[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼  KAI NE JARUMI💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAH *NOTE*: BA SABON RUBUTU BANE TSOHUWAR AJIYA CE. *Dan Allah kamar kullum ina kira akan ko bai maki dad'i ba yanzu ki adana saboda gaba wataqila ya miki* Page 1: Alhaji Hamza Muhammad Jambulo, d'an asalin garin kano ne gaba da bayan shi ma'ana uwa da uba dika kanawan dabo ne,Allah ya azurta shi da macen aure mai suna Maimounatou,da Yara biyu mata Rashida da Sakeenaa, Maimounatou ta fito daga tsatso na masu akwai, iyayen ta hamshaqan masu arziqi ne, ta na da kyau daidai misali, ta kasance kafin auren su da Hamza tana da masoya da yawa,manyan yaran attajirai,yaran 'yan kasuwa kamar mahaifin ta da yaran 'yan siyasa dik cikin su bata ga Wanda zuciyar ta ta aminta da shi ba dan haka sai ta qi zab'en kowa a cikin su dik da takura da azalzalar ta da iyayen ta suke akan ta fidda mijin aure. Hamza shi ne saurayi na farko da ta fara so, ta had'u da shi a hanyar ta ta zuwa gidan Goggon ta, shi Kuma ya dawo daga 'yan bige bigen shi na neman kud'i,ya had'a zufa ya gaji liqis, dik da yanayin shigar shi da Kuma ganin yanayin shigar da ta yi ya San ba sa'ar shi bace, amma kyan ta da kamalar ta ya sa shi tsaida ita ya gabatar da Kan shi, Kuma ya Sanar da ita abinda ke zuciyar shi, tare da neman sanin inda take zaune saboda a cewar shi mace mai Kamala kamar ta be Kamata a tsaida ita a hanya ba, tin daga nan Hamza ya sace zuciyar Maimounatou ta ji dik duniya ba Wanda take so ya zama mijin ta sai shi, ta na son namiji da confidence irin nashi,babu b'ata lokaci ta masa kwatancen gidan su, ko a fuska bata ga tsoro da fargabar komai a tattare da shi ba, kamar yanda take gani a fuskokin wasu in ta sanar da su ko ita wace ce. A hankali soyayya mai tsafta ta yi qarfi a tsakanin su, Iyayen shi sun San wacece Maimounatou a wajen shi, sun sha bashi hakuri akan ya barta ya nemi wata, duba da har a wannan lokacin bashi da tsayayya Kuma kwakkwarar sana'a, amma ya roqi da su ci gaba da Yi masa addu'a in rabon shi ce Allah ya bashi, in ba rabon shi bace Allah ya musanya mashi da Mafi alkhairi. Bangaren Maimounatou kuwa ba Wanda ya San shi sai mahaifiyar ta, mahaifiyar ta ta yi iyakar qoqarin ta dan ta fahimtar da Maimounatou irin tazarar da ke tsakanin ta da Hamza amma ta kafe sai Hamza,haka ta hakura ta kyale ta sannan ta gabatar da buqatar ta wajen mahaifin Maimounatou, da labari ya riske shi Shima kafewa ya yi ba zai aura mata talaka ba, ya Saida akuya ta dawo ta na ci masa danga, sai dai a cikin yaran abokan shi hamshaqan 'yan kasuwa ya aura mata Wani, Maimounatou da Jin haka ta hau kuka, rashin lafiya kuwa har da kwantawa a asibiti, akan dole iyayen ta suka  hakura suka aura masu junan su. Tinda Hamza ya auri Maimounatou be tab'a zuwa wajen kowa roqon ko da allura bane, ya jajirce ya tsaya da qafafun shi Kan jiki Kan qarfi,da dad'i da wuya, rana da iska, damina da rani ya nemi kud'i dan rufa wa Kai da iyalin shi asiri,shine dako, shi ne share sharen manyan shagunan 'yan kasuwa, shi ne garuwa shi ne faci shi ne Saida kayan miya, dik wata sana'a da Hamza ya San za ta kawo masa kud'i be zauna ba ya tab'a ta, be dogara da kwalin makaranta ba , su na nan a haka yau da dad'i gobe da d'aci har Allah ya azurta su da yaran su biyu 'yammata kyawawa. Rasheeda itace babba, sannan Sakeenaa, tsakanin su akwai tazarar shekara biyu, Yau da gobe Hamza ya na 'yan bige bigen shi har Allah ya sa ya samu tsayayyar sana'a ta Saida shaddodi manya da qanana da yadi Shima manya da qanana sai jallabiyyu na maza, albarka ta yawaita cikin kasuwancin shi nan da nan sai arziqi ya zauna masa Shima aka fara sharafin duniya na masu akwai da shi, a da ana Kiran shi da Hamza Kai tsaye, yanzu kuwa Alhaji Hamza Muhammad Jambulo da shi aka San shi. Wata rana suna zaune da matar shi Maimounatou da 'ya'yan su inda  Rasheedah ke da shekara goma Sakeenah kuwa na da shekara takwas, Maimunatou na zaune kusa da mijin ta ta dora qafar ta daya a cinyar shi shi kuma yana matsa mata, a cewar shi ta gaji da aikace2n gida dole ya mata tausa, " Tawan ki duba fa ki ga yanda Allah ke hukuncin shi, an hana ni ke a baya ba dan komai ba sai dan talauci, amma yanzu daga ni har ke bama qirga zuwan mu qasa mai tsarki nawa  mu da yaran mu, a yanzu kowa dai ya shaida Hamza me buga can buga nan ya zama Alhaji Hamza" A hankali ta zame qafar ta ta matsa sosai jikin shi, kwantar da kan ta ta yi a kafad'ar shi sannan tace, " Mijina KAI NE JARUMI NA dogaro da Allah da jajircewar ka ne suka Kai ka matakin da ka ke Kai a yanzu,sannan ka sani tun a  baya na yi alqawarin ko da shi ko bashi kai zan aura Kuma na aure ka d'in a halin baka da shi,amma ba gashi ba yanzu Allah ya dube ni ya sa ka kaima ka zama mai akwai din, dan haka godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai, Allah ya raya mana zuri'ar mu," "Ameen Jaruma ta" Sumbatar ta ya yi a  goshin ta suka ci gaba da hira akan samu da rashi, Wanda yake faruwa da izinin Allah, Rasheedah dake gefen su kuwa kyab'e baki ta yi ta tashi ta yi dakin ta. Rasheedah: Rasheedah Hamzah, ta kasance Fara ce irin farinnan mai matuqar kyau da daukan hankali, sannan akwai ta da kyau daidai misali, ga gashin ta baqi mai cika saidai bai da tsaho sosai, Rasheedah kwata2 ba ta dakko halayyar iyayen ta ba ko kad'an , tana da wasu irin halaye masu wuyar sha'ani,Rasheedah na da tsananin qin talaka, 'yar Qarama da ita se girman Kai, kwata2 ko qawaye ba ta yi sai da yaran masu akwai, da yanda take son kuɗi da abin duniya haka take son ibada da anyi salihar mace. Sakeenaa: Sakeena sab'anin rashida ce daga halitta har kuma halaye, domin kuwa ita baqa ce irin baqinnan mai matuqar kyau, gashin ta baqqiqirin Mai yalwar tsahi da cika, girar ta kamar an gyara mata ita take a ko da yaushe ka kalla, makaranta bari na taqaita maku akwai kyau wajen Sakeenaa, ta bangaren halayyar ta kuwa tayo halayyar  mahaifan ta sak, kai har za a iya cewa ta d'ara su kyan hali,akwai ta da  son ibada, tin Kan ta Iya sallah take qoqarin gwadawa har ta Iya sallah, a qarancin shekarun ta in ta ga iyayen ta na azumi zata kame bakin ta tace itama yau azumin take kowa nata ne da talaka da mai kudi, bata ware wa, gashi a duniya tana son 'yan uwan ta musamman Rasheedah. Wannan sune 'Yammatan Alhaji Hamzah. A kwana a tashi a sarar mai rai,Rasheedah da Sakeenah sun zama manyan 'yammata, bayan saukar qur'ani da suka yi tin su na Yara, sun sake yin wata a yau,inda suka samu kyaututtuka masu yawa musamman Sakeena da ta yi haddar ta ba algus, baqin ciki kamar ya kashe Rasheedah dan ganin yanda ake ta ba wa Sakeenah mahimmanci a makarantar, amma ba yanda za ta yi dole ta danne ta bar abun a ran ta. A hanyar su ta komawa gida ne suka  had'u da wani kyakkyawa Kuma kamilin saurayi,babu b'ata lokaci ya tsaida su,sallama ya yi musu, Sakeenah ce kawai ta amsa, Rasheedah kuwa qa'idar ta ne se ta fara kallon mutum in ta ga ya mata sannan ta amsa Kiran shi ko sallamar shi, in be mata ba ko mutum zai shekara yi mata sallama ko a zuci ba zata amsa shi ba, ta na kuwa juyawa idanun ta suka sauka a saman fuskar shi ta Kai duban ta kowanne bangaren na jikin shi nan da nan  kyaun shi ya yi gaba da ita ta ji ya yi mata, se dai kashhhh a qafa ya zo, dan bata ga alamun Yana tare da wani abun hawa ba, ko da ace machine ne kuwa, kawai sai ta had'e fuskar ta ta juya ta fara sauri dan Isa gida,Sakeenaa ce ta tsaya ta amsa masa sallamar shi sannan suka gaisa, yana kallon yanayin Rasheedah a ranshi yace, 'Gwanda da Allah ya rufan asiri ba ke nake so ba,lallai yau da na san se na wahala wajen neman soyayyar waccan nunar ranan' A zahiri kuwa gabatar da kan shi ya yi a wajen Sakeenaa in da ta nuna mai gidan su da suke hangowa sannan tace, " Na gode da soyayyar da ka furta ka na min Adnan, amma zan baka hakuri, ba dan ka na da makusa ba, sai don ina son kabi doka da tsarin mahaifina, shi ya kamata ka fara samu ya baka izinin ganina, domin shi zai aurar da ni, kaga bai kamata na fara kula ka ba da izinin shi ba ko?" Wata kyakkyawar ajiyar zuciya ya sauke dan a da ya d'age nunfashin shi ne saboda tsoron kar ta yi rejecting d'in shi,se Kuma ya ji magana ta hankali da tarbiyya daga bakin mace Mai daraja murmushi ya sakar mata sannan yace, "Amma kin matuqar tsorata ni,kar na ja ki da hira yanzu sai nazo gidan na ku,meye sunan malamar na gabatar maki da kaina da suna na amma ke ki na min rowar naki," Murmushi ta yi daya qarawa fuskar ta kyau, sannan ta sanar da shi sunan ta, suka yi sallama ta tafi,yana ta kallon ta har ta shige gidan su. Bakin ta d'auke da sallama ta shiga gidan nasu, bata tarar da kowa a parlour ba har  tsakar gidan, dan haka sai ta wuce d'akin su direct ta tarar har Rasheedah ta cire kayan ta ta saka wasu ba tare da ta yi wanka ba, al'adar ta kenan ita tsafta bata cikin agender din ta, kad'a kai Sakeenaa ta yi ta wuce ta cire kaya ta dau towel din ta na  wankan ta shiga bathroom, tsaki Rasheedah ta yi sannan tace, "Aikin banza ace wai duk kyaun da Allah ya miki, ki tsaya sauraran wancan abun, da ganin shi ba qaramin matsiyaci bane, me zaki da shi? So kike duk sanda zanje gidan ki na qulle abinci na a leda ko a food flask na je? Me yaci da zai baki? Kin wani tsaya kina ta rangwad'a kina karairaya, ko dai kyaun shi ne ya rude ki? " Tsabar mamakin kalaman yayar ta ta ne yasa ko juyawa ma ba ta yi ba ta tsaya cak can Kuma ta fice ta bar Rasheedah na ta zagin ta akan tsayawa da Adnan,abubuwan da ta fada mata sun matuqar qona ranta, amma dake itan ba mai ruqo bace kan ta fito wanka ta manta, haka suka shirya suka ci abinci, kome suke sai ta mata mita akan ta rabu da wannan talakan tin kan abun ya kai kunnen mahaifin su, bata ganin nata saurayin Auwal mai kuɗi ne, dan ma yace ba zai na b'ata ta da kudi ba yanzu har sai sun yi aure kar iyayen ta masu ra'ayi su ce ba son Allah yake mata ba,a haka har dare ya yi Abban su ya dawo. Suna zaune a babban parlorn su, as usual ana ta hira bayan sunyi sallar isha'i, sun ci abinci, sallama aka yi , wanda take Sakeenaa ta gane mai muryar amma ta dake, Abban su ne ya miqe ya yi waje dan ganin waye, Sakeenaa ma tashi ta yi tai ma maman ta sallama akan sai da safe yau ta gaji bacci take son yi da wuri, miqewa itama Rasheedah ta yi tabi bayan ta, ba ko sallama ma maman su  ta yi daki kai tsaye, addu'ar shiriya Maman su ta mata a ranta, ganin halayen yaran nata sun banbanta kamar ruwa da wuta sai ta yi tasbihi ga Allah ta nema musu shiriya baki daya, bayan jimawa kadan Abban su ya dawo, ya na murmushi. " Maimunatou na barkan mu , da  dikkan alamu bana zan aurar da yaran nan, da izinin Allah, " Cikin farin ciki da zumud'i take tambayar shi me ya faru, " Abban Rasheedah me yasa kace haka, wanene ya shigo Kai tsaye cikin gida?" Dariya ya danyi sannan ya bata labarin zuwan Adnan, kuma ya shaida mata cewar, ya masa izinin ya ci gaba da  zuwa  in sun daidaita Kan su to, in yarinya ta ga be mata ba ba zai wa 'yar shi auren dole ba, ya sanar da shi qa'idar zuwa zancen shi a sati sau d'aya ne, sannan kuma daga bayan la'asar ne zuwa kafin magrib, kuma a cikin parlourn shi babban nan zasu na hirar ba a waje ko farfajiyar gidan ba, kuma baya son saurayi yana kashe wa d'iyar shi kud'i, in ya aure ta ko kantin kwari ne ya sai mata, Adnan ya ji dad'in hakan sosai ba kad'an ba, hakan ya qara masa so da qaunar Sakeenaa, ya tabbata zai yi aure gidan mutunci, Adnan maraya ne, dan haka yake son ya samu macen da zata riqe shi da gaskiya da amana. Bayan wata shida da haduwar wadannan masoyanne akai auren su, inda gidan Rasheedah ke a kabuga, ita kuma Sakeenaa take a can cikin Jambulon tsakanin ta da gidan su akwai tafiya sosai, anyi aure cikin rufin asiri da kwanciyar hankali, wanda wannan aure ba qaramin dagawa Rasheedah hankali ya yi ba, ta gano Auwal ba wani mai kud'i bane, dan daga gidan da take ma ya nuna mata hakan, gidane irin na qasar nan amma yasha siminti da fenti,daki biyu ne a gidan,sai band'aki ko arziqin kitchen babu, da alama da murhu za ta na amfani. Gidan Sakeena kuwa ya sha banban da na Rasheedah, gida ne makeke na masu hannu da shuni, kowa ya yi mamakin ganin irin gidan da Adnan ya ajiye Sakeenah duba da yanda ya zo kamar bai da komai. Bayan wata daya da kwanaki ne Rasheeda ta matsawa mijin ta akan se ta je ta ga gidan 'yar uwar ta dan ta ga shin abinda ake fad'a gaskiya ne? Daga nan ta je gida gaida iyayen ta, sanda ta fara bi ta gidan iyayen su mahaifiyar su ta bata tabbacin irin daular da aka Kai Sakeenah kasa boye baqin cikin ta ta yi, dan takaici da baqin ciki har kuka ta je tsohon dakin su ta sha ta gode Allah, kafin ta shirya ba ko sallama ta wuce gidan da aka mata kwatance shi ne na Sakeenah, ba tare da ta shiga gidan ba ta tsaya ta na kallon shi daga nesa ta na hawayen danasanin auren Auwal hawayen ta ta share ta samu adaidaita sahu ta yi gida, tin daga ranar ta yanke masu zaman jin dad'i da nishad'i ita da mijin ta Auwal.... [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼  KAI NE JARUMI💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 2: A hankali Sakeenaa ta fuskanci irin qiyayyar da 'yar uwar ta ke mata, ba qaramin baqin ciki ta yi da ta gano hakan ba,ta yi kuka sosai akan baqin ciki, ita dai ta san tana matuqar son yayar ta ta, bata son duk wani b'acin ranta, a baya ta zaci kawai haka halin ta yake yawan kushe abun wasu da son ta burge mutane, ta zaci kowa ma haka take masa, bata tab'a tunanin wai hassada take mata ba me qarfi haka. Duk sanda Sakeenah  zata kai mata ziyara kuwa sai ta debi abubuwa sosai ta kai mata, kama daga dangin abinci, sutura ,abin sha,da dai sauran su ta Kai ta na Mai nuna wa yayar tata abinda ta mallaka nata ne ba banbanci dik dan ta sa ta dena nuna mata qiyayya a zahiri, amma inaaa sam basa burge Rasheedah ita dai so take ta zama Sakeenah, Sakeenan ta koma ita, dan haka ta na kawo mata kayayyakin nan za ta mata tatas, ta yi mata rashin mutunci,Kuma ta karb'e tare da fad'in raba arne da makami ai ibada ne, kalmar nan na matuqar qona ran Sakeenah wato ma ita ce arniyar. Abinda ya faru kenan a yau da Sakeenah ta kawowa 'yar uwar tata ziyara, domin a cewar ta Bata son zumuncin su ya lalace koma mene ne ita ce qarama dole ta bi yayar ta Dan sada zumunci, sannan Allah da Manzon sa ba su son duk bawan da yake yanke zumunci, ta na kwadayin ladan da Allah ke ba wa masu Sada zumunci ranar gobe kiyama. Sanye ta ke da wani leshi Mai sauqin kud'i saboda gudun kar ta saka Mai tsada 'yar uwar ta ta ce ta je nuna mata azziqin tufafi, haka zalika takalmi da jakar da ta d'auka dik masu sauqin kud'i ne Wanda ta siya na musamman saboda zuwa wajen Rasheedah, Adnan ya Kai ta da Kan shi har qofar gidan ya ajiye ta, ya fitar mata da kayayyakin da zata Kai wa Rasheeda, kudi ya qara mata ya ce ta Kai wa Rasheedah, sannan ta gaishe su in ta gama ta kira shi ya Maida ta gida. Dubu goma ne ya bata ya ce ta ja jari, sallama su ka yi ya wuce, shigar ta ke da wuya ta tarar da Raheedah tana hura murhu zata dora abincin rana, aje maficin ta yi tana yatsina fuska ta ce, " A'a kaga matan alhazawa matan da suka ci suka tada kai,ku ne a tafe cikin rana haka?" Murmushi Sakeenaa ta yi sannan ta shige parlour dan ta san sarai magana ta faɗa mata, zama ta yi tare da cire hijab din ta da niqab, sallama Rasheedah tayi ciki ciki ta shiga, tare da dage labulen sakamakon duhun da wajen ke da shi in ba wuta, gaishe da ita Sakeena ta yi cike da farin ciki tace, " Rasheedah ga Apple na kawo maki dan na kula mun samu dan baba, na san zaki so shi Allah ya raba ku lafiya ya bada mai albarka," tana maganar ta na bud'e ledar da ta sako fruits ciki. Dan gajeran tsaki Rasheedah ta ja sannan ta ce, "Hmmm dake an fada maki talaucin namu ya kai yanda in nayi sha'awar ta ba za a siyo min ba ko," Sakeena ta hadiye rashin Jin dad'in Kalaman yayar ta se ta yi dariya ta ce, "Niii ina na isa na fara wannan tinanin ma, kawai dai tawa gudummawar na kawo dan d'ana ko 'yata su fara cin abun auntyn su, amma ai Yayah Auwal na iya qoqarin shi," Kauda kai ta yi ta yatsina fuska, talaucin Auwal ba qaramin damun ta yake ba, "Ke dalla can wane qoqari ya iya banda qoqarin yi min ciki ba kayan da zasu qara min kuzari, kullum cikin wahala, duba fa ki gani kamar ni ace ina hura murhu, gaba d'aya na yi baqi, haskena ya dishe, kamata ya yi ace yanda nake da cikin nan na qara haske da kyau amma jibi yanda na qare na lalace," Sakeenaah kuwa zuba mata Ido kawai ta yi ta na kallon ta,rashin godiyar yayar ta ta kullum da alama gaba yake ba baya ba, bud'e baki tayi dan ta mata nasiha amma sai ta dakatar da ita ta miqe ta ce ta na zuwa,kayan miyan da ya kawo ta dakko ta baje a qasa ta hau ware wa, ledar nama ta aje a gefe ta gyara ta dora tafashen nama, sannan ta yi jajjage, ta soya kayan miyan ,ta tsaida ruwan dafa dikan taliya, sannan ta dakko tafasasshen naman ta zuba ta saka maggi da dan kayan qamshi ta rufe sannan ta dawo, duk abinda take a kan idon qanwar ta ta, "Uhumm ina jin ki," "Abinda nake son fada maki Rasheedah shine ki godewa Allah, akan abinda ya baki, ki fa diba ki gani taliya zaki dafa, sannan ki gani ba zallan ta bane haka nan har da naman miya, da damar mutane suna cikin matsalar rashin abin da zasu ci, amma ke kin samu kina kai qarar Allah akan bai baki ba wajen bayin shi, in a rayuwa kk ce ba zaki duba na qasa dake ki godewa Allah ba, to kuwa in kina kallon na saman ki sai dai ki butulcewa Allah, kuma Rash......." "Ke dakata in wa'azi zaki min riqe abun ki, ba zan qara fada maki damuwa ta ba, akan wane dalili zaki saka ni gaba ki ta faman min wa'azin da kk san ba dauka zan ba, meye aibun abinda nace? Bayan komai na fada gaskiya ne, ko dan ke kinga Allah ya baki shine ni dan na fadi halin danake ciki ya zama laifi?" Sakeenah hadiye bacin ranta ta yi dan tabbas yanda tai mata maganganun cikin daga murya da tsantsar rashin mutunci da wata ce sai ta mayar mata ba dad'i, amma sai ta miqe ta dauki hijabin ta da niqabin ta ta dakko dubu goman ta aje mata akan kayan ta tace mata, " Allah ya baki hakuri ba niyyata na zo na bata ranki ba, gaishe ki na zo yi tinda na gaida ki zan wuce, Allah ya raba ku lfy, ya qara arziqi," Cikin halin rashin kulawa tace, "Tafiya zaki bazaki ci abincin talakawa ba ko, hhhh ai na sani , ki gaida gida , sai munzo cin arziqi gidan masu da shi," Bata ce mata komai ba ta fita,a soron gidan ta hango motar shi, yana mata murmushi, take ta ji baqin cikin ta ya ragu, qarasawa ta yi tana masa murmushi dik da niqabin dake fuskar ta bai gaza gane me take mai ba, amma a hakan sai da ya gano zuciyar ta ba dadi a lokacin da ta shiga motar, saurin d'auke niqab din ya yi yace "Me ta maki yau kuma, na kula kullum kk zo gidannan sai ta bata maki rai ke kuma baki son fad'a min, a gaskiya zaki daina zuwa in haka ne, ita ta dinga neman ki ba shikenan ba," "Sam ba za ai haka ba, in banje wajen yayata ba wajen wa zani? Kuma ni ban ce maka ta min wani abu ba ai ko? Ina son yayata ina qaunar ta, kome zata min yayata ce , komai zatai man ba zai taba canja wani abu daga son da nake mata ba," Ta qarasa muryar ta na rawa, idon ta taf kwallah,bata son ta kuma cewa komai sai ta jingina kanta a kujera bayan ta maida niqab din ta, jan motar ya yi yana hararar gidan Rasheedan, daidai lokacin da mijin ta ya ke qoqarin shiga gidan, ya na shiga kuwa ta miqe ta karb'e ledar hannun shi ta ce, "Meye wannan a ledar?" Miqa mata ya yi ya koma ya zauna a gajiye, aikin gini yake, gaba d'aya ya gaji, tsaki ta ja sosai sannan ta kalle shi, "Yanzu Auwal meye wannan tsakani da Allah? Ya zaka kawon wani zogale sai kace tsohuwa? Ga abubuwan kwadayi da qarin jini nan da masu ciki ke ci amma ni ka ban wannan?" Cike da takaici ya kalle ta, se kawai ya mata shiru dan in ya biye mata sai ya faffalla mata maruka, miqewa ya yi ya kewaye ta ya fita tsakar gida dan wanke hannu da qafa, sanin halin shi ne yasa tayi gum da bakin ta da ta ga ya miqe, se da ya fita ta dauki zogalen ta na mita ta kwadanta yawun ta har zuba yake ta yi maza ta goge da bayan hannun ta,ta zauna zata ci kenan ya fito, dariya ya barke da ita,sannann ya yi maza ya karb'e kwanon daidai lokacin da zata zira hannu dan diba ya kama hannun nata da qarfi ya sid'e , cikin kuka ta fizge hannun ta shi kuma ya shige d'aki da shi ya rufe qofar, ihu ta saka tana kiran ya bata ta ci amma ya qi ya na ta dariya ya ce "Ba zan bayar ba ai ina kallon ki, jira dama nake ki gama had'a min tinda ke ba so kk ba, kin raina abinda na baki saboda kin fi qarfin shi ko? To ni da ban fi qarfin shi ba bari na ci abuna" Cikin kuka take masa magiya shi kuwa ya yi kamar be ji ba, se kwasar zogalen ya ke ya na kaiwa baki, tare da lumshe idanun shi, hannun da ya sid'e ta kalla ta ga akwai saura se ta hau sid'e hannun nata,Wani irin dad'i ne ya gauraye mata baki har tsakiyar kan ta ta ji shi. " Auwal kai min rai ka bani na ci, cikinnan zai iya zubewa in ban ci abinnan ba," "Wa ya yi cikin da izinin Allah? Ba dai Allah ni ya bawa ikon dura abubuwan da cikin ya samu ba?  Kar ki damu ya zube na qara maki wani," kuka ta zube a wajen tana yi,dan tabbas ta san ba zai tab'a bata ba, sai da ya gama tass d'an burbudin kwanon ya dangwara a gaban ta ya yi wajen taliyar da ta dahu har ta dan fara qauri, saukewa ya yi ya d'iba ya dawo parlorn ya na ci , kallon shi ta yi cike da harara da tsiwa, ranta na suya dan ba qaramin b'ata ranta ya yi ba daya cinye, " Allah sai ya saka min Mugu azzalumi kawai tinda ai ka san sarai ina da buqatar irin wadannan abubuwan a jiki na tin da ciki gar..," Kan ta rufe baki ta ji ya bige mata baki da bayan hannun shi, nan take kuwa ta buga ihu ta Kai hannun ta baki se ga jini, qara rikicewa ta yi da kuka, shi Kuma ya miqe ya na nuna ta da yatsa ya ce, "Ni kk zagi ki ke had'awa da Allah?dan ma kin samu ina maki qoqari ko? za ki ga iskanci kuwa ganin idon ki mun d'aura daga yau, tin da qoqarin da nake a ban da shi kin raina muje zuwa da Auwal kk magana," Wajen tukunyar ya nufa ya kwashe sauran naman tass ya wuce uwar d'aki ya zauna ya sa gaba yana ci, wani yunquri ta yi da sauri dan ta je ta ci itama,Wani mugun kallo ya wurga mata se da hanjin ta ya kada, qunquni take  ta na ja masa Allah ya Isa kamar wata qaramar yarinya,Auwal na ganin haka ya janye kwanon zai miqe ta kwasa waje da gudu, "Da ki tsaya mana qaramar mara kunya, kwatakwata baki da hankali baki San me duniya take ciki ba, zan koya maki zaman duniya ne, shashasha kawai" A tsakar gida ta ja ta tsaya, can Kuma ta qarasa ta ja tukunyar taliyar ta hau cin abinci tana kuka, ko gamawa bata yi ba ta tuna da abubuwan da Sakeenah ta Kai mata, da sauri ta nufi parlour ta dauki ledojin ta hau bubbud'ewa,da  soyayyan nama ta fara yin karo se fruits da fresh milk,sannan kud'in da ta aje mata, d'aya ledar Kuma rigar bacci ce da turare da man shafawa se d'ankunne, kyabe baki ta yi tace, " Ko banza na mora, duk da ba haka na so ace wai qanwata ke min ba, ai kyanta ace ni ce zan dinga bata ta na karb'a ba wai ni ta dinga kawon ba" Ci ta hau yi ba ko bismillah, ko me ta tina oho, se ta  miqe ta shiga daki ta zauna gaban Auwal tana ci tana waqe2n habaici, ko kula ta bai ba, dan ya san wa ya kawo, shi a nashi b'angaren dik da yasan ya mata qarya wajen auro ta, amma yana tsananin son ta, sannan in ta bishi a sannu zasu zauna lfy, kuma iya qoqarin shi zai mata duk abinda ya sawwaqa tinda harkar gini watarana a samu me yawa ne watarana kad'an amma ita inaaa bata San wannan ba, sai da suka yi aure duk wasu halayen ta da bai ma san ta da shi ba musamman na tsanar qanwar ta da duk wani wanda ya fita qumbar susa suka fito masa fili se ya dauki hakan a matsayin Allah ne ya tura shi wajen ta dan ya yi maganin ta, halayen munana bai rage masa son ta ba sam, sai ma qaruwa da yake, dan ko ba komai yana morar ta ta wani wajen. *************************** Cikin dare Sakeenah ta miqe tana safa da marwa a d'aki, juyi Adnan ya yi se ya ji bata jikin shi,idon shi ya bud'e kad'an da magagin bacci ya kalli gefen shi ya ga ko ta mirgina gefe ne ya jawo ta jikin shi se ya ga bata nan, sun riga sun Saba wa junan su kwana a manne da juna,rashin ganin ta a gadon ne ya bashi damar bud'e  ido sosai a tsaye ya gan ta tana safa da marwa, cikin damuwa ya sauke qafafun shi tare da zira takalmin shi ya riqe kafad'ar ta ya ce, " My love lafiya ki ke kuwa? Me ya same ki, ko na maki wani abu ne da ya b'ata ran ki ban sani ba?" Da sauri ta fada jikin shi tana kuka sosai, "Mine abun nan na damuna sosai, ka duba ka ga qawayena da akai auren su bayan namu duk da ciki, Rasheedah da aka mana aure rana d'aya ciki ne da ita ba wai baqin ciki nake ba ko Wani abu makamancin haka ka fahimce ni kawai nima na so ace Ina da shi amma shiru har yanzu," Ta qarasa maganar  cikin matsanancin kuka, sake baki ya yi da farko yana kallon ta, sannan daga baya ya yi murmushi ya kamo ta ya dora a kan cinyar shi, "Habaa my love, yanzu ina ilimin ki ya tafi, ki dinga zance irin na Wanda suka manta Allah na yin yanda ya so a lokacin da ya so Kuma akan Wanda ya so? Habaa gaskiya ban ji dad'in Jin haka daga gare ki ba, ke da na sani ki na da tawakkali da aiki da ilimin ki na addinin da na boko ma, Ina hankalin ki ya tafi ?habaa kar kina saka wannan a ran ki, Kuma dai na ga ni ban ma gama cin amarci na ba" Ya na fad'a yana sunsunar wuyan ta, yana shafa bayan ta, sannan ya yi amfani da d'ayan hannun shi yana qoqarin janye mata rigar dake jikin ta, itama cikin zaquwa da abinda mijin nata yake mata ta juya ta bashi hankalin ta dika, wasanni suke kamar zasu cinye juna, ina ganin haka nace tooooo Haermee an zo wajen manya fece🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀ [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼  KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* Page 3: " Wayyo Allah na shiga uku na lalace, da nasan haka zan sha wahala da ban auren ba ma, wayyo mama na Abbana ku taimaka min,Auwal ka cuce ni ka Kai ni ka baro Allah ya saka min, ga talauci ga ciki ka had'a ni da shi zan mutu wajen haihuwa Auwal Allah ya tsin..." Midwife d'in da ke karb'ar haihuwar ta ce ta rufe mata baki da sauri ta ce, "Subhanallahi baiwar Allah ya ki ke abu kamar ba musulma ba ne? Se zage zage ki ke yi tinda aka kawo ki, yanzu mijin naki Zaki tsinewa kamar wasu Wanda suka samu cikin ta haram? Kin manta ma da addu'o'in da ya Kamata ki yi, kin manta da buqatun ki da ya Kamata ki roqi Allah a wannan yanayi da ki ke ciki saboda Allah na karbar addu'ar masu naquda, me yake damun ki? Ga ki kamar wayayyiya amma kina abinda jahilai ma basa yi, mtsss" Takaici da haushin Rasheedah ya gama cika nurses da midwifes tare da likitan dake cikin d'akin haihuwar, gaba d'aya kamar Jira suke kuwa suka yi mata caaaaa, banza ta yi da su ta ci gaba da zage zage ta na Kiran dan ba su bane suke Shan wahalar shi ya sa,Allah ya d'ora musu masifar da take ciki su ji idan da dad'i,Auwal na waje ya na Jiyo dik abinda take yi, ya yi zukud'i ya zabga tagumi se fata yake Allah ya sauke ta lafiya, gaba d'aya tausayin ta ya gama cika masa zuciya, ta Wani fannin kuma haushin ta yake ji,tinawa ya yi da abinda ya faru kafin su zo asibitin.... 'Yanzu baza ki daina wannan iface2n ba ki kira sunan Allah? Sai kin gama tara mana mutanen unguwa a zo jin me ke faruwa, Ki qoqarta ki tashi na kai ki asibiti nan ma kin qi, kin san sarai ni ba iya d'aga ki zan ba saboda yanda ki ka yi qiba se na taimaka maki mu taka zuwa waje ga me adaidaita can na kira ya na ta Jira, Iya jiran shi Iya kud'in da zan bashi Kuma gashi bamu je asibitin ba balle mu ji nawa zan kashe,' Hannun shi ta damqo ta matse tare da gasa masa Wani wawan cizo tin qarfin ta, ihun shima ya saki, d'aga hannun shi ya yi da niyyar wanke ta da mari sai ya hakura ya sauke, yace mata,' 'Bashi kk ci zan rama ne nima,' A haka ya qoqarta d'aga ta, ya shirya ta da kyar tana fizge2 kamar wata 'yar bori, a haka suka shirya zuwa asibitin Imam Wali dake cikin Jambulo, suna zuwa malaman asibitin suka ji yanda take ihu suka san akwai darga da wannan rikitacciyar da tin a zuwa awo wasun su suka San halin ta,da kyar ta bari aka shiga da ita dakin haihuwar, suna shiga ya lalubi qurqurar wayar shi ya kira surukan shi da Sakeenaa ya sanar da su suna asibiti haihuwa ta zo, doguwar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama wannan tinanin, a Fili ya furta, "Allah ya kyauta, Allah Kuma ya sauke ki lafiya ya bamu masu albarka" Tinda Auwal ya Sanar da ita maganar haihuwar ta ke a cikin tsananin zumud'i tare Kuma da  tausayin yayar ta ta, shiryawa ta yi Adnan ya dakko ta dan ya Kai ta asibitin, kan ta fito sai da ta dakko kayan shayi, da dik wasu abubuwan da tasan za a buqata Wanda ta dinga tanadi kamar ita ce zata haihu, hatta da kayan jariri se da Sakeenah ta tanada, dan tasan halin Yayar ta ta,ba lallai tai hakan ba, suna isowa tana haihuwa, murna a wajen su ba a magana, Sakeenaa kam har da kukan dad'i, aka buqaci kayan da zasu gyara yaro a saka shi nan Auwal ya yi qifi2 da ido, miqawa ya ga Sakeenaa tayi, nan take zuciyar shi ta bata waje mai katuqar girma da mahimmanci, dan ya tabbatar ita mace ce me kirki ba kamar yayar ta ba, murmushi ya sakar mata na godiya dan bai da bakin yin ta, Adnan ne ya bi Doctor bayan ta fita daga dakin, Office yaje ya tambayi kud'ad'en da za a biya be fito ba kuwa se da ya  biya kudin komai, fitowa ya yi ya miqa ma Auwal receipt fuskar shi ba yabo ba fallasa,dan shi haushin yanda Rasheedah ke wa matar shi yake, shiyasa haushin Rasheedan ya shafe shi,  hawayen da yake maqalewa ne ya gangaro masa, nan take ya hau godiya ba iyaka, sai can yamma aka sallame su suka wuce gida. Sun isa gida lafiya, nan da nan Sakeenah ta Maida hankali ta dora ruwan wanka, Rasheedah na d'aki ta saka baby a gaba ta na kallo, cike da so da qauna irin ta d'a da mahaifiya. Can gidan iyayen su kuwa tinda maman su ta ji an sauka lafiya, se ta yi musu girki mai rai da lfy ta aiko masu da shi, Sakeenaa ita ce ta ke wuni a wajen ta tin da akai haihuwar dan gidan d'aki d'aya ne ba zai Yu ta kwana ba shi ya sa sai dare ta ke tafiya, komai da ya kamata a ce ta tanada kan haihuwa ashe babu, ran Auwal ya yi matiqar baci, ashe duk 'yan kud'in na shi da take tattarewa ta ce zata sai abu saboda haihuwa ba siya take ba? Qwafa ya yi yace Allah ya basu rai da lfy se ya yi maganin ta. Ranar suna Sakeena akwati daya qarami ta yi musu na kaya a shaqe yake da kayayyaki na jariri da na uwar, sai dubu ashirin da ta kawo ta ba wa Rasheedah, har yanzu ta kasa reading face din yayar ta ta, fatan ta Allah yasa daga wannan lokacin qiyayyar da take mata ta tafi, Allah ya maye gurbin qiyayyar da son ta a zuciyar 'yar uwar ta. Yaro yaci suna Yousuf, ya ci sunan mahaifin Auwal se dai mu ce Masha Allah yaro ya ci sunan dan kuwa akwai kyau, mahaifin Auwal mutumin kirki ne sanda ya na raye shi yasa ya Masa takwara, Auwal saboda maraici ya sha wuya a rayuwa sosai, ga ba wani ilimin zamani sosai,gwanda ma na addinin, yana da shi, shima ba wani sosai ba, a qalla dai ba za a kira shi jahili ba, yace suna kiran yaro da sunan shi bai son wani iyayin b'oye suna, haka ko ake kiran shi da Yousuf din shi. Yau kusan shekara ɗaya da rabi kenan da haihuwar yousuf, Rasheeda na dauke da wani cikin ba tare da ita Kan ta ta kula da hakan ba, Yousuf ya yi wayo sosai, yawon shi yake ko ta ina, ga surutu Dan dik abinda ya gani ya San sunan shi, zai iya baka labari tsaf ka fahimci abinda yake fad'i kowa na mamakin wayo da qoqari irin na Yousuf. Sakeenaa kuwa a wannan lokacin hankalin ta in ya yi dubu ya tashi, saboda rashin haihuwar da bata samu da wuri ba har qasashen waje sun je, ance lafiyar su qalaou su dika,a dik sanda Adnan ya gan ta cikin damuwa ya Kan zaunar da ita ya ce, " Haba my love ki daina kukan nan haka ya isa, ki zama mai tawakkali ga Allah kar ki nuna wa Ubangiji ke kinfi qarfin ya jarabce ki, haihuwa ta Allah ce fa, in ma tsoro kk zan qara aure na maki alqawarin ke daya kin ishe ni rayuwar duniya, ni har qasan zuciya ta ban da sha'awar tara mata da yawa, sai dai in Allah ne ya qaddara min, ki yi hakuri kin ji My love?" Kukan ta kan ragu amma ba dan ta daina ba ba kuma dan ta daina jin zafin rashin haihuwar da batai ba. Hankalin ta bai qara tashi ba sai wata rana da ta ziyarci Rasheedaa ta gan ta, ta tabbatar ciki ne da ita, a cikin zuciyar ta ta hau godewa Allah da neman gafarar shi sannan ta yi wa yayar ta addu'ar Allah ya qaro mata zuri'a ta gari me albarka. Hira suka ta sha wanda gaba d'aya akan qorafin Babu da talaucin Auwal ne, qaiqayin baki ya Kai Sakeenah da fad'a wa Rasheedah hasashen ta na ko dai Wani cikin ne da ita? Shiru Rasheedah ta yi ta na tinanin rabon ta da period da Kuma hali na kasala da yawan amai da zubda yawu da take, Wani irin tashin hankali ne ta ji ya mamaye ta,nan da nan ta fara zage zage da qudirin zubar da cikin,Sakeenah ta yi data sanin Sanar da Rasheedah hasashen da ta yi, tin Rasheedah na fad'a da zage zage Sakeenah na gane wa har ta dawo ta dena gane komai, kalmar Rasheedah ta qarshe ce ta daki kunnen ta, da sauri ta kalle ta da kallon amma baki da hankali ko? Sanan ta ce mata, "Kin kuwa San me ki ke fad'a? Wai ke me ya sa a kullum ki ke adawa da dik wata ni'ima ko jarabawa da Allah ya ke maki a rayuwa? Kin kuwa San hakan da ki ke babban laifi ne? Ki kalle ni mana ban ishe ki misali bane, tare fa aka mana aure amma ko b'ari ban tab'a yi ba, ga qawayen mu da aka wa aure a bayan mu dik sun haihu, shine ke dan kin samu Allah ya baki ki ke so ki masa butulci?" "Dalla malama rufe min baki, tinda Allah ya wanke miji d'an gaske ga dukiya ya baki dole ki ce haka mana, ni da ni ke cikin daular da ki ke Kuma bana haihuwa me zai damen, ba se kawai na ci duniya ta da tsinke ba, amma ki dube ni fa ki gani, dik gayu na da kyau na na b'ige a auren magini, maginin ma qaramin magini talaka, haka kawai se na hau tara Yara tsufa ya kamani da wuri, ga babu ga tsufa nan da an kwana biyu ya ce zai qara aure ko? To ba zai Yu ba,idan ba zaki goyi bayana ba ki kama gaban ki dama ban gayyace ki ba, ni banda baqin naci ma ban ga me ya sa ki ke min sintiri a gida ba, mtsww aikin banza" Sakeenah na zubar da hawaye yau ma ta bar gidan yayar ta ta, ta na qudirta anya ba zata bi shawarar Adnan ba ta dena zuwa tinda ba ta San darajar ta ba. Tafiyar Sakeenah ba jimawa Rasheedah ta hau kukan baqin ciki da data sani ta yi tsarin iyali, a qalla Yousuf ya qara wayo Kuma wataqila Kan nan arziqi ya same su, se ta ji dad'in sake jiki ta haihu, amma ga talauci ga taron Yara kamar a idi, inaaa ba zata Iya ba. Auwal na shiga gidan ta je da gudu ta fad'a jikin shi, se kuka take ta na shagwaba tare da buga qafa a qasa, ya na mugun son wannan bangaren nata na shagwaba da runguma da narkewa da take a jikin shi, ya na sa ya ji kamar shi kad'ai ne Wanda ta jingina a jikin shi take neman ya warware mata wata matsala ko damuwar ta, qara rungume ta ya yi shima tsam a jikin shi, ya ja ta suka shiga d'aki, a bakin gado sika zauna ya hau tambayar ta meyake damun ta, " Auwal na kasa cin abinci yau, zuciya ta na ta tashi, ga jiri danake yawan gani, wai shine fa daga  zuwan yarinyar nan ta kallen wai ciki garen," Ta qarasa cikin matsanancin kuka, murna ce ta kama Auwal, ganin haka yasa ta tsagaita da kukan ta, ta kalle shi, " Ya naga kana murna?" Amsa ya bata da, "Ba dole ba Allah mai kyauta da qari ya qaran, Allah na gode maka, Allah ka sauke ta lafiya ka raya mana abinda ke cikin ta" yana ta zabga addu'o'in shi ta ture shi tana bin shi da wani mugun kallo, "To ni yaushe ma na warke da zan sake wata haihuwar? dika2 ko shekara biyu ban ba da haihuwa na sake wata? Ehhh tin da ba da duwawun ka za ai haihuwar ba kuma ba a cikin ka za a kwanta ba kayi murna mana" Cikin kuka ta fice tana surutai, shidai bai ce mata komai ba, dan tabbas ya san ta wahala, ci gaba da cire kayan shi ya yi yana ta murna,ita ko parlor taje ta kwanta tana ta rusa kuka,har Yousuf yazo yana kuka sosai shima dan ganin ta na kuka, daka masa tsawa ta yi ta kore shi, shiru ya yi yaron yaqi tafiya kuma yana ta kallon ta, daga baya haka ta yi bacci a wajen, Auwal gyara mata kwanciya ya yi ya rab'a mata Yousuf ya fiddo mai cikakkun nonon ta ya bashi ya yi ta sha,har shima baccin ya dauke shi. ***************************** Sakeenaa ce kwance ta yi zugum idonun ta sai tsiyayar da hawaye su ke, ko dai zuwa za ta yi wajen Maman ta ta sanar da ita rashin haihuwar ta wataqila zata sama mata wata mafita, Kai koma ba ta samu mafita ba a qalla zata samu ta yi sharing damuwar ta da Wanda zai damu da damuwar tata, ba kamar Rasheedah ba da bata damu da dik Wani hali da take ciki ba, shawara kawai take da zuciyar ta wani tinanin ya fad'o mata........ [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼            WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* Page 5: Duk wani qoqari da yunquri na Hana tafiyar nan Rasheedah ta yi ta gaji, dan kuwa bata samu nasara ba, har nuna wa Abban su rashin dacewar karbar tayin tafiya makka da Adnan ya musu sai da ta yi,ta ce kar mutane su ce sun aura mashi 'yar su ne saboda abun duniyar da yake da shi, da ta ga Abban zai gano irin hassada da kyashin da take wa qanwar tata, sai ta fake da cewar wai a ganin ta tinda shi Abban na da azziqin shi shima ai be Kamata ya bari har Adnan ya ce ze biya masa ba, sannan ai ba yau ya fara zuwa hajjin ba, Abba kuwa ya ce mata, "Rasheedah ai Adnan ko a hanya muka had'u ya biya min makka na koma Hajji da gudu zan karb'a ballantana ya na auren 'ya ta, Kuma ni ban banbanta a tsakanin surukai na da yaran da na haifa ba, musamman da abun ya zo da dikkan su marayu ne, dan haka mu yanzu ranar tafiya kawai muke Jira mutane kuma sai su yi ta fad'an abinda suka ga dama, ni dai Ina maki nasiha da ki riqe zumunci domin Allah, ki so 'yar uwar ki kamar yanda take son ki ko sama da haka, Allah ya had'a min Kan ku ya muku albarka" Cike da yaqe dan ba haka ta so ba, ta amsa addu'ar shi sannan itama ta hau musu addu'o'in Allah ya Kai su lafiya ya dawo da su lafiya, har lokacin tafiya ya yi Kuma ba ta yi magana da Sakeenah ba akan tafiyar, har gidan ta Sakeenah ta je dan yi mata sallama da ta d'akko maganar tafiyar se ta kauce, ta hau yi mata Wani maganar, ko Kuma ta yi shiru ta qi cewa komai. Ranar da zasu tafi kuwa ko gida bata je ba dan yin sallama da iyayen ta, ta waya ta kira su ta maqale murya ta ce bata da lafiya ba zata samu zuwa ba, fatan samun sauqi suka mata, suka yi sallama ta waya, Sakeenah na karb'a dan su yi sallama ta kashe wayar ta ta na zage zage. Auwal kuwa ya ce mata, "Shi yasa ma har yanzu ki ke a haka cikin talaucin da ki ke zagi, ke ce me qashin tsiya shi yasa har yau ban kudance ba, hassada Kuma ga Mai rabo taki in ji bahaushe" hararar shi ta yi suka ci gaba da fad'i in fad'a a tsakanin su. Ko da suka Isa qasa Mai tsarki babu wasa babu kama hannun yaro dikkanin su se suka dirfafi ibada da yin abinda ya Kai su, Sakeenah ta dage da neman gafarar Allah da Kuma  fatan Allah ya bata zuri'a mai albarka,  Allah ya gafarta wa iyayen ta da dikkan musulmi, tayi addu'a sosai har wataran takan kasa furta me take so ta roqa se kawai ta fashe da kuka, Allah ya san abinda bawa ke so kafin ya furta. kwanakin su na cika suka hau haramar dawowa Nijeria daga Makkah,inda su Mama da Abba suka dawo su kuma suka qara gaba yawon shaqatawa da bud'e ido, dan ya mata alqawarin jin dad'i matuqar yana raye da rai da lafiya kuma da arziqin shi, spain suka fara zuwa dan Sakeenah na son qasar ta na gani a TV yanda masoya ke shaqatawa, inda suka yi sati d'aya ji ta yi kamar kar  su  bar qasar, daga nan suka wuce Cairo, anan ne suka samu waje suka yi zaman su dama ya na da gida a qasar tin Wanda mahaifin shi ya siya musu saboda in sun je hutu su sauka a muhallin su ba hotel ba, rabi da kwatan kasuwancin Adnan dama a  nan ya fi yawa, su na nan zaune har  sai da Rasheedah ta haihu,mutanen gida na ta tambayar ta yaushe za su dawo ne? Sai ta ce musu su na nan tafe, a hankali ta fara gajiya da zaman qasar tinda watarana in ya fita ya na jimawa kafin ya koma gida sai ta yi ta kewar shi ta ji gidan ya mata girma ita kad'ai, a hankali ta fara masa kukan ita ta na so ta dawo gida, ganin hankalin ta ya yi gida ne ya Sanya shi siyan ticket din komawa Nija, Sakeenah dai na qaurnar dawowa qasar ta ta gado Nigeria (Allah ya qara mana lafiya da zaman lafiya a qasar mu ta gado ya zaba mana shugabanni na gari) shiri take cike da murna da doki, ta matsu ta ganta a gida she really want to see her family ta yi kewar su da yawa. Adnan ya lula duniyar tinani Sakeenah na ta had'a musu kaya, a da yaqi su koma gida, so ya yi har sai ta samu ciki ta haihu, sannan su koma da jariri ko jinjirar su a hannu, ba dare ba rana kullum yana kan yin abu daya, kawai dan ya samu ta samu ciki ko hankalin ta ya kwanta ga addu'a su na ta yi amma shiru, a kullum tinanin me zai dan ya sama mata farin ciki yake,a wannan karon ya tabbatar da cewa komai son ya faranta mata Allah ya fishi son ta, kuma shi ya gadama bai bata ba dan haka sai ya ja baya ya barwa Allah ikon shi, har ta gama had'a kayan be sani ba ya na riqe da rigar ta da ya d'auka dan ya taya ta ninkewa,ta kalle shi ta jinjina Kai, dan ta san wannan dogon tinanin ba ya rasa nasaba da halin da take ciki, ita Kan ta ta San ta yi dacen miji Wanda kowacce mace a duniya zata yi fatan ace mijin ta ne, amshe rigar ta yi ta aje a saman gado, sannan ta raba qafafun ta ta zauna a jikin shi tare da saqale hannyen ta biyu a wuyan shi, ta hade goshin su waje d'aya ta ce, "Tinanin me kk bayan gani kusa da kai, daka miqa hannun ka kuwa  zaka tab'o ni, ni kuma daka tab'o ni zan taso willingly to give u what ever it is u desire from me," Murmushi suka yi a tare, ya lakace hancin ta, a binda bata so kenan ya lakace mata hanci shi Kuma sarar shi kenan, ai ko kan ya sauke hannun nashi  ta kama ta ciza ta sauka da sauri ta gudu parlour,tabbas ya ji cizon ya shige shi,dan haka be b'ata lokaci ba ya bi bayan ta yana yarfe hannu kamar wadda ta gutsure wa yatsan, yana raki, " Ka dena abu kamar wani karamin yaro mana please, se kace Wanda na cire wa yatsan? Maganin ka kenan tinda baka Jin magana....my love ka ga gobe zamu koma gida ka yi hakuri kar ka rama sai mun isa gida please ," "Lallai ma yarinyar nan, ni Zaki yi wa wayo? Se da ki ka cijen ki ce Zaki bani hakuri? Lala lala in ji larabawa, anan ki ka min anan zan rama" Bin ta ya yi suka fara kewaye gidan,ga Sakeenah da gudun tsiya da  zamiya,kullum suka fara irin haka sai dai ta basshi ya kama ta kawai in ta ga ya wahala, amma ba dai ya kamo ta da kan shi ba, ai ko gudu ta saka suna ta zagaye gidan, tana mai dariya yana mata warning ta tsaya shi ba abinda zai mata, tace tabb in ba abinda zai mata meyasa yake bin ta,kitchen ta shige ta boye a qasan dinning table da ke ciki, " My love ki fito ki ji, ya isa wasan haka, kin shige nan in iska ta maki kadan fa,na yafe maki, i promise ba abinda zan maki," "Ka yi alqawarin?" " Yes na yi alqawarin,just come out kin ji na yafe miki" A hankali take tashi dan ta San halin shi be San inda take bane shi yasa yake mata wayo da ta fito ya kama ta, haka kuwa aka yi,dan tana fitowa ta na waige waige ta ga ta Ina ya tsaya  ta ji ya cafke ta ta baya,qara ta saka, sannan ta yi ta dariya, sama ya yi da ita yana fad'in " Wa na kamaa?" "Please Mine ka kyale ni,ka fa yi alqawarin ka yafe min" " Yes na maki alqawarin ba zan rama ba, amma ai ban maki alqawarin hana ki soyayya ta ba ko?" Yana fada yana dorata kan dinning table dake cikin kitchen din yana dariya, dariyar ta ta rage tana jifan shi da Wani mayataccen kallon da ya sake birkita shi, nan da nan zuciyar shi ta hau tsananin bugawa, idanun shi sun nuna zallar yanda ya ke Jin ta a zuciyar shi, gani na yi kamar ba layin Yara suka fara d'auka ba se na ja qofar kitchen d'in na koma kallon cartoon a parlour. Washegari da misalin qarfe takwas na safe jirgin su ya tashi daga Ciro international airport zuwa Nigeria,tafiyar awanni biyar ne da 'yan mintuna ta iso da su Aminu Kano international airport,cikin baccin da be jima da daukan ta ba ta ji ana sanar masu isowar su gida Nijeria, zasu sauka ta garin kano, dad'i ne ya kamata, cikin zuciyar ta take jin dama ace tana sauka taga mutanen gidan su da Rasheedah da babyn ta, inama ta bude ido ta ganta gaban ta ta rungume ta ita da abinda ta haifa da Yousuf. "Tinanin me kike?" "Tinanin Mama da Abba da Rasheedah da iyalan ta nake, ba qaramin son na gan su nake ba," "karki damu ko da dare ne zan kai ki wajen su in baki gaji ba ," Maqale hannun shi ta yi dan murna, ji ta yi in ya mata haka ya gama mata komai,suna sauka drivern shi ne ya zo daukar su, bakin shi yaqi rufuwa dan murnar ganin iyayen d'akin nashi, koba komai suna cin mai kyau, suna shan mai kyau sanda Hajiya na nan,amma tin da suka tafi sai dai su saya su ci, ko su ci girkin masu aikin ta mata, a cewar su kuwa basu Iya komai ba. Wanka da sallahr azahar  kawai Sakeenah ta yi ta hau bud'e akwatuna da jakunkunan da ta yo wa mutanen gidan su tsaraba, ta hau ware na kowa ta na sa wa a inda ya dace lokacin da ta gama qarfe uku na rana ta yi, gani ta yi da sauran lokaci kafin su fita, gashi ta Saba wa Adnan da cin abincin ta, tashi ta yi ta fad'a kitchen sai hana ta yake ya na cewa ta zauna ta huta, ta ce, "Se kace wadda ta tuqo jirgin? Ni da na sha bacci na ma ka bari kawai na sama mana abu me sauqi yanzun nan" Cikin ranta ta na ayyana ai dole ne ta kyautata masa duba da yanda yake kyautata mata  da iyayen ta Shima, ko a can waje da suka je, ita ke masu girki, har abokan shi na can yake kawowa, suci su qoshi Kuma su na yaba mata sosai. Dama da suka dawo ta tarar da gida a share a goge fes, sai dakin shi da nata ne kawai ba a gyara ba, saboda basu bar ma key ba balle a gyara, da niyyar in ta gama girkin zata shiga ta gyara  ta na zuwa da kayan shara da goge goge ta ga har ya sauya zanin gado, ya wanke bathroom, godiya ta masa sannan ta ce ya bata waje ta qarasa shi Kuma ya qi, ya ce sai dai su yi tare, ba yanda ta iya da shi haka suka had'u suka gyara dakunan su tare, har mamaki Adnan ke bata in ya na ayyuka irin wannan a gida, kamar ba shi ne hamshaqin Mai kud'in nan ba, Wanda ake nunowa a TV ya na baza babbar riga da baza turanci, lokuta da dama in ta masa qorafi akan yanda yake mata aikace aikace sai ya ce mata, "Sakeenah dik dukiya ta da d'aukaka ta da Wani qasaita ta bata Kai ta fiyayyen halitta ba, ni ba kowa bane a Kan shi amma Yana yi wa iyalan shi hidima, shi ne Wanda ya fi kowa kyautata wa iyalan shi, ni Kuma Ina so na yi koyi da shi, ko da ace ban yi komai da yake yi Sak da Sak ba Ina so na kwatanta, sannan in ban miki ba wa zan yi wa ban da uwa banda uba bani da Yaya bani da qanne se kawunai da baffani ke shaida ce Ina kyautata musu Ina sada zumunci na da su, amma ke ce a yanzu ya zama dole na ba wa kulawa sama da kowa a rayuwa ta" Duk sanda ya fad'a mata haka ta kan ji wai shin ita me ma take masa ne a rayuwar zaman su na kyautatawa? Su na kammalawa suka yi wankan su a tare, kamar ko da yaushe doguwar riga ta saka da ta siya a can Ciro,ta yi rolling Kan ta da mayafin rigar ruwan Zuma da ta sha adon stones da saqa me kyau a jikin ta,ta yi matuqar kyau, baqin ta irin mai sheqin nan ya na ta d'aukan Ido sosai, duk wanda ya kalle ta sau daya sai ya yi na biyu,niqab din ta ta daura, ta samu waje tana jiran shi ya idar da sallah, su na wanka ta ga baqon ta ya zo (period) se kawai ta ke tasbihi daga zaunen, subhanallahi wa bihamdihi subhanallahil azeem, astaghfirullah wa'atubu ilaik ya rahman, subhanallah, Alhamdu lilLAAH, Allahu Akbar, subhanallahi wa bihamdihi adadakhalqihi waridhanafsihi wazinatu arshihi wamidadakalimatih,su take ta maimaitawa,dama Sakeenah ta riga ta Saba da yawan tasbihi ko aiki take ana samun ta tana hailala, da hauqala,ko hira take a ka dan yi shiru to fa za a ga ta na tasbihin ta( hakan na sa mutum ya zama mai kwarjini bayan ladan da zai samu, Allah zai so shi, dan shima yana son Allah, sai kana son abu kk ambaton shi, sannan Allah zai sa bayin shi na gari su soka kaima, akwai fa'idodi marasa adadi wajen ambaton Allah, wadda ta