*ZARGE* _(Mugun Ƙulli)_ BY SALMA AHMAD ISAH & ZAHRA ROYAL STAR بسم الله الرحمن الرحيم Page 01 *Sabon Titin kwaɗo, Katsina state...* Wata matashiyar budurwa ce zaune a cikin wani babban ɗakin da a kallon farko za ka shaida cewa na 'yan mata ne... Domin ɗakin ya ƙunshi gadajen kwanciya har guda biyu, sannan dressing mirror ma biyu ne... Hatta da wardrobe biyu ce, yawan tarkacen dake cikin ɗakin bai sa ɗakin ya kasa yin kyau ba. A hankali ta miƙa hannu ta janyo kwalin cart ears headphones, peaches color, ta kunna shi tana taunar cingam a nutse, sannan ta yi connecting da warta, ta saka a kanta tana gyara ɗaurin ɗan kwalin kanta... TikTok ta shiga, sannan ta soma recording video tana ta wani marfi kamar 'yar tsana mai batiri. A ƙalla sau uku tana recording tana sakewa, domin duk ciki ba ta ga wanda yay mata ba... Tana shirin sake ɗaga wayar domin recording wani videon a karo na huɗu, aka buɗe ƙofar ɗakin da take ciki. Hakan yasa ta sauƙe wayar tana amsa sallamar da aka yi, tare da kallon wadda ta shigo ɗakin. Wata farar matashiya ce, wadda take kama da ita sak, amma idan ka kallesu ka san cewa wadda ke zaune a ɗakin ita ce babba, domin alamun girma sun fi bayyana tattare da ita, sanye take da uniform ɗin Katsina State College of Health science and technology. Hannunta na dama riƙe da wata teddy backpack, yanda ta jingina da garu, da kuma yanda take buɗewa tare da lumshe idanuwanta yasa 'yar uwar tata ta gane cewa a gajiye take. 'Yar dariya ta yi tana maida hankalinta kan wayarta, yayin da ita kuma ɗayar ta ƙaraso cikin ɗakin tana tafiya a gajiye. Yaraf ta zube a kan gado tana sauƙe ajiyar zuciya. “‘Yan makaranta manya! Da wa ya gaya miki Borno gabas take?” Cewar ta cikin ɗakin tana ci gaba da dube-dube a cikin wayarta, sannan tana taunar cingam. A gajiye ta kalleta ita ma, sannan tace. “Wai fa hakan ma dan mota ake kaini ake dawo dani... Ba dan haka ba ai da na banu!” “Ai duk abin da ake faɗa miki ba ki ji! Sai yanzu da kika fara zuwa kika gane ma idonki!” “Humm! Ke dai bari! Calss ɗin 2-4 bai yi ba!” Cewarta tana tashi zaune da ƙyar! Sannan ta sa hannu ta cire hijabin jikinta, kana ta cire takalmin ƙafarta. “Amira! Amira!” Wata murya ta shiga ƙwala ƙiran sunan tun daga ƙasa, hakan yasa Amiran ta amsa da sauri. "Na'am Mummy!” Ta aje wayarta dake hannunta ta miƙe tsaye, lokacin da ɗayar ke cewa. "Ni na ma manta da tace na ƙira mata ke!..." Ba ta kai ga rufe bakinta ba aka buɗe ƙofar ɗakinsu da ƙarfi, hakan yasa suka yi saurin kallon ƙofar, duk da sun san wa zai buɗe ƙofar... Wani irin kallo na ɓacin rai Mummy ta shiga binsu da shi. Hakan yasa Amira ta sha jinin jikinta ta kama susar wuya cikin alamun rashin gaskiya. “Sau nawa na ƙiraki?” Mummy ta tambaya tana haɗe rai. “Yanzu ne fa na...” “Rufa min baki! Tun sanda kika shiga wanka na ce miki idan kika fito ki zo ki ɗora mana abincin dare! Shi ne da kika fito daga wankan kika zauna ki kai kwalliya, sannan kika dasa camera a gaba kin video da ɗaukar hoto! Ko?” “Mummy mana! Ki yi haƙuri!” “Kar ki zo ki yi abinda na ce, ki ga yanda zan yi da ke!” Mummy ta ƙarashe tana kallon ɗayar dake zaune a kan gado tana cire uniform ɗin jikinta. “Ke ma ZAHRA! Idan kin.gama hutawar sai ki fito ki tayata! Domin ni ba zan zauna na sa ku a gaba ina kallo ba tare da kun iya komai ba! A kai ku gidan miji ba tare da kun iya tafasa ko fa ruwan zafi ba! Dan haka ki je ki yi wanka ki sauƙo ki tayata!” Wadda aka ƙira da ZAHRA ta jinjina kanta, sannan ta sake bajewa a kan gadonta tana susar wuya. Ita kuwa Amira da sauri ta sauya kaya, sannan ta sauƙa ƙasa ta shiga kitchen, gudun kada ran Mummy ya ɓaci a kan wannan girki! Domin in ba ta yi ba na lahira sai ya fi ta jin daɗi, ita ma Zahra ba ta ga ta zama ba, duk yadda take a gajiye haka nan ta daure ta fito suka yi girkin tare da 'yar uwarta Amira. *Nigerian Law school, Bwari, P.M.B 170, Garki, Abuja Nigeria.* "YABINTU! YABINTU! YABINTU!" Cikin tarin dandazon ɗaliban shari'a da suka fito daga ajin Trots Law... Wata baƙar matashiya ta shiga ƙwala ƙiran sunan tana tattage, wai ko za ta samu danar hango YABINTUn da take ta ƙira. “Yabintu! Khadija na ƙiranki!” Faɗin wata budurwa dake sanye da baƙar mini skirt, tare da farar shirt, wadda ta ɗorawa baƙar suit a sama, wuyanta saƙale da legal collar a maimakon tie, ta riƙe legal gown a hannunta da kuma legal wig, yayin da take kallon wata farar budurwa, wadda ita kuma take sanye da dogon baƙin matching trouser, da farar riga, sannan akwai suit a saman dress shirt ɗin, kamar sauran ɗaliban shari'ar ita ma legal collar ne saƙale a wuyanta... Sai da ta yi rolling wani farin mayafi a kanta, sannan ta ɗora legal wig a sama, hannunta na dama na riƙe da legal gown ɗinta, na hagun kuma na riƙe da wasu ɗima-ɗiman litattafai... Ba ta cika tsayi ba, amma tana da dirarren jiki, kuma fara ce, fari irin mai kyau ɗin nan, tana da kyakkyawar fuska, abar son kallo, gwanar birgewa ga mutane!... Cike da nutsuwa ta juya ta kalli Laura da ta mata magana, kafin fararen idanuwanta suka juya daga kan Laura zuwa baya. Hakan ya bata damar ganin Khadijan dake ƙwala mata ƙira, lokaci guda kuma ta dakata, ganin Khadijan ta nufosu tana gudu. "Bar tab Ɗinki kika manta!” Cewar Khadijan tana haki, yayin da take miƙa mata bar tab ɗin, Yabintu ta saki wani sassanyan murmushi, sannan ta saka hannu ta karɓa. “Kin kuwa kyauta! Dan da ba ki bani ba da wata ƙila sai zuwa gobe zan yi ta naimansa na rasa! Na gode” Khadija ta yi dariya tana girgiza kanta. "Ba komai ai! Ina ku ka yi ne?" Ta tambaya yayin da suka jera su uku suna tafiya a tare. “Ni dai cafeteria nake son zuwa!” Cewar Laura. "Ni kuma a gajiye nake, da hostel nake son wucewa" "To me zai hana mu fara zuwa mu ci wani abu, sai mu wuce hostel ɗin, dan na san ke ma a gajiye kike liƙis! Ba lalle ki iya girka komai ba" Cewar Khadija. “To ba damuwa, mu je ɗin...” Yabintu ba ta gama rufe bakinta ba suka jiyo horn ɗin motar da duk duniya mutum ɗaya ta san yana yin irinsa, da sauri idanuwanta suka zarce zuwa wurin da ta san ya saba aje motarsa... Kuma kamar yanda ta yi zato, motar tasa na fake a wurin, ya buɗe ƙofar driver seat, ya fito da ƙafarsa ɗaya waje, yayin da ɗayar kuma take cikin motar, hannunsa ɗaya na kan sitiyari yana kallonta ta saman baƙin glasses ɗin da ya saka. "Ai fa! Da ma na san ba lallai ace ya bar ki kin je ba! Dan haka mu mun wuce, sai mun haɗu a hostel" Cewar Khadija, sannan da sauri ta ja Laura suka nufi wata hanyar da ban... Yayin da Yabintu ta nufi wurin da motarsa take fake murmushin kan fuskarta na yalwata. Tun kafin ta ƙaraso ya fito daga cikin motar, ya rufe ƙofarta sannan ya jingina da ita yana kallonta har ta ƙaraso inda yake. “Barka da rana Habibi!” Ta faɗa cikin muryarta mai daɗin saurare. Umar ya girgiza kansa yana ƙare mata kallo. "Barka da rana Hayati! Ya rana ya gajiya?" "Duk ba wanda babu, dan yanzu haka ma cafeteria za mu je mu ci abinci, daga nan sai mu wuce hostel!" "Ai bai kamata ki je cafeteria ba ina nan! Dan haka kawai ki zo mu fita waje mu je mu ci abinci!" Da mamaki Yabintu tace. "Da waɗannan kayan?" Umar dake shirin buɗe ƙofar motarsa ya fasa shi ma yana binta da kallon mamaki. “Eh! Mi ye aibin kayan naki?" "Ai da ka bari na koma hostel na ciresu, sannan na watsa ruwa na sauya wasu!" Umar ya rufe motar baki sake. "Hayati kin san irin kyan da kayan nan suke miki kuwa? Allah da ace kin sani da ba lalle ki ci gaba da saka wasu kayan saɓaninsu ba, ni da ma da su na fara ganinki, har na ji kin kwanta min a rai, dan haka kayanki ba su da wata tawaya!" Yabintu ta yi murmushi tana rufe bakinta da books ɗin dake hannunta. "Ki yi sauri mu tafi kafin rana ta gama gasa mini ke a nan" Wani murmushin ta sake, sannan ta zagaya zuwa inda ya buɗe mata ta shiga, sannan shi ma ya zagayo ya shiga ya tada motar ya ja suka fice daga Law school ɗin. Fatima Haruna Bakura ke nan, wadda aka fi sani da Yabintu, matashiyar budurwa wadda ta taso da burin zama lawyer tun a yarinta, kuma burin nata ya samo asali ne sakamakon mahaifinta Alhaji Haruna Bakura babban alƙali ne, wanda a halin yanzu ya yi retire. Su biyu ne kaɗai a wurin iyayenta, kuma ita ce ta farko, sai ƙaninta Khalid dake bin bayanta. Asalinsu 'yan jahar Zamfara ne, kuma har zuwa yanzu suna gudanar da rayuwarsu a cikin garin Gusau. Yabintu da Khalid sun samu gata sosai a wurin iyayensu, domin mahaifinsu mutum ne mai kula da duk wani da ahalinsu suke so. Hakan tasa ko a lokacin da Yabintu ta fara tasowa tare da burin zama lawyer ya tsaya kai da fata wurin tayata cimma wannan burin nata. Kuma shi da kansa yake ƙarfafa mata gwiwa kan hakan abu ne mai matuƙar kyau, wanda idan ta yi shi za ta saka shi alafahari. Kuma tun daga lokacin da ta taso har zuwa sanda ta gama jami'a, ta shiga law school ba ta samu wata tangarɗa daga iyayenta ba, ga shi yanzu tana daf da gama law school ɗin. Sun haɗu da Umar saurayinta ne wattani takwas da suka wuce, lokacin tana sabuwar zuwa a law school, kuma daga wannan lokacin suka fara soyayya har ta kai ga manya sun shiga maganar, domin ana jiran ita Yabintun ne ta kammala Law school ɗinta sannan a yi aurensu. *Unguwar Samaru, Gusau, Zamfara state, Nigeria.* Gwan! Gwan! Gwan! A karo na uku aka sake ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin da wata budurwa ke ciki, kwance take a saman gado, ta yi kwanciyar rubda ciki, yayin da kanta yake a ƙarshen gadon, ƙafafunta kuma suna ta saitin allon gadon. Bacci take hankali kwance, har da su minshari, babu ko alamar tana jin bugun ƙofar da ake. "Falak! Wai ba za ki buɗe ƙofar nan ba?" Wata farar dattijuwa ta faɗa a ƙufule, cikin fushin dake nuna cewa tana daf da fasa ƙofar ɗakin. Sai a wannan karon ta motsa ƙafafunta, kafin ta buɗe idonta da kalarsa ta sauya zuwa ja, ba ta haura sakan guda ba ta sake lusmhe idon nata, dan ji take kamar wani abu ke janta kan ta rufe idon nata. "Falak! Wallahi idan ba ki zo kin buɗe ƙofar nan ba sai na ci ub*nki!" Dattijuwar ta sake faɗa a ƙufule, tana jin kamar ta ɓalla ƙofar, ta finciko Falak ɗin dake ciki, sannan ta lakaɗa mata duka. Kuma maganar da ta yi a wannan karon yasa Falak ɗin ta sake buɗe idonta, ta tashi zaune tana hamma, kafin ta shiga sosa wuyanta, tana jin kwata-kwata ita baccin ma bai isheta ba. A daddafe ta miƙe ta nufi ƙofar ɗakin tana layi, alamun kayan da ta ja jiya ba su gama sakinta ba, kuma da ma ita ta san za a rina, shi yasa tacewa Khamis ba za ta iya shanye kwalabe huɗu ba, amma haka ya tilasta mata ta shanyesu tas, duk kuwa da ta nuna ƙin amincewarta kan hakan... Wani matsiyacin kallo Hajiya ta bi Falak ɗin da shi, lokacin da ta buɗe ƙofar tana buɗe idanuwanta da ƙyar a kan mahaifiyarta, domin ji take kamar za ta faɗi. "Baccin ub*n me kike bayan kin san yau akwai school?" Cewar Hajiya tana binta da kallon sama da ƙasa, cikin ƙarfin hali Falak ta buɗe jajayen idanuwanta a kan Hajiyar, sannan ta furta. "Ayi haƙuri Hajiya, ban san baccin ya ɗaukeni ba!" "Kin yi sallahr Subhi?" Hajiya ta sake cillo mata tambayar tana nazarinta, Falak da idanuwanta ke gaf da rufewa gaba ɗaya ta yi saurin buɗesu, sannan ta jinjina kanta ba tare da ta san ma wace tambaya Hajiyar ta mata ba, tsayuwar da take yanzu haka ji take kamar za ta faɗi, ba dan ƙofar da ta riƙe ba da tuni ta faɗi ƙasa. "Sai ki je ki yi wanka ki shirya ki sauƙo ki yi breakfast ki tafi school! Dan ita Bilkis ta jima da tafiya abinta, ba kamar ke ba da kika kwanta baccin asara!" Hajiya ta ƙarashe tana wurga mata harara, Falak ta sake jinjina kanta. "To Hajiya!" "Tun wuri ma gara ki raba kanki da wannan lalacin, dan Wallahi idan FAISAL ya dawo ya iskeki kina wannan lalacin ba za ki ji da daɗi a hannunsa ba..." Ita dai Falak kanta kawai take jinjinawa, domin ba komai take ganewa a cikin kalaman Hajiyar ba, burinta kawai Hajiya ta bar ƙofar ɗakin, domin ta daddafa ta shiga bathroom ta watsa ruwa a jikinta domin hayyacinta ya dawo. Cikin ikon Allah kuwa Hajiya na gama banbamin nata ta tafi, hakan ya bata damar garƙame ƙofar ɗakin, tana layi ta nufi bathroom, kafin ta kai cikinsa sai da ta faɗi ƙasa sau biyu, da ƙyar da jiɓin goshi ta shiga ciki, ta samu ta watsa ruwan kamar yanda take fata, kuma sai ta samu ɗan kuzari, domin ba gaba ɗaya mayen ya gama sakinta ba. Tana fitowa daga bathroom ta gabatar da sallahr safiya, yo sallahr safiya mana, domin a ƙalla lokacin 10 na safiya, domin ba ta yi sallahr da asuba ba kamar yanda tace. Tana idarwa ta miƙe da sauri, sannan ta shirya cikin wata abaya maroon color, ba ta yi kwalliya ba, sneakers kawai ta saka a ƙafarta, ta fesa turare mai sanyin ƙamshi, ta ɗauki wasu abubuwanta na buƙata ta fita. Lokacin da ta sauƙa falon ƙasa, Hajiya tare da Mama ne zaune a falon, yayin da suke hira a kan wasu kaya da aka siyo. Da kallo suka bita har ta iso inda suke, har ƙasa ta tsugunna tana gaishe da Hajiya da Mama. "Hajiya ina kwana" "Lafiya" Hajiya ta amasa, Falak ta kalli Mama dake murmushi. "Hajiya ina kwana!" "Lafiya lau Falak! Fatan kin tashi lafiya" Hajiya ta faɗa tana ta fara'a, kamar ta saka zani ta goya Falak. Ta amsa tana miƙewa, ganin ta nufi ƙofar fita yasa Hajiya faɗin. "Ba za ki karya ba kafin ki fita?" A hankali ta ɗan juyo ta kalli Hajiyar, sannan tace. "Na makara sosai, zan ci a waje" "Ai da kin tsaya kin ci" Cewar Mama, dan yadda take kula da Falak ya fi yanda take kula da Bilkis ɗiyar cikinta. "A'a Mama, kada ki damu zan ci a can... Na tafi" "To a dawo lafiya, Allah ya tsare, ya bada sa'a" Ta amsa da amin, lokacin da ta fita waje, maimakon ta hau ɗaya daga cikin motocin gidan sai ta fita waje tana amsa wata waya. "Baby Baby Babe! Kin tashi lafiya" Muryar Khamis ta fito ta cikin wayar. "Na tashi lafiya Baby! Amma yau asiri ya kusa tonuwa! Don Wallahi bacci na yi ta yi kamar gawa, yanzu haka maganar da nake maka ba su gama sakina gaba ɗaya ba, ji nake kamar zan faɗi! Allah ne ya rufa min asiri Hajiya ba ta ganeni ba" Tana iya jin sautin dariyar da Khamis ɗin ke yi. "Haba Babe! Sai ka ce ba wayayya ba? Ya ma za ayi ki bari ki yi abin da Hajiya ko wani na gidanku zai gane?" Ta girgiza kanta lokacin da ta tsaya a bakin titi. "Ba za ka gane ba ai! Yanzu kana ina?" "Gani nan a bakin titi, ina iya ganinki ma" Da sauri ta kalli wata mota ƙirar Honda Accord, wadda ta san cewa tasa, ba tare da tace komai ba ta katse ƙiran, sannan ta nufi motar ta buɗe ta shiga. "Yaushe ka zo?" Ta tambaya tana binsa da kallo, mutumin da ta danƙawa ragamar rayuwarta, mutumin da soyayyarsa tasa ta soma ɗabi'un da ba nata ba, mutumin da ya sauya duk akalar tunaninta. "Na ɗan jima a nan, kuma ma san za ki fito" Khamis