Showing 1 words to 1489 words out of 1489 words
Chapter 1 - AUREN MAHAUKACI PAGE ONE Complete Book By Ummu Rufaida.txt
AUREN MAHAUKACI
Story and Written by
UMMU RUFAIDAT
Alhamdulillah!!ina godiya ga Allah ubangiji,mahaliccin kowa da komai,Allah yayi dadin tsira bisa shugabanmu,Annabinmu,fiyayyen halitta Muhammadur rasulillahi (S.A.W)da ahalinsa, da sahabbansa,dama wadanda suka bishi a tafarki madaidaici daga yanzu har izuwa ranar tashin Alkiyama.
SADAUKARWA!!!
Gareki kawa,yar uwa,kuma Aminiya.
HALEEMA MUHAMMAD
ABDULLAHI
(HALEEMATOU)
(Kagengen labari)
Page 1
Bismillahir Rahmanir Rahim.
"Haba don Allah!meenah ya za'ayi ace waini mahaukaci za'a auramin,yanzu duk samarin dake garinnan da masu sona ana korarsu amma ace an rasa wanda za'a bani sai mahaukaci!!kuma wanda ba'asan asalinsa ba?saboda kawai na rasa mahaifana!saiya zama bani da gata ko kadan???"
Ta karashe maganar tare da fashewa da wani kalar kuka mai cin rai.
Haba don Allah Hannah!mai yasa zaki tada hankalin ki akan abunda kinsan ba fashi?kuma tada hankalinki shine zai kara faranta musu rai,
Nidai rokona a gareki don Allah ki nuna kamar abun bai dameki ba,kuma kibi mijinki karkiyi tunanin kasancewar sa Mahaukaci kice zaki masa abun da ranki yaso.
Shine bashi da hankali amma mahaliccinmu yana sane da duk abuda yake faruwa.
Ki kasance gata a garesa,kiyi zaman Aure dashi,ki masa biyayya tamkar kina tare damai hankali.
Hannah duk son da nake miki ban tabajin banason Aurenku da wannan mahaukacin ba.
Daga kai tayi ta kalli Meenah,tare da fashewa da kuka tace"yanzu shikenan AUREN MAHAUKACI ya tabbata akaina"?
Goge mata hawayen meenah tayi tare da fadin hakuri zakiyi.
Mu tafi gida kar a nemeki a rasa inna ta dukeki.
To gantalalliya!tambadaddiya!daga gidan ubanwa kike nake nemanki na rasa,uwarki ce zata miki abincin?kiyi gaggawar gama abinci kafin yarana su dawo yunwa ta hudaminsu,gantalalliya kawai!shiyasa nace a hadaki gantalalle irinki zakufi dashi...
Kin bani waje kosaina karyaki?dangin mayu ai dama mahaukaci yafi dacewa dake,ko kin cinyeshi ba matsala tunda dama ba'asan asalinsa ba.
Goge hawayen dake fuskarta tayi,tare da fadin Allah ya huci zuciyarki...
Talla!rufemin baki munafuka.
Bata sake magana ba tayi hanyar
Madafi.
Ango!Ango!! cike da shakiyanci suke tsokanarsa hade da sakin dariyar zolaya.
Daya daga cikinsu ne ya fara magana....
Aini nafi kowa farin ciki da Auren nan,saboda saida naje nace inasonta tayi burus da magana ta ai gashi dai mun gani,karshen alewa kasa.
Yanzu AUREN MAHAUKACI ya kamata,kuma mahaukacinma wanda ba'asan asalinsa ba.
Gashi madoki ba! dayan ya karbe da fadin haka.
Na ukun dake gefensu ne,yace "nikam wallahi tausayin Hannah nakeji,ace duk kyanta,da iliminta,amma ta kare da AUREN MAHAUKACI????"
Yo Allah na tuba ba ita ta jawa kanta ba,data soni da tuni dani za'ayi.
Kai dallah me Hannah zatayi dakai?garama mahaukacin duk da haukar sa yafika kyan gani......
ya isheka wawa kawai! Nine zakace mahaukaci yafi ni kyan gani.......
