Showing 18001 words to 21000 words out of 33406 words
Chapter 7 - ABU NAKA Book 3 end Writing by SODANGI.txt
kowane lokaci ina jikinki ba Aisha, amma in na tuna wai ta hakan ne na sanya miki ciwo sai in ji na haqura”.
Ba ta kalle shi ba ta ce mishi, “Wannan kuma ruwanka, kai ka zavarwa kanka hakan ba ni ba, balle ko ka ce na takura maka. Kuma ma ni daga yanzu kar ka sake yi min wannan maganar tunda muna shan magani maganar ta qare a wurina na barwa Ubangijina”.
Ya ce, “Haka ne Aisha”.
Shekara guda da auren Saddiqa da Mus’ab, tana kwance a xakinta bayan ta karanta katin murnar cikarta shekara guda da zuwanta Ajakuta, wanda Mus’ab xin ya aiko mata da shi, zuciyarta ta shiga tunanin Gwaggonta da daxewar da ta yi ba ta je gabanta ba. Anya na yiwa Gwaggo adalci kuwa?
Tana cikin tunanin Mus’ab ya shigo xakin cikin yanayin da ta san akwai abin da ya yi dalilin dawowar nashi, cikin murmushi yake rage kayan jikinshi yana cewa, “Dawowa na yi ki bani goron cika shekara guda da zama ango”.
Ta kawar da fuska ta ce, “In don wannan ne ai babu wani goron da za ka samu, sai dai ko hukunci. Tunda shekara guda kenan rabon da in ga Gwaggona, tunda na zo kuma baka tava kai mata ni ba ko sau xaya don ta ganni”.
Ya iso gareta yana faxin, “Bari dai yau kam ina ganin ya kamata in tsaya muyi maganar zuwa wurin Gwgagon nan”.
Tsawon lokaci yana jikinta yana yin yanda yaso, har sai da ya kai ga samun yanda yake so ya huta ya koma cikin nutsuwarshi, zai soma yi mata wata hirar sai ta ce mishi, “To, Yaya ai ka ce yau kam za ka zauna mu yi maganar zuwa wurin Gwaggon”.
Yana jin haka ya yi maza ya rage fara’ar dake tare da shi.
“Kin fa matsa min a kan maganar nan, babu halin ki ganni ina hutawa sai kin kawo min maganar zuwa Misau, da wani wanda bai san zaman aure bane? Ina ce kwanan nan Bilkisu da Hamida suka tafi?”
Ba ta kalle shi ba ta ce, “To ai shi kenan zan daina damunka, amma dai in ka dawo gida baka sameni ba kar ka ce ranka zai vaci, don na gaji ina so in je in ga uwata, zuwansu Anti ai ba zuwanta bane”.
Jin haka da ta ce yasa ya shigar da maganar wasa.
“Kina so in xaure muku hanya kenan direban ya rasa inda zai bi”.
Ya sake jawota ya maqale yana faxin, “To ke aikin aure da haqquwan cikinshi wasa ne da za ki ce don kin shekara baki je gida ba sai ki tafi ba da izinin mijinki ba, bari daga nan zuwa gobe zan ga abin da zan iya yi a kai”.
Ta ce mishi, “To”.
Washe gari suna karyawa Saddiqa ta ce, “Yauwa, Yaya Mus’ab ka ce zamu yi maganar tafiya Misau yau”.
Ya ce, “Kai ni Mus’ab”. Ya sauke cokalin dake hannunshi ya ajiye ya kalli Saddiqa ya ce, “Na ga dai alamar in ban yi maganar tafiya Misau xin nan ba za ayi min tawayen da zai hanani shan ruwan da zai tsriga min a gidan nan. Faxi yaushe kike so mu tafi”.
Ta yi murmushi ta ce, “Ko gobe”.
Ya xan motsa kafaxarshi ya ce, “In kinga za ki tafi ba tare da kin tsaya yi musu tsaraba ba sai mu tafi tunda Juma’a ne mu dawo lahadi, amma ni ina ganin me zai hana ki qara yin haquri kaxan tunda zan fara hutuna na qarshen shekara a qarshen wannan watan, in ma bamu yi hutun duka a can ba sai muyi ko da wata guda ne”.
Ta ce, “To, Ubangiji yasa mu gani”.
Ya ce mata, “Amin”.
Tun daga ranar Saddiqa ta kasance cikin shirin tafiya, kullum da irin lissafin da za ta baiwa Mus’ab, Yaya yi haquri na sake tunawa da gida, kaza da kza ta sake ba da wani sabon lissafin, ko na mance da saka gidan su wance su wance ba a lissafin.
Ana gobe za su tafi Mus’ab ya dawo gida bai samu Saddiqa ba, al’amarin ya yi matuqar ba shi mamaki, don kuwa hakan bai tava faruwa ba.
