✍ 👨‍⚕️ Doctor Shazim👨‍⚕️ Daga alƙalamin KHADIJA ( M ) ABDULWAHAB KAINAAT... ✍ *_KING AND QUEEN WRITING CHAMBER_* Proud to my first novel Ina alfahari da kasan cewar wannan littafi na farko agareni 📚 Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah ma ɗaukakin sarki mai kowa mai komi da ya bani ikwan rubuta wannan littafi. Ya ubangiji al'arshe kabani ikwan rubuta abin da zai amfani muslinci da muslmai, ka bani ikwan rubuta abun da zai amfaneni duniya da lahira 🙏 ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ ✖️ Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na littafin nan ba ta kowace hanya, ba tare da an nemi izni a wurina ba. idan kunne ya ji jiki ya tsira! Wannan labari ƙagegen ne ,sannan ban rubuta shi ba da niyyar muzanta wani ko cin mutuncin wani ba, duk wanda ya ga wani abu yayi shige da halayyar shi arashi ne. Season one Free Episode 1_2 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ_ 12 June 2003 _Ƙarfe 12:30 Am Yanayin sanyin da gari yayi, da iskar da ke kaɗawa wanda ya haddasa ganyayyakin bishiyu yin rangaji, tare da ba da wata sassanyar iska. Yadda sauran ruwan saman da ƙasa bata gama shanyewa ba, da wanda yake gudu acikin kwalbatoci zai tabattar maka da lallai damuna ta kama. Shiru anguwar take sai kace ba kowa a cikin ta saboda yanayi na dare haɗi da damuna, duk da daman ba'a cika samun mutane na kai kawo a cikin irin waɗannan anguwannin ba ko da kuwa da rana ne, sai hasken bulbs daya haske anguwar haɗe dana street lamps kaɗai ake gani. Anguwace irin ta masu faɗa aji a cikin ƙasa, domin kuwa daga shahararrun yan kasuwa sai manya a gwamnati ke a cikin ta. Motace ta shararo da gudu daga kwanar dake hannun dama a cikin anguwar, yayin da wasu ba ƙaƙen motoci guda huɗu ke biye da ita. Gudu motar take sosai har ta fita daga cikin anguwar ta hau babban titi, still wa ɗannan moticin na biye da ita a baya Daga irin gudun da mamallakin motar ke yi zaka san cewa yana gudu ne tsakanin rayuwa da mutuwa. ta mirror ɗin motar yake hangen fitilar motocin da ke binsa, yana gudu motocin na bin sa har suka hau kan titin da zai fitar da kai daga garin, gudu suke har suka fita daga garin, in ban da salati da neman ɗauki daga ubangiji babu abun da mai motar nan ke yi. domun shi a yau ya san tashi taƙare, saboda ya galabaita a dalilin dukan daya sha, tukin neman ga garar sa yake, ƙarfinsa ya kusa ƙarewa, dubawa yayi ta cikin mirror motar amma bai ga alamun waɗannan motocin ba, tunani ya fara to ko ya tsre masu ne, amma duk da haka bai fasa gudun da yake ba, wani mummunan Bugun da yaji an kaima ma motar shi ne yasa shi fahimtar ce wa kenan wata hanyar suka bi amma suna biye da shi mirror ɗin motar ya kalla, amma sai yaga ba waɗan cen motocin ba ne, wata ƙatuwa truck ce ke binsa yanzu saɓanin waɗancen motocin, ba shiri ya karya kwana ya faɗa cikin daji, gudu kawai yake amma ba wai ya san inda yake dosa ba ne, tsintar kansa kawai yayi a bakin wani ƙaton rami mai zurfin gaske, dole tasa shi taka birki ba dan ya shirya ma hakan ba sai dan baya da wani zaɓi, kawai ya sadakat kwanan shi a yau sun ƙare. bai gama wannan tunanin ba yaji me truck ɗin ya kaima motar shi wani mumunan bugu wanda ya haddasa mashi buguwar kai nan take ya suma. Sake ja da baya me truck ɗin yayi ya kaima motar wani bugun wanda yafi na ɗazun, nan take motar tayi cikin ramin, ko karar faɗawar ta ba'a ji saboda tsananin zurfi irin na ramin . parking me truck ɗin yayi a bakin ramin tare da leƙa ramin ta hanyar hasken motarshi daya bari a kunne. wani irin ramine me zurfin gaske, wanda tsananin zurfin shi zai sa ka kasa ganin abunda ke ƙasan ramin. dariya yayi me sauti da amo tare da cewa yanzu kam nasan zan samu cikwan kuɗina domin wannan sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba. komawa yayi cikin motar shi, anan yasamu wayar shi na ringing ɗaukar wayar yayi boss shine sunan daya bayyana a jikin screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi tare da sa wayar a handspree tun kafin yace wani abu me kiran nashi yace " Ina fatan kagama dashi? " answer ya bama boss ɗin da cewa " ai wannan tashi ta ƙare sai dai uwar shi ta haifi wani amma ba dai shi ba, dan a yanzu yana can ya gana da magabatan sa" "amma naji daɗin jin haka" boss ɗin ya faɗa . "amma boss ya kake ganin za'ayi da matar shi da yaran shi ?" me truck ɗin ya tambaya. "Kar ka damu da wannan big boss. zaiji da komai , yanzu dai katuraman da account number ka domin natura maka Sauran kuɗin aikin ka " "thank you so much boss" me truck ɗin ya faɗa. boss ɗin ya ce "don mind" Kit ya kashe wayar account number ya turama boss tare da yima motar key ya bar wajen WANNAN KENNAN. 🌹~ _Kainaat_ ~ 🌹 Gida ne matsa kaici shi ba ƙarami ba shi kuma ba babba ba chan sosai ɗan dai dai. gida ne namasu rufin a siri kuma yan boko naji da faɗa. Painting ɗin gidan ya kasance white and blue color ne, haka ma get ɗin gidan blue and white ne. daka shiga compound ɗin gidan zaka fara cin karo da ɗakin mai gadi daga hannun hagu Sai parking lot daga hannun dama wanda ke ɗauke da rides masu kyen gaske da tsada na fashion a ƙallah za su kai guda 5 a parking lot ɗin. Sai garden mai kyen gaske ga suke suke masu ɗaukar hankali. Sai boys quarters dake bayan part ɗin masu gidan. Masha Allah na furta a ya yin da nayi arba da parlorn gidan wanda aka ƙawata shi da furniture's masu kyen gaske da tsada, komai na cikin parlor onion and pitch color ne, daga gefen daman parlor twin up stairs ne me kyau Sai kitchen dake gefan hagu wanda yake haɗe da store kusa da shi kuma dining area ne mai ɗauke da chairs guda 7,Sai wani ɗan corridor daga gabas ɗin parlor mai ɗauke da 4 bedrooms, daga chan kuma up stairs ɗin ya kasu kashi 3,part ɗin matar gidan dake haɗe dana yaranta ke hannun hagu Sai na me gidan dake hannun dama sai chan gaba na yaron gidan ne namiji. daga part ɗin dake hannun hagu naji anata kwala Kiran Aaimah! Aairah!! Aairah!!!. Wata kyakyawar mace ce tafito daga ɗaya daga cikin bedroom ɗin ta nufi wanda ke kallon nata ta na cigaba da Kiran " Aaimah " da "Aairah". Fara ce sosai tana da jiki ba sosai ba ita ba rammama ba Ita ba mai ƙiba ba a kalla zata kai kimanin shekara 50 . jikin ta sanye yake da sleeping dress riga da wando masu santsi yana yi da Pakistan dress pink color. ba ƙaramin kyau suka yima surar jikinta ba. "Kun kuwa san ƙarfe nawa" ta faɗa yayin da take tura ƙufar bedroom ɗin ta shiga. Masha Allah na faɗa domin kuwa bedroom ne me kyan gaske, komai na cikin sa ya kasan ce pink and white color ne , yaji kaya masu kyan gaske bawai cike yake da kaya ba. bed ne sai bed side drawers, sai dressing mirror gefen shi kuwa wardrobe ne wanda clothes set ne ciki sai jikin ƙofar shigowa kuma jere suke da ƙofar bathroom sai wani ɗan corridor inda ya kasan ce laundry basket ne da shoe rag ne sai bag hanger , bags ne masu kyau na gayu dana school kowace bag set biyu ce kuma color ɗaya. turus ta tsaya ganin ta kwance har yanzu akan bed, " Aairah lafiya kike kuwa da baki tashi ba ina Aaimah take Ita ma, ko yau baku zuwah school ne iye. " Ƙarar buɗe ƙofar bathroom taji juyawa tayi, wata kyakyawar budurwa ce ke tsaye jikinta ɗaure da towel iya gwiwarta jikin ta sai raɓar ruwa yake, alamar wanka tayi, fara ce Ita ma kamar mahaifiyar ta tana da dogon gashi har ƙugunta, ga matsakai tan idanu masu ɗauke da brown eyeball da zara zaran eyelashes, hancinta ma ɗan dai dai dogon bamai yawa ba sosai, ga small mouth me ɗauke da pink lips, tana da shape mai ɗaukar hankali sannan tana da tsayi amma ba sosai ba chan. masha Allah kawai zamuce, akalla zatai kimanin shekara 18 a duniya. "Ok kintashi kenan Aaimah ce kenan bata tashiba." "Wallahi mom tunɗazu nake tashin ta amma taki tashi wai Ita batagaji da bacci ba." "Tafi ke ki shirya, rabu da Ita yanzu ai zata tashi ba dan halinta ba " mom ta faɗa a lokacin da ta ƙarasa jikin bed ɗin , "Aaimah! Aaimah!! wake up, its time for school , ko kina sone kuyi late ne iye autar mom . " "Uhm uhm uhm haba mom wai miyasa kike cema Aaimah auta nifa" Aairah tafaɗa yayin da take buga ƙafa tan turo baki haɗe da rike ƙugu. ai kuwa nan Aaimah ta tashi tana ma Aairah dariya harda gwalo, dama duk abunda mom ke faɗa tana ji, tashi ne kawai bata yi ba "mom kinganta ko dariya take man harda gwalo"Aairah ta faɗa sai wani turo baki take da hura hanci. "Ke da'alla rabu da Ita, ai kema autah ce" mom ta faɗa tana dariya ganin yarda Aairah kema Aaimah dariya harda tsalle, "oho dai ai ni aka fara cemawa" mom ta katse ta da cewa " To ya isa haka maza kushirya ABIE na nan yayi shirin tafiya , kunsan dai yau zai koma wurin aiki abuja." "to shikenan mom gamu nan zuwa" har suna haɗa baki wurin faɗin haka. fita Mom tayi daga bedroom ɗin haɗe da jawo masu ƙofa, ta shi Aaimah ta yi ta nufi bathroom tana faɗin my twin sister dan Allah kifito man da uniform ɗina kafin na fito"Aairah ta ce " to sannu mom kinji koh" "haba twin sister dan Allah fa nace" Aaimah ta faɗa tana lan gwabar da kai , Aairah ta ce " hmmm sai shegen daɗin baki kamar ta Allah" " Pls twinee" Aaimah tasake faɗa "shikenan ba dan halinki ba"Aairah ta faɗa tana ya tsine fuska,murmushi Aaimah tayi tana faɗin "yawwa twenny Ni na san nafi kowa Sa'ar Yar uwa a duniya shiyyasa nake alfahari dake baki sani ba fah irin daɗin da nake ji Idan naganki kusa dani ba" , baki kawai Aairah ta saki tana sauraron ƙar yar da Aaimah ke shirga mata. "wallahi Aaimah kin bani ki rinƙa jin tsoron Allah , ko kunyar ƙarya ba kyaji " gwalo Aaimah tayi hadi da jawo ƙofar bathroom ta shige, dariya kawai Aairah tayi haɗi da girgiza kai tana faɗin " Allah ya shirya ki Aaimah da karya" wurin dressing mirror ta wuce Vaseline ɗin dove ta shafa tare da farar powder kaɗan ta shafa a fuskar ta sai kwalli da tasa ma eye's ɗin ta, wurin wardrobe ɗin su ta wuce buɗewa tayi , kaya ne masu yawan gaske komai set biyune, wurinda hijaban su suke daban haka ma sleeping dress ɗinsu da ban suma dogayen riguna da atamfofi wurinsu suma da ban haka ma uniform ɗin su na school dana Islamiyya, uniform ɗin school ta ɗako masu set biyu itada Aaimah wurin bed ɗin su ta koma da kayan a hannun ta domin ta shirya. shaf shaf ta shirya cikin uniform ɗin ta masu ɗan karan kyau, riga ce da skirt, rigar white color ce, skirt ɗin wanda ya kasance iyakarsa gwiwarta pink color sai sock's fara me ratsin pink daga sama sai top wacce itama ta kasan ce pink color sai Yar baby hijab it kuma white color ce, wurin corridor ɗin su ta nufa shoe da school bags ɗin su ta ɗauko masu, white color ne takalman snikers sai school bag pink color. "Sis kin ɗauko man nima uniform ɗin" Aaimah ta faɗa wacce fitowar ta kenan daga bathroom. amsa Aairah ta bata da "Eh Amma fa kiyi sauri ki shirya kona tafi wurin Abie na barki" wurin dressing mirror Aaimah ta nufa tana faɗin" sorry karki damu yanzu zan shirya ki bani 5 minute insha Allah " shaf shaf itama ta shirya cikin nata uniform ɗin Masha Allah Itama ba ƙaramin kyau tayi ba saboda itama Aaimah kykyawa ce sosai a bun da kawai Aairah zata nuna mata tsayine shima ba wani finta tayi ba sosai ka mannin su ɗaya da Aairah tsayinne dai kawai banbancin su shima sai insun jera zaka fahimci hakan. Snickers ɗin ta itama ta saka tare da amsar bag ɗinta dake hannun Aairah a tare suka fita daga bedroom ɗin direct part ɗin Abie suka nufa, hannun su cikin na juna suka shiga parlor ne mai matuƙar kyau, dan yafi na down stairs kyau da haɗuwa domin ya ƙawatu da expensive furniture's, komai na cikin parlorn sky blue ne da fari. wani kykyawan matshin tsohone wanda Akallah zaikai ki manin shekara 60 a duniya, yana da haske shima sosai, zaune yake akan 2 siter " abie " kenan tea yake sha wanda mom ta haɗa mashi, sallama sukayi tare da ƙarasawa ciki suna faɗin "abie ina Kwana antashi Lafiya "suka faɗa yayin da suke samun wuri kusa da abie suka zauna, "lafiya lau alhmdllh my daughters ina fatan kuma kuntashi lafiya" "Alhmdllh abie " suka faɗa, Abie ya ce "to Masha Allah haka ake so" "amma Abie zaka tafi yau shine baza ka yi breakfast damu ba" Aaimah ta faɗa tana turo baki "Sorry my daughters duk da ma laifin kune tunda tun ɗazu ya kama ta ace kuntashi amma kuka yita bacci gashi ni kuma sauri nake, ai daya ke bajima wa zanyiba wannan time ɗin, zandawo very soon kunji koh." "shikenan abie Allah ya dawo da kai lafiya"da ameen abie ya amsa tare da kai cup ɗin tea bakin sa. "to uwayen surutu atashi aje ayi breakfast time na kurewa, abar shima abie ya samu ya gama nashi breakfast ɗin karya makara "mom ce ke magana wacce fitowar ta kenan daga bedroom ɗin abie hannun ta riƙe da jakar kayan shi da zaiyi tafiya da Ita "Uhmmmmm haba mom dan Allah kibari muƙara sa yin ban kwana mana" Aairah ta faɗa tana turo baki, dariya kawai Abie ke masu "Kinci gidan ku nace kutashi kuyi breakfast yana chan baba larai tashirya maku, nima abarni nayi ban kwana da mijina" "ah mom sai kice mutashi soyayya ta motsa, to bari muyi ta kanmu," Aairah ta faɗa tareda yin dariya "Kunci gidan ku jairan banza marasa kunya kawai "abie ne ya faɗa tare da yi masu daƙƙu wa dariya suka kwashe da Ita, " abari muga soyayya tukunnan sai mu tafi" Aaimah ta faɗa hadi da gyara zaman ta, wurin su mom ta nufo ai bashiri suka mike da gudu suka fita daga part ɗin suna dariya....... "Kaga man jairan yara marasa kunya"mom ta faɗa yayin da take zama kan hannun sofa da abie ke zaune, dariya abie yayi tare da cewa "Allah ya shirya, dan inkika biye ma su Aairah sai su samaki ciwan kai" "wallahi kuwa ai abdallah ne kawai maganin su, yama shigo kuwa" mom ta faɗa. Aa ina jin baigama shirin zuwa hospital nasan daya gama zai shigo muyi sallama, haka ne kuma mom ta faɗa tare da cewa" yanzu dai ba wannan ba yaushe zaka dawo? " "2 week's kawai fa zanyi " "ashe kuwa kashirya zuwa dani abuja kenan Indai 2 week's zakayi ƙafata ƙafarka, murmushi abie yayi haɗi dacewa "to su fa yaran ki kibarma wa su iye" " dan Allah kabar ma maganr yara Sai kace wasu yan goye saunawa Nake zuwa abujar batare da su ba" Assalamu Alaikum sukaji an faɗa katse labarin dasuke sukayi haɗi da amsa sallamar, wani matashin saurayi ne kyakyawan gaske wanda ko ba'a faɗa maka waye shi ba kamanin sa da abie zaitabbatar maka da cewa ɗan sane, DR. ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM kenan matashi maiji da waye wa ga ilimi both side boko da Islama, farine shi ma sosai yana da tsayi dai dai misali gashi irin mazannan ne masu motsajiki dan yana da kirar jiki mai kyan gaske ga ƙasumba irin ta yan gayu domin kuwa daga ganin ta kasan tana shan gyara, jikin sa sanye yake da uniform ɗin sa na aiki hannun sa riƙe da briefcase ɗin shi, ƙarasawa ciki yayi wuri ya samu ya zauna,yana faɗin " inakwana abie mom ina kwana", lafiya lau alhmdllh suka amsa mashi abie ya ɗaura da cewa "har anyi shirin fita aiki kenan? " " eh abie dayake ina da shiga thearter ƙarfe 10:00," "masha Allah , Allah ya taimaka," "ameen ya rabbi , abie dawuri zaka wuce ne yau? " "eh dawuri zan wuce saboda gobe tunda safe ina da shiga court ‍, amma insha Allah bazan jima ba zan dawo ina ma tuna nin two days zanyi na dawo" "to shikenan abie Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya" da ameen suka amsa mom na faɗin "breakfast ɗinka nachan dining, sannan su Aairah na nan kawuce dasu school in baza kayi late ba, "amma mom mi ya hanasu bin school bus yau? " " uhm kai dai bari, shegiyar shiririta ce irin tasu , kasan halin su yanzu haka idan akace maka suna can basu kammala breakfast ɗin su ba ba'a gardama, narasa gane shiririta irin tasu Aaimah wallahi yara sai kace ba masu jini ba ajiki suyita abu kamar basu sanyi, Allah dai ya shirya su, ameen abdallah ya faɗa tare da cewa "bari naje nayi breakfast ɗin sai na dubasu" "ok muma ga mu nan sakkowa"tashi yayi ya fice ya nufi dining, tunkafin ya isa yake jin hayaniyar Aaimah da Aairah sunata zagaye dining Aairah ta ɓatama Aaimah baby jiba da tea itakuma Aaimar nacewa saita rama shine fa suke ta zagaye dining baaba larai sai cewa take su bari amma ina kamar ƙara zugasu take. Tsawa abdallah ya daka masu tare da cewa "ashe ku shasha shune ban sani ba, zaku dawo ku zauna ko sai ranku ya baci sakarkarun banza da wofi, wallahi kushiga hankalin ku kullum girma kuke amma ɗabi'un ku sak na yara. bashiri kowace cikin su ta nemi wurin zama, baaba larai ce ta matso zatayi serving ɗin ya abdallah tana faɗin " abdallah an tashi lafiya" "lafiya lau baaba, ina kwana," Alhmdllh tace "mizan zuba maka" "a'a kibarshi kawai baaba Aairah ta zuba man," "to shikenan ni bari nawuce kitchen" Aairah yace ma tayi serving ɗin sa ita kuma Aaimah tayi sauri ta chanzo hijab ɗin ta tunda sungama breakfast ɗin su , to tace haɗi da tashi ta nufi bedroom ɗin su. Abie ne ke saukowa shi da mom hannun ta riƙe da jakar kayan sa , "abie kafito " ya abdallah ya faɗa ayayin da yake kar ɓar jakar kayan a hannun mom,yana faɗin "abie muje koh" yayin da yake fita daga parlorn , bayansa suka bi har da Aaimah wacce sakowarta kenan daga bedroom ɗin su dataje chanzo hijab,"adawo lafiya, alhaji Allah ya kiyaye hanya yakai ka lafiya ya dawo da kai lafiya" "ameen ya rabbi baaba larai" abie ya bata amsa, fita sukayi compound ɗin gidan wurin motar abie suka wuce wacce baka driver ya daɗe da fito da ita dan har ya abdallah ya saka ma abie kayan shi a booth ɗin motar bankwana suka shigayi su Aairah har da hawaye abie sai lallashin su yake. abdallah ne yace" dan Allah abie ka kyale yarannan sai sun sa kayi late", "kuyi hakuri bazan jimaba zan dawo may be na dawo nan da 2 days kunji" "to abie Allah yatsare hanya" ameen abie yace abdallah ne yace "to kuwuce ciki ku ɗauko school bag ɗin ku na ajiye ku a school, abie Allah ya tsare" ya faɗa haɗi da tasa keyar su Aaimah zuwa ciki, mom ce ta matso kusa da abie tana cewa "wallahi barrister kamar kar ka tafi nake ji" " tofah yara shagwaɓa uwa shagwaɓa toni wazan kama" ya faɗa yana dariya "uhmm kaima kasan wanda zaka Kama" ta faɗa tana ɓata rai, "yau naji shiyyasa kenan kika ƙi magana sai da yaran ki suka shige ciki zakiyi man adawo lafiya , ashe shagwaɓa za'ayiman ban sani ba ", mom tace "ok hakama zakace "ta faɗa haɗi da juyawa zata nufi ciki , hannun ta abie ya riƙo yana faɗin "Sorry kubrah, kema kinsan wasa nake , karki damu bazan jima ba zan dawo insha Allah" "to shikenan Allah ya dawo man da kai lafiya" ameen abie ya faɗa yayin da yake shiga cikin mota sit ɗin baya ya zauna bala driver na gaba key yayima motar, hanu mom ke ɗaga ma abie shima yana ɗaga mata,suka nufi gate,buɗe masu gate baba mai gadi yayi yana faɗin a dawo lafiya " mom na nan tsaye har sai da motar tafita daga gidan sannan ta juya tashiga ciki , dasu Aairah tacikaro suma sun fito a dawo lafiya tayi masu tawuce ciki abdallah ne ya sauko daga upstairs part din sa Yana ce masu ku wuce mu Tafi. 🌹~KAINAAT~🌹 Fita sukayi wajen mota suka shiga abdallah ya jasu gate suka nufa wanda tun fitar abie baba megadi yabar masu shi buɗe gaishe dashi suka yi ya amsa yana masu adawo lafiya da ameen abdallah ya amsa yayin da suke fita daga gidan, abdallah ne yace" dama ana duka school ɗin ku wallahi dasai nasa yau anmaku dukan tsiya. " "dan Allah ya abdallah kayi hakuri bazamu ƙara ba" "kundai ci sa'a kawai ba'a duka da kungane kuranku yau da daga yau bazaku sake baccin safe ba, ace wai kuna bacci har school bus tatafi kuga yan hutu koh" Kayi hakuri dan Allah wallahi baza mu ƙara ba" , "ni da'allah kuyi man shiru sai bada hakuri sai kace masu tuban gagaskiya bayan nasan ƙarawa zakuyi" ya faɗa yayin da yake hawa kan titin ring road in da nan ne school ɗin su take bakin gate ɗin school ɗin yayi parking tare da cewa "kufito kuwuce ciki, fita sukayi suna yi mashi adawo lafiya Allah yasa yace motar yayi ma key yabar wajen tare da Kama hanyar hospital ɗin da ya Episode 3_4 . LITTLE ANGELS PRIMARY AND SECONDARY SCHOOL. shine sunan school ɗin Kamar yanda school uniform ɗin suka kasance pink and white color haka paint ɗin school ɗin shima pink and white color ne. Cikin school ɗin suka shiga Masha Allah school ce mekyan gaske ta yayan masu arziki Upstairs ce makarantar wanda ya kasan ce down na yara up kuma na manya ne, up stairs suka nufa domin an daɗe da gama ASSEMBLY shiyyasa suka nufa class, S. S. 3 shine class ɗin su , shiga sukayi ciki for master ɗin su suka samu yana ma shirin fita domin ya gama abunda ya kaishi. "Aairah And Aaimah Muhammad hashim , why are you coming late" for mastern ya faɗa, Sorry sir we have wake up too late that the reason why we came to school late and it will never Happen again Aaimah ta faɗa yayin da Aairah ke ta bata fuska irin tafi ƙarfin ta bashi amma sa. this should be the last, get sitet for mastern ya faɗa hadi da fita daga class ɗin . Kallan juna sukayi haɗi da kwashewa da dariya, Aairah tace Why are you coming late tana kwai kwa yona maganar for master ɗin , dariya suka sake kwashe wa da Ita, Aaimah tace this should be the last. wannan karan duka yan class ɗin ke dariya. Sit ɗin su suka zauna suna cigaba da dariya, Allah ya shirya ku twins domin yanzu abun naku sai adu'a mu samma make Aairah da uncle Hamza na magana sai wani harar sa kike," bazaki gane bane "Aeesha" Aairah ta faɗa wacce akakira da Aeesha tace to ganar dani. "Ke wallahi haushi uncle hamza ke bani dafa Ina masa kallon mutumin arziki ashe dan banza ne, baki ji munce ya dai na zuwa gida yi mana lesson ba, Ai korar sa ya abdallah yay, saboda abun da ke kai shi bashi yake yiba, Ko kunya baijiba yace wai yana son Aaimah sai kuma yana lesson kiga yana kokarin taɓa ma mutun hannun ai kuwa rannan ashe duk abun da yake faɗa a kunnan ya abdallah, shine fa ya kore shi yace karya Kara ganin sa, to Wallahi inta kaice maki komu dukan da mukasha wurin ya abdallah sai kin tausaya mana dan Wallahi buguwa mukayi kamar gangar church kuma mom tace ba ruwan ta gashi abie baya gari, shiyyasa innagan shi Nake jin kamar na shaƙe sa"Aairah ta faɗa tana hura hanci, Allah ya shirya sa to Aeesha ta faɗa , Ameen dai. be silent biology teachern su ne yace haka wanda shigowar sa kenan yasame su sunata surutu, natsuwa suka yi suna sauraron lesson ɗin dayake masu. _F. M. C MEDICAL CENTER_ zaune a office ɗin shi da ke Amenity, waya ce a kunnan sa da alama waya yake. "haba dude ai dole nace haka tsawan shekarar mu nawa muna tare ace baka taba ziyarta taba su mom ma a suna ka ɗai suka sanka sai waya, ai tare bata ce haka ba amma nasan maganin ka zan haɗa ka kawai da ammy ne nasan ita zata saka kazo ba dan kashirya ba konasa mom takiraka may be kazo ya abdallah ne ya faɗi haka,, On the other hand nacikin wayar yace,, sorry my man ba haka bane nima ina san zuwa to ayyuka ne suka min yawa shiyyasa amma insha Allah ina nan zuwa very soon,, ai nima ina da tarin ayyuka amma Nake ajiye su na ziyarceka,, inkuma Sai zanyi aure zaka zo inji to, duk da in zanyi sai tare da kai don ina samun mata zan haɗa ka da ammy kaima ka fito da taka ko aba da kai sadaka" abdallah ya faɗa yana dariya. "haba kaima kasan wa za'a ba da sadaka Indai aure zakayi bisimillah ban hanaka ba amma ni ba yanzu ba. "shikenan tun da kai bazaka chanza ba kullum ace mutum amsar sa ɗaya, ina gaishe da su ammy "ya abdallah ya faɗa . "zasuji insha Allah nima ka gaishe man dasu mom kace mata ina nan zuwa very soon " "Allah yasa domin kuwa na san halinka," Karka damu dude zan zo insha Allah, to shikenan sai anjima , abdallah ya faɗa , ok nagode sai anjima kashe wayar yayi shiri yayi haɗi da fita daga office ɗin dakin tiyatar yanu fa. 10:00 am LAGOS. _EKO HOSPITAL._ Patient ne zazaune wanda da alama sun zo ganin likita ne. wata Nurse ce tafito daga Office aƙalla zatayi kimanin shekara 25 jikin ta sanye da fararen kaya riga da wando hulace kawai akan ta saɓanin wasu nurses ɗin da ke sanye da baby hijab, baka ce amma ba baki sosai ba wurin patient din tanufo, hadi dacewa DR. Is on the way, yayin da take amsar Katin patient ɗin wani dattijo ne zaune bai bada card ɗin shi ba da alama ma baiji mi nurse ɗin tace ba,"hey bring your card" nurse ɗin ta faɗa ganin bai ba da nashi Katin ba," ƴata ni bana da Kati yau nafara zuwa".dattijon ya faɗa dakyar alamar ba karamin kamu ciwan yayi masa ba ,cikin harshen hausa tafara mgn duk da batayi Kama da hausawa ba kuma bawani iya hausar tayiba sosai " to ya kake so ayi Katin ka keso nabaka ne komi" "a'a naji ance ana bada magani kyauta shiyyasa nazo" dattijon yafada, wani kallon rainin wayau take ma dattijon har ya gama magana, cikin karaji tace "hey hausa people nabani mamaki, to bari kiji nan ba charity hospital bane dan hk kitashi kiba mutane wurin, in ban da abunki ta ina wannan hospital ɗin tayi Kama da charity hospital koh ance maki irin hospital ɗiin kune na arewa" nurse din ta faɗa hadi da nuna masa hanyar fita. " haba Victoria kin man ta me doctor yace duk time ɗin da marasa ƙarfi suka zo ne " wata kyakyawar nurse ke faɗin haka chocolate color ce a ƙalla zatayi kima nin shekara 23 itama sanye take da fararen kaya rigada wando sai farar baby hijab, zuwan ta ke nan tasamu victoria nayima dattijo masifa Ita bahaushiya ce sabanin victoria, "ina ruwana ai yan zu ba ya nan sai dai inkece zaki faɗa masa Kasa tashi dattijon yayi jikinsa sai rawa yake, tsawa ta dakama dattijo, haɗi dacewa "I said get out from this hospppppp, kasa karasawa tayi adalilin saukar wani mahaukacin mari dataji a kuncinta batai aune ba tasake jin wani marin a dayan kunchinta bashiri ta kife ƙasa, gaba ɗaya hankalin patient dana nurses ya dawo kan wanda yayi marin. Tsaye yake jikinsa sanye da blue uniform ɗin sa na aiki, kafarsa na sanye da black din takalmi sai hannunsa dake riƙe da briefcase da lab coat ɗin sa, dogone yana da tsayi, farine sosai kyakyawan gaske ya nada dogon hanci sai eyes masu black ɗin eyeball, small mouth me ɗauke da red lips, sumar kan sa wacce tasha gyara koma take kan shan gyara black color ta sauko saman neak ɗin shi ya sha rawani irin na larabawa, dama da ka ganshi kai tsaye zaka ce balarabe ne kukuma half cast , akallah zai yi kima nin shekara 29 zuwa 30. Good morning sir, nurses ɗin suka shiga gaishe da shi hannu kawai yake ɗaga masu yayin yake kiran security ƙara sowa security ɗin sukayi suna gaishe da shi cikin girmamawa, amsa masu yayi yana nuna masu dattijon haɗi da cewa kushigar min dashi office yayin da yake ba daya daga cikin securityn key din office ɗin shi, kamashi sukayi suka ɗaurashi akan keken daukar marasa lpy wannan nurse ɗince wacce tayima victoria mgn ta matso kusa da shi hannu ta mika zata anshi briefcase ɗin dake hannun shi dakatar da Ita yayi, magana ya fara cikin harshen turanci nurse "hidaya me nace ne gameda masu zuwa neman tai mako? " " kace duk wanda yazo neman tai mako ah EKO aturashi ABNOOR, kuma itama nurse Victoria tasani kuma sai da nasake faɗa mata da tana ma datijjon faɗa" "shikenan koma dai miye Wannan yazama nakarshe ina ba haka ba dukkan ku sai ranku ya ɓaci "ya fada haɗi da nufar office ɗin shi 🌹~ KAINAAT ~ 🌹 Tasowa victoria tayi daga duƙewar datayi domin ta maru, haryanzu bata dawo dai dai ba, masifa tafara yima nurse Hidaya akan Ita ta haɗa ta da dr haryayi mata wannan marin, "to bari kiji Victoria garama tun wuri kifita daga harkata basai da na gar gaɗe kiba amma mikika ce ke kina ganin dr shazim bazai iya yimaki komai ba ke yar gaban goshi, kedai kawai za fin mari ne yasa zaki sauke a kaina mizai hana shi dr bazaki bishi office kiyi mashi masifar ba "hidaya ta faɗa tana dariya sauran nurses ɗin ma dariya suke saboda sun san magana ce hidaya ta faɗa ma victoria saboda ba ƙaramin so take ma DR. SHAZIM ba, mutsww victoria taja tsaki saboda haushin dariyar dasuke mata ta kuma gane miyasa su dariya wuce wa tayi office ɗin dr saboda itace ke tura mashi da patient, Shiga tayi cikin office ɗin haɗi dacewa, good morning sir zaune yake yana rubutu ajikin file wanda da alama na wannan dattijon ne yayin da shikuma dattijon yake kwance bisa gadon marasa lafiya a office ɗin , ko kallon inda take bai yiba sake gaishe da shi tayi, call nurse hidaya for me abun da kawai ya ce mata kenan, hakuri ta shiga bashi dan bazata iya daina aiki dashi ba domin in har chanzata zaiyi da nurse hidaya to sai dai tabar hospital ɗin saboda bazata juri ganin shi tare da wata ba, tsawa yada kamata domin yaga bata da niyyar fita daga office ɗin yace " get out from my office" haɗi da nuna mata hanya, fita tayi daga office ɗin zuwa office ɗinsu na nurses fashe wa tayi da kuka, tana faɗin bazai yuwu ba wlh dr shazim nawa ne ni ka ɗai babu wacce ta isa ta raɓesa sai ni taƙara fashewa dawani kukan, wata nurse ce tashi go office ɗin wacce itama daga ganin ta ba muslma bace tana cewa , "ai yanzu kika fara kuka victoria, dama ba sai da na faɗa maki ba kitashi tsaye amma kika kiji to wallahi Idan bakiyi wasa ba kina nan sake dabaki hidaya zata kwace shi, sai dai kizama ƴar kallo" "haba destiny yaza ki man wannan mumu nan maganar, kisan kuwa yanda nake son dr shazim kuwa da kinsan yanda nake son shi da baki ce haka ba" " victoria kenan inaga bakisan halin hausa peoples bane zaki sha mamaki inkika tsaya wasa domin kuwa Ita hidaya yarensu ɗaya bayan nan religion ɗin suma ɗaya kina ganin zai kula ki ne yana ganin hidaya, kawai kitashi tsaye" "to ya zanyi ki bani shawara pls"wani munafukin murmushi destiny tayi haɗi da cewa yanzu dai kifara kiramashi hidaya tukkun nan zuwa anjima sai muyi magana " " haba destiny yazakice nakirata sai dai yaji haushi amma ni bazan kira taba wlh" "kaji sakarya in ban da kina sakarci in baki kira mashi ita ba taya zai gane kintuba kuma itama hidayan ki roketa akan ta tayaki bashi hakuri nasan zatayi," "uhmmm shi kenan ta faɗa haɗi da barin office ɗin domin kiran hidayar, dariya destiny ta kwashe da Ita haɗi da cewa "zaki gane baki da hankali Victoria zakisan cewa ni ba kanwar lasa bace yanda kika ki brother samuel to haka zaki rasa shazim shima sakarya kawai" . wurin su hidaya Victoria tanufa,ta zuwa ta tsaya hannunta riƙe da ƙugu tace" kizo dr . nakira tana faɗa ta juya kai gefe, "wakenan acikin mu?" watace cikin nurses ɗin dake zaune ta faɗa , "tasan kanta ai acewar Victoria , sarai sungane hidaya take nufi sbd sun San tana yar tsama da Ita amma sai suka nuna basu gane ba "hidaya kinsanfa ke nake nufi amma kinyi kamar baki ganeba zanje na faɗa masa bazaki zoba" " kejiman Victoria da karfin halin, kin faɗi sunan tane daza kice ta ƙizuwa" "ah to gane mana hanya sister maryam" acewar wata daga cikin nurses ɗin "haba Victoria nina rasa me hidaya ta tare maki a hospital ɗinnan,ai ko bakomi ƴar uwarki ce tawurin aiki, amma ace kullum baki da abokiyar faɗa sai Ita" karka faɗa man mgnr banza mana Joseph ina ruwanka" "sorry shawara ce" barin wurin yayi wanda akakira da Joseph "mike faruwa ne anan cewar destiny wacce isowarta kenan, a'a hidaya Victoria bata faɗa maki dr nakira ba nagan ki zaune ko har kin dawo daga wurin shi "A'a destiny yanzu zanje, ok destiny ta faɗa haɗi dacewa kefa Victoria naga kinyi tsaye kutafi mana bin bayan hidaya destiny da Victoria sukayi suna ɗan yin nisa da sauran nurse's ɗin destiny ta ɗan taba Victoria alamar ta roki hidaya akan ta taya ta ba dr haƙuri ganin baza tayi ba yasa destiny dakatar da hidaya haɗi da cewa "kiyi hakuri hidaya akan abun da Victoria tayi maki haushin dariyar da kuka yi matane ɗazu, amma kiyi hakuri" "shikenan bakomi, ni da man bawani riƙe taba" "shikenan amma ki taya ta ba ma dr hakuri pls karya cireta daga cikin nurses ɗin dake tura mashi patient pls, a ranta take faɗan"ok shiyyasa kenan tazo ta ciman mutun ci"amma a zahiri sai tace "bkm yawuce insha Allah zan taya ta" thanks Victoria ta faɗa yayin da suka kawo office ɗin shiga ciki sukayi sallama hidaya tayi yayin da Victoria ke bayan ta, dr gani hidaya ta faɗa, ok a saka patient a layi amma mutum 15 kawai zan duba sauran kiturasu office ɗin DR KABIR, sorry sir ni ina iya tura su a cewar Victoria data ga yayi kamar bai san tana wurin ba, as from today this is the last time dazaki Kara zuwa office ɗin na I hope you understand, a fuwan sir kayi mata haƙuri bazata ƙara ba hidaya ta faɗa gaban ta na faɗuwa tsoron kar itama ya koreta, nagama magana get out ƙasa Victoria tayi akan gwiwo winta tana ci gaba da bashi haƙuri harda kuka, I said get out from my office ya faɗa da tsawa yana nuna mata hanyar fita, fita tayi tana kuka kamar ranta zai fita ,kema zaki iya tafiya" Ok sir hidaya ta faɗa fita itama tayi " wajen office ɗin ta samu Victoria da destiny suna ganin ta suka nufe ta rokonta suka shigayi a kan ta taya victoria ba ma dr haƙuri " shikenan insha Allah zan taya ta kar ku damu hidaya ta faɗa hadi da sharema Victoria hawayen dake fuskarta ta cigaba da kwantar mata da hankali godiya sukayi mata sannan suka koma office ɗin da suke zama ita kuma ta wuce wurin patient domin tura ma dr su . haka ya cigaba da ganin patient shikuma wannan dattijon ruwan da aka sa mashi na ƙarewa yasa driver ya mai dashi ABNOOR aka bashi gado , bashi ne ya bar EKO ba sai wurin 12:30 sannan ya wuce ABNOOR nan ma yaga patient dayawa saboda da nan yafi jimawa a nan a kan eko , abnoor hospital ɗin sane halak malak Ita kuma eko aiki yake a chan, sau biyu yake zuwa eko a sati idan yana lagos saboda yana visiting wasu Hospital ɗin , kuma in yaje 2 to 3 hours yake yi yaje abnoor , amma standard in da yafi zama abnoor ne saboda chan har ranar Saturday yana zuwa in yana lagos ,sai wurin 6:00 ya tashi daga aiki dan har an fara kiraye kirayen sallar magrib masallacin hospital ɗin ya nufa domin gabatar da sallah sai bayan angama tukkun nan yanu fi gida, horn yayi a bakin wani katafaren gida naji da faɗa dake Victorian Ice land , gida ne har gida wanda daga gani ba sai an faɗa maka ba kasan cewa an narkar da kuɗi, me gadine ya bude masa gate, ciki ya shiga ya nufi parking lot da ke chan cikin gidan,ɗakin mai gadine farko daka shigo gidan sai boys quarters daga chan gaba sai kayi ƴar tafiya sannan zaka iso part ɗin masu gidan sai parking lot dake gefe sai wani katon garden dake bayan part ɗin masu gidan hade da Wani katon swimming pool me kyen gaske,ride's ne gasunan kala kala a kallah zasu kai 6 a parking lot ɗin , parking yayi cikin gidan ya nufa tura ƙofar shiga part ɗin yayi bakinsa ɗauke da sallama,parlor ne me kyan gaske komai na cikin sa ya kasan ce golden and white color ne royal sofas ne masu kyan gaske set biyu sai wani ƙaton dining table mai chairs kusan guda 10 , sai wasu bedroom guda 3 dake hannun dama sai kitchen da store atare, wani corridor ya nufa inda yana shiga nan ma wani madaidaicin parlorn me dauke da sofa a set 1 komai na cikin sa golden color ne sai dining mai dauke da chairs guda 5 sai two bedroom, daya daga cikin su ya nufa bakinsa ɗauke da sallama, wata kyakyawar mace ce zaune a kan sallaya itama farace sosai suna Kama da dr banbanchi Ita mace ce shikuma namiji zata yi kimanin shekara 50 , sanye take da hijab hannun ta reke da chasbaha tana ja , da a lama sallah ta gama, sallamar da yayi ta amsa mashi yayin da yake ƙarasa wa inda take zaune wuri ya nema ya zauna "an wuni lafiya ammy, ya gida"ya faɗa , amsa mashi tayi da" lafiya qlu Alhmdllh ya aiki ya fama da patient, alhmdllh ammy, Masha Allah ta faɗa haɗi da cewa katashi ka shiga ciki domin kasamu ka huta zansa fatima ta kawo maka dinner ɗinka , dama shi ba ma'a bocin cin abinci a dinning bane, to shikenan ammy bari na wuce ciki, fito wa yayi daga bedroom ɗin yanu stairs dake parlor wani part ya shiga wanda da alama nasa ne tura ƙofar yayi haɗi dayin sallama, ya kutsa kai ciki parlor ne shima ma dai dai ci me kyan gaske komai nacikin sa ash and black ne bedroom ya nufa wanda shima bedroom ɗin kayan cikin sa ash ne hattada furnitures ɗin ciki ash ne ɗan corridor ya nufa cloth set ne sai gefe laundry basket, kayan jikin sa ya shiga ragewa ya koma daga shi sai boxer bathroom yanu fa domin watsa ruwa after 15 minutes ya fito jikin sa sanye da bathrobe wurin clothes set ɗinsa ya nufa jallabiya ya saka ajikin sa bathroom yakoma domin ɗauro alwallah sbd time ɗin sallah isha yayi masallachin gidan ya nufa dan gabatarda sallah anagama sallah part ɗin sa ya koma a parlor ya zauna kan sofa bai jima da zama ba yaji ana nocking tambaya yayi waye ne " fatima " ce Yaya ok shigo ya faɗa , turo ƙofar tayi tashigo bakinta ɗauke da sallama kyakyawar matashiya ce akalla zatayi kima nin shekara 18_19 fara ce itama tana kamada ammyn su amma ba sosaiba dr dai shine ke kama da Ita sosai " ina wuni Yaya andawo lafiya, lafiya qlu , dama ammy ce tace nakawo maka dinner ɗin ka, ok ajiye kan table, ajiye mashi tayi haɗi dafita jawo table din yayi , serving ɗin kanshi yashiga yi, yana kammala cin abincin bedroom ɗinsa ya koma laptop dinsa ya jawo dake kan bedside aiki yashiga yi..... KATSINA.... Su Aaimah ne zaune a falon mom suna kallo, sanye suke da pajamas sky blue, mom ce tafito daga bedroom ɗin ta, ita ma sanye take da pajamas purple color, waya ce a kunnan ta da alama waya take wuri tasamu kan sofa ta zauna tana cigaba da wayar " mom abie ne Aaimah ta faɗa yayin da take matsowa kusa da mom, daga mata kai mom tayi alamar eh" mom dan Allah kice muna gaishe shi munkira shi bai ɗauka ba, to kaji Wai twins ɗinka nagaishe da kai wai sunkiraka baka ɗauka ba mom ta faɗa , mika ma Aaimah wayar tayi da a lama cewa yayi a basu wayar, amsa tayi haɗi da cewa" inawuni abie ya Abuja, ya kuma aiki " on the other hand abie yace" lafiya qlu Alhmdllh ya gida ya kuma school " Alhmdllh abie ta bashi amsa, abie ko kace ina nake Aaimah ka ɗai kasani" Aairah ce ke mgn wacce ƙara sowarta kenan "afuwan yanzu zance kina ina sai kuma gaki ya gida ya schll" Alhmdllh abie yaushe zaka dawo, jibi insha Allah zan dawo " to Allah ya kaimu abie , ameen ya faɗa sun jima suna waya sannan suka yi sallam, bedroom ɗinsu suka nufa domin bacci dan mom ta daɗe dashige wa nata bedroom ɗin .... Episode 5_6 _FRIDAY......._ sauko wa yake daga stairs jikin sa sanye da baƙaƙen coat hannun sa riƙe da briefcase , ammy ce zaune kan sofa ƙaraso wa yayi kusa da ita " Ina kwana Ammy ina fatan kintashi lafiya " ya fada yayin da yake samu wuri kusa da Ammy ya zauna " lafiya lau Shazim har kafito," eh ammy ya bata amsa," ga breakfast din ka nan kan dinning" "to,ammy kinkuwa yi waya da NORAIZ "( kanin sa mai bimasa yayan fatima dayake baya nan yana kasar portland yana masters akan business ) ya fada yayin da yake nufar dinning "eh naji yace yana nan zuwa ranar sunday ( lahadi ) , ammy ta fada " eh ammy haka yake fada man jiya, "to Allah ya kaimu lafiya" Jiya uncle ɗin ku ya kirani, yace kai ka ɗai suke jira" shiru yayi baice komai ba sai da ammy ta sake cewa "da kai fa nake magana, ni ban san mikake nufi ba , da anyi magana sai kayi shiru, tun yaushe ake abu ɗaya sai yawo kake ma mutane da hankali" "kiyi haƙuri ammy, wlh ban gama abun da nake ba, kuma nifa bani da wata wacce zance ina so, nafi son su barin harsai na samu wacce nake so" "to bari kaji na faɗa maka ni ba ruwana daga yanzu bazan sake shiga maganar ba duk hukuncin da suka yanke akan ka babu ruwana "shazim yace "dan Allah ammy karkice haka idan kika zare hannunki innah zata iya zuga su su yanke man hukuncin da duk sukaga dama" "to idan har baka son haka tafaru to dole sai ka nema ma kanka masalaha" "insha Allah ammy" "to Allah ya yarda, ameen ammy ". fatima ce ta fito daga bedroom dinta dake kusa da na Ammy jikinta sanye da uniform , dinning ta nufo Ita ma domin breakfast " Ina kwana Yaya dafatan antashi lafiya " lafiya qlu ya bata Amsa, yana gama breakfast ya mike hadi da daukar briefcase din shi " Ammy ni zan wuce, to a dawo lafiya Allah ya bada sa'a, ameen Ammy fita yayi zuwa parking lot, gaisawa ya tsaya yi da masu aikin gidan tun daga kan maibama flower ruwa Har izuwa kan maigadi sannan ya fuce daga gidan, ABNOOR ya nufa domin yau baya zuwa EKO. ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN PRIVATE HOSPITAL ( ABNOOR ). Direct office din sa ya nufa briefcase din sa ya aje akan table zama yayi hadi da bude laptop dinsa Aiki yafara kafin time din daya ke duba patient yayi. sallama a kayi hadi da turo kofar wani matashin saurayi ne wanda zasu yi sa'anni da shazim din. Amsa mashi sallama yayi, shigowa yayi daga ciki hadi da mikama shazim din hannu suka yi musa baha , sannan ya zauna kan kujerar dake gaban table din " shazim amma yanzu ka shigo ko dan nazo baka nan, eh shigowata kenan nakama aiki , ai ku manya ne agogo sarkin aiki, haka dai kake gani majeed karfin haline kawai, wlh kuwa ai kana kokari, to ya za'ayi, dole a nema" "hakane dama maganar kayan da suka kusa ƙarewa ne" "kai ai kuwa gara daka tuna man dan har na manta, zanyi magana da su yau insha Allah " "to shikenan nibari nakoma office" "to shikenan nima yanzu zanje duba patient insha Allah sbd da time din sallah nayi zan tashi sai kuma gobe Idan Allah ya kaimu, ameen majeed ya fada hadi da barin office din shima baijima ba ya fita dakin marasa lafiya nufa sai 12:10 sannan ya dawo office yana shiga bawani jimawa yayi ba ya hada kan kayansa ya fito direct gida ya nufa bedroom din ammy ya fara zuwa gaisawa kawai sukayi ya nufi part din sa bedroom din sa ya nufa kayan jikin sa ya shiga ragewa ya nufi bathroom after 10 minutes ya fito kugunsa daure da towel dressin mirror ya nufa mai ya shafa mai dankaran kamshi, comb yasa ya shiga combing din kansa sannan ya shafesa da man aloe da hair spray clothes set dinsa ya nufa shaf shaf ya shirya cikin wata shadda ƴar ubansu milk color ba karamin b kyau yayi ba sannan ya dauko hula ya daura brown color, feshe jikin sa yayi da turare mai ƙamshi,sannan ya nufi shoe rag dinsa takalmi ya dauko me kyan gaske shima brown color. masha ALLAH kawai zamuce dan ba karamin kyau yayi ba wayoyin sa dake bedside ya dauka fita yayi daga bedroom din yana zuba kamshi, ya nufi down stairs parlorn ammy zaune ya sameta tana karatun Al'qur'an tana kai aya tace " sai masallaci kenan, eh ammy ya bata amsa , to shikenan a dawo lpy nima zanje gida domin na ƙasa duba jikin baba , to saikin dawo Allah ya bashi lfy nima insha Allah yanzu daga masallachi zan biya na gaishe shi saina dawo ya fada hadi da kama hanyar fita Ammy nacewa a dawo lpy , da innah asabe ya cikaro ( mai Aikin su) zata shiga wurin Ammy, gaishe da Ita yayi ta amsa mashi da " Lafiya lau Shazim har za'a tafi masallachi kenan, eh ya bata amsa hadida fice wa daga falon ya nufi parking lot mota yashiga mai gadi ya bude masa gate ya fuce......... _KATSINA......._ AIRAH Zaune take bakin gado jikinta daure da towel da alama wanka zatayi . "sister gaskiya kiyi sauri kifito nima nayi wanka kinsan yau abie zai dawo kuma mom tace muje gidan granny mu gaishe ta har so nake muje gidan aunty safiya ( kanwar MOm wacce suke uwa daya uba daya) mun kwana biyu ba muje ba "Aairah ta fada. fitowa Aaimah tayi daga bathroom jikinta daure da towel " bawani sis zaki ziyara ne kodai zakije ganin ya MUS'AF dan nasan halinki sarai, Amma wlh Aaimah kin bani da sharri yau she nace maki saboda shi zanje gidan ni dai ziyara zani bawai saboda ya mus'af , dan wlh ki bari karki jaman ya usman yaji wannan maganar , ai kuwa saina fada masa ince bakiji gargadin da yayi maki ba, ni wlh har mamaki kike bani kirasa dawa zakiyi soyayya sai ya mus'af harka duk ta yarin ta, eh naji matar babban mutum sai mi koda ace na girmi ya mus'af ina ruwan ki Aairah ta fada tana huro hanchi, Allah ya baki hakuri Aairah ni nayi nan Aaimah ta fada hadi da nufar dressing mirror bathroom Aairah ta nufa shaf shaf Aaimah ta shirya cikin atamfa super Red color ɗinkin riga da skirt tana nan tsaye tana fesa turare Aairah ta fito sai bata rai take shiryawa itama tayi cikin atamfa color daya data Aaimah tana gamawa ba tai ma Aaimah magana ba taka ma hanyar fita daga bedroom din, murmushi Aaimah tayi hadi dacewa " ki nafa iya cewa kinji haushi, bata bata amsa ba sai tsaki data ja, haba twin sis kiyi hakuri bazan sake ba kinji ta ya mus'af sorry pls Aaimah tafada hadi da matsowa kusa da Aairah sake bata hakuri tayi tare da cewa haba abun gidan ya mus'af kiyi dariya mana dan Allah tafa da yayin da take langwabar da kai, murmushi kawai tayi hadi da cewa wallahi Aaimah ki daina kushe man ya mus'af Indai kina so mu zauna lafiya da ke, kaina bisa wuya na daina insha Allah Aaimah ta fada hadi dajan hannun Aairah suka fita bedroom din mom suka nufa samun ta sukayi zaune gaban dressing mirror tana saka sarka a wuyan ta sanye take da wani hadaden less brown color ta sha daurin ture kaga tsiya hannunta ya sha dan hannu da zobe na gold kalar sarkarta, har suna hada baki wurin fadin masha Allah , Aaimah ce ta ce "kice yau an tashi rikita mana abie kenan , wannan kwaliyya haka mom ai sai ya ka sa gane ki yayi tuna nin sabuwar amarya aka kawo masa, Aairah tayi charab tace ba kiga harda ture kaga tsiya ba, lallai duk wanda ya ture ya taro match ba yan ball, murmushi kawai mom tayi hadi da cewa kun rainani ko, na lura ni kuka maida granny da dadi, Aa wane mu kawai dai munga kin hadu kar abie ya riki ce, ALLAH ya shirya ku mom ta fada ameen suka amsa, Aairah tace daman mom daga gidan granny zamu wuce gidan aunty safiya dan Allah, shikenan Idan kunje kuce ina gaishe ta , to shikenan mom zataji Insha Allah amma sai abie ya shigo sannan zamu tafi , to shikenan mom ta fada.. Ya usman ne ya shigo bedroom din jikinsa sanye da shadda maroon color sallama yayi hadi da shigo wa gaishe da shi su Aairah su kayi hadi da ficewa falo zama sukayi kan sofa suna kallo. a chan kuma bedroom din mom gaishe sa Ita usman yayi, amsa mashi tayi hadi da cewa har ka dawo daga masallachin, eh mom ya bata amsa, abinci fa, a kai maka part dinka ko zaka sauko kachi a dinning, a'a a barshi nan zan sauko Idan abie ya shigo sai muci tare da ku , dan nayi waya da shi da ina kan hanya wai ashe ya dawo yana gidan dadi (kakar su ta wurin uba mahaifiyar Abee) amma yanzu zai taho, to shikenan bari nasa ajera abinci kan dinning sai muci tare da dashi dama nayi tuna nin basu kusa isowa ba, to shikenan mom ni na wuce part dina kafin ya kai da shigowa ya fada hadi da ficewa itama mom fita tayi direct kitchen tawuce a chan tasa mu baba larai na zuba abinci cikin warmers "yawwa baba kice harkin kwashe kafin nazo, halan kinga najima ban dawo ba sallah nayi sai nace bari kawai nayi har da wanka tun da nasan san da zan dawo nasan a bincin ya nuna kuma barrister na hanya shiyyasa, A'a nima sai da nayi wankan da naga baki sauko bane kuma ya nuna sai nace bari kawai na kwashe, to shikenan bari na jerasu a dinning mom ta fada hadi da daukar warmers din ta nufi dinning bala driver ne ya shigo hannun sa dauke da kaya suna cikin gaisawa mom sukaji sallamar abie daga bayan su sauko wa su Aairah sukayi da gudu jin sallamar abie, nufar sa su kayi da gudu hugging din su yayi yana murmushi sun bi sun makalkale shi mom ce ta matso tana cewa ku sake sa man, kunbi kun makalkalesa , haba mom kwana biyu fa baya nan, to ko baya nan fa , ya kwaso gajiya shine zaku kara masa wata, ku sake sa mana , sakin sa su kayi kan sofa suka zauna, shi kuma up stairs ya hau shi da mom , bala ne ya sake shigowa da wasu kayan na abie, jakar kayan abie ka dai bala ya kai sama sauran kayan kuma kitchen ya nufa dasu . AFTER 25 minutes........ abie ne da mom ke sauko wa daga up stairs abie har ya chanza kayan jikin shi da alama wanka yayi dinning suka nufa ta sowa su Aairah sukayi suma suka nufo dinning din " Aairah maza kije ki kira yayan ku mom ta fada, tashi Aairah tayi direct part din ya abdallah ta nufa tsit parlorn shi, ba kowa sai kamshi kawai dake tashi ya hadu parlorn golding color ne komai na ciki , bedroom din sa ta nufa nocking tayi tambaya yayi waye, Aairah ce, yaya mom tace ka sauko abie ya dawo ta bashi amsa, gani nan zuwa yace, fita tayi daga part din ta koma wurin su mom , yace ga shinan zuwa ta fada yayin da take samun wurin zama serving din su Aaimah ta shiga yi sai ga ya abdallah shima ya sauko jikin sa sanye da jallabiya karaso wa yayi yana gaishe da abie da gajiyar tafiya, amsa mashi abie yayi tare da tambayar shi ya aiki,amsa ya bama abie da alhmdllh shima serving din sa Aaimah tayi , abinci suka shiga ci ba magana sai dai karar spoon dake tashi, su Aairah suka fara tashi, ba dai har kun ta shi ba, abie ya tambaya yana binsu da idanu, eh abie zamuje gidan granny ne shiyyasa kuma fa mun koshi, Aairah ta bashi amsa, to shikenan sai kun dawo kar dai ayi dare , a dawo dawuri kunji, Insha Allah abie baza mu kai ba, Allah yasa, ameen suka fada hadi da nufar up stairs , abie suna gama cin abinci kan sofa suka koma suna fira shi da ya abdallah ,mom kuma tattare dishes din da su kayi amfani dasu tayi ta nufi kitchen, baaba larai ce ta fito daga corridor din da da kinta yake wurin su abie ta nufo hadi da gaishe da abie tana tambayar shi ya gajiyar hanya amsa mata yayi da, "lafiya lau alhmdllh, ya gida ya kuma muka same ku, alhmdllh muke naga sako nagode Allah ya saka da alkairi, ameen nagode bakomi abie ya bata amsa ( nasan masu karatu zasu ce godiyar mi baaba larai keyi ma abie , kudi ya ba ma mom ta ba ma dukan hadiman gidan dama ya kan yi haka duk In zaiyi tafiya.) Kitchen ta nufa anan ya samu mom na wanke dishes din da suka ci abinci " ah hajiya dakin bari nazo na wanke ai, A'a bakomi baaba kema ki huta mom ta bata amsa, to shikenan bari muyi tare" inji baaba larai, A'a dakin bar shi Allah kinga na kusa gamawa ai, to shikenan , su Aairah ne suka sauko sun sha jalbab har kasa sai bag kalar ta kalmin dake ka farsu kara sowa su kayi wurin su abie hadi da cewa sai mun dawo,abdallah ne ya ce" mudi na nan waje shi zai kaiku" to suka ce hadi da nufar wurin mom sun cewa sai mun dawo a dawo lafiya tayi masu , ficewa su kayi harabar gidan, a nan suka samu mudi na jiran su , motar suka nufa, shiga su kayi, key yayi ma motar suka fice da ga gidan dama me gadi ya bude masu gate labari kawai Aaimah da Aairah keyi shi dai mudi nashi saurare har suka isu gidan granny horn mudi yayi a bakin gate din gidan bude masa gate din a kayi ya shiga daga ciki ya na parking suka fito gidane dan dai dai me kyau cikin gidan suka nufa wata kyakyawar tsohowa ce suka samu zaune a parlor tana kallon SUNNAH TV ( granny kenan mahaifiyar mom ce) sallama su kayi da gudu suka nufi yar tsohuwar, granny tace " karku kuskura ku fado man , salon ku ida kara sa man yan kafafun da nake fama dasu" Aaimah tace "haba granny daga munyi murnar ganin ki sai kice zamu ida karasa maki yan kafafun"ta fada tana turo baki, Aairah ce tace " shiyyasa yau zan zuga tsoho yayi maki kishiya tun da baki da kafafu" granny tace " sai dai ke ayi maki kishiya, amma ba dai ni ba, saboda ni ba wacce zata iya kishi dani, in kuma kece kishiyar inji tunwuri" dariya suka kwashe da Ita su duka Aairah tace " wah wai ni , ai kuwa da kin sha kwar kwasa da kisi si na, murmushi kawai granny tayi hadi da fadin Allah ya shiryeki yan biyu ( dayake haka take ce masu kokuma Hassana da hussainah) gaishe da Ita sukayi suna tambayar tsoho na nan, ( wato mijin granny) granny ce ta basu amsa da "yana parlor da yake ganin dalibn sa, inajin ma karatu suke saboda yau juma'ah ( malamin addini ne shi duk da ya tsufa hakan bai hana shi koyar da daliban sa ba) Aaimah tace" to shikenan granny bari muje gidan aunty safiya mu dawo, kilan time din ya gama, to sai kun dawo ku gaishe man da ita granny ta fada Aairah ce tace zataji insha Allah fita sukayi harabar gidan nan suka samu mudi zaune kan benchi suna fira da me gadin gidan, gannin sun fito yasa shi ta sowa Aairah ce tace "kabar shi kawai ba nisa za muyi ba gidan aunty safiya za muje, to ya fada hadi da koma wa kan benchi ya zauna su kuma fita su kayi daga gidan, tafiya su kayi a kafa ba mai nisa ba suka iso gidan tura yar kofar dake gefen gate su kayi hadi da shiga gidan, gida ne mai girma ba laifi dan har ya kusa girman gidan su, part din masu gidan suka nufa da sallama a bakin su suka shiga parlorn, yan yara suka samu na wasa a parlorn mace da na miji a kalla za suyi kimanin shekara 10, suna jin sallamar su suka nufo su da gudu suna masu "oyoyo aunties ya gida ya mom" su Aaimah suka ce"lafiya lau hisham sai ku ka dai a parlor kai da hibba, wata matashiya ce ta leko daga up stairs jin haya niyar yaran zata yi sa'anni dasu Aaimah tana ganin su Ita ma da gudu ta sauko tana fadi "oyoyo lovely sister da kuka ce kun fasa zuwa" Aairah tace "kedai bari najma, dafa har mun fasa saboda abie zai dawo yau, to da muka koma gida daga school mom take ce ma ai yama kusa isowa, to shine fa muka shirya tana dawo wa muka taho, najma tace "gaskiya naji dadi, da Allah har nayi fushi, Aaimah tace "yanzu dai ba wannan ba naji banji mutsin Ummah ba ( Aunty SAFIYA suke cema Ummah sbd su najma ) ko bata nan ne , tana dakin abba najma ta bata amsa hadi da jan hannun su tana cewa kumu tafi part din abban daga nan sai ku gaisa dashi ko , ok muje, part din abban suka nufa, sallama su kayi yayin da suke shiga cikin parlorn zaune suka same su kan sofa, amsa masu sallamar suk ayi aunty safiya tace "ah lallai yau ina da mn yan baki" abba yace " lallai kam yau muna da man yan baki, ya mom din ku da abie ya kuma school, alhmdllh abba suka amsa mashi, to masha Allah abba ya fada najma ce tace " to ku tashi mutafi daki, da to suka amsa mata hadi da mikewa suka fice direct bedroom din najma suka nufa suna shiga suka yada zango akan bed din ta Aairah ce tace " wai nikam ina Yaya mus'af ne najma,Aaimah ta ce " uhmm dama nasan hali har ni zakiyi ma bariki wai ziyara za muzo bayan nasan karyane, eh din naji komi za kice kice Aairah ta fada tana murguda ma Aaimah baki ,najma ce tace" ya Isa haka inkuka fara sai kuba mutun haushi wlh , ya mus'af ne deko to yana part dinsa bari nakira maki shi a waya koke kikira shi ba shi kenan ba, Aaimah tace aikin san wasa nake maki ko rabin rai , niban wani sani ba Aairah ta fada, to yanzu kinsan shikenan ko ta wuce, bari ni na kira maki shi da kaina a cewar Aaimah hadi da ciro wayarta tayi dealing number sa kiran na shiga ta mikama Aairah wayar picking call din yayi hadi da ce " Aslm, wslm ta bashi amsa, sai cewa yayi" Aaimah ya kike ya gida yasu mom da ya abdallah, ina kuma sweetie nah take, bubbuga kafafu ta shiga yi tana turo baki hadi dacewa" haba Qalbei nice kenan baka gane ba , su najma miza suyi inba dariya ba suna cewa a she soyayyar bata kaiba da har ake kasa gane muryar juna , fa shewa da kukan shagwaba Aairah tayi hadi da cewa ka gani koh Aaimah da najma nayi man dariya, on the other hand yace " sorry sweet heart nayi tuna nin Aaimah ce, kinga ai numberta ce amma kiyi hakuri kinji my, najma na gidan kune, Aa fa kai da nazo nayi surprise dinka, amma sai ka bata komai baka gane ni ba Aairah ta fada, sorry kinji tawan fada man kina ina kinji, turo baki gaba tayi hadi da cewa " Ina bedroom din najma , am coming sweet heart ya fada hadi da kashe wayar,ajiye wayar tayi Ita ma hadi da yima su najma gwalo "oho dai ke da ba'agane ba najma ta fada hadi da tafawa ita da Aaimah" nocking sukaji ana yi da sauri Aairah ta nufi kofar tana bu dewa wani matashin saurayi ne tsaye jikin sa sanye da jeans da T-shirt na kamfanin Gucci farine kyakyawan karshe a kalla zai yi kimanin shekara 20 murmushi Aairah ta sakar mashi shima martanin murmushi ya mayar mata, gaishe da shi Aaimah tayi, ficewa su kayi daga bedroom din, su Aaimah kuwa fira kawai suke har aka kira sallar asr, sallah suka tashi su kayi a lokacin Aairah itama ta shigo domin yin sallar Aaimah ce tace ma Aairah ai nayi tunanin nisa ku kayi da naga kun fita ashe kuna kusa, banza Aairah tayi da ita ta nufi bathroom domin yin alwala, basu ne suka bar gidan ba sai wajen 5:00 sannan suka koma gidan granny najma da Aaimah na gaba yayin da Aairah da mus'af ke bayan su , suna shi ga granny tace a she zaku dawo harna yi tuna nin kun wuce gida a she kuna nan, kallon mus'af tayi tana fadin" kai kuma lafiya kayi man tseye a kai , aure ne dai banyi ehe" dariya mus'af yayi hadi da cewa sai mi, dama ni yarinya nake so me jini a jika ba tsohuwa ba, dariya suka kwashe da Ita su duka, haba kai dai kawai dan ba zaka samu bane , ya safiyar take ina su Hibbatu da hisham , lafiya lau suke granny, fira suka shiga yi da granny tana tsokanar su a nan tsoho ya same su, gaishe da shi suka yi , dashi suka taru suna ta firar ba sune suka bar gidan ba sai kusan 5:50 sannan mudi ya mayar da su gida duk da mus'af ya so mai da su, amma suka ce ya barshi tun da da driver suka zo ,da shigar su gida bedroom suka nufa domin time din sallar magrib ya kusa kayan jikin su suka cire suka sanya ma rasa nauyi, sau kowa su kayi down stairs direct kitchen suka nufa wurin mom da baaba larai dake shirya dinner , kama masu aikin su kayi har suka kammala kowa ya nufi bedroom dinsa domin gabatar da sallar magrib wacce ake kira. KAINAAT _Lagos....._ Innah asabe ce a kitchen ita da fatima suna girki kiran sallar da a ke yine yasa fatima cewa "Innah kije kiyi sallah zan karasa aikin, to amma kefa, karki damu Innah kitafi kawai ( da yake tana fashin sallah ne) To shikenan, fita tayi daga kitchen din ta nufi dakin ta, shazim ne ya shigo cikin gidan jikin sa sanye da farar jallabiya da alama daga masallachi yake par Ammy ya nufa bai isketa ba sai yawuce bedroom din ta nan ma bata nan fitowa yayi daga part din ya nufi main parlor fatima ya gani ta fito daga kitchen hannun ta rike da food flask " Ammy bata dawo bane, eh bata dawo ba , ok ya fada hadi da Komawa part din sa, sanda Innah a sabe zata koma kitchen har fatima ta gama komai da yake sai da ta jira aka kira sallah isha tayi, kama mata kawai tayi suka gyara kitchen din, falo fatima tafita kiran daya daga cikin ma aikatan gidan tayi a waya domin yazo ya daukar masu a binchin su, sallama a kayi daga kofar falon hadi da turo ta, fateemah ce tace yawwa ilya hadi da shiga kitchen fitowa tayi hannun ta dauke da food flask din masu aikin mika mashi tayi , part dinsu ita da Ammy ta nufa bedroom din ta ta shige kayan jikinta tacire towel ta daura bathroom ta wuce domin yin wanka 10 minutes ta fito daga bathroom din dressing mirror ta nufa mai kawai ta shafa ta nufi clothes set dinta dama ta sanya pad tun a toilet shiryawa tayi cikin pajamas lemon green ta yafa mayafi white mai dan girma feshe jikin ta tayi da turare mai dadin kamshi fita tayi daga bedroom din a falon Ammy ta zauna kan sofa wayar ta dake charge tacire ta shiga chatting wurin 9:00 sai ga Ammy wacce shazim ya dauko falo ta tsaya shi kuwa up stairs ya haura sai 9:30 fatima da Ammy su kayi dinner dan shi shazim cewa yayi takai masa part din sa suna kammala wa fatima ta kwashe kayan da suka yi amfani dasu ta kai kitchen nan falo ta zauna suna fira da Ammy sai wuri 10:00 su katashi kowa ya shige bedroom dinsa , zaune yake kan sofa dake bakin bed dinsa yana aiki a laptop dinsa sai wurin 12:00 ya rufe laptop din toilet ya nufa bayan 5 minutes yafi to jikin sa da danshin ruwa da alama alwala yayi, wardrobe dinsa ya nufa sallaya ya fito da Ita ya shim fida shafa'i da wutiri yayi ya jima kan sallayar yana adu'oi sannan ya niketa ya maida ta cikin wardrobe, bed dinsa ya nufa hadi da kashe bulbs din dakin bedside ya kunna, zama yayi daga bakin bed din adu'a yayi ya sha fa a fuskar sa sannan ya ida hawa kan bed din kwanciya yayi hadi da jan blanket yarufe iya kugunsa. To nace Asuba tagari doctor nima bari naje na nemi nawa makwanchi.😴 Washe gari....... Zaune Ammy da fatima suke kan dinning suna breakfast, shazim ne ya shigo jikin sa sanye da jogging suit black color sai p-cap white hannun sa rike da water bottle wurin su Ammy ya nufa " ina kwana Ammy fatan kin tashi lafiya ya fada Ammy tace "lafiya lau alhmdllh, yau baka zuwa abnoor ne, amsa ya bata da " A'a Ammy zanje, ok naga har 10:30 tayi Ammy ta fada , shazim yace " eh wlh nayi late wurin tashi daga bacci amma yanzu zan shiga ciki nashirya Insha Allah, to shikenan sai ka shirya ga breakfast dinka nan na jiran ka a dinning, to Ammy ya fada hadi da nufar part din sa............. ✨ _Victoria_ . ✨ Anguwace ta christianity irin ta masu kara min Karfi, destiny naga ni ta fito da ga wani gida ta nufi wan da ke opposite din inda ta fito jikin ta sanye da gown iya gwiwarta purple color kanta da kitson kalaba na attachment ka farta sanye da flat shoe, gidan dan karami ne, ko ina ya sha cement dakuna biyu ne a gidan nufar daya daga cikin kofofin tayi knocking hadi dacewa" excuse" daga cikin dakin naji ance "come in" tura kofar tayi hadi da shiga Victoria ce acikin dakin tana ta faman jan straight gown taki shigar ta destiny ce tace " lallai Victoria a she bakima shirya ba kin kuwa san nisan da wurin ya ke da shi sai fa munfita Lagos kuma fa kinsan yau ana zuwa church da yamma, sorry destiny yanzu zan shirya mu tafi, abun da yasa ma nayi late bari nayi sai momy ( mahaifiyar ta ) ta tafi market sannan domin in tasan inda zamu ba zata bari mu tafi, Victoria naga ma shiryawa suka fita gidan tafiya sukayi sai da suka hau kan titi tukun suka tsai da mai mashin suka hau, tafiya su kayi mai dan nisa sannan suka kawo wani dan karamin kyauye duk duwatsu suna kawowa inda mashin bai wuce wa suka sauka, kudin sa suka bashi su kuma suka cigaba da tafiya nanma sai da su kayi tafiya ba laifi tukun suka kawo wata yar bukka ita kadai a wurin sai mutane jere a bakin bukkar suna karaso wa suma suka bi layi, sun jima a tsaye layi bai zo kansu ba, victoria harta gaji da tsayuwa ta duƙa, lokacin da layi ya zo kansu shiga sukayi tare cikin bukkar, wani mutum ne zaune gaban sa wasu kahuna ne sai kawunnan mutane kwaran gwal jikin sa sanye yake da jajayen kaya fuskar sa duk ta sha digedige fari sai idanun sa kewaye da bakin fenti gaishe dashi sukayi dawani irin yare mara dadin ji shi kuwa kwashewa yayi dawata irin dariya sannan ya tambaye su meke tafe dasu, destiny ce ta kora masa bayani a kan abun da yake tafe dasu, dariya ya sake kwashe wa da Ita sannan yayi yan surkullen shi wani magani ya dauko cikin wani bakin tulu ya basu destiny tasa hannu ta karba ita kuwa Victoria sai zare idanu take kudi suka dauka masu yawan gaske suka ajiye a gaban bokan sannan suka fice daga bukkar ta hanyar da suka biyo ta nan suka bi sai da suka kawo cikin kyauyen tukun suka samu wani mashindin ya dawo dasu gida, gidan su destiny suka wuce dan lokacin kafe 4:15 dakin destiny suka nufa zama sukayi suna huce gajiyar tafiya destiny ce tace" ina zuwa" tana fada ta fice daga dakin batafi 1 minute ba ta dawo da kwano a hannun ajiye shi tayi gaban Victoria fita ta sake yi sai gata ta sake shigowa hannun ta rike da pure water guda biyu zama tayi hadi da bude kwanon sakwara ce da miyar okra ( kubewa) suna cikin ci saiga wani namiji ya shigo dakin sanye ya ke da crazy jeans sai singlet gashin kansa kuwa yasha dada ( yanda yan iska keyima gashin su ya koma kamar lagwani )da kaga yana yin sa zaka san a buge yake, ya na ganin Victoria ya kama washe baki daure fuska Victoria tayi tana ganinsa , kusa da Ita ya matso kamar zai yi hugging din ta ba shiri ta mike tsaye hadi da daka mashi tsawa tana cewa" which kind of this nonsense samuel " bangane wulakanci ba Victoria you are my wife ya fada yana washe baki, destiny dai na gefe tana kallon su bata ce masu kala ba sai da taga Victoria na niyyar fita da ga dakin sannan taba Victorian hakuri shi kuma Samuel ce mashi tayi "ya fita ya basu wuri tun da shi ba shi da hankali , Victoria tace bata son shi to mi yasa zai ta kura ma rayuwar ta, Komawa Victoria tayi ta zauna sai wani cika take tana batsewa, suna kammala cin a binci fita su kayi bakin wani fanfu suka wanke hannu Victoria ce tace "destiny zan tafi gida domin nayi shirin zuwa church din kuma kin ga momy bata san nafita ba kar ta dawo bata ganni ba, kawai dai kinson zuwane amma aikin san bata dawo ba, da ta dawo da mun iske momy ( mahaifiyar destiny ) a gida itama ta dawo tun da wurin business din su daya, kuma tare suke fita su dawo tare, to kawai Victoria tace, komawa su kayi dakin, destiny tace " kinsan fatan da nake kuwa Victoria, Aa sai kin fada Victoria ta fada tana sauraron mi destiny zata ce, so nake wannan wawuyar hidaya ta taya ki bama dr hakuri kamar yarda da tace, a samu sa'a shi kuma ya maida ki uhmmm zata sha mamakin abun da zamuyi mata dan sai munrabata da eko ma gaba daya yan da ba zata sake ganin dr ba, nima haka nake so zata sha mamaki In dai ya mai da ni wuri na, dariya sukayi harda ta fawa suna nan suna shirya yan da za su yima hidaya sai ga mahaifiyar destiny tashi go , suna jin shigo warta suka fito daga dakin gaishe da Ita su kayi yayin da destiny ke amsar kayan da momyn ta ta shigo dasu, Victoria ce tace "ni na tafi" to saina shigo destiny ta fada tana fita gida ta shiga momynta ta samu a dakin zaune cewa tayi" good afternoon momy , afternoon daga ina kike na shigo baki nan momyn tafa da , ina gidan su destiny ne momy, ok kawai momyn tace, wurin 5:00 suka shirya domin zuwa church ( suna zuwa church su duk ranar Asabar domin gyaregyre sbd lahadi ) gidan su destiny , Victoria taje daga chan suka wuce church din......... _Katsina......_ Mom ce zaune a main falo suna fira da baaba larai abdallah ne ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya wurin su mom ya zu hadi da cewa fira kuke ne nagan ku zaune, wlh kuwa sai ina haka naga kasha jallabiya mom tafada amsa ya bata da cewa zan danje wani wuri ne daga nan zan tsaya sai angama sallah sannan zan dawo, mom tace" ah kace wurin diyata za'a amma sai kaje mata da jallabiya sai kace wani limami, murmushi kawai yayi hadi da cewa " mi za kiyi da wata diya keda kike da yan biyu duk mata a gaban ki, mom ce tace " duk da ina dasu kari ai bai kin dadi koh baaba larai" haka ne kuwa hajiya baaba larai ta bata amsa, Mom ce ta kuma cewa" ni dai yau she zaka kawo man surukata gidan nan" abdallah ne yace " ki bari mom dana samu wacce ta dace dani zan kawo maki Ita har gida, uhmmm Allah ya shirye ka abdallah wata kan har yanzu baka samu wacce tada ce da kai ba ko, nasan maganinka ai sawa xanyi abie dinku ya zabo maka mata tun da kai ka kasa Mom ta fada, abdallah yace" haba mom kamar ni za'a za boma mata, ai kuwa dana bani , yo ai sai abokaina suyi man dariya, mom tace" to In dai baka son auren dole to ka fito da mata kayi aure, kai ko kunya bakaji shekara 30 fa amma ace baka da mata haba ina amfani ' dan Allah mom kibar batun auren, dolenan , In dai aure ne very soon zanyi in Allah ya yarda, Allah ya yarda mom ta fada, ni na wuce sai na dawo ya fada hadi da nufar kofar fita, a dawo lafiya mom ta fada , fira mom suka cigaba Ita baaba larai suna nan zaune sai gasu Aaimah sun shigo da'a lama daga Islamiyya suke dan jikin su sanye suke da hijabi blue color gaishe da su su kayi sannan suka nufi bedroom din su wanka su kayi hadi da alwallar magrib sannan suka sanya kaya marasa nauyi a daki suka zauna har sai da su kayi sallah isha tukunnan suka fita falo fira sukeyi a kan Islamiyya anan mom tasa me su har da abie wanda baijima da dawowa ba daga masallachi nan sukai ta fira har 9:00 sannan su kayi dinner kowa ya wuce dakin sa suna shiga daki wayar Aairah na ringing dauko wayar tayi dake ajiye kan bedside murmushi tayi data dauki wayar taga mai kiran Aaimah ce tace " halan ya mus'af ne, daga mata kai Aairah tayi to sai da safe domin nasan ke ba yanzu ba Aaimah ta fada hadi da hayewa kan bed taja blanket Ita kuwa Aairah zama tayi bakin bed ta cigaba da waya ba Ita bace ta gama wayar nan ba sai wurin 10:55 sannan ta haye bed adu'a tayi ta shafa hadi da shafa ma Aaimah sannan taja blanket Ita ma bayan ta kashe bulbs da bedside lamp..... Asuba ta gari yan biyu 😴 Episode 7_8 Mom ce zaune a main parlor suna fira da baaba larai ya abdallah ne ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya wurin su mom ya nufo hadi da cewa "fira kuke ne nagan ku zaune? " "eh , sai ina haka nagan kasha jallabiya" mom ta fada amsa ya bata da cewa zan danje wani wuri ne daga nan zan tsaya sai angama sallah sannan zan dawo, mom tace" ah kace wurin ɗiyata za'a, amma Sai ka je mata da jallabiya Sai kace wani limami," murmushi kawai yayi hadi da cewa " mizakiyi da wata diya ke da kike da yan biyu duk mata a gaban ki, mom ce tace " duk da ina dasu ƙari ai bai ƙin daɗi koh baaba larai? " haka ne kuwa hajiya baaba larai ta bata amsa, Mom ta kuma cewa" ni dai yaushe zaka kawo man surukata gidannan? " abdallah ne yace " karki damu mom, dana samu wacce ta dace dani zan kawo maki ita har gida, uhmmm Allah ya shirye ka abdallah wata kan har yanzu baka samu wacce tada ce da kai ba ko, na san maganin ka ai, sawa zanyi abie dinku ya zabo maka mata tun da kai ka kasa Mom ta fada, ya abdallah yace" haba mom kamar ni za'a zaɓo ma mata , ai kuwa dana ji kunya, yo ai sai abokaina suyi man dariya, mom tace" to In dai baka son auren dole to kafito da mata kayi aure kai ko kunya bakaji shekara 30 fa amma ace baka da mata, haba ina amfani ' dan Allah mom kibar batun auren dolen nan In dai aure ne very soon zanyi in Allah ya yarda, Allah ya yarda mom ta fada, ni nawuce sai na dawo ya fada hadi da nufar kofar fita, a dawo lafiya Mom ta fada , fira mom suka cigaba Ita baaba larai sai gasu Aaimah sun shigo daga Islamiyya jikin su sanye da hijabi blue color, gaishe dasu su kayi sannan suka nufi bedroom din su , wanka sukayi hadi da al'walar magrib sannan suka sanya kaya ma rasa nauyi a daki suka zauna har sai da sukayi sallah isha tukunnan suka fita parlor,kan sofa suka zauna suna fira islamiyya a nan mom ta same su harda abie wanda baijima da da wowa ba daga masallachi nan suka zauna suna fira har 9:00, sannan sukayi dinner kowa ya wuce dakin sa , suna shiga daki wayar Aairah na ringing dauko wayar tayi dake ajiye kan bedside tana murmushi ganin mai kiranta, Aaimah ce tace " halan ya mus'af ne, daga mata kai Aairah tayi, to sai da safe domin nasan ke ba yanzu ba Aaimah ta fada, bed ta nufa ta kwanta taja blanket , Ita kuwa Aairah zama tayi bakin bed ta cigaba da waya, ba ita bace ta gama wayar nan ba sai wurin 10:55 sannan ta haye bed, adu'a tayi ta shafa ta shafa ma Aaimah sannan taja blanket Ita ma bayan ta kashe bulbs da bedside lamp..... _Washe gari........_ Zaune suke kan sallaya suna adu'a da tasbihi, tashi Aaimah tayi daga kan sallayar ta nufi inda suke Ajiye Alqur'ani , guda ɗaya ta ɗauko, kusa da Aairah ta dawo ta zauna hadi da mika mata tana cewa" sister amsa in karanto maki haddar da nayi, inda nayi kuskure saiki gyara man," to in dan na gama maki nima sai ki amsar man"to Aaimah " karatu ta fara cikin ƙira'a mai daɗi ,Aairah na sauraron ta inda tayi kukure sai ta gyara mata, sai da suka gama amsar ma junan su hadda tukunnan suka mai da qur'anan wurin da suke a jiye su , fita suka yi daga bedroom saboda gari ya waye Ƙarfe 7:00 na safe, main parlor suka nufa a kitchen suka samu mom da baaba larai suna hada breakfast gaishe dasu sukayi , amsa masu su kayi cikin kulawa Mom tace " ina fatan dai kungama hardar ku ta yau, eh mom , to masha Allah, baaba larai tace " kace muna da bikin hadda dana kammala makarantar gagarumi gidan nan, to Allah ya taimaka ya nuna mana lokacin lpy" har hada baki suke wurin cewa ameen, kama masu aikin su kayi harsuka gama sannan su Aairah suka jera kan dinning, bedroom din su suka koma domin shirin zuwa Islamiyya ( Islamiyyar harda suke, in suka tafi tun safe sai yamma duk ranar weekend, Idan kuma ba weekend bane karfe 2:30 suke zuwa sutaso da yamma, amma ban da ranar Friday in kuma an yi hutun school to kullum ne ban da friday .) Aaimah ce ta fara shiga toilet domin yin wanka ita kuma Aairah uniform dinsu na Islamiyya ta dauko masu tare da bags dinsu , Aaimah na fitowa itama ta shiga shaf shaf Aaimah ta shirya cikin uniform din san da Aairah ta fito har Aaimah ta gama shirin ta ita ma cikin kankanin lokaci tashirya suna gamawa suka fice zuwa main parlor dinning suka nufa domin yin breakfast suna gamawa part din abie da na mom suka nufa domin ce masu zasu tafi , a dawo lpy suka yi masu , fita su kayi harabar gidan anan suka samu mudi na jiran su dan shine ke kaisu, sai wurin 10:00 su mom su kayi nasu breakfast din saboda weekend........ ✨ _SHAZIM_ ✨ Yau sunday baya zuwa aiki , kwance yake kan sofa a bedroom din sa ya baje papers da laptop din sa yana, tun da ya gama sallar asuba ya ke nan wurin yana aiki har bacci yayi awan gaba da shi, jikin sa sanye yake da jallabiya, wayarsa ajiye saman cikin sa yayin da ya sa ɗayan hannun sa ya rufe fuskar sa, wayar sa dake saman cikin sa ce ta fara ringing, hannun sa dake kan fuskar sa ya janye yana ya tsina fuska alamar an katse mashi baccin sa , daukar wayar yayi "Brother" shine sunan daya bayyana akan screen din wayar picking call din yayi hadi da Kara wayar a kunne " hello Yaya na cikin wayar ya fada, "ba zaka chanza ba ko noraiz , ina amfanin wani hello kana muslim " " a fuwan big bro noraiz ya fada, Allah ya shirye ka, ameen Yaya ka tashi lpy yasu Ammy da fatima? , lafiya lau suke kaifa, Ina fatan kai ma kana lafiya? , ina lpy Yaya, oka Masha Allah shazim ya fada hadi da cewa ya maganar da wowar ka yau, domin da naga kiranka nayi tuna nin kace man ka iso dan nasan halin ka da chanza lokaci idan zaka dawo , A'a ba haka bane Yaya ina nan zuwa yau din Insha Allah , kawai dai ban samu biyo jirgin safe bane shiyyasa nakira ka na fada maka sai dai da yamma insha Allah, ok Allah ya kawo ku lpy, ameen Yaya sai an jima, ok kawai shazim ya faɗa hadi da kashe wayar ya ajiyeta kan center table, sai da yayi 5 minutes a kan sofar sannan ya mike, papers din da ya baza ya kwashe da laptop ya saka cikin din briefcase, cire jallabiyar dake jikin sa yayi ya koma da gashi sai shorts toilet ya nufa ya jima a toilet din sannan ya fito ya nufi dressing mirror anan ma ya jima yana yan shafe shafe sai kace mace sannan ya nufi clothes dinsa shiryawa yayi cikin jeans and T_ shirt fita yayi daga bedroom din part din Ammy ya nufa a parlor ya same ta Ita ka dai, fatima na Islamiyya, gaishe da Ita yayi , amsa mashi tayi wuri ya samu ya zauna kusa da ita, Ammy tace " ga breakfast dinka chan kan dinning tun dazu har nayi tuna nin yau baka fitowa a daki za kayi weekend , wane ni Ammy , kina a gida na zauna daki, ai dole na fito na tayaki fira, tun da auta na Islamiyya kuma rigimenmen ki baya nan duk da yau zai dawo , murmushi kawai Ammy hadi da cewa kunyi waya da shine naji yace da safe jirginsu zai taso, kin dai san halin ka yanki Ammy da chanza lokaci inzai dawo, wai kuma yanzu sai yamma tukun, Allah ka shirya mai babban suna kai dai, ameen Ammy ya fada hadi da tashi ya nufi dinning, warmer din dake kan dinning din ya shiga bu dewa yana duba abun da ke cikin su. cup ya dauka ya hada tea sannan ya zu ba arish, wurin Ammy ya dawo ya zauna suna fira shi da Ammy yayin da shi kuma yake cin abincin sunjima suna fira har aka fara kiran sallar zuhur sannan su ka tashi Ammy ta nufi dakinta shi kuma ya nufi part din sa domin yin alwala..... ✨ _HIDAYA_ ✨ Flat house ne me kyan gaske Masha Allah na masu rufin asiri kutsa kai nayi cikin parlorn gidan wanda komai na cikin sa brown color ne, hidaya naga ni zaune kan dinning ta lunch ita da mahaifiyar ta kamanin su ɗaya, tashi hidaya tayi mahaifiyar ta tace " mi ki ke nufi, naga kin tashi ? " " na ƙoshi ne mama" wai ni kam hidaya mike da munki ne, a ce kwata kwata mutum baya son cin abinci, ko baki da lafiya ne," " lpy ta kalau mama, dan nayi breakfast a makare ne , amma lafiya ta qalau, to shikenan, bedroom din ta ta nufa, kayan jikin ta ta cire ta shiga toilet ta dan jima sannan ta fito jikinta daure da da towel, dressing mirror din dake dakin ta nufa simple make-up tayi sannan ta nufi wardrobe din dake kusa da dressing mirror din, gwon ta dauko ta atamfa da mayafi, shiryawa tayi cikin kayan Masha Allah dan bakaramin kyau kayan sukai ma fatar taba, da yake hidaya chocolate ce ita ba faraba sannan ita ba baka ba, wayarta dake kan bed ta dauka da jaka wurin da takalmanta suke ta nufa ɗan flat shoe ta dauko tasa , fice wa tayi daga dakin bedroom din ta nufi na mamar ta zaune ta same ta kan gado sallama tayi hadi da cewa" mama zan tafi gidan su maryam" mama tace " to shikenan sai kin dawo ina gaishe da hajiya lubabatu, sannan karfa kiyi yamma kinsan dai Baban ku yana gari, insha Allah mama bazan jima ba zan dawo, to saikin dawo fita tayi daga bedroom din hadi da ficewa , a bakin gate ta tsaya tana neman abun hawa bata jima ba ta samu napep shiga tayi sannan ta yima mai napep din kwatancen anguwar da zai kaita, tafiya sukayi mai dan nisa balaifi sannan suka iso wata anguwa bakin gate din wani gida yayi parking me napep din fita tayi hadi da bashi kudinsa ya wuci ita kuma ta nufi gidan, mai gadi ta samu zaune akan ɗan benchi, gaishe da shi tayi, ya amsa mata yana faɗin "yasu mama ku, suna lafiya da alama ya santa shiga tayi cikin gidan, part biyu ne gidan daya daga ciki part din ta nufa shiga tayi tai parlor gidan yake kamar ba kowa wani dan corridor ta nufa ɗakuna ne kusan guda hudu ƙofofin su na kallon juna wanda, ke farko ta shiga bedroom ne mai kyau , bed ne sai wardrobe da toilet da dressing mirror, ba kowa dakin sai karar ruwa daga cikin bathroom alamar a kwai mutum a ciki wuri tasamu gefen bed din ta zauna batajima da zama ba sai ga maryam ta fito daga bathroom daure da towel " a she dai zaki zo maryam din ta fada , wlh kuwa , zan zo mana, ykk ya gida ya su mama, lpy qlu suke maryam ta fada hidaya tace " bakowa ne gidan sai ke kadai? " " A'a suna nan , kawai dai suna ɗaki ne, ok, naji shiru ne da na shigo , A'a suna nan bari dai nasa kaya dai" maryam ta fada haɗi da nufar wardrobe, kaya ta dauko riga da skirt na martial , shaf shaf ta shirya sannan ta dawo wurin hidaya ta zauna tana fadin " wai ni kam sister ya kuka kare da Victoria kinsan tun ranar da ku kayi fada da ita, bamu sake wata magana ba, ya kuka kare naga dr ya mai da ki wurin ta, kin kuwa san dadin da naji, domin nasan insha Allah burinki ya kusa cika" hidaya tace " bakomi , bamu sake wata magana da ita ba da sunan sa in sa ba, dan har roƙuna su kayi ita da destiny akan na taya ta bama dr hakuri ya maida ta wurin ta, to ke saikika ce mata mi? Maryam ta fada ta na tsare ta da idanu , hidaya tace " mazan ce kuwa maryam, tun da ta roƙe ni mi zai hana, amma wallahi hidaya baki da hankali sai kawai kije kice ma dr dan Allah yayi ma Victoria hakuri koh, uhmmm ko dai yanzu kin haƙura da shi ne baki son sa yanzu? Maryam ta jefa mata tambaya hidaya tace " wlh maryam bazan boye maki ba ina son dr har zuciyata, to amma shine zaki taya ta kuma kinsan cewa son shi take, dama kawai take jira ta raba shi da kowa , to ya zanyi maryam, komi tayi dan kanta tun da har ta roƙeni zan taya ta mana,maryam tace " uhmm sannu uwar masu tausayi tun da ta rokeki ai sai ki bashi haƙurin, wlh ke ba kisan wacece Victoria da destiny ba, su kan su muna funtar junan su suke yi inma baki sani ba to kisani ita kanta destiny din son dr take muna funtar Victoria kawai take, shiyyasa kike fadan haka ni da na daɗe dasu ni zan baki labarin ko su su waye garama tun wuri ki mai da hankalin ki a kan dr ki kyale wata Victoria da destiny chan , amma fa inkinji shawarata, dan wallahi kika tai make su, sai kinyi dana sannin haka, amma fa inkinji, shikenan ngd sosai da shawarar ki , amma sister sai nake ganin kamar dr bazai soni ba, kina ganin in ya shigo hospital duk matan dake hospital din bamu isheshi kallo ba, amma zan ciga ba da rokwan Allah in har shi alkairi ne a rayuwa ta Allah ya tabbatar man, to ameen, amma ya ka mata kisanar dashi cewa kina son sa, ko ba komai zai san ke masoyiyar sa ce, koya kike gani, zanyi kokarin haka insha Allah, amma gaskiya ina tsoron abun da zai biyo baya karma ya zo ya da katar dani kamar yan da yayi ma Victoria , abun da bazan soba kenan Maryam c tace " to idan baki fada masa ba taya zai gane kina son shi , ki fada masa kawai insha Allah ba abun da zai biyo baya sai Alkairi kuma insha Allah zan taya ki da adu'a, smeen sister nagode sosai Allah ya barmu tare, ameen karki damu maryam ta fada chanza firar su kayi zuwa wata suna nan zaune har a kayi sallar asr , sallah suka tashi su kayi sannan suka fita daga dakin suka nufi parlorn gidan Wannan kenan.......... ✨ _Ammy_ ✨ Zaune take kan sallaya a bedroom dinta bata jima da gama yin sallah ba wayar ta da ke kan dressing mirror ce tayi ringing hannu tasa ta dauko wayar murmushi tayi hadi dacewa "Allah sarki mai babban suna ina jin ya kara so, daga wayar tayi hadi da Kara wayar a kunne sallama tayi da murmushi a fuskar ta, on the other hand na cikin wayar yace wa'alaikumus salam my Ammy ya gida, lafiya lau mai babban suna ya hanya, alhmdllh ammy mun kusa sauka insha Allah , nan da Karfe 5:30 shiyyasa na kira ki fada ma ilya yazo ya dauke ni na kira Yaya bai dauka, may be baya kusane Ammy ta fada" to Ammy ki fada ma ilyan, yanzu kuwa Allah dai ya kawo ku lpy, ameen Ammy wlh harna ƙosa na ganni kusa da ke, Allah dai ya dawo da kai lafiya, ameen ya fada, kashe wayar tayi , mike wa tayi daga kan sallayar parlor ta fita kan sofa ta zauna , number ilya ta shiga nema cikin wayar ta sai ga fatima ta dawo daga Islamiyya wurin Ammyn ta nufo hadi da cewa " barka da gida Ammy, mikike yi zaune ke kadai s parlor? , ta fada yayin da take samun wuri kusa da Ammy ta zauna, amsa Ammy ta bata da "number ilya nake nema saboda zai dauko mai babban suna , ya noor ya dawo ne ta fada hadi da mikewa harzata nufi upstair Ammy tace " dawo uwar zumuɗi cewa nayi zai dauko shi bawai ya dawo ba" da wowa tayi tana turo baki gaba hadi da cewa "to Ammy ƙarfe nawa zai dawo , Ammy tace" ƙarfe 5:00 insha Allah jirgin su zai sauka, shiyyasa yace a kira mashi ilya yaje ya dauko sa;; Ammy dan Allah zanbi ilya inzai tafi, cewa Ammy tayi" to shikenan maza kije " bata ma tsaya sauraron mi Ammy zata ce ba ta nufi dakin ta da sauri, wanka ta fara shiga bata jima ba ta fito sanye da bathrobe shaf shaf tashirya cikin doguwar riga abaya tayi rolling da gyelen a kanta, wayar ta kawai da jaka ta dauka ta fice daga dakin inda tabar Ammy nan ta sa meta, ƙara sowa fatima tayi wurin ta tana fadi" yawwa Ammy na shirya kinyi ma ilyan magana " A'a bari nayi sai kin shirya tukunnan , ai a kwai sauran lokaci, duka yanzu ƙarfe 4:00 kuma kinga cewa yayi sai 5:30 jirgin zai sauka Ammy ai da kinyi mashi magana, kinsan fa a kwai nisa Airport din zamu yi kusan 20 to 30 minutes bamu kai ba fah kuma ga go slow" Ammy tace "haka ne nasha'afa ne shiyyasa amma bari na kira ilyan ya fitar da mota sai ku tafi ta fada yayin da take kiran ilya a waya yana picking tace " ilya ka fitar da mota zakuje Airport kai da fatima domin dauko mai babban suna yana hanya, to Ammy insha Allah yanzu kuwa zan fito da ita ilya ya fada da yake shima Ammy yake cewa, to shikenan ga fatimar nan fito wa Ammy ta fada hadi da rejecting din kiran, mike wa Fatima tayi hadi da cema Ammy sai sun dawo a dawo lafiya Ammy tayi mata sannan ta tashi ta nufi , kitchen innah Asabe ta samu a kitchen din tana gyarashi domin fara shirye shiryen dinner , Innah asabe na ganin ammy tace " barka da fitowa hajiya, da yawwa Ammy ta amsa mata" kina bukatar wani abune ? Innah asabe ta fada saboda ganin Ammyn datayi a kitchen a wannan lokaci " eh kinsan mai babban suna na hanya to shine nake son a daura dinner tun yanzu , kuma shima shazim bai ci komai ba ya fita ga fatima ita ma kuma, kinga in aka gama da wuri zai fi ai, innah asabe tace"ah yaufa muna da babban bako,shiyyasa naga fatima ta wuce da gudu dan bata ma lura da niba Ammy tace" kinsan halin Fatima da zumuɗin, ai ina ce mata yana hanya duk tabi ta rude tana chan tabi ilya Airport, dariya Innah Asabe tayi hadi dacewa" Allah dai ya kawo shi lafiya, ameen Ammy tace shirye shiryen daura dinner suka shiga yi.. ✨ _SHAZIM_ ✨ shigowa yayi main parlor bakinsa dauke da sallama, da alama daga waje yake baya cikin gidan, su Ammy dake kitchen suka amsa mashi sallamar, fitowa Ammy tayi daga kitchen din tana cewa" kai ashe baka gidan, ka kuwa yi waya da ƙanin ka? ya ce man ya kira wayarka baka dauka ba " " Eh na ɗan fita ne tun dazu har bedroom din ki nazo na same ki kina bacci, wayar na silent ne sai daga baya naga kiran sa, yace man ai kunyi waya akan kitura mashi ilya ya dauko shi, eh Ammy ta fada hadi da Komawa kitchen din shikuma part dinsa ya nufa, bedroom dinsa ya wuce kayan jikin sa ya rage ya nufi toilet bayan kamar 15 minutes sai gashi ya fito sanye da bathrobe dressing mirror dinsa ya nufa hadi da zama kan stool din dake gaban mirror din, ya jima yana yan shafe shafensa sannan ya nufi wardrobe , shiryawa yayi cikin kana nun kaya riga da wando, wandon baki iyakar sa gwiwarsa sai rigar fara mara nauyi mai gajeran hannu, wurin dressing mirror ya koma feshe jikin sa yayi da turare sannan ya fita daga bedroom din ya nufi down stairs parlorn Ammy, dinning ya nufa yaga bakomi, fita yayi daga parlorn ya nufi kitchen wurin su Ammy yana shiga yace " Ammy akwai abinci, yunwa nake ji, gashi nan ana girkawa saura ka dan mukarsa Ammy tafada, gaskiya Ammy bazan iya jiraba sosai nake jin yunwar babu wani abu koda mara nauyi ne? Ya tambaya, Ammy ta ce" bari na yanka maka fruit ta fada hadi da bude fridge ta dauko fruit ta wanke yanka mashi tayi ƙanana ta zuba mashi a ɗan bowl ta mika mashi amsa yayi hadi da cewa " nagode sosai Ammy sannan ya fice daga kitchen din, main parlor ya koma TV ya kunna hadi da daukar remote yana chanza channel zuwa TVC news, zaman shi yayi kan sofa yana shan fruit tana kallo Wannan kenan............ 