RAMIN MUGUNTA Ka gina shi dai-dai da kai WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN MMN HIBBA SADAUKARWA NA SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH) AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA. Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljanna yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. GARGAƊI littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 07073193332 1-2 Ƙarfe sha biyu na dare dai-dai babu abin da kake ji se kukan tsin tsaye daga can kuma se harbin bindiga ta ko ina ji kake tau tau darammmmm har sashi se wuce wa yake kamar ruwan sama nan da nan garin ya kuma yin shiru, a daidai wani tanƙa meman gida ƴan fashin suka tsaya dukkan su fuskokonsi arufe suke wasu daga cikinsu ne suka ɗa ne katangar gidan ɗakin me gadi suka shiga inda suka rakumi shi se gashi atsaye yana rarraba ido ya buɗe baki ze yi ihu ɗayan yace. “idan ka kuskura kayi mana ihu sena sa bindiga na fasama ƙwa ƙwalwa wallahi” tsutt me gadin ya tsuke magan sa kamin wannan lokacin tini ya fitsare wandan sa da firsari jikin sa se kyar ma yake janyo shi suka yi xuwa harabar gidan biyu daga cikin su ne suka buɗe wa sauran gett suka shigo inda suka yiwa gidan ƙawanya me gadi suka sa a gaba suka ce ya nuna musu sashin me gidan tiryan tiryan ya kai su duka ɗaya oga su ya yiwa Ƙofar ta buɗe suka shiga farlon, nan ya bawa yaran nasa izinin da su taso masa masu gidan cikin mintina ƙalilan suka tasosu bayin allah dik sun ruɗe musamman me gidan , yana kuka yana basu haƙuri tara da cewa in dai kuɗi suke so xe basu amma su kai ƙema da gass suka ce su ransa suka zo ɗauka kuma turosu akayi. “gwaja” “na'am” oga “miƙo min bindiga ta” miƙa masa yayi ya amsa tara da saita kan alhajin kalmar shahada ya Shiga yi yana kaiwa ƙarshe. harasashi ya fasa kansa take ya faɗi ƙasa wata ƙara matar ta saki bata gama ƙarar ita ma ya sakar mata bulet nan da nan jini ya wanke ɗakin, MANAL wacca take ɗakin ta ta jiyo ƙarar bindiga tayo waje a zatan ta wani gurinne taji tsoro ta fito dai-dai lokacin da ɗan fashin nan ya harbi mahaifiyar ta ƙara ta saki tara da yin wurin iyayan nata wanda suke kwance cikin jini, “ABBA MOMY ABBA ku tashi ku tashi dan Allah MOMY ki tashi kufa kuka min alƙawarin zaku kaini gurin wasa gobe shine.. se kuma tayi shiru tara da juyawa gurin ƴan fashin cikin zafin nama ta warci bindigar... “kun kashe min iyaye na kun rabani dasu me suka muku na san iyaye na masu kirki ne amma yau gashi kun raba ni da su dan Allah ni ma ku kashe ni se ta saita kanta da bindigar data ƙwata a hannun su , ogasu ne yayi saurin amshe bindigar yace “ ba a ce muka sheki ba dan haka mungama ai kin mu se an jima” yana gama faɗar haka yayi waje ragowar suka mara mai baya aka bar ta daga ita seme gadi wanda tini yayi suman tsaye, itama MANAL faɗuwa ƙasa tayi sumammiya gari na waye wa unguwa ta ɗauka ƴan fashi sun kashe ALHAJI SA'AD ME DALAH kan kace kwabo zance ya yaɗu gidan rediyo talabijin kai har A jarida a buga dik wanda yaji labarin se yayi kuka yayi ala-wadai da dik wanda yake da sa hannu acikin kisan domin kowa ya san ALHAJI SA'AD mutumin kirki ne ga temakon, talakawa haka itama matarsa hajiya ZARAH. mutuniyar kirki ce ga faran faran da mutane, ƴan jaridu da masu bincike sunyi iya ƙoƙarin su wajan binciko wa inda suka yi wannan ta asar amma basu samu wata Hujja ba MANAL kuwa da ƙyar aka samu kanta dan tayi doguwar suma bayan an haɗa su aka ce tazo tayi musu addu'a dan a kaisu makwan cin su anan ne MANAL ta kuma shiga wani sabon tashin hankalin kan gawar iyayan nata ta faɗa tana kuka me ban tausayi se da ta bawa kowa tausayi da kyar aka janye ta aka saikace su sannan aka kaisu makwan cinsu., tin da aka fitada gawar wani su MANAL ta kuma suma har aka dawo daga Kai su bata far faɗo ba se da aka dan gana da asibiti shima da kyar a kasamu kanta sannan akayi mata allurar bacci, se magariba ta farka tana ƙarewa ɗakin da aka kwantar da ita kallo hawaye na bin gefen idonta, “haƙuri zakiyi MANAL haka Allah ya ƙaddara musu ta wannan hanyar Allah ya karɓi rayuwar su su kuma wa inda suka kashe su Allah ya ganar dasu” ko bata juya ba ta san waye me magana wato ALHAJI BUKAR ne ƙanin mahaifin ta uwassu ɗaya ubansu ɗaya, wani sabon kukan MANAL ta ƙara fashewa da shi ganin ƙanin mahaifinta amma babu mahaifin ta agurin nan suka yo kanta shi da matar sa da ƴa ƴansa suna rarrashin ta “ki dena kuka MANAL in sha Allahu ba zaki yi rashin iyaye ba zan maye miki gurbin ɗan uwana kuma ga maman su NABILA nan itama zata nake miki uwa kinji ƴa ta, ni dai fatana kirki sa damuwa aranki wani abin ya same ki ina so naga jinin ɗan uwana dan Allah MANAL kiyi haƙuri ki fawwalawa Allah komai kinji” kai ta gyaɗa mai alamar to ta juya ta kalli su NABILA da ZAINAB wa inda suka yi jugum murmushin ƙarfin hali tayi tara da yi musu alama da su matso gare ta nan kuwa suka ƙaraso ta ruƙo hanna yansu tana kallansu ba tara da tace komai ba. To bayan sadakar bakwai dik wasu kadarori na ALHAJI SA'AD ME DALAH suka zama mallakin MANAL tin agurin ALAJI BUKAR ya nuna ƙin amince warsa, se dai a raba dukiyar biyu A bashi rabi inda aboka nan margayi wato ALAJI SA'AD suka ce a ah hakan baze yu ba yayi haƙuri ƙarshe dai aka rabu baran baran har alaji bukar yana cewa, kila ma su suka kashe mai ɗan uwan sa .. BAYAN ANYI ARBA'IN. Gaba ɗaya alaji bukar da ƴaƴan sa suka kwaso kayan su suka dawo gidan kowa ya zaɓi inda ze zauna tin daga nan MANAL ta fara ganin sauyin rayuwa babu wanda yake bi ta kanta idan gari ya waye akayi abin kari babume kiran ta se dai ta jiyo hayaniyar su suna shewa ita kuwa tana ɗaki kullum cikin karatun alƙur'ani take. tana nema wa iya yanta rahama wajan ubangiji tina nin iya yanta ya dame ta kullum se ytayi mafarki dasu musamma MOMYN ta yau ma kamar kullum cikin bacci tazo mata tana yi mata nasi ha da taji tsoran allah kada ta kus kura ta saɓa mai idan ta tsinci kanta awani yana yi dik yanda tasamu kanta tayi haƙuri ta kuma gode masa dan wata rana se labari, firgigit ta tashi daga baccin da take saka makon dukan da taji an ɗala mata NABILA ta gani tsaye akan ta tana binta da wani irin kallo wanda ta kasa gane ma'anarsa “ idan kin gadama kixo in ji DADY " daga haka NABILA ta fice daga ɗakin gami da banko mata ƙofar kallan mamaki MANAL ta bita da shi bata kawo komai a ranta ba ta miƙe tare da shiga tolet tayi wanka ta sauya kayan jikin ta ta saka hijab ɗin ta har ƙasa ahankali take tafiya kamar ba itaba, canjin yana yin data gani akan fuskokin su ya bata tsoro musamman DADY, kusa da shi taje ta zauna akan kafet tace “ina kwana DADY” “da ban kwana ba zaki ganni tin ɗazu na aika akiraki se yanxu kika gadamar zuwa?” girgiza Kai tayi gamida cewa “kayi haƙuri DADY” tsaki yayi yace. “so nake ki bani dik wasu takaddu da aka baki wanda akace kinci gado” da sauri MANAL ta ɗago kanta tana duban sa. “ eh ai na san kinji me na ce ” ya faɗa cikin tsawa wadda ta ƙara firgita ta . “to DADY bara na kawo maka” ta faɗa cikin muryar kuka da razana tin da take ba'a taɓa yi mata tsawa ba sega shi yau bayan ran mahaifan ta taga sauye sauye, cikin mitina ƙalilan ta kawomai jakar takar dun da dik wasu kadarori da aka bata karɓa, yayi yana washe baki „zan ajiye miki a guri na dannaga ke biki ɗauke su da mahimmanci ba” to kawai tace mai dik da bahaka taso ba. Ahankali rayuwa tayiwa MANAL ƙunci dik wannan ƙibar da hasken yanxu babu su yanxu ne ta san meye rayuwa ya akeyin ta gaba ɗaya ta fita a hayya cinta ta lalace, sakamakon baƙae wuyar data kesha A gurin ƙanin mahaifin ta dama matar sa da ƴaƴan su sun mai da tamkar baiwa MANAL da bata san sn shiga kicin ba yanxu ta sani wanki shara wanke wanke dik ita keyi inka ganta ba zaka taɓa cewa ta taɓa rayuwar jin daɗi ba wani. gigitaccan mari NABILA ta wanke ta da shi hagu da dama tace “ dan ubanki haka ake wanki? ji yanda kika bari kaya na suka ɓaci da ƙasa to wallahi se kin kuma wanke su kuma ki zauna anan har sesun bushe kinji Me nace ?” da suri MANAL tace “to” tsaki NABILA tayi, "shasha kawai dabba da bata san komai ba wallahi dama na tsane ki yanxu ba kida wani zaɓi daya wuce ki bimu in ba haka ba muna kasa ki, wannan kyan naki da kike taƙama da shi se na disa she shi kin zama mujiya acikin muatane.” tana gama faɗin haka tayi gaba. durƙushewa MANAL tayi ta saki kuka m ecin rai, mutuwa men min yan kan ƙauna kin raba ni da iyaye na tin ba aje ko ina ba na fara ganin sauyi wanda nake tina nin ze share min hawaye na shine A sahun gaba wajan ganin an kuntata min a yanzu ni MANAL ko suturar kirki bani da ita suna NABILA sun kwashe babu hutu kullum cikin aiki babu abinci me kyu babu gurin kwana me kyau ƙarshema aɗakin baƙi nake kwana wayo ni MANAL ya Allah ka kawo min ɗauki........” MMN HIBBA CE RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER✍️ SUMAYYA ABDULLAH ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.✍️ littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 3-4 Haka MANAL ta kuma wanke kayan dik da sanyin da ake su rawa , sannan ta zauna zaman jiran su bushe “kee kee kee MANAL” mamy ce take ƙwala mata kira, jiki na kyarma taje ta tsuguna “gani mamy" ta faɗa cikin rauna nan niyar murya dan tasan yau kashin ta ya bushe bata gama tina nin da take yi ba taji an rife ta da duka, ta ko ina ihuu take tana bata haƙuri amma kamar tana tunzura ta ƙafa tasa ta ringa haurin ta har se da taga ta galaɓai ta san nan ta ƙyale ta zuwa wannan lokacin MANAL ji take gwara mutuwa da wannan azabar da take ciki, ƙafa tasa ta taka mata hannu wata razananninyar ƙara ta saki se kuma ɗif babu alamar rai ajikin ta , “kuma wallahi ki tashi ki je ki ɗora abin cin rana ki gyara gidan nan dan baƙi na sun kusa ƙaraso wa ” se ta kuma harbin ta da ƙafa ta juya cikin gida abin ta, ahankali MANAL ta soma buɗe idon ta da suka mata nauyi tafi minti talatin da far faɗowa daga suman da tayi amma ta kasa motsa wa ji take kamar hannun ta ba'a jikin ta yake ba, tazo zata miƙe jiri ya kuma ɗibar ta, ta kuma faɗuwa ta yi haka ya kusa sau uku kafin Allah ya bata sa'a ta miƙe tana ɗingisa ƙafa haka ta shiga kicin ɗin dik da ba gani take sosai ba ta jima tana girki ita ce ɗora wannan sauke wannan se la'asar sakaliya ta gama, sa shin msmy ta nufa wanda ada yake mazaunin na MOMYN ta da sallama ta shiga amma ba'a amsa ba hakan yasa ta kuma yi wata sallamar ZAINAB ce ta fito daga ɗakin ba tara da ta kalli inda take ba tayi gaba ganin haka yasa ita ma MANAL ta fito daga ɗakin A hanya sukai karo da mamy tayi saurin durƙusawa ƙasa baki na rawa tace “momy na gama girkin ko da abin da za'ayi miki ?" wani matsiyacin kallo ta bita da shi kana tace, “au so kike in kuma mai mai ta miki to cewa na yi ki gyara ko ina na gidan nan”, sunkuyar da kai MANAL tayi hawaye na bin kun cin ta cikin tsoro da gudin abinda zeje ya dawo tace “ dan Allah mamy ki bani abinci yinwa nake ji yau kwana na biyu banci komai ba ” “ehhh lallai yarin ya kin giga ina magana kina cewa abinci zaki ci shegiya acici to ka zakici ba maza maza ki tashi kiyi abinda nace miki” ta faɗa cikin tsawa jiki na ɓari, MANAL ta tashi har tana neman faɗowa daga matattakalar benan haka ta gyara gidan tana yi tana faɗuwa sabida yinwar da taci ƙarfin ta, tana gamawa taja jiki da kyar ta shige ɗakin ta , sallah ma a zaune tayi ta, tana idar wa ta ɗan kishin giɗa. nan take wani azababben bacci me haɗe da yinwa yayi gaba da ita tara da wasu muna nan mafarkai, tayi nisa cikin baccin da bawani daɗinsa take ji ba cikin taji ankwara mata ruwa me sanyi kamar daga cijin fireza aka ciro shi . tini jikin ta ya hau tsuma ta koma gefe ta kure kamar tsumma., wata wulaƙan tacciyar dariya ZAINAB tayi tana kallon yanda haƙoran MANAL suke gwaruwa kamar mazari “shigiya me suffar aljanu se kizo DADY na kiran ki yau kam se kin ƙwammace ƴan fashin da suka kashe iya yanki kema sun haɗa dake mayya” daga haka ZAINAB ta juya tana sakin wani shu'umin murmushi kayan da suka jiƙe ta canza dik da suma wa'inda tasa ba wankakku bane raban da tasa kaya masu kyau wankakku har ta matan shekarun gashin kanta kuwa ba'a magana yayi dauɗa ya cukur kuɗe shima se tashin wari da hamami da yake yi ko ɗan kunne babu a kunnan ta ta koma tamkar namiji se idanu da suka yo waje sabida baƙar azaba da kuma yinwa,. Ras rasssss gaban ta ya yanke ya faɗi yanda taga fuskokinsu ya tabbatar mata da akwai abinda yake faruwa, can nesa da su ta samu guri ta ta kure “Keeeeeeeeee MANAL ina sarƙar gold ɗin da kika ɗauka?” cikin firgici gamida razana bakin ta har harɗewa yake wajan faɗin “sassa sarƙa kuma DADY wallahi ban ɗauka ba bamma san a'ina aka ajiye ta ba,” “Kam bala'i, to idan bake kika ɗauka ba uban waye ze ɗauka ko kina nufin su NABILA ne suka ɗauka to wallahi fito min da sarƙa ta kona kashe ki” cewar MAMY “wallahi wallahi MAMY ba ni na ɗauka ba.” ZAINAB ce ta ce . “ amma naga kin shiga ɗakin MAMY ɗazu kuma naga kin ɓoye wani abu a zanin ki dana tambaye ki me kika ɗauka kika ce babu komai kona miki ƙarya?”girgiza kai MANAL tayi dan in tace ba haka bane ba zasu yarda ba “DADY aje a duba ɗakin ta”cewar NABILA, meze faru ana xuwa ɗakin aka ga sarƙar aƙar ƙashin tsummo karanta kuka MANAL take iya ƙarfin ta tana gaya musu ba ita ta ɗauka ba DADY ne ya dunƙule hannun sa ya sakar mata abaki tini haƙoran ta biyu suka yo waje be tsaya anan ba falo ya jata yace ta kwanta aƙasa ta kuma ɗaga rigar ta wata mirtikekiyar dorina ya ɗakko wacca da ita ake dukan dokuna, dokunan ma na gidan sarauta wa inda suka giga. babu imani babu tausayi DADY ya shiga sauke mata wannan dorinar agadan bayan ta , tin MANAL na ƙara har ta dena ne man ɗauki NABILA da ZAINAB se ihuuu suke suna cewa ƙara mata DADY karka ƙyale ta har se ta mutu se da yaga ta de na motsi sannan ya bar ta. haka suka tsallake ta suka wuce ko a jikinsu hasali ma daɗi suke ji Dady kuwa cewa yake “Allah yasa ta mutu kowa ma ya huta dan so yake yayi wadaƙa da dukiyar ta, MANAL kuwa bata far faɗo ba kuma babu alamun zata farka ɗin inda sukabar ta nan suka dawo suka same ta kamar gawa kanta ya kumbura kamar ze fashe haka ma idanun ta suka koma kamar lemon zaƙi dan kumburi, bayan sun gama karyawa NABILA taje inda MANAL ke kwance tasa ƙafa ta harbe ta amma kamar ta taɓa dutse shewa ta saki gamida ƙwallawa su Dady da mamy kira suzo su ga MANAL ta mutu burin su ya cika , zasu ci karan su babu babbakaaaaa suma ihuuuuu su kasa suna murna Allah ya rabasu da alaƙakai, dariya ZAINAB tayi gamida cewa "shi kenan Dady dukiya ta zama tamu dik wanda ya tambaya me yasa Meta se muce karuwan ci ta shiga har ta kwaso cutar , H.I.V wato ƙanjamau ita ce ta kashe ta kaga babu wanda ze zarge mu ” “haka za'ayi zee kin kawo shawara me kyau, nan suka bar ta kowa ya shige ɗakin sa acewar su se sunyi wanka sun gama abinda suke sannan zasu gayawa mutane mutuwar MANAL, MANAL kuwa wacca ta mance a'ina take aduniya ko alahira ta dai fi zoton alahira take, cikin azaba da radaɗi ta fara motsawa dishi dishi ta soma gani hakan yasa ta maida idon ta ta rufe , bayan minti tala tin ta sake yin ƙurin sake buɗewa dik hazo hazo take ganin komai ga bakin ta da yake shatatar da jini sakamakon haƙoran ta da suka fita cikin ranta tace “shi kenan na zama me wawulo sun raba ni da haƙora na, Hannun ta da ƙafar ta wa inda suka zama kamar tirmi dan kumburi suma ta kasa motsasu se yanxu ne ta sake tabbatar da rashin iyaye ba ƙaramin musiba bane ashe haka rayuwa take? Ashe dama mutane kowa da kalar zuciyar sa dama in kuka fito ciki ɗaya da mutum halinku ba iri ɗaya bane kowa da nasa ? Allah sarki ABBANA ashe yanda ka. ɗauki ɗan uwanka shi ba haka ya ɗauke ka ba ashe ba sonka yake ba afili yake nuna ma yana sonka a Zuciyarsa kuɗin ka yake so Allah Sarki iyaye na kun tafi kun bar ni alokacin da nake matuƙar buƙatar ku Allah sarki ABBA na kullum kana gaya min cewa ko bayan ranka ƙanin ka shine wanda ze riƙe ni ze bani kulawa kamar kai, se gashi shine yake neman makasa ta baya so ya buɗe ido yaga ina numfashi sabida abin duniya wanda kaima daka tara su kuma kake alkairi dasu ka tafi ka barsu ina ma mutuwa tazo ta ɗauke ni, na huta da wannan uƙubar hawayen azaba ne suka ringa xubo mata kanta ya kuma yi mata nauyi, tamkar dutse Wata ƙara taji an saki wan da ta san NABILA ce nan ta shiga ƙwalwa su mamy kira “Dady mamy kuzo ku ga wannan baƙar mayyar ashe bata mutu ba” sabida sauri dady har neman sulewa yake nan suka tsaya akan ta . wani ƙululun baƙin ciki ne ya kama DADY wannan waca iriyar yarinya ce me baƙin naci dik wannan wahalar da ya bata be sa ta mutu ba tsabar takai ci daya cika shi cewa yayi “ kar wanda ya kuma sauraran ta kuma kar a kuma bata abinci har se yinawa da ƙishiriwa sun kashe ta yana gama faɗar haka ya haye saman be ne yana ta masifa ɗakin sa ya shiga yana ta faman huci se zagaye ɗakin yake ya riga da ya gama tsara komai game da yanda ze yi da dukiyar MANAL idan ta mutu se gashi ta far faɗo tsaki ya kuma yi a fili ya ce“ dole ne ki mutu bazan ci gaba da zama a haka ba tin da mahaifin ki baya doran duniya kuma ke kaɗai ya bari aka mallaka miki dukiyar sa dole ke ma ki mutu ko ta halin ƙaƙa se kin bar dunyar nan ni ma na fanta ma da dukiyar ɗan uwa na! na yi facaka da ita zaki mutu zaki mutu zaki mutu MANAL” ya faɗa yana jefar da hular kansa. KEEEEE DUNIYA INA ZAKI DAMU NE ANYA WA INNAN MUTANAN SUNA JIN TSORAN ALLAH YA ALLAH KASA MU FI ƘARFIN ZUCIYAR MU ALLAHUMMA AMEN IDAN HAR KE MASOYIYA TA TA TSAKANI DA ALLAH KUMA KINA JIN DAƊIN LITTAFIN NAN TO KI TAYA NI TURAWA CIKIN WASU GRP MMN HIBBA TANA GODIYA DA TARIN MASOYA DA ADDU'AR DA KUKE MATA SHAWARA D'AYA ZAN BAWA MASU KARATUN LITTAFIN RAMIN MUGUNTA SISTER BAN CE KARKI KARANTA LITTAFIN NAN BA AMMA IDAN KIN SAN KINA DA RAUNIN ZUCIYA TO KARKI KARANTA DOMIN BA'A FARA KOMAI BA YANZU MANAL ZATA FARA SHAN WUYA WANNAN SHARAR FAGE NE. ƙalamin mmn hibba ne✍️ RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER✍ SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi Shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 5-6 Kamar yanda DADY ya faɗa hakan ce ta kasance yau kwanan MANAL huɗu ba tara da tasa komai acikin ta ba se dai ta sha ruwa nan da nan ta kuma tsotsewa ta koma kamar ƴar tsana kana iya ganin ƙasusuwan jikin ta , ƙafar ta ta kumbura har ta soma xubar da ruwa amma babu wanda yaji tausayin ta sema abinda ya kuma yin gaba yau ta kama litinin NABILA da ƙawayan ta sun cika gidan se shaye shaye suke abin babu kyan gani maza da mata, ne sunyi wata iriyar shiga wacca da ita gawamma babu kowacce da saurayin ta suna holewar su, gefe guda hakimar tasu uwar gayyar ce jikin wani saurayin ta babu kunya babu tsoran Allah gaba ɗaya gidan ya kauraye da warin wuy wuy da sigari se guntsa suke suna fesarwa. MANAL, ce ta fito tana bin bango dan ko tsayuwar kirki bata iyayi sabida yinwa gaba ɗayan su suka bushe da dariya, kamar mahaukata sabbin kamu MANAL kuwa ko ajikin ta ita bata damu ba dik da tasan da ita suke. ɗaya daga cikin samarin ne yace. “BEBY NABEE ina kuka samo wannan ƙasusuwan jifa ƙashin ta ina iya irgasu zama da irin wannan matsala ne se su goga muku talauci” hhhhhhhhhhhhh, suka kuma sa dariya irin ta gogaggun ƴan duniya tsaki NABILA tayi gami da cewa “kai dai bari Beby wallahi daga ƙauye aka kawo mana ita take mana shara da wanke wanke baku ga yana yin ta kalar na ƴan ƙauye ne ba ?” suka kuma bushewa da wata wula ƙantacciyar dariya, “keeeeee, MANAL baki ga mutane bane zaki wuce baki gaida su ba ?” a san yaye tace “kiyi haƙuri aunty NABILA” se ta juya gurin ƙawayan nata har ƙasa ta tsuguna tace “sannun ku” babu wanda ya amsa a cikin su se ma wani ƙas-ƙantaccan kallo da suka bita da shi. “da halla ni jeki dafa mana shayi ki kawo mana kuma wallahi kika daɗe sena miki bille afuskar ki” ta faɗa cikin ɗaga murya, kicin ɗin ta shiga dafe da cikin ta da yake ƙugin yinwa tana addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki da gaggawa. wani ragowar abinci ta gani an ajiye da alama bana yau ba ne dan har ya fara yami ALLAHU akubar, haka MANAL tayi zaman dir shan tana ci kwa nan nan abinci da ko dabba baza'a bawa ba ita kuwa murna, take yi ta samu abin da zata sawa cikin ta. ta manta da wani dafa shayi se da taji NABILA na ƙwala mata kira bashiri ta miƙe jiki na ɓari, kamar mazari gass ɗin ta kunna ta haɗa komai da ake buƙata na shayi kan kaceme har ta gama ta juye musu a' filas ɗin shayi ta ɗauki ƙana nun kofuna na shan shayi ta fita kanta aƙasa dan bata son haɗa ido da wa innan ƙartin. gaban NABILA ta kai filet ɗin ta ajiye ta juya zata tafi “ uban waye ze zuba mana shayin da kike ƙoƙarin tafiya ko kinji na ce ki tafi ne?” girgiza kai ta yi gami da dawo wa ta zuba wa kowannen su sannan ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana miƙa musu “NABEE dama haka kuke dafa shayi agidan ku?” NANSY ta faɗa gami da furzo, shayin daga bakin ta . nan suma sauran suka kai cup ɗin shayin bakin su ai kuwa suma suka furxo da shi suna ya mutsa fuska, haushi ne ya kama NABILA ta ɗauki cup ɗin shayin ta kai bakin ta ai kwa ita ma ta furzo shi ashe ba siga MANAL tasa acikin shayin ba gishiri ta saka a madadin siga haushi ne , ya kama NABILA yanda MANAL ta kunya ta ta agaban ƙawayanta MANAL kuwa ta rakuɓe jikin ta se kyarma, yake cikin ɓacin rai, NABILA ta cika cup ɗin da yake gaban ta da shayi bata ɓata lokaci ba ta sheƙawa MANAL afuska wata gigitacciyar kara, MANAL ta saki sabida azaba da raɗaɗi NABILA kuwa ko ajikin ta wani cup ɗin ta kuma cika wa ta kuma sheƙa mata, azaba tai azaba Uƙu ba tai Uƙu ba gaba ɗaya fuskar MANAL babu kyan gani domin kuwa ƙunar ta shige ta fatar fuskar ta ta saɓule tin daga wuyan ta da sauran sassan jikin ta hakan bai ishi NABILA ba seda ta haɗa mata da duka tana zagin ta dama iyayan ta da suka rigamu gidan gaskiya. se da aboka nan sha shancin nata suka riƙe ta wai ta bar ta haka Ahakan ma taji jiki . “ NABEE wannan ƙunar da kika yi mata be dace ba idan aka bar ta ahaka fuskar ta ze iya samun matsala kamata yayi mu kaita asibiti tin da wuri” cewar JAMSY. wata uwar harara NABILA ta jefi JAMSY da ita kana tace. “wallahi babu inda zani se dai ta mutu idan ma ta mutu waya damu da ita. fuuuuu, ta wuce kamar zata tashi sama. suma sauran suka fice daga gidan suka kama gaban su akabar JAMSY kaɗai ita kuwa tausayin MANAL ne ya cika ta dan haka ta ƙudiri aniyar ce to rayuwar ta ɗaukar MANAL tayi kamar gawa babu alamar rai atare da ita bayan mota ta saka ta sosai take gudu, tamkar zata tashi sama tin kanta isa asibitin ta yiwa Dr. ɗin waya abinka da ƴaƴan masu kuɗi babu wani bincike ko ace se tazo da ƴan sanda aka shiga da MANAL ɗakin tiya ta jim kaɗan Dr ɗin ya fito yace. "JAMSY ta same shi a office ɗin sa baya nin da Dr JAMAL yayi wa JAMSY ya ɗaga mata hankali, ya tabbatar da cewa. fuskar MANAL tayi dameji In kuwa ana so ta dawo dai-dai to fa se an kashe maƙudan kuɗi wanda aƙallah sun kai million goma da dubu ɗari bakwai da hamsin sosai hankalin, JAMSY ya tashi ta san Ko ta gayawa su NABILA ba zasu biya kuɗin ba, dan haka tayi alƙawarin zata ɗauki nauyin aikin tinda tana da kuɗin da suka fi haka a Account ɗin ta nan ta cewa Dr. su fara aikin zata biya na dai ta cike komai da komai aka shiga da MANAL ɗakin tiya ta.... Can gidan kuwa babu wanda ya tambayi inda MANAL take har kokin gaban su kawai suke likafa taci gaba DADY ya mallakawa su ZAINAB da BABILA motoci kowacce uku tara da dan ƙara musu maƙudan kuɗaɗe a account ɗin su haka ita ma MAMY ya ɗauki gida sukutum guda ya bata wanda aƙalla ze kai million hamsin bayan haka ya biya musu kuɗin tafiya ƙasar India dama sauran ƙasashe wai suje su huta duniya sabuwa DADY se wadaƙa yake da dukiyar ƴar ɗan uwan sa ba tara da yasan abinda zeje ya dawo ba. su NABILA da ZAINAB sun samu yanda suke so mahaifinsu ya basu damar su zagi kowa su daki uban kowa kuma su zauna lpy hakan ya ƙara musu girman kai da jin cewa suma ƴaƴan masu kuɗi ne hakan yasa suka kuma dulmiya cikin ƴaƴan masu kuɗi abin dai ba kyan gani sune shaye shaye Kwan a hotel dik wani gidan fati in dai a kano yake to fa sun san shi samari ta ko ina se ɓullu musu suke suna kashe musu kuɗi kamar basa so musamman ma NABILA dan tafi ZAINAB mutane kai in kaga manya manyan masu kuɗin da