Ya fito waje ya tsaya don ganin ta inda za ta vullo. Kusan minti talatin da tsayuwa kafin ya hango shigowar motar da ta fita a ciki. Tana shigowa ya juya ya shiga cikin falonshi ya ja ya tsaya yana jiran isowarta.
Fusrkarshi a xaure ya tambaye ta, “Ina kika je?”
Ta tsaya tana kallonshi cikin murmushi.
“Haba Yaya, babu ko sannu da zuwa?”
“An qi ayi miki sannu da zuwa, na aike ki ne? Ko kuwa don kina gadarar za ki yi tafiya sai ya zama kowane lokaci za ki rinqa zarar mota kina fita? Kuma ta kai ma har ba za ki gaya min ba ma sai kawai in zo in tarar bakya nan? Ki bari raina ya vaci da tafiyar ki gani in ban hanata ba gaba xaya in ce na fasa in ga qaryar zumuxi”.
Idanuwanta suka cicciko karo na farko da ta ga irin wannan vacin ran a tare da Mus’ab, ta sunkuyar da kanta qasa cikin rawar murya ta ce mishi, “Ka yi haquri magungunan da kake sha na je sayowa don na duba na ga ba za su kai mu dawo ba, sai na ji tsoron kar su qare a inda bamu san inda zamu same su ba, na kuma ta yi maka waya in gaya maka baka xauka ba”.
Ta kasa danne kukan nata, don haka ta yi maza ta wuce ciki ta barshi nan wurin a tsaye yana kallon wayar tashi. Miss call har shida, duka kuma nata ne. Ya bi bayanta zuwa wurin nata.
“To mene ne kuma na kukan? Da kika yi bayanin na yi wata magana ne? Amma ai kema kin san ba qaramin tashin hankali zan shiga ba idan na zo gida ban same ki ba ban kuma san da fitar naki ba, ai sai in yi zaton gudu kika yi kika barni”.
Ba ta kalle shi ba ta xan yi murmushi don ta san zolayarta yake yi.
“Zo nan ‘yar shatuwallena”.
Ya qanqameta a jikinshi.
“In mun je Misau a gidanmu zamu sauka daga can ne za ki rinqa zuwa duk inda za ki kina dawowa gida kina kwana”.
Ta ce, “To”.
Tare suka tafi gidan Idris suka yi mishi sallama, daga nan suka wuce gidan Liman, shima sallamar suka je mishi.
GARIN MISAU RANAR TALATA DA YAMMA
Direban dake janye da motar su Mus’ab ta yi parkin a qofar gidansu da misalin qarfe huxu da rabi na yamma, Mus’ab yana karanto addu’o’in godiya ga Ubangiji bisa kariyar da ya yi musu suka iso lafiya.
Bai san sanda Saddiqa ta fice daga cikin motar ba, ya shiga gida yana riqe da jakarta da takalminta da ta fita ta bari a motar tana rungume da Gwaggo Habiba tana kuka. Fitowar Malam Abdullahi daga xakinshi cikin hamdala ya dawo dasu cikin nutsuwarsu.
“Sannunku da zuwa, sannunku da zuwa”.
Abin da yake ta faxi kenan. Mus’ab ya ja ya tsaya daga bakin zauren.
“Shigo mana Mus’abu ka tsaya daga can kamar wani baqo?”
Ya bi bayanshi zuwa cikin xakinshi kamar yadda Saddiqa ma ta bi bayan Gwaggonta suka qule cikin nasu xakin.
Mus’ab da babanshi suna gaisawa ita ma Saddiqa ta yi sallama ta shigo, cikin ladabi ta tsuguna tana gaishe shi.
“Iko sai Ubangiji, jiya Habiba take maganarku ashe kuna tafe. To kun zo lafiya ko?”
Ta ce, “Lafiya qalau”.
“Ya ya abokan zama?’
Ta amsa cikin girmamawa, “Duka sun ce a gaishe ku”.
Ya ce, “Madallah, Ubangiji ya yi muku albarka”.
Ta tashi ta fita ta barsu ta sake shigowa, ta ajiyewa Mus’ab kwanon furar da Gwaggo Habiba ta dama mishi da kanta, wanda ba a tava yin hakan ba sai dai tasa ayi mishi.
Saddiqa tana zaune a kicin tana ta taya Gwaggonta aikin abincin da take yi suna kuma hirarsu, duk lokacin da ta kalle ta sai ta ga ita take kallo.
Ta yi murmushi ta ce, “Gwaggo kina kallona kina mamakin rashin zuwana gabanki shekara guda ko?”
