💍 *AL_HUBB* 💍 The love💘 By Aysha b. Naseer Episode 01: ASSIDDIQUE RESIDENCE Bismillahir Rahmanir rahim Dukkan godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala daya bani ikon fara wannan littapi ubangiji Allah yasa mu karu mu amfana da darusan dake ciki ya yafe kurakurai.. Its another bright saturday weekend dukda ma a gurinta ba weekend din bane, tunda har saturday ma setaje aikin, tana jin dadin aikin ko ba komai yana dauke mata kewar zama cikin wannan tangameman gidan da sam babu dadin zama ba kuma dan babu ba sai dan yawan yayi mishi yawa, ga rashin Albarkar mutane, Satinta daya ne kadai yanxu da zuwa, Ta janye hijab din dake kanta ta miqe daga kan dardumar da tun sallar asubahi take kai tana jero bukatunta gurin wanda shi kadae tasan ze biya mata su, a hankali ta karasa bakin mirror ta kalli kanta, yes yau ne kadai ta yarda ta rame tunda taji ana cewa ta rame din, tai azamar juyawa mirror din baya saboda ruwan hawaye dataji sun soma taruwa a idanunta, hakan ya baiwa idanunta damar sauka kan tamfatsetsen zanen frame din na fuskarta, tai azamar shiga bandakin dake cikin dakin, mintina 30 suka isheta gama shiryawa, a hankali ta tura kofar bedroom dinta, ya sadata da corridor din dakuna, sannan ta karasa fita sarari kafin wani tangamemen falour ya bayyana a idanunta, da farko kafin tazo gidan ta ayyana dole dama ze zama super unique amma datazo se taga gabadaya an karar da tunaninta, babu abinda ya hana ta zama er kauye a lokacin, ta sauke numfashi ta gangara kasan benen dashi kanshi ya isa abin kallo, (picture din falourn is on wattpad) Motar da aka ajiye domin kaita gurin aiki ta shiga already driver na jiranta, ta lumshe ido tana jin sanyin A.C na ratsata, a hankali take rewinding abubuwan da suka faru cikin kankanin lokacin komi ya sauya Gama jami'arta, Auren minnatullahi, barin gidan Anty siyama zuwa nan Abuja gidan As_siddique, fara service dinta, She recalled the day she was posted to camp in Abuja, she was confused, tasan battada kowa a Abuja, ta fadawa dai Abbah jabir da Anty siyama inda akae posting dinta, haka ta tattara ta tapi dan tama mance a nan Abuja minnatullahi take aure, sae bayan sun kusa gama camping tana shirin relocating kawai Anty siyama ta kirata tace kar tayi relocating ta zauna nan *gidan As_siddique* ... Wani katon mall driver ya karasa da ita, it was beyond expectation of a mall, yayi girma, a yadda a ke fadi ma shine the first biggest mall cikin garin Abuja babu kamarshi, Har kofar inda zata shiga driver yyi parking ta fita batareda ko hasken rana ta tabata ba, Mall ne mai different shops and places, cikin wani hadadden gurin cin abinci ta shiga, wani kamshi mai saka kasala ya ratsa ta, bata tsaya ko ina ba ta wuce direct inda nata aikin yake, duka anyi desserts din safiyar, ita daya ake jira tazo tai tasting, Tayi sterilizing hannunta dukda a tsaftace suke, sannan ta fara da samosa, sau daya ta tauna ta zubar, angrily ta kalli chef din da yayi girkin ta nuna mishi barin hannun damanta, ya ja tray dinshi ya koma, Sai tea cikin transparent disposable, ta karba tayi sipping shima din bata karasa hadiya ba ta zubar rai a bace, Gabadaya 11 dishes din da suka kawo saida tayi disqualifying 10 dishes, sandwich ne kawai yayi shima yana buqatar ingredients to look more enticing and stimulating... Thats about *zainab* she loves to cook its in her blood.. Meeting na kusan 1hr sukai itada manager din data tarar a gurin sanda tazo wanda ke kula da restuarant din(SALEEM), atlast suka karkare kan zasu rufe gurin for some few weeks, a weeks din kuma zatayi training cooks din... A ranar akayi shutting down restaurant din, a daren ta tsara yadda classes din duka zasu tapi ba tareda wani takura ba. kashegari kuma suka dinga zuwa gida daukan courses, cikin kwanaki 3 aka kammala duk wani dessert sannan suka shiga main dishes gadan gadan, she taught them everything su kansu sunji dadi sosai In a week suka gama aka bude resutuarant din aka faraa girkuna, And a wannan ranar ne masu gidan suka dawo daga doguwar tapiyar da suka dauka Tana daki a zauna tana duba Al'quranin ta, karfe 8 harda mintuna bata jima dayin sallar isha'i ba, Er hayaniya taji irin daga can nesa dayake gidan nada zurfi ta miqe ta fita bolcony din dake cikin dakin, daga inda take tana iya hangen kasa, hadaddun motoci ne a jere guda 5, black with dark tint, sun jima da tsayawa, duk securitues sun gama fitowa sannan a hankali ta zuro fararen kafafunta, ta fito tana kallon komai a yatsine, ta dayan bangaren ya fito, looking calm as ever, AS_SIDDIQUE, Ya zagayo suka hade hannayensu, they look perfect, zainab ta fada tana murmushi She will love to see their kids, ohh damn cute Kafin su karaso cikin falourn kasa ta rigasu sakkowa, tana sanye da blouse da skirt, sanann gyale a kanta, Tana tsaye a falourn aka bude musu kofa, suka shigo and everything seems like a dream to her, this is the second time data kasance gata ga As_siddique, amma sai taji da banbanci sosai, wancan karon batasan shi ne ba, wancan karon bata damu da sanin ma waye shidin ba, kuma wancan karan be cikin zuri'arsu, but today, tasan shi ne As_siddique, the billionaire's heir, the most beloved child a cikin family, kuma mijin minnatullahi wacce take kalla kamar yayarta dukkuwa da ba wani shirin kirki sukeyi ba She couldn't say a word, "Zainab how re u?" Shine kalmomin da suka fito a bakin minnatullahi, zainab ta dauke idonta daga kallon datake mishi, ta dubi minnatu tace "Ya mint am good and okay" sai ta dubeshi kadan tace "u're welcome" Minnatu ta subale hannunta cikin nashi sannan tazo ta wuce ta gaban zee ta soma hawa stairs din kamin tace "pls zainab zan dan huta a dakina banason disturbance, Zaianb ta gyada kai, sannan ta dawo da dubanta gareshi, shikuma ya juya yana sallamar securities din, cikin dumbin mamaki maimkon ya hawa sama shima ya huta sai ya sule takalmanshi a nan ya zauna kan couch din falourn ya miqe kafa, Ganin haka yasa zee juyawa, and for the first time taji muryarshi yace "Hlo zainab right" Ta juyo ta gyada kai tana fata gaske ne Ya yafito ta da hannu ta karaso kuwa amma sai ta zauna kan capet din dayake, yace noo pls tashi ki zauna kan couch, batayi musu ba ta miqe ta zauna kan kujerar "He's nice" ta fada a ranta "gaskiyar Anty hawwer (her only sister)" So tell me meke gudana a FC (food_court, restaurant dinshi da take aiki) Tai shiru tana tunanin "shi bae gaji bane?" Am all ears ya katse tunaninta Tai gyaran murya sannan ta dora hannayenta kan kafarta (cinyarta) tana facing dinshi a karkace ta soma da fadin "well i thought saleem updates you, buh i ll say it all since u ask, actually most of the chefs re not well trained, so i had to give them a classes,,," ta fada mishi duk yadda sukai da achievement din da aka samu" Beyi smiling ba but he's impressed, okay i will test u too" Ta dago ta dubeshi, wai itane zeyi testing a fannin girki? Oh wow she'll love that U ll prepare a coffee now, tai nodding sannan ta miqe ta tapi cikin kitchen din dake kasa wanda a cikin shi akwae bene daze kaika har kitchen din sama She prepared the coffee dama batayin bacci sai ta sha coffee dan haka tai two cups ta dauka ta miqa mishi daya, amma se yaqi karba yace tai tasting tukunna ta zauna tayi sipping ta kuma miqa mishi kuma ya karba at once ya shanye tas Zee ta zuba mishi ido, ya miqo hannu ta miqa mishi na hannunta shima ya shanye, Ya zuba mata ido sai ya lumshe idanun kuma, ba tareda ya bude ba yace "So u're hawwer's sisster...?" Wayarshi tai kara ya bude idanunshi yayi picking "Okay mom sai kunzo" yayi dropping call din "Muzakkir's wife?" Ya karashe tambyar, zainab ta tsaya kallonshi "how comes ya ganeta da wuri haka, tasan yazo gidan Anty hawwer sanda tana nan amma ai basu hadu ba" Kamar yasan tunanin datake kenan yace "i don't forget taste, i remember how all the dishes tasted plus the tatse of ur coffee" Muje zuwa..🥰 💍 *AL_HUBB* 💍 The love💘 By Aysha b. Naseer Episode 02: His personal cook Ranar aiki ce dan haka tayi shirinta da wuri, ta fito and everywhere was quiet, har zatayi descending downstairs, sai ta koma bangaren data tabbatr na minnatu ne, ta karasa bakin wata kofa ta kwankwasa amma shiru dan haka ta murda kofar, falour ne mai girma amma baikai waiting falourn kasa girma ba komi shiru sai karan na'urori, dispenser nata aiki, aircon na nata, "I hav told you to hire a cook but u refuse" Shine abinda taji minnatu na fadi har muryarta na tashi, Zee ta dan daga murya tace "ya mint zan fita" minnatu tace "karaso" Ta karasa dakin babba ne sosai dakin, yana zaune kan sofar dake dakin ya dora kafa daya kan daya looking calm as always saedae daga shi sai singlet da shots, Itakuma minnatu na kwance kan gadon dake facing sofa dukda akwae tazara tsakanin gadon da sofar tana aika mai da harara, ganin zee yasa ta dan mata murmushi, pls STAR zaki hadama abin kari zae fita ne da wuri" zee tace to Sannan ta fita, zee na juyawa minnatu ta aikamata da harara, Ya dubeta muryarshi calm yace "wai kekam mene matsalarki, ni kin harareni dan nace kimin abin kari, itakuma mene nata laipin da kika harareta" Muryarta kamar zata dokeshi tace "kai wlh kana da matsaala star, nipa ba wani son zuwanta gidana nakeyi ba, dan kawai karka takuramin da aikin girki ne yasa nace tazo, nasan zata dafa maka duk abinda kakeso" Zee tayi diff "Dama shine dalilin dayasa Anty Siyama tace tazo kenan, tun ba yanxu ba tasan halin Anty siyama da son kanta, wato ta moreta ta kawo wa kanwarta ma ta moreta, me suka maidani ne? Baiwarsu?" Ta matsa daga bakin kofar a hankali dama tazo ta tmbyi me za'a dafa mishi ne, kunnunwanta sukae mata wnn jin And everything became clear to her, ko a da basa shiri d minnatu balle kuma yanxu da ta auri Nigerians billionaire, Ta shiga kitchen din smaa tayi preparing simple dessert for him, ta koma ta kai mishi, a falour ta sameshi shi kadae ta ajiye ta juya ta fita tana maijin haushin kanta na zuwa gidan minnatu saedae ynxu kam aikin gama ya rigada ya gama Ayyukan zee a FC ya ragu dan duka cooks din suna kokari gurin inganta abinci kuma ga salim shima wanda diman daeman yana gurin yana kulawa da harkokin Karfe 2 ta iso gidan, akwae karuwar motoci... Ta alakanta hakan da en sannu da zuwa ne Takai kofar faloyrn kenan aka banko kofar duk nauyin kofar nan da fadinta zee tai baya da sauri ganin za'a lahantata, manyan mata su uku ne suka fito jikinsu yasha adon gwala gwalai, kai da gani kasan masu arziki ne, dukkansu babu wacce ta kula da zee kowacce taje ga motarta drivernta yaja ta suka fita, zee ta sauke ajiyar zuciya ko sudin su waye kuma, Tana shiga taga minnatu tana ta taunar cingam abinta babu wani abinda ya dameta "ya mint sannu da hutawa" ta fada tana kokarin wuceta" yawwa ta amsa a takaice Ta taka steps uku kenan ya shigo falourn, bai lura da zee ba yake fadin "Whats ur problem please sune fa yayye na, kinsan sarae irin en ubancin da akeyi cikin gidan nan amma kikae ignoring komai kika musu rashin mutunci" minnatu ta miqe "mukayiwa juna dae, ai kasan en uwanka basu da kirki nikam bazan juri iskanci ba wlh ai basu nake aure ba," ta haye sama abinta Ya zauna a nan din yana lumshe ido, zee ta juya ta cigaba da hawan steps dinta "What's wrong with them both?" Ta tambayi kanta, and minnatu is like she dont respect him, shikuma ya fiya sanyi a yadda ta gani... Karfe 6 na yamma "Pls dear kiyi mata mgana mana" minnatu ra kalleshi, "aikin ta ne tasani karka damu zatayi maka" ya futa daga dakin nata ganin bata niyyar yin abinda ya sakata din, da kanshi ya karasa bangaren zee ya wuce falour ya shiga corridor din ya karasa bakin kofar dakin dayasan anan take ya kwankwasa, ta bude ta bashi hanya ya shiga ya zauna itakuma ta tsaya tana mamakin shigowarshi har cikin dakinta baze turo bane? Amma dae tai shiru " in bazaki damu ba, anjima by 10pm inada important meeting kuma kece zaki dauki nauyin abinda za'ayi serving, zan turo Rafiq yazo ya tayaki,... kamar mutun nawa? Ta katseshi, "Just 10" tace is okay basae an tayani ba i can manage" ya tsura mata ido yadda take mishi magana with lots of respect yayi nodding sannan ya miqe har ya kai kofa yace "Ammm please add that coffee to the menu" idanunta na kasa tace okay sir... Ta dauki wayarta tai dialing number favourite cousin sis dinta, babu dadewa ta dauka "mutanen Abuja ya garin" "Zakiyya wae barrister baisan Assiddique ya dawo bane? Wasu abubuwan fa duk da kanshi yakeyi" zakiyya tai murmushi "ya sani mana zee, shima barristern baya kasar kuma Assiddique ne ya aikeshi kinsan role biyu yake mai playing role din personal Assistant da role din barrister shiyasa aikin ke mishi yawa, kuma yaqi appointing wani P.A din kinsan beda yadda" Zee ta zauna tana tinani "can u imagine duk girman gidan nan duk yadda matsayinshi yake babu cook, ma'aikata 5 ne masu share share suma suna ida aikinsu suke koma quaters dinsu, nice dae meyi musu girki se meyiwa ma'aikata da security girki a can quaters din" Zakiyya tace "ai baki sani ba, yana da personal cook da, duk tafiyar dazeyi da ita yake kafin yayi auren, kuma Mami (qanwar mamanshi) ce ta bashi cook din saboda matsalolin tsaro, amma yanayin aure ya maidawa mami ita, shi yana tunanin minnatu zatana mishi girki, nan kuwa besan buhun uban girman kanta ba, yanxu kuma baze koma gurin mami yace mata ta maida mishi ba" Zainab ta jinjina kai (Barrister shine mijin Zakiyyan shiyasa take sanin wasu abubuwan dake gudana a gidan) Sunyi hira daga baya suka katse kiran... Karfe 9 da rabi na daren ranar, zee ta kammala abubuwan datasan zasu bukata har ta yi wanka ta fito a wanka, wayarta tai ringing, ganin bakuwar lamba ya saka ta mishadi sosai ta dauka da sauri, amma sai taji yace Yusuf Assiddique here, zee ta hadiye ruwan hawayenta sannan tace "good day sir, everything is ready" yace ze turo azo a tayata dauka sai tayi arranging kafin time ya cika dan wasunsu sun fara zuwa suna can wani kebantaccen falour, Atampa ce jikinta riga da skirt sun zauna dam, ta dau hijab ta dora a kai, sannan ta leqa kasa inda taga maaikata biyu tsaye da security daya yana jiransu, ta kitchen tabi ta sakko sannan tace su shigo kitchen din, saedae kafin a fara daukan kayan security din yayi mata magana a kunne da cewar "oga yace se tayi tasting kafin a kai musu", ta daga kai ta dubi CCTV din dake kitchen din wadda batasan da ita ba sai dazu tana girki taje dakko abu, a ranta tace "ko wannna ma ai bazata bari na zuba komi ba, Shi securityn ne ya zaba mata wanda yakeso tayi tasting kuma tayi sai da suka jira 10mints kafin aka dauka itama tabisu da wasu, Wata kofa ce a cikin falourn daga can gefe siririn carpet ne a shimfide a dogon corridor din, sai hanyar farko daga hannun dama suka shiga anan wani katon dakin taro ya bayyana kamar conference room, bama kamar this is a conference room, to dayake mutanen da zasui meeting din bassu da yawa sai akayi jere da cushion a gefe na mutun 10, sukai placing komi neet sanann ta fita, duk abinda takeyi Assiddique na kallanta, yayi smiling, tun farkon zuwanta gidan yana sane da duk motsinta and now is high time yayi abinda mind dinshi ke raya mishi Ya dau waya ya kira Abbah jabir (qanin babanta wandaa ke riqonta), yayi mishi explaining komi and ya nemi izini, Abbah jabir yaji dadi sosai, koba komai zee made him proud... Cikin bacci taji bugun kofa, ta dubi agogo karfe 1 harda mintuna 10 na dare, this is the first time da aka buga mata kofa a wanann lokacin, ta tashi tana mitstsike ido, bisa ga dumbin mamakinta ta ganshi a tsaye sanye da farar jallabiya, kwan fitilar dake corridor din mai bada different colours ya dinga haskashi, zee ta kura mishi ido deep in thoughts "Tunda zakiyya ke yabon launin fatarta, sae taga tata ba komi bace compared to tashi, ba fari bane kuma ba baki bane, irin caremel mai dan haske, kuma tana bada sheki kamar golden, sai taji tamkar ta taba taji irin taushinta, dogo ne kuma mai murdadden jiki, a yadda take ganinshi sai taga yanxu yapi ko yaushe yin kyau a idanunta, sai kuma ta tuna ko yaushe yana sanye da spec baki banda yanxu, hakan yasa ta kalli idanunshi... Ya katse tunaninta da cewar Come with me sannan ya juya yana tafiya majestically, ta bishi tana sunne kai, kitchen ya shiga, ya zauna kan work top yayi folding hannayenshi, "a mug of coffee pls" Zainab ta daga idanunta tana kallanshi a hankali wani murmushi ya subuce mata, "in aka ce girman kai to shi wannan baima sanshi ba, anya shine billionaire din datakeji ana fada" Without any hesitation ta shiga hadamai shikuma yana kallon duk wani moves nata, A hankali yace "inaso nayi hiring dinki a matsayin personal cook dina" zee ta kalleshi tana tuna hirar da sukai da zakiyya, "i ask Abbah jabir and he agreed" bata kalleshi ba tace "bani da wani jaa tunda har Abbah jabir ya amince and cooking will be my pleasure" yaji dadin hakan, Shiru na en dakiku sanann yace "gobe bazakije FC ba, yayye na maza su hudu zasuzo kuma zaki musu girki, in kina buqatar wani abu just dial Bashir's number (security din daxu) ta jinjina kai okay sir, dan sanda tazo duk muhimman ma'aikatan gidan sun bata mumbers dinsu incase of emergency 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 03: His father's Son Zainab ta tashi da annashuwa, kodan tasan zatai girki ne oho, as early as 9am ya kira wayarta, tai picking da sallama meet me at my apartment tace okay sir, ta rike wayar tana jujjuyawa, anya tasan falournshi kuwa ta dae san bangaren datake zargin nashi ne amma batada tabbas Ta zira hijab da slippers dinta, ta karasa waje, ta wuce bangaren minnatu sannan ta isa last part, a hankali ta tura kofar, falour ne kamar na minnatu, tayi tsaye tana kallon kofofin dake cikin falourn wayarta tai ringing, yace ta shiga kofar hannun damanta, ta juya ta tura kofar, sai stairs, yace "descend down" ta soma taka steps din tana kaiwa karshe taga wani hadadden falour an kwatashi da Arya sofa and dining set (the pic is on wattpad) Shi kadae ne zaune yana kallan tv da spec din a idanunshi, ta karaso ta tsugunna ta gaidashi ya amsa ya nuna mata kusa dashi yace ta zauna, ta zauna Tunda yanxu kin zama personal cook dina u need not to worry about the FC zamu cigaba da aiki tare, and by 4 yayye na danake fadamiki zasu zo, A nan falourn zaki dinga serving duk girkin da kikayi, breakfast, lunch and dinner zan dawo cinsu a gida, zee tace to Daga nan yace taje tayi planning girkin da zatama yayyenshi gobe se ta fara nashi Har ta juya zatabi ta inda ta fito yace "no zoki bi ta nan and ta nan zaki na shigowa ko yaushe" ya nuna mata wata kofa anan kasa, databi kofar sai gata a wannan corridor din da aka shimfida carpet, inda kofar conference room yake, karshe ya sadata da main falour din, Everything went smoothly as planned, abu hudu ta mishi presenting tace ya zabi wanda zata musu atlast ya zabi grilled fish da barbeque, Komi ya kammala tayi serving nasu kan dining (pic on wattpad), minnatu ma tace akai mata nata daki dan babu yadda zakaji kamshin nan baka fara salivating ba, Sunyi dogon meeting shida yayyen nashi kuma kowannensu ya yaba da girkin da akayi presenting... Yana tsaye yana tsane ruwan dake kanshi, fitowarshi a wanka kenan ta karaso dakin nashi, she's dressed attractively in nighties, yayi placing brief smile a fuskarshi, dan yasan wani abu tazo buqata "My Star ya su yaya sukaje gida" ba mutun ne mai riko ba yace "lpia qalau", meyasa bakizo kun gaisa ba kuma kinsan na fadamiki zasuzo Ta yatsina fuska kaina ke dan min ciwo, yace Allah ya sawwaqe "Star ya maganar komawata makaranta? Da kuma aikina zaman gidan nan ya gundireni" Yace don't worry im working on that Amma bakya ganin abin zeyi yawa, ga aiki ga school, musamman profession dinku da kin rabu da masters din ko kuma ki haqura da aikin for now, "Karka damu i can handle them all, beside 2nd degree is not that stressful i can manage" Yace "okay good, yanxu suna arranging hospital dinnan kinsan aikin dayawa, so da zarar sun gama zaki fara aiki ne, nd for the 2nd degree sedae kiyi nan abuja tunda kinaso ki hada harda aiki, taji dadi sosai sannan ta qarasa gadonshi ta kwanta, "yau anan zan kwana" yace next week zamuje gaida mami daga nan zamu tsaya mu sauke umarah... Tayi diff kamar batasan yana mgana ba... Kashegari tun asuba yayi mata tex na abinda yakeso, da time din dayakeso tayi serving nashi, ganin da safene yasata tashi da wurwuri, ma'aikata duk sun gama aikinsu na safe, ta shiga kitchen tayi preparing pancake din kamar yadda yace dayake ba abu ne mai wahala ba da wuri ta kammala, ta koma daki tai wanka dukda batai wani datti ba, ta dan dora hijab mai saukin nauyi sannan taje ta dauki pancake din da kamar ya balle kamar baze balle ba kuma dan laushi da taushi, Baya falourn dan haka tai mishi matsuguni a dining area ta juya, Har takai kofa taji motsin sakkowarshi daga sama, ta juyo ta rissina tana mai gaidashi ya amsa looking cool as always, Karfe 8 ne daidai amma har ya gama shirinshi tsaf da alama fitar dazeyi mai muhimmanci ce yayi kyau in blue ya karasa kan couch ya zauna ya lankwasa kafa daya kan daya sannan ya dan juyo ya kalleta (Pic on wattpad) "Dakko breakfast din" Ta dakko tazo tai serving dinshi ya sakko daga couch ya baje a kasa, ta miqe zata tapi yace a'a ta zauna becin abinci shi daya, last cook dinshi ma tasaan da hakan koda bazataci ba buh ta zauna... Ta zauna amma hnkalinta be gurinshi, be bar komi a plate din ba datai serving, yayi hamdala sanann ya miqe Tana serving lunch minnatu ta sakko cikin falourn, zee tace "barka da warhaka ya mint" yawwa barkanmu dae, ta qarasa gurinshi yana zaune kan couch din ta zauna kusa dashi, "ina kwana star" yace lpia qalau kin tashi lpia" tace lpia lau Zee ta gama serving din yace "bata wannan" ta miqa wa mint "doramin shi kan dining ya mutun zeci abinci a kasa ga dining" zee ta qarasa ta ajiye ta dawo ta soma seving nashi, Har minnatu ta miqe yace "jiya na miki mganar tafiya saudi bakice komai ba, kuma kinsan tunda akayi bikin nan bakije kun gaisa da mami na ba" ta bata rae taja kujera ta zauna "nipa bance maka bazanje ba" yace good Wani dadi ne ya tsirga zuciyar zee dan tasan dole itama zae tapi da ita, kuma zata roki alfarmar ya barta taje gidan aanty hawwer, Haka kawae murmushi ya subuce mata, ya kalleta "why is she smiling all alone"? Gurin yayi kama da library saboda yadda aka kawatashi da qananun kujeru da glass cabinet, saedae yayi kama da bolcony saboda yadda yake daga gefen falourn, "Wannan gidan wae ashe har yanxu ban gama kallo ba" zee ta ayyana hakan a ranta, ta taho da mug of coffee din dayace ta hada mishi, he smiled at her, zee ta tsinci kanta da tunanin why is he smiling?, dukda zata iya cewa this is the first time dayayi smiling a gabanta, ta ajiye mug din yace "sit Batayi musu ba ta zauna, "tell me dazu da rana naga kina smiling why?" At once murmushin ya bayyana a face dinta, and he couldn't stop looking at her innocent face, "she's a natural" ya fada a ranshi, "Am excited by the fact we re going to visit my most beloved land" A hankali yayi recalling haduwansu na farko cikin plane, she's blushing all alone "Zakiyi visiting sister naki shiyasa right?" Ta gyada kai feeling so much happiness A ranta tace he don't know Anty hawwer is more than a sister she's a mentor, a friend, a mom, Tell me the secret behind ur cooking skills, i must say i like every bit of ur food how each and every dish taste, smell, the aroma is simply amazing, Zee tai dariya a hankali tana tuna yadda Anty hawwer tace ya yabi girkinta sanda ya faraci, This man and food..... Satin tapiyarsu ya zagayo, sukayi duk shirye shirye, gidansu Suka fara biyawa dats gidan iyayen Assiddique, Motoci biyar sukayi convoy, zee tana ta biyu ita da bashir (head of securities) Assiddique da minnatu na motar bayansu, ranar zee tasha kallo, mansion ne mai kama da royal one, apartment apartment, Haka suka dinga ketawa da motocin har daga karshe suka tsaya wani apartment dayafi dukkan sauran kyau na ban mamaki, Suka fito duka, amma basu motsa daga bakin motar ba, sai da yayi appearing Ba tsoho ne can sosai ba, amma akwae shekaru tattare dashi, yana rike da wata stick mai azabar kyau, gabadaya bakinshi ya kasa rufuwa, dayake fuskarshi ba boyayyiya bace yasa zainab ta gane shine the real Assiddique wato mahaifin yusuf,,, shi yayi musu jagora har falournshi, minnatu ta gaida shi haka zainab ma, Maimakon yusuf yabi matan daidaya yana gaidasu a'a sune suke zuwa daidaya suna gaidashi, su hudu ta karshen itace sukayi hira mai tsayi kuma bata bar gurin ba sabanin sauran da kowacce tazo sai ta tashi ta koma tana yatsine yatsine, Yayyenshi maza da mata haka suka dinga zuwa suma suna gaidashi wasu suyi musabiha wasu su dan daga mai hannu dan ji suke kamar su shake shi, zainab dae a yadda ta dinga irga yayyenshi saida mutun goma sha daya maza da mata, kuma magidanta, Abu daya dayake a bayyane shine irin tsananin qauna da mahaifin yusuf ke nuna mishi bama iya wannan ba harda fifikon da yake nunawa karara, a bayyane yake cewa yapi sonshi fiyeda duk sauran yaranshi, wannan yasa momy ta samu gurbi mai karfi a zuciyar yallabai, dan duk wanda ze nuna yusuf yace yana sonshi to ya zama abin kauna gurin yallabai, Dukda momy itace amaryarshi amma tapi sauran matanshi wayau, taja yusuf sosai a jikinta sakamakon mahaifiyarshi bata gidan duniyar ma gabadaya A bangaren yusuf kuwa sam bejin dadin yadda yallabai ke nuna karara yafisonshi akan yayyenshi ba, dan yasan hakan ba karamar kiyayya ze jawo mishi ba a matsayinshi na Auta a gidan, kuma wanda ya pita dabaan da sauran en gidaan domin mahaifiyar shi ba er kasar nigeria bace er ethopia ce, shiyasa sam be cika zama cikin gidan ba ko kafin yayi aure, yau yana waccan kasar gobe yana wannan Gidan mami (qanwar mamanshi dake saudi) ne kadae yake zuwa ya dade ya sake,,, Sai yamma Yallabaai ya barsu dan su tapi shi a cewarshi bai gaji da ganinshi ba, sun tattauna business matters a inda yallabai ke jaddada mishi lallai ya cigaba da kula dan kusan rabin kasuwancinshi a hannun yusuf yake, danma shi yusuf din yaki yarda ne da tuni ya sakar mishi kusan komai, amma sai ya nuna mishi ai ga sauran en uwanshi nan kuma mostly maza ne suma suna buqata.... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 04: Mint's Husband Private plane sukabi shida dumbin securities dinshi, tarbar mai kyau mami tayi musu sai nan nan take da minnatu a matsayinta na matar yusuf, Abincin da akayi serving nasu ya dan taba kadan duk yaji be mishi dadi, dandanon nata yapi mai kowanne yanxu, Sae bayan an kwashe abincin yace da mami ta nunawa zainab (wacce ya gabatar da ita matsayin qanwar minnatu kuma personal cook dinshi a yanxu) kitchen ta dafa mai abu mara nauyi yaci kamin ya kwanta, haka kuwa akayi seda tayi mishi girki sannan ya samu yaci ya koshi, kashegari shi da kanshi yace ta shirya ze kaita gidan Anty hawwer, ya shiga dakin da aka sauke minnatu "zanje nakai zainab gidan yayarta ko zaki rakamu?" Ya tambayi mint tace a'a taja blanket ta rufe fuskarta alamun bacci bae isheta bama, ya girgiza kai kurun,, shima yanaso yaje su gaisa da muzakkir din dan haka suka tapi da mota daya, shi dama ba wani son wannan convoy din yake ba yallabae ne be yarda dole se ya dinga yawo da securities A waje suka tsaya yace da zee ta shiga ta musu iso, zee kamar ta sa gudu tadae yi sassarfa ta qarasa, saedae babu kowa gidan sai nihal da binafat er aikin Anty hawwer Zee tai murmushi "gidan en boko kenan" ta koma tace dashi ya shigo, ya shiga yana cewa "muzakkir din baya nan ne" tace eh duk basa nan Ya dau waya yace da securities din su tapi ze taho anjima, Ruwa da lemo ta kawo mishi ya sha ruwan kadan, sai taga yayi relaxing kan kujerar yana kallon news, harda daukan remote ya kara volume, tace "kana bukatar wani abu? Yace no, so nake na dan huta ni kadae na gaji da hayaniyar securities, duk inda kayi suyi ta binka" ta jinjina kai tana dan jin nauyinshi Lura da hakan dayayi ne yasa yace "zo" ta kalleshi, zo? Ta maimaita a ranta, sae kuma ta miqe daga kujerar datake ta koma kan capet kusa da kafarshi, yayi en danne danne a wayarshi sannan ya miqa mata wayar, garin karban wayar hannayensu suka hadu, taji taushin fatarshi it was wow "Dubamin apartments dinnan wanne ne ginin shi da tsarinshi sukapi kyau a naki ra'ayin" ta soma dubawa a hankali, da gani kasan bana kasarmu bane, "Sir wannan yapi kyau" ya gurgiza kai, "don't call me sir again" ta daga ido ta kalleshi yayi nodding ta sauke idanunta, to me zata kirashi idan ba sir ba, Ina kallonki matsayin er uwar matana, bugu da kari u re my personal cook, nd that makes u someone close to me. A haka ya saka zainab ta saki jiki dashi, ganin lokaci ya dan ja yasa tace zata hadamishi lunch mai sauki, haka kuwa akayi ta kammala ta kawo mishi ya sakko ya baje ya ci abinshi cikin jin dadi, abin mamaki duk dadewar da yayi gidan Anty hawwer minnatu batama san bai cikin gidan mami ba balle ta daga waya ta kirashi, ta dauka ya dade da dawowa, kammala cin abincinshi keda wuya sae gasu su biyu sun dawo Anty hawwer da Uncle muzakkir, Wani tsalle zee tai ta fada jikin er uwarta, suma su Assiddique suka yi musabiha, nan suka zauna aka danyi hira sannan yace ze wuce, Zainab ke sanar da Anty hawwer yadda zaman ta ke gudana gidan minnatu da kuma matsayin personal cook daya bata, Anty hawwer tace "kice kin sha kwana, lallai ki rike amanarshi dan naga ya saki jiki dake" zee tai murmushi "amma seda na sha gwaji ai, kuma fa ko a kitchen din nashi akwae cctv" "Yes ai yanada gaskiya, danma yanada taka tsantsan da kuma kariyar ubangii amma wadaannan en uwan nashi ai da tuni sun batar dashi, to zakaran da Allah ya nupa da chara ko ana muzuru ana shawo sai yayi" Kwanakinsu hudu gidan mami itakuma tana gidan Anty hawwer, yakan lekota lokaci zuwa lokaci idan yaji yayi kewar girkinta, daga nan sukayi ziyara suka kuma wuce makkah, sati daya sukayi bayan sun sauke umrah suka dawo gida, a lokacinne kuma barrister shima ya dawo, Komi da suka tsara da minnatu ya tapi smooth, aka kammala shirya hadadden asibitin da akayiwa ado da kayan aiki wadatattu, hakan yasa aka budeshi sannan ta fara aiki, makaranta ma ana jira sunfara diban sabbin dalibai Dadi kam gurin minnatu kamar kamar me, Satinta daya da fara aiki, duk taji yusuf ya gundireta babu damar tayi bacci zezo ya dameta, a nashi bangaren shima halin minnatu yana damunshi babu damar yazo neman hakkinshi zata fara complain ita a gajiye take blah blah blah.... Suna falournshi tana danne danne a system, zainab na serving dinner yace "Sweetheart inada labarin da zan baki" ta dago a kufule "haba star wae meye haka, Allah ka fiya surutu" he was stunned, ya miqe a zuciye yace da zainab "serve me upstair" zee ta bishi da kallo, ko ba'a fada ba ranshi ya baci amma mint ko damuwa batayi ba ta cigaba da abinda take Zee tai serving mint ta ajiye kan dining nashi kuma ta dauka ta haye sama dashi, ta kai mishi har inda yake tana mai yi mishi murmushi, lokaci daya duka bacin ranshi yayi disappearing, yaji tamkar ta zuba mishi ruwan sanyi ne kan tafasasshiyar zuciyarshi dake hayaki, ta zauna ta tankwashe kafa kamar yadda yayi shima tana facing dinshi yana cin abincin yana dagowa lokaci lokaci yana kallonta, yana kammalawa sae ga mint ta shigo a shirye harda jakarta tace "star inada emergency zanje na dawo maybe kuma a can zan kwana" ya jinjina kai "a dawo lpia" Daga haka ta fice, zee ta miqe ta kwashe kwanukan dayaci abinci, tana kitchen tana ajiyewa sae gashi, ya jawo kujera ya zauna, ta dan kalleshi kadan tae murmushi sanda ta gama sannan yace tazo palournshi na sama A kan couch ta sameshi yana danna system hannunta rike da bowl na fruit salad ta karasa ya jawo dan karamin table ta dora a kai, taje ta dakko pick ta ajiye mishi, ba dan qaramin birgeshi tayi ba, shikam duk me kula da cikinshi ya gama mishi komi, Ta zauna kusa dashi with a smile on her face shima yayi murmushin calmly and brief, "so how do you know this Assiddique need something to taste while working" tai er dariya "afterall its my duty, added to that its my pleasure to serve a unique person like you" Ya kalleta sannan ya soma kai fruits din baki "tell me more how unique am i?".... "U re not only unique, u're amazing, u re simple, kindhearted, and u re cool" ta karasa fada muryarta low Interestingly yake nodding, ko mint bata ta6a yabonshi haka ba, kuma a yadda yake kallon zee sanda tana fadi he knows the words re coming straight from her heart, she's the first person da cikin kankanin lokaci taga farinshi har take yabonshi with outmost sincerity, Ya dan dauke hannunshi daga kan system din sannan yace "na maida ke personal cook dina and u didn't inquire about ur salary why?" Zainab answered him with "U told me u spoke with my uncle (Abbah jabir) about me being your personal cook, hakan yasa ban ja ba bankuma ce komai ba dan nasan duk abinda ya yanke daidai ne" ya gyada kai sannan yace come closer, ya fada yana matsawa shima gun system din,zee ta matsa ya soma mata explaining aikin dayakeyi da en abinda zata tayashi, sun shafe kusan 1hr suna aiki, hakan ya tabbatr mata he trust her, shima yasan yayi trusting dinta yanxu tunda already ya gwada ta kuma ya lura da motsinta, yayi observing nata from the first day she came to the house dukkuwa da cewar bai nan.... After like a month komi na mint ya kammala ta soma zuwa school kuma tana aikin data kwallafa duk wani buri na rayuwarta a kanshi, babban burinta bae wuce taje interview gidan tv ba sunanta ya rabu dana Assiddique kuma a medical doctor itakm burinta ya cika, jin kanta take tamafi Assiddique din, dan ita kadae tasan abubuwan datae dan ta ganta cikin gidan Assiddique Tafiya ce ta taso mishi ya sameta a daki tana shirin aiki, "Dear na miki maganar tapiyata and u show no concern" tace tana daura agogo "u re free mana star u can fly to any where u want to, nima next week ina da conference da zanyi attending and its a must" "And u didn't feel its necessary to mention it to me, se yanxu?" Ta yatsina fuska "sometimes in kana behaving kmr mara ilimi wlh" his face turned red, amma yayi kokarin calming kanshi ya samu kujera ya zauna ta tallapi chin dinshi da hannu biyu, Bata damu ba ta kama hanyarta tai waje Wacce irin mata ce ya aura haka, konda wasa besan haka take ba, if not baze soma aurenta ba, gabaadaya baza'ayi conversation na minti daya da ita ba bata fadi wata baqar maganar ba, imagine calling ur husband mara ilimi, Ya furzar da iska sannan a hankali ya zame yayi relaxing kan kujerar, It is the one thing he lacks all his life, ya dauka idan yayi aure ze huta ze samu abinda yayi lacking amma it never seem to happen, he lost his mom even before he know her, 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 05: Bussiness Trip Assiddique ya sanar da zee mgnr tapiyar da zasuyi tace mishi to amma barrister baze bisu ba saboda ze zauna nan ya kula da wasu harkokin, Kudi ya dauka ya bata yace taje tayi siyayya dan yanajin zasu jima in suka tapi, kwanaki biyu bayan nan komai na tapiyarsu ya kammala, ya debi wasu securities din ya barwa minnatu wasu, ko kadan ba wani son tapiyar nan takeyi ba musamman da taji zasu dan dade dukkuwa da btasan wacce kasa zasuje ba, Mota uku sukayi, yana ta tsakiya a baya itakuma zee a gaba sae driver, sanda suka shiga plane baccinta tayi batasan sun karasa ba, har suka isa masaukinsu bata gane inda sukazo ba, Irin Apartment din data zaba tace yapi kyau sak shi taga sun sauka, bangaren security na gefe sae ciki kuma daki biyu da falour a tsakiya sannan kofar kitchen, ya nuna mata dakinta shima ya shiga nashi, tana cikin unpacking ne ta zaro frame din, a hankali ta sule ta zauna kasan dakin, its exactly the date, wasu hawaye masu zapi suka biyo kuncinta, ya murda kofar dakin ya shigo, bata san da shigowarshi ba ta sunkui da kai tana shessheqa, ya matso ya tsugunna a gabanta ze zare frame din amma ta rike gam as if her life depend on it, saesanann ta gane yana dakin ta goge hawayenta tana sauke ajiyar zuciya, ya kalleta itama ta dago ta kalleshi, why re u crying? Do u miss home? Ta girgiza kanta, ya lura batason fadamishi komai sae bai matsa mata ba, i hav meeting to attend now, Ya fada yana miqewa tsaye, a sanyaye itama ta tashi "pls akwae kayana a daki hop u wont mind unpacking them" ta gyada kai, yace "do you know where we re?" Ta girgiza kanta yace "europe" da sauri taja baya kamar ya zuba mata ruwan attaruhu jikinta ya soma 6ari, Tai kokarin saita kanta tana sauke numfashi kamar tayi kokawa da en dambe, yace se na dawo, hop ba wani matsala? Tace no babu, yace good I will wake u up when im back" tace okay yace take care Ta koma da baya ta zauna kan gadon da6as, "europe" furucin ya fito tareda ruwan hawayenta, a hankali wani tunani ya shigo ranta, sae taji saukin tsoron daya mamaye ta, kuma taji tamkar tayi tsuntsuwa ta fita ta dinga bin lungu da sako na garin ta dauki frame dinta ta rungume a kirji, sae ta ajiye ta nemi bandaki tae alwala, ta gabatar da salloli sannan ta dade tana jera addu'o'i, ta miqe ta karasa gyara nata kayan sannan ta wuce nashi dakin, komi neat kayan ne kawae ba'ayi unpacking ba, zee a ranta tace "Allah wadaran mata irin mint dae, Ace kanada mata amma bakasan dadinta ba, mata mara kishin mijinta, har ta yarda ta barshi ya taho wata kasar shida wata batareda ta damu ba Ta soma gyara mishi kayan nashi a nutse, ta kammala komi, sae ta tsinci kanta da sake gyara mishi dakin, ta dan kara abin kamshin daki, juyowar da zatae ta ganshi tsaye bakin kofa tae saurin jaa baya da farko saboda ta razana sae kuma murmushi ya biyo baya dan gajere, Yace "its late i thought ma kinyi bacci" "U work day and night without complain, what's there when i overworked too, afterall u re the boss" Yaji dan dadi cikin ranshi, she cared, "I need something simple pls, my stomach hurts", tai brief smile, sannan ta wuce kitchen din, 20 minute yayi mata yawa tayi preparing noodles ta kai mishi, tare suka zauna sukaci abincin dan itama bataci ba, ta kwashe kwanukan yace ta dawo ta tayashi aiki, tace to Zama sukai suka baje a falourn, inda yake mata bayanin ayyukan da sukeyi na kafa reshe anan din dan cigaban kasuwancinsu (anya zee iya aikin personal cook kawae take mishi) Har karfe 12 na dare zee ta soma haamma ta dan saci kallonshi, Gabadaya he's focused kan abinda yakeyi, babu alamar ya gaji, ta jinjina kai tunda ubangida bae gaji ba matayi ma bayace ya gaji ba, suka cigaba Yace akwai takardu a daki ta dakko mishi suma so yake ya gama aikinsu yau, kamar zata fadi saboda bacci haka take hada hanya Tana shiga bedroom din taji wani sanyi da kamshi, ta kalli gadon da ta gyara dazun sae taji muradin dan kwanciya,,, Mintuna fiye da 15 sun shude amma bata dakko ba, shidae a iya saninshi takardun a bayyane suke be musu wani boyo ba, ya miqe ya nupi dakin, ya murda kofar dakin, murmushi mai sanyi ne ya subuce mishi ganin ta kwance kan gado tana ta barci abinta amma kafafunta a kasa, ya karasa ya kura mata ido, tana bacci peacefully, a hankali ya gyara mata kafarta ya maida sama sai kuwa tayi juyi ta kuma bararrajewa kan gadon, ya lumshe ido sae yanxu dayaga tana bacci yaji wani gajiya da son yin bacci, ya fita falour ya miqe kan resting sofa ba dadewa shima baccin ya daukeshi Koda Asuba bae samu sallah ba dan ya makara itakuma da magagi a idonta tai sallahr tana idarwa tabi kan daddumar abinta bakinta dauke da lazumi baccin ya dauke ta, karfe 10 ta farka tana tasbihi, ta bude idanunta tangaran, ta dubi agogon dake dakin sae kuma tabi dakin da kallo, kamar wacce aka tsikara ta miqe daga kan daddumar, sannan a hankali ta soma tuna abinda ya faru, ta fita a dakin ta taddashi a falour yana ta bacci kan resting sofa, ta qarasa nesa kadan dashi tana kallonshi, a hankali ta girgiza kai "may you find eternal happiness in life u deserve it" the guy is the real definition of gentle Dakinta ta koma tai wanka ta sauya amma harta fito be tashi ba dan haka ta shiga kitchen dan dora mishi abin kari kafin ya tashi, da duba babu wasu en abubuwan dan haka ta fita gurin securities Ta sanar dasu babu wasu abubuwan kuma tanason mishi girki kafin ya tashi ne, daya daga cikinsu yace ze rakata ta siya dan yakan basu kudi koda wani abu zeyi araising in be nan, ta koma tai rolling kan pink abayar jikinta, Mall ne amma in ka shiga kamar kasuwa kanta kanta abubuwa daban daban kusan duk abin cefane akwai wasu ma mutun be sansu ba, ta sissiyi duk abinda zata buqata harda wasu spices din datake nema a nigeria ma duk ta samu A hanyarsu ta dawowa ne wani bature yayi ta binsu dayake a kafa sukaje babu nisa sosai kuma itama zee din tana so taga garin, security din yace "mu tsaya suka samu gefe sukaja suka tsaya, ba kunya kuwa ya karaso su, se washe wa zee baki yake, zee ta turbune fuska hakan yasa security ya rungume hannayenshi yana kallonsu dan ba karamar dariya ke cinshi ba "U re beautiful dear" baturen ya fada da yaren nasara, ta kara hade rae tana yiwa Afzal(securityn) signal ya korar mata shi amma shikam bayaso show din ya kare tun yanxu Bata iya amsashi ba ya kuma cewa from which country? And where do u reside?" Taji tamkar ta shaqe shi dan haushi kawai sai tai gaba fuuuu Hakan yasa Afzal tsaidashi yace matar aure ce kuma babban soja take aure, ya zaro id ya nuna mishi da cewar shima security dinta ne, a fusace ta bude kofar falourn ko lura da bayanan ma batai ba ta zauna tana ciccin magani, Afzal ya kwankwasa kofar sannan ya shigo shima, yana ganin yadda take kumbure kumbure sae ya fashe da dariya, kuma fa gayen ya hadu" ya fada da sigar tsokana ta sake murtuke fuska, bude kofar dakinshi yayi ya fito, sanye da jallabiya da alama har yayi wanka ma, Afzal ya miqe yayi mai salute sukai musabiha sanna Ya ajiye kayan ya fita, utama ta tsugunna ta gaidashi bae amsa ba strictly yace "wanne gaye ne yake magana" zee ta dan sassauta bacin ranta "wani bature ne ya dinga biyomu abin haushi", Ya miqe "karki kara fita" ya wuce, zee ta dan yatsina fuska "kamar ranshi ya baci".... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 06: Blessed hands Ta dauki kayan cefanen ta wuce kitchen wondering about his mood, baya bata rae har haka musamman yadda ya bayyana kan fuskarshi karara, kuma bata ga aabin bacin rae ba, Tana chopping Onion ya shigo kitchen din, she's deep in thought da batama san da shigowarshi ba, ya karasa gurin dispenser ya tari ruwa yana kallonta, is like she enjoy loosing in the world of thought, ganin onion din datake chopping ya kare batama sani ba tana kokarin yankan hannunta, yasashi ajiye ruwan hannunshi ya isa gareta yana mai rike hannunta wanda wukan take, ta dago ta kalleshi a dan razane, ya saki hannunta, "What in the world re u thinking about" ta ajiye wuqar ta sunkui da kai, "life's dynamic" ta fada a takaice da rashin son yin wani karin bayani, ya juya ze wuce tai saurin cewa "Im sorry" ya juyo ya dubeta "about?" Ya tmbya da sakakkiyar mind, sai kuma ya dawo inda take, ta sunkui da kae tana wasa da fingers dinta, a hankali tace "dazu naga ranka ya baci kuma na pita ne saboda akwae abin da zan siya babu" yace is okay, What re u preparing ta kalli kayan cefanen da ta ware wanda zatai amfani dasu "scrambled eggs croissant" ya samu guri ya zauna Ya akeyi?", tace its simple, bowl din data fasa kwai me yawa ta dakko ta ce kagani already na fasa kwai da dan dama, sannan na saka ingredient din danake buqata, ta dora saucepan kan low heat sannan ta zuba kwan tana juyawa a hankali sae gashi ya zama scrambled, ta tabbatr yayi ta kashe wutar sannan ta dakko croissant din ta ska a oven ta danyi preheating a oven ta fiddo shi tayi spliting amma ba duka ba yadda ze dan bude sannan ta zuba scrambled eggs din, guda hudu tayi musu tayi plating me kyau, ya tayata dauka itakuma ta dakko mugs din da zata masu tea, kamar wasu brother and sister suka zauna sukaci abincin, Bayan sun kammal ta kwashe yace taje daki ta dakko takardun jiya in kuma tayi bacci to" Tayi er dariya cikin jin kunya ta wuce ta dakko ta fito, ya amshi takardun ya miqe qafa dama kan carpet yake already, zee ta lura yana qaunar zama kan carpet, Itama ta zauna ta facing nashi kamar yadda sukeyi, maimakon yayi mata bayanin aikin da zatae sae ya Amshi takakrdun ya ajiye a dayan side dinshi, sannan ya kalleta, yace "tell me about ur family i heard u re an orphan" zee sunkui daa kai tana tuna abubuwan da suka faru iri iri," tai shiru kamar bazwtace komai ba sae kuma ta mishi bayanin kanta da iyayenta da danginta (sae a gaba me kaaratu zeji komi), yayi shiru yana sake jimanta mata rasuwar iyayenta sannan ya bata haquri ganin da yayi kamar da dawo mata da abin sabone yadda idanunta ke zubda ruwan hawaye, Wannan yasa Assiddique tunanin maybe shine dalilin dayasa take kuka rannan daga haka suka cigaba da aikinsu Rannan yana falour be dade da shigowa ba, zee tayi bacci already dan mostly meetings dinsu se da re sukeyi, wayarshi tae kara yaga sunan mint ya bayyana, wanann shine karo na biyu data kirashi tun zuwanshi kusan sati biyu kenan, sae dae ya kira yaji ya take wataran ma in ya kira bata dauka kuma bata biyowa hakan yasa ya rage yawan kiranta, ya daga wayar yana tunanin da wacce bukata kuma tazo yanxu, Kamar tanajin bacci take maganar kasa kasa, her voice is one of his fav, "star ya kake?" Ya amsa da Alhamdulillh, tace ka duba net yau nayi hira da Arewatv, mantawa nai ban fada maka ba, kuma gobe zanje kano yin wani aikin" Yaji ranshi ya soma baci "amma kinsan ke matar aurece ko?, meyasa in zakiyi abu bazakina neman permission ba" tace permission kuma sekace a kulle nake" yayi ajiyar zuciya a hankali yace "karki sake ki fita daga garin Abuja" ta dan kara sautin muryarta "me kake nupi kenan, haba kaima wasa kake wlh, nagama arranging komai tafiya kuma dole ce, yace nidae na fadamiki, tun kafin ya kashe wayar ma ita ta katse tana tsaki Zee ta fito daga dakin da nighties a jikinta tana hamma idanunta a rufe da bacci sosai, ta karasa fridge ta dauki ruwan gora, ta bude ta samu guri ta zauna tana sha, ita batasan dashi cikin falourn ba musamman dayake idanunta da bacci kuma wutar falourn a kashe take, shikuma tunda ta fito yake kallonta, ganin yadda ta zauna tana shan ruwan yasa shi dariya ya murmusa cike da birgewa, bata shanye ruwan ba kuma bata rufe gorar ba Ya karasa ya karbi gorar ganin zata iya zubda ruwan, yace tashi ki koma daki" ta wuce abinta ya bita da kallo, Abu daya yayi realizing a yanxun, mint na batamishi rae zee take shigowa picturen ta gyara mishi mind dinshi that made him feel good, he feels great for having her by his side" Kwana biyu bayan nan, da maraice suna waya da barrister, zee ta fito falourn alamun tayi wanka ne sae bulbula kamshin arabian perfume dinta take, gabadaya attention dinshi yana kanta sae yaji ma kamar be gane bayanin da barrister ke mishi, ya miqe ya barta a falourn, itakuma ta kwanta kan kujerar ta chanja channel tana kallo, sae bayan ya gama waayar ya dawo falourn, ya shigo kallo daya yayi mata ya dauke kai ya zauna ta kalleshi tace "yaya_na yaushe za'a fita dani naga gari" be kalleta ba yace "babu inda zakije kina gida, in wani abu kike buqata ki bada a siyo miki," tace "a'a bakomi kawae fita nakesonyi, yace "NO Shiru ya ratsa dan tun zamanta da assiddique be taba bata ranta ba se yanxu da ya dage babu inda zataje kuma gashi tana so ta fita din, ta miqe daga kwancen zataje daki yace zo, ta dawo ta zauna, acct. Details dinki nake buqata, ta bashi yace "ki shirya anjima da dare zamu fita amma ki samu hijab ki saka" taji dadi har ranta tace "to Taji dadi yadda yake protecting dinta kamar kanwarshi, koba komai tasan tana da muhimmanci itama a gurinshi ba iya matsayin cook ya dauketa ba, Ta dakko wayarta ta bude mishi tace "yaya_na kaga hirar da ya mint tayi a gidan tv", sanda mint tace ya duba ya gani sam yaji beson gani amma yamxu da zee ke son nuna mishi sai yaji muradin gani, Tare suka kalla hirar, farko tayi shigar less (lace) coffee da pitch sae dae dinki ya kamat gashi wuyan off shoulder ne, duk kirjinta a waje, hakama kanta ta zame dankwalin gaban gashin kanta ya fito hakama jelar attach din ta baya ya fito, gyalenta kuwa a tsintsiyar hannunta yake babu amfanin dayakeyi, ya girgiza kai, Al'amarin mint se ita... Zee batta da hijab kato dan duk kusan abaya ne ta taho dasu, dan haka ta saka wata A_line gown wacce ta fidda shape dinta ta material, sannan ta dora hijab din a jikinta ya tsaya iya cikinta, ta kalli kanta a mirror ta girgiza kai ta dakko wani gyalen ta dora akan hijab din daga shoulder, Tana fitowa shima yana fitowa ya gama shiryawa ya kalleta yace banason gyale ta dan bata fuska "hijab din beda tsayi ne" yace to dakko free Abaya ki saka, Ta koma ta chanja zuwa abaya da hijab din in complete black, yace yawwa better, suka jera suka fita da securities Zainab taita kallon hanya ko zataga wanda ta sani, sunje gurare sosai, zee taji dadin fitar shi kanshi ma haka, suka nemi ice sweet ya siya mata yace "taste it its good" ta karba tayi tasting, shima ya karba yasha, yes its nice yace yh, suna tafiya yana irga mata restuarant, duk arean da sukazo ze fadamta restuarants din da suke arean sedai in sun tashi ne ko kuma an sake sabbi, sun irga su sunpi 50, a wajesukayi dinner sai wajen karfe 11 suka dawo gida a gajiye, suna ta dariya duk suka fada kan kujera, saeda ta huta sannan ta dauki chocolate din daya siya da wasu lemuka ta kai deep freezer, tana sakawa ne yace "dazu baki tambayeni dalilin dayasa nake irga miki restuarant ba, ta juyo ta kalleshi "obviously i thought its because u like their dishes" ya girgiza kae "No Na irga miki su ne just to tell u the taste of ur dish is totally unique, different from all the restuarant i know, ur hands Ta kalli kalli hannayenta yace "yes ur hands are blessed" and she blushed.... Kashegari tana tashi data kunna wayarta taga alert, ta bude tana murna anyi allawee (kudin da ake biyan coppers), amount din data gani yasata sanin wannan kudin ba daga FG bane, ta duba wanda ya turo Abubakar kawae ne a name din kuma its like a company, Ta cigaba da harkokinta amma abin na ranta, suna zaune suna break tace "yayana kaga wani abin mamaki, an turo min kudi kuma na rasa gane waye" ta dan daga mata hannu sae ta tuna in yana cin abinci bae magana, ta cigaba da cin nata abincin itama, sae bayan sun gama yace "first salary dinki ne as the personal cook of this YUSUF ABUBAKAR ASSIDDIQUE" sae yanxu ta tuna jiya fa ya karbi Acct. Details dinta, tae shiru tana so tayi korafin yawan kudin sae yace "karkiyi tunanin na karamiki ne haka kudin suke, ko waccen cook din tawa ma haka nata albashin yake" a cikin ranshi kuma yace saedae nakki harda karin allowance, u re more than a personal cook, 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 07: more than personal cook Godiya sosae tayi mishi sannan yace "kinfi karfin haka gurina, i feel like u re my best friend someone i can feel free with, kinsan harkar manyan nan se a hankali, u don't have time, u dont have friends, babu wani lokaci da zakayi spending naka na kanka its all on bussiness, buh still u manage to make me feel good all the times" Kwanaki biyu bayan nan suna hirar wani film da daddare yace "off