ke yi Koda yaushe zata fi gane me nake fad'a)tana zaunen ya shigo kallon' kina burge ni Sakeenah ta' ya bita da shi, dan ba qaramin kyau ta masa ba a hakan, hanun ta ya kama ya miqar da ita su na Yi wa junan su Murmushi, sannan ya dauki akwatuna biyu da jakar ta suka fita Gate me gadin gidan su ya bud'e wa Adnan ya fitar da mota shi ba su tsaya a ko Ina ba sai a qofar gidan su Rasheedah, da sauri Sakeenah ta bud'e motar ta shige ciki tana kwalawa yayar ta ta kira dan gidan Rasheedah ya fi kusa da gidan ta akan gidan iyayen su shi yasa suka fara zuwa nan, yousuf na zaune yana cin tuwon masara miyar kubewa d'anya, ta ji kifi, ai ko ta d'aga shi sama ta yi tana masa wasa, yana ta dariya, dik da lokacin da suka tafi yana qarami, shekarar shi bata fi daya da watanni ba, dan haka ba wani gane ta ya yi sosai ba, "Ina baby Sulaiman yake? Da kewar ku na dawo Yara na a ban Sulaiman na gan shi, gani na dawo a bani yaro na in ganiiiii" Yatsina fuska Rasheedah ta yi ganin irin shigar alfarma da kyaun da qanwar ta ta sake yi kamar wata baqar balarabiya,miqa mata shi ta yi ta na yatsina, Auwal kuwa na mata sannu da zuwa tare da miqa mata yaron da ke hannun shi ya na bacci, Rasheedah ce ta kasa boye yanda take ji game da kyan da Sakeenah ta yi, madadin ta yabe ta Kai tsaye se cewa ta yi, "Ko dai ciki ne da ke naga kin qara kyau," Murmushi Sakeenah ta yi ta d'an rungume Rasheedah da gefen hannun ta na dama ta ce, "Ba ciki bane, dan yanzu ma bani da tsarki" " kaiii Sakeenaa halin ki na yarinta na damuna ni dan Allah sake min kafad'a kar ki karya ni ki takaici Yara na, tinda kin d'auke shi gashi nan ki gan shi kafin ya yi fushi ya ce se yau kk zo ganin shi" Sakeenah dai bata kula ta ba, dan yau Cike take da farin cikin ganin su,ba zata biye mata ba ta b'ata mata rai a banza, sake  rungime yaron ta yi ta sumbace shi a chiks din shi both side,fuskar ta na dauke da murmushin da ke bayyana hushiryar ta, itama dai Rasheeda yau duk baqin halin ta sai da ta murmusa, ganin yanda qanwarta ke son yaran ta kamar ita ta haife su, wata mummunar zuciyar ta ce  ta ce mata, 'ke mara wayo ja can dan bata taba haihuwa bane take son yaran  ba dan wai tana qaunar su ba har ran ta, da ace ta na da nata ko kallo basu ishe ta ba, yanda suke cikin daula ba ganin ta ma ba Zaki na Yi ba, ki duba ki ga jimawar da suka je suka yi a qasar waje kamar ba za su dawo ba' 'Dan gajeren tsaki ta yi ta zauna, Sakeenah kuwa waje ta yi ta miqawa Adnan yaron ya ko yi masa addu'a Auwal ma bin ta ya yi dan su gaisa da Adnan d'in, yana isa ya washe baki ya ce, "Larabawan makka da Madina barka da dawowa yallabai, ai na zaci ba Zaku dawo ba na ce dan Allah a kawo min qanwata ta zo ta ga d'an ta, .....ya ka tsaya a waje  Bismillah malam Adnan mu shiga ciki," Adnan kad'a kai ya yi ya na dariyar barkwancin Auwal sannan yace, "Da azahar muka dawo fa qanwar nan taka Mai rikici ta kafe ita se ta ga Mama da Abba da yaran ta, ni Kuma ka San burin ta kamar umarni ne a gare ni, dole ne na cika mata shi....amma da ka fara shiga kaga yanayin wajen zai yu na shigo kai tsaye?" Auwal yaji daɗin hakan dan ya San halin gimbiyar tashi, ya baro ta zaune da daurin qirji dama haka take yawan zama a gidan, ko a same ta da  riga daban zani daban kamar mara tufafi, ko da baya samun d'inka mata kaya masu tsada, amma baya rabo da sai mata kayan sawa daidai qarfin shi, Kuma a gida ma ana mata sutura Sakeenah na kawo mata, ta saka complete ne take ganin asara. Shiga ya yi ya mata magana za su shigo da Adnan,dan kwalin ta ta ware ta yafa tana qunqunin za a hana ta sakewa ita da gidan ta, dan rowa da son abun duniya irin na masu kud'in yanzu, su barta ta je masu oyoyon shine ba za su bari ba, sai da suka biyo ta dan kar ta je ta dangwali arziqi, kan ta rufe bakin ta da mitar ta ga an jawo akwati an shigo da shi, cike da takaici Sakeenaa ta kalle ta dan kuwa ita da Adnan ba abinda basu ji ba....... Rasheedah a sauya hali...... . [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262*   Page 6: Wani yawu ta had'iya ji ka ke  "maqawat" se zare Ido take,idanun ta akan akwatin da ke hannun Adnan, kallo suka bita da shi jin maganganun da take sun tsaya cak, ba kunya ba Jin nauyin kowa Rasheedah ta miqe daga inda take zaune ta Isa gaban su,hannun ta na rawa fuskar ta d'auke da murmushi da zumud'i ta durqusa gefen Adnan tana masa sannu da zuwa, tare da qoqarin karbar akwatin hannun shi,nan  take Auwal ya watsa mata wani mugun kallon da yasa ta ja baya tana zumburo baki, Adnan da Sakeena kad'a kai suka yi dan tsananin takaicin halayen ta, miqa mata akwatin Adnan ya yi har tana tuntube da qafar Yousuf ta karb'e,kuka Yousuf ya sa dan taka shin da ta yi,ko ta kan shi bata bi ba, ta kama akwatin ta yi parlour ta dora saman kujera, qoqarin budewa ta hau yi abun ta, ba godiya ba komai, ba tambayar na waye? Adnan ne yace mata, "Ga tsarabar ku nan Daga Sakeenah ta had'o harda kayan bbyn ta da aka haifa bata nan, Allah ya raya ya sanya albarka, ni kuma ga nawa a sai wa yaro wani abu," Ya zaro kud'in da ban gane ko nawa bane, ya miqawa Auwal, zumbur ta yi ta matso da niyyar karb'a taga har Auwal ya karb'a, wani haushin ta ne ya kama dikkan su, a wannan lokacin ko Sakeenaah idon ta ya cika fam da hawaye, qoqari kawai take wajen riqe su, tin da ta zo fa duk d'okin ganin yayar ta ta, ita ko a jikin ta ba ta nuna ma tana farin ciki da ganin ta ba, kuma bata mata kyakkyawan sannu da zuwa ba, amma da ganin abun duniya ta rud'e, anyaaa???? "To mu zamu wuce dare na yi asuba ta gari,dan a yau muka so duba su Mama ma, amma da alama se dai mu bari zuwa gobe saboda dare ya yi" Adnan ne ya furta hakan ganin yanda matar shi take gab da fashewa da kukan baqin ciki,  kamo hannun ta ya yi, a hankali ta furta masu, "Sai da safen ku Yayah Auwal ... My boy kayi bacci lfy ko Allah ya muku albarka," Kuka Yousuf yasa sosai da zasu tafi,ya maqale ta, sai zabga ihu yake yana fad'in zai bisu, Sakeenaah ce ta ce, "Yayah Dan Allah ku bamu shi mu tafi da shi mana, in ya so gobe in zamu je gidan Mama sai mu kawo shi" Cikin Jin dad'in yanda Sakeenah ke son yaran su Auwal ya ce, "Dakko mai kayan shi ya bisu,dan kin san shi da kafiya ko sun tafi ba zai daina kukan nan ba ya samu abin yi kenan yau," Wani mugun kallo Rasheedah ta watsa wa Auwal, sannan ta kalli yanda Sakeena ta kwantar da yaron a kafadar ta yake ta ajiyar zuciya, ita kuma tana shafa bayan shi cikin lumshe ido da kaunar yaron, " A'a a ,a bar min d'ana a gidan uban shi domin shi bai saba da gidan masu akwai ba, da gidan talakawa ya saba,haka kawai ya je ya ji dad'in gidan masu arziqi nan gidan ya gagare shi zama, ba zai yu ba," Cike da rashin mutunci na ba sani ba sabo take maganar, cikin kuka mai qarfi Sakeenaa ta dire yaron ta fita da gudun ta, tana kuka, Adnan ji ya yi kamar ya shaqe Rasheedah, wani mugun kallo ya watsa mata ya matsa daf da ita ya na nuna ta da yatsan shi manuni ya ce, "Wai ke wace iriyar mahaukaciyar mata ce wadda bata San menene zumunci ba, bata San mene ne so da qauna irin ta 'yan uwantaka ba? Anya Rasheedah ki na da zuciya a qirjin ki kuwa? To ga d'an naki nan an bar maki Dan Allah ki jiqa shi ki shanye shi idan ana sha wawuyar banza kawai, kuma in Allah ya yarda in dai ni ne mijin Sakeenaah ba zaki qara ganin ta taka qafar ta ba a gidan ku, sai dai in kin canja hali, Allah ya cece ki na ga qafar ki Kuma a gidan masu halin ki ga yanda zan maida ki, shashasha kawai," Cike da fushi ya fice, Auwal kuwa daskarewa ya yi a wajen , kunya, tsoron halin matar shi, da kuma tausayin Sakeenaah ne danqare a zuciyar shi, kasa ce mata komai ya yi, dan yana ganin in dai ya yi magana ta mai shirme sai ya kirb'e ta kamar kubewa a turmi, d'aukan Yousuf ya yi da yake ta tsala kuka, ya zaro alawa a aljihun shi ya b'are masa ya bashi, da qin karb'a ya yi da fari, amma da wayo da dabara ya hakura ya karb'a ya yi shiru, nan da nan bacci ya dauke shi, a haka ya dauke shi suka je tare ya rufe gidan sannan ya wanke masa hannu da baki, daya ci tuwo dazun, ya kai shi ya kwantar da shi a shimfidar shi, ya dakko Sulaiman ma ya kwantar, sannan shima ya bi lafiyar gadon su ya yi masu addu'a dika ya fara bacci, gimbiyar na can tana d'aga wannan ta aje, ga murnar samun kaya, ga baqin cikin sanin Daga inda kayan suka fito danqare a ranta, wannan wai tsarabar su ce daga qanwar ta, Allah kada'i yasan ita wanne irin kaya ta lodowa kan ta, oh duniya, taya za a ce qanwarta ita ke da arziqi sai dai ta na sammata, amma ita tana zaune hmmm Allah ya kyauta, Hassada kenan, kana nuna wa Allah be Iya rabo ba, subhanallah, to Duk me wannan halin ya shirya shiga tashin hankali duniya da lahira, hassada yanzu ta yi wa mutane yawa da katutu a zuciya, d'an uwa na yi wa d'an uwan shi hassada, miji ko mata na wa juna hassada, maqoci da maqoci hassada, yanzu a social media ma da baka tab'a ganin mutum ba, da ka ga Wani ci gaba ya same shi se ka dau hassada ka sa a ran ka akan shi, zaman lafiyan da wata ke yi da mijin ta ko da iyayen ta ko da maqotan ta ya zama abun hassada a wajen wasu, kar muna mantawa dai hassada na tattare da babban mummunan sakamako Allah ya mana tsari da ciwon hassada. Gama surutan ta ta yi ta miqe ta shige d'akin nasu bayan ta rufe akwatin, tana shiga ta hau cire kayan ta ta kwanta kusa da Auwal, duk sha'awar da ya ke ji, kan ya shigo gidan, yanzu ta kau, me zai da ita yanzu? Shi tsoro ma take bashi yanzu, in dai zata iya nunawa qanwar ta qiyayya haka to shi waye? Shafa shi ta somayi, ya rintse ido, nan da nan jikin shi ya fara karbar saqonnin ta,amma saboda kafiya da dauriya, ya tura ta, "Dalla malama meye haka? Kar ki ban haushi kici dan banzan duka da daren nan,ki ja zumman jikin ki ki yi bacci, sai da safe, ke kin ma San me? Gaba d'aya kin fara fita a raina Rasheedah, ban San kalar zuciyar da ki ke da ita ba,qanwar ki uwa d'aya uba d'aya ki ke wa irin wannan qiyayyar? Bayan yarinyar nan bata da burin da ya wuce na ta ga ta kyautata maki da iyalan ki, amma ke kullum burin ki ki nuna mata hassada qiyayya da kyashin da kk ke yi mata a fili, kar fa ki manta ko iyayen da suka haife ta bata je ta gani ba ta zo nan, dik da sun fara zuwa ne dan nan ne a hanya amma da ta so da can gidan ku ta wuce, ashe rabon ki b'ata mata rai da farin cikin ta ke cikin ran ne,tirrr da halin ki Rasheedah, magani na kenan na bin auren kyau, kyan ki ya rud'e ni na aure ki, kyan ki ne ya sa ni yi miki qarya har se da na mallake ki, ashe kyan d'an maciji ne, gashi nan ki na ta sarar kowa a hankali, Allah ya shirye ki, ki janye jikin ki kafin na lakad'a miki na jaki a Daren nan na fad'a miki" Ya na magana ya na nuna ta da yatsa, kafin ya juya mata baya, amma da yake yar duniya ce, ta san Auwal baya tab'a wuce tayin jikin ta komai fushin da ya yi, ita ce ma ke hana shi Kan ta lokuta da dama, se ta ce se ya siyo mata kaza ko tsire ko balangu kamar tsohuwar mayya, in Yana da shi ya siyo, in babu ya banqare ta kamar kazar ya gama abinda zai da ita, daga baya ya lallashe ta su yi baccin su dan haka ta San lagon shi sosai,yau Kuma gashi itan ma a buqace take da shi, binshi tai ta zira hannin ta a jikin shi tana shafa sensitive areas din shi, tare da bashi hakuri da 'yan surutan soyayya a kunne, tini ya juyo,........ Sai da sika lafa tana kwance a qirjin shi yana wasa da gashin kan ta yace, "Dan Allah yau Ina son sanin menene dalilin ki na nuna wa qanwar ki uwa ɗaya uba ɗaya qiyayya haka?," Numfasawa ta yi ta gyara kwanciyar ta sannan tace, "Na fara tsanar Sakeenaa ne tin muna yara, ba dan komai ba sai dan soyayyar da iyayen mu ke bata ya bambanta da nawa, suna nuna banbanci kwarai ainun a tsakanin mu, ni ce babba amma kamar Sakeenah ce gaba da ni, saboda yanda ake d'aukan girman da qanqantar dik a bata, in bata da lafiya gaba d'ayan su yi suke kamar sune ba lafiyar, amma in na kwanta ciwo ba Mai zuwa inda nake se dai ana min sannu Daga nesa,a ban magani a min allurai shikenan ba wata kulawa da nuna tausayawa, kafin a sai min Abu sau d'aya an sai mata sau biyar, komai suke da shi za ka ji sunce na  Sakeenaa ne, ko ka ji su na cewa sakeenaa ta fiki hankali,Sakeenaa ta fiki ilimi, Sakeenaa ta fiki tausayi, Sakeenaa ta fiki kyau, Sakeenaa Sakeenaa Sakeenaa, sunan ta ya min yawa a kaina, sunan ta ya cika zuciyata da baqin ciki, duk qoqarina iyayena da malamai na dama kowa baya gani sai na Sakeenaa, akan me? Ni ba halitta bace,ko ba su suka haifen ba,gashi saboda mugun bakin da suke min kullum akan ta fini komai na b'ige da auren ka a matsayin talaka,ba wai kai na tsana ba ko nake dana sanin aure,A'a ina jin haushin babun da kk ciki ainun, ita tana cikin halin yalwa, na baka labarinnan ne dan kasan dalilin qiyayya ta akan ta, ba dan ka ban shawara ko ka qara min abinda zai sa na ninka tsanar ta a zuciya ta ba, dan haka yanda ka ji kai shiru da bakin ka," kad'a kaii kawai Auwal ya yi yana mamakin wannan wauta ta Rasheedah,duk da yasan laifin ya samo asali daga mahaifan su ne, domin duk son da kk wa d'a a cikin yaran ka ba a son kana yawan nuna wa, ka danne kowa ya zaci shi kafi so a yaran ka, ana so kowanne yaro ya ji cewa an fi son shi sama da d'an uwan shi har se da Kan su sun gane cewar ashe fa Mama da Baba Suna son kowannen mu equally ba banbanci, amma ku a ranku Kun San wa ku ka fi so,da Kan su  zasu fahimci cewar ashe mahaifan mu na son mu ne gaba daya ba wanda suka ware? To sai soyayar ku ta mamaye zuqatan su, sannan kuma su samu had'in kai mai girma,( Allah ka sakawa iyayena da alkairi da dik iyayen da suka zamanto masu adalci a wajen yaran su, Allah ka yafe wa iyayen da suka nuna wa yaran su banbanci Ameen). Juyawa ya yi ya kwanta, ita ma ta kwanta,amma idon ta biyu, ko wanka basu yi tinanin zuwa suyi ba, kullum sai a suba suke yin tsarki su. ( wanda ba daidai bane hakan, ba a ce hakan haramun bane amma rashin dacewa ne,ka kwana cikin rashin tsarki, akwai mugayen da in kai me riqon ibada ne sun rasa hanyar cutar ka to da wannan damar zasu cuce ka, sannan baka San yaushe ne lokacin mutuwar ka ba, ai ko ba komai da dad'i a same ka cikin tsarki,dan haka ko haila mace keyi ake son ta na yawaita tasbihi, da karanta qur'ani kai koda iya qulhuwallahu ahad ta haddace tai ta maimaita wa) Bangaren su Sakeenah kuwa Adnan na fita waje ya tadda ta jikin motar su ta kifa kan ta sai kuka take, bud'ewa ya yi ya saka ta ciki, ya ja suka wuce gida, suna isa gidan motar na tsayawa ta bude ta faɗa gidan da gudu tana kuka, d'akin ta ta wuce ta rufe qofar ta kwanta a gado tai ta kuka, tana dana sanin zuwa a ranar, biyo ta ya yi ya murda qofar ya ji ta a rufe, bugawa ya hau yi, yana mata magiyar ta bud'e, amma sam taqi, bata taba fushi haka ba, Kuma bai tab'a ganin b'acin ranta irin na yau ba, ta bangaren ta kuwa tinani take, me taiwa yayarta data tsane ta haka,tin tasowar su, ba ta san soyayyar 'yar uwar ta ba, sai dai ta ga wasu suna son junan su abun na bata sha'awa da burgewa  amma banda su, in ta mata abun burgewa sai ya dawo na rashin mutunci da cin fuska, me ya yi zafi haka? Kukan ta ne ya qaru nan da nan zazzabi ya rufe ta dama ga gajiyar hanya bata ko bari ta huta ba wai ita me 'yar uwa ta tafi wajen ta, se abun ya taru ya saukar mata da ciwo biyu, quncin zuciya da zazzafan zazzabi, ta na cikin kukan ne ta ji qarar  abu ya fashe se Kuma ta jiyo Adnan yayi qara,ai da gudu ta sauka daga gadon ta na ganin jiri ta yi waje, shi kuma ya yi haka ne dan ta fito tinda ya saka key din shi ya ji akwai Wani a jikin qofar bazata bud'u ba kenan,se kawai  ya je ya dakko plate ya sake a qasa ya tarwatse sannan ya ya yi qara, ya dawo bakin qofar ya tsaya, aiko budewar nan da za ta yi suka yi karo, a  gigice ta fito tana kwada masa kira,cikin gaggawa ya rungume ta ya maida ita d'akin ya na mata  dariya tare da fad'in, "Wa na kamaaa, yau se kin karb'i hukunci mai girma a waje na, hukuncin rufen qofa da kuma kukan da ki ka yi  kika wahal min da jikin ki ji jikin ki yanda ya yi zafi fa, Dan Allah ki kwantar da hankalin ki kar ki jawo mana Wani ciwon" Bata San sanda ta sake barkewa da sabon kuka ba sakamakon tinawa da abinda ya faru a gidan Rasheedah da ta yi,bai hana ta kukan ba,sai kawai ya rungume ta yana buga bayan ta a hankali, sai da ta yi ya ishe ta sannan ta fara ajiyar zuciya dik jikin ta ya saki, ga Wani mugun zazzafan zazzabi da ke nuqurqusar ta,ji ya yi nauyin ta ya qaru jikin ta ya sake, yana dubawa yaga ashebacci ne ya d'auke ta, juyar da ita ya yi ya fara zame mata kayan ta hankali, cikin nutsuwa ya qarasa cire mata  kayan jikin nata dika, dubawa ya yi yaga pad din ta ta baci, ya dakko wani pant din ya sauya mata wata,ya zame na jikin ta ya aje gefe ya sa mata wanda ya haɗa, daukan wancan ya yi ya kai toilete, ya cire pad din ya nannade ya sa a dustbin,sannan ya wanke mata pant ya shanya ya d'ebi ruwa me rangwamen sanyi da qaramin towel ya je ya goge mata jikin ta ko zai samu zafin ya ragu, bayan ya gama ya Sanya mata sassauqar rigar bacci, ya koma bathroom din ya yi wanka ya je ya kwanta a jikin ta,(namiji d'an gaske Kuma JARUMI ne kawai zai iya kyautata wa matar shi haka) ji ya yi jikin ya rage zafin da ya yi sosai, tsananin tausayin yanda take son yayar ta amma bata samu hakan ba in return yake, ji ya yi cikin bacci tana magana, daya kasa kunne ya ji tana, "Me na yi miki ne da baki sona? Ni ina son ki Rasheedah ta" Tab'a ta ya yi dan ya farkar da ita Daga mafarkin da take, ta na Jin saukar hannun shi a jikin ta ta juya gaba d'ayan ta ta qanqame shi, ji ta yi zuciyar ta na tashi,a hankali ta fara bud'e ido can Kuma ta miqe da gudu ta yi toilet, tana sheqa amai bin bayan ta ya yi shima ya riqe ta, jikin ta zafi kamar wuta, amai take tana qarawa,tana gamawa ta zame a wajen za ta kwanta ya yi maza ya riqe ta, ta kwanta jikin shi, sai ta saka kuka, "Sannu my love, ko zamu je asibiti ne?" Da sauri ta girgiza masa Kai bata so su je asibiti, "To sannu bari mu bari gari ya waye se mu je ko?" 'Daga masa kai ta yi ya kama ta suka koma d'akin ya kwantar da ita shi Kuma ya koma ya gyara wajen da ta yi aman. Washe gari...... [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262*   Page 4: Da sauri ta girgiza Kan ta, tare da tashi ta zauna da kyau a fili ta ke fad'in, " kaiii inaa da kunya na je ina cewa  Mama ta nema min magani na haihu, kaii ba zan iya ba ma, to ya zata kalle ni ma? Ai se ta ce bani da kunya ma" Tana nan zune har qarfe hudu na rana ta buga ga kiraye kirayen sallar la'asar nan dik ya karad'e ko Ina, gani ta yi zaman ba zai yi mata maganin komai ba ga lokacin sallah ya yi kawai  se ta fad'a bathroom ta dauro alwala  ta fito ta zira doguwar riga da hijabi ta tada sallah, ta dade tana addu'ar neman gafarar Allah, da yiwa mijin ta da iyayen ta addu'a sannan taiwa dikkan musulmi addu'a kafin ta yi wa kan ta ta neman haihuwa me albarka ta dad'e sosai cikin sujjadar ta ta na maimaita addu'ar ta, sannan ta d'ago tai tahiya ta yi sallama, tana idarwa ta faɗa kitchen ta haɗa masu abinci dan qarfe shida Adnan ke dawowa, tana girki tana qara gyara gidan, ta je toilet din shi ta qara wankewa, ta fidda masa kayan da zai saka in ya dawo, sannan ta fito,bayan ta kammala girkin ne da gyare gyaren ta koma d'akin ta ta cire kayan ta ta d'aura towel ta shige bathroom dan yin wanka, had'a ruwan wankan ta yi cikin kwamin wanka ta zuba dik wasu abubuwa da take amfani da su wajen wanka, ta d'aga qafarta kenan zata shiga ta ji motsi alamar Adnan ya dawo kenan,Murmushi ta yi na farin cikin dawowar mijin nata ta qarasa shiga, kafin ta zauna ya bud'e qofar ya shiga, da sauri ta zauna ta na dariya, dan Sakeenah mace ce Mai kunya,har yanzu bata Iya bari Adnan ya gan ta ba kaya, se dai ta na saka qananan kayan da za a ce da su da babu dik d'aya ne, to ta fi son haka akan ta zauna ya gan ta ba komai a jikin ta, Murmushi ya yi Shima ya qarasa shiga bathroom din ya hau cire riga, se ni Kuma Hamidatuwa na jaaawo musu gambu na koma Ina jiran su a parlour. Ina zaune na ji dariyar su tare da maganar Sakeenah ta na fad'in, " Zaka fara ko? ko wanne kyau na yi a hakan, bayan ka dawo da wuri, ni da na so se na tsara kwalliya irin ta 'yan gayu se ka dawo" "Tabb ashe kin shirya sumar da bawan Allah marayan Allah se Kuma Allah ya dube ni ya dawo da ni akan Kari, Sakeenah ni Adnan zan iya rantsuwa da Allah ban tab'a ganin macen da ta min kyau Kuma take min kyau a kowanne yanayi take ba sama da ke, ko kin yi wanka, ko baki wanka ba ke Mai kyau ce, ki dinga godewa Allah domin kuwa se a tara mata dubu kafin a samu irin ki goma" Idan Adnan na kod'a kyan ta se ta dinga Jin ta kamar ta fi kowacce mace a dik duniya kyau da kyakkyawan hali, saboda ba ya barin wata kafa ta jikin ta ko ta halayyar ta ba tare da ya yaba ba, " hmmm na gode"  shine kawai abinda ta Iya furtawa ta na Wani tsadadden murmushin da ta San  ya na sake rikita shi, su na cin abinci a saman dinning ma Adnan be shiru ba, ci gaba ya yi da ziga ta da yaba dad'in girkin da had'uwar shi, "Mine ka dena sa wa Ina Jin kaina kamar zai fashe dan girma, wannan irin yabo haka? Ai dik yanda na zama a gidannan Kai ma ka na da babban kaso a Kan hakan, saboda mace na zama ta kirki ne a wasu lokutan gwargwadon irin adalci da kulawar mijin ta a gare ta, kenan ka ga Kai ya fi cancanta a yi wa yabon da ka ke min" "Ba Zaki gane matsayin da ki ke da shi a zuciya ta ba ne, ke dai Allah ya qara min lafiya da arziqi na ci gaba da Baki kulawa kamar sarauniya " "Ameeen, Ina son ka mijin Sakeenah," "Ina son ki matar Adnan" Murmushi ta yi kafin su miqe Daga saman dinning din su yi masauki a kujera Mai cin mutum biyu, kunna TV ya yi ya Kai NTA, kwantawa ta yi a jikin shi ta na shafa qirjin shi sannan ta ce, "Yauwaa my love dan Allah bana muje hajji mana, kaga sai mu samu mu yi ibada kuma mu yi addu'ar da muke da buqata akai ko" Lakace hancin ta ya yi sannan ya sumbaci tsinin hancin nata ya ce, " kamar kin karanci zuciya ta,anya baki min leqen asiri a zuciya ta ba?wannan na cikin tsari na a shekarar nan inshaa Allahu zamu koma hajji ni, ke, Abba da Mama ma duk zamu da su, dan ba zamu tafi ba muje da iyayen mu ba ko," Wani irin dad'i ne ya kama ta ta miqe ta kwanta rubda ciki a kan shi, tana facing din shi tare da rungume shi sosai, shi Kuma sai dariya yake fitarwa a hankali ba abinda ke bashi farin ciki sama da ya ga Sakeenah na farin ciki a rayuwa, kallon shi ta ke cike da tsananin so da qaunar shi da suka ninku a zuciyar ta, d'an qaramin leben ta na qasa ta ciza a hankali cikin kashe murya da kashe Ido ta ce, "Bani da bakin da zan Maka godiya mine sai dai na ce Allah ya jiqan iyayen mu da suka gabata ya kyautata makwancin su ya sa su yi alfahari da samun ka a matsayin d'a na gari Ameen" "Dama ai ba godiya nake so ba, Dan nima iyaye na ne, addu'ar ki kawai nake buqata Dan kuwa addu'ar ki a gare ni haske ce, Kuma alkhairi ce, Dan tinda na had'u Dake alkhairai kala kala ke bibiyata wadannan addu'o'in naki na daga cikin abinda ke qara min ci gaba a rayuwa, kin ga kuwa ni ne ma zan maki godiya ko?" Lips din shi ta kama da yatsan ta ta Dan ja, ta miqe ta gudu d'aki, da qarfi ya furta, "Invitation aka bani in zo kenan? To Gani nan zuwa" da sauri ya bi ta d'akin suka rufe qofar abin su, Bai fito ba sai da aka kira magariba, ya wuce masallaci. Sallah ta gabatar da azkar ta sake gyara abubuwan da suka b'ata, ta Dan watsa ruwa ta saka rigar baccin ta Mai kyau, ga tirarukan da  ta Sanya masu sanyin qamshi, sai ta Dora hijabin ta ta na jiran a yi isha'i, bayan ta idar da sallar isha'in ne ta shiga kitchen ta sama masu fruit salad da  chicken and potatoes salad sai Dan abun sha da ta had'a na abarba  qarfe tara na dare ya shigo, ya na hamma, "Wai kin San ana idar da sallar isha'i kawai se bacci ya dauke ni, maqocin mu ne da zai tafi ya tashen shine muka taho" "Ai dole bacci ya dauke ka, ka wuni aiki, ka dawo ban barka ka huta ba, I am sorry mine" Kamo ta ya yi ya na Murmushi ya ce, "Ni fa da na gan ki da qaton hijabi haka na San akwai wata harkar a qasa, zo nan in gani ba wata I am sorry," Guduwa ta yi suka hau zagaye kujerun Suna dariya, da kyar ya kama ta suka zube a kujera su na dariya, "Dan Allah zo mu je mu ci abinci yunwa nake ji, na San kaima yunwa ka ke ji" Da kyar ya barta suka jera ya na riqe da qugun ta, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna Shima, ta zuba musu abinci suka fara ci. Bayan sun kammala a tare suka gyara waje Wanda suka rage suka saka a fridge ya taya ta wanke kwanukan, suka kashe kayan kallo suka wuce d'aki, ni dai ban bi su ba dan lamarin su Adnan in kana binbini se ka ji kunya. Bayan ya tafi aiki da safe ita Kuma da hantsi ta shirya ta ja motar ta ta yi gidan su ta sanar da iyayen su game da tafiyar da Adnan ya ce za su yi zuwa Hajji, ba qaramin murna suka yi ba, cikin tsananin farin ciki Mama ta sa waya ta kira  Rasheedah ta Sanar da ita abin farin cikin da ya same su dan ta taya su murna,wayyo Allah, Rasheedah ji ta yi kamar ta mutu dan baqin cikin daya kama ta, tana kashe wayar ta hau kuka,  Auwal ne ya riqe ta yana tambayar waya mutu cikin tashin hankali, banza ta yi da shi sai da tai kukan ya ishe ta sannan tace, "Wannan banzar yarinyar ce zata makka,da su Mama, zan so ace ni na fara kai su, ba ita ba, amma dubi yanzu sabida auren talaka qanwar bayana ita zata kai iyayen mu makka," Ta qarasa cikin kuka, wani haushin ta ne ya kama shi kamar ya shaqe ta, ya na mamakin yanda bata Iya b'oye baqin ciki da hassadar ta har se ta yi kuka,anya Rasheedah ba 'yar tsuntuwa bace a gidan? Dan shi yanzu ba safai ya ke Jin haushin zagin da take masa na talauci ba, Cikin Jin haushin maganganun ta ya yi tsaki ya fice daga d'akin, d'aga kan ta  ta yi ta kalle shi ta murguda baki tare da hararar shi, sannan ta ce "Ni ba dan son da nake maka ba na rantse da tini na bar gidan ka na auri mai kudi, haba namiji ace yau ko atampa super ko Holland din nan ba ka tab'a siya ka ce na Kai gida ba, balle shadda me d'an maiqo, kamar Kai ka kawo talauci duniya" Yousuf ne ya shigo yana kuka yayi kashi, wani haushi ne ya qara kamata kamar ta kama yaron ta yi ta duka, da mai kud'i ta aura yanzu ai da tana da masu aiki, ga Sakeenah nan masu aikin ta kusan biyar, wai a haka ma bata son masu girki, gyara parlourn ta guda uku da sauran dakuna kawai ake mata se kula da tsakar gidan da fulawowi da wankin su da sauran abubuwa, amma dik wata hidimar Adnan da kanta take yi,cikin fushi ta miqewa ta daka masa tsawa akan  ya bar mata kuka kan ta doke shi, aiko qara b'are baki ya yi, tako kama shi da jibga,ba ta yi aune ba ta ji maruka masu lafiya ta kowanne gefen fuskar ta, ihu ta kurma ta hau bori, "Dan iskanci kina nan kina shashanci da muguwar hassada yaro ya dakko po zai hau ya kasa cire wando har yayi a jiki shine zaki hau d'a da duka,ke wa ya dake ki a jakancin da kike wa mutane",( makaranta kuji fa har jaka mijin ta ke kiran ta sabida tana mai halayen su) kuka ta ke sosai, ga baqin cikin da ke cin ta in ta tina tafiyar su Sakeenah,ga duka taci a hannun miji,sannan ya sata gaba ta wanke kashin dole,ta na kuka take  wanke masa ta shirya shi, ta koma ta kwanta, tinanin wannan tafiyar da zasu yi take ta yi anyaa zata bari a yi tafiyar nan kuwa?........... *Readers barkan mu da safiya, anya Rasheedah na da head kuwa?* [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAINE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* Page 7: Kafin washegarin ranar aman da ta yi ya fi uku, duk ta fita hayyacin ta, da asuba sallah kawai Adnan ya yi ya kwashe ta sai asibiti, suna zuwa aka hau duba ta, nan take suka gane zazzabi ne kawai ke damun ta, saboda damuwa da ta yi mata yawa, qara mata ruwa aka yi saboda ta samu kwarin jikin ta dan aman da ta yi ya galabaitar da ita, se aka had'a mata da magungunan da za su saukar da zazzabin, likita Kuma ya bata shawarwari na ta qoqarta ta yi avoiding duk Wani abu da zai sa ta shiga damuwa saboda kiyaye Kan ta daga kamuwa da cutar hawan jini, daga baya ya ce wa Adnan ya biyo shi office d'in shi ya na so ya yi magana da shi. A tare suka shiga office din , Dr. Uwais ya zagaya ya zauna a kujerar shi sannan ya wa Adnan nuni da kujerar da ke gaban shi ya ce ya zauna, zama ya yi Suna fuskantar juna likita ya cire gilashin shi ya kalli Adnan ya ce, "Alhaji Adnan a iya sanin da na Maka na San Kai me kula da lafiyar ka da ta iyalin ka ce, amma garin yaya ka bari wannan ciwo ke qoqarin kama matar ka? Ka sani fa matar ka na gab da kamuwa da hawan jini, binciken mu da Kuma tambayoyin da na mata ya nuna akwai matiqar damuwa a tattare da ita, wataqila akwai abinda kk mata na rashin jin dad'i ya sa hakan ke Shirin faruwa da ita, Wanda in haka ne zan yi matuqar mamaki, Iya sani na da Kai Kai mutum ne Mai kula da dik Wanda ke qarqashin shi ballantana matar da kowa ya shaida kana so Kuma kana kula da ita fiye da Kan ka na sani tsakanin miji da mata sai Allah, amma dai dan Allah ka duba kai qoqari ka gyara, ka dinga faranta mata kamar yanda ka saba, ka ci gaba da  kula da amanar da Allah ya baka, in kuma ta wani wajen take samun damuwa ka qoqarta kaga ka toshe mata wannan kafar damuwar, gaba ake gudu,ina fatan ban yi maka katsalandam a harkokin iyalin ka ba,shawara ce a matsayi na na d'an uwan ka Kuma likitan iyalin ka,wadda Ina ganin in kabi a sannu zata samu sauqi da wuri Kuma za a gujewa wannan mugun ciwo na hawan jini," kad'a wa likitan kai Adnan ya yi cikin sauri da kuma gamsuwa da bayanan shi, "Sam Uwais raina be b'aci ba,ta  ya zaka bata min raina akan gaskiya? na ji dad'in shawarwarin ka ainun, amma ina mai sanar maka daga yau damuwar ta zata kau da yardar Allah,Kuma Ina so ka sani bana daga cikin silar damuwar ta amma na san musabbabin hakan Kuma zan d'au mataki akai, haba Kai ma ka San yanda nake son Sakeenaah ba zan cutar da ita ba, na gode Uwais in ka je gida ka gaida su Baffah bari na koma wajen ta,Ka wuni lfy" Uwais cousin d'in Adnan ne, Baban Uwais Yaya ne ga mahaifin Adnan,anan asibitin suke ganin likita, Kuma suke zuwa medical check up. Sallama suka yi da juna, ya wuce d'akin da aka ajiye ta,ya tarar da ita waje d'aya ta dafe kai,tana ta tinani kala2 bama ta san ya iso ba, "Kin gani ba, yanzunnan aka maki maganar rage damuwa amma kin zo kin takura kan ki anan, haba Sakeenaah so kk ki kamu da ciwon da ni zai zame wa masifa da bala'i? Tinda sanin Kan ki ne dik halin qunci ko rashin lafiyar da ki ke ciki na fi ki shiga damuwa, in Kuma ba so ki ke ki rasa ni ba gaba d'aya Dan Allah ki Dena shiga damuwa"   Cikin hawaye ta gyada kai, "To in dai baki son rasa ni ki daina damuwa, komai da ya faru ki d'auka bai faruba ba zan yafewa kaina ba idan wani abu ya same ki,?" Dr. Uwais be sallame ta ba sai yamma,kafin a sallame tan Adnan be Sanar da kowa halin da suke ciki ba shi da masu aikin su ne sukai ta dawainiya da ita, kama Daga Kan abinci ne da Duk wata kulawa dai da take buqata har aka sallame su da la'asar. Bayan sun dawo gida wanka ya mata da ruwa mai dumi sosai jikin ta ya gasu sosai, ta ji dad'in wankan, shima yayi, qananan kaya suka saka dan su sha iska daga nan se suka koma parlor,amfani ya yi da comb ya hau taje mata gashin ta suna ta hira ya na bata labarai na abun dariya, ita Kuma ta na ta sheqa dariya abunta kamar bata da wata sauran damuwa a duniya,da kanta ta sa band ta daure Kan nata ya dawo gaban ta ya kalle ta ya qara ya ga yanda ta yi kyau se qamshi take budawa,rungume ta ya yi ta na mishi dariyar yanda yake ta yabon kyan ta daga baya ya sake ta ya je ya kunna mata kallo ya sunkuya ya sumbaci goshin ta sannan  ya wuce kitchen,bayan shi ta bi da kallo ta na yi masa addu'a a zuciyar ta,murmushin ta mai kyau dake bayyanar da hushiryar ta ta saki,ya na juyawa suka had'a Ido kuwa ,ya ji dad'in ganin wannan tsadadden murmushin nata, hakan na nuna masa ta fara warewa kenan, a qasan ranta tana qoqarin mantawa da komai, daga zancen haihuwar har abinda yayar ta ta ke mata,so take ta fifita farin cikin mijin ta da ita Kan ta akan kowa yanzu,yanda Adnan ya damu da halin da take ciki ya na bata tausayi sosai dan har  'yar rama ya yi a dare d'aya, tana wannan tinanin ya iso dauke da faranti babba a hannun shi, tarkacen kwalamar ta da ta Saba ci ya deb'o mata dan kawai ranta ya yi fari, dangin su Chocolate da biscuit ne da ice cream, sai Apple,shi dai kawai ya lodo komai da ya Kan ga ta na ci dan bai san me zai fi faranta mata ba a yanzun da bata da lafiya,aiko tana gani ta hau masa dariya, dan ta fuskanci gaba daya bai ma san me zai kawo mata ba, "Ko kina son wani abu da ban saka ba ne a cikin nan? ko banana kk so, ko kina son juice ? Aikuwa kin ga na manta ban dakko ba bari na kawo miki," Miqewa ta yi ta amshi farantin ta aje a center table, ta je gare shi, d'afe shi ta yi kamar wata mage haka ta shige jikin shi, ya d'aga ta da kyau ita ko ta saqale qafafun ta a qugun shi,ta kwantar da fuskar ta a wuyan shi, a hankali, numfashin ta na dukan wuyan nashi, kama ta ya yi da kyau sannan ya samu waje ya musu masauki a kujera, a hankali ta ke masa rad'a a kunnen shi, "Ina son ka mijina,ina qaunar ka, Allah ya faranta maka yanda kk faranta min, Allah ya jiqan iyayen ka ya sanya su a aljanna,Allah ya kyautata makwancin su, kafin a samu namiji kamar ka a wannan zamanin sai an sha wahala, KAI NE JARUMI na ni Sakeenah Allah ya barmu tare har abada, Allah ya bani iKon kyautata Maka sama da ya da ka ke kyautata min" Wani irin dad'i addu'o'in ta ke masa tare da narkar da zuciyar shi a kogin qaunar ta da girmama ta,lumshe Ido kawai yake ya na bin ta da kallon qauna,Sakeenah na kashe masa gab'ob'in jiki da addu'ar da take wa iyayen shi iyayen shi shi kad'ai suka haifa amma samuwar Sakeenah a rayuwar shi ya sa Yana Jin kamar su biyu suka bari a duniya, bata gajiya da yi musu addu'o'i a kowacce Rana ta duniya ko Mai ya mata in ta ji dad'i sai ta musu kyakkyawar addu'a,ya tallabo fuskar ta ya dago ta sosai suka fuskanci juna,magana yake son yi ya kasa furta komai, ji ya yi ta ce masa "Dauke ni mu je d'aki miji na" Murmushi ya saki ya manna fuskar shi a jikin ta, ba musu Adnan ya sungume ta sukai d'aka abun su Suna dariya, tin a hanya ta fara gigita shi, dana ga haka nace tabbas ba wani rahoto daidai ni bari na cinye kwalamar ta ta☹ (To jama'atul musulmi Dan mace na period ba shi zai hana ta shiga aza room da mijin ta ba, saduwa ce take haramun, dik abinda za su yi da be sab'awa Allah ba suna Iya abun su Dan faranta ran junan su) *************************** Rasheedah ce ke ta sharar baccin ta tin daren jiyan bata farka ba balle ta yi wankan tsarki ta yi sallah, ko kuka yaron ta ya yi Auwal ke Kara shi jikin Nono ya sha ya koma bacci se kace wadda tai aikin qarfi,ta na nan kwance har sai da Yousuf ya tada ta ya yi kashi a poo ya na so a wanke masa sannan ta miqe, ta je ta wanke masa ta yo wanka ta sa kaya ta tada sallah rana na kallon ta gatso gatso,a hanzarce ta jejjefa sallar ta ninke sallaya  ta zo ta dafa masu taliya, da manja da yaji, ta duba kayan da aka kawo mata jiyan, wasu qananan kaya ne masu matuqar kyau riga da wando kalar orange, masu matuqar kyau da tsada ta dauka har zata saka, can wata zuciyar ta ce mata 'ke me zaki saka kayan qanwar bayan ki kiyi da su? Kawai kije ki siyar ki sai wasu sauran kudin kin kashe wata hidimar da su' Ta yi amanna da shawarar kuwa dan haka ba b'ata lokaci ta samu Sulaiman ta masa kwaskwarima Yousuf ma ta masa,ta saka masu wasu kayan ta dau wad'anda take ganin zata siyar suka rufe gida su ka yi gaba, suna fita wani babban shago ta je a layin nasu da suke saida yan kayyaki haka,taje ta masu bayanin kawo mata akai jiya ita kuma ba ta son sawa tace bari ta saida, aiko yana gani shima dan son banza ya hau d'aga wa ya na kalla, wasu riga da wando ne suka dauki hankalin shi ya riqe wandon ya na kallo, tambayar ta ya yi nawa zata siyar masa wandon, ta ce ko nawa ne ya bata dan ba sanin kud'in su ta yi ba,iya wandon dake mahad'in rigar zaiyi k, amma haka ya hada dika da rigar da wandon ya bata 4k, sauran ma haka ya yi ta musu siyan wulaqanci, a haka ta tashi da 37k dad'i ne ya kama ta kamar ta suma,   kasuwa ta wuce daga nan ta siyo atampopi uku, ta saiwa yaran suma yan kayan da ba Wani tsada gare su ko quality ba, ta hado kan sauran canjin ta ta yi cefane har da kaji biyu, tayo gida. A qofar gida ta ganshi ya cika ya yi fam,sai a sannann gabanta ya fadi, dan kwata2 ta manta da shi, salati ta hau yi, kan ta iso qofar gidan itama ta dake ta b'ata rai sosai kamar yanda ta ga ya yi, yana ganin ta ya Isa gaban ta ya miqa mata hannu, makulli ta zaro ta bashi, ya bude gidan, ya wuce bai tanka ta ba, sai ta yi dariya tace, "ka isa yanda na b'ata rannan ka tanka ni dama humm da ka ga ruwan rashin mutunci mtseww" karaf a kunnen Auwal kuwa. Tana aje Sulaiman a gado Yousuf  ya haye kujera ya hau baccin wahala dan ba kad'an ta wahalar da yaran nan ba, ga rana ana kod'awa, juyowar nan da za ta yi ya kifa mata mari guda uku kyawawa, tsabar gigicewa matse qafa ta yi saboda matse fitsarin da ya taho mata ba shiri,daka mata tsawa ya yi ya ce, "Fita waje ! In ki ka min fitsari anan se kin gwammace kid'a da karatu, mahaukaciya da bata San ciwon Kan ta ba" Da gudu ta yi waje kafin ta Isa band'aki fitsari ya kufce mata, anan tsakar gidan ta gama shi ya na gama zuba kuwa ta rushe da matsanancin kuka, tana zage2 akan me zai dake ta? Me ta masa in ba cin zali ba Allah ya isan ta ,kamar Jira kuwa ya ke ya fita a sukwane ya hau jibgar ta, Yousuf da ya farka tin a tsawar da aka daka mata ne ya tafi da gudu ya na kuka ya tsaya a tsakanin su ya kalli wannan ya kalli wancan , Sulaiman ma da ya farka ganin ana ta koke2 se ya saki nashi,nan fa gida ya rikice da koke koke kamar gidan makoki, shigewa daki Auwal ya yi yana tinanin hali irin nata, ta na nan ta na sharar bacci bata basu abun karyawa ba, ya na tinanin in Yara suka tashi me za su ci Kan a yi girki? Shi ne dalilin da ya sa ya tafi siyo masu indomie da d'an kwai tinda jiya Adnan ya basu kud'i,ya na dawowa ya gan ta da qatuwar leda ta nufi shagon da ke unguwar su ta na magana ana d'aga kayan, daga nan ya fahimci me take yi, a gaban idon shi ta hau machine da yaran shi dika ta bar unguwar, ya na nan zaman jiran ta, Kuma dan ta raina masa hankali ta dawo tana Wani cin magani tana fad'in maganganun rainin hankali akan shi ita gawurtacciya ko? Shiru Auwal ya yi ya dor'a hannun shi a Kan shi da yake Jin yana sara masa ga yunwa da ke mugun cin shi,tsaki ya ja Mai qarfi ya kalli sauran kayan da ta barbaza wasu a akwatin wasu a qasa,yanzu tsabar hauka ace ta sai da kaya masu daraja da tsada ta shigo da tarkace a madadin su,haushi kam ya shashi har ya rasa wajen aje saura, addu'ar shiriya ya mata ya miqe ya fita dan nemawa kan shi abinda zai ci da d'an shi, kwance ya ganta kan kujera tana ta kuka, tausayin ta ne ya kama shi domin ba duka qanqani ya mata ba, banza ya yi da ita ya fita, har ga Allah yana son matar shi, amma bata da hali mai kyau, qyashi da hassada, da baqin ciki sun wa rayuwar ta yawa shi Kuma ba matar da ya zaci ya aura ba kenan...... Wanda ya sai rariya ya San zata zubda ruwa ai ko? [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* Page 9: Da asuba bayan sun idar da sallah sun gabatar da duk wasu ibadun da suke yi bayan kowacce sallahr farillah, baccin su suka koma mai cike da nishadi, Adnan ji yake kamar ya dawwama a jikin  Sakeenaah ya zamana dik inda za shi ko me zai yi ta na tare da shi, Sakeenah wata ni'ima ce da Allah ya bashi a rayuwar shi, ita alkhairi ce a gare shi ta kowacce fuska,yarinya ce ita da ta San qima da darajar Kan ta da ta mutane, ga uwa uba nutsuwa da sanin ya kamata, mace ce mai ibada da tsoron Allah, lallai shi kam ya yi dace, Allah ya dubi maraicin shi ya had'a shi da macen da ta tattara komai da yake buqata,akan ce mace ta auri mijin marainiya in ta yi dacen miji, to shi Kam ya auri matar maraya za a ce, qara qanqame ta ya y, ya kai bakin shi bayan ta ya na sumbata, cikin baccin ta take jin hakan, juyowa ta yi gaba daya itama ta rungume shi suka ci gaba da baccin su. Basu farka ba sai wajen tara na safe, miqewa ta yi ta fara ayyukan da ta dora wa Kan ta tinda ta na da masu aiki amma ta gwammace ta yi hidimar mijin ta da kan ta, abincin karyawa ta musu sannan ta dora girkin da zata Kai wa iyayen ta, ta matsu lokacin tafiya gidan ya yi ta yi kewar su sosai,( ba lallai bane Dan Zaki gidan ku ki yi masu girki ya na dai Daga cikin kyautatawa, Dan ba kowanne miji bane Zaki dauki abincin shi ki Kai gidan ku be sa Ido akai ba, amma in gidan iyayen shi Zaki Kai se ki ga be damu ba,kaiwa naku gidan se ya zame maki abin magana Dan haka in Zaki Kai abinci gidan ku ki tabbata ba zai zama da zubewar mutuncin iyayen ki ba) qarfe  1:15pm ta gama komai, Adnan kuwa  ya na gama karyawa ya zauna a dan qaramin parlourn su da laptop d'in shi yana ayyukan shi tare da duba emails din shi, shiga goma fita goma sai ta bi ta gefen shi, ta dan masa wassanni, in ko ta wuce bata kula shi ba ze shagwabe mata fuska kamar qaramin yaron da maman shi ke aiki ta manta da shi, a haka ta gama ta hada masu ruwan wanka ta fiddo masu kaya, inda ta dakko masu wata shadda ruwan toka da ta sha aiki me kyau, daka ganta ka san an kashe kudi wajen siyan ta da dinkata, anko ya masu shi da ita, zuwa ta yi ta zauna ta ja laptop din gaban ta ta yi saving masa ayyukan shi sannan ta yi hibernating laptop din, ta juya gare shi ta na kallo shi cikin wani salo na musamman shi ɗin ma qura mata ido ya yikamar ranar ya fara ganin ta, d'an hade fuska ta yi sannan ta ce, "To a tashi haka nan muje wanka ko" Adnan na ganin haka ya sake shigewa cikin kujera,ya na matuqar son yanda take tarairayar shi kamar Wani qaramin yaro, a gaban ta ne kawai ya ke Iya sakin jikin shi ya yi Duk abinda yake so,hamma ya yi tare da miqa shi a dole ya gaji kamar Wanda ya yi aikin qarfi, Sakeenah na ganin haka ta girgiza Kan ta ta na Murmushi, yau Adnan shagwab'a yake ji,ita kuwa zata Yi pampering din shi kamar jinjiri, tashi ta yi ta tsaya a gaban shi, ta bashi hannun ta guda d'aya dan ya kama, Cike da kasala ya miqa mata hannun shi d'aya, yunqurawa ya yi kamar zai tashi ya ja ta ta fad'a jikin shi, dariya ya Sanya mata, "Kin gani? Wata 'yar yarinya da ke a wajen ki ke son d'aga ni," Tura baki ta yi Cike da shagwab'a, sannan ta ce, "Ni dai Dan Allah Mine mu je mu yi wanka, wannan dai ba wuni zani gida ba, tinda yanzu har kusan 2:30pm fa" Tashi ya yi tsaye tare da ita jingine a gefen shi suka wuce wanka, sun fito ya ga ta na ta daure fuska ta qi fara'a ya kalle ta Cike da kulawa ya ce, "Babyn Adnan me ya faru ki ke b'ata fuska?" "Ba Kai bane ka sa muka b'ata lokaci kalli time fa, yanzu wajen 3:11pm ko sallah ba mu yi ba, ni dai gaskiya se in bar tafiyar ma se gobe na je da wuri wannan ai zuwan yamma za mu yi" Janta ya yi jikin shi ya na qarasa balle mata bra d'in da take sanyawa, ya dauki under skirt din ta ya zura mata ya Sanya mata doguwar rigar shaddar ta sannan ya miqa mata dankwalin kayan Dan ya San yanda take saurin nan ko Kwalliya ba zata tsaya yi ba, "I am sorry My love, yanzu zamu tafi, ki ka sani ko jinkirin da muka Yi ya zama alkhairi Adnan ya zama Daddy?ko bakya so?" Wata iriyar kunya ce ta kama ta ta saki murmushin jin dad'i ta kwantar da jikin ta a nashi, "Allah ya nuna min wannan ranar da na fi kowa farin ciki a rayuwa ta" "Ameen" Qarasa shiryawa suka yi ta shafa lipstick da powder se ta sa kwalli ta kafa dauri me kyau, Kan ta gama ya qarasa shiryawa Shima se suka tada sallah, su na idarwa suka yi addu'ar su suka rufe sashen su sai gidan su Sakeenatuwa. **************************** A gidan Rasheedah kuwa tun safe ta yi wa yaran wanka, amma sai bata saka masu kaya ba domin ta kwana da burin zuwa gida a ranar, yousuf ta yanka wa warning din kar ya fito tsakar gida ya b'ata jikin shi, Auwal na kallon su be ce mata komai ba, Dan shi yanzu gaba d'aya lamarin ta ya fita akan shi, haka ya gama komai ya shirya ya fita bata gama abin karyawa ba,a haka ta gyara waje sama2,  ta dora masu abinci suka ci, cikin daya daga atampopin da ta siyo bayan ta Saida kayan da Sakeenah ta kawo mata tsaraba ta Kai aka dinka mata, se ta dakko  mayafin da ya dace da kayan wani shara2 me bala'in kyau ta sab'a goyon ta sannan ta yafa mayafin, ba qaramin kyau Rasheedah ta yi ba, dama can ita me kyau ce rashin halin kirki ke sa ake mantawa da kyan nata,shape din ta ya bayyana sosai a waje, ta riqo hannun Yousuf da ta wa kwalliya da kayan da Sakeenaa ta had'o masu tsaraba, shima Sulaiman kwalliyar da ta masa kenan, ga takalmi mai tsini ta saka,ta feshe jikin ta da turarukan da Sakeenaa ta kawo mata tsaraba, Arebians, qamshi ko ta ina na tashi kamar wadda tai barin turaruka a jikin ta, haka ta tako fuskar nan ta sha ado, a haka ta ja qofar gidan ta rufe da makulli ta yi gaba. Duk inda ta gilma haka zaka ga  idon mutane na bin ta yuuuuu,a haka ta tako ta zo bakin titin unguwar su, ta dad'e tsaye tana neman abun hawa bata samu ba, masu manyan motoci sai qara rage gudu suke suna kallon ta, har wani fari take tana yanga, cikin ranta kuwa fad'i take, "Kaiiii arziqi yayi a rayuwa, dube ni kalar babbar mota,Sam be kamata kamar ni ace yawo nake a qasa ba Mtseeww Allah ya tsinewa talauci," Dogon tsakin da ta ja ne ya sa Yousuf ya daga kai ya kalle ta, a haka ta samu adaidaita suka kama hanya sai gida,suna isa qofar gidan, suma su Sakeenaa na sako motar su, wani qululun baqin cikin ganin su ne ya taso mata, ji tai kamar tace a maida su gida, amma ba hali, sai su raina ta suga ko shakkar su take , ita ko Sakeenaa ta bangaren ta ba qaramin farin ciki ne ya lullube ta ba, yau zasu yi yini tare da yayar ta a gida,ta San Mama zata ji dad'i sosai, Adnan kam in ranshi yai d'ari ya baci,ji ya yi kamar su koma gida kawai, da yasan wannan uwar raqai din zata zo da basu  zo ba yau, d'aure fuska ya yi sosai ya kalli yanda matar shi ke murnar ganin yayar ta, sai ya sassauta dan kar ya b'ata ran ta,ya San halin ta yanzu tana iya jin haushin shi, fita ya yi ya buɗe mata, ta sako qafar ta waje,sai da Rasheeda ta hadiyi yawu, dan ba qaramin burge ta suka yi ba, sannan ga wani arnen takalmi a qafar Sakeenaa, mai a daidaita sahu ne yai magana, "Malama ki ban kudina nai gaba ina da abin yi in ke ba ki da shi," Da ya San wacece Rasheedah da be tsokano wa Kan shi jidali ba, kamar Jira take kuwa duk wani haushin dake ranta ta fara sauke masa shi a ka, hayaniyar su ce ta ja hankalin mazan dake zaune a d'an nesa da su, daidai Sakeenaa da Adnan sun dakko warmers da suka sako abinci suna takowa wajen, sun riga matasan isowa dan haka Mai adaidaita Sahu ya maimaita me ya faru ita Kuma ta ce qarya yake zagin ta ya yi, Adnan na ji ya San me adaidaita sahu ya fita gaskiya, matasan na zuwa suka fara hayya hayya za su daki me adaidaita Adnan ya hana ya sallame su, sannan ya sallami Mai adaidaita ya bashi hakuri shi kuwa Mai adaidaita ya ja adaidaitan shi ya yi gaba ya na fad'in " 'Yar bala'i da baqin ciki tinda ki ka hango su a mota luqeqiya ki ka hau hanqoron nishin baqin ciki ke da shiga irin motar nan kuwa se dai a qiyama in ana shiga shegiya 'yar has," " Uwar ka ce 'yar has d'in dan uban ka matsiyacin banza ni Wani ya Isa na Masa hassada ne kaf duniyar nan, shege mara mutunci kawai," Hannun ta Sakeenaa ta riqe ta ja da niyyar su shiga ciki ta fisge ta kama hannun Yousuf, "In ki ka kama hannuna wa zai kama na d'ana? Ko dan baki san zafin su ba sai na shige na bar shi anan?" "Ke ! ko da wasa kar ki kuskura ki b'atawa mata ta rai, ba dan  ke ta zo ba, ni da na san yau zaki zo ma da ban bar ta zuwa yau ba, to ki kiyaye ni, duk abinda ya samu iyalina ta dalilin ki ranki sai ya yi mugun baci shashasha kawai" Cikin fushi ya wuce cikin gidan ya barsu tsaye har Sakeenaah be kula ba Dan ya San a hakan ma haushin shi take ji ya yi wa yayar ta ihu,cikin yaqe Sakeenaah ta kama hannun Yousuf suka shiga, ita kuma 'yar jarabar tana ta fama, suna isa suka tadda Adnan gaban su Abba, suna gaisawa, Mama bakin ta har kunne ganin yaran nata ga jikokin ta, cikin ranta godewa Allah kawai take tare da fatan Allah ya azurta Sakeenah itama da haifi nata, suma zama suka yi a qasa suka gaida iyayen nasu, Yousuf Abba ya kira,yana zuwa kuwa ya kama guiwa shima ya yi gaisuwa, dariya aka sa a wajen dika, banda Rasheedah, Sakeenah cikin dariya ta ce, "Lallai Yousuf ka gaji ni wajen gai suwa ko Maa? Haka kk ce ina yi sanda ina qarama ko?" " kwarai kuwa haka kk yi, ko wa kk gani har wanda baki sani ba sai kin dafe guiwa kin kai gaisuwa," Dariya aka qara sawa, Rasheedah kuwa da haushin maganar su ya kama ta se ta kyab'e baki ta ce, "Hmmm to ai sai ki bari in kk sillibo naki sun yi koyi dake, amma wannan mahaifin shi ya gada, dan baban shi ma haka yake," Ta qarasa maganar ta tana wani marmara ido, baki iyayen suka sake, Sakeenaah ko yaqe ta yi tace, "Auu habaa, Allah sarki," Ba ta son iyayen su San cewa har yanzu basu jituwa, amma Abba sai da ya gane, cikin d'an had'e fuska ya ce, "Ke wai dan Allah yaushe zaki yi hankali, yaushe zaki gane irin son da qanwar ki take maki, bazaki na koyi da kyawawan halayen ta ba kema ki zama ta gari? Kullum qara baud'ewa kike kamar saniya?" Aiko ran Rasheedah in ya yi dubu ya baci da Jin Kalaman mahaifin nata akan ta, wato ita ce ma saniyar? Adnan kuwa na Jin haka ya yi caraf ya cafe maganar da cewa, "Ai Abba dama ina da niyyar zuwa na fad'a maku irin wadannan abubuwan da Rasheedah ke yi wa Sakeenah, amma in na tuna Sakeenaa ta ji na kawo qarar Rasheedah wajen ku ranta zai b'aci yake sa na bar maganar,amma damuwar da Rasheedah ke kunsawa Sakeenaa ba kad'an bace da kuwa kwanaki har likita cewa ya yi ta rage damuwa dan ko gab take da kamuwa da hawan jini, kuma wannan baiwar Allah itace sanadi," Dik abubuwan da ke faruwa Adnan be rage ba ya sanar da iyayen nasu, wanda hakan ba qaramin kuka ya saka Sakeenaah ba, sannan ta ji haushi matuqa da Adnan ya zayyana wannan abu gaban iyayen su, a nashi bangaren ya fad'a ne dan wataqila in iyayen suka yi ma Rasheedah fad'a zata nutsu ta kyale masa matar shi ta dena hantarar ta da nuna mata tsanana fili, bai san cewa duk fad'an da za a wa Rasheedahn ba qara mata tsanar Sakeenaahr ze yi fiye da da, ji take kamar ta tashi ta shaqe ta ta mutu kowa ya huta, hakuri iyayen suka bata bayan sun gama wa Rasheedah fada, hira aka koma yi, ana raha amma zuciyoyin su ba dad'i,musamman Sakeenaah data ke jin haushin Adnan na fadan wannan abun, ga kuma yanda hankalin ta ke tashe da kallon da yayar tata ke mata,a haka dai aka kira la'asar suka tashi zasu masjid Abba da Adnan kenan sai Yousuf da shima yace zashi, Sakeenaa da Rasheedah ne suka miqe zuwa tsohon d'akin su dan yin sallah,Mama kuwa d'aki ta tafi Dan d'akko ma Rasheedah hijabi, tinda mayafin jikin ta ya yi shara shara da yawa ba zai sallah ba, Sakeenah na ninke  Hijab din ta ta ji an dafa kafadar ta, tana juyowa taga Rasheedah wadda fuskar ta ke d'auke da Wani irin yanayin da ba zai fad'u ba, "Rasheedah lafiya?"