🌹~ _KAINAAT_ ~ 🌹 _MURTALA MUHAMMAD INTERNATIONAL AIRPORT Mutane ne iri iri wasu najiran time din da zasu hau jirgi, wasu kuma sun zo daukar yan uwan sune, wasu na cikin mota wasu na zaune akan chairs din da aka ta nada domin masu zama. Motar su fatima ce ta kara so cikin airport din parking lot din dake wurin ilya ya nufa parking yayi, fatima ce tabfara fitowa sannan shima ya fito, cikin airport din suka nufa inda mutane ke zaune fatima ta nufa, wuri ta samu ta zauna , wayar ta da ke cikin bag ce ta fara ringing fito da ita tayi "YA DR" shine sunnan daya bayyana akan screen din wayar, picking call din tayi hadi da sallama, on the other hand nacikin wayar ya amsa mata sallamar " ina wuni ya dr , ya gida ya kwana biyu, lafiya lau Alhmdllh Bintalo, turo baki Fatima tayi cikin shagwaba tace" haba Yaya nace fa bana son sunnan amma baka dai na ceman ba, ta fada tana dan bubuga kafafu, dariya na cikin wayar yayi, ai kuwa nan tashiga yi mashi kukan shagwaba tana cewa " dariya ma na baka koh" "sorry fatimaaaaaa" ya fada hadi da jan sunan, Uhmmm kawai tace, sake mgn nacikin wayar yayi "bana ce kiyi hakuri ba, ai duk laifin kine kinsan fa nace kibar ceman ya dr nan da kika kware wurin kirana dashi, shiyyasa nima nace maki haka kinga nima na rama kenan, amma kiyi hakuri bazan sake ba kinji" "shikenan Yaya ya wuce" "Yawwah koke fa, yasu Ammy kina ina ne haka naji hayaniyar mutane? amsa ta bashi da " Ina airport , munzo daukar ya noor ne " " ok yau zai dawo kenan, kice ina gaishe dashi ina mashi ya gajiyar tafiya " " to zai ji Insha Allah yaya " " ok take care of your self for me pls, bye" ya fada, itama " bye" tace masa hadi da rejecting call din, game ta shiga bugawa a wayar tana nan zaune aka fara sanar war iso war jirgin 5:30 tashi tayi ta koma inda mutane ke tsai tsaye domin tarbar yan uwan su passengers ne suka fara biyo wata kofa da aka rubuta EXIST da manya harafi wacce domin su aka tana de ta fatima dai na nan tsaye, mutane kuwa wanda suga yan uwan su nata rugawa da gudu suna tarbarsu, ita dai sai zare idanu take sokawai take taga ta ina ya noor din ta zai bullo. Wani matashin saurayi ne ya bullo jikin sa sanye da ƙananun kaya jeans and T -shirt na company gucci, jaka rataye a kafadar sa baka jikinta an rubuta ADIDAS da farin paint da manyan haruffa, hannun sa rike da trolley yana ja P-cap ce a kansa sai face mask akallah zai yi kimanin shekara 25 a duniya. Fatima ce ta rugo da gudu tana fadin ya NOORRR tana nufar wannan saurayin, sakin trolley din dake hannun sa yayi fa dawa tayi jikinsa tana dariya hadi dacewa " shine kawani boye face dan nasha wahala wurin gane ka koh " janye ta yayi daga jikinsa yana cewa " Autar Ammy kedai haryau Allah baisa kinsan cewa kingirma ba koh, fatima tace " haba ya Noor haka ma za kace koh, shikenan tunda baka yi farin ciki da ganina ba " ta fada hadi da juyawa zata bar wurin, hannun ta ya riko yana cewa " sorry my yar qanwerh, wasa fa nake maki, kema kinsan nayi farin ciki da ganin ki autar mu " ya fada hadi da jan kumatunta tana dariya " koke fah " ya fada hadi da cire facemask din da yasa MASHA ALLAH nafada daganin wannan kyakyawar fuskar ta Noraiz kamannin sa daya da fatima , dan dai shi namijine ita kuma mace. ilya ne yakaraso inda suke yana washe baki Noraiz yace " kice tare kike da ilya Ammy " ya fada yana mikama ilya hannu domin suyi musabaha. ilya yace " ina wuni, ya hanya, ya aka baro mutane turai " dariya fatima da Noraiz sukayi jin ilya yace wai ya aka baro mutanen turai, amsa mashi Noraiz yayi da " alhmdllh ilya ya gida " amsawa ilya yayi da " lafiya qlu " ilya yace hadi da daukar trolley din Noraiz suka bar wurin, parking lot suka nufa booth ilya ya bude ya saka trolley da jakar Noraiz, shiga sukayi cikin motar Noraiz da ilya naga ita kuma fatima na baya, key ilya yayi ma motar suka bar airport din, hanyar gida suka nufa suna tafe suna fira Noraiz ne yace " wai ina ya shazim fatima " amsa ta bashi da "may be yana gida , danni banjima da dawowa daga Islamiyya ba na biyo ilya" "ok " kawai Noraiz yace yayin da suka iso anguwar su horn ilya yayi time dinda suka iso bakin gate din gidan, megadi ne ya bude masu gate din, ilya ya danna kan hancin motar ciki, parking lot ya nu fa parking yayi, fitowa su kayi daga motar suka nufi cikin gidan, ilya na biye da su a baya hannun sa dauke da trolley da bag din Noraiz. Shiga sukayi cikin gidan bakin su dauke da sallama Da sauri Noraiz ya nufi shazim dake zaune kan sofa, hugging din sa yayi hadi da cewa nayi missing din ka yy sosai shafa kansa shazim yayi kamar wani karamin yaro yana cewa " to ai yanzu komai ya wuce tun da gaka nan ka dawo" " haka ne kuwa yaya " Noraiz ya fada Ammy ce ta fito daga kitchen ita da Innah Asabe wurin su suka nufa Ammy nace wa" oyoyo mai babban suna " tashi Noraiz yayi ya nufi Ammy hugging dinta yayi yana cewa " nayi kewar ki sosai Ammynah " nima nayi kewar ka mai babban suna " Ammy ta fada, Innah Asabe ce ta matso tana cewa " marhabun lale mai babban mutum, ya hanya, ya kuma karatu " Amsa ya bata da " alhmdllh " nan suka shiga firar yau she gamo, ilya haurawa yayi upstairs domin kaima Noraiz kayan sa part din sa, baijima ba ya sauko yana cema kayan na part dinka nakaima maka. godiya Noraiz yayi mashi, ficewa ilya yayi ya koma bakin gate wurin mai gadi dama nan take zama. Noraiz ne yatashi yana cewa " zanshiga na watsa ruwa na fito naga time din sallah magrib yakusa" ya fada yayi da yake haurawa upstairs. Ammy c tace " shazim abincin fa koba yanzu ba " "A'a Ammy sai an jima in mun dawo sallar magrib sannan" to shikenan " Ammy ta fada , tashi yayi ya nufi upstairs shima Ammy ma da Innah Asabe nasu bedroom din suka nufa aka bar fatima ta gyara kitchen da jera abinchi kan dinning ( sbd bata sallah ) tana gama wa itama ta nufi nata bedroom din wanka tashiga ( dama tana yin wanka kusan sau hudu arana intana period ) ✨ _NORAIZ_ ✨ Fitowa yayi daga bathroom sanye da bathrobe ( part din sa shima ya hadu sai dai bai kai na shazim girma ba, amma dai masha Allah yayi kyau ) dressing mirror yanufa mai kawai yashafa ma jikin sa yanufi clothes set dinsa jallabiya ya dauko black color yasa wurin kayan sa da ilya ya kawo masa ya nufa, turare ya dauko cikin jakar sa ya fesa gadi da mai dashi Ficewa yayi daga part din dama yayi alwala tun a toilet , part din shazim ya nufa dake kusa da nashi yana shiga shazim din na fitowa daga bedroom din shima sanye ya keda jallabiya Ficewa kawai sukayi suka nufi masallachin dake chan main gate din gdn basune suka dawo cikin gidan ba sai da su kayi har isha tukun suka dawo cikin gdn parlorn Ammy suka yada zango fatima kadai suka samu zaune a parlorn suna zama sai ga Ammy ta fito wuri ta samu ta zauna tana cewa " to a tashi ga abinci chana najira " to suka cemata hadi da nufar dinning din Fatima ce tayi serving din su....... ✨ _KATSINA_ ✨ Zaune suke kan dinning suna dinner su duka gidan baka jin komai sai karar plate da spoon Suna gamawa abie da abdallah da Mom suka koma kan sofa yayin da su Aairah ke gyara dinning din, suna gamawa wurin su abie suka dawo suka zauna fira suka shiga yi abie na tambayar su yaushe zasu fara exam din SSCE " saura 3 weeks abie " suka bashi amsa " to Allah ya bada sa'a, da Ameen suka amsa " abie wace school zaka kaimu in mungama " Aaimah ta tambaye shi" ban gane inda zan kai kuba , kuda kuke da school a cikin grinku, a i ba sai kunje wani gari ba " abie ya fada yana tsare su da idanu " A'a gaskiya abie Muyi primary school da secondary school a nan sannan kuma ace munyi high school a nan gaskiya abie s chanza mana " to sai dai kunga ma exam din tukunnan, to shikenan abei " chanza firar sukayi zuwa wata, sai kusan 9:30 sannan su Aairah suka nufi dakinsu sbd sun fara karatun exam gakuma zuwa school gobe Suna shiga bedroom din su wanka sukayi hadi da sanya pajamas dinsu sannan suka dauki books dinsu suna dubawa sai wurin 12:00 sannan sukayi bacci....... Episode 9_10 Sanye suke da uniform din su na school, ko wacce rataye da school bag din ta, ficewa su kayi daga bedroom din suka nufi main parlor su Mom suka samu kan dinning suma basu jima da zuwa dinning area ba, gaishe dasu su kayi hadi da samun wuri kan dinning din suka zauna, abie ne yace " yau yan biyu an shirya dawuri kenan " amsa suka bashi da " eh abie " "to Allah ya taimaka ya ba da sa'a" da ameen suka amsa, mom ta miko masu tea da ta hada masu " thanks Mom" suka fada hadi da sa hannu suka Karba, basu fi minti 10 ba suka tashi suna goge bakin su da tissue paper suna fadin sai mun dawo , a dawo lpy su mom suka yi masu fice wa su kayi suna fadin Allah yasa. Suna fita daga gidan sai ga school bus dinsu ta shigo anguwar, sai da ta kawo dai dai inda suke tayi parking, kofar bus dince ta bude shiga su kayi daga ciki suka nemi wuri suka zauna kusa da wannan friend din ta su Aeesha Aeesha tace "twin friends yau wace rana kun fito da wuri kun hau bus first round " ta fada da murmushi a fuskar ta " kedai bari kawai Aeesha sa'a ce kawi yau " Aairah tafada yayin da Aaimah ke cewa " sai kace kema kullum da wuri kike zuwa Aeesha " dariya Aeeshar tayi hadi da cewa " ai wlh duk da haka gara ni dai " "bawani nan, wlh kema muguwar let comer ce " Aaimah tafa da yayin da bus din keshiga cikin School bus stop, bus din tanu fa parking tayi aka bude kofar student nata fita suna nufar assembly ground Inda ss 3 ke tsayawa nan su Aairah suka nufa annan suka samu sauran yan class din su wanda suka zo dawuri, gaisawa suka shiga yi. bayan 30 minutes aka gama assembly kowa ya nufi class din su ✨SHAZIM✨ Saukowa suke daga upstairs shi da Noraiz parlor Ammy suka nufa, kan dinning suka same ta , gaishe da ita su kayi Noraiz yace " ammy ina fatima nagan ki ke kadai kan dinning? " amsa ta bashi da " Fatima ai ta wuce school" " kai na manta fah, amma Ammy yau she take gama wa ne " " tace man dai next month zasu fara exam, daga wannan week din ma ta gama zuwa school sai kuma exam " " Allah ya taimaka ya bada sa'a, yaya " Noraiz ya kira Shazim dake zaune yana sauraron su, da na'am ya amsa mashi , Noraiz yace " amma dai yaya fatima a abuja zatayi university kamar yanda take bukata intagama secondary school "sai da yayi kusan 5 seconds sannan yace "A'a nan za tayi school din ta gata ga ammy, " ya fada fuskar sa babu a lamun wasa, hankan yasa dole Noraiz ya kama bakin sa yayi shiru amma baiji dadin shawarar da yayan nasu ya yanke ba, saboda fatima ta ƙwallafa rai akan zuwa abuja saboda sa'ada , " Allah ya taimaka " kawai yace yaci gaba da breakfast din sa, Ammy duk da ta fison fatimar tayi karatu kusa da ita.amma sai tace "wai shazim mi yasa kake haka ne, tun da kai ka janye jiki da abuja, mi yasa suma zaka sa dole sai sun janye jiki da abuja ne wai, miye ai bun dan tayi karatu a can, duk ni ma nafi son tayi kusa da ni" ɗan nisawa yayi sannan yace "ammy ni ba haka nake nufi ba, kwai naga zaki yi kaɗai ci ne, ke kaɗai a gida "katse shi ammy tayi da cewa "in dai dan ta nine karka hanata zuwa abuja, idan bata nan baga ku nan ba kai da noraiz " "ammy mu ba zama muke ba, idan muka fita tun safe sai dare fa muke da wowa" "to naji sai dare kuke da wowa, itama idan ta je makaranta ba sai da yamma zata riƙa dawowa ba? " ta ƙarasa faɗa da sigar tambaya tana tsare shi da idanu "ammy dan Allah kiyi haƙuri tayi karatun ta nan, itama sai ta fi jin daɗi karatun, chan haya niyar innah kawai ta ishe ta " uhmm kawai ammay tace ba tare da ta sake cewa komi ba , Ba wanda ya sake magana cikin su har suka kammala breakfast din , shazim ne ya fara ajiye fork din da yake cin arish hannu ya mika ya yagi tissue din dake kan dinning ya goge bakinsa sannan ya dauki robar ruwa ya sha, ya mike ya nufi sofar da ya ajiye briefcase dinsa ya na fadin "Ammy nizan wuce" cup din tea din da ta kai baki ta janye tana fadin " a dawo lafiya , Allah ya ba da sa'a, an jima ka dan zanje gidan baba may be baza ka same ni sanda zaka dawo, dan zanjima kilama sai dare ma zan dawo " " ameen, ina gaishe da malam, sai na dawo" ya fada yayin da yake shirin barin parlorn, Noraiz yace " a dawo lafiya Yaya, Idan na ajiye ammy gidan malam zan biyu ta wurin ka insha Allah " " Allah ya kawo ka lafiya " kawai ya fada hadi da ficewa, parking lot ya nufa motarsa wacce yasa aka wanke masa ya nufa, bude kofar motar yayi briefcase din sa ya aje da lab coat, sannan ya zagaya driver seat ya zauna , key yayima motar ya nufi main gate , gaisawa yayi da ma'aikatan gidan sannan ya fice daman mai gadi yariga da ya bude masa gate,eko ya nufa yana tafiya yana sauraron karatun alqur'ani a motar.... ✨HIDAYA✨ Tsaye take gefen titin anguwar su tana jiran abun hawa, kusan 5 minutes tana nan bata samu abun hawa bata samu ba, wata bakar motace ta shigo anguwar tasu, tunda motar ta shigo anguwar tasu take ma motar kallon kamar tasan mamalakinta, motar na ƙarasowa kusa da ita tana rage gudu, kallon motar kawai take sai da ta kawo dab da ita sannan aranta tace" wannan ai kamar motar dr kabir " parking motar a kayi hadi da sauke glass din motar, kyakyawan saurayine fari amma ba sosai chan ba, akallah zai yi kima nin shekara 28 zuwa 30, sanye yake da blue din kaya complete riga da wando sannan fuskar sa sanye take da glass, hidaya tace" ina kwana dr" amsa mata yayi da " lafiya lau , mikike yi tsaye anan " hidaya tace " ina jiran abun hawa ne dr" ok yace sannan kuma ysake cewa " to shigo ciki mu wuce " " A'a dr katafi kawai zan samu abun hawa insha Allah " hidaya ta fada, glass din dake fuskar shi ya cire hadi da cewa " to fah, hidaya ko dai kina tsoron na sayar dake ne iye " murmushi tayi hadi da cewa " A'a ba haka bane " ajiyar zuciya ya sauke hadi da cewa " to inhar ba haka bane, to kishiga mu wuce " to kawai tace hadi da zagayawa ta shiga ciki, key yayima motar yana cewa " wlh kina bani mamaki hidaya, sai kace wata ƙara mar yarinya in ki ka yi wani abun " murmushi kawai tayi masa ba tare da tace komai ba, haka sukai ta tafiya yana janta da fira har suka iso eko , parking lot din asibitin ya nufa hadi dayin parking, har tasa hannu zata bude kofa ya da katar da ita yana cewa " wai hidaya tsorona ki keji ne, naga har wani sauri kike ki fita" "A'a " kawai tace hadi da duƙar da kanta ƙasa, " shikenan bakomi kina iya tafiya "ya fada ficewa tayi daga motar shikuma ya tsaya tatara kayan sa dake back seat, tana fitowa motar shazim na parking, dr kabir ne ya fito hannun sa riƙe da tarkacen sa yana cema hidaya su tafi , tafiya suke sunkusa kawo inda motar shazim take sai gashi ya fito,miƙa masa hannu dr kabir yayi sukayi musabaha, hidaya ta gaishe da shi, da lpy kawai ya amsa mata , wuce wa tayi tabar su shi da dr kabir tayi cikin asibitin, office din su da nurses kezama ta nufa, ba kowa ciki sai friend ɗin ta maryam da alama wadan da suka zo duk sun fita. " lafiya yau ki ka yi late ? " maryam ta tambaya , ƙarasowa inda take hidaya tayi tana cewa "ke dai bari, banyi bacci bane jiya dawuri shiyyasa nayi late" dafa kafadar ta maryam tayi tana cewa " kingama yanke shawara yan da zaki tunkari dr da maganar koh " " a'a gaskiya, maryam ina jin tsoro ne, ban san ya dr zai dauki maganar tawa ba " hannun hidaya maryam taja suka zauna sannan tace " ki kwantar da hankalin ki hidaya Insha Allah alkairi ne zai biyo baya, kinji" ajiyar zuciya hidaya ta sauke tana cewa " to Allah yasa haka maryam " da ameen maryam ta amsa mata hadi da cewa " tashi mufita" ta fada tana jan hannun hidaya, fice wa su kayi suka nufi inda yan uwansu nurses suke, gaishe da junan su suka shigayi , office din dr Shazim hidaya ta nufa tana cema maryam " sister bari naje office din dr na dawo" "ok sai kin dawo " maryam ta fada, office din hidaya ta nufa hadi da tura kufar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. amsa mata sallamar yayi, sannan tace "dr asa patient a layi " amsa ya bata da" eh " har zata fice sai kuma ta dawo sai da tayi 2_3 seconds sannan dai ta daure tace" afuwan dr dama ina so ne Muyi wata mgn " ɗago kansa yayi daga aikin da yake ya tsare ta da idanu alamar ina sauraronki, magana ta fara " dama dr maganar Victoria ce " daga mata hannu yayi alamar ya isa haka " ya zama na ƙarshe da zaki ƙara man maganar ta a nan, in ba haka ba kema zaki bita , fatan kingane " " ok sir insha bazan sake ba " ta fada hadi da ficewa daga office din , direct wurin patient ta wuce, ta shiga aikin ta , a haka Victoria da destiny suka same ta, wuri suka samu suka zauna kusa da ita , gaisawa su kayi sannan Victoria tace " hidaya ya maganar mu ne" ajiyar zuciya hidaya tayi sannan tace " gsky kiyi haƙuri Victoria, ko yanzu daga wurin dr nake nayi nayi ya haƙuri amma yaki, dan har cewa yayi kona daina masa magnar ki ko nima ya koreni " wani kallon banza Victoria tayi mata sannan ta ce " munafukar banza, wannan nasan duk shirin kine, to kisani kamar yanda kika rabani da dr nima sai na rabaki dashi " mikewa hidaya tayi tana cewa" kije kiyi duk abun da za kiyi Victoria, tun da ke baki da mutunci " fada sosai ya kaure tsakanin su har Victoria na neman kaima hidaya duka, destiny na jenye ta, su maryam ne suka zo wurin saboda hayaniyar Victoria data jawo hankalin su, nan suka shiga cewa gsky baki da mutunci Victoria, komawa Victoria tayi kansu tana ce masu munafukai tasan ai da hadin bakin su, ai kuwa abun yayi masu zafi nan suka shiga maida mata da martani, Hayaniya ce ta damesa harta na neman haddasa masa ciwan kai hakan tasa shi dole ajiye abun da yake yi, telephone ️ din dake office din ya dauka, dialing numbers yayi ana picking call din yace kasa meni a office dina yana gama fada yayi rejecting kiran bayan 30 seconds sai gashi anturo kofar, wani security ne ya shigo gaishe da shazim yayi hadi da cewa dr gani " wai hayaniyar mi nake ji ne" afuwan dr bari naje na duba " ok kawai yace masa, fita security yayi inda su Victoria suke ya nufa nan ya same su har lokacin basu dai na fadan da suke, hidaya sai kuka take saboda a rayuwarta ta tsani fitina, su maryam ne ke maida ma Victoria martanin, ɗaya daga cikin nurses ɗin mata security ya tambaya mike faruwa amsa ta bashi " zuwana kenan na same su suna hayaniya sai dai ban san miye maƙasudun faɗan na su ba " " to shikenan " shine kawai abun da security ya faɗa ya komawa office ɗin shazim ya sanar dashi cewa " sir su nurse Victoria ne ke hayaniya, ina jin dai wani abun ne ya ha dasu " "Mutsww"shazim yaja tsaki a ranshi yace "nonsense kawai dasu, zasu wani tada ma mutane hankali , sakarkaru banza " achan kuwa waje dr kabir ne ya fito daga office ɗinsa ya nufi inda su Victoria suke shima hayaniyar su ce ta dame shi, yana isowa wurin dukan su su kayi shiru tsaki yaja hadi da cewa" wlh kunbani mamaki matuƙa , ashe bakuda hankali " ya fada hadi danuna hidaya ya nace wa " wacece nan , mi kuma akayi mata take kuka" da yake duƙe take shiyyasa bai gane ko wacece ba, maryam tace "dr hidaya ce" matsowa yayi kusa da ita yana fadi "mike da munta ne " amsa maryam ta bashi da cewa " Victoria ce ke ci mata mutunci ita kuma bata iya ramawa shine take kuka, mukuma " hannu ya daga ma maryam hadi da cewa "ya isa haka, oya tashi " yace ma hidaya, mikewa tayi fuskar nan duk tayi sharkaf da hawaye "wuce muje" yace, binsa tayi a baya har office ɗinsa , toilet ya nuna mata " shiga ki wanke fuskar ki " shiga tayi ta wanke fuskarta sannan ta fito wuri ya nuna mata kan sofa da ke cikin office din zama tayi tana sauke ajiyar zuciya ita bakomai yafi bata haushi ba wai a ce daga taimako Victoria zatayi mata haka, gyaran murya dr kabir yayi haɗi da zama kan sofar yana fuskantar hidaya yace " hidaya nasan wannan ba halinki bane miyasa kike biye ma mutane irin waɗanna, ke da ita bafa ɗaya bane al'adar ku ba ɗaya ba kwata kwata ita batasan kunya ba saboda ba'a koya mata ba amma ke duk wanda ya ganki zai yimaki kallon wacce bata san mutuncin kanta ba, pls hidaya karki sake" " insha Allah hakan ba zata sake faruwa ba nagode " " bakomai karki damu tashi ki tafi kicigaba da abun da kike yi " " ok" ta faɗa hadi da mikewa ta fice, wurin patient ta koma ta cigaba da turama dr su. ✨noraiz✨ Parlorn ammy ya shigo jikinsa sanye da kananu kaya farar riga da bakin wando, yana shigowa Ammy na fitowa daga bedroom dinta sanye take da hijab har kasa, Noraiz yace " yawwa Ammy harkin shirya kenan " "eh" Ammy ta fada, ficewa su kayi, parking lot suka nufa wurin wata bakar mota rang rover suka nufa Noraiz ne ya bude mata kofa sannan ya zagaya driver seat ya zauna hadi da yima motar key ya nufi main gate, megadi ne ya tashi ya bude masu gate gaishe da Ammy mai gadin yayi amsa mashi tayi cikin kulawa sannan Noraiz yayima motar key suka fice tafiya su kayi sosai sannan suka sha kwanar wani road mikewa suyi sosai sannan suka tsaya abakin wani gida horn Noraiz yayi abakin gate din gidan. ƙofar dake jikin gate din gidan aka bude wani mutum ne ya leko yana ganin motar Noraiz ya koma da sauri gate din gidan aka bude ciki Noraiz ya danna hancin motar ciki, parking lot din dake gidan Noraiz ya nufa hadi da yin parking, fitowa su kayi shi da Ammy suka wuce cikin gidan part biyu ne gidan , ɗaya daga cikin part ɗin suka nufa da sallama abakin su suka shiga cikin parlorn parlorn ne mai girman gaske wani dattijone zaune kan carpet sai wata yar tsohuwa dake kusa da shi tana mika masa magani da ruwa wurin su suka ƙarasa wannan yar tsohuwar ce ta dago tana amsa ma su sallamar da su kayi, haɗi da cewa "oyoyo ango saukar yaushe" noraiz na murmushi yace "jiya "yayin da suke wuri zama kan carpet, ammy tace "ina kwana ummy, ya jikin baba " ummy tace "lafiya lau, jiki alhmdllh" masha Allah Ammy tace , sannan ta kalli baba tana faɗin "ina kwana baba, ya ƙarfin jiki" " jiki alhmdllh da sauki wa nake gani kamar NURADDEEN? " Baba ya tambaya Noraiz yace " shine mlm ya ƙarfin jiki? " " jiki alhmdllh nuraddeen saukar yaushe" " jiya" Noraiz ya bashi amsa " masha Allah ya karatu?" "Alhmdllh mlm" masha Allah malam ya faɗa nan suka shiga fira har baba yana tambayar noraiz ina wannan ƙaton gwawron yyn nashi,mai gudun aure, murmushi kawai Noraiz yayi yana bashi amsa da yana hospital " Masha Allah, Allah ya taimaka " ya fada, sunjima suna fira har kusan 12 sannan Noraiz yace " mlm zanje wurin yaya " " to a dawo lafiya " "Allah yasa " Noraiz ya fada hadi da nufar kofar parlorn ya fice, daga gidan, kallon ammy malam yayi yana faɗin" jiya ahmad ya kirani kan maganar shazim, sun ji shi shiru, kuma suna ta kiran shi basu samu, har mansoor sai da ya kirani shima bai samun shi " "eh haka yace man nima da ya kirani " "kin faɗa ma shazim ɗin?" "eh na faɗa mashi, amma har yanzu ce man yayi bashi da wacce yake so " ɗan nisawa malam yayi sannan "na lura so yake mu cire hannun mu daga maganar, mu ƙyale shi da su ahmad ɗin su yanke mashi duk hukuncin da suka ga dama " " haka nace mashi, zamu cire hannun mu a lamarin suyi duk abun da suka ga dama" ummy tace "ba haka za'ayi ba malam, ina ga a ƙara mashi lokaci ko da ba mai tsayi ba" malam yace "lokaci na nawa za'a bashi zainab, tun yaushe ake bashi lokaci " "duk da haka dai, a ƙara mashi ko da wata ɗaya ne "malam yace "to shikenan" Noraiz yana shiga cikin eko parking yayi a parking lot, fitowa yayi s ya nufi cikin hospital, da yake office din shazim chansama yake hakan yasa shi hawan lifter yana fitowa daga lifter office din Shazim ya nufa nocking yayi daga ciki aka bashi iznin shiga ƙofar ya tura ya shiga, shazim ya samu zaune yana aiki cikin laptop sallamar da yayi shazim ya amsa mashi wuri ya samu cikin daya daga kujerun office din ya zauna " ya aiki yaya? " "Alhmdllh " kawai shazim yace yana yana tambayar jikin malam " alhmdllh yaya , yaji sauki" dr kabir ne ya shigo office din yana ganin Noraiz yace " saukar yaushe Noraiz " " jiya Yaya, ya Aiki " Noraiz ya fada "Alhmdllh Noraiz, ya school " "school alhmdllh " "masha Allah" fira suka shiga yi ta yaushe gamo shida dr kabir shazim na sauraron su yana aikin gaban sa, kiran sallar zuhur ne ya katse masu firar suka fice zuwa masallaci domin yin sallah daga cana abnoor shazim da Noraiz suka wuce......... ✨ Aairah ✨ dawowar su kenan daga school dan ko uniform basu cire ba suka haye bed saboda ba ƙaramin gajiya su kayi ba ' dan Aairah da wani irin zazzabi ta dawo Mom ta shigo ɗakin su tana cewa " lpy kuke, ko uniform baku cireba kun lama bacci " "wallahi mom mun gajine sosai shiyyasa, kuma ma Aairah bata jin daɗi , zazzabi ne a jikin ta " "wani aiki ku kayi ne a makarantar" mom ta fada yayin da take ƙarasawa kan bed, hannun ta ta ɗaura saman wuyan Aairah "ya salam " mom ta fada saboda jin zafin dake fita daga jikin Aairah " mi ke damun ki?" " zazzabi ne da ciwan kai" " ok yaka mata kitashi ki cire uniform ki watsa ruwa, bari naje na dauko maki magani kafin yayan ku ya dawo" tashi tayi zaune mom tace ma Aaimah ta shiga bathroom ta hada mata ruwan wanka, to tace hadi da nufar toilet, ficewa mom tayi daga daki Uniform ɗin jikinta ta cire ta daura towel, Aaimah ta fito tana cewa sister kishiga ga ruwan chan " to nagode sister " ta fada toilet ta nufa kayan jikinta ita ma ta cire Aairah na fitowa ta shiga kan gado Aairah tahau hadi da jan blanket saboda data yi wankan wani sanyi take ji Mom ce ta shigo hannun ta ɗauke da tere wanda ta hadoma Aairah abinci " wai kwanciyar kika sake " wurin ta mom ta nufo, table ɗin dake ɗakin ta jawo ta daura teren da ta shigo dashi, hawa tayi kan gadon tana fadin " tashi kici abinci ga maga ni nan " tashi tayi zaune " baki sa kaya ba kenan? " mom ta fada hadi da nufar wardrobe dinsu, riga mara nauyi mom ta dauko mata " tashi kisa,, mom tafada yayin da take mika mata rigar amsa tayi hadi da tashi ta sanya rigar sannan ta dawo kan gadon ta zauna abincin da ta haɗa mata tamika mata tana gama ci mom ta bata magani tasha sannan ta koma ta kwanta blanket Mom taja mata ta haɗa tiren da Aairah taci abinci ta fice da shi yayin da take cema Aaimah inta gama shiri ta fito taci abinci ita ma shaf shaf Aaimah ta shirya sannan ta dawo kusa da Aairah "sister ya jikin naki" "da sauki " Aairah ta fada "ok Allah ya kara sauki, bari naje naci abinci na dawo " gyada mata kai Aairah tayi alamar sai kin dawo ficewa Aaimah tayi daga bedroom din , parlor ta nufa Mom ta samu kan dinning ita da abie ƙarasawa tayi wurin su tana cewa " ina wuni abie " " lafiya lau , yanzu Mom din ku ke fada man Aairah bata jin dadi, ya jikin nata? " " da sauki abie " " to Allah ya bata lafiya, Idan abdallah ya dawo sai ya duba ta, inma taka ma ayi mata allura, koh mi kenan dai " abie ya fada, Aaimah a jiye spoon din dake hannun tayi tana dariya hadi da fadin " kace yau akwai buduri , Aairah za a yima allura tashin hankali kenan " " ka jita sai kace ba jirgi daya ya kwasu ku ba, kema son allurar kike ne " Mom tafa da hadi da mangare ma Aaimah kai, sosa inda Mom ta mangare ta tayi tana turo baki da fadin " Allah gara ni da Aairah Mom" "Bawani nan " Mom ta fada,suna gama cin abincin abee ya mike yana cewa " bari naje na duba jikin ta " ya fada yayin da yake nufar dakin su, samunta yayi kwance kan gado kamar yanda Aaimah ta fita tabar ta duk ta rufe jikinta da blanket har fuska, ƙarasawa gaban gadon abie yayi yana fadin " Aairah " "na'am abie " ta amsa mashi hadi da danjan blanket din ta fito da fuskarta " ya jikin naki " " da sauki abie " " to Allah ya ƙara sauki, Idan abdallah ya dawo sai ya duba ki kin ji" zanbur ta tashi daga kwance tana fadin " amma dan Allah abei idan ya dawo dan Allah karka bari yayi man allura, yaba ni mgni kawai " ta fada hadi da maida fuskarta kalar tausayi " to shikenan kwantar da hankalin ki magani kawai zai baki, kinji koma ki kwanta " " to abie " " Allah ya baki lafiya " abie ya fada hadi da nufar kofa ya fice.... ✨SHAZIM ✨ Sai bayan da akayi sallar magrib suka bar abnoor shi da Noraiz , direct gdn malam suka nufa domin ammy na chan har da fatima wacce daga school chan ta wuce Suna shiga gidan parking su kayi sannan kowanen su ya fito daga motarshi saboda Noraiz da motar shi yaje eko wurin shazim part din malam suka nufa zaune suka same shi a parlorn shi yana duba wani littafin addini sallama su kayi hadi da shiga cikin suka nemi wuri suka zauna Amsa masu sallamar yayi yayin da yake cire medical glass din dake fuskar gaishe dashi shazim yayi yana tambayar shi ya jiki " alhmdllh ya aiki " '' alhmdllh malam'' "to Allah ya taima ka" " ameen malam" fira suka shiga yi sai da aka kira sallar isha sannan suka tashi masallachi suka nufa harda malam ana gamawa suka dawo ciki,za su nufi part ɗin ummy malam yace noraiz ya tafi, shi kuma yana son magana da shi, wuce wa noraiz yayi, su kuma shi da malam suka shiga part ɗin malam, part ɗin ummy noraiz ya nufa, ammy da ummy ya samu a parlor fatima da yarinye kuma na kitchen Zama yayi kan sopa kusa da ummy yana mata shagwaɓa akan yunwa yake ji "ga abinci can su fatima na girkawa" "gaskiya ni bazan iya jiran su gama ba "ammy tace "to sai dai karka jira ɗin"ummy tace "a'a baza ayi haka ba, bari naje kitchen ɗin baza a rasa abun da zai ci ba kafin su gama "ta faɗa haɗi da tashi ta nufi kitchen ɗin , ammy tace "da kin ƙyale shi ummy, sai kace ba namiji ba " "A'a ke dai, wasa da ciki ai bai da amfani sai ulcer ta kama mutum" "wallahi kuwa ummy" jifan shi ammy tayi da pillow. A chan parlorn malam, "shazim bana son mu cire hannun mu akan lamarin su yanke maka hukuncin da baka so ba, gara tun wuri ka nema ma kanka masalaha" "insha Allah malam,zanyi ƙoƙari,ka basu haƙuri" "haka kake cewa kullum, har hakan yasa suna tunanin ni ke goya maka baya, kuma miyasa idan sun kira ka, ba su samun ka, mansoor ma ya kirani yace yanata ne manka amma baya samu " "bakomi, inajin network ne " "to kayi ƙoƙari ka kira su"da to ya amsa,tashi yayi yace zaije wurin ummy su gaisa, da to kawai malam ya amsa, part ɗin ummy ya nufa, a parlor ya same ta noraiz na kusa da ita yana cin abinci, wuri ya samu ya zauna yana gaishe ta amsa mashi tayi cikin kulawa hadi da tmbyr shi ya aiki "aiki Alhmdllh ummy, ya malam da jiki " ummy tace " jiki da sauki Alhmdllh " "to masha Allah, Allah ya ƙara sauki " " Ameen" fatima ce ta nufo idan suke, gaishe da shazim tayi tana cema ummy sun gama, ga abinci can kan dinning, da to ummy ta amsa, wurin dinning fatima ta koma tana cewa"ummy na malam fa, part ɗin sa za'a kai masa" "A'a, zai shigo "bata rufe baki ba sai ga malam ɗin ya shigo, tashi sukayi dukan su suka nufi dining ɗin, bayan da suka gama,shazim ya sake duba jikin malam ya sake rubuta mashi magunguna Sannan suka yi masu sallama,suka kama hanyar gida Ammy da shazim mota daya suka koma yayin da fatima da Noraiz suka shiga tasu suma Suna shiga gida Innah Asabe ta fito tana masu sannu da zuwa da tmbyr ya jikin mlm nan Ammy ke fada mata jiki da sauki alhmdllh, sannan kowa yakama hanyar bedroom dinsa, ita ma Innah Asabe nata dakin ta nufa........ Episode 11_ 12 Har yanzu kwance take kan gado kamar yanda abie ya barta sallah ce kawai take tashi tayi, Aaimah na zaune kusa da ita tana duba book dinsu na school saboda exam dasuke facing, nocking suka ji anayi Aaimah ce tace "waye" daga chan wajen taji ance "zaki zo ki buɗe ko sai kingama tambayar waye sannan" bashiri ta sauko daga gadon hartana niyyar faduwa saboda jin muryar wanda ke nocking din bakowa bane face ya abdallah, buɗe kofar tayi tsaye yake jikinsa sanye da gajeran wando iya gwiwa sai riga mara nauyi mai gajeran hannu Matsawa Aaimah tayi gefe shi kuma ya wuce ciki daidai bakin bed din ya tsaya yana cema Aairah ta tashi, tashi tayi zaune, shima zama yayi bakin gadon yana fadin "minene ke damun ki" "kaina ke ciwo sai zazzabi, amma naji sauki dan yanzu bana jin zazzabi" "ok" ya fada yana kallon ta domin yasan karya take allurace kawai bata so kuma dole sai yayi mata ita , hannun shi ya daura saman wuyanta zafi yaji zau "ki kace ya sauka zazzabin bayan gashi nan jikin ki da zafi" "to yaya dan Allah ka bani magani kawai, wlh bn son kayi man allura dan Allah" "a haka zaki zama likita kina gudun allura, wa zai zauna kiyi mashi ita kenan bayan ke bakiso" "dan Allah dai yaya" tafa da hadi da hada hannu wanta wuri ɗaya alamar yayi hakuri. "shikenan to" ya fada hadi da ficewa daga dakin dawowa Aaimah tayi kusa da ita tana cewa "ai kuwa nasan allurar zai maki , tun da jikin ki har yanzu da zafi" mi Aairah zatayi inba kuka ba , kuka rurus kamar wata ƙaramar ya rinya Aaimah kuma sai ƙara bata tsoro take tashi tayi daga gadon ta fice daga dakin bedroom din Mom ta nufa, Mom fitowar ta kenan daga bathroom Aairah ta shigo kamar wacce a ka koro, bed din mom ta nufa ta haye hadi da jan blanket ta rufe jikinta tana cigaba da kuka kusa da ita mom ta ƙaraso tana fadin " ke kuma lafiya kamar an koroki, mikike ma kuka ne" "Mom ya abdallah ne zaiman allura" "Yau ni naga takaina ni kubrah, shine kika shigo kamar an koroki " Mom bata rufe baki ba sai ga ya abdallah yashi go hannun sa rikeda leda, yaje dakin su bai sameta ba tada Aairah mom tayi magani yafara bata da kuwa zai mata allura sun sha buduri har Mom , sai da yayi mata jan ido tukun a ka samu a kayi allurar dama haka yake fama dasu ita da Aaimah Indai a kace basu lafoya tofa sai sun kusa tara masu mutane a gida saboda allur kawai, amma kullum Iƙirarin su shine su zama likitoci Kuka Aairah tasha Banida kuka ba, sai dai ta kwana dakin Mom Aaimah ma nan ta dawo ta kwanta saboda bata iya kwana dakin su ita kadai... WASHE GARI... Alhmdllh tatashi da jikin da sauki sosai bedroom dinsu ta koma tayi wanka tasa kaya mara sa nauyi ko da Aaimah ta shigo tana tambayar ta ya jikin "da sauki sosai" "to Allah ya Kara sauki, hajiyar allura " harara ta bugama Aaimah, ita kuwa mi Aaimah zatayi inba dariya ba tana fadin "wlh sister duk mijin da ya aure ki zai sha fama musamman idan shi likita ne, dan wlh nasan tara mashi mutane zaki rikayi muddin baki da lpy yace xai maki allura" "kice duk mijin daya aure mu dai, sai kace kema allurar kike so zaki wani tasa ni gaba kina man dariyar banza" "ai wlh kinsan gara ni dake wllh" "wlh karya ne bawani nan" "to uwayen musu da safiya zaku fara ma mutane musun tsiya da kuka saba, ba kamar ke Aairah daga samun sauki harzaki fara dan banzan surutun da kuka saba" Mom ta fada wacce shigowar ta kenan tasame su suna ta gaddamar da su ka saba "ke kinyi wankan kokodai sai kungama musun sannan" "A'a yanzu zanyi" Aaimah ta fada hadi da nufar toilet ta shiga, kusada Aairah Mom ta matso tana fadin "ya jikin, duk dama kinji sauki tunda gashi harkina musu" murmushi tayi hadi da daura kanta saman kafadar Mom tana cewa"da sauki Mom, Aaimah ce da raini wayau waini take ma sharrin bana son allura saika ce ita ma so take" murmushi kawai mom tayi tana fadin Allah ya shirye ku "ameen Mom" Aairah ta fada ✨VICTORIA✨ sanye take da uniform din ta, fita tayi daga office din su direct lifter ta nufa numbobi ta danna kofar lifter ce ta bude wasu nurses ne ciki shiga tayi ciki itama Lifter na tsayawa kowa ya fice alamar sun kawo inda zasu, fita tayi itama direct office din Dr Shazim ta nufa saida ta zo bakin kofar office din tukun ta tsaya, waige waige tashiga yi alamar rashin gaskiya saida ta tabbatar ba mai ganin ta tukun ta sanya key din dake hannun ta ta bude office din da sauri ta shige ciki saboda jin alamar kamar mutum na tunka ro office din tsi office din yake alamar ba kowa a cikin sa , sai ac dake aiki wurin freezer dake office din ta nufa. - to fa nace mi Victoria ke shirin yima dactor A office ne🤔- bu dewa tayi, cike yake da drinks kala kala, gani nayi ta dauko kwalin daya daga cikin drinks din ta a jiye saman wani dan ƙara min table dake kusa da fridge Sannan ta sake dauko wani, a ta kaice dai sai da ta ɗauko kusan kowace color dake ciki sannan ta maida ta rufe. Hannu tasa cikin aljihun wandon kayan ta, ta fito da wani gari cikin wata yar ƙara mar ruba fari tas dashi , buɗe marfin kowane kwali na drinks din tayi sannan ta dibi wannan garin ta zuba ta girgiza, daya Bayan daya sai da ta tabbatar ta girgiza kowane ya girgizu sannan ta mai da ta rufe maida su tayi ciki ta jera su kamar yanda ta same su, rufe fridge tayi sannan ta kama hanya ta fice ta nufi lifter ta sake danna numbobi kamar dazu sai ga kofar ta bude sai da gaban ta ya fadi saka makwan ganin hidaya da maryam da tayi ciki tasan dole suyi zargin wani abu saboda a wannan floor din daga office din dr shazim sai na dr kabir sauran wuraren ɗakin marasa lpy ne da inda patient ke zama dan ganin likita in sun zo, kuma gashi lokacin da patient ke zama bai yi ba, an dai bu ɗe offices domin sharewa da moping. dan doctors babu wanda yazo kallon kallo suka shiga yima juna itada hidaya dan ita maryam harara kawai ta bita da ita Itama harar maryam din tayi hadi da tsaki ta shige cikin lifter fita suka yi dama nan suka nufo "Aikin bazan harara a cikin duhu, yar wahala kawai" maryam ta fada hadi da jan hannun hidaya suka wuce , itama tsakin tayi hadi dacewa "oho dai dr ne dai saina rabata dashi, kuma kema zan dawo kan kine inna gama da ita" Haka dai taita ban baminta a banza har ta kai inda zata sauka A chan kuma hidaya ce ke ce ma maryam "nifa kinsan gani nake Victoria kamar bata da gsky," "mikika gani? "Maryam ta tambaya "bakiga tana ganin mu ba duk tawani sha jinin jikinta, bayan haka ma mita zo yi floor ɗin su Dr yanzu ba lokacin fara aiki ba, ni sai nake ganin kamar wani abun tayi" "Uhmm haka ne kumafa hidaya, ke ita ta sani chan taje taji da rashin gaskiyarta, si Allah na sama yana kallon duk wani abu da zatayi, koma mi tayi dan kanta hidaya ita da Allahn daya halicceta" "Wlh kuwa ita da mahaliccinta" hidaya ta fada abun da ya kawo su suka shiga yi, suka ture zan chan Victoria gefe Tana shiga office din su destiny ta samu da wasu daga cikin nurses din da suke zama office din wurin destiny ta kara sa tana fadin "sister shigowar ki kena? " "Eh yanzu nazo, nama yi tuna nin bakizo ba sai da naga ka yanki a locker sannan, amma daga ina haka.? " "Mufita daga waje na fada maki, nan kinga mutane, kuma kinsan su da bakar gulma yanzu zakiji magana wani wuri." "hakane kuma" destiny ta fada hadi dajan hannun Victoria suka fice daga office din sai da suka shiga wani dan corridor ku sada office din su sannan Victoria tace"daga office din dr nake" "kai da gaske kike" "da gaske nake mana, kaji destiny na taɓa maki wasa ne, daga chan nake" "Amma ina fatan ba wanda ya ganki ko, kuma kinyi yanda gurutu yace muyi" "Sosai ma kuwa, ai kamar yanda yace nayi haka nayi" "Yawwa yanzu sai dai mu tsaya jiran saka mako kawai" "hakane kam, kinga mu koma office kar wanima ya fito" "kumafa haka" Office din suka koma dumin shirin fita dan da suka shiga office din ba kowa ciki duk sun fita , suma basu wani jima ba suka fice.. ✨Hidaya✨ Zaune suke ita da maryam da sauran nurses din asibiti fira suke yi kafin doctors su shigo kowa ya kama gaban sa zuwa inda yake nasa aikin suna nan zaune dr shazim ya shigo shi da dr kabir da Noraiz, yana gaba su Noraiz na bayan shi gaishe da su nurses din su kayi Noraiz da Dr kabir ne kawai suka smsa masu Shazim kuwa hannu kawai ya iya daga masu Suna zuwa bakin office din shi briefcase dinsa dake hannun Noraiz ya amsa saboda shi Noraiz office din Dr kabir zai wuce Office din ya shiga, ko ina fes an gyara sai kamshin fresheners tarkacen sa ya ajiye saman table hadi da zama kan chair dinsa laptop dinsa ya jawo ya fara aiki a ciki, nocking aka yi "Come in" ya ba da izin, hidaya ce ta shigo bakin ta dauke da sallama, hannun ta riƙe da file,amsa mata sallamar yayi "GM Dr, dama nace zan iya fara turo patient" kai kawai ya daga mata alamar eh "ok" ta fada hadi da ficewa ta koma wurin patient wurin 12:00 ya gama ganin patient din dazai gani time din har Noraiz ya dawo office din , "Yaya wai baka da wani abun cine a office dinnan" Noraiz ya fada yayin da yake bude fridge dake office din "to a cici ni bana aje komai daya danganci abinci a eko , zaka iya bari Sai munje abnoor tukunnan" kwalin lemu ya ɗauka sannan ya rufe fridge ɗin , yana fadin "bari nasha wannan kafin mu tafi " wurin zaman shi kan sofa ya koma ya zauna hadi da bude marfin lemun, Dr kabir ne ya shigo da sallama a bakin sa hannun shi ɗauke da basket din abinci yana cewa "wlh Momma har yanzu kallon yaro take man, wai abinci tasa aka biyo ni dashi saboda kawai banyi breakfast na fito ba" "dama ai kai yaro ne" shazim yafa da yana murmushi "haba dai kai ka san wanene yaro wlh" "ai duk auta yaro ne"da yake kabir shine auta a wurin momman shi "lallaima Shazim wlh ka rainani" maganar Noraiz ta katse su yana cewa "wlh Momma ni ta tai maka kamar tasan yunwa nake ji" kallon shi Shazim yayi yana girgiza kai da fadin "wlh Allah ya shiryaka Noraiz, duka ƙarfe 12 amma sai wani complain din yunwa kake, sai kace wani karamin yaro" "Yaya kasan fa ina fama da ulcer" ya fada yana shafa cikin sa "bawani ulcer kawai ragon cine" Shi dai dr kabir binsu kawai yake da idanu yana murmushi "to yanzu dai ku kale wannan musun, kai Noraiz zo ka zuba abinci kaci" Dr kabir ya fada dawowa Noraiz yayi kan sofar da Dr kabir yake , plate ya dauka da serving spoon ya buɗe food flask farar shinkafa ce, zubawa yayi sannan ya bude dayar flask din wacce pepper soup ce ciki, duka dai y sai da ya buɗe kowane flask dake cikin basket din sannan ya koma gefe yana ci, Dr kabir ya zuba ma Shazim yana cema noraiz "wato ɗan tsako sami ka ki dangi ko" dariya kawai Noraiz yayi "Ok bakin maganar ya mutu kenan" Dr kabir ya fada yana murmushi, shima dai Shazim murmushi yayi yana cewa "baka san waye noraiz ba a kan abinci" daga nan su kayi shiru kowa na aikin bama cikin sa sai da suka gama Dr kabir ya nufi fridge ya dauko masu lemu da ruwa Shi noraiz ruwa kawai ya amsa saboda ya dauko lemu tun dazu sai da suka gama tsab sannan suka tashi shazim Duka tarkacen sa ya haɗa saboda da sun dawo sallah abnoor zasu wuce shida Noraiz....... ✨Aairah ✨ Alhmdllh jiki yayi sauki sosai dan yanzu haka zaune take parlor suna fira ita da Mom da Aaimah wacce taki zuwa school saboda Aairah bata je ba abie ne ya shigo daga masallachi sallar zuhur wurin su ya nufa zama yayi kan sofar da Aairah take yana faɗin "ah lallai jiki yayi sauki Masha Allah" hadi da shafa kanta Mom tace"Jiya kana part ɗinka da ka ga budirin yin allura" abie yace "Allah dai ya shirya yaran nan da dan bazan tsoron allura, a haka zaku zama Drs din da ku ke so kuna tsoron allura" Aaimah tace"duk da haka abie muna iyawa Allah" abie yace "to Allah dai yasa" Aairah tace "ameen abie" sun jima suna fira har wurin ƙarfe 3:00 sannan suka tashi ✨ Shazim ✨ Yau da wuri suka bar abnoor saɓanin kullum da sai yayi sallar magrib da isha sannan ya ke ko mawa gida, duk da yanzun ma ba gida suka nufa ba gidan malam suka nufa domin sukara duba jikin sa Zaune suka same shi a parlorn shi yana duba littafi, sallama su kayi hadi da shiga cikin , cikin parlorn amsa masu sallamar yayi yana tambayar su ya aiki, da alhmdllh suka amsa mashi Shazim ya ce"ya ƙarfin jiki" "Masha Allah jiki alhmdllh , yanzu ko ina ina iya zuwa alhmdllh " "Masha Allah Malam Allah ya ƙarl sauki da Nisan kwana mai amfani" "Ameen ya Rabbi" "Malam kodai lokaci ne yayi, muyi shirin cin gumba" noraiz ya fada yana dariya dakkuwa malam yayi mashi "lallai nuraddeen ni kake ma fatan Mutuwa koh, to sai dai mahaifiyar ka ta mutum amma bani ba, ja irin banza" dariya Noraiz ya kwashe da ita yana fadin "yanzu nan malam baka san mutuwa" Shazim dai na gefe yana jin su in ban da murmushi ba abun da yake "mutuwa na kan kowa nuraddeen , yaushe musilmin kwairai zai guji mutuwa, kawai dai ana tsoron mi za'a riska in an je chan" "haka ne kam Malam, Allah dai yasa mu mutu muna masu Imani" da Ameen suka Amsa su duka , nan mlm ya shiga yi masu nasiha a kan ruƙo da gaskiya da kuma aiki da ita da tsare mutuncin kai, sannan ya ƙara yima shazim fada a kan ya fitar da mata yayi Aure shekarun sa ƙaruwa suke ba raguwa ba, kuma mahaifiyar su bata da wani buri daya wuce taga ta aurar dasu baki daya shine kwanchiyar hankalin ta, saboda dangin mahaifin su gani suke kamar ita da malam suka hana shi yin aure, "Shazim ko baka so naga jikokin jajirtaccen jika na ne" duƙar da kanshi yayi ƙasa yana cewa "ba haka bane Malam, Insha Allah zanyi kokari nayi nan kusa" "to Allah ya yarda, ya kuma za ba maka mace tagari kai da ɗan uwanka, itama fatima Allah ya bata miji nagari" da ameen suka amsa su duka har da ummy wacce shigo war ta kenan parlorn taji suna adu'a shine itama ta amsa da ameen.gaishe da ita su kayi , cikin kulawa ta amsa tana tambayar su ammy, shazim maganar kasuwancin shi da yake son noraiz ya cigaba da kula da su yayi ma malam da noraiz ɗin kan shi, "eh wannan shawara ce mai kyau,dama ya kamata ka rage ma kanka wasu abu buwan," "hakane, dama jiran dawuwar sa nake na tattara komi na miƙa masa " "yayi hakan Allaha ya tai maka,amma ko da noraiz ɗin ya amsa ka bar hameed su cigaba da kula tare, duk da noraiz abun da ya karanta kenan, zai ƙara samun wasu daba ru wurin hameed" "eh daman shawarar da na yanke kenan" "to Allah ya tai maka"da ameen suka amsa sun jima sosai gidan malam dan sai wajen Karfe 10 na dare sannan suka tafi gida , mlm ya sha maganin sa , kuma yana sa shi bacci . Suna shiga gida parlorn Ammy suka nufa inda anan suka sameta ita da Fatima zaune sallama suka yi , amsa masu Ammy tayi tana cewa "nayi tuna nin baba ya rike ku chan ku sai kwana, ashe zaku dawo" "Wlh kuwa zamu dawo, ya gida" "gida alhmdllh gashi nan" fira suka ɗan taba Ammy nace masu ga dinner din su chan kan dinning suka ce sun koshi dan sun ci dinner gidan malam basu jima ba kowa ya nufi dakin sa saboda dare da yaja sosai..... Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wataran dadi wataran akasin haka su Aairah sun fara zana jara bawar gama secondary school har sun kammala, haka zalika fatima ma ta gama Noraiz watan shi 2 da sati 3 da dawowa kenan. Zaune ammy take bakin bed, wayar tace da ke kan bedside ta fara ringing ɗaukra wayar tayi tana kallon mai kiran, ya ahmad shine mai kiran, dafe kan ta tayi tana faɗin ya salam, Allah ya sa bawani abun bane, picking tayi haɗi da kara wayar a kunne tana sallama, amsa mata sallamar na ciki wayar yayi, gaisawa suka yi, tana tambayar yasu hajiya asiya ds su kairiyya, da lafiya lau ya amsa mata sannan yace"wai aisha mi kuke nufi ke da shazim ne, tun yaushe nake faɗin idan na kira shi bana samun shi" "kayi haƙuri yaya, tun ranar da kakira na faɗa mashi ya kira ka, na yi tuna nin ya kira" "yaushe zai kira, kar mi mashi maganar da ya tsana, ko ba mu kai matsayin da za muyi mashi ita ba" "ba haka bane yaya, dan Allah kayi haƙuri, zanyi mashi magana ya kira ka yau" "to, daman na kira ne dan in faɗa maki ina son ganin shi shi da ƴan uwan shi cikin wannan watan" "to yaya, zan faɗa mashi" "to shikenan, sai anjima" "to Allah ya kaimu"da ameen ya amsa haɗi da yin rejectin, a jiye wayar ammy tayi tana faɗin" na rasa gane halin shazim, idan har bai jaman abun magana ba wurin su hankali shi baya kwanciya, amma na san maganin shi ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi part ɗin shi, yana parlor zaune, tambayar shi tayi ina wayar shi, "gata nan ammy, lafiya" "kira ya ahmad yanzu nnan " "amma ammy mi yasa" "zaka kira shi kukuwa sai ka gama tambaya ta dalili" "A'a kawai yace haɗi da ɗaukar wayar yayi dialing number uncle ahmad, tana fara ringing, aka ɗauka, sallama yayi haɗi da cewa "ina wuni uncle "da lafiya lai uncle ahmad ya amsa, sannan ya ɗaura da cewa "shazim laifin mi muka maka da idan mun kiraka baka ɗauka, kuma kai bazaka iya kiran mu ba? " "bakomi uncle " "to shikenan, ina son ganin ka abuja kai da ƙannan ka cikin watannan"shiru yayi baice komi ba, uncle ahmad ne yace "baka ji mi nace ba ne " "A'a naji, amma uncle aiki na ya zanyi da shi" "Ina sauraron zuwan ku kana ji na ko" "eh naji" rejecting uncle ahmad yayi batare da ya saurari mi shazim ɗin zai sake cewa ba, "sai ku shirya kai da su" "haba ammy, ni bazan je ba " "to wallahi bari kaji bazaka dinga ja man zagi ba wurin su kaji na faɗa maka, gara ma tun wuri ka shirya ku tafi" "to, amma sai next week " "Allah ya nu na mana"ammy ta ce haɗi da ficewa ta bar part ɗin ..... 🖊 Episode 13 ✨Noraiz-Fatima✨ zaune suke parlorn Ammy, fatima na duba wani novel yanzu ba school sai Islamiyya, shikuma yana aiki a laptop ɗin sa, aje novel din tayi tana cewa "ya noor ka kuwa tuntubar man big bro maganar school ɗin dan Allah " ture laptop ɗin yayi yana cewa "kima bar wannan maganar , dan wlh yace kusa da Ammy za kiyi karatu , ki tambayi Ammy ma a ga banta yace haka, har sa baki tayi amma yace a'a" "hai wai shi ya Shazim miyasa yake haka dan Allah , to yaya ita Ammy mi zai hana tace sai nayi " "kawai kiyi haƙuri kiyi karatun ki anan a kwai makarantu masu kyau kamar na can zaki samu duk abun da kike so, kuma na san zai sama maki mai kyau da tsada" "ya noor ya zanyi dole na hakura, Allah ka ɗai yasan da lilin sa na hana ni" "nasan bazai wuce saboda innah ba ya hanaki " "anya dai, Allah yasa haka alkairi ne" "ameen "Noraiz ya faɗa (Suna da saurin fahimtar dan uwansu saboda sun ɗauke shi tamkar mahaifin su da suka rasa tun basu san kansuba, saba nin wasu yan uwan idan akace mahaifin su baya da rai, zaka samu insuna son abu dan uwan su yanu na masu illar abun maimakon su fahimce shi, sai kasamu suna kullatar shi a rai wasu harsu kai da faɗin dan yaga mahaifin su baya da rai shiyyasa yake masu abun da duk yaga dama,zasu dunga ɗaukar shi a matsayin mai tauye masu haƙƙi abu buwa dai iri iri, Allah kasa mana ƙaunar ƴan uwan mu da fahimtar su ka bamu ikwan rufa ma junan mu asiri ameen 🙏 ) Ammy ce ta fito daga bedroom dinta tana cewa "yaya da kanwa mi ake shiryawa ne, aketa ƙusƙus" "sirri Ammy ki zauna ayi dake" Noraiz ya fada yana nuna mata kan sofa, zama tayi tana faɗin " ina sauraro kuwa, wane sirrin ne ake shiryawa"fatima tace "ammy maganar makaranta ce" "mi ya faru " "bakomi, ya noor ya sanar dani yan da ku kayi da ya shazim" "hakane sai dai kiyi haƙuri " "dama ya zanyi ammy dole na haƙura, amma ban san mi yasa ya shazim bai son zama na abuja ba " "nima kaina ban san dalili ba nasan dai bai wuce innah" sun jima suna tattaunawa kan maganar, sai ga shazim ya shigo da alama daga abnoor yake saboda yau friday dama bai cika jima wa ba saboda zuwa masallaci, wurin su ya nufo ya na faɗin " Ammy ina wuni, mi a ke shiryawa ne nagan ku zazzune a parlor" "lafiya lau ya aiki, sirri ne kaima zoka zaune" murmushi yayi yana neman wuri kusa da Ammy ya zauna, gaishe da shi su fatima sukayi noraiz nace wa " ashe dama na bika naga ka dawo da wuri" "ai kafi son zaman gida ne saikace wata mace, zan ga yan da zaka ƙare idan kafara business " "ai koh lallai " Ammy ta fada hadi da mangare ma shazim kai, sosa wurin yayi yana fadin "Ammy haka ne fa, in ba mace ba miya haɗa namiji da zaman gida" dariya fatima da Noraiz suka yi ganin yan da shazim ke bata fuska , maka masu harara yayi, shiru suka yi suna ƙumshe dariya, basu wani jimaba suna fira suka tashi domin shirin zuwa masallaci ammy kuma da fatima suka tafi daki domin yin sallah suma.... ✨KATSINA✨ Abie ne da abdallah ke sauko wa daga up stairs zasu tafi masallaci, da Mom suka ci karo a parlor ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke da food flask" Masha Allah irin wannan kyau haka barrister, gaskiya kar ka sa matan mutane suyi ta kalle man miji" dariya abie yayi abdallah kuwa duƙar da kai yayi yana murmushi a zuciyar shi yana fadin " Mom duk da an tsufa amma ana kishi, Allah ya bani mace irin Mom" nace ameen dr "da har ina cewa zan ƙara maki a bokiyar zama, amma kike faɗin haka" "tab wallahi kaima kasan wasa kake, ai auren mu inkaji ana auren zobe, ba saki ba yaji ba kishiya" dariya abie ya sake kwashewa da ita yana faɗin "za kuwa kisan ba wasa nake ba, dan daga nan zance zan wuce" in ban da dariya ba abun da abdallah ke ma iyayen nasa, yana kallon su cikin birgewa "ka dai faɗa , nawa jine kawai" "ai kuwa zaki san bawasa nake ba, kaga abdallah wuce mu tafi kar mu makara" ficewa su kayi suna jin Mom na masu a dawo lafiya bedroom ɗin su Aairah ta wuce bude ƙofar tayi ta shiga shiri ta same su suna yi "yawwa kun shirya kenan" "eh"suka bata amsa "yawwa kuyi sauri ku ƙarasa , ga abinci can kitchen mungama, ku jera kan dinning sannan su mudi ma ku tabbatar kun kai masu nasu nizan shiga nayi wanka ne kunji" Aairah tace "ok Insha Allah za muyi yan da kika ce, amma Mom wai ya maganar walimar mune, munga ba'a fara shirin komai ba, kuma fa jibi ne" Mom tace" tana nan mana ba jibi bane, jira nake anjima yayan ku ya kaimu shopping ko kuma abie dinku, saimu siyo duk abun da ya dace" Aaimah tace"to shikenan Mom Allah ya kaimu an jimar" ameen Mom tace hadi da fi cewa daga dakin tana sake tuna masu aikin da ta sa su, suna gama shirin suka fita domin yin abun da Mom tasa su, suna kammalawa nan main parlor suka tsaya suna kallo su abie ne da ya abdallah suka shigo, sannu da dawowa su kayi masu hadi da gaisawa, amsa masu su kayi abie ya samu kan sofa kusa dasu ya zauna ya yin da shikuma ya abdallah ya haye up stairs, fira su qka shiga yi da abie akan walimar da za'a yi masu , sun jima suna fira har Mom ta sauko tana cewa "shiyyasa naga barrister bai shigo ba, ashe kuna nan kun tasa shi gaba da abun da kuka saba watan surutu " Aairah tace"kai Mom bafa surutu muke masa ba, maganar walimar mu fa mu keyi" dinning Mom ta nufa tana faɗin "to yayi, sai ku taso ga abinci na jiran ku" ta sowa suka yi har da abie suka nufo dinning din, abie nace ma "Aaimah jeki ki kira yayan ku, kinji" "to sbie" ta fada hadi da nufar up stairs ta nufi part din abdallah , samun shi tayi yana waya jira tayi sai da ya gama sannan tace yaya kazo mu ci abinci, da to kawai ya amsa mata, ya yin da ita kuma ta fice tabar ɗakin ko mawa dinning din tayi wurin zaman ta na ɗazu ta koma ta zauna plate taja wanda Mom tayi serving ɗin kowa, shiru kowa yayi anata bama ciki hakkin sa, sai da suka kusa kammalawa sannan abdallah ya sauko ya nufo dinning ɗin, Mom tace "lafiya baka fito ba tun time din da aka kira ka" "Ina wani ɗan aiki ne shiyyasa" ya fada hadi da neman wurin zama ya zauna plate ɗin abinci Mom ta miko masa, thanks ya faɗa hadi da dau kar spoon ya fara cin abincin, suna gama wa su Aaimah suka gyara wurin yayin da su Mom suka koma kan sofa, suma suna gamawa wurin su Mom ɗin suka dawo, firar walimar da za'ayi masu suka shiga yi, basu tashi ba sai da lokacin sallar asr yayi sannan su abie suka wuce masallaci, suma daki suka shiga domin gabatar da tasu.. mom ce ta fito daga bedroom ɗinta jikinta sanye da atamfa ɗinkin riga da zani da mayafi sai jaka a hannun ta, ɗakin su Aaimah ta nufa samun su tayi duk sun sha abaya black color sunyi rolling da gyelenta sai side bag da ko waccen su ta rataya sai glass irin na gayu ɗinnan, shirin fita suke daga ɗakin sai ga Mom ta shigo "yawwa kun shirya kenan to ku fito mu wuce abie dinku da yayan ku na waje mu ka dai suke jira" Aaimah tace "Mom ba kice munyi kyau ba" yan yatsu kawai Mom ta haɗa al'amar komai yayi, ficewa su kayi zuwa compound din gidan inda anan suka samu abie da ya abdallah, shiga su kayi cikin motar ya abdallah ke driving yayin da abie ke kusa da shi, sukuma suna baya su da Mom, a dawo lafiya su mudi su kayi masu yayin da abdallah ya fice da motar suka hau kan titi, wani ƙaton shopping mall ya nufa dasu, parking su kayi a parking lot dake wurin wanda aka tana da domin masu siyayya, sai da ya gama dai dai ta parking din motar, fitowa suka yi, cikin mall din suka nufa, barka da zuwa waiters su kayi masu,inda ake ajiye cart suka nufa, guda biyu suka ɗauka, Aaimah na tura daya tana biye da abie da ya abdallah , yayin da Aairah ke tura daya tana biye da Mom,siyayya suka yi sosai, sun jima a shopping mall sai da suka tabbatar sun tanadi abun da suka san zasu buƙata sannan suka nufi wurin biyan kudi, abdallah ya biya duk abun da suka siya ma'aikatan wurin suka ɗaukar masu kayan zuwa booth, wurin da ake sai da snacks suka wuce pizza da shawarma da ice cream ya abdallah ya sai masu daga nan suka wuce gidan dadi, suna isa bakin gate din gidan ya abdallah yayi horn, mai gadin ne ya leƙo, ganin motar abdallah yasa shi komawa ciki da sauri hadi da bude masu gate, ciki ya shiga da motar parking lot dake compound din gidan ya nufa hadi da yin parking, sannan suka fito,booth abdallah ya buɗe, snacks ɗin da suka siya ya ɗauko haɗi da miƙama su Aairah , cikin gidan suka nufa, parlor ne dan dai dai matsakaici yasha royal sofas masu kyan gaske , wata yar tsohuwa ce (dadi kenan) zaune ita da wata mata aƙalla zatayi kima nin shekara 38 zuwa 40 ( Aunty Rabi kenan, ƙanwar abie ce, zaune take da dadi tun lokacin da Allah yayi ma mijinta rasuwa, kuma gashi Allah bai bata haihuwa ba shiyyasa ta dawo kusa da mahaifiyar ta tana kula da ita) sallama su kayi, aunty rabi ce ta amsa masu sallamar hadi da cewa "wannan shi ake kira tafi da gidan ka, wannan ziyarar bazata haka yaya" dariya abie yayi hadi da cewa "ke dai bari kawai rabi, munje siyayya ne saboda walimar su Aairah, shine muka biyu ta nan" nan suka shiga gaisawa, wurin dadi suka matsa itama suna gaishe da ita amsa masu tayi cikin kulawa hadi da taya su Aairah murnar kammala makaranta da hadda nan suka shiga fira "Muhammad yaushe ne walimar su yan biyu" dadi ta tambaya, amsa abie ya bata da" jibi ne Insha Allah" "to Allah ya kaimu" da ameen suka amsa , miƙama aunty rabi snakcs ɗin dake hannun su suka yi, amsa tayi tana ma abie godiya, Aairah tace "amma dai dadi zaki zo koh" "Insha Allahu kuwa, ai audu zai zo ya ɗauke ni da kansa, koh audu" tafada tana shafa kan abdallah dake kusa da ita, ɓata rai yayi yana cewa, "wai dan Allah dadi bazaki daina ce man audunnan ba, nifa suna na abdallah , ba audu ba" dariya su ka kwashe da ita su duka ban da abdallah dake zabga ma su Aairah harara saboda dariyar da suke mashi "ai inba kishiya kayi man ba, bazan daina cemaka haka ba, shima abun da zaisa na daina kawai dan kar ta raina min ango ne, amma da bazan bari ba" "to shikenan ashe baki ba cin kaza kuwa, tunda haka ki kace" dariya suka sake kwashewa da ita, dama duk abdallah da dadi suka haɗu wuri daya tofa zaka sha dariya , mai aikin dadi ce ta fito daga kitchen wurin su ta nufo tana gaishe da su abie,mom tace "uwani ashe kina nan, ya kwana biyu" "Alhmdllh" wace aka kira da uwani tace, su Aairah ma gaishe da ita suka yi, amsa masu tayi da lafiya lau"an kammala girkin " uwani ta faɗa , aunty Rabi tace "to shikenan, Aairah ku ɗauki wannan snack's kuje da shi kitchen sai ku taya ta jera abincin kan dinning" da to suka amsa mata, tashi suka yi suka bi bayan ta , Aaimah tace "wai Aunty uwani ina Nuratu ne naga kwana biyu idan muka zo bama ganinta"( diyar Aunty uwani nin ce nuratu) Aunty uwani tace "Nuratu na kauye, an kusa bikinta ina fatan za kuzo "cike da mamaki su Aairah suka ce "aure fa kikace Aunty Uwani, yanzu nan nuratu harta isa aure"Aunty uwani tace "eh mana, duk sa'annin ta dake chan duk anyi masu aure har ma wanda basu kai taba ana masu aure, dan dai kawai ku kuna birni ne shiyyasa kuke ganin kamar bata isa ba" Aairah tace " to Allah ya nuna mana lokacin, Insha Allah kuwa zamu je" haka suka ciga da fira Aunty Uwani na basu labarin ƙauye su kuma suna mamaki har suka kammala jera abincin kan dinning, sallar magrib da aka kira ne yasa su abie nufar masallaci shi da abdallah Mom ɗakin Aunty Rabi ta nufa domin gabatar da sallah , su Aairah kuwa ɗakin Dadi suka nufa domin yin tasu sallar, sun riga su mom dawo wa parlor su da Dadi,suna ta zuba mata surutu su abie suka shigo hara da uncle mustafa ( kannin abie wanda ke bi masa, su biyar ne ɗiyan dadi abie shine na farko sai uncle mustafa daga nan sai aunty Rabi sai uncle Ahmad sai Aunty Asma'u itace yar autar su, da Uncle mustafa ne ka ɗai ke katsina, kafin Abie ya dawo nan shikuma uncle Ahmad har yanzu yana abuja sai Aunty Asma'u dake aure kano, Aunty Rabi kafin Allah yayi ma mijinta rasuwa barno take Aure time din .) bakin su dauke da sallama suka shigo,amsa masu sallamar su kayi yayin da su Aaimah ke cewa "uncle ina wuni" amsa masu yayi cikin kulawa yana cewa "ya school naji yaya yace kun kammala, to Allah ya tai maka yasa a samu saka mako mai kyau" da ameen suka amsa mashi,dadi tace "yawwa mustafa naji daɗin zuwan ka, kamar kasan ina son ganinka kai da Mahammad " abie yace "to fa mama Allah yasa lafiya " "lafiya lau,maganar dai da na saba ce, mu shiga daga ciki" da to suka amsa haɗi da miƙewa suka bi bayan dadi, bedroom ɗin ta suka shiga, wuri suka samu bakin gado suka zauna, kallon su dadi tayi sannan tace"a kullum bazan gaji da maku maganar ɗan ƴar uwata ba, ba shi da wani a duniyar nan da zai kalla a matsayin uwa a gare shi bayan ni , ban san wane hali yake ciki ba, ƴar uwata zata ce ban riƙe alƙawari ba " uncle mustafa yace "kiyi haƙuri mama, insha Allah zamu nemo shi a duk idan yake a faɗin duniyar nan " "mustafa kullum haka kuke cewa, amma har yau baku nemo man shi ba, kullum sai nayi mafarkin shi yana cikin damuwa, yana buƙatar tai mako na "abie yace "ki ƙara haƙuri mama, insha Allah za'a gan shi, zanje har garin ku, nasan baza'a rasa wanda yasan inda ya koma da zama ba" "to shikenan Muhammad, zan zuba ido har lokacin da Allah zai bayyanar da shi"da ameen suka amsa, dadi tace "ku tashi ku koma parlor kuci abinci "to mama suka faɗa haɗi da miƙewa suka nufi parlor, a dinning suka samu su mom, wuri suka samu suma suka zauna,aunty rabi tayi sarving ɗin su , sai wurin karfe 9 da kusan minti 50 sannan suka bar gidan harda uncle mustafa suka nufi gida, suna isa gida, baaba larai ta fito tayi masu sannu da zuwa, kowa ɗakin sa ya nufa, snacks ɗin da suka zo dashi baaba larai ta kai kitchen ckin fridge bayan ta ɗauki wanda zataci, ɗakinta ta nufa ta kwanta ita ma 😴.....🖊 Episode 14_15 WASHE GARI Tunda suka yi sallar asuba basu koma bacci ba saboda ɗokin zuwa wurin ƙunshi da gyaran kai da za suje, ko da gari yayi haske wanka kawai suka yi suka shirya sannan suka nufi ɗakin Mom, koda suka shiga basu sameta ba kitchen suka wuce anan suka same ta ita da baaba larai suna shirya breakfast gaishe dasu sukayi, Mom tace"wai ba dai har kunshirya ba" "munshirya , tafiya ma zamuyi" suka bata amsa Mom tace"to sai ku bari kuyi breakfast tukunnan" Aairah tace "ba fa direct saloon din zamu wuce ba, sai fa munje gidan Aunty Safiya mutafi da Najma " "duk da haka dai kujira kuyi breakfast sannan"mom ta faɗa, da to suka amsa mata, dole suka tsaya sai da suka yi breakfast ɗin sannan mudi ya kaisu gidan ya dawo, basu wani jima ba saboda ko da suka je Najma harta shirya su kawai take jira, basu wani bata time ba mus'af ya kaisu shagon saloon ɗin da zasuje, wurin ya haɗu babu wani nau in gyaran jiki da basa yi, kama daga wankin kai har izuwa kunshi da gyaran ƙafa...... Wannan Kenan ✨Ammy_Fatima _Noraiz ✨ Zaune suke kan dinning suna breakfast, shazim ya shigo jikin sa sanye da jogging suit white color,sai p_cap black color , wurin su Ammy ya nufo yana faɗin"ina kwana Ammy" da lafiya lau Ammy ta amsa mashi "Ammy ai da kun bari na dawo sai muyi breakfast ɗin tare" "kai da shigowar ka ba yanzu ba, waye zai tsaya jiranka" "amma Ammy ba gashi nashigo da wuri ba" "yau koh" Ammy ta faɗa Noraiz ne ya ce "yaya da ƙarfe nawa zaka je abnoor yau" "yau bazan jeba" "amma yaya saboda mi" "haka nan, zamu je wani wuri ne shiyyasa, idan kun kammala breakfast ɗin, Ammy ku shirya" Fatima tace "wannan wane bazata ne haka yaya " Ammy ma cewa tayi "ina zaka kaimu" murmushi yayi haɗi da cewa "surprise ne, ku dai kawai ku shirya" daɗi suka ji saboda sun san wani abun mamakin ne yake son yi masu bazata dashi, saboda shi idan ya so fa akwai wasa da dariya, in kuwa baiso ba tofa zaka same shi kadaran kada ham, duk da da man akwai kyakyawar alaƙa tsakanin sa da ahlinsa, wani lokacin in yana tare da su zaka same shi kamar bashi ba, cigaba su kayi da breakfast, shi kuma part ɗinsa ya nufa domin watsa ruwa sannan ya dawo yayi breakfast , san da ya kammala nasa breakfast din dukan su sun shirya shima ko mawa yayi part dinsa ya shirya cikin wani haɗaɗen yadi wanda yasha ɗinkin zama ni" wurin su ya dawo, Ammy ce tace "kai Masha Allah ba ƙaramin kyua kayi ba" "nagode sosai ammy" gaba yayi yana faɗin "to ku taso mu tafi" tashi su kayi su ka bi bayan shi zuwa compound din gdn, anan suka samu motar da zasu fita da ita ilya ya gama gyara ta ya fito da ita compound , nufar motar suka yi, shi ya shiga ma zaunin driver ya yin da Noraiz ke kusa da shi Ammy da fatima kuwa baya suka shiga, reverse yayi ya nufi gate, a dawo lafiya su ilya suka shiga yi masu, driving yake , su Ammy sun zuba ido ne suga shin ina kuma zasu, wani katafaren shopping mall na ji da faɗa ya nufa dasu,sabon mall ne daga gani ba'a jima da fara aiki a cikin sa ba, parking yayi a parking lot ɗin wuri sannan yace "Ammy ku fito, mushiga ciki " to kawai Ammy tace sannan suka fito,sai da suka fito su duka sannan yace "kowa ya kalli sama " kamar yan da yace haka suka ɗaga kansu suna kallon saman shopping mall, in da aka rubuta (WHITE HOUSE SHOPPING MALL) da man yan baƙi ammy sauke kanta tayi tana kallon shazim cike da alamar tambaya, ganin kallon da ammy keyi masa yasa shi murmushi yana faɗin "surprise " cike da mamaki ammy tace "wai ni kam ina zaka kai son kuɗi ne shazim"matsowa yayi kusa da ita haɗi da dafa kafaɗar ta yace"ammy ina da ku idan ban nemi kuɗi ba mizan yi" "haba shazim business nawa kake " "Ammy koma nawa nake, wannan ba wani abu bane, ki sa mashi albarka " "to Allah yasa albarka ya ba da sa'a "da ameen suka amsa su duka, shazim yace "Mu shiga ciki" ciki suka shiga ya na gaba suna binshi a baya,wani matashin saurayi ne a ƙalla zai yi kimanin shekara 27 ya nufo su, gaishe da ammy yayi da shazim,gaishe da shi noraiz da fatima su kayi, da fara'a a fuskar shi ya amsa masu, shazim yace"ya aikin hameed " "alhmdllh, komai na tafiya dai dai" "masha Allah,muje ina son nu na ma su ammy ko wane part " "ok to shikenan "ciki su ka wuce, wura re ya shiga nuna masu shi da hameed , sai da ya kaisu ko ina a cikin mall ɗin sannan suka ya da zango a office ɗin shi, hameed kuma ya koma wurin ma'aikata ,office ɗin ya haɗu sosai kamar ba office ba, ammy na kan sofa su fatima na ƙasa kan carpet, shi kuma yana zaune kan swivel chair,ammy ta ce"shazim wuri yayi kyau Allah ya taimaka " "ameen Ammy" ammy tace "yanzu wa zai kula da nan? " "a kwai wani ƙanin hameed shi zai kula da nan, hameed kuma noraiz sai su cigaba da kula da wan can business ɗin " "to shikenan, hakan yayi kyau" sun jima a office ɗin sai da rana tayi sanyi suka fito,yace su shiga ciki kowa ya zabi abun da yake so, da sauri fatima ta jawo masu cart, suka shiga jidar abun da ransu yayi masu musamman Fatima da Noraiz, Ammy kuwa shazim ke tura mata nata cart din tana daukar abun da take so, sai da kowa ya dauki abun da yake so, ma'aikanta wurin suka kwashe kayan suka zuba masu a booth, sallama suka yi ma su ammy,har parking lot hameed ya raka su,( bayan aikin asibiti shazim yana business sosai tun kafin ya fara aiki da buɗe abnoor yake business, yana sai da motoci wanda hameed ke kula da shi yana da boutique da gidan gona sai white house da ya buɗe yanzu, amma ba shi ke kula da su ba kula mashi ake da su ) mai makon ya kaisu gida wata hanyar ya kuma sake ɗauka , in da ake sai da laptop's ya nufa dasu yana parking suka fito shi da noraiz , su ka shiga ciki, noraiz ya zaɓar ma fatima laptop mai kyan gaske shima,kuɗi ya biya suka fito zuwa mota, daga nan wuren bu ɗe ido yai ta kaisu, Ammy ba ƙaramin dadi tajiba saboda rabon ta da ta shiga gari da sunan miƙe ƙafa har ta manta, sai da yamma likis sannan suka koma gida, godiya su duka suka shiga yi mashi, shi kuma yana cewa "dan Allah su bari mana,wannan ai wajibi ne a gare sa daya yi masu fiye ma da haka" Ammy tace "duk da haka shazim, bakaji mi hausawa suka ce ba?, yaba kyauta tukwici, tunda bamu da tukwicin dazamu baka shine muke godiya" "to shikenan " kawai ya iya cewa , ilya ne da mai bama flowers ruwa suka shigo da kayan da suka zo dasu, su kuma kowa daki ya nufa domin watsa ruwa ,Fatima na shiga ɗaki wayanta dake cikin bag ta ciro daketa ringing, ya dr ne ke kira, katsewa kiran yayi zata kira sai kuma wani kiran ya sake shigowa,picking tayi haɗi da sallama amsa mata sallamar yayi hadi da cewa"yar ƙanwata ya kike ya gida ya su Ammy? " "lafiya lau Yaya" "masha Allah, ina gaishe da su sosai" "zasuji Insha Allah " "miye labari " "ai ni yaya fushi nake da kai, " "to fah, kaina bisa wuya ni kuwa mi na ai kata" "wai ace in gama secondary school, Amma yaya ko irin text dinnan na congratulations ban samu daga gareka ba kai da ya mansoor " "Allah sarki fatima, kiyi hakuri kinji, so naima ace nazo har Lagos din, amma kuma wasu yan abu bu wa ne suka sha kaina, amma kiyi haƙuri kinji" "shikenan yaya bakomi, dama yanzu baka wani ji dani," "kai , ya za ki ce haka " "haka ne mana, yau she rabonka da zuwa Lagos, tun kuna mutunci da ya shazim sosai " murmushi yayi mai sauti yana cewa"waya ce maki bama mutunci sosai yanzu" "to baga shi nan ba yanzu baka son zuwa Lagos " Fatima kenan, ya fada a zuciyar shi , a zahiri kuwa cewa yayi"fatima yana yin aiki ne kawai ba wani abu ba, amma Insha Allah ina nan zuwa Lagos very soon " "to Allah ya kaimu ya nuna mana lokacin" da ameen ya amsa fira suka shiga yi da bisani suka yi sallama, ya mansoor ta kira shima tayi mashi ciwan baki ra shin kiranta, haƙuri ya shiga bata, sun jima suna waya, a chan parlor kuwa Ammy ce ta fito daga ɗakin ta, Innah asabe ta samu a kitchen tana jera kayan da suka siyo, gaishe da Ammy tayi, amsa mata Ammy tayi cikin kulawa, Inna asabe tace "mi za'a dafa yau da daddare " "A'a ba sai an dafa komai ba munyi takeaway da muka fita" "to shikenan "kawai Inna Asabe tace, gyara kitchen din kawai suka yi..... ✨Victoria✨ "destiny wai kina ganin abun da gurutu ya bamu yana aiki kuwa, kusan fa wata daya kenan bawani chanji" Destiny tace"karki damu na yarda da Gurutu, mukara lokaci kawai, idan ma muka ji shiru mu sake Komawa kawai" "gaskiya abun da za'ayi kenan gara kawai mu koma" destiny tace "to shikenan amma mu ƙara lokaci mugani " ✨Hidaya✨ Zaune take bakin gado wayar ta dake gefan ta ce ta fara ringing picking tayi hadi da manna wayar a kunne tana fadin "hello maryam ykk ya gida"on the other hand maryam tace"lafiya lau hidaya" hidaya tace "Masha Allah" "mi kike yine haka naji kamar muryar ki tayi ƙasa? " maryam ta tambaya, amsa hidaya ta bata da "lpy qlu, kawai dai ina kwance ne" Maryam tace"ok to yayi, ya labari doctor kinsan kwana biyu ban shigo hospital ba, ina dai fatan kin fada masa abun da ke ranki" sauke ajiyar zuciya hidaya tayi, sannan tace"ina fa maryam, wlh da na gansa rasa duk wani kwarin gwiwata nake, sai kawai naji na kasa fada masa" Maryam tace"gaskiya hidaya kina da aiki, yanzu nan fada masa dinne kika kasa yi " "uhmm maryam kenan dan dai kawai bake bace a matsayi na ba ne shiyyasa" "ba haka bane hidaya, daurewa kawai zakiyi ki fada masa" "to shikenan maryam zanyi kokari naga na fada masa nagode sosai" "bakomi idan ma kin kasa sai mu nemi number shi, kota waya ne sai ki fada masa, fata na kawai shine ya amince dake amatsayin abokiyr rayuwa, in ga ta tsiyar su destiny da Victoria " "to Allah yasa ya soni koda bai kai wanda nake masa ba" hidaya ta fada "to ameen sister, ki cigaba da adu'a Insha Allah dr naki ne ke kadai" "to Allah yasa" da ameen maryam ta amsa mata sun dan jima suna wayar daga bisani suka yi sallama...... ✨Aairah_Aaimah✨ Ana kammala masu saloon din da kunshi mus'af yazo ɗaukar su, mus'af ne yake cema Aairah " kai masha Allah sweetie irin wannan kyau haka kin kuwa ga yanda kunshi nnan yayi matukar yi maki kyau" "nagode sosai" Aairah ta fada Aaimah ce tace "da yake ya mus'af Aairah ka dai ka sani shiyyasa kace nata yayi kyau mu ko ka kalli namu, abun yar wariyar launin fata ce" "No Aaimah ba haka bane, na qalbie ne ya ɗauke man hankali, amma kuma naku yayi kyau sosai"cewa Aaimah tayi "shikenan ya mus'af bakomi" "mu tafi koh"mus'af ya faɗa nufar motar suka yi, Aairah ta shiga gaba, sai Aaimah da najma a baya, gidan su Aairah ya nufa dasu, parking yayi a compound , su Aairah suka fita , masu decoration suka samu a compound din suna decorating, main entrance din gidan suka nufa, koda suka shiga ciki baaba larai da Mom da Aunty rabi suka samu a parlorn, suna aikin zuba souvenirs cikin jakunkuna masu dauke da sunan Aairah da Aaimah, shiga suka yi parlorn bakin su ɗauke da sallama, amsa masu sallamar su Mom suka yi, da gudu su Aairah suka nufi Aunty rabi, suna fadin "oyoyo Aunty, ashe kin zo" Aunty rabi tace "na zo Mom ɗinku ke faɗa man kuna wurin salloon, buɗe mugani " ta faɗa tana cire ɗan kwalin Aairah " kai masha Allah, gaskiya yayi kyau" "na gode sosai Aunty" Aairah ta fada, Aaimah cewa tayi" to ni bari na tashi, tun da na lura Aunty baki tani ta Aairah kike" Aunty rabi tace "sorry Aaimah, ke ma ina ta ke, mu ga naki kema" mom ce tace " to tunda abun ƴar wariyar launin fata ce ,matso kinji ƴata naga naki harda ƙunshin" ta faɗa tana miƙama najmah hannun, da sauri najmah ta ƙarasa wurin Mom, nan tashiga nuna mata Ina wuni, suka ji mus'af yace, Mom ce tace "wai dama mus'af tare kuke" "eh" yaba Mom amsa, gai sawa su kayi har da su Aunty Rabi da baaba larai , mus'af bai wani jima ba yayi masu sallama ya wuce gida, shi ka ɗai ya tafi, a nan Najma zata kwana. zama su kayi nan parlor suna taya su mom aikin da suke, har suka kammala sannan suka wuce daki, wanka ko wace cikin su tayi da sallah magrib wacce ake kira, basu fita daga daki ba sai da suka yi harda sallar isha sannan suka fice daga dakin suka nufi parlor , yanzu ma mom da Aunty Rabi suka samu a parlorn, zama suka yi sai ga abie da ya abdallah sun shigo, nan suka zauna suna fira, ✨Lagos✨ Ammy da Fatima ne zaune a parlor bayan sunyi sallar magrib da isha suka dawo parlor suna duba kayayya kin da suka yi shopping, fatima tace " wlh kayan nan sunyi kyau sosai Ammy " Ammy ta ce"ai kuwa sunyi kyau sosai" Fatima tace" amma Ammy yaushe yaya yace zamu tafi abuja , amma dai sai cikin wannan week ɗin ko " "to sai dai Idan ya dawo in tambaye shi, dan gsky ni bai faɗa min yaushe zaku tafi ba, duk da munyi magana yace next week amma ban ga yana wani shiri na alamar tafiyar ba " "ok to shikenan Ammy" nan suka shiga duba kayan suna yaba kyan su, Noraiz ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, amsa mashi sallamar su kayi, Ammy na ce wa "ina ka baro Yayan naka" Amsa Noraiz yaba ma Ammy da "tare muke dashi, yana compound yana amsa waya" Ko rufe baki noraiz bai yiba shazim ya shigo, shima wurin su Ammy ya nufo, gaishe da Ammy yayi , ya nemi wuri kusa da Ammy kan sofa ya zauna, Ammy ce tace "ga abinci, kan dinning" "to " ya bata amsa, dinning din suka nufa, suna kammala dinner din, fatima ta gyara wurin , su kuma kan sofa suka koma, Ammy na tambayar shazim yaushe zasu tafi abuja "gaskiya ina tunanin sai upper week,zanje jos wani hospital ne suke son ganina next week" "amma shazim naso ku tafi next week, jiya sai da Ibrahim ya kirani shi da innah nace masu kuna nan tafe next week, yan zu idan suka kira nace kun fasa gani za su yi kamar ni ke hana ku kuzo" shazim yace "to ammy suyi haƙuri na dawo mana kiran emergency ne, patient sun fisu buƙatar gani na " "shikenan Allah ya kaimu upper week ɗin" da ameen suka amsa su duka, fira suka dan taba sannan kowa ya nufi ɗakin sa domin bacci...... ✨katsina ✨ Kwance suke kan bed ko waccen su sanye take da pajamas ɗinta , Aaimah da najma color ɗaya white sai Aairah dake da pink color , labari kawai suke a kan yanda walimar zata ka sance Aairah tace "wallahi harna ƙosa naga gobe tayi" Aaimah tace "faɗi kike anaji, ni baki san yan da nake jiba, Allah dai ya nuna mana goben lpy" da ameen suka amsa, sun jima suna tattaunawa a kan yanda walimar zata kasance , har bacci yayi awon gaba da su.... WASHE GARI Tun da safe suka tashi, shirye shirye kawai suke na walima, har mai makeup Mom ta ɗaukko, wacce zata yi masu kwaliyya, zuwa anjima, Idan lokacin walima yayi , su Mom kuwa suma tun da suka yi sallar asuba suke cikin kitchen ita da Aunty Rabi da baaba larai, suna ida shirya abubuwan da basu gama shiryawa ba jiya. a chan compound kuwa yasha decoration, mai kyan gaske. wurin karfe biyu na rana gidan ya fara cika da mutane, saboda bayan la'asar za'a gabatar da walimar , har gida ya abdallah ya je ya dauko Dadi, sai Aunty safiyya wace mus'af ya kawo,yan uwan abie ba wanda baizo ba da ƴaƴen su , sai wasu daga cikin ƙawayen Mom , hakama ƙawayen su Aairah na islamiya da boko duk sun zo, sai abokan abie dake nan katsina ba laifi suma sun zo , gida dai ya ciki Alhmdllh..... ✨Ammy ✨ Zaune take kan sallaya tana adu'a, wayar ta dake bedside drawer ce ta fara ringing, miƙa hannun ta tayi ta ɗauki wayar haɗi da yin picking bakin ta ɗauke da sallama on the other hand cikin wayar muryar wata dattijuwar mace tace wa'alaikumu salam, ammy ta ce"ina wuni innah " amsa ma ammy tayi da "lafiya " ammy tace "innah yasu alhaji ahmad da su hajiya turai" da katar da ammy matar yi da faɗin "dakata aisha bawai na kira ki bane dan kiyi taman tambayoyi, na kira ne kan maganar da muka yi da ke, naga yau kusan wata kenan amma bangan su sunzo ba" ammy ta ce "dan Allah innah kiyi haƙuri, ko jiya da daddare munyi maganar da shazim akan zowan naso,to shine yake sanar man anyi mashi kiran gaggawa jos baza su samu zuwa ba sai sati na sama " katse ammy tayi da faɗin "dallah dakata man aisha kina nufin sai abun da shazim yace kenan, ko mi kike nufi"ammy ta ce "ba haka nake nufi ba innah" on the other hand "to mi kike nu, tun yau she muke magana sai dai kice man ranar kaza zasu zo amma kuma basu zo sai anyi magana ki kawo ma mutum wani uziri" shiru ammy tayi tana sauraran ta, da kaga fuskar ammy kasan cike take da damuwa " to bari kiji in gaya maki, baku isa ba daga ke har wannan mara kunyar, zumunci ne Allah ya riga da ya haɗa kuma dole ne ayi shi, bar ganin nayi shiru na barmaki yaran a hannun ki bawai hakan na nufin bazan iya ƙwatar su ba daga hannunki bane, saboda yara basu da wasu dangi a duniya bayan mu ɗinnan dai da kika gama rainawa kikasa ƴaƴanki suke ganin kamar bamu da amfani" sosai matar ta rufe ammy da masifa ammy na bata haƙuri tana gama faɗar abun da zata faɗa ko jiran mi ammy zata ce bata yiba ta kashe wayar, shiru ammy tayi ta ƙura ma wayar ido, chan kuma ta ɗaga hannun ta sama tana adu'a wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, gefen hijabin ta ta sa ta goge tana faɗin "Allah sarki abubakar, Allah ya jiƙan ka ya haskaka kabarin ka " na ce ameen ammy, tashi tayi daga kan sallayar ta linke ta ta saka cikin wardrobe da hijabin da tayi sallah fita tayi daga ɗakin, fatima ta samu zaune kan sofa tana ta latsa sabuwar laptop ɗinta wacce shazim ya saya mata, ɗago da kanta tayi tana faɗin"barka da fitowa ammy "da yawwa ammy ta amsa mata haɗi da neman wurin zama ta zauna, fuskar ta duk a ya mutse, lura da hakan fatima tayi yasa ta cewa"lafiya dai ammy na ganki cikin da muwa " ce mata ammy tayi ba komai mikika gani "nagan ki duk wani iri ne ammy " amsa ammy ta bata da gajiya ce, "to ammy da kin kwanta kin ɗanyi bacci kafin la'asar tayi "to"shine kawai a bunda ammy ta ce mata..... ✨KATSINA✨ Sai bayan da a ka gama sallar asr ɗakin su Aairah ciki yake da ƙawa yen su na boko da islamiya , mai makeup ta fara tsara ma Aairah makeup mai kyan gaske, wayar Aairah ce ta fara ringing cema Aaimah tayi ta duba mata taga wake kira , Amsa ta bata da alaramma ne ( malamin su na Islamiyya ) haɗi da yin picking, tayi sallama, ba'a jin me na cikin wayar yake ce wa, kawai dai naji Aaimah ta ce to shikenan malam, sannan tayi rejecting tana ce ma Aairah "ya ce sun ƙara so, suna waje" Aairah tace " to pls ki fita keda aeesha ku shigo da su, ko ki faɗa ma abie sai ayi ma su iso " Aaimah ta ce " bari dai na faɗa ma abie ɗin kawai, dan na san babu hanyar wuce wa" Aairah ta ce "to shikenan faɗa ma abie ɗin kawai" dialing number abie Aaimah tayi, picking abie yayi yana cewa "lafiya Aairah , kun gama shirya wa ne" "Aaimah ce abie " "Ok kun gama ne" "A'a abie dama su alaramma ne suka iso" Abie ya ce " to bari na sa abdallah ya shigo da su, amma fa kuyi sauri bana son lokaci ya ƙure" "to abie insha Allah mun kusa" "to shikenan"abie ya faɗa haɗi da yin rejecting din call din Aairah ta ce " sis ya abie ɗin ya ce " Aaimah ta ce"gashi chan zai sa ya abdallah ya shigo da su" Aairah ta ce "to kira su ki ce ga ya abdallah nan fi towa" kiran su Aaimah tayi ta faɗa masu, sannan ta ajiye wayar, ana kammala ma Aairah ita ma aka yi mata, sanan najma, sai friend din su Aeesha, sosai suka yi kyau kamar ka sace su ka gudu mu samman ma su Aairah , dan ba ƙara min kyau suka yi ba, shiryawa su kayi cikin wata atamfa super ɗinkin riga da skirt, sosai ɗinkin ya amshi jikin su ba ƙara min kyau atamfar tayima fatar su ba, sannan su ka ɗaura farar alkyabba saman atamfar, faɗin kyan da alkyabbar tayi masu ɓata lokaci ne, kamar wasu ɗiyan sarakai, mom ce ta shigo ɗakin jikin ta sanye da wani haɗaɗɗen lace ɗinkin doguwar riga, wuyan ta da kunnan ta da hannu sanye da gold, mom ta ce "kai masha Allah kuce kun shirya, kai amma kunyi kyau sosai, kamar zan kai ku gidan miji" dariya friend ɗin su da ke ɗakin suka yi suna ce wa"mom ai wannan ranar sai sun fi haka bada kala" su dai su Aaimah ban da murmushi babu abun da suke, "mom ta sake cewa "to kuzo ku fita ku ka ɗai ake jira " da to suka amsa mata, fice wa mom tayi daga ɗakin, suma tashi su kayi suda friend ɗin su suka fice chan compound, suna gaba friend ɗin nasu na