the tv i want ask u something" ta kashe tvn sannan ta maida focus dinta gareshi yace "baki da sha'awar kara karatu i mean second degree" zee har ranta bata wani muradi amma take taji ra'ayinta ya chanja sakamakon wani tunani daya fado mata, tace ina muradi, munyi magana da Anty hawwer kuma tace idan na gama service na koma gurinta se na cigaba" yayi shiru ya zuba mata ido "Noo bazakije gurinta ba zanyi kokarin settling sae na nema miki school" "Gobe akwae bakin da zamuyi na gayyacesu suzo nan muyi meeting din dan na gaji da cin jagwalgwalon da suke serving gurin meeting so nake ki zage ki mana snacks masu dadi, yadda zasuji kamar su taune hannunsu, i know u offer the best" tace "in shaa Allah" Zama tai ta nutsu ita daya tayi list na abubuwan da zatae sannan ta mishi presenting yace duk sunyi, sae ki duba abinda babu a kitchen kiyi magana na bada a siyo, itakam daso samu ne suje tare da me siyan amma tasan baze barta ba, ta nemi takarda tayi list na abinda take buqata ta bada, komai ya kammalu, ranar tun da safe ta shiga kitchen ta saka Apron sanin datai aikin ba na mutun daya bane, dukkuwa daba yawa garesu ba amma ta shirya yin varieties iri iri, tana cikin rolling flourn ya shigo tace "yawwa pls taimaka min ka dauremin" ta fada tana nuna mishi Apron din data kwance kuma hannunta duk flour, ya karaso, a hankali yasa hannu ya kama igiyar, sannan ya daure idanunshi a kanta, Bayan ta kammala wadannan ne ta koma kan drinks ta debo wasu chocolates din da suka siyo tayi garnishing chocolate milkshake din da tai, sannan ta ajiye a fridge dan lokacin yamma maa tayi, gabadaya baya gidan ma shima yana da aikin tun kafin azahar ya fita da tuni yana nan yana tayata koda surutu ne, Sae after magrib ta tapi yin wanka duka komai ya hadu ta kowanne bangaren, Shikuma tunda ya shigo yaji kamshin dadi ya koma nashi dakin yayi wanka ya fito ya sauya ammaa daya fito falour be ganta ba, waayarshi tae kara bakin suka sanar dashi sun karaso, ya fita yaje ya tarosu, yaa kaisu kebantaccen gurin dayasa aka danyi decorating sannan ya dawo still bata falour ya kira sunan ta amma shiru, ya kwankwasa kofar dakinta still shiru ya murda kofar dakin abinshi, tana zaune kan dressing mirror da waya a kunnenta suna ta hira tana nishadi da batama san ya shigo ba Towel ne a jikinta, gashin kanta data wanke ya kwanta a gadon bayanta yana digar ruwa ya rufe bayan nata ma, ta sauke wayar a kunne tana kallonshi ta cikin mirror, tayi gyara murya tana jawo wani towel din ta rufe kanta, yace "ki dan hanzarta sun iso fa" sae ya juya ya fita da sauri kamar zeyi tuntube, Tai saurin miqewa ta shirya, dan ko mai ma bata shafa ba, tunda ta fito a wanka zeenat(her bestfriend) ta kirata suke ta waya saboda sukan jima basuyi waya ba dan bata nigeria tun watannin baya da akae bikinta, mostly sunpi haduwa ta chat Suna zaune ta karaso tana ta kamshi mai sanyi na arabian perfumes din, ta musu presenting snacks din sannan tayi plating ma kowansu cikin jan hankali, tana cikin aikinne dayansu yayi magana da yaren nasara "your wife is gorgeous, i like the colour of her skin" ta dago a hankali ta kalli yusuf, shima ya kalleta fuskarshi babu yabo babu fallasa, bayan ta gama ta wuce suna mata godiya, ta tsaya gaban katon mirror n dake falourn, gabadaya jikinta a rufe yake ruf, face dinta da tafikan hannayenta ne kawae a waje, kenan fuskarta ya kalla har ya gane skincolour dinta. Kuma yace his wife amma be gyara musu da cewar ba matarshi bace.... Rannan suna falour sunata faman aiki, ya kalli yatsanta yace "your ring" ta dago da sauri ta rike yatsan da zoben yake, "who gave you" ta saki yatsan tace Ammi Be sake tofawa ba se can yace "yau zamu fita and in the next three days zamu koma gida" farinciki ya bayyana karara a fuskarta Allah ma ya sani tana son komawa nigeria ta gaji da kasar turawan nan Suka shiga katon mall din, zee tayi iyakacin kokarinta kar tayi kauyanci ya dinga lodo mata kaya dan ta tabbatr ba nashi bane saboda idan ya dakko abu guda biyu ze tambyeta wanne tapiso in ta zaba ze debi irin shi kamarr guda 4 ko 5, atlast suka karasa gurin perfumes, yace "i like ur scent, zaki iya fadamin sunan perfumes dinki inaso nima na dinga amfani da irinsu" Nan ta nuna mishi su harda wadanda suka fi nata kamshi da tsada ma duka ya siya da nata da nashi, haka suka dawo gida Sun kammala duk shirye shiryensu ya fadamata wadannan kayan natane yanaso tayi tsaraba dasu taita godiya kuwa har saeda yaji dadi a ranshi As scheduled suka koma gida nigeria kamar yadda suka tsara, ranar sunsha tarba daga jama'ar yallabai se kace ba business trip yaje ba, a gajiye ya koma gida ya tadda mint tana ta bacci, ya dubi wristwatch din hannunshi, karfe 4 ne na yamma, kuma tasan sarae ze dawo amma ta kama bacci, ya shiga bathroom yayi refreshing ya fito, abincin dare yayi musu ordering dan yasan zee ta gaji kuma beson takura mata, a bangaren zee itama wanka tayi ta kimtsa wasu kayan da suka dawo dasu, ta ware wanda zata bada laundry, Tana cikin aikin raba tsaraba ya kira wayarta, its after isha'i ta dauka yace taje, tana zuwa ya bata abincin ta cikin takeaway ta karba tayi godiya tayi mai saeda safe, yace no coffee? Tai murmushi tace later? Yace yeah... Ta koma ta cigaba da aikinta sae da tagama warewa kowa nashi tsaraban sanana ta zauna taci abincin, tana kammala wa wayarshi na shigowa Tasan tuni ne zeyi mata dan haka taqi dagawa ta tashi ta tattara gurin ta wuce kitchen, tana cikin aikin ya shigo, ya zauna suna hira jepi jepi, ta gama ta bashi nashi itama ta zauna tasha nata a nan, ya ajiye mug din da fadin "jazakillah bi khair" ta amsa da Amin, sannan yace "goodnight" Yana shiga dakin mint ya taddata falour tana cin abincin tayi mishi killer smile datasa ya manta da duk haushinta dayakeji, welcome home Star Yace "thanks my dear ya zauna kusa da ita, bayan ta kammala ta jawo system yace bacci nakeji, ta fahimci me yake nupi sae ta share da fadin to kaje ka kwanta, yayi shiru yana kallonta "ke bazaki kwanta ba" ya tambaya tace eh inada aiki da zanyi ai ban dade da tashi a baccin ba, Ya matsa kusa da ita yayi whispering a kunnenta, tayi murmushi wanda yayi kama da na mugunta tace sedae na rakaka kai bacci se na cigaba da aikina yace eh naji, Suka tapi daki, yayi juyin duniya duk abinda zeyi yaja hankalinta amma taqi tana bashi uzurin seta gama aikinta, daga karshe yace ya yarda to ta gama aikin ze jirata, ta koma falour ya biyota amma ko a gefen slippers dinta, atlast se bacci ne ya daukeshi kanshi a kafadarta..... Kuyi haquri da wannan, biki tinz 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 08: Asma'ul Husner Gabadaya yusuf ya fita harkar mint dan yaga alamun aikin ta da karatunta sunpi mata komai, Yinin yau zee bata saka yusuf a idonta ba, ko breakfast baice ta hadamishi ba, ta tura mishi list na abubuwan da zatae ya zaba kamar yadda suka saba amma beyi reply ba, kuma da alama be gidan, mint ma bata gidan se ita daya, Da yamma likis mint ta dawo, lokacin zee na kitchen, suka gaisa sannan tace "girki ake tayi kenan in kin gama ki kawomin nawa falourn Star na kasa" Sae after magrib ta kammala taje ta kai ma mint nata sannan ta koma daki, tana shiga taji alamun shigowa cikin gida tae saurin fita bolcony ta leka, motocinshi ne suka shigo, taji dadi a ranta dan ta damu da bata ganshi yau din ba, tun kafin ya shigo gidan ta fita kitchen tayi warming hadaddiyar rice din da tayi sannan ta soma yanka salad Ta kammala hadawa duka ta tapi taje falournshi inda yace ta dinga serving ta ajiye a spot din datasan suna zama cin abinci, tana cikin jerawa taji karan steps, ya sakko sanye da kaya masu sauki, ya karaso har gabanta fuskarshi dauke da murmushi, ya zauna ya tankwashe kafa itama ta zauna tana mai gaidashi ya amsata sannan ta soma serving, ya kusa kammala cinhe abincin tace "ya aiki ya gajiya, yau gabadaya banyi aikina a kitchen ba sae yanxu" ya dago tana goge bakinshi "naje gurin yallabai ne tun safe, na dauka zan dawo da wuri amma abin yaci tura" tace "Allah yayi jagora ya bada sa'a cikin al'amura" ya amsa da amin, ta debe kwanukan zata wuce yace ki kai ki dawo tace to A gaban system ta sameshi yana ta aiki, ta karaso ta zauna gefenshi tana tayashi da jera wasu taakardu, dan yanxu ta san mafi yawan ayyukanshi yadda yakeyinsu, suna tsaka da aikin ne tace "ina neman alfarma ne" ya janye idanunshi daga kan screen din ya kalleta "gameda me fa?" Ta cigaba da aikin tana mai bayani "inaso naje kano ne na kai tsarabar da ka siyo min saedae kuma bansan ya za'ayi data anty hawwer ba" Be ce komai ba har suka kammala guraren 12 na daren yace "i will think about it" Mint kuwa tun sanda taji alamun shigowarshi ta shiga wanka, saboda tana so tayi spending quality time dashi amma data fito ta leka se ta tadda shi yana cin abinci tare da zee, taita jiranshi shiru shiru, ta leqa again taga suna aiki, ta koma ta cigaba da jiranshi amma be zo ba har tayi bacci Sae sannnan mint ta lura yusuf ya pita harkokinta gashi en kwanakin nan wata kewarshi take ta rasa dalili, kuma sae ta soma jin haushin zainab, Tana zaune tana mamkin jin gidan yayi shiru, sanin da tae aikinta sae yamma yasa tun asuba ta koma bacci bata tashi ba sae yanxu karfe 1 na rana, ta fita kitchen amma babu alamun anyi girki yau, ta shiga part din zee taga ba kowa a gyare tsaf, yusuf kam bataa nemeshi ba dan tasan ya fita ma, Wayarta tai soma ringing, ta dauka tana murnar fanin kiran Anty siyama, suka gaisa tace "meyasa baki biyosu ba?" Da rashin fahimta mint tace "su wa?" Anty siyama tace "mijinki mana shida zee, yanxu suka bar gidana ta kawomin tsaraba ta bawa Abbah jabir kudade dayawa wae albashinta na farko ne" wata ashariya mint tayi Amma yarinyar nan se naci ubanta kuwa, harni zataci amana, duk security babu wanda ze bita in gida takeson zuwa se shi, ni zataiwa bariki, kan ubaan can" haka taita zage zage kamar zautacciya daga karshe ta kashe wayar batama tsaya jin abinda Amty siyaman ke fadi ba, Su zainab kuwa shi da kanshi ya dinga rakata suna bawa en uwa tsarabarsu, har gidan zakiyya ma sunje dasu kubra, khairi kuma da bata garin aka bada nata itama anty hawwer aka aika mata nata ta plane, Plane sukabi suka dawo, Itakuma mint data kashe wayar anty siyama sai ta soma tunanin me zataiwa zainab ta huce, hankalinta ya koma kan abubuwan da suka faru, yadda yusuf ya chanja mata a kwanakin baida abokin hira sae zee Wayarta tai pinging alamun shigowar notification ta dan jawo tana dubawa, a hankali akalar tunaninta suka koma kan calendar ta datai notifying dinta, she's been so busy da tama sha'afa shaf, ta je gaban mirror tana jujjuyawa tana kallan kanta, "what?" Ta fada daa dan karfi ganin zarginta na tabbata, bata tsaya testing a toilet ba ta dau driver suka wuce clinic, da kanta taje lab tace su debi jininta ga test din datakeso suyi mata, nan sukayi kmaar yadda tace, babu jimawa result ya fito, ta karbi takardar tana jujjuyata, wani kyakkyawan murmushi ya subuce mata "she has been pregnant for the past 4 month amma bata sani ba" Ta fita a asibitin tace da driver ya kaita gidansu Assiddique saboda tasan yallabai baya nan, tun a hanya kuma ta kira mami, harda dan kukanta ta hada karya da gaskiya ta fada mata wae Anwar (haka suke ce mishi a gida) bae kula da ita ya maida hanakli kan cook dinshi, sae su kwana biyu bae mata magana ba, wani sa'in in tayi mishi se yana amsa mata ciki ciki, Mami ta bata haquri sanann tace zata kirashi ta mishi fada "yanxu yana ina ke ma kina ina" Ta dan ja numfashi muryarta na cracking tace "ni mami na gaji gsky na taho gidan yallabai, kuma naje asibiti nayi test ina dauke da juna biyu, tun safe yau bani da lpia ashe yabi ta sun tapi kano wae rabon tsaraba" ran mami ya sake baci, ta lallaba ta sanann tace taje gurin momy Taji dadi soaae dan tasan mami wanke shi zatae tas, suna hanyar karasowa gida yaga wayar mami, ya dauka yana murmushi "amma se fadanta ya tadamishi hankali yadda take ta fada kan mint ta kawo kararshi be kula da ita, sannan a karshe ta kare da fadin yaje gida ya dakko ta tana tareda momy" ta kashe wayar baice uffan ba kuma bata sanar dashi maganar cikin ba saedae har ranta tana farinciki da cikin Yayi biting lower lips dinshi cikin rashin jin dadi, wanann abu da me yayi kama, yana shiga gida ya wuce nashi bangaren, zee taga chanji karara kan fuskarshi, ta girgiza kai ta wuce nata bangaren, Ya fito a wanka yaga wayarshi na haske, over 4 missed calls duka kumaa momy ce, ya lumshe ido ya salam, ya girgiza kai "mint shouldn't hav done this, komi ya haqura dashi in tayi mishi amma ya zata hadashi da iyayenshi, ya zauna ya nade kafa abinshi, Kwana biyu amma shiru yusuf baeje ko inda mint take ba, yasan idan yaje yanxu momy se tayi mishi fada, shikam ya za'a na mai fada kan abinda baeyi ba, wacce kula ce be bata ba kuma, koda cewar aurensu hadi ne amma be rage ta da komai ba infact he likes her tun a farkon ganinta dashi sae dae ita zuciya tana son mai kyautata mata, she already wiped all the love, Gobe ake saka ran yallabai ze dawo kasar dan haka sae goben zeje gidan, ya san kuma dole yallabai bayanshi zebi, yayi murmushi, a bangaren mint tunda taji labarin dawowar yallabai a gobe ta hada ya nata ya nata ta komo gidan yusuf ta sani sarae beson lepin danshi Allah yasa randa ce da ita ba ciki ba, babu abinda ya mai zapi indae kan yusuf ne Yana wanka ta shigo gidan dan fita ma zeyi, ta je ta ajiye kayanta sanna ta dawo bangarenshi lokacin ya gama shiri, ya tsaya yana kallonta ta taho gurinshi tana murmushi ya tabe baki ya dau turarenshi ya soma fesawa, tayi hugging dinshi ta amshi turaren ta ajiye ta soma shafar sumar kanshi, im back ta fada yace u're welcome, sae ta bashi takardar dake hannunta, ya karba yana dubawa at once kuma ya mance da komai yana mai bayyanar da faffadan murmushi, "are u serious?" Four month pregnant? Tayi nodding with a smile, Ya yi hugging nata da kyau yana godiya ga Allah, masha Allah, ya xaunar da ita yana matsa kafarta... Da yallabai ya dawo kasar da kanshi yaje yayi mai Albishir zo kuga bakinciki karara a fuskar mafi yawan mutan gidan, shikuwa yallabai ya mata kyautar kujerar makkah guda biyar sannan a take ya zuba mata 5mil a acct. Ranar mint taga gata, Dadi ya isheta ta rikice jin uban kudaden da aka zuba mata a acct., tun daga nan mint ta dinga rashin mutunci a gidan, kuma duk abinta kan zee yake karewa ko zee tapi mai kaulayin shan wahalar cikin wasu abubuwan kuma duk mint tana sane duka dan ta kuntatawa zee dinne se kace ba itace ta nemi tazo gidan ba, se zee ta dafa abinci kala shida mint tana cewa beyi mata ba, amma baiwar Allah bata nuna mata ta damu, dukkuwa da takanji babu dadi Inma sharar dakine sae ta hana kowa shigowa ta dage se zee ce zatai mata, har tausa take mata amma batayi a gaban yusuf se baya gidan, a haka cikin mint yayi ta girma zama da kyar tashi da kyar, addu'a kuwa sosae yusuf ya dage da ita yakuma tilastawa mint yinta dan sanin yawan makiyan dake harin wannan cikin, kujerun makkan da yallabai ya bata kuwa tuni ta rabarma yan uwanta tana fadi wai ita matar billionaire, sanda lokacin haihuwar yayi ta saka aka gayyato wani mashahurin likita daga india yayi mata c.s ya fidda babynta katuwa mace, zokuga farinciki gun yusuf sae hamdala yake wa ubangiji akwae shi da son yara sosae... Wannan yarinya tasha gata ko iya towel din da aka sakata a ciki ma ihun kudi yake, tasan tazo gidan dukiya, akayi suna aka sakamata sunan mami, (Asma'ul Husner) suna ce mata Husner Gurin momy mint ta koma tayi wankan jego, abu daya da suka lura dashi shine yadda babyn batada ishasshiyar lpia musamman zainab da itace ta kasance mai raino dan ko yaushe Husner na gurinta indae mint ta karbeta to abinci zata bata... Na kusa tsayawa da typing dan bana jin ruwan comment, se ku karanta kuyi mukus 😡 nima kuwa zakujini tsit, my wattpad people is it dat had to vote and comment? 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 09 : Selfish Gabadaya a gidan momy t zauna har tayi arba'in kuma tace lallai zee ce meyi mata raino, hakan yasa yusuf kusan koyaushe yana gidan, dan babu yadda za'ai zee tai nisa dashi kodan cikinshi,,,, Bayan Arba'in dinne ta shirya zuwa kano gidan iyaye da enuwanta, yusuf yace ze hadata da ma'aikatan momy amma zee bazata bita ba, ta kama hanya kuwa ta tapi abinta, a ranar ne ta saka atampa, akayi mata hoto (its on wattpad) Saeda ta shafe satika biyu sannan ta dawo, amma da ganinta kasan akwae matsala, ta koma shiru shiru gabadaya, tun data dawo ta hana kowa taba husner, ita kadae ke hidima da ita, daga karshe ma tace ma yusuf zata ajiye aikinta sae husner tayi wayau, shi kuma bawan Allah zokuga murna gurinshi, hakan ya tado da tsohuwar soyayyarta a ranshi da ta danyi saura, zama suke najin dadi sosae duk son duniya ya kwallafa shi kan husner dukda ba zama yake a gidan bama, idan ya dawo kuma mafi yawan lokuta tana bacci ne abinta Rannan yusuf baya a gidan daga mint sae zee,,, zee tazo wucewa ta hanyar falourn mint taji kamar kuka, ta danyi knocking sannan ta shiga tana daki tana kuka tana fadin "Dan Allah doctor Raghav ka kara rufamin asiri yadda besan zancen nan ba tun a farko karka fasa kwae, im trying my best na ganin na boye, i can't afford loosing Assiddique, im his one and only wife the mother of his kids"...... Zee ta shiga thinking, me hakan ke nupi mint tayi wani abu? Har dare tunanin abu daya ne a ran zee "tasan babu yadda za'ayi mint ta ajiye aikinta kawae dan ta kula da husner dole akwae wani boyayyan al'amari amma me yayi zapi da har zesa yusuf ya rabu da ita,,,, Tun daga ranar kuma zee ta soma lura da abubuwan mint, se lokacin ta lura duk kusan kwana biyu sae ta fita ita da husner amma basu dadewa suke dawowa shiyasa ma batasan tana fitar ba tunda kowa da nashi part din, Wata ranar lahadi da dare, mint da husner sunyi bacci yusuf yana zaune yana yaba chanji da mint tayi a ranshi, zee kuma tana serving dinner dinshi aka kira wayarshi, yayi picking tunda yayi sallamar farko be sake tofawa ba, ya kuma nutssu ya maida hankaali kan bayanin da ake mishi, bayan ya ajiye wayar ne ya miqe yana zirga_zirga a falourn Zainab ta tsaya tana kallonshi, "meke faruwa haka" tasan ba karamin abu ne ze tadashi daga gaban abinci ba, sun jima a haka yana kaiwa yana kawowa daga baya kuma yace ta tashi taje, ta fita tana wondering what's wrong, Kashegari da wuri ya fita, yau zee tai shirin bin mint a baya dan ta sa a ranta sae taga inda take zuwa, tana da kudi a hannunta dan haka bata wani damu ba, bayan mint ta fita itama ta shiga napep ta bita a baya, asibitin da take aiki taje, zee ta tsaya a compound din tana kallon mint dake shiga cikin asibitin, ta saka kafa zata fita a napep.din kenan motocinshi suka shigo guda uku, dan ko a maafarki babu abinda ze hanata sheda motocin yusf, ranshi kamr a bace bema jira driver yayi kyakkyawan parking ba ya fito ranshi na suya, ya shiga a fusace, ganin a yadda ya shiga yasa zee fitowa ta sallami mai nepep ta kama hanyar shiga ciki da hanzari, Mint na office din dr. Suraj ya shigo yana huci, ta miqe ba tareda aanyi wani furuci ba ruwan hawaye suka soma ambaliya a fuskarta, daedae nan zee ta karaso har tana haki amma ta tsaya daga dan nesa yadda zatana ganin komi, A hankali ya juya jin kamar motsi suka hada ido da zee ta lumshe mishi ido da sigar rarrashi dukkuwa da batasan me mint din tayi ba, ita mint dake ciki da dr. Basu lura da zee ba, duk fushin daya taho dashi dayake tunanin ze iya shaqe mint a lokaci daya ya kaita barzahu yaji yana cooling, yayi folding hannayenshi biyu a kirji yana kallonta, ya furzar da iska waje ya girgiza kai kawae ya fita, zee ta bishi da sauri, Mint kuma ta tsaya inda take cikin rashin kwarin gwiwar binshi, Gida suka koma zee tana ta biye dashi har ya karasa falournshi na kasa ya zauna kan kujerar ya cire hular kanshi ta dafe kan nashi, zee ta tsugunna a gefenshi itama tai tagumi, sun dade a hakan "she's selfish" furucinshi ya sata kallonshi, mint is a selfish woman" kawae sae hawaye suka zubo mishi, wayarshi ce tai kara yaga yallabai ne ke kiranshi ya tabbatr labari yaje kunnenshi ne, ya daga da fadin barka da warhaka, yallabai yace "Anwar divorce her, bazata zauna cikin zuri'a ta ba, THIS IS NOT A MISTAKE" ya katse wayar, yusuf ya ajiye wayar yana jimami, mint cee ta shigo a rikirkice ta karasa gaban yusuf tayi kneeling fuskarta da hawaye, pls don't divorce me, pls yusuf duk abinda nayi saboda ina sonka ne" ya girgiza kai, "no kina son kanki dae" ta hadiyi daci a makogwaronta, idan yusuf ya sake ta itakam ta kade, "Menene wannan innocent child din tayi miki, now its all over mint" ya fada yana wucewa ciki, bata bishi ba sae ta dubi zainab dake zaune tana kallonsu kanta a kulle da tmbyoyi fal ranta, "zainab pls ki bashi haquri ki tayani bashi haquri" zainab tayi nodding tana tashi itama ta wuce Kwnaki biyu suka shude gidan nan a birkice yake kowa hankalinshi be jikinshi, gashi yallabai ya takura sae yusuf ya saki mint, zee kuma duk tabi ta damu, gashi batasan mene ya faru ba batakuma san wa zata tunkara ya mata bayani ba, damuwarta kuma yadda be tmbyar ta girka mishi abinci ta sani kuma ba ci yake ba saedae yasha tea kawai, ta miqe yau kam se taji mene ya faru, falournshi na sama da qasa duk be nan kuma tasan be fita ba tunda ga securities ga motoci a gida, wannan bolcony din ta karasa hoping ta saameshi a can, aikuwa ta sameshi din yana zaune ya tsurawa flowers din gurin ido, ta ja kujera ta zauna kusa dashi, barka da warhaka ya dan juyo ya kalleta sannan ya dauke kai, ya ciji lower lip dinshi, tace "bana ganin husner a gidan nan" kawae sae hawaye suka gangaro daga idanunshi, ya miqe tsaye kamar ta kunna shi ya soma bayani "Banyi sa'ar mace ba zainab, do u know what she did?" Zee ta girgiza kai jiki a sanyaye " she killed my innocent poor child husner is gone kukan ya kwace mishi, kawae sae ta fara hawaye itama, musamamn data tuna irin son dayakewa husner, ko ita mint din darajar husner takeci duk wasu shegantakarta yana daga mata kafa Idanunshi jajawur ya girgiza kai, nagaji da haquri zainab, wadanda suka kulla auren sunce na warware" zee tace "say it say it all Ya soma mata bayani kamar haka "ina zaune abina, yallabai yaa kirani yace ya samamin matar da zan aura he'll sent her pics, tunda ake kawomin proposal na aure yallabai be taba hadani da kowa ba, and he specifically told me "Anwar she's beautiful u'll love her" Wannan shine kuskuren da nayi na biyewa yallabai da kyawunta ya rudeshi, ba tareda dogon bincike ba dukkuwa da yallabai yasan gidansu gidan mutunci ne amma karin bincike kan halayyarta ma nada muhimmanci tunda itace zan zauna da ita, i accepted the proposal, because i love that man, yes i love my dad i can never turn his proposal down, yana turamin picture dinta from the first glimpse nayi realizing she's a beauty, she's beautiful naji a raina irin matar daya dace na aura kenan, komi na biki ya cigaba da gudana nida ita bamu taba ko magana ba dan bana kasar a lokacin, kafin a tsaida rana yallabai ya nemi ayi genotype saboda yasan ni AS ne bayan tayi nata sukayi presenting result kuma aka tabbatr she's AA pattern.... babu dadewa aka tsaida rana aka soma shirin biki, ranar da suka shirya event din kamu a kano shine ranar dana fara ganinta, se naga ai hoto ma karya yayi min, she's beyond all my expectation and that made me felt so excited,,,, i feel relaxed knowing that i got a wife, and now do you know what happen?, she lied her genotype is not AA pattern its AS she tempered with the result as she's a medical doctor" ya sunkui da kanshi, a hankali zee ta soma bitar maganganunshi " kenan hakan na nupin husner is a sickle cell baby?" Ya gyada kai, and the worst part of it shine ta sani since from day 1, amma taki fada sae da jikin ya fara tsanani ta nemi hutu ta zauna a gida, tana kaita asibiti ana dubata, kuma ta sani sarae ba abinda yankamata ayi kenan ba, she need proper treatment, that poor baby has been seriously sick, and at last she's in comma, even the doctors gave up" Zee taji wani hawaye me daci ya zubo mata how could a mother do this, for her selfish reasons? Oh Allah its so bad, har haka takeso sunanta ya ra'bu dana Assidique, all she cares is fame, money in short worldly attachments Ranar zee da kyar tayi bacci da ta fara sae taga fuskar husner sanda tana jinjira sosae, the baby is cute 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 10: RIP Kashegari husner tace ga garinku nan, rae yayi halinsa, aka fito da ita daga cikin na'urorin, aka kaita gidan yallabai, tunda yusuf yaji labarin gawar husner na gidan yallabai yaqi koda motsawa, labarin rasuwar husner ya shiga ko ina cikin dangi amma babu wanda yasan cewar SS ce, Yayi karfin halin shiryawa, mint kuwa tana daki ko falour bazata iya fitowa ba, zainab kuma tana ta kaiwa da komowa a falournta, tunda taji labarin gawar husner na gidan yallabai taketa leqa motocin yusuf ko ze fita amma shiru kakeji, kmr a mafarko taji an tadasu tasan ya kusa fitowa kenan, tai saurin daukan gyalenta dama a shirye take ta sauka da sauri, ta karasa gun motocin taja ta tsaya itada sauran securities suna jiran fitowarshi, kamar walkiya se gashi ya fito, fuskarshi ba a hade ba kuma ba a sake can ba, saeda zee taga motar daya shiga itama tayi wuf ta shige, bece mata komai ba suka soma tapiya, a hankali tace "ya haqurinmu" ya gyada kai kawae, Tana kallon titi tace " Allah yasa mai ceto ce" sae lokacin ya amsa da Amin" A haka suka karasa jefi jefi zainab na yiwa husner addu'a wanan yasa zuciyar yusuf tayi calming dama abinda take buqata kenan... Suna isa ta koma bangaren momy ko ina jama'a ne, akayi mata sallah sanannn aka miqata gidanta na gaskiya...Sae yamma likis ya kira zee yace ta fito su koma gida Wanna karan ma motar dayake ciki ya shiga, suna tapiya zee tace "forgive her" kamar ta yanki naman jikinshi yayi mata wani kallo, "pls badan ita ba saboda Allah, dukkanmu mutane ne, we all make mistakes, im sure she learned from her mistake, kuma abinda yake a rubuce baze chanja ba, Allah yayi husner ba me zama bace, muma kuma duka can zamu tapi duniyar ba gurin zama bace, Allah yana tare da masu haquri, nasan ka fini ilimi kuma ka fini sanin ya kamata bazakayi abinda Allah yake qi ba, abinda al'arshin ubangiji ke girgirza sakamakon shi (saki), please give her another chance" be ce mata komai ba har sukaje gida amma yana juya maganganunta a ranshi, bayan sun shiga ne yace ta sama mishi fruits, tace to, ya shiga ya samu kujera ya zauna yana huce gajiya, Idanunshi a lumshe suke hakan yasa besan da shigowarta ba se kama kafarshi datai yaji, ya bude idanunshi, "please Anwar im sorry, ka dubi girman Allah kayi haquri, wlh nayi kuskure" ya zuba mata ido, she's crying ya ayyana a ranshi, hawayenta suka cigaba da zuba tana rokonshi da Allah karya saketa, zee ta karaso rikeda fruits din ta ajiye gefenshi sannan ta d'aga mint ta zaunar da ita kan kujerar gefenshi.ta fita ta basu guri tana fatan zeyi considering magananta karya saki mint Wayarshi ya saka ya kira yallabai ya saka a speaker, bayan sunyi gaishe gaishe yusuf yace "yallabai ta bani haquri kuma na haqura yanxu hukunci na hannunka, kaine ka hada, kuma kanada ikon sakani warwarewa" yallabai yace "tunda ka haqura shikkenan amma fa ka sanar mata ni ban haqura ba se na huce tukunna" sukai sallama mint ta sauka qasa tasaka guiwarta a kasa tana rike hannayenshi cikin kuka tace "nagode mijina nagode, Yayi shiru be amsata ba ta dago ta dubeshi, sai taga jikinshi ya saki, a hankali yake binta da kallo, sae kuma idanun suka rufe ya fadi dayan side din kujerar, a rikice ta miqe tsaye, ta soma girgiza shi "yusuf, yusuf yuuusuuf" Kafin kace me zance ya karade ko ina yusuf Assidique ya suma ba'asan mene ke damunshi ba, suna tsaye duka harda zee manyan likitoci nata kaiwa suna komowa, amma sun kasa gane mene ya dameshi Tunda aka kwantar dashi a asibiti haankalin yallabai ya tashi, kwanaki uku amma babu cigaba dan haka yallabai yace su fita dashi gun dr. Raghav, yallabai ya sanar a sanarwa zee da ita da wani yayanshi zasuje mai suna Abdul, a ranar suka wucee indian an sha fafutuka da kyar suka samu ya farfado, ranar yallabai saeda yayi sadaka sosai, dan ya ajiye komi yana kula da danshi tsoka daya a miya, zainab kuwa a nata bangaren ba karamar tashin hankali ta shiga ba addu'a take babu dare babu rana babu wanda ake bari ya shiga inda yake se yallabai iyakacin ta dashi saedae kallo daga nesa ta glass, Ranar daya farfado tana tsaye a jikin glass din tana hangenshi ya bude ido yana yatsine fuska dukkan alamu sun nuna bejin dadin jikinshi, ya juya kanshi kenan ya hangeta tana kuka tana goge hawaye, tana dagowa taganshi yana kallonta da idanunshi, tayi gaba da hanzari sae ta buge kai, sae sannan ta tuna ashe glass ne ta koma da baya har suna karo da nurses, Kwanakinshi biyu komai ya samu sauki sosai, saedae abu daya da doctors suka kasa ganewa shine yadda be magana kuma be responding, amma jikinshi ko ina lpia qalau, Kwanaki biyar suka diba suna duba kunnenshi amma komai normal har zuwa brain dinshi atlast suka fadama yallabai abinda ake ciki "Komai nashi is normal, amma bayaji kuma be maidawa ma'ana baya magana, munyi duk iyakacin kokarinmu ganin yayi responding amma shiru kuma mun duba komai a kunnenshi normal ne tun daga external ear har zuwa brain" yallabai ya shiga tashin hankali mai tsanani taya za'ace Assiddique heirs be magana kuma beji, its impossible, ya daukeshi ya chanja mishi asibiti, amma same problem, se ya chanja kasar gabadaya suka koma America sunyi sati anan amma babu wani cigaba, Saida yallabai ya kusa zagaye kasashen duniya duk gurin neman maganin yusuf amma abu yaci tura, kamar zeyi hauka, Yusuf da kanshi ya nemi pen and paper ya rubutawa yallabai kamar haka "lets go back home" A ranar yallabau ya zubda hawaye, "duk dukiyarshi amma ya gaza nemawa dan dayake mafi soyuwa a gareshi magani Yusuf ya taso yazo inda yake yasa hanky ya goge mishi hawayenshi dan ya gane duk irin zapin da yallabai yake ciki, a haka ya rarrasheshi suka komo gida, duk inda zasuyi kuwa in babu zainab sai yusuf yaja ya tsaya, suka dawo gida amma aka boyewa media batun rashin jinshi da maganarshi, Da farko yallabai cewa yyi yusuf baze koma gida ba saedae ya bishi amma yusuf ya rubuta mishi cewar ai ga zainab nan zata kula dashi kuma mint ma tana nan sannan idan ya koma gida abin ze zama kamar tonan asiri ne, Da wannan dalili yallabai ya barshi ya koma gida, amma abin mamaki suna zuwa gidan a ranar mint ta hada kayanta ta karasa gabanshi ta dan doki kirjinshi, "ka zama dutse nikuwa bazan zauna da musaki ba, aji na ya wuce nan" Zee ta tsaya kamar statue tanajin rashin halacci irin na mint, dukda beji me tace ba amma ya bita da ido har ta fice, Zainab da kanta ta dakko takarda biro ta rubuta divorce her, har wani huci take bazeyi arguing da zee ba ya rubuta saki daya ma mint, zee ta bita dashi tana Allah wadae da halayyarta, ya zauna a kujerar, kamar dazu daxu ne fa mint tazo ta durqusa tana kuka kar ya saketa, and now, ya gane saboda beda lpia ne yasata tapiya, zee ta shigo ta sameshi yana tunani idanunshi sun kada sunyi jawur, ta dakko paper ta rubuta 'what's wrong' ya karanta sanann ya amshi pen din ya rubuta, "please don't leave me" ruwan hawayenta suka zubo ta rufe fuskarta da tafin hannunta, tana girgiza kanta kamar bazata dena ba, ya dora hannunshi kan nata, ta san zapi da dacin rabuwa dda masoyi, laushin hannunshi dataji kan nata yasata dagowa Ta sharce hawayen idanunta ta rubuta mishi "in life's trial, in hardship and ease, in sorrow and happiness, i ll accompany you, ubangiji Allah ya baka ikon cin wannan jarabawar", ya dunkule hannunta cikin nashi ya dora kanshi kan hannayen hawaye mai zapi ya zubo mishi Ayi haquri da wannan 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 11: Faruq Barrister ne ya amshi wasu ayyukan nashi saura kuma suka koma hannun yallabai, tunda shidae ba yadda za'ae ayi meeting dashi, wannan abu na kara dugunzuma mishi hankali, zee ta lura gabadaya walwalarshi ta ragu sosae duk soyayyarshi da abinci kuwa yana faraci zeji ya fita a kanshi, wani sa'in ma se yaji tmkar ya bar duniyar ya huta, gashi brothers dinshi na kara rura wuta, wajen yawan damunshi da kira dukda be dauka amma abin na bata mai rai, idan be dauka ba kuma se su mishi da tex da ya jikin Allah ya sawwaqe, zainab ta sanar da Anty hawwer duk yadda suke ciki a nan ne ta bata shawarwari gameda abinda zatayi "Ki kyale duk wata harka ta asibiti, ki tuno karatukan ammi, zan turo miki da zamzam sae mu tsara yadda addu'o'in zasu na tapiya ina fata dae ze yarda" zee tai jinkirin amsawa kamin tace "eh a tunani na dae bazeyi musu ba" Bayan kwanaki uku kuwa aka turo da zam zam din, da kanta taje ta sanar dashi abinda take kokarin farawa, beyi wani jaa ba ya bata go ahead, Farko da laqad ja akum ta soma ta tofa mishi gwargwadon yadda zata iya sannan ta karanta suratu ra'ad kafa 7 da niyyar koma mene ke damunshi Allah ya saukaka mishi ya bayyana, ya karbi ruwan data tsiyayo a cup ta miqa mishi yasha da bismillah acikin ranshi, kwanaki bakwae suka jera sunayin wannan, kuma a kwanaki bakwan ta lura walwalarshi ta soma dawowa amma yakan zauna shi daya ya rike newspaper kamar yana karatu amma ba karatun yake ba, Yauma yana zaune rike da news paper din ta karaso bema san da zuwanta ba ta amshe newspaper din sannan ta bude Al'qur'ani mai girma suratur rahman ta miqa mishi, ya karba ya soma karantawa, ta fita ta kyaleshi yana karatun a zuci, be dena ba seda ya kai nasi, ya kuma ji dadi, sae ya soma istigfari, shikam yaushe rabonshi da bude Al'qur'ani ya ruqe ya karanta shi haka saedae ya saka a audio ya saaurara ko yana mota yace da driver ya saka musu, amma wannan nutsuwar da ladan rikewar da kallar ma ya rasasu, gashi yanxu da beda wani abu dayakeyi ya dauko ya karanta, tabbas d'an adam ba abakin komi yake ba, yanxu gashi ya koma kamar mara amfani, yayi hamdala daya tuno wasu ni'imomin ubangijin... Yallabai kuwa dayaji maganar tafiyar mint hankalinshi ya tashi dan bazeso taje ta tonawa d'anshi asiri ba, gashi bemaji labarin tapiyar tata ba sai da tai sati da tapiya, ya dau waya ya kira Abbanta, bayan sun gaisa yallabai yake sanar dashi abinda mint tayi, dan da alama ma be sani ba, Abban ta yace "karka damu yallabai in shaa Allah zata dawo, yanxu bana kasar ne shiyasa ma bansan hakan ta faru ba amma idan na dawo zamu ga yadda za'ai" Next abinda zee tai shine ayatus_shifa da ayatul_rukiya, to dayake sunada yawa yasa ta dan dau lokaci mai tsayi ma tana tofasu, suma kamar wadancan ta bashi yakesha da kadan kadan, rannan sunyi sallar magrib itada shi suna zaune a gurin da aka kebe domin yin sallah cikin falournshi, bayan sun kammala addu'a ne ya juyo ya kalleta ta mishi alama da ya dan dakata da hannunta, ya juyo yana dubanta ya tankwashe kafafunshi, ta dakko Al'qur'anin ta soma rera mishi kira'a, hakan yasata tunawa da Amminta, yayi shiru yana saurarenta da annashuwa a fuskarshi, bayan t ida ne ta dago ta kalleshi kawai ya sakar mata murmushi a take zuciyarshi ta ayyana mishi muradinta, Zee zata iya cewa yau ce rana ta farko dayayi murmushi har haqoranshi suka bayyana tun sanda wannan abun ya sameshi, ba karamin dadi taji a ranta ba ganin Assiddique din data sani yau da dawo, Kwanaki biyu bayan nan barrister yazo ya sameshi da maganar wani award night da akayi organizing tun last month kuma sunce shine babban bako me bada awards, Assiddique yyi shiru ranshi babu dadi dan already sun fadamishi tun yanada lpia kuma yayi accepting.. ya rubuta ma barrister "i will think about it" daga haka suka gimtse maganar, ya kammala shan ayatur rukiya da shifa sae wasu ayoyi na warware sammu suma ta sake tofa mishi, rannan suna kitchen yana zaune kan worktop, gabadaya zee ta sha'afa beji, yanata binta da ido tana harkokinta ji yake kamar ya dakko takarda ya sanar da ita sakon zuciyarshi, sae yaji tace "yaya_na tea ko coffee" sae kuma ta dago tunawa da tae baiji amma sae taga ya jawo memo ya rubuta "i can hear u, i will prefer tea" taa kalleshi da dumbin farinciki batasan sadda ta dinga jera Alhamdulillh ba har saeda ya zuba mata ido yana murmushi, ta rufe bakinta cikin tsananin jin dadi, sae ya dau takarda da pen din yana rubutu "jiya bayan na saka karatu a daki na kwanta dukda ba ji nake ba, har bacci ya daukeni, banyi awanni biyu ba nayi mafarki mai tsoratarwa na tashi ina gumi, a lokacin naji sautin karatun yana ratsa kunnena, now i can hear ur sweet voice" Tayi blushing tana kara godewa sarki Allah a nan ya sanar mata da maganar zuwanshi Award night nextweek ya nemi shawararta, itakam yanxu base ta rubuta mishi ba tunda yana jinta, tace mai eh yaje din tundaa har yayi alqawari kuma babu wanda ze gane baya magana tunda yanaji, ze miqa award din itakuma zatai speech" da haka sukayi concluding Kowacce rana kowanne second kowanne minti sae Assiddique yaji kamar ya zauna ya rubutawa zee tsararriyar wasiqar da zata bayyana sirrin cikin zuciyarshi amma sae yake danne zuciyarshi akan har se ya samu lpia zepiso ya sanar da ita wannan muhimmin al'amari da bakin shi, tabbas ita zuciya tanason mai kyautata mata, zee ce ta zaba mishi kayan da ze saka in zasu tapi award night din, akwae labarae dayawa dayakeson bata gameda artist din da za'a karrama amma babu baki kuma yayi tsayi ya rubuta mata su, zee tana daki ta kammala kwalliya, sam ba ma'abociyar kwalliya bace ta dade sosai rabonda tayi kwalliya irin haka ta saba shafa lip gloss kawae da er powder shikkenan, ta sakke kallon kanta a mirrorn tayi murmushi (pic on wattpad), sannan ta dauki dan kwalinta ta daura Bayan ta fito ta taddashi cikin motar a zaune, yayi kyau zee ta ciro wayarta tayi mishi hoto (pic on wattpad) ganin yau ba spec a idanunshi yasa tace "kafi kyau in bakasa wannan bakin tabaran ba" yayi dariya sannan ta zagaya baya ta shiga, Sanda suka karasa ma an dade da fara taron, shine ya fara shiga itakuma ta tsaya amsa wayar zeena tana sanar da ita ta dawo nigeria, tace okay zamuyi waya anjima, A lokacin har ya shiga m, ta bishi da dan sauri, akwae mutane dayawa a wajen, ta hangeshi yana bama wani matashin saurayi award, ta karasa ta samu guri ta zauna ta dauki lemo kenan, Assiddique ya matsa fuskar matashin saurayin ta bayyana, glass cup din hannunta yyi crashing lemon data saka a baki ya kwareta harda fitowa ta hanci, wannan ya jawo hankalin mutane ciki harda saurayin, amma se ya tsaya daga nesa yana kallonta, Yusuf ya karasa da hankali yana dan bubbuga bayanta idanunta suka kada ssukai jawur ta daga su ta zuba cikin nashi, yana nan tsaye rike da award a hannu, Ta ture Assiddique dake gabanta ta karasa gabnshi sae yayi saurin fita waje, itama ta bishi a hanzarce, Yusuf kuma ya bisu da ido kawae amma ganin baze jure ba ya dagawa me taron hannu sigar neman excuse Da dan duhu a inda suka fita suka tsaya ta kare mishi kallo tun daga sama har kasa "faruq" ta furta kamar bataso, Be amsa ba kuma be dena kallonta ba, sae ta durqushe a gurin why, why faruq, ka tapi ka barni, u always make me missed u Tana kuka sosae take wadannan maganganun, wanda ta kira da faruq din ya bita ya tsugunna a gabanta, da hannu biyu ta dinga dukan kirjinshi, "u left me, kayi tafiyarka on our anniversary without a goodbye, u always love it when u make me miss u" Sae lokacin yace "zainab" da muryarshi mai bala'in dadi, ya cire hannunta daga kirjinshi, sannan ya fara tari mai karfi, Assiddique dake nesa dasu yana sauraronsu ya karaso Zee data rikice ta koma gun assiddique pls help him, har jini ne ke fita a bakinshi, suka daukeshi suka saka a mota unconsciously, Dukka sukai jigum jigum, sae shessheqar zee lookaci zuwa lokaci Da suka karasa ma sae aka bashi gado dan za'a mishi gwaje gwaje sosae, zainab duk ta rude hankaulanta sun dugunzuma, Shikuma Assiddique babu baki balle yace mata wani abu ko ya lallasheta ya zuba mata ido, da kanta ta kwantar da hankaalinta amma tana jin daci a ranta, ita tace mishi su koma gida tunda dare yayi, Tun a mota ya rubuta mata who is he, idanunta suka taru da hawaye tace " the owner of this ring" ta daga yatsanta wannan zoben datace mishi ammi ce ta bata yayi shiru yana tunani, sai ya rubuta mata tel me about him, tai murmushi kadan sannan ta gyada kanta i will 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 12 & 13: Begining Zee ta soma tuno masomi kuma mafarin lamarin . . . Gabanta ya sake faduwa a karo na barkatai,,,, sam bata gane lecturen da malamin keyi, kanta ya shiga sarawa, a hankali ta dukar da kanta kan desk din cikin ajin tana mai jin juwa na dibarta, Zeena ta dan rankwafo da nata kan saitin nata tace " zee mene ke damunki ne wai?" Zee ta daga mata hannu kurun tana mai maimaita sunan Allah akan labbanta, wayarta ce ta shiga vibrating ta zaro ganin sunan Anty hawwer yasakata dagowa ta kalli malamin dake karkare darasin dan ya fita, ta dan sauke numfashi sannan ta maida wayar jaka, malamin na fita ta zaro wayar ta kira Anty hawwer, tayiwa zeena alamun tana zuwa saboda hayaniyar dalibai, da sauri ta karasa inda keda saukin hayaniya lokacin Anty hawwer tayi picking, "Anty mene ya faru?" Anty hawwer tai dariya, "kamar ya mene ya faru, meze faru kuwa?" Zee tai shiru batareda sanin amsar da zata baiwa Anty hawwern ba, Anty hawwer ce ta katse shirun da fadin "ke tsiyata dake se ki shiru kinajin mutun na magana, ke kika jiwo, dama ce miki zanyi in kin gama lecture din ki biyo gun maman fatima naje wankin kai sai mu wuce gida kawai", zee tace to Anty hawwer, ta fadi a sanyaye sannan suka katse kiran, Cikin ajin ta koma ta tarad da zeena da en tsirarun dalibai da basu fita ba, zeena ta kalli agogon hannunta tana miqewa, "zee karfe biyar (5) fa yanxu har da rabi, muje gida ko? Zee ta gyada kai itama tana karban jakarta sannan suka fita daga cikin theatren, Bayan sun fito suna tafiya kan kwaltar cikin makarantar Zee tace "Zeena Anty hawwer na gurin maman fati zan biya ta can sai mu wuce gida" okay to muje kawai, Zee tai murmushin jin dadi dan ta tsani tafiya ita daya, Bayan sun futa cikin school din suka tsallaka titin sai gasu gaban wani tafkeken Beauty pala, gurine na gyaran jiki, gyaran gashi, kafa, fuska da duk wani gyara na mata, harda bangaren makeup a ciki,, sliding glass in sukayi suka shiga katon gurin, daidai shigarsu suka tarad da Anty hawwer na kimtsawa itama an kammala gyaran, zeena da Zee suka karasa gurinta, zeena ta Amshi bbynta mai suna Nihal, sannan duk suka gaidata "Anty hawwer barka da yamma" tai murmushi yawwa barkanku daga haka suka fita zuwa motarta," Anty hawwer ke tuki, Zee na baya ta kwantar da kanta a kujerar ta baje abinta, zeena da nihal kuma suna gaba, hirarsu suke su biyu sai lokaci lokaci Zee ke sako baki "Anty Abbah ya dawo kuwa?" Zee ta tmbya, Eh ai tun wajen 2 ma yana kasar nan, dan na barosu a gida shida Ammi," Zee taji dadi jin Abban nata ya dawo, Zeena tace "Anty yanxu dagaske jibin zaku wuce saudi?" "Eh zeena ni kaina har na fara kewarku, ko na tafi ki kulamin da waccan shiru shirun kawartaki kinji zeena" zeena tai murmushi tana kallan fuskar Zee ta mirror, baki da matsala Antynmu,ku kula da karatunku dan Allah banda wasa, banda abokan banza da samari barkatai, Haka taita musu nasiha har suka karasa unguwar mai titi a tsakiya da gidaje bangaren hagu da dama, tun farkon layin suka sauke zeena tana musu sai gobe zata shigo ta gaida Abbah ta mai sannu da hanya" sukuma sukai gaba, bayan Anty tace lallai sai Zee ta dawo gaba, haka ta dawo ta dau nihal, Tafiya suka sake saida suka kai karshen layin sukai kwana sannan suka hangi dandazon jama'a hayaki ya saka gurin ya kara duhu, Zee ta dan dafe kirji tana jin kanta na sarawa tamkar an buga mata karfe a tsakar ka, Hasbunallahu wa ni'imal wakil ta furta a hankali, Jikin Anty yayi sanyi ta dubi Zee dake dafe da kirji tana saita numfashinta, cikin dakewa ta taka accelarator kadan suka kara gaba, yawan mutanen dake gurin yasa suka toshe hanya dan haka a tilas Anty hawwer ta samu guri tai parking tana mai danne zuciyarta da fatan Allah yasa tunaninta ya zama karya, tun kan Anty ta ida parking Zee ta bude motar, a tsawace anty tace "ke kula dalla zaki yar min da 'ya" Zee da sam tama sha'afa akwai nihal kan cinyarta tai saurin riketa tana rungumewa a kirji gam kamar za'a kwace ta, babu wanda ya iya sake cewaa dan uwanshi ko Qala suka fito suka rife motar, sai kuma suka zama kamar masu san'da suke tafiyar a hankali a hankali, har suka ida karasawa, Abbah jabir ne a tsaye yana waya hankalinshi a matuqar kidime, Zee ta daga kanta sanda ta ganta a gaban konannen gidan daya kone rumus,,, ta kada kai tana mai sake kallan gidan a karo na biyu, sai lokacin Abbah jabir ya kula dasu, Anty ce tai karfin halin fadin "Abbah jabir, gobara akayi?" Ya kada kai kurun, Zee ta sake kankame nihal tanajin wani abu mai zafi na kuna a kirjinta, Sama sama taji muryar Abbah na fadin "kuyi haquri Allah ya musu rasuwa"..... Shine kalmar dataaji ta karshe, wata murya taji a kanta tana fadin "sun rasu, sun rasu, Ammi da Abbah sun rasu, wayyo mun shiga uku", "Ta rasu? Ammi rasu?, dan Allah karki tafi ki barni" ta kumajin karajin muryar tamkr zata fasa mata dodon kunne tana mai hautssinewa da dukkan neurons din cikin kwakwalwarta, sai aka fasa wani kuka mai azabar karfi da razanarwa, daidai nan ta bude idonta cak ta dena jin komi tsit Lokaci daya ta bude dukkan idanuwanta tana mai kallon cieling din dakin datake, sai ta kalli gefen daga sama ta hangi abin karin ruwa, take ta soma motsa sassan jikkunanta, hakan yasa tabi karin ruwan da kallo har zuwa inda ruwan ke shiga wato hannunta, asibit? Shine abinda ya fado mata, Zee ta maida idanunta ta kulle sannan ta bude, ta kalli gefenta, dakine mai girma babu kowa kuma a cikinshi, ta dauki tsayin seconds sai aka bude kofar dakin, su uku suka shigo Zeena tai saurin karasowa gurinta tana mai danne kukan dayazo mata , Zee Zee, ta maimaita sunan nata Sannu Zainab, Abbah jabir ya fada, Kallo daya Zee tayiwa Anty hawwer ta kauda kanta, saboda yadda fuskar Anty hawwern ta chanja, ya bayyana karara tasha kukane kuma tana kan sha, Sun rasu ko? Zee ta tambaya a matuqar sanyaye, Zeena dake zaune gefen gadon ta kamo hannun Zee ta hada da nata kurun tana mai shanye nata kukan, cikin dakewa Anty hawwer tace "Zee baki da lpia kiyi kokari ki cire duk wata damuwa a ranki, daga haka ta fice da sauri, A hankali hawaye suka gangaro gefen idanun Zee dake kwance, shima Abbah jabir din fita yayi, Wani abu zeena ta hadiya kamin tace "hawaye kuma Zee, namene haka, kinajin dai abinda Anty ta fadi", Cikin karfin zuciya Zee ta dan dago daga kwancen, zeena ta taimaka mata ta saka mata pillow a bayanta, bayan ta zauna ne, ta kuma matse hannun zeena dake cikin nata har saida zeenan ta kallin hannu ta kuma kalli Zee, "Zeena na rasa Ammy shikkenan Ammy na ta tafi, zeena kinfi kowa sanin wace Ammi, kin kuma fi kowa sanin ya Ammy take," zeena ta sunkui da kai jin Zeen na kokarin karyar mata da zuciya, Zeena Ammy zeena Ammy, zeena ta kalli Zee da bakinta ke ambata sunan Ammy idanunta babu hawayen kuma, Ki kwantar da hankalinki Zee, Zee ta murmusa kadan dan akwaita da haquri kam, dukkansu shiru sukai yayinda Zee ta lula duniyar tinanin Amminta A hankali take tariyo rayuwarta tareda Ammi, Amminta mace ce mai hakuri, mace mai tarin ilimi, tundaga na boko zuwa na addini, ga ilimin rayuwa, Her whole best moment in dis life is her moment with Ammi, Kasantuwarta autar Ammi yasa tafi samun kusanci da Ammi, sukai muguwar shaquwar ko a bacci ta kanyi mafarkin Ammi Wasu zafafan hawaye masu dumi suka gangaro mata, Koyaushe kuma kowacce rana baza ta kare ba Ammi bata karar da ita da wani sabon ilimin ba, A gurin Ammi ta koyi karatunta na Alqur'ani wanda sukeyi duk bayan idar da sallar magrib har zuwa isha'i, duk wata rayuwa kamilalla Ammi ta nuna mata, kuma duk wani gata na duniya Abbanta ya sama mata Ta sharce siririn hawayen da suke zuba sakamakon tuno iyayen nata da tai, mutane mafi soyuwa a gareta duk duniya, mutane datafi shaquwa dasu duk duniya, haka kuma mutane mafi daraja a rayuwarta A bangaren zeena ma, sarai tasan halin Ammi halin dattako, koda ita ba diyar Ammin bace amma ta samu abubuwan karuwaa dayawa tun daga kuruciyarsu har zuwa yanxu da za'a iya cewa sun mallaki hankalin kansu tunda suna da shekaru 19 ne a duniya, Ammi ta sanar dasu darusan zaman rayuwa kuma tana kan sanar dasu, ashe zaman nasu bazaiyi nisa ba, ashe Ammin bazataga auren autarta ba Duka su biyun basu an kara da junansu ba, basu san cewar duka hawayen suke ba, Anty hawwer da shigowarta kenan ta tsaya tana kallonsu Kasa jurewa tayi ta karaso ta rungumesu duka tana mai share kwalla Sai a lokacin da Zee ta jita jikin yayarta kwalli daya duk duniya ta saki wani kuka mai cin zuciya, haka take kukan tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi lokaci lokaci..... Dan kansu suka dena kukan, sai bayan kwanaki biyu aka sallami Zee, ta rame sosai, dan kasa dena zubda hawaye tayi, gabadaya jitai duniyar ta fita a kanta babu abinda keyi mata dadi, gidan Anty hawwer ta koma ta zauna, Abbah jabir (kanin Abbansu) shine ke ta dawainiya dasu, matanshi ma duk sunzo duba Zee sanda tana asibitin, zeena kuwa kusan koyaushe tana hanyar asibitin har aka sallameta dayake a gidan yayanta take, dan har matar yayanta ma tazo tayi musu ta'aziyya dan kowa ya zauna da Ammi yasan halayyarta ta dattako, haquri da tsananin Addinin islama dukda tayi boko kuwa, shiyasa duk wani d'a da Ammi zata raina to ze taso a nutse ne dan ya samo tarbiyya tun daga tushe, dan ma Allaah bai azurta Ammin da yawan 'ya'ya ba.... A gidan Abbah jabir ake zaman makoki, dayake Zee battada lpia yasa Anty hawwer tace tai zamanta kurun a gidanta itakuma kullum zataje da safe ta dawo da yamma, har akayi sadakar bakwai, To dama kamata yayi tun kwanaki hudu baya, Anty hawwer zata wuce saudi, inda mijinta ke karatunshi na masters degree kuma ze dora da PHD itama antyn zatai masters din tunda shi yama kusa kamamla nashi, to se kuma wannan kaddara ta faru, mijin Anty hawwer yaso zuwa gaisuwa amma Anty hawwern ta hanashi dan yana tsakiya da yin jarrabawa ne, yaqi yarda sam saida ta hadashi da Abbah jabir sannan ya haqura, dan shim Abban be goyi bayan ya taho din ba, bayan sadakar bakwai din ne Abbah jabir da wasu en uwa na nesa suka hadu dan tattaunawa, dayake duk babu wani dan uwa na kusa daga bangaren ammin har Abbah se Abbah jabir duk sauran cousins ne ko na Ammi ko kuma cousins din iyayensu Ammi da Abbah haka... Kowaa ya hallara su biyune kadai mata sai kuma nihal dake hannun Zee, wacce ta rame tai duhu dama ba farar bace amma kuma ba baka sosai bace, sabanin Anty hawwer datake da haske Abbah jabir ne ya soma musu bayanin abinda ya tarasu "Bazamuja da tsayi ba, muna sakeyi muku ta'aziyar rashin iyaye da enuwa, dan ni kaina sun wuce yayuna saidai nace musu iyaye, yadda suka kula dani tun rasuwar namu iyayen, to dama haka rayuwar take, dududu nawa take, kuma babu komai cikinta sai zallar haquri ga wanda keson cin riba, Allah yajiqansu ya gafarta musu muma ya kyauta namu zuwan, saida aka sakewa su Abbah addu'a sanan Abbah jabir ya dora "Hawwer munyi magana