ya bata amsa. "Yanzu ina za mu je?" "Mu je mu shana mana!" "Woooo! Babe, kamar ka san yau ba na son zuwa school! Mu je kawai!" Ta faɗa cike da jin daɗi, Khamis ya yi dariya, sannan ya tada motar ya ja suka bar unguwar, inda suka nufi gidan da suka saba sheƙe ayarsu dake cikin filin jirgi. Alhaji Ali Makama haifaffan garin Zurmin jahar Zamfara ne, attajirin mai kuɗi wanda Allah ya masa rasuwa shekaru goma sha biyar da suka wuce... Ya mutu ya bar matansa biyu, Hajiya Aisha, wadda ake ƙira da Hajiya, da kuma Hajiya Laraba, wadda ake ƙira da Mama... Hajiya Aisha na da yara biyu tare da Alhaji Ali Makama, FAISAL shi ne na farko cikin 'ya'yanta, kuma haka ma a wurin Alhaji Ali Makama. Wanda a halin yanzu yake riƙe da muƙamin Major a hukumar sojan Nigeria. Kuma a halin yanzu yana Ikorodu Barrack dake Lagos. Duk da ana sa ran yana daf da dawowa cikin garin Gusau domin da ma can a Zamfaran yake, sauyin wurin aiki yasa ya koma Lagos ɗin. Mai bi masa kuma Falak ce, wadda ta kasance auta cikin 'ya'yan Hajiya, Bilkis kuma ita ce auta a gidan gaba ɗaya, kuma ita ce tilon 'yar Mama. Kasancewar akwai fahimta tare da jittuwa a tsakanin matan biyu yasa bayan rasuwar mijinsu ba su yi ƙoƙarin barin gidan ba, sun ɗauki haƙuri, sannan suka rungumi 'ya'yansu domin ba su tarbiyya mai kyau. Tsakanin Hajiya da Mama babu wani abu da za ka ce ga shi ya taɓa haɗasu, a zahiri suna zama ne kamar 'yan uwa ba kishiyoyi ba, amma idan aka tona ba lalle hankali ya yarda da ƙulle-ƙullen da ake kan ƙullawa ba. Bayan rasuwar Alhaji Ali Makama, FAISAL shi ne ya zama kamar uba ga su Falak! Domin akwai tazarar shekaru tsakaninsa da su sosai ba kaɗan ba, kuma a lamarin FAISAL babu ɗaga ƙafa ga duk wanda ya shiga gonarsa, tun tasowarsa yake da wani irin murɗɗaɗen mutum, sai kuma ga shi ta shiga aikin soja, wani abu da ya ƙara dagula ɗabi'unsa. Sai dai duk da wannan zafin nasa bai san abin da ƙannen nasa ke aikatawa ba, domin hatta su Hajiya babu wanda ya san cewa Falak na shaye-shaye, a wasu lokutan ma ba ta kwana a gida ba tare da kowa ya sani ba. Kuma tarbiyyarta ta fara wargajewa ne a lokacin da ta haɗu da wani shaiɗanin saurayi wai shi Khamis. *. *. *. ZARGE isn't free, dan haka free pages 7 kwai muke da su... Domin samun naku cikin sauƙi za ku biya ₦500. Yanzu aka soma tafiyar🔥 *ZARGE* ©Zahra Royal Star & Salma Ahmad Isah Page 02 *Channels Television station, Abazie Ifeanyi Close, Guzape, Abuja.* Wata baƙar mota ce ta ƙetara babban gate ɗin station ɗin, ta wuce har zuwa parking lot. A lokacin da motar ta faka kuma ba jimawa aka buɗe ƙofarta... Ba tare da ɓata lokaci ba wani dogon baƙin mata shi mai cike da haiba, kamala da kwarjini ya fito yana saisaita sakin hullar Zanna Bukar dake kansa, sanye yake da wani plain yadi milk color, babu aikin komai jikin rigar yadin. A hankali ya kai hannunsa na hagu ya buɗe gidan baya na motar, sannan ya sunkuya ya ɗauki wata bag da kuma wasu 'yan tarkace dake wurin, yana ɗauka ya miƙe tare da rufe ƙofar motar, sannan kamar kullum, cike da kuzari ya nufi ƙofar shiga station ɗin. Duk inda ya ratsa sai an gaishe shi ko an ɗaga masa hannu, ba wai dan shi ne shugaba ba, ko dan ya fi kowa, sai dan sanin ya kamatansa da iya mu'amalantar al'umma yasa yake da farin jini a duk inda zai zauna. Lokacin da yake taka stairs ɗin da zai sada shi da office ɗinsa dake sama aka ƙira shi. "BILAL!" Hakan tasa ya dakata, sannan ya juyo a hankali. Ganin abokinsa Aliyu ne yasa ya yi murmushi yana binsa da kallo har ya iso inda yake, sannan ya miƙa masa hannu suka gaisa. "Wai ina ka je wajen sati guda ke nan rabon da na ganka?" Ba tare da Bilal yace komai ba ya juya ya ci gaba da tafiya, yayin da Aliyu ya biyo shi yana faɗin. "Na san duk yadda aka yi case ɗin 'yan matan nan ne ba ka rabu da shi ba!" Bilal ya kalle shi, kafin ya kuma girgiza kansa yana murmushi, haka Aliyu ya matsa masa kan sai ya sanar da shi dalilin ƙin zuwansa wurin aiki a kwanakin da suka wuce, domin ya san abokinsa Bilal ƙuli-ƙuli ne, ba shi gaba, duk yadda ka kai ga wayonka ba lallai ka iya gane inda ya sa gaba ba, akwai shi da zurfin ciki da kuma wayo na ban mamaki, hakan tasa duk wani labari da ya samu ba ya bari a yaɗa a gidan TVn nasu ba tare da ya tabbatar da shi ba, kuma ko shi kansa ba ya kawowa labaran da ba su da tushe, duk kuwa da yanda yake saka rayuwarsa a haɗari wurin samo labaran a wasu lokutan. "Why don't you tell me abin da kake ɓoyewa?" Cewar Aliyu lokacin da Bilal ya buɗe office ɗinsa suka shiga ciki, amma har ya aje kayan da ya shigo da su a kan table bai tanka masa ba, sai da ya ja kujera ya zauna, sannan ya buɗe wata jaka da ya shigo da ita, ya fito da wani flashdrive, ya cillawa Aliyu, shi kuma ya cafe, kafin ya shiga kallon flashdrive ɗin yana juyawa. “Ga amsar tambayoyinka nan!" Kawai Bilal ɗin yace, sannan ya fito da system ɗinsa ya fara sarrafata. "Ban gane ba" Faɗin Aliyu yana jan kujera tare da zaunawa, Bilal ya ɗaga idonsa ya kalle shi. "Tambayoyin da kake min game da rashin zuwana aiki tsawon sati guda! Duka suna cikin nan... Kamar yanda mu ka yi hasashe tun farko cewar wannan ƙungiyar ta GKL suna ɗaukan 'yan mata da sunan za su sama musu aiki a ƙasashen waje, daga baya sai su ɓige da safararsu suna cinikinsu zuwa wasu ƙasashen da ban da waɗan da aka alƙauranta musu hakan ta tabbata!" Cikin irin mamakin da Bilal ya saba jefa kowa a ciki idan har ya bankaɗo wata gaskiya da ake ganin wuyar tonuwarta Aliyu ya sake kallon flashdrive ɗin. "Ke nan duk tsawon satin nan kana Lagos?" "Eh ina Lagos! Kuma ban dawo ba sai da cikakkiyar hujja a kan abin da shuwagabbanin ƙungiyar suke aikatawa! Wannan flashdrive ɗin na ɗauke da videon 'yan matan da ake safara yayin da ake sakasu cikin container a tashar jirgin ruwa dake Lagos! Ba wannan kaɗai ba, hatta da videon cinikayyar 'yan katan da suke akwai! Na ɗauko komai, kuma na samo komai" Aliyu ya ƙyafta idonsa yana ƙarewa Bilal kallo, kawai sai ya yi dariya, domin ya tuna da wani lokaci can baya da ya taɓa cewa anya kuwa Bilal Mutum ne? Domin abubuwan da yake sun zarce tunani, duk yadda ƙungiyar GKL ke ƙoƙari wurin ganin ta kare sunanta dan kada ya fito a cikin waɗannan harƙallolin na cinikin 'yan mata daga Nigeria zuwa ƙasashen waje sai da Bilal ya bi hanyar da ya san zai iya tona musu asiri. "Ban ma san me zan ce maka ba" "Kawai ka ce Allah ya rayani!" Faɗin Bilal yana murmushi. "To Allah ya rayaka! Yanzu kuma mene ne next?" Bilal ya jingina da kujerarsa yana juyata a hankali, kafin ya ɗaga hannayensa yana motsasu wuri guda, can kuma sai yace. "Mu dai namu kawai shi ne mu binciko duk wasu abubuwan da ake zargin an binnesu a ƙarƙashin ƙasa, kuma an hanemu da yaɗa labaran bogi, yanzu kuma da na tabbatar da hakan za mu miƙa videon zuwa ga manager, sai manager ya tantance kafin labarin ya isa ga al'umma da kuma mahukunta, idan kuma ya fita ya rage ga hukuma su san abin yi!... Mu dai mun yi namu mun gama" Aliyu ya girgiza kansa. "Ni da kaina zan kai wannan bayanin zuwa ga manager!" Bilal ya taɓe bakinsa yana gyara zaman hularsa. "Ai tuni ya san da batun... Domin tun jiya da na dawo na sanar da..." Bai rufe bakinsa ba wayarsa dake aje a kan table ta soma ringing, dan haka gaba ɗaya hankalinsa ya koma kan wayar, musamman ma da ya ga mahaifiyarsa wadda ke zaune a garin Gusau ce mai ƙiran. Kafin ya ɗaga ya yi wa Aliyu alama da zai iya tafiya kawai, kafin ya ɗaga ƙiran, ya soma magana cike da ladabi. Kana ganin yanda yake wayar za ka san cewa da wani mai matuƙar muhimmanci a gare shi yake wayar. *Sabon Titin Kwaɗo, Katsina state...* *08:23 na dare.* ZAHRA POV. A hankali ta rufe ƙofar kitchen, bayan ta fito daga ciki hannunta riƙe da bowl, wanda ta haɗa cereal a ciki. Sanye take da wide blue trouser, sai farar free size T-shirt, kanta ɗaure da wani farin viel, ƙafafunta cikin farin Crocs mai ado a jiki. "Zahra kin sauƙe min miyar nan daga kan gas?" Mummy ta tambayeta lokacin da ta iso cikin main falo tana shirin cire Crocs ɗin ƙafarta. "Eh na sauƙe" Ta amsa lokacin da ta zauna a kan carpet, sannan ta janyo center table gabanta, ta ɗora bowl ɗin hannunta a kai, ta ci gaba da kallon film ɗin da ake haskawa a Hijra Tv, tana yi tana cin cereal ɗin da ta haɗa, domin ita ba ta cika cin abinci da daddare ba, sai cereal ko abu makamancinsa. "Amira!" Mummy ta ƙira Amira dake kwance a kan kujerar zaman mutum uku, ta saka waya a gaba tana latsawa. Jin ba ta amsa ba yasa Mummy ta kalleta. "Amira!" Ta kuma ƙira tana binta da kallo. "Na'am Mummy" Ta amsa tana tashi zaune a firgice. Domin har ga Allah ba ta ji ƙiran farkon da Mummyn ta mata ba. "Ke wai haka kullum rayuwarki za ta ƙare a kan waya? Baki da aiki sai na latsa waya? Wallahi Amira a kan wayar nan za mu samu matsala da ke?" Amira ta sauƙe kanta ƙasa tana ɓata fuska. "Ki tashi ki je ɗakina ki ɗauko min wayata, na ji kamar tana ringing" Ta miƙe da sauri ta yi sama, sannan ta je ta ɗauko wayar da ƙira yake shigowa a karo na uku. Ta dawo falon ta miƙawa Mummy, da yake wayar mai muhimmanci ce yasa Mummy ta tashi daga falon, domin mahaifiyarta ce ta ƙirata. "Kin san jiya sau biyar wannan Kamal ɗin yana ƙiran wayata?" Faɗin Zahra tana kallon Amira wadda ta ci gaba da aikin da ta saba, wato latsa waya. Amira ta dubeta. "Kuma me ya sa ba ki ɗaga ba?" "Na ɗaga na ce masa me? Me zan ce?" Amira ta kwashe da dariya, har da tafa hannuwa. Ta aje wayarta tana bin Zahra da kallon mamaki. "Oh yarinya! Wai ke ba ki san yanda ake magana da saurayi ba ko?" Zahra ta girgiza kanta. "Sanin me zai amfane ni da shi? Saboda ni dai yanzu karatuna na saka a gaba! Ba zan ɗauki zancen wata soyayya ba" Amira na shirin sake faɗar wani abin wayarta ta shiga ruri, ganin me ƙiran yasa ta ja tsaki ta saka wayar a silent mood. "Waye?" Zahra dake kaiwa spoon bakinta ta tambaya tana kallon wayar Amira da ta kuma kawowa haske alamun wani ƙiran ne yake shigowa. Amira ta juya idonta. "Zai wuci wannan mara mutuncin!" "Haba Yaya! Yanzu fa ya kusa zama mijinki, ki daina ce masa mara mutunci mana" Amira ta ƙanƙace idonta tana kallon Zahra. "Ba ki san abin da yace mini jiya ba! Wai na ɗora video a status yace na yi maza-maza na sauƙe! As if shi ne Ubana!" "To a hakan kike cewa na fara soyayya? Ku dai da kuka ga za ku iya sai ku yi, amma mu kam ba yanzu ba, kuma ta wani ɓangaren ya fiki gaskiya Yaya! Dan ba ko wani saurayi ne zai yarda ya riƙa ganin video ko hoton matar da yake son aure a duniya ba!" "Duniya? Yanzu dan na ɗora a status shi ne zai baza duniya?" Zahra ta yi murmushi mai sauti, sannan ta jinjina kanta. "Kin san Allah kar ki yi mamakin ganin videon ki a Instagram ma, domin dan kin ɗora a story yanzu wani zai iya sauƙewa a kan wayarsa, wani ya gani ya tura, shi ma waji zai iya tura daga wayarsa, daga haka za ki ga yana bazuwa har ki ganshi a inda ba ki yi zato ba" Wayartata suka sake kalla, sakamakon wani hasken da ta kuma kawowa dalilin shigowar ƙiran Mahmud saurayin Amiran. Wanda ake sa ran zai zama mijinta nan da wasu wattani, domin hatta kayan aurenta an kawo, an kuma yanke ranar auren tun bayan da ta gama karatunta na gaba da secondary. "Allah sarki bawan Allah! Ki ɗaga, ba ki san abin da zai faɗa miki ba, wata ƙila ma zuwa ya yi" Amira ta yatsina fuska tana hararar wayar, kamar da aka ce ita ce Mahmud ɗin. "Ai Wallahi zai yi ya gama, amma ba zan ɗaga wayarsa ba, zai gani idan ina da mutunci ko a'a" Zahra ta yi dariya. "Wallahi yana ƙoƙari da halinki Yaya..." Kafin Amira ta kai ga bata amsa aka buɗe ƙofar shigowa falon. Daddynsu Alhaji Musa Gyaza ya shigo falon yana gyaran murya. Sanin cewa shi ne yasa suka miƙe da sauri suna amsa sallamar da ya yi, kafin suka masa sannu da zuwa. Daddy ya amsa yana murmushin ganin 'ya'yan nasa mata biyu kacal a duniya. "Kallo kuke ne?" Daddy ya tambaya yana ƙarasowa cikin falon. "Eh Daddy!" Zahra ta amsa shi. "To mashaallah... Aminatu" Daddy ya ƙarashe da ƙiran sunan Amira na gaskiya. "Na'am Daddy" Amira ta amsa tana matsawa kusa da inda yake. "Mahmud ya zo tun ɗazu yana waje yana ta jiranki! Yace wai idan ya ƙira wayarki ba ta shiga!" Zahra da Amira suka haɗa ido, na jin yanda Mahmud ya ɓoye laifin Zahra a idon Daddy, duk dan kar ya san abin da ta yi ya mata faɗa. "Ya na ga kuna kallon juna? Ko ba haka ba ne?" Daddy ya katsewa ko waccensu zancen zucin da suke. Dan haka Amira ta yi saurin kallonsa. "Eh, eh haka ne Daddy" "To sai ki fita ki je ki same shi, dan Sani Mai gadi yace ya daɗe a compound tsaye yana ta jiranki!" Ta amsa da to, sannan ta yi sama ta ɗauko mayafi ta sauƙo ta fita, lokacin kuma Daddy ya zauna a falon, yana tambayar Zahra ina Mummy, tace masa tana sama, dan haka ya umarceta da ta ƙira masa ita. *Nigerian Law school, Bwari, P.M.B 170, Garki, Abuja Nigeria.