Showing 1 words to 441 words out of 441 words

Chapter 1 - DARIYA DA MURMUSHI Labarun ban dariya Hausa Novels Document 2025.txt

Yahya So   

22 Dec 2024

2529

ο»ΏπŸ˜‚πŸ€£πŸ˜‚ LABARAN BAN DARIYA ZALLAH πŸ˜‚πŸ€£πŸ˜‚


πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡
ALLAH YA ISA SHADAI DAIπŸ˜‚


Wani ma' aikacin gwamnati ne ya sami kudi masu yawan gaske daga rashawa da 6uruntun gwamnati, ya gina gida kasaitacee a garinsu. Ranar da zai tare, sai ya kira walima, amma kafin a fara sai ya nemi a yi masa addu'a. To dama akwai wani malami da aka gayyata, kuma Megida ya roke shi ya yi masu addu'a.


Malam ya ce,


"Toh jama'a! Sai mu yi Allah Ya isa sha-dai-dai" πŸ˜‚


Jama'a suka yi tsit, wasu na neman dariya, wasu kuma cikin mamakinπŸ€” wannan abu. Amma, Malam tuni ya fara: "Allah Ya isa, Allah Ya isa ..... " Da ya gama sha dayan, sai kuma ya ce,


β€œA yi Allah wadai uku uku .... "πŸ˜‚πŸ˜πŸ˜‚


πŸ˜‚πŸ˜„πŸ˜‚LABARAN_BAN_DARIYA_ZALLAHπŸ˜‚πŸ˜„πŸ˜‚πŸ˜„


.
Wani dattijo ne yayi niyyar Noman gyada da
damina, Ranar da aka yi ruwa mai yawa sai ya je
Gona, ya na fara huda sai kawai ya ji ance kai Ku
taya shi mana!!! Kawai sai yaga an hude gonar baki
daya, washegari ya zo da nufin yayi shuka, yana
sarawa zai fara shuka sai ya ji an ce kai Ku taya shi mana!!! Sai ya ga an shuke gona duka. Haka dai
duk lokacin da yazo aiki a gona sai ya ji ance kai Ku
taya shi mana. Har sai da Gyada ta isa roro ya zo ya
fara aiki sai ya ji an ce kai ku taya shi mana. Nan
take aka gama aikin roron Gyada. Sai ya dan dauki
daya ya ci. Kawai sai ya ji an ce kai ku taya shi mana. Nan da nan suka cinye Gyada. Ashe aljanu
ne.
kai ku tayani mana!!!! ----> Amma fa dariya.HHHπŸ˜‚πŸ˜‚


πŸ˜‚πŸ€£πŸ˜‚ LABARAN BAN DARIYA ZALLAH πŸ˜‚πŸ€£πŸ˜‚


πŸ‘‰πŸ‘‰DAN FULANIπŸ‘ˆπŸ‘ˆπŸ˜‚πŸ€£


wani Bafillatani, wai shi Na-Rana, ya kamu da cutar ajali, sai ya ba da wasiyyar in ya mutu a binne shi da sandarsa. Haka kuwa aka yi. A wajen ta'aziya, sai Malam Adamu ya hango Jauro a gefe yana ta juyayi yana ta cewa, 'Cofdi jom! Mm, Mm, Mm!' Malam Adamu ya tambaye shi ko lafiya? Jauro yana kada kai cikin takaici, ya ce, 'Ai ba mutuwar Na-Rana ba, hushin Na-Rana!' Salman ya sake nisawa, ya yi ajiyar zuciya, ya sunkui da kansa, ya sake dagawa, ya kaIli Malam Adamu ya ce, 'Watau ... , ga walakiri da tombayor kwakwa, ga kuma Na-Rana da zushiya'. To ya kenan laura? 'Mhm! Ai molom, na tabbata yanzu suno nan suna gwobazawa. Da ma ka san shi Na-Rana shewa yo yi in ya mutu a bunne shi da sondarsa, gashi kuma da iya fadan sonda!' "To, Allah Ya sawwake," inji Malam Adamu.πŸ˜‚πŸ€£

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login