da maigidan naki, yacemin kun gama tattaunawa kan zaki dauki Zee ki cigaba da riketa a can gurinki, Anty hawwer ta gyada kai alamun hakane, Zee ta dubesu dan ita batamasan da wannan mgnr ba, Maganar Abbah jabir ya cigaba "Muma nan mun tattauna bayan munji ta naku bangaren, Hawwer se muke ganin kamar zepi idan Zainab ta zauna nan gurina" lokaci guda gaban Zee ya tsinke ya fadi tana mai jin hawaye na taruwa cikin idonta, Allah sarki rayuwa, sati daya baya bazata taba cewa har lokacin da za'a dinga neman inda zata zauna zezo ba, amma gashi iyayenta tmkr basu wanzu ba komi ya kone, gida, mota, su kansu komi ma, A wayance ta saka gefen gyalenta ta share er kwallar dake zubowa, bawai zaman gidan Abbah jabir ba amma matan Abban duka sedai hamdala kuma kowa yasan da hakan Maganar Abbah jabir ya cigaba da fadin "Mun duba ne munyi la'akari da karatunta, tunda yanxu suna karshen semester karshe a level one idan ta kammala wannan semestern sukayi hutu setaje gurinki din tayi hutu in aka dawo kuma seta dawo ta cigaba da karatunta har itama lokacin da Allah ze kawo nata mijin" Wannan hukunci na Abbah jabir shida sauran manya yayi daidai a kunnen kowa har da Anty hawwer hakan yasa itama Zee ta amshi kaddararta tana mai fatan Allah yayiwa iyayenta rahama, Daga haka aka cigaba da maganar gadonsu, Abbah jabir ya sanar dasu dukiyar Abba ta cikin gidan sun rigada sun kone kamar yadda kowa ya sani, abinda ya rage sune kudade cikin account da wasu filaye da takardun ke hannun wani Abokin Abbah dukda haka suna cigaba da binciken wasu...." Bayan an kuma tattaunawa su Zee suka koma gidan anty hawwer wacce itama gobe zata koma saudi, tunda suka taho a hanyar babu wanda yayi magana, Zee ma zamewa tayi takwanta sosai kan kujerar tana rungume da nihal dake bacci, itama ta lumshe idanunta,Anty hawwer tace "Zee" Zee ta dan bude idanunta da sukai mata nauyi sannan ta kalli gefen da Anty hawwern take tana tuki ta dan kakalo murmushi sanda Antyn ta dan juyo ta kalleta Ajiyar zuciya kurun Anty hawwer ta sauke tana mai maida kanta ga titin , basu dadeba a hanya suka isa gidan Anty hawwern, madaidaicin gida da aka tsarashi tsari irin na en boko, Har anyi sallar la'asar ma sanda suka iso, hakan yasa suna shiga Anty ta amshi nihal ta wuce daki, Zee ta ajiye hijab dinta sannan ta shiga bandakin falourn dan bata muradin shiga ciki, a ciki tai Alwala ta fito, ta nemi dadduma ta shimfida tai sallah, bayan ta idar da sallar ma ta dade tana addu'a sosai ga iyayenta har ta kare da kukan dayaci karfinta ta kifa kanta kan abinsallar tana mai tsananta kukanta, Anty hawwer ta durquso tana mai dafata ganin ta tsagaita da kukan tana ajiyar zuciya, ita kanta anty hawwern tausayin Zee takeji, tasan tanada haquri sosai hakan yasa inma abu ya bata mata rai bata fiya kulawa ba, abinda ze sakata kuka kuwa ba karamin abu bane, musamamn sanin irin shaquwar dake tsakaninta da Ammi.... Zee ta dago sanda sukai ido hudu da Anty hawwern sai ta sake rukunkumeta, cikin kuka take fadin "Anty ke kinji dadi, ko ba komai Ammi da Abbah sunga aurenki, nikuma fa?, burin Ammi bai wuce taga ranar da zataga bikina ba, Anty hawwer kema tafiya zakiyi ki barni!!! Rarrashi sosai Anty hawwer take saida tai kuka takoshi sannan ta share hawayenta Anty hawwer ta soma mata nasiha kadan kadan "Rayuwar gabadaya nawa take ma Zee dita, komi sai kinyi haquri zakiga yazo ya wuce babu wani dawwamammen abu a duniya komi se ya wuce wlhy kmr yadda muma din zamu shude watarana, meyasa bazaki dauki kaddara ba Zee, kigafa har faduwa kikai Zee, nikuma ya kikeso nayi da tawa rayuwar, all the expections danake yi gameda su Ammi, duk tanadin danayi musu ashe babu wani rabo, to ki kwantar da hankali ki dau komi ba komi ba Zee ta, we hav to be strong, muci jarrabarwarmu Zee, mu fawwala lamuranmu ga ubangijin talikai, Kukan Zee ya tsananta amma babu sauti cikin jimammin wannan rayuwa, yau kaine gobe kuma bakai bane, "Dududu ma kwana nawa ne kun kare semestern kinzo gurina, in kuma kinaso na fasa tafiya ne wallahi zan fasa Zee, banida wata data fiki yanxu, idan kin ida semestern se mu koma tare" Zee ta dago ta share hawayenta dan tasan tsaf Anty hawwern zata iya kuma tasan zata shiga hakkin Abban nihal ne, "a'a anty hawwer " A sanyaye antyhawwer tace "Zee" Zee ta dago da kanta tana kallan Anty hawwern, Ta dafa kafadar Zee tace "ki Zama jaruma, babu abinda Ammi da Abbah sukke bukata kamar Addu'arki idan kuma kinje gidan Abbah jabir, ki maida komi ba komi ba, kiji kiqi ji, kuma ki gani kiqi gani, dan sai kin toshe kunnuwanki kuma rufe idanuwanki, ni kuma na yarda Zee din danasani , Zee rainon Ammi, Zee one and only sistern hawwer zatayi overcoming duka wani diffuciultie with faith kimin alqawari Zee" Zee ta kamo hannun Anty hawwer, tayi rapping hannunta cikin nata tace "nayi miki alqawari Anty hawwer, na kuma karbi kaddarar rashin Ammi da Abbah, Allah ya musu rahama"...... Kashegarin ranar tun wajen 12 duka suka kammala shirinsu dan anty hawwer tafiso takai Zee da kanta sannan ta tafi, kulle ko ina sukayi dama already sunyi waya da Abbah jabir kan karfe 1 zasu zo dan haka yace to ze jirasu, en sauran kayan Anty hawwer dake gidan na sakawa da wasu na amfani ta kwashe duka suka zuba komi a mota, saida suka kulle ko ina sannan suka fito, suka kulle gidan ma, suka shiga motar suka hau titi, boutique suka biya Anty hawwer ta saiwa Zee wasu kayan sakawa tunda battada su, wanda take sakawa ma a kwanankin na Antyn ne, sannan ta siya mata atampopi, ta kuma ce zata tura mata kudi cikin account dinta, Zee taji dadi taita godiya kuwa, #the sister's love Bayan sunje gidan Abbah jabir, sukaa tarar dashi a driven din gidan ya kafa wata kujera yana karanta jarida, sukayi parking suka fitto, nan suka shiga gaisawa sannan yace su shiga daga ciki, jakar kayan Zee aka futar a motar da wasu en kayan da Anty ta bar mata, aka bar na Antyn a motar, Idan ka baro driven din gidan ma, tsakargida zaka tarar, sai kuma falour a gefe, sannan dakunan yaran gidan, na matan gidan kuma yana saman benen, Duk yawancin su suna falourn a zaune dan nan suka fi zama, gidan kam ba'a cewa komi dan a jagalgale yake nan buta, nan kwanukan wanke wanke, ga bandaki a hangame kudaje kuwa ta ko ina, hmm Zee tai ajiyar zuciya kurun dan abin ma ba'a magana, saida suka huta aka kawo musu abinci dukkansu babu wanda yaci abincin, Bayan sunyi sallar la'asar ne, Abbah ya kirasu falournshi dake can gefe cikin gidan, suka sake gaisawa, Duka yaran gidan sun hallara mata 8 ne sai kuma maza 4, nan Abbah ya sanar dasu zuwan Zee kuma zata cigaba da zama a gidan, babu wanda yace ko kala, haka ya gama jawabinshi, Anty siyama itace amaryar Abbah jabir kuma matarshi ta uku, kasancewar bikin nasu bai wani dadeba yasa battada 'da ko 'ya a cikin gidan, wannan dalili yasa Abbah fadin "na damka alhakin komi na Zee a hannun siyama" tunda dama dole se an sama mata uwar daki itama kamar kowanne 'da," Anty siyama da bata fiya surutu ba tace "Allah ya tayamu riko" duka sukace Amin,,, Anty hawwer ma ta dora da fadin "Abbah jabir, nima ga tawa motar nan se Zee ta cigaba da zuwa makaranta da ita dukda bata iya ba amma tana koya kadan kadan" Abbah jabir yace to ba matsala zai sama mata driver kurun se su dinga tafiya tareda sauran yaran gidan" (babu motar yara a gidan Abbah jabir dan ba wani dukiya ce mai yawa gareshi ba, mota daya ce kuma tashi ce) Sai magariba sannan Anty hawwer ta soma shirin tafiya filin jirgi, Abbah jabir da Zee ne kurun suka mata rakiya, Koda sukaje rabuwa Zee ta rike hannun anty hawwer kamar karta saki, sai kuma tai murmushi tace Allah ya tsare ya kaiku lpia, sannan tai kissing nihal tana mai murmushin da baiyi mata dadi, Anty hawwer ce ta kalleta tace "haka nakeson jarumar kanwata, idan na sauka zan kiraki" daga haka sukai waving juna... Wasu en hawaye suka dan digo daga idanun Zee tana murmushi cikin tunanin sabuwar rayuwar dazata tsinci kanta a gidan Abbah jabir da kewar iyayenta da er uwarta... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 14 & 15 : first glimpse Kashegarin wannan rana Abbah jabir ya soma shirin barin garin dan komawa gurin nashi aikin (yana aiki ne a garuruwa daban daban kasancewar shi mai aikin dan sanda mai mukamin D.P.O. yasa akanyi mai transfer zuwa garuruwa daban daban lokaci zuwa lokaci, kuma yakan dauki matar dakeda girki ya tafi da idan idan tayi kwanakin ta wato sati daya se wata taje), Abbah jabir seda ya tabbata ya wadata iyalanshi da abinda suke bukata kamin ya tafi shida uwargidanshi dasuke kira umman Halipa, ita tanada yara 7, Halipa ne babba wanda yaci sunan Abbanshi shekarunshi 25 se tahir shekarunshi 24, Usama (22yrs), Kubrah (19yrs), Hassana & Hussaina (15yrs), da Kausar (11yrs). Sai kuma matar Abbah jabir ta biyu, tanada yaranta 5, suna kiranta maman khairi, Khairi ce babba (18yrs), sannan Zakiyya (17yrs), iklima (15yrs), Ammar(13yrs) da Hindu (10yrs) zee ma ranar talata ta koma makaranta, batada matsala da duka takardunta dukda sun kone amma already they are scanned on gmail..... tun Asuba da zee ta tashi ta share dakin da suke bacci itada Kubrah da Khairi dukda su basu tashi din ba, sannan tai karatunta na safe da sukanyi da Ammi, zee ta rike littafin tana mai tuno nasihun Ammi kowacce Safiya.... "zainab ki kasance mai haquri da duk halin da zaki tsinci kanki a rayuwa, ki kula kuma ki nutsu ke macece, dabi'unki, mu'amularki da mutane, kalamnki, suturunki sune zasu fadawa mutane ko ke wace, dan haka ki kiyaye harshenki, ki tauna magana kafin ki fidda ita, ki kiyaye tufafinki su zamto masu nuna darajarki ba masu fidda tsaraici ba...." bubbuga kofar dataji ne ya sakata dawowa tinaninta ta dubi agogo karfe 6:30 ne gari bai kammala wayewa baa kuma dukda haka babu wacce ta tashi kaf gidan, dan ko da Asubahi bataji motsin kowa ba se mazan da suke can boysquaters, baba maigadin gate din gidan yazo ya budema ladi kofar kamar yadda ta saba zuwa tana aiki tazo da sassafe ta shirya en makaranta tayi breakfast sannan ta tapi wajen 12 inta gama duka ayyukan gidan, sai kuma wajen 3 ko 4 ta sake dawowa tayi ayyukan yamma da wanke kwanukan da akaci abincin rana da yamma, girkin rana dana dare kuma wacce keda girki ce zatai in kuma tana da yarinya se ta sakata, in kuma suna makaranta tilas tayi dakanta.... Wannan kenan zee ta dade tana jerama Ammynta da Abbanta addu'o'i kamin ta miqe taje dan yin wankan safe kmr kullun, ta tarar har ladi ta ida wanke bandakin kuwa, sai karfe 7:45 zee ta kammala dukka shurinta dan tanada lecture ta 8 kuma gashi ma ta makara, lokacin dukka kowa ya tashi, wasu na wanka wasu na shiri, wasu kuma na breakfast, haka suka gurgunda suka gama karfe 8 suka dunguma cikin motar da Anty hawwer ta bada su kusan rai 7 (ba dukansu ne keda lecturen safe ba wasunsu zasu bi zeen ne saboda samun bati dan Abbah jabir ya shaidama drivern iya hidiman zee ne kurun wanda kuma ze fita a lokacin dazata fita se su tapi tare tunda dai ba shine ya sayi motar ba ta gado ce). Usama ne a gaba (shima yana zuwa wata private college), zee, khairi, kubrah, hassana da iklima kuma suna baya, sai hussaina data zauna a gaba kusada Usama dan babu waje a bayan, Ammar, hindu da kausar kuma makarantarsu babu nisa su qananan, zakiyya kawai aka bari a gida, ita ta gama sec. Schl amma bata fara wata schl ba tukun se nxt session in za'ayi sabon diban dalibai Hassana da hussaina da iklima aka fara saukewa a wata private sec. Schl, sannan aka sauke kubrah a school of nursing sai kuma usama a Aminu dabo college of health, ya rage daga zee se khairi, tun kan su karasa Zeena keta faman kiran zee, zee da wayarta ke cikin jaka ma sam bataji ba dan mostly a vib. Ko silent take saka wayarta Dayake tafiyar akwai d'an tsayi kafin a karasa yasa zee ciro wayarta dan debe kewa, ganin kiran Zeena rututu yasakata bin kiran amma se zeena tai rejecting, zee ta tsaya tana kallan wayar da mamaki, can kuma babu jimawa sakon zeena ya shigo yana fadin "ki hanzarta zee malamin har ya shigo" zee tai shiru tana kara kallan time takwas harda talatin da biyar ta sauke boyayyiyar ajiyar zuciya, zata iya cewa tun da ta fara makaranta wannan shine karo na farko data taba makara haka, dan Ammi jajirtacciyar uwa ce, wacce take kulawa da dukkan al'amuran gidanta danma bata samu haihuwa da wuri ba wasu yayun zee da anty hawwer kuma sun rasu, wasu ma tun suna ciki suke barewa, iya su biyu kadai Allah ya tsayar mata, zee tai murmushi tuno Amminta da tayi lokaci guda kuma idanunta suka ciko da kwallar tunowa da tai bazata sake ganinta ba... Allah sarki, Rayuwar kenan... zee aka kai har cikin makarantar... Tsohuwar jami'ar Bayero dake kano, sannan aka wuce da khairi jami'ar maitama sule (northwest uni). Qarfe 2 suka kammala lecture itada Zeena da sukeyi tare dama already driver yasan by 2 zata gama dan ta fada mai, suka taho itada zeena aka kai zeena har gida, itama ta shiga ta gaida matar yayan zeena datake gurinsu sannan suka wuto gida, kasancewar zee ba raguwa bace dan ko sanda tana gida tareda Ammi itake girki indai babu abinda take, and there's something special about zee's cook... Tana shiga dama already tayi sallar zuhr dinta tun a school ta cire kayanta ta shiga ta watsa ruwa dan gidan shiru yake yaran duk sun tapi islamiyar karfe 2:30, zakiyya bacci take hakama matan gudan kowacce na dakinta dan haka itama ta koma daki tana mai jin kadaici, dan da ace da ne da tana jikin Amminta suna hira ko shawarar abinda za'a dafa da daddare, tashi tayi ta shiga kitchen din gidan fot th first time, kitchen is d best place in d world dake daukewa zee kewa, is the best place that makes her feels comfortable and okay, shiyasa girkinta ma dabanne da wani sinadarin da idan kaci sai kaso ace baie kareba u ll be craving for more and more babu kosawa babu ginsa (secret na girkin zee wanda ta koya da taimakon Ammi da kuma nata soyayyar da girki) Gyara kitchen din tayi saboda ladi batazo ba tukun kuma zakiyya da tai girkin rana bata gyara ba, coffee ta shiga hadawa, the best drink of hers, bayan ta kammala ta juye cikin wani karamin cup data gani, sannan ta fita a kitchen din, its been a while since she had it, al'adarta ce itada Ammi basu kwanciya bacci basu sha akalla 2 mug of coffee din da zee ta kware wajen hadawa, yanxu kuwa kusan more than a week ma batasha ba, hakan yasataji wani dadi bayan tasha coffee din Dukka yaran gidan wadanda suke higher institute se kusan magrib suka soma dawowa, zee ta cigaba da zama gidan Abbah Jabir bayan umman halipa tayi sati daya ta dawo umman khairi ta tapi, Cikin zaman da tai a gidan yasata fahimtar abubuwa da dama, Ta fahimci akwai hassada da suke ma juna a tsakaninsu, kuma kowa be damu da al'amarin kowa ba, wani bai taimakon wani kowa na kyashin taimakon dan uwansa indai ba shine ze amfana ba, ga shegiyar lalaci gun matan gidan harda yaran gidan, zakiyya ce kurun me dama dama hakan yasa sukafi shiri da ita kaf gidan dukkuwa da ba sa'arta bace amma tasu kam tazo daya, Wata ranar lahadi su zee suna shirin fara jarrabawa, ta maida hankali sosai karatunta take dama ba daga nan ba kam,yau girkin na Anty siyama ne (uwar dakin zee), zee taje ta gyara mata dakinta da bandakin dan indai tana gida itake mata aikin dakinta, sannan ta fita zuwa main falour inda mafi yawan yaran suke, Anty siyama kuma tana kitchen tana kokarin daura sanwar rana, zee ta karasa tace "Anty siyama kawo yau nayi girkin tunda ina gida," ba musu ta bar mata girkin sannan ta soma mata bayanin abinda zata girka, "jallof ce ta shinkafa zanyi dan inaga zatapi min sauki" zee tace to Daga haka ta fita a kitchen din, Zakiyya ta shigo tana cewa bari na tayaki da en yanke yanke, zee tai murmushi (note: zee takan taya itama zakiyyan aiki sosai a baya hakan ne ya saka ma zakiyya kaunarta itama tai kwadayin tayata) Akwai komi da zee ke buqata dan haka ta soma girki, this is the first time dazatayi girki a gidan, Kan kace me gida ya dau kamshi, daya daya yaran kan leqo kitchen wannan yace mukam me ake dafamana, wani yace "ah'ah yau kece a kitchen kenan" hmmm koni na kagu naci wnn girki, cewar zakiyya dake tsaye ta jingina tana kallon yadda zee ke sarrafa kayan kitchen To a wannan rana kam ansha santin girki, dukda jallof ce mai sauki tayi musu amma kam sunji banbanci da abincin gidan... Cikin masu santi hardasu kubra dake fadin "ai kawai zee kizo ki bude kafteria a school dinmu wlhy zakiy ciniki" me za'ayi inba dariya ba, itakuma har ranta take fadi.... Suna nan duka suna santin abincin Abbahjabir ya kira wayar Anty siyama, ta dauki wayar yace "ta miqawa Zainab,, " Anty ta miqa mata wayar sai bayan da suka kammala wayar da zee ne, yace ta kirashi da numberta anjima da wasu bayanai, sannan ta miqawa Anty wayar Bayan taje daki ta dauki wayarta ta kira Abbah jabir din kmr yadda yace shikuma yace ta tura mai acct. Numberta koda ze bukata a gaba, bayan sun gama wayar kuwa tamai sending.... Karatu fa yayi zafi yanxu zee da zeena basa barin school da wuri dan tare suke karatunsu, ita zee tana part of Basic medical sciences ne, zeena kuma Allied health science, lectures dinsu duk na level 1, iri daya ne sai en practicals da ake warewa, daga level 2 kuma kowannensu ze kama bangarenshi but still akwai lectures din da zasu dinga haduwa.... "Zee nikam yanxu kin gama zama typical late comer, kin shahara a makara duk sanda muke da lectures da safe" Zee ta dara tana kallan yadda Zeena ta dage tana jaraba, "kyayi dariya mana, nidai Allah yasa da exams dinma karki makara dan akwai na safe sosai a ciki, Zee tace "ai da wuri zan dinga tashi, ni na isa na makara da exams" Kiran Anty hawwer ne ya shigo wayar Zee ta fadada annashuwarta tana maijin dadi ta dauki wayar, gaisawa sukai tana tmbyar ina nihal Anty hawwer tace duk suna nan qalau "Yanxu Zee saura sati uku ki taho ko? Dan ina nan ina lissafi" Zee ta jinjina kai cikin tsananin murna, eh Anty na, "kina school yanxu?" Zee tace eh "to ayi karatu dayawa, Allah ya baku sa'a, ki gaida zeena dakyau," daga haka suka yanke wayar.... Exams suka fara lami lapiya, dukda Zee kan samu rashin jin dadin karatu dan indai ba a makaranta tai ba to beyi mata dadi sedai ta fita tsakar gida da daddare, dan yaran gidan akwai hayaniya kuma dakin nasu su uku ne babu inda zataje ta kebe,, babu wani aiki datakeyi yanxu dan sanda zasu fara exams din ma Anty siyama ta tapi gun Abbah jabir, kuma ta kulle dakinta, Rannan zasuyi exams Zee bata samu tayi wani karatun arziki ba, gashi kuma ta sassafe ce, dan haka magrib nayi ta kwanta bacci saboda ta tashi sai ta saita alarm dinta, Karfe 10 ta tashi ta watsa ruwa, tayi sallolinta sannan ta fita tsakargida wani dan lungu, dayake akwai kwan lantarki a gurin yasa sauraye basu dameta ba, taita karatunta, sauran yara da mata kuwa kowa ya koma daki ita ko abinci ma ta mance bataci ba dan sai la'asar ma tai lunch, Ji tayi karatun be shiga hakan yasa ta gane something is wrong tasan kanta mutun ce me son karatu, ajiye pen din hannunta tai ta shiga safa da marwa da son tuno me ta manta? Mene yasa karatu ya zama boring, Tana cikin tinanin taga Zakiyya ta pito daga dakinsu dauke da mug na shan tea/coffee, ta dan murmusa sannan ta ajiye takardun hannunta ta nupi gun zakiyya wacce batama kula da ita ba, saida Zee ta dafata sannan ta waigo a dan razane, Zee tasa mata dariya, zakiyya ta tsaya kallonta for some seconds sannan tace Zee kinsan wani abu? Zee ta dena dariya tana girgiza kai ganin serous face din da zakiyya tai "U re really awesome, u hav dat inner beauty" Zee ta kankance idanu cikin rashin fahimtar inda ta dosa sannan tace "and why re u complimenting all of d sudden?" "Zee wlhy dagaske nake as u laugh now i just saw a gorgeous Zee in you, or maybe it's bcos u hardly laugh, u smile more our silent Zee our damsel" Zee tai murmushi kawai tana girgiza kai tai gaba "i donno wat come into u dis night maybe u met with a sprit" ta karasa fadi tana acting horror face... zakiyya tai dariya kadan itama tabi bayan Zeen dake nupar kitchen A kitchen din Zee ta soma tattara kayan da zatai amfani dasu, Zakiyya tana dariya ta ajiye mug din hannunta "to me za'a dafa mana kuma bari na tsaya nai kallo" Zee tace "tsaya ki gani ko na girka dake ne?" zakiyya tace eh ayi dani, Zee tace okay.... Shiru ne ya biyo baya kamin zakiyya tace "wlhy zee fa dazu gaskiya nake fadamiki, kingane ko, irin silent beauty dinnan gareki wanda ba kowanne ido ne ke iya gani ba, se mai idon basira irin mu" Zee tai murmushi jin hirar zakiyyan, to sannu masu idon basira....Zakiyya bataa fasa ba ta cigaba, "just look at u in kaji ana fadin the real african beauty to kece kat" Zee ta tura mata mug of coffee din, "ungo ya isa dama cin hancii kike bani to gashinnan asha lpia" zakiyya ta karba, itama Zee ta dauki nata duka suka fito, saida zakiyya taje gun karatun nata sannan tasha tana ta santi, itama Zeen shan nata take, zakiyya tace " the taste is milky sugarcy,no juicy, no tasty indeed its superb" ta fadi tana hade babban yatsanta da manuniya ya bada zero...👌🏻 Coffee din da Zee tasha yayi boosting energy dinta na karatu ya dawo... Haka wannan semester ta kare bayan sunsha exams, yanxu Zee har ta saba da zaman gidan Abbah jabir, musamman kasancewa da zakiyya wacce ta kasance wadda sukafi kusanci acikin gidan, Zakiyya ta maida jakar ta rufe, ta karaso inda Zee ke zaune tana danna waya, "nima gaskiya inaso na biki mu tapi gidan Anty hawwer tare, Zee tai er dariya "to ai Abbahjabir zaki fadima ba ni ba" zakiyya ta tabe baki "badai kyaso muje tare amma da kinaso ai da kinyi mai magana" Zee ta dafa zakiyya "er uwa kiyi haquri yanxu kinga lokaci ya kure tunda gobene tapiyar ki bari next in shaa Allah zanyima Abbah magana sai muje tare" Zakiyya tace to Allah ya nuna mana daga haka suka shiga wata hirar har khairi tazo ta taddasu itama tai joining, Kashegari kamar yadda aka tsara din Zee ta tattara komi nata ta kama hanya dama already sunyi magana da Abbahjabir ta waya ya tabbatr komi ya kammalu sannan ta hau jirgi suka daga saudiyya bayan rakiyar da su zakiyya sukai musu... Dadi kam da annashuwar da Zee ke ciki ma har ba'a magana, ta rungume hannayenta biyu a kirji tana doki da son haduwa da er uwarta tsoka daya a miya bayan jirgin yayi balance a sama ne ta cire belt din tana mai relaxing kan kujerar sannan ta lumshe idanunta tana mai murmushi lokaci zuwa lokaci, Ya sake kallonta a karo na barkatai, anya wannan kalau take kuwa, she's just smiling and blushing alone, ya dan ja tsuka bamai sautin qara ba, Koda masu tmbyar abinda mutun zeci suka zo gun Zee cewa tai itakam ruwa ma kadai ya isheta, dan batajin zata iya cin wani abu yadda take dokin nan bata ma son cin komi, na kusa da ita aka tmbya, itakam se yanxu ta tuna akwai mutun ma kusa da ita, Dayake shine a window itakuma tana baki,,, sanda tazo ma zamanta kurun tai bata kalli inda yaake ba, shima din bai damu da hakan ba, sama sama ta dan kalli fuskarshi, sai kuma ta sake juyawa ta kallleshi, his face seems familiar, amma a ina tasanshi, ganin kallon nata yayi yawa ne yasa ya kwanta ya rufe fuskarshi da hanky, Zee ta tabe baki a ranta tace aikin banza, amma a ranta tanaso ta tina inda tasan fuskar matashin saurayin da be wuce shekaru 31 ba a duniya, Dayake jirgin nasu direct saudi ne yasa basui tsaye tsaye ba, koda jirgin su Zee ya sauka uncle muzakkir (mijin Anty hawwer) ne yazo ya dauketa da kanshi danma saida tasha jira yana kiranta yana ta bata haquri kan gashinan, hakan yasa mutane da dama sun tapi sun barta a gun... A gajiye ta karasa tsararren gidan na Anty hawwer inda suke zaune da maigidanta a birnin madina, uncle muzakkir ne ke sanar da ita Anty hawwern tana school bata dawo ba, er aikinta Binafat kurun ta tadda, dukda gidan kuwa ba wani kato bane, selfcon ne mai dakuna hudu, sai kitchen babba da toilets in each bedroom, akwai dining area, gidan kam tsararren mai kyau, wannan shine zuwan Zee na farko gidan, uncle muzakkir ya nuna mata dakin da zata zuba kayanta, ta karasa takai kuwa, sannan yace shima ze fita anjima ze dawo, Ruwa ta shiga ta watsa lokacin karfe 11 da mintuna ne na rana a saudiyyan, hakan yasa ta kwanta, bata tashi ba sai karfe kusan 12 da en mintoci ta tashi ta wanke fuskarta ta fito ta shiga inda ke sakata nishadi dan har lokacin anty hawwern bata dawo ba, Binafa ta tarar tana aikin chopping veges din da zatai girki dasu, suka sake gaisawa da Zee sannan tace "wat are we having for lunch?" Binafa tace "am yet to decide" Zee ta jinjina kai tana kallan kitchen din da sake dubawa, ta kalli kayan da Binafa tai chopping sannan tace okay just leave the rest to me i will cook today" binafa tai shiru tana tinani "but ma i dont think ma'am will like d idea i think is better u let me do my job pls" Zee ta jujjuya kanta, sannan ta dafa binafa "just trust me she'll not only like d idea but she'll love every bit of it, hav faith in me" Binafa ta jinjina kai tana murmushi kadan nervously, dukda haka bata bar kitchen din ba tana tayata da miko wannan miko wancan, Special rice ta dafa wacce tasa veges da curry (wanna see d pic? Its on wattpad) snan tai sauce da kaji kamar pepper chicken.... Tun kan ta karasa suka jiyo motsin taba kofar shigowa falourn wanda ya tabbatr musu cewar Anty hawwern ce ta dawo, dan gurin parking din ba hade yake da gidan ba, underground parking space ne saboda su basu fiya parking motoci cikin gida ba sunfi gane su haqa kasa sui underground, duk mostly haka gidajensu yake.... Shigowar datai ne yasaka taji wata kasala ta shigeta saboda kamshin girkin daya turare gidan, (cikin sirrikan girkin Zee shine yanada tashin kamshi ta iya hada simple spices kuma su bada kamshi mai tashi da zai cika duk wani lungu da sako ya tadama da yunwarka, Wani kasaitaccen murmushi Anty hawwern tayi "this is my sister's handwork for sure" ta fadi tana nupar kitchen din da nihal dake kafadarta tana bacci, Zee na tsaye ta harde hannaye tana jiran shigowar anty hawwern dan tasan tabbas zata shigo din, aikuwa ta shigo tana mai zumudin son haduwa daa qanwarta, dukkansu murmushi suka sakar ma juna mai cike da tarin sakonni, Zee ta karasa gun Anty hawwer dake tsaye dauke da nihal, ta saka hannu ta amsheta tana mai shafa bayan diyan, sannan kuma sukai sidehugging juna, Binafa tana kallonsu tana ta murmushi abinta dan sun burgeta, so classy Saida Anty hawwer tace a bude mata tayi tasting abincin dake bada wannan kamshi dan ko tantama batayi tasan shinkafa ce saboda sanin soyayar dake tsakanin Zee da shinkafar.... Sanda ta tauna shinkafar ta kusa hadiyewa sanna ta jujjuya idonta, "ohh i really love it," Zee tai dariya ta kalli binafat "haven't i told u she will love it" Anty hawwer tace definitely its yummy"..... Koda uncle muzakkir ma ya dawo, ya yaba da girkin Zeen dukda dama ya sabacin abincika masu dadi daga gurin matar tashi, but still there's special taste in Zee's blessed hands"... Tunda Zee tazo Anty hawwer ta dena tapiya da nihal makaranta, take barinsu tare a gida, kuma Zee ta karbe girkin gidan daga hannun binafa, sedai in Anty hawwer na nan suyi tare abinsu 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 16: challenge Ba kadan ba Zee ke enjoying zama tareda Anty hawwer ta sake koyan wasu sirrikan girkunan gun Anty hawwern, dana waje dana gida dan har tuwo ta sake kwarewa a wajen girkawa dukda ba wai ita abincinta bane, duk ranar da Anty hawwer battada school sukan fita shaqatawa taita nuna mata gurare, wani sa'in ma idan karatunnata ba yawa tare suke zuwa makarantar su dawo, hakan yasa yanxu Zee tasan gurare dayawa har masallaci ma tana zuwa dakanta in an kira sallah, dan gidan nasu baida nisa da masallacin madinan,,, Its another bright saturday, weekend, duka su biyun sun kimtsa ko ina babu abinda ke tashi sai kamshin turaren wuta, dukda sukanyi gyara amma aikin na yau na daban sakamakon bakon da zasuyi a gidan, Zee tace da Anty hawwer "ni fa i don't get it, wats so special about dis guest dat u two are all cautious as if its d sheikh al sudais dats visiting" Anty hawwer ta girgiza kanta tana tabe baki, "mind ur tongue u girl u re so annoying wallah" Zee itama tabe bakin tayi, okay acikin mu naga waye annoying ai... Haba hav been pleading with since dis morning for u to tell me who is visiting but u re dodging" "Okay yanxu bari na fadamiki ko hankalin kowa zai kwanta, Jiya da Abban nihal yaje sallan magrib a masjid ne, suka hadu da wani old friend of his tun school time, kuma babban mutun ne a kasarmu nigeria, dan nasan wa'inda basu san face dinshi ba daddaiku ne," Who is he? Zee ta tbaya "The great Alh. Yusuf Abbakar As_siddique, the As_siddique's CEO, the young billonaire, the African's third billionaire, the Nigerians number one billonaire" So are u satisfied my lil sis?" Zee ta jijjiga kai kmar kadagaruwa jin wannan uban kirari da ake mishi, Kuma kinsan meyasa yace zezo? Zee ta sake jujjuya kanta a sanyaye "Saboda Abban nihal ya fadamishi babu inda ze samu well served delicious food, se a gidanshi" ta karasa fada tana nuna Zee a matsayin ita kenan me wannan girki, The moment he heard about d nice dish he quickly agreed without any hesitation, do u know why?" Zee ta sake karkada kai a hankali "Well bcoss he loves food my dear, he's addicted to nice dishes and he hardly get the time to eat due to his tight schedules" Miqomin wayata na nuna miki pics dinshi, Zee ta janyo wayar Anty hawwern, itakuma ta tapi searching sunanshi a insta, saidai taga acct. Din nashi private ne, dan haka ta sauya akala ta koma Wikipedia, nan da nan sai ga hoton, Alh. Yusuf ya bayyana, Zee ta amshi wayar tana kallon hoton, he's d same guy data hadu dashi a jirgi sanda zata taho, her jaw drop.... a cikin ranta take fadin "idan dai har shidin billonaire ne kamar yadda anty hawwer ta fadi, meyasa ya biyo flight bebi private jet ba?, and ya akayi yake da time haka da har ze iya sparing yazo dinner kuma why is he all alone sanda ta ganshi babu wani guards, ko P.A atleast"..... Da idanuwa Anty hawwer kebin abincika da kallo kamar ta cinyesu duka, they re all served in an inviting way, plated so nicely and lovely, but u won't judge until the mastication starts, Karfe 7 ta buga daidai sanda suka ida parking motocinsu suka shigo cikin gidan, sunata hira jepi jepi abinsu, bazaka kalli As_siddique kace shine As_siddique dinba a yadda yake free abinshi saidai in ka kalli suturar jikinshi zaka san naira tayi ihu, already everything is served on d dining area, koda suka shigo falourn babu kowa, ya sule takalmanshi tun daga bakin kofa, kyawawan kafafunshi suka bayyana, ya karasa dining area batareda ya jira uncle muzakkir ya mishi iso ba, "I just can't wait seeing d dining full already" ya karashe mgnr yana murmusawa, shima Uncle muzakkir yai dariya, babu wani damuwa ya zauna sosai ya sakko da abincikan kasa dan ba al'adarshi bace cin abinci a sama, yayi serving kanshi dan already, his mouth is watering, Bai tsaya jiran ayi mishi bismillah ba ya soma ci, uncle muzakkir kuma dakinsu ya wuce ya tarar da Anty hawwer taa fito daga wanka tana shiryawa ma almost done, dankwali kurun ya rage, haka ya saka ta daura tasa gyale suka fito, Koda ta shigo falour mamaki ya kamata ganinshi tsakiyar falour yana baje koli abinci, ta kunshe dariyarta dan da alama ko ganinsu beyi ba, gyaran murya uncle muzakkir yayi, sannan suma suka zauna, uncle muzakkir yai joining dinshi, "Abban nihal ina Zee?" Ta fada tana dube dube, bayan sun gaisa da As_siddique.... uncle muzakkir dake kokarin fara kai abincin baki, yace gaskiya ban ganta ba tun shigowata, Miqewa tai ta karasa kitchen dan ta barta tana cewa sai tayi fruit salad, ya mutun zeci abinci babu fruit da zasu taimakwa abincin yai digesting, aikuwa tana ta aiki Anty ta taddata, ta kammala hada fruits din sai coffee datake saukewa, Ta rike haba, lallai sannu ke bama kya gajiya da girki naga alama Zee tai murmushi To kizo muje ku gaisa, Zee ta zaro ido, a hakan? Haba Anty ai kawai ki karasa musu dashi nikam wanka zanje nayi kmr yadda kikai wanka, idan na gama basu gama ba ma gaisa, Okay cewar anty hawwern, "To yanxu mene amfanin wani coffee" "Ai anty dinner babu coffee lami ce" wananan kuma ke kika sani, ta dauki bowl din fruits din ta soma kai musu itakuma Zee ta shige dakinta zuwa bandaki, da kamar bazata kai musu coffeen ba amma se ta haqura dai ta kai gudun kada Zee taji haushi, Lokacin har ya kamaamala cin abincin be bar komi a plate dinba, haka dabi'arshi take indai abinci ya mishi dadi, bai kula fruit ba bisa mamaki taga yakai hannu ya dau coffee yana fadin "kinsan shi idan ya huce bazeyi dadi ba" Dadin girkin da As_siddique yaji ne yasaka ciro kudi irin naamu na gida nijeria ya ajiye sanda yazo tafiya yace abama wacce tai girki tukuici,, dan Anty hawwer ta sanar dashi ba itace tai ba, "Looking forward to see her" shine abinda ya fada sannan ya musu sallama ya tafi, Zee na zaune gaban dressing mirror tana shafa mai, taji alamun sun fito, ta dan yaye curtings din saidai bayansu ta hanga kurun.... Abban nihal yaita bama Zee labarin irin santin da Yusuf As_siddique ya dinga mishi bayan fitarsu itakuma se dariya take, wai harda cewa ban taba cin abinci mai dadin wannan ba kamar ba'a duniya ba, its out of d world" Duk suka saka dariya, Anty hawwer ce tace "ai gaskiyarshi girkin Zeen is out of d world" uncle muzakkir ya dora da "exactly" "Yace ma fa badan satar hanya yayo ba da se ya kawo personal cook dinshi ta koyi one or two things" "Au nan ba'a san ma yazo ba kenan" cewar Anty hawwer "Ai yallabai baze barshi ba shiyasa kika ganshi single babu ko guard balle cook ko P.A".... Zee a ranta ta samu amsar tmbyarta ta dazu Zee ta dauki kudin ta raba biyu ta basu rabi rabi dan sunyi mata komi itakam yanxu tasan battada kamarsu a rayuwa tunda ta rasa su Ammi, gudun kada taji babu dadi yasa suka amsa, Satikan Zee biyar da kwanaki uku a gidan Anty hawwer zeena ta kirata, tasan tunda taga kiran zeena zancen daya ne dan shi aketa nanatawa cikin en kwanakin nan a cewar zeenan duk sanda sukai waya, A sanyaye tace "zeena an kafene?" Zeena tace "eh Zee dazu da safe aaka kafe, nima yanxu haka aka turomin na samu 3.55 CGPA kuma 3.41, Zee ta sauke numfashi ta zaqu taji nata sakamakon, Nikuma fa? Ta tambayi zeenan? Kema haka Zee saidai ke kam akwai carryover, gwale idanu tai jin tanada C.O, "practical ce ko?" Zeena tace eh a sanyaye, hawaye suka ziraro daga idanunta, shikkenan karantunta ya soma tabarbarewa tunda tai rashin su Ammi Bata baki sosai Zeena takeyi daga haka harta haqura tana mai kara karfafa mata gwiwa da cewar zata iya din.... Da Anty hawwer ta dawo ta tarar da ita babu wani kuzari ta tambyeta, Zee taji ruwa na taruwa a idonta, C.O akwai cin rai, ta rungume Anty hawwer tana kuka, lallashi Anty hawwer ta shigayi dukda batasan dalilin kukan ba saida ta dena dan kanta ta soma ma Anty hawwern bayani "Result dinmu ne ya fito Anty, kuma inada C.O guda daya" wasu hawayen suka sake ballewa, Anty hawwer ta rike haba, wai dama duk saboda C.O kwalli daya ake wannan kukan, "Kuma wlhy Anty sau uku ne banyi attending practical dinba, lokacin da nai rashin su Ammi ne danayi sati da kwanaki banje ba, ashe malamin yayi ta fixing classes kuma yace du wanda baya zuwa to bazeyi passing course dinshi ba, ta sake sarce hawayen takaici Saida Anty hawwer ta jira ta gama sannan ta soma bata baki cikin kulawa tana mai bata haquri da fadin samun C.O bawai yana nupin karshen karatunta bane a'a yana nupin ta kara kaimi ne cikin karatunta..... Kaimi kam Zee ta kara Saura sati biyu su fara registration, an kafe musu yawancin courses din da zasuyi dan haka Zee taita browsing littafai tana ajiyewa, saida ta tara harda vedios na karatu sannan ta soma, da biochemistry ta fara karatun nata, to koda aka fara registration Zee ta turawa zeena kudin tayi mata online a can, Anyi resumming school da sati daya sannan Zee ta soma shirin komawa sanin da tai koda an koma da farko ma ba wasu abubuwa za'ai dayawa ma daga cikin lectures din du ba'a faraba, kuma tana jin dadin karatun datake a can din.... Wayar da zakiyya tayi mata kuwa tapi dari dukdan ta dawo fa an fara lectures, dayake itama ta samu admission a BUK din amma ita computer ne ma to ita a new campus tke.... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 17 & 18: Stranger Ranar litinin da safe ta sauka a nigeria, bayan goma ta arziki da Anty hawwern ta hadata dashi dan seda ta hadawa kowa tsarabarshi a gidan sanann itama Zee nata daban ma.... Hakama Abban nihal ya karbi acct numberta gun Anty hawwer ya tura mata kudade,,, bawai dan Abbah jabir ya gaza ba sai dan basaso taji kamar itadin marainiya ce ta nemi wani abu ta rasa kuma ta kasa samun wanda zata tmbya Hutawa tai a ranar litinin din ta kuma rabawa kowa tashi tsarabar, kashegari talata kuma zata koma school, saida ta tabbatr ta kimtsa komi nata, ta duba timetable din da aka turo dazu a watsapp group dan rabonta da watsapp tun barinta Nigeria,, karfe 8 ne lectures din goben, kuma Classrep. Ya tabbatr malamin zezo kuma yayi gargadi da zuwa a makare dan malamin bayaso, Ganin lecturen biochemistry ne yasa bata wani damu ba tunda already ta karantashi sosai abinda ya rage kawai taje taji sabon lectures din malamin shikuma ta kara da nata ilimin dan wannan semestern bazata saka wasa ba Abinda Zee take gudu shine ya faru dan kuwa ta makara hakan yasa taketa zabga sauri gashi sai kiranta hudiyya (course mate dinta, saboda yanxu lecturen su ya rabu da zeena) take tana jaddada mata malamin fa ya shiga cikin aji... Karfe 8:40 (2hrs lecture ne 8 to 10am) aka sauke ta ta karasa bakin kofar lecture theatre din mai dauke da mazaunan dalibai kusan dari biyu... Zee ta chanja akalarta zuwa siririyar kofar dake ta bayan theatre din dan ganinta inta shiga ta baya zepi mata sirri dukkuwa da sanin datai malamin nasu me lecture yau bai son makara kuma idanun dalibai du kanta zasu dawo kuma sits din gaba duka tasan an cikesu, da wannan tinani nata tabi ta kofar baya, lecture hall ne me kama da class ba irin sauran theatre dakeda bene ba, sanda Zee ta shiga malamin yanata bayaninshi kamar be lura da shigowarta ba hakan yasaka ta zama daga baya baya sit na biyun karshe inda ta hangi space ta fada gudun kada malamin hankalinshi ya kawo kanta, maida hankali tai ga lecture din da malamin keyi saidai addababben kamshin turarenshi ya debi hankalinta, ta dan lumshe ido tana mamaki wai namiji da Arabian perfume, dan ko bata juya ba tasan namiji ne, tanason Arabian perfumes musamman in tai mixing da humra, A nashi bangaren shima, yajiyo sanyayyen kamshin turarukan datai mixing dukkuwa daba masu tashi ne sosai ba, yanason kamshin nan dayakeji na tashi a jikinta, a hankali ta dan waiga hannun ta na hagu inda saurayin ke zaune, sanye yake cikin yard mai laushi da saukin nauyi, fari kar kafafunshi rufe cikin bakin takalmi, hannunshi dake kan teburin ta kalla ya'daura bakin agogo yatsuntsi kuma biyu sanye da azurfa sai sheqi suke, daga ido tai dan son ganin fuskarshi kadan ta saci kallonshi amma sai taga batasan fuskarshi ba cikin en department dinsu ta basar ta cigaba da jin lecture din dukda a baya take amma tanaji, shima a nashi bangaren ya dan saci kallonta,, ba fara bace kuma ba baqa bace kuma tapi chocolate haske, somehow sandy complexion, "she's cool" ya fada a ranshi..... Babu zato balle tsammani malamin ya nuno Zee yana mai cillo mata tmbya "Explain all dat i hav explain" hakan dayayi ya tabbatr yaga sanda ta shigo, dan haka yakeyiwa duk wani makararren daya shigo ajinshi a karshe, idan baka iya ba kuma ya disga ka Zee ta miqe ta soma jawabi wanda yasa duka ajin juyowa gareta amma sam malamin yace shi bejin me take fadi tafito waje, with her full confidence ta fita fuskarta babu yabo babu fallasa kuma babu ko digon tsoro a fuskarta dan taga alamar malamin dan rainin hankli, Bayan ta daidaita tsaiwarta ne ta fuskanci class din ta soma da fadin "good morning class" dukka aka zuba mata na mujiya da mamakin harda wata gaisuwa ma, sai ta fara bayanin CHO (carbohydrate) din kamar yadda yace tayi Tun daga bayanin mene shi carbohydrates ta fara wanda bata nan ma sanda yayi sannan ta cigaba da bayani kan CHO (carbohydrate) din amfaninsu na main source of energy for all living organism sannan ta dora da structural component na CHO da inda ake samunshi kamr a structure na DNA da kuma plant cells (cellullose) Ta cigaba da fadin CHO contains mainly carbon, hydrogen and oxygen atom (C-carbon, H-hydrogen, O-oxygen atom) sannan ta fadi molar ratio din da ake samun atoms din wato 1:2:1 ma'ana carbon 1 hydrogen 2 Oxygen 1, Ta cigaba da bayanin types na CHO, sune mono-saccride, Di-saccharide, oligo-saccharide and poly-saccharide Zee ta dora da fasa musu me ake nupi da shi saccharide, which comes from a greek word for SUGAR Ta cigaba da fadin "let look at each types of dis carbohydrate, their structure and their formation, Ajin ya sakeyin tsit saboda jin lecturen nata so intresting, yadda take baje bayani dalla dalla yadda kwakwalwar kowannensu zata dauka Zee ta karasa ta dauki marker, dake jikin white board din nasu, ta soma rubutu, shi kanshi malamin kallonta kurun yake Monosaccride ta rubuta as a heading Sannan ta juyo ta kallesu tana musu bayanin shi monosaccride a matsayin simple sugar, kuma smallest unit dat make up any CHO Sannan ta juya ga allon ta soma zana structures guda uku a kasan kowanne structure ta rubuta sunansu, Glucose, Galactose and fructose ta juya tana cigaba da musu bayanin kowanne CHO (carbohydrate) Sanda takai gurin fructose sannan maalamin ya tsaida ita dan yaga battada niyyar tsayawa, Aikuwa nan da nan ajin da dauki tapi ana shewa ana ihu, wani kasaitaccen murmushi ya bayyana a fuskar Zee wanda ya bayyaanar da asalin kyawunta, Saida malamin ya tsawatar sannan ajin akai shiru, yace "wats ur name" Zee tace "Zainab muhammad sir" Dalibai suka dauka zainab zainab zainab, yanxun ma saida malamin ya sake tsawatarwa, sanann ya kalli Zee yace "u earn 5marks u really impress me i must say" Cikin jin dadi Zee tace thank you sir, sanann yace ta koma sit dinta Kusa dashi ta koma, a nashi bangaren shima kamar yadda Zee ta birge kowa shima din hakanne, tazauna tana mai saita numfashinta dan ita kanta tasan ba karamin kokari tai ba, A haka har aka tashi a lecturen, Abinda Zee tai ya saka da yawan daliban suke magana da ita duk inda suka ganta sukan gaisa both mata da mazansu, har wasu ke ce mata 'kwaruwa.... Sai yamma Zee ta shigo gidan itada zakiyya da suka biya newsite suka dakkota tun daga parking lot din suke ganin ana fito da kayan furnitures, zee ta kalli zakiyya, "yau kuma mene ke faruwa a gidan, kamar kayan Anty siyama nake gani", zakiyya tace "Au ashe ke fa bakya nan bakisan me ya faru ba" kedai yanxu mu shiga mu huta tukun zan baki labari... Gidan a dan hautsine suka sameshi, zee ta kai jakarta daki ta hau sama dakin Anty siyama, saidai tun kan ta karasa ta jiyo hayaniyar hirar su Anty siyaman da autarsu *Minnatullahi* Zee ta karasa falourn inda ta tarar du an kwashe kayan ciki hatta carpet da electronics, kujeru ne kawai ba'a dauke ba, Zee ta gaidasu duka su biyun suka Amsa, dan minnatun ma ta girmeta da kusan shekaru 4, Sai bayan sallar magriba, zakiyya ta shigo dakinsu Zee, Zainab na kokarin fita daga dakin sukai kacibus, dan kusan duk yaran gidan suna babban falour, Zee tace "ai yanxu gurinki nake shirin zuwa na dauka ma ko kina falour ne", Zama zakiyya tai, kedai zauna kiji labari, itama zee ta zauna, "ai bayan tapiyarki ko ince daf da zaki dawo nan, ranar Anty siyama bata dade da dawowa ba, mukaji sunata rigima da umman halipa, wai Abbah yace kar ta sake ta raaba mishi gida, mamanmu ma data dawo tace itama yace ta sake jaddada mata tunda ta dena daukar wayarshi, se a gurin ya_kubra nakejin abinda ke faruwa wai ashe abban Anty siyama ne, ya gina mata wani gida mai kyau, itace tace mai ta gaji da zama gidan yawa" Zee tace "to yanxu babu izinin Abbahjabir zata koma gidan?" Zakiyya tai dariya "Inafa ya rigada ya yarda dan baze iya ja da sirikinshi ba, kinsan fa dama a yadda mukaji ba wani son Abbah take ba, Abbanta ne ya bashi daya nema, su kuma a gidansu dama shine ke zabawa kowacce 'ya mijin da zata aura, kuma mutun ne dake spoiling yaranshi in suka mai biyayya, dan abinda yapi gida ma ze siya mata tunda ta auri zabinshi" Zee tace "Allah mai iko, kowa da nashi tsarin rayuwar"... "Eh fa kuma har kayan daki du ze chanja mata, kuma ance wlhy gidan me kyau ne irin tsarin en gayu dan harda wallpaper ya saka mata bayaga aircorn gashi ya kubrah tace solar ma ake hadawa yanxu da tuni ta tare" zee ta rike haba, "kice yanada kudi" Zakiyya tace "sosai ma, dukda yanxu duk ya rabawa yaranshi maza kasuwancinshi, kuma yanada manyan mutaane a kasar nan, saidai shi baya zuwa neman aure ma 'yarshi, saidai gidan maza suzo shikuma idan ya yaba da hankalin mutun se ya aura mai"...... Weekend ya kama ranar tarewar Anty siyama a sabon gidan nata, dan hatta kayan sakawarta ta gama hadawa kuma kowa yasan tareda zee zata tapi tunda a gurinta take, hakan yasa itama ta kintsa komi, rakiya sosai akayi musu kowa yaje gidan sai sambarka... Duk gidan babu wanda zee ke jimamin rabuwa da kamar Zakiyyan, tapi shaquwa da ita fiyeda kowa a gidan, gashi dama basu wani shaqu da Anty siyaman ba, iyakaci ta sakata aiki ne itakuma tayi shikkenan danma aikin gidan beda yawa tunda an dauke wanke wanke da wanki da kuma sauran ayyukan da mai aikin takeyi, Zakiyya, khairi kubra da Zee kurun aka bari sunata sake kallan gidan sunce sai magariba zasu dawo, sauran yara kau du an maidasu da iyayensu, iyakacin dangin Anty siyama ne kurun a gidan suma din daga Minnatu autarsu se ya Hibba wacce ke tsakanin Minnatu da Anty siyama amma ita mamanta daban dasu, Zakiyya da Zee suna kitchen Anty ta sakasu hada musu abinci da drinks, Zakiyya tace "yanxu zee babu ruwanki da hayaniyar gidanmu kinji dadinki, saidai abinda ban gane ba tayaya Duk girman gidan nan Anty siyama bata dauki mai aiki ba.... Bata ida zancenta ba, khairi ta fado kitchen din tana dariya-dariya kadan, Zee da Zakiyya du suka zuba mata ido, ta matso tsakiyarsu da sauri, ta soma magana a hankali "Kunsan me na jiyo yanxu naje zan shiga dakin Anty siyama na mata sallama?" Duk suka girgiza kai "wai ciki ne da ita na wata hudu da satika,. Se qanwarta tace meze hana ta dauko er aiki tunda gidan da girma kunsan me tace?" Suka sake girgiza kai suna kallanta "wai ai baga zee ba budurwa mene amfaninta, kuma ita batta son kazantar en aiki wai gwamma dai ke din" khairi ta ida tana kallan zee din, har cikin ran zee bataji dadin furucin da khairi tace Anty tayi a kanta dinba, me hakan ke nupi?.... Anty siyama bata bar su Kubra sun tapi ba saida suka gyara gidan tsaf, sannan suka tapi, ya Hibba ma ta tapi sai minnatu aka bari wacce ba yau din zata tapi ba, gidan Anty siyama dan kyau kam yayi kyau, Gidane mai babban falour bayan driven, a cikin falour akwai dakuna hudu amma daya babu kaya a rufe yake, sai fantameman kitchen daga baya haka amma ta cikin falourn akwai kofa, sai kuma bandaki a falour da kuma cikin dakuna biyu, daki daya mai bandaki Anty siyama ta dauka ta barwa zee dayan.... Su Zee suka wayi garin ranar lahadi cikin koshin lpia a sabon gidan Anty, dama tun sanda tai sallar Asubahi bata koma ba tana kan daddumar, da misalin karfe 8 na safe Anty ta kwankwasa dakin da zee take, ta tashi taje ta bude mata dukda bata saka key ba, Anty ta shigo dakin , zee kuma ta gaidata da fadin "An tashi lpia, ta gyada kai kurun sannan tace "Kinga yau i need something early for breakfast, pls" Zee da tasan Antyn na halin laulayi ne tace me za'a dafa Anty?" "For now ko sandwich ma will be okay, ki duba akwai duk abin bukata a kitchen and pls ki hadomin da coffee" zee ta gyada kai kurun, Mintuna marasa yawa zee ta dauka ta kammala hada sandwich din mai sauki na bread da minced meat da cheese, sai kuma cup of coffee din, zee bata hada da kanta ba dan ba al'adarta bace shan coffee da safe, Dakin Anty ta nupa ta kwankwasa, aka bata izinin shiga da yes, ta tura kofar,, kafafunta suka luma cikin foot mat mai laushi dake shimfide a bakin kofar dakin, Minnatu na kwance kan gadon daga can cikin dakin itakuma Anty na zaune kan cushions din da aka jera cikin dakin, zee ta karasa ta aje mata a kan glass center table din mulmulalle mai kyau sannan tace "gashi Anty", sannu shine amsar Anty sannan ta dora "Kinga naga falourn yayi kura dan share ki goge" zee tace to ta fita ta hau aiki, ba laipi yana da fadi falourn dukda set daya na kujeru ne cikinsa amma akwai wahalar shara ga bangaren dining, abu kamar wasa haka Anty tai ta saka zee aiki ita ko sedai tace to, itace ta musu komi a gidan Yanxu haka ma girkin abincin rana ta sauke, babu komi cikinta sai tea data dan kurba da biscuit, tayi serving kanta nata abincin ta bar musu nasu a warmers dan Anty bacci ma take minnatu kuma na wanka, karfe 5 na la'asar minnatu ta kammala duka shirinta ta dubi Anty dake zaune kan cushion din dakin ta miqe kafa, "Gaskiya girkin dazu yayi dadi, ke kam anty kin samu cook a bagas" Anty tai murmushi "tsuntsu ne daga sama gashasshe Allah ya aikon" duka suka saka dariya... Minnatu ta kammala nata shirin itama ta tapi, Sanda zee sukai waya da Anty hawwer ta sanar mata duk abinda ke faruwa cikin gidan Haquri shine abinda Anty hawwer ta bata da fadin "kiyi mata biyayya Zee karki sake ki nuna mata wani abu dan in kinyi mata ba faduwa kikai ba, ki bari ku rabu lpia dan ko kinyi mata rashin kunya ma babu abinda ze kareku daga ke har ita" Wanke_wanke, Shara, goge goge a takaice duka ayyukan gidan zee keyinsu, wanki ne kurun Anty keyin abinta a washing machine Ranar litinin ma saida zee taiwa Anty aikin gidan sannan tayi nata shirin na makaranta, saukinta ma tapiyar ita kadaice kuma yanxu a sharada suke dukda akwai er tazara amma ba kamar daa da suke darmanawa ba, Dayake lecturenta na yau ma safe ne amma practical C.O dinta ne Ta dora labcoat kan kayanta ta shiga lab din, bayan sun kammala practical dinne ta fito ta nemi wayar zeena, Kina ina? Ta tmbya zeena tace ina class amma lecturer'n ma bezo ba da alaama bazezo ba, okay zee ta fadi Sannnan ta nemi layin hudiyya, hudiyya ta dauka tana fadin "zee ina kika shiga ne" ta fada muryarta kasa kasa alamun bataso ajita Zee tace kardai akwai lecture hudiyya tace "eh mana munada embryo mana tun 9 ya shiga yanxu saura 1hr ya gama" ganinan to.... Tai tsaye a bakin kofar ajin tana jimamin shiga, kofa daya ce da class din kuma ta gaba babu yadda zata shigaa ba'a ganta ba kuma dole ta gaban malamin zatabi, Wannan gaurayayyen arabian scent ya daki nostrils dinta lokacin iska ta kado zee ta juya gefen hannun damanta inda ta hangeshi yana cigaba da tahowa iska na karkada gyalenta da kayanta suna yawo, he's dressed in a pure white male Nigerian kaftan well ironed, walking majestically, his right hand buried in his pocket... Ganin da tayi yana nufo inda take yasata saurin dauke idanunta daga kallon datake mishi, ya karaso yana mai shafa beard dinshi da gyaran murya, zee ta daga kanta tana sake maida kwayar idanunta kanshi a karo na biyu, Cikin cracky voice dinshi yace "Assalamu alaikum" ta janye daga kallanshi zuwa gurin datake hange wasu korayen flowers, sannan ta amsa mishi sallamarshi "It seems we re on the same plane... we late" Zee ta jijjiga kai, tace "u also part of the embryology class?" Ya dan lashi lips dinshi sannan ya gyada mata kai, Ta dan saki fuska "so am not alone" yace yes am also not alone" sukayi murmushi duka har nashi ya fidda sauti, Suna nan tsaye babu dadewa malamin ya fito har ya gama... Karfe 12 na cika zeena ta kirata lokacin tana tare dasu hudiyya cikin theatre suna dan duba lecturen da aka musu, zeena tace "hey latecomer" zee tayi silent smile dinta as always tace "ina department" "okay hurry up mu hadu a cafteria yunwa ze kassheni" zee tace "okay my chop_chop" saida suka karkare karatun da hudiyya sannan tace mata "muje cafteria zeena tana can" hudiyya tace no kuje banjin yunwa, to dayake dama they're not dat close yasa ta wuce Tana shiga cafterian taji presence dinshi a ciki, ta soma waige waige inda zata hangeshi, he's calmly seated, hannunshi daya rike da waya a kunne yana magana amma idanunshi suna kanta tun sanda ta shigo, suna hada ido gabanta ya yanke ya fadi, ta sauke idanunta kafin ta sake dagasu amma sai ta chanja musu direction, hannun zeena ta gani yana flying a sama hakan yasa ta karasa inda take jiki a sanyaye, Already zeena tayi ordern sakwara da miyan alayyahu dan har ta soma ci, ta dubi zee "kin zauna kinyi shiru ke dai matsalarki dabance a rayuwa wlh" zee ta dubeta kurun bata damu ba sai kai lomomi take, "me zakiyi order? Dan nasan shegen iyayinki inyi miki order ki yarfani kice bakici kowanne abinci a gurinki beyi ba se naki" zee tace "easy mana duka wannan surutun fa ko so kike se kin kware" zeena ta tabe baki ta cigaba da aikin cin abincinta, Zee kuwa gabadaya jinta take a takure dan ko tantama batayi tasan kallonta yakeyi, tai tagumi.... tanaso ta juya ta kalli bari dayake amma bataso su hada ido, suna nan zaune taji kamshin nashi ya matso kusa da ita, ta daga kanta ta ganshi gefenta yana tafiyarshi cikin izza still yana magana a waya har ya fita, Kin sanshi ne? Shine furucin zeena sanin da taiwa aminiyar tata kallo be cikin dabi'arta balle har ta bi mutun kuma namiji ma... Yaddaa take batason alaka da mazan, Zee ta sauke numfashi ta kalli zeena "i donno, i just feel like i know him, its like we re connected" zeena ta kurama zee ido "are u okay?" Zee tayi banza da ita dan tasan shaqiyancinta, Ta saka bayan hannunta tana taba wuyanta tana cewa "Allah yasa ba fever ya kamaki ba kike sambatu" cikin sanyi zee ta cire hannun zeena daga wuyanta Zeena bata fasa zuba ba "Yau zee kike maganan wani saurayi ai na dauka kece zee dake tsoron mu'amula da samari" zee ta girgiza kai kurun ta kyale zeena... Sauran lectures dinsu akace duka babu dan haka zee ta kama hanyar gida zeena kuma tana class time din Koda ta isaa gidan ta tadda Anty a falour suka gaisa ta wuce daki tai refreshing sannan ta fito neman abinda zata saka a cikinta danko la'asar ma yanxu ne ake kira, girkin daren ranar ma zee ta yishi gabadaya dai komai anty ta sakar mata ita keyi Akwai rashin sabo nayin ayyuka masu yawa haka bayaga zirga_zirgan makaranta hakan yasa zee battajin dadin jikinta sosai Yauma kafin ta fita lectures haka saida ta kammala ayyuka dukkuwa da jikin nata ba dadi zazzabi kadan takeji da dan ciwon kai wanda kan haifar mata da jiri lokaci zuwa lokaci * * * * * Zee ta samu guri ta zauna tana fidda haki na gajiyar tapiyar da tai dukkuwa daba wata doguwar tapiya bace cikin department din nasu ne daga class zuwa lab, Ta dan dago kanta da kyar jin gaurayyyen kamshin turarukanshi, ta bude idanunta da sukai ja alamun ciwon kai, yana tsaye kanta, a hankali ya jawo kujerar stool ya zauna kamin ya mata cikakkiyar sallama, Cikin makoshi ta amsa sallamar tashi ta ko yaushe, "Zainab" ya fadi very low and cracky, Zee da mamakin yaa akayi yasan name dinta ta dubeshi, tana mai sauke hannunta daga kanta, saidai kanta taji ya sake sarawa ta maida kanta kasa tana mai jin ciwon kan, Wat is wrong with her"? Tambayar da lab attendant din yayi yana mai dubansu sanda ya karaso kusa da su "I think she's not okay sir" saurayin ya fada cikin jimamin yanayin daya ganta, "Take her to the clinic then" lab attendant ya fada in i don't care manner Okay sir shine furucin saurayin sannan ya durquso kanshi saitin kunnenta kadan yace "zainab can u walk?" Tace yes a hankali Okay let me accompany you to the clinic... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 19: Lonely Tafiyar suke sunayi suna hutawa, tun kan su fita a department ta miqa mishi wayarta tace "pls ka kiramin bes, yace okay password? Ta fada mai yayi unlocking sannan yayi searching sunan da akayi saving da bes yayi dialing, kira yayi sau biyu amma ba reply, yace she isn't picking" ta amshi wayar tana jimami da tinanin ina duka suka shiga yau ba zeena ba hudiyya dan tun da tazo school yau basu hadu da hudiyya ba ko lectures batazo ba balle zeena da ba tare suke lecture ba gashi kuma bata picking call, Suna fita wajen department, yayi waving wata mota dayaga tana tapiya, mai motar ta karaso ya mata bayanin "mara lpiace zata taiamak sukaita clinic" tace okay" Zee ta shiga baya shikuma ya shiga gaba dayake clinic din nada nisa daga cikin school, Bayan anyi examining zee ne doctor ya mishi bayani da cewa "its just stress ba wani abin damuwa bane" ya musu prescribing magunguna da en advice, * * * * * Zee ta dube shi ganin zasu rabu kuma bata san koda sunanshi ba, A hankali tace "Ammmm nace ba...." Ya watsa mata lazy eyes dinshi cikin nata, still yayi pocketing hannayenshi "Ur name?" Yace sorry ban fadamiki sunana ba, Am *faruq usman jabbar*... "Nice meeting u faruq" Yayi shaking head dinshi and at once his face displayed a stunning smile, precised.... Daga haka ta shiga mota driver yaja Karfe 6 harda mintuna, ta shiga falourn Anty, tana zaune tana karkada kafa, ko gaisuwa bata bari sunyi ba "Zainab kinga lokaci kuwa karfe nawa yanxu, wato nagane nupinki dan kada kiyi aiki shine kike zuwa makarata ki shantake, to in bakiyi ba nice zanyi miki aikin, muna zaune tare dole kece zakiyi" ta karashe tana mai jan tsuka," Zee dai sam bata fadan Anty take ba ta jikinta take, ta karaso gaban anty ta tsugunna ta bude jakarta ta fiddo magungunan, tace "clinic naje Anty banda lpia" sannan ta jawo hannun Anty ta saka a wuyanta" Jikin Anty yai sanyi "to ai da sekimin bayani mana sannu, jeki watsa ruwa zakiji daidai se kisha magungunan kizo ki bar girkin zan samu wani abu me saukin nauyi naci, kema sai ki duba ko flakes ne kisha" Ta sake juyi kan katifar tata, She just can't get him off her mind, oh Allah his voice, his looks, his dress his matured sense of humor, just everything about him "Faruq" tai furucin dayayi daidai da karan wayarta, ta jawo wayar tana tinanin Anty hawwer ce Ganin da tai na sabuwar number yasata jinkirin dauka, amma se tai picking ba tareda tace komi ba, Kamar koyaushe dai wannan cikakkiyar sallamar tashi yayi mata, voice dinshi so cool and cracky as always, Saida zee ta danyi gyaran murya ta saita numfashinta sannan ta amsa mishi sallamarshi, "Yaya jikin naki en mata" zee tai murmushinta mai sanyi tace "Alhamdulillah, yace good masha Allah" Ina fata kinsha maganinki kuma kinci abinci zee ta amsa mai da yes duka nayi, Itace ta dora da tmbyar "ina ka samu number ta? Kuma ya akayi kasan sunana and wanne department kake?" "Okay okay, duka zan amsa miki su but bari ayi one by one, First na samu numberki ne daxu bayan kin tapi... A gurin wata friend dinki, i think hudi... Something ne name nata" Ohh hudiyya zee ta fadi Yace "yes tazo tana tmbyata kina clinic ne ance mata nine na rakaki so i told her u hav already left, dats wen i asked her of ur number.... Ina fata bayanina ya gamsheki" Zee tace um Good... Sunanki kuma nasanshi ne sanda kikayi mana lecture a biochemistry hall na CHO" Zee tace "ohh yes" And nikuma a same department muke nida ke, na shigo ne with D.E in case ma zakice baki sanni ba a baya i recently joined u guys" "Kin gamsu ko? Tace eh na gamsu kuma nagode akan dazun nan, Yace bakomi ai ba wani abu bane Zee tace wani abu ne mana "u sacrificed ur practical class" kai kadai ne ka iya wolunteer ka kaini clinic" Wannan ba wani abu bane ni a gurina ki manta ma ya faru, Daga haka sukayi sallama yana mata Allah ya kara sauki Xxxxxxxxx Cikin ikon Allah zee ta tashi tana maijin karfin jikinta Tana kitchen tana hada musu break ne ta jiyo hayaniyar Anty da alama waya takeyi "Wallahi ya_bilki bazan bar gidana ya mutu babu inda zee zataje, in kuwa ba haka ba nima ba inda zani wallahi"... Itadai zee ta fito danta kammala ta taddata a falour ta miqe kafa tai shiru alama bayani akeyi mata a wayar, sai kada kai take "To shikkenan zan gwada hakan amma idan fa yaqi yarda sedai yayi haquri shima"... Itadai zee ta wuce ta hau shirin makaranta harta gama ta wuce * * * * * * Tai tsaye bakin lecture hall din, "lallai.ta bakin zeena ne na zama typical late comer" ta sake jaddadawa kanta, Tana so ta shiga kuma tana gudun wulaqancin malamin, Daga ido tayi tana tunanin mafita, sai ta yanke shawarar samun guri ta zauna, gefen class din tayi saboda sanin da tai akwai kujeru gurin, koda ta karasa shi kadai ne zaune yanata faman pressing phone dinshi idanunshi da hankulanshi gabadaya sunaga abinda yakeyi,,, tayi sallama ta samu guri dan nesa kadan dashi ta zauna, A hankali ya dago yana kallanta, sai kuma ya dubi wrist watch din dake daure a wrist nashi, ya maida kallonshi kan wayar yana nodding kanshi kurun, Zee ta shiga laluben wayar hudiyya saidai bata dauka ba harta tsinke, se kuma sako ya shigo "Wlh kar ki shigo dan malamin beda kyau yanxu se ya manna miki C.O yace kinyi disrespect ing dinshi, gara idan be ganki bama..." A sanyaye ta sake karanta sakon kamar wacce tai mantuwa cikin sakon, Muryarshi ta tsinkayo yana fadin "nikuwa na dauka nafi kowanne dalibi makara ashe duk makarata ma kekam kin fini" Ta daga kai ta dubeshi hmm shine abinda kawai tace A ranta tace "yau da ace Ammi nada rai da hakan sam bazata faru ba, gashi tundaa aka dawo semester kowacce safiya sai na makara Allah yaji kanki Ammi, uwata gari," ko kadan batasan tana zubda hawaye ba saida taji damshinsu a kuncinta, Ta dubeshi ganin ya taso ya nufo inda take, ta saka hannu tana goge kwallar idanunta "Kiyi haquri i don mean to hurt u zainab" Tayi nodding "i know nima ba maganarka ce ta sakani kuka ba na tuna Ammi na ne" Ya sauke numfashi kadan "Ur mom?" Ta daga mai kai, yes d best mom in d world" yai murmushi yes mom are d best Itama sai ta tsinci kanta da murmusawar, "But i hav loose mine she's gone forever, Allah ya jikanki yaaa_ummee (يا امي) " ya fada in a broken way Ta sake dagowa ta kalleshi "innalillahi, u also lost ur mom?," yace "Yes tun banyi hankali ba, i was just 8 then.." "I also lost my Ammi recently, not only her but i lost my Abbah too" she donno why kawai saita tsinci kanta da rufe fuskarta tana kuka She felt as if they just died, and dis new environment she's into, she don't like it at all, "yes is okay u cry my dear, but they need ur du'a, more"..... Tai nodding kawai * * * * * Tun 1 suka gama lectures, sauran duka practicals ne kuma ba'a soma su ba, Sanda taje masjid tai sallah, sam bata bukatar saka wani abu cikin cikinta, she just needs to be alone, tasan idan ta koma gida yanxu aiyyuka na babu gaira Anty zata dinga kwakulo mata Earpiece ta samu ta toshe kunnuwanta sannan ta dauki hanyar zuwa library, Tana zaune tana juya pen din hannunta "her life now?, she's totally not herself, ta zama tamkar wata 'yar aiki a gidan Anty siyama, bawai bata aiki bane no takanyi girki ma ammi da, kuma tana share mata daki ta wanke toilet, amma wanke wanke, wankin kayanta wannan duka bai cikin aikin datakeyi, she terribly missed Ammi plus Anty hawwer," kodayake bakomi komi ze wuce amma da kamar wuya.... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 20 & 21 : crushing my crush Can i sit? Ya fada yana kallonta, Zee ta daga kai tinaninta na katsewa, yana tsaye yayi folding hannayenshi a kirji yana lumshe ido time to time, song din datake saurare a earpiece dinma harta kare bata sani bama, ta zare earpiece din, Yaja kujera ya zauna dukkansu suna kallan juna, littafin dake gabanta ya jawo yana kalla,, "physiology?" Ya fadi bayan ya gama duba littapin yana kallanta, bata kalleshi ba amma tanajin me yake fadi, So tell me something about the blood and body fluid (physiology course) Zee ta daga kai a sanyaye ta dubeshi Ta girgiza kai "i donno" ta fada a takaice kuma a hankali "Are u okay?" Ya tambayeta saboda yanayinta No am not ta amsa shi a takaice Ya dora duka hannayenshi kan desk din yana sake kallanta a tsanake "Wats wrong with u?" Ta kalleshi a takaice kuma ta janye kallanta ta sunkui da kanta, "So wats even wrong with me?" Ta fada cikin ranta Kamar mai counting words yace: "La haula wala kuwwata illah billah"..... Furucinshi yasaka ta dagowa tana dubanshi cikin son neman karin bayani "Dats wat u re supposed to say" A duk duniya babu wani abu mai bakinciki muddin ka rabu da iyaye lpia kuma ka kyautata tsakaninka da ubangijinka da mu'amularka da mutane, zainab ki dena barin abu yana zama cikin ranki har yana wasa da farincikinki, duk abinda ya dameki akwai wasu da nasu ya ninka naki, mene ma abin bakinciki ko damuwa a gareki, da kike daa cikakkiyar lapia kike bakida nakasu kina da ilimi daidai gwargwado, da sauran abubuwan ni'ima daa Allah ya hore mana" Kalamanshi sun zo a daidai gurbin daya dace, kuma sun samu karbuwa To mene ma na dorawa kai damuwa a rayuwar da karewa zatai, rayuwar da Allah ne ke da iko akan komai, rayuwar da rabonka bai wuce ka," Zee ta sauke numfashi "Allah ya bamu wucewa lpia" furucinta kenan dayaja hankalinshi gurin faadin Amin Sai ta jawo note din nata cikin sakin fuska da sanyi "dagaske fa nake ban san komi gameda blood and body fluid ba, physiology is not my fav" "Are u serious?, oh u re d first person dat i met who dont like physiology" Tai murmushi, "the course is not dat interesting" idanuwanshi ya kura mata cike da mamaki "lady u re different" Furucinshi ya sata dan darawa kadan, Yes if physiology is not interesting den wat would.... Biochemistry? Or Anaatomy?" Yadda yayi furucin yana zare ido yasata fashewa da dariya..... "Damn cute" Furucinshi kenan wanda shi kanshi baisan ya furta ba, itakuma batama jishi ba Zee ta kare dariyartata da placing wani dakakken murmushi, he just couldn't take off his eyes, ya ilahi Furucinshi ya sata zuba idanunta cikin nashi tana neman karin bayani, Gabadaya he feels uncomfortable ya miqe da dan hanzari yace "i gotta go chat later" ya dauki key da phone nashi daya ajiye yayi gaba da sauri Da dumbin mamaki ta bishi da ido, he's doing okay just now and wat happen all of d sudden" Tayi furucin a fili tana kallonshi yana kule mata da gani, Ta sauke ajiyar zuciyar "i hop everything is ok and good... Atleast he made my whole week not a day for dat matter" Wayarta tai kara ta duba taga sunan zeena ta dauka ranta wasai, "kina ina?" Ina libry but am done" zeena tace okkay i tot ma ko kin tapi already "No yanxu dai nakeson kiran drivern" "To ki sameni a waje akwai labari" zee tai dariya to ganinan da gudu ma" sukai cutting call din Kiran zeena na katsewa na zakiyya ya shigo Ta dauka da murna Zakiyya tace "er uwa kin bar makaranta kuwa?" Zee tace a'a Zakiyya tace to jirani dan Allah akwai story nasan beje miki ba zee tace "too lallai se kinzo din" itama daga haka sukai cutting Zee ta juya kwayar idonta "mene abin bakinciki gaa wanda ke zagaye da mutane kamar su zakiyya da zeena" ****** A wajen ta samu zeena zaune tana waya murya caan kasa kan wasuu kujerun gini a kasan bishiyar darbejiya, ta karasa gurin tana sake kallan zeena dake sallama dana wayar, zaman zee yayi daidai da ajiye wayar tata Ita kanta zeena seta bawa kanta Dariya ta kuwa kyalkyala abarta Zee ta tsaya kallon ikon Allah Da kanta ta nutsu tace "ke nayi sabon kamu" zee ta tabe baki au shine dama labarin yo inde kece ai bakya gajiya da sabbin kamu, inaga sekinyi samari dubu tukun zaki zabi na aure" Zeena tace "gara ni dai akan ke da kike korarsu, amma wlh ki tsaya kiji dagaske nake miki... Allah nima na fara sonshi" "Tooo waye shi din haka me sa'a" cewar zee Zeena ta gyara zama sunanshi Imran, abokin yaya ne (daama na fada muku gidan yayanta take zaune), amma ya taba aure matar ta rasu gun haihuwa ita da baby tun shekaru hudu baya, Zee jin tai shiru yasata fadin shikkenan labarin? Ko dai ba'ason fadamin wani karin bayanin? Uhm to masoya Allah ya bar love" Haka suka kare tana tsokanarta, har zakiyya tazo saiga driver shima, duka su ukun suka dunguma, A hanya ne zakiyya tace "kinsan kuwa an sake yiwa Abbah transfer" zee tace "daga jigawan? To zuwa ina?" Zakiyya tace har port Harcourt pa, yaso zuwa nan kafin ya wuce amma be samu halin hakan ba wai akwai abubuwan dazeyi a can din" Zee tace to Allah yasa haka yapi alkhairi, Ni bama wannan ba ai baakisan meke faruwa ba, cewar zakiyya Zee tace meke going kuma?" Ai in gaya miki da akayi maai wannan transfer din yanxu bayan yabi jirgi yaje, to anty siyama ce da zuwa se abbah yace ai kikoma cikin mu ma'ana ki dawo gida a rufe nata, ta tubure wallahi babu inda zakije wai bazata rufe gida ba ya lalace har wata guda" Wata guda kuma? Zee ta tambaya "Eh sun kara kwanakin yanxu tunda garin da nisa" "To Allah ya kyauta kuma ya aka kare" Zakiyya tace "ai kin amincewa tayi shine tace akwai yayarta suna ce mata ya_bilki mijinta ya mutu sai 'danta daya yana bording itace zata dawo ta zauna dake, nima mama take fadamin wai na shirya kayana mu tapi yau tunda a BUK nake tapiyarmu zatai daya" "To yaushene tapiyar antyn?" Zakiyya tace a yadda naji ma yanxu yaci ace ta tapi tunda ya rigada ya mata booking flight, nima ai yanxu in mukaje gida dakko kayana kawai zanyi mu wuce dan na gama shirya su" Maganganun Anty siyama na daxu da safe suka fadowa zee datake fadin "Wallahi ya_bilki bazan bar gidana ya mutu.... babu inda zee zataje, in kuwa ba haka ba nima ba inda zani wallahi"... Haka suka miqa zeena gida zee na fadin "to tattabara uwar alqawari a gaidamin sahibin" zeena ta mulmula mata dakuwa me zakiyya zatai kuwa in ba dariya ba, itama zee ta dara Zakiyya taje ta debi kayanta ta saka cikin booth sukai sallama da mama da umman halipha suka wuce du yaran gidan basa nan na islamiya na can en boko ma na boko... Yadda zakiyya ta fadi kuwa haka zee ta gani a gidan Anty siyama Dattijuwa ce takai shekaru arba'in da en kai, ya bilki da suke cewa yaayaa, bama ita kadai ba har da minnatu autarsu Anty siyama kuwa already ta rigada ta tapi,. A dakin zee zakiyya ta saka kayanta, koda suka shiga gidan ma babu wanda yace ci kanku, dan mint ma sam batasan ma sun shigo ba, hankalinta naga wayar salulanta dataketa faman latsawa tana tauna chewing gum tana fasa kwai iri iri, Yaayaa kuwa waya take yi, bata tarbesu da komi ba se kallon banza Zakiyya ta zauna kan gadon tana yaye gyalenta ta zuba tagumi "Munga ta kanmu mukam, zee kinga kallon da yaayaa ta mana kuwa" Zee tai takaitaccen murmushin dole tace "se haquri daga haka ta shige bayi Wata sabuwa cewar zakiyya... "Motar tazo fa sis" Ya fadi calmly Ta daya bangaren tace "Allah yaa sanya alkhairi my fuj" yace Amin Duka sukayi shiru na seconds Ta katse shirun "Fuj tell me wats wrong, u sound dull" Ya zame daga zaman kujerar dayake yayi relazing sosai, ya luma yatsunshi cikin gashin kanshi yana mai hura iska waje "Sis akwai matsala fa" I know, ta fada Tell me wats d prob. Ya dan ciji lips dinshi kadan ranshi babu dadi yace "I think am falling" "Falling? Falling where, falling on wat?" Ta tambaya cikin rashin gane inda ya dosa "For her" Dukda baya ganinta saida yaji yadda ta mirgina akan gadon "Ya ilahi.... Fuj Are u serious?" Yai ajiyar zuciya, "Seriously its killing me" Muryarta wasai sounding excited tace "Pls just drop everything and love her, fuj continue to love her pls dont kill urself," Ya dafe fuskarshi "and dad?" Ta sauke ajiyar zuciya "we'll see to that later just love the lucky girl" Ya girgiza kai kawai "u re not serious" Ya katse wayar cikeda confusion, haka taita kiranshi amma yaqi picking X x x x x x Bayan zee ta fito a wanka aka soma kiraye kirayen sallah magrib, already ta dauro alwala ta sa kaya wando da riga sakakku, sannan ta zumbula hijab babba har kasa ta tada sallah, zakiyya kuwa tuni rabar A.C ta sata bingirewa bacci ya kwasheta, Idar da sallar zee yai daidai da shigowar yaayaa, Tai tsaye bakin kofa ta kama kugu, zee tace "barka da warhaka yaayaa" "Sannu ku shafaffu da mai ko, kun shigo bako gaisuwa kuma kun kule cikin daki to wallahi iskancin da kukewa siyama ni baza'ai minshi ba" Hayaniyar fadanta ya tada zakiyya ta soma mittsike ido tana hade rai cikin jin zapin tada ta da yaayaa tai bayan duk uwar gajiyar data kwaso, "To ku fito kowacce aikinta na nan yana jiranta tunda banice zanyi muku aikin ba" Ta fice daga dakin Zee ta miqe ta cire hijab din tace kije ki watsa ruwa ni bari naje nayi aikin, Zakiyya tace "ba yanxu zanyi wankan ba se zan kwanta yanxu dai zan sauya kaya ne kurun" Daga haka zee ta fice Kitchen Anty ta nuna mata, zee ta shiga taga yayi dakal_dakal, du a tsakude, tiles din yayi shatin sawayen kafafuwa da datti ga kwanukan abincika birjik da alama tun fitarta da safe ba'a gyara ba, Haka ta hau gyarawa ta wanke kwanukan tai mopping sannan ta fita falour ta tadda zakiyya na goge dining ta gama sshara, Yaayaa tace "jeki maza ki wanke bandakinmu" zee tace to ta wuce Koda ta shiga dakin anty siyaman da suka sauka, minnatu ce gaban mirror tana shafa foundation a face dinta da alama makeup takeyi zata wani guri, Zee ta wuce zuwa bandakin ta gyara musu se tashin kamshi yake ta fito, yanxu kuma tana tsaye tana daura turban Tasha wata black fitted gown data fidda tsantsar kyau da halitta da ubangiji ya zuba, Tabbas ko wace kuma ko wane ya kalli minnatu se ya sake juyowa ya dubeta, Fara ce tas kamar ka taba nono ya zubo, tana da dan jiki, irin wanda bature ke cewa chubby, shape dinta kam shine muradin kusan kowanne d'a namiji, full option coca-cola shape Har zee takai kofa taji minnatu tace "Kinga zoki share nan ma" Kamar bazata juyo ba amma seta juyo tace to sanan ta fita dan dakko broom, fitowar zee ba dadewa minnatu ma ta pito, tashaa makeup kam abinta kamar wata baby dull, idan ka dubeta zaka rantse bazataji yaren hausa ba, zakiyya da zee suka bita da ido, taiwa yaayaa sallama ta fice..... X X A gajiye zakiyya ta shiga daki itaama zee ta shigo ta tadda ta, zakiyya tace "nipa yunwa nakeji" zee tace nima haka wlh dan ko lunch banyi bama ni" Zakiyya tace to bari naje na nema mana abinda zamuci dan naga couscous a dining dazu, a dining ta samu plate, zata fara zubawa taji yaayaa na fadin "Ke mene haka" Zakiyya ta kalleta tana bata rai Wannan abincin na mint ne pa, malama in yunwa kikeji ki shiga kitchen mana ki dafa... Dire plate din zakiyya tai ranta a bace wlh badan yaayaa zatai sa'ar mama ba da seta gaggaya mata bakaken maganganu, tana kunkuni ta wuce fuuu Itakuwa zee tun fitar zakiyya tunanin shi ya fado mata, haka kurun speed din zuciyarta kan kara gudu inta tuno wani abu nashi ko shi kanshi, innalillahi ta furta, what's all this? Ta tambayi kanta amma ba amsa sai ma shigowar zakiyya data katse mata tinani Zakiyya a kufule take zazzagewa zee yadda sukai da yaayaa "Kuma fa kiga minnatun taci kwalliya ta fita da daren wai taje birthday, a can din inace ai akwai abinci ne, Allah zee badan ke ba da tuntuni na tattare kayana nayi gaba, haba duk uban aikin da mukayi bayan gajiyar makaranta sannan ace abincinma babu" Zee ta kammala sauraran zakiyyaa sannan tace kwantar da hanakalinki, ni bari na dafa miki abu mai sauki, beside dama ni kodaa kin kawo abincin ma ba lallai ya birgeni ba nafiso na dafa da kaina, ai shiga kitchen abin jin dadi ne..... X Kashegari Tare da zakiyya suka tafi school, aka ajiye zee,, sannan aka wuce da ita sabuwar jami'a, Tana sauka wata arniyar bakar mercedes tai parking dan nesa da ita, kyawun motar ya ja hankalin zee ta zuba ido tana son ganin me saukowa, bangaren me zaman banza aka fara budewa, Wata budurwa ta fito tana magana da na ciki kuma ta wuce Babu jimawa aka bude bangaren drivern, faruq ya fito cikin shigarsu ta farare da suke bal'in amsarshi, sai kamshi yake, Yana fitowa idanuwanshi sukai tintibe da fuskarta tsaye tana kallonshi, Fuskarta a hade yai saurin jaanyewa daga kallonta, itama zee ta juya ta wuce "Basabanba yau ba'a yi latti ba" Taji muryarshi a kanta sanda take zaune daga baya cikin ajin da babu dalibai dayawa" Ta danyi yake "bamuyi ba zakace" yayi wata dariya cikin makoshi Sannan ya zauna gefenta, "ina friends din naki?" Basu karaso ba tukun" Shiru ya ratsa na dakikai kafin ya katse shirun da cewa "Nikuwa in bazaki damu ba zainab inaso ki kara ganar dani biochemistry, yana daga cikin courses din danake faduwa kuma ban ganewa ko da can" Zee tace "Inace yanxu ne farkon yinmu ko ka tabayinsu? Ya amsa da "eh na tabayinsu tace "To Sedai idan nima zaka koyamin physiology dan yana bani wahala bansani ba kodan farkon yi na ne" Ya lumshe ido kamin yace "karki damu da wanann" Tun daga wannan rana kusancinsu ya sake karuwa fiyeda baya, a sati sukan ware rana daya suyi karatu bamai yawa ba yadda kowanne ze gane yana jin dadin karatu da ita yadda take farfasa mai komi daki daki, itama tana jin dadin karatunsu, har takai dalibai suka fara gulmarsu Wasu suce ai en uwa ne wasu suce saurayi da budurwa kowa dai da abinda ze fadi Zeena ma saida ta zaunar da zee amma finfiris zee taqi cemata ko kala domin ita kanta zee ta kasa gane mene tsakaninta da faruq balle har taiwa wani bayani Ana haka ne aka tapi hutun sati daya na mid semester break Xxxxxx "Anty hawwer nidai Allah inaga kamar na fara sonshi" Zee ta fada tana kara jaddadawa anty hawwern Ta cikin wayar tace "Nima jikina ya bani yana sonki kamar yadda kike sonshi koma fiye".... This is the first time danaji kin firta wai kinason wani da namiji,,, kuma hakan bawai ya nuna gazawarki bane a'a dat makes u a human with emotions with feelings, nidai koma mene i ll still support u as a sister as an elder, fatanmu shima ya soki kuma ya furta miki yana sonki, dan tunda har kika firta nasan ya chanchanta ne i hop ur intentions towards him are clean".... Ghost readers 😕 kunsan kanku 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 22 : propose Bayan sunyi cutting call din Zee ta mirgina akan gadon Asking her self "Why do i even love him?, how and when did i fall for him?" Zee ta lumshe idanunta tana hango siffarshi tun daga kasa har sama Faruq? Faruq is a tall guy, his complexion? yanada haske sosai sekace mace, dan sajenshi dayayi daidai da face dinshi his nose, lips and his lazy eyes, Ita kadai take ma kanta tambaya kuma take amsawa, Tai saurin bude idanunta "what am i doing?" Wani bangaren zuciyarta yace "u re asking why u fall for him" Ta sake lumshe idanunta "Sassanyar muryarshi, dabi'arshi ta kama kanshi daga kula en matan banza, shigarshi ta mutunci, furucinshi dake nuna tarin hankalinshi..... X x x x x x x x "Er uwar fuj, fuj fa ya rasa ya zeyi" Ya fada very low Tace ta cikin wayar "Nida aka watsar dani kuma shine ake sake nemana yanxu, na kirakaa har seda na gaji na dena kira baka tashi nemana ba se yanxu kuma" Ya dan goge zufar dayaji tana taruwa a goshinshi "Dan Allah karki bar dan uwanki lokacin dayake matuqar buqatar shawararki" "Shikkenan naa tausaya yanxu me fuj yakeso" Yai shiru yana jimami Tace zan kashe wayata fa in bazakai magana ba Ya hadiyi wani yawu kamin ya ce "Zuciya batai min adalci ta fada soyayya a sanda bai dace ba sam," "Inji waye yace maka be dace ba... Kaga shawarar dana baka kwanaki itace zan sake baka, kaje ka sameta ka sanar mata sakon ranka, na tabbata bazatayi denying ba," Yai ajiyar zuciya "Amma kinfi kowa sanin halin daanake ciki a yanxu, bakya ganin furta mata so kamar yana nupin zanyi wasa da rayywarta ne, idan na cusa soyayyata a ranta kuma mene makomar soyayyar tamu a gaba, yaya kike tinanin dady zeyi dani? Kina ganin nata iyayenta zasu barta taa cigaba da zaman jirana akan wannan mummunar akidar" A sanyaye tace "Bawai banyi tinanin wadannan bane yasa nace ka fada mata, banaso ka tsinci kanka cikin irin halin dana tsinci kaina, banaso ka biye wa mummunar akidar ta tarwatsa taaka rayuwar kamar yadda tai gaba da nawa farincikin ta kuma barkaa da danasani da tarin nadama kamar yadda ta barni" Ta fashe da kuka mai ciwo wanda yasata tsinke kiran Gaskiyar Anty-Safiyya ne....... * * Kwanci tashi babu wuya gurin Allah, haka sati dayan hutunsu ta kare, duk su biyun babu wanda yayi contacting wani bawai kuma dan basuyi kewar juna ba, a'a saidan kowanne na tsoron kara fadawa soyayyar dan uwanshi in yaji daga gareshi... * Dayake gidan nasu estate ne kowa da nashi bangaren gidaje ne kusaan 8 iri daya, faruq nashi gidan a kasa yake, yayinda na sarah ke gefen nashi, Yauma a tare suka fito dan haka suka wuce makaranta cikin motar tashi da bai dade da siyanta ba... Tana tsaye bakin department din nasu ta hangi motar, tasan tabbas ta faruq ce, ta kasa janye idanunta daga kan motar, kamar ko wacce rana cikin kwanakin nan haka yau ma ta fito daga cikin motar sannan shima ya fito, who is she? Ta tsinci kanta da fadin hakan, Sam bata lura ya karaso gurinta ba seda taji kamshin perfume sannan ta ankara Allah ma yasa bai jita ba, Yayi mata cikakkiyar sallamarshi, itama ta amsa a sanyaye, sannan suka jera zuwa class Sai bayan ta zauna sanann ta tina tsaiwar jiran hudiyya takeyi a wajen ta tabe baki"Allah dai ya sawwaqe min" ta fadi a ranta... Muryarshi ta tsinkayo yana fadin "Yau da karfe nawa zamuyi karatu naji an fara scheduling test's" Tace "inaga bayan wanann lecturen babu wani, duk sunyi postponing so we hav enough time" * * Ta dakko note dinta ta bude zata soma bayani sai ta daga kai Yana zaunen amma ya zuba mata kasalallaun idanunshi,, wani kasala ce ke shigarta idan tana kallon fishy-like sleepy eyes nashi "Faruq" ta fadi a hankali Ya sauke numfashi kadan ya shafi beard dinshi "I want to tell u something" ya fada Ta rufe littapin "am all ears" Ya sake gyara zama idanunshi kyam a kanta "Zainab as i told u ealier am faruq usman jabbar, my mom is no more, Allah ya mata rasuwa tun banyi wayo sosai ba, my dad is a professor...." Sai kuma yayi shiru na wasu dakikai yana tinanin ta ina ze lalubo bakin zaren ya soma warware mata" A hankali ya cigaba da cewa Mahaifina dan asalin jihar katsina ne, su hudu ne gurin kakanninmu "Mu biyar ne gurin ummee da dady, Anty safiyya itace babba tana da shekaru 35 yanxu, se ya halisa tanada shekaru 31, sannan ni sai kuma Aisha kanwata shekarunta 25 da auta Hamra dake 20yrs of age... Duka basa kasar nan, suna europe sauran danginmu kuma suna katsina wasu kuma Abuja" Shiru ne ya sake ratsawa Shi da kanshi ya katse shirun gabadaya muryarshi ta chanjaa ta sake low and cracky wacce zata iya sakaka bacci muddin kaa cigaba da saurarenta na tsawon wasu sakanni "Will u please give me a chance" Jitai duk kasala ta shigeta saboda yanayin yadda yai da muryarshi, ta dago ta dubeshi saidai sam bazata iya jure kallan abinda take gani cikin kwayar idanunshi ba, ta sauke idanunta kasa gabanta na fat fat, sun dauki tsayin mintuna 2 a haka sannan ta saita kanta ta kalleshi a takaice tace "i will think about it" ta miqe ta kwashe notes dinta zata tapi har ta wuceshi yana nan zaune ya kirayi sunanta da fadin "Narnarh" Ta tsaaya cak batareda ta juya ba, "lemme drop u home pls" ya kare yana jan please din karshe Still batai responding ba kuma tana nan tsaye, har ya karaso inda take sannan ya zagaya ya bude mata kofa Jikinta a matuqar sanyaye ta shiga shima ya zagaya driver's seat Haka suka kama hanya kowannensu yai shiru ta shiga tinani sosai, haka suka fita a school din suka hau titi, sai a sannan ne ta kwatanta mishi inda take ma'ana unguwarsu, a haka faruq ya dinga mata labarin kanshi kama daga inda yake zaune, (estate dinsu da bashi da nisa da school din wajen unguwar jan bulo) da kuma labarin makociyarshi sarah wacce take same estate dashi, ya cigaba da fadin "she's in applied biology 100level" zee dai tana ta saurarenshi tana kuma kwatanta mishi to dayake ma ba gurine mai wahalar ganewa ba se gashi sun iso har kofar gidan Anty, ta mishi sallama da godiya tabude murfin motar, a hankali yace "pls don't keep me waiting" ta jijjiga kai kurun ta fice ya bita da ido har ta bude gate ta shige gidan.... Driver yayi mamakin ganin ta dawo ba tareda ta kirashi ba dan sunyi da zakiyya seta gama lecture sannan se su taho tare, ta wuce cikin gidan inda ta tadda yaayaa da minnatu a falour, kallo yaayaa take minnatu kuma tana danne-danne a system daake gabanta, tai sallama ta gaida yaya ta wuce daki, ta shige dakin tanajin yaayaa na fadin "to tunda Allah ya dawo dake da wuri se ki fito ai aikinki suna nan" zee taji sarai amma batace ko ufan ba dan yanxu tapi buqatar lokaci tai tinani dan gabadaya ma batajin wani kuzarin yin aiki A nashi bangaren tunda ya koma gida ya chanja kaya yake ta saka da warwara gabbadaya ya kasa nutsuwa, expression din fuskarta ne sam be gane inda ta dosa ba, "karfa tai rejecting" ya sanarma kanshi, yai saurin kauda tinanin ta hanyar girgiza kai, no dont worry fuj she won't... ya lumshe ido Sai bayan la'asar zakiyya ta dawo bayan tama driver waya ya dakko ta, har lokacin zee na daki ko leqowa batayi ba dan ko er yunwa ma bataji, Tana kwance a rigingine idanunta a bude tana kallan ceiling zakiyya ta shigo, tai sallama amma bataji amsar kowa ba, Ganin zee datai kwance kuma bata amsa sallamarta ba yasa tasan ta tapi tinani, ta karasa tana cire gyalenta ta jefa mata a fuskaa, a dan razane ta miqe tana yakice gyalen daga fuskarta, sai kuma taga zakiyya tsaye gaban dressing mirror tana cire en kunne.... Wattpad @AyshabNasir 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 023: butterfly "Kai zakiyya ni wlh kin bani tsoro ma" "Ai dole na baki tsoro zee har na shigo nai sallama amma duk bakisan da zuwana ba", zee ta dan yi murmushi kadan zakiyya tace "iyayen tunani yau kuma tinanin me akeyi?" Zee ta tashi da saurin jin wata azababbiyar yunwa, bata samu amsawa zakiyya tambayarta ba sedai tashi da tai ta fita, zee yaau kam tssha fadan yaayaa har cewa tai ta maidata mahaukaciya tana mata magana ta shige daki ta kulle, haka dai bata ce komi ba sukai aikinsu da zakiyya sannan ta nemi indomie ta dafa musu mai dan karan dadi.... Suna cikin cin indomiensu a falourn aka kwankwasa kofar falourn dan lokacin har karfe 7 da rabi an kusa sallar isha'i, zakiyya tace bismillah, aka bude kofar bisa ga mamakinsu zeena ta bayyana a gabansu, zee ta yalwata fuskarta da matuqar murmushi, zakiyya kuwa har da miqewa ta rikota duk a farincikin ganinta, Zeena ta dan hade rai tace "zakiyya ni gurinki kadai nazo waccaan kuwa na dena kulata" Zee ta dan yi murmushi, dan tasan fishin na mene, zee ta matso kusa da ita "ki rufamin asiri kiyi haquri besty ni nasan laipina kuma duk na amshi laipina" Zeena ta tabe baki ta kalli zakiyya tace "kinsan dan rashin mutunci wai yarinyar nan tana ta soyayya a makaranta amma sam taki fadamin tama maanta damu ko hudiyya seda tace ta dena karatu da kowa seda shi, haka kuma a class suna tare ko yaushe kuma fa dan d.e ne gashi aance da shegen girmankai" Tun sadda zeena ta soma jawabi kan faruq, zee taji gabaanta ya buga, a wayance ta saisaita numfashinta, zakiyya ta dafata "Zee dagaske ne abinda zeena ta fadi? Me ya kaiki? Soyayya da dalibi a school?" Ba zato balle tsammani sukaga hawaye na silalowa daga idanunta tasa hannu ta rufe bakinta tana mai cigaba da kuka, A tsorace sukayo kanta suna bata haquri da mata sannu dukkuwaa da basu san dalilin kukan nata ba haka siddan, "Innalillahi, zee kuka kuma? Me yayi zafi haka?" Cewar zeena Tai saurin goge hawayen idonta, ni ba soyayya muke da faruq ba mutinci ne ya hadamu, zeena tace to ai shikkenan" a haka suka rufe hirar Zeena ta miqe tace "dama Anty ce ta aikeni wani gida kusa da nan shine na biyo bari na tashi na tapi kar dare yayi" Zee ta saka driver ya kai zeena gida... * * * * * * * Tana zaune cikin library tunda tazo yau bata je ko department ba saboda batada lecture karatun test kurun take ko ta kan su zeena da hudiyya batabi ba kowa ya kama harkokin gabanshi kasancewar semester tazo gangara komi ya dau zafi Ta sake jujjuya note din gabanta, ya ilahi" shine abinda ta furta Karatun jarida kawai take na kusan minti talatin kuma babu abinda take fahimta, She never like physiology Ta dan daga kanta kadan ba zato kyallin fararen kayanshi hadi da hasken fatarshi sukai reflecting a idonta, ta maida kallonta inda take tunanin ta hangeshi, Majestically yake hawowa steps din cikin libry din, taji gabanta ya fadi, numfashinta ya sarke ta sauke idanunta kan littafinta dake ajiye kan table din,,,, gabanta na dagawa, a sanyaye cikeda nutsuwa ya sauke idanunshi a kanta sanda ya ida hawowa steps din, ya lumshe idanu silent beauty dinta na fizgarshi "she's natural...purest" Ya fadi haka cikin mind enshi, Koda bata daga kanta ba tasan daga inda yake tsaye kallonta yakeyi, gashi turarenshi mai sanyi ya mata sallama Ya tako zuwa inda take da cikakkiyar sallama a bakinshi kmr ko yaushe, hakan dabi'arshi ce, Bata dago ba sema bude shafi nagaba datai cikin littapin dake ajiye a teburin gabanta, ta amsa mai sallamar yaja kujerar dake fuskantar tata ya zauna, "Zainab mun wuni lpia?" Ta gyada mishi kai tana kokarin kaucewa kallon idonshi, Ya saka hannu ya ja littapin gabanta yana kalla "shine dan kimin wayo kikazo yin karatunki ke kadai babu gayyata" Tai murmushi trying hard to look comfortable, Am i disturbing? Ya tambya ganin gabadaya ta takura Tai shiru tana nazarin amsar data dace ta bashi Lowering voice dinshi yayi with lots of emotion har cracking takeyi yace "even if am disturbing I'll not leave u zainab" ta dago a karon farko tun zuwanshi ta dubi face dinshi Bata iya controlling kanta haka numfashinta yake fita da sauri da sauri, amma tayi averting gaze dinta daga fuskarshi She's unable to say even a single word....., in front of any man she never felt wat she's feeling now .... Relax zainab lets read" ya fadi Taja numfashi ta sauke ajiyar zuciya" ya rufe note din gabanta without thinking twice ya fara mata explaning course din na PYS deptment Ta yadda zata gane yake mata bayani sanin da yayi bata iya shi ba, filla filla yake fede mata,,, Thank you Faruq, ta fada batareda ta kalli face dinshi ba, its my pleasure ya amsa mata, "Are u heading home?" Ya fada yana duban agogon hannunshi, tace "no i hav a class" Ya danyi tinani "to my knowledge i don't think we hav any class" "A C.O course" ta fada tana nuna mishi labcoat din dake ajiye a gefenta" ya jijjiga kai Okay I'll wait for you den, taji mamakin jin wai zai jira ta tace okay kawai Sai 4 da en mintina suka fito, straight masjid ta wuce danyin sallah ta idar da sallar ta cire labcoat din tana cikin ninkewa wayarta tai kara sunan faruq ya bayyana kan screen ta dauka tana amsa cikakkiyar sallamar daya mata, Kina ina? Masjid ta amsa Okay ina waje tace to, ta dau labcoat din da jakarta ta fito, Tana gabanta suna tafe, hakan yasa koda suka fita ta rigata fita kuma ta rigata bayyana a idon faruq, ta karasa inda yake Yace "sarah u still in d school" daidai nan itama zee ta karaso, ta kalli budurwar fuskarta ba yabo ba fallasa, sarah tace yes Yace "zainab meet sarah, and sarah this is my zainab" sarah ta kalli zainab kallo na kurilla zee ta murmusa tace "sannu sarah yakike?" Sarah itama ta dan murmusa "lpia qalau" sai kuma ta dubi faruq "pls are u heading home?" Ya saci kallon zainab yaga ta maida dubanta kan titin dake dan gabansu, "eh to i hav to drop my zee first" Zee a ranta tace "naji ikon Allah nikuma yaushe na zama tashi" Maganar sarah ta katse tunanin zee "mind if i join u guys?" Ba zato se ganin faruq tai gabanta yace "madam she's asking if she can come with us" A hankali kirjinta ke dagawa, saboda yadda ya matso daf da ita, ta sauke idonta kasa ta gyada mai kai kurun, daga haka suka wuce gabadayansu, saida suka sauke zee a gida sannan suka nupi hanyar nasu gidan, Yauma zee ta riga zakiyya dawowa dan haka ta shige daka bataga kowa a falour ba dama, Wayar Anty hawwer ta soma laluba cikin damuwa babu jimawa ta soma ringing hakan yasa ta katse cos ko ta dauka ma zatace bari ta kirata ne, Tana katsewa kiran ya dawo ta dauka ba bata lokaci, a sanyaye suka gaisa Anty hawwer tace "me faruq din yace miki?" Zee da mamaki tace "ya akayi kikasan magnrshi zanyi miki" "Bayan Ammi kema kinsan babu wanda ya kaini sanin halinki so muje magana" Zee ta gyyara zama ta zayyane mata duk abubuwan dake gudana a tsakaninsu harda propsing din dayayi mata sai bayan ta gama labarta mata ne Anty hawwer tace "Na fuskanta, kinsan mene? Zee tace a'a Ya rigada ya gane kina sonshi zee, domin shi SO abune da bazai taba buya ba, muddin mutun kaana mishi so na haqiqa to bazaka iya boyewa ba sam, shiyasa ya fahimta bawai dan kinyi sakaci ba, a'a saidai Son da kike mishi na haqiqa ne, Shima kuma yana sonki zee, Abu na farko mafi muhimmanci yanxu shine kiyi istikara ki mutsu kiyi addu'a, sannan abinda zakiyi shine kawai ki maida hankali ku cigaba da karatunku, tunda semester din kun kusa karkare ta, in yaso daga baya kyayi mishi mgnr Amsarshi amma ki buqaci karin bayani sosai game dashi akan danginshi kafin ki bashi amsar daya muradi"..... Rayuwa ta cigaba da garawa a haka,, zee tai istikara kuma tana cigaba da addu'a sosai, shaquwa kuma na kara kulluwa tsakanin faruq da zee dukkuwa da taki furta mishi kalmomin dayake matuqar so amma ya danne kuma ya dage da kulawa da ita sosai, A haka suka shiga satin soma exams, Pls masu cewa zee ta jira faruq ya soma proposing inaga baku fahimci last episode ba dan faruq ya rigada ya bayyana mata sirrin dake ranshi, sannan masu so labari ya kare im sorry to say ba yanxu labari ze kare so ku dauki coca cola mu cigaba da gashi kawae..... Loads of love from ur fav. Writer😍😍 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 24 $ 25: Inlove Ba dan karamin karatu sukeyi da faruq dinba a school har a gida ma, idan zeyi se ya kirata cikin dare itama ta tashi tayi, tun bata saba ba harta saba, se ya zama komi zatayi seta tuntubeshi, a haka suka kare exams din nasu cikin jin dadi, Zee har tausayi faruq din ke bata yadda be gajiya da hidimarta sam, gashi ya bude mata kwakwalwa musamman kan physiology, ta matuqar ji dadin semestern fiyeda kowacce semester, It was their last day at school ending first semester, Ya tsaya bakin kofar class din yana jiran ta fito daga last papper din nasu, He never thought zasu kai har wannan lokacin batace mishi komai ba, all he knows is dat they both love eachother but why is she behaving like dis? Why is she not saying anything? Its like she's playing with his heart and life in whole, at first he's relaxed knowing she'll accept his love soon but the soon never come the soon is turning forever He's damn curious...... Tayi mishi sallama da sanyin muryarta, "here she comes with her damn sexy voice" ya fada a ranshi yana mai katse wancan tunanin nashi ya juyo ya dubeta, She looks pale a hankali ya buda labbanshi gurin fadin "Are u sick?" Ta jingina da karfen gurin cikin rashin jin dadin jikinta Tai nodding, "wat's with u?" Ya tmbya da son sanin meke damunta yana kara kallonta ganin kmar ta dan rame ma, its just a slight headache, maybe due to exam stress... Lemme take you to the clinic den, da kamar zatace a'a sai kuma tace okay dan ita tasan meke damunta (just a period pain) Koda sukaje clinic din, tace da faruq ya barta taga likitan ita kadai, beyi musu ba ya zauna a mota kawai ya jirata ta gama ta fito suka wuce... Suna cikin tafiya idanunta a lumshe shikuma yakan dubeta lokaci zuwa lokaci, a sanyaye ta bude idonta jin motar ta tsaya alamun sun zo, Bin gurin tai da kallo ganin ba gida sukazo ba sai a lokacin ta gane ba hanyar gida ya dakko ba, horn din dayayi tasaka mai gadi zuwa ya bude mishi, "Hop ban bata miki lokaci ba" tace a'a yace okay pls wait for me ta jijjiga kai Cikin estate din ya shiga nashi apartment din ta bishi da kallo dan ta gane gidan da yake ne, tana nan zaune ba jimawa ya fito da wata er leda a hannunshi, yana locking kofar ne sarah ta shigo duk ta gaji da alaama Ta karasa tana mishi murmushi ya saci kallon motar da zee ke ciki sai kuma ya maida dubanshi gareta, zee taji wani haushin sarah kawai musamman yadda taketa yi mai iyayi tana murmushi gashi dukda a gajiye take hakan bai kara mata komai ba ma sai kyau, dayake farace chubby irin ajebon nan, Faruq yace "my madam is waiting for me chat later" dagaa haka ya juya ta biyo bayanshi ta karaso Bangaren da zee take ta karasa, "Anty zee ina wuni" zee ta amsa da kina lpia ya exams ashe baku gama ba" sarah tace "eh amma saura paper daya ta rage" "Allah ya bada sa'a" Sarah tace Amin ta miqa mata wayarta "bani numberki sai mu dinga gaisawa" zee tai jimm sai kuma ta saka mata digits din tace zata kirata yaja suka wuce sarah ta bisu da ido kamin tace "lovebirds" Haka kawai hankalin zee be kwanta da waannan saran ba, ga salon data fito dasu wai Anty zee ko yaushe ta zama Antynta, dukda zee din batafi 20 ba amma tasan ta girmi sarah dan girman jiki kawai tai saidai mene na wani laqana mata Anty kuma ko uban me zatai da digits dina" tai tsaki a sarari batareda tasan ya kubce mata ba, Faruq dake tuki ya dan juyo ya kalleta, itama ta dubeshi da sauri bata bari yace komai ba tace "im sorry" yayi nodding, Er mitsilar shopping nylon din dake cinyarshi ya dauka ya dora a nata cinyar Ta dauke kanta daga titin datake kalla ta kalli cinyarta jin ya aje abu, yace "take a look" Ta dauka ta bude, ring ne cikin gida me kyau sai sarka bamai girma ba itama a wani gidan, Tace "for?", yace You ofcourse, tace and why? Bai san sadda yaja wani brake ba Allah yasa babu mota gabansu da bayansu da tabbas se ya hada dan karamin accident dan babu abinda ze hana na bayanshi ya buga mishi, A hankali kuma ya gangara gefen titin, a tsorace ta zare idanuwanta tana kallan danyan aikin dayayi na kokarin kashesu... Ya watsa mata nashi idanun muryar shi low and lil upset yace Idan nayi miki kyauta har sai kin tambayi why?, zan baki abinda zai cutar dake ne? Kokuma bani da wannan matsayin a gurinki? Ko kuma kin raina ne" his voice clearly show how upset He's Girgiza kanta take a hankali, ko daya wallahi... Ya juyo da jikinshi sosai yana kallanta den why? Zainab why? Is it dat u don't love me? Na dami rayuwarki right? Shiyasa kika share duk wata maganar soyayyar dana miki, can't u understand how much patient am putting just for you, isn't dat enough to tell u how much love i hav for u" Yanxu kam duk jikinta yayi sanyi she's damn confused akan maganar nan tuni ta sauke idanunta Shi kanshi yana ankare da yadda speed din zuciyarta ya karu ta yadda kirjinta ke dagawa...kanta na qasa she want to tell him she loves him too but something is pinching her, Tana ta tadin zuci sai ji tayi sun fara tafiya, ta kalleshi ta kalli titin ta lumshe ido ranta be mata dadi a haka suka karasa gida, yayi parking a kofar gidan ta bude kofar jiki a mace, har zata fita kuma sai wayarshi tai ringing ta juyo duka suka kalli wayar tashi dake ajiye sunan sarah ya bayyana, kan screen din ya kai hannu zai dauka zee tai saurin dauke wayar tace "will u please come in?" A mamakance ya dubeta sai kuma ya maida duban kanshi da kayan dake jikinshi, dukda sun danyi squeezing but he's okay, yayi nodding... Ita ta fara fita a motan sannan shima ya fito yana locking motar zakiyya ta karaso tana mai shimfida murmushi a fuskarta, ta gaidashi ya Amsa sannan duk su ukun suka shige su biyu a gaba, faruq na biye dasu a baya, gefen garden din gidan ta kaishi ya zauna kan kujerun Alfarmar dake gurin, sannan ta koma ciki dan tuni zakiyya ta shige, Batareda ta damu ba ta shiga ta watsa ruwa ta saka bubu peach mai ratsin coffee ta daura turban mai sauki sannan ta dauki gyale bayan ta fesa turaruka duka batafi 15 mins ba, ta shiga kitchen dan tun tana bandaki ta yanke shawarar hada mishi fruit salad kawai, tai turus tana kallan zakiyya da ta kammala yanka fruits din in cubes, zee ta karaso, "Ke kuma haka akeyi se ki bar bako babu ko ruwa" cewar zakiyya taana juye salad din cikin mazubinshi na tangaran mai garai garai, Zee ta karasa bakin window din kitchen din dake dan lungu ta hangi faruq zaune yana sipping juice, Ta dawo tai hugging zakiyya ta baya "godiya nake er uwa, "kinfi haka ai a gurina zee" Kije zan kawo wannan din ko bayan shi akwai abinda za'amishi" zee tace a'a Har ta kai kofa zakiyya tace "he's perfect" zee tai displaying wide grin sannan ta fice tana blushing Ta kofar kitchen din tabi ta baya yadda zepi mata sauki, yana zaune ya dago ya dubeta "she's looking cute in d attire" yaji zuciyarshi na mishi gulma, ta karaso ta zauna "How re u feeling now?" Tace "na warke ai dama na dan lokaci ne gajiyan" Yace to Allah ya sawwake, daidaai nan zakiyya ta kawo bowl din fruits salad da pick biyu, ta ajiye a table din tsakiyansu, sai sanaann zee tai musu introducing juna, sannan zakiyya ta koma ciki, Zee ta dubeshi ta kama idanunshi cikin nata sai ta bude bowl din ta dau pick daya ta mika mishi daya, ita ta fara sha sannan shima, its really good, faruq ya fada yana kallonta, tai murmushi sannan ta ajiye pick dinta In serious tone tace "i never deny loving you, even if i do is just a big fat lie" "I loved u when i gave up my heart will love someone, not like i hav been inlove before, i truly don't even know how the emotions are, all i know about love is the love of my Ammi, my Abbah, and sibling affection" I hav got all the care i needed from them, my best friend, my secretkeeper, my first love, duka Ammi ce, so am never lonely, shiyasa ban taba maida hankali kan guys ba" tai shiru "I understand nernerh" "Saidai kuma abinda ya sakani yin jinkirin amsar soyayyarka saboda bani da tabbas kan soyayyar da zamu gina, ban sani ba ko mai riba ce ko mara riba, idan nace mai riba shine am talking about the future, sincerely i don't want to love someone without getting married, wannan soyayyar shirmen irin ta en makaranta wacce ana kare karatu shikkenan an rabu banajin zan iya yinta and i want to know more about u" Now he understand, "Se yanxu ne na fahimci dalilin dayasa kikamin shiru har na tsayin wadannan kwanakin, u re afraid, u think i ll just love u, waste ur time without making u my wife.... Never zee never, dukda bamusan future ba, but wlh ban taba kallanki da wata manufa ba inba na aureki ba, kuma in shaa Allah i promise I'll do all what it takes to make u my wife," And about me what is it u want to know? Cos i think i've told you who i am, from where and about my family but dont worry ull get to know everything slowly, tunda wani abun ma mancewa akeyi" Duka bayanan daya mata taji ta gamsu, ta kalleshi kadan, "now u already know my answer den" yace "noo say it" tai murmushi shima yana murmushin "Dont tell me kunyata kikeji" ta rufe fuska da hannayenta, ba karamar dariya ta bashi ba yai dariyar sannan ya miqe yana kallan wrist watch