Karya nayi,ai wllh wannan mahaukacin da kuka raina da ace bai samu matsalar kwakwalwa ba,dako inda kake bazai kalla ba,duk da haukarsa tsananin kyansa bai buya,kawai dai dan in mutum yana da tabin kai to shikenan bashi da wata daraja a wajen al'umma.
Ya bude baki da niyar magana sukaga ba Asali (haka suke kiran mahaukaci) yayo kansu da niyar duka kamar yadda ya saba dukan duk wanda ya shiga safgarsa,dama wanda bai shiga ba.
Habawa kafa mai naci ban baki ba!!
Tuni koya ya arce don sunsan in ya kama daya acikinsu saidan buzunsa.
Ana haka saiga Hannah,ta bishi da kallo,don ita dama can ko ya hana kowa bin hanya in tazo zai barta,abinda take mamakinsa kenan don har baffanta ya taba duka da kyar aka ceceshi.
Ko silar hadasu Aurenma dalilin dukan da yayiwa Inna ne.
Binta yayi da kallo kamar yadda itama take kallosa,share hawayen daya zubo mata tayi,tana tausayawa kanta,tana kuma tausayin ba Asali.
Tana tunanin ranar da zasu zauna daga ita saishi,tana tsoron karta masa wani abu ya jibgeta bamai cotonta.
Tazo daidai saitinsa taga yasha gabanta,ya mika mata hannunsa yana kuma kallon cikin idonta.
Kallo hanunsa tayi,ta kuma kalli abinda yakeso ta bashin wato a awarar Inna ta aiketa ta siyo mata.abinciTasan bamai bashi ya karba,amma kuma yau da kansa ya bukata?
Gani tayi bazata iya hanashi ba,amma tana tsoron hukuncin da za'a mata inta bashi.......
Bata gama tunin ba taga ya kara jijjiga mata hannunsa,alamar ta bashi.
Daga ido tayi ai kuwa caraf!sai acikin nasa,wani irin kwarjini taga ya mata.
Saboda haka batasan lokacin data sake masa ledar da awarar ke ciki ba.
Wani kalar murmushi yayi wanda saika fahimta zaka gane yayi murmushin.
Tafiya take amma gaba daya hankalinta baya jikin ta abu biyu ya shamata kai,irin hukuncin da Inna zata mata dalilin bayar da awararta,da kuma tunanin mahaukaci, tabbas akwai wani abu tattare dashi wanda take tunanin ita kadai ta fahimci hakan.
Yana dakyau mai daukar hankali, wanda yanzu dalilin haukarsa ba kowa ke fahimta a kallo daya ba,saidai duk inda mutum ya nutsu ya kalle shi zaisan kyakkyawa ne ajin farko.
Yana da wata nutsuwa wadda in mutum yanada lura zai fahimci hakan.
Assalamu Alaiku.......
"Ina sakona dan uwarki!
Cewar Inna ba tare da barta ta karasa cikin gidan ba,
Um um um...dama..dama..dam....
Dama me!shegiya mai kashin tsiya,
Yanzu dama da gaske ne kin bawa wancen matsiyacin mahaukacin awara ta?
Ai kuwa zakici ubanki!don bazanyi asara ba saina fanshe kudina wllh.......
Ji kake dum..dum...ta rufeta da duka tako ina,
Ihu take tana neman taimako,saidai kash!!!babu mai taimakonta a wannan lokacin.
Sosai ta jigata kafin ta rabu da ita tana haki.
* * *
Bagaren ba Asali kuwa,tunda ta bashi awarar ya bar wajen, yana tafiya yacin kayarsa har yaji ya koshi,
Saura uku ta rage ya jefata a bola,kana yaci gaba da tafiyar da baisan inda ya dosa ba.
Tun ana saura sati daya baffa ya sayar da babbar gonar mahaifin Hannatu(Hannah),
Wacce ya siyarta kimanin naira dubu dari tara da hamsin,wadda ya siyar da ita ne kawai,bawai don haka ya kamata ya siyar ba.