suke zuwa gurin ta abin se ya baka mamaki hakan be taɓa damun iyayen su ba hasali ma daɗi suke ji ƴaƴan su sun zama man yan yara yau kwanan NABILA huɗu bata gidan abige ta shigo gidan tana tangaɗi gamida layi da surutai bar katai irin na ƴan maye, SUNA WANI LITTAFINA DANA KESON RUBUTAWA MAI SUNA (ƳAR SHAYE SHAYE ) Yaune ake saran kwance tiya tar da aka yiwa MANAL wanda rabin jin yar tata ya ta'allaƙa akan Dr. JAMAL wanda JAMSY ta bashi amana da kuma gayamai irin halinda MANAL ke ciki sabida ita tayi tafiya ƙasar KAMBIRIC dan iyayen ta acan suke da zama shi ne suka bugo mata waya lallai tazo suna son ganin ta hakan yasa ta damƙa amanar MANAL a hannun sa masha Allah aiki yayi kyau sosai su kansu likitocin da suka mata aikin sunyi mamakin aikin basu taɓa tsammanin zeyi kyan haka ba. sosai MANAL ta saba da Dr. JAMAL dan mutum ne me sakin fuska ga kuma faran faran, da mutane ai kuwa MANAL tayi kayu jikin ta da kyan ta da hasken ta suka soma dawowa dik wannan kasusuwan yanzu sun koma. kullum idan MANAL tayi sallah bayan ta yiwa iya yanta addu'a se ta yiwa JAMSY da Dr. JAMAL yau watan ta uku cifff a asibitin Kuma yau ne za'a bata sallama se dai abinda yafi bawa Dr. JAMAL mamaki ya kuma ɗaure mai kai yanda MANAL ta shafe wata uku s asibitin amma babu wanda yazo yace shi ɗan uwan MANAL ne sosai yake mamaki yana so ya tambaye ta se dai baya son shiga hurimin da ba na sa ba dan haka yaja bakinsa ya zuge. MASARAUTAR ZAKI Yau ma kamar kullum yarima SUHAIL ne kwance akan taf keken gadon sa wanda ya sha zanin gado na al-farma. bacci yake sosai amma se juyi yake yi kamar wanda yake ganin wani abu cikin baccin nasa frigigit ya tashi yana salati se gumi yake kamar wanda yayiwa sarki ƙarya ƙafafunsa ya xuro ƙasa yasa wani tattausan ta kalmi mafarki da ya saba yi kullum yau ma shi yayi se dai be taɓa ganin fuskar ta ba kawai abinda ya sani shine tana yawan zuwar mai a mafarki tana kuka tana neman tema konsa kuma wai acikin wata rijiya me zurfi da duhu take ga macizai da kunamu suna ta saranta shi kuma yazo wuce wa ta gurin ya ganta cikin wannan halin da zarar yaje gurin domin ya temaka mata se rijiyar ta dinga matsawa ahaka ahaka har ta yi mai nisa “wace ce ke a ina kike wana irin temako kike so na yi miki” me yasa ba zaki bayyana min kanki ba?” yayi wa kansa tamabayar da bashi da me ba shi amsar ta. tashi yayi jikin sa babu ƙwari kamar anyi mai duka toilet ya shiga yayi wanka gaban mudubi ya wuce wasu tsadaddun mayuka masu ƙamshi kamar tirare ya shafa a jikinsa wasu kaya masu taushi da santsi kamar Auduga kuma farare yasa sosai suka yi mai kyau jikinsa ya feshe da turare me ƙamshi da daɗin ji al-kyabba ya ya ɗora akai sosai ta ƙara mai kyau waje ya nufa cikin takun sa na ƙasai ta irin na sarakuna gaba ɗaya bodi gad ɗin sa da dogarawa da suke bakin ƙofar suka zube suna kwasar gaisuwa kai kawai ya gyaɗa musu. Bodi gahd ɗin suka take mai baya su kuma dogarawan suka zauna gadin sashin nasa dik inda ya gifta bayi da ƙwarori sai sun tsugunna sun kwashi gaisuwa kai kawai yake gyaɗa musu kun san masu mulki busu fiya son magana ba domin tana yi musu wuya. Kai tsaye FADA suka nufa. “An gaishe ka yarima ɗan sarki jikan sarki wanda yagaji sarauta gaba da baya taka lafiya yarima mejiran gado kaga ɗan Sarkin sarakuna kaga ɗan Sarkin daya san sarauta gaba SALAMUN baya SALAMUN ɗan sarki jikan sarki wanda suka gaji sarauta kaga masu abu da abun gado ba taka haye ba”. Abin da dogarawan suke ta faɗa kenan har yarima ya shiga fada yayin da mutanan dake ciki suka fito suka basu guri wannan Umar nine daga sarki muddin yarima zezo fada dik wanda yake cikin fadar ya fito ya basu guri sun gana in yaso bayan ya tafi se su dawo yana shiga ya rungume Mahaifin nasa yana dariya kamar wani ƙaramin yaro bayan sun gaisa memartaba yake tambayar sa yau she ne ze gudanar da bikin buɗe asibitin sa da ya gina Sosa kai yayi yace, “ehh to ranaka ya daɗe ban tsaida rana ba amma zan kira JAMAL se mu tsaida rana” "to toto shike nan yarima Allah ya bada Sa'a nima in an tashi taron asanar da ni da wuri dan ina so in halarci taron kuma nima ina son na bada tawa gudummawar” “to memartaba” In sha Allahu muna godiya Allah ya ƙara girma da buɗi ya baka lafiya me ɗorewa gaba ɗayan su suka amsa da Amin. ɗakin mahaifiyar sa ya shiga wato uwar gidan sarki bayan sun gaisa ya shiga sashin kilishi itama suka gaisa sannan ya shiga sashin gwaggo wato ƙaramar matar sarki acan yayi karin kumallo dan dama yafi sabawa da ita kome zeyi in dai yana neman shawara to ita yake gayawa in dai bata gidan bace. ko Sarki da suka fi shaƙuwa da shi fiya da kowa be fiya gaya mai wasu matsalolin nasa ba A cewarsa girma ya kamashi be kamata yaringa ɗaga mai hankali da nasa matsalolin ba ya maji da mulkin da yake kai, jefi jefi suna taɓa fira da gwaggo damma yarima be fiya son magana ba. (Kunji fa masu karatu ya tsallake ɗakin mahaifiyar sa yazo yana ci aɗakin kishiyar ta shin me yakawo hakan??????) miƙewa yayi yace. “Gwaggo se anjima” “to se ka dawo Allah ya tsare ” “amen gwaggo se na dawo har ya kai bakin ƙofa yaji ankira suna shi . “YAYA SUHAIL,” ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin sakkowa daga saman be ne tana zuwa ta ware hannunta alamar ya ɗauke ta ɗaukar ta yayi ya shiga jijjuya ta kamar wata ƴar tsana ita kuwa se dariya take. Sauke ta yayi ya lakace kumatun ta yace. “ ƴar lukutar gwaggo ya akayi ne na san wannan kiran da akamin Akwai magana” baki taturo tace. “ba kai bane jiya kace inka fita zaka sayomin dogayan riguna kuma baka siyamin ba” ta faɗa cikin muryar shagwaɓa “sorry MEENA mantawa nayi ungo ATM ɗina kisa Direba ya kaiki kuma kice sikiruti suraka ku kinji” tsalle tayi, gamida cewa “yawwa YAYA na nagode amma fa se wani satin zani sabida akwai abinda zanyi” “wannan kuma ya rage naki ga dai A.T.M nan na baki” Gwaggo na zaune tana kallansu se yanxu tasa musu baki da cewa. “A'A tin da ba yau zata je ba karɓi A.T.M ɗinka kar ta wullar maka ka san ta da shirirta” “a'ah gwaggo kibar mata kawai idan ma ta ɓatar se na sake yin wani ko autr mu?")” “Eh yaya na” “to Shi kenan ni zan wuce” “to seka dawo Allah ya tsare” da “Amin” ya amsa “kai tsaye sashin sa ya koma wayarsa ya ɗauka ya kunna wadda tin jiya ya kashe saƙwani nine suke ta shigowa cikin wayar na abokansa dama na ƴan matan da suke son sa shi kuma baya son su , saƙwan JAMAL kawai ya duba dariya yayi afili yace. “kai JAMAL se abarka ba dai tsokana ba” number sa ya kira . dai-dai lokacin da JAMAL yayi fakin a'kofar gidansu MANAL Wanda ya koma na su Dady ɗaukar wayar yayi yana dariya yace. “Se yanxu ka ga damar kira na wallahi SUHAIL idan kayi aure se dai mu dinga zuwa inda kake danna san mantawa zaka yi damu” kome yace mai Seya kwashe da dariya yace. “Ina xuwa zan kiraka naje wata unguwa ne oky sena kira ɗin” ya faɗa tara da sauke wayar daga kunnen sa ya dawo da duban sa gurin MANAL wacca dik tabi ta fiegice ta gigice. Maganar sa ce ta dawo da ita daga tina nin da take . “kiyi haƙuri MANAL dik da ban sanki ba amma na fuskanci kina cikin damuwa da alama ke marainiya ce ki cigaba da haƙuri da kai wa Allah kukan ki haƙiƙa Allah maji roƙon bayinsa ne ba zaki taɓa dana sani ba muddin kika riƙe sallah da addu'a zaman wannan gidan yafi miki alkairi idan kika ce zaki bar gidan nan zaki tsinci kanki a yana yinda ba aso addu'a itace makamin mumini zaki ga ribar haƙuri ga wannan kuɗin ni ne na baki kisiyi kayan sawa dana kwalliya” girgiza mai kai tayi tace “A'ah kabar su Na gode da temakon da kukayimin Allah ya saka da alkairi” “Amin amma ki karɓi kuɗin nan” ganin ya dage yasa ta karɓa yasa ta amsa tara da ƙara yimai godiya fitowa yayi ya buɗe butt ɗin motar ya fito mata da sauran kayan ta da magun gunan ta sannan suka yi sallama ta jima a tsaye tana bin motar da kallo harta ƙulewa ganin ta . Dam dam gaban ta yashiga bugun tara, tara lokacin data kalli makeken git ɗin gidan ƙwan ƙwasawa tayi me gadi ya buɗe mata tafiya take kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki afarlo tayi arba dasu suna karyawa sabida safiya ce gaba ɗayan su suka xubo mata ido kamar zasu cinye ta musamman BABILA da taga babu abinda fuskar ta yi “ To ƴar iska kin gama yawon barikin naki kin dawo?” cewar Dady rintse ido, MANAL tayi sosai taji zafin maganar, “kayi haƙuri Dady wallahi ba yawo bariki naje ba ” Cikin ƙaraji, DADY yace. “Karki kuma ce min Dady ni ban haifi mazinaciya ba kin ga ƴaƴa na nan ƴan albarka akusa dani kije can ki nemi mataccan ubanki wanda mugun abinsa yaja masa har ƴan fashi suka kasheshi yanzu yana inaaa? dukiyar da take sawa yana min wulaƙanci ya tafi ya barta ni ɗin da bayaso nine akan dukiyar nake yanda na gadama da ita da gani se ƴaƴana kema da suka barki don ki gaji dukiyar wahalace zata kashe ki abanzaaaaaa”.. ALLAH KAI MANA DA KYAU KA RABA MU DA SON ZUCIYA MMN HIBBA CE RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 7-8 TUSHAN LABARIN. ALHAJI Sa'ad mai dalah wato mahaifin MANAL da alhaji bukarr uwassu ɗaya ubansu ɗaya tun suna yara mahaifin su yara su ya barsu hakan yasa ɗawainiyar su ta dawo kan mahaifiyar su ita ce cin su ita ce shan su , haka suka taso cikin yana yin rayuwa yau daɗi gobe akasin haka ga rashin kuɗi ga karatun su uwa uba cida sha, koda ta samu dangin mahaifin su da maganar gona kinsu na gado suka ce ba zasu bayar ba ƙarshe ma se suka kulle mata baki ta hanyar bin malamai tin daga nan bata Kuma yin maganar gadon ƴaƴan ta haka suka ci gaba da faɗi tashi ita da yaran ta SA'AD tun yana ƙarami Allah yayi mai baiwa dik abin da ya taɓa to in sha Allahu se Abin yayi albarka da haka ya fara ƴan seda sede na kayan kanti cikin ikon Allah Allah yasa musu albarka da wannan kayan da yake siyar wa da su suke ci da su suke sha, suke biyan kuɗin makaranta. ABUBAKAR wato ALAJI BUKAR tun yana ƙarami yake da wani irin bauɗaɗɗan hali ga baƙar zuciya kamar kuturu. saɓanin ɗan uwansa SA'AD wato ALAJI SA'AD ME DALAH babu ruwanshi da kowa harkar kasuwanci sa da karatun sa kawai yake Sannu ahankali shagon sa ya bunƙasa ya zama babban ɗan kasuwa Wanda duniya tasan da zaman sa har ƙasashe yake fita domin sarin kayayyaki lokacin da suka isa aure mahaifiyarsu tace ya kamata suyi aure dama shi ALAJI SA'AD ME DALAH bame kula kulan mata bane mace ko ƴar uwassu ce iya kacin su da shi gaisuwa daga haka baya wani fira da mace saɓanin BUKAR da yake biye biyen mata shi yasa da aka ce su fito da matan Aure yace yanada wacca yake so me suna BILKISU BILKISU dai irin mutan nan ne wa inda ba kwaɓa ba harara gabin malamai da bokaye gaba ɗaya gidan su haka suke . shi kuwa SA'AD cewa yayi ake komai mace me hankali da nutsuwa ze aura. haka kuwa akayi mahaifiyar su ta nemo mai wata yarinya wacca suke maƙota dasu mai suna, ZARAH Marainiya ce ba uwa ba uba tana zaun ne agurin kakar ta ta gurin uwa haka akasha biki bayan bikin su da sati biyu Allah ya yiwa mahaifiyar su ALAJI SA'AD rasuwa sunyi kuka sosai musamman SA'AD.. A kwana a tashi ba wuya gurin Allah ALAJI SA'AD ME DALAH ya zama shahararren ɗan kasuwa Wanda sunan sa ya zaga duniya Mutum me mutumci da karamci ga temakon talakawa kullum gidan sa cike yake da mutane saboda kullum se yayi sadaka abinci da kuɗi da Kayan sawa hakan yasa dukiyar sa kullum daɗa bunƙasa take rumfar kasuwa uku ya sewa ƙaninsa da motoci nahawa guda uku da danƙareran gida na gani na bugawa a jarida dik Kwana biyu yake aika mai da kayan abinci da kaji da kayan marmari sannan ya tura mai kuɗi ta account ɗinsa sannan idan lokacin aikin hajji yazo tare suke tafiya da mata yan su . Amma duk da haka ALAJI BUKAR baya gani kullum cikin yi mai ƙorafi yake kuɗin da yake ba shi basa isar sa hakan be dame sa ba sema ƙara masa daya ke yi haka rayuwa taci gaba da juyawa har Allah ya bawa BILKISU ciki wato matar ALAJI BUKAR ta haifi ƴar ta mace ALAJI SA'AD ya nemi ɗan uwan nasa da yasa sunan mahaifiyar su amma yace baze sa ba koda ya koma gida ya gayawa BILKISU uban ashar ta ƙunduma tace. "wllh baza'a sawa ƴar ta AMINA ba ƙarshe dai a kasa sunan mahaifiyar ta wato ZAINAB. ranar suna Alaji Sa'ad ne yayi komai raguna biyar aka yanka banda shanu da raƙuma kyautar mota ya bawa BILKISU tara da kuɗi shi kuwa uban gayyar ba,a magana. BILKISU se hura hanci take tana homa ta haihu hada yiwa ZARAH habaici bata haihuwa hakan bedamu ZARAH ba Kuma bata taɓa gayawa mijin ta ba tasan haihuwa nufine na Allah idan Allah yayi zata haihu zata haihu. Se da ZARAH ta shekara goma sannan ta samu ciki lokacin ZAINAB ƴar gidan ALAJI BUKAR na da shekara huɗu aduniya lokacin haihuwa yayi ta haifi ƴar ta mace kyakkyawa fara sool mai kama da mahaifinta ranar suna yarinya taci suna AMINA amma ana kiranta da MANAL MANAL yarinya ce mai hankali da nutsuwa kuɗin mahaifin ta be rufe mata idoba babu ruwan ta da duniya kamar dai iyayen ta tin MANAL na ƙarama take fuskantar ƙalubale daga wajan ƙanin mahaifin da matarsa in dai taje gidan da ɓacin rai zata dawo gida tun abin baya damunta har ya soma damun ta ko da ta gayawa iyayen ta basu bata goyan baya ba se cewa su kai tayi haƙuri wataƙila dik sanda zata je ransu aɓace yake MANAL da ZAINAB makaranta ɗaya Alaji Sa'ad ya saka su dik abinda ze yiwa MANAL to se yayi wa ZAINAB da suka kammala secondary school Alaji Sa'ad yace su zaɓi ƙasar da suke so su ƙarasa karatun su MANAL tace ita India take so ZAINAB ma tace nan take so da maganar taje kunnan Alaji bukar se cewa yayi ƴar sa ba zata je wata ƙasa karatu ba haka kurum ta lalace se dai shi ya kai ƴar sa amma baze ba da tasa ƴar ba Haka aka biya wa MANAL kuɗin komai na karatu ta tafi ita kuma ZAINAB aka sama mata wata anan garin Kano kamin wannan lokacin BILKISU ta kuma haihuwar ƴar ta mace wanda ba haka taso ba so tai ta haifi namiji kamar dai ko yaushe Alhaji SA'AD ne yayi komai na suna a lokacin MANAL ta kammala karatun ta ta dawo da sakamako me kyau hakan yasa mahaifinta ya shirya mata walima da kuma yi mata Al-ƙawarin kaita gurin shaƙatawa gefe guda kuma BILKISU ta saka alhaji bukarr tana yi mai huɗubar sheɗan wai ɗan uwansa ya asir ce shi dan kar yayi kuɗi kamarsa ga kuma wulaƙanci da yake musu baya jansu ajiki so sai ALAJI BUKAR ya hau ya zauna kan zugar da matar sa BILKISU take yi mai dan haka ALAJI BUKAR ya wanke ƙafar sa yaje gidan ALAJI SA'AD ME DALAH kan ya bashi kuɗi zeja jari shagunan sa sunyi ƙasa babu kaya aciki gashi kuma bashi da kuɗi sannan million goma yake so ya bashi tunda yake zuwa karɓar kuɗi gurin ALAJI SA'AD be taɓa yi mai musu ba amma wannan karon yace. yayi haƙuri ze bashi amma se an da sati ɗaya dan shima babu wasu isassun kuɗi agurin sa saboda yayi odar kaya daga ƙasashen da yake odar amma in sha Allahu nan da sati ze ba shi nan fa Alhaji bukarr ya soma wasu munanan magan ganu yana cewa dama be damu da shi ba baya te maka mai daga shi se ƴar sa da matar sa magan ganu dai marasa tushe shi kuwa ALAJI SA'AD yaji zafin abinda ɗan uwan nasa yayi mai har ya kai su gayin sa'in sa Abin da busu taɓa yi ba haka ALAJI BUKAR ya bar gidan cikin fushi da ɓacin rai yana zuwa BILKISU ta kuma ɗora shi akan network ya kuma fusata. washegari misalin ƙarfe huɗu na yamma aka gudanar da gagarumar walima da aka shir yawa MANAL walimar data haɗa manya manyan ƴan kasuwa da masu kuɗi kai harda ɗan sarkin marautar *ZAKI* daya halarci taron a madadin *SARKI* kyaututtuka kam tashasu daga me bata mota seme bata gida sema bata fili dame bada cek ɗin kuɗi har da wanda ya biya mata aikin hajji. Shima ALAJI BUKAR yaje gurin walimar shima ya bata kyauta fuskar nan tashi wasai kamar babu abinda ya faru.an sha hotuna sosai kowa ka gani yana cikin farin ciki ba dan komai ba se dan karamci da mutunci irinna alaji sa'ad me dalah. *INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJU'UN* A daran ranar ƴan fashi suka haura gidan ALAJI SA'AD ME DALAH suka kashe shi shi da matar sa Wanda awashe garin Ranar da akayi walimar MANAL suka yi mata Al-ƙawarin kaita gurin shaƙatawa gurin shaƙatawar da basu je ba kenan Abin da yafi ɗaurewa mutane kai shine yanda ALAJI BUKAR be wani nuna damuwa akan mutuwar ɗan uwan nasa ba kamar ma ba ɗan uwan sa ba ne ya rasu. WANNAN SHINE LABARIN MANAL DANA IYAYANTA WANDA IDAN ME KARATU BE MANTA BA KISAN DA AKAYIWA ALAJAI SA'AD ME DALAH SHINE FARKON FEGE ƊIN MU TO KUNJI DAI ALAJI BUKAR KANINE AWAJAN MAHAIFIN MANAL BARA KUMA MU KOMA CIKIN LABARIN DAN MUJI KALAR RAYUWAR DA MANAL ZATA CIGABA DAYI BAYAN DAWOWAR TA DAGA ACIBITI.... Cigaban labari Sosai magan ganin Dady suka yiwa MANAL zafi, tin da suke zagin ta ko ai bata ta taɓa jin zafi irin na yau ba ace dik irin halaccin da ABBAN ta yayi musu basu gani ba sema zagi da tozarci daya biyo baya kuma wani babban abin takaicin ma ɗan uwansa shine yake yi mai haka dama masu iya magana sunce Naka shi yake bada kai NABILA ce ta taso dan har yanzu bata gama yar da cewa fuskar MANAL ce ba wasu ƴan iskan kayane A jikin ta wanda dasu ƙwamma babu se da ta gama ƙarewa MANAL kallo tana wani yamutsa fuska tamkar taga kashi tace. “Sannu da dawowa karuwar waje ina fatan dai su ƴan iskan naki sun sallameki dan naga kinyi kyau ba lefi gaskiya kin shiga bariki da ƙafar dama" se ta finciko ledar dake hannun MANAL kayan da jamsy ta siya mata ne aciki se magun guna da aka bata da wanda zata sha da wanda kuma zata shafa se kuma kuɗin da Dr. JAMAL ya bata waro ido, NABILA tayi gamida cewa. “Ehhhhy lallai yarinya ki ce da gaske ƙanjamau gareki" ta faɗa tana ɗaga wani kwalin magani wanda maganin goge tabo ne wato (NIYO SIKIN) aka bata saboda sauran ragowar tabon dabe goge ba ya goge, amma shine NABILA take kira da maganin ƙanjamau saboda toshewar basira. Juya wa tayi gurin su Dady tana nuna musu kuɗin “ kun gani ko? Dady kalli wannan kuɗin ku gani” nan da nan Dady ya kuma hassala yace NABILA ta ba shi kuɗin karɓa yayi yazura a ajjihu sa ya cika rigarsa da iska. MOMY kuwa cewa tayi yo “allah na tuba idan bata yi bariki ba se allah ya tambaye tako kun manta labarin babart a dana baku ita ma ai ƴar barikin ce" Da sauri MANAL ta bar gurin dan ba zata iya jiyewa kanta wannan ɓacin ran ba dan haka taja ƙafafunta ta shiga ɗakin ta wanda babu komai aciki se tsummo karan ta zama tayi tana sauke numfashi kamar wadda tayi tseran gudu fuskar ta ta taɓa taji sumul afili tace. “Allah na gode ma daka haɗa ni da su JAMSY da DR JAMAL da dan su ba da tini na zama makauniya ko kuma kuturwa eh mana kuturwa yo fuska ta ƙone kuma ba ni da wanda ze te maka min da se abinda Allah yayi karshe ma na dinga ɗoyi mutane su dunga gudu na kiran da NABILA take ƙwala mata ne ya katse mata dogon tina nin data lula a sanyaye ta fito tsuguna wa tayi gamida cewa. "gani" wani mitsiya cin kallo ta bita da shi kana tace “ Idan kin gama tina nin ƴan iskan naki kije ga wanki na kimin idan kin gama ki dafa min abinci merai da lpy zanyi baƙo kuma kwana zee yi” daga haka ta juya ta fara tafiya haj tayi taku biyu se ta dawo . “Au na manta idan kin gama kije gurin ajiye motoci akwai farar mota ta ki wanke min da wanki zan kai se naga keee ya kamata ki wanke ta saboda baki da wani kima da daraja dan haka kiwanke min ita tassss ke ba komai bace face baiwar mu shi yasa da Dady ya ce ze koreki na hana ko dan mu na kasa ki” ta faɗa tarada kama kunnan MANAL ta murɗe da iya ƙarfin ta har seda MANAL tayi ƙara ƙafa tasa ta harbe ta sega MANAL aƙasa kanta ya bugu da ƙasa, tashi tayi tana shafa kanta taji koya fashe se taji be fashe ba lokacin da taga kayan se da gaban ta ya faɗi ta tuna dokar Dr. JAMAL da ya kafa mata na kar ta yawai ta sunkuyo da aikin ƙarfi saboda har yanzu fuskarta da saura kuka ne ya ƙwace mata ya Allah ka kawo min ɗauki cikin gaggawa ka raba ni da Rayuwar cikin gidannan wallahi gwara zaman gidan yari da zaman gidan nan sosai take kuka me tsuma zuciya dakyar ta samu ta gama wankin sannan ta shiga kicin ta ɗora girkin rana bayan ta gama ta ɗora wanda NABILA tasa ta nan da nan gidan ya kaure da ƙamshi ta ko ina. ƙarfe biyar ta gama komai dan haka tayi sallar la'asar sannan ta fito wajan ajiye motocin kai daga ganin motar kasan babu wani datti ajikin ta amma saboda tsabar zalunci tasa ta wanke mota. Ruwa ta ɗebo A botiki ta zuba kilin sannan ta soma wanke motar nan da nan motar tayi fesss kamar masu wankin mota ne suka wanke agajiye ta shiga gidan tana jan ƙafafu se dai mee tana shiga taji an ɗauke ta dawasu gigittun maruka kuma lafiyyayu har seda ta kifa ta dungura ta kuma dungurawa...... Muje zuwa fan MMN HIBBA✍️ RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba. GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 9-10 A gigice, MANAL ta ɗago hawaye fal fuskar ta“ke waca iri yar mahaukaciya ce da bakya kallan gaban ki jibi yan da kika taka ni” "ki yi haƙuri momy wallahi ban gani ba” to dama ina zaki gani kina tafiya bagazar bagazar da halla matsa ki bani guri” jiki na kyarma MANAL ta matsa kai tsaye ɗakin ta ta nufa ɗauro alwala ta gabatar da sallar magrib ta tana kaiwa allah kukan ta da nema wa iyayan ta gafara wajan ubangiji sosai taji xuciyar ta tayi sanyi dik wata damuwa da take ciki ta gushe lallai dik wanda ya miƙa lamuran sa ga ubangiji subhanahu watala ala baze taɓa dana sani ba tana nan zaune har aka kira sallar isha'i tayi kwanciya tayi bacci ɓarawo yayi awan gabada ita. innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn, abin da nake ta maimaita wa kenan lokacin da idona ya sauka a kansu NABILA ita da saurayin ta keeee duniya ina zaki da mu abin babu kyan gani bayan sun gama ai kata masha'arau suka shiga banɗaki tara sukayo wanka suka haye gado suka kwanta babu abinda ya same su cikin dare kwar-tan NABILA ya tashi ita kuwa se sharara bacci take saɗaf saɗaf ya fice daga ɗakin yana tafe yana waige waige ɗakin MANAL️ ya nufa ahankali ya tura ƙofar ya maida ya rufe MANAL dake bacci sama sama taji ana shafa ta juyi tayi bata ra da ta kawo komai aranta jin an ci-gaba dayi harma anxarce yafi na da yasa tayi xumbur ta miƙe “waye” abinda bakin ta iya faɗa kenan jikin ta na ɓari tsoro ya kama ta ko ƴan fashi ne suka dawo ita ma su kashe ta aiko da tafi kowa jin daɗi kawai se taji bakin ta yana faɗin. “ kune kuka dawo nima Ku kashe ni dan Allah kuyi saurin kashe ni ni ma na gaji da rayuwar nan gwarama na mutu ko na huta” "ke basu bane ni ne saurayin NABILA kuma nazo gare ki ne dan ki temaka min ko ince mu temaki juna tin da na ganki naji sha'awar ki ta kama ni naji ina son kasance wa dake dan haka kawai ki amin ce muji daɗi tare ke ma kifi ta daga cikin wannan gidan kisiyi naki ki samu kuɗaɗe ki se mota ke ma ki koma babbar yarinya irinsu NABILAA in dai kika bani kanki to zaki samu dik waɗan nan abubuwan dana lissafo miko” ya faɗa yana shafa jikinta tsoro ne ya kuma kamata ta cure guri guda jikin ta se rawa yake kamar maxari ta tina nasihar da momyn ta take mata cikin mafarkin ta “dan Allah ka rabu dani ni ba ƴar iska bace in dai se nabi maza sun samu kuɗi na ƙwammace talauci ya kashe ni, kuɗi basu dame ni ba domin ina da zuciya me kyau” “haba beby ki gwada mana kiji wallahi da kanki se kin neme ni” ya faɗa yana kai hanninsa kan fuskar ta da sauri ta bige hannin ta ƙwallla ƙara me raxanar wa gaba ɗaya ƴan gidan suka fito suna ta zagin ta ta tashe su daga bacci. “ wai me yasa meki da kike mana ƙara acikin gida?” cewar ZAINAB “wa wa wani ne ya shigo ɗaki na wai yana so na bashi kai..” se kuma tayi shiru jikin ta na kar-kar wa tsaki ZAINAB tayi gami da cewa “ yo Allah na tuba ko kwarto ne ya shigo gidan nan me zeyi dake abu A ko maɗe dahallah rufewa mutane baki” NABILA dai kasa magana tayi domin tana zargin wani abu game da saurayin ta lokacin da MANAL tayi ƙara data tashi bata gansa aɗakin ba afusace ta nufi ɗakin nata, tana hura hanci tana xuwa ta ganshi akwance kuma idon sa biyu cikin masifa, ta soma magana “wannan wan irin wulaƙanci ne zaka kama kashiga ɗakin ƴar aikin gidan mu ai seka jamin raini sannan daka fita idan wani ya ganka fa ?” dariya yayi irin tasu ta ƴan bariki yace. “ haba beby ke ma kin san babu abin da zanyi da waccan kucakar yarinyar koda kuwa mata sun ƙare A duniya ke kaɗai kin ishe ni kawai naje wuce wa ne naga Ƙofar ta a buɗe shine na janyo mata ƙofar shi ne ta tsorata da kike cewa idan wani ya