nashi, Itama ta miqe smiling slowly, "i ll be on my way we'll talk" ya fada yana kallanta ta miqa mishi wayarshi, ta rakashi har wajen motar sannan tai waving ta koma ciki Ko karasa shiga ciki batai ba wayarta dake hannunta ta fara ringing, ta duba taga sunan faruq, ta dan yamutsa fuska sannan ta ja second kamin ta dauka "Nerhnerh ince dai yanxu bakya jin kunya ta tunda phone call ne" Tai dariya tai hanyar komawa bolcony din, so tell me nerhnerh, not now ta fada tana mai kashe wayar da sauri, faruq dake tuki yai mirmusshi ya ajiye wayar ranshi fes, bai karasa gida ba seda ya kira Anty safiyya ya fada mata yadda sukai da zee ba karamin dadi taji ba, tace "FUJ Allah ya barku tare ya kauda idon makiya yace Amin Anty na.... Zee da zakiyya suna kitchen sunata aikin abincin dare "wai meyasa yau baki kira driver ya dawo dake ba" zee ta tambayi zakiyya, "kawai nagama da wuri ne kuma banason zaman school din nace bari na d'ana hawa napep" "Zee wannan shi kuma waye? Shine wanda ke dawo dake kullum shiysa kikace in na gama na dinga kiran driver kawai" zee tai nodding... Shine faruq kenan, "Ya akayi kikasan sunanshi" zee ta tmbyi zakiyya "Kinmanta sanda zeena tazo tace kuna soyayya kikaqi yarda harda mana kuka" zee tai dariya kawai Amma yayi kam he's handsome.... From which state is he? Cos he look like pure Fulani A takaice zee tace katsina... Good,, wish u best of luck.." Zee tace. Thank you" Tun last week minnatu ta koma U.S inda tke krtu, sai yaayaa cee kawai a gidan itama bata fiya zama ba in suna nan, Tun jiya da faruq ya kirata sukai wayar nan bayan fitarshi be sake kira ba, agogo ya buga karfe 12 na rana, kamar ta kirashi amma se taki, tana fadama kanta "maybe he's busy" Ta idar da sallar azahar tana zaune bisa dardumar tana kare lazuminta, wayarta tai ring, tasa hannu ta jawo wayar dake kusa da ita kan mirror, sunan Anty hawwer ta gani bata wani ji dadi ba ta dauka, sai kuma hira ta barke zee ta sanaar da ita komai yadda sukai da faruq jiyan.... Tayi juyi kan gadon nata batajin bacci sam, zakiyya dake dayan bangaren a kwance itama ba baccin take ba tace "zee zamuje saudin kuwa a wannan hutun dan naga beda yawa 2 weeks ne kawai" a kasalance zee tace "no Abbah jabir yace se mun gama session din kamar last time, koni naso zuwa".... Karfe takwas na safiya suna ta ayyukan gidan, sukaji karan shigowar motoci dan yaayaa ma bata tashi ba, window zakiyya ta leka, zee na karasa mopping, Zo ki tayani ganin abin Al'ajabi kamar motocin gidansu Anty siyama, ai bata rufe baki ba ta gano Antyn na fitowa daga mota, Keee dama yau Anty zata dawo? Zee da sam batamaji me take cewa ba, gabadaya tunaninta naga faruq, yanxu kam ya fara bata mata rai, atleast he should hav called she's patiently waiting for his call, she missed dat cracked voice of his," jijjigata da zakiyya keyi yasata kikkifta idanu cikin jin gajiyar zuci, Bata kaiga cewa komi ba Anty siyama ta bayyana gabansu ta kofar falourn, duka suka tsaya suna kallonta kamar sunga abin mamaki, Zee ce tai karfin halin karasawa gareta tana gaidata dayi mata sannu da zuwa, ta dubi falourn sama da kasa babu abinda ke tashi sai kamshi, tai murmushi tace yawwa sannunku da aiki,, yaayaa ce ta fito jin karabniya, nan suka bude sabon babin yiwa juna sannu da jin dadin ganin juna.. Ranar Aikin dasu zee sukeyi se da ya karu, dan ko wanki daya anty bata bada ba na kayanta saida ta dawo ta basu suka saka a engine suka dinga aikin wankewa, ga girki da ta dinga saka zee Abinka da mai ciki se an girka tace kamshin be mata ba, Allah sarki zee haka taita wahala dan zakiyya daki ta rufe tai kwanciyarta... Karfe 6 na magriba, zee ta kammala girkin daren ranar, a gajiye take ta koma daki. Turus tai bakin kofa tana kallan zakiyya dake hada kaya a trolley, ta karaso da sauri kuma, "Kardai tapiya zakiy ki barni" zakiyya tace zanje gida nayi sati daya se na dawo nan zance mama tayiwa Abbah magana yama Anty siyama magana na cigaba da zama a nan tunda mkrntarmu daya ne karatun da tapiyar zatapi sauki" ba karamin dadi taji ba tace "to sai kin dawo Allah yasa ya amince" zakiyya tai er dariya, ze amince ma sedai kiyi addu'ar Allah yasa me gidan ta amince" zee ta jinjina kai... Bayan tapiyar zakiyya zee tana kwance a dakin ko dinner bata fita tayi ba, gabadaya ma ta rasa mene ke mata dadi, Wayarta tai ringing ta zabura tana son ganin sunan faruq kan screen din, cikin sa'a sunan nashi ya bayyana, wani dadi ya ratsata ta dauka da sauri ta rike har zatai picking kuma se ta tuna kawai haushin takeji, wato ma duk kewarshi datai shi beyi ba ai da ba haka yake mata ba dan basu taba kwaana biyu basui waya ko kuma ta ganshi ba, Ta yatsina fuska ta ajiye wayar gefenta raanta wasai, tana kallan wayar kiran farko ya katse na biyu ya shigo, shima ya katse na uku ma, seda ya kirata sau 5 bata dauka ba Ya haqura, sai a sannan wata yunwa ta dameta ta mike ta fita neman abinci, ko ba komai tasan yanason magana da ita kuma ya tina da ita wannan ma kadai ya wadatar dukda har ranta tanaso ta dauka taji ya yake, A haka ta tuttura abincin ta koma dakin, anan ta sami wayar tana ta ringing kuma shi dinne, ta karasa ta dauka sannan ta gyara zama tai picking call din, Da sallamarshi da ko yaushe ya fara, wani sanyi mai kamada na kankara ya ziyarci zuciyarta, ta lumshe ido sannan ta gyara muryarta ta amsa mishi sallamar, "Nernerh kuma shine inata kiran wayar kika sha re ni" ya fada muryar nan kamar wani mai shagwaba, ta hadiyi yawu tana maida numfashi akai akai, ta gaza fadin komi, "Nayi laipi ban kira ba ko nernerh?, can kasan makoshi tace "uhm" Yace "to nerhnerh meyasa baki kirani ba" har yanxu muryarshi kamar ba ta faruq din data sani ba he sound emotional A wannan gabar kam batada Amsar dazata bashi, "Nasani nine ya dace na kiraki but idan kinji shiru seki kiraa kiji ko lpia" ta gyada kai tmkar yana ganinta, Ya cigaba da fadin "naje katsina ne cikin dangi acan zanyi hutuna" tace ohh, to ya kike? Ya gida? Ta amsa da lpia qalau, a hankali ya soma janta da hira tun bata amsa mishi sosai harta ware ta cigaba da amsa mishi, sunfi 1hour suna waya yana bata labarai kala kala duk dan ta sake dashi, daga karshe sukai sallama yayi mata saida safe sannan yace ta kula da kanta... Kashegari da tex dinshi ta tashi, taji dadin tex din daya mata ta mishi reply da thank you, dukkuwa da ba sune kalaman da suka dace tayi mishi reply dasu ba,, tana ta ayyukanta na yau a cikin gidan amma hankalinta naga wayarta... Faruq kawai take tunani gashi ita nata jin kan ya hana ta kira taji ya yake shima tun tex din safe be kira ta ba, duk tabi ta damu wayarta nayin motsi kadan zata duba, tana zaune bakin mudubin tana juya wayar tana tunanin kawai gwamma ta kirashi, kiran sallar magrib akayi duka babu wata nutsuwa a tare da ita ta tashi tai sallah, bayan ta idar ko addu'ar kirki batai ba ta jawo wayar, sai kuma tai wurgi da ita kan gado cikin jin haushin kanta, duk tabi ta damu kanta akan wanda bema damu da ita ba, hawaye taji sun silalo mata meyasa zuciyarta zatai mata haka wanne irin fadawa so ne haka tafar daya, meyasa be damu daa ita kamar yadda ta damu dashi ba.... A hankali ta kwantar da kanta jikin gadon dake gefenta, hawayen idanunta basu tsaya ba, kewar Ammi takeji sosai, tun rasuwarsu bata ji kewarsu ba kamar yau bama kaamar Amminta, da tuni suna hira ko karatun qur'ani, ta share hawayenta ta dago ta jawo qur'anin ta soma karantawa amma sam babu nutsuwa a tare da ita, ta rufe ta dakko wayar ta saka karatun ta kwantar da kanta tana saurare, har akayi sallar isha'i tana nan ta miqe itama ta gabatar da nata sallar sannan ta hau gado dan sam bata jin yunwa ma, a haka har bacci ya sureta, cikin baccin ta dingajin ringin din wayarta ta tashi a dan firgice tana ambatan sunan faruq a bakinta, aikuwa sunan nashi da tai saving da dear ya bayyana kan screen din, wani sanyi taji a ranta, atleast tasan bai manta da ita ba, a matuqar sanyaye ta jawo wayar tai picking ta kara a kunne cikin sleepy voice ta Amsa sallamar tashi, "My queen har kin kwanta" cikin makogwaro tace "uhmm" yace "to ya kike? Ya yau din?" Tace Alhamdulillh yace "masha Allah" "I hope kinyi dinner" tai shiru a ranta tace "ko ya d'ance ma yayi missing dina, bata ida karashe maganar ba yace "yau nayi missing dinki dayawa" tai mishi banza ta fada a ranta "liar" Ya cigaba da cewa "kinsan abinki da family issue, wlh ban samu zama ba i was very busy, daga a aikeka can se a aikeka nan... Haka yaita mata hira tana binshi da umm har kuma daga baya ta saki jiki dashi suka dinga labarai ranta yai fes,, ita har mamaki take ko nawa yake kashewa a sayan card? Wacce sana'a yake kodayake daga ganinshi kasan he's from a wealthy family, daga karshe chats suka koma dan ce mishi tai ta gaji da wayar amma bawai ta gaji da hira dashi ba nan ma suka bude sabon babi, datace mishi bataci abinci ba ya sakata gaba saida tai snapping abincin data hada ta turamishi kuma ta zauna taci tana mai jin annashuwa... Ba zee tai bacci ba se wajen 12 ta gota ma, a tarihinta kuwa wannan ce rana ta farko data kai ya wannan lokacin batai bacci ba saidai in karatu take ko kuma batada lpia.... Assalamu alaikum Ina mai baku haquri jina shiru da kukayi jiya, hakan ya faru ne saakamakon rashi da muka samu, Allah yayiwa yayan Abbanmu rasuwa, pls ku sakashi cikin addu'o'inku Ubangiji Allah ya kai rahama kabarinshi Allah ya jiqanshi Amin 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 26: message Haka lamura suka cigaba da garawa tsakanin faruq da zee, a satin biyun da sukai na hutunsu kuwa ba er qaramar soyayya suke xubawa ba dukkuwa da wani sa'in se ya yini ya kwan be kirata ba itakuma ya barta da tinaninshi, idan kuma ya kira ya bata uzuri a haka suka dawo makaranta, A bangaren zakiyya ma Anty siyama ta yarje mata dawowa gidan da zama, yanxu su uku ne cikin gidan dan yaayaa ta koma gida tuni, Karatu zee tayi daidai gwargwado dan wannan seemestern ma tanaso tayi abin arziki dukkuwa da result din wancan semester din be fito ba amma tanaji a jikinta tayi abin kirkin,, A satin da suka koma a satin ya dawo garin, kuma yana shigowa garin be zarto ko ina ba sai gurinta dan ko apartment dinsu beje ba,, yauma zakiyya ce tayi mai iso sannan daga baya zainab din tazo, tun daga nesa take kallanshi, yayi haske akan wanda tasanshi da, siririn sajenshi ya sake kwanciya saidai bai kara kiba ba kuma bai rame ba, amma kuma yau ba fararen suturar bane jikinshi, besan ta karaso ba yanata pressing wayarshi saida sanyin breeze din data taho ya hurashi hadi da qamshin arabian perfumes dinta suka hade da scent din flowers dake gurin, a matuqar sanyaye ya lumshe ido yana sauke numfashi, a hankali ta mishi sallamar shima ya amsata sannan ta zauna gefenshi, sai sannan ya daga idanunshi ya kalleta, ya kai mintuna 2 kwarara yana kallanta, wanda yasata takura gabadaya, ta dan yi gyaran murya tace "anzo lpia ya hanya"... Ya dauke kanshi bai amsata ba, bata damu ba ta sa hannu zata zuba mishi lemon da zakiyya ta kawo, ya amshi lemon yana girgiza kai... "Banda abinki wake saka sarauniya aiki" ya zuba nashi itama ya zuba mata ya miqa mata dukkansu murmushi sukeyi,, kurba daya tai ta ajiye ta bata fuska "ni ka dena kallona" Wani murmushin gefen baki yayi "baki isa ba" a mamakance tace "ikon Allah", Sai kuma ya kalli jikinshi ya kalleta, "shine har da yin irin shigar da nai ko" ta kalleshi itama tana murmushi, dukkansu black sukayi shi yasa black getzner se shining take itakuma ta saka black Abaya tasha duwatsu tana shining, A hankali murmushin fuskarshi yayi fading sounding serious yace "u really look good nerh_nerh" Har wani melting zuciyarta keyi in taji yace mata nerh nerh nan wlh, Ta kikkifta idanu kamar mara gaskiya "ai ban kaika ba" Ya zare idanu "karkiyi sa6o dan kin fini nesa ba kusa ba," hakan ya sakata displaying wannan murmushin dayake mata kyau, har ya bayyanar da haqoranta dake shining "So bright" ya fadi "' shine abinda ya fara sanarmin da feelings dinki a kaina, zainab kina da wani silent beauty ba kowanne idanuwa ke gani ba se mai idon basira" Wait wani ya taba fadamin haka, zee ta ayyana a ranta, a hanakali kuma ta tuna sanda zakiyya ta fadamata tun a wancan gidan a lokacin ta dauka wasa ne kawai, amma gashi still faruq ya sake fadamata".... Basu dade va suka karkare hirar tace yaje gida ya huta tunda yayi tapiya, suka kuma tsaya a kan next week zasu koma lectures sanin halin malamai dasukayi in an koma hutu akan dan kara lokaci akai.... A falour ta tadda zakiyya, ta karasa kusa da ita ta zauna tana facing dinta, zakiyya tai tsaki, wai mene haka ne kina gani fa kallo nakeyi, zee ta juya ta dubi tv din da ake wani indian film a starlife, ta karasa ta kashe tvn sannan tace we need to talk, ihu ne kawai zakiyya bata kurma ba dan seda ta ma zee dundu, Say it quick pls" Zee tace dama rannan da kikace am beautiful dagaske kike ? Zakiyya tayi wani murmushi, Faruq ya fadamiki same abinda nace right? Ta gyada kai, "ni a nawa tinanin irinsu Anty hawwer ne kyawawa da irinsu..." Se kuma tai shiru bata karasa ba, "Minnatullahi ko?" Ta gyada kai how do u know ita zan fadi?" Zakiyya tace "Saboda mostly haka mutane ke gani, ina nupin idan kai ba fari bane to ba kyakkyawa bane, yawanci anfi alaqanta farare da kyau, saboda nasu kyawun yafi daukar ido da hankali dats attraction, amma irin naku kyan daban ne, u re unique, ko colour din skin naki ma abin kallo ce dan koni akace na fadi category din skin colour naki faduwa zanyi cos baki cikin farare kuma baki cikin bakake, irin naku silent beauty din se masu idon basira suke gani"...... Sunyi resuming karatukansu cikin ikon Allah kuma komai yana tafiya daidai, da farko faruq ne ke zuwa daukanta da kanshi kuma ya maidata amma se ta hanashi tace ya dinga maidata kawai tunda akwai mota a gidan, basu dade da komawa ba akayi pasting result, bata shiga school ranar ba hakama faruq dan indai daya beje ba to dayan ma haka, Shi da kanshi ya kirata lokacin tana kitchen tana girkin abincin rana cikin annashuwa, Anty siyama ce ta kawo mata wayar, Gashi wayarki na ringing tun dazun (ta barta a falour ne) ta dauka batareda ta damu da wani banzan kallo da anty siyaman keyi mata ba, "Soulmate An kafe fa" ajiye serving spoon din hannunta tayi ta nemi guri ta jingina, "Dear me muka samu?" Yace zan miki sending ta whatsapp, ta bata rai "ni banason wannan jan ran naka kawai ka fadamin in banyi abin arziki ba ai shikkenan" a hankali yace "soulmate komai na Allah ne, kuma kowa rabonshi ze samu," faduwar gabanta ta tsananta "Kin samu clear pass nima haka" ya karasa fada yana kyalkyalewa da dariya, itama dariyar ta saki sannan ta furta Alhamdulillh Ba karamar kwarinta faruq yayi ba dan kuwa 4 point ya kawo itakuma 3.7 dukansu suna upper, wannan news yayiwa Anty hawwer dadi ba kadan ba, A bangaren faruq ma ya sanarwa Anty safiyyanshi, yace ta fadawa dady, itadai Anty safiyya fadi kawai take lallai zainab Alkhairi ce FUJ ka kula da ita dan Allah".... A karshen satin akayi sadakar cikar shekarar rasuwar Ammi da Abba, tareda faruq akayi komai, sai zee taji tamkar ta samu faruq ne a madadinsu, Wataranar litinin zee ta shiga school da safe basuyi waya ba, tun jiya da yamma dayace mata zai tafi birthday din wani friend dinshi, tana falour wayarta tai ringing ta dauka tana murmushi ganin sunan faruq kan screen din, bayan sunyi en gaishe gaishe kamarr kullum yace "soulmate, zanje birthday na wani friend ne sun gayyaceni, a nan kusa damu yake, he's my neighbor, amma fa in baki yarda ba bazanje ba" murmushi mara sauti zee tayi tace "karka damu na yarda ma" yace thank you my queen" tace "karfa ayi dare" daga haka sukai sallama, har tayi bacci kuwa be kira yace mata ya dawo ba kuma bataga tex dinshi ta watsapp ba Taji wani bacin rai tunawa da yadda sukai jiya, ko tex din safe daya saba mata ma beyi ba, ta cigaba da takawa zuwa hanyar department din nasu, tana kokarin shiga sarah na qoqarin fitowa daga department din, zee tai mamakin ganinta dan basuda alaka ko ta lectures da zata kawo department din, Harda er sassarfa ta hada ta karaso gaban zee, zee ta kare mata kallo, babu kwalliya a tareda ita sam kamar va safiya ba kamar ma ko mai bata shafa a fatar tata ba, saidai fatar ta boye hakan kasancewar oily skin me shining gareta, Kuma tayi kalar a rikice take, "zee faruq," sarahn ta fada a dan hargitse batareda ta kula da irin kallon da zee ke kare mata ba, zee ta hautsine "me ya sami my dear, meya faru da my faruq" sai hawaye suka fara zubowa kamar dama jira sukeyi, zeenat ce ta karaso sakamakon hango su datai a kofar department din, harda dan gudunta ta isosu, ta rike zee tana tamabyar sarah datai sororo tana kallon zee meya faru, sarah ce ta soma fadin, "tun jiya en sanda suka kamashi dayaje birthday, dan nima naje amma banje da wuri ba dan an kusa tashi ma, kuma ba tare muka taho ba" to me yayi musu suka kamashi?" Zeena ta tambaya, "wai yayi violating rules na driving" Wanne police station ne?, sarah ta sanar musu dagaa haka suka dunguma suka tapi, Koda suka karasa tun basu shiga ba zee ta hangi bayanshi yana cike wasu takardu, da rigarshi a hannu, sai daya gama komai ya fito sannan ya gansu tsaye a waje sai faman kuka zee take babu sauti, Ya tsaya a gabanta kawai batareda yasan me ze ce mata ba,, zeena taja gefe, zee ta sunkuy da kanta tana cigaba da zubda hawaye da sheshheka lokaci zuwa lokaci, gurin zeena ya karasa ya amshi tissue, sannan ya dawo gabanta ya miqa mata, ta amsa babu musu tana goge hawayen idanunta, kallonta yake tayi kwalliya cikin coffee gown wacce ta fidda tsayinta, sai gyalenta medium data nade kanta dashi, kyalli fatarta ya karu tamkar ka hangi golden ring yana kyalli cikin rana yana daukar ido hakama tata skin din, hancin nan tubarkallah, ya dan kauda fuskarshi, itakuma ta dago bayan ta gama goge fuskarta, ya maida dubanshi kan innocent face nata, yau sai yaga tayi mishi kama da er baby, Har gida suka rakashi itada zeena ya musu bayanin cewa "wai ya karya dokar tuki ne a yadda suka fada shiyasa suka kulleshi" zee dai batace komai ba sai jimami hakama zeena, bayan kwanaki biyu da faruwar wannan, zee tana gida bata da lecture na safe se karfe biyu ma, ta kammala wanke wanke tayi goge goge ko ina tas, ta koma daki taa zauna tana tinanin yin wanka ta hada ruwa zata shiga kenan wayarta tai pinging alamar shigowar sako, ta shiga batareda ta duba ba, bayan ta fito ne ta shirya ta dakko wayar sai taga wani sako dake neman tarwatsa kwakwalwarta kamar haka; "Zainab ki fita harkar faruq ba mutumin kirki bane, d'an shaye shaye ne idan kuma baki yarda ba ki duba watsapp dinki" Wani mugun bugu taji kirjinta nayi mata kamar zai tsage Naga sakon ta'aziyarku dayawa, nagode Allah ya bar zumunci, 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 27: F.U.J Gabadaya ji tai wani jiri yana dibanta ta rintse ido ta rike bedsheet din ta damke shi a hannunta, takai mintuna 10 a haka sannan cikin karfin hali ta jawo wayar taana ta girgiza kanta da fatan Allah yasa ba gaskiya banee abinda ake fada mata, ta bude watsappa bayan messages sun gama shiga ta hangi message na bakuwar lamabar datayi mata tex, ta shiga da hanzari Vedio ne ta bude, tunda ta fara kalla ta kasa kifta idanunta, tabbas faruq dinta ne, yana zaune kan kujera yayi balance, gabanshi kuma wani karamin table ne an jere kwalabe da gani ma ya fita hayyacinshi ga kwalayen sigari da daya a hannunshi, sai sha yake, a zaunen ma layi yake Wasu zazafan hawaye suka sakko mata, wani tex ya shigo ta watsapp din ta karanta kamar haka, "wannan shine dalilin dayasa en sanda suka kamashi saboda he's drunk and he drive, Allah ma yasa beji wani rauni ba, dont try calling me cos u wont get through" Ta ajiye wayar cikin kokarin controlling kanta, ta zame kasan tiles din zuciyarta na mata zafi, faruq be mata adalci ba, me yasa ze yaudareta, innalillahi wa inna ilahi raji'un, kuka sosai takeyi, har daga karshe ta kwanta a kasan hawaye na bin kumatunta, Bazata iya kayyade tsayin awannin data dauka a hakaba, tamkar matacciya haka takejin jinkinta ya mata nauyi, ko dan yatsanta kasa dagawa tayi, wayarta kuwa tayi ringing yafi sau ashirin amma sam bata ma ji ba A hankali ta turo kofar ta shigo dakin a gajiye, ta subale jakarta kamar ance ta kalli inda take ta sake waiwayawa dakyau, yes mutun ne a gurin, da sauri ta karasa gurinta inda take a zube, jikin nan ya dau zapi rau, ta dago ta amma jikin nata a sake yake gabadaya, zakiyya ta jijjigata "Zee mene haka, meya sameki, na shiga uku zee yi magana", idanunta a bude sun chanja kala kuma sai kallon zakiyyan take," da sauri ta saketa ta fita ta nemi Anty siyama, Allah yasa driver be tapi suka sakata a mota, Alluran bacci akai mata hakan yasa batasan meya faru tsakanin kwanaki biyun ba tana ta bacci, Ta bude idanunta da guntun hawaye a gefe, cikin rashin sa'a tai tozali dashi tsaye duk ya birkice, ya karaso gabanta da sauri ba tareda ya damu ba ya tsugunna a gaban gadonta kan guiwarshi, ta rintse idonta hawaye masu zapi suka soma ambaliya,, muryarta a dashe sosai dan bata fita, koda dama can sanyi gareta, "Dan Allah ka tapi ka kyaleni banason ganinka" shock ya shiga, shida ya matso ya tausheta, ya dauka zatai farincikin ganinshi ya dauka zataji dadi ne idan ta ganshi ya dauka zataji saukin zazzabin datakeji ne ya dauka zatai appereciating efforts dinshi gameda zirga zirgar daya dingayi cikin asibitin amma se sabanin haka,? Kuma a iya saninshi beyi mata laipin daze saka tace batason ganinshi ba, bayan wayarsu ta karshe ma suna annashuwa sukayi da son ganin juna in lokacin lecture yayi, Bai iya furta mata komai ba se kallonta dayakeyi ta sake maimaita mishi cikin fusata da tsana "nace ka tapi ka kyaleni banason gaaninka, ka rabu dani dan Allah" Furucin nata ya sanar dashi lallai dagaske zee ke fadamishi hakan, ya tapi ya barta? Kamar yaya wai? Ya tmbayi kanshi, Zeena ce ta shigo dauke da flask a hannunta, duka suka dubeta, zee tai yunkuro tana kama hannun zeena sanda ta karaso "dan Allah kice mishi ya fita ya barni, banasonshi a rayuwata" zeena ta zubama faruq ido, a matuqar sanyaye ya juya ya nufi haanyar fita ya rike handle din kofar sai kuma ya saki, lokacin zee ta kifa kanta jikin zeena tana sheshheka a tunaninta ya tapi, Dawowa yayi a hankali ya tsaya gabanta yayi folding hannunshi kurun, bata san yana dakin ba "zeena faruq ya cuceni, ya boyemin gaskiyarshi, se yanxu danayi nisa a soyayyarshi sannan , Allah ne kadai zai mana sakayya," Zeena batace komai ba sai kallon faruq da takeyi wanda ya zuba ma zee ido, sai kuma yayima zeena alamu da yatsanshi ta fita, ta zame jikinta ta fita sakamakon hakan kuma zee ta dago tana kallonshi bacin rai ya zanu a fuskarshi amma who cares tunda dai ita hakan ko a kwalar rigarta, Ya karaso itakuma ta zuba mishi ido cike da tsanarshi, "Me nayi miki da zakice Allah ne ze sakamiki? Na yaudareki ne?" Ya tambayeta da dan fada fada, ta mishi banza ta kauda kai gefe, zuciyarta na dagawa da sauri da sauri, shiru duk sukayi batace mishi komi ba shima bai sake maimaita tmbyar ba, yafi mintina 20 a haka sai ya juya a hankali ya fita daga dakin ranshi na tafarfasa, Tabi bayanshi da kallo ya fita ya rufe kofar daidai nan ta saki wani marayan kuka cikin karyewar zuciya, A ranar aka sallami zee ta koma gida bayan likita yayi gargadi da ta dena saka damuwa dayawa a ranta, zee da zakiyya a motar driver na jan su, "Zakiyya banga Anty ba kwata kwata" zakiyya tace "ai Anty itama babu lpia tana hospital tana ta lebour tun daren jiya" duk rashin kwarin jikin da zee keji sai taji wani karfi, "wanne asibiti? Kardai wanda muka baro" zakiyya tace shi , Amma saboda Allah shine baki kaini na dubata ba, maida wuqar to tsokanarki nake Ta haihu har sun sallameta dazu Dadi zee kamar ita ce ta haihu, "me muka saamu?,ya jikinta?" Ki bari in munje kya gani keda likita yace ki huta duk kinbi kin dami kanki.." Aikuwa da sukajee gidan a dan cike yake, da en gida da kuma en uwan Anty harda yaayaa, Anty ta samu namiji kuma tana lpia Gabadaya satin bataje school ba suna gida sunata hada hada, ranar suna gidansu ta tapi akayi suna, aka sakama yaro sunan muhammad saghir *** Ta kammala shiryawa domin tapiya makaranta tayi shigarta ta bakar abaya dukda cewar ba fara ce tas ba amma tayi kyau ta yafa gyalen abayar dayasha ado da duwatsu, Driver ya ajiyeta gaban department tama zakiyya sallama sannan ta fita a motar, ta dan waiga ko zataga motar faruq dukda haushinshi da takeji amma sai babu ita, haka aka gama lectures din ranar amma babu shi babu alamarshi, sai kuma taji tana son sanin halin dayake ciki, Ta danne ranta ta tafi gida, kwanaki uku zee ta jera tana zuwa makaranta amma bataga ko me kama da faruq ba, duk iya kokarinta na danne rashin damuwar da tai hakan ya faskara sai ta tsinci kanta cikin matsananciyar damuwa na rashin ganinshi Bata kira driver ba yau kuma bata jira ta gama lecture ba ta fita ta gate din baya ta tari napep ta fadamishi inda ze kaita, Ta kai mintuna 5 a tsaye a kofar gidan tun da mai napep ya ajiyeta, can dai ta tattaro confidence ta tura kofar gate din, motoci ne parked in the drive in, can gefe a lungu taga motar faruq kasan rumfa har tayi kura, Ta karasa gun motar tana lakatar kurar data gani ta waiga ta dubi kofar apartment dinshi kaamar kuma wacce magnet ke jaa ta soma tafiya zuwa apartment din nashi, ta tura kofar taji a bude, ta soma hawa matattakalar benen dake bakin kofar, ko gajiya batajiba ta gama haye steps din ta ganta a bakin wata kofa, tasa hannu ta tura Er kara kofar ta bayar ta sule takalmanta sannnan ta shiga, da dan duhu a falourn dan duka fitilu a kashe suke hakama curtains a sauke suke, amma hakan bai hana ta ganin royal cushion set din da akayima falourn ado dasu ba, masu launin royal blue sai carpet sky blue da ratsin black babu wasu tarkace cikin shi daga set na kayan kallo sai dispenser, ta karasa wajen wagegen window din ta yaye curtains sannan taga switch ta kunna fitilar falourn, take haske ya gauraye falourn, a tsaftace yake amma akwai kura alamun kwana biyu ba'ayi shara ba kuma kamar babu me shiga cikinshi, Cikin rashin tsoro ta nupi kofar dakin datake kallonta, ta tura kofar kamar waccan tayi kara itama, sai tayi baya da sauri kuma bada nisa ba, sai kuma ta dawo ta shiga dakin, Tun a bakin kofar dakin take tuntube da guntayen sauran sigari, haka ko ina a kasan dakin wasu ma ba'a kunna ba Kaca kaca dai dakin ta dubi saman bedsheet din, yayi rubda ciki dukda er kurar dake dakin ma sam be dameshi ba, can gaban gadonshi taga wani frame na hoto, da gani mahaifiyarshi ce a jikin hoton da wata wacce zee tayi concluding da cewar yayarshi ce Anty safiyya datakanji labarinta a gurinshi, Tana nan tsaye ya miqa hannu yana kokarin jawo sigarin dake kan drower, yayi sa'a ya jawo ya kai baki, zee ta ajiye jakarta ta karasa ta rike sigarin, Sai a lokacin yaji kamshin perfume dinta, jikinshi a mace ya daga dara daran idanunshi ya dubeta a raunane, kawai ji tai bazata iya rike hawayenta ba, ta tsugunnna a nan ta dora kanta a gadon tana shessheqa, ya miqe zaune cikin rashin jin dadi, dan kanta ta dena kukan ta dago ta kalleshi yana nan zaune "Ashe dagaske ne kai dan shaye shaye ne?, shine ka boyemin? Ka yaudareni" tai concluding Ya zuba mata ido kawai, tayi shiru kuma ta kasa miqewa ta tafi.. Can ta tattaro confidence ta miqe, Da cracked voice dinshi yace "i miss you nerhnerh" ta kalleshi zuciyarta ta raunana, wani sonshi ya taso mata, "Nerhnerh" ya kirata Ta zuba mishi idonta na wasu lokuta kafin ta dauke idonta trying hard to control her feelings, "YES is true i smoke but i hav stopped drinking years back " lokaci daya taji wani abu ya soki zuciyarta, ta durqusa cikin kurar tiles din sakamakon rawar da kafafunta suka dauka, "nerh nerh wallahi i stop taking alcohol, i dont drink anymore" Hawaye suka sillo mata, she's totally broken, kenan dai da gaske ne faruq is a drunkard A hankali ya tsugunno gabanta shima kan gwiwowinshi, kanta na kasa shikuma itadin yake kalla, am sorry zainab Sunanta ya fita tar a bakinshi tamkar shi ne ya rada matashi, I love you pls don't leave me, bata iya ce mishi komai ba se shessheqar da takeyi lokaaci lokaci, dukkuwa da tsananin tasirin da kalamanshi keyi a kanta, ya miqe tsaye yace pls come with me, ta miqe ta bi shi jikinta a sanyaye, wani daki nan kusa dasu ya bude a cikin falourn, Dakin a gyare yake ba kamar bedroom din ba, saidai babu komai cikinshi sai art accessories, at first in ka shiga zaka fara hangen wani glass yana ta shining kuma an manna qananun fitilu a jikinshi suna bada different colours hakan ya kara mishi sheki, FUJ in bold shine a jikin glass din sai kuma board mai fadi gefen board din akwai table da su colours da different painting materials, Sai kuma frames da dukansu an juya bayansu hakan ze saka bazaka gane mene jikin frames din ba, wasu kuma an rufe su, Stool ya jawo mata yace sit, ta zauna tana goge sauran hawayen idonta, ya karasa gaban glass din mai kyau, abinka da mai tsayi bai nemi karawa ba ya ciroshi a hankali, cautiously da alama abin is very precious to him, ya nufo ta dashi, zee ta dinga kallon abin tana burin ta taba shi, ya miqa mata shi, ta amsa tana kalla, sai da yazo hannun ta sannan ta gane ashe award ne, sauran rubutun jiki duk kananu ne, F.U.J ne kawai akayi shi babba yadda ko daga nesa kake zaka ganshi tmkr yana yawo cikin ruwa garai garai, F.U.J shine abinda bakinta keta mmaimaitawa The name seems familiar, ohh ta tuna akwai wani frame da akayi designing flower a jiki lokacin Amminta ce ta siya mata shi, a can kasan frame din an saka F.U.J, Wats the meaning? Ta tmbya tana shafa frame din "Not only its meaning, u ll get to know me" Ya fita ya koma bedroom ya dakko wayarshi ya dawo, yayi kira, sannnan ya ajiye wayar yaja kujera ya zauna nesa da ita gefen board din amma ita yake facing '"Faruq usman jabbar is the literal meaning of FUJ" She looks suprised and he knows she will hakan yasa bai damu ba ya cigaba da bayaninshi Professor J.B is my dad, she looks suprised yet again, 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 28: Faruq 2 Asalinmu fulanin katsina ne kauyen dutsin ma, asalin en kauye, fulanin ruga, irin masu tsabar dukiyar gonaki da dabbobi, kakanmu na gurin abbana (paternal grandpa) shine ya soma yin boko cikin su duk cikin kakanninmu shine yayi boko saboda yana da son bokon amma iya kacinshi primary ne, kuma a wannan lokacin sune asalin en boko, suna da tsabar dukiya na shanuwa da gonaki da suke nomawa... Allah ya albarkaceshi da yara har hudu, maza 2 mata 2, babban yayansu ibrahim Allah yayi mishi rasuwa da dan dadewa, sai ta biyu momy suwaiba, sannan Abbana sai autarsu suna ce mata Inno, taci sunan mahaifiyarsu, To kasancewar mahaifina shi kadai ne namiji a cikinsu bayan rasuwar baba ibrahim kenan, sai babansu ya kwallafa rai kan Abbana yayi karatun boko tunda sauran mata ne yasan aure zasuyi dukda hakan kuwa sunyi iya secondary, Cikin sa'a shima Abbana ya taso da kaunar bokon wacce har tapi ta maihaifinshi karfi ma, irin su ake cema Allazi boko, Yayi karatu yayi karatu har saida ya kai matakin professor, a lokacin dayake jami'a ya kammala degree dinshi na farko ya dawo ya tarar mahaifinshi yana cikin jinya babu lpia, hakan yasa suka yanke shawarar kaishi asibiti tareda mahaifiyarshi, Basuma karasa ba Allah ya karbi rayuwarshi, Sauran yaran mata kuwa sunyi aure a lokacin daya Abuja aka kaita (momy kenan) dayar kumaa katsina ta zauna (inno) bayan kammala sadaka da jimami na rasuwa, akayi rabon gado, sai mahaifina ya tashi da kamasho mai yawa tunda shine namiji, ba karamar damuwa ya shiga ba saboda rashin Abbanshi kasancewar sun shaqu matuqa ga yadda ra'ayinsu kan zo daya kan fannoni dayawa, sai yaji duk bokon ma ta fita a kanshi, ya zauna kawai yana kulawa da dabbobi da gonakinshi dana mahaifiyarshi, ba'a dade ba sunan masu scholarship ya fito kasancewar yayi applying schorlarship din tun da dadewa, aikuwa ya samu, yaji matuqar dadi sanda ya samu kanshi cikin wadanda gwamnati zata dauki nauyin karatunsu, hakan ya kara mishi kwarin gwiwa ya soma processing yana shirin tapiya, Innarshi bamai son magana bace sosai amma hankalinta yapi kwanciya idan yayi aure ita ba son bokon take ba, Abbana kuwa lokacin ma babu auren a ranshi sam, ya kama hanya ya tafi europe karatu, ya damka komi na harkokinshi gun inna da kawunnanshi Dayake yana son karatun sai ya maida hankali kuma ya dinga sa'ar cin jarabawarshi da research,, a nan ya ga ummi na, nutsuwarta da hankalinta ya debeshi gata itama fulani ce asalin jihar Adamawa, yana gama masters dinshi ya dawo gida yayi bautar kasa ya kuma saka a nema mishi auren ummi na sanin da yayi irinsu ba karamar wahalar samu sukeyi ba, Lokacin da akayi bikinsu yana da shekaru 38 saura kiris ya cike arba'in, dayake yanason bokon kuma ya dan fara kasuwancinshi a europe se ya dauke inna da matarshi suka koma europe gabadaya, a nan ya kafa harkokinshi da iyalinshi, kuma ko a lokacin be haqura da boko ba ya cigaba da phd.... Haka muka taso mahaifinmu na tsananin burin muyi boko, a europe aka haifeni cikin turawa, amma ko sanda aka haifeni ma inna ta rigamu gidan gaskiya, Rayuwarmu duk cikin turawa mukayita addininma dan ummee tana tsawatarwa ne, kamar yadda na fada miki a baya mu biyar ne yaran umme da Abban, ya safiyya, ya halisa sai ni faruq sannan Aisha da auta Hamra, tun sanda Ummee ta haifi Aisha kanwata take ta rashin lapia wani irin ciwon ciki, wanda shine yayi ajalinta Aisha na shekaru 4 nikuma ina 8 Ummee na ta rasu, faruq ya goge wani hawaye daya sillo mishi alamun har yanxu yana jin zapin mutuwar ummeen shi... Hamra ba ummee na ce ta haifeta ba, 'ya ce a gurin cousin din Abbah ya rasu shine ya karbeta ya riketa, Ina gama primary school Abbah ya daukeni ya kaini U.S inda bani da kowa babu mai kwabata, a ganinshi ni namiji ne dole se ina zagayawa, kuma ko ina aka kaini zan zauna, sannan yana da burin nabi footsteps dinshi a boko, saidai kash, America gari ne na holewa babu mai kwabarka, babu cikakken addini, Nayi en mata a america dukda lokacin ina yaro ne kuwa irin soyayyar nan ta secondary school musamman dayake ni fulani ne sai nake da farinjini sosai kowa faruq, nan ne masomin tabarbarewar tarbiyyata, mune beach mune bar, mune clubs, a nan na koyi shan wannan sigarin, da alcohol Nayi disappointing Abbana, sam ni da shi bamu yin shiri, tunda ya gane abinda nakeyi ya dawo dani europe na karashe secondary school dina da kyar, saboda karatun ya riga ya fita a kaina, ga zuqar hayaki ga yawon jaraba, watarana ma a buge nake dawowa nasha nayi tatul , duk mutanen gidanmu sunsan ina shan ta, My fav. Sister ya safiyya har kuka takeyi idan Abbah yayi punishing dina, dan indae result ya fito to ba abin arziki nake ci ba, wataran ya zaneni wataran ya kulleni a daki na kwana na yini babu abinci balle sallah ko salati, Saida takai ta kawo ya kwace duk wani source da zan sami kudi ya cemin indae naci exams to zae bani packet na sigari har se na gaji da sha, Naji dadin hakan na maida hanakli kuwa naita karatu a haka na samu naaa kammala sec.school, Zee batasan sanda hawaye suka gangaro a cikin idonta ba, wanann wanne irin bala'ine akan boko, aikuwaa ya cika alkawari dayaga nayi abinda yakeso ya siyo packs na cigarette ya bani ..... Ya safiyya na itace meyimin nasiha ta dinga tinamin Allah da annabi, a hanakli kuma taa dinga jan ra'ayi na, na soma gane rayuwa mene ne ma amfanin zuwanmu rayuwar Domin muyi bauta ne kawai ga Allah, a hankali na soma chanja dabi'una marasaa kyau zuwa masu kyau, musamman in na tina wuta da Aljanna, idan na tuna mutuwa, har asibiti takan kaini naga marasa lpia,, ta sakani na kara godewa Allah dayayi ni da raena da lpiata, Haakan ya dasa min sonta a raina fiyeda na kowanne dan adam bayan ummee na, ita ce ta sakani tsaida sallah, ta koyamin wasu surori daga cikin alqur'ani, Ubangiji madaukakin sarki yace "hakika ita sallah tana kauda Alfahsha da aikin munkari" kuma tabbas na yarda, na kuma gamsu tunda ni ganau ne ba jiyau ba, Na dena duka yawace yawace, na dena shan alcohol gabadaya, cigarette ce kawai na kasa yakicewa dukkuwa da cewar na rage sha sosai Abbana ya sake maidani U.S cigaba da bokon datazama jazaman garemu duka, na fara level one na gama nayi level 2 amma sukayi min withdraw saboda ban kai marks din da suke muradi ba, kasancewar fannin medicine ne suna da tsauri, Na dawo gida still, saidai wannan karan ran Abbana ya baci ganin na raina mishi wayau banayin karatun ne wanda nikuma har raena nasan ina kokari na, gashi shi mutun ne dayapi so kayi karatun da kanka bawai a saya maka result ba.... To wannan dalili ne yasaka shi turoni nigeria yin karatu, a matsayin punishement a nashi ganin ko zan nutsu idan naga yadda ake shan wahalar karatu a nigeria, na shigo BUK da D.E amma ban samu medicine ba sai basics, yanxu haka so yake idan na gama naje nayi medicine din dayake muradi, Now zainab this is all about faruq usman jabbar, faruq wanda be koyi saukar alqu'ani ba, faruq is a smoker addict, faruq dont know how to recite the qur'an properly, faruq a drunk in the past Yadda yake fadin abubuwan gameda kanshi zakasan abin nayi mashi ciwo matuqa, ya hadiya wani abu mai daci, ya karasa gaban board din ya yaye, zane ne a jiki na zainab, ya karasa jikin sauran hotunan ya jujjuyo dasu, Zanuka ne masu matuqar kyau, "This is my passion zainab" Ba wani medicine danake so painting is all i want, but Abbana baze barni ba, dats y na zama secret artist, nake zane ina sayarwa, and dis, Ya matso kusa da incomplete painting din zee yace "this is all i did when u said u dont want to see me anymore" Zainab kam is speechless, so dama faruq painting yakeyi saboda tace ya rabu da ita, and this beautiful painting,..... Kwankwasa kofar akayi, faruq yace yes, gayen ya bude kofar da abin shararshi, Faruq yace "are u done?" Gayen ya gyada kai, "Okay i will call u later u can leave" Sai yanxu zainab ta tuna kafin ya fara bata labari yayi kira a wayarshi ashe masu shara ya kira, asalin ajebo kenan Ta raya hakan a ranta, agogon hannunta taa kalla, sannan ta miqe "i will get going" ya zuba mata ido, itakuma bata kalleshi ba ta tattara jakarta ta fito yabi bayanta, lemme drop u home, Ta kalleshi he's half naked A hakan?, ya kalli kanshi ya shafa sumarshi tai murmushi tace talk later take care, Ya bita da kallo har ta fice, be tsaya a nan ba seda yabita da kallo ta bolcony tana fita kuwa ta sami napep, ya koma kan kujerar ya zauna yana ajiyan zuciya mai karfi Yasan zee bazata gujeshi ba, is never his fault daya taso a haka, but he is trying to make himself a better person" Gabanshi ne ya fadi daya tuna akwai abinda bai fada mata ba ya boye mata kuma yana da muhimmanci ta sani, But abin ze tada mata hankali ne kawai, ya share yaji kwarin jikinshi kam yanxu ya dawo, his life is fully coloured with zainab in it And totally empty without her, ya tuna kwana biyun nan yadda ya zama depressed, Kamar yana counting words yace "I love you nana zainab" Show me some love and follow my Wattpad page @ AyshabNasir Me love u😅 Assalamu alaikum warahmatullah ina yiwa daukacin musulmi barka da sallah dafatan munyi sallah lpia Allah ya karbi ibadunmu, wannan annoba muna rokon Allah ya yaye mana ita Amin Episode 29: we 're Humans Zainab a nata bangaren sanda taje gida ma yamma tayi sosai, gabadaya tinaninta na ga faruq ne, so this is who he is, now is left for me to decide to continue with the relationship after knowing about him or to leave him, Yanxu yaayaa ce ke zaune da Anty tana mata wanka Tana aikin wanke kwanukan da suka bubbushe saboda tun safe wasu ke ajiye a base din, her mind is not there, gabadaya tunaninta faruq da abinda ya fada mata, Kuma she needs to know more about su ya safiyya, suma haka Abbansu ya tursasa su ya dorasu kan akidar boko? Dan ita dai bataji faruq yayi mentioning inda dayansu tai aure ba, dukkuwa da sudin manya ne, A haka ta kammala wanke wanke ta gama duka ayyukanta tai wanka, tayi sallah sannan ta kwanta kurun ta kashe fitila, bata dade da kwanciya ba zakiyya ta turo dakin, "Zee yau bacci da wuri haka" tana jinta amma bata amsata ba "ai da bari kikae kikayi sallar isha" ita kadai tai kidanta tai rawarta kuma duk a tunaninta bacci zee keyi, Bayan fitar zakiyya ta nutsu sosai tana buqatar tattaunawa da kanta, "Ina son faruq, fadin hakan ma kamar bata baki ne, and now i found faruq as a drunker and smoker, though he said drinking was his past habit he dont anymore, and he reduce smoking too, Ta tuno hadisin da ma'aiki ke cewa Prohet SAW said "all the children of adam will commit sins and the best of them are those who repent" We 're humans we 're not perfect, and seeing how deep he loves me i just can't leave him, leaving faruq now is never an option for us both, i love him he loves me, A yandaa na fahimta shi kanshi abin na damunshi shiyasa har ya kasa fadamin hakan tun farko, yes abin na damunshi ko daga yanda yake baani labarin ma da kuma yanda yayi concluding, he felt ashamed of himself, he need guidance yana bukatar kulawa, yana bukatr wanda yasan addini, inama ammi na tana raye, da na kawo mata faruq ta dinga mishi karatun nan nata na alqur'ani mai matuqar dadi, karatun fiqhu, sirah, hadisi... Allah ya miki rahama Ammi na Allah ya jikanka abbana, Bazan gujeka ba faruq, i will try my possible best to see u become the better person u wanted to" A haka ta kare tinaninta har bacci ya debeta da tarin mafarkai na faruq, kashegari zee ta tashi amma duka jikinta babu kwari kamar irin mutun yayi zazzabi da dare ya sauka da safe, tana kwance har zakiyya ta gama shiryawa, "Zee yau bazaki school ba" ta gyada kai "banajin dadi" sannu to Allah ya sawwaqe daga haka ta pita, Tana nan kwancen wani tinani ya fado mata, Wane ne yasan faruq na taking cigarette bayan en gidansu, dan dole wanda ya mishi vedio dinnan yasanshi, ta karaci tinaninta babu amsa, Wayarta tai kara, ta dakko tana murmushi "Nerh_nerh yau ba school ne naga school din empty ba kowa?" Surprisingly tace "ba kowa kuma?, kuma pa yanxu zakiyya ta tapi itama" "In my world u re the only persons i see clearly, so dole makarantar tayimin duhu mana tunda baki cikinta" Now she get where he's heading "Ohhh ta fadi tana smiling", i don't feel good today" So that means u re not coming? Then i hav no place in the school today, Bata ce mishi komai ba yace "what's with you?" Hop bakije kinyi overstressing kanki jiya ba," bata ce mishi komai ba yanxun ma Jin shirun yasashi fadin "that means im right, u overthink and why please" In kince na barki ne..... Sai kuma yayi shiru be karasa ba Seconds sukai flashing dukkansu mute, a tare kuma kamar hadin baki suka ce Shi yace "bazan barki ba itakuma tace "bazan barka ba" And all boost in laughter Sukai dariyarsu sannan tace ai na dauka cewa zakai zaka rabu dani, yace "nidin banza" in nayi asararki na cuci kaina wlh, irinki ke kadai ce a duniya, lemme tel u u're uniquely unique," Hakan daya fadi ya sake bata dariya , Gaba daya ma sai taji duk ta warware, dama curiosity yaja mata sanyin jiki, curious about not making the right choice, and faruq here keeps reminding her, keeps assuring her he's is not only the right one buh the best she could ever imagine" Alhamdulillh she conclude knowing only Allah will give her a partner like him, there's no perfect relationship only we makes it our own definition of perfect... I hop u re feeling good now? Ya tmbya tace "yeah yeah, Alhamdulillh" yace great, now ki tashi ki samu kici abinci kiyi wanka da ruwan dumi u'll feel good tace angama yallabai_na And that makes him feel the throne, yes he's her king "Stay safe" haka suka kare wayan, and ta miqe tayi kamar yadda yace se gashi ta warware sarai abinta har yin ayyuka ma, Karfe 12 ta kamamla komi tana zaune amma gaba daya zaman beyi mata dadi, ta miqe ta koma daki tayiwa faruq tex tana son ganinshi after zuhr aamma ba'a gida ba, ta mishi kwatancen inda zasu hadu, Itama ta shirya, bayan sallah ta tapi, a can ta sameshi, garden ne a gefen wani mall akwai karancin mutane da yawan korayen flowers, cool breeze tana kadawa, Tun daga nesa yake kallanta, as she walks she resembled a peacock, naturally beautiful And the cool breeze blowing makes her cloths float in air, and damn she look not only breath taking buh mind and soul taking, Alhamdulillh ya furta, kallonta kawai tare da dumbin nutsuwarta ya isa ya saka mishi nutsuwa da nishadi hadi da farinciki (mar'atus_saliha) balle ace tayi magana, maganganunta masu cike da tarin hankali, nutsuwa da fikra ga balaaga, ma'ana iya sarrafa harshe, tabbas zee kam Allah ya bata, saidai kara godewa mahalicci da Amminta, annabi yayi gaskiya dayace mu nema ma 'ya'yanmu uwa ta gari, domin iyaye sune copy na abinda kakeso 'ya'yanka su zama, ba iya uwa ta gari ba harda uba na gari...... Ta katse mishi tinaninshi ta hanyar sallamarta, kamar yau ya fara jin muryarta gabadaya yaji ta sake zaqi da dadi, Ya amsa yana mai annashuwa, ta kalli sit din ta kalleshi ya gane nupinta yace "sure gimbiyata most welcome to sit" Ta zauna "wato dan zaki zauna ma shine se kin tmbya" tai murmushi "haka ya dace"... Bani 3 mins pls" tace na baka Ya miqe ya tapi cikin nutsuwa, ta bishi da kallo, bai jimaba ya dawo hannunshi rike da cool drinks guda biyu, ya aje daya a gabanshi dayan a gabanta, Ya kuma dauki na gabanta ya bude mata yace "bismillah" Ta amsa ta fara sha, yace "so u ask me out" ta kalleshi a nutse ta ajiye robar, "yes dont i hav the right to?" Ta fada a zolayance, Yayi dariya, "ke kadai keda wannan right din" taji dadi har cikin ranta, So now lets talk serious, Nayi tinani ne kan abinda ya faru saedai abinda ke bani mamaki shine who sent the vedio to me?" Dif ya dauke wuta alamar maganar ta tabashi, murmushin fuskarshi yayi fading ya lumshe idanunshi tareda tallafar goshinshi "Ur expression and the sudden change in ur mood left me with no choice buh to believe u know something, tell me about it my dear" calmly tai maganr Ya furzar da iska waje, ya dan shafi beard din shi " labarin da na baki a iya karan kaina ne, ban sanar dake komai gameda sauran en uwa na ba, Ta sake tattara nutsuwarta dukkuwa da ganin da tai kamar beson fada "Bari mu soma da ya_safiyya, ita ce diya ta farko gun Abbana da ummina, shekarunta 35 yanxu haka, nasan zakiyi mamaki idan nace miki ko auren fari batai yi ba, yes bata taba aure ba, she's totally broken, tun bayan rasuwar ummee abba be sake aure ba, ya safiyya ke kula da duk hidindimun mu, bata da wani son karatu sosai, hakan yasa tapison tayi course mai sauki dan a nata burin ma in tayi first degree ya wadace ta, saidai Abbah ya saka mata law a matsayin course din da zatae a university, batai musu ba dan akwae ta da kawaici, ta tapi ta soma karatunta na law, a nan ta hadu da wani guy yazo ziyartar kaninshi a europe yana karatu a same school din, in takaice miki suka kulla soyayya mai karfi, tana shekara ta karshe suka sanar da Abbah sun rigada sun gama duk plans dinsu na aure da kasancewa tare, amma me? Abbah yaqi sam yace se ta gama karatun ta kaf dukkuwa da tana kan hanyar gamawar ne, haka sukaita lallaba shi da alqawarin ze barta tayi duk karatun datakeso, amma daga karshe sai Abbah ya ci mishi mutunci da cewar baze taba bashi safiyya ba, domin shi ba dan boko bane irin en kasuwaan nan, qualifications dinshi kuma iya first degree ne itama da kyar ya karasa, amma akwai dukiya sosai na albarkar kasuwancin, kuma maraya ne babanshi ya rasu shine ke kulawa da qanneshi da mahaifiyarshi, a cewar Abbah kuwa Shi yafiso diyarshi ta auri wani professor ko doctor atleast, ko wani mai muqami a gwamnati ba wanda ya dogara da kasuwanci ba, shima a nashi bangaren mahaifiyarshi ta dameshi akan lallai ya rabu da ya_safiyya itama batason dangin en boko wai mu bamuda tarbiyya mun taso a cikin turawa, kuma ai gaskiyarta ne tarbiyar tamu tayi karanci She cried her eyes out, a lokacin ne taji maraicinta, ta rasa tudun dafawa, bata kuma da ikon daga baki tai magana, and it all ends, saidai zuciya irin tata ta saka a ranta bazatai aure ba har abada, she still loves him amma shi har yayi aure ma, a yadda naji mahaifiyarshi ta nema mishi matar shima beyi musu ba ya yarda, kuma a hakan ya_safiyya take cigaba da sonshi, its exactly 10years now, ten good years,,, atlast ta zama lawyer din dayake so saidai result dinta beyi ma abbah kyau ba, shi yaso da irin first class ta gama, hakan yasa basu wani dasawa da ita.. Sai ta biyu ya_Halisa, hmmmmmmmm Zee ta dubeshi jin yadda yaja ajiyar zuciya "Er gaban goshin Abbah kenan, fitinanniyar gidan, zee duk fitinar da nayi napila ce akan tata, ta gama gane Abbah, da ita kadai yake shawara, bata taba kawo mishi maganar aure ba har yanxu da take da shekaru 31, kullum boko boko boko, am ashamed to call her my sister wlh, bawai fa bokon takeyi ba, tana bada mutuncinta ne ga malamai dan su siya mata result, ga uban samari ga yawon jaraba, saidai shi abbah duk besan abubuwan datake ba tunda an kawo mai result me kyau ai shikkenan cikar burinshi, babu kuma wanda ta tsana a gidan nan sama dani, ji take dama a namiji tazo dan ta zama er gaban goshin Abbah sosai, To sai Aisha baiwar Allah, itama tayo halin ya_safiyya ne akwai kawaici, akwai haquri, irinsu ne ko yatsa ka saka musu a baki basu taunawa, auta hamra kuma footstep din ya_halisa tabi, dats in short kenan Now what i want to say here is dat, ni na sani babu ko tantama akwai saka hannun ya halisa cikin tura vedio dinnan, cos duk wani abunda nake a garin nan suna sane da takuna itada Abbah and babban burinsu shine su kawo karshen mu'amularmu, Gaban zee ya fadi idan akwai abinda take tsoro bayan mutuwarta yanxu bai wuce rabuwa da faruq ba Saidai na rigada na saka duk shirinsu a kwandan shara kema kuma ki manta dasu, ni faruq bazan yarda na rasaki ba, ke din Alkhairi na ce, all i want is ur good character ur behavior, a wife that will lead me to jannah and i found her in you"... Follow my page on wattpad @AyshabNasir Episode 30: our promise Mid semester break din wannan karan yapi wancan dadi dan gaba daya tare sukai spending ita da faruq din nata, ta'ba kid'i taba karatu haka suke abinsu, sun tsara ma kansu duk abubuwansu, Zee tana kwance tana imagining yadda rayuwarsu zata kasance da faruq, ace yau anyi bikinsu gata cikin gidan faruq, tayi dariya mara sauti ita kadai ke blushing abinta, Anty ta gama wankanta hakan yasa yaayaa ta tapi.. Sunyi resuming school, soyayyarsu bata hana su yin karatu saima citta datake karama karatun, lol. Yana zaune cikin motar yana jiran fitowarta daga masjid, ta fito tana tapiya a hankali har ta karaso gun motar ta bude ta shiga ta zauna, rufe kofar da zatai tayi er kara, "wayyo hannuna na" alamun murfin motar ya datse mata hannu, A sukwane ya zagayo yana 'barin jiki, subhanallahi nerh nerh kina kula dan Allah, har ya tsugunna ya kama yatsanta yana dubawa, sai ta fashe da dariya ta kwace hannunta, Ni sakeni yayi sororo yana kallanta, is dis a joke? Ya fada yana wani cin magani, Ta kifta idanunta, no its reality, ya miqe yana karkade rigarshi, Se kin biya kudin wankin kayan nan da kikasa na batasu da kasa, Haka ya ajiyeta sunata wasa da dariya