[ NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 3 Da k’yar Umma Ta runtse idonta ta furta “Innalillahi wa inna ilaihirraji’una…” wasu hawaye na zubo mata. Abba cikin k’arfin hali ya saki kansa da ya ji ya masa wani irin duum ya furta “Uban me kika masa ya sake ki” Ban amsa ba illa damk’e hannun Mami da na yi a cikin nata hannun cikin tashin hankali kaf jikina rawa kawai yake yi. “Kin ga ko Fateemah abinda nake gaya miki, wannan shagawab’atan da kike yi ba hanya bace mai b’illewa, ga shi nan yanzu abin da ta janyowa mana ba mamaki bata kai budurcinta gidan Miji ba” Umma ta furta cikin wata irin karyayyiyar murya da ta bayyana karyewar zuciyarta. Mami a kufule ta furta “To hasashenki bai zama gaskiya ba, tunda ga shi a rubuce ya furta da kansa bai d’ora mata idda ba, idan kuwa haka ne ta ya zai san bata kai wani budurci ba? Kawai dai butulcin y’ay’a maza zai nuna muku.” Abba ya saka hannu ya wafce takardar da take hannun Mamin idanunsa ya zuba akan gajeran rubutun mai saka dubban bak’in ciki a zuciya. Ya lumshe idonsa bayan ya tabbatar da abinda Mamin ta fa’da. Wani irin bak’in ciki ne yake nuk’urk’usar zuciyarsa don har yana jin wata irin suka a zuciyar tasa. Ya lumshe idonsa yana tunanin Halaccin da Ustaz Ahmad zai yi masa kenan? Duk da k’ank’antar y’arsa ya cireta a makaranta ya ba shi aurenta shine yau daga tarewarta ya saketa? Ya d’ago idanunsa jajur yana kallona ya furta “To me kika masa ya sake ki Aysha? Don kalmar bakomai ba zan yarda da ita ba ko duk jikina kunne ne.” Na runtse idona ina sake jin takaicin Ahmad a raina. Ji dai yadda ya sanya iyayena b’acin rai. Umma da Mamina hawaye suke. Shi kuma Abba nasa idanun ya tara hawayen sai dai ba su kai ga zubowa ba. Amma bakinsa har rawa yake. “Wallahi Abba ba abinda na masa, ka kirasa ka tambayesa ka ji idan baka yarda da ni ba…” “kira kam Ai ya zama dole….” Ya fa’da yana mik’ewa ya fice daga parlorn yana danna wayarsa fuskarsa a murtuke. Umma kallo guda ta mana ni da Mami itama ta mik’e ta shige d’akin Abba. Ni na san a lokacin ji take kamar zuciyarta ta fito don tsananin b’acin rai. Mami na ta dafa ni tana furta “Share hawayen ki Aysha, ni na san ba abinda kika masa. Iskancine kawai da kuma nunawa mutane isa, ba su suka nuna masa sha d’in wata tsiya ba ce. Kwanta abinki ki yi barci don na san jiyan ba wani isashshen barci kika samu ba. Bari na je na samu dandazon munafukancan y’an saka ido na san me Zan gaya musu. Daga haka itama ta mik’e ta fice tana d’an murmushi tana cije bakinta ha’de da k’wafa duka lokaci guda. Lumshe idona na yi wasu hawaye suna zubo min. Na saka hannu na share hawayen ina sake tsinewa Ahmad a zuciyata. Madadin barci tunanin rayuwata ne ya dawo min daki-daki cikin kwanyata girmana k’iruciyata da ha’duwata da Ahmad da zan ce a yanzu ha’duwar tamu ta zame min mummunar k’addarar da zan ce da ina da iko da na koma baya na goge ta tas daga cikin shagon rayuwata….. ★★★ Alhaji Imam Khalil shi ne sunan mahaifina, da kowa ya san shi. Asalin sunan Abdurrahman ne, amma sakamakon ya ci sunan kakansa ne yasa ake ce masa Imam. Mahaifina su biyu ne kacal a wajen iyayensa, daga shi sai k’anwarsa Dije, da muke kira Umma Dije, sun taso cikin tsananin soyayyar Iyayensu game da kulawa. Kasancewar mahaifinsa babban malami hakan ya sa ba su ingantacciyar tarbiyya, don duk wanda ya ha’da da su dole ne ya yaba da nutsuwarsu, da hankalinsu. Mahaifina tun yana shekara ashirin da uku aka masa auren fari, da Ummana Sa’adatu, y’ar k’anin Babansa wanda da kansu suka k’ulla soyayyarsu, kuma kowa ya yi tsananin murna da farin ciki da hakan ta kasance. Abbana da Ummana sun yi zaman aminci, ta yadda suke ganin girman junansu, suka kuma gina rayuwar aurensu da soyayya mai tsafta da babu algus a cikinta. A shekara ta biyu da aurensu ne Umma ta ta samu cikin Yaya Muhammad, bayan shi aka haifi Yaya Sadik, sai Yaya Umar, sai Yaya Usman, lokacin da aka haifi Yaya Usman babu da’dewa Abba na ya auro Fateema Mami na, haifaffiyar fulanin yola. Su kuwa su Abbana fulanin potiskum ne. Tunda Mami ta shigo gidan ta fuskanci Umma na bata kishi da ita matsayin k’anwarta ta d’auketa, sai itama ta zubar da shawara da zugar k’awaye itama ta kwantar da kanta suke zaune lafiya. Shekararta d’aya a gidan, Umma ta sake haifo Yaya Ali ita Kuma ko b’atan wata bata yi ba tunda ta zo gidan. Bayan shekara d’aya da rabi sai Umma ta sake samun ciki ta haifo Yaya Hamza. A kansa ne Umma ta ce ta bawa Mami shi duniya da lahira lokacin da ta tabbatar da shigar cikina bayan wata uku da haihuwarsa. Sai dai me? Wani ikon Allah yana komawa hannun Mami da wata d’aya Ubangigji ya karb’i ransa. Mami ta shiga damuwa sosai, don haka Umma ta ce ta kwantar da hankalinta tana haihuwa zata bata abinda ta haifa. Tunda likitoci sun tabbatar Mami ita da haihuwa sai wani ikon Allah. Cikin farin ciki ta dubi Umma na ta ce “Ko mace ce?” Umma ta ‘d’aga kai duk da a k’asan ranta tana jin Anya zata iya bada y’a mace, tunda abu ne da take mafarkin son samunsa saboda duka yaranta maza ne. Shima Abba ya sha furta mata duk sanda ta haifi Mace zata sha gatan da baa tab’a yiwa wani a gidan ba. Lokacin da aka tabbatarwa Umma da ta haihu kuma mace ta ce da ni ta ji hankalinta ya tashi matuk’a, ta kuma yi dana sanin furtawa Mami bada kyautar abinda ke cikinta. Sai dai ba yarda ta iya ba zata iya kallon idon Mami ta ce ta janye kyautar ta ba. Ga likitoci sun tabbatar mata ya zama dole ta hak’ura da haihuwa in dai tana son lafiyarta ta ‘dore. Don haka ranar suna Umma ta ce ta bawa Mami ni. Ba wanda bai dinga mata kallon mamaki ba. Mami kuwa tsabar murna rungume Umma ta yi tana hawayen farin ciki. Ba wanda bai fa’di wautar Umma ba sai dai ta saka yatsa ta toshe kunnenta ta kuma kulle duk wata k’ofa da y’an gulma zasu mata tasiri. Ta mik’awa Mami ni ta ce “Na bar miki ita Fateema duniya da lahira shayar da ita kawai zan dinga yi.” Mami ta rungumeni tsam a k’irjinta cikin tsabar farin ciki tana yi mata godiya don da gaske ta ji da’din kyautar. Mami da kanta ta saka min suna Nana Ayshatu, Saboda ta da’de tana son sunan. Ba wanda ya k’i amincewa tsakanin Umma da Abba duk da su ma cikin su kowa nada sunan da yake burin saka min. Amma suka amince da Ayshatu da Umma ta saka min. Ta mayar da ni hannunta, sai dai idan ina son Nono ta kai ni na sha wajen Umma da daddare kuwa k’arfi da yaji ta mayar da madara ce abincina don ba zata yarda na dinga kwana a wajen Umma ba. A farkon shekaruna na taso cikin matuk’ar shagwab’a da sangarta, Don Mami bata son ko fa’da a min balle duka yanzu duk girmanka zata maka rashin Mutunci. Ana min magana zata ce a k’yaleni yarinya ce, Ko Umma da take yawan tsawatar min sai da suka yi tashin hankalin da ta tattara ni ta watsar ta daina yi min fa’da. Ta ce min sai dai kawai a koda yaushe bakinta cikin yi min addu’a take. Idan kuma ta faki ido ko idan Mami bata nan tas take wanke ni da fa’da. Wani lokacin nasiha. Tun ina yarinya ban saba saka manyan kaya ba sai k’ananan kaya don haka na tashi kamar y’ar turawa, musamman ina da hasken fulani da gashi mai tsayi. Ina da tsiwa ta gasken gaske da rashin kunya don haka yayyena ke cin Uba na. Adon gashi Mami take min sosai a wannan shekarun duk inda na shiga sai an yaba ni. Mami cikin jin da’di da farin ciki Zata ce “Tubarkallah, maye ya ci kansa kurwar AYSHA ya fi gaban ci.” Umma da taga na yi shekara goma cikin kwantar da murya ta dinga bawa Mami shawarar a dinga saka min kayan hausawa ko na saba da su. Amma Mami ta yi funfurunfus ta k’i har ma ta fa’dawa Umman maganar da ta tsaya mata a rai cewa ta yi “Umma kada wata rana fa ki ce zaki karb’e AYSHA a wajena, don naga kamar kina tantama da tarbiyyar da nake bata?” Hankali tash Umma ta dinga bata hak’uri tana furta “Ba nufi na kenan ba Fatima, amma Allah ya baki hak’uri In sha Allah ba zan sake magana akan abinda ya shafi AYSHA ba.” “Ya dai fi.” Mami ta fa’da fuskarta a ha’de ta kuma ja hannuna muka bar wajen. Tun daga ranar bata sake magana ba. Su Yaya Muhammad ne ma basa gani su k’yale su kuwa Mami wankesu take tas. A makaranta na taso da hazak’a da wata irin kwanya mai d’auke karatu duk girmansa. Ina shekara goma na sauke Alkur’ani. Shekara sha d’aya kuwa ina Js One. Sanda na shekara sha biyu ne, ba zan manta ranar da komai ya sauya a gidan mu ba. Aka wayi gari Mami na ta tattara duk wasu kayan sawata ta rabar da su. Na sha kuka a ranar don ina matuk’ar son kaya na. Bata kulani ba ta dai ja ni mun fita. Kasuwa muka shiga ta dinga siya min atamfofi da laces da yadin Hijabai. Da after dress masu kyau. Muka biya wajen tailor ta saka ya auna ni don a yi min d’inki. Ta kuma ce masa urgent take so. Tun a shagon ta saka min d’aya daga cikin dogayen hijabs d’in da aka d’inka min. Ta Kuma saka sabon nik’ab. Farin ciki ne ya cika zuciyata don ni kaina ina son yin shigar da dinga suturce jikina musamman tuni na gano Na fara shiga sahun y’an matanci. Muka dawo gida. Umma da su Yaya suna zaune suka bi mu da kallo baki sake, don kuwa na d’age Nik’ab d’in ina kallonsu ina murmushi. Mami itama dariya take tana bin su da kallo. “Lokaci ya yi da AYSHA zata dinga suturce jikinta ba don komai ba sabida bana son wani ya min shigar sauri. AYSHA ba zata yi aure ba sai ta yi masters, don haka har fuskarta ban amince ta bayyanata a waje wani ya gani ba……” Ga duk mai son bibiyar littafin nan don Allah ya shiga link d’in nan don ba lallai na jure yawon tafiya group group yin posting ba. Abin da yawa Nagode…🤗 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 1★ Wannan page kacokam d’insa sadaukarwa ne ga members na MIKIYA WRITERS… ★★★★★★★★★★★★★★ Yau ne k’arshen shagalin da ake gudanarwa a ranakun bikin aurena, yau ne dinner party wacce aka shirya ta ta mata zalla a Amani Event center. Ban ha’da dinner ta da maza ba kasancewar daga ni har angon ustazai da bama son gurb’ata bikinmu da abubuwan da suka sab’awa shari’a da Addinin musulunci. Neman albarkar auren kawai muke ba neman suna a duniyar social media ba, don haka bikin nawa ya zama kamar lami miya ba nama saboda rashin warwasawa da na k’i bari y’an mata su yi. Asalima ko ki’da baa saka ba sai ranar kamu ne ma aka saka ki’dan k’warya shima na hana kowa ya yi vedio gudun ya’da b’arna a bayan k’asa. Hakan da na yi ya burge mutane da dama yayin da wasu suke ganin tsabar iyayine da son a sani ba wai addini ba. Ban da mu ba don na san Allah da zuciya yake aiki. Kuma mahaifina ya yi farin ciki da hakan sosai musamman ganin k’ank’antar shekaruna bai saka na ajiye addini da koyarwar Manzon Allah ba. Hankalina gaba d’aya ba ya wajen dinnerr duk da ina tsintar wa’azin da Malama Zainab Jafar take yi a wajen Dinnerr ka’dan-ka’dan. Farin cikin da nake ciki ne ya yi min yawa sanin cewa yau zan angwance da masoyina wanda nake mafarkin kasancewa matarsa a koda yaushe. Ji nake kamar na jawo lokaci a tashi daga dinnerr ko ma koma gida mu je mu shirya a sada ni da gidan Mijina wanda nake matuk’ar d’oki shauk’i da son gani. Tabbas fuskata kawai zaka kalla ka tabbatar da zakwa’din da zuciyata take ciki. Duk da gefe guda na zuciyar tawa a sanyaye yake da kuma rauni wanda zan iya cewa ina jin sa har k’asan raina ba na komai ba ne sai na rabuwa da gidan mu da Ahalin da suke cikinsa. Ina son iyayena kamar yarda zuciyata bata son rabuwa da Yayyena maza da na kasance mace k’wal a cikinsu. Ashe ban sani ba wayo a kai min daga wajen Dinnerr zaa kai ni gidan Mijina ba don komai ba sai don an san yanayin shak’uwata da Abbu a lokacin rabuwarmu tabbas sai mun saka jama’a kuka, musamman kuma kada Yayyena maza suji labari. Mamana da Mamina suna wajen su sun halarci wajen Dinnerr don haka bayan tashi daga dinnerr suka zame suma ban sake ganinsu ba sai jin hannun Aunty Sharifa na yi tana fa’din “Tashi Aysha mu je daga nan sai gidan Mijinki kuma shikkenan Aysha ta girma.” Sai sannan zuciyata ta sake tsinkewa fargaba ta shige ni sanin cewa da na yi daga nan sai gidan Mijina shikkenan ana nufin na yi sallama da iyayena? Idanuna na zubawa Aunty Sharifa murya a raunane na ce “Mami na fa..” “Mami ta tafi gida Aysha ba zata iya ganin kukan ki ba..” Jikina ne ya yi sanyi don tun safiyar ranar na lura da rashin walwalar Mami duk da k’ok’arin dannewa da take, amma hakan bai b’uya a cikin k’wayar idanunta da suka tara ruwa ba. Ni na san Mami bata son wannan auren don dai ba yarda zata yi ne a matsayin ta na marik’iyata kawai kuma kishiyar uwa ba wacce ta haife ni ba. Shi yasa bata da damar da zata nuna hakan. Wata ajiyar zuciya na saki da na hango Mamina na tahowa fuskarta d’auke da damuwa sai dai tana k’ok’arin dannewa wajen sakin murmushi ta iso wajen. Ta zare hannuna daga na cikin Aunty Sharifa ta maye da nata ta ja ni ba tare da ta yi magana ba muka wuce. Hakan da mutane suka gani yasa suka biyo mu wasu da yawa a wajen Mamina ta burgesu yayin da wasu na san ba mamaki abinda ta yi d’in su kira shi da iyayi. Mamina da kanta ta shigar da ni d’akin aurena, hannuna damk’e cikin nata tana gaya min addu’oin da zan yi a cikin kunne na. Na lumshe ido ina fa’dar addu’ar da duk da na iya ta a yau saboda raunin zuciya sai na ji ta b’ace min b’at. Lokacin tafiya na yi wani kuka ya kufecewa Mami ta rungumeni ina kuka tana kuka da k’yar mutane suka lallashemu aka samu aka b’anb’are Mami daga jikina aka fita da ita. Kukan na sake ruhshewa dashi ba wanda ya yi mamaki don an san shak’uwar da take tsakaninmu da Mamina. Haka ina ji ina gani kowa ya tafi daga gidan aka bar ni ni ka’dai kamar mayya. Sai sannan fargaba ta sake shiga jikina saboda ina da tsoro musamman na san gidan babban gaske ne. Tun ina saka ran shigowar ango har na saduda na yaye mayafin dake jikina zuciyata cike da mamakin ko me ya hanashi shigowa haka. Har na d’au wayata zan kira shi sai na ji ina jin kunya kada ya ce har na matsu da ganinsa na kira shi don haka sai na mayar da wayar kawai na ajiye na cigaba da kewaye d’akin da idona, wani irin farin ciki ya ratsani ganin irin namijin k’ok’arin da iyayena suka yi don su fitar da ni kunya. Sai sha biyun dare sannan na dinga jin takunsa kamar daga corridor hakan yasa na yi saurin jan mayafi na na suturce jikina. Daga jin yarda yanayin bugun zuciyata ya sauya na san shi ya shigo jikina kuma ya ba ni ni yake kallo, amma ko me ya hana shi k’arasawa inda nake. Ta cikin mayafi na dinga lek’ashi sanye yake cikin wata irin Alkyabba mai kyau da santsi kalar blue black da ta amshi farar fatarsa. Saman jallabiyar Alkyabba ce golden kamar yarda dai ya saba shigarsa a kullun yauma hakan ne. Kansa da hula mai shegen kyan tsiya wacce hausawa suke cewa Tashi ka fiye naci sai dai wannan mai tsadar ce. Tuni d’akin ya baje da wani irin k’amshin turaruka da ya danne nawa da na wutan da aka saka a d’akin. Kana jin k’amshin turaren zaka san mai tsada ne na masifa… Sai da na kai idona kan fuskarsa sannan gaba na ya yi wani irin fa’duwa ganin yarda fuskarsa take a ha’de murtuk kamar bai tab’a dariya ba. Kamar ba Ustazuna mai yawan fara’a ba. Me zai saka ya ha’de rai a wannan daren da yafi ni zakwad’in zuwansa? Duk da dama ba ma’abocin dariya da k’yakyatawa bane amma ma’abocin murmushi ne don ya ce dariya na rage imanin Mumini. Ganin ya fara taku zuwa inda nake yasa na sake jan mayafi na k’udundune fuskata don ban shirya amsa sunan mara kunya a wajen Ustazuna ba. Yanayin takunsa yanayin yarda bugun zuciyata ke sauyawa da k’arfin gaske don na san dai ba mamaki yau Ustaz ya kai min runguma abinda muka da’de muna mafarki don da gani har shi na san mun yi dauriya… “AYSHA!” Ya fa’da cikin jarumar muryarsa da take bayyana kasantuwarsa Namijin gaske.. Mamaki ne ya kusan kasheni jin a yau ya ambaci sunana gatsau ba wani sakayawa kamar yarda ya saba kira na da “Eesha ko ya ce Aysha ta..” Duk da haka ban yi nawar d’agowa ba na zuba masa ido ina kallon yarda yake kallona fuskarsa a ha’de ya mik’a min takardar hannunsa tabbas yanayinsa ya firgita ni… “Ungo wannan.” Ya fa’da da wata irin shak’akkiyar murya, yana d’auke kallonsa daga gani na. Leda ce ya mik’a min. Daga haka ya juya ya fice a zatona zuwa zai yi shirya ya dawo. Duk da zuciyarta na gaya min akwai matsala ba haka Ustazuna ya kamata ya tare ni ba ni da nayi zaton runguma da kyakykyawan kiss da na da’de ina mafarki…. Ko dai na masa wani laifi ne da ban sani ba? Ajiyar zuciya na saki ina jan ledar da sauri. K’amshin kazar Yahuza suya ya dake ni da Ice cream masu sanyi. Jikina har rawa yake don idan ban manta ba rabona da abinci tun safiyar ranar don haka kawai sai na samu kai na da fara cin kazar na sha ice cream d’in. Na saka hannu na jawo leda zan d’au lemo idona ya kai kan wata farar enveloped. A zatona mantawa ya yi don haka ban ma bu’de ba na ajiye a gefe ina jan kwalin exotic na fara d’addaka shi a cikina. Na tattare kayan idona ya sake sauka kan enveloped da a bayansa na ga sunana b’aro b’aro. AYSHA IMAM KHALIL… murmushi na saki ina tunanin ko wata kyauta Ustaz d’in ya bani don haka na jawo da sauri na farke enveloped d’in da yake ta zuba k’amshin turarensa. 𝒜𝓈𝓈𝒶𝓁𝒶𝓂𝓊 𝒶𝓁𝒶𝒾𝓀𝓊𝓂.... 𝒩𝒾 𝒜𝒽𝓂𝒶𝒹 𝒮𝓊𝓁𝒶𝒾𝓂𝒶𝓃 𝒮𝒶ℯℯ𝒹 𝓃𝒶 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝓂𝒶𝓉𝒶𝓉𝒶 𝒜𝓎𝓈𝒽𝒶 ℐ𝓂𝒶𝓂 𝒦𝒽𝒶𝓁𝒾𝓁 𝓈𝒶𝓀𝒾 𝒹𝒶𝓎𝒶 𝒷𝒶𝓉𝒶 𝒹𝒶 𝒾𝒹𝒹𝒶𝓉𝒶 𝒾𝒹𝒶𝓃 𝓉𝒶 𝓈𝒶𝓂𝓊 𝓂𝒾𝒿𝒾 𝓉𝒶 𝓎𝒾 𝒶𝓊𝓇ℯ...... Kasa k’arasawa na yi saboda yarda na ji numfashi na yana neman d’aukewa na dinga ware ido ina jin zuciyata na wani irin bugu.. Tabbas NAGA RAYUWA Me yake shirin faruwa da ni ne? Saki a daren aurena daren da muke d’oki da zakwa’din zuwansa ni da mijina ya da’de yana gaya min yana jiran ranar da zai rungumeni dtazo saboda kiyeye dokar Ubangiji. Me na yiwa Ustazuna ya sake ni? Na shiga uku!! Haka na furta a zuciyata.. To fa! ko me AYSHA ta yiwa Ustaz Ahmad ya zabga mata saki a daren aurenta? Duka yana cikin littafin NAGA RAYUWA da zai dinga zuwa muku daga Alk’alamin….. 𝒥𝒾𝓀𝒶𝓇 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 2. ★…..✍🏽 Kuka ne sosai ya kufce min, irin kukan nan da kake jin d’acinsa har k’asan ranka. Kuka mai sauti da Amon muryar karaya a cikinsa. Me Na masa? Shine tambayar da nake wa kaina na kuma kasa lalubo amsar. Abinda zuciyata take gaya min nake k’aryatawa ko nak’i ko na so dole ne na gasagata zuciyar tawa dole Butulcin d’a namiji ne ya biyo ta kai na. Ko kuma ya yi haka ne don ya gwada mizanin soyayyarsa a zuciyata. Amma ya rasa ta hanyar da zai gwada sai ta kalmar saki? Kai abinda kamar wuya Ustaz da wayonsa ba zai yi wasa da saki ba Halak d’in da ya san Allah baya so, kuma idan aka aikata shi ar’ashi tana girgiza. Dole ba don na so ba na amince da shawarar da zuciyata take ba ni, na danganawa sashensa na je na tambayeshi abinda ke faruwa… Tsam na mik’e na shiga laliben sashennasa, kasancewata bak’uwa a gidan bai saka na sha wahalar gane k’ofar sashen nasa ba. Daga can corridor tsakanin k’ofar da zata kai ka nawa sashen. A hankali na tura k’ofar na shiga. Shiru babban parlorn nasa baka jin k’arar komai sai na A.c da take ta aiki ba ji ba gani. Fitulun wajen ma a kashe suke. Karatun k’ur’ani ne kawai yake tashi a parlourn cikin k’ira’ar shureim. Na gama zagaye parlorn da idona ban gan shi ba, don haka na isa k’ofa guda da take parlorn da na tabbatar nan ne d’akin nasa. Yana zaune a gefen gadon daga k’asa saman sallaya ya kifa kansa a jikin gadon. Jin motsina ya saka shi d’aga kai. Wata irin fa’duwar gaba ce ta same ni ganin yarda idanunsa suka ka’da suka yi jawur kamar gaurashi. Idan ba idanu na ne suka min gizo ba sai naga kamar hawaye ne a kwance a k’asan idanun. Mayar da idonsa ya yi ya lumshe bai sake kallona ba alamu sun nuna baya son gani na. Zuciyata a jagule tana wani irin bugu da k’arfin gaske na k’arasa wajensa. Zama na yi a gefen gadon murya cike da rauni na furta “Ustazuna, wata takarda na gani a cikin kayan da ka kawo, zuciyata ta kasa amincewa hannunka ne ya rubuta ta. Ban kuma fahimceka ba.” Shiru kamar ba zai amsa ba, idanun dai still a lumshe daga inda nake ina ganin yarda k’irjinsa yake bugu. “Ustaz, magana fa nake.” “Taki ce.” Ya fa’da muryarsa a shak’e. Ido na waro ina furta “Saki Ustaz!” Ya bu’de idon nasa ya nutsasu cikin nawa, a hankali ya d’aga lab’b’ansa kamar baya so ya furta “K’warai kuwa AYSHA, don haka ki tabbata kin fice kin daga gida k’arfe bakwai na safe….” Ina daga zaunen na dinga jin wani irin jiri yana d’ibana. “Ko zan san dalili?” Wannan karan madadin amsa min mik’ewa ya yi yana zabga tsaki ya furta “Ban sani ba…” Shiru na yi na lumshe idona ina hak’ilo da yak’i da b’acin ran da yake son dannen numfashi. “Tashi ki fita zan rufe k’ofata..” Ya furta yana nuna min k’ofa.. Ya fa’da yana juya min baya… Jikina a salub’e na mik’e ina jin kamar k’afarta wa ba Zata iya d’aukata ba saboda rawar da jikina yake yi na zallar tashin hankali. Da k’yar na ja jiki na isa bak’in k’ofar daidai lokacin da na jiyo ina kallon Ustaz ina cije leb’ena shima kallon nawa yake hawaye ba zuba daga idonsa. Na ja k’ofar da k’arfin gaske na fice daga d’akin. Zuciyata har Tafasa take saboda tsananin b’acin rai. Na zauna a gefen gadona ina mayar da numfashi tabbas Uztaz ya cuceni a shekaruna sha takwas kacal ya mayar da ni k’aramar bazawara? Shin halaccin da zai yiwa Iyayena kenan? Tabbas ya amsa sunansa Butulu? Yanzu me Zan je na ce a gidan mu? Ya rasa irin sakin da zai yi min sai irin wannan na tozarci da wulak’anci saki a ranar aurenka daren amarcinka? Yaya mutane za su yiwa abin fassara? Dole ne a jefa min ayar tambaya musamman kowa da ya san Ustaz ya san Babban Malami na da ake watsa tafseer d’insa a gidajen sunna na t.v. Babban Malami ne da gwamnatin k’asa baki d’aya take ji da shi duk da dai ba wani shekaru ne da shi ba ba zai wuce shekaru 32 ba. Toilet na shiga bayan da zuciyata ta tabbatar min ba ni da wanda zan fuskanta a wannan gab’ar sai Ubangiji. Don haka na yi alwala na fito na tada sallah akan daddumar da Abba ya bani d’azu da safe ita da Alk’ur’ani da Riga da Hijab na sallah farare tas har da carbi da wani turare mai k’amshin gaske, yana furta “AYSHA, kin ga wa’dannan sune garkuwarki a gidan miji idan kika rik’esu kin samu makamin k’are dangi.” Ina sallahr ina hawaye na kaiwa Allah kuka na, na bayyana masa rauni na na kuma rok’eshi ya shige min gaba a dukkan lamari na.” Ban tashi daga sallaya ba sai k’arfe uku da naji kaina ya fara ciwo abin mamaki sai na ji na samu k’arfi da nutsuwar zuciya. Na ji komai ya faru gareni daga Allah yake duk da tabbas Ustaz ya cuceni. Abu guda nafi buk’ata a yanzu na ji dalilin sakin da ya yi min, sai dai na yi alk’awarin ni da kai na ba zan sake tambayarsa ba don ko don ganinsa bana yi. Barci ne sosai ya d’auke ni, kasancewar garin sanyi ne dare yana tsawaita don haka sallar asuba sa daf da k’arfe shidda ake yi, shi yasa na samu barci sosai duk da ba wai zance na yi isashshe ba ne. Ina sallame sallahr ko kayan sallar ban cire ba na fice da su da sauri a jikina. Shiru layin amma a haka na dinga tattaki har na je bakin titi. Allah kuma ya taimakeni na samu adaidaita sahu. “Shara’da phase 2 kawai nace masa. Har k’ofar gidanmu ya ajiye ni ta hanyar kwatance da na masa. Duk da a tsorace nake da ganin Abbana hakan bai hana ni shiga gidan da k’warin gwiwata ba. Y’an biki ko watsewa ba su yi ba, don wasu daga garuruwa daban daban suka zo. Sai dai gidan shiru da alama kowa gajiyar biki ta saka ana sallah an kwanta sai wa’danda suke aiki a bayan gidan ta can na dinga jin d’an hayaniya da sautin kwanuka na tashi. Jama’ar da suke kwance a Parlor wa’danda duk k’annen Mami na ne da na Umma na suka dinga bi na da kallon mamaki baki a sake. Anty Sharifa ta ce “Ke AYSHA lafiya?” Mami da fitowarta daga d’akinta kenan itama hangame bakin ta yi tana ware ido ta furta “Ni Fa’dima me Zan gani haka? Ke Aysha Uban me ya fito da ke da sassafe haka?” Ta fa’da tana jan hannuna hankali a tashe ta furta “Ai dama sai da na gayawa Abbanku kin yi k’ank’anta da aure, shekara sha bakwai don ko sha takwas d’in baki cika ba, yanzu haka wani bak’on al’amari kika gani da yafi k’arfinki yasa kika gudo?” Anty Sharifa k’anwar Umma ta ce “Ah haba! Sai kace ba y’ar yanzu ba, ai duk da take k’anwar Maza na san ta san me aure ya k’unsa ko da ta hanyar k’awaye da karance karancen littafine…” Mami ta d’an harareta “Me AYSHA ta sani? Karatun littafin take ita? Ko k’awayen arziki AYSHA bata da su balle su sanar da ita aure da abinda ya k’unsa…” Ta fa’da tana jan hannuna muka shige Uwar d’akinta. Zaunar da ni ta yi a bakin gado, bayan ta koma ta rufe d’akin da key tana furta “Bana son saka ido da munafunci yanzu duk ido zai dawo kan ki, kema kin yi wauta Aysha. Me ya kai ki fitowa don kawai Mijinki ya kusanceki Ai shine auren muma duk haka ake mana da haka kuma kowa yake sabawa… kowace macen aure da kika gani haka ne yake faruwa da ita koda yaushe, don haka tun kafin sauran mutane da Ubanki su ji ki tashi maza naje na mayar da ke, bana son na ji komai wannan sirrinki ne ke da Mijinki. Maza tashi mu tafi kafin mutane su fara miki kallon mara wayo mai gudun Miji.” Hawaye ne suka fara zuba min, ganin ita Mami na inda take hange daban da abinda ya kawo ni gidan. Na turo bakina ina furta “Ni fa ba wannan bane, ko hannu bai rik’e min ba fa.” Mami ta d’an bu’de idonta ta furta “To menene idan ba wannan ba?” “Ya sake ni…” Wani irin ja da baya Mami ta yi idonta a waje tana kallona baki a bu’de ta shiga shock sosai cikin wani irin yanayi ta furta “What? Ya sake ki Aysha? Shi Ahmad d’in ne ya sake ki? A kwana guda da kika yi a gidansa to Uban me kika masa?” Hawaye ne suka fara ambaliya a fuskata na gayawa Mami duk abinda ya faru ban b’oye mata komai ba. Dariya Mami ta yi tana furta “Sharrin D’a Namiji! Ga abinda nake gudu ya zo. Sai ki tashi mu je wajen Abbanki na bashi tukuicin alheri da Ahmad ya kawo masa, ya mayar masa da y’a k’aramar bazawara Ahmad dai mai nagartattun halayen da Ubanki yake faman b’ab’atu akai.” Ido na waro waje ganin tana ja hannuna “Tashi mu je mana.” Na ja hannun ina girgiza kai “Mami, ba zan iya zuwa wajen Abba ba, Allah ina tsoro, ban san yarda zai d’au lamarin ba.” Wani kallo ta min cikin b’acin rai ta furta “Tashi na ce miki mu je ko? Iyakacinsa dai dake fa’da, tunda ba zai iya zare miki ranki ba.” Ta fa’da a fusace ta kuma fincikeni muka fita wajen. Abin haushi Jama’a an fito gaba d’aya kowa sai baza ido yake ana kallon mu. Kallo guda Mami ta musu suka dinga bajewa suna ba mu hanya. Ban yi mamaki ba don ni da kai na na san an samu topic. Abba na zaune yana lazimin safiya. Umma ce a gefensa tana ha’da masa coffee da ya saba sha duk safiya. Da alama shi bai san abinda ya faru ba. Balle Umma da tun jiyan bata fita daga sashensa ba. A razane duk suka zuba mana idonsu musamman Umma da har Cokalin hannunta yake fa’duwa. “FATIMA lafiya kuwa? Naga Aysha da sassafe.” Umma ta fa’da tashin hankalinta na sake bayyana a saman fuskarta. Zama Mami ta yi a gefen Kujerar da yake kusa da Abba, ta saka ni a gefenta ta furta “Lafiyar kenan Umma, sai dai d’an gaban goshin naku ya muku Aiken tukuicin sakamakon alherin da kuka masa…” Abba da yake laziminsa ya d’ago ya d’an zubawa Mami ido don ya san halin kayarsa sarai danger ce wutar baya. Umma kuwa cup d’in ta ajiye tana sake furta “Me ya faru to? amma fa Mammin Aysha ya kamata ki yiwa y’ar taki fa’da ta san fa ta girma, aure kuma ba wasan yara ba ne. Idan ban da shashashanci menene na dako wannan Uban sammakon, koma menene ba ga waya ba me yasa ba zata sanar miki ba? Sai ta d’ebo jiki ta taho ta saka y’an biki su tafi da ita a bakin duniya tunda ko gama watsewa ba su yi ba. Aa sam wannan wauta ce da shirme.” Mami wani kallo ta mata sai kuma ta cije baki. “Kamawa ta yi, ta dako uban sammakon babu gaira ba dalili ba abinda zai sakata fitowa daga gidan Mijin da aka kai ta jiya.” Mami ta fa’da tana hura hanci da jijjiga k’afa. Umma dai shiru ta yi don ba mamaki ta lura idan ta cigaba da magana tata ce zata yi zafi. Abbana yana jin su bai yi magana ba ya cigaba da laziminsa. Sai da ya idar sannan ya ‘d’au coffee d’insa ya shanye ya zuba min kallon da na kusan jin kayan cikina suna shirin fitowa. “Ke wace irin shashasha ce Aysha? Daga kai ki gidan Miji jiya yau ki fito? Kin d’auka auren wasa ne? Me ya fito da ke?” Madadin amsa masa jiki na ne ya dinga rawa kamar yarda zuciyata take bugawa. “Ba magana nake miki ba?” Ya sake fa’da da Tsawar gaske, hakan da yasa har ban san sanda na rik’e Mami da kyau ba ina makyarkyata “A’a Alhaji, kada ka sake hargitsata Ai ba laifinta ba ne fitowar dole ne ta fito tunda ya saketa…..” Gaba d’aya bakinsu a ha’de suka furta “Saki Fatima?” Ta jijjiga kai tana murmushi ha’de da furta “Sakamakon halaccin da kuka masa ne, duk duniya kuna ganin ba wanda ya cancanta kamar Ustaz Ahmad. Kullum zancenku nagartaccen mutum ne mai ilimin addini da ya shahara a duniyar Malamai. Yau ga ilimin nasa nan ya fara nuna muku….” D’akin tsit ya yi Abba jikinsa har rawa yake. Umma kuwa zama ta yi jab’ar a k’asa ta rik’e kanta kawai jikinta na rawa…. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR NAGA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 4.. Da mamaki Umma take kallonta su Yaya Muhammad suma suka zuba mata ido. Ya Usman da ya kasa shiru ya ce “Au ke kuma auren ne ba kya son ta yi? Shi yasa zata ke k’unshe fuskarta, amma kamar wannan ba dabara ba ce..” Harara ta watsa masa tana furta “To kanari Uban surutu, ni na ce maka bana son ta yi aure? Auren ne dai ba yanzu zata yi shi ba sai ta yi dogon karatun da na tabbatar zata iya k’watar y’ancin kanta a Wajen namiji sannan zan amince ta yi aure, haka kawai ba za’a aurar da ita da duhun kai ba shikkenan ta zama sai kace baiwa wajen namiji…” Cikin mamaki suka zuba mata ido, Umma kanta ta yi mamakin furucin Mamin, sai dai data tuna Mamin gidansu gangariyar y’an boko ne sai bata yi mamaki ba ta saki ajiyar zuciya kawai tana furta “Allah ya taimaka, ya nuna mana lokacin…” Yaya Muhammad gyara zama ya yi yana tab’e baki ya furta “Amma dai wannan kamar ba shawara ba ce mai b’illewa, Saboda kowa yanzu burinsa a ce y’arsa ta yi aure sai ta yi karatun a nata gidan Mijin….” “Sai ka bari sai ka haifi taka y’ar Muhammad ba wannan ba…” ta fa’da a zafafe tana nuna ni. Ta ja hannuna muka wuce samanta. Tana banbamin fa’da har da rantsuwar nan gaba idan Muhammad bai yi wasa ba sai ta mare shi. A kashegarin ranar kuwa bayan na yi wanka Mami ta tsantsara min kwalliya cikin shigar kayan hausawa da suka min matuk’ar kyau. Murna na dinga yi don kam dama ina son su Mamin ce bata ba ni damar sakawa ba. Sanda na fita tsakargida idanun masu aiki duk a kaina suke, sunan ta dariya ganin kwalliyar da aka min. Har Iya ta kasa shiru ta ce “Lallai Aishatun Mami ta girma… Ma sha Allah a yi shekaru irin na dabino.” Abba da yake zaune daga can gefe shi da su Yaya Muhd, baki sake ya dinga kallona yana furta “Inye Aishatun ba, irin wannan Kwalliya haka? Waye ya siyo Miki kayan hausawa…” ina dariya na zauna daf da shi an furta “‘Mami na ce, ita ta siyo min su da yawa ta ce na daina saka wa’dancan kayan yahudun.” Jan hancina Abba ya yi ya ce “Ai ke ce Yahudun.” Sannan ya juya yana kallon su Ya. Muhd ya furta “Kun ga abinda na gaya muku ko? Na gaya muku kada ku tada hankalinku a kan yarinyar nan Fatima ba zata yi sanadin gurb’acewar tarbiyyarta ba..Fateema mace ce data san abinda take yi.” Shiru su ka yi suna cigaba da shan kununsu Ya Ali ne ya furta “Ba shakka, to Allah yasa dai ba da wata manu…” wani kallo naga Umma ta masa sai ya ja bakinsa ya tsuke yana dariya. Tun daga ranar ya zama na saba saka kayan hausawa, kuma ko aike na waje za’a yi Mami na bata bari na fita ba nik’ab har hakan ya zame min Jiki. Sai dai a fuskar Umma Wani lokacin ina kallon yanayinta kamar hakan baya mata da’di, sai dai ba yarda zata yi ne. Duk inda na je kuwa sha’awar shigata ake, don kowa ya ganni ya san d’iyar wacece? D’iyar mace mai mutunci wacce ta san ciwon kanta, kuma yake bawa y’arta tarbiyya, ba wacce da kanta take saka y’a’yanta shigar banza ba don kawai su kawo mata mazan aure ta dinga kuma zuga su da fa’din sun yi kyau. Sanda na fara period kuwa, Mami hana aikena ta yi. Saboda wani irin kyau da na dinga zubawa, mak’erin y’an mata na ji suna cewa ya fara k’era ni. Don haka ta shiga taka tsantsan da ni. Idan Ya. Muhd ya yi magana ta hau masa masifa don haka ya gani ya zuba mata ido kamar yarda kowa ya yi. Sanda maganar aurensu ta bujiro da y’ay’an abokin Abba Mami na jin iya secondary kawai suka gama. Ta dinga tab’e baki tana fa’din “Amma Sadik kun yi bak’ar dabara, yanzu meye riba a auren k’wailayen mata?” Ya Muhd don takaici kasa mata magana ya yi, Ya. SADIK MURMUSHI ya saki yana furta “Ai auren irinsu Mami ya fi riba, ko bakomai zasu bi duk wani tsari da aka shar’anta musu..” Ta ja tsaki ta furta “Mugunta zaku musu ba, ai shikkenan shi yasa duk bala’i ba zan yarda AYSHA ta yi aure daga gama secondary ba dole ko degree sai ta yi, idan ma bata yi masters ba…” Ya Muhd da yake tsaye ya tura hular sa goshi yana furta “A dai rage dogon buri, idan yarinya ta yi girma da yawa yanzu mazan ma gudun aurenta suke, don sun san tafi k’arfinsu…” Yana ji ta k’unduma wani zagi ya shige d’akinsu yana dariya. Haka kuwa aka yi, bayan wani lokaci aka gudanar da bikin Ya. Muhd da Ya sadik. Muhd da Khadija, Yaya Sadik kuma da Nafisa a lokacin ina Js 3. Amma duk wata cika ta matantaka ta bayyana a surar jiki na. ★★★✍️ Ina SS 2… al’amarin ya faru. Mun taso daga Islamiyya ni da k’awata Asma’u, muna tafe muna hira a hankali cikin nutsuwa. Ranar ganin ba kowa a layin sai na ‘dage hijabi na. Asma’u ta kalleni da mamaki ta ce “Yau kuma Aysha? Lallai kina son idan Mami ta ji labari har ni ta ha’da ta ci mutunci na kenan?” Tab’e baki na yi, ina yamutsa na fuska na ce “Ai layin ba kowa….kuma ma waye bai sanni a layin nan ba?” Cigaba ta yi da bani labarin wani series da ake yi a Mbc bollywood wanda na yi missing ban kalla ba, sabida girki da Mami ta saka ni a daidai lokacin. Murmushi kawai nake saki… Zuciyata ce ta wani irin bugawa daidai lokacin da muka ha’da ido da shi yana tsaye a gefen wani gida da ake gini ba’a k’arasa ba…” Da sauri na ja nik’ab d’ina na mayar ina jin yarda sautin bugun zuciyatta ya tsananta. Tabbas na san fuskarsa a sunna t.v matashin Malamine da yake tafseer a duk azimi. Ba wanda bai san Ustaz Ahmad ba. Saboda yarda yake d’an gayu komansa mai kyau ne yana kuma ji da tashen Naira. Asma’u ta furta k’asa k’asa “Ke AYSHA kamar Dr. Ahmad sulaiman ko?” Ban amsa mata ba, k’irjina dai ya cigaba da bugu. Sam zuciyata kasa cigaba ta yi da saurarar labarin da Asma take bani saboda wani yanayi da na fa’da mai girman gaske.. Tabbas tunda nake ban tab’a ganin mutumin da jallabiyya ta yiwa kyau kamar wannan mutumin ba. Ga wani azababben k’amshin turarensa da ya maye wajen gaba d’aya. A kallon da na masa sai naga ashe har ya fi kyau a fili. Yana da haske sai dai ba sosai ba. Idanunsa farare tas kuma mayalwata. Cikakkiyar gira ce da shi da gashin ido kamar yarda gashin kansa yake cikakke kuma bak’i si’dik. Duka wannan na gani ne a guntun kallon da na masa. Asma tana shiga gida nima na fa’da gidanmu da sauri tunda mak’ota muke da su. Shi kuma Ustaz gidan da yazo gidan yana kallon gidanmu. Ban bari kowa ya ji shigowata ba na haye sama da sauri na shiga d’akina. Haka kawai nake don sake ganinsa don na san windown d’akina yana kallon gidan da yazo. Ina d’aga labulan kuwa na hango shi yana tsaye still suna magana da Lawal da ya kasance d’an mak’otan mu. Idanunsa na ga ya juyo yana kallon gidan mu kamar mai nazarin wani abu… Daidai lokacin Mami ta shigo tana k’wala min kira. Da sauri na saki labulan windown alamar rashin gaskiya bayyane k’uru k’uru a cikin idanuna. Ba ta yi min magana ba sai takowa da ta yi zuwa gaban windown ta d’aga labulan tana furta “Uban me kike kallo anan d’in?” Idanunta ya sauka akan Ustaz da sauri ta juyo tana kallona baki sake ta furta “Namiji kike kallo Aysha? To Uban me ya ha’da ki da shi?” Hantar cikina ta ka’da… bakina na rawa na furta “Babu komai Mami…. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ Wancan group d’in ya cika Wanda Bai samu Shiga group 1 ba ya Shiga 2. Amma don Allah idan kana group 1 kada ka Shiga 2 don duk Abu d’aya ne. A shiga group, ba Zan juri posting a kowane group ba, ba kuma Zan juri a dinga cewa Na tura daga farko ta private ba. Hankalinka kwance ka shiga group kawai. Nagode[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 5. Mami ta zabga tsaki tana sakin labulan tana kallo na ta furta “Idan ma shi kike kallon, ki tsaya ki saurareni da kyau.” Ta fa’da tana jan kunnena “Koda wasa kada ki sake ki saka wani namiji a ranki, a yanzu dai kam don ko me zai faru ba zan bari a aurar da ke ba, sai na cika burina na kin zama wani abu a fannin ilimin boko.” D’aga kai na na yi, ina lumshe idona. Ta fice da sauri ina jin b’acin rai ma ya mantar da ita abinda ya kawo ta. Bu’de idona na yi a hankali ina sakin ajiyar zuciya. Ba tare da damuwa ba na sake yaye labulan d’akin. Daidai lokacin da Ustaz ya d’ago yana sake kallon gidan mu, ban damu ba na tsaya na kalleshi sosai don na san ba zai ganni ba, glass d’in yana da duhu daga waje ba’a ganin wanda yake ciki. Na saki ajiyar zuciya ina kallon sanda ya shiga motar sa yana sake bawa Lawal hannu suka yi misabiha. Ya ja motar ya bar wajen. “Allah ya yi halitta…” Na furta a hankali ina kai wa saman gado na zauna. Har a lokacin yanayin bugun zuciyata bai koma daidai ba. Shikkenan na samu abin yi tun daga ranar da na gan shi, ban sake komawa daidai ba. Kullum cikin tunaninsa nake da burin sake ganinsa koda sau ‘d’aya ne a rayuwata. Ranar da sati ya zagayo ranar wata lahadi still mun dawo Islamiyya da Asma’u kamar wancan lokacin. Asma ce take ta surutunta ni kuwa bakina shiru, don wani irin yanayi nake ji a zuciyata ga bugun zuciyartawa ya sauya. Muna doso layinmu na ji mayataccen k’amshin turarensa wanda ba zan tab’a mantawa ba. Da sauri na sauke Nik’ab d’in don kuwa na tabbatar shine duk da bayansa kawai na gani still sanye yake da jallabiya mai kyau brown kansa da hula tashi ka fiya nace mai tsadar. Muna doso ta inda suke zamu wuce don dole sai ta nan d’in na ji k’afafuna sun fara rawa kamar ba zasu d’aukeni ba. Duk da nik’ab ne a idanuna na ga ya ‘dago yana kallon inda muke sai kuma suka yi shiru da hirar da suke. Da k’yar na saita kaina na nutsu muka shige su. Sai da na shiga gate d’in gidanmu sannan na saki ajiyar zuciya a hankali ina furta “Ya rabbi! Me ke faruwa da ni ne?” Bayan kwana biyu ina zaune a ajin mu ja Islamiyya. Aka aiko kirana. A matsayin da nake kai na shugabar makaranta na san ba wani abu bane don an aiko kirana d’in, amma wannan karan sai na ji zuciyata ta buga sosai. Ido na tsurawa mai kiran nawa. Har ya ji haushi ya furta “AYSHA magana fa nake.” Da sauri na amsa da “To gani nan.” A Office d’in Headmaster na tsaya ina knocking a hankali. Muryar Malam d’in na ji yana furta “Bismillah Ayshatu…” Na yi sallama na shiga, k’amshin turarensa ya doso hancina har ban san sanda na ware ido ganin Ustaz a zaune ba idonsa akan wani littafi da ke hannunsa. Wallahi Allah ne ya yi ba zan fa’di ba, Saboda zallar rashin nutsuwa. Sunkuyar da kaina na yi ina wasa da yatsuna. Har Malam ya gama rubutunsa ya d’ago yana kallona “Gaisuwa fa Ayshatu?” Da sauri na juya na kalli Ustaz da ya yi kamar bai san da ni ba a wajen. “Ina yini?” Bai d’ago ba na ji dai ya masa murya a k’asa “Lafiya..” D’an tab’e bakina na yi duk da na ji haushinsa, na mayar da hankalina kan Malam. “Ki je maza ki sanar da duk ajujuwa akwai assembly idan an idar da sallah..” Na amsa da sauri don burina fita daga office d’in kafin halin da nake ciki ya bayyana…” Haka kuwa aka yi, ana idar da sallah ba wanda ya tashi daga babban filin harabar makarantar. Kowa ya zauna ya kuma nutsu ana jiran fara assembly. Duka Malaman makarantar suna zaune sun kame akan kujerunsu. Mu kuma muna tsaye don lura da masu surutu. Wajen tsit baka jin saurin komai. Malam Kawu ne ya nuna ni da nufin nazo wajensa. Ina isa ya furta “Ki fara karatu, Yanzu Malam Babba zai zo.” Na mik’e na d’au speaker d’in ina fara karatu ya yi daidai da shigowarsu. K’asa kawai na yi da kai na na cigaba da karatuna kawai cikin muryar Shureim da na k’ware da karatu da ita. Ina kallo Ustaz kawai ya lumshe idonsa yana jijjiga k’afa a hankali. Sai da nace sadak’allahul azeem sannan ya bu’de idon nasa ya sauke su a kaina. Ji na yi tsigar jikina ta tashi. Da k’yar na ja jiki na koma inda nake na zauna don kam ba zan juri tsayuwa ba. Malam Ahmad ne ya fara jawabi da sanar da su babban cigaban da makaranta da ta samu na zuwan Ustaz Ahmad da son d’aukar wani darasi a makarantar…” Kabbara da ihu d’aliban suka saka cikin matuk’ar murna da farin ciki. Bayan ajiye loudspeaker d’insa Malam Kawu ne ya d’auka ya ‘dan yi barkwancinsa sannan ya sanar da cewa ya barwa Ustaz abinda har zuwa sanda zai bar makarantar.” Ta cikin nik’ab na ware ido jin abinda ya ce don ajin Malam kawu nan ne ajin mu, gefe guda kuwa na zuciyata wani irin farin ciki ne mara misali a cikinta. Haka aka tashi zuciyar kowa cike da farin ciki. Ina ji y’an mata suna ta yaba Ustaz haka kawai sai na ji raina ya b’aci tsananin haushi ya shiga zuciyata, ban sani ba ashe wannan shine kishi. Kashegari da wani irin ‘doki na yi shirin makaranta, karo na farko har da mutstsika Lipstick a lab’b’ana sai naga na yi kyau da sauri na saki nik’ab d’ina tun kafin Mami ta gan ni da jambaki ta min masifa. Sai dai na makaro ina d’aga kai na hangota ta cikin mudubi fuskarta a ha’de take kallona. Ta iso inda nake zuciyata ce ta dinga harbawa da k’arfi. Saka hannu ta yi ta cire nik’ab d’in, ta kuma saka yatsa tana zagaye lab’b’ana tana sakin murmushi ta furta “Jambaki AYSHA? Jambaki kika saka zaki makaranta? Me kike son b’oye min ne?” Lumshe idona na yi ina jin zuciyata na bugu da mugun k’arfi. “Kada ki fara AYSHA, kada ki fara abinda zamu zo muna k’aramin yak’i da iyayenki a gidan nan. Goge shi tas idan baki yi wasa ba tsaf zan cireki daga Islamiyyar na samu Malamin da zai dinga koya miki…” Da sauri na rik’e hannunta “Don Allah Mami kiyi hak’uri kada ki raba ni da makarantata, In sha Allah ba zan sake sakawa ba. Kuma wallahi bana kula kowa ko Asma ki tambaya…” Murmushi kawai ta saki ta janye hannunta. “Zan bincika..” Daga haka ta fice bayan ta saka ni na goge jambakin dama ni ko kalli bana sakawa ina da kwallina daga indallahi. Na saki ajiyar zuciya ina fita daga d’akin. Shiru makarantar da alama ni da Asma ne muka fara zuwa. Muna shiga aji Asma ta fice don itace da Duty ranar. Sai na zauna ni ka’dai na bu’de kur’ani na soma tilawa. Don dokar Tahfiz ce duk wanda ya fara zuwa shi yake fara karatu a lokacin…. K’amshin turarensa da sallamarsa ne ya saka ni yanke karatun cikin fa’duwar gaba. Na kuma kasa bu’de baki na amsa sallamar… Tsaye ya yi yana kallona bai shigo ajin ba, ga shi nik’ab d’ina a d’age yake. Na saka hannu zan ja nik’ab d’in k’asa ya furta “Ba kya amsa sallama ne Malama…” Wallahi jin muryarsa ka’dai sai da ya razanar da zuciyata. Muryata na rawa na ce “Alaykassalam…” Murmushi ya d’an saki ya isa wajen zamansa. Sai da ya zauna ya furta “Ina sauran y’an ajin? Ni fa bana son makara, don haka dole a kiyaye…” shiru na masa don bani da nutuswar da zan iya cigaba da amsa masa. “Cigaba da karatunki…” Ji na yi kamar na zunduma ihu. Ta ina zan iya karatu wallahi ba zan iya karatu daga ni sai shi a yanayin da nake ciki ba… d’ago ido ya yi ya d’an kalleni ya sake furta “Cigaba na ce….” Ji na yi kamar na zunduma ihu. Allah ya taimake ni sai ga Asma ta ranga’da sallama cak ta tsaya ganin sabon Malamin. Gaisheshi ta yi ya amsa mata yana d’an tsuke fuska. “Kin makara ki juya…” Da sauri ta ce “Wallahi Malam ba makara na yi ba, na je duty ne ka tambayi AYSHA ma ka ji…” “AYSHA?” Muka ji ya fa’da, wanda yasa na yi saurin d’aga kai don a zatona kirana ya yi, sai naga kawai ya yi murmushi ya girgiza kai ya ce “Ku bu’de Manhajjul Muslim… A ina kuke?” Asma ce ta amsa ni kuwa sam hankalina baya wajen… Tunda ya fara karatun bai ‘dago ya kallemu ba y’an aji kuma duk wacce tazo sai ya tsayar da ita ya ce ta makara… ga karatun da yake mana mai mugun saka kunya don karatu ne akan yarda ake wankan janaba da abinda yake sabbaba shi.. “Yanzu kun gane yarda ake wankan ko? Da kuma sabbabinsa?” Asma ce kawai ta ‘d’aga kai, ya juya yana d’an kallo na.. “AYSHA kin gane menene janaba, sababinta da kuma yarda ake wankanta?” Runtse idona na yi jikina har ya fara rawa musamman idanunsa duka ya zubesu a kaina. “Ba kya ji ne? D’auke wannan bak’in k’yallen ki min cikakken bayani….” “Ya ilahi na furta ina jin kamar na zunduma ihu ta ina zan fara wannan abin kunyar…. “Ke samo min ruwa a office mai sanyi, ke kuma ina jin ki?” Ina kallo Asma ta fice tana dariya k’asa-k’asa. Ji na yi kamar na ruga na gudu musamman da ya jawo kujerarsa daf da ni, ina sake shak’ar Mayen turarensa… “AYSHA” ya fa’da cikin wata irin husky voice “D’ago ki kalleni..” Da k’yar na d’ago sai dai na kasa kallon nasa. Kallona yake shi kuwa kamar ya samu Tv fuskarsa d’auke da murmushi ya furta “Answer my question before na ha’da duk makarantar nan ki musu lecture akan haka…. menene janaba? Hukuncin ta a musulunci da yarda ake wankanta?” 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ Albishirinku! Albishirinku!! Yau ne fa! Yau ne litattafan Bright pens za su fara zuwa muku da izinin Ubangiji…. 1.K’arfe a wuta. AYSHA cool marubuciyar k’anwar maza. Hadarin gabas Nazeefa Sabo Nashe. marubuciyar Me Zan Yi da ita? Mutallab daga harzik’ar marubuciya Nimcyluv Zaytoon zai zo daga Alk’alamin Malamar Adabi Zee kumurya. Za’a fara sakar muku K’arfe a wuta kafin zuwan sauran In sha Allah. Don samunsa a sauk’ak’e ku yi joining wannan link d’in… ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/FTFuiA4woYJCgNQrcBYGX4 [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Page d’in kacokam naki ne k’anwata Nimcyluv hope na goge lefina Masoyiya 🤣 Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 6 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR Ji na yi zuciyata ta cigaba da bugu, na kasa amsa masa tambayar ya bi kuma ya tsare ni da ido. Hannayena kawai nake matsawa don ban san me zan ce masa ba. “Ba ki ji ba? D’age wannan bak’in k’yallen don ban sani ba ko hararara kike..” K’iris ya rage na fashe da kuka saboda yanayin da ya saka ni, ga mayen turarensa ya bi ya hana ni sukuni… “ki d’aga na ce, Are you dumb?” Hannuna na rawa na saka na d’age nik’ab d’in. Na runtse idona saboda har ga Allah ba zan iya cigaba da kallonsa ba… ina ji ya sauke ajiyar zuciya yana furta “Kin yi passing wannan Oya tashi ki fita sallah…” Tun kafin ya kai k’arshe na mik’e da sauri ban san yarda aka yi na isa bakin k’ofa ba, ni dai na gan ni a waje. Na tsaya ina sauke numfashi hannuna dafe da k’irjina da take matsanancin bugu… Ina jin k’amshin turarensa alamar nan yake tahowa na zuba sauri har da ‘dan gudu don kada ya riskeni a wajen… Yanayin tsarin karatun nasa ya saka y’an aji aka daina makara saboda ana son karatun nasa sosai. Na san wasu y’an matan da yawa ba don Allah suke zuwa da wuri ba. Ga shi su cab’o Uban kwalliya a fuska a baza k’amshin turare ana yi ana zuba iyayi duk don Ustaz ya yaba. Shi kuwa sam baya kulasu idan zai shigo ma bak’in glass yake sakawa ya rufe idonsa… Wata rana da ta kasance ranar Talata ce. Sam kasa yarda na yi na je makarantar saboda da na duba maddar da zamu yi sai naga fik’hu ce. A rayuwata ina kunyar Ustaz shi yasa sam ba zan iya zama ya karanta Fik’hun a gaba na ba, kada a yi irin ta ranar da muka karanta Babul janabati… Don haka yau ina duba littafin naga za’a yi bayani ne akan ruwa kashi uku da yake fitowa daga gaban mace na ji sam ba zan iya zuwa ba. Sanda Asma ta biyo min ta shiga d’akina tana kallona ta furta “AYSHA me ye haka?” Nima kallon nata na yi nace “Me kika gani?” Ta saki tsaki tana kallon agogo “Yau kuma wani sabon abu zaki tsiro da shi, makara? Abinda ba halinki ba. Kin san dai Ustaz Ahmad ya jaddada rashin son makara ko?” D’an yamutsa fuska na yi “Ke makarantar ce fa ba zani ba.” Ta waro ido “Dalili?” “Bana jin da’di ko na je ba fuskantar karatun zan yi ba. Ki ba shi uziri na.” Asma ta ‘d’au jakarta tana furta “Allah ya baki lafiya, amma kamar ciwon naki bai kai inda ba za’a iya zuwa makaranta ba..” Ban mata magana ba har ta fice daga d’akin. Na saki ajiyar zuciya duk ina son zuwa makarantar ko don naga Ustaz wannan karatun da zai yi yau ne zai hana ni zuwa. Allah ya san ba zan iya zama yana zayyano min karatun nan me saka kunya ba… Kashegari da wuri na shirya musamman ganin maddar Hadith da Tajweed ne da mu. Asma ta biyu muka tafi.. Ajin har ya cika y’an mata sai baza k’amshi suke. Muka shiga muma muka bi ayari muka zauna. Ina ji wata sanda Ustaz ya shigo k’asa k’asa ta saki ajiyar zuciya “Wallahi Zahra mutumin nan ya gama sace zuciyata..” Zahran ta harareta tana furta “Ke ka’dai? Ai kowa nan da kike gani yana fatan ya taya shi…” Wani abu ne ya tsaya min a zuciyata. Na d’aga idona na kai duba na gare shi duk da idona a cikin nik’ab yake ina kallon yarda ya tsuke fuskarsa ya shigo ya ja kujera ya zauna. Fuskar a yamutse ya furta “Kada na sake ganin wata da kwalliya a fuska a ajin nan ba gidan biki za ku ba, kuna jina? Wannan wace irin tarbiyya ce zaku zo Islamiyya ku wani fece kwalliya wa kuke son burgewa?” Gaba d’aya masu kwalliyar k’asa suka yi da kansu na san kunya ce ta rufe su. Wani farin ciki ya rufe ni a raina na ce don ma baka ji k’amshin turarukan da suke ba. Na cije leb’e na ina furta “Marasa aji kawai, ni ko sonsa zai kashe ni Ai ba zan bari ya gane ba…” “AYSHA Imam Khaleel…” Ya fa’da cikin muryarsa da ta ratsa kunnuwan duk y’an ajin. Ni kuwa tunani na tafi na wuncin gadi ina ganin kamar ba sunana ya kira ba. “Ba kya ji ne AYSHA?” Ya fa’da wannan karan da alamar fushi a muryar.. da sauri na mik’e jikina har shaking yake ka’dan. “Me ya hanaki zuwa jiya? Don ban yarda da uzirin da k’awarki ta bayar ba…” Shiru na yi ina wasa da yatsuna.. “Cire abin fuskarki, kada kuma ki sake zama min da shi a aji…” Na d’age nik’ab d’in idanuwa na na son kawo ruwa. Na yi k’asa da kai na… “Bana jin da’di ne..” na furta muryarta na rawa.. kallona yake sosai kafin ya saki wani d’an banzan murmushi ya furta “Ko?” Na d’aga kai na ina kallonsa ya tsuke fuska. “Bayan an idar da sallah ki tabbata kin samu wata ta miki karatun jiya, ki zo office ki same ni zan miki tambaya akan karatun don na tabbatar kin gane bana son tafiyar kura….” Da sauri na furta “Ai na iya, bama sai ka tambayeni ba…” Kallona ya sake yi yana girgiza kai ha’de da murmushi ya furta “Jayyeed, na san kin iya k’wararriya ina son na tabbatar da iyawar ne kamar yarda na tabbatar da na abokan karatun ki…” Yarda kika san na zunduma ihu haka na ji, wani irin mutum ne wannan.. “Malam ka tambayeta mana anan…” wat daga d’aliban ta yi tsagal ta fa’da. Da alama ko haushi ta ji. Kallon Maryam ya yi idonsa cikin nata ya furta “Idan na k’i fa? Maddar Hadith d’in kike so na bari na koma fik’hu. Ko kuwa ma Am I talking to you?” Shiru ta yi tana k’ikkifta ido… da alama ta ji haushin disgin da ya yi mata. “As I told you earlier, ki tabbata kin zo after asr, kuma ina son ki gudu kin ji…” ya fa’da yana d’aukar littafinsa… Tsit ajin ya yi, ni kuma na zauna ina sauke numfashi. Na sake mayar da nik’ab d’ina. K’afata kuma a d’an mik’e a wajen. Ni da kaina na san ina da kyan k’afa sosai, amma ban damu da rufeta kamar fuskata ba. Yana d’agowa ya kalleni. “How many times zan gaya miki ki cire k’yallen nan a fuskarki.. kin san bonono?” Na yi saurin girgiza kai “To shi kike yi, rufin k’ofa da b’arawo ba. Wannan da kike bari a waje ita yafi kamata ki rufe, don ana ake gane a wani aji mace take.” Ya fa’da yana nuna k’afata. “Duk namijin da ya san abinda yake idan zai so mace k’afarta yake fara dubawa saboda akwai wani karatu na musamman akan k’afar…” Da sauri na ja k’afata na cukuikuye tun kafin na ji ma menene karatun. Murmushi ya yi ya girgiza kai ya kalli y’an ajin “Kuna son ku sani?” Da wani irin ihu da farin ciki suka furta Eeh Malam. Ji na yi kamar na tashi na rufe su da duka. “Ta hanyar k’afa ake gane Mace Khareeja ce ko Mutawassi’da ko Dakhilatun… kun san ma’anarsu?” Cikin karsashi suka furta “A’a” musamman manyan ajin da suna son irin wannan karatun. Na san sun sani don suna ta k’us k’us da murya suna dariya. “Mace Kharija itace mai yawan sha’awa….” Runtse idona na yi ina sake jan nik’ab d’ina. “Baki ji warning d’ina ba kenan?” Hawaye ne kawai na ji suna cika min ido ganin yarda ya tsira min ido cikin wani irin narkakken kallo da na kasa fassara shi. “A k’afafunku yanzu kowacce zan iya gaya mata ajin da take..” Ya fa’da yana d’an ha’de ransa… Da sauri kuwa suka dinga tura k’afafunsu ni da Asma da wasu biyu ne kawai ba mu tura ba. Ya dinga kallonsu yana tab’e baki ya furta “Kunya itace cikar mutuncin y’a mace ku dinga koyi da d’abi’ar y’an uwanku…” Ya fa’da yana nuna mu. Sannan ya sha kunu ya cigaba da karatun sa na Hadith. A k’aida idan aka fita sallah, sai duk y’an aji sun fita sannan Malam zai fita. Haka kowa ya mik’e amma ni na kasa mik’ewa sai mutsu-mutsu nake a Hijba bana son tashi ne don kada Ustaz yaga k’afata. Ina kallon yarda yake dariya k’asa k’asa. “AYSHA tashi ki fita sallah.. ko kina Off?” Waro ido na yi na yi saurin sakin Nik’ab d’ina, ina martaba rashin kunyar ustaz a cikin zuciyata. “Jira fa nake ki tashi ki fita..” Asma da ta ga ban fita ba ita ta sake dawowa tana kallona. “AYSHA taso mana.” Na yafito ta da hannu. Ra’da na mata. “Pls ki samo min safa ko a k’afar waye don Allah..” Asma ta k’unshe dariyar da take son yi ta fita tana kallon ustaz. “Me kike ce mata? Ko kina needing wani abu ne?” Na yi saurin girgiza kai. Zama ya yi yana danna wayarsa har sanda Asma ta dawo ta mik’a min sucks d’in. Na yi saurin amsa na dinga zira wa ta cikin Hijab d’ina. Ina kallon yarda Ustaz yake min wani kallo… Sai kuma girgiza kai ya fita..” Na sauke ajiyar zuciya. Asma ta zauna kusa da ni tana furta “Kamar Ustaz fa ya fa’da son ki..” Ban amsa mata ba saboda kiran sallah na ik’ama da aka yi. Muka fita da sauri. Ana idar da sallah ina zaune a harabar makarantar muna Jiran yara su gama shigewa. Wata yarinya tazo tana kallona. “Anty Aysha, Ustaz Ahmad yana kira…” waro ido na yi ina kallon Asma da take ta dariya na harareta na ce “Don Allah ki raka ni?” “Wa? Ni? Ai idan kika gan ni a lahira kai ni aka yi. Me ya aikeki fashin makaranta jiya? Ga shi nan abinda kika gujewa shi kika tarar yau har Gwara ma jiya a cikin mutane ne, yau fa daga ke sai shi…” Ban manta magana ba saboda haushi da ta bani. Na tashi cikin sanyin jiki da na zuciya na bi step d’in da zai kai ka Office d’in Ustaz Ahmad. Duk da ban Tab’a shiga ba na san nan ne, don ina jin yarda y’an mata ke wassafa kyau da tsaruwar office d’in. Sai da ya saka aka kashe masa ku’di sosai kafin ya fara zama cikinsa. Knocking na yi sosai kafin daga can a ce “Shigo kafin ki saka min ciwon kai.” Zuciyata na bugu na mur’da handle d’in k’ofar na shiga. Shiru office d’in sai wani irin azababben sanyi da k’amshin turarensa da ya zauna ra’dam a office d’i. K’ofar na bari a bu’de, sai dai tun kafin na kai ga zama ya furta “Ita k’ofar zata rufe kanta kenan?” Tsaye na yi ina wasa da yatsuna don kam ba zan wani kulle k’ofa ba, a haka ma ji nake kamar zuciyata zata fito don tsabar tsoro. Bai kulani ba ya mik’e ya isa k’ofar ya rufe ya dawo ya zauna. Yana d’aukar cup d’in Hot coffee d’insa idanunsa akai na dana kasa zama sai rawa k’afata take. Tsawon mintuna biyu yana shan tea d’insa ya lumshe ido ni kuma ina tsaye… “Na gama ganin surarki idan ita kike son ki nuna min sai ki zauna Ai…” Ban san sanda na zauna ba.. Ina haki kamar wacce ta yi gudu tsabar firgicin da maganarsa ta saka ni. A yanayin fuskarsa naga yarda yake ha’diye dariyar da yake son yi. “Mun yi karatu jiya, akan ruwa uku da suke zubowa daga gaban mace, sababinsu da hukuncinsu Islamically.. su nake son yanzu ki jero min ki kuma gaya min me Ke sabbabasu da hukuncinsu a musulunce tunda kin ce kin sani…” “Cabd’i…” na furta a hankali ina jin wani irin bugu da zuciyata take yi… wayarsa ya ‘d’auka ya danna yana furta “Ina jin ki, ina son in san da gaske kin iya orally kafin lokacin da zan sani a aikace…..” 