* YABINTU POV. A karo na uku, Khadija da suke zaune ɗaki ɗaya ta sake kwashewa da dariya, har da guntuwar ƙwallarta. Cike da mamaki Yabintu dake zaune kan gadonta na kwanciyar mutum guda ta ɗaga kai ta kalleta, yayin da take duba wani abu a cikin system. "Wai ke dariyar me kike ne tun ɗazu? Sai ka ce wadda ta samu taɓin ƙwaƙwalwa?" Dariya ba ta gama cin Khadija ba ta tashi zaune a kan gadonta, tana riƙe da cikinta tace. "Littafin FULANI na Khadeeja Candy nake karantawa!... Wallahi daga ɗan iska sai Faɗime, wai Shattima ne ya bata waya, kuma ba ta faɗawa Inna ba har ta dawo gida waya na ringing, Inna tace kamar ƙaran waya take ji, Faɗime tace ba waya ba ce... Inna tace in ba waya ba ce mene ne, buɗar bakin Faɗime sai cewa ta yi wai Memory ne ta haɗiye, da Inna tace a ina aka taɓa jin memory na waƙa a cikin mutum sai cewa ta yi da ta je birni ne ta tsince shi, sai ta haɗe da ruwa, shi yasa yake waƙa a cikinta!" Lokacin da ta ƙarasa bawa Yabintu labarin ita kanta sai da ta yi dariya, domin abin ne akwai ban dariya. "Allah ya kyauta" "Humm! Dan ma ba ki ji abin da ta yi wa Iya mayya ba..." Khadija na shirin ci gaba da bata wani labarin ƙaran wayarta da aka ƙira ya hana ƙarasa labarin, dan haka ta ɗauki wayar ta amsa ƙiran da yake shigowa da sauri. Domin mahaifiyarta ce ke ƙira. "Mummy ina yini?" Daga ɗayan ɓangaren Hajiya Ramatu ta amsa da. "Lafiya lau Yabintu! Ya makaranta ya karatun?" Yabintu ta yi murmushi tana rufe system ɗinta, kafin tace. "Komai yana tafiya yanda ake so Mummy!" "To mashaallah Allah ya taimakeku" "Anti Bint!" Ta jiyo muryar ƙaninta Khalid ta cikin wayar, alamun dai yana kusa da Mummy ne. "Ni ina ruwana da kai? Kai da na fi wata uku da dawowa, amma ko sau ɗaya ba ka ƙirani ka ji ya nake ba" Tana jin sanda ya karɓi wayar a hannun Mummy, kafin yace. "Wai da ma Mummy ba ta gaya miki ba? Tun washe garin ranar da kika tafi phone ɗina ta lalace, kuma Daddy ya ƙi sauya min wata, yace wai dole sai na gama SS3" Yabintu ta yi dariyar jin yanda Khalid ya ƙarashe maganar cikin alamun dake nuna cewa zaman rashin wayar ya ishe shi. "Dan Allah Anti Bint ki sa baki ya sai min wata" Ya faɗa ƙasa-ƙasa, kuma hakan yasa ta gane cewa duka suna zaune ne tare da su Daddy a falon. "Ok give him the phone" Da sauri ya matsa kusa da Daddy dake cin abinci a falo, sannan ya miƙa masa wayar, Daddy ya dube shi, kafin ya kalli wayar. "Anti Bint ce take son magana" A hankali Daddy ya miƙa hannunsa na hagu, sannan ya karɓi wayar ya kara bisa kunnensa. "Daddy barka da dare! Da fatan kana cikin ƙoshin lafiya" Cewar Yabintu daga ɗayan ɓangaren. "Lafiya ƙalau Fatima! Ya karatun ya makarantar?" "Komai lafiya yake tafe Daddy" "To mashaallah haka ake so ai" "Daddy magana ce a kan wayar Khalid! Yace tasa ta lalace, kuma kai ka ƙi sai masa sabuwa" A jikinta ta ji cewar lokacin da ta gama maganar, sai da Daddy ya kalli direction ɗin Khalid, kafin ya bata amsa. "Ai da yace miki na ƙi sai masa sabuwa ya kamata ace ya faɗa miki dalilina" "Eh haka yace wai kace sai ya kammala secondary school" Daddy ya girgiza kansa yana murmushi. "To ai ba gaskiya ya faɗi miki ba... Gaba ɗaya Khalid ya tattare hankalinsa ya mayar kan waya! Ba shi da aiki sai chat, game da kuma kalle-kallen banza da wofi! Ko ta karatunsa ma ba ya yi, duk wannan maida hankalin nasa a kan karatu yanzu babu, abin takaicin ma shi ne, last exams ɗinsu C4 ya ci a mathematics, B2 kuma a English! Shi yasa lokacin da wayar tasa ta lalace na ji daɗi, kuma ko da ace ba ta lalace ba zan karɓeta, kuma ba zan ba shi ba sai zuwa lokacin da ya gane cewa karatu shi ne kaɗai gatan da zan iya ba shi a yanzu!" Yabintu ta jinjina kanta. "Ƙwarai kuwa Daddy kana da gaskiya, kuma hukuncin da ka yanke ya yi dai-dai. Amma kuma idan aka duba za a ga cewar ita ma wayar tana da amfani Daddy, domin ko karatun ma zai iya yinsa ta waya, assignment da sauransu... Dan haka ni dai da za bi tawa da an sai masa wata, amma kuma ba za a ba shi ba sai an kafa masa dokoki da ƙa'idoji, wanda idan ya kiyayesu to ya shafawa kansa lafiya, idan kuma ya ƙi sai a ƙwace wayar!" Daddy ya kuma kallon Khalid da ya sunkuyar da kansa tun lokacin da Daddyn ya fara faɗawa Yabintu abubuwan da ya yi, kafin ya jinjina kansa. "Shikenan Fatima, inshaallah za mu duba iyuwar hakan...! Zuwa yaushe za ki leƙo gida ne?" "Yauwwa Daddy Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana... Batun zuwana kuma zan iya shigowa Zamfara nan da next week, domin mun kusa samum Mid-semester break, so zan zo na yi good 1 to 2 weeks a gida, kafin mu dawo a ci gaba da fafatawa!" "To Allah ya kawoki lafiya, sannan a ci gaba da dagewa a kan karatun nan, tun da yanzu ƙiris ya rage a gama" Ta jinjina kanta tana murmushi. "Haka ne Daddy..." Ba su jima suna magana da Daddy ba Mummy ta karɓa, ita kam sun ɗan sha hira, kafin suka yi sallama, Khadija ba ta ƙarasa bata labarin Faɗimen Bandalo ba ƙiran Umar ya shigo wayarta, dan haka ta jingine komai ta tsaya yin waya da shi kaɗai. Salma Ahmad Isah ✍️ Zahra Royal Star 🌝 _____________ _ZARGE paid book ne a kan ₦500 kacal. za ku tura kuɗinku ta account details ɗin da zan rubuta a ƙasa._ 5487270431 Salma Isah Monie point Sai kuma a tura shaidar biya ta 0813 047 9973. *ZARGE* _(Mugun Ƙulli)_ BY SALMA AHMAD ISAH & ZAHRA ROYAL STAR بسم الله الرحمن الرحيم Page 03 *Room No. 19 Gamji Royal Hotel, Gusau, Zamfara State Nigeria* Ringing ɗin wayar a karo na uku ne ya sa su tsaida albidar da suke kan yi, da ƙyar kyakkyawar matashiyar ta miƙa hannu ta ɗauki wayar tana ɗan ɓata fuska kaɗan. Shi ko saurayin dake rungume da ita har yanzu bai fasa abunda yake mata ba sai kiss yake kai mata kota ina. "Hello Mama me ya faru ne? Muna cikin aji ana cikin lecture kin sani fa" Daga cikin wayar Mama ta ce "Haba Bilkis tun ɗazu fa nake ta faman neman wayarki amma ba'a ɗauka... Kuma ga shi har yamma ta yi ba ki dawo ba". "Mama kin san cewa idan muna aji ba'a ɗaukar waya, yanzu ma sai da na fito tukunna na ɗauki wayar taki". "To shikenan sai kin dawo, kuma dan Allah ki kula, karatun nan da aka sa a gaba a dage a yi shi!". Bilkis ta ɗaga idonta tana juya shi cike da gundura da maganar Mama a kan wani karatu, ƙasa-ƙasa tace. "To inshaallah" Daga haka ta yanke wayar tana jan ɗan guntun tsaki, kamar wacce tayi waya da ƙawarta ko abokiyar gabarta. Saurayin dake naniƙe da ita ya saki wani murmushin gefen baki yana cewa. "Ke fa shegiyar kan ki ce Baby Bilkees. Uwar da ta haife ki, ki ke ma haka?". "Hmm kai dai kawai asha sha'ani. Duk ɗaukarsu fa school nake zuwa kullum, shi ya sa fa nasa aka raba mana school da Yaya Falak, saboda ba na son abin da zai kawo min cikas a harkata. Duk ɗaukarsu ni nitsatssiya ce mai jin magana wacce karatu kawai ta sa a gabanta, shi ya sa kullum nake riga Falak fita daga gida, a kan hakan kullum sai Hajiya ta mata faɗa, tana cewa ta riƙa yin ɗabi'u irin nawa, wai ko ta ga dai-dai a rayuwarta... Shi ko Ya Faisal da ya bawa Falak kyautar abu gara ya bani, kuma sai ya ƙirani sau biyar bai ƙirata sau uku ba, kullum gani yake cewar na fi Falak nutsuwa". Saurayin ya yi dariya. "Gaskiya kin iya takunki, da ba ki bari an haɗa muku school ɗaya da 'yar uwarki ba, da sai ta tona miki asirin cewa baki yawan zuwa school". "Ai ko da na karya Shegiya, dan ita ma ƙarara take nuna ƙiyayyata dake zuciyarta, ni ma dannewa kawai nake ina kulata, domin na sa a ga laifinta, amma Wallahi ko ni ba na sonta, ita ma ga shegen baƙin halin tsiya". Saurayin nata ya ƙara ja musu bargo yana cewa. "Manta da zancen kawai... mu hole kawai kan ji?". FALAK POV. zaune take a tsakiyar samari Maza da Mata, can nesa kad'an dasu kid'a ne ke tashi sosai 'yan mata da maza sai rawa suke suna chashewa. Wasu kuma a zazzaune suna shan giya da sigari da wasu ƙwayoyin maye. Daga inda suke Falak da Khamis na zaune waje ɗaya, sai lallaɓata yake kan yauma ta sha ƙwaya, amma ta ce ita fa yau ba ta jin za ta iya shan wani abu, domin yau saura kaɗan asirinta ya tonu wajan Hajiya. Kallonta ya yi yana kamo hannunta, da sauri ta fisge tana cewa "No Khamis na sha gaya maka cewa ba na so kana yawan taɓani, a tsaya iya shan kayan maye kawai, amma ba na jin zan iya baka kaina, ka sani kuma ba na so kana yawan kawo hannunka jikina please". Ta ƙare maganar fuskarta a murtuke, da sauri Khamis yace "Ohhh I'm so sorry Baby luv, na manta ne, Amma..." Dakatar da shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu, za tai magana wani abokin Khamis ya zo wajen, ya ja hannun Khamis suka ɗan bar wajan. Falak dake bin ko ina da kallo, idonta na gane mata yadda wata budurwa da saurayi dake nesa da inda take zaune suna kissing juna. Wani dogon tsaki Falak ta ja, tana kauda idonta daga garesu, har hakan ya jawo hankalin wasu kanta. Dan ita kam kwata-kwata ba za ta iya yarda da wannan ƙazantar ba, ta fi gane kawai ta sha tayi mankas abinta, amma fa bata yarda wani shege ya raɓeta ba. Wasu 'yan ƙwayoyi ta ɗakko tasa a baki ta kora da wani maganin mura kwalba guda, tsabar yadda take jin ranta a ɓace yasa ta ɗauki ƙwayoyin da Khamis ya mata tayinsu ɗazu amma ta ƙi sha. Bayan wasu mintoci ta fara jin kanta ya fara juya mata, idonta na lumshewa a hankali. Lokacin da jikinta ya saki ta kwanta a kan kujera tana jin duk hayaniyar da ake a wurin na tashi sama-sama. A lokacin kuma wani matashi ya shigo wurin, kuma yana shigowa ya wuce wurin abokansa da suka gayyato shi. Bai jima da tsayawa kusa da su ba ya hangi Falak, wadda ta ji duniyar ta mata nauyi, hakan yasa ta tashi zaune kanta na juyawa. Ba tare da ya bari kansa ya kulle ba kawai ya nufi wurin da take, domin har ga Allah ya ɗauka cewar ita ma kamar sauran 'yan matan dake wurin ce, ma'ana mace mara kamun kai, domin ba shi kaɗai ba, duk wani wanda zai ga wata mace a wurin haka zai ɗauketa, domin da ma wurin ba na 'ya'yan mutunci ba ne. A kusa da ita ya zauna yana kallon yanda take ta layi daga zaunen da take, kansa ya juya ya kalli mutanen wurin, sannan ya sake matsawa kusa da ita, hannunsa ya ɗaga ya kai jikinta zai taɓa hannunta yana lasar baki kamar maye. "‘Yan mata barka da yamma!" Ya faɗa yana taɓa hannunta, duk da Falak na jin jikinta ya yi nauyi sosai hankalinta bai gushe ba, domin ba ƙaramar ƙwaya za ta sha ta sa hankalinta ya gushe gaba ɗaya ba, kuma hakan ya samu nasaba ne sakamakon jininta da yake da ƙarfi. Ba wai mayen ne ba za ta yi gaba ɗaya ba, a'a za ta yi maye, amma hankalinta na jikinta, so duk abin da za'a mata ko a furta kusa da ita za ta ji, kuma za ta riƙe a kwakwalwarta kamar tana cikin hayyacinta. "Kyakkyawa kamarki bai kyautu ace kina zaune ke kaɗai ba, ya kamata ki bani dama a yau ɗin nan na nuna miki soyayya!" Ya kuma faɗa yana taɓa damtsen hannunta, a lokacin kuma ta yi ƙarfin halin bige hannunsa daga jikinta, tana watsa masa jajayen idonta. "Kar... Kar ka sake...!" Ta haɗe kalaman da ƙyar tana nuna shi da ɗan yatsanta a kasalance. Saurayin ya yi murmushi, sannan ya sake kaiwa hannunsa jikinta a karo na uku, ganin ba za ta iya jurewa ba yasa ta tattaro duk waji guntun ƙarfi da ya rage mata, sannan ta ɗaga hannunta ta kwaɗa masa mari. "Kar ka... Ka sake taɓani na ce... Ɗan akuya kawai!" Marinsa da ta yi, da kuma kalaman da ta furta yasa gaba d'aya hankali ya dawo kansu, shi kuma saurayin ya miƙe tsaye yana tunanin irin abin da zai mata, yana shirin rama marinsa da ta yi wata budurwa cikin waɗan da suka gayyace shi wajen ta zo ta ja hannunsa suka bar Falak kwance. "Kai kuwa me ya kai ka zuwa wajan budurwar Khamis? Wadda duk wajan nan an san cewa ba ta da mutunci, to ko shi Khamis ɗin yana son ɗanata amma taƙi ba sa damar hakan". Cewar budurwar da ta jan ye shi. "Shi ya yarda har yake lallaɓata, tana a bige ma zai iya mata illa ba ta sani ba". "Kayya! Ai ba zai taɓa iyawa ba ne shi ya sa, kamar ta mass asiri, hatta wannan shaye-shayen da take da ƙyar ya shawo kanta ta farasa, amma mu'amala da Maza, kam taƙi". "To wata ƙila sonta yake da gaske shi ya sa ba zai iya rage zafi da ita ba, ko kuma asirin ta mai, ni da ace ni ke da waccan ai Wallahi da tuni na gama da ita ta wannan wajan" *Sabon Titin Kwaɗo, Katsina State, Nigeria* ZAHRA POV. Zama Amira tayi a kan gado, bayan ta dawo daga wurin Mahmud. Zahra dake kwance akan ɗayan gadonta, tana karanta wani book ɗinta na school ta tashi zaune tana cewa. "Ya na ga kin dawo sai sakin murmushi kike, hala an shirya ba?". Wani murmushin Amira ta ƙara saki tana cewa. "Uhum an shirya, kawai tausayi ya bani wallahi, bawan Allahn nan yana sona sosai." Zahra ta yi dariya tana rufe book ɗinta. "Ai dole, ni ma wallahi ya birge ni, sai kuma ki ɗan rage ɗora hoton naki tunda dai kinga ba ya so, ki yi ƙoƙarin faranta masa kema... Kuma da ma kwana nawa ne ya rage ki shiga daga ciki?". Amira dake kallon Zahra tace "Ohhni 'yasu wai yau kece ke bada shawarar a kula da saurayi, keda ba abin da kika sani a cikin soyayyar ma?" Murmushi kawai Zahra ta yi tana ɗan gyara zamanta a kan gadon tana cewa. "Hmm ba wani abu na ce ba ai, shawara ce na baki kyauta, ku da kuke soyayyar sai ku yi ta fama ai, kullum raine a ɓace kai da mutum shi ya sa kwata-kwata ba ta birge ni". "Hmm lallai yarinya, za ma ki yi ne nan gaba kaɗan, sanda zata kamaki ta kanainaye miki zuciya ba ma zaki sani ba". "Bana ganin ranar za ta zo kuwa". Da ɗan mamaki Amira ke kallon Zahra ta ce. "Kambu! Anya yarinyar nan baki da iskokai a kanki kuwa? Yo idan ba haka ba, ta ya za ai ka ji dad'in rayuwa babu masoyinka a kusa da kai?, Kina da babban aiki fa a gabanki wallahi. Ko da yake Mummy zan sa ta rinƙa amso miki rubutu gaskiya ki rinƙa sha". Dariya kawai Zahra tayi tana girgiza kanta ta koma ta kwanta, domin gobe da safe zata fita, tana da lecture d'in safe. Yayin da ita kuma Amira ta tashi ta shiga bayi tana ta mitar halin Zahra, a lokacin wayar Zahra dake aje a gefen pillownta ta yi ringing, hakan yasa ta ɗauka ta duba. "Hello Zahra Beauty" Cewar wata murya wadda daga ka ji ta za ka san cewa mai ita ta iya tsiwa. Zahra ta yi dariya. "Yane Kulsum mummuna" Suka kuma yin dariya a tare. "Wai A. Sani cewa tace gobe bayan mun gama class ɗin 8-10 za mu tafi Aldusar Parks mu je mu huta a can!" Zahra ta girgiza kanta, dan da ma ta san zancen gizo ba zai wuce na ƙoƙi ba. "Yanzu ku bayin Allah ana daf da fara exam kuna zancen zuwa hutu? Ina muka ga hutu a lokaci irin wannan?" Tana iya jiyowa sautin tsakin Kulsum ta cikin wayar. "Ke! Tsakanin mutuwa da hisabi babu wanda za a fasa, dan haka gobe kawai ki shirya mu tafi, kuma ki taho mana da shepherd's pie... Na san kin iya yinsa sosai!" Kulsum ba ta damar cewa komai ba ta katse ƙiran, murmushi kawai ta yi ta aje wayar, tana yo wa Kulsum ɗin addu'ar shiriya. *Channels Television Station, Abazie Ifeanyi Close, Guzape, Abuja Nigeria* BILAL POV. A hankali ya sauƙe wayar dake manne a kunnansa yana ɗan juya kujerar da yake zaune akai. K'arar bud'e k'ofar Office d'insa ne ya sa shi d'an d'aga kai yana duban mai shigowa, ganin Aliyu ne yasa ya miƙe tsaye ya soma tattata kayansa yana faɗin. "Zan wuce gida, gaskiya yau da wuri nake son tashi". Aliyu bai zauna ba yana tsaye ya ce "Oga ne yake son ganinmu gaba ɗaya fa". Ɗan kallon Aliyu Bilal ya yi kafin ya saki ƙaramin tsaki yana faɗim "Cewa za kai ɗan rainin wayo ke son ganinmu, hala wani abu ya ji dan gane da binciken da na ke yi ko?". "Naga alamar hakan daga garesa. Amma dan Allah Bilal kar ka nuna irin zuciyarka a wajansa, ka bi komai a hankali please, na san halinsa bai wuce ya ce, kwata-kwata ka cika shiga abin da bai kamata ba, ko kana son basu matsala a gidan Tvnsu ba, ka san abin da ka binciko abu ne babba sosai, wadda ya ƙunshi ɗaya daga cikin manya-manyan ƙasar nan, so da ma dole ka fuskanci matsaloli tare da k'alubale". Bilal ya sauƙe kansa yana ɗan lumshe idonsa sai kuma ya buɗe, dan har sun sauya launi sunyi ja kaɗan, saboda matsalar k'asar da take yawan ci masa tuwo a ƙwarya. "Shin idan shugabanni na haka sai zuwa yaushe ci gaba zai wanzu a ƙasar nan Aliyu? Taya za a yi ka binciko gaskiya ga abu k'iri-k'iri, an san cewa gaskiyar ce amma a tauyeta?, A gaskiya ba zan ci gaba da lamuntar hakan ba, kuma shi yasa muke samun matsala da Sir, domin shi duk abin da za a binciko sai yasa an rage wani abu daga cikin binciken da aka yi, saboda yana tsoron bada rayuwarsa ne?, Ko kuwa cin hanci suke kawo masa? Ni na rasa gane inda ya dosa" Da sauri Aliyu ya ce "Haba Bilal wane irin cin hanci kuma, gara ma dai kace ko tsoro yake ji kar mutanan suje har inda yake su ce za su cutar da shi, domin ba Allah a ransu, duk wani abu da zai basu matsala kawar da shi suke, shekara nawa suna aikata irin haka, ka ji an taɓa kawo ƙarshen abin?". Bilal ya ɗan saki murmushin da ya fi kuka ciwo ya ce "To mi ye aikin Jaridar da ma?, ba taimakon al'umma da hukuma ba ta hanyar bankaɗo abubuwan da aka ɓoye ba ne?, Kuma in dai kana da tsoro ko shakka a ranka to ba za ka tab'a aikin jarida yadda ya dace ba, in dai kuma baka da gaskiya shi ma bazaka tab'a aikinka yadda ya kamata ba, za ayi ta cutar jama'a ne, kai kuma mai gaskiyar tsoro sai ya saka ka danne gaskiyar taka, ka bada dama ke nan domin a cuci jama'a, komi kake fa Allah sai ya tambaye ka ranar gobe?". Jikin Aliyu ya yi sanyi ya ce "To Bilal Sir fa ba zai tab'a fahimtar wannan ba, amma ban sani ba ko ya fahimta idan ka masa bayani kamar yadda kake min haka, amma mu ma kanmu muna kasada da rayuwarmu ne Wallahi". "Ni ko zan rasa rayuwata a wannan aikin ba na jin zan damu, burina shi ne, na bankaɗo gaskiya komai ɗacinta". Yana idasa maganar ya nufi k'ofa, shi ya fara fita kamin Aliyu ya take masa baya. Zahra Royal Star🌝 Salma Ahmed Isa✍️ _____________ _ZARGE paid book ne a kan ₦500 kacal. za ku tura kuɗinku ta account details ɗin da zan rubuta a ƙasa._ 5487270431 Salma Isah Monie point Sai kuma a tura shaidar biya ta 0813 047 9973. *ZARGE* BY ZAHRA ROYAL STAR & SALMA AHMAD ISAH Page 04 *Nigerian Law school, Bwari, P.M.B 170, Garki, Abuja Nigeria.