......... 😱😱😱😱😱😱 *Meke shirin faruwa ne? Jama'a ku kawo dauki* [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* Page 8: Sakeenaah ta ji sauqi sosai, ta dawo normal kamar bata yi ciwo ba a kwanaki ukun da suka gabata, duk da cewar period take ba abinda ya canja na ma'amalar auratayyar ta da Adnan sai abu daya, (Saduwa) ban da shi ji yake kamar ma bata priod d'in saboda  irin kulawar da take bashi, ba qaramin gwana bace wajen iya kwantar ma da mijin ta buqatun shi, dan ba ta son tauye shi ko tawace fuska saboda Shima yanda yake kyautata mata,  sabanin mutuniyar ku Rasheedah, ita sai tana so ma aka fi yin abun, in ko tana period ko hannun ta ya tab'a da sunan wasa to pa kamar ya aikata sab'o,ta dinga nana ta masa she is on her period fa, kwata2 baya wani samun yanda yake so a wannan lokacin. Yau Sakeenaa ta gama period din ta, Adnan yana wajen harkokin kasuwancin shi abubuwa sun masa yawa duba da tsawon lokacin da ya d'auka baya zuwa kamfanin nashi guda biyu d'aya na sarrafa rake a Maida shi zuwa sugar, d'aya Kuma shigowa suke da kayayyakin sawa daga qasashen waje kala kala,yau kayan su da suka yo order daga Hong Kong za su iso,shi yasa Adnan ke son zuwa gani da Kan shi, kan ya fita dama ya fad'a mata yana sha'awar tuwo,saboda haka yau tuwo zata Yi masa tinda shi yake so. Shamsiyya me aikin ta ta sa ta jiqa mata shinkafar tuwo daidai yanda zata ishe su ,ta Kuma Sanya ta b'arza mata wake a blander tare da bushe shi sannan ta jiqa mata,ita Kuma ta wuce d'akin Adnan ta na gyarawa dik da ba Wani datti ya yi ba ma, da ta gama ta wanke toilet, sannan ta koma nata ta gyara , mai yi mata shara Harsa'u dama ta share parlour da dika gidan ko Ina qalqal se d'aukan Ido yake, sai da ta fara dora tuwo ta had'a miyar waken ta da ta qara da gyad'a dan ta yi qard'i,ta kawo ganda da busasshen kifi ta zuba da kayan qamshi da dik abinda ya Kamata dai,se ta fara tinanin yin farfesu,dake Adnan na son farfesun naman zabo kawai sai ta yanke shawarar shi zata masa, deep freezer ta bud'e ta d'akko naman zabon ta gyara Shima ta yi masa had'in da ya dace da shi ta zuba masa kayan qamshi na  MummyJaf miscellanea special curry ya na matuqar d'auke qarnin kaza ko kifi da Kuma naman zabon, idan Miya kuwa ka ke yi da shi har maqotan maqotan ka sai sun Jiyo qamshin ta, (sai an gwada akan San na kwarai 08039469116 shine no da Zaku Kira Dan mallakar naku) sannan ta wuce wanka. Cikin gayun ta ta fito sanye da Wani material Mai laushin gaske kalar makuba da ratsin fari a jiki, ta kafe dauri me kyau da dankwalin shi, ta saka siririyar sarqar ta ta zinare me siririn abun hannu da zobe, ta yi wa fuskar ta saussauqar Kwalliya se tashin qamshi take, masu aikin ta sai yaba mata suke, ita kuwa Murmushi ta yi ta yi musu godiya, tambayar ta suka yi ko akwai abinda take so a mata? Kallon su ta yi ta ce, "Shamsiyya kin tace min zob'on kuwa? " "Eh Hajiya na ma so na qarasa had'a shi sai na ga kamar kin fi son had'a wa Alhaji abun sha da Kan ki, amma fito maki da kayan marmarin na wanke su Suna nan aje se dai in kin shiga kin ga akwai abinda za a maki Kuma se a yi Uwar d'aki na" "To na gode,ku na iya tafiya kawai ai Kun yi qoqari,da fatan Kun d'iba ko?" "Eh Hajiya ai wannan girki qamshin shi kawai ya Isa mutum ko ba a bashi ba ya d'iba ballantana ma komai ki ka ci a gidan nan muma sai kin bamu" Dariya suka yi gaba d'ayan su, Shamsiyya akwai barkwanci, gata ba wata babba bace sosai da kad'an ta girmi Sakeenah dan dika dika ba zata fi shekara ashirin da takwas ba sa'anni ne ita da Rasheedahn Sakeenah, bazawara ce mijin ta rasuwa ya yi ya barta da Yara biyu mata, dik weekend ta na kawo su gidan su zauna da ita a can sashen masu aiki, sanda Sakeenah ke Jin nishad'i sai ta sa a shiga da su su yi wasan su wajen ta. Sallamar su ta yi suka koma bangaren su, ta shige kitchen dan qarasa had'a zob'on da ya sha abarba da cucumber da kankana, ga kayan qamshi da na'ana'a, goruba da ta zuba a ciki, hummm makaranta wannan zobo da gani se ya yi dad'i, fruit salad ta had'a ta Saka a bowl ta rufe ta Saka a fridge se ya dawo zata d'akko Dan a sha shi da sanyi sanyin shi. Gani ta yi sun qarasa tuqa mata tuwon sun kwashe miyar ma ta yi sun zuba a inda ya dace sun jera mata komai a dinning table har ruwa sun aje, ajiyar zuciya ta yi ta yi Murmushi Shamsiyya ta na matuqar taimaka mata a gidan nan sosai, ganin ba abinda ya rage da za ta yi se kawai ta koma parlour ta zauna ta hau tasbihi a ranta, kalmar La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,se Rabbi inni lima anzalta ilayya min khairin faqeer, da rabbana hablana min azwajina wa dhurriyatina qurrata a'ayunin waj'alna lil muttaqeena imama ke fita a bakin ta, in ta gama tai hasbulallahu wa ni'imal wakeel, haka haka dai, har taji tsayuwar motar mai gidan, dai dai ana kiran magrib hijab din ta ta saka tana murmushi, tasan tana da alwala in yazo ya ganta ba sallah take ba sai ya bata kwalliyar nan bai mata gani mai kyauba,dan haka sallah ta tada, sai da ta kai raka'a daya ya shigo, kallo ya bita da shi, baki sake, dan a hakan ma ba qaramin kyau ta masa ba, wucewa ya yi yana shaqar qamshin gidan yana lumshe ido, aje jakar shi ya yi tare da wucewa kan dinning table direct Dan kuwa ya dawo da matsananciyar yunwa a tattare da shi tin Karin safe ko ruwa be sha ba da ya fita, warmers din ya hau bud'ewa Wani qamshi ya daki hancin shi, yawu ya hadiya nan da nan kuwa cikin shi ya fara kukan yunwa ya ga abinci, ji ya yi kamar ya fara ci kan ta zo, amma ya daure ya zauna zaman jiran ta,tana idarwa ta yi istighfar sau uku se ta miqe ta je gare shi ta na takun ta me burge shi, d'an rankwafawa ta yi ta sumbace shi a Kuncin shi sannan ta gaishe shi tare da Yi masa sannu da dawowa, Shima sumbatar goshin ta ya yi tare da yaba Kwalliyar ta, godiya ta masa ta na Wani yauqi ta hau zuba musu abincin, d'an duqawa ta yi Cike da tsokana ta ce, "Bismillah me gida ka ci abincin kada ya huce" "My love yau Kuma Wani sabon salo ne hakan? Wai me gida kamar a qauye"dariya suka saka a tare, "Ka San da yake yau gidan ya koma na gargajiya shi yasa ka koma me gida kaima" "Ohhhh haka neeee" Gira ta d'aga masa guda d'aya Murmushi ya yi me sauti suka yi Bismillah suka fara cin abinci, ko magana Adnan ya kasa tsabar yanda abincin ya yi masa bala'in dad'i, hannu kawai yake d'aga mata ya na jinjina mata, ita Kuma ta na Masa dariya, "Yau santin kurma ake kenan, ka San a makaranta an koya mana Santi kala kala, to Kai yau na kurma ka ke yi ko?" (Hauwabuna can relate) Kai ya d'aga nan ma be ce komai ba, sai da suka kammala dika ne ya dinga Sanya mata albarka ya na yabon abincin daki daki, kama daga Kan yanda tuwon ya yi dad'i Kuma ya tuqu, zuwa yanda farfesun naman zabon ke Wani fitar da d'ad'anon me dad'i da qamshi me gamsar wa, zuwa yanda miyar ta yi zaqwai,Sakeenah godiya ta yi masa, suka miqe a tare, jakar shi ta koma parlour ta d'akko suka wuce d'akin shi. Ba abinda Adnan yake banda kallon yanda take sarrafa mazaunan ta wajen tafiya, ya shagala sosai a kallon ta har suka Isa d'akin ma be kula ba, in dai Sakeenaa na gaban shi yakan manta komai, wanka suka shiga ta taya shi daga baya ta fita ya yi alwala, ta fidda masa kayan da zai saka kafin ya fito, daya fito bai gan ta a d'akin ba ya San ta wuce nata ta bashi waje ne ya samu damar yin sallahr da be ba, kan ya fita ta d'akko ragowar zobo ta aje musu a center table na parlourn su ta kunna kallon Wani indian film na 'Hamara Rishta' ya na idarwa inda take ya nufa, Adnan shi da kallo bai wani dame shi ba yafi so ya Kai channels TV ko NTA, gani ya yi ita Kan ta sarkin kallon yau hankalin ta baya Kan TVn ta qura masa ido ta na kallon shi daga saman har qasa "Yau Adnanu ya zama TVn Sakeenatuwa" Murmushi ta yi ta rufe fuskar ta alamun ta ji kunya ya kama ta ta na kallon shi, dariya suka saka a tare ya lakuce mata hanci, harara ta sakar masa, dan ita bata so ana lakuce mata hanci, dariya ya sa ya d'aga hannu yana bata hakuri, tace sam sai ta rama , "Habaa my love yanzu tsakanin mu ba yafiya?" "Ni dai gaskiya banda ta nan bangaren ai ka San bana so ana tab'an hanci amma kullummmmm se ka yi" "To gashi zo ki rama," ai kuwa da sauri ta miqe zata Kai hannun ta ta rama ya miqe ya yi d'akin shi, ya na tafe ya na fad'in, "Ki biyo ni nan ki rama in kin Isa" "Ai kuwa gani nan zuwa yau se na kusan gutsure Maka hancin ka dama ya yi tsawo da yawa" Tsaye ta gan shi saman abun sallah ya na qoqarin tada sallah, "Auuuu ta nan ka biyooo? To bari na je na sake alwala sai ka jamu" Shi Kan shi ba shi da alwalar ya yi haka ne dan ta bari su yi sallahr isha'i, in ya so ta masa koma me ta ga dama, ta na fita ya shiga bathroom ya yi alwala ya fito, tsaye ta sake tadda shi, dan haka se kawai ya tada sallah suka yi sallar su tare, su na idarwa suka fara karanta qur'ani suka yi ma iyayen su addu'a da musulmi baki d'aya da kan su, a zuciyar ta ta yi addu'ar... 'Ya Allah ka bamu zuri'a Mai albarka idan alkhairi ne a tare da mu da addinin mu, idan ba alkhairi bane Allah ka bamu hakuri da juriya da dangana Ameen' "Ameen" Adnan ya fad'a ya na kallon ta da tausayawa, dan ya San hawayen da ke zuba mata baya rasa nasaba da addu'ar da take a zuciyar ta, addu'ar kuwa ba zata wuce ta neman haihuwa ba, matsawa jikin shi ta yi ta kwantar da kan ta a qirjin shi  sannan ta ce, "Yaushe zaka kai ni naga Mama da Abba? Ka ga su suka zo duba ni da banda lafiya a madadin ni na je gaishe su da muka dawo" "karki damu gobe ma sai mu je ai," A hankali yake shafa bayan ta, ta d'aga Kai su ka qura wa junan su Ido Cike da so da kulawa daga nan salon su ya sauya, nace to bari na leqa yaya babba naga me take yi ita Kuma? Kwance take ta yi d'aid'ai a gado sai hura hanci take ita ga mara M, Auwal Kuma sai bin kanta yake akan  ta taimaka ta bashi hadin kai,ko yayane ya samu ya rage zafi amma taqi sam, "Ni fa na jima da sanin ba so na ka ke ba, jiki na ka ke so,wato so kake ka cuceni ko hutun shekara biyu ni ba zan samu ba a rayuwa ta na zama kamar akuya bini bini haihuwa ko? dika2 yaronnan sherar shi fa d'aya ne,haka kawai ka wani zo ka maqalen ka dirkan ciki ni Kuma inzo ina ta fama ko? ga goyo ga laulayi kamar yanda na yi na Yousuf to gaskiya ni kam na gaji ba zan iya ba, ni ba akuya bace ko mage ehe"  Cike da lallashi Auwal ya ce, "Haba mata ta abar so na uwar 'ya'ya na, naga in ma Cikin ya samu ke ba mai wahalar laulayi bace,Imma fa ya samun kenan, Dan Allah ki taimaka min kar ki bari na fad'a halaka, Ina da mata na tsaya wajen matan banza,yanzu ke Rasheedah Dan Allah baki ganin Sakeenaah neman haihuwar nan take bata samu ba har yau tare fa akai auren ku, gashi ke Allah ya baki amma kina qi? Ki daure ki taimaka min a matuqar matse nake," Cikin muryar tausayi ya yi maganar ba dan ba zai iya murd'e ta ya yi abinda yake so ya tashi ba, sai dan kawai ya na so su gyara zaman su su dena abu kamar wasu 'yan bariki, wannan abun daya fad'a ne ya bata qarfin guiwar gyarawa da kyau ta yi tunani, wato ita se yanzu ta gane ma ni'imar da Allah ya mata,ya bata haihuwa ya hana Sakeenah, Wani irin farin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta, ko ba komai itama yau ta fahimci akwai abinda take da shi Wanda Sakeenah bata da shi a duniya murmushi ta yi ta ce masa, "Taso taso miji na gani na baka dama in ma cikin 'yan biyu zaka min yau d'in nan shirye nake da d'aukan shi ka haska min yau Wani duhu da na jima a ciki" Auwal bai fahimce ta ba shi dai murna ya hau yi ta yarda da shi dan haka ya kora ni waje suka rufe qofar su Burin ta kawai yanzu be wuce ta sake samun ciki ba ko dan ta qunsa wa Sakeenah haushi kamar yanda Sakeenan ke qunsa mata haushi a kullum........... Niko na ce ki ke qunsawa Kan ki dai [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* Page 10: Sakeenaah na had'a Ido da Rasheedah ta ji gaban ta ya yi wani irin mugun faduwa, saboda yanda taga tsantsar tsanar ta da qiyayyar ta a fuskar yayar tata, cikin rawar murya ta ce, "Rashee....." "Dakata min tsohuwar munafuka, dama had'awa ki ka yi da mijin ki in kunzo ku min wulaqanci gaban iyaye na ku min munafurci da annamimanci? Ku fada masu abubuwan da na maki dan su qara tsanata? Gaki an taba 'yar so Kuma 'yar gwal ko? To bari kiji na fada maki wani abu da wataqila baki sani ba Sakeenaah, ni Rasheeda na yi alqawarin ba zan tab'a son ki ba a rayuwa ta har abada,ko me ki ka zama, ko me zaki zama,ko me ki ka mallaka, ke zuri'ar ki ma ba ni ba su ko da kuwa duniya zaki haifa dan yawa nan gaba ni dasu ba zancen soyayya, na tsane ki ! Na tsane ki !! Na tsane ki !!!" Numfashin Sakeenaah ne ke mata wahalar shaqa, ido ta lumshe wanda tin da Rasheedah ta fara magana take zubda hawaye, wannan wace irin rayuwa ne,wace iriyar qiyayya ce haka me zafi? Me ta yi mata? Anya Rasheedah bata da aljanu da ke had'a su fad'an ba gaira babu dalili? Dan ita har yanzu bata San menene takamaimai abinda ya janyo wannan mahaukaciyar qiyayyar me zafi ba a tsakanin su, a bayyane take nuna mata tsana, kyashi, hassada, da qiyayya, yau ko kafira ce ita ai se haka,abun takaicin shine tama qi sanar da ita asalin dalilin da yasa ta ke qin ta,dan dalilan da ta sani gani take kamar ba su bane, a wajen ta basu kai wanda za ai mata tsana haka ba, kuka take sosai, ta na nan tsayen ta wani jiri na d'iban ta, ta kuwa tafi luuu zata fadi, Rasheedah da ke saitin wajen kawai se ta buga tsaki ta kauce, ai kuwa ji ka ke  'tiimmm' Sakeenah ta fadi a qasa. Zagaye Sakeenah Rasheedah ta yi zata shige toilet abun ta,tana gab da shiga toilet din ta ji muryar mahaifiyar su da ta je d'akko wa Rasheedahn hijabi saboda sallah, dan tin da ta shigo take kallon kayan sun yi tsiraici da yawa amma bata mata magana ba, da niyyar zata bata hijabi kalar kayanta ta dinga had'awa da shi, cikin matsanancin kuka ta ce, "Yanzu ashe irin yarinyar dana haifa kenan ban sani ba? Ina murna ina da yara biyu kyawawa, ashe na yi kuskure, yarinya ta d'aya cekyakkyawa me kyan hali ce, d'ayar kuma baragurbi, yanzu da kan ki kike zayyana wa qanwar ki uwa d'aya uba d'aya wadannan abubuwan? Wace........" Wani nishi da Sakeenaah ta ja ne ya yi sanadin rugawar Mama da gudu gare ta, tana danna qirjin ta, alamar dawowar su Abbah maman ta ji ta kuwa kwala masu kira a gigice, a firgice suka shigo dan sun ji kiran nata kamar da kuka a ciki, Adnan ne a gaba har yana tuntube da Hijab din da Mama ta kawo wa Rasheedahn, sauran qiris shi din ma ya fadi. Yana ganin matar shi a kwance a qasa shame shame, ya yi saurin kallon Rasheedah wadda ta nuna ita fa yanayin da Sakeenah ke ciki ko a jikin ta, cikin ran ta da fari ta tsorata, amma daga baya da ta ga yanda hankalin kowa ya tattara ya koma Kan Sakeenaah cikin madaukakiyar damuwa da tashin hankali sai hakan ya qara sa ta jin tsanar Sakeenaah ta ninku a ran ta,wai akan ta ake wannan rawar duwais din, ji harda Abban su, kad'a ido sama ta yi ta ja gajeren tsaki zata shige, Mama ta yi wani kukan kura ta janyo ta, daidai lokacin Abba ya shafawa Sakeenaah ruwa ta dawo normal, kifa mata kyawawan maruka mama ta dingayi ta na kuka, tare da fad'in baqaqen maganganu akan Rasheedahn,ko gezau Rasheedah bata yi ba zuciyar ta ta bushe ta dake da qiyayya da hassadar qanwar ta, Adnan ne ya riqe hannun Mama yana bata hakuri, "Ka barni kan ta kashen yarinya mai yi mana biyayya da son mu da kulawa da lamarin mu gwanda ni na kashe ta, ban tab'a sanin haka Rasheedah ki ke da baqar zuciya ba, a zato na d'an kishin nan ne dake tsakanin 'yan uwa Saqo da saqo,ashe ke kina nan kin gina zuciyar ki akan mummunar qiyayya me zafi haka,mu kuwa me za mu yi da mai halayya irin taki? Ta ina na gaza a baku tarbiyya ni da mahaifin ku har kk deb'o wannan mummunan halayen bamu sani ba? Wannan wacce irin yarinya na haifa? anya bata da  mugayen aljanu a tattare da ita kuwa?" Abba ne ya zaunar da Maman a gefen bakin gadon d'akin, ya rungume ta ya na lallashin ta, "Zubar hawayen ki a gurin ta masifa ne,zai sa ta qara lalacewa ne kawai, ki kwantar da hankalin ki da izinin Allah zata so Sakeenaah, kwatankwacin yanda iyaye za su so 'ya'yan su, ki basu lokaci, ke Kuma Rasheedah mu na Mai baki hakuri akan dikkan abinda ki ke ganin mun aikata maki ba daidai ba da ya ja ki ka tsani qanwar ki da ku ka fito ciki d'aya har haka" Sakeenaah da ta jingina da pillow, a hankali tace zata sha ruwa, ruwan Adnan ya bata, yana mata kallon so,qauna da tausayawa, kallon ta ya ci gaba da yi ya ga yanda take kallon Rasheedah, takaici duk ya ishe shi, a hankali ta Maida kallon ta zuwa ga Adnan ta ga yanda ya damu akan ta, shi Kuma bin ta yake da kallo tare da maganar zuci, 'Baki da wayo my love har yanzu ya Kamata  ki farka ki gane wannan ba zata taba son ki ba,' A hankali Sakeenah ta furta " Rasheedah kiyi hakuri da dikkan abinda na miki, wanda na sani da wanda ban sani ba, ko menene shi ki wa girman Allah ki yafe min, rayuwar nan ta duniya ba komai cikin ta face rud'in shaid'an , ni ina son ki,ina son ki, ina son ki,ke yayata ce, bayan iyayen mu banda kowa bayan ke, sai mijina, in baki so na ya zanyi?" Kuka ne yaci qarfin ta, haushin ta yanzu Adnan ya ke ji, na farko kenan ma baya list din masoyan ta na fari wannan banzar da bata son ta ta ma fishi matsayi, sannan ga shi sai wahala yake da ita amma ko kallo bai ishe ta ba, tari ne ya sarqe ta ta kasa qarasa maganganun da take yi,tsaki Rasheedah ta yi ta d'au gyalen ta da jakar ta ta bar dakin, parlor ta je ta tadda yaran ta duk sunyi bacci, goya Sulaiman ta yi ta dau Yousuf a hannu, ta yi waje, ranta baqiqqirin, da kulawar da ake bawa Sakeenaah, bayan ta manta itace silar koma me ya sami Sakeenahn har ake bata kulawar. Abun nasu ya zama wata iriyar jarabawa, Allah ya jarabci Sakeenah da tsananin son yayar ta ta, ita Kuma Rasheedah na tsananin qin qanwar ta ta. (Dama haka Kan faru, sanda Wani yake tsananin son Wani, to shi wannan da ake so sai a yi rashin sa'a lokacin yake tsananin qin Mai son nashi) Mai adaidaita Sahu ta tsare ta hau ta yi gida,Su kuma suka fito da Sakeenaah dan kai ta asibiti, suna zuwa likitoci suka karb'e ta suka kwantar aka gwada Bp din ta ya hau sosai, sannan aka d'ebi jinin ta suka yi gwaje gwaje, matsalar hawan jinin ta suka hau dubawa dan shine yafi, a haka Mama, Abba,da Adnan, suka shiga jinyar Sakeenaa,har kusan kwana sha d'aya a asibiti, Sakeenah ta d'ashe ta yi haske sosai, kusan kullum cikin amai da zazzabi take,amma kullum idon ta rufe taqi budewa kome ake tana ji tana sane, amma bata son yin magana, tinanin tin da ta fara wayo, zuwa 'yammatancin su take, har ranar auren su, ko akwai abinda ta yi wa yayar ta mara kyau da ya ja mata mummunar qiyayyar nan? Amma ta rasa,dawowar Abba daga kasuwa kenan ya biyo, ya na tambayar jikin Sakeenah a wajen Mama da Adnan da tinda Sakeenah ta kwanta be je ko Ina ba, dik abinda ake da buqatar shi ko signing ko ganin Wani file d'in se dai a kawo masa nan ya yi a mayar, tattauna wa suke akan matsalar musamman jinin ta da ya qi daidaita sai su ka ga hawaye na zuba ta gefen idon ta, Adnan da Abba har suna rige2n zuwa gare ta,Adnan ya kama hannun ta ya ce, "My love pls ki yi magana mana ki fad'i abinda ke ran ki ki cire damuwar ran ki ko zamu samu ki ji sauqi, nasan kina jinmu ba wanda yace ki tsani yayar ki, amma baki ganin sata arai har ki samu matsala haka babbar illa ce ga rayuwar mu? Kin sani in Wani abu ya same ki ba zan rayu ba, ke kad'ai nake da a duniyar nan, ki yi hakuri ko dan  abinda ke cikin ki?" Da sauri ta bud'e ido tana kallon shi, dan duk abinda su keyi tana ji amma meyasa bata ji zancen ciki a jikin ta ba? Gyada mata kai ya yi idon shi tab hawaye, " Eh ciki, jiya likita ya tabbatar mana kina dauke da qaramin ciki" Sunkuyawa ya yi daidai kunnen ta nima ko na kai nawa naji me zaice amma inaaa ya iya qusqus banji komai ba☹ murmushi ta saki ta rufe idon ta, sai kuma ta saki kukan farin ciki, da kyar suka lallashe ta ta yi shiru, murna a wajen ta ba a magana,banda hamdala ba abinda ta ke maimaitawa, tini damuwar da take ciki ta Kau ta maye gurbin damuwar da farin ciki, roqon shi ta yi daya d'aga ta ta je toilet, alwala ta yi tazo ta yi sallah raka'a biyu ta godewa Allah da ya amsa addu'ar ta a wannan lokacin. Se da suka qara kwana biyu aka tabbatar da lafiyar ta sannan aka sallame su, gidan su suka wuce, Mama da Abba ma suka wuce nasu, cike da farin ciki. Makaranta ba sai na fad'a maku irin lelen da Sakeenaa ke sha ba wajen Adnan kai har ma da Mama da Abba ba, kullum cikin shagwaba ta suke, komai tace tana so sai sun bata, kan kuce me Sakeenaah ta zama Masha Allah barakallah, ta yi 'yar qiba me kyau ta masu ciki, jikin ta kamar ba ita ba, ta yi haske akan baqin ta se kalar ta ta zama Mai d'aukan hankali da idanun Mai kallo, Adnan in yasata a gaba da kallo, har sai ta soma shagwabar kallon ya yi yawa. Wani abu dake qara burge Adnan kuma shine her demand of sex increases, duk a harkar cikin wannan bangaren ya fi burge shi, kusan kullum ba fashi sai anyi wataran har sau uku,kai wataran har hudu ma, ba qaramin morewa yake ba,ji yake kamar ta tabbata haka ko bayan haihuwa, ita kuma in an gama sai ta hau bashi hakuri tana kuka, akan tasan tana takura masa, amma ba yanda zata yi ne, ya yi hakuri data haihu zasu koma normal, kawai sai ya gyada kai, a ranshi ko yace ba amin ba Allah sa a dawwama a haka mu na morar juna. Lokacin da cikin Sakeenaah ya kai wata bakwai, Adnan ya na yawan ganin ta tana rubuce2, in ya yi qoqarin gani,ta saka kukan shagwaba akan yana mata leqe, haka zai hakura ya je ya hau yin wani abun ya barta, a girman cikin da take da shi haka take ci gaba da dukkan ayyukan da muka san ta da shi, sai dai kawai wannan karon akwai sauyi, in kasala ta rufe ta sai ta hakura sai ta ji normal sannan ta tashi ta yi ayyukan ta. Cikin ta na wata takwas ta shirya ba da sanin Adnan ba ta tafi gidan Rasheedah....... *Kai ni ku ban madoki na tsane Sakeenaar nan, me ya kaita kuma zuwa gidan Rasheedah, mara zuciya kawai😡*[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 11: Tana zuwa ta yi parking nesa da gidan kadan, daga inda take ta na ganin duk Wani Mai shige da fice a layin,ta yi wajen  minti ashirin a zaune a motar da ta kunna wa karatun qur'ani gefen ta ruwan sha ne a 'yar robar ta me kyau da take saka abun sha a duk sanda zata fita saboda yawan Shan ruwan da take,hango shi ta yi ya dawo daga aiki, tin daga nesan ta gane shi, da sauri ta bud'e motar ta ta fita cikin d'aga murya yanda zai ji ta ta kira sunan shi, jinkirtawa ya yi da tafiyar da yake ya waiwaya,Murmushi ya saki dan kuwa ya gane ta,ita ce macen da ya sani ta na saka niqab da dogon hijab ko kuma doguwar riga da niqab d'in, matsawa ya yi fuskar shi na sake fad'ad'a murmushin, can Kuma ya koma yaqe dan ya tuna abubuwan da Rasheedah ta yi mata a baya, ya so k'warai ya je har gida ya bada hakuri Rasheedah ta dinga ci masa mutunci ta na Kiran shi da d'an kalan dangi da sauran munanan sunaye dan haka se ya fita a maganar ya dinga musu addu'ar Allah ya daidaita tsakanin su,amma fa tun lokacin Auwal ke jin kunyar Sakeenaah ko da kuwa sunan ta aka ambata Kuma duk tsahon lokacin nan basu hadu ba, sai gashi yau ta bashi mamaki da zuwan ta, " A'a Sakeenaah ke ce yau a unguwar tamu, ya baki qarasa ciki ba? Bismillah mu shiga ciki mana" Murmushi ta yi ta gyara tsaiwar  ta sosai, yanda cikin ta zai fito, aiko yana gani ya fadada fara'ar shi tare da d'aga hannayen shi sama ya na godewa Allah, tsananin farin cikin da ta gani a tattare da shi ya sa ta kwad'ayin dama ace Rasheedah ce haka da sauri ta kawar da tinanin nan dan yanzu ta na qoqarin kiyaye duk wani abu da zai tada mata da ciwon ta, Cike da murna Auwal ya ce, "Kaiii masha Allah, Allah maji roqon bayin shi, Allah ya raba ku lafiya ya sa ki haifi mai albarka, lallai in mace ce na yi wa Yousuf kamu tin yanzu, kuma ina fatan ta yo gadon halayen ki Sakeenah na ji dad'i na yi farin ciki da ganin ki d'auke da ciki, dole ne na yi wa waccan mara hankalin albishir," kwallace ce ta taru mata a ido ta qara murmusawa sannan ta fara magana, " Yah Auwal, nazo nan ba dan komai ba sai dan na roqe ka wata alfarma, guda d'aya zuwa biyu, ka san dai dik abinda ke faruwa tsakanina da yayata, to wannan dalilan dake tsakanin mu ne yasa nake son dan Allah kar ka Sanar da ita Ina d'auke da ciki a yanzu, sannan Ina roqon alfarma inna haihu lafiya 'yata ko d'ana zai dawo hannun ku da zama, dan yanda nake jina Ina jin kamar ba zan rayu da abin da zan haifa ba, ina son yaro ko yarinyar su dawo hannun Rasheedah,sannan alfarma ta biyu kome zata yanke akan abinda na haifa karka musa mata, kome zata ma abinda na haifa karka mata fada,tsakanin ku ya zama nasiha, domin so nake ko ta wanne hali Yayata ta so ni da abinda na haifa, sannan ta gane mene ne kalmar so na 'yan uwantaka, so nake ta san mahimmancin zumunci, na roqe ka ko wanne hali abinda na haifa zai shiga indai ba sabon Allah bane ta sanadin yayata kar ka rabu da ita, kar ka tsawatar mata na bata abinda na haifa halak malak,ban San me yasa ba jiki na na bani rayuwa ta ba zata Yi tsaho ba Yah Auwal, dan Allah ka riqe min wannan wasiyya ko bayan ba raina,in Kuma Allah ya sa na haihu lafiya da raina da rayuwa ta, Ina so in abinda na haifa mace ce a qulla zumunci mu had'a su aure, Ina fatan zaka min wannan alfarmar" Kuka ne ya ci qarfin ta ta kifa kai a jikin motar ta tana kuka, shi ma kukan yake sharb'a a daidai wannan lokacin,yana jinjina irin soyayyar da Sakeenaah kewa Rasheedah, inama Rasheedah zata fahimci haka, "Kar ki damu na d'aukar maki wannan alqawarin komai zai faru ba zan rabu da Rasheedah ba, kuma ba zan hana ta komai akan riqon da zata yi wa abinda kk haifa ba, sai dai dole ko taso ko bata so ba zan saka abinda kk haifa a makaranta, sannan batun mutuwa da kk danganta kan ki da ita ba lallai bane, Allah ne kawai yasan gawar fari,Allah ya raba ku lafiya ya bamu Mai albarka" kad'a kai ta yi tana murmushi,ta masa godiya sosai sannan suka yi sallama, tana qoqarin tafiya ne ya ce mata, " Af na manta ban sanar dake ba, ai ko itama Rasheedan tana can dauke da cikin ta shiga watan haihuwar ta dai yanzu amma bata yi nisa ba," Murna ta yi sosai da Jin hakan, sannan ta yi mata fatan ta haihu lafiya, suka sake yin sallama ta ja motar ta ta nufi asibiti, wajen likitan ta taje aka auna jinin ta, nan suka hau mata fada sosai,akan tana saka tinani da damuwa a ranta sosai, ko meye matsalar ta ya kamata ta aje ta a gefe ta samu lafiya,in ta haihu qalaou sai ta yi facing damuwar ta ta warware ta, consultant guda ce ta samu ta yi ta bata shawarwari tare da kwantar mata da hankali ta nuna mata yanda zata kula da Kan ta da abinda ke cikin ta, aiko ta sake samun sauqin damuwar ta sosai, haka ta fito ta kama hanyar gida, a hanya ta na tafe ta na tunani, ita ta san ta rage damuwa sosai, tinda a baya bata da aiki sai kuka da baqin cikin halin da suke ciki ita da yayar ta, amma yanzu se ta wuni ma bata yi tunanin ta ba, ta dai rasa me ke yawan sanya ta fad'uwar gaba da Jin tashin hankali, wannan abun da take ji shi ke sanya ta ganin kamar ba zata rayu da abinda ke cikin ta ba, hakan Kuma ke qara jefa ta cikin damuwa. Mai gadi ne ya wangale mata gate ta shiga, masu aikin gidan na ta gaishe ta ta na amsa wa, Shamsiyya ce ta bud'e mata qofa ita Kuma ta yi sallama ta shiga gidan,a parlourn ta ci burki Dan ganin Adnan a tsaye ya na ta safa da  marwa,yana ganin ta ya aje robar ruwan dake hannun shi ya kamata ta zauna, da alamar gajiya a tattare da ita ta furta, "Mine ka yi hakuri na fita ban sanar da Kai zani asibiti ba, na ji bana d'an Jin dad'in jiki na ne shi yasa na tafi dan na ga likita" "Haba My love ai da kin min ko da text message ne in na gani shikenan ba zan shiga halin damuwa da tashin hankali irin haka ba, gaba daya kin sani damuwa da fargaba, hankalina ya tashi,na zaci Wani abu ne ya same ki" " kwantar da hankalin ka Mine gani na dawo ai ko? Jiki na ne ban gane masa ba shine na tafi na San in na Sanar da Kai kana Iya barin aikin ka ka taho bayan zan iya Kai kaina, ai hakan be Kamata ba ko? Alhamdulillah zuwa na ya yi amfani dan kuwa na samu shawarwari masu mahimmanci daga wajen likita, na samu kwarin guiwa da kwanciyar hankalin da nake buqata, amma har yanzu Ina da damuwata guda d'aya," Cikin sauri ya ce, "Meye damuwar ki?" Murmushi ta yi mai ciwo, "Damuwa ta ka riga ka santa ka qi kawai ka karb'e ta ne, bama ka so na dinga fad'a, kuma ina kyautata zaton in ban samu wannan alfarmar daga wajen ka ba ko mutuwa na yi ruhina ba zai  samu nutsuwa ba," Kuka ta saka sosai harda shessheqa, "Ki daina kuka mana, amma kin san abinda kk nema a wajena mai wahala ne, kar ki manta fa nima banda kowa makusaci a yanzu sai ku, ya zan iya hakuri ina kallon abun da na san nawa ne zai wulaqanta kuma na kasa tab'uka komai, dan na yi imani da Allah zuri'ar ki ta shiga hannun wannan muguwar yarinyar ba za su ji da dad'i ba, sannan wa ya fad'a maki ma zata yarda ta riqe maki yaro ko yarinya? Kuma wama ya Sanar da ke ba Zaki rayu da abinda Zaki haifa ba? Kar ki manta fa ni da ke abu d'aya ne, ba ke kad'ai ke so na ba, nima Ina son ki, to ta ya ya Zaki dinga yin maganganun da za su kassara zuciya ta, ko so ki ke Nima na kamu da Wani ciwon?" Cikin kuka ta ke kad'a Kai alamar Ah ah, rungume ta ya yi ya na shafa bayan ta a hankali ya ci gaba da fad'in, "Haka aka ce maki daga haihuwa d'aya mutum zai mutu ko me? ko kuwa mutane nawa ne masu hawan jini kuma sike haihuwa su rayu? Ni ki daina ma wannan maganar dan Allah kina sawa ina shiga damuwa sosai," Share hawayen ta tayi sannan ta qoqarta tashi zaune da kyau ta shige daki, sai magana yake mata bata kula shi ba,ai kuwa hankalin shi ya tashi, ko dai da gaske mutuwa zata yi ta bar shi?  komawa ya yi ya zauna ya fasa bin ta, hannun shi biyu ya Sanya ya tallabe  fuskar shi ya saki kuka mai d'aci, zuciyar shi ya ji ta matse masa waje d'aya ta  na quna, " Ya Allah kar ka raba ni da mata ta, ina son ta, Allah ka sauke ta lafiya da abinda ke cikin ta Allah ka fini son ta Allah ka mana zab'in alkhairi," Abinci ta fito zata deb'o ta Jiyo kukan shi da addu'ar shi, sai ta koma da baya ta jingina da gini,itama kukan take,daga baya ta share hawayen ta ta fita, kitchen ta wuce ta fara diban abinci,zuwa ya yi ta bayan ta ya kwantar da kan shi a bayan ta cikin matacciyar muryar da ba a son yin magana da ita ya ce, "Na amince da buqatar ki ki daina saka damuwa a ranki, Allah ya sauke ki lafiya" Murmushi ta yi ta juyo ta hau sumbatar shi, sai da ta dangana shi da jikin gas sannan ta sake shi tana ta godiya, yaqe kawai yake haka ta debi abincin ta suka koma parlour ta na ci ta na sake nuna masa dalilin da ya sa take son aikata hakan, Wanda shi Sam be dauki hakan a Wani babban dalili ba Banda takurawa abinda zata haifa da Sanya shi cikin damuwa da baqin ciki kamar yanda ta rayu a cikin su saboda yayar ta ta. A kwana a tashi yau cikin Rasheedah da Sakeenaa ya shiga watan haihuwar su wato watanni tara cip2, wanda Sakeenaah ko alamar naquda bata ji, amma Rasheedah kam tin kwana biyu da suka wuce take fama da ciwon baya da mara, yau abun ya tsanan ta, cikin taimakon Allah Auwal ya kaita asibitin da ta saba haihuwa,bayan gumurzu da artabu a d'akin haihuwar ta sillub'o diyar ta mace mai kama da ita sak kyakkyawa masha Allah, labari ya iske ma su Sakeenaah, inda cikin zumud'i ta hau girke2 da shirin zuwa asibitin dan ganin jinjirar, Adnan kamar ya hana ta amma dai ya yi shiru, dan bai son ya b'ata mata rai a wannan stage  d'in,haka ta gama ta shirya ya kaita, da sallama ta tura qofar suka shiga tare da Adnan, Rasheedah na bud'e idon ta ya sauka akan cikin Sakeenaah, wani uban ashar ta saki  sannan tace "Me nake gani kamar ciki a jikin ki Sakeenaah?" Adnan cikin qasaitaccen murmushi yace, " kwari kuwa, da yake Allahn da yake bayarwa ba ta hannun oo yake miqa abun ba sai gashi muma ya bamu," Sakeenaah ce ta dan dungure shi da hannu kan ya yi shiru , qarasa shiga suka yi,aiko Rasheedah ta had'e fuska, tana sababin ita bata son gayya haba abu a dami mutum daga haihuwa sekace ya yi shela? Ba wanda ya kula ta, Sakeenaah ta had'a mata tea mai kauri ta zuba mata farfesun naman kaji da yasha dankalin turawa, carrot,  da green beans da kayan qamshi nan take wajen ya kuwa kaure da qamshi, yawu Rasheedah ta had'iya sannan ta leqa kwanon, tana miqa mata ta amshe tana wani yatsina,ta hau ci kamar mayya, sai Wani zaro ido take, dariya Adnan ya kunshe, Sakeenaah ta harare shi, Auwal ne ya so magana shima tare da yin dariya Sakeenaa ta hana da ido, haka suka qunshe dariyar su, har ta gama, ko kwana basu yi ba aka sallame su dan Suna cikin qoshin lafiya ita da jinjirar. Yau kwanan Rasheeda hudu da haihuwa, Sakeenaa ta tashi da matsananciyar naquda mai tsananin azaba, gaba d'aya Adnan ya rasa jarumtar shi da kullum Sakeenah ke Kiran shi da JARUMIn ta kuka ya ke wiwi kamar shi ne ke naqudar, tausayin ta ya gama ragargaza naman jikin shi da tinanin shi Bangaren Sakeenaah kuwa........ Ku d'an Jira ko zuwa anjima mun ji mi nana ka hwaruwaaaa.... [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼    WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 12: Wata iriyar wahalalliyar naquda Sakeenaah ke yi,ta wani fannin ta sanya matsanancin tsoro da fargabar shin zata rayu da abinda take ta fata Allah ya bata shekara da shekaru ko Kuma mutuwa za ta yi? Wannan dalilin ne ya janyo jinin ta ya yi bala'in hawa, ba abinda take sai addu'o'i, wanda kusan rabin addu'ar tana nemar wa kanta rahamar Allah ne, sai kuma daidaito a tsakanin zumuncin ta ita da yayar ta, anyi inducing din ta kafin ta samu haihuwa, kukan jaririyar su ne ya karade ko ina, na dakin har da Wani sashe na asibitin ma. Dik halin nan da Sakeenah ke ciki Adnan na gefen ta ya na riqe da hannun ta ko yatsina fuska ta yi sai ya mata sannu,in ko ya ga hawaye a idon ta na gangara haka Shima nashi idon zai ta zubar da ruwa addu'a kuwa bai San Iya adadin abinda ya roqar mata ba da abinda zata haifa, sai da naqudar ta taso gadan gadan ne aka tada shi d'aga wajen ta ya tsaya a gefe, ma'aikatan lafiyar suka duqufa dan taimaka mata ta haihu. A lokacin da kukan jinjirar ta su  ya shiga kunnuwan shi kuwa rikicewa ya yi da murna da kuka, ba b'ata lokaci ya dora goshin shi a qasa dan godiya ga Allah, ya na d'agowa ya je jikin gadon ko gama gyara Sakeenaah ba a yi ba ya rungume ta ya hau sumbatar ta yace, "Sannu my love dama na fad'a maki ke Jaruma ce, kin ga qoqarin da ki ka yi ko?Allah ya miki albarka, Masha Allah Atiyyah (Kyauta )ta iso Allah ka raya mana ita da imani,ka ba maihaifiyar ta lfy, ni kuma ka qaran arziqin kula da ita," Murmushi Sakeenaah ta yi mabayyani, bayan an dora mata yarinyar tasu a jikin ta ta kalle ta ta sake  murmusawa a karo na biyu sannan ta ce, "Tabbas Ablah(cikakkiya daga kyaun halitta)  ta iso, Masha Allah ka ga yarinyar nan ba inda ta baro mu," Ta daga kai tana kallon mutane hud'u dake dakin, Doc. Midwifes biyu, da mijin ta Adnan, dan ta samu tabbacin maganar ta, gaba dayan su kad'a kai suka yi cikin yarda da maganar ta sosai, "Tabbas wannan gaskiya ne madam, barakallah yarinyar nan ta na da kyau anya mun tab'a karbar kyakkyawar haihuwa irin wannan kuwa?" inji likitan, "Gaskiya tinda muke bamu taba karbar haihuwar kyakkyawa irin wannan ba, kalar ta daban ne, Allah ya raya maku ita da imani," in ji d'aya d'aga cikin midwifes din, " Ameen" Suka amsa dika, nan take Adnan ya karbe ta ya mata addu'oin da suka zo  a sunnar Annabi Muhammad ana yi wa jarirai, sannan ya miqa ta ga Sakeenaah ta tauna dabino ta bata, nan danan ko ta tsotse shi tass, tana gamawa aka bata nono ta sha, sannan Doc. Yace su bada ta ai mata wanka a kawo masu ita, dai dai nan Mama da ta gaji da Jira a  bakin qofa ta shigo, itama ta na ganin yarinyar sai da ta yi sujjada dan godewa Allah, sannan tace a basu su dika su tafi ba maganar wani wankan asibiti tinda sun goge ta tas, haka kuwa aka  yi Sakeenah da baby na gama cika awannin da ake bayan an haihu a asibitin aka sallame su suka yi gida, gidan ta aka wuce da ita, dan basu shirya tafiya wankan gida ba, Adnan tuni ya sanar da ita baya so, shi a barshi komai a nuna masa zai mata Mama ta ce inaaa zaman biqi ba aikin namiji bane, ya dai bari a mata anan d'in tinda baya so ta je gidan ita ta zauna mata dan Maman ta kula da gaske baya son ta yi nesa da shi,suna isa kuwa ya daura ruwa a qatuwar tukunya, Mama ta shiga ta mai sannu tana tsokanar shi angon qarni, yana sunkuyar  da kai yana shafe qeya, fita ya yi yaje d'aki, ya isko Sakeenaah na ta bacci, tea ya hada mai kauri ya tada ta ta amsa tasha,su Shamsiyya kuwa dama ba yau suka Saba ganin yanda yake wa matar tashi hidima ba, Adnan mutum ne da ke kyautata wa matar shi kwatankwacin yanda take kyautata masa koma a ce fiye da hakan. Kitchen ya sake komawa ya bud'e fridge da freezer dan ya tabbatar in akwai komai da suke da buqata ko Kuma akwai buqatar qarowa, ya na tsaye ya na nazarin wajen ya hango wata roba da aka shaqe da farfesun kayan ciki dakkowa ya yi ya bud'e ya ji yanda qamshi ke tashi Shamsiyya ya kwalawa Kira ta zo cikin hanzari ta durqusa ya miqa mata tare da bata Umarnin ta dumamawa Sakeenaah. "To uban gida na ni ai da Ina Jira in ka fita ne ma in sama mata abinda zata ci, amma tinda ga wannan shikenan," "Kar ki damu a dumama wannan din ma ba komai, anjima sai a yi sabo," Mama na can na wanke jinjira, shi Kuma ta cikin matar shi yake, wata tukunyar ya gani ta tafaso ya ji qamshin abubuwan be tab'a Jin irin shi ba, tambayar Shamsiyya ya yi menene wannan? Amma dai ba matar shi za a bawa ta sha ba ko? Murmushi ta yi sannan ta ce, "Uban gida na wannan ai ba na sha bane, na zama ne, ruwan wanka tinda dama akwai na zafin a tolas d'in ku ba se an d'ora ba shine Hajiya Mama da ta zo se ta dora wannan d'in, tinda cikin Uwar d'aki na ya Kai wata takwas Hajiya Mama ta aiko da su" "To amma dai ba a tafashen zata zauna a ciki ba ko?" "Ah ahhhh Uban d'aki na, se ya huce daidai yanda zata iya zama" Sanda aka gama dumama farfesun Adnan da kan shi ya karb'a dan ya Kai mata, ruwan tea Mai kauri da ya sha kayan qamshi Shamsiyya ta dafa ta  sake had'a mata ta d'ora masa saman trey ta bashi, ya na Kai mata kuwa ba b'ata lokaci ta gyara zaman ta a saman gadon,yunwa ta ke ji sosai dama, sannu ya yi mata ya zauna gefen ta ya fara bata a baki be bari ba sai da ta qoshi sosai. Doc. Ya bada Umarnin  kar a sa mata ruwan wanka mai zafi sosai saboda hawan jinin ta dan haka ruwan da baida zafi Mama ta had'a mata ta taya ta wanka suka fito, Adnan na can d'ayan d'akin d'auke da jinjirar ya na ta kallon ta Cike da so da qaunar yarinyar,Kafin awa uku Baby da mama sun yi fes sun fito shar da su. Adnan da Mama waya suka dinga yi wa 'yan uwa da abokan arziqi Suna Sanar da haihuwar, cikin qanqanin lokaci gida ya cika da dangi da ke kusa da su both na Adnan d'in da Sakeenaah,har su Rasheedah sai da aka sanar wa ta hanyar Kiran Auwal da Adnan ya yi amma daidai da Allah ya raya bata San ta ce ba, ta dai tambayi abinda aka haifa aka Sanar da ita, can se ta kyab'e baki sannan ta cewa Auwal da ke mata albishir d'in haihuwar, "To da ka ke Wani fad'a min barin tawa jinjirar zan na tafi wajen tata jinjirar kenan ko me? Ni fa bana son jaraba haba" Kallo Auwal ya bita da shi, dan yanzu abin nata ya d'auke shi a matsayin bugun mugun baqin aljani ba yin kanta bane, magani ya Kamata ya nemar mata ko Allah zai sa a dace. Babyn Rasheedah taci sunan Farhah, bayan kwana bakwai itama Sakeenaah babyn ta taci sunan Mama, Haleema, inda Baban ta ke kiran ta Atiyyah, maman ta ke kiran ta da Ablaerh, Mama tace wannan sunan sai su ita ba ruwan ta Hali dubu zatana kiran takwarar ta, Abba yace Matas zai na kiran masoyiyar shi, Sakeenaah kam sai dai tai dariya, domin gata da so ba wanda bata gani wajen miji da iyayen ta, ga shi Kuma 'yar ta ma ana nuna mata soyayya Mai qarfin da ta fi wadda ake mata " Mama ya kamata ki je wa Rasheedah, kin ga zaman da kk min zai dad'a ja min qiyayyar ta, amma ki hakuri inna Fad'i ba daidai ba," "Zan tafi na je mata, amma da na je ba jimawa zan yi ba zan koma gidana tinda kin ga ita haihuwa ta uku ce fa ta San Kan komai,ke din ma tinda dai ga masu aikin ki dattijai biyu da Shamsiyya sun Iya komai Suna da amana Suna qaunar ki ga kuma mijin ki da yake Jin zai iya komai ma da kan shi dik za ku Iya kula da wannan mai manyan idon, Rasheedah kuwa tin da ta haihu na je wajen ta ta nuna bata buqata ta, amma shikenan ai bana biye mata ba, zan je d'in kamar yanda ki ka ce, Allah ya miki albarka," "Ameen Mamana, sai dai akwai wata alfarma danake son na nema a wajen ki," Qasa ta yi da murya sosai ban ji me tace ba, amma naga Mama ta miqe cikin fushi, "Dama jira nake ki min wannan maganar banzan da Abban ku yace kin masa tin wata biyu da suka wuce,shi ya hane ni da tinkarar ki da maganar duba da rashin lafiyar da ki ke fama da shi, idan shi ya maki alqawari, to ni ban yi ba, kuma ba zan taba yi ba, sanin kan ki ne Rasheedah ta tsane ki, da duk wani abu daya dangance ki, hauka kk da zaki ce haka," Kuka ta fara sosai, harda shessheqa, hankalin Mama ba qaramin tashi ya yi ba,dan ko kad'an bata son damuwar Sakeenaah, Sakeenah irin yaran nan ne da ke da shiga rai saboda tsananin biyayyar su da kyawawan halayen su, shi ne dalilin da ya sa suke son ta ainun, cikin sassauta murya Mama ta ce, "Abun har ya kai haka,to tsaya, ki bar kuka mu yi magana, fad'an dalilin ki kwakkwara na aikata hakan?" Hawayen ta ta share ta fuskanci Maman ta ce, " Maa ni nafi son koma meye dalilina daga baya kun gani, ni bana son furta meye uzurina, alfarmar nan kawai zaku min ku nuna min soyayyar ku cikakkiya a gareni bayan ba ni a doron qasa, Ina so wannan abun da zan yi ya zama wasiyya a gare ku kin ko San Mama wasiyya indai ta alkhairi ce dole ne a cika ta ko?," " Akul na kuma jin maganar idan bake dinnan kina karyan zuciya sosai Sakeenah, wa ya ce maki Zaki mutu yanzu? Dan Allah ki dena wannan maganar mara dad'in ji" murmushi ta yi kawai sannan ta rungume Maman,hawaye na bin kuncin ta, a haka ta samu ta fara gyangyadi, Adnan ne ya dan leqo ya gaida Mama, da hannu ta masa nuni da ta yi bacci, a hankali ta zame jikin ta daga na Sakeenah ta gyara mata kwanciya shi Kuma ya gyarawa Baby Atiyyah kwanciya  sannan suka ja masu qofa suka fita, daukan Mama ya yi a mota dan ya Kai ta gidan Rasheedah,ya zauna a qofar gida dan tace a yau zata koma gidan ta ba zama za ta yi ba, " Aaa Mama ce a gidan namu yau Kuma,to  sannu da zuwa, ya kuma kk bar mai jego da jikar so," Baki Mama ta saki ta bi Rasheedah da ta yi maganar da kallo, lallai wannan rashin kunyar ta ta na buqatar gyara,har da ita abun zai tab'a ashe "Gidan ku Rasheedah, ni kk kalla ki fadawa haka? A jikokina wa na ware, haihuwar ki nawa? Ita haihuwar ta nawa? Meyasa kk haka? Ke yanzu ba zaki daure ki sawa zuciyar ki salama ba,to sai anjima dama leqowa nayi a gaisa naga jaririya, Allah ya raya mana da imani" Cikin maganar shi ta yara Yousf yace zai bita, daukan shi ta yi ta fice tabar Rasheedah na mata Allah ya kiyaye, dan ita a ganin ta ta fadi abinda ke ranta, dama lokaci zuwa lokaci Yousuf kan je mata ya yi kwanaki, duk da ba safai Rasheedah ke yarda ba. **************** Atiyyaerh da Farhah na da saurin girma da ga wayo, sai dai Atiyyaerh tafi Farha girman jiki, kamar itace babba, in Mama ta fada ace ai ta yi son kai,bayan abun a buɗe yake, amma Rasheedah na jin an ce Atiyyaerh ta fi Farhah  jiki sai ta fara fad'in "To abinka da jikar so", Mama ta yi nasiha ta yi zagin,ta yi fad'an ,amma inaaa, ita haka take ganin anfi son Atiyyaerh bisa ga Farhan ta, a kullum Sakeenaah qara zama shiru take, duk da Adnan baya son hakan, amma haka take roqar shi ya kaita gidan yayar ta,cin ranshi ji yake kamar ya yi bindiga, ita ko Rasheedah in sun je ba ta da aiki sai habaici da mugayen kalamai akan Atiyyaerh, dan kawai taga ko ta ina ta wuce Farha, hasken fata kawai Farha zata nuna ma Atiyyah, kamar dai ita da Sakeenaa. Yau yaran suke cika shekara biyu cip, inda Sakeenaah ta saka yarinyar ta a gaba mai tsanain wayo da magana kamar ta shekara uku ta na ta yi mata addu'o'i, Abban ta ne ya shigo ya dawo daga shopping ya siyo mata wasu sarqoqi masu kyau sosai na zinare da wasu kayayyakin na sawa, Sakeenaa ta yi ta mitar kaya sun mata yawa ya dinga tinawa akwai wasu yaran a dangi Yana taimaka musu mana, sannan ya daure ya dena  shagwaba ta haka,yakan ce, "Haba My love ita kadai fa muke da ita,in ban mata ba wa zan yi wa?" Rausayar da kai kawai ta yi, ta qawata fuskar ta da murmushi, sannan ta ce, " Allah ya qara maka bud'i Abu Ablaerh," "Ameen, Zo ta nan ki zauna kusa da ni, nifa sai na ga kamar kin d'an fara kyallin goshi, ko dai Atiyyaerh ta yi qani ne," Ya qarasa ya na mai sumbatar kuncin ta, rungume juna suka yi Adnan ya d'aga Kai ya kalli qofar d'akin Atiyyah dake a rufe ya ce, " Ni fa na kula tin da aka haifi yarinyar nan wasan parlour ke gagarar mutum, tashi ki gani muje na duba ki, ko akwai ajiyata a jikin ki" Dariya ta yi sosai, "Ka duba ni ka ga akwai ajiya ko kuma ka yi ajiyar yau, dan dai ni nasan ban da komai," "Muje dai an gani duk kin gama rudan rutsuwa da wannan qamshin naki, " ni ko na ce tooooo da kyau Sakee baby☹ Maganar Adnan ta tabbata, ashe Sakeenaah dai ciki har ya yi wata uku ba su sani ba, sun gano hakan ne ta hanyar amai da ta gama sheqawa bayan ta sha tea da safe ta na kukan yanda take Jin kasala sai Adnan ya ce, " Na fada maki na yi ajiya kin qi yarda