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢✍️ https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR Group 1 ya cika. Ga wanda bai samu damar shiga ba ya danna link d’in nan ya shiga group 2 daga gobe In sha Allah a iya groups d’in zan dinga posting. Kada a dinga bina private ana na bayar daga farko. Allah ya sani bani da jumurin hakan… [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 7. Duum haka na ji maganar Ustaz ta min saukar bazata a kunnena. Na sunkuyar da kaina ina mamakin yarda shi Sam ba ya Jin kunyar fa’dar duk abinda ke bakinsa. “Ina Jin ki…” Ya fa’da yana sake sanya idanunsa cikin nawa. Muryata na rawa na furta “I can’t..” kafin na yi aune hawaye ya fara zubowa a fuskata don har ga Allah ya fara takura min. Shi bai san duk sanda ya rutsa ni ba, Wani irin yanayi nake shiga mai wuyar kwatance… “Kuka ki ke? Daga tambaya?” Ya furta muryarsa a k’asa sosai. Na sake runtse idona na k’ara k’arfin kukan nawa. “Ki min shiru.. tunda ba amsa just wipe your tears..” ya fa’da yana mik’a min handky d’insa. Amsa na yi na shiga goge idon nawa amma hawayen still basu tsaya ba. “Ki tsayar da hawayen nan yanzun nan bana son shagwab’a. Me aka miki daga cewa ki yi karatu..” Ya furta a hankali cikin wani husky voice da zan iya cewa yana sane yake min magana da ita.. “Zan gaya miki Laa Haya’u fiddeeni, idan baki tsaya kin koya ba ta ina zaki iya? Ko ni ne ba kya son na koya miki?” Da sauri na d’aga kai, murmushi ya saki mai kyan gaske.. yana furta “Why?” Yana shigar da idonsa cikin nawa “Gaya min dalili sai na k’yaleki..” Shiru na masa idona a k’asa ina cigaba da wasa da handky d’in hannunsa.. ina ji ya saki ajiyar zuciya bayan ya gama k’are min kallo tas, don a jikina na ji ni yake kallo… “Dole zai fito muku a exam don haka dole ki saurareni na miki gamsashshen bayani. Kuma bana son ki rufe min ido. Ki tsaya ki kalleni kamar yarda kowace d’aliba take sauraran malaminta idan yana mata karatu. Tunda ni ba saurayinki ba ne, balle ki ce kina jin kunyata…..AYSHA..” Na d’ago da niyyar kallon nasa sai dai sam idanuna sun kasa ba ni dama. “Kalleni ki saurareni..” Na girgiza kai “Don Allah Ustaz ka yi hak’uri zan je Asma ta koya min, inda ban gane ba..” ta gefen ido naga ya tab’e baki. “Ban yarda ba Aysha, na Riga na d’au alk’awari zan karantar da ku don haka dolena ne na yi miki yarda na yiwa kowa..” “To ka ha’da ni da wani Malamin.” Na furta muryata na rawa. “Saboda ni surikin ki ne? Ko saurayin ki?. Ruwa uku ne yake fitowa daga al’aura akwai Maniyyi, akwai wadiyyi akwai maziyyi kina ji na? Maniyyi shine ruwan da yake fitowa mutum yayin babbar sha’awa, saduwar aure wato jima’i….” Ban san sanda na kai kaina bakin k’ofa ba, na fice da sauri don na lura Ustaz so yake kawai ya kashe ni da salonsa. Saboda wani irin abu da na dinga ji a jikina. Ina ji yana k’wala min kira amma na k’i komawa na shige wani lungu ina mayar da haki. Ina goge hawayena da handky d’insa da ya cika da k’amshin turarensa sai sannan ma na lura da handkerchief d’in. Na cusa shi cikin aljihun hijab d’ina ina mayar da haki. In dai zan shiga aji a haka dole ne ma a fuskanci bana cikin nutsuwa don haka kawai na fice daga makarantar don ba zan iya sake ha’da ido da Ustaz ba, a dai ranar yau… Ina zuwa gida d’aki kawai na shige ba tare da na bari su Mami da suke kitchen su ganni ba. Na shige toilet saboda wani irin fitsari da na ji ya matseni. Ban yi mamakin ganin discharge mai yawan gaske a undies d’ina ba. Kwanciya na yi saman gadon ina sakin haki tare da shak’ar k’amshin Ustaz da yake jikin Handky d’in. Murmushi nake saki ni ka’dai ina tuna drammerr da muka sha da Ustaz d’in. Gwara ya dokeni akan na zauna yana min wannan karatun nasa… na raya a zuciyata. A kwancen nake har 6:30. Daidai lokacin da na ji shigowar Mami da Asma. Tana fa’din “Wani irin ta taho gida, ni ban ganta ba amma bari na duba d’akinta.” Turus ta yi tana kallona “Ke lafiyarki kika taho daga Islamiyya tun kafin a tashi.” Lumshe idona da ya yi nauyi na yi na furta “‘Mami bana jin da’di ne.” Ta saki ranta tana kallon Asma da take tsaye da Jakata a hannu. “Shine zaki shigo d’aki ki kwanta? Anan wa ya san baki da lafiya?” Ta yi tsaki tana ficewa daga d’akin “Dama ki taso ki sha magani yanzunnan, don na san rashin son magani ne yasa kika k’ulle kanki a d’aki.” Asma Mami na fita ta tuntsire da dariya “Daga zuwa wajen Ustaz kuma sai ki gudo gida.. ko ya fasa miki sirrin zuciyarsa ne?” Na wurga mata harara “Mhmn” ta furta tana zama gefen gadon “Ni sai na ji ma d’akin kamar k’amshin ustaz d’in yake..” Da sauri na danne handky d’insa da k’afata ina furta “A’a Ustaz d’in ne na b’oye ba k’amshinsa ba, y’ar rainin hankali kawai…” “Zaki ga y’ar rainin hankali, Dama ya ce na gaya miki gobe kada yaga k’afarki cikin ajinsa..” “Ta fi Nono fari wallahi, Sai na canja aji..” Asma ta tsira min ido tana furta “Ke ce zaki iya barin Ibn kaseer? Ki dai ba shi hak’uri kawai ki koma. Wai me ya miki?” Zama na yi na bata labari ta dinga tuntsira dariya tana kifawa ta furta “Wallahi Aysha mutumin nan sonki yake, shi kuma tasa salon soyayyar kenan, kan bala’i Amma fa ya burgeni…” kallo na watsa mata ina nuna mata k’ofa. “Maza ki ta surutu Mami ta ji ta tsireni, ni ba wani so na da yake.. kawai dai ya lura ina jin kunyarsa ne..” “Kema aI sonsa kike tunda kina jin kunyar ya miki irin wannan karatun…” Ta furta tana dariya duka na kai mata ina jan hannunta na furta “Fice min daga d’aki Malama..” Ta fita tana furta “Ko baki ce ba, amma wallahi kun dace wai! Ai kuwa zuciyar y’an matan ajin nan zata buga don yau ma baki ji zagin da kika sha ba, da kika bi shi office..” Na tab’e bakina ina furta “Y’an wahala, su suka ga zasu iya. Don Allah Asma tafi gida kawai..” ta fita tana murmushi.. Na zauna ina nawa murmushin nima. Ina ma ya furta yana so na da nafi kowace mace sa’a… Kashegari ma k’in zuwa makarantar na yi na fake da bani da lafiya don sam ban ji zan iya zuwa na kalleshi ba. Tsawon kwana uku ina k’aryar ciwo kullum Asma ta dawo sai ta biyo gida ta koya min abinda aka yi. Ranar laraba ta shigo d’akina tana murmushi ta ce “Aysha yau fa Ustaz ya kasa dauriya, sai da ya tambayeni ina kike bayan ya kira ni office d’insa. Na ce masa baki da lafiya baki ga murmushin da ya saki ba na irin na raina masa hankali ya furta “Ki gaya mata ranar asabar ta dawo makaranta…” Murmushi kawai na saki na ce “Allah ya kai mu. Asma ta fita tana furta “Ke mutumin nan da gaske ya faller kawai furtawa ne bai yi ba..” samun kai na na yi da sakin murmushin nima ina furta “Allah yasa. Kashegari ya kasance ranar alhamis ce, na tashi da wuri na yi shirin makaranta don Exams zamu fara third term SS 2. A gaggauce na sauko daga sama ganin lokaci ya ja. Na isa kitchen wajen Umma da Mami da na tabbatar suna kitchen d’in. Saboda koda yaushe tare suke girkin su. Wani kallo Mami ta zuba min mai cike da zargi da tuhuma, na lura kwana biyu irin kallon da take min kenan. Na yi k’asa da kai na ina sake gaishesu. Na mik’e ina cewa sai na dawo bayan sun amsa gaisuwar. “Abincin fa?” Mami ta fa’da tana tsare da kallo. Na d’an girgiza kai ina turo baki na ce “Mami, yau bana son yin breakfast fast…” “Wasa kenan, wuce Malama ki ha’da tea ki sha ga chips nan ki cinye tas kafin ki wuce… ina lura da ke kwana biyu ba wani abincin kirki kike ci ba, jiki kamar sillen kara… Uban me ke damunki?” Da sauri na furta “Allah bakomai Mami..” K’wafa ta yi, ta cigaba da aikinta kafin ta furta “Ina fatan Bakoman ta zama bakomai d’in…” Umma da take jin mu dariya ta yi tana furta “Ke ma dai Fateema, kamar AYSHA ce sai an tsaya cewa ta ci abinci sai ka ce yarinya, idan kika ga bata ci ba ta k’oshi ne…” Mami a tunzire ta furta “To Ayshan nawa take? Shekara sha bakwai Ai har yanzu yarinya ce, ko yanzu ta kama d’aukarta zan yi na cafeta na goyata da zani. Gaskiya a daina jawo mata girma balle ido ya dawo kanta…” Umma d’auke kanta ta yi tana furta “Allah ya taimaka, aure dai idan lokacinsa ya yi ko an jawo girma ko baa jawo ba yinsa za’a yi…” Mami wani kallo ta yiwa Umma sai kuma ta furta “Allah Umma kada ki fa’di maganar nan wajen Abbansu ya ji, don wallahi ko sama da k’asa zata ha’de a shekaru dai irin na Aysha ba zan bari a mata aure ba, sai na ‘dauketa mu bar garin ina dalili?” Ni dai ina daga gefe dariya tana son kama ni, koda yaushe drammerr Umma da Mami na kenan. Na gama kurb’ar tea d’in a gaggauce na fice ina amsa addu’ar da suke min da ameen.. Ina zaune a ajin mu na makarantar boko intercontinental nake zuwa. Aka turo kira na daga office d’in principal. Ban wani damu ba sanin cewa ina da mik’amin da zaa iya nemane koda yaushe. A hankali na saka hannu ina knocking d’in k’ofar. Daga ciki principal ya amsa da “Yes come In.” na saka kai na direct cikin office d’in. Daidai lokacin da idanuwana suka sauka cikin na ustaz hancina ya shak’i k’amshinsa. Ji na yi k’afafuna kamar ba a jikina suke. A raina na ce “Nan ma ka biyo ni ne?” “Da principal zai lura lokacin zai ga yarda k’irjina yake bugun gaske idanuna suka tara k’walla. Na shiga office d’in a nutse da sallama. “Good morning sir!” Na furta muryata a nutse. Ina satar kallon Ustaz da ya yi kamar bai ganni ba. “Morning AYSHA Imam. Baki ga bak’o ba?” Na juya ina satar kallonsa murya a k’asa na furta “Good morning.” Ya d’ago daga kallon wayar da yake fuskarsa a ‘dan tsuke ya furta “Morning…” Daga haka bai sake magana ba ya mayar da kansa kan abinda yake na daddanna waya. Principal ya mik’e min wasu files “Maza ki kaiwa Emeka, ki ce masa ya yi signing before a fita break..” Na amshi files d’in ina d’an durk’usawa. Na fita raina a b’ace. Zuciyata cike da mamakin kallon da Ustaz ya min kamar bai sanni ba. Sai na ji sam ban ji da’di ba. Haka dole na koma Islamiyya ba don raina na so ba, sai don zuciyata ta kasa dauriyar rashin ganin ustaz. Ranar ma ko kallo ban ishesa ba, ya yi karatunsa ya fita fuskarsa a d’an tsuke. Ina komawa gida na tarar da abinda ya kusa fasa min zuciya. Tun daga bakin gate nake jiyo hayaniya a cikin gidan mu. Muryar Mami a sama take sake furta “Wannan ma ai zance ne, kuma ba mai yiwuwa ba, Ayshan nawa take da za’a d’auko maganar aurenta yanzu, to wallahi in dai ina numfashi ba mai aurar da ita a wannan lokacin..komai zai faru sai dai ya faru…. Gabana ne ya yi wani irin mugun fa’duwa na waro ido a hankali na furta “Aure kuma? Ni Ayshan za’a yiwa aure yanzu?” Murya a sanyaye na yi sallama, gaba d’aya suka zubo min ido, kamar sun samu Tv. Take na gasgata abinda zuciyata ta gaya min. Aurar da ni za’a yi. Gefe na ja na zauna idanuna tuni suka fara bulbular da hawaye ina kallon Mami na na ce “Mami aure za’a min?” Mami da itama nata idanun suka yi jajir suna son zubo da hawayen, ta furta “Kul Aysha! Kada ki sake ki zubar min da hawaye anan, wannan maganar ki ‘dauketa tatsuniya wallahi in dai sunana Fateemah y’ar halak kuma cikin iyayena sai na cika burina a kan ki… babu wanda ya isa ya aurar da ke a wannan k’ananan shekarun sai kace a karkara. Ko su karkarar yanzu an daina irin wannan auren. Wuce ciki ki zauna…” Na kasa wucewa cikin zuciyata sai kakkarwa take, ni na san halin Abba yana da kafiya da naci akan abinda ya saka gaba, ba wanda ya isa ya canja masa ra’ayi, baya ma tank’waruwa ko ka’dan, irin mutanannan ne da ake cewa taurin kai kamar mutanen farko. Don haka ban san sanda na kece da wani irin kuka ba musamman da na tuna shikkenan son da nake wa Ustaz ya zama tarihi kenan, ba zan aureshi ba? Mami hankalinta ya sake tashi, ta ja hannu da k’arfi muka hau sama cikin b’acin rai da k’unar zuciya take furta “Ba zai yiwu ba, ki gaya masa ma tun farko kada ya yi abinda zamu zo muna samun sab’ani da shi. “An da’de baa samu sab’anin ba, aure ne dai ba fashi sai dai ki yi duk abinda za ki yi. Haka kawai ba zan ga samu naga rashi ba. Nagartaccen mutum irin wannan ya zo neman auren y’ata ko a primary take tsigeta zan yi na ba shi…” muka ji muryar Abba a sama yana fa’da yana tsaye a k’ofar shigowa… Mami ta juya a fusace tana furta “Kada mu yi haka da kai Abban Aysha…. Tsaki ya ja kawai ya shige parlor jin ana kiran sallah. Bayan Sallahr Isha, a al’ada irin ta gidanmu bazuwa ake, a tsakargida kan tabarma a ci abinci. Yau d’in ma haka ce ta kasance sai dai ni ina daga wani d’an lungu a zaune kamar yarda Mami ta umarce ni. Abba ya juya yaga kowa bai ganni ba. Ya kalli Mami ya ce “Ina Aysha?” “Ina zaka ga Aysha anan? Alhali ka birkita mata kwanya tun d’azu take kuka..” “Ta shirya fara na jini, don aure ba fashi, ki kuma sanar da ita k’arfe takwas bak’onta zai zo. Don Allah ki sata ta wulak’anta martabar gidan nan kiga abinda zan Aikata.. Babban mutum ne da ba zai juri rashin kunya ba…” Daga haka bai saurari surutun Mami ba ya wanke hannunsa ya saka a cikin tuwo ya fara ci… Ina tsaye ina jin k’afata na rawa. Babban mutum nake ta nanatawa a zuciyata it means mai iyali dattijo. Na runtse idona ina jin wani zafi a k’asan zuciyata. Ina jin yaro ya yi sallama aka amsa masa ya ce “Wai akwai bak’o a waje…” Na ji zuciyata ta wani irin hantsilawa har sai da na dafe k’irjina. Muryar Abba na ji yana cewa “Kai ALIYU jeka ka shiga da shi sitroom, kai kuma Usman jeka ka kira min Aysha… Ji na yi kai na ya wani irin sarawa. Usman da ya nufo inda nake ya tsaya yana kallo na. “Au da kina tsaye kina ji?” Hawayen idona na d’auke na d’aga masa kai na. “Ki je in ji Abba kina da bak’o… Saura ki je masa da wannan banzan hawayen shashasha tun baki san wa ne me neman aurenki ba kin sakawa kan ki damuwa…” Ban bi ta kansa ba na nufi inda Abba yake. Mami kuka take tana sake rok’onsa ya janye maganar sa. Kallona Abba ya yi ya ce “Ki je ki shirya ki je sitroom kina da bak’o saura ki je ki nuna masa rashin tarbiyya…” Na juya jikina a sanyaye madadin na je na canja kayan Wucewa na yi wajen haka idona a damalmale da hawaye na tura k’ofar, muryata cike da k’unci na masa sallama.. k’amshin turaren Ustaz na ji ya baibaye hancina zuciyata na bugu nake son d’agowa naga ko shine ban dawo daga tunanin da nake ba, na ji ya ce “Aysha Imam ya gida?” Ko daga barci na tashi na san muryar Ustaz na yi saurin d’ago kaina idona ya sark’e cikin nasa, yana zaune yana matse yatsunsa cikin na juna fuskarsa d’auke da murmushi….. Cikin mamaki na furta “Ustaz!” Ya d’aga gira yana murmur ya furta “Ayshatu…. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ ‎ Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 8 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR Kasak’e na yi ina kallonsa, shi kuma sai sakin murmushi yake ya firta “Kin yi mamakin gani na ko? Koda yake na san ba lallai ki yi mamakin ba don tini zuciyarki ta sanar da ke zan zo d’in ko ina so ko bana so, haka ne?” kallonsa kawai nake kafin na Ankara da abin kunyar da na so aikatawa na runtse idona ina jin yarda zuciyata ke harbawa da k’arfin gaske. Bana son na bu’de idona balle na tarar da Mafarkin da na saba ne.. “Ki yi hak’uri nazo gidanku ba tare da saninki ba, ban kuma nemi amincewarki ba ko? Na yi hakane saboda koyi da sunnar manzon Allah s.a.w, na fara Neman izinin iyayen yarinya kafin ita yarinyar. Na san tuni ki fuskanci manufata ba ke ba ma wasu da dama a ajinku sun san inda zuciyata da ruhina suka karkata, kema kuma a idonki na gano zallar son Ustaz da k’aunarsa…” Da sauri na waro idona ina kallonsa. Ya ‘daga min girarsa guda da ta bada wani shape mai kyan gaske. Yana lumshe idon. “Don't pretend Aysha na san kina so na, albushir guda da zan miki ina miki so ninkin miliyoyin naki…” wani sanyi na ji yana ratsa zuciyata ban san sanda na saki wata siririyar ajiyar zuciya ba. “Ba ki ce komai ba?” Na sunkuyar da kai na wani murmushi da ban shirya zuwa masa ba yana kufce min. Cikin siririyar murya na furta “Me Zan ce Ustaz…” “Ki ce I love you too…” Da sauri na saka tafin hannu na rufe fuskarta, ina ji Ustaz ya saki ajiyar zuciya ya furta “Yawaitar kunyata a idanunki ya tabbatar min da zazzafar soyayyata a ranki. Amma naga kafin ki fito kamar kin yi kuka ko dai baki so fitowar ba ne?” “Ai ban san kai ba ne…” Na yi saurin toshe bakina jin abinda bakin ya furta. Murmushi Ustaz ya saki ya furta “Ni na sani ai, da kin san ni ne kwalliya mai kyau zaki cab’a min ki fito kina iyayi irin yarda budurwa take wa Habibinta ko?” “Kai Ustaz!” Na furta ina d’an satar kallonsa “Kai ko gaskiya, next zuwan da zan yi dama ki tabbatar kin fito min a y’an matanki caras a bu’de min kuma jiki tunda ya halatta ko sau d’aya ne kaga matar da zaka aura ki saka min kaya mai kyau.. Kin ji ni ina ta surutu ban tabbatar ma ana so na ko a’a ba…. AYSHA d’ago ki kalleni…” na d’ago a hankali ba don zan iya kallon nasa ba, sai don bana son na masa gaddama. “Kina so na za ki aure ni?” K’asa na yi da kai na in furta “Kana da mata?” Wata irin dariya ya yi da har sai da ya bayyana wasu points a gefen hancinsa. Ya furta “Kishi kumallon mata, kada dai ace AYSHA na da kishi?” Girgiza kai na yi “Ni ba ni da kishi, ni dai kawai ba zan auri mai mata ba..” Dariya ya yi sosai ya furta “Mhmn, ba amsa kenan, don wannan amsar bata cika gamsashshiya ba.” In a serious tone ya furta “I have a wife AYSHA da yara biyar…” wani irin waro ido na yi, k’walla na taruwa a k’asan idon nawa. Na girgiza kai. Ustaz kuwa idanunsa ya kafa min yana sakin murmushi k’asa k’asa. “Gaskiya na gaya miki, ki je ki yi shawara zan dawo jibi idan kin amince sai ki gaya min. Ko ta cikin waya ne.” Ya fa’da yana ajiye min wani kwali a cikin leda “Idan kin kunna akwai layi a ciki, na yi setting komai, ban amince da Instagram da duk wasu tarkacen Social media ba sai whatsapp kawai. I repeat Whatsapp only AYSHA…. Anjima zan kira na san a waya dai may be zaki amsa min sosai ba za’a dinga min maganar bebaye ba, mai rowar murya kawai…” Murmushi kawai na saki ha’de da fa’din “Na gode.” Cikin sanyin murya don kam Ustaz ya sanyayar da ita, tunda ya gaya min yana da mata. “Numberta kawai, Sai Siblings d’inki da parents ban da su bana son ganin any number.” Na ce “Toh!” Ya ‘dan kalli table ya tab’e baki “Budurwar k’auye ba ruwa ba lemo haka ake saukar saurayi ko?” Da sauri na girgiza kai ina y’ar dariya ka’dan. Na lura Ustaz sam bai da bak’unta. Komansa free yake. “Ki gaida kowa na cikin gida sai na dawo.” Ya fa’da yana ficewa daga d’akin. Sakin ajiyar zuciya na yi, ina lumshe ido. A wata duniya na dinga ji na, mai girman gaske. Da na san Ustaz ne yazo wajena ba ta yarda za’a yi na zubar da hawaye na a banza, tunda Burina ne dama burina zuwan wannan ranar. Abu guda ke fa’dar min da gaba Mami na! Ban san yarda zata fuskanci lamarin ba. Ni kam ina son Ustaz kuma na shirya Aurensa koda Ba Abba ne ya ce ba, balle shi ya ce. Na ‘d’au kwalin wayar, ba kowa a tsakargida shiru gidan, dama Mami ce mai son hirar tsakargida da alama tunda bata da sukuni a zuciyar ta sai kowa ma ya kama kansa. Umma dai itace da girki na san tana wajen Abba. Step na fara hawa ina jin tsoro na yana sake yawaita. A hankali na tura k’ofar parlorn Mami, Kamar yarda na zata tana zaune tana kallon tashar Arewa24. Ta amsa sallamar ba tare da ta kalleni ba. Jikina a sanyaye na zauna a gefenta ina nazarin fuskarta na ji ta furta “Yaya kika ganshi? Wani dattijo ko? Mai gemu buya-buya tunda na ji ance Ustaz ne, yanzu haka ma k’azami ne..” Kallon Mami ina mamakin kalamanta, tabbas bata san Ustaz ba, da bata yi wani furucin ba, ba mamaki da zata gan shi taga kamanninsa itama ta so ya zama surikinta.. ina cikin ko a cikin maza millions za’a tsame Ustazu na a matsayin wanda yafi kowa kyau da tsafta.. Mami ta zaci in dai ance mutum Ustaz ne sai ya zama wani mara fasali. Ai yanzu Ustazai akwai d’aukan wanka da kwalliya sosai ma. Ban san me yasa ba sai na ji wasu siraran hawaye suna zubo min, wanda na san ba hawayen komai ba ne sai na zallar farin cikin cikar burina, tunda na ji sanyinsu har k’asan raina da cikin jikina.. A zaton Mami kukan bak’in ciki nake. Ta mik’e tsam daga kujerar ta ta dawo inda nake ha’de da dafa ni, ta furta. “Daina zubar da hawayenki a banza Aysha, in dai ina numfashi babu mai miki wannan auren tozarcin ko me ma zai faru ya faru… wani irin tsalle zuciyata ta buga, na ‘dago da sauri ina kallonta na furta “Mami, kada ki ce haka, Mu yi hak’uri kawai mu yarda da k’addara, Saboda ba mu san abinda Allah ya b’oye ba….” “Rufe min baki Aysha…” Ta furta cikin wani irin zafin rai, da har huci take fesar wa. “Kada kice min zuciyarki har ta amince da wannan mutumin? Wato har kin ji a zuciyarki zaki iya aurensa? So kike ki ba’da min k’asa a ido? Duk da yak’i da hak’ilon da nake na nema miki y’anci a wajen iyayenki da ba su san mutuncin ki ba? To bu’de kunnenki ki ji da kyau, ko son sa zai kasheki ba zaki auresa ba…” Ta fa’da tana fancakalar da hannu na ta mik’e a zuciye ta shige d’aki. Shiru na yi zuciyata na harbawa na zubawa hanyar da ta bi ido. Ina mamakin duk furucinta. “Anya Mami tana cikin hankalinta kuwa?” Ras take” zuciyata ta bani amsa tsabar son boko ne da ak’idar bokon yaja mata haka. Na d’an tab’e baki ba ina tunanin tabbas za’a samu matsala, don yarda nake son Ustaz bana jin wani hargitsin Mami zai saka na rabu da shi. Na shige d’akina. Ina bu’de ledar da ya ajiye min. Waya ce mai kyau IPhone 13 sai turaruka masu kyau guda biyu. Na shinshina turaren d’aya irin turarensa ne sak, a jikinsa ya rubuta “For Night only…” Murmushi na saki, ina tunanin sabida me zai ce sai dare kawai zan saka.. Na san Abba ya kwanta, don haka sai da safe zan kai masa wayar ya gani, idan ya amince sai na cigaba da rik’ewa idan kuma bai amince ba sai na mayar wa Ustaz. Wanka na yi na saka sleeping dress sannan na fesa turaren da Ustaz ya sanar da ni sai dare kawai zan dinga sakawa. Sai da na kwanta sannan na gane dalilinsa na cewa For Night d’in. Don k’amshin sosai ya dinga tuno min da Ustazun. Na dinga sakin murmushi ni ka’dai. Kafin na ji wayar na vibrating. Idona na kai kan screen d’in wayar sai ga hoton Ustaz a ciki yana sakin murmushi an rubuta “Farhatul K’alb..” (Farin cikin zuciya) ina sallama ya saki ajiyar zuciya kafin ya amsa ya furta “murya mai da’di…” shiru na yi “Ba gaisuwa AYSHA? Me ya hanaki bacci k’arfe d’ayan dare?” Da zan iya cewa zan yi Tunaninka. Sai dai na ji na kasa na furta “Bakomai…” “Gaskiya ban yarda ba.. ni na san me ya hanaki barci..” “To menene?” Na fa’da cikin sanyin murya. “Cewa zaki yi To menene Habibeey?” Ya fa’da yana koyan muryar y’an mata dariya ya bani sosai na dinga yi kuwa ba k’akkautawa “Tunanin D’an Ugly saurayinki ko?” Na ware ido.. “Ba zaki amsa ba. Zaki iya vedio call please.” Da sauri na girgiza kai ina cije leb’ena na furta “A’a” “Me yasa?” Duban jikina na yi na ce “Ni dai bana so…” “Mhmn..” Ya ce cikin wata irin murya “Allah ya baki hak’uri, amma ki saka Hijab mana mu yi, wallahi son ganin ki kawai nake ko zan iya barci, kin bi kin rufe idona ke kawai nake gani.” “Shikkenan ma, kaga ba sai ka ganni ba kenan…” Dariya ya saki ya ce “Aysha!” Sunan da na ji ya tsarga har k’aramin yatsan k’afata “Kin san sunana?” “Uhm” na ce masa. “Okay fa’da na ji please, ni dage sai fa’dar naki nake kamar ni na ra’da miki. Ya sunana?” “Ustaz!” Na fa’da cikin muryar da ni kaina ban san na iya ta ba. Shiru ya yi tsawon seconds Hamsin har na zata ko ya kashe ne. Na furta “Hello..” ya saki ajiyar zuciya yana firta “Ina jin ki Aysha… kin tafi da numfashi na ne, Allah ya baki wata irin murya da zan yi kishin wasu mazan su gaba da jinta in dai za su yi feeling abinda nake ji yanzu… Ba zan iya ba, ki tashi ki yi sallah yanzu ki rok’a mana dukkan alheran da suke cikin neman auren nan kin ji?” “Toh” na amsa “Kina sallahr ai ko? Ko ba kya sallar dare?” “Ina yi.” To maza ki yi sallahrki zan kira da safe na ji feedback akan maganarmu.” Ya fa’da yana kashe wayar bayan ya furta “I love you…” cikin k’asa da murya. Sai da na ware ido ina tunanin Anya kuwa Ustaz ne.. ashe Ustazan nan suma ba baya ba wajen bawa soyayya hakkinta? In dai kuwa haka ne tabbas na dace.. Sallahr na yi na dinga rok’on Allah musamman akan Mami da niyyar Allah ya karkato mata da zuciyarta ta amince ta kuma so auren nan. Da sassafe na tashi, cikin matuk’ar karsashi da wani farin ciki da ya kasa b’oyuwa a fuskata. Idona kawai zaka kalla ka karanta abinda yake k’asan raina na zallar farin ciki. Kasancewar lahadi ce na fita Parlorn Abba inda anan ake zama duk ranar lahadi a karya. Tun daga tsakargida masu aiki suke bina da kallo har na isa parlorn. Su ma su Abba da mamaki suke kallo na ganin yanayin sauyin fuska a tare da ni ba kamar jiya ba da na tashi fuskar kamar hadarin kaji. Mamaki ya ishi Abba ya kasa shiru har sai da ya furta “Ayshan Mameeyn ta, ta samu ne naga kina wani farin ciki.” Sunne kaina na yi ina dariya da girgiza kai. Na mik’a masa kwalin wayar hannuna don na b’oye turarukan. Wayar ya bi da kallo yana furta “Wannan fa Aysha?” Cikin k’asa da murya ina kallon Mami da take min wani kallo na furta “Mutumin jiya ne ya ba ni.” Abba ya ‘dan ware ido yana furta “Ma sha Allah, labarin zuciya a tambayi fuska. Fateemah ya naga haka kuma? D’iyar take da alama ta yi na’am da zanka’de’den mijinta, ke tun baki tsaya kin ji waye ba kike kumfar bakin ba kwa son sa. Ustaz Ahmad Sulaiman Sa’eed babban Malamin nan, yaro da kwanyar manya shine fa yake son ta…” Cikin wani yanayi Mami ta ‘dago idonta tana furta “Ustaz!” Da mamaki a idonta, ta furzar da wani huci tana furta “Shine ma abinda ba zai yi wu ba cab’di! Kama sake nazari….” 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 9 ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LSB89Dp71pHETB3hpaWohR “Kamar ya?” Abba ya furta yana saka k’wayar idonsa cikin ta Mami. Amma sam yau Mamin wannan kallon na Abba na da alama bai ratsa ta ba, don tab’e bakinta ta yi murya a sama ta furta “Kamar komai ma Abban Aysha.. Ta yaya za’a aura mat Uztaz hakan na nufin makarantar da na ci buri akanta ba zata yi ba kenan? Wani Ustaz ne zai bar matarsa tana yawo a titi fisabilillah, da ma wani d’an boko ne da sauk’i. Amma wannan ha’din sam bai ha’du ba, in dai za’a min adalci akan Aysha a tuna bani da wata da nake gani a matsayin y’ata a bar Aysha ta yi karatu…” Ta fa’da idanunta suna zubar da k’wallar da ta sanya duk jikina sanyi. Amma ban hango sanyin gwiwa a wajen Abba ba, kamar yarda na hango shi a wajen Umma, don a raunane ta ce “Abban Aysha ka yi hak’uri ka janye maganar auren nan….” wani kallo ha hurgawa Umman da ya sata shiru da bakinta tana kallon Mamin a raunace. “Ba zan janye ba, har abada kuwa, don ba zan ga samu naga rashi ba, wani irin solob’iyon Uba kuke so na zama? Allah ya kawowa y’ata nagartaccen Mijin da kowane Uba yake fata sai na masa butulci sabida wani karatun boko na banza da na wofi. Mutumin da ko y’ay’a d’ari yake so za’a ba shi a rana guda, duka ta tsallake ya ce Aysha ce ta masa Aysha yake son aure sai na zuba masa k’asa a ido, Saboda wata maganar banza da wofi. Ita ka’dai ce fa y’ata mace da nake fatan ta yi dace da Mijin k’warai.. ko yanzu yake so na tsame ta a boko na mata aure wallahil azeem na shiryawa haka, ba abinda kuma zai saka ni fasawa. Karatu dai idan ya ce zata yi a gidanta falillahil hamdihi idan ya hanata ma gaba d’aya wallahi ba zan tursasa shi ba. Saboda ku iyayen banza ne ku da zaku saka ta ta yarda ku rarrasheta ku ke sakata ta bijire min? To ku je ku yi na da ku a ga wanda zai ci riba…” Daga haka yaja bakinsa ya tsuke ya kuma wanke hannunsa ya tsoma cikin tuwo ya cigaba da ci. Fuskarsa a ha’de sosai alamar duk abinda ya fa’da har k’asan zuciyarsa hakan yake. Mami ta ture kwanon tuwon da muke ci ni da ita da Umma ta mik’e fuska a ha’de ta fice daga parlorn. Jikina a sanyaye na mik’e zan bi ta Abba ya saka baki ya kira ni muryarsa a dake. “Dawo Ayshatu, zauna ki ci tuwonki, ba cutar da ke zan yi ba, har ga Allah alheri nake hango miki game da aurenki da Ahmad..” Na d’aga kai na ina wasa da zoben hannuna. “Ki kuma bu’de wayarki ki fara amfani da ita, na san ba zai cutar da ke ba. Ban kuma amince da duk wani tarkacen social media ba…” Na d’aga kaina don shima Ustaz garga’di da ya min kenan. Na san tunda suke ta jaddada min to social media d’in ba abu ba ne mai kyau. Cin tuwon kawai nake ba tare da ina fahimtar d’and’anonsa ba, don dai kada Abba ya yi magana ne na zage na ci tuwon kafin na mik’e cikin mutuwa jiki na haye sama. So nake na je naga Mami da halin da take ciki. Jikina a sanyaye na murd’a k’ofar d’akinta don bata parlour kamar yarda ta saba zama. A saman gado na sameta hannayenta dafe da k’unci da alama ta yi zurfi cikin tunanin da take. Zama na yi daf da ita ina d’ora kaina a saman kafa’darta. Sai na ji ta saki ajiyar zuciya. Ta rungumoni sosai a jikinta tana furta “Aysha, yanzu kin amince d a auren da Abba zai miki?” K’asa na yi da kaina idona na zubar da k’walla. “Mami kema ki yi hak’uri please…” Janye jikinta ta yi tana sakin wani malalacin murmushi “Na yi hak’uri Aysha? Na yi hak’uri Ustaz ya cuceni ya raba ni da duk wani farin cikina? Ya kuma ruguza min da duk wani shirina a kan ki da na shekara da shekaru ina shiryawa?” Ta girgiza kai tana taune leb’enta ta furta “Wallahi bai isa ba, mu zuba ko ni ko shi?” K’asa na yi da kaina saboda ba zan iya sake cigaba da juriyar kallon idanun Mami ba, don wani abu nake gani a cikin idon… Zamewa ta yi ta kwanta tana mayar da numfashi idanunta a lumshe. “Tashi ki tafi AYSHA, ta shi ki wuce d’akinki…” Ta fa’da a zafafe da sauri kuwa na mik’e ba fice don ban saba ko na ce ban tab’a ganinta a irin wannan yanayin ba… na lura daf take da fara Aljannu… Da safe har na shirya na gama shirin makaranta Mami bata tashi ba. Hakan yasa na nufi d’akinta ina nocking a hankali. A zafafe ta furta “Waye ne?” “Nice Mami…” ta bu’de k’ofar tana kallona idanunta kuwa da k’yar take lumshe su. Ta ja hannuna tana murzawa a hankali cikin wata irin murya ta furta “Ayshatu…” Na d’ago ina kallonta ta d’an sunkuyar da kai sai kuma ta saki hannun nawa. Tana sakin Malalacin murmushi ta furta “Har kin yi shirin makaranta?” Na d’aga mata kai “Ina kwana Mami?” Amsawa ta yi tana d’an ja baya ta furta “Wuce ki tafi AYSHA, ni ba abinda zaki ce min tunda kin zab’i farin cikin iyayenki a kaina. A jiya na yi takaicin rashin haihuwa da ni na haifeki da kaina na san ba zaki bujire min ba….” Kuka ne yazo min sosai ban san sanda na fa’da jikinta ba na saki wani irin kuka. Mami ta rungumeni sosai a jikinta ina jin yarda take sakin ajiyar zuciya. A kunne ta ra’da min “Kada ki bujire min Aysha, kada ki guje ni zan shiga wani hali AYSHA….” Da k’yar ta zame jikinta daga jikina ta juya bayanta tana furta “Je ki ki rufe min k’ofa…” Jikina a sanyaye na fice daga d’akin nata. A kitchen na tarar da Umma na tana ta aikinta ita ka’dai. Sai na ji duk ban ji da’di ba don koda yaushe tare suke aikinsu da Mami. Da wayona dai ba zan tab’a cewa ga ranar da suka yi aiki ba tare ba. Kallo guda ta min ta d’auke kanta tana amsa gaisuwata. Na juya zan fice ta furta “Ba zaki k’arya ba ne?” “Umma na k’oshi…” Umma ta bi ni da kallo mai kama da harara tana furta “Ki yi ta k’oshin mana Aysha? Cikin wa? Kin zata ni d’in uwarki ce da zan ta bin ki ina lallab’aki, kin bi kin k’i ki kwantar da hankalinki balle na uwarki ya kwanta sai kace a kan ki aka fara auren early marriage, sanda Ubanki ya auro ni 15yrs nake, ban ma kai ki ba me ya same ni? Mahaifinki dai kaifi d’aya ne, ba mai saka shi ba mai hana shi don haka ki nutsu ki san abinda ki ke. Ban tab’a jin kan Fateemah da Abbanku sai a yanzu da take son ta bujire masa, me ye ribarki idan kin haddasa sab’ani a tsakaninsu? Na ce meye ribarki AYSHA?” Shiru na mata ina bulbular da hawaye. Me yasa Umma zata ga laifina ce mata na yi bana son Ustaz? Bata san nafi kowa son haka ba? Tashin hankalin Mami ne kawai bana so nake b’oye hakan a raina.. “wuce ki bani wuri, ki shirya bujire masa kece zaki wahala don kin san ko magagin mutuwa kike Ubanki sai ya sadaki da gidan mutumin nan…” Na ja k’afata na fice daga kitchen d’in zuciyata a k’untace ranar na isa makaranta. Har na dawo daga makaranta ranar Mami bata mik’e daga saman gadonta ba. Ko kayan barcin bata cire ba. Na shiga na sameta na sanar da ita na dawo. Ta bi ni da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya ta nuna min gefenta. “Zo AYSHA ki kwanta ki huta…” Ban k’i tayinta ba don ina buk’atar hakan na san kwanciya kusa da itan ne kawai zai saka na daina jin b’acin ran da nake ciki. Sau tari idan na saka jikina a jikinta ina samun nutsuwa idan ina cikin tashin hankali ko b’acin rai. Ta jawo ni na shiga jikin nata sosai. Hannu ta saka a bayana ta shafawa a hankali kamar yarda ta saba min. Muryata a k’asa sosai ta furta “Aysha me yasa kike son bujire min? Kada ki cuci kanki ki yi aure at your young age, zaki cuci kanki, zaki yi nadama nan gaba rayuwa ta canja. Ke ka’dai nake da hope a kanki AYSHA don Allah kada ki bujire min, ko me za’a miki kada ki amincewa auren Ustaz.. kin yarda.” Na d’aga kai sai naga ta saki ajiyar zuciya ta bani peck a kumatu tana sakin murmushi ta furta “Thanks my beautiful Baby, I love you..” Shiru na yi sai da ta d’an ja kumatu na ta furta “Ba zaki mayar min ba? Ko fushi kike da ni?” “I love you too Mamy..” na fa’da kamar yarda na saba fa’da koda yaushe idan ta furtar kalmar. Ta lumshe ido tana sake jana jikinta ta furta “Oya sleep…” zan yi magana ta furta “Shsssh!” A kunne na hakan yasa na lumshe idon dole. Take ni da Mamy barci ya d’auke mu. Barci da ba mu tashi farka wa ba sai da aka yi kiran sallahr la’asar. Na bu’de ido da sauri don na san tabbas yau na makara a makaranta. Mami bata san Ustaz yana koyarwa a makarantar mu don haka bata saka ido a kaina da zuwa makarantar ba. Ta bu’de idonta da k’yar tana kallona “Ya dai Aysha?” Na sauka daga gadon ina furta “An yi sallah Mamy, kuma zani Islamiyya.” Kanta ta rik’e a hankali tana d’aga min kai. Na fice da sauri. A gaggauce na watsa ruwa na yi shirin Islamiyya na fito da sauri. A d’aki na samu Mami daga ita sai rigar wanka. Ta mudubi take kallona ta furta “Kin shirya Aysha?” Na d’aga mata kai. “Zo ku shafa min mai a baya na.” Na isa wajenta da d’an sauri na zuba nan a hannuna ta zame rigarta na fara shafa mata. Ban wani damu ba don na saba shafa mata d’in. Kuma Mami ba ta damuwa da suturce kanta koda ina wajen abinda ya danganci k’irjinta kam bata damu ta b’oyeshi ba. Tun ina jin kunya har na saba. “Ada lafiya ta fa’da tana mik’o min chocolates masu d’an yawa. Tana furta “Ki tabbata kin cika min alk’awarina Aysha, kada ki sake ki amince da auren Ustaz..”