* YABINTU POV. Cikin hanzari take shiryawa, domin sun yi da Umar kan zai zo ya ɗauketa dan ya kaita ta duba jikin mahaifiyarsa dake kwance a asibiti ba lafiya. Gaggawar da take ta yi ce ta sa Khadija da Laura da ta kawo ziyara ɗakin nasu suka shiga dubanta. "Wai Umar ɗin ya zo ne?" Laura ta tambaya tana kama baki. Ba tare da Yabintu ta kallesu ba ta saka clip ta riƙe veil ɗin da ta yafa a kanta, kafin tace. "Ya kusan ƙarasowa dai! You all know that I don't want keep him waiting" Laura da Khadija suka yi dariya, har da tafawa. "Oh soyayya ruwan zuma..." Cewar Khadija, ba ta ƙarasa ba Laura ta caɓe da. "In ka sha ka ba masoyi" Ita dai Yabintu murmushi kawai ta yi tana kallon fuskarta a mirror. Lokacin kuma wayarta ta shiga ƙara alamun shigowar ƙira, da yake da ma ƙiran nasa take jira sai ta yi saurin ɗaukan wayar ta amsa. "Hello Hayati gani nan a ta wajen babban gate!" Faɗin Umar ta cikin wayar, dan haka Yabintu ta yi murmushi tana juyawa a jikin mirror. "Okay gani nan fitowa" Tana gama faɗin hakan ta sauƙe wayar, sannan ta ɗauki handbag ɗinta, ba ta fita ba sai da ta kuma gyaggyara jikinta, kafin ta fita, su Laura na mata dariyar shaƙiyyanci. A inda yace mata ya faka ta same shi, shi da kansa ya fito ya buɗe mata motar ta shiga, yana ta yabawa da irin kyan da ta yi. "Wai me ya samu Umma da faja'atan ta kama rashin lafiya?" Ta tambaye shi lokacin da ya ɗauki hanyar zuwa asibitin da aka kwantar da mahaifiyarsa. Umar ya dubeta yana driving da hannunsa ɗaya, yayin da yake shafa sumarsa da ɗayan hannun nasa. "Jininta ne ya hau ba gaira ba dalili! Amma dai su likitocin sun ce da alama ta ci ɗaya daga cikin abubuwan da hawan jinin ya haramta mata ne" Cike da tausayawa Yabintu ta girgiza kanta. "Allah ya bata lafiya" "Amin ya Rabbil izzati" Har suka isa Abuja Continental Hospital yana bata labarin yanayin ciwon mahaifiyar tasa. Shi ya mata jagora har zuwa ɗakin da aka kwantar da ita, lokacin da suka shiga kuma suka iske ƙannensa huɗu a cikin ɗakin, Mata uku na miji ɗaya. Su huɗun gaba ɗaya sai da suka gaisheta cikin girmamawa, ta amsa tana ta murmushi, kafin ita kuma ta miƙa tata gaisuwar ga mahaifiyar su Umar ɗin. "Lafiya ƙalau Fatima Bintu! Ya makaranta ya karatu! Ya kuma wajen su Umman taki?" Mahaifiyarsu Umar tace yayin da suke gaisawa da Yabintu. Kan Yabintu a ƙasa tana murmushi ta amsa da. "Wallahi komai lafiya Umma, su ma suna lafiya, nan da jibi ma zan je hutu gida..." "Ahhh to mashaallah! Allah ya taimaka..." Ta jima a asibitin suna ta hira da ƙannen Umar, domin da ma can sun saba da ita. Sai da lokaci ya fara ƙurewa sannan tace za ta tafi, ƙannen Umar mata sai da suka rakata har zuwa parking space dake ƙasa, kafin suka koma, shi kansa Umar a hanya sai da ya tsaya ya mata siyayyar guzirin da za ta kai gida. Kafin ya dawo da ita cikin hostel ya tafi. *House No. 17, Aguiyi Ironsi Street, Off Ahmadu Bello way, Durumi District, Abuja.* *Da misalin 09:13 na dare.* BILAL POV. Cike da kula ya ɗaga electric kettle ɗin dake ɗauke da tafasasshen ruwan zafi, ya tsiyaya ruwan zafin a cikin wani mug da ya saka ganyen shayi, sai da ya zuba ruwan yanda zai isheshi, kafin ya mayar da kettle ɗin ma'ajinta ya aje. Ya kashe socket ɗin da kettle ɗin ke jone a jiki, kafin ya koma kan sandwich ɗin da ya haɗa. Duk da dare ne ba ya jin zai iya cin wani abu bayan sandwich ɗin, domin bayan tarin gajiya da ayyukan da suka shige masa ba ya jin yana da lokacin zama ya girka wani abin mai nauyi. Fitowa ya yi daga kitchen hannunsa riƙe da plate mai ɗauke da yankan sandwich biyu da kuma mug mai ɗauke da tean da ya haɗa. Lokacin da ya ratso ta falon da babu hasken komai cikinsa sai na Tv ya yanke shawarar zama a falon domin ya ci sandwich ɗin a nan. Sanda ya zauna ya janyo center table ya aje mug tare da plate ɗin da yake riƙe da su a kan table ɗin. Sannan ya ɗauki remote control ya sauya channel daga StarPlus zuwa Channels Tv, domin yana so ya ga ko za a saka rahoton da ya kawo bayan yin cecekuce tsakaninsa da shugansu na wurin aiki, duk da sun tsaida magana kan za a fitar da rahoton tunaninsa bai gama yarda kan za a saka ɗin ba, gara ya gani da idonsa. Remote control ɗin ya aje, lokacin da ya ga har an yi nisa a rahoton ƙarfe tara na dare da ake haskawa, ya ɗauki mug ɗinsa ya kai baki ya yi sipping tea ɗin dake ciki kaɗan, hankalinsa gaba ɗaya yana kan Tvn, rahoton da yake ta tuƙuburin gani shi ne na ƙarshe a cikin rahotannin da aka gabatar, sai dai duk da haka ya yi farin cikin ganin labarin, domin babu abin da aka rage na daga wanda ya kawo. Sai da aka gama haska labaran bai ci ko rabin sandwich ɗin da ya haɗa ba, duk kuwa da muguwar yunwar da ya kwaso daga wurin aiki. Sai da aka gama ɗin ne ma kafin ya samu sukunin cinyewa, ya ɗauke kayan ya kai kitchen, bai fito ba sai da ya wanke duk abubuwan da ya ɓata. Lokacin da ya fito daga kitchen ɗin wayarsa dake gurzawa a kan sofa ta ja hankalinsa. Ko da ya ɗauki wayar har ƙiran ya katse, a nan ya ga 3 missed call daga Aliyu, kasancewar wayar a vibration mode take yasa ƙaran wayar bai fito ba. Murmushi kawai ya yi, ganin ƙiran Aliyu ya sake shigowa wayar a karo na huɗu, kuma ya san me yasa yake ta jera masa wannan ƙiran kamar wanda yake binsa bashi. "Yane?" Kawai yace yana ɗaga wayar. "To! Buri ya cika, an haska labarai kuma an bada rahoto, yanzu sai mu koma gefe mu ga abin da zai wakana!" Wani murmushi mai kyau Bilal ya yi yana shafa kwantaccen gashin sajensa, kafin yace. "Inshaallah komai zai tafi kamar yanda muke fata, ko hukuma da gwamnati ba su ɗauki mataki ba wannan rahoton ya isa ya wayar da kan al'umma game da illar tura yaransu mata ƙasashen waje zuwa aikatau! Kuma ka ga ko ta nan ma mun yi nasara!" Ya ji alamar Aliyu ya gyaɗa kansa, kuma ƙasa-ƙasa yake jiyowa muryar tilon yaron Aliyun yana wasa. "Ina madam da Boy?" "Suna lafiya gwauro!" Bilal ya yi dariya yana zaunawa a kan sofa. "Ka yi ka bar ni! Komai lokaci ne, kuma na Allah ne, mu ma inda rai da rabo namu na nan tafe" "Allah ya nuna mana..." Wayar tasu ba ta tsawaita ba ta ƙare, saboda ƙiran Adebisi wata abokiyar aikinsu da ya shigo ya kori na Aliyu. "Yanzu na gama kallon labaran da aka haska yau! Gaskiya ka yi na mijin ƙoƙari B. Liman!" Faɗin Adebisi cike da farin cikin abin da abokin aikin nata ya yi. Bilal ya shafa kansa yana faɗin. "Ƙoƙarin ba nawa ne ni kaɗai ba, har da ke Ade, domin ke ma kin taimaka da taki gudunmawar!" Ade ta yi dariya. "Komai zan maka zai zama kamar na yi wa kaina ne B. Liman!" Ta kuma ƙiran sunansa da ta saba ƙiransa da shi, wato B. Liman, cikakken sunansa kuma Bilal Bashir Liman, ana taƙaitawa ne da B. Liman ɗin kawai dan ya fi sauƙin faɗa ko a baki. "Zuwa yaushe za ki dawo?" Ya tambaya, dan yanzu haka ita Adebisi tana garin Enugu. "Nan da sati mai zuwa zan dawo" "Ki kawo min tsarabar doya" Shi kansa da ya yi batun sai da ya yi dariya, ballantana kuma ita da ya shaidawa. "Wa zai girka maka doyan idan na kawo? Ko Mama za ka kaiwa?" Ya girgiza kansa yana taɓe baki. "Ni zan ci abata!" "To zan kawo maka, kar ka damu" "To na gode, ni zan sauƙa a kan layi!" "Okay bye" Ya aje wayar a gefensa, sannan ya ɗaga kansa yana shafa sumar kansa, sabon aikinsa da ya saka a gaba yana yawo cikin tunaninsa. *Sabon Titin kwaɗo, Katsina state...* Mummy ta aje flask biyun da take riƙe da su a kan center table, kafin ta waiga ta kalli Daddy dake operating wayarsa. "Ga abincin nan" Ta idasa maganar tana zama kusa da shi, kafin ta ɗauki plate ta shiga zuba masa abincin, har sai da yace ya isa, ya aje wayar hannunsa sannan ya karɓi plate ɗin ya soma cin abincin. "Su Zahra sun kwanta ne?" Daddy ya cillowa Mummy tambayar, yayin da take zuba masa drink a cikin cup. A hankali Mummy ta aje cup ɗin da ta zuba masa drink ɗin next to plate ɗin abincinsa. "Ba lalle ba, ita Zahra ɗazu ta dawo daga Aldusar Park, kuma na san a gajiye take, yanzu haka ba za ta kasa baccin ba, ita dai idon screen ina da tabbacin ba ta yi baccin ba" Abba ya yi dariya jin sunan da ta ƙira Amira da shi. "To ko zuwa gobe da safe ne ki sanar da su, zuwa gobe su shirya, tun da Saturday ce na san Zahra ba ta da class, za mu je Gyaza mu duba Hajiya!" Mummy ta yi murmushi tana shafa cinyarta. "Ai ba sai gobe ba, yanzu ya kamata na gaya musu, domin su shirya tun yanzu, duk da na san ba kwana za mu yi ba kamar yanda muka saba!" Daddy yana taunar abinci ya jinjina mata kai. ZAHRA POV. Yayin da Amira ke soyewa tana ƙonewa da Mahmud saurayinta a waya ita kuwa duk ƙauri ne ya cika mata hanci. Tana kwance a kan gadonta, ta kunna kallo a system ɗin Amira tana kallon wani indian series. Duk da a gajiye take daɗin Film ɗin ya hanata kwanta da wuri, don so take ta gama kallon wannan episode ɗin sai ta kwanta, saboda yau Kulsum da A. Sani wato Aisha Sani ƙawarsu sun bata wahala kamar me, dan bayan Aldusar Parks and Zoo da suka yi niyyar zuwa tun farko har Maryam Park suka ja ta. Sai da ta yi nadamar binsu zuwa wannan yawon, kuma tsabar tijara duka da uniform suka fita, kowa ya gansu ya ga ɗalibai. Rabi da rabi hankalinta na kan wayar da Amira ke yi da Mahmud, wadda ke kwance tana wani juyi, alamun wayar tana kai mata har ka, ta wani kashe murya kamar ba ita ba. Ita har mamakin kalaman da Amiran ke amfani da su a wayar take, dan ita kam ji take ba za ta iya ba. A wani ɓangaren kuma zuciyarta ce ke raya mata cewar anjima kaɗan za ta shukawa Mahmud tsiya, domin Amira ba a abin arziƙi da ita, ko sun shirya to fa sai ta yi abin da zai sa su ɓata. Har episode ɗin ya ƙara Amira ba ta gama wayar ba, da yake ta gaji sai ta rufe system ɗin, ta ɗorata a kan side drawern da ta raba gadonta da na Amira. Sannan ta ɗaga bargonta ta rufa a kan ƙafafunta, ta lalubo hula ta saka a kanta, sannan ta shiga yin addu'o'in bacci da na kariya. "Ya Amira mu kwana lafiya" Ta faɗa tana shirin kwanciya, shigowar Mummy ɗakin ce ta katse abubuwa biyu lokaci guda, kwanciyar Zahra da kuma wayar da Amira ke yi da Mahmud. "Au! Har yanzu ba ku kwanta ba ke nan?" Mummy ta tambaya tana binsu da kallo. "Yanzu dai zan kwanta... Ya Amira kuma waya take" "In ji wa? Ni ma kwanciyar zan yi ai!" Cewar Amira tana harar Zahra, alamun dake nuna ke ke ba a rufin asiri da ke?. Mummy ta yi murmushi, kafin ta furta musu wasu kalmomi da za su zama sanadiyayyar rabuwarsu da juna na har abada. "To! Daddynku yace ku shirya, zuwa gobe za mu tafi wurin Hajiya a Gyaza!" Zahra ce ta fara zumbur ta tashi zaune tana kallon Mummy. "Dan Allah Mummy?" "Da ina muku wasa ne?... Sai da safe" Ta ƙarashe tana rufe ƙofar, dan da ma ba ta gama shigowa cikin ɗakin gaba ɗaya ba. Zahra da Amira suka dubi juna, cike da farin cikin batun tafiyarsu Gyaza, domin gaba ɗayansu babu wanda bai son zuwa Gyaza, wato mahaifar Daddynsu, inda 'yan uwansa da mahaifiyarsa suke zaune... Dalilin son zuwansu Gyaza shi ne, ana nuna musu gata sosai, duk sanda za su je suna ganin gata a wurin 'yan uwan ubansu... Kakarsu ma haka na matuƙar ji da su, duk da tun da yanzu lamuran tsaro suka ɓaci idan sun je ba sa kwana a can, zuwa suke su yini su dawo cikin garin Katsina. A cikin daren suka tashi suka fara shirya kayan da za su saka gobe idan za su tafi, kai kace zuwa za su su yi wata a can. Kuma tun a cikin daren Amira ta faɗawa Mahmud batun tafiyarsu zuwa Gyaza... Wata tafiya da za su yi nadamar yinta, a lokacin da nadamar ba za ta amfanesu da komai ba. Salma Ahmad Isah ✍️ Zahra Royal Star 🌝 _________________ ZARGE littafin kuɗi ne, domin more naku sai ku biya ₦500 to. 5487270431 Salma Isah Monie point Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973 *ZARGE* BY ZAHRA ROYAL STAR & SALMA AHMAD ISAH Page 05 *Unguwar Samaru, Gusau, Zamfara state, Nigeria.* *08:22 na dare.