baya, maƙil suka iske compoud ɗin da mutane, wurin da aka tana da domin su suka nufa suka zauna, ba ɓata lokaci aka shiga gaba tar da walima, alaramma yayi wa'azi, sannan su Aaimah suka yi karatu, sosai walimar tayi kyau ta kuma ba da ma'ana, su Aairah ba ƙara min burge mutane suka yi ba, sun kuwa sumu kyauta daga islamiyyar su, haka ma abie, mom, ya abdallah , dadi, granny, papi,aunty safiya, ƙannan abie duk sun basu kyauta, sosai suka tara kyaututtu ka daga wurare daban daban, su aunty rabi da aunty safiya suka yi rabon souvenirs, sai wurin karfe 6:40 ana shirin kiran sallar magrib sannan aka tashi, kowa ya tafi yana yaba hazaƙa irin ta su Aairah da kuma ganin nagartar islamiyar su ....... Episode 16_17 Sallah isha Aaimah ta kammala tana zaune kan sallaya Najma ta shigo hannunta ɗauke da wani madai dai cin kwali, Aaimah ce tace "ke kuma daga ina haka da wannan ƙaton kwalin" amsa najma ta bata da"saƙwan Aairah ne inji ya mus'af " ta faɗa yayin da take ajiye kwalin kan bed, ta sowa Aaimah tayi daga kan sallayar tana faɗin "ya mus'af dai, mugani" buɗe kwali suka shiga yi, Aairah ta fito daga bathroom jikinta ɗaure da towel tsayawa tayi tana kallon najma da Aaimah dake ko kuwar baɗe kwali, kayan da ke cikin kwalin suka shiga fitowa, qur'an ne da carpet sai watch na mata da turare, kwalin turaren su Aaimah suka buɗe suna ta fesa ma jikin su suna faɗin "ah lallai ya mus'af abun yar wariyar launin fata ce, to bari muji kalar ƙamshin turaren" ita dai Aairah ban da bin su da idanu babu abun da take, dan kwata kwata bata fahimci mi suke nufi ba, barin bakin ƙofar bathroom ɗin tayi ta nufi dressing mirror tana faɗin "wai ku lafiyar ku ƙalau kuwa, dare ne amma sai wani fesa ture kuke baji ba gani, wai ma ina kuka same shi ne" najma ce tace "naki ne inji ya mus'af, tun da mu bazai bamu ba shine muke fesawa" taso wa Aairah tayi daga gaban dressing mirror ɗin tana faɗin "kuji tsoron Allah, shine kawai za kuyita fesawa koma ku faɗa man" Aaimah ce tace to yan zu an faɗa maki shikenan ko, kayan Aairah ta shiga dubawa tana faɗin "kai amma nagode sosai ya mus'af, Allah ya bar ƙauna"da ameen su najma suka amsa, tashi Aairah tayi ta shirya cikin pajamas ɗin ta sannan suka shiga buɗe sauran kyaututtu kan da suka samu, sai da suka gama harma sun kwanta sannan ta ɗauki wayarta ta kira mus'af, sunjima sosai suna waya har su najma suka yi bacci, itama suna gama wa bacci ta kwanta.... Wannan kenan ✨lagos✨ Fatima da ammy ne a kan dinning suna dinner, fatima ce kawai ke cin abincin dan ammy bata wani ci sosai ba ta tashi tana faɗin "nizan shiga ciki, idan yan uwan ki sun shigo kice masu na kwanta sai da safe " fatima ce tace " to ammy, amma lafiya naga kin tashi ba tare da kinci komai ba" "naƙoshi ne fatima, sai da safe "ammy ta faɗa, bedroom ɗin ta ta nufa, binta kawai da kallo fatima tayi, aranta tana faɗin "ko mike damun ammy ne yau"shiru tayi dan bata da mai bata amsar tambayar ta, ammy bata jima da tashi ba shazim suka shigo shi da noraiz bakin su ɗauke da sallama, amsa ma su sallamar fatima tayi, dinning ɗin suka nufo , warmars ɗin da ke kan dinning noraiz ya shiga buɗewa yana faɗin "mi aka dafa ne autar ammy " girgiza kai Shazim yayi yana faɗin "ina ammy ne naganki ke kaɗai? " "ta shiga ɗaki " "lafiya dai koh? "fatima ta ce "gaskiya yaya da sauƙi dai". shazim ya ce "mi kuma ya same ta yanzu" "wallahi yaya har yanzu mood ɗin ta sai ahankali kuma na ƙara tambayar ta mike da munta, sai cewa tayi wai lafiya qlu, kuma fa yanzu bata ci komai ba wai ta ƙoshi" ɗan shiru Shazim yayi kamar me nazari chan kuma sai ya ce" ok shikenan sai da safen ku " ya wuce part ɗin sa, noraiz yace "nifa ina tunanin wani abu ke damun ammy wan da baza ta iya faɗa mana ba"fatima ta ce"abun da nake tunani ke nan ya noor"sun ɗan jima suna tattaunawa a kan chanza war mahaifiyar su, sannan suma suka tashi suka nemi wurin kwanciya su.... WASHE GARI... Ammy na kan sofa a parlor, Shazim ya shigo da ga motsa jiki, wirin da ammy ta ke ya ƙara so, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi cikin kulawa, tashi yayi da nufin barin parlor ammy ce ta ce"ina zaka je? " Shazim ya ce "zanje ne na watsa ruwa nayi shirin ta fiya yau zan tafi jos " ammy ta ce " ok ashe yau zaka tafi? " "eh ammy" ya bata amsa, ammy ce ta sake magana tana faɗin "to dawo ina son magana da kai " to kawai yace haɗi da dawowa ya samu wuri ya zauna, ammy ce ta fara magana tana faɗin "wai ni kam shazim mike da munka ne kai da ƙannan ka.? " ɗago da kansa yayi yana faɗin "bakomai ammy, mikika gani ne.? " "ba komai, kawai dai naga nayi maku maganar zuwa abuja amma babu wanda ya sake ce man komai akan tafiyar, Noraiz ma da na tambayeta shi ceman yayi ya manta " ajiyar zuciya Shazim ya sauke sannan yace "ba komai ammy, ni aiki ne ya sha kaina shiyyasa " ammy tace "to yanzu bangane mikake nufi ba?" shazim ya ce "ammy ina ganin sai dai kawai fatima da noraiz su tafi, tun da ni jos zani kuma na faɗa maki, da ace zan iya zuwa ranar na dawo to da kawai sai na kai su ni sai na dawo " wani kallo ammy ta bishi da shi har ya gama faɗan abun da zai faɗa sannan ta ce "yanzu dai mi kake nufi ba zaka je ba ko kuma dai wani abun kake nufi??? " "A'a ammy da na dawo zanje insha Allah " ammy ta ce "maganar sai ka dawo jos bama ta taso ba, yanda su fatima zasu je haka kaima zaka je,kai ka ɗai ne likita da baza su ne mi wani ba, in kuma maganar aikin ka kake nasan kafin kaje ka dawo hameed zai ji da komai na abnoor har ka dawo, in kuma eko ne da ka ɗauki permission nasan zasu baka, kuma duk abund a ya kamata ace kayi ai kabir na nan" kallon ammy kawai shazim yake, dan shifa har zuciyar shi baya son wannan tafiyar, shiyyasa ma ya kawo mata excuse ɗin zuwa jos dan kawai ta cire shi cikin masu tafiyar, amma daga ganin yanda take magana yama san bazata haƙura ba, katse mashi tuna nin ammy tayi da cewa "sai wani kallona kake kana tunani, tafiya ce dai dole kayita shazim" ajiyar zuciya ya sake saukewa yana faɗin "ammy bawai bana son zuwa bane,a kullum ke kike faɗaman ka taimaki mai ne man tai mako da gwar gwadan abun da Allah ya hure maka, ammy yau ke kike cewa su ne mi wani, dan Allah ki bari naje in dai abuja ne zanje idan ma kikace na wuce daga jos ɗin sai na wuce amma dan Allah karki hanani yin wannan taimakon" "babu wani excuse fa da zaka kawo man, nariga da nagama magana, garama kawai kayi shiru dan bazan saurari excuse ɗin ka ba" "shikenan ammy kwana nawa kike so muyi" "sati biyu nake son kuyi sannan ku dawo" ɗago kai shazim yayi da sauri yana kallon ammy jin tace sati biyu zasu yi"haba ammy ina laifin kwana biyar" "sati biyu fa zaku yi kaji na faɗa maka" "dan Allah ammy kiyi haƙuri, ki maida shi kwana biyar" "to naji sai dai kai kayi biyar ɗin, ammy fatima da noraiz sai sunyi sati biyu cif sannan su dawo" ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce "ammy ina dai laifin ita fatima tayi sati biyun" "bangane ba shifa noraiz mizai sa bazai sati biyun ba? " "Ammy kinga nace shi zai cigaba da kula da business ɗina ai kinga bai kamata ace yayi sati biyu ba" "ban amince ba to, ina masu kula da business ɗin time ɗin da yake makaranta" "suna nan ammy" "to su cigaba da kula da shi kafin su dawo"miƙewa shazim yayi yana faɗin "to shikenan ammy, nizan shiga na shirya time yana ƙurewa" da to ammy ta bisa har zai wuce, tace "idan kaje jos ɗin kwana nawa za kayi?" murmushi yayi dan dama ya san bazata taɓa hana shi taimako ba,ba tare da ya juyo ba yace "dama kwana biyar zanyi, amma tun da kince ba sai naje ba zan tura majeed yaje kawai" "to na fasa kaje ka dawo sai ku tafi" murmushi yayi yana cewa "A'a ammy ki bari kawai majeed ɗin yaje" "kaci gidan ku nace kaje zaka wani ce man majeed yaje bayan nasan kana son zuwa"murmushi yayi mai ɗan sauti yana faɗin"to shikenan "haɗi da wai go wa ya dawo kusa da ammyn yana ƙara faɗin "nagode sosai ammy na "dun gure mashi kai tayi tana faɗin"ni kake ma dariya ko, dan kasan dama bazan taɓa hanaka zuwa ba ko" "a'a ammy ba da ke nake ba" "to shikenan, tashi kaje ka shirya kar lokaci ya ƙure"da to ya amsa haɗi da miƙewa ya haye sama , fitowa fatima tayi daga bedroom ɗin ammy, wurin da ammy take kan sofa ta zauna tana faɗin "na kammala jera kayan ammy" ammy ta ce "masha Allah, Allah ya biyaki" "Ameen ammy" fatima ta ce, innah asabe ce ta shigo parlorn gaisawa suka yi ita da ammy sannan take cewa "hajiya an kammala karin kumallon " "Masha Allah sannu da ƙoƙari, Allah ya saka " "Ameen hajiya "innah asabe ta amsa sun nan suna ɗan taɓa fira shazim ya sauko shi da noraiz, gaishe da ammy noraiz yayi danshi shazim sun gaisa tun ɗazu,sannan suka gaishe da innah asabe, sannan suka tashi suka nufi dinning, shazim da norai basu wani jima ba suka miƙe shazim na ma su ammy ban kwana sai ya dawo sai sun dawo, adawo lafiya ammy da fatima suka yi mashi, suna fita parking lot suka nufa, mota suka shiga noraiz ke driving, suna tafe suna fira har suka kawo airport, sai da jirgin shazim ya ta shi noraiz yabar airport ɗin ya wuce abnoor wurin majeed, acan ya wuni sai da yamma ya koma gida. kamar yan da shazim yace kwanan shi biyar ya dawo daga jos, san da ya dawo har ammy tasa fatima ta shirya kayan ta. Wannan kenan. sauko wa yake jikinsa sanye da jeans da t_shirt, wurin ammy ya nufo dake zaune kan sofa, gaishe da ita yayi, cikin kulawa ta amsa mashi tana tambayar "yau batare zasu fita da noraiz ne ba " "tare zamu fita yana shiryawa ne "ko rufe baki bai yi ba sai ga noraiz ɗin ya sauko cikin sauri yana faɗin"yaya na shirya, ina kwana ammy" "lafiya lau "ammy ta amsa, tashi suka yi suka fice suna cewa sai mun dawo, adawo lafiya ammy tayi masu,fi cewa su ka yi zuwa parking lot, wata sabuwar mota suka nufa suka shiga, shazim na driving, noraiz na kusa da shi,buɗe masu gate mai gadi yayi suka fice, sai da suka kawo kwanar da zata kaisu eko shazim ya cema noraiz "yaushe zaka fara kula da business ɗin" Noraiz ya ce "yaya duk sanda kace na fara, sai na fara " shazim ya ce "to shikenan, idan nagama kammala tsara komai zanyi maka magana sai ka fara" "to shikenan yaya, Allah ya kaimu " da ameen shazim ya amsa yayin da ya ke shiga cikin eko ɗin, parking lot ya nufa, yayi parking,sannan ya fito suka shiga ciki, yana gaba Noraiz na biye da shi, har suka kawo office ɗin Shazim bu ɗewa yayi suka shiga ciki, wuri noraiz ya sumu kan sofa a office ɗin ya zauna, shi kuwa Shazim wurin zaman shi ya nufa ya zauna, ba ɓata lokaci ya fara aiki, nocking ɗin kofar office ɗin aka yi , izini shazim ya bada , hidaya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama, amsa mata sallamar suka yi, gaishe da su ta yi sannan ta ɗaura da cewa "doctor patient zasu iya fara shigowa kai kawai shazim ya ɗaga mata alamar eh yayin da ya ke mayar da kansa kan laptop ɗinsa dake gaban sa ya cigaba da aikin da yake yi , ok ta ce haɗi da ficewa daga office ɗin.... KATSINA Su Aairah ne zaune parlorn mom suna kallo saboda yanzu ba school islamiya sai weekend ( saboda tunda suka gama hadda alaramma ya ware masu ajujuwa suna koyar wa du da abokan haddar su ) mom ce ta fito daga bedroom ɗin ta, ta nufo parlorn tana cewa "kufa yanzu baku da aiki sai zaman gida" Aairah ta ce "mom ai na wani lokaci ne, da mun tafi school shikenan sai mun dawo " "haka ne kuma " acewar mom Aaimah ce ta ce "mom wai har yanzu abie bai yanke shawarar school ɗin da zamu je ba "mom ta ce "har yanzu gaskiya banji yace komai ba shi da yayan ku, amma ina tuna nin bai gama yanke shawarar inda zaku tafi ba " Aairah ta ce"mom dan Allah kisa baki ya bar mu muje wani gari muyi karatun pls " sai da mom ta ɗan nisa sannan ta ce "gaskiya bazan yi maku wannan alƙawarin ba, saboda ba shi ka ɗai ba nima nafison kuyi karatu kuna kusa da ni, hankali na sai yafi kwanciya"Aairah ta sake cewa "haba mom yaza ki ce haka, duk inda muke Allah na nan zai tsare mu da tsarewar sa " kallon su kawai mom tayi amma bata ce komai ba, tasowa suka yi daga inda suke suka matso kusa da ita haɗi da dafa ƙafar ta suka ce "pls mom " har suna haɗa baki, sauke ajiyar zuciya mom tayi , sannan ta ce "shikenan zanyi mashi magana duk abun da yace to " "yawwa mom, Allah yasa ya amince " mom tace " ameen "Aairah ta ce "mom yau she abie ya ce zai dawo" mom ta ce "to ya dai ce kwana biyar zai yi " Aaimah ta ce "Allah ya kaimu, ya kuma dawo dashi lafiya" amsawa su kayi da ameen.... Lagos.... Hidaya ce zaune a reception ita da maryam suna magana, maryam ce ta ce "gaskiya ya kamata ace zuwa yanzu komai ya wuce" hidaya ta ce "baza ki gane bane maryam, abun da wahala " "haba dai hidaya miye abun wahala a ciki" hidaya ta ɗan nisa sannan ta ce"baza ki gane bane maryam, wlh dana ganshi sai na rasa duk wani ƙwarin gwiwar da nake dashi " Maryam tace "gaskiya daurewa za kiyi, dama ace na samo number sa ne to da ko a waya ne sai ki faɗa masa, duk da gaskiya zai fi kyau ace face to face kika faɗa masa, ko ya kika gani " "haka ne, matsalar bazan iya ba, kuma ina tsoron ya wulaƙanta ni" Maryam tace "kicire duk wannan tuna nin na cewa wai zai wula ƙanta ki, saboda gaskiya doctor bai yi kama da wanda zai iya yin haka ba" ɗan ajiyar zuciya hidaya ta sauke, sannan ta ce "shikenan, amma dan Allah ki samo man number kawai " Maryam tace "shikenan zanyi ƙoƙarin hakan, amma mi zai hana ke ki tambayi dr kabir nasan ma zai baki" hidaya ta ce "kai gaskiya bazan iya tambayar shi ba " "saboda mi baza ki iya tambayar shi ba? " maryam ta tambaye ta "kinsan in dai na tambaye shi sai ya tambaye ani mizan yi da ita,ba wannan ba ma gaskiya bazan ma iya tambayar shi ba" "haka ne kuma, amma ga shawara mi zai hana ki rubuta mashi sai ki ajiye mashi a office kan table ɗin sa, nasan dole zai gani kuma zai karanta " "haka ne kuma maryam kin kawo shawara, hakan kawai za'a yi " "sai kiyi ƙoƙari wurin ganin kin tsara mashi kala mai wanda zasu tafi da imanin shi "maryam ta faɗa tana yar dariya ita ma hidaya dariyar tayi, wata nurse ce ta nufo wurin su tana faɗin " mi ake tattaunawa ne, naga kuna ta dariya? "juyuwa maryam tayi tana kallon wacce tayi magan tana faɗin "sirri ne sister Aisha " gyaɗa kai Aisha tayi tana faɗin "ah bari na zauna nima ayi da ni " murmushi hidaya tayi, maryam ce tace mata "zauna kuwa kisha sirri" dariaya suka yi su dukan su,fira suka shiga yi akan aikin su , suna nan sai ga victoria da destiny sun fito daga office ɗin da suke zama, wani kallon banza victoria ta bishu da shi, tsaki maryam taja haɗi da cewa "aikin banza aikin wofi, haka dai zaki ƙare yar wahala kawai " a harzuƙe victoria ta nufo wurin su tan nuna maryam da yatsa tana faɗin " ke maryam kar ki kuskura kice zaki gaya man magana, kibari sai nayi lokacin ki tukunnan "tashi maryam tayi daga zaunan da take tana kallon victoria tun daga ƙasa har sama, sannan ta ce "idan aka faɗa maki maganar miza kiyi"girgiza kai victoria tayi tana faɗin "wallahi da sai kin gane baki da wayau, dan zan nuna maki cewa ni ba sa'ar yin ki bace " dariya maryam ta kwashe da ita tana ce ma victoria " wallahi ni har mamaki kike bani wahalalliya kawai " a masife victoria tace "kinga wahalalliya nan bayan ki"ta faɗa haɗi da nuna hidaya dake zaune wacce tayi kamar ma bata san da zaman victoria awurin ba, maryam tace "wallahi kin dai san ku wacece wahalalliya, waye a hopital ɗinnan baisan cewa ke yar wahala bace "a harzu ƙe victoria ta matso tana shirin kaima maryam duka dan ba ƙara min haushi maganar maryam ta bata ba, riƙe ta destiny tayi tana faɗin "lafiyar ki kuwa, duka fa kike shirin kai mata " victoria ta shiga kiciniyar ƙwace kanta daga riƙwan da destiny tayi mata tana faɗin "rabu dani na koya mata hankali" tana huci, ita kuwa maryam cewa take "dan Allah ki ƙyaleta destiny ta duke ni" fizgewa victoria tayi daga riƙwan da destiny tayi mata sosai ta kaima maryam duka, ramawa maryam tayi ita ma, sosai faɗa ya kaure tsaka nin su , hidaya ce ta riƙe maryam tana faɗin "dan Allah maryam kiyi haƙuri ki ƙyale ta pls" "haba yaza kice in ƙyale ta baki ganin cin mutuncin da take man ne,duka fa ta kaiman, ki barni kawai na nuna mata cewa bafa wai ana tsoron ta bane " destiny ce tace "pls maryam kiyi haƙuri "jan hannun victoria tayi suka bar wurin, saida suka shiga wani corridor sannan destiny ta saki hanun victoria tana faɗin "wai miki damun ki ne victoria nace ki fita daga harkar su, ki fuskan ci a bunda ke gaban ki, kin dai san mi gurutu ya ce mana, amma kin zo kina sakarci" ajiyar zuciya victoria ta sauke tana faɗin "wallahi idan naga yarinyar ne sai kawai naji wani baƙin ciki ya turniƙe ni" "uhmmm koma mi kike ji game da ita bai kamata ki bari yayi ta siri ba tunda dai kinsan mi gurutu ya ce " "shikenan zan kiya ye " "da dai ya fi maki"destiny ta faɗa haɗi da barin wurin, bin bayan ta victoria tayi... ✨Shazim ✨ Kayan shi dake kan table ɗin shi ya shi ga tattarawa yana zubawa cikin briefcase ɗin shi yana cema noraiz "tashi to kai , time ɗin sallah yayi" ok kawai noraiz ya ce, haɗi da miƙewa amsar briefcase ɗin yayi daga hannun shazim, ficewa suka yi daga office ɗin suka nufi masallaci koda aka gama sallah abnoor suka wuce, suna shiga a compound ɗin hospital ɗin suka ci karo da majeed wanda dawowar sa kenan daga sallah asr hango sabuwar mota ne yasa shi tuna nin koh shazim ne, tsayawa yayi, sai da Shazim ya gama dai daita parking sannan suka fito shida noraiz, ƙaraso wa majeed yayi wurin su, gaisawa suka yi majeed na faɗin "noraiz kenan ɗan gidan yayan sa, ai dama karatun doctor kayi, kaga ni kullum kuna tare duk da ma yanzu haka ne "ɗan sosa kai noraiz yayi yana kallon shazim chan kuma sai ya mai da kallon shi wurin majeed yana faɗin "wallahi kuwa ya majeed abun da naso kenan amma yaya yaƙi yarda " Shazim ne yace "to parrots zaku fara naku surutun koh, to ni kun ga tafiya ta "ya faɗa yana nufara entrance ɗin hospital, bin bayan sa suka yi suna cigaba da firar da suke yi har suka iso office ɗin Shazim, sun ɗan jima a abnoor dan sosai shazim ya duba patient anan sai da suka yi sallah magrib da isha sannan suka nufi gida, koda suka isa gida gaishe da ammy kawai shazim yayi ya nufi part ɗin sa domin ba ƙaramin gajiya yayi ba dinner ɗin sa ma sai dai fatima ta kawo masa nan part ɗin sa, wanka yayi ya shirya cikin kayan bacci white color, parlor ya dawo akan center table ya samu dinner ɗin sa da fatima ta kawo masa, serving ɗin kansa ya shiga yi yana kammala dinner ya wuce bedroom ɗin sa toilet ya wuce ba'afi five minutes ba ya fito jikinsa na danshin ruwa da'alama alwala yayi da brush, wurin wardrobe ya nufa ya fito da sallaya shimfi ɗawa yayi, shafa'i da wutiri yayi, ya ɗan jima yana adu'a, sannan ya tashi ya nufi bed ɗinsa ya hau adu'a yayi sannan ya kashe bulb ya kunna bedside lamp.... Episode 18 _19 A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji, har an ciye sati da wasu yan kwana ki da maganar tafiyar su shazim abuja, kullum da kalar excuses ɗin da zai ba ma ammy har dai suka yi wannan kwana kin basu tafi ba, a gefe kuma innah ta addabi ammy kullum cikin kira take akan miyasa ba su zoba har yanzu sai dai ammy ta bata haƙuri, yau ma tun da sassafe ta kirata, tun da ammy taga kiran innah sai da gabanta ya faɗi tasan da tace mata ba yau ba zata rufe ta da cin mutunci, haka nan ta ɗaga wayar kamar yanda ammy tayi zargi hakan ce ta faru dan sosai innah ta cima ammy mutuncin san ranta, baiwar Allah ammy harda kukan ta, tashi tayi daga bakin gado da take zaune ta nufi part ɗin Shazim, bata same shi a parlorn shi ba hakan ne ya sata nufar bedroom ɗin sa tayi nocking buɗe ƙofar yayi, jikin sa sanye da uniform ɗin sa da'alama ma ya gama shirin tafiya hospital ne, ganin ammy tsaye bakin ƙofar bedroom ɗin sa yasa shi mamakin ko lafiya ta zo da kanta maimakon tasa fatima ko noraiz ya kirasa, gaishe da ita yayi, amsa mashi tayi da lafiya, daga yana yin da ta amsa mashi yasan cewa gaskiya ba lafiya, domin tun da yake da ammy bai taɓa ganin ta cikin irin wannan yana yin da ya ganta ciki ba yanzu, kafin ya sake cewa wani abu ya ji tace "wai ni kam shazim yaushe ka zama mara jin magana ne, wai har ace nizan saka abu amma kafi ƙarfin kayi abun da nake so koh" kallon ammy jin abun da tace danshi aiya sanin shi baisan mi take nufi ba dan shi harga Allah ya manta sunyi wata magana ta zuwa abuja "ammy dan Allah kiyi haƙuri wallahi ban san akan mi kike magana ba" wani irin kallon ammy ta bishi da shi tana cewa"watau saboda kagama rainani shiyyasa ka manta da maganar da mukayi da kai koh, wai nikam Shazim wane irin yaro ne kai maganar zuwa abujar ce ka manta saboda ka raina mutane koh " sai yanzu ya ma tuna da wata maganar tafiya dan shi duk atuna nin shi ammy ta bar maganar ganin ta kwana biyu bata sake yi mashi maganar ba " dan Allah ammy ki daina cewa haka ta yaya zan raina ki dan Allah kiyi haƙuri wallahi yana yin aiki.... " bai ƙarasa faɗar maganar da zai faɗa ba ammy ta da katar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa "da kata man bana son jin wani excuse naka, umarni nake baka ba shawara ba kashirya gobe tun da safe ku tafi " cikin rashin jin daɗin hukuncin da ta yanke yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri sai jibi " tsawa ammy ta daka mashi tana faɗin "wallahi kaji na rantse gobe zaku tafi indai na isa da kai sannan kamar yanda su fatima zasu yi sati biyu kaima sai kayi shi , in kuma ban isa ba zaka iya yin duk yanda ka ga dama " tana gama faɗar haka ta juya tafice daga part ɗin, komawa Shazim yayi cikin bedroom ɗin shi ya zauna bakin bed yana dafe kansa dan harga Allah baya son tafiyar nan gashi ammy tayi fushi, bashi da wani zaɓi banda ya shirya kawai gobe su tafi ko hakan zai sa ta sauko daga fushin da tayi dashi, ammy na fita daga part ɗin shi main parlorn ta nufa, noraiz da fatima ta samu kan dinning suna breakfast gaishe da ita su kayi, amsa masu tayi tana tambayar su " kun shirya kayan ku da nace ku shirya? "fatima tace "eh ammy saura kaɗan ingama shiryawa yawale nake jira ya kawo kayan guga sai na gama " ammy ta ce "ok anjima zai kawo daya kawo kishirya su yau " da to fatima ta amsa, mai da kallon ta tayi kan noraiz tana faɗin "kai fah ka shirya naka " "a'a ammy, wai ba anfasa tafiyar ba " kallon shi kawai ammy tayi bata ce komai ba, "wallahi ni ammy da kin haƙura da maganar tafiyar nan, dan ni wallahi bana son zuwa ko dan saboda wannan tsohuwar, tayi ta zagin mutum bayan ba wani abu mutum yayi mata ba, tana faɗin wai dama ba sonta kike ba shiyyasa muma bamu sonta wai da papah na raye bamu isa muyi nesa da ita ba " katse shi ammy tayi ta hanyar ɗaga mashi hannu tana cewa "ya isa haka, kar in ƙara jin kace wani abu inba so kake yanzu nan ranka ya ɓaci ba " shiru noraiz yayi ganin kamar ran ammy ya ɓaci. shazim ne ya sauko daga part ɗin sa ya nufo main parlorn, fuskar shi cike da damuwa, zuwa yayi wurin ammy ya durƙusa gaban ta yana faɗin "dan Allah ammy kiyi haƙuri " kau da kai tayi kamar ma bata son ganin shi tayi banza da shi, haƙuri ya shiga bata amma ko ta ɗaga kai ta kalle sa, tashi yayi daga durƙuson da yayi yana faɗin"dan Allah kiyi haƙuri, na wuce office " ko yan zu bata ɗaga kai ta kallesa ba, noraiz ne yace" yaya bazaka yi breakfast ba "ganin shazim ɗin ya nufi hanyar fita batare da ya kalli dinning ba"na ƙoshi "abun da kawai ya cema noraiz, ficewa yayi daga parlorn ko da ya shiga motar shi ya daɗe bai tada motar ba gaba ɗaya baya jin daɗin fushin da ammy ta ɗauka da shi, sai da ya kusan 15 minutes a motar bai tafi ba sannan yayi mata key ya bar gidan ko gaisuwar da megadi keyi mashi shida ilya bai amsa ba ɗaga masu hannu kawai yayi ya fice.. a parlorn kuwa noraiz ne ya taso daga kan dinning ya dawo kan sofa kusa da ammy yana faɗin "ammy wai mike faruwa, naga kamar kina fushi da yaya lafiya " amsa ammy ta bashi da "ba komai tafiya ce bai so kuma dole sai kunyi ta " noraiz ya ce "dan Allah ammy ki janye maganar tafiyar nan ni ban san miyasa kike son sai munyi wannan tafiyar ba,kinsan halin innah bawani son mu take yiba kema kinsani,su uncles ne kawai suka damu da rayuwar mu lokacin da muke buƙatar kulawar su " ammy tace "ya isa haka,dama kai da shazim na lura halin ku ɗaya, to tafiyace sai kunyi ta gobe ma bawai jibi ba kunji na faɗa maku " " ammy gobe fa ki kace " "ƙwarai kuwa gobe nace, idan kuma ban isa ba sai inji "noraiz ya ce "kin isa ammy, Allah ya huci zuciyar ki , insha Allah ba zamu sake cewa komai ba game da wannan tafiyar ba, yanzu zamu fara shirya kayan mu goben zamu tafi insha Allah "ammy tace "da ma dai ya fiye maku " ta faɗa haɗi da tashi ta nufi bedroom ɗin ta, da idanu kawai suka bita, sai da su kaga shigewar ta ɗaki sannan suka kalli juna noraiz ya ce "nifa gani nake kamar akwai abun da ke damun ammy, yan da tayi fushi akan tafiyar nan abun yayi yawa, kawai dai tana ɓoye mana ne, amma alamu sun nuna cewa tana cikin damuwa yan kwana kinnan, kuma nasan hakan da sa hannun innah "ɗan nisawa fatima tayi tana cewa "na daɗe da lura da hakan ya noor, kuma na tambayeta ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba tana ce man wai ba komi, abun da kawai ya ka mata shine mu shirya kawai gobe mu tafi, may be zata huce dan naga tayi fushi sosai" "haka ne fatima, amma kinsan yaya baya son tafiyar nan "fatima ta ce "amma dole yayi ta ya noor tun da ammy ta nuna ɓacin ranta, na san ko dan haka dole ya tafi " noraiz ya ce" haka ne dan bansan mi ya haɗa su ba naga tana fushi da shi kuma daga part ɗin sa ta ke " "ina tuna nin tayi mashi maganar tafiyar ne ya nuna bazai je ba " noraiz ya ce "to ƙila, nima yan tashi zanyi naje na shiraya kayana, dan wallahi nasan ta wai waye mu baza mu ji da daɗi ba yanda tayi fushin nan" "dama ni ya noor tun da tayi magana nashirya kayan ganin ba'a yi tafiyar ba ne yasa na saka wasu daga cikin kayan da zani walimar school ɗin mu"noraiz ya ce " ki daman murna kike da wannan tafiyar" "murmushi fatima tayi taan faɗin"ina son zuwa naga sa'ada da ya kairiyya ne kawai" noraiz ya ce"za kuma ki haɗu da innah guyaba "dariya fatima ta kwashe da ita, tashi yayi yana faɗin "bari nima tashi yanzu na kammala shirya nawa kayan tun da ba inda zani" ya faɗa hadi da tashi ya nufi part ɗin su, tashi ita ma fatima tayi ta nufi nata bedroom ɗin.... ✨SHAZIM✨ Zaune yake a office ɗin shi ya bar baza ta kardu kan table ɗin shi ya zuba masu ido yana kallon su da alama hankalin shi baya kansu, yayi zurfi cikin tunani ya ji ana nocking, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya bada izinin shigowa, hidaya ce ta shigo hannun ta ɗauke da files, gaishe da shi tayi hannu kawai ya ɗaga mata, ganin hakan ne yasa hidaya fahimtar yau baya san magana dan haka kawai ta matsa kusa da table ɗin ta ajiye mashi files, ɗago da kanshi yayi yana kallonta, fahimtar mi ya ke nufi ne yasa ta cewa "dama files ɗin patient ne dake waje" sai yanzu ya buɗe baki ya ce "kwashe su ki kaima dr kabir, bazan samu damar du ba kowane patient ba yau" daga ganin yana yin da yake maganar zaka san cewa baya jin daɗin," dr baka jin daɗin ne" hidaya ta tambaye shi, kai kawai ya ɗaga mata, ɗaukar files ɗin tayi ta fice, direct office ɗin dr kabir ta nufa, nocking tayi aka bata izinin shiga, shiga tayi bakin ta ɗauke da sallama, zaune ta same shi yana aiki a laptop "good morning sir "hidaya ta faɗa, ɗago da kansa yayi yana amsa mata gaisuwar da tayi tana kallon files ɗin sa ke hannun ta"lafiya dai koh hidaya, ina zaki da wannan files ɗin? " amsa ta bashi da "dr Shazim ne yace na kawo maka, bazai samu da mar duba patient ba yau" "ok ajiye " ya faɗa yana maida kansa kan aikin da yake yi, hidaya tana ajiyewa ta fice daga office ɗin, saida ya gama aikin da yake yi sannan ya miƙe ya fice daga office ɗin, ya nufi office ɗin Shazim, shiga kawai yayi batare da yayi nocking ba, samun shi yayi zaune kan sofa dake office ɗin dafe da kanshi, jin alamar an buɗe ƙofa ne ya sa shi ɗago da kanshi yana kallon dr kabir da ya shigo, amsa mashi sallamar da yayi yayi, ƙara sawa dr kabir yayi haɗi da ne man wurin zama ya zauna kusa da shazim yana faɗin "hi dude, what's wrong with you, naga kasa nurse hidaya ta kai man file ɗin patient " kallon shi Shazim yayi sannan ya ce " am not feeling better " "ya salam, mike damun ka " ɗan nisawa shazim yayi sannan ya ce "wallahi ammy ce wai dole sai natafi abuja, da na kawo mata excuse fushi ma tayi dani " kabir ya ce " to minene aciki da har zaka sama kan ka damuwa irin haka, shawarar da zan baka anan kawai kashirya ka tafi, hakan ka ɗai zai sa ammy ta huce " "baza ka gane ba kabir, kwata kwata bana son zuwa abujar nan " "to ya zakayi haka nan zaka yi haƙuri ka tafi tun da ammy ta ce katafi, yaushe ne tace ka tafi " "gobe fah "kabir ya ce "to Allah ya kaimu gobe, kai ka ɗai zaka tafi " "a'a harda su noraiz " "ok, Allah ya kaimu goben, karka wani damu "shazim ya ce "ameen nagode" "bakomai kar ka damu " "ina ma tuna nin tashi zanyi na tafi abnoor dan ban gaya ma majeed ba, sannan zan koma gida daga chan" Kabir ya ce "eh gaskiya ya kamata, da ƙarfe nawa zaku tafi ko dai sai munyi waya " "ina tuna nin da safe, dan wallahi ammy tayi fushi sosai " "to Allah ya kaimu " "ameen " Shazim ya faɗa hadi da tashi ya nufi table ɗin sa ya fara haɗa kayan shi yana maidawa cikin briefcase, yana gama haɗa wa kabir ya taso domin yi mashi rakiya, su hiday na zaune a reception suka zo suka wuce, suna wuce maryam tace "lafiya naga dr ya tashi lokacin tashin shi bai yiba " hidaya ta ce "baya jin daɗi ne, dan koda na kai masa files ɗin patient cewa yayi na kaima dr kabir, ina tuna nin ba zai iya zama ba shiyyasa zai tafi gida " maryam tace "Allah ya bashi lafiya " da ameen hidaya ta amsa, chan maryam tace"kinsan wane tuna nin nayi? " hidaya ta ce "a'a sai kin faɗa " maryam tace "kawo kunnan ki kiji" matsawa hidaya tayi kusa da maryam, magana ta faɗa mata, sauran nurses ɗin dake wurin suka ce "dan muna kusa shine abun harada su raɗa ko maryam" murmushi maryam tayi sannan ta ce "komai fa na son sirri, wannan magana ce tsaka nina da ita" wata acikin nurses ɗin ce ta ce "in tayi wari maji" ƴar dariya maryam tayi haɗi da cewa "bama zata yi ba " har parking lot dr kabir ya raka shi, saida dr kabir yaga tafiyar Shazim tukun ya koma cikin hospital ɗin, ya zo zai shiga office ɗin shi yaji maganr hidaya tana cewa"doctor " juyowa yayi yana kallonta sannan ya ce "na'am " duƙar da kanta tayi ganin ya kafe ta da idanu "lafiya dai koh hidaya,? kin tsayar dani kin kuma yi shiru " magana ta fara yi bata re da ta ɗago da kanta ba "dama dr tambayar ka zanyi mike damun dr ne " kallon ta kawai dr kabir keyi, sannan ya ce "baya faɗa maki baya jin daɗi ba " "eh haka ne " "to baya jin daɗi ne, gida ma ya tafi yanzu" "ok, am dan Allah ko zaka bani number shi nakira shi nayi mashi ya jiki"magana take still kanta na duƙe, wani kalar kallo dr kabir ya shiga binta da shi, ita kuma jin baice komai ba yasa ta ɗago da kanta, tana ɗago wa idanun ta suka sauka cikin nashi daya kafe ta dasu, kusan 5 seconds bai ce komai ba, chan ya ɗan nisa sannan ya ce "dama baki da number shi" girgiza mashi kanta tayi alamar eh, "ok shikenan ina wayar ki na sa maki number " hannu ta sa cikin aljihun rigar uniform ɗin ta ta ciro wayar ta ta miƙa masa, amsa yayi ya sa mata number, miƙa mata wayar yayi tasa hannu ta karɓa tana faɗin" nagode" shi dai dr kabir kallonta kawai yayi ba tare da ya ce mata komai ba harta juya ta bar waje bai daina kallonta ba, sai da ya ga ta ɓace ma ganin sa tukun ya murɗa handle ɗin ƙofar office ɗin shi ya shiga..... ✨ Shazim ✨ yana barin eko direct abnoor ya nufa, yana parking ya fito ya nufi main entrance ɗin hopital ɗin ba tare da ya ɗauki briefcase ɗin sa ba, yana shiga direct office ɗin dr majeed ya nufa nocking yayi, daga ciki aka bashi izinin shiga, kama handle ɗin ƙofar yayi ya tura ya shiga, bakin sa ɗauke da sallama, zaune dr majeed yake yana duba files dake gaban shi, amsa mashi sallamar yayi, wuri shazim ya samu ya zauna, hannu ya miƙama dr majeed suka yi musabaha, dr majeed ya ce " lafiya kuwa yau nagan ka a wannan lokacin? " "lafiya qlu majeed, maganar tafiya abuja nan ce ta taso, ammy tayi fushi dole sai mun tafi gobe "majeed ya ce "to fah, kwana nawa zaka yi " "kai dai bari kawai wai sai nayi sati biyu inji ammy" majeed ya ce "shiyyasa fa tun time ɗin da kace tace ku tafi ya sa nace maka ka tafi kawai ni zan kula da komai, amma kaƙi, yan zu ga irinta nan ta soke kwana biyar ɗin da tace " "bazaka gane bane kawai majeed, wallahi bana son zuwa ko nan da chan shiyyasa " "to ya zaka yi zumunci ne dole ayi shi" "haka ne" "yanzun goben da ƙarfe nawa zaku tafi? " "da safe"shazim ya bashi amsa " ok Allah ya kaimu " da ameen ya amsa , sun ɗan jima suna magana akan magunguna da allurai da zasu yi order, sai da shazim yayi sallamar asr bayan yaba ma majeed duk abun da zai bashi, sannan suka yi sallama ya nufi gida, tsit ya iske parlor alamar ba kowa, hakan yasa shi nufar bedroom ɗin ammy amma nan ma ba kowa, fita yayi ya nufi up stairs part ɗin noraiz ya shiga, samun shi yayi a parlor zaune kan sofa yana aiki cikin laptop, ɗagowa noraiz yayi jin anbuɗe ƙofa , yana ganin shazim ya miƙe yana faɗin "sannu da dawowa yaya"da yawwa shazim ya amsa yana cewa "ina ammy? , naga kamar bata gida kuma banga motarta ba a parking lot, nama yi tuna nin kokai ka fita da motar" "tun da ka fita ta fita ko breakfast bata yi ba, na tambaye ta ina zata, sai cewa tayi yanzu zata dawo, amma haryan zu bata dawo ba" jinjina kai kawai shazim yayi haɗi da ficewa ya nufi part ɗin sa, yana shiga parlorn shi wayar shi dake cikin aljihun wandon shi ya ciro number ammy ya shiga kira, tana ringing amma ba'ayi picking ba harta katse ya sake kira sai da yayi kusan 3 times amma bata ɗauka ba, fita yayi ya koma part ɗin noraiz, yana shiga yace "noraiz ina wayar ka? " "gata nan yaya " noraiz ya bashi amsa "kira number ammy "da ok noraiz ya amsa, nan shima ya shiga kiran wayar amma ba'ayi picking ba, ƙofar parlorn suka ji an buɗe fatima ce ta shigo da waya a hannun ta "yaya na shiga ɗakin ammy naji wayar ta na ringing, sai da na duba naga ashe kai ke kira, shazim bai ce komai ba ya fice daga part ya koma nashi, number malam yayi dialing, picking malam yayi haɗi da Sallama yana faɗin "likita bokan turai" "ina wuni malam" "lafiya lau, ya aiki" "alhmdllh " "to masha Allah " ɗan shiru Shazim yayi, jin yayi shiru ya sa malam ce wa "lafiya dai koh shazim? " "lafiya lau malam, dama ammy ce " sai kuma yayi shiru, malam " yace miya samu aishar? " "bakomai malam, tayi man magana ne akan zuwa abuja to nace mata ina da uziri wirin aiki, to sai bata sake maganar ba tun daga ranar, yau kawai " nan ya shiga bashi labarin yan da suka yi da ammy yau , har fushin da tayi da kuma dawowa da yayi yanzu bata gida da kuma kiranta daya ke bata ɗauka, ɗan nisawa malam yayi sannan ya ce "ta faɗa man komi ke faruwa, gaskiya banji daɗi ba, baka kyau ta ba, shi zumunci Allah ne yace ayi sa, kuma komi ya faru tsakanin ka da su ai kai ne baka kyauta ba " sosai malam yayi mashi faɗa da nasiha, akan bai kyauta ba daya bari har sai da ran ammy ya ɓaci "ayi haƙuri malam insha Allah hakan bazata sake faruwa " "shikenan Allah ya kyauta gaba " da ameen malam ya amsa, sannan shazim ya ce "to malam ammy tana nan ne " "eh tana nan " ajiyar zuciya shazim ya sauke, sannan suka yi sallama da malam, bedroom ɗin shi ya wuce, jifar da wayar shi yayi kan gado yana shiga, kayan jikin shi ya cire daga shi sai boxer yanufi bathroom, kusan 15 minutes ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, shiryawa yayi ciki ash ɗin jallabiya wuri ya samu kan sofa ya zauna, laptop ɗinshi ya jawo yashiga dan dannawa.... ammy bata dawo gidan sai da yamma liƙis, ta shigo, gaishe da ita fatima da noraiz dake parlor zaune, amsa masu tayi, haɗi da samu wuri ta zauna kan sofa, hijaba ɗin ta ta cire ta miƙa ma fatima tan cewa "kai man ɗaki" da to fatima ta amsa ta tashi ta kaima mata, tana fitowa ammy ta ce "ina innah asabe? " amsa ta ba ammy da "tana ɗakin ta" "ok " Noraiz ya ce "ammy wai ina kika je ne, yaya ya dawo tun ɗazu yana ta ne manki " fuska a ɗaure amma ta ce "in da ya aike ni chan na tafi" noraiz ya ce "dan Allah ammy kiyi haƙuri ki dai na wannan fushin, goben zamu tafi kamar yanda kika ce" "karma ku tafi " ammy ta ce, magana noraiz zai yi, ta ɗaga mashi hannu tana ce "ya isa haka kar ka takura man daga dawuwa ta " da jin haka dole noraiz ya kama baikin sa yayi shiru, sau kowa shazim ya ke daga up stairs ya nufo parlorn, hango ammy da yayi, yana isowa parlorn ammy ta miƙe ta nufi ɗakin ta, tsayawa yayi chak ganin tana ganin shi ta tashi, binta yayi har ɗakin, yana shiga ya ganta tsaye bakin dressing mirror, ta cikin mirror ta hange shi, yi tayi kamar ma bata san da shigowar shiba, ƙara sowa yayi har gaban dressing mirror ɗin yana faɗin "ina wuni ammy" amsa mashi tayi da "lafiya " daga nan ta ɗauke kanta ta koma bakin gado ta zauna, binta yayi har bakin gadon, durƙu sawa yayi yana dafa gwiwar ta, haƙuri ya shiga bata, da ƙyar ta haƙura, ganin ta haƙura yasa cewa "dan Allah ki rage satin da ki kace zanyi zuwa kwana biyar " "idan har kana son zaman lafiya da ni to kawai kayi shiru "da to kawai ya amsa mata, sannan ya fice daga ɗakin ya koma part ɗin shi domin yin alawala saboda lokacin sallah da yayi,yana fita ita ma ammy tashi tayi ta nufi toilet domin alawa, yana ko mawa part ɗin shi alawala kawai yayi ya fito suka wuce masallaci da noraiz dake parlor yana jiran shi yana saukowa suka wuce, anagama sallah suka wuce gidan malam basu bane suka dawo gidan ba sai wurin ƙarfe 10 sannan suka dawo, koda suka dawo ammy da fatima har sunyi bacci, suma part ɗin su suka wuce kowa ya nemi ma kwancin shi .........🖊 Episode 20 _21 Washe gari... Iliya ne ke saka trolleys ɗin su fatima a booth ɗin mota da zai kaisu airport, ammy da fatima da noraiz sai Shazim zaune suke kan sofa a main parlor, ammy nayi masu nasiha sai da ta gama faɗa masu duk abun da zata faɗa masu sannan suka tashi suka kama hanyar fita daga parlorn, fatima da noraiz harsun fice ammy ta tsaida shazim, tana faɗin "dan Allah shazim karnaji kar na gani dan Allah, kayi haƙuri da komi zaka gani har Allah yayi maku dawowa " "to ammy insha Allah "fitowa suka yi ammy ta raka su har parking lot suka shiga mota, tana masu Allah ya tsare hanya da ameen suka amsa mata, sannan ilya yaja motar suka fice daga gidan ammy na ɗaga masu hannu, saida taga mai gadi ya rufe gate sannan ta juya ta koma ciki, cike da kewar su yanzu sai ita kaɗai cikin gidan, fatan Allah ya kaisu lafiya ya dawo dasu lafiya.. suna fita daga gidan direct gidan malam suka wuce dan suyi mashi ban kwana, sosai malam yayi masu nasiha da fatan isa lafiya, suna fita ilya ya kama hanyar airport, koda ya kaisu sai da ya jira har jirgin su ya tashi sannan ya dawo gida..... ✨Abuja✨ Airport, passengers ne suka fara fitowa ta ƙofar da aka rubuta exist wacce aka tana da domin passenger, su shazim ne suka ɓullo ta wannan ƙofar yana gaba fatima da noraiz na biye da shi abaya da trollys ɗinsu a hannu, wata kyakyawa matashiya ce wacce zasu yi sa'anni da fatima fara ce sai dai bata kai fatima haske ba, ta nufo fatima da gudu tayi hugging ɗin ta tana faɗin "oyoyo sister" fatima da fara'a a fuskar ta tace "ya kike sa'ada" wacce aka kira da sa'ada, tayi murmushi tana faɗin "lafiya lau ya hanya" sannan ta juyo tana cewa" ya Shazim ina wuni" amsa mata yayi da "lafiya lau" sannan ta juya tana gaishe da noraiz, da fara'a a fuskar shi yace "ai nayi tunani fatima kaɗai kika gani " da murmushi a fuskar ta tace "a'a ya noraiz kuma ai na gan ku " suna nan tsaye wasu ƴan mata kyawawa su biyu suka iso farare ne sai dai ɗaya tafi ɗaya haske, mai hasken sosai tana kama da sa'ada sai dai ita daka ganta zaka san tana ƙara wa dana kanti, jikinsu sanye da ɓakar jallabiya sunyi rolling da gyelen jallabiyar, wurin su suka nufo, mai kama da sa'ada cike da yanga take faɗin "hi ya shazim "haɗi da nufar Shazim da nufin tayi hugging ɗin shi, kasa ƙarasawa tayi ganin wani mumunnan kallo daya bita dashi fuskar shi a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, kwal kwal tayi da ido kwalla na taruwa ciki tace " haba ya shazim miyasa kake haka , daga na nuna farin cikin ganinka " banza yayi mata kamar ma ba da shi take ba,gaishe da shi ɗayar tayi, cikin sakin fuska ya amsa yana faɗin "ya kika kairiyya " "lafiya lau, ya hanya?"da alhmdllh ya amsa mata,hugging ɗinta fatima tayi tana faɗin "nayi kewar ki aunty kairiyya" da fara'a a fuskar ta tace "nima nayi kewar ki", wasu maza ne suka ƙaraso wurin su su biyu sanye da uniform, suna ƙarasowa suka ce "barkan ku da zuwa ranka ya daɗe " kallon su shazim yayi yana cewa "barkan ku dai aminu ya kwana biyu" "alhmdllh ranka ya daɗe" wanda aka kira da aminu ya ce, ɗayan ne ya ce "yallabai ya lagos " shazim na kallon shi ya ce "alhmdllh kamal, ya aiki" "lafiya lau ranka ya daɗe"sannan suka gaishe da noraiz fuska ɗauke da fara'a ya amsa, sannan fatima ta gaishe da su, amsa mata suka yi cikin kulawa fuskar su da fara'a, suka amshi trollys ɗin noraiz da na shazim dake hannun noraiz aminu na cewa "mutafi koh ran ka yade "ok kawai shazim yace ya kama hanya, su aminu na gaba da trollys ɗinsu, sa'ada ce ta amshi na fatima, wannan budurwar wuce su tayi fuuu kamar zata tashi sama, fatima ce tace "aunty feenah abun ba magana "juyowa tayi ta kalli fatima sama da ƙasa fuska a haɗe tace "sannu" ta juya tayi gaba, da idanu kwai fatima ta bita, taɓe baki noraiz yayi, fuskar sa'ada da ɗan damuwa ta kama hannun fatima tana faɗin "sorry sister " ɗan yaƙe fatima tayi tana faɗin "bakomai" tsaki kairiyya ta ja a zuciyar ta tana faɗin "ko yaushe feenah zata dai wannan banzar ɗabi'ar " parking lot ɗin airport ɗin suka ƙara so time ɗin har shazim ya shiga bayan mota ya zauna, aminu na saka kayan su cikin booth, amsar trolly ɗin dake hannun sa'ada kamal yayi ya saka a booth, buɗe ma su baya yayi, noraiz ya shiga sa'ada ta ce " kamal mu zamu tafi a motar aunty kairiyya " "to shikenan hajiya " kama hannun fatima tayi suka nufi inda motar kairiyya ta ke, tsaye suka same ta bakin mota, sa'ada tace "lafiya dai aunty kairiyya" "babu komi, ku nake jira ne " sa'ada tace "aunty feenah tafiya tayi?" eh kawai kairiyya tace haɗi da buɗe motar ta shi, suma shiga sukayi fatima na gaba kusa da kairiyya sa'ada na baya, key tai ma mortar haɗi da yin reverse tabi bayan motocin da su shazim ke ciki, suna tafiya kamal na tambayar noraiz ya lagos da ammy, da alhmdllh noraiz ya amsa mashi sosai suke fira da shi har suka kawo wata danƙareriyar anguwa ta ji da faɗa, gidajen dake anguwar ka ɗai sun isa su sa ka fahimci cewa anguwa ce ta manyan mutane, gidaje ne naji da faɗa, road road ne gasunan kala kala kowane road kalar tsarin ginin gidajen ta da ban, karya kwana animu yayi ya shiga wani road bin bayan shi su kamal suka yi shi da kairiyya , masha Allah wani haɗeɗen estate ne naji da faɗa, aƙalla gidajen dake cikin estate ɗin zasu kai 20 duk da akwai wainɗan da anyi foundation ba'afara gina su ba, tsarin gidajen dake cikin estate ɗin yafi na sauran gidajen dake sauran road ɗin haɗuwa da tsari,komai na gidajen iri ɗaya ne, tafiya suka yi mai ɗan tsayi, sannan suka kawo bakin main gate ɗin estate ɗin ,securitys ne zaune kan bench a bakin gate ɗin estate ɗin, ɗaya daga cikin su ne ya taso ya nufo motar, sauke glass ɗin motar aminu yayi, gaisawa yayi da security ɗin, tambayar shi securityn yayi daga ina, amsa aminu ya bashi "daga airport muke, yallabai shazim ne ya zo " liƙawa security yayi yana cema shazim "ranka ya daɗe barka da zuwa, ya hanya "da alhmdllh shazim ya amsa masu, sauran security ɗin ma ta sowa su kayi suna gaishe da shazim sannan suka nufi motar dasu noraiz ke ciki suna gaishe su, cikin sakin fuska suka amsa masu, buɗe masu gate security yayi ,ciki aminu ya danna kan hancin motar kamal na biye da shi, sai da suka ɗanyi nisa da tafi sannan suka iso bakin wasu gidaje biyar dake jere duk da akwai yar tazara tsaka nin su , huɗu girman su ɗaya, ɗayan kuma yafi su girma sosai, mai girman dake tsakiyar su aminu ya nufa , parking aminu yayi bakin wannan ƙaton gidan wanda yafi sauran gidajen girma da haɗuwa parking lot ɗin gidan ya nufa yayi parking, motoci ne da a ƙalla zasu kai biyar an rufe su, fitowa aminu yayi ya buɗe ma shazim ƙofa amma sai shazim yace kawai ya ɗauki kayan ya wuce, hakan yasa shi nufar booth ɗin motar ya fito da trollys ɗinsu, ya nufi entrance ɗin shiga gidan ya tsaya, kamal ma ya nufo nan yayi parking a parking lot fitowa noraiz yayi, su fatima kuma wani part kairiyya ta nufa da su tayi parking, fitowa sa'ada da fatima suka yi, sa'ada ta buɗe booth ta fito ma fatima da trolly ɗin ta, fatima leƙa ta window tana faɗin "aunty kairiyya sai mun shigo " da to kairiyya ta amsa, reverse tayi ta nufi wani part tayi parking, ficewa tayi ta nufi cikin part ɗin. kallon motar feenah dake parking lot ɗin sa'ada tayi, aranta tace kenan gida aunty feenah ta dawo , trolly ɗin fatima ta ja suka nufi entrance ɗin gidan ,kamal na parking noraiz ya fito ya nufi aminu dake tsaye yana jiran fitowar shazim ya kai masu trolly ɗin cikin gidan amma bai fito ba noraiz na isowa ya tambayi aminu lafiya, amsa aminu ya bashi da shazim ya ke jira ya fito noraiz ya ce " ok muje kawai" da to aminu ya amsa yana gaba noraiz na baya, buɗe ƙofar aminu yayi suka shiga har time ɗin shazim bai fito ba yana zaune cikin mota, haɗeɗen parlor ne mai kyan gaske dan inka shiga sai kayi tuna nin ba acikin estate ɗin kake ba, babu motsin kowa aciki sai ƙarar ac dake aiki ita kaɗai,kota ina ƙamshi ne ke tashi cikin parlorn, up stairs aminu ya nufa , ɗakuna ne saman sosai, wata yar hanya aminu ya bi nanma wani parlorn ne wanda yafi na ƙasa haɗuwa da tsari, wani stairs ɗin suka ƙara nufa nanma parlor ne shima ya haɗu ga tsari mai kyau,sannan suka nufi wani ɗan corridor , bedrooms ne kusan guda huɗu anan aminu ya tsaya yana ajiye trollys ɗin yayi ma noraiz sai anjima, godiya noraiz yayi mashi sannan ya ja trolly ɗin shazim ya shiga ƙofar dake kusa da shi, ɗan ƙaramin parlor ne mai kyan gaske kusan tsarin shi ɗaya da parlorn shazim dake lagos, nan kamshi yake mai daɗin gaske ga sanyin ac, bedroom ya nufa nan ma ya haɗu shima kamar na lagos ne sai dai yafi na lagos girma da wasu abubuwan, har cikin wardrobe noraiz ya saka ma shazim trollys ɗin shi sannan ya fice daga ɗakin yanufi nashi, shima nashi ya haɗu sosai banbancin shi dana shazim bawain mai yawa bane bedroom ya nufa ya rage kayan jikin shi ya nufi toilet domin ya watsa ruwa .. ✨Shazim✨ wayar shi dake cikin aljihu ya fiddo, number ammy yayi dialing saida ta kusa tsinkewa sannan ammy tayi picking bakin ta ɗauke da Sallama, amsa sallamar shazim yayi yana faɗin ammy ya gida, da lafiya lau ta amsa tana tambayar shi ya gajiyar hanya da kuma mutanen abuja "gajiyar tafiya akwaita ammy alhmdllh" murmushi ammy tayi mai ɗan sauti tana cewa "gajiya sai kace wanda yaje a mota ko a ƙafa" kwantar da kanshi yayi jikin saet ɗin motar yana shafa kanshi ya ɗan lumshe ido yana faɗin "da gaske nake ammy " ammy tace "to yayi, ya mutanen gidan? " "wallahi ban saniba dan ban shiga ba" "to saboda mi, ina fatima da mai babban suna? " "fatima na part ɗin uncle Ibrahim, noraiz kuma na part ɗin mu " "to kai kana ina? " "ina cikin mota, yanzu muka iso ne ammy, na tsaya in kira ki ne " "ok miyasa ku baza ku sauka part ɗin ibrahim ba kona yaya ahmad " "bakomai ammy, shi da kanshi uncle Ibrahim ɗin yasa aka gyara mana nan" "duk da haka shazim da kuna zauna part ɗin shi, nasan shima dan ya san halinka ne ba zaka zauna part ɗin shi ba yasa aka gyara maku nan " "ammy ba haka bane" "to yaya ne in ba haka ba? " "kawai ya san zamufi sakewa ne apart ɗin mu shine kawai" "shikenan shazim, amma da mun gama wayar nan ku shiga part ɗin innah ku gaishe ta dan Allah " "to" kawai yace dan wallahi kwata kwata bai son ganin tsohuwar, "to sai anjima, in ka shiga kace ina gaishe dasu dan Allah " "to insha Allah zasuji "daga haka yayi rejecting ɗin kiran,number malam ya lalubo bugu ɗaya malam ya ɗauka da Sallama, gaishe da shi noraiz yayi, cikin kulawa malam ya amsa da tambayar shi hanya da su fatima, sunjima sosai suna waya da malam sannan suka yi Sallama, cikin aljihu wando ya maida wayar, sannan ya buɗe motar ya fice, ya nufi part ɗin su ko da ya shiga bedroom ɗin shi ya nufa yayi wanka ya kwanta kan bed, nocking ya ji anayi daga parlor, shiru yayi kamar yana bacci dan ya san bazai wuce noraiz bane, kuma ya san ya zo ne dan su tafi parts ɗin uncles ɗin su, shiyyasa yayi shiru dan bai shirya zuwa wurin kowa ba yanzu, jin shiru yasa noraiz tuna nin koh yayan nashi barci ya ke, barin bakin ƙofar yi ya fice daga gidan, gidan dake kusa da wanda kamal ya aje fatima da sa'ada noraiz ya shiga da Sallama, parlo ne mai girma ya ji furnitures masu kyan gaske, tsit yake ba kowa a ciki, wani ɗan corridor ya nufa ya shiga wata yar ƙofa,nan ma wani ɗan ƙara min parlor ne, shiga ciki yayi da sallama, kyakyawar tsohuwa ce zaune kan carpet jikinta sanye da atamfa ɗinkin riga da zani sai feenah da ke kan sofa kusa da ita fuskar ta duk hawaye jin sallamar norai ne ya sa feenah goge hawayen da ke fuskar ta,zuba ma noraiz ido tsohuwar tayi har ya ƙara so cikin parlorn ya neman wuri ya zauna kan sofa yana faɗin "inawuni innah " amsa mashi tayi da "lafiya, ai nayi tuna nin kaima kafi ƙarfin kazo ka gaishe da ni kamar ɗan uwan ka mara kunya, dan nasan idan ba Ibrahim ya kira shi ba bazai ta ɓa shigowa nan ba saboda aisha ta riga da tasa ya gama raina ni baya ganin mutunci na " "kiyi haƙuri innah yana nan shigowa bacci ya kwanta saboda jiya bai samu yayi bacci sosai ba " "kai da Allah yi man shiru, wane haline kuma na abdulƙadir wanda ban sani ba, itama fatima tafi ƙarfin tazo ta gaishe ni koh" "A'a innah tana tare da sa'ada nasan zasu shigo ne "ta ɓe baki innah tayi tana faɗin "Allah sa" da ammen noraiz ya amsa haɗi da miƙewa yana faɗin" innah zanje part ɗin uncle Ibrahim" bai jira mai zata ce ba ya fice abun shi, da harara feenah ta bishi yana fita tace "kingani koh innah shima noraiz wulaƙanta ni ya ke, dan tunda suka zo ko kallon banza bai yi min ba, da ya shazim ya dizgani a airport dariya yayi shida fatima " "rabu da yan banza, zanyi maganin su ne daga su har uwar ta su, kuma shi wannan mara mutuncin nasan miye maganin sa, bari dai kawunnan nashi su dawo" "yawwa innah shiyyasa nake sonki wallahi " "ai karkiji komai,su dai dawo, zai san dani yake magana, sai dai kuma abun da nake so a wurin ki shine ki kama kanki ki daina son taɓa jikin shi dan nasan halinki da ɗabi'ar banza " "Insha Allah innah na bari bazan sake ba " "Allah ya sa " da ameen feenah ta amsa, suna nan zaune suna fera sa'ada suka shigo ita da fatima ko da fatima ta gaishe da innah cewa tayi" sai yanzu kika ga damar zuwa, ai da kinyi zaman ki baki shigo ba "haƙuri kawai fatima ta bata, ko kallonta bata yiba suka cigaba da fira ita da feenah, ganin haka ne yasa fatima cema sa'ada ta tashi suje part ɗin su aunty kairiyya, tashi sa'ada tayi suka fice zuwa part ɗin uncle ahmad, anan suka samu noraiz shida mahmud,gaishe da mahmud fatima tayi, sannan suka shiga bedroom ɗin mama ( asiya mahaifiyar su mansoor ) suka gaisa tana tambayar fatima ya su ammy, sun ɗan jima suna fira da ita sannan suka tashi suka nufi bedroom ɗin kairiyya. wani matashin saurayi ne ya shigo parlorn da sallama hannun shi riƙe da briefcase, da sauri noraiz ya nufe matashin yana cewa "oyoyo ya mansoor,nayi kewar ka sosai"rungume shi mansoor yayi yana cewa " lil bro saukar yaushe? " " tun ɗazu, ina ta zuba idon ganin ka, ya aiki" shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "alhmdllh,ya su ammy da auta? " muryar fatima sukaji fitowar ta kenan daga ɗakin kairiyya tana cewa "gani anan yaya "juyawa mansoor yayi yana cewa "autar ammy, yan graduation kice tafiyar harda ke"ɓata fuska fatima tayi tana faɗin "ai ni fushi nake da ku kai da ya dr, ko ɗan text message na happy graduation" matsowa kusa da ita mansoor yayi yana faɗin "sorry lvly sis bahaka bane munso muzo har lagos ɗin Allah ne dai bai nufa ba, amma kiyi haƙuri gift ɗinki na nan na ajiye maki"washe baki fatima tayi tana faɗin "tnxs big bro" "to shikenan autar ammy ni zan shiga ciki na watsa ruwa " mansoor ya faɗa haɗi da nufar up stairs,"to sai ka fito "fatima ta faɗa, tashi noraiz da mahmud su kayi suka fice su fatima kuma suka zauna kan sofa suna fira ita da sa'ada. shazim daga wannan kwanciyar bacci yayi awan gaba da shi ba shi bane ya tashi ba sai gab da magrib, yana tashi ya nufi toilet yayi wanka haɗi da alwala,sannan ya shirya ya fito daga bedroom ɗin ya nufi dinning, abinci yaci kafin ya fice daga part ɗin,ya nufi masallacin dake cikin estate ɗin ,ana gama sallah ya fito ya nufi part ɗin uncle ahmad,kairiyya da su fatima ya samu a parlor , gai she dashi kairiyya ta sake yi tana cewa" ya gajiyar tafiya ya shazim " amsa mata yayi da Alhmdllh sannan yace" uncle fah? " yana sama ta bashi amsa, tashi yayi ya nufi up stairs ya shiga wani ɗan ƙaramin parlor, zaune uncle ahmad yake kan carpet, mama na kusa da shi,sallama yayi ya shiga ciki, amsa mashi sallamar sukayi, wuri ya samu kan carpet ya zauna yana gaishe da su amsa mashi sukayi cikin kulawa uncle ahmad na tambayar su malam da ammy,"suna lafiya" uncle ahmad ya ce "masha Allah, kaje wurin Ibrahim?" shazim yace" a'a yanzu dai zan tafi " uncle ahmad yace "to shikenan, bari sai ka ci dinner tukunnan sai ka tafi " "bana jin yunwa uncle yan zu na ci abinci" uncle ahmad yace "to shikenan tashi kaje wurin Ibrahim ɗin " da to shazim ya amsa haɗi da miƙewa ya fice,yana fita bedroom ɗin mansoor ya nufa, zaune ya same shi yana waya, harara ya watsa ma shazim, murmushi yayi haɗi da samun wuri kusa da shi ya zauna yana faɗin"my lover bro wannan hararar ta mi cece" katse wayar mansoor yayi yana faɗin"amma wallahi ka rainani shazim ni nema lover ɗin koh " "eh mana, yaya " "ni nama manta nayi maka magana fushi nake da kai " "kaina bisa wuya minayi kuma lover bro "duka mansoor ya kai mashi ya kyauce "Allah zanyi maganin ka idan har baka daina ce man lover bro ɗinnan ba" " sorry na dai na" "da dai ya fiye maka, kuma ka tashi ni ka bani wuri " "afuwan ya mansoor " juya mashi baya mansoor yayi yana faɗin "ka tashi nace ka bani wuri" hannu shazim ya sa ya riƙe kunnuwan shi alamar ban haƙuri yana cewa"haba ya mansoor dan Allah fa"kallon shi mansoor yayi yace "Uhmm , ya hanya, ya su ammy da malam" "suna nan lafiya " "masha Allah" dafa kafaɗar shazim mansoor yayi sannan ya ce "bro wai miya farune ake ta kiran ka amma baka ɗaga waya wani time ɗin ma akashe, kasan ka ɓata ma su abbah rai sosai " kallon mansoor shazim yayi "yaya su abbah sun ta kura dole sai nayi aure ni kuma yanzu bana da ra'ayin yi" "ƙanina kasan mi? " girgiza mashi kai shazim yayi,alamar a'a, ɗan nisawa mansoor yayi sannan yace "miyasa baka son yi aure yanzu, duk wani rufin asiri na duniya Allah ya baka shi, to miyasa bazaka godema ni'imar da yayi maka ba " kwantar da kanshi yayi saman kafaɗar mansoor sannan yace " yaya bawai bana son auran bane kwata kwata' a'a nafiso su ƙara man lokaci har nasamu wacce take sona nake son ta, amma yaya kowa yaƙi fahimta ta " shafa kanshi mansoor yayi yana faɗin "karka damu bro ni na fahimce ka insha Allah suma su abbah zasu fahimce ka " "Allah yasa yaya" "Ameen "( a kwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin shazim da mansoor, mansoor ya girmi shazim bawai sosai ba, tare suka taso har makaranta tare suka yi ) "tashi muje part ɗin uncle Ibrahim dan nasan ba inda kaje tun da kazo " "nayi baccine shiyyasa " "ok tashi muje "tashi sukayi suka fice direct part ɗin uncle Ibrahim suka nufa, bakin su ɗauke da sallama suka shiga,momy suka samu zaune kan sofa ita da aliyu, da gudu aliyu ya taso yayi hugging ɗin shazim yana faɗin "oyoyo yaya "ɗaga shi sama shazim yayi yana faɗin "haidar ykk,ya school" "lafiya qlu yaya" masha Allah shazim ya faɗa haɗi da sauke shi ƙasa yana faɗin "momy anwuni lafiya " "lafiya lau alhmdllh, ya hanya, yasu ammy da malam " "lafiya qlu Alhmdllh "mansoor yace "momy ina wuni " "lafiya qlu Alhmdllh, ya aiki " "alhmdllh momy, uncle na ciki " "eh yana part ɗin shi" "ok bari mushiga momy " to momy tace sukuma suka nufi corridor dake kallon parlorn ,wani ɗan ƙaramin parlor suka shiga, shiru parlorn yake bakowa sai ƙarar tv da ta ac, mansoor ne yace su zauna may be uncle ɗin na ciki, zama sukayi kan sofa, muryar uncle Ibrahim su kaji daga bedroom ɗinshi cikin faɗa yana cewa "wannan ai maganar banza ce maganar wofi, amma kabani mamaki, to bari kaji tun wuri kasan yan da za'ayi " muryar wani matashi sukaji daga bedroom ɗin yana ba shi haƙuri "dan Allah dady kayi haƙuri, wlh mistake aka samu amma insha za'a dawo dasu, ko yanzu nayi magana da c.p dake chan yace suna nan suna bin ciken idan suka shige da sun samu zasu sanar da ni " "da dai yafi, dan bazan yi asarar million dollars ba a bazan, in ma ban da shashan ci irin na yaran yanzu ina ake samun matsala irin haka ai tun chan ya kamata ka duba bawai sai kun zo nan ba " "sorry dady insha Allah zasu dawo " "Allah ya sa, ina so yanzu daka fita kasake kiran c.p ɗin kaji a wane mataki suke " "to" fitowa saurayin yayi da wani kallon yabi su shazim dake zaune kan sofa sannan ya kama hanyar fita daga parlorn, mansoor ne ya daka mashi tsawa yana faɗin "kayi hauka ne luqman, sa'annin wasan ka ne mu daza kallemu ka wuce kafi ƙarfin ka gaishe da mune " wanda aka kira da luqman ne yace "sorry yaya ban lura da kai bane " "idan baka lura dani ba, baka ga shazim bane ko kafi ƙarfin ka gaishe da shi ne " "a'a" "oya koma ka gaishe shi kafin ranka ya ɓaci " juyawa luqman yayi ya koma cikin parlorn, sai da yaje har gaban shazim sannan ya ce "ina wuni ya hanya " idan har bango na magana to shazim ya amsa mashi gaisuwar, dan yi yayi kamar ma bai san da wata hallita ba wai luqman a parlorn, duk abun da ke faruwa uncle Ibrahim na tsaye bakin ƙofar badroom ɗin shi yana kallon su, sake gaishe da shi luqman yayi still bai amsa ba,gyaran murya uncle Ibrahim yayi, hakan yasa gaba ɗaya suka mai da hankali su kan shi ƙara sowa yayi cikin parlorn yana faɗin "shazim baka ji ana gaishe da kai? " maimakon shazim ya bashi amsar tambayar da yayi mashi sai ma cewa yayi "uncle anwuni lafiya" ganin ya waske ne yasa uncle Ibrahim amsa mashi gaisuwar yanama luqman alama ya tafi da ido , ficewa luqman yayi daga parlorn ( luqman ɗan uncle Ibrahim ne, shine babban ɗan shi sai feenah daga feenah sai sa'ada da aliyu, uncle ahmad kuma mansoor ne babba sai faisal daga faisal sai mahmud sai kairiyya sai salma ) Episode 22_23 Kallon shazim uncle Ibrahim yayi yana cewa "shazim ya su ammyn ku da malam?" "lafiya qalau suke " "to masha Allah, ya gajiyar hanaya " "alhmdllh " "ka shiga wurin innah kuwa? " "a'a, daga part ɗin uncle ahmad nake, amma daga nan chan zan tafi " "haba shazim ai tun da kuka zo chan ya kamata kufara shiga, bawai sai yanzu ba " "haka ne uncle, na ɗan gajine to shine sai na ɗan kwanta " "ah to gaskiya tashi ku tafi,inya so sai ku dawo "da to suka amsa haɗi da miƙewa suka nufi ƙofa, suna fita uncle Ibrahim ya ciro wayar shi daga aljihu dake ringing, picking yayi yanufi bedroom ɗin shi. A bakin part ɗin innah suka tsaya shazim na faɗin " muna shiga da masifa zata tare ni nasani " murmushi mansoor yayi yana cewa "lamarin ka kai da innah ai sai Allah " "ai big bro innar ce ta cika matsala " "kai kuma baka ganin zarau sai ka tsinka " "innar ce ai sai da irin haka " "haka dai kace, wuce mu shiga karka ƙara bata lokaci tace da ka bari sai gobe " dariya suka kwashe da ita yayin da suke shiga part ɗin bakin su ɗauke da Sallama, feenah suka samu kan sofa tana charting a wayarta, tashi tayi zaune tana amsa masu sallamar da sukayi, zama su kayi kana sofa, sai kallon shazim take, shi kuwa tun da suka shigo ya ɗauke kai kamar bai ganta ba, mansoor ne yace" ina innah take? " "yanzu ta shiga ciki " "ok ce mata gamu nan " ta miƙe kenan sukaji muryar innah tana faɗin "dama kunyi tafiyar ku dan bana da lokacin ku yanzu nima"murmushi shazim yayi a zuciyar shi yana faɗin "sarki,baki taɓa shanye raɗa" kamar daga sama yaji muryar innah na faɗin "kayi murmushi mana tun daga mahaukaciya sabon kamu na magana" kallonta shazim yayi batare da yace komai ba, hakan dayayi ne ya harzuƙa ta daman a harzuƙe take "kai ni daina kallona da waɗannan idanun ka, karka cinye ni " da buɗar bakin shazim sai cewa yayi "dagama kin samu ina maki kallon love "riƙe haɓa innah tayi tana faɗin " riƙe kayan ka bana buƙata " "ke dai da kin karɓa " tsaki innah ta ja tana faɗin "sai yanzu kayi lokacin zuwa ka gaishe ni kenan, koko sai yanzu uwar taka tace kazo ka gaishe ni? " "kusan haka, yan zunma sa'a kika ci har kika ganni " "ba shakka mara mutunci, to koh ita uwar taka in tazo bata isa ba tace sai lokacin da ta gadama zata gaishe dani ba, bare kai " "kuma fa hakane, dole ta gaishe da ke kamar yanda ke ma kike gaishe da magabata so ina ganin bawani abun tashin hankali bane"mamaki ne ya kashe innah takasa cewa komi, mi shazim yake nufi,ta shi shazim yayi yana faɗin "big bro ta shi muje bacci nake ji" sannan ya kalli innah yace "asuba ta gari tsohuwa mai ran ƙarfe" sannan yayi gaba abun shi sallama mansoor yayi mata haɗi da bin bayan shazim da harara innah ta raka shi tana faɗin " bauɗaɗɗe kawai maramunci " feenah ce tace innah "wai miyasa ya shazim yake maki haka ne?" "mi yasa fa,ai ba komi bane face abun da uwar shi ta koya mashi, ai zanyi maganin su daga shi har ita dani suke magana" suna fita part ɗin uncle ahmad suka wuce zuwa bedroom ɗin mansoor, zama shazim yayi bakin bed mansoor na tsaye yana waya shazim ne yace " nizan tafi na kwanta naga ka kama waya" "ok sai da safe " ficewa shazim yayi ya nufi part ɗin su, yana shiga ya nufi bedroom ɗin shi kayan jikin shi ya rage ya shiga toilet, bayan minti biyar ya fito ƙugun shi ɗaure da towel, clothes set ɗin shi ya nuf, pajamas ya ciro riga da wando masu taushi ya saka sannan ya nufi wayar shi dake haske alamar kira zama yayi bakin bed haɗi da ɗaukar wayar dan yaga mai kiran shi,majeed ne picking yayi bakin shi ɗauke da sallama " on the other hand majeed yace "mutanen abuja, ya gajiyar hanya " "alhmdllh majeed, ya aiki?" "aiki alhmdllh, ina ka ajiye wayar kane ina ta kiran wayar ka bakayi picking ba " " wlh kuwa majeed, time ɗin da kakira ina bacci ne dana tashi kuma naje part ɗin uncles ɗina ne,yan zu na dawo, ya ake ciki" "dama maganar kayan da mukayi order ne sun iso " "masha Allah, ka duba duk abun da mukayi order sun sako mana shi " "eh na duba, sai dai akwai matsala" "matsala, tami fah? " "ina jin sunyi mistake ne, dan gaskiya kayan da mukayi order basu suka kawo mana ba amma ina tuna nin mistake ne suka samu, amma kakira kaji" "ok to shikenan, amma abun da mamaki " "wlh kuwa nima nayi mamaki sosai, musamman kayan dana gani a matsayi namu " "wane irin kaya ne?" "abun da mamaki, amma bari na turo maka kagani da idonka"ok kawai shazim yace haɗi dayin rejecting, ba'afi one minute ba sai ga saƙo ya shigo wayar, shiga cikin saƙon yayi,yana buɗe saƙon ya ci karo da kayan maye su cocaine, India he ga alcohol iri iri masu matuƙar tsada da haɗari ga lafiya ɗan zaro idanu yayi yana faɗin "ya Allah, miye kuma wannan , daga ina, na waye? " ɗan dafe kanshi yayi, sai kuma chan yayi dialing number majeed tana fara ringing yayi picking "kanaji majeed, kasan mi za'ayi " "a'a saika faɗa " "kawai kusa su a store, ba sai an maida masu ba, ina son na san ko na waye " "to shikenan, amma ya za'ayi da magungunan da suka kusa ƙarewa " "karka damu zan sake ordern wasu, amma waɗannan ku bar maganar su kawai har sai na dawo sannan " "ok to shikenan, sai da safe" "ok mu tashi lafiya" yace sannan yayi rejecting ɗin kiran,tashi yayi yashiga toilet ya ɗaura alawala 2 minute ya fito ya nufi carpet ya shimfiɗa ya kabbara sallah, yana gama mawa ya ɗauki quran, ya shiga karantawa ƙarar shigowar message yaji awayar shi sharewa yayi sai ga wani message ɗin ya sake shigowa bai koma takan wayar ba har sai da ya kammala karatun sannan ya ɗauki wayar ya nufi switch ɗin ɗakin ya kashe light nan take bedside lamps suka kawo,hawa yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe iya waist ɗin shi, sai sannan ya jawo wayar, message ya gani da baƙuwar number buɗa message ɗin yayi,yana gama karan tawa ya danna power yayi switching ɗin ta, adu'a yayi ya shafa sannan ya kashe bedside lamps, ƙara jan blanket yayi zuwa chaist ɗin shi cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi........ Washe gari bayan ya dawo daga masallaci sallar asuba komawa yayi ya kwanta, sai wurin 8:30 ya tashi yayi breakfast bayan ya gama ya nufi part ɗin uncles ɗin shi domin gaishe da su,daya je part ɗin uncle Ibrahim, bayan sun gaisa yake tambayar shi yaje ya gaishe da innah kuwa, ce mashi yayi eh bayan bai je ɗin ba yace eh ne dan ya san cewa zai yi yaje, shikuma bai shirya ma tujararta ba tun da safe, yana fita daga part ɗin bedroom ɗin mansoor ya nufa, yana shiga ya same shi yana shirin tafiya office, gaisawa sukayi, sannan mansoor yace mi zai hana ya bishi su tafi office ɗin tare, bai yi gardama ba, dan shi kwata kwata baya son zaman gida kamar mace, shiyyasa a kullum yake ma noraiz faɗa saboda zaman gida, shiryawa yayi suka tafi tare,sai da yamma liƙis sannan suka dawo, a bakin ƙaramin gate ɗin estate ɗin mansoor ya hango feenah ta fito daga motar wani sauray, riga da wando ne a jikinta tayi rolling da ɗan ƙaramin gyale, sai waige waige take kamar tana tsoron wani ya ganta, kwata kwata bata lura da motar su ba tana sauri ta shiga , kallon ta mansoor kawai yayi har ta shige ciki sannan yace" narasa gane mike damun ya rinyar nan, amma zanyi maganin ta " shazim ne yace "lafiya dai ko bro,kai da wa??" " ni da feenah mana kana nufin baka ganta ba "girgiza kai yayi alamar a'a, sarai ya ganta amma sai ya fake a bai ganta ba, dan shi gani yake kwata kwata babu abun da ya shafe shi da lamarin feenah, tun da iyayen ta suna sane da abunda take, kuma tushen lalacewar ta daga kakarta ne tun da ita ke goya mata baya akan duk abunda take so, so mizai hana tayi abun da taga dama tun da ta samu ɗaurin gindin kakarta da kuma mahaifin ta.ta babban gate suka shiga, sai masifa mansoor yake, shazim na jinshi bai ce komi ba suna shiga ciki part ɗin innah mansoor ya nufa, yana parking yace ma shazim ya fito su shiga su gaishe da innah, shazim yace "gaskiya ni nagaji zan wuce ciki, anjima na zo na gaishe ta kawai " "miyasa bazaka shiga ba, duk fa yau bamu gaishe da ita ba yaka mata ace kazo mun shiga bafa wani jimawa zamuyi ba, dan nasan bawani anjimar da zaka zo, kawai ka fito mu shiga " "nagaji ne bro, ka bari sai anjima " "pls bawani jimawa zamuyi ba "ok kawai shazim yace ba dan yaso,ya so mansoor ɗin ya bari sai anjimar fitowa yayi haɗi da bin bayan shi suka shiga ciki,innah suka samu zaune a parlor mai aikin ta na mammatsa mata kafa,sallama su kayi haɗi da ne man wurin zama,gaishe da su mai aikin tayi, amsa mata sukayi mansoor na faɗin "barka da yamma innah, ya gida " "lafiya lau, ya aiki" "alhmdllh" "shi wannan fanɗararen yafi ƙarfin ya gaishe ni ne " "a'a innah, kin tari numfashin shi ne " "bana ra'ayi ne yau "acewar shazim, hararar shi innah tayi tana faɗin "riƙe kayar ka, bawai ina jiran taka ba" taɓe baki yayi,yana faɗin"dama ance abun da baka samu haɗa shi da baka so " tsaki innah taja ba tare da ta sake cewa komi ba sallamar feenah suka ji,yanzu sanye take da doguwar riga ta material maima kon riga da wando da suka ganta da su ɗazu a bakin gate , amsa mata sallamar sukayi,harara mansoor na watsa mata harara, gaban ta ne ya ɗan faɗin ganin hararar da ya ke jifanta da shi dan ita a sanin ta batayi mashi komi ba, wuri ta samu kusa da innah sannan ta kalli shazim tana faɗin "ina wuni Ya shazim "yi yayi kamar ma bai san da shi take ba,innah ce ta ja tsaki tana faɗin "Allah dai wadar mai wulaƙanta ɗan adam"banza yayi da ita duk da yasan da shi take, sosai sharetan da yayi ya sosa mata zuciya dan har idanunta sun tara kwalla, tana matuƙar son shazim amma sai wulaƙanta ta yake yana share ta kamar bai san daga inda ta fito ba, mai da idanun ta tayi kan mansoor tana faɗin "ina wuni ya mansoor "bai amsa mata gaisuwar ba sai ma hararar ta da yayi,innah ce tace "tofa yau ina ganin ikwan Allah, daga me shareta sai mai harara, kenan kai ma kakoyi baƙin hali irin nasu o'o "tsuke fuska shazim yayi dan ya san ba da kowa take ba face shi, kallon yan da ya tsuke fuska tayi tana faɗin "aikin banza aikin wofi,wai duk dan kar a raina shi" yanzu ɗauke kai shazim yayi kamar bai san dawa take ba, feenah da duk ta sha jinin jikinta, tace ma mansoor "Yaya mi nayi kake hararata " "zaki sani ne"innah ce tace "kai wai lafiya mansoor mi tayi ne" "wlh sai na bata ɗan banzan kashi a gidannan "da buɗar bakin innah sai cewa tayi "ai sai ingani tun da kakoma zalunci" "wai miyasa innah kike haka ne, duk ke ke ɗaure mata gindi take duk abun da ta gadama " "to na ɗaure mata gindi sai aka yi yaya"kallon feenah mansoor yayi yana faɗin "wlh kinji na faɗa maki duk ranar da kika bari na kama ki jikin ki sai ya faɗa maki shashasha kawai"turo baki tayi tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri yaya ni ban san minayi maka ba " "uban waye na ganki da shi yanzu a bakin gate, kinyi shiga kamar ba musluma ba " gaban ta ne ya faɗin, dan bata yi tunanin wani ya ganta ba ,duk dan kar a ganta ne yasa tabiyo ta ƙaramin gate, kenan tanan shima ya biyo kuma hakan na nufin shazim ya ganta,ya salam, ƙatse mata tunani yayi ta hanyar cewa "tambayar ki nake? " kame kame ta fara"am.... imm dama wani class mate ɗina ne "wanka mata mari mansoor yayi, ai ba shiri tayi bayan innah tana kuka, mansoor ne ya ɗaura da cewa "ni zakiyi ma ƙarya,saboda kin rainani, ban hanaki bin wannan ɗan iskan yaron ba,saboda ban isa in faɗa maki kiji ba shine kuka koma haɗuwa waje yana ajiye ki a baya dan kar wani ya ganki ko"fashewa ta sake yi da kuka tana faɗin "dan Allah kayi haƙuri, wlh ba shi bane " hannu mansoor ya kai zai jawota daga bayan innah, kakkare ta innah tayi tana faɗin "wai miye haka mansoor so kake kaji mata ciwo ne, to wai ma miye a ciki dan ta kula shi kai waya san adadin matan da kake kulawa"duk wannan budiri da ake shazim na zaune yana daddana wayar shi hankali kwance kamar baya ɗaki,mansoor ne yace "wlh ko mi feenah tayi laifin ki ne innah, tun da ke ke goya mata baya " "eh na goya mata bayan sai aka yi yaya, da Allah ni ku tashi ku bani wuri" "haka zaki ce innah? " "Eh haka na ce, sai akayi yaya" "to shikenan "shine kawai abun da mansoor ya ce yaja hannun shazim suka fice, da harara innah ta rakasu har suka fice , suna fita ta rufe feenah da faɗa ta inda taje shiga bata nan take fita ba, haƙuri take ba innah akan bazata sake ba insha Allah "wannan kuma ke kika sani, kar Allah ma yasa ki daina, dan ni ba ruwana tun da duk abu da nake faɗa maki bawai yana shiga kunnen ki bane, abun da kikaga dama shi kawai kike yi" "dan Allah kiyi haƙuri innah wallahi bazan sake ba, yan zun ma ban san zasu ganni bane " "karma ki daina, kina ji kina gani zakiyi ma kanki tsiya da kanki, kuma wallahi muddun baki shiga cikin hankalin ki ba, shi wan da kike son kinaji kina gani zaki rasa shi, a banza" "insha Allah na daina " "da dai ya fiye maki ". Shazim suna fita daga part ɗin innah part ɗin su ya wuce shi da mansoor a parlorn shi suka ya da zango, mansoor ranshi duk a ɓace saboda feenah yasha hanata mu'amula da wannan saurayin amma ta ƙi daina wa saboda yasan halin yaron ɗan isaka ne amma bata ji,ga shigar banza iri iri ta iya, ta kasa gane abun da yake nuna mata,shazim ne ya fito daga bedroom ɗin shi ya cire kayan da yasa daga shi sai boxer da vest, dafa kafaɗar mansoor yayi yana faɗin "lafiya, tuna nin mi kake"ajiyar zuciya mansoor ya sauke yana faɗin "wallahi banajin daɗin abun da feenah take, ita kuma innah sai goya mata baya take " "haba bro miyasa zaka damu kanka, duk fa wani abu da take laifin innah ne kuma uncle na gani" "hakane shazim, amma da ban haushi kwata kwata innah bata kyautawa, ace yarinya na aikata ba dai dai ba amma ta hana a tsawatar mata " "gaskiya kam bata kyautawa, amma da Allah ka share da komi ka je ka watsa ruwa " "ok to shikenan "ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi hanyar fita yana faɗin "sai na dawo " "ok sai ka dawo" shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi bedroom ɗinshi, toilet ya shiga bayan 5 minute sai gashi ya fito sanye da bath robe, dressing mirror ya nufa mai ya shafa ma jikin sannan ya fesa turare bakin bed ɗin shi ya dawo haɗi da ɗaukar wayar shi yayi dialing number ammy, tana fara ringing tayi picking, sallama yayi sannan ya gaishe da ita, on the other hand ta amsa mashi cikin kulawa haɗi da tambayar shi ya su innah da su uncle ahmad, amsa ya bata da suna nan lafiya lau, sannan ta tambaye shi sun faɗa mashi dalilin kiran shi da sukayi amsa ya bata da "a'a basu yi faɗa man ba" "to shikenan, ina auta da me babban suna? " "auta na part ɗin uncle Ibrahim wurin sa'ada, mai babban suna kuma na part ɗin uncle ahmad wurin mahmud, ni ka ɗai suka bari " "a'a kaima laifin ka ne, ai da sai ka sauka wurin mansoor " "a'a nafi jin daɗin zama ni ka ɗai ne " "to ai kaika sani " sun ɗanjima suna waya sannan sukayi sallama, malam ya kira suka gaisa har da ummy, shima malam sun ɗan jima suna tattaunawa sannan shima sukayi sallama, kwanciya yayi kan bed ɗin cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, hara sai da mansoor ya zo sannan ya tashe shi suka wuce masallaci saboda anfara kiran sallar magrib, sai da suka tsaya akayi har isha sannan suka fito, daga masallaci part ɗin uncle Ibrahim suka shiga, a part ɗinshi suka same shi, bayan sun gaisa ne yake tambayar sunyi maga da uncle ahmad, amsa shazim ya bashi da a'a "amma mi yasa muke kiran ka ba mu samun ka?? " ɗan sunnar da kai yayi dan bai taɓa tunanin uncle Ibrahim zai mashi magana akan haka ba duk da yasan dole zasu tambaye shi, jin yayi shiru ne yasa uncle Ibrahim cewa "magana nake kayi shiru baka ce komi ba " amsa ya bashi da "bakomi kawai yana yin aiki ne" ɗan jin jina kai uncle Ibrahim yayi duk da ya san yana sane yasa ba'a samun shi a waya, amma a fili sai ya ce "to shikenan Allah ya kyauta gaba" da ameen suka amsa, chanza firar uncle Ibrahim yayi zuwa wata, sun ɗan jima awurin shi dan anan sukayi dinner tare da shi, sai wurin shaɗaya saura suka baro part ɗin,ra buwa suka yi da mansoor kowa ya nufi part ɗin su, shazim ko daya shiga part ɗin su bedroom ɗinshi ya nufa, laptop ɗinshi ya ciro daga cikin bag ɗin shi ya shiga aiki, ba shi bane ya kwanta ba sai ɗaya saura sannan ya kashe laptop ɗin ya nufi toilet ya ɗauro alwala, ya dawo ya kabbara sallah, ya jima yana nafilfilo sannan ya tashi ya nufi bed ɗin shi bayan ya kashe bulbs ɗin ɗakin, kwanta yayi haɗi da jan blanket ya rufe jikin shi, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba dashi.... Episode 24_25 WASHE GARI tun da safe suka fita shi da mansoor, sai da yamma liƙis suka dawo a gajiye, shazim part ɗin su ya nufa, wanka yayi ya ɗan kwanta, duk da ya san bacci a lokacin bai da amfani, amma haka nan ya kwanta saboda ba ƙarmar gajiya ya kwaso ba, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba dashi, ba shine ya tashi ba sai gab da magrib, toilet ya shiga ya sake wani wankan da alwala, sannan ya shirya cikin wani farin yadi, ficewa yayi zuwa part ɗin uncle ahmad wurin mansoor, a parlor ya ci karo da mansoor, juyawa yayi suka wuce masallaci, sai da suka yi har sallar isha tukun suka fito daga masallacin, part ɗin uncle Ibrahim suka nufa, aliyu ka ɗai suka samu a parlor yana kallon cartoon, ya na jin sallamar su ya nufi shazim da gudu, ɗaukar shi shazim yayi yana faɗin "sai kai ka ɗai ina su momy " "tana part ɗin dady "sauke shi shazim yayi yana faɗin "to yayi, tafi ka cigaba da kallon ka " to aliyu yace haɗi da komawa kan sofa ya zauna yan cigaba da kallon shi, mansoor yace"aliyu shazim ka ɗai ka sani ko" "a'a, ai kai kullum muna tare " murmushi kawai mansoor yayi, haɗi da cewa "ok haka ne, ai shazim ɗin zai tafi zai barni da kai, babu ruwana da kai daga yanzu" "sorry ya mansoor, wasa fa nake " "ba wani nan"shazim yace "ƙyale shi kaji, idan zan tafi da kai zan tafi ai, kana zuwa lagos koh" ɗaga mashi kai aliyu yayi yana dariya, mansoor yace "zamu gani ai "aliyu sai tsalle yake zai bi shazim lagos. sama suka wuce zuwa parlorn uncle Ibrahim, zaune yake shi da momy da alama suna tattaunawa ne, sallama suka yi haɗi da shiga ciki, amsa masu sallamar su kayi, wuri suka samu kan sofa suka zauna,gaishe da uncle Ibrahim da momy su kayi, amsa masu gaisuwar su kayi uncle Ibrahim na tambayar su ya aiki, da Alhmdllh suka amsa, ta shi momy tayi ta fice,fira suke jefi jefi, luqman ya shigo kamar wan da aka jeho yana faɗin dady! dady!! ,binshi suka yi da idanu, mansoor ne yace "lafiya kake luqman zaka shigo wuri ba sallama kamar wanda aka jeho" "kullum faɗa nake masa saboda ɗabi'ar banza da ta wofi,ko kafiri bai shiga wuri ba sallama bare kai ɗan muslimi, kiran mi kake man haka?" duƙar da kan shi yayi ƙasa yana faɗin "ba komi" bai son yin maganar saboda su shazim daya gani,mansoor da shazim sun fahimci bai son yin maganar ne saboda ya gan su, fahimtar hakan ne yasa uncle Ibrahim cewa "fice to ka bani wuri" ba musu ya kama hanya ya fice,tsaki uncle Ibrahim yaja yana faɗin "lamarin luqman sai adu'a" mansoor ya ce "narasa mike damun shi uncle, tun da suka fita karatu waje ɗabi'un shi suka canza" "hakane, Allah ya shirya"da ameen mansoor ya amsa, shazim dai na jinsu amma baice komi ba, sai da uncle Ibrahim yace" shazim kayi shiru kamar baka a wurin" "uncle wai ni " "a kwai wani shazim ɗin ne anan bayan kai "murmushi kawai yayi ba tare da yace komi ba, uncle Ibrahim yana lure da shazim duk wani abu idan ya shafi luqman da feenah to fah ba ruwanshi , ko kau mizai same su . mansoor ya ce "uncle bari mu wuce sai da safe, shazim tashi mu tafi" tashi shazim yayi yana cema uncle Ibrahim "sai da safe uncle " "Allah ya tashe mu lafiya"da ameen suka amsa, haɗi da ficewa suka bar part ɗin, tashi uncle Ibrahim yayi ya fita daga parlorn shima,bedroom ɗin luqman ya nufa, tura ƙofar yayi ya shiga, samun shi yayi yana safa da marwa, sai kai kawo yake cikin ɗaki, a hanzarce ya juyo jin an buɗe kofa , ganin mahaifin shi ne yasa ya nufe shi da sauri yana faɗin "dady daman wannan cp dake bincike ne ya kira ni yace sun samu idan suke sai dai basu da tabbaci, amma suna nan suna bincike da sun tabbatar zasu kira ni, ya kira wayarka baka yi picking ba shi ne ya kirani, shi ne nazo faɗa maka ban san wannan ɗan rainin wayau yana nan ba shi da ya mansoor " uncle Ibrahim yace "ok,wayar tana bedroom ɗina ne ban san ya kira ba, naji daɗin jin haka" "dady yanzu zaka mai do man da motata da ka amsa ko" "cewa nayi sai sun bayyana sannan" "pls dady " "kama bar bani haƙuri, dan ba baka zanyi ba har sai na gansu ido da ido tukunnan, kaga daga yau idan na saka ka abu ba zaka sake shashanci ba" "dan Allah dady ka bani, insha Allah hakan ba zata sake faruwa " uncle Ibrahim yace "ni kaga tafiya ta , daga yau sai ka kiyaye " yana gama faɗa ya fice daga ɗaki. Suna fita daga part ɗin uncle Ibrahim, part ɗin su shazim suka nufa, a parlor suka ya da zango, wayar mansoor dake cikin aljihun wandon shi ce ta fara ringing,ciro ta yayi yana kallon screen ɗin wayar baby shine sunan mai kiran shi , murmushi yayi haɗi da picking yana faɗin "sorry beb, yanzu nake shirin kiran ki" muryar mace ce tace "bawani nan, da ban kiraka yanzu ba da ba zaka kirani ba " "haba dear ya zaki ce haka, kin san da ace na gama abun da nake da zan kira ki" "uhmm dama haka zaka ce " "haba dear, pls kiyi haƙuri " tsaki shazim yaja yana faɗin"rainin wayau" hararar shi mansoor yayi yana nuna shi da ɗan yatsa, taɓe baki yayi haɗi da cewa "rainin wayau mana, ka zauna ƙaramar yarinya ta maida ka kamar wani wawa" harara kawai mansoor ya maka mashi ba tare da ya ce komi ba ya cigaba da wayar shi. hannu yasa ya riƙe kunnan shi yana faɗin "afuwan na kama, bazan sake ba pls " ta shi shazim yayi ya fize wayar daga kunnan mansoor yayi rejecting,da kallon mansoor ya bi shi , rasa mi ma zai ce mashi yayi, gaba ɗaya ya kashe shi da mamaki sai kace shi akace ya kama kunne, komawa yayi mazaunin shi ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai wani cin magani yake, matsowa kusa da shi mansoor yayi yana faɗin "ɗan rainin wayau bani wayata" "wallahi bazan ba da ba" "saboda wayar ka ce?" "ko ba tau bace bazan ba da ba, tunda kai zubar ma kan ka aji ba komi bane a wurin ka ba" "dallah ka bani wayata, ina ruwanka koma mi zanyi" "wallahi kaji kunya, wai yarinya zata saka ka kama kunne, kamar wani teddyn wasan ta " "ko ƴar tsana ta ɗauke ni ina ruwanka tunda ba kai ta ɗauka ba" "Allah ma ya kiyaye, wane ita sai dai irinku da kuka raina kanku" "wallahi ina tausayin ka shazim, duk randa so yayi maka mugun kamu, zaka gane baka da wayau" "haba dai, ko zanyi so ba irin naka ba na rainin wayau " "indai da rai zamu gani, zaka zo nan ne ka same kana kuka saboda mace" "Allah ma ya kiyaye, nafi ƙarfin mace tasa na zubar da hawaye, sai dai kai, dan da alama har kuka kake mata" "uhmmm shazim kenan, idan da rai da lafiya zamu gani ai" "ba abun da zaka gani sai alkairi, dan Allah muma bar wannan zancen" "za'a yi shine wata rana " "naji koma yaushe za'ayi shi" kai kawai mansoor ya girgiza yana murmushi ba tare da yace komi ba, sun ɗan jima suna fira daga bisani mansoor yayi mashi sallam ya fice. tashi shima yayi ya nufi bedroom ɗin sa, toilet ya shiga ya ɗauro alwala yayi shafa'i da wutiri yana gamawa ya nufi bed ɗin sa bayan ya kashe bulbs ɗin ɗakin hada bedside lamp, wayar shi da ya ajiye kan bedside drawer ce ta fara ringing , hannu yasa ya jawo wayar yana duba mai kiran shi unknown number ce, tsaki yaja haɗi da rejecting,yana rejecting wani kiran ya sake shigowa "wai waye wannan zai ta kura man ne "ya faɗa haɗi da sake rejecting kiran, sai ga message ya shigo buɗe message ɗin yayi yana karanta wa, yana kammala karantawa , tsaki ya sake ja, kashe wayar yayi baki ɗaya, blanket yaja ya rufe jikinshi baki ɗaya har kai washe gari weekend Momy ce da su sa'ada a kitchen suna haɗa breakfast feenah ta shigo jikinta sanye da pajamas masu santsi white color, sun bi shape ɗin jinkata kanta sanye da black ɗin hula, hugging ɗin momy tayi ta baya "inakwan momy " "lafiya lau, kin tashi kenan? " fatima tace "ina kwna aunty feenah " banza tayi da fatima har sai da momy tace baki ji ana gaishe da ke ne "naji " "ok amsawar ce baki iyawa " kallon fatima feenah tayi tana faɗin "lafiya " tsaki momy ta ja haɗi da mai da kanta kan abun da take, fatima ma nunawa tayi ko ajikinta abun da feenah tayi mata, abu yayi matuƙar ɓata ran sa'ada kasa daurewa tayi har sai da tace "gaskiya aunty feenah abun da kike baki kyautawa " "ni kike gaya ma haka" momy tace "ai gskiya ta faɗi" jan hannun fatima sa'ada tayi sai hura hanci take tace " zu mu fita parlor " "a'a bari mugama aikin " "kizo kawai mu tafi " da hararar feenah ta raka sa'ada "zan kamaki ne yarin ya, zaki san wa kike hura ma hanci" kallon momy tayi tana faɗin "mi kike dafawa ne momy?" "to acici bansani ba " "momy dan Allah ki dai na ceman acici" "bazan dai na ba " bubbuga ƙafa ta shiga yi cike da shagwaɓa, luqman shigowar shi kenan kitchen ɗi yaga feenah na momy shagwaɓa , daga shi sai boxer black color, mangare mata kai yayi yan faɗin"sakaryara banza ji kayan