Showing 24001 words to 27000 words out of 33406 words
Chapter 9 - ABU NAKA Book 3 end Writing by SODANGI.txt
da shi a hankali ta cusa hannayenta cikin rigarshi tare da kwantar da kanta a qirjinshi, a hankali cikin kalamanta mai sanyi ta ce mishi, “In ka haifi mace guda to Gwaggona fa Yaya?”
Kwanaki ashirin sun cika saura guda xaya tal! Saddiqa tana xakinta a kwance Mus’ab ya shiga ya sameta, ta yi maza ta share hawayenta tare da sakin fuskarta don kar ya gane abin da take ciki. Shima ya yi kamar bai gani ba.
Matsawa kusa da ita ya yi ya kwanta, ya miqa hannu ya jawota jikinshi yana sansanar qamshinta. Ta yi qoqari ta xan ture shi ya xan matsa kaxan.
“Mene ne haka?”
Ba ta kula tambayar tashi ba ta yi maza ta miqe ta zauna.
“Da ka tsaya mun yi magana tukunna”.
Ya ce, “Ba zan yi ba sai na yi abin da ya kawoni tukunna”.
Bai yarda ya bari ta sake ce mishi komai ba ya shiga sarrafata, sai da suka samu nutsuwa sai ta ce mishi, “Ni Yaya baka da damuwa ne, gobe ne fa aikin nan?
Bai kalle ta ba ya ce, “Bani da ita, takin ma bana son ki gaya min addu’a kawai na ce ki rinqa yi”.
“To ai ni munanan mafarke-mafarken da nake yi ne suke bani tsoro, in zan gaya maka abin da na gani kuma ka ce wai baka son ji”.
“To a ina kika ji an ce a ba da labarin mummunan mafarki? Ina ce addu’a aka ce a rinqa yi mishi?”
Bai tsaya ba ya tsallaketa ya shiga banxaki ya yi wanka ya fito tare da alwala, ya shiga gabatar da nafila. Ita ma ta bi bayanshi, basu daina ba har sai da aka kira sallar asuba.
Yana dawowa daga sallar asuba ta je kusa da shi don ta gaishe shi, ya jawota ya rungume a jikinshi yana shafata.
“Santsin jikinki kaxai ya isheni ni’ima Aisha”.
Ta yi maza ta zame daga jikin nashi ta ce,
“A’a, Yaya kana faxa ne kawai don in ji daxi, amma in da haka ne ai da ka haqura da wannan tiyatar da za ka tafi yau, tunda na gaya maka ni kam Yaya Mus’ab ina sonka rashin haihuwa kuma ba zai rage komai ba a tsakaninmu da kai”.
“Na sani Aisha”.
Ya faxa cikin jin daxin kalaman nata.
“Na sani Aisha, na san za ki iya zama dani da lalurata. To amma mene ne tukuicin son da muke yiwa juna? Ina son ganinki da ciki”.
Ya faxi hakan cikin raxa har ya sata jin kunya.
“An jarrabi zuciyata da son in ganki a hakan, in san nine, mutanen duniya ma su tayani shaida hakan a ce matar Mus’ab juna biyu ne da ita”.
Ta yi murmushi, yana ganin murmushin nata ya yi maza ya miqe ba tare da ya ba ta damar da za ta sake narke mishi ba.
“Bari in yi wanka Aisha in shirya kafin su Idris su iso”.
Kafin ya fito daga wankan sai ga Idris da matarshi Abida sun shigo, ‘yan mintoci kaxan kuma sai ga Sani shima ya iso tare da amaryarshi.
Saddiqa tana tsaye a xakinta jikinta sai rawa yake yi, Mus’ab ya shigo sanye da jallabiya mai ruwan shuxi, silifas xin wanka ne a qafarshi, qamshinshi na kullum yana tare da shi.
Ya kama hannayenta duka biyu ya riqe a cikin nashi, ya sunkuyo da idanuwanshi cikin nata da tuni suka fara zubar da hawaye.
“Ai nima zan bika, zan je ayi komai a kan idona ina gani”.
A hankali ya ce mata, “A’a, Aisha yi haquri ki yi zaman ki a gida, ga ‘yan’uwanki mata nan sun zo za su tayaki zaman gidan zai fi miki sauqi da nutsuwa”.
Za ta yi magana ya yi maza ya ce mata, “Shhhhhh!” Kan ta yi wani abu ya yi hanzarin sanya bakinshi a nata, kusan minti guda kafin ya saketa.
“Kar ki yi min musu, addu’a kawai za ki yi min”.
“To Yaya”.