* FALAK POV. Zaune take a falo, hannunta na dama riƙe da smoothie jar, yayin da take juya straw ɗin dake ciki a hankali da hannunta na hagu... Jin takun mutum ta wurin stairs bai sa ta kalli wurin ba, dan kowa ya yi wa Falak shaidar shariya da rashin kunya, wai kuma hakan ma ko kaso biyar cikin ɗari na halin ɗan uwanta Faisal ba ta ɗauka ba... "A dawo lafiya Bilkis, dan Allah ki kula, ki duƙufa ki yi karatu sosai!" Muryar Mama da ta ji ce ma tasa ta samu arziƙin kallon wurin da suke tsaye ita da Bilkis, ta sha dogon Hijab har ƙasa, domin da ma ita ba ta da shigar da ta wuce dogon Hijabi, a wasu lokutan ma idan za su fita tare da Falak sai tace ba za ta je da ita ba, don ita ba za ta bita da dogon Hijabi kamar matar takaba ba... "Inshaallah Mama" Faɗin Bilkis kanta a ƙasa, sai da Mama ta gama mata nasiha, sannan tace mata ta tafi, ta gaban Falak ta zo ta wuce tana mata sai da safe, wani ɗan iskan kallo Falak ta bita da shi, wanda yasa lokaci guda Bilkis ta kama kanta, sannan ta fita daga falon da sauri. "Falak! Kallo ake ne?" Mama ta tambaya yayin da take zaunawa a kan settee, Falak na zuƙar smoothie ɗin dake cikin jar ɗin hannunta ta kalli Mama, kafin ta ciro straw ɗin daga bakinta tana murmushi. "Umm kallo nake" "Ke ba za ki yi karatun ba?" "Wani karatu kuma Alaji?" Ta furta ba tare da ta damu da zancen karatun ba, domin a yanzu ba shi ne a gabanta ba, a duniya idan tana da maƙiyi to bai wuce karatu da makaranta ba, shi yasa a wasu lokutan take haura sati ba tare da ta leƙa makarantar ba, duk kuwa da yanda Kawunsu Alhaji Sammani wanda ya ci gaba da kula da kasuwancin mahaifinsu bayan rasuwarsa yake kashe mata kuɗi sosai a kan makarantarta. A wani ɓangaren ma za ta iya cewa damuwar karatu ce ta saka ta fara shaye-shaye, ba wai dan ba ta gane karatun ba, haka kawai take jin cewa ta tsani makaranta da duk wani abu da ya shafeta, a lokacin da tace ba za ta ci gaba da zuwa makaranta ba Hajiya ta balbaleta da faɗa, har ta kai ga tace idan ba ta maida hankali kan karatunta ba sai ta tsine mata, kuma daga lokacin ta fara shaye-shaye. "Ba exams za ku fara ba?" Ta ɗan kalli Mama kaɗan, kafin ta girgiza kanta. "Na sani, amma ni ba yanzu zan fara nawa karatun ba..." "Sai zuwa yaushe ke nan? Uwar malalata" Muryar Hajiya ta katse mata hanzari, dubanta ya kai kan Hajiyar dake tsaye jikin banister. "Ai in dai ba za ki maida hankali a kan karatunki ba mun yi ta samun matsala da ke" Ita dai ba tace komai ba, jar ɗin hannunta kawai ta aje a kan center table, Hajiya ta ƙaraso cikin falon, lokacin da Mama ke faɗin. "Haba Hajiya? Ai ba haka za ki riƙa mata ba! Cikin lallami za ki na mata nasiha, ki kuma nuna mata hanyar da kike son ta bi" "Humm! Maman yara ke nan! Yanzu Falak ba ta yi hankalin da za ta yi wa wani faɗa ba? Da wannan girman nata zan wani zaunar da ita ina lallaɓata?" Ita dai Falak ƙala ba tace musu ba, dan idan ta faɗa ɗin ran Hajiya ne zai ɓaci nan take, kuma za ta iya yin kanta da faɗa, wata ƙila ma ta bugeta, yawan faɗan Hajiya yasa gaba ɗaya ba su yi wata shaƙuwa da ita ba, kullum cikin tsare gida take, babu wani lokacin samun kusanci irin na 'ya da uwarta a tsakaninsu, ita kuma ba ƙawa gareta ba ballantana idan damuwa ta mata yawa ta samu wani da za su tattauna da shi domin samun mafita... Shi ko Faisal kar ma ta soma tunkararsa da batun shawara ko wani abu, mutumin da sai su yi wata ba su ga farin haƙorinsa ba, saboda sam shi dariya ba ta dame shi ba, kullum fuskar nan a ɗaure tamau, kamar haddarin da ya so zubar da ruwa, wasa na wa da ƙaninsa ma ba ya haɗata da shi, ballantana har ta kai su ga hira, kuma shi in zai yi magana umarni yake bayarwa, ka ƙi bi kuma jikinka ya gaya maka. "Ina Bilkis ne? Ban ji motsinta ba" Faɗin Hajiya, Mama ta yi murmushin jin daɗi. "Ta tafi makaranta, tace yau a hostel za ta kwana saboda suna da exams gobe, so tana so ta yi karatu sosai..." Hajiya ta wurgawa Falak dake latsa wayarta harara. "Kin ji fa? Yarinyar kirki, wadda ba ta sa shashanci a gaba ba, ita karatun ne kawai a gabanta..." "Ai ita ma Falak ɗin tana karatun Hajiya, kawai dai sai san barka" "Ina fa..." Ƙofar falo da aka ƙwanƙwasa yasa hirar tasu dakatawa. "Falak tashi ki duba waye" Falak ta aje wayar hannunta, sannan ta nufi ƙofar ta buɗe, tana arba da wanda yake bayan ƙofar ta ja tsaki a fili tana ɗauke kai. "Falak waye?" Hajiya ta tambaya tana zaune daga cikin falo. "Sirikarki ta gobe ce" Ta faɗi maganar cikin shaguɓe, tare da buɗe ƙofar gaba ɗaya, Maryam budurwar Faisal kuma ƙanwar Mama ciki ɗaya ta bayyana ga su Hajiya. Lokaci guda Hajiya ta washe baki tana miƙewa tsaye. "Maryam? Ke ce tafe?" Maryam dake tsaye a bakin ƙofa ta shiga ciki, yayin da Falak ke binta da wani kallon rashin kunya, duk da ta lura sai ta ɓoye, da yake ita ma 'yar bariki ce sai ta matsa kusa da ita za ta rungumeta tana faɗin. "Ohhh my little sister..." Dakatawa ta yi, lokacin da Falak ta ɗaga mata hannu alamun ta dakata. "Ja jikinki a nawa!..." Kawai tace, sannan ta juya ta ɗauki wayarta ta yi sama, shi ma wannan Maryam ta shaƙa, amma ganin Hajiya da Mama yayarta yasa duk ta shanye komai, ta nufi wurin Hajiya tana gaisheta kamar ta Allah. Hajiya ko kamar ta saka zani ta goyata, dan ita kanta ba ta ce ga dalilin da ya sa take son Maryam ba, kuma soyayyar da take mata ce tasa lokacin da ta nuna cewa tana son Faisal Hajiyar ta yi Uwa ta yi makarɓiya ta tilasta Faisal amincewa da soyayyar Maryam, duk kuwa da shi ɗin ba ya sonta. "Amma dai a nan za ki kwana ko?" Cewar Hajiya lokacin da ta kawowa Maryam drink. Maryam ta yi sipping drink ɗin, kafin tace. "A'a, yanzu ma zan koma, mun yi magana da Major ne a kan wani book da na daɗe ina naima, yace mini shi kuma yana da shi, shi yasa na zo karɓa" Hajiya ta kama baki tana 'yar dariya. "Ikon Allah! Ai kuwa kin ga bai barwa kowa keyn ɗakinsa sai Bilkis, ita kuma yanzun nan ta fita!" Kamar da gaske Maryam ta ɓata fuska cikin rashin jin daɗi. "Oh oh, amma ban ji daɗi ba Wallahi" "Ah haba Maryam? Kar ki ji ba daɗi mana, bari na saka Falak ta zo ta duba miki" "Za ta yarda kuwa? Kin san halin Falak fa?" Hajiya ta ja tsaki. "Ita ta haifi kanta?" "A'a Hajiya, amma bari dai na ƙira wanda zai iya sakata ko da ranta bai so ba" Ta ƙarashe tana latsa wayarta, a cikin contact list ta naimo lambar 'Heart beat' sannan ta aika masa ƙira. Falak na shiga ɗakinta ta kwanta a kan gado, damuwar Hajiya da abin da mata duk sun bi sun hanata bacci... Da ta ga ba za ta iya ba sai ta tashi zaune, sannan ta sauka daga kan gadonta ta sunkuya a ƙasan gadon, ta miƙa hannunta ta janyo wata jaka dake ƙasan gadon, ta fito da wasu kwalaban kayan maye guda biyu, ta mayar jakar ƙasan gadon, sannan ta zauna a kan gado, ta buɗe kwalba ɗaya tana shirin ɗurawa cikinta wayarta ta dakatar da ita... Tsaki ta ja, sannan ta rufe kwalbar tana miƙa hannunta saitin wayar, ganin sunan 'MR. BEAST' ya fito ɓaro-ɓaro a kan screen yasa ta zaro ido. Ta yi saurin aje kwalbar, ta goge bakinta, har da su kimtsa kanta kamar wadda ya ƙira videocall. "Assalamu alaikum! Ya Faisal ina yini" Ta faɗa a salihance, domin ko kusa ba ta son abin da zai haɗata faɗa da Faisal, dan sai ta gwammaci barin zaman gidansu gaba ɗaya a kan Faisal ya yi fushi da ita. Daga cikin wayar, wata murya mai kauri, wadda ta ƙunshi zallar kamewa da kwarjini ta fito ta doki dodon kunnenta. "Da ban wuni ba za ki jini haka? Kina ina?" Falak ta juya idonta, a ranta kuwa faɗi take. _"Masifaffe"_ "Ina zan je a lokaci irin wannan? Ai ina gida?" "Ok! Maryam ta zo, ki je ɗakin Bilkis ki ɗauko keys ɗin ɗakina, ki je ki buɗe, a cikin wannan shelf ɗin da yake kusa da desk za ki ga wani book mai suna 'The Inner Child' ki ɗauka ki bawa Maryam" Cike da takaici Falak ta cije leɓenta na ƙasa, dan ta san da gangan Maryam ɗin ta aikata mata haka. In dai kuwa haka ne yanzu za ta gasa mata maganar da za ta hana mata sukuni. "Shikenan yanzu zan je na ɗauko mata... Yaushe za ka dawo ne Yaya?" Abin ka da ɗan uwa, sai ta samu kanta da tambayarsa hakan, duk da ta san ba lalle ta yi gwaninta ba, dan wata ƙil ma gwasaleta zai yi, kuma sai ya yi abin da take hasashen. "Ban sani ba" Kawai yace a dake, dan haka ita ma ba ta sake cewa komai ba ta aje wayar tana kallonta, duk da bai katse ƙiran ba, shi a rayuwarsa ba a yanke masa ƙira, ko da kuwa kai ka ƙira shi ba shi ya ƙiraka ba, saboda a wasu lokutan ya kan manta abin da zai ce, sai bayan wasu mintoci kuma zai tuna, sai ka ga ya faɗa maka, wani lokacin kuma maganar ta ƙare, amma saboda isa da gadara ba ka isa ka kashe masa waya ba sai in shi ya kashe. Har bayan shuɗewar wasu sakkani, kafin Falak ta ga ƙiran ya katse, a bayyane ta ja tsaki, sannan ta ɓoye kwalaban da ta fito da su, ta ɗauki wayarta ta kuma fita. Ɗakin Bilkis ta shiga, ta ɗauki keys ɗin, sannan ta sauƙo ƙasa tana bin Mama da Maryam dake hira da kalll, dan zuwa lokacin Hajiya ba ta falon, wani ɗan iskan kallo ta wurgawa Maryam, kafin ta yi ƙwafa ta fice daga falon. Part ɗin Faisal dake gidan ta shiga, sannan kamar yanda yace mata haka ta yi, har ta samu book ɗin. Lokacin da ta fito take kulle part ɗin nasa ta ji muryar Maryam a bayanta. "Yauwwa Sister, kin ɗauko mini?" Ta juyo tana kallonta. "Ga shi na ɗauko ƙuda sarkin naci!" Ta faɗa tana danƙa mata book ɗin a hannunta, a karo na uku Maryam ta shaƙa, dan tun da ta zo Falak ke mata abubuwan da ba su mata daɗi. "Kar ki damu sister, yayanki ya kusa zama nawa" Falak ta yi murmushi mai sauti tana harɗe hannayenta a ƙirji. "Idan ma bacci kike to ki farka! Domin jelar raƙumi ta yi nesa da ƙasa Maryam, kuma ko da girgiza kurna ta fi magarya, dan haka Ya Faisal ya fi ƙarfinki, na san kina ganin kamar kalamaina a matsayin shashanci ko wauta. Duk ki cire wannan, batu ne na gaskiya nake miki, Faisal ba zai taɓa aurenki ba" Maryam ta yi murmushi tana juya book ɗin dake hannunta. "Zan so ace na ga yanda za ki yi ranar da na mallaki yayanki a tafin hannuna!" Falak ta yi taku biyu zuwa gabanta, sannan ta ɗaga hannunta dake riƙe da wayarta ta dafa kafaɗarta. "Wannan ranar ba za ta zo ba Habibty 'yar wahala" Tana gama gasa mata maganar ta janye hannunta daga kan kafaɗarta, sannan ta raɓata ta wuce tana karkaɗe hannunta da ya taɓa Maryam ɗin, kamar wadda ta ɗauki buhu mai datti. Haka Maryam ta bi bayanta da kallo a kufule, tana hasaso kalar abubuwan da za ta yi wa Falak bayan ta shigo gidan a matsayin batar Faisal. YABINTU POV. Gaba ɗaya ƙawayenta ne suke zazzaune a ɗakinsu, yayin da suke hirar tafiyar da za ta yi, duk da wasu daga cikinsu su ma za su je gida. "Ni fa ji nake kamar na biki mu tafi Zamfara tare!" Cewar Khadija... Yabintu ta wurga mata hararar wasa. "Kamar da gaske, ke ɗin da tsoro ya cika miki ciki kika kasa zuwa last time da muka yi za mu tafi da ke?" "A'a ni fa ban ga laifinta ba! Yo ai ko ni ba zan iya zuwa yankinku a halin da ƙasar nan take ciki ba" Faɗin wata daga cikin friends ɗin nasu. "Kai duk fa wannan abubuwan da kuke ji ana yi bakinsu ƙauyuka... Ba su shiga cikin gari" Cewar Yabintu. "To ai ka fin a isa garin dole sai an ratsa ta ƙauyen ko?" Cewar wata tana taɓe baki. "Wallahi duk kallonku nake, kawai dan abin bai zama muku dole ba ne shi yasa!" "Ke da ya zamewa dole sai ki je... Mu dai Allah ya yaye mana" Yabintu ta yi dariya kawai. "Amma dai da Umar za a je ya yi rakiya?" Faɗin Laura a sigar tsokana. "Ai shi ba rago ba ne kamar su o'o, tun da shi da 'yan uwansa suka tashi tun daga Abuja har zuwa Zamfara suka je naiman aurena!" Gaba ɗaya su shida suka sheƙe da dariya. "Oh Yabintu da Umar soyayya kamar ba za a rabuba! Mu dai Allah ya kaimu lokacin bikin nan mu cashe!" Faɗin Khadija tana ɗaura ɗankawalin kanta da ya since, Yabintu ta yi murmushin jin daɗi. "Amin" Ta amsa tare da sauran... Su da kansu suka tayata shirya kayanta, domin zuwa gobe za ta bi jirgi zuwa Sokoto, daga nan kuma za ta hau mota ta kaita cikin Gusau. Sai da aka gama shirya kayan kuma aka dawo aka ci gaba da hirar da rabinta ya fi karkata a kan karatunsu da suke daf da gamawa. Salma Ahmad Isah ✍️ Zahra Royal Star 🌝 _________________ ZARGE littafin kuɗi ne, domin more naku sai ku biya ₦500 to. 5487270431 Salma Isah Monie point Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973 *ZARGE* BY ZAHRA ROYAL STAR & SALMA AHMAD ISAH Page 06 *Channels Television station, Abazie Ifeanyi Close, Guzape, Abuja.* BILAL POV. Zaune yake a office ɗinsa yana wasu rubuce-rubuce, sosai ya maida hankali kan rubutun da yake, lokacin da ya ɗiga aya ya miƙa hannunsa na dama ya ɗauko wata takarda, kamin ya fara wani rubutu a kanta, shigowar Aliyu office ɗin ce ta sa ya dakatar da rubutun da yake, na tattara wasu bayanai game da binciken da yake son farawa. Kuma kallo ɗaya ya masa ya sake maida hankalinsa kan rubutun da yake. Aliyu dake kallonsa tunda ya shigo ganin yadda aiki ya sha masa kai, yasa shi zama kawai. Ƙara kallonsa Bilal ya yi, ganin yadda ya yi shuru ya sa Bilal ture tarin takardun dak gabansa, kamin ya ɗan murza goshinsa yana runtse idonsa, kamin ya ware hannunsa ya d'auki wata takarda yana ta kallonsa, jin shirun ya yi yawa yasa shi ya fara magana. "Me ya faru ne na ganka a haka?". Ya tambaya ba tare da ya kalle shi ba, A hankali Aliyu ya aje masa fallan jaridar da ya shigo da shi a kan table ɗinsa. Bilal ya bi takardar da kallo, kuma kafin ya kai ga karanta abin da ke rubuce a jiki Aliyu yace. "An kama shugaban ƙungiyar GKL hukuma tace za su gudanar bincike a kansa da ƙungiyarsa" Bilal ya sa hannu ya ɗauki jaridar, sannan ya bi hoto haɗe da rubutun dake jiki, ya miƙe tsaye yana ci gaba da kallon jaridar. "Ban sani ba ai, saboda tun da na tashi yau wani aiki ya sha min kai... Alhamdulillah". Ya faɗa muryarsa ɗauke da murnar yin nasara, ya koma ya zauna yayin da Aliyu ke murmushi. "Ɗazu Victor ke sanar min cewa wai ka ɗauki hutun sati guda... Yanzu kuma wani sabon aikin za ka yi?" Bilal ya aje jaridar da yake ta riƙe da ita, sannan ba tare da jin komai a ranaa ba yace. "Bincike a kan 'yan bindigar cikin daji! Waɗan da suka addabi mahaifata da maƙotanmu!" Ido waje Aliyu yake kallonsa, ya tabbatar Bilal ba zai bar aiki ba sai ya jawowa kansa da ma su gabaki ɗaya mutuwa. "Lallai ka d'auko bincike mai tsananin had'ari tare da rikitarwa, domin kuwa shi ma wannan akwai sa hannun wasu hafaffu da mai a ƙasa, me yasa wai kai ba ka da aiki sai binciko abubuwa maau haɗari irin waɗannan?". Bilal ya yi murmushin gefen baki. "Kawai addu'a za ka min, ku sai ku tsaya a matsayarku, amma ni dai na sa a raina cewar sai na binciko duk wata badaƙalar da ake a ban ƙasa... Zuwa gobe zan wucw Zamfara". Bilal bai tanka masa a kan maganarsa ya farko ba, domin ya san maganarsa ba ta isa ta sa Bilal ya fasa abin da ya yi niyya ba... Tun da har yace zai yi to zai yi, dan haka ya tsallake wannan maganar yace. "Za a je duba Mama ke nan?" "Eh ka san na kwana biyu ban je ba, kuma idan na je can zan fi samun wasu bayanai daga wurin mutane" "Gaskiya kam, to Allah ya tsare, ya kaika lafiya, a miƙawa Mama saƙon gaisuwata, sai mun yi waya". "Yeah, amin thank you". Daga haka Aliyu ya tashi ya fita ya bar shi zaune yana nazarin ta inda zai fara aikin da ya ɗauko. *Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, Nigeria.