abinsu, Zee tana sipping coffee dinta tana duba takardunta sitting comfortably, wayarta tai kara, duk a zatonta faruq ne harda dan yatsina fuska tana mita a ranta "shikkenan mutun baze barka kayi karatu ba, yanxu fa muka gama wayar nan" Amma data dauki wayar sai taga sa6anin haka, lamba ce sabuwa kuma bata kasar nan ba, kawai sai tinaninta ya kawo mata Anty safiyya ce, Ta dauka "Prof. J.B here, kamar saukar aradu haka taji gabanta ya buga, "I called to warn u girl,, kin hanashi karatu a school, im warning you, leave my son he will never marry u, hop im clear" ya datse wayar, tsit komi ya dauke mata na wasu seconds sai kuma tayi sighing heavily, Allahumma ajirni fiy museebatee, ta ajiye takardun dan karatun ma bazeyu ba, Xxxxx Yayi nodding cikeda frustration, wai me tsohon nan ke nupi dashi ne, he's interfering too much in my life, "Shikkenan ya_safiyya na gane don't worry" Kashegari as expected zee bataje school ba, batareda wani dogon tinani ba ya nupi gidansu, ya shiga yayi sallama da kanshi dan ko ya kirata ma yasan ba picking zatai ba... Tana zaune a falourn taji sallama a bakin kofa muryar kuma kamar ta faruq dinta, ta miqe tsaye tana sauke numfashi da daidaya, babu tsammani kawai ta ganshi cikin falourn, Faruq nan gidan matan aure ne fa, yace "nima auren nake nema" daidai nan kofar dakin Anty tafara kara alamun zata fito, da sauri ta jashi waje, zuwa baya, Meyasa zaka shigo baka nemi izini ba, Meyasa bazan shigo ba nanah, na kira kinqi picking, kuma kinqi zuwa school, kawai saboda prof. Ya kira ki, shikkenan se ki rabu dani?" Ta tsaya tana kallanshi da mamakin a ina yasan maganar kodayake ba abin mamaki bane tunda mahaifinshi ne, zama tayi a sanyaye shima ya rakata ta hanyar tsugunnawa a gabanta hannayenshi kan lamps dinta, ta ture hannayenshi, be musa ba ya janye su, pls nanah wannan ba wani issue bane da ze saka har kice zaki rabu dani ba, soyayyarmu tapi haka kwari, Taji idanunta sun kawo ruwa, "to ya kakeso nayi dear he personally called saying i should leave his son, his son will never marry me" Se taji hawayen sun zubo, "ni kaina my heart is aching" Ya sunkui da kanshi, "nanah i promise to marry u since from the first beginning... alkwarinmu yana nan" Ta gyada kai cikin rashin gamsuwa, "Ni ya fara kira tun ba yanxu ba, halisa already told him wai nayi budurwa a school, they re monitoring each and every move i make inside the school, he knows many people there, has so many agent that will keep updating him of every single move i make,,,, now look into my eyes nerhnerh" Batayi musu ba ta kalleshi kadan ta dauke fuska, hakan kuma baisa yaqi cigaba da fadin abinda ze fada ba "I promise to marry u nerhnerh, nine zan aure ki ba prof ba, im against anyone that will not approve of me marrying u" Ta miqe tsaye da sauri tana girgiza kai,hawaye suka zuba a fukarta "U cant go against ur dad bcos of me, i won't let u do so, hakan ma bame yuwuwa bane, ni kuma mene farincikina idan naga saboda ni ka tarwatsa familynka, mene farincikina idan saboda ni kayi aure kuma dukanmu bamusamu Albarkarshi ba" Kaje kawai kaje kabi umarninshi, tana kaiwa nan tayi hanyar da zata kaita falour, Da sauri ya cafko hannunta ya dawo da ita... Voice dinshi low yace "Baki isa ba, dubi idanunki sun karyata abinda labbanki ke fada, tayaya zaki yanke mana wannan danyan hukuncin bayan duka ni da ke munsan abu ne da bazeyu ba... Ta katse shi ta hanyar fadin "meyasa baze yu ba" Saboda nasan dukkanmu munason junanmu, we leaving this relationship now is something that's gonna be hard, haba mana zainab, ina mafarkanmu da mukeyi tare, ina alqawarirrika da zamu cikasu tare, ina mafarkinmu nason muga munyi aure mun zama mata da miji mun haifi namu zuri'ar danake muradin su taso da tarbiyya irin taki, itakuma soyayyar da ke ranmu muyi yaya da ita?" Think nerhnerh think" Sai yanxu ya sake mata hannunta kuma kukan nata ya karu dukda beda wani kara, shima be hanata ba, she feels she cant life without him, faruq ya zama jinin jikinta, amfaninshi tattare da ita har yapi amfanin Ruwa a jikin dan Adam, ashe So na iyayin zurfi har haka, she realize that now that she's thinking of loosing him, Shima a nashi bangaren kallonta kawai yake still bata dena kuka ba, and just like a gentle man, ya kara taku daya kusa da ita sosai, takwantar da kanta kan kirjinshi,, sanyin dadin turarukanshi, tareda shi kanshi daya mata rumfa yasata jin nutsuwa gamammiya tana sauka, take ta nemi kukan ta rasa, sai ajiyar zuciya take saukewa a lokaci guda kuma tana jin shima tashi saukar ajiyar zuciyar, bazasu iya kiyadde tsayin mintunan da suka dauka a haka ba, dan kanta kuma ta janye kanta ajikinshi a hankali ta daga idanunta ta dubeshi a tsanake, yana tsaye hannayenshi bunne cikin aljihun wandonshi har lokacin bai motsa ba, kuma yana kallanta, ta sauke nata idanun,saitin kunnenta yace "nerh nerh stop thinking of leaving me please" ta gyada kai kurun batace komai ba, ya lashi lips nashi sannan ya lumshe idanunshi ya bude, he believed true love does exist.... "Jeki gida ki huta nerh nerh, gobe zamuyi magana sosai kinji, inaso ki huta sosai" Ta gyada kai fuskarta babu annuri, yayi waving dinta itama tai waving dinshi, tana shiga falourn ta tadda Anty siyama zaune tana bama little saghir ruwa Har ta wuce taji tana cewa "baqo kikayi?" Zee tace eh, "meyasa baki ce mishi akwai mutane a gidan ba" Next time in shaa Allah, cewar zee din ta kuma wuce daki batada bukatar wata doguwar magana.. Kashegarin wannan rana kamar yadda suka shirya suka nemi guri suka zauna, "To muje magana" zee ta fada ganin beda niyyar cewa komai, ya dakko wayarshi yayi dialing numbers sannan ya saka a speaker, babu dadewa akai picking, Muryarta very clear with a fluent english with lil twist "Hloo Fuj" "Anty safiyya we together" ya fada in short, tace " okay yawwa, zainab hope u can understand my twisted english, zee tai murmushi tace "afternoon Anty safiyya" "Oh gosh u even knows its me before i introduced myself well not bad,, Fuj seems u said alot about me already, Now serious talk zainab, what i want to clarify here is, please don't make the mistake of breaking this relationship Faruq yana sonki sosai keda shi ku kasance tare through thick and thin, fight for your love, its worth it, so u wont regret later, hope im clear" Zainab ta gyada kai, a sanyaye tace "yes, thank you Da haka suka karkare wayar, Zee ta kalleshi, me kaje kace mata nayi? Abinda kikayi mana shi na fada mata kinyi, Ta marairaice fuska, kuma ai ni bance zan barka ba, im ready to fight the world for you, a hankali kalamanta suka juyo da attention dinshi gabadaya zuwa kanta, ya janye idanunshi daga kallon wayar ya maida kanta "Impressive, amma na dade banji kalamai da suka huda zuciyata ba kamar wadannan wow wow we surely will fight together" Tare suka ce "bazan barki/ka ba" sai yayi winking dinta, ta sunkui da kai tana blushing "Nana zainab dina muyi magana mana, inaso muyi planning future namu" Ta tattara nutsuwarta gareshi they all sound serious, "yanxu so nake na gabatar da kaina gurin Abbah_jabhir first, but before then mun tsara da Anty safiyya cewar zanyi ma momy magana, (wannan yayar Abbanshi datake Abuja) Zee tace eh nagane ai, "yawwa to ita zan fadawa nasan zatai supporting fully, kuma akwai manya da zasuyi ma Abbah magana, dan ita kanta baki ji fadan da takeyi ba kan Abbah ya tara 'ya'ya manya a gabanshi duka babu aure, hmm tana da fada fa, so in yaso idan muka gama school sai sauran shirye shirye ko?" Zee tai dariya cike da jin dadin kalamanshi, sannan ta dora nata "nidae dear nafiso koma me zamuyi ya zama da yardar Abbah ne, Yace karkiji komai nasan momy duka zatai min handling wannan, itama fa ya safiyya a lokacin batada wanda ze bata shawara ne, dan da ace momy ta sani da duk hakan baxe faru ba".... To Allah yayi mana jagora yace Amin Amaryata Fadi ra'ayinka/ki gameda wannan littapin Sharee Episode 31: surprise Kowanne dare yanxu ta rigada ta sadaukaar dashi ma faruq, mafarkinshi sun zama abin yinta, har ta dena damuwa, kuma tana tashi a bacci sakonshi ne keyi mata barka da safiya, ba karamin dadi anty hawwer taji ba jin komai yana tapiya daedae, Zee tayi ado cikin maroon gown wacce aka dinka da wanann yard da ake yayi wato scoober, flair gown cee amma tasha ado da flower, ta saka silver jelweries sai gyalenta shima maroon, kamshin perfumes dinta sunyi sanyi sosai, ta dauki waya ta kirashi dan yanxu ko be kirata ba ita ke kiranshi dan sabon da sukai batajin ta tabayinshi da wani mahaluki, she's very free and comfortable with him "Amincin Allah ya tabbata a gareki sarauniya mai mulkin zuciyar Umarul_Faruq" "Ameen Kaima Amincin ya tabbata ga wanda yayi nasarar tapiya da zuciyar wannan sarauniya mai tsada" Yace Amin, ai ba karamar sa'ar samun ta nayi ba, so wats up? Tace im set se tapiya, yace nima im set dear, hop bakiyi bacci dayawa ba kin tsaya yin boko, tace point of correction mun tsaya yin boko dai kuma mun raya daren mu wajen ambaton mahalicci" ya kara sautin dariyarshi, wannan haka yake To ki tabbatr kin dauki I.D card dinki base kinzo kina min kuka na dawo dake gida ki dauka ba" Tai dariya tunawa da tai sunyi hakan a wata exam da dan dadewa, Haka suka karkare wayar suna annashuwa, yau suka fara papers din nasu Kwanci tashi babu wuya, satinsu biyu suka ida duka exams din nasu Yau ce last papern su, ta fito a gajiye kamar ko yaushe dayansu yana jiran daya wanda ya riga gamawa, ta tadda shi yana jiranta ta karasaa tana mai murmushi, "Da alama yau paper tayi onga" tayi dariya, Ai kapi kowa sanin amsar tmbyr, "Wlh ai bazaaki gane ba, da ace bantsaya kin koyamin micturation reflex (Renal physiology) dinnan ba ai da ina ruwa tsundum" Sai yanxu tai dariya "Dama se da na fada maka DDW (daidai wajen, #only student can relate) ne amma kaqi yarda, shiyasa na saka dole ka iya shi tunda nima haka kakemin dole na iya wasu abubuwan dukda ma baka iya zaban DDW ba" Suka saka dariya, muje ki rakani unguwa to mana, Side look ta mishi "zuwa ina kenan?" Yace "abinci zaki rakani saya yunwa nakeji" tace okay muje gauro na" Yayi murmushi kawai dan yasan tsokana ce, suka wuce restuarant din, yayi musu ordern shinkafa da kaza, Kafin a kawo ordern yace "yanxu yaushe zaku wuce saudin?" Tace eh to se naji yadda Abbah_jabir yace tukunna shine ze bamu go a head" "This time around a ina zakai spending hutunka? Ko KT " "No zanje gurin momy ne zamuyi wannan maganar a Abuja zan zauna abina" tace "not bad" Daidai nan waiter din ya kawo abinci suka soma ci bayan sun kammala suka tapi, har gida ya kaita ..... Faruq ya rigasu tapiya Abuja gurin momy, kamar yadda suka tsara wannan karan da zakiyya zata tapi amma bazasu kare hutunsu duka a can ba zasu dawo saboda su Antyn zasu zo suma ganin familyn Abban nihal din, duk taje tayi ma su zeena sallama da matan Abbah jabir, ta kammala shirinta tsaf kuma koyaushe suna waya da faruq din da yanxu kwanakin shi biyar a Abj, sanda zasu tapi airport tana wayar dashi yace "Akwai news dear amma sai kin sauka" tace akan mene ne? Maganar mu ce, jiya nayi ma momy maganarki da plans dinmu sauran details kuma ba yanxu ba" Basu suka dena wayar ba har saida zasu shiga jirgi yayi mata addu'o'i sannan sukai sallama, sun sauka a birnin madina cikin koshin lpia, zakiyya se masha Allah take furtawa, sanda sanyin madina ya daketa, suna nan tsaye suna jiran d'an aiken da ze zo daukansu saboda uncle muzakkir yayi nisa se ya turo musu wani Dukda a taxi yazo zee bata kasa gane cewar shi aka aiko ba, saboda kamar da yakeyi da uncle muzakkir a fizge dan yapi uncle muzakkir tsayi kuma yapishi duhu, ya karaso gurinsu yana tapiya a nutse, zainab right? Ya fada yana kallan zakiyya dan bema kula da zee ba, zakiyya tace yeah ta dauka zolaya ce, "Yacemin ku biyu ne ina dayar?" Zakiyya ta kalli zee dake gefenta, ya danyi turning oh ashe gaki, so u re zakiyya den" zee tace yes, ta fada tana hade rai, zakiyya ce tace "how comes ka ganni ita kuma baka ganta ba alhalin muna tsaye tare" Ya dubesu duka su biyun duka gowns ne jikinsu daya is darker than the other Darker one din ta saka golden and blue ankara, wacce tapi hasken dukda ba hasken gareta ba, ta saka black abaya, "Maybe bcos she dress in black and she's black too" ya fada a zolayance dukda yasan she's not black as he said Zakiyya ta ce "i guess u re blind" Zee kuwa wannan karan murmushi kawai tayi mai suka shiga motar ya tayasu diban kaya, koda suka karasa diba ma shine ya karbi na zakiyya duka yace ze tayata shiga dasu itakuma ta taya zee, Anty hawwer na falour, nihal wacce ta soma tapiya lokacin ta taho da dan gudu gurin zee aikuwa ta dauketa ta jujjuya suna dariya, zakiyya ta karasa ta baje kan kujera wlh na gaji dayawa, Shima ya zauna amma ba kan kujerar da take ba, itakuma zee ta karasa kujerar da Anty hawwer take, "sannunku da zuwa, sannu mujaheed" ta fada tana kallan wanda ya rakosu, Zakiyya tace "anty hawwer wai kinji be gane zee ba dama be santa ba" "Eh shima wannan ne karanshi na farko a nan kuma basu taba haduwa ba," "Amma Anty hawwer ko kama ai ze gani" cewar zakiyya tana murguda mishi baki, Yayi dariya a ciki ciki kadan "na ganeku fa kawai inaso na tsokani sister inlaw ne", ya fada yana maida dubanshi kan zee Da murmushi dama a fuskarta ta miqe taja nihal daki tace "ni nayi nan", Har zee tai wanka ta sauya kaya ta kwanta bataga gilmawar zakiyya ba, mamaki duk yabi ya isheta suna can suna hira a haka bacci mai nauyi yayi gaba da ita," Dayake bayan zuhr ne sanda ta kwanta bata tashi ba sai la'asar, ta tadda zakiyya zaune a gaban dressing mirror da alama tayi wanka itama dan gashi ta chanja kaya, ga nihal a gefenta tana baccin itama, Tashi tayi tayi sallah sannan ta jawo wayarta a nan taci karo da missedcalls din faruq, tun da rana yake kiranta kusan 5 missedcalls, tayi dialing numbershi amma sai bata tapiya ta ajiye ta haqura Mujahid ya sakasu a gaba sai sunje masallaci sallar magriba, Anty hawwer tace "kaidai barrister baka gajiya da surutu wallahi, ka rabu dasu su huta tunda basu son zuwa" Zee tace "Au Anty barrister ne?" Zakiyya tace "eh mana" zee a mamakance take kallon zakiyya "Ke kuma yaushe kika san hakan" Zakiyya bata amsaa ba sai mujahid ne ya amsa da cewar "ba kin tapi baccinki dazu ba, mukuma nan muka sha hirar mu babu ke" zee tace yayi, Aikuwa se ga kiran sallah, yace to minti 2 kuje kuyo alwala" babu musu zakiyya ta miqe dan dama itakam tanason fita, zee ma ta tashi, Duk sukai Alwala suka dauki nihal itama, dukda babu nisa sosai amma sai suka taddashi a bakin mota yana jiransu, (motar uncle muzakkir ce yakan barta a gida idan school zeje cos basu da wani nisa sosai) Zee tace "ya mujahid a kafa zepi dadi" yace "salon mu rasa sallah ko"? Ya dubi zakiyya dake rike da nihal yace "mutuniyar zo ki shiga abinki", ya bude mata gidan gaba, zee ta tabe baki ta shiga baya "Ba mutuniyar ba aljanar ce".... Ta zaro wayarta ta sake dialing number faruq amma har lokacin bata tapiya, jikinta taji duk yayi sanyi, sukakarasa masallacin ya saukesu suka shiga bangaren mata ya zagaya bangaren maza, Bayan an idar da sallar, nihal taja hijabin jikin zee, tace "ya akayi" Cikin gurbatacciyar hausarta Tace "fitsari", suka kalli juna da zakiyya, tace muje nasan bandakin, Zakiyya ta shiga tareda nihal zee kuma ta tsaya jiransu a waje ta sunkui da kai tana dialing number faruq amma babu network gurin dan haka ta fita er harabar, ta dan daga kanta kenan ta shaqi wani kamshi da yake familiar, a take kuma kwakwalwarta ta sanar mata da waye, ta juyo a hanzarce.... Yana tsaye ya rungume hannayenshi ya jingina jikinshi da pillar cikin harabar masallacin datasha ado.. Ayi haquri da typos #not edited Episode 32: Madeena yayi winking dinta yana mai murmusawa a tausashe Jikinta ya dau bari ji take kamar taje ta rungumeshi, wani sonshi tkeji ana karamata buhu buhu, ta hanzarta sunkui da kai tana kallan katon hijab din dake jikinta har kasa, "God knows i love him" ta fadi hakan cikin ranta kirjinta na dagawa wanda beyi mata hakan sai sadda ta hadu da faruq, Tayi baya kadan da jingina da pillar din itama dan ji take bazata iya tsaiwa ita daya ba, Allah yasa ba mafarki nake ba ta ayyana ma kanta hakan a fili, Dagowa yyi daga jikin pillar ya soma takowa, bataso ta daga kai taa kalleshi the next second ta tsinci idanunta cikin nashi, haka har ya karaso hannayenshi birne cikin aljihun wandonshi, yauma whites dinne amma yard ne mai laushi da haske karrr Bai bari dayansu yayi magana ba yace "Assalamu alaik ya habibtee" ta kasa dena kallonshi kuma kirjinta ya kasa dena dagawa, Sun shude seconds a hakan kafin ta samu ta sauke idanunta zuwa kan bakaken takalmanshi da sukayiwa farar fatar kafarshi mai dauke da dogayen en yatsunshi kyau, A hankali ta bude bakinta tace "wa'alaikassalam warahmatullah" Ta fada murmushi na subuce mata, yayi dariya itakuma ta rufe bakinta da hannayenta "Ashe dai kaine" ta fada still tana dariya mai cike da annashuwa, Yana facing dinta a tsayen shima murmushin yake "ashe dai nine" ya kwaikwayi muryarta, takuwa kyalkyale da dariya.... Wayarta da take faman ringing ta katse musu jin dadi, Zakiyya ce ke kiranta "ya akayi?" "Kuje kawai ina tare da SHI" sai kuma ta sake dariya ta katse kiran, Su dinma jerawa sukai suka fita a masallacin, yace ta kaishi ya gaida Anty hawwer tace to Saukar yaushe?" Yace yanxu fa babu dadewa nace bari na tsaya nai sallah, ashe rabon naga tauraruwata ne, no wonder naji wani magnet na jana" Zee ta dubeshi ta dubi sorrounding dinsu, babu mutane sosai inda suke, gashi sama tayi kyau, Ji take kamar ta mutu dan dadi, ga ta ga faruq a birnin madina, no moment is will be greater saidai ko ranar bikinsu, Ya katse mata tunanin da fadin "tinanin me kikeyi? Ta tsugunna da sauri da wayyo kafata Shima ya tsugunno a hanzarce me ya sameta, sai ta daga kai ta dubeshi duka suna tsugunnen, a kasalance tace "so nake mu huta na gaji da tapiya", yayi smiling briefly sannan yace zo Ta kalleshi taga dai ai kusa suke Ina? Yace ba kin gaji ba? goya ki zanyi sai ta miqe da sauri wasa fa nake maka, ta fada a kunyace Haka suka jera har gidan Anty hawwer zee se wani shagwaba take mishi abin kuwa se birgeshi yake, Koda suka karasa sukai knocking a bude take suka shiga babu kowa a falourn sai ita daya, ya tsaya daga waje itakuma ta shiga harda dan gudunta, ta fada kan kujerar ta boye fuskarta cikin dankwalin anty hawwer tana dariya da tarin nishadi "Ke mene Haka" "Anty SHI NE" Tai tsaki kadan tana fizge dan kwalinta ni matsa in kin gama dariyar kya fadamin inda kika barosu barrister" Zee ta dago "au wai basu dawo ba" da mamaki Anty tace "to ba tare kuka fita dama ina zasu dawo kuwa" Zee ta fadawa Anty hawwer yadda sukai sannan ta dora da bata labarin zuwan faruq, "Kiji sakara dan Allah kuma kika barshi tsaye kikazo kinata babbakamin dariya" ta tashi tsaye Jeki ce mishi ya shigo, sannan ta wuce bedroom ta sako hijab, kafin ta dawo har ya shigo kuwa Anty da kanta tai serving dinshi da drinks, ya tsugunna har kasa kuwa ya gaidata dukkuwa da yasan ya girmeta amma ya tabbata ta bawa zee shekaru kusan 5 koma fiye, Bai wani dade ba urgent call din momy ya shigo a wayarshi ya dauka ya amsa with respect sosai sannan yayi musu sallama, zee ta rakashi a hanzarce ya fita da fadin ze dawo gobe in shaa Allah tunda yana gari,, bayan tapiyarshi kuwa ba kadan Anty ta dinga yabawa da hankalinshi ba, "Kai zee amma gayen nan ya samu tarbiyya massha Allah, ga yadda ya gaidani, ga yadda yake magana da tarin ilimi" Zee tai shiru kawai sai ta tsinci kanta da tunawa da rayuwar faruq, har yanxu batada tabbas ko ya dena shan sigarin ko be dena, amma tasan koda be dena ba to ya rage sosai, bata taba jin warinta a jikinshi, hakama bazaka taba kallanshi kace yanasha ko ya tabasha ba, jajayen labbanshi har wani spark suke badawa, a ranta tace A gida zee tai sallar isha'i sai after isha'i su zakiyya suka dawo, bayan anty ta gamawa zee mitar "ni dama tunda naga suna wani kirki nasan akwai wata a kasa tsakaninsu wato shine ya kwasshi mota suka kama hanya suka fice aikuwa bazan kirawo su ba in sun gadama karsu dawo ma" Da en ledoji suka dawo a hannu, zakiyya ta ajiyesu a falour sai wani annaashuwa takeyi, nihal kam tayi bacci, iya zee kadai suka tadda a falourn, ya mujahid ya wuce nashi dakin, zakiyya tace "zee zo kiga gowns din da yaya ya sai min Dayake zee mayyar gowns ce aikuwa se gata a gabansu ta dinga budawa tana nuna mata kala 4 ne sunsha adon stones kana gani kasan ba karamin uban kudade ya kashe ba, sai guda daya ta zee din, sak kalar fatar zee golden brown, zee tasa ihu, tana karawa a jikinta tana kalla a mirror din dake dining area, wayyo Allah gobe ita zan saka idan zamu hadu da SHI, Haka suka gama santin gowns itama Anty hawwer tazo ta gaggani ta saka albarka, harda su chocolate da shawarma ya siyo, dasu sukai dinner ranar Tun tapiyar faruq jiyaa basui waya ba ya barta da tarin kewarshi dan ko ta kirashi ma be shiga, hakan yasa yau duk ranta babu dadi tunda ta tashi, Ko da wasa ko kadan bataso taga sunyi nisa itada faruq, ya zama jini da tsokarta, cewar tana sonshi ma ya zama bata furuci, a gaban kowama bazataji kunyar cewar tana sonshi ba,, a haka ta cinye ranar lugus da ita, duk zakwadi da burin su hadu din kuwa ya tashi a babu ta dauki gown din ta maida wardrobe, daga ance za'aje sallah kuwa zata riga kowa yin alwala, amma haka har isha'i, Kawai sai ta samu kanta da shiga toilet ta zauna a seat din toilet din tana dialing numbershi tana kuka, basu fasa ce mata wayar a kashe ba itama bata fasa kirannashi ba, daga karshe ta rungume wayar ta saka mudubi a gaba tana kallon kanta tana zubda hawaye, kanta har wani sarawa yake, Zuuu wayar ta dau vibration, next second fuskarta tai displaying wide grin, sakamakon idonta da suka sauka kan sunan dear calling, kamar ba ita ce ke kuka ba Tai picking wayar amma ta tsinci kanta da kasa cewa komai, yau baiyi sallamar ba "Nerh nerh shine furucinshi na farko" Ta sauke numfashi can ciki kuma tace na'am Yace im so sorry kinji" Tace me kayi kke bada haquri?, yace "jiya kinsan muna tare momy ta kirani so dama batasan na bar kasar ba, nd she call me back urgently, so im back to 9ja" Ta gyada kai ita daya, tace okay lets chat yace okay kawai... saboda cost din kudin Ta chat yake sanar da ita kamar haka "So i was supposed to update you today kan maganr mu danacee miki akwai labari" Sorry its short Sharee Episode 33: Challenge II "Tace eh" "To munyi magana da momy tun sanda nace miki zan fada mata, and her respond was superb baby" Zee tai juyi kan gadon cike da jin dadi, "yace ta goyi bayana 100% kuma zata saka ayi bincike a kanki tace "indai abinda na fada akanki hakane to kar mu damu duka zata fadawa dady na" Shine jiyan ta sameshi da maganar ta phone tace mishi ina gama makaranta aure zatamin ko yanaso ko beso, so ranshi ya baci yayi ta fadaa sosai daga karshe ya kashe wayar, Daga baya kuma ya kirata yace "ta fadamin ya yarda in na gama school nayi aure amma da sharadi daya" kuma sharadin shine, se munje anyi genotype nidake, im pretty sure he knows my genotype and i know mine too" Da sauri zee tai typing "Wats ur genotype?" Yace "AS" So it all depend on urs now, Tace " i dont know mine dear buh im pretty sure im not AS" Duka sukai shiru for some seconds kamin yace "okay don't worry in kin dawo din zamuga yadda zamuyi" tace to Bata sanarwa da ko Anty hawwer abinda suke ciki ba, faruq a nashi bangaren ya gyara kwanciyarshi baayan kammala hirar su, a hankali memorynshi ya tapi kan asalin maganar sai yaji tmkar yanxu ne momy ke sanar dashi "Sharudanshi guda biyu ne faruq, na farko shine zakuyi genotype dakai da ita dan already yasan naka so indae ita ba AS bace shikkenan yace ya yarda... Sharadi kuma na biyu shine saidai idan zaka hada ta itada Hamra ka aura, yace ya rigada yayiwa kanshi alqawari tun a baya ita ze aura maka saboda maraicinta,.... Yaji wani abu mai karfi ya tokare mishi makogwaro, "its impossible, never possible, babu wata hamrah daze aura ma kawai zeyi kamar ya yadda ne rigimar tsohon nan tapi karfinshi" (ni Aysha b nace anya Zaka iya yiwa dady wayo kuwa) abu kamar wasa soyayya tsakanin zakiyya da barr. Tayi karfi gwanin ban sha'awa kowannensu burinshi ya farantawa dan uwanshi, tun suna boyewa ma har suka dena dan an rigada an gano su, sai zee taji inama ita da faruq ne cikin gida daya wayyo da an buga soyayya kuwa, Wannan karan dama ba dadewa zasuyi ba, dan haka kafin su wuce 9ja suka biya makkah gabadayansu sukayi umarah sannan suka dawo gida 9ja, tun daga airport gidan Anty suka wuce dukkansu, yayi kura babu laipi to dayake sunada yawa sukai ta aiki, shikuma uncle muzakkir ya fita neman abinda babu, ya siyo bayan sun kammala kowannensu yayi wanka sukaci abinci suka huta, a daren ranar uncle muzakkir ya daukesu duka sukaje gaida hajiyarshi, Danginshi suna son Anty hawwer, itama sosai tayi ma kannenshi mata guda biyu tsaraba, hakama hajiyarshi dayake shine ke kulawa da qannenshi tun bayan rasuwar mahaifinsu, har shi kanshi barr. Ma da taimakon uncle muzakkir yayi karatu mai zurfi har haka kuma yake aikinshi a kano yanxu ma hutu ya dan dauka yaje can gurinsu Anty hawwern, se kuwa ya hadu da zakiyya dama hajiyarshi ta matsa mishi da maganar aure, su zakiyya se wani sunne kai take, wai ita anzo gidan surukai Se kusan 10 suka bar gidan suka bar barr. Tunda dama nan yake zama da cewar gobe zasu dawo, Kashegari kuwa tun bayan tashinsu da safe suka ida komai suka kama hanya gidan Abbah jabir, suka kai tsaraba a can suka bar zakiyya, sannan gidan Anty siyama itama suka kai ma little saghir tashi da tata tsarabar, a can suka tadda minnatullahi itama ta dawo kasar ta gama karatunta na medicine a U.S tana cukucukun service shine ta dawo gidan Anty, zee bata zauna ba tabi Anty hawwer gidan hajiyar uncle A can suka yini ranar, har zee ta fara sabawa da su bahijja da badi'a (qannen uncle muzakkir) Nihal kam gabadaya gidan ma ta koma, hajiya tace su bar mata ita tunda ba yanxu zasu koma saudi ba, Zee babu kunya taqi komawa gidan Anty siyama tana gidan Anty hawwer abinta Kwana biyu bayan nan, su biyu ne kawai cikin gidan tunda nihal tana gurin hajiya uncle ma ya fita Zee tana zaune basu dade da gama waya da faruq ba, duk ta gaji da zaman gidan sai yanxu ta gane irin shaquwar da sukai da zakiyya da ko hira ce tana nan tana yi mata ko mitar wani abun Sallama taji ta amsa tana miqewa jin kamar muryar zakiyya aikuwa se gasu su uku da kubra da khairi da ita, Nan fa aka dinga murnar ganin juna, suka baje hira har suka tada Anty dake bacci itama ta fito suka gaisa Zakiyya harda jakar kayanta, aikuwa zee ji tai kamar ta hadiyeta dan dadi, Anan suka yini khairi da kubra suka tapi suka bar zakiyya, "Zakiyya tace "haba inaaa zee ai yanxu bazan iya zaman gidan nan ba shiyasa na gudo wlh ni yanxu ai na saba dake" suna cikin hira yayo sallama Zee ta kalli zakiyya da tuhuma "Kodai bazaki iya zama babu shi ba, kin saba dashi" zakiyya ta dauke kai oho dai.... Wannan time din zee tare da faruq sukai karatun semester me zuwa ta level 3 yayinda zakiyya kuma zata shiga level 2 Result na wancan semester din shima ya fito, zee da faruq sunyi wuta shi 4.4 itakuma 4points dot, Sai bayan sunyi registration sannan Anty hawwer da uncle suka koma suma su zee suka koma gidan Anty siyama, ta tarbe su sosai kuwa dan tayi missing dinsu, ta gane amfaninsu sosai sanda basa nan, Zee da faruq sun shirya kan ranar laraba zasuje ayima zee test din dan sanin genotype dinta, momy da kanta ta hadasu da wani doctor ma ba lab attendant ba, a bisa umarnin dady din Suna zaune jigum suna jiran result tabbas idan aka auna bp dinsu a lokacin ya hau, Sun dan sha zama danma sune sunsan doctor din da saidai suje su dawo, aka miqo result din faruq ya karba sukai musabiha da doctorn, Sai da suka shiga mota sannan faruq ya soma budewa, zee tai jigum tana kallanshi, har dauke numfashi tayi sanda ya bude gabadaya AS pattern shine abin da ya bayyana... Ya ajiye yana mai dora kanshi kan sitiyarin, Zee tasa hannu ta dau takardar hannunta na karkarwa "How comes AS" bata ta6ayin genotype ba amma babu AS a gidansu tasan both Amminta da Anty hawwer AA ne Abbanta ne dai bata sani ba tadai san ba SS bane Hawaye yabi kuncinta murya a raunane tace "shikkenan karshen alaqarmu tazo?, itama momy bazata yarda ba, Abbah ma baze ta6a yarda ba,, luck is not on our side" Ta fashe da kuka "Only if they knows" ta dago tana maimaita furucinshi kan labba, only if they knows, they will for sure mana faruq, doctor ya sani kuma ze fadawa momy" "Ko duk duniya zasu hadu babu wanda ya isa hanani aurenki balle wannan takardar" ba zato ya kunna motar yaja a guje, sautin mumfashinsu ne kadai ke tashi har ya isa kofar gidan ya ajiyeta, saidai batakoyi yinkurin fita a motar ba shima baice mata fita ba Sun shafe mintina goma a haka sannan ya dago ya zuba idanunshi a kanta, Itama ta dubeshi a raunane, gabadaya ya sauya, idanunshi sun zama abin tsoro har wani red suke badawa da orange dan huci, kan hancinshi da kunci da labbanshi ma sunyi orange orange, ta sunkui da kanta hawaye ya digo mata "Nasani ko nawa en uwan idan suka san result din nan bazasu bar wannan alaqar tamu ba, yanxu an waye se da genotype kafin ayi aure a mafi yawan lokuta..." Ya katseta "Me kike nupi nerhnerh? Ki dubi tsabar idona kice zaki rabu dani, Ta shiga girgiza kanta, Wannan kuma nayi karya Yadda nakejin zuciyata namin zafi watakil ko rabin haka bakiji, bazan rabu dake ba, ni ne mijinki, ina qaunarki ina sonki nerh nerh, jeki gida Kmaar an hankada ta Ta bude kofar da sauri ta fice taja ta tsaya har ya bar gurin sannan ta goge hawayenta ta shiga gidan Kusan sati biyu bayan nan bata sakejin wani maganar genotype daga bakin faruq ba, harkokinsu kawai sukeyi, itama kuma bata ko tmbyeshi ba, da kanshi yazo ya sanar mata "Nerh nerh dady ya amince da auren mu, ya yarda muyi aure in muka kammala karatu" Da rashin fahimta ta kalleshi, irin suspicious look dinnan, like mganar daya fada gaibu ce Sai ta dauke kanta ta cigaba da danna wayarta, dayake kan kujeru suke a sararin school din, ya tsugunno gabanta yana kallanta, "Nerh nerh pls say something" ta miqe tsaye kawai, shima ya miqe da sauri, "Me kake shirinyi ne?, me kaje ka shirya ka fada musu? Domin dani da kai duka mun sani ko momy ko dady bazasu goyi bayan wannan auren ba" Ya saka hanky ya goge gumin dake tsattsafowa a goshinshi dukda iskar dake kadawa a gurin, "Tsorona Allah tsorona karki ce zaki barni, my life will be empty, pls zee wannan ba wani abu bane da har ze saka mu sadaukar da soyayyar da muka gina da kyakkyawar niyya" A hankali ta koma ta zauna ta tallafi chin dinta da dukkan hannayenta, Ta girgiza kai "ya akayi soyayya ta rufe maka ido har haka FUJ?, sukuma yaranmu fa? Se muna sara muna duban bakin gatari fa" Be zauna ba yana tsayen "wai meyasa bazaki gane irin son da nake miki ba, meyasa bazaki gane irin loneliness din danake ciki ba kafin shigowarki rayuwata,, haduwar mu ta samamin abubuwa da dama dana rasa, zainab kin cike min gurabe dayawa a rayuwata, kin haska rayuwata, wallahi ke alheri ce a rayuwata, na rasa ummee na bana so na rasaki pls zainab" Ya karasa yana mai zaunawa a sanyaye Ta dubeshi "she feels for him, yes she love him, itama kanta datake maganar batajin zata iya rabuwa dashi din" Har kin manta sanda kika ce min u're ready to fight the world for me, ko kuma dama duka zance ne? A sanyaye tace "ko kadan kalamai na ba iya labba suka tsaya ba har zuwa jini da tsoka zuciya da ruhi tareda ilahirin jikina" ta hadiyi yawu mai daci "now tell me, me kacewa su momy da har dadyn ku ya yarda?" Dont forget to follow my wattpad page, comment and share @AyshabNasir 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 34: For how long Yace "i just bribed the doctor not to reveal the real result to them, and he agreed" yayi pausing da rashin son karasa fadin abinda ya soma tace "So u lied fuj? U lied to them? And whose idea was that?" Ya shafa kanshi "Anty safiyya" Sai kuma ya kalleta da kyau, "hav faith in our love zainab, stop worrying about the future, its all in the hands of the Almighty, we shall continue praying for the best and i hope u re my best, i know u re" Komai ya cigaba da tafiya watarana farinciki watarana kuma akasin hakan kwana a tashi babu wuya ga mai rai da lpia, su zainab suka kammala jarabawar first semester na level 3, babu abinda yaa ragu a soyayyarsu sai ma shaquwa mai karfi dake kara danko tsakaninsu Yau sukai last paper ya kaita har gida sannan ya dakko abinda ya saka a mota a back seat, ya miqa mata ki rike da kyau kuma se kinje daki zaki bude, my regards to zakiyya and Anty" Tace okay bye take care and thank you, Sukai waving juna ya tapi, haka ta dauki katon abin datake kyautata zaton frame ne ta wuce dashi har daki kuwa, dayake su zakiyya sun gama exams dinsu tun last three days da suka wuce ta tadda ta a dakin, Zee ta shimfide shi a kan gadon ta soma kiciniyar budewa da zumudin son sanin menene, Daidai sanda ta karasa unwrapping, hoton data gani a gidan faruq ya bayyana a fuskarta, amma wancan half done ne wannan kuwa cikakke ne ya kammala zana ta zane mai kyau so smooth fully blended, zakiyya ta karaso tana karewa zanen kallo Muryar zakiyya ce ta dawo da zee daga duniyar tinanin data tapi, Wow amma wannan F.U.J dinnan sun iya zane, ya akayi suka zanaki? Zee tace "uhm, ehhh, sun iya sosai wlh, nima faruq ne ya bani as a gift," Daidai nan waayar faruq ta shigo, zakiyya tace "oh dan halak yaqi ambato, zee ta dauka tana kara kallan zanen zakiyya kuma ta fice a dakin "So how do u like it my dear" Tayi smiling, "i dont just like it, im so much inlove with it" Tohm so nake ki bani dama kiyi placing dinshi cikin dakinki a saman bed ko a side, yadda duk sanda kika gifta zaki ganshi, Tace wannan ai abu ne mai sauki, "Tunda kin manta ni bari nayi reminding naki, "its our anniversary gift, look closely at the frame, akwai rubutu a jiki, i love you nerh nerh" Se yanxu ta tuna today 10th june is exactly their anniversary, Gosh Taa rike goshi, bayan sun gama wayan da faruq ta zuba ma frame din ido, yes akwai rubutu kam dagaske written in a golden shinning colour amma se mutun ya zuba ido ze gano shi a gefe yake kasa, "It's exactly 10th of june, its exactly the day i met the only person in the world that I want beside me every day and every night for the rest my life. Having you by my side makes me the happiest, most grateful and luckiest person in the world. Here is my vow to you, i vow to be with you until the end of forever.... Happy anniversary soul mate Gurin "i vow to be with you until the end of forever" sai yayi bold kuma yafi fitowa akan sauran rubutun, ba karamin nishadi kalamnshi suka saka ta ba, ba kankanuwar kwanciyar hankali da nutsuwa suka kara mata akan relationship dinta da faruq din ba, Watanni hudu suka shude bayan nan, hakama rayuwar na cigaba da garawa, sun kammala level 3 successfully hakama zakiyya ta kammala level 2, kubrah da usama sun gama college dinsu, khairi kuma itama level 4 zata shiga yanxu A wannan semestern data kare babu wani abun daga hankali daya faru se wata jarabawa da sukai ta human genetics, a ranar ba guri daya suka zauna ba, cos faruq yazo late time din har an fara ma, ya zauna daga baya, wani dan P.G aka barwa yayi supervising nasu sukuwa dalibai da sukaga sun sami salala sai akaita bude waya kuma mostly en baya ne keyi inda faruq yake, en gaba ma basu san wainar da ake toyawa b, se bayan sun gama ne faruq ke bawa zee lbarin abinda ya faru a exam hall din taita mamaki, ai bakiga yadda suka dinga fidda waya naked bama da kinsha mamaki, yanxu karatu duk ya baci, yai ta mata mita.... maneman su kubrah sun nemi gaanin Abbah jabir tun kwanaki, se Abbah jabir din ya saka rana zuwa ending september in shaa Allah ze zo gida dan yana saka ran an kusa mishi transfer zuwa guri kusa, to shima faruq se yace in Abban yazo zeje ya gabatar da kanshi Anty shirye shirye take sosai na tarban Abban dan gidanta ze sauka saboda ita keda girki a wannna lokacin, tareda maman su khairi ya dawo ya fara sauka wancan gidan sannan ya dawo gidan ta, minnatullahi bata gidan a lokacin taje Abuja gidan yayansu, dama service din nata suna ne kawai, tunda harkar nigeria a saki kudi ne kawai a wuce gurin Rana daban daban ya basu, iyayen Bashir (meson kubra) su suka fara zuwa, sun yi magana sosai dan har da niyyar kawo kudi ma sukazo amma abbah yace su bashi wata daya zeyi bincike ya kuma sanar da en uwa, sai na khairi (Bukar) shima same Abbah ya sanar dasu dan duka a shirye suke dama, sai kuma ya mujahid (na zakiyya qanin uncle muzakkir), shima Abbah ya fada mishi hakan dukda yasan ta bangarenshi ba wani matsala tunda yasan en gidansu tun kan uncle muzakkir, Faruq ne yazo a karshe saidai shi nashi ba kamar na sauran ba, ya sanar da Abbah shi ba da wurwuri yakeso ba dan be kammala shiryawa ba, se sun gama karatu tukunna, shima Abbah yacemishi ba matsala zeyi bincike kanshi, Zee tai shiruuu tana tunani Tunda faruq ya sanar mata Abbah yace zeyi bincike taji jikinta yayi sanyi, indae kuwa za'ayi bincike kan faruq da prof. to akwai matsala tattare da gidan nan... Wata daya bayan nan, Abbah yayi bincike kan maneman, komai na biki ya cigaba da tafiya aka saka bikin kubrah da khairi da zakiyya, duka rana daya za'a daura auren on may na sabuwar shekara me kamawa, Kafin Abbah ya koma ya samu transfer din kuwa amma zuwa kaduna ne hakan yayi ma kowa dadi dan ko ba komai yapi kusa, Komai na tafiya kaamar flash lokacci babu wuya a gurin Allah, level 4 first semester tayi musu sauqi sosai, dan courses sun ragu duk kamar karashe ne, ba kullum ma suke shiga school din ba, Sukayi duk jarabawarsu suka kare, shagulgulan bikin su kubrah aketa faman shiri, Sunyi kamu kawai sannan aka daura aure, kubra a nan kano zata zauna, zakiyya ma haka, khairi ce dai aka kaita katsina, Zakiyya aka fara kaiwa tunda itace karama, sannan daga baya akayi asubanci aka kai khairi, sai kuma kubrah itama Tun da suka dauki hanyar katsina kai khairi, zee taji gabanta nata faduwa, bata samu damar kiranshi ba har suka dawo, suna dawowa ma kubrah suka tapi kaiwa, zee tai jigun tana lissafa tun ranar kamu dayazo yace mata bejin dadi ya tapi be dawo ran daurin aure ba, ta kirashi sau daya wayarshi a kashe, bata samu lokaci ba suka kai zakiyya sai khairi yanxu gashi sun kai kubra, Ta jawo wayarta ta danna lambobinshi, tayi ringing ta katse no answer ta kuma dialing tai ringing ta kusa katsewa sannan ya dauka, da wata murya da batasan faruq da ita ba yace zee, shima kamar da kyar ya fada, tana dai jin numfarfashi sama sama, sai kuma wayar ta katse, ta miqe a zabure Innalillahi faruq mene ya sameka, sai tai realizing a gda tke ta yi kokarin calming kanta, sannan ta dauki gyalen dake kan gadon ta dau wata 500 ta fita da sauri dan nutsuwar ma taki zuwa, batasan sadda ta fara hawaye ba, ta saka gyale tana gogewa amma yaqi goguwa, dan tana gogewa wani na fitowa Ta dau napep ta fadamishi inda zai kaita, ta zabga tagumi tana hawaye "ashe ni ina can ina shan shagalin biki shi yana nan wayasan ma mene ya sameshi" haka suka karasa tana ta bama kanta laipi, ta sallami mai napep and without thinking twice ta danna kai cikin gidan, bata tsaya ko ina ba sai bakin apartment dinshi, ta tura kofar Silent taji dakin, falourn very neat komai a tsaftace, ta subale takalmanta harda er sassarfa ta wuce bedroom dinshi, yana kwance marabarshi da gaawa kadan ne, ta rike bakinta saboda kada kukan ya fito, Ta karasa bakin gadon da sauri ta zauna tana kallanshi, idanunshi a lumshe suke ya budesu a hankali yana kallanta, Ya kara haske akan wanda tasanshi, labbanshi sun bushe fuskarshi ta rame, idanunshi sunyi ciki kamar wanda yayi jinya ta watanni, Muryarshi ce ta ja hankalinta Ta dan kara tauri da karfi yace "taimakamin na zauna, batayi wani tunani ba ta riko kafadarshi kusan gabadayanshi a kirjinta yake, ta taimaka mishi ya zauna sannan itama ta zauna gefenshi, tari ne ya rikeshi, wanda har saida idonshi ya fidda ruwa sannan ya sauka Itama taji nata idon ya kawo ruwa amma ta hadiye kukanta, kai kana kallan faruq zakasan yana jin jiki, Da muryar tashi da ta sake rashin dadi yace "nerh nerh ya gida? Ya hiddima?" Ta gyada mishi kai kurun Mene ya sameka? Kuma bazaka iya kirana ba, kaje asibiti?" Ya lumshe ido tarin ya sake yi sannan yace "mura ce kawai sai ciwon kai, na kira wannan doctorn na momy yazo ya dubani har ya bani magunguna kuma masu aikina na kulawa dani ba wani abin damuwa" A kufule ta dubeshi "har ni zaka cema babu wani abin damuwa" Yayi shiru yana kallanta a kasalance bece komai ba, sannan yace ki jirani a falour zan shiga bandaki Tace to, ya miqe dakyar kamar iska zata kadeshi ya fadi, jallabiya ce jikinshi, sai lokacin ta lura ramar ma har jikinshi ne, Ganin yana tangadi kamar dan maye, yasa ta zuba mishi ido cikin tausayawa, kasa yayi luuuu Saukinta a tsaye take ta tafi da sauri ta riko kugunshi Dukansu sai suka zube a kasa, gyalen nata ma ya riga yayi nashi guri, numfashinshi takeji gaba dayaa fuskarta da kirjinta shine yayi saurin tashi a kanta sannan itama ta miqe, im... Im sorry Ya fada tace "are u sure u can manage, ya lumshe ido i will Sai wajen la'asar ta tafi tayi mishi girkin rana, first time daya ci girkin zee a nan ya banbance me ake nupi da girki me dadi, dukda beda lpia amma yaci abincin dayawa, sai ta gane rashin lpiar nashi harda loneliness ma, rashin samun wanda zeyi hira dashi, wanda ze tsaya ya kula dashi ya bashi abinci, Saida tamishi girkin dare kapin ta tafi, Ya tsaya jikin curtains din yana hangota har ta fita sannan ya dawo ya zauna, Hawaye ya biyo kuncinshi "how would she feels in ta gane asalin abinda ke damun faruq dinta? Wanann shine Abu kwalli daya daya boye mata tun ba yanxu ba kuma har a yanxu bejin ze iya fada mata shi, Devastated, heartbroken, heartache wadannan duk sunyi kadan su fassara azabar da zatajii a kokon ranta, radadin da zataji a fatar jikin, da kuma zafin da zataji cikin nama da kashi da bargon jikinta, For how long zan iya keeping wannan secret din daga gareta?....... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 35: Heartbreak A week after Komai na tapiya normal, saura sati daya hutunsu na first semester ya kare su koma second semester, wanann lokacin ma kamar kowanne lokacin suna ta6a karatun next semester danma babu wasu course project ne ma me dan wahalar kuma already sunyi proposing topics anyi approving sunma fara chapter 1, jikin faruq yayi sauki tari ne kawai har yanxu akwai saura da er rama amma bame yawa ba, Zee takan ziyarci gidan zakiyya lokaci zuwa lokaci, Next month zasuyi anniversary dan haka wannan karan zee ta shirya suprise ma faruq A haka suka koma school suna ta kaaratunsu da project abinsu dan kusan course dinma duk sunyi covering, zeena ma an fara maganar bikinta da Imran, to nata course din dayake 5years ne yasa suka tsaya kan idan ta gama level 4 za'ai bikin se ta karasa final year a gidanshi Ranar laraba ana gobe anniversary dinsu, Anty ta hana zee zuwa school da cewar ta taimaka mata da girkuna zatai baki, zee bata damu ba tace to tunda itama bason zuwa school din take ba sakamakon suprise din datake shiryawa goben, Sun sha ayyuka da kusan duka zee ce karfin aikin, tayi abincikan masu dadi da kamshi, Tana daki ta fito a wanka suna waya da faruq guraren karfe 4 taji sallamar su a falour, dama taji tsaiwar motocinsu, Ta cigaba da shan soyayyarta, saida suka gama wayar ta nemi kayanta ta saka atampa ce brown da pink ta kashe daurinta na zahra buhari Anty ce tayi kiranta ta amsa, Mutun uku ne da yara biyu, Wadanda ke facing dinta sanda ta fito ta gani alamu mata da miji ne manya, sai mace daya da bataga fuskarta ba sai gashin kanta kasancewar ta juya mata baya, Saida tazo inda zata gansu duka ta gane ai minnatullahi ce, zee ta gaidasu duka Anty tace "wannan shine babban yayanmu wanda ke abuja" zee ta sake kallanshi babba ne kam dan akalla ze haura 40, se matarshi Ta sake gaidasu sannan ta gabatar musu da abincin da ruwa ta koma daki, Sai bayan isha'i suka tapi suka bar minnatullahi, a daren wata mata itama tazo gidan da wasu kayayyakinta Jin anata amarya amarya yasa zee gane cewar bikin minnatullahi za'ayi Aikuwa tana shiga daki ta tadda zakiyya nata kwala mata kira, ta dauka "Ina kika shiga ne haka labari mai zafi na neman hucewa" "Fadamin mene ne ya faru?" Ki bari gobe kizo gidana kawai musha labarin, zee tai jimm eh to gobene anniversary dinmu kuma akwai shirye shiryen danake but still i will squeeze tunda kece"... Da en kudaden da suke hannunta ta shirya musu candle light dinner, taje tayi booking sannan ta kirashi tace mishi by 6 yazo tana jiranshi yace okay, sannan yace "Nima level coordinator ne yake nemana yanxu xan shirya naje befre the time Tace okay to seka dawo daga nan ta wuce gidan zakiyya, Bayan sunyi settling take ce mata "kinsan wani babban business tycoon a kasar nan ummm" tai shiru tanaa kokarin tuno sunanshi yawwa "yusuf Abubakar As-siddique" zainab itama ta shiga nazari ta tabajin name din amma a inaa, zakiyya ta katse nazarin nata ta hanyar nuna mata hotonshi a wayarta kinganshi "Yes yanxu ta tuna shine bakon uncle muzakkir zuwanta saudiyya na farko da Anty hawwer tace yayi satar hanya, Ta gyada kai "yes yes na sanshi" yawwa To in gaya miki shine wai zai auri minnatullahi" zee ta wara idanu wai dama beda aure? Zeyi 30 fa koma fiye, kuma ina ya ganta yace yaanaso kodaayake ai kina ganinta kinsan dole se gidan hutu gidan nera" Zakiyya ta dora "ai bikin ma hadi ne amma fa ance yana sonta yaga kyakkyawa duk ya rikice, a yadda naji fa kenan nima ya kubra ke bani lbari, to shine bikinsu yanxu next month ne,... Zee ta katseta "ai ta dawo nan naga har an fara mata gyaran jiki ni gani nake ma cigaba ne dan yadda fatarta ke wani shining" Ahh kekuwaa ai dole gidan As_siddique fa zata shiga, hmm za'asha shagali ai ni dai Allah yasa su gayyaceni" Zee tace "Allah ya sanya alkhairi" Ai da can ya aka kare gani take tapi kowa balle yanxu kuma ai gani zatai mu ko darajar kiyashi ma bamu kai ba, cewar zakiyya Itadai zee bata kuma tofawa ba... Karfe 6 harda rabi kamin zee ta kammala shiryawa, tasan ma faruq har se ya rigata zuwa, tayi kwalliyar ta da wani less purple and pink da ratsin black ash, kamshi ne kawai ke fita a jikinta, se fatarta dake bada wani unique shine, ta 'kagu taga faruq dinta suyi spending quality time Har ta karasa bata kirashi ba shima bataga shigowar nashi kiran a wayarta ba, Bisa ga mamkinta ko a kofar gurin bataga motarshi ba, "ashe dai makarar ba tawa bace ni kadai" ta je ga special table dinsu da tai reserving yasha kwalliya cikin wani grass isolated place ta zauna tana dialing number dinshi amma to her suprise taji ta a kashe, at once duka smile din dake face dinta yayi vanishing, Ta zauna tana kallon hanyar shigowa gurin after like 15 minutes ta kuma daukan wayarta tai dialing still suka sanar da ita a kashe, ta kalli kanta ta kuma kalli hanyar shigowa, she just hope faruq will show amma inaa Tun tana hoping har ta fidda rae and it was all dark, garin ya sake duhu tana nan zaune aka ida sallar isha'i har wasu mintuanan na shudewa buh all she's doing is looking at the way, A hankali taji takunshi ta kuma zuba mishi ido dayake duhu keda hanyar shigowar bataga fuskarshi ba sanda haske ya dan haska shi kuma sai ta gane ma'aikatan gurin ne, yazo yake cema lokacin da tai reserving ya kare, kamar an fizgeta daga kujerar datake ta son tashi tun dazun ta miqe ta karasa cikon payment dinta dukkuwa da bata taba abincin da sukai serving ba, Ta fita daga gurin, Gefen titin ta soma bi a hankali tana tapiya hawaye yana zubowa kan kuncinta lokaci lokaci tana ajiyar zuciya har ta karasa gida ,, she just hope yana lpia, duk disappointment din be dameta ba kamar yadda tunanin mene ya faru dashi, Ko dinner batai ba ranar tai sallah ta kwanta amma bacci yayiwa idanunta qaura, ta ajiye wayar cikin gajiyawa, meyasa faruq ze na yi mata haka, meyasa ko abu ze faru be tashi faruwa se yau" sune tunanin datake ta ayyanawa cikin ranta, Ta janyo wayar tana dubawa through contacts dinta, a hankali tayi scrolling baya, ganin lambar datake nema ta bayyana a idanunta, Tayi dialing jiki a sanyaye, bata da wani option daya wuce ta kira sarah, ita ce kadae zata iya sanar da ita halin da faruq yake indae yana gida, tun ranar da sarah ta karbi numbern ta, tayi mata magana ta watsapp, kuma sukan gaisa lokaci lokaci, amma basu taba waya ba Ringing ta dade tanayi sai daf da zata tsinke ta dauka, Hello ant. Zee" saran ta fada zee ta dan yi gyaran murya tana duban agogo jin muryar saran kamar bacci takeyi, karfe 12 ne na dare, sai taji dama bata kira ba, hello, sarah ta sake maimaitawa, oh hello sarah, ya kike? Dafatan kina lpia Lpia qalau, ya gida, zee ta amsa da Alhamdulillh, sarah tace masha Allah, dafatan dae lpia dan naga dare yayi yanxu, cewar sarah "Eh lpia qalau, na dae kira ne naji ko kinsan ya faruq yake, wayoyinshi basa tapiya" sarah tai shiruu cikin rashin sanin abinda zata sanar da ita, shin ta fada mata gaskiya ne ko kuma tayi shiru ta kyale ta, Kinyi shiru sarah, Allah yasa dae yana lapiya," sarah tai gyaran murya, why not gobe kizo da kanki, tana kaiwa nan ta katse wayar ta kuma kashe gabadaya, zee ta rike waya a hannu tana jimami, hakan da sarah tayi ya sake dulmiyata kogin tunani da tarin tambayoyi, dakyar ta samu ta rintsa en en awannin da basu gaza biyu ba, Tun asuba data tashi ta kasa komawa, ta tsurawa agogo lokaci tana jiran gari ya waye, ta sake jawo wayarta ta lalubi numbernshi amma babu chanji daga abinda ake fada mata jiyan, ta ajiye wayar jikinta yayi sanyi gabadaya Tun karfe takwas tayi wanka tana gama ayyukanta, sae kuma taga 8 yayi safiya ta fita, ta zauna tana sake danna lambar tashi, aka sanar da ita switch off, itakam da zataga matar dake ce mata switch off data shaqure wuyanta, haushi yasata miqewa, takuma gaji da jira, bata damu ba koda asuba ne ba safiya ba, ta gaji fita zatai Ta dauki er karaamar handbag dinta ta yafa gyalenta kan daurin dankwalin atamparta, dukda cewa hankalinta a tashe yake hakan bai hanata yin kyau ba dukda batae kwalliya ba, Ba ta dauki lokaci ba ta isa kofar gate din estate din su faruq, tunda ta taho gabanta ke faduwa har yanxu data tsaya a gate din, bata wani damu ba ta shiga bayan sun gaisa da maigadi, saedae part dinshi a kulle yake gam da padlock, ta tsaya tana karewa part din kallo "Meyasa faruq ke min hakane, meyasa beda burin daya wuce na daga hankalina na damu a kanshi, banda wani sukunin tinani se nashi cikin halin da ban sani ba, kodae be sona ne" hawaye masu dumi suka gangaro mata, ta saka hannu ta sharesu cikin gajiyawa, haqiqa so wahala ne kawae Tana nan tsaye tana tadin zuci, sarah ta fito, dan tun shigowwarta ta ganta, Zee ta juya ta kalli sarah dake karasowa inda take, sanda ta karaso suka gaisa, sarah tace "in bazaki damu ba muje ciki mana" tayi gaba zee tabi bayanta zuwa bangaren sarahn... Aysha_bee ce https://www.instagram.com/p/CBI14BnhMto/?igshid=exzlz4093xe3 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Ina masoyana suke ku firfito ku marmatso kuji... Amma