ganni ba kin ce min sun san da zuwa na ba?” “eh sun sani amma basu san kwana zakayi ba” daga haka suka ɗora daga in da suka tsaya. *MASARAUTAR ZAKI* “wai daga ina kake naga ka jima baka ƙara so ba?" cewar SUHAIL. “wallahi naje wata anguwa ne shi yasa kaga na jima” JAMAL ya faɗa lokacin daya zauna. “ ya ake ciki na san maganar bata wuce ɗaya maganar buɗe asibiti ya faɗa yana ƴar dariya" "eh wallahi ita ce sabida Me martaba yayi min magana kan yaushe ne xan buɗe nace mai se na zauna da kai munyi shawara” taɓe baki JAMAL yayi “wai shawara se kace wani ƙaramin yaro” gaba ɗaya suka sa dariya, nan dai suka tattauna kan yanda za su gudanar da komai. MEENA ce ta shigo ɗakin tana ƙwalawa SUHAIL kira, “YAYA YAYA SUHA....” se kuma tayi shiru sakamakon ganin JAMAL da tayi shi kuwa JAMAL dariya yayi yace." a'ah matar ya kika tsaya ƙaraso mana ko dan kin ganni ne?” a'ah wallahi ni ba matar ka bace dube ka fa tsoho da kai fuskan ka dik gemu wallahi da zan auri tsoho ba” ta ƙarasa faɗa tana turo baki, ga baki ɗaya su suka sa dariya harda riƙe ciki. haba MEENA ta ya zaki min haka so kike a yi mana dariya in dai gemu ne zan aske se ki dena ganin tsufa na ko?” kai ta gyaɗa mai alamar eh “yawwa mata ta ƙaraso kusa da mijin ki” ƙarasawa tayi ta zauna shi dai SUHAIL ido ya zura musu a ransa yace. “Oh ko yaushe MEENA zata yi hankali? yarinya kusan shekara shabiyar amma tana abu irin na ƴan shekara biyar shi kuma ƙaton banza ya zauna se biye yarinya ƙarama da bata san me ne ne so ba bare ta soka SUHAIL ya faɗa cikin ransa be san maganr ta fito fili ba se ji yayi JAMAL yace. “ehh gwara/ni ina da wacca nake so dik da ƙaramace kai kuwa fa ko budurwa baka da ita” tsaki SUHAIL yayi gami da cewa. “to ai seka ci gaba da zaman jiran randa zata yi hankali se ka aure ta ai kin banza kawai ” dariya JAMAL yayi yace. “ ni da yarin tar ta nake son ta babu ruwa na da rashin wayon ta” SUHAIL kuwa ya faɗa duniyar tinani kan mafarkin yarinyar daya keyi wanda harya zame mai jiki shi dai fatan sa Allah ya bayyana masa ita ta ko ina. “SUHAIL ya dai tina nin me kake yi se magana nake kayi shiru?” fir gigigit ya dawo daga duniyar tina nin daya lula “babu komai kawai dai ina tina nin wani abu ne amma karka damu ba wani abun damuwa bane” “okay allah ya shige magana gaba” dikkan su suka amsa da ameeeeeeen. daga haka JAMAL ya tashi da nufin tafiya gida har mota suka rakashi MEENA na ɗaga mai hannu... kamar yan da Alhaji bukar ya tsara zasu je yawon buɗe ido shi da iyalan sa hakan ce ta kasan ce aƙalla zaswuje ƙasashe kusan biyar daddare yasa aka kira masa MANAL guri ta samu ta zauna ne sa da su ta ta kure kamar tsumma. wani kallan tsana DADY ya bita da shi “ to ƴar iska ragowar kantiti mu dai ta fiya zamu yi ba zamu dawo ba zuri ba amma ki sani ba wai bamu tafi mubar ki agidan nan bane dan kiyi yanda ranki yake so se mun kulle ko ina na gidan nan ko ruwan sha ba zmu bar miki ba bare abinci dan haka ya rage ya naki ko ki nema wa kanki abinci da zaki ci koki zauna da yinwar ki wannan matsalar kice kinji abinda nace miki?” ya faɗa cikin tsawa., “ehhh naji in sha Allahu zaka same ni a me bin umar nin ka” tsaki NABILA tayi gamida cewa. “kai ma dai DADY ina ita ina zama da yinwa tana da ƴan iskan kwaratan samari ai babu zan can yinwa tare da ita bare tana ganin bama nan ai se abin da ta gada ma zata yi waƙila ma ta kawo mana kwarye cikin gida” “taɓ ɗi wallahi da tayi dana sanin haihuwar ta da akayi ta shigo mana da kwartaye cikin gidan mu na sunna” cewar MOMY. ZAINAB kuwa cewa tayi. “ caɓ da ta gane shayi ruwa ne wallahi kinji na ranste dik randa kika kawo mana kwato cikin gida haɗuwa zamu yi mi miki dukan kawo wuƙa banza ballagaza ƴar isaka wacca tayo gadon uwarta Anzo a ban za za'a koma a iska” ira iran waɗan nan magan ganun suka dinga faɗawa MANAL ita dai jinsu kawai take a ranta tana addu'ar Allah ya tsare ta daga aika ta zina masuyi yi ma allah ya shirye Su. washegari kamar yanda DADY ya faɗa seda suka kulle ko ina na gidan sannan yasa aka raba wutar gidan da fam-funan ruwan gidan ƙarfe bakwai jirgin su ya ɗaga. MANAL na ɗakin ta tsoro ya kama ta yanxu ita kaɗai zata kwana A wannan tanƙa meman gidan wanda zeci mutane sama da dubu gashi babu fitila babu ruwa lallai akwai matsala gagaruma.. YANXU AKASOMA KUDAI KUBIYO NI DAN JIN KALAR RAYUWAR DA MANAL ZATAYI ITA KAƊAI ACIKIN GIDAN BABU ABINCI BABU RUWA GASHI BABU FITILA WOHOHOOOOOOOOOOO WATA MIYAR SE'A MAƘOTA MMN HIBBA CE RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 11/12 A yau ne yarima SUHAIL yake gudanar da bikin ƙaddamar da buɗe katafaran asibintin da ya gina shi domin talakawa komai kyauta ne kama daga duba mara lafiya magun guna kai hatta katin daza'a rubuta maka magani kyauta ne sosai gurin ya cika da al'uma manya manyan mutane masu ji da kan su , ƴaƴan sarakuna maza da mata suma sun zo kai hatta da wasu sarakan na garuruwa sun halar ta shi kan shi memartaba ya halar ci taron SUHAIL ne tara da babban aminin sa wato JAMAL sune akan gaba al'makashi aka bawa SUHAIL ya yanka farinn ƙyallan da aka saka agurin ai ko gurun ya kaure da tafi, nan aka gama komai taro ya tashi lafiya tara da sanar da mutane sati mai zuwa za'a fara aiki a asibitin tara da manya manyan ƙwararrin likitoci daga haka taro ya tashi. MANAL ta koma tamkar ƙwarangwal sabida yinwa ashe da ba rama tayi ba yanxu ne tayi rama tayi baƙi ta rame ta lalace ta ƙwanjame kamar mai curar H.I.V sabida yinwa har ta kai ta kawo bata gani sosai ganin yinwa na neman halaka ta yasa ta yanke shawarar fita tayi bara ko zata samu abinda zata bawa ƴan hanjin ta wanda suka dunƙule guri guda kamar an sa mata dutse a cikin ta., kome gadi bata tsaya saurara ba domin shi ma DADY yayi mai wonin idan ya sake ya bata abinci to A bakin aikin sa shi yasa ko da wasa bata tin kari inda yake ba, bakin titi ta fito tana tafiya tamkar mara hankali dik inda ta gifta se an kalle ta wasu ma sun ɗauka mahaukaciya ce.saboda kayan dake jikin ta basu da maraba dana mahaukata ita dai tafiya kawai take har ta shiga cikin kasuwa shago shago ta ringa bi tana a temaka mata da abin da zata ci yinwa take ji har tsugunawa ƙasa take yi tana roƙon mutane amma babu wanda ya saurare ta se data zagaye kasuwar amma bata samu ko sisi ba tink ƙarfin ta ya ƙare juwa ta soma ɗibar ta ganin ta ya ɗauke kawai se gani akai ta faɗi nan da nan mutane suka yo kanta ruwa me sanyi aka fesa mata ta farfaɗo tana bin mutanen da suka yi cirko cirko akan ta “ ke yarinya me ke damun ki” cewar wani dattijo da kyar ta buɗe baki tace. “yinwa nake ji yau satina ɗaya banci komai ba dan Allah ku bani abinci kar yinwa ta kashe ni ku temaka min ba ni da kowa ba uwa ba uba,” se data bawa dik wanda yake gurin tausayi har da masu kuka wani mutumi ne yasa aka kamo ta aka kawo ta shagon wata me siyar da abinci ya bada dubu biyu yace azuba mata taci ta ƙoshi a zuba mata wani ta tafi da shi godiya ta shiga yi mai tara da yimai addu'a har mutumin ya bar gurin ba ta de na yi mai addu'a shinkafa da miya da nama aka zuba mata ci take tamakar zaki yaga nama hannu baka hannu ƙwarya kan takai wata lomar ta ɗebo wata mutanan gurin se kallan ta suke tana gama ci ta kora da ruwa me sanyi a take a nan bacci ya ɗauke ta se ƙarfe biyu ta farka salati tayi tara da miƙe wa, ta saka siɗaɗɗun takalman ta zata tafi me abinci tace. “ga sauran abinci ki ” karɓa tayi tara da yin godiya ta cewa me abincin idan mutumin ya dawo ta yi mai godiya sannan ta kama hanyar gida Hannun ta ɗauke da kwalin tec'awaye. tana zuwa ta ƙwanƙwasa me gadi ya bude mata ta shi fiyo watan da aka bata da shi ta yi alwala ta jero sallolin da ake binta sannan ta janyo abinci ta soma ci tare da yiwa Allah godiya tana gamaci tayi sallar isha'i sannan ta kwanta bacci me daɗi yayi awangaba da ita wanda ta manta rabon d atayi irin shi . tin daga wannan ranar MANAL seta fita bara shago shago wani xubin ta samo kuɗi wani zubin abinci ko garin kwaki da haka take samun abinda zata sawa ƴan cikin ta MASARAUTAR ZAKI “SUHAIL SUHAIL SUHAIL me yasa baza ka te maka min ba? me yasa ka kasa ƙaraso wa gare ni? ko ba zaka temaka min ba duba kaga yanda macizai suke sarana kuna mu na harbi na ka dubi maraice na ka cecen i daga wannan baƙin ramin me duhu da ƙunci da azaba babu komai acikin sa se uƙuba nice nice MANAAAAL” A matuƙar razane, ya tashi gaba ɗaya ya jiƙe kamar an yi mai wanka da ruwa durowa yayi daga kan gadon kamar zararrre jikin sa se ɓari yake bakin sa, na faɗin “MANAL MANAL MANAL a ina zan ganki a ina kike?” se kuma ya soma hamdala ga Allah buwayi gagara misali gagara kwai kwayo. “Allah na gode ma daka nuna min wannan baiwar taka zan temaka mata zan kutsa lungu da saƙo in ne mota adik inda take” wayar sa ya janyo lambar JAMAL ya lalubo ya danna kira gami da karawa akun nan sa bugu biyu JAMAL ya ɗauka be bari sun gaisa ba “JAMAL dik abin da kake ka bari kazo Ina son ganin ka yanxu dan Allah ” “ lafiyarka ka kuwa ka duba a gogo ƙarfe bakwai na safe meke faruwa ne ko baka da lafiya ?” tsaki SUAHIL yayi tara da cewa. "kaga malam idan ba zaka zoba kace ba zaka zoba ” daga haka ya katse kiran. murmushi JAMAL yayi yace. “kaji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa haka kurum zaka kira ni da wannan uwar safiyar kamar wani zararre wallahi se na gama abin da nake zanje in yaso ma shawota ” SUHAIL bayan ya katse wayar ta gumi ya rafka ya tsurawa guri ɗaya ido idanuwan sa suna ƙara hasko mishi fuskar MANAL ji yake kamar a zahiri ya gan ta. ji yayi an da fashi yayi saurin ɗagowa “MANAL ke ce?”sororo JAMAL ya tsaya yana kallan abokin nasa ya kuma maimaita. “MANAL kuma” ji yake kamar ya taɓa jin sunan. "SUHAIIL wai meke faruwa ne tin da safe ka kira ni kace nazo yanxu kuma naji kana kiran sunan wata MANAL plsssss me ya faruwa ?” "ban sani ba JAMAL ban santa ba ban san wacece ita ba A mafarki take zuwar min tana neman temako na amma ban taɓa ganin fuskar ta ba se yau ta bayyana min kanta ta kuma gayamin sunan ta MANAL” shuru JAMAL yayi yana bin abokin nasa da kallo lallai ya tausaya mishi kuma ga dikkan alamu ya faɗa soyayya da yarinyar da take xuwar mai a mafarki caɓɗi akwai cakwakiya “ JAMAL a ina zamu nemo ta ba zan iya cin komai ba idan ban nemo ta ba kuma A yau ɗin nan” wata uwar harara JAMAL ya watsa mai yace. “sannu shugaban mahaukata na didduniya ta ina zamu nemo ta yarinyar da bamu santa ba hasalima amafarki ka ganta wai waya gaya ma ana yin haka? kawai daga kaga mace amafarki seka dage seka nemo ta to idan kai ka haukace ni da hankali na wallahi wama ya sani ko aljanu ne suke xuwar maka amafarki da yake kasha giyar wake seka tafi neman ta Allah ya bada sa'a seka dawo amma ba dani ba danni ban shirya wahalar da kai na ba kai da kaga zaka iya ga hanya nan Allah ya tsare ” "haba JAMAL ya zaka yimin haka a tina nina abokin kuka shi ake gayawa mutuwa amma se gashi kana neman juya min baya” “ dole in juya maka baya badan komai ba se dan lafiyarka baka san wacece ita ba kawai tana xuwar maka a bacci se ka dage seka nemo ta gaskiya ba zan goyi da bayan ka ba” A fusace, SUHAIL ya miƙe ya ɗauki mukullin motar sa yayi hanyar waje motar sa ya shiga tarada bata wuta ya buga wani uban ham da gudu ya fice daga gidan har yana ƙoƙarin taka masu gadin gidan kowa mamaki yake tunda suke basu taɓa ganin yarima SUHAIL a irin wannan yana yin ba shima JAMAL motar sa ya shiga ya bi bayan sa ganin gudin da SUHAIL yake shararawa ya ɗagawa JAMAL hankali,,, tsoran sa ɗaya kar yaje suyi karo da wani da kyar ya samu yasyha gaban sa saura ƙirissss su yi karo gaban sa yaje ya tsaida motar dole SUHAIL yaja birki ji kake ƙiiiiiiiiiiiiiiiiii. fitowa JAMAL yayi daga tasa motar ya buɗe ta SUHAIL ya shiga “yanxu SUHAIL da kake wannan gudin baka gudin wani abun ya same ka?” SUHAIL daya kifa kan sa A kan sitiyarin ɗin motar ya ɗago tini ida nin sa, suka sauya launi daga fari zuwa ja “dik abin da ya same ni ba matsalarka ba ne ka fitar min a mota zanje in nemo ta dik inda take ba zan kuma ne man temakon kowa ba” “Shi kenan SUHAIL zan taya ka neman ta dik inda take ka kwantar da hankalin ka” bara na kira azo a ɗauki mota ta se mu tafi a taka haka kuwa akayi JAMAL ya kira Direban sa ya ɗauka suka tafi a tasa lungu da saƙo suka shiga su kutsa nan su kutsa can amma babu me kama da ita har wajan da almajirai mata suke zama se da suka je amma ba su ganta ba ko mace suka gani ahanya se SUHAIL yace su tsaya su ga fuskar ta ko ita ce A hanya magariba tayi musu sunyi laushi kamar fulawa musamman JAMAL dole suka koma gida tin daga wannan rana se sun fita neman ta se dai har yau ba A dace ba sosai jikin SUHAIL yayi sanyi gashi kullum se yayi mugayan mafarkai da ita tana neman temakon sa hakan yasa hankalinsa ya kuma tashi,,,, dik ya rame yau kima nin sati uku suna fita neman ta Allah be sa sun ganta ba yau ma kamar kullum JAMAL ya shiryo tsaf se dai me ganin mutumin nasa yayi a kwance babu alamun shirin fita a tara da shi a bakin gadon JAMAL yayi wa kansa masauki gamida cewa. “yau baza mu fita ba ne?” “eh mubari se gobe kai na ne yake ciwo” “to Allah ya sawaƙe kasha magani ?” kai ya ɗaga mai alamar eh "“yawwa SUHAIL bara na nuna maka Hotunan wasu takalma da naga anyo odar su JAMAL ya faɗa tarada fito da wayar sa daga ajjihun sa ya shiga gurin hotina “ka gansu wallahi sunyi kyau sosai kuma nasan zaka so su ” ya miƙa mai wayar karɓa yayi yana dubawa “eh gaskiya sunyi kyau ”seya cigaba da dubawa kamar wanda akasa ya cigaba da dubawa hotina har ya wuce hotunan ta kalman Zumbur ya miƙe hannunsa dafe da ƙirjin sa jikin sa na ɓari,,,,, kamar mazari shi kuwa JAMAL firgita yayi yace. "SUHAIL lafiya kake wannan zaburar ” “ita ce ita ce ita ce wallahi JAMAL ita ce MANAL ce JAMAL dama kasan ta ? me hotan ta yake yi a wayarka ? ko ƴar uwarku ce ?” "wai wace ce kake magana akanta ni ban fahimci komai ba” “baka santa ba me ya kawo hotan ta cikin wayar ka?” SUAHIL ya faɗa tarada nunawa JAMAL hotan MANAL wanda ya ɗauka lokacin da aka yi mata tiyata JAMSY ce tace ya ɗauki MANAL a hoto ya tura mata dan taga yanda fuskar ta tayi shi ya ma manta daya ɗauki wata MANAL a hoto dama ita ce SUHAIL yake gani cikin mafarkin sa ohhhh Allah me iko tabbasa koda ba ita bace to sunan yaxo iri ɗaya. MMN HIBBA RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi sho dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE SADAUKARWA NA SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH) AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA. 13-14 “Dan Allah JAMAL ina zan ganta? wallahi ita ce nake gani cikin mafarki na dan Allah aboki na ka temaka min na san kana da masaniya akan ta tin da ga hotan ta awayar ka plsssss JAMAAL” ajiyar xuciya JAMAL ya sauke gami da cewa. “tabbasss na santa amma ban san komai game da ita ba hasali ma wata ce ta kawo ta asibiti na lokacin da aka ƙona mata fuska har ma seda akayi mata aiki wato tiya ta domin gaba ɗaya fatar ta ya saɓule kuma gaskiya ina ganin yarinyar nan marainiya ce don gaskiya babu iyayan da zasu bar ƴar su ta shafe watanni ba suzo inda take ba kai bakaga wani abun mamaki bama seda na rakata gidanna su wallahi gidane na masu kuɗi kuma shahararrru dan wannan gidan daka ganin wanda ya gina shi ba ƙaramin me kuɗi bane kai wallahi yafi gidanmu tsaruwa da komai wannan shine abinda na sani akan ta gaskiya kuma na faɗa maka zazzafar iska SUHAIL ya furzar daga bakinsa, yace. “ka gani ko abin da nake gaya maka ai ni na san wannan mafarkin dana keyi da ita da akwai magana gashi kai da kanka ka faɗa tana cikin wani yana yi ya zama dole yau ɗin nan muje gidan su” be jira abin da JAMAL zece ba ya faɗa ban ɗaki agurguje yayo wanka ya fito mai kawai ya shafa ya zura kaya gamida fesa turare yace. “ ma iya tafiya” ba musu JAMAL ya tashi suka shiga mota se gidan su MANAL.... kamar kullum yauma MANAL ta fita bara wannan karon harda robar ta shagunan kasuwar ta ringa shiga tana bara se dai yau se ahankali babu sa'a gashi jiya bata samo na kirki ba dan data gaji da yawo se ta samu wata rumfa inda bakowa bane yake xuwa gurin ta zauna tarafka tagumi har aka kira la'asar amma MANAL bata samu ko ƙanzo ba dan haka ta kamo hanyar gida a hanyar ta ta dawowa ne ta gamu da wani mes eda lemo da ayaba da kankana tsayawa tayi agurin ta dubawa baron lemon ido bata ko ƙiftawa se zare idanu, take kamar wacca taga nama shi kuwa me lemon kallan mahaukaciya yake mata don haka ya ɗauki guda ɗaya ya bata saboda murna har haɗawa take da hannin sa tayi mai godiya shi kuwa me lemo mamaki ne ya kashe shi wai dama tana da hankali? tafiya take tana shan lemon ta kamar mahaukaciya sabon kamu se jan lemon take tana tura wa cikin bakin ta dai-dai ƙofar gidan su JAMAL yayi fakin ɗin motar dikkan su suka fito daga motar SUHAIL se kallon gidan yake ji yake kamar ya taɓa shiga gidan “INNALILLAHI WA,INNA ILAIHI RAJUN” abin da SUHAIL yake ta nana tawa ke nan afili yace. “wannan ai gidan ALAJI SA'AD ME DALAH ne wanda a shekarun baya ƴan fashi suka shiga suka kashe shi shida matar sa” cikin mamaki JAMAL yace... “ kar dai kace min wanda she karun baya memartaba ya wakilta mu muzo gidan sa saboda walimar da yayiwa ƴar sa lokacin data kammala karatun ta?” “ ƙwarai ma kuwa JAMAL ita ce to amma abin tambayar shine waye yake ruƙon ƴar tasa? kuma su waye a cikin gidan?” “ ba wannan zamu tsaya yi ba gidan ya kamata mu shiga koma me nene zamu gani” cewar JAMAL ƙarasawa suka yi tara da ƙwanƙwasa ƙofar gidan me gadi ne ya buɗe ƙaramar ƙofar suka shiga bayan sun gaisa JAMAL yayi saurin amshe zan can dan baya so SUHAIL yayo musu katoɓara yana so yaji komai abakin me gadin . “dan Allah malam me gidan nan alaji sa,ad muke nema” “Ayya ai ALAJI ya jima da rasuwa hala dai kuba ƴan garin nan bane ko?” “eh gaskiya mu ba mazauna nan bane” me gadi “shi yasa baka samu labarin kisan da aka yiwa alaji ba” JAMAL yace. “wallahi ban sani ba to ina matar sa da ƴar sa suke?” "kayya ai shida matar tasa aka kashe yanzu ƴar sa ce kaɗai ta rage” “ Ko zamu iya sanin inda take kuma su waye acikin gidan?" shiru me gadi yayi yana Nazarin abinda ze ce can ya nisa kana yace “ ai tin ran sadakar uku ƙanin sa ALAJI BUKAR ya dawo gidan da zama ƴar sa kuma tana nan gidan wato MANAL bata jima da fita bara ba yanxu zakuga ta dawo ” “BARAH!!.” SUHAIL da JAMAL suka haɗa baki gurin faɗa “ƙwarai ma kuwa ta tafi bara saboda ƙanin mahaifin nata basa nan shi da iyalan sa sun tafi yawon mema kuke cewa ko yawon zaga gari na dai manta.” INNALILKAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UNA abinda SUHAIL da JAMAL suke ta nana tawa MANAL ce, ta turo ƙaramar ƙofar get ɗin ta shigo har lokacin tana shan lemon ta wanda babu komai aciki se fata se gwaguya take sam bata lura dasu ba ganin tana neman shigewa ciki yasa JAMAL ya ƙwalla, mata kira “MANAL” da sauri ta wai go kasa ƙarasawa tayi sema kafe shi da ido da tayi can kuma tace. “laaaaaaaaaah Dr,. JAMAL kai ne dama zaka kuma zuwa in da nake ina JAMSY ban kuma ganin ta ba” gabaɗaya ta jeromai tambayoyin a lokaci guda kuma cikin murna, “waca tambaya zan amsa miki?" dariya tayi tace. “wallahi dik na ruɗe ne ” se yanxu SAUHAIL ya magantu dace wa. “ ki cire wannan ɓawon lemon daga bakin ki, ” se yanxu ta lura da SUHAIL cire wa tayi cikin jin kunya ta kuma sunkuyar da kanta ƙasa. “ daga ina kike ?” cewar JAMAL in ina tasomayi “uhum uhum naje barane kuma ban samo komai ba se wannan lemon da kuka gani” da suri SUHAIL ya juyar da fuskar sa sabida wasu hawaye da suka taho mai ace yarinya ƴar masu kuɗi wadda batasan wani abu waishi talauciba ita ce take yin bara kai duniya ba matabbata bace.... “me yasa kika fita bara bacin na san da mutane agidan kuma da abinci” JAMAL ya kuma jefo mata wata tambayar. ƙwallace ta silalo daga idon ta tace. ai basa nan sunyi tafiya amma sun kusa dawowa” ta faɗa yayin da ƙwallar data maƙale akwarin idon ta ta samu damar gan garowa. iska me zafi , SUHAIL ya furzar yace. “ka gani ko JAMAL na faɗama nina san ganin ta da nake yi a mafarki ba'a banza ba dan Allah ka duba kaga wannan tanƙameman gidan ace ita kaɗai zata kwana acikin sa dan haka yanzu zamu tafi da ita gida ba zata sake kwana a cikin gidan nan ba ” “A'AH SUHAIL hakan bame yuwa ba ne gwara mu barta anan nina san yanda zamu muɓullowa lamarin dan haka kabar komai a guna ” Seya juya inda MANAL take tsaye ta tsura musu ido cike da tsoro dan gani take kamar cutar zasu yi “kin ga MANAL ki kwantar da hankalinki baxa mu cutar dake ba hasalima ceton ki zamu yi kishiga ciki xamuje mu dawo kin ji ” kai ta ɗaga mai alamar to fita suka yi daga gidan suka shiga motar su SUHAIL ya kalli JAMAL yace. “ina zamu?” “kasuwa zamuje muyi mata siyayyar kaya dana abinci danna lura akwai yinwa atare da ita in yaso gobe se mu dawo kafin nan ta dawo hayyacin ta ” “ eh kuma fa haka ne” cewar SUHAIL. tin daga burosh kilin sabulun wanki dana wanka kayan kwalliya takalmi kayan sawa hijab dogayan riguna pants shimi brxy kai kaya kawai suke jida kamar za'a haɗa lefe shi kuwa SUHAIL komai ya gani ɗauka yake har seda JAMAL yace ya isa ɓan garan kayan abinci suka nufa komai da ake buƙata na girki seda suka siya mata sannan suka se mata da faffe gurin biyan kuɗi suka je suka biya akasa musu amota sannan suka dawo gidan mamaki ne ya kashe MANAL kai ba ita ba hatta dame gadi se da yayi mamaki gainin tulin kayan da suka shigo dasu ɗakinta suka kai suka dire mata tarada gaya mata gove zasu dawo zokuga kukan farinciki gurin MANAL se godiya take musu SUHAIL kuwa se kallon ta yake ji yake kamar ya tafi da ita ya raba ta da wannan wahalalliyar rayuwar amma bara ya jira yaga wana mataki JAMAL xe ɗauka shima megadi ba,a barshi abaya ba seda suka danƙa mai kuɗi masu yawa suka ce yasa musu ido akan MANAL kada ya kuma bari taje ko ina. sannan suka kama hanyar gida..... Cikin dare SUHAIL ya kasa bacci fuskar MANAL kawai yake gani koya rufe idon sa ita yake gani yanda yaga rana haka yaga dare gari na wayewa yayi wanka yaje ya gaida memartaba ya gaida mahaifiyar shi da sauran matan baban shi. ko karin kumallo be tsaya be yi ba ya kama hanyar gidan su JAMAL. “a'ah lale marhabin yau kai ne agidan namu SUHAIL lallai yau za'ayi ruwa da ƙanƙara” cewar wata dattijuwar maga wacca ba-zata wuce shekara hamsin ba. sosa ƙeya SUAHIL yayi yace. “ina kwana” “ MOMY lpy lau ja'iri dole ka sunkuyar da kai dik yanda akai akwai abin da ya kawo ka danna san ruwa baya tsami banza har da zaka dako wannan uban sammakon ka taho seka shiga shima ɗayan mashirir cin ɗan uwan naka yana ciki be ma tashi daga bacci ba”. “to MOMY na barki lafiya” sim sim ya shige ciki yana shiga ɗakin ya ganshi akwance bashi da niyyar tashi duka ya ɗala mai, agigice JAMAL ya tashi har yana bigewa da bango dariya SUHAIL yasa har da riƙe ciki shima JAMAL ya daddage ya ɗala mai dindu tsut SUHAIL ya dena dariyar sabida yaji zafin dukan “ashe babu daɗi ni kayi min ” gabaki ɗayan su sukasa dariya. “kaga malam katashi Ka shirya Mu tafi in yaso ko ahanya ne seka karya danna matsu inji yaya MANAL ta kwana” harara JAMAL ya ɓalla mai yace. “saboda wata MANAL se naƙi karyawa agida na tafi hanya ina cin abinci to bara kaji babu inda zani se na karya kuma anutse Idan zaka jira kajira” tsaki SUHAIL yayi tarada faɗawa kan gadon, shi kuma JAMAL ya shige banɗaki wanka yayi ya shirya sannan suka nufi babban farlon gidan karyawa sukayi sannan suka kama hanya. “kace akwai ta inda zaka ɓullowa lamarin yarinyar nan ta yanda zamu kuɓutar da ita cikin sauƙi" SUHAIL ya faɗa lokacin daya karya kwana.” "eh ƙwarai haka ne a gani na ba shigar sauri zamu yiwa waɗan nan mutanen ba danna lura wannan ALAJI BUKARR ɗin ba ƙaramin mugu bane don haka cikin hikima da bara zamu bi komai zamu sa me gadin gidan yarin ga yi mana si ai din dik abinda yake faruwa da zaran anxo gaɓar daya dace mu tema keta semu te maka mata ammafa shima ba bayyana kan mu zamu yi ba se dai mu tura wasu idan suka gan mu tarada ita tofa zata kuma shiga wani halin Ko suyi mata wani abun kaga kenan lamari ya ɓaci" cike da gamsuwa SUHAIL yace. “haka ne dik abinda ka faɗa yayi Allah yasa mu dace” gaba ɗaya suka amsa da amin. daidai lokacin JAMAL ya cinna hancin motar cikin gidansu MANAL bayan sun gaisa dame