* YABINTU POV. Zaune take a cikin motar Umar, isowarsu ke nan filin jirgin, kuma dalilin da ya sa ba ta fito ba wai sallama suke, kuma lokacin tashin jirgin da saura, dan wajejan awa ɗaya sauya. Kallon Umar ta yi, ganin yadda yake kallonta kamar zai cinyeta, murmushi ta saki tana ɗan gyara zamanta a cikin motar ta ce. "Ya da wannan kallo kuma? Sai kace wacce ba za ta dawo ba?". Umar ya sauƙe ajiyar zuciya, yana ɗan shafa sumar kansa kamin ya ce. "Ji nake kamar kar ki tafi ne, kuma sai da muka zo filin jirgin na fara jin hakan". Wani murmushin Yabintu ta saki tana cewa "Uhum kamar fa yau ne za ka ga na dawo, ai hutun ba mai yawa bane, it's just 1 to 2 weeks... And whenever you missed me you can give me a touch abi?". Ba ta san sanda ya kamo hannunta ba, sai ji ta yi yana murza shi kaɗan-kaɗan, haka kawai yake jin kamar idan ta tafi za su rabu ne har abada... Tun da Yabintu take da shi bai tab'a gigin koda tab'a d'an yatsanta ba, shi ya sa take kallonsa cike da tsananin mamakinsa. "Hayati na ga jikinka ya yi sanyi, ka daina damuwa please lafiya lau zan dawo inshaallah". Cewar Yabintu ganin duk jikinsa ya yi sanyi. Lumshe idonsa ya yi, kafin ya buɗe ya shiga binta da wani kallo wadda bai tab'a mata irinsa ba, muryarsa a sanyaye ya ce. "Na sani ba dad'ewa za ki yi ba, amma wallahi haka kawai nake ji kamar a fasa tafiyar nan taki". A hankali ta d'an murza hannunsa dake cikin nata tana kallon cikin kwaryar idonsa. "Ba na so ina ganin damuwa a kan fuskar nan taka fa please, ni da zan tafi a jirgi, kuma insha Allahu 'kalau zan dawo ka ji?". Daga haka ta yi saurin janye hannunta daga cikin nasa, a hankali tasa hannunta na dama ta murɗa murfin motar ta fita, shi ma fitar ya yi yana kallon terminal, ya zagoyi inda take, suka fara tafiya, a ƙofar Terminal suka rabu, suna ta waving ma juna hannu kamar kar su rabu. Daga ƙarshe ma dai tace masa ya zo su ɗan zauna a ciki kafin lokacin tashin jirginsu, bai ƙi ba, domin har ga Allah shi ma bai gaji da ganinta ba. A kan wasu kujeru suka zauna, Yabintu sai baza idonta take, domin hatta ita kanta zuciyarta ba ta mata daɗi. Suna zaune a wurin wayar Umar ta yi ƙara. A hankali ya zaro wayar ganin mai kiran nasa yasa shi ɗauka da sauri. "Okay ga ni nan zuwa yanzu insha Allah". Abin da ya ce ke nan bayan ya gama sauraron abin da na wayar yace. Kallonsa Yabintu ta yi ganin yadda ya tashi da sauri yasa ta ce "Me ya faru?". "Wai Umma ce taƙi shan magani, tace dole sai na zo na ba ta da kaina, na san duk salon kar ta sha maganin ne, saboda na san ba son maganin take ba, ga shi jikin nata sai a hankali har yanzu. I'm so sorry cuz I have to leave before you leave" Yabintu ta saki murmushi, sannan ta miƙe tsaye tana kallonsa. "Haba ba komai, ka je kawai, tun da kai ka kawo ni har airport". Murmushi ya sakar mata yana ƙara jin ƙaunarta har cikin ransa, sai da ya furta mata i love you kamin ya bar wajan. Yana niyyar saka key ya tayar da motarsa domin tafiya kawai kamar an ce ya waiga ya hango wata jakar Yabintu da ta manta ta, hannu ya miƙa ya ɗauko jakar, ya fito dai-dai da wayarsa na sake ringing. Yana fitowa daga motar su kai k'aro da wani, tsabar saurin da Umar yake bai ma lura da shi ba. D'agowa ya yi domin bawa wanda ya bige haƙuri, sai idonsa ya gane masa wani tsohon friend ɗinsa Bilal B. Liman. Murmushi kowanne d'auke a kan fuskarsa Umar ya ce "Ah-ah B. Liman?". Bilal ya gyara zaman hular dara dake kansa yana murmushin ganin tsohon abokinsa. "Na'am Faruk Yola" Dariya suka yi, sannan suka yi musabihi. "Ya na ganka a nan? Ko aikin jaridar ne ya kawoka?" Bilal ya girgiza kansa. "Ko kaɗan, ganin gida zan je?" Umar ya yi dariya. "Sai ka ce wata mace... Za a leƙa Zamfara ke nan?" "Wallahi da yake na d'an kwana biyu ban je ba". Umar zai sake magana ya sake jin k'arar wayarsa, da sauri Umar ya kalli Bilal ya ce. "Ohhh sorry friend dan Allah ga wannan jakar ka bawa Yabintu, wallahi sauri nake Umma ba lafiya, za ka ganta zaune wajan waiting chairs, ba mu gaisa sosai ba, Allah ya tsare hanya Kuma". Yana damƙa masa Umar ɗin ya yi saurin buɗe motarsa ya shiga, ko damar tambayar wace ce Yabintun ma bai ba shi ba, domin shi bai san wacece budurwar Umar ɗin ba. Bilal ya bi abin da ya basa da kallo. Shi ya za'ai ya gane ta, tunda ba wani saninta ya yi ba, koda yake ya yi masa uzuri da alama jikin Umman nasu ne ya sake tashi, kuma Mahaifiya ai ba abar wasa ba ce, shi ya sa Umar d'in duk ya bi ya rud'e, "Uwa mai dad'i." Cewar Bilal a zuciyarsa. Murmushi ya saki sanda ya fara tafiya yana nufar inda waiting chairs ɗin. Dai-dai lokacin da ya iso wurin, aka fara wata sanarwa cewa jirgin da zai tashi k'arfe 9AM, wadda zai tashi daga Abuja zuwa Sokoto an soke tashinsa sakamakon wasu 'yan dalilai da ba su bayyana ba, suka kuma ƙara da bawa fasinjojinsu haƙuri game da wannan tangarɗar da aka samu. Hankali a tashe Yabintu ta mik'e, sai kuma ta saki wani dogon tsaki, a dai-dai lokacin, a wannan wurin, zuciyarta ta ƙissima mata wani abu da ya zama sanadiyyat faruwar ƙaddararta ta rayuwa. Tunanin take kan ba za ta iya jira sai zuwa gobe ba, ta riga ta yanke cewar yau a kan gadon ɗakinta na Gusau za ta kwana, dan haka gara ta hau motar Kaduna daga Abuja, idan an sauƙeta a Kaduna kuma sai ta hau motar Gusau. Duk da da ba haka tsarin yake ba, idan ta hau jirgi zai sauƙesu ne a Sokoto, daga nan kuma za ta hau kota zuwa Gummi, daga Gummi kuma za ta hau motar Gusau. Mutane da yawa sun ji haushin tsaida masu tafiya da akai, wasu kuma sun bada uzurin ko jirgin ne akwai matsala ko kuma sun dai hango wani abun ne. Shi ko Bilal dake tsaye kusa da Yabintu bai ji wani abu ba, Allahn da ya yi hau shi ya yi gobe, kuma goben ma kamar yau take... Tsayawa da ya yi sauraron sanarwar ya mantat da shi saƙon da aka ba shi, juyowar da zai yi suka kusan cin karo da Yabintu da ta ɗauki bags ɗinta. Kuma hakan ya sa ya tune da saƙon da aka ba shi, sai ya dubeta yayin da ita ma shi take kallo. "Oh sorry Pleas" Bilal ya girgiza kansa alamun ba komai, kafin yace. "please ko ke ce Yabintu girlfriend d'in Umar?". Da ɗan mamaki Yabintu ta ƙara kallonsa, dan ba ta sansa ba, shi ina ya santa? Sai kawai ta samu kanta da d'aga masa kai kawai. Murmushi ya saki yana mik'a mata jakarta dake hannunsa yana cewa "Ga wannan Umar ne ya bada ya ce a baki, kin manta tata ne a cikin mota, yana sauri, shi ya sa ya bani na baki. Kuma gashi an samu matsalar tashin jirginmu". Murmushi ta d'an sakar masa, jin wajan Umar ya santa ta amsa tana godiya ta ƙara da. "Eh amma ni ba zan iya jira har sai gobe ba, yau zan wuce gaskiya". "Ohh amma baki tsoron hanya?... Saboda akwai hatsari sosai fa". "Ba wani abu da yardar Ubangiji lafiya lau zan isa". D'aga k'afad'arsa ya yi kamin ya bata bata waje yana mata fatan sauƙa lafiya, lokacin da ya fito faga terminal ya shiga motarsa sai ya ƙira mahaifiyarsa ya sanar mata da cewa an soke tashin jirginsu, sai zuwa gobe zai zo. A lokacin kuma Yabintu ta fito daga terminal da kayanta, ta tare taxi wadda za ta kaita tashar motar da za ta hau ta Kaduna... A kan idonsa ta shiga taxi ɗin, kuma har taxi ɗin ta bar wurin bai gama wayar ba, sai da ya gama sannan, ya sauk'e numfashi, yana jin kamar bai yi dai-dai ba, da ya bar ta ta tafi, kuma ya san motar haya za ta hau, mi ya sa bai hanata ba? Ko ma ya bita su tafi tare, haka kawai yake jin kamar bai kyauta ba. *Ƙauyen Gyaza, Kankia Local Government, Katsina State, Nigeria.* *12:44 na rana.* ZAHRA POV. A hankali Zahra ke matsama Hajiya kakarsu k'afarta. Amira kuma na zaune kusa da Hajiyar tana cin kwaɗon rama da aka musu, duk sun zagaye Hajiya suna mata hira. Hatta Mummy na kusa da Hajiyar suna ta lallaɓata, domin yanda suke son tsohuwar sosai. Shi ko Daddy yana can wurin 'yan uwa, abin ka da mutan ƙauye, akwai son sada zumunci. "Wash! ke ki bi min k'afa a hankali fa, ja'ira karki k'arasa ni". Hajiya ta k'are maganar cike da wasa da zolaya. Turo baki Zahra ta yi tana cewa. "Haba Hajja? yanzu ai sai kisa amin dariya, ina malamar asibiti guda?" Ai kuwa dariyar Amira ta kece da ita, tana cewa "Yo da ma ke mai yima Hajiya gwaninta ai saiya shirya, ke ce da gulma wai sai kin mata tausa, na san hakan sai ta faru ai, shi ya sa ban ma yi gigin cewa zan yi mata ba". Ta ƙarasa tana cusa rama a bakinta. Hajiya dake dariya a hankali ta jawo Zahra jikinta tana cewa "Ke rabu da ita dan Allah, wasa nake miki fa, ci gaba da min tausar jikalle, da ma so nake na gane masu jin yaushin ana min tausa kuma na gane ki". Ta k'are maganar tana mintsinin cinyar Amira. Amira ta janye jikinta, sannan ta miƙe riƙe da robar da take cin ramar da ita tana faɗin. "Bari na tashi kar ki ƙarasawa saurayina ni" "Ai sai na ƙwace saurayin naki ma! In ya so na ga ta tsiyar" Ita dai Amira ƙin tanka mata ta yi, ta fita tana cin ramarta. Mummy ta yi dariya kawai tana firfita da muhuci, bawai dan gidan babu nepa ba, sai dan Hajiyar ba ya son iskar fanka, domin babu ta inda za ka ga gidan ka ce a ƙauye yake, domin gini aka yi mai matuƙar kyau. Sai wajejan yamma Daddy ya shigo tare da ƙannensa biyu. "To Hajiya! Mu fa za mu kama hanya kin ga magariba ya kusa, kuma ina tsoron kwana a garin nan, bare ma na d'an zaga an san na shigo garin". D'an nisawa Hajiya ta yi kamin ta furta kalamomin da za su yi sanadiyyar wargaza farin cikinsu gaba d'aya. "Shi ya sa ai ban so ka nausa cikin garin nan ba har wasu su san da zuwanka. Ga shi dare ya farayi, ni kuma ba zan bari ku tafi yanzu ba gaskiya, sai dai ku bari zuwa gobe". Daddy ya yi k'asa da kansa cikin bin umarnin Hajiyar ya ce "Shikenan Hajiya za mu kwanan zuwa gobe sai mu wuce". Ya faɗa ba wai dan hankalinsa ya kwanta da hakan ba, dan ya san zamansa a garin haɗari ne... Su ko su Zahra daɗi suka ji, domin sun sha roƙon idan suka zo garin kan ya barsu su kwana, amma bai bari, sai yanzu da Hajiya ta faɗa, suna ta murna ba tare da sanin abin da zai biyo bayan hakan ba. "Yawwa insha Allah ba abin da zai faru. Duk da dai a kusa-kusa damu d'in nan ana 'yan bindigar suna yawan shigowa, shi yasa abin sai a hankali". Cikin Amira ne ya bada wata k'ara tsabar tsoro ta ce "Hajiya to miye na bada labari kuma? Kawai ki yi shiru dan Allah wallahi ni dai har kin samin tsoro, har na fara jin kamar ma kar mu kwana Wallahi". Zahra tayi saurin cewa "To amma Hajiya kuke zaune a haka? Ku ma ai nake ganin duk masu kud'in garin sun tashi sun koma cikin birni, ke ma Wallahi kawai da yarda kika yi, idan za mu yafi mu tafi tare da ke". Wata dak'uwa Mummy ta jefa ma Amira da Zahra, hakan ya sa ba shiri suka kama bakinsu suka yi shuru. Hajiya ta d'an yi murmushi tana cewa. "Kyaleta kawai, ai tana da gaskiya, ni kuma gara na mutu a garin nan da kuke gani, ai da zan tashi daga cikinsa da tuni na tashi, ga ubanku nan zaune, ba yadda bai yi i da ni ba domin na koma kusa da shi nak'i, ina dai nan inda nafi wayo, muna ta kuma addu'a a kansu, kuma cikin ikon Allah abin nasu ya yi sauk'i, amma kwanakin nan dai sai Addu'a domin ba ranar banza da za'a tashi da safe ba ki ji labarin cewa sun shiga wani gari nan kusa damu ba, an kashe wani ko an d'auki wani, amma nan dai gaskiya har yanzu ba'a tab'a shigowa ba". Ɗaya daga cikin ƙannen Daddy yace "Hajiya da za ki yarda yanzu ma zaku iya tafiya domin alamu sun nuna cewa hankalin Yaya Musa bai wani kwanta da ci gaba da zamanki a garin nan ba" Hajiya ta girgiza kanta. "Su dai sa tafi zuwa gobe, amma ni kam zama a garin nan yanzu na farasa" Salma Ahmad Isah ✍️ Zahra Royal Star 🌝 _________________ Page ɗaya ya rage a free pages ɗin da muka alƙauranta... Domin ci gaba da karanta littafin ZARGE za ku biya ₦500 ta lambar wayar da za mu rubuta a ƙasa... Muna masu tabbatar muku da har yanzu ba mu yi komai ba. 5487270431 Salma Isah Monie point Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973 *ZARGE* BY SALMA AHMAD ISAH & ZAHRA ROYAL STAR Page 07 *Ƙauyen Gyaza, Kankia Local Government, Katsina State, Nigeria.* ZAHRA POV. Bacci suke hani'an a wani ɗaki da aka ware musu ita da Amira, yayin da Amira ta jibga mata ƙafafunta, dan da ma can Amira mummunar kwanciya gareta, hakan yasa ma aka raba musu gado tun suna yara... Tsaki ta ja cikin magagin bacci ta kai hannu ta ture ƙafafun Amiran dake kan cinyoyinta. Amma ba a fi minti uku da yin hakan ba Amira ta sake lafta mata ƙafafun nata a karo na bayu. Tsakin da ta ja a wannan karon ya fi wanda ta ja da farko tsayi, idonta ta buɗe tana ɓata fuska, sannan ta sake ture ƙafar Amira tana haɗawa da faɗin. "Ke Yaya kin danneni" Amira da ba ta san me take cewa ba cikin magagin bacci ta yi wani gwarancinta da ya so bawa Zahra dariya, dan yanzu da ace gari zai waye tace Ya Amira kin yi kaza Wallahi har ƙur'ani za ta dafa kan ba ta aikata ba. Juyi ta yi tana laluben pillow, ta ɗauko guda, sannan ta rungume tana lumshe idonta. Sakan uku ba ta haura da lumshe idon nata ba ta ji kamar ana buga ƙofar sashen da suka sauƙa, domun tsabar girman gidan da Alhaji Musa ya gina sashi sashi aka kasa shi, na Hajiya da ban, na ƙannensa da matansu ma da ban, haka kuma ya yi nasa ma da ban. Jin ƙaran ƙwanƙwasa ƙofar a karo na biyu yasa ta buɗe idonta, kafin kuma ta tashi zaune tana mamakin jin bugun ƙofar a lokaci irin wannan. Domin ta tabbatar da wani abu guda ta sauƙa daga kan gado, tana laluben wani dogon mayafinta data ɗaura a kanta lokacin da za ta kwanta, ta ɗauka ta ɗaure kanta, sannan ta nufi ƙofar ɗakin, sanye take da wasu pyjamas riga da wando masu santsi, duk da kalar kayan mai duhu ce bai sa kayan ya fasa sheƙi cikin duhun daren ba. Lokacin da ta buɗe ƙofar ɗakin ya yi dai-dai da sanda shi ma Daddy ya buɗe tasu ƙofar. Kuma tana leƙowa da kanta suka haɗa ido da shi, ta fito yayin da Daddy ke mamakin rashin baccinta a lokacin, dan shi kam bai samu bacci ba, tun da ya kwanta har zuwa yanzu da ƙarfe ɗaya da mintuna ta yi. "Zahra me ya hanaki bacci har yanzu?" Daddy ya tambaya yana kallonta, kamin ta samu zarafin amsa masa aka kuma ƙwanƙwasa ƙofar falon, hakan yasa Daddy ya kauda batun, ya nufi ƙofar zai buɗe, sanda ita ma Mummy ta fito daga ɗakinsu tana hamma. "Isah lafiya?" Daddy ya tambaya lokacin da ya buɗe ƙofar ya ga ƙaninsa Isah, hasken fitilun dake waje ne ya ba shi damar ganinsa da kyau. Isah ya sharece gumi, sannan a gaggauce yace. "Ku yi maza-maza ku fito! Domin an samu gayu sun shigo garin nan a cikin wannan daren!" Wani irin sautin ƙulululu na tashin hankali cikin Daddy ya yi, sannan hantar cikinsa ta shiga kaɗawa, take gumi ya yanko masa, yana jin wani tashin hankali na masa sallama. "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Daddy ya furta bakinsa na rawa. "Sun shigo gidan nan ne?" Daddy ya tambaya bakinsa na rawar tashin hankali. "A'a ba su shigo ba, shi yasa muke ƙoƙarin mu fita daga gidan kafin su shigo!" Isah bai rufe bakinsa ba Daddy ya ji sautin harbin bindiga da kunnuwansa. Idanuwansa ya zaro waje yana innalillahi wa inna ilaihirraji'un. "Me yake faruwa ne wai?" Mummy dake tsaye tare da Zahra cikin rashin sanin abin da yake faruwa ta jefo musu tambayar. Amma Daddy bai amsata ba ya juyo cikin falon, ya tsaya yana kallonsu. "Ina Amira?" Ya tambaya gaba ɗaya ilahirin jikinsa na rawa. "Ta... Ta na ɗaki!" Zahra ta amsa tana haɗiyar miyau, dan ita ma ta ji tashin bindigar. "Maza jeki ki tasota ta zo mu fita" Da gudu Zahra ta koma ɗakinsu, sannan ta shiga tashin Amira dake bacci hankali kwance, kamar