Cikin rawar murya ta faxi hakan. Bai jira ya ji sauran maganar ba ya yi maza ya fita daga xakin, ya samu su Idris da Sani a waje da suka zo don suyi mishi rakiya.
Saddiqa ta nemi wuri ta zauna a qasa tana ta faman kuka Abida tana rarrashinta.
“Ki yi haquri Aisha, ki yi ta addu’a kawai Ubangiji dai yasa ayi a sa’a”.
Ta xago ta kalleta cikin hawaye ta ce, “Iyayenmu fa basu san da aikin ba, na yi na yi mu gaya musu ya qi, wai yana tsoron kar su hanashi gara in an yi kawai su ji”.
Abida ta jinjina lamarin, nan take kuma sai ta ba ta shawara.
“To yanzu tunda ya riga ya tafi ai sai ki gaya musu su sani, don kuwa ai yana buqatar addu’arsu”.
Ta yi maza ta miqe ta xauko wayarta, lambobin Gwaggonta ta danna, tana jin muryarta ta soma kuka.
“A’a, me ya sameki Saddiqa ba dai wani abin ne ya faru tsakaninki da mijin naki ba ko?”
Saddiqa ta ce, “Eh, Gwaggo”.
Gwaggo ta yi maza ta ce, “Yau to ai yanzu muka gama magana da shi ya kirani muka gaisa, mun kuma xan jima muna magana ban ji alamar damuwa a tare da shi ba”.
Cikin nutsuwa Saddiqa ta tambayeta ya gaya miki daga ina ya kira ki Gwaggo? Da sauri ta ce mata, “A’a, bai gaya min ba, wani abu ya faru ne?” Ta yi tambayar a yanayi na nuna damuwa.
“A’a, Gwaggo babu abin da ya faru, amma shi yana asibiti wai za a yi mishi tiyata”.
Da sauri ta tambaya, “Tiyata? Ba shi da lafiya ne?”
Tana share majina tana maganar, “Lafiyarshi qalau a kan dai maganar nan ne, na yi na yi ya qi ya bari, na kuma ce ya gaya muku wai ba zai faxar muku da gaba ba, bayan haka kuma yana tsoron kar ku hana”.
Shiru Gwaggo ta yi na wani lokaci alamar jikinta ya yi sanyi, a hankali cikin nutsuwa Saddiqa ta jita tana cewa, “To Ubangiji yasa ayi mishi aikin a sa’a”. Ta ce, “Amin”.
Tana ajiye wayar kiran Mus’ab ya shigo.
“Albishirinki Aisha”.
Ta yi maza ta ce mishi, “Goro”.
Yana murna ya ce mata, “Yau hira sosai muka yi ni da Inna da na kira ta”.
Ta ce, “Kai Yaya Mus’ab, wannan ne abin albishir xin, ni ina ce ma za ka ce min an fasa yin tiyatar ne”.
A hankali ya ce, “A’a, Aisha ai likitocin da za suyi aikin ma sun riga sun iso tun xazu, Dr. Usman ya gaya min cewar shi da wasu likitoci uku ne za suyi aikin. Kin san wani abu?”
Ta yi maza ta ce mishi, “A’a, sai ka faxa”.
Ya ce, “To zan shiga tiyatar ne hankalina a kwance bana tsoro ba kuma na fargaba, na kuma yarda cewar duk wani abin da ya faru ko zai faru, to daga Ubangiji ne, na roqe shi ya yafe min zunuban da na yi ta aikatawa waxanda suka zama sanadin da na cutar da lafiyata.
Ke kuma na gode miki Aisha, na zauna dake zama mai daxi, kowane lokaci a cikin tattalina da kyautata min kike, kin yi komai don ki faranta min. Mafi alherin al’amarinki kuma shine, kin zama sanadi na daidaituwar tsakanina da mahaifiyata, in ban fito daga wannan tiya…..”
Ta yi maza ta saki wayar a qasa saboda firgitar da ta yi tare da faxin “Na shiga uku!” Nan take kuma ta soma kuka.
Da qyar ta iya yin shiru saboda rarrashi da kalaman qarfafa gwiwa da su Abida suka yi ta yi mata.
“Gaskiya ba zan iya zaman nan ba gara min kawai muje asibitin”.
Abida ta ba ta haquri. Jimawa can ta sake cewa, “Nifa gara min kawai in tafi don ban ga amfanin zaman da nake yi a nan ba”.
Tasa hannu ta kira layin Mus’ab don ta gaya mishi ya barta kawai ta zo asibitin don ta ganshi. Sani ne ya amsa.
