Showing 12001 words to 15000 words out of 33406 words
Chapter 5 - ABU NAKA Book 3 end Writing by SODANGI.txt
mata jikin, saboda baka da haquri. Ai ni bana son rashin haquri, in aka yi haquri aka bi a hankali ma mene ne wata rana ba sai labari ba?”
Kalaman Abu suka gunduri Mus’ab, ya juya ya fita ya je ya sallami likitan dan ya san Abu ba za ta bar Saddiqa ta fito ba. Ya yi kamar ya bi bayan likitan shima ya yi tafiyarshi don kalaman nata suna sa shi jin kunyarta da yawa. To amma in ya yi haka ita Saddiqa fa?
Ya shiga wurinshi ya gama abin da zai yi ya fito cikin shiri da qamshi, ya sake komawa wurin nasu har lokacin Saddiqa tana kwance, bacci take ko ido biyu bai sani ba.
Ya kalli Abu cikin yanayin murmushi ya ce, “Amma Abu…..”
Bai qarasa ba ya yi shiru, ta gane inda ya dosa. Ta xan taya shi murmushin haxi da cewa, “Babu komai jeka abinka ka dawo za ka zo ka samu matarka ta yi tsaf na kintsa maka ita, ruwan zafi ai shine maganinshi sadidan, sai ko gasasshen nama, farfesu da kuma yaji-yaji, wannan kuwa duk akwai a gidan zan kula maka da ita”.
Ya ce, “To Abu”.
Ya juya zai tafi ta yi maza ta sake kiranshi.
“To zo mana”.
Ya dawo yana sauraron ta. Cikin nutsuwa ta ce mishi, “Zanin gadon naku za ka xauko min in tafiwa uwarku da shi don ya zama mata albishir”.
Mus’ab ya tsuke fuska ya ce, “A’a, Abu ni bana son irin wannan abin da kuke yi tonon asiri ne kawai”.
Nan da nan ta taso cikin fushi, “Za ka bani zanin gadon ne ko sai ka yi dalilin vacin raina a gidanka?”
Ya yi maza ya ce, “A’a, Abu wane ni in vata miki rai”.
Ta ce, “To maza xauko ka kawo min”.
Ya ce, “To”. Ya je ya kawo mata ya juya ya fita ya barta rungume da zanin gadon tana ta faman sanya musu albarka.
Ofis rannan a nishaxi mai yawa Mus’ab yake, ba yau ya fara sanin mace ba a rayuwarshi, amma bai tava samun kansa cikin nishaxin da ya samu kanshi ba jiya.
Kai girma da darajar aure yawa ne da shi, in ban da shaixan ma to me za a yi da matan banza ne? Ya tuna tsawon lokacin da Kawu Gixe ya yi yana fama da shi ya yi aure yana qi, wanda inda tun a wancan lokacin ma ya furta cewar Aishan yake so ya san ba zai hana shi ita ba duk da qanqantar tata.
Sannu a hankali Mus’ab ya yi ajiyar zuciya tare da lumshewar ido, cikin zuciyarshi ya yi tunanin al’amura masu yawa, kafin daga bisani ya saki wani lallausan murmushi, a hankali kuma sai ya furta sunan nata a bakinshi Aisha kenan.
Kafin ya isa gidan da yamma aiken shi biyu, abubuwan amfanin gida yake ta aikewa, cikin zuciyarshi yana tunanin yana zuwa zai tura gidan Idris a kawo mishi Zainab don ta taimakawa gidan nashi.
Abin mamaki yana zuwa sai ya tarar da komai a kintse a kammale a kan tsari, Saddiqa tana zaune a falonta tana cin tuwo miyar kuka da Abu ta yi da naman rago, ga yajin daddawa.
Ya kalli Saddiqa ya kawar da kanshi, har lokacin idanuwanta basu wattsake daga kukan da ta yi ba, iyaka dai ta yi wanka ta kuma yi kwalliya ‘yar kaxan.
Sannu da Abu tana fara’arta ta amsa, sannu da qoqari Mus’abu ka dawo ba?
Ya ce mata, “Eh”.
“To sannu da zuwa, Ubangiji ya yi muku albarka ya rufa muku asiri, ya kuma sa ku gama da duniya lafiya”.
Ya ce mata, “Amin Abu”. Ya juya zai tafi wurinshi.
Ta ce mishi, “Ga abincinka nan a kicin sai ka shiga ka xauka”.
Bai kalle ta ba ya ce, “Aisha ba ta ji sauqi bane Abu? Ki bata ta kawo min mana”.
Ba ta tanka mishi ba don haka ya biya ya xauka ya tafi da shi wurin nashi.