Gwaggo Habiba ta ce, “A’a, Saddiqa ba shi bane, aure ai ya wuce haka, ya kan kuma sa ayi abin da ya fi haka. Canzawarki ce take bani mamaki, ban tava zaton za ki zama haka ba, gaba xaya kin sauya min, sai nake tunanin ashe dai yayanku zai riqe aure”.
Saddiqa ta yi ‘yar dariya ta ce, “Uhm! Gwaggo kenan, wai ku me kuka mai da Yaya ne?”
Gwaggo ta tayata yin murmushin ta ce, “Ke dai kawai an godewa Ubangiji ga shi shima……”
Ta fasa faxin abin da za ta faxa xin saboda b ta saba zancenshi da kowa ba. Saddiqa ta gane abin da take nufim, ta miqa hannu cikin ladabi ta karvi ludayin miyar dake hannunta don ta yi mata abin da take son yi, daidai lokacin kuma tana yi mata bayanin Yaya Mus’ab ai masu ganinshi kullum ma suna mamakin yanda ya zama, to balle wanda ya shekara bai ganshi ba, to ya dena komai Gwaggo, baya shan taba balle barasa, duk wani abin da kika sani ya bari.
Cikin jin daxi ta ce mata, “Iko sai Ubangiji, ashe a kan bari?”
Ta ce, “Eh, to shi dai ya daina, na kuma yarda ya daina don baya faxin abin da ba gaskiya bane”.
Wani daxin ya sake kama Gwaggo saboda irin shaidar da matarshi ke bayarwa a kanshi. Ta ce, “Eh, haka dama waxanda suka sanshi nake jin suna faxa, to Ubangiji ya qara shirya mana”.
“Aisha!”
Ta fito ta zo ta same shi. Ya ce, “Gayawa Inna ta yi haquri Baba ya ce muje masallaci magariba ta gabato, sai mun dawo zan zo mu gaisa”.
Ta ce, “To, sai kun dawo”.
Ta koma tana gayawa Gwaggon nata, su kuma suka fita. Malam Abdullahi yana gaba yana ba shi wani labari, shi kuma yana biye a yanayi na girmamawa da amsawa cikin ladabi.
Da daddare xakin Gwaggo Habiba ya cika da jama’a ‘yan sannu da zuwa, qannen Mus’ab mata duk sun zo, ga maqwabta da suka shirshigo ana hira, Abu tana basu labarin irin borin da Saddiqa ta yi ranar da za ta barosu, tana yi kuma tana kuka tare da faxin ni zan biki, ni zan biki ki kaini gun Gwaggona, ana ta dariya.
Ta kalli Saddiqa dake kwance kan qafar Gwaggon nata ta harareta tare da faxin, “Ashe-ashe duk gulma ne da iya shege, jira take yi in tafi in basu wuri ta sa hannu biyu ta rungume al’amarin mijinta, tunda ga shi ba ta zo gaban Gwaggon nata ba sai yau shekara guda har da kwana goma sha takwas”.
Gwaggo Habiba ta yi maza ta ce, “Yanzu kwanakin dawowarki daga can kenan Inna?
Ta yi maza ta ce, “Eh mana, to ko dawowarmu daga aikin Hajji yau wata nawa ne?” Ta hau lissafi.
Gwaggo ta girgiza kai ta ce, “Kai kwanaki suna gudu, Ubangiji dai ya azurtamu cikawa da imani”. Gaba xaya aka amsa “Amin-amin”.
Abu ta sake juyawa kan Saddiqa, hannu tasa ta kai wa kuturinta duka ta ce, “Ke, tashi mki zauna kema kamar kowa, kin zo gabanta za ki yi ta tumurmusar ta, in kin koma wurin miji ki mance da ita. Waxannan mazaunan da kika ajiye in baki zauna a kansu ba mene ne amfaninsu?”
Saddiqa ta soma shure-shure da kuka sai dai hawayen sun qi zubowa.
Gwaggo ta ce, “Ba fa laifinta bane Inna, kuma da kanku kun yi ta faxa bai zauna ba, ga kuma qarin girma da ya samu, to ai ita ma ba ta zauna ba tunda tare da ita yake yin tafiyar”.
Mus’ab ya tsaya daga tsakar gida ya kira Hamida, ta yi maza ta tashi ta fita, ba ta daxe ba ta dawo ta ce, “Anti wai ki je yana kiranki”.
Saddiqa ta xaure fuska ta ce, “Gaskiya ni bana son Antin da kuke ci min, a kirani da sunana kawai”.
Ta miqa hannu ta buxe jakarta tana xiban magunguna. Abu tana faxin, “Ai tunda kika auri tsoho mai tsofaffin qannen da suka haifeki, to dolenki kema ki karvi tsufan”.
Saddiqa ta yi dariya daidai ta xauki kofi da robar ruwan swan tana faxin, “Uhm! Abu kenan, yanzu nan Yaya Mus’ab xin ne tsoho?” Ta fita ta barsu suna dariyarta.