“Hello! Aisha akwai wani abu ne?’
A hankali ta tambaye shi “Yaya fa?”
Ya ce, “Ai tun qarfe takwas da rabi suka shiga dashi, dama shine mutum na biyu a tiyatar da za suyi yau”.
Cikin Saddiqa ya ba da sautin qulululuuu! A lokacin da idanuwanta suka kai kan agogon dake wurin, qarfe goma sha xaya har da kwata, kusan awowi uku kenan da shigarwar da aka yi mishi. Ko a wane hali yake ciki yanzu? Oho! Ta yi maza ta ajiye wayar ta nufi banxaki saboda kaxawar da cikinta ya yi.
Wunin ranar zirga-zirgar da ta yi ta yi kenan. Wajen azahar ta isa asibitin bayan ta riga ta yi sallarta a gida.
A hankali ta tura qofa ta shiga xakin da aka nuna mata cewear shine nashin inda aka bashi, jallabiyar da ya baro gida da ita ne a ajiye a kan gadon.
Ta miqa hannu ta xauka ta ninke ta sanya cikin jakar dake hannunta, ta ajiye jakar a kan gadon ta nufi inda ta hango Sani da Idris a tsaye.
Tana isa wurin ta gane a kusa da xakin tiyata suke tsaye. Su dukansu biyun babu wani annuri a tare dasu, gaba xayansu idanuwansu sunyi zuru-zuru, bakunansu sun bushe.
“Sannu Aisha”.
Idris ne ya yi mata gaisuwar a yanayi na qarfin hali. Ta yi nufin wucewa zuwa inda ta hango qofar da aka rubuta Theater room a jiki, da sauri suka ce mata, “Ai ba a zuwa nan, iyakar wurin tsayuwar kenan inda muke xin nan, ki dawo kawai ki yi haquri ko kuma ki koma can xakin ki samu su Abida in an fito da shi ai nan xin ne dai za a kawo shi”.
Ba ta yi magana ba kuka kawai take ta yi.
Dr. Usman ya zo wucewa tana kallon shi yana magana da su Idris ba ta iya qarawa ta ji abin da suke faxa ba, tana dai kallon fuskokinsu zuciyarta kuma tana raya mata, ta gaji da kallon nasu ta yi qoqarin matsawa kusa dasu don ta ji me yake gaya musu haka wanda bayanin ya qi qarewa.
“Yanzu dai sai mu qara haquri mu haxa da addu’a”.
Qarshen maganar likita da ta ji kenan.
“Me ya faru? Me ake ciki na ji yana cewa ayi haquri?”
Ta yi musu tambayar a firgice saboda ba ta same shi ba ya riga ya wuce. Tun kafin su san me za su ce mata ta fara kuka.
Da sauri Idris ya soma yi mata bayanin “Ba fa wani abu bane mai tsanani al’amari ne da yake faruwa da mutane da yawa, kin san kowa da yanda qarfin jininshi yake, an gama aikin sai dai bai dawo sosai ba ta yanda za su iya fito da shi”.
Yana nan kenan tsakanin akwai da babu. Zuciyarta ta raya mata. Nan take jiri ya xebeta ta tafi za ta faxi, da sauri wata mace dake wucewa ta bayanta tasa hannu ta tare ta, su Abida suka yi maza suka kama ta aka kaita xakin aka kwantar da ita.
“Ki fa kwantar da hankalinki kar kuma shi a fito da shi ke kuma kin samu matsala”.
Kukanta kawai take yi ba ta ko kallon su balle ta amsa.
Awa xaya baya aka fito da Mus’ab. “Gareka nake ya Ubangiji, gareka nake neman taimako”. Abin da yake ta nanatawa kenan.
Gaba xaya ana tsaitsaye a kanshi cikin sauraro.
An fito daga sallar magariba kenan sai ga Kawu Gixe da Abu sun iso asibitin, nan da nan Saddiqa ta xan samu nutsuwa a tare da ita.
“Iko sai mai shi, haka al’amarin yake? To Ubangiji ya ta da kafaxarshi”.
Gaba xaya aka amsa “Amin”.
Kalaman Abu ne wannan bayan ta amsa sannu da zuwa da gaisuwar da aka yi ta yi mata.
“To a nuna min inda zan yi sallah”.
Saddiqa ta wuce za ta nuna mata, ta tarar tuni har Kawu Gixe ya idar. Ta tsuguna a gefe tana gaishe shi.
“Ya ya aka yi aka yi irin wannan aiki haka baku sanar da gida ba?”