Kwana biyu a jere Abu tana cikin hidimar tarirayar Saddiqa, kulawa da shagwava, har dai Mus’ab ya gundura da abin saboda ko kusa da ita ba ta barinshi yaje.
Ya shiga kicin inda ya hangeta tana gashin nama, ya same ta cikin nutsuwa ya ce mata, “To wai ni Abu ni kuma ni shi kenan ne?”
“Shi kenan kamar ya ya?”
Ta yi tambayar tana kallon shi. Ya xan yi murmushi tare da miqa hannu wajen tayata aikin da ya tarar tana yi.
“To ba kema na ji kiuna ce mata ba cutarta na yi ba, kuma ban zalunce ta ba?”
Ta ce, “Eh”.
Ya ce, “To tunda haka ne ba sai ki lallavata ki xan rinqa turo min ita ba, kina gani fa har yanzu ko magana na yi mata ba ta amsawa”.
Abu ta yi dariya ta ce, “Naqi in lallava maka itan, ai sai daxin ya yi maka yawa, randa na tafi na barku ku biyu a gidanku ka san yanda ka yi ka lallava abinka”.
Satin Abu guda a gidan ta sanar da Mus’ab shirinta na komawa Misau a kwanaki biyu masu zuwa a gaba.
“Da sauri haka Abu?”
Ta yi murmushi ta ce, “Ai na zauna muku Mus’ab ina laifi, in ban da gidanku kai da matarka ina za ni in yi wannan zaman?”
Cikin nutsuwa da girmamawa ya ce mata, “Ai mun gode miki Abu, Ubangiji ya qarawa rayuwarki albarka”.
Daga gefenta Saddiqa ta yi magana a yanayi na sanyin jiki.
“Zan biki gida Abu”.
Abu ta waiwaya ta kalle ta, tuni har hawaye sun fara zuba a idanuwanta.
“A’a, Saddiqa dena wannan kukan ki share hawayenki ki ji abin da zan gaya miki, ki bini gida Misau kina so mujewa iyayenku da abin da zai baqanta musu rai ne?
Ai ni jakadiya ce ta alheri a garesu, zan je musu ne da labari mai daxi mai faranta musu rai. Na zo na same ku lafiya, na kuma barku lafiya har ga albishir mai daxi zan je musu da shi”.
Ta ci gaba da maganarta da cewa, “Aure ai girma ne, girma kuma haquri ne, don haka ki yi haquri ki zauna tare da mijinki, ki yi mishi biyayya, yi na yi bari na bari, ba ki ga irin kai kawon da yake yi a kanki ba? Yana sonki, to in kin tafi ki barshi da wa Saddiqa? Kar ki yi haka”.
Mus’ab ya tashi ya tafi ya basu wuri. Tana ganin fitar Mus’ab ta qara mai da hankalinta wurin Saddiqa.
“Sa hannu biyu ki rungumi al’amarin mijinki, kar ki yarda ki yi wasa da aurenki, kullum ki je ki gaishe shi, kullum ki karkaxe mishi shimfixarshi, kullum ki yi mishi abinci mai daxi. Ki sa ido sosai a kan shi, kar ki yarda hannunshi ya tava wata mace in ba ke ba ce, kar ki yarda ya mai dake qaramar mace, kina gida a zaune shi yana can wurin matan banza a waje. In tafi dake gida to ki barwa wa shi? Ki barwa matan bariki ko? Ke bakya kishi ne?”
Ta tsareta da ido.
“Ni kuwa ai kishi ne dani, ban tava barwa wata mace mijina ba shi yasa ma bayan rasuwarshi ban yarda na sake yin wani auren ba, sai na yi zamana kawai saboda na fi so ko a lahira a ce shine mijina na aljanna cikin yardar Ubangiji”.
Yanda Abu ta yiwa Saddiqa nasiha da kalamai masu daxi, haka ta zaunar da Mus’ab ta yi mishi irin wanda za ta yi mishi, sai dai shi kam ba irin rarrashin da ta yiwa Saddiqa ta yi mishi ba.
“Kar ka zalunceta ka yi haquri da ita, ka yi mata adalci, ka sani ba ta da kowa a garin nan in ba kai ba”.
Ya ce, “To Abu, na gode Ubangiji ya saka miki alherinki a gareni”.
Ta yi murmushi ta ce, “Amin Mus’abu ya saka mana tare”.
Duk kalaman da Abu ta yiwa Saddiqa na rarrashi da kwantar da hankali, da yanda zuciyar Saddiqan ya karvi maganganun da ta yi mata bai hana zuciyarta ta karaya ba har ta yi ta zubar da hawaye tana kuka tare da faxin, “Zan bi ki Abu”. A lokacin da ta ga ana ta fitar da tsarabar da Mus’ab ya yi mata ana jibgawa cikin motar da za ta mai da ita gida Misau.