Minti kusan biyar da fitar Saddiqa sai gata ta dwo tana kuka, gaba xaya aka yi tsit! Ana kallon ta.
“Mene ne kuma na wannan kukan da kike yi?”
Tana sharve ta baiwa Abu amsa da cewa, “Wai dole sai na fita mun tafi can gidan mun kwana”.
Da sauri Abu ta ce, “Ke wuce ki shiga xakin uwarki ki hau gadonta ki yi kwanciyar ki ko ‘yar hira ku yi ku xebewa juna kewa kin ji?”
Saddiqa ta yi hanzarin bin umarnin nata ta wuce cikin xakin ta hau gadon ta kwanta, ta barta tana faxanta.
“Haba, ni bana son fitina, fitanannen mutum kawai mara haquri, shekara guda baka kawo yarinya gaban uwarta ba kuma kun zo ba za ka barta ta sake ba?”
Da haka hirar ta watse kowa ya nufi gidanshi.
Washe gari da sassafe Saddiqa ta fito daga wanka kenan tana zaune kusa da Gwaggonta tana shafa, sai ga Abu ta shigo tare da sallamarta.
Ta kalli Abu ta ce, “Gaskiya ko tare dake muka kwana iyakar sammakon da za ki yi kenan ki shigo mana xakinmu”.
Ta zauna kusa da Saddiqan suka gaisa tana kallonta.
“Ni kina da ciki ne?”
Ta ce, “Nima ban sani ba”.
Ta yi tsaki ta ce, “Kar ki sani”. Ta juya wurin Gwaggo Habiba, “Ba ta ce miki komai bane?”
Cikin nutsuwa ta ce, “A’a, ba ta da komai Inna, ta dai ce wai tana da matsalar al’ada. Na ce daga baya kenan hakan ya sameta ko? Tunda ita ai ba mai irin wannan lalurar ba ce”.
Abu ta ce, “To ba sai a karvo mata magani ba?”
Saddiqa ta fito cikin kwalliya sosai sai sheqi take yi, ta yi kyau har ba a magana. Abu sai binta da kallo take yi.
Ta kalli Abun ta yi murmushi ta ce, “Kar ki karvo min magani don ba zan sha ba, Yayana yana kaini asibiti”. Ta wuce ta fita saboda jin isowar Mus’ab, daga fitar nata ta dawo ta zauna.
Mus’ab ya shigo ya nemi wuri ya zauna kan tabarma, ya yi kwalliyar manyan kaya babbar riga da ‘yar ciki da wando na farin yadin voil, ga hularshi ta zauna d ata yi matuqar sakuwa. Tuni qamshinshi ya gauraye ko’ina. Ya shiga yiwa Innarshi bayanai tana sauraro har tana faxin haka ne, abin da baya faruwa a tsakaninshi da ita.
Hatta Abu dake tayata sauraron daxi ne ya kamata. Saddiqa ta tsuguna a gefen Mus’ab riqe da kofin ruwa da kuma magani a hannunta, tana jin ya yi shiru ta yi maza ta ce mishi, “Ga shi ka sha’.
Yasa hannu ya karva ya sha saboda ba zai yi musu da ita a gaban Innarshi ba.
Abu ta ce, “A’a, ni wane irin magani ne wannan kike xura mishi? Ba ki gaishe shi ba ba ki ba shi abin da zai ci ba kin kawo qwayoyi kin ba shi. Haka jiya yana kiranki kika kama xiban qwayoyi. Baka da lafiya ne Mus’abu?’
Kafin ya amsa Saddiqa ta ce mata, “Sai ana ciwo ake shan magani? Kema ba na ga safe da yamma kike sha ba?”
Bai biyewa Saddiqa ya mayar da maganar wasa ba sai ya ce mata, “Bani da lafiya Abu”.
Abu ta kalle shi ta ce, “Wane irin ciwo ne wannan da bai hanaka qiba ba, bai kuma hana fatarka gogewa ta yi kyau ba? Ko kuwa dai irin shagwavarku ta ‘ya’yan yau ku yi ta xirkawa kanku qwayoyi haka siddan?”
Ya ce, “A’a, ciwo nake yi sosai”.
Abu ta riqe baki cikin mamaki ta ce, “To hala ciwon ne ya mai da kai haka?”
Ya yi murmushi ya ce, “Ba shi bane, ina zaune lafiya ne a gidana na yi sa’a Aisha ta karvi lalurata ba ta tayar da hankalinta ba balle nawa ya tashi, ban da haka kuma na daina shan abubuwan da da nke sha, shi yasa kika ga na canza da yawa. Amma ina buqatar ku qara yi min addu’a”.