tsumma a randa. "Amira! Ya Amira!" Ta faɗa tana ɗaka mata duka a cinyoyinta, amma a banza man kare. Cikin tashin hankali Zahra ta cije leɓenta na ƙasa, dan gaba ɗaya ma ta rasa yanda za ta yi, ba ta taɓa sanin cewa wata rana wannan nauyin baccin na Amira sai ya kusa janyo musu halaka ba sai yau. "Ina Amiran wai?" Daddy da ya faɗo ɗakin ya tambaya, Zahra ta nuna masa ita. "Ta ƙi tashi" "Ke Amina! Amina" "Na'am" Aka yi sa'a wannan karon ta amsa. "Ki tashi mu tafi" Cewar Daddy. Da yake ba ta san wainar da ake toyawa ba sai ta yi juyi tana faɗin. "Ina kuma za mu je cikin daren nan Daddy? Ba Hajiya tace sai gobe za mu tafi ba?" "To Bandits ne suka shigo Gyaza!" Ai Zahra ba ta gama rufe bakinta ba Amira ta zabura ta miƙe zaune, take jikinta ya kama rawar tsoro, hawaye kuma suka yanko mata. "Wayyo Allahna mun shiga uku Daddy za su kashemu!" Ta faɗa bakinta da jikinta gaba ɗaya na rawar tsoro. "Ki yi shiru kin ji? Babu abin da zai sameku! Tashi mu je" Cewar Daddy yana kamo hannunta, kamar wata sokuwa haka ta miƙe tsaye, ya ja hannunta yayin da Zahra ma ta kama ɗayan hannun nata, tsaye suka iske Mummy da Isah a falo cikin tashin hankali, ba tare da ɓata lokaci ba suka fita daga sashen Daddy, suna tafiya a hankali kamar masu shirin yin sata. Lokacin da suka isa babbar harabar gidan suka ji an daki babban gate da mugun ƙarfi, hakan yasa Zahra da Amira suka tsorata, suka rungume juna Amira na fashewa da kuka. "Na shiga uku, Daddy mun mutu" Ta faɗa jikinta na rawa, Mummy ta kamasu ta jasu cikin matan ƙannen Daddy su biyu da, da kuma Hajiya da aka tarasu a tsakar gidan. Kowa ka kalla a cikinsu hankalinsa a tashe yake, domin abu makamancin wannan bai taɓa faruwa da su ba, dan ba a taɓa shiga ƙauyen nasu ba, har gara ma ƙauyen maƙwabtansu... Kafin su samu mafita wasu daga cikin gayun suka dirƙo ta katanga, lamarin da ya ƙara ruɗa duk wani mai jini da hankali a jika dake wurin... Musamman ma da suka nunasu da bindiga, tare da umartarsu kan su durƙushe a kan gwiwoyinsu. Abinka da wanda yake gaɓar ceton rai, babu musu suka zube a ƙasa, kowa jikinsa na rawa, ciki har da Hajiya tsohuwa, ita ko Amira har da fitsarin tsoro ta saki a wando. Kasancewar su biyu suka dirƙo, ɗaya ya tsaya gadinsu, yayin da ɗaya ya ƙarasa ya buɗe gate ɗin da yake a kulle, sauran abokan tafiyarsu dake tsaye a waje suka shigo, kowa cikinsu riƙe da muggan makamai. Haka suka musu ƙawanya suna kallonsu. "Ku mana shiru dan Ubanku! Kafin duk mu bi mu kasheku yanzun nan!" Cewar wani daga cikin 'yan bindigar yana zare jajayen idanuwansa a kansu, tsawar da ya daka musu ce tasa Amira ta ƙara firgita ta ƙanƙame Zahra dake aikin kuka, amma babu sauti sai hawaye. "Ina Alhaji Musa?" Tun da suka ji wannan tambayar kuma suka tabbatar da cewa shikenan! Ta faru ta ƙare, da ma sun zo ne dan su kashe shi, ko su tafi da shi. "Ba magana ake muku ba kun yi shiru!?" Suka sake daka musu tsawa jin babu wanda ya amsa, kuma yanzun ma tsoro ya hana kowa furta komai, sai Zahra da ta fashe da kuka mai sauti tana matsawa kusa da Mummy da ita ma ke hawaye. Ganin abin nasu rainin hankali ne yasa wani cikin 'yan bindigar ya ɗaga bindigar dake hannunsa, cike da rashin imani ya ɗorata a kan Hajiya da jikinta ke rawa, ba tare da kowa ya fuskanci abin da suke son aikatawa ba suka ji ƙaran bindigar da ya harba ya tashi. Hakan ya sa suka sake ruɗewa, ɗaya cikin matan ƙannen Daddy ta ƙwalla ƙara, yayin da Zahra ta toshe kunnenta jikinta na ƙara ƙaimi wurin rawar da yake, ita ko Amira hayyacinta ne ya shiga ƙoƙarin ƙaura daga jikinta... Take Daddy ya ɗaga hannunsa yana kuka, a lokaci guda kuma yana kallon gawar mahaifiyarsa yashe a ƙasa. "Ni ne!.? Ni ne" Ya furta har sau biyu. "Wato rainin hankali ne ya sa ka yi shiru ke nan?" Daddy ya girgiza kansa. "Kai! Ku kama mana shi da 'ya'yansa biyu mu tafi" Jin batun waɗan da za a ɗauka har da 'ya'yansa yasa Daddy ya haɗa hannayensa ya shiga roƙonsu. "Dan Allah karku taɓsu! Na roƙeku da girman Allah! Dan Allah ni ku kasheni, ko ku tafi da ni!... Amma su kam ku ƙyalesu" Har ƙasa Daddy ya kifa yana ƙoƙarin roƙonsu, amma ba su saurare shi ba suka kamo Zahra da Amira dake jikin Mummy suna kuka, cikin ƙoƙarin kare 'ya'yansa Daddy ya riƙo mutumin da ya riƙe Zahra, aiko yana juyowa ya bugawa Daddy bakin bindiga a tsakiyar kansa, yana faɗuwa ƙasa wani da ban da wanda ya daki kansa ya harbe shi har sau uku, hakan yasa Zahra da Amira suka fasa ihu tare da Mummy suka yi kansa, yayin da ita kuma Mummy ta soma yin abu kamar mai hauka, tana ihu tana riƙe ƙafar ɗaya daga cikin 'yan bindigar da ya harbi Daddy, ita ma bai yi wata-wata ba wurin harbin ƙoƙon kanta, abu goma da ashirin suka haɗu suka taranma Zahra da Amira, duk sai suka rasa me za su yi. "Daddy! Daddy!" Amira ta ƙira da ƙarfi tana jijjiga shi, tashin hankali bai ƙara kamasu ba sai da suka ji an ce a kashe kowa dake wurin... Ai take Amira ta yanke jiki ta faɗi, Zahra ce mai taurin ran da ta ga komai, aka yi komai a kan idonta... Amma kuma kunnuwanta gaba ɗaya sai da suka daina aiki, domin ƙaran harbe-harben da suka yi a wurin ya sa jinta ya yi nisa, ta yanda har suka saɓi Amira ita kuma suka soma janta zuwa wajen gidan ba ta sani ba. Ba wai ta mutu ba ne, ba suma ta yi ba, kuma ba haukacewa ta yi ba, kawai dai lamarin da ya faru a kan idonta ne ya kasa fita daga cikin tunaninta... Babu abin da yake maimaita kansa sai harbin da suka yi wa Daddy guda uku, da kuma wanda suka yi wa Mummy a cikin kanta. Ba iyaka su kaɗai aka ɗauka a ƙauyen ba, har da wasu 'yan mata da maza dake ƙauyen aka haɗa, tsabar yawan 'yan bindigar a tashin farko ba ka isa ka ƙirgasu ba... Yawansu ya kai intaha, kamar 'yan rali, wasu a kan babura, wasu kuma a ƙasa, suka saka mutanen da suka ɗauko a tsakiya, waɗan da matan cikinsu suka fi yawa... 'Yan mata ire-iren Zahra da Amira sun fi yawa, amma duk da haka har da mata masu goyo da kuma tsofi waɗan da shekarunsu suka fara gazawa, kawai tafiya suke, ba tare da sunsan inda za a kaisu ba, ita dai Zahra ba ta cikin hayyacinta, domin ba ta san inda ƙafafunta suke takawa ba, tafiya kawai take saboda ta ji kowa na tafiyar. YABINTU. Bayan kwashe tafiya ta tsawon awanni uku da 'yan mintuna motar hayar da ta hau ta isa garin Kaduna... Kuma ba tare da wani ɓata lokaci ba ta naimi motar da za ta kaita Gusau. Lokacin da aka nuna mata motar sai da ta tsaya ƙarewa motar kallo, kafin ta shiga ciki, yayin da ake saka mata kayayyakinta a bayan motar. Ta yi waige-waigenta ta gama, amma ba ta ga alamun akwai wani fasinja bayan ita ba, hakan bai ɗaga mata hankali ba, musamman da ta tuna cewa yanzu ta yi rabin tafiyarta. A hankali ta kalli fuskar wayarta da ta kashe tun bayan da ta shiga mota a tashar Abuja. Bawai dan tana tasammanin ƙiran wani ba, domin ta san babu yanda za ayi ƙira ya shigo wayar a rufe. Kuma dalilin da ya sa ta rufe wayar shi ne, ba ta son Daddy, Ummanta ko Umar su san cewa a mota taho, domin ta san idan suka ji za su iya hanata, shi yasa ta rufe wayar tata, duk da ta san ba lalle ma wani cikinsu ya ƙirata ba, tun da sun ɗauka cewar ta riga ta hau jirgi ne. Tun tana jiran cikar motar da fasinjoji kafin su ɗauki hanya har ta cire rai, domin har bayan shuɗewar awanni biyu babu fasinja ko guda da ya zo yace zai je Gusau. Ganin kamar lokaci na ƙurewa ya sa ta kalli ɗan yuniyal ɗin dake kusa da motar. "Baba dan Allah wai babu yanda za ayi mu tafi yanzu? Na ga rana na takewa!" Mutum biyun dake zaune kan wani benci suka dubeta, kafin ɗayan cikinsu ya furta. "A'a 'yar nan, indai za ki biya kuɗin sauran kujerun me zai hana ku tafi yanzu!" Tsaki ta ja, ita da ta san da wannan ma ai ba za ta ɓata lokaci har haka tana zaune ba. Dan da ma ita ba ta son takura, gara ma a kaita ita kaɗai, dan haka tace. "Nawa ne kuɗin kujerun duka?" Aka ƙira direban motar akai lisaffi, ta lale kuɗinsu tas ta biya. Amma kafin su tafi sai da ta naimi su mata alfarma ta samu abinci kafin su tafi. Da yake ta biyasu kuɗinsu yanda ya kamata yasa basu musa ba. Fita daga tashar ta yi, ta je ta hau agwagwa da buje in ji Zamfarawa (keke napep nake nufi🤣). Ta je wani supermarket ta yi siyayyan kayan ciye-ciye da drinks, ta hau wata keke napep ɗin ta dawo tasha, tana dawowa ta shiga mota, da yake ita ake jira kawai sai suka kama hanya. Tafiya ce doguwa, wadda ta fara tun daga Kaduna. A hanya sun wuce ƙauyuka da garuruwa. Tun da suka ɗauki hanya sau biyu suka tsaya, na farko sun tsaya sun sha mai a wani gidan mai, sai kuma a wani ƙauye da drivern ya sake tsayawa suka yi sallah. Sannan suka ci gaba da tafiya, hira wannan ba ta haɗata da drivern ba, sai sanda take cin cake tai masa bismillah yace alhamdulillah, ta maida hankalinta kan hanya kawai, zuciyarta da bakinta ko sun duƙufa wurin ambaton Allah da naiman kariya daga gareshi. Har bacci sai da ta yi a motar, lokacin da ta farka kuma yamma ta yi liƙis, a nan ma sun tsaya a wani ƙaramin gari sun yi sallah, sannan suka ci gaba da tafiya. Yabintu ba ta fara jin kwanciyar hankali na tunkarota ba sai da ta ga sun shigo jahar zamfara, duk da ta wani ɓangaren akwai wani tsoro da ya ɗarsu a zuciyarta, ita dai ba ta ce tsoron na miye ba, amma ta san tana jin tsoro. Ba ita kaɗai ba, hatta drivern kansa a tsorace yake lokacin da suka fara wucewa ta ƙauyukan da 'yan bindiga suka kaiwa hari. Shi yasa shi ma ya riƙi addu'a, ya shiga jan motar da gudun gaske. Sai dai kuma duk yadda za ka kai ga gujewa abu, matsawar Allah ya hukunta cewa sai ya faru da kai to ba yadda za ayi ka tsere masa. Tun daga nesa direban ya fara hangen motoci biyu fake a kan hanya, hakan yasa ya rage gudun motar, domin yanda motocin suka tsaya sun tare titin ta yanda motarsa ba ta isa ta wuce ba. "Lafiya? Me ya faru?" Yabintu da gabanta ya soma bugawa ta tambaya tana leƙen window. "Ina jin sikyuriti ne!" Ya faɗa yana son tantance abin da yake wajen, domin bai yarda ya ƙarasa kusa da motocin ba, ba su tabbatar da abin da yake faruwa ba sai da suka ji ƙaran harbin bindiga. Ai tuni cikin yabintu ya kaɗa, ta gwalalo ido tana. "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" Basu rabe ɗayan biyu ba suka hango Bandits sun nufo motar tasu, ashe su ne suka tare motocin dake gabansu. "Mun shiga uku 'yan bindiga ne" Cewar direban yana buɗe motar, sannan ya fita ya falfala da gudu, ya bar Yabintu zaune cikin motar, tsoro ya hanata ko motsi. Ban da innalillahi wa inna ilaihirraji'un babu abin da take furtawa. Jin ƙaran tashin wata bindigar yasa ta waiga ta kalli bayan motar, inda ta ga direban motar ya faɗi ƙasa yana ƙwala ƙara, alamun dai shi suka harba. Kuka Yabintu ta fashe da shi, sannan ta ƙanƙame jikinta tana toshe kunnenta, tun da ta zo duniya tashin hankali mai kama da wannan bai taɓa raɓar inda take ba sai yau. "Fito!" Ta ji an daka mata tsawa. Hakan yasa ta razana ta ɗago kanta, ta kalli wasu mutum uku dake tsaye a jikin motar, sun buɗe ƙofarta, tashin hankali da yanda ƙwalla ta cika idonta yasa sam ba ta ce ga kammanin fuskarsu ba. "Dan uban ubanki ba magana ake miki ba!" Ta ji sun sake faɗi, amma tsabar rikiɗa sai ta kasa tantace yaren da suke, ta saki baki kawai tana binsu da kallo. Tasss kake ji, wani cikin 'yan bindigar ya gaura mata mari, take ta dafe wurin da ya mareta tana ganin gilmawar taurari a idonta. "Za ki fito ko sai mun ci ubanki yanzu a wurin nan?" A wannan karon marin da ta sha ya dawo da nepar da ta ɗauke a kanta, dan haka jiki na ɓari ta fito daga motar, ƙafarta ɗaya sanye da takalmi ɗayar kuma babu. A hankali ta juya ta kalli wurin da gawar direban nan ke kwance, da sauri ta ɗauke kanta ganin yanda aka yi raga-raga da kansa. "Wuce mu je!" Suka kuma daka mata tsawa suna turata, wani marayan kuka ne ya kufce mata, ta sake shi tana taka ƙafarta, kuma har zuwa lokacin hannunta na dama na kan kuncinta da har yanzu bai daina zogin azabar marin da ta sha ba. Kanta a ƙasa, tana kallon ƙafarta da babu takalmi guda kuma da takalmi... Ban da innalillahi wa inna ilaihirraji'un babu abin da take faɗa, domin sai yanzu ta san da cewa ta faɗa wata duniyar azallumai da babu wanda zai ceceta sai ubangijinta. Zahra Royal Star 🌝 Salma Ahmad Isah ✍️ _________________ Page ɗaya ya rage a free pages ɗin da muka alƙauranta... Domin ci gaba da karanta littafin ZARGE za ku biya ₦500 ta lambar da za mu rubuta a ƙasa... 5487270431 Salma Isah Monie point Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973 *ZARGE* BY SALMA AHMAD ISAH & ZAHRA ROYAL STAR Last free chapter... 08 *House No. 17, Aguiyi Ironsi Street, Off Ahmadu Bello way, Durumi District, Abuja.