gadi sukace yayo musu magana da MANAL.... tin da ta doso su SUHAIL ya saki baki yana kallan ta har seda JAMAL ya xungure sa sannan ya ankare sanye take cikin hijab ruwan ƙasa yayi mata kyau tsakanin jiya da yau ta canza ta fara dawo wa MANAL ɗin asali har ƙasa ta tsuguna ta gaida su suka amsa tace “su Shigo ciki binta suka yi har xuwa ɗakin ta ruwan da suka seyo mata ta kawo musu suka sha gefe ta koma tana wasa da yatsun hannin ta shiru babu wanda yace komai. JAMAL ne yayi gyran murya gamida cewa... “MANAL” ɗagowa tayi ta kalleshi yaci gaba dacewa “sunana JAMILU UMAR ABDULLAHI ɗan gidana seneto UMAR ABDULLAHI amma amfi sani na da JAMAL. wannan abokin nawa sunan shi SHAMSIDDIN ɗa ne ga sarkin masarautar *ZAKI* ana ce mai SUHAIL shine wanda ake sa ran ze hau milki nan ba da jimawa ba kinji daga inda muke dan haka kema munaso musan labarinki.” gefan hijab ɗin ta tasa ta share ƙwallar data xubo mata nan ta shiga basu labarin ratuwar ta tin daga farko har ƙarahe ba itaba su kansu seda suka xubar da hawaye musamman SUHAIL wai dama da gaske ana irin wannan ratuwar ace ɗan uwan mahaifinka ya dinga axabtar dakai har da yi maka mummunan fata ke duniya ina zaki damu rarrashin ta suka yi sannan sukai mata sallama tara da yi mata alƙawarin zasu dinga zuwa suna ganin ta tin daga wannan rana sesu SUHAIL sun xo tarada yo mata siyayyaya nan da nan MANAL ta murmure hasken ta ya dawo kyawun ta ya kuma fitowa tayi ƙiba fatar nan tayi luwai kamar ta Jarirai gwanin sha'awa ta samu kayan more rayuwa uwa uba kwanciyar hankali babu kyara babu tsan gwama bare marin manca hanya. MMN HIBBA RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 15-16 FILIN SAUKAR JIRAGE NA MALAM AMINU KANO. A hankali jirgin ya sauka ƙasa tara da sakin wata lafiyayyar iska me ratsa zuciya, sannu a hankali fasinjoji ciki suka soma fitowa ɗaya bayan ɗaya canna hango ALAJI BIKAR da iyalan sa sun yi kyau fatar nan see sheƙi take su NABILA da ZAINAB sun koma tamkar ƴan india dan kyau musamman NABILA fatar nan tayi luwai luwai kamar ba ƴar hausawa ba idan ba magana tayi ba zaka taɓa cewa ta san wani abu wai shi hausa DIREBA ne yazo ya ɗauke su dam dam dam gaban MANAL ya yanke ya faɗi lokacin data jiyo maganar su a tazane ta juya ta kalli ɗakin ta wanda yake shaƙe da kayan abincin da su SUHAIL suka kawo mata jiya innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai take ambato hijab ɗin ta ta saka ta fito harabar gidan dan gudin kar ace bata zo tare su ba tin da ta fito suke bin ta da kallo DADY da yake waya kasa ci-gaba da yin wayar yayi ya saki baki galala yana kallonta ita kuwa MANAL tsugunawa tayi har ƙasa tace. “DADY sannun ku da dawo wa ya hanya” babu wanda ya iya tanka mata se na mujiya da suka zuba mata NABILA kasa ɓoye abin da ke ranta tayi tace. “ke muna fuka ƴar iska ƴar tasha mu xaki yiwa daɗin baki gidan ubanwa kika samu kuɗin da har kika ɗinka sutura masu tsada irin wannan se ta juya gurin DADY wai dady baka gani ne baka kayan da suke jikin ta ba? ka duba da kyau komu da muke da gata bamu taɓa sa irin wannan tsadaddun kayan ba dama na faɗa muku in dai taga bama nan se ta kawo kwarton ta gidan nan kuma gashi idan ba maza take biba uban wa ze siya mata kaya masu tsada kamar haka” “kin faɗi gaskiya NABILA don haka DADY muna so ka ɗauki mummunan mataki akan ta ko dai ka kore ta ko kasan yanda zaka yi da ita na gaji da ganin wannan shegiyar yarinyar me kama da aljanu” ceawr ZAINAB. “kuma dai kwa faɗa ƴaƴan nan dana bashi shawarar yanda zeyi da ita ai ƙiyawa yayi gashi nan tana kawo mana ƴan iska cikin gida." cewar MOMY ta faɗa a fusace. DADY kuwa cewa yayi. “komai yazo ƙarshe insha Allahu za'a yita ta ƙare ba dai maza take biba to zan aura mata wanda ya dace da ita kuma kyauta zan bayar da ita ko in ce sadaka” daga haka DADY ya shige ciki suma suka mara mai baya suka bar MANAL tsaye jikin ta dik ya mutu, yanxu ƙiyayyar da suke mata har ta kai a bayar da ita sadaka?. kururuwar, da NABILA take yi ne ya dawo da ita daga duniyar tina nin data lula a ƙofar ɗakin ta, ta gansu NABILA na cikin ɗakin tana fir fito da kayan dasu SUHAIL suka kawo mata se da ta fito da komai hatta da kayan sawa seda NABILA tayi musu filla filla. “magana ta ƙare kuna gani har da kayan abinci hummm ƴar gata wato ruwan roba ma take sha gaskiya ne kin samu sake to wallahi ba zaki kuma amfani da su ba mu zamu ɗauka” gaba ɗaya NABILA ta kwashe kayan bata bar mata ko tsinke ba se kayan jikin ta ɗakin ta ta kai kayan na abinci kuma ta kai su kicin tofa rayuwar MANAL ta kuma koma ruwa tinda suka dawo bata samu zama aiki kawai take kanta gama wannan ance tayi wannan nan da nan ta koma gidan jiya. yau da daddare DADY yasa aka kira mai MANAL gyaran murya yayi yace. “to ƙaramar karuwa tin da kin nuna auare kike so zanyi miki aure zan sa a nemo min faƙiri matsiyaci matalauci wanda bashi da cin yau bare na gobe na aura masa keee, kije can ki ƙawata da iskancin ki zan sa me gadi ya nemo min koma waye dik tsufan sa koda sadaki ko babu haka zan bashi ke tin da baki da galibu” kuka ne ya ƙwace wa MANAL me tsuma zuciya yi take kamar ran ta ze fita dariya su NABILA suka sa gamida tafawa ZAINAB tace. “gaskiya DADY kayi abinda ya dace dama auaran take so magana ta ƙare seta tafi Allah ya raka taki gonaaaaaa.NABILA ta amshe da cewa “ni kam DADY wata alfarma nake so kamin” “faɗi dik abin da kike so ni kuma zan miki shi” “ dama ba wani abu bane face ina so ayi auran cikin satin nan bana so aja lokaci sannan kasa afara yi maka bin ciken wanda ya dace da ita” “an gama ƴar lele ai ko yau kika ce a ɗaura auran yau za'a ɗaura shi” dikkan su suka sa dariya ”kukan MANAL ya kuma tsanan ta yi take kamar zata shiɗe, tsawa DADY, ya daka mata yace. “tashi ki bani guri ƴar iska kawai kukan ubanki kikeyi” Murmushi mugunta NABILA ta yi kana tace “ƙyale ta DADY wai ita muna fuka." Washegari da safe Dady ya samu me gadi ya faɗa mai abin da yake so kan cewa ya nemo mai mutumin da yasan matalauci ne bashi da cinyau bare na gobe. “to Alhaji insha Allahu Zan nemo maka Amma ranka ya daɗe idan an nemo mutumin me zaka yi mai Idan wani aikin ne nima zan iya” "ba aiki bane ba Malam rabe ina so in yiwa MANAL aure ne shi yasa kaji nace ka nemo min matsiya ci faƙiri irin ta sabida ta da cewa da shi ” shiru mai gadi yayi can kuma yace. “kuma fa ALAJI kayi gaskiya dan wallahi auran yafi da cewa da ita ina gaya ma yarinyar nan bata jin magana kaga yanda take kawo ƙartai cikin gidan nan da nayi mata magana seta nemi zagi na shi yasa naja baki na na zuge kuma insha Allahu zan kawo maka irin mutumin da kake so koma wanda ya fishi talauci” “ ai kuwa Malam rabe da nayi maka kayuta me tsoka” baki Rabe ya washe “An gama ranka ya daɗe " ƙofa ya buɗe mai bayan fitar alaji BUKAR me gadi ya koma ɗakin sa gamida turo ƙofa wayar sa ya ɗakko wacca tasha ɗaurin ƙirji da kyauro number JAMAL daya bashi yace idan yaga wata matsala data shafi MANAL yayi gaggawar sanar dashi, “hello ranka ya daɗe malam Rabe ne me gadi ne na gidan su MANAL” daga ɗaya ɓan garan JAMAL yace.“ okay ya kake ya MANAL ɗin tana lafiya dai ko?” cikin rawar baki RABE me gadi yace. “eh tana lafiya se dai akwai abin da yake faruwa wato yanxun nan ALAJI BUKAR ya same ni da wata magana wai na samo mai mutumin da bashi da cin yau bare na gobe nan ya kwashe dik yanda suka yi da ALHAJI BUKAR ya faɗa mai ya ƙara da cewa “ ya bani nan da kwana biyu in nemo mai mutumin shi yasa nace bara na gaya maka .” “to ranka ya daɗe an gama se naji ka, daga haka ya kashe wayar. Afili yace. “ ƙarshan ku yazo mugaye azzalumai marasa imani.” MASARAUTAR ZAKI SUHAIL ne, zaune gaban memartaba gyaran murya yayi yace. “SUHAIL jibi in Allah ya kai mu kan tura Ka London gurin MUHAMMAD zaku tattauna kan yanda za'ayi game da harkar kasuwanci daga nan kuma zaka wuce Amerika ka amso min sako gurin aminina LAWAN” cikin girmamawa SAUHAIL yace “ an gama RANKA YADAƊE na barka lafiya .” ɗakin sa ya koma wayar sa ya ɗauka ya kira JAMAL kan yazo suje gidans u MANAL saboda jibi ze bar garin “okay Shi kenan seka zo ɗin” mintina ƙalilan JAMAL ya ƙaraso. “yawa ka ƙara so ai ba seka zauna ba muje kawai” kallansa JAMAL yayi ya kawar da kansa kana yace. “so kake mu janyo mata wata masifar to masu gidan sun dawo dan haka ka saurara min da wannan soki burutsun naka" cikin tashin hankali SAUHAIL ya ce “ kana nufin s ta koma wannan wahalalliyar rayuwar?” ƙwarai ma kuwa amma na samu hanyar da zamu te maka mata nan JAMAL ya kwashe yanda su kayi da RABE me gadi ya gaya mai sosai hankalin SUHAIL ya tashi ,. ganin haka yasa JAMAL cewa. “ka kwantar da hankalin ka a wannan lokacin ne ya kamata ka temaka mata” “ ta waca hanya zan temaka mata ?” “ta hanyar auran ta ” zaro ido SUHAIL yayi yace. "auran ta fa kace kai ma kasan hakan beme yuwa bane memartaba baxe taɓa amince ba” gyara zama JAMAL yayi yaci gaba dacewa. “in dai da gaske kana son ka t temaka mata to ka aure se dai idan ba tausayin ta kake ji ba” shiru SUHAIL yayi tarada furxar da zaxxafar iska kana yace. “shi kenan JAMAL ya kake ganin za'ayi?” " tun da ka amince ka bar min komai a hannu na san yanda zanyi” kamar yanda ALAJI BUKAR ya bawa malam RABE me gadi umarni ya kawo mai mutumin da bashi da cinyau bare na gobe hakance ta kasance wani tsoho ne tukuf har ya ranƙwafa saboda tsufa ƙafafunsa dik gidan memery wato faso takalmin ƙafarsa kuwa silifa ne lamba gomasha ɗaya yadin jikin sa kuwa irin ya din nan ne da ake cewa ishirinka maraya shima dik ya fefe har ya fara fashewa cikin gidan suka shiga inda suka iske dika mutanan gidan har MANAL bayan sun gaisa RABE yayi wa alaji bukar baya nin mutumin da yace a samo mai. washe baki DADY yayi gamida cewa. “ƙwarai kuwa yayi yanda nake so ”MOMY ma cewa tayi “gaskiya kam yayi ga dikkan alamu talauci yayi mai kanta kuma ya dace da ita se dai bamu san kenan shi ba?” “suna na SUNUSI kuma ni almajiri ne ina da mata uku ƴaƴa na sha takwass sannan banida sana'a ruwa nake siyar wato garuwa” “masha Allah haka ake so”cewar ZAINAB. “gaskiya kam dady yayi se taje ta riga tuƙa tuwo a lamaba talatin ina ga shima ba kullum ake cin tuwon ba” inji NABILA kenan. “kin faɗi gaskiya yarinya se muyi sati bamu ɗora tukunya ba se dai na basu ashirin ashirin su se garin kwaki su jiƙa su sha” inji SUNUSI kenan, “shi kenan malam SUNUSI dama wannan yarinyar zan aura maka kuma kyauta na baka da idan har ka amince to gobe ka turo magaba tanka a ɗaura kuma na gaya maka bana son komai daga gare ka ko sadaki bance ka kawo ba” “haba ALAJI wa za'a yiwa wannan kyautar yace baya so ai se dai in bashi da hankali wannan kykkyawar yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa in sha allahu gobe zan turo” SUNUSI ya faɗa yana washe bakin sa me ɗan karan wari haƙoran nan kamar jar dawa dan dauɗa “to shi kenan idan kazo da ƴan uwan naka ka samu malam RABE shi na wakilta a matsayin wanda ze aurar da ita️” Jama'a muji tsoron ubanguiji mu ku sani akwai mutuwa akwai kwanciyar kabari akwai hisabi WANNAN AL-ƘALAMIN MMN HIBBA NE RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba. GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 17/18 Washe gari misalin sha ɗaya na safe SUNUSI da ƴan uwan sa suka bayyana a gidan su MANAL sun sha yadin su mamar dik ya ya muste kamar an ƙwato su daga bakin kura fuskar nan komai ba su shafa ba takalmin nan dai na jiya shi ne be canza wani ba haka aka ɗaura auran ko sadaki babu, MANAL kuwa tana ɗaki taji anɗaura mata aure da sa'an kakan ta taci kukan ta, ta ƙoshi zazzaɓi me zafi ya rufe ta daddare SUNUSI ya turo wasu dattawa sune ƴan ɗaukar amarya a cikin A daidaita suka zo jakar tsummo karanta ta ɗauka ta fito har lokacin kuka take yi , A farlo ta same su babu nasiha babu komai DADY yace. “gata nan ku tafi da ita ni dai na gama nawa na fita haƙƙin ta tin da na aurar da ita ga wanda ya fi dace wa da ita" se a sannan kukan MANAL ya ƙaru , taje gaban DADY tana roƙon sa da ya yafe mata dik laifin da tayi mai sannan taje gurin MOMY da su NABILA amma babu wanda ya tanka mata illah wani mugun kallo da suke bin ta da shi . tana kuka tana komai dattawan nan suka sata a ɗan sahun da suka zo da shi suka ɗau hanya sun jima suna tafiya sannan taga an ɗauke hanyar cikin gari an shiga cikin wani sur ƙuƙin daji doguwar tafiya kafin suka isa wani gidan jar ƙasa dik da a duhu ne hakan be hana MANAL ta ƙare mai kallo ba irin ginin nan ne na da wanda akeyi da jar ƙasa shi ma ya mutu kana iya hango na cikin gidan ɗaku nan ma ana hango su A taƙaice dai ba shi da maraba da wanda yake waje shiga cikin gidan suka yi caɓal MANAL taji ta tsoma ƙafar ta cikin ruwa wasu zafafan hawaye ne suka sirnano daga idan ta zuwa kuncin ta cikin ranta tace “ inna ilaihi wa inna ilaihi raju'un na shiga uku ni MANAL nan kuma ƙaddara ta jefo ni Allah ya sa nan ɗin ya zame min Alheri ya sa ƙarshen wahala ta ce tazo ya Allah ka ba ni ikon cinye wannan jarabawar ” ɗakin da dattawan suka shiga nan ta nufa taxo shiga ta ƙume ji kake gummm, ashe irin ƙofar nan ce ta ƙauye da seka tsuguna zaka shiga sosai ta bugu sukuwa dattawan se sannu suke rattabo mata kai kawai ta ɗaga musu. Ƙarfe goma na dare SUNUSI ya shigo da abokanan sa se washe wargajejan bakin sa yake hakan yasa dattawan miƙewa suka yi mata se da safe. nanfa MANAL ta kuma takure wa sabon kuka ya ɓalle mata, kamar famfo yau ne ta ƙara tabbatar da maraice babu daɗi idan iyayan ta suna raye ko rasa mijin aure tayi baza su aura mata wannan tsohon ba sallamar da aka yi ne ta dawo da ita daga tinanin da take kasa amsa sallamar tayi illah miƙewa tsaye da tayi bakin ta na rawa tace. "Dr. JAMAL kai ne? ya akayi kazo nan? waya gaya ma a ɗaura min aure? ya aka yi kasan ina nan?” dariya JAMAL yayi kana yace. “ai nine na ɗaura miki auran.” “kai ne ka ɗaura min aure ? ta yaya hakan zata faru bacin dazu aka daura min aure da Wannnan bawan Allah kuma kace kai ne ka daura min Aure plsss JAMAL me ke faruwa da ni ne ka gaya min gaskiya ina cikin Rudani ko kai ma cutar da ni zaka yi dan Allah karka min wani abu ka bar ni da tashin hankalin da nake ciki na yi ƙanƙanta da Wannan tashin hankalin.” ta karasa fada tara da zubewa ƙasa tana kuka me tsuma zuciya. tausayin ta ya kama JAMAL tabbas ba tai ƙarya ba ta yi ƙanƙanta da kalar rayuwar da take ciki ba ko wace mace ce zata iya fuskantar haka ba tare da ta sama wa kanta mafita ba. “ ki yi shiru MANAL ba ni da nufin cutar dake ina me miki albishir da cewa daga yau kin de na hawayen baƙin ciki se dai na farin ciki ki tsaya ki saurari abin da zan gaya miki”. “ a hankali ta ɗago tana kallan sa kallo me cike da tambayoyi. ME KARATU BARA KOMA BAYA DON JIN YA AKAI HAKAN TA FARU INYASO SEMU CIGABA JAMAL yaci gaba dacewa. "malam RABE me gadi ya sanar dani cewa ƙanin mahaifin ki yana shirin aurar dake ga mutumin da yaso kuma wanda bashi da sana'a hakan yasa na samu SUHAIL da maganr bayan mun gama tattauna wa nace mai shiya kamata ya aure ki dan ya ceto ki daga wannan masifar da ake neman jefa ki cikin ta na samu malam RABE na gaya mai halin da ake ciki na kawo mai SUNUSI a matsayin shine wanda ze aure ki in da allah ya temake mu ALAJI BUKAR ya danƙawa malam RABE me gadi ragamar ɗauri auren ki hakan yasa muka yi amfani da wannan damar muka ɗaura auran wanda A zahiri muka cewa alaji BUKAR da SUNUSI aka ɗaura a baɗini kuma da YARIMA SUHAIL aka ɗaura miki aure kinji yanda abin ya kasance ”. “ƙwarai ma kuwa yarinya gaskiya ya gaya miki hatta da wa in nan tsofaffin da kika gani sun taho dake suma haya muka ɗakko su kuma wannan gidan ba gida na bane hayar shi muka yi ko da su alhaji bukarr zasu biyo mu shi yasa kika ga an kawo ki gidan nan wannan shine gaskiyar lamari kuma ba da ni aka ɗaura miki aure wannan kayan da kika gani a jiki na suma aro shi mukayi ba wai kaya na ba ne” cewar SUNUSI, cikin rawar murya MANAL tace. “yanxu kuna nufin ni matar yarima ce? kuma ɗan sark? ko dai tsokana ta kuke yi don allah ku gaya min gaskiya karku yaudare ni idan da shi aka ɗaura min aure wannan ba damuwa bane danni bana buƙatar wasu kayan more rayuwa na san zan ƙare rayuwa ta acikin baƙin ciki mutuwa ta nake jira danna fison mutuwa akan komai”. “haba MANAL se kace ba musulma ba biki yarda da ƙaddara bane kiyi gaggawar yin istigifari”cewar JAMAL. " astagafirillah astagafirillah astagafirillah astagafirillah MANAL ta shiga nanatawa “SUNUSI yace "ƙwarai MANAL kuma ki gode wa allah kina da xuciyar imani da yarda da ƙaddara wallahi da wasune da tuni sun fantsama duniya Allah yana gani ba kowa ba ne ze iya jure wannan uƙubar da kika sha, dan haka ki gode wa Allah ki kuma gode wa, wa innan bayin Allah da suka tsaya kai da fata wajan ganin ba a kuma jefa ki cikin wani tashin hankalin ba daga ƙarahe dai ina miki fatan alkairi kuma insha Allahu daga yau na san kin dena wahala komai yazo ƙarshe bi ixinillahi”. daga haka SUNUSI ya tashi yayi musu se da safe hannu JAMAL ya zura a ajjihu ya ɗebo kuɗi da be san adadin su ba ya miƙa mai godiya yayi mai ya kuma yimusu seda safe. “muma tafiya zamu yi na kaiki gidan ki kafin angwanki ya dawo ”dariya MANAL tayi dan JAMAL yabata dariya. gida ne me kyau sosai wanda ya gaji da kyau ba babba bane sosai se dai daga gani kasan an kashe kuɗi ba kaɗan ba, hon yayi me gadi ya buɗe musu JAMAL ya cinna hancin motar ciki, cikin gidan suka shiga dik da bawani tarkace bane acikin farlon amma yayi kyau matuƙa sosai ya tafi da MANAL ai ko ta ware ido tana kallon ko ina. " to MANAL wannan shi ne gidan ki a ciki zaki zauna har se SUHAIL ya dawo zan ringa xuwa ina duba ki fatan dai baza ki damu ba se yasa hannu a ajjihunsa ya zaro waya babba acikin kwalin ta ya miƙa mata gashi idab kin samu nutsuwa ki duba kiga tayi miki idan ba tayi ba se'a canza miki” karɓa tayi tara da yimai godiya sannan ya zaga da ita gidan ya nuna mata ko ina sannan sukayi sallama ya tafi ita kuma ta dawo ciki ta kulle ƙofa. ɗakin da ya nuna mata a matsayin nata nan ta shiga kai tsaye wanka tayo wanda rabon da tayi irin shi har ta manta se da ta wanke lungu da saƙo na jikin ta har gashin kanta se data wanke bayan ta fito gaban mudubi ta zauna ta shafa mayukan data gani masu tsada ga ƙamashi sannan ta fesa ture cover ta buɗe taga kaya himili kuma dukka sababbi ne ɓan garan atamfofi da leshi da ban ɓan garan ƙana nun kaya daban wata rigar bacci me santsi da laushi ta saka tayi matuƙar yi mata kyau kamar dan ita akayi ta. alwala tayo ta gabatar da sallar magarib da isha'i. sannan ta haye luntsumeman gadon me laushi kamar burodi lumshe ido tayi tana jin wani sabon yanayi har ta manata raban data hau katifa wayar da JAMAL ,ya bata ta janyo ta fito da ita daga kwalin sosai wayan ya burge ta komai an sakawa wayar hatta da sim an saka mata kunnawa tayi kamar jira ake ta buɗe massage ya shigo wadda taga anyi sevin ɗin number da SUHAIL shiga cikin massege ɗin tayi ta buɗe ga abinda akace. "slm MANAL ya kike ya gida fatan kina ciki ƙoahin lfy? daga YARIMA SUHAIL.” bata san sanda murmushi ya suɓuce mata ba se ta tsinci kanta da mayar mai da amsa kamar haka. "lafiya ƙalau fatan kai ma kana cikin ƙoshin lafiya” ta tura mai nan ta tsinnci kan ta da tina nin sa , lallai ta yarda komai lokaci ne bata taɓa tina nin zata kuma yin rayuwar jin daɗi ba bare ta kuma yin dariya da haka bacci me daɗi yayi awan gaba da ita.... MMN HIBBA✍️ RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE. SADAUKARWA NA SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH) AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA. 19/20 Kiraye kirayen sallar asubah da ake yi ne ya farkar da MANAL, daga ni'imtaccan baccin data jima batayi irin shi ba banɗaki ta shiga ta dauro alawala ta gabatar da salla sannan tayi azkar kamar yanda ta saba bayan ta gama ne ta naɗe sallayar ta mai da ta ma'ajin ta ta kuma koma wa bacci se ƙarfe takwas ta tashi ta gyara gidan ko ina yayi fesss se ƙamshi da yake tashi kicin ta koma shima ta gyarashi sannan ta ɗora shayi ƙwai ta soya bayan ta kammala ɗakin ta ta koma wanka tayo ta sauya rigar baccin da take jikin ta zuwa doguwar riga wato A baya green color tayi mata kyau sosai, dik da ba wani kwalliya tayi ba man leɓe kawai ta shafa ta kalmi felet ta saka sannan ta fito farlo ta soma karya wa cikin nutsuwa take cin abincin cikin ranta tana gode wa Allah yanzu ne ta tabbatar da karin maganar gaskiya ne wadda bahaushe yake cewa mai haƙuri ya kan dafa dutse yasha har ma da roman sa sam bata taɓa tina nin zata fita daga ƙangin wahalar data shiga a gidan su se gashi Allah ya yi ikon sa a kanta, a fili tace. “alhamdulillah Allah na gode ma da ka haɗa ni da wa innan bayin naka ko ya su DADY suke? ko suna tinawa da ni? nama san ba zasu damu da ni ba tin da babu wanda ya rako ni gidan miji na ” ƙofar da ake ƙwan ƙwasawa ne ya katse ta daga tuna nin data lula miƙewa tayi taje ta buɗe JAMAL ne ta bashi hanya ya wuce . “Ina kwana Dr. ya kaje gida jiya?” ta faɗa tara da tsugunawa har kasa, murmushi, JAMAL yayi kana yace. “lafiya ƙalau amaryar mu ya baƙunta da Kaɗai ci ?”