dake jikin ki, ko kunya ba kiji, ko aliyu bazai yi abun da kike ba " "ina ruwan ka dani da zaka dake ni mugu kawai, kai bakaga kayan dake jikin ka ba sai ni azzalumi " "ke dan ubanki ni kike faɗama haka" "eh an faɗa maka " duka yazo kai mata da gudu ta ɓoye bayan momy, ture ta momy tayi tana faɗin" matsa ki bani wuri mara kunyar banza, kai kuma fice ka bani wuri " "haba momy yaza kice haka, rashin kunya take man fa kuma ji kayan dake jikinta " "fice nace ka bani wuri kai bakaga kayan dake jikin na ka bane, ko kunya baka ji da ƙannan ka kake irin wannan shigar kana yawo cikin gida" gwalo feenah tayi mashi "wallahi zan kama ki ne "yana faɗa ya wuce kamar zai tashi sama, kallon feenah momy tayi tana faɗin "kema wuce kije ki canza waɗannan kayan tun kafin ranki ya yi mummunan ɓaci" "haba momy, miye aibun wannan kayan dan Allah " "ki fice nace " "dan Allah momy kiyi haƙuri "banza momy tayi da ita, kama ma momy tayi suka kammala breakfast ɗin,mai aikin momy ce ta shigo ta kwashe flaks ta kai dinning, dawo wa tayi tana faɗin"momy ina na yallabai shazim yake " "gashinan " momy ta faɗa haɗi da miƙama mai aikin, charab feenah ta amshe flaks ɗin daga hannun momy tana faɗin "jeki kawai zan kai masa" "A'a hajiya da kin kawo na kai masa" "nace kije zan kai masa"da to mai aikin ta amsa haɗi da ficewa ta bar kitchen ɗin, fita itama feenah tayi tana faɗin "momy bari na kai masa na dawo" bata jira mi momy zatace ba kawai ta fice. kwance yake a bedroom ɗin sa , cikin bacci yaji ana nocking ƙofar bedroom ɗin sa, farkawa yayi batare da ya motsa ba ya dai buɗe idon shi, sake nocking ɗin kofar aka yi, ta shi yayi ya nufi ƙofar ya buɗe, feenah ce tsaye , kallon sama da ƙasa ya sahiga binta da shi, ganin kallon da yake mata ne ya sata duƙar da kai "inakwan ya shazim "bai amsa mata gaisuwar ba sai cewa yayi"mi ya kawo ki part ɗi na?" "yaya dama momyce tace na kawo maka breakfast " juyawa yayi yana faɗin "ok kina iya ajiyewa kan dinning " "haba ya shazim, dan Allah wai mi nayi maka a rayuwa ne kake wulaƙan ta ni, ko gaisuwa ta baka amsawa" shigewa yayi cikin bedroom ɗin batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba, kamar ta fashe da kuka saboda tsabar baƙinci, tarasa mi tayi ma shazim ya tsane ta a duniyar nan kwata kwata baya ƙaunar ta ya tsane ta, parlor ta koma kan dinning ta ajiye mashi haɗi da ficewa tana sharar ƙwalla, tana shiga part ɗin su ɗakinta ta nufa, kan bed ta faɗa, sai a lokacin ta fashe da kuka. wanka yayi sannan ya fice ba tare da ya zuwa part ɗin uncle ahmad,sai da ya gaishe da mama sannan ya wuce sama wurin uncle ahmad,gaisawa suka gaisa ya nufi bedroom ɗin mansoor,tura ƙofar yayi bakin shi ɗauke da sallama, zaune yake yana aiki cikin laptop , ɗago da kan shi yana kallon shi "ai nayi tunanin sai na zo tuk zaka tashi? " "ai da kazo ɗin " "kunyi waya da a hashim kuwa? "girgiza mashi kai shazim yayi alamar a'a "ya kirani ɗazu yake ce man ya kira ka bai samu ba" "na kashe wayata ne da zanyi bacci may be ya kira ya ji akashe" "to ba mamki, sai ka kira shi" ok kawai yace, wayar shi ya jawo yayi dialing number kairiyya, tana picking yace "ki kawo man breakfast part ɗin mansoor "yana gama faɗa yayi rejecting ba tare da ya tsaya yaji mi kairiyya zata ce ba, kallon shi mansoor yayi yana faɗin "ɗazu fa da su fatima suka shigo mama tace su zo su kaimaka breakfast suka ce sun baro feenah zata kai maka, bata kai maka ba? " "ta kai" "to mi yasa ba ka ci ba?" "saboda bana jin yunwa lokacin " "ba ka jin yunwa ko ko dai bazaka ci ba saboda ita ta kawo, wai mi yasa kake haka ne shazim " "dan Allah ka rabu dani, bana ji yunwa ne lokacin, yanzu kuma ina ji shine kawai" girgiza kai kawai mansoor yayi ba tare da yace komi ba ya mai da kan shi kan aikin da yake, nocking ɗin kofar aka yi, ba da izinin shiga mansoor yayi, kairiyya ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama hannun ta riƙe da tray, amsa mata sallama suka yi, ƙasa ta ajiye tray ta jawo center table ta ajiye gaban shazim tana faɗin "ina kwana ya shazim " da lafiya lau ya amsa mata, tray ta ɗaura kan table ɗin tayi serving ɗin shi,thanks yace haɗi da ɗaukar spoon ya fara cin abincin, ficewa tayi daga ɗakin, a hankali yake cin soyayen arish kamar baya son ci,sai da yaja time kafin ya kammala, wayar shi dake gefan shi ce ta fara ringing, ɗaukar wayar yayi yana duba mai kiran, ammy ce, picking yayi haɗi da sallama yace,om the other hand ammy ta amsa mashi sallamar tana faɗin "mutanen abuja " shafa sumar kanshi yayi yana faɗin "ina kwana ammy" "lafiya lau, ya uncles ɗinka da innah " "suna nan lafiya " "ina gaishe da su, ina auta ta na kira wayar ta bata ɗauka ba " "yanzu haka ta jefata wani wuri " "to idan ka ganta kace ta kirani"da to ya amsa yana faɗin "ammy ga mansoor zaku gaisa "ya faɗa haɗi da miƙama mansoor ɗin wayar, amsa yayi yan kara wayar a kunnen shi, gaisawa su kayi ammy na faɗin "mansoor kayi mana hijira koh " "a'a ammy aikine ke riƙe ni" "dama ku ai baku da wani excuse sai na aiki, yaushe rabon ka da zuwa lagod" "insha Allah ina nan zuwa " "to Allah ya yarda, ka gaishe man da su baban ka" "za su ji insha Allah " "to nagode "ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting, miƙama shazim wayar yayi, amsa yayi yan dialing number, malam ringing ɗaya biyu malam yayi picking, gaishe da shi shazim yayi, cikin kulawa ya amsa mashi yana tambayar ya abuja, sun ɗan jima suna magana daga bisani suka yi sallama, majeed ya kira amma tana ringing ba'a ɗauka ba, mai da akalar kiran yayi kan a hashim, shima tana ringing ba ai picking ba, ajiye wayar yayi kusa da shi, fira suke shiga yi shi da mansoor jefi jefi, har lokacin sallar zuhur yayi, ta shi suka yi suka ɗauro alwala suka fice a main parlor suka ci karo da kairiyya ta fito daga kitchen mansoor ne yace ta shiga part ɗin shi ta kwaso kayan breakfast ɗin da takai ma shazim da to ta amsa haɗi da nufar part ɗin sa, ficewa suka yi zuwa masallaci, da aka gama sallah mansoor yace su shiga part ɗin innah, da sallama suka shiga part ɗin bakowa sai mai akin innah da ta fito daga kitchen jjn ana sallama, amsa masu sallamar tayi tana gaishe su haɗi da cewa, innahr ta shiga sallah yanzu, ok mansoor yace wuri suka samu kam sofa suka zauna, shazim wayar shi da ke cikin aljihu ya ciro yana ɗan daddana ta, fitowa innah tayi hannun ta riƙe da ɗan kwalinta kanta duk furfura an mata kitson zane guda shidda da gake tana da suma ba laifi, kallon su tayi tan riƙe haɓa "ku kuma daga ina da wannan ranar" mansoor yace "ina wuni innah " lafiya lau ta amsa, kallon shazim dake ta aiki dan gwala waya innah tayi tana cewa "shi kuma wanccan ya fi ƙarfin ya gaishe ni ne ko mi"ɗan taɓa shi mansoor yayi "ana magana" ɗago da kanshi yayi yan kallon mansoor yace "ni wai "wani kallon raini wayau mansoor yayi mashi jin tambayar da hake mashi bayan yasan tun da innah ta shigo ya san da shigowar ta, innah ce tace "a'a ba kai ba mu ɗan rainin hankali " murmushi shazim yayi haɗi dacewa "anwuni lafiya, ai ban san kin fito ba ranki ya daɗe "tsaki innah ta ja tana faɗin "da ban wuni ba zaka ganni haka ne " d murmushi a fuskar shi yace"ai ban sani ba " "ai kin banza "shine kawai abun da innah tace, basu wani jima ba suka fice daga part ɗin, da harara innah ta raka su harsuka fice, parking lot suka nufa, motar Shazim suka shiga, estate ɗin suka bari ✨KATSINA ✨ zaune suke kan sofa part ɗin abie,jinkin sanye da riga da skirt na material Aairah tace "abie wai yaushe zamu tafi ne" "yayan ku zaku tambaya" "yaya fa abie " "eh, shi zai kaiku " "amma dai baza mu wuce gobe ba ko, tunjiya mun gama shirya kayan mu " "to wannan ne ban sani ba, idan ya dawo sai ku tunbaye shi " "to abie " wayar abie ce ta fara ringing, miƙa masa Aaimah tayi tana faɗin uncle mustafa ne, amsa abie yayi yana picking, ficewa su kayi zuwa bedroom ɗin a kan bed suka ya da zango, Aaimah tace "Allah ya sa ya ce gobe zamu tafi " "ammen Aaimah , wallahi na gaji da zaman gidan, ko ba komi zaka ga wurare kala da ban da ban " "Allah dai yasa yace goben " Aairah tace "to ameen,harna ƙosa na ganni a can nasan zamu sha ya wo da Ameera, bari na kirata ma" Aaimah tace "eh ki kira ta " wayar ta ta ɗauko tayi dialing number Ameera, ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin sister wai yaushe zaku zo, abba yace yau amma gashi har dare baku zo ba" Aaimah tace"ke ko sallama babu " "bazaki gane bane na ƙosa na ganku ne, yaushe rabon da na ganku" "sai ya abdallah ya dawo shi zai kawo mu ne" "aikuwa kiran shi zanyi ince dan Allah ya kawo ku gobe" nan sukai ta labari kan school, har time ɗin sallar asr yayi, alawala suka yi suka gabatar da sallar suna nan zaune kan carpet mom ta shigo jikinta sanye da gown ta shadda white color anmata kwalli da black ɗin net, hannun ta riƙe da hijab da jaka da alama fita zata yi, gaishe da ita suka yi Aairah na faɗin"mom jar kin shirya" "eh na shirya, ku tashi kuje kitchen baaba larai na can tana aiki ku kama mata " "to mom yau she zaki dawo " "sai dare gaskiya, dan daga gidan granny zan shiga gidan safiya, sai dai dare" Aairah tace "da na san zaki can da tun ɗazo muka shirya muka bi ki " "A'a ko da ku shirya bazan je ko ina da ku ba" "saboda mi mom " "koma saboda mi ku bari wani lokacin kun tafi "hanyar fita mom ta kama tana faɗin "ku taso kuje ku kama mata aikin "da to suka amsa suna tashi suka bi bayan ta, har compound suka rakata abie suka samu tsaye jikin mota yana jiran mom, tare zasu fita zai ajiye ta gidan granny shi kuma zai wuce gidan dadi, a dawo lafiya suka yi masu sannan suka koma ciki, kitchen suka nufa wurin baaba larai, kama mata aikin suka yi suna ɗan fira, sun ɗan jima suna aiki sai gaba da magrib suka kammala, cema baaba larai su kai ta tafi kawai zasu gyara kitchen ɗin da jera abinci kan dinning, da to baaba larai ta amsa haɗi da ficewa ta nufi ɗakin t, Aairah ta kaima su bala na su dinner ɗin Aaimah kuma ta jera kan dinning, sai da suka tabbatar sun kammala duk wani abu da ya dace sannan suka nufi ɗakin su domin yin sallah, bayan sun gama sallah parlor suka dawo zama suka yi suna kallo,har akayi sallar isha, ɗaki suka koma domin gabatar da sallar, sai bayan sallar isha mom da abie suka dawo, dinner su kayi, bayan sun kammala su Aairah suka nufi ɗaki domin bacci ....... Episode 26_27 '''''''''''''''Wayar Aairah ce ta fara ringing, Aaimah cewa tayi "to ni sai da safe, dan nasan indai ya mus'af ne to ke kam ba yanzu ba, duba mai kiran tayi, mus'af ne picking tayi fuskarta ɗauke da murmushi tace "hubby barka da dare " "barkan ki dai my love, ya gida " "lafiya lau "cikin sauƙin soyayya suke wayar, anan mus'af yake sanar da ita next week zai wuce uk ( can ya kuma da karatun ) , Aairah kamar tayi kuka dan taso ace suna ƙasa guda da shi, bata son yayi mata nisa, ta dai yi mashi fatan alkairi sun ɗan jima suna waya daga bisani suka yi sallama. ✨SHAZIM✨ tsaye ya ke bakin window ya riƙe curtain (labule) yana waya da a hashim, fuskar shi a sake suke fira, a hashim na cewa "saboda mansoor ne kawai zan shigo gobe amma da dan kai ne bazan zo ba " "to ko yanzun ma kakar ka shigo tun da ina nan" "kai dai kawai saboda mansoor " "ai da kayi zaman ka " sun ɗan ɗauki tsawan lokaci suna fira sannan su kayi sallama,ya juya kenan zai bar bakin window ya hangi wasu manyan truck's guda ukku suna shigowa cikin estate ɗin da alama ta ƙaramin gate suka shigo,mamaki ne ya kama shi,waɗannan truck's daga ina kuma minene suka ɗauko, ya jima tsaye yana kallon truck's ɗin har suka yi parking a bakin babban store ɗin estate ɗin, mutum uku uku ne su ka fito daga cikin kowace truck, bayan truck ɗin da ke gaba suka nufa, mutum biyu ne suka buɗe truck ɗin suka shiga miƙoma sauran wasu manyan kwalaye suna shiga da shi cikin store ɗin, barin bakin window yayi ya nufi toilet ya ɗauro alwala, sallah ya gabatar ko da ya gama sallah ya jima zaune kan carpet bai ta shi ba, tunani ya shiga yi game da kwalayen da yaga masu truck ɗin na shiga da su cikin store,shin kwalin minene kuma na waye, ya jima a zaune har sai da ya fara jin bacci sannan ya ta shi ya kashe light ɗin ɗakin ya nufi bed ya kwanta, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awan gaba da shi. washe gari kamar jiya feenah ta kawo ma shazim breakfast kamar yan da ya tsallake jiya baici ba haka ma yau baici ba ya nufi part ɗin uncle Ahmad a can yayi breakfast tare da mansoor,fita su kayi shi da mansoor. ✨KATSINA✨ ......... zaune su ke kan dinning suna breakfast, kallon abie Aaimah tayi tana faɗin "abie dan Allah idan zaka je gidan dadi ka tafi da mu" "safiya ce yanzu ku bari sai da yamma sai kuje " Aairah tace "dan Allah abie, muna so ne muyi mata wuni "girgiza kai mom tayi tana faɗin "ku shikenan tun aka ce ba school daga nan ƙafa fuwan ku suka dai na zama wuri ɗaya " "ba haka bane mom mun jima ba muje gidan ba ne " "ba ma kunjima baku je ba, ina tunanin ko ranar friday kuje gidan" Aaimah tace "dan Allah dai mom "abie ne yace "kuyi sauri ku shirya " haɗa baki sukayi wurin cewa "yawwa abie mungode "da sauri suka bar dinning area suka nufi bedroom ɗin su. abie ne a parlor tsaye yana jiran su Aairah , mom ce ke sau kowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya black color, wurin abie ta nufo tana faɗin "ba su fito ba ko " "eh kinsan su da shiririta, duk ta ƙare tafiya zanyi idan ya so daga baya mudi ya kai su" "afuwan abie ga mu nan" cikin sauri suke taka stairs case ɗin, sanye su ke da hijab har ƙasa onion color ,ƙara so wa su kayi, kallon mom abie yayi yace "sai mun dawo "a dawo lafiya tayi masu haɗi da juyawa ta nufi kitchen, fita su kayi abie na gaba suna bin shi a baya har compound, motar su ka shiga, Aaimah na gaba kusa da abie yayin da Aairah take baya, fira suke cikin kwanciyar hankali har suka iso gidan dadi,horn abie yayi a bakin gate mai gadi ne ya leƙo ganin motar abie yasa shi komawa ciki da sauri,ya buɗe mashi gate, ya shiga ciki parking lot ya nufa, sai da ya gama dai daita parking ya kashe motar Aairah ce ta fara fitowa sannan sai Aaimah, jiran abie su ka yi har ya fito su ka shiga cikin gidan tare,cikin parlor su ka shiga suna sallama tsit parlorn yake babu kowa,wuri abie ya samu kan sofa ya zauna har zasu nufi ɗakin Aunty Rabi sai gata ta fito tana amsa masu sallamar da su kayi, gaishe da ita su Aairah su kayi da fara'a a fuskar ta amsa masu sannan ta nufi wurin abie "yaya ina kwana " "lafiya lau, ya gidan " "Alhmdllh" "mama na ciki ne?" abie ya tambaya "eh tana ciki " "bari na shiga mu gaisa "da to Aunty Rabi ta amsa, ta shi abie yayi ya nufi bedroom ɗin dadi, zaune take kan sallaya ta gama sallar walha tana adu'a, zama abie yayi gefan gadont har sai da ta gama adu'a, waigowa tayi tana kallon abie ta ce "Muhammad kai ne tafe " "eh mama, ina kwana " "lafiya lau, ya su kubra " "suna nan lafiya, tana gaishe ki " "ina amsawa"su Aairah ne su ka shigo da gudu su ka nufi dadi suna faɗin "dadi munyi kewar ki" basu ƙarasa ba abie ya dakatar da su da faɗin "lafiyar ku lau kuwa,za ku wani nufe ta da gudu hak, salan ku danne mata ƙafafu fa bayan kun san fama take dasu, Allah yasa in ƙara ganin irin haka " ya faɗa cikin faɗa, tsaya wa su kayi suna kallon dadi kamar za su yi kuka dadi tace "a'a da ka barsu ƙafafu ai sunyi lafiya ba abun da zasu man" "kar kice haka mama,ji fa yanda suka nufe ki da gudu, waɗannan yaran wani lokacin jinsu su ke kamar wasu ƙananun yara" "duk da haka dai da ka barsu, ku zo nan"dadi ta faɗa tana miƙa masu hannu, matsawa su kayi kusa da ita su ka zauna "inakwna dadi " "lafiya lau, ya gida " "lafiya lau" "masha Allah" fira su ka shiga yi da dadi, abie dai na zaune yana jin su, tashi yayi yana faɗin "mama ni zan wuce " "zauna ina son magana da kai" komawa abie yayi ya zauna yana faɗin "to Allah ya sa lafiya" "lafiya lau" ta faɗa tana kallon su Aairah ta ce ku ɗan bamu wuri " da to suka amsa haɗi da ta shi suka fice, dadi tace " dama magana ne akan ɗana, tun ranar da nayi maku magana kai da mustafa ban sake jin wani ya ce komi ba dangane da maganar " ɗan nisawa abie yayi sannan ya ce "haka ne mama, naje har garin na ku, amma ban samu wanda yace ya san inda ya koma ba, an dai ce man a kwai wani abokin baban sa da suke kasuwanci tare, amma yanzu baya garin, lokacin da bai da lafiya babban ɗansa yazo ya tafi da shi, sun dai faɗa man ɗanna sa yana kaduna da zama"hannu dadi ta ɗaga sama tana faɗin " ya Allah, Allah ka bayyanar da shi, hankalina ta shi yake duk lokacin da nayi mafarkin habiba,ban riƙe amana ba " ta faɗa hawaye na sauka a fukar ta,lallashin ta abie ya shiga yi, hannu yasa ya share mata hawaye yana faɗin "ki dai na kuka mama, insha Allah za'a gan shi, ki daina cewa ba ki riƙe amana ba Allah yaga niyyar ki" "Muhammad dole na ce haka, amanar yaron nan ta bar man , da ace da ubansa ya nuna bazai bar man shi ba na cigaba da kula da shi ina ziyartar shi, amma sai na fita batun shi, kaga kuwa ban kyauta ba " "kiyi haƙuri komai zai wuce da izinin ubangiji, za muyi iya bakin ƙoƙarin mu ganin mun samu inda yake " "to Allah ya yarda " "Ameen " abie ya ce "Muhammad wai ya jikin abokin ka, kwana biyu ba muyi waya da safwan ba da mahaifiyar shi , ban kuma tambaye ka ba " "jiya munyi waya da safwan, ya sanar min an ma kusa sallamar shi , ya nemi alfarmar a bar shi can wurin su" "ai gara yayi zaman shi can, ko dan saboda azzaluman mutanen nan " "gaskiya a gani na gara ya dawo nan, har Allah yasa memoryn shi ya dawo" "to Allah ya ƙara sauki , amma kana ganin idan ya dawo ƙasar nan mutanen nan zasu barshi, baza su cigaba da bibiyar rayuwar shi ba " "haka ne muddin suka san yana raye baza su ƙyale shi ba,ko da nace ya dawo nan bawai zai koma can bane, a nan zai zauna tare da mu har memoryn shi ya dawo ya tuna da iyalan shi,ta hakan ne za mu iya samun sa'a akan su, amma idan yana can ba lallai ne ya iya tuna baya ba " "gaskiya hakan shi ya fi, dan ya ji jiki da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi, kuma yan da ya manta da abun da ya faru za su iya ƙara cutar da shi muddin ya koma " ɗan nisawa abie yayi yace "haka ne, shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun ƙare shiyyasa suka samu galaba a kan shi har su ka kashe shi" "insha Allah , Allah zai toni asirin su" "Ameen, burina kwai ya dawo cikin hayyacin shi, ya tuna da baya " " ameen, Allah ya bashi lafiya " da ameen abie ya amsa, sun ɗan jima suna tattaunawa akan abokin abie, daga baya yayi ma dadi sallama, parlor dadi ta nufa wurin su Aairah da Aunty Rabi. ✨Abuja✨ Zaune ya ke kan carpet a parlor yana aiki a laptop, sanye yake da short black color iya gwiwar sa, sai t_shirt ita ma black color, wayar sa da kan hannun sofa ce ta fara ringing , jawo ta yayi haɗi da du ba mai kiran, murmushi yayi ganin A hashim, picking yayi tun kafin yace wani abu A hashim yace " hey man gani a bakin gate ɗin estate, kasan halin securityn ku da ɓakar tambaya " "kai kuma tambayar ce baka so?" "ni dai ka kira su bana son surutun tsiya" "ai kuwa sai dai kai ta tsayuwa, dama ba kace wurin mansoor ka zo ba, to mi ya hana baka kira mansoor ɗin ba, shi sai ya kira su " "ok dan na kira ka shine zaka ɓata man lokaci, Allah ko ka kira su su barni na shigo ko na koma in da na fito " "yo ka kuma "kashe wayar a hashim yayi ba tare da yace komai ba, number ɗaya daga cikin security ya kira yana faɗin "ɗan rainin hankalin yana iya ko mawa " picking security yayi yana faɗin "good evening sir"ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace "friend ɗi na na waje ku bar shi ya shi " "ok sir "security ya faɗa, rejecting kiran yayi, aikin sa ya ci gaba. security ne ya nufi motar A hashim da ke bakin main gate , baƙar mota ce ƙirar ferrari 250 ta sha tinted, security na ƙara so wa, hannu ya sa yayi nocking window motar , sauke glass a kayi a hankali, arba nayi da kyakyawar fuskar ( DR ABDALLAH MUHAMMAD HASHIM , A HASHIM, BI MA'ANA YA ABDALLAH ) sanye yake da farin yadi, ya sha ɗinkin zamani, kallon security yayi yace"barka da aiki" "alhmdllh, dama yallaɓe shazim ne yace ka shigo" ok kawai ya abdallah yace, reverse yayi ya nufi cikin estate ɗin, direct part ɗin uncle ahmad ya nufa, parking yayi a parking lot,dai daita parking yayi, wayar shi ya ciro daga aljihun gaban rigar shi number mansoor ya lalubo haɗi da dialing, bugu ɗaya mansoor ya ɗauka yana faɗin "ka iso ne , kana bakin gate" "gani a parking lot na shigo ciki" "ok, ai da ka shigo " "ka fito dai mu shiga tare" "ka ji ka sai kace estate ɗin ba ƙon ka ne, gani nan zuwa " ok ya abdallah yace haɗi da yin rejecting,fitowa yayi daga cikin motar ya jingina da ita yana jiran isowar mansoor, bayan kamar seconds goma sai ga mansoor ya fito, parking lot ya nufo wurin shi,yana iso wa suka yi hogging ɗin juna cike da farin cikin haɗuwa da juna mansoor ya ce"barka da zuwa, ya KT" "KT alhmdllh yasu abbah da mama " "lafiya lau suke, kwana da yawa" ya abdallah yace "alhmdllh " "ka kira shazim kuwa?" mansoor ya tambaya, ɗan ya taine fuska ya abdallah yayi yana cewa "rabu da ɗan rainin wayau kawai"murmushi mansoor yayi yana cewa "ai kun fi kusa, da man can ku sababbo ne,sai in baku haɗu ba, mu shiga daga ciki ku gaisa da mama mun tsaya a waje muna ta surutu"ok ya abdallah yace, ciki suka nufa,main parlor suka shiga bakin su ɗauke da sallama, kairiyya ce da su fatima a parlor, jin sallamar su ya sa su wai gowa, ware idanu fatima tayi,tana faɗin "ya dr a abuja" da gudun gaske ta nufi ya abdallah zata yi hugging ɗin shi tana faɗin "ya dr a abuja, un believable "tare ta mansoor yayi yana faɗin "yau ina ganin ikwan Allah, hugging ɗin sa za kiyi a gaba na "duƙar da kai fatima tayi tana faɗin "a'a yaya nayi missing ɗin shi ne sosai"bin ta da wani kallon mansoor yayi yana faɗin" to sannu " ya abdallah ne yace" rabu da shi kawai fatima " ma tsowa tayi kusa da shi batare da tayi hugging ɗin shi ba tace "ya dr, nayi mamki sosai, dama kana abuja shine ko ka faɗa man zaka zo bayan ka san ina abuja " "sorry fatima , na ƙi faɗa maki ne dan nayi surprise ɗin ki, ya kike " "lafiya lau yaya, amma a nan zaka kwana ko? " "a'a, anjima zan tafi "bubbuga ƙafa fatima ta shiga yi "haba dan Allah yaya, gaskiya nan zaka kwana" muryar kairiyya su kaji tana cewa "watao ya abdallah fatima kawai ka gani ko, har muke gaishe da kai ni da sa'ada baka ji ba " murmushi yayi "no ba haka bane kairiyya, ya kike ya kwana da yawa" "lafiya lau alhmdllh, ya hanya " "Alhmdllh " "ya abdallah nima kenan baka ganni ba ko"sa'ada ta faɗa tana turo baki "sa'adatu sa'ar mata, ya gida" "lafiya lau ya kt da su mom" "suna nan lafiya " mansoor ne ya ja hannun shi yana faɗin "mu shiga ciki ka zauna, idan ka biye masu za ku kwana ne a tsaye "bin bayan mansoor yayi har cikin parlor, zama yayi kan sofa, kusa da shi fatima ta zo ta zauna, sai sakin murmushi take kamar gonar auduga, ba ƙaramin farin ciki tayi ba da ganin abdallah ( su fatima ba zama, yau gata ga ya dr ) ya mansoor ya ce "sa'ada shiga kikira mama "da to ta amsa haɗi fa nufar bedroom ɗin mama, ta shi kairiyya tayi zuwa kitchen "ruwa da lemu ta kawo mashi " sake komawa kitchen ɗin tayi sai gata ta fito ɗauke da wani bowl ci ke da yankakun fruit ta ajiye gaban shi, tnxs yace haɗi da ɗaukar ruwa ya sha,fitowa sa'ada tayi mama na bayan ta har suka iso parlor, zama mam tayi kan sofa,"abdallah yau kai ne a garin namu " "eh mama, ina wuni, na same ku lafiya" "lafiya lau abdallah, ya su momyn ku da uncle ɗin ka " "lafiya lau su ke " " masha Allah " ta shi mama tayi ta koma ɗakin ta, kairiyya ma tashi tayi ta dalilin kiran wayar ta da a kayi, ya rage parlorn daga mansoor, abdallah, fatima da kuma sa'ada, sai zuba mashi fira fatima take wani ya bata amsa wani kuma yayi murmushi, sun ɗan jima tare da su fatima har aka fara kiran sallar magrib, sannan su ka shiga ɗakin kairiyya do min gabatar da sallah su kuma suka nufi masallaci,a can ya abdallah su ka haɗu da shazim, yi yayi kamar ma bai gansu ba, murmushi kawai mansoor yayi yana girgiza kai, ya san shazim yana wannan fushin ne saboda Abdallah , bayan an sallame sallah, suka fito daga masallacin,tsayawa su kayi har sai da uncle ahmad da uncle Ibrahim su ka fito abdallah ya gaisa da su, suna tambayar shi su mom da abie "suna nan lafiya " uncle ahmad ya ce "masha Allah, ya uncle ɗin ka " "yana nan lafiya " "ina gaishe da shi "uncle ahmad yace, tafiya su ka yi shi da uncle Ibrahim, sai a lokacin abdallah suka gaisa da shazim,ta fiya suke shazim na faɗin "ai nayi tunanin tun tuni ka tsufa da komawa gidan uncle" "ɗan rainin wayau ai ba dan kai na shigo ba" "hmmm koma dai miye, sannun ka da zuwa, ya hanya " "yawwa, Alhmdllh, ya kwana biyu " "Alhmdllh" ya faɗa a dai dai time ɗin da su ke kawowa part ɗin su shazim , ciki su ka shiga ba kowa a parlor,dama shazim ne ka ɗai ke zama part ɗin,noraiz da man tun ranar da suka zo ya koma part ɗin uncle Ahmad da zama, direct sama su ka nufa part ɗin shazim, a parlor su ka ya da zango, abdallah na cewa "wai shazim yau she zaka je katsina " "zanje insha Allah, amma saboda mom da abie zani amma ba dan kai ba " "ya kamata dai, har yanzu fa mom bata sanka ba, gara ma abie kun taɓa haɗuwa sau ɗaya" mansoor ya ce "gaskiya baka kyauta ba, ace duk tsawan shekarun nan baka taɓa zuwa katsina ba, gaskiya nayi mamaki" shazim ya ce "to ni dai ya isa haka kar ku cinye ni, katsina dai ce ko to zani inasha Allah " Allah ya yarda, suka faɗa, fira su ka shiga ta yaushe gamo, sai da aka kira sallar isha sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, bayan sun fito daga masallaci part ɗin uncle ahmad su ka nufa, suna tafiya shazim yace "amma zaka kwana nan ko" "a'a komai dare sai na koma gidan uncle " "pls ka kwana nan" "sai ranar da kaje katsina sannan zan kwana nan" shazim ya ce"kai ka sani kuma wannan, kar Allah yasa kwana " time ɗin da su ke shiga cikin main parlor, kamar ɗazu ma fatima da sa'ada su ka samu a parlor suna kallo,sallama su kayi, amsa masu sallamar su kayi , sama mansoor ya wuce ya bar su a parlor "ya dr har na yi tuna nin ka tafi" fatima ta faɗa "ina nan ban tafi ba" "zaka kwana nan ɗin" "a'a yanzu zan tafi " "dan Allah ya dr ba dan ni ba " sa'ada ma tace "pls yaya,mi yasa ba zaka kwana ba " "ba komi sa'ada " fatima tace "pls ya shazim kasa baki dan Allah ya kwana" " idan ya kwana wani abun zai maki ne? " girgiza kai fatima tayi tana faɗin "a'a kawai dai naga mun daɗe ba mu haɗu ba " " to tun da babu abun da zai maki karki damu mutane" kwal kwal fatima tayi da idanu alamar kuka, kallon shazim abdallah yayi yana ta ɓe baki yana faɗin "kar ki damu zan dawo gobe insha Allah " "pls ka kwana dai dan Allah" "shikenan fatima zan kwana saboda ke " taɓe baki shazim yayi yana faɗin "aikin banza " abdallah ya ce "wannan kuma kai ta shafa, ɗan rainin wayau " tashi fatima tayi su ka je kitchen ita da sa'ada, "wallahi kaji kunya wai fatima zata saka kwana " "ina ruwan ka kuma " tsaki shazim yana faɗin "girma dai ya faɗi" "ya daɗe bai faɗi ba" mansoor ne ya fito "ina ta jiran ku shigo, naji ku shiru" ta shi su kayi su ka bi bayan mansoor ba tare da sun ce komi ba, a parlorn shi suka zauna, fira suke cikin kwanciyar hankali, nocking su kaji, mansoor ne yace wanen,"fatima ce yaya, " ok shigo kawai mansoor ya faɗa, turo ƙofar su kayi ita da sa'ada kowace hannun ta ɗauke da tray, kan center table su ka ajiye fatima na faɗin "ya dr ga dinner "tnxs abdallah yace, ficewa su kayi ita da sa'ada, mansoor ne yayi serving ɗin su. kan carpet su ka zauna suna cin abinci, da suka gama mansoor ya kira fatima ta zo ta kwashe dishes ɗin, fira su ka ɗan taɓa, sai wurin 9:30 su ka yi mansoor sallama su ka nufi part ɗin su shazim, suna tafe suna fira,suna kawo bakin part ɗin su shazim, mota ce shararo da gudu ta shigo estate ɗin ta ƙaramin gate,bin motar su kayi da kallo har tayi parking a part ɗin uncle Ibrahim, mace ce ta fito daga motar, jikin ta sanye da hijab har ƙasa,fuskar ta da face mask ,cire face mask ɗin tayi, tazo ta gaban su zata wuce,taɓo shazim abdallah yayi yana faɗin....... Episode 28_29 ..................... Taɓo shazim Abdallah yayi yana faɗin "dude wannan ba ɗiyar uncle Ibrahim bace feenah" yayi maganar yana nuna ma shi ita lokacin da zata shiga part ɗin su, sauri kawai take bata ma lura da su ba kallon sosai shazim yayi, sai a lokacin ya gane ta , ce wa yayi "ita ce, wani abun ne? " girgiza ya Abdallah yayi yana faɗin "amma daga ina take a wannan lokacin, sai kace ba mace ba " amsa shazim ya bashi da "sai ka bita ciki ka tambayeta, tun da ka fara aikim jarida ban sani ba " murmushi ya Abdallah yayi yana cewa "kai fa matsalar ka ke nan, daga tambaya sai ɓakar magana" shazim ya ce "ai kai ne da shiga abun da ba ruwan ka, ni ina zan san daga ina take " "dole nai magana, naga ƙanwar ka ce" "duk da ƙanwa tace, ban san daga ina take ba a wannan lokacin ba, kuma iyayen ta suna sane" ya faɗa haɗi da jan hannun Abdallah yana faɗin "dan Allah ma wuce mu shiga ciki, kasa mun tsaya muna maganar da bata da amfani "ciki su ka wuce,a bedroom ɗin shazim suka yada zango , zama Abdallah yayi kan bed, shazim kuma ya shiga toilet,Abdallah wayar shi ya ɗauka yayi dialing number uncle, ahmad bugu biyu ya ɗauka, tun kafin Abdallah yace wani abu uncle ahmad yace "Abdallah lafiya baka dawo ba har yanzu " "a nan zan kwana ne uncle " "ok to shikenan, sai da safe" "Allah ya ta she mu lafiya" da ameen uncle ya amsa, rejecting ɗin kiran Abdallah ya yi, fitowa shazim yayi daga toilet jikin sa sanye da bath robe , clothes set ɗin shi ya nufa, pajamas ya ɗauko ash color ya sa, ta shi Abdallah yayi shima yayi wanka, pajamas shazim ya ɗauko mashi white color ya sa kwanaciya su kayi suna fira sama sama har bacci yayi awan gaba da su. washe gari tare da mansoor su ka dawo part ɗin daga sallar subhi fatima da sa'ada ne su ka kawo masu breakfast. ✨LAGOS✨ EKO zaune su ke a reception maryam ce ta kalli hidaya tana faɗin "wai har yanzu dr jikin ne yasa bai zo hospital ba tsawan wannan kwanakin" ɗan nisawa hidaya tayi sannan tace"maryam nima ban sani ba, gashi ina kiran shi bai taɓa ɗauka ba, amma ina tuna nin dan yaga baƙuwar number ne yasa bai ɗauka" maryam tace"ba mamaki, may be shima yana cikin mutanen da basu ɗaukar baƙuwar number, Allah dai yasa lafiya, kwana biyu da bai zo ba ameen " hidaya tace "har nayi tunanin tambayar dr kabir sai kuma na fasa, kar yayi tuna nin wani abu " "a'a da kin tambaye shi, ba abun da zai yi tunanin, tun da yasan dr boss ɗin ki ne kina da right ɗin da zaki tambayi lafiyar shi " "haka ne kuma, idan naje office ɗin shi anjima zan tambaye shi naji, wallahi duk na damu da rashin shi kwana biyu,fata na dai ace yana lafiya" "insha Allah lafiya lau yake " "Allah ya yarda " da ameen maryam ta amsa, canza firar su kayi zuwa wata, har lokacin da zasu fara aiki yayi kowa ya tashi ya nufi aikin gaban sa, hidaya tattara files ɗin patient tayi ta nufi office ɗin dr kabir, bakinta da sallama ta shiga, zaune yake yana du ba wasu paper's, gaishe da shi tayi tana faɗin "dr ga files ɗin patient, za su iya fara shigowa " eh ya bata amsa,haka ta shiga tura mashi patient har lokacin sallah yayi, da katawa yayi ya nufi masallaci domin yin sallah, sai da ya dawo daga masallaci hidaya ta same da tambayar dr shazim, cewa kabir yayi "a fuwan ban faɗa maki ba, yana abuja ne wurin uncle's ɗin shi, shiyyasa ki kaga kwana biyu baya zuwa, amma ba kin amshi number shi ba ai da kin kira shi " "eh, idan nakira ne baya ɗauka " "gaskiya ba zai ɗauka ba dan ba kasafai yake ɗaukar baƙuwar number ba ba, amma nasan insha Allah next week zai dawo " "to Allah ya kaimu nagode " "ba komi "dr yace, ficewa tayi daga office ɗin ta koma reception wurin maryam, sanar da ita tayi yanda su kayi da dr kabir, maryam tace "dama duk yawan aikin da dr yake da shi, har yana iya barin garinnan da sunan ziyara ba aiki ba " "to aiko gashi nan " hidaya ta faɗa, maryam tace "wai nikam na tambaye ki mana?" "ina sauraron ki" hidaya ta faɗa "kin kuwa tura mashi text ɗin da muka yi magana da ke " "na tura mashi ma" "kai aikuwa ina ganin shine dalilin da yasa da ki ka kira shi bai ɗauka ba" "a'a gaskiya, saboda da number mama na kira shi, kawai dai baya ɗaga baƙuwar number ne" "Allah dai yasa ya karanta " " zai yi wahala ace bai duba ba " "haka ne " "kar ki damu, ki cigaba da tura mashi nasan wataran zai du ba " "to Allah ya sa " da ameen maryam ta amsa, tashi su kayi suka nufi office ɗin da suke zama, suna shiga tar kacen su su ka haɗa domin lokacin tashin su yayi. ✨KATSINA✨ Abie ne da uncle mustafa a garden suna tattaunawa game abokin abie da za'a sallama daga asibiti zai dawo nigeria, uncle mustafa ne yace "yau she safwan ɗin yace zasu sallame shi" "yace man next week su ke sa ran a sallame shi " "to Allah ya kai mu next week ɗin" ameen abie yace " amma yaya kana ganin ko a nan baza su iya bibiyar shi ba " "insha Allah baza su taɓa sanin yana raye ba, har sai lokacin da asirin su zai tonu, su duk a tunanin su ya daɗe da mutuwa " "Allah dai ya toni asirin mutanen nan, sun cutar wannan bawan Allah kamar mi, da da ƙarar kwana da tuni sun kashe shi " "haka ne yaya shi da yake mahaifin safwan kwanan shi sun kare ,ai sun kashe shi" "kisa na wulakanci ma ,amma ai Allah na nan zai toni asirin su tun a nan duniya kafin kiyama " "haka ne kam " Abie tace"burina bai wuce naga memoryn shi ya dawo ba,da a ce lokacin da na mai da shi China na rika bibiyar iyalin shi da ko baya nan zan iya hada hujjujin da zan maka su court ,amma yanzu dole sai yana cikin hayyacin shi zan iya hada duk wata hujja da nake nema " "haka ne kam dole sai ya dawo cikin hankalin shi ,Allah dai ya bashi lafiya" "shiyyasa nace idan an sallame shi zan dawo da shi Nigeria,saboda dole sai a nan zai iya ganin abun da zai sa yatuna da baya har a samu memory shi ya dawo" "haka ne ,amma yaya idan su ka dawo ina zasu zauna" "shi kadai zai dawo ban da safwan da mahaifiyar shi ,saboda mahaifiyar shi ta tsorata sosai ,ko da safwan din yace zai zauna bazata bari ba " "ai dole ta tsorata ,baji bagani aka kashe mata miji,kisan wulakan ci" Su Aairah ne su ka shigo garden din dauke da bowl din fruit da ruwa da lemu ,kan table din dake wurin su ka ajiye masu ,suna gaishe da uncle mustaf ,amsa masu yayi yana fadin "anata hutu ko ,ya hutun " da Alhmdllh su ka amsa hadin da barin garden din ,kallon abie uncle mustafa yayi yace"yaushe za su yi joining university ne ,naji wasu makarantun har sun fara lectures " abie yace "Abdallah nake jira ya dawo daga abuja ,komai na makarantar su yana hannun shi " "gaskiya ya kamata ya hanzarta ,yaushe ya ce zai dawo " "yace man dai next week za su dawo shida Ahmad din ,na san ya san wasu makarantun sun fara lectures" "ya kamata gaskiya ya hanzarta " abie yace "su matsalar ne sun nace ne akan dole sai sun tafi wani gari ba su son nan" "da gaskiyar su yaya ,fara su fita inda idanun su zai kara budewa ,ko ba komai zasu iya mu'amula da mutane " "haka ne ,ni ba komi yasa bana son su yi Mesa dani ba ,kasan halinsu wani lokacin ba jin magana suke ba" "haba yaya duk rashin jin su sun kai ihsan ne ,amma haka nan na turata jos karatu duk da a gidan kanwar mahaifiyar ta take da zama ,ka bisu da adu'a kawai ba abun da zai faru da su insha Allah, idan ma tsoron tura su kake inda ba su san kowa ba ,ai ga abuja sai su zauna gidan Ahmad ,kaga duk lokacin da su ka tashi lectures gida zasu dawo" "hakan dai ne zai fi ,dan zaman hostel ne ban so ,zan kira Ahmad din inyaso kafin su zo sai su nema masu admission" " to shikenn yaya hakan yayi,Allah ya taimaka " ameen abie yace ,canza firar su kayi zuwa wata ,sun jima a garden din suna tattaunawa har sai da lokacin sallah yayi ,sannan su ka tashi su ka nufi masallaci . ✨ABUJA✨ Momy ce ta fito daga bedroom dinta ,numfashi taja a zuciyar ta tace "wannan kamshin daga ina kuma " kitchen dan tana kyautata zaton daga canne , tana tun karar kitchen kamar ana huro mata mashi , tun a bakin kofar kitchen take fadin "wai yau mi ake girka mana ne ,gida duk ya cika da kamshi " ta fada yayin da take Shiva cikin kitchen din ,turus ta tsaya ganin fatima da sa'ada sai kai kawo a kitchen aiki kawai suke bilhakki "to fah kace yan mata na ne a kitchen,duk su ka ciki gida da kamshi, ashe yau zan ci girkin manya " fatima tace "yawwa momy daman neman mai testing muke " "to a zubo man, naji ƴaƴan nawa sun iya girki" sa'ada ta shiga buɗe ma momy warmers, bin abinci da kallo momy tayi tana faɗin "kai masha Allah, wannan ko bakai testing ba kasan ya yai daɗi " plate da serving spoon sa'ada ta ɗauko ta zuba ma momy fried rice da cos low spoon ta sa mata haɗi da mi ƙa mata tace " momy gashi "amsa momy tayi ta samu wuri kan kujerar da ke kitchen ɗin ta zauna,spoon ɗaya tayi, sai kallon su tayi tana zaro ido,faɗuwa gaban su yayi kar ace abicin bai yi daɗi ba sai faɗin "momy miya faru "su ke, murmushi momy ta saki tana faɗin "kai masha Allah, wannan girki naku yayi daɗi sosai masha Allah " rungume juna su kayi suna tsalle suna faɗin "mun gode momy " feenah ce ta shigo tana ya tsine fuska da alama daga bacci take "kukuma lafiya, kuke ta ihu duk kunbi kun addabi mutane " tsayawa su kayi da murnar da su keyi su kai, sa'ada tace "girki fa mu kai, kuma momy tace yayi daɗi, shine muke murna " tsaki feenah taja "girki kodai ja gwal gwalo,ku nan har wani girki kuka iya " hararar ta momy tayi tana faɗin "ki fara ci kiji kafin ki kushe masu girki " zaro ido feenah tayi tana faɗin "wah ni, Allah ya kiyaye " sa'ada tace "wallahi Aunty feenah kin dai san munfi ki iya girki " jinjina kai feenah tayi "ke ni kike faɗama haka " "yo ai gaskiya na faɗin " duka ta kaima sa'ada da sauri ta ɓoye bayan momy "momy wai daga faɗar gaskiya zata dake ni " dukan ta sake kai mata a bayan momyn, fatima dai na tsaye tana binsu da idanu, riƙe hannun feenah momy tayi "kar ki sake ki dakar man yarinya, koma mi ta faɗa maki ke kija, idan bazaki yabi girkin su ba ai bai kamata ki kushe masu ba" "amma momy baki ji mi tace man ba " "koma mi tace, ai ba ƙarya tayi ba, kin iya girkine " ran feenah in yai dubu to ya ɓaci jin momy ta goyi bayan sa'ada "momy wai miyasa kike haka duk abun da sa'ada zata man idan na ce zan dake ta sai ki hana " "dole na hana, saboda komi tai maki laifin ki yafi yawa " "shikenan momy tun da haka ki kace " tana gama faɗa ta wuce fuuuuu kamar zata tashi sama, sa'ada tace azuciyar ta "nasan daga nan sai part ɗin innah" babu wanda ya bi ta kan feenah daga momy har fatima, aikin dake gaban su suka kama, sai da suka kammala komi suka jera abincin kan dinning,Abdallah kuma cikin basket suka jera mashi shi da shazim, dama girkin saboda shi su kayi shi bayan sun gama su ka wuce bedroom ɗin sa'ada domin yin wanka, fatima ta fara shiga wanka sa'ada kuma ta ɗauko masu kayan da zasu sa, fatima na fitowa sa'ada ta shiga , shaf shaf suka shirya su ka fice zuwa kitchen, basket ɗin da suka jera ma Abdallah suka ɗauka, direct part ɗin su shazim suka nufa,tsit part ɗin kamar ba kowa, sama su ka wuce zuwa bedroom ɗin shazim, sa'ada ce tayi nocking shiru ba'a basu izinin shigaba sake nocking ɗin tayi still shiru, fatima tace "ko dai suna part ɗin uncle Ahmad " "ba mamaki suna can " fatima tace "amma bari nayi nocking ɗin ɗakin ya noor may be shi yana nan" juyawa tayi zuwa bedroom ɗin noraiz tun kafin tayi nocking a ka buɗe ƙofar , noraiz ne ya fito shi da mahmud da alama fita zasu yi, bim su da kallo su kayi noraiz yace "ku kuma lafiya ku kayi curko curko da basket a hannu " fatima ce tace "daman su ya dr muka kawo ma abinci, munyi nocking shiru" "to ku ajiye kan dinning mana" "a'a gaskiya ya noor, idan kuma basu dawo part ɗin ba da wuri fa, zai iya yin sanyi " "to tun da gudun yayi sanyi kuke mu sai ku bamu muci " "a'a wallahi ya noor, ba fa naku bane, idan zaku ci yana can part ɗin momy" mahmud yace "mu da yake bamu da galihu ko " "ni ba haka nake nufi ba" hannun noraiz ya ja "wuce mu tafi" ficewa su kayi su fatima su ka bi bayan su zuwa part ɗin uncle Ahmad,suna shiga part ɗin mansoor su ka nufa, nocking su kayi, izinin shiga aka basu, tura ƙofar su kayi suka shiga zaune su ka samu Abdallah da mansoor shazim na kwance kan three seater idanuwan shi a rufe da a lama bacci yake, sallam su kayi, amsa masu sallamar su kayi "ina wuni ya dr " fatima tace, gaishe da shi sa'ada tayi, amsa masu yayi cikin kulawa, sai sannan suka gaishe da mansoor ƙin amsawa yayi sai ma hararar su da yayi "ok sai yanzu kuka san da zamana ko " haɗa baki su kayi wurin faɗin "a'a yaya " "ba wani nan, ai na san zaman da nake da ku " "a'a yaya " "shikenan dai, mi aka dafa mana, naji tun da kuka shigo nake jin ƙamshi " fatima tace "abun daɗi, kuma na ya dr ne " zaro ido mansoor yayi "ai haka, abun ƴar wariyar launin fatace kenan dai " dariya fatima tayi "wasa fa nake yaya, kaima kasan na ku ne" fatima sun shantake sai surutu su ke ganin boss na bacci,firar su kawai su ke, abun da basi sani ba idon shi biyu yana jin su banza kawai yayi da su, sai da yaji da gaske ba fita zasu yi ba sun samu wurin zama yasa shi buɗe ido yana faɗin "ke tashi ku ba mutane wuri " simi simi suka tashi su ka fice, mansoor ne yace "miye haka zaka wani kore su " "an kore su ɗin " banza kawai mansoor yayi da shi bai sake cewa komi ba, tsaki Abdallah yaja yana faɗin "sai kace wani kafi rashin san surutu, zaka wani kore su " ta shi yayi ya nufi bedroom ɗin mansoor batare da yace masu ƙala ba, suma fita lamarin shi su kayi, mansoor ne yayi serving ɗin su basu jira fitowar shazim ba su ka kama cin abincin su, lokacin da zai fito har sun kusa kammalawa, zama yayi yana cema mansoor "nima sai ka zuba man ko" "in dai ni zan zuba maka sai dai kar kaci ɗan rainin hankali " ɗaukar plate shazim yayi yana zuba abinci ba tare da ya sake ce ma mansoor ɗin komi ba. mansoor zamu sa ƙafar wando ɗaya da kai kai da Abdallah kun fa damu shazim tam 😏 fira mansoor da Abdallah su ke shazim kuma na cin abinci, da ya kammala fatima ya kira ta kwashe dishes ɗin, sai da yamma liƙis Abdallah ya koma gidan uncle ahmad , fatima kamar tayi kuka, sai da yace mata zai dawo tukunnan ta haƙura, tare su ka tafi da shazim da mansoor a motar Abdallah, Abdallah ke driving mansoor na kusa da shi yayin da shazim ke baya, fira suke shazim na baya yana jin su amma bai sa masu baki ba har suka iso gidan uncle ahmad....... Episode 30_31 ............ Horn Abdallah yayi a bakin gate ɗin gidan, ta ƙaramar ƙofa mai gadin gidan ya leƙo ganin motar Abdallah yasa ya koma da sauri ya buɗe mashi gate, ciki ya shiga da motar ya nufi parking lot yayi parking. Kai masha Allah gidan ya haɗu ba'a cewa komi, part biyu ne gidan,ɗaya yafi ɗaya girma,ba laifi gidan yana da girma, fitowa su kayi suka nufi ƙaramin part ɗin, ciki su ka shiga bakin su ɗauke da sallama, wata yar matashiyar budurwa su ka samu a parlor kwance kan sofa ta juya ma ƙofa baya, sallamar da suka yi ce ta sata tashi zaune haɗi da amsa masu sallamar,kyakyawace fatar jikin ta chocolate color,baza ta wuce shekara 19 zuwa 20 a duniya, jikin ta sanye da english wear's riga da skirt, cikin parlorn suka shiga, haɗi da samun wuri kan sofa suka zauna, gaishe da su wannan budurwar tayi, sannan tace ma Abdallah " yaya jiya mu kai ta jiran ka ka dawo baka dawo ba " "yanzu ai gashi na dawo ko " "amma sai da yamma, wai ma ina kaje" "to uwar masu iya surutu, ban sani ba wuce ki kira mana ummah" "yaya nice ma mai surutun ko " "zaki wuce ko sai ranki ya ɓaci " barin wurin tayi tana turo baki, wata ƙofa ta nufa, ba nocking kawai ta buɗe ƙofar ta shige bayan kamar minti biyu sai ga wata kyakyawar mace ta fito daga ɗakin jikin ta sanye da gown ta material, a ƙallah zata yi kimanin shekara 40 a duniya, ba fara bace amma bazaka kira ta da baƙa ba chocolate ce kamar ɗiyar ta, ƙara sowa tayi cikin parlorn tana faɗin "Abdallah daga bari naje na dawo sai kwana " murmushi Abdallah yayi ba tare da yace komi ba, gaishe da ita su shazim su kayi,fuska ɗauke da fara'a ta amsa tana faɗin " daga ziyara sai ku riƙe mana shi harda kwana " mansoor ne yace " ai gashi nan mun dawo da shi " "ai duk da haka " fira suke da matar cikin nishaɗin amma ban da shazim, dan shi yama ƙosa su tashi, tashi tayi tana faɗin "sai fira muke ba'a kawo maku abinci da ruwa ba " mansoor ne yace "a'a ba komi yanzu zamu wuce " "a'a gaskiya sai kunci ko da snacks ne, bari na sa Ameera ta kawo maku " tana faɗa ta koma ɗakin da ta fito ɗazu,shazim yace "ba sai ta kawo ba A hashim tafiya zamu yi " rai a ɓace Abdallah yace"wallahi baku isa ba kuna nan har sai uncle ya dawo " ganin ranshi ya ɓaci ne yasa mansoor cewa su jira ɗin, fasa tafiyar su kayi, Ameera ce ta shigo parlorn hannunta ɗauke da tray ruwa ne da lume, ajiye wa tayi a gaban su shazim, inda ta fito inda nake kyautata zatun kitchen ne chanta koma, sai gata ta fito hannunta ɗauke da snacks wata na biye da ita da bowl ɗin kayan marmari, a gaban su shazim ta sake ajiyewa, wacce suka fito tare ce ta gashe da su shazim, barin parlorn su kayi suka koma inda su ka fito, sai da Abdallah yayi da gaske sannan shazim yaci wani abu daga cikin abun sa aka kawo ma su, sun jima a gidan har sai da uncle Ahmad ya dawo suka gaisa, uncle ahmad yana matuƙar kama da abie sai dai abie ya fishi hasken fata,sun jima suna fira dashi, yanda ya sake masu kamar abokin su,da zasu tafi shida Abdallah su kayi nasu rakiya har parking lot. lokacin da su ka koma estate lokacin kusan ƙarfe goma da rabi na dare, kowa ma kwancin shi ya nufa, alawala yayi ya kabbara sallah,daya gama adu'a kwai yayi ya kwanta. Haka kwana ki su kai ta tafiya har shazim sunyi tsawan sati ɗaya da kwana biyar da zuwa abuja,a cikin kwana kin nan kunsan kullum sai Abdallah yazo wurin su ko su suje, fatima ma da sa'ada zuwan su gidan uncle Ahmad biyu, har lokacin su uncle ahmad basu sanar da shi kiran da suke mashi ba, shi kuma bai tambayi kowa ba ya dai zuba masu ido idan har basu sanar da shiba, yayi alƙawarin bazai tambaye su ba zai haɗa kayan ahi ne kawai ya koma logas, ya gaji da zaman abuja, aikin shi ne kawai ke damun shi, shi da yazo da niyyar kwana biyar, ya kai wannan lokacin ne saboda Ammy, amma da ba dan haka ba da tuni ya daɗe da komawa,har ammy ya kira yace shi dai zai dawo, amma sai ta hana shi tace ta zauna har sai in sun sanar da shi kiran da suke mashi, ba dan yaso ba ya haƙura. kullum idan mansoor zai tafi aiki tare suke tafiya. kwance yake kan bed ringing ɗin wayar shi ne ya tashe shi,lalubo wayar, a hashim ne ke kira , picking call ɗin yayi haɗi da yin sallama sannan ya ɗaura da cewa"lafiya kira da sassafe haka? " banajin mai a hashim ke cewa, na dai ga shazim yayi murmushi da alama a hashim ya bashi amsar da ta dace da maganar da yayi,sannan ya ce "kar ka damu very soon" sun ɗan jima suna waya sannan suka yi sallama, tashi yayi ya nufi toilet, bayan kamar minti 5 sai gashi ya fito ƙugun shi ɗaure da farin towel,clothes set ɗin shi ya nufa cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin wani yadi fari da baƙi mai taushi da ɗaukar hankali, gaban dressing mirror ya nufa kwalbar turare ya ɗauka ya feshe jikin shi,wayar shi dake kan bed ya ɗauka sannan ya fice ya nufi hanyar fita tana zuba ƙamshi, part ɗin uncle ahmad ya nufa a bakin ƙofa yaci karo da mansoor, mansoor na ganin shi yace" dama wurin ka zani, naga har kusan 11 baka fito ba kana can kwance "ɗan ya tsine fuska yayi yana faɗin " wallahi kuwa abun da ban taɓa yi ba kenan, amma yau ban san ya akai ba "hannun shi mansoor ya ja yana faɗin "mushiga ciki kayi breakfast may be gajiyan jiya ne "ciki suka shiga mama da kairiyya suka samu a parlor gaishe da mama yayi kairiyya ta gaishe da shi mama na faɗin "ga breakfast ɗin ku chan kan dinning " tashi sukayi suka nufi dining ɗin, kairiyya tayi saving ɗin su tana kammalawa ta dawo kan sofa, mahmud ne yashigo shi da noraiz, wurin su shazim suka nufa suka gaishe da su, suma suka zauna domin yin breakfast ɗin. suna kammalawa shazim da mansoor suka fice daga part suka nufi na uncle Ibrahim. zaune take kan sofa ta juya ma ƙofa baya sallamar su ce tasa ta juyowa, fuskar ta da fara'a ta nufe tana gaishe da su, mansoor ne ya amsa amma shazim ɗaure fuska yayi kamar an aiko masa da saƙon mutuwa "bro ana gaishe da kai " "naji" shine kawai abun da yace,kuka ne ya ciyo feenah ta rasa mi tayi ma shazim yake wulaƙanta ta, ace ko gaisuwar ta baya iya am sawa, juyawa tayi da sauri ta nufi bedroom ɗin ta kukan na neman kufce mata "gaskiya baka kyautawa, narasa miya sa ka tsani feenah kwata kwata baka son ta, in ta gaishe ka baka son amsawa wai miye duk hakan " "ka gama"fuska da alamun ɓacin rai mansoor yace "ok ni kake cema nagama ko yayi kyau" riƙo hannun shi yayi yana faɗin"sorry bro kai." bai ƙarasa maganar ba saboda fisge hannun shi da mansoor yayi yana faɗin "ra bu dani bana son jin komi daga gare ka" yana gama faɗa ya juya ya bi bayan feenah, ɗaga kafaɗa shazim yayi irin abun bai dame shi ba,sama ya nufa wurin uncle Ibrahim,yazo shiga kenan yaji yayi karo da mutum har sai da ya ɗan ja baya ,ɗagowa da kanshi yayi yana kallon luqman dake gaban shi tsaye yana liliya goshin shi da alama yaji zafin karon da sukayi, kallon shazim yayi yana faɗin "kayi hauka ne" tun kafin ya ƙarasa shazim ya ɗauke shi da wani mummunan mari har sai dai ya kusa faɗuwa, cikin azabar zafi ya ɗago yana faɗin "wannan wane irin zalunci ne azzalumi kawai mugu"sake wanka mashi mari shazim yayi har sai da ya duƙe kasa, amma duk da haka bai fasa ce mashi azzalumi ba,shaƙo wiyan rigar shi shazim yayi haɗi da kai mashi duka a baki, wahalalliyar ƙara luqman ya saki dan ba ƙaramin zafi yaji na har bakin shi ya fashe,uncle Ibrahim ne da ya fito sai ga mansoor da feenah har da momy sun nufo sama ta dalilin ƙarar da luqman ya saki,ganin yanda ya shaƙe mashi wuya ne yasa uncle Ibrahim cewa "shazim miye haka kashe shi zaka yi ne, wai ma miya haɗa ku ne, kake mashi wannan dukan" cikin kukan wahala luqman yace" ba abun da nayi mashi ya hau duka na, da yake azzalumi ne shi "wani sabon naushin ya sake kai ma luqman a baki, cikin sauri uncle Ibrahim ya ƙaraso kusa da su dan tun da ya fito yana tsaye ne a bakin ƙofa, hannun shazim ya fize daga riƙwan da yayi ma luqman yana faɗin "shazim baka da hankali ne illata shi kake son yi ne?" ran shazim ne ya ɓaci da maganar uncle Ibrahim, yasan cewa luqman bai da kunya kwata kwata kuma ya raina shi ya san dole sai da dalili zai mashi wannan dukan,amma da alama laifin shi yake gani, ce mashi yayi"eh, tun da shi bashi da hankali, bai san ina ke mashi ciwo ba" "shazim ni kake faɗa ma haka?" banza yayi da uncle Ibrahim sai ma kama hanyar fita yayi, riƙo shi mansoor yayi yana faɗin "bakaji ana maka magana zaka fice "cikin ɓacin rai shazim ya ce "sakar man hannu na mansoor" ƙin sakar mashi hannu mansoor yayi, ganin bazai sakar mai hannu bane yasa shi fizge hannun shi ya fice daga part ɗin bin bayan shi mansoor yayi yana ƙwala mashi kira ,da kallo uncle Ibrahim ya bi su har suka bar part ɗin ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli luqman yana faɗin"maganin ka kenan luqman, tun yaushe nake maka faɗa akan ka daina shiga harkar shi amma baka ji, yanzu da bama kusa Allah ka ɗai yasan irin illar dazai yi maka "cikin kuka luqman yace"yanzu dady goyan bayan shi kake, duk irin wannan dukan da ya yi man" "dole na goyi bayan shi dan na san halinka da rashin kunya, kuma haka nan bazai rufe ka da duka ba batare da kayi mashi komi ba "cikin ɓacin rai luqman yace "tun da haka ne dady, wallahi sai na rama bazai dake ni a banza ba wallahi"juyawa yayi zai bar wurin da sauri uncle Ibrahim ya jawo hannun shi yayi yana faɗin "ashe baka da hankali ban sani ba,dallah wuce ciki sakarai kawai " ya faɗa haɗi da janshi suka shiga parlorn shi aka bar momy da feenah tsaye, feenah ce tace "wai miyasa ya shazim ya tsane mu ne, ji dukan da yayi ma ya luqman dan Allah" ɗan nisawa momy tayi sannan tace "idan har da laifin shazim to na innah yafi yawa dan ita ta haddasa komi, ita tasa luqman bai ganin shazim da mutunci" "haba momy yaza kice haka,ba ruwan innah, dama chan ba son mu yake ba" "nace hakan,duk ba ita ta haddasa komi ba tasa kuka tsane su kuke mashi rashin kunya,ke ma duka yaushe kika dai na raina shi, dalla wuce ki bani wuri" wucewa feenah tayi tana turo baki ta nufi ƙofar fita zuwa part ɗin innah, a bedroom ta same ta mai aikin ta na shirya mata kaya a wardrobe, kallon mai aikin feenah tayi tana faɗin "ke tashi ki bamu wuri"ta shi talatu tayi ta fice, kallon feenah innah tayi tana faɗin "ke kuma lafiya kika korar man mai aiki? " zama tayi bakin bed ɗin tana cewa "tacika sa ido ne da gulmar tsiya" "to aikuwa ke zaki ƙara sa man tun da har kika kore ta "ɗan ya tsine fuska feenah tayi tana faɗin "ai yanzu zan tashi sai ta zo ta ida maki"sannan ta ɗaura da cewa "innah kin san mi ya faru kuwa?"gyara zama innah tayi tana faɗin "a'a sai kin faɗa,mi ya faru" "uhmm ya shazim ne yayi ma ya luqman dukan tsiya har da fasa mashi baki"zaro ido innah tayi haɗi da rike haɓa tana faɗin "wallahi bazai yiwu ba, shikuma sai luqman ɗin ya tsaya kamar wani sakarai har ya zubar mashi da jini" "to kema innah in ban da abunki ina ya shazim ina ya luqman "miƙewa innah tayi tana cewa "to wallahi bai daki banza, ka gaman azzalumi yaro"ficewa tayi daga bedroom ɗin tana masifa ta nufi part ɗin uncle Ibrahim, momy da ke zaune kan sofa tun daga waje ta fara jiyo masifar innah, sai gata ta shigo, tana ganin momy tace "ina Ibrahim ɗin yake? " sama momy ta nuna mata da hannu, fuuuu innah ta wuce zuwa sama tana ta zazzaga masifa,tana shiga parlorn ta samu uncle Ibrahim shi da mansoor dake kwance kan sofa, ko sallama babu ta faɗo tana faɗin "wallahi bazata saɓuba bindiga a ruwa,ina luqman ɗin yake"miƙewa luqman yayi ya nufe ta "dan mi zaka tsaya wannan yaron mara mutuncin yayi maka duka irin haka sai kace jaki" uncle Ibrahim ne yace "haba innah yaza kice haka,bayan kin san halin luqman da rashin kunya dole yana da laifi" "hakama zaki ce yaron yayi mashi irin wannan dukan, amma kace shine mai gaskiya" "ba wai na goyi bayan shi bane, a'a nasan halin luqman ne da rashin kunya shine kawai , kuma kema nasan kinsan halin shi sosai" tsaki innah taja tana faɗin "shima ai ba kunyar bace da shi, kuma wallahi bai daki banza ba, idan da ya dake shi nayi shiru lokacin da yake yaro yanzu bazan yarda ba ace da girman shi ya dake shi ba in zuba ido ina kallo idan kai bazaka ɗauki mataki ba ni zan ɗauka da kaina" "yawwa innah shiyyasa nake ƙara sonki kin fi dady sona " "karka damu zanyi maganin shi, fita ka bamu wuri zamuyi magana "da to innah ya amsa sannan ya kama hanyar ficewa daga parlorn, kallon uncle Ibrahim tayi sannan tace "kai kuma zauna "zama yayi kan sofa dake kallon wacce innah ke zaune.. Da yamma innah ta aiki feenah kiran uncle ahmad, tana zuwa part ɗin ta samu su noraiz a parlor, yi tayi kamar bata san da su a parlorn ba ta nufi sama,faisal ne yace "lallai ma wannan yarin yar uncle ahmad na zaune a parlorn shi, mama na zuba mashi fura a cup ta shigo da sallama,amsa mata suka yi uncle ahmad na cewa"mamana zo ki zauna "ya faɗa haɗi da nuna mata kusa da shi, zuwa tayi kusa da shi ta zauna,"daga ina mamana? " " daga wurin innah na ke , tace na kira mata kai " "to, kice mata gani nan zuwa" da to feenah ta amsa haɗi da ficewa ta bar part ɗin ta koma na innah. lokacin da suka fita daga part ɗin uncle Ibrahim part ɗin su ya nufa ya shiga bedroom ɗin shi,da ƙafa ya tura ƙofa da ƙarfi har yaso da tsema mansoor hannun dake bayan shin, ja da baya mansoor yayi yana kallon ƙofar kamar shazim ɗin a wurin,tura ƙofar yayi ya shiga zaune ya gan shi bakin bed, ƙarasawa cikin yayi ya zauna kusa da shi yana faɗin "shazim miyasa ka dake shi, mi yayi maka"banza shazim yayi da shi har saida ya ƙara tambayar shi, still banza yayi da shi ran mansoor ne ya ɓaci, cikin masifa yake ce ma shazim "wai bakaji ina maka maganane, ko nima shashasha ka ɗauke ni ban sani ba" ɗan nisawa shazim yayi, sannan yace"dole nayi banza da kai mana" "ok haka kace koh " "eh" abun yayi matuƙar ɗaure ma mansoor kai, cikin lallashi ya ce"kayi haƙuri nasan kana ganin kamar na goyi bayan luqman ne"shiru shazim yayi kamar ba da shi mansoor yake ba "haba shazim na san kana jina" "ina jinka mana" haƙuri mansoor ya shiga ba sai da ƙyar ya sa mu ya shawo kansa har ya dai na fushin da ya ke. innah da feenah ne zaune a parlor, feenah ta kwanta tana daddan wayar ta, innah kuma na zaune ta ƙurama tv ido, sallama su uncle ahmad su ka yi haɗi da shigowa, amsa ma su sallamar innah tayi, wuri suka samu su ka zauna, uncle ahmad yace "innah gani feena tace kina kira na, Allah dai yasa lafiya " "lafiya lau " innah ta faɗa haɗi da kallon feenah tace "takwara tashi ki bamu wuri " da to feenah ta amsa haɗi da miƙewa ta fita, laɓewa tayi a bayan ƙofar part ɗin innah, maganar da su innah ke yi take saurare sai sakin murmushi take, alamar buɗe ƙofa taji za'a fito taji, hakan ya sa da gudu tabar bakin ƙofar ta ɓoye bayan part ɗin, uncle ahmad ne da uncle Ibrahim su ka fito daga part, tsayawa tayi har sai da taga shun nufi part ɗin uncle Ahmad sannan ta nufi part ɗin innah da sauri, a bedroom ta samu innah da waya kare a kunnen ta, zama tayi tsakiyyar bed ɗin innah tana faɗin "dan Allah innah kiyi sauri ki gama wayar nan pls" da ƙuwa innah tayi mata, dariya feenah, ganin wayar innah ba mai ƙarewa ba ce yasa ta kwanciya kan bed ɗin sai sakin murmushi take kamar wacce aka yima albishir da gidan aljanna, innah ta ɗan ɗauki lokaci tana waya,lokacin da ta kammala, zama tayi ita ma kan bed ɗin "ke kuma lafiya kika zo zaki ta kura man " ta shi feenah tayi tana ɗan ya tsine fuska tace " dama nazo ne naji ya kukayi da su dady " riƙe haɓ innah tayi tana faɗin "sannu uwata, to ban sani ba" murmushi feenah tayi tana faɗin "ai naji komi kuka ce " ɗan zaro ido innah tayi tace "dana ce ki fita kenan laɓewa ki kayi kina sauraron mi muka ce " "a'a ai ba duka naji abun da kuke cewa ba " "ƙarya kike kinji komi" "Allah a'a, yau she uncle ahmad yace su Aunty uwani zasu zo " "ban sani ba, tashi ki bani wuri " "dan Allah innah ki faɗa man " innah tace "naƙi in faɗa" roƙonta feenah ta shigayi akan ta faɗa mata yau she zasu zo, amma ƙiri ƙiri innah ta ƙi faɗa mata. ✨SHAZIM✨ Kayan shi ya hau haɗawa dan yayi alƙawarin sai ya bar abuja gobe da izinin ubangiji, ya gaji da zaman jiran jin kiran da su ke mashi, shiyyasa kawai ya yanke shawarar tafi gobe ko da shi kaɗai ne ban da su fatima, inyaso daga baya sun dawo, yana cikin haɗa kayan mansoor ya shigo bedroom ɗin, turus ya tsaya yana kallon shazim dake ta faman haɗa kaya, yi yayi kamar ma bai ga shigowar mansoor ba yaci gaba da abun da yake matsowa mansoor yayi kusa da haɗi da dafa kafaɗar shi yace "wai shazim kana nufin har yanzu baka haƙura ba" ba tare da ya kalli mansoor ba yace "wa yace maka fushi nake " "to idan ba fushi kake ba, miye na wani haɗa kaya, dan nasan halinka kana iya cewa lagos zaka koma" "faɗi kake ana jinka " "haba shazim miye abun fushi a nan" "wai dan Allah wa yace maka fushi nake, kawai ina son na koma ne saboda aiki na da baro, luqman har ya kai matsayin da zai ɓata man rai ne na koma lagos " ɗan ajiyar zuciya mansoor ya sauke "to shikenan, amma ka bari su abbah su ce ka tafi ko" "mansoor baza ka gane bane, aikina fa na baro tsawan sati ɗaya da wani abu haba " "haka ne shazim, amma duk da haka ya kamata ka jira kaji mi zasu ce " "ai ba tafiya zan yi ba batare da na sanar da su ba, zan faɗa masu in son in tafi gobe " "to shikenan "mansoor yace, kama mashi yayi ya haɗa duk wani kayan shi da ya zo da su, bayan sun gama masallaci su ka nufa su kayi sallar magrib har da isha daga nan part ɗin uncle Ahmad su kaje, dinner su kayi bayan sun kammala ne shazim ya samu uncle ahmad har part ɗin shi ya sanar da shi yana so zai koma lagos gobe, ko da ya faɗa mashi cewa yayi ya bari sai nan da ranar lahadi, saboda family meeting da za su yi ranar asabar, ba dan ya so ba ya haƙura, part ɗin su ya koma kwata kwata baiji daɗin hana shi tafiya da uncle Ahmad yayi ba kuma, ammy ya kira ya sanar da ita, ce mashi tayi yayi haƙuri ya jira, ko ba komi zaiga ƴan uwanshi da ya daɗe bai gani ba dama waɗan da bai san su ba, dan bashi da yanda zai yi ne yasa ya haƙura, baya farin ciki da wannan family meeting ɗi. ✨Ammy ✨ kwance take kan gadon ummy, gama wayar su kenan da shazim ta kwanta, tunda su shazim suka tafi abuja kullum tana gidan malam, wata ranar ma a nan take kwana, yau ma anan zata kwana, ummy ce ta shigo ɗaki da sallama, amsa mata sallamar ammy tayi, bakin bed ummy ta zauna tana wash, yanzu indai tayi tafiya ko yaya take sai ƙafafun ta su kama ciwo, sannu Ammy tayi haɗi da cewa "anya ummy baza muje asibiti ba saboda ciwan ƙafafun nan" "a'a ba sai munje asibiti ba, yaushe ango na zai dawo? " "yanzu nayi waya da shi da gobe zai dawo, amma yanzu sai ranar lahadi saboda meeting da za suyi na family " "to Allah ya kaimu, su Ahmad ɗin sun sanar da shi kiran da suke mashin ne" "a'a basu faɗa mashi ba har yanzu, ya dai ce man dawowar shi zai yi ko ba su faɗa mashi ba wai ya gaji da zama fa aiki ya bari, na daice yayi haƙurin su faɗa mashi " "eh gaskiya ya ka mata ya tsaya yaji kiran mi suke mashi " "kin san halin shi ummy wani lokacin da baƙar zuciya " "ai kuwa dole ya rage ta, tun da komi ma su kayi mashi shi ya jawo ma kansa " "haka ne, ummy yaushe su mamy su kace zasu dawo?" ammy ta faɗa "ta ce man wani watan idan Allah ya kaimu " "Allah ya kaimu, ina son idan za su koma na bi su na kwana biyu banje Morocco ba " "gaskiya ya kamata kije har da yarannan " "da su nake son zuwa musamman shazim da bai son shiga mutane " Ummy tace "ai lamarin angon nawa ne sai adu'a " firar su suke har sai da bacci ya fara ɗaukar su, sannan ummy ta tashi ta tafi ɗakin malam..... Episode 32_33 ......... Washe gari ta kasan ce friday, sun tashi da shirye shiryen tar bar baƙi, uncle Ahmad ne yace ma Kairiyya ta samu Feenah da su Fatima su gyara part ɗin da ke kusa da na innah. A part ɗin innah ta same ta kwance kan gadon innah da a'lama ma a nan ta kwana, ko da Kairiyya tayi mata magana cewa tayi "mizai hana a sa masu aiki su yi gyaran" Kairiyya tace "wannan kuma abbah zaki faɗa ma haka bani ba, tun da bani nace ayi gyaran ba " innah na zaune kan carpet tana jin su amma bata ce komi ba "To gaskiya ni bazan iya ba,gara ma tun wuri kije ki samu masu aiki kuyi gyaran tare, amma ni bazan iya ba" abun yayi matuƙar ba Kairiyya mamaki duk da daman tasan Feenah, ba kasa fai ake sata aiki tayi ba, in dai batayi niyya ba to fa bazata yi ba, amma ba ta yi tunanin cewa Abbah zai iya sata abu tace bazata yi ba, "yanzu dai mi kike nufi " " bana jin daɗi, bazan iya ba "ta bata amsa kai tsaye, Kairiyya tayi tuna nin Innah zata sa baki jin abun Feenah tace amma sai taga innah tayi kamar ba bata san da zaman su a ɗakin ba , kallon Innah tayi tace "Innah kina jin mi tace ko " Innah tace "dan Allah ni karki dame ni, tun da tace bata jin daɗi, to sai ki ƙyale ta, ai sai da lafiya ake komai " jinjina kai Kairiyya tayi haɗin da cewa "haka ne kam, gaskiya ne " tana gama faɗa ta tashi ta fice daga ɗakin, innah tace "yau ga fitinanniyar yarin ya"da harara Feenah ta rakata tana faɗin "sai kace an ce mata nima yar wahala ce irin ta " ta faɗa haɗi da jan tsaki, juya kwanciyar ta tayi tana kallon Innah tace "Amma dai Innah su gwaggo uwani na zuwa yau za a yi meeting ɗinnan ko " "sannu uwar yan gaggawa, saboda cin rabo ne abun kawai daga zuwa sai a kama meeting, ai a bari su huta " "shikenan da ƙarfe nawa tace zasu baro kurfi" "wannan ne kuma ban sani ba ". Kairiyya ko da ta fita daga part ɗin Innah part ɗin uncle Ibrahim ta nufa, sumun Fatima da Sa'ada tayi, tace su zo su tai maka mata su gyara part ɗin da ke kusa da na Innah, ba musu su ka taso suka bi bayan ta, lokacin da suka isa part ɗin a buɗe su ka same shi, duk a tunanin Kairiyya Abba ne ya buɗe shi, sai da suka shiga ciki su ka samu laure mai aikin mama da saude mai aiki momy suna ka kaɓe ƙura, cewa tayi "ai da kun barshi " laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa Ashe laure ce ta amshi key wurin mama ta buɗe part ɗin ta kira saude ta taya ta su graya pary ɗin, a ganinta ga su a estate ɗin mi zai sa su Kairiyya su yi akin, Kairiyya ta ce"ai da kun barshi, tun da gani ga fatima da sa'ada " laure tace "A'a aikin zai yi maku yawa, ki bari kawai muyi " Kairiyya tace "Allah kuwa da kun barshi za mu iya" "A'a duk da haka dai " ganin sun nace ne yasa Kairiyya cewa sai dai suyi aikin tare,a haka su ka cigaba da aikin suna fira sun ɗauki tsawan lokaci kafin su gama,sai wurin sha biyu da minti arba'in da wani abu su ka kammala, part ɗin uncle Ibrahim su Fatima su ka nufa, wanka su kayi da sallah kowace ta nemi wurin kwanciya ba tare da sun nemi abinci ba duk da suna jin yunwa. ✨SHAZIM✨ Kwance yake kan gado a rigingi ne kanshi yana kallon sama, idanun shi a rufe da a lama bacci ya ke, wayar shi dake kan bed side ce ta fara ringing, har kiran ya katse bai motsa ba,wani kiran ne ya sake shigowa, mutsu mutsun buɗe idanuwan shi ya shiga yi , bu ɗe su yayi yana kallon saman ceiling, ya ɗauki kusan five seconds yana kallon, kiran na shirin katsewa ya zura hannu ya jawo ta, picking yayi ba tare da ya du ba mai kiran na shi ba, muryar majeed ce ta daki dodon kunnen shi yana sallama, sallamar ya amsa cikin kasa lelliyar murya ta masu bacci yake faɗin"majeed kai ne " "eh nine, kamar ma bacci kake?" majeed ya tambaye shi amsa ya ba shi da "kai dai bari, ya aiki" "Alhmdllh, dama na kira ka ne saboda kayan nan da ke store, masu su fa sun fara bibiyar kayan " "mi ya faru kace haka? " "jiyan bayan tashi na security ya kira ni yake ce man wa su mutane sun zo bayan tafiya ta, wai sun zo da shigar jami'ain kiwan lafiya, an turo su ne dan su yi bin cike a abnoor a kan ana ba da magani ba bisa ƙa'ida ba , sun nemi da su buɗe masu store" "store kuma, su yi mi kenan a ciki " "shima tambayar su yayi mi za su yi a store shine su ka ce wai suna son su bincka magungunan da muke da su, bai dai buɗe ma su store ɗin ba dan cewa yayi ba shi ke da makullin store ba,da ya faɗa masu haka sai tambayar shi su kayi wai hospital ɗin na waye, so ya dai ceman bai faɗa masu saboda bai yadda da su ba, in dai har da gaske turo su a kayi yasan baza su zo a wannan time ɗin ba, sun dai ce zasu dawo" "ok yaushe su ka ce zasu dawo " "ba su faɗa mashi ba, sun dai ce kawai za su dawo " "ok to shikenan, nima ranar sunday zan dawo, idan na dawo za mu san yan da zamu bullo ma al'amarin insha Allah, buri na dama su fara bibiyar kayan" "Allah ya kaimu ranar sunday ɗin" Ameen ya amsa, sallama su kayi, mai da wayar yayi kan bed side, tunanin ya shiga"wai su waye masu wannan kayan ne?" tambayoyi yayi ta jefa ma kanshi bashi da mai bashi amsar su, ya jima a kwance shi bai koma bacci ba shi bai tashi ba, sai da aka fara kiran sallar asr, sannan ya sauka daga kan gado ya shi toilet, wanka ya sake da al'wala, shiryawa yayi cikin wani yadi mai taushi brown color ya sa hula milk color, feshe jikin shi yayi da turare mai ƙamshi, masha kamar ka sace shi ka gudu, shoe rag ɗin sa ya nufa ta kalmi ya ɗauko brown color ya sa , wayar shi ya ɗauka da key ɗin mota ya fice zuwa parking lot, wata farar mota da bai taɓa hawa ba tun da su ka zo ya nufa, shiga yayi cikin ta yayi reverse ya nufi main gate, ya na nufar main gate wasu motoci guda shidda su ka shigo cikin estate ɗin,ko mawa yayi yana tafiya slowly time ɗin da ya iso bakin gate ɗin har sun gama shi gowa, ficewa yayi ya bar estate ɗin,part ɗin innah motocin su ka nufa, parking su ka yi, na cikin motocin ne su ka fara fitowa,wata kyakyawar mata ce ta fara fitowa fara ce amma ba sosai ba a ƙallah zata yi kimanin shekara 51 zuwa da biyu Aunty uwani kenan, part ɗin innah ta nufa, ɗaya bayan su ke fitowa daga motacin, harda wata mata mai matuƙar kama da wacce ta shiga part ɗin innah sai dai tafi waccen haske nesa ba kusa ba,a ƙallah za tayi kimanin shekara 49 Aunty sadiya sunan ta ƙanwar Aunty uwani ce , su uku suka fito daga bayan motar ita da wasu matasan mata ɗaya da yaro a hannun ta ɗayar kuma da goyo, mai yaron bazata gaza shekara 32 ba a duniya, sunan ta Aunty Zainab ɗiyar gwaggo Halima ce ita ce babbar ɗiyar ta, ɗayar kuma bata wuce shekara 30,ita kuma sunan ta maryam ɗiyar gwaggo Uwani ce, motar da ke bayan su wasu ƴan mata ne su ka fito su hudu uku daga baya ɗaya kuma daga gaba ta fito, wacce ta fito daga gaba a ƙallah zata yi ki manin shekara 23 sunanta farida ɗiyar gwaggo Halima ce ita ma sai ƴan mata guda uku biyun zasu yi sa'annin baza su wuce shekara 27 ba Asma'u da Amina kenan,dukkan su suna da aure sai dai ba wacce ta haihu Amina Anwar take aure ɗan gwaggo Halima , ɗayar kuma bata wuce shekara 25, sai motar da ke bayan su yar matashi yar buduwar wa ce ta fito baza wuce sa'annin su kairiyya ba, sai maza su uku, motar da bayan su kuma duka maza ne manya su huɗu,du kan su part ɗin innah su ka nufa da sallama a bakin su, innah na zaune kan sofa ita matar da ta fara shigowa , tashi innah tayi tana faɗin " lale marhabun , sannun ku da zuwa" wurin zama ko wannan su ya samu, wa su kan sofa wasu kan carpet, feenah ce ta shigo da gudu daga ita sai vest da da wando gyelen da ta ɗaure kan ta da shi a hannu ta shigo da shi ta nufi wannan matashiyar wacce za su yi sa'annin, hugging ɗin ta tayi "oyoyo sister yau she rabon da na ganki " "ai baki son zumunci ne feenah " "kaji sai kace kema zumunci kike so" "wallahi kin san gara ni da ke " "ba wani nan, yau she rabun ki da abuja, zaki wani ce gara ke " babban da ke cikin su ne ya daka ma feenah tsawa yana faɗin " ke baki da hankali , baki ganin mutane zaki wani shigo da gudu ko sallama babu, ji kayan da ke jikin ki " faɗuwa gaban ta yayi dan shaf ta manta da wane kaya ne jikin ta, ta kuma manta cewa harda ya usman za'a zo, dan bala'in shakkar sa take "iskanci ki na nan ko,ki shiga hankalin ki da ni, kina son kafin na bar garinnan jikin ki yayi tsami, sa karya kawai " innah tace "A'a usman da kata daga shigowar ka baza ka ta kura ma yarinya ba, kai shikenan bazata nuna murnar ganin ƴar uwar ta ba " wannan matar ce wacce ta shigo daga baya gwaggo Halima tace "dama mama har yanzu baki daina goyan bayan feenah ba, ki duba fa yan da ta shigo ko sallama babu, ji kayan da ke jikinta " "dan Allah ya isa haka sadiya, daga zuwan ku za ku ta kurama yarin ya, sai ɗoki take ku zo amma kun zo za ku fara tasa ta gaba da masifa " "to shikenan , nayi shiru " Usman yace "zaki fice kije ki canza kayannan ko sai na ɓaɓɓalaki wa wuya kawai" jan hannun matashiyar budurwar feenah tayi su ka fice, su Fatima ne su ka shigo su da momy bakin su ɗauke da sallama, amsa masu sallamar su kayi cikin parlorn su ka shiga, gaisawa momy ta shiga yi da su gwaggo uwani, su fatima gaishe da su su kayi,gwaggo Halima ce kawai ta amsa gaisuwar da fatima tayi masu , amma gwaggo uwani yi tayi kamar ma bata san da fatima ba a parlorn sai ma tashi da tayi ta nufi ɗakin innah,da idanu kawai fatima ta bi ta idanun ta na kawo ƙwalla, gwaggo Halima ce ta lura da halin da fatima ta shiga, dafa kafaɗar tayi "Fatima ya Ammyn ku, ina su noraiz da shazim " tayi mata tambayar ne dan ta kau da mata hankali daga abun da gwaggo uwani tayi mata, "ya noor na tare da ya mahmud, ya shazim ne dai ban san inda yake ba amma ina tunanin yana tare da ya mansoor " "masha Allah, ya su malam" "lafiya lau su ke " janta da fira tai tayi har sai da ta saki ranta "Fatima mu baki ganmu ba ne " wata kyakyawar budurwa ce zaune kusa da sa'ada "Allah sarki Aunty farida so nake mu gama gaisawa da gwaggo, ina wuni, ya hanya?" "lafiya lau fatima, ya lagos, ina Ammy" "Ammy na lagos " ɗaya bayan ɗaya fatima ta bisu tana gaishe da su, wasu su amsa wasu yi banza da ita,har da masu sarka mata habaici, da ta gaji da ganin abun da suke mata tashi tayi ta bar part ɗin ta nufi na su, hawayen da take ɓoyewa ne su ka shiga gangaro mata, tarasa miyasa gwaggo uwani bata ƙaunar su ita da ƴaƴen ta, ta ci kuka kamar mi ita ka ɗai a part ɗin har bacci ya ɗauke ta kan sofa. A can part ɗin Innah kuwa, gwaggo Halima ce ta kalli su Aunty maryam da su Aunty Amina tace "yanzu ku da hankali ku da wayan ku kuke abu kamar wasu ƙananan yara, musamman ke maryam da girman ki zaki biye ma su Asma'u " Aunty maryam tace "mi nayi kuma mama " "ina kallon ku ke da su Asma'u Fatima ta gaishe ku Zainab ce da Fiddausi kawai su ka amsa mata, miyasa kuke haka da hankalin ku" "mun fa amsa baki lura bane " tsaki ya usman ya jaya " wallahi har mamaki ki ke bani maryam ko yaro ƙaramin bazai yi abun da kike yi ba , ku kuma ku shiga hankalin ku" ya faɗa haɗi da nuna su da yatsa, mama ce ta shigo su ka gaisa da gwaggo Halima, bata wani jima ba ta koma part ɗin ta, mai aikin momy da mama ne suka shigo da manyan tray ɗauke da ruwa da lemu, bayan sun ajiye masu gaishe da su suka yi, sannan su ka fice suka kawo masu abinci da snacks . Mansoor ne ya shigo parlorn, wuri ya samu kan sofa yana gaishe da su gwaggo uwani wacce fito war ta kenan daga bedroom ɗin Innah, hannu ya miƙa ma usman su ka gaisa "ya usman kwana da yawa, ka shige jos ba'ajin ɗuriyar ka" "ba wani na shige jos, ai kai da shazim ba mutunci ne da ku ba, musamman shazim sai ya shigo jos sau ba a dadi amma ban taɓa ganin ƙeyar shi ba" "Ka san shi da aiki ya Usman, may be shi ke hana shi zuwa in da kake" "ba wani aiki kawai dai ba ya son zumunci ne" gwaggo Halima ce tace"mansoor yana ina ne abokin naka " "wai shazim?" "Eh shi " "Ina tunanin yana part ɗin su,na kira maki shine?" "a'a ƙyale shi na san zai shigo " tsaki gwaggo uwani ta ja tana ce ma mansoor "kai je ka kira shi, tun da shi ya fi ƙarfin ya shigo gaishe da mutane" "da kin ƙyale shi yaya, na san zai shigo zuwa anjima kuma ma duka mintin mu nawa da shigowa, ra bu da shu Mansoor ba sai ka kira shi ba " "haka ku ke dama ke da su yaya, yaro yaita abun da yaga dama amma ku baku gani, da ance kaza za ku kare shi" "ba haka bane, idan har kika ga munyi goyi bayan shi to fah yana da gaskiya, haka nan baya abu batare da dalili ba" " haka ku kaci rani, in dai shazim ne za mu gani " banza gwaggo Halima tayi da ita kamar ma ba da ita take maganar ba, Mansoor yana nan zaune noraiz da mahmud su ka shigo, wuri suma suka samu kusa mansoor su ka zauna, gwaggo uwani ce tace " ai nayi tunanin kai ma kafi ƙarfin gaishe da mutane kamar ɗan uwan ka " bai amsa mata tambayar ta ba sai ma gaishe ta da yayi, haushi abun ya bata , ta so ya bata amsa amma sai yayi kamar ma ba da shi take ba, da lafiya ta amsa mashi suna gama gaishe da su , su kayi fice war su, su noraiz basu jima da fita ba ba mazan ma su ka tashi har da mansoor suka fice, shi da anwar part ɗin su shazim suka nufa sauran kuma suka nufi part ɗin da aka tana da domin su, a can su saude su ka kai ma su abinci. bedroom ɗin sa suka nufa, mansoor yayi nocking har ya gaji, wayar shi ya ciro daga aljihu ta lalubo number shazim ya kira, har ta tsinke bai yi picking ba sai da ya sake kira sannan yayi picking, yana ɗauka mansoor yace "kai wai kana lafiya ake ta nocking " kwance yake kan bed ɗin Abdallah a gidan uncle Ahmad, ɗan ya tsina fuska yayi yana faɗin "bafa na nan, na fita tun ɗazu" "ok kana ina ne?" "ina wurin Abdallah " "yaushe zaka dawo,su Anwar fa sun zo kuma gwaggo Halima na neman ka" "may be sai dare ko gobe" amsar wayar Anwar yayi yana faɗin "muna gidan zaka ce wai sai gobe, wasa dai kake ko" "Anwar ya hanya " "Alhmdllh, ina nan ina jiran shigowar ka" "to shikenan sai na shigo " "ok ina zama jira "yana gama faɗa yayi rejecting kiran, barin part ɗin su kayi zuwa part ɗin mansoor. Sai da yamma liƙis su Abbah suka dawo daga wurin aiki nan part ɗin innah su ka yada zango a parlor, suna firar yaushe gamo da ƴan uwan su, Auny uwani ce tace" yaya ba naji kamar kace shazim da noraiz suna garinnan ba da muka yi waya da kai " Uncle Ahmad yace "eh suna nan, basu shigo kun gaisa ba ne " "banga ƙeyar ko ɗaya daga cikin su ba, dama noraiz me ɗan iya gaishe da mutane inya gansu, shi ko wannan uban marasa kunyar yafi ƙarfin gaishe da kowa" Uncle Ahmad yace "haba uwani, wai miyasa a kowane lokaci kike ma shazim musammanar fahimta ne,yanzu haka baya nan ne , shi yasa baizo ya gaishe da ku ba " "dama nasan haka zaka ce yaya, da anyi magana kan shi sai ku goyi bayan shi " gwaggo Halima tace"bawai an goyi bayan shi bane, kece dai baki fahimci shi ba, kuma ai noraiz ya shigo nan kun gaisa da shi " "to naji, ai naga ke yazo ya gaishe ki ke da kika fahimci shi" girgiza kai kawai gwaggo Halima tayi ba tare da tace komi ba, Uncle Ahmad yace "ya isa haka, idan ya dawo zai shigo ku gaisa " "Allah yasa "a cewar gwaggo uwani sunjima a part innah suna fira, sai da aka fara kiraye kirayen sallar magrib su ka bar prt ɗin zuwa masallaci, su ma gwaggo Halima ta shi su kayi su ka shiga ɗakin Innah domin gabatar da ta su sallar, har sai da su kayi isha sannan su ka dawo parlor , sai bayan sallar isha kairiyya ma ta shigo gai she da su, su Aunty maryam kamar su cinye ta dan bata zo tun ɗazu ba, haƙuri ta ba su akan bata jin daɗin ne shiyyasa ba shigo ba, bata wani jima ba ita ma ta koma part ɗin su. feenah tun korar da usman yayi mata bata sake shigowa part ɗin ba sai yanzu ta shigo ita da ilham, a nan parlor suka zauna suna fira da su Aunty maryam. Wuraren ƙarfe 9 ya motar shi ta shigo estate ɗin, a hankali yake driving kamar baya son yi, part ɗin su ya nufa yayi parking, ya jima zaune a mota yana waya, sai da ya kammala wayar shi tukunnan ya fito ya nufi cikin part ɗin tsit babu motsin kowa kamar ko wane lokaci, bedroom ɗin shi ya nufa, kayan jikin shi ya shiga ragewa bayan ya ajiye wayar shi da key ɗin motar da ya fita, toilet ya shiga, bayan kamar 10 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe, bakin window yaje ya tsaya yana kallon cikin estate ta baya kamar mai tunanin wani abu , ya jima a tsaye a wurin,daga baya ya saki curtain ya bar jikin window ya nufi clothes set ɗin shi, pajamas ya ɗauko riga da wando, wandon iya kar shi gwiwa sai riga mai garen hannun,cire bathrobe ɗin jikin shi yayi daga shi sai short, pajamas ɗin ya ɗauka ya sa, bayan ya gama sawa,cap ya ɗauko irin ta sanyi black color ya sa,fehe jikin shi yayi da turaren shi mai ƙamshi, wayar sa da ya ajiye kan bed ya ɗauka ya zura ta cikin pocket ɗin wando, flip flops ya zura a ƙafar shi, fita yayi daga bedroom ɗin main parlor ya nufa fita yayi daga part ɗin zuwa part ɗin mansoor,yana shiga main parlor su Amina, Asma'u da farida ya samu zaune kan sofa suna fira sai kairiyya da ke kwance kan sofa,ɗauke kai yayi daga kansu, amsa mashi sallamar da yayi su kayi, gaishe da shi su ka shiga yi, ba tare da ya tsaya ba ko ya kalli inda su ke ba yace lafiya, iya abun da yace kenan ya haura sama wurin mansoor, tura ƙofar parlorn yayi ya shiga, samun mansoor yayi zaune kan doguwar sofa shi da Fiddausi suna fira ( ɗiyar gwaggo Halima ce, ita ce budurwar shi da suke waya ) a bakin ƙofa ya tsaya yana kallon su, daga baya kuma ya shigo cikin parlorn, mansoor yace "ok ashe zaka dawo " ba tare da ya amsa mashi tambayar da yayi mashi ba, fuska a ɗaure ya kalli Fiddausi yace "ke tashi ki ba mutane wuri Episode 34_35 ............. Wani ɗan iskan kallo shazim ke bin mansoor da shi "kasan Allah ko ma wane irin kallo zaka man sai dai kayi amma ba in da zata, tun da ba kai ka kawo ta ba " "ok haka kace " "Kwarai kuwa haka nace, kayi duk abun da ka ga dama " Fiddausi dai na bayan mansoor tana zare idanu ƙes take jira ta watsa a guje, kallon ta shazim yayi yana faɗin "ke zaki zo ki wuce ko sai ranki yayi mumunnan ɓaci " fitowa tayi daga bayan mansoor zata fice, jawo hannun ta mansoor yayi yana faɗin "in wasa da ke ne " hawaye suka fara sauka daga fuskar ta, girgiza mashai kai tayi alamar a'a, "to koma kan sofa ki zauna " ƙin komawa tayi saima sake ɓoyewa da tayi bayan mansoor ɗin, nufo su shazim yayi gadan gadan, ai ba shiri ta watsa da gudan, dan bata san mi zai yi mata idan har ya kamta,sai da ta kusa shiga parlor sannan ta tsaya kan stairs case tana mai da nufashi, kallon ta su Asma'u su kayi, Amina tace "ke lafiya daga ina haka, sai kace wacce wani abun tsoron ya biyo " bata bata amsar tambayar da tayi mata ba sai ma binsu da take yi da idanu, sai da ta ɗan dawo cikin hankalin ta sannan ta ƙaraso cikin parlorn ta nemi wuri kan sofa ta zauna,sake tambayar ta Amina tayi "yo yana wuce ya shazim ne ya koro to" acewar Asma'u, Amina tace "wai baza ki yi magana bane" Sai a lokacin ta samu damar cewa "ya shazim ne ya koro ni ya mansoor yace ba inda zani, ganin yace ba idan za ni ne yasa nayi zama na, wallahi ina faɗa maku kaɗan ya hana bai make ni ba " Asma'u tace "dama nasan za'a rina, ni narasa miyasa ya shazim yake wannan isa da mallakar, samun ya mansoor ɗin yayi " Amina tace "Wallahi kuwa rainin wayaun shi yawa gare shi, sai kace wani ɗakin shi da zai wani koro ta " Asma'u tace " samun ya mansoor ɗin yayi da har zai nuna mashi wannan isa da mallakar " farida ce tace "wallahi babu ruwana kun ga tafiya ta, dan zai iya fitowa a kowane lokaci kuma kun san mi zai biyo baya idan ya kama ku kuna gulmar sa " tsaki Asma'u taja tana faɗin "matsoraciyar banza da wofi kawai, yo to sai mi dan ya kama mu " "Wallahi kun san mi zai biyo " "duk abun da zai biyo baya bawai muna tsoron shi bane " "ok haka kuka ce Allah ya fito da shi inga ta tsiyar cika baki " tana gama faɗa ta shige war ta ɗakin kairiyya *✨SHAZIM✨* A can bedroom ɗin mansoor, bayan fitar Fiddausi da gudu, kallon shazim mansoor yayi yana faɗin "wallahi kaji kunya, sai kace kai ka kawo ta da zaka wani kore ta, idan kai baka soyayya an gaya maka kowa irin ka ne wanda bai san in da ke mashi ciwo ba" "Wannan kuma ki ake ji, ko yanzu nasa ke ganin wata acikin su sai na ɓata mata rai yanda baka tunanin, inga abun da zaka iya " "Zan kira ta sai inga abun da za kayi, mara mutuncin kawai " "Oho dai koma mi zaka ce ka daɗe baka ce ba, na mamajo kawai " "Naji ni na mamajo ne, wanda bai san inda ke mashi ciwo ba fa " "Kai ake ji idan ma ka fita kasa kairiyya ta kawo man tea " ya faɗa haɗi da neman wurin zama kan sofa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya "Wannan ne kuma baka isa ba "tsaki shazim yaja ba tare da ya bashi amsar maganar shi ba, ficewa mansoor yayi daga bedroom ɗin zuwa parlor, kamar yanda Farida ta bar su Asma'u na gulmar shazim haka mansoor yazo ya same su,bakin benan ya tsaya yana sauraron duk abun da suke faɗa, kairiyya ce da ke kwance ta hange sa ta witsiyar ido, gyaran murya tayi masu amma hakan bai sa sunyi shiru ba sai sake ba da ƙaimi da su kayi wurin yin maganar "da alama sara kuke baku duba bakin gatarin ku " jin haka ne yasa fahimtar akwai abun da take son su fahimta, ɗagowar da Amina zatayi karab idanunta kan mansoor daya harɗe hannuwan shi kan ƙirji yana kallon su, duƙar da kai su ka yi ƙasa , ƙara sowa mansoor yayi cikin parlorn"sannun ku da ƙoƙari ko " ya faɗa yana binsu da idanuwa,ba wacce ta ce ƙala a cikin su saima tashi da su kayi sumi sumi su ka bar parlorn , tashi Fiddausi tayi zata bi bayan su , muryar mansoor taji yana faɗin "koma ki zauna " dawo wa tayi ta nemi wuri kan sofar da ta tashi, ɗuƙar da kai tayi tana wasa da ƴan ya tsun hannunta, tashi kairiyya tayi zata bar wuri da katar da ita mansoor yayi ta hanyar cewa "ki kaima shazim tea " da to ta amsa haɗi da nufar kitchen,haƙuri mansoor ya ba Fiddausi akan abun da shazim yayi mata" bakomi ai yaya " fira suka cigaba da yi ciki shauƙin soyayya, zuwa kairiyya tayi ta wuce ta gaban su zuwa sama hannun ta ɗauke da trayn da ta haɗo ma shazim