kafin nan bari mu kammala karatu Episode 36: Aches Cikin falourn sarah ta zauna tana mai jin kanta na juyawa, sarah tai serving dinta drinks, zainab a ranta kuwa sam ba wadannan ne a gabanta ba, Wata takarda ta zaro ta miqa mata, zainab ta karba tana son ganin mene cikin takardar dan zuciyarta na fada mata sakon faruq ne, tai hanzari budewa sanann ta soma karantawa cikin ranta "Assalamu alaikum warahmatullah zainab dina By the time da zakiyi receiving wanan papern im already gone, so far, yes zainab, amma banaso kiyi tunanin hakan na nupin wae karshen soyayyarmu ne yazo, ko kadan wannan ne ma mafarin soyayyarmu, inda hali ki jirani zainab ina nan zan dawo, in shaa Allah zan kiraki, i will definitely call" Zainab ta sake karanta takardar cikin rashin fahimta, sae ta dago ta kalli sarah, ina faruq yaje? Meyasa bemin sallama ba? Ya akayi ya bar wannan takardar a hannunki? Sarah ta kalli zainab cikin tsanaki tace " faruq yaje gurin malamin ku (levelcoordinator) right, Zainab ta gyada kai yes "B.u.k sunyi withdrawing dinshi from the department, accusing him of examination malpractice" zee ta miqe "Sarah are u drunk, are u okay? Kinsan me kike fada man kuwa, faruq dinne yayi exam malpractice? How comes?" Sarah tayi sighing "zauna kiji, zee ta zauna kwakwalwarta na kokarin fassara mata abinda sarah ke fada ko zata yarda amma ina, "Nidae shi ne kawae abinda na sani gameda wanan if you need more info u can contact your levelcord" zee tayi baya ta jingina kanta a jikin kujerar tana jin juwa, sarah ta dakko wayarta ta miqa mata, zee ta amsa tana maida idanunta kan pictures din, Ta dan mirje idanuwanta ganin wani almara a cikin wayar, "what the heck" ta fada on top of her voice, Ta kalli sarah idanunta tap da hawaye, meye haka sarah?" Sarah bata samu courage na kallan idanunta ba ta dan sunkui da kai, hakane zainab wanann shi ne babban dalilin dayasa faruq ya tapi beyi miki ko sallama ba, saboda ya kare mutuncinki ne, saboda yana qaunarki fiyeda yanda yake qaunar kanshi, Hawayen suka gangaro daga idanunta ta saka hannu ta rufe bakinta tana mai cigaba da kuka zuciyarta na pounding, ta dade tana wannan kuka me qaramin sauti, ta jima tana shatatar hawaye, dan kanta ta lallashi kanta bawae dan kukan ya isheta ba sae dan tana buqatar komawa kebantaccen guri tayishi son ranta A maimakon ta koma gida sai ta wuce school, ko sau daya ka kalleta sai kasan tayi kuka, idanunta sunyi luhu luhu, still tana tafiyar hawaye na zuba time to time, saedae ta saka bayan hannunta ta sharce, direct office din levelcord ta wuce amma se bata sameshi ba, ta fito ta koma bin titin, duk inda ta waiga cikin school din sae ya tuna mata da faruq, hakan kan kara ingiza kukan nata, can bayan school ta samu kasan wata bishiya, gurin tsit yake dan kamar daji ne saedae wucewar motoci kawae zaka na ji, Ta tsugunna kasan wata bishiya ta sunkuyar da kanta cikin raunin zuciya hawayenta ke diga kan tafin hannunta, What a mysterious life, ko a mafarki jiya i yanxu bazata ce faruq ze tapi ya barta ba cikin kankanin lokaci haka, ta ciro wayarta tana sliding pictures din, me hakan ke nupi, meyasa sarah zatace sune dalilin tapiyar faruq?, Bata samu amsarta ba se kurawa pictures din ido da tayi, shot hudu ne kuma sun dauku tarr koyaya imdae kasan zainab zakasan ita da faruq ne cikin hotunan a wani yanayi... Zee tana tuna sanda abin ya faru, lokacin da aka gama hidimar bikinsu zakiyya, taje gidanshi ta taddashi cikin mawuyacin hali, har tayi kokarin taimaka mishi Bari mu dan koma baya kadan From episode 34: "Ta karasa bakin gadon da sauri ta zauna tana kallanshi, idanunshi a lumshe suke ya budesu a hankali yana kallanta, Ya kara haske akan wanda tasanshi, labbanshi sun bushe fuskarshi ta rame, idanunshi sunyi ciki kamar wanda yayi jinya ta watanni, Muryarshi ce ta ja hankalinta Ta dan kara tauri da karfi yace "taimakamin na zauna, batayi wani tunani ba ta riko kafadarshi kusan gabadayanshi a kirjinta yake, (first shot) ta taimaka mishi ya zauna sannan itama ta zauna gefenshi, (another shot) tari ne ya rikeshi, wanda har saida idonshi ya fidda ruwa sannan ya sauka Itama taji nata idon ya kawo ruwa amma ta hadiye kukanta, kai kana kallan faruq zakasan yana jin jiki, Da muryar tashi da ta sake rashin dadi yace "nerh nerh ya gida? Ya hiddima?" Ta gyada mishi kai kurun Mene ya sameka? Kuma bazaka iya kirana ba, kaje asibiti ne?" Ya lumshe ido tarin ya sake yi sannan yace "mura ce kawai sai ciwon kai, na kira wannan doctorn na momy yazo ya dubani har ya bani magunguna kuma masu aikina na kulawa dani ba wani abin damuwa" A kufule ta dubeshi "har ni zaka cema babu wani abin damuwa" Yayi shiru yana kallanta a kasalance bece komai ba, sannan yace ki jirani a falour zan shiga bandaki Tace to, ya miqe dakyar kamar iska zata kadeshi ya fadi, jallabiya ce jikinshi, sai lokacin ta lura ramar ma har jikinshi ne, Ganin yana tangadi kamar dan maye, yasa ta zuba mishi ido cikin tausayawa, kasa yayi luuuu Saukinta a tsaye take ta tafi da sauri ta riko kugunshi (3rd shot) Dukansu sai suka zube a kasa, gyalen nata ma ya riga yayi nashi guri, (last shot) numfashinshi takeji gaba dayaa fuskarta da kirjinta shine yayi saurin tashi a kanta sannan itama ta miqe"...... Karashen maganarsu da sarah ta soma tariyowa "zee tace "amma meyasa hotunan suka zama dalilin tafiyarshi, in ze tapi ma kuma meze hanashi yimin sallama" sarah tace "nidae i dont know much abinda yace min shi ne "sarah ki fadawa nana zainab dina, ko zan bada rai na fansa bazan bari a taba mutuncinta ba, haka kuma makircinsu baze sakani rabuwa da soyayyarta ba" Wani tinani ne yazo kanta "kenan su ya halisa sunyi amfani da wannan pictures sukayi manupulating faruq har ya tapi ya barni, meyasa soyayyarmu ta tsaya musu a rai har haka, nikam mene nayi musu a rayuwa da basa son tarayyata da faruq" Kwanakin zainaab biyu tana zazzabi harda amai da matsanacin ciwon kai, sam taqi zuwa ganin likita, tana dai shan magunguna kuma tana ayyukanta na gida amma sam bata zuwa school, kuma koyaushe tana daki, dayake anty bata wani damu ba itama tana ta hidimar lil saghir yasa bata lura ba, Tana kwance a daki wayarta tayi ringing, tasa hannu da ciro ta a chargi dan tun ranar da sukai magana da sarah tai watsi da wayarta dama babu chargi se ta mutu, se dazu ta tuna ta saka ta a chargin, Sallama tai da wata irin murya mai kauri alamun bata da lpia, anty hawwer ta amsa tana tmbyar lpia zainab, ina kika shiga inata neman wayarki tun jiya, zainab ta lumshe ido A hankali hawaye mai zapi ya biyo kuncinta ta hadiyi yawu mai daci, Anty haww.... Bata qarasa ida furta sunan antyn ba kukan ya kwace mata, bata cire wayar a kunnenta ba kuma bata fasa kukan ba, Anty hawwer kuma bata ce mata komai ba, kuka take tana ajiyar zuciya da shan majina duk lokaci guda, Sai kuma ta soma mata bayani cikin kukan "faruq ya tapi ya barni, sun sakashi tapiya bada son ranshi ba Anty, sai kuma ta soma warware mata abinda ke faruwa tun daga last call dinsu dayace mata zeje gurin levelcord, her anniversary suprise, yadda sukai da sarah kashegarin ranar, har zuwa yadda takeji yanxu, Anty zuciya ta zapi takemin, nagaji nagaji Anty, Ammi ta tapi, Abbah ma ya tapi yanxu kuma faruq ne, shima ya tapi Anty nasan kuma baze dawo ba, Anty ta katse ta "wane yacemiki baze dawo ba, inace cikin takardar har cewa yayi ze kiraki ya akayi kika kwallafa ranki kan faruq har haka, yanxu ki tashi kiyi wanka zan kira zeena tazo ta rakaki asibiti, banason wannan zaman dayan da kike, kina nupin bazaki karbi kaddara bane ke kam a rayuwa, kina kokarin butulcewa ubangiji, haba mana zee" Ta share hawayen ta gabadaya rayuwar babu dadi "maza ki tashi kinji" ta gyada kai tohm ta sake goge hawaye "kuma banason wannan kukan kinyi kuka kuma ya isa haka, kina da abubuwan yi da hawayenki, zee tace to bawae dan hawayen sun dena zuba ba Yadda anty tace hakan tayi ta tashi ta nemi ruwan dumi cikin heater ta gasa jikinta tun daga kai zuwa tafin kafarta ta saki shower, sanan ta cuda jikin nata kadan dan babu wani kwari, Tana fitowa taga kiran zeena ta dauka jiki a sanyaye "gani nan tafe kinji sannu" tace to, mintunan da basu gaza 15 ba zeena tayi sallama a falour, Anty siyama dake fitowa a kitchen ta amsa mata suka gaisa sannan tace zee din tana daki, zeena ta wuce dakin ta tadda ta zaune karshen gado ta rungume jikinta, zeena ta karasa ta dafata, zee ta daga ido ta dubeta tana mai kokarin kada hawayenta su zubo, zeena batace mata komai ba ta miqe ta dau hijab ta saka suka fice a gidan, bayan sunma anty sallama Mabiya kuma masoya Al_hubb Wannan dama ce tazo da dumbin masoya zasu nunamin kauna, yau ina neman alfarma a gurinku karku watsamin kasa a ido, zanji dadi idan kuka karfafamin guiwa 🙏🏻 Please ku biyoni a shafi na na instagram @Ayshabnaseer @aysha_bee_couture Karku karanta ku wuce inma searching zeyi wuya ga link nan https://www.instagram.com/p/CBI14BnhMto/?igshid=exzlz4093xe3 Pls surprise me, inaso ku bani mamaki na tashi na tadda followers bila adadin, yadda ban gajiyawa gurin typing dan following dai nasan kuma bazaku dauke kai ba, Show me love😥 Surprise me Nima se na cigaba da baku mamaki wajen typing❤ I will love to see my true fans💝 https://www.instagram.com/p/CBI14BnhMto/?igshid=exzlz4093xe3 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 37: Tawakkul Basu jima can sosae ba a asibitin suka dawo, likitan ya bata shawarwari da magunguna sannan yace ta dena saka abu a ranta haka nan, gidan Anty siyaman zeena ta rakota suka zauna falourn, zeena na sake mata sannu, ta lumshe ido tanajin kanta na sake mata ciwo, a lokacin anty siyama ta fito ita daya da alama wanka tayi ba dadewa, ta karaso inda suke tana kallan zee sannunku da dawowa, zeena ta amsa Sai ta kalli ledar magungunan tace "bata da lpia ne" dan harga Allah se yanxu ta lura zee din ta rame, zeena ta amsata da "eh wlh, kuma taqi sanarma kowa batada lpia seda Anty ta tuhumeta" anty siyama ta girgiza kai kadan, bataji dadin hakan ba, amma tace "Allah ya sawwaqe cikin jimantawa Daki zee ta tashi ta wuce ta kwanta kan gado, zeena ta dibi magungunn ta bita itama, a kwancen ta tadda ta, ta karaso ta zauna saitin kanta, "kiyi haquri zee, ki kara haquri kinji" cikin karfin hali ta daga idanunta ta kalli aminiyar tata sannan ta lumshe ido kamin tace "ai nayi zeena" wani tausayinta ya rufe zeena din Zee ta tashi zaune ta gyara zamanta ta saka hannunta cikin hannun zeena ta rike, zeena itama ta kara rike hannun da kyau, zeena tace "naji dadi da kikayi haquri kuma inaso kimin alqawarin cire damuwa a ranki dan babu abinda zata rage ko ta kara sedae ma ta sace miki kwanciyar hankalinki amma bazata dawo da faruq ba" zee ta gyada kai sannan ta dafa kafadarta "zeena karki damu in shaa Allah zan daure kuma indae faruq mijina ne nasan ze dawo ya aureni" "Naji dadin jin wadannan kalamn a bakinki" tai murmushi sannan tace muje na rakaki, zeena tace "a'a karki damu" "And whoever relies upon Allah, then he's sufficient for him, indeed Allah will accomplish his purpose, Allah has already set for everything a [decreed] extent" Q65:3 Bugu da kari Wasu lokutan Allah yakan rabamu da abu saboda ba alkhairi bane, ko kuma jarrabawa, koda kin rasa faruq kada imaninki ya ragu kokuma kiji kamar Allah be sonki ne, inaso ki dauka a ranki Allah yana jarabtar bayinsa dayafi so ne, gwargwadon imaninsu, I heard yasmin talking about tawakkul "What exactly tawakkul means?, it means i dont see the solution, i dont know what's gonna happen tomorrow but i do know one thing FOR SURE and that's 'inna ma'iya rabbi sayahdeen' indeed my lord is with me and he'll guide me through, When we have that kind of attitude Allah promise of something, He'll spilt cease for us, that situation that look impossible Allah will make a way out, that situation we dont see a solution Allah will give a solution' Zainab ta kara gyara zama tana sauraron jawabin da Anty hawwer ke mata tana mai qara jin kwarin gwiwa da sallamawa ubangiji dukkan lamuranta, zuciyarta na cooling Sannan ta dora da fadin Again cikin alqur'ani mai girmaa Allah yana cewa "wani lokaci zakuqi wani abu amma shi ne Alkhaiirnku, wani lokaci kuma zakuso wani abu amma ba Alkhairi bane a gareku" a karshe yace "Allah shine mafi sani, mukuma bamusan komai ba" Tunda Allah shine ya sani se mu miqa lamuranmu gareshi muyi fatan ya mana zabi na alkhairi cikin rayuwarmu, mukuma karbi al'amura da haquri da tawwakali sannan a karshe mu tsarkake zukatanmu", Ubangiji ya kan jarrabemu ne gwargwadon imaninmu" Zainab ina fata zakiy aiki da abinda na fadamiki kuma kiyi nazari sannan ki nutsu ki kumaa godewa Allah cikin lamuranki, domin idan kika gode mishi ze qara miki" Zainab ta gyada kai kmar kadangaruwa, "Se nakeji a rayuwa nafi kowa sa'a, samun 'yar uwa kamarki abu ne da se an tona, nagode Anty Allah ubangiji ya raya miki zuri'a, Allah kuma ya biya mana bukatunmu na alkhairi" Tana cikin scrolling wayarta a twitter tayi karo da wani post da mufti menk yayi "Quit worrying especially over things you can't control. If you want peace of mind hand things over to the Almighty after you hav done your best. You hav played your part so now let Him take over. Remember whatever you let into your mind has the potential to manifest in your life".... With all the encouragement she finally get back to school, Saukinta ma duka courses din sun fara karatunsu da faruq kuma project ne me muhimmanci dan haka ta maida hankali dukda wasu lokuta she feel lonely and so empty, wasu lokutan kuma bata iya controlling tears dinta, as duk idda ta juya ze na tuna mata da faruq ne, amma se take rarrashin kanta, with "this too shall pass" Result ya fito (na previous semester) kuma tayi abin arziki kmaar ko yaushe taji dadi ta gode Allah, and she smiled lightly saboda tunawa da faruq da tai, babu wani abu dawwamamme Ta sami levelcord a office bayan sun gaisa ta nemi inda hali ya sanar da ita wata magana gameda withdrawing din faruq a school amma yace baze iya disclosing wani details ba, all he can say is "an kama faruq yayi exam malpractice kuma an koreshi, kumaa ba shi kadai bane harda wasu students dinma, Bikin minnatullahi ya matso sosae shirye shirye ake ta ko ina, saukinta ma mostly a Abuja suke shirin nasu tunda can gidan mijin yake, Takan zo gidan Anty siyaman idan ta gaji da hayaniyar biki, se ta shigo ta huta, A haka bikin yazo, bangaren amarya zasuyi Dessert party itada friends dinta sannan sai mother's eve na iyaye, wanda ke a mazaunin kamun amarya da Ango, sanda akazo rabon iv zee batai tsammanim za'a bata ba sekuwa aka bata itada da zakiyya wae baza'a bama kubra ba saboda tanada ciki me laulayi zata batamusu biki, khairi kuma ba'a garin take ba Aikuwa kubra tayi bala'i tace dama ko sun bata bazuwa zatae dangin marasa mutunci kawae, zakiyya me zatae inba dariya ba, tace mukuwa zuwa babu fashi... Yau za'ayi kamun da aka gayyacesu, zakiyya dama tun ba yau ba fadi take, "zainab muyi ado mu kece raini, in ta fadi haka zee sae tayi murmushi kurun, Zee Ta fito a shower tana goge jikinta, a ranta take tinanin wanne irin kamu ne bayan magarib kamar za'ayi dinner, ta sauke idanunta kan wannan frame din da faruq ya bata na anniversary dinsu, tayi murmushi wanda baikai zuci ba, ta juya ta cigaba da shiryawa, ta jawo drower kenan zata dauki eye pencil idanunta suka sauka kan wata jotter daya taba designing da kanshi, anyi painting front page din da zanen rose yayi kyau (pic on wattpad) Ta dakko ta ta dora kan mirror, sanda ta kammala shiryawa seta dubi kanta a mirror, da lokacin da suke tarene idan tayi kwalliya haka zece mata "ki dauka min hotonki na fara gani" takan ce mishi abinda makaranta zanzo zaka ganni" se yace "a'a banaso kafin ki karaso wani yaa rigani ganinki" Yanzun ma seta tsinci kanta da daukan hoton kanta dukda babu faruq din da zata ma sending Ta jawo jottern ta dauki red pen ta soma rubuta "Dear heart Being apart is more difficult than i ever imagined. I see reminders of you everywhere i looked, and they make me ache to be near you again. I cherished every moment we spend together, i love you even more in the moments when we re apart. Tonight As i write this letter it's like you are right here with me. I miss you my omar" ta rufe jottern ta maida cikin drawern tana mai jin tarin kewar shi Ta kurawa kanta idanu ta cikin mirror din wondering how can love be so deep, ta lunshe ido.. Turo kofar dakin zakiyya tayi tana sallama zainab ta amsa tana mai juyawa fuskarta dauke da murmushi Dukka suka hada baki gurin fadin WoooW Zakiyya ta riga cewa "zee kinga kyan da material dinnan ya miki" dariya ta subuce ma zee tace "ke kinga kyan da less din ya maki, dukka dariyar suke Ita zee material ne pale pitch yana da yanayin santsi da sheki aka mishi ado da duwatsu bakake masu dan girma da suka qara mishi kyalkyali, se gyalenta dark Ash da yyi bala'en shiga da kayan, kanta kuma ta daura head pale pitch, sarka da dan kunnenta duka black ne, makeup din face dinta kuma nude babu wata hayaniya, Ita kuma zakiyya lace ne royal blue da ratsin sky blue se touch din plain white kadan kadan, tayi dinkin buba da zani da sukai mata kyau dan ta sakeyin er kiba, dankwalin lace din ta kashe daurin zara buhari, sannan tayi ado da silver jewelries, hakama gyalenta da jaka da takalmi... Tare suka jera suka fita falourn suna annashuwa, babu kowa a gidan se anty dake dakinta da alama wadanda ke gidan antyn sun tapi gurin event din, zakiyya ta zauna kan kujerar snn tace jeki ce mata mun shirya fa dukda tasan mun shirya din dan na gaisa da ita, Zee batai wani yunkuri ba sega Antyn ta fito itama a shirye, ta kashe kala, har gida me makeup tazo tayi mata ta tapi, dan seda tace zee ma tazo a mata tace a'a saboda batason makeup me yawa a face dinta, ta iya simple one kuma yayi kyau Ko ban fada ma me karatu ba nasan yasan labari yazo karshe...kiris ya rage 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 38: He's back Tare duka suka dunguma gurin event din, saedae da sukaje mutane dayawa sunje dukda bikin na manya ne amma da mutane dukda haka kuma komai a tsare akeyi kuma a nutse, sai karfe 10 amarya tazo, akayi kamu sannan aka sanar da shigowar Ango da abokanshi, karkuso kuga idanun jama'a bama kamar kawayen amarya daketa rangwada ko wani abokin ango ze kyasa Ya shigo tare da abokanshi, gabadaya idanunshi naga kan amaryarshi da take ta walwali, tayi makeup kai baka ce a kasar nan take ba, a lokacin ne mutane dayawa suka fuskanci Assidduque mutun ne mai fara'a daga yadda yake ta murmushi yana blushing, barima inya dubi amaryarshi se wani nishadi ya taso mishi itama a nata bangaren kanta ya sake girma ji take babu ya ita a fadin duniya, ace ta hada zuri'a da dangi kamar na assiddique, A tsakiyar filin ya tsaya yayi folding hannayenshi, daya daga cikin abokan angon wanda ya kasance barrister mijin zakiyya ya amshi mike ya soma fadin "ango na jiran amarya tazo ta tareshi" (barrister bawae abokin Assiddique bane, yana mai aiki ne kuma yana jin dadin aiki dashi, yayanshi wato uncle muzakkir mijin anty hawwer shine abokinshi kuma shi ne ya hadasu) Qawayen amarya suka tapi gurinta suma suka zagayeta sannan cikin isa ta taso tana taku bride's maids na take mata baya, 'dan nesa kadan dashi taja ta tsaya itama, shi da kanshi ya karaso inda take, ya hade hannayensu suka karasa gurin zamansu. Bayan sun zauna yayi whisper a kunnenta "u re more than beautiful" Tayi blushing Haka aka kare taro cikin annashuwa dajin dadi.. Bayan daurin aure da kai amarya abuja wanda zee bata je ba, aka hada mother's eve a can ma suka rakashe, Abubuwa suka cigaba da tapiya smoothly da taimakon mai duka, har zee ta kammala semestern data rage mata a makaranta, lokacin service dinsu akayi posting dinta a camp a garin Abuja, shine mafarin zuwanta Abuja kamar yadda na fadi a first page Zee ta karkare labarin tana mai duban Assiddique wanda ya sunkui da kai Tace "kaji yadda ta kasance tsakani na da faruq, shi ne masoyina wanda na rigada na bama zuciyata ba tun yau ba" "Nikuma ya zanyi da tawa zuciyar" a bazata taji kalamnshi sunzo mata Ya dago yana kallonta a nutse tareda shauqi mai yawa Ta dubeshi batareda ta kula maganar da yayi ba "yayana kaji kana magana" ta fada excitedly... Be amsata ba se murmushin dake kwance kan fuskarshi, a hankali kuma ya zame kasan falourn ya miqa sujudus_shukur Ganin da sukai dare ya tsala ya sakasu neman makwanci tareda barin sauran batutuwa ma gobe idan mai duka ya kaimu.. Zee kuwa ta kasa kwanciya dakyau se juye juye take kan gadon dakin nata, damuwanta da hankulanta sunaga faruq ne "batasan mene ke damunshi ba amma abin ya tsaya mata a rai, bayan tsayin watannin data dauka tana kewarshi yau gashi gareta amma cikin wani yanayi, Akalar tunaninta ta karkata ga Assiddique, sarae taji furucinshi na daxun "Nikuma ya zanyi da tawa zuciyar" Da sassafe ta tashi kai da ganin idanunta kasan ko kadan bacci bai isheta ba, Ta kammala wanka da shirinta kenan idanunta suka sauka kan wayar farruq data taho da ita jiya, ta jawo ta ta kunna Abinda ta fara gani shine wani hadadden hotonshi kan wallpaper The first time data ganshi da kananun kaya, ba irin namu na gida nigeria ba, kai da ganin hoton kasan ba anan kasar aka daukeshi ba (Pic on wattpad) A hankali kida mai taushi ya soma tashi daga wayar na waqar Alan Walker "lily" amma se ta fara daga gurin "Follow everywhere I go Top over the mountains or valley low Give you everything you've been dreaming of Just let me in, ooh....... Everything you wantin' gonna be the magic story you've been told And you'll be safe under my control Just let me in, ooh....... Just let me in, ooh" Har wayar ta katse wani kiran ya sake shigowa sannan ne zee ta ankara kira akeyi ta dauka tana mai gyara muryarta Gaisawa suka somayi da ya Safiyyan dan taga sunanta jikin screen din Surprisingly tace "Zee ko ba zainab bace?" Zainab taji heart dinta tayi melting tace "nice Anty har muryarta na shaking, Nan ta sanrma ya safiyya abubuwan da suka faru jiya sannan ta dora da fadin yanxu ma asibitin zamu wuce, itama ya safiyyan tace yanxu zata shirya su hadu a can.. Tayi cutting call din, zee tabi wayar da kallo does that means tana garin nan? Tare da Assiddique suka tapi asibitin, suka fara duba jikin faruq har a lokacin be farka ba, da alama an mishi allurar bacci ne, zee tayi kokarin danne kukanta ta hanyar rufe bakinta, duk abinda take Assiddique na lura da ita, Sanda suka sami doctor ya soma musu bayanin abinda ke damun faruq "Matsalar hunhu (lungs) ce, da alama ta dan jima a jikinshi dan har cancer din tayi developing takai matakin da dole sai an mishi aiki kuma in so samu ne kawae a fita waje a mishi aikin saboda hadari da aikin keda shi..." Suna fitowa a office din doctor sukai kacibis da ya safiyya, ai zee me zatai, se hawayen dataketa riqewa suka soma bulbulowa, "na shiga uku Anty, faruq keda lung cancer" Rarrashinta ta shiga yi daga baya suka nemi guri suka zauna inda take zayyane mata abubuwan da suka faru shikuma ya barsu ya wuce gidan yallabai saboda nemanshi dayakeyi "Faruq ya koma europe ba a son ranshi ba, school authority sun mishi sharrin yin exam malpractice sakamakon sunanshi daya fado cikin wa'anda suka zauna a gurin da akayi na wata exam wai human genetics" Sarai zee ta tuna sanda faruq ya fada mata anyi malpractice amma ai shi beyi ba, tana da tabbacin faruq be satar amsa dan da yanayi da ta sani duk dadewar da sukai, da baze na karatu sosai haka ba "Wannan lung cancer din kuma bata jima da tashi mai ba, shi ne dalilin zuwanshi amsar wannan award din domin ya saida ya biya expenses na aikinshi" "Dady ya samu matsala da harkokinshi na europe, duka muna nan Abuja gurin momy, yanxun ma hada kudin tafiyarshi aketa famanyi amma dake aikin me tsada ne sosae yasa kudin basu hadu ba" Zee tace "Kenan yasan da ciwon a jikinshi?" Ya safiyya tace eh"... Zee ta koma gida devastated, abu daya ke zuwa kanta taje ta samu Assiddique ya biyawa faruq kudin aiki, tasan ko nawa ne yanadashi, kuma yanada kirki tasan ze bada kudin, ta tura kofar falourn ta danna kai ciki, har ta soma hawa sama taji kamar muryar mutane cikin gidan, tasan Assiddique be gidan tunda ya sanar da ita zeje gun yallabai, Ta wuce dayan part din datake jin kmr magana, cikin falournshinna kasa ta tadda minnatu da Anty siyama, mamaki tai ya akayi ko motarsu bata gani ba, kodayake hankalinta be gurin ba lallai ta lura ba Gaisawa suka shiga yi Minnatu se wani hade rai takeyi tana cika tana batsewa, zee ta tashi Anty siyama tace "zainab dawo kiji mana" zee ta koma ta zauna "Kinga dai a gidan nan aiki kikeyi kuma biyanki akeyi, to dan Allah ki tsaya iya boundaries dinki, banaso na cigaba da jin kananun maganganu, gida dai minnatu keda gida, babu ruwanki cikin abinda ya shafi itada mijinta in sun ga dama su daki juna babu ruwanki, dan naji kece kika ingizashi ya rubuta mata takarda, ba haka nasan halinki ba kuma bana fata ki sauya,, tun ina miki ta lallami ki kyale mata mijinta suyi zaman lafiya" Zee ta jinjina kai kurun ta tashi tabar gurin A ranta take saqa maganganun Anty "ita sam yanxu bata da lokacin wannan abinda ya dameta ma ya shallake tunanin wata minnatu, fatanta Allah yasa Assiddique ya amince da buqatarta, tana son faruq dinta dadin dadawa tana matuqar qaunarshi.... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 39: fishy Ta zabga tagumi da hannaye biyu sam bata ji maganar dayake tayi mata ba sai da ya zuguri fuskarta da spoon Ta kifta idanu tana mai hadiye kukan dataji yana kokarin tahowa, ta sunkui da kai batareda tayi wani tunani ba ta soma fadin "dan Allah yayana ka taimaka min ka taimaki faruq, dan Allah badan ni ba, yadda Allah ya taimakeka..." Se ta kasa karasa maganar ta sunkui da kai cikin jin zafin zuci, Tashi yayi daga gaban abincika sannan yace ta biyoshi, Wannan gurin mai kama da library ya karasa sannan ya jawo kujera ya ce da ita "zauna, zee ta zauna tana sauke ajiyar zuciya "Kiyi kokarin kwantar da hankalinki, in shaa Allah faruq ze samu lafiya, kinji" ta gyada kai "Good, munyi magana da doctor and yayimin recommending UK so yanxu ma mun soma processing ne, karki damu by God's grace ze tashi" Zainab ta tsaida idanunta kanshi tana mai jin wani dadi na ratsa ta Tayi hour daya a kwance kan gadon amma juye juye kurun take faman yi abubuwa dayawa ke yawo a kanta A bangaren ubangidan nata, lokaci daya taji yayi furuci bayan ranakun daya kwashe bai magana a sanda ta ida bashi dogon labarin, shi kanshi a yadda ta lura furucin nashi ya bashi mamaki, Kuma koda be fada mata ba tasan me maganar tashi ke nupi, yes tasani sarai yana sonta, amma tai ignoring ta lumshe idanunta tana qara hasko fuskarshi daxun dayake mata bayanin shirye shiryenshi gameda faruq, A yadda ta fahimta Kawae yana danne feelings dinshi ne yana dora nata saman nashi, maybe zata iya kiran haka a matsayin asalin qauna, saidai ita da shi ta sani sam abu ne da bama zeyu ta hango ko ta hasaso ba, tamkar hada ruwa da wuta ne guri guda, Challenges take hanga ta ko ina, bama kamar bangaren uwargidan nashi, All she can do is to keep ignoring his feelings for now koda hakan zeyi hurting dinshi ne, ya kamata ya fahimci inda akalar zuciyarta ta tapi, shima ya maida hankali ya kula da gidanshi, bazataso ta zame mishi tashin hankli ba sam, zata cigaba da mishi addu'a Allah ya bashi farincikin duniya da lahira hadi da gamammiyar kwanciyar hankali.. Kafin kace me shirye shirye sunyi nisa, saidai Assiddique yace kar a sanarma da familyn faruq cewa shi ne ya dau nauyin aikin da sauran expenses, ya fadama zee kar ta fada musu nan ma, Amma still seda ta sanar da Ya safiyya kadai tace "yace beso a sani to dan Allah kar ki fada, a barshi a matsayin wata foundation ce ta dau nauyin komi" Ranar Anty safiyya har kwalla ta zubda, tayi murmushi duka lokaci daya " dama seda na fadama FUJ kedin Alkhairi ce" sukai hugging juna Mutane biyu suka tapi tareda faruq, safiyya se wani likita da Assiddique yace ya bisu saboda sauqin abubuwa, dan dady beda ishasshiyar lafiya shima, zee taso ta bisu amma Assiddique yace ta kwantar da hankalinta ta zauna har su dawo, haka tana kuka tayi waving dinsu a airport, shikuma yana daga bayanta yana kallon komi, Yana sonta sosai amma ba yadda zeyi dole zeso abinda takeso, salloli ta maida hankali sosae tanayi ba dare ba rana, rokonta da addu'arta Allah yasa ayi aikin a sa'a faruq ya dawo lafiya, har takai ma yanxu Assiddique yana mata uzuri da girki, duk yadda yakai ga son girkinta yakan haqura saboda mafi yawan lokuta bata tashi da wuri saboda kwana datake tana ibada, har ya fita, hakan yasa yapi missing breakfast da lunch amma takanyi kokarin hadamishi dinner Bangaren mint kuwa ta koma school da aikinta halayan na nan dai saidai yanxu tana damuwa na yadda star din nata ko kallon inda take beyi, in kuwa tazo inda yake ma yakan tashi ya bata guri ko ya soma fake call Satinsu faruq daya da zuwa aka kammala komi na aikin, akayi mishi zainab tana zaune ta rike waya a hannu gabanta na dukan tara tara, Tafi awa uku a zaune a wajen in ta gaji ta tashi ta dan zagaya sannan ta sake dawowa ta zauna, a haka wayar datake ta jira ta shigo mata Ko ringing daya batai ba tai picking da fadin "ya safiyya an ida? Anyi sa'a? How was it?" Se taji shiru ya biyo baya tace "hello" Ya safiyyan tayi sighing da fadin Alhamdulillh zee it was successful sun mashi lobectomy kuma zasu dorashi a chemotherapy afterward" Zee ta fidda haki mai kara tana mai dafe kirjinta sannan wasu siraran hawayen farinciki suka zubo mata "Alhamdulillh" Asibitin sunso discharging faruq saboda expenses da kuma yadda jikinshi ke responding ma treatment yadda ya kamata domin ana samun progress yadda ya kamata, ga kuma uban kudaden da ake kashewa Amma sai Assiddique yace "kar a sallameshi tukunna nafiso ya warke sumul yadda ze iya takawa yazo har gaban zainab da kafafunshi, kuma to avoid further complication a barshi ya huta da kyau" Ya safiyya ta kira zee tana sanar da ita abin Alkhairin da Assiddique yayi na barin faruq din "nima kamar yasan abinda ke raina kenan, idan akace za'a dawo dashi a yanxu jikin ze iya rikicewa ko kuma a samu delay na progress, dan Allah ki sake mishi godiya zee ubangiji Allah ya faranta mishi ya biya mai buqatunshi yasa ya cika da kyau da imani" zee bakinta har kunne amsawa kawai take da Amin Amin Zee taje ta samu Assiddique shi daya yana aiki da system ya dago ya dubeta, tana tsaye da katon murmushi kan fuskarta tama kasa tsaiwa dakyau se rausaya take, sai ya samu kanshi da murmusawar shima, sannan ya nuna mata seat din kusa dashi yace "zauna Ta zauna tana mai kallonshi and for the first time taji abu cikin zuciyarta gameda shi, ta sunkui da kai tana murmushin ita daya, ya girgiza kai sannan yace tunda kinzo, ga aiki ki tayani, ya fada yana dora wasu papers kan cinyarta Har lokacin murmushi take ta rike takardun sannan ta sauka daga kan kujerar ta zauna tana facing dinshi ta dubeshi amma sai taga ya mata kwarjini ta maida kanta kan takardun a hankali ta soma fadin "Allah ya saka da Alkhairi, mungode ubangiji Allah ya biya maka bukatunka na Alkhairi ya baka zuri'a dayyaba" Yace "Amin a takaice dukda yaji dadin addu'ar har ranshi, cikin ranshi yake fadin "inama zaki ji yadda nakeji gameda ke zainab"... Tunaninshi ya katse sakamakon ganin mint dayayi kamar an jehota, ta tsugunna ta watsar da takardun kan ciyar zee sannan taja hannunta ta tura waje ta rufe kofa, ya tabe baki yana kallonta sai kuma ya cigaba da abinda yakeyi, Zee ta sa dariya dan ita abinma dariya ya bata, a yadda take cikin farinciki batajin wani abu da mint zatai mata ze bata ranta "Amma star idan aiki kake buqatar ayi maka ni yafi cancanta ka saka, ita girki ne kadae aikinta cikin gidan nan" Yayi shiru be tankata ba, Magana fa nakeyi, yace "eh ina sauraronki Tayi kwafa Amma dai kasan nafi karfin wulaqanci ko, ka dubeni da kyau wlh nafi karfin ka hadani da zee Beson yi mata magana amma yanxu kam se yayi "dama ai ke da zee babu hadi ma" ya fada yana mai murmusawa Ita ma tai murmushi dan da alama dukkansu da yadda kowannensu ya fahimci maganar, a ranshi yace "zee tafiki komai minnatu, a yanxu ma ta fiki matsayi cikin raina" Jikin faruq na sauki sosai dan yanxu yakanyi abubuwa da dama da kanshi batareda an taimaka mishi ba, dukka update daga gurin ya safiyya zee ke samunsu, duk sanda tace ya safiyyan ta bama faruq suyi magana se tace yana bacci ne har abin ya fara damunta Dan indai da gaske jikin faruq yayi kyau kamar yadda suke fada amsa waya dai ai baze gagara ba... Comments dinku na sakani nishadi... Alhub novel Group dina ina yinku Bama kamar in naji team faruq da team Assiddique na ja'inja kuna dan lukutin birgeni a cigaba da gashi #team faruq #team Assiddique Which team 're u? 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Asslm alaikum inaso na danyi clarifying abubuwa kamin mu cigaba saboda wasu na cewa basu fahimta ba se nake ganin bayani nada dadi 1. Ana cewa Assiddique baya magana lokacin data fara bashi labari amma bayan ta kammala labari sae ya cigaba da magana Ai idan me karatu ze tuna abinda na fada a page din data kare bashi labari, ita kanta zee dayayi maganar seda tai mamaki tace yayana kaji kana magana shima kanshi murmushi yayi sannan ya sunkuya ya miqa sujudusshukur Ma'ana yana godewa Allah da bakinshi ya bude yayi magana 2. Maganar mint da a ke cewa an saketa kuma ya akayi ta dawo, ai kafin zee ta soma bawa Assiddique labari yallabai mahaifinshi ya kira babanta har sukayi magana yace baya kasar amma in ya dawo ze dawo da mint din So shine dalilin zuwan Anty siyama gidan tunda Anty siyama ai a kano take amma dalilin dawowar mint tazo abujan har tayi ma zee kashedi ta rabu da mijin mint Episode 40: Married Watanni biyu cur suka dauka a UK kuma Alhamdulillh jiki yayi sauki sosae, dayake ta hanyar Assiddique ne sai aka hada shi da wani doctor a nan nigeria daze cigaba da kula da lafiyarshi, Ta zauna gaban mirror din a gajiye, gabadaya ma ta rasa gane wanne irin kwalliya zatai ma faruq din tun sanda ya safiyya ta sanar mata da dawowarsu a yau din takejin feelings iri iri, Ta dubi kan gadonta da tai mishi kaca kaca da kaya ta rasa wacce irin sutura zata saka ji take komi ma beyi ba, ta kalli fuskarta tana tunanin wanne irin makeup zatai da ze faranta ran faruq din nata Tapi awa daya tana wadannan sake sake daga baya dataga lokaci na sake kurewa sai ta sami wata black abaya mai adon flower red and white, ta sami black veil tayi rolling ta kalli face dinta babu kwalliya kamar mafi yawan lokuta ta saka lipgloss sannan ta dauki purse dinta, Lambar Assiddique ta shiga nema sakamakon fadamata da yayi da kanshi ze kaita, dan zeso yaga farincikin daze sauka kan fuskarta idan taga faruq, bazeso missing ba "Ya dauki wayar da sallama, bai bari tace komai ba yace "pls kiyi haquri wasu en ayyuka sun tsareni nayi ma driver magana ze kaiki, tace to yayana Ta sauka batareda tayima mint sallama ba dan gabadaya damuwanta be wuce taje taga faruq ba, hankalinta na gareshi, saida ta fito farfajiyar gidan taga garin yayi duhu hadari ya hadu sosae, tai murmushi tana jin dadin iskar dake kadawa tana kada kayanta da flowers din gurin a hankali Zee ta dubi agogonta tabbas ta makara tace da drivern dake tuki "dan Allah kayi sauri nasan sun sauka yanxu" Koda suka isa ta fito da hanzari har tana gurde kafa, driver shima ya fito ya soma vedio kamar yadda ubangidan nashi ya sakashi dan a cewarshi bazeyi missing kyakkyawar fuskarshi zee ba in tana murmushi Daga nesa ta hangeshi cikin katuwar farfajiyar filin jirgin, dukda bayanshi take ganni amma tasan shi dinne, yau ya saka wasu sutura da ba farare ba, iskar gurin take kada gashin kanshi fuskarshi na fitar da annuri, juyowa yayi kadan hakan ya bata damar ganin gefen fuskarshi yayinda murmushi mai taushi ke fita a fuskarshi, bayanshi ya safiyya ke tahowa gurinshi ta gabanshi kuma wasu mutanene da ta tabbatar su dady ne, itama tana tunkarar inda yake, cak zainab taji kafafunta sun kasa karasawa kamar an saka kusa an kafeta a gurin,Take wani abu ya tokare mata makogwaro, sakamakon furucin ya safiyya dataji tana fadin "Hamra dama kin haihu shine dady be sanar mana ba, wow faruq ka zama dady yanxu, Allah yayi kaine zaka fara bawa dady jika" Zee ta hadiyi yawu mai daci, akan idanunta faruq yasa hannu ya amshi yaron dake hannun daya daga cikin kannen nashi biyu wanda bata gane wacce Aisha ba wacce hamra Jaririne jawur dashi, dady ya karasa ya rungumesu tare duka su biyun, ya dan bubbuga bayanshi yace "welcome back my son" Ruwan saman daya soma sauka ne yasa kowa na wajen ya fara neman mafaka harda su faruq ma suka bude umbrella, zee ta bisu da kallo batareda tayi yunkurin hana zubar ruwan a jikin ta ba.. tana kara gasgata murmushin dake kan fuskar faruq da yadda ya kama hannun hamra ya hada da nashi, Denajin dukan ruwan tai a jikinta hakan yasa ta gane umbrella ce aka saka mata ta daga ido ta kalleshi a raunane, sai kuma taji kamar an sassauta rikon da akaiwa kafafunta ne, ta kuwa kwasa da gudu batareda ta damu da yadda ruwan yayi mata sharkaf ba, bata tsaya ko ina ba sai a gaban faruq wanda ke tsaye cikin wani glass place hakanan inda ruwa baze tabasu ba, haki take fiddawa tana ajiye tagwayen ajiyar zuciya,, ya safiyya ce tayi saurin karasowa ta lulluba ma zee wani showel da aka raba musu cikin jirgi, faruq ya saci kallon dady yaga suna magana da doctor din dasukazo tare sannan ya kalli hamrah yaga tana zaune comfortably itada Aisha suna hira, ya miqawa ya safiyya babyn sannan yaja hannun zee da sauri Tana ta kokarin fizge hannunta amma bata cimma nasara ba seda suka sha kwana ta fizge tana huci tana kallonshi Sai kuma hawaye masu dumi suka kwaranyo kan kuncinta masu sanyi, taja numfashi tana mai lumshe ido, Ita ce tai breaking silence din ta hanyar fadin "Faruq dagaske ne kayi aure harda d'a?" Ya lumshe ido ya bude sannan yace "gobe by 4 ki sameni a garden palace we'll talk" ya juya ze tapi sai kuma ya dawo yace ki tayani yima Assiddique godiya ya safiyya ta fadamin komi" yayi mata brief smile sannan ya fice ya tapi, ta bishi da kallo kamin ta zube kan guiwowinta tasa hannunta ta rufe fuskarta, Kamshin turarukanshi taji yasa ta dago da fuskarta ta kalleshi yace tashi muje, ta tashi amma sai taji jiri ya debeta tai saurin dafe bango, ya akayi? Ya tambyeta ranshi be mishi dadi, ta daga ido ta kalleshi sannan ta murmusa cikin karfin hali tace bakomai yaya_na ya jinjina kai Kan hanyarsu ta komawa dukansu sunyi shiru jigun jigun, is it true? Taji ya jeho mata tambayar unexpectedly, kawae sai ta saka mishi kuka ya furzar da iska waje, saeda tayi mai isarta dan kanta ta dena, motar ta tsaya alamun sun iso, yace "goge hawayenki banasonsu" ta daga jemammun idanunta t kalleshi taji wasu ruwan hawayen na taruwa Ta bude kofar ta fita kawai, ya bita da kallo "ko kadan bayason damuwarta, dayasan abinda faruq ze mata kenan dabai soma barinta taje inda yake ba, yakasa gane indai a kanta ne be iya controlling kanshi, duk yawan ayyukanshi amma ya tsallake ya taho gareta dukda yace mata baze samu damar zuwan ba amma ya gaza nutsuwa..." Zainab ta kira Anty hawwer muryarta very low alamun sun bayyana gabadaya she's depressed, "Mene ya faru zee ya naji voice dinki haka" Zainab ta soma mata bayani tanayi tana shessheqa Shiru ya biyo baya, dan iskancin faruq ya matuqar bata haushi, daga alama kuma cikin abinda ta fada mata ta gane Assiddique na son zee din, tayi murmushin takaici "Yanxu me kike ganin zakiyi?" Zee tace "bansani ba Anty shiyasa na kiraki "Kin sani zainab, wallahi kinsan mene ya dace kiyi, wannan karan bazan cemiki komai ba na barki ki yanke wa kanki hukunci, saidai ki sani komene zakiyi kiyi abinda ze samar miki da kwanciyar hankali zainab" Kashegari Ta shirya cikin sanyin jiki ta fita ta samu driver babu abinda yake dan haka tace ya kaita anguwa, bataso assiddique yasani shiyasa bata sanar mai ba, Karfe 4 da mintina 10 ta isa palace din, can gefe ta hangeshi zaune kan wani dan dutse da aka maidashi kamar bench yana zagaye cikin kananun duwatsu da bishiyu Ta karasa tana mai yi mishi sallama, kukan tsuntsaye na tashi yayi mata murmushi amma sai ta samu kanta da jin haushin murmushin nashi Ta samu guri ta zauna yadda zata fuskanceshi, nana zainab kin wuni lafiya, ta gyada mishi kai kawae Ya lumshe idanu ya bude, ya dubi en tsutsayen dake shawagi a gurin yace "its been a while" Nan ma tai mishi shiru Duka sukayi shiru tsayin mintuna kafin daga baya yace "ina fatan bawai fishi kike dani ba" ta girgiza kai kawai, Then talk mana zainab, talk, tell me how much you've missed me Sai ta samu kanta da zubda kwalla "So kake na fada maka nayi kewarka dan ka sakejin dadin kuntatawa zuciyata, Dududu watanni nawa ne?, Watanni goma sha takwas ne, shekara daya da rabi amma har kayi aure har ka rufe babin zainab a rayuwarka, harda yaro" Ta lumshe idanunta yayinda hawaye suka sauka kan lashes dinta "Pls don't cry zainab i never deserved your tears" Ta miqe a kufule, idan baka da abin fada ni inada abinyi, yayi saurin shan gabanta Nike da abubuwan fada zainab ki bani kadan daga lokacinki dan Allah, ta koma ta zauna tana mai hadiyar yawu lokaci lokaci Ko kadan nasan ban kyautata miki ba zainab, hakane nayi aure na auri hamra bayan komawata europe, ki fahimce ni dan Allah nayi hakanne a bisa umarnin dady Ta katse shi da fadin na fahimci wannan sai kuma wanne? "Kema kinsan ke nakeso dake nake son karashe rayuwata amma a bisa kaddara da kuma dalilin rabo yasa alakar mu da hamrah ta kai haka, zainab ina nan a kan baka ta har yanxu ina sonki nasan kema kina sona ko?....." Uhmmm nayi shiru bakina akwai goro #Aysha b. Ina mai farincikin sanar da ku ni marubuciyarku Ayshab, nayi attending fashion school ta @malaabis_by_mymz inda nai syllabus dina a yanxu haka kuma nake dinki, mafi yawan wadanda ke garin kano nasan kunsan dinkunan malaabis base na tofa ba kira na gareku masoyana musamman mutanen garin kano, ku kawo dinku nan ku, be it ankara, or material that will look like ready to wear i assured you wont regret in shaa Allah, ur fabric re in the right place n safe.. Patronize ur writer show love And dont forget follow my IG page @Ayshabnaseer @Aysha_bee_couture 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 41: Breakup Kema kinsan ke nakeso dake nake son karashe rayuwata amma a bisa kaddara da kuma dalilin rabo yasa alakar mu da hamrah ta kai haka, zainab ina nan a kan baka ta har yanxu ina sonki nasan kema kina sona ko?....." Ta zuba mishi idanunta batareda ta ce mishi komai ba, ganin da tai baida niyyar fadin komai ya sakashi fadin "Yanxu me kikai deciding" ta lumshe idanu taja ajiyar zuciya, batareda tasan me zata ce mishi ba gabadaya kanta ya kulle, sai kuma yace "zainab let's end everything" Kwarewa tai jin kalaman nashi, sai kuma ta dan saita kanta dukda speed na heart beat dinta be ragu ba sema karuwa dayayi da tsananin gudu, yayi shiru yana kallonta, da dumbin tausayinta cikin ranshi, kiyi haquri zainab amma ina ganin hakan shi ne mafita, ya miqe itakam tana nan, "anya wannan faruq dina ne?" ma'assalam taji ya fada tai saurin tashi tasha gabanshi, anya kaine faruq din dana sani, ina duka alqawarukan mu, ina batun soyayyarmu, ina kuma batun auren mu, duka kayi watsi da komai" Ya hadiyi yawu sannan a hankali ya zagayeta ya tafi, ta zube kan guiwarta "ya ilahi what's all this" Ko zatai expecting komai daga faruq batai expecting kalmar rabuwa ba, A nashi bangaren ya tabbata suyar da zuciyarshi ke mishi ya fi wanda nata keyi mata, "soyayyar dayake mata ce yasa baze jure kallanta cikin bakinciki haka ba, ko a baya ta sadaukar da abubuwa sosai saboda shi, tayi mishi halacci, bata taba cin amanarshi ba, ta dauki duka hope dinta ta saka a kanshi, to mene amfaninshi indai zaina saka ta kuka, mene amfanin soyayyar da bazata sama mata farinciki ba, bayaga wannan ma dalili na biyu shi ne, shi yanxu baida abubuwan da zasu sama mata farinciki, shi be kammala makaranta ba, baida certificate, bashi da aikinyi ta ina ze fara aurenta ya kula da ita da hamrah, baze iya sama mata jin dadin daya kudira ba, he lacks and na uku kuma, danginshi basu sonta tayaya ze so kanshi yaa jefata inda yasan ba dadin zaman zataji ba saidai tayi ta haquri ana cutarta Wadannan dalilai dama wasu suka sakashi haqura da ita a ranshi bawae dan baya sonta ba, tun komawarshi babu abinda yake se fafutukar yadda ze kula da ita yadda ze dawo ya aureta amma dady ya bijiro mishi da zancen hamrah, babu yadda zeyi in yanason auren zee kuma idan yanaso dady yayi supporting dinshi financially ya bashi abinyi sedai ya aureta, sanda akai auren kuma yaga batada wata matsala, zaman nasu sai ya zama babu hayaniya saboda tana sonshi sai take avoiding duk wani abu da tasan bayaso.. Zainab tana komawa gida ta sulale kan gado a take ta soma jin zazzabi da ciwon kai, ta jaawo blanket ta lullube jikinta sai can dare bayan isha'i ya kwankwasa kofar dakinta, ta bude idanunta da sukai mata nauyi bibbiyu take gani dukda a kwance take amma jiri takeji, ta maida idanun ta rufe, ganin da yayi babu alamar akwae mutun cikin dakin ya sakashi bude kofar ya shiga, duhu ne cikin dakin dan haka ya nemi switch ya kunna fitila, haske ya gauraye can ya hangota ta dunkule guri guda cikin blanket, yayi saurin karasawa gareta "Zainab mene ya sameki?" Baki da lafiya ne? Ya tambyeta Bata iya amsashi ba sai kallonshi da tai ta kuma maida idanun ta rufe, ya fita da sauri ya nemi mint ta taimaka mishi suka fito da ita aka kaita asibiti saida tai kwanaki hudu a kwance kamin aka sallameta, to dama tayiwa Assiddique magana tun jiya, dayazo dubata tace "yayana dan Allah ka barni naje naga Anty hawwer zanfi jin dadin zama a can din" Dukda beji dadin hakan ba amma sai yace "shikkenan ba matsala in shaa Allah zan hada komai na tafiyarki in aka sallameki sai ki wuce" Ta kammala hada komai na tafiyarta, driver ya kaita har airport, bata dadeba jirgin nasu ya tashi zuwa birnin madina, duk wani abu data sani zai tuna mata da faruq sai data tattareshi ta watsar, hatta frame din daya bata da duk wasu takardu ta kone, hakama cikin wayarta ta goge duka hotunanshi tayi taking deep breath sannan a hankali ta furta "May Allah S.W.T make it easy on us" Jirginsu ya sauka lafiya a birnin madina, suka zauna sukai magana sosae da Anty hawwer, zainab ta sanar da ita "na rigada na haqura da faruq, idan so cuta ne to haquri magani ne, time heals every wound, haka nan ba komai ne mukeso muke samu ba, kuma ko ba komai na koyi darrusa zamana da faruq" Anty hawwer tace "kina ganin kin yafe ma faruq har cikin ranki" Zainab tai murmushi sannan tace "wanann ne kuma ban sani ba tukunna" "Ina mai baki shawara daki yafe ma faruq saboda hakanne kadai zai sa ki manta da komai, rikeshi cikin ranki will do more damage kema ze shafeki ne, amma da zaran kin yafe mishi zakijiki sakayau, daga nan sai ki bama Assiddique dama" Zainab ta daga ido ta kalli Anty hawwer "Ke kike fadin haka da kanki" Tace "yes Amma kinsan mijin mint ne ko Tace "and so? Se mene dan mijin mint ne, ai bawai yana nupin dan ita daya aka halicce shi ba Zainab ta girgiza kai nikam gaskiya banajin ma inasonshi, Anty hawwer tace "shiyasa nakeso ki yafe wa faruq, hakanne zai baki damar cigaba da gudanar da al'amura har ki bawa wani dama, amma muddin kina rike dashi a ranki to bazaki cigaba ba" "Duk wannan abin da kikeyi Anty shifa bama cewa yayi yana sona ba" "To tayaya ze fada kuwa kin kashe mishi kwarin guiwa kin nuna mishi duk duniyarki babu ya faruq, in yayi magana ma sharewa kikeyi".... Zainab na kwance a falourn Anty tana kallo, wayarta tai ringing, ganin Assiddique ne sai taji kamar kar ta dauka sai data kusa tsinkewa sannan ta dauka da sallama, ya amsata muryarshi cikeda annashuwa sannnan yace "na dauka zee ta manta damu ne, tunda kika tafi kuma ko er waya" Tayi shiru batace mishi komai ba "yace yaushe zaki dawo ne ko kinyi resigning ne ban sani ba" In shaa Allah nan bada jimawa ba, yace to Allah ya dawo dake lafiya ina ta neman cook amma har yanxu na gaza samun ya ke, sai na fahimci ke din ke d'aya ce" Tayi murmushi a takaice sannan tace "ya Ayyuka yayana" "Gasu nan sunsha mana kai sai hamdala, ina tunanin gobe in Allah yaso zanje egypt, so ki cigaba da min addu'a" Tace to Allah ya tsare... Watanni daya bayan nan, Assiddique yaga zee bata da niyyar dawowa gashi zaman nasu da mint babu dadi gabadaya bejin dadin zaman gida, kullum aikinta complain beyi kaza ba beyi kaza ba, ko kuma ita dama dole akai mata ta dawo in be somta ya sawwaqe mata, har ya gaji da jin ita dole akai mata Zainab ta fito a kitchen din bayan kammala hada musu lunch ta shiga daki tai wanka ta fito ta tadda Anty a falour wacce take dauke da juna biyu na kusan watanni shida, tare sukai lunch harda nihal da tayi wayo sosae yanxu, da la'asar ta saka mata hijab tace da anty safiyya sun tafi masjid dan sunyi missing zuhr, A kafa suka je kuma suka dawo, zee tai turus a kofar gidan Antyn ya mata murmushi mai taushi sai ta samu kanta da kasa mayar mishi its short though not too short lol 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 43: Result Kashegari kuwa likitan har gida yazo dayake Assiddique yana hutu a yau din, Duka suna falourn su ukun, mint na aikinta shikuma ya saka zainab tayashi duba wasu designs, Akayiwa likitan iso ya shigo falourn bayan an nemi izinin Assiddique, ya shigo sukayi musabiha Ya zauna ya ciro takardar ya miqawa Assiddique, yusuf ya karba yana jujjuyata, zainab kuwa ta kurawa takardar ido, ji take kamar ta fizge ta bude,,, Assiddique ya bude takardar sai ya kurama result din ido sannan ya dubi zainab, ta hadiyi yawu, ya miqa mata tasa hannu ta karba, a hankali wani murmushi ya subuce mata, dama jikinta ya rigada ya gama bata hakan Tashi likitan yayi shima Assiddique ya bishi yi mai rakiya, mint ta juyo ta kalli zainab tace "tashi ki bani guri" da mamaki zainab ta dubeta hannunta rike da takarda sai kuma ta miqe ta bar gurin badan tsoro ba saidan bata muradin wani tashin hanakli yanxu, ta karasa daki ta kira Anty hawwer tana sanar da ita abinda ya faru, zainab tace "Anty kinga result din wai ya bayyana am AA" anty tace masha Allah zee tace "gaskiya nikam Im confused" Tayaya mutun zeyi test sau biyu kuma result yana differing, anya baki ganin ya yusuf ya saka son zuciya cikin lamarinshi, nifa dama tunda suka dibi jinina naji jikina ya bani result din dole ze fito yadda suke so ne," Anty hawwer tace "hakane abin is confusing gaskiya amma banaso ki nuna mishi baki yadda da result dinshi ba, ki bari in kinzo kano muje na rakaki kiyi inda munsan baza'ayi manipulating result ba, kinga dole cikin biyun nan wani sai ya sake maimaituwa, either na faruq ne ba daidai ba ko kuma na Assiddique" zainab ta gyada kai cikeda gamsuwa Zainab ta tashi as early as always domin hada mishi breakfast, bayan ta kammala ta kai mishi falour, already ya kammala shiryawa,mint ma ta fito, batayi musu ko sallama ba ta wuce hanyar da zata sadata da babban falour tai tafiyarta, zainab ta zauna sosai itama tai serving nata lokacin shikuma ya soma ci, Ba al'adarshi bace magana idan yana cin abinci amma wannan karan yayi niyyar hakan, yace "me kike gani gameda alakarmu" ta dago tana dubanshi ta karasa hadiye abincin sanann ta tsame hannunta daga cikin abincin gaba daya "Zainab inaso ki zama matata, dagaske wannan yusuf din ya fada soyayyar zainab, kuma aurenta zaiyi" Ta dauki ruwa da hanzari ta kurba ta ajiye, batayi tsammanin maganar soyayya da aure daga bakinshi dukda tasan yana sonta din, amma shi baze duba alaqar dake tsakaninta da matarshi bama, Ta tattaro duka confidence dinta tace "kayi haquri yayana amma ni yanxu karatu nakeso na dora ba aure ba" Dukda yaji zafin maganarta amma sai yayi controlling kanshi ya cigaba da cin abincin nashi, amma gabadaya tunani ya cika kanshi "Tayaya za'ace the able Assiddique wai ya buda baki yace yana son yarinya amma ta bashi haquri" y tashi tsaye abinshi sannan ya wuce Zainab ta bishi da kallo tana tunanin mene ma ya hana ta amshi soyayyarshi, bayan shidin babu abinda ya rasa saidai tawaya irin ta dan adam da kowannenmu yana da fault, Inaso nayi karatu mai zurfi kodan na nunawa faruq nidin wata ce kuma na sakashi yin nadamar abinda yayi, im yearning for success badan nawa ra'ayin ba sai dan inaso faruq yaji bakincikin ganina as a successful person,,, Da kudaden aikina zan tara na koma makaranta Sati daya bayan nan, Assiddique yace zee ta shirya sunada tafiya jibi tace dashi to, Birnin UK jirginsu yayi landing, zee ta fito tana shan iskar dake kadawa mai dadi haka suka wuce masaukinsu, tana mamakin yadda yasan mutane a kasar, a ranar ita daya ta kwana a apartment din daya sama musu dan shikam ya tafi wasu ayyukan, sai kashegari da sassafe ya dawo ya chanja kaya ya dan miqe, A yammacin ranar yace ta shirya su fita, aikuwa ta shirya cikin Abaya mai kyau, zagayawa yayi da ita makarantun dake kusa dasu sannan yace "zainab ki zabi makarantar da zakiyi karatunki ni zan dauki nauyi" Ji tayi kamar ta daskare a gurin ta washe baki cikeda jin dadi, Kafin kace me Anty ta turo credentials dinta, wasu universities din basa offering msc a course dinta dan haka suka nema a oxford, ji take kamar a mafarki, tanajin labarin oxford yau gata zatayi karatu a ciki, Assiddique na son cika mata burinta, Sanda suka koma gida ta nemi zuwa kano na kwana biyu ya barta dan shima ba zama zaiyi a Abujan ba wata tafiyar gareshi, Zee taje gidan Anty hawwer cikin dumbin farinciki, itama Antyn murna take tana godiya ga Allah sai taji duk hankalinta ya kwanta da Assiddique din, aikuwa kashegari suka wuce Asibitin akayi ma zainab test din, yace ko su dawo da magrib su karbi result ko kuma gobe, zainab bata iya jira har gobe ba taje ita daya ta karbo ta dawo Tun a hanya takeson budawa amma tanajin gabanta na faduwa, ta haqura saida taje gida sannan ta miqawa Anty Tasa hannu ta buda sai me? AA pattern a karo na biyu, Anty ta girgiza kai, ashe dai Assiddique ne mai gaskiya ta miqawa zainab tace amshi Zainab ta amsa tana kalla, haka nan taji wani abu ya taso mata gameda ubangidan nata, in banda abinta ma taya zata soma tunanin zeyi manupulating result amma ya akayi wancan da sukai da faruq ya bayyana AS Ta rasa amsa ta ninke takardar tana yima Anty murmushi itama maida mata tayi dan ta gane manufar murmushin, "Kar ki sake rejecting dinshi idan ya sake zo miki da maganar soyayya" zainab ta gyada kai a gamsashe, Ta koma Abujan kamar yadda tai niyyar amma Assiddique be cikin gidan daga dukkan alamu baima dawo daga tafiyar da yayi ba, hakama mint bata gidan, ta zauna a gadon tana murmushi "lallai burikanta suna gab da cika" Basu hadu da mint ba a ranar sai kashegari da safe, zainab ta kaima mint abinci sanin da tai mai gidan bai nan, ta zabga mata harara itakuwa zainab ko a gefen slippers dinta Saida ya sake sati sannan ya dawo, haka nan zainab taji tana zumudin dawowar tashi bama kamar dayayi mata tex personally ya sanar mata da dawowar tashi sannan ya dora da ina fatan zan samu tarba mai kyau" Hakan yasata zuwa inda tafi k'wari ta zage kuwa ta mishi sabbin dishes wadanda ta tabbatr zaiji dadinsu dan indai fannin cikinshi ne ta gama gane wannan bangaren, Mint sai shige da fice take itama tun sanda ya sanar da ita dawowar tashi, itace zuwa pedicure manicure, gyaran jiki gyaran kai duka dai, Ya sauka cikin koshin lpia, saida ya biya gidan yallabai tukunna ya wuto gida, Gidan yayi shiru sai karan na'u'rori, ko wanne glass sai sheki yake, ga kamshi mai sanyi na fita daga kowanne bangare na gidan, yayi smiling sanda ya shigo, bai tsaya ko ina ba sai falournshi na kasa bayan ya wuce main falour, ya zauna kan kujerar Zainab tunda taji alamun zuwanshi ta tashi ta dauko hijab ta saka sannan ta sauko ta wuce falourn, daidai shigarta mint ma ta shiga, Suka hada baki gurin fadin "Sannu da dawowa" ita zainab da hausa ta fada mint kuma da yaren nasara "welcome home" Ya kalli zee sannan yace "yi serving pls" mint ta dan bata rai "Na dauka zakai shower ne" ya girgiza kai wannan yafi muhimmanci beside mura ke neman kamani" Tace ayyah sannu.. zainab rage mishi gudun AC din, zee ta dau remote ta rage, Tayi gurin abincin tana kokarin serving mint tace jeki kawae zanyi serving" zee taji babu dadi a ranta amma ya ta iya sai ta miqe, Yace "a'a barta tayi mint, nafison yadda take plating" mint ta hade rai Bai kula ba Ya cigaba da fadin "she plate so nicely, it looks impressive always" Mint tayi cilli da farin plate din dake hannunta, ya bi tiles ya tarwatse Ta miqe ta kalli zee dake tsaye "fita a nan" zee ta juya tana tabe baki Ya dan hade rai sannan ya furzar da iska waje "ya ilahi" ya fada a hankali yadda zataji, sai ya miqe ya wuce sama ya barta gaban abincin, Takaici ya sakata daukan bababn warmer din ta fita dashi ta bawa securities, wasu kananu kuma duka ta zubar a waste bin..... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 42: Back to work Ta gaidashi ya amsa sannan ta shiga ta mishi iso, ya shigo bayan ta mishi iso, zee ta tarbeshi da abubuwa kala kala, harda abincin da tai dazun data ajiyewa uncle, rabonda yaci abiincinta ya dade hakan ysa ya sauka ya baje, zainab da anty hawwer suka bashi guri, suka bar mishi nihal, tare suka kwashi garar abincin tana mishi surutanta na yara yana biye mata, Bayan ya kammala ya nemi yin magana da Anty hawwern ya rage su biyu ne a falourn, "Alfarma nake nema gurinki" tai shiru tana saurarenshi itakuwa wacce irin alfarma mutun kamar Assiddique zezo nema a gurinta "inda hali zanso idan zan wuce gida nigeria gobe na tafi tareda zainab ta koma bakin aikinta ina ganin zama hakan ba dadi ai" Anty hawwer ta nisa kamin tace "wannan gaskiya ne amma kaga yanxu jikin nawa yayi nauyi shiyasa bazanso tai nisa ba tana taimaka min da wasu abubuwa, koda zata koma aikin sai in Allah ya saukeni lafiya ina fatan zakayi mana haquri kayi mata wannan alfarmar" Baiji dadin maganar ba amma da alama baida wani choice yace "shikkenan ubangiji Allah ya saukeki lafiya ya kaimu lokacin" ta amsa da Amin sannan tace bari na turo ta ku gaisa Zainab ta kalleshi da tausayawa, ta sani sarae ya zafin so yake, kuma tasani alaqarta dashi bame yuwuwa bace a yanxu dai bata gama fidda abinda ya dace tayi ba amma babu batun soyayya ko aure a ranta nan kusa, Ta zauna kan kujerar tana yin murmushin dabai kai zuci ba, shima ya maida mata a tausashe, "Kin dai qi aikin zainab, ko ni ake gudu ne?" Tai smiling nervously "Ko daya" ta bashi amsa a takaice, naji abinda ya faru tsakaninki da faruq dagaske ne you two broke up? Who told you? Ta tmbya yace my driver but why mene ya faru? Taji wani tukuki ya bugi zuciyarta idan akwae abinda ta tsana yanxu bai wuce taji wata magana dangane da faruq ba, how dare he walked away just like that without any explanation, Ganin da yayi mood dinta ya sauya ya sakashi chanja akalar maganarshi, inaga zan wuce, sai gobe zan biyo kafin na tafi in shaa Allah, ta jinjina kai sannan ta bishi da kallo ya tashi ya fita batareda ta mishi rakiya ba.... Anty hawwer ta zaunar da zee trying hard to convince her, ki yafemishi zainab, wannan shi ne karo na karshe da zan roki ki yafema faruq ko dan nutsuwar ruhinki, u'll feel free Zainab tace "Anty bana tsallake umarninki, bakuma na qin karbar shawararki haka bana bijirewa duk abinda kikazo min dashi amma wannan karan banajin zan iya, idan nace na yafe mishi nayi miki karya ne kawae iya fatar bakina bawae har zuci ba wlh, ki saka kanki a matsayi na, tayaya zakiy tunanin zan iya yafe mishi, farko he left da Alqawarin zai kirani, amma bai kiraba har shekara ta shude, na rarrashi zuciyata ina mishi tanadin kaina, duk tsayin jiran danai finally na hadu dashi, kinsan yadda naji kuwa dana ganshi, tmkar naje na fada mishi duk tsayin kewarshi da nai na nuna mishi duka notes din dana dinga rubutawa idan nai kewarshi, amma hakan bazeyu ba sakamakon baida lpia, kinsan tsoro da firgicin dana shiga kan kar na rasashi, all the sleepless nights n tiring days, and lokacin da za'a mishi aiki, i spent almost all my night kan dadduma ina kuka ina roka mishi sauki gurin Allah, duk saboda ina sonshi, i endured almost everything, but what? He came back am so anxious, exicited and happy to meet him, sai kuma naga wai yanada mata harda da, duk wannan bai sa naji a raina zan rabu dashi ba, naje na sameshi muyi magana hoping zai ce min zainab kiyi haquri, i still love you n i will marry you, amma kash, sai yace dani muyi ending komai, kuma batareda yayimin wani bayani ba ko ya bani kwakkwarar hujja, kawae yayi tafiyarshi ya barni batareda nuna kulawa ba" Ta karashe tana goge hawayen dake zarya a idanunta, "bai cancanci yafiya ta ba Anty, zan nuna mishi nafi karfinshi i will do everything in my power to become successful, i'll make him regret" ..... Zainab ta cigaba da zama a gurin Anty, har watan haihuwarta ya kama a cikin watanni ukun nan Assiddique yakan ware lokaci yazo ya ziyarci zee dukda busy schedules dinshi, A daren da Anty zata haihu, ranar zee bata kwanta da wuri ba, tana falour tana kallo kawai sai ji tai ana buga kofar dakin Antyn, ta tashi sanin da tai uncle muzakkir ya fita ba dadewa, a bakin kofar ta tadda Anty cikin mawuyacin hali, Zainab ta fita ta nemi waya ta kira shi, Allah yasa yana kusa, A asibitin ta kwana sai gabanin Asuba ta santalo yaronta, murna ba'a magana, bayan an tabbatar ita da jaririn duka lafiya suke aka sallameta, Dukkansu sunyi mamakin haihuwarta a lokacin sakamakon E.D.D dinta bai cika ba, amma likita ya tabbatar musu babu wani abu, Bayan anyi suna yaro yaci sunan Abbansu Anty wato muhammad suke kiranshi Sanda Anty ta cika kwanaki arba'in suka shirya dawowa gida, dama tun kafin haihuwarta sunyi shawara da uncle muzakkir din zasu koma nigeria tunda karatun da suke duka sun kare kuma akwai gida a can din nasu, saidai wasu business daya fara a madinan zai na zuwa time to time shi kadai, Haka suka tattara suka bar madina suka dawo gida nigeria, dadi kamar Assiddique ya zuba ruwa a kasa ya sha jin sun dawo yasan zee ta kusa komawa bakin aikinta, Rannan kamar Almara tana daki tana shirin zuwa gidan zakiyya wacce itama takeda ciki ya soma girma sannan su wuce gidan kubra suga yaranta twins data haifa, wayarta tai ringing ta dauka da mamakin ganin sunan Assiddique jiki, yace da ita yana garin ya kawo mint gida tayi mishi kwatance yazo Mamaki tayi sosai takuwa yi mishi kwatance aikuwa babu dadewa sai gashi da wasu securities ya barsu a waje, zee ta mishi iso ya shiga, Sun dan taba er hira sannan yake sanar da ita sai nan da kwana biyu zasu koma kuma yana fatan in zasu koma ta shirya su wuce tare, tace dashi in shaa Allah, Bai wani jimaba ya tafi, A daren ranar da uncle muzakkir ya dawo ya sanar da ita lallai lallai ta shirya ta koma bakin aikinta idan su Mint zasu koma ta bisu su tapi tare, batayi wani musu ba dama itama din tanason komawa aikin dan akwae abinda ta kudura Ta hada duka kayanta, shi da kanshi yazo ya dauketa, sannan ya shiga ya kira su mint, ko kadan mint bata san tareda zee zasu koma ba, Motoci sunyi convoy mint da Assiddique suka shiga ta biyu yayinda zee ke cikin ta uku, saida suka isa airport sannan zee ta fito mint ta ganta, Mint Ta kalleshi sannan tace "itakuma daga ina?" Yace "aikinta zata koma", zee tace "ya mint kinyini lpia" tayi mirsisi taki amsawa Haka sukai tafiyar kowa da abinda yake sakawa cikin ranshi, kan kace me sun sauka Kwanaki biyu bayan nan, zee ta kammala mishi gurkinshi sannan tasa waya ta kirashi yace "kawomin office bazan samu zuwa gida ba", ta shirya ta nemi driver suka wuce office din, yana cikin office din FC (food court) ya biyo duba ayyukansu ta shiga ta ajiye mishi kan wani table karami dake gaban sofa, ya fita itakuma ta soma serving bai dade ba ya dawo amma wani mutun na biye dashi a baya yasha coat da wata kit a hannunshi, Suka zauna suka soma cin abinci su biyun har zata fita yace tai zamanta, bayan sun kammala dayan mutumin yace "ita ce kenan" ya gyada kai eh bismillah Zainab ta soma kallonsu daya bayan daya yayinda mutumin ya bude kit dinshi ya ciro kayan aikinshi, Assiddique yace "bashi hannunki (cubital fossa) zainab" ta kura mai idanu tana kallon allurar dake hannun mutumin Mutumin yace "karki tsorota, ba wani abu bane sample na jininki zan diba kadan zamuyi test ne" kamar kar ta miqa hannun amma duk sun kafeta da idanu haka tanaji tana gani ta miqa ya zuqi jininta cikin syringe. Bayan nan Assiddique ya hana zainab komawa gida yace yau tare zasu koma, tace "girkin dare kuma fa" yace "ai a nan zaki zauna a hada dinner dake sai muyi takeaway" tace mishi to Ya tafi ya barta a restuarant din sukai aiki tareda ma'aikatanshi, bayan magrib yazo ya dauketa suka koma gida tare, Mint na tsaye a bolcony tana jin dadin iskar dake kadawa, sai taji alamun dawowar mai gidan nata, ta dan zagaya ta daya bangaren da zatafi ganinshi da kyau, bisa madaukakin mamakinta sai ganinsu tai a tare su biyu dayake itama bata dade da dawowa daga gurin nata aikin ba,, haka nan taji wani tukuki ya mamaye zuciyarta, a take tsanar zainab ta ruru cikin ranta, Dama har akwae macen data isa Assiddique ya kalleta, ai ta dauka babu ita, ta dauka duk fadin duniya ita kadaice ze kalla, amma da yanayin kallon dayake ma zee yasa taji ta tsani zee din amma sai ta danne zuciyarta da fadin "aiki kurun take mishi," ta yarda akan hakan dan gani take babu fa wata da zata iya samun gurbi a zuciyar star dinta domin gani take ta mamaye ko ina... Zainab ta dubi Assiddique a sanda yake cire hadadden covered shoe din kafarshi "Yayana genotype za'ayimin ne shiyasa aka dauki blood sampls dina ko?" Yayi nodding,, ta tabe baki sannan ta wuce nata dakin... 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 44: wedding bell Abinda mint keyi yana kara bakanta ta gurin Assiddique ne kawai shikuma yana karajin son auren zainab har ranshi Shirye shiryen makarantar zee ya kammala komai akayi yana updating zee saboda ta zauna cikin shiri,, ranar tafiyarta yazo, a lokacin baya nan dan haka dole ita daya ta hau jirgi ta tafi, duk wannan abin da ake mint bata san karatu zee ta tafi ba, sai da Anty siyama ta kirata take sanar da ita, karkuso kuji zagi kala kala a bakin mint nan fa hankalinta ya soma tashi ta fara tsinkewa da lamuran mijin nata akan zainab Zainab kuwa batasha wahalar gane abubuwa ba sam, hakama a cikin makaranta da taimakon GPS, tsakanin Apartment dinta da school din babu nisa hakan yasa bata buqatar Abin hawa, ita kanta ma tafi son tafiyar da kafa Assiddique ne ya kama mata tun kafin ta zo room and falour ne da kitchen da toilet a cikin room din, cikin estate yake, Sukanyi waya da Assiddique din sosai in baya aiki wani sa'in kuma suna dadewa basuyi ba idan ayyukan suka tashi, Haka ma su Anty duk sunayin waya, fannkn karatunta kuwa zee ta maida hankali kan MSC dinta dan ma babu wani stress a farkon Cikin satin nan zee ta lura sun dan jima basu gaisa da Anty ba dan haka ta dauki waya ta kirata, Antyn ta dauka amma daga ji inda take akwai hayaniya, zee tace "Anty kin fita ne" tace "a'a zainab biki akeyi, wai dannar kirji akazo" Waye za'ai wa kishiya, zainab din ta tambaya Anty tace "Abban nihal ne yake angwancewa gobe daurin aure" Zainab ta kusa daskarewa a gurin "aure fa kikace Anty" Anty tace "eh zainab aure fa, Zainab bata sake yarda ba saida ta kira Zakiyya itama ta tabbatr mata da hakane, zainab ta zabga tagumi kai kace ita ce za'aiwa kishiya, abin ya tsaya mata a rai, zataso taje taga wacce ce wannan ta auri mijin yayarta Bayan komai na biki ya lafa zainab ke tambayar Anty hawwer wai wace ce ya aura, tayaya uncle muzakkir zaici amanarki yayi aure Anty hawwer tace "Dan ya kara aure bawai yaci amanata bace, Allah ne ya halasta mishi kan me ze haramtawa kanshi, ki dena wadannan tunanin zainab, idan namiji ze kara aure wlh ko zaki hada sama da kasa indai yayi niyha sai yayi, haukan da mata keyi ma shi ne ke kara tunzura maza kan lallai se sun karo ma ko dan su gwada ma mace karfin ikonsu, idan kinndaga murya kin tada jijiyar wuya, ki sani kin ragewa kanki mutunci ne a idonshi amma da zamu gane mu kwantar da hankalinmu, shi fa komai a rayuwa Allah ya rigada ya rubuta, idan Allah yayi mata hudu Abban nihal zai aura zainab a rubuce yake tun ran gini tun ran zane, tabbas akwai ciwo dama dole akwae ciwo amma dole haka mutun ze danne yayi addu'ar Allah ya hadashi da abokiyar zama nagari, mun karanta wannan abin cikin Alqur'ani, meyasa zan jahilci lamarin, fatanmu Allah ya bamu jarrabawar da zamu iya ci" Zainab ta gyada kanta cike da gamsuwa haqiqa maganganun Anty haka suke Zainab na kitchen tana kallon fool din dake bayan gidan nata, takanga mutanen dake estate din suna zuwa zama itama yau sai taji muradin fita gurin ta zauna, Ta kammala wanke abinda zata wanke haka nan taji muradin dora abinci yau dan takan jima batai girki ba musamman breakfast da dinner, dan lunch mostly a school takeyi saidai ranakun da bata fita ba Rich Faten dankali tayi ma'ana yasha kayan dadi, kama daga kifi, naman kaza, da ganyayyaki masu dadi da kamshi, Ta ida ta sauke ta dauka ta kai fridge ta saka, haka nan taji tayi kewar Assiddique, ta sake kallan falourn, ko nawa ya kashe mata haka, tai murmushi sannan ta dau littafinta da wayarta tayi kofa, Tana bude kofar shima yana karasowa, ta tsaya tana jujjuya kwayar idanunta dan tunani take mafarki ne, ya sake matsowa yace "Barka da yau zainab" Muryarshi ce" taji zuciyarta na rada mata, A take murmushi y samu gurbi kan fuskarta, sai ta matsa daga bakin kofar ta koma ciki shima ya bita ya shiga ya zauna kan kujerar, Abincin t dauka ta sake sakawa kan wuta sannan ta zauba mishi ta kawo ta dakko ruwa da lemo ta ajiye mishi Ya sakko kasa, itakuma ta koma kitchen din ta zuba nata Bayan sun kammala cin abinci tace "yaushe kazo?" Yace "tun jiya" . Nazo ganin gidan da zamu zauna ne, na bada ayimin aikinshi" Da rashin fahimta ta dubeshi gidan da zasu zauna shi da wa? "Ko bazaki aureni ba zainab?" Ya fada kamar zeyi kuka, haka nan dariya ta subuce mata sai tasa gyalenta ta rufe fuskarta Yace "to tashi maza ki shrya mu fita" tace yayana karatu zanyi fa, yace bazamu dade ba Babu nisa da inda gidanta yake can sosae, sai gasu gaban wani babban building, da alama gida ne ake renovating dinshi kuma ake sake mishi fasali, yace wannan ne gidan da zamu zauna in shaa Allah zainab ni da ke matsayin mata da miji, Ta kara daga kai ta kalli gidan, wannan ko gidanshi na nigeria ma ai Albarka Wasa wasa soyayya mai karfi ta soma shiga tsakanin zainab da Assiddique koda dama wancan karan ma ita ce taqi bashi hadin kai, idan makaranta zataje tare zasu fita ya kaita, idan karatu zatai shima sai ya debo taakrdu yana nashi aikin tana nata karatun Sai da yayi sati daya sannan ya soma shirin komawa nigeria, gabadaya zee taji babu dadi, "yanxu sai yaushe zaka dawo" yace "im not sure amma nan kusa in shaa Allah, zanje gurin Abbah jabir na mishi maganar mu" Ta sunkui da kai cike da kunya, haka tanaji tana gani ya tafi, Ashe dagaske ne da hausawa sukace shi SO tsuntsu ne, bata taba tunanin zuciyarta zata iya samun gurbin wani mahaluki ba bayan faruq amma da haquri da lokaci gashi komai ya wuce gabadaya sai taji zuciyarta ta sassauto akan tsanan faruq bawai kuma soyayya ba amma kuma ta rage jin haushinshi, A bangaren mint kuwa ta lura mijin nata gabadaya ya sauya mata dakyar magana ke hadasu idan ma yana garin fa kenan dan taga ya tsiri tafiyu iri iri baya ma cika zama a gidan, ta kudurce a ranta koda zainab ta dawo to bazata dawo mata gida ba, ya nemi wata cook din amma ba zee ba, Assiddique ya sanar da yallabai maganar zainab, yallabai ya zuba mishi ido "Ita yarinyar ina ce a karkashinka take aiki, kuma ita kakeso ka aura" yace eh yallabai "To ya maganar genotype kuma" yace munyi yallabai babu wani matsala AA ce Hakan yayi wa yallabai dadi yace "Amma ka gyara tsakaninku da minnatullahi kafin ka kawo wata sannan ka zauna ka tsara ayyukanka kafin ka auro er mutane ka kasa kulawa da ita" Ya gyada kai cike da ladabi to yallabai Gaskiyar yallabai ne shi ba mutun ne da zai iya rike mata biyu ba a halin da yake ciki dan haka dole ne a samu mafita kar ya tauye wa wata hakkinta, Yallabai da kanshi yaje ya samu Abbah jabir suka tattauna magana, a take aka tsaida biki bayan ta kammala wannan shekarar kafin ta juya se a daura sannan ta cigaba, wannan abu yayiwa Abbah jabir dadi sosai, yallabai ya nemi Abbah jabir yayi shiru gameda maganar tukunna har sai Assiddique ya shawo kan matarshi da kanshi... Yusuf ya samu minnatu tana aikin nata na kullun a gaban system din da har ta soma kashe mata idanu yanxu in zatayi aiki sai da glasses Ya zauna, ta dan kalleshi ta watsar ta dauka bukatarshi ta kawoshi ammma sai taji yace "minnatu magana zamuyi, in Allah ya yarda nan da watanni biyar za'a daura min aure" Idanuwa ta zaro waje sakamakon yadda maganar ta daketa, "Aure, Aure, Aure fa kace yusuf" Yayi blinking idanunshi "Hakane" "Kai dama wai har ka isa ka kara aure? Har akwae macen da ta isa nai kishi da ita, tukunna ma wacce karyar ce take bimin miji" yayi shiru bai amsata ba sai ma maida hankali dayayi ga TV Amma dai kai kasan wlh nafi karfin wukaqanci, kuma kasan dai babu macen data isa ta shigo min gidana Kawai sai tayi daki fuuu tana kuka, nan da nan ta kira Anty siyama a waya ta sanar mata tana rantse rantse be isa wlh yayi aure ba, tafiya zanyi na bar mishi gidan Anty, kokarin kwantar mata da hankali take amma ina ita kawai gani take yaci mata mutunci ne Dakyar Anty ta shawo kanta ta fasa tafiya Sai ta dauka tsokanarta yakeyi ganin ya cigaba da Al'amuranshi dan haka taje ta sameshi "Na yarda kayi aure amma kan sharuda guda biyu" 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 45: forgive n forget Batareda ya kalleta ba yace "fadi sharudanki" Tace "sharadi na farko bazaka kawo amaryar ka wannan gidan ba, saidai ka nema mata wani gidan dan bazeyu ta zauna min a gida ba" ya jinjina kai yana jin karfin hali irin na mint yace "na biyun kuma fa" Tayi rolling idanunta sannan tace "ka nemi wata cook din ka sallami zainab bana so ta dawo bakin aikinta" ya gyada kai yana tabe baki Shikkenan naji, amma ki sani na yarda da sharudanki ne badan ina tsoronki ba bakuma wai dan sai na yarda ne auren ze yu ba, a'a saboda masalaha tsakani na dake ne da kuma kyautatawa ta zaman tare wacce na lura ke sam baki san da ita ba, kuma inaso ki zauna ki gyara halayyarki indai ba so kike amarya ta kwace miki ni ba dan saura kiris ma Maganar zainab dama can banine na kawota gidan ba, kece kika nemi tazo saboda bazaki iya da hidimar mini girki ba, gida kuma naji bazan hada ku ba Mint ta jima tana juya maganganunshi musamman inda yace "ki zauna ki gyara halayyarki" hakan yasa ta soma zargin ko tana da wata mummunar halayya ne, kuma me kyautatawa take nupi a zamantakewa irin ta aure Zainab t kammala shekararta ta farko ta dawo gidan Anty dan dama jira kawae take ta dawo a hau mata gyara, itace sha wancan sha wannan duka dai, Rannan zainab tana daki tana bacci ta jiwo hayaniya cikin babban falourn Anty hawwern ta tashi ta dubi kanta a madubi, tasa hannu ta shafi skin dinta ita kanta burgeta skin din keyi, tayi kyau ta murje sosai, yau saura sati biyu cif a daura aurensu fa.... Anty ce ta turo kofar dakin ta shigo tace "saka hijab ki fito ku gaisa" zainab tace Anty su waye tace "amaryar Abban nihal da qaninta" ta fita tana murmushi zainab ta dan tabe baki ko mene abin murna dan amaryar mijinka t ziyarce ka, ta saka hijab ta fita falourn, A hankali take takawa tana kara gasgata abinda idanunta ke fada mata "su kuma me sukeyi a nan, mene hadinsu da amaryar uncle muzakkir" Anty tace karaso zainab, zainab ta karasa tana mai dubansu duka Ta dan danne mamakinta Ta gaida su ciki ciki, ita kadai ce ta amsa amma shi bai amsa ba idanunshi na kallon kasa ne kawae Anty hawwer tace " Zainab ita ce Amaryar Abban nihal" "Ya safiyyan?" Zee ta tambaya a mamakance tanaji kamar kar ta yarda a ina Abban nihal ze san su faruq,,, sunzo ne domin suyi magana da ke zainab, Zee a ranta take ayyana "wato Anty tasan ya safiyya Mijinta ya aura shine bata samarmin ba" Anty hawwer ta tashi ta basu guri ya rage sai su uku cikin falourn Ya safiyya ta matso kusa da zainab ta kamo hannayenta "Zainab nasan ko wace faruq yayiwa abinda yayi miki bazaki yafeshi ba ni banga laipinki ba Bawai kuma ina nema mishi afuwa bane dan shidin dan uwa nane ba" rabuwarki da faruq yayi ne domin kwanciyar hankalinki zainab, nan Anty ta sanar da zee reason din faruq duka" Zainab taji jikinta yayi sanyi "bata taba tsammanin faruq na sonta har haka ba dama mutun yana nashi ne Allah ma na tashi" Ta dubi faruq din wanda a yanxu ko ishasshiyar lafiya ma bata isheshi ba balle abin kula da iyali "Nayi tunanin bazan iya yafe maka ba a baya amma yau na yafe maka faruq kuma gaskiyanka a lokacin da ka fadamin dalilanka da bazan yarda ba saboda im blindly inlove, im desperate to become ur wife ban ganin laipinka ko kadan, bazan gane meke jira ba a time din bakuma zan karbi uzurinka ba, madalla da wannan soyayya taka a gareni faruq, haqiqa yanxu kam nagode maka kuma a tsakani na dakai babu komai sai mutunci da zumunci" Sai a lokacin yayi smiling yace "nagode zainab Allah ya sanya Alkhairi a aurenki" tace Amin kaima kuma haka Haka nan zuciyar zee tai mata wasai, wannan shi ne beauty of forgive and forget, if you keep holding grudges it will keep affecting you, zai shafi lafiyar mutun, kullun tunanin mutun zai tsaya ne kan ya zan raam abinda wane yayi min, gabadaya zaka manta goals dinka na rayuwa kayi focusing kan mutun daya jal wansa haka zeyi tasiri wajen rashin cigaban rayuwar mutun ne, dan Allah mu zamo masu yafiya ko muma ubangiji ya ji 'kan mu Zainab ta sanar da Anty duk yadda sukai dasu faruq, Anty taji dadi sosai, dan zataso er uwarta ta shiga gidan aurenta babu wani digon tsana a ranta, yadda zata bada zallar soyayya wa mijinta Anty tace "Lokacin da Abban nihal yace zeyi aure nayi kokarin sanin wace ya sanar dani wata tsohuwar budurwarshi ce daya taba haduwa da ita a europe sanda yake zuwa gurin barrister dake karatu a can, tun kafin muyi aure ya sanar dani magaanr ta kuma ni shaida ce yana kaunarta kawai dai dadynta yaqi yarda shima hajiyarshi taqi amincewa a lokacin har ta nema mishi aurena A sanadin gorin da Abbanta yayi mishi na cewar baida ilimi ya sakashi komawa makaranta bayan munyi aure nima ya sakani nayi masters, mafarin zuwanmu karatu saudiyya, gashi yanxu yakai matakin PHD har yana sake wasu research din" A hankali zainab ta dinga relating labarin da faruq ya taba bata na Ya safiyya da saurayinta a europe da labarin Anty hawwer, sai taji ta gane komai, ikon Allah kenan gashi a karshe dayake ya safiyya matar uncle muzakkir ce bayan tsayin shekaru sun sake haduwa kuma ya aureta din Allahu Akbar ta furta tana ganin iko irin na ubangijinmu maiyi yadda yaso, shikuwa dady yanxu ya saduda a yadda Anty hawwer ta bata labarinshi ya halisa kuma ana kwance ana jinya rae a hannun Allah, an ma kasa gane mene ke damunta Zainab tace da Assiddique bata buqatar wani event amma Anty ta shirya musu kamu iya mata zallah, yace "to shikkenan" Tayi mamaki dayayi saurin yarda ma, ranar kamu kuwa ana mata makeup an kusa kammalawa Anty tazo ta sameta tace "kuyi sauri zainab ango yana waje yana jiranki zaki karbamin sako" Aka kammala ta lullube fuskarta da gyalen rigar me kamar net, complete white tayi sai touch na sky blue, ta fita ta sameshi cikin mota yace ta shigo Ta shiga motar ranta bayaso dan bataso ta dade gurinshi, da tarin mamaki taga yaja mota sun soma tafiya, Ta zare ido "banfa dakko clutch ba ina zaka kaini" yace kiyi shiru kawai mu tafi cikin salama Ta dan harareshi Sai gasu gurin katon gurin event, basu dade da zuwa ba su Anty ma suka karaso tazo ta kawo mata clutch Nan fa guri ya dauka ai amarya da Ango sunzo suka shiga ciki kawayenta da abokanshi na take musu baya, sai taga sam wannan ba kamu bane tamakar wata mashahuriyar dinner ce, duk taku daya da zatai camera man yana fitar da hoto fitacce, Mint bata san me akeyi ba, tana can gidan yayanta dake Abuja itama tana sake gyara, dan kin zama tai a gidan tun saura sati biyu da bikin, a cewarta gara taj cikin en uwa zatafi jin dadi, Anty siyama tana daga cikin taron, dan ita kadai ce tace zataje cikin matan Abbah jabir sauran duka cewa sukai ai abin na en mata ne, tun saura wata 1 bikin ta gane Mijin kanwarta zee yake nema kuma zai aura, amma gudun husuma yasa tai shiru koma mene sune suka kai zee gidan yanxu basuda bakin yin complain, tana tausayawa mint dan idan ta gane abinda ake ciki kowa bazeji dadi ba Duka yaran Abbah jabir daidaiku ne basu halarta ba, bama kamar su zakiyya da ake ta rawar kai dan ji take tama fi zainab jin dadin wannan auren Mint na zaune matar yayan nata ta kkwalla mata kira babu kakkautawa, Jin kiran dai yaqi karewa yasa ta nupi dakin da take, ta wulla mata wayar hannunta "dama wannan ce matar mijin naki, ni kamar na ta6a ganinta ma a gidan siyama" Mint ta dauki wayar tana son ganin amaryar mijin ta " Ta rike wayar baki bude domin ba wata high makeup ne a fuskar zainab din ba, Dariya tayi amma mai tafe da hawaye, "Anty zainab ce fa" Sai ta saki wayar ta dora hannu aka Wallahi Anty sai na musu rashin hankali, dama amanata suke ci ban sani ba" Sai dure duren ashariya ya biyo baya not edited 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 46: knotted Matar yayan nata ta kada kai kana tace "to ke yanxu dan Allah mene haka, ji abubuwan da kike fada" mint ta dubeta idanunta sun fara cikowa da kwalla tace "Amma Anty idan banda namiji ma, mene ya rasa tattare dani, kalleni fa, babu abinda bani dashi" Ta tabe baki tace zauna mint kiji Kamar bazata zauna din ba amma ta zauna ranta na mata k'una "Naga alama duk cikin yayyanki babu wacce zata fadamiki gaskiya mararanta shiyasa ni zan fadamiki minnatu, na lura sam bakisan me ake nupi da zamantakewa irin ta aure ba, abinda kikeso kuma kikaga yayi miki shi kike aikatawa wanda hakan kuma ba daidai bane, akwai sadaukarwa akwai haquri akwae hidimtawa juna akwae juriya dukka a zamantakewa irin wannan, Ko ita siyama da kikaga tana zaune gidan mijinta lafiya dole tana haquri ne saidai in bazata fada miki ba, inaso ki sauke wannan girman kan da kika dorawa kanki domin baze amfaneki da komai ba, shifa aure bauta ne ta ubangiji ki tsaya ki kyautatawa mijinki tayu ki samu rabauta duk wadannan kyale kyalen da kike dauka shi ne aure sam basu da wani muhimmanci, Minnatu ki sani shi fa zaman tare dole saida kyautatawa kuma ita zuciya an gina ta abisa son wanda yake kyautata mata, indai dagaske kina son mijinki kamar yadda kike ikirari to sai kin mishi biyayya, shi namiji shi ne shugaba, kuma wallahi badan mijinki me haquri ne bama baxe taba jurar wannan cin kashin da kike mishi ba, da tuntuni yayi waje dake Abinda nakeso dake shi ne ki yarda kina da laipi, domin idan kika yarda kika amshi laipinki shi ne zaki samu ki gyara alaqarku keda mijinki Itafa gaskiya a bayyane take ke da kanki kin san abinda kikeyi ba daidai ba, idan mijinki na kyautata miki kinsani idan ma kece kika tura shi bango ya dena kyautata miki kinsani, idan mijinki na ganin kimarki wallahi kinfi kowa sani, balle ma kuma Assiddique Ke da ace wani ne keda wannan dukiyar kuma kike mishi abinda kike ma yusuf ke kinsan wulaqancin da zaki fuskanta ba kadan ba ne dan ba er kankanuwar wahala zakisha hannunshi ba Shawarata anan ki kwantar da hankalinki, karki sake ki tadawa mijinki hankali domin indai kikai asararshi ko kika bari ya subuce miki a tunaninki na zaki sami wani to wallahi kece zaki kwana a ciki ke mutunce kuma mai cikakkiyar hankali ki tsaya ki gyara halayyarki dan ke kanki kinsan zama dake abu ne mai wahala, Dan Allah ki saka kanki a mazaunin Assiddique idan shi ne yake miki abinda kike mishi ya zakiji? Zaki iya jurewa" Mint tayi shiru tana sauraren maganganun Anty hakika ita gaskiya dama daci gareta, taji dacin maganganun Anty amma can kasan zuciyarta tana ji kamar gaskiya ne, idan da ita ke da matsayin yusuf a kasar nan, da bazata ma soma auren yarinya a nigeria ba, gani zatai duk ta girmi tunaninsu, da ita keda matsayin yusuf kuma matarshi ta mishi abinda ni nayi mishi bazan zauna da ita na sscond guda ba.... Anty ta katse mata tunaninta da fadin to shiyasa a alaqa irin wannan uzuri yake da dadi, yanxu naki turn dinne ki saka wa Assiddique da haqurin da yayi na zama dake kowa idan yayi aure kwanciyar hankali yake nema, amma du kinbi kin tada naki hankalin da nashi kin hana muku zaman lafiya, kije gurin malaman islamiya su kara sanar dake zamantakewa dan ni ba malama bace kuma ki nemi yafiya gurinshi dan kin dauki hakkinshi.. A bangaren Amare kuwa ana can ana shagali, ba kananun kudi aka liqawa zee din ba, bama kamar angon nata daya bude bakin aljihunshi yayita watsa mata nera da doollar saida t rike hannunshi a kunyace tana blushing shima ya dan murmusa sannan yace "ur wish my command my queen" Hotunan bikin nan sunbi social media sosai, zakiyya ji take ina ruwa ta zuba a kasa tasha, yau zainab dinta ta auri mijin minnatu An daura auren daya samu halartar dumbin jama'a manyan mutane na kasar sannan aka soma shirin kai amarya dakinta, zainab na daki itada su zakiyya Anty ta kira wayarta tace "ta fito" ta saka gyale a kai ta fita, tana sanye da atampa Ash and white, da farin gyalenta, ta sami Anty itada Abokiyar zamanta ya safiyya suna hira abinsu kai kace ba kishiyoyi bane abin sha'awa Gefe ta ga faruq zaune kan kujerar dayake ba anan ake daura aure ba yasa babu jama'a gidan sosae ba kamar gidan Abbah jabir ba Ta gaidasu suka amsa, Ya safiyya tace "zainab ina tayaki murna Allah ya sanya Albarka a aurenku" sai tayi murmushi ta daga kai ta kalli faruq yace "na tayaki murna qanwata" Fuskarta da dumbin farinciki tace "Nagode yayana" Daga haka ya tashi ya basu guri dama yazo yi mata Allah sanya Alkhairi ne, su Anty suka saka ta a gaba da nasihu kala kala gameda zamantakewa, daga karshe akayi shirin daukan Amarya Komai ya tapi lafiya aka kai amarya gidan yallabai gurin kowacce matarshi, sannan aka kaita gidan mint, tana waiting falour a zaune tasha ado itama aka ajiye amarya a gabanta aka gama nasihu suka tashi batace dasu ko uffan ba Zainab ta danyi mamakin mint, sai taji dadi da batai tashin hankali ba kamar yadda tayi tsammani, A gidan yallabai zainab da wadanda suka kawo amarya suka kwana, da shirin kashegari amarya zata wuce gidanta dake UK, su Anty duk sun niyyaci zuwa ganin gidan Amarya amma fafur Abbah jabir ya hana yace babu wanda zaibi amarya, Hakan nan suka haqura suka koma gida a kashegarin, Zainab na zaune a dakin da aka saukesu, ta dubi kanta a mudubi sai sheki take exactly yadda Amarya ya kamata ta kasance, sai taji tayi kewar yusuf, tun ranar dinner dinnan rabonda ta ganshi dukka sun shiga busy ko waya basu samu sunyi ba, ta rike wayarta tana jujjuyawa kamar ta kirashi amma sai t kasa, Kwankwasa kofar dakin akayi, ta bada izinin shigowa, Daya daga cikin hadiman gidan yallaban ta shigo ta ajiye mata Accessories din tace "hajiya tace "ki shirya Anjima Angonki zaizo" tana kaiwa nan ta fita, Zee ta matsa kusa da kayan tana kallansu, ta jinjina kai lallai wannan kaya kowa ya gansu yaga zallar dukiya, Ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin less din da aka kawo mata, ta daura dankwali fuskarta fayau babu makeup ta dora gyalen dake ta walwali a kanta, ta jawo wayarta taga lokaci karfe hudu harda mintuna, ko ba'a sanar mata ba tasan lolacin sallah yayi ta tashi ta gabatar da la'asar dinta Daidai ta idar wasu en mata suka shigo dakin, daya tace "ki fito wai ana jiranki", ta zura kafafunta cikin rufaffen golden shoe dinta sannan suka fita Sai da suka wuce falour wannan bangaren aka kaita har falourn yallabai, a can taji presence dinshi dukda fuskarta a rufe take amma tasan yana cikin falourn, En matan da suka mata rakiya suka zaunar da ita sannan suka koma, Yallabai yayi musu tashi nasihar sannan yace zasu iya tafiya, zainab taji an kama kafadunta tasan ba maigidan nata bane amma batasan waye ba, har mota ta shigar da ita sannan tace "Amarya a dawo lafiya, daga jin muryar tasan ta mint ce da sukaje filin jirgi taji motarsu ta tsaya a ranta tanata tunanin ina mijin nata ne wai, meya hanashi shigowar motar datake, bude kofar motar akayizee taji an yaye gyalen fuskarta, ta fara tozali da takalman kafarshi, ta daga ido ta kalleshi, looking exactly like Ango, "To ai mun baro gidan yallabai kya iya bude fuskarki, tayi smiling, ya hada hannayensu ya fito da ita, sai lokacin zainab ta lura da tulin securities din da zasui masu rakiya tace "na dauka mu biyu zamu tafi" ya girgiza kai "Yallabai baze taba yarda ba" Sun sauka lafiya cikin birnin na london a ranar dukkansu baccin gajiya sukasha babu ma kamarshi daya tara uwar gajiya 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 47: His bride Kashegarin ranar da magarib ya shigo gidan da leda a hannunshi, zee tana can falournta tana kallo abinta, sai taji kamar motsinshi ta ruga daki d sauri ta nemi hijabi ta saka ta koma bakin windown cikin dakin tana kallan wasu flowers a bolcony Har cikin dakin ya shigo yana fidda kamshi, yasha ado bata juya ta kalleshi ba Ya ajiye ledar hannunshi da cewa Amarya ga kazarki, tai shiru tana rarraba idanu, ya bude ledar kamshi ya shiga lungu da sako, ya taka ya karasa har inda take tsaye ya zagaye kugunta da hannayenshi, ta dan matse jikinta ya saka kanshi a kafadarta Tun zee bata saki jiki ba ya saka saida ta saki jiki bayan sun kammala cin kazar yace "ki dan cire hijab din mana kisha iska, ta girgiza kai ai babu zafi, yayi murmushi Nidai Ayshab na koma daga falour na jawowa amarya da Ango daki dan naga Assiddique niyyar kashe boss yake lol Satin Assiddique daya gurin zainab ya koma Nigeria cikin sati dayan nan kuwa soyayya babu kalar wacce basu kashe ba, sanda zai tafi ma sai zainab taji gabadaya bataso, har da yi mishi kuka amma haka ya lallaba ta da cewar ta bashi 1 week zai karasa wasu abubuwan a Nigeria sannan ya dawo Mint taji dadin dawowarshi, shima kuma yayi mamaki sauyi daga gurinta, ta chanja kamar ba ita ba, bakaken kalamai, ji da kai, rashin kulawa, duk ta rage su sosai, hakan yasa Assiddique yabonta, a lokacin ta nemi yafiyarshi kan abubuwan da tayi ta mishi, ya kuma ce ya haqura har ranshi Zainab tana nunawa masu aikinta abubuwan da suka kamata taji wayarta na ringing ta dauka tana jin dadin ganin sunan Anty hawwer, sunyi er hira sannan tace mata "naga abin Alkhairin da mijinki yayi wlh na matuqar ji dadi Allah ya saka mishi da gidan Aljanna" Zainab ta shiga nazari mene yayi din haka tace "Anty me kenan" zee tace duk yadda abin Alkhairin sa yayi ya bi social media ke baki sani ba Tace "a'a Anty" Antyn tace "to ki duba news nasan zaki gani" Ta shiga kafar news dake cikin wayarta, tana ta dubawa aikuwa saiga sunanshi "Shahararren d'an kasuwar nan wanda ya kasance d'an gaban goshin yallabai wato yusuf Abubakar Assiddique yayi abin da ya bawa kowa mamaki" Ta shiga cikin full labarin ta soma karantawa, har ta fahimci abinda angon nata yayi, Har cikin kokon ranta taji dadin abinda mijin nata yayi, "zuciyarshi wankakkiya ce he's pure" ta tabbatar wa da kanta tana mai murmushi Ashe abinda zaiyi kenan dayace na bashi sati daya, ta sauke numfashi cike da jin dadi, ta kudurce bazatai mishi maganar ba sai ya dawo Ranar da zai dawo kuwa shiri ta maida hankli tanayi sosae, ta gama tsara duka abinda zatai mishi hatta da kayan da zata saka wajen tarbarshi sai da ta fidda su ta ajiye, cikin gidanta kuwa kamshin turaren wuta yake na musamman da Anty hawwer ta saka akayi mata hadinsu, su kajiji, damsu, sandal da sauransu, dayake kullun saita kona ta turara jikinta sai gidan ya kama sosai hakama jikinta Ta maida hanakli ta shiga kitchen, karfe 2 ta soma girke girken itada wata baturiyar yarinya dake dan taimaka mata batai wasu abincika masu yawa ba dan haka da wuri ta kammala Karfe 4 da mintina ta fada wanka dan sai 5 jirginsu zai sauka, ta fito taci ado bamai yawa ba looking as natural as always, tana jera abincikan a dining dinshi taji an murda kofar falourn, ta dubi wajen kofar tana jiran ganin mai shigowa dan kuwa tasan da dan sauran lokaci kafin karasowarshi, "Yana so yayi suprising dinki" taji zuciyarta na rada mata, ta saki baki tana kallonshi ya tako yana mata murmushi, Har ya karaso gurinta tana kallonshi, ya dan ja hancinta yace "bazaki amsa sallamar tawa bama" ta sunkuyar dakai "sannu da hanya" Ta karbi briefcase din hannunshi, ta ajiye, Tace "abinci ko wanka" yace zabamin tace muje na wanke ka to, yayi brief smile yace kafin nan muje kiga Ya zagaya bayanta ya saka hannayenshi ya rufe mata ido yace muje Tana murmushi ta dinga tafiya batareda tasan ina suke tafiya ba, Sanda suka tsaya ta tabbatar harabar gidan ce saboda iskar dake kadata ya dauke hannunshi daga idanun nata hakan ya bata damar bude idanunta yayinda rantsattsiyar motar ta bayyana a gabanta ta karasa gurin motar sannan ta juyo tana kallonshi yana tsaye, "Sabuwar amarya mukayi?" ya girgiza kai, kikayi dai matata, ta zare idoo "Ni kuma" tasa dan yatsanta ta nuna kirjinta" yayi nodding "kwarai ma" ta bude bakinta widely "like seriously" Ya saka mata dariya ganin yadda take acting, sai ta ruga zuwa gurinshi, ta fada kirjinshi... Sanda sukaje wanka daga ita har shi sai da sukai wankan Saida ya kammala cin abincin ta soma mishi maganar "Naji Abin Alkhairin da kayi kuma naji dadi sosae Allah ya kara Arziki" Yayi smiling "shiyasa ban fiyason yin abubuwan taimako dayawa ba, yanxu zai bi social media, sai ya zama kamar ma dan riya ne mutun yayi" tace "ka tsarkake niyyar ka ka kuma toshe kunnuwanka mijina, Allah ne zai biyaka ba mutun ba" yace "lokacin da najewa yallabai da maganar ki ya nunamin cewar bazan iya rike mata biyu ba saboda yanayi na ayyukana bana samun zama kuma ni kaina na yarda da hakan a lokacin ne nai niyyar yin abinda na dade inaso nayi, tun daga nan na soma duba cikin Al'amuran Kasancewar duka harkokin yallabai na hannuna ne, shidai yakan duba wasu abubuwa ne lokaci zuwa lokaci amma jagoranci gaba daya a guri na suke wanda ni kaina hakan sunmin yawa, shi ne fa nayi analysis na fitar da abinda zan baiwa kowanne domin su tayani kulawa da harkokin tunda ba ni kadai ne d'anshi ba," Sanda ya ida bayaninshi zee ta ce "kuma yallabai ya aminta da abinda kayi?" Dafarko da na kira meeting yaqi yarda, daga baya da kanshi ya kirani yace "meyasa ban fara fada mishi abinda nake shiryawa ba" na bashi haquri, sannan yace shikkenan ya amince indai ina ganin hakan da nai daidai ne, Na sake kiran meeting na musu bayani in details na kuma damkawa kowannensu dukiyar da zai cigaba da kulawa da ita a cikin dukiyar mahaifinmu" Zainab ta daga thumb dinta, thumbs up Ango na, Allah ya kara girma yasa Albarka, Ya sake mike kafarshi kan kujerar "Kinga zamusha soyayyarmu cikin kwanciyar hankali bazan damu da ayyuka ba nima na samu sassauci" Ya safiyya ta kira zainab tana mata godiya, zainab tace "mene kuma ya faru" "Kinsan faruq is struggling da neman abinyi sakamakon baida certificate yasa gurare da dama suka dinga rejecting dinshi dukda abokan dady ne wasunsu, wannan raba dukiya da Assiddique yayi yasa daya daga cikin yayyen nashi ya dauki faruq aiki a masana'antar shi a bisa umarnin Assiddique Zee taje ta sameshi da maganar daukan faruq aiki, yayi smiling "ina sane da duk moves dinshi ai zainab tun rabuwarku, kawae ina neman ways da zan rama miki abinda yayi miki amma sai na lura ba yadda na dauka yake ba, he's struggling to live, bayaga rashin wadatacciyar lafiya ga responsibilities na iyali, iyaye da yayye thats when nayi niyyar sama mishi abinyi atleast ya barmin ke" ya karasa fada yana pecking cheeks dinta tayi dariya ta rike cheeks din Suka raba kwanaki tsakaninsu, Assiddique ya zama d'an gata tsakanin mint da zee, sun koma makaranta, babu wani stress, Watanni hudu bayan nan zainab ta fahimci bayyanar ciki a jikinta, sanda Uban gayyar ya fahimta sai ya hanata komai yace babu abinda zatana yi shikam ya haqura, dukda haka takanyi wasu abubuwan idan baya kasar Zainab ta kammala karatunta sucessfully lokacin cikinta nada watanni 7 har ya fito, taso komawa gida amma ya hanata saboda cikin ya tsufa yace a nan zata haihu, sanda mint taji labarin cikin zee tayi nadama har cikin ranta, ta tuna kyakkyawar yarinyarta Asma'u, haka nan ta barwa Assiddique zainab har zuwa ta haihu tace yaje ya zauna da ita tana buqatar wani kusa da ita, Ba kadan ba mint ta birgeshi yaji babu ya ita a wannan lokacin, Zuwa yanxu zanso naji daga bakin mai karatu wanne darasi kuka tsinta cikin wannan labari 💍 *AL_HUBB* 💍 The love 💘 By Aysha b. Naseer Episode 48: Finale Las las las Zainab ta haifi beautiful daughter dinta, skin clour na Assiddique, amma kusan gaba daya kamar zainab tayo, Ranar suna aka maida wa yarinyar Asma'ul husner, zainab ta dawo nigeria inda tayi wankanta a gidan Anty hawwer, bayan ta gama wanka ta zagaya gidajen 'en uwa har gidan Anty siyama tayi mamakin yadda Anty siyaman ta sake mata sai gashi harda hirarsu, Raanr da zainab zata koma gidanta da kanshi yazo daukanta, motoci uku ne kawae, zo kuga zumudi gurin Assiddique dan ba karamar kewar Amaryar tashi yayi ba, zainab tayi kwalliya tayiwa husner ma, Anty hawwer ta sake mata hade hade na gyara wanda zata cigaba koda ta koma gidanta, Har ya shigo gidan Anty ta bashi abinci ya san taba bai ganta ta ko gilma ba, ya kammala ya tashi yace to Anty zamu wuce, ya fita ya tsaya jiranta Tana sanye cikin atampa da babban gyalenta Anty na rike da husner suka fito, ya zuba mata idanu yana murmushi shi daya,Anty ta miqa mishi husner tace "to Allah ya tsare" yace Amin Anty Ya zagaya ya shiga, zainab tayiwa Anty sallama ta shiga itama Ya kalli husner dake hannunshi "tubarkallah har tafiki kyau" zee ta dan bata fuska "haba dai" yace kwarae ma kuwa ko baki yarda ba" tayi mishi shiru Ya kamo hannunta yace "kinyi shiru" tace "kasan yadda na soma sonka?" Yace "A'a tell me how" Ta ce "i fell inlove with you the way you fall Asleep slowly and then all at once" Idan kika kalleni how do you feel Tayi murmushi idan na kalleka i remember the verse "So which of the favors of your lord will you deny" (Cikin suratu Arrahman fabi'ayyi'alaa i rabbi kumaa tukazziban).... Wannan karan gidan yallabai suka sauka saboda nemansu dayakeyi, zainab ta sunkui da kai gaban yallabai kamar yadda taga Yusuf yayi, shikuma yallabai yana rike da husner yana wasa da en yatsunta Wasu takardu aka kawo, yallabai yace da mutumin ya miqawa zainab, zainab ta saka hannu biyu ta karba yace "Lokacin da er uwarki ta samu juna biyu nayi mata irin wannan makamanciyar kyautar, dukda nata kudi ne, kekuma takardu ne na makaranta, Tunda sakamkonku ya fito kuma yayi kyau yadda ake buqata na tambayi mai gidanki wanne aiki kike sha'awa sai ya sanar dani baki muradin aikin Asibiti kin fison koyarwa so samu a university ko college, wannan makaranta health college ce kuma mallakinki ce, komai na bukata An zuba sai dai in kika sake dubawa sai muga me ne akai missing tunda harka ne na project kuma mutun ajizi" Zainab sai taji hawaye ya zubo mata "Nagode Abbah ubangiji Allah ya raya zuri'a Allah ya jikan magabata ya kyautata namu karshen" yayi matuqar ji dadin Addu'arta yayi murmushi irin nasu na manya ya cire wani zoben azurfa dake hannunshi ya saka a karamin hannun husner yace itama ga nata tukuicin Sai yamma likis suka baro gidan yallabai zainab sai murmushi take ita daya tana ta fadin Alhamdulillh ala kulli haal, Hanyar gidan mint suka dauka zainab dai batace komai ba, har suka karasa amma sai yasa akai packing a kofar gidan, suka fita suka shiga da kafarsu Gaba daya taga gidan ya sauya, maimakon su yi hagu sai sukai dama, taga wani tamfatsetsan gini ya bayyana gabanta, barka da zuwa sabon gida sabuwar Amarya, ta juya ta kalleshi kawai sai ta rungumeshi Dukda gidan zee baikai na mint girma ba amma tsararre ne sosai, kuma duk a hade suke, wancan na uk kuma duk wacce ya tapi da ita sai ta sauka tunda dukansu ayyukansu a nan nigeria yake Shekarun husner hudu kafin zainab ta samu wani cikin a lokacin zainab kana kallonta kasan ta amsa sunan matar Assiddique din, naira da dollar sun zauna, itama mint bayan bayyanar cikin zainab t gane ta samu rabo, batareda kowa ya sani ba tayi running test domin a gane genotype din yaron aikuwa cikin sa'a ya fito As ranar sai da tayi kuka ta koshi dan murna ta kuma godewa sarki jalla, ta sanar da mijin nata komai, shi kanshi yaji dadi sosai bama kamar ganin irin farincikin dake kwance kan fuskarta, Assiddique yana iya kokarinshi wajen yin Adalci tsakaninsu Tammat bi hamdillah, Alhamdulillh Allah yayi na kawo karshen wannan littafi nawa, idan kun karanta kuma kunji dadinshi kun karu da wani abu nima kuyimin Addu'a nagode Ga tattaunawar da mukai tsakanina da 'yar uwata fatima gameda wannan littafin Fadima: Wai nikam in tmbayki Me yasa Baki aurawa Faruq Zee ba Aisha: 1. Haka na tsara labarin 2. Zee loves him too much irin wannan soyayyar da Allah ya hana 3. Inaso mutane su gane ba kowa ne zakuyi soyayya ze zama dole mijinka ne ba 4. Ya kamata mint ta gane wasu darussan Fadima: 2 dai is d strong one Kinsan me yasa na gne hkan Sbd Ina wurin da Prof ya kirata yyi mta warning Kinsan Faruq ya shigo gidan Yana lallashinta 1. Ya rike mata hannu 2. Ta kwanta akan kirjinshi Bata San ma tsawon time din da suka dauka ba 3. Zuwa gidanshi da tkeyi Kuna masoya Kuna kebancewa is not fine Duk wnn sun sabawa Allah sbd soyayar da ta rufe musu Ido Kuma Bata taba Jin ma Alamar nadama ba . Number 4: Kingane Sosai ma kuwa kaii a wnn ma Kamar ba mace ba, Akan wani dalili zan bar wata tanawa Mijina girki Ya dauke ta su bar kasar for weeks da sunan cook wllh ba wnn mgnar tab! Aisha: yes yes Kawae wahala zatasha hannunshi da rashin kwanciyar hankali Kuma ya kamata ta girbi sakamakon tawakkalinta Bawae dan faruq baya sonta ba Fadima: Yh I understand Amma sometimes rabuwar yna Zama maslaha Shikam Yusuf is d lucky one Allah ya biya Masa ladan hakurin da yyi da Mint Ina fatan 'en kungiyar Assiddique #teamAssiddique zaku gane dalilin dayasa na aura mata shi bawae dan kun rinjayi en team din faruq ba... Allah yasa mu dace Nan bada dadewa ba in shaa Allah zan fara sabon book Gaisuwa gareku masoyana Ayshab ✍🏻🤝🏻