Showing 1 words to 568 words out of 568 words

Chapter 1 - MATATTARAR BAN DARIYA Mukyakyata Mu Sha Dariya Zallah by kanopost.ng.txt

Yahya So   

22 Dec 2024

2151

Matattarar Ban Dariya
By Mansur Usman Sufi
0813723707


LABARAN BAN DARIYA ZALLAH 😂🤣😂##


Malam Audu ne ya ziyarci wani abokinsa Kuturu. Yana shiga zauren, sai ya ga Kuturun yana ajiye kwanon fura wadda ya shanye tas. Sai ya ce, 'Kash! Ina ma akwai sauran furar nan' .





Kuturu ya ce, 'Wallahi ta kare, amma za a iya yin dakan-ka. Ko a yo ne?' Malam Audu ya ce, 'Da kuwa na yi godiya'. Kuturu ya shiga cikin gida ya dauko gero. Sai ya sa a baki ya tauna ya tauna sannan ya zuba tukar a cikin kwano. Da ya gama, sai ya zuba mata nono ya kawo wa Malam Audu, ya ce 'Ko a kara maka sukari ne?' Malam Audu ya ce, 'Zubo shi sosai'. Sannan ya kar6a ya yi ta kikkifiar fura, har da side kwano.





Ya yi gyatsa ya ceo 'Kai Musa dan Kuturu! Wannan fura da dadi take. Ni dai ban ta6a shan irinta: ba. Wai don Allah, ya ake yin wannan dakan-ka ne?'





Malam Audu ya 6ata fuska ya ce, 'La haula wala kuwati! Yanzu haka ka yi min?' Dan kuturu ya ce,' To ai haka dakan-ka ya ke'.


'Dan Kuturu (da sauti irin na kutare) ya ce, ai geron ake ta taunawa a baki a tofa tukar a kwano, sannan a kara no no da sukari'. Ai kafin kace wannan, Malam Audu sai amai kwaaa, kwaaa. Dan Kuturu ya ceo 'Af! Yanzu kuma ba ta da dadi ne?' Malam Audu ya kalle shi ya ce, 'Allah Ya isa.😂😂😂😂😂




Alpha ka je ka nemi ilimi da ku’di kawai


Lamarin da yawa daga cikin masu iqirarin su alfofi ne na da ban dariya da ban tausayi. Ba sa janyo aya ko hadisi, asali ma da yawan matsayarsu sun sa’ba nassosi. Ba za ka ga sun quoting wani malami ko littafin ilimi ba ko qididdiga wato ‘facts and figures’. Kullum cikin bayar da labaran soki burutsu.


Da yawa ba su yi shekaru goma ko talatin da aure ba ballantana a ce su bayarda sirrikan nasarar aure ba. Kai ko a cikin abokai ba su ne shugabanni ba balle ka ce su na da charisma don haka su ba ka leadership secrets. Kawai dai zafin rai da surutu su ka fi kowa.


Da kuma za ka koma ilimin Psychology irin na su Freud da sai ka fi tausayawa ma su, ko ka yi ta tunanin ko an samu matsala a yarinta ne.


Idan Ka na so ka zama tsayayyen namiji da ya isa da gidanshi ka je ka samu tsayyayun maza su yi ma ka karatu. Za ka ga a kowacce unguwa su ne tsiraru saboda jajircewa ba wasan yara ba ne kuma fa zafin rai ba ne.


Mallam ka je ka nemi ilimi da ku’di sannan ka zagaya duniya ka yi kallo. Zafin kai da qunar zuciya za ka ga duk sun ragu! Ni na san ma su tsattsauran ra’ayi lokacin mu na jami’a, da yawansu duniya ta yi mu su karatun ‘ta nutsu’ yanzu.


Ta yaro kyau ta ke………🤣🤣


Kuyi mana mentioned din alpha guda daya daka sani✅

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login