ko," Bata fuska ta yi ta ce, " Ni ba wata ajiya da nake da shi," "Tinda baki yarda ba to tashi muje asibiti in ba tsoro ba," Dariya ta yi tace ta dai ji tsoron take, a qasan ranta tana godewa Allah, in dai hakan ya zama gaskiya,a nutse ta futa "Na yarda muje " "Bismillah mu je" Tashi suka yi suka shirya tsaf sai asibiti, gwajin farko aka gano ciki dan wata uku, murna kam ba sai na fada maku irin wadda suka yi ba ranar,biyawa ya yi da ita super market, ta kwashi kayan zaqin ta, suka dawo gida, suna isa ta sauke Atiyyaer, dake cin biscuit, sannan tai kitchen, tea ta hado ta zauna zata fara sha kenan, Atiyyaerh ta zubar mata da shi wajen qoqarin itama sai ta sha, fada ta mata ta kora ta wajen Abban ta, ita kuma tai kitchen dakko mopa, ta dawo tana ma Adnan bayanin kukan Atiyyaerh bata kula ba santsi ya kwashe ta, ta fada kan center table, kanta ya bugu, qafarta ta zame ta kifu ta gaba, wata qara ta sake tana kiran sunan Allah, Adnan da gudu ya qaraso,......... *wayyooooo niiii Ummu Ablaerh plssss don't die, makaranta zasu sambaden wallah,ki tausayan😭😭😭* [30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼   WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *Dan Allah masu tambaya daga farko ku yi hakuri a gama gaba ɗaya a haɗa document sai a tura maku...masu tambayar KUN MAKARO daga farko dan Allah ku tambayi mutanen group ɗin da kuke ciki maybe ba za a rasa wanda ba ya clearing chats ba sai a Baku ko ku buɗe document da na tura group ɗin da kuke ciki ku karanta ta nan. Kar ku manta KYAKKYAWAR FAHIMTA ne kawai sabon littafin da nake yi a yanzu waɗannan dika reposting nake yi na jima da yin su...Na gode* Page 13: Kafin Adnan ya isa ya taimaka mata ta Kai qasa,gaba daya jini ya jiqe wajen, daukan ta ya yi suka yi waje dan zuwa asibiti,ganin halin da take ciki ne ya sa aka shiga emergency room da ita aka shiga duba ta, hankalin Adnan ya Kai qololuwa wajen matuqar tashi, jikin shi sai rawa yake ya kasa yin komai, so yake ya yi kuka ma ko zuciyar shi ta sake daga qullin da ta masa, amma inaaa hawayen sun qafe sun qi zuba,suna nan a haka ya yi tinanin Ablaerh ya baro ta ita d'aya a sashen su ga su Shamsiyyah na can wajen su ba lallai su ji me ke faruwa ba, wayar shi ya zara jiki ba kwari ya kira Shamsiyya ya Sanar da ita ta dauki Ablaerh su koma shashen su da ita, sannan ya yi wa Mama waya ya sanar da ita komai, a sannan ne ya ji Wani kuka ya zo masa sosai, kashe wayar ya yi ya kife fuskar shi a tafukan hannayen shi, ya na jin matiqar tsoro, domin yanda yaga jini na bin qafafun ta da kanta,in dai daga  jikin ta ya fito to tabbas tana buqatar wani ko kuma Wani abu mara dad'i ya same ta, yana tina hakan ya miqe da gudu ya yi inda aka kwantar da ita, yana masu magana da qarfi yana kuka, akan su bude ya ga matar shi, da kyar aka rirriqe shi ya samu ya zauna ya had'e kai da guiwa yana ta zubda hawaye, ba a fi minti 20 ba Mama da Abba suka zo, tare da Yousuf, sai Ablaerh da suka biya suka d'akko,  yana nan zaune suka tadda shi, Abba ne ya dafa kafad'ar shi, ya d'ago rinannun idanun shi ya kalle su, kad'a mashi kai kawai Abba ya yi, domin shima daurewa kawai yake, "Ka yi hakuri ka k'warara zuciyar ka, kai mata addu'a kaji," Adnan na jin kalmar addu'a ya tashi  kamar wanda aka mintsina, ya samu waje ya zauna ya daga hannaye sama, yana ta roqon Allah akan ya bata lfy, ko abinda ke cikin ta bai tsira ba yana roqon Allah ya bar masa matar shi, ba qaramin tausayi ya ba Mama da ke ta kuka ba a gefe, suna haka likitoci biyu sika fito, dayan ne ya cire glasses din shi, ya sharce zufa, miqewa suka yi a tare baki d'ayan su suka nufe su dan jin me ke faruwa, d'aya daga cikin likitocin ne ya kalli Adnan ya ce, "Alhaji Adnan Bismillah Ina son magana da kai" Abbah ne ya kalli likitan ya ce, "Zaka iya fad'a mana ko me ke faruwa baki d'ayan mu Doc. ni mahaifin ta ne, wannan mahaifiyar tace," "Ok to ku biyo ni," Shigar su office din ke da wuya suka samu mazauni suka zauna, inda Adnan ya samu gefe ya tsugunna ya yi jugum kawai, Doc. Ya fara magana kamar haka, "Gaskiya 'yar ku na cikin hadari sosai Alhaji domin kuwa ta zubda jini sosai ba kadan ba, mun samu mun qara mata da hanzari, dan bari sai an nemo a dangi ma bata lokaci ne, i am very sorry to inform u that we have really tried to save the baby amma mun rasa shi, sannan ta samu rauni mai zurfi a kanta, wanda a qallah zai dau wani tsahon lokaci kafin ta warke,..... Sannan Kun San dama tana d'auke da hawan jini" Tin da ya fara magana salati kawai Abba yake, Mama na share kwalla, tinani kawai take, ita kuma Sakeenaah haka Allah ya jarabce ta da faruwar al'amura haka, addu'a take mata na samun cin wannan jarabawa, " Eh mun san tana dauke da shi," in ji Abbah da ya ji yanda wajen ya d'auki shiru, banda shassheqar kukan Adnan ba a Jin komai sai qarar AC. "Ya na da matuqar mahimmanci a kula da lafiyar ta saboda a wannan yanayin da take ciki bamu da buqatar abinda zai dame ta in har Allah ya sa ta farka, hakan ba zai faru ba har sai Kun taimaka mata ta hanyar yi mata dik Wani abinda take so, kar ana dinga sanya ta cikin damuwa,... zata iya farkawa daga nan zuwa gobe amma sallamar ta sai yanda muka ga jikin nata ya yi sauqi dan haka ku kwantar da hankalin ku a yi Imani da Allah shine Mai warkar wa Alhaji zata samu lafiya, ka daure ka ci gaba da bata kulawar da muka sanka da shi, ni anjima zan tafi d'an uwan ka zai zo ya ci gaba da bata kulawa,(cousin din Adnan dake aiki a wajen) Inshaa Allah zata samu lafiya, Allah ya bata lfy," " Ameen" suka amsa dika, miqewa suka yi zasu fita,har a wannan lokacin Adnan na tsugunne, Abba ne ya kama hannun shi suka fita, d'akin da aka kwantar da ita suka leqa ga tanan kwance  kamar matacciya, wasu hawaye ne masu zafi suka wanke fuskar Adnan, zuwa ya yi ya zauna kusa da gadon a kujera, ya jingina kan shi da gadon, ya kama hannun ta, kuka yake kamar qaramin yaro, Ablaerh ta matsa kusa da shi, ta kwantar da kan ta a jikin guiwar shi, itama tana kukan, ba qaramin tausayi suka ba Abba da Mama ba, fita suka yi waje, wannan karon Abba ma kukan yake, "Kar ki tafi ki barmu, muna matuqar buqatar ki a wannan lokacin, yarinyar mu is just 2years she needs u, pls ki taimaka ki zauna da mu, Yah Allah ka d'aga kafadun ta, ka sa mata kaffara, Yah Allah ina son mata ta, ni maraya ne,ka ban ita dan ta zama haske a rayuwata, Allah ka rayan ita ta ci gaba da tallafa ma maraicina," Adnan shiru ya yi da magana dan Yana tsoron kar ya yi sab'o,ci gaba ya yi da kuka ya na riqe da hannun Sakeenaah, kukan shi ne ya sa Ablaerh qara fashewa da kuka, d'aga ta ya yi ya na rarrashin ta,dan shi yanzu ta matar shi yake, a hankali ta yi bacci se ya rungume ta a qirjin shi. Har safiya ta waye Sakeenaa shiru ba alamar motsi a tattare da ita, hankalin Adnan da su Abbah  ya yi matuqar tashi, nan da nan Adnan ya miqe ya fita, a waje yaga su Abba da tin jiyan Suna nan basu tafi ba, Suna leqa su lokaci zuwa lokaci, tashi suka yi suka nufe shi ganin tashin hankali a kwance a fuskar shi, "Me ya faru?" In ji Abba da tin da gari ya waye ya ga bata farka ba yake cikin damuwa, " Abba har yanzu bata motsa ba, zuwa zan na kira Doc." Ya qarasa magana  idon shi taf da kwalla, numfashi Mama ta sauke, dan ta matuqar tsorata, Doc ya kira, ya je d'akin, duba ta ya yi yace zata tashi nan da kamar awa d'aya inshaa Allah, zama Adnan ya koma ya yi a gefen ta, Mama da Abba suka zauna a saman gadon dake d'akin a gefen ta , tin daren jiyan dama ya kwantar da Ablaerh akai, ido suka zuba mata baki d'ayan su kawai, kowa bakin shi da addu'ar Allah ya bata lafiya ya bata iKon farfad'o wa........ [01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 15: Ko da na bi inda Rasheedah ke kallo sai na hango Mama d'auke da Atiyyaerh a cinyar ta, tana shafa bayan ta a hankali a haka har ta yi bacci, komai akan idon Rasheedah ke faruwa, d'auke idon ta ta yi ta zumbura baki gaba dan ganin ga ta ta yarinyar a gefe amma a qasa ko Maman ta d'an jingina ta da jikin ta, nan da nan abun na ta ya motsa, ta d'aure fuska, ta kira Afrah, maqe kafada yarinyar  ta yi taqi zuwa, sai ta matsa kusa da Mama sosai, daidai wajen Atiyyaerh, itama ta kwantar da kanta, murmushi Mama ta yi ta shafa gashin ta, a qasan zuciyar ta tana nema wa Atiyyaerh sauqin zama a wajen Rasheedah Koda  ta hanyar Afrah ne. Bakwai na cika dangi na nesa da na kusa kowa ya tattara ya koma mahallin sa, Mama sai ta wuce da Atiyyaerh gidan ta, Rasheedah ba qaramin Jin dad'in hakan ta yi ba, dan a zaton ta sun manta da wasiyyar da Sakeenah ta bar musu, ko Kuma tinda sun San halin ta ba za su yarda yarinyar ta zauna a wajen ta ba, Dan haka gida ya rage Daga Masu aiki sai Adnan,Adnan d'in kuwa dama shi ko zaman makoki da ake a farfajiyar gidan shi ba zama yake a wajen ba, ko waye ya je masa gaisuwa sai dai ya tarar da su Abba ya musu gaisuwar  ya juya, Koda yaushe ya na sama cikin d'akin shi, daga sallah sai tasbihi da roqar wa matar shi da iyayen shi Rahamar Allah, Jin shi yake kamar ba zai tab'a Iya ci gaba da rayuwa Mai dad'i ba a yanzu da ya rasa jigon rayuwar ta shi. A qarshen satin Abba yace ma Adnan ya qoqarta had'awa Atiyyaerh kayan ta da dik Wani abu da ya dace dan damqa ta wajen sabuwar Uwar ta ita wasiyya ana so a gabatar da ita da gaggawa,  hankalin Adnan ba qaramin tashi ya yi ba, yayi kuka ba iyaka, da kan shi ya lallashi kan shi, dan ya san cika umarnin Sakeenaahn shi zai yi ya riga ya mata alqawari, yana daga cikin wasiyyar ta da ta dinga jadaddawa kafin ta mutu, kuma ya kamata a cika mata ita, had'a kayan Atiyyaerh ya shiga yi idanun shi na zubar da hawaye, yana cikin hadawar ne ya ga wasu takardu guda biyu, daya duba sai yaga *Zuwa Ga Ablaerh My Love* Sai dayar kuma an rubuta, *KAI NE JARUMI NA* Daukan ta Atiyyaerh ya yi ya ajiye a  gefe ya bude tashi, gaba d'aya fuskar shi ba komai sai hawaye, tayi jawur da ita, *Mijina* *Kai ne jarumi na, kai ne hasken idaniya ta, kaa zauna dani cikin so da qauna, tare da amana, ka zama jigon rayuwa ta, kai ne Wanda  in nayi kuka kk sharen hawaye na, in nayi dariya kk tsayawa ka kalli kyau na ka yaba min,in nayi girki kai santi ka yabi aiki na* *Jarumi na, ina qara roqon ka akan ka daure akan abinda na yi wasici akai, ba dan ba ka da iko akan d'iyar ka ba, sai dan na san Jarumtar ka zata sa ka yi hakuri, dan cikar burina, fatana ka yi ta min addu'ar samun sa'a akan quduri na kar ya zama ba nasara* *Allah ya had'a fuskokin mu a jannatul firdaus, mu d'ora rayuwar aure fiye da wadda muka yi a nan duniya Mai Cike da tsafta da jin dadi, INA SON KA MIJINA JARUMI NA* *DAGA MATAR KA SAKEENAA* Saka takardar ya yi a qirjin shi yana kuka, a qasan zuciyar shi kuma yana jin kwarin guiwar rabuwa da gudan jinin tashi, ci kaba ya yi da had'a kayan ta, bayan ya gama da kayan nata ne  ya dauki wayar shi ya koma d'akin shi, (ban san me ya ke fada ba tinda ya rufe ta ciki☹) bayan zuwa kamar awa d'aya cur ya fito d'auke da wasu akwatuna da jaka a rataye a kafad'ar shi, qasa ya sauka ya kira driver din shi, bayan ya shiga ya gaishe da Adnan,sai Adnan ya bashi umarnin d'iban akwatunan daya d'akko daga d'akin shi zuwa qasa, sanan ya koma ya dakko kayan Atiyyaerh, ya zauna a kujera ya na kallon cikin gidan, daga baya ya miqe ya fita cikin hanzari yana share kwalla, zuciyar shi na tinano masa irin zaman so da qauna daya faru tsakanin shi da Sakeenaah a cikin gidan, d'aya motar ya bude ya zuba kayan Atiyyaerh  a ciki,ya ja da kan shi, ya nufi gidan Mama, yana zuwa ya yi parking a farfajiyar gidan sannan ya shige ciki, Atiyyaerh na ganin shi ta daka tsalle ta d'ale shi tana masa surutai, wani ya gane wani Kuma bai ganewa, shi dai ba ya buqatar ganewar ma, kallon ta kawai yake kamar wanda ba zai sake ganin ta ba, Abba ne ya fito Mama na biye da shi, "Aa Adnan kaine tafe, barka da zuwa, Bismillah zauna mana ka ke tsaye" Isa gaban Abba ya yi ya bashi hannu kan shi a qasa kamar yanda suka Saba gaisawa, bayan sun gaisa ne ya gaida Mama ta amsa cikin sakin fuska da tausayawa, janyo kayan Atiyyaerh ya yi gaban su, sannan ya miqa wa Mama dan akwatin da ake saka mata kayan adon ta, musamman na gashi, share hawayen da ya gangaro masa ya yi sannan yace, " Abba ina neman izinin ku akan tafiyar dana yanke hukuncin yi, zuwa Dubai, domin ci gaba da kasuwanci na, a yanzu banda sauran dalilin zama anan, sai dai inna tafi zan din ga zagayowa domin ganin ku,ku kad'ai nake kalla a matsayin iyaye, dan haka ba zan dad'e ba zan dinga zuwa ganin ku, sai dai duk abinda nake fad'a yanzu sai fa Kun bani izinin ku zan aikata shi," Kan shi a qasa, yana sauraran amsar su,ya na addu'ar Allah kar ya sa su dakatar da shi, dan baya Jin zai iya ci gaba da Zama a Nigeria kusa da 'yar shi ya na ji ya na gani ta na rayuwa a hannun Rasheedah, "A gaskiya Adnan dole na jinjina Maka domin kuwa na yarda da sunan da Sakeenaah ke Kiran ka da shi na  *KAI NE JARUMIN ta* domin kuwa a iya tsahon rayuwar ka ka ga abubuwa kala2, dan haka ina son wannan karon ma ka zama jarumin wajen sanyawa zuciyar ka hakuri, in dai tafiyar ka zata sama maka kwanciyar hankali ni dai na maka izinin tafiya, Allah ya sanya albarka, ya kare mana kai dik inda ka shiga, nasihata a gare ka ka zama mai tsoron Allah, kar ka zama mai sab'a masa ko ketare dokokin shi, in kai haka Allah zai kare ka ya kiyaye ka,sannan Kuma ka samu ka je wajen Baffanin ka da Kawunan ka ka musu sallama kar ka tafi ba tare da sanin su ba" Kallon Mama suka yi da ta sha majina irin na masu kukan nan, "Adnan Allah ya maka albarka, ya faranta maka, Allah ya jiqan mahaifan ka da Sakeenaah ya raya abinda kuka haifa Allah ya kare mana Kai a dik inda ka shiga, Allah ya habaka kasuwancin ka Ameen," Amsawa suka yi dikan su da "Ameen" sannan sika miqe don raka Adnan zuwa waje, wasiqar da ya ga an rubuta sunan Atiyyaerh ya zaro a aljihun shi ya damqa a hannun Mama sannan ya yi gaba zai fita,Atiyyaerh ce ta riqe shi tana kuka, tana kiran Mummyn ta, Adnan zuciyar shi ta cika fam da quncin rabuwa da mutanen da yafi so a rayuwar shi, bai san sanda ya yakice ta ba ya shige motar ya ja da gudu yana kuka, Mama da ta sunkuya ta d'aga Atiyyaerh dake birgima a qasa, kukan itama take, Abba share kwallar shi ya yi ya taimaka mata sika d'aga ta, dan ji ta yi ta yi mata nauyi, sai tirjewa take, tana kiran Daddy da Mummyn ta, a haka sika shiga,Mama ta goya ta,yar wayar shi Abba ya lalubo ya kira Auwal. Ba su fi awa biyu a zaune ba Auwal da Rasheedah suka shigo, bayan gaishe2 ne, Abba ya sanar masu da dalilin kiran nasu dika, ya kira su ne dan damqa amanar da marigayiya Sakeenaah ta bar masu, Rasheedah ce ta bata rai sosai, sannan ta ce.......... [01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼     WRITTEN  BY HERMEEBRAERH Page 16: Bakin ta da ta bud'e za ta yi tijara kamar yanda ta Saba ta kulle gam dan ganin yanda kowa ya d'aure fuska dan son ganin qarshen rashin mutunci da qiyayyar da take wa 'yar uwar ta ta, musamman ma Auwal da yake jin in tace zata yi wani gangancin nuna ita fitsararriya ce ba abinda zai hana shi yau a gaban iyayen na ta ya jibge ta ai hukunta ta ya yi tinda Rasheedah dai kamar jakka take sai ta ci bugu take nutsuwa yau kuwa a shirye yake da ya hukunta ta gaban iyayen nata, tana fuskantar hakan daga wajen Auwal sai ta ce, "Ba sai ka tashi ka dau akwatin mu tafi ba, aiki ma malam kawai ina fama da wasu qananan a gaba na a tashi a wani jonan wata," Ta na kaiwa nan ta yunqura ta dau qarama daga jakunkunan Atiyyaerh ta yi waje ta na mita addu'ar shiriya iyayen ta da mijin nata suka bita da shi, Mama sai share hawaye take ta na kukan tausayin marainiyar Allah, da ace Sakeenaah ta yi shawara da ita kafin dasa wannan tunanin a zuciyar ta ai da ta hane ta, ta sauya mata da wata shawarar Mai billewa, domin a iya hangen nesanta na manya bata hangowa Atiyyaerh Jin dad'i wajen Innar tata ba sai wahala, Abba ne ya dinga lallashin ta ya na bata baki ya na nuna mata abinda ya sa Sakeenah yanke wannan hukuncin, fatan su Allah ya sa yarinyar ta yi SANADIN shiryuwar Rasheedah. Rasheedah na fita waje ta ga mota mai matuqar kyau sosai a fake a harabar gidan, gefen motar kuwa drivern gidan marigayiya ne jingine da ita, drivern ne ya duqa kad'an ya gaishe ta, sannan ya tambaye ta inda mijin ta yake, amsa masa ta yi da, "Ya na ciki akwai Wani abu ne?" Sai Wani zaro ido take, komawa gefe drivern ya yi yana jiran fitowar Auwal, zuwa ta yi kusa da shi tace, "Malam ba aiko ka aka yi ba ne? To ka isar min da saqon mana in ya so in ya fito se na Sanar da shi," Kallon ta ya yi kawai dan yana da labarin ta tsaff dik Wani kalar wulaqanci da qiyayya da take nuna wa Madam din su ya sani, dan haka cike da jin haushin ta ya kalle ta ya ce, "Amma ai da na zo kk ga na maki magana hakan na nuna maki cewa na san ko ke wacece,shi  ya sa ma na tambaye ki mijin ki, To saurin Jin saqon da yake ba naki ba na mene ne? Ki Jira ya fito mana mtswww" Cikin tsananin mamaki da shakkar drivern ta ja baya tana qunquni, dan ba qaramin jibgegen mai qarfi bane, fuskar nan baqiqqirin ba wasa a tattare da shi, komawa ta yi ta qame sannan tace, "Ka gama b'oye2n uwar da zaka b'oye duk uwar da zaka fad'a zai dawo kunne na ne" Cikin fushi ya matsa daf da ita yace, "Uwar wa kk nufi?" Su Abba ne suka fito dan rako Auwal da Atiyyaerh dauke da akwatunan yarinyar, Abba ne zai Kai su tinda Auwal ba shi da abun hawa,kicibus suka yi da abinda ke faruwa tsakanin Rasheedah da driver,kallon Rasheedah suka yi wadda ido ya firfito waje ya mata gulu2 se wara su take cike da tsoro, a firgice take da mutumin kamar ka ce mata kyatt ta saka gudu, hanlalin ta ya yi mugun tashi to dukan ta wannan basamuden ze yi ko me? "Niiiii....niiii...ni.. ban ce uwarr ka baaa.. ai," Ta qarasa maganar tare da damqe bakin ta da ke rawa, tsoro ne ya mamaye ta ta ji kamar ta saki fitsari saboda maimaita kalmar uwar ka da ta yi, tana kyalla ido taga su Auwal na fitowa da gudu ta kwasa ta yi wajen su tana maida hawayen daya taru mata, Auwal na ganin yanayin ta sai ya ji be ji dad'in hakan ba, ko ba komai ya na son matar shi, halayen ta ne baya so ko kad'an, cikin yanayin daure fuska ya ce wa mutumin, "Malam lafiya  zaka sa min mata a gaba kana muzurai? Kai ba drivern Alhaji Adnan bane?" Cike da girmamawa ya qaraso, ya gaishe su, sannan ya sanar dasu ya kai Adnan Airport ne se ya bashi umarnin ya kawo motar gidan Auwal,ya je gidan nasu ya tarar ba kowa shine tunanin shi ya bashi ya zo nan, ya San ba za su wuce nan d'in ba, godiya su ka yi sosai, Mama hawayen tausayin Adnan da qaramar 'yar su ne kawai ke kwaranya a idanun ta, shikenan yanzu ya tsallake wata qasar dan kawai ya manta da damuwar rashin matar shi,anya kuwa ba za su nemi fatawa wajen malamai ba? Anya ba a cutar da shi ba? ta na wannan tunanin ta ga Suna Saka kayan Atiyyaerh a motar, sannan Auwal ya ce, "Mu je ka aje mu ka dawo da motar, Dan ka ga dai mu bamu da inda za mu ajiye ta, kar a sace a wannan unguwar tamu, gwanda a barta nan kawai zai fi" Da Jin haka sai driver ya ce, "Ai Yallab'ai cewa ya yi na maida ku can gidan shi, in yaso ko in akwai wani abu da kuke buqata a can gidan naku kun je ku dauka daga bay,amma yafi son ku koma gidan nashi da zama tinda ba kowa ciki se masu aiki" Auwal ya so ya qi karb'ar tayin komawar su wannan katafaren gidan Rasheedah ta hau rantsuwar ba zata koma tsohon gidan su ba ga gida sun samu daga sama su tsaya Wani halin qauyawa, Abba ma tausar shi ya yi akan ai ba komai ya karb'a su koma can d'in zai fi maslaha, da kyar Auwal ya amince za su koma d'in, murna Rasheedah ta hau yi ko kunya bata ji bakin ta har kunne, ashe da rabon ta a cikin wannan makeken gidan,kaiii jama'a daɗi kashe ta,  haka suka d'unguma suka yi gidan, suna isa bayan sun fitar da kaya ne ta shiga ciki da Farha da Ayiyyaerh, driver na ganin ta wuce ya zagaya gefen Auwal ya fad'a masa wata magana qasa2, sannan suka yi sallama ya tafi, yana waiwayen gidan yana hawayen kewar iyayen gidan nashi masu son shi, masu karamci, addu'ar samun Rahamar Allah ya yi wa Sakeenaah sannan ya nema wa uban gidan shi sauqi a wajen Allah daga halin quncin da yake ciki,kafin su rabu se da Adnan ya bashi jari mai tsoka da qaramin gida, shida me gadi, su Shamsiyya ma sai da ya musu ihsani sosai kafin ya sallame su, dik da ya basu zab'i in suna so Suna Iya ci gaba da zama idan sabuwar matar gidan bata da matsala da hakan. Tana isa ta aje Afrah dake hannun ta ta saki hannun Atiyyaerh da ta tattaka ta nufi sama dan dubo Mommyn ta, ta na tafe ta na kiran mommyn nata da Daddyn ta, Rasheedah kuwa  juyi ta hau yi tana kallon gidan, wani daɗi ne ya kama ta, yanzu ta zama hajiya kenan, ga sauran suturun Sakeenaa nan, dan da akai rabon gadon Sakeenah surutun ta kaf an bar wa Rasheedahn ne tinda kusan girman su d'aya, murjewar fata kawai Sakeenaah zata nuna wa Rasheedahn saboda banbancin Jin dad'in rayuwa,a lokacin da aka ce an barmata suturun  qunci ta dinga yi ta na fad'in ba a bata komai ba, gani take duk uwar dukiyar su ace ba ta da abin gada na qanwar ta ta se sutura? Auwal ta gani ya shige ta ya yi dakin da aka kwatan ta mai direct, bin bayan shi ta yi da azama,daf  zai bud'e qofar d'akin dan ya shiga ne ya juyo ya wurga mata wani kallon da yasa ta koma gefe da sauri, shiga ya yi ya saka key, inda aka masa kwatance nan ya leqa,baya ya yi da sauri, dan bai tab'a ganin abinda ya gani ba a rayuwar shi, kud'i ne maqudai masu yawan gaske, a cikin wata jaka qarama, gaba daya ya rud'e se zufa yake samun gefen gado yi ya zauna,yana kallon kudin daga nesa, takardar dake Kai ya dakko ya bude, karantawa ya hau yi a zuciyar shi, idonun shi sai zubar da hawaye suke, nan danan ya saki kuka sosai, tausayin bayin Allahn nan yake ji matuqa,a yau ya tabbata dukiya ba ita ce kad'ai farin cikin rayuwa ba,komai Allah ya baka ko da tsinke ne ya nufa ta SANADIN  shi ne za ka yi farin ciki to kuwa za ka yi farin cikin,nan take ya ji duk soyayyar da yake wa Rasheedah a baya ta kau, domin ta dalilin ta ne wannan qunci ya sami wannan mutum na rabuwa da gudan jinin shi, domin ba dan qiyayyar da ta nuna wa Sakeenaah ba da tini yana tare da diyar shi, daure fuska ya yi ya miqe ya adana kud'in ya cire key d'in ya fita daga d'akin a bakin qofa ya gan ta ta na muzurai, Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya Isa d'akin da ya ke Jiyo kukan Atiyyaerh ya d'auke ta suka bar gidan, bin shi ta yi da kallo da son qarin bayani akan me ya Kai shi cikin d'akin Kuma me ya faru ta ga kamar ya yi kuka, Auwal kuwa ya fita ne saboda baya son ganin ya ta yanzu kwatakwata, ji yake kamar ya rufe ta da duka, ya rasa me zai gaya mata ya fidda mata wannan halayyar tata a jikin ta, kyabe baki ta yi ta ci gaba da exploring gidan. Ana Kiran sallar azahar Auwal ya dawo da Atiyyaerh ya shige d'aki ya yi alwala zai wuce masallaci, Atiyyaerh da ke Jin yunwa ce ta ke tab'a Rasheedah ta na maimaita mata kalmar, "Mummy tea, Mummy tea, Mummyyyy" Jin da ta yi bata amsa mata ba sai ta fashe da kuka sosai, Afrah da ke tsotsar hannu lokaci zuwa lokaci ta tashi zaune tana ta kallon ta tana tsotsar yatsan ta babba, a fusace Rasheedah ta juya ta kalli Atiyyaerh da ke kuka ta ce, " Wacce irin jaraba ce wannan, ke ba zaki bar mutane su huta ba? Dubi yanda kika tasar min yarinya, kin koma kin zauna a can ko sai kin ci uban ki yanzu," Cikin zare ido da d'aga murya take maganar, abinda Atiyyaerh bata tab'a sani ba kenan a rayuwar ta, ai ko ta fashe da wani rikitaccen kuka,ga yunwa na damunta, tin da suka dawo bata ci abinci ba, gashi har azahar ta yi Auwal ya so ya tsaya ya had'a Mata tea d'in amma kawai ya wuce masallaci. Ko da ya fita ma tinanin halin da ya baro yarinyar yake, kukan ta har cikin ranshi yake jin shi, maqotan su Rasheedah basu tab'a jin kukan Atiyyaerh haka ba,unguwar ta talakawa ce Adnan ya yi gini a ciki domin ya na kwadayin taimakawa marasa shi, ya tabbata in ya yi gini a manyan unguwannin masu kud'i daidai da abincin da za a bayar sadaka ba lallai a samu masu buqata ba, dan haka ya yanke shawarar gina gida anan,Kuma yake taimaka masu sosai, tausayin yarinyar ne ya kama su dan a  tinanin su Atiyyaerh na kukan rashen mahaifiyar ta ne, "Ahhh lallai naga alama zaki fara cin ubanki kuwa,nace ki yi shiru se ki baren baki? Ke baki san menene shiru ba ashe? Tsit nace" Ta dora yatsan ta a baki tana zaro mata ido, cikin kuka da gigicewa yarinyar  ta kwantar da kanta a gadon tana runtse ido, dan a tsorace take da zaro idon da Rasheedah ke mata,amma ta kasa yin shiru, a hasale kuwa Rasheedah ta kaiwa bakin duka tana fad'in, "Shiii nace kar na sake jin kukan ki" Damqe bakin ta ta yi tana ci gaba da kukan a hankali, tare da ajiyar zuciya, a haka ta samu ta yi bacci, tana ta ajiyar zuciya, miqewa Rasheedah ta yi ta fice tana banbamin fad'a, Auwal ne ya dawo a gaggauce hannun shi d'auke da biscuits da madarar gwangwani babba da na Ovaltine, sai millo. "Ki ji tsoron Allah akan amanar da aka baki, Ina jiye maki sanda amana zata ci ki, Marainiya ce fa? Wanne irin hali gare ki? Na yi matuqar danasanin had'a zuri'a da ke, na yi danasanin sanin ki a rayuwa ta, amma bawa baya wuce qaddarar shi, Rasheedah ke ce mummunar qaddara ta a rayuwa ta, Ina roqon Mai dika da ya bani iKon cin jarabawar nan,dana san haka kk da ba zan taba hada zuri'a dake ba?" Ya na gama magana ya ajiye mata ledar ya wuce d'akin shi dan yin sallah tinda ya San yanzu Kam an riga da an idar a masallaci. Wani irin haushin Atiyyaerh ne ya qara kamata,yanzu a Kan wannan yarinyar take ganin wutar qiyayya da tsabar tsanar ta a idon Auwal? Ina soyayyar da yake mata ? A Iya sanin ta dik laifin da za ta masa Kuma ko me zai faru tsakanin su Auwal be tab'a dena son ta ba, hawaye ta ji na bin kuncin ta, da sauri ta goge su, ta na ayyana kala kalar muguntar da zata gana wa Atiyyaerh. Bata ba wa yarinyar nan komai ba kuwa na ci sai dare da suka zo cin abincin dare, ai kuwa ta na gama cin abincin ta hau amai, saboda yunwar da ta mata yawa a cikin ta, masifa da bala'i Rasheedah ta fara yi ta na dungure mata Kai, a haka ta gyara wajen ta na zage zage, tea ta had'o mata ta dangwara mata a pida ta haye sama, dan ta riga ta qudurta yau sai ta gwangwaje a sabon gidan nan halin da Atiyyaerh ke ciki kuwa ba zai hana ta hakan ba, Auwal kuwa tinda ya fuskanci take taken ta ya wuce d'akin yaran shi maza ya yi kwanciyar shi da su bayan ya gama nuna masu su dinga kula da qanwar su, duk abinda take so Suna yi mata daidai Wanda za su iya, Wanda ba za su iya ba su na barin Maman su ta yi, budar bakin Yusuf kuwa sai cewa ya yi, "Abbah ai na ga Mama bata son Ablaerh dukan ta kawai take da zagin ta ko da yaushe" Auwal rasa amsar da zai bawa yaron ya yi Dan haka sai ya hau basu tarihin Annabawa har bacci ya d'auke su, su na nan kwance ya ji an bud'e qofa, Rasheedah ya gani sanye da wasu fitinannun kaya, sun bala'in mata kyau, da dane ba abinda zai hana shi zuwa gare ta, amma yanzu Wani irin kyankyamin sake kusantar ta yake gani yake tsabar munin halin ta duk ya manne a jikin ta ba zai so ya kwashi halin ta ba kuwa, Gani ta yi ko kallon azziqi bata ishe shi ba balle na tsiya, cikin shagwaba da tura baki ta ce, " ko ka tashi mu koma mu yi abun mu can dakin mu ko kuma muyi anan," Kallon baki isa ba ya mata,in Kuma ki na iyawa zo ki yi na gani, murmushin mugunta ta yi ta fara cire rigar saman Yousuf da be bacci ba ya kalle ta,zata cire zanin ta kenan Auwal ya yi sufa ya cafke cikin rad'a mata magana a kunne ya ce, "Baki da hankali ne? Meye haka kk yi a gaban yara? Muje can jarababbiya kawai mahaukaciyar banza wadda bata bawa abun kunya mahimmanci ba a rayuwar ta," Sallama ya wa yaran ya rufe su tare da dafa Kan su ya musu addu'o'i ya kashe fitila ya tura qeyar ta sika tafi, dariyar mugunta ce fal ranta,tin kan su isa ta qarasa cire zanin daga ita sai wata yaloluwar riga ciki babu komai, kallon ta ya yi cikin tsananin Jin haushin ta, kenan da a gaban yaran zata cire ta tsaya a haka? Lallai be tab'a sanin ya auri mahaukaciya ba sai yau,ita kuwa ko a jikin ta sai wani juyi take a gaban shi,kasa jure kallon ta ya yi ya fizge ta da mugunta ya wurga ta d'akin nasu ya banko qofa a ran shi ya na ayyana irin muguntar da zai mata tinda ta d'age se an yi🙊 Auwal tin Yana mata na mugunta har zuciyar shi ta yi laushi ta saki dan kuwa Rasheedah na da matuqar tasiri a wajen shi ta nan bangaren in dai zai kusance ta to damuwar shi na raguwa, halayen ta ya tsana matuqa dan se ka kwana tinani baka gano wanne ne na gari a halayen ta ba, da misalin qarfe uku na dare ya tashi ya zauna bakin gado ya na kallon ta ya na tinani kala kala akan halayen ta, ita kuwa  tana ta kwasar baccin ta, a hankali ya tashi ya nufi bathroom Dan yin wanka, ya na fitowa ya Sanya gajeren wando da vest ya Dora jallabiyya sannan  ya tafi kitchen ya hadawa Atiyyaerh madara, mai kauri, da ruwan dumi, sai ya dakko cake da ya gani a fridge ya je dakin su ita da Afrar,kwance ya ganta amma idon ta biyu, tana son yin kuka tana tsoro, hawaye sai zuba yake a gefen idon ta,tana ganin shi ta fara irin abunnan na hadiyar zuciya na masu kuka, da sauri ya isa gare ta ya rungume ta tsam a jikin shi tare da fad'in, "shsssssss, kar ki kuka kinji baby Ablaerh na," Qanqame shi ta yi sosai tana kuka, danna mata cup ya yi a baki,nan danan ko ta kama, ta hau sha, tana gama sha ya bata cake din taci kad'an can kuma ta fara bacci ragowar  cake d'in a hannun ta,tausayin ta ne me tsanani ya kama shi ya goge kwallar da ta taru a idon shi, ya dauke guntun cake din ya goge mata hannu da tissue, sannan ya goge mata baki, ya gyara masu kwanciya ya masu addu'a ya tashi ya fice, d'aki ya koma ya kwanta, yana tinanin wannan ruqo da aka basu, tabbas ba zai iya bari ana ma yarinyar nan horon yunwa ba, dole ko yaya ne yana kula da cin ta da komai nata, ko a bayan idon Rasheedah ne. Washegari bayan ta kammala komai da ya dace se ta shiga d'akin yaran ta tada su, suka yi brush, ta koma kitchen aka fara had'a abinci, hankalin ta kwance ga wata murna dake ranta, wai yau ita ke da wannan gidan? A haka ta kammala tana 'yan waqe waqen farin ciki, tana kammalawa ta jere a saman dinning table,yaran na zaune already Suna jiran ta kamar yanda ta umarce su, zuba musu abincin ta fara sannan ta zuba wa Kan ta da Afrar dan a baki take da niyyar bata, Auwal ne ya fito sanye cikin shadda Mai kyau da ta karb'i kalar fatar shi se zabga qamshin turare yake, ya na qarasa balle maballin rigar,yaran ne suka gaishe shi ya amsa Cike da fara'a zama ya yi ya ga be ga Atiyyaerh ba gashi ta tasa yaran ta a gaba da dankali da kwai da soyayyar kaza an had'a shayi Mai kauri ba 'yar masu gidan, "Ina Atiyyaerh?".......,.. [01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 18: A tsorace Atiyyaerh ta ja da baya,cab'al qafar ta ta shiga cikin kashin, yanda Rasheedah ke matsowa tana masifa haka Atiyyaerh ke ja da baya, tana tattaka waje da kashin, wata tsawa Rasheedah ta sakar mata akan ta tsaya ta daina yad'a mata kashi a ko ina, gigitaccen kuka yarinyar ta saki mai qarfi jikin ta babu inda ba ya rawa, Yousuf kanshi sai da ya firgita, ya durqusa gaban Ummar tasu ya na kuka ya ce, " Umma dan Allah kar ki daki Ablaerh, ki yi hakuri, zan gyara maki wajen," Haushi ne ya qara kama Rasheedah ganin yanda d'anta ke kuka akan wannan sokuwar yarinyar, aiko sai ta ci uban ta yau, kallo ta watsa masa da ya sa shi miqewa ya yi gefe ba shiri, zuwa ta yi ta damqi Atiyyaerh da gashin kanta ta wanka mata mari biyu masu kyau, sannan ta kama kunnen ta ta yanka mata warning din daga yau kar ta sake ganin qafafun ta a parlor in dai ba ita ta kira ta ba, sannan ta tsaida ita gefe ta je d'akko abubuwan da zata gyara waje da shi, in banda a jiyar zuciya yanzu ba abinda Atiyyaerh keyi, dan ta kasa kukan ma, zuwa ta yi tana goge wajen tana zagin ta, bayan ta gama ta dauke ta a wulaqance tai bayi da ita, wanke mata ta fara yi da tsintsiya,a cewar ta bazata saka hannun ta ba bata son taba kashi, ko wa ya ke wanke wa Afrah Kashi oho? duk haka ta sossoke mata duwais da tsintsiyar yarinyar kuwa haka ta dinga kuka saboda azabar zafin da take ji, sai da ta rage kashin sosai sannan ta saka leda a hannun ta ta wanke mata, da ruwa mai sanyi, hankado ta ta yi waje tace taje ta kwanta ta yi bacci, cikin ajiyar zuciya irin ta wadda ta gaji da kuka Atiyyaerh ta tafi ta kwanta, jikin ta ba kaya sanyi duk ya dame ta, a fusace ta bar dakin, Yousuf ne ya shiga da gudu ya je ya rungume qanwar tashi suka yi ta kuka tare, tin daga nan ya dasa qiyayyar mahaifiyar shi a zuciyar shi, domin ganin mugun abun da take aikatawa qaramar yarinya, ruwan d'umi ya samo da taimakon Sulaiman a saman dinning na cikin flask dan basu Iya kunna ruwan zafin bathroom d'in ba da ruwan sanyi suka had'a daidai wanka suka mata wanka me kyau,Suna gamawa suka hau duba kayan da ya dace su Sanya mata a garin haka ne suka yi kaca kaca da wajen kayan sawar nata ba tare da sun Wani damu ba suka zab'ar mata wata riga da wando na sanyi suka sa mata,ba jimawa bacci Mai nauyi ya d'auke ta sai ajiyar zuciya take saki. Cikin tashin hankali Sulaiman ya kalli Yousuf dan ganin b'arnar da suka tafka na fasa flask din ruwan zafin da suka yi wa Atiyyaerh amfani da shi, Rasheedah na jin qarar ko ta fito kamar wata mahaukaciya, "kan uban can , a cikin ku waye ya fasan flask, ko uban ku ne ya siyo da za ku fasa min?" " Umma ni ne na fasa ba da sane na ba, amma kuma ai kema ba ke kk siyo ba, Mummyn Ablaerh ce ta siyi abin ta," in ji Yousuf da ya kafe ta da Ido Shima cikin rashin kunya. Mari ta daga hannu zata kai masa, Auwal da ya shigo da manyan ledoji niqi niqi a hannu ya ce, "kina taban yaro yau na lahira sai ya fiki jin dad'i, dan se na maki dukan da ban taba maki irin shi ba jakar banza wadda bata da hankali, Rasheedah a kullum garin Allah ya waye se na zagi Kai na na Kuma yi wa kaina Allah ya qara dan son zuciyata ya kaini yi maki qarya na aure ki, ga sakamakon abinda na aikata nan Ina girba, ke din wata iriyar jarabawa ce mummuna a gare ni, a kullum Ina danasanin sanin ki a rayuwa ta, yanzu me ya faru? Me ya miki ki ke so ki dake shi? Ina Afrah da Atiyyaerh?" Ido ya zuba mata Yana son Jin qarin bayani, Kalaman shi sun yi matuqar sukan zuciyar ta,ta ji zafin kalmar shi na ita d'in mummunar qaddara ce a gare shi, hawayen ta ta mayar ta na sauraron Yousuf da ke rattaba masa bayani akan abinda ya faru, kallon ta kawai ya yi da takaici ya ja hannun yaron suka wuce ciki, Yousuf Jin shi yayi kamar wani JARUMIn maza, da qananan shekarun shi ta dasa masa qiyayyar ta, da son kare Atiyyaerh ko da zata dake shi shima,ya qudurta ko kashe shi ma zata yi sai dai ta kashe shi amma ya dena shiru in tana zaluntar Atiyyaerh,shi yanzu ma ya dena son ta Mummyn Ablaerhn shi yake so, in ta dawo daga tafiyar da Abban su yace sunyi ita da Abban Ablaerh wajen su zai koma da zama. *BAYAN SHEKARA UKU* Yousuf ne ya fito da shirin zuwa makarantar *AL-ANSAR* da ke unguwar maqotaka da su, Atiyyaerh ce ke kallon shi Cike da sha'awa, Yousuf d'in ne ya Sanya ta zamo Mai tsananin son karatu, tinda  yana koya mata karatu idan ya dawo ko sanda baya komai a gidan, Atiyyaerh na ganewa sosai kuma ta na da saurin daukan karatu,dafa Auwal ta yi da yake Saka takalmin shi a zaune a gefen kujerar da ke kusa da qofar fita daga parlourn, " Abba nima ina son a sani a school din su yaya," Murmushi Auwal ya yi sannan ya d'aga ta sama yana mata wasa suna dariya, Afrah na gefe tana tsotsar hannun nata da ta saba, Rasheedah ce ta fito ta kalle su ta kalli d'iyar ta a gefe dake kallon su tana murmushi tana tsotsar hannu, "Ikon Allah, wannan shine agola yafi dan gidan," Sannan ta wuce kitchen, sai da ta dawo ne Auwal ya bata amsa da, "Tabbas wannan shine agola yafi d'an gida, domin ke da kk zo da gayyar ki gidan yarinya har da mijin ki, ke kk neman mallake wa yarinyar gidan ta, makaranta nake son saka ta, da kud'in ta, dan ubanta ya bada kud'in zuwan ta makaranta, har jami'a, sannan ya had'a da naki yaran, dama lokaci nake jira, dan haka gobe2n nan ba jibi ba zan d'auke su ita da Afrah na kai su makaranta suma," Tsallen murna Atiyyaerh ta saka, Yousuf na mata dariya, ya ja hancin ta, ita ko Afrah kuka ta saka, ita bata son makaranta, duka ake in ji Yah Sulaiman, da kyar Auwal ya rarrashe ta ya mata bayanin yanda lamuran makaranta yake in baka Jin magana baka karatu to fa zaka daku, amma in kana Jin magana Kuma ka na da qoqari se dai a baka kyauta amma ba duka ba, ta na Jin haka se ta yi shiru, had'e su ya yi dika ya fita dasu ta ci kanta dan tinda ya ce zai Saka Atiyyaerh a makaranta ta ke bala'in kashe kud'i za a yi a banza,se da ya qara saiwa yaran abun kwalama sannan ya aje su a makatanta,  yawatawa ya yi ta yi da su Afrah,kafin su nufi hanyar gida Afrah ba wani ci take ba dan tafi ganewa tsotsar hannu, Atiyyaerh kam ta dage ta yi ta ci, dan ta san wataqila da sun je gidan shikenan ta gama ci kenan, ya maida su gida ya yi shirin fita aiki, ya qara jan kunnen Rasheedah akan amanar da aka bata, yana fita kuwa tace da wa Allah ya had'a ta bada Atiyyaerh ba, dukan ta ta hau yi tana zagi, "Munafuka mai halayya irin na uwarta sak, ku dinga simi2 da kai, kamar na Allah, kuna cutar da wanda kuke tare da su, sarai kin san Afrah bata son makaranta kike wani tsalle, dan za a saka ku, dan kija ace ke mai hankali ko? Ita mara son makaranta ko? Kuma wane munafikin ne ya ce ki ce asaka ki ? Yau sai kinci ubanki, gobe in ya ce zai kai ku kice zaki kigani yanda zan kakkarya ki a gidan nan" Sai da ta mata lilis sannan ta tura ta d'aki ita d'aya, Afrah ma miqewa tsaye ta yi zata bi bayan Atiyyaerh, Rasheedah ta daka mata tsawa akan ta koma ta zauna, aiko ta saka kuka sosai, taqi komawa ta zauna d'in, hannu ta miqa dan ta ja ta jikin ta ta hana ta, yarinya kuwa ta kwasa da gudu ta yi dakin, tana shiga ta kulle, kuka ta tadda Atiyyaerh nayi, bata ce mata komai ba ta zauna gefen ta ta saka hannun ta a baki tana tsotsa hawaye na zuba mata, a haka har su ka yi bacci suna ajiyar zuciya. Bayan Yousuf sun dawo ne yake tambayar ina suke , Auwal ma tambayar ta ya yi inda yaran suke da ido ta yi nuni da d'akin su,kallon su ta yi ta ga yanda suka bi hanyar Suma da idanun su, se kawai  ta yi murmushi, dan ta san qaryar da zata yanka masu, kwata2 bata son Atiyyaerh taje makaranta, bata son ta samu Wani abu na ci gaba a rayuwar ta sam........ [01/07, 12:42 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH Page 17: "Ina plate din Atiyyaerh?" "Bata tashi ba in ta tashi na had'a mata nata," Tinawa ya yi jiya yarinyar bata samu bacci da wuri ba, ya tabbata bacci ne mai nauyi ya d'auke ta yanzun, se kawai ya ce, "Ok," kafin su gama Atiyyaeh ta farka, ta fito, tana murza ido, gashin ta duk ya hargitse, ya sauka a saman kafad'un ta, direct wajen Rasheedah ta nufa,da sauri Rasheedahn ta hankada ta baya, yarinyar ta bige cup din tea da yousuf ya d'aga zai Kai bakin shi,zafin tea d'in da ya zuba a hannun ta ne ya Sanya idanun ta cika da hawaye, kallon Rasheedah Atiyyaerh ta yi sannan ta fashe da kuka, "Shiiiii ki rufen baki,mai shegen kukan tsiya, uban wa zaki zauna wa a cinya? Ko Afrah ga ta nan a zaune tana karyawa da kan ta,ko kuwa se ke 'yar  gwal zan d'auka? To maza samu waje zauna nan na hada maki abinci, kuma ki min shiru ko ki daku yanzunnan" Miqewa ta yi rai a b'ace taje ta hado mata shayi tsalalo ba Wani wadataccen Madara da millo balle sugar, sannan ta soyo kwai guda d'aya, ta kawo ta dangwara mata ta yanko bread ta dora a saman K'wan ta ce, "Ga shi nan ki cinye dan in kk tsaya min shegen kukan nan naki zane maki jiki zan kina ji na ko," kyab'e baki Atiyyaerh ta yi kamar zata yi kuka tana ci gaba da kallon Rasheedahn, cikin wata iriyar murya mai tsananin nuna gajiyawa da halayyar Rasheedah Auwal ya ce, " Rasheedah ki ji tsoron Allah, wannann yarinyar da ko kyakkyawar magana mai ma'ana ba zata iya maki ba sai ta had'a da shirme kasancewar ba ta da cikakken wayo, ita ki ka zauna ki na wa wannan abubuwan na zalunci, dubi abinda kk bamu dubi wanda kk bata,ita da gidan ubanta, kayan abincin ubanta, kaiii amma baki da imani Rasheedah Sam sam" ya na kaiwa nan ya ja kujerar da yake Kai ya miqe da niyyar barin wajen. "To a min gori tinda Ina gidan uban ta, na ga dai gidan qanwata ne Kuma Ina da gadon qanwata dole na zauna na ci azziqi na bar azziqi a mazaunin shi,sannan ba ni na roqi uban nata da ya ban wajen zama da abincin da zan ci ba, haqqin ka ne ciyar dani me kyau da ban wajen zama mai kyau,sutura mai kyau da kulawa, amma ka gaza wasu mazan sun tara kaima ka zauna cin azziqi, dan haka daga yau kar a sake min gorin azziqi da ka tara da ban ci na wasu ba, Kuma na ga ai zaka iya bata naka in kana so ba Wanda ya hana ka ai, da ta tashi da wuri ai da haka bata faru ba," komawa mazaunin ta ta yi ta ci gaba da cin abincin ta, gaba d'aya abun da Rasheedah ke yi a Kan idon Yousuf Kuma ya na gane halin muguntar da take wa Atiyyaerh da rashin azziqin da take wa mahaifin su,yaron yana da wayo sosai, shekarar shi bakwai, tashi ya yi da dan guntun tea din shi a hannu ya je ya had'e waje d'aya  dana Atiyyaerh sannan ya sake raba masu, nata yafi yawa sosai, sannann ya miqa mata k'wan shi, ya d'au guda d'ayan da aka soya mata, ya na juya shi sai ya ga a qone ma yake ta baya, kawai sai ya hau cire qonannen Yana zubawa a gefen plate d'in shi ya na cin Wanda be qone ba, hakan da yaron ya yi yayi bala'in burge Auwal,komawa saman dinning d'in ya yi ya d'auki nashi Shima ya yi mixing da na Atiyyaerh ya sake raba musu Sulaiman ma ya aikata irin abinda ya ga Yayan shi da Abban shi sun yi,Afrar ce ta tashi dugui dugui zata yi itama Rasheedah ta daka mata tsawa, "Meye haka? Meye wannan zaku dinga wa mutane qazanta wai ku masu tausayi,hana ta abincin aka yi da za ku dinga wa mutane qazanta? Ko dake wannan ma ai tausayin munafurci ne, ba za ku burge ni ba sai na ga kun fasa cin abincin kun bata naku dika," Buga tsaki Rasheedah ta yi sannan ta miqe zata wuce d'aki, Atiyyaerh na zaune ta na Shan tea ta dafe hannun ta a qasa,Cike da masifa Rasheedah ta wuce ko ganin gaban ta bata yi ta kuwa take hannun marainiyar Allah da ke zaune a qasa,wata iriyar razananniyar qara ta saka ta d'auke hannun ta ta na yarfewa tare da Kiran Mommyn ta, Auwal ba qaramin qoqarin danne zuciyar shi ya yi ba na barin ta be mata dukan tsiya ba, d'aukar Atiyyaerh ya yi ya lallashe ta ta yi shiru, sannan ya bata abincin, tare duk sika hade k'wai da dankalin turawan a plate d'aya suka qarasa karyawa, bayan sun gama ne ya shirya ya fita, fitowa ta yi ta kama kan yaran ta ta masu wanka, Atiyyaerh na ganin haka ta hau murna, tsakanin ta da wanka akwai amana, kayan ta ta hau cirewa a d'akin su Wanda a da na Sakeenah ne a yanzu Rasheedah ta maida shi na yaran, d'akin Kuma da yake mallakin Atiyyaerh sai ta maida shi na Afrah, kamar yanda Atiyyaerh ta ke Jin su Yousuf na ce mata Umma itama haka ta fito daga d'akin ba kaya, a bakin qofar toilet suka had'u da Rasheedah wadda ta dakko  Afrah a hannu kamar wata jinjira, da kallo Rasheedahn ta bi yarinyar ,ita kuwa se dariyar farin cikin za a mata wanka take, cikin muryar ta mai dad'i ta ce, " Umma nima a min wanfa" Fuskar ta d'auke da  fara'ar da ta ke qara mata kyau, b'ata rai Rasheedah ta yi sosai sannan ta ce, " Uwar ki ce zata miki wankan? maida wandon ki mai shegen iyayin tsiya kawai," Ta wuce gado ta ajiye Afrar kamar wata jinjira sannan ta fara shirya ta, Yousuf da Sulaiman already ta shafa musu mai ita suke Jira ta basu kayan da za su Saka, a ran ta ta na ayyana dole ne a sauya musu kaya, dan ba zai yuwu Suna a cikin Irin wannan qaton gidan a ce yaran ta na Saka gwanjo ba, kayan sawar su yousuf ta d'akko ta basu,ta hau taya su Sanya wa, Atiyyaerh kuwa ganin ana ta yi ba ita sai ta zuba mata Ido ta na bin ta da  kallo, can  ta kuma cewa, " Umma wanfa," wannann karon idon ta ya kawo ruwa dan tsaf ta na Jin me Rasheedah ke fad'a ai, ta Gane bata so ta mata wankan ne, cikin fushi Rasheedah ta ja ta suka fad'a bathroom d'in, Atiyyaerh kuwa na ta murnar za a mata wanka, tap ta kunna ta tara ruwa a robar da ta yi wa Afrah wanka, ta na gamawa ta d'auke ta ta tsumbula ta cikin ruwan sanyi zata yi mata wankan da shi,kara ta sake ta miqe tsaye tana karkarwa, dariyar mugunta Rasheedah ta saki kamar wata qaramar yarinya me mugunta,zare Ido ta yi ta umarci Atiyyaerh da komawa cikin ruwan ta zauna, qi ta yi ta ci gaba da kukan ta a tsaye, da qarfi ta zaunar da ita cikin ruwan , yarinya na kuka ta qarasa mata wankan, daga ranar ruwan sanyi ya koma na wankan Atiyyaerh, se dai idan ruwan zafin wankan yaran ya ragu, tsabar mugunta ce ta sa ba zata kunna tap din ta sake had'a mata me zafi ba, tinda akwai heater a bathroom d'in,ta gwammace ta d'ebi na sanyi ta yi wa yarinyar amfani da shi. ******************************* Mama  na zaune ta na tinanin ko ya Atiyyaerh take ? Dan ta riga ta San halin Rasheedah bata Jin zata Iya kyale yarinyar ta wataya a gidan su,se kawai ta yanke shawarar zuwa dan ganin ya suke tafi da riqon amanar da aka bar mata, bayan ta sanar da Abba ya bata izini,sannan ya fita shago a unguwar ya siyo abubuwan kwalama na yara yace akaiwa Atiyyaerh da su Afrah, sallama suka yi ta hau abun hawa sai gidan su Atiyyaerh. Tana isa gidan ta bud'e gate da kan ta ta shige, tinda ba mai gadi yanzu, harabar gidan ta kalla ta ga ba motocin gidan hatta da ta Auwal d'in babu, alamu ne na ya fita kenan, da  sallama ta Isa qofar shiga cikin gidan, ta kama hannun qofar ta murd'a, sai ta ji ta a bud'e, sallama ta ci gaba da yi amma ta ji shiru ba Wanda ya amsa, a can ta hango Atiyyaerh k'wance akan kujera ta takure waje d'aya, ta na rawar sanyi,ga parlour ya d'auki wani duhu saboda kashe fitulu da aka yi Kuma labulaye a sake suke, zuwa ta yi da sauri ta Isa gaban yarinyar ta d'aga ta tana tab'a jikin ta, zafi taji rauu, nan danan ta d'aga ta hankalin ta tashe, kwalawa Rasheedah kira ta hau yi amma shiru, miqewa ta yi ta bubbud'e d'akuna biyu na farko da maibin shi taga wayam, sama ta hau can inda d'akin yaran yake a nan ta gansu, Rasheedah ce a tsakiya yaran sun kwanta a jikin ta sun rufu suna kallo, kwalin popcorn zaune a gaban su suna kallo suna ci, mamaki ne mai tarin yawa a ran Mama, "Me nake gani haka Rasheedah? kin saka yaran ki a gaba Kuna kallo amma kin bar wannan tahalikar ita daya a waje, da Wani barawo ne ko me mugun abu ya shigo gidan fa? Shikenan sai a cutar da ita ke kina nan Kuna more rayuwa da yaran ki? habaa Rasheedah, a ina ki ka koyi wannan rashin imanin ne haka? Wacce iriyar zuciya ce a qirjin ki? Tinda ki ke da ni Rasheedah baki taba gani koda bera na wulaqanta ba, haka mahaifin ki, me zakice wa Allah randa ya tambaye ki amanar marainiyar da aka bar maki?" Cike da takaici mama ta bar d'akin, zuwa ta yi tana hawaye ta na tina Sakeenaah baiwar Allah, ta duba kitchen ta d'akko maganin zazzabi na Yara ta had'a tea Mai d'umi ta bawa Atiyyaerh tea d'in da magani, sannan ta dakko towel da ruwa mai rangwamen sanyi ta yi ta goge mata jiki da shi, kafin minti 5 ta fara zufa bacci mai nauyi ya d'auke ta. Bayan fitar Mama Yousuf ya qurawa mahaifiyar su ido, domin ta masu qarya, d'aga kafad'a ta yi tace wa yaron da ya kafe ta da kallo, "Meye kuma kk tsare ni da wannan manyan idon naka," " Umma kin ce tana bacci a d'akin mu," "Eh mana fitowa ta yi dan munafurci amma ai a can na barta ta na baccin" Sauka ya yi daga gadon ya fito ya zo wajen Kakar su ya zauna, nasiha ta hau yi masa sosai game da qanwar tashi kamar wani babban mutum haka yake sauraron ta kuma dik abinda take fad'a masa yana shigar shi matuqa, Rasheedah ce ta fito tana hura hanci ta zauna a d'age ta gaishe da Mama, ko kallon ta mama bata yi ba, ta miqawa Yousuf ledar su tace masa shi da qannen shi, wannan kuma na Atiyyaerh ne,Abba ne yace a basu, cikin fushi Rasheedarh ta fara magana, "To baga shi ba, yaran ma sai kin nuna banbanci, tsakani da Allah ai da hadowa kawai za ai ace gashi a ba yara,ba kiyo ledar kowa daban ba, ta haka ne yara ke tashi kai a rabe," Cikin fushi Mama ta fara magana, "Ai tinda dama zuciyar ki ba mai kyau bace dole ki ji b'acin rai akan hakan, haba ke kuwa, ki dinga sanyawa kan ki salama, ki