GARIN MISAU A RANAR ALHAMIS DA YAMMA
Gwaggo Habiba tana cikin kicin xinta tana qoqarin dama kunun tsamiyar da za suyi buxa bakin azumin nafilan da suke ita da mijinta.
Tsayuwar motar da ta ji ‘jiiyim’ kusa da qofar shigowa zauren gidan yasa ta fitowa da sauri ta zo ta tsaya a tsakar gidan tana kallon hanyar shigowa gidan, cikin zuciyarta tana faxin wannan motar dai da qyar in ba Inna ta kawo ba.
“Assalamu alaikum”.
Muryar Abu cikin fara’a da murmushi ta shigo gidan tamkar ba ta wahala a tafiyar tata ba.
“Lah! Ashe kuwa ke ce Inna, Inna sannu da zuwa, dama tunda na ji tsayuwaar motar dama na ce wataqila kece a ciki, sannu da zuwa, Inna kun shawo hanya”.
Suka nufi xakinta tana shimfixa mata tabarma tana faxin “Tun shekaran jiya muke sa rai dake a gidan nan”.
Abu ta yi murmushi irin wanda ta daxe ba ta yi ba.
“Gidan Mus’abu fa na je a yau xin ma da ya ya na baro shi? Duka yaron nan ki gani in ya gama shigo da kayan tsarabar nan ki samu abin da kika ba shi ya ci, duk da dai ba yunwa muke ji ba”.
Gwaggo Habiba ta yi murmushin jin daxin yanayin da ta ga mahaifiyarta a ciki, ta nufi wajen direban tana faxin “Wannan doguwar tafiyar da kuka yiwo Inna ki ce bakwa tare da yunwa”.
“A’a, baya fa ba ta kaxan, kar dai a ce xan fitar nan da na yi ne Inna ta dawo a bayana?”
Abu ta yi maza ta ce mishi, “Ai kuwa dai nice malama, hala tarin tsarabar da ka gani a tsakar gidanka ne yasa ka gane hakan?”
Ya ce mata, “Eh”.
Ta yi murmushi ta ce, “Aikin Mus’abu kenan”.
Da daddare bayan sallar isha’i Gwaggo Habiba da Abu suna falonta, sun gaisa sun ci abinci suna hira. Ta qosa qwarai Abun ta ba ta labarin yanda ta baro Saddiqa, ita kuma sai ja mata rai take yi.
Malam Abdullahi ya shigo falon ya same su a dalilin ya dawo daga sallar isha’i.
“Gwaggo sai yau?”
Ta yi dariya ta ce, “To yau xin ma da ya ya? Ai dagewa kawai na yi na ce in dai ba tayaku zaman auren naku zan yi ba, ai gara ku barni nima in koma wurin iyalina”.
Malam Abdullahi ya yi dariya, ita kam Gwaggo Habiba sai murmushi take yi, ya yin da kanta ke sunkuye.
“To ya ya kika baro su Gwaggo?”
Ta yi maza ta ce, “Sai alheri, ga tsaraba can ya ce a kawo a rabawa ‘yan’uwa da maqwabta, in kuma gaya maka cewar kai da Kawunshi ku yi shirin tafiya aikin Hajji, ni kuma ni da uwarsu zamu je Umara na ce mishi a’a, ni kam Hajji zan ce don ban sauke farali ba, ga kuma girma ya riga ya kama ni, gara in je tun ban kai ga ba zan iya ba. Ya ce, to sai yanda muka shawarta”.
Cikin farin ciki Malam Abdullahi ya ce, “Eh to, Gwaggo ai sai ku je Hajjin ke da Yaya Gixe mu sai mu tafi Umarar da Habiba”.
Abu ta ce, “A’a, ni da kai dai mu yi Hajji, ita da xan’uwanta suyi Umarar, ai tafiyar da kai za ta fi min dai-dai”.
Malam Abdullahi ya ce, “To, Ubangiji ya yi musu albarka”.
Abu ta yi ta faxin “Amin-amin”. Har ya tashi ya fita saboda sallamar da aka yi da shi.
Gwaggo Habiba dake zaune shiru a gefe ta xago ta sake tambayar ta, “To ya ya kuwa Saddiqa Inna?”
Abu ta kalle ta cikin murmushi ta ce, “Duk wannan labari da nake bayarwa bai isheki ba sai kin ji na Saddiqa ita kaxai? To lafiyarta qalau na barota tana ta hidimar aurenta, ta ce a gaisheki, ga kuma saqo ta ce in kawo miki”.