Tunanin mai zai kuma siyarwa yake,don ya kudurti samun kudi sosai a Auren nan,tunda in hakane ba halin cin komai.
Tunanin sane ya tsaya wajen daukar gidaje biyu daga cikin kadarar mahaifin nata,daya gida ne da zaikai kimanin milion daya da rabi,sai kuma dayan daya kasance gida irin na talaka mai daki uku wanda marigayin ya siya ne don Almajirai su zamu wajen zama suyi karatu.
Amma tun bayan rashinsa,baffa ya kori duk Almajiran acewarsa ya zama na magada.
Bayan siyar da gidajenne ya sayawa Hannah da mahaukaci gida,wanda ya kasance ginin bulo mai dauke da daki daya sai bandaki da kicin da kuma rumfar baranda.
Tafiya tana tunani wanda yanzu ya zame mata jiki,bata ankara ba saiji tayi tayi karo da mutum....
Sosai ta tsorata kafin cikin dar dar ta dago da idonta,karaf!suka hada ido da Angon nata,fuskarban tasha bula da gawayi,sai yayi wani abun tsoro gashi sai zare dara-daran idonsa yake.
Abu biyu taji ya dira mata,wato tsoron sa da kuma tausayinsa. Kallonta yake kamar yadda take kallon sa.....
Bata zata ba saiji tayi ya kama hannunta ya fara tafiya da ita..
Sosai ta kara tsorata dashi.
Bai saki hannunta ba saida yaje tsakiyar bola kafin ya saki hannunta ya zauna,tare da kamo hannunta ya jata alamun ta zauna....kallon wajen tayi cikin bola ne fa duk datti wajen ba fasali,ta fada a ranta tare da dosanuwa a kan wani karamin dutse da ta gani a wajen.
Kallonta yayi tare da fadin "abinci zanci" kallonsa tayi,tana tunani a ranta,ita yanzu a ina zata samu abinci?
Bayan a gida itama sai Haajara ta dauko mata a boye kafin ta samu naci(Haajara 'ya ce a wajen Inna da baffa wacce ita sam bata dauko halin iyayenta ba).......
Abinci zanci!!!!ya kuma fada da karfi!
Dai dai lokacin da meenah tazo zata wuce,karar maganarsa ce tadau hankalinta zuwa wajensu.
Dariya ya sheke da ita,tare da fadin "ga Amarya ga Ango" soyayyar akeyi ne haka a ciki bola?lailai kauna tayi nisa.
Banason shime meenah!nidai don Allah karaso na nemi taimakonki........
Waaa?tab in kin ganni a lahira kaini akai,amma da kafata ba zanzo inda za'a rabani da wani sashe na jiki naba.
Mutumin dako babba ya kama ba'a iya cetonsa ta fadin rai!balle ni inya damkeni ko ban mutu ba may be da karaya zan koma gida.
"Haba don Allah meenah don Allah kizo ba abinda zai miki"
Allah ya kareni da zuwa wajennan kedai da yake dama jininku da gauraye dana juna shiyasa damacen duk abinda yake in kinzo zai jira ki wuce kafin ya dora.
To shikenan tunda bazaki zoba,amma don Allah ki taimakeni inda a abinci a gidanku ki kawomin yanzu.
To yanzu naji magana, ina zuwa.
Tana fadin haka ta koma gida.
Sunanaan zaune harta dawo da kwanon silba mai rufi a hannunta.
Gashi na kawo,to ki karaso mana....... Aaaaaaa nidai kizo ki karba!!!
Yunkurawa tayi da niyar tashi taji ya rike hannun,
kallon sa tayi tare da fadin ina zuwa abincin zan karbo maka.
Kallonta ya tsaya yi kafin kuma taga ya kece da dariya kamar an aikoshi.
Dariya yake sosai harda yar dungure,hakanne ya bata damar zuwa karbar abincin a wajen meenah wacce take kamar kace kyarat!ta fece.
Tana amsa kuwa meenah ta arta da gudu.