. Na amsa na fice da sauri.. Ina shiga makarantar na tabbatar Ustaz na nan don ga motarsa nan, gaba na ya fa’di don na san na makara ba ta wasa ba. Amma haka na d’aure na nufi ajin. Harabar makarantar shiru duk an yi sallah an koma aji. Zuciyata na bugawa na isa k’ofar ajin fuskata a ha’de don ya kamata na fara janyewa Ustaz don na cikawa Mami alk’awarinta, ya zama dole na mata halacci musamman ganin ita bata haihuwa kada zafin ya mata yawa… Idanu y’an ajin suka zubo min, Har shi Ustaz d’in da ya tsayar da karatun da yake yana kallona. Na sake ha’de raina na nufi wajen zama na. “Aysha Imam Khaleel kin makara.” Ya fa’da cikin dakakkiyar muryarsa cak na tsaya ban k’arasa inda zan zauna d’in ba. Fuskata a ha’de na d’ago ina kallonsa. Ina ji kallon ne ya bashi mamaki. “Me yake damunki?” Juyawa na yi na fice kawai daga ajin. Ustaz na ji yana kiran “Aysha!” Na k’i na juyawa na koma saman step d’in na zauna kawai kaina a saman cinyata idanuna suna zubar da hawaye. “Tashi ki shiga aji.” Na ji muryarsa a kaina. Ban d’ago ba, ban kuma shiga ajin ba. “Ba kya ji ne Aysha?” Na d’ago a zafafe ina kallonsa na furta “Ni ba zan shiga ba, ka k’yale ni…” Cak ya tsaya yana kallona cikin narkakkun idanunsa ya furta “Ma Asabaki?” Wanda akan lab’b’ansa kawai na ji furucin. Ya lumshe idonsa ya furta “Tashi ki shiga..” Ba musu na mik’e jikina a sanyaye kamar zan shiga ajin sai na yi hanyar fita daga gate d’in. Ina ji Ustaz yana fa’din “Aysha tsaya…” Amma Ina na bawa banza ajiyar sa na fice har da d’an sauri na… Ina fita gate na juya naga Ustaz ya d’an rik’e kansa yana kallo na yana cije leb’ensa….. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://www.arewabooks.com/chapter?id=669e462086c5cb5aff79fe08 https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 11 ‎Runtse idonsa naga ya yi da sauri, kafin ya girgiza min kai, “Kada mu yi haka da ke Aysha, kada ki sakawa zuciyata ciwon da zai yi wahalar warkewa.” Sai naga ya durk’ushe a gabana idanunsa sun tara wata k’walla da ya k’ara idanun nasa kyau. Duk da akwai tazara a tsakani na da shi sosai ma, don na lura yana taka tsantsan k’warai da gaske wajen ganin ya kiyaye dokar Allah. “Ki taimaka min don Allah ki amince na aureki, ba yarda idan kin gama secondaryn sai Ai mana auren, duk da haka ma sai na yi k’ok’arin gaske kafin na iya daurewa, ni ka’dai na san me nake ji a kanki, ni na san irin yarda girman son ki yake a zuciyata, Please AYSHA will you marry me?” Runtse idona na yi ina jin yarda zuciyata ke matuk’ar gudu da tarin k’aunarsa a ciki, da gaske dauriya nima kawai nake da kuma son cika alk’awarin da na yiwa Mameey Amma ina ji a raina rashin Ustaz a rayuwata daidai yake da rasa rayuwar tawa. “Ki amsa min AYSHA, please za ki aure ni?” Wallahi ban san sanda na d’aga kai ba, Saboda wani irin kallo mai azababben kyau da Ustaz ya dinga zuba min da narkakkun idonsa. Gani ya yi ya dunk’ule hannunsa duka biyun yana sakin ajiyar zuciya ya furta “Shukran ya Rabbi, Shukran ilaiki Ayshata…” Ya mik’e yana sake kallon Table bayan ya ajiye wata leda a kusa da ni. Ya furta “Yau ma AYSHA ko ruwa babu?” Sai kunya ta kama ni na yi k’asa da kai na, ina wasa da zoben hannuna. Murmushi mai sauti ya saki. “Shikkenan tunda rowa kike min, na gode..” ya yi furucin da karyayyiyar murya. Da sauri na girgiza kai ina furta “Ai ban san zaka zo ba…” “Ta ya zaki san zan zo bayan kin k’i picking call d’ina, kina hora ni saboda kina tunanin kin yi yarinya sa aure ko?” Ya furta yana d’an murmushi ha’de da cije leb’ensa ka’dan. “Allah ya nuna mana lokacin, Jibi zan wuce Egypt, zan samu one week a can. Idan na dawo kashegari zai kama litinin anan zan sha ruwa. Ina jiran girki mai kyau daga wajen kyakykyawar budurwata, za ki yi min?” D’aga kai na yi da sauri ya yi dariya “Kamar gaske Allah yasa kin iya girkin.” “Allah kuwa na iya..” Ya mik’a min hannunsa “Zamu gani ai, Allah ya kai mu ranar kuma ban amince kowa ya tayaki ba. Kina girkin muna vedio call, ba ni zoben hannunki.” Na waro ido ina girgiza kai. “Ai ya yi maka ka’dan, ji fa hannunka.” Ya kai duba zuwa hannunsa “In dai ba rowa zaki min ba, ai sai ki bani na gwada na gani, ko ya yi min ka’dan ina so zai min rakiya Egypt..” Na zare zoben ya nuna min gefen kujera “Ajiye a nan, Zan d’auka.” Na kuwa ajiye ina sake girmama halin Ustaz na kiyaye dokokin musulunci. Ya ‘d’au zoben ya saka a k’aramin yatsansa sai ga shi kuwa ya ‘dan shiga. Sumbatar zoben ya yi a hankali yana lumshe ido ya furta “Ina sonka zobe, Saboda ka fito a hannun AYSHA ta..” Ban san sanda na saki murmushi ba ina jin kamar ni Ustaz ya sumbata.. Daga haka ya fice daga sitroom d’in yana sakin murmushi… Tunda na saka k’afata a benen Mami, na ji gabana yana fa’duwa, fatana Allah yasa ta yi barci. Da san’da na tura k’ofar parlorn sai dai ba kamar yarda na yi tsammani ba, Mami na nan idonta biyu. Tana zaune a kan kujera ko T.V bata Kunna ba. K’afarta ta ‘dora ‘d’aya saman d’aya tana girgiza ta fuskarta a ha’de sosai. Jikina a sanyaye na k’arasa kusa da ita na zube a gabanta… “Mami na, don Allah ki yi hak’uri ki yafe min laifi na, wallahi ban yi don na b’ata miki rai ba, na yi ne don bin umarnin Abba….” “Abba ba? Dole ki bi umarninsa tunda shi ya kawoki duniya, ni mecece a wajenki da na wuce Uwar goyo, ba abinda zaki ce min kin zab’i iyayenki a kai na sakamakona kenan a wajen ki Aysha? Duk da tarin k’aunar da na nuna miki?” Ta fa’da wata k’walla na zubo mata. Nima kukan na saki, jijiyoyin kaina suka d’aure na dinga kuka mai tafe da ajiyar zuciya. Ta matsar da ni daga jikinta tana mik’ewa ta nuna min k’ofa “Sauka min daga bene AYSHA ki koma wajen iyayenki da kika fi k’auna….” A tsorace na dinga kallonta jin furucinta kuma na hango tabbas da gaske take har k’asan zuciyar ta . Hannunta na kama da sauri ina furta “Me yayi zafi haka Mami na? Duk duniya ba ni da kamarki, Abba da Umma kawai haihuwata suka yi, amma ke kika ci dukkan wahala da ni, kika bani tarbiyya kika kula da ni da jiki da aljihunki me yasa zan bujire miki?” “Zaki bujire min ne AYSHA saboda d’a namiji, d’a namijin da nan gaba idan ya kuntaka miki iya shege sai kin yi dana sanin ha’duwa da shi, d’a namijin da idan nan gaba ta ciyoshi zai auro wayayyiya mai ilimi ke kuma ya mayar da ke Bagidajiyar gida… Ilimi shine garkuwarki don haka ki yiwa kan ki fa’da ki rabu da shi ki zab’i karatunki…” Runtse idona na yi na furta “Ya ce zai bar ni na yi karatun har sai na ce ya isheni…” “K’arya yake AYSHA yana samunki, zai manta da wannan alk’awarin, bana burin nan gaba ki zama k’ask’antacciya nafi so ki zama tauraruwa a cikin duniyar mata masu ilimi, ta yarda zaki shiga ko ina a goga da ke… Ki bijirewa auren nan AYSHA in dai ba so kike na ‘d’auka har a raina don kun san bana haihuwa ba ne bani da kuma y’ar da zata shafe min hawaye…” Fa’dawa jikinta na yi ina furta “Zan share miki Mami, wallahi zan share miki kuma na hak’ura da Ustaz ko da hakan na nufin rasa dukkan farin ciki a rayuwata…” Murmushi ta saki tana sake rungume ni a jikinta. “Ba wani farin ciki da zaki rasa Aysha, farin ciki yanzu ma kika fara in dai zaki rabu da wancan mutumin ni kuma zan baki farin cikin da har sai kin dinga mamaki, zan maye miki gurbin Uba, Uwa da shi kansa Mijin…” na d’aga kai ina sakin ajiyar zuciya a hankali. “Ba ni wayar da ya baki?” Hannuna na rawa na mik’a mata. Naga ta danna wajen kashewa ta kasheta tana murmushi “Bak’in mugu sai dai ka auri wata ba AYSHA ta ba…” ta fa’da tana mik’ewa ta shige d’akinta “Ki je ki yi wanka ki kwanta, Maganar wannan mutumin close har abada…” wani irin yawu na ha’diye da k’yar ina mik’ewa na ji kaina ya sarawa na rik’e kan da k’yar na isa cikin d’aki, ina ji kamar Mami ta raba ni da wani sashe ne na rayuwa ta.. Tun daga ranar na rasa duk wani farin ciki da walwala. Sai dai ina k’ok’ari sosai wajen danne hakan don kada Mami ta gane. W Ranar kwana uku da faruwar lamarin Mami ta fita, Umma ta hawo sama, ta shiga d’akin da nake a kwance ta sameni idanuna na kallon ceiling ta tsaya a gefen gadon. Ganinta ya saka ni yin firgitgit ina kallonta. Ajiyar zuciya ta saki ta zauna a gefen gadon tana furta “Ta shi Aysha magana za mu yi, a matsayina na uwar da ta haifeki na san kin kwana da sanin cewa ba zan cutar da ke ba.” Jikina a sanyaye na mik’e na zauna idanuna na kawo ruwa sai na ji kawai ina son na yi kuka a jikin Umma na. Fa’dawa jikinta na yi na saki kukan bata hana ni ba sai ma sake rungume ni da ta yi a jikinta. Na yi kukan sosai kafin ta ‘dago ta share min hawaye ta furta “Me ke damunki?” Girgiza mata kai na yi “Bakomai Umma.” Murmushi ta saki tana gigiza kai “Ba zai zama bakomai ba AYSHA tabbas Akwai komai, ni na san kina son mutumin nan Kuma kin amince da aurensa, me yasa kuma kwana biyu kika canja? Ga shi kullum kina d’aki ba kya walwala, Aysha ina son ki bu’de kunne ki ji ni da kyau. Bin Umarnin mahaifinki wajibi ne gareki, ki amince da auren nan kafin ki zo kina nadama, me yasa ba kya amsa wayarsa alhali kin san baya gari? Ya kira Abbanku yana tambayar lafiya idan ya kira wayarki bata yi? Ina wayar taki take?” Umma ta furta tana min kallo mai cike da k’auna da rarrashi. A hankali na furta “Tana wajen Mami.” Murmushi naga ta yi ta mik’e tana fa’din ki tashi ki yi wanka ki sauko ki ci abinci bana son zaman ‘d’akin nan.” Na mik’e a hankali na shige toilet d’in. Umma har ta tara min ruwa na shiga wankan sannan ta fita daga d’akin. ———— Kashegari da safe naga duk k’annen Abba maza sun zo gidan. Ban san me ake ba ni dai na shirya na tafi makaranta. Da na dawo kuwa rigima na tarar a gidan wai ashe ku’din aurena aka kawo da sa rana gaba d’aya.. Shine Mameey ta fito tana masifa a tsakargida na ganta da Umma tana janta da akwatin ta tana furta “Wai Fateema meye haka kina cikin hankalinki kuwa? Saboda za’a aurar da Aysha zaki bar gidan nan…” A zafafe ta janye hannunta. “Cika ni, gwara na tafi meye amfanin zama na a gidan da baa san daraja da k’imata ba, ashe dama kun bani y’ar ne don ku wulak’antani ku nuna min bani da iko da ita. Zan bar gidan tunda ba Uban da na ajiye, ku je ku yi ta aurar da ita….” Da gudu na iso wajen na zube a jikinta, jikina yana kakkarwa na furta “Please Mamy ba inda zaki, ba Zan aure shi ba wallahi, tunda dai baki amince ba…” “Ashe kuwa sai dai idan ba ni Iman ba ne na haifeki Aysha, aure ba fashi..” Mami ta juyo tana kallonsa “Kada Allah yasa ka fasa Imamu, ga y’arka nan ka aurar da ita, amma ni na gama zaman gidanka…” Hanya ya nuna mata yana juyawa a zafafe cikin parlorn sa. Mami ta wancakalar da ni ta ja akwatin ta da sauri zan bi ta Abba ya daka min tsawa da sauri na durk’ushe a wajen ina jin tashin motar Mamin. Na runtse idona da k’arfin gaske, ina jin wani irin b’acin rai Yana dugunzuma zuciyata… Wannan wani irin bal’ai ne tabbas zuwan Ustaz rayuwata ba abinda ya haifar sai fitina a cikin gidan mu, abinda ban tab’a gani ba, sa’insa tsakanin Iyayena da Abba. Ranar sam zuciyata bata da nutsuwa na ji a raina sam na shirya rabuwa da Ustaz. Nan da nan labari ya kara’de danginmu an bada ni an saka min rana. Aka yi ta zuwa Allah ya sanya alheri. Mami kuma bata dawo gidan ba tashin hankalina kenan… Ranar lahadi Ina zuwa makaranta naga motar Ustaz. Mamaki ya kama ni na fara tunanin a yau d’in da ya dawo yazo kenan. A aji na same shi a zaune da wasu tsirari daga cikin ajin. Ido ya ‘dago yana kallona sai naga kamar har rama ya yi a ido. Na rusunar da idona kawai na isa wajen zama na na zauna. Sai da ya gama karatu wanda duk rabi ba fahinta nake ba sannan ya ‘dago yana kallon y’an ajin ya furta “Bissalam, ku je ku yi sallah.” Ni ce ta farkon fita. Ana idar da sallah aka ce koda kowa ya mik’e, anan muke jin ashe yau ustaz zai yi sallama da makarantar. D’alibai da yawa ba su so ba, musamman y’an mata da suke ta maganar k’asa-k’asa. Ustaz ya yi alheri sosai ga makarantarmu. Sanda Malam Kawu ya masa godiya a madadin y’an ajinsa na Ibn Kaseer ta cikin loud speakerr Ya furta “Bayan jaddada kalmar godiyar mu, sannan ina son y’an makaranta su taya Ustaz Ahmad murnar samun matar Aure da ya yi, a cikin makarantar nan. An saka musu rana da hazik’ar mu, Hafizar mu Aysha Imam Khaleel, Head girl d’in mu ta wannan makaranta. Duk da nik’ab ne a fuskata sai da jikina ya fara rawa musamman da kabbarar mutane ta dinga shiga kunnuwa na. Na runtse idona a hankali. Ina hango yarda bakin Ustaz ya kasa rufuwa yana ta sakin murmushi. Y’an mata kuwa duk fuskokin wasu ba walwala. Har gaba na aka dinga zuwa ana sake taya ni murna. Ni dai kasa bu’de fuskata na yi na samu na na silale na gudu… Ina zuwa layin gidan mu naga yarinya ta biyo ni da gudu “Malama Aysha take ta furtawa. Na tsaya ina kallonta sai da ta d’an yi haki na alamar gudun da ta ci sannan ta mik’o min envelope ‘din mai matuk’ar kyau. Da tun kafin na bu’de na san waye saboda k’amshin mayen turarensa. “Ba ruwana da fushinki, duk da na ji haushi amma abu guda na sani dole a cika min alk’awarina zan zo shan ruwa gobe around 7:30pm. Your’s Ustazun Aysha. Ajiyar zuciya na saki. A raina ina tunanin ta inda zan rabu da Ustaz ba tare da na saka shi a damuwa ba.. Kashegari nima tashi na yi da azimin kawai na samu kai na da son yiwa Ustaz d’in girki, duk da ina ji a raina a ranar zan rok’e shi ya janye daga maganar aurena ko don dawo da farin cikin gidan mu, kuma Mami ta dawo gidan mijinta. Girkin na masa, Masa da sinasir sai miyar taushe na kuma yi kunun tsamiya da zob’o da ya ji kayan k’amshi. Haka kawai na ji gwara na masa abincin mu na gargajiya. Umma dai sai kallona take kafin ta gaji da shirun ta furta “AYSHA wa kike wa girki ne?” Kunyace ta kamani na ce “Umma cewa ya yi zai zo ya sha ruwa.” Gani na yi ta yi murmushi ta d’an’dana girkin da lemon ta girgiza kai ta furta “Kin yi k’ok’ari, sai ki ha’da masa da zogale tunda naga harkar gargajiya kika masa. Ko ke fa? Ki rabu da Mami zata dawo da ikon Allah, gobe ma Na ji Baffaninku suna za su je gidan…” Na d’aga kai kawai ba wai don zan janye maganar rabuwa da Ustaz ba da na shiryawa a yau. Daidai lokacin da zai zo kuwa sai ga Yaya Ali ya shigo d’akina yana kallona ya furta “Bak’onki ya zo kandala.” Turo baki na yi ina fa’din “Kai Ya Ali me ye haka? Kai ma ya kamata ka yi aure ka bar gidan nan.” D’alle min baki ya yi yana furta sai ki aurar da ni, ashe dai kina son mutumin ji wani uban kwalliya da kika yi har da su jambaki?” Harararsa kawai na yi na shige na sauka k’asa. Kafin na je ma har Umma ta saka an kai masa abincin sitroom. Ina shiga yana zaune na same shi. Idonsa a lumshe sai dai daga yanayin fuskarsa na tabbatar akwai abinda ke damunsa. Sallamar da na yi bai saka ya bu’de idon ba ya dai amsa nima na ga haka ne ta hanyar d’aga lab’b’ansa da ya yi. Tsawon mintu biyu bai bu’de idon ba duk da a jikina na ji yana kallona da lumsassun idanun nasa. “Zuba min ruwan tea.ban sha ruwa ba dabino kawai na ci.” Ya fa’da still idanunsa a lumshe. A daburce na fara ha’da masa shayin. Ina shirin sake zuba sugar ya furta “Enough madam, wa ya gaya miki ana son maza su dinga shan zak’i sosai?” Ya fa’da yana ware idonsa ka’dan a kai na. Maik’on k’wallar ido yana k’arawa idonsa kyau. Hawaye naga sun d’an gangaro masa. Hakan ya saka jikina ya yi sanyi. Na ajiye cup d’in shayin a kan table da ke kusa da shi. “Na gode” ya furta cikin raunin muryar da ta saka har na ‘dago na kalleshi da sauri na ce “Kuka ka ke?” Ya ‘d’aga min kai. “Kuka nake AYSHA, dole na yi kuka me yasa ba kya so na? Kike wahalar da ni, kin san kalar azabar da kika bani a kwanakin nan, Sana’a na je yi k’asar mutane amma na zama sam bani da nutsuwar da zan gudanar da sana’ar na kira waya a kashe har na gaji na kira Abba. Amma still you don’t on your phone why? Me na miki da na yi deserving this kind of purnishment a wajenki? Kin san bana k’asar balle nazo na ji dalili. Ki gaya min gaskiya me ya faru kin daina so na ne?” Da sauri na d’aga kai ina kallon sanda ya matse tea cup d’in hannunsa duk da zafinsa na runtse idona. Sai na ji ya saki ajiyar zuciya ya ajiye cup d’in. Ya furta “Na gode AYSHA, amma may I know the reason?” Ji na yi na kasa b’oye masa na ce “Mami na bata son relationships d’inmu da kai, ta fi so na yi karatu…” “Maminki?” Ya furta yana kallona kallon da yasa na ji wani mugun tausayinsa ya kamani. Sai naga ya cije leb’ensa ya mik’e kawai ya ajiye cup d’in ya fice. Ji na yi kamar na bi shi amma k’afafuna sun kasa sai b’alle war hawaye na ji daga cikin idona. Ai kuwa na saka kukan sosai ina yi ina mayar da ajiyar zuciya…. Shikkenan na san na rabu da Ustaz idan ba’a yi wasa ba rabuwa ta har abada! 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢. Kin fara karanta k’arfe a wuta kuwa? Kin ji da’din labarin Arfa da Viper? Idan baki fara ba maza ki fara tunda ke kan ki kin san Alk’alamin Aysha cool baya rubuta shirme. Rubutu ne take yi mai inganci wanda take rubuta abubuwan da suke faruwa zahiran da hanyar warwaruwar matsalar. Kada ki manta marubuciyar k’anwar Maza ce gaba da gabanta, cutarwa… maza ki fara ana kan free pages ina tabbatar muku ba zaku yi nadama ba. K’ARFE A WUTA…….. Don samun page 12 na Naga rayuwa ga wanda ba za su iya jira ba, ku duba arewabooks an saka. Ga link d’in nan. Nagode [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 10 ‎Da daddare muna zaune a ‘daki ni da Mami. Kalba take min tana sake zuga ni akan kada na yarda na auri Ustaz. Umma ta yi sallama ta tura k’ofar ta shigo. Idanunta zube a kan mu. Mami kuwa tana ganinta ta tsuke fuska. Zama ta yi a gefen gadon Mamin tana furta “Yanzu Fateema abin har ya kai haka? Ni ban ga abin d’aga hankali a wannan maganar ba, har kike neman ki tsiro da wasu halaye na daban da ba masu kyau ba. Wa’dannan abinda kike bakomai ba ne sai raina Abban su, kin koma san sarai makomar macen da ta raina Mijinta. Ni ban ga aibun Abinda Abbansu zai yi ba. Kamar fa gata ya yi muku ke da y’ar taki, auren namiji kamar Ustaz Ai duk uwa ta gari zata so wa d’anta……” Kallon da Mamin ta mata ne yasa ta tsuke bakinta tana kallonta da mamaki a fuskarta… “”Ke ce dai baki ga abin tada jijiyar wuya ba, ni na hango shi, kuma kuka d’auki maganar nan k’arama ni na shirya fito na fito da duk wanda ya ce zai mata aure a wannan y’an shekarun nata, wallahi ko Human right sai na kai mutum, in dai da gaske har zuciyarku kun bar min y’ar, ai sai ku bar ni na yi abinda zan yi da ita, sai dai idan nuna min za ku yi, ban isa da ita ba don ba ni na haifeta ba….” “A’a Fateema, duk maganar bata kai ga haka ba, Allah ya baki hak’uri.” Umma ta fa’da tana mik’ewa ta fice daga d’akin. Wani tsaki da ya tab’an zuciya Mami ta ja tana furta “So kike ta yi zaman aure da gidahumanci kamar yarda ke kike yi…” Sai na ji kalmar ta min girma a kai, na kuma samu raina da b’aci Umman ce gidahuma kenan? Sallamar Abba muka ji a kan mu bayan kusan mintuna 30 da fitar Umma, har a sannan kuma Mami bata fasa zuga ni ba. Ido ya zuba mana cikin tsukakkiyar fuskarsa da ban tab’a sanin yana da ita ba. “Tashi ki je sitroom kina da bak’o…” Mami ta ja hannuna ta rik’e k’am. Ba zata je ba..” Ta furta idanunta cikin na Abba. Wani kallo ya wurga mata mai cike da nuna zallar b’acin ransa ya furta “Kada mu yi haka da ke Fateema, kada ki kai ni bango, abin ba zai mana da kyau ba. Cika mata hannu…” Hannun ya fincike a nata hannun ya ja hannuna muka fice. Har d’aki ya raka ni. “Ki shirya sosai ki same shi a sitroom, idan kin so ki watsa min k’asa a ido ki zubar da martabar gidan nan…” Jikina kawai rawa yake, na kasa aikata komai sai share hawayen fuskata nake. Ga Abba ya ce yana tsaye a parlorn Mamin yana jira na. After dress kawai na zura akan kayan na fita duk zuciyata a furguce take ba ni da nutsuwa ko ka’dan. Don ban manta kashedin Mami ba na kada na yarda da zuwa wajen Ustaz idan kuwa na amince ta san na nuna mata bata isa da ni ba, kuma ba ita ta haifeni ba. Wannan magana ita take firgitani nake kuma rasa nutsuwa tabbas sun saka ni a tsaka mai wuya. Hannuna Abba ya sake ja, muka sauka ina kallon Mami da take tsaye ta saka hannu ta share hawayenta sai na ji nima nawa hawayen sun zubo. Na d’an tsaya Abba ya juyo yana kallona. “Kina son na b’ata miki rai AYSHA? Kada ki saka na d’aura miki aure da shi yanzun nan…” Da sauri na girgiza kai. Sai da ya ga na shiga sitroom d’in sannan ya juya ya koma cikin gida. Zuciyata kawai bugu take, musamman da na ji k’amshin turaren Ustaz ya mamaye sitroom d’in. Na yi sallama can k’asan mak’oshi. Shima a k’asan mak’oshin ya amsa yana sakin ajiyar zuciyar da tasa na d’ago na kalleshi. Jallabiya ce bak’a wuluk a jikinsa, yau bai saka Alkyabba ba. Kansa dai da farin Ihrami. Idanunsa sanye da farin glass da ya k’ara fito da kyan fuskarsa. “Shigo ki zauna..” Kamar ba zan shiga ba. Sai dai na shiga na zauna a kujerar da take nesa da shi. “Dawo wannan kujerar bana son magana da k’arfi, I feel headache zuwan na dole ne..” Na kalli kujerar da take kallon tasa na tashi na koma na zauna fuskata a tsuke ina wasa da yatsun hannuna. Shiru ya yi kansa a k’asa kafin na ji muryarsa mai cike da rauni yana furta “Ba gaisuwa AYSHA?” Sai na ji kunya ta kamani na d’ago kamar dole na ce “Ina wuni?” Bai amsa ba, wani kallo kawai yake jifana da shi da yasa yanayin jikinsa sauyawa, sai naga ya lumshe ido yana murza goshinsa ya furta “Gaya min laifina Ayshatu? Kike hukunta ni da wannan sigar, na kira waya kin yi rejecting text no answer, makaranta kin k’i zuwa, gaya min me ya faru?” Shiru na masa kawai idanuna na zubar da hawaye da zan iya a lokacin kai tsaye zan furta masa ya janye maganar aurena, amma wallahi na kasa ya min wani irin kwarjini da ba zan iya kallon idanunsa na furta masa hakan ba. Gashi a k’asan zuciyata wata irin soyayyarsa mai zafi ce take sake ragargazar zuciyar. Kallona dai yake kafin na ji ya sake kiran sunana. Kiran da naji har tsakiyar raina. “AYSHA! D’ago ki kalleni ina son mu yi maganar gaskiya, bana son k’unbiya k’unbiya kuma…. Zan baki tarihin kai na da baki tab’a tambaya ba, zan sanar da ke waye ni da k’arfin soyayyarki a zuciyata, idan kin amince da aurena to, idan kuma kin ji ban kwanta miki ba bayan sanin wanene ni sai na k’yaleki na yi fatan Allah ya ha’da kowa da rabonsa…. Ahmad Sulaiman Saeed shine Cikakken sunana, sunan da iyaye suka saka min, sunan da kowa ya san ni da shi. Sai dai a yanzu a makarantar ku da gidanmu na ji sun canja min suna zuwa Ustazun Aysha….” Jin abinda ya fa’da ya saka ni saurin d’agowa ina kallonsa. D’aga min kai ya yi “Banda tambaya har sai na gama, abu guda da na sani ina jin da’din Sunan da aka canja min, ina kuma fata ya ‘dore har abada idan da alheri a cikin zama na da ke… Mu uku kacal na gani a gidan mu, nima ban san dalilin da yasa suka zab’i su haifemu mu ukun ba kamar a k’asar turawa duk da dai d’abiun turawan suke amfani da su… na so a ce gidanmu muna da yawa kamar yarda nake sha’awar duk wani babban gida ya kasance, sai dai hakan bata samu ba. Amma na ce alwashin duk matar da na aura sai ta haifa min yara bila adadin ina son naga y’ay’ana sun kai hamsin…” waro idona na yi ina kallonsa ya ‘d’aga min kai “Don haka sai ki shirya dafatan Allah ya bamu masa albarka….” Runtse idona na yi saboda tsananin kunya a raina nake raya sai kace nace masa zan aureshi? Ahmad Sulaiman Sa’eed shine Babba, sai Khadija Sulaiman Sa’eed wanda kafin a haifeta sai da na shekara goma cif. Itama tsakaninta da d’an autanmu shekaru goman ne, shi yasa na ce miki su iyayena rayuwar turawa suke ko don a can k’asar masu jajayen kunnuwan suka taso. Mahaifina ya da’de yana aiki a Canada kafin ya dawo Nigeria ya kafa kasuwanci. Mahaifina su Talatin ne a gidansu ba zan iya jero miki su ba, sai dai na san mutanene masu zumunci masu son kuma auren zumunci, nima bijirewa na yi na musu tsallen baka’dai na gaya musu AYSHA kawai zuciyata take so. A d’akin su Abba na akwai Umma Amina itace Babba sai Umma Jamila, Daddynmu sai Abba Kabeer, Abba Ali, Abba Naseer da Umma Shatu.. autarsu kenan kuma mate d’ina ce mai sunan Ayshata… A gidansu Umma na kuwa su Ashirin ba biyu ne, sai dai a d’akinsu su biyar ne kacal. Ramla Mahaifiyar Ahmad Sulaiman, sai Saudat Tasleem, Taiba da Nihad. Nan fa wai su mahaifiyarsu balarabiya shi yasa ta sakawa yaranta sunan larabawa don Kakata buzuwar Yamen ce.. sai kin hankali da su idan muka yi aure don mutane ne masu felek’e da iyayi na gaske. Duka karatu na tun daga matakin yarinta har na girma, na yi su ne a lebanon school, sai da na gama secondary sannan na tuburewa Daddy na ce Jami’atul Madeena za’a kai ni. Ya so ya bujire don shi burinsa na zama iyalen Elizabeth ni kuma na ce nawa burin na zama dangin King Fahad ne, an kai ruwa rana kafin ya amincewa buk’atata na tattara na tafi Jami’atul Madeena ban kuma dawo ba sai a waccan shekarar… Ina isowa Nigeria na tsunduma aikin k’wadago ina ha’dawa da noma da kiwo da kuma safara daga can k’asashen waje zuwa tamu k’asar. Ranar da na fara ganinki, rana ce mai matuk’ar girma a wajena, da ba zan manta da ita ba. Kamar ba zan fita daga gida ba saboda hadari da ya lullub’e sararin samaniya sai dai wayar da Kabeer yake min ta isheni na zuwa ganin wani gida da Zan gani a layinku. Na mik’e na shiga wanka kamar ba zan yi kwalliya ba sai dai na samu kaina da tsara kwalliya ashe zan ha’du da matata ne… Ina tsaye da abokina na dinga jin zuciyata na wani irin harbawa. Mamaki ya isheni na juya don ganin dalili sai idona ya fa’da kan wata zuk’ek’iyar yarinya doguwa fara mai suffar larabawa. Numfashina ne ya kusa d’aukewa duk da na Yi matuk’ar daurewa wajen yi miki kallon da shari’a ta amince da shi kallo guda. Sai da kika wuce sannan na saki ajiyar zuciya ina kallon Kabeer na furta “Wacece wannan?” Kabeer dariya ya yi sosai yana cewa “Ai kuwa in dai sonta ka ke ka dace da macen k’warai, Saliha managarciya da kowa ke so.. duk layin nan ba nutsuwar yarinyar can wallahi…” na d’an yi dariya ina furta “Dalilinka na cewa haka Kabeer?” “Saboda kai daga gani shigarta ka san ta ha’da duk qualities d’in da ake son mace ta gari ta zama..” ya furta yana kallona cikin son tabbatarwa. Dariya na yi nace “Idan kuma Basaja take fa?” Kabeer ya ware ido ya ce wallahi ba wani Basaja idan baka amince ba kuma ka yi bincike..” “Bincike ya zama dole Kabeer, don aure nake son mu yi ta zame min Uwar yara na kaga kuwa dole na binciki sahihancin tarbiyyarta..” Kabeer ya jinjina min kai. “Ina tabbatar maka Ahmad duk binciken da zaka yi akan yarinyar nan magana guda zaka samu Mai tarbiyya ce…” Na saki ajiyar zuciya ina d’aga kai na windownku na hango kamar ana lek’e jikina kuma ya bani ke ce ko?” Waro ido na yi ina kallonsa. Ya saki murmushi yana d’aga min gira. “A jikina na san ke ce, na san kuma kema kin fa’da soyayyata daga yanayin yarda idanunmu suka sark’e da juna…” Daga ranar na kafa d’anbar bincike ka’in da Na’in. Shine dalilin da yasa na je har makarantarku neman koyarwa. Kuma daga ranar kullum a kan idona kike tafiya makaranta duk da ba na bari ki ganni, na kuma lura duk sanda kika zo wucewa sai kin dinga d’an juyowa kina dubawa. Ina sane na dinga miki duk tambayoyin da nake miki a aji sai na samu kina da matsananciya kunya. Wannan ma ya sake k’ara miki k’ima a idona. Hakan yasa kai tsaye naje gida da buk’atar azo min neman izinin fara zuwa zance wajenki. A take Abba ya ce wallahi in dai nine nake sonki ya ba ni ke, sai dai zai rok’i alfarmar a barki ki gama secondary saura shekara guda. Ba wanda ya ja da haka sai dai ni ba haka na so ba, na so a ce a yi bikin cikin wata biyu idan yaso ki k’arasa makarantar a gida na. Mommy ce ta dinga tausata. Abin kamar almara kullum Aysha k’ara min wutar sonki ake.. Yau da na ganki kina kuka a makaranta da k’yar na k’arasa musu karatun da nake musu. Allah ne ka’dai ya kai ni gida. Na dinga rok’on Daddy yazo a d’aura aure kawai amma ya k’i ya ce dole a bi maganar Abbanki ko shine ba zai aurar da y’arsa bata gama secondary ba. Still yanzu ma nazo naga kina kuka, AYSHA ki gaya min gaskiya ba kya son auren ne?” Ajiyar zuciya na sauke a hankali na d’aga kai na. Waro ido ya yi har yana mik’ewa ya iso gaba na a tsayen da yake hannayensa a k’irji ya furta “Ki gaya min gaskiya, da gaske ba kya so na, idan Kika sake tabbatar min zan hak’ura…” Jikina ne yake rawa na sake d’aga kai na.. Zama ya yi yana rik’e kansa naga sai murza goshinsa yake. Sai kuma na ji cikin sark’akkiyar murya ya furta “Ki furta da bakin ki, cewa ba kya so na…” Na d’aga leb’ena a hankali ina kallon k’wayar idonsa muryata na rawa na furta “Na ba yanzu zan yi aure ba sai na yi ko degree ne, am too young to marry…..” Ga mai son next page ya duba shafina na arewa zai samu page d’aya ko biyu bayan wannan. Page 11 @ ArewaBooks Danna link d’in nan Zai kai ka har page 11. https://arewabooks.com/chapter?id=669d122dc1b845b878dad215 Saboda yawan complain d’inku yasa na yi haka… dafatan za’a ni ha’din kai. Group 1 and 2 ya cika ga group 3 nan wanda bai samu ba ya shiga. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 12 ‎ Kashegari na lallab’a na yi shirin makaranta, don kawai na zame na je gidan su Mami na. K’arfin hali kawai nake don ko barcin kirki ban samu na yi ba. Don ma a ‘d’akin Umma nake kwana tunda Mami bata gidan. Ganin juye juyen da nake ya yi yawa, hakan yasa ina ji Umma ta saka baki ta kira suna na. “Mik’e AYSHA ki shiga toilet ki yi alwala ki yi sallolin nafila tunda barcin ya gagara. Na mik’e kuwa jikina a sanyaye na aikata abinda ta ce d’in, sai naga na samu sauk’in abinda nake ji a cikin raina. A kitchen na sameta tana dama kunun gya’da. Na furta “Umma zan tafi.” Ta ‘dago tana kallona kafin ta mik’o min cup d’in hannunta mai cike da kunun gya’da mai zafin gaske. “Shanye shi tas kafin ki tafi, kina nan kin sakawa kan ki k’wazzaba duk kin bi kin rame.” Ban mata musu ba na sha kunun don ni da kaina ina ji a jikina na matuk’ar ramewa don har kamar iska zata kwasheni. Ina shiga motar na ce da Baba Driver “Gidan su Mami zaka kai ni ba makaranta ba Baba.” Ya juyo yana kallona ya ce “Yau ba zaki makarantar ba Ayshatu?” Na d’aga masa kai, sai bai ce komai ba ya ja mota ya nufi da ni court road don anan gidan su Mamin yake. Shiru gidan har na shiga cikin harabar gidan ba kowa, don gidan sam ba yara sai Maman su Mamin duk an musu aure mazan gidan kuma wasu suna k’asashen waje karatu. Na shiga Parlorn gidan da yake k’asa inda anan step d’in benen yake. Mama ta dubeni tana bu’de baki. “Yarinyar Mami ce a gidan nan da safe haka, ina makarantar?” D’an murmushi na saki ban yi mata wasan da na saba mata ba ni jika da kaka. Na zauna a gefenta ina furta “Mama ina kwana?” Ba zan amsa ba Aysha, kin ga yarda kika dawo kuwa? Wace irin masifa ce kuka jefa kan ku haka ke da Uwar taki, ita ba nutsuwa ke ba nutsuwa, ku wato ba zaku yarda da hukuncin Allah ba kenan, dole sai kun ja da mahaifinki alhali dukkanku a k’ark’ashinsa kuke, ai ni ya min daidai wallahi wani Sokon Uba ne shi da alheri na binsa zai saka k’afa ya doke saboda wani bokon banza da wofi… ai idan nice a ranar da aka zo neman auren ma zan d’aura auren kowa ma bai ji ba bai gani ba. Mutum kamar Ustaz Ahmad da yake burge kowa, a cikin lafazin karatunsa zaka gane mutum ne mai nagarta…” idanuna ne suka kawo k’walla na yi shiru kawai ina jin zancenta. Ina ma y’arta zata zauna ta gane abinda Maman take fa’da. Amma Ai mun bari gini tun ran Zane, ni na san Ustaz ya yi zuciya ya bar ni daga yanayin kallon da ya min jiya. Ai shi ba k’aramin mutum bane da zai zauna ina masa walagigi da hankali. “Tashi ki je can wajen Uwarki, kada ki min kuka anan ba zan wani lallasheki ba, don ni bana bayan rashing gaskiya..” Na Mik’e kawai ina harha’da hanya na hau saman don na san a can zan samu Mami har yanzu yaran gidan kowa da d’akinsa. Na tura k’ofar na shiga, Mami tana kwance a saman carpet idanunta a lumshe kamar mai barci. Ta bu’de ido tana kallo na. Da sauri na isa wajenta, mik’ewa ta yi zaune tana bu’de min hannunta alamar na shiga. Na kuwa shiga ta Mayar ta rufe i ruf tana sakin ajiyar zuciya. “I missed you Mami na.” Ta lumshe ido tana furta “I mish you too Baby na.. Ina school d’in baki tafi ba kika biyo nan.” Hawaye na fara yi. Ta saka yatsa tana wasa da hawayen fuskata tana sakin murmushi a hankali ta kai min sumbata a gefen k’unci. “No more crying Baby na..” “Zaki koma gidan? Ni na yarda ba zan aure shi ba.” Ta saki murmushi ta ja hannuna ta matse cikin nata ta furta “Zan koma Aysha, don ba zan iya rayuwa ba tare da Baby na ba..” Murna na fara yi ina jin abinda ya tsaya min a zuciyata yana tafiya. So nake na tambayeta ta amincewa alak’ata da Ustaz amma sai na ja baki na yi shiru don bana son b’acin ranta. Ina kallo ta shiga wanka ta fito ta shirya a gabana sannan ta zura hijab d’inta muka sauka k’asa. Mama bin mu ta dinga yi da kallo ganin yarda nake jan akwatin Mamin. Murmushi kawai ta furta “Lallai Fateema, yanzu ba wanda bai rarrashekiba aka dinga baki hak’uri kika k’i komawa gidan mijinki sai yanzu da Aysha ta zo? Ai shikkenan Allah ya kiyaye hanya..” Mami murmusawa kawai ta yi muka fice daga gidan. Muka shiga cikin motar Mamin sai gida. Umma tana tsakargida tana ware kayan miya da naman da za’a saka a freezer ta ji sallamar mu. Da mamaki ta ‘dago tana kallonmu. Mami murmushi ta saki tana furta “Kallon fa?” Umma ta ce “Ba dole na kalleki ba Fateema, yanzu ba wanda bai je biko ba har ni kishiya, amma kika k’i dawowa Mahaifinki ma ba yarda bai yi da ke ba, shima kika ja kika kafe sai yanzu kawai naga ficilar yarinyar ta dawo da ke..” Mami Murmushi ta saki. Ta ce “Hakan zai nuna muku mahimmacin ta gareni a rayuwa ta…” Umma ta ce “Ba shakka, To Allah ya kyauta na gaba…” Daga ranar da na furta masa ba zan aure shi ba, bai sake nemana ba har tsawon kwanaki biyar. Zuwa lokacin duk na fige na lalace sai kace wacce ta yi watanni tana ciwo. Ba wanda ya sake bi ta kaina balle a min zancen Ustaz. Da yamma sai ga Yaya Muhammad ya shigo gidan muna tsakargida duk muna aiki. Ya d’an dubi Mami yana sosa kai ya furta “Hajiya Mami, Aron Aysha zaki bani, Khadija na fama da laulayi ni kuma tafiya kaduna ta kama ni zan kwana biyu a can…” Mami ta masa wani kallo kafin ta furta “Muhammad bana son jaye jayen magana, ita ina y’an gidansu ba za’a kai mata su ba, sai Aysha? AYSHA ce zata je ta mata wahalar laulayin kenan? To ba sai yiwu ba ka samar mata y’ar aiki idan ma bata da y’an uwan da zasu zauna mata.” Muhammad ya d’an rusuna, duk da ba wani girmansa Mami ta yi ba, bai fi 2 yrs ta bashi ba, amma yana girmamata a matsayinta na matar ubansa. “Ki taimaka, ko don nan gaba idan Aysha ta yi aure bata da y’an uwa mata itama fa y’an uwan Mijin ne zasu kula da ita.” Mami ta girgiza kai “Wallahi don dai kai ne, amma da Umar ne Allah ba zata gidansa ba..” Dariya Muhammad ya yi don ya san Mami da Umar sam basa shiri haka ma Usman. Ya dinga dariya yana kallona ya furta “Ke d’ebo kayan da zasu miki kwana biyar, ki yi sauri ina mota ina jiranki…” Na mik’e na hau sama, a raina sam bana son zuwa saboda ina yawan fita da yamma naga ko zan ga Ustaz amma bana ganinsa. Na shirya kaya na na bi Yaya Muhammad gidansa. A parlor na samu Anty Khadija daga yanayinta na hango tabbas laulayin take. Gaisheta na yi ta amsa tana murmushi na mata sannu. Da kanta ta raka ni ‘d’akin da zan zauna. Hijab d’ina na cire na fito parlorn ba mayafi a jikina sai hula. Tas na gyara gidan don ya yi k’ura ka’dan. Kafin na shiga kitchen na tuk’a musu tuwon semovita da Yaya Muhammad ya ce shi ka’dai take iya ci. Tsaf na shirya musu table d’in duk zuciyata ba da’di balle ganin tunda suka shige d’aki basu sake fitowa ba wai bata son k’amshin kayan miya. Mijinta sai wani lallab’ata yake. Haushi ma abin ya bani don haka bayan na yi wanka kawai na fita k’aramin parlorn na kwanta. Ina kallon wani Korean series. Anty Khadija da Ya Muhd suka shigo hannunsu sark’afe cikin na juna sai wani janta yake a jiki, ita Kuma tana sake narke masa. Kunya da takaicin su ma duk suka ha’du suka sake jagule min zuciya ta. Khadija na kallona ta furta “Sannu Aysha..” na amsa mata ina mayar da kaina na kwanta. “My love wallahi duk jikina ciwo yake, so nake ka yi min tausa…” Gani na yi kawai ya sunkuya ya ‘dagata cak tana Zillo tana komai ya fice da ita kamar Babyn roba. Lumshe idona na yi ina tunanin dama nice da Ustaz a haka, da na tabbata ba wani da zai kai ni farin ciki a duniya. Sai kawai na samu kaina da zurarowar hawaye. K’amshin turarensa da na dinga ji yana sake yawaita ne ya saka ni bu’de lumsassun idanuna…. Da wani irin sauri na mik’e ganin Ustaz ne da Ya Muhd a parlorn. Ustaz d’in a zaune idanunsa akan wayarsa. Hula ce kawai a kaina, itama ta zame don haka gashi na ya bayyana sosai. Kayan jikina kuwa T.shirt ce da ta d’an kamani ka’dan sai siket. Ido na dinga warowa ina k’ank’ame jikina. Sai na lura Ustaz ko kallona bai yi ba, ya cigaba da hirarsu da Yaya Muhd, kamar ma basu san ina wajen ba. “Bari na kawo maka ruwa” Ya Muhd ya mik’ewa yana ficewa. Sai sannan na furta “Ya zaka shigo ba sallama, ai dai ba kyau shiga gidan mutane ba sallama, ga shi nan ka shigo ko Hijab babu a jikina…” Wani irin kallo ya min. Kafin naga ya ‘d’auke kansa ya mayar kan waya ya furta “Ba wajenki na zo ba, kuma mai gidan ne ya bani izinin shigowa.” Raina ne ya sake b’aci a kufule na ce “Sai ka tashi ka fita, ina son zan wuce cikin gida…” “Na hanaki ne?” Ya furta yana zuba min narkakkun idanunsa.. Turo bakina na yi sai ga Ya Muhd ya shigo yana kallona “Tashi ki samo masa snacks a kitchen Malama…” Ji na yi kamar na yi ihu. Na kalleshi na ce “To ka bani Hijab d’ina a cikin gida…” Tsaki Ya Muhd ya yi kafin ya fice sai ga shi ya dawo da Hijab ‘din ya hurga min. Ina kallo Ustaz ya ‘dan tab’e bakinsa na zura Hijabin na fice da sauri. A kitchen na tsaya ina mayar da ajiyar numfashi dafatan Allah yasa Ustaz aurena yazo sake nema.. Ban dawo daga hayyacina ba sai da Ya Muhd ya shigo kitchen d’in yana wurga min harara ya furta “Ki zuba abinci ki kai masa Malama ki ha’da da snacks.” Ya fice da sauri. Na sauke ajiyar zuciya. Na ha’da abincin da snacks d’in sannan na shiga d’akin da yake zuciyata na wani irin bugawa. Har na ajiye abincin bai d’ago ba. Na ja na tsaya don na kasa fita daga sitroom d’in. “Zuba ka’dan.” Ya furta cikin wata irin husky voice. Kamar ba zan zuba ba, sai dai na zuba tunda neman sulhu nake. Na ajiye akan table ya d’ago yana kallona kafin ya d’au abincin ya tab’e bakinsa. Na rasa dalilin wannan tab’e baki don haka na fara kallon jikina ko wani abin ya gani ban ga komai. Don haka na koma kujera na zauna. “Ki tashi ki koma ba wajenki na zo ba..” Da wani irin zafin rai na ‘dago ina kallonsa sai naga shi ko kallona ba ya yi tuwonsa kawai yake ci. Haushi ya kamani na mik’e da sauri zan fice daga ‘dakin. Na ji muryarsa a waya yana furta “Aysha, zo ku gaisa da zab’in alheri da Allah ya min, ga matar da za’a aura min aure da ita jibi….” Wani irin rawa jikina ya fara na juya da sauri don ganin matar da yake nuna min a vedio call. Zuciyata ce kawai bata fito ba, Saboda tashin hankali. Ya mik’a min wayar ba tare da ya kalleni ba. Take hankali yazo min kada a yi abin kunya na karb’e wayar ina kallon kyakykyawar yarinyar a cikin waya sai sakar min murmushi take. Yarinya kamar ita ta k’era kanta fara jajir da ita. Idan ma zata girmeni da ka’dan ne. “Sannu Aysha..” ta furta cikin zak’in muryarta. Kokawa na dinga yi da numfashi na na ja iska da k’yar na fesar ina k’ak’aro murmushi na ce “Sannunki…” ta lumshe ido tana furta “Yaushe zamu ha’du ki taya ni shirin biki?” Ji nayi kamar na k’unduma mata zagi. Na ha’diye wani abu da ya tsaya min a mak’oshi na ce “Ki yi hak’uri ina school ba ni da time, Allah ya sanya alheri..” Daga haka na mik’a masa wayar da sauri, ina jin zuciyata na wani irin hantsilowa. Bai karb’i wayar ba ya nuna min gefensa “Ajiye min anan, kin ga zab’in da Allah ya yi min ko? Wani baya auren matar wani, she is my cousin jibi za’a d’aura mana aure don a shekaruna ba zan iya jiranki wani degree ba, duk sanda kika gama degree d’in idan kina da niyyar aure na the door is open…” Ya fa’da yana kurb’ar lemo da min kallon da na tabbatar na rainin hankali ne. “Ba wani aurenka da zan yi, ce maka aka yi ni kuma kwantai zan yi da zan auri Mijin wata, ragowar wata Allah ya kiyaye Mijina zan samu Wallahi nima dallele na aura…” na furta ina huci kamar wacce ta yi tsere. Murmushi ya saki yana yamutsa fuskarsa ya furta “Allah ko? Amma dai kin san ba zaki samu wanda ya fi ni ba… Idan haka kika zab’a Ai shikkenan, ina fatan ita dai kin ganta idan bata fi ki ba, ke ba zaki fita ba…” Ya ‘d’au key d’insa yana furta ki turo Min Muhammad zan ba shi Invitation card d’in Abba ya kai masa…..” “Ba zan turo shi ba ‘din…” na furta kai tsaye idona na cikin nasa, duk wata shakkarsa da nake ji ranar ta kau, Saboda tsananin kishi da ya rufe min ido na. Murmushi ya saki ya furta “Bakomai, bari na kira shi a waya…” Cije leb’ena na yi ina ji yana furta “Muhammad idan ba damuwa d’an fito na baka cards d’in Abba na d’aurin aure na special guests…..” Daga haka ya saka kai ya fice ya bar ni a tsaye kamar statue gaba d’aya naji duniyar na juya min na runtse idonsa sai ga wasu k’walla masu turiri sun fara zubo min.. fuskar budurwarsa still a cikin Idanuwana…… 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 13 ‎ Tabbas bata inda zan ha’da kaina da matar da zai aura, ta fi ni komai kyau ilimi wayewa, da kuma gata, daga ganin gidansu inda ta d’au hoton in dai ba y’ar feck life ba ce to na san Ubanta yafi Abba ku’di nesa ba kusa ba. Me ya ja min? Na ce na fasa auren Ustaz gashi nan na jawowa kai na sakiyar da ba ruwa. Da k’yar na mik’e na fita cikin gida, daidai lokacin da na ji Motar Ustaz ta fita daga gidan a guje. Na lek’a ta window sai naga Yaya Muhd ya shigo gidan . Fuskarsa a ha’de yake kallona. Kafin naga ya yi k’aramin tsaki ya shige bedroom d’insa. Da alama haushina yake ji ta yarda nayi watsi da duk abinda suke so na zab’i farin cikin Mami fiye da nasu. Wayata na jawo na fara kiran Ustaz da sauri amma wayar na ringing Ustaz bai ‘d’auka ba. Na ja tsaki ina cilla wayar kan kujera tare da zama dab’ar ina rik’e kaina da naji yana sara min da k’arfin gaske. Idona na lumshe amma still Ustaz da Amaryarsa nake hangowa a wani yanayi na soyayya. Zuciyata ta dinga bugu da k’arfin gaske. Wasu hawaye masu zafi suka dinga zubo min. Ban san sanda na ja wayar na danna masa msg ba. “Ka ‘d’aga wayar magana za Mu yi….” In seconds ya dawo min da amsa “It’s too late, ki yi barci zan yi magana da safe, yanzu muna discussing da amaryata ne.” Na yi cilli da wayar ina jin wani d’aci har a mak’wagoro na. Cije leb’e na kawai nake yi ina mamakin wulk’ancin da Ustaz yake son ya fara min. Da dai naga babu sarki sai Allah, sai kawai na mik’e da sauri na nufi bedroom ‘din da nake, direct washroom na shige na sakarwa kaina shower da kayana a jiki da komai, burina naji abinda nake ji ‘din ya ragu. Sai dai ba abinda ya ragun daga zafin zuciya da nake ji. Na ‘d’auro alwala na shiga sallah ba ji ba gani… Kashegari da k’yar na tashi na hau gyaran gidan don duk kawai na kawar da abinda nake ji a raina. Da yamma sai ga Mami na tazo gidan. Da sallama ta shigo na yi saurin ‘d’aga kai ina kallonta. Zama ta yi tana tana jikinta ta furta “Ke Baby! What happened to you na ganki so pale haka?” Daurewa na yi ban sakar mata hawayen da suke son zubo min na ce mata bakomai…” Sai sannan ta amsa gaisuwar da Khadija ta mata. Tana fa’din “Ina Muhammad ‘din?” Anty Khadija ta ce “Ai bai dawo ba..” Gani nayi Mami ta girgiza kai ta ce “Yaushe ya ce zai dawo daga Kadunan?” Khadija ta ce “May be gobe.” Ni mamaki nake yi don dai Yaya Muhd yana nan a cikin gidan nan me yasa Anty Khadija zata ce bata nan… Mami ta ‘dan ja tsaki ta furta “D’an bamu waje Khadija zan yi magana da ita…” Kamar jira take tayi saurin mik’ewa ta fice. Mami ta saki ajiyar zuciya tana jawo wata leda a jakarta. “Dama yana dawowa ki dawo gida, a goben, kin ji na gaya miki.” Na ‘daga kaina ta zaro wata roba mai cike da wani abu kamar rubutu tana furta “Bu’de ki shanye, ban yarda da lamarin wancan mutumin ba..” Na karb’a hannuna na rawa na bu’de na sha duk da sam hankalina ya kasa yarda da rubutun, abu ne da na sani a gidan mu Abba d’an izala ne shi yasa baa ta’ammali da rubutu, zan iya cewa tun tashi na ma ban tab’a ganin rubutu a gidan ba. Yana dai yin tofi. Ina shanyewa ta saki ajiyar zuciya sannan ta ciro wani turare a jakarta ta shafa min. Turaren sam ba shi da da’din k’amshi. Daga haka ta mik’e bayan ta bani chocolates da ta siyo min da biscuit da yawa ta ta ce “Zan tafi AYSHA na gaya miki ki taho yana dawowa gobe..” Na ‘daga kaina ko sallama bata yi da Khadija ba ta fice. Sai ga Yaya Muhd ya fito daga bedroom fuskarsa a ha’de ya zuba min ido yana kallona. “Me ta baki kika sha?” Na waro ido ina furta “Bakomai fa…” “Bakomai d’in Uwaki, ba ina kallo ta baki abu roba kika shanye ba…” ya furta yana tsare ni da ido. Yana bu’de k’ofofin hancinsa da alama k’amshin turaren yake shak’a. “Wannan wani irin turare ne kamar na y’an bori? Tashi kije ki yi wanka don Ubanki shashasha da bata san ciwon kanta ba…” Yaya Muhd ya furta a zafafe kamar ya mangare ni. Da sauri na shige d’aki ina turo bakina alamar na ji haushin abinda ya yi min ‘din. Ina ji ya zabga tsaki. Da na yi wankan, zama na na yi a ‘d’aki fuskata a ha’de don na ji zafin abinda ya yi min. Sai gashi ya shigo d’akin yana kallona ya furta tashi magana zamu yi AYSHA….” Na mik’e na zauna still fuskata a ha’de. “Haushi kike ji ko? Baki da hankali yarinya har yanzu baki san me duniya take ciki ba, ina sane na kawoki nan don ban yarda da wannan matar ba…” Wani irin waro ido na yi na furta “Mamin nawa?” Harara ya zuba min, Yana fa’din “Saura kuma don Ubanki ki je ki gaya mata, na ce ban yarda da ita ba, tunda da alama ta shanye miki zuciya har kina k’ok’arin gasa taki zuciyar saboda ki sanyaya tata, kan ki Kika cuta ba wani ba na tabbatar ko gama karatun kika yi ba zaki samu kamar Ustaz Ahmad ba, shi na daban ne ina gaya miki, gashi nan kin cuci kanki zai yi aure ya bar ki, saboda ko farantawa wata k’atuwa rai shi kuma Abba da hakkin ki masa biyayya yake kanki kin bak’anta masa nasa ran a matsayinsa na mahaifinki, Kin nunawa duniya bai isa da ke ba. Ina sane na kawo ki nan amma nan ‘din ma sai da ta biyoki. To wallahi ki kiyaye kan ki na gaya miki bakomai zata sake baki ki yi amfani da shi ba. Ki ‘dau waya kuma ki kira Ustaz idan ya amince yazo gidan nan sai na tayaki bashi hak’uri, Allah yasa ya hak’ura ya aureki.” “Ameen” na furta ba tare da na san ameen ‘din ta fito ba. Ya Muhd ya bi ni da wani irin kallo kafin ya yi murmushi ya ce “Shashasha, kina so kina kai wa kasuwa..” Na sunkuyar da kai ina d’an dariya. Ya furta “Ki kira shi yanzu.” Ya fita daga d’akin. Sai da na yi addu’a sosai sannan na kira shi, Ringing ta yi sosai kafin ya ‘d’aga. Cikin Husky Voice ‘d’insa ya ce “Assalamu Alaiki, K’anwata AYSHA ya aka yi?” Wani irin waro ido na yi raina ya b’aci da sunan da ya kira ni da shi. Wai k’anwata ina ma laifin Habibteeyn… da yake fa’da. Ba dai ji haushi ba na furta “Ina yini?” Sai da ya yi ‘dan jum sannan ya furta “Lafiya lau, Babyn Mamy me ya faru na ji muryarki so weak…” Hawaye na ji sun silalo min na yi k’ok’arin tsayar da su ina furta “Zaka zo yau please…” “Ina zan zo?” Ya furta a hankali cikin k’asa da murya “Gidan Ya Muhd please Ustaz…” Sai da ya ja fasali sosai sannan ya furta “Me Zan zo na yi? Ko kin shirya amincewa aurena ne?” Shiru na masa zuciyata na bugawa da sauri na ce “Ni dai kazo don Allah…” ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya. Yana fa’din. “Sai dai gobe yau a gidan su Habibteey zan sha ruwa..” wani irin wuntsilawa zuciyata ta yi don haka naja baki na tsuke ina hucin da na tabbatar yana jin sa ta cikin waya.. “Kada ki fashe, don naji fushin ya bayyana har ta numfashinki, zan zo Amma ina son a min irin funkaso da masar rannan ki saka man shanu a cikin miyar.” Ya furta a hankali. Wani farin ciki naji na ce “Ai baka ci abincin ran nan d’in ba, ta ya aka yi ka gani? Bayan baka bu’de ba…” Y’ar k’aramar dariya ya saki ya furta “Little girl, bayan kin gama kuka a sitroom na saka Drivernku ya ‘dauko min Warmers ‘din na tafi gida da su, ranar duka kowa a gidan mu sai da ya ci abincin AYSHA Momeey na ta mamakin iya girkin ki da murnar ki zama surikarta ashe ba zaki zama ba….” “Wa yace ba zan zama ba?” Na furta da sauri. Na ‘dan Jim ya yi bai ce komai ba, kamar ma ba zai ce ‘din ba sai kuma ya ce… “Ke kika zab’i rabuwarmu Aysha… Ga shi Yanzu it’s too late, koda yake sai nazo za mu yi magana, take care ki ha’da min zob’o bana son kunun aya…”Ina ji ya kashe wayar. Nima ajiye wayar na yi cikin sanyin jiki, ina runtse idona wasu zafafan hawaye suna zubo min.. Na dubi agogo naga akwai sauran lokacin da zan iya masa da funkaso, tunda sai a lokacin ma 3:30 ta yi. Da sauri na mik’e na isa kitchen ‘din Anty Khadija. “Alhamdulillah” na fa’da ganin duk abinda nake buk’ata akwai shi a kitchen d’in. Nan da nan na fara shirin girki, don kam Alhamdulilah Umma da Mami sun hora ni da girke girke iri-iri, don haka duk inda na je basu da fargabar a bani girki. Sai shidda daidai na gama girkin. Gidan sai zuba k’amshi yake. Wanka kawai na yi na samu kaina da tsantsara kwalliya ta fitar hankali, wai duk don na kamo matar Ustaz a kyau. Amma still walainiyar fuskarta kawai nake gani. Don haka na saki tsaki na goge makeup ‘din tas hawaye na bin idona. Sanda aka yi sallah kuwa dabino kawai na samu na ci, don nima na yi azimin. Zaman dafi’an na yi akan sallaya. Ina ta lazimi da addu’ar Allah ya ‘dorani akan Ustazuna ya janye batun auren waccan yarinyar mai kama da zabiya, idan har ya amince ni na yarda ko kashegarin ranar ne a ‘daura min aure da shi. Daga baya zan san yarda na yi muka shirya da Mami. Ina zaunen akan sallaya Ya. Muhd ya shigo, ‘Dan duba na ya yi sai kuma naga ya tab’e baki ya furta “Ki taso Malama, bak’onki ya zo.” D’aga kai na yi gabana na cigaba da matsanancin bugu. Na mik’e cikin mutuwar jiki da kasala. Dama na jera masa komai a sitroom ‘din. Fuskata fayau ko kwalli babu na fita wajensa cikin shigar doguwar riga bak’a da na yi rolling da mayafinta. Jikina ruf ba inda ake gani sai fuskata don hatta k’afata a rufe take. Da sallama na shiga parlorn yana zaune ya tank’washe k’afa suna hira da Ya. Muhd har ya fara cin abincinsa. Ya ‘dago kai ya kalleni ya mayar kan abincinsa. Ya. Muhd mik’ewa ya yi ya fita. Ni kuma na zube a k’asa daga gefensa ‘dan nesa da shi ka’dan. “Ina yini?” Ya ‘dago yana kallona. Kafin ya furta “Lafiya Lau Ukhteey..” Turo baki na yi, na ce “Ni ba y’ar uwarka ba ce..” ware idonsa ya yi ka’dan ya furta “Then ke mecece?” Sunkuyar da kai na na yi ina wasa da yatsun hannuna. Ustaz bai bar kallona ba don ina ‘d’agowa muke sake ha’da ido da shi. “Amsa min mana ke mecece? Tunda kin ce ba kya so na, ni yanzu kallon k’anwa nake miki..” Idona ne ya kawo ruwa na zuba masa idanun nawa da naga ya k’ank’ance nasa idon ya saka cikin nawa ya Kuma lumshe su. Cikin wata irin murya ya furta “Matsayin Yayan ma ba zaki bani ba kenan?” D’aga kai na yi. Ya yi dariya sosai har wushiryarsa na bayyana ya ce “Shikkenan nagode. Matsayin me zaki ba ni? Gaya min AYSHA?” Mutsu-mutsu na fara yi shi kuma ganin hakan bai saka ya d’auke idonsa ba. Kallona yake kawai yana murmushi yana kuma kurb’ar ruwan zob’onsa. “Ba zaki gaya min ba? Ai shikkenan bari na tashi na tafi Habibteey na jira na, na gode da girki ya yi da’di sosai mijinki ya ji da’dinsa Wallahi na masa murna. Nima Allah yasa dai Habibteey ta iya girki…” Turo bakina na yi na furta “Ni ka daina min zancen zabiyar nan…” ware idonsa ya yi yana furta “Habibteeyn ce zabiya? Lallai ma, to idan ita zabiya ce ke kuma mecece?” Ban san sanda na harareshi ba. Na furta “Allah ya sawwake ni Ai fari na ba irin nata ba ne. Fari na yafi nata kyau…” Ya tab’e baki yana dariya ya ce “Ko dai kishi ne? Idan banda haka kiga yarinya zubin larabawa ki ha’da kanki da ita. Zan tafi ta ce ma Na gaisheki, amma kafin na tafi ina son na san matsayina sannan don Allah a min alfarma ki halarci event ‘dinmu ko guda ‘d’aya ne….” “Wallahi ba zani ba…” Na furta da sauri, har muryata na sark’e wa saboda tsabar takaici da bak’in cikin da zuciyata take ciki. Na lura ba k’aramin so yake mata ba kuma duk ni na jawowa kai na. Da sauri na fice daga ‘dakin ina sake fa’din “Ba zan je ba, sai kace wata mara zuciya…” Ban san sanda hawaye ya dinga rigegeniya a kan fuskata ba… Ranar kam ba barcin da ya ‘daukeni, ko b’arawon ma hak’ura ya yi ya k’yaleni. Da safe kam da ciwon kai na tashi. Kuma ko shara ban yi ba. Ina kwance a ‘d’aki Anty Khadija ta shigo tana kallona ta ce “AYSHA kin tashi, naga yau ko fitowa ba ki yi ba. Ki je in ji Yayanki.” Ban amsa mata ba, don haka kawai na samu kaina da k’uncin zuciya da jin haushin kowa ma. Na mik’e da rigar Barcin da take jikina na fita parlorn. Kaina ko gyara babu. Idona ya yi k’ozai-k’ozai. Zuba min ido Yaya Muhd ya yi kafin ya furta “Ke baiwar Allah, lafiya kike? Kinga yarda kika dawo kuwa?” Kallonsa kawai nake ban amsa ba ganin yarda yake walainiya cikin sabuwar shadda fara k’al da ita. Ya tab’e baki ganin bani da niyyar amsawa ya ce “Allah ya kawo sauk’i, ke Khadija mu je na sauke ki a asibitin tunda ita bata shirya ba, balle ta raka ki, ni zan wuce wajen d’aurin auren Ustaz… Hararar gefen ido kawai nake watsa masa, ina ganin Ya Muhd d’in kamar wani gagarumin mak’iyina. Ganin ba zan amsa ba ina kallo Suka fice shi da matarsa suka rufo min k’ofa… Na cusa hannuna cikin gashin kaina ina jin zuciyata na wata irin suya. Hawayen ma k’in zubowa suka yi. Kawai wani irin kuka nake na zuci. Ban san iya lokacin da na ‘d’auka a kwance a wajen ba, sai ji na yi wata ta yi k’ara na duba naga msg d’in Ustaz ne ya shigo wayata. Tsaki na zuba kamar ba zan karanta ba sai dai na bu’de sai naga ya saka “Alhamdulillah an ‘d’aura aure na, ina jiran fatan alheri daga k’anwata….. Duum naji na daina ji da gani… [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group for updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more https://chat.whatsapp.com/FuUV3xjAcKgDaquGHnOnjw https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 14 14….. Tun daga kwanyata nake jin wani irin zafi, har k’asan zuciyata. Jikina ya yi sanyi sosai kukan ma ya kasa zuwa sai wani b’acin rai nake ji mai dugunzuma zuciya, ya raunata gabban jiki. Da k’yar na sulale na zame na kwanta a k’asan carpet ina lumshe idona. Tafarfasar da zuciyata take yi yasa na dinga jin kai na yana neman yin tsawa. Gashin kaina na burkita gaba d’aya ina jan gashin da k’arfi kamar shi ya min laifin. Kuka nake son yi amma kukan ya