tea,zaune yake kamar yan da mansoor ya barshi,ƙafa ɗaya kan ɗaya yana latsa wayar shi, ciki ta shiga da sallama a bakin ta, sallamar da tayi ya amsa, ƙara sawa tayi cikin parlorn kan table ɗin dake ɗakin ta ɗaura mashi trayn, tnxs yace, fice wa ta yi zuwa parlor ta wuce su mansoor zuwa ɗakin ta, shazim yana gama shan tea ɗin wayar sa ya saka cikin pocket ya nufi main parlor, kallo ɗaya yayi ma mansoor da Fiddausi dake parlorn, hararar shi mansoor yayi, ɗaga kafaɗa shazim yayi yana faɗin "aikin banza " haɗi da kama hanya ya fice daga part ɗin, yana fita a waje ya ci karo da uncle Ahmad zai shigo, gaishe da shi shazim yayi, amsa mashi yayi yana faɗin "wai ina kaje ne tun ɗazu bayan kasan yau su uwani zasu zo, ai ko ba komi da ka tsaya kun gaisa tukunnan " amsa shazim ya bashi da "naje wurin Abdallah ne saboda wani aiki da muke " "Ok to kashiga part ɗin innah ku gaisa da su suna can " da to ya amsa haɗi da nufar part ɗin, ciki uncle ahmad ya shiga lokacin har mansoor ya koma part ɗin shi ita kuma Fiddausi tana ɗakin kairiyya a nan zata kwana, sama ya wuce zuwa nashi bedroom ɗin. Shazim tsayawa yayi a bakin part ɗin Innah kamar zai shiga kamar bazai shiga ba daga bi sani dai ya shiga bakin shi da sallama ciki ciki, in ba ka kalli bakin shi ba baza ka taɓa cewa yayi sallama ba,gwaggo Halima ce da innah sai Aunty zainab da ke ba yaron ta abinci sai maryam a parlorn, amsa mashi sallamar da yayi Aunty zainab tayi, bawai dan taji sallamar da yayi ɗin ba sai dan sanin ba zai taɓa shiga wuri ba tare da yayi sallama ba, wuri ya samu kan sofa ya zauna, kallon gwaggo Halima yayi yace " ina wuni Aunty "da yake haka yake kiran ta "lafiya lau shazim, ina ka shige tun ɗazu nake ta cigiyar ka " "na je wani ɗan aiki ne " "Agogo sarkin aiki, a nan ɗin ma baka huta ba" murmushi yayi ba tare da yace komi ba, Innah ce tace "da yake uwar ka kawai ka sani shiyyasa ka gaishe da ita " "to idan ban fara gaishe da ita ba ke zan gaida " "wah ni, ai ba jiran ta ka gaisuwar nake ba " "Koma kina so ba wai zan gaishe da ke ɗin bane " harara maryam ta maka mashi jin yan da yake mai da ma innah magana yan da ran shi ya so "bana ma so, gida cike yake da ƴaƴan albarka, kuma sun gaishe da ni, ba taka nake jira ba " har ya buɗe baki zai mai da mata martanin maganar da tayi, gwaggo Halima ta katse shi ta hanyar cewa " shazim ya su Ammyn ku da malam " tayi hakan ne dan ta hana shi ba innah amsar maganar da tayi dan tasan abun da zai fito daga bakin shi ba mai daɗi bane "Ammy na lafiya haka ma malam " "masha Allah " Aunty Zainab ce tace "shazim ya kwana biyu, ya lagos " "lafiya lau alhmdllh, ya gajiyar tafiya " " ba gajiya" jan shi da fira gwaggo Halima tai ta yi har su ka ɗan ɗauki lokaci, tashi yayi zai tafi, da katar da shi gwaggo tayi ta hanyar cewa " ka jira yaya ta fito ku gaisa " kallon maryam tayi "maraya je ki kira ta su gaisa " tashi tayi ba tare da ce ƙala ba ta nufi bedroom ɗin innah, "zauna shazim kafin ta fito" da to ya amsa haɗi da komawa kan sofa ya zauna yana amsar yaron Aunty zainab, tun da ya shigo yaron ke miƙo mashi hannu alamar ya ɗauke shi,amsar shi yayi haɗi da tambayar ya sunan shi "gaskiya shazim mutuncin ka ra gage ne yanzu bama ka san sunan shi ba kenan " gwaggo Halima ta ce " a'a kar ki ga laifin shi,yaron da ba'a nan kika haife shi ba, kuma ma duka yaushe kika dawo ƙasar ne " Aunty Zainab tace " haka ne, sunan shi Aayan " " Allah ya raya " yace da Ameen Aunty zainab ta amsa, Maryam samun gwaggo Uwani tayi kwance kan gadon innah amma ba bacci take ba, zama maryam tayi bakin bed ɗin tana faɗin "mamy wai shazim ne ya shigo, Aunty halima tace kizo ku gaisa " "ɗan rainin hankali sai yanzu yayi lokacin zuwa kenan" maryam tace " ko dai aka ce ya zo ba " "haka ne kuma yanzu haka wani cikin su yaya ne yace yazo ya gaishe da mu" " ba ma mamaki " tashi gwaggo Uwani tayi tana faɗin "bari naje na same shi" ta faɗa haɗi da kama hanya ta fice, bin bayan ta maryam tayi. firar suke cikin kwanciyar hankali shazim dai na sauraron ya ƙagara ta fito dan ya samu ya koma part ɗin su bacci ne cike da idanun shi. gwaggo Uwani ce ta fito marya na bayan ta, a bakin ƙofar ɗakin innah ta tsaya tana faɗin " isashe ai nayi tunanin kafi ƙarfin gaishe da mutane "banza yayi da ita yana yi ma Aayan wasa duk da ya san da shi take ba tare da ya kalli in da take tsaye ba "Eh dole kayi banza da ni saboda ga mahaukaciya sabon kamu na magana "ko kallon in da take yanzu ma bai yi ba,tsaki yaja a ranshi yana faɗin "da ya san masifa zatayi mashi da bai tsaya ba " masifa take ta in da take shiga ba tannan take fita ba, da dai ya gaji da jin banbamin da take, ajiye Aayan yayi kan sofa haɗi da kallon gwaggo halima yace "sai da safe " "Allah ya tashe mu lafiya " da ameen ya amsa haɗi da kallon Aunty zainab yace "sai da safe " " to Allah ya kaimu " ficewa yayi yana jiyo muryar gwaggo Uwani tana zazzaga masifa kamar ta ari baki " zanyi maganin abun da yake damun ka mara mutunci " gwaggo Halima tace "gaskiya yaya kina abun da bai da cewa, yaron nan fa har ya tashi zai tafi na tsayar da shi dan ku gaisa amma kin fito kin rufe shi da faɗa mara tushe bare asali " "Ok ni zaki ce ma haka saboda wannan yaron, ai da kin sani da baki tsayar da shi ba da kin bar shi yayi tafiyar shi " "gaskiya yaya ki chanza, dan ko ɗazu banji daɗin abun kika yima Fatima ba, ya rinya ƙarama mi tasani game da abun da kike nufi " "Wai sadiya magana kike son faɗa man saboda waɗannan yaran ko mi kike nufi " "ni ba magana nake son faɗa maki ba kawai dai ina son ki san abun da kike aikatawa bai dace ba kwata kwata " " a'a maganar dai kike son faɗa man a kan yaran da ban sani miye haɗin ki da su ba " "Amma nayi mamaki yaya da ilimin ki kike faɗin haka,bayan kin san jinin da ke yawo a jikin ki shike yawo ajikin su amma kike faɗin haka " "jinin da dai ke yawo a jikin ki amma ba jiki na ba " "Ai kuwa ko kin ƙi ko kin so jinin da ke gudana ajikin ki shi ne dai ajikin su" "Wa ni Allah ya tsari gatari da saran suka, ni bani da wata alaƙa da su " "Ke kuwa ke da alaƙa da su, saboda uban su da kika haɗa uba da shi " "dan na haɗa uba da uban su ba ahi ke nuna cewa sun zama jinina ba" "Wannan kuma kin faɗi san ranki ne " "Wai sadiya miye ribar ki idan kin goyi bayan yarannan ne, wata riba gare ki " "ni kuwa ke da riba, saboda zumunci Allah ne yace ayi shi kuma na riƙe shi da hannu bibiyu " "wahalar banza kike, yau da ace uban nasu kafin ya bar duniya ya bar wani abun arziƙi to da nace kina yi ne dan ki samu wani abu a wurin su " "ko mi nake inayi ne dan Allah, kuma maganar mahaifin su dake, ina tuna nin ko bai bar komi ba da zai rasu ina tananin sai da ya rufa maki asiri ke da ƴaƴan ki da ƴan uwanki kafin ya bar duniyar" "Wai dakata sadiya, gori kike son yi man kan abun da sadiq yayi man " "Ni ba gori nake maki ba saboda ba ni nayi maki ba, ina tuna maki ne da abun kika manta " "gorin dai kike man sadiya kuma na gode " "duk yan da kika ɗauka yaya, Allah dai yasan mi nake nufi " Innah tace "wallahi kin bani mamaki sadiya, ƴar uwar ki kike ma gori akan abun da wani yayi mata, miye dan gan takar ki da shi da har zaki ba ɗe baki kiyi ma ƴar uwar ki ta jini gori " "mama sai dai ku ƙi fahimta ta amma ni ba gori nike mata ba, kuma innah ki dai na cewa ba ni da alaƙa da su, duk duniya basu da wasu da zasu nuna a matsayin dangin uban su bayan mu, muma haka kamar yan da zamu nuna su mansoor a matsayin ƴaƴan yan uwan mu haka suma dole mu nuna su a matsayin haka" gwaggo Uwani tayi cab tace" ki dai nuna su amma ba dai ni ba, bari kiji sadiya na san ko mi yasa kike wannan faɗe faɗen " Aunty Zainab ce tace " dan Allah mama Aunty kuyi haƙu ku dai na wannan gan ganun ba dan ni ba " "taya zaki ce haka zainab, gara dai ta ƙarasa yi man gorin da ta fara " "Ni dai ko mi ki kace naji, kamar yan da muke zuminci lokacin da yake raye yanzu ma bazan fasa ba " maryam tace " haba mama dan Allah karku zama ƙana nan yara a gaban mu, mu ya kama ta ace munyi haka kunyi mana faɗa amma ba wai ku ba" ta shi gwaggo Halima tayi ta fice daga part ɗin zuwa na uncle ahmad, bedroom ɗin mama ta nufa, tsit ta same shi ba kowa mama na ɗakin abba, hasken ɗakin ta kashe haɗi da hawa kan bede ta kwanta zuciyar ta duk ba daɗi. Lokacin da ya bar part ɗin innah part ɗin su ya nufa, a main parlor ya zauna kan sofa, gaba ɗaya ji yake zaman abujar nan kamar yana kan ƙaya yanke shawara yayi gobe ko da da yamma ne sai ya bar abuja ya koma lagos, ya ɗan jima zaune sannan ya tashi zai nufi sama zuwa bedroom ɗin shi, karab idanun shi suka sauka kan mutum dake zaune kan dinning ya duƙar da kai kan table , tashin farko bai gane ko waye ba sai da ya matsa dinning area sannan yaga ashe macece kuma fatima, ƙara sa wa yayi haɗi da kiran sunan ta amma ko motsi bata yi ba, bubbuga table ɗin yayi still bata motsa ba abun ya ɗaure mashi kai wane irin bacci ne take yi haka har bata ji kiran da yayi mata ba, gaskiya ba lafiya, hannu yasa ya ɗago da kanta, ya salam ya furta ganin ko numfashi bata yi, ruwan da ke kan dinning ɗin ya ɗauka buɗe marfin jirkar yayi ya ɗan zuba a hannun shi shafa mata yayi a fuska amma bata motsa ba, sai da yayi haka kusan sau uku sannan ta ja wani dogon numfashi "mi ke damun ki? " ya jefa mata tambaya, biji biji take kallon shi saboda nauyin da idanun ta su ka yi mata, sake jefa mata tambayar yayi, ware idanun ta tayi a kan fuskar shi, "da ke nake magana, mike damun ki " da ƙyar ta iya furta "babu komi yaya, nayi dinner ne shine bacci ya ɗauke ni ba tare da na sani ba " "ok da man a nan kike dinner " "a'a yau ne nayi a nan " "Zaki faɗa man mike damun ki ko sai na ɓata maki " "da gaske nake yaya ba komi " tsawa ya daka mata yana faɗin "ina wasa da ke ne, zaki faɗa man ko sai na ci mutuncin ki " fashewa tayi da kuka " Aunty Ilham ce ta mare ni " "ta mare ki da kika yi mata mi keken " "Wai dan momy tace na kira su su zo su ciki abinci, to shine sai tayi magana ni kuma ban ji ta ba, dan kawai nace banji ta ba shine ta mare ni Aunty feenah ta shaƙe man wuya " "Ok shine kika zo nan kina kuka har sai da numfashin ki ya ɗauke ko " "ba kuka nayi ba, bacci ne ya ɗauke ne " "ok yayi, kinsha magani " "Eh sa'ada ta kawo man " " to yayi, ina so gobe tun da safe ki haɗa duk wani kayn ki dake can part ɗin gobe zamu koma lagos ina fatan kin ji ni" "Eh yaya naji " "ta shi ki wuce kije ki kwanta " da to ta amsa haɗi da nufar ƙofa zata fita " ina za ki " "zanje na kwanta ne " "Ok shine kika kama hanyar fita " "Zanje ɗakin sa'ada ne " " ba can zaki ba, ɗakin ki zaki wuce " da to amsa haɗi da nufar sama ta shiga ɗakin ta bata taɓa kwana a cikin shi ba, tashi shima yayi ya nufi na shi bedroom ɗin,a jiye wayar shi yayi kan bed ya shiga toilet ta ɗauro alwala, carpet ya shimfiɗa ya shiga gaba tar da nafilfilo da yake yi duk dare, bayan ya gama light ɗin ɗakin ya kashe haɗi da hawa gadon shi ya kwanta, bacci ya ɗauke shi cikin ƙan ƙanin lokaci *WASHE GARI * Bayan ya dawo daga masallaci ɗakin fatima ya fara liƙawa dan ganin a wane hali take ciki, zaune ya same ta kan carpet ta gama sallar subhi, gaishe da shi tayi, amsa mata yayi yana faɗin "ya kike jin jikin ki yanzu " "lafiya lau" "to masha Allah, ki ƙara shan maganin ki " da to ta amsa mashi, ta shi yayi ya bar ɗakin ya nufi nashi, wayar shi ya ɗauka ya kira ammay ya sanar da ita yau zasu dawo, cewa tayi sai dai shi ya dawo yau amma ban da fatima,bai faɗa mata cewa fatimar bata jin daɗi ba ya dai roƙi ta bar su su dawo yau amma tace a'a, ganin bazata haƙura bane ya sa shi yi mata sallama, mai da akalar kiran yayi ga malam bugu ɗaya malam ya ɗaga yana faɗin "likita bokan turai ka shige abuja ba a ko jin ɗuriyar ka " "ai insha Allah ina nan dawowa yau " "Allah ya nuna mana "da ameen ya amsa yana faɗin "na kira ammy na faɗa mata yau zamu dawo ta ƙi amincewa wai sai dai ni na dawo ni kaɗai " "To ai ba wani abu bane dan ka baro su can, sai su dawo da kan su " "ba wai barin su bane matsala malam, su gwaggo Uwani suna kuma kasan halin ta da ya ranta shiyyasa bana son su zauna musamman fatima, dan ko jiya ban san mi ya haɗa suba har sai da su ka yi sana din tashin ciwan ta" "Subahanalilahi, yanzu ya jikin nata " "taji sauƙi, ina tsoron abun da zai biyo baya ne yasa nake son mh dawo tare " "E gaskiya ya kamata ku dawo tare, ku shirya ku tahu zanyi magana da Aishar " "To shikenan malam mun gode, sai mun dawo " Allah yasa malam ya faɗi sallama suka yi, kiran noraiz yayi awaya yace ya same shi a ɗaki, ko da yazo ce mashi yayi ya haɗa kayan shi yau zasu koma lagos, da fara ko uziri noraiz yafa kawo mashi akan ya bari sai gobe ko monday, ganin babu wasa a fuskar shazim ne yasa shi kama bakin shi yayi shiru. Cikin parlorn su ka shigo hannun su ɗauke da basket, dinning area suka nufa, feenah ce ta fito da flaks ɗin abinci tana jerawa kan dinning Jin motsin mutum ne yasa fatima fitowa parlorn, ganin su feenah yasa ta tsayawa a bakin ƙofar ɗakin ta, Ilham ce tace" ke zo nan " banza tayi da ita " ke bada ke nake magana ba " banza fatima ta sake yi da ita ganin bazata zo bane yasa Ilham tashi ta nufe ta " ke har ni zan kira ki kiyi banza da ni " da buɗar bakin fatima sai cewa tayi " eh nayi banza da ke ɗin sai aka yi mi " da sauri feenah ta ƙara so tana faɗin "lallai wuyan ki ya isa yanka " hannu Ilham tasa zata ɗauke fatima da mari bata kai da kai mata marin ba taji saukar lafiyyen mari a fuskarta har sau biyu, ɗago da fuskar ta tayi tana kallon shazim da ke tsaye gaban su, feenah zata buɗe baki tayi magana kenan ya ɗauke ta itama da wani a zabeben mari har saida ta dafe ƙarfen bene dan ba ƙaramin maruwa suka yi ba" ya shazim mi mukayi ka ma... " bata ƙarasa ba yasake ɗauke da mari ganin haka ne yasa Ilham watsawa da gudu ta nemi hanyar fita , magana ya fara cikin kakkausar murya "wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da wata banza a cikin ku zata sake ɗaga hannu ta daki fatima" yana gama faɗa ya wuce ta nan tsaye dafe da kumatu tana kuka, fatima ɗakin ta ta shige ta turo ƙofa, Ilham ce ta dawo ganin shazim ya fita ta kama hannun feenah suka bar part ɗin........ _Episode 36_37_ ........ Ilham ce ta dawo ganin shazim ya fita, ta kama hannun feenah suka bar part ɗin zuwa part ɗin Innah, feenah sai kuka take kamar wata ƙaramar yarinya, gwaggo Halima su ka samu akan sofa a parlor da cup a hannun ta tana shan kunun gyaɗa, da sauri ta juyo tana kallon feenah da ke ta kuka kamar wata ƙaramar yarinya "ku kuma lafiya daga ina haka?" basu bata amsar tambayar da tayi masu ba, sai ma neman wurin zama da su kayi kan sofa, feenah har wani ƙara ɗaga murya take duk dan innah da gwaggo uwani su ji su fito "wai ku ba da ku nake magana ba,ke kuma ko ki man shiru ko wallahi na make maki baki, sakar yar banza kawai" Ilham tace " mama ya shazim ne fa ya same mu yayi ta marin mu baji ba gani " "wani iskancin kuka yi mashi ko " "ba abun da muka yi mashi, abinci kawai muka je kai mashi shine ya haumu da mari " "ke Ilham ƙarya kike shazim ba zai mare ku ba haka nan dole da abun da kuka yi mashi, kuma ma ko ba abun da kuka yi mashi ya mare ku yayi man dadai dan kun cancanci fiye da haka " jin abun da gwaggo Halima tace ne yasa feenah ƙara sautin muryar kukan da take, sai Aunty maryam ta faɗo parlorn kamar an jehu ta "mi nake ji, ba dai wannan mara mutuncin ba ne ya mare ku" tsawa gwaggo Halima taa daka mata " ke maryam ki shiga cikin hankalin ki na ƙara jin kin faɗi wani abu a nan ranki zaiyi mumunnan ɓaci shashasha kawai kema" turo baki maryam tayi tana faɗin "haba Aunty mi yasa zaki ce haka, du ba fa kiga fuskar feenah duk sahun hannun shi, in ban da zalinci mi suka yi mashi har haka " gwaggo Uwani ta fito tana faɗin "wallahi bai mari banza ba " gwaggo Halima tace "yaya sai dai fa ki ga laifin shazim, amma ko rantsuwa nayi bazan kaffara ba su ke da laifi " "dama haka zaki ce tunda da man ba son ganin laifin shi kike ba " "Wai miyasa a kullum kike cewa, ina goyan bayan shi ne, ni ba goyan bayan shi nake ba kawai ina goyan bayan gaskiya" " to ai sai ki ta goyan bayan gaskiyar, amma wallahi bai mari banza ba sai ya gane kuskuren shi " "to shikenan in dai shazim ne ga kai ga fata " "Wallahi Aunty laifin su " sa'ada ta faɗa wacce shigowar ta part ɗin keknan,juyawa su kayi su duka suna binta da idanu, gwaggo Uwani ce tace" munafuka ubanwa yasa bakin ki daga shigowar ki " turo baki sa'ada tayi " wallahi ba ƙarya nake ba,Aunty Ilham ce ta mari fatima kawai dan tayi magana bata jita ba, ita kuma Aunty Feenah tasa ɗan kwalinta ta shaƙe mata wuya bayan tasan tana da matsalar numfashi " tafa hannu gwaggo Halima ta shiga yi tana salallami " yanzu da kashe ta ku ka so yi kenan, dan uban ku ku sau nawa mutum ke maku magana kunayin banza da shi bayan kuna jinshi , wallahi da ni na riƙa ku da sai kun yaba ma aya zaƙinta mutanen banza kawai " gwaggo Uwani tace "ke yanzu kenan harkin yarda da maganar wannan shashasha yarinyar " "dole na yarda da ita dan na san sa'ada bazata yi masu ƙarya ba" Feenah tsagai tawa tayi da kukan da take ta kalli sa'ada tana faɗin "wallahi kika bari na kama ki sai kin gane baki da wayau " duka gwaggo Halima ta kaima feenah "dan ubnki idan kin kama ta kiyi mata bungun da zata kasa tashi mar mutunci, kuma wallahi daga ke har Ilham ɗin sai nasa Usman yayi maganin ku " " a kan mi zaki haɗa su da shi, duk wannan marin da wannan mara mutuncin yayi masu bai isa ba " "ai mai sauƙi yayi masu, gara nasa usman yayi masu dukan da ko wani su kaga zai dake ta sa hana, bari ma kiga yanzu zan kira shi " "a'a sadiya kar ki kira shi a bar zancen kawai ya mutu " "idan har kinga zancen ya mutu to sai idan ita fatimar ce tace ta yafe masu " "wallahi baza ki ja masu raini a wurin yarinya ba, tun da dai zancen ya wuce a barshi kawai " " idan fa ba ita tace zancen ya wuce ba to fa bazai wuce ba, sa'ada kira man fatimar " da to sa'ada ta amsa haɗi da fita,ko da taje part ɗin shazim ta samu a parlor, gaishe da shi tayi, harta miƙe zata nufi ɗakin fatima yace mata bacci take saboda maganin da ya bata, koma wa tayi part ɗin Innah , ganin ta dawo ita kaɗai ne yasa gwaggo halima tace " ina fatimar take " "ya shazim na samu a parlor yace bata jin daɗi ya bata magani bacci take" "to yaya kin dai ji ko, har sun kaita ga kwanciya, wallahi ko suje har part ɗin su bata haƙuri ko yanzu nasa Usman yayi maganin su " "dan Allah dai ki ƙyale su,tun da harya bata magani zata ji sauƙi ne " "sai fa sunje sun bata haƙuri, idan ba haka ba kuma tam" "ba inda zasu, wai ke sadiya mi ke damun ki, to kisa usman ɗin ya dake su " innah ta faɗa wacce shigowar ta kenan daga part ɗin uncle Ahmad "mama dukan fatima fa su kayi bayan sun san tana da matsala " "koma mi su kayi mata baza su bata haƙuri ba " "shikenan mama, amma bana jin daɗin abun da kuke yi " "dallah ni yiman shiru tun da baki san ciwan ƴaƴan ki ba " "Allah ya huci zuciyar ki " kawai gwaggo halima ta faɗa haɗi da tashi ta shiga kitchen, zama innah tayi kan sofa hannu ta miƙa ma feenah " zo nan ƴar albarka dai na kuka zai gane bai da wayau, yi shiru kinji " matsowa tayi kusa da innah ta ɗaura kanta saman kafaɗar ta "kar ki damu sai yayi dana sanin marin da yayi maki har ita munafukar fatimar, Allah dai ya kaimu anjima" lallashin feenah innah tai tayi har sai da taga ta shiru. ✨SHAZIM✨ duk wani shiri da zai masu na tafiya yau ya kammala , shi ka ɗai yake kiɗan sa yake rawar sa, bayan mansoor ba wanda yasan da shirin shi na tafiya yau jira kawai yake su uncle su yi taron su da yamma su kuma su wuce, fatima ce ta fito daga ɗakin ta parlor ta nufo har kan sofar da take kwance, gaishe da shi tayi sannan tace mashi za ta je part ɗin uncle Ibrahim ta ɗauko kayanta,da to ya amsa mata haɗi da ce mata kar ta saki ta daɗe, to tace ta fice zuwa part ko da ta shiga ba kowa a parlor ɗakin sa'ada ta shiga samunta tayi zaune gaban dressing mirror tana shafa powder zama fatimar tayi kan gado tana kallon sa'ada da ke kallonta ta cikin mirrorn "Wai lafiya sister kike kallo na kamar baki sanni ba " "Fatima ai dole na kalle ki, wai daga bari ki ɗauko magani shikenan ko " " wai dama dalilin da yasa kike man wannan kallon ne " "Ok tambaya ta ma kike " ganin kamar ran sa'ada ya ɓaci ne yasa fatima cewa"sorry, ya shazim ne yace na kwana can " "Ok ya jikin na ki " "da sauƙi " "Allah ya ƙara sauki, yau ɗin zaku tafi?" "yanzu ma kaya na nace mashi zan ɗauko" "ok naso ace ya shazim ya bari ko da zuwa gobe ne " "nima naso amma ya zanyi" fira su ka shiga yi duk akan tafiyar da su fatima za su yi sa'ada kamar zata yi kuka, anan fatima tayi wanka , bayan sun shirya ita da sa'ada sallah su kayi batan sun gama ne su ka nufi ɗakin momy , da sallama su ka shiga momy na zaune kan carpet ta gama sallar, jiranta su kayi har ta kammala, fatima tace "ina wuni momy" "lafiya lau fatima, ya jikin ki " "naji sauƙi" "to Allah ya ƙara sauki, kiyi haƙuri kinji" "bakomi momy" "momy wai ya shazim yace zasu tafi, dan Allah kice ya bar fatima nan shi ya tafi " "A'a gara dai su tafi, kuma ma fatimar ba makaranta zata fara zuwa ba " "eh momy amma ai da sauran lokaci " "duk da haka dai " "momy baki son su tsaya ne " "kinci gidan ku " turo baki sa'ada tayi tana faɗin "dan Allah idan kina so su tsaya ki roƙi ya shazim ɗin pls" " sai kuma kiyi" " shikenan momy tun da baza ki ba shi haƙuri ba bari na faɗama dady shi sai ya bashi, dama dady bai san zasu tafi yau ba " ( da yake suna gida shi da uncle Ahmad ) ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi ƙofar fita " kika saki ko ƙafar ki ta taka waje sai ranki ya ɓaci dan baki da hankali bai faɗama dadyn ku ba shine ke zakije ki faɗa mashi kin dawo kin zauna kafin ranki ya ɓaci " da wowa tayi tana turo baki " momy to dan Allah ke ki bashi haƙuri ya barta " "Kima daina yi man magiya,gara su tafi ko itama ta huta " ba yanda sa'ada bata yi ba amma momy tace bazata ce ma shazim ya bar fatima ba, har part ɗin uncle Ahmad su kaje nan ma sai da sa'ada ta roƙi mama kan tasa baki shazim ya bar fatima amma ita ma tace ba ruwan ta, tama fiso su tafi dan sarai tasan halin su gwaggo Uwani a ka bar fatima wahalar su kawai zata sha kafin su tafi. Kamar yanda su uncle Ahmad su kace zasu yi meeting a yau, basu fasa ba yanzu ma haka sun hallara a babban parlorn da su ke meeting, Innah ce kawai sai su gwaggo da su uncle ba yaran, tattaunawa su ka fara daga bisani uncle Ahmad yace ayima Zainab magana tattaro kan ƙannanta, a waya gwaggo Halima ta kira ta, zaman jiran shigowar yaran su kayi,Aunty zainab ce ta fara shigowa sai Aunty maryam da Amina da Asma'u,Farida sai Fiddausi, kairiyya da su fatima ta shigo sa'ada na ɗauke da salma ƙanwar kairiyya ce, feenah da Ilham suka shigo wuri guda matan su ka zauna sai mazan ya usman tare ya shigo da su Anwar, Mahammad, mahmud, luqman, noraiz, faisal, mubarak, Umar, musa harda ƙananan Aliyu da Aminu duka mazan sun hallara mutum biyu ne babu shazim da mansoor, ganin babu su ne uncle Ahmad yace "usman ina sauran ƙannan naka"tun kafin yace wani abu gwaggo Uwani tayi carabtace " na san dai mansoor zai shigo wannan mara mutunci sai dai wani daga cikin ku yaje ya kira shi amma bazai zo ba " gwaggo Halima tace " yaya baki ganin zarau sai kin tsinka, yanzu idan ya shigo ɗin batare da wani ya kira shinba fah " ta buɗe baki kenan zata mai da ma gwaggo Halima amsa, sai ga mansoor ya shigo da sallama a bakin shi shazim na bayan shi, jikin shi sanye da baƙin wando cargo sai t_shirt fara, kallon gwaggo Uwani gwaggo Halima tayi tana faɗin "to yanzu gashi nan ya shigo " tsaki gwaggo Halima tayi batare da tace komi ba, wuri su shazim su ka samu kusa da su usman su ka zauna,uncle Ibrahim ne yace Faisal ya buɗe masu taro da adu'a, tashi Faisal yayi yayi adu'a bayan ya gama ya koma mazunin shi ya zauna,sallama uncle Ahmad ya fara sannan ya ɗaura da nasiha , kowa ya baza kunne yana sauraron shi har ya gama nasihar da ya fara sannan yace " a taƙaice dai maƙasu dun wannan taro ba komi bane face a kan maganar ranar da muka tsaida ce ta auran wasu daga cikin ku, tun tuni munso ace an kammala komi ranar auran kawai muke jira, sai dai hakan bai samu ba dalilin wasu da basu shirya ba a cikin ku muka ɗaga masu ƙafa zuwa wani lokaci, wasu sun gabatar da waɗan da suke so wasun ku kuma har yanzu shiru, yanzu dai munyanke hukuncin tsaida rana ga duk kanku da wanda suka gabatar da wanda su ke so da wanda su kayi kunnan uwar shegu da maganar,dama ɗaya ce zan ba ma wanda basu gabatar da zaɓin su ba tuntuni shine yanzu su gabatar mana, idan ba haka ba zamu zaɓa masa duk wanda ko wacce ta dace " ɗan nisawa uncle Ahmad yayi sannan ya ɗaura da cewa" shazim da mansoor sai faisal ina magan ne a kan ku,tun a wancan lokaci na yi maku magan akan ku gabatar man da zaɓin ku amma shiru, abun da nake so na sani shine baku da raɓine ko kuwa wani abun kuke nufi na da ban, to kun daiji mi nace yanzu idan kuna da magana muna sauraron ku kafin mu zartar da hukuncin da muka yanke, muna sauraron ku " tun da uncle Ahmad ya fara magana su ka sadda kai ƙasa, kowa dake parlorn zuba masu ido yayi domin yaji abun da zasu ce,faisal ne yace " ni ina da wacce nake so " Uncle Ibrahim ne yace "to muna sauraron ka" "uncle dama farida ce " shiru su kayi basu ce komi ba,fiddausi kamar tayi kuka jin mansoor ya ƙicewa komai, shi kuwa mansoor so yake shazim ya gabatar da wacce yake so duk da yasan da wahala , uncle Ibrahim ne yace " muna sauraron ku kunyi shiru,ko kawai mu cigaba da abun da ya tara mu " da sauri Mansoor yace"uncle ni ina da wacce nake so" ajiyar zuciya ta sauke jin yace yana da wacce yake so Uncle Ibrahim yace " to masha Allah kana iya faɗa mana wacece " "dama uncle ba kowa bace Fiddausi ce " murna kamar ta kashe Fiddausi jin mansoor ya ambace ta " to masha Allah" Uncle Ahmad ne yace " to saura kai shazim muna sauraron ka " ɗagowa yayi ya kalli uncle ahmad sai kuma ya sake mai da kanshi ƙasa, tsit kowa yayi jiran abun da shazim zai ce kawai su ke, tsawan 4 minutes shazim baice komi ba "to idan na fahimta har yanzu baka fitar da zaɓin naka ba kenan" sai a sannan ya buɗe baki yace "a'a uncle " "to muna sauraron ka " "ina so a ƙara man lokaci,bayan na su mansoor sai ayi nawa " "wannan ne baka isa ba shazim,da cewa mu ƙara maka lokaci yau kusan shekara kenan, sai yanzu kuma ka sake cewa mu ƙara maka wani lokacin abun da bazi yuwu ba kenan " Uncle Ibrahim ne yace " to yanzu dai munji ra'ayin wasu daga cikin ku,mansoor ya gabatar da Fiddausi a matsayin zaɓin sa faisal farida, Muhammad dama tuntuni mun san ya gabatar mana da kairiyya a matsayin zaɓin sa, to sai wasu da suka nuna ra'ayin yin aure yanzu duk da munfiso mu fara gamawa da manyan su amma tun da sun nuna ra'ayin su na son yin auren yanzu insha Allah za mu yi masu yanda su ke so, kafin nan ina so na sanar da hukuncin da muka yanke akan ga duk wanda bai gabatar da zaɓin shi ba " Uncle Ahmad yace "shazim ina so ka sauraremu da kayau, tun da munce ka fitar da wacce kake so kaƙi, to mun yanke hukuncin haɗa ka aure da ƴar uwar ka hauwa'u " tuna ni shazim ya shiga shin wai wacece hauwa'u cikin yaran dan bai ma san wacece mai wannan sunan ba Uncle Ahmad ne ya katse mashi tunanin da yake ta hanyar cewa " kayi shiru banji kace komi ba " carab innah tace "yo mi zai ce, daga ma anyi mashi gata " "duk da haka innah muna son jin ta bakin shi, ina jinka shazim " shiru kamar bazaice komi ba can dai yace "Uncle bangane wacece kake magana a kanta ba " riƙe haɓa innah tayi tana faɗin "lallai ɗan iskan gaye wato hauwa'un ce baka sani ba saboda ka raina ma mutane wayau ko, to ba kowa bace face takwara ta feenah ince ita ka santa " wani mumunnan faɗuwa gaban shazim yayi,a zuciyar shi yake faɗin " amma an raina mashi wayau arasa da wacce za'a haɗa shi sai wannan daƙiƙiyar yarinyar, lallai sun shiraya ganin ɓacin ranshi kenan" uncle ahmad ne yace "to ka dai ji ko wacece, mi kace a game da hukuncin " banza shazim yayi da shi kamar ma ba da shi yake magana ba, har sai da mansoor ya zungure shi yace "bro ana magana kayi shiru " ɗago da kanshi yayi idanun shi sun kaɗa sunyi jawur tsantsar ɓacin rai ne a cikin su ya wurga ma mansoor wata mummunanar harara wacce tasa mansoor kauda kai dan bai taɓa ganin ɓacin rai a fuskar shazim ba irin na yau, mai da kanshi yayi ya ɗuƙar, gwaggo Uwani tace "yau ga rainin wayau, yan isaka ka ɗauke mu ana magana kayi shiru "wani ɗan iskan kallo ya jefeta da shihar sai da gabanta ya faɗi innah tace " kayi fiye da haka ma mara mutunci, aure ne dai sai kayi " feenah dai sai zare ido take tsoron ta kar shazim yace bai son ta ganin ya mai da su mahaukata ne yasa uncle Ahmad girgiza kai ya cigaba da faɗin"waɗan suka buƙaci a sa ranar da su " ban da murmushi babu abun da ke fita daga fuskar luqman tun kafin ma a kira sunan shi Uncle Ahmad yace "luqman da mahmud muna sauraron ku ku gabatar da zaɓin naku muna ji " jin uncle ya ambace su ne yasa farin cikin luqman ƙaruwa, sai da uncle ya sake magana tukunnan mahmud yace "Ilham itace zaɓin da na kawo maku " "to masha Allah Ilham muna so muji daga bakin ki kinji abun da ɗan uwan ki yace " duƙar da kai Ilham tayi cike da kunya tace " uncle na amince " "masha Allah, Allah ya nuna man lokaci " da ameen kowa ya amsa, sannan uncle ahmad yace "to kai luqman mauna sauraron ka " gyara zama luqman yayi yana kallon Innah da wani munafukin murmushi a fuskar shi yace " uncle ni ba kowa bace zaɓi na face fatima " kamar saukar aradu haka fatima taji maganar luqman, ita yau she harma su ka samu jituwa da zai ce wai yana sonta anya ba kunnuwanta bane suka jiyo mata ba dai dai ba, shazim mamaki abun ya bashi dan shi bai san da wani zacen soyayya ba tsakanin luqman da fatima ba kuma da ace ya sani da tuni yayi ma tufkar hanci amma ko yanzu bawai lokaci ya ƙure bane in dai da ranshi da lafiayar shi zai ga wanda zai masu auren dole, watau meeting ɗin nasu ne ma ke nan dan su aka tara wannan taron kenan maganar uncle Ahmad ce ta dawo da su cikin hayyacin su " to fatima kinji abun da yayan ki yace miye ra'ayin ki " kasa cewa komi fatima tayi sai ma kuka da ta fashe da shi " yau ga iskanci, daga tambaya sai kuka, zaki buɗe baki ki ba mutane amsar tambayar da aka yi maki ko kuwa " gwaggo Uwani ce ta faɗi haka cike da masifa, sake fashewa da kuka Fataim tayi " haba yaya kamata yayi kiji dalilin kukan ta bawai ki rufe ta da masifa ba, zo nan fatima " ta faɗa haɗi da miƙama fatima hannu ta zo kusa da ita, tashi fatima tayi ta nufe ta " yi shiru dai na kuka kinji, miyasa kikayi kuka baki son shi ne " carab innah tace " haba dai wane ita tace bata son shi, ta dai faɗi mi take ma kuka" "dan Allah innah kiyi shiru, idan tace bata son shi ba wanda zai mata dole " acewar uncle ahmad "idan tace bata son shi kenan biye mata zaku yi kenan, idan ba'ayi mata aure ba jiƙata za'ayi a sha " shazim dai na sauraron su dan yayi rantsuwa inda da ranshi babu wan da ya isa yayi mata auren dole kuma ma da wannan sakaran yaron "shi nagani, wallahi ko tana so ko bata so sai ta aure shi tun ba jiƙata za'ayi ba... " katse ta uncle ahmad yayi yana faɗin "ke uwani kar na sake jin bakin ki a nan, kinji na faɗa maki " " a kan mi zaka ce haka amadu, idan ba'ayi mata auran ba mi zata yi ma mutane " tashi fatima tayi ta fita da gudu tana kuka kamar ranta zai fita, tashi luqman yayi ya bi bayan ta ba tare da kowa ya lura da shi ba Shazim yace "idan bata da abun da zata yi maki ke, a kwai waɗan da suke da abun zata yima su, kuma wallahi da raina da lafiya ta babu wanda ya isa yayi mata auren dole " gaban innah ne ya faɗi jin abun da shazim yace,fashewa da kuka innah tayi tana faɗin "ni kake ci ma mutunci a gaban ƴaƴana da jikoki na, saboda baka ganin darajata dan bani na haifi ubanka ba " gwaggo Halima ce tace "kiyi haƙuri mama ki daina kuka, taya zaki ce bai ganin mutunci ki saboda ba ke kika haifi mahaifin shi ba,kin kasa fahimtar shi ne amma..... " bata ƙarasa ba innah tace " yi man shiru ai duk abun da yake aikatawa na lura akwai sa hannunki mara mutunci" uncle Ahmad ne yace " dan Allah innha kiyi haƙuri kiyi shiru " "taya zanyi shiru kuna ganin yaro na ci man mutunci a gaban ku kun kasa ɗaukar mata ki " "Kiyi haƙuri dai dan Allah " ya faɗa haɗi da kallon shazim yace "shazim mu kake faɗa ma haka koh, na lura ka raina innah ko, kenan ba mu isa mu yanke hukuncin ba a kan ku kenan ba" "uncle ba da ku nake ba, amma tun da ta nuna bata son shi a ƙyale ta kawai tun da bawai tayi girman da za'ace ta isa aure ta ƙiyi ba " "ok kai zaka nuna mana abun da ya dace kenan ko " a cewar gwaggo Uwani, banza shazim yayi da ita kamar ba da shi take magana ba, duk abun da ake uncle Ibrahim baice ƙala ba saboda a kan ƴaƴan shi ake magana,bazaka iya gane awane hali yake ciki ba jin su shazim sun nuna basu san ƴaƴan shi. Uncle Ahmad ne yace "to naji ba da mu kake ba,sai ka faɗa man da wanda kake " shiru yayi baice ƙala ba ganin bazai ce komai bane yasa uncle ahmad ɗin cewa " kace babu wanda ya ida yayi mata auren dole,mi kake nufi?" yanzu ma shiru yayi baice komi ba, ɗan nisawa uncle Ahmad yayi yace "to bari kaji hukuncin munriga da munyanke aure babu fashi " "Uncle wannan yarinyar da kuka haɗa ni da ita bana son ta,a yana yin kukan da fatima keyi alama ce ta bata son shi, i dan kuka tursasa dole sai mun bi umarnin ku komai zai iya faruwa " yana gama faɗa ya tashi ya bar parlorn, da idanu kowa dake parlorn ya bishi,tashi feenah tayi zata bi bayan shi sai a lokacin uncle Ibrahim yasa baki tsawa ya daka ma feenah yana faɗin "dawo ki zauna, shashasha banza " innah ta nufa ta faɗa kan jikinta fashewa tayi da wani mahaukacin kuka sai ihu take kamar wacce uwarta ko ubanta ya mutu basu taɓa tunanin shazim zai iya shuka masu rashin mutunci ba irin wannan musamman uncle Ibrahim da ya kasance ƴaƴan shi ne na cikin shi, tashi uncle Ibrahim yayi ya nufi feenah dake jikin innah ya ɗauke ta da wani mumunnan mari haɗi da jan hannun ta ya bar parlorn, bin bayan su innah tayi tana mashi masifa dan mi zai mareta, yarinya na son shi yace bai son ta ya barta da baƙin cikin da ya ƙunsa mata.. gwaggo Uwani ce tace "yaya yanzu kenan haka za'a zuba ma wannan yaron ido yana cima ma mutane mutunci kuma baka ce komai ba " gwaggo Halima tace " mi kike so yace, tunda yace bai sonta a ƙyale shi kowa Allah ya haɗa shi da rabon shi " "dallah sadiya kiyi ma mutane shiru ke dama tuntuni nasan cewa baki tare da mu, hada ke cikin masu zuga wannan yaron " "ni dai komi zakice kice,goyan bayan gaskiya nake, kuma tun da ya nun..... " bata ƙarasa ba uncle Ahmad yace" dan Allah ya isa haka, kowa zai iya tashi ya tafi na sallami kowa " ɗaya bayan ɗaya yaran suka fara ta shi suna fita wasu naji haushin shazim da fatima wasu kuma na ganin yana da gaskiya duba da rashin tarbiya da feenah ke da shi, uncle Ahmad ka ɗai aka bari a parlorn yayi shiru damuwa ƙarara a fuskar shi. _*✨SHAZIM✨*_ Tun da ya bar parlorn part ɗin su ya nufa, bedroom ɗin shi ya shiga trollyn shi da ke bakin gadon shi ya jawo ya kai shi parlor wayar shi ya ciro ya kira noraiz bugu ɗaya noraiz ya ɗauka tunkafin yace wani abu shazim yace ka same ni a ɗaki ƙit ya kashe wayar, bayan kamar 10 seconds noraiz ya shigo da sallama, ko sallamar da yayi shazim bai amsa ba yace "wuce ka ɗauko kayan ka " kwata kwata babu sauƙi a fuskar shazim, da to noraiz ya amsa haɗi da ficewa ya nufi bedroom ɗin shi ya fito da trollyn shi zuwa parking lot da mansoor yaci karo zai shigo part ɗin, ba wanda yace ma ɗan uwan shi wani abu, ciki mansoor ya shiga zuwa ɗakin shazim yana shiga shazim na fitowa hannun shi riƙe da jakar laptop ɗin shi, kayan da ke jikin shi ne ɗazo a jikin shi sai p cap da yasa yanzu da baƙin glass, tsaye mansoor yayi yana kallon shi.......... _Episode 38_39_ ...........Ƙarasa wa ciki mansoor yayi yana kallon shazim sama da ƙasa sanna ya fara magana "shazim ka bani mamaki matuƙa, ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba " "mamaki na baka ko?" "tambayata kake ma " "mansoor idan har baka ga laifin abun da akai man ba bai kamata ni kaga laifina ba " "dole naga laifin ka, a gaban mu fa kake faɗa masu magan son ranka " "sai dai kai ta ganin laifi na amma bazan zauna a tauye man haƙƙina inaji ina gani, mi fatima tayi da za'a yanke mata wannan hukuncin kuma su rasa dawa zasu haɗa ta sai wannan ɗan iskan " "ko da yace yana sonta kaji sun ce zasu aura mata shi ne?" "Koma dai mi ne ne, bazan taɓa bari a ci zalinta ba, kuma ni kaga tafiya ta "yana gama faɗa yaja trollyn shi ya bar mansoor tsaye yana kallon shi, bin bayan shi mansoor yayi a bakin ɗakin fatima shazim ya tsaya tura ƙofar ya shiga tsit ya samu ɗaki alamar ba mutum a ciki, tunani yayi ko ta fita tare da noraiz, fita yayi mansoor na tsaye "wai shazim fushi kake dani ko mi " banza shazim yayi da shi ya nufi stairs case janye da trollyn shi, sake magana mansoor "magana nake maka shazim " "inajin ka, mikake so nace maka ne " " ok haka kace " a taƙaice yace eh, fita su kayi zuwa parking lot aminu ne ya amshi trollyn da ke hannun shazim ya sa a booth, dawowa yayi ya buɗe mashi bayan motar ya shiga rufe ƙofar aminu yayi, mansoor na tsaye bakin part ɗin yana kallon su, noraiz ne ya ƙaraso parking lot ɗin shi da mahmud, tambayar shi shazim yayi ina fatima "tana ɗakin ta " "bata can " noraiz yace " kila tana part ɗin uncle Ibrahim " "mi take a can kuma?" shazim ya tambaya "nima ban sani ba " "to kaje ka kira ta " da to noraiz ya amsa haɗi da juyawa ya nufi part ɗin uncle Ibrahim shi da mahmud,da sallama su ka shiga part tsit main parlorn babu kowa, bedroom ɗin sa'ada suka a bakin ƙofar ɗakin suka tsaya mahmud ne yayi nocking, zaune take bakin bed tana kuka taji ana nocking, tashi tayi ta nufi ƙofar ta buɗe mahmud ne yace " sa'ada kice ma fatima ta fito su tafi " cikin muryar kuka sa'ada tace "ai bata nan, ina tunanin tana ɗakin ga " noraiz yace "bata can " maimaita maganar sa'ada tayi "bata can yaya, to ina ta tafi?" "shine ba mu sani ba, mun ma yi tunanin kuna tare " "ai tun da ta fita a parlor na biyo bayan ta ban san ina ta shiga ba da na zo ɗaki banganta ba sai nayi tunanin ko tana ɗakin ta , to ko dai tana tare da Aunty kairiyya " sa'ada ta faɗa, fita su kayi zuwa part ɗin uncle Ahmad mahmud da sa'ada ne suka shiga part noraiz wurin shazim ya nufa, yana isowa shazim yace "wai ina fatimar ne kasan ƙarfe nawa yanzu " "yaya gata nan zuwa, bata tare da sa'ada ne " ok kawai yace, gaba kusa da driver noraiz ya buɗe ya shiga, mahmud ne ya fito shi da sa'ada wurin su suka nufo tun kafin su ƙara so noraiz yace "tana ina " sa'ada ce tace "can ma bata nan " shazim yace "bata nan" ɗaga mashi kai sa'ada tayi alamar eh, wayar shi ya ciro ya shiga dialing number ta tana ringing amma ba'a ɗauka ba, tsaki shazim yaja yana faɗin "amma sai na ci mutuncin yarinyar nan" sai da yayi mata kusan 5 missed call bata ɗauka ba, ganin dai da gaske fatima ba ɗaga wayar zata yi ba ne yasa shazim cewa "noraiz ku shiga ciki ku duba ta ko tana ɗakin ammy, ko ina dai ku duba ta " da to suka amsa noraiz ya fito su ka nufi part ɗin su, ba inda basu duba har bedroom ɗin shazim dana noraiz ɗin amma ba fatima ba dalilin ta,ne man fatima har part ɗin innah da na su Aunty zainab,su da zasu bi jirgin ƙarfe biyar na yamma sune har aka yi sallar magrib ba su tafi ba suna ne man fatima,abun da ya ɗaga masu hankali ganin wayar ta da suke ta faman kira a main parlorn part ɗin uncle Ibrahim kan sofa sa'ada har ta fara kuka, hankalin shazim yayi ƙololuwar tashi, ina fatima taje. duk wannan bidir da suke na ne manta babu wanda su ka faɗa ma suna ne manta, zaune suka yi a main parlorn part ɗin su shazim kowa yayi ta gumi tunanin kawai suke ina fatima ta shiga, sa'ada kuwa sai kuka take mahmud na lallashin ta,har aka yi sallar isha basu san in da ta shiga ba, tashi sukayi su ka nufi masallaci, sa'ada kuwa part ɗin su ta nufa wurin momy , ko da ta shiga samun momy tayi zaune bakin gado tayi tagumi, damuwa ce ƙarara a fuskar ta, da gudu fatima ta faɗa saman jikin ta tana kuka, ɗago da ita momy tayi tana faɗin "lafiya ke kuma daga ina haka, mi kike ma kuka kuma " cikin shashekar kuka tace "momy ba'aga fatima ba " da sauri momy ta ɗago da fuskar ta tana faɗin "ban gane ba, ina ta je " "momy tun ɗazu muke nemanta ni da su ya shazim ba mu gan ta ba, muna ta kiran wayar ta ashe tana a nan parlor ta barta " dafe kai momy tayi tana faɗin "ya salam, ina taje , kun du ba har part ɗin su innah da na su Auntyn ku?" "eh momy babu inda bamu duba ba amma bata nan" "har ɗakin feenah kin duba " "a'a momy ban duba ba " "to ta shi muje mu duba " ta shi su kayi zuwa ɗakin feenah babu in da basu duba har cikin toilet sai da su ka duba babu almun ta,ɗaya bayan ɗaya duk wani ɗaki da ke part ɗin sai da suka duba amma bata ba alamar ta, date kai momy tayi kamar mai tunanin girgiza kai ta shiga yi tana faɗin " ba gaskiya bane , hakan ma bazata taɓa faruwa ba, idan ko haka ne na shiga uku ni turai " "momy miya faru, miye kuma ba gaskiya ba?" sa'ada ta jefa mata tambayar haɗi da tsare ta da idanu "bakomi sa'ada,kije part ɗin su Kairiyya ku sake duba ta " momy ta faɗa tana nufar part ɗin dady,fita tayi zuwa part ɗin su shazim yan da ta bar su ɗazu zazzaune kan sofa yanzu ma haka ta same su amma ban da shazim "ya noraiz an ganta " girgiza mata kai kawai yayi, fashewa tayi da kuka sai kace ƙaramar yarinya, mahmud ne yace" dan Allah sa'ada kiyi mana shiru, ba ɓacewa tayi ba za'a ganta" ficewa tayi daga part ɗin. Su Asma'u ne zaune a main parlorn part ɗin uncle Ahmad, fira su ke duk a kan meeting ɗin ɗazu da abun da shazim yayi, kowace na tofa albarkacin bakin sa, kairiyya ce ta saukko daga sama part ɗin mansoor hannun ta ɗauke da tray da alama dinner ta kai masa ta shigowa parlor sa'ada na banko ƙofa kamar zata ɓallata ta shigo fuskarta jage jage da hawaye,da sauri su ka juyo suna binta da idanu gaban su sai faɗuwa yake jira kawai suke su ji tace ga wanda ya rasu dan duk a tunanin su mutuwa akayi , sai kuka take ta kasa cewa komi,magana su ka shiga yi mata "ke wai mi akayi ne kike kuka, wani ne ya rasu " sai jefa mata tambayoyi suke amma ta ƙice masu ga abun da take ma kuka, karshe ma part ɗin mansoor ta nufa da gudu, ta shi su kayi suna binta da idanu har ta haye sama, kallon kallo su ka shiga yi ma juna, fitowar shi kenan daga bedroom ɗin shi yaji an banko ƙofar parlor ɗin shi kamar za'a ballata har sai da ya ɗan tsorata da ganin sa'ada idanunta sunyi luhu luhu "ke lafiya daga ina haka " bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma ƙara sautin kukan da tayi, har sai da mansoor ya kwatsa mata tsawa yana faɗin "ke lafiya kike wannan kukan mi a kayi maki " cikin shashekar kuka tace "fatima ce..... " bata ƙarasa ba mansoor ya katse da "fatima ce tayi mi, kiyi magana mi ya samu fatimar " fashewa tayi da kuka tana faɗin "tun ɗazu muke nemanta ba mu ganta ba" tsaki mansoor ya ja yana faɗin "ina fatimar zata je, ki je dai ki sake du bata " "wallahi yaya ba inda ba mu duba ta ba amma ba mu ganta ba ni da su ya shazim " ya salam mansoor ya furta yana faɗin "an kira wayar ta kuwa " "tun ɗazu ya shazim ke kira amma tana ringing ba'a ɗauka " ok bari na zo mansoor ya faɗa haɗi da nufar bedroom ɗin shi da sauri ya tura ƙofar ya shiga, wayar shi da ke kan sofa ya nufa ɗauka yayi ya shiga dialing number fatima tana ringing amma ba'a ɗauka ba kamar yan da sa'ada ta faɗa mashi kusan 5 missed call, ɗan dafe kanshi yayi yana furta "ya Allah " fita yayi daga bedroom ɗin in da ya bar sa'ada a nan ya same ta ƙofar fita parlorn ya nufa bin bayan shi sa'ada tayi, su Asma'u har yanzu suna nan tsaye hankalin su duk a tashe, ganin ya mansoor da sa'ada da sauri kairiyya ta nu fi mansoor tana faɗin "yaya wai mike faruwa ne " ficewa yayi batare da ya bata amsa tambayar da tayi mashi ba ganin haka ne yasa ta jawo hannun sa'ada tana faɗin " sa'ada wai mike faruwa ne " "ya kairiyya fatima ce ake nema ba'a ganta ba " dafe ƙirji kairiyya tayi tana faɗin "ba'a ganta ba " "Eh, tun ɗazu muke nemanta ni da su ya mahmud amma bamu ganta ba, ko ɗazu da na shigo nan ita muke ne ma" Asma'u da Amina har haɗa baki su ke wurin jan tsaki da faɗin "aikin banza kawai saboda kawai ba'a ganta ba zaki wani shigo ma mutane kamar wacce wani nata ya rasu " mutsww su ka sake jan tsaki, kairiyya ce tace " amma nayi mamakin abun da ya fito daga bakin ku wallahi, haba Aunty Asma'u cewa tayi fa tun ɗazu ake nemanta ba'a ganta ba " Amina ce tace "ke kairiyya ki kam kan ki, ko cewa tayi ta mutu ina ruwan mu " kairiyya tace "wallahi ku dai canza dan wannan ba rayuwa ba ce " hayayyaƙo mata su kayi da masifa Fiddausi tace "gaskiya fa ta faɗa ko da ace ba ƴar uwar ku ba ai ita muslma ce bare jinin ku ɗaya da ita, gaskiya ku gyara " kallon juna su kayi suna faɗin "yau ga ƴan isakan yara wa'azi za ku yi mana " kairiyya tace " ba wa'azi za muyi maku ba gaskiya ce muke faɗa maku " "to ba mu so " a cewar Amina, jan hannun sa'ada kairiyya tayi su ka bar part ɗin zuwa part ɗin innah wurin gwaggo Halima, ita ka ɗai suka samu a part ɗin gwaggo Uwani da innah ba su nan, suna asibiti wurin feenah data yanke jiki ta suma lokacin da uncle Ibrahim ya fitar da ita daga parlorn da suka yi meeting ɗazu, abun dake faruwa su ka faɗa mata,sosai hankalin ta ya tashi, wayar ta ta ɗauka ta shiga dialing number uncle Ahmad da yake shima bai nan yana tare da su innah , korma uncle Ahmad bayani tayi akan abun da yake faruwa, sosai ya nuna tashin hankalin shi, tamabayar gwaggo Halima yayi "ina su shazim ɗin su ke " "ina jin suna part ɗin su, nima su kairiyya ne suke faɗa man abun da ke faruwa " "ok gani nan zuwa " ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran. "ga Abban ku nan zuwa, amma da mamaki abun ina zata nufa, ku tashi muje, ke sa'ada je kikira man usman kice ya same ni a nan part ɗin " da to ta amsa haɗi da tashi ta fita. Lokacin da mansoor ya fita part ɗin su shazim ya nufa, noraiz ya samu a parlor mahmud ya fita, tambayar shi yayi "ina shazim ɗin" amsa noraiz ya bashi da "ya shiga ciki yanzu " ok kawai mansoor yace haɗi da nufar sama part ɗin shazim,ba nocking ba komai ya tura ƙofar da ƙarfi ya shiga ɗago da idu shazim yayi jin yanda mansoor ya shigo kamar an jeho shi da idanu shazim ke binshi, magana ya fara "yanzu dan wulaƙanci shazim ace kun nemi fatima baku ganta ba amma ka kasa faɗa man sai da sa'ada ta faɗa man, wai wannan haushin nawa da kake ji na minene" "dan Allah ka barni naji da abun da yake damu na" "ok abun da ke damun ka ko " "haba dan Allah kaine da wata magana, yanzu fa nake shirin kiran ka sai gaka ka shigo " "uhmm" kawai mansoor yace sannan yace "to ina ta tafi " "nima ban sani ba, bawani wuri ta sani ba bare nayi tunanin ko tana can" dan jinjina kai mansoor yayi yana faɗin " haka ne gaskiya" can kuma ya matso kusa da shi ya zauna yana faɗin "ɗan kira number a hashim kaji ko fatima taje gidan su" wani kallo shazim yayi mashi " ban gane ba, mi zai kai fatima gidan a wannan lokacin " "dan Allah dai ka kira shi " "ni bazan kira shi ba, kai mi zai hana ka kira shi " mansoor yace " kai matsalata da kai kenan, to bani wayar ka na kira shi tun da baza ka kira shi" ɗaukar wayar yayi ya shiga kiran number A Hashim, bugu biyu yayi picking ko sallamar da yake mashi bai amsa ba yace "Fatima na tare da kai?" "Fatima kuma?" a hasale shazim yace "taya ina tambayar ka kana tambayata" "ba dole na tambaye ka ba, ni yau she rabon da naga Fatima,in ba ma rainin wayau ba a wannan lokacin zaka tambaye ni fatima " har ya ɓuɗe baki zai yi magana mansoor ya fisge wayar dan ya san abun na iya koma masu faɗa, kara wayar yayi a kunne yana faɗin "sorry Abdallah, ka gane neman ta muke ne, an kira wayar ta bata yi picking ba tun ɗazu mu ke neman ta , shine sai nayi tunanin ko tazo gidan uncle ne wurin Ameera" hankalin A Hashim yayi matuƙar tashi jin ya ce ba'aga Fatima ba, cikin tsantsan tashin hankali yace "amma ina taje mansoor " "wallahi shine ba mu sani ba" Abdallah yace "ya ilahi" haka kawai ya ce haɗi da yin rejecting ɗin kiran, ta shi mansoor yayi ya fita daga parlorn ya nufi main parlor, yan da ya bar Noraiz haka ya same shi har da mahmud da ya shigo yanz, gwaggo Halima ce ta shigo ita da kairiyya da sa'ada sai usman , har time ɗin kuka sa'ada keyi, kairiyya na lallashin ta, kusa da su mansoor ya matsa, haƙuri ya shiga ba ta akan insha Allah za'a ganta, fitowa shazim yayi bedroom ɗin shima ya nufo main parlor wuri ya samu kusa da noraiz ya zauna, ya usman ne yace " shazim tun yaushe ne kuka duba baku ganta ba " "tun fitar da tayi ɗazu da ana meeting, nayi tunanin ko tana nan ɗakin ta ko wurin sa'ada " "ya salam" ya usman ya furta haɗi da cewa "amma ba inda kake tunanin zata " "ina zata je yaya bayan ba wanda ta sani abuja " kallon sa'ada ya usman yayi "ke sa'ada kin kira ƙawayen ki ko taje wurin wata daga cikin su " "yaya ai ni bana da ƙawaye,kuma ma tun da tazo gidan su momy kaɗai muka je sai gidan uncle ɗin ya Abdallah " "waye kuma Abdallah "ya usman ya tambaya, mansoor ne yace "wani course mate ɗin shazim ne kuma ma mun kira shi bata can " shiru sukayi ba wanda yasake cewa komai, kowa na tunanin inda ta shiga, shazim kuwa alƙawari ya ɗauka duk abun ya same ta wallahi bazai ƙyale kowa dake cikin estate ɗin ba tunda ai sune silar shigarta wannan halin har tasa ƙafa ta bar estate ɗin, damuwarshi yanzu shine ina taje awane hali take dan yasan duk in da take zai yi wuya ace ciwanta bai tashi ba, ya usman ya tashi yana faɗin "ina zuwa wannan zaman bazai mana maganin komi ba " tashi ita ma gwaggo Halima tayi "haka ne usman bazama ya kamat muyi ba " tashi su kayi duk suka fita aka bar mansoor da shazim mansoor yace "ina mamakin inda taje, to wai mi zai sa ta bar estate ɗin nan" shazim yace " wallahi muddin wani abu ya sameta ran kowa sai ya ɓaci " shiru kawai mansoor yayi baice komi ba, can kuma sai yace "yo wai ma an tambayi security ko sunga fitar ta " sai da mansoor yayi maganar sannan hankalin shazim ya kai ga nan "hakane kuma mansoor wallahi ni duk banyi wannan tunanin ba " "idan tafita dole zasu ganta ko da ta ƙaramin gate ta fita, tashi mu tafi " mansoor ya faɗa haɗi da ɗaukar wayar shi su ka fita zuwa main gate da ya usman suka ci karo shima main gate ɗin ya nufa, a tare suka ƙara sa, securityn na zaune kan benchi da suke zama,su ƙara so inda su ke, gaishe da su security su kayi a taƙaicw suka amsa masu mansoor na faɗin " tambayar ku muke son yi" babban cikin su ne yace "Allah yasa mun sani yallabai " a hassale shazim yace " kunga ficewar fatima " "gaskiya yallabai ba muga fitar ta ba, motar Alhaji ce kawai ta fita shi da su innah in ba dai atare da su ta fita ba " Mansoor yace "kun tabbata baku ga ficewar ta ba, kuma bawani driver da ya fita da mota " "gaskiya babu, bayan Alhaji Ahmad ba wanda ya fita da mota " wuce wa shazim yayi batare da ya jira su mansoor ɗin ba, juyo suka yi suma zasu bi bayan shi sai ga mota ta nufo main gate daga waje, tsayawa su kayi dan suga waye, ɗaya daga cikin security ne ya nufi motar ba kowa bane face ya Abdallah ya kasa zama hankalin shi ya ƙi kwanciya tun da aka ce ba'aga fatima ba, izinin shiga ciki security ya bashi, ciki ya shigo ganin su mansoor ne yasa shi tsayawa wurin su sai da yayi parking sannan mansoor ya gane shi, mansoor ce mashi yayi" ya shiga ciki kawai shazim ma yanzu ya wuce" ciki ya shiga yayi parking a parking lot, part ɗin kawai ya nufa , tsaye ya samu shazim a parlor, gaba ɗaya hankalin Abdallah a tshe yake tsare shazim yayi da tambayar ina taje ne Fatimar, amsa kawai shazim ya bashi da bai saniba, gashi malam da Ammy sai kiran shi su ke yace zasu dawo yau gashi har dare yayi babu su babu labarin su. Sa'ada lokacin da suka fita daga part su shazim part ɗin su ta nufa, ta shiga bedroom ɗin momy ta shiga bata same ta ba tunawa da tayi ɗazu momy part dady ta nufa ne yasa fita ta nufi part ɗin dady, tunkafin tashiga ta fara jin muryar momy tana faɗin "amma ban taɓa tunanin baka da hankali ba luqman sai yau, dama ashe shashasha ne kai ban sani" muryar dady taji yana faɗin "dan Allah ki daina ɗaga murya turai " "ok in daina ɗaga murya ko.... " bata ƙarasa ba saboda tura ƙofar da sa'ada tayi ta shiga tsaye ta samu momy da dady sai luqman da ke zaune kan sofa jikin shi sai rawa yake kamar wanda zazzaɓi yayi ma mugun kamu,jin anturo kofa ne yasa shi tashi da gudu ya nifi bedroom dady,ganin sa'ada ce yasa shi tsayawa yana haki kamar wanda yayi wasan tsere, dady ne yace "ke kuma daga ina haka " "dady fatima fa ake nema ba'a ganta ba " "to naji fita ki bamu wuri" " dady amm..... " bata ƙarasa ba ta dalilin tsawar da dady ya daka mata yana faɗin "nace fita ko so kike sai ranki ya ɓacin" ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu......... _Episode 40_41_ ............ba shiri ta fita, amma sai ta ƙi tafiya ta tsaya tana sauraron mi suke cewa, bana ji mi take ji naga dai taja baya da sauri tana kallon ƙofar can kuma ta fita dagu tana kuka, bedroom ɗinta ta nufa tana shiga ta faɗa kan bed fashewa tayi da wani matsanancin kuka, kuka take kamar ranta zai fita sai birgima take kan bed ɗin tana faɗin "wayyo Allah nah, Allah kasa abun da kunnuwana suka jiman ba gaskiya bane, idan har haka ta kasance bazan taɓa yafe maka ya luqman " sai kuka take tana ta roƙwan Allah yasa ba gaskiya bane tashiga tashin hankali da jin abun da su dady ke tattaunawa sai ta baka tausayi yan da ta dage tana rokwan Allah yasa ba gaskiya bane,can kamar an tsikareta ta tashi ta fita daga bedroom ɗin da gudu ta nufi sama part ɗin dady har tasa hannu zata buɗe ƙofar part sai aka turo ƙofar dady ne sai momy dake bayan shi da kaganta kasan tana cikin damuwa idanun ta duk sun kumbura ba ƙaramin kuka tasha ba,tsaye su kayi suna kallonta sai kuka take dady ne yace "wai wannan kukan da kike na minene, miya dawo da ke nan ba nace ki wuce ba " ƙara sautin kukan tayi ba'a ma jin mi takecewa sosai " dady ƴar uwata " "dan Allah kiyi haƙuri sa'ada za'a ganta yanzu ma wurin su shazim ɗin zan tafi, kiyi shiru kinji" ya faɗa cikin sigar lallashi "to dady, amma maganar wa naji kunayi, wacce ya luqman....... " bata ƙarasa ba dady ya katseta ta hanyar daka mata tsawa" wai ke wace irin yarinya ce sa'ada, nace maki za'a ganta kuma maganar da kike cewa munayi ba'a kanta bane, ki kwantar da hankalin ki " ya ƙarasa maganar yana lallashin ta " amma dady dan Allah ka bari naga ko wacece pls " "miyasa baki jin magana ne sa'ada, wuce ki tafi bedroom ɗin ki ki kwanta kar ki haddasa ma kanki ciwan kai kinji za'aga fatima " fashe tayi da kuka "ni dai dady ka bari naga ko wacece " tsawa ya daka mata "ina wasa da ke ne, ko ki bar wurinnan ko ranki ya ɓaci shashasha" hawayen da momy ki ɓoye wa ne suka zubu "wallahi Alhaji in jiye maku abun da zai biyo baya da luqm" dady yace "dan Allah turai kiyi man shiru, kija ta ku bar nan wurin " "dole na faɗi haka Alhaji, an cuc..... " bata ƙarasa ba dady ya dakatar da ita ta hanyar cewa "wai miyasa kike da taurin kai ne turai, nace ki jata ku bar nan " jan hannun sa'ada tayi tana faɗin "zo nan kinji kiyi haƙuri ki daina kuka, kinji jikin ki harya ɗauki zafi " momy ta faɗa haɗi da jan hannunta, fisgewa sa'ada tayi ta nufi ƙofar zata buɗe, da sauri dady ya fisgota ɗauke ta yayi da wani mumunnan mari har sau biyu, tangal tangal tafara zata faɗi ƙasa, fa sauri momy ta taro ta zuwa jikinta ta rugume ta tana kuka " kijata ku bar nan" "ba inda zan kai tai, ku faɗa ma yara in da ƴar uwar su take, ko wallahi naje na kira su duk abun da zai biyo baya ya daɗe bai biyo baya ba " "turai haka kika ce, kin kuwa san mi kike faɗa kuwa, kina cikin hankalin ki kuwa" "cikin hankali na nake, nasan mi nake, wannan ai zalunci ne " tana gama faɗa ta ɗago da kan sa'ada tana faɗin "sa'ada tashi ki kira man mansoor ko shazim " shiru sa'ada bata amsa ba bakuma ta motsa ba, ashe tun marin da dady yayi mata momy ta tare ta suma tayi batare da sun sani ba, da sauri momy ta ɗago ta kalli dady tana faɗin " ta suma Alhaji, Innalillahi" ta faɗa tana bubuga ta tana faɗin "tashi kinji, dan Allah ki tashi " momy gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, key dady yasa ma part ɗin shi ya rufe ya yafita ya bar momy da sa'ada durƙushe a ƙasa momy sai kuka take,daƙyar ta samu ta ɗauki sa'ada ta nufi ɗakinta da ita, kwantar da ita tayi kan bed sannan ta nufi dressing mirror ɗakin ta ɗauki jirkar ruwan da take ajiye wa duk dare, a hannu ta tarfa ruwan ta nufi fuskar sa'ada ta yayyafa mata sai da ta sake yayyafa mata sannnan ta ja wani dogon numfashi,Alhmdllh momy ta furta hadi da kiran sunan sa'ada, jin muryar momy ne yasa ta tashi zambur kamar wacce aka zungura " momy ina fatima, ina ƴar uwata take, momy dan Allah ki faɗa man in da take " ta ƙarashe maganar tana kuka "kiyi haƙuri sa'ada ƴar uwar ki bata ɓata ba kiyi shiru kijin, kar ki ja ma kanki ciwo " "amma wacece a part ɗin dady naji kuna faɗin ya luqman yayi raping" da ta faɗi haka har sai da gaban momy ya faɗi " momy kinyi shiru,idan har ba ƴar uwata bace pls momy wacece " hawaye ne suka taru a fuskar momy, girgiza mata kai tayi " sa'ada nima ban san wacece ba, dadyn ku yaƙi bari naga ko wacece " "momy amma a ɗakin na same ki pls momy ki faɗa man " shiru momy tayi batace mata ƙala ba, tana son kowa ya san halin da ake ciki amma ta tsoron wane irin hukunci luqman zai fuskanta take, ganin tayi shirune yasa sa'ada faɗin "momy ki faɗa man, ko naje na kira ya shazim da ya mansoor su zo su ɓalle ƙofar ɗakin dady " "sa'ada karki kira su ba fatima bace " "idan har banga kowa cece ba hankalina bazi taɓa kwanciya ba" tana gama faɗa ta fice daga ɗaki da gudu,k'wala mata kira momy ta shiga yi tana fad'in ta dawo ,amma ina ko wai wayen momy bata yi ba , fashewa momy tayi da kuka "ya Allah ka kawo sassauci a wannan lamarin ya Allah " sa'ada ɗakin momy ta faɗa dagu ta maida ƙofar ta rufe, wani sabon kukan ta sake fashewa da shi, sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta kamar wacce ciwan hauka ya kama hau buɗe buɗen drawer's tana neman extra key's gaba ɗaya ta hargitsa ma momy ɗaki ta hauka ta shi kayan ta da ke cikin wardrobe duk ta watso su ƙasa, har da su ɗaga mattress sai nishi take ta haɗa uban gumi amma bata gan su ba fitar da rai tayi da ganin su sai hawaye take kayan da ta watso ta fara kwashe wa tana mai dawa cikin wardrobe,sai da kwashe su tasa ta maida ta rufe wardrobe ɗin, zama tayi ƙasa dirshan tana share hawayen dake ta zarya a kumatun ta, tazo tashi kenan zata fita idanun ta suka sauka akan keys ɗin da take ta wahalar nema, ashe wajen watso kaya ta watso da su batare da ta sani ba , ɗaukar keys ɗin tayi ta fice da sauri. Dady na fita daga part ,part d'in uncle Ahmad ya nufa ,a parlor ya same shi shida su mansoor da ya usman ,noraiz ,mahmud sai gwaggo halima da mama ,sunyi jugum jugum,kowa hankalin shi tashe yake da rashin ganin fatima, ya usman ya yanke shawarar kiran police ya sanar da su halin da ake ciki , Abba ne yace kana ganin za su zo,na ga dare yayi kuma ka san yana yin jami'an tsaron k'asar nan yan da su ke" "haka ne Abba,ai wanda zan kira aboki na ne kuma nan kusa office d'in su yake " "to shikenan " Abba ya fad'a, ya d'aga waya kenan zai kira su sai ga dady ya shigo ,fasa kiran yayi,amsa mashi sallamar da yayi su kayi ,wurin su dady ya k'ara so ,Abba ne yace " wai dama kana nan?, amma dai baka san mike faruwa bane ko?" Dady yace "na sani ,akan maganar ne ma nake son mutattauna" " in taso ne " da eh dady ya bashi amsa had'i da juyawa ya fita ,bin bayan shi Abba yayi, garden su ka nufa ,zama su kayi akan kujerun dake wurin ,shiru dady yayi bai ce komai ba har sai da Abba yace " kace za muyi magana mun kuma zo kayi shiru ,ina fatan dai lafiya ,d'an nisawa dady yayi sannan ya fara magana "yaya kasan halin yaronann luqman bai da hankali koko alama ..." sai kuma yayi shiru, ganin yayi shiru ne yasa Abba da sauri yace " kayi shiru kuma mi luqman yayi ,kar dai kace man duk neman yarinyar nan da ake luqman ne ya d'auke ta?" "da ace d'auke ta yayi yaya ai da sauki , saboda bai da hankali bai san in da ke mashi ciwo ba k'okarin yi mata fyade ya so saboda kawai ta nuna bata son shi " zanbur Abba ya mike yana fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un ,dama yaron nan bai da hankali ban sani ba ,amma Ibrahim miyasa tun d'azun baka sanar da ni ba, yanzu tana ina" "tana bedroom ɗina, na so tun lukacin na sanar dakai ,amma ganin kuna asibiti ne yasa ban sanar da kai ba" "haba Ibrahim idan bana nan ka kirani ai dole na dawo ,kuma ai da ka sanar da shazim ,yanzu idan ya san cewa tun d'azu tana part d'in ka ,mi kake tuna nin zai biyo baya ,kana gani d'azu cewa kawai fa yayi yana son ta amma ji irin bacin da ranshi yayi da maganganun da ya fad'ama," "wallahi yaya tsoron irin hukuncin da zai ma luqman ne yasa ban sanar da shi ba " "ai da ko mansoor ka fad'a mawa shi zai iya controling d'inshi ko halima, da sai su kai ta hospital adu bata ,amma yanazu ba k'aramin kuskure kayi ba na kin fad'a tun d'azu " "ya salam amma yaya minene ma fita " "mafita d'aya ce a sanar da shi halinda take ciki " "amma yaya yana iya illata luqman da duka " "to koma mi zai mashi ai shi ya ja tun da bashi da hankali ,kuma zamu k'i fad'a ne saboda kar ya hukunta shi, kuma idan mu kayi haka ba muyima yarinyar nan adalci ba kamar yan da luqman yake a wurin haka take a wurin mu " "hakane, bari na kira dr sai ta zo ta du bata " dady ya faɗa haɗi da ciro wayar shi daga aljihu yayi dialing number dr su. _*✨SHAZIM✨*_ "Shazim ni ina mamkin in da fatima zata je ,ko ina a estate d'innan kun du ba kuwa " a cewar Abdallah d'agowa shazim yayi yana fad'in "duk in da nake tunanin zata iya shiga mun duba amma ba mu ganta ba" "gaskiya abun nan da mamaki ,tun da dai ba inda zata je,nifa zargi nake tana cikin estate d'innan" d'an nisawa shazim yayi had'i da cewa" nima zargina kenan,sai dai duk inda nake tunanin zata iya shiga ko za'a iya kaita sai da na duba,dan na daina tunanin wani wuri ta tafi yanzu nafi zargin sace ta akayi " "abun da kawai ya kamata yanzu shine mu kira police kawai dan wannan zaman da muke bawai zai amfana ma wani abun arzik'i bane ,amma ya ka gani" "gaskiya wannan itace mafita kawai " Abdallah wayar sa daya d'aura kan hannun sofa ya d'auka ,number wani police abokin uncle ahmad yayi dialing Mansoor ne ya shigo part ɗin wuri ya samu kan sofa kusa da Abdallah ya zauna, kallon shi Abdallah yayi yana faɗin " mansoor har yanzu ba wani labari " " "babu Abdallah,gashi tun ɗazu ya usman ya kira wani abokin shi police amma har yanzu baizo ba, na rasa gane lamarin ƙasar nan " "sai haƙuri, nima yanzu na kira wani abokin uncle na san shi insha Allah zai zo " " Allah yasa " Mansoor ya faɗa, shazim dai na gefe yana jinsu baice ƙalaba wayar sa ce tayi ringing , dafe kai yana faɗin " ya Allah, wallahi na rantse duk wanda na kama da sa hannun shi hmmm... " kawai yace ba tare da ya ƙarasa ba, kiran ne ya sake shigowa wayar mansoor ne yace "idan bazaka ɗauka ba ka kawo na ɗauka, dan rashin ɗaukar ka shi zai ƙara jefa su cikin tashin hankali " "idan na ɗauka mi zance masu mansoor?, idan har su ka sani hankalin su sai ya fi tashi akan wanda suke ciki yanzu saboda rashin ɗaukar kiran su da banyi ba " "duk da haka shazim da ka ɗauka sai kace masu kun fasa dawowa ne yau, amma hakan zai sa su cikin tashin hankali matuƙa " "uhmmm " kawai yace suna nan zaune jigum sa'ada ta bankaɗo ƙofa ta shigo har tana tuntuɓe tana shirin faɗuwa,sai haki take kamar wacce wani abun tsoro ya biyo, fuskar ta sharkaf da zufa mansoor ne ya taso da sauri yana faɗin "wai miyasa ba zaki zauna wuri ɗaya bane sa'ada , ji yan da ki ka shigo kina shirin illata kanki, yanzu miya ya dawo da ke nan" sai haki take maganar ta ma da kyar take fita "yaya dama.... " maganar ce ta sarƙe mata sai sauke numfashi take "dan Allah ki kwantar da hankalin ki kiyi man baya nin abun da ke faruwa " bata ba shi amsar tambayar sai ma nufar shazim da tayi da sauri, keys ɗin dake hannun ta miƙa mashi tana "ya shazim gashi " ɗagowa yayi yana kallon ta "key ɗin ɗakin dady fatima na can " kamar saukar aradu haka su ka ji maganar ta mansoor da Abdallah da sauri suka nufe ta suna faɗin "da gaske kike sa'ada " ɗaga masu kai tayi tana faɗin " eh yaya da gaske nake tana can ita da ya luqman " "luqman kuma?, kin tabbata sa'ada? " "yaya fatima ce fa, wallahi tana can " "ya Allah, amma mi ya kaita can mi ta ke yi tare da luqman a ɗakin uncle" ƙarar rufe ƙofa su kaji da sauri ko wannen su ya kalli ƙofar basu ga kowa ba mansoor ne yace "shazim tashi mu je.... " bai ƙarasa ba ganin sofar wayam ba kowa, basu san da ya bar wurin ba sai yanzu su ka fahimci cewa ashe rufe ƙofar da suka ji shi ne ya fita, ba yan sa suka bi da sauri ko da suka fita ko mai kama da shi basu gani ba a compound, zuciyar mansoor sai bugawa take yana tsoron abun da shazim zai yima luqman,da sauri suka isa part ɗin direct sama suka nufa shazim har ya shige ya maida ƙofar da key ya rufe, bubbuga ƙofar su ka shiga yi suna kiran sunan shi amma ko motsin shi basu ji ba bare su sa ran zai buɗe masu, sai haɗa shi da Allah mansoor yake akan ya buɗe masu amma shiru. Lokacin da ya shiga parlorn ba kowa hakan ya sa shi wu cewa bedroom ɗin dady tura ƙofar yayi ya shiga, kwance ya hangi fatima kamar matatta an rufe mata rabin jikinta da blanket, ƙara sawa yayi bakin gadon saitin in da fuskar ta take,sai fitar da numfashin wahala take kanta ko ɗan kwali babu sumar kanta duk a ya mutse fuskara tayi fayau da ita bakin ta ya bushe ƙamas duk ya faffashe goshinta ma a fashe yake da gefan bakin ta fuskar ta tayi jawur , siraran hawaye ne ke fita daga gefen idanuwanta da suka kumbura su kayi suntum,wuyan ta da ƙirjinta duk sawun ya kushi, sai jan numfashi take da ƙyar ta fitarwa, wasu zafafan hawaye ne suka taru a idon shi zuciyar shi sa ta farfasa take, hannu biyu yasa zai ɗauke ta ƙarar buɗe ƙofa da yaji ne yasa shi juyawa dan ganin wanene ya shigo, ido biyu su kayi shida luqman da ke tsaye bakin ƙofar bathroom ɗin dady daga shi sai bathrobe, tun ɗazu yake cikin toilet ɗin jin motsin mutum ne yasa shi fitowa duk a tunanin shi dady, ai kuwa yayi daya sanin fitowa, wani mumunnan faɗi gaban shi yayi ganin wanda bai yi tsammani ba da sauri ya juya zai koma toilet ɗin sai kafin ya ja ƙofa ya rufe tuni shazim ya cimma sa, roƙwanshi ya fara akan dan Allah yayi mashi haƙuri wallahi ba da gangan yayi mata haka ba, kuma ba abun da yayi mata " sai magiya yake mashi amma ina shazim bai ma san yana yi ba, buga mashi kai yayi da bango nan take goshin shi ya fashe ya fara zubar da jini, wani wahalallen ihu luqman ya saki yana cigaba da rokwan shi da yayi mashi afuwa bazai sake naushi shazim ya kaima bakin shi dake yake rokwan na shi,naushin shi ya shiga yi ta ko ina yana buga mashi kai da bango tun luqman na da bakin bashi haƙuri har ta kai muryar shi bata fita saboda azaba. Su mansoor na bakin ƙofar part ɗin suna aiki bugawa da roƙon shazim akan karyayi ma luqman wani abu amma ko alamar yana jin su basu jiba, hankalin su duk ya tashi akan halin da luqman yake ciki, sa'ada sai kuka take tana kiran sunan luqman da fatima, momy ma sai kuka take tana ro kwan shazim karya kashe luqman, ganin da gaske shazim ba jinsu yake ba yasa momy fita da part ɗin a hargitse ta nufi part ɗin uncle Ahmad kamar an jeho ta haka ta faɗo cikin parlorn su mama da gwaggo Halima da su ya usman da sauri suka miƙe cikin tashin hankali su ke tambayar ta lafiya, momy sai hawaye take ta nuna masu bayan ta bayan nata suka kalla su basu ga komai ba, sai da ƙyar ta samu ta kalmomin " sha zi m zai ka sh e luqman " ta ƙarasa maganar a rarrabe,salati gwaggo halima ta rabka tana faɗin " na shiga uku ni halima, mi ya haɗa su kuma Innalillahi " da sauri su ya usman suka nufi part ɗin su momyn, bin bayan su su mama su kayi momy sai sharar hawaye take, a bakin ƙofar part ɗin suka tsaya suma su ka hau bubbuga ƙofar suna rokwan shazim da ya buɗe amma ina ya usman ne yace su sa ƙarfi kawai su ɓalla ƙofar kawai dan ko zasu kwana a nan shazim ba wai zai buɗe masu bane har sai ya fitar da mansoor daga hayyacin sa, haka su kai ta ƙoƙarin ɓalla ƙofar, duk wanna budirin da ake dady da Abba suna garden jiran dr basu san mike wakana ba, ba irin ƙoƙarin da su mansoor basu yi ba ganin ƙofar ta buɗu amma ina, momy ce tace mahmud yaje ya kira su dady a kwai key a jikin shi, da sauri luqman ya tafi kiran su, su kuma su mansoor na ta aikin ɓalla ƙofar yayin da Abdallah yake sake kiran number wannan police ɗin dan yaga sun jima basu zo ba gashi ana shirin kisan kai. sai ga dady da Abbah sun shigo hankali a tashe da sauri dady ya nufi ƙofar yana ciro key ɗin dake aljihun shi matsawa su mansoor su kayi suna bashi wuri key ɗin yasa ya shiga kiciniyar buɗe ƙofar amma ina ta ƙi buɗuwa saboda key da shazim ya bari jikin ƙofar da ya shiga, kuma yayi hakan ne dan kar ma su samu sa'ar buɗer ƙofar Shazim sai da yayi mashi lilis duk ya farfasa mashi goshi da bakin shi shaƙe mashi wuya yayi har sai da yaga baya motsi ko ɗan yatsa baya iya motsawa tukun ya sake shi ya faɗi ƙasa yarab ba numfashi, bai bi ta kanshi ba ya nufi gadon da fatima take hannu biyu yasa ya ɗauke ta irin ɗaukar da ake yima jarirai ya fice da ita yana zuwa bakin ƙofar su mansoor na samun nasarar ɓalleta suka shigo da sauri ganin shi da fatimar ne yasa suka nufe shi sa'ada da sauri da shigo tana kuka haɗi da cewa "ƴar uwata miya same ki, ya shazim naga kamar bata numfashi " sai tambayar shi suke wane hali take ciki dan ganin fatima. ya sa sun man da luqman da ke can yashe a bedroom ɗin dady, dadyn kawai ya nufi bedroom ɗin da sauri har sai da gaban ya faɗi da yayi arba da luqman yashe a ƙasa babu alamar ma yana numfashi, bayan shi Abba ya biyo da sauri shima ya ja burki ya tsaya yana bin luqman da ke kwance ƙasa, kuka ne ya kubce ma dady yana faɗin "luqman dan Allah ka tashi kar ka mutum, dan Allah na roƙe ka katashi " sai jijjiga shi dady yake yana roƙwanshi da ya tashi amma ina ko motsi wannan bai yi ba Abba ne ya ƙaraso kusa da su dafa kafaɗar dady yayi " Ibrahim ai shuma yayi " sai a lokacin dady ya lura da cewa suma luqman ɗin yayi jiyawa Abba yayi ya nufi toilet ya ɗebo ruwa yazo ya yayyafa ma shi a fuska a firgice luqman ya farka sai sambatu yake yana faɗin "dan Allah ya shazim kayi haƙuri wallahi babu abun da nayi mata, dan kar ka kashe ni wallahi bazan sake ba plea.... " da sauri dady ya kira sunan shi, zambur luqman ya miƙe zai nufi toilet dan duk a tunanin shi shazim ne tashin farko bai gane muryar dady bace sai da Abba yace "dawo luqman ina zaka ba shazim bane mune " sannan luqman ya tsaya yana sauke numfashi da sauri ya nufi dady yayi hugging ɗinsa fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro "dady ya shazim kashe ni yaso yi, baya ƙaunata sai ce mashi nake ba abun da nayi mata amma sai da ya dake ni , miyasa ka bar shi ya shi go " dady yace "luqman duk laifin ka ne, yanzu ai kaga irin abun da nake guje maka ko " "dady wallahi ban yi mata komai ba, Allah bazan sake ba, dan Allah kar ka bari ya raba ni da ita wallahi ina son ta " "kama dai na faɗar haka luqman dan yanzo ko mutuwa zaka yi shazim bazai taɓa bari ka aureta ba ba shi kaɗai ba har ita kanta fatimar da su Aisha " "dan Allah dady" Uncle Ahmad ne yace "ya isa haka, zo muje mansoor ya duba ka ko mu tafi asibiti goshin ka da bakin ka sai zubar da jini su ke " "Abba banzan iya zuwa wurin ya mansoor ba nasan shima fushi yake da ni kuma ina tsoron na fita mu sake haɗuwa da ya shazim, momy dai ta zo nan ta duba ni " hannun shi Abba ya jawo "zo mutafi ba abun da zai sake yi maka ai ina tare da kai " "ni dai momy nake so ta duba ni" "to shikenan zo mu tafi " duk da yace haka ƙin binshi luqman yayi sai da dady yace "nima ina nan ba abun da zai maka kaji " sannan ya bi bayan su suna gaba yana baya sai zare ido yake har suka shigo main parlor ba kowa duk su mansoor sun fita sai momy dake zaune kan sofa ta buga uban tagumi, tana ganin su da sauri ta taso tana "luqman yanzu kaga irin ta ko " da sauri ya nufe ya yayi hugging ɗinta " momy wallahi bazan sake ba Allah " Abba ne yace "turai kiyi mashi dressing ɗin wannan ciwukan "sai a lokacin momy ta lura da ciwo kan da kae jikin shi,medical room ɗin su ta nufa da sauri zama su kayi kan sofa suna jiran ta fito, kamar daga sama suka ji ƙarar jiniyar motan ƴan sanda Abba ne yace "Innalillahi ba dai usman sai da ya kira ƴan sandan nan ba, ya Allah " da sauri luqman ya tashi yana zazzare ido " na shiga uku dady ni su kazo kama wa ya shazim ne ya kira su" dafe kai dady yayi "shazim wai wane irin yaro ne yaya, yanzu duk wannan dukan da yayi mashi bai isa ba sai ya haɗa shi da ƴan sanda " shi dai Abba yayi shiru bai ce komi ba "dady dan Allah kar ka bari su tafi da ni, dan Allah ba dan ni ba dady" duk ya bi ya ruɗe jikin shi sai rawa yake dafa shi dady yayi "kwantar da hankalin ka ba abun da zasu yi maka kaji... " ko rufe baki bai yi ba a ka turo ƙofar parlorn a shigo ƴan sanda ne su uku suka shigo, da gudu luqman ya boye bayan dady, Abba ne ya nufe su da sauri yana faɗin " yallaɓai lafiya?" babban cikin su ne yace " munzo ne da sammacin kama luqman Ibrahim Nuraddeen " Abba yace " wa ya baku izini ke nan?" "nine ya ji an faɗa daga bayan su " matsawa yan san da sukayi a dai dai lokacin momy ta fito hannunta riƙe da first aid box Abdallah ne tsaye bayan su ya harɗe hannuwa a ƙirji da mugun mamaki su dady ke kallon shi Abba ne yayi ƙarfin halin cewa "a kan wane dalili kenan, duk dukan da shazim yayi mashi bai isa ba" Abdallah yace "pls Abba kayi haƙuri" ya faɗa haɗi da kallon jami'an tsaron da ke tsayae yace " yallaɓai kuyi aikin da ya kawo ku " matsowa dady yayi ganin ya matsa ne yasa luqman da sauri ya nufi sama "dan Allah yallaɓai ku dakata dan Allah " tsayawa su kayi suna sauraron mi dady zaice kamar daga sama suka ji ihun luqman yana kiran sunan dady a tamanin suka juya suna kallon sama, shazim ne su ka hango ya damƙi wuyan luqman ya nufo parlorn da shi ba wanda yaga san da ya shigo part ɗin, ya gaji da jiran police ɗin ne au fito da luqman ganin sun jima ne yasa shi ya shigo shine yaji dady nacewa su dakata ya kuma hangi luqman zau shige part ɗin dady, har wurin su ya ƙara so da luqman ya miƙama ɗaya daga cikin police yace "arrest him" kama hannun luqman police ɗin yayi ya sa mashi handcuff ya fice da shi,kan sofa dady ya zube, Abba ne yace " why shazim why, yanzu duk dukan da kayi mashi bai isa ba, shima fa ɗan uwan ka ne kamar fatimar " kallon Abba shazim yayi da idanun shi da suka kaɗa su kayi jawur tsantsanr ɓacin rai da masifa ce a cikin su hannu kawai ya haɗa ma Abba alamar haƙuri ba tare da yace komai ba ya fice daga part ɗin sai a lokacin momy ta fashe da kuka. ciki mota su ka sa luqman suka tafi da shi sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady.......... _Episode 42_43_ ................ Sai ihu luqman yake yana kiran sunan dady. Shazim ba irin haƙurin da su ya usman da su mahmud, faisal mama gwaggo halima, har da su Asma'u da kairiyya basu bashi ba amma ko kallon in da suke bai ma yi ba sai ma kama hanya da yayi ya bar part ɗin tare shi mansoor yayi yana faɗin " haba shazim miyasa zaka yi haka duk haƙurin da ake baka yaci ace ka haƙura, dan Allah kar ka bari su tafi da shi, a nan ma zaka iya hukunta shi, please " ya ƙara sa magana cikin sigar roƙo, amma ina ko kallon shi shazim bai yi ba sai ma bi ta gefan shi da yayi ya wuce, bin bayan shi mansoor yayi yana ci gaba da roƙon kwan shi amma kwata kwata babu alamar ma zai saurare shi, ko mawa yayi kan Abdallah yana faɗin " haba Abdallah miyasa zaka kira su tun da har shazim ya ɗauki doka a hannu ai da an barshi yaji da iya wannan " "mansoor kafi kowa sanin halin luqman tun da kai ke tare da shi, ji irin abun da yayi ma fatima ace ma bai mata komai ba, halin ciwan da ya sata ya kyauta kenan " "na san bai kyauta ba amma hukuncin zai mashi yawa " "kai ka ga haka " Shazim ne ya ce " ko da bai kira su ba ni sai na kira su, kuma wallahi na tabbatar da ya ci mutuncin fatima, wallahi kaji na rantse sai yayi daya sanin sani na a rayuwar shi, sai ya gommaci kiɗa da karatu daga shi har mahaifin na shi daya iya ƙoƙarin ɓoye ta dan kar wani ya sani " yana gama faɗar haka ya shige part ɗin su, mansoor yana ji yana gani ba shi da yanda zai yi haka police ɗin suka fice da liqman daga estate ɗin cikin dare, bin bayan su shazim yayi dan ya duba jikin fatima. kusa da dady Abba ya matsa " Ibrahim kayi haƙuri kar ka sa kanka a damuwa insha Allah ba abun da zai faru da luqman zai dawo gobe da izinin Allah, ka kwantar da hankalin ka " "amma yaya mi nayi ma shazim a rayuwa da zai saka man da irin wannan abu, ai ko darajar kasan cewa ta ƙanin mahaifin shi ya duba ya ƙyale luqman, amma saboda bai ɗauke ni a bakin komai ba bayan yayi mashi dukan mutuwa shine ya haɗa shi da jami'an tsaro, mi nayi mashi har haka " "ka kwantar da hankalin ka ba abun da kayi mashi kawai ranshi ne ya ɓaci, amma nasan nan da zuwa wani lokaci zai huce kuma zai nemi afuwan abun da yayi maka " "shikenan yaya, ya jikin feenah na manta tun ɗazu ban tambaye ka ba " "jikinta da sauƙi gobe da safe za su ma dawo gida insha Allah" "Allah ya kaimu " dady ya faɗa, da Ameen Abba ya amsa haɗi da tashi yana faɗin "ka tashi kaje ku kwanta, ka lallashi turai naga hankalin ta yayi matuƙar ta shi " da to dady ya amsa haɗi da tashi ya nufi ɗakin momy, ficewa Abba yayi zuwa part ɗin shi lokacin da ya shiga duk sun shige ɗakunan su hakan yasa ya nufi ɗakin shi ya kwanata Zaune dady ya samu momy bakin gado tayi tagumi sai share hawaye take,abun zallah ban tausayi tana ji tana gani an kama mata ɗa bata yanda zata yi, zama dady yayi kusa da ita, ɗan shiru yayi na wani lokaci can ya dafa kafaɗar ta " dan Allah turai kiyi haƙuri, ko mai zai wuce da izinin ubangiji, insha Allah gobe luqman zai dawo kiyi haƙuri kinji " fashewa tayi da kuka mai tsuma rai dady shima kukan ne yazo mashi amma sai ya danne shi bai yi ba, jawota yayi jikin shi yayi hugging ɗinta yana ɗan bubbuga bayan ta haƙuri ya cigaba da bata har sai da tayi shiru ta koma tana sauke ajiyar zuciya, a haka har bacci ya ɗauke ta, kwantar da ita yayi kan bed haɗi da jan blanket ya rufe mata jikin, sannan ya nufi toilet ɗinta bayan kamar ten seconds ya fito, switch ɗin ɗakin ya nufa ya kashe masu sannan ya nufi gadon ya hau sai da ya rufe jikin shi da blanket sannan jawo ta jikin shi yayi hugging, idanu ya rufe ba bacci yake ba tunani ya shiga na abun da ya faru ya daɗe yana tunani har shima bacci yayi awan gaba da shi. Fitowar shi kenan daga toilet ta farka a firgice tana kiran sunan shi da Ammy da malam har noraiz sai bige bige take tana ƙoƙarin cire drip ɗin da aka sa mata da sauri ya ƙarasa wurin ta yana sa hannu ya riƙe hannuwanta da take bige bige yana kiran sunnan ta da cewa " dai na kuka gani nan a kusa da ke " jin muryar mutum ne a kusa da ita yasa ta ƙoƙarin fisge hannun ta tana kiran sunan shazim a ruɗe " ya shazim ka zo ka taimake ni kashe ni ya luqman zai yi dan Allah ka taimake ni " gaba ɗaya a firgice take ta dai ji muryar shazim amma bata san yana ina ba dan bata san shine a kusa da ita ba duk a tunanin ta luqman ne, sai ko kawa take zata ƙwace hannun ta da shazim ya riƙe jawo ta yayi jikin shi da sauri yana faɗin " kwantar da hankalin ki ni ne a kusa da ke ba luqman ba " duk da haka bata daina yunƙurin fisgewa daga riƙowan da yayi mata ba, ganin dai da gaske a tsorace take bazata tsaya ba ne yasa shi jawo ledar magungunan da yasa aka siyo mata allurar da ke ciki ya ciro dama ya haɗata, hakan yasa bai tsaya wata wata ba ya yayi mata allurar a damtsen hannun ta,dan danan allurar ta fara aikin ta cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗauke ta, jin jikinta yayi sanyi ne yasa shi fahimtar tayi bacci, kwantar da ita yayi kan gadon ya ja mata blanket, ya daɗe zaune yana kallon ta saƙawa da kwan cewa kawai yake , muddun gwajin da ya tura asibiti sakamakon ya fito, abun da yake zargi ya tabbata , ya rantse babu abun da zai hana shi yin shari'a da luqman har da mahaifin shi, ya jima yana saƙawa da kwancewa daga bisani ya tashi ya nufi parlor wurin Abdallah da mansoor, zaune ya same su kan sofa kowa yayi shiru yana tattaunawa da zuciyar shi, wuri shima ya samu kan sofar ya zauna Abdallah ne yace " har yanzu bata farka ba " ɗaga mshi kai kawai shazim yayi, yan da suka ga rana haka suka ga dare kowannen su a zaune ya kwana, har luqman da ke station a tsaye ya kwana har gari ya waye _*WASHE GARI*_ Haka su ka tashi da jiki su ku ku ba bu walwala, har lokacin kuma fatima bata farka ba, kowa da ke estate ɗin ya shigo ya duba jikinta har da dady,sa'ada ke zaune kusa da fatima ta zuba mata idanu. da safen ma ba irin haƙurin da su ya usman basu ba shazim ba akan ya haƙura a saki luqman, amma fir yace bai san wannan zancen ba dole sai anyima fatima gwaji ya tabbatar da luqman bai mata komai ba sannan, har station ɗin suka je ko za'a basu bail shi amma ina saboda shazim ya hana ba yanda su ka iya haka suka dawo estate suka zuba ma sarautar Allah ido, ba wanda ranshi bai ɓaci ba da shazim, shi kuwa abun da ke gabansa kawai yake, har estate ɗin ummah matar uncle ahmad ta zo domin duba fatima kuma duk wani gwaji da shazim ke so ayi ma fatima ita tayi mata da yake likita ce tafiya tayi zuwa hospital dan ta bicika awan da tayi ma fatima,kowa zaman jiran dawowar ta yake da saka makon da zata zo da shi dan shazim yace dole sai sai yaga sakamakon ko da zai yarda aba da bail luqman, shiyyasa suka zauna zaman jiran tsammani kowa adu'ar shi Allah yasa luqman bai mata komai ba kamar yanda yake faɗi, kafin ummah ta dawo su Innah su ka dawo daga asibiti da feenah, ta ji sauƙi kamar ba ita ba sai dai damuwa da take ciki, kwata kwata bata da walwala,har ƴar rama tayi duk a kan shazim, part ɗin innah su ka nufa gwaggo halima da mama ne suka shigo su kayi ma feenah ya jiki, feenah na kwance kan sofa tayi matashi da cinyar innah , su ya usman ma sun zo gaishe ta ganin noraiz ne yasa innah cewa " ai ku nayi tunanin kun tsufa da tafiya ashe kuna nan, kenan zuciyar da uban naku hau ba wata bace" shiru noraiz yayi bai ce mata ƙala ba gwaggo halima ce tace "dan Allah mama kiyi haƙuri daga dawowar ki " tsaki kawai innah ta ja ba tace komai ba,can kuma tace " ina su Ahmad ne " gwaggo Uwani tace " nima dai naga ban gan su ba, kuma wai mike damun ku ne nagan ku duk sai a hankali " "nima abun da zance kenan, sai kace kunyi zaman makoki" innah ta faɗa tana tsare gwaggo halima da idanu "ba komai innah kawai saboda jikin feenah ne, amma tun gashi kun dawo Alhmdllh " shiru kawai su innah su kayi bawai dan sun yarda da abun gwaggo halima ta faɗi ba, feenah ce ta tashi tana cema innah zataje part ɗin su dan ta watsa ruwa, da to innah ta amsa mata, tashi tayi Ilham ta bi bayan ta, a bayan part ɗin innah su ka tsaya feenah tace " dan Allah Ilham ki faɗaman mike faruwa ne na ganku duk sai a hanli " ɗan nisa wa Ilham tayi sannan ta faɗa mata duk abun da ya faru da basu nan, kuka feenah ta fashe da shi tana faɗin "wai dan Allah mi yasa ya luqman bai gudun abun magana ne wani lokacin mi zai sa yayi ma fatima haka laifin mi tayi mashi har haka " Ilham tace "gaskiya kam bai kyauta ba, amma baki ga irin na damar da yayi ba, yayi daya sanin yimata haka " "ba abun da dady yayi a kan ya luqman ɗin " "ba abun da yayi, domin ya shazim ya hana a bada bail shi wai har sai ya tabbatar da bai mata komai ba " "shikenan " feenah ta faɗa part ɗin su suka nufa, tsit suka same shi ba motsin kowa, bedroom ɗin momy su ka nufa zaune su ka same ta bakin bed ta zuba uban tagumi gaba ɗaya damuwa tayi mata da bai bayi, sai sallama suke bata ma san suna yi ba tayi zurfi cikin tunani har sai da feenah ta dafa ta sannan ta san da shigowar su, ajiyar zuciya ta sauke haɗi da wai gowa tana kallon su, shafa kan feenah tayi tana faɗin " kun dawo kenan " ɗaga mata kai feenah tayi " to ya jikin " da sauki feenah ta faɗa " momy ina dady yake " "yana ɗakin shi " "ok, momy abun da ya luqman yayi kenan " ta faɗa idonta na tara ƙwalla shiru momy tayi batace komai ba "momy wai miyasa ya luqman bai jin magana, yanzu yana ganin ta kyauta, duk ya saku a cikin damuwa " "feenah dan Allah ki bar maganar nan abun da ya faru yariga da ya faru " " amma momy..... " da katar da ita momy tayi " daga dawowarki ki feenah, kar ki dawo man da abun da yariga ya wuce, insha Allah ba abun da zai faru " "shikenan momy, bari naje ɗakin dady " ɗaga mata kai kawai momy tayi, hannun Ilham taja zuwa ɗakin dady basu same shi a parlor ba hakan yasa feenah ta nufi bedroom ɗin shi Ilham kuma ta zauna kan sofa, a bakin ƙofar ta tsaya haɗi da yin nocking, izinin shiga dady ya bata a hankali ta tura ƙofar ta shiga tsaye ta same shi sai kai kawo yake, sallama tayi haɗi da maida ƙofar ta rufe, juyowa dady yana kallon har ta ƙaraso kusa da shi tayi hugging ɗin shi, shafar sumar kanta yayi " ya jikin naki " "da sauki " "Allah ya ƙara sauki " da Ameen ta amsa sannan tace " dady yaushe za'a bada bail ya luqman " "daga dawowar ki waya faɗa maki abun da ke faruwa, nima ban sani ba feenah, amma insha Allah na san zuwa anjima za'a sake shi " " to Allah ya kaimu " da Ameen dady ya amsa, ta ɗan jima a part ɗin dady daga baya ta fita ita da Ilham , duk abun da ke faruwa har lokacin innah da gwaggo Uwani basu sani ba har sai da ummah tazo da sakamakon gwajin da tayi ma fatima, sanna su innah suka san abun da ke faruwa, innah tasha kuka zagi kuwa na duniyar nan ba irin wanda bata yima shazim ba, har papah dake kwance cikin kabarin sa bata bari ba sai da ta zage shi tasa da maifiyar shi kakar su shazim, har part ɗin su taje ta samu shazim, zaune ta same shi a part ɗin su ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, su Abdallah da ummah har da Ameerah duk suna zaune kan sofa, kowa ya zuba ma shazim ido, jira kawai su ke ya gama karanta takar dar suji minene sakamakon gwajin fatima , kamar daga sama suka ji muryar innah tana faɗin " dama ubanka ko da ya bar duniya sai daya tozar ta man ɗana, wallahi duk abun da ya samu luqman bazan bar ka ba daga kai har uwar taka, mara mutunci kawai" masifa iri iri sai da innah ta sauke ma shazim, zagi kuwa ba wanda innah bata sauke ma shazim ba duk masifar da take mashi ko kallon in da take bai yi ba,takardun dake hannun shi kawai yake aikin dubawa, gwaggo halima ce ta shigo tana bama innahr haƙuri amma ina masifa ta rufe ma innah ido har su dady sai da suka sa baki amma taƙiyin shiru, shazim yana gama karanta takar dar gawajin , sallama yayi ma ummah da godiya, ba tare da yace ma kowa ƙala ba ya tashi ya nufi bedroom ɗin sa inda ya kwantar da fatima,sai magana su mansoor suke mashi akan ya faɗa masu sakamakon amma yayi banza da su ya nufi ɗakin shi , ummah su ka tambaya ce masu tayi itama bata karanta ba, shikenan kawai su kace, rakata parking lot mansoor da Abdallah su kayi, sai da ta tafi sannan au ka dawo parlorn, Kamar dai yanda take jiya yauma haka take kwance,goshinta da bandage jikinta duk a bushe yake, sa'ada na nan zaune kusa da ita ta zuba uban tagumi, ɗagowa tayi jin shigowar mutum da kallo ta bi shazim daya shigo,ce mata yayi taje bedroom ɗin fatima ta ɗauko mashi trollyn ta, da to ta amsa mashi haɗi da ficewa ta nufi ɗakin fatima, noraiz ne ya taso ya nufe ta yana faɗin" ya akayi naga kin fito " "kaya yace na ɗauko ma fatima da trollyn ta " Ok kawai noraiz yace haɗi da nufar bedroom ɗin shazim ɗin samun shi yayi a bakin wardrobe ɗin shi, sallama noraiz yayi mashi haɗi da faɗin " yaya minene sakamakon, hankalin kowa a tsahe yake kai kawai su ke jira ka faɗa masu sakamakon ka kuma taso ka shigo ɗaki.... " "dakata man dan Allah noraiz, ka wuce ka fita yanzu zamu wuce " "amma yay.... " "bana son jin komai daga gare ka, kayi abun da nace kawai " da to kawai noraiz ya amsa haɗi da nufar bedroom ɗin shi laptop ɗin shi ya ɗauka haɗi da kashe duk wani abu wuta a ɗakin sannan ya fito dama trollys ɗin su suna cikin mota tun jiya bedroom ɗin shazim sa'ada ta koma da trollyn fatima da ta ɗauko, lokacin da ta shiga shazim harya canza kayan jikin shi zuwa baƙar t_shirt da cargo trouser shima baƙi da p_cap sak shigar da yayice jiya sai dai ba kayan bane wasu ne yasa irin su, a tsakiyar ɗakin ta tsaya da trollyn "boɗe ki ciro mata doguwar riga mara nauyi " shazim ya faɗa, da to sa'ada ta amasa haɗi da ɗora trollyn bakin gadon, buɗe shi tayi doguwar rigar abaya mara ɗauyi ta ɗauko mata ajiye ta tayi gefe ta rufe trollyn , kallon shi tayi tana faɗin "yaya gashi " "ok,kina iya samata?" "eh " ta bashi amsa, jinjina kai yayi haɗi da jan trollyn fatimar ya fice. da ya fito wata takarda ya ciro daga cikin aljihun trouser ɗin shi ya miƙama mansoor, amsa mansoor yayi yana faɗin " thank you,zan same ku kuwa kafin na dawo " ɗaga mashi kai shazim yayi, hugging ɗin shi mansoor yayi " shikenan sai na dawo bro " ok shazim yace, a tare su ka fita shi ya sa trollyn fatima a booth mansoor kuma ya shiga motar shi ya fice daga estate ɗin. Mansoor na ficewa AMBULANCE ɗin asibitin su ummah na shigowa, ita ta turo da ambulance ɗin dan su samu sauƙin zuwa airport da fatima,tsayawa shazim yayi har sai da tayi parking sannan ya gaisa da drivern ambulance ɗin sannan ya shiga ciki yana faɗi inazuwa da to drivern ya amsa, ha zai shiga ciki wayar shi dake aljihu tafa ringing, tsayawa yayi yana amsa kiran ✨SA'ADA ✨ Rigar ta shiga kiciniyar sanya ma fatima, tasha wahala kafin ta sama ta rigar saboda jikinta duk a sake yake kamar wacce ta mutu babu inda ke motsi a jikinta,bayan ta sa mata rigar ne ta nufi dressing mirror ɗin shazim main shafawa ta ɗauko ta ɗan shafa mata a hannuwan ta da ƙafafuwan ta saboda jikin ta duk ya bushe tana gama shafa mata ta fice zuwa waje lokacin da ta fita Abdallah da noraiz ka ɗai ta samu su Abba duk sun fita, fita tayi itama zuwa parking lot inda anan ta samu shazim tsaye yana waya jira tayi har ya gama wayar sannan tace " ya shazim idan tafiya za kuyi, dan Allah ka tafi da ni " " ki bari idan mansoor zai zo sai kuzo tare " "dan Allah ya shazim, wallahi hankalina bazai kwanta ba,dan Allah ya shazim " kai kawai ya ɗaga mata alamar to shikenan "nagode sosai ya shazim ta faɗa " haɗi da nufar part ɗin su da sauri, zazzaune ta samu su Abba da su gwaggo halima harda innah,sallama kawai tayi masu bata jira sun amsa ba ta nufi ɗakin ta da sauri, shaf shaf ta canza kaya ita ma doguwar riga ta sa, gyalen ta kawai ta ya fa sai side bag ɗinta da wayar ta da ta ɗauka, da sauri ta fice kowa dake parlorn da idanu ya bita, gwaggo uwani ce tace " ke kuma ina zaki " "lagos zan bi su ya shazim" kawai tace haɗi da juyawa ta fice,da sauri feenah ta tashi jin wai shazim zai tafi, gwaggo Uwani ce ta jawo tana faɗin "dawo nan " dawowa tayi ta zauna sai turo baki take, innah tace " amma wannan ɗiya anyi ƴar banza, kenan waɗannan marasa mutuncin zata bi " Abba ne yace " ai ba komi innah dan ta bi su, nasan tana son zama da ƴar uwarta ne har ta samu sauƙi " "amma kuma bata ga abun da yayan yarinyar yayi ma yayan ta ba da zata wani bisu kamar wasu ƙannan uwar ta " "kiyi haƙuri innah,shima luqman ɗin yana da laifi " "dama nasan bayan shi zaku bi" gwaggo Uwani ce tace " bansan mi yake nufi ba tafiya zai yi ba tare da yasa an saki luqman ɗin ba komi " "ke bari kiga naje na samu wannan mara mutuncin " innah ta faɗa haɗi da miƙewa ta fice bayan ta su gwaggo Uwani suka bi har da su Abba, tana fita shazim na fitowa ɗauke da fatima a kafaɗar shi kamar wata gawa, noraiz da Abdallah na bayan shi sai sa'ada data fito hannun ta ɗauke da jakarta da jakar laptop ɗin fatima,drivern Ambulance ɗinne ya buɗe mashi ƙofa ya saka fatima, zama yayi kan wata ƴar chair dake cikin ambulance ɗin,ledar magungunan fatima ya amsa a hannun sa'ada haɗi da maida ƙofar ya rufe,wani drip ɗin ya sake sama fatima sai da ya komai na tafiya yan da yaso sannan ya fito, motar mansoor ce ta shigo estate ɗin, gaba ɗaya hankalin su kan motar ya koma har yazo parking lot yayi parking buɗe motar yayi ya fito nufo su yayi luqman ne ya fito jikin shi duk a sanyaye har ya ɗan faɗa dare ɗaya kawai, da sauri innah ta tare shi yana ganin ta shima da sauri yayi hugging ɗinta hawaye na bin idanuwan shi , su dady ma nufo su su kayi binsu yayi tayi ɗaya bayan ɗaya yana hugging ɗin sai kuka yake, dady ne yayi hugging ɗin shi yana lallashin shi,sa'ada ƙin zuwa tayi wurin luqman haushin shi take ji, mansoor ne ya ƙaraso wurin su shazim, hugging ɗin shazim yayi "tnxs bro " ɗago da shi shazim yayi yana faɗin " godiyar ta isa haka, yaushe zaka zo " "Insha Allah next week zan zo " "to Allah ya kaimu " da ameen mansoor ya amsa, raba jikin su su kayi, "ku kuzo mu wuce " shazim ya faɗa haɗi da nufar Ambulance ɗin da fatima ke ciki zai shiga, gwaggo halima ce ta ƙaraso kusa da shi " shazim baza ka bari ko breakfast kuyi ba sannan ku tafi " "ba komai Aunty, idan mun isa cana za muyi " "shikenan, Allah ya kai ku lafiya, ina gaishe da Ammyn ku sai nazo " "zataji insha Allah, sai kinzo " "to shikenan " ta faɗa haɗi da ko mawa wurin su innah,mama Allah ya sauke su lafiya tayi masu,dady ma da Abba sai da suka yi masu Allah ya kiyaye haɗi da adu'ar Allah ya ba fatima lafiya, ƙin amsa masu shazim yayi dan duk haushin su yake ji musamman dady kowa sai da yayi masu Allah tsare ban da mutum uku innah, gwaggo Uwani,sai momy dake part ɗin ta bata fito ba dan bama ta san luqman ya dawo ba, sai luqman ɗin dake tsoron yazo wurin saboda shazim, amma yaso ya ga ya jikin fatima yake,mota su ka shi ga, shazim na cikin ambulance da fatima sai mansoor da noraiz Abdallah da sa'ada a motar mansoor , kairiyya taso ta bi su amma Abba yace ta bari sai zasu je sai su tafi tare, feenah taci kuka kamar ranta zai fita haukace masu tayi ita a dole sai tabi shazim tun ana lallashin ta kan ta bari sai su dady zasu har ta kai ga ba mutane haushi dady ya wanke mata fuska da mari, Allah ya ƙara kowa ke mata. Luqman ya so ya raka su airport amma dady yace a'a. Suna nan tsaye har motocin su suka bar estate ɗin, sai da suka ga fitar su sannan kowa ya koma part ɗin shi Suna zuwa airport ba daɗewa lokacin tashin su yayi,har filin in da jirgi yake Ambulance ɗin ta shiga , shazim ne ya turo ɗan gadon da take kwance, da sauri mansoor da Abdallah suka fito daga cikin mota suka shigar da ita cikin jirgin. . Allah sarki fatima ta zo da ƙafar ta cikin ɗoki da nisha ɗi amma zata koma cikin halin jinya, dama haka rayuwa ta gada in yau kai ne gobe ba kai bane, Allah ya baki lafiya mai amfani Ameen. sa'ada da noraiz ma fitowa su kayi su ka shiga. Sallama mansoor yayi masu, da yake harda Abdallah zasu tafi. Sai da jirgin su ya tashi sannan mansoor ya koma cikin motar ya bar airport shi ka ɗai cike da kewar su. Sai da suka kusa isa lagos sannan shazim ya kira malam ya sanar da shi suna hanya sun ma kusa isowa , faɗa sosai malam yayi mashi saboda ƙin ɗaukar wayar su da baiyi ba,duk ya bi ya tayar masu da hankali,haƙuri ya shiga bashi ,ƙin haƙura malam yayi sai ma kashe wayar da yayi yana faɗin "zaka dawo ka same ni ne ai " number majeed ya lalubo ya kira shi ya sanar da shi suna hanya ya turo mashi da Ambulance suna tare da patient ne, bai jira mi majeed zai ce ba yayi rejecting kiran yasan dole majeed zai tambaye shi waye bai da lafiya. ✨LAGOS✨ Kiran Ammy malam yayi ya sanar da ita su shazim na hanya "amma shazim bai da hankali baba, yanzu da lafiyar su lau amma mu kai ta kiran shi baya ɗaga wa" "Allah dai ka ɗan yasan dalilin da yasa bai ɗauka ba" "amma ko ma minene, ai ya ɗauki kiran mu idan baza su dawo a jiyan ba " "yanzu dai sai sun shigo, kisa ilya yaje ya ɗauko su dan yace sun kusa isowa " da to Ammy ta amsa haɗi da yin rejecting, kiran ilya tayi ta sanar da shi su shazim na hanya yaje ya ɗauko su. Suna gama waya da Ammy bai jira komai ba ya shirya ya nufi airport shi da ɗayan drivern gidan mai suna ɗan Auta, shi ba kasa fai ya cika driving ba yafi yawan zaman gida. Ko da suka isa airport ɗin su majeed sun daɗe da zuwa da Ambulance tun da shazim yace mashi suna tafe da patient hankalin shi yaƙi kwaciya sai da ya zo dan yaga waye ba lafiya, basu wani jima ba jirgin su shazim ya ƙaraso. hankalin majeed yayi matuƙar tashi da yaga fatima,bawan Allah ilya har da ƴar ƙwallar shi, shigar da ita su kayi cikin Ambulance ɗin , bai ma lura da Abdallah ba hankalin shi naga fatima, har sai da shazim yace" wai lafiya Abdallah na maka magana hankalin ka na wani wajen baka ji " sai a lokacin ya lura da Abdallah dake mashi magana, gaisawa su kayi da shi. Mota kowannan su ya shiga, yanzu ma shazim Ambulance ya shiga shi da Abdallah sai majeed daman a nan yazo,majeed na gaba shida driver yayin da Abdallah ke kusa da fatima shi da shazim, ganin duk sun shige nan yasa noraiz da sa'ada nufar motar da ilya yazo ɗaukar su, ɗan auta kuwa empty ya koma ba kowa a motar da ya zo da ita, Ambulance ɗin ke gaba su ilya na binsu a baya. Kasa haƙuri majeed yayi har sai da ya tambayi shazim mike damun fatima, duk ya bi ya damu, abun har so yayi ya ba Abdallah haushi ganin yanda majeed ya ruɗe kan ciwan fatima, amsa shazim ya bashi da ciwan ta ne ya tashi, tambayar shi majeed yayi miye dalilin "majeed ka kwantar da hankalin ka, da sauƙi jikin ta " tsaki Abdallah yaja,shi kuwa majeed hankalin shi naga fatima bai ma san Abdallah nayi ba, shazim kawai ya lura da shi, girgiza kai kawai yayi ba tare da ya ce ma kowa komi ba "to amma hospital za'a nufa da ita " majeed ya faɗa, tsaki Abdallah ya sake ja yana faɗin "wai lafiya majeed ka bi duk ka tashi hankalin ka, ance maka jikin ta da sauƙi, amma sai tambaya kake " "daga tambayar lafiyar ta zaka wani ce na damu mutane jiman ƙarfin hali" " dan Allah ya isa haka, gida za'a kaita duk wani abu da ya dace ayi mata zan iya yi mata shi a can ba dole sai a hospital ba " shazim ya faɗa Majeed yace "to shikenan , Allah ya bata lafiya " "Ameen ya Allah " shazim ya amsa, babu wanda ya ƙara cewa komai cikin su har suka ƙara so gida, horn su kayi da sauri mai gadi ya buɗe masu, ciki su ka shiga, a compound drivern yayi parking da Ambulance ɗin, jin jiniyar Ambulance ne yasa Ammy dake parlor zaune fitowa da sauri gaban ta na faɗuwa, tana fitowa su shazim na fito da fatima, da sauri ta ƙara so kusa da su dan taga waye kuma ba lafiya, ai ko da tayi arba da fatima kwance kamar matacciya,wani mummunan faɗuwa gaban ta yayi, jiri ne ya fara kwasarta ta tafi luuu zata faɗi babu wanda yalura da ita sai noraiz,da wani masifafen gudu ya ƙaraso wurin ta yana kiran sunan ta cikin ƙaraji ya ganin ta tafi luuu zata faɗi,ririƙeta yayi,ƙasa suka nufa shi da ita dan tuni har ta sume, gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim a tamanin ya ƙaraso wurin su saura kaɗan ya faɗi...... _Episode _44_45_ _..........Gaba ɗaya hankalin su shazim ya dawo kanta, shazim a tamanin ya ƙara so wurin su saura kaɗan ya faɗi, tallabo kanta yayi yana kiran sunan ta "Ammy! Ammy!! pls ki tashi dan Allah " sai ro ƙwan ta yake da ta tashi duk ya bi ya firgice sai jijjiga ta yake, noraiz ban da kuka babu abun da yake, ilya ne ya shiga ciki da sauri, ruwa ga ɗauko a kitchen da sauri ya fito ya dawo wurin su, Abdallah ne ya amsa ya nufi ammy da ke kwance a jikin shazim, da sauri ya kwance marfin robar ruwan ya shiga yayyafa mata sai da ya yayyafa mata kusan sau ukku sannan ta ja wani dogon numfashi, Alhmdllh su ka shiga furtawa, hawaye ne suka taru idanuwan ta " mi ya faru da fatima??, kar ka saki kace man ta mutu " tana faɗa hawayen da suka taru a idanuwan ta na zuba, abun tausayi su Abdallah ma sai da zuciyoyun su suka karaya ganin yanda Ammy ke zubar da ƙwalla "ki kwantar da hankalin ki Ammy, ba wani abu bane ya same ta lafiyar ta lau " "taya zaka ce man tana lafiya bayan na ganta a haka " "da gaske nake Ammy, ki kwantar da hankalin ki " ya faɗa haɗi da kallon su majeed yace " majeed ku shiga ciki da ita " da to majeed ya amsa, shi da Abdallah su ka shiga da fatima, da sauri Ammy ta tashi ta bi bayan su, bin bayan ta noraiz yayi ya na share hawaye , shazim kallon sa'ada da ke gefe rakuɓe gefe sai hawaye take yayi yace " shiga ciki mana " da to ta amsa haɗi da bin bayan su noraiz ta shiga ciki,komawa yayi cikin Ambulance ɗin ledar magungunan fatima ya ɗauka sannan yayi ma drivern sallama, bai shiga ciki ba waya ya ciro daga aljihun wandon shi, dialing ɗin wata number yayi,wanda ya kira na ɗagawa bai ko amsa mashi sallamar da yake yi ba yace " kayi sauri ka kawo man na dawo " yana gama faɗa yayi rejecting kiran, ciki ya nufa, bai same su a main parlor ba hakan yasa shi nufar medical room ɗin su dake kusa da part ɗin shi, tura ƙofar yayi ya shiga ciki, tsai tsaye ya same su fatima kuma na kwance kan gadon marasa lafiya gaban gadon ya ƙarasa haɗi da ajiye ledar da ke hannun shi kan ɗan table ɗin dake gefan gadon wani drip ya sake fiddowa daga cikin ledar haɗa shi yayi duk su Ammy na nan sun zuba mashi ido harya gama haɗa shi ya sama fatima, sai da ya gama dai data komai sannan ya kalle su yace " mu fita mu bata wuri " ficewa su kayi zuwa waje, ban da Ammy matsawa ma tayi kusa da gadon ta zauna kan wata kujer ta roba dake gefan gadon "Ammy mu fita bata son kowa kusa da ita yanzu " shazim ya faɗa "babu inda zani, ina nan har sai ta farfaɗo ta faɗa man abun da ya same ta " lallashin ta ya shiga yi akan ta tashi su fita amma ƙiri ƙiri tace bata fita, saima tsare shi tayi akan dole saiya faɗa mata abun da ke damun fatima shiru yayi yana kallon Ammy ba tare da yace mata komai ba "magana nake maka shazim mike damun fatima ka wani tsare ni da idanuwa kana kallo na" Ammy ta faɗa da damuwa a fuskar ta, duk ta damu da son jin miya samu ɗiyarta "kiyi haƙuri Ammy kamar yan da nace maki ciwanta ne ya tashi " " haba shazim sai kace dai ban san yan da ciwan nata yake ba, kuma yaushe rabon da ya tashi ina tuna nin tun tana ƙarama kuma kai da kanka kace man ta samu sauƙi idan ba abu yayi tsanani ba ba lallai bane ciwan ya tashi" "haka ne Ammy, amma ai bai zama dole sai abun yayi tsanani ba" "shazim! shazim! ! shazim!!!, sau nawa na kira sunan ka " "sau uku Ammy " "to ka faɗa man mike damun ɗiyata mi ya haddasa mata wannan ciwan tun kafin ranka ya ɓaci, idan ma laifi tayi maka ka dake ta ka faɗa man dan na fara zargin laifinka ne ciwan ta " "Ammy kema kin sani bazan taɓa sa sannu na daki fatima ba ko kau mi tayi man " "to naji faɗa man mi yasa same ta " baya son ya faɗa mata ne dan kar ta tashi hankalin ta sosai, "kayi shiru?" "zan faɗa maki Ammy, amma yan zu ina so na ɗan watsa ruwa, zan zo part ɗin ki na same ki " "na lura dai faɗaman ne baka son yi " "ba haka bane Ammy zan faɗa maki amma yanzu ki bari na watsa ruwan, ko fa breakfast ba muyi ba mu ka taho" jin yace ko breakfast basu yi bane yasa tace " to shikenan na ji zan koma part ɗina, amma kar ka shanya ni, zan sa Innah Asabe ta shirya maku breakfast a dinning " "insha Allah da na shirya zan shigo " "to shikenan " fita su kayi daga ɗakin, bin bayan Ammy noraiz da sa'ada su ka yi , a parlornta ta zauna kan sofa, kusa da ita noraiz yazo ya zauna, sa'ada kuma kan sofa ta zauna tana faɗin " ina kwana Ammy " kwata kwata Ammy bata san da sa'ada aka zo ba sai yanzu da ta gaishe da ita sannan ta san da ita su ka zo " lafiya lau sa'ada tare ku ke kenan " " eh Ammy, ya gida " " Alhmdllh, ya su momyn ku " "suna lafiya " "Masha Allah "Ammy ta faɗa Innah Asabe ce ta shigo parlorn, gaishe da ita noraiz da sa'ada su kayi, cikin kulawa ta amsa tana tambayar ya mutanen abuja. _*✨SHAZIM✨*_ A bakin part ɗin shi ya sami su Abdallah sun yi tsaye, kowa da abun da ke damun shi majeed gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake burin shi ɗaya su keɓe da shazim yaji miye ke damun ta yayin da Abdallah ke gefe guda sai cika yake yana batsewa duk dan saboda majeed dan duk ya lura da take taken shi, da kallon shazim ya bi su, murmushin gefen baki yayi yana faɗin "lafiya dai dakarun yaƙi, duk kun wani yi ma mutane cirko cirko sai kace wasu body guard " majeed ne yace " dan Allah ka ajiye wannan wasan a gefe, ka ƙi ka faɗa man mi ke damun fatima dan na daɗe ban ganta aciki irin wannan halin ba " Abdallah ne yayi saurin cewa "wai kai dan Allah wannan damuwar ta micece ne, duk ka wani bi ka damu mutune da mike da munta sai kace in an faɗa maka ɗauke mata ciwan zaka yi " wani ɗan iskan kallo majeed ya bi Abdallah da shi can kuma sai yace "in abun da ya dame ka ne wai da tambayar da nake tun da ba kai nai mawa ba, wai ma miye naka a ciki ne ina ruwan ka da ni ne ma" "wannan kuma matsalar kace" Abdallah ya faɗa haɗi da jan tsaki ya shige part ɗin shazim, shazim dai na tsaye yana bin su da idanuwa dariya ce ke cin sa amma sai ya ɗaure fuska bai yi ba amma a zuciyar shi dariya kawai yake mas. Majeed ne yace " ni wallahi abun a hashim ma mamki yake bani, dan na tambayi abun da ke damun ta laifi nayi ne zai wani dage shi a dole kar a tambayi mike damun ta sai kace wani mugun abu " Shazim ne yace " kar ka damu ranshi ne kawai a ɓace ba wani abu ba " "dan ranshi na a ɓace shine zai ta wannan ƙarfin halin" " ya isa dai yanzu kayi haƙuri, komai ya wuce " hmmm kawai majeed yace dan ba ƙaramin ɓaci ranshi yayi ba da abun da Abdallah yayi mashi, "kayi tsaye mu shiga ciki " shazim ya faɗa, ok kawai majeed yace haɗi da bin bayan shazim su ka shiga ciki, zaune su ka samu Abdallah kan sofa ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya jin alamar shigowar su ne yasa shi zaro wayar shi da ke cikin aljihun shi yayi dialing number Abie, yana picking ya tashi ya fita zuwa waje, a bakin ƙofar part ɗin ya tsaya amsa sallamar da abie yayi yayi sannan yace " ina kwana abie, ya su mom " "lafiya lau, ya su shazim ɗin ya kuma jikin ƙanwar tasa " " lafiya lau abie, jikin ta da sauƙi " " to Allah ya ƙara sauƙi, shazim ɗin na kusa " " eh bari na bashi " " to " abie ya faɗa, ƙofar ɗakin ya tura ya shiga ciki, zaune majeed yake yayin da shazim ke tsaye bakin fridge, ƙara sawa Abdallah yayi kusa da shi miƙa mashi wayar yayi yana faɗin " abie ne ke magana" ok shazim yace haɗi da amsar wayar ya kara akunnen shi " ina kwana abie " "lafiya lau shazim, ya kwana biyu, ka yada mu ko " murmushi yayi yana cewa " ba haka bane abie, ya mom " "haka ne mana shazim,ban taɓa ganin ƙafar ka a katsina ba idan ba abuja kaje ba nima ina nan ai ban taɓa ganin ka ba " "Insha Allah abie ina nan zuwa , zan maka zuwan baza ta " "to Allah yasa, ya jikin fatima " "da sauƙi abie " "to Allah ya ƙara sauƙi, ga mom ɗin ku nan za ku gaisa " abie ya faɗa, to shazim yace , muryar mom yaji tana cewa "shazim ya gida " "lafiya lau mom,ina kwana " "lafiya lau, ya su ammyn ku " "lafiya lau su ke " "Ashe fatima ba lafiya,to Allah ya bata lafiya " "Ameen ya Allah " "Ammyn ku na kusa " "A'a tana part ɗin ta " "to shikenan ka gaishe man da ita dan Allah " "insha Allah zata ji " "yawwa to nagode sai anjima " mom ta faɗa haɗi da yin rejecting,cire wayar yayi daga kunnan shi haɗi da miƙa ma Abdallah , amsa Abdallah yayi. bedroom shazim ya shiga, kamar yanda yace ma Ammy wanka yayi jallabiya ya sa ya fice zuwa part Ammyn zaune take kamar ɗazu, sai dai yanzu ita kaɗai ce noraiz na part ɗin shi sa'ada kuma na ɗakin fatima, zama yayi kan aofar da kusa da wacce Ammy ke zaune "Ammy " ya kira sunan ta a hankali , juyowa tayi tana kallon shi, magana ya soma cikin natsuwa "Ammy kiyi haƙuri da abun da zan faɗa maki " "ina sauraron ka shazim, haƙuri kuma ya zama dole tun da bazan guge abun da ya riga ya faru ba " ajiyar zuciya ya ɗan sauke, duk abun da ya faru a Abuja sai da ya sanar da ita har da irin matakin da ya ɗauka a kan luqman sai da ya faɗa mata, Ammy taci kuka kuma taji haushin hukuncin da su uncle Ahmad su ka yanke ma shazim dan kwata kwata bata son feenah , saboda rashin tarbiyar ta da rashin kamun kanta taso ace da kairiyya suka haɗa shi bawai da feenah ba, sannan ranta yayi matuƙar baci da luqman ta so ace shazim yayi mashi hukunci fiye da wanda yayi mashi, ta san duk abun da ya faru a kwai sa hannun innah da gwaggo Uwani "na sara miyasa innah bata ƙaunata da su shazim wai mi nayi mata ne a rayuwa, duk abun sadiq yayi mata amma da wannan zata saka mashi, ya Allah ka kawo man ƙarahen wannan al'amarin " Ammy ta faɗa a zuciyar ta kallon shazim tayi tace " yan zu yaushe su ka ce sun tsai da ranar bikin " "ni ban san yaushe za su tsai da ba, bana ma so na san lokacin " "shi luqman da yace yana son fatimar sun amsa cewa zasu bashi " "a lokacin basu amsa ba, amma na san zasu amsa ne,amma ki kwantar da hankalin ki Ammy babu mai ma fatima auren dole da wannan yaron in dai ina raye " "shazim bana son ka nuna ba su isa da kai ba ko dan yan Ibrahim ya kula da rayuwar ku " "Ammy ni bazan nuna masu basu isa da ni ba, amma bazan bari su zalinci fatima ba" "shikenan, amma auren naka da feenah fa, na so ace da kairiyya su ka haɗa ka ba wai feenah " "dan Allah ma Ammy ki bar wannan zancen, ni bazan auri wannan yarinyar ba ko kuwa mi zasu yi" "shikenan, fatima yan zu miye yake damun ta " "jikin ta da suƙi kawai dai alurar da nake mata ce ke sata bacci saboda firgitar da take yi ne, amma insha Allah nan da zuwa anjima ma zata iya farkawa " "Allah ya bata lafiya, amma gaskiya luqman bai kayuta man ba, mi yasa zai yi man haka a rayuwa" "Ammy kar ki damu da batun luqman yanzu abun da yaso ya aikata Allah bai bashi sa'a ba ta dalilin ciwan fatimar daya tashi sai yaji tsoro bai mata komai ba, dan haka ki kwantar da hankalin ki kawai " _Abun da ya faru, lokacin da fatima ta fice daga parlorn da suke taro,luqman shi kuma haushin ta nuna bata son shi ne yasa shi fita ya bi bayanta ya tare ta yana mata masifa ita harta isa tace bata son shi daga zai taimaka mata shine zatace bata son, angaya mata shima son ta yake, kawai dan an haɗa shi da Allah ne akan yace yana son ta ne yasa yace yana son ta,maganar daya faɗa ce ta wai an haɗa shi da Allah yace yana son tace ta ɓata mata rai ta kai ga zazzaga mashi masifa son ranta hartana ce mashi ɗan shaye shaye, shikuma haushin rashin kunyar da tayi mashi ne yasa cewa yau sai ya nuna mata cewa shi cikaken ɗan iska ne, shine fa ya saɓeta kan kafaɗa, tana kuka ta kai mashi duka a baya har cizon shi tayi amma ya ƙi sauke ta har sai da ya isa ɗakin shi sannan yayi wurigi da ita kan gadon shi haɗi da maida ƙofa ya rufe ba tausayi ya afaka mata,kuka ta shiga yi tana roƙwanshi daya ƙyale ta amma sam sam bai saurare ta ba,dan ma kar ta sa wani ya jisu ne yasa shi rufe mata baki da nashi,sumbatar ta ya shiga yi ba arziƙi tun tana kuka har ta kai ga fara kai mashi duka ta ko ina har da cizo da ya kushi, wani ya kushi ne da takai mashi a gadon bayan shi ne yasa shi haɗa ta da bango har kanta ya fashe ta kifa ƙasa azabar zafin da taji ne yasa ta fasa ƙara wanda hakan ya jawo hankalin dady daya shigo part ɗaukar key ɗin mota saboda suma da feenah tayi zai kaita asibiti, da yake ɗakin luqman ɗin yana kusa da na shi shiyyasa yaji ihun da fatima ta tayi, har ya shiga ɗakin ya same ta ya she a ƙasa shikuma luqman tsaye yana zare ido duk ya tsorata, anan sai da dady ya wanke shi da mari kafin yasa shi su ka kama fatimar suka shiga part ɗin shi da ita duk yayi hakan ne dan kar shazim ya san abun da ya faru yayi tunanin suma kawai tayi na tsoro bai san lalurar ta ce ta tashi ba, sai da suka ya yayyafa mata ruwa ta ƙi tashi sannan hankalin dady da na luqman ɗin kanshi ya ƙara tashi momy kuma motsin su ne yasa nufar part ɗin dadyn amma sai ya hanata ganin fatimar ba irin tambayar da bata yi mashi ba dan taji ihun fatima amma dady yace ba komai, da sa'ada ta faɗa mata ba'aga fatima bane yasa ta zargin ko dai fatima ce_ "shikenan shazim, amma taya zan yarda bai keta man haddin yarinya ba" "nasa matar uncle ɗin Abdallah tayi mata awo kuma sakamakon ya nuna cewa ba abun da ya same ta " "to shikenan Allah ya bata lafiya, kaga ma ko gaisawa ba muyi da Abdallah ba nagama kamar har da Abdulmajeed ku ka shi go " "Eh tare muke da shi " "to bari nasa sa'ada ta kawo maku breakfast naji kace bakuyi break ba kuka taho " "Eh Ammy " shazim ya faɗa haɗi da tashi ya nufi part ɗin shi wurin su Abdallah. Ɗakin fatima Ammy ta nufa, zaune ta samu sa'ada bakin gado ta zuba uban tagumi Sallama Ammy tayi sa'ada bata amsa ba ganin kamar hankalin ta baya tare da jikin ta ne yasa shiga ciki kusa da sa'ada ta ƙarasa, dafa kafaɗar ta tayi tace " sa'ada lafiya kika zuba uban tagumi ina sallama bakya ji " " ba komai Ammy " "ya za kice ba komai bayan na ganki cikin damuwa haka, ko dai duk a kan fatima ne " ɗaga mata kai sa'ada tayi alamar eh "ki kwantar da hankalin ki za ta samu sauƙi insha Allah " " to Ammy " "yawwa, zo ki je part ɗin shazim ki kai masu breakfast,ke ma kizo kiyi " "to Ammy ta faɗa haɗi da miƙewa su ka fita zuwa dinning, jera mata kayan breakfast ɗin Ammy tayi a tray, trayn ɗin bai ɗauke kayan duka ba hakan yasa Ammy cewa taje ta dawo sai ta kai masu sauran da to ta amsa har ta kama hanya zata nufi sama sai ga noraiz ya sauko amsar trayn yayi yace taje ta ɗauko sauran dan yaji lokacin da Ammy ke cewa taje ta dawo ta ɗauki sairan, " to ya noraiz " ta faɗa haɗi da komawa ta ɗauko sauran ta bi bayan shi, a bakin ƙofar part ɗin suka tsaya. Sa'ada tayi nocking, shazim ne yazo ya buɗe masu, amsar trayn da ke hannun sa'ada yayi noraiz kuma ya shiga da wanda ke hannun sa, juyawa sa'ada tayi ta koma parlorn Ammy "yawwa har kun kai masu " "Eh " "to kema jeki kiyi naki breakfast ɗin" da to ta amsa haɗi da nufar dinning ta zauna ,noraiz ma da ya shigo parlorn dinning ɗin ya nufa samun wuri yayi ya zauna , sa'ada tayi serving ɗin shi Ammy kuma ɗakin ta ta nufa ta kira malam da ummy ta sanar da su da wowar su shazim da kuma rashin lafiyar fatima, malam ranshi yayi matuƙar ɓaci ya kuma ce wallahi babu wanda zai Aura ma fatima luqman, idan da yayi shiru innah na abun da ta gadama akan su yanzu bazai yi shiru ba sai dai duk abun da zai faru ya faru. "insha Allah ina nan zuwa anjima na duba jikin fatimar " "ai baba da kun barshi, jikin nata da sauƙi " "A'a, sai na zo " "to shikenan Allah ya kawo ku lafiya " da Ameen malam ya amsa, rejecting kiran yayi. wanda shazim ya kira a waya ne yazo, magungunan ne ya kawo mashi wanda zai cigaba da ba fatima. sai bayan sallar asr majeed ya tafi gida, akan zai dawo da daddare ya sake duba jikin fatimar,Abdallah kuwa kamar ya shaƙe majeed haka yake ji, shima majeed ɗin haushin Abdallah yake ji dan gani yake duk wannan abun da yake yana yi ne saboda kishi, ya lura son fatimar yake ko wannan su kishi ne ke ɗawai niya da shi. Kamar yanda malam yace da daddare su ka zo shi da ummy, majeed ya dawo shi da mamar shi daya faɗa mata fatimar bata da lafiya shi ne tace zata zo ta gaishe da ita, sun daɗe a gidan daga baya su ka tafi, su malam kuma shazim cewa yayi dan Allah su kwana nan, "A'a aboki gida zan koma, ai nace sai ranar da ka zama babban mutum tuk zan dawo gidan nan " "dan Allah dai malam iya yau fa " "ahab sai dai kayi kuma, komai dare sai na tafi gida fatimar dai ta farka " ba yanda bai yi da malam ba amma yace a'a bazai kwana ba ba dan ya so ba ya haƙura, tun suna sa rana farkawar fatima har suka fara fdda rai malam ma har ya ce ummy ta zo su koma gida, Ammy ma ta so ace sun kwana Amma yace A'a gobe dai zasu dawo idan ta farka, rakiya su kayi masu har parking lot idan drivern malam yake sai da suka ga tafiyar su tukun suka koma ciki. kowa shirin kwanciya yayi ya nufi ɗakin shi, Ammy ta so ta kwana medical room ɗin wurin fatima gudun kar ta farka cikin dare amma shazim yace ta bari shi zai kwana ɗaki ita ta tafi ta kwanta kawai, tafiya tayi amma gaba ɗaya hankalin ta na kan fatima ko da ta tafi ɗakin ta bata kwanta ba alwala tayi ta shiga nafilfilo tana roƙwan Allah ya fatima lafiya, sa'ada kuma a ɗakin fatima ta kwana. Shazim bedroom ɗin shi ya shiga yayi wanka ya canza kayan da ke jikin shi zuwa na bacci parlor ya dawo wurin Abdallah dake zaune yana latsa wayar shi shima sanye yake da pajamas, kallon shi shazim yayi yace " ka shiga ka kwanta ni zan kwana wurin fatima dan ina kyautata zaton zata iya farkawa a kowane lokaci " "bana jin bacci, kai idan kana ji zaka iya kwanciya ni sai na zauna na jira ta farka " murmushi shazim yayi dama ya san in dai yace zai haka to Abdallah bazai kwanta ba "ko ina jin bacci dole na haƙura" "kai kana ma ji ke nan " "na san kai ma kana ji sai dai ka ƙi kwanciya " "to ina ji bazan kwanta ba" "to ai shikenan " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya ɗauki laptop ɗin shi, tashi Abdallah yayi ya bi bayan shi, medical room ɗin su ka nufa kan sofa suka zauna, shazim na aiki a laptop yayin da Abdallah ke aikin latsar waya...... _Episode 46_47_ ..........Medical room ɗin su ka nufa kan sofa suka zauna, shazim na aiki a laptop yayin da Abdallah ke aikin latsar wayar shi,suna ɗan taɓa fira jefi jefi, har shazim ya gama abun da yake a laptop fatima bata farka ba, wajen Asuba ta fara mutsu mutsun farkawa, da sauri su ka ƙara sa wurin ta, sai kiran sunan Ammy take da shazim,sai ƙoƙarin tashe take mai da ta yayi ya kwantar "ya shazim ina Ammy " fatima ta faɗa " Ammy tana ɗaki bacci take, ya jikin naki " "ya shazim ina nake " "kina gida ya jikin " "ya shazim ina ta kiran ka amma baka zo ba " "yanzu ai gani a kusa da ke " "ya noor ma da Ammy duk na kira su amma basu amsa man ba, ya luqman so yayi ya kashe ni ya shazim " ta faɗa hawaye na bin idanuwan ta, sosai ran Abdallah ya ƙara ɓaci da abun da fatima ta faɗa "kiyi haƙuri kinji, bazan sake bari wani abu ya faru dake ba insha Allah, ki kwantar da hankalin ki " "dan Allah ya shazim kar ka bari su Aura man shi wallahi bana son shi " "bazan taɓa bari su aura maki shi ba karki damu " "ya ina son ganin Ammy " "Ammy bacci ta ke fatima, dare ne yanzu ki bari sai da safe zata zo kinji " Abdallah na gefe ya ƙira mata ido ji yake kamar ya mayar da ciwan a jikin shi tsabar yan da yake jinta a cikin jikin shi "zaki sha ruwa ne " shazim ya faɗa ganin tana miƙa hannu alamar wani abun zata ɗauka, girgiza mashi kai tayi " Eh ya shazim " hannun yasa ya ɗauko ruwan da ke kan table ɗin da magungunan ta ke kai cire marfin jirkar yayi da kanshi ya bata a baki, bata wani sha sosai ba ta kauda kai, ajiye jikar shazim yayi yana cemata " ki koma ki kwanta " da to ta amsa haɗi da komawa ta kwanta drip ɗin da ke jikin ta ya cire mata "zaki sha tea ko " ya tambaye ta, ɗaga mashi kai tayi alamar eh "Ok bari na kawo maki sai kisha maganin ki daga nan " ya faɗa haɗi da tashi ya bar gaban gadon kallon Abdallah dake tsaye ya zuba ma fatima ido kamar ya cinye ta yayi " lafiya dai ko?" ya tambayi Abdallah haɗi da tsare shi da idanu, kawat kawata hankalin Abdallah na kan fatima bai ma san shazim na mashi magana ba, har sai da shazim ya ɗan taɓa shi tukun ya dawo cikin hankalin shi, zuba mashi ido yayi yana kallon shi "malam lafiya ka wani tsare ni da idanu " Abdallah ya faɗa yana wani shana mur "kai zan tamabaya ai wannan " shazim ya faɗa yana zuba mashi harara, jin muryar Abdallah ne yasa fatima jutuwa da sauri ta kalli inda suke tsaye shi da shazim "Ya dr " fatima ta kira sunan shi cikin kasalelliyar murya ta marasa lafiya, matsawa yayi kusa da ita yana faɗin " "na'am fatima, ya jikin ki" hawaye ne su ka taru a idanuwan ta tace " ya dr, yaushe kazo " "tare muka zo da ke, ya jikin " ya faɗa haɗi da neman wuri bakin gadon ya zauna, fita shazim yayi zuwa part ɗin shi . hannun ta Abdallah ya kamo yana faɗin "fatima ina tambayar jikin ki kinyi shiru " "ya dr da sauƙi " "Allah ya ƙara sauƙi " "Ameen" shazim ne ya shigo hannun shi ɗauke da cup ɗin tea sai turiri yake,kusa da gadon ya matso, amsar cup ɗin Abdallah yayi yana faɗin "tashi ki zauna kisha tea ɗin " yunƙurin tashi tayi, aje cup ɗin yayi kan table domin ya tai maka mata ta tashi tun kafin ya ajiye shazim ya kamata ya tayar da ita zaune, " thanks" Abdallah yace, harara shazim ya zuba mashi murmushi kawai Abdallah yayi da kanshi ya shiga bata tea shazim kuma na duba mata magungunan da ya kamata ta sha, da ta kammala sha amsar magungunan Abdallah yayi ya miƙa mata da kanshi tasha, matsowa shazim yayi da allura a hannun shi yana faɗin " to malam matsa " juyowa Abdallah yayi yana kallon shazim dake tsaye hannun shi riƙe da allura, "ka matsa nace bawai ka kallan ba " matsawa Abdallah yayi yana faɗin "ka dai yi a hankali dan nasan halinka, ban da mugunta" "ka san Allah zanyi maka ita idan baka yiman shiru ba ɗan rainin wayau kawai " shazim ya faɗa yana nuna ma Abdallah allurar da ke hannun sa " zaka iya " Abdallah ya faɗa haɗi da nufar kan sofa ya zauna, fatima dai sai binsu take da idanu abun ba ƙaramin burgeta yake ba, matsowa shazim yayi kusa da ita yana faɗin "miƙo man hannun ki " hannun rigar da ke jikin ta taja haɗi da miƙa mashi hannun, a damtsen hannun ta yayi mata alurar yana tsirawa ta rintse ido da sauri Abdallah yace "wai Allah, dan Allah kayi mata a sannu " " ka takura man fah, ai da zuwa kayi ka amsa kayi mata da kanka " shazim ya faɗa " bana iya yi mata allura ai " tsaki shazim yaja " aikin banza da na wofi " " kai kaga aikin banza " fatima sai murmushi take dan ba kaɗan su ke sata nisha ɗi ba, lura da hakan ne ma yasa shazim biye ma Abdallah har sai da wani baccin ya sake ɗaukar ta tukun su ka bar ɗakin dan lokacin sallar asuba yayi, alwala su kayi a part ɗin shazim su ka nufi masallaci tare da noraiz su ka tafi, lokacin da su ka dawo Ammy da sa'ada su ka samu a medical room ɗin tare da fatima da ta sake farkawa, gaishe da Ammy su kayi haɗi da zama kan sofar da ke ɗakin har sai da gari yayi haske tukun su ka tashi su ka bar Ammy da sa'ada Innah Asabe ma ta shigo ta duba jikin fatima,da ta tashi tafiya kitchen bin ta sa'ada tayi ta shirya ma fatima lafiyayyen breakfast, duk da bakin nata ba daɗi haka Ammy da sa'adar su ka tasa ta gaba sai taci, ganin sun damu taci ne yasa ta daure badan tana jin da ɗin shi ba taci sosai sa'ada taji daɗin ganin taci, fatimar ma daɗi taji ganin yanda kowa ke nan nan da ita ta kuma ji daɗin ganin ƴan uwan ta a tare da ita, ko da Ammy ta kira malam ta sanar da shi farkawar fatima hamdala yayi ma ubangiji kuma da safen ya sa driven shi ya kawo su shi da ummy, da shazim bari yayi sai anjima yaje ya ɗauko su da kanshi sannan ya sanar da su farkawar fatimar, amma sai Ammy ta riga shi kiran malam sai dai kawai ya gansu sun zo, majeed ma ya zo shi da mamar shi sun daɗe gidan sosai sannan su ka tafi,shazim da har ya shirya zai je Abnoor sai ga kabir ya zo duba jikin fatima, tun jiya ya kira wayar shazim bai ɗauka ba shine ya kira noraiz, shine noraiz ɗin ya sanar da shi ai sun dawo da rashin lafiyar fatima, shine daya fito daga gida zai je eko ya fara zuwa nan dan ya duba jikin ta,da kabir ɗin zai wuce ne ya shirya su ka tafi tare ba yanda bai yi da Abdallah ba akan ya bishi su tafi amma yace zai tsaya idan lokacin shan maganin fatima yayi zai bata har ce mashi shazim yayi ai Ammy na nan amma ƙiri ƙiri ya ƙi binsu, tafiya shazim yayi ya bar sa shima bai wani jima ba ya wuce Abnoor can ma ana yi sallar asr ya dawo, Abdallah da ya zauna gida kulawa sosai ya ba fatima da tace kaza jiki na rawa zai yi mata shi tun yana ba Ammy mamaki har ya dai bata mamaki, dan sosai ya cire duk wata kunya daya ke ji ta Ammy,su malam kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin yanda Abdallahn yake kula da fatima a gaban su, har kiran Abie da mom yayi ya ba Ammy da malam har da ummy su ka gaisa su ka kuma yi ma su ya mai jiki, sai da daddare su malam suka tafi akan gobe ma zasu dawo su sake duba jikin ta. haka fatima ta cigaba da samun kulawa daga wurin kowa a cikin su har ta ɗan samu sauƙi ta ma koma ɗakin ta da zama yanzu ba'a mata allura magunguna kawai take sha, kwanan Abdallah huɗu ta wuce katsina dan tun tuni uncle ahmad ya tafi, ya tafi ne akan zai dawo ya sake duba jikinta shi da su Abie, kamar tayi kuka da zai tafi taso ace ya ɗan yi kwana ki da yawa cematan da yayi zai dawo ne yasa ta haƙura. Shazim kullum kafin ya tafi aiki sai ya tabbatar da taci abinci kuma tasha maganinta, noraiz ma ya fara aiki kulawa kowa yake bata hakan yasa ta ƙara jin daɗi kuma jikin ta Alhmdllh masha Allah dan ba inda bata zuwa, kuma taji daɗin da sa'ada ta biyo ta. Satin su ɗaya da dawowa lagos su uncle Ahmad su ka zo da uncle Ibrahim, kairiyya, feenah, gwaggo Halima , luqman har da momy da mama, mansoor bai samu zuwa ba saboda aiki amma yace insha Allah yana nan zai zo idan ya kammala, ba yanda ba su yi da innah da gwaggo Uwani su zo ba amma tace wallahi ita ba zata zo ba ta so ma ta hana su uncle Ahmad ɗin ma zuwa amma su kace su sai sunzo sun gaishe da fatima. Fatima gaba ɗaya hankalinta tashi yayi da ta ga luqman dan ta tsorata da shi,bawan Allah duk ya sha jinin jikin shi ganin yanda take ɗari ɗari da shi, ga wani kallon tsana da shazim ke binshi ga Ammy kwata kwata ta ƙi bashi fuska ko da ya gaishe da ita kadarn kadaham ta amsa mashi ƙarshe ma tashi yayi ya bar parlorn ya nufi parking lot ya zauna a mota , haɗa kan shi yayi da siti yarin mota duk ji yayi ya tsani kan shi yayi kuma daya sanin abun da yayi mata, ganin duk ya damu ne ya kuma ware kanshi ne yasa Ammy ta ɗan saukko tanuna ba komai komai yawuce har ta sa noraiz ya kira mata shi, ko da yazo haƙuri ya bata akan abun da yayi fatima, ta kuma ce ta yafe mashi amma a zuciyar ta ɗauki alƙawarin ba zata bari ya auri fatima ba Fatimar ma ba yanda ba'ayi da ita ba akan ko magana tayi ma luqman ɗin ko da bazata yafe mashi ba amma taƙi. Fennah sai ƙoƙari take taga shazim ya kula ta amma ya ɗure fuska ko kallon banza bata ishe shi ba,da su uncle su ka tashi tafiya ƙin binsu feenah tayi dole ita a nan zata zauna, ganin ta dage ne yasa Ammy cewa a barta idan mansoor yazo sai su koma tare harda kairiyya ma, sa'ada daman ba mai maganar ta dan cewa tayi tun da fatima baza tai karatu abuja ba to ita zata yi lagos , ko da tace haka dady bai yi musu ba ya amince mata. da zasu wuce sai da suka je gidan malam,su ka kuma roƙi afuwar shi akan abun da luqman ɗin yayi, ya kuma haƙura yayi masu Allah ya kiyaye hanya. Shazim fa har su ka tafi ban da gaisuwa babu abun da ya haɗa shi da su har su ka bar garin. Abdallah kamar yan da yace kwanan shi biyar da tafiya, ya dawo shi da uncle Ahmad mom da ummh, abie bai samu zuwa ba saboda wani uziri daya tsare shi, hakan yasa su ka zo su ka ɗai ban da shi, Ammy taji ɗadi sosai ta kuma yi masu godiya, fatima kamar tayi dan bata taɓ gaini mom ba a zahiri sai dai photo da waya sai ga shi yau taga mom ido da ido. wani abu da na lura da shi kallon da mom ke ma ammy da wanda ammyn ke ma mom kamar sun taɓa ganin juna ko, duk da sun kasa tuna inda su ka taɓ ganin juna. A ranar su mom su ka koma katsina Abdallah kuma sai da yayi kwan biyu tukun ya koma. _* to masu karatu kar ku manta an tafi an bar Feenah da kairiyya akan idan mansoor ya zo za su tafi tare da shi , yanzu wasan zai fara amma kafin nan ina so na sanar da ku waye shazim*_ _*WANENE DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN ( SHAZIM) *_ Dr shazim ya ka sance ɗane daga zuriar alhaji nuraddeen ahmad sharani. Alhaji nuraddeen sharani, mutum ne mai rufin asiri, ya ka sance ɗan kasuwa ne mai sayar da kayan masarufi, alhaji nuraddeen yana zaune ne a garin kurfi dake jahar katsina, anan cikin garin yake gudanar da harkar kasuwancin shi da ƙauyakun da ke kusa da garin kurfi. Alhaji nuraddeen yana da mata ɗaya tilo mai suna habiba ana kiran ta da ruma, ita ma yar cikin garin kurfi ce, barumiya ce kyakyawar gaske, shekarar su goma cif da aure Allah bai basu haihuwa ba, ruma kullum cikin tashin hankali take saboda tsangwamar da iyah ( mahaifiyar nuraddeen ) ke mata ita da ƴaƴen ta, har ta kai ko hidima suke ruma bata zuwa saboda kyara da tsangwama da suke mata, ganin yanda hankalin ruma yake atashe yasa nuraddeen ya shiga kwantar mata da hankali yana nunamata cewa Allah yana sane dasu kuma zai basu haihuwa karta damu da duk abunda ƴan uwan shi ke cewa, sosai yayi mata nasiha akan su cigaba da adu'a kawai, kwantar da hankalin ta tayi ganin mijinta bai damu da rashin haihuwar ta ba, mahaifiyar nuraddeen ta takura ma shi akan dole fah sai ya ƙara aure tunda matar shi bata haihuwa, nuna mata yayi baya buƙatar ƙara aure, indai haihuwa ce Allah zai ba ruma, sosai ran iyah ya ɓaci jin abunda ya ce ta kuma ɗauki fushi da shi akan ƙinbin umarnin ta da yayi, har gida taje ta samu ruma tayi mata cin mutunci, duk a tunanin ta ita ta hana nuraddeen ƙara aure saboda ta shanye shi, sosai tsanar da yan uwan nuraddeen kema ruma ta ƙaru saboda ƙin ƙara aure da yayi, ruma ba ƙaramar wahala take sha ba awurin iyah , dan kusan kullum sai ta zo har gida ta ci mata mutunci, hakan yasa tayi ta roƙwan mijin nata akan ya bi umarnin mahaifiyar shi da nuna mashi mahimmanci bin umarnin nata, da farko ƙin amincewa yayi sai da ruma ta rinƙa tasa shi gaba tana yi mashi kuka akan ya ƙara auren, haka nan ba dan ya so ba ya amince da ƙarin auren, iyah da kanta ta nema mashi auren ɗiyar aminiyarta, ba a ɗau wani lokaci ba aka ɗaura auren nuraddeen da amayar shi hauwa'u ana kiran ta da maijidda, ranar da aka kai hauwa'u gidan shi ya haɗa su ita da ruma yayi masu nasiha akan suyi haƙuri su zauna lafiya, hakan ce ta faru dan sosai ruma da maijidda ke zaman lafiya, ruma ta ɗauki maijidda kamar ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya........ _Episode 48_49_ ........... Watan maijidda ɗaya da satittika a gidan nuraddeen Allah ya albarka ce ta da samun ciki , zo kaga murna wurin nuraddeen da ruma, da iyah taji labarin cikin maijidda har gida ta zo tayi ta sakar ma ruma habaici tana ce mata juya, ita kuwa ruma babu abun da ya dame ta tasan Allah da ya bama maijidda yana sane da ita, sosai take kula da maijidda, cikin na kaiwa wata biyar ta hana maijidda aikin komai a gidan daga sallah sai bacci da cin abinci take yi,da cikin ya isa haihuwa iyah ta mai da maijidda gidan ta, a cewar ta a gaban ta zata haihu, watan cikin maijidda tara da kwana goma ta haifi ɗa namiji kyakyawa mai matuƙar kama da nuraddeen, zo kaga murna wurin angon jego da iya, ruma ma ba'a barta a baya ba tayi murna da farin ciki sosai, da ranar suna ta zagayo yaro ya ci sunan mahaifin nuraddeen Ahmad ana kiran shi da magaji, sai da maijidda tayi arba'in ta koma ɗakin mijinta,ruma ta cigaba da kula da ita da yaron ta har yayi ƙwari, shekarar magaji biyu maijidda ta samu wani cikin ta haifi ɗiyarta mace wacce taci sunan iyah watau maryam suna ce mata uwani haka maijidda tayi ta haihuwa amma ruma shiru bayan uwani maijidda tayi halimatu daga kan halimatu ne ta ɗan dakata bata ƙara haihuwa ba, yaranta sun taso cikin soyayyar mahaifin su da abokiyar zaman ta, sosai ruma ke son yaran kusan kullum suna tare da ita dan halimatu ma awurin ruma ta taso, haka rayuwa ta cigaba da tafiya,iyah ta tasa nuraddeen gaba akan dole sai ya saki ruma dan bataga amfanin ta ba tunda bata haihuwa, hankalin nuraddeen da ruma sosai ya tashi, amma bai saki rumar ba, ganin ba shi da niyyar sakin ruma ya sa ta sa aka kira mata shi har gida, tayi mashi faɗa sosai akan ya ƙi bin abun da ta ce har ikirari tayi mashi akan ko dai ya saki ruma ko kuma ta tsine mashi , ba shida wani zaɓi a lokacin bayan ya ai watar da abun da mahaifiyar shi ta ce, haka ya samu ruma yace taje gida sai ya nemeta, hankalin ruma ya kai ƙuloluwar tashi da jin abun da nuraddeen ya faɗa, haƙuri ta shiga bashi ita da maijidda, nuna masu yayi bashi da wani zaɓi ne, kuma ai ba sakin ruma yayi ba, cewa kawai yayi ta tafi gida insha Allah zata dawo idan komai ya daidai ta tsakanin shi da iya, dole ruma ba dan ta so ba ta haɗa kayanta ta tafi gidan iyayen ta, sun sha kuka ita da maijidda san da zata tafi, haka ta tafi gida rai babu daɗi, koda ta tafi gida nan ta samu yayarta bilkisu da ke aure cikin garin katsina ta zo, ran mahaifiyar ruma da na ƴar uwarta ba ƙaramin ɓace yayi ba akan abun da nuraddeen yayi, ko da bilkisu ta tashi tafiya tasa ruma tayi a gaba akan ta haɗa kayan ta su tafi katsina da farko ruma ƙin amincewa tayi akan zata tsaya har sai komai ya dai daita tsakanin ta da nuraddeen, hakan yasa mahaifiyarta ta yi mata faɗa sosai ba dan ta so ba ta bi bilkisu zuwa katsina, bayan tafiyar ruma katsina nuraddeen ya zo gida wurin mahaifiyar ta ya bata haƙuri akan abun da ya faru ya kuma nuna mata bashi da yanda zai yi ne umarni ne daga mahaifiyar shi, mahaifiyar ruma ta fahimci shi ta kuma yi mashi uziri, sannan ta ce yayi ma mahaifiyar shi biyayya ka wai ya saki ruma,hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba jin tace wai ya saki ruma, ƙin amincewa yayi, sai ma haƙuri da ya ba mahaifiyar ruma. Sosai rayuwar ruma ta chanza a gidan ƴar uwar ta, soyayya da kulawa ta ke samu daga wurin ƴar uwar ta da mijin ƴar uwar ta, hakan ya sa ta saki jikinta sosai a gidan ga kuma yaran ƴar uwarta da take kallo kamar ƴaƴen da ta haifa da cikin ta, ko wane lokaci tana tare da su, suma da sun dawo makaranta zaka same su manne da ita, watan ta ɗaya a gidan ta ƙara fresh tayi kyau hasken fatar ta ya ƙara fitowa har yar ƙiba tayi,zazzabin dare ne ya taso ta gaba,sai ta wuni lafiya amma da dare yayi sai zazzaɓi ya rufe ta, ko da bilkisu ta fahimci haka sai ta ce mata ta shirya su tafi asibiti amma ruma ta ƙi, wata rana suna zaune kan dinning zasu ci abinci daga buɗe warmer ƙamshin abincin ya daki hancinta tashi tayi da gudu ta nufi toilet, amai tashiga ƙwarawa kamar zata amayar da ƴan hanjin cikin ta , biyo bayan ta bilkisu tayi tana mata sannu da faɗin "nace muje asibiti amm kin ƙi saboda taurin kai, yanzu ai dole ki shirya mu tafi" da ƙyar ruma ta buɗe baki tace " ba sai munje ba yanzu da nayi aman na samu sauƙi " ƙin sauraran ta bilkisu tayi sai ma ficewa da tayi ta nufi ɗakin ta tana faɗin " ki shirya kawai mu tafi bana son taurin kai" tasa ta gaba bilkisu tayi ta shirya suka je asibiti, koda suka je aka yima ruma aune aune anan likita ya shaida mata cewa ruma na ɗauke da ciki tsawan wata uku da sati biyu, zo kaga murna wurin ruma da bilkisu, Allah sarki abun da suka da ɗe suna nema har ake mata gori ake kiranta da juya yau gashi Allah ya ba ta , koda labari ya isa kurfi sunyi murna da jin wannan labari, har gida mahaifiyar ruma ta sa aka kira mata nuraddeen ta sanar da shi, bawan Allah harda kukan shi saboda tsabar farin ciki, yana koma wa gida ya sanar da maijidda, ita ma tayi farin ciki kamar mi, koda iyah ta ji labari ita ma harda kukan ta musamman da ta tuna cin kashin da suka yi ma ruma ita da ƴaƴan ta har suke kiran ta da juya, har gida ta je ta bama mahaifiyar ruma haƙuri akan ruma ta dawo ta haihu ɗaki mijin ta, da farko ƙin amincewa mahaifiyar ruma tayi sai da iya tai ta bata haƙuri tukun ta haƙura kuma tayi mata alƙawari akan rumar zata dawo, iyah taji daɗi kuma tayi ma mahaifiyar ruma godiya, hakan ce ta faru, bilkisu da kanta ta shirya ruma ta dawo da ita gidan mijinta, soyayya da kulawa iyah ta shiga bama ruma tana tattalin ta kusan kullum tana gidan nuraddeen kamar wannane jika na fari da za'a haifar mata, haka shima nuraddeen kamar ba'a taɓa yi mashi haihuwa ba , wani ikwan Allah maijidda sai ta fara jin haushin kulawar da iyah da nuraddeen ke yima ruma, tana ganin kamar sun fi son ruma akanta , ƙi ƙiri ta fara nuna hassadar ta a fili, iyah kuwa da nuraddeen basu ma san tana yi ba, da cikin ruma ya kai watannin haihuwa kamar yanda iyah tayi ma maijidda haka tayi ma ruma ta mai da ta gidan ta da zama, yan da iyah ke son ruma ta ke bata kulawa kamar ta ɗauke mata nauyin cikin haka ta ke ji, saboda cikin ba ƙaramin wahalar da ruma ya ke ba, kullum nuraddeen ya nan manne da ita sai dare yake koma wa gida, sosai ran maijidda ya ƙara ɓaci saboda dawowar da nuraddeen ya ke yi da daddare da kuma wunin daya ke yi wurin ruma, gani take kamar saboda cikin ruma ya banzatar da ita da yaran ta,sosai tsanar ruma ta ƙaru a zuciyar ta duk ta manta rawar ƙafar da nuraddeen yayi lokacin da tana da cikin magaji, cikin ruma sai da ya kai wata goma da satittika bata haihu ba, hankalin nuraddeen ya tashi sosai ganin har tsawan wannan lokacin bata haihu ba, kwantar mashi da hankali iyah ta shiga yi akan ya kwantar ta hankalin shi ana samun irin haka, amma fir ya ƙi amincewa har sai da ya ɗauki ruma zuwa asibiti, ko da likita ya duba ruma anan ya gano cewa bazata iya haihuwa da kanta ba sai anyi mata cs, lokacin da bilkisu ta zo asibitin duk wani abu da ya kamata a yi na cs ɗin nuraddeen yayi har an shiga da ita theater room, bakin theater room ɗin suka tsaya shi da bilkisu suna jiran tsammani, har kusan awa huɗu ta shuɗe amma likitocin ba su fito ba lokacin ana ta kiran sallar asr, masallaci nuraddeen ya tafi ya bar bilkisu, har ya je ya dawo ba'a fito da ruma ba likitocin ma ba wanda ya fito, hankalin nuraddeen ya kai ƙololuwar tashi, sai da wasu awannin suka shuɗe sannan wata nurse ta fito daga ɗakin hannun ta riƙe da jariri cikin towel, da sauri nuraddeen da bilkisu suka nufo nurse ɗin suna tambayar ta jikin ruma,miƙa ma bilkisu jaririn tayi tana faɗin "ana gyarata ne,idan an maida ta ɗakin hutu sai ku ganta" da to su ka amsa mata , amsar jaririn bilkisu tayi tana kallon shi kyakyawan gaske a cikin kamannin ruma babu abun da ya baro kamar tayi kaki, idonun shi rufe da a lama bacci ya ke, barin wurin su nurse ɗin tayi, hankalin nuraddeen duk a tashe so kawai ya ke yayi ido biyu da ruma, sake buɗe ƙofar theater room ɗin aka yi dr ne ya fito yana cire safar hannun shi, da sauri nuraddeen ya ƙarasa wurin shi yana tambayar shi wane hali matar shi ke ciki, " Allah ya bamu ikwan cetan jaririn amma mahaifiyar shi ta sha wahala sosai, yanzu dai munyi mata allurar bacci tana ɗakin hutu,ko da za ku ganta sai zuwa anjima" "to shikenan dr, nagode "ya faɗa haɗi da miƙa ma mashi hannu su kayi musaba ha, dr yace "babu komi, Allah ya bata lafiya"da ameen nuraddeen ya amsa, wuce wa dr yayi zuwa office ɗin shi,nuraddeen ko ma wa yayi idan da bilkisu take ya amshi jaririn yana kallon shi, ji yake kamar ya mai da shi ciki tsabar yanda ya ke son shi, ruma bata farka ba sai wajen ƙarfe 9, nurse ce tazo ta sanar da su farkawar ruma, ta shi su kayi suka bi bayan nurse ɗin nuraddeen har yan tuntuɓe saboda sauri. Kwance take kan gadon marasa lafiya, jin an buɗe ƙofa ne yasa ta buɗe idanuwan ta dake rufe, binsu take da idanu ko ɗan ya tsanta bata iya ɗagawa, ba ƙaramin jin jiki take ba, zama nuraddeen yayi kan kujerar dake kusa da gadon, bilkisu kuma ta zauna kan gado, sannu su ka shiga yi mata,bata amsa masu ba sai ma hawayen da ke bin kumatun ta, hannu nuraddeen yasa yana share mata hawayen"ki daina kuka ruma Allah zai baki lafiya" jinjina kai tayi, hankalin nuraddeen duk ya ta shi ganin ko magana bata iyayi, yun ƙurin tashi take zaune,pillow yasa ya tai maka mata yayi ta ɗan jingina da bango sannu kawai su ke mata, kiran sunan nuraddeen tayi , da sauri yace na'am, hannunta ta miƙa ganin tana son kama hannun shi ne yasa shi sauri kama nata hannun yana ƙara mata sannu, da ƙyar ta buɗe bakinta tana tamabayar ina abun da ta haifa, da sauri bilkisu ta miƙa mata jaririn da ke hannunta, amsa tayi ta zuba jaririn ido tana kallon shi hawaye na bin idanun ta, gaba ɗaya duk tabi ta karya masu zuciya da kukan da take, ta ɗauki tsawan lokaci tana kallon jaririn daga bisa ni ta miƙa ma nuraddeen shi,amsa yayi yana kallon ta, murmushi ta sakar mashi, da ƙyar magana take fita daga bakinta tace "ina so kasa mashi sunan mahaifina dan Allah, sannan kayi man alƙawarin baza ka taɓa bari yayi maraici ba, ji nake kamar bazan tashi ba " "dan Allah ki dai na cewa haka cuta ai ba mutuwa bace insha Allah zaki samu lafiya " Bilkisu hawaye ne kawai ke zuba daga idanunta duk ta karaya "ina so dai ka ɗaukar man alƙawari " "Insha Allah zanyi maki yan da kike so fatana Allah ya baki lafiya " nuraddeen ya faɗa,"na gode, ina so kowannan ku ya yafe man duk wani abun da nayi mashi, duk wani wanda kuka san na taɓa mu'amula da shi ina son ku roƙar man shi yaya feman " sai haƙuri su ke bata ciwo ba mutuwaba ne, sai dai tayi murmushi idan su ka faɗa mata haka, nurse ce ta shigo ta sanar da nuraddeen likita na son ganin shi, tashi yayi ya bi bayan ta har office ɗin dr , wurin zama dr ya nuna mashi, zama yayi yana zuba dr ido yana sauraron mi zaice, magana dr ya fara " da man ba wani abu bane yasa na kira ka, game da jaririn ya kamata a nemo mashi madara saboda lafiyar shi zuwa wani ɗan lokaci sai mahaifiyar ta shi ta cigaba da shayar da shi,sannan ita ma akwai wasu magunguna da ya kamata ita mahaifiyar tashi ta riƙa sha " dr nagama faɗa ya rubuta mashi sunan magungunan da madarar da ya kamata a riƙa ba yaron kafin mahaifiyar shi ta cigaba da shayar da shi, yana gama rubutawa ya miƙa mashi, amsa yayi haɗi da yima dr godiya ya fice zuwa ɗakin da ruma take kwance,yana buɗe ƙofa ya samu bilkisu ta kifa kai da bango sai shashekar kuka take ruma kuma jikinta rufe yake da farin ƙyalle,wani irin faɗuwa da gaban shi yayi jikake dam dam, dafe saitin zuciyar shi yayi yana nufar gadon da take kwance hannun shi na rawa ya yaye farin ƙyale da aka rufe ta da shi, fuskarta ta bayyana idanuwan ta a rufe suke fuskarta da alamun murmushi, suma tsaye nuraddeen yayi lokacin guda ya tsinci kanshi ciki wani yanayi mara daɗi, hawaye ne suka shiga sakkowa daga idanun shi,zubewa yayi ƙasa kan gwiwowin shi yana faɗin "yanzu shikenan na rasa ruma har abada,kai hakan bazai yiwuba " sai sambatu yake kamar wanda ya zare, jin maganganun da yake ne ya ƙara karya zuciyar bilkisu ta ƙara sautin kukan da take. _*ALLAH SARKI RUMA UBANGIJI ALLAH YA JIƘANKI DA RAHAMA ABUN DA KIKA BARI ALLAH YA RAYA SHI*_ A wannan yana yin faɗa maku tashi hankalin da nuraddeen, bilkisu, iyah, mahaifiyar ruma suka shiga ɓata lokaci ne suna shiga tashin hankali mara misltowa. bilkisu ta ciga da kula da jaririn har aka yi adu'ar uku, sannan nuraddeen yayi ma yaron huɗu ba da suna Abubakar sadiq,ya ciki alƙawarin da ya ɗaukar ma ruma, har akayi arba'in da rasuwar ruma sadiq na hannun bilkisu, da ta tashi komawa katsina da sadiq ta tafi har aka yaye shi, san da aka yaye shi mijin bilkisu ya nemi da abashi sadiq,amma sai nuraddeen yace a'a shima yana son yaron shi ya taso a gaban shi,bilkisu ta so ace nuraddeen zai bar mata sadiq a hannun ta amma bata da yan da zata yi haka ta dawo da sadiq hannun mahaifin shi,lokacin da mijinta aka tura shi ƙasar china jakadancin nigeria, har kurfi ta zo ta sake roƙon nuraddeen daya bata sadiq ɗin ta tafi da shi, amma yace a'a idan dai sun zo nigeria zai riƙa zuwa masu hutu, taji haushin ƙin bata sadiq da nuraddeen yayi amma bata da yan da zata yi tun da ɗan shi ne dan dole ta haƙura ta tafi da kewar yaron. Kulawa sosai sadiq ke sa mu wurin mahaifin shi da kakar shi iyah, ganin yan da iyah da nuraddeen ke kula da sadiq ya sa maijidda ɗaura mashi karan tsana duk da yake ƙaramin yaro, ƴan uwan shi na son shi amma ta hana su ma'amula da shi, ko wasa suke ya zo wurin su sai ta sa su kore shi ko su da ke shi, tun basu ɗaukan abun da take sa su har hakan yayi ta siri da sadiq ya shiga cikin su zasu yi ta kyarar shi da hantarar shi, haka zai raɓe yana kuka ta kuma ja mashi kunne akan muddin ya faɗa ma nuraddeen sai tayi mashi bugun tsiya, bawan Allah haka zai shiru bai taɓa faɗa ma mahaifin shi ba, wani munafuncin na maijidda idan a gaban nuraddeen sai ta nuna tana tausayi sadiq tayi ta ririta shi amma idan nuraddeen baya gida wahala iriri babu wacce bata sa sadiq har aiki wan da ya fi ƙarfin shi sa shi take yi lokacin yana da shekara shidda amma sai ta sashi abun da ya fi ƙarfin shi,lokacin ta ƙara haihuwa yaron na da shekara ɗaya a duniya, sunan yaron Ibrahim kyankyawa ne dan yafi su magaji kyau shiyyasa ita ma tafi son shi a cikin su, haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq ya taso cikin ƙiyayyar yan uwan shi, kwata kwata baya jin daɗin zama da su, sauƙin shi ɗaya idan mahaifin shi na gida ko kuma yaje gidan iyah ko su magaji na makaranta daya ke ba makarantar su ɗaya ba ta nan kawai ya ke samun sauƙin wahalar da yake sha ta su magaji dan har tafi wacce yake sha wurin maijidda, wurin iyah ya koma da zama dalilin wani bugu da su magaji suka yi mashi har suka ji mashi ciwo, daya je gidan iya ya faɗa mata har gida tazo ta sami maijidda tayi mata zagin wulaƙanci akan ita ta sa su magaji su ka daki sadiq, haƙuri ta shiga bama iyah ta na cewa "kiyi haƙuri dan Allah iyah, wallahi sadiq ƙarya ya ke faɗuwa yayi amma ba dukan shi su magaji suka yi ba " ji suka yi an ce "wayyayi iyah cu yaya ne cuka buge ci" Ibrahim da ke tsaye bayan maijidda ne yayi maganar lokacin yana da shikara uku, maijidda kamar ta nutsi saboda baƙin cikin abun da Ibrahim ya ce yaro ne amma sai wayen tsiya,gashi kuma bala'in son sadiq yake dan wani lokacin idan maijidda ko ƴan uwan shi suka daki sadiq nan zai zauna yana kuka da kuma mahaifin su ya dawo zai sanar da shi, murmushi iyah tayi tana faɗin "kaga ɗan albarka, dama na san ƙarya kike, da ma chan na lura ba son sadiq kike ba saboda kinga mahaifin shi ya fi son shi, idan bai fi son shi ba ya ki ke so yayi yaron nan ana haihuwar shi mahaifiyar shi ta rasu to dan mi mahaifin shi bazai nuna mashi kulawa ba, amma kinbi kin tsani yaro kin ɗaura mashi karan tsana kin hanashi wasa da ƴan uwan shi kin sa sun tsane shi saboda tsabar zalunci, to bari kiji wallahi ki shiga hankalin ki in ba haka ba zakiyi mamakin abun da zanyi maki shashasha kawai" tana gama faɗa ta ja hannun sadiq suka koma gidan ta, haka rayuwa ta cigaba da tafiya sadiq na hannun iya har ya kusa gama primary school, yan primary 5 lokacin magaji ya kammala secondary yana bin mahaifin su kasuwa , uwani na ss1 halimatu na jss 3 Ibrahim kuma na primary 2 Allah yayi ma iyah rasuwa sosai sadiq ya shiga tashin hankali mara misltowa ya ci kuka kamar ranshi zai fita ana bashi haƙuri, bayan an gama zaman makokin iya sadiq ya koma gidan mahaifin shi da zama, sadiq ya ga rayuwa, wahalar maijidda yake ci sosai ba kaɗan ba ita da uwani, saboda magaji tun da ya girma ya watsar da huɗubar mahaifiyar shi ya kama ɗan uwan shi ganin magaji yana son sadiq yanzu yasa halimatu ita ma take janshi a jiki dama shi Ibrahim baya da matsala tuna farko, uwani ce dai dama can ita bata da mutunci sak halin maijidda gare ta, sosai sadiq ke shan wahalar ta kai sai ayi rabon abinci a manta da shi sai dai halimatu da Ibrahim su bashi nasu a ɓoye dan idan maijidda ta sani dukan tsiya take masu shi daman magaji baya gidan yana kasuwa tare da mahaifin shi, haka rayuwar sadiq ta cigaba da tafiya kamar mara galihu mara gata, shi da gidan mahaifin shi amma bashi da sakewa sai in mahaifin shi da yayan shi magaji na gida, wata rana wani aminin nuraddeen alhaji abdulƙadir wanda suka taso tun ƙuruciya,lagos yake tun bayan rasuwar iyayen shi ya koma wurin ƙanin baban shi da zama acan yayi karatun shi ko da ƙanin mahaifin nashi ya rasu bai dawo kurfi ba a lagos ya cigaba da zama , du da yana lagos nuraddeen na kurfi tare suke harkar kasuwanci , sai dai shi alhaji abdulƙadir yana zuwa har ƙasashen waje ,alhaji abdulƙadir yafi nuraddeen ƙuɗi nesa ba kusa ba, matar shi ɗaya hajiya zainab balarabiyar ƙasar Morocco ce, sun haɗu ne a chan ƙasar har Allah yasa suka yi aure, shekarar su kusan goma amma basu da ɗa ko ɗaya, zainab tana haihuwa amma ƴaƴan basu zuwa da rai, ko da ya kawo ma nuraddeen ziyara bai nufi kasuwa ba gidan shi ya nufa direct , nan ya ci karo da sadiq bakin ƙofar gida yana kuka,dafa kafaɗar sadiq alhaji abdulƙadir yayi yana cewa "yaro yaya sunan ka? " cikin shashekar kuka sadiq yace "sunana sadiq " "masha Allah, amma miyasa kake kuka, ina mahaifin ka? "sadiq ya ce "bakomi, babana yana kasuwa" "to ko zaka iya rakani wurin shi? " da to sadiq ya amsa mashi, har kasuwa ya raka shi wurin nuraddeen, sosai nuraddeen yayi farin ciki da ganin alhaji abdulƙadir dan sun ɗan dade basu haɗu ba, gida suka koma, nan suka shiga firar yaushe gamo, anan alhaji abdulƙadir ya nuna yana son ya tafi da sadiq logas ,ƙin amincewa nuraddeen yayi, saboda ba ƙaramin son sadiq yake ba baiso ko kaɗan yayi nesa dashi, ko da ya shiga gida fuskar shi da ɗan damuwa, tambayar shi maijidda tayi akan mike da munshi, nan yake faɗa mata "wallahi wani aminina ne yazo, to shine ya buƙaci da na bashi sadiq, to gaskiya gani nake kamar zai ƙara ma kan shi wahala ne, dan nafi shi rufin asiri ne sa ba kusa ba, to abunda ya sa ki gannin ciki da muwa ban so yaga kamar na hanashi sadiq ne saboda ni Allah ya bani , da yake shi bai da ɗa ko ɗaya " wani da ɗi ne ya rufe maijidda tana ganin wannan ce hanya mafi sauƙi da zata raba sadiq da nuraddeen, kuma da taji mutumin talaka ne abun ya ƙara mata daɗi sai dai bata ji daɗin ƙin amincewa da nuraddeen yayi ba , ta so ace ya ba da sadiq ɗin ko dan ta huta da ganin shi, kuma tana ganin idan sadiq ya tafi daga nan nuraddeen bashi da wanda zai so sai ƴaƴanta, haka ta shiga zuga nuraddeen akan ya ba abdulƙadir sadiq, ita duk a tuna nin ta da gaske abdulƙadir talaka ne bai da komi,dan bai faɗa mata Abdulƙadir bane dan ta san Abdulƙadir sosai rashin faɗa mata ko waye yasa tai ta zuga nuraddeen,kallon ta kawai nuraddeen yake, dama yace mata aminin shi ne kuma talaka ne dan yaga mizatayi yayi ne daman dan ya gwada ta, sai kuma yaga farin cikin ta, hakan ya ƙara tabbatar mashi da cewa da gaske maijidda bata son sadiq ko ƙaɗan, ko da magaji yaji labari shima haɗa mahaifin shi da Allah yayi akan ya bari a tafi da sadiq ko ba komai zai samu kwanciyar hankali, sai daga baya shima nuraddeen da yayi tunani yaga da cewar ya ba abdulƙadir sadiq, ko dan shima sadiq ɗin ya huta da tsangwamar da maijidda keyi mashi , dan abdulƙadir mutumne mai mutunci, yana da kirki sosai kuma zai ruƙe sadiq kamar ɗan daya haifa,ya san kuma rayuwar sadiq zata chanza, har ma sauki ya samu abdulƙadir ya faɗa mashi ya amince zai bashi sadiq, ba ƙaramin daɗi abdulƙadir yaji ba ya kuma yima nuraddeen godiya sosai, sannan yace ya shirya sadiq ɗin gobe da man zai koma lagos da safe , sunjima suna fira har kusan yamma sannan nuraddeen yayi mashi sallama, yana komawa gida yasa halimatu ta haɗa kayan sadiq cikin jaka, Ibrahim sai kuka yake za'a tai mashi da ɗan uwan shi wani wuri, lalla shin shi sadiq yake amma ya ƙi haƙura, ita kuwa maijidda sai jin daɗi take sadiq zai shiga cikin wahala. Washe gari da safe wurin ƙarfe takwas abdulƙadir yazo domin tafiya da sadiq, halimatu ce ta fito da kayan sadiq har ƙofar gida, amsar jakar drivern abdulƙadir yayi da ga hannun halimatu ya sa a bayan mota , nuraddeen ne da abdulƙadir suka fito magaji na riƙe da hannun sadiq, ban kwana abdulƙadir yayi ma nuraddeen sannan ya ja hannun sadiq suka shiga mota, sadiq na ta ɗaga ma magaji da Ibrahim da halimatu hannu, suma suna ɗaga mashi hannun har motar ta bar anguwar,kasuwa nuraddeen da magaji suka wuce halimatu da Ibrahim kuma suka koma gida, abdulƙadir koda ya kai ma matar shi sadiq, sosai tayi murna kuma ta karɓi sadiq hannu bi biyu, gata da kulawa sadiq ke samu wurin abdulƙadir da hajiya zainab, abdulƙadir ya saka sadiq makaranta,sai dai makarantar basu sa shi ajin daya tsaya ba ya fara ne daga primary 4, kuma kamar yan da ya faɗa duk akayi hutu sadiq na zuwa kurfi, zuwan shi na farko kurfi maijidda kamar tayi huaka dan baƙin ciki ganin yanda sadiq ya koma, yayi kyau yayi fresh hasken shi ya ƙara fitowa, tayi data sannin sa baki nuraddeen ya bada sadiq, nan ta nace akan idan sadiq zai koma lagos sai ya tafi da Ibrahim, sosai nuraddeen ya ci mata mutunci ya kuma ce shi ba mutum banza bane, sadiq abdulƙadir yace yana so to dan haka bazai tura Ibrahim ba, bala'i sosai maijidda tai ta yi akan wai nuraddeen ya nuna ya fi son sadiq shiyyasa da abdulƙadir yace ya bashi shi ya ɗauka ya bashi,kullum cikin ɗaga ma nuraddeen hankali maijidda take har sadiq ya gama hutun shi ya koma, shekarar sadiq ɗaya a lagos Allah ya azurta zainab da samun ciki, zo kaga murna da farin ciki wurin zainab da abdulƙadir sadiq ma sai murna yake za'a haifa mashi ƙani ko ƙanwa, daya dawo daga school zai tasa zainab gaba yana faɗin ummy yaushe zaki haifa man ƙani, wani lokacin idan yayi mata tambayar sai dai tayi dariya, cikin zainab na shiga watan haihuwa, ta matsa ma abdulƙadir akan dole sai ya kaita Morocco ta haihu acan, ba dan ya so ba ya kaita, sadiq ma yasa rigima akan dole sai ya bita, haka abdulƙadir yayi masu visa yakai su shi kuma ya dawo, satin zainab ɗaya a morocco ta haifi ɗiyar ta kyakyawa mai kama da ita,ba'ayi suna a morocco ba suka dawo nigeria, da sati ya zagayo yarinya ta ci sunan mahaifiyar zainab watau Aisha, har lagos nuraddeen yazo ranar sunan aisha, sosai sadiq yayi murna da ganin mahaifin shi, da nuraddeen ya tashi tafiya maƙale mashi sadiq yayi akan sai ya bishi, zainab tasa ƙanwarta wacce suka zo tare da ga morocco ta haɗa ma sadiq kayan shi da zai bi nuraddeen......... _Episode 50_51_ ............. Koda nuraddeen ya koma da sadiq kurfi, bala'i maijidda ta tada akan dole sai sadiq ya dawo kurfi da zama tun da daman dan abdulƙadir bai da ɗa ko ƴa yasa aka bashi sadiq to tun da yan zu matar sh ta haihu sai sadiq ya dawo gida, sai da nuraddeen ya biyo mata ta bayan gida sannan ta kama kanta, sadiq bai gama hutun ba nuraddeen ya haɗa mashi kayan shi ya mai da shi lagos , a kwana a tashi asarar rai sadiq ya kammala secondry school lokacin aisha na da shekara bakwai a duniya,a lokacin tana primary 4, daya ke tun tana 4 year alhaji abdulƙadir ya sata makaranta, akwai soyayya da shaƙuwa tsakanin sadiq da aisha bacci kawai ke raba su, ko wane lokaci zaka same su suna tare da juna, musamman da yanzu sadiq yake zaune a gida yana hutu kafin ya fara zuwa jami'a, da sadiq zai tafi kurfi kuka aisha ta sa a dole sai ta bishi hajiya zainab da sadiq su kaita lallashinta sadiq yayi mata alƙawarin idan zai koma bikin su halimatu zai tafi da ita sannan ta haƙura,ko da sadiq yaje kurfi anan yake samun labarin rasuwar kakar shi wacce ta haifi ruma, yayi kuka sosai dan ba ƙaramin son tsohuwar ya ke ba saboda ita ma tana son shi,hutu na ƙarewa ya koma lagos , bai wani jima da dawowa ba ya fara zuwa school, kullum kafin ya tafi school sai ya fara ajiye aisha a school sannan yake wuce wa , saboda da zai fara zuwa jami'a mota abdulƙadir ya siya mashi, idan an tashe su kuwa driver ke ɗauko ta ranar da bashi da lectures kuwa shi ke kaita ya ɗauko ta, haka rayuwa taci gaba da tafiya an tsai da ranar bikin su uwani ita da halimatu, bikin su na saura sati ɗaya sadiq ya shirya zai tafi kurfi maƙalewa aisha tayi sai ta bi shi, shirya mata kayanta hajiya zainab tayi suka tafi,suna isa kurfi da Ibrahim suka ci karo zaune ƙofar gida shida abokan shi, yana ganin su ya taso da fara'a a fuskar shi yana ma sadiq barka da zuwa yayin da yake amsar jakar kayan da ke hannun shi, gaishe da shi aisha tayi, ya amsa mata da fara'a yana ce ma sadiq su shiga ciki, gidan suka nufa, suna shiga halimatu na zaune kan kujera yar tsugunno tana wanke wanke, ta so wa tayi da sauri tana ma su barka da zuwa suna nan tsaye maijidda ta fito daga kitchen hannun ta riƙe da kwano, wurin su ta ƙaraso tana bin aisha da ido, sadiq ya ce "ina wuni innah, mun same ku lafiya " daga mashi kai kawai tayi tana tambayar wannan fah, sadiq ya bata amsa da aisha ce ƙanwa ta, fuska a ya mutse tana kallon aisha ta ce"ba shakka, sannu ko " duƙara da kai aisha tayi tana cewa ina wuni da lafiya lau maijidda ta amsa sai kuma tace" yasu mamar ki kun baro su lafiya" da fara'a aisha tace" lafiya lau suke suna gaishe da ku" "muna amsawa "maijidda ta faɗa sannan tace ma halimatu " ki kaita ɗakin ku, kunyi tsaye "tana gama faɗa ta juya ta nufi ɗakin ta, da kallo suka bita fuskar su da mamaki dan ba su taɓa tuna nin zata yima aisha ko kallon arziƙi, kayan ta da ke hannun sadiq halimatu ta amsa haɗi da jan hannun ta suka nufi ɗakin su, sadiq ma ɗakin su suka nufa shida Ibrahim yana tambayar shi ina su baba da magaji sai da yamma magaji suka dawo daga kasuwa shida nuraddeen, sosai magaji yaji daɗin ganin sadiq hakama nuraddeen yayi farin ciki sosai musamman da yaga aisha, kulawa sosai aisha ke samu wurin dangin sadiq mu samman halimatu dan ta ɗauki aisha kamar ƙanwarta, uwani ce kawai ba ruwan ta da aisha amma har maijidda na jan ta a jiki, abun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, ana gobe ɗaurin aure gida ya cika da baƙi alhaji abdulƙadir yazo shida hajiya zainab, tarba mai kyau suka samu wurin nuraddeen da maijidda, washe gari aka ɗaura aure aka kai amare gidajen mazajen su aisha gidan halimatu ta kwana, sai washe gari ta dawo gidan su sadiq saboda ranar zasu koma lagos harda sadiq, da zasu tafi kiran sadiq maijidda tayi ɗakin ta akan mizai hana su tafi tare da Ibrahim tun da ya kusa gama makaranta, haƙuri sadiq ya bata yana cewa ko jiya yayi ma baban su maganar yana so su tafi tare da Ibrahim amma yace bai amince ba, haushi kamar ya kashe maijidda, gani take nuraddeen baya son ƴaƴan ta sadiq kaɗai yake so, kwantar da murya tayi tana cewa "kana jina sadiq ka rabu da maganr baban ku, da kace ma alhaji abdulƙadir kana son tafiya da ɗan uwanka nasan zai amince "maganar nuraddeen suka ji daga bayan su yana cewa "to wallahi ban amince ba , idan har kana son zaman lafiya da ni kar na sake naji kayima abdulƙadir wannan maganar kaji na faɗa maka "maijidda ta ce" wai miyasa kake haka ne, yaro na son tafiya da ɗan uwan shi amma ka hana haba dan Allah "ko kallon inda take bai yi ba yace ma sadiq "kama hanya ka wuce suna waje suna jiran ka "da to sadiq ya amsa yana ma maijidda ban kwana, Allah ya tsare kawai tace tana bin nuraddeen da kallo da zai fita, har ƙofar gida nuraddeen ya samu su sadiq yayi ma abdulƙadir ban kwana dayi mashi godiya, da motar su zata bar anguwar Ibrahim harda kukan shi, sannu sannu bata hana kaiwa sai dai ajima ba'a kai ba magaji ma yayi aure lokacin halimatu da uwani na da ƴaƴa ɗai ɗai uwani na da namiji mai suna usman halimatu kuma mace sunan ta zainab. soyayya ce ta ƙullu tsakanin sadiq da aisha hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma abdulƙadir da nuraddeen ba, dama basu da wani buri daya wuce haka zainab abun yayi mata daɗi dan baƙaramin so take yima sadiq ba tamkar ɗan cikin ta haka ta ɗauke shi , da sadiq ya kammala degree ɗinshi,kullum suna tare da aisha dan har binta yake makaranta, alhaji abdulƙadir ya ɗaura sadiq kan kasuwanci kafin ya fara aiki, sai da sadiq yayi kusan shekara ɗaya da rabi yana gudanar da kasuwanci sannan alhaji abdulƙadir ya sama mashi aiki a Abuja duk da sadiq ɗin yaso yayi a lagos saboda kwata kwata baya son abun da zai sa yayi nisa da aisha, da zai tafi kuwa aisha har da kuka abun ma mamaki ya ba ma hajiya zainab,sadiq bai daɗe da fara aiki ba nuraddeen da abdulƙadir suka tsai da rana auren su da aisha akan da ta kammala makaranta za'a yi bikin, hakan ce ta faru aisha na kammala makaranta aka fara shirye shiryen biki,ana saura wata ɗaya ƙanwar zainab tazo daga Morocco ta tafi da aisha, chan zasuyi mata gyaran jiki sai ana saura sati za su dawo da ita, ana saura sati ɗaya bikin Aisha ta dawo daga Morocco ita da yan uwan hajiya zainab , gida ya cika da baƙi aka fara shirye shirye an je anyi ma aisha jere gidan sadiq, shagali sosai alhaji abdulƙadir ya shirya haka ma nuraddeen ba'a barshi a baya ba, ana saura kwana uku yan kurfi suka zo part guda alhaji Abdulƙadir ya ware ma Nuraddeen ya ajiye duk wani baƙo daya zo mashi da yan uwan shi, maijidda kuwa ita da su uwani da yaran su suna part ɗin hajiya zainab , ranar juma'a aka ɗaura auren Abubakar Nuraddeen Ahamad Sharani da amaryar shi Aisha Abdulƙadir murna wurin ango da amarya ba'a cewa komai da yamma Alhaji abdulƙadir da nuraddeen suka haɗa aisha da sadiq su kayi masu nasiha,sannan suka je wurin hajiya zainab,nasiha sosai tayi masu da fatan alkairi, aisha na kuka ƙannan hajiya zainab suka yi mata rakiya gidan mijinta, ranar lahadi yan uwa da abokan arziƙi suka fara tafiya , ƴan kurfi kuma washe gari zasu tafi litinin kenan , da yamma maijidda tasa aka kira mata sadiq ta sake mashi maganar Ibrahim, cemata sadiq yayi "innah baba ya hana, ina kuma tsoron abun da zai biyo baya idan nace dole sai Ibrahim ya tsaya"bal bale shi da masifa maijidda tayi, wai bai son zumunci dan yaga Allah ya ɗaukaka shi shine zai fara ƙyamar ɗan uwan shi,abun yayi mugun bama sadiq mamaki, bai taɓa tuna nin maijidda zata ce mashi haka ba arayuwa, haƙuri kawai ya bata, washe gari da safe sadiq yaje gidan alhaji abdulƙadir domin gaisawa da su ya kuma yima su nuraddeen rakiya saboda da safen zasu tafi, koda ya gaishe da nuraddeen bai san miya faru kawai nuraddeen ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yana cewa "kenan ni ban isa na hana ka abu ka hanu ba ko " haƙuri sadiq ya shiga bashi batare da yasan miya aikata ma mahaifin nashi ba, sai da zasu tafi halimatu ke bashi haƙuri haɗi da faɗa mashi abun da ya faru, wai ashe lokacin da ya bar ɗakin da maijidda ta sauka, fita tayi daga ɗakin taje har ɗakin hajiya zainab ta roƙe ta akan dan Allah tunda sadiq da aisha basu gidan yanzu za su ji duk ba daɗi mizai hana Ibrahim ya dawo gidan da zama, to shine hajiya zainab ta sami alhaji abdulƙadir da maganar shiku ya samu nuraddeen akan dan Allah ya bar mashi Ibrahim ɗin, to shine nuraddeen yayi tuna nin sadiq ne ya faɗama abdulƙadir ɗin shine ya rufe shi da faɗa, koda halimatu tagama faɗama sadiq bai ji daɗin abunda maijidda tayi ba yaso ace ta bari ya lallaɓa baban nasu harya amince, amma ta ɓata mashi komai gashi baban yayi fushi da shi, kafin su wuce sai da sadiq ya sake bama nuraddeen haƙuri,ya haƙura amma akan da Ibrahim zasu tafi daga baya sai ya dawo amma ina abdulƙadir yaƙi amincewa , ba yanda nuraddeen ya iya dole ya bar Ibrahim, maijidda daɗi kamar ya kashe ta, nuraddeen na lure da ita bai dai ce komai ba,sai da suka isa kurfi yayi mata tatas dan ya san ita zata sa sadiq duk shirin ta ne, nunawa tayi ko a jikin ta burinta dama Ibrahim ya zauna a lagos to burinta ya cika komi zai ce bawai zai dame ta bane, watan sadiq da aisha ɗaya dayin aure suka wuce abuja aka bar Ibrahim a lagos saboda makaranta da ya ke zuwa, cikin ƙan ƙanin lokaci Ibrahim ya goge ya zama ɗan gayu,saboda ba ƙarmin kulawa yake samu daga wurin su hajiya zainab ba,sadiq watan su bakwai a abuja ya nema aisha admission ta fara zuwa makaranta, idan zai tafi aiki tare suke fita ya ajiyeta a makaranta ranar da take da lectures ɗin yamma kuma ya ɗauko ta, mota ya siya mata ranar da take ra'ayin driving da kanta sai taje da kanta ta dawo da kanta , akwana a tashi aisha har ta kai aji uku a jami'a matar magaji ta haihu ta haifi ɗa namiji kyakyawan gaske sunan yaron mansoor lokacin Aisha tana ɗuke da ciki na tsawan wata biyar, sosai take samun kulawa daga mijin ta da cikin ya isa haihuwa lokacin suna hutu zasu shiga aji huɗu, hakan ya sa sadiq ya ɗauki hutu wurin aiki suka tafi lagos dan ta haihu a chan, cikin yardar ubangiji da komawar su ba da jimawa ba Allah ya sauketa ta samu ɗa namiji kyakyawan gaske mai matuƙar kama da ita, murna wurin sadiq ba'a cewa komai, hakama iyayen aisha da ƴan kurfi sunyi matuƙar farin ciki, da sati ya zagayo, yaro ya ci sunan Alhaji Abdulƙadir suna kiran shi da {shazim} malam yayi matuƙar farin ciki da wannan ta kwara da sadiq yayi mashi,haka ma aisha taji daɗi sosai,kulawa sosai take samu wurin ummy, da tayi arba'in suka tafi kurfi ita da sadiq,Ibrahim ya so su tafi tare da shi amma makaranta ta hana saboda yana shekarar ƙarshe a jami'a, sun samu tarba ta musamman daga wurin maijidda haka ma magaji da nuraddeen hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma sadiq ba, matar magaji kuwa komawa su kayi tamkar ƙawaye ita da aisha, yaron ta mansoor shekarar shi ɗaya da rabi a duniya, kafin su koma lagos Aisha sai da ta zaga gidajen ƴan uwan sadiq, ta kuma je gidan uwani da halimatu, suna komawa lagos basu jima ba suka wuce abuja , haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ibrahim ya gama makaranta, sadiq yace ya dawo abuja yayi masters, shazim ya taso cikin kulawa da soyayyar iyayen shi da dangin shi musamman Ibrahim duk abunda ya siya zai ce na Shazim ne, haka ya taso cikin kulawa da gata,da shazim ya isa yaye lagos suka kai shi wurin ummy, har sai da yayi shekara ɗaya a lagos lokacin yayi wayau sosai, ya iya tafiya ga surutu, haka zaka same shi ya tasa hajiya zainab gaba da surutu abu kaɗan yace ummy { da yake shima haka yake kiran ta saboda yaji ammyn shi na kiran ta da haka} *_WANNAN KENAN_* .... Ibrahim ya fara zuwa makaranta Aisha kuma na shekarar ƙarshe, shazim nada shekara uku a duniya sadiq ya ajiye aiki ya kama kasuwanci gadan gadan riba sosai yake samu, cikin ƙanƙanin lokaci ya zama attajirin gaske ya buɗe katafaren company da yake sarrafa kayan masarufi musamman shinka fa, kasuwancin shi na ta haɓaka , ɗaura Ibrahim yayi kan wasu harkokin kasuwancin yana kula mashi da su, gida ya gina mai girman gaske ya kuma biya ma baba, innah, malam, ummy makka , sai shi da aisha, farin ciki wurin su ba'a cewa komai ya sha adu'a wurin su, kafin ya tafi ya tare a sabon gidan da ya gina, da zasu tafi ya ce ma magaji ya dawo Abuja da zama shida matar shi da ƴaƴan shi , da ma gidan da ya gina yayi shine saboda su, magaji yayi godiya sosai ya kuma tattara komai nashi dake kurfi sun dawo abuja shi da matar shi asiya, sunje sun sauke farali, a abuja su ka sauka da ma ta nan suka tafi, sai da malam su kayi sati shi da ummy sannan suka wuce lagos, baba kuwa da innah nan zasu zauna part ɗin su da ban, har da ibrahim da baiyi aure ba part ɗinsa da ban , innah sai nan nan take da sadiq ta ɗauki son duniya ta ɗaura mashi tun bai sakin jiki da kulawar da take nuna mashi har ya fara sakin jiki, abun ba ƙaramin ba nuraddeen mamaki yake ba, yan da ta sauya. Shekarar shazim 5 sadiq ya sa shi makaranta shi da mansoor aisha ta sake haihuwar ɗa namijin mai matuƙar kama da sadiq, sosai sadiq ya yi murna haɗi da gode ma Allah, ranar suna yaro yaci sunan baba watau nuraddeen suna kiran shi da { noraiz} baba yaji daɗi,satin noraiz uku da haihuwa asiya ta haihu ita ma ɗa namiji sunan shi mahmud, Ibrahim ya samu mata yayi aure sunan matar turai, yar kano ce amma iyayen ta anan abuja suke da zama, shekarar ta ɗaya ta haifi ɗa namiji mai suna luqman lokacin noraiz da mahmund nada shekara ɗaya da kusan rabi, shazim shidda mansoor bakwai faisala ukku ƙanin mansoor, wani abun mamaki tun da matar Ibrahim ta haihu innah ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa aisha da asiya kamar sunyi mata wani laifi, duk da wannan chanji da take nuna masu hakan bai hana su kyautata mata ba, kuma kan su haɗe yake dan matar Ibrahim ba ruwanta hakama yaran su kansu haɗe yake ko wane lokaci suna tare da juna musamman shazim da mansoor dan ko school tare zaka gansu da ƙanin su faisal da yake ansa shi makaranta shi ma , noraiz ne dai da luqman sai mahmud ba'a kai da sa su ba , sai daga baya aka sa noraiz , luqman da mahmud makaranta, shazim da mansoor kullum sun part ɗin baba kakansu wani lokacin har da su noraiz kullum haka suke in basu part ɗin baba suna part ɗin papah { sadiq} ko hutu shazim zai je lagos tare suke zuwa shida su mansoor luqman ne dai bai taɓa zuwa ba. _*WANNAN KENAN*_. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau daɗi gobe akasin haka sadiq ganin duk aboka nan shi na siyasa ne ya shi samu baba da batun yana so ya shiga shiyasa ƙin amincewa baba yayi hakan yasa abokan sadiq su kayi zuga suka zo wurin baba dan su roƙe shi akan ya bar sadiq, ai kuwa faɗa sosai baba yayi ma sadiq ya ce kenan dama su suka hure mashi kunne ya ke son shiga shiyasa,dole ta sa sadiq haƙura ganin baba yayi fushi sosai, lagos yaje ya sanar da malam abun da ke faruwa, hakan ya sa malam wanke ƙafa yazo har abuja wurin nuraddeen, tattaunawa suka yi malam kuma ya roƙe shi akan ya bar sadiq ɗin, ba dan hakan ya kwanta ma baba arai ba ya amince,sosai sadiq yaji daɗi, da matakin ɗan majalissa ya fara ,cikin ikwan Allah ya samu,shekarar su uku da fara mulki ya ida ginin estate ɗin daya fara opposite da gidan shi, suna gab da sauka daga mulki da jam'iyar su zata tsai da ɗan takara suka tsai da shi, ƙin amincewa yayi dan shi baya da burin yin muƙami mai girma irin wanna,matsa mashi suka yi ba dan ya so ba yace "to shikenan, amma sai yayi shawara da iyayen shi, duk abun da suka ce da shi zaiyi amfani ", ko da ya samu malam da baba da maganar cewa suka yi yayi haƙuri ya yi, ai abu ne mai kyau insha Allah zasu taya shi da adu'a, yaji daɗin hakan da suka ce ya kuma samu ƙwarin gwiwa, cikin ikwan Allah ana zaɓe sadiq ya samu,daya ci zaɓe sai Ibrahim da magaji suka koma estate da zama,sadiq ya so malam ya dawo abuja da zama lokacin daya zo yi mashi fatan alkairi daya ci zaɓe amma ƙiri ƙiri malam ya ƙi amincewa, baba ma da farko cewa yayi sadiq ya bar shi anan gidan shi amma sadiq ya ce a'a ya fi so ya zauna tare da shi yanda zai riƙa bashi shawara, sadiq ya fara mulkin shi cikin adalci mutane na jin daɗin mulkin shi,aiki ya ne ma ma Ibrahim da magaji dan tun dawowar shi abuja sadiq ya ne ma mashi admission ya jona karatu sai dai iya kar shi degree saɓanin Ibrahim da ke da master's ,business ɗin shi kuwa ya ɗaura wani aminin shi daya ke da amana, lokacin daya kusa gama zagayen farko na mulkin shi , Allah yayi ma nuraddeen rasuwa mutuwar da ta girgiza ahalin ga ba ɗaya musamman sadiq ya fi kowa fita hayyacin shi, sun shiga alhinin mutawar nuraddeen kamar mi, malam yaji mutawar aminin shi kamar mi, lokacin da aka yi adu'ar bakwai maijidda tace zata koma estate da zama wurin su magaji bayan da sadiq bai yi da ita ba amma ta ƙi zama ko da takaba ta gama amma ina ba dan ya so ba ya sa aka kaita, time ɗin da akayi arba'in ɗin nuraddeen matar Ibrahim ta sake haihuwa ta samu ɗiya mace kyakyawa mai suna hawa'u innah kenan suna kiranta da feenah,innah taji daɗi da Ibrahim yayi mata ta kwara ai kuwa ta ɗauki son duniya ta ɗaurawa feenah,bayan haihuwar feenah da sati biyu asiya ma ta haihu, ita ma ɗiya mace ta haifa mai suna kairiyya, watan nuraddeen tara da rasuwa za'a sake sabon zaɓe sadiq ya bar gidan gomnati ya koma gidan shi inda ya fara zama, awannan zaman ana saura sati ɗaya zaɓe Allah yayi mashi rasuwa, ta dalilin haɗarin mota, sunje wani ƙyauye ne a hanyar su ta dawowa su kayi haɗari wasu a nan take suka mutu sadiq kuma sai da yayi jinyar kwana biyu sannan Allah yayi mashi rasuwa ,mutawar sadiq ta girgiza dan gin shi kamar mi, aisha ta shiga tashin hankali mara misltowa da rasuwar sadiq hakama ƴaƴan ta sunci kuka kamar ransu zai fita duk da bawani wayaune da su ba sosai har dama dama shazim, kusan zaucewa aisha tayi, malam ma ya shiga alhini wanda ya fi na lokacin mutuwar nuraddeen , ummy taci kuka kamar mi dan ba ƙaramin son sadiq take ba tana mashi kallon babban ɗanta. _*ALLAH SARKI NIMA NAJI MUTUWAR KA KAMAR NAI HAUKA ABBA ALLAH YA JIƘAN KA DA RAHAMA AMEEN*_. A estate akayi zaman makokin shi har aka yi kwana bakwai, laulayin ciki Aisha ta fara na tsawan wata biyu sai bayan rasuwar sadiq cikin ya bayyana , ta sha kuka kamar ranta zai fita, tana tausa yin abun da zata hai fa zai taso batare da ya san waye mahaifin shi ba, ko da maijidda taji labarin cikin aisha baƙin ciki kamar ya kashe ta, ta fara nuna ma aisha tsana da tsangwa ma, hakan ne ya sa aisha ta ce zata koma lagos da zama, amma si malam da ummy suka ce ta bari ta gama takaba sannan, haka ta haƙura har ta kammala ta kaba, amma da zata tafi sai Ibrahim da magaji suka roƙeta akan dan Allah ta zauna har sai ta haihu sannan saita koma lagos ɗin, hakanan ta haƙura ta zauna ba dan ta so ba dan kwata kwata yanzu bata jin daɗin zama da innah, ta ware ta su asiya kawai take so su da ƴaƴan su ta ɗauki karan tsana ta ɗaurama su Shazim ba hali su shiga cikin ƴan uwan su ko su je part ɗin ta ta fara kyarar su kenan da hantarar su, ta kuma sa su mansoor tsanar su babu hali su raɓu da juna, tun abun bai damun Aisha har ya koma yana damun ta, har ta kai da samun innah dan ta bata haƙuri ko tayi mata laifi ne batare da sanin ta ba , amma sai innah ta rufe ta da masifa wai tayi mata rashin kunya, haƙuri kawai aisha ta bata, lokaci ya shuɗe har cikin aisha ya shiga watan haihuwa, a lokacin ma ta so ta koma lagos ta haihu a chan amma ƙiri ƙiri innah ta ce bata isa ba sai dai ta tsaya ta haihu a nan in ya so daga baya bayan ta yaye abun da ta haifa sai ta tafi tabar masu ƴaƴan su, maganar innah ta girgiza Aisha ba kaɗan ba tun tana boye ma malam da ummy irin zaman da suke yi ita da innah har ta kasa haƙuri ta kira ummy tana kuka ta zayyane mata duk abun da ke faruwa tun daga mutur sadiq har yan zu, abun yayi matuƙar ba ma ummy mamaki dan ita bata san halin innah ba kallon mutuniyar kirki take mata ashe ba haka take ba, ko da ta sanar da malam shima abun ya bashi mamaki dan bai taɓa tuna nin haka daga wurin ta ba, haƙuri suka bata akan tabi komi a sannu in sha Allah komi zai wuce kuma baza su bari a rabata da ƴaƴan ta ba, Ibrahim yana bata kulawa sosai , hakan ya sa ta kwantar da hankalin ta taciga da kula da ƴaƴan ta , shazim tun da ya lura da innah bata son shi da mahaifiyar shi kuma su mansoor ma basa son su yanzu sai kawai ya yanke shawarar fita harkar kowa da ke cikim estate ɗin , ko part ɗin su ya dai na zuwa, da tare su ke tafiya makaranta dasu mansoor amma ganin yan da suke takura ma shi shi da noraiz ya sa ya dai na tafiya tare da su, yasa ammy ta ba ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan makullin motar ta yana kai su, abun yayi matuƙar bata ran innah, ta tasa aisha bala'i tana son raba zumunci, ta kuma amshe makullin motar daga hannun drivern, ran shazim ya ɓaci da abun da innah tayi, ai kuwa har part ɗin ta yaje ya ɗauke key ɗin motar lokacin tana cikin toilet wanka su mansoor kuma na parlorn zaune dama cikin drawer ta sa shi,innah na fitowa feenah ta faɗa mata shazim ya shigo mata ɗaki kuma ya ɗauki key,mamaki abun ya ba innah ba shiri ta fice sai part ɗin Aisha tun daga bakin ƙofa ta fara masifa tana zage zage aisha na zaune kan kujera ita da mai aikin ta tana matsa mata ƙafafun ta dake ciwo ta ji haya niyar innah, ta na shirin tashi innah ta shigo ta hau bala'i tana zagin ammy, haƙuri ammy ta shiga bata dan bata san mi tayi mata ba, suna nan sai ga shazim ya shigo innah na ganin shi ta shaƙo wuyan rigar shi tana faɗin " ɓarawon banza ɓarawon wofi,bani key ɗin da ka ɗauko ɗaki na munafuki" gaban ammy ne ya faɗin jin abun da innah tace, shazim kuwa cike da masifa ya ce "wallahi ni ba ɓarawo bane, kuma key bazan ba da ba tun da ba naki bane " suman tsaye ammy tayi jin rashin kunyar da shazim ke ma innah, mamaki da tsoro ne ya kama innah jin abun da shazim ya ce mata, yaron da ko yatsa kasa mashi a baki bazai tauna ba amma shine yau yake faɗa mata magana cike da rashin kunya, katse mata tunani yayi ta hanyar figewa daga riƙwan da tayi mashi ya nufi up stairs ya haye, bin shi kawai tayi da kallo har ya ɓace ma ganin ta, ammy tace "dan Allah kiyi haƙuri innah zan amshi key ɗin in maido maki" fashe wa da kuka innah tayi tana faɗin "munafuka nasan ke zaki zuga shi yayi man rashin kunya, kuma wallahi ki sani dani kike magana" tana gama faɗar haka ta fice daga part ɗin.......... 🖊 _Episode 52_53_ ............ Innah na fita ammy ta wuce bedroom ɗin ta, noraiz ne ya shigo yana kuka, har zai nufi ɗakin ammy sai ya fasa saboda maganar shazim daya ji yana ce mashi"lafiya kai kuma kake kuka, waya dake ka ? " cikin muryar kuka noraiz ya ce "su ya mansoor ne da luqman " balbale shi da masifa shazim yayi dan mi zai tsaya luqman ya dake shi bayan ƙanin shi ne, shiru noraiz yayi, tsaki shazim ya ja haɗi da cewa "suna ina? " noraiz ya bashi amsa da "part ɗin uncle Ibrahim " shazim bai ce komi ba ya kama hanyar fita daga part ɗin ya fice, yana fita part ɗin uncle Ibrahim ɗin ya nufa, luqman da feenah ka ɗai ya samu zaune a parlor suna kallo, bai yi wata wata ba ya haushi da duka sai da yayi mashi jina jina sannan ya kyale shi yana kuka, feenah ce ta miƙe tana faɗin "ya shazim dan mi zaka dake shi" buge mata baki shazim yayi yana faɗin "rufe man baki koke ma na haɗa da ke " kuka ta kama yi tana faɗin Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na faɗa ma dady da innah" kwata kwata feenah bata da kunya koko alama, kuma hakan ya samo asali daga wurin innah saboda mugun son feenah take kamar mi, ita ta shagwaɓa ta kuma ta zuga ta akan dun wanda ya dake ta tace bata yafe ba idan bazata iya ramawa ba, hakan ya sa ta taso a sangarce ga rashin kunya iri iri feenah ta iya ta , abu ƙaɗan tace innah ko faɗa dadyn ta yayi mata tana kuku zata faɗa ma innah, ita kuma tai ta bala'i,saɓanin kairiyya da ba ruwanta, kuma tana son su noraiz dan kusan kullum tana part ɗin ammy,ita ba ruwan ta shiru shiru ce, mari shazim ya kaimata ta ruga da gudu tana kuka ta shige bedroom ɗin momyn ta,yazo fita yaci karo da mansoor da faisal zasu shigo part ɗin, cakumo wuyan rigar mansoor yayi, faɗa sosai ya kyaure tsakanin su har sai da momy {turai} ta fito ta raba su, mansoor na kuka saboda ciwan da shazim ya ji mashi, wuce wa shazim yayi zuwa part ɗin su, yana tura ƙofa yaci karo da ammy tsaye , "daga inah kake? " shine abun da ammy tace, shiru yayi bai bata amsa ba,jin yayi shiru ne yasa ta sake mashi tambayar, shiru ya sake yi , saukar mari kawai yaji a kumatun shi, abun da ammy bata taɓayi mashi ba, rufe shi tayi da faɗa sosai,tana gamawa ta juya, yana dafe da kumatu yace "dan Allah ammy kiyi haƙuri " wuce wa tayi batare da ta kalli inda yake tsaye ba, bin ta yayi har ɗaki yana bata haƙuri sai da ƙyar tace taya fe mashi kuma ya ɗauko key ɗin daya ɗauko ɗakin innah ya kawo mata, da to ya amsa haɗi da ficewa ya bar ɗakin, key ɗin ya ɗauko ya bata, ƙarar buɗe main ƙofa sukaji da ƙarfi, sai kuma haya niya fita ammy tayi zuwa parlor, innah suka gani ruƙe da hannun feenah su luqman na bayan ta tana ta zazzaga masifa, uncle Ibrahim ne ke bata haƙuri yana faɗin " dan Allah innah kiyi haƙuri" "wlh ba zan haƙura ba, yan da ya dake su wlh sai na rama masu " ammy ce tace "mike faruwa ne? " tun kafin ya bata amsa innah tayi saurin cewa " munafuka annamimiya, kina iya cewa baki san mi wannan fitsararen ɗan naki yayi ba, bayan ke kika sa shi munafuka kawai " muryar shazim suka ji yana cewa "gaskiya innah ki dai na ce ma ammy na munafuka dan ba munafuncin da tayi maki, dukan noraiz su kayi ni kuma na rama mashi, kuma wlh suka ƙara dukan shi sai nayi masu mafiyin haka tun da ba jakin su bane " tsawa uncle Ibrahim ya daka mashi yana cewa " kai baka da hankali ne shazim, innar kake faɗa ma wannan kala man, kar na sake jin bakin ka " innah tace "ai da ka barshi yayi man abun da uwar shi ta koya mashi, na san nan gaba har duka na tana iya sa shi tun da ba sona take ba" uncle Ibrahim yace "kar Allah ya nuna mana hakan, dan Allah kiyi haƙuri ki koma part ɗin ki" tasa ƙeyar su feenah tayi zuwa part ɗin ta tana tafiya tana zagin shazim,Aisha tayi tsaye ta kasa ko motsi, uncle Ibrahim ne yace "dan kiyi haƙuri da halin innah, karki sa abun a zuciyar ki kinga dai halin da kike ciki,ce mashi ta bakomi nagode haɗi da nufar part ɗin ta, faɗa tayi ma shazim har da duka, tana faɗin saboda zuwa makaranta yayi abokai marasa kunya shine zai zo gida yana ma manya rashin kunya, ta kuma gargaɗe shi kar ta sake jin yayi faɗa da wani cikin estate ɗin, cemata yayi to, bawai dan ya dena ba, ya zame ma yaran gidan abun tsoro dan ko kallon da bai yi mashi ba kayi mashi to zai hauka da duka ne ba ruwan shi, tun ammy na mashi faɗa har dai ta zuba mashi ido tana adu'a Allah ya shirya shi, dan komawa yayi mar kunyar ƙarfi da yaji har jira yake wani ya tsokane shi ko noraiz, dole tasa yaran tsoron shi. Wata rana wasu mutane suka zo da ga hukumar efcc, har part ɗin ammy wai ana zargin marigayi Abubakar, da satar kuɗin gomnati,dan haka ammy ta tattaro duk wani takardun dukiyar sadiq ta basu tun daga kan filaye har zuwa na company, abun yayi matuƙar bama ammy mamaki haka ma su uncle Ibrahim,ai kuwa kaca kaca ammy tayi masu ta kuma ce "babu wan da ya isa yasa ta bada koda allura ce daga cikin dukiyar sadiq, mutumin da yake hukunta duk wan da aka samu da laifin sata shine zaku ƙullama wannan sharrin , kuma abun ta kaici bayan ba ranshi, wallahi Allah bazai bar kuba" wani daga cikin mutanen ne yace " hajiya ki kwantar da hankalin ki, mu bamu zo dan rigima ba aikin mu kawai muke yi, muna so ki fito mana da duk wani takarda daya shafi Abubakar in ba haka ba zamu sa jami'ai su duba mana" ammy ta ce" sai dai kuyi duk abun da zaku yi amma ni bazan ba ku komai ba, tun da na san ƙarya kuke munafuncin ne kawai " ganin dai da gaske bazata yi masu abun da suke so ba ya sa suka miƙe suna faɗin " to shikenan tun da haka kika ce, Ibrahim mu zamu wuce, amma bawai hakan na nufin baza mu sake dawowa ba " suna gama faɗar haka suka fice da harara ammy ta raka su, har inda suka yi parking Ibrahim ya raka su sannan ya dawo part ɗin ammy, magana ya fara yi ma ammy yana cewa "ina so ki fahimce ni " "ina sau raron ka "ɗan nisawa yayi sannan ya ce " ina so ki gane cewa tun da kikaga an turo su to daga hukumar sune, kuma ba sharri zasu yi ma yaya ba dole akwai abun da mu ba mu sani ba, amma ina so kiyi haƙuri mu bi komi a sannu ko dan halin da kike ciki, insha Allah komi zai dai dai ta " ko mi akayi sai yace saboda halin da take ciki bai da wata magana bayan wannan "to shikenan Allah ya shige mana gaba kuma zan yi magana da lawyern, sadiq, tun da a high court yake aiki " uncle Ibrahim ya ce "hakane ni da kaina zanyi magana da barrister, ba sai kin kira shi ba " sun ɗan jima suna tattaunawa ta yan da zasu bullowa al'amarin, uncle Ibrahim na barin part ɗin ya kira barristern sadiq ya faɗa mashi duk abun da ke faruwa,sannan ya samu uncle Ahmad ya faɗa mashi lokacin da suka zo baya gida, ammy ma ta kira su malam ta sanar da su,lallashinta su kayi,ko da su uncle Ibrahim suka sanar da innah abun da ke faruwa cewa tayi to sai mi su ɗauki haƙƙin muta ne su ba su mana , sadiq ɗin waliyyi ne shi da bazai iya satar ƙuɗin mutane ba , abun yayi matuƙar basu mamaki dan basuyi tsammanin jin haka daga wurin ta ba, kwana uku da zuwan efcc ammy ta haihu ta haifi ɗiya mace kyakyawa mai matuƙar kama da noraiz, farin ciki wurin ammy ba'a cewa komai dan tana matuƙar san ɗiya mace,kwanan ammy biyu da haihuwa turai ita ma ta haifi ɗiya mace kyakyawa, farin ciki wurin uncle Ibrahim ba'a cewa komai, duk wani abu da uba zai yima ɗiyar shi sai da yayima babyn ammy da tashi,da ranar suna ta zagayo aka sama babyn ammy fatima babyn turai kuma sa'adatu suna kiranta da sa'ada. Shiru har tsawan wata uku efcc basu dawo ba kuma basu shigar da ƙara ba. watan fatima da sa'ada biyar da haihuwa kwatsam sai ga sammaci kama uncle Ibrahim da ga court efcc sun shigar da ƙara, hankalin kowa yayi matuƙar tashi musamman uncle Ibrahim da akayi arresting, Innah sai kuka take tana ma ammy masifa uncle Ahmad na bata haƙuri akan tayi shiru , amma ina sai zagin ammy take tana cewa " mijinta yaje yayi sata shine zata liƙama ɗan ta, wallahi duk abun da ya samu Ibrahim sai ta gane bata da wayau" Allah sarki ammy ban da kuka babu abun da take,noraiz ma sai kuka yake ganin mahaifiyar shi na kuka shazim kuwa in ban da haɗiyar zuciya babu abun da yake, zazzaɓi ne ya rufe ammy bayan ta shiga part ɗin ta,wayar ta shazim ta ɗauka ya kira malam ya faɗa mashi abun da ke faruwa, hankalin malam yayi matuƙar ta shi sosai, ya kuma cema shazim insha Allah suna nan zuwa shi da ummy. innah taci kuka kamar ranta zai fita ta tsine ma ammy yafi aƙira akan laifin da bana ta ba, takuma ƙara jin tsanar ta, turai ma sosai taji zafin ammy in ta tuna saboda laifin sadiq aka kama mijin ta duk da bata nuna mata a zahiri ba,kwana biyu da kama uncle Ibrahim uwani da halimatu suka zo daga kurfi su da ƴaƴan su , har suka yi kwana ɗaya da zuwa ammy bata san sun zo ba, dama halimatu ce mai zuwa wurinta to innah ta hana, sai washe gari da safe ta shigo part ɗin ammy suka gaisa, sai a sannan ammy ta san da zuwan su, daga ranar kullum sai halimatu ta shigo sun gaisa saboda tun da abun ya faru ammy ta dai na fita tana part ɗin ta koda yaushe ita da ƴaƴan ta, ta ɗan samu natsuwa saboda kullum sai malam da ummy sun kira ta sun kwantar mata da hankali sun kuma faɗa mata sunan zuwa hakan yasa ta dai na damuwa sosai taci gaba da adu'a, kullum lawyern sadiq sai ya zo har aka tsai da ranar shiga court, ana gobe za'a shiga court malam da ummy suka zo amma basu sauka a estate ɗin ba sai suka sauka a gidan da sadiq ya fara zama , can ammy taje ta same su ita da su noraiz, anan suka kwana, washe gari da zasu tafi court gida aka bar su shazim tare da mai aikin ammy, suna isa court ba'a daɗe ba alƙali ya zo aka fara gaba tar da ƙara, da lawyer ya fara gabatar da ƙara abun yayi matuƙar bama ammy mamaki dan anƙara akan abun da efcc suka faɗa time ɗin da suka zo gida, an mai da zargin kan ana zargin sadiq da reƙe hannun jarin abokanan kasuwan cin shi, sannan gomnati na zargin shi da satar maƙudan ƙuɗin da sunan aiki, an kuma kama container biyar da kayan maye da sa hannun shi, alƙali ya buƙaci ganin abokan kasuwan cin sadiq da wanda sune maƙa su dun shigar da ƙarar, abun yayi matuƙar ba ma ammy mamaki , saboda waɗan da suka shigar da ƙarar abokai ne ga sadiq na ƙut da ƙut wasu daga cikin su tun kafin ya shiga shiyasa yake tare da su, haka ƙara ta ciga ba da tafiya duk yan da lawyer sadiq ya so kare sadiq abun ya ci tura dan mutanen sun gabatar da hujuji masu matuƙar ƙarfi, ammy na ji na gani aka ɓata sunan mijinta bayan ran shi kuma aminan shi,duk wani company na sadiq sai da kotu ta amshe har da wasu gida jen shi, a taƙaice daga gidan shi dake lagos sai estate ka ɗai kotu ta bari, rayuwa tayi ma ammy zafi, taci kuka kamar ranta zai fita, sai da malam da ummy suka yi ta bata haƙuri da nasiha, malam yace ta yita yi ma mijinta da ƴaƴen ta adu'a,sun kwantar mata da hankali sun kuma nuna mata mahimmanci haƙuri da ƙaddara, hakan ya sa ta ɗanji sauki a ranta,amma abun na damun ta ba ita kaɗai ba har da malam da su uncle Ahmad dan sun san wannan duk sharrine, innah kuwa kamar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda tsabar jin daɗi an saki uncle Ibrahim,kwata kwata bata damu da halin da Ammy take ciki ba, yanke shawara ammy tayi idan su malam zasu koma lagos ƙafarta ƙafarsu kuma da ƴaƴen ta zata tafi komi innah zata ce sai dai tace dan a yan da take ji har kotu tana iya kai ta idan tace zata amshi ƴaƴen daga wurin ta,ko da ta faɗa ma su uncle Ibrahim shawarar data yanke, haƙuri suka shiga bata har da halimatu amma ina, sunyi sunyi amma taƙi haƙura, har zuwa su kayi wurin malam ko zai sa baki ta zauna amma sai yace shima yana buƙatar ta a kusa da shi, ya dai yi masu alƙawarin zata riƙa ziyartar su insha Allah ita da yaran,sun so ko noraiz a bar masu amma malam yace a'a,ba yanda suka iya haka suka haƙura, tsab ammy ta haɗa duk kayan ta dana yaranta dake part ɗin su, duk wani abu da tasan tana so sai da ta ɗauka sannan ta fitar da wanda zai lalace taba ma'aikanta estate ɗin sannan ta kashe duk wani abu na wuta, har part ta samu innah tayi mata ban kwana tayi tunanin innah zata ce wani abu amma sai taga saɓanin haka, turai da asiya sun sha kuka da ammy zata tafi ,maƙalewa kairiyya tayi akan dole sai ta bi ammy, haƙuri ammy taita bata, mansoor ma sun shirya da shazim shima har da kukan shi innah har gida ta samu su malam tayi masu sallama, tun da safe suka kama hanyar lagos cike da kewar mutanan abuja. Tunda suka koma lagos malam da ummy suke bama ammy kulawa ta musamman dan ganin ta kwantar da hankalin ta,hakan baƙaramin kwantar da hankalin ammyn yayi ba ta rungumi ƙaddarar ta, kullum cikin yima mijinta adu'a take da ƴaƴen ta, malam ya saka shazim da noraiz makarantar boko da islamiya,shazim na jss one noraiz kuma primary two, makarantar su ɗaya, su noraiz ƙarfe 12 ake tashin su amma noraiz baya komawa gida sai an tashi su shazim 2:30 pm sannan su tafi tare, da sun dawo wanka suke su ci abinci sai su wuce islamiya, malam ya tsaya tsayin daka akan rayuwar su duk wani abu na rayuwa wanda uba kema ƴaƴen shi malam na masu shi,hakama ummy babu abun da ba ta masu, uncle Ibrahim da uncle Ahmad ma suna matuƙar ƙoƙari akan su sosai su ke basu kulawa duk da basa a tare da su, kuma lokacin bayan lokacin uncle Ibrahim yana kawo masu ziyara har lagos, haka suka taso cikin soyayyar kakannin su da mahaifiyar su, malam ya so ammy ta ƙara wani auren musamman da uncle Ibrahim ya nuna yana ra'ayin auren ta, malam ya so tayi ko da ba uncle Ibrahim ɗin ba mutane sun sha zuwa suna nu na ra'ayin aurenta amma tace a'a tafi son ta zauna tare da su malam da ƴaƴen ta, ƙyaleta malam yayi sai ma nema mata aiki da yayi, da farko ƙin amincewa tayi da aikin sai da malam ya zaunar da ita yanuna mata amfanin yin aikin sannan ta amince tafara aikin. haka rayuwa ta cigaba da tafiya ammy na zuminci sosai da su asiya, suna waya time to time, lokacin da turai da asiya suka haihuwa har abuja taje ita da fatima bata tafi da su shazim ba saboda makaranta. Akwana a tashi shazim harya kammala secondry school lokacin noraiz na jss one fatima kuma na nursery one, uncle Ibrahim yazo lagos ya roƙi ammy da ta bashi shazim yayi karatu a hannun shi tare da su mansoor, ƙin amincewa ammy tayi da zaman shazim a abuja saboda innah, tana tsoron zaman su tare saboda ta lura kwata kwata innah bata ƙaunar shazim, da kuma shi kan shi shazim ɗin ta san bazai taɓa raga ma innah ba tana tsoron abun da zai biyo baya, babu yan da uncle Ibrahim bai yiba amma tace a'a,ganin bazata amince bane yasa ya sanar da malam da ummy, faɗa malam yayi ma ammy dan mi zatace a'a, Ibrahim ba uba ne wurin shazim ba yana da ikwan da zai iya mai da shi wurin shi da zama bama karatu ba, ba dan ammy ta so ba ta haƙura,sosai uncle Ibrahim yaji daɗi da ta amince kafin ya tafi sai da ya amshi takardun shazim duk, ko da ya koma abuja addimission ya nema ma shazim da mansoor cikin ikwan Allah suka samu kiran ammy uncle yayi ya sanar da ita ya kuma faɗa mata time ɗin da zasu fara lectures, malam ta samu ta sanar da shi yaji daɗi ya kuma kira uncle Ibrahim yayi mashi godiya, ya kuma ce mashi insha Allah ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim zai zo,hakan ce ta faru ana saura sati biyu su fara lectures ɗin shazim ya shirya ya tafi abuja, da zai tafi noraiz harda kukan shi, ko da ya isa abuja mansoor ne yazo har airport shi da driver ɗaukar shi, farin ciki sosai mansoor ya nuna na zuwan shazim ɗin da kuma kasan cewa da zasuyi a tare,ko da suka isa estate ɗin tarba ta musamman shazim ya samu daga wurin uncle's ɗin shi da matan su, sosai suka nuna farin cikin zuwan shi har da yaran su, feenah ce dai da innah sai luqman ko a jikin su, lura da hakan da shazim yayi ne yasa ya ɗauke kan shi daga innahr yayi kamar ma bai san da zamanta a estate ɗin ba, feenah kuwa ko kallon banza bata ishe shi ba daga ita har luqman ɗin dama ba son rainin wayau yake ba kuma ita da ma yar rainin wayau ce ga rashin kunya, da zasu fara zuwa makaranta uncle Ibrahim ya sai masu motoci masu kyan gaske, sunyi farin ciki sosai, da farko shi da mansoor kowa tafiyar shi yake shi kaɗai har da haɗi da ba department ɗin su daya ba shazim na karantar medicine and surgery mansoor kuma yana karantar medicine,abokin shazim ɗaya a department mai suna A hashim,shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim, mansoor kuwa yana da abokai ba laifi , sai daga baya mansoor ya ce mizai hana su dunga tafiya tare, amincewa shazim yayi suna tafiya tare, ta dalilin haka shaƙuwa sosai ta shiga tsakanin su kowane lokaci suna tare da juna ko a school ko a gida, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma uncle's ɗin shi ba dan dama burin su yaran su haɗe kan su, innah ce kwata kwata hakan bai mata daɗi ba dan ba haka taso ba, har kiran mansoor tayi tana mashi faɗa dan mi zai shige ma shazim, shazim ɗin ba ba son su yake ba san da suna yara, shikuma ya ce mata ko ada laifin su ne , su suka nuna ba su son shi shiyyasa shima ya nuna bai son su, ba ƙaramin haushi maganar mansoor ta ba innah ba hakan yasa ta ƙara jin ta tsani shazim musamman ma yan da yayi fatali da ita a estate ɗin, dan sai ayi sati bata sa shi a ido ba kuma kullum sai mansoor ya zo gaishe da ita da safe amma bata taɓa ganin shazim ba, ƙarar shi ta kai wurin uncle ahmad akan bai zuwa yana gai she ta, kiran shi uncle ahmad yayi yayi mashi faɗa da nuna mashi hakan bai dace ba, haƙuri ya bashi ya kuma yi alƙawarin gyarawa, tun daga ranar kullum da safe idan mansoor zai je gaishe da ita tare suke zuwa, kullum kuma yaje gaishe da ita ta rinƙa faɗa mashi baƙaƙen maganganu, in tana yi yi yake kamar ma bai san mitake yi ba, hakan kuwa ba ƙaramin haushi yake bata ba, sai daga baya daya lura abun nata ba mai ƙarewa bane yasa intace mashi a to sai ya kai mata har z, bata yi mamaki ba tun da daman tasan halin shi tun yana yaro ba ragamata yake ba, wata rana suna dawowa daga makaranta mansoor ya ce suje su gaishe da ita ko da suka je gaishe da ita basu same ta ba tana part ɗin uncle Ibrahim sai su feenah da kairiyya suka samu a part ɗin suna kallo, gaishe da su kairiyya tayi amma feenah mansoor ka ɗai ta gai da, dama tun da shazim ya zo kowa na gaishe shi amma ban da ita, lura da bata gaishe da shi bane yasa mansoor rufe ta da faɗa maimakon ta gaishe shi sai tashi tayi tafice tana ƙunƙunai, a kwai wata rana da uncle Ibrahim ya kira shazim part ɗin shi daya je part ɗin ba kowa a parlor sai ita kaɗai da yayi sallama ta ƙi amsawa sai ma ɗago da kai tayi ta kalle shi ta kauda kai tana jan tsaki , abun yayi matuƙar bata ran shi ya tsani rainin wayau da rashin kunya hakan yasa ya ɗauke ta da mari har sau biyu har sai da ta duƙe saboda zafin da taji ai kuwa ba shiri ta nufi ɗakin momyn ta tana kuka, da ta shiga ko da ta sanar da momyn ta taso ƙeyarta tayi har parlorn ta bashi haƙuri, dole ta bashi haƙuri tun da ga ranar kuwa ta dai na yi mashi koda kallon banza bare aje ga tsaki. Lokacin da su shazim su kayi hutu da zai tafi lagos tare suka tafi da mansoor har hutun su ya ƙare suka dawo, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shaƙuwa ce sosai tsakanin shazim da A hashim dan A hashim yana yawan zuwa lagos wurin shazim hakan ne yasa kowa ya sanshi tare da shazim musamman fatima ba ƙaramin son a hashim take ba idan ya zo lagos to tana nan maƙale da shi, tun wata rana da noraiz ya ji ciwo yayi mashi alura shine ta tambaye shi daman ya iya alura kamar ya shazim sai yace mata eh ai su dr ne tunga ranar ne ta sa mashi suna ya dr. Cikin ikwan Allah sun kammala degree zasu joining masters,maganar aure su uncle ahmad suka yi masu amma sai suka ce su ba yanzu ba sai sun kammala masters sun fara aiki tukunnan, ko da suka ce haka su uncle ahmad sunyi na'am da hakan, tunga time ɗin basu sake masu maganar auren ba sun barashi a sai sun fara aikin,business malam yace shazim ya fara kafin su fara masters, da zai fara malam ya bashi jali, cikin ikwan Allah san da zasu tafi business ya haɓaka Allah ya sa ma abun albarka,da zasu tafi malam ya samo wani yaro mai gaskiya da ruƙwan amana ya ɗaura shi akan business ɗin kafin shazim ɗin ya kammala karatu,cikin ƙanƙanin lokaci business ɗin ya ƙara haɓaka,saboda yaron na kula da business ɗin shazim cikin aminci ga gaskiya da ruƙwan amana, lokacin da suka kammala master business ɗin shazim ya haɓaka sosai dan malam na kula da komai ga kuma hameed hakan yasa business ɗin haɓaka. lokacin da suka kammala masters lokacin su noraiz shi da mahmud da luqman suna aji biyu a jami'a. Basu jima da kammala masters ba suka samu aiki su duka,har da a hashim, uncle Ibrahim ya so shazim yayi aiki a abuja amma yace ya fi son lagos saboda business ɗin daya ke hakan yasa uncle Ibrahim haƙura,shazim yana aiki awata babbar asibiti dake garin lagos, haka rayuwa ta cigaba da tafiya shazim yana aiki hameed na kula mashi da business,yanke shawarar yin phd yayi, ko da ya sanar da uncles ɗin shi da malam goya mashi baya su kayi ,amma sai malam ya bashi shawarar yin phd ɗin ta online, sosai hakan yayi mashi daɗi ko ba komi zai samu ya dunga zuwa aiki wani lokacin yana kuma kula da business ɗin shi,cikin ikwan Allah yana kula da aikin shi da business ɗin shi ya kammala phd,ƙarin girma ya samu a wurin aikin shi bayan nan kuma yana visiting wasu hospital ɗin,ganin komai na tafiyar mashi dai dai yasa ya yanke shawarar buɗe privet hopital, daya samu malam da maganar , goya mashi baya malam yayi ya kuma tai maka mashi da wani abun wurin gina hospital ɗin, cikin ikwan Allah aka gama gina hospital ɗin , ammy ma ta tai maka mashi da wani abun da zai zuba kayan aiki, sosai yaji daɗi ya kuma yi ma ammy godiya,kayan aiki masu inganci ya zuba, sai da komi ya kammala sannan ya ɗauki ma'ikata,ya kuma ɗaura wani abokin shi mai suna majeed wan da su kayi islamiya ɗaya,da yake iyayen shi talakawa ne masu rufin asiri, kuma da man yayi karatu a harkar lafiya hakan yasa shazim ya ɗauke shi aiki ya kuma ɗaura shi a matsiyin babba mai kula da harkokin Hospital ɗin idan baya nan ko yana wurin aiki........... _Episode 54_55_ ........ Uncle Ibrahim da uncle ahmad tasa shazim da mansoor gaba suka yi akan su fito da mata suyi aure, amma sai su kace ba yan zu ba, faɗa suka yi masu sosai suka kuma ce sun basu nan da wata huɗu ko dai su fito da mata ko kuma su zaɓa masu da kansu ganin haka ne yasa mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru ta business ɗin shi kawai yake dan ya ma manta da wata magana ta aure,ganin mansoor ya gabatar da wacce yake so amma shazim shiru yasa uncle Ibrahim shiryawa yaje har lagos ya samu malam da batun, ya kuma sanar da shi sun yanke shawara kodai ya fito da mata yayi aure ko kuma su aura mashi duk wacce suka ga dama, malam bai ba da goyan baya ba akan hukuncin da suka yanke yace su bar shi da shazim ɗin shi da kansa zai sa ya fito da matar , kwata kwata ba haka uncle Ibrahim ya so ba yaso ace malam ya goyi da bayan su, ba dan ya so ba ya amince ya koma abuja, koda ya koma ya sanar da uncle ahmad yan da suka yi da malam faɗa ya kama yana cewa kenan malam ke goya mashi baya shiyyasa da suka yi mashi magana yayi kunnen uwarshegu da su, ya kuma yanke hukuncin dole tare za su yi mashi aure shi da mansoor da su feenah dake shirin kammala makaranta, {su noraiz sun gama masters kawai suke jira} ko yana so ko baya so, sosai uncle Ibrahim da innah suka amince da hukuncin da uncle ahmad ya yanke, uncle ahmad da kan shi yakira malam ya sanar da shi cewa sun ƙarama shazim ɗin wata biyu kacal ko dai ya fito da mata kokuma su aura mashi duk wacce ransu ya so,abun yayi matuƙar ba malam mamaki yan da suka ɗau abun da zafi sosai har haka, shima yana so yaga shazim ɗin yayi aure amma ya fiso abi komi a sannu gudun dana sani. Ammy da ummy malam ya kira ya sanar da su abun da uncle ahmad ya ce, suma basu ji daɗin hukuncin da suka yanke da zafi haka ba,suma babu abun da suke buri sama da shazim ɗin yayi aure. Kiran shazim malam yayi ya sanar da shi hukuncin da uncle ahmad ya yanke,sannan yace mashi komi yake ya fito da mata suma sun fi son yayi auren tunda dai dai dai gwargwado Allah ya bashi rufin asiri, to sai ya gode ma Allah shima yayi aure ya tara iyali, cewa yayi insha zaiyi ƙoƙari ganin ya fitar da mata yayi auren, malam yaji daɗi da ya amince zai yi auren ya kuma yi mashi adu'a Allah ya zaɓa mashi mata tagari. Tun ranar da su kayi magana da malam har tsawan wata biyu shazim bai kawo matar ba bai kuma sake maganar ba, tun su uncle ahmad nasa idon ya zo yace ga wacce yake so har suka gaji,su kai fushin har suka gaji ganin wanda suke yi dan shi yayi kamar ma bai san suna yi ba,gajiya malam yayi da shirun nashi ya sake mashi maganar, ko da yayi mashi maganar sai cewa yayi gini yake yanzu so yake sai ya kammala tukunnan,malam yace to ya kamata ya kira su uncle ahmad ya sanar da su, da to ya amsa, ya kuma kira su ya sanar da su, balbale shi da faɗa uncle ahmad yayi dan mi bazai sanar da su ba tuntuni sai yan zu da lokacin da suka bashi ya ƙare, haƙuri ya bashi ya kuma sanar da shi ya kusa kammala gini ai saura ka ɗan , jin yace hakane yasa uncle ahmad haƙura ya ƙara mashi wasu wata uku, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma shazim ba dan shi kwata kwata bai shirya yin aure yan zu ba neman kuɗi kawai yasa a gaban shi,tun da uncle ahmad ya amince da maganar gini daya ce yana yi yasa ya fake da ginin har akayi shekara ɗaya bai kammala ba bai ce ga mata ba, sai da malam ya tasa shi gaba da faɗa sannan ya kammala,gida ne mai girman gaske kusan part uku ne gidan, kuma yana kammalawa yace su koma gidan da zama, malam cewa yayi sai dai shi da ammy da fatima su koma(da yake noraiz na makaranta shi da su mahmud) amma shi ba yanzu ba sai yayi aure sannan zasu dawo shi da ummy, ba yan da bai yi da malam ba amma ya ƙi amincewa dole tasa shazim haƙura suka koma shida su ammy duk da da farko da malam yace bazai koma ba ammy cewa itama tayi bazata koma ba sai tare da su malam amma sai malam yace ta koma suma sunan za su dawo. _*CIGABAN LABARI*_ ........ Aunty safiya ce tsaye bakin ƙofar parlorn mus'af tana nocking amma ba'a buɗe ba , ba kuma a bata izinin shiga ba, da dai ta gaji da tsayuwa ne yasa ta fara kiran sunan mus'af ɗin tana faɗin " wai lafiya kake ne? , ana nocking amma kayi shiru ka kuwa san ƙarfe nawa yanzu kowa na waje kai ka ɗai ake jira " daga ciki mus'af yace " gani nan zuwa, ina gama shirya wasu kayan ne " "amma kai ko anyi shiriritacce, yanzu da baka gama shirin ba kenan, yayi maka kyau, to kayi sauri ina nan ina jiran ka " zaune yake bakin gado sai dialing number Aairah yake amma bata ɗaga wa ga umma dake bakin ƙofa tana faɗa mashi shi kaɗai su ke jira, ganin dai da gaske ba ɗagawa zata yi bane ya sa shi haƙura da kiran ya miƙe trollyn shi da ke bakin gadon ya ja haɗi da sanya wayar cikin aljihu, da kaga fuskar shi zaka tabbatar da cewa yana cikin damuwa kwata kwata ba walwala a fuskar shi duk dan saboda kiran Aairah da yayi bata picking, da ya fita tsaye ya samu ummah tana jiran shi ya fito, da kallo Aunty safiya ta bishi " wai mus'af mike damun ka ne, tafiyar ce baka son yi ko mi" "a'a ummah " "idan ba ita bace ba ka sonyi ba, ace tun last month kasan da wannan tafiyar amma ace har yau baka gama shirin da zaka yi ba " "kiyi haƙuri na gama yanzu " gaba tayi tana faɗin "ka taho mu wuce kowa na waje yana jiran ka " bin bayan ta yayi, a compound su ka samu abba da su najma su kawai su ke jira, suna isowa wurin su ba ɓata lokaci kowa ya shiga mota su ka fice faga gidan zuwa airport, mus'af duk a takure Aairah ta ƙikiran shi, bini bini ya duba waya amma shiru har su ka kawo airport tun yana sa ran ganin kiran ta har ya fidda, parking su kayi a parking lot ɗin airport ɗin, fitowa su kayi su ka ɗunguma zuwa ciki, saura 25 minutes jirgin su ya tashi, zama su kayi kan chair's ɗin da aka tana da domin zama, mus'af gaba ɗaya ya kasa su kuni sai zuba idon ganin Aairah yake amma shiru har dai Abba da ummah su ka lura da halin da yake ciki, Abba yace " lafiya dai ko mus'af" "lafiya lau Abba " "A'a ba dai lau ba, ko a kwai wanda ka ke jiran zuwan shi ne " girgiza ma Abba kai yayi alamar a'a, har lokaci ya rage saura 15 minutes jirgin su ya tashi Aairah bata kira shi ba ba kuma ta zo ba, sai da ana saura 8 minutes sai ga su sun zo ita da Aaimah harda mom ya Abdallah ya kawo su, sunje gidan mai gadi yake sanar da su ai sun tafi airport ɗin tun ɗazu, shine fa su ka biyo bayan su, mus'af har wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke da yaga Aairah,da sauri ya nufe ta ganin mom da ya Abdallah ne yasa shi waskewa ya nufi mom ɗin, murmushi Aairah tayi dan ta san wurin ta ya nufo sai so yake su ƙeɓe domin suyi ban kwana amma Abdallah ya kasa ya tsare,sai dai kowannan su ya ƙura ɗan uwan shi ido ba yanda su ka iya dole su kai ban kwana kamar kowa,kowa da kewar ɗan uwan shi, jirin su na ta shi kowa ya nufi mota, mom bin su Aunty safiya tayi zata je gidan granny, da mom zata tafi Aaimah ba yan da bata yi ba akan tana son su bi mom gidan granny amma ya Abdallah ga hana, Aairah da man bata tanka ba dan ta mafi so su tafi gida,suna isa gida parking yayi a parking lot,yana gama parking ko kashe motar bai yi ba Aairah ta buɗe ta fice, bedroom ɗin su direct ta nufa,tana shiga ta faɗa kan bed fashewa tayi da wani kuka mai tsuma zuciya sai kace wacce akayi ma wani abu, a haka Aaimah ta shigo ta same ta, kallo ɗaya Aaimah tayi mata haɗi da taɓe baki tace " amma wallahi kin haɗa kanki da aiki, da man wannan cika da batsewar da kike yi a mota kuka ne kike ɓoyewa ashe, ah lallai sannun ki " banza Aairah tayi da ita sai ma ƙara sautin kukan ta da tayi, tun Aaimah nayi mata iya shege har dai ta koma lallashin ta " dan Allah Aairah kiyi haƙuri in dai ya mus'af ne zai dawo ki kwantar da hankalin ki, karatu kawai fa yaje ba wani abu ba " haka Aaimah tai ta lallashin ta har ta sa mu ta ɗan yi shiru sai sauke ajiyar zuciya take. "ni banga abun da zai sa ki tashi hankalin ki ba Aairah, in dai ya mus'af ne zai dawo karatu ne ya tafi ba wani abu ba " magana Aairah ta fara cikin muryar kuka " ni fa ba tafiyar da yayi bace ta sani kuka ba " "idan ba ita bace to minene ya saki kuka ana zaman lafiya?" "ya Abdallah fa shi ya hana mu muyi ban kwana, ya tsare mu da idanuwa ni na rasa mi yasa baya son soyayyar mu ni da ya mus'af, shima abie baya goyan baya" dafa kafaɗar ta Aaimah tayi "sister ba wai baya son soyayyar ku bane, kawai dai abun da nake tunani ya na ganin ƙanƙantar ku ne ku duka " "amma idan haka ne miyasa mom da Aunty safiya da Abba basa gani sai shi da Abie kawai " "to Allah ka ɗai ya san dalilin su, amma tabbas na san ba wani abu bane " "Allah yasa haka, amma wallahi ina matuƙar ƙaunar ya mus'af ban san ya zanyi ba idan su abie su ka ƙi goya mam baya ba, ina son shi sosai " "ki kwantar da hankalin ki insha Allah za su amince,amma kiyi ta adu'a Allah ya zaɓa maki abun da yafi zama alkairi, nima zan taya ki da adu'a " Kwantar da kanta tayi saman kafaɗar Aaimah tace "Ameen sister nagode" mangare mata kai Aaimah tayi haɗi da cewa tace" dama a kwai godiya tsaka nin mu " murmushi Aairah tayi tana shafa inda Aaimah ta mangare ta " sorry my lovely twiny" Aaimah tace " sister ni fa ko na ƙagara mu samu addimisson mutafi makaranta na gaji da zaman gida " "nima Allah na gaji, ai naji ya Abdallah yace cikin satinnan za su fara ba da wa " "Allah ya kaimu, har na ganni a school nama so ace a hostel zamu zauna amma abie yace A'a " "ni daman nafison gida, ko ƙarfe nawa zan kai gida dai zan dawo " a cewar Aairah "gaskiya na fi son zama hostel dan sai na fi karatu a can " "ko a gida idan ka sa kanka zaka yi ai " "ki kace koh, amma ni nasan sai na fi jin daɗin yi a hostel " sun jima suna firar sai daga baya su ka nufi main parlor Abdallah su ka samu kwance kan sofa da waya kare a kunnan shi, raɗa Aaimah tayi ma Aairah a kunne tana faɗin " ina fa zargin yaya buduwar yayi, any time yanzu cikin waya yake" jinjina kai Aairah tayi haɗi da cewa " ni ban ma lura ba " "kice jirgi ya bar ki tashi, wallahi tun da ya dawo daga abuja ya koma waya kowane lokaci " "ah lallai kam jirgi ya bar ni a tasha " Aaimah tace " wallahi kuwa, zan so naga wacece yaya yake kashe ma murya hak..... " bata ƙara sa ba ta dalilin make kanta da aka yi Aairah tun kafin taga wanene ta watsa dagu sai kitchen sai da ta shige ne tafara leƙen parlorn, ya Abdallah ta hango riƙe da kunnan Aaimah yana mata ƙoso a kai sai faɗin " dan Allah yaya kayi haƙuri wallahi da zafi " ta ke "amma gulma bata da zafi ko " "wallahi yaya ba gulma muke ba kuma ba da kai muke ba labarin school nake bata " "Allah ko " Abdallah ya faɗa, ɗaga mashi kai tayi cikin sauri tana faɗin " ka tambaye ta kaji " tana faɗin haka Aairah da ke leƙen su da sauri ta koma cikin kitchen haɗi da turo ƙofar ta rufe, abun ma har so yayi ya ba Abdallah dariya, sake jan kunnan Aaimah yayi yace " daga yau idan na sake jin kuna maganar wani ko da batawa bace sai nayi maganin ku " ɗaga kai Aaimah tayi kamar ƙadangaruwa tace " wallahi baza ma mu sake ba dan Allah kayi haƙuri dai " mangare mata kai yayi yana faɗin "wuce ki bani wuri " yana sakar mata kunne da gudu ta nufi up stairs tana sosa kunnen ta, Aairah dake cikin kitchen jira kawai take taji ana nocking ta shige store. mai da wayar yayi a kunnen shi yana faɗin " hello ƴar qanwer ta " daga cikin wayar fatima tace "ya dr kai da waye naji kamar kana magana da wata "ta faɗa cikin muryar da ke nuna bata ji daɗin jin yana magana da wata ba, duk abun da yake faɗa ashe duk tana jin shi ,up stairs ya nufa yana murmushi haɗi da cewa " ba nace maki ina gida ba " a shagwaɓe tace " eh haka kace, amma wacece kuke magana " "to ai sai ki tsaya na faɗa maki, wata younger sister tace " "twins?" ta fafa cikin sigar tambaya "eh ɗaya daga cikin su ne " "yaya yaushe zaka basu waya mu gaisa " "yanzu bana kusa da su amma ki bari zan kira ki sai na ba su " "shikenan yaya, yaushe zaka zo " "very soon zan zo " sun jima suna waya daga ƙarshe su kayi sallama *_✨SHAZIM✨_* Zaune yake a office ɗin shi dake eko yana aiki a laptop , wayar sa ce ta fara ringing, hannu yasa ya jawo wayar yana ganin mai kira yayi tsaki haɗi da yin rejecting ya cigaba da aikin da ke gaban sa,wani kiran ne ya sake shigowa ,banza yayi da wayar aikin da kegaban sa kawai ya ke ,haka wayar taita ringing mai kiran bai daina kira ba shi kuma bai yi picking ba ,message ne ya fara shigowa ba k'ak'autawa,papers d'in dake gaban sa ya ture da laptop ,dafe kansa yayi yana fad'in "da alama yarannan so su ke na koya ma su hankali " ya fad'a had'i da jawo wayar yana shirin kashe ta wani message d'in ya shigo wata number ce da ban bu d'e message din yayi ya fara karantawa _GM dr da fatan ka wayi gari cikin k'oshin lafiya, a ko da yaushe dai ina k'ara miko k'ok'on barata fatan zaka amshi tayi na wata rana ,ka huta lafiya daga ni masoyiyarka 🌹.._ yana gama karantawa ya ja wani dogon tsaki yana ,a zuciyar shi yana fad'in " dole nayi maganin ki yau" yana gama fad'a ya jawo landline din dake kan table din,dialing wasu numbobi yayi ,ana picking ko sallama da na cikin wayar ke mashi bai amsa ba yace "Am waiting for you" yana gama fad'a yayi rejecting had'i da tashi daga kan kujerar da yake zaune ya koma kan sofa. bayan kamar 5 second akayi nocking k'ofar office din ,izinin shiga ya bada ,turo k'ofar tayi ta shigo ,kamar ko da yaushe sanye take cikin uniform din ta farare ,sallama tayi had'i da cewa "dr gani " batare da ya amsa sallamar da tayi ba yace "ina wayar ki take " gaban ta ne yayi wani mummun fad'uwa ,da sauri ta d'ago tana kallon shi ,cikin in ina tace " wa...ya.. ta ...kuma d..r? " ta k'arasa maganar cikin sigar tambaya , jifar ta yayi da wani sakaran kallo had'i da cewa " A'a tawa" "dan Allah kayi hak'uri dr mi zaka yi da wayata?" "bana son jin wata magana ,zaki bani wayar ko saina b'ata maki rai " _abun da hidaya bata sani ba tun lokacin da ta amshi number shi a hannun dr kabir ta fara tura mashi messages yasan cewa ita ce ,dan dr kabir ya kira shi ya fad'a mashi cewa zata kirashi ta damu akan yanayin da ya bar hospital ranar ,saboda yasan zai yi wuya idan ta kira shi ya d'auka dan ba kasa fai yake d'aukar bak'uwar number ba_ hawaye ne ke sauka daga bisa fuskar ta ,hannu tasa cikin aljihun rigar ta ta fiddo da wayar hannun ta na kyarma ta mik'a mashi ,amsa yayi ,number ta da ke cikin wayar shi yayi dialing tana fara ringing ya d'ago da kanshi ya na kallon ta ,duk'ar da kai tayi tana share hawayen da ke bin kuma tunta, magana ya fara da kakausar murya "kema ashe baki da hankali ban sani ba, ina maki kallon wacce ta san ciwan kanta ashe ba haka kike ba, daga yau sai yau kar na sake ganin ƙafar ki acikin office ɗina " wasu zafafan hawaye ne suka sake wanke mata fuska, cikin muryar kuka tafara magana " dan Allah kayi haƙuri kar kace ka kore ni, wallahi kuskure ne bazan sake ba insha Allah.... " tsawa ya daka mata "fita ki bani wuri tunkafin ranki yayi mummunan ɓaci " kuka sosai hidaya ta fashe da shi tana bashi haƙuri, amma kwata kwata bai saurare ta ba, haka ta ja ƙafarta ta fice daga office ɗin ranta duk a jagule sai data sanin biye ma shawarar maryam take, da ta san wata rana zai ganota kuma har ya koreta da bata biye mata ba, tana fita daga office ɗin da dr kabir ta cikaro tsaye bakin ƙofa ya harɗe hannuwa a ƙirji, da alama ba tun yanzu yake a bakin ƙofar ba kuma yaji duk abun da ya faru tsakanin ta da shazim, dagama yan yin kallon da yake mata ta san cewa ba abun da baiji ba...... _Episode 56_57_ .........Fuskar shi a murtike yake bin ta da kallon ƙasa da sama, idanuwan shi sun ƙaɗa sunyi jawur,tsantsar ɓacin rai ne a cikin su, bi tayi ta gefan shi zata wuce, da sauri ya sa hannun shi ya fisgota, har sai dai da tayi ƴar ƙara saboda zafin da taji, janta yayi har office ɗin shi suna shiga ya yarfar da hannunta har sai da ta kusa faɗuwa , magana ya fara cikin kausashiyya murya dake nuna tsan tsar ɓacin ran da yake ciki " dama duk abun da ke faruwa saboda shi ne, duk irin wulaƙancin da kike man dama duk saboda shi ne?, amma kinyi matuƙar bani mamaki,banyi tuna nin haka daga gare ki ba mi nayi maki da zaki yi man haka, da me ya fi ni da har zaki zaɓi zubar da mutuncin ki na ƴa mace a idanuwan shi, why ! why !! why hidaya " ya ƙarasa maganar da wata kalar murya da ke nuna ya karaya,har ya buɗe baki zai sake faɗin wani abu sautin kukanta daya karaɗe office ɗin ne ya dakatar da shi, matsawa yayi kusa da ita, ɗurƙushe take a ƙasa sai zubar da hawaye take,tausasa murya yayi yace " saboda na nuna ɓacin raina ne kike wannan kukan, ko dan saboda ya nuna baya sonki?? " shiru tayi bata ce ma shi ƙala ba, sake kwantar da murya yayi yana faɗin " da ke nake magana kinyi shiru, idan ma dan nayi maki faɗa ne kike wannan kukan kiyi haƙuri, dole raina ya ɓaci ina ta fama da ke akan ki ƙarɓi soyayyata ki so ni ko da bai kai kwatan kwacin yanda nake sonki ba amma kin ƙi, ashe duk wahalar da nake baki gani, miyasa kika yi man haka, ko ina da wani haline wanda bai yi maki ba, idan har ina da wani abu wanda baki so ki faɗa man zan daina amma dan Allah ki rabu da shazim, shazim bazai so ki ba ya san cewa ina sonki kuma gani yake soyayya rashin aikin yi ce, kuma zuwan da yayi abuja uncles ɗin shi sun zaɓa mashi matar da zai Aura yanzu haka tana gidan su " Gabanta ne yayi mummunan faɗuwa jin furincin shi na ƙarshe, da sauri ta ɗago tana kallon shi da rinanun idanuwanta " ya kabir da gaske kake?" jinjina mata kai yayi alamar eh , fashewa ta sake yi da wani kukan, da sauri ta tashi ta bar office ɗin da gudu, da sauri shima ya tashi ya bi bayan ta,ko da ta fita bata tsaya ko ina ba sai bakin gate ɗin hospital ɗin tana fita tayi sa'a samun abun hawa, lokacin da dr ya ƙara so bakin gate ɗin mai napep ɗin daya ɗauke ta yana barin wurin, dafe kan shi yayi yana faɗin " wai mi kike so ne hidaya? dan Allah kar ki zautar da ni " haka yayi ta sambatun shi shi ka ɗai a bakin gate da dai ya gaji, komawa yayi cikin hospital ɗin direct office ɗin su ya nufa, a bakin ƙofa ya samu maryam ta fito, tsai da ta yayi yana faɗin "please maryam kayan hidaya zaki ɗauko man " "dr lafiya dai, mi ya samu hidayar, yanzu muke tare da ita dr shazim ya kira ta " "ba komai ki kawo man ina office" yana faɗa ya wuce office ɗin shi ok kawai tace haɗi da komawa cikin office ta tattaro kayan hidaya ta nufi office ɗin dr kabir da wayarta a hannun tana dialing number hidaya amma bata shiga. Tana yin nocking yana buɗe ƙofar, miƙa mashi jakar hidayar tayi tana faɗin " dr gashi, amma mi ya sameta ina ta kiran wayarta bata shiga " Amsar jakar yayi yana faɗin " bata jin daɗi ne ta tafi gida" "dr ai da kabari sai na tafi mata da kayan " "A'a ki barshi kawai zan kai mata kafin na wuce gida " "to shikenan Allah ya bata lafiya " da ameen ya amsa, wuce wa yayi ya barta anan tsaye sai mamaki take azuciyar ta tana faɗin " mi ya samu hidaya yanzu yanzu, Allah dai yasa ba wani abu bane ya haɗa ta da dr shazim ba dan ta san abun da zai sa hidaya tafiya a wannan lokacin dole yana da alaƙa da shazim tun da shine ya kirata" A zahiri kuma tace "Allah dai yasa lafiya " office ɗin su ta koma tana cigaba da dialing number hidayar amma har yanzu bata shiga daga ƙarshe ma jin wayar tayi a kashe, hankalinta ya ɗan tashi jin wayar a kashe kuma " to wai mike faruwa da hidaya ne?, amma zanje gidan inji ko lafiya nake kiranta bata ɗauka" haka tai ta jefa ma kanta taambaya tana haɗa kayan ta ita ma. Da ya bar hospital ɗin wani shopping mall ya nufa,parking yayi ba tare da ya shiga ba wayar ya fiddo yayi dialing wata number wanda ya kira na picking sallamar da yayi kawai ya amsa ma shi sannan yace "ina waje " shine kawai abunda yace yayi rejecting kiran, bayan kamar 5 seconds sai ga wani matashi ya fito hannun shi ɗauke da wani madaidaicin kwali ya nufo motar dr kabir, yana iso wa dr kabir ya buɗe mashi gefan shi , saka kwalin yayi ya maida ƙofar ya rufe, zagayowa yayi wurin dr yace "a sauka lafiya ranka ya daɗe " da Ameen dr ya amsa haɗi da yima motar key ya bar harabar wurin. A bakin gate ɗin gidan yayi parking, fitowa yayi haɗi da zagayawa ya ɗ jakar hidaya daya kwalin daya amso ya nufi gate ɗin, ƙofar da ke jikin gate ɗin yayi nocking, mai gadi ne ya buɗe ƙofar, kallon dr kabir yayi yana faɗin " ranka ya daɗe barka da zuwa, an wuni lafiya, ai da kayi horn sai na buɗe maka " "lafiya lau, kar ka damu wuce wa zanyi, dan Allah wannan saƙon nake so ka ɗan miƙama hidaya " "to shikenan yallaɓai,amma da ka shiga " "karka damu , yanzu dai amshi kayan ka kaimata " ya faɗa yana nuna ma maigadin jakar, amsa mai gadin yayi yana faɗin " shikenan ranka ya daɗe sai anjima" hannu yasa a aljihu ya ciro 5k ya miƙa ma mai gadin yana faɗin sai anjima, hannu mai gadin yasa ya amsa yana yi mashi godiya. Wurin motar shi ya koma ya shiga,reverse yayi ya bar anguwar, a hankali yake tuƙi har ya kawo wani ƙaton gida yayi horn a bakin gate, mai gadi ne ya leƙo yana ganin motar ya koma da gudu haɗi da buɗe mashi gate ɗin, ciki ya shiga da motar a compound yayi parking,yana gama parking ya fito ba tare da ya kashe motar ba a buɗe ya bar ƙofar haka ma key a jiki ya bar shi ya nufi main entrance ɗin gidan. Gida ne bani da gida ba, babba ne sosai dan ya fi gidan su shazim girma nesa ba kusa ba, part part ne gasu nan bila adadin, tsayawa faɗa maku yana da gidan yake ɓata lokaci ne. Ma aikatan gidan ne su ka shiga gaishe da shi, hannu kawai yake ɗaga masu, dan a yanayin da yake ciki ba zai iya magana ba. Da sauri wani matashin saurayi ya nufi motar ya kashe haɗi da buɗe back seat ya ciro mashi briefcase ɗin da laptop, key ɗin ya zare ya rufe motar da sauri ya bi bayan shi. parlor ne ƙato da royel sofas a ƙalla za su kai set huɗu milk color. Up stairs ya nufa matashin saurayin nan na biye da shi da kayan shi da ya kwaso masu, suna zuwa wani ɗan corridor matashi saurayin ya ɗan da kata yana faɗin " ranka ya daɗe ina zan kai maka kayan? " "main parlorn na" shine kawai abun da ya faɗa yayin da yake tura wata ƙofa da ke cikin corridor,juyawa saurayin yayi ya nufi wata ƙofa dake can ƙarshen corridor ya shiga wani parlor ba laifi yana da girma kamar dai yanda main parlor yake,komai na cikin shi brown color ne, ya tsaru iya tsaruwa, kan tow seater saurayin ya ajiye mashi kayan ya fice. Ƙaton parlor ne sosai dan da ƙaɗan parlorn da suka fara shigowa zai nuna mashi girma da tsaruwa, wata ƙofa dake facing ɗin shi ya nufa haɗi da tura ƙofar ya shiga,nan ma wani parlor ne ɗan madai daici, lab coat ɗin dake jikin shi ya cire haɗi da yin wurgi da ita kan sofa sannan ya cire top ɗin da ke jikin shi ita ma yayi wurgi da ita ya koma daga shi sai dogon wando da riga long sleeve, wani ta ƙofa ya nufa tura ta yayi ya shiga ciki, masha Allah nace da ganin wani danƙareren bedroom dake ɗauke da royel bed mai kyan gaske, komai na cikin bedroom ɗin white color ne, faɗawa yayi kan bed ɗin yayi kwanciyar rub da ciki, ya rasa mike mashi daɗi a duniyar nan, gaba ɗaya ji yake ya tsani kan shi, magana ya shiga yi da zuciyar shi " miyasa hidaya zaki yi man haka,gaba ɗaya kin gama zubar man da mutunci, dan mi zaki ƙi ƙarɓar soyayya ta kice wai shazim kike so, wai da mi shazim ɗinnan ya fini ne da har zata iya cewa tana son shi amma ni ta ƙi ƙarbar soyayya ta" haka ya cigaba da saƙawa yana kwance wa, daya juya ƙaɗan ya buga tsaki. turo ƙofar bedroom ɗin akayi wata mata tsaye sanye take ciki less ɗin kin doguwar riga, hannun ta riƙe da kayan shi da ya zubar a parlor, bakin bed ɗin tazo ta tsaya "Auta mike damun ka ne ka zubar da kaya a parlor sannan kazo nan ka kwanta, lafiya dai ko?? " shiru yayi bai ce komai ba, bai kuma juyo ba daga kwanciyar da yayi, kayan da ke hannun ta ta ajiye gefan bed ɗin, sannan ta hau kan bed ɗin, hannu tasa ta shiga shafa sumar kan shi, cikin lallashi ta fara magana " wa ne mai tsau tsayin ne ya taɓa ɗan gidan momy yau ya kwana a kulle, faɗa man wanene yanzu na ɗau mataki a kan shi kaji ɗan gidan mama,ko na kira yayyen ka ne " shiru yayi nan ma baice mata komai ba "yanzu Auta har akwai ɓacin ran da zaka shiga kayi fushi da momyn ka tana magana kayi banza da ita" sai a lokacin ya ɗago da kanshi ya kalle ta ba tare da yace komai ba, murmushi tayi tana faɗin " mike damun bugun zuciyata ne faɗa man naji yanzu nayi maganin sa" hawaye ne suka kwararo daga idon shi, ɗuƙar da kai yayi ƙasa, da sauri ta sa hannu ta taro fuskar shi tana " ya salam Auta mi zan gani haka, waye ya ɓata maka rai ne har haka yasa ka zubar da hawayen ka, maza ka faɗa man ko waye yanzu na ɗau mataki saboda saman auta koka da yayi " faɗawa yayi jikinta yayi hugging ɗinta so tightly, fashewa yayi da kuka kamar wani ƙaramin yaro, shafa bayan shi ta shiga yi " dan Allah ka dai na wannan kukan ka faɗan man abun da ke damun ka, ko so kake nima ka sa ni kukan kasan kukan ka tashin hankali ne a gare ni " shiru, ajiyar zuciya ya shiga saukewa, cikin muryar kuka ya fara magana ba tare da ya raba jikinshi da nata ba "momy ashe wahalar banza nake bani take so ba " yana faɗin haka ta fahimci akan hidaya yake magana dan komai na shi na rayuwa ta sani ko shawara zai yi da ita yake yi babu wani sirrin shi da bata sani ba, ba ya iya ɓoye mata komai. "ban gane ba, itace tace maka bata sonka?" raba jikin su yayi , komawa yayi ya kwanta ya ɗaura kanshi saman laps ɗinta, shafa sumar kanshi ta shiga yi " ka kwantar da han kalinka babana nasan tana sonka, babu wata ƴa mace da zaka ce kana so a duniyar nan ta ƙi amincewa da kai insha Allahu hidaya matar ka ce bata da wani miji a duniyar nan bayan kai" "to ai momy yau da kunne na naji bani take so ba " "ba kai take so ba, to wa take so?" "momy shazim wai take so bani ba " "shazim dai " "Eh momy, shi tace tana so " "tofa ana wata ga wata, to shi shazim ɗin yana son ta ne" "A'a momy, ai ya san ina sonta kuma ma anyi mashi mata a familyn su " "to ai ta kwana gidan sauƙi tun da shi ɗin ba wai yana sonta bane kuma har kace an yi mashi mata " "amma momy ta zubar man da mutunci, kullum faɗi nake tana da kamun kai tana da natsuwa amma ta buɗe baki tace ta son wani bani ba " "kar ka damu ina tuna nin bata san kana sonta bane ai baka faɗa mata ba " "momy na faɗa mata kin manta ne " "yanzu dai ka kwantar da hankalin ka ni zan san yarda zanyi zan sanar da dadyn ku , insha Allah sai ka Auri ta kar ka damu kaji " ta faɗa tana share mashi hawayen da suka ɓata mashi fuska, murmushi tayi haɗi da jan gemun shi tace "babana kafa girma ka rage wannan yarintar ko so kake ɗiyar tawa ta raina man kai ne " ta faɗa haɗi da lakuce mashi hanci, murmushi yayi haɗi da cewa "momy ai bazan yi a gabanta ba, ke kaɗai zan mawa tun da daman ke maganin kuka na ce " "duk da haka dai, kar ka haifa man jikoki masu kukan banza kamar kai " murmushi yayi "momy har kin fara maganar jikoki, duk wanda ke a gaban ki " "to babana idan ban yi maganr su ba maganar mi kake so nayi, jikoki kuma ai na babana na da ban ne " "haka ne my lovely mom" " ta shi kaje ka watsa ruwa, abinci na nan kan dinning yana jiran ka " "momy ni a nan zanyi" "to shikenan tashi kaje kayi, amma ka kusa daina shigar man toilet " "kai momy, saboda mi?" "saboda ka girma, ka kusa aje iyali " ta bashi amsa haɗi da miƙewa ta bar bedroom ɗin, tana fita shima ya tashi ya nufi toilet ɗin, bayan kamar 15 minutes ya fito jikin shi sanye da bathrobe. Ficew yayi daga bedroom din yanufi parlor ,zaune ya samu momy ita da su ya mustafa ( yayyan shi, su ba kwai ne y'ay'an momy ,maza biyar mata biyu ,dr kabir shine karamin kanin su shi ka dai ne bai yi aure ba ,ya mustafa shine babba sai umar,khalid,aliyu,safeenah,azeema sai dr kabir,duk acikin gidan maza suke zaune da matan su ) binshi da kallo suka yi , ya mustafa ne yace " yau ina ganin ikwan Allah ,wai kai da man har yanzu baka girma ba ,wanka a bedroom din momy ko kunya " turo baki yayi gaba yana fadin " wallahi da na san kuna nan da ban fito ba ,haka nan ku hana mutum saket " rike baki ya umar yayi yana fadin " Allah ya shirye ka junior" ( da yake haka su ke ce mashi ) "Ameen" ya ce yana murgud'a ma ya umar baki kamar wata mace ,tsaki ya khalid ya ja ba tare da yace komai , ya aliyu kuwa cewa yayi " gaskiya ku kyale shi ya huta,idan bai ma momy da mu ba wa zai mawa ,ku barshi ya shana wata rana sai labari" Matsowa kabir yayi kusa da Aliyu yana fadin "yawwa ya Aliyu shiyyasa nake sonka" "mu kuma baka son mu ko saboda muna fada maka gaskiya " ya khalid ya fada Ya mustafa yace " ai shima jirgi daya ya kwaso su shi da Aliyu dama ce kawai shima bai samu ba " "fadi kanka tsaye ,da ace ni ne shi sai nayi abun da yafi wanda yake yi Allah" ya Aliyu ya fada ,momy dai na gefe sai murmushi take tana kallon su cikin alfahari. Ya Aliyu ne yace " kaji Autan momy ta shi kaje ka sa kaya ka dawo na san baka ci abinci ba ,kazo da kai na zan baka a baki " "Allah dai wadaran naka ya lalace ,yanzu wannan katon zaka ba abinci a baki amma dai gaskiya kaji kunya Aliyu " "A'a ya khalid bari ,wane irin naji kunya ba wata kunya da naji kanina ne fa ko ba haka ba momy " ya fada yana kallon momy dake bin su da idanuwa "rabu da shi Aliyu na lura adawa yake da babana" "haba momy wane irin adawa ,wannan katon ne zai ba abinci a baki " "Ai ba haramun ba ne ,idan kai bazaka bashi ba ,sai ka bar mai bashi ya bashi " "Allah ma ya kiyaye na zauna ina ba junior abinci a baki sai kace ban da aikin yin " "to ni zan bashi idan kai bazaka iya ba,je ka sa kaya kaji Autan momy " ya Aliyu ya fada yana kallon dr kabir gwalo dr kabir yayi ma ya khalid ,tsaki ya khalid din yaja yana fadin " wallahi kaji kunya kato da kai kana abu sai kace wata mace " Dariya su ya mustafa su kayi suna fadin " da gaske dai adawa kake da shi " Tsaki ya khalid yaja ba tare da yace masu komai ba ,kwata kwata baya son ganin kabir na taɓara abun haushi yake bashi . Shaf shaf ya sa kaya ya dawo parlorn samun su yayi zaune a dinning su duka har da dady wanda shigowar shi kenan ,kusa da dady yaje ya zauna ,shafa kanshi dady yayi yana fadin " likita bokan turai yau da wuri aka dawo kenan? " "Eh dady" "sannu to ,ya aikin?" "Alhmdllh dady" "to masha Allah" dadyn ya fad'a "juyo na baka abincin kar ya khalid yaji dadi" ya Aliyu ya fada yayin da yake d'ebo abincin a spoon ,bude baki kabir yayi ya Aliyu na ba shi a baki dady ma na bashi sai murmushi yake yana ma ya khalid dake jifan shi da harara gwalo ,karshe dai daya gaji ganin abun kunya jifan shi yayi da spoon da sauri ya duke yana fadin " wayyo Allah dady zai cire man ido " _kai dr ban da dai sharri_ "wallahi zan sa k'afar wando d'aya da kai khalid idan baka fita harkar junior ba " "haba dady baka ga yanda ya k'ara sangar cewa ba kuma fa duk dan kuna goya mashi baya ne " "An goya mashi bayan " momy ta fad'a ,shiru khalid yayi bai sake cewa komai ba, dr kuwa sai murmushi yake kamar wani zautacce Haka suka cigaba da lunch suna fira cikin ni sha di ,da suka gama ma kan sofa su ka koma momy ke sanar da dady maganar hidaya, haƙuri ya ba dr ya kuma ce insha zaiyi iya bakin ƙoƙarin shi ganin ya amsar mashi auren hidaya, da dady ya faɗi haka da sauri ya rungume shi yana faɗin "na gode sosai dady " saboda sangarta da rashin kunya har da su rawa. Su ya mustafa nayi mashi dariya, ya khalid kuwa ban da tsaki babu abun da yake. _nace daman dr haka kake, dole shazim ke ce maka yaro duk da shima yaron ne_🤓 Wannan ahali akwai nisha ɗi a tattare da rayuwar su, Allah ya dawwamar da farin cikin a gare su, hidaya ina taya ki murna idan kika shigo wanna ahali mata ga junior ɗan gata momy da dady da su ya khalid 😜. wai zaki sha gata abun ba'a magana, amma fa idan kin ƙyale wannan mai kan kwakwar, bari dai na zuge baki na kar um um um ta watsa man tafi ba sai dai na ƙasara ba bakina a lekum 🤐 Haka suka cigaba da fira cikin nisha ɗi sai da lokacin sallah yayi tukun suka nufi masallaci. _*✨HIDAYA✨*_ "Wai hidaya zaki buɗe ƙofar nan ne ko sai ranki ya ɓaci" zuwa tayi ta buɗe ƙofar idanuwan ta duk a kumbure alamar taci kuka, tana buɗe ƙofar ta koma ciki, bin bayan ta ummah tayi tana faɗin "yanzu abun da ki ka yi kina ganin shi ne dai dai ko, wai zaki faɗa man abunda ke damunki ko sai na kira Abban ku" "Ummah kai na ne ke man ciwo " "Ƙarya kike hidaya,har ni zaki ɓoye ma damuwar ki " "umma ki yarda da ni kaina ke man ciwo " Shikenan shine abun da ummah ta faɗa "kije to ki watsa ruwa kizo ki ci abinci ki sha magani " ummah na gama faɗa ta fice ta bar bedroom ɗin, komawa tayi ta kwanta a rigingine kanta na kallon ceiling , tayi shiru gaba ɗaya ta rasa mike damunta, dagske dr kabir yake anyi ma shazim mata a familyn su,hawaye ne suka gangaro mata daga cikin idanuwanta, hannu tasa ta share turo ƙofar ɗakin akayi, tsaye tayi tana binta da kallon daga baya ta shigo, zama tayi kan bed ɗin, ta dai ji almar shigowar mutum amma bata san waye ba duk a tunanin ta umma ce sai fa taji shiru ne yasa ta tashi daga kwanciyar, zuba mata ido maryam tayi tana kallon ta "lafiya kike man wannan kallon " ta faɗa cikin kasalalliyar murya "idan ma da akwai abun da yafi kallo kin cancanta hidaya,yanzu kan dr kike son sama kanki ciwan da zai zame maki masifa a rayuwa, miyasa bazaki rabu da shi ki kama wanda ke sonki naga dai ba wani abu da dr shazim zai nuna ma dr kabir, kuma tun da ki kaga kina roƙon Allah a amma kuma baki samu abun da kike so ba ki haƙura mana inaga haka shine mafi alkairi a rayuwar ki " "maryam amma kin fi kowa sanin yanda nake son dr, mi zai sa kice in rabu dashi " "idan baki rabu da shi ba ya zakiyi hidaya, bafa a so dole kin sani, tun da kikaga ya nuna baya ra'ayin ki ki haƙura mana ko dan ki sama ma kanki sauƙi" "ni dai shawarar da zan baki shine ki fitar da shi a zuciyar ki ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine a rayuwar ki Allah ya tabbatar maki amma idan kinji " "maganar gaskiya ina son dr so mai ƙarfi wanda nake jin bazan iya daina son shi ba " "to aikuwa kina da aiki mai girma a gaban ki" "ba wani aiki insha zan cigaba da roƙon Allah wataran na san zai so ni " "gaskiya hidaya baki cikin hankalin ki, naga Allah kika roƙa akan idan shi ba alkairi bane a rayuwar ki ya sauya maki da alkairi, yanzu ga alkairin ya zo amma kin kasa fuskantar gaskiya " "bazan ɓoye maki ba maryam wallahi bana son dr kabir idan nace na amince da soyayyar sa zan cutar da kaina ne kawai tunda bana son shi " "ba cewa nayi ki amince da shi ba, A'a ina son ki fitar da tunanin dr shazim a zuciyar ki ki roƙi Allah idan har dr kabir alkairine Allah ya tabbatar maki, amma kina ɓata lokacin ki ne akan shazim " "bazaki gane yanda nake jinshi bane a raina maryam" "bazan gane ba ko dai bazaki gane ba " Haka suka cigaba da magana a tsakanin su kowa so yake ɗan uwan shi ya fahince shi har dai ummah ta shigo ta same su, tana shigowa su kayi shiru binsu da idanu tayi daga baya tace, "maryam ɗan bamu minti biyu baban ta na san magana da ita " da to maryam ta amsa, kallon hidaya ummah tayi tace " ta shi ki wuce Abban ku na kira " gabanta ne ya faɗi , yanzu idan Abba ya tambayeta mike damun ta mi zata ce mashi "ummah nace maki fa kaina ne kawai yake ciwo " "zaki tashi ki wuce ko kuwa " tashi tayi ta nufi ƙofa ta fice zuwa parlorn Abban ta zaune ta same shi kan carpet yana duba jarida, sallama tayi ta shiga ciki, amsa mata sallamar yayi yana nuna mata wurin zama, zama tayi inda ya nuna mata kusa da shi, gaishe da shi tafa ra daga bisani tace "Abbah gani ummah tace kana kira na" "miyasa kika dawo gida yau da wuri, sannan mi ya sameki a wurin aikin na ku da har yasa kika dawo gida kina kuka, sannan miye haɗin ki da kabiru ɗan gidan minister mai wada daya kawo maki jakar ki sannan wannan kwalin na minene ??? " ya faɗa yana nuna mata jakarta da wani ƙaton kwali da ke gefan shi. gabanta ne yayi wani mumunnan faɗuwa jikake daram, a zuciyar sai faɗin " mi ya kawo dr gidan nan sannan wannan kwalin na minene " katse mata tunani yayi ta hanyar cewa "da ke nake magana kinyi man shiru " "Abbah bana jin daɗi ne kaina na ciwo shine na dawo gida" "to shi wannan kwalin na minene??, hidaya kin san dai bana wasa da ke ko? " _lokacin da dr kabir ya zo ashe Abba na bayan shi harya bada jakar da kwalin, da ya tafi ne ya tambayi mai gadi kayan miye kabir ya bashi, a nan ya sanar dashi cewa hidaya yace a ba_ "Eh Abbah da gaske nake maka bana lafiya ne shine ya ɗauko man jakata wannan kayan kuma na maryam ne " "Yau kika fara rashin lafiya ne da zaki kama kuka " shiru tayi "idan kika bari na bincika na gano ta ƙamai mai abun da ke damunki baza kiji da daɗi ba " " da gaske nake Abbah " " shikenan ɗauki jakar ki da kwalin ki wuce" da to ta amsa haɗi da ɗaukar jakarta da kwalin ta fice, da ummah taci karo zata shiga part ɗin Abbah , fuskarta a ɗaure babu alamun sassauci, fasa shiga tayi tace " biyo ni ina son magana dake " kawai ta faɗa, ajiye kwalin tayi a main parlor ta bi bayan ummah har bedroom ɗin ta, tsaye ta samu ummah a bakin gado, kallon ta ummah tayi tace. " hidaya miye haɗin ki da kabir yaron mai wada?" " ummah ba komai " " kar kiyi man ƙarya hidaya, maryam ta sanar dani duk abun da ke faruwa" "ummah maryam ƙarya take" "ƙarya? , maryam ɗin ce zata yi maki ƙarya " "A'a ummah" "ki shiga hankalin ki dani hidaya kinji na faɗa maki " "to ummah " "tafi amma ba wai mun gama maganar bane kina jina ko " "eh ummah " ta faɗa haɗi da kama hanya ta fice, da idanu ummah ta bita hara ta fice. ɗaukar kwalin tayi da jakar ta ta wuce ɗakin ta, zaune ta samu maryam kamar yanda ta bar ta ɗazu, mai da ƙofar ɗakin tayi ta rufe, tana zuwa tsakiyar ɗakin tayi jifa da kwalin harda jakar ta, da sauri maryam ta kalleta tana faɗin " ke kuma lafiya miya same ki kike jifa da kaya" "Ki barni kawai maryam, wai ashe dr gidannan ya zo har Abba ya ganshi " wani wawan tsaki maryam ta ja tana faɗin " aikin banza da wofi, shine zaki shigo kina wannan jifar da kaya, wai dan Allah miye laifin wanda yace yana sonka ne, kuma kema kin sani in ban da so na so wallahi bazai ce yana sonki ba dan kin fi kowa sanin shi ba sa'anki bane kawai dan Allah ya jarabce shi da son ki shine zaki riƙa yi mashi wannan wulaƙan cin" "maryam na lura bazaki taɓa fahimta ta ba " "in dai akan wannan haukan da kike yi ne bazan taɓa fahitarki ba, kuma ki sani zan sanar da ummah duk abun da ke faruwa tsakanin ki da dr shazim kin dai san abun da zai biyo baya idan taji kin buɗe baki kince kina son wani ɗa namiji " " maryam bana son irin wannan wasan, ke yanzu sai ki faɗa mata " "kina wasa ne ki cigaba da wulaƙanta dr ki gani idan ban faɗa mata ba, ke har ma abun da bakiyi ba sai nace kinyi wallahi" "komai zakice sai dai kice, amma maganar gaskiya bana jin son dr a zuciya ta " "zaki ma koya ne malama, kwalin minene wannan da kika jefar " maryam ta faɗa yayin da take nufar kwalin da ke ƙasa yashe, ɗaukar shi tayi ta buɗe, wani kyakyawan teddy bear ne pink sai heart fari a gaban cikin shi an rubuta am sorry dear da baƙin fenti, kwashewa maryam tayi da dariya tana faɗin " soyayya ruwan zuma, lallai dr " ta fa ɗa haɗi da sake buɗe kwalin ta fito da sauran kayan da ke ciki, sweet ne da uban chocolate masu ɗauke da sorry a jikin ledojin su, ba maryam ba har ita kanta hidayar sai da ta dara........... _Episode 58_59_ ............. "Amma fa dr na matuƙar son ki hidaya " maryam ta faɗa yayin da take buɗe wani chocolate ta kai baki, taɓe baki hidaya tayi "ke ki kaga haka " "wai ke haryanzu kina a kan bakanki na baki son shi " Kwanciya tayi haɗi da juya mata baya batare da tace komai ba, binta da ido maryam tayi tana faɗin "karki fasa zaki sha mamakin abun da zanyi maki kuwa " "ke maryam kin daɗe ko mi za kiyi ana so dole ne " "haka ki kace? " "eh haka nace " tashi maryam tayi zata fice, da sauri hidaya ta riƙota "wai ke ƴanzu ko kunya bakiji sai kije ki faɗama ummah " "sakar ni" maryam ɗin ta faɗa taba fisgewa daga riƙon da hidayar tayi mata ta nufi ƙofa, a sukwane hidayar ta rigata isa bakin ƙofar, abun ma dariya ya so ba maryam amma sai ta ɗaure fuska bata yi ba tace " ki matsa man a gabana " "wallahi bazan matsaba tun da ke baki san wasa ba " "wasa ko zakiga wasa " maryam ɗin ta faɗa tana ƙoƙarin janye hidaya "dan Allah maryam kiyi haƙuri wasa fa nake " "Ina ruwana da wasanki ni bani hanya na wuce " haka su kai ta jayayya har ummah tayi nocking ta hidaya sai roƙon maryam take akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, gajiya ummah tayi ta sake wani nocking ɗin tana faɗin "wai lafiya kuke da baza ku buɗe man ba " da sauri hidaya tasa hannu ta buɗe tana yima maryam alama da da ido akan dan Allah kar ta faɗa ma ummah, ummah na shigowa kallon su tayi tana faɗin "ku lafiya naga duk kunyi wani tsaye cirko cirko " hidaya ce tayi carb tace " ba komai ummah magana muke" "maganar ce har sai kunzo bakin ƙofa? " maryam tace " tafiya zanyi ne daman" "tun yanzu zaki tafi maryam?, ga abinci can a dinning, ki bari sai kinci sai ki wuce gida " " naci abinci ummah kafin na fito daga gida daman saboda naga ta dawo ne da wuri kuma ina kiranta bata ɗauka ba yasa nayi tunanin ko lafiya " "to shikenan, ki gaishe da mamar ku " "za taji insha Allah " jinjina kai ummah tayi haɗi da ficewa ta ba ɗakin "shine zaki wani ce zaki tafi " "idan ban tafi ba mizan yi maki ne, ko so kike na zauna ki cigaba da ɓata man rai " "haba dan Allah wane irin ɓacin rai kuma " "koma dai minene ni tafiya zanyi yi " "Amma ai kin tsaya na baki wancan kayan " "bana so" shine kawai abun da maryam ta faɗa ƙofar ta nufa ta buɗe bin bayan ta hidaya tayi tana bata haƙuri amma taƙi sauraronta,ba yanda ta iya haka maryam ta tafi ba tare da ta amshi chocolate ɗin ba ko ban kwannan arziƙi ba su yi ba, juyawa tayi ta koma ciki dinning ta nufa wurin ummah . _*✨KATSINA✨*_ Abie ne da uncle Ahmad da uncle mustafa zaune a parlorn suna magana Uncle mustafa ne yace " yaya yanzu yaushe zaka tafi kenan" Amsa Abie ya bashi da "da wannan week ɗin nace amma yanzu ina jin sai wani week ɗin saboda safwan da za su zo gobe " "to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen abie ya amsa, uncle Ahmad ne yace " wai yaya idan sun zo su safwan ɗin anan za su zauna?" "eh mana Ahmad idan ba nan ba ina zasu zauna " "a gaskiya yaya da zaka ji shawara ta da ba su zauna anan ba " "saboda mi? " "yaya bawan Allah nan yana cikin tashin hankali, rayuwar cikin barazana take, sai nake ganin zaman shi a nan kamar akwai gangance " "Ahmad bawani gangance nasan da lilin da yasa nace ya zauna nan " "to shikenan yaya,bawani abu Allah ya bashi lafiya " "Ameen shi ne kawai, yaushe zaka koma Abuja ne " abie ya tambaya "tuna ni nake ranar friday zan tafi " "ok Allah ya kaimu, wai addimisson ɗin su Aaimah shiru " Uncle Ahmad yace "Inajin fa basu fara ba dawa ba kuma kaga late aka nemar masu addimisson ɗin Amma na san bazai wuce wannan week ɗin ba tun da makarantar next month su ke fara lectures " "to shikenan Allah ya kaimu " da Ameen su ka amsa su duka, dadi ce ta fito ta zo wurin su ta zauna kan sofa gaishe da ita su kayi, amsa wa tayi da kulawa a fuskar sannan tace " mi ake tattaunawa ne tun ɗazu? " uncle Ahmad ne yace " magana muke ta yanda zamu nemo maki yaron ki " "mai makon naji kunce kun nemo shi sai kuce magana kuke ta yanda zaku nemo shi, na lura so kuke mu sa ƙafar wando ɗaya da ku kafin ku nemo shi " Abie ne yace "ba sai an kai ga haka ba" "to yauahe zaku kawo man shi gidannan? " Amsa Abie ya bata da "insha Allahu nan bada jimawaba, da wannan satin zan tafi kadunar to amma saboda zuwan su safwan yasa na fasa sai wani satin" "Allah sarki gobe ne kenan zasu zo, to Allah ya kawo su lafiya " "Ameen " su ka amsa su duka, fira suka shiga yi cikin nisha ɗin har sai da lokacin sallar zuhur yayi sannan suka nufi masallaci dadi kuma ta nufi ɗakin ta. _*✨SHAZIM✨*_ Lokacin da hidaya ta fita daga office ɗin shi bai wani jima ba shima ya nufi Abnoor Aiki yayi sosai sai daga baya yanufi office ɗin majeed,bai same shi a ciki ba hakan yasa yayi tunanin ko yana duba patient ne zama yayi kan sofa yana jiran ya dawo, wayar shi dake ringing ya jawo duba mai kiran yayi, Mansoor ne, picking kiran yayi sallama yayi, amsawa mansoor ɗin yayi yana faɗin "kai dai babu ruwanka yanzu da neman mutane, idan mutum bai nemeka ba shikenan kai ba ruwan ka da shi " ɗan yatsine fuska yayi yace "kai ai na lura neman mutanen kae yi " "gashi kuwa na neme ka " "to naji, yaushe ne ma kace zaka zo " "ok ka ma manta yaushe nace zan zo, nalura kamar baka son zuwana saboda zan zo na ɗauke maka habibtyn ka " "wait mansoor idan ba so kake nayi maka rashin mutunci ba to ka daina haɗa ni da wannan sakaryar yarinyar" "lallaima shazim sakaryar kace?" "ƙwarai kuwa ba sakayar bace, ni da zaka taimaka wallahi da zuwa kayi yau ka tattarata ka mai da ma iyayen yanta ita dan nagaji da zama da muke yi a gida ɗaya " "Amma nayi mamaki shazim ko da ace yau baka san taba ai baka faɗi haka ba bare ma tana ƴar uwar ka " "ni dai da zaka taimaka da kazo gobe ka tafi da ita " "bazan zo ba ɗan rainin wayau, idan da gaske ne ka gaji da zama da ita ja dawo da ita da kanan " "bana da wannan lokacin kuma " "to nima bana da shi " "Alright haka kace " "Kwarai ma kuwa " yana faɗar haka yayi rejecting kiran, murmushi gefan baki yayi haɗi da cire wayar daga kunnan shi, kwanciya yayi kan sofar latsar wayar shi ya shiga yi, anan majeed ya shigo ya same shi, zama yayi yana faɗin " yaushe ka shigo?" hannu ya miƙa mashi su kayi musabaha " tun ɗan ɗazu na shigo " "Ok naje duba patient ne, lafiya dai ko" " lafiya, maganar waɗan nan kayance nake so muyi " " ok , wanda ke hannun mu ko wanda kace a tura " " eh wanda nace ku aika " "anyi kamar yanda kace" "yawwa nagode sosai " "Amma shazim baka gani gara mu miƙa kayan nan hannun ƙungiyar drugs " "a'a majeed, idan mu kayi haka kamar mun ba masu kayan kayan su ne, kasan yanda cin hanci yayi yawa a ƙasar nan muna bada kayan nan masu su za su fito ne su ba cin hanci su amshi kayan su " "haka ne, amma to idan mun bar su nan mi za muyi da su" "ba abun da za muyi da su, kawai ina son yin amfani da au ne wajen gane mai kayan daga nan sai na ɗauki matakin da ya dace akan shi " "to shikenan, amma a canza masu wurin zama daga store " "ka jika da wata magana, idan ba nan ba ina zamu kai su, a nan zamu bar su har Allah ya toni asirin masu " "shikenan " majeed ya faɗa canza firar su kayi zuwa wata, ana kiran sallar asr su ka fita su ka nufi masallaci, da suka gama sallah majeed office ɗin shi ya koma shazim kuma yace mashi briefcase ɗin shi kawai zai ɗauka gida yake son ya koma saboda fatima, sallama su kayi majeed na faɗin yana gaishe da fatimar. Yana shiga office ɗin kamar yanda yace briefcase ɗin kawai ya ɗauka ya rufe office ɗin, motar shi da yayi parking a parking lot ya nufa, shiga yayi yayi mata key haɗin da yin reverse ya nufi gate , mai gadi na ganin shi da sauri ya tashi ya buɗe mashi gate ɗin , yana ɗaga mashi hannu har ya bar hopital ɗin. yana fita wata ɓakar jeep ta fito daga bayan Abnoor, ta mirror ya hange ta abun yaso ya bashi mamaki saboda ya san bawani titi ko wani gida da za'a mota zata iya fitowa daga wurin, tuƙi yake yana kallon motar da farko yayi tunanin hanya ce ta biyo da ita may be ko matsala ta samu ne yasa ta tsaya a bayan Abnoor ɗin, sai da yaga ya bar titin abnoor ɗin ya hau wanda zai kai shi gida yaga motar tana nan tana binshi, tafiya ya fariyi a slowly abun mamaki sai kawai yaga mai motar yayi parking,murmushi ne ya so kufce mashi dan abun yayi matuƙar bashi mamaki, key yayi ma motar ya cigaba da tafiya, shima mai jeep ɗin key yayi mata ganin haka ne yasa shi yin kwana ya sauka daga titin da zai kaishi gida, shima mao motar canza hanya yayi zuwa wacce shazim ɗin ya bi, yanke shawara kawai shazim yayi daya tsaya ya ga ko waye kd binsa a baya, gangarawa yayi bakin hanya yayi parking kashe motar yayi ta zare key ɗin motar ya fito, mai motar na ganin ya fito da sauri yayi reverse ya a wani irin masifan gudu ya shiga wata kwana, jinjina kai yayi yana faɗin " ƙaramin ɗan iska ai da ka tsaya sai naji dalilin bin nawa da kake " komawa yayi cikin motar ya kama hanyar gidan malam, yana isowa horn yayi mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga , parking yayi sannan ya fito ya shiga ciki, parlorn ummy ya fara zuwa zaune ya sameta ita da mai aikinta tana ɗan daddana mata ƙafu saboda fama takeyi da su kwana biyu, ƙara sawa yayi ciki bakin shi ɗauke da sallama Amsa sallamar da yayi ummy tayi tana faɗin " lale marhabun da bokan turai " wuri ya samu kan sofa kusa da ita ya zauna, mai akin ummy ce tace " ina wuni " "lafiya lau " ya amsa mata haɗin da kallon ummy yace "ina wuni ummy, ya ƙafafun " "da sauƙi ya aiki " "Alhmdllh" "o ya fatima da jiki " "Alhmdllh taji sauƙi sosai " "to masha Allah, Allah ya ƙara sauƙi " "Ameen " sun ɗan jima suna ɗan taɓa fira da ummy kafin daga bisani ya nufi part ɗin malam Samun shi yayi a kan carpet yana duba wani littafi,sallama yayi mashi haɗi da ƙara sawa ciki ya samu wuri ya zauna kan carpet ɗin, amsa sallamar malam yayi sannan yace "daga ina haka da yamma " "daga Abnoor nake, shine nace bari nazo na duba ku kai da ummy " "ai kuwa ka kyauta,ina nuraddeen da fatima " "Fatima dai na gida, noraiz kuwa yana mall kasan yanzu su noraiz an daina zaman banza " murmushi malam yayi yana faɗin " haka ne kam su aboki na an girma yanzu ba'a zaman banza, to Allah ya taimaka" "Ameen " "fatima jiki yayi sauƙi ko " "ta samu sauƙi dan ba inda bata zuwa yanzu " "to Allah ya ƙara sauƙi" "Ameen " "yau she zata fara zuwa makaranta? " malam ya tambaya "insha Allah nan da wani watan zasu fara karatu, da yake makarantar basu jima da bata addimisson ba " "Ah abu yayi kyau Allah ya kaimu nan da wani wata " " Ameen malam" "ya wajen su kawun ka sun sake kiranka kuwa " "A'a ba wanda ya kira ni cikin su " ya faɗi hakan kawai saboda bai son malam na mashi maganar yayi haƙuri ya ƙyale su "shazim kenan, ina so kasa haƙuri a zuciyar ka, ko jiya Ahmad ya kirani yace suna nemaka ba su samun ka, abun da ya faru shazim yariga da ya faru tun da yaron nan yayi nadamar abun da yayi kayi haƙuri mana, yanke alaƙa da su bai da amfani saboda su ɗin jinnin ka ne " "amma ai malam su basu ganin haka" "wayace maka basu gani sun sani kuma duk wani abu da kaga suna yi maka suna yi ne dan suna sonka a matsayin ka na ɗan ɗan uwan su " "malam kai kaɗai kake fahimtar haka, amma su ba haka bane a ransu ba " "idan zaka biye wannan tuna nin naka bazaka taɓa fahimtar abun da nake so ka fahimta ba" " malam na fahimce ka kuma nasan mi kake nufi" "da ka fahimta da baka ɗauki wannan fushin da kake yi da su ba, ko ka manta lokacin da kana yaro miye wanda uba ke yima ƴaƴanshi wanda Ibrahim bai yi maku ba" "malam baka san waye uncle Ibrahim ba shiyyasa kake cewa haka, kawai yayi ne saboda wani dalilin shi " "hmmm lallai shazim,duk da ban zauna da Ibrahim ba sosai amma ina tabbatar maka da cewa mahaifiyar shi da yayan shi kaɗai za su nuna man sanin Ibrahim,suma sai dai su nuna man wani amma Ibrahim na san shi sani bana wasa ba a halayen shi babu wanda ban sani wanda ko ƴan uwan nashi basu san shi da shi ba, tun da kaji nace kayi haƙuri ka maida komai ba komai ba kayi hakan kawai" "shikenan malam, amma wane hali ne nashi wanda ka sani har kake cewa ƴan uwan shi basu san shi da shi ba?" "abun da ya wuce shazim ya riga da ya wuce sai dai kuma mu fuskanci gaba " "Amma malam da ka sanar da ni " "ka kwantar da hankalinka, idan akwai ƙaddarar ka sani zaka sani, amma karka sama ranka wani abu ba komai bane fatana kawai ka daina wannan fushin mara amfani da kake yi da su " "shikenan malam insha Allah zan dai na" "kaji ɗan albarka ko kai fa " malam ya faɗa yana shafa kan sa, canza firar suka yi zuwa wata, ya jima sosai a gidan dan sai bayan da yayi sallar magrib sannan yayima malam da ummy sallama ya kama hanyar gida, yana shigowa layin su ya hangi wannan baƙar jeep ɗin tayi parking a ƙofar gidan su mai gadi na tsaye bakim motar da alama magana su ke da mai motar, ƙara sawa yayi bakin gate ɗin, mao gadin na ganin shi da sauri ya nufi gate ya buɗe mashi, ko kallon inda jeep ɗin nan take bai yiba ya shige ciki, yana shigewa mai gadi ya maida gate ɗin ya rufe, parking yayi a compound kashe motar kawai yayi ba tare da ya ɗauki kayan shi da cikiba ya fito ya nufi mai gadi dake ƙoƙarin ficewa zuwa wurin wannan mai jeep ɗin, da hannu ya dakatar da shi,alama yayi mashi da ya zo, da sauri mai gadin ya nufo shi,yana isowa yace " barka da dawowa ranaka ya daɗe " ba tare da ya amsa mashi ba ya jifa mashi tambaya "wanene a bakin gate da na ganku a tare? " "wani mutumi ne" "wani mutumi? kana nufin baka san shi ba" "eh ranka ya daɗe " "ok, maganar mi na hango ku kuna yi? " "tambaya ta yake wai da yaushe zaka dawo gida, to shine sai gaka ka dawo " "shine kawai abun da na hango ku kuna tattaunawa " da sauri mai gadin yace "eh shine ranka ya daɗe" "am wa kake da suna ina fatan kasan halina, ka faɗa man maganar da kuke tattaunawa da shi karka bari nayi bincike na gano gaskiya" "yallaɓai dai Allah kayi haƙuri, wallahi ina tsoron matakin da zaka ɗauka a ka ina, amma maganar gaskiya ya tambaye ni ne akan wai kai ke da asibitin abnoor, nace mashi eh naka ne to shine yace wai mahaifiyar shi ce bata da lafiya wai yaji ance a asibitin ka kuna duba mara lafiya kyauta wai bai san ta yanda zaiyi magana da kai ba shine yake so wai dan Allah na bashi wani haske ta yanda zai samu ayi ma mahaifiyar shi aiki" "wane kalar haske kenan" "wai so yake na haɗa shi da Ammy, to dana ji yace haka ne sai nace yaje asibitin ya kai ta za'a du bata ba dole sai Ammy ta sa