Cikin sauri Gwaggo Habiba tasa hannu ta karva tana warwarewa ta ga abin da ke jikin zanin gadon ta yi maza ta rufe tana salati, cikin sanyin jiki ta kalli Abu.
“Irin wannan cin zarafin ya yi mata Inna? Wannan ai rashin tausayi ne”.
Abu ta galla mata harara.
“Ke kam ai ba za ki yaba mishi ba, ina can ne fa abin ya faru amma baki kalli haqurin da ya yi da ita ba, kin kuma san a kan ‘yarki ne maza suka fara yin haka. Ya dai ce in gaishe ki in kuma roqa mishi ke ki yafe mishi abubuwan da ya yi miki”.
Ta miqe tana tafiya tana yafa zanin rufar ta.
“Ni gidana za ni in kwana, in yara sun shigo ki xora musu kayana su biyoni da shi”.
Gwaggo Habiba ta bi bayanta tana faxin, “Ki huta gajiya Inna, sai na zo miki ban gajiya”.
AJAKUTA
Mus’ab yana zaune a qofar gidanshi cikin shirin yin alwalar sallar magariba, ya kalli agogon hannunshi bayan ya kalli yanayin sama, zuciyarshi ta raya mishi da sauran lokaci.
Nan take ta sake raya mishi yanzu kam cikin yardar Ubangiji in har komai ya tafi daidai kamar yanda ake fata, to Abu ta isa gida tana can tana bai wa su Inna labarin Aisha ta kai budurcinta, ya san babu wani labari da zai fi wannan daxin bayarwa a wurin Abu.
Ya xan yi shiru kaxan cikin wani tunanin, zuciyar tashi ce dai take sake tuna mishi da irin wunin da ya yi tare da Saddiqa bayan tafiyar Abu a ranar cikin kuka da takura mai yawa, wanda ya yi dalilin da ko aiki bai samu damar zuwa ba.
Son shi ne ba ta yi yasa take waxannan abubuwan ko kuwa? Ya yi maza ya kawar da wannan tunanin saboda dalilai guda biyu. Na farko mu’amalarshi da ita a farko, yanda ta bijirewa auren Sadisu ta nemi a barta kawai ta yi mata yanda ita da kanta ta gayawa Gwaggonta ita xin shi take so, da yanda ita da kanta ba tare da ya nemi ta yi mishi hakan ba ta voyewa Abu halin da suke ciki a lokacin da ta zo gidan.
Waxannan dalilai guda biyu sune suka qarfafa zuciyarshi ya xan ji sanyi, ya kuma qarfafa zuciyar tashi a kan himmatuwa wajen ganin ya shawo kan lamarin nashi.
Hadari ya taso tare da iska mai tsanani, wanda ya yi dalilin da liman ya bayar da umarnin haxa jam’in magariba da isha’i a masallacin.
Ya shigo gida daidai ruwan saman yana saukowa, zuciyarshi ta yi mishi daxi saboda sanin da ya yi Saddiqa matsoraciya ce. Wurinta ya fara isa bayan ya gama rurrufe qofofin gidan.
“Kin yi sallah kuwa?”
Ta amsa mishi da eh. Ya wuce ta yana tunanin irin takurar da ya ga ta yi, ina ma dai NEPA su xauke wutar lantarkin. Yana yin wannan tunanin ya miqa hannu kan mitar gidan ya kashe wutar, duu ya bayyana a ko’ina. Ya wuce ya nufi wurinshi.
Bai daxe da shiga wurin nashi ba ya ji motsin Saddiqa a cikin falon nashi.
“Waye aa nan?”
Ya yi tambayar don ya gane maganar ne ba ta son yi. A hankali ta ce mishi, “Nice”.
“Kina son wani abu ne?”
Ta xan yi shiru kafin ta daure ta ce mishi, “Wuta aka xauke ni kuma bana son duhu “.
Cikin nutsuwa ya ce mata, “Eh, Aisha duhu ai ba shi da daxi”.
“Ko za ka sa a kunna Jean?”
Ya ce, “To, sai dai ruwan ya yi yawa bai kamata in fitar da shi a cikin ruwan ba, saboda kuna Jean ai kinga babba ne mu xan bari mu gani ko ruwan zai yi sauqi”.
Ta yi shiru.
“Ko kina tsoro ne?”
Ta ce mishi, “Eh”.
Ya yi kamar ya ce ta shigo wurinshi sai ya fasa, ya fito ya zo inda take ya kama hannunta ya ce, “Muje in rakaki wurinki”.
Da hikima da lallami ta yarda