k’i zuwa. Rigar barci ce a jikina ban kuma damu da na cireta ba, don bata wankan nake ba. Sai yanzu na ji ina jin haushin biyayyar da na yiwa Mameey, kamar na cuci kai na kamar ni na jawowa kai na. Ina kwancen cikin tafasar zuciya idanu na a kulle. Na ji kamar wani na tsaye a kai na. Da k’yar na dinga bu’de lumsassun idanuna sai na ga Ustaz ne a tsaye sake mayar da idon na yi na kulle don ina tunanin imagination d’in da na saba ne. Daf da ni na dinga jin k’amshin mayataccen turarensa, don haka na ware idona sosai na zuba su a kansa. Yana zaune daf da ni idanunsa a kaina yana sakar min murmushi. Da sauri na mik’e cikin razana ina neman ko Hijab ne da zan suturce jikina don rigar barci ce a jikina itama iya gwiwa mai santsin gaske, sanda suka tafi na ji abin duniya ya min zafi ban san sanda na wancakalar da Hijabin can gefe ba. Hijabin yana daga can bakin k’ofa. Ga shi sam ba zan iya tashi ba. Na takure gefe guda ina rufe jikina duk da na san ba abinda bai gani ba, don ban san tsawon wani lokaci ya ‘d’auka a wajen ba. Murya a sark’e na furta “Ya zaka shigo min haka? Ba sallama ka bani Hijab ‘dina…” Still kallona yake yana murmushi kawai bai kuma mik’o min Hijab d’in ba. “Please Ustaz, ka bani Hijab ‘dina….” Na furta kamar na yi kuka. Muryarsa a sark’e ya lumshe ido… ya furta “Idan na k’i fa?” A tunzire na furta “Amma dai ka san haramun kake kalla ko?” Sake k’ura min ido ya yi kafin murya can k’asa ya furta “Da jikin da Mai jikin yau duk mallaki na ne, Matar Ustazunta…” wani irin ware ido na yi don ni duk ban fuskanci manufarsa ba. “Tashi ki ‘dau Hijabin naki…bari na rufe ido na..” Ya fa’da yana rufe idon nasa. Ban san sanda na wani irin mik’ewa da sauri ba don ‘d’aukar Hijabin, sai ji na yi kawai ya jawo ni na fa’do jikinsa ya saka hannu ya rungumeni sosai yana sakin ajiyar zuciya. Idona a waje nake furta Ustaz me ye haka? Ina matar taka?” “D’aya matar tawa tana gidansu Aysha, ga uwargidan anan.” Ya fa’da min cikin wata murya a kunnena. Da sauri na wani kalar Zillo na bar jikinsa ina kallo ya yi baya ya jingina da kujera idanunsa a lumshe yana sakin ajiyar zuciya… ni kuwa kallonsa kawai nake ina mamakin jin abinda ya ce da gaske an ‘d’aura mana aure shi? Kuma mu biyu da wata. Duk da na yi farin ciki amma kishi bai barni na bayyana farin cikin ba. Zuciyata na sama da k’asa na dinga kallonsa still idonsa a lumshe.. na furta “Wai da gaske aurena aka ‘d’aura ni da kai da wata kuma?” Idanunsa a lumshen ya ‘d’aga kai. A zafafe na ce “Tab’di! Ni Allah ban ce maka ina son mai mata ba…” “Aysha bana son surutu, ki tashi ki shirya mu je gidanku, Abba yana jiranki abokai na suna jira su ga matata za su koma garuruwansu. Ba lallai ku sake ha’duwa ba sai lokacin tariya.” Ya fa’da yana mik’o min wata leda mai kyan gaske. Ledar na bi da kallo ina amsa ya jawo ni jikinsa. Kissing ‘din lips ‘dina ya yi ka’dan yana jan karan hancina ya furta “Am sorry for this, na da’de ina jiran wannan ranar. Sai ga shi Allah ya bani ku ku biyu… “ Turo baki na na yi cikin matuk’ar jin kunya na sauka daga jikinsa. “Wa yace ki sauka? Kin san dai ba haramun ba ne ko?” “Ni dai bana so, ka je wajen waccan matar.” Na fa’da idona na zubar da hawaye. Murmushi ya yi yana furta “Don kuwa baki ga yarda ta yi kyau ba, ta yi kwalliya sai zabga wani irin k’amshi take mai sanya tunani a rai. Ke kuwa ko wankan bana jin yau kin yi, saboda kina Cikin tashin hankalin kin yi rashin santalelen saurayi irina ko?” Turo baki na yi na shige ciki da sauri. Ina jin sautin murmushin Ustaz. Sai da na murza key a ‘d’akin don naga kamar Ustaz yau ya cire kunyarsa gaba d’aya. Wankan na yi sosai har kamar fatata zata futa, don duk dole ina son nafi waccan matar kyau. Ina cikin zura rigar lace a jikina na ji muryarsa a bakin k’ofa. “Bu’de Aysha..” wani irin waro ido na yi na furta “Na bu’de na Maka me?” “Idan ba zaki bu’de ba, answer your phone..” Sai sannan na kai idona kan wayar naga numberrsa da na yi saving da Ustazu na, tana ringing. Amsa wayar na yi. “Kada ki yi kwalliya, kada ki saka turare kuma don zaku gaisa da abokaina…” Ya furta yana kashe wayar. Ban saka turare ba, amma na yi kwalliya don haka kawai ba zan bari wata can ta fi ni kyau ba. Na fito tsaf da ni cikin laffayar da ta zauna das a jikina ta fitar da shape ‘dina sosai. Idon Ustaz a kaina yake kallona ya furta “Cab a hakan zaki fita?” Na ‘dan turo bakina “To ba kai ka kawo kayan ba?” Mik’ewa ya yi ya isa kusa da ni, yana jana jikinsa da sauri na fara turjewa ya rik’e ni sosai yana furta “Bana ce kada ki yi kwalliya ba, wa yace ki yi, tsaya na goge jambakin nan.” Cak na tsaya a zatona gogewar zai yi sai na ji bakinsa a saman leb’ena yana tsotsa a hankali. Da sauri na waro ido. Ya sake ni yana murmushi ya bushe min idon da iskar bakinsa. Yana furta “Gobe ma ki sake k’in bin umarnina, ki je ki sako Hijab, ba zaki fita da wannan abin ba, Ji k’irjinki ji yarda ta fitar da zahirin Suffar Aysha…” Ya fa’da yana shafa gefen Hips ‘dina. “Anya Aysha zan iya jira ki gama secondary ‘din nan, kamar yarda Abba ya buk’ata? Ba zan iya ba zan wahala sosai wallahi, duk da dai ina da wata matar, amma kuma zuciyar tana nan…” Ya fa’da yana ‘dage min gira ka’dan. Turo bakina na yi ina jin zuciya ta na shirin tafasa na furta “Ni ka daina min zancen matarka.” Yatsansa ya saka yana zagaye leb’ena da su, yana murmushi ya sake ba su sumbata sannan ya lumshe idonsa ya furta “I like those kissable lips, na da’de ina mafarkin wannan ranar.” Shiru na masa ina jin sauyawar yanayi tare da ni. Sakin ajiyar zuciya ya yi yana furta “Wannan karatun boko…. Shikkenan maza ki je ki saka Hijab Madam, ana jiran mu.” Na juya d’akin Anty Khadija. A drawernta na samo Hijab mai kyau da ya shiga da kayan na saka. Ina fitowa na tarar Ustaz har ya mik’e yana waya k’asa k’asa na ji yana furta “Ki jira na ce, zan zo yanzu ko Habibteey…” Wani irin duum na ji a raina. Ya mik’o min hannu yana furta “Zo Aysha ku gaisa da Habibteey…” Banza na masa idona na shirin zubo da hawaye na fice daga gidan da sauri. Sai ga shi ya biyo bayana na kulle k’ofar. Banda ina son zuwa gida cewa zan yi ba zan bi shi ba. Ya shiga mota ni ma na shiga fuskata a ha’de shima bai min magana ba ya ja zuwa gidan mu. Sai da na ganni a k’ofar gida sannan hankalina ya dawo jikina na tuna da batun Mami ko ta amince da auren? Gaba na ya fa’di sanin cewa ba lallai ta amince ba tunda ko jiya da ta je gidna Ya Muhd ban ga alamar haka a tare da ita ba. Zan fita daga Motar ya ja hannuna ya rik’e cikin nasa yana kallona. “Idan baki saki fuska ba zan mayar da ke.” Na ha’diye tashin hankali na na furta “Ba wajenta zaka ba?” “Ina ruwanki, ki yi abinda yake gaban ki, and kada ki sake ina magana ki yi gaba hakan raini ne, kin ji ko? Idan baku gaisa kun saba ba sai yaushe zaku gaisa, idan na gama da ke, zan tafi wajenta da daddare kuma ki shirya zan zo na kai ki wajen su Mommy kafin su yagalgala nama na…” Yawu na ha’diye ina sauka daga motar bayan na sake nik’ab ‘din fuskata don haka kawai sai na ji ina jin kunyar ha’duwata da jama’ar gidanmu ban san kalar tsiyar da suka tanadar min ba. Dariya Ustaz ya yi ganin yarda sam na kasa sake jiki na fita. Ya juya yana kallon cikin harabar gidanmu. Kafin ya furta ko na kira miki Muhammad ya shiga da ke?” Da sauri na ‘d’aga kaina. Don hakan zai fi kin sauk’i akan na shiga da kai na. Ina kallo ya dannna wayar hannunsa ya kira Ya.Muhd. Bai ko d’au lokaci ba, sai ga shi ya fito fuskarsa d’auke da murmushi yana kallo na. “Amarya..” Turo bakina na yi na furta “Ya.Muhd, bana so, shine baka gaya min ba sai da aka d’aura auren.” Murmushin ya sake yi ya ce “Ba gashi yanzu kin sani ba, gaya min are you happy or not?” Ya kama hannuna muka nufi cikin gidan. Ina ji Ustaz yana fa’din idan na gama yana jirana a sitroom. Tsakargidan taf da mutane, ta cikin nik’ab ’dina na dinga ganinsu, y’an Uwan Umma, Y’an Uwan Abba da y’an Uwan Mami sai hira ake cikin annashuwa da farin ciki. Har sama Muhammad ya kai ni bai bari an ganni ba, ya shigar da ni parlorn Mami. Parlorn nata shiru ba kowa. Sai k’arar Tv. “Ki shiga Mamin tana ciki, ki san yarda kika yi kika kwantar mata da hankali, don tun safe ta k’i bari kowa ya ganta, ta yi fushi sosai don har kuka yau ta yi a gaban Abba, ta furta Kalmar da ta tsayawa kowa a rai, don an ga ita Allah bai bata haihuwa ba….Jikin kowa kam ya yi sanyi, don haka ki rarrasheta..” Ya Muhd ya fa’da yana saka yatsansa guda a idonsa ya ‘d’auke k’wallar da ta tarar masa a k’asan idon. Wani irin fa’duwar gaba na shiga, idona a waje cikin tashin hankali na furta “Ba da sanin Mami ba, aka ‘d’aura min aure?” Muhammad ya ‘d’aga kai “An yi kuskuren da kowa yake dana saninsa, don kam baa kyauta mata ba, shi kansa Abban zan iya cewa ya yi nadama, amma ba hak’urin da bai bata ba ta k’i saurararsa ta ce sai ya saketa tunda bata da wani amfani a wajensa…” Wannan karan sai dana dafe k’irjina jin abinda ya ce na zube a kan kujera ina mayar da ajiyar numfashi. Ina ji Yaya Muhammad ya fice yana sake jaddada min na aikata abinda ya ce ‘din. Na kai mintuna biyar kafin na daure na isa d’akin nata cikin tashin hankali na mur’da k’ofar. Sai na jita a kulle, a hankali na fara nocking in kiran sunan Mamin cikin tashin hankali. Tsawon lokaci kafin ta bu’de k’ofar, na ‘dago idona ina kallonta hawaye ne yake zuba a idon nata ya yi jajur, cikin tashin hankali na zube a jikinta, amma sai naga ta janye ni tana min wani kallo da ya kusa ‘d’auke min numfashi na….. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ ‎ Kin shirya Siyam lunch box ko duk wasu kayan yara na buk’ata musamman yanzu lokaci ne da za’a koma makaranta. To akwai tanadin da Tinysteps_ng ta yi muku na samun duka abinda kike so da ya danganci back to school akan farashi mai rahusa… abin buk’ata kawai garzaya da gudu ki shiga cikin group ‘din, ta hanyar danna link. Zaki ganki tsundum cikin companyn Tinysteps_ng… Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group fouf updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more https://chat.whatsapp.com/ https://www.arewabooks.com/chapter?id=66a2a58ee86f6001e809b915 Akwai page 15 a arewa, ku duba ku Karanta a can. Gobe ina biki ba zan samu posting ba. Na gode [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 15. ‎Kin shirya Siyam lunch box ko duk wasu kayan yara na buk’ata musamman yanzu lokaci ne da za’a koma makaranta. To akwai tanadin da Tinysteps_ng ta yi muku na samun duka abinda kike so da ya danganci back to school akan farashi mai rahusa… abin buk’ata kawai garzaya da gudu ki shiga cikin group ‘din, ta hanyar danna link. Zaki ganki tsundum cikin companyn Tinysteps_ng… Hello! We are Tinysteps _ng do well by joining our group fouf updates on our unique kid’s dress back to school supplies toys and lots more https://chat.whatsapp.com/ ★✍️ Idanunta zubar da hawaye kawai take, tana pointing d’ina da hannunta, bakinta na rawa so take ta furta furucin da yake kan harshenta sai dai da alama harshen nata ya kasa bata ha’din kai. Sai kawai na ji ta kamani ta min wata irin kyakykyawar runguma tana sakin kuka kamar zata mayar da ni cikinta. Zuciyata da ta ta duka a tare suke wani matsanancin bugu. Kukan kawai nake nima don na kasa jurewa. Ban san tsawon lokacin da muka ‘dauka a haka ba. Sai da Mami ta gaji sannan ta ‘dago ni tana share min hawayen ido na. Tana sakin wani guntun murmushi ta furta “Ina miki murna AYSHA, ina wa iyayenki Murna….” Da wani irin zafin nama na rufe mata baki ina girgiza kai. Muryata a shak’e alamar na ci kuka da yawa na furta “Kada kice haka Mami, Wallahi bani da wasu iyaye bayan ke, ke nake wa kallon Uwa tunda ke na bu’de ido na gani a matsayin uwata. Wannan auren nawa tabbas k’addara ce don Allah Mami ki yi hak’uri, ki daina nuna fushinki, kada mutane su yiwa abin wata fassara…” “Fassara?” Ta furta tana cije leb’en bakinta, sai kuma naga ta saki murmushi ta furta shikkenan na san k’addara ce Aysha na kuma yarda da ita, In sha Allah zan daure zuciyata, duk da na san ba zan tab’a iya kawar da damuwar da take zuciyar ba, amma zan yi hakan musamman don idon mutane da kika ce..” Da farin ciki na rungumeta ina sakin ajiyar zuciya. Ta ja ni jikinta ta bani kiss a gefen kumatu. Tana jan karan hancina ta furta “Yanzu AYSHA ke matar aure ce ko? Ustaz zai raba ni da ke da zarar kin gama secondary?” Sai kawai ta ciji leb’enta ta ja hannuna zuwa cikin d’akin. Tana furta “Cire Hijabin nan, abin wani banbarakwai amarya da hijab. Cire maza na gyara miki fuska mu fita a gaisa da mutane, idan da mai hoto a Mana..” Duk da ban manta da garga’din Ustaz ba haka na amince Mami ta zauna ta tsantsara min kwalliya. Don Mami gwanar kwalliya ce. Sai ga shi na zuba wani irin fitinannen kyau. Laffaya sabuwa dal ta ‘d’auko ta na’da min. Ta kuma saka min wasu irin turaruka masu mugun k’amshi. Zuwa lokacin naga kiran Ustaz yafi nawa a wayata. K’arshe da ya gaji sai ya turo min text. “AYSHA kina ina ne? Ki zo yanzu mun gama cin abinci tafiya za mu yi. Ban da makeup banda turare pls!l” k’irjina ne ya d’an buga ganin ya sake warning ‘dina a kan hakan, sai dai ban isa na bujirewa Mami ba. Tana murmushi ta ja ni jikin mudubi ta rungumoni muka d’au hoto da wayarta, mun yi masifar kyau sosai. Ta d’an ja hancina, tana furta “You look Gorgeous Ayshan Mami.” D’an murmushi na saki itama ta yafa nata mayafin mai kauri muka fita tsakar gida. Mutane suna ganinmu aka taho wajenmu da sauri ana muna gu’da a kai. Mami murmushi kawai take tana amsa Allah ya sanya alherin da ake mata. Nan aka fara mata d’an biki ana fa’din Mami girma yazo an samu suriki. Ya Muhammad ne ya shigo yana fa’din Ina AYSHA take ne? Ke kizo in ji abokan ango. Na mik’e zuciyata na wani irin bugu na ja hannun Asma da wata k’awarmu muka nufi sitroom d’in. Kaina a k’asa kawai yake, ina jin ‘dan bikin da suke min, bayan amsa gaisuwar su Asma da suka yi. Sai jin hannun Ustaz na yi a jikina yana ja na d’akin su Aliyu da yake cikin sitroom d’in. Aka saka masa dariya gaba d’aya. Bai kula su ba sai da muka shiga cikin d’akin ya kullo k’ofar da k’arfi ya zuba min tsumammun idonsa. Lumshe idon na yi ina jin bugun zuciyata na tsananta don na san ni mai laifice a wajensa. Madadin na ji ya yi magana kawai jin bakinsa na yi saman nawa yana tsotse jambakin bakina kamar ya samu alawa. K’wace jikina nake son yi amma ya k’i bani dama don ya rungumeni tsam a jikinsa. A kunne yake ra’da min cikin wata irin murya “Rashin kunya ko? Da kunnen k’ashi, bana ce kada ki yi kwalliya ba kada ki saka jambaki, ki kuma fito da hijabi shine baki ji ba kika yi kunnen uwar shegu kika na’do wannan abin kika fito?” Ya fa’da yana zagaye hannunsa a shaffafen cikina zuwa saman k’irjina “Ji fa Aysha, ji nan wajen duk sun fito tsaf a cikin kayan, kowane banza ya kallesu kike so? Bayan mallaki na ne….” Tsaf na rufe idona, cikin matsananciyar kunya, kamar yarda na Ustaz ‘din ma suke a rufe, Murya na rawa na ce “Ustaz ka bari kai fa Malamin addini ne.” “Malamin addini baya soyayya? Baki san annabi ma ya yi soyayyar da ta fi wannan ba?” Ya fa’da min cikin wata irin murya yana shinshinar wuya na. “Turarenki Aysha yana jefa ni a wani yanayi ya sunan sa?” Kuka nake son na saka masa don duk wani yanayi nake ji a jikina. “Pls Ustaz ka bari!” “I can’t Aysha, na da’de ina jiran ranar da zan gan mu a haka, pls kice a gida kina so ki tare zaki yi karatun a gida….” Ya fa’da yana bu’de lumsassun idanunsa da suke dawo wata colour cikin nawa… “Your Love gonna make me crazy Aysha…” Ka’dan ya rage ban sume ba, a yanayin da ya yi maganar…. Kasa furta ko kalmar ‘a’ na yi, saboda matsananciyar k’aunarsa. Na Dai d’an janye jikina ina furta “Ustaz, mutane fa suna jiran mu.” ya min wani kallo kafin ya girgiza kai “Ba zaki ko ina ba, a haka zaki wajen maza? Wa’dannan halittun nawa ne ni ka’dai, Allah ni ka’dai ya mallakawa.” Daga haka ya fice da sauri yana jan k’ofa. Ban San ya suka yi ba, ya dai lek’o yana furta min “Wifey zan dawo around 7:30, ki shirya.” Na ‘d’aga kai na. Ina kallo ya fice wani haushi ya cunkushe min zuciya, na san ba mamaki wajen waccan zabiyar zai je… haka na ce a raina kafin na mik’e a kasalance na fice daga ‘dakin jin su Asma suna kira na. Saman Mami na sake hawa da su, suna ta min iya shege iri iri saman ma ba kowa da alama Mamin ta sauka. Na zauna akan kujera ina kallon Asma da bakinta ya k’i rufuwa. Ta furta “Wallahi lamarinku da Ustaz, AYSHA abin sha’awa, ta k’wayar idonsa ake gane zallar k’aunar da yake miki.” Murmushi kawai na saki ina gyara zama na. Sa’ada ma murmushin ta yi ta furta “Ke mai sa’a ce AYSHA, irin sa’ar da kowace mace take son ta samu. Allah ya baku zaman lafiya amma na san yau fa kin tarwatsa farin cikin y’an mata da yawa, don ko a Islamiyya Ustaz Ahmad ya tafi da zuciyar y’an mata da yawa…” Haka dai muka yi ta hirarmu. Har nake sanar da su zamu fita da Ustaz da daddare Amma ina tsoron na gayawa Mami. D’an waro ido Asma ta yi sai kuma ta tuntsire da dariya “Mhmnm Fa Aysha, ba wai na ji ance ba yanzu zaki tare ba, kada Ustaz…” Ta fa’da tana rufe bakinta tana dariya… Na yi tsaki ina dukanta a cinya na furta “Ni y’ar yarinyata da ni, me Ustaz zai ‘d’auka a jikina…” “Abubuwa da yawa mana, ai shi ya ga mai ya gani ya nace miki, Allah dai ya kai mu next year mu sha biki…” Sa’da itama ta fa’da tana dariyar… shigowar Mami ce ta saka muka ja baki muka yi shiru. Ta ‘dan kallemu tana murmushi ta furta “Aysha ki sauka k’asa, ku gaisa da mutane…” na mik’e su Asma suka bi ni suka saka ni a tsakiya muka sauka. Babban parlorn da ya kasance na Abba nan muka fara shiga, inda y’an uwan Abba suke. Da fara’a duk walwala suke amsa gaisuwata. Umma Dijah ta kasa shiru tana furta “Ai kin dace Aishatu, Ubangiji Allah ya sanya albarka a auren ya nuna mana ranar tariya.” Kaina a k’asa na kasa amsa ameen ‘din sai wasa nake da zoben hannuna. Daga nan muka shiga parlorn Umma. Zo kiga farin ciki yarda suka rungumeni suna ihun ga amarya ga amarya. Murmushi kawai nake saki. Inna laddu kuwa k’anwar Babar Umma cak ta saka ni a cinyarta tana furta “Ma sha Allah tubarakalla dole Ahmadu ya tubure sai an d’aura aure. Haka kika sake zuba kyau.” Na ‘dan yi dariya kawai ina kallon Umma na, da ko kallona ba tayi ba sai dai murmushi sam ya kasa barin fuskarta. Na da’de anan d’in kafin na zame jiki na koma sama, inda y’an uwan Mami suka cika wajen. Suma da farin cikin suka tare ni. Mami kuma Ta ware a cikinsu sai farin ciki take. Na zauna daf da ita na kwanta a jikinta kaina a saman cinyarta na lumshe ido. Barci mai nauyin gaske ya ‘daukeni, na san barcin da ban yi bane a daren ranar yake d’aukata. Mami bata tashe ni ba sai daf da la’asar na ‘dan ware idona. Ina kallon wajen, ba kowa sai Mamin da k’awayenta guda biyu. Duk suka zubo min idon da yasa har na ji kunya na mik’e na bar wajen da sauri na shige ‘dakina. Sallah na yi ina idar da sallahr na sauka k’asa wajen Umma. Har lokacin jira nake na ji Ustaz ya kira ni amma bai kira ba. Kawai sai zuciyata ta dinga bani yana can wajen amaryarsa. Don takaici har wata k’walla ce ta so zubo min. Na matse ha’de da tura k’ofata parlorn Umma. Ba kowa a parlorn da alama duk bak’in sun tafi. Sai Umma ita ka’dai da k’anwarta suka ‘dago suna kallo na. Umma ta d’auke kanta. Sai Anty Zee ce ta ce “Shigo mana Aysha kin ci abinci?” Na ‘d’aga kai na “Na ci Anty.” Ta yi murmushi tana fa’din amaryar da ba lalle, wannan aure naki Aysha Ai shine bagatatan. Yaushe ya ce zaki ki gaida iyayensa?” Wani farin ciki ya shige ni don abinda nake son na ce kenan, amma ba kasa gayawa Mami balle Umma. Na gyara zamana ina furta “Yau ya ce Anty..” Ta saki murmushi tana fa’din “Kin ji ko Yaya, ai na san wallahi kawai zan ce ne, ace kawai mutum ya auri mace sai ya zuba mata ido alhali sabon shiga ne a aure a ce wani sai ta k’arasa karatu, karatun me Allah na tuba a gidanta ba zata yi karatun ba, wallahi kada ki bi ta wani karatu ki tattara y’a ki mik’a d’akin Mijinta….” Umma ta waro idonta tana furta “Rufa ni ki saya, ni meye nawa da za’ace ni zan saka a kaita d’akin Miji, ki bar uwarta y’ar a lallab’a da yaya ma aka samu aka shawo kanta a yau d’in. Shekara kamar yau ne, Idan Allah ya kai mu.” Anty ta yi d’an tsaki tana kallon Umman ta ce “Allah ya kai mun, idan da rabon an yi taron suna ne ba taron biki ba sai mu ce san barka…” Da sauri na mik’e na fice daga ‘dakin cikin matsananciyar kunya. Na koma saman Mami. Bak’in sun tafi sai ita ka’dai zaune ta zuba hannunta a k’unci. Har na zauna daf da ita ba ta sani ba sai da ba dafa ta sannan ta juyo a razane tana d’an kallo na. Ta furta “Aysha ce?” Cike da tausayinta na ce “Mami kin ci abinci?” Ta ‘d’aga min kai tana d’an murmushi. Na yi shiru ina wasa da yatsuna na furta “Mami Ustaz ya rok’i alfarmar yana son na je gidan su yau after magriba….” Mami ta ‘dago tana kallona, idanunta suka bayyana tashin hankalin da zuciyarta take ciki. Ta gyara zamanta tana sakin ajiyar zuciya sai kuma ta kama hannuna murya a raunane ta ce “Ba zan hanaki bin sa ba AYSHA, don yanzu duk duniya ba wanda yake da iko da ke sama da shi. Sai dai zan rok’i alfarmar ki tsare jikinki, don maza mayaudara ne idan dama jikin naki yake so da zarar ya kusanceki zai iya sakin ki tun kafin ki tare…. Ki min alk’awarin ba zaki bari Ustaz ya kusanceki ba..” Na d’aga kai na, ina ji har a zuciyata na amince da abinda Mamin ta ce. Ta sakar min murmushi ta furta sai ki shirya da wuri kada yazo yana jiranki amma banda saka turare… na d’aga kai. Da magriba ina idar da sallah Mami ta shigo d’akin hannunta d’auke da wata leda. Ta zauna a gefen gado. Tana bu’de ledar wata doguwar Riga ce mai masifar kyau kalar bak’a da stone golden ta yi matuk’ar kyau. “Ki saka wannan, sai ki je gidan nasu, idan kin je kuma bana son rawar kai ki nuna musu ke mai tarbiyyace.” Na amsa ina godiya. Bata amsa ba ta wuce ta fita. Da wata irin murna na zura rigar a jikina na shafa powder sama sama, sai na yi rolling. Ba k’aramin kyau na yi ba ni da kai na na sani. Sanda na fita parlor sai naga Mami bata nan. Na san tana k’asa na sauka k’asan don Ustaz ya isheni da kiran waya. Yarda na zata kuwa suna tsaye a kitchen ita da Umma. Suka juyo suna kallo na. Anty Small ta furta “Ma sha Allah, Allah ya yi halitta.” Mami ta dafa ni tana furta A dawo lafiya, and take care AYSHA. Ga wata leda nan ki kaiwa Inlaw d’inki abinda ke ciki…” Na d’au ledar ina murmushi na fita k’ofar gida don na san Abba yana masallachi sai dai su Umma su gaya masa. Cikin takun nutsuwa na isa bakin motar na saka hannu na bu’de k’ofar gaban motar. Gaba na ya yi wani irin mugun fa’duwa ganin Habibteeyn Ustaz a gaban motar, ta sha kwalliya ta yi masifar kyau tana zabga k’amshi. Murmushi ta ‘dan saki ni kuwa fuskata a tsuke na juya da nufin komawa gidanmu don wallahi in dai da wannan za’a ba zan je ba…. Kai bana jin ma zan iya kishi da zanka’ded’iyar mace irin wannan habibteeyn ta Ustaz ba. Ta ko ina ta fi ni…. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 16. ‎16… AYSHA! Na ji Ustaz ya fa’da cikin muryarsa da take bayyana ginshira. Na ja na tsaya sai dai ban jiyo ba, Saboda bana son na jiyo d’in naga Habibteeyn Ustaz. Rufe k’ofar Motar da aka yi ya tabbatar min da ya zo wajen. A daf da ni ya tsaya. Kafin na juyo na ji hannunsa a cikin nawa hannun. Da kansa ya juyo da ni yana k’ok’arin lalubar idanuna ni kuwa na ja na runtse idon. “Wuce mu tafi.” Ya ce cikin wani cool voice da ta so ta saka raunin da yake zuciyata ya bayyana… “Ni ba zan shiga ba..” “Me yasa?” Ya fa’da bayan jin abinda na ce. Na d’an turo bakina ina furta “Ka je kawai, ka je ka kaita ni na hak’ura..” wani murmushi ya saki yana furta “Tafiya da ita ne ba kya so?” Na d’aga kai na. “Me yasa zaka zo da ita?” Na fa’da hawaye suna son zubo min. Ustaz murmushi kawai ya saki ya ce “Maza ki yi kuka a gabanta ta raina ki.” Na matse hawayen ina kallon cikin idonsa da suke lumshewa kamar me… “Ku je zan saka Ya Aliyu ya kai ni a motar Abba..” cute smile d’in ya sake yi yana jan hannuna har kamar zan fa’da jikinsa. Ya furta “Yanzu dai ba kya son Third Party a Cikin tafiyar mu ko?” Da sauri na d’aga kai. Sai naga ya saki hannuna yana murza goshinsa a hankali. Kallon k’asan ido yake min kafin ya jefa min tambayar da ta so saka ni zubewa a k’asa tsabar yarda jikina ke rawa. Cewa ya yi “Kina so mu ka’daice, in har kika yarda muka tafi mu ka’dai zaki min deep kiss a cikin motar…” ya fa’da yana murza hannuna. Da sauri na janye hannun ina furta “Mu je kawai, amma ta koma baya tunda nice Uwargida.” “Done wifey ya furta yana dariya k’asa-k’asa. “Hannunki AYSHA so soft, har bana son na daina tab’awa…” Da sauri na janye hannun ina dubawa naga ko Maigadi ya ji, sai na ga ma baya wajen. Muka isa bakin motar hannuna cikin nasa yana ta murzawa. Ja na yi na tsaya ina jin zuciyata kamar ta buga, ganin yarda Ustaz ya durk’usa daf da ita yana gaya mata magana. Sai naga ta ‘dan ha’de rai ta fito tana min wani kallon banza ta shiga bayan motar. Murmushi na saki ina jin duk wani bak’in cikina ya yaye. Na shiga gaban Motar cikin jin haushin yarda da ta zauna a motar… “Baku gaisa ba?” Muka ji muryar Ustza daga sama bayan Mun fara tafiya. Shiru kowa ya yi har sai da ya sake furta “Ba kwa ji ne ina magana…” Sannan ta furta “Ina yini?” A ciki na amsa don sai naga kamar ta fini sauk’in kishi. Wani irin wawakeken gate muka shiga, inda muka tarar da makeken fili. Ustaz ya yi Parkin ina kallo ta fice cikin takun isa da son ta nuna min ita ta san gidan tunda cousin ‘d’insa ce. Na d’an ha’de rai ina cije leb’ena idona suka kawo ruwa. Ustaz ya sunkuya yana kallona ka’dan, tunda mu ba mu fita daga cikin motar ba. Ji na yi ya kaiwa bakina sumbata ya kuma lashi d’an guntun hawayen da ya zubo min. “Kukan menene?” Ya furta a cikin kunnuwa na. Da sauri na rintse idon, don na lura Ustaz so yake ya kashe ni da salonsa. “Mu je mana Zauj, ko sai na d’aukeki..” na d’an turo bakina ina furta “Ba ga shi can har ta wuce ba, so take ta nuna min lallai ta fi ni iko da gidan ku.” Yatsa ya saka yana zagaye lab’b’ana. “Wato ashe bakin nan ya iya tsiwa? Amma da kike kasa sak’at idan kin ganni a wuri. Mu je na raka ki kin ji tunda ita ta nuna mana gidansu ne ta tafi ta barki.” Ya fita ya zaga ya bu’de min mota. Zai rik’e min hannuna na janye ina d’an duban hanya na furta “Ka bari mana, kada wani ya gan mu?” “And so what? Idan an gan mu Ai ba haramci muka aikata ba ko?” Ya fa’da yana tsotsar bakina ka’dan. Na lura lips d’ina suna burgeshi. “Ke halak d’ina ce Aysha, a yanzu ba wani shamaki tsakaninmu da ke, sai wancan karatun da Maminki ta kafe sai kin yi, Wallahi ba ruwana duk ranar da ta wayi gari ta ganki da ciki….” Da sauri na waro ido jin abinda ya fa’da. Ya lumshe ido yana d’aga kai ya ce “Am serious Eesh baki san yarda nake ji akan ki ba…” ya fa’da yana jan hannuna. Da sauri na janye hannun nawa ganin yarda mutane suka fara fitowa daga k’ofofi daban daban an ware ki’dan larabawa suka zagaye mu da Ustaz. Sai fa’dar Marhababuki lale suke. Kana ganinsu kaga jinsin larabawa don farare ne k’al da su. Ustaz d’an murmushi ya saki ya yi saurin zamewa ya bar ni da su. Matar mai kama da Ustaz kwabo da kwabo ita ta k’araso inda nake ta kama hannuna tana ha’dani da jikinsa tana fa’din “Marhababuki Ibnateey…” Wani irin sahihin k’amshi ne kawai yake fita ko ta ina a gidan. Suka ja hannuna zuwa cikin gidan. Kaina a k’asa k’irjina sai bugu yake, amma matar bata cika hannuna ba. Sai da muka isa cikin babban parlorn gidan. Tabbas gidan su Ustaz ba k’arya ya ha’du kana ganinsa ka san sun ci sun tada kai da naira, babu gami sam tsakaninsa da namu gidan. A kan kujera ta zaunar da ni, amma sai na zame na zauna a k’asa. Ina gaishesu a kunyace. Kishiya ta ce tazo kusa da ni ta zauna. Tana kama hannuna na ji kamar ta zubar garwashin wuta a hannun, da sauri na janye sai na ji ta yi dariya ta furta “Am not his wife, he was just joking… ni k’anwarsa ce the only Sis da yake da ita….” Innalillahi na furta a hankali kunyar rashin mutuncin da na mata nake ji, dana sani ya shige ni sosai. Ta yi dariya sosai ta fara bawa mutanen parlorn labarin acting d’in da nake idan ta ce musu ni matar Ahmad ce. A raina na ji ba zan k’yale Ustaz ba sai na rama, wannan ai ba wasa ba ne. Dariya sosai mutanen parlorn suka fara. Mommy ce ta ce “Ahmad ba zai miki kishiya ba, ke ka’dai kin ishesa In sha Allah, Son da Ahmad yake miki ba a kwatancensa Allah ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba.” Ta juya tana kallon k’ofa. Ta furta “Ibnateey maza kirawo min shi, a yi addu’a kafin a fara cin abinci..” Da sauri kuwa naga Habibteey ta mik’e ta nufi inda zata kira shi. Sai ga shi ya fito cikin wata jallabiya brown color yana shigowa da ni ya fara ha’da ido. Na d’an turo bakina ina masa hararar gefen ido, kafin na sake jan mayafi na rufe fuskata. “Ahmad kazo ka ciyar da matarka kamar yarda al’adarmu take at first day of marriage.” Wata mai kama da Mommyn ta fa’da tana sake janyo Ahmad zuwa inda nake. Zuciyata kawai bugu take ina tunanin ta yaya zai ciyar da ni? Daf da ni ta zaunar da shi har jikina yana ha’duwa da nasa. Ta kawo masa kayan abincin gabansa. Da kansa ya yi serving d’inmu. Kafin ya ‘dago yana kallon auntyn nasa, ta ‘d’aga masa kai “Oya ka fara mana, ina jira zan yi pic..” Hannunsa ya saka ya ‘d’aga mayafi na. Da sauri na runtse ido, ganin ya kai dabino guda baki na. A hankali ya furta bu’de bakin…” “Amma ka san ba haka muke ba ko?” Anty ta fa’da ranta a b’ace. Ina kallo ya d’an yi dariya, sai kuma ya mayar da dabinon bakinsa ya gutsira ka’dan ya tauna ban yi auneba na ji bakinsa cikin nawa yana zuba min taunannen dabinon. Jikina ne ya fara rawa da sauri na rik’e numfashina da yake son d’aukewa ganin still YUstaz bai cire bakinsa a cikin nawa ba sai juya harshensa yake cikin wani salo da lumsassun ido, sai da ya tabbatar na ha’diye sannan ya janye yana ‘dan murmushi. Ihu da Kabbara suke kawai a gidan. Aka dinga mana hotuna ni kuwa duk kunya ta saka jin jikina wani iri na sunkuyar da kaina kawai na kasa ha’da ido da kowa. Anty ce ta ce Khadija ta tafi da ni d’akinta sai a kai min abincin can tunda na kasa sakewa da su, su al’ada garinsu ce haka, ba abin kunya ba ce, rana ce mai mahimmanci a wajensu da ake wa saurayin da bai tab’a aure ba, don a ga yanayin da zai shiga a yi dariya idan an ga abinda zai yi a first deep kiss ‘d’insa. Ni dai tuni na bi bayan Khadija jikina na rawa muka isa ‘d’akinta. Muna shiga ta janye mayafin fuskata tana dariya. “Bud’e fuskar Anty AYSHA na ganki da kyau, tunda dai nan daga ni sai ke..” Knocking muka ji. Khadeeja ta furta “Yes come in..” k’aninsu ne ya shigo yana d’an hararar Khadija ya furta “Mhmmn, I know kina nan kin saka ta a gaba da surutu kamar parrot…” ta wani waro ido tana furta “Ridwan am I play with you? Ni kake kira parrot iya get out from here…” Ya turo bakinsa ka’dan yana furta “Aiken Mommy ne, ta ce ki rakata part d’in Yaya Ahmad su ci abinci da shi tare…” Na wani irin waro ido, kamar na yi kuka nake kallon Khadija na ce “Ki gaya mata na k’oshi don Allah…” Khadija ta waro ido tana furta “Ban kai nan ba, idan ba so kike Ya Ahmad da Anty Danger su gididdiba ni ba..” tana jan hannuna amma na kasa ta shi. Sai kawai ta fita sai gata ta dawo da wacce na tabbatar ita suke cewa Anty Danger na ji ta ce “Anty Tasleem to gata nan, ki gaya mata da kan ki.” Murmushi ta saki tana jan hannuna ta furta “Ta so Inlaw, yau ranace mai muhimmanci ga duk mai son Ahmad, shima kuma yau rana ce da zai so ku kasance tare tunda dai ba yanzu za’a kai ki gidan sa ba. Muje ku ci abinci ku yi hira sosai.” A kunyace na mik’e na bi bayanta hannuna cikin nata, muka ratsa ta wata k’ofa, Khadija na bin mu a baya, sai da muka wuce wani fili mai kyau kafin mu dangana da wani d’an gini mai kyau duk da bai cika girma ba. Anty Danger ta saka hannu a k’ofar ta yi nocking sai ga shi kuwa ya bu’de ina ji Anty Danger ta furta “aka tabbatar ta ci ta k’oshi ka kuma bata gift mai tsadar gaske wanda ba zata manta ba, na san ka san me nake nufi ko?” Hannuna na ji cikin nasa kafin ya kalli Khadija ya furta “Ke bar nan..” Da sauri kuwa ta juya tana dariya ta furta “Su Ya.Ahmad da mata Ai sai Allah. Anty Danger ma ta juya ya ja hannuna zuwa cikin k’aramin parlorn mai masifar kyau na zata anan zamu tsaya sai naga ya shiga da ni wata k’ofa da ta kai mu ainahin wani babban bedroom d’insa… muna shiga naga ya jani jikinsa ya rungume sosai cikin wani irin sautin murya ya ra’da min “Bari na fara baki gift d’in da surikarki ta rok’a na baki…” k’ok’arin zame jikina nake Amma ina ji na yi kawai yana zame d’ankwalin kayana ya cusa hannunsa cikin gashin kaina a kunnena na ji yana furta “Alhamdulillah Eesh komanki is beautiful ina fatan cikinki yafi wajenki kyau….” Jikina rawa kawai yake shi kuma bai daina shinshina k’asan wuya na ba.. “AYSHA ina son ki sosai ke ce rayuwata ki amince min yau d’aya kawai….” 