Ba ta iya ce mishi komai ba in ban da kukan da take yi, saboda ta riga ta gama tsorata da yanayin da aka fito da shi a ciki.
Har suka bar asibitin ran nan bai wani dawo cikin hayyacinshi ba, ita kam ta so a ce an barta ta kwana a wurinshi Abu ce ta ce gara su tafi wai in sun zauna me za suyi mishi bayan ga likitoci suna ta kaiwa da kawowa, ga kuma Kawu Gixe da Sani suma a nan za su kwana?
Sun dawo gida Saddiqa sai bin Abu da kallo take yi, zuciyarta tana raya mata duk halin da Mus’ab ke ciki hankalinta a kwance yake, da kanta ta xebo abinci ta zauna ta ci ta xora da ‘ya’yan itace, ta yi wanka ta hau gado ta yi kwanciyar ta tana tambayar Saddiqa,. To don kin qi ci kin qi sha sai me? Ina ce duk iya shegenku ne ya jawo hakan? Da kin hanashi ai da bai yi ba.
Saddiqa ta zuba mata ido tana kallon ta cikin matsanancin takaici, ta ma rasa me za ta ce mata.
Dare ya yi nisa sanda ta farka ta duba agogon wayarta uku da rabi ne na dare, ta shafa inda Abu ke kwance ba ta nan, ta tashi ta tura qofar banxaki a hankali don ta gani, nan ma ba ta nan. Ta fito falo ba ta ganta ba.
Har ta zuwa za ta koma xaki sai ta tura qofar xaya xakin, Abu tana ciki a zaune kan sallaryarta hannayenta duka biyu a xage zuwa sama, kuka take yi hawaye sai gudu suke yi a fuskarta.
“Ya Ubangiji, wannan yaro Mus’abu….”
Abin da kawai Saddiqa ta iya ji kenan. A hankali ta mai da qofar ta rufe ta nufi xaki ta je ta kama tata harkar.
Suna idar da sallar asuba suka isa asibitin, har lokacin Mus’ab yana kwance a rigingine kamar yanda suka barshi, bambancin kawai shine a yanzu yana furta kalmomi da wanda ke kusa da shi yake iya ji.
“Cikina, cikina, a san min ruwa in sha”.
Saddiqa ta kalli mahaifinta ta ce, “Baba wai zai sha ruwa”.
Kawu Gixe bai kulata ba sai Sani ne ya yi mata bayani, “Sun ce kar a ba shi komai”.
Tausayin halin da yake ciki yasa Saddiqa ta soma zubar da hawaye. Da sauri Kawu Gixen ya ce mata, “Ke, kar fa ki kawo mana iya shege a nan? Kuka? Ba ki san za a yi hakan bane da kika ingizashi yaje ya yi? Wannan fitina da me ta yi kama? Dole ne sai kowa ya haihu? Waxanda basu haihu ba basa rayuwa ne? Yanzu babu bayin Allah mutanen kirki da su basu haihun ba?”
Abu ta tave baki ta ce, “Uhm! Nima dai abin da na ce mata kenan”.
Sani ya yi maza ya ce, “A’a, Kawu Aisha kuwa babu yanda ba ta yi da shi ba shi ya qi”.
Da sauri Kawu Gixe ya ce, “To me yasa ba ta faxa ba ta ja bakinta ta yi shiru?”
Cikin nutsuwa Sani ya ce, “Kawu ina ganin tuna an riga anyi sai ayi addu’a kawai ayi dace, ita Aisha kam Kawu kowa ya ganta ai ya san ta shiga wani al’amari, tunda ai ko shekaran jiya gidansu ba haka na ganta ba, daga jiya zuwa yau ne fa ta yi wannan zabgewar”.
Kwanan Mus’ab uku kafin ya dawo cikin hayyacinshi sosai ya san abin da yake ciki da waxanda suke tare da shi.
Kowa sai murna yake, yana fara samun sauqi Abu ta yi xib! Ba ta ko kallon inda yake kwance, ko ya yi qarfin hali ya yi mata magana ba ta wani kulawa balle ta amsa.
Saddiqa ta kalle shi ta ce, “To kai ka yi haquri mana ka yi shiru dole ne sai ka kula Abu?”
Abu ta galla musu harara dukansu biyun, ta ce, “To ni don ba a kulani ba sai me? Ni ai bake ba ce ya dena kulani mana. Fitinannun mutane masu neman fitinar tsiya, ana zaune lafiya ku tada mutane a tsaye”.
A hankali ya buxa baki ya ce, “Ki yi haquri Abu, Aisha ba ta da