sawa kan ki tausayi, da soyayya, ko kin mori kyaun da Allah ya miki, domin wannan baqar zuciyar taki ke tauye ki" Kauda kai Rasheedah ta yi tana qunquni, Mama bata ce komai ba ta aje Atiyyaerh ta miqe zata tafi, sai da taje qofa ta juyo tace, "Abinda kai a duniyar nan za a maka, wanda bai ba ma an masa balle kayi, kuma Allah ne shaida ban ma iyayena haka ba, mahaifin ku har iyayen shi suka rasu sina saka masa albarka,ki bi duniya a sannu shi haqqin maraya nauyi ne da shi, nauyin shi ya fi dutsen Dala Rasheedah ba Zaki Iya d'aukar nauyin haqqin marainiya ba ki samawa Kan ki salama ki ajiye qiyayyar nan mara tushe, kin Yi wa mahaifiyar ta hassada da zazzafar qiyayya ta bar maki duniyar, yanzu madadin ki yi karatun ta nutsu ki tina kema watarana Zaki inda mahaifiyar yarinyar nan ta tafi amma ki ke toshe kunnen ki ki ka rintse idon ki ki ke wa yarinya azaba, kar ki ce ban fad'a maki ba Rasheedah na fitar da haqqin da ke tsakanin mu na uwa da 'yar ta na fad'a maki gaskiya ruwan ki ne ki bi, ruwan ki ne ki barta kar ki bi" Tana kaiwa nan a maganar ta ta fice, dan guntun tsaki Rasheedah ta ja sannan ta d'auki ledar Atiyyaerh ta debi kayan ciki ta qara a na su Yousuf, Sulaiman da Yousuf na tsaye suna kallon ta tare da Afrah ta debi biscuits da sweets ta basu, Yousuf qin karba ya yi, sai ita Afrah ce ta karba, Sulaiman kuma da aka bashi, zuwa ya yi ya aje gaban Atiyaerh ya koma ta bashi wani, cikin qara da hargowa ta fara magana, " 'Yan iskan yara masu halin uban su kar ku ci d'in ku kuka sani," Ta kwashe ledojin zata shige d'aki sai ta ji muryar Auwal na fad'in, " Allah na gode maka da basuyo halin ki ba duk da banji me ya faru ba, da sunyo halayen ki da na shiga uku na lalace da haifar mugun iri," Cike da rashin kunya ta murgud'a baki ta shige d'aki, Yousuf ne ya labarta masa dik abinda ya faru da baya nan,nan take ya d'ebe su a amota zai Kai Atiyyaerh asibiti, likita ta gani ya duba ta ya rubuta magunguna, sannan ya yi hani akan a rage yawan yi mata amfani da ruwan sanyi Kuma a kiyaye bata ruwan sanyin ta na sha,suna kammalawa da asibiti suka bi suka sai magungunan da aka bata, sai sukaje wajen cin abinci, aiko Atiyyaerh ta kwashi gara, taf ta cika cikin ta, sannan suka dawo gida, direct d'aki ya kaisu, dan basu buqatar abincin dare ranar, cikin Atiyyaerh ne ya motsa, ya yi qara, nan take ta sake wata muguwar tusa mai wari, su Yousuf ne suka toshe hanci suna tsokanar ta, wasa suke suna ta guje2, can kashi ya matse ta, " Yaya zan yi kashi," "To bodara mu je ki gayawa Umma," kama hannun ta ya yi ya tafi da ita wajen Rasheedah, suna zuwa tsakiyar carpet din wajen Atiyyaerh riqon kashi ya kwace mata, tako sake shi a wajen, tana kuka, daidai Rasheedah ta fito dauke da kwanon data gama cin farfesun kifin da ta yi da basa nan,wani wari ne ya daki hancin ta,cikin toshe hanci da yatsina fuska ta kalli su Yousuf da ke zare Ido ta ce, "Meye wannan? Me nake ji haka, Kashi ki ka min a qasa? kan ubancan kayyasa, yau se na ci kut......Uban ki Ina zuwa,........... [01/07, 8:47 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 19: Auwal mamakin yanda Rasheedah ke ta hidima da shi a daren yake,ita ce Yi masa girki mai dad'i da ya fi so, had'a masa ruwan wanka har da su zuba kayan wankan da suka tarar a bathroom d'in masu gyara fata na maza, Yana fitowa ya tarar da kayan da zai Saka na jiran shi, ita ta taya shi shiryawa ta feshe shi da turaruka masu dad'in qamshi, ga wata uwar Kwalliya da ta fesa Kai ba zaka ce ta tab'a haihuwa ba ma balle ace ta ajiye Yara har uku,sai Wani yauqi da shisshige masa take, ya gaji da Shan mamaki qarshe dai ya kama ta suka zauna a bakin gado ya zuba mata idanun shi da ke bala'in burge ta, ya ce, "Fad'a min wannan sauyin halin na menene, domin ke ba abar yadda bace Rasheedah" Wani abu ta ji ya soki zuciyar ta me zafin gaske, Auwal baya fad'in abinda ba haka ne a zuciyar shi ba, hakan na nufin da gaske mijin ta me son ta da qaunar ta a da yanzu be yarda da ita ba?hakan fa na nufin ya dena son ta,dan se akwai yarda soyayya ke samun wajen zama,laifin waye dika wannan? Laifin Sakeenah da 'yarta ne? Tabbas laifin su ne, saboda da alama ya fi son su sama da ita da take matar shi, qoqarin danne baqin cikin ta tayi sannan ta yanko murmushin yaqe ta ce. "Haba Abban Yousuf me na yi Maka a rayuwa Mai zafi haka? Ni dai dan Allah ka yi hakuri bana son tone tone, shi mutum in Yana aikata laifi ya gane kuren shi ai se ya gyara tin kafin a nusar da shi ko Kuma lokaci ya qure masa ko? Na gane kuskuren da na ke aikatawa gaba d'aya shi yasa nake so na gyara,ka yi hakuri ka dawo min da soyayyar ka da qaunar da ka ke min a baya" Kuka ta fashe da shi Wanda ta tabbata sai ya lausasa zuciyar shi, duk fad'a ko dukan da zai mata tana sane da baya son kukan ta, taurin Kai ne irin nashi ke hana shi lallashin ta,a hankali kuwa ya ji ya yarda da neman gafarar da ta yi, amma be San me yasa ba ya kasa sakewa da ita, Yana Jin kamar akwai Wani abu da take qullawa, share mata hawayen ta ya fara tare da rungumar ta a jikin shi Yana lallashin ta. "Shiiiii ya Isa haka, ki dena b'ata hawayen ki, kin San bana son kukan ki ko?" Shessheqar kukan ta ne ya ragu, ta sake shigewa jikin shi, ta na Wani abu kamar qaramar yarinya, Auwal ya yi kewar ta da yawa, ya yi kewar shagwabar ta da soyayyar ta, tinda suka zo gidan komai yi yake cikin qunci da Kuma cewar ya zame masa dole ya mata abinda take so kar ta masa haukan ta, amma ba Dan Yana so ba, a hankali suka fara wasannin su, Rasheedah ta sake masa jikin ta sosai ya na yanda ya ga dama da shi, cikin wata iriyar muryar da ke rikita Auwal ta fara magana, "Abban Yousuf da gaske kenan gobe za ka Kai Atiyyaerh da Afrah makaranta?" Auwal na Jin haka ya rintse Ido,ya fara qoqarin janye jikin shi da ya mata rumfa da shi Yana wasa da ita, Jan shi ta sake yi jikin ta ta na Masa wasanni masu rikitar wa, ta tabbata a yau ba zai iya fushi da ita ba saboda yanda ta sashi yake ji, ci gaba ta yi da magana daya gefen kuwa ta na Masa wasannin da ya sa maganganun ta ma basu wani shigar shi sosai, "Abban Yousuf kar ka fahimce ni ba daidai ba, na tambaye ka ne saboda ni nake zaune da yaran nan a gida, na San me kowa ke so, Ita fa yarinyar nan Auwal ba ta son makaranta,na sha jin maganar su da yara tana fad'in ita tafi son yayan ta yana koya mata a gida, dan haka ni shawarata da ka barta a gida....in su Yousuf suka je suka dawo daga makarantar kaga sai yana mata karatun a gida,ta haka ne shima zai samu kwarewa sosai," wani kallon baki da hankali kuma ke bama ki iya makircin ba ma Auwal ya mata ba tare da ta sani ba, domin yanda yake Jin ta birkita shi ba zai iya jurewa ya yi fushi da ita ba, gurnani kawai ya mata da "Uhmmmmm" Jin hakan da Rasheedah ta yi se ta qara qaimi wajen rud'a Auwal, ni dai tattarawa na yi na basu waje, na koma d'akin Yara muka kwana. Washe garin ranar kuwa Rasheedah na can na baccin gajiyar da Auwal ya tara mata, ya farka ya yi wanka ya yi sallah ya shirya sannan ya nufi d'akin yaran, da kan shi ya tada su suka yi brush suka yi alwala Yousuf ya ja su sallah Auwal na murmushin Jin dad'in yanda Yousuf ke da hankali,da kan shi ya shiga bathroom ya had'a ruwan wanka yayi wa yaran wanka har da Atiyyaerh da Afrah, qasa ya tarkata su suka sauka ya soya masu kwai ya had'a musu tea suka sha da bread, sai cake da ya siyo na tafiya makarantar yara da ya dibar wa kowa da juice da suke had'awa da shi, ya d'auke su sai makaranta, suna zuwa ya yi duk wani cuku2 na Saka Afrah da Atiyyaerh makaranta ya gama komai, sannan ya damqa su a hannun hukumar makaranta ya ja ya tsaya dan ganin ajin da za a Saka su, Atiyyaerh direct primary one aka saka ta, Afrah kuma suka bashi hakuri sai dai ta fara daga nursery saboda ita komai bata Iya ba Banda A zuwa F, Atiyyaerh kuwa har sunan ta da na Daddyn ta ta Iya rubutawa Yousuf duk ya koya mata, tana Jin turanci already, ta Iya had'a wasu kalmolin dik da ba dika ba,dan haka Auwal be Wani damu ba yace ba komai, don yasan qoqarin kowa a cikin su, zai tafi Afrah ta dinga kuka, da kyar aka bambare ta akai aji da ita, Atiyyaerh kuwa sai murna take sosai, tinda dama abun nema ne ya samu, dad'in dad'awa an aje ta aji d'aya da Sulaiman, hankalin ta kwance ta samu malamin ajin ya mata wajen zama kusa da wata yarinya mai kyau  itama mai suna Amal wadda ba zata wuce sa'a da Atiyyaerh ba,murmushi suka yi wa juna, sannan Atiyyaerh ta maida hankalin ta in da malamin ke tambayar sunan ta, nan ta fad'a masu sannan ta qara da "Mummyna na ce man Ablaerh, Daddy na na ce min Atiyyaerh, a gidan mu ma Atiyyaerh su Yaya ke kirana," Malamin su Murmushi ya yi, sannan ya ce,ta maimaita maganar da ta yi da turanci, tinda ta iya, nan da nan kuwa ta maimaita da turancin ta na Jin dad'i yau gata a makaranta,murmushi malamin su ya sake yi, yaran aji kuwa suka saka dariya, karatu suka fara, ta yi matuqar maida hankali akan abinda ake koya musu Dan sai ta ji kamar karatun makaranta da na Yousuf akwai banbanci wannan na da wahala, na Yousuf kuwa babu wahala Sam Sam,nan da nan take gane nashi, dan haka duk abinda bata gane ba bata bari a wuce wajen se ta yi ta tambayar malamin su, shi kuwa haka zai dawo baya ya mata bayani daidai fahimtar ta a haka ne ma wasu da basu gane ba suke shiru suke fahimta,a haka suka gama karatun su na wunin ranar har aka tashe su,iya malaman da dik suka shiga ajin shi Atiyyaerh sai da suka san anyi baquwar daliba. Ban garen Afrah kuwa, da ta gama kukan sai ta saka hannu a baki ta hau tsotsa abunta har baccin ya d'auke ta,an tada ta yafi sau nawa, qarshe in suka dame ta ta saka kuka, haka suka barta ta sha baccin ta. ******************************* Rasheedah bata tashi farkawa ba sai qarfe tara na safe, agaggauce ta gama wanka ta yi sallah ta sauka qasa, ji tayi gidan ba kowa shiruuu, d'akin Yaran ta nufa ta ga wayam ba kowa, wajen kayan Atiyyaerh ta duba ta ga alamun an tab'a kayan, Murmushi ta yi ta zauna bakin gado tana Jin Wani b'acin rai na yunquro mata, wato ita Auwal zai yaudara? Ya gama more ta jiya ya qi bin maganar ta? Lallai za a yi tashin hankali kuwa, Cike da b'acin rai ta hau watsar da kayan Atiyyaerh qasa ta na tattakawa, ta na gamawa ta fita daga d'akin cikin fushi, zata sauka qasa ta ji alamun bud'e qofa, tsayawa ta yi ta hard'e hannayen ta a qirji ta na kallon qofar, idanun ta sun kad'a sun yi jawur dan b'acin rai,Auwal da ya shigo ya Maida qofa ya rufe, ya ajiye key din motar a center table sannan ya kalli yanda take Wani cika tana batsewa, Murmushi ya yi a ran shi a fuska kuwa ya kalle ta da kulawa ya ce, "Ah ah Rasheedah lafiya na ga fuskar ki ta sauya haka? Ko dai Kashi ki ke ji ne? Dan na San ki ke da shiga toilet kamar akwai amana kamar wata quda haka ki ke dan shegen yawan kashin ki" "Kan uban can, ni ce ma me yawan Kashi? To malami dakata ka ji,idan ma ka d'akko wannan shirmen ne Dan na manta me ka yi to wasan ka be karb'u ba, ni zaka yaudara? Ni zaka ci wa amana?" "Amana Kuma? Rayuwar auratayyar mu ki ka ji na yayata a duniya ko me? Ko so ki ke na Sanar da duniya yanda mugun abun ki be tsaya a Iya fatar baki ba har se kin Yi amfani da jikin ki kamar wata wadda bata San ciwon Kan ta ba? Ke Rasheedah ki kiyaye ni ni ba banzan namiji bane,ba Kuma soko bane ni, sarai na San me yasa ki yin abinda ki ka yi jiya, kin ga kenan duk wahalar da ki ka sha jiya Baki samu lada ba,ba lada ba la'ada, kin Yi asarar lokacin ki da energy din ki wajen kyautata min na qarya da yaudara, ke ba dan Sakeenah ce da kan ta ta yi wasiyyar ki kula da Atiyyaerh ba saboda tana maki kwadayin samun Rahamar Allah akan Wanda suke sada zumunci ai ganin yarinyar nan ba me barin ki kiyi muguwa azzaluma kawai, wato ke naki yaran su je makaranta su samu ilimi ita da kud'in uban ta da uwar ta ta zauna da jahilci ko? Sannu muguwa" Zagaye ta ya yi ya wuce ta gaban ta zai shige d'aki, har ya gota ta ya dawo baya ya ce mata, "Rasheedah ki sauya halin ki da wuri da gaggawa, kar ki zo ki na danasanin da bashi da amfani," "Ba zan sauya halin nawa ba, azzalumi me cin amana kawai, ta je makarantar na ga yanda ilimin zai zauna a Kan ta, aikin banza kawai " A fusace Auwal ya juya Dan ya lallasa ta ta na ganin ya na biyo ta ta zura da gudu qasa ta shige kitchen ta rufe, tare da ci gaba da fad'a masa baqaqen maganganu, kwafa ya yi ya koma d'akin su ya kwanta a gado ya rintse idanun shi Yana Jin qiyayyar Rasheedah na samun wajen zama a zuciyar shi, be fita ba ranar se da aka tashi yaran ya wuce ta a parlour har ta zabura zata gudu taga ko kallo bata ishe shi ba, ya wuce d'akko Yara, ya biya da su restaurant suka ci suka sha suka qoshi, sannan ya dawo da su gidan, da kan shi ya yi wa su Afrah da Atiyyaerh home work, sannan ya fita ya bar gidan tare da mummunan gargad'in daidai da harara aka wa yarinyar in ya dawo Shima zai d'au mummunan mataki sannan ya fita, Rasheedah kuwa ji ta  yi kamar ta yi bindiga, shi yasa ta Saka hijabi ta fita zaga unguwar da qafa Dan ta rage baqin cikin da ke ran ta. **************************** Kusan wata biyu kenan suna zuwa makaranta batare da wata matsala ba,yanzu mutuniyar ku Atiyyaerh in za ta yi magana sai da turanci take yi dik da dama sun Saba yi da iyayen ta, amma lokacin bata da Wani wayo sosai yanzu ne take gane komai dalla dalla turanci ya zama second language d'in da ta ke ji ta Kuma kware akai sannan larabci dan ana yi musu shi a makarantar, Afrah kuwa bata san bihim ba da ake koya musu dan bata Wani Maida hankali akan karatun, kullum taje daga kukan banza sai bacci, in kuwa aka matsa za ai karatu a gida sai ta gudu wajen Umman su,ta ce ita bata so, Rasheedah ko ji take kamar ta mata dukan tsiya dan haushi kullum gori take mata da cewa, "Shiritacciya kawai,ke ba zaki Maida hankali ki yi abinda zai amfane ki ba kin tsaya shiririta, ga waccan mara galihun ma tana karatu balle ke, so kk ta girma ta fi ki ilimi tana aiki ke kina zuwa maula ko? To ki tsaya ki ji da kyau daga yau se yau, bana so na sake ganin ki na wannan wawancin so nake ki fita komai da komai ma ni ba karatu kad'ai ba kin ji ko?," Ita dai Afrah sai dai ta tsotsi hannu ta ci gaba da kallon ta kawai. Yau Lahadi, zasu je gidan kitson dake maqotaka da su, Atiyyaerh bata son zuwa ko kadan, duk da yawan gashin dake kanta, bata qin kitso, amma dalilin yaron gidan kwata2 ta tsani kitson da zuwa gidan, yaro ne sa'an Yousuf,mai suna Ahmad, ba qaramin son ganin Atiyyaerh yake ba shi kuma a rayuwar shi,dan yara abokan shi ma cewa suke budurwar shi ce,ya yi ta jin dad'i kuwa, in ya ganta ya je ya yi ta mata surutu,kala2, gashi baya zuwa makaranta shi, se ball da wasa a unguwa dad'in dad'awa kuma qazami ne , haka gidan da suke zuwa kitson ma qazamai ne matan gidan, Suna shiga gidan Atiyyaerh ta labe bayan Yousuf daya rako su shida Sulaiman, aiko Ahmad na hango su ya tashi ya je inda suke,yana jan hannun ta Atiyyah, kallon Yousuf ta yi ta kyab'e baki zata yi kuka, aiko yana ganin haka ya kaiwa hannun Ahmad duka yace, "Dalla sake mata hannu, wani qazami da kai," Aiko da jin haka Ahmad ya saki hannun ta ya kaiwa Yousuf naushi, dambe ya kaure a tsakanin su, Afrah ta matsa gefe tana tsotsar hannu tana kallon su, ita ko Atiyyaerh saka hannu ta yi aka fara damben da ita sosai, Ahmad ya fisu qarfi, Sulaiman mugun matsoraci ne, baya ya yi yana ta zare ido, idon shi sunyi jawur yana son yin kuka, wani abokin Ahmad ne ya taso suka hadu suka zane Yousuf, ana gama damben Ahmad ya fizge hijab din Atiyyaerh aiko gashin ta da ke dunqule a matsattsen hijab din ya baje, kuka take sosai da qarfi, wanda ya ja hankalin matan gidan suka leqo soron, Maman Ahmad ce tace, "Me zan gani haka, Yousuf waya fasa maka baki? Me ya faru haka?" Kan ta gama tambaya Ahmad ya kwasa da gudu da abokin shi sun bar wajen, Sulaiman ne da yanzu ya fara kuka ya fad'a mata komai, Yousuf ya kumbura sai nishi yake, bai ce komai ba, ya d'aga Atiyyaer, ya kama hannun ta suka yi gida, Maman Ahmad na ta kwala mai kira yaqi juyowa, suka shige gida Afrah ma bin su ta yi, sannan Sulaiman, suna shiga Rasheedah na kitchen ta fito, ganin fuskar Yousuf da jini ga shi sun yi biji biji shi da Atiyyaerh sai mamaki ya kama ta ta ce, " Ah kunyi saurin dawowa lafiya? Me ya faru na gan ku haka?" Sulaiman ne ya mata bayani, aiko kan ya qarasa ta gane Atiyyaerh ce ta ja aka ma Yousuf haka, wani irin Mari na rashin Imani ta sakar ma yarinyar da ke kuka, ta kamo ta ta hau duka ba ji ba gani tana fad'in, "Dan uban ki da ya gudu ya bar min wahala kashen d'an ki ke so a yi? dubi yanda jini ya ke zuba a bakin shi,shegiyar yarinya tin yanzu kin fara hulda da maza ko, to bari kiji in aure ne ki bari ki tasa aurar dake zamu yi da wuri mu huta da wahala, shegiya mai kama da mayu," Ta wurga ta gefe ta shige ciki ta na Kiran yaran nata, Yousuf kuwa kuka yake sosai, duk abinda aka masa bai ji kuka ba sai da aka dake ta, ranshi ya yi mugun b'aci da hakan, d'aki ya kwasa da gudu ya shige, Sulaiman ma ya bi shi, kallo Rasheedahn ta bisu da shi, "Shashashai in ban da ku ma,kuna gani yanda kowa ke nuna yafi son ta akan ku, kuke manne mata, har wani haushi ka ji kenan dan na hukun ta ta akan dukan da ta sa aka ma? Kai ka sani wawan yaro kawai," Ta yi shigewar ta kitchen ,ta ci gaba da aikin ta, kuka sosai Atiyyaerh take, Afrah ta je ta zauna kusa da ita, tana shan hannu, bata ce mata komai ba amma sai kallon ta take,idon ta ya cika taf da hawaye itama. Da daddare bayan Auwal ya dawo sun gama cin abinci Suna kallo,se na ga Yousuf na yi wa Abban su rad'a  a kunne, cikin fushi sosai kuwa ya shiga d'akin shi, tana kwance ta yi d'aid'ai a gado tana kwasar rab'a , aiko ya samu qaton hannun shi na magina ya yanka mata duka a cinya, a gigice ta farka, "Wayyo Allah,waya d'anan Iron a cinya me zafi haka?" Tana kuka ta na  murza wajen tana yarfe hannu, "Ni ne nan na dake ki, mai shegen son kai kawai, ke wace irin mata ce da baki san Annabi ya faku ba? Meke damun ki ne, wannan yarinyar marainiyar Allah me ta ci maki? Ki shiga hankalin ki ina fada maki baki ji ko? Zan mummunan saba maki akan ta," "Kan uban can akan waccan yarinyar ka daken? To bari kaji, wahala a hannuna yanzu ta fara shan ta kala2, indai ni ce Rasheedah, sai dai ka kashe ni inna dake ta, ta zabura tai waje da gudu har zanin ta na kwancewa, bin bayan ta ya yi shima,tana zuwa ta samu Atiyyaeh na home work, ta dauke ta da mari, ta sake dauke ta da wani, yarinya ta gigice gashi marin da bata san da zuwan shi ba, ta kasa ma kukan, bude baki  ta yi tana qaqalo kukan ya qi zuwa, Rasheeda bata ankara ba itama ta ji maruka na sauka a kuncin ta, yana dukan ta tana dukan Atiyyaerh tana zage2, d'aga ta ya yi cak, ya yi d'aki da ita ya rufe ya shiga kirbar ta, kamar an aiko shi, "In kince ba zaki fasa dukan ta ba baki haifu ba, ko bana nan kika dake ta na dawo sai kin karbi naki dukan kema tinda kin zama baqar jaka, muguwar banza kawai," kuka take sosai, tana jin wata muguwar tsanar Atiyyaerh sabuwa na sake kama ta, " Lallai Auwal ka ja mata, ka ja mata d'and'anar azaba a wajena kala2, baka san me zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba har yanzu," Ta tashi da kyar ta fada toilet tana kuka...... *Hummmmmmmm* [01/07, 8:47 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅 Page 20: Tin daga wannan ranar, ko hanya ce ta biyo da Atiyyaerh ta inda Rasheedah take sai dai ta bar wajen da kuka, danko sai ta mata wani abun muguntar da zai saka ta kuka, kullum Yousuf dayasanin fad'a ma mahaifin shi abinda ya faru yake, sannan ya qudurta a ranshi sai ya kama Ahmad ya baje qarfin shi akan shi, tinda shine silar abinda yake faruwa da Ablaerhn shi . Kwance take a d'akin su bayan sun dawo daga islamiyya, ko kayan ta ta kasa cirewa, ashe da empty lunch box ta tafi ranar, sai da ta je zata ci abinci taga wayam, gashi da safe iya tea ta sha, tea din ma ba wani had'in kirki aka masa ba, Auwal tin da ya kula the more yana shiga harkar su the more Rasheedah na qara haukacewa da musgunawa yarinyar sai ya ja baya da shiga lamarin nasu,saboda ya kula idan zai jinyata Rasheedah ne akan Atiyyaerh da ta samu dama sai ta ninka abinda ya mata akan yarinyar,kawai sai ya koma yi mata addu'ar shiriya,dan haka lokuta da dama yana ji Kuma ya na ganin ta tana mata mugunta amma haka zai kasa tanka mata,yau har ya tashi zai Saka wa Atiyyaerh extra cake a jaka sai ya ga ta saka mata lunch box a jakar sai ya fasa aiwatar da qudirin shi,hakan kuwa shi bahaushe ke Kira da rashin sani ya fi dare duhu dan kuwa ba komai a cikin lunch box d'in,ko da suka dawo Atiyyaerh ta tambayi abinci Rasheedah ce mata ta yi ta je d'aki ta cire kaya tazo su ci da 'yan uwan ta, tana shiga ta biyo ta d'akin, tace in ta sake ta koma parlourn sai ta ji a jikin ta,ta zauna har sai ta kira ta, su Yousuf basu gane komai ba, suka zauna jiran ta, " Afrah ku ci abinci mana ko kun cinye akwai da yawa a kitchen zan qara maku na zuba mata wani, maza kuci," Fara ci suka yi, amma Yousuf kwata2 bai jin dad'in ci ba tare da Atiyyaerh ba, a haka ya tura suna gamawa tace su je daki su yi wanka, su huta kafin lokacin islamiyya ya yi,'yan mazan tashi suka yi suka tafi d'akin su, Afrah ma ta nufi  d'akin su ita da Atiyyaerh, se ta ga Atiyyaerh kwance tana kuka, ta riqe ciki, yunwa duk ta gama rarake mata ciki, Afrah ce ta je ta zauna a gefen ta ta tambaye ta meye, cikin kuka ta fad'a mata yunwa take ji, " Umma tace mu cinye zata zuba maki wani,ki je ki ci naki a wajen Umma" Cikin jin dad'i da kuma tsoron me zai je ya zo Atiyyaerh ta miqe ta fita, zaune ta ganta ta d'ora qafa d'aya kan d'aya ta na kad'a ta, rara gefe ta fara cikin sanyin jiki da murya tace, " Umma yunwa nake ji, kamar zan mutu," " Laaaaa kaji munafukar yarinya,yanzu ke a ina kk san mutuwa? Iyyeee, waya fada maki ana mutuwa in an ji yunwa, wahala kawai zaki sha ba zaki mutu ba in ma tsoron mutuwa kk kar ki bi uwale, matsa ki ban waje munafuka ki je ki shirya, ki saka kayan ki,na islamiyya lokaci ya kusa," "Umma abincin fa? Yunwa nake ji yau ban ci abinci ba fa" "Dan uban ki Adnanu ba Zaki bar nan wajen ba se na b'ab'b'alla ki? Dan munafurci salon Wani ya ji a ce bana baki abinci ko? Kin b'ace min da gani ko se na mammake ki?" Tini hawaye ya gama wanke fuskar Atiyyaerh, hankalin ta a matuqar tashe, dan ba qaramin yunwa take ji ba, haka ta koma d'akin,ta fara saka kayan ta na islamiyya, tana sharce hawaye, Afrah ma kukan ne ya kama ta, dan ta ji komai, haka suka gama shiri suka fita, Afrah ce ta gaya ma Yousuf komai, hankalin shi ya tashi sosai da jin haka, gaba d'aya tausayin  qanwar tashi ya gama lausasa zuciyar shi,dan bai san ya zai ya bata a binci ba tare da Umman su ta gane ba, dabara ce ta fado masa,yace su yi gaba zai taho. Sallama ya yi ya shiga gidan ya riqe ciki, da gudu ya yi band'aki, ta bi shi, "Yousuf lfy? Meya same ka? Ko gudawa kk ne?" " Eh Umma, inna fito zan bi kitchen na sha magani na koma makaranta," "To Allah ya sawaqa, ni nayi d'aki ka tabbatar ka ja min qofa sosai kan ka fita," " To Umma" Murmushi ya yi, bayan ta haye sama da dan mintuna kamar biyar ya fito ya yi kitchen ya nemo leda, ya d'ebi abinci, da ruwa a roba, ya d'au maganin gudawa ya fice da gudu, Atiyyaerh ta jingina a jikin windon ajin su tana hawaye tana kallon waje yunwa take ji ba ta wasa ba,can  ta hango Yousuf na gudu, da leda a hannun shi, mamaki ne ya ishe ta,bata gama tambayar kanta meye a ciki ba ta ga ya shiga ajin su yana neman izinin an aiko shi wajen Atiyyaerh dan ta taho bata ci abinci ba aka ce ya kawo mata, " Ablaerh ki taso yayan ki na neman ki a waje kar ki dade," in ji malamin su da ke tsananin son ta, saboda qoqarin ta, bayan haka Atiyyaerh yarinya ce Mai shiga rai, sannan Kuma ba Wanda ya qi yaro me kyau ai. Cikin hanzari da rashin kuzari ta isa, suna fita ya bud'e mata abincin a wata 'yar kwana a yunwace ta hau d'iban girkin ta na ci idon ta na kwalla, haka ta cinye abincin tas ta sha ruwa, Yousuf kuka yake har da majina, ba qaramin tausayi ta bashi ba,samu ya yi ya goge mata bakin ta sosai da ya yi maiqo, "In mun koma gida Umma ta baki abinci ko kin qoshi ki karba, in ba haka ba zata gane na baki abinci ta dake ki ta dake ni, kin ji," kad'a kai ta yi alamar ta ji,sannan a hankali cikin sanyin murya tace, " Na gode Yaya," Murmushi suka yi wa juna sannan suka tafi ajujuwan su, Yousuf sai da ya sha bulalar latti, sannan aka barshi ya shiga. *Bayan shekara bakwai* Atiyyaerh an fara zama budurwa ita da Afrah, Sulaiman da Atiyyaerh na  JSS 2, Yousuf Kuma  ana SS 2, Afrah na JSS 1 daga baya ta Maida hankali a karantun ta dik da cewa har yanzu bata Kai Atiyyaerh hazaqa ba amma ta fi da fahimtar abinda ake koya musu a makaranta, Atiyyaerh ta zama budurwa me cikar halitta da haiba, duk da cewar ba qaramar wahala take sha ba a gidan duk wanda ya ganta zai d'auka ta fi shekarun ta, tana da girman jiki, Afrah ma hakan take a bangaren ta ba laifi sun yi gadon kyau wajen iyayen su maza da mata, duk wani aikace aikacen gida Atiyyaerh ke gabatar da su kama daga kan wanke2 share2, wankin kayan ta na gida da uniform, watarana har na Rasheedah da Afrah haka za a sa ta yi dole, dik da cewa akwai washing machine a gidan, wataran in za su gidan Mama gaida ita, in ta ga ta je can musamman a week end sai ta ce ita a barta zata yi mata weekend to anan take samu ta huta da aikace2, ta samu ta maida hankali a kan hardar ta ta Qur'an da karatun bokon ta. Kayan kwalliya wajen Afrah ba a magana, ko abun wankan ta daban ne, daidai misali Auwal harka ta bud'e masa ga aiken kud'i da baya yankewa daga wajen Adnan, kudin da Adnan ya bar masa ya kula da Atiyyaerh ma juyawa yake yi Yana yin blocks da Saida siminti tinda ya fi kwarewa a wannan harkar, dan haka Yana qoqarin wadata iyalin nashi da duk Wani abu da suke buqata, Atiyyaerh kam har ta cire rai da amfani da kayan kwalliya, domin tasha gargad'i wajen Umman su akan kar ta sake ta ganta da kwalliya, ko ta ji ta yi amfani da tirare ko abun wankan Afrah, roll on kawai take sai mata Shima acewar ta kar ta kashe su da warin balaga, duk qoqarin Afrah na ganin Atiyyaerh tayi amfani da su ko a boye ne amma inaa Atiyyaerh taqi Sam domin ta ma riga ta Saba da rashin kwalliyar, in ta matsa sai tace mata "Afrah kar ki damu, ni Kwalliya bata gabana yanzu, fatana na gama da duniyar nan lafiya ko so kk na saba umarnin Ummana? Wace irin yarinya kk so na zama kenan an hana ni yin abu Kuma na aikata? A haka ma alhamdu lilLAAH bana buqatar Kwalliya na gode da nuna kulawar ki a gare ni, best friends for everrrr," Sai ta Kai wa Afrah runguma ta na dariya,lokuta da dama da sabulun wanki take wanka, sannan ta shafa  basilin, har cikin ranta bata Jin Wani damuwa akan hakan,duk randa karambanin Afrah ya Kai ta ta saka wa Atiyyaerh tiraren ta a jiki kuma Rasheedah ta ji qamshin ranar Atiyyaerh sai ta daku, Afrah kuwa haka za tai ta kuka tana bada hakuri tare da Yi wa Umman nasu rashin kunya, Auwal ya sha yo musu shopping ya siyo kayan Kwalliya da turare domin Atiyyaerh amma haka Rasheedah zata kwashe, Yana so ya yi magana, ya na gudun ja wa yarinyar duka ko Wani zagin a wajen muguwar Auntyn tata. Watarana ba da niyya ba Afrah ta dauki hijabin islamiyyar Atiyyaerh ta feshe shi da turare a zaton ta nata ne tinda iri d'aya ne, sai da ta gama shiri zata fita daga d'akin Atiyyah ta fito daga wanka d'aure da towel, ta kula da hijabin ba Wani baqin ruwan biro a jiki, fari ne qal, se ta tsayar da Afrah ta mata bayanin wannan nata ne, Dan kuwa na Afrah ya baci da ruwan biro, hakuri Afrah ta bawa Atiyyaerh ta miqa mata hijabin ta, ta koma ta d'auki nata ta Saka,sannan ta sauka ta ce wa Atiyyaerh Suna jiran ta a qasa, bayan kammala Shirin ta ne tsaf ta Sanya hijabin ta sauka qasa itama Gani ta yi Afrah ce kawai su Yousuf sun yi gaba, ta na zuwa kuwa hancin Rasheedah ya shaqi qamshin turaren Afrah a jikin Atiyyaerh, tini ta kama masifa da bala'i ta na fad'in Atiyyaerh ta raina ta bata Isa ta hana ta abu ta hanu ba, bud'e baki Atiyyaerh ta yi dan ta mata bayani, ta kuwa tashi a fusace ta Kai mata duka, bata kyale yarinyar nan ba se da ta lallasa ta tas sannan ta barta ta haye sama ta na ci gaba da zagin Atiyyaerh, kallon Afrah da ke kuka kamar ita ake duka Atiyyaerh ta yi sannan ta ce, "Afrah in dai kina so na da gaske baki son ana dukana kamar mara gata ko galihu, ko dake bani da gatan ma ai, Dan Allah da son Annabi ki daina qoqarin sai nayi amfani da kayan ki, na gode da qaunar ki a gare ni yayata, bana fatan Allah ya gajiyar dake a wajen tausaya min keda Yayah Da Yah Sulaiman amma Dan Allah ki dinga taya ni kiyaye abinda za a dinga dukana akwai zafi, ba wai iya zafin jiki ba, Ina Jin zafi a nan d'ina, Ina Jin zafi Afrah a cikin zuciya ta, ba zan iya kwatanta miki ya zafin yake ba, ba na fatan ki ji irin wannan zaf'in Afrah akwai ciwo sosai,na riga na gama yarda Mommy na ta rasu Daddy na Kuma baya so na saboda Mommy na ta rasu shi yasa ya barni anan na sha wahala, na ji na amince zan jure komai, zan shanye komai, amma dan Allah ki taimaka min zamana anan ya min sauqi, ba zan iya ci gaba da jure irin wannan wulaqanci da quncin ba Afrar akwai ciwo sosai," Afrah ta kasa magana sai kuka, da gudu ta fad'a jikin Atiyyaerh ta rungume ta sosai kamar zata tsaga jikin ta ta shige ,banda gunjin kukan su baka Jin qarar komai a parlourn, Yousuf da Sulaiman tini sun Isa makaranta saboda a tinanin su Afrah ce ta tsaya kyale kyalen ta da ta Saba zata sa su makara, dan haka basu San wainar  da aka toya aka cinye ba,sai da suka yi kuka suka gaji suka tsaya a tap din tsakar gida suka wanke fuskar su sannan suka tafi makarantar. A haka Atiyyaerh ta saba da rashin kwalliya,ta Saba da azabar Rasheedah har ta dena wa duk Wani duka ko zagi kuka, sai dai ta yi Murmushi me ciwo ta bata hakuri,bangare guda kuwa duk wanda ya ganta zai rantse bata da damuwa, Atiyyaerh na da natural kyau Mai d'aukan hankalin me kallo, gata da nutsuwa da kamun kai. *DUBAI* Kwance yake a makeken gadon shi, yana ta tinani kamar kullum, har wannan lokacin bai yi aure ba, wayar shi ya lalubo ya danna kiran Abba, Abba na gani ya yi murmushi, ya d'aga kiran, bayan sallama da gaishe2, ne yace "Abba akwai Wani abu da kuke buqata? Ka San bana so a wannan shekarun naka kana wahalar da kan ka, hutu ka ke buqata a yanzu Abbana" "Alhamdulillah bamu da matsalar komai sai ta kewar ka, satin can na sama Ablaerh tazo mana  hutun qarshen mako,kullum tazo zancen ta bai wuce mu bata labarin mahaifan ta ba, ka daure ka dawo ka ganta,domin kwanciyar hankalin ta dan ita gani take kamar baka son ta ,in ka dawo mu ma namu hankalin ya kwanta, gashi kaqi aure, wannan shine matsalar mu Adnan, to a gaskiya zan fad'a Maka bamu da wata matsala a yanzu se wannan, ka daure ka jure ko dan raya sunnar Annabi Muhammad ka yi aure, Kai fa ba ma'asumi bane Adnan, akwai lokacin da dole Dan Adam Yana buqatar mace,dan Allah ka daure ka yi aure,babbar soyayyar da zaka nunawa Sakeenah kenan ka tsare Kan ka daga fad'a wa halaka ta hanyar yin aure," Rintse ido Adnan ya yi cike da jin zafin mutuwar matar shi da kullum ke tab'a shi, ga kewar d'iyar shi dake dawainiya da shi, amma baya jin lokaci yayi da zai je ganin ta, " Abba ka yi hakuri zan zo ne, amma ba yanzu ba, inshaa Allah zan zo ne,Kuma maganar aure zan duba na gani, Abba na kasa dena tuna ranar da ta barmu, Abba wa ka ke ganin zan aura bayan zuciya ta bata da Wani ragowar gurbin da wata zuciyar zata samu mazauni a cikin ta? Ina tsoron na yi aure na zama silar zubar hawayen wata Abba, Abba ku ci gaba da taya ni addu'a Allah ya sauqaqa min ya min zab'in alkhairi" "To Adnan Allah ya kare mana kai, ya sa da rabon ganawa,Allah ya sauqaqa Maka radad'in da ka ke ji a zuciyar ka, Allah ya Maka zab'in alkhairi, ka kula da kan ka,ka kare kan ka daga zina,da shayen²n matasan yanzu in an ga kud'i da wadata sun samu se a dinga shaye shaye da neman matan banza, in ka ji wani abu na son mace na taso maka ka yi azumin alkhamis da litinin, ko ka samu ka yi auren ka,kar ka jefa kan ka halaka bayan Allah ya rufa maka asiri Adnan," Cike da jin dad'in addu'o'i da nasihar Abba Adnan ya yi godiya suka yi sallama ya koma ya kwanta, yana matiqar jin dad'in yanda Abba ke matuqar son shi,yake masa nasiha da take ratsa masa jiki ta dasa masa tsoron Allah. ****************************** Shirin tafiya kitso Atiyyaerh take ita d'aya, gobe akwai makaranta, Afrah ta riga da ta yi nata tin jiya, tana cikin tafiya ta kusa shiga gidan ne ta ji ana kiran ta, cike da b'acin rai ta d'aure fuskar ta, dan bata qaunar ko da jin muryar shi ne balle ganin shi.. . . . *Thank u guys for ur comments ina jin dadi sosai, kuma yana sa na qara sambada maku typing ba tare da naji gajiya ba. ME LOVE U DA YAWA❤*[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERHMEEBRAERH Page 21: Tsayawa ta yi cak a inda take, dan bata son ya bita cikin gidan yana mata surutai marasa tushe da ma'ana a cewar ta,su Kuma matan gidan na biye masa ana cewa budurwar sa ce ita, da fuskar ta mai d'auke da gajeren Murmushi na ba yabo ba fallasa ta juyo, yana tozali da fuskar ta ya ji wani sanyi a ranshi,ba kadan yake son Atiyyaerh ba,shi in za a taimaka mishi yanda baya makarantar nan ba wata uwar yake tsinanawa ba sana'a se d'aukan magana to a bashi auren ta kawai,cikin washe dikkan haqoran shi ya ce, " Hajiya Atiyyaerh, meye na sauri kawai dan kin ji ina kiran ki, ki kwantar da hankalin ki, in Allah ya nufa nine mijin ki ko ba dad'e ko ba jima sai na aure ki," Cikin jin haushin kalaman shi ta gyara tsayuwar ta ta kalle shi Ido cikin ido, amma dake bata son ya gane meye a zuciyar ta sai ta sake fuskar ta ta, ta shanye b'acin ran ta sannan ta ce, "Haba Ahmad yaushe ka ga Ina sauri ni? Sannan a gani na tinda ka san da haka me zai sa mu yi ta bata lokacin mu mu dika muna tsayuwa hira a titi? Mu Jira mu gani in har akwai qaddarar aure a tsakanin mu, sannan dika dika ma nawa nake? Kai Kan ka shekarun ka nawa har da ka ke hango aure? To gwanda gwanda ma ni mace ce tinda ana wa mata aure da wuri kafin maza, ballantana ma ni yanzu karatu nake, bana buqatar soyayya yanzu,ka bari inna gama makaranta munyi maganar soyayya da auren ma gaba d'aya dan Allah, ka dena bina kana surutan da ka ke please" "Da gaske kin amince  za mu yi magana in kin gama karatun ki? Hakan fa na nufin zaki ban dama na shiga neman auren ki?" D'aga masa kai ta yi da murmushi, suka yi sallama ta shige gidan nasu. A tiyyaerh na da samari a wadannan shekarun nata, dan kowa ya ganta zata yake tafi ainahin shekarun ta, duk sanda manyan motocin masu hannu da shuni suka tsaida ta a hanyar islamiyya ta kanyi murmushi ne kawai ta ci gaba da tafiyar ta, a haka ne ta samu wani, Hassan, ba qaramin son ta yake ba,iyayen shi manyan masu kudi ne, ba zai wuce shekara 25 ba, ya takura ta matuqa, Afrah kan ce mata "ki bashi dama, ko da secondary ne ki ka gama a aurar dake ki huta, wannan rayuwar gidan in baki barta ba zaki samu ciwon zuciya wata rana," Takan yi murmushi tace, "Afrah nawa muke ne da muke tinanin aure ne, we are still young,getting married at young age will not solve my problems, kawai zan ta addu'a Allah ya zaban mafi alkairi," Afra kan amsa da " Ameen" amma tana matuqar tausayawa qanwar ta ta, ta wani bangaren kuwa Yousuf ba qaramin tausaya mata yake ba, ya qudurta inshaa Allahu zai jiyar da Ablaer daɗi fiye da yanda take tinanin samun sauqi a rayuwar ta, to taya zai samu wannan damar? ******************************* A kwana a tashi asarar mai rai, yau su Ablaerh ke rubuta jarabawar su ta qarshe a makarantar sakandire ta Al'ansar, Atiyyaerh da Amal na hango sun had'e kai tare da rungume juna suna ta kukan rabuwa da junan su,sun bala'in ba wa qawayen su tausayi, dan kowa ya san yanda suka shaqu, babban abinda ya sasu kukan dama shine an saka ranar bikin Amal, kuma ba a qasar nan zata zauna ba ma, Ghana za a kaita, can dangin mahaifin ta, biki ma a ta can zasu yi shi  na al'adun su ba anan ba balle ta samu damar zuwa, da kyar aka raba tsakanin su kowa ta tafi cike da kewar 'yar uwar ta, sun iso gida kan Atiyyaerh na matuqar ciwo, ta rasa ina zata saka kanta ta ji dad'i, dan ko magani tasan ba ta da arziqin da za a bata a gidan, shigewa d'akin su ta yi bayan ta gaida Abban su da Umma dake zaune, Abban su ya taya su murnar kammala secondary school da suka yi, sannan ya na burin saka su a makarantar gaba da sakandire in har results din su ya yi kyau dik da bashi da tantama akan yaran nashi musamman Atiyyaerh, sai dai bai fad'a masu hakan ba, ya bar abun a ran shi,  yanayin yarinyar  yasa yana son ya je ya ji me ke damun ta, amma yana tsoron iya masifa tace yana banbanci, addu'ar samun sauqin koma meke damun ta ya yi mata a ran shi. Tana shiga ta fara cire kayan ta, ta ninke ta saka a basket din wankin su, daga ita sai pant da brah, da dogon skirt, a hankali ta warware gashin ta ko zata samu sauqi daga daurin da ta masa, ya zubo a bayan ta, ta sa hannu a can qasa ta buda shi sosai,dan ta sha iska, tana cikin haka aka bude aka shigo, a zaton ta Afrah ce, " Ban San me yasa ki ke son shigo wa waje ke ba sallama ba kullum, sai kin tsorata mutum kizo kina Wani yi hakuri my sister," Tana nuna yanda Afrahn take mata, juyowar da zata yi idon ta ya shiga cikin na Yousuf, cikin in ina tace, " Yah....yah..yayah?" Daga mata kai ya yi, cike da murna ta tafi da gudu da niyyar rungume shi kamar yanda ta Saba da tana yarinya,sai kuma ta tsaya agaban shi, tana ta dariyar farin cikin ganin shi, yau wata shida kenan daya koma makaranta, a zariya, " Yayah yaushe ka zo, ba ko sanarwa?" Shiru ta ga yayi har lokacin bai motsa ba, bai kuma kifta ido ba, sannan kuma bai ce mata komai ba, kallon inda ya qurawa ido ta yi ta ga ya hadiyi wani yawu , daidai qirjin ta ta ga yana kallo, wata siririyar qara ta saki, ta juya tare da dafe wajen,tana zare ido, gashin ta ta barbaza a jikin ta ya rufe mata kafadu , cikin tafiyar sauri ta sunkuya tana jan bedshit din su, sun irin cusa shi can cikin nan, ya qi fita, kawai sai ta duqa a wajen cike da kunya ba kadan ba, dariya yake sosai, harda kama ciki, "Yayah go out pleaseeeee," " No, i can not just go out,In kuwa na fita sai dai na koma zariya kin yarda?" Cike da tsokana ya fad'i hakan, " Yayahhhhh pleaseeee manaaa" Ta qara fad'a cike da shagwaba da muryar dake nuna alamun gaf take da Saka masa kuka, dariya ya yi sannan ya ja qofar ya fice,kan ya qarasa fita yace mata, "In kin shirya ki samen a dakin mu na baki tsarabar ki," Bayan ta amsa shi da "To" ne ta ji dariya ta kama ta, nan da nan ta nemi azababben ciwon Kan ta rasa se sama sama take Jin shi,ta na Saka kaya ta na tinanin irin kyaun da yayan nasu ya qara kamar ba shi ba, dafe qirjin ta ta yi, data tina wani kallo daya mata, sannan ta tina inda ya kalla, buga qafar ta ta yi a qasa, tana tirje2, tana kukan shagwaba, jikin ta na ta motsawa,Afrah ce ta bude qofar zata shigo, tana shigowa ta ga Atiyyaerh na hakan, "Ke kuma lfy, me yake damun ki?" Cike da shagwaba ta bud'e baki ta fara magana da cewar, " Ba yayah bane ya shigo mana daki ba ko sallama kuma ban maida kaya a jikina ba," Dariya ce ta kama Afrah sosai, cikin dariyar ta ce, " Ayyaa so sorry love, kuma gashi ya gama gane maki wannan tula tulan naki, kaiiii sorry u," Zaro ido Atiyyaerh ta yi dan ta tabbata ba da jimami qaramar yayar ta ta tayi maganar ba, ( in baku manta ba Afrah ta ba Ablaerh kwanaki ne) cike da shagwaba ta miqe ta maka mata pillon dake hannun ta, ta wuce wajen kayan ta,dake cikin wata jaka , dan Rasheedah ta hana ta saka kayan ta a wajen na Afrah,duba doguwar riga ta yi, a kayan ta aje a gefen gado,ta dauki duk abinda take buqata in ta yi wanka zata saka ta aje, sannan ta wuce Afrah da har yanzu bata daina dariya ba tana tsokanar ta, dan ta san yanda Atiyyaerh ta tsani a ga jikin ta,musamman qirjin ta, dan Allah ya hore mata su, sannan ga shi wai Yayahn su da take tsananin jin kunya tin da suka fara girma,yanzu kuma shi ya ga qirjin ta da wanne Ido zata sake kallon shi? " Kin ji da shi dai ki ta tsokana nan ki ka fi kauri dama ai, laifina ne ma da qaiqayin baki na na fada maki," Cikin tura baki tai shigewar ta bathroom d'in, wanka ta yi ta d'aura alwala sannan ta fito, ta shafa Vassilin din ta, da yar farar powdern ta, sai kwalli data zizara, ba qaramin kyau ta yi ba. Afarah ta gani itan ma ta cire kayan ta ta sa wasu ba tare da ta yi wanka ba,cikin jimanta lamarin Atiyyaerh ta ce, "Wai ke meyasa baki son wanka ne? Munje mun dawo daga makaranta, mun gama shan qura a hanya mun dawo ga zufa amma ke baki san ki qara wanka ba," "Ke ni banni da shegen son wankan nan irin naki kamar agwagwa ba zan iya ba," Ta rausaya jikin ta mai kama da na Ablaerh, jerawa suka yi suka fita parlour kamar wasu tagwaye, direct dakin Yousuf da Sulaiman suka nufa, Sulaiman na kwance yana bacci, Yousuf yana zaune alamar tinda ya baro dakin su Afrah yake zaune a wajen, ya yi zurfi a tinanin Atiyyaerh Afrah ta taba shi, " Yah gamu mun zo a bamu tsarabar," Murmushi ya yi ya sauke idon shi kan Atiyyaerh, ita kuma ta yi saurin juya baya tare da sunkuyar da kan ta qasa,dariya suka saka mata baki d'ayan su, miqewa ya yi yana tambayar su ya jarabawar ta yi sauqi kuwa? Haka dai suka yi ta hirar yaushe gamo, ya dakko tsarabar kowa ya damqa mata, Ablaerh yaa bata wata doguwar riga ne mai kyau baqa da ratsin pink a jiki, sai Afrah itama diguwar riga ce da rastin red a jiki, sai tsallen murna suke kamar wasu yara, dakko chocolate ya yi da tarkacen sweets ya ba Ablaerh, dan ya matuqar saba mata da shan su a boye, in baya nan tai kwadayin su har kuka take, ba mai bata, cikin murna sosai ta zube gaban shi, tana godiya,a nan ta bud'e ta fara sha ta rufe ido tana taunawa, tana wani girgiza kai, ba Yousuf ba dake namiji,har Afrah sai da ta yaba da kyaun ta, a hankali ta bude idon ta ta ga suna kallon ta,ta miqe ta fita cike da jin kunya, Sulaiman ne ya farka shima sai murna da ganin dan uwan shi yake, haka suka ci gaba da hira bayan ya amshi nashi tsarabar. Yauce rana mafi muni a wajen Atiyyaerh, ranar da ta yi kukan rashin uwa da uba , kukan maraici, kukan Ina zata Saka ran ta da abinda ke tinkarar rayuwar ta ta gode Allah,😭😭........ [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *Yesterday was our 15 years wedding anniversary my beautiful fifulll please say a prayer to us... thank you.* Page 22: komawar Yousuf makaranta da kwana biyu kenan, su Atiyyaerh na zaune a Parlour su uku, Rasheedah, Atiyyaerh, da Afrah, yaran na ta hirar makaranta da Kuma qawayen su, Rasheedah na zaune ta na danna waya ta na kallon su lokaci zuwa lokaci, a dik sanda zata had'a Ido da Atiyyaerh sai ta zabga mata harara, ita kuwa ta d'auke Kan ta ta ci gaba da hirar ta, in ana sabawa da mugun abu to Atiyyaerh ta saba da na Rasheedah,buga gate da akai ne yasa su dika ukun da suka saurara da hirar da suke suka nutsu dan su ji waye, kallon Atiyyaerh Rasheeda ta yi, in an buga gida irin haka mazan basa nan dama ita take zuwa duba waye, miqewa ta yi ta dauki hijab din ta ta saka tai waje, tana budewa ta yi arba da qatuwar motar Hassan a waje, cike da murmushi yake kallon ta, "Ashe lallai bugun zuciyata bai kasala ba wajen sanar dake zuwana," kad'a ido ta yi sama sannan ta isa gare shi, bayan ta yi masa sallama ta gaida shi tace, "A gaskiya ni ban da abin fada maka kuma daya rage wa bakina Hassan, soyayya tsakanin mu ba mai yuwa bace, ka taimaka ka rabu dani, wai wa ma ya fada maka nan ne gidan mu?" "Atiyyaerh ba zan iya rabuwa dake ba gaskiya,ina son ki sosai, duk da ni d'in ina fuskantar qalubale a gidan mu wajen neman auren ki da nake son shigowa, amma hakan ba zai hana ni na gwada sa'a ta ba,kuma dangane da tambayar ki na waya nuna min gidan ku, na biyo ki shekaran jiya da kuka raka yayan ku," Ajiyar zuciya Atiyyaerh ta sauke sannan ta   bud'e baki za ta yi magana suka ji budewar gate da qarfi , tana juyawa ta yi Ido hud'u da Umman su, nan da nan ta rab'e gefe da niyyar ta shige gida, cikin fushi Rasheedah ta janyo ta baya,sannan ta ce, "Ki jira na fad'i duk abinda nake so na fad'a a gaban ki Kan ki tafi, malam kalle ni nan, ni ce uwar ta, ba zamu baka auren ta ba, domin mun mata miji tin tini, in ma baka sani ba ka sani, kalli can, ka ga wancan gidan na kusa da mu?....." Ta yi nuni da hanyar gidan su Ahmad ta ci gaba da magana, "To a can gidan yaron yake,sunan shi Ahmad,tun Suna Yara suke soyayya kuma an yi magana gemu da gemu, iyayen shi sun kawo komai na aure,dama ana Jira ta kammala secondary school ne, Kuma alhamdulillah,da alama daga gidan mutunci ka fito dan haka kasan dai ba kyau neman aure akan aure ko? To ka tafi in da rabo sai kaga Allah ya kawo maka wata ta gari," Cikin tsananin daci da qunar rai Hassan ya kalli gidan su Ahmad, a ranshi yana jin haushin tsayawa Sanya da Wani bibiyar ta da ya dinga yi ba tare da ya d'au matakin neman auren ta ba,yau gashi wancan talakan ya riga shi, ko sallama bai masu ba yaja motar shi ya tafi, duk da ba son shi Atiyyaerh ke yi ba abun ba qaramin sosa zuciyar ta ya yi ba, ya za a ce wai yayar Mummyn ta ce zata mata wannan aikin, cikin kuka ta shige gida, tana zuwa zata shige daki ta ji Umman nasu ta daka mata tsawa da cewar, "To uwar son maza, uwar jaye jaye, ke kenan  baki da aiki sai jaye jayen maza ga Afrah nan ta kame Kan ta har yau ba Wanda ya biyo ta sai ke kin ballagazar da kan ki maza na faman binki dik inda ki ka shiga,yanzu gashi daga je ki duba waye shine kk tsaya sakin zance ko, to ki kwantar da hankalin ki in namiji ne sai kin gaji da shi, yanzu2 zan leqa gidan su Ahmad na yi ma Babar shi magana in da gaske suke to fito," Cike da tashin hankali Atiyyaerh ta kwasa da gudu ta tsugunna a gaban Rasheeda ta kama qafar ta cikin gunjin kuka ta ce, " Ummana dan Allah ki yi hakuri, kar ki gurbatan rayuwa ta, zan shiga halin qunci fiye da kullum in aka ce Ahmad ne mijina, Umma ni na yarda ku barni na zauna ba aure har abada akan a hada ni aure da wancan jahilin ko islamiyya fa bai zuwa," "Iyyyeee lallai ne bari ki gani na ga alamar kin zaci wasa nake ko?" Sama ta nufa a guje ta Sako hijab d'in ta, zata fita, Afrah da Atiyyaerh suna kuka suka riqe ta Suna bata hakuri, juyo wa ta yi ta hau kai masu duka dukkanin su a haukace, Afrah ta yi baya amma Atiyyaerh sam ta qi matsawa, kuka kawai take ta rasa me ke mata dad'i, fizgewa Rasheedah ta yi daga riqon da tai mata ta yi gaba, da sallama ta shiga gidan ba b'ata lokaci ta shige d'akin mahaifiyar Ahmad d'in, ta na zama aka gaisa sama sama sannan ta sanar dasu cikin nan da sati biyu su yi komai na Shirin auren Ahmad da Atiyyaerh su turo ai auren in suna so in basu so zata ba wa wani Atiyyaerh, cike da murna su ka yi godiya ta kamo hanya ta koma gida abunta kamar ta je bada auren 'yar tsana. Atiyyaerh ce zaune a qasan carpet ta jingina da kujera, kanta na qasa ta na shassheqar kukan baqin ciki, da kewar iyayen ta,Auwal na zaune  saman kujera ya raba qafafun shi daya ɗora hannayen shi akai ya haɗe yatsun hannayenn shi  waje d'aya, sai kad'a jikin shi yake Cike da masifar da ke cin ran shi, anya Rasheedah bata yi nasarar Sanya masa ciwon hawan jini ko na zuciya ba kuwa saboda yanda yake ji a zuciyar shi? A d'aya gefen nashi kuwa Afrah ce zaune a qasan carpet itama tana ta kuka,da sallama ta qarasa cikin parlourn, tana isowa ya miqe ya ja wuyan rigar ta daf da shi, ya na zare mata idanu, ya ce, "Ke mahaukaciyar ina ce? Ke zaki aurar da ita da har zaki je ki yi wa iyayen yaron can magana akan auren ta? Banda zagin cin mutuncin da ki ke mata a kullum safiya,meke damun rayuwar ki ne gaba d'ayan ta Rasheedah?" Cike da hargowa ta fara magana, "Ina ce dai da uwar ta zata mutu duk ta sanar daku ni ke da iko akan wannan yarinyar? In dai ka tina haka ka barni nai abinda na ga ya dace da ita in dai ba sab'a wa wasiyyar ta ta da kuka dame ni da sai na cika za kayi ba," Iya abinda ta sanar da Auwal kenan ta sa kai ta haye sama zuwa daki abinta cike da fushi,yo bama dole ta aurar da wannan shegiyar yarinyar ba? Na farko tinda take bata tab'a jin Afrah ta yi saurayi ba, na biyu kuma duk da kyaun Afrah in ta jera da Atiyyaerh sai ka ga Atiyyaerh ta zarta ta, sannan ga samari da Atiyyaer ke yawan yi amma Afrah shiru, amma in ta tafi zata samu itama ta samu mai kud'in da zai kula 'yar ta ta, sannan haushin ta dik samarin Atiyyaerh masu kud'i ne, Ahmad ne kawai talaka, kuma jahili, dan haka shine daidai ita. "Ki yi hakuri Atiyyaerh tabbas Rasheedah ta fini gaskiya, wannan umarnin mahaifiyar ki ne akan mu barwa Rahseeda ke da duk Wani abu da zata zartar akan ki, ban tab'a zaton Rasheedah rashin Imanin ta ya Kai haka ba, ban San me Sakeenaah ta tsare mata ba dik da bata rayen ma, na rasa yanda zan shawo Kan wannan qiyayya da matsala da ke afkuwa a tsakanin ku, na yi nasihar, na tsawatar, na yi duka, na yi addu'a amma shiru,ni yanzu ban san dalilin ta na wannan qiyayyar ba har yanzu,domin na raina dalilin da take bayarwa, ko da yake ita hassada mugun ciwo ne, ita ke Kai mutum da aikata manyan zunubai Dan kawai ba ya son Wani ko baya qaunar ci gaban shi ,babu komai kar ki damu Atiyyaerh na, Wani hanin ga Allah baiwa ne Kuma ina kyautata zato ga Allah ya sa kome zai faru ya kasance mai kyau, dan haka ki rungumi qaddarar ki Allah ya miki albarka," Cike da tashin hankali take kallon shi,me yake nufi, bari zai yi a mata auren dole da jahili? Ita fa ko masallaci bata tab'a ganin shi ya je ba sai majalisar su ta shaye2, kuka take sosai ta miqe ta yi d'aki da gudu, Afrah ce ta bi hanyar da Atiyyaerh ta bi da Ido cikin tsananin tausayin 'yar uwar tata, cikin kukan tausayin Atiyyaerh ta ce, " Abba ka tausaya mata, ka duba ka gani tin tasowar mu take Shan wahala a wajen Umma, bata tab'a roqon kowa akan ya taimaka mata ba, wannan fa maganar aure ake yi a tsakanin ta da wannan d'an iskan, Abba in ni ce zaka iya bari haka ta faru akai na? Haba Abba ka sa baki mana, Atiyyaerh bata cancanci wannan tozarcin Daga wajen ka ba Abba,a yanzu ne lokacin da ya Kamata ta huta tinda aure za a mata ta bar gidannan da yake a matsayin kurkuku a gare ta,Abba ai ya kamata ace zata kasanace ne cikin farin ciki ko? Abba pls do samething" Afrah ta qarasa cike da kuka, Auwal  ya yi shiru, zuciyar shi na tafasa, ji yake daya sani da bai dau alqawarin nan ba, da ya sani ko mai nacin da Sakeenah ta masa ya qi amincewa da buqatar ta, tabbas da ita kanta Sakeenah ta San 'yar uwar ta ba zata tab'a sakkowa daga d'okin da shaid'an ya dora ta akai ya bata fadawan shi take ganin ta kamar wata sarauniya a duniyar ta ta zalunci da bata bata gudan jinin ta ba, ba abinda zai iya yi a yanzu, sai dai ya bi lamarin da addu'a, Yana roqon Allah da ya sa hakan ya juye ya koma alkhairi ma Atiyyaerh. A can d'akin su Atiyyaerh kuwa ta na can ta na cin kuka, kamar wadda aka yi wa rad'a Kuma ta miqe tsaye, da hanzari ta had'a Kayan ta dika a jaka, ba tare da ta fad'a wa kowa ba da sassafe kowa na barci ta gudu gidan Mama, tana shiga ta fasa kuka,Mama ta fito daga daki a firgice, "Me zan gani haka, kukan me ki ke haka Atiyyaerh? Me ya same ki? Waya mutu?" " Mama ku taimaka min, Umma zata min aure da Ahmad maqocin mu, Mama in aka auran shi an tauye rayuwa ta,ku taimaka min, ni bance sai mai kudi zan aura ba amma a qalla aban mai ilimi musamman na addini," Kamota ta ji anyi ta baya tana juyawa taga Abban su Rasheedahn, fadawa ta yi qirjin shi ta saki sabon kuka, hakuri suka had'u suka bata, dan basu da abin yi akai Suma, umarnin mahaifiyar ta ne akan kar a sawa Rasheeda baki akan kome zata yanke akan Ablaerh,Kuma sun kula so take ta nuna masu iyakar su, wato tinda an dage se an cika wasiyyar Sakeenaah bari ta yi wannan rashin mutuncin, fatan su kawai Allah ya sanya albarka a rayuwar ta ya kare ta daga sharri kowanne iri ne,kallon su kawai take cikin share hawaye ta na Murmushi Mai ciwo da qona zuciya ta ce, "Yanzu kenan ban da gata? Banda mai taimako na a cikin ku, banda wanda zai tsaya min? Kome zai samen ba ni da wanda zan fad'awa na ji dad'i? Na tab'a kawo qarar Umma a dik irin abinda take min? Ah ah ban taba kawo maku qara ba sanda take dukana, ko sanda ta ke hanani abinci, ko sanda take zagina da iyaye na, ban taba fad'a maku komai ba, amma yanzu na kawo kukana akan future life d'ina kun kauda kai, Allah shi ne Mafi sani an cutar dani, an zalinceni, amma Allah na nan," D'aukan kayan ta ta yi ta fita a gidan suna kiran ta amma ko juyawa bata yi ba, kuka kawai take suma kukan suke, kwarai zasu so su hana faruwar komai, za su mata magana su lallashe ta ko zata sauya qudirin ta akan wannan mummunan lamarin da take so ta zartar,basu tab'a zaton rashin Imani da tausayin Rasheedah ya Kai haka ba. Atiyyaerh na komawa ta tarar da Rasheedah na tsaye ta na masifa akan rashin ganin ta da kayan ta da ba ta yi ba,cikin had'e fuska da baqin rai ta ce, "Gidan uban wa ki ka je da sassafen nan?" " Umma ki yi hakuri wajen Mama naje," "Ohhhh kin je ne ki fad'a masu ne dan su kashe ni ko su tsine min?  