. murmushi kwai tayi gami da cewa. “Ina godiya a gare ka dakai da abokin ka Allah ya biya ku ya kai haske cikin rayuwar ku, daku da duk ahalinku Allah ya saka muku da gidan aljannar firdausi.” “Amin Amin ya Allah muma muna matuƙar godiya da wannan addu'a sannan daga yau bana so ki kuma yimin godiya Allah ne ya ƙaddara haɗuwar mu, kuma shine silar komai dan haka shi zamu gode wa ” “ haka ne Dr.” ”Zo ki ci-gaba da karyawar ki ko nine na tare miki guri?” A kunyace ta tashi ta koma kan dainin table ɗin tana shan shayin kamar me koyan sha, “SUHAIL ya kira ki kuwa?.” “A'ah be kira ba ya dai yi min massage” " “amma ya faɗa min yau da safe ya kira ki biki ɗaga ba” "da yake na bar wayar a ɗaki shi yasa daya kira banji ba” "okay idan kin gama abin da kike se ki kira shi ni zan wuce ko kina da buƙatar wani abun?" ''A'ah bana bukatar komai'' sallama yayi mata ya tafi . yana fita kiran SUHAIL ya shigo tsayawa yayi a bakin motar sannan ya ɗaga wayar gami da karawa a kunnan sa, "wai dan Allah JAMAL me kake jira tin ɗazu baka tafi ba kabar ƴar mutane ba kaje ka duba lafiyar ta kaga a wana hali ta kwana haba meye hakan" SUHAIL ya faɗa cikin ɓacin rai, shi kuwa JAMAL be katse shi ba har se da ya dasa aya kana yace. "to ranka ya daɗe ko kuma nace baba na kagama faɗan naka ko kuma da saura?" JAMAL ya faɗi hakan cikin son ya ƙular da SUHAIL, ai kuwa ya kuma tunxura ta inda yake fita bata nan yake shiga ba, da JAMAL ya gaji faɗan nasa yace. "to tin da dik abinda nake yi maka ban birge kaba seka dawo ka kula da ita ya faɗa tarada gimtse kiran. ko kaɗan JAMAL beji haushin SUHAIL ba dan idan da sabo ya saba dariya ce ta kamashi, daya tuna abinda SUHAIL yace. "wai ya bar ƴar mutane ita kaɗai se kace wani abu ze kama ta ya lura SUHAIL ya kamu da son MANAL ba tun yau ba. “allah yasa ita ma tana son shi” JAMAL yaɗa lokacin da yayi fakin a harabar gidansu. **** shi kuwa SUHAIL yana can abin duniya ya ishe shi shima ya san abinda yayiwa JAMAL be kyauta ba ko ba komai JAMAL abokin sa ne na haƙiƙa me ƙaunar shi tsakani da Allah amma ya iya da xuciyar sa ita ce ta axal xale shi dan yaji yanda MANAL ta kwana gashi ya kira wayan ta amma bata ɗauka ba faɗawa kan luntsume man gadon yayi wanda ya sha zanin gado na alfarma silin ɗin ɗakin ya ƙurawa ido yana tina nin mafita amma ya gaza samun mafita koɗaya dole dai ya koma wajan JAMAL ɗin iska mezafi ya furxar ya miƙa hannin sa kan allon gadon ya janyo wayarsa kira biyar yayi wa JAMAL be ɗaga ba shi kuwa JAMAL yana kallan kiran amma yaƙi ɗagawa se ana bakwai sannan ya ɗaga babu Wanda yayi magana a cikinsu sun ɗauki kusan minti tala tin sannan SUHAIL yace. "sorry JAMAL na san ban kyauta ba amma kamin afuwa kai ma kasan ba halina bane" "ni babu abunda kamin SUHAIL kaima kasan ba zanyi fushi da kai ba kawai dai na baka lokaci ne idan ka huce kamin magana" JAMAL ya faɗa yana ƴar dariya daga nan fira ta ɓalle wanda firar tasu akan MANAL sukeyin ta cikin firar tasu ne SUHAIL ya cewa JAMAL. "wallahi ina tsoran ran da zan tunkari ME MARTABA da zan can MANAL wannan shi ne karon farko dana aika ta abu ba tara da sanin sa ba" "gaskiya ne SUHAIL ba kai bama ni kai na ina jin tsoro amma babu yanda muka iya dole mu gaya musu tunda baze yu mu ɓoye wannan maganar ba dole wataran asirin mu xe tonu in ban da abinka ai ME MARTABA yasan mahaifin ta ni A ganina baze ɗauki zafi damu ba " ajiyar xuciya SUHAIL yayi yace. "ba wannan xaka duba ba JAMAL auran da nayi batara da sanin su ba shine matsalar kasan halin me martaba idan ya ɗauki zafi" ƴar dariya JAMAL yayi kana yace. wallahi idan naga hukun cin da'ayi mana me tsauri ne zame wa zanyi in barka ko nace ban san anyi ba gaba ɗayan su suka sa dariya ƙarshe dai sukai sallama kan inya dawo zasu tunkari SARKI da maganar... "Kwanciyar hankali da hutu yasa MANAL ta fara komawa MANAL ɗin asali kyawunta ya kuma fitowa fatar nan kamar ta jatirai dan laushi da santsi tayi ƙiba abinta ɓul ɓul kamar ba itava dirin ta da surar ta da baiwar da Allah yayi mata ta cikar ƙirji sun kuma fitowa kai hatta da gashin kan ta daya ƙuƙƙulle saboda wahala ya ware dik na mijin daya kalle ta se ya kuma kallanta kai bama na miji ba mace ma, seta kuma wai wayawa ta dube ta kullum se JAMAL yaxo ya duba MANAL tarada tambayar ta ko akwai abinda take so ga kuma wayar ta wacca take ɗebe mata kewa akai-akai SUHAIL yake kiran ta dik da bawani fira suke yi ba daga gaisuwa se ya kake, Daga banɗaki ta fito jikin ta ɗaure da tawul ga kuma wani ahannunta tana goge jikin ta , da alama wanka tayo abinda bata taɓayi ba yau shi tayi wato kwalliya haka kurum ta tsinci kanta da tsarawa fuskar ta kwalliya ita kanta seda ta kuma duban kanta saboda kyan da tayi cover ta buɗe tana duba kalar kayan da xata sa ta jima tana xaro kayan dik wanda ta ɗakko se taga be mata ba a haka har hannun ta ya kai kan wani farin leshi me ratsin golden ajiki doguwar riga ce bubu sosai ɗin kin ya mata kyau sauran kayan data janyo ta mayar sannan ta saka kai tubarkallah masha allah kyau iya kyau gashi ɗin kin yayi mata ciff kamar dan ita akayi ɗaurin dan kwali tayi gamida feshe jikinta da turaruka masu ƙamshi wayar ta ɗauka ta koma farlo tana gemm lokaci lokaci takan ɗagowa ta kalli agogo kamar wacca take jiran wani. Filin saukar jirage na malam aminu kano JAMAL ne tarada dogarawan masarautar zaki suna jiran fitowar SUHAIL sun jima sannan suka hango shi yana sakkowa daga sitef ɗin jirgin cike da takun ƙasaita kai daga gani sa kasan babu ƙarya ya haɗa iri da jinin sarauta yana ƙarasowa suka rungume juna shi da JAMAL sannan suka shiga mota tun a hanya SUHAIL yake tambayar JAMAL ya faɗawa MANAL yau xe dawo?" "a'ah ban gaya mata ba saboda ina so in shammace ta naga ya zata yi idan ta ganka" dariya suka sa gami da tafawa SUHAIL yace. "wallahi JAMAL baka da dama wato kaga yanda zata yi tome zata yi idan ta ganni bacin ba yau ta saba gani na ba," "dik da bayau ta taɓa ganin ka ba amma wannan shine karan farko da zaku kalli juna amtsayin miji da mataaaa" dai dai lokacin suka fito daga cikin mota bayi da ƙwarori se kwasar gaisuwa suke gami da yi mai sannu daxuwa gefe guda kuma algaita na tashi inda ake ta yimai kirari tara da yi mai barka da dawowa, kai tsaye ɗakin sa suka nufa wanka SUHAIL yayo ya sauya kayan jikin sa sannan suka tafi fada kamar yanda fadawan suka saba tashi sukayi suka basu guri JAMAL ne ya fara gaishe da me martaba sannan SUHAIL se sunne kai suke daga gani kasan basu da gaskiya, " lafiyar ku kuka zo kuka min gurfane anan naga tun ɗazu muka gama magana daku ko dai wata tsiyar kuka tafka ban sani ba ?" Cewar SARKI. JAMAL ne ya ƙiftawa SUHAIL ido, dan kar ya ce komai, "kaga shaƙiyyan yara ina magana kunyi shiru kuna magana da ido to kutashi ku bani guri tunda yau shaƙiyan cin naku ne ya motsa" sarki ya faɗa tara da rarumo maficin da yake gefan sa . da gudu suka miƙe suna dariya gami da cewa. "allah ya huci zuciyar, sarkin sarakuna kabari in tayi tsami zamu gaya ma " " kai ku tafi cann ni kun ishe ni da iya shege dikkan su suka sa dariya, Suna fita SUHAIL ya dubi JAMAL gami da cewa "me yasa ka hana na gaya mai?" "saboda ba yanxu ne lokacin wannan maganar ba kabari seda daddare semu gaya mai ko kuma xuwa gobe da safe yanxu dai muje in kai ka kaganta danna san ka matsu ka ganta" JAMAL ya faɗa tarada kashe mai ido ɗaya, duka SUHAIL ya kai mai yayi saurin gocewa, mota suka shiga suka kama hanaya da isar su magadi ya buɗe musu. MANAL dake kwance kan kujera two sita tana gem awayn ta sam bata ji tsayuwar motarsu ba sallamar su kurum taji da sauri, ta miƙe gamida cewa Dr. kai... bata ƙarasa abinda take son faɗa ba SUHAIL ya shigo ido suka haɗa tayi saurin sunkuyar da kanta jikin ta ya hau rawa kasa tsayuwa tayi da gudu tayi cikin ɗakin ta da ta saka keey tarada jingina bayanta a jikin ƙofar har yanxu ƙamshin tiraransa yana manne a hancin ta ga ƙirjin ta da yake dukan uku uku dama haka yake da kyau kamar shi yayi kansa wannan ai yama fita kyau kuma bama ajinta bane yafi ƙarfin ta gashi ɗan gidan sarauta" se da kallo ɗayan data yi mai taji ta kamu da son shi wannan shi ake kira da kallo ɗaya takk, Can farlo kuwa JAMAL se ha tintsire da dariya se yi yake shi kuwa SUHAIL yanda kasa an dasa gunki yama kasa cewa komai seda JAMAL yayi me isarsa yace. "gaskiya SUHAIL ka firgita ƴar mutane gashi kasa ta shige ɗaki harda garƙama mukulli seya tsuguna ya ɗauki wayar MANAL data yarda aƙasa ya miƙawa SUHAIL karɓa yayi ya doshi ƙofar ɗakin nata cikin muryarsa me sanyi da daɗin sauraro yace. "MANAAL buɗe ƙofar ko nine baki son gani?" Ahankali ta buɗe ƙofar har yanxu kanta aƙasa yake miƙa mata wayar yayi yace. "wato guduna kikeoyi amma bakya gudun JAMAL saboda ni kama ki zanyi ko cinye ki zanyi ko?" girgixa mai kai tayi alamar a'ah "baki da baki ne ?" cikin shagwaɓa tace. "ina da shi" "to amma bakiyin magana" kayi haƙuri dan Allah zanyi" ta faɗa har yanxu kanta aƙasa. "wai me yasa ba zaki kalle ni ba se rowar fuskar kike min dama bani kika yiwa kalliyan ba?" SUHAIL ya kuma jefo mata wata tambayar baki ta turo gaba kamar zatayi kuka tace. "eh ba kai na yiwa ba" ta faɗa tara da ƙara kawar da kanta shi kuwa SUHAIL gaba ɗaya ya shagala da kallan ta yanda tayi maganr yaji wani abu ya soke shi be san sanda ya kai hannin sa kan fuskar ta ba ya ɗago da haɓar ta suka ƙurawa juna ido gaba ɗayan su suka ji wani abu ya fixge su,, MANAL tai saurin rumtse idon ta tana jin wani irin yana yi da bata taɓa jiba. shima a nasa ɓangaran SUHAIL hakan take dakyar ya saita kansa yace. "se kin gaya min wa kike xumɓuro wa wannan bakin ya faɗa yana jan leɓantea da yasha manleɓe. turo shi ta kuma yi kana tace. "ni bada kai nake ba" "to dawa kike sekin gaya min" "dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan kuma ba" ta faɗa cikin shgwaɓaɓɓiyar murya. sakin ta yayi yace. "na haƙura idan kika sake se na hukunta bakin" Hannun ta ya kama suka zauna kan gadon har yanxu Hannun ta na cikin nasa yace. "kee biki iya yiwa mijin ki sannu da xuwa ba? ?" ko irin girkin nan da mata suke wa mazajen su ni biki yi min ba se shagwaɓa da turo baki" "to ai ban san yau xaka dawo ba da nayi maka idan kana so se nayi maka yanxu" "me ze hana in dai baxan takura ki ba " girgixa masa kai tayi tace. babu wani takura" okay muje ki yimin yanxu danna dena cin abin cin kowa sena mata ta" ɗagowa tayi ta kalle sa gira ya ɗaga mata yace. "eh mana koba mata ta bace.?" "itace" ta faɗa tarada rufe fuskar ta data fin Hannun ta . lallai Allah ya kashe ya bani mace mai hankali da nutsuwa ga kunya uwa uba ilimi ga addini ibada ya faɗa cikin ransa tare suka fito farlon inda suka iske JAMAL zaune hararar wasa ya jefa musu yace. "Sannu romiyo wato shine kuka bar ni anan kamar wani shara ko?" Dariya SUAHAIL yayi kana yace. "haba kai kuwa ai kayi mana uzuri koh daga fitawar mu, ka hau mu da faɗa" harara ya kuma ɓalla mai yace. "Ai gobe ma rana ce sena rakoka zaokamin wannan dogon waulakan cin" nan sukai ta fafatawa.... MANAL kuwa tuni ta shige kicin ta ɗora girki sun ann zaune se ta shin ƙamshi suka ji kallon kallo suka ringa yi Ita kuwa MANAL cikin mintuna ƙalilan ta gama haɗa komai ta zuba a kula sannan ta dakko filet da cokula ta ɗora akai ta kai ta ajiye musu ta juya zata tafi ta jiyo Muryar SUHAIL yana cewa "muza mu zubawa kan mu ?" ya faɗa yana mai kafe ta da maya tattun idanun sa wanda suke ƙara hargitsa ta dawo wa tayi ta zuba musu sannan ta koma daki bayan tafiyar MANAL su SUHAIL suka baje se kwasar girki suke JAMAL kuwa saboda santi harda cire hula ya ajiye a gefe yana kwasar abinci. "A gaskiya SUHAIL ka more mata dan ba kowace maca ce ta iya girki kamar haka" dariya SUAHAIL yayi yace. "Kai dai bari ai wallahi a yanzu ina ji a raina ko me martaba be yarda da aure na da ita ba to akwai matsala " "Allah ko''. ''ƙwarai ma kuwa'' SUHAIL ya bashi amsa. bayan sun gama kwasar girkin SUAHAIL ya shiga ɗakin dan ya faɗa mata zasu tafi kwance yasa Meta ta ƙurawa sili ido, yayi sallama yafi a irga amma bata ji ba seda ya bubbuga gadon sannan tayi firgigit ta tashi ido suka haɗa tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da ƴan tsun ta " mu dai zamu wuce se kuma zuwa gobe in sha Allahu idan muka dawo tara zamu tafi dake" '' To Allah ya kaimu Allah ya tsare hanya" MANAL ta faɗa har lokacin kanta na ƙasa. Murmushin jin daɗi yayi sannan ya fita daga ɗakin da kallo MANAL ta bishi tana kuma mamakin wai yau ita ce matar SUAHAIL mutumin da kowa yake son gani amma babu dama se gashi ita ta gan shi kuma a matsayin mijin ta yake ikon Allah se dai kallo. WASHE GARI...... SUAHAIL da JAMAL ne zaune gaban me martaba , bayan sun gama kora mai dik abin da ya faru kama daga mafarkin da SUHAIL yake yi har zuwa lokacin da suka ɗaura auran MANAL da SUHAIL ba tara da sanin ALAJI BUKAR. shi kanshi me martaba seda ya tausaya wa MANAL, "ƙwarai da gaske na san ALAJI SA'AD ME DALAH abokina na ne kuma mutumin kirki ne sosai bashi da abokin faɗa" cewar me martaba, "yanzu ina ita yarinyar take?" sosa kai SUHAIL yayi gami da cewa "tana gida na a nan na ajiye ta mun yake sharar s sanar da kai idan ka amince se ta dawo nan" "haba ku kuwa yaza ku ajiye ta ita kaɗai acikin wannan gidan lallai lallai gobe kuje ku ɗakkota ku kawo ta nan dan akula da ita'' gaba-daya suka haɗa baki gurin faɗin godiya muke ranka ya dade'' sannan suka fice daga fadar....... MMN HIBBA RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi Shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba. GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE🤝 21/22 SHIN WANE NE SUHAI?. SHAMSIDDEN MUHAMMAD shi ne cikakken sunan sa ɗa ne ga Sarkin masarautar zaki, masa rauta ce babba wacce ta jima tana mulki tun iyaye da kakanni MUHAMMAD SHAMSIDDEN shine sunan mahaifin SUHAIL kuma sarki a masarautar zaki ya gaji sarauta agurin mahaifin sa Sarki MUHAMMAD sarki ne me adalci ga al'ummar sa baya zalinci ko kaɗan kuma baya bari ayi zalunci hakan yasa kowa yake son shi ba zaka taɓa ji ance ga aibun sa ba se dia alkairin sa, SARKI MUHAMMAD matansa biyu HAWAU'U wato uwar gida (Kilishi) se HAJARA wacca suke kirada gwaggwo ƴaƴan sa guda biyar ZAINAB ita ce babba se LUBABATU me bi mata se kuma SUAHAIL shine na Uku Kuma shi kaɗai ne namiji hakan yasa duk wani burin sarki ya ɗora shi akan SUHAIL se ƙanwarsa BILKISU se kuma ƴar autar su AMINA wacce ake kira da MEENA, ZAINAB BILKISU LUBABATU anyi musu aure harma da ƴaƴan su, suma ƴaƴan sarakuna suka aura, yanzu sai MEENA kawai tarage wacca daga ita ba'a kuma haihuwa ba. "JAMAL kuma ɗane ga UMAR ABDULLAHI wato ɗan gidan seneto kuma aminin sarki ne hakan yasa JAMAL da SUHAIL suka shaƙu da juna duk da wani zubin SUHAIL yanda miskilan ci. WANNAN KENAN BARA KUMA MUDORA DAGA INDA MUKA TSAYA. Da safe SUHAIL da JAMAL suka shirya tsaf suka yiwa gidan da MANAL take dirar mikiya lokacin MANAL ta koma baccin safe bugun ƙofar su ne ya tashe ta addu'a tayi sannan ta miƙe taje ta buɗe musu sam ta manta da rigar bacci ce ajikin ta kunya ce ta kama ta JAMAL kuwa yayi saurin ɗauke kansa shi kuwa SUHAIL wani baƙin ciki ne ya tokare mai xuciya ya za ayi ta fito haka bacin ta san tare suke da JAMAL dik da JAMAL abokin sa ne na ƙwarai kuma ya san koshi waye amma ai be kamata ta fito haka ba dan takai ci be san sanda ya daka mata tsawa, ba MANAL ba hatta da JAMAL se da ya tsorata, nan da nan idon sa ya kaɗa yayi jajir kamar garwashi se huci yake, ita kuwa MANAL saboda firgici, da tsoro ɗaki ta shige jikin ta na rawa tinda take ba'a taɓa yi mata irin wannan tsawar mesa ƴan hanjin mutum su girgiza, rakuɓe wa tayi a ƙuryar gadon jikin ta se rawa yake kamar maxari gani take SUHAIL dukan ta zeyi. "haba SUHAIL ya zaka daka mata wannan tsawar? se kace Aradu a haka kake cewa kana sonta to wallahi in dai haka zaka ringa mata zaka sha wahala ka sani cewa su mata abin a lallaɓa ne idan kace zaka mata horan tsawa da hantara tofa zata fanɗare maka idan wata ranka mata tayi shiru wata ran rama wa zata yi kaga kenan zance ya ɓaci mata da kake gani ƙaramar ƙwaƙwalwa gare su tunanin su gajere ne in suka shiga damuwa tofa ba duka bane suke yin tawakkali abinda xuciyar su, ta raya musu shi suke yi” Ajiyar zuciya SAUHAIL ya sauke kana yace ”kai ma kasan abinda tayi bata kyauta ba inda wani ne ya shigo shike nan ya gama ƙare mata kallo,” dariyar da take cin JAMAL ce tafito fili yayi me isarsa ya gano kishi ne yake ɗawai niya dashi dan haka yace. “kaga yanxu dai ka tashi kaje ka rarrashe ta dan wallahi ta firgita idan yaso daga baya seka kafa mata duk dokar daka gadama JAMAL ya faɗa yana kuma ƙunshe dariya tsaki SUHAIL yayi gami da miƙewa yace “wallahi seta raina kanta dan bazan lamunci haka ba.” “to wai kai an gaya maka haka take wannan ma akasi ne kuma daga bacci ta tashi ya kamata kayi mata uxuri malam me mata ” ya faɗa tarada sakin dariyar ƙeta, can ƙuryar gado ya hango ta ta cure guri guda, jin an turo ƙofar yasa MANAL ta kuma tsurewa nan da nan hawaye ya wanke fuskar ta ta rufe idanin ta ji tayi an danƙo hannun ta se gata atsaye kamar gunki saboda tsoro saura kaɗan MANAL ta saki fitsari a wando se ma kyar kyata take, kamar me zazzaɓi. “ YAYA dan allah dan annabi kayi haƙuri wallahi ba zan sake ba na tuba wallahi.” murtike fuska SUHAIL ya kuma yi gami da ƙara matse hannun ta ƙara ta saki tara da yin tsalle ta kuma rintse idanin ta “wallahi na tuba YAYA na tuba bazan kuma ba dan Allah kayi haƙuri ka sakar min hannu karka ɓalla ni,” ta faɗa tana me marai raice murya ga hawaye jage-jage a fuskar ta. sassauta mata ruƙon yayi yana kallan ta kana yace “naji na haƙura wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe muddin kika kuma fitowa a haka sena miki wanda yafi wannan ban yarda ki cire hijabi a wani gurin ba musamman idan da maza agurin kinji ko biki jiba?” “na ji ” maza tashi ki shirya mu tafi gida me martaba yace in zo in tafi dake” tashi tayi da nufin shiga ban ɗaki domin yin wanka se kuma ta tuna yana cikin ɗakin tsayawa tayi tana kallan sa , “ya dai kika tsaya kina kallo na ko wankan ma sena nuna miki yanda zakiyi?” girgiza mai kai tayi alamar a'h. “to meye?.” cikin turo baki tace " ka tashi ka tafi zanyi wanka” kallan ta yayi ya kawar da kansa gefe seda ya gama shan ƙamshin sa, sannan ya fita, da ido ta bishi afili tace "ohhh ni MANAL Allah ya haɗa ni da ƙarfan ƙafa,” wanka tayo tana fitowa, mai kawai ta shafa ta saka doguwarriga tayi rolin da mayafin rigar filet ɗin takalmi ta saka ta fito farlo har ƙasa ta tsuguna ta gaida JAMAL ya amsa cikin sakin fuska shi kuwa hakimin wani kallo yake jifan ta da shi kawai se gani su kai ya tashi ya shiga cikin ɗakin jim kaɗan se gashi ya fito hannin sa riƙe da hijab ruwan ƙasa miƙa mata yayi “oya jeki cire wannan matacin kokwan da kika saka bata ce komai ba ta amsa ta shiga ɗakin ta cire mayafin ta saka hijab ɗin daya bata tana fitowa taga b har sun fita amota ta same su dan haka ta buɗe baya ta shiga JAMAL yaja motar suka ɗauki hanya cikin ikon allah suka isa, yau dai ga MANAL acikin masarautar ZAKI gab da zasu shiga fada suka ci karo da MEENA ta fito kallonsu ta tsaya yi idon ta ne ya sauka akan MANAL wacca take gefan JAMAL nan da nan annurin fuskar ta ya ɗauke yanda kasan taga mala ikan mutuwa. kasa jure abinda ke xuciyar ta tayi tace " YAYA JAMAL wace ce wannan kar dai kace min budurwar ka, ce.” kafin JAMAL yayi magana SUAHAIL yayi caraf yace “eh budurwar sa, ce kuma da ita akasa musu rana ƴar uwar sa ce auren zumunci za'a yi musu” dafe kirji MEENA tayi gami da maimaita kalmar “ auren zumunci” ɗumi taji akan kuncin ta tasa hannu ta taɓa taga hawaye ne juyawa tayi ta cigaba da tafiya hawaye na kuma ɓulɓulowa daga kwarin Idan ta. “MEENA! MEENA!! MEENA!!! JAMAL ya shiga ƙwalla mata, kira amma bata saurare shi ba. se da ya haɗa da gudu sannan ya samu ya sha gaban ta. "Tsaya kiji MEENA, wallahi ba budurwa ta bace matar sa ce ya faɗa ne dan ya haɗa mu rigima plsss ki yarda da ni kin san bazan miki ƙarya ba" "MATAR SA" MEENA ta mai maita dai-dai lokacin su SUHAIL suka ƙarasa inda suke, JAMAL se hararar shi yake, Shi kuwa SUHAIL nunawa yayi kamar be san me yake yi ba ɓan garan mahaifiyar SUHAIL suka yi inda suka iske kafata nin mutan gidan hatta da memarta ba yana gurin guri suka samu suka zauna bayan an gama gaisawa memar taba yayi gyaran, murya ya fara magana kamar haka. "to da farko dai zan gaya muku wata muhimmiyar magana gameda wannan yarinyar yaefaɗa tarada nuna MANAL wadda tunda suka shigo mutanan dake cikin ɗakin suke bin ta da kallon mamaki ya cika su kowa da abinda yake saƙawa a ransa jira kawai suke sarki ya gama magana su tambayi wace ce ita. ME MARTABA yaci gaba da cewa "ina fatan xaku bani haɗin kai kamar kullum se dai wannan maganar ina so ku ɗauke ta a matsayin ƙaddara da kuma ikon Allah kuyi imani da Allah ku sani kuma buku wuce Allah ya jarabe ku da kowaca irin ƙaddara ba dan haka kuyi haƙuri. ” sai ya nim fasa sannan yaci gaba da cewa "wannan yarinya da kuke gani ƴar aboki na ce kuma kun san shi wato ALAJI SA'AD ME DALA "ehh ƙwarai ranka ya daɗe mun san shi " Allahu akbar ai ranka ya daɗe naji ance ya jima da rasuwa" cewar uwar gida KILISHI. "ƙwarai da gaske ya rasu kuma wannan yarinya ita kaɗai Allah ya bashi se kuma ɗan uwansa nan sarki ya kwashe dik abinda ya faru bayan rasuwar mahaifin MANAL har xuwa lokacin da ya nemi ya ɗaura mata aure da wani ƙarshe auran ya juya kan SUHAIL. ya ɗora da cewa “dan haka yanxu wannan yarinyar MATAR SUHAIL ce se dai idan ita ce tace bata son shi wannan kam batzan mata dole ba" Gaba ɗaya ɗakin babu wanda beyi kuka ba saboda tausayin MANAL a gaskiya ba kowa bane ze iya jure wannan uƙubar ba "Allah ya temaki sarki mu bamu da ta cewa dik hukun cin da ka yanke yayi mudai muna musu fatan alakari gaba ɗayan su su kuma wa'in can Allah ya shirye su yasa su gane gaskiya" cewar gwaggo wato babar MEENA. gaba ɗaya suma sauran suka amsa mai da haka "masha Allah alhamdullih Allah ya kara haɗa kanku koda bayan raina ku zamo tsin tsya ɗaya ma ɗauri ɗaya dan haka nan da ƴan kwana ki za'ayi taron bikin a bata sadakin ta tunda dama an ɗaura aure sadaki ne be bayar ba sannan bana so kowa yaji wannan maganar abar ta iya nan ni, zanji da komai Allah ya shige mana gaba" gaba ɗaya suka amsa da Amin. "To MANAL ga baban nin ki, nan duk abinda kike so ki tambaye su nan gidan ku ne ki yi komai kanki tsaye India be saɓa faɗar Allah ba duk Kuma wanda kika ga ze miki ba dai-dai ba to kizo ki gaya min in ɗau mataki kinji ko"? ''insha Allahu ranka ya daɗe nima kuma zaka same ni ame yi muku biyayya har ƙarshen rayuwa ta Na gode sosai Allah ya ƙara maka lafiya'' suka amsa da ameen ameen. "Ni dai ranka ya daɗe ina so a bani ita danna kula da ita'' cewar Gwaggo. Murmushi, me martaba yayi yace. ''an baki ita uwar yara na san zaki kula da ita dan bani da shakku akan ki,''. ''godiya nake ranka ya daɗe Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana'' ''Shike nan nima na samu abokiyar fira kuma a ɗaki na zamu ringa kwana'' cewar MEENA tana dariyar farin ciki, Harara SUHAIL ya banka mata dan haka tayi tsit ne san me martaba yana kallon sa ba seji yayi yace ''sannu baba na da wannan kallon da kake mata me tayi maka? dan kawai tace zasu kwana guri guda shi ne kake hararar ta wato kai me mata ko'' da sauri SUHAIL da JAMAL suka fice daga farlon suna dariya. To rayuwar MANAL a cikin gidan sarauta ta zama tamkar ƴar gold kowa ririta ta yake babu wanda ya taɓa yi mata koda kallon banza duk inda take so zata shiga ko tayi abinda take so duk inda kaga MEENA to zaka ga MANAL sun zama tamkar ƴan biyu. yau da daddare bayan sallar isha MANAL ce kwance akan gado tana danna waya kiran SUHAIL ya shigo ta ɗauka tara da karawa akunnan ta tayi sallama amsawa yayi ciki ciki ya ɗora da cewa ''wato MANAL dana ce kizo shine kika ƙi zuwa se kace zan cinye ki ko, shikenan Nagode'' ɗifff ya katse kiran da kallo tabi wayar ita ma ta san bata kyauta ba jikin ta ne yayi sanyi ace tun daga yanzu ta fara ɓatawa mijin ta rai amma ai ba lefinta bane gwaggo ce ta hana ta zuwa sakkowa tayi daga kan gadon ta ɗaura hijab akan rigar baccin da take jikin ta, ta ƙofar baya tabi dan kar Gwaggo ta ganta tana zuwa masu gadin shi suka bata hanya ta shiga bata same shi a farlo ba dan haka ta wuce cikin ɗakin kwance ta same shi ya ƙurawa silin ido yana kallo kamar me naza rin wani abu ''YAYA gani'' ko kallan inda take be yi ba bare tasa ran xe bata amsa. Zama tayi abakin gadon ta kamo hannin sa ta haɗa da nata tace ''plsss YAYA SUHAIL dan Allah kayi haƙuri wallahi Gwaggo ce ta hanani zuwa yanzu ma bata san na fito ba. Zaga yawa tayi inda ya maida fuskar sa ta marai rai ce tana bashi haƙuri ''yanzu kina nufin ban isa ince kiyi abu kiyi na san kinyi karatun addini kin san hukuncin macen da bata bin Umar nin mijinta amma shine har kike gayamin cewa wai Gwaggo ce ta hanaki zuwa kenan ita take auran ki ?'' "a'ah amma naga ita uwace a guri na idan nayi haka ba-zata ji daɗi ba seta ga kamar dan ba ita ta haife ni ba shi yasa banji maganar ta amma kayi haƙuri'' hannun ta ya kuma riƙe wa yace ''ya na iya tunda ina son ki'' bata san sanda tace ''nima ina sonka''. da sauri ta rufe fuskantar da tafin hannun ta dariya yayi yace ''me kika ce ɗan mai mai ta banji ba'' baki ta turo gaba, kana tace ''wallahi kaji kawai dai kana so na kuma faɗa ne'' ''eh naji amma sekin kuma mai mai tawa'' Ina son ka Ina son ka YAYA SUHAIL har Cikin, zuciya ta tun randa ka dawo daga na ganka naji zuciya ta ta Amin ta da kai,'' '' da gaske MANAL kina so na amma naji daɗi sosai da kema kina ƙauna ta atina nina ni kaɗai nake sonki'' murmushi ta sakar masa wanda ya bayyanar da farin ciki, hancin ta yaja yace ''yanxu ki koma kar Gwaggo ta gane ba kya nan'' miƙe wa tayi ya raka ta har bakin ƙofar yana jin wani son ta na Kuma shigar sa , tana komawa ta ta tarar da MEENA tayi shirin kwanciya ga waya akunnan ta da alama waya take yi itama kwanciyar tayi MEENA ce ta juyo ta kalle ta se wani murmushi take ita kaɗai ''Anty MANAL ina kika je tun ɗazu nake neman ki yanzu kuma kin shigo kina ta murmushi ko dai gurin yaya SUHAIL kika je ?'' harara ta jefa wa MEENA tace ''idan ma gurin sa naje ina ruwan ki naga miji na ne''''' ''iyeeeeeee lallai kema kin zama irin yaya SUHAIL yanzu babu kunya kike cewa mijin ki ne nifa ƙanwar mijin kice tamkar suruka nake awajan ki'' duka MANAL ta kaiwa MEENA ta goce tana mata dariya, kwanciya ta yi tana cewa zaki gane kuran ki.” WASHE GARI ya kama juma'a aranar ne aka kawo lefan MANAL wanda daga ƙasar India aka siyo su zo kuga kaya kamar an buɗe kantin kwari aka kira MANAL tazo taga kayan lefan ta kuka MANAL ta saka wannan kayan ko iyayan ta ne iya kacin abinda su suyi mata ke nan da kyar aka samu tayi shiru se godiya take musu. SARKI yasa aka kirawo ta yayi mata nasiha Sannan yace kar ta kuma yimai godiya in kuwa tayi yasan bata ɗauke shi a matsayin mahaifin ta ba sannan yace idan akwai abinda be mata ba ta faɗa A canza mata Kuma ta zaɓi kalar kayan ɗakin data ke so seta gayawa su Gwaggo Asiya mata ya danƙa mata sadakin ta Wanda bata san iya adadin su ba sannan ga mulkin mota ɗaya SUHAIL ne ya bata ɗaya kuma shi ya bata sannan Kilishi ita ma ta bata Sai kuma Gwaggo wacce ta zama babar amarya MANAL ita kuma ta bata kyautar GIDA dan ƙarere. Yau ne ya kama asabar kuma yau ne ran da aka shirya taron bikin, kowa