* *10:33 na dare* BILAL POV. Kai kawo yake a cikin falon da babu komai cikinsa sai hasken TV dake a kunne, domin ko kaɗan Bilal bai son hasken wani da daddare, shi yasa a ko da yaushe bulb ɗin gidansa suke a kashe. Hannunsa ya goya a bayansa, zuciyarsa na masa ba daɗi. Domin har kawo yanzu ji yake hankalinsa bai kwanta ba game da lamarin budurwar Umar. Ga shi ba shi da contact nata ballantana ya ƙitaya ya ji wani hali take ciki. A hankali ya shafa wuyansa yana haɗiyar wani abu a maƙoshinsa, wanda ya sa Adam's Apple ɗinsa ya motsa sama da ƙasa. Kujera ya dafa, sannan ya zauna a kan kujerar yana furzar da huci kaɗan, duk ya rasa me ya kamata ya yi. Wani abu ya tuna, dan haka ya ɗauki wayarsa, sannan ya lalubo lambar Umar ya aika masa da ƙira. "Barka da dare B. Liman! Da fatan kana cikin ƙoshin lafiya" Shi ne abin da Umar yace daga ɗayan ɓangaren. "Haka nake fata... Ya jikin Umma?" Batun jikin Umma da ya ambata yasa Umar bai bawa maganarsa ta farko muhimmanci ba, dan haka yace. "Umma ta ji sauƙi, dan zuwa gobe they can discharge her" "To Allah ya ƙara lafiya... Na ce ko ka ƙira girlfriend ɗinka ka ji yanda ta sauƙa gida?" Bilal ya tambaya zuciyarsa na rawa, na kokwanton amsar da zai iya samu. "Eh to! Da yake ka san jirgi ta hau yasa ban ƙirata ba, kuma har zuwa yanzu da nake tabbacin tana gida ma ban ƙirata ba, saboda na bata lokaci ne ta huta, zuwa gobe sai na kirata, amma duk da haka na yi mamaki da ita ba ta kirani tace min ta sauƙa lafiya ba!" Bilal ya rintse idonsa, sannan ya saka hannunsa ta riƙe kansa. "Lafiya kake tambaya? Ko wani abu ya faru da ku ne a hanya?" Umar ya sake tambaya jin Bilal ya yi shiru, a hankali Bilal ya buɗe idonsa, sannan ya girgiza kansa yana ajiyar zuciya. "Flight ɗinmu zuwa Sokoto bai tashi yau ba, sanda na je bata jakarta aka sanar da cewa an soke tashin jirgin... A lokacin ban san dalilin hakan ba, sai ɗazu nake jin an ce wai an samu labarin an kai hari ne a wani ƙauye dake kusa da Sokoton, shi yasa suka soke tashin jirgin..." "Wait a minute B. Liman, ban gane ba? What are trying to say?" Umar ya katse shi. "Ina so na faɗa maka cewar Yabintu ba a jirgi ta tafi ba, bayan an soke tashin jirgin take shaida min cewar ita ba za ta iya jira sai zuwa gobe ba, fan haka za ta je ta hau motar haya!..." "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Umar ya furta, ba tare da ya bar Bilal ya sake furta komai na ya katse ƙiran, Bilal ya aje wayarsa a gefensa, zuciyarsa na harbawa da ƙarfi, domin yanzu alamu sun nuna cewa yarinyar nan tana cikin matsala. Duk kuma sai yake ganin laifinsa, domin ya kamata ace lokacin da ta nuna son tafiyar ya bata shawarar kada ta tafi, ko bai hanata kai tsaye ba sai ya sanar da Umar. Amma bai yi hakan ba... Yanzu ga abin da ya faru da ita!. ----******---- Umar na katse ƙiran Bilal ya shiga naiman lambar Daddyn Yabintu. Amma jar ta gama ringing ta katse bai ɗauka ba, hankalinsa a mugun tashe ya miƙe tsaye, ya soma safa da marwa a cikin ɗakunsa yana sake dialing lambar. A wannan karon ya yi sa'a Alhaji Haruna Bakura ya ɗaga wayar. Da ƙyar Umar ya iya saita kansa suka gaisa da Daddy lafiya-lafiya, amma duk da hakan sai da Daddy ya fuskanci akwai matsala tattare da shi. Duk da su ma yau sun yi busy da yawa, na jiran zuwan Yabintu amma shiru har yanzu da dare ya yi. Kuma ko sun ƙira wayarta ba ya shiga, shi yasa ma suka fara tunanin ko dai ta fasa tafiyar ne. "Umar fatan lafiya? Dan na ji yanayin naka kamar ba lau ba" Cewar Daddy. Kamar mai jira Umar yace. "Daddy Fatima ta iso gida?" Dimmm! Kunnuwan Daddy suka yi, domin tun da ya ji haka ya san cewa Yabintu ta baro Abuja. "Daddy kana ji na?" Umar ya sake faɗa jin shirun ya yi yawa. "A'a har yanzu ba ta ƙaraso ba, idan an ƙirata ma wayarta ba ta shiga, shi yasa ma muka fara zargin ko dai ta fasa zuwan ne?" Gwajab! Umar ya koma ya zauna a kan kujera, saboda wata irin zufa da ta keto masa. "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!" Ya furta yana kama kansa da ya sara nan take. "Me yake faruwa ne Umar?" Daddy ya kuma tambaya. "Daddy yau aka soke tashin jirgin su Yabintu, hakan yasa ita kuma ta yanke hukuncin tafiya a mota, kuka ta tafi ɗin, amma yanzu da kake sanar da ni cewar ba ta isa Gusau ba yasa na fara tunanin ko dai wani abin ya sameta a hanya!" Duk dariyar Daddy sai da ya ji wani abu ya soki ƙahon zuciyarsa, domin babu tantama kan lalle a halin yanzu 'yarsa tana cikin haɗari... Amma me ya sameta? Haɗarin mota suka yi? Ko kuma Bandits ne suka sacesu a hanya? Wannw daga ciki hankalinsa zai kama? Wanne? *Gusau, Zamfara state...* MARYAM POV. Kwance take tana bacci a ɗakin hotel ɗin da suka kama, ƙaran wayarta ne ya tasheta a bacci, dan haka ta miƙa hannunta ta janyo wayar, da ƙyar ta buɗe idonta ta kalli mai ƙiran, a zabure ta miƙe zaune tana murstika ido. Sannan jiki na rawa ta amsa ƙiran ta kara a kunnenta. "Barka da safiya Major" Na cikin wayar bai bari ta gama magana ba ya dakatarta cikin alamun dake nuna cewa ransa a ɓace yake. "Me kike da har na jera miki ƙira 2 ba ki ɗauka ba?" Maryam ta juya idonta cikin takaici, wai dan ya mata ƙira biyu shi ne yake faɗa kamar wanda ya jera mata ƙira sittin... Ita yanzu ya fara gajiya da halin Faisal, ba dan ita tace ta za ta iya ba da tuni ya rabu da bawan Allahn nan. "Wato ga ɗan iska ko? Na miki magana shi ne kika min shiru?" Wannan karon a tsawace ya yi maganar, dan sai da ta zabura kamar wadda ke tsaye a gabansa. "Na... Na shiga wanka ne! Ka yi haƙuri dan Allah!" Ya yi shiru kawai, can kuma yace. "From now till Saturday zan iya shigowa Gusau! Na faɗa miki ne kawai dan kina yawan min ƙorafi kan ba na sanar miki da zuwana!" Maryam ta yi murmushin jin daɗi, kafin tace. "To Allah ya dawo da kai lafiya My Major!..." Ya kuma yin shiru, kuma hakan yasa a gane cewa ya gama magana, amma ba ta isa katse masa waya ba tun da ta san hali, dan haka ta aje wayar a gefenta tana kallo, har ya gaji dan kansa ya katse ƙiran. Wani dogon tsaki ta ja tana jan rigarta da ta yar a ƙasa. "Ai kuma shikenan, yanzu zai dawo ya ishi jama'a da tsirfa da bala'i" Ta ƙarashe maganar tana saka rigar a jikinta. "Ke da wa kuma?" Wani baƙin Alhaji mai ƙaton ciki da ya fito daga bayi ya tabayeta yana binta da kallo. "Saurayina Faisal" Allhajin ya yi dariya yana zaunawa a kan gadon, yayin da ita kuma take mayar da tufafinta da ya cire ɗazu. "Tun yaushe nake cewa ki rabu da shege? Da ace ke me jin magana ce da tuni kin rabu da shi kin zo na aureki!" Maryam ta yi murmushi tana taɓe bakinta. "Ai ba za ja gane ba Alhaji Sadi, ba na jin zan iya rabuwa da Faisal, ko da kuwa zai riƙa yankar naman jikina yana cinsa ɗanye!" "Yo ai kima a banza man kare! Tun da mun riga shi samun wurin" Ta juyo ta kalleshi. "Idan ka gama bani kuɗina zan wuce" Ganin kamar ba ta son zancen yasa shi ma ya share, yace ta je zai mata transfer. Da haka suka yi sallama ta fito daga guesthouse ɗin Alhaji Sadi da suka saba haɗuwa suna sheƙe ayarsu lokaci zuwa lokaci. Tana shirin tsaida napep a bakin titi wayarta ta shiga ƙara, ganin Mama ce mai ƙiran yasa ta ɗaga wayar ta kara a kunne. "Wai kina ina ne?" "Na je wurin aiki" "Wurin aikin ubanki? Wallahi ko kaffara ba zan yi ba kan wurin wannan mayen Alhaji Sadin kika je ki! Wai Maryam sau nawa zan ce da ke sai kin kama kanki kafin ki mallaki Faisal a hannunki?" Cewar Mama daga cikin wayar cikin faɗa. Maryam ta juya idonta irin kanki ake ji ɗin nan. "To wai sui Faisal ɗin wa ya san tsiyar da yake shukawa a Lagos ɗin? Waye bai san sojoji da shegen biye-biyen matan banza ba? Ni Wallahi ba zan daina ba sai aurena da shi ya kusa? Haka kawai zan hana kaina jin daɗin rayuwa saboda wanda bai damu da ni ba!" "To shikenan! Ki zauna kina kallon ruwa har kwaɗo ya miki ƙafa, ke shaida ce kan yanda muka sha wahala na bin malmai, kafin muka karkato da hankalinsa kanki, idan ba ki yi wasa ba Wallahi Faisal sai ya kufce miki!" Maryam ta ja tsaki. "Ni karki tara min jama'a, yanzu ina bakin hanya, ɗazu ya ƙirani yace zai iya dawowa daga yanzu zuwa Saturday, dan haka zan zo sai mu tattauna a gida!" "To sai kin zo" Daga haka ta katse wayar yana rantsuwa a ranta har da Allah kan babu mai hanata holewa da samarinta, tun da auna bata kuɗi yanda ya kamata. *Ikorodu Barrack, Lagos, Nigeria.* Zaune a farfajiyar wasu gajerun gine-gine na ofisoshin manyan sojoji dake barrack ɗin, wani farin mata shi ne, sanye cikin complete Nigerian camouflage uniform (kakin sojoji). Ya jingina bayansa da jikin kujerar da yake kanta, kansa a sama, yayin da ya saua idanuwansa cikin shade, yayinda ya ɗora ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya, hularsa kuma a kan gwiwar ƙafarsa wadda take sama. Nauyin manyan boots ɗin dake ƙafarsa ba su sa ya fasa jijjiga ƙafarsa ba, hannunsa na dama kuma riƙe da fidget spinner (Ban san sunanta da hausa ba, amma na ji ana cewa katantanwar hannu). Duk da idanuwansa a rufe suke haka yake kaɗa sppiner ɗin, yayin da kunnuwansa ke jiyo masa wata waƙa dake tashi a can nesa da inda yake. "Major Makama" Take ya ja tsaki jin ƙiran da aka masa. A hankali ya daina jijjiga ƙafarsa, sannan ya sauƙeta daga kan 'yar uwarta yana gyara hularsa dake aje a kan gwiwar tasa, sannan ya ɗago yana saka ɗan yatsansa tare da gyara glasses ɗinsa da ya zamo. Kuma har zuwa lokacin bai daina kaɗa fidget spinner ɗin dake hannunsa ba. Major Khalil abokinsa da ƙira shi ya iso wurin da yake zaune yana shan iska, ya ja ɗaya daga cikin kujerun dake wurin ya zauna. Murmushi kawai ya yi yana kallon sppiner ɗin dake hannunsa. "Kai da wa kuma?" Ya tambaya, dan ya san ba a rasa nono a riga, abu ne mayuwaci ka gan shi cikin walwala, shi ba a rasa abin da yake ɓata masa rai duk kwanan duniya. Kuma daga zarar ransa ya ɓaci za ka ganshi riƙe da fidget spinner ɗin nan, yana wainta, wai ko ya rage ɓacin ran da yake ciki. Tsaki kawai ya ja, sannan ya saka hannu ya cire shade ɗin da suka saya kyawawan madaidaitan idanuwansa, masu rikitar da 'yan mata da kuma waɗan da suke ƙasa da shi. Duk da a zaune yake za ka iya gane cewa shi dogo ne, amma faɗin da yake da shi ya ƙarawa hallitar tsayin nasa kyau, ba shi da wani jiki sosai, amma ko dantsensa ka kalla za ka san yana motsa jiki. Ba fari ba ne sosai, kuma ka zalika shi ba baƙi ba, amma hakan bai rage komai na daga kyawun hallita da Allah ya ba shi ba. Ba shi da gemu ko saje, amma ayana da wani ɗan siririn gashin baki dake tsakanin ƙofofin hancinsa da laɓɓansa. Kuma idan daga nesa sosai kange shi ba lalle ma ka ce yana da gashin bakin ba, sai in ka matso kusa, domin babu gashi sosai. Sumar kansa ba ya da tsayi, domin ya yi askin buzz cut ne, irin askin da sauran sojoji 'yan uwansa ke yi yawan yi. "Ba magana?" Major Khalil ya sake tambaya yana binsa da kallo, Faisal ya ja tsaki yana ɗauke idonsa daga kan Khalil. "Wannan mara kamun kan ne!" Major Khalil ya yi dariya. Dan ba sai ya zauna ya masa dalla-dalla ba, ya gane waye mara kamun kan. Shugabansu ne General Audu Kazaure. "Me ya faru?" "Wai ɗazu ina zaune mutumin nan ya ƙirani yace na zo na same shi a office, da na je na iske shi da wata karuwa, duk da haka ban fita daga office ɗin ba na tsaya domin jin dalilinsa na ƙirana, amma wai sai ya kalleni yace na jw, idan an jima zai ƙirani... Ma'ana ba shi da lokacina sai ya gama da ita!" Major Khalil ya Kuma yin dariya, ganin Faisal na matse spinner ɗin hannunsa da ƙarfi, kamar wanda ita ce ta masa laifin. "Ban da abinka Bilal! Da ma shi General kowa da halinsa ya sanshi!" "Idan bai yi wasa ba ai mata ne za su kashe shege!" Shi ko Khalil yace me zai yi in ba dariya. "Wallahi ba za ka kasheni da dariya ba... So nake mu je siyayya, tun da ka ga jibi za mu tafi" Cewar Khalil yana miƙewa tsaye. Faisal ya bi shi da kallo, kafin ya sa hannu ya ɗauki hularsa dake kan ƙafarsa, sannan ya miƙe tsaye yana faɗin. "Me za ka siyo?" "Komai ma" Faisal ya ja tsaki. "Kai fa ba ka da hankali! Wato ba ma ka san abin da za ka siyo ba?" Khalil ya kuma darawa, kafin ya dafa shi yana faɗin. "Ni dai in za ka rakani ka ce min komai ma, tun da na saba!" Da ƙyar dai ya samu ya shawo kansa ya yarda zai raka shi ɗin, duk da iyaka au kaɗai za su fita ba, har da masu tsaron lafiyarsu. *Huda University Gusau, Eastern Bypass Road, Sokoto Road, Gusau, Zamfara state.* Wata farar mota ƙirar Audi RSQ ta faka a bakin gate ɗin shiga makarantar. Daga cikin motar, wata farar bafulatanar yarinya ta ɗauki jakarta da sauri yana faɗin. "Na gode ya FU'AD!..." Bafulatanin saurayin dakw zaune a mazaunin direba, sanye da suit gray kala ya dubeta yana murmushi. "To Allah ya taimaka!" "Amin" Yarinyar ta amsa tana buɗe ƙofar motar ta fita, tana fita ta rufo masa ƙofar motar, sannan ta nufi gate da sauri-sauri, yayin da shi kuma matashin da ta kira da Fu'ad ya tada motar ya soma ƙoƙarin barin wurin, sai da yavkusa barin layin kafin ya ankara da wani book da ƙanwar tasa ta manta a kotar. Murmushi ya yi kawai yana girgiza kai, kafin ya dawo baya, wannan karon har cikin makarantar ya shiga. Ya fito daga motarsa riƙe da littafin nata, ya nufi faculty of Law, inda ya san cewa a can ƙanwar tasa take. Tun daga nesa ya hango wata budurwa sanye da abaya blue, tashin farko zuciyarsa ta raya masa cewar ƙanwarsa Umaima ce. Dan haka ya soma ƙwala mata ƙira yana nufar inda take, amma ba ya juyo ba har sai da ya isa kusa da ita, ua saka hannunsa ya riƙo damtsen hannunta, ya juyo da ita yana faɗin. "Ke wai ba ki ji ne ina ta ƙwala miki..." Bai kai ga ƙarasa furtawa ba saboda wani lamari da ya faru unexpected. FALAK POV. Kasancewar yau Khamis yace mata ba ya gari yasa ta shirya ta tafi Makaranta, ba wai dan tana so ba sai dan ya zame mata dole. Kuma tun da ɗazu Hajiya ke faɗa mata cewar Faisal zai dawo ta hango kamawar watan tashin hankalinta na shirin kamawa. Domin idan yana nan dole ta rage wasu abubuwan, sannan dole ta yi wasu da ba ta yi a baya. Tsabar murɗɗaɗen halinta yasa ba ta da ƙawa ko kaɗan, ba a makarantar ba ba a gida ba. Ita kaɗai take tafiya a cikin makarantar, tayin da ta nufi Library, dan ba ma ta jin za ta iya attending class ɗin. Kamar daga sama ta ji an riƙo damtsen hannunta hannunta, sannan aka juyo da ita, ɓacin ran rainin hankalin da ta ga ana shirin mata yasa ba ma ta tsaya ta ji abin da mutumin ke faɗa ba, ta rufe idonta ta ɗaga hannunta ta shararawa matashin marin da yasa ya ɗauke wuta. "How dare you touch me this way?" Ta furta idanuwanta zare a kansa, ba ta duba girmansa ba, ba ta duna kamalarsa ba, ba ta duba kimarsa ba ta zage ta ci mutuncinsa yadda taso. Shi ko Fu'ad kuncinsa kawai ya dafe yana kallon yarinyar da ya san ba ta kai Umaima ƙanwarsa a haife ba, amma gata tsaye a gabansa tana ci masa mutunci, tasa jama'a na ta kallonsu. "Ke! Falak! Kar ki sake furta wata mummunar kalma a kan yayana! Dan Wallahi idan har kika sake ni ma sai na mareki!" Umaima da ta ga abin da ya faru ta faɗa, tana isowa wurin, wani irin kallo Falak ta yi wa Umaiman dake sanye da abaya blue, kusan shigen wadda ke jikinta. "Shi yayan naki ba shi da ɗa'a ne? Ko gyatuma ba ta koya muku a gida ba? Ya kamata ace kin ba shi labari cewar babu wani ƙazamin saurayi da ya isa ya yi gigin taɓa Falak..." "Ke har kin isa!..." Umaima ta faɗa tana ɗaga hannunta za ta mari Falak, amma sai Fu'ad ya riƙe hannun nata. "Ya isa Umaima! Tana da gaskiya, kin mance book ɗinki ne a car, shi ne na zo zan baki, da na ganta da farko na ɗauka cewar ke ce, shi yasa na riƙe hannunta a bisa rashin sani, dan Allah ki yi haƙuri!" Ya ƙarashe yana kallon Falak dake binsu da kallon sama da ƙasa. Wani dogon tsaki ta ja, sannan ta juya ta barsu tsaye a wurin ana ta kallonsu. "Ka yi haƙuri Ya Fu'ad! Kowa ya san halin Falak kan ba ta da mutunci!" Cewar Umaima tana duba gefen fuskarsa da ya yi ja, alamun a nan ya sha marin, abinka da farin mutum. Fu'ad bai amsata ba, saboda bayan Falak kawai ya bi da kallo, sakamakon wani abu da ya karanto a cikin idonta, wani abu! Wani abu! Tabbas wani abu!. _____________ _Hello!_ _Free pages sun ƙare daga nan oo... Domin ci gaba da karanta wannan book ɗin za ku biya ₦500 kacal_ _Humm! Akwai gwarama fa!_ _A ganinku wani hali Amira da Zahra za su kasance a ciki?_ _Wani hali Yabintu ke ciki?_ _Sannan ga Falak ga kuma Fu'ad_ _Ga Maryam ga Faisal!_ _Me kuke ganin Faisal zai yi a kan Maryam, Mama, Bilkis da Falak idan jar asiri ya tonu... Domin ku sani, ƙarya fure take ba ta 'ya'ya._ _Ina mai tabbatar muku fa har yanzu ba mu yi komai ha a tafiyar nan_ Domin biyan kuɗin book ɗin za ku tura kuɗin ta: 5487270431 Salma Isah Monie point Sai ku tura shaidar biyanku ta 0813 047 9973. Zahra Royal Star 🌝 Salma Ahmad Isah ✍️