baki ba, shine yace wai zai bani dubu ɗari dan na haɗa shi da Ammy " "sai kace mashi mi kenan" "zan bashi amsa ne sai gaka ka dawo" "ok shine kawai abun da kuka tattauna" "shine kawai ranka ya daɗe" "to amma mi yasa naga kana ƙoƙarin komawa wurin shi " "zan koma nace mashi ne idan da gaske yake ya zo ya sameka kuyi magana, " "zaka iya tafiya, amma ba sai ka koma wurin shi ba " "to shikenan nagode" mai gadin ya faɗa haɗi da komawa bakin ƙofar ɗakin shi ya zauna . Ciki shazim ya shiga,ba kowa a main parlorn , sama ya nufa zuwa part ɗin shi, yana tura ƙofar ya shiga wani ƙamshi ne ya bigi hancin shi,ba irin wanda ya saba jiba a ɗakin , wani irin ƙamshi ne gashinan dai, bin ko ina na ɗakin ya shiga yi da kallo sai gani yayi kamar an canza mashi fasali , azuciyar shi yace "wannan wane irin ƙamshi ne " ya faɗa haɗi da nufar bedroom ɗin shi nan ma ƙamshin yaji irin na parlorn, mai da ƙofar ɗakin yayi ya rufe , gaba ɗaya ƙamshin ya addabe sa dressing mirror ɗin shi ya nufa inda yake ajiye room fresh ya jawo ƴar locker room fresh iri iri a cikin locker, daya daga cikin su ne ya ɗauka haɗi da maida locker ya rufe, fesa room fresh ɗin ya shiga yi sai da ya tabbatar ya canza ma ɗakin iskar shaƙa tukun ya maida turaren wurin zaman shi, kayan jikin shi ya shiga ragewa, toilet ya nufa sai kamar bayan minti biyar ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani a hannun shi yana goge kanshi, ajiye towel ɗin yayi daya gama guge kansa,zama yayi kan kijrar dake bakin dressing mirror ɗin nan ya shiga shafe shafen shi sai da ya ɗauki kusan minti biyar zaune yana abu guda daga baya ya nufi corridor da wardrobe ɗin sa take,ash ɗin jallabiya ya ɗauko ya sa, komawa yayi bakin dressing mirror ya feshe jikin shi da turare, yana shirin barin wurin yaji anturo ƙofar bedroom ta ciki mirror ya zuba ido dan ganin wanene wannan daya fi ƙarfin yi mashi nocking, a iya sanin shi dai ko Ammy bata shigar mashi ɗaki babu nocking, turo ƙofar tayi ta shigo hannunta ɗauke da tray data shirya mashi abinci, zuba mata ido yayi yana kallonta ta cikin mirror har ta gama shigowa ta nufi ɗan table ɗin dake tsakiyar ɗakin ta ajiye mashi juyowa tayi tace " dinner ne na kawo maka " banza yayi da ita kamar ma bai san da zamanta a ɗakin ba, matsowa tayi kusa da shi kamar zata shige jikin shi tana fa ɗin " ya shazim wai minene matsalar, ina sonka kuma kaima nasan kana sona to banga wani abu aciki ba da zaka rinƙa wulaƙanta ni " baƙaramin ɓaci ranshi yayi ba wai yau wannan yarinyar ce ta samu power har ta iya tsayawa a gabanshi tana faɗa mashi waɗannan magan ganun, bai gama fita daga mamaki ba yaji ta kai mashi runguma ta baya 😲....... _TASHIN SENS FEENAH WALLAHI BA RUWANA_ _Episode _60_61 ...........................Please duk ka ajiye wani fushi a gefe da kake yi dani,abun da ya wuce ai ya riga da wuce " ta faɗa tana wani ƙara manne mashi ajiki haɗi da zagayo da hannunta tana shafa ƙirjinsa, ranshi ne yayi wani mumunnan ɓaci har bai san lokacin da yayi wurigi da ita ba bata faɗa kan komai ba sai kan table ɗin dake tsakiyar ɗakin gaba ɗaya ta faɗa kanshi tray ɗin da tashigo da shi ya kafa abincin da ta kawo mashi ya zube ajikinta, azabar zafin abincin da taji ne yasa ta fasa wata uwa ƙara gashi hannunta ya bugu sosai, bata gama dawowa hayyacin ta ba ya ɗago da ita wanke ta yayi da lafiyayyun maruka har sau huɗu tangal tangal ta shiga yi juwa ta kwashe ta sai ƙasa jikake tim ta faɗi ba ƙaramin buguwa ƙugunta yayi ba, fashewa tayi da wani matsannancin kuka tana faɗin " wayyo Allah nah momy zai kashe ni, na bani innah kizo ki taimake ni ya ɓallaman ƙugu " tsawa ya daka mata yana faɗin " tashi ki fita ki bani wuri kafin ranki ya ɓaci" wani kukan ta sake fashewa da shi dan bazata iya tashi ba dan ba ƙaramin azaba take ji a ƙugunta ba gashi idanuwan ta bata wani gani sosai saboda marukan da yayi mata har jini ya kwanta gefan indanta na hagu,ganin bata da niyyar tashine yasa shi jan hannunta data bugu ƙiyyy ya jata har bakin ƙofa yana zuwa yayi wurgi da ita wani ihu ta kwala zaiyi wuya ace su Ammy basu ji ta ba dan kware baki tayi sai ihu take tana tabani ta lalace hannunta ƙugunta,maida ƙofar bedroom ɗinshi yayi ya rufe nan ya barta sai kuka take tana kiran su Kairiyya su zo su kawo mata ɗauki. Noraiz ne ya shigo a sukwane jin ihun mutum, bai ɗauki murya ba ya dai ji ihu da kuke kuke sunyi yawa kuma a part ɗin yayan shi hakan ne yasa shi shigowa a guje,a nan durƙushe ya sameta sai kuka take "wai wacece ke wannan ihun lafiya?, miya sameki?" bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba sai ma sake fashewa da wani kukan da tayi, su fatima ne suka banko ƙofar ɗakin har rigen rigen shigowa suke Ammy na bayan su, noraiz sai magana yake ma. ta amma taƙi shiru gashi bai gane ko wacece a cikin su ba bare ma ya san minene ke damun ta, sai da ya ga shigowar su kairiyya sannan ya fahimci cewa ita ce , tsaki yaja haɗi da cewa " yo wai ashe ke ce ki ka wani addabi mutane da ihu, ai ba wani ya aiko ki part ɗin nasa ba koma mi yayi maki wallahi Allah ya ƙara " abun da yasa ya faɗi haka yasan dole ita da shazim ne wani abun tayi mashi har yayi mata "wane irin sakarci ne wannan noraiz, bakaga halin da take ciki ba kake mata Allah ya ƙara kenan ma kasan abun da ya sameta?" Ammy ta faɗa yayin da take matsawa wurin feenah da kairiyya ke ta ƙoƙarin ɗagawa amma ta kasa saboda da ta ɗago feenahr take komawa saboda bata iya tashi "yana wuce wani abu tayi ma ya shazim, tun da daman ya hanata shigo mashi part amma da yake ba jin magana take ba ai gata nan ta shigo " noraiz ya faɗa yayin da yake ƙoƙarin juyawa ya nufi ƙofa, da katar da shi Ammy tayi ta hanyar cewa "na ga kana shirin fita ina zaka ko bakaga halin da take ciki bane kuma yaushe shazim ɗin ya shigo gidan " "na gani Ammy mi zan yi mata?" "lallai noraiz tambayata ma kake yi ko" "A'a Ammy mi zan yi mata to" "kira man shi yayan naka da yayi mata haka, ai sai ya zo ya san yanda zaiyi da ita idan ma hospital zai kaita" " to noraiz yace haɗi da nufar ƙofar bedroom ɗin shazim ɗin yayi nocking shiru ba'a bashi izinin shigaba ba kuma a buɗe ƙofar ba,Ammy tace "lafiya?" "da alama dai bai ciki, dan ban ji motsin shi ba " kallon feenah Ammy tayi tana faɗin " wai ma mi ya sameki da nayi tunanin ko ke da shazim ne?" "Ammy shi ne ya mare ni ya kuma haɗa ni da table ɗin bedroom ɗin shi ko nan shine ya jeho ni " sai da tayi magana tukun Ammy ta lura da jinin daya kwanta a gefan idon ta ga sawun hannuwan shi nan a fuskar ta ra ɗau, mi noraiz zai in ba dariya ba jin tace wai ya jehota, sa'ada ma ɓoyewa tayi bayan fatima ta sha dariyar ta, daƙuwwa Ammy tayima noraiz tana faɗin "ya jeho ki dai ?, sai kace wasu kayan wanki " wata dariyar noraiz ya sake kwashewa da ita yana faɗin " kayan wanki fa kika ce Ammy " wani ƙululun baƙin ciki ne ya tukare feenah ganin yan da noraiz ya dage sai kwasar dariya yake yana mata Allah ya ƙara " Noraiz wallahi zanci mutuncin ka kai da sa'ada, ku wane irin mutanene wai, tana wani hali kuna mata dariya saboda rashin tausayi " " Ammy kina ji fa tace a bedroom ɗin shi ya mareta, in ba tsabar iskanci ba irin nata mi ya haɗata da bedroom ɗin shi " noraiz ya faɗa tsaki Ammy taja haɗi da nufar bakin ƙofar bedroom ɗin shazim, nocking ta shigayi tana kwala mashi kira amma babu alamun ma yana ɗakin, kallon feenah tayi tace " ko fita yayi? " girgiza mata jai feenah tayi tana faɗin " yana nan ciki, daya jeho ni waje mai da ƙofar yayi ya rufe " dariyace ta kusa kufce ma noraiz jin ta ƙara cewa ya jeho ta, da sauri ya sa hannu ya tushe bakin sa haɗi da sadda kai ƙasa " shazim kana jina shine kayi banza dani ko saboda tsabagen rainin wayau ko " Ammy ta faɗa yayin da take sake nocking ɗin ƙofar still shiru babu alamun zai zo ya buɗe mata, ganin dai da gaske ba zuwa zai yi ba ya buɗe mata ba ne yasa tace su Kairiyya su kama feenah, haka su ka talalla bata kamar kayan wanki da take faɗi su ka fice noraiz na bayan su yana dariya mara sauti dan gudun kar Ammy ta ji shi, haka su ka saukko da ita daga saman stairs un expected su ka hangi shazim kwance saman sofa three seater ya ɗaura hannun shi na dama saman kanshi yayin da hannun shi na hagu yake saman cikin sa da alama ma bacci yake jallabiyar da yasa ce ɗazo a jikin shi , abun har so yayi ya ba feenah tsoro tun da ita dai ta san lokacin da ya fito da ita bedroom ɗin shi ya koma abun mamaki kuma gashi a parlorn Ammy, Noraiz ne yayi surin cewa "to ga ya shazim a parlor kin gani kenan ƙarya take da tace shine ya mare ta Ammy " zuba shazim ido Ammy tayi baccin shi kawai yake kwasa abun shi hankali kwance,zama kusa da shi Ammy tayi tana kiran sunan shi haɗi da bubbuga hannun sofar, duk abun da ke faruwa idon shi biyu yana jin su, sai da Ammy ta dake kiran sunan shi tukun ya buɗe ido yana kallon ceiling sai da ya ɗau sakanni sannan ya mai da duban shi ga Ammy "lafiya na ganka nan kwance?" Ammy ta jefa mashi tambayar, ɗan ya tsine fuska yayi haɗi da yun ƙurawa ya tashi zaune "kai na ne keman ciwo shine na sha magani na kwanta " "Amma shazim mi feenah tayi kayi mata haka?" "wacece kuma feenah?" ji wani tambayar rainin wayao nan wurin shazim "ok baka ma santa ba " "Ammy naji kina wata magana ne bayan ni tun da na dawo ina nan kuma ni banga kowa ba, shiyyasa na tambaye ki " fashewa feenah tayi da kuka tana faɗin " wallahi ya shazim mun haɗu ba dinner naje kai maka ba kuma ma ai tray ɗin yana bedroom ɗin ka " hannu Ammy ta ɗaga ma feenah tana faɗin " ya isa haka feenah, yanzu kai ai sai kaje da ita medical room ka du ba hannun ta " tashi yayi yana faɗin " Ammy cewa fa nayi kai na keman ciwo, bazan iya duba kowa ba a yanayin da nakeji kai na noraiz ya kaita asibiti " yana gama faɗa ya kama hanyar tafiya part ɗin shi "tafiya ma kake?, kayima yarinyar mugunta sannan kace baza ka duba ta ba " wai gowa yayi yana faɗin " bana jin daɗi ne Ammy kuma ni ban ma san akan mi kike magana ba " yana gama faɗa ya haye sama, da kallo kawai Ammy ta bisa tasan ƙarya yake shine ya dake ta amma zai ce wai bai ma san akan mi take magana ba "Kairiyya ku ka mata zuwa waje noraiz ya kaita asibiti, kai kuma maza ka ɗauko key ka kaita asibiti " ammy ta faɗa tana kallon noraiz da ke tsaye, turo baki yayi yana faɗin "Ammy ni bacci nake ji " ko kallon shi Ammy bata yiba tace " ku fita da ita kunji, gani nan zuwa " da to su ka amsa haɗi da nufar waje da ita, Ammy kuma bedroom ɗinta ta nufa , ganin shirin ɗauko key take ta kai feenah da kanta yasa noraiz bin bayan ta yana faɗin "dan Allah kiyi haƙuri zan kaita da kai na " ko kallon shi bata yi ba ta shige bedroom ɗin , wardrobe ɗin ta ta nufa buɗewa tayi ta ɗauko hijab sannan ta koma wurin dressing mirror ɗinta locker dake ji ta jawo key ɗin motar ta dake ciki ta ɗauka, "Pls Ammy wallahi zan kai ta " roƙonta yayi tayi sai da ƙyar ya samu ta bashi key ɗin , tana bashi ya fita a tsaye ya samu su fatima riƙe da feenahr sai ruri take tana kuka yan ƙara so wa wurin su yace "Allah ko kiyi mana shiru ko wallahi na koma, ƴar rainin wayau kawai wani ya aike ki ɗakin shi da zaki ta wani cika ma mutane kunne " ya faɗa haɗi da nufar motar Ammy da ke parking lot, da harara feenah ta raka shi duk buguwar da tayi bai hanata rashin kunya ba, fito da motar yayi zuwa compound in da su ke tsaye sa'ada ce ta nufi motar ta buɗe ƙofar baya su Kairiyya su ka shigar da ita, kairiyya ce ta zauna a baya tare da feenah fatima kuma ta shiga gaba, sa'ada ta koma ciki dan ɗauko masu hijaban su saboda duk cikin su babu mai hijab sai fatima ita ma gama sallar ta kenan taji ihun feenah,bayan kamar 5 seconds sai sa'ada ta fito hannunta riƙe da hijab ɗin kairiyya da ta feenah,miƙa masu tayi su ka amsa sannan ta koma ɓangaren da feenah take ta shiga ya zama sun sata a tsakiya ita kairiyya, reverse noraiz yayi ya nufi gate da tun fitowar shi ya sa mai gadi ya buɗe masu, ficewa yayi daga gidan hanyar Abnoor ya ɗauka idan su ka zo in da za su sha kwana da mugunta yake shan kwanar dan duk ya sha kwana sai fennah ta saki ƙara, sa'ada dariya kawai take kwasa a zuciyar ta tana faɗin " Allah ya ƙara maganin mai shishigi kenan, mutum yace baya so to ina dalilin maƙale mashi, in dai ya shazim yanzu kika fara gani " haka tai ta ma feenah dariya da Allah ya ƙara har su ka iso Abnoor, horn noraiz yayi mai gadi ya buɗe mashi ya shiga da motar ciki,parking yayi yana gama daidaita parking yace su sa'ada su kama ta su shiga ciki, fitowa su kayi har da fatima su ka kamata sai ɗangesa ƙafa take har su ka shiga ciki yayin da shi kuma yake bayan su, sun shiga nurses ɗin dake night su ka amshe ta,noraiz ne yaje office ɗin majeed ya sanar da shi abun da ke faruwa da yake yau bai tashi da wuri ba, "Ya salam " majeed ya furta haɗi da cewa " shazim baya gida ne?" " yana nan baya jin daɗi ne shiyya sa bai duba ta ba" " amma wane irin rashin jin daɗi ne wannan da har zai hana shi duba patient " abun da yasa majeed ke faɗin haka noraiz ce mashi yayi faɗowa tayi daga bene koma yana zargin ta karye shiyyasa duk hankalin majeed ya tashi. "muje na ga jikin nata" majeed ya faɗa yayin da yake tashi daga kan kujerar da yake, fice wa yayi noraiz ya biyo bayan shi har inda feenah take sai uban kuka take kamar yarinyar goye, nurses ɗin da ke wurin duk haushi ta ba su kawai abun da yasa su kayi shiru su ka ƙyaleta tana cika masu kunne saboda kawai sun ganta tare da masu asibiti amma da ta sha masifa _*kun san halin wasu nurses ɗin namu ko yawan kuka su ka ga mutum nayi yanzu zai sha masifa su ce bai da dauriya bayan suma fa ba ita gare su ba*_ majeed na ƙara sowa tambayar ta ya shiga yi mike damun ta ina da ina ne ta bugu , bata bashi amsa ba sai sake ɓare baki da tayu tana wani kukan , noraiz ne yace " dallah malama an magana, idan kuma ba inda ke maki ciwo mu tashi mu kuma gida " "da kata noraiz saboda mi zaka yima ihu bakaga sai kuka take ba dole akwai inda ke mata ciwo kuma ka ce faɗowa tayi daga bene ba " "haka ne faɗowa tayi " ya faɗa fuska a ɗaure shi a dole gaskiya ya faɗa, jin abun da yace ma majeed ne yasa feenah buɗe baki tace "wurgi ya shazim yayi da ni har na faɗa kan table hannun ya bugu da ƙuguna amma ba faɗuwa nayi ba " norai a ranshi yace " shashasha ana so a rufa mata asiri amma da yake bata san ciwan kanta ba take tona ma kanta asiri sai kace wani abun arziƙi ne dan ta sanar da ya majeed ya shazim ne ya ji mata ciwan" tsaki yaja sannan a zahiri yace " ka rabu da ita kawai ya majeed ka duba ta ka gani ko ta samu karaya a ƙugunta dare yayi " ihu feenah ta sa jin noraiz na faɗin ko ta samu karaya, abun ma har so yayi ta ba majeed dariya, in ba sharri irin na noraiz ba yaushe daga wannan faɗuwar zata karye kuma a ƙugu "ya isa haka dan Allah noraiz " nurses ɗin dake wurin yasa su ka kamata zuwa emergency room,cikin ƙanƙanin lokaci majeed ya shiga du bata daya kama hannunta sai ta fashe da kuka,hakan yasa ya gane cewa ta samu targaɗe ne a hannun,wurin gayran targaɗen sai da ta so ta tara mashi mutane da dai ya gaji tsawa ya daka mata yana faɗin wallahi ko dai tayi shiru ko kuma ya ƙyaleta da ciwan, nurses ɗin da ke ciki suna taimaka mashi tsaki kawai su ka ja duk ta ba su haushi sai kace ba mace ba wata cewa tayi " zanga ranar da kika zo haihuwa ƙila ranar mutuwa zaki dinga yi kina dawowa" "ai kam dai" harara kawai feenah ta maka ma su "yo ashe abun iskanci ne tun da har kina da idon hararar mutane " "ya isa haka " majeed ya faɗa Sai da ƙyar ya samu feenah ta tsaya ya gyara mata targaɗen sannan yayi sannan yayi ma ta allura,magunguna ya ɗauko mata a pharmacy wanda zata sha har da wanda zata shafa a fuskar ta da hannun ta da na ɗigawa a ido saboda jinin daya kwanta mata sannan ya sallame ta, _*Allah sarki masu abu da abun su, su sai dai kawai a ɗauko masu ba tare da sun siya ba*_😜 fitowa tayi sai ɗan gesa ƙafa take hannu ya sha uban ɗauri, duk sai ta ba su fatima tausayi idan ka cire sa'ada da noraiz dan su ko kaɗan ba su ji tausayin ta ba sai ma Allah ya ƙara da su ke mata suna faɗin gobe ma idn halinta ne ta sake komawa part ɗin shi. Godiya noraiz yayi ma majeed sannan suka nufi hanyar fita, tsaida fatima majeed yayi yana tambayar ta ya ƙarfin jiki da bata haƙuri na rashin zuwa kwana biyu da baiyiba ya duba ta "babu komai ai ya majeed naji sauƙi sosai " "to shikenan Allah ya ƙara sauƙi, amma duk da haka zan zo har gida na sake duba ki " "to shikenan ya majeed sai na ganka " "ok insha Allah " ya faɗa har in da noraiz yayi parking su ka yayi mata rakiya lokacin da su ka iso har su Kairiyya sun shiga cikin motar ita kawai suke jira, sallama tayi ma majeed sannan ta shiga ciki, tsaye yayi har sai da ya ficewar su sannan ya koma ciki ya haɗa kayan shi ya bar asibitin. Lokacin da suka iso gida tuni baccin wahala ya ɗauke feenah sai da kairiyya ta tashe ta tukun ta sana sun iso gida, fitowa su kayi su ka shiga ciki a parlor su ka samu Ammy tana jiran dawowar su, wurin ta su ka ƙaraso, "ya jikin feenah?" Ammy ta tambaye ta, amsa ta bata da " da sauƙi Ammy " "Allah ya ƙara sauƙi, ki tafi ɗaki ki kwanta " da to ta amsa haɗi da nufar ɗakin da suke kwana ita da kairiyya kusa da ɗakin fatima. "noraiz mi majeed yace ya samu hannunta na ganshi a ɗaure?" Ammy ta tambaye shi "targaɗe ne wai ashe da ni har nayi tunanin karyewa tayi jin yanda take neman fasa ma mutane kunnne " "ban dan shashancin banza noraiz" "to Ammy ga key ɗin ki nan sai da safe" ya faɗa haɗi da miƙama Ammy key ɗin motar ta ya nufi sama zuwa bedroom ɗin shi Ammy ma cewa tayi suma su fatima su wuce suje su kwanta dare yayi da to su ka amsa mata haɗi da wucewa ɗakunan su, kairiyya ɗakin su ita da feenah ta nufa da ledar magungunan feenah,tura ƙofar ɗakin tayi ta shiga ciki. Masha Allah ɗakin ya haɗu sosai family bed ne acikin sa mai girma wanda mutum huɗu za su iya kwanciya ba tare da sun takura ba, dan gadon duk yafi na ɗakunan su Ammy girma da faɗi. Zaune ta samu feenah kan gado sai zuba uban kuka take tsaki kairiyya taja dan tun abun bai bata haushi har abun ya fara bata haushi, ciki ta ƙarasa kan dressing mirror ta ajiye ledar magungunan feenah ta nufi toilet, alwala ta ɗauro ta zo ta gabatar da sallar shafa'i da wutri da ta saba yi duk daren duniya, har ta kammala sallar ta canza kayanta zuwa na bacci feenah bata bar kuka ba da dai abun ya ishe ta cewa tayi " wannan kukan da kike yi ki sani bawani amfani da zai yi maki dama kinyi shiru kin kwanata dan zai fiye maki, komai ma ta sameki feenah laifin ki ne kin san halin ya shazim sarai ba sai an baki labarin shi ba tunda kika ga baya ra'ayin ki inaga da haƙura kika yi da shi kika fita batun shi amma duk wannan shishige mashi da kikeyi bazai amfana maki komai ba face ma kiyita shan wahalar sa kina dai gani yau da da tsautsayi da tuni ya karta ki, shawa..... " bata ƙarasa na feenah ta daka mata tsawa tana faɗin "da Allah dakata man kairiyya dama ba tun yau ba nasan cewa ke ƴar baƙin ciki ce , kina bakin ciki na samu ya shazim, to wallahi aniyar ki ta biki dama sai da innah tace mana kema son shi kike dama ce kawai baki samu ba shiyyasa kike man baƙin ciki, to wallahi kiyi ki gama ni da ya shazim nan gani nan bari ɗumaman mayya e he " ta ƙarasa maganar haɗi da dallama kairiyya harara kamar idanuwanta zasu zazzago ƙasa, abun yayi matukar ɗaure ma Kairiyya kai wai ita feenah ke ce mawa tana mata baƙinci kuma wai innah da bakinta ta ke ce ma feenah wai tana mata baƙin ciki tun da take bata taɓa tunanin wani cikin su zaiyi tunani maka manci haka ba, "Allah ya tsare ni feenah da yi maki baƙin ciki,gaskiya ce nake faɗa maki " "to bana so kitsaya a matsayin ki kawai ban son gaskiyar taki " feenah ta faɗa "haka kika ce?" "eh haka nace gaskiya ko in dai da ga wurin ki ne bana so na ya fe " "shikenan wahala ta ya shazim yanzu kika fara shanta " kairiyya ta faɗa haɗi da jan blanket ta juya mata baya ta rufe jikinta ruf, tana jin feenah na faɗin " aniyar ki ta biki, ni da ya shazim sai alkairi duk baƙin cikin mutum wallahi sai dai ya mutu" tana jin ta amma tayi banza da ita kamr ba da ita take magana ba, itama da ta gaji da banbotan kwanciya tayi. _*ɗan adam kenan duk yanda kairiyya ta damu da ita amma ji irin maganganun da tajefa mata, Allah ya shiryeki feenah, nima nace in dai shazim ne muzu ba mugani ke da shi wa zai ci riba*_ _WASHE GARI_ ........... zaune su ke kan dinning suna breakfast, kowa na ci abinci amma ban da feenah da bata iya ko da ɗaga hannunta balle ta samu taci lura da hakan ne yasa Ammy cewa " feenah lafiya kowa yana breakfast amma ban da ke " Kwalla ce ta taru a idanuwan ta tace " Ammy bazan iya ci ba saboda hannun" ta faɗa hawayen da ke idanunta na zubowa Sai da ta faɗi haka sannan Ammy ta tuna da cewa tayi fa targaɗe a hannunta, "ta so ki dawo kusa da ni sai na riƙa baki, ke sa'ada koma in da ta taso " Ammy ta faɗa, turo baki gaba sa'ada tayi tana faɗin "Ammy tana fa iya ci da kanta " "kimci gidan ku zaki tashi ko sai naci mutuncin ki, wai ko wane irin mutanene wai" miƙewa sa'ada tayi haɗi da ɗaukar plate ɗin da take cin abinci ta koma in da feenahr ta tashi "wallahi Ammy ke ke ƙara biye mata wani bata iyaci da kanta ba sai kace wacce ta karye, ai da karyewa kika yi ƙila komai sai ayi maki k....... " kasa ƙara sawa yayi ya duƙe ƙasan table da sauri sakamakon jifar shi da Ammy tayi da spoon, dariya ce ta kubce ma fatima dama haushin abun da yake ma feenah tun jiya ta ke , yana a ƙasan table bai ɗago ba yace " na rantse da Allah na kamaki fatima sai ranki ya ɓaci zaki san ni kike ma dariya " hannu ta sa ta toshe bakin ta tana faɗin "A fuwan ya noor bazan sake ba " "kima sake yarinya , dan Allah Ammy kiyi haƙuri " Ya faɗa ba tare da ya ɗago ba, tsoro yake ya ɗago Ammy ta sake jifan shi "Ammy kinyi shiru baki ce kinyi haƙuri ba " sai kace wani yaro "Sai baƙin tsoro ga jan faɗa " Ammy ta faɗa, jin tace haka ne yasa shi fahimtar cewa ta haƙura, ɗagowa yayi yana zuba ma fatima harara, tsit wurin yayi baka jin motsin su sai na cokulan da suke cin abinci, shazim ne ya shigo daga motsa jiki,wurin su ya ƙara so Ammy kawai ya gaida ya nufi sama daman tun da su feenah su ka zo ya daina breakfast a dinning dama can ba gwanin zama dinning ba ne, suna kammalawa fatima ta shirya mashi na shi a tray da zata kai mashi noraiz cewa yayi mo zai hana ta ba feenah ta kai mashi, cika feenah tayi ganin da gaske noraiz bazai barta ta zauna lafiya ba shikenan ya samu abun da zai riƙa tsokanan ta. Shazim bayan fatima ta kai masa breakfast ɗin shi yaci shirya wa yayi ya wuce EKO. Su hidaya ya samu zaune a reception, gaishe da shi suka yi amma ba wacce ya amsa mawa acikin su gaba yayi abun shi, victoria ce ta taɓo destiny tana nuna mata hidaya kwashewa su kayi da dariya ashe duk abun da ya faru tsakanin ta da shazim sun sani wani munafukin aka samu ya sanar da su shiyyasa yau suka zauna a reception kawai dan su sa mata ido, abu kaɗan su saki dariya, tun hidayar bata gane da ita su ke ba har ta fahimci cewa ita su ke yima dariya, gajiya tayi da dariyar da su ke yimata tashi tayi ta nufi office ɗin da suke zama,wata dariyar shaƙiyyan ci suka ƙara kwashe wa da ita, abu yayi matuƙar ɓata ran maryam aikuwa ta tashi tana faɗin "Amma dai wallahi wasu anyi dabobi,ku wani tasa mutane kuna yi masu dariya sai kace wasu mahaukata,Allah dai wadaran wanda bai san ciwan kanshi ba " nurses ɗin da ke wurin har haɗa baki su ke wurin faɗin " ke dai bari maryam wasu mutanen dai basu san ciwan kan su ba" tsarguwa su victoria su kayi ganin kowa sai faɗin abun da yazo bakin sa yake yasa victoria miƙewa tan faɗin " kushiga hankalin ku dan naga take taken ku da duk wacce tace zata zage mu sai ta gane bata da wayau" "wai dakata victoria kike ko wa wai ma wakike faɗa ma wannan maganganun " "da uban da ya tsargu nake " "ai fa kaji matsalar bamuguje " maryam ta faɗa haɗi da kwashe da dariya dan ta san victoria bata san mi kalmar bamaguje take nufi ba sauran ma dariyar su ka kwashe da ita, haka su kayi ta jefa ma victoria baƙaƙen magamganu da hausa ganin bata fahimtar mi suke cewa, baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshi nan ta shiga zunduma masu zagi da yaren su, banza sukayi da ita kowa ya kama harkar gaban sa su ka barta ita kaɗai sai ɓaɓatu take kamar wata mahaukaciya, destiny ce tace " haba victoria sun maida ke mahaukaciya amma ki baki gane ba sai wani gazi kike " da yaren su tayi maganar dan kar su maryam su fahimci mi take faɗa mata amma abun da bata sani ba daga yana yin yanda victoria tayi shiru su ka fahimci cewa wani abun ta faɗa mata, jan hannun ta destiny tayi suka bar wurin zuwa office ɗin su da suke zama samun hidaya su kayi tana karatun alqur'ani mai girma,zama su kayi suna sauraron ta wani abu na Allah kamar tace su zauna suyi shiru, haka suka zauna sai satar kallon ta su ke ita bata ma san da zuwan su ba, karatun ta kawai take, wayar ta ce dake cikin jaka ta fara ringing,sai da ta kai aya tukun ta buɗe jakar ta ciro wayar duba mai kiran tayi , dr kabir shi ne mai kiranta, latse wayar tayi ta sata a silent ta cigaba da karatun ta, haka yayi ta kira ba tare da ta sani ba. Zaune yake a office ɗin shi abun duniya duk yabi ya ishe shi sai kiranta yake Amma taƙi ɗauka kuma ya san taga kiran shi ɗauka ne kawai ba zata yi ba,sai dai daya juya yace " wai hidaya kashe ni kike sonyi ne, mi nayi maki ne dan Allah da kika zaɓi ki azabtar da ni " haka yake ta sambatu bawan Allah duk ya zama abun tausayi ƙarshe dai kiran Momy yayi tana picking ya fashe da kuka yace " momy so take sai zuciyata ta buga momy bata sona ban san mi nayi mata ba " "ya Allah Auta ba dai acikin hospital ɗin kake man wannan kukan ba " "momy a nan ne mana gaba ɗaya so take ta zautar da ni ban san mi nayi mata ba" "yanzu dai daina wannan kukan da kake yi kamar wani yaron goye" "to momy na dai na, amma dai yau dady zaije wurin baban ta ko" "eh yau zai je insha Allah ka kwantar da hankalin ka, idan kana saurin karaya bazaka iya shawo kanta ba, ka daina saurin karaya ka sama ranka ƙwarin gwiwa ka nuna mata soyayya na san zata so ka my Auta" "to shikenan momy na dai na " "yawwa, yanzu tana ina tana gida ne ko ta zo hospital ɗin" "momy nima ban sani ba ko ta zo ba " "ai kai kana hospital ɗin ko?" "eh momy " "to kaje ka du bata " "to momy" ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran, ta shi yayi ya fice daga office ɗin ya nufi reception, yana zuwa si maryam su ka shiga gaishe da shi amsa masu yayi sannan yace " maryam ina take ko bata zo ba yau " tun da ya faɗi haka maryam ta gane hidaya hake nufi "tana office, a kira maka ita ne " "a'a bari naje da kaina " ya faɗa haɗi da nufar office ɗin na su, binshi da kallo nurses ɗin su kayi kowa da gulma a bakin shi, maryam duk ya bata tausayi yana matuƙar son hidaya kuma shi ba ruwanshi ko a ina nu na sonta yake ba ruwan shi,jin nurses ɗin na ta ƙusƙus ne yasa maryam cewa " to uwayen surutu za ku fara, abun nema ya samu " "daga faɗin alkairi sai abun ya zama surutu " wata ta faɗa "eh, ai idan kayi maganar mutum ba tare da ya sani ba gulma ce" "to munji ba sai kin yi mana wa'azi ba" "ba ku son gaskiya na lura" maryam ta faɗa. Yana zuwa bakin office ɗin ya jiyo muryar ta tana raira karatun alqur'an, ajiyar zuciga ya sauke yana faɗin "ya Allah ka mallaka man wannan baiwar " ya faɗa haɗi da tura ƙofar da sallama a bakin sa,ɗagowa su victoria su kayi su ka kalle shi, abun ya basu mamaki mi ya kawo dr kabir office ɗin su, gaishe da shi su kayi , hannun ya ɗafa masu ba tare da ya amsa ba, jin suna gaishe da shi ne yasa hidaya ɗa gowa ta kalle shi, da sauri ta duƙar da kai, kallon su victoria yayi yana faɗin " Please excuse us" ta shi su kayi su ka fita, amma sai su ka laɓe bakin ƙofa dan son jin mi zai ce mata matsawa yayi ya samu wata kujera ya zauna kusa da wacce take zaune,binta kawai yake da kallon sai wasa take da ƴan yatsun hannun ta, cikin ƙasa da murya ya fara magana " beb wai mi nayi maki ne, pls idan da abun da nayi maki wanda baki so ki faɗa man kinji zan daina" kanta na a duƙe tace " babu abun da kayi man" "to amma mi yasa kike man wulaƙan ci, ko dai baki sona har yanzu shazim kike so " girgiza kai tayi "magana nake so kiyi man, hidaya ki fahimce ni ina sonki tsakani na da Allah ne, ina son ki fahimce ni pls " har ga Allah bazata ce dr kabir baya birgeta ba, amma son da take ma shazim ne na daban ne wanda take jin bazata iya haƙura da shi ba har ta so wanin sa ba, "ya kabir maganar gaskiya bazan ce baka burge ni ba amma ina so ka fahimce ni ya shazi.... " tsawa ya daka mata yana faɗin "dan Allah dakata man hidaya shazim ne dai ko to ga shazim nan " yana gama faɗar haka ya tashi ya fice daga office ɗin,ya tsani maganar shazim da take yi mashi duk sai taji ba daɗi amma ba zata iya haƙura da shazim ba, ta shi tayi ta bi bayan shi. _*✨KATSINA✨*_ ........ Su Aairah ne ke ta gyaran part ɗin da ke kusa da na Abie saboda zuwan su safwan, tun safe su ka tashi da shirye shiryen tarbar su Abie ma na gidan dadi saboda zuwa da za suyi su ɗauko su a airport shi da su uncle mustafa da Abdallah, mom da matar uncle Ahmad suna kitchen suna shirya masu abinci da ƙarfe huɗu na yamma jirgin su zai sauka. _*NA KUSA KAMMALA SEASON ONE*_ _GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM _ _KHADIJA M ABDULWAHAB ( KAINAAT ) 09132289761_ _WHATSAPP KAWAI BANDA PHONE CALLS_ ✍ _ _Episode 62_63_ .............. Hidaya lokacin da ta bi bayan dr kabir,ko da ta fita bata ganshi ba hakan yasa ta bi shi office ɗin shi, zaune ta same shi kan sofa ya ɗaura hannun shi na dama saman kai, idanuwan shi a lumshe ya rasa mi ke mashi daɗi a duniyar nan, ƙara sawa tayi wurin shi "Dr are u ok " banza yayi da ita duk da ya. gane ita ce, tunaninta bai ji ta ba ne hakan ya sa ta sake kiran sunan shi, "Please hidaya leave me alone " ya faɗa da ɗan ɗaga murya "kayi haƙuri, na san abun da nayi maka ne ya ɓata ranka,dan haka nake haɗa ka da Allah da kayi haƙuri " hannun shi daya ɗaura saman kanshi ya cire duk a tunanin ta ya haƙura ne Amma sai ganin shi tayi ya kama hanyar ficewa daga office ɗin "ba dan halina ba kar ka fita, idan nice baka son gani zan fita amma kai dan Allah karka fita" ya faɗa yayin da take miƙewa ta nufo ƙofar, tsaya wa yayi cak shi bai fita sanna kuma bai dawo ba,zuwa tayi har gaban sa tana faɗin " ina so ka fahimce ni Please, duk abun da ka ga ina faɗa maka ina faɗa maka tsakani na da Allah ne" "naji hidaya, ai na ce maki kije gaki ga shazim ba shikenan ba" " am dr......... " "please ya isa haka bana son jin komai daga bakin ki" " saboda mi" "saboda duk abun da zai fito daga bakin ki ba alkairi ba ne a wurina, dan haka ni kawai ki fita ki barni da abun da ya ishe ni pls" ya ƙarasa maganar haɗi da haɗe hannuwan shi wuri ɗaya,kan sofa ya koma ya zauna " shikenan zan fita na baka wuri" tana faɗa ta buɗe ƙofar office ɗin ta fice, wurin su maryam ta nufa , tun kafin ta ƙara so maryam ke jefan ta da harara "lafiya wai ki ke hararata?" hidaya ta faɗa yayin da take samun wurin zama ku sa da maryam ɗin "kinfi kowa sani" "ni babu wani abu da na sani " "yayi kyau " maryam ta faɗa, fira su ke ɗan taɓawa jefi jefi, suna nan zaune har aka fara kiran sallar zuhur, dr kabir ne ya fito daga office ɗin shi ya shiga na shazim, yana shiga ya same shi yana tattara files ɗin da ke kan table ɗin alamar ya tashi sai kuma wani lokacin. Sallam kabir yayi mashi haɗi da shi gowa ciki, kallon shi shazim yayi yana amsa mashi sallamar "Autan momy lafiya dai?" shazim ya faɗa dan ganin kabir da yayi duk sai a hankali ga idanuwan shi a kumbure kamar na wanda ya sha kuka "lafiya lau, mi ka gani?" "bakomai" shazim ya bashi amsa "mu tafi ko " shazim ɗin ya sake faɗi saboda ya gama haɗa duk wani kayan shi, gaba kabir yayi shi kuma ya bi bayan shi su ka nufi masallaci, da aka gama sallah shazim sallama yayi ma kabir saboda shi zai wuce Abnoor kabir ma cewa yayi shima da anyi sallar asr gida zai tafi hakan ce ta faru ana gama sallah bai daɗe ba shima ya kama hanyar tafiya gida. _*FEENAH*_ ......... zaune take bakin gado a ɗakin su ita da kairiyya, wayarta da ke kan bedside drawer ta ɗauka number innah ta shiga dialing bugu biyu innah ta ɗauka tana faɗin "sai yau kikayi lokacina?" "kai innah daga kiran ki zaki fara da complen" "oho ni kike cema haka ko" "innah ai kece daga kira sai ƙorafi" "to naji , miyasa kika kira ni dan na san ba dan Allah kika kira ni ba" "haba dan Allah innah" "ba wani haba, ƙarya na faɗa tun da nake da ke kin taɓa kirana haka nan kawai da sunan ki gaishe ni tun da kika kama ƙafa kika koma lagos da zama " "naji ni dai innah, kima tsaya ki saurari mi ke damuna amma sai wani faɗa kike man" "to naji, yanzu faɗa man mike damunki da yasa kika kirani " "dama ba komai bane, yaushe su Abbah su ka tsaida ranar Auran mu da ya shazim, dan ni nagaji da wulaƙancin da yake man ga wannan munafukar kairiyya a gefe " "wannan ko ƴar banyar yarinya a nan ɗin ma sa maki ido take ke nan " "Ai wallahi innah sai ma abun da ya cigaba jiya har da wani tsare ni zata yi man wa'azi saboda naje part ɗin ya shazim ya mare ni " "mi?, mari fa kika ce?" "eh kawai dan na taɓa shi, fuskata fa duk ya kumbura man ita hannuna har da targaɗe kuma da Ammy tace ya duba ni ƙinyi yayi, shiyyasa na kira ki kisa su Abbah su tsai da ranar Auran mu nasan dai ya Aure ni ƙarya yake yace zai dake ni " "amma kin bani haushi feenah, bana hanaki taɓa sa ba ke mi yasa baki jin magana ne, yanzu da ya illata ki da ya kenan, shi bai da asara saboda daman ba sonki yake ba" "ai bazan ma ƙara ba, dan wallahi ba ƙaramar azaba na sha ba jiya da ana gyara man hannuna " "to dadai ya fiye maki, dan shi ba ruwan shi dan ya yi maki illa" "to innha yanzu yaushe zaki sa a sa ranar bikin mu " "kar ki damu ki barni da su ni na san mi zanyi " "yawwa innha ta shiyyasa nake sonki " "kar ki ji komai, kawai ki bi abun da na ce maki " "to insha Allah " "sai anjima, na manta in faɗa maki mansoor na nan zai zo nace ya barki ya dawo da su sa'ada amma na san halin shi duk yanda zai yi karki saki ki biyo shi kinji na faɗa maki " "insha Allah innha bazan biyo shi ba" "yawwa, sai anjima " innah ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran faɗawa tayi saman gado tana faɗin "yawwa innha shiyyasa nafi kowa sonki don baki bari na zubar da hawaye " _*a dai juri zuwa rafi feenah wata ran tulu zai fashe*_ _*✨KATSINA✨*_ ...... Abdallah ne ya shigo wrin su mom dake kitchen ita da ummah da baaba larai ya nufa, da sallama a bakin sa ya shiga kitchen ɗin, amsa mashi mom tayi tana faɗin "wai da kai baka bi su abie ɗinka ba?" "eh naje na dawo ɗaukar takardun su Aairah ne , makarantar ta fara ba da addimisson yanzu wani abokin uncle Ahmad ya kira shi yake sanar da shi Ameerah ta samu , shine uncle Ahmad yace na zo na ɗauki na su Aairah na tura ma Abokin na shi wanda ya duba ma Ameerah sai suma ya duba masu suma" "masha Allah kace ƴan biyu na sun kusa tafiya school ƙwanda ta kwanta, kullum na huta da mom wai yaushe ya Abdallah yace za'a fara ba da addimisson kullum maganar su ke nan " Ummah tace " ai gara su da Ameera, yanzu hankalina ya kwanta tunda Allah ya sa ansamu addimisson yanzu hankalina zai kwanta " "ai yaran nan idan ka bari suka ta so ka gaba kaga ta kanka " mom ta faɗa Ummah tace " Allah dai ya shirye su " da Ameen su ka amsa Abdallah ya ce "ni zan wuce" Mom tace "yaushe Abie ɗin naku yace za su iso" "sai ɗan anjima ka ɗan yanzu ma ni su ke jira " "Ok sai kun dawo, su kuma Allah ya kawo su lafiya" "Ameen, sai na dawo" ya faɗa haɗi da ficewa ya bar kitchen ɗin. Su Aairah ne su ka shigo da gudu daga garden Ameera na riƙe da wayar Aairah Aairah na biye da ita tana faɗin " wallahi Ameera ki bani waya ta kafin ranki ya ɓaci " "wallahi ban badawa kin bi duk kin ishi mutane, ban badawa idan kina da ƙarfi ki zo ki karɓa " Ameera ta faɗa tana ma Aairah gwalo, sai zagaye parlor su ke Aaimah na tsaye tana masu dariya tana faɗin "wallahi karki bata " "Aaimah ban san wulaƙanci dan mi zaki ce karta bani " "ai wallahi ko bata ce haka ba bazan baki ba dama kin daina bi na " Ameerah ta faɗa sai haki take, awannan yana yin ne Abdallah ya fito daga part ɗin shi ya gansu, tswa ya daka masu yana faɗin "wai ku wane kalar yara ne kun girma amma kwata kwata baku san ciwan kanku ba, wallahi ko ku natsu ko ranku yayi mumunnan ɓaci sakarkaru kawai " "yaya wayata fa ta amsa Aaimah na ce mata wai karta bani "Aairah ta faɗa tana turo baki "na dai faɗa maku " Abdallah ya faɗa haɗi da ficewa ya bar parlorn , suna ganin ya fita kamar yace su cigaba sai kace ƙananan yara haka su kai ta zagaye parlor duk sun cika gidan da hayaniya. _*✨Airport✨*_ Mutane ne ta ko ina suna kai kawo, kowa da baun da yake, masu jira jirji da masu jiran ƴan uwan su, motar su Abie ce ta shigo cikin Airport ɗin Abdallah ke driving motar da su Abie suke ciki yayin da uncle mustafa ke driving motar shi, parking lot su ka nufa haɗi da yin parking su ka shiga fitowa, Abie da uncle Ahmad ne su ka fara fitowa sai uncle mustafa sai ya Abdallah, cikin Airport ɗin su ka nufa abie da su uncle Ahmad suna ɗan fira sama sama, wani ƙyatattce wuri su ka nufa zama su kayi kan chair's ɗin da ke wurin , su abie kaɗai ne su ka zauna ya Abdallah kuma can gefan su ya samu wuri ya zauna wayar shi ya ciro yayi dialing number fatima,bakin ta ɗauke da sallama tayi picking call ɗin tana faɗin " ni nayi fushi, sai yanzu daga bari na dawo " " da ya dr ki kayi fushi?" ya faɗa cikin sigar tamabaya "ai duk laifin shi ne, ya bar ƙanwar shi tana ta jiran shi" a shagwaɓea tayi maganar "kin san dai idan ba wani abu ya tsare ya dr ba bazai bar ƙanwar shi tana jiran shi ba " "shikenan tun da haka kace " "haka ne fah ba wai nace ba " "kana ina yanzu?" fatima ta tambaya "ina airport" "ya dr ba dai wani wuri zaka je ba?" "zanyi tafiya ne, kina so na zo maki da wani abu ne" nan take yana yin muryarta ya canza, rai a ɓace tace "bana so, sai ka dawo" ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, murmushi ne ya suɓuce mashi yana faɗin " fatima manya " tashi yayi daga inda yake zaune ganin su Abie sun ta shi, bin bayan su yayi. Wani kyakyawan matashin saurayi ne ke saukowa daga mata ƙalar benen jirgin da ya sauka, fari tas da shi hannun shi ɗauke da madai daicin trolly sanye yake da baƙin cargo trouser sai t_shirt wacce ita ma ta kasan ce baƙa da p_cap red color da ɓakin glass, ba ƙaramin fito da kyawun shi da na fatarshi kayan su kayi ba,saukowa yake cikin natsuwa yayin da wani dattijon mutum ke bayan sa jikin sa sanye da kayan mu na hausawa riga da wando na yadi mai taushi,shima fari tas kyakyawan gaske zai su yi sa'annin juna shi da Abie duk da yawan shekarun shi haka bai hana kyauwun shi fitowa ba, tafiya su ke shi da matashin har su ka iso inda mutane ke tsai tsaye, Abie ne ya ƙara so da sauri wurin su fuskar shi ɗauke da tsantsar farin ciki,su uncle mustafa na bayan shi, yaan ƙarasowa yayi hugging ɗin wannan dattijon yana faɗin " masha Allah, barkan ka da zuwa ƙasar ka, barka da dawowa " murmushi shima dattijon yayi yana faɗin "nagode" raba jikinsu su kayi su uncle Ahmad ma matsowa su kayi kusa da shi hannu su ka miƙa mashi su kayi musabaha, suna mashi barka da zuwa, ya Abdallah matsawa yayi wurin wannan matashin yana faɗin " safwan manyan ƙasa yau dai gaka a nigeria, ina tsoron naka ya tafi " murmushi safwan yayi haɗi da cire glass ɗin dake idon shi yace "Abdallah ka raina ni, wani ya ce maka ina tsoro ne " "sosai ma kuwa tsoro kake, in ba tsoro ba mi yahana ka zuwa tun tuni sai yanzu" "saboda kai ma baka zuwa " "ba wani nan tsoro ne ya hanaka zuwa " "haka ka ce " "eh haka na ce " "zamu gani ai ni da kai wake tsoron" safwan ɗin ya faɗa haɗi da matsawa wurin Abie ya shiga gaishe da su. Ɗunguma su kayi zuwa parking lot in da su kayi parking ɗin motocin su, safwan shi da Abdallah su ka shiga motar shi yayin da Abie da uncle Ahmad su ka shiga motar uncle mustafa, barin airport ɗin su kayi ba su nufi ko ina ba sai gidan Dadi. Horn su kayi a bakin gate ɗin gidan dadi, mai gadi ne ya buɗe masu ciki su ka shiga,parking lot su ka nufa haɗin da yin parking, fitowa su ka shiga yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun gama fitowa ciki su ka nufa, abie gaba ɗaya a cikin farin ciki yake da zuwan wannan bawan Allah, da sallama a bakunan su suka shiga ciki, parlorn tsit yake kamar ba kowa, Aunty Rabi ce zaune kan sofa tana karatun al'qur'ani mai girma,sai da ta kai aya sannan ta tsaya haɗi da amsa masu sallamar da su kayi, ciki su ka ƙara sa haɗi da samun wurin zama kan sofa's su ka zauna, gaishe da wannan dattijon ta yi tare da yi mashi barka da zuwa ,cikin kulawa ya amsa mata, da fara'a a fuskar safwan ya gaishe da ita, amsa mashi tayi tana faɗin " safwan yau dai gaka ga nigeria, ya gajiyar hanya " "lafiya lau Alhmdllhl" safwan ya faɗa "masha Allah , ya ka baro momyn ka " "tana lafiya ta ma ce a gaishe da ku " "muna amsawa " abie ne yace " ina mama, ko tana ɗaki?" " eh yanzu ta shiga bari naje nayi mata magana" ta faɗa haɗi da tashi ta nufi ɗakin dadi,wannan dattijon ne ya kalli abie yace " sai dai ban gane nan ina ne ba?" "nan gidan mama mahaifiyar mu" "oho Allah sarki " mutumin ya faɗa Aunty Rabi ce ta fito ita da dadi,ƙara sowa wurin su su kayi wuri dadi ta samu kan sofa ta zauna tana kallon wannan mutumin, ta sowa yayi ya dawo kusa da ita yana faɗin " mama ina wuni " wani iri dadi taji jin ya kirata da mama, duk sai ya bata tausayi, shikenan waɗannan mutanen sun cuce shi yanzu baya iya tuna komai da ya shafi rayuwar shi ya manta ko shi wanene ya manta iyalan shi da ƴan uwan shi. Kallon Abie yayi yace "naji tayi shiru ko ba ita bace mamar ba?" "ita ce bata ji ka bane" abie ya faɗa "lafiya lau nake, ya hanya" dadi ta faɗa fuskar ta da ɗan murmushi wanda da ka ganshi kasan na dole ne "Alhmdllh " mutumin ya faɗa, fira suka shiga taɓawa shi da dadi kamar ɗan da ta haifa da cikinta, tun bata saki jiki da shi ba har ta saki jiki su ka sha fira duk da firar ba wata bace tambayoyi ma da yake mata duk sunfi yawa. Aunty Rabi ce ta kawo masu ruwa da lomu, sun jima a gidan sannan abie yace su tafi can gida amma sai wannan bawan Allah yace bazai je ba shi yana nan tare da mama, abie ne yace mashi ai idan sun je zasu dawo dadi ma tace zuwa za kuyi ku dawo to sannan fa ya bisu suka tafi. Lokacin da suka isa gida su Aairah na nan zaune a main parlor suna kallo, jin sallamar abie ne ya sa su tashi da sauri suka nufe su, suna faɗin "oyoyo ga abie" haɗi da gaishe da su uncle Ahmad, ciki su Abie su ka shigo abie na faɗin "ina su mom ɗin ku sai ku ka ɗai a parlor " "yanzu su ka shiga ciki" Aaimah ta faɗa Abie yace " ba kuga uncle sadiq ba " ya faɗa yana nuna wannan mutumin, da sauri su ka nufe shi suna faɗin " uncle sannu da zuwa, ya gajiyar hanya " "Alhmdllh, ya kuke " "lafiya lau mu ke" "masha Allah " ya faɗa Wuri su ka samu kan sofa su ka zauna yana tambayar su Aairah ya sunan su, ɗaya bayan ɗaya suka shiga faɗa mashi sunayen su yan jinjina kai. Ameera ce ta tashi ta tafi kiran su mom , ba ta daɗe da tafiya ba sai gata tare da su mom , ƙara sowa su kayi ciki, nan suka shiga gaishe gaishe, abie na nuna ma uncle su da sunayen su, sun jima anata fira har sai da aka fara kiraye kiyaren sallar magrib sannan su ka tashi su ka nufi masallaci, su mom ma da su Aairah ɗakunan su auka nufa domin gabatar da tasu sallar, bayan sun kammala ne mom tace su je su jera dinner kan dinning,tafiya su kayi su ka jera komai da ya kamata sannan suka koma kan sofa suna cigaba da kallon da suke yi ɗazu, su abie ba su dawo gidan ba sai bayan da su kayi sallar isha tukun su ka dawo, suna shigowa dining su ka nufa,su Aairah mom tace suje suyi serving ɗin su, su kuma su kawo masu na su abicin nan kan carpet saboda dining ɗin da yayi masu ka ɗan. bayan sun kammal serving ɗin su kamar yan da mom tace kan carpet su ka kawo masu na su abicin su ka ci. Bayan sun kammala dinner a nan mai parlor su ka zauna suna ɗan taɓa fira amma banda su Aairah da suka gama dinner bedroom ɗin su suka nufa, Abdallah ma da safwan part ɗin Abdallahn su ka nufa su ka bar su Abie ka ɗai a parlor suna fira. Sai wurin ten uncle mustafa ya tafi gida uncle Ahmad kuma ya tafi part ɗin da su ka sauka shi da ummah, abie kuma shi da uncle sadiq su ka tafi part ɗin shi. _har ya manta da yace a mai da shi gidan dadi to kwakwalawa ce ta koma ta ƙananun yara_ bayan sun shiga part ɗin abi, wani bedroom abie ya kaisa wanda ke kusa da nashi, da suka shiga ciki pajamas abie ya ɗauko mashi sannan ya nuna mashi wani corridor da wardrobe ce ciki yace ya shiga ya canza kayan jikin shi , bayan ya canza abie yace ya shiga toilet yayo alwala, da to ya amsa mashi haɗi da nufar toilet ɗin ɗakin bayan 1 minute ya fito jikin shi da danshin ruwa. Nuna mashi bed abie yayi yace ya zo ya kwanta, matsowa yayi ya hau gadon zaman abie yayi shima kusa da shi sannan yace" zan riƙa karanto maka adu'ar kwanciya bacci sai ka maimaita " to ya faɗa nan abie ya shiga karanto mashi shi kuma yana maimaitawa har abie ya gama karanta mashi, sannan yace ya kwanta, kwanciya yayi abie yaja mashi blanket sannan yayi mashi sai da safe haɗi da nufar ƙofa ya kashe mashi light ɗin ɗakin tare da jawo mashi ƙofa, cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba da shi........ _*Allah sarki babban mutum da shi amma bai san komai ba a rayuwa ya dawo kamar ƙaramin yaro komi yanzu sai an koya mashi, wannan zalunci har ina, mutane wallahi muji tsoron haɗuwar mu da ubangiji mu *_ _*NA KUSA KAMMALA SEASON ONE*_ _GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM_ _KHADIJA M ABDULWAHAB ( KAINAAT ) 09132289761_ _WHATSAPP KAWAI BANDA PHONE CALLS_ _Episode 64_65_ ............... Abie ɗakin shi ya koma, shima alwala yayi sannan ya zo ya gabatar da safa'i da wutiri sannan ya kashe light ɗin ɗakin ya kwanta, duniyar tunani ya shiga, yanzu baya da wani buri face yaga Allah ya toni asirin mutanen nan, ya jima a kwance yana saƙawa da kwan cewa ba tare da bacci ya ɗauke shi ba, sai da dare ya raba sosai sannan bacci ya fara kama idon shi,ta shi yayi yaje ɗakin da uncle sadiq yake a bakin ƙofa ya tsaya leƙashi yayi, hango shi yayi ta hanyar hasken bedside lamp dake kunne yana ta sharar baccin shi hankalin shi kwance, mai da mashi ƙofar abie yayi ya rufe, bedroom ɗin shi ya koma kwanciya yayi dan da nan bacci yayi awan gaba da shi..... _*WASHE GARI*_ Masallatai na fara ƙwala kiran sallar asuba abie ya farka,toilet ya nufa ya ɗauro alwala sannan ya dawo ya canza kayan dake jikin shi zuwa jallabiya, fita yayi ya nufi ɗakin da uncle sadiq yake ciki, lokacin da ya tura ƙofar hango shi yayi a zaune a bakin gado da alama ma har alawala yayi saboda danshin ruwa dake jikin shi, da sallama Abie ya shiga , ɗagowa uncle sadiq yayi yana kallon abie, yace" yawwa harka tashi kenan" "eh" uncle sadiq ya bashi amsa "ta so to mu tafi masallaci " abie ya faɗa haɗi da kama hanyar fita, bin bayan shi uncle sadiq yayi, a main parlor su ka samu uncle Ahmad da su Abdallah, su na sakkowa ficewa su kayi zuwa masallaci,lokacin da su ka dawo abie da uncle sadiq a parlorn abie suka zauna abie na koya mashi karatun al'qur'ani mai girma, sun jima abie na koya mashi, har sai da gari ya waye sosai tukkun su ka ajiye karatun, uncle Ahmad ne ya shigo parlorn da sallama a bakin shi, amsa mashi sallamar su kayi, wuri ya samu kusa da abie ya zauna yana faɗin " ina kwana yaya, fatan an tashi lafiya " amsa mashi abie yayi da "Lafiya lau alhmdllh" sannan uncle Ahmad ya kallin uncle sadiq yana faɗin " ina kwana, an tashi lafiya" "lafiya lau Alhmdllh " ya amsa shi ma kamar yanda yaji abie ya amsa, fira su ka ɗan shiga taɓawa,nocking ɗin ƙofar parlorn akayi abie ne ya ba da izinin shigowa, turo ƙofar su Aairah su kayi su ka shigo bakunan su ɗauke da sallama hannun su ɗauke da manya tray da mom ta shirya ma su abie breakfast ɗin su, amsa ma su sallamar su abie su kayi, table ɗin da ke tsakiyar parlorn su ka nufa, trays ɗin su ka sauke su ka ɗaura kan table ɗin haɗi da gaishe da su,cikin sakin fuska su ka amasa ma su musamman uncle sadiq,tsayawa su kayi sai da su kayi serving ɗin su tukun su ka nufi hanyar fita, parlorn su ka nufa wurin su mom da ke zaune kan dinning suna breakfast, dinning ɗin su ka nufa har sun ja kujeru za su zauna mom tace " yayan ku fa, kun kai mashi abinci ne " "mom bari mu kayi sai mungama, ba su isa tashi ba yanzu " Aairah ta faɗa Carab Ameera ta ce " ba su tashi ba fa mom" daƙƙuwa ummah tayi ma Ameerah, mom na faɗin " kunfi kowa sanin halin Abdallah kar Allah ya sa ku kai masa zai fito ne ya same ku " "mom Allah ba isa tashi ba yanzu" "ku dai kuka sani amma ni ba ruwana ya fito ya same ku ba ku kai ma shi abinci ba" Ameera cewa tayi " ni dai Aairah ta so muje mu kai masa wallahi ina tsoron abun da zai biyo baya " "sai kin dawo, gaskiya ni yunwa nake ji" "ok haka kika ce ko " "eh" Aairah ta faɗa yayin da ta ke kai bread a bakin ta hanyar kitchen Ameerah ta nufa tana faɗin "wallahi idan baki zo mun tafi ba saina cema ya Abdallah ke akace kikawo masu ki kace baki zowa " ɗan ɗaga murya Aairah tayi tana faɗin "idan kin fasa uwar yan jan sharri " daga kitchen Ameerah tace "wallahi zaki san ni kike cema uwar ƴan jan sharri " "eh ɗin in sani, ai na san dalilin da yasa kike son jaman sharri kuma ko mi zakiyi bazan ba da ba ehe " ɗaga murya Ameerah tayi yan da Aairah zata jita sosai tace " wannan kuma ke kika sani kar Allah yasa ki ba da ƴar rainin hankali " gwalo Aairah tayi mata sai kace tana gaban ta tace "oho dai, ban ba dawa " Ameerah na jin ta amma tayi bazan da ita, Aaimah dai na jin su bata ce ƙala ba sai zuba ma cikin ta abinci kawai take, Ameerah ce ta fito hannun ta ɗauke da trayn da ta shirya masu breakfast, zata wuce kenan Aaimah ta dakatar da ita tana faɗin " kawo na ɗaukar maki naga kamar kayan sun yi maki yawa, ke kuma wallahi Aairah sai kin gane baki da wayau " " dan Allah ku rabu da ni zuwa dai ne nace bazanyi ba koma mi zaki faɗa kin daɗe" "ai dai haka kika ce " Aaimah ta faɗa, amsa Aairah ta bata da " sosai ma kuwa, duk abun da zaku faɗa mashi kun daɗe " ta ƙarasa maganar tana murguɗa ma Aaimah baki "haba yarinya kamar a gabansa kika yi haka" "dan Allah ya isa haka, ke Aairah tashi ku tafi ko gaisawa ai kunyi da safwan" "mom zanje idan na gama " Aairah ta faɗa, kallon su Aaimah mom tayi tana faɗin " to ke wuce ku tafi ba dole sai kunyi zuga ba ke da Ameerah ma ai ya isa " "mom ai ta je ta gaishe da ya safwan ko " "zataje ai tace idan ta gama, maza ku wuce ku" da to su ka amsa haɗi da nufar part ɗin, suna tafe suna surutun da suka saba amma fa acewar Abdallah, suna isowa bakin part ɗin Ameerah ce tayi nocking har ta ɗaga hannu zata sake wani nocking sai gashi an buɗe ƙofar, safwan ne tsaye jikin shi sanye da ɓakar jallabiya, da fara'a a fuskar Ameerah tace " ya safwan ina kwana, fatan an tashi lafiya " fuskar shi shima da fara'a yace " lafiya lau, ina su ummah " "suna main parlor suna breakfast, ga naku nan kai ma mun kawo maku kai da ya Abdallah " murmushi yayi a zuciyar shi yace " Ameerah ba dai surutu ba, Aaimah ce tayi gyaran murya tana faɗin " to ni dai a bani wuri na wuce dan na gaji da tsuyuwa" girgiza kai safwan yayi da murmushi a fuskar shi yace " Aairah uwayen ƙorafi, zo ki wuce kar ki faɗin ƙasa " ya faɗa haɗi da matsa mata hanya, ciki ta shige tana faɗin " wai dan Allah mi yasa ya safwan kake ce man Aairah ne, ba fa ita bace wannan Aaimah ce " ta faɗa yayin da take ajiye tray ɗin kan carpet, Ameerah ma bayan ta ta bi ita ma ta ajiye wanda yake hannun ta "to naji ina ita Aairah take na ganku ku ka ɗai, ita bata zuwa a gaisa ba" "tana parlor wurin su mom " Aaimah ta faɗa yayin da take nufar ƙofa "to ki kira man ita " da to Aaimah ta amsa haɗi da nufar ƙofar fita su ka fice, tana zuwa wurin su mom tace " Aairah kije ya safwan yana kira " ɗagowa Aairah tayi tana faɗin ni kuma "A'a ba ke ba ni " Aaimah ta faɗa yayin da take jan kujera ta zauna "dallah daga tambaya zaki wani mai da man da baƙar magana " "an mai da maki, dallah malam idan zaki tashi kije ki tashi idan kuma bazaki tashi ba kiyi ta zama ƴar rainin wayau wai ni A'a ni " Aaimah ta faɗa tana kwai kwayon yanda Aairah tayi magana, Aairah tace " mom kina jinta ko daga maganar ariziƙi sai ta tsiya " dafe kai mom tayi tana faɗin " ya Allah, ke Aaimah kar na sake jin bakin ki ke kuma Aairah tashi kije kira da yake maki " tashi Aairah tayi tana hararar Aaimah, taɓe baki Aaimah tayi tana faɗin " inga sun zazzago ƙasa sannan zan san kina harara"tsaki Aairah taja haɗi da wuce wa ta nufi part ɗin Abdallah, girgiza kai ka wai mom tayi ba tare da tace ma su komai ba. Nocking tayi, izinin shiga aka bata, tura ƙofar tayi ta shiga, zaune yake kan sofa kamar yanda su Aaimah su ka barshi hannun shi ruƙe da cup ɗin tea sai turiri yake,yayin da Abdallah ke zaune kan carpet yana haɗa breakfast fitowar shi kenan daga bedroom ya samu an kawo masu breakfast, safwan ɗago da fuskar shi yayi ya zuba mata ido haɗi da amsa mata sallamar da tayi, gaishe da su tayi tana faɗin " ya safwan gani Aaimah tace wai kana kira na " amasa mata gaisuwar yayi yana faɗin " dama ba wani abu bane kawai naga baki zo bane shine na ce su kira man ke mu gaisa tunda ke baki zo ba " " zan zo ya safwan breakfast nake ne shiyyasa " " ok yayi kyau, kin tashi lafiya " " lafiya lau " " masha Allah " " ina iya tafiya " ta faɗa dan duk ta gaji da tsayuwa da kuma kallon da yake mata " eh kina iya tafiya dama kiran kenan " "to sai anjima " ta faɗa haɗi da ju yawa zata wuce Abdallah ne yace " ki dawo anjima ki kwashe wannan kayan " ya faɗa yana nuna mata kayan breakfast ɗin da ke gaban sa, da to ta amsa haɗi da kama hanyar ficewa, idanu safwan zuba mata har sai da ta ɓace ma ganin sa tukun ya janye idon sa, karb su ka haɗa ido da Abdallah, hararar shi yayi yana faɗin " lafiya da wannan kallon malam " taɓe baki Abdallah yayi yana faɗin " aiki ya zo ga ma iya " " ƴan sa ido ba " safwan ya faɗa " mi zan sa ma ido a nan, Allah ya kiyaye " Abdallah ya faɗa yana mai da kanshi kan breakfast ɗin da yake yi "Ohon maka kuma wannan " safwan ya faɗa shima yana kai cup ɗin tea dake hannun shi baki, babu wanda ya sake cewa komai cikin su. _*✨LAGOS✨*_ Zaune yake a office ɗin shi yana aiki, files ne gaban shi na patient yana duba wa, wayar shi ce ta fara ringing, hannu ya sa ya ɗauko ta, du ba mai kiran shi yayi, privet number shine abun da ya gani, tsaki ya ja haɗi da yin rejecting kiran ya cigaba da abun da ke gaban shi, wani kiran ne ya sake shigowa, ko kallon inda wayar take bai yi ba haka taita ruri har ta gaji tayi shiru alamar mai kiran ya gaji sai ga message ya shigo, ɗaukar wayar yayi dan ganin wanene ya turo mashi message, baƙuwar number ce ya gani kuma da alama bata nigeria ba ce, buɗe message ɗin yayi ya fara karan tawa kamar haka _DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN,manya yan aji bakwai ba'a ɗaukar baƙuwar number ganinka kuma sai an cika form,wow i like your style keep it up na san nan gaba zai yi maka amfani, ba komai bane ya sa nake neman ka ba face ina so na sanar da kai illar dake cikin yaƙin da kake son jefa kanka aciki,manyanka ma sunyi ba suci riba bare kai ƙaramin alhaki ko da yake hausawa na cewa barewa baza tai gudu ɗan ta yayi rarrafe ba malam Abdulƙadir o afuwan dr Abdulƙadir kar kace na mai da kai malamin makaranta 😊, ya ta kwaranka kuma kakan ka mun kwana biyu ba mu gaisa ba amma da alama yanzu na lura kana so mu dawo da zumunci dake tsakanin mu , fatan yana lafiya shi da hajiya zainab ina nufin ummy????, Abdulƙadir ina mai baka shawara idan har kana son zamanka lafiya a duniyar nan to ka tsame hannuka daga abun da kake shirin aikatawa gudun aikata abun da zai jefa ka cikin matsala kai da iyalanka, fatan zaka ɗauki shawarata duk da na san kai mai taurin kai ne amma ina mai baka shawara._ Wani wawan tsaki shazim ya ja lokacin da ya kawo ƙarshen message ɗin yana faɗin " aikin banza matsora cin banza da wofi kawai, mu zuba mu gani ni da kai da duk wani mai hali irinka shege ka fasa " ya faɗa yana maida kanshi yayi kan abun da yake, wani tsakin ya sake ja yana sake faɗin " aikin banza matsoracin banza da wofi kawai " Ƙofar office ɗin yaji an turo an shigo, majeed ne ya shigo a uzirce kamar wanda aka jeho, wurin shazim ɗin ya matsa yana faɗin " amshi shazim ka gani " ya faɗa yana miƙa ma shazim wayar shi, amsar wayar shazim yayi yana duba abun da majeed ɗin ke nuna mashi, text message ne shima aka turo mashi da irin number da aka turo ma shazim yanzu, karanta message ɗin shazim ya shiga yi _ABDULMAJEED MA'ARUF WAKILI,na san za kayi mamakin wanene ni da kuma sunan ka da na ambata, kar kayi mamaki yanyi ne yasa haka. a taƙaice dai abun da ke tafe da ni, ba wani abu bane face ina so na ja maka kunne kai da abokinka, ku rufa ma kanku asiri ku fitar da kanku acikin yaƙin da iyayen ku su ka kasa,idan kuma ba haka ba zaku sa kan ku cikin bala'in da ba kuyi tsammani ba ku da iyalanku, shawara ce idan kun ɗauka ku zata yima amfani idan kuma kun ƙi to duk abun da ya biyo baya kuyi kuka da kanku._ Tsaki shazim yaja yana miƙa ma majeed wayar shi, amsa majeed yayi yana faɗin " ni dai shazim a ganina mu fitar da kan mu a wannan matsalar ko dan su Ammy " " tsoro kaji ne wai majeed?" " dole naji tsoro shazim, barazana fa yake mana, ni abun da nake ganin zai fi shi ne kawai kayan nan mu miƙa ma hukuma su " " to dan yana mana barazana sai mi, ya isa yayi mana abun da Allah bai nufa ba ne, sannan kaya da kake cewa mu miƙa ma hukuma su tamkar munji tsoron ne kuma Allah zai kama mu da laifi duk wanda ya cutu a kan kayan " " bai isa ba shazim,kuma Allah bazai kama mu da lafin wani ba tunda hukuma muka ba kayan kuma muna kyautata zaton tayi adalci ne" "majeed ina so ka fahimci wani abu a lamarin ƙasar nan cin hanci yayi yawa muna ba da kayan nan zai ba da cin hanci ne a bashi batare da tausayin bayain Allah ba da aka ɓata ma rayuwa ba, yau da ace ƴaƴansu zasu ba da bazan da mu amma inaji ina gani bazan bari a cuci al'ummah ba " "haka ne shazim, amma duk da haka mu miƙama hukuma ko dan su Ammy dan gaskiya ina jin tsoron abun da zai biyo baya idan muka cigaba da riƙe waɗannan kayan " " to idan kana jin tsoro ka kira shi kace kai ba ruwanka, Amma ni ba gudu ba ja da baya " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya nufi wata ƙofa dake kallon in da yake zaune, tashi majeed yayi yana faɗin " miyasa zaka ce haka shazim, ko da naji tsoro ai bazan iya tsame hannu na ba na barka " Shigewa ciki yayi ba tare da yace mashi komai ba, bin bayan shi majeed ɗin yayi, tura ƙofar ɗakin yayi ya shiga, ma daidai ci ɗaki ne mai kayan gaske harda ɗan madaidaici family bed a cikin sa da sofa masu kyau guda, tsaye ya hango shazim bakin wani ɗan ƙaramin fridge ya na ɗauko robar ruwa, sofa dake ɗakin ya nufa haɗi da samun wuri ya zauna, shima zama majeed yayi yana faɗin " Please shazim ina so ka fahimce ni ne, bana so mujefa wani daga cikin ahalin mu acikin matsala ne shiyyasa na ce haka" ajiye robar ruwan shazim yayi yana faɗin " majeed akwai wani ɗan adam daya isa yayi ma bawa abun da Allah bai ƙaddara ba " "A'a shazim " "to inaso ka fitar da wannan tsoron a ranka ka fuskanci gaskiya, duk wani barazana da zai yi mana yana yi ne dan muji tsoro " "to shikenan, yanzu ya zamuyi " "karka damu zanyi shawara komai na yanke zan sanar da kai " "to shikenan bari na koma office na barshi ba kowa " "to shikenan, ka ja man ƙofar idan ka fita" shazim ya faɗa, tashi majeed yayi ta fita haɗi da rufe mashi ƙofar kamar yan da yace. Zamewa yayi ya kwanta kan sofar, idanuwan shi ya rufe kamar mai bacci. Duk yinin ranar a wannan ɗakin yayi shi ko sallah a nan yayi ta, sai da yamma bayan sallar asr ya tashi ya koma cikin office ɗin kayan da ke kan table ɗinshi ya tattara ya zuba cikin locker sannan ya ɗauki briefcase ɗin shi da wayar shi ya fice zuwa parking lot in da ya ajiye motar shi, briefcase ɗin ya fara ajiye wa sannan ya zagaya ma zaunin driver ya zauna, key yayi motar haɗi da reverse ya nufi gate, da katar da shi mai gadi yayi ta hanyar ɗaga mashi hannu, parking yayi a bakin gate ɗin yana ce ma maigadin " lafiya dai ko?" "lafiya lau ranka ya daɗe, dama wasu mutanen suka zo neman ka ɗazu" "Suna ina?" "ban barsu sun shigo ba yallaɓai sun tafi " "saboda mi mudi, nan fa asibiti ce dan mi zaka hana su shigowa idan suna tare da patient ne fa " "yallaɓai abun da yasa na hana su shigowa shine basuyi kama da marasa lafiya ba yallabai wallahi da ƴan dambe su kayi kama duk sun wani sha baƙaƙen kaya kamar sheɗanu " "mi suka ce maka da suka zo?" "wai maigindan su ne ya aiko su wurinka,daga ganin ba su da gaskiya shiyyasa ni da su isya muka hana su shigowa " "koma dai minene, daga yau idan su ka sake zuwa ka kirani ka faɗa man kaji ko " "eh naji ranka ya daɗe, insha Allah su ka sake zuwa zan kiraka na sanar da kai " "to shikenan, buɗe man gate na wuce" "to yallaɓai " mudi ya faɗa haɗi da nufar gate ya buɗe mashi, ficewa yayi ya daga Asibitin ya hau kan titin da zai sada shi da gida. Wayar shi dake ciki briefcase ɗin shi ce ta fara ringing, banza yayi da wayar dan ya san bazai wuce wannan shashashan mutumin ba ne, wani kiran ne ya sake shigowa, tsaki yaja yana faɗin "sai kuma kayi ta yi" Kira ne yai ta shigowa ba ƙaƙautawa amma ko kallon briefcase ɗin bai yi ba bare ya ɗauki wayar har ya iso gida, horn yayi a bakin gate mai gadi ya buɗe mashi, ciki ya shiga yayi parking a parking lot ya jima a motar bai fito ba wayar shi ya ciro cikin briefcase ɗin dan ganin wane mahaluƙin ne yayi tayi mashi wannan kiran duk da yana da ya ƙinin waɗannan mutanen ne sai dai kuma da ya duba mai kiran nashi number mansoor ya gani da ta Ammy sai noraiz da fatima, faɗuwa gaban shi yayi yana faɗin "Ya Allah, mike damun su Ammy su ke man wannan kiran" a hanzar ce ya buɗe motar ya fita ko briefcase ɗin shi bai ɗauka ba ya fice zuwa cikin gida yana shigowa main parlor tsaitsaye ya samu su Ammy har da mansoor wanda zuwan shi kenan, sallama yayi ya nufi Ammy yana faɗin "Ammy lafiya mike faruwa ne ??" "Feenah ce ta fita tun ɗazu da safe tace man zata je gidan su ummy to shine tun ɗazu bata dawo ba da muka yi waya da ummy nake ce mata feenah wai yaushe zata dawo naga yamma tayi ko nan zata kwana shine take ceman wai wace feenah ita duk yau bata ganta ba, na kira wayarta ni da su fatima yafi a ƙirga amma a kashe kuma ka san bata da lafiya " A jiyar zuciya shazim ya sauke yana faɗin " wallahi Ammy ba kuji yan da kuka tayar man da hankali ba, yanzu duk dan wannan yarinyar ta fita ne kukai ta man wannan kiran kuma kuka tashi hankalin ku" "shazim ba asan inda taje ba fa nace maka kuma an kira wayarta a kashe amma kake faɗin haka " "Ammy ina wannan yarinyar zataje da har zata ɓata, kawai dai taje yawan banzan ta da ta saba amma kina nan zata dawo da ƙafar data fita " ran mansoor ne ya ɓaci jin abun da shazim ke faɗi ya rasa miyasa shazim bai ƙaunar feenah , amma sai yayi shiru baice komai ba "haba shazim ya za kace haka, feenah fa yarinya ce ina zata je a garinnan da bata sani ba dama a abuja ne sai nace taje gidan su mahaifiyar ta ko gidan ƙawayen ta " "Ammy ki kwantar da hankalin ki in dai akan wannan yarinyar ne ba in da zata shige a garin nan ta ɓata, tana yawan da ta saba ne amma ba ɓata tayi ba " " wai shazim minene tsakanin ka da feenah duk kabi ka tsani yarinya kawai dan ta nace tana sonka shine zaka riƙa jifar ta da waɗannan kalaman " a slowly shazim ya juya yana kallon mansoor dake tsaye bayan shi fuskar shi a murtuke tsan tsar ɓacin rai ne a idanuwan shi, side smile shazim ya saki yana faɗin " kai kuma saukar yaushe?" " ban sani ba " mansoor ya faɗa " to fa daga tambaya " "ka riƙe tambayar ka bana so " murmushi shazim yayi wanda har ya bayyana kyawawan haƙuran shi "wai wannan fushin duk na minene ƙarya na faɗa bata yawan ne " shazim ya faɗa yana ɗaga mashi gira "kanka ake ji kuma " mansoor ya faɗa "dan Allah ya isa haka, ya muna cikin wani hali ku kuma daga haɗuwar ku zaku kama yi ma mutane jaraba " Ammy ta faɗa mai da kallon shi yayi ga Ammy yana faɗin " kar kia damu fa Ammy zata dawo ne dan kanta " yana gama faɗar haka ya nufi sama zuwa part ɗin shi da kallo kawai su ka bishi, sun rasa wace irin tsana ce shazim ke yima feenah da har bai damu da ɓatan ta ba kuma ya san bata da lafiya. Zaune su kai a parlor ko wa yayi shiru suna jiran tsammani har akayi sallar magrib ba feenah ba labarin ta, wasa wasa dai har tara na dare feenah bata dawo ba kuma duk in da suke zargin za su ganta sun je amma ba labarin ta, fidda rai su kayi da zata dawo, mansoor ne yace su tashi kowa yaje kwanta idan bata dawo ba gobe za su je police su shigar da ƙara kawai, kowa ya aminta da maganar mansoor haka ne yasa su ka tashi kowa ya nufi ɗakin baccin shi. Ammya na shiga ɗaki wayarta na fara ringing, abun yayi matuƙar bata mamaki ganin number feenah bayan yanzu ta gama kira a kashe, picking call ɗin tayi da ko sallamar da feenah keyi bata amasa ba tace " feenah ina kika shige duk kin bi kin tayar mana da hankali " daga cikin wayar fashewa da kuka feenah tayi tana faɗin " Ammy ni bana son na koma abuja " " haba feenah idan baki son komawa sai ki faɗa man amma ba wai ki bar gida, yanzu kina ina?" "ina gidan su wata class mate ɗina , dan Allah karki bari ya mansoor ya tafi da ni " " shikenan bazan bari ya tafi da ke ba amma kar ki ƙara irin wannan shashancin kinji na faɗa maki" " to Ammy bazan sake ba insha Allah " " to shikenan, gobe ki dawo da safe " " to Ammy " " yawwa sai da safe " ammy ta faɗa haɗi da yin rejecting kiran, fita tayi zuwa part ɗin shazim,nocking tayi mansoor ne ya zo ya buɗe mata, a bakin ƙofa ta tsaya, mansoor yace" ki shigo mana Ammy " " A'a ba sai na shigo ba, feenah ce ta kirani yanzu " da sauri mansoor yace " ta na ina Ammy?" "tana gidan wata ƙawar ta" Shazim dake zaune kan sofa taɓe baki yayi a zuciyar shi yana faɗin " ni ai na sani " " amma feenah bata da hankali shine bazata faɗi ba zata tayar ma mutane da hankali dan sakarci" " kai dai ka bari kawai mansoor, wai abuja ne bata son komawa shine tayi tafiyar ta " " lallai ma yarinyar nan, zata dawo ai ta samu mutane " a zuciyar shi kuma yace " na san ba kowa zai sata ba sai Innah " " abun da nake mansoor idan zaka tafi ita ka barta nan ɗin tun da tana son zama" "Amma Ammy gata ga sa'ada abun zai yi yawa. " "haba mansoor wane irin yawa ana zaman lafiya, idan ita ma Kairiyya bazata bika ba ka ƙyaleta lokacin da su ke san komawa sai su koma " _ita sa'ada a nan zatayi school tare da fatima shazim ya nema ma su addimisson_ " shikenan Ammy" mansoor ya faɗa " yawwa, sai da safen ku " Ammy ta faɗa haɗi da ja masu ƙofar, sai da safe su yayi mata, bedroom ɗin shazim ya nufa dan shi har ya shige. _SAURA PEG ƊAYA YA RAGE A SEASON ONE_ _ZAN ƊAN JE HUTU KAFIN NA FARA SEASON TOW_ _GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM 300 NE BA YAWA_ _3169482544 MUKHTAR HADIZA FIRST BANK_ _SAI A TURA SHAIDAR BIYA TANA WANNA NUMBER 09132289761 KO 08133650574_ _Episode 66_67 ........... Kamar yanda Ammy tace ma Feenah tun da safe ta dawo, sosai mansoor yayi mata faɗa kamar ya daketa,arziƙin Ammy kawai taci ya rabu da ita, washe gari da zai tafi ma faɗa yayi mata sosai akan ta kama kanta, in dai ta bari yaji ta aikata wani to zai zo ne da kanshi ya tafi da ita komai kuwa zatayi, ce mashi tayi inasha Allah ta bari bazata yi wani abu ba, noraiz da fatima da sa'ada su ka raka su airport shi da kairiyya dan shazim tun faɗan da su kayi ba su wani shirya ba shiyyasa bai raka shi ba. _*✨KATSINA✨*_ Addimisson ɗin su Aairah abokin uncle Ahmad ya amso, sai dai kuma ba anan branch ɗin su dake abuja ba su ka basu Addimisson, branch ɗin su dake lagos su ka tura su,ko da uncle Ahmad ya sanar da abie cewa abie yayi baza su tafi lagos ba sai dai ya nema masu wata school ɗin anan katsina amma baza su lagos ba saboda shi baya son su zauna a hostel, mom ma da taji cewa tayi gaskiya sai dai suyi a nan amma bata bada goyan bayan suje lagos ba,su kuma suna so ba yanda ba suyi da abie ba akan ya amince yace A'a, sai ma kiran wani abokin shi yayi da ɗiyar shi ke school of nursing yace idan ba su gama bada addimisson ba yana so zai sama ma su Aairah. " gaskiya ina tunanin sun gama ɗaukar ɗalibai amma zan bincika naji" " to shikenan, komai kenan sai ka kirani ka sanar dani " " to insha Allah " abie ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran " haba yaya miyasa zaka ce haka, tunda dai suna son makarantar yaya ai banga aibu ba, kabi su da adu'a kawai insha Allah babu abun da zai faru da su har su gama " uncle Ahmad ya faɗa " Ahmad ni bazan bar yarannan ba su zauna a hostel ko da ace a cikin garinnan ne bare ba nan ba can wata uwa duniya, gaskiya bazan iya ba " "yaya wai mi kake tsoro ne aciki, tarbiyya dai daidai gwargwado suna da ita nasan baza suyi abun da za muyi da mun sani ba, dan Allah ka bar yarannan suyi karatun su inda su ke so, ka bi su da adu'a kawai " "dan Allah abie ka bar su, insha Allah wani abu bazai faru da su ba sai alkairi " Abdallah ya faɗa wanda zuwan su kenan shida safwan yaji uncle Ahmad nama abie magana akan makarantar "Ai kai daman bakin ku ɗaya da su " "ba haka bane abie, tunda suna so kuma kai kan ka ka yarda da nagartar makarantar ka barsu kawai dan Allah" "yaya idan kana tsoron rayuwar da za suyi ne, ni ina da wani aboki dake cikin makarantar a nan yake zaune da iyalin shi sai kawai su zauna a gidan shi amma dan Allah karka hana su " "Yanzu dai sai Alhaji umar ya kirani na ji, idan an samu nan ɗin to nan kawai za su yi idan ba'a samu bane to" "dan Allah dai ka bar su kawai suyi karatun su a inda su ke so " "Kaga wanda kake magana abokinka ne kar mu takura mashi " "Idan kana ganin haka yaya to su zauna a hostel ɗin shi sai ya riƙa lura da duk wani shigi da ficen su " "abie wallahi ina mamakin yanda kake ko kwanto akan su Aaimah" "dole nayi kokwanto Abdallah, yara ne yanzu ka haife su ne baka haifi halin su ba " "haka ne abie, abun da nake gani kawai mizai hana su zauna a gidan su shazim kawai dama fatima a can shazim ya nema mata addimisson kaga kawai sai su riƙa zuwa tare suna dawowa tare, hankalin ka ma sai ya fi kwanciya " "to zan dai fi yarda da hakan, amma kana ganin baza'a ta kura su ba " Uncle sadiq dai na gefe yana sauraron su kamar yana fahimtar mi suke faɗa, safwan ma sauraron na su yake amma baice ƙala ba "haba abie wane irin takura kuma shazim fa nace maka ba wani ba,yanzu idan yaji kace haka ai bazai ji daɗi ba" "duk da haka Abdallah, ka san halin su Aairah ba jin magana su ke ba kana gani a nan idan iya shegen su ya motsa yanda ake fama da su" "wannan abie duk rashin aikin yi ne ke damun su, Amma da sun fara zuwa makaranta za su daina wasu abubuwan " Fitowa su kayi daga cikin gidan Aairah na ɗauke da tray wanda snacks ne a ciki, Aaimah kuma ruwa ne acikin trayn dake hannun ta yayin da Ameerah bowl ne babba a hannun ta yanka kun kayan marmari ne a ciki, wurin su abie su ka nufa dake zaune a garden, ƙarasawa wurin su su ka yi,ya Abdallah ne ya nufe su trayn dake hannun Aaimah ya amsa safwan kuma ya amshi na hannun Aairah yana ce mata " sannu da ƙoƙari " Yawwa tace tana ya mutse fuska "to fa ni da yake bani da galihu shiyyasa ba'a amshi na hannu na ba " Ameerah ta faɗa, dungure mata kai Abdallah yayi yana faɗin "bani nan uwar yan ƙorafi " turo baki tayi tana faɗin " yo ai dole nayi magana ya Abdallah an amshi na hannun su amma ni ban da ni " "to naji Abdallah ya faɗa yana ajiye bowl ɗin da ya amsa a hannunta kan table ɗin da ya ajiye saura kusa da su abie. "to oya a koma ciki" Abdallah ya faɗa, juyawa su kayi su ka nufi cikin gidan wurin su abie ya koma,zama yayi kan kujerar da ya taso ɗazu yana faɗin " abie babu wata matsala za su iya zama a can " " amma Abdallah baka ganin za'a takura su, ni dai da ka bari kawai na nemar masu wata a nan" " abie babu wani takura, amma idan baka son zaman su a can to dan Allah ka bari su zauna hostel babu abun da zai faru da su inash Allah, Amma na san Ammy bazata ji daɗi ba ace tana garin au zauna a hostel " "A'a gaskiya ba za su zauna a hostel ba " " to shikenan ka bari kawai nayi ma Ammyn magana " _Duk wannan dagewar da Abdallah yayi yana yi ne dan shima ya samu dalilin zuwa lagos ɗin a kai a kai shiyyasa duk yabi ya dage_ " to shikenan, kira ta ni sai nayi mata baya ni da kaina" to Abdallah yace yayin da yake zaro wayar shi dake cikin aljihu yayi dialing number Ammy, tana picking ya miƙa ma Abie tana faɗin gashi abie, amsa yayi haɗi da kara wayar a kunne, muryar Ammy yaji tana sallama haɗi da faɗin " Abdallah " "bashi bane abie ɗin sa ne, an wuni lafiya " " lafiya lau Alhmdllh, ya aiki" " Alhmdllh, ina su shazim " " suna nan kafiya, ya su hajiya kubrah da ƴa ƴa na, har yau dai sunƙi zuwa ko daya ke ba'a kawo man su ba zance ?" " suna nan lafiya saboda su ne ma yasa na kira " " to, Allah yasa lafiya?" "lafiya lau, maganar makaranta ne mun nema masu makaranta ne a abuja to da suka basu addimisson sai suka tura su branch ɗin su dake nan lagos, bana son su zauna a hostel ne saboda yara yanzu suna gaban ka ma sai a hankali bare ace basa gaban ka shine nace nake son su zauna nan sai su dunga zuwa suna dawowa " " Amma gaskiya banji daɗi ba,yanzu akan su Aairah har sai ka ka kira da kanka, haba dan Allah " " ba wani abu bane, faɗin ai yana da daɗi " "duk da haka dai banji daɗi ba " " to ayi haƙuri " "shikenan ya zanyi tunda anriga an gama, yanzu yaushe za su fara lectures?" " nan da sati uku ne " "to Allah ya nuna mana, nan ai gida ne ko da ka ma barsu a hostel naji labari bazan bar su ba " "to shikenan nagode " "wane irin godiya kuma" "to shikenan sai sun zo ɗin " " to Allah ya kawo su lafiya " "Ameen ya Allah " abie ya faɗa sallama su kayi ammy na faɗin tana gaishe da mom, miƙa ma Abdallah wayar abie yayi , amma bai san yana yi ba saboda hankalin shi ba anan yake, _har wani ajiyar zuciya ya saki daya ji ammy tace ko da sun zauna a hostel zata dawo da su ne gida, yanzu ko ba komi ya samu kafar da zai riƙa zuwa lagos ba tare da wani yayi tunanin wani abu ba_ zaungurin shi safwan yayi cikin magana raɗa raɗa ya ce " hankalin ka yanzu ya kwanta ko" "sosai ma kuwa " Abdallah ya faɗa a hankali yanda su abie baza su ji ba " "Amshi wayar ka na ce " abie ya faɗa yana sake miƙo mashi wayar, amsa yayi yana faɗi "ka gani ko Abie, na san ma bazata ji daɗi ba " "duk da haka dai tunda an faɗa mata ai shikenan nan " murmushi uncle ahmad yayi yana faɗin "yanzu sai da ka samar ma su idan ka fi yarda sannan hankalin ka ya kwanta yaya" "bazan ɓoye maka ba gaskiya sai yanzu naji zan iya bari suyi ne sa da ni " "to ai shikenan tun da ka amince " Cikin gida su Abdallah su ka nufa shi da safwan, suna shiga main parlor da hayaniyar su Aairah su ka fara cin karo suna ma Ameerah dariya tana kuka saboda ba su samu addimisson a abuja ba, ta so suyi makaranta tare amma Allah bai nufa ba shine suka tasa ta gaba suna mata dariya. "ku har gobe baza kuyi hankali ba, ai gara ma da abie yace anan za kuyi karatu saboda baku da hankali " Tsi su kayi, Ameerah kuma bata bar kukan da take ba tsawa Abdallah ya daka mata yana faɗin " billahil'azim ko kiyi man shiru ko ranki ya ɓaci " shiru tayi amma hawaye basu daina zuba ba, tsaki yayi ya nufi part ɗin mom, safwan kuma zama yayi kan sofa Aaimah tace "dan Allah ya safwan da gaske abie bai amince ba " ɗaga mata kai yayi alamar eh,ɓata fuska Aaimah tayi tana faɗin " Amma miyasa abie zai ƙi amincewa " dariya Ameerah ta kwashe da ita " wallahi Allah ya ƙara naji daɗi da abie ya ƙi amincewa " "yar baƙin ciki insha Allah zai amince" "bazai amince ba insha Allah" tashi safwan yayi yana faɗin "Aairah ki kawo man tea please " turo baki tayi tana faɗin to, dama tun da ya zauna wurin bata sake cewa ƙala ba, haka nan ita fa shishige matan da yake yi ba burgeta yake ba,tashi tayi ta nufi kitchen ɗin shaf shaf ta haɗa mashi tea ta nufi part ɗin Abdallah, nocking tayi, da kanshi yazo ya buɗe mata ƙofar matsawa yayi gefe yana faɗin ki shigo ciki " mom ke kirana " ta faɗa so kawai take ya amsa ta gudu, amsa yayi yana faɗin" to muje can main parlor sai na sha a can idan kin dawo daga wurin mom sai kizo " to tace haɗi da yin gaba yana binta a baya har main parlor, kan table ta ajiye mashi ta nufi ɗakin mom da Abdallah ta ci karo zai fito, yana ganin ta yace "harkun biyo ni kenan" "yaya ba kai na biyo ba wurin mom na zo " " ba wani " ya faɗa haɗi da ficewa, ciki ta ƙarasa tana faɗin " mom kinji dai ko abie bai amince ba" "to ya za kuyi sai haƙuri " " ya muka iya tunda bai amince ba " ta faɗa kamar zatayi kuka bed ɗin mom ta nufa ta kwanta, murmushi mom tayi " yanzu fa kina iya kuka " " A'a mom ba kuka zanyi ba" " ai nayi tunanin shi za kiyi, to wasa yake abie ɗin ku ya amince " " dan Allah mom da gaske " " A'a da ƙarya " " sorry mom, farin ciki ne yasa nace haka, amma naji daɗi da abie ya amince " tana gama faɗa ta fice ta nufi parlor wurin su Aaimah, dariya ta fara yima Ameerah kafin ta sanar da su abie ya amince,ƙululun baƙin ciki kamar ya kashe Ameerah, saboda dariyar da Aairah ke yi mata. Aaimah kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha da Aairah ta sanar da ita abie ya amince, haushi da takaici kuwa wurin Ameerah ba'a magana. _Wannan kenan_ Lokacin da Ammy su ka gama waya da abie,parlor ta fito wurin su fatima take sanar da fatima zuwan Aairah, fatima kamar tayi hauka dan daɗi da ma ta jima tana son ganin su har cewa take idan su ka samu hutu sai taje katsina ko dan taga waɗannan yan biyun na su ya dr, yau gashi burin ta na ganin su zai ciki har ma za su zauna tsawan wa su shekaru,taji daɗi sosai da wannan labari da Ammy ta sanar da ita Ammy na barin wurin ta ɗauki wayar ta ta kira Abdallah dan sake ji daga bakin shi, ƙara tabbatar mata yayi da sunan zuwa nan da three weeks. "ya dr dan Allah su zo next week, wallahi na ƙosa na gan su " "one week da three weeks ai duk ɗaya fatima, in dai da rai da lafiya za ki gansu har ma sai kin gaji " "duk da haka dai ya dr" "to ni dai babu ruwana hukuncin abie ne wannan " "shikenan Allah ya kaimu, ka basu wayar to mu gaisa " "sai dai na tura maki number Aairah ko ta Aaimah" "kai ya dr, to naji ka tura man duka " "to shikenan zan tura maki " "yawwa ya dr nagode bye " "Wait naga sai wani rawar ƙafa kike, karfa su zo ni ki share ni kuma dan saboda ke nasa abie ya amince za su zo dan nima na samu damar ganinki" ya faɗa yana ɗan murmushi, rufe ido fatima tayi ita a dole kunyar zancen shi taji "kinyi shiru idan haka ne gara tun wuri na sani " "haba ya dr dan Allah ka daina faɗar haka, kaima ka san babu abun da zan samu da zai ɗuke man hankali har na share ka " "na sani, nima wasa nake maki, naga dai kina ta rawar ƙafa ne " "na ƙosa na gansu ne" "very soon zaki gan su " "to shikenan, katuro man number" to ya faɗa haɗi da yin rejecting kiran, bayan kamar minti ɗaya sai ga number ya turo mata duk da ta Aairah da Aaimah,ko kiran shi tace taga number bata yi ba saboda zumuɗi, number Aairah tayi dialing, da sallama Aairah a bakinta tayi picking kiran, a hanzar ce fatima ta amsa mata sallamar tana faɗin "sister ya kike, ya gida " "lafiya lau, pls wake magana " Aairah ta faɗa, murmushi fatima tayi sannan tace " na san bazaki gane ni ba, fatima ƙanwar ya shazim abokin ya Abdallah" "ooo Allah sarki, ya kike ya su Ammy " "lafiya lau su ke, yanzu take faɗa man zaku zo lagos ke da Aaimah" "Eh" "dan Allah kuce ma abie ya barku ku zo next week ba dole sai nan da sati ukku ba pls " abun mamaki ma ya ba Aairah ganin yarda fatima ke zumuɗin zuwan su duk da ba su san juna ba a zahiri, hakanan taji fatima ta kwanta mata arai ita ma taji ta ƙagu da taganta " shikenan insh Allah zan roƙe shi ni da Aaimah " "yawwa nagode sosai, ina Aaimah take?" " tana wurin mom " " ok dan Allah ki bata mugaisa harda mom ɗin " " to shikenan, kashe idan naje wurin su sai na kiraki " " to " fatima ta faɗa haɗi da kashe wayar. Wani wawan tsaki feenah taja, dama tun da taji Ammy ta faɗin zuwan su Aairah taji ranta ya ɓaci hakanan taji ta tsane su duk da bata san su ba amma taji bata ƙaunar su zo " haba ya feenah miye abun tsaki kuma?" " dole nayi tsaki, saboda ke shashasha ce baki san mutane ba amma dagaji za su zo sai wani zumuɗi kike " " bangane bata san su ba, ke dai idan baki san su ba to kiyi shiru amma ita ta san su ko nima nan da kike gani na san su " sa'ada ta faɗa tana hararar feenah "ƙannan uwarki ne su da zaki ce kin san su,kuma wallahi na kama ki zaki san ni kike harara" " ba ƙannan uwata ba ne, amma ai su muslmai ne kuma muslmi ɗan uwan muslmi ne, to wai ma ina ruwanki idan sun zo ke dai ba a kanki za su zauna ba kuma ai dai inji nan ba gidan dady bane bare har sai kin zaɓi wanda zaizo kema kara ki akayi " sa'ada ta faɗa tana miƙewa tsaye dan ta san abun da zai biyo baya tsakanin ta da feenah ba mai kyauba ne, tashi feenah ita ma tayi ai tana gani haka ta kwasa da gudu sai ɗakin Ammy tana faɗin " Allah yasa idan su ka zo su koya maki hankali, tunda ta ƙamarki yi ma mutane wulaƙanci sai kace ma nan ɗin gidan ku ne " "ai da kin tsaya inji uban da kike faɗa ma wannan maganganun " gwalo sa'ada tayi mata tana faɗin "da karyeyyen hanun " ta faɗa tana langabar da hannun ta irin ciwannan taji tana faɗin " wayyo Ammy wurgi ya shazim yayi da ni " A harzuƙe feenah ta bi bayan ta, da gudu sa'ada ta shige ɗakin Ammy jikake garam ta banko ƙofa ta rufe da key, bubbuga ƙofar feenah ta shiga yi tana faɗin "wallahi sai na ci ubanki na kamaki " daga cikin ɗakin sa'ada tace " ki kashe ni idan kin tashi " " zaki san da ni kike magana feenah ta faɗa haɗi da barin bakin ƙofar, ta koma cikin parlor, samun fatima tayi tana waya da mom da Aaimah, haushi kamar ya kashe feenah, ta shima tayi ta nufi bedroom ɗin ta da take kwana, wayarta ta ɗauka tayi dialing number Innah, tana picking ko sallama bata ti ba ta zayyane mata komai dan gane da zuwan su Aairah har da ƙari _aikin banza sai kace Innar wani abu zata iya😏_ Baƙin ciki da takaici ne ya cika Innah ƙala bata ce ba ta kashe wayar, haushi kamar ya kashe feenah jin innah bata ce komai ba. Shazim da ya dawo gida Ammy ke sanar da shi zuwan na su, Allah ya kawo su shine kawai abunda yace. _dafta ban san wulaƙanci fah ehe_ A kwana a tashi babu wuya wurin ubangiji yau ya rage saura kwana biyu su Aairah su zo lagos, duk wani shiri da za suyi sun kammala, ranar da zasu tafi kawai su ke jira, Abdallah ne zai kai su, sai ya gama su komai a school sannan zai dawo. Ameera sun koma Abuja tun last week, ta sha kuka kamar mi bata yanda zata yi dole ta haƙura, taci ƙurin suyi school tare amma bai nufa ba. Washe gari ranar da za su tafi har gida su ka je su ka yi ma dadi sallama, sannan su ka je gidan granny da gidan Aunty safiya, najma ma kamar ta haɗiye zuciya dan baƙin ciki za su tafi su barta, saboda ita dadyn ta a nan ya samar mata da school, sai da daddare sannan su ka koma gida.......... _WASHE GARI_ _SEASON TOW KENAN, MU HAƊU A SEASON TOW DAN JIN YARDA ZATA KAYA ZAMAM SU AAIRAH A LAGOS, GA FEENAH YAR BAƘIN CIKI_ _SHIN WANENE SU SHAZIM SUKA RIƘE MA KAYA YAKE MA SU BARA ZANA, YA MAGANAR AURAN SHAZIM DA FEENAH DUKA WANNAN AMSAR TANA CIKIN SEASON TOW_ _ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN DOCTOR SHAZIM SEASON ONE_ _ZAN ƊAN JE HUTU KAFIN NA FARA SEASON TOW_ _GA MAI SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN DOCTOR SHAZIM 300 NE BA YAWA_ _3169482544 MUKHTAR HADIZA FIRST BANK_ _SAI A TURA SHAIDAR BIYA TANA WANNA NUMBER 09132289761 KO 08133650574_ Masu cewa ban sa Account number to ga shinan na sa.