Uwar ki ma ta yi ta bari indai had'a ni da iyaye na ne,ke bari ki ji in kk ga ba ai auren nan ba kin mutu, ko kin mutu a dakin ki za ai maki wanka,na gidan Ahmad, wuce ki ban waje ni," Shigewa ta yi tana ta kuka gashi bata da waya balle ta gayawa Yayan ta,wataqila ya sama mata mafita, alwala ta shiga ta d'auro ta hau salloli tana kuka tana sanar da Allah, Afrah tsabar taya ta baqin ciki itama ta amshi maruka biyu bayan fitar ta, da taje ta mata magana akan auren. Kwana biyar tsakani su Ahmad suka kawo kudin aure dubu goma, sannan da akwatinan lefe biyu, dika kayan ciki basu fi goma ba, sai takalma biyu, da jaka biyu,mayuka ne da yan kayan kwalliya kamar an roqo gasu nan, komai a tsiyace, a wannan lokaci kowa yaga Ablaerh sai ya mata kuka, komai ya k'wace mata, bata immm bata imm imm, wani lokacin zaune za ka ganta ta yi zurfi a tinani kawai hawaye na bin fuskar ta, d'an gyaran nan na amare wa take da shi da ma zai kula ya mata? Kullum tinanin ta ina mahaifin ta yake tinda an ce shi Yana raye, me yasa ya tafi ya barta? Meyasa bai taba waiwayar ta ba? Wata irin qiyayyar mahaifin ta ne ta d'arsu a zuciyar ta, a wannan matakin ta cire komai ta qudurta auren Ahmad kuma zata masa biyayya,kawai yanzu tafi qaunar ma ta bar gidan ta huta. Sauran kwana biyu biki Yousuf ya dawo daga makaranta, Sulaiman ya zo shima daga Hostel, dan sunyi magana da Yayan shi Abban su ya neme su, akan wata mahimmiyar magana, tin a hanya gaban Yousuf ke tsanan ta bugawa, ya tambayi duk wanda yake ganin zai samu haske akan kiran Abban su amma ba wanda ya fada masa komai, lokacin da ya shigo gidan dare yayi, Sulaiman ya tarar idon shi ya yi jawur, kamar wuta, kasa kallon qanin nashi ya yi, dan bai tab'a ganin shi cikin tsananin fushi haka ba, yasan ko ya masa magana ba zai kula shi ba, wannan dalilin ne ya sa shi tambayar Afrah dake gefe tana kuka meke faruwa? Sanar da shi komai ta yi, cikin tsananin b'acin rai ya ce , " Inaaaa ba zai yu ba, ba zai tab'a yuwuwa ba, taya za ai a Yi irin wannan kwad'on, ni na kai son Ablaerh ina? Ya za a min haka, ya za a zauna ta qarfi da yaji sai an cuci marainiya?" Wani mugun kallo Rasheeda da ta fito daga kitchen take bin Yousuf d'in da shi, "Sannu ubana, sannu mad'aurin auren ta, waya damu da son ta da kk? Ko kana son ta wa zai zauna da ita cikin gida d'aya? Kai wama zai yarda ta zama surukar shi? bari kaji, yanda d'an uwan ka ya zauna ya yi shiru to kai ma ka sa min ido, mahaifin ku ya kira kune dan bai son ai auren baku nan, dan haka ku kiyayen dikkan ku zan matuqar sab'a maku akan wannan haukan da kuke, kana Ina take tarawa mutane samari a qofar gida kamar gidan magajiya? Ka na Ina samarin ke tare ta a hanya da sunan soyayya? Kai kana ma da tabbacin wannan yarinyar bata San Wani namijin ba?" Cikin qunar rai Yousuf ya bud'e Baki zai magana Dan ya San wacece Ablaerhn shi ba ta aikata abinda ake fad'a akan ta ba,amma Atiyyaerh ta riga shi, " Nifa Yayah komai ya wuce Allah ya sa hakan shine Mafi alkhairi a gare ni, i can not stop her from doing what she wants, komai ta ce daidai ne akaina, and i will obey her command indai bai sabawa Allah ba, ka kwantar da hankalin ka Yayah, rayuwa ta bazata wulaqanta ba indai zaku na min addu'a," Tana kaiwa nan ta shige d'aki da sauri tare da toshe bakin ta da take shirin kuka, zama ya yi dab'ar a kujera mafi kusa da shi, tare da rintse idon shi da suka yi jawur, ya dafe kan shi dayake jin kamar zai tarwatse, shassheqar kukan sulaiman ne da Afrah kawai ke tashi a wajen, tambayar su ya yi Mama da Abba sun sani? D'aga masa kai suka yi alamar eh sun sani, me suka ce ya sake tambaya, Afrah ce ta labarta masa duk abinda Atiyyaerh ta fad'a mata, shima kukan ya fara sosai, anya irin wannan wasiyyar ya halatta a cika ta? wacce irin qiyayya ce tsakanin Umman su da Mummyn Atiyyaerh as much as he could remember mummyn Atiyyaerh was a very kind hearted woman, she is so loving, caring , and beautiful, she is so cool and sweet,me ya sa Umman su bata son ta? Miqewa ya yi ya ce masu sai da safe, " Yah ina zaka?" Tambayar da suka hada baki suka yi masa kenan, "Makaranta zan koma zamana baida amfani," " ka yi hakuri Abba ya dawo shi ya kira mu fa," "Bazan iya ba, shima hakuri kawai zai ban, and i don't want to hear it from him, zanga matuqar gazawar shi, ku bari kawai na koma," " Yah in ka tafi baka ma Ablaerh sallama ba abun zai mata ciwo sosai" Jingina ya yi da bango ya d'age kan shi sama dake barazanar tarwatse masa, tabbas yasan haka ne in ya tafi ba su yi sallama ba ba zata ji dad'i ba,a hankali ya fara taku ya je d'akin nasu, kwance take tana kallon sama, hawaye na gangare wa a idon ta, ko motsawa bata yi ba, wurga idon ta ta yi gefe inda ta ji motsin shiga d'akin ta ga shine, bud'e mata hannu ya yi akan ta je gare shi, kukan ta ne ya qaru, a hankali ta miqe ta je ta fada jikin shi for the first time a rayuwar ta bayan ta girma, kuka take sosai, kamar zata hadiye zuciya, shima kukan yake, baisan yana son ta ba sai yanzu, itama bata zaci wannan yaba shi da zuciyar ta ke yi ba sone sai yanzu, suna tsaye a haka Rasheeda ta banko qofar ta shiga.... [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 23: Hannu ta sa ta damqi damtsen Atiyyaerh ta janye ta daga jikin Yousuf ta kwad'a mata mari, cikin qanqance Ido da d'aga murya ta ce, "Ai dama na San za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, tinda na ga gilmawar ka kayo nan jikina ya ban akwai Wani abu, a gidan nawa zaki nuna min karuwanci? To ki kwantar da hankalin ki kwana nawa neèe ?daga gobe ne fa za a yi bikin naku, jibi an daura aure an kai ki gidan mijin, kin je can ki ci uwar da zakici a can amma ba a nan ba," Ran Atiyyaerh da Yousuf ba qaramin b'aci ya yi ba, musamman kalmar karuwancin nan da ta ambata ta sosa zuqatan su, amma dake Atiyyaerh akwai hakuri, tin kallon farko da ta mata na b'acin rai bata sake ko da kallon ta ba,ta juya ta koma gado ta kwanta ta dora pillo a  kanta, sannan ta ja bargo ta rufa, Yousuf ne har yanzu ya ke tsaye ya kuma tsare Umman tashi da ido, yana son ya yi magana amma ya rasa mai zai furta da Allah ba zai fushi da shi ba, tabbas in zai magana ko ashar ya dura ba zai ji sauqin zuciyar shi ba, wannan matar me mummunan halin da be tab'a ji ko gani ba a rayuwar shi mahaifiyar shi ce, kalaman shi dole su zama masu taushi a gare ta in Yana son Rahamar Allah, a wannan gab'ar kuwa bai da kalamai masu wannan taushin, hadiye wani abu ya yi mai mugun d'aci ya sa kai zai fice, "Ina zaka je kuma?" "Makaranta zan koma," kafin ta furta wani abun ya fice, daidai zai bude qofa Abban su shima ya kama zai shigo, murmushi Abban ya masa amma ya kasa maida masa da martanin Murmushin, dan haushin Abban ma yake ji sosai ai ba kowacce wasiyya ake cikawa ba, wannan akwai cutarwa a cikin ta, ace shi bai isa da gidan shi ba,saboda kawai wasiyya sai kowa ya rufe ido, fadar Allah nawa sike takewa duk da ba zai iya nunawa ba, amma tabbas yasan suna aikata Wani abun mara kyau ko da a b'oye ne, sai wata wasiyya ce zata hana su kyautata wa marainiya, wannan ko uwar ta na da rai ba zata so hakan ba, komai son ta yi mending abubuwa tsakanin ta da Umman su, kafad'ar shi Abban ya dafa ya d'an matsa kad'an,ai kuwa kamar ya matso da kuka, kuka ne ya kwacewa Yousuf, wanda Abban nasu ya ji dad'in zuwan kukan, dan ya kula tin ba yau ba d'an nashi yake son Atiyyaerh, sai dai a wancan zuwan da ya yi ya tabbatar da zargin shi ,se kuma ga wannan mummunan had'in aure da ake son a Yi wa yarinyar, rungume shi ya yi sosai a jikin shi dan ya yi kukan shi ba me hana shi, sun fi minti 5 a tsaye, sannan ya kamo hannun shi suka qarasa shigowa, zaunar da shi ya yi a kujera kusa da Sulaiman da idon shi har yanzu yake kamar gauta, duk da yayi kukan amma har yanzu zuciyar shi na nan da takaicin wannan had'in auren, ji yake kamar yaje ya batar da Ahmad din, in ba a ga ango ba wa zai aure ta d'in? Afrah ce ta je ta debowa Abban nasu ruwa da abinci, zama ya yi yaci tukunna, yaran na mai kallon lallai Abba har abinci kk iya ci? Bayan ya gama ya yi hamdala sannan ya fara magana kamar haka, " kuyi hakuri, kuyi hakuri, kuyi hakuri, shine kalmar da zan iya had'a ku da ita, ku sani uwa ta wuce wasa, kar kuce zaku yi fushi da mahaifiyar ku, tabbas uwa ba abar wasa bace, ku yi hakuri da hukuncin da ta yanke, ni kaina zan so hana wa, amma a wannan karon ina son, itama ta ga irin abun da Sakeenaa take son ta gani, na fahimci inda komai yake dosa yanzu haka, ku qara hakuri, zuciyata tafi taku b'aci, badan komai ba sai dan ganin nine mai gidannan, ina da ikon sawa kuma na hana, amma qiriqiri gidana yafi qarfi na, dan haka dole na bamu hakuri dika, Yousuf kai hakuri a daura aure sai ka koma," Yana kaiwa nan ya miqe da jakar shi ya wuce ciki, wata qara yousuf ya saki ya koma da baya ya kwantar da jikin shi akan kujerar, sunan Allah kawai ya fara ambato, dan yasan shine kawai mafitar shi a halin da yake ciki cikin iKon Allah kuwa sai ya ji ya fara samun sauqin zuciyar shi, umarni ya ba Afrah akan taje wajen Atiyyaerh, ita kuma bata son zuwa kunyar ta take, wannan zalinci har ina, me zata ce mata? Da wanne idon zata kalle ta to? Amma haka ta miqe ta shiga dakin, tana zuwa ko taga Atiyyaerh na rawar sanyi, tab'a tan da zata yi se ta ji jikin ta rauuuu, kamar wuta, sai karkarwa take, miqewa tai a kid'ime zata fita, ita kuma ta tattare duk qarfin ta da ya rage ta cafko ta, " Kar ki sanar da kowa, in kk fita raina zai fi haka baci, ki barni wataqila mutuwa tace tazo dan ta sauqaqa min komai dake faruwa dani, ina zan saka kaina, na zama marainiyar qarfi da yaji da ubana, ina mahaifina? Meyasa bai waiwaye ni ba ya nunan ina da uba? Me yasa bai zo ya tsaya min ba? Afrah ba mai jin kukana ko nayi, a banza, ko nai roqon a taimakan a banza, amma ba komai, akwai Allah, kuma baya barci," Afrah kuka kawai take ba qaqqautawa, Atiyyaerh ko idon ta yanzu ya bushe, bata jin kukan ma, sai suyar zuciya, a haka aka kira sallar isha'i suka miqe, dan ranar ko magrib ba wanda ya yi,alwala Atiyyaerh ta d'auro da taimakon Afrah, mazan suka yi jam'i suka rama magrib da ke Kan su sannan suka maida isha'i, tinda suka yi sallah Atiyyaerh ke zaune a wajen bata motsa daga wajen ba, domin ta kula sallar da ta yi ta yaye mata wani kaso mai tsoka daga damuwar ta, miqewa ta yi ta ci gaba da jero nawafil, bata samu ta zauna ba sai da taji qafafun ta sun kasa tsaiwa, saida taji idon ta na rufewa sannan ta kwanta a wajen, cikin zuciyar ta addu'a kawai take na neman zabin Allah, tana roqon in laifi ta yi wa Allah ya ke mata wannan horon ya yafe mata, in jarabawar rayuwar ta ce haka tana roqon Allah daya bata ikon ci, kar ya sa ta sab'a masa,a haka bacci ya dauke ta,Afrah ita kuma sai wajen hudu ta tashi ta yi ta nata nawafil din da addu'o'i, kowa a gidan bai rintsa ba banda Rasheedah da ta yi d'aid'ai a gado, tana ta kwasar barci harda saleba. A yau ne aka daura auren Atiyyaerh da Ahmad, akan sadakin su da suka bada dubu goma,bakin shi kamar zai tsage dan murna,hakoran nan nashi farare da suka rine da hayaqi sai kyalli  suke , ba laifi Ahmad na da dan kyau,daidai misali, but he is not that extremly handsome, abokan shi 'yan ganye kamar ruwa a wajen, haka aka tashi Abban su Rasheedah  kamar zuciyar shi ta fashe, ko gidan su Atiyyaerhn bai shiga ba ya sa kai ya tafi gidan shi Mama kuwa dama bata zo wannan auren baqin cikin ba, ta dai Kira Yousuf a waya ya had'a ta da Atiyyaerh, ta mata nasiha sosai Kuma ta bata hakuri akan abinda ke faruwa, su Yousuf da Sulaiman daga wajen suka yi makaranta, dama Sulaiman a shekarar ya shiga first semester yake ya na so ya Maida hankali dan ya samu GP me kyau kamar yanda Yousuf ya ke nuna masa mahimmancin hakan, ba wanda ya dauki ko tsinke a cikin su suka wuce,kafin Sulaiman ya San Kiran da ake musu ya sa ran samun wani abu wajen Abban su amma yanzu ji yake in ba kud'in makarantar da ya zama dole ba bai da buqatar komai wajen su ba qaramin haushin su yake ji ba dikan su, Auwal ne ke ta gaisawa da abokan Ahmad, sai abun qauraye suke masa, a haka taron ya tashi, Auwal ya shige gida, direct d'akin shi ya nufa, dan gidan kamar ba aure ake ba, a dangi ba wanda yazo, sai wasu qawayen Rasheedan su uku, suma d'aya ce halin su ya zo d'aya da ita, sauran biyun ne suka samu suka gyara Ablaerh, suka sa ta ta yi wanka, bata masu musu ba ta yo ta fito, bayan ta dauro alwala, zama ta yi suka shafe ta da mayuka masu kyau da suka zo da shi, masu qamshi, a cikin su wata tayo mata humrah mai qamshi sosai, suka shafe mata da turaruka , suka mata kwalliya daidai yanda kyaun ta zai qara fitowa, mamakin kyaun ta suke, the more suna kallon ta the more suna qara ganin kyaun ta, Afrah kam ko jambaki bata saka ba bare kwalli, haka ta zauna kamar wadda take takaba, fuskar nan ba walwala ko ta sisin kwabo, haushin ma Ablaerh da ta zauna ake mata wannan shirmen take, murmushi ta mata ta dafa ta bayan qawayen Umman su sun fita, " Bana son damuwar ki, in na tafi ina tinano fuskar ki cikin damuwa hankalina zai dinga tashi ne, ki sassauta wa zuciyar ki, ni yanzu na sallama wa Allah ragamar rayuwata na san ba zai tsaran abinda zai zama cutarwa a gare ni ba, zan shiga gidan aure na da son zaman gidan mijina ba da wata niyya ba, tinda ya zama mijina ba zan masa musu ba, zancen halayen shi da kk tsoro kuma kar ki damu, duk fa wanda yaso zama lfy shi yaso,ki sama min nutsuwa ta ganin kyakkyawar fuskar ki cikin annuri,ta haka ne inna tafi zan dinga jin dad'in tunawa da ke, ki min alqawarin zaki dinga zuwa wajena Ina ganin ki, ta haka ne kewa ta zata ragu," Afrah gyada mata kai kawai take cikin kuka,daga qarshe suka rungume junan su, Atiyyaerh ta yi matuqar qoqari wajen maida hawayen ta ta hadiye su, dan bata son ta bawa Afrah qarfin guiwar ci gaba da kuka, bud'e qofar aka yi aka shigo, qawayen Umman su ne da umman tasu, dayar mai halin Ummar tasu ce tace, " Yar nema mai kan buta meye na kukan? Ke za a aurar ko neman gindin zama a wajen ta? Kar na qara ganin kin zubda hawayen ki a banza," kallon tsana suka bi ta da shi, ba wanda ta tanka ta a cikin su, " To Ablaerh kin ji dai abubuwan da muka fada maki d'azu, aure ibada ne, ki jaddadawa zuciyar ki haka kar ki saka mata wani tinani bayan wannan Allah ya albarkaci rayuwar auren ki ya kare ki daga dikkan Sharrin da ke cikin ta ya had'a ki da alkhairin da ke cikin ta," Daga nan suka miqar da ita dan raka ta gidan auren ta dake maqotaka da su, d'an tsayawa ta yi sannan ta tafi wajen Umman su ta durqusa, " Ummana na gode da kulawar ku Allah ya qara girma ya biya maku buqatun ku na alkairi, Ummana ki yafen dukkan bacin ran dana kasance ina saka ki a ciki a dik sanda ki ka kalle ni, ki yafe min dan na tafi da albarkar ku," Sheqe2 ta kalle ta tace, " Na yafe maki Allah ya maki albarka, ai wa miji biyayya a zauna lfy dan nasan halayen ki kaf na taurin kai," kallon ta Afrah ta yi ta kauda kai, sannan ta fice, miqar da ita qawayen Umman suka yi sai gidan su Ahmad, ba laifi, an masu tarbar mutunci, an girmamasu, d'akin Atiyyaerh kam ya sha kaya,Auwal ba qaramin qoqari ya yi ba wajen cika d'an madaidaicin d'akin da kaya masu tsada, dakin ciki da parlor ne,sai wani d'an kewayayyen waje nan ne toilet, sannan kitchen din su na kwano ne waje ne na had'aka dika matan gidan nan suke girki, a haka kowa ya fara watsewa, dan atiyyaerh bama ta san sanda Afrah ta zame ta tafi ba, tana komawa gidan dakin su ta tafi ta fada gado ta yi ta kukan baqin ciki, kukan tausayin halin da 'yar uwar ta zata shiga anan gaba. Ango ne ya shigo da ledar shi a hannu, ya ajiye, direct wanka fad'a ya na gamawa ya fito daga makewayin nasu,ya saka wasu kayan, ledar da ya shiga da ita ya janyo ya kuma kamo hannun Atiyyaerh ya zaunar da ita a gaban ledar dake daf da shi, budewa ya yi se ga qatuwar kaza ta bayyana, " Amarya kin sha qamshi , amar ya baki laifi ko kin kashe dan masu gida," Murmushin yaqe ta d'an yi masa, dan gaba daya tsoron shi ma take ji, "To bismillah amarya mu ci kazar amarci dan ni dai yunwa nake ji" Yankowa ya yi ya miqa mata a baki cikin Jin kunya ta d'an kauda Kan ta gefe, dariya ya yi yace, " Yarinya gwanda ma ki ci dan ga qarar da cikin ki yake yi nan kema,alamar kin bar kan ki da yunwa, na riga Kuma da nasan gidan ku ba yunwa, in baki ci bama ni ba fasa wa zan ba atoh," "Menene ba zaka fasa ba? Ni fa bana Jin yunwa ne kawai na qoshi" "Lallai yarinya yarinya ce, wato baki san ma me za a yi ba, tabdijam, to ke dai ci ko ba Kya Jin yunwa ci Dan Allah ba Dan ni ba" karb'a ta yi a kunyace ta fara ci, murmushi ya mata, ta mayar masa itama, a haka suka gama ci, bayan sun gama ne, ta tashi ta d'aga komai ta goge qasan da aka saka maiqo, ta je ta yi alwala ta wanke bakin ta, shima wanke bakin ya yi ya zo ya kwanta, sallah ta yi ta zauna ta jira ta ji ko zai ce zasu yi nafila tare, kaya taga yana cirewa, daga shi sai gajeren wando, duk halittar jikin shi tana gani, wani wawan faduwar gaba ne ya kamata, cikn in ina tace, "Ammmm naaa zaci....zaaa mu yi nafila neee, irin na sabon aure da ake yi?" Tashi ya yi zaune yace, " ke ni kyale ni, yau dai saboda na aure ki Allah ya ban iko har isha'i na yi,amma ni kam ba wata nafila da zan yi gaskiya" Wani baqin ciki ne ya kama ta,da ace Ahmad ba jahili bane haka, da wataqila har son shi zata daure ta koya wa zuciyar ta bayan biyayyar auren, amma inaaa ba zata iya son shi ba samm, cikin kwantar da kai ta miqe ta je gaban shi ta durqusa, ta kamo hannayen shi,sannan ta ce, "Haba miji na, kai da ka yi raka'a har hudu wannan kuma biyu ne fa kacal, kuma godewa Allah zamu yi akan baiwar da ya mana ta aurar da mu ga junan mu da ya yi, ka ga ai ya Kamata mu nuna godiya da farin cikin mu ta hanyar bauta masa tinda ka ga dai ba za mu yi rawa da waqa ba, magana ake ta Allah,ba Wani ba" Da Jin haka sai ga Ahmad ya miqe ya zura riga ya je ya yo alwala, yazo ya jasu sallah tayi mamakin yanda ya dan iya ba haka ta zata ba ma sam,a zaton ta komai be Iya ba, "To yanzu munyi sallah sai gado ko?" Ya fada yana kamo ta jikin shi ya na qoqarin cire mata hijabin ta,Wani mummunar fad'uwar gaba ne ya kama ta Jin ta a jikin shi da ta yi,a hankali ta saki jikin ta ta kwanta a nashi tace, "To ai baka min addu'ar da na ji ance angwaye na wa amaren su ba na neman tsarin Allah daga sharrin matar da suka aura da neman Allah ya hada su da alkairan da ta ke da shi, ko so kk na dinga ma rashin kunya ko qin bin umarnin ka?" Kad'a kai Ahmad ya yi, sannan yace "Nan da d'aya Atiyyaerh ke kin San da ya na iya karatun sallah ma? Ni ai ban wani iya addu'ar ba, se dai in ke Zaki koya min" Ba musu kuwa ta koyar da shi, nan take ya dafa Kan ta ya yi mata sannan ya fara mata wasanni, cike da tsoro cikin zuciyar ta, amma ta dake, dan bata son ta yi zaman k'unci a gidan Ahmad, koma me zai je yazo so take kar ta walaka a wajen shi, taurin kan da zata mai shi zai nuna yanda ta zab'i ta  zauna a gidan tinda aure dai an riga da an d'aura shi ba Kuma fasa kusantar ta zai yi ba, ko ba jima ko ba dad'e se anyi, to gwanda ma ta hakura ta sawa zuciyar ta salama,ji yake kamar zai had'iye ta, ko ina tabawa yake, yau wai shine da wannan zuqeqiyar a matsayin mata, dole a tanadi addu'a ta godiyar Allah, tun suna wasanni a qasa ya miqar da ita ya kaita gado, ina ganin yazare masu komai na jikin su na basu waje,nace a ci amarci lfy🤭 Ablaerh ta wahala ba kadan ba wajen Ahmad, ta yi kuka ta gode Allah, kukan takaicin rasa budurcin ta ga wanda ba ta taba zata ba shine yake dawainiya da ita, rarrashin ta yake sosai, yace, "Ashe ku da ku ka yi boko ake cewa yan iska duk qarya ne, wanda basu yi makarantar ba sune yan iskan, dan kinga fiddausin bayan layi gaba daya a bude take," zaro ido Atiyyaerh ta yi waje, cikin razana da tsananin tsoro ta kalle shi ashe har neman mata yake bayan shaye shaye???????? [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH *Makaranta ku yi hakuri ku jira ku ji ya abun zai kasance har zuwa qarshe,sannan kar mu na manta cewar  kowa fa da qaddarar shi a rayuwa, ba lallai ne a halicce ka ka ji daɗi all ur life ba, we ar not in this dunya to have fun, we ar here to worship Allah, kuma a cikin bautar shi ne ya ke jarabtar  mu da abubuwa kala2, in ma ya jarabce mu da arziqi, ko talauci, ko ya haɗa mana dika, gaka mai arziqi amma ma talauci, ko gaka talaka amma mai arziqi, (mai wadatar zuci talaka,da mai kudi mara godiya) dan haka nake cewa ku qara hakuri, akan kome zaku karanta har mu Kai qarshen labari thank you.* Page 24: Ahmad a kwanakin nan ji yake duk duniya ba wanda ya fishi morewa da matar aure, ta bangaren Atiyyaerh kuwa ta sani bata yi irin auren da take so ba, Kuma har yanzu bata son Ahmad a ranta, amma ta na Jin dad'in yanda yake kula da ita, yake nuna mata soyayya, ta bangaren surukan ta ma bata da matsala da su, Inna Abu da Baba Garba basu da wata matsala, su suke ci da su ita da Ahmad d'in, dan haka ta kan fita ta ya Innar aiki bayan ta gama da na bangaren ta,Ahmad yana da Yayah da matar shi, wadda take da qananan yara biyu,Sadiq da Umar,yaran ba qaramayen marasa kunyan yara bane, yanda uwar su take ba kunya komai a tsattsaye haka suma yaran suke, Yayan Ahmad Muhammad sunan shi kowa na ce masa Yayah, bai da matsala, amma wani lokacin akan yaran shi sai a buga da shi a tsakar gida, nan ma yana samun pampo ne wajen matar shi,me suna Hajar, Hajar ko sunan surukar ta katsal take fadan shi ba sakayawa wato Abu, shiyasa yaran suma suka dauka, Abuu, Baba Garba ne kawai suke ce wa Baba, su abincin su daban suke yin shi a gidan, in ta ga dama ta zuba ta bawa surukan in bata yi niyya ba suci da yaran ta da mijin ta. Atiyyaerh ta kasa ce ma surukar ta Abu, sai take ce mata Inna kamar yanda taji Ahmad da muhammad na kiran ta, ta kula da yanda surukan ta ke son ta, har Yayah, sannan kuma ta kula da yanda Hajar ta tsane ta, sai tana yada mata magana akan kyaun ta ai na d'an maciji ne a Jira lokaci kad'an mummunan halin Atiyyaerhn zai bayyana ne nan gaba, amma ba ta taba tanka ta, to yaushe ma tazo gidan? Kuma ma in ta dad'e me zai kaita biye mata? Ita fa a rayuwa bata son hayaniyar fad'a, rayuwar bala'i da masifa a ciki ta taso, to me zai dame ta kuma? Dan haka ganin halayen Hajar take nafila akan inda ta baro ba Wani damuwa bane a wajen ta. Ta gama wanka kenan ta yi kwalliya daidai ita abin ta, dan rashin sabon da ta yi ne ma da Kwalliyar yasa wataran sai ta yi wanka sai ta manta bata yi Kwalliya ba se ta tina yanzu fa a gidan miji take sai ta dan yi kwalliyar kadan, to ranar Kuma an yi sa'a Ahmad a gida yace zai wuni, ita kuma kullum tana nuna masa fita neman na kai ya na dojewa dan be Saba ba, sai ya ce mata shi fa ba sana'ar da bai gwada ba basa kar bar shi ne, haka take hakura, ta biye mai ya yi ta jagwalgwala ta, bata so amma bata tab'a nuna masa ba,kuma bata taba kyamartar shi ba, dan daidai misali bai da qazanta yanzu, tana sashi gyara a inda taga bai mata ba, da dabara da Jan hankali zata nuna masa me take so ya gyara, misali wata rana suna zaune yana ta bata labarin yan ganyen abokan shi, , " kinga kafin na aure ki ,nida Baba Qarami sai mu sha ganye nadi shida a rana, ba abinda ya mana zafi, amma kinga nine yanzu har na d'au sati biyu ban sha koda sigari ba, sai sau d'aya,randa kk shiga yiwa Inna tuwo na sha da kk dawo na buga qasa nace ban sha ba🤣 , kika yi kika yi na kafe na ce miki ban sha ba, kin san me?" Kada masa kai ta yi tana dariyar tina kafiyar da ya mata yana zaro ido kamar mage ta sha wanka, "A ranar sai na ji wani haushin kaina dan me zan sha abinda ba ki so, bayan ke tinda na aure ki ba ki da burin da ya wuce na ki faranta min? Shiyasa na yi ta qoqari na daina, dana ji ina son shan Wani abun maye gwanda na zauna a gida na yi ta Koda kallon ki ne Ina Jin nishad'in da bana Jin irin shi a cikin kayan Mayen, shine zakiga na dame ki na maqale maki, ke kuma nasan kin gaji amma a haka ki ke  hakuri dani,na gode Atiyyaerh 'yar aljannah ki ta taya ni da addu'a kin ji? Watarana inshaa Allahu zan dena ne" Tausayi ya bata ta daga masa kai kawai alamar "To" tare da tsagaita dariyar ta, a hankali ya ja ta jikin shi, bakin shi ta ji yana wani bugawa, zuciyar ta ta hautsine kamar zata yi amai, tabbas ta bari ya kai bakin shi nata zata yi amai ne kawai,dan haka cikin dabara ta janye ta na murmushi, ta ce Masa, "Mijina ina zuwa na je na yi brush, nazo na maka wani abu, dan yau sai na baka ladan qoqarin ka na daina shaye2, duk kuma randa ka min alqawarin daina neman mata ni kadai na san me zan maka a gidannan," Ta shi ta yi tana taku mai Jan hankalin da ita Kan ta se da ta yi mamakin yaushe ta Iya hakan?  ya kwanta yana hango ta yanda take tafiya jikin ta na juyawa cikin salo, hankalin Ahmad in ya yi dubu to Atiyyaerh ta d'age shi, brush din ta ta d'auka ta saka toothpast, sai ta juya tana kallon shi, tace, "Mijin Ablaerh na saka maka ne kaima ko na bari?" Cikin zumudi yace, "Saka min nima , ai dole nima na tsaftace nawa bakin kar naiwa kaina mugunta, bansan dad'in da za a ban a ciki ba," Dariyar samun nasara ta yi, suka je suka wanke baki, a zuciyar ta tana mamakin ina ta iya irin wadannan abubuwan?( niko nace Ablaerh ko wacce mace jaruma ce, mai ilimi ce, kuma mai fasaha ce, dan haka mace mai wayo da dabara ita zata iya sarrafa wadannan abubuwan, kowa Allah ya halicce ta da kissar ta a tare da ita, ya dangan ta da wacece ke kafin ki mori abinda Allah ya baki na baiwa, in ke cikakkiyar mace ce zaki amfana da sirrikan dake tattare dake, in mata kk rako to komai kina zaune ki na jiran sai an fada maki, sai kin ce baki iya ba a koya maki, bayan a take zaki iya maganin matsalar ki da kalaman ki, da jikin ki, sannan da kallon ki,) can na hango malama Atiyyaerh na kwance saman jikin Ahmad, Ahmad ya rude sai sambatu yake, ta gama susuta shi, qara maimaitawa yake, "Daga yau na maki alqawarin bani ba shan ganye,bare sigari, har abada, Ablaerh ki dinga min irin wannan kullum," Hajar ce ta zo wucewa ta ji duk abinda ke faruwa, kad'a kai ta yi ta tafi, bayan sun gama.abinda suke ne, suka yi wanka a makewayin su, ta saka wasu kayan tace masa bari ta shiga ciki ta taya Inna aiki, dama tin dazun take son zuwa , suka zauna hira, cewa ya yi da shi za a, ta yi iya yin ta kar ya bita amma inaa ya qi, hakura ta yi suka shiga ciki tare, tankad'e ta tarar Inna nayi, ta yi sauri ta karb'a ta ja kujera ta miqa masa dan ya zauna, ita Kuma ta tsugunna ta ci gaba da tankad'en, Innace ta bata ta ta kujerar amma taqi karba, tankad'e take suna hira, sannan tana duba ruwan tuwon, dan yawanci abincin su baya wuce tuwo miyar kuka, se juma'a a dafa shinkafa ko taliya 'yar murji, Atiyyaerh ce ma data zo ta sa ake d'an canja miyar kala2,in yau an yi kuka gobe a Yi kubewa ko ayoyo, Hajar ce ta shiga sashen Inna Abun itama ta samu bakin qofar d'akin Innar ta zauna ta ce, " Au nan ku ka shigo ashe, ai zuwana wajen ku wajen sau uku kenan ina komawa, gaba d'aya kun rikita mana gida da sambatu kamar Kan ku aka fara aure" Wata uwar kunya ce ta kama Atiyyaerh kamar ta tsaga qasa ta shige, hannun ta kasa riqe rariyar ya yi, sai ta ji ta mata nauyi, kula da hakan ne ya bata ran gogan nata,cikin son baqantawa Hajar Shima ya ce, " Eh muna can muna abinda muka yi aure domin shi, kin ganta nan na san ba sona take ba, amma bata rowa,kuma 'yar albarkar ba sai an siyo mata tsiren Talle mai nama ba kan a kusance ta, a bata so na take hakuri da babu na, duk da ita gidan ubale akwai, kuma a......" " Dan Allah ka yi hakuri ka rabu da bata amsa irin haka, baka kula Inna ta tashi ta bar wajennan ba sabida kunyar maganganun ka? Ni kaina ka ja min kunya yanzu da wanne ido kk son na kalle ta?" Ta qarasa cike da shagwaba, wanda dama da ita take qara susuta shi, matsawa ya yi daf da ita ya fara bata hakuri, Hajar da ta cika ta yi fam,dan bata tab'a zatan Ahmad duk yasan wadannan abubuwan game da ita ba, gaskiyar shi ne kuma a haka wai tana son Muhammad, akan shi ba abinda ba zata yi ba dan kar ya mata kishiya,amma fa haqqin shi in zai sauke sai jama'a sun ji, indai ba ita ke so ba, "Sannu 'yan bariki,ni zaku gwadawa bariki? To bari ka ji mu zuba ni da ku a gidannan naga wa ya fi wani bariki, kina wani sunne kai kamar ta Allah, yanda aka ce gidan ku akwai tarbiyya ashe qarya ne, kin gama rabawa gayu a titi, dan dai qarya kk kice a nan kk koyi komai," Bata ankara ba ta ji an kafe ta da mari, jikin Ablaerh na rawa ta ja shi, amma inaaa yau dabar ta motsa, ita kan ta Hajar ta tsorata,dan ko a bige yake bai tab'a bata tsoro kamar na yau ba, dama tinda Hajar ta miqe ta na magana da qarfi gidan ya d'auka da ana fad'a tsakanin amarya da Hajar, nan da nan 'yan d'aya gefen da ke zaman haya suka leqo, dama ashe ana rade2n tunda tai boko bama budurwa bace, dan salin, alin suka yi abunsu, bata yi wani iface2n da maqota zasu ji ba,to shikenan ake zargin ta, se yau Hajar ta fallasa qus qus d'in da ake akan ta, " Amadu kai hakuri ka tafi sashen ku," In ji Innah Abu da ta fito daga d'aki, Jikin Ahmad kuwa se b'ari yake cikin rawar murya ya ce da Innar tasu, "Qazafi fa ta yi wa mata ta Innah, waye ya kusantar min ita har da ya ji ba budurwa bace? Yau se na illata ki a gidan nan Hajar" Zabura ya yi ya sungumi tab'arya zai rantama mata akai Atiyyaerh ta riqe ta na hawaye ta ce, "Dan Allah Bappan Umar ka yi hakuri, mu tafi, tamun qazafi kuma Allah mai hisabi ne akan kowa da komai, Allah zai mun sakayya, muje bana son daga zuwana a na samun hayaniya haka," kwalla ce ta sakko mata a kunci, aiko yana ganin haka ya qara zabura zai make hajar, cikin zafin nama ta janye, ashar ya dinga durawa irin na asalin yan tashan nan, " Matar tawa ce ta rabawa gayu jikin ta? Uban wa ya kwantan da ita daren farko ya ji ta a matsayin budaddiya da har zaki ce haka? Ni da mata ta ki mata sharri a gabana? Yau na lahira sai ya fiki jin dadi Hajara se kin fad'an gayen da ta rabawa jikin nata ko na yi maki dukan mutuwa"......... [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 26: Da abincin su ta shiga dakin ta aje a parlour, sannan ta shige uwar d'aka, kwance ta gan shi ya na bacci, kallo ta bishi da shi daga fuskar shi har zuwa yatsun qafar shi, Ahmad ba shi da makusa in ba ta ilimin shi ba, shi d'in ma zama da ita ya sa ya fara koyan wasu abubuwa masu mahimmanci a rayuwa musamman ta bangaren da ya shafi ibada da bautar Allah,ya fara Iya koyon rubutun Hausa da karatu, bashi da girman Kai wajen zama ta koyar da shi Dan ya San ya yi wasa da damar shi be je makaranta ya Iya ba, Allah ya bashi wadda zata koya masa ba tare da ta masa gori ba sai kawai ya saki jiki ya na koya abun shi, a cikin zuciyar Atiyyaerh kuwa ta sani kwata2 bata jin son shi, sai dai ya na da Wani matsayi Mai girma a gare ta na mijin da take aure,ta San girman matsayin miji a Islamiyya ana koyar da su, qawayen Rasheedah sun mata nasiha akan haka, Mama ta mata nasiha ta waya akan hakan, Dan haka bata tab'a manta matsayin shi da girman da iKon da yake da shi akan ta,ta d'auki Ahmad a matsayin aboki saboda zaman su ya musu sauqi ya Kuma Yi musu dad'i, ta haka ne ta ke zaune lafiya kamar wadda ta yi ninqaya a cikin son shi da jimawa,wannan dalilin ne ya sa ba zata tab'a barin shi yana neman mata ba ko dan kare mutuncin ta, cire kayan ta ta yi tai wanka ta dawo d'akin ta gyara jikin ta ta sauya kaya, sannan ta tashe shi, ta ce, "An kusa kiran magrib, ya Kamata ka tashi haka ,ruwan wankan ka na bayi, in ka gama ka dawo sai muci abinci," "Na gode, amma gaskiya na dad'e ina bacci ban San lokaci ya tafi haka ba sannu da aiki," Murmushi ta masa ta miqa masa hannu dan ya tashi, kama wa ya yi ya tashi ya fice, kan ya dawo ta dakko masa kayan da zai saka, sannan ta zauna tana jiran kiran sallah, kan ya shigo an kira sallah, da Shirin masallaci ya bar d'akin sai zabga qamshin yake yi, tana sallah ta ji qarar faduwar abu da mugun qarfi, sai da ta idar da sallar ta ta leqa dan ta ga meye, tana fita ta fad'i qasa, sakamakon santsi daya d'ebe ta, "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, meye haka Umar?" Dariya suka saka mata,"ke Aunty Amaryar nan baki iya abinci ba, gaba d'aya kin tuqa tuyo ya yi wani gudaji, sanan kin mana miya tsululu kamar ruwan wanke kai," Cewar Sadiq da yake babba akan Umar,a hankali taso tashi amma ta kasa, sakamakon gurdewa da qafar ta ta yi, da rarrafe ta bar wajen da miyar ta zube ta koma gefe ta na matsa qafar ta da ke mata radad'in zafi, ta ce, "Ku yi hakuri Sadiq inshaa Allah gobe za ku ci mai dad'i, amma ku sani wannan abun da kuka yi ba abu bane mai kyau,yaran da basu da tarbiyya su ke yin hakan, sannan kuma kunga kunyi almubazzaranci da kuka zubar da abinci, Allah yace duk almubazzari dan uwan shaid'an ne, dan haka ni bana son ku kasance daga 'yan uwan shaidan, ko kuna so?" Girgiza mata kai suka yi, ganin maganar ta kamar na shigar su se ta ci gaba da cewa, "Da kyau yaran Bappan su, Allah ya muku albarka, nan gaba ko wani ya sa ku yin haka kuce yi wa babba rashin kunya haramun ne Allah ya haramtawa yaran kwarai 'yan albarka yin rashin kunya, kun ji, kuma duk mai saka ku rashin kunya baya son ku, so yake ku shiga wuta, in baku so ku shiga wuta sai ku qi yi kun ji?" D'aga mata kai suka yi jikin su duk yayi sanyi,sun fahimci Auntyn nasu na son su, Umman su so take su shiga wuta, ita Kuma Atiyyaerh daga yanda ta ji Sadeeq na tsara zance ta San Saka su aka yi, tinda a baya Suna mata biyayya dik da ba su da kunya,cikin Murmushi ta ce musu, "To me ake cewa wanda aka yi wa laifiiiiii?" Ta fad'a tana karkata kai tana murmushi, " Kiyi hakuri," Suka fad'a a tare, umartar su ta yi da su tafi ba komai, suka juya jikin su ya yi sanyi, duk a kunnen Hajar, in ranta ya yi dubu to ya b'aci, qwafa ta yi tace, "Zamu had'u ne ai gaba," Ta shige sashen ta kafin yaran su fito, kafin Ahmad ya dawo a durqushen da take ta gyara wajen, yana dawowa, ya ganta ta had'a zufa,ga qafarta miqe ta kumbura,cikin damuwa kwance a saman fuskar shi yace, "Me ya same ki? Ya naga qafar ki ta kumbura?," "Zamewa na yi na fad'i a bakin qofa, shine qafata ta yi haka, kuma zafi take min," Ta qarasa cikin kuka, dan ba qaramin zafi take ji ba, da kyar da sidin goshi, ta yarda ya ja qafar, ta sha kuka kuwa sosai, amma da ikon Allah yana ja mata se ta mata sauqi sosai,ciki ya kama ta suka shiga suka ci abinci,su na gamawa a wajen ta yi bacci, bayan kiran isha'i ne yace gida zai sallah ba za shi masallaci ba dan ba ya son ya fita ta sake samun wata matsala, " Allah ne mai kare bayin shi fa, in ma ka zauna Allah ya nufa se wani abu ya samen zaman ka ba zai hana ba, kaje kawai," Murmushi ya mata cike da gamsuwa da bayanan ta ya fice,tashi ta yi ta na d'an d'ingisawa tai alwala ta yi isha'i sannan ta tafi ta kwanta, tsabar gajiya ko minti 3 batai ba bacci mai dad'i ya d'auke,ko da ya dawo se ya ga har ta yi bacci abin ta,kwanciya ya gyara mata shima ya rab'a gefe ya kwanta, duk da gajiyar da tai bai barta ba sai da ya d'aga ta cikin dare ya sauke buqatar shi, amma ko a fuska bata nuna masa b'acin rai ba dik da bata so hakan ba,haka ta hakura ta sallama masa kanta,ta sani ladan ta na wajen Allah, ba ta koma bacci ba sai da ta tsarkake jikin ta, sannan ta dora da nafila da karanta qur'ani, sannan ta koma. Wataranar asabar da safe, rana ce da Atiyyaerh ba zata tab'a mantawa ba a rayuwar ta ta gidan auren  Ahmad, Ya gama sauke buqatar shi ta auratayya kenan, se Atiyyaerh ta ji ya fara fad'a ya na kumfar baki, "Ni fa na gaji da gafara sa ban ga qaho ba,shekara biyu da watanni ba ki tab'a ko da b'atan wata ba ne haba, ai a qalla ko b'ari kinyi, kullum sai munyi abunnan, wataran har sau uku a rana, dubi Hajar kwanan nan ta haihu, amma ke shiru, gaskiya na gaji,kullum Inna da Baba in suka ji kina zazzab'i fatan su ace ciki gare ki, ni dai gaskiya na gama maki kawaicin haihuwa nake so," Kallon shi ta yi cike da takaici, ta bud'e bakin ta da ke rawa saboda kukan da take son yi ta ce, "Amma dai Bappan Umar ka san ba ni ke bada haihuwa ba ko, a wannan lokacin da ilimin addini ke shigar ka ya kamata ace kasan waye Allah, kasan Allah shi ba a masa dole, ni kaina zan so na haihu amma Allah bai nufa ba, ya kk so nayi," "Bawani nan dama Hajar tace tsarin iyali kk, saboda kina son komawa karatu, to bari ki ji ba a gidana ba, bazan lamunta ba, ki haihu ko d'aya ne in yaso sai ki tafi karatun naki" Mamaki ne ma ya hana ta magana ta zauna a kujera dabas, se da ta nisa sannan ta ce, " Hajar? Yaushe ka fara zuwa kuke hira har da zata fad'a maka hakan, ko ni yaushe nake magana da ita da zan fad'a mata Ina so na koma karatu? Kayi tinani fa, matar nan tin da nazo ta sa min ido, dan kawai kana so na, Inna da Baba na sona, shike nan fa, kuma tayi qoqarin Yayah ya daina so na, su Umar su daina kula ni suna min rashin kunya, amma ta kasa samun hakan, shine yanzu ta b'ullo ta nan, Allah na nan, yafi mu sanin abinda muke aikatawa," Ta miqe ta shige d'aki, zugum ya yi yana tinani, tabbas kusan duk abinda ta fad'a gaskiya ne, to amma baya mantawa randa Atiyyaerh ta tafi gidan Mama gaida Abba ya yi rashin lafiya, sunyi magana akan ci gaba da karatun ta,har ta nuna masa tana da sha'awar hakan, kuma ta bashi shawara ya koma makaranta, ta boko tinda yanzu yana zuwa islamiyya, ya mata zancen haihuwa tace ita duk abinda Allah ya yi shine daidai, to shiyasa da Hajar ta fad'a masa hakan ya yarda, ji ya yi bai ji dad'i ba da bai yi dogon tinani ba ya yanke hukunci, amma shifa gaskiya yana son haihuwa, tashi ya yi ya shige ya kwanta, bai kula ta ba, tana ta jiran ya bata hakuri ta ji shiru, juyawa ta yi ta ga yana qoqarin yin bacci, ta tada shi, yana miqewa ta saka kuka, rikicewa ya yi ya hau dudduba ta ya na son leqa fuskar ta, ita Kuma ta na kauda kai, "Subhanallahi, Atee na me ye, meya same ki?" Kuka take kawai tana abun shagwabbabu, tana karya kai, da kyabe baki, tashi ya yi tsam ya d'ora ta a kan cinyar shi, "Ni ne ko, ni ne na qi kula ki? Ni ne na zarge ki akan kin qi haihuwa ko?" ... in ya yi magana sai ta d'aga kai sama ta ci gaba da kuka tana yarfe hannu, tana juya jikin ta a nashi, "Shiiiii to kiyi hakuri, ba zan sake ba, ba zan qara ba kin ji, wancan ma akasi aka samu, kin fahimci mijin ki ko, zaki yafe masa ko yar albarka?" Sai d'aga kai take komai yace, gefe ya yi da kan shi yana dariyar rikici irin nata, in tana irin haka ba qaramin burge shi take ba, kuka ta bare baki  ta saki irin na shagwabar nan, tana turje qafa, tana jijjiga jikin ta, hannu ya sa ya tsaida ta amma jikin ta be dena motsin ba, "Kin ga ki na ta bawa jikin ki wahala,  se jijjiga shi ki ke,ko kina tinanin Zaki Iya kuka ba tare da jikin ki ya motsa ba?" kallon shi ta yi ,ta ce, "Ai zan iya me zai hana" "Da gaskeeee to yi na gani," Aiko nan take ta ci gaba da jijjiga jiki tana qanqame jikin, amma still jikin ya qi dena rawa ,dariya suka saka dikkan su a tare, daga nan suka hau hira Suna wasannin su. Hajar da ta had'a fad'a dan ta je rabo se  ta ji shiru, sai ma wata soyayya da ta kula suna qara zubawa abun su,haushi kamar ya kashe ta( hassada babban ciwo ne, jama'a mu sani hassada tana cinye kyawawan ayyuka kamar yanda wuta ke cin busasshen ciyawa, mai hassada na samun dusashewar hasken fuska, ya zama cikin baqin ciki koda yaushe, zuciyar mai hassada bata tab'a haske saboda a koda yaushe cikin tinani da saqe2n mugunta yake, hassada illar ta na da yawa ba iyaka,mu kiyayi hassada mu zauna lfy, ba sai mutum ya maka wani abu ba in kana da cutar hassada kk mai hassadar, ba sai mutum ya ma san kana mai hassada zaka fara ba, balle kuma wasu na ma mutum hassada ne da ga zarar ya kyalla ido yaga dan uwan shi ya fishi wasu abubuwan, dan haka kar kai mamaki dan kaga wani ya tsane ka ba dalili, ba komai ke kawo haka ba sai hassada, Allah ya kare mu). "Ina son yau na je gida gaida Umman mu, da Abba na san yana gida in na je da wuri, na dad'e ban je ba," "Ba komai ki na iya shiryawa yanzu ki je,in kin je ina gaida su, a gaida Afrah sarkin kunya, ina mamakin yanda ta kasa sakewa da ni har yau," Murmushi ta yi tace, "Haka take fa, ita dama magana bata dame ta ba,balle ta ce min wai kai sai ka dinga mata maganar manya," Dariya suka saka, ta na qarasa gyara gadon, ya maida ta kai, ta miqe tana masa hararar wasa, "Ni Allah bana son haka,dubi sai da na gyara zaka wani bata min," Burgima ya yi, ta ko bi shi ta janyoshi, dama haka yake so, nan da nan salon wasan su ya koma na manya, (lols) sai da komai ya lafa ne sannan ta kai masa dukan wasa, "Duk kasa sai na b'ata lokaci duk sammakon da na yi wajen tashi da wuri yau," Dariya ya yi sosai sannan ya ce, "To ai mun taimaki juna ko ba komai" Shige shi ta yi ta tafi bayi tai wanka ta zo ta shirya, bayan ta gama ne ta masa sallama yana kwance kasala ta rufe shi ta tafi, bayan ta fada masa ya tashi ya yi wanka. ****************************** Da sallama ta shiga gidan a bakin ta,ba laifi duk Wanda ya gan ta ba zai ce tana cikin wahala ba, saboda Mama na aika mata da sutura ba tare da Rasheedah ta sani ba,da 'yan kud'ad'e Abbahn su Rasheedah ma na mata aike akai akai,dan haka ba ta da wata matsalar sutura da kayan ado,  sai dai hasken fatar ta da ya ragu, ta shiga parlour bakin ta na maimaita sallama, Afrah ce ta tafi da gudu ta rungume ta tana mata sannu da zuwa, itama cike da farin cikin ganin 'yar uwar ta ta rungume ta,cikin murya mara hargowa Rasheedah ta ce, "Meye haka kufa baku girma," Qasan ran ta kuwa ta na baqin cikin ganin Atiyyaerh na da aure ga Afrah nan ko mashinshini ta rasa ga Kuma Atiyyaerh da ganin ta bata da wata matsala a gidan auren ta, tinda dik tsahon wannan lokacin ba su tab'a Jin ta kawo qara ba, shi Kan shi mijin duk Wanda ya gan shi zai ga alamar nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare da shi, ( Oh Allah, ina zamu saka kanmu mu Fans din Atiyyaerh, an mana auren mugunta Dan a ga mun tagayyara ,an ji shiru,yanzu gashi Kuma an zo ana Jin haushin me yasa mu ka yi aure Afrah na gida ba aure, to wai shin laifin na waye?) Sunkuyar da kai qasa ta yi ta duqa gaban Rasheedah ta ce, "Barka da safiya Umma ya gida? Da fatan na same ku lafiya?" A ciki ta amsa gaisuwar kamar bata so,Abba ne ya fito sanye da kyakkyawar shiga da alama fita aiki ze yi, cikin sauri Atiyyaerh ta miqe ta Isa gaban shi ta na murmushin farin cikin ganin shi, shi din ma bakin shi ya qi rufuwa cikin murnar ganin ta ya ce, " A Ablaerh ce a gidan namu da wuri haka,ko dai ba a son ai missing ganin Abba ne yasa aka yi sammako?" Cikin fara'a ta ce, " Eh Abbana,na san inshaa Allah na fito da wuri zamu had'u,gashi kuwa Allah yasa, ina kwana Abbana?" Amsawa ya yi tare da zama, "Lafiya qlou 'yar albarka, da fatan Kuna lafiya ba dai wata matsala ko Atiyyaerh ? " Cikin Jin kunya ta saukar da kan ta qasa ta ce, "Abbana muna lafiya ba wata matsala gaskiya alhamdulillah, ya ce ma na gaishe ku sosai in na zo" "To alhamdulillah Allah ya qara maku zaman lafiya Ameen, dama na jima Ina son ki shawarci mijin ki zancen komawar ki makaranta in ya amince,akwai kud'in ki da mahaifin ki ya bari da za'a saka ki a makaranta,dan haka ku yi shawara abinda ya ce se ki Sanar da ni ko ta waya ne, ni ina sauri yanzu zan fita yanzu mun Yi magana Daga baya, ki gaida shi," " To Abba zan Sanar da shi gaisuwa ka, zancen karatu kuma na fasa ci gaba Abba, dan ban ga amfanin kud'in da ya bari ba Abba, ba na buqatar su, in zanci gaba da karatu zan ci gaba da kud'i na na kaina, Ina tinanin fara sana'a ne Abbah inshaa  Allahu, amma na gama amfani