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️[8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 18. 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 18. ‎Da sauri na kalleta kafin na girgiza kai na. Wasu hawaye na shirin zubo min, wanda bana komai ba ne sai na jin haushin tsanar da Mami na ta yiwa Ustaz, alhali shi yana sonta yana daraja ta, don kai tsaye zan iya cewa Ustaz kallon Uwa yake wa Mami. “Zaki amsa min, ko sai kin gama k’are min kallo? Na ce kin mik’a masa kanki ne?” Girgiza kaina na yi jin abinda Mamin ta ce. Sai naga ta saki wata ajiyar zuciya da har ta bayyana ta saman k’irjinta. Tana kallona ta furta “To wankan me kika yi? Ko da yake…” sai naga ta ‘dan cije leb’enta tana furta “Mhmn, ina ya kai ki bayan gidansu? Don naga da’dewar da kika yi ta yi yawa, kin saka na kasa barci fargaba ta d’aya kada ya mayar da ke cikakkiyar mace…•” K’asa na yi da kaina kurum. Na ce “Gidansu kawai ya kai ni, kuma na da’de ne saboda duk y’an uwansa suna gidan sun ‘dan ha’da Walima, wai su haka al’adarsu take, ranar da aka d’aura aure dole a yi Walima ta nuna godiya ga Allah…” Ta ‘dan tab’e baki. “Bayan walimar sai kuka zauna hira da mahaifiyarsa? A matsayinki na maras kunya ko?” Da sauri na girgiza kai na ce “Wallahi a’a Mameey, kawai dai ina zaune da sisters d’insa suna jana da hira…” na nuna mata kayan da suke kan gado na ce “Su suka bani.” Ko kallon kayan bata yi ba, ta fice da sauri daga ‘dakin tana furta “Ina ruwana da wasu kayansu, tunda dai bai kusanceki ba Ai shikkenan, ki gaya masa kuma fita an yi ta farko an yi k’arshe ba zai ya bu’dar miki da ido ba, ya zuba miki karatun da sam bana son ki fahimceshi a yanzu…” daga haka ta ja k’ofar da k’arfi ta bar ni da bu’dadden baki ina kallonta. Na saki ajiyar zuciya kafin na zura kayan sallah ta na tada sallahr isha’i da ban yi ba. Bayan na gama tunanin irin rigimar Mami, tabbas idan ka fahimci halinta tana da da’din zama amma kafin ka fuskanceta zaka saka ta a b’angaren mutane masu bau’dadden ra’ayi. Sanda na kwanta kuwa kiran wayar Ustaz ne ya isheni, kunyarsa da nake ji na abubuwan da suka wakana a tsakaninmu ne ya hana ni d’aga wayar, sai da ya yi kira ya kai biyar sannan na saka wayar a kunnena. Wata ajiyar zuciya ya saki. Yana furta “Na kasa barci Eeesh, kina ta yi min gizo duka surar jikinki ta baibaye tunani na, da na san haka ne da ban fara janyowa kaina ba….wani feeling nake ji mai zafin gaske AYSHA, na kasa controlling kaina na samu barci… please ki amince min even once… na kusanci halak d’ina..” K’it na kashe wayar ina mayar da numfashi. Lamarin Ystaz yana neman ya girmi kaina. Kiran duniya ban amsa ba. K’arshe ya turo min msg. “Shikkenan tunda ba zaki amsa ba, I really missed your cutable lips…. And…boo….” Sai ya yi alamar murmushi bai k’arasa ba. Wani irin waro ido na yi a fili na furta “Na shiga uku me yasa Ustaz sam bai da kunya, amma idan ka ganshi a fili ba zaka zaci zai aikata haka ba. A lumshe idona yake Amma duk wasu feeling ina jinsa nima kamar Ustaz d’in kawai daurewa nake don ban san ya zan yi ba idan ba dauriyar ba, na san ko giyar waje na sha ba zan amincewa buk’atar Ustaz ba, idan ba so nake Mami ta yi yaga yaga da nama na ba. Da safe sanda na isa makaranta ashe labari tuni ya baza makarantar kunya ta dinga isata jin ana ta min Allah ya sanya alheri. A islamiyya ma kasa katab’us na yi duk da dai da nik’ab a fuskata. Tunda aka d’aura aure sai gidanmu ya zama nasu Ustaz, don in dai yana gari baya jure rashin iya zuwa. Mami kuma ta kasa ta tsare don k’iri k’iri wani lokaci da ya tambayeta zan raka shi unguwa ta ce “Ahmad, ka saurareni da kyau ba zan amince ka dinga fita da AYSHA bata tare ba.” Ya ‘dan ware ido yana kallonta ita kuwa ba abinda ya dameta ta mik’e ta shige bedroom d’inta. Ustaz ya ‘dan dubeni yana sakin ajiyar zuciya. Na mik’a masa lemon da na ha’da masa, don anan saman Mamin muke zance da kanta Kuma ta buk’aci hakan. Ranar da yazo bayan d’aurin aure da kwana biyu zan fita sitroom ta ce “AYSHA hau da shi sama na, ai ya zama d’an gida, bai kyautu a dinga barinsa a parlorn waje ba, sai kace wanda yazo zance.” Gaba ‘d’aya wajen ba wanda bai d’ago ya kalleta ba, hatta Abba sai da zancen ya bashi mamaki. Ita kuwa ta maze tana murmushi ta ce “Da ne nake adawa da auren AYSHA, banda yanzu da k’addara ta Riga ta tabbatar da hakan. Allah ya sanya musu albarka a auren.” Abba murmushinsa ya kasa b’oyuwa kamar yarda bakin Umma ya kasa rufuwa. Shikkenan tun daga ranar Ustaz ya samu sake, mafi yawan lokuta ma tare ake zama a ci abincin dare da shi. Ya d’auki iyayena kamar nasa kamar yarda nima kullum muke gaisawa da Mommynsa a waya idan har na sha’afa ban kira ba, da kanta take kira na. Khadija kuwa ta zama uwa k’awata tsabar shak’uwar da muka yi, duk da ta girme min. Gefe guda al’amarin Mami na bani mamaki a zahiri a gaban kowa ta hak’ura amma a ba’dini ni ka’dai na san yarda muke zaune da ita, musamman duk ranar da Ustaz zai zo ta dinga ha’de rai kenan tana min masifa komai na yi kuma laifi yake zama a wajenta. Ban gayawa kowa ba, don bana son kowa ya sani balle a ji haushinta. Mafi yawan lokuta idan Umma ta fara mata zancen da ya rage na watannin tariyata tsam take mik’ewa ta bar wajen. Wannan abu yana tab’a min ruhina har na ji sam ban ji da’din abinda take yi d’in ba. In dai batun karatu ne, da bakin Ustaz ya mata alk’awarin sai nayi karatu a gidansa har sai nace ya isheni, tunda shima ta wani fannin d’an boko ne da ake damawa da shi a bokon. June-july, shine watannin da muke saka ran zamu gama makaranta. Kwanci tashi sai ga shi lokacin har yazo. Ina ji ko mu da zamu zana jarrabawar bamu kai Ustaz lissafa kwanakin ranar graduation d’in mu ba. Wata rana muna waya. Ya ce “AYSHA, na k’agu ki gama wannan makarantar na sauke buk’atar da ta min cunkoso a jikina….” Waro ido na yi kafin na furta “Wace buk’ata kuma?” Sai da busar da iskar da take bakinsa, har na ji sautin ta ta cikin waya sai na ji ya ce “Kashe mu yi vedio call, zan gaya miki buk’atar…” “Ni dai A’a, na yafe.” Na fa’da a shagwab’e. Ya saki murmushi kafin ya furta “Ashe kin san buk’atar tunda kina jin kunyar na gaya miki, bari na miki ta Malam bahaushe, wallahi AYSHA na gaji, gangar jikina tana buk’atar maha’dinta, ina son jin d’umin Aysha zahirinta ba tare da shamakin tufafi ba…” da sauri na kashe wayar ina mayar da ajiyar zuciya. Ni da kaina na san Ustaz ya yi hak’uri gashi yanzu ko rungumar baya samu ya yi min Mami ta kasa ta tsare, sau tari sai muna zance sai ta shigo parlorn da niyyar d’aukar wani abin. Wani lokacin Ustaz kasa sakin jiki yake yi. Shi yasa yace min sau da yawa shi yasa baya zaman Nigeria yake tafiyarsa wata k’asar ya kwana biyu. Burina kawai na fito da A1 a duka subject d’in da nake, don haka na dage da karatu Ka’in da na’in. Ustaz ma a wannan lokacin ya mugun d’aga min k’afa sai dai ya kira ni a waya. Har rama na yi saboda bani da isashshen lokacin kaina ko waya a gaggauce nake amsa masa, sau tari sai ya nuna fushin sa sannan nake bashi lokaci na. Ranar da muka gama makaranta, rana ce mai matuk’ar mahimmanci a wajena. Duk da Ustaz ya hana ni ko saka kwalli a ranar, hakan bai hana ni zuba wani Uban kyau ba na kwatance. Wata doguwar Riga mai masifar kyau na saka wacce Mommyn Ustaz ta kawo min. Da takalmi half cover wanda zai matching da adon rigar golden brown. Na yi rolling kaina. Sanda Ustaz yazo zamu tafi hararata ya dinga yi yana tsaki k’asa k’asa. Muna isa wajen ya kulle motar yana zuban narkakkun idanunsa. Kafin ya kaiwa bakina sumbata ya furta “Me yasa? Me yasa ko baki kwalliya ba sai kin yi attracting idon mutane..” Murmushi kawai na masa. Sai naga ya bu’de dashboard ya ciro nik’ab Sabo fil a leda da kansa ya saka min nik’ab d’in yana furta “fuskar Matata haramun ce ga dandazon maza.” Ustaz ya kasa ya tsare ta dole ya nunawa mutane ni matarsa ce, don bai ji kunyar ko su Abba ba sanda za a bani kyauta ya rik’e hannuna muka hau kan step. Shi ya karb’i kyautar da Mataimakin governor ya bani sab’anin sauran matan da suka dinga amsa da kansu. Tafi aka dinga yi da wani irin ihu. Da aka tashi bai barni na yi hotuna ba, ya saka ni a mota yana furta “Is enough kuma, idan ba so ake Ustaz zuciyarsa ta yi bombing ba..” ya tada Motar yana jan hannuna da yake saman cinyata yana murzawa a hankali ya furta “Saura 2 weeks na mallaki komai da komai na jikinki Ayshatu na, har nan ko?” Inda hannunsa ya sauka ne ya saka ni ware ido ina runtse su da sauri da k’arfi. Sai naga ya daki sitiyari yana murmushi ya furta “na godewa Ubangiji da ya mallaka min kamilar mace, da nake jin In sha Allah nine nan d’an mukullin wancan abin da ake killacewa, I love you Ayshatu na….ina son ki fiye da son da nake wa ruhina, I wish to spend the rest of my life with you…” ya fa’da yana d’an jan hancina. “Na kusa cire kunyar nan gaba d’aya. Just 2 weeks za’a saka, a haka ma ni ba haka na so ba na so a ce 1week after Graduation kawai, amma ya zan yi Mommy ta kafe basu gama shirye shirye ba.” Gani na yi kawai ya ja gefen hanya ya yi parking. Ya kwantar da kujerar yana kallona da wasu lumsassun idanunsa. Tsigar jikina ce take tashi kawai. Iya zallar kallon Ustaz yana canja min yanayi inaga ranar da zan ganni da ga ni sai shi a matsayin ma’aurata. “Say something AYSHA, ko da yau ka’dai ne kice Ustaz I love you na ji sanyi a raina…” Lumshe idona na yi, Karon farko na ji yau ina son shayar da Ustaz mamaki. Murya a sark’afe cikin wani irin sauti na furta “I… Love…You Ustaz with All my heart Ustazu na.” Jina kawai na yi a jikinsa yana bani wasu zafafan kiss. A kunne ya ra’da min “Me kika tanadar min a ranar da zamu tare?” Na runtse idona. “Kada ki ji kunya My Eesh ba kunya tsakanin Miji da Mata say it…. Kin tanadar min duka kan ki…” na d’aga kai na na ji ya bani sumbata a forehead d’ina da tsinin hancina. Ya saki ajiyar zuciya a hankali ya mayar da seat d’in yarda ta ke ya ja muka tafi. Sanda muka isa gida, na hau sama Mami na tarar tana cika tana batsewa a cikin parlornta, idanunta sun ka’da jajur tana kallona kafin ta zauna ta rik’e kan nata. Jikina a sanyaye na yi hanyar da zata kai ni d’akina, na ji muryar Mami a kaurare ta ce “AYSHA! Zo nan!” Cak na tsaya kafin na juya a hankali na isa inda ta ke. Na zauna a gefenta. Ta nuna min cards… “Ga cards d’in bikinki nan, burinki da na iyayenki ya cika, ina muku murna, ba zan b’oye miki ba AYSHA sam bana farin ciki da aurenki, zan kuma amince da aurenki ne idan kika amince da wasu shara’di da zan baki…. As from today zaki dawo kwana a d’akina ba kuma naso ki gayawa kowa, sannan ban amince ko gayawa kowa wannan shara’din nawa ba, sannan ki sanar da shi daga yau ba waya tsakaninku sai mesaage……. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA 17. https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 17. ‎ Jikina na rawa na kauce fuskata daga sumbatar da yake kai min. “Ustaz shine ka min k’arya?” Na fa’da ina janye jikina daga nasa na zauna a kan kujera. Zaman dirshan ya yi a gabana ya zuba hannunsa a kan cinyata yana kallona cikin wani yanayi ya furta “AYSHA k’arya kuma? K’aryar me?” Magana yake cikin wata irin murya da na kasa tantance a wani mahalli zan sakata. “Kace min Khadija matarka ce.” Na fa’da ina yin k’asa da idona don bana jin zan iya jure wannan kallon da yake min. Wani murmushi ya saki da har ina iya juyo sautinsa da numfashin da ya sakar min ya ratsa fuskata. Yana dariyar ya furta “D’ago ki kalleni…” na k’i d’agowar da ba zan jure ba. Hannuna ya kama ya matse cikin nasa. A hankali ya furta “Ranar da kika ce ba kya so na, kin fasa aurena hankalina tashe na taho gida. Ni da kaina na tabbatar ikon Allah ne kawai ya kawo ni gida, Saboda tashin hankalin da zuciyata take ciki. Sanda na isa gida ko ciki ban shiga ba kamar yarda na saba. Na shiga part d’ina na zauna hankalina a tashe. Duk na ji duniyar bata min da’di. Ashe Mommy taga shigowata ta camera ta aiko Khadija taga ko lafiya ban shigo ba kamar yarda na saba. Yanayin da Habibteey ta ganni ne ya sata zubewa cikin tashin hankali a gabana tana kama hannuna ta furta “Subhanallah Ya Ahmad lafiya kuwa?” Na ‘dago idona da suka yi jajir na zube a kanta sai kawai na ga ta ru’de ta fara magana “Ya Ahmad ka yi magana me ya sameka?” Ajiyar zuciya na saki cikin wani irin rauni na sanar da ita dukkan damuwata. Madadin naga ta cigaba da damuwar sai naga ta tuntsire da dariya ta furta “Ya Ahmad wallahi AYSHA na sanka, kawai dai akwai wani dalili da yake nema ya mata Katanga da son naka zai kuma iya togaceku daga aure idan baka yi gaggawar sakawa a d’aura muku aure ba ina tabbatar maka nan gaba zaka rasa AYSHA…” shiru na yi ina murza goshina kafin na ce “Khadija ta yaya kike zaton Iyayenta zasu yarda su aurar da ita a S.S 2.” Ta sake murmushi ta ce “Ka je musu da buk’atar auren kawai banda tariya idan yaso idan ta gama secondary school sai ku tare…” Shiru na yi ina nazarin zuciyata duk gwiwata ta yi sanyi don na san mawuyacin abu ne Abbanki ya yarda da abinda zan je masa, ni kaina ina tunanin yarda zan yi aure na kuma zuba miki ido bayan auren a zuwan sai an tare na kusanceki ko ba so akwai sha’awa balle ke da nake so nake kuma mafarki kullum Akan wancan gwadaben sai na ji abin da kamar wuya. Gefe guda kuma ina jin tsoron ko kin daina so na don ba zan iya auren matar da bata so na ba, don haka kai tsaye na ce da Khadija “Idan kuma bata so na fa?” Dariya ta yi sosai, dariyar da ta dinga saka min wani irin d’aci a zuciya, a zafafe na ce “Khadija wai meye haka? Ya nazo miki da matsalata zaki saka ni a gaba kina dariya?” Dariyar ta sake yi kafin ta ce Tabbas Ya Ahmad na yarda kai sabon shiga ne a fagen soyayya, duk mutumin da zai Soka da farko ya dawo ya k’i ka da k’arshe to ba k’in ka yake ba sai dai idan akwai wani dalilin da zai saka ya janye soyayyar… ka bincika kuma zaka ce na gaya maka. Kana so ka gane tana sonka ko bata son ka?” Da sauri na ‘d’aga kai, don shi na fi buk’ata. Ta gya’da kai ta furta “zan baka hotona, ka kaiwa AYSHA a zuwan ni ce matar da zaka aura, idan har kaga ta shiga tashin hankali to tabbas tana son ka, idan kuwa kaga bata damu ba to gaskiya sonka bai je ko ina ba a zuciyarta.” “Good idea!” Na furta cikin jin da’di. Da k’yar na bari kashegari ta yi, kafin na kai kaina gidanku, sai dai me? Ina zuwa aka ce min kina gidan Yaya Muhammad. Wani farin ciki na ji. Na saka aka min kwatance sai gidan Muhammad. Sanda na baki hoton Khadija, lab’e wa na yi ba tafiya nayi ba, ina son naga reaction d’inki. Wani farin ciki ya mamaye ni ganin yarda kika nuna damuwa da hoton da kika gani. Ya Muhd shi ya sanar da ni komai da abinda ake ciki game da Maminki. Hakan shi ya bani k’warin gwiwar zuwa na tari Daddy na da zancen son zuwa a nema min aurenki. Da fari bai amince ba sai da na masa rantsuwar zan amince na barki ki yi karatu sannan ya yarda zai je nema min aurenki da shara’din idan Abbanki bai amince ba zan hak’ura. Na yarda da hakan. Kashegari kuwa aka je nema min aurenki, abin mamaki take Abbanki ya ce ya amince banda ma yana tausayawa Maminki kada zafin ya mata yawa da yace na tare da matata kawai. Bokon me? Bokon Ai ba fa’dar Allah ba ce. Na ji da’din wannan labarin na tabbatar na auri y’ar babban gida irin matar da Manzon Allah ya kwa’daita mana mu aura. Muhd ne ya bani shawarar zai ‘d’auke ki ya kai ki gidansa har sai bayan an ‘d’aura auren don ya lura kamar damuwar da Mami take ciki ne yake neman tunzira zuciyarki. Ki bujirewa auren. Wannan shine abinda ya faru My Eeesh dafatan zaki yafe min?” Na lumshe idona kawai ina jin yarda yake murzar min hannuna a hankali. “Ana ahubbuki kaseer kaseer Eesh.” Murmushi kawai na saki ina janye hannuna na ce “Ustaz mu tafi gida kada dare ya yi.” Sumbata ya kaiwa hannun yana furta “wani gida kuma Aysha? Kina da gidan da ya wuce nan ne?” Idona na ne ya kawo ruwa na zare hannuna ina furta “Please Ustaz! Kada mu yi haka da kai mana..” Shiru ya yi yana sake matsar da hannuna saitin bakinsa idanunsa a lumshe yake sumbatar yatsun yana furta “Shshsh, idan kika cigaba da min magiya you will spend your night anan…” na waro ido. Jin abinda ya ce bai fasa kissing hannun nawa ba. Sai da ya gaji don kansa ya janye hannun yana sakin ajiyar zuciya ha’de da kallona da burkitattun idanunsa ya mik’e naga ya shiga wata k’ofa da na tabbatar toilet ne, bai wani jima ba naga ya fito da rigar wanka a jikinsa yana goge jikin. Da sauri na runtse idona na ji ya saki dariya mai k’aramin sauti ya furta “Idan baki wasa ba zaki shafa min mai….” Ai ban san sanda na isa bakin k’ofa ba, ina sakin haki na tsaya a bakin k’ofar da zata fitar da kai daga parlorn. Tsawon mintuna biyu sai ga shi ya fito sai zabga k’amshi yake fuskarsa very fresh. Ina ganinsa na yi saurin murza handle d’in k’ofar zan fita sai dai hakan bai samu ba don key ‘din na hannunsa ya k’araso daf da ni, kansa a saman wuya na ya rungumeni ta baya yana sakin ajiyar zuciya, a kunne ya ra’da min. “Kin saka ni wankan dole Ayshata…” wani irin runtse ido na yi na furta “Please Ustazu Ka Bari am too young fa..” naga ya d’an yi murmushi kawai ya kaiwa bakina sumbata ya furta “Mu je kafin Maminki ta k’arar da charging wayarki ta miki missed calls ya fi hamsin…” waro ido na yi ina kallon wayar da Ustaz yake mik’o min, a raina na furta shikkenan na ka’de yau har ganyena…. Da zan tafi Mommynsa da Aunty’s d’insa suka ha’da ni sha tara ta arziki. Tabbas a idanunsu na hango sun yi na’am da ni. Sanda muka isa k’ofar gida, da sauri na kai hannu zan bu’de k’ofar sai na ji ta a kulle gam. Na juyo ina kallon Ustaz na ce ya haka?” D’an lumshe ido ya yi yana turo min lab’bansa “I need kiss AYSHA in dai kina son ki fita, ina son ki min abinda zan dinga tunawa da shi da zarar na rufe ido da niyyar barci…” “Allah Ustaz ba zan iya ba…” Ji na yi kawai ya yi baya da seat ‘d’insa ya janyo ni da k’arfi na zube jikinsa a hankali ya fara bani wani irin passionate Kiss. Mun d’au tsawon mintuna biyar a haka kafin ya sake ni. Ya danna lock motar ta bu’de “Sweet dream Ayshata, ki yi mafarki na pls…. I mean romantic mafarki…” Da sauri na fice daga motar. Don kamar lamarin Ustaz yana neman girman kwanyata. Sa’daf Sad’af na shige bedroom ‘dina. Don bana son na yi k’wak’wkwaran motsin da Mami zata ji ni. Ina shiga d’akin kuwa kayan jikina na cire da duk suke k’amshin turaren Ustazu, idan ba hanci na bane ya ji ba daidai ba, sai na ji kamar jikina ma k’amshinsa yake. Da sauri na fa’da toilet don a jikina nake jin ya wajaba na yi wanka. Ina wankan na dinga jin ana buga k’ofar toilet d’in da k’arfi gabana na wani irin fa’duwa na fito. Ina fitowa kuwa idanuna suka sark’e da na Mami da yake wurga min wani irin kallo mai nuni da zallar jin haushi. Idanunta a burkice banda bata shaye shaye sai na ce ma a buge take… cikin rawar murya na furta “Sannu…sannu Mami, ke ce?” Ta sake wurga min kallon tana mik’ewa ta iso daf da ni. Kallon sama da k’asa take min kafin ta saka hannunta cikin sumar gashi na ta furta “Wanka AYSHA? Wankan me kika yi na ji gashinki a jik’e don’t tell me kin mik’awa wancan wawan kan ki?” ★✍️ 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢 [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA♥︎♥︎♥︎ 19. 𝒩𝒶𝓏ℯℯ𝒻𝒶𝒽 𝒩𝒶𝓈𝒽ℯ★✍️ Free Book.. MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Arewabooks @nazeefah https://chat.whatsapp.com/HfGu1Pozgx9IxjCYqW7ZCZ Wattpad@Nazeefah381 08033748387. ★★★★★ 𝒫𝒶ℊℯ 19. 19. Wani iri na ji kaina ya yi, na kasa d’aga ko ido na kalli Mami jin yarda nake jin wani irin d’aci a mak’ogwaro na, na tabbatar b’acin rai ne ya haddasa min haka. Bata jira jin abinda zan ce naga ta mik’e ta shige bedroom d’inta hakan ya tabbatar min bata buk’atar yarda ta ko rashin yarda, umarni ne kai tsaye ta bani da take tunanin tilas ne na bi shi. Hawaye naji suna zubo min masu d’imin gaske wanda suke narkar da duk wata damuwata da take k’asan zuciyata. Jikina a salub’e na shige d’aki, Ina ji lokaci ya yi da ya kamata na nunawa Mami nima y’ar Zamani ce, zan iya jurar komai banda rashin waya da Ustaz, ya Riga ya saba narkar da zuciyata da kalamai masu narkar da zuciya. Furucinta kam tamkar d’igar dalma ne cikin zuciyata gwara ta min komai banda hana ni jin muryar ustaz wallahi. Bayan Isha, still Ustaz yazo gidan mu. Kamar yarda ya saba wannan karan ma da shi aka ci abincin dare. Ya kalleni bayan ya mik’e bai ji kunyar Abba ba balle su Mami ya furta “AYSHA, zo mota ki amshi sak’o.” Ta gefen ido nake kallon Mami da take zuba masa banzan kallo. Na mik’e jikina a salub’e na bi bayansa. Har ya shiga cikin mota. Hakan yasa na masa knocking glass. Bu’de motar ya yi ya furta “Shigo mu fara tsara yarda shirin bikin zai kasance, bana son hira a saman Mami, I can’t feel comfortable…” Na shiga Motar jikina a sanyaye. Ya janyo paper da biro ya mik’o min. “Lissafo min abinda duk kike so a yi a bikin, da duk abinda za’a kashe.” Ya furta yana kallona. Kafin ya d’an tab’e baki ya ce “Why are you so quiet yau ne? Ko har kin fara tunanin aure ne?” Lumshe idona na yi ina girgiza kai. Na furta “Bakomai fa, kawai stress d’in exams ne yake tambaya ta.” Ya girgiza kai yana jan hab’ata ya furta “Oh I see, am so sorry dana sani ban zo yau ba. Jeki gida zan shigo gobe ko jibi, ina hoping by that time kin wartsake stress mu samu mu shirya bikin sosai, duk da bana son event da za’a ha’da maza da mata please ko hoto mace nake so.” Na d’aga kai. Ya ja hannuna ya yi kissing kafin ya mik’a min ledar hannunsa. Mai kyan gaske tun kafin na bu’de na san turare ne a ciki saboda wani k’amshi na fitar hankali da naji yana fita a ciki. “Sweet dream…” Ya furta a hankali cikin Wata husky voice mai dashewa. Na amsa ta hanyar d’aga kai. Na fita daga mota. Sanda na shiga gida duk sun watse daga tsakargida, na hau saman Mami bayan na lek’a na yiwa Umma sallama. Mamin bata parlor na shiga d’akina. Kyaututtukan da na samu na dinga bu’dewa ina binsu da kallo. Sai daga k’arshe na bu’de ledar Ustaz wani rantsatstsen turarena da charbi da sallaya da aka saka sunana a jiki da haruffan larabci “Zaujaty Ayshatu…” Murmushi na yi ina rungume d’an zoben gold d’in a k’irjina bayan na fesa turaren mai k’amshin na Ustaz sak sai dai shi wannan na mata ne k’amshin bai kai na Ustaz k’arfi ba. Lumshe idona na yi. Sai jin tafi na yi a kai na. Da sauri na ware idona ganin Mami a tsaye idonta a kaina. Ta furta “Weldone Aysha, kin kuma burge ni.” A daburce na furta “Mami me na yi?” Ta tako zuwa inda nake, ta saka k’afarta d’aya ta tokare a saman gado tana kallona ta furta “Me kuwa kika yi AYSHA? Ba abinda kika yi illa kina so ki nuna min ke ma kin girma. Ahmad ya fara shayar da ke da’di da zumar da ke cikin aure, tunda ga shi har kin san ki rungume kyautar sa a jikinsa, alamu ya nuna kin fara sanin soyayya kin kuna san menene sha’awa, tabbas lokaci ya zo…” Ta fa’da tana lasar leb’enta “Uban me kika tuno da yasa ki lumshe ido da murmushi? Kin hango yarda yake rungumeki ko? Ke a tunaninki wai na amince da aurenki ne? Ko ka’dan har yanzu zuciyata bata so ina kuma adawa da haka. Na k’i jinin tarayyarki da wannan mutumin da yazo ya wargaza min duk wani tanadi na a kan ki…. Sak na yi ina jin furucin Mamin kamar d’igar dalma a cikin k’irjina. Ji nake kamar ana soya zuciyata saboda tsananin hucin da nake ji a k’asan raina. “Mik’o min turaren.” Ta yi furucin cikin b’acin rai. Na saka hannu na mik’a mata turaren. Ta fice da shi tana furta “Kin bar amfani da duk wani abu da zai baki, musamman turare waya sani ma ko asiri ya miki a cikinsa. Shegen mutum mai azababben naci..” Ta gama zaginsa ta fice daga d’akin sai sannan naji wani kuka mai tafe da takaici ya zo min, ba shiri na saka kukan kuwa sosai. Raina ya b’aci sosai don haka bayan na yi wanka na shirya nan je ‘dakin nata ba kamar yarda ta min umarni na yi zama na a ‘d’aki. Wajen sha biyun dare ta shigo d’akin cikin shigar wasu silk kayan barci sai baza k’amshin gabbasa take. Ina kwancen ta zauna a gefen gadon. Da sauri na lumshe idona don ko ganin Mamin naji bana son yi. Sunkuyo da kanta ta yi saman fuskata ta bani kyakykyawan kiss a gefen kumatu. A kunne ta ra’da min “Tashi Babyn Mameey, don’t tell me fushi kike da ni, na san dai idonki biyu.” K’in motsa wa na yi. “Ba zaki tashi ba?” Ta sake furucin a hankali sai ji na yi kawai ta burkito ni jikinta a hankali ta saka hannunta a gefen cikina ta min cakulkuli da sauri na bu’de idon ina d’an ja jikina ba furta “Kai Mammy, am not that young fa…” Sake janyo ni ta yi jikinta tana ha’da fuskata da tata ta furta “You are still my little Aysha, har yanzu kallon Babyn Mameey nake miki. Sau tari raina ne yake b’aci bana son kusancinki da Ustaz wallahi ina jin haushin hakan sosai a raina. A yanzu ba zan k’i ki auri wani ba ki bar Ustaz ba don komai ba sai don na san zai yi tsauri zai kuma takura miki zamantowarsa Malami, ba zai bari ki mori rayuwarki ba, balle….” Sai naga ta ciji leb’en bakinta na k’asa ta yi shiru bata k’arasa ba. Ta d’an girgiza kai sai naga ta ja pillow kawai ta kwanta ta furta “A dole za’a raba mu abinda bana so, ba yarda zan yi ne, shi yasa nake so mu dinga kwana tare ina jin ki kusa da ni, don na san wata rana ba zan samu damar hakan ba….” Kafin na yi wani yunk’uri naji Mami ta kwanta daf da ni sosai tana sakin ajiyar zuciya… ni dai a ‘darare na yi barci a ranar da mamakin wasu daga halayyar Mamin… Bayan kwana biyu da faruwar hakan aka ce za’a kawo lefe don haka ranar da wuri na shirya duk raina ba da’di musamman takura ni da Mami take yi na kwana a d’akina ko nata ko itace da girki sau tari sai ta dawo don kawai ta hanani waya da Ustaz. Waya kam sai a sace nake yi da shi. K’asa na sauka cikin shigar doguwar Rigar abaya da na na’de kaina da mayafinta, na saka nik’ab kuma. Mami da Umma na gani a kitchen sai masu aikin mu suna ta hidimar ha’da abubuwan da za’a tarbi bak’i da su. Bayan gaishesu Umma naga ta zuba min ido kafin ta juya wajen Mami ta ce “Fateemah, wani abu ke damun y’ar taki naga tayi wata Uban rama? Ko dai duk tunanin auren ne?” Mami ta d’an tab’e baki tana kallon Umma ta furta “Me kike tsammani daga yarinya kamarta da za’a mata aure a k’ananun shekaru, ba dole ta yi tunani ba tunda ta san abinda zata tarar gidan Mijin ba mai sauk’i ba ne…” Umma d’auke kanta ta yi tana furta “Allah ya kyauta, aure ne fa ba rayuwar azaba ba, menene na sakawa kai tunanin? Sanda aka yi aurena shekaru sha biyar gareni kuma ba abinda ya same ni, ku san dai na yi gaskiya ko Sabaya ki fara d’irka mata gaskiya… don ramar ta yi yawa.” Mami ta tab’e baki ta furta “Idan taje gidan Mijin, ta fara samun abinda kuke so ta samu Ai zata ciko. Zo ki wuce AYSHA kafin mutane su zo su tarar da ke, ki gaida Aseeyar sai kuma yamma zaki dawo. Driver na nan a waje ya sauke ki.” Na d’aga kaina ina fita daga kitchen d’in. Bayan na sake kallon Umma da ta zubo min ido… A waje na tarar da Asma don tare zamu tafi. Driver ya taso don ya kai mu, na girgiza masa kaina “Bar shi ma Baba, Ustaz zai kai mu, amma don Allah kada ka gayawa Mami na.” Murmushi ya yi ya d’aga kai jin abinda na ce. Da sauri na ja hannun Asma muka fice don Ustaz ya isheni da kiran waya. Muna isa kuwa ya wurga min harara gaisuwata ma bai amsa ba sai ta Asma. Ban wani damu ba don na san laifukan da na yiwa Ustaz a lokutan nan ba zasu lissafu ba. A hanya Asma ta masa zancen zamu je fitar da anko. Ji nayi yana furta “Waye zai je kasuwar? Ba dai AYSHA ba wallahi gwara na rasa miliyoyin naira da na barta ta shiga kasuwa ku fa’di colorn da kuke so da adadin ku zan saka a kawo muku.” Asma murmushi ta yi ta kuma furta “Mun gode Allah ya k’ara arziki.” Muka gama tsara bikinmu da y’ay’an Anty Aseeya k’anwar Mami, kafin Ustaz ya sake dawowa d’aukar mu. Sanda muka isa gida Asma tana fita ya saka hannunsa ya rik’e hannuna. Tsawon minti guda yana murza hannun kafin ya ware idonsa a kaina. “Me yasa ba kya amsa wayata da daddare?” Muryata a hankali na furta “Barci Ustazuna barci ne ke hana ni sak’at.” Ya cije leb’ensa yana narkar da idonsa cikin nawa ya furta “Ki yi barci ki more AYSHA, gwara ki yi barcin yanzu don ina tabbatar miki ranar first night d’inmu ba barci till down zamu yi mai zafin gaske….” Da sauri na lumshe ido na. Ya saki hannun yana furta “Good night, abinda bai yi ba a lefe feel free ki gaya min.” Na girgiza kai na ina furta “Na san Ustazu na ya iya zab’e zan kuma yi farin ciki da dukkan abinda ya fito daga hannunka.” “Jikina fa?” Ya furta yana d’aga gira da sakin murmushi… da sauri na fice ina furta “Har jikin…” Sai naga ya waro ido ya buso min iska alamar kiss yana sakin murmushi ya furta “I love you till my last breath…” na shige gida cikin wani irin zallar farin ciki. Tun a gate Asma ta wani rungumeni tana furta AYSHA ke mai sa’a ce kin ga lefenki kuwa?” Murmushi kawai na saki wata kunya na sake baibayeni wai ni Aysha yau ake zancen aure na a gidanmu. A parlorn Abba na tarar da su da yake na san lefen suke kalla hakan ya saka ni guduwa sama don har ga Allah ba zan iya zaman kallon lefen ba… Da daddare Mami ta shigo still yau ma cikin shigar wata shegiyar rigar barci sai zabga k’amshin turare take. Gashinta a sake sai baza k’amshi yake da alama ta yi gabbasar gashi. Glass cup ne a hannunta mai d’auke da madara ta zauna a gefen gadon ta mik’a min cup d’in. “Tashi ki sha AYSHA.” Na karb’a na kafa kai na shanye. Mami ta zuban ido tana saki wani malalacin murmushi ta furta “Yau zan sanar da ke abinda baki sani ba Aysha Zan koya miki yarda zaki mallaki Ustaz in a romantic way…. “ Dishi dishi na dinga gani a idona na fara kallon Mami bibbiyu da duk abinda take furtawa yana shiga kunne na kafin na ga ta saka hannu ta baje gashin kanta ta ‘dago tana min wani kallo….. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️😉‎ [8/5, 1:21 PM] Nazeefah Nashe: NA GA RAYUWA…….20. Gaskiya ku min kara, ku yi dandazo ku nuna wa Littafin mu ja Bright pens na Aysha Cool. K’arfe a wuta….. soyayya wacce zata girgiza media… a fito a siyi k’arfe a wuta ko na yi yajin aikin rubutu na sati guda 😒 yauwa eeehe. Don samun littafin kai tsaye ka tuntub’i AYSHA COOL MARUBUCIYAR K’ANWAR MAZA. Kowa dai ya san yarda labarin ya kara’de Media.. tuna da sunan K’ARFE A WUTA. I dedicated this page to my lovely sis Nimcyluv. “Saboda sonki da littafin Na ga rayuwa na mallaka miki wannan page d’in. Really appreciated 🥰. Masu bina private kan na mayar da shi na ku’di saboda na dinga musu posting 2 times a day. Ku yi hak’uri Na ga rayuwa dai kyauta na bada shi don haka In sha Allah zamu gama cikin nasara idan ku'din ne ya muku yawa ku siyi books 'dinmu na Bright pens. 🤗 _____________ Cikin lumsassun idona nake kallon abubuwanda Mamin take min a sunan tana koya min yarda zan mallaki zuciyar Ustaz. Har k’afata ta ja a hankali tana matsawa cikin wani salo. “Hakan da nake miki Aysha shine romantic tausa kuma haka ake son ki yiwa Mijinki, ba kunya tsakanin Miji da Mata ki zage ki nemi zuciyar Mijinki ko ta wani hali….” Wasu abubuwan daga baya sam kasa fahintar su nayi, sabida wani irin barci da ya dinga fisgata k’arshe dai ban san ya aka yi ba sai wayar gari nayi naga asuba ta yi. Har gari ya fara haske. Na juya Babu Mami a d’akin idona na lumshe duk abinda ya faru a daren ranar ya shiga dawo min daki-daki. Ajiyar zuciya na sauke kafin na mik’ na shiga toilet don abin na Mami ya girmi kwanyata. Da yake na san alhamis ce ban wani damu da neman abin kari ba. Still bayan naje ba gaishesu barcin na ji ina sake ji don haka na koma d’aki kawai na sake kwanciya. Daga ranar ya zama kullum Mami sai ta bani wannan madarar na sha da daddare ina sha kuma barci mai nauyin gaske zai d’auke ni ba zan farka ba sai asubahi. A haka kwanakin bikin suka dinga matsawa na dinga zuba wani kyau ga k’irjina ya cika k’ugu na ma haka na yi k’iba ta ban mamaki. Don bana manta wata rana muna zaune a parlorn Abba ana auna ni d’inkin da za’a min wata k’wararriyar tela da ta yi shuhura a ‘dinkin Amare cike da mamaki Umma yake kallo na ta ce “Fateema kin ga yarda AYSHA ta cika ta yi k’iba kuwa kamar ma har ta tare a gidan Mijin? Ko dai har kun fara shan sabayar?” Mami murmushi kawai ta yi ta ‘d’auke kanta tana kallona k’asa k’asa. Da yamma kuwa ina dawowa daga Islamiyya na shiga parlorn Mamin sai naga ta yi bak’i wasu manyan mata, da kana ganinsu kaga y’an duniya… Sak na yi ina kallonsu a zaune sun ci matsatstsun kaya dole na yi mamaki don ban saba ganin irin su ba a gidanmu. Gaba d’aya k’irjinsu a waje yake, sun baza gashi ga sark’a a k’afarsu. Mami na gani na ta tsuke fuska, k’ok’arin Gaishesu na yi amma sai ta dakatar da ni. “AYSHA sauka k’asa wajen Umma na gama da bak’i tukun.” Sak na yi na juya sai na ji d’aya a cikinsu tana furta “Ma sha Allah, Fateema wannan yarinyar fa komai ya ji akwai kaya gaskiya…” “Ita nake baku labari…” Shine kawai abinda naji. Na sauka k’asa jikina a sanyaye saboda mamakin abinda Mami ta ce na yi. Bata tab’a ce min na sauka k’asa don na yi bak’i ba, sai yau bak’in ma irin wa’dannan marasa kamun kai. Parlorn Umma na shiga sai na sameta tana waya. Da ido ta bi ni da kallo har na zauna a kujerar da take kusa da ita. Sai da ta gama wayar ta juyo tana kallona ta furta “Ke AYSHA lafiya? Naga kin shigo sukuku da ke.” Girgiza mata kai na yi “Bakomai, Mami ce ta ce nazo nan saboda ta yi bak’i.” “Ki zo nan?” Umman ta furta cikin mamaki don itama abin da bata saba gani ba ne. Na d’aga kaina a hankali. Sai naga taja ajiyar zuciya ta ce “Tashi ki je kitchen maza cikin fridge ki d’auko min wasu jarkoki guda uku suna nan. Ki ha’do da cup.” Na mik’e na shiga kitchen d’in Umman da yake cikin parlornta. D’auko biyu na yi saboda da d’an girmansu kafin na koma na d’auko d’aya da cup. Umma ta bu’de ta farkon ta zuba Rabin cup ta mik’o min “Karb’i ki sha, ba kuma wai don da’di ake shan irin wannan kayan ba don na san ki da shegen kwa’dayi.” Na runtse idona na shanye. Ta sake zuba min na sauran gororin tana furta “Kullum ki dinga zuwa cikin fridge kina bu’desu ki sha, Ko Mamin naki na baki?” Na girgiza kai bata bani komai. Na so gaya mata sai madarar da take bani duk dare da take saka ni barci sai dai na kasa. Ina kallo ta d’an cije leb’enta ta furta “Ai shikkenan, da ni da ita duk d’aya ne, ki dage sosai wajen shan su, akwai wasu ma da zan saka a kawo miki duk da dai na san ko da wannan kika tsaya kin fita zarra Magungunan Anty Surayya mai Bojuwa herbals ba k’arya ba ne, suna da amfani k’warai a jikin mutum. Zan kuma baki numberr wayarta don ki dinga tuntub’arta don samun ingantattun magani na gyaran zamantakewar aure…. Ta mik’e sai gata ta dawo da wata roba. Zuba y’an k’wayoyin maganin ta yi a hannunta ta ha’da min da dabino tace na taune. Sauran kazar sababi tace a satinnan zata kawo miki. Na san komai don haka kunya ta kamani don ina karatun litattafai saboda haka na san magungunan da Umman ta bani da dalilin ba ni su. Da Mami ce ba zan ji kunyarta ba kamar Umman don ita Umma sam bata saki jiki da ni ba. “Gyaran jiki dai ba kya buk’atarsa don fatar ki mai kyau ce ba abinda kike buk’ata, sai zuwa saloon a miki predicure da manicure zuwa jibi ki shirya ki je.” Na d’aga mata kai. Daga haka ta mik’e ta shige kitchen na san ba kunya ce ta saka ta barin wajen. Na d’an saki murmushi kawai ina jin soyayyar Umman da wani irin tausayinta a raina. Ni kenan y’arta mace amma ta iya kyauta da ni ta kuma d’auke kanta a kaina. Lallai Umma ta cika fulanin k’warai masu kunya kara da d’auke kai. Sai dare sannan bak’i Mami suka tafi. Ina shiga parlorn naga sun yi kaca kaca da shi. Tab’e baki nayi na shige mai aikin da take gyarawa. Wata litinin abubuwan suka fara faruwa tsakanina da Ustaz, litinin d’in ana saura kwana hu’du a fara bikin. Na san anan yake shan ruwa in dai ya yi azimi. Shirin bikin bai hanani tashi na fara shirya masa abin shan ruwa ba, duk da yinin Ranar sam bai kira ni ba. Nima kuma na shiga busy shi yasa ban kira shi ba. Azimin ne nima a bakina, amma haka na daure na fara shirin yi masa abin bu’de baki. Kunun kwakwa nake son masa, rashin ganin flavour ya saka ni fitowa daga kitchen d’in zuwa d’akin Mami. A bakin k’ofa na tsaya ganin ba Riga a jikinta tana shafa mai. “Shigo” na ji ta ce. Kamar ba zan shiga ba sai kuma na shiga kaina a k’asa. Tsaki ta zabga tana furta “wani munafuncin kuma kika tsuro da shi na tsayawa a bakin k’ofa?” Girgiza kai na nayi na ce “Aa naga kina saka kaya ne..” ta d’an yi tsaki kafin ta ja towel ta rufe k’irjinta “Yau kika saba gani na ba riga?” Na girgiza kai. “Flavour nake so Mami zan saka a kunun kwakwa..” na furta don son barin d’akin. “Yana gidan Uban Ahmad…” Mami ta furta cikin wata irin murya mai bayyana tsananin b’acin rai. Na d’ago ina kallonta idona yana kawo ruwa, ta iso gaba na cikin b’acin rai ta ce “Kike kallo na, na ce yana gidan Ubansa Sulaiman Sa’eed ba, ko da abinda zaki yi?” Hawaye ne kawai suka shiga zuraro min na saka k’afa da sauri na juya na bar d’akin jikina har rawa yake yi. Da k’yar na koma kitchen na k’arasa girkin a gaggauce na fa’da wanka. A raina ina jin ko me Mami zata yi ba zan rabu da Ahmad ba, amma fa zuciyata sai suya take yi. Shima bayan magribar da yazo sai naga fuskarsa sam ba annuri, kallona kawai yake da k’yar ma ya amshi cup d’in da ba zuba masa Kunun, naga yana kurb’a a hankali kamar yana shan magani, idonsa da suka jirkita zuwa brown colour a kaina. Kawai sai na samu kaina da rushewa da kuka. Bai hana ni kukan ba kamar yarda bai fasa kallona ba, abin mamaki shima sai naga gangarowar hawaye a nasa idon. “Me ya sameki?” Ya ce cikin wata irin murya da yasa na d’ago ina kallonsa… ban amsa masa ba illa cigaba da kukan da na yi, ya saka hannunsa ya mik’o min “Zo ki gaya min…” Ji na yi ba zan iya masa musu ba na isa wajensa jikina a sanyaye na zube a gabansa. Durk’ushe wa ya yi a gabana ya d’ora cup d’in kunun a bakina. A hankali na fara sipping. “Gaya min damuwarki?” Ya furta min a hankali. Na ce “Kai zan tambaya Ustaz, kai zan tambaya ji fa k’walla a idonka. Kana cikin damuwa yau gaba d’aya fa ko kira na baka yi ba…” ya saka hannunsa a goshina yana murzawa a hankali bayan ya jani jikinsa bakinsa ya saka a saman nawa yana lasar lips d’ina. Kafin ya lumshe idonsa yana cigaba da shafa goshin nawa ya furta “Ki yi shiru baki da lafiya ga kanki nan yayi zafi jijiyarsa ta tashi.” Ni da kaina na yarda ba ni da lafiya sai dai shima na ji nasa hannun shima ya ‘d’au zafin. Tafin hannunsa na kama na rungume a fuskata ina shak’ar k’amshin turarensa na furta “Ustaz kai ma jikinka zafi.” Idonsa a lumshe ya d’aga min kai. “Bani da lafiya ne AYSHA, wani irin ciwo zuciyata take min, ina kika je jiya da daddare, na kikkira wayarki baki d’aga ba?” Girgiza kai na yi ina mamakin furucinsa na furta “Ina zan je ban gaya maka ba, kaima ka san ba inda zan iya zuwa.” Still idonsa a lumshen ya sunkuya ya sunbaci tsinin hancina ya janye ni daga jikinsa sai naga ya mik’e yana kallona ya furta “Good night, idan kinga baki ji sauk’i ba ki fa’da a gida a kaiki asibiti..” Da mamaki na ce masa “Baka ci abincin ba ai?” “Am okay.” Ya fa’da yana fita da sauri kamar har a lokacin da k’walla a idonsa. Na mik’e zuciyata na bugawa na shige cikin d’aki duk hankalina a tashe. Tun daga ranar Ustaz ya canja gaba d’aya, baya kira na sai dai na kira shi. Khadija ma har waya take min ta ce sun rasa kansa a gida. Amsa guda nake bata nace nima anan d’in ban san me ke damunsa ba. Sau tari ma idan na kira shi cewa yake yana busy ya kashe wayar. Tun jikina na bani bakomai har nazo na yarda tabbas akwai wani abin da Ustaz yake b’oye min. Mami kuwa hankalinta kwance cikin zallar farin ciki take gudanar da shiryen shiryen bikin. Dukiya yake kashe min bata wasa ba, lamarin har ya fara firgita tunani na. Kullum kulawa take bani ta musamman. Na yi wani irin fitinannen kyau da kowa ya gani sai ya tanka. Ranar da za’a kamu, sanda aka min kwalliya wallahi idan ba fa’da aka yi ba zata zaka yi India ce, Saboda fitinannen kyan da na yi a cikin Indian dress d’in da aka min complete kwalliyarsu. Jikina a rufe yake ruf. Duk da fuskata da walwala sai dai sab’anin zuciyata da take cike da takaicin Ustaz na rashin kulawa da ya kamata ya bani, musamman a irin wannan lokacin da amarya da ango suke buk’atar zuwansa. Mai kwalliya na gama min Mami ta shigo wajen. Wani irin bu’de baki ta yi ta furta “Wow! Ya subhanallah Ayshata haka kika dawo? Fatabarakallahu Ahsanul Khaleek’in, Tabbas Allah ya yi halitta…” murmushi kawai na saki ina kallon yarda Mamin ta rungume ni a jikinta ana d’aukarmu hotuna ko ta ina. Na so ace Ustaz ne a madadinta. “Sai ki kirashi ku tafi.” Mami ta furta fuskarta a d’an tsuke kamar ba ita ta gama dariya yanzu ba. Wayata na d’auka na fara kiransa ta dinga ringing bai d’aga ba kamar yarda ya saba a kwanakin nan. A fusace na ji ya yi furucin “Wai menene?” Mamaki ya kamani jin tambayar rainin hankalin da ya yi min, na dinga kallon wayar ina son na tabbatar da gaske daga shine. “Na gama shiryawa” na furta a hankali. “Ki ce Mami ta kai ki.” Ya furta yana katse wayar. Ido na d’an ware kafin na sake danna wayar na tura masa text “Amma dai ka san kai ya kamata ka kai ni ko?” Ban zaci zai dawo min da amsa ba, sai naga ya turo min da “To ki jira…” na d’ago ina kallon Mami da suke magana da mai kwalliya ta kalleni itama ta ce “Ya taho?” Na d’aga kaina kawai ina furta “Eeh ga shi nan.” Tun a mota nake kallon yanayin Ustaz d’ina tamkar ba shi ba, fuskarsa murtuk babu annuri ko ka’dan a cikinta, na zata zai yaba kwalliya ta sai dai ko kallona bai yi ba. Ya ja mota muka tafi bayan Asma ta shiga. Hankali ne tashe nake kallonsa na ce “Baka da lafiya ne Ustaz?” Bai ko kalleni ba balle ya amsa min, ya cigaba da driving zuwa inda ake gudanar da shirin. Shiru motar tafiya kawai muke kamar kurame sai sautin k’ur’an da yake cikin motar cikin suratun nisa’i. Muna isa wajen Dinnerr Asma ta fita. Ni kuwa kasa fita na yi ina bin Ustaz da kallo da idanuwana da suke kawo ruwa. “Ya dai?” Ya furta yana d’an Cijan bakinsa da kawar da kai, na san kwallar da ke idonsa ce baya son na gani. Hannunsa kawai na kama k’am cikin nawa. Na furta “Gaya min ustaz, gaya min ko laifi na maka na baka hak’uri bana son irin wannan horon da kake min zuciyata ba zata ‘dauka ba…” cigaba ya yi da danna wayarsa idanunsa duk sun ka’da sun yi wani iri. “Baka da lafiya ko?” Na fa’da ina son lalubar k’wayar idonsa. A fusace ya ce “K’alau nake Ayshatu, just go and live me alone….” Kallonsa nake yi idonsa a runtse kafin na janye hannuna a hankali na fice daga motar idona na zubar da k’walla ban damu da b’acin kwalliyar ba damuwata sanin wani laifi na yiwa Ustazun Aysha.. 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢★✍️NA GA RAYUWA…21. Ina neman alfarma Don Allah da Manzonsa 😭🤲 don Allah ku shiga link ɗin nan ku yi mana voting MIKIYA WRITERS ASSOCIATION https://www.facebook.com/share/p/ChZaudpRhnBicHZ5/?mibextid=C7JYKg Idan kun shiga zai nuna requesting ana yin approving sai ku danna mini don Allah. Masoya Ustazun Aysha. A nuna mata kara… Daga kungiyata abar alfaharina. In dai kuna son na cigaba da rubutu cikin da’din rai… Ganin irin yawan mutanen da suka zo wajen kamun biki na, ya wanke min duk wani b’acin rai na da bak’in cikin dake nuk’urk’usar zuciyata. Wani farin ciki ya ziyarce ni, da na tuna duka wa’dannan mutanen sun zo ne saboda ni. Zuciyata ta yi haske walwala da fara’ar fuskata suka dawo. Mai hoto ce ta dinga d’aukata duk inda na saka k’afa, har zuwa sanda na isa wajen zama na. K’awayena suna bina a baya. A haka na zauna ina ta sakin murmushi. Ki’dan larabawa ne kawai yake tashi a wajen, da wani irin k’amshin turaren wuta masu da’din gaske. Ba’a rawa kowa yana wajensa a zaune sai mai gabatar da shirye shiryen bikin ce kawai a tsaye a filin wajen, tana ta yiwa manyan bak’i barka da zuwa. Kowa yana zaune cikin aji kai daga gani ka san mutane ne masu aji da wanda ilimi ya ratsa su suka halarci wajen. Ba wani hayaniya kowa yana zaune a inda aka tanadar masa ya zauna ya hanyar ganin Table no. D’insa a card d’insa. An ci an sha, kowa ya yi nak, an kuma yi barkwanci Malamai mata suka yi wa’azi sosai. Bayan tsawon lokaci aka tashi daga wajen. Dangin Ustaz ma sun zo sun kuma yi min kamu akan ku’di masu daraja. Ustaz ne ya mayar da ni gida bayan an tashi sai dai ko kallon arziki bai ha’dani da shi ba balle magana ta fatar baki. Tattarashi na yi na watsar don ni sam ban san wani laifi guda da na yi masa ba. Sai sha biyun dare na kashe wayata saboda naga da gaske dai Ustaz bai kira ba. Da Asuba kuwa ina kunna wayata kiransa ya shigo. Na saki ajiyar zuciya na saka hannu na amsa kiran cikin matuk’ar farin ciki, don rabon da ya yi min kira irin wannan har na manta. “Hello Habeeby…” Na kira shi da sunan da ban tab’a kiransa da shi ba. Madadin ya amsa sai ji na yi ya yi k’aramin tsaki ya furta “Ina ki ka je jiya da daddare, ba kira wayarki a kashe?” Zuciyata ta wani yunk’oro da tsananin b’acin rai na ce “Ina kuwa zan je da daddare? Wace irin tambaya ce wannan barci nake ji shi yasa na kashe wayar na kwanta… na san ba kira zaka yi ba shi yasa ban ma saka a kai ba.” “Kada ki raina min hankali mana, ki mayar da ni wani sokon namiji wanda bai san abinda yake yi ba, ke…….” D’if na kashe wayar da sauri, jin mamakin furucinsa, a muryarsa nake jin wani b’acin rai wanda na tabbatar har k’asan zuciyarsa yake. Ba zai yiwu na cigaba da waya da shi ba, don nima tawa zuciyar a hassale yake shi yasa na kashe. Na runtse idona ina jin wayar tana ta ringing kuma na san Ustaz ne don ringing d’insa daban ne. Hannu na saka na d’au wayar ba rubuta masa gajeran sak’o. “Allah ya huci zuciyar manya, ka yi hak’uri Habibeey idan zuciyarka ta yi sanyi ka kira ni. Ina tura masa na kashe wayar gaba ‘d’aya cikin wani irin tashin hankali naji hawaye na zubo min daga idona. Me na yiwa Ustaz me zafi haka da nake hango jin haushina a tsakiyar k’wayar idonsa? Ranar ne aka yi Dinnerr bikina a AMANI… Shima tsaf aka tsantsara min kwalliya ta cikin Black material wanda zab’in Ustazuna ne, kwalliyar ta min kyau matuk’a da gaske. Stone peach ne a jikin material d’in don haka aka min amfani da Shoe and clutch peach sai sark’ar wuyana ta zallar Zinare zubin English golden. Baa min kwalliya ba ranar saboda hawaye ya k’i barin idona ba kuma hawayen komai bane, sai na rabuwa da gidanmu Abba na Ummana, da Mami na. Ga su Ya Usman ma duk wai yau zamu yi ban kwana, zan tafi rayuwar da kowa yake gaya min sai hak’uri. Zuciyata ta yi rauni sosai musamman da aka kai ni wajen Abba mu yi sallama. Abba ya d’ago cikin jarumta ya saki murmushin da na tabbatar na k’arfin hali ne. Hannu yasa ya ya fito ni jikin sa. Muryarsa cike da k’arfin hali ya ce “Matso AYSHA ta….” Na matsa kuwa jikinsa na kafa kaina a saman cinyarsa ina zubar da wani irin hawaye. Hannu ya saka ya bubbuga baya na alamar rarrashe cikin wani irin furuci ya ce. “Ki yi hak’uri Ayshatu na, haka kowace mace ta gada kuma shine abin alfaharin ta. Aysha, ina son ki yiwa mijinki biyayya kwatankwacin biyayyar da Rabi’atul Adawiyya ta yiwa Mijinta, ko ki samawa zuri’ar gidanku k’ima da daraja a idanun Mijinki. Ba na son AYSHA ki yi abinda Mijin ki zai tsaneki har ta kai ga yazo yana dana sanin aurenki. Alhamdulillah ina alfahari da iyayenki mata ina so kuma ki yi koyi da su. Na fi son a fito min da gawar Ki daga gidan Ahmad Aysha, haka shine cikar burin Uba na gari, musamman da ke ke ka’dai ce d’iyata Mace da Allah ya bani. Soyayyar da nake miki ce ta saka na aurar da ke da k’ananun shekaru ba k’iyayya ba, Saboda na san Ahmad mutum ne na k’warai zai kuma rik’e min ke tsakaninsa da Allah. Ki kiyaye Ayshan Mami Allah ya miki albarka.” Ameen na ji jama’ar parlorn sun amsa Daga haka Abba ya ja hannuna ya damk’a min Alkur’ani ya saka min wata jaka mai kyau a gefena. “Alk’ur’ani ya zamo abokin hirarki, sallaya ta zama inda zaki sujjada ki kaiwa Allah kukanki, bana son kawo k’ara, mutuniyar kirki bata fiye kai k’arar Mijinta ba gudun b’ata masa suna. Kin ji ko?” Na d’aga kai ina jin zuciyata kamar zata tafasa saboda tsananin b’acin rai. Ranar kam Ustaz k’in zuwa ya yi ya kai ni wajen dinner, kiran duniya ya k’i d’agawa k’arshe ma sai ya kashe wayar tasa gaba d’aya. Jan bakina na yi na tsuke ban gayawa kowa ba sai su Mami ne suka tafi dani wajen dinner. Wannan shine labari na da duk wata soyayya da muka gudanar da Ustaz. Hawayene ya gangaro daga idona na mik’e daga saman kujerar da nake ina bin d’akin Abba na da kallo. Tunani ne ya shiga yi min suntiri a zuciyata so nake na gano dalilin da yasa duk son da Ustaz yake min ya riki’de ya koma zazzafar k’iyayyar da ta kasa b’oyuwa a ransa har ta kai shi ga furta min kalmar saki a daren auren mu. Daren da Ustaz ya da’de yana gaya min ya ci buri iri iri a kansa. Burin ganin Aysharsa a zahirin Aysharsa ba tare da shamakin tufafi ba. Sai ga shi daren yazo mana a wani irin hagunce da namu burin. Menene sila? “MAMIN KI!” Na ji zuciyata ta amsa min a tsawace.. Da sauri na runtse idona ina girgiza kai da k’arfin gaske. Daidai sanda aka bu’de k’ofar d’akin aka shigo. Na dawo hayyacina ina binsu da kallo cikin dishi dishin idona. Yaya Muhammad, Ya Sadik, Ya Umar, fuskarsu a murtuke ba fara’a suke zubo min ido. Suka shigo cikin wani irin taku da yake nuna zallar b’acin ran da suke ciki. Zuciyata ta shiga bugu da k’arfin gaske na dinga bin su da kallo ina kallon yarda suka dogara k’afafunsu akan kujerar suka zagaye ni da idanunsu… Wani irin kallo suke jifana da shi, wanda na rasa a mizanin da zan saka kallon nasu. Na san dai kallo ne na Allah wadaran halinki… Sautin zuciyata ya sake bugu da k’arfin gaske jin Ya.Muhd ya kira sunana da sark’akkiyar muryarsa. “AYSHA! Gaya mana laifin me kika yiwa Ahmad ya sake ki a daren farko? Kada kice mana bakomai don hakan ma kin san ba zai yiwu ba. Ba auren k’iyayya aka muku ba, Ustaz kuma bai d’ora miki iddarsa ba balle a ce auren d’and’ano ya yi da ke? Me kika masa?” Ya fa’da a tsawace. Hawaye ne kawai yake kwarara daga ido na. Na shiga masa rantsuwa da a idonsa ka’dai na san rantsuwa ta ba inda ta je. Na ba shi labarin abinda na sani dangane da canja min da Ustaz ya yi a kwanaki ka’dan da Suka rage na bikin mu. “Mak’aryaciyar banza, wa kike tunanin zai yarda da wannan tatsuniyar taki? Ta yaya kike tunanin mutum ya aureki yana tsananin son ki Sannan ya sake ki a daren da aka d’aura muku aure? Dole akwai wani abu ki gaya min gaskiya kawai… kada ki bari zargin da nake a zuciyata ya tabbata don ni zuciyata na gaya min tabbas ke da uwarki sun san komai, Mami ba, tabbas akwai saka hannunta a cikin lamarin haka nake ji a raina…. Ji muka yi an turo k’ofar da k’arfin gaske, an shigo, idanuna suka fa’da cikin na Mami da suka ka’da suka yi jajur. “Umar! Ni kake zargi da mutuwar auren Aysha?” Ta furta a tsawace idanunta suna zubar da hawaye… Umar ya cije bakinsa yana jijjiga kai ya furta “Ai ba abin mamaki ba ne, tunda kowa ya san kina adawa da auren….” “Faruk!” Umma ta fa’da a tsawace tana nuna shi da yatsa. Tashin hankalin da kake son ka jawo mana kenan a gidan nan. Ta yaya kake tunanin Fateema zata cutar da Aysha ta hanyar kashe mata aure? Kada na sake ji… bana so wani irin zancen banza ne wannan..? Kana cikin hayyacinka kuwa… Gani muka yi Mami ta juya zata fita daga ‘dakin, sai dai shigowar Abba ya hanata don da k’arfi ya turo k’ofar shima idanunsa akan Umma ya furta wai menene?” Nan Umma ta shiga ba shi labari Mami dai bata ce komai ba illa ficewa da ta yi tana hawaye. Madadin Abba ya yi fa’da sai naga ya girgiza kai ya kalli su Ya. Muhd ya furta “Ku tafi masallaci Muhammad an yi sallah.” Suka fice a hankali. Umma ta dubeshi yana zama yana danna waya ta ce “Amma ka barsu suka fita baka wa Umar fa’dan abinda ya yi ba?” Jingina ya yi da kujera yana lumshe idonsa ya furta “Nima ina tunanin da Umar yake….” Ba shiri Umma ta zauna tana furta “A’a Abban Aysha kada ka fara irin wannan maganar don Allah…” wani kallo ya mata kafin ya cije bakinsa. Ya furta “Ina zargi na ce, kuma tabbas idan na tabbatar da zargina wallahi sakinta zan yi, ina jiran feedback d’in Ahmad, mun yi waya da mahaifinsa ya gaya min su basu san labarin sakin ba, amma sun yi waya da Ahmad ya sanar masa yana airport d’in Abuja zai wuce egypt, amma Babansa ya dakatar da shi ya ce ya juyo lalle a daren nan zai zo ya gaya mana koma menene…” Umma jikinta a salub’e ta mik’e tana furta “Allah ya kyauta.” Ta bar ‘d’akin. abba ya sake d’agowa a karo na biyu yana kallona ya furta “Kin tabbata baki san komai ba?” Na d’aga masa kai na. Ya girgiza kansa shima ya mik’e ya fice daga d’akin. Tausayin kaina ya sake kamani. Kuka nake sosai ba wanda ya sake bi ta kaina, tun bayan da Umma ta shigo ta kawo min tea ta rutsa ni sai da na shanye. Sannan ta fice daga d’akin. Har dare gidanmu tsit ba wani mai walwala, y’an biki tuni suka watse bayan an sanar musu ba wani abu bane, Ustaz ne tafiyar gaggawa ta same shi. Bayan Isha’i Iyayen Ahmad suka zo, Abba ya saka aka shiga da su parlorn sa na cikin gida. Ni dai gaba na kawai fa’duwa yake. Ba su wani da’de ba suka tafi. Sai ga Ya.Umar ya shigo da gudu yana furta “Umma fito Abba ba lafiya jikinsa rawa yake…” Da wani irin sauri Umma ta fito nima ban san sanda na fito daga d’akin Abba ba, na bi bayansu sitroom d’in Abban. Da wani irin tsawa Abba ya ce min “Fice Aysha haihuwar ki ba ta min rana ba, ku d’auka ku dubi hotunan nan ku ga irin b’atancin da cutarwar da ta yiwa nagartar gidan nan…..” K’afafuna na rawa na zube a wajen ina kallon takardun da Ya Muhammad ya zubo min, ido na ware ganin ba abinda ya b’uya a hoton daga tsiraicina komai na a waje, k’irji and everything gefe guda wani mutum ne zaune kusa da ni yana shafa k’irjina…. Na zunduma wani Uban ihu, ina jin numfashina na neman barin gangar jikina… Kash! Ina mai baku hak’uri, anan Book 1 ya k’are, sai dai ba zan yi jumurin kawo muku shi a kullum ba ta kafar whatsapp saboda wani dalili mai girman gaske, zan mayar da posting Litinin talata laraba da alhamis. Wato sau hu’du a sati. Sauran ranakun zan dinga posting a arewabooks. Y’an Arewabooks zasu dinga samu kullum In sha Allah. Dafatan za’a min uziri. Na gode sosai. Masu so arewa ku yi searching @nazeefah ko kuyi searching sunan Book d’in. Labari yanzu aka fara AYSHA bata ga komai ba sai nan gaba. Akwai book 2 akwai Book 3. Ganin rayuwar yana gaba… 𝔍𝔦𝔨𝔞𝔯 𝔑𝔞𝔰𝔥𝔢✍️