mamaki yake a ina SUAHAIL ya samo matar aure A'lna ma aka ɗaura auran? dik iyakar me gulma an kasa gane kan zaran duk wanda ya tambayi me martaba se yace ƴar ɗan uwan sa ce daga haka kowa yaja bakin sa ya zuge . Biki yayi biki, bikin da ya haɗa manya manyan sarakuna da ƴan siyasa da masu kuɗi kaɗe kaɗe da bushe-bushe kawai ke tashi faɗar kyan da MANAL tayi ɓata lokacine tayi kyau iya kayu ga alkyabba da akasa mata ta fito a matar a saki seta juye ta zama jinin sarauta daloli aka ringa watsawa kai kace shara ce ko takardu ne Se yamma likisss biki ya tashi wajan ƙarfe tara na dare aka raka amarya ɗakin ta wato ɓan garan SUHAIL ƙarfe sha ɗaya abokan ango suka rako shi bayan anyi siyan baki aka ɗora da nasiha Sannan akayi addu'a kowa ya kama gaban sa aka bar amarya da ango sallah sukayi bayan sun idar ya kama goshin ta yayi mata addu'a sannan yayi mata wasu ƴan tambayoyi Game da addinin ta, ta kuma bashi amsa yanda ya kamata kajin da ya shigo dasu ya ɗakko sukaci suka kora da madara kamar kowa na angon da aka kai mai amarya ɗakin sa kuma suke raya sunnar ma aiki (s.a.w) haka suma daran ya kasance a gare su sun nunawa juna kulawa sosai SUHAIL kuwa ya godewa Allah daya mallaka mai MANAL a matsayin mata kuma ya same ta abudurwa. WASHE GARI da safe kamar yanda al-adar masarautar take farin ƙyallan da aka basu aka fito dashi kowa ya gani wannan shine shedar MANAL ta kawo budur cinta gidan miji ''MANAL MANAL MANAAL ki tashi mana gari fa ya waye ki tashi kiyi sallah'' SUHAIL ya faɗa yana yaye bargon data lulluɓa da shi shashsheƙar kukan ta yaji, dafe kansa yayi kana yace '' me kuma aka yi miki MANAL? na ce bazan ƙara ba kiyi haƙuri mana ki tashi kiyi sallah lokaci na ƙurewa '' ''bazan iya tashi ba yaya SUHAIL don Allah ka kiramin Gwaggo wayoo Allah na zan mutu'' se ta fashe da kuka me ɗaga hankali gaba ɗaya tabi ta ruɗa SUHAIL shima ji yake kamar yayi kukan fita yayi cikin hanzari ya nufi sashin Gwaggo kamar an wurgo shi Gwaggo kizo dan Allah MANAL ce bata da lafiya se kuka take kuma ke take kira hankali tashe, Gwaggo tabi bayan shi yanda yabar ta haka suka zo suka sameta se yanzu hankalin Gwaggo ya kwanta dan ita atuna nin ta MANAL ɗin bata lafiya ne ashe ciwon da kowace mace take ji ranr daran ta na farko dan haka Gwaggo tace ya fita ya basu guri da kyar ya fita bayan fitar sa Gwaggo ta shiga bayi ta cika baf ɗin ruwan zafi Sannan tace ta shiga ƙara ta saka tana yarfe hannu ahaka har seda ta sauya mata sau uku sannan ta haɗa mata me tirarakan jiki tawshiga bayan ta gama mata wannan tasa aka kawo mata madara ta haɗa mata da wani magani wanda ze sassauta mata zafin da takeji tace ta kwanta ta huta bayan fitar Gwaggo SUHAIL ya shigo kan gadon ya hau tara da kamo hannun ta yana kallon fuskan ta ''sannu ko ya jikin naki'' tashi tayi zaune ta ɗora kanta a, kafaɗar sa ''da sauƙi'' shafa kanta yayi gamida ''to Allah ya ƙara sauƙi dana san haka zata faru da ban zo inda kike ba ji nake kamar ban kyauta ba” Cikin shagwaɓa tace. ''habaaa yaya SUHAIL kai ɗin fa miji na ne kuma Allah shiya halasta yin hakan tome zesa kace haka wannan ai ba abun damuwa bane kuma haka kowace mace take tsintar kanta ran daranta na farko idan har ta riƙe Mutun cinta ni dai ina alfahari da kai kai ɗin jarumi ne ta ko ina'' ta faɗa tarada rungume shi shima rungume ta yayi nan suka lula duniyar masoya. MMN HIBBA✍️ RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba_ GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE 23/24 GIDAN ALHAJI BUKAR. Tin bayan barin MANAL daga gidan suka buɗe, sabon shafin rayuwa sun manta da wata MANAL karan su suke ci babu babbaka kuɗi kuwa kamar yayi mosu suke yi an samu dukiyar marainiyar Allah anata ci, NABILA ce ta fito daga cikin gidan tara da wani mutum babba kuma baƙiƙƙirin yake kamar gawayi amma me kuɗi ne na gasken gaske idan ba kuɗi ba babu abinda ze sa NABILA ta bashi fuska wajan da yayi fakin ɗin motar sa suka, nufa wata jib gegiyar mota cd mai numfashi ita kanta NABILA bata taɓa ganin Irin ta ba. Cikin kwar kwasa da yauƙi gami da yin fari da ido tace'' yanzu beby se yaushe zaka dawo kasan bana son kayi nesa dani ji nake kamar bani da lafiya'' ta ƙarasa faɗa cikin shagwaɓa. ''haba swet ki kwantar da hankalin ki, mana sati biyu fa kawai zanyi sannan inna dawo za'ayi maganar auren mu, danna gaji da zama babu aure ''to Shi kenan seka dawo ɗin pls ka kula min da kanka kaji beby'' mota ya shiga ya ɗakko wata ƴar ƙaramar akwati ya miƙa mata yace ''ga wannan kiyi mane ji dasu kafin na dawo'' karɓa tayi ta sunkuyo kanta dai-dai kuma tunsa tayi mai kisss wani jaɓarrrrr yayi a motar yana lumshe ido, wai shi yaji daɗi ''shi yasa nake so ayi maza-maza a bani ke dan kin haɗa komai da nake buƙata ta fannin ƴa mace'' dariya tayi mai shi kuma ya tada motar ya fita suna ɗagawa juna hannu. ''mommy mommy zo kuga Abin arziƙin'' da sauri mommy ta fito tana cewa ''kar dai kice harya tafi Allah yasa dai ya baki kuɗi masu yawa'' ta faɗa sa'ilin data zauna akan kujera buɗe akwatin tayi sega kuɗi fal akwatin kuma ba nera bace daloli ne jikin mommy har rawa yake, saboda murna bandir ɗaya ta dauka tana wul wulasu kana tace ''NABILA yanzu ne kika samu mijin da ya kamata ki aura dama wannan ranar nake jira kuma gashi tazo dan haka ki ce mai ya turo da maga batansa kawai ayi magana babu ruwan mu da koshi waye mu dai kuɗi k muke so kinga se a haɗa dana ZAINAB a yi mun huta dukiyar mu zata kuma haɓaka kina auran me kuɗi ita ma ZAINAB tana auren me kuɗi kai Allah Nagode maka, ƴaƴa na masu farin jini ga ƙashin arziƙi''' hhhhhh suka sa dariya NABILA tace '' mommy shi ma seda yayi min maganar yanzu yace shi baya so aja lokaci'' to mu meya ruwan mu ko yanzu ya fito bashi ke, zamuyi India da wannan ai bamu da matsala ta faɗa tana karkaɗa bandir ɗin dalolin dake hannun ta. Daddare ALAJI BUKAR ya dawo Bayan ya gama cin abinci mommy ta kawo mai kuɗin da saurayin NABILA ya bata ta ɗora da faɗin "kuma yace inya dawo ze aiko da manyan sa ayi maganar bikin su ," washe baki Dady yayi yana ɗaga kuɗin yace '' ko yau yace a ɗau musu aure da ita ai bashi ita zanyi me za mu, tsaya jira muga samu muga rashi" '' nima haka nace kaga faɗuwa tazo dai-dai da zama se ahaɗa dana ZAINAB'' cewar mommy. jin jina, kai Dady yayi alamar gamsuwa da maganar ta, "kaga tunda wannan shegiyar yarinya ta bar gidanna muke, ta samun alkari dama na gaya maka kasan yanda kayi da ita idan ba haka ba wallahi muda ci-gaba se dai muga ana yi yanzu gashi duk yaran mu, sun samu mazajan aure masu kuɗi na kere sa'a''. taɓe baki ALHAJI BUKAR ya yi kana yace ''ni fa wallahi na manta da wannan ƴar iskar yarinyar kuma banaso a dinga tuna min da ita taje can ta ƙaraci Iskan cin ta,'' kamar yanda saurayin BABILA ya faɗa in ya dawo ze aiko iyayan sa hakance ta kasance suka zo akayi magana saboda tsabar idon su ya rufe basu tsaya binciken ko shi waye ba, daga ina yake suwaye iyayansa. sati biyu aka saka Kuma yace karsuyi komai na kayan ɗaki shi zeyi NABILA kawai yake so akawo masa ko tsinke kar akawo ta dashi murna da farin ciki suka mamaye su, ita ma ZAINAB haka nata saurayin yace shi ze mata komai su ZAINAB da NABILA se gyaran jiki akeyi inka gansu kamar ka sace su, dan kyau tun ranar Laraba aka fara biki kuma duk fita akeyi tunda aka fara bikin ba'a liƙa nera ba Daloli kawai ake amfani dasu mommy kuwa se fan kama take cikin ƙawayan ta tana homa yaran ta sunyi dacen mazaje masu kuɗi se bisha sha akeyi da kuɗi kamar ba'a so Raƙuma da shanu aka yanka na girkin biki Banda naman kaji wanda akakai aikin su wajan masu girkin abincin biki ko suna Yau Lahadi kuma yaune aka ɗaurawa su ZAINAB aure akan sadaki masu tsoka NABILA akan sadaki million hamsin ZAINAB kuma million tala tin bayan ɗaurin aure duk wanda ze tafi se anbashi jaka wanda aka manna hotan amare da angwaye ajiki kayan ƙwalma da ma kulashe ne aciki se kuma tsabar kuɗi nera duba ashirin haka aka ringa rabawa duk wanda suka halarci bikin maza da mata shaɗaya na dare angwaye suka turo moto cin ɗaukar amare domin kai su gida jansu dik cikin motocin babu motar ƙasa da million ashirin se walainiya suke da ɗaukar ido haka akasa kowacce amota domin kaisu gidan jansu... MASARAUTAR ZAKI A ɓan garan amarya MANAL soyayya kawai suke sha ita da mijin ta SUHAIL gaba ɗaya ta miƙa masa kanta se yanda yayi da ita kulawa da soyayya kawai suka sani basu san wani abuba waishi ɓacin rai. MANAL ce a kicin tana ƙoƙarin ɗora grlirki SUHAIL ne ya shigo kicin ɗin bayan ta ya zagaya ya ruƙo kugun ta ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yace ''ni gaskiya ina buƙatar mata ta a kusa dani plsss ki ajiye wannan girkin kiji dani'' ya faɗa yana turo hannunsa cikin rigar ta. Juyowa tayi suka fuskanci juna tace ''wallahi kafiya ta kura fa baka barina na huta ko kaɗan tunda garin Allah ya waye kake abu ɗaya kaƙi bari in ɗora mana abinci rana ko sokake ka maida ni, fanko ne''? ta ƙarasa maganar tana jan hancinsa taɓe baki yayi kamar ƙaramin yaro yace. '' koma me zaki ce se dai kice Ni na san ba daga ni bane daga ke ne ke ɗin ta musamman ce'' hannu ya kai ya kashe gass ɗin data kunna batai aune ba taji yayi sama da ita wutsil-wutsil ta soma yi ''da Allah ka sauke ni babu inda zani mutum se kace doki kai baka gajiya da abu ɗaya'' be ajiye ta ko ina ba se kan gado hararar wasa ta sakar mai shi kuwa dariya ya mai da mata. a haka ya soma sarrafa ta har samu gamsuwa kwanciya ta yi ajikin sa tana ta zuba mai shagwaɓa shi kuma yana aikin rarrashi har suka yi wanka MANAL bata dena kuka ba daya gaji se cewa yayi ''wallahi in biki yi min shiru ba sena ƙara'' wata uwar harara ta banka masa tace ''aikuwa da ni da kai har abada kona gudu wajan Gwaggo'' ta faɗa tana murgu ɗa ɗan ƙaramin bakin ta, hannu ya kawo xye buge bakin ta goce tana turo baki shi ''wallahi yau se nayi maganin bakin nan mara kunya sena hukunta shi ya faɗa tarada miƙewa yana binta da gudu, MANAL tayi farlo aikuwa ya biyo ta suka ringa zagaye ɗakin ganin da gaske so yake ya kamata seta fita waje tayi sashin KILISHI wato mahaifiyar sa, shima kuwa ya bita duk inda sukai se an bisu da kallo kowa yana sha'awar su, wasu ma dariya sukeyi wai yau SUHAIL ne yake gudu yana bin matar sa ?.kamar anjefo ta ta faɗa dakin bayan ANNAH ta ɓuya se haki take '' a'ah MANAL Lafiya kike wannan uban gudu haka ke dawa ?" Kafin MANAL tayi magana SUHAIL ya shigo ɗakin shima yana haki, ''wayyoooooo Allah ANNAH kiyi mai magana don Allah karya duke ni,'' se ta ƙanƙame ANNAH. yarinya gwara ma ki fito dan babu abinda ze hanani dukan ki ba dai junin ki rashin kunya ba to daga yau baza ki kuma murguɗa wa kowa wannan bakin ba'' ya faɗa yana ƙoƙarin zagayawa bayan ANNAH ''kai SUHAIL kafita idona na rufe kai Yanzu ko kunya bakaji ba ka biyo ta kuka keto gidannan kuna gudu to naga ka taɓa ta ɗin'' ''haba ANNAH ya zaki goyi da bayan ta bacin itace bata da gaskiya'' ya faɗa kamar xeyi kuka ita kuwa MANAL se xuro kai take tana masa gwalo. tsaki yayi sannan ya fita yana gun guni bayan fitarsa ANNAH ta dubi MANAL kana tace '' Idan kika kuma tsokano shi bazan hana shi dukan ki, ba dan SUHAIL baya kunyar dukan ki ze yi ba, shi kamar ƙaramin yaro haka yake'' baki MANAL ta turo gaba tace ''ni wallahi babu abinda nayi mai kawai dai muguntar sa, ce ta motsa'' na dai gaya miki dan haka fito min daga baya duk kinbi kin yamutsa min kaya. MANAL bata bi takan ANNAH ba ta ɗauki furar data gani kusa da ita tasha nono se ƙamshi take nan MANAL ta gyra zama ta fara antawa Cikin ta tana yi tana lumshe ido, ''hummmmmm wannan yarinya da fi'ili kike naga ca kika yi baki shan fura yanzu kuma me ya haɗa ki,da ita har kike zalama haka?'' "uhum uhum ''nima ban san ya aka yi ba naji ina son sha kuma in ban sha ba ba zan iya sukuni ba'' taɓe baki ANNAH tayi tace ''kya ji da shi uwar tsugudidi'' To, rayuwar MANAL acikin gidan mijin ta rayuwa ce me tsaf ta gaskiya da ruƙon amana duk abinda take so se an mata tayi kyau tayi ɓul-ɓul da ita tayi ƙiba tayi fari fatar nan kamar ta jarirai SUHAIL na iya ƙoƙarin sa Wajan faranta mata yanda ya kamata. Cikin dare MANAL zazzaɓi me zafi ya rufe ta wanda dama tun jiya yake nuƙur ƙasar ta daurewa kawai take yi can Kuma ta ringa kyalaya amai hankalin SUAHAIL ya tashi kan kace me har ta gala ɓaita bata ma san wanda yake kanta gashi duk ta ɓata ɗakin da amai SUAHAIL ya rasa ya zeyi fita yayi harya doshi ɗkin Gwaggo seya tuna yau itace da girki ɗakin ANNAH ya shiga ya tarar tana bacci tashin ta yayi ya gaya mata abinda yake faruwa tara suka taho suka tarar da MANAL kwance kamar gawa bata ko motsi ''innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn MANAL MANAL me ya sameki dan Allah ki tashi karki tafi kibar ni wallahi bazan iya rayuwa da wata mace ba idan ba ke ba'' cewar SUHAIL yana share ƙwalla ruwa ANNAH ta ɗakko a firixa ta juye mata shi ajikin ta, ajiyar zuciya, tayi wata robar ruwan ta ɗakko ta miƙawa SUHAIL tace "ungo wannan idan kaga tayi irin haka ka zuba mata ni zan koma na ɗakko ta kalmi se mutafi asibiti'' karɓar robar ruwan yayi ita kuma ta fita ƙura mata ido yayi baya ko ɗif tawa gani yake idan ya ɗauke idonsa ze iya rasa MANAL ɗin sa, Kafin ANNAH ta dawo ai harya cicciɓo MANAL a bakin ƙofa suka ci karo kawai se ta juya suka shiga mota da kanshi yake tuƙin ga masu gadinsa na biye dasu awata motar Lokaci-lokaci ya kan waigo yaga yana yin jikinta sosai yake gudu kafin su isa ya kira JAMAL awaya kuma akayi Sa'a yau aikin dare JAMAL yake yi suna zuwa aka kaita Emergency aka fara bata agajin gaggawa dirip a kasa mata domin ta jigata sosai gashi tayi amai yafi a'irga wajan rabin awa JAMAL da sauran Dr. cin suke kanta bayan gwaje-gwaje da akayi aka tabbatar da MANAL tana ɗauke da juna biyu na tsahon sati huɗu wanda hakan yayi dai-dai cikar satin bikin su huɗu a ranar da aka kaita tasamu Cikin. Bayan sun gama komai kuma har ta dawo hayya cinta suka fito inda suka tarar da ANNAH da SUAHAIL a inda aka ta nada cikin hanzari SUAHAIL ya nufo inda JAMAL yake itama ANNAH ta biyo bayan shi dan san sanin awana hali MANAL take ciki '' JAMAL me ya ke damun ta? ina fatan dai yanzu ta dawo hayya cinta?'' cewar SUHAIL yana kallon JAMAL dan jin mexe ce ''ka kwantar da hankali ka, SUAHAIL babu abinda yasa meta kuma taji sauƙi sosai yanzu ANNAH ki shiga ki zauna agurin ta kai, kuma ka biyo ni Office zamu yi magana ɗakin ANNAH ta shiga su, kuma suka tafi Office ''zauna mana SUHAIL muyi magana seka ce wanda ake min tsini'' ''kaga JAMAL ba zama bane ya kawo ni ka gaya min abinda yake damun mata ta'' dariya JAMAL yayi, kana yace ''idan kuma naƙi faɗa maka fa me zaka yi kaga SUHAIL in zaka zauna muyi magana ka zauna dan wallahi bazan gaya maka ba kana tsaye se kace wanda ya haɗiyi muciya'' tsaki SUHAIL yayi sannan ya zauna shi kuwa JAMAL zama ya gyra kana yace ''albishirin ka, ''goro'' ya bashi amsa ata kai ce. JAMAL ya kuma cewa ''fari ko jah'' wayyo Allah SUHAIL ji yayi kamar ya rufe JAMAL da duka amma ya daure dan yasan halin JAMAL idan zasu shekara to seya amsa masa tambayoyi Sannan ze gaya mai abinda ke damun MANAL dan haka yace ''fari kal-kal'' murmushi JAMAL ya kuma yi kana yace ''MANAL ɗinka tana da juna biyu'' kamar wani dolo haka SUAHAIL ya ringa bin Jamal da kallo bakin sa har rawa yake wajan faɗin ''da da dan Allah JAMAL da gaske kake MANAL na da ciki'' ''ƙwarai ma kuwa SUHAIL matar ka nada juna biyu na tsahon sati huɗu ina taya ka, murna aboki na Allah yara bata da shi lafiya'' SUHAIL sauka yayi Daga kan kujerar da yake ya kai goshin sa , ƙasa yanawa Allah godiya sannan ya tashi ko sallama be yiwa JAMAL ba ya fita ɗakin da aka kwantar da MANAL ya shiga lokacin tana zaune tana shan furar da ANNAH tasa aka kawo mata sabida bata son komai idab ba fura ba. tunda ya shigo ya kafe ta da ido baya ko ƙif tawa ƙarasawa yayi ya zauna akan gadon yana kallon furar data kesha kanta ya shafa kana, yace ''beby na ina godiya agare ki, da irin wannan kyautar da ki ka min naji daɗin haɗuwa dake seya shafa fuskar ta zuwa wuyanta. Ture hannun sa tayi, ta nuna namai inda ANNAH take tana sallar asubah. ANNAH na idarwa take tambayar SUHAIL me yake damun. MANAL sosa kai, yayi yace ''dama ba Wani abu bane yake damun ta ba illah ƙaruwar da muka samu MANAL na da ciki'' ya faɗa tara da saurin barin ɗakin saboda kunya dama kuma beyi sallar asubah ba. itama MANAL ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige don kunya furar data ke, sha ta ajiye ta koma ta kwanta tana mai jin kunyar ANNAH ita kuwa ANNAH ko a jikinta , se godiya da tayiwa Allah dama tana so taga ƴaƴan SUAHAIL se gashi Allah ya amsa mata. Gari na waye.wa asibitin ya cika da muta ne hatta dasu LUBABATU da ZAINABA sunxo kowa se nan nan yake da MANAL, se azahar aka sallame su suka dawo gida nan fa aka ɗora daga inda aka tsaya kowa burin sa ya faran tawa MANAL sarki da kansa yazo yayi mata ya jiki kai MANAL taga gata iya gata ko wasshhh, tace se an tambaye ta inane yake mata ciwo ko Akwai abinda ta ke so, Se dare SUHAIL ya shigo ya same ta Ita da MEENA suna fira gaisawa sukayi da MEENA ta tashi ta basu wuri zama yayi ya kamo hannunta yana kallon idon ta Sannan yace ''ya jikin naki ina fata dai kinci abinci?'' ''eh naci sosai ma kaima kaci ko''? ta faɗa tarada shigewa jikinsa, ''hannu yasa ya ɗaga ƴar yo loluwar rigar baccin data saka yana shafa cikin ta yace '' in dai mata ta da beby na sunci bani da matsala domin sune farin ciki na'' hannu tasa ta saƙalo wuyansa tace '' indai baka ci abinci ba to muma baxa mu iya ciba kai ɗin katanga ne agare mu taya kake tunanin in baka da wal-wala muma zamuyi" ira Iran wa'inna kalaman suka ringa wa junan su ɗaukar ta yayi suka shige beed room.... Nima dai nace Bara inyi ta kaina domin wannan kalaman soyayya da suke, zayya nowa juna haka kamar ba gobe MMN HIBBA CE. RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER✍️ SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN MMN HIBBA 07073193332 SADAUKARWA NA SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH) AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA. 25 -26 Tin da aka ɗauki amare a motocin da angwaye suka turo domin kai su gidan su, na aure ana cikin tafiya duka motocin da mijin NABILA ya turo suka lalace A hanya gashi kuma babu mutane sosai agurin dan haka yace Bara ya turo wasu motocin a mai da su gida idan yaso ' daga baya sa zo suga gidan hakan kuwa akayi aka kawo wasu motocin aka juya dasu shi kuma ya ɗauki matar sa , awata mota suka tafi seda aka wuce wani ƙungurmin daji sannan akazo gidan shi kaɗai ne agurin babu gida ko ɗaya agurin tunda NABILA take bata taɓa ganin gida me kyan wannan ba kai amma Allah ya kashe ya ba ni irin wannan gida haka se kace wanda aka gina da zinare malam ko ina se walainiya yake ta faɗi hakan cikin ranta, koda suka shiga gidan se taga ashe ɓangare biyu ne ko wanne dana sa kalar fentin wanda yafi tsaruwa suka shiga faɗar dukiyar da aka kashe wa gidan ɓata baki ne kai kace aƙasar waje kake idan ba fitowa kayi ba ba zaka taɓa cewa a Najeriya kake ba, sallah sukayi Sannan ya baje mata nama kala-kala na kaji da na rago da na shanu har da na Raƙumi bayan sun gama yaja ta suka shige ɗaki tun ƙarfe sha biyu na dare ALAJI yake abu ɗaya har seda aka kira sallar asuba sannan ya saurarawa NABILA ta jigata ba kaɗan ba tunda take yawan barikin ta bata taɓa haɗuwa da namiji irin Alhaji daze kwana yana gurzar ta abin mamaki shine tunda tazo gidan sau ɗaya taga yayi Sallah idan tace beyi Sallah ba se yace yayi awaje kafin ya shigo, a haka har aka shafe wata biyu idan aka kai amarya ɗakin miji ƙiba take yi tayi kyau amma banda NABILA Gashi dai zata ci me kyau tasha me kyau ta kwanta ame kyau kai hatta da aikin gidan ba tayi saboda Akwai ƴan aiki agidan amma hakan be sa NABILA ta samu kwanciyar hankali ba saboda jaraba irin ta Alhaji kullum cikin abu ɗaya yake baya taɓa barin ta ta huta wani zubin ma yana gama saduwa da ita idan yaje ya dawo ze kuma komawa ruwa tun abun baya damun ta har ya soma damun ta ga ramar da tayi dik ta koɗe se wasu iyayan ƙasusuwa da sukayi mata sarƙa awuya watan ta biyu agidan tasa mu ciki nan fa abun ya kuma rin caɓe mata gashi ya amshe mata duk wayoyin ta bare ta kirawo wani nata ta gaya mai halinda take ciki, ita ba abokin fira gare ta ba, su, kansu masu aikin gidan basa wani yin doguwar fira da ita, saboda Alhaji yaja musu kunne gashi Allah ya haɗa ta da ciki me laulayi na masifa amma duk da haka ALAJI baya raga mata ka ida ne idan ya fara se asuba kuma yana gama wa ze fice daga gidan bashi ze dawo ba se magrib ta ƙwanja me ta bushe ta. tayi baƙi ta Lalace kamar ƙwaran gwal se uban ciki daya yo mata gaba kamar ba NABILA ba yau dai NABILA ta shirya tsaf domin zagaye ko ina na gidan sannu a hankali take tafiya har takai ɗaya ɓan garan shiga tayi cikin farlon shi ma dai kamar wancan yake har ma ya fishi tsaruwa zama tayi a ɗaya daga cikin farlon tana hutawa ta kai kusan awa biyu a ɗakin sannan ta tashi zata tafi magan ganun mutane ta juyo ƙasa ƙasa Dama da akwai mutane Acikin gidan nan to amma ai alaji yace min babu kowa aciki mu kaɗai ne ta faɗi hakan cikin ranta tsintar kanta tayi da son shiga ɗakin dan taga suwaye. Innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn, abinda kunnan ta ya jiye mata ne yasa tayi suman tsaye dama ALAJI ɗan mafiya ne?'' tayiwa kanta tambayar da bata dame bata amsar ta. ''yawwa Gali zuwa yanzu na san cikin matar ka, ya kai wata biyar kuma kasan alƙawarin da aka yiwa dodo idan kayi aure matar ka, ta samu ciki zaka bashi jinin matar da kuma abinda ke cikin ta dan haka lokaci yayi da zaka yi hakan gobe ka kawo mana ita dan DODO yana ƙishiruwar jinin su," buɗar bakin ALAJI se cewa yayi "angama ya. shugaba na ai, dama na gaya maka zan kawo wa DODO Kalar jinin daya ke so shi yasa da naga wannan yarinyar na kuma sa akayi min bincike akan iyayan ta se faɗuwa tazo dai-dai da zama naji labarin suna da san kuɗi se na siye su da kuɗi banza ye wawaye ko bin ciken asalina basu yi ba suka bani auran kai in taƙai ce maka ko sunan basu sani ba, dama ni,ba sonta nake ba na auro tane kawai danna bawa DODO jinin ta Ni kuma na samu dukiya na zarce kowa'' ALAJI ya faɗa cikin ƙwarin guywa da karsashi. Sulalewa NABILA tayi a ƙasa ta ɗora hannu aka zata fasa ihu ta tuna idan tai zasu ji ta dan haka ta toshe bakin ta tana rizgar kuka jin motsin za'a fito yasa tayi saurin barin sashin ta koma nata sashin hankali tashe shi kenan ta mutu ta lalace yanzu bata da wani maceci se Allah gashi babu wanda ya taɓa zuwa inda take, agefe guda kuma ALAJI duk sati seya aika da kayan abinci gidan su NABILA da kuɗaɗe masu tarin yawa Sannan yace NABILA tana gaishe su, in suka samu lokaci zasu zo shi da ita basu samu zama bane saboda suna xuwa ƙasashe yawan cin amae ci, hakan yasa su mommy suka Kuma sakewa da shi se yai kiran su awaya su gaisa busu tambayi NABILA ba a cewar su, me zata musu tunda Allah ya bata miji me kuɗi tana can tana wadaƙa da dukiya suma kuma suna samun rabon su , da haka sha-shan iyayan nata suka sha shance basu ko damu da kiran ta awaya ba, su dai a basu kuɗi kawai, Allah ka tema keni ka fidda ni daga wannan gidan'' cewar NABILA wadda ta miƙa lamurran ta ga Allah, kullum kaga NABILA da unab hijab yanzu sallolin nan biyar basa wuce ta saɓa nin da dase ta share wata da watanni ba tayi ba gashi a kwa nan nan ALAJI ya ƙara matsa mata ta fanni saduwa har yanzu bata faɗa mai ta san ko shi waye ba, Ranar Laraba da misalin karfe Uku na yamma ALAJI ya shigo yasa Meta a zaune ba tarada ya kalle taba yace ''zoki raka ni wancan sashin nawa yau acan nake son kwana kema kina ta ƙorafi baki taɓa shiga cikinsa ba to yau Allah ya nufa seki shirya mu tafi yanzu'' cikin NABILA ne ya bada wani ƙuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu, ƙirjin ta ya shiga duka tara-tara nan da nan jikin ta ya hau rawa kamar ana kaɗa mata gangi hawaye share-share a fuskan '' dan Allah ALAJI kayi min rai kada ka kai ni wajan dodon tsafin ku wallahi ni yanzu kuɗi basa gaba na, na roƙe ka da kabar ni da raina'' ta faɗa cikin shashshekar kuka, "hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh, ALAJI ya bushe da wata wula ƙantacciyar dariya lokaci guda kuma ya maida fuskarsa tamakar ta shanu yace ''ashe ma kin riga da kin san inda zan kai ki , to babu damuwa base nayi miki jagora ba ki wuce muje kawai kuma ki sani kome zaki yi se dai kiyi amma babu fashi sena samu abinda nake so na yiwa dodo alƙawarin bashi ke, da Kuma abinda ke cikin cikin ki, sha-sha kawai, hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh seya kuma fashewa da wata kafirar dariya tunda nake ban taɓa ganin mahaukatan iyaye Irin naki ba, basu san ko ni waye ba suka ɗauke ki, suka bani Saboda kuɗi ya rufe musu ido ki tashi muje ko kuma Ni, na kaiki da kaina nan da sati ɗaya za'a bawa DODO jinin ku, ke da abin da ke cikin ki,'' tashin hankali wanda ba'a samai rana kuka NABILA take tana bashi haƙuri amma ina, wata tsawa da ya daka mata seda abinda ke cikin cikin ta ya juya, da hannu yayi mata nuni da ƙofar bata da zaɓin da yawuce tayi abinda ya Umar ce ta, hankali NABILA be kuma tashi ba seda ta ganta acikin ɗakin matsafa babban ɗaki ne gari guda yara ƙananu da ƴan mata da datti jawa ta gani wasu an musu aski wasu kuma ba'a musu ba sannan kowanne an rubuta mai lamba a jikinsa ƙara ta saka lokacin da idan ta yasauka akan sassan jikin mutanan da aka yanka anyi musu gunduwa gunduwa kuma babu alamar ɗigon jini ko ɗaya agurin kenan an bawa DODO jinin su ya shanye? kenan nima haka za'a bada nawa jinin ta faɗi hakan cikin ranta wasu yara ta gani su biyu daga ganinsu kasan daga makaranta aka ɗakko su saboda yunufom ɗin da yake jikinsu, ''shugaba gata nan na kawo ta Ni, na gama nawa dan yanxu ma haka tafiya zanyi ƙasar Amurika naje na huta ina fatan za'a kulamin da komai'' wanda aka kira da shugaba yace '' karka damu kaje duk inda zaka DODO ze baka kariya adik inda kake'' mai da kallan sa yayi kan NABILA yace ''to NABILA na gode ƙwarai da gaske da irin gudummawar da kika bani wajan ganin na kawowa DODO ke dan haka Allah ya haɗa mu, acan'' daga haka yasa kai ya bar ɗakin hannu ta ɗora a kai ta runtuma îhu tana birgima a ƙasa tun NABILA na kuka har ta dena ta dake kwa nan ta biyu acikin ɗakin a kazo aka ɗauki wata mata shiyar budurwa aka shiga da ita ɗakin da DODON yake dariyar su, suka jiyo alamun dado ya shanye jinin yarinyar kawai se gani sukai an jawo gawarta an warɓar aƙasa wani basa muden mutum yazo da wata wuƙa me mugun kaifi da tsini ya kwakule idon ta da ƙirjin ta da kuma gaban ta sannan ya fita wani ma ya shigo shi da tasa wuƙar har da roba ya cire kan ta da ƙafafunta da kuma hannayan ta shima ya tafi wani ma ya kuma shigowa shima dai kamar sauran da tashi wauƙar ya zauna ya gididdiba sauran sassan jikin ta gaba ɗaya se kace naman kaji yaxu ba a robar ya tafi can kuma suka jiyo wani gur-nani ashe dodan ne yake yin haka dik lokacin da aka ba shi jinin mutum in dai yayi masa to seyayi wannan gurnanin hakan ya nuna yayi farin ciki kuma buƙata zata biya. *Bara kuma mu wai waya gidan ZAINAB muji ita kuma awana hali take* ABUJA GARIN GWAMNA Tunda aka kai ZAINAB gidan bata taɓa jin daɗin zaman gidan ba ashe ƙarya itama saurayin nata ya shirga mata yanada mata har da ƴaƴa zagada zagada kuma matar tashi mugun kishi gare ta dik macan daya aura itace ajali ta gata da bin bokaye ko aure yayi seta gama wahalar dake sannan tasa bokan ta ya miki asiri ki kasa guduwa daga gidan dan haka ya tura su, London wai suje suhuta dan baya son matar tasa tasan yayi aure bugu da ƙari ashe ba ZAINAB kaɗai ya aura ba asabar aka daura mai Aure da wata mai suna KHADIJAH washe gari lahadi aka ɗaura mai da ZAINAB mata biyu a lokaci guda itama waccan ɗin budurwa ce kamar ZAINAB ɗin, a daran da aka kai ta aka fara tar zoma domin kuwa ce mata yayi tsohuwar matar sa ce da ya saka ya dawo da ita KHADIJAH tana ji tana gani ya shirga mata ƙarya itama taci kukan ta ta ƙoshi, ZAINAB kuwa kwana tayi kuka tana ya cuce ta amma da yake namiji ɗan duniya ne seya lallaɓa ta ya samu abinda yake so awurin ta satinsu biyu agidan Uwar gidansya ta dawo ita da ƴaƴan ta nan fa aka shiga ɗauki ba daɗi ita dai KHADIJAH duk abinda suka ce da ita shi take yi shi yasa basa takura mata saɓanin ZAINAB data lashi ta kobin babu macan da zata yiwa biyayya hakan yasa HAULE da yaran ta suka sako ZAINAB a gaba wahalar yau da ban ta gobe da ban kwatsam ZAINAB ta samu ciki HAULE ta ƙra sako ta, a gaba har da cin alawashin seta salwantar da cikin, rayuwa tayiwa ZAINAB zafi gashi ba wata kulawa take samu agurin mijin nata ba raban data ganshi har ta manta watannin sedai ta jiyo Muryar sa, shida matarsa da ƴaƴan sa, zaune take ta rasa abinda yake mata daɗi gashi cikin jikin ta ya dame ta motsi ji tayi an banko ƙofar ɗakin anshigo SUHAIMA ce ta tsaya kanta tace "ZAINAB tashi ki dafa min in domi yanxu ita nake sonci Sannan kiyi sauri karki ɓata min rai kuma karki samin attaruhu da yawa bana so tayi yaji saffa saffa nake so tayi'' shiru ZAINAB tayi ƙwalla na gan garowa daga idon ta Aranta tace ''yanxu wannan ƴar ficiciyar yarinyar ce take sani aiki kuma cikin gadara da izzah. maganar suhaima ce ta katse mata zan can xucin data keyi ta hanyar faɗin ''wai keeeeee ZAINAB ba Magana nake miki ba kikayi banza dani ko kina nufin ba zaki yi abinda nasa ki ba ?" ta faɗa cikin tsawa da ɗaga murya, cikin kuka ZAINAB tace '' dan Allah SUHAIMA kiyi min afuwa wallahi bazan iyayin girki yanxu ba marata ciwo take yi'' ahayeeeeeeeeeeeeeeeeeeee Nana ye to wallahi bari kiji ba ciwan mara ba ko haihuwa zakiyi se kinyi abinda nace'' ''SUHAIMA bazan iya ..'' bata ƙarasa abinda take son faɗa ba SUHAIMA ta wanke fuskarta da wasu lafiyayyun maruka hagu da dama se ganinta da jinta suka ɗauke na wuccin gadi SUHAIMA bata tsaya anan ba ta haye ruwan cikin ta ta ringa kai wa cikin bugu ta ko ina tun ZAINAB na kuka da Neman agaji har ta dena saboda azaba se da SUHAIMA tai mata dukan. fitar hayyaci Sannan ta ɗaga ta tarada barin ɗakin babu wanda ya kuma bi ta kanta bare ya temaka mata SUHAIMA na fita daga ɗakin ta gayawa mahaifiyar ta duk abinda ya faru tace tayi dai-dai gwara da tayi mata haka. Cikin axababban ciwo ZAINAB ta far faɗo daga doguwar suman da tayi cikin ta wanda ya de na motsi ta taɓa taji yana nan a zaton ta babu cikin ajikin ta gaba ɗaya jikin ya kumbura kamar wadda tasha sha kafashe ga jini da yake zuba kamar anbuɗe famfo da kyar ta samu jinin ya tsaya tun daga wannan rana ZAINAB ta shiga taka tsan tsan da dik abinda ta san zesa jikin ta yayi tsami ita kuɗi kawai take so ta samu ta gudu idan ba bata bar gidan ba to sedai a tarar da gwar ta, ga cikin ta Da yayi mata nauyi, ba ko da yaushe yake motsawa ba se yafi kwana da kwanaki be motsa ba ga yinwa da taci ta cinye ta gaba ɗaya ta zama tamkar mahaukaciya ko wanka ba tayi idan ta doso ka kai kace mushe ne. Ita kuwa Khadijah tabi Allah tabi ma aiki tabi HAULE da yaranta se abinda suke so, take yi shi yasa ita bata shan wuya kamar ZAINAB, yau ZAINAB ta tashi da naƙuda ta kai awa ɗaya tana abu ɗaya amma babu sauƙi se gurin Allah da kyar ta rarrafo daga ɗakin ta, ta shiga ɗakin HAULE a bakin ƙofar ɗakin ta dur ƙushe tana kallan su cikin fitar hayyaci tace MUKUTAR ANTY ku temaka min mutuwa zanyi dan Allah kukai ni wajan iyaye na kar na mutu ban gansu ba'' ta faɗa cikin azaba da raɗaɗin naƙuda wannan ne karo na farko da MUKUTAR yaji ze iya tema kawa ZAINAB duk da yana tsoran HAULE amma dole ya ajiye komai agefe ya temaka mata idan ya so daga baya kome ze faru ya faru miƙewa yayi da nufin zuwa inda ZAINAB take adur yaji HAULE ta daka mai wata uwar tsawa ba shiri ya koma ya zauna jikin sa na ɓari , tashi tayi ta ƙarasa inda ZAINAB take tasa hannu ta ɗauke ta da mari ta finciko ta, ta kaiwa cikin ta naushi tasa hannu ta kama gaban rigar ta, ta yaga nan jikin ZAINAB ya bayyana a fili yaran kuwa suka ɗauki shewa suna cewa ''se Mommy wallahi kinyi dai-dai'' cikin bala'i da masifa HAULE tace '' dama na gaya miki duk randa kika kuma shigo min ɗaki sena keta miki mutunci banza ƴar masu son Abin duniya wato ke, kina tina ƙaho kin auri me kuɗi zaki zo ki bararraje ko ai kin ga bararraje wa '' ta ƙarasa faɗa tara da hanka ɗata ta faɗi wata razananniyar ƙara tasaki se kuma ɗif alamar ta suma koma ta mutu se jini daya yanke mata kan kace me jinin ya mamaye gurin da gudu MUKUTAR yayi kanta yana kiran sunan ta amma ina bata ko motsawa be saurari tsawar da HAULE take daka mai ba ya ɗauke ta yasa amota se asibiti. Suna isa aka ɗora ta akan gadon marasa lafiya Emergency aka nufa da ita ana bata te makon gaggawa Dr sunyi iya yinsu wajan ganin jinin da yake zuba ya tsaya amma abin ya citura dole tasa aka nemi MUKUTAR yasa hannu domin ayi mata oforeshen nan da nan aka shiga da ita ɗakin tiya ta awa ɗaya da rabi, aka kammala tiya tar sedai ɗan bezo da raiba bayan angama komai aka bawa MUKUTAR gawar ɗan domin yaje ya binne ita kuma suka yi mata allurar bacci sedai inta farka suga yana yin jikin nata, MUKUTAR yayi kuka sosai daya ga ɗan da ZAINAB ta haifa se dai bezo da rai ba tunda ake mai haihuwa be taɓa yiwa ɗa soyayyar da yake yiwa ɗan da ZAINAB ta haifa mai ba ZAINAB ta far faɗo likitoci suka yi mata ƴan gwaje gwaje don a tabbatar da ta samu lafiya sedai ana dubawa aka gano ta gamu da lalurar yoyan fitsari wannan dalili yasa ZAINAB ƙara shiga wata damuwar seya zamana tama dena Magana se dai ta kalleka kawai kwanan ta biyar a asibiti aka sallame ta suka dawo gida ta ci gaba da fuskantar ƙalubalen data saba, babu me raga mata ga yoyan fitsari da ya kuma yin gaba idan ta zauna aguri ta tashi kai kace ruwa kofi ɗaya aka zuba agurin Ranar wata Alhamis HAULE da yaran ta suka fita supar makeet don yin siyayya har da KHADIJAH suka tafi ZAINAB kaɗai aka bari ta shiga tunanin ta yanda zata gudu can ta tuna da wata da Bara ɗakin HAULE ta shiga ta hau bincike lokar mudubi ta janyo idonta yayi tozali da kuɗaɗe masu tarin yawa ɗiba tayi ta mai da lokar cikin sauri ta fito daga ɗakin ta koma nata ɗakin Hijab da takalmi tasaka ta fito sauri take kamar zata kifa tayi Sa'a me gadi baya nan tayi wufff ta fice ɗan sahu ta hau tace ya kaita tashar da ake hawa motar Kano** minti goma ya kai su tasha tayi Sa'a motar Kano ta cika saura gurin mutum ɗaya ta shiga me mota yaja suka ɗau hanya se a sannan ZAINAB ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tarada fashewa da kuka me tsuma zuciya ƙarfe shida na yamma suka iso Kano ɗan sahu ta hau ya kawo ta har ƙofar gida su, kuɗi ta bawa me ɗan sahun bata jira ya bata canji ba ta kwasa da gudu tana zuwa ta ringa dukan gettt ɗin gidan da iya ƙarfin ta me gadi ne yazo yaga waye wannan me bugun tashin Hankali yana buɗewa ZAINAB ta faɗo gidan har tana bangaje me gadi da gudu shima RABE me gadi ya rufa mata baya yana faɗin ''jama'a ku temaka mana mahaukaciya ta shigo gidan nan jama'a ku kawo ɗauki wallahi mahaukaciya ce'' Turusss ZAINAB taja ta tsaya lokacin data shiga cikin farlon se kuma ta sulale ƙasa sumammiya dai-dai Lokacin RABE me gadi ya shigo Mommy ce ta sakko daga saman bene cikin shiga ta Alfarma ''wai kai RABE ihun me kake mana ne haka ka san bana son wannan halin naka , idan kayi wasa yanxu xan kore daga gidan nan'' ' kiyi haƙuri hajiya ina zaune naji ana bugun ƙofar shine na buɗe ƙaramar dan naga waye ina buɗewa naga wannan mahaukaciyar kafin nayi yin ƙurin rufe ƙofar ta bangaje ni ta shigo'' ya faɗa tarada nuna inda ZAINAB take kwance da sauri Mommy tayi baya dan ta tsorata cikin faɗa tace '' da halla malam fitar min ita daga gida ko sokake tamin illah?" ''kiyi haƙuri Hajiya zan fitar da ita'' ya faɗa tarada kama hannun ZAINAB a yin ƙurin sa na ganin ya fitar da ita, dai-dai lokacin ZAINAB ta far faɗo daga suman data yi fizge hannun ta tayi ta mike tana zazzare ido kamar mahaukaciya sabon kamu waige waige ta soma yi idan ta ne ya sauka akan mommy wacca tabi ta tsure bata ɓata lokaci wajan yin gurin mommy da gudu ta ƙanƙame ta tana kuka mommy kuwa saboda tsoro saura kaɗan tayi fitsari awando tana cewa ''RABE ka temaka min kafitar da wannan mahaukaciyar kar ta yimin rauni cakkk ZAINAB ta saki Mommy bakin ta na rawa tace "mo mo mo mommy biki gane ni ba ta faɗa cikin Muryar kuka '' inna lillahi wa inna ilaihi raji'un ZAINABBBBBBB kece meya same ki, hatsari kuka yi ina mijin naki yake '' gaba ɗaya ta jera mata wa in nan tambayoyin alokaci guda kuma cikin tashin hankali, girgiza kai ZAINAB tayi tace '' kaico mommy kaico da auren MUKUTAR kaico da auaran me kuɗi Mommy naga rayuwa kuma na san meye rayuwa yanxu haƙiƙa Allah baya bacci kuma tun a duniya yake sakayya. Sai ta nisa ta cigaba da cewa ''mommy abu ɗaya zangaya miki yanxu cewa na gamu da lalurar yoyan fitsari'' innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn '' mommy ta faɗa cikin firgici ZAINAB kuwa kuka ta cigaba dayi kamar ranta ze fita, itama mommy kuka ta saka kana tace '' ZAINAB har yanzu biki gaya min abinda ya faru ba bayan kaiki gidan mijin ki, da akayi'' ajiyar zuciya ZAINAB ta sauke tace '' Mommy MUKUTAR ya cuce ni ashe dama yanada mata har da ƴaƴa baya ga haka bani kaɗai ya aura ba mu biyu, ya aura nan ZAINAB ta zayyanewa mommy duk abinda ya faru da irin wahalar da tasha dama cikin data samu, kuka mommy take yi wuy-wuy tana tsinewa MUKUTAR tarada cin alawashin se tayi Shari'a dashi, '' ZAINAB kije kiyi wanka ki cire kayan da suke jikin ki, se kici abinci'' to ''mommy'' ZAINAB ta faɗa tara da miƙewa ta shiga tsohon ɗakin ta, wanka tayo taci abinci ta dawo farlo ta tarar da mommy azaune a inda ta barta zama tayi suna ɗan taɓa fira jefi jefi wanda mafi yawancin firar tasu akan wahalar da ZAINAB ta sha ne. Cikin tashin hankali ALAJI BUKAR ya shigo farlon kamar wanda aka wurgo shi sabida labarin da RABE me gadi ya kwararo mai ''ZAINAB da gaske kece kika dawo haka?" Dady ya faɗa lokacin daya shigo farlon da gudu ZAINAB taje ta rungume mahaifin nata tana kuka tace ''nice nice dady kaga yanda rayuwa ta mai da ni ko?,'' '' ki kwantar da hankalin ki, ZAINAB wallahi in dai ina raye sena sa anyiwa MUKUTAR abinda bexe kuma yiwa wata ya mace ba ze san ya taɓa ƴar gidan ALAJI BUKAR'' ''a'ah Dady ka rabu da shi na barshi da Allah'' shi kenan ZAINAB tunda kin haƙura amma wallahi da sena saka a raba shi da ransa, ƙarasa shiga cikin farlon yayi suka zauna '' ZAINAB tace '' wai Dady ina NABILA na san zuwa yanzu ta haihu ?" Dariya Dady yayi yace '' ai ZAINAB ina gaya miki NABILA tayi dace da miji wallahi tunda ya aure ta yake mana alheri banda kayan abinci har kuɗi seya aiko mana kwana biyu ma beyi kira na ba ko Lafiya'' ya faɗa tara da zaro wayar sa daga cikin ajjihu ya danna lambar mijin NABILA sedai me a kashe ake ce masa mayar da wayar yayi yace ''ƙila wayar tasa ba caji bari zuwa anjima sena sake gwada wa, NABILA. har anyi mata aski an rubuta mata lambar randa za'a bawa DODO jinin ta, duk yawan cin mutanen data gani acikin dakin matsafan duk a yanka su, se kuma sababbi da aka kawo suma anyi musu aski rana ɗaya za'a bada su NABILA dai tariga da ta sallama jira take randa za'a bawa DODO jinin ta tazo kawai abada ta ta huta yanxu duniyar bata gaban ta addu'a kawai take yi sallah kuwa babu damar yi ana i, gobe za'a bawa DODO su NABILA suka dena jin motsin mutanen da suke gadin su, hakan ya tabbatar da Sun tafi wani gurin wata mata ce tace '' alhamdullih Allah ya kuɓutar da mu, dan haka ku tashi mu tafi gaba ɗayan su suka miƙe kowa yana addu'ar da duk tazo bakin sa, fitowa sukayi waje dan neman hanyar da zasu gudu amma babu hanaya wata doguwar kanta ga ce me uba tsayi nan kowa ya tsaya babu wata alama da zata nuna cewa akwai hanya agurin can suka ga katangar gidan ta tsage gaba ɗayan su suka haɗa baki wajan faɗin alhamdulillah nan fa suka bawa kafafun su amanar ƙasa gudu sukeyi aciki dokar dajin da basu san kowana daji bane sun share kusan awa ɗaya suna tiƙar gudun ceton rai sannan suka zo bakin titi gaba ɗayan su suka zube atiti suna haki NABILA kuwa kamar zata shiɗe da kyar take iya fuzgo numfashin ta ...... MUJE XUWA FANS RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba. GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE SADAUKARWA NA SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH) AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA. 27/28 sun jima axube abakin titin Sannan Allah ya kawo wani me tirela tin kanya ƙaraso suke ɗaga mai hannu tsaya wa yayi suka ce dan Allah ya temaka musu daga gurin ƴan mafiya suka kuɓuto ai wannan direba yana jin haka yace suyi sauri su,shiga kar su biyo su nan suka soma rigegen shiga wannan na bangaje wannan sunci uwar tafiya me nisan gaske sannan suka shigo garin Kano kai tsaye ofishin ƴan sanda ya kai su yayi musu baya nin komai. Wasu daga cikin su, sun gane gidan su , wasu kuma basu gane ba ciki har da BABILA data dena yin magana se dai tayi nuni da hannun ta ga uban ciki da yayo gaba kamar ya fito waje gidan rediyo dana talabijin aka kai su tara da ɗaukar hotunan su, ko Allah zesa adace. Ranar asabar daddare su, Dady da da mommy da ZAINAB wacce ta fara dawowa cikin hayya cin ta suna zaune a falo fira suke cikin kwanciyar hankali Dady yace ''wallahi har yanzu Ban sami number mijin NABILA ba gashi mu, babu wanda yasan gidan bare muji ko lafiya suke, ƴar dariya Mommy tayi kana tace '' wallahi ALAJI kana bani mamaki, meye wani abun damuwa ka sani ko sun tafi yawon cin amarci kama dena damun kanka, ina da yaƙinin babu abinda ze sameta ai ita Allah ya kashe ya bata ka duba kaga yanda yake ɗawai niya damu ba kamar mitsiya cin nan ba mijin ZAINAB ba'' ''kuma fa haka ne wannan ba abin damuwa bane ina musu fatan su, dawo lpy mu,kuma a cigaba da bamu dukiya'' ya faɗa tarada miƙewa ya shige ɗakin sa dan dare yayi mommy ma tashi tayi tacewa ZAINAB seda safe'' to mommy Allah ya tashe mu lafiya nima yanxu zan tashi naga goma ta wuce'' ''okya'' to sekin taho itama mommy ta shige nata ɗakin labaran ƙarfe goma da akeyi ne suka ja hankalin ZAINAB ta maida hankali tana sauraro ''A yaune wani direban wata tirela ya haɗu da wasu bayin Allah wanda ƴan Mafiya suka sace ciki harda ƙananan yara wasu daga cikin sun gane gida wasu kuma basu gane ba dan haka ake cigiyar iyayan su ko ƴan uwan su, nan aka fara hasko fuskokin su , ana tambayar su, suwaye iyayan su , ya sunan su , kowa ya bada amsa me gabatar wa ya cigaba da cewa ''wa innan sune mutanan da ake neman ƴan uwan su sedai ayanzu sun tabbatar da ba zasu iya gane gidajen suba, se aka hasko fuskar NABILA ''itama wannan ɗaya daga cikin wa'inda ƴan mafiyan suka ɗauka ne sedai ita bata iya magana amma ga dukkan alamu da Kuma bincike da mukayi cikin hikima ta faɗa mana sunan ta wato NABILA ABUBAKAR. wata gigitacciyar ƙara ZAINAB ta saki bakin ta na rawa wajan faɗin NABILAAAAA, dai-dai Lokacin Dady da mommy suka fito suna tambayar ta Lafiya da hannu ta nuna musu tivi ɗin sabida ta kasa yin magana a kuma lokacin ne aka ƙara hasko fuskar NABILA tarada faɗin sunan ta dana mahaifinta saura kaɗan Dady ya faɗi, saboda tashin hankali'' yace "me ya samu NABILA ina mijin nata? yake koma. Sun yanka mijin nata ita kuma ta tsira'' Mommy kuwa kuka tasa tana '' na shiga uku ni, BILKISU meke faruwa da ƴaƴa na,'' ZAINAB ma kukan takeyi tana astagafurillah Allah na tuba ka yafe min ashe itama NABILA batayi dace da miji ba? Ko kuma da gaske ƴan mafiya ne suka ɗauke su, ita da mijin nata'' ta yiwa kanta tambayar da bata dame bata amsar ta. Dady kuwa sambatu ya cigaba dayi yana faɗin se yaje ya amso ƴarsa yanxu ya faɗa tarada nufar ƙofar '' da sauri ZAINAB tasha gabansa tace'' kayi haƙuri Dady mubari se gobe tunda mun san inda take kaga yanzu sha ɗaya na dare idan ka fita ahaka akwai matsala gashi garin nan babu wani tsaro na roƙeka Dady ka bari seda safe semu tafi mu godewa Allah da yasa aka ganta''' da kyar ZAINAB ta shawo kan Dady ya haƙura. Ranar babu wanda ya runtsa acikin su, seka ce wa'inda akayiwa mutuwa washe gari da sassafe suka ɗun guma se Ofishin ƴan sanda nan sukayi bani sannan aka haɗa su da D.P.O kiran NABILA akayi dan a tabbatar da suɗin iyayan ta ne. tana ganin su ta fashe da kuka tana son yin magana sedai babu halin yi da hannu D.P.O ɗin ya tambaye ta iyayan tane. Kai ta ɗaga mai alamar eh, su, DADY suman tsaye suka yi lokacin da suka ga yanda NABILA ta zama wata tsohuwa ZAINAB ce tayi ƙarfin halin ƙarasawa inda NABILA take se yanzu NABILA taga ZAINAB Cikin firgici tayi mata alamar da ''ZAINAB kece meya same ki ,'' rungume ta ZAINAB tayi suka cigaba da rizgar kukan su, bayan Dady ya cike wasu takaddu aka basu NABILA kai tsaye asibiti suka nufa yace aduba mishi NABILA aga meya hanata magana inda suka tabbatar mai da babu komai kawai dai akwai abinda ta gani wanda ya ɗaga mata hankali dan haka addu'a kawai zasu yi mata nan bada jimawa ba zata dawo dai-dai gida suka juyo cikin damuwa da tashin hankali mara misal tuwa NABILA kuwa mamakin yanda aka gyara gidan su take dan haka ta tambayi ZAINAB ko Dady ya kuma yin kuɗi ne' ZAINAB tace mata a'ah '' mijin ki, ne yake turo musu da kuɗi da kayan abinci gidan ma shiya gyra shi Nan da nan ZAINAB taga NABILA ta ruɗe har tana neman fita daga hayyacin ta, '' NABILA meya sameki daga yi miki maganar mijin ki, seki shiga tashin hankali meke faruwa?'' Cikin kuka NABILA tayi alama data kira mata su, Dady n taje ta kira su , ''NABILA kinsa ankira mu, Kuma kinyi shiru ki gaya mana abinda yake damun ki'' cewar mommy hawaye ne ya kwaranyo daga idon ta tarada yi musu bayani cikin maganar kurame ta shiga basu labarin dik abinda ya faru da ita, '' innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn dukan su suka faɗa alokaci guda gami da dafe ƙirji '' NABILA dama wanda kika aura ɗan mafiya ne bamu sani ba?'' cewar Dady jikinsa na kyarma kai ta ɗaga mai alamar eh ''MOmmy dan firgici suma tayi nan sukayi kanta ZAINAB na kuka ta buɗe firij ta ɗakko ruwa me sanyi ta yayya famata ajiyar zuciya ta sauke, tana binsu da ido hawaye na bin fuskartar, ana cikin haka wayar Dady tayi ƙara cikin rashin ƙwarin jiki ya fito da wayar ganin sunan yaron sa ne wanda yake kulamai da shagunan sa, da runfunan sa, na kasuwa yayi saurin ɗagawa gami da karawa akunnan sa, daga ɗaya bangaran yaron nasa yace ''ALAJI se dai kayi HAƘURI gaba ɗaya shagunan ka, da runfuna sun ƙone babu abinda ya tsira nima yanzu naje danna buɗe shago naga ni wallahi ALAJI ba'a tsira da ko tsinke ba, kawai se gani sukai Dady ya faɗi kasa tummmm da gudu sukayi kansa suna kiran sunan shi se momy ma ta kuma sumewa ZAINAB ce ta fita da gudu tana ƙwallawa direba dame gadi kira, cikin farlon suka shiga ZAINAB tace su temaka musu sukai su, asibiti mota aka sasu suka tafi asibiti ana zuwa aka fara duba su, tashin hankali wanda ba'a samai rana likitoci sun tabbatar da DADY ya gamu da cutar ɓarin jiki '' munshga uku wai me ke faruwa damu ne? daga wannan se wan can'' cewar ZAINAB tana kuka. MASARAUTAR ZAKI Sannu a hankali ta fito daga banɗaki jikin ta ɗaure da towul da alama wanka tayi cikin ta ya turo gaba sosai dakyar take tafiya ji tayi anyi sama da ita ana juya ta ƙanƙame shi tayi dariya yayi yace matsoraciya kawai duka ta kaimai aƙirji tace ''eh naji ai tsoro halak ne'' murmushi ya kuma yi yace '' albishirinki'' ''goro fari ƙal-ƙal'' kumatun ta yaja harse da tayi ƙara yace '' ansaka ranar auran su, MEENA da JAMAL nan da sati ɗaya zamu sha biki'' ''cikn farin ciki tace '' dan Allah Beby da gaske kake karfa ka shirga ni dan na san halinna ka'' ta faɗa cikin shagwaɓa da turo baki, bakin ya matse yace ''har yanzu wannan bakin be dena halin sa ba ko?" kuma turo bakin tayi tare da shigewa jikin sa tace washhhhhAllah'' da sauri ya ɗago ta yace ''me nene inane yake miki ciwo'' ya faɗa cikin firgici ''turo baki tayi kana tace '' ba ba ba bebyn ka bane ya takura min ba, se da muna yake yi da motsi plssssssssssss kace ya dena dan Allah'' ta faɗa cikin kuka tana matso ƙwalla kai daga gani kasan kukan dole ake yi mai shikuwa SUHAIL ruɗewa yayi yana rarrashin ta har da cewa idan ta haihu ze goya ta da kyar dai ya samu tayi shiru zaunar da ita yayi akan lokar mudubi ya ɗauki mai yana shafa mata bayan ya gama ya shafa mata fauda tare da gyara mata gashin ta yasa mata ribom COVER ya buɗe ya ɗakko mata wata yar yololuwar rigar bacci wadda duk rabin ta nettt ne yasa mata sannan yaja ta zuwa farlo ya xuba mata abinci kaɗan taci tace ta ƙoshi dole ya ƙyale ta ya ɗauke ta zuwa bedroom suka kwanta. To Aɓan garan su DADY abin Ba'a cewa komai, komai ya rinca ɓe musu musamman Dady da yazama se ankwantar antayar babu. ɓarin jiki mommy itama gata nan dai yau da lafiya gobe ba lafiya NABILA ma haka ga ciki da yayo gaba har watannin haihuwar sa ya wuce dik ta rame kamar me sikila ZAINAB ce kawai me ɗan dama-dama Acikin su, Gaba ɗaya rayuwa ta juya musu baya dukiyar da suke taƙama da ita ta gudu ta barsu gidan da suke cike kawai yayi rage masu aikin gidan duk sun gudu saboda babu kuɗi mota ɗaya ce ta rage acikin gidan itama taji jiki da ita suke malan jawa suna zuwa asibiti da ita domin duba lafiyar DADY. MMN HIBBA. RAMIN MUGUNTA (Ka gina shi dai-dai da kai) WRITER SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MMN HIBBA) 07073193332 Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya. littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba GARGAƊI ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na. NA GODE MASARAUTAR ZAKI. Dik wanda ka kalli fuskar sa, kasan akwai farin ciki ga kaɗe-kaɗe da bushe bushe da suke tashi saboda yaune ake shagalin bikin ƴar auta MEENA bikin daya haɗa manya manyan sarakuna su MANAL sune matan yayye kuma sune ƙwayan amarya sune daga gaba-gaba sunyi kyau har sun gaji da haɗuwa gagarumar walima aka shirya SUHAIL abokin ango kuma yayan amarya kaya iri ɗaya suka saka da MANAL hatta da ta kalma iri ɗaya sedai ace nasa na maza ne ita kuma na mata duk inda MANAL ta gitta akan idon SUHAIL ji yake kamar yasa ta arigar sa, saboda kishi ita kuwa MANAL rabon abinci suka shiga yi ita da ƙawayan MEENA ko wana tebl se sun ajiye sannan suyi gaba MANAL ce ta ɗakko zata ajiye wa wani saurayi daya Hakim ce shi kaɗai yana ta faman daddana waya ajiyewa tayi ta juya dan ta ɗakko wani filet ɗin taji an daka mata tsawa juyowa tayi tana kallan sa ''ke wace iriyar jaka ce zaki zuba min abinci a jiki'' ashe maya fin MANAL ne ya janyo filet ɗin lokacin da tazo zata juya. ''dama ku ƴaƴan talakawan nan haka kuke daga an gayyato ku gurin biki seku zaƙalƙale ku ringa yiwa mutane hauka aguri'' mutumin ya faɗa kamar ze kaiwa MANAL duka, Dik abinda yake faruwa akan idon SUHAIL nan da nan idon sa ya kaɗa yayi jajur kamar garwashi kamar wanda aka mintsina ya tashi inda su, MANAL suke ya nufa yana xuwa beyi wata wata ba ya ɗauke gayan da mari jikake tauuuu kauuuuuu kamar ana dukan roba kwalr rigar sa ya kama yana wujijjiga gayan Muryar sa na rawa yace "matar tawa kake zagi kai wana irin kidahumi ne shin baka san darajar mace ba koba mace ce ta haifeka ba da har zaka kiramin mata jakaaaaaaa'' SUHAIL ya faɗa cikin ƙaraji hankalin mutanen gurin ya dawo kansu anyi anyi SUHAIL ya sake shi amma yaƙi dukan sa kawai yake sarki da kansa yazo amma ina SUHAIL yayi nisa baya jin kira jibagar sa, kawai yake kamar Allah ya aiko sa duk wanda yaxo da nufin ceton sa SUHAIL seya haɗa da shi nan akayi carko carko ganin abin bana ƙarau bane yasa MANAL kutsawa cikin mutanan da turtsetsan cikin ta tana zuwa ta riƙe SUHAIL cikin kuka tace "ya isa haka dan Allah na roƙeka kabar shi, haka in dai danni kake yi to naya fe masa, cakkk, SUHAIL ya tsaya da dukannasa ta kama hannunsa suka bar gurin tini gayan ya arce, ɓangaran su ta nufa riƙe da hannun SUHAIL wanda yake ta huci kamar kububuwa zaunar dashi tayi akan kujera ta buɗe firij ta ɗakko ruwa me sanyi ta xuba a Cup ta kafa mai abaki shanye wa yayi ta kuma ƙara mai sannan tasa mu guri ta zauna tarada kamo hannunsa tana jamai yatsun sa wanda take ja tasaki ta kama ɗayan shima ta jima tana mai har seda taga jijiyoyin sa sun saki sannan ta soma magana cikin sanyin murya tace '' Allah ya huci zuciyar yarima na, fatan dai ze manta da dik abinda ya faru'' ta faɗa tana shafa sajan sa, ɗauke kansa yayi alamar har yanzu be huce ba, '' haba nawan ni kaɗai har abada, Kisss ta manna mai agoshi To ance tsakanin mata da miji sai Allah cikin hikima da Bara MANAL ta shawo kan mijin nata ta hanyar gaya mai kalamai masu kwantar da hankali, daga haka ta miƙa masa kanta dan tasan shine abu, na biyu da yake ƙara kawantar wa, da SUHAIL hankali adik sanda ranshi ya ɓaci washe gari aká ɗaura auran MEENA da JAMAL akan sadaki mafi inganci daddare aka kai amarya gidan ta SUHAIL ne ya kai MANAL dan yace baya so, tasha wahala tunda ba ita kadai bace an kai amarya gidan ta me kyau da tsari Kowa ya kama gaban sa akabar amarya da ango, agajiye liƙisss MANAL ta kwanta salla ma, da kyar tayi ta bata tsaya jiran SUHAIL ba tayi kwanciyar ta ga zazzaɓi da ya rufe ta, cikin dare MANAL taji wani axababban ciwo wanda tunda take bata taɓa jin Irinshi ba, tun tana daurewa har ta, kasa cikin azabar ciwo ta tashi SUHAIL da yake ta rafsa baccin,sa fita yayi ya kira Gwaggo tana zuwa taga naƙuda MANAL take ba tara da ɓata lokaci suka tafi asibiti ɗakin haihuwa aka shiga da ita minti biyar Nos ta fito ta samu SUHAIL tace abasu kayan haihuwa su sun manta da wani Kayan haihuwa saboda ruɗewa dole se siya akai acikin asibitin minti biyu Nos ɗin ta sake fitowa ta kalli SUAHAIL tace ''ranka ya daɗe albashirin,ka'' cikin zaƙuwa SUHAIL yace ''goro'' yanda yayi maganar seda yasa Nos ɗin tayi dariya kana tace ''MADAM ta sauka lafiya kuma an samu 'yan biyu duka maza'' dan farin ciki SUAHAIL kasa yin magana yayi se motsa bakin sa yake goshin sa ya kai ƙasa yayi wa Allah godiya '' ''Alhamdullih Allah abin godiya SUHAIL ya zama uba cewar Gwaggo sosa kai SUHAIL yayi yana sunne kai wai kunya yake ji bayan an kai MANAL ɗakin hutu suka shiga ga gadanta gana yaran ta wanda aka naɗe su cikin kayan jarirai masu kyau da tsada tunda SUHAIL ya shigo idon sa na kan yaransa inya ɗauki wannan seya ajiye wannan ya kuma ɗaukar dayan har ya bawa MANAL haushi wato ba ta ita yake ba ta ƴaƴan sa yake nan ta cika tayi fammmm, ya kusa 30 minit yana kallon yaran sa, sannan yazo gurin MANAL maganar duniya yayiwa MANAL amma tayi burusss da shi, se cika take tana batsewa Ita dai Gwaggo tana kallan su bata ce ta tafas ba, bare a sauke ''kuka MANAL tasa mai tana cewa shi kenan yanxu ta san baya son ta ƴaƴan sa yake so, shi,kuwa SUHAIL dariya ma, ta bashi, nan dai ya lallaɓa ta suka rabu lafi, kangari ya waye SUHAIL ya ɗora photo yaran a MIDIA anyi masa haihuwa Kan kace me, ƴan uwa da abokanan arziƙi sun sani kankace kwabo ƴan barka sum a cika acibitin ba masaka tsinke ƙarfe goma na safe aka basu sallama sabida basu da wata matsala daga me jegon har yaran ta kai tsaye sashin Gwaggo aka kai MANAL dan akula da ita da kuma yaran ta, zo kuga yanda ake nannan da MANAL kai ba zaka taɓa cewa bata da iyaye ba, shima SUHAIL yana can gurin abokanan sa sunata yimai tsiya se dare ya samu shigowa cikin gidan ɓangaran su, ya nufa cike da ɗaukin sake ganin yaran sa amma me babu kowa fitowa yayi yanufi sashin Gwaggo dan yafi zaton tana can ilaikuwa ya sameta tana cin tuwan dawa miyar ɗanyar kuɓewa data sha manshanu da yajin daddawa wanda Gwaggo da ta,shiga kicin ta dafa mata shi . ƙarasa wa inda take yayi se faman Binta da kallo yake kamar ze cinye ta, huremai ido tayi ''kallon fa haka'' dariya yayi yace "gani nai kinyi kyau kuma kin manta dani tunda gashi har kina iya cin abinci batara dani ba, sunkuyar da kanta tayi kana tace ''kayi haƙuri nima dan babu yanda zanyi ne duk duniya na fiso na ganka kusa dani bana so, naga kayi nesa dani dan Allah kada kaga na haihu kace zaka min kishiya wallahi bazan iya sheres ɗin ka da wata na fiso ka zauna dani ni ɗaya takkkk kayimin wannan alƙawarin'' ta faɗa fuskar,ta cike da kishi'' shiru SUHAIL yayi yana mamakin dama MANAL nada irin wannan baƙin kishin haka? tambayar da bashi dame bashi amsar ta ''kayi shiru ko Kanada wata budurwa awaje baka gaya min ba?''' ta tambaye shi idonta fal hawaye da sauri SUHAIL ya girgiza kansa yace ''wallahi kiyar da dani tunda nake ban taɓa ssuraran wata ƴa mace ba hasali ma su, suke cewa suna sona,'' ajiyar zuciya MANAL tayi tace shi kenan na yarda da kai, danna san baza kamin ƙarya ba, dai-dai lokacin yaran suka tashi suna kuka da alama yinwa sukeji ɗakko su, yayi, ya bata HASSAN shi kuma yana jijjiga USAINI bayan tagama bawa Hassan ya miƙa mata usaini ya mutsa fuska tayi ''wallahi na gaji plssssssssssss ka siyo madara a dinga basu ta faɗa tana turo baki''' Kallan da SUHAIL ya bita da shi ne yasa ta karɓi Usaini tana bashi nono tana gama bashi ta miƙa masa ɗansa ta juya musu baya ya jima a zaune yana yiwa yaran addu'a ya kuma yi musu huɗu ba kwantar da su, yayi yasa hannu ya juyo da MANAL yana kallan cikin ƙwayar idon ta, '' ko bayan raina kika bawa yara na madara ba zan yafe miki ba saboda lafiyar ki ƙalau ki faɗi duk abinda kike so zanyi miki amma kada ki, kuskura ki bawa ƴaƴa na madara'' ya faɗa cikin faɗa da ɗaga murya idanun sa sunyi ja kamar garwashi fita yayi daga ɗakin zuciyar sa, na suya. tun daga nan SUHAIL ya dena shigowa ɗakin idan ma yaxo iya kacin sa farlo yace amiƙo masa yaran sa idan ya gama ganin su ya bada abinda ze bada ya tafi hakan ya ɗagawa MANAL hankali tana ji ze ringa waya da ƴan mata yana dariya kullum cikin kuka take ga kishin mijin ta da yake damun ta ga watsin da yayi da ita. Gida ne ginin jar ƙasa Irin na da ko albarkacin ƙofa babu se buhun siminti da akasa aka rufe gidan shima duk ya yayyage kana iya ganin wanda yake ciki Ahankali yake magana cikin sarƙewar numfashi yace '' kaico na ni, ABUBAKAR ban riƙe amanar yar ɗan uwana ba gashi yanzu nayi biyu babu ba dukiyar ba lafiya tari ne ya kamashi ya kusa minti 30 yana yi kafin ya lafa masa yaci gaba da cewa '' tabbasss Allah ba azzalumi bane tun aduniya yake hukunci base anje lahira ba BILKISU ZAINAB BABILA ya kira sunan,su. Suka amsa cikin kuka yace '' hakiƙa na kasan ce me son kaina a koda yaushe saɓa nin ɗan uwana da ba haka yake ba, baya taɓa nuna ban-banci duk abinda nake so yana min baya taɓa gajiwa dani amma bana duban haka wata rana naje gidan sa nace ya bani kuɗi zan yi jari yace to amma in yi haƙuri babu kuɗi agurin sa saboda shima yayi odar kaya amma nan da sati inzo in karɓa, alokacin na rufe ido na, nayi mai rashin mutunci wanda shima hakan ya fusata shi, har mukayi musayar yawu na dawo gida na gayawa mahaifiyar ku, itama ta zuga ni nan dai na kuma hawa dokin zuciya cikin daran na fita na haɗa kai da ƴan fashi na basu kuɗi nace su kashe ɗan uwana ALAJI SA'AD ME DALAH nace kar su kashe MANAL saboda idan ba ita bazan samu duka kadarorin dana keso ba Lokacin zuciya ta ƙeƙashe bana ganin komai, cikin dare kuwa ƴan fashin nan suka kashe shi, shi da matar sa wanda daga nan ne MANAL ta dawo gurina da Zama itama ba'aje ko ina ba na amshe dukiyar ta nasa agaba mukai taci ita kuma muka barta cikin wahala da azaba. Wannan shine babban zunubin dana ai kata wanda ban taɓa gayawa kowa ba, wanda na san alhakin ɗan uwana ne yake ta bibiya ta dani daku, babu kuɗi babu gidaje ba motoci ba shaguna komai ya ƙare munsiyar da komai abincin da zamuci ma gagarar mu, yake ƙarshe ga inda muka dawo gidan da bashi da maraba da titi wayyoooooooooo Allah na ina zanga MANAL na roƙe ta gafara ta yafe min ko naji sanyi ta wani ɓangaren na san tawa tazo ƙarshe ba lallai na tashi ba dan haka nake jan hankalin ku, da kuguji duniya domin babu komai Acikin ta se ɓata. NABILA wacce itama ta haihu sedai ɗan nakasashhe ne bashi da ƙafa gashi ita kuma ta gamu da cutar H.I.V wanda mijin da ta aura yasa mata har taci ƙarfin ta tace '' in sha Allahu DADY zamu nemo duk inda MANAL take mune mi, yafiyar ta dan mun azabtar da ita ga mugayan kalamai da muke faɗa akanta wanda kan mu, suka dawo'' ta faɗa cikin kuka me nuna tsantsar nadama Mommy da ZAINAB ma kukan suke "yanxu idan mukace zamu nemo MANAL ina zamu, bamu san inda take ba sannan bamu san gidan wanda aka aura mata ba cewar mommy gaskiya ne mommy amma Ni, aganina mu nemi, RABE me gadi ina ganin ze san gidan tunda shi ne wanda ya nemo mijin da aka aura mata cewar ZAINAB gaba ɗaya sukai na'am da zancanta. Kwana biyu suna neman Rabe wanda da kyar suka Ganshi suka taho dashi,. Shi kanshi RABE seda ya tausaya musu amma daya tuna rashin imanin da sukayi wa MANAL se yaga be Kama tama yaji tausayin su ba, Nan Dady ya kuma faɗawa RABE me gadi Irin aika aikar da yayiwa ɗan uwan sa ya ƙara da cewa ''Rabe ina roƙon ka, daka kai ni gurin MANAL na roƙi gafarar ta kona samu sauƙin ciwon dana keji a jiki na kai kaɗai kasan inda take shi yasa nasa aka nemo min kai kate maka RABE,'' DADY ya faɗa cikin sarƙewar tarin daya kamashi wanda har da jini seda ya lafa sannan Rabe yace '' gaskiya ALAJI bazan ɓoye maka ba wanda na kawo maka bashi MANAL ta aura'' ''wata aura?'' cewar mommy nan RABE ya kwashe duk yanda akayi gurin ɗaurin auren ya gaya musu yaci gaba da cewa ''yanxu haka shekaran jiya na sami labarin MANAL ta haihu kuma ƴan biyu zancan nan da nake muku MANAL matar ɗan Sarkin masarautar ZAKI ce, Gaba ɗaya ɗakin yayi tsittt kamar ruwa ya cinye su, '' DADY kuwa cewa yayi "alhamdullih Allah Nagode maka daka juya wannan lamari RABE na gode da baka aurawa MANAL wanda ka kawo ba ina fata zaka mana, jagora don muje mu nemi yafiyar MANAL” insha Allahu ALAJI duk sanda kuka shirya kuyi min magana zan kai ku Allah ya tsare gaba yasa mufi ƙarfin zuƙatan mu, suka amsa da Amin kowannan su, yana mamakin yadda akayi haka lallai ikon Allah da girma yake, MASARAUTAR ZAKI SUHAIL ne zaune a farlon Gwaggo yazo ganin yaran sa Bayan an kawo masa su, ya zauna yana ta ɗaukar su, a photo se zabga murmushi yake MANAL ce ta shigo farlon cikin shiga ta alfarma tayi kyau sosai sallama tayi ya amsa ciki-ciki dan har yanzu fushi yake da ita. Guri ta samu akan kujerar da yake kai ta zauna tara da yi mai sannu da zuwa banza yayi mata duk da haka bata haƙuri ba tace '' kayi haƙuri YAYA wallahi b...'' da sauri ya ɗaga mata hannu yace "ya isa haka MANAL bana son jin komai daga gare ki kin riga da kin nuna min koke wace ban taɓa tina nin zaki yiwa yara na wannan horon ba mena rage ki, da shi me kika nema kika rasa da har zaki ce ba zaki shayar da su ba shi kenan ai bake kaɗai ce mace aduniya ga mata nan birjik aduniya ko nawa nake so zan aura da har zan zauna ina kallo ki ringa yiwa ƴaƴana horan madara '' kuka MANAL ta saka mai har cikin ran sa yake jin kukan nata Amma ya maze dan baya so ko kaɗa nan gaba idan ta kuma haihuwa tace zata bawa ɗan sa madara dan haka yayi banza da ita taƙaraci kukan ta, miƙewa yayi ze tafi ta riƙe rigar sa cikin kuka tace '' saboda bani,da kowa shine kake min duk abinda ka gadama har kake iƙirarin zaka ƙara aure shi kenan SUHAIL ina so ka sani kafin na bar gidan ka seka bani yara na dan sba naka bane da abina ka ganni ko yanzu kace in tafi tafiya zanyi amma da yara na zan tafi" Jikin sa ne yayi sanyi da yaji ta amci bata da kowa se kuma ta basa dariya da tace yaran ta ne cikin son ya ƙular da ita yace '' bazan bayar da yaran ba duk inda zaki kije amma bada yara na ba sannan da kike cewa yaran ki, ai duk wanda yaga yaran nan yasan ƴaƴa na ne saboda kamar da muke yi dasu'' dan takai ci MANAL magana tayi Fuuuuuuuuuuuuu ta bar farlon ranta aɓace shi kuwa SUHAIL dariya yayi yace yarinya se rigimar tsiya wai kaji yaran ta Saboda tsabar rigima Irin Tata, ranar suna yara suka ci sunaye HASSAN akasamai sunan me martaba USAINI kuma akasamai sunan mahaifin MANAL wato SA'AD, anyi taron suna me jego da yaran ta suka samu kyautittika da dama har da wani abokin. SUHAIL daya biya mata kujerar maka idan tayi arba'in zata tafi. cikin ikon Allah MANAL tagama wanka yaran ta sunyi kyau sunyi ɓul-ɓul kamar ba haihuwar fari ba randa zata koma sashin su, Gwaggo tasa aka gyara ta da magun gunan mata ga Gara da akayi mata daddare aka rakata ɓangaran ta, washe gari da yamma me martaba yasa aka kira masa SUHAIL da MANAL basu ɓata lokaci ba suka je Gaban MANAL ne ya yanke faɗi lokacin da tayi tozali da su DADY wanda daga ganin sa kasan ba shi da lafiya sabida akwance yake, kasa zama tayi har seda me martaba yace ta zauna sannan ta zauna nasiha me ratsa zuciya SARKI yayi musu sannan yace '' MANAL duk abinda kika ga ya sami mutum to daga Allah ne dama ya riga da ya ƙadar maka haka tun kan kazo duniya na san baki manta da wa'innan mutanen ba to dan haka kiyi haƙuri kiya fe musu duk abinda suka miki saboda manzon Allah (s.a.w) yana son me yafiya'' '' Hakiƙa MANAL munzalin ce ki, ina me roƙon gafara agurin ki, da ki yafe min kona samu Salama a rayuwa ta haƙiƙa ban riƙe zumunci ba na biyewa duniya ina ganin kamar bazan mutuba se gashi tun aduniya Allah ya nuna min iya kata ki yafe min MANAL nina san tawa ta ƙare Allah baxe bar ni ba kodan Abinda nayiwa ɗan uwana Nana ya gaya musu cewa shine yasa aka kashe mahaifin MANAL innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn MANAL ta faɗa tarada miƙewa tsaye cikin kuka tace “ dad da da dama kai ne kasa aka kashe min Abba na momy na?'' ta faɗa cikin kuka se Kuma gani su kai ta sulale ƙasa sumammiya da sauri SUHAIL yayi kanta yana kiran sunan ta ruwa ya ɗakko ya fesa mata ajiyar zuciya tayi kuka take me tsuma zuciya rungume ta SUHAIL yayi ajikin sa yana rarrashin ta, '' bazan taɓa yafe maka ba tunda ka raba ni da iyaye na kuka saka rayuwa ta cikin wahala'' Mommy da ZAINAB da NABILA suka durƙusa gaban MANAL suna neman afuwar ta. ''kinga yanda na koma ko MANAL jibi yanda rayuwa ta juya min baya yanzu haka na kamu da cuta me karya garkuwar jiki ZAINAB Kuma ta gamu da yoyon fitsari mommy kuma Cutar farfaɗiya ce tasa Meta muna roƙon ki da ki yafe mana mun san da wuya ki manta da irin abubuwan da muka yi miki'' cewar NABILA tana kuka kamar ranta ze fita Allah sarki MANAL me zuciyar imani '' Shi kenan na yafe maku Allah ya yafe mana baki ɗaya yasa hakan ya zama IZINA ga yan baya''' gaba ɗaya suka amsa da ameen ZAINAB ce tace ''muna godiya MANAL kuma ina ƙara roƙon ki dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri ki yafe wa DADY'' share hawaye MANAL tayi kana tace '' na yafe masa seya nemi yafiya gurin Allah, Allah ya tsare gaba'' ''na na nagode sosai MANAL tabbasss ke jinin SA'AD ce na gode Allah yayi miki albarka dake da xuriyan ki, ya kare ku daga mugun ji mugun gani na gode ƙwarai da gaske'' cewar DADY yana kuka ga wani numfashi da yake fitarwa sama-sama me martaba yasa aka kaishi asibiti sannan ya basu abinci da kuɗi masu yawan gaske sannan yace idan wata matsalar ta taso suxo su gaya mai Godiya suka yi mai. Kwanan DADY biyu a asibiti Allah yayi mai rasuwa saka makon tarin daya ci ƙarfin sa wanda likitocin sukayi iya ƙoƙarinsu amma ina rai yayi halin sa . Lokacin da labari ya riski MANAL tayi kuka sosai koba komai shi ma ubane awajan ta rayuwa taci gaba da juyawa yau daɗi gobe akasin haka an samu ci gaba sannan kuma anyi rashe rashe ciki kuwa harda Mutuwar SARKI wato mahaifin SUHAIL mutuwar da tadaki kowa bayan arba'in aka naɗa SUHAIL amatsyin sarki, Wanda kowa yayi na'am da haka kwanciyar hankali ta wanzu ɓangaran su MEENA da JAMAL suma ba'a cewa komai dan kuwa itama MEENA ta haihu ƴa mace wadda taci sunan mahaifiyar JAMAL suna kiran ta da KAISAR NABILA ma tayi aure inda ta sami me irin cutar ta ta amince masa suna zaune cikin rufin asiri ZAINAB ma ta koma gidan tsohon mijin ta MUKUTAR wanda tun bayan tafiyar ZAINAB asirin da HAULE tayi mai ya karye ya danƙara mata saki suna zaman su cikin so da ƙauna ita da yaran HAULE wanda ta fita ta bari MOMMY kuma SUHAIL ya siya mata gida sannan lokaci-lokaci suna xuwa su gaishe ta, MIJIN NABILA da ta aura ƴan sanda sunyi nasarar danƙe su gaba ɗaya su Wanda dama tun lokacin da aka kaisu NABILA wajan su suka sa musu ido yana dirowa garin ƴan sanda sukayi ramm da shi. aka kuma ka masu Gaba ɗaya. BAYAN SHEKARA TAKWAS. Wasu kyawawan yara na hanga cikin wani ƙaya taccan farlon suna wasa wasu kuma suna karatu. wata mata ce ta fito cikin shiga ta alfarma gefanta kuyangu ne guda uku hannayen su riƙe da kwani ka, ɗaya kuma tana ɗauke da jariri da alama dai ɗan matar ne lokacin da suka ƙaraso seda na murza ido na danna ƙara tabbatarwa da gaske ne Abinda ido na yake gane min ko kuma gizo ne. Murzawa nayi da kyau na kuma buɗe su fesss akan. Matar da gaske ne MANAL ce agaba na ta zama big Madam komai nata ya sauya ta zama. Babbar mace. Gaba ɗaya yaran suka taso suna mata magana kowa da abinda yake cewa bata saurare su, har seda ta sallami Kunyan gun ta karɓi jaririn gaba ɗaya sun. Cika mata kunne tama rasa yanda zata yi dasu tsawa ta daka musu tsittt suka yi kamar ruwa yaci su '' haba gaba ɗaya kun dame Ni, dame zanji se kace ku kaɗai ne ƴaƴa wallahi duk wanda na sake jin bakin sa sena zane shi'' ta faɗa cikin zare musu ido, USAINI dake zaune kan kujera yana danna computer yace '' kema mommy idan da sabo yaci ace kin saba da hayaniyar wa'inna ɓerayan na ki'' '' ƙyale su, baba na sena ringa zane su tunda basa jin magana musamman kai NAUFAL me taurin kan tsiya irinna baban,ku'' dai-dai lokacin SUAHAIL ya shigo farlon ''naji duk abinda ake cewa ƴaƴa na masu tauri kai irin nawa'' ya faɗa tarada Zama akan kujera gaba ɗaya sukayo kansa kowa yana so ya hau cinyar sa, ɗaukar su yayi ya ɗora su, yana musu wasa cikin so da ƙauna NIHAL da baza ta wuce shekara huɗu ba tace '' DADY gobe ina son ka Kai ni gurin wasa nayi wasa'' '' shi kenan mama na zan kai ki , shi kuwa NAUFAL cewa yayi '' DADY Ni kuma so nake ka saya min kayan wasa mota da jirgi'' an gama kaima Allah ya kai mu duk zan siya muku'' kallan MANAL yayi wadda take bawa SUHAILA nono yace '' shi kenan abinda kuke so?'' Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin '' yesss DADY'' murmushi yayi kana yace '' to maza ku tashi kuje ku kwanata kuce yaya HASSAN yayi muku addu'ar kwanciya kunji '' to DADY seda safe Mommy seda safe suka faɗa suna barin ɗakin. Tashi SUHAIL yayi ya matsa kusa da MANAL da take ta yamutsa fuska a ranshi yace '' me hali baxe taɓa de nawa ba har yanzu MANAL bata son bawa yaro Nono'' afili kuwa cewa yayi '' maman yara dare fa yayi ya kamata muje ki kwanta nima kuma aji dani'' ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya '' wai dan Allah kai ABBEN WTO YINS baka girma da wannan abun '' ta faɗa kamar zatayi kuka '' kin taɓa ganin wanda ya gaji da raya sunnar ma'aiki nifa so nake yau ɗin nan na baki ajiyar wani BEBYN'' yasa hannu ya ɗauki SUHAILA wadda ta jima da yin Bacci ɗaki ya kaita sannan ya dawo ya ɗauki MANAL da take ta turo baki be dire ta ko ina ba se kan gado yaje ya rufe musu ƙofar sannan ya dawo kan gadon ya hau ya janyo MANAL jikin sa yana shafar bayan,ta cikin tattausar Muryar yake gaya mata kalamai masu sanyaya zuciya daga haka suka lula duniyar ma'aurata bayan komai ya lafa MANAL ta riƙo hannu sa kana tace "alhamdullih Allah Nagode maka da ka bani mijin marainiya me share min hawaye na dama ance me HAƘURI shi ke dafa dutse yasha har da roman ,sa ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH. INA ALFAHARI DA ZAMO WAR KA UBAN YAYA NA. LEFIN DAƊI ƘARE WA. Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin na RAMIN MUGUNTA ina fatan wannan yazama darasi ga ƴan baya kunga dai yanda ƙarshen Dady ya kasance sanadiyyar biyewa san zuciya da yayi da son Abin duniya harya kaisa ga aurawa ƴaƴan sa wa'inda besan ko suwaye ba bema san asalin su, ba wanda hakan yasa ya kamu da Cutar shanyewar ɓarin jiki NABILA kuma ta gamu da Cutar H.I.V, ZAINAB kuma yoyan fitsari mommy kuma Cutar farfaɗiya wannan kaɗai ya isa yasa mutum yasan cewa duniya ba mattabba bace ALLAH YA TSARE MU DA AIKATA IRIN WANNAN ZALUNCI YASA MUFU ƘARFIN ZUCIYAR MU, YASA DUNIYA TA ZAMO A HANNUN MU, BA'A ZUƘA TANMU BA GODIYA TA MUSAMMAN A GAREKI KHADIJAH ABDULLAHI UMAR (OUM SHARIFAT) GARKUWA JARUMAI KUMA (BESTY NA🥰🥰) ALLAH UBANGIJI YA BIYA MIKI BUƘATUN KI, NA YAU DA KULLUM DAGA MARUBUCIYAR 1 - MATAR YARO 2 - NI DA YAYA OMAR 3 - IZINAH 4 - GANI GA WANE 5 - RAMIN MUGUNTA 6 - ƳAR SHAYE SHAYE 8 - MIJIN BERA 9 - KISHIYAR UWA CE SANADI ️ SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MAMAN HIBBA) SHA RUBUTU.. nake cewa bissalama ASSALAMU ALAIKUMA BAYIN ALLAH SE MUN SAKE KASANCE WA DAKU A CIKIN WANI SABON LITTAFIN NAWA ALLAH YA ƘADDARA SADUWAR MU AMEN.