da dukiyar shi, ya maida ni marainiya gaba da baya, ba Mummyna, ba Daddyna,rayuwa ta gaba d'aya bata tafiya min yanda nake son ta,ba haka nake son rayuwa ta ba Abbah, amma Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, Abba da Daddyna zai dawo, da zai zo na dinga ganin shi, daya mayen gurbin Mummyna, da na rage jin radad'in da zuciya ta take min game da shi," Tausayin ta ne ya kama Auwal da Afrah, Auwal ne ya ce, "Kiyi hakuri Atiyyaerh, Daddyn ki na matuqar son ki, wannan dalilin ne yasa baya son ya dawo qasar nan ba tare da kin gama karatun jami'a ba, na masa alqawarin daga sanda kk gama jami'a daga ranar zan fad'a masa, shi kuma a satin zai dawo, shiyasa tinda akai auren ku kika ga ina ta bin kan ki, akan ki ci gaba da karatu kk qi, na sani kina da hujja mai qarfi, ba lallai sai kinyi karatu ne zai dawo ba, a ganin ki karatun ki bai da alaqa da dawowar shi,haka ne, amma ni banda masaniya akan dalilin shi na fadar hakan, ki daure ki shawarci mijin ki akai ya na da matuqar mahimmanci ki ci gaba da karatun a wajen Daddyn ki" Gyada masa kai kawai ta yi tana ci gaba da kuka ita ta riga ta San Daddyn ta be son ta Abbah na kwantar mata da hankali ne kawai, Rasheedah ce ta kyab'e baki a ranta ko tana ayyana ta ga yanda zata bar Atiyyaerh ta ci gaba da karatun, fatan ta Allah ya sa kar mijin ya yarda ma, ita yanzu damuwar ta rashin auren Afrah, ga Atiyyaeeh na da aure, wata mummunar dabara ce ta fado a ranta tai murmushi, bayan Abba ya fita ne itama ta fita ta barsu da ita da Afrah, taje chemist din unguwar su ta dawo, hira suke suna taya Umman nasu girkin rana, ta wuce su ta je jakar Atiyyaerh ta saka wani abu ta zuge ta koma ta zauna, kamar ba ita ba. Bayan Atiyyaerh ta wuni a gidan ne ta yi wa su Afrah da Umman ta sallama tace ma Afrah, "Ga saqo Afrah ki ce wa Yah Sulaiman wannan karon in ya dawo ya taimaka ya zo, tinda ya je min sau d'aya bai qara zuwa ba," Amsawa ta yi da "Inshaa Allah tare ma zamu zo," "Allahu ya yarda, Yayah wannan watan zai gama bautar qasa ko," " Eh in Allah ya yarda, " "kaiii amma na ji dad'i,Allah ya bada sa'a,a randa ya dawo nake so ki zo ki gayan na zo na mai congrats kin ji," "To in Allah ya yarda kuwa" kamar kar su rabu haka suke ji, haka ta fita Cike da kewar su,ta yi 'yar tafiya kadan ta fada gidan auren ta, Ahmad ta gani zaune a bakin qofa yana kad'a qafa, mamaki da tsoro ne kwance a fuskar ta,bata taba ganin shi haka  ba cikin b'acin rai, "Bappan Umar me ya same ka haka?" Wani mugun kallon da ya hautsina mata ciki ya wurga mata, ja da baya ta yi dan tsoro, tsawa ya daka mata ya ce, "Ban jakar ki," Da sauri ta wurga masa jakar  ta ja baya, bud'ewa ya yi ya duba sai ga magani a ciki, hannu ya sa ya dakko,se ta ga ya zira hannu a aljihun shi ya dakko magani ya had'a da na jakar ta ta se ya ga tabbas wannan shine wanda Umman ta ta nuna masa, hawaye ne ya fara bin fuskar shi, " Haba Atiyyaerh, me na yi miki da zafi haka? ko dan ina son ki shi yasa ki ka tsane ni haka Ko zuri'a baki son had'awa da ni? Atiyyaerh kin sani tun ina qarami na nake son ki, ban tab'a dainawa ba har girma na, umman ki da kanta ta nuna min irin b'arnar da ki ka dad'e kina min, ashe magani kk sha kar ki haihu? Ta fadan ta gani a jakar ki ta ɗauka ta je shago ta tambaya aka ce mata na hana haihuwa ne, shine ta zo ta tambayen da sanina nake barin ki kike tsarin iyali? To ina ma kk taba ciki bare mu haihu balle mu tsara iyalin? Ba zan iya zama da ke a haka ba, na hakura da ke Atiyyaerh tinda na kula ba Zaki tab'a so na ba har abada, qarshen qiyayyar da zaki min kenan ki nuna kyamar had'a zuri'a da ni, zan zauna har qarshen rayuwa ta ina nadamar son ki da nake yi, saidai zan miki godiya wataqila dama Allah ya kawon ke ne cikin rayuwa ta dan na samu shiriya, na gode maki da wannan qoqarin da ki Kai Dan ganin na zama mutumin kirki, Atiyyaerh ki je na sake ki saki d'aya, biyu, uku Atiyyaerh, bana son na sake ganin ki ki je ba zan iya zama da macen da take tsananin qi na ba a fuska ta nuna min ba komai," Atiyyaerh kusan suma ta yi a wajen,shi kuwa ya shige dakin ya dakko biro da takarda a irin littafan da take koyar da shi ya yaga ya rubuta mata ya wurga mata ya koma dakin ya saka sakata ya na kuka sosai. Ba tare da ta Iya furta komai ba, jiki ba kwari ta d'auki jakar ta da magungunan da ya zubar a qasa ta kama hanya zata tafi gida,Innar shi ta zo ta na mata magana bata Iya bud'e baki ta amsa ba tsabar baqin cikin da take ciki,Hajar Kan ta da ke son a tsani Atiyyaerh abun ya zo mata a bazata,cikin kuka ta koma gida. Rasheedah ta tarar zaune ta na Shan juice din orange, Suna kallo ita da Afrah, cikin zubar hawaye ta kalle ta ta zaro magungunan ta nuna mata sannan ta share hawayen ta da ke zuba ta ja majinar kuka ta ce, " Umma me na miki a rayuwa tane? Me  na tsare maki? Me kk so ki fad'a min na bar miki shi har abada? Ba zan iya daukar wannan baqin cikin ba, Ahmad ya sake ni saboda abinda ban san na aikata ba, ashe na koya mai karatu da rubutu ne dan ya saken da su, bana son shi amma na saba da shi, na saba da nunamin yanda yake so na, na saba da kalaman shi masu taushi, na saba da nuna min yafi sona sama dake, me zai sa ki lalata rayuwata? Wannan karon ba zan zauna da ke ba, ba zan bi wasiyyar Mummyna ba ke Kuma ki nakasa min rayuwa ta ba" Afrah kanta ya kulle, d'aukar takardar ta yi ta bud'e, zubewa ta yi a qasa kwaraf, hawaye na zuba mata, kallon Umman ta ta yi ta kalli Ablaerh "Meke faruwa ne, me ya sa ya sake ki daga komawar ki ko kin masa Wani abu ne kafin ki fito dama?" " Ki tambaye ta, ban san me na mata ba, ta je ta nunawa Ahmad maganin tsarin iyali wai ni nake sha, Ahmad na da son haihuwa sosai fiye da komai a rayuwar shi, gashi ta sa ya yanke hukunci cikin fushi ya yi min saki har uku a lokaci d'aya, na rasa wace iriyar qiyayya take min, yau ko 'yar tsuntuwa ce ni ba Zaki na mata wannan abubuwan ba Umma, ballantana a ce ni d'in jinin ki ce ko kina so ko baki so, idan Kuma kin gaji da gani na ne a duniya ki kashe ni kawai ki huta" Tana gama fad'a ta haye sama da gudu ta na kuka, Afrah qarasa zauna wa ta yi a wajen, ta saka kuka, tana kallon Umman su da take rarraba, ido, tabbas ita ta had'a komai, amma yanzu jikin ta ya yi sanyi,dan tina me zai je yazo da ta yi, in Auwal kuwa ya sani ta ta ta qare, sannan ga Yousuf da Sulaiman, tana tinanin nan ta ji sakkowar Ablaerh daga sama da ta hau cikin sauri da b'acin ran da bata tab'a nunawa a fuskar ta ba,ta dauki mayafin ta dake  qasa, ta koma gidan ta ta kwashi kayan ta a kwati, ta kama hanya...... [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼  WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 25: Duka ya sake kai mata ta goce, Atiyyaerh ce ta ya yi sauri ta shiga tsakiyar su, ta kwab'e baki kamar na me Shirin yin kuka, dan kuwa ji take kamar ta Saka kukan Sam bata ji dad'in abinda ya faru ba a tsakanin su,se take ganin kamar za a ga laifin ta, tinda sa'insa bata tab'a had'a su ba balle ya ce zai Kai wa matar Yayan nashi duka irin haka. "Dan Allah Bappan Umar ka yi hakuri ka rabu da ita, matar Yayah ce fa? In ka dake ta kamar ka d'au hannu ka daki Yaya ne fa, na san ba zaka iya dukan Yayah ba ai ko? To ka rabu da ita ta min qazafi ita da Allah,Allah baya zaluntar bayin shi sai dai su su zalunci Kan su" Kallo ya bita da shi Yana masifar son salon da take magana da shi a yanzun, ba qaramin burge shi ta yi ba, sai kace irin qananan yarannan masu shegen kyau haka ta koma,tsaki ya ja mai qarfi zai wuce sashen su dan in ya ci gaba da zama a wajen ba zai kyale ta ba,ya na juyawa ze fita ya ga Yayan shi a tsaye da Baba Garba, dafa kafad'ar shi Yayah ya yi yace masa su je ciki ya na son magana da shi,cikin rausaya kai na irin fushi fa nake dinnan ya bisu, Yaya kuwa kallon matar shi ya yi da Atiyyaerh yace su biyo shi, wani d'aki suka shiga, ba komai sai tabarmi, da ledar tsakar d'aki, sai littattafai, na Baba Garba , bayan sun zauna ne, Atiyyaerh ta miqe ta deb'o masu ruwa, suka sha suka yi mata godiya, sannan Baba Garba ya yi gyaran murya, ya yi sallama suka amsa,ya ci gaba da magana kamar haka, "Zancen gaskiya ban ji dad'in yanda mun fita dan mu je nemo maku  abinci amma mu dawo mu taddaku kuna fad'a ba, har da kai namiji a fad'an, kenan zaman ka a gidan bai da wani amfani in dai mata zasu na fad'a ka shiga? Ina son sanin abinda ya faru daga bakin ki Atiyyaerh kuma bana son ki boye laifin kowa, ki fad'an gaskiyar me ya faru," Sallama ta yi itama kamar yanda ta ga Baba Garba ya yi Kan ya fara magana,se suka amsa mata sallamar, sannan ta labartawa Baban komai, bata rage ba bata qara ba, wani kallo mijin Hajar ya bita da shi, Wanda yasa ta sunkuyar da kai, "Wato ke lab'e kike masu kenan, tinda da alama a maganganun da Atiyyaerh ta fad'a ya nuna ba yau din ne kawai kk lab'e masu ba tin da aka kawo ta kk masu labe'n, "  In ji Baba Garba da ya kafe ta da Ido ya na jiran jin me zata ce. Cikin jin kunya Atiyyaerh ta dan matsa gefe ta takure, lura da hakan ne yasa Baba gaggauta maganar da yake son yi, "Da ga yau zuwa har a bada bana son na sake ganin fad'a a gidannan, bana son a sake taruwa anan, ran kowa zai ya b'aci, matan su tashi su je a ci gaba da aiki, kuma bana son gaba ko qananun magana, ina fatan kun gane, ke kuma Hajar bata hakuri," kallon Atiyyaerh ta yi cike da tabbb wannan zan ba hakuri dinnan, amma mijin ta na daka mata tsawa se ta ba Atiyyaerhn hakuri, Atiyyaerh kuwa sanar da ita ta yi cewar ba komai Allah ya kyauta na gaba komai ya wuce,kowa ya amsa da ameen suka miqe suka fita, bayan fitar su ne Baba ya ma yaran shi nasiha, akan kar su kuskura mata su had'a su, su b'ata masu zumunci, komai zai faru kuma suna zurfafa tunanin su da binciken su kafin yanke hukunci, godiya suka yi sannan Yayah ya bama qanin shi hakuri for his wife's behavior, nuna masa ya yi ai ba komai ya wuce, sannan suka fita. Hajar ta rasa yanda zata yi dan ta dasawa mijin ta tsanar matar qanin nashi, dan haushin Atiyyaerh take ji matuqa,kowa na son ta a gidan, dan ita tin kan auren Ahmad ba son ta ake ba a gidan, balle yanzu an samu surukar so, tasan ita kam tata ta qare, duk wata hanya a 'yan kwanakin nan tabi amma shiru, dabara ce ta fad'o mata, tabbas tasan yaran ta basu da kunya da su zata yi amfani,dan in akwai abinda Muhammad ya tsana bai wuce wani ya tab'a masa yara ba...... ******************************* Afrah ce ke zaune a Parlour ta na kallo, Rasheedah ta fito ta ci uwar kwalliya,tinda ta aurar da Ablaerh hankalin ta ya kwanta, dan a zuciyar ta tana raya tana can tana fama da d'an wiwi, wataqilama ta sha duka yafi a qirga, ga faccala ga suruka, wahala goma da ashirin, murmushi ta yi da tai wannan mummunan tunanin, ta zauna a kujerar dake kallon ta Afrah da take daure fuska a duk sanda ta ga Mahaifiyar ta ta, dan tayi2 ta bar ta taje taga 'yar uwar ta amma ta hana ta, haushin hakan take sosai, , " 'Yar Umman ta me yake b'ata ranki ne? Sai na ga kina b'ata rai kwanakin nan, ko zaki gaida Mama da Abba ne?" Cike da zumudi Afrah tace, " Eh Ummana," Komawa kusa da Rasheedah ta yi ta zauna bakin ta ya qi rufuwa, " Ummana dan Allah daga nan na biya gidan Ablaerh na gan ta?" Wani mugun kallo ta buga mata tare da harara kamar idon zai fado qasa ta ce , "Ki mata uwar ki in kin je? Tashi in zaki gaida iyayena ki je in bazaki ba ki bari," Ta jaye jikin ta ta bar parlourn, daf zata shiga d'akin ta ja burki ta tsaya, ko me ta tina oho ta juyo cike da fara'a tace, " ki je amma kar ki dade, kin gano mana d'akin amarya da halin da take ci" Cike da zolaya ta fad'i hakan, ta shige d'aki abinta, miqewa Afrah ta yi cike da murna ta shige daki, shiryawa ta yi, tai kwalliyar ta da ta saba, ta fice, direct gidan Mama taje, Mama ta yi murna da ganin ta, ta tambaye ta ta je gidan Ablaerh kuwa? Ta ce yau zata, saqo ta d'akko mata daga d'aki, a leda biyu ta fiddo ta miqa mata,tace, "Wannan garin kayan qamshi ne dana niqa mata, komai zata ci ta saka ko a girki ko a abun sha, na zamanin nan da kuke hadawa da kayan marmari, wannan kuma ridi ne(kantu) na niqa mata shima, zata na sha da madara, sai wannan garin aya ne shima na niqa mata, zata iya sha da had'in kantunnan da garin ayar da kayan qamshinnan da madara, in kinje ki mata bayani dalla dalla, ciwon qafar nan ne ya ke damuna amma dana ji dama zan je na ganta,wannan Kuma turaruka ne da kayan ado naku na 'yan zamani, wannan kud'in Kuma ki bata ko zata buqata, maza ki je kun sha hirar yaushe gamo," Tashi Afrah ta yi cike da murna, ta ce ta gaida Abba in ya dawo ta fad'a masa in ji amaryar shi ta yi kewar shi sosai,yaushe zai je zance, dariya mama ta yi tace zata fad'a masa, bayan ta fita ne ta tsaida abin hawa ya maida ta unguwar su, direct gidan Ablaerh ta shiga, ta je Ablaerh na wanka, se ta shige har uwar d'aka ta zauna, sai kallon ko ina take, a gyare, ga kayan namiji nan aje wankakku a goge, da kayan Ablaerh shima a ajiye a wanke a goge, bata kawo komai ba tana zaune tana raba idanu ta jiyo dariyar Ahmad, yana tsokanar Ablaerh akan rashin sakewa da shi da take, kukan shagwabar ta yake koya, ita kuma tana murmushi, har yau ta kasa wani sakewa da shi sosai, ko dan ba soyayyar shi a ranta ne oho? da takalmin Afrah suka fara cin karo, wanda yasa Ahmad shiru cann yace, "Ko dai baquwa muka yi ne?" Atiyyaaerh ce tace bari ta duba to ta gani, Afrah dawowa ta yi parlor ta zauna, dan ta gama jiyowa ita da Ahmad ne suka dawo daga wanka, kunya duk ta kama ta, dama bata zo ba yau, ta rasa ina zata kai kunyar da take ji, bata son had'a ido da su, (kuji fa🤣🤣 saura ke Afrah kina layi) Atiyyaerh na ganin Afrah, ta tafi da gudu tana ihun murna ta d'ale ta, dariya suke ta yi tare, Ahmad ya leqo ya ga ita da wa? Sai ya ga Afrah, shima dariya ya yi yace, "Ashe babbar baquwa muka yi, mu da Muke Shirin  zamu bi ki har gida tinda kin yada mu kin qi zuwa," Cike da Jin kunya ta sunkuyar da kai tace, "Lokaci ne ban samu shi yasa, nike taya Umma aiki,.....malama d'aga ni ni kin yi qiba kin zo kin zaune min 'yar siririyar cinya ta" Qara zama Ablaerh ta yi tana dariya tace, " Allah ni ba wani qibar da na yi, ni sai nake ganin ma kamar na rage nauyi,ko ?" Ta kalli Ahmad, da sauri ya daga kai, "Sosai ma, aike baki da wani nauyi, tinda inna daga ki ji nake kamar baki fi a hada nauyin Umar da sadiq ba," Kunya suka qara ba Afrah, "Ni dai gaskiya in haka kuke a gidannan ba zan din ga zuwa ba, first kun fito wanka tare,second kunzo kuna min wani maganar manya anan," Dariya suka saka dikkan Su, Ahmad ya wuce d'aki yana tsokanar ta da cewa, "sauran ke yarinya," Atiyyaerh ce ta bishi,suka shirya sannan yace mata, "Ina son fita na je a gaisa da abokai Kuma an kwana biyu ba a had'u ba, yanzu har fushi suke da ni wai tinda na yi aure na yada su, Ina nuna masu na fi qarfin su yanzu ko Kiran nawa ma sun dena" Nan da nan idon Ablaerh ya kawo kwalla,gani kawai take in ya fita cikin abu biyu sai d'aya ya faru, ko ya je wajen matan da yake harka da su a da , ko ya tafi wajen shaye2, kamo fuskar ta ya yi ta kalle shi, ya sumbaci bakin ta a hankali ya ke lumshe ido Yana kallon ta, itama idon ta ta lumshe ta sauke akan nashi da har lokacin suke a lumshe,a hankali ya bude idon shi sosai ya sarqe shi cikin nata, "Na miki alqawarin ko kina tare dani, ko baki tare dani, na canja rayuwa ta,har abada bazan komawa sab'on Allahn da na bari ba,na bar aikata sab'o dan Allah ba dan kowa ba Ablaerh,ki sani ke mace ce d'aya tamkar da ba iyaka, kin isar min Kuma kin wadatar Dani daga duk wani hayaqi da kuma matan banza, kin shayar dani ruwan daya kauda min wadancan qishin, kuma har abada ba zan dai na jin qishi daga ruwan da kk shayar dani tin a daren farkon mu ba, Ina fatan za ki ci gaba da kashen qishirwa ta a dik sanda na buqaci hakan, dik da na San har yanzu ban da Wani cikakken matsayi a ran ki, amma ba zan gaji da gode miki akan hakuri da ni da ki ke ba" Murmushin gamsuwa da kalaman shi ta yi sanna tace, "Allah ya Karen Kai ka je lafiya ka dawo lfy, ka kula da kan ka, in lokacin sallah yayi a duk inda kk ka tashi kayi, sannan lokacin cin abinci in yayi ka dawo gida ka ci" Sumbatar shi ta yi a kuncin shi dika biyun, shi kuma ya mata a goshi da lips, suka fito, Afrah kan ta na qasa, dan d'akin nasu ba wani sirri ana Jin abinda suke tattaunawa akai,Ahmad Kuma sallama ya wa Afrah cikin barkwanci har ya fita yana tsokanar ta akan yanda take Jin kunyar shi,bata ce masa komai ba,yana fita ta sauke ajiyar zuciya, "Ba zan sake zuwa gidan ku yana nan ba, wannan sai kun qarar wa da mutum kunyar shi," Dariya Ablaerh ta yi, gaisawa suka yi a tsakanin su,se Kuma suka hau hirar yaushe gamo, ta bata saqon Mama, kwalla ce ta cika mata ido,tana kewar su sosai, musamman Yayah, gashi Afrah ta fad'a mata tinda ya tafi ko waya bai sake wa kowa ba, gwanda Sulaiman ya dawo sau daya shima, kuka take yanzu kam, dan gaba d'aya sai ta ji kewar su da take qoqarin dannewa kullum tana taso mata, har Rasheedah dake azabtar da ita dai sai ta ji tana son ganin ta,balle Abban su da ke son ta,share mata hawaye Afrah ta yi tace, "Taso muje na gaida surukan ki, in ce dai ba mai takura maki a gidan?" D'aga mata kai ta yi ta bata labarin ya suke mata a gidan, sai dai ta boye mata halin faccalar ta,farin ciki ne ya kama Afrah da jin hakan, ta miqe suka shiga wajen Inna, Baba na nan duk suka gaisa, sannan ta kaita wajen Hajar, sun gaisa ba yabo ba fallasa, suna komawa bangaren su Afrah tace, "Anya wannan matar Yayan naku na son ki kuwa Ablaerh?" Ce mata ta yi, "Tana sona mana, me ki ka Gani? in ma bata so na to ni dai ban sani ba," "To in ma bata nuna maki ba to tabbas bata son ki, sai ki kula," D'aga kai ta yi tai murmushi, hira suka sha abun su kamar kar su rabu, daga baya Afrah ta yi mata sallama zata tafi, da kuka suka rabu dan basu san yaushe zasu sake haduwa ba, bayan ta koma ne Rasheedah ta ke tambayar ta ya taga Ablaerh, cike da zumud'i ta fada mata komai, ran Rasheedah baqiqqirin dan haushi ba haka taso ba, amma bata ce komai ba ta shige kitchen tace Afrah ta je ta taya ta aiki. Yau tin safe Atiyyarh ta shirya take gyara gidan, har bangaren su Inna,  bayan ta gama sharewa da gyarewa ne, ta d'ora girki, Ahmad na maqale da ita duk inda ta yi, tayi2 ya ma je d'aki ya jira ta gama yaqi, sallama wata budurwa ta yi ta shiga gidan, daidai lokacin Afrah na tankad'en gari, kallon ta Ahmad yake kamar zai kife qasa, yarinyar siririya ce ta sa ka dinkin da ya d'ame ta sosai, yan qananun bootyn ta sun sha d'ama da kyau, tana tafe tana kada su, tana tauna cingam, sai d'an qaramin mayafin ta dake rataye a kafad'ar ta, fuskar nan har ta qone  tsabar shafe2, qafar baqaririn da hannayen, haushi ne ya kama Ablaerh, ko da bata son shi ai mijin ta ne, a hankali ta zame zanin ta cinyar ta da take zaune ta sha mai ta yi luwai2 ta bude, ko mace ta kalla sai ta yaba, tari ta yi sosai kamar irin ta kware d'innan,nan da nan Ahmad ya dawo da hankalin shi kanta da sauri, aiko yana arba da cinyar nan a bud'e sai ya daburce, ruwa ya deb'o mata a randa ya bata, d'akin Hajar baquwar tayi, tana shigewa Atiyyaerh ta bata rai tace, "Ni ka tafi d'aki nace, inna gama ai zan shigo ko," Nan take ya gane me take wa hakan, dariya ya quntse yace , " To ina jiran ki kar ki dad'e," D'aga masa kai ta yi ran ta a d'an b'ace ta rufe cinyar ta da ya qurawa ido, ta d'an murguda lips dinta, dariya ya saki yanzu kam ya kasa riqewa, bayan ya shiga d'akin ne ya fara taka rawar murna, Atiyyaerh na kishin shi, tsalle ya yi ya d'ale gado, yana ta birgima kamar qaramin yaro, Allah, Allah yake ta shigo........ *Kuna tinanin Ablaerh na son shi kuwa? Ko dai kawai tai haka ne don hana mijin ta kallon wata?* [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN .BY HAERMEEBRAERH Page 27: Gidan Mama ta samu abun hawa ta hau ta nufa, kuka ta saka kanta a cikin mayafin ta ta ke ta yi ba qaqqautawa har suka isa, tana fita ta miqawa mai adaidaita sahu 200, wanda zai bata canjin 150,amma ko canjin bata tsaya karb'a ba ta wuce ciki, shi kuwa Mai adaidaita se magana yake mata ba ta kula shi ba ta fada gidan, da kuka ta shiga, Mama dake bakin pampo tana wanke alayyahu ta isa wajen ta da sauri tana gyara zanin ta a rud'e ta ce, " Lafiya Atiyyaerh ki ka shigo ki na kuka haka ,Meya faru, me aka miki, ke da uwar taki ne ko Kuma mijin?" Mama ta jero mata wadannan tambayoyin. Bata kula Mama ba ta sa kai ta wuce d'akin da tin asali yake mallakin Iyayen nasu, in tazo nan take sauka, tana shiga ta danna qofar ta rufe ta da  jam lock, Mama tsaye ta yi ta yi ta bugun qofar tare da Kiran sunan Atiyyaerh amma ta qi budewa, kukan ta ta zauna a gado ta na yi, sai da ta ji ana kiran sallar magrib ta miqe tana had'a hanya saboda yanda take Jin kan ta kamar zai fashe dan ciwo, ga zuciyar ta dake mata wani irin zafi wai yau ita aka yi wa saki har uku, dika dika nawa take? Shekarun ta ba zasu wuce ashirin da biyu ba,an Maida ta qaramar bazawara a banza a wofi,alwala ta yi tai sallah, sannan ta yi azkar na yamma kamar yanda ta saba, karatun qur'ani ta fara rerawa da ka har aka kira sallar  isha'i, sannan tai sallah ta silale a wajen ta kwanta ta na lumshe ido,ji ta yi mama na magana cikin Shan majina ta na fad'in, "Eh tana ciki, tin da ta shigo da kuka ta zo ta rufe kan ta anan bata bude ba na yi Kiran na yi magiyar amma ta qi bud'ewa,amma dai na jiyo ta na karatun qur'ani, sai kuma yanzu naji shiru ba alamar motsi, Ina Jin tsoro Abban su dan Allah ko b'alle qofar ne ka sa a yi" "iKon Allah to me ya same ta haka da girma har ta kasa tsayawa ta sanar da ke damuwar ta, kin tabbata bata ce miki komai ba ta wuce? Saboda ba halin Ablaerh bane irin haka" "Haram bata ce min komai ba ta wuce ni" "Ikon Allah, Allah ya sa lafiya to,muje na ji," Hannu ya daga da nufin kwankwasa qofar ya ji tace, "Ni ku barni kawai, ba zan magana da kowa ba yau, i just want to be alone, sai gobe mayi magana, dan ko na fito ba zaku gane komai daga waje na ba," kuka ne ya ci qarfin ta, juyawa Abba ya yi zai tafi,Mama ta kalle shi, itama idon ta ya cika da kwallah ta ce, " Yanzu tafiya zamu yi mu barta? Abban su ya kamata mu tsaya mu ji meke damun ta, in mace tace a kyale ta ba wai tana nufin hakan bane,tana buqatar kulawa, ko mai zata ce hakuri za ka yi har ta daidaita,mu qara gwadawa," Komawa ya yi ya fara mata magana, " Haba yar gidan Abban ta Auwaluuu,ki bud'e ki fad'an me ya same ki, me aka miki, na maki alqawarin wannan karon ina bayan ki, ba zan bari kowa ya cutar da ke ba, ina tare dake," Tana jin haka ta ja jikin ta ta jingina da qofar ta kwantar da kan ta a jiki hawaye na ci gaba da zuba, a hankali ta ce, " Abba kayi alqawarin kana bayana fa kace a wannan karon,ka tabbata komai na fad'a ina so zaka min shi?" "Na yi alqawari,domin na san tabbas cutar dake aka yi da yawa abinda ki ka yi d'innan ba halin ki bane,baki tab'a hakan ba," Miqewa ta yi a hankali ta bude qofar, Mama na ganin ta ta nufe ta ta rungume ta,ita kuma ta ci gaba da kukan ta,cikin kukan ta ce musu, " Mama Ahmad ya sake ni sakin wulaqanci saki har uku a lokaci d'aya ba tare da haqqina ba, ban masa laifin komai ba, Mama Umma Rasheedah ce ta min sharri a wajen shi ya sakeni,saki Uku, Mama na saba da Ahmad, koda bana son shi, me na yiwa Umma Rasheeda da bata so na,in wani tarihi ne da ni da yasa ta tsane ni ku sanar dani, in wani abu ne take so dana mallaka ku fad'a min shi na bar mata shi bana son abun, na tsane shi, Na shane shi, bana buqatar shi in dai zai ja min tsana irin wannan a wajen Ummana," Kuka take kamar wadda akai wa sabuwar mutuwa, Mama ma kukan take, Abba ne cikin tausayawa ya kamo ta suka zauna bakin gadon ya ce, "Atiyyaerh bari na tina maki ma'anar sunan ki, ke takwarar Maimunatou ce,Mahaifin ki ya sa ka maki suna Atiyyaerh ma'ana kyauta, Mahaifiyar ki ta sa maki Ablaerh, wato mai kyau, wadda kuma aka tsara wajen halitta, dukkan nin su basu yi qarya ba, qiyayyar da Rasheeda ke maki ba komai bane illa hassada, hassada kuwa mummunan ciwo ne mara kyau,in ya kama mutum maganin shi na wahala, dan haka wannan ciwo ke damun Umman ki, fatan mu mu zama masu mata addu'a Allah ya yaye mata, ba  akan ki ta fara ba, ta fara da qin mahaifiyar ki ne abun ya dawo kan ki, ba abinda kk mata, ba abinda kk riqe mata, ina fatan kin gane, dan haka ki kwantar da hankalin ki, game da sakin da Ahmad ya miki, ina mai baki hakuri, da fatan Allah yasa hakan shine yafi maku alkairi da ke da shi" A da zuciyar ta cike take da qunci, amma yanzu komai sai ta ji ya kwaranye mata se abinda ba a rasa ba na kewar Ahmad, ta samu sauqin baqin cikin ta,cikin nutsuwa ta musu godiya, sannan tace, " Abba Mama dan Allah zan zauna da ku ba zan koma wa Umma ba, zan zauna nan har Daddyna ya gaji da zaman can in ya tina yana da 'ya ya dawo,har ya...," Kasa qarasawa ta yi saboda kukan da ya sarqe muryar ta, bata son tina wai tana da uba amma ya banzatar da ita sabida wani shirmen dalili, tabbas ba dan tana son shi ba,tana son ganin shi da ta yafe shi, da ta manta itama tana da uba, kamar yanda ta dauka shima.ya manta da ita, hakuri su Abba sukai ta ba ta, Mama ta debo mata tuwon shinkafa,miyar taushe, ta sata gaba, da kyar ta iya ci, dan ji ta yi gaba d'aya bata son cin komai, bayan sun d'an taya ta hira ne suka bata waje, ta koma tai addu'ar kwanciya bacci ta shafa a jikin ta ta kwanta, baccin kasa d'aukan ta ya yi, sai tinanin Ahamd ne ya cika mata zuciya, ko me yake yi a yanzu? Ko su Baba sun san ya sake ta? Allah shine masani a haka bacci barawo ya dauke ta. ******************************** Da asubar fari Baba Garba da Yayah suka zo gidan Abbah, inda Suna buga qofar gidan tare da sallama daga baya  Auwal ya zo shima, nan fa aka hau gaishe2, da jajanta wa juna abinda ya faru, can nesa da su kad'an suka ga Abba na tahowa ya dawo daga masallaci,yana isowa ya miqa masu hannu aka gaggaisa, sannan ya bud'e gidan suka shiga, parlour suka tafi dika, bayan sun zauna ne suka qara gaishe2, Baba Garba ne ya fara magana ya ce, " Malam Hamza, bayan mun dawo gida jiya wajen magrib, muka ga Ahmad ba yanda yake,sai an kwantar se an tayar sai da muka kai shi asibiti, jikin shi zafi saboda zazzabi, sai sambatun kiran Atiyyaerh yake,yana fadin ya cuci kanshi,ya yanke hukunci cikin fushi, da sauran kalaman nadama, da na matsa mai da tambaya ya sanar da mu duk abinda ya faru, mahaifiyar shi yanzu haka tin jiya take kukan mummunan aikin da ya jiqa mana, yarinyar nan ta zama 'ya mace d'aya da bamu samu ba a tsakanin mu, ni da mahaifiyar su, tinda ta je ita ke mana komai, ita take taya mahaifiyar su aiki, ta zama abokiyar hirar ta, girmama ni take kamar ni na haife ta, ga Yayan su nan, bata taba gaida shi a tsaye sai ta durqusa, yaran shi duk rashin kunyar su sai da ta shanye har ta sa suka zama yaran kirki, tin jiya suma suke ta neman ta da suka ji abinda ya faru kuka sukai tayi, suna a dawo masu da Aunty Amaryar su, ba munzo bane dan mu bada hakuri a maida ta ba, domin mun san saki uku ne tsakanin su, munzo ne dan bada hakurin abinda yaro ya aikata mara kyau, a yi hakuri, a yafe mashi, tabbas ya yi rashin hankali, da rashin hakuri, wanda ya jefa kan shi a nadama da dana sani, kuma muna fatan zumuncin mu zai ci gaba ba zai yanke ba," " Wannan haka yake Malam Garba yaro ya yanke hukunci cikin fushi, wanda ya sa su gaba dayan su a tashin hankali, sai dai mu yi fatan Allah ya kiyaye gaba, ya sa hakan shine mafi alkairi," In ji Abban su Rasheedah, Auwal kuwa ya ce, "Nima Dake ban dawo da wuri ba sai qarfe goma na dare, saboda wata kwangila da kamfanin bulo na ya samu kwanan nan, ko da na dawo ba a Sanar da ni da wuri ba, se da na nemi Afrah ban ganta ba, Ina shiga d'aki na gan ta tana kuka, da na yi bincike se na ji mummunan labarin, na so zuwa tin a daren amma na bari zuwa yau da safe na zo, to dama rayuwa bawa baya wuce qaddarar shi, muyi fatan yanda muka roqi auren ya zama alkhairi sakin ma ya zama alkhairi,Allah ya had'a kowa da rabon shi na alkhairi" Amsawa dika suka yi da 'Ameen" sanan suka miqe da niyyar zasu tafi, zasu wuce asibiti, wajen Ahmad, Auwal ne ya ce "Wanne asibiti ne inna tashi nima zan zo duba shi," Fada masa suka yi sannan sukai sallama suka tafi, bayan sun zauna ne Abbah ya kira Mama da Atiyyaerh, suka zauna, kan ta a qasa dan ganin Abban nata cikin damuwa, da alama shima bai yi bacci ba, gaida shi ta yi sannan ta gaida Abbahn su Rasheedah da Maman, bayan sun amsa ne Auwal yace, "Ablaerh ki yi hakuri da wannan mummunan abu da ya faru,jiya na dawo gida na tadda mummunan labari akan abinda ya faru, wanda ba kowa ne sila ba illa Rasheedah, na zo ne domin na baki hakurin komai da take maki, daga wannan lokacin inshaa Allah komai ya qare ba zan sake saka ido ta b'ata rayuwar ki ba, dan haka nake baki hakuri da ki zo mu koma gida," Kan ya qara bude baki ta riga shi da sauri ta ce, " Abbana ka yi hakuri,ba zan iya komawa qarqashin inuwa d'aya da Umma ba, irin qiyayyar da take min ban zaci ta kai haka ba, sai jiyan, na ci alwashin ba zan sake zama guri d'aya da ita ba, in kuwa wannan karon kuka kafe sai na zauna da ita dan cika wasiyyar Mommyna to tabbas zan bijire maku, zan iya barin gidan nan akan na zauna da ita," Ta qarasa maganar cikin kuka, wanda gaba d'ayan su saida suka tausaya mata, "Shikenan yanzu magana ta qare ba inda zata tafi, ina nan tare da ita, nima ina son kasancewa da ita tin fari, kawai dan an fi qarfina ne yasa na hakura, amma tin fil'azal da anbi tawa da Atiyyaerh ma bata zauna da Rasheedah ba a wannan qiyayyar da take mata, dan haka mu yi fatan alkairi a rayuwar ta kawai ta ci gaba da zama nan" "Haka ne, kema kin kawo hanzari mai kyau Hajiya, dan haka abinda kk fada yayi daidai ta ci gaba da zama anan kawai," Abba Auwal ba haka yaso ba amma shima addu'ar fatan alkairi yayi suka ci gaba da tattaunawa da Abbah akan matsalar Rasheedah,anan ya karya sannan ya tafi,kafin ya Isa gida se da ya tsaya ya biya asibiti wajen Ahmad,ya tadda Ahmad cikin mawuyacin hali, duk ya fige kamar wanda ya yi ciwon watanni, bayan ya gaida shi ne ya wuce gida, kwata2 ya dauke wa Rasheedah wuta, baya kula ta baya cin abincin ta, baya komai da ita na ma'a malar aure, dan gaba d'aya ta fice masa a rai, Afrah ma ba kula ta take ba banda gaisuwa, sai ta qarata zage2n ta da fadace2n ta amma ko mai ba zata ce ba, Sulaiman a satin ya dawo, lokacin da ya ji labarin kasa cewa komai ya yi ya qurawa mahaifiyar tasu ido, saida jikin ta ya hau kyarma, ba dan komai ba dan bata tab'a ganin fushi da tsana a idon d'an nata ba irin wannan lokacin, tinanin ta ya kai kan me Yousuf zai ce kenan idan ya ji???? *BAYAN KAMMALA IDDAR ATIYYAERH* Atiyyaerh na zaune a Parlour ta na hutawa  bayan kammala aikin gidan da ta d'auke wa Mama tin zuwan ta, zaune take cikin Kwalliya mai kyau da d'aukan hankali wadda ta jima ba ta yi irin ta ba, haka kawai yau ta ji ta na sha'awar yin Kwalliya, wayar da Abba ya sai mata take dannawa,wani qamshi ne mai dad'in shaqa da kwantar da hankali ya daki hancin ta, sannan sallama ta biyo baya da muryar da ba zata tab'a mantawa da ita ba a rayuwar ta, d'aga kan ta ta yi a hankali idanun su ya had'e dana juna, sun dad'e suna kallon juna kafin ya katse kallon da cewa, "Ba za ki min iso ciki bane, anan zaki bar baqon naki?," Cike da jin kunya ta kauda kan ta daga kallon shi, ta yi masa nuni da ya shigo, miqewa ta yi ta shiga ciki,shi kuwa ba abinda yake face bin kyakkyawar surar ta da kallo,wani yawu ya hadiya da qarfi sannan ya ce, " Allah ka mallaka min qanwar nan tawa a matsayin matar aure na a wannan karon" Dawo wa ta yi sanye da mayafin da ya rufe jikin ta yanda ya Kamata,hannun ta d'auke da farantin da ta d'ora jug din da ta zuba zob'on  da ta had'a ba jimawa Wanda ya sha kayan qamshi da cucumber da abarba, sai lemon zaqi da na'ana'a, ta aje masa a gaban shi,sannan ta sanar da Mama zuwan shi ta dawo, zama ta yi ta gaida shi, ya amsa idon shi kamar zai fad'i qasa Dan kallon ta, " Yah Kallon fa? " Cike da shagwaba ta fad'i hakan shi Kuma cikin kashe murya ya ce, " Ya ba zan kalli dimond dina ba, sannan kina Wani abu kamar baquwa? Ko gaisuwa ma Babu, any way na yafe gaisuwar, kallon ki ma da na yi ya wadatar da ni,na San ke Baki ma yi kewa ta ba, dama wanene ni a wajen ki da Zaki kewa ta? Ni kuwa kin ga kullum cikin kewa da tinanin ki nake,na jima rabona da na saki a Ido na,ke Kan ki yaushe rabon da ki ganni? Tin lokacin da na dawo na tadda daddad'an labarin nan,na wuce kaduna wajen abokina, na hau fafutukar neman aiki, har Allah yasa na dace, a kullum sai na yi waya da Afrah na ji ya kk, takan ce min tazo kun yi hira kala kaza da kaza, nai ta jin dad'i, saboda so nake na dawo da kwari na Ablaerh bana son rasa ki wannan karon,akwai sanda na sa ta ta yi min recording muryar ki inda kk ta dariya akan labarin miyar da ki kai wa Mama mai yaji, na ji matuqar dad'i kasancewar fara'ar ki ta dawo, na qudurta dawowa tin a lokacin to kamfanin da nakewa aiki, na sarrafa kayan gine2 ba zai ban damar tafiya daga fara aiki da su ba,sai da na yi wata hud'u da su sannan na dawo, tinda na dawo na so zuwa amma ina tsoron me zaki ce game da buqata ta a wajen ki," Cikin sauri ta daga kan ta tace, "Wacce buqata ce zata tsorata ka zuwa waje na Yayah, kasan yanda na yi kewar ganin ka kuwa, a lokacin da komai ya faru na so kana nan, nasan zaka ban kafad'ar ka na koka baqin ciki na amma baka zo gare ni ba Yayah , nasan zaka min tattausan lafazin ka domin na kwantar da hankali na ammma shiru ba ka zo gare ni ba Yayah Babu kai babu dalilin ka, Yayah na zata kai zaka taimaka ka dawon da farin cikina amma haka ka tafi ka barni ba wata kulawa Daga wajen ka, sannan yanzu ka zo da wata buqata a gare ni?" Kuka take sosai dan tinawa da yanda ta tsallake ramukan baqin ciki ita d'aya ba mataimaki a gare ta, hawayen ta duk ya bata mata kwalliyar da ta yi, tashi ya yi ya zauna kusa da ita, ya goge mata fuska, sannan ya dafa kafad'ar ta yace, "Ablaerh my dear ki daina kuka,ki yi hakuri ki yafewa Yayan ki, na sani ni Mai laifi ne a wajen ki,amma inshaa Allah komai yazo qarshe, ni zan maye maki gurbin duk abinda ki ka rasa a rayuwa, Ina fatan na zama *JARUMIN KI* " " Yayah na san da hakan sanin cewa *KAI NE JARUMI NA* ne yasa na ji takaicin rashin ganin ka a lokacin da nake da buqatar ka,babu Kai babu Daddy na, Yah ka taimaka min Daddy ya dawo gareni na kasa yin fushi da shi dik yanda zuciya ta ta so tsanar shi sai na kasa, ka taimaka min yayah " "Share hawayen ki nace ai ko?  yanzu gani na dawo, kuma ba zan sake barin ki ba ko mai rintsi komai wahala, ina tare da ke, ina fatan zaki qarawa Yayan ki matsayi ya tashi daga Yayah ya koma masoyi?" Wata kunyar shi ce ta kama ta ta miqe ta shige ciki da gudu, a hanya suka had'u da Mama, mama ta ce, "Ke meye haka zaki ture ni na fadi?" Bata kula ta ba ta shige d'aki ta rufe ta jingina da qofa, tana ajiyar zuciya, tare da murmushi,ta dafe qirjin ta dake bugawa da sauri da sauri, hawayen ta ta share ta ce, " Oh Ya Allah kasa Yayah ya zama farin cikin rayuwa ta, nima ina son ka Yayana na baka dama ka zamo masoyi a gare ni," Da qarfi ta fada gado ta hau juyi tare da murnar kalaman shi a gare ta, bayan ya gaida Mama sun tab'a wasanni na jika da kaka ya yi mata sallama ya tafi, dan yasan yanda Atiyyaerh ta tafi ta na Jin kunyar shi ba zata dawo ba. ****************************** Zaune suke dikkan nin su a parlour kowa da abinda yake yi, Muryar Yousuf ta karad'e parlourn da.... " Abba game da maganar na nemo mata da ka min ina son sanar da kai cewar  Atiyyaerh itace macen da ta kwanta min a raina Kuma nake son na aura," a zabure Rasheedah da ke jefa inibi a baki ta hau tari sakamakon Wani guda d'aya da ta jefa Dan ta tauna ya wuce mata maqoshi da kyar ya fito, cikin Maida numfashi ta ce, "A ina za a yi hakan, a wanne gidan, sai dai bayan raina kai da ka auri wannan yarinyar Yousuf na fad'a Maka, gwanda ma tin wuri ka janye wannan banzar maganar mara amfani da ka yi " "Sannu uban shi me Iko da gidan Baki d'aya, Kuma in ji waye ya ce ba zai auri Atiyyaerh ba? Ke? To in kece dan Allah yanzu ma ki fad'i mana, mu kuma ana arba'in din mutuwar ki zamu d'aura auren Yousuf da Maimunatou,shashasha kawai, Kai Yousuf ka kwantar da hankalin ka wannan karon da kaina zan tsaya Maka sai ka auri Ablaerh" Miqewa ya yi ya shige d'aki,ya bar Yousuf  da sauran 'yan uwan shi a wajen, yana ganin zata fara surutu ya miqe shima ya yi dakin su, fad'a take kamar zata ari baki, ba mai kula ta "To a yi mu gani, in dai ni Rasheeda ina raye d'an dana haifa ba zai aure ki ba Ablaerh... [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼        WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 28: " A gaskiya ba zan lamunci abinda ka ke shirin aikatawa ba na fada maka,ta ya za a ce d'an nawa ya auri ragowa yana saurayi? Ba zai yu ba ba zan lamunta ba, saboda nima ina da haqqi akan shi, ni nai cikin shi wata tara ba tare da kowa ya taya ni da riqon shi ba, ina da 'yancin zabar ma d'ana abinda ya fi dacewa da shi,"   "Zaki matsan a hanya ko sai na make ki? Domin ke ba matar da za a ragawa bane saboda qima ko daraja, dan baki tare da su, in ba a taya ki daukan cikin shi ba ai bake kikai wa kan ki cikin shi ba ko? Sannan abubuwan da kk ci a cikin nashi da kulawar da kk samu ko da kudin asibitin da aka biya na haihuwar d'an naki iyayen ta ne suka biya in kin manta na tina maki butulu, matsan ni malama ina da abin yi," Matsawa tai tana qunquni, dan rabon da ta ga ya b'ata rai haka ta manta,amma wannan karon komai da gaske yake d'aukan shi. Afrah ce ta shirya ta nemi izinin Abban ta zata gidan Mama, amince mata ya yi tare da bata dubu d'aya,yace ta tsaya a hanya ta d'an sai masu ko da lemo ne, godiya ta yi,ta fice, ta dad'e a bakin titi tana jiran abun hawa kafin wani matashin saurayi, mai matsakaicin kyau da haske ya tsaya a gaban ta, motar shi kadaran kadahan ba wata me tsada bace, shi ba talaka bane da alama kuma ba mai kudi bane, sallama ya mata ta kauda kai gefe tare da amsawa a hankali, qara gaba shima ya yi inda ta tsaya ya sunkuyar da kan shi daidai tsahon ta ya ce, " Malama Afrah bismillah mana, kina tsaye rana zata maki illa ai" Cike da mamakin sunan ta da ta ji ya ambata a bakin shi ta matsa gefen shi tace, " Malam ina ka sanni?" " ke ba qanwar Sulaiman bace? Sulaiman abokina ne ai, tare mukai makaranta, muka gama, naga hoton ki ne a wayar shi, ba Yousuf ne yayan ku ba, kuma kina da qanwa ne ko yaya me suna Ablaerh?," D'aga masa kai ta yi ta d'an murmusa lallai wannan ya san ta, bud'e mata motar ya yi ya ce ta shiga, "Na gode matuqa, amma gaskiya ba zan shiga ba, na ji dad'in tayin da ka min, ba ya daga cikin dacewa mace ta shiga motar wanda ba muharramin ta ba a wannan zamani da muke ciki, domin kuwa kamar misalin kasancewar su ne a d'aki d'aya na ukun su zai iya zama shaidan," Ba qaramin burge shi ta yi ba, cike da jin dad'i ya bud'e motar ya fito, adaidaita sahu ya sama mata, ya biya kud'in, ta masa godiya, ta tafi. Tin a hanya take tunanin fuskar ajnabin da bata tambayi sunan shi ba, data tuna murmushin shi sai itama tai murmushi,  a haka suka isa ta sauka ta shiga, tana shiga ta tarda Mama da Atiyyaerh, Mama na wanke wa Atiyyaerh kai da kalkashi, da kwai, tare da man shampoo, sai dirza kan take tana mitar, "Gashi sai uban yawa da tsaho baza ki gyara ba, gashi nan duk amosali ya danqare maki akan ai, in ba dan kina tare da tsohuwar da kullum ki ke tsokanar na tsufa ba wa zai baki wannan maganin amosalin dake danqare akan ki? " "Kaiiii jama'a dad'i na dake mita, " Dundu Mama ta d'ima mata,ta kuwa gantsare tana kukan shagwaba?dariyar Afrah ce ta sa su duba inda take tsaye ta na Jin dramar su duk da idon Ablaerh a rufe yake ta san ita ce, oyoyo ta fara mata, itama ta wuce daki ta yi ta cire kayan ta ta daura zani, tazo ta zauna a kujera 'yar tsuguno ta gaida Mama ,bayan sun gaisa ne tace, " Mama nima a wanken da karkashin, kaina se ya yi ta qaiqayi ya na kuma karyewa," "To taho, kk min raki kisha d'ima kema, ai rashin sani ne, wanke kai da karkashinnan yana da amfani sosai, gyara kai yake da qarawa gashi tsaho, sannan ya yi maganin amosali, kuma yana sa laushin gashi," Bayan sun gama wanke kai ne, suka tafi d'aki suka fara drying gashin su da hand dryer, suka mulke shi da man kwakwa, mai had'in man rid'i da na alayyadi, da man habbatussauda, sai man zaitun, ba qaramin kyau gashin su ya yi ba se sheqi yake ya yi baqi sosai, ga santsi da yake, Ablaerh ce ta nade shi cikin shower cap ta shiga wanka, ta dirje jikin ta sosai, tare da shafe tsakanin cinyoyin ta da Alovera, dan ya yi haske, ( shafa alovera, lemon tsami, lemon zaqi, kindirmo asalin mai kyau, tomeric da lemon zaqi ahade, yana saka tsakanin cinyoyi ya yi haske, ko kuma duk inda yake baqi a jikin ka kana son ya yi haske mai kyau in ka shafa duk d'aya daga ciki ya yi kamar 30mnts yana haskaka wajen, amma tomeric da lemon zaqi hada su ake a shafa) fes ta fito kamar a dauke ta a gudu, Allah ya ma Atiyyaerh kyau mai ban sha'awa, sannan ga gyaran jiki natural da Mama ke mata kullum, Afrah ta gani tana ta murmushi ita daya, " Hmmm who is the lucky guy?" In ji Atiyyaerh na tabbatar da wannan Murmushi na tinanin masoyi ne Dagowa ta yi da idon ta masu kyau ta kalli 'yar uwar ta ta, ta sake sakin murmushi bata ce komai ba, itama zuwa ta yi ta qara watsa ruwa, dan jikin ta ya dan baci da kumpa, bayan ta fito ne su ka yi kwalliya,sannan Afrah ta nisa tace, "Ammm game da abinda kk tambaya dazu ki ka ji na yi shiru banda amsar da zan baki ne, domin ban san me zance ba, zan fada maki how stupid i am to fall in love with a stranger? Ko zan fada maki cewar ko sunan shi ban sani ba? Amma shi yasan sunan mu ya san Yah Sulaiman," Cike da murna, Atiyyaerh ta daka tsalle, ta rungume ta, , " U ar not stupid my love, so haka yake, banga laifin ki ba, fatan mu ubangiji yasa shine mafi alkairi a rayuwar mu, baki daya, ki fad'awa Yah sulaiman cewar kin ga abokin shi har ya taimaka kk samu abun hawa da sauran su ya mai godiya kinga in ma ya manta ki ai ya tuna ki, dan ba zamu bari ya kufce mana ba yanda naga alamar son shi a tare dake," Murmushi Afrah tai sosai daya bayyana haqoranta masu kyau, suna haka Mama ta shigo suka ci gaba da hira da ita, Afrah a gidan ta kwana dan kwata2 yanzu bata son bud'e ido ta ga Rasheeda, da ana canja uwa da ta canja ta ta amma ba a yi sai dai tai mata addu'ar mai canja zuqata daga mummuna zuwa kyakkyawa ya canzawa Umman nata halayen ta. Tin safe suka gyarawa Mama gidan Afrah ta shirya komawa gida, a hanya ne Ablaerh na dawowa daga rakiya Tsohon saurayin ta Hassan ya tare ta, tayi mamaki sosai daya gane ta, gaisawa suka yi ya fad'a mata yana sane da mutuwar auren ta, yasha wahala kan ya gano inda take, yau dama ya so zuwa gaida Kakan nata ya gabatar da kan shi, sai kuma gashi sun hadu, "Mu qarasa gidan dan na kula maganar ba ta tsaye bace ko malam Hassan?" " wannan haka yake , bismillah na qarasa dake," " A'a ba damuwa, ai mun kusa,ba sai na shiga ba, muje kawai," A gefe ya yi parking d'in motar tashi sannan ya kulle ya bi bayan ta...... *Hahaiiiii casssssss, Malam Hassan samawa kan ka lfy muna da miji a hannu*🙄 [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼       WRITTEN    BY HAERMEEBRAERH Page 29: Parlour ta bude mishi ta mai izinin shiga sannan ta shiga ciki ta sanar da Mama, kafin ta d'ebi zobo mai sanyi da meatpie da suka yi ita da Afrah ta kai mishi, sai da ta koma ciki ta d'an bashi waje sannan ta dawo, ya d'an ci kad'an dan shi damuwar shi bai wuce tazo su yi magana ba, ita kuma ta rasa ta yanda zata b'ullo masa, zaman ta keda wuya Yousuf ya yi sallama ya shiga, ganin baqo kuma ga Dimond d'in shi a zaune ta sha kwalliya ya sa ya yi kicin2n da rai, fuskar nan kamar bai tab'a dariya ba, hankalin ta in ya yi goma ya miqe tsaye, a daburce ta furta, " Sasssannu.. da zuwa Yayah," ko kallon ta bai ba ya amsa, idon shi na kan Hassan, yana jiran qarin bayani, daga tsayen ya harde hannayen shi a qirji yana kallon su, "Ammm dama wannan shine Hassan.." Se kuma tai shiru, Yusouf yace , " Ehemmm? Sai yazo yin me?" Hassan ne ya miqe tsaye ya je ya ba ma Yousuf hannu dan su gaisa, kamar ba zai miqa masa nashi hannun ba, ya miqa mai  ya koma d'aya daga kujerun parlourn ya zauna ya hard'e qafa, qasa ta yi da kan ta, da a ce zasu kasa kunne da sun ji yanda zuciyar ta ke bugawa, Abbah ne ya yi sallama a tsakar gida, nan da nan ta yi wata ajiyar zuciya me qarfi, fit ta tashi da sauri ta fita waje, zuwa ta yi ta kama hannun Abba suka shige dakin su, tana shiga ta fara buga qafa irin na shagwab'ar da ta Saba yi wa Abban, " Abba tin d'azu nake jiran ka, Hassan yazo ga Yayah can yana ta b'ata rai , yayi fushi, ni kuma bani na kawo Hassan ba, ganina ya yi a hanya muka gaisa, na zo da shi dan bana son mu tsaya a waje, ina son na masa bayani, akan ina da wanda nake so, amma Yayah kamar ba zai gane hakan ba gaba d'aya ya b'ata rai," Hawaye ne ya gangaro mata, Abba murmushi ya yi dan ya gane a rud'e take sosai, " kwantar da hankalin ki ina shi Yousuf d'in yake? Muje na gan su" Noqe kafad'a ta yi ta zauna gefen Mama da ta fara bacci, ," A'a Abba ni dai bana son na sake ganin Fuskar Yayah sai ya sakko, tsoro nake ji," Dariya ta ba Abban ya fita, ta kama hannun ta ta saka a baki tana cisgar farcen ta tare da qurawa qofa ido, ta kasa kunne sosai dan ta ji me za a ce, Abba ne ya musu sallama ya Samu waje ya zauna suka gaisa da Hassan ya bashi baki akan ga abinda ke akwai na auren Yousuf da Atiyyaerh,  hankalin shi ya yi matuqar tashi a karo na biyu, hawaye ne suka zubo ya yi saurin d'auke su, amma ya makara a kan idon Yousuf, jikin Yousuf ya yi sanyi, dan ya tabbatar ba qaramin so yake wa qanwar tashi ba, amma sawun giwa ya take na raqumi, shima in ba ita rayuwar shi zata shiga hatsari, hakuri ya ba Hassan cike da dakewa ya nuna masu ya gode zai wuce amma yana son a mai alfarmar ganin ta ko da sau d'aya ne, kishin Yousuf ne ya motsa ya dan had'e rai, ya ce, " Minti 5 na baku danni sauri nake zan tafi nima," Murmushi Hassan ya yi dan ya gano Yousuf d'in kishi ke damun shi, se ya dafa kafad'ar shi yace , "Ni minti 2 ma ya ishen," Abbah ne ya yi murmushi ya miqe ya shiga ciki, tana ganin Abba ta miqe tana zaro ido da son Jin me ya faru, cikin tsokana Abbah ya ce, "ki je yayan ki na can na fada akan kin kawo wani," Hawaye ta fara tana yarfa hannaye, Abba dariya ya saka yace, "Matsoraciya waya fad'a maki ana tsoron miji? Ba tsoro tsakanin ma'aurata sai dai biyayya, da ladabi, in kina jin tsoron namiji sai ya ci kashi akan ki, amma in kina mai biyayya sai rayuwar ku ta zama abin burgewa, kin ji ko, share hawayen ki wasa nake maki," Sharewa ta yi, maganar Abbah ta shige ta sai ta samu gwarin guiwa ta fita, a waje ta tadda Hassan, Yousuf kuwa d'an d'aga labule ya yi yana leqen su, Atiyyaerh ta hango shi, amma shi bai kula ba, he is busy wajen kallon Hassan,murmushi ta yi mai sauti, har haqoran ta suka fito, Hassan yace, "Wato kina murna zaki auri dan uwan ki ba ni ba ko?" Cikin sauri tace " A'a ba haka bane, kawai naga yanda ka fahimci Abba da sauri ne," " To ba dole ba, wannan yayan naki kamar zai doke ni, sai muzurai yake," Dariya suka saka, a tare, ya taka zuwa wajen motar shi, ya d'akko wata leda da kwali a ciki ya bata ya mata fatan alkairi ya tafi, yana shiga mota ya kifa kan shi ya fara zirarar da hawayen rasa ta a karo na biyu, da kan shi ya rarrashi kan shi ya tafi, tana shiga ciki ta gan shi ya had'e rai sosai, itama jiman tawa Hassan take, kan ta tsaye ta je ta zauna akujerar dake kusa da tashi, miqa masa ledar hannin  ta ta yi tace, " Yah kaga Hassan ya ban ya tafi, sai na ji ya ban tausayi," " Eh shiya sa naga sai dariya kuke kamar kema kina son shi kar ya tafi ko?," Dariya ce ta kama ta amma ta dake,ta ce " Laaa Yah ya akai ka gani?" "Ina tsaye jikin labulen nan na ga komai ai," Dariya ta saka sosai harda duqawa, tin yana tsumewa shima ya saka dariyar,ya ce, " kinga laifina ne? Na sani ko ya yi yunqurin gudar min da amarya?" Dariya suka dad'a sawa, " kai jama'a ayi ai auren nan na huta, ina qailula gaba d'aya kun cika mana kunne da dariya, haba," "In kin gaji da ganin mu gobe ma a daura mana aure ki ga in ban d'auke mata ta mun tafi ba" Haka suka yi ta zolayar juna kafin daga bisani ta basu waje su ka sha hirar su ta masoya. Auwal ne a qofar wani gida, na masu qaramin qarfi,  yana tsaye da alama wani yake jira, wata budurwa ce da zata kai sa'ar su atiyyaerh , ko ta girme su da kadan, ta fito tasha kwalliya, anyi daurin ture kaga tsiya, sai taku take cikin isa da rausaya, tana leqowa waje sosai naga kyaun ta ba laifi,ta hadu, ga shape mai kyau, murmushi Auwal ya yi, ciki naga ta masa jagora suka shiga, a soron gidan an shimfida tabarma da abinsha a jug, da qaramin cup, sai flask da alama abinci ne a ciki,cikin zazzaqar muryar ta ta ce, "Sannu da zuwa," washe Baki Auwal ya yi ya ce, "Ke za a yi wa sannu da qoqari, sai kace wani babban baqo ko Wani saurayi zaki min wannan tarba ta musamman haka," Dariya ta yi mai cike da jan hankali sannan ta ce, "Ai kai saurayi na ne, dama ba na kowa ba," Se ta yi wani farrr da ido,habaaaa suman xaune Auwal ya yi, (Hahaiiiii cassssss Auwal ya je zance💃🏻💃🏻💃🏻) A haka dai suka gama hirar su Auwal ya bata kud'i ta qi amsa, shi kuwa ya matsa da kyar ta amsa, ta masa godiya ta shige gida, Auwal ma ya ja motar shi ya koma gida cike da farin ciki, Rasheedah ya gani tsaye ta riqe qugu, cikin rashin kunyar ta da ta Saba ta ce Masa, "Wai ni ban gane maka ba kusan yau sati biyu kenan, sai ka na kaiwa dare, in ka fita, ko kana zaune ka shirya ka ci kwalliya ka fita Ina ka ke zuwa? " Ko ci kan ki bai ce mata ba, dan har yanzu baya kula ta, domin ya kula sam bata risina ba sai ma abinda ya yi gaba, cire kayan shi ya yi ya shiga wanka ya fito ya juya mata baya ya kwanta abin shi, ta yi ta bambami bai ce mata bari ko ci gaba ba. Washegari da yamma ,Sulaiman ne ya shiga gidan shi da wani abokin shi,se da  ya nuna ma baqon nashi wajen zama sannan shi kuma ya shiga ciki, dakin Abban su ya kwankwasa, Rasheedah ce ta fito, ya ce mata Abban su na nan, fuskar shi ba walwala, kallon shi ta yi na wasu 'yan  sakonni sannan tace masa yana ciki, kafin ma ya ce mata komai Abban ya fito cikin shiga ta kamala, yace, "Mu je ko," Gaba Sulaiman ya yi shima Auwal ya bi bayan shi, Rahseeda ce ta kama haba, ta ce, " Yau nake ganin ikon Allah, akan waccan shed'aniyar yarinyar kowa ya juyan baya, lallai dani take zance," Juyawa ta yi ta koma dakin. Bayan Abokin Sulaiman mai suna Qaseem ya gaida Abba ne, ya gabatar da kan shi a matsayin wanda yake son Afrah, kuma yana aiki da Aminu kano Teaching Hospital tare da Sulaiman, sannan iyayen shi suna nan a unguwar Kabuga, bayan ya gama ma Abba bayani ne, Abba ya masa izinin ci gaba da zuwa wajen Afrah dan su fahimci juna, kuma in da hali yana son had'a auren ta dana dan uwan ta, Qaseem ya yi matuqar farin ciki da hakan,dan godiya ya dinga yi kamar zai kwantawa Auwal,Suna gama tattaunawa Auwal ya miqe ya koma ciki, Auwal d'in na shigewa Qaseem ya miqe ya daka tsalle, ya fad'a kujera ya na murna,Sulaiman ya Kai masa duka a kafad'a ya ce, "Kaiiii shegen a gidan surukai kk dai a rage wannan rawar kan," "Kai ka ga haka, ni yanzu na gama zama d'an gida, je ka kiran masoyiya ta mu gana," "Tab yaro ni yayan ka ne ai ba wai qanin ka ba," Durqusawa Qaseem ya yi a qasa yace, "Dan Allah yayah kiran qanwar ka na zanta da ita," D'age kai sulaiman ya yi ya dora qafa d'aya kan d'aya, yana kad'a qafar shi a dole ana neman alfarma wajen shi, kwafa Qaseem ya yi ya miqe tare da zama a kujera ya ce, "Kar kaje d'in nima za ka zo zance wajen walida na ga uban da zai kira ta, ni haka nake maka?" Ai da sauri Sulaiman ya miqe ya shiga dakin Afrah ya sanar da ita zuwan Qaseem, " Yah wane haka?" " Abokina da kk ce ya taimaka maki kwanaki, shine yazo, Abba ya masa izinin ganin ki," Cikin tsallen murna ta sakko daga gado, ta rungume Sulaiman, tana murna, kiss ta masa a kumatu ta fad'a toilet, hab'a ya kama, sannan ya kama qugu ya tokare qafa d'aya ya bud'e baki yana kallon qofar da ta shige, Murmushi kawai ya yi sannan ya fita waje,wato dai kenan itama tana son shi, kad'a kai ya yi ya sanar da abokin nashi tana zuwa shi ya shiga in sun gama ya masa waya. Tana can ta rasa ma wacce kwalliya zata yi, daga qarshe ta yanke kawai bari ta shafa powder ta shafa mai a bakin ta da kwalli, dan bata son bata masa lokaci, tana gamawa ta saka doguwar riga ta yane kan ta da mayafin rigar, ta fesa turaruka masu sanyi ta fito, ta zo ta same shi, kan ta a qasa sai murshi take shima haka, zama ta yi a kujerar da ke d'an nesa da shi sannan suka gaisa, ya qara jaddada mata me ya kawo shi, ta yi na'am da shi, suna cikin hira ne Rasheedah ta fito, ta gan su, kallon inda suke ta yi ta tsaya turus, wadannan kuma yaushe suka jone, dan ta san yaron, amma ita wannan had'i sam bai mata ba, yaron fa ba wani mai arziqi bane, ita ko so take Afrah ta auri hamshaqi, yanda zata fantama itama, kan ta gama nazarin ta taji yana gaida ta cike da girmamawa, amsawa ta yi ta shige kitchen ta fara abubuwan da zata yi, ba su jima ba ya mata sallama ya fita,ya kira Sulaiman suka tafi, Kamar daga sama Afrah ta ji Rasheedah ta ce, " ke meye had'in ki da wancan kuma? Yaron da bai aje ba bare ki saka ran zaki mori wani abu a wajen shi shine ki ka tsaya b'ata lokaci da shi?," "Umma tinda ya mallaki soyayyata ba ruwana da abinda ya tara, Abba ya aminta da shi, Yayah da Yah sulaiman sun aminta da shi, haka Atiyyaerh ta san da zaman shi, Umma ke me zai sa ki nuna rashin amintar ki? Saboda ba shi da abin duniya? Har yanzu zamana a gidan ba mashinshini be ishe ki ba ko? " Auwal ne da ke Jin dik abinda suke magana akai ya ce wa Afrah " Ba ita zata aurar da ke ba dan haka shige ki kama abinda zaki ni na fita anjima in na kusa dawo wa ki hadan kunun ayan nan da kk min rannan, Allah ya miki albarka," wuce wa suka yi suka bar Rasheedah a tsaye baki sake. *DUBAI*............ *Allah ya sa Daddy ya dawo😭😭* [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 30: Iska ya shaqa tare da lumshe ido, ya d'auki a qalla second fiye da 20 kafin ya bud'e idon shi, kallon filin jirgin Aminu Kano yake kamar wani baqo a qasar, yayi matuqar kyau, fuskar shi ta yi fresh ya aje gemu me tsaho me sheqi kamar Wani baqin balarabe,fatar shi mai ruwan chakulan ta yi luwai luwai irin na 'yan hutu, ba qaramin kyau ya yi ba, yana kalle2 ne ya buge wata matashiyar yarinya, da ba zata wuce shekara 27 ba, juyowa ta yi cike da nutsuwa fuskar ta sanye da niqab ba a ganin komai a jikin ta sai idanuwan ta, hatta da hannayen ta da qafar ta sanye suke cikin safa, doguwar rigar da ta Sanya ta yi mata das a jikin ta gwanin sha'awa sai ta yafe Kan ta da mayafi baqi, Ido suka had'a da wanda ya buge ta, tsayawa ta yi tana kallon shi, ba qaramin tafiya ya yi da ita ba,tin bayan rasuwar Sakeenaah be tab'a tozali da idon macen da ya fizgi hankalin shi ba sai yau,yarinyar ta yi matuqar burge shi, yana yin shigar ta sai ya tina masa da margayiya, nan take ya d'auke kan shi, tare da bata hakuri, dan a tinanin shi matar aure ce, murmushi ta masa ta nuna mai ba komai, bayan ya fita ne ya tadda drivern shi, sai washe baki yake ,bakin nashi yaqi rufuwa, da gudu ya isa ya rungume uban gidan nashi, har hawayen farin ciki sai da suka zuba masa, shima cike da murna ya rungume shi, budurwar nan tana kallon su cike da sha'awa, itama motar da zata d'auke ta ne ta tsaya gaban ta, shiga ta yi drivern ta ya ja ta,Adnan Shima ya shiga tashi suka fara tafiya, drivern shi na ta bashi labarai akan abubuwan da ya Saba Sanar da shi tin bayan tafiyar shi ba tare da kowa ya san shi d'in ido da kunnen Adnan d'in bane,cike da jiman ta sabbin abubuwan da ya ji a yanzu ya ke jinjina Kan shi,har suka isa wani jibgegen gida Mai matuqar kyau da tsaruwa, bud'e masu gate d'in aka yi, tin kan motar ta gama shiga gidan wannan motar da ta d'auko yarinyar nan ta shiga gidan dake kallon gidan da Adnan ya shiga, juyawa ta yi ta kalli gidan, kan a rufe gates d'in kowanne gidan a tsakanin su, Mai gadi ma da sauri ya duqe gaban Adnan yana kukan farin cikin sake ganin shi, "Ashe da raina Allah zai nufa na sake saka ka a ido na, kaiii Allah na gode maka," Daddy ne ya d'aga shi, ya miqar da shi, ya rungume shi suka gaisa a haka, sannan baba Mai gadin ya koma ya qara tabbatar da rufe gidan suka dunguma suka shiga ciki baki d'ayan su, direct d'aki Adnan ya shiga,ya rage kayan jikin shi, ya shiga bathroom ya yi wanka, ya dad'e yana zubawa kan shi ruwa, yana tsaye yana tina masoyiyar shi wadda bata tab'a barin zuciyar shi ba ko da da minti d'aya ne, haka ya fito ya shafe jikin shi da mayuka, ya fesa turaruka, ya saka jallabiyya, ya fita dinning dan kukun shi ya yi masa waya ya sanar da shi abincin is ready, zuwa ya yi yaci ya sha, sannan suka zauna dika suka sha hirar yaushe gamo, suma wannan abincin da yaci shi suka ci, Adnan ne ya ce, "Da daddare zamu je ka kaini gidan mu na ga Abbana, da Mama na, ba qaramin kewar su na yi ba, ni yanzu Atiyyaerh ce babbar damuwa ta,ka na ganin in ta ganni ba zata ji haushi ba? Wanne irin reaction ka ke ganin za ta yi?" Ya na gama fad'in haka se ya sadda kai qasa, idon shi, ya cika da kwalla,cikin tausayawa driver ya ce, " Ranka ya dad'e kar ka saka wannan a rai ya dame ka, inshaa Allah fushin ta ba zai wuce yau ba, ka kwantar da hankalin ka, yarinya ce da ta haifu daga wajen marigayiya, yarinya ce mai biyayya da hakuri da yafiya, indai zata yafewa Waccan shaid'aniyar to ko zata yafe maka," Adnan ya gamsu da bayanin driver ya kad'a kai, a haka suka d'an taba hira ya je ya yi sallar la'asar, bayan ya idar ne ya fita dan shan iska, daga saman balcony ya hango wata kyakkyawar halitta, baqace doguwa mai shape mai kyau, ta saka riga mai siririn hannu, fara sol, sai gashin ta da yake a d'aure, ya zauna a dokin wuyan ta irin gashin nan ne na 'yan Afrika Mai cika da tsaho,hannun ta riqe da mug ta na kora baqin shayin da ke turiri, sai d'ayan hannun tana danna wayar ta, direct wajen wata kujera ta nufa, da qaramin table a wajen, ta aje mug d'in ta ci gaba da danna wayar ta, band din da ta d'aure gashin kanta ta cire ta baza gashin, tai gaba da shi sannan ta saka hannun ta ta baza qasan shi, kamar mai susa kamar me son shan iska a cikin gashin nata, Adnan bakin shi a sake ya na bin ta da kallo, d'agowar nan da zata yi, tana lumshe ido dan dad'in susar da take wa Kan ta,idanun ta suka sauka akan fuskar shi, dake kallon ta, cike da kunya ta fara dabur2 din me zata yi, d'aga hannu ya yi alamar ta yi hakuri, murmushi ta yi tai saurin miqewa ta nufi hanyar da zata shigar da ita d'akin ta, ko mug d'in bata tsaya d'agawa  ba tai gaba, daidai zata shiga ciki ne ta juyo suka sake had'a ido, murmushi suka yi wa juna ta shige ciki, Daddy ne ya shafa gemun shi, mai cilli2n furfura a jiki, ya yi murmushi, ya koma d'akin shi, fuskar ta kawai yake hangowa,can ya ce, "Subhanallah in tana da aure fa?" Tashi ya yi daga kwantawar da ya yi, yana nazari, nan jikin shi ya yi sanyi, dan yanayin ta ya mai kama da marigayiyar shi, "Allah kasa bata da miji, tabbas zan gabatar ma da su Abba daddad'an labari na samun matar da zan aura na San za su yi farin ciki sosai, baffana har ya yi fushi ya dena d'aukan wayata saboda sun bani Umarnin neman mata na yi aure na qi, in Allah ya cika min buri na sai dai na je Sanar da su maganar aure"  Da wannan zantukan ne ya miqe ya fad'a bathroom dan d'aura alwalar sallar magrib da ya ji ana ta Kira, sannan ya fita masjid dan yanzu ba gajiya a tare da shi kamar d'azu, ya na fita suka had'u da wani dattijo da in zai girme shi bai fi da irin 4 to 5 years dinnan ba, suka gaisa, suka shiga masjid d'in a tare, bayan anyi sallah ne sun fito zasu koma gidan su, suka qara gaisawa, inda mutumin yake sanar da shi shi maqocin shi ne ashe, sanar da shi ya yi sunan shi Alhaji Haladu Gwandu, yana da mata da d'iyar su da ta dawo ba jimawa d'azu daga Dubai  mai suna Fauziyyah a can ta yi karatun ta, ita d'aya Allah ya basu, shima sanar da shi ya yi taqaitaccen tarihin shi,nan take mahaifin Fauziyya ya masa ta'aziyyar rasuwar Sakeenaah, sannan ya masa fatan samun mace ta gari, sukayi sallama da juna kowa ya shige gida, direct d'aki ya je ya shirya cikin shigar da kowa ya gan shi sai ya qara, dan kuwa komai ya ji, fitowa ya yi yana baza qamshi, ya yi wa Auwal waya yace su had'u a gidan Abba, fita ya yi inda motocin shi suke ya shiga wadda driver ya tada, Baba me gadi ma tini ya bud'e gate shi kad'ai ake jira dama, driver ya ja su sai gidan Abba. Kowa ya shirya cikin shiga mai kyau da Kamala kamar masu zuwa Wani event, Rasheeda ta tambayi inda za a je yafi sau ba adadi ba wanda ya kula ta, haka suka d'au hanya, ana tafiya ta gane ina za a ta ja tsaki da qarfi da yasa kowa kallon ta, "Da ace min gidan gyatumin nawa za a ake ganin asarar hakan Allah ya kyauta to," Ko ci kan ki ba wanda ya ce mata, suna isa suka tadda wata jibgegiyar mota me numfashi a qofar gate d'in gidan, kowa sake baki ya yi yana kallon motar musamman Rasheedah da ta dinga zuba santin motar, suna tsayawa Auwal ya fito, shima Adnan ya fita daga cikin motar da taimakon driver ta hanyar bud'e masa motar ya tsaya a gefe Suna wa juna murmushi, dan tinda yazo gidan suke a tsaye a nan saboda ya rasa ta ina zai fara sa qafa ya shiga cikin gidan, kallon shi su Afrah suke, Yousuf kam tabbas ya san wannan shine Daddy, Auwal kam hawayen dad'in ganin Adnan ne suka wanke masa fuska, shima Adnan d'in haka,Rasheedah da ta fito daga baya tana mitar tsaiwar me suke, tana ganin Adnan d'in kusan zama ta yi a qasa a wajen, Afrah da Sulaiman ne suka taro ta, Cikin wata iriyar murya me rawa ta ce, "Waaa nake gani haka kamar Adnan?" Cike da jin d'acin labaran da ya ji daga mutanen shi ya kalle ta,ya kauda kai, ya kalli Auwal ya taka ya rungume shi, shima qanqame shi ya yi kamar wanda aka ce wa zai sake komawa inda ya fito,yaran ma rungume shi suka yi,banda Afrah da ke gefe hawaye na ta zarya a idon ta, dama wannan shi ne Daddy kenan? Shine abinda take ayyanawa a ranta, me zai sa ya tafi ya bar Atiyyaerh, ta sha wahala wajen Umman su? Bayan da ga dukkan alama yana cikin rufin asiri, kauda kai ta yi ta shige gidan da gudu, dan in Atiyyaerh bata yafe masa ba itama bazai ga fara'ar ta ba, a ranshi ya tabbatar da labarin da yaji game da shaquwar Atiyyaerh da Afrah, jikin shi ya yi sanyi sosai da ganin hakan, ya tabbata akwai had'in kai,a tsakanin su, d'unguma suka yi ciki baki d'ayan su, har lokacin Rasheedah bata daina kallon shi ba. Da kuka Afrah ta shiga, ta fada cinyar Atiyyaerh da take zaune ta shafa hadin Cinnamon da lemon tsami,kwai, zuma da d'an sugar kad'an a ciki ta shafe a jikin ta, tana ta danna waya,tana kallon hotunan Yayahn ta, daga ita sai qaramar riga iya guiwa, data matse ta daga sama, sannan ta sake daga qasa, mai siririn hannuwa,rigar na da aljihu a jikin ta, kalar yellow, ta daure gashin ta ta nannade shi, ta yi masifar kyau, wayar ta ta zira cikin aljihun rigar  hankalin ta tashe take tambayar Afrah me ya faru? Amma ta kasa magana, sallamar Abban su Auwal ne ta katse mata tambayar, tafe dashi akwai wani mutum mai cikar kamala, da zati wanda ta kasa tantance waye, amma zuciyar ta sai qara qarfi take wajen bugawa......[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼          WRITTEN   BY HAERMEEBRAERH *Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA?   To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️* *Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin  sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal* Page 31: Mama ce ta fito  daga d'akin su Abbah na biye da ita a baya, tana neman Atiyyaerh dan ta raba masu musun da suke akan kwanan wata, " ke zo ki raba mana wannan gaddamar, yau nawa ga watan bat......." Dakatawa ta yi da zancen ta,dariyar Abbah ce ta d'auke lokaci d'aya mamaki ya maye gurbin ta, "ADNAN" Suka had'a baki wajen fad'a,Juyawa Adnan ya yi daga barin kallon Atiyyaerh ya Maida idon shi Kan dattijan guda biyu, Cike da tsananin farin ciki ya tafi wajen Abbah da Mama da idanun su suka ciko da kwallar farin ciki,rungume Abbah ya yi, ya fashe da kukan murna, Abbah ma kyakkyawar runguma ya Masa ya na bubbuga bayan shi,bakin Mama ya qi rufuwa saboda farin ciki, "Shekara 19 kenan rabon mu da Sanya ka a idanun mu Adnan sai yau Allah ya yi zamu sake saka a idon mu, ya ilahi kullum tinani na baya wuce Allah kar yasa na mutu ban sake ganin ka ba, mu nemi yafiyar ka akan sakaci da kuma cika wasiyyar da bata zamo alkhairi ba, dan babu abinda Atiyyaerh ta tsinta wajen Rasheedah sai uquba da bala'i gashi ita wadda aka yi domin ta har yau Imani da tsoron Allah da son zumunci be shiga zuciyar ta ba,a qoqarin cika wannan wasiyya Adnan mun zalunci marainiyar Allah,ka yafe mana Adnan, ka yafe mana," Kuka ne ya ci qarfin Mama a dole ta yi shiru da maganganun da take ta zubawa, Abbah ne ya samu waje a kujera ya zaunar da ita, yana lallashin ta, don yasan kusan kullum sai ta yi kuka akan hakan , ko yana gida ko ya fita, "Mama ni ne zan nemi yafiyar ku, ku yi hakuri da saku cikin kewa da tinani da na yi, inshaa Allah na dawo gare ku kuma na dawo wajen 'yata ba abinda zai sake rabamu da ku, ina fatan kun yafe min?" Atiyyaerh ce ta ke bin shi da Wani irin kallo, cikin qasa da murya ta fara magana, " Yafiya? Yafiya fa kace Daddy? All this years? What have you been doing that is so important da ya sa ka yi abandoning din mu? u ar there leading a luxery life, ni ina nan ina azabtuwa, kamar marainiya mara gata, mara galihu, mara dangi, sai mariqiyar da ta min riqo kamar bamu had'a jini da ita ba,me na muku, kullum na tina halin dana shiga ni d'aya ji nake kamar zuciya ta zata fashe ta tarwatse, Umma bata riqe amana ba, bata riqe zumunci ba, Mummy ta yi zaton zata iya canja mata halaye idan ta bata ni, bata san kuskure ta tafka ba, ta azabtar dani, ta azabtar dani, ta azabtar dani, ta min auren da bana so,na koma bazawara, na had'iyi baqin ciki irin Wanda in aka wa mutum auren da baya so ya yi hakuri ya danne domin biyayyar Allah da ta iyaye ya d'and'ana,Yan zu Kuma Ina had'iyar baqin cikin rabuwa da mutanen da na Saba da son su, saboda son zuciya irin nata, su nake gani na ji ina da iyaye, domin sun d'auke ni a matsayin d'iyar su ta cikin su, ba suruka ba, Ahmad ya gwadan soyayya mai tsanani da kulawa, kowa nawa ya gujen har ba a so a zo wajena, na San a lokacin nan dik uzirin da mama ke bani na rashin lafiya da ta so zuwa waje na a mota za a kawo ta ta zo ta ganni, amma har na gama rayuwa da Ahmad bata San ya d'aki na yake ba, na yi hakuri na shanye, hakan ta faru ne saboda ita ta dalilin ki ne Umma ke ce silar komai, ke ce silar shiga ta matsala da damuwa a rayuwa, habaaa ba zuciya a qirji na ne? Kar ku Yi zaton bana Jin zafi da radad'in yada ni da kuka yi, na zab'i na Maida komai baya na ne Dan kwanciyar hankalin kaina, amma ba Dan na manta ba,su kan su 'yan uwana da ke so na da Abbana da ke so na sai dai na ga soyayyar su daga nesa amma ba za a nuna min soyayyar ba yanda zan ji dad'i na San yess ana so na, Afrah ce kad'ai ke take duk wata doka ta nuna min so, me na aikata mara kyau? Me yasa ku ke tsoron ta ku ke kyale ta har ta ke abinda ta ga dama, ba zan tab'a yafe miki ba Ummaa, ba zan yafe ba, ba zan yafe ba, dan haka kar Wanda ya nemi yafiya ta," Duk maganganun nan da take tana yin su ne cikin kuka da buga qirjin ta da qarfi da hannayen ta bibbiyu,Yousuf ji yake kamar ya riqe hannun ta dan gani yake zata jima kan ta ciwo, ga kuka tana yi kamar zata hadiye zuciya, ba wanda baya kuka a wajen, Rasheedah tin tana kukan a tsaye sai da ta durqusa, kukan tsananin nadama take Wanda bata tab'a tinanin zata yi shi ba nan kusa,a zaton ta duk abinda take yi rama banbancin da aka nuna mata tsakanin Sakeenah da ita ne,kuka take sosai irin kukan da take jin asalin tsanar kanta,da halayen ta, muryar Atiyyaerh ce ta sake karad'e kunnuwan su baki d'aya, " Bana buqatar ka Daddy, zan ci gaba da rayuwa ni d'aya cikin raina Ina ji na kamar marainiya, kamar yanda ka saba min tin fil azal shekara 19 baya, ai na d'auki darasin rayuwa yanzu Kuma, zan iya ci gaba da qarasa rayuwata ba kai, tinda haka kk so kuma ka zaba min,I am ok with the kind of love I am receiving from my family, zan yi bakuri da kalar soyayyar da kowa ke nuna min, na riga na Saba da hakan and it is ok for me," Da gudu ta zo zata shige ciki, cikin zafin nama Daddyn ta ya riqe ta gamm a jikin shi yana kuka, yana son yi mata magana ya bata hakuri amma ya kasa, sai qoqarin kwacewa take ta shige ciki, amma sam ya hana ta, duk ta b'ata masa riga da kurkur din da ke fuskar ta, data gaji da qoqarin kwace kan nata ne ta kwanta a qirjin shi tana ta kuka,jikin kowa ya yi mugun sanyi a wajen, sai yau suka San cewa ashe kallon kowa take, a zaton ta har cikin ran su ba sa qaunar ta, to me zata fahimta dama a yanayin yanda abubuwa suka dinga faruwa? Ai ta ma yi hakuri da su, tinda Suna ji su na gani ta ke azabtuwa ba Wanda ya tsaya mata tsayin daka dan ganin ta kubuta daga hannun Rasheedah, " Atiyyaerh my love, ki duba girman Allah da soyayyar ki da Annabin rahama ki yafe min,iyakar abinda zan iya ce wa kenan, bani da bakin magana, nafi son cika wasiyyar Mummyn ki fiye da komai a rayuwa ta a wannan lokacin,wannan dalilin ne yasa na bi umarnin da ta bayar, na tafi na barki zuciya ta na tsananin son ki,ina son jinina a kusa da ni nima, amma ba yanda zan yi, dana zauna naga ana wulaqanta ki, wanda na san dole za ai hakan tinda kowa ya San Rasheedah bata son 'yar uwar ta da suka fito ciki d'aya ba Kuma ta son abinda ta haifa, shi yasa na tafi, kome kk ciki ina sane da shi ta hannun mai gadi na da driver na,  a kullum sai na yi kukan qunci, ta haka ne na samu ciwon zuciya, amma alhamdulillah Allah ya yaye min yanzu na samu sauqi da yardar Allah ciwon be yi nisan da ba zai warke ba Allah ya taqaita min shi,a lokacin da na ji daddad'an labarin da kullum Mummyn ki ke fatan ya tabbata sai na ji hankali na ya yi na dawo gida, musamman tin tana raye ta yi min umarnin in naga maganar auren ki da Yousuf masoyin ta da ke ta taso na tsaya tsayin daka dan ganin auren ya tabbata, ga takardar ki da ta rubuta maki, ki yafe ni ki karba ki karanta,zata maki bayanin komai a nan," Cikin sauri ya hau kiciniyar zaro takardar daga aljihun shi,ya damqa mata, kamar ba zata karba ba can kuma ta saka hannu ta karba, *Atiyyaerh My Love*   *Ina fatan sanda takarda ta zata isa hannun ki, kina cikin qoshin lfy, da cikar imani, My baby, ki yi hakuri,ki yafe min, ki yafewa Daddyn ki, sannan ki yafewa Yayata, abar qauna ta, kome da ta miki a rayuwa, na san ba zata miki mai kyau ba, ba zata so ki ba kamar yanda ta ambata, amma ina roqon alfarmar ke ki so ta, ki qaunace ta kamar ni, ki zama mai yafiya, ki zama mai biyayya, in burin raina ya cika, wato auren ku ke da d'a na Yousuf, ki zama mai ladabi da biyayya ga mijin ki, baki da wanda ya fishi a duk duniya, haka yake ga duk wata d'iya mace, a lokacin da ta yi aure qoqari take ta zama mace ta gari a wajen mijin ta, ki kasance mai tsafta, iya girki, iya kwalliya, da magana, ki zama mai tsoron Allah, da nema a wajen Allah, kar ki zama mai shirka, mai neman wani biyan buqatar ki wajen wanin Allah, in kina haka Allah zai so ki,mala'ikun shi zasu so ki, mutane zasu so ki, mijin ki zai so ki ya qaunace ki.* *" Abalerh dear ban bar ki a hannun yayata dan ki wulaqanta ba, na bar ki ne dan ta koyi riqo da zumunci, ta san me ake kira da zumunci, ta cire tsananin son kan ta da take da shi, sai kaso wani sannan son d kk wa kan ka zai amfane ka, in kana da yawan qiyayya a ran ka zaka rasa soyayyar Allah, data mala'iku, da ta mutane, sannan kowa naka zai qi ka, soyayya ita ke jawo soyayya, ba yanda za ai qiyayya ta jawo soyayya, amma soyayya na jawo giyayya ta koma so, shi nake fatan ki bawa Rasheedah yayata soyayyar ki, dan qiyayar ki ta koma so a wajen ta,"* *A qarshe ina mai tabbatar maki ina son ki, ina qaunar ki, amma wanda ya fiki sona ya kira ni,ki kula da kan ki.*          *I love you so much Ablaerh na* A yanzu kam zuciyar Rasheedah ta gama kakkaryewa in to million pieces, tabbas ta karbi soyayyar 'yar uwar ta da 'yar 'yar uwar ta, ta yi nadamar qiyayyar da ta nunawa Sakeenah da abinda ta haifa ashe haka so yake?saboda kwanciyar hankalin da ta ji ta lullube ta a yanzu ba zata Iya misalta shi ba, Wani qunci da quntata da zuciyar ta ke d'auke da shi na shekara da shekaru se ta ji babu shi, ta rasa ta ina zata fara bada hakuri sannan wa da wa ya dace ta fara bawa hakuri dan kuwa ta cutar da kowa, sai kawai ta yi dif kamar an d'auke ruwa, ta kasa bud'e bakin ta ta ce Ummm ko A'ah, kowa a zaton shi kawai halayyar ta ta ce ta motsa, sai dai ta yi ta bin mutane da ido. Atiyyaerh juyawa ta yi ta rungume Daddyn ta bayan ta gama karanta masu wasiqar da Mummyn ta ta bar mata, sai murna kuma suke, Daddy ne ya kalli Afrah yace, " Yanzu dai tinda qanwar ki ta yafe min ai na san kema zaki yafe wa Daddy ko?" Cike da jin kunya ta miqe ta je gare shi, had'e su ya yi ya rungume, a haka wannan iyali suka kwana ana hirar yaushe gamo, kamar daren sallah, haka suka kasance dan farin ciki, cannn suka ji Rasheeda ta fashe da kuka sosai har tana siqewa, dan tinda suka ga ta ja ta yi shiru kowa ya yi banza da ita, kowa ya nemi yafiyar Atiyyaerh Kuma ta furta ta yafe ma kowa, ganin Rasheedah bata kula su ba ne ya sa mama ta ja su suka nufi kitchen ake ta hidimar azziqi aka barta a wajen, wannan shine dalilin da ya sa a yanzu kowa ke mamakin kukan ta "Na roqe ku da ku yafe min, ku yafe min, ku yafe min, ku...ku...ku yafe min,in ba ku yafen ba Allah ba zai yafen ba, ku tausaya mun ku yafe min ba dan hali na ba sai domin Allah da manzon shi da zumuncin da kuka yi riqo da shi ni na wulaqanta shi, ku yafe min ko zan ga haske a qabari na da rayuwa ta na shiga uku na lalace ni Rasheedah Ina zan Kai haqqin zumunci da marainiya wayyoooo Allah na na shiga uku na," kuka take sosai na tsananin nadama da danasanin abinda ta aikata,Afrah ce ta kalle ta ta kauda kai,zuciyar ta ta yi rauni ganin yanda mahaifiyar ta ke kukan da bata tab'a irin shi ba,amma a haka ta kauda Kan ta gefe dan in dai har  Atiyyaerh bata yafe mata ba itama ba zata ci gaba da sake mata fuska ba, matsawa ta tashi ta yi daga in da Umman tasu take, ta koma kusa da Sulaiman da shima ya b'ata rai sosai, dan shi ya na ma tantamar sahihancin wannan kukan nadamar,anya ba Dan ta ga Daddy ya ninka da arziqi bane? rarrafawa Rasheeda ta fara, ta kama qafar wannan ta saki ta kama ta wancan ta saki, Daddyn Atiyyaerh 'yar shi kawai ya ke kallo, dan Shima ya na jin in bata yafe mata ba shima ba zai yafe mata ba, cike da kukan nadama da kaico take roqon su, Atiyyaerh ce ta taka ta je gaban ta, ta durqusa ta d'aga ta, bata ce komai ba ta rungume ta, wata runguma Rasheeda ta mata kamar zata maida ta ciki, sai da Atiyyaerh ta zaro ido ta yi qara kadan sannan ta ce, "Ummaaaa haqarqarina zasu hade waje d'aya ai" Cike da shagwaba ta fadi hakan, gaba d'aya wajen aka saka dariya,a hankali kowa ya nuna ma Rasheeda ya yafe mata, suka ci gaba da hirarrakin su tare, ita dai banda matsar kwallar da take lokaci bayan lokaci ba abinda take, ta kasa Saka baki a hirar, Wani irin nauyi da kunyar su take ji, anan ne Abbah ke tambayar Daddy cewar, "Wai ni Adnan ba za ka yi aure ba ne, shekara da shekaru ka qi kula kowa,ai ba ka zauna haka ba,kar ka manta har yanzu fa kana da sauran quruciyar ka, dan ba zaka wuce 46 ba ,to dan me zaka tauye kan ka?" Sosa qeya ya yi irin na samarin da aka wa maganar aure sun ji kunya,kawai se kowa ya saka dariya,Adnan kallon Abbah ya yi ya ce, " Abba na ga wadda ta kwantamin a rai a yau d'innan a airport, amma ban magana da kowa nata ba, ko ita bata sani ba,aban wani lokaci tukunna,Abba in ka ganta,kamar su d'aya da marigayiya, komai nasu iri d'aya, banbancin su wannan tafi margayiya tsaho da haske, hatta shigar da margayiya ke yi itama wannan irin ta na ga ta yi, " Cike da mamaki kowa ke sauraran bayanan shi, fatan alkairi Abba da mama suka yi.masa, sannan Auwal ya yi magana cike da Jin kunya, ya ce, " Abbah ina ganin in ya fiddo mata ai sai a had'a da namu ayi ko, tinda Sulaiman ya samu mata shima qanwar wanda ke neman Afrah yake so, gani nima na samu macen da zan qara, a kusa da mu take, yarinya ce sa'ar Sulaiman," Ya qarasa maganar yana sinne kai, wai shi kunya, dariya aka saka a wajen,mutuniyar ku kuwa suman zaune ta yi, cikin wata iriyar muryar da kowa ya kasa fassara ta ta ce, " Aure? Aure fa Auwal? Da yaushe ka qulla wannan abun ban da masaniya?" "Da lokacin da ki ka rufe ido kina cin zarafin marainiyar Allah, kuma ki ke qoqarin hana d'an ki auren d'iyar da ya kamata ace ke kk had'a auren su da kan ki tin fil azal" Cikin matsanancin kuka Rasheedah ta ce, "In dai dan haka ne ka yi wa Allah ka yi hakuri na amince a yi auren su amma kar ka min kishiya,ka sani aduniya bana son kishiya Auwal na tsani komai da zai zama kishiya a wajena dan Allah kar ka min kishiya na canja hali na ba zan sake ba, Mama Abbah dan Allah ku bashi hakuri na sauya daga mummunan halin da na d'orawa kaina na zab'i kyakkyawan hali, dan girman Allah kar ka min kishiya Auwal "  Mama ce ta tashi tsaye ta na nuna Rasheedah da yatsa ta ce, "Ai kuwa sai ki fara son kishiya tin yanzu, mara mutunci, wato halin naki zaki dawo da shi ko? To in baki fasa ba baki cika Rasheedah me mugun hali ba," Abba ne ya riqe Mama dake tashi tsaye tana masifa, Rasheeda kuka take sosai da ya fi na d'azu, ita za a yi wa kishiya yanzu, ba a mata kishiya ba tin da yarintar ta da ruwan jikin ta se yanzu da ta tara manyan yara?..... . *Hahaiiii cassssssssssss Rasheedancy za ai mata kishiyancy, su waye zasu yi qawayen uwargidancy, 🤣🤣🤣🤣🤣* [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH *Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA?   To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️* *Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin  sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal* Page 33: Se da ya gama lallab'a ta sannan ya tambaye ta abinda take so ta karya da shi, nan ta shiga zayyano masa abubuwan da take so Cike da shagwab'a shi Kuma ya na haddacewa , da kyar ya samu ta yi bacci sannan ya rufe ta ya ja mata qofar a hankali ya fito. Yanda suka barta a haka ya tadda ta, be damu ba ya hau bata umarnin ta dora abin karyawa saboda kar amarya ta tashi ba abinci,  Kuma amarya ta na so a yi mata farfesun kayan ciki dan tana buqatar abu me d'an yaji yaji da ruwa ruwa,ta had'a da chips sannan ta soya qwai, sai ta mata kunun gyad'a, yanda yake fad'an saqon amaryar cike da umarni da izza abun ya gama gigita Rasheedah yau ita ake bawa Umarnin yi wa kishiya girki? Ga shi a yanda yake mata maganar ba wargi bata isa cewa dan me ba shiru ta yi dan tana gudun ya liqa mata duka ya qarasa zubar mata da d'an mutuncin da ya yi saura gaban 'yar cikin ta, ita yanzu gaba d'aya tsoro ma yake bata, ba qaramin canjawa ya yi ba, yana juyawa zai tafi ya yi Wani mugun murmushi, dan tabbas ya san amaryar shi mai Suna Khadeejah na da kirki sosai da sanin ya Kamata, ga ilimin addini da na zamani daidai misali, amma fa ya san tana da wani hali guda d'aya wato tsanar duk wani mai mummunan dabi'u wanda kuskuren da ya yi kenan wajen neman auren ta da ya yi ta hanyar zayyane mata halayen matar shi, a da yayi haka ne dan ita in tazo ta tausayawa Atiyyaerh ta bata kulawar da Rasheedah ta gaza bata,se ga shi ma bata ci gaba da zama da su ba ta koma wajen su Mama, amma yanzu ya gane kuskuren da ya yi na fad'a wa macen da zai aura halin matar shi ta gida,dan ya kula amarya so take ta ci qaniyar Rasheedah da kyau, zai bar su kuwa har zuwa lokacin da Rasheedah zata yi hankali Yana tafiya ya na magana shi kad'ai, "Ai ko ba zan hana ba, yanzu ne zata san a ina ya kamata mace ta yi kishi sannan shi kishin ya ake yin shi," Ya sake yin wani murmushin mugunta ya fad'a d'aki, Khadeejah kuwa har ta tashi ta shiga wanka sai shima kawai ya fada suka yo wankan su fes bayan soyayyar su da suka sha, dik da ta na Jin kunyar shi a matsayin ta na mace Kuma budurwa, burin ta a gidan yanzu shine ta na so ta yi maganin Rasheedah dan haka in Auwal ya yi mata wani abu musamman wanda ya ke sata dariya topa zata ware murya ne tai ta dikar dariya,sedai ba irin dariyar nan mara dad'in sauraro take yi ba,ah ah ta na Yi ne cike da salo da yanga a ciki,Auwal d'in duk na kula da ita,ya kan sha dariya sosai shi d'aya ya jinjina kaidi irin na mata a ran shi. Bayan sun kammala shiryawa ne ta ce Masa, " Honey ni na gaji da zaman d'aki, muje Parlour, yunwa nake ji sosai, kaga tana gamawa kawai sai muci ko," Ta fad'a tana wani rausaya, aiko Auwal kamar raqumi da akala haka ya rungume ta a jikin shi suka nufi Parlour, Rasheedah kuwa da ta d'akko palates zata aje a dinning ce ta d'aga Kai ta hango su suna fitowa manne da juna, Khadeejahn ta Wani maqalqale shi sai shagwab'a take ta na Washhh ita jikin ta ciwo yake, suka samu kujera suka baje, suna maida nunfashi, cikin dariya Khadeejah tace, " Honey kasan me?" Ya girgiza kai dan ba qaramin kai shi duniyar wata take ba, "Lips din ka wani zaqi suke da shi kamar zuma, bana gajiya da sumbatar su" Ta qarasa maganar ta da Kai bakin ta nashi, ba wata wata kuwa Auwal ya cafke nata ya na Wani lumshe idon, Khadeejah kuwa ta haka ta yi dabarar d'agawa Rasheedah hannu tare da zaro ido kamar tana yi da wata 'yar ta ta mata nuni da ta bar wajen, da sauri ko Rasheedah ta yi gaba dan ba zata Iya jure ci gaba da kallon su a wannan halin ba, zuciyar ta kamar zata fashe haka take ji, hankalin ta a matuqar tashe yake, yau wace irin jarabawa take gani? " Oh Allah ka min maganin wannan tashin hankali da nake ciki, ashe haka zafin kishi da radad'in shi yake?" Aje plates din ta yi ta koma, ta qarasa soya kwai tana yi ta na sharar hawaye, bayan ta gama ne, ta kai komai zata wuce Auwal yace ta tsaya ta karya, taso yin musu Khadeejah ta sa baki, "Habaaa Yaayaah ki yi wannan aikin sannan ki tafi baki ci ba pls ki zauna muci, kinga cin abinci a tare ya na qara hadin kan iyali" Cike da kissa take maganar tana kashe idanu, mamaki yarinyar ke bawa Auwal dan kuwa kowa ya San ta da kunya da girmama na gaba da ita mutane na tsananin yaba mata, shine dalilin da ya Kai shi neman aure wajen ta, wata zuciyar ke Sanar da shi cewa. 'laifin ka ne Auwal, ka riga ka b'ata matar ka uwar 'ya'yan ka a gaban wadda ba ka aura ba, dole raini ya shiga tsakanin su' Zama Rasheedah ta yi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki,ga masifa tana son yi, amma sai ta kula wannan da gani ta ci uwar ta a bala'i da kissa gashi ba dama ta yi magana Auwal zai mata rashin mutunci a gaban kishiya, sannan in suka yi fad'a da Khadeejah da alama ita zata kwana a ciki, dan kowa laifin ta zai gani musamman Mama zata ga bata sauya halin ta ba dama qarya take, duk girman ta da manyan yara ace wai wata na juyata haka hummmm rayuwa kenan? Amarya ce ta debi chips ta had'a da kwai ta kai bakin Auwal, cike da jin dad'i ya bud'e baki ya amsa,cikin ran shi ya ke ayyana... ' Oh rayuwa kenan ashe nima da rabona a soyayya' A hankali ya tauna yana lumshe ido, ji yayi an sumbaci saman idanun shi dake rufe,ya bud'e ido se ya ga Khadeejah ce cikin yanga ta ce, "An kuwa tab'a fad'a maka kai d'in kyakkyawa ne? Da kai haka baka ji yanda kasa zuciya ta gudu ba, tab'a ma kaji," Kafin Auwal ya yi magana ta ja hannun sa ta dora akan qirjin ta, shiko yana jin ya damqi cikakku kuma tsayyayun na fillos har wani danna hannun shi yake wai zai jiyo zuciyar ta ta, dukan table d'in Rasheedah ta yi da hannayen ta biyu ta miqe tsaye,nan take suka maida hankalin su kan ta, " Ba zan iya d'aukan wannan barikancin ba Auwal akan me....," Maganar ta ce ta katse saboda kallon da Amaryar ta wurga mata me matuqar rikitar wa,ai kuwa ba qaramin kidimata kallon ya yi ba, anya yarinyar nan ba asiri ta musu ba dika? Ta mallake miji dan kawai ta gana mata azaba,kamar daga sama ta ji Amarya ta fashe da kuka, harda shessheqa, cikin b'ata rai Auwal ya ce wa Rasheedahn, "Bata hakuri," Rasheedah kuwa Imani ya mata yawa kawai se ta sake baki,cike da wata gigittaciyar tsawa da tinda suke bata tab'a ji ya yi irin ta ba ya maimaita cewa ta bawa Amarya hakuri,a rud'e ta ba Amaryar hakuri, kamar an kashe redio kuwa ta yi dif, ta lafe a jikin Auwal, sannan ya umarci Rasheedah da ta koma ta zauna, hawaye ne kawai ke gudu a idanun ta, quncin da take ji a zuciyar ta bata Jin zata Iya ci gaba da zama a gidan nan, saboda da dikkan alamu amaryar nan ta zo ne da niyyar kassara rayuwar ta,Auwal d'in ta ne fa, Wanda ke shanye dik Wani rashin mutunci da wulaqanci ta, Auwal d'in ta da ke susucewa akan ta ya b'ata lokaci wajen gwada mata soyayya, Auwal d'in ta ne fa uban yaran ta, amma a yanzu Yana neman fin qarfin ta, cikin kwana d'aya yarinya qarama ta gigita shi ta sa ya fita hayyacin sa, anya zata Iya rayuwa a haka kuwa? A hankali ta koma ta zauna ta na share hawayen ta da suka kasa dena zuba "Zauna ki ci abinci da kyau Ina Gani salon ki zo yunwa ta kama ki ki rame ko ciwo ya kama ki ace bana adalci a tsakanin ku ko?" Zama ta gyara tana hawaye tana tura abincin, yau 'yar cikin ta ke mata mugun abu haka? Oh duniya kenan juyi2, Auwal ne ya d'ebi farfesu ya Kai bakin shi sannan ya deb'o ya ce wa amarya ta bud'e baki ba zafi, ta na bud'e wa ya zuba mata a bakin ta hau taunawa cikin yanga, itama ta d'auki spoon ta d'iba ta bashi,  a haka suka ciyar da juna suka qoshi, Suna ta zuba soyayyar su,zuciyar Rasheeda kamar ta daina aiki haka take ji,ango da amarya sun lula duniyar soyayya ta zame jikin ta a hankali ta yi d'aki, ta na shiga ta rufe qofar da qarfi ta saki wani wahalallen kuka, yi take tana qarawa ba mai lallashi, haka ake ji a kishi, ko ita kad'ai ce ke jin haka? Tinda ita bata son a had'a ta da kishiya a komai nata, sai ta ji baqin cikin duniya ya mamaye mata rayuwar ta, ashe kishin miji ya fi zafi akan kowanne kishi, da kyar ta daddafa ta hau gado,ta jima kafin bacci mai dad'i ya d'ebe ta. Bayan sun gama ne sukai wanka,suka shirya cikin shiga mai kyau, zasu tafi gaidan  su Abban, Leqawa Amarya tai dakin Rasheedah tace mata, ya kamata ta fara hada abincin rana zasu dan zagaya gidan su dawo,cike da umarni take fadan hakan, kuma fried rice za tai da coleslow, sai salad din dankalin daban, dan ita bata son ganye, Auwal yaci wancan, ita taci wannan, sai ta hada masu kunun aya, sannan ta gasa masu nama ya yi dan ruwa-ruwa, " kinsan ni har yanzu ba wai na warke daga ciwukan da honey  ya jiman bane, lallai kina fama dama haka yake? Ayi ta abu d'aya ba ya gajiya? Lallai ki na fama" Cike da zolaya ta sa kai ta bar d'akin ta bar Rasheedah na sharar kwalla, a mota ta same shi, zaune ya na jiran ta, bud'e mata ya yi ta hanyar miqa hannun shi ta shiga ta zauna ya ja su sai babban gidan su Adnan, inda su Mama da Abban su Rasheedah ke zaune a yanzu.  Suna Isa Mai gadi ya bud'e masu gate, suka gaisa da Auwal da Khadeejah sannan suka qarasa ciki, hannun Khadeejah na cikin na Auwal suka Isa bakin qofar shiga sashen su Mama, da sauri ta karb'e hannun ta Cike da Jin nauyi ta yi gaba, abubuwan ta na ba shi mamaki, a gida ta zage ta na ta zuba masa soyayya, amma yanzu wai kunya take ji, Murmushi ya yi ya kad'a Kai ya bi bayan ta. Zaune ya hango su Yousuf da Atiyyaerh wadda ta shagwabe ma Yousuf d'in kamar zata shige cikin shi shi kuma yana ta wani lallashin ta, suna ganin su Abba Auwal suka nutsu, suka durqusa su na kai gaisuwa, a hankali kowa ya hallara a parlourn da yake Babba sosai, Sulaiman da Walida, Daddy da Fauziyya ustaza wadda ta sha doguwar riga ta nade kan ta da mayafin ta,fuskar ta ba wata kwalliya sosai amma tayi kyau daidai ita,Mama da d'an tsohon mijin ta ne suka zauna a kujera Mai d'aukan mutum biyu, nan aka hau barkwanci da gaishe2 ana tsaka da gaishe gaishen kowa ya kula ba Rasheedah suka zo, Atiyyaerh ce tace, "Abbah ina ummana?" Khadeejah ce ta amshe da cewa, "Tana bacci ne da za mu fito se naga bai kamata mu tada ita ba, shiyasa muka taho," kallon ta Atiyyaerh ta yi tai murmushin yaqe,dan gani take kamar ba gaskiya ta fad'a ba, ana ta hira ta yafici Yousuf suka zame jikin su suka bar gidan, a motar Yousuf d'in da Adnan ya sai masa suka fita, ko da suka shiga gidan sun same ta ne a zaune, Umman nata ta rafka uban tagumi tana kuka dan tin da amarya ta gama mata bayanin me zata dafa take zaune take kuka,ba abinda ya bata ranta sai kalmar ta ta qarshe, akan halittar mijin da take taqama nata ne ita daya, yau ga wata 'yar cikin ta na yabawa  halittar shi a gaban ta, tina hakan ne ya sa ta fashe da kuka, Da gudu Atiyyaerh ta Isa gaban ta ta durqusa tare da kama hannayen ta ta ce, "Subhanallahi, Ummana me ya faru? Me matar can ta yi miki, dan da ganin matar nan za ta yi mugun hali, " Cikin tsananin kuka Rasheedah ta sake riqe hannun Atiyyaerh da kyau ta na qoqarin durqusawa a gaban ta ta ce, " Atiyyaerh ki yafe min, in baki yafe min ba ba zan tab'a ganin daidai ba a rayuwa ta, matar nan so take ta sa zuciyata ta tarwatse, ban tab'a sanin haka kishi yake da ciwo ba sai yanzu, ashe da hassada ce ke d'awainiya da ni, na rasa gane tsakanin cutar hassada data kishi waccece tafi zafi, gaba d'aya ina da su Yousuf, tabbas ina daf da fad'awa jerin masu ciwon zuciya, Atiyyaerh ba kiji yanda qirji na ke bugawa ba," Tana kaiwa nan a maganar ta se ta tina d'azu da Amarya ta dorawa Auwal hannun shi akan qirjin ta,wani kuka ta saki me qarfi kamar wata qaramar yarinya, hakan da ta yi ya yi matuqar ba Atiyyaerh tsoro, kar Umman tasu ta kamu da wani ciwon fa, kamar wadda aka mintsine su ka ga umman sun ta miqe ta daura dankwali ta yi waje,bin ta Atiyyaerh ta yi itama, a kitchen ta same ta, tana qoqarin d'ora abinci, haduwa suka yi ta taya ta suka yi komai a tare suka gama, Atiyyaerh ce ta dinga d'iban abincin ta na sa wa a motar Yousuf , sannan suka shirya har Rasheedah suka nufi can babban gidan. Khadeejah na ganin Suna shiga da warmers na abinci se ta yii murmushi kawai, tare da jinjinawa zuciya mai kyau irin ta Atiyyaerh, dan in itace sai Rasheeda ta gane shayi ruwa ne, bata ce komai ba ta yi mata sannu da aiki, itama bata nuna mata komai ba ta amsa, da yauwa, Atiyyaerh ji ta yi an dafa kafad'ar ta sannan aka ce, "Abun haka ne Aunty Atee ba gayya a aikin? Yaushe ma ki ka bar gidan?" Ta na juyawa se ta ga walida ce ashe matar Sulaiman, Murmushi ta mata kawai, ta ce, "Ba komai amaryar mu ki huta,wataran kema zaki yi naki ai," Tashi suka yi dikan su suka gyara inda za a ci abincin, kallon Rasheedah da ke rakub'e a kujera Atiyyaerh ta yi kamar kazar da kwai ya fashewa haka ta biyo su zalo2, gaisuwa ta kai wajen su Abbah da Adnan da hankalin shi ke kan matar shi,ita kuma sauran yaran suka gaida ta,ana ta hira amma banda ita ta yi shiru kamar marainiya, Auwal na ta saka ta a hirar amma shiru kk ji, dan ita yanzu tsoron su take, in sunkoma kuma su gasa ta, bangaren Mama kuma ta ji dad'in ganin sauyawar ta, a tinanin ta jan girman ta take yi. A haka suka tashi bayan sunci sun sha, mazan suka wuce masjid matan suka tattara wajen suka gyara kowa ta yi bangaren ta, Atiyyaerh ta taya su Rasheedah debe kaya suka mayar mota su Rasheedah suka shiga mota suka bar gidan. Atiyyaerh ta kasa bacci cikin dare, sai juya abinda ta gani take a ran ta, ta San irin rayuwar kana so ka yi abu amma a hana ka, ta yanda ko magana ba ka da izinin yi sai an Hana ka, juyi ta yi ta rungume Yousuf da ya yi shiru ya na kallon sama, a hankali ta ce " Yayah ni kam nace ko za a samo wa Umma yar aiki ne, kasan bata wani saba da aiki ba,gashi yanzu ba ita kad'ai bace akwai kishiya, kar aiki yazo yana mata yawa," "Batta kawai zata iya, aikowa neman ladan aure yake itama a barta ta nemi ladan nata auren" Ya ja ta jikin shi da kyau,ya kwantar da ita, gaba d'aya hankalin ta baya jikin ta, ya na can wajen tunanin halin da Umman ta ke ciki. Cikin ikon Allah Walida da Atiyyaerh nada wata biyar a gidan suka samu ciki,cikin walida nada wata uku, Atiyyaerh na da wata hud'u, ba qaramin murna kowa ya yi ba da samuwar cikin nasu, musamman ma cikin Atiyyaerh Mama ta ji tsoron kar itama ta yi jinkiri irin na Sakeenaah se gashi cikin qanqanin lokaci ta samu,se da ta yi wata rashin lafiya ne kowa ya San ta na da cikin dan boyewa take, wai kunya take ji, Sulaiman ya sha fadawa Yayahn shi hasashen shi na anya Atiyyaerh bata da ciki kamar walidan shi?  Sai Yousuf d'in yace, "kaii anya kuwa ! Yanzu Kai wannan marar ce za a ce akwai d'an mutum? Inaaa bana Jin ta na d'auke da ciki gaskiya" Haka Sulaiman ke barin maganar ba dan ya yarda cewar babu d'in ba,to fa sai da ta yi wannan zazzabin mai zafi aka je asibiti aka tabbatar akwai sannan Yousuf ya yarda,ranar kuwa kowa ya ga rawar Kai a wajen shi ji ya dinga yi  kamar zai hadiye ta dan murna, ta roqe shi ya rage rawar Kai ya qi, Suna barin asibiti basu zame ko Ina ba sai gida, a babban parlour ya kwaza labarin samuwar cikin nata, ta hanyar tsokanar Mama zata samu d'an jikar ta ta wajen su ba da jimawa ba, aiko Atiyyaerh ji ta yi kamar qasa ta bud'e ta shige dan kunya. "To da ka ke ta fad'a wa mutane ai ba ni kad'ai bace, har da Walidah da Afrah," Ta fad'a ta na tura baki, dariya aka Sanya Baki d'aya, Mama na ta godewa Allah a cikin zuciyar ta da bakin ta, ganin yanda ta gama rayuwa da Ahmad ba labarin ciki ya Sanya ta tsoron ko itama zata yi jinkirin haihuwa irin na Sakeenah se gashi abun farin cikin ya samu da wuri, Daddy Adnan kuwa kallon 'yar tashi yake Cike da so da qauna da tausayawa irin ta d'a da mahaifi, fatan alkhairi da Sanya albarka iyayen nasu suka musu, tsabar kunya ko amsawa bata yi ba ta gudu d'aki aka bar Yousuf da amsawa da bada labarin sunan da yake so a Sanya in macece, in namiji ne ga sunan da yake so,dariya kawai akai ta mishi saboda sai halin shi na 'yan fari ya bayyana a ranar, Sulaiman ne me Jin kunya shi kuwa Sam be ga abun kunya ba a wajen. Sanda labarin ya riski Rasheedah kuwa ta yi murna sosai,ta Sanya albarka tare da fatan Allah ya sauke su lafiya. Bayan shekara shida, gidan su Atiyyaerh ya zama babban gidan iyali, Atiyyaerh na da yara hud'u,haihuwar ta ta fari ta samu d'iya mace suka Sanya mata sunan marigayiya wato Sakeenah sai Kuma aka samu Mai sunan Abbah daga baya Kuma ta haifi 'yan biyu mata, Walida Kuma nada yara uku,dika maza, babban dan Afrah a nan gidan yake da zama, mai sunan Adnan, takwaran daddy kenan, khadeejah na da Yara biyu mace da namiji aka sake maimaita sunan Sakeenaah  namijin Kuma Hisham, sai Fauziyyah wadda ke dauke da cikin fari yanzu, Adnan yana fatan ta haifi mace ya Sanya mata sunan Sakeenaah,gani yake in za a cike gidan da suna Sakeenaah ba laifi bane. Atiyyaerh da Yousuf ne Kwance a babbar kujera a parlourn su Suna ta hirar wajen aikin Yousuf d'in Yana Sanar mata qarin matsayin da ya samu ta na ta zuba masa addu'a, suka Jiyo kukan Little wato Auwal qarami, Wanda shi ne autan Atiyyaerh, Rasheedah ce ke d'auke da shi a hannun ta, ta na tafe ta na mitar ya hana su bacci,kwanan ta goma sha uku a gidan ta zo wajen Mama dan jinyar ta saboda fama da take da ciwon qafafu ,kukan da ya sake tsanyarawa ne ya sa Atiyyaerh tashi zaune da kyau dan ta ji shin shi din ne ko yaya? Da sallama ta shiga parlourn ta miqa wa Atiyyaerh shi sannan ta ce, "To ga shi nan na dawo da Kai wajen Ammin taka,dan nema me rikicin tsiya, in sake zuwa ka ce zaka bini, ya hana mutane bacci,sai kace a dawa yake, ba a cikin gida ba," Dariya Atiyyaerh ta yi ta rungume shi sannan ta ce, "Yi shiru Babana na kainaaa, Umma dai haushi take ji ka ce baka auren da ita, shi yasa rabu da ita ba za ka sai mata ragon sallah ba bana" "Yo wannan Banda aukin zuba Kashi da fitsari a tsaye me ya sani?" A hankali Atiyyaerh ta lallab'a shi ya koma bacci sannan ta je d'aki ta kwantar da shi ta dawo, "Haka yake yi fa ko cikin dare sai ya baro d'akin su yazo wajena,Abbin su ya yi ta fad'a wai ni ke sangarta shi shi ya sa ya cika d'afa,ko yaron ma nawa yake oho" "Aiko dai ya cika d'afa da gaske haba, Ina ne baya shiga da wannan siraran qafafun nashi kamar na sauro, amma da ya yi bacci a Wani wajen se an kawo miki shi" Dariya suka yi dika Yousuf ya ce "Ai gobe zai je ya ga budurwar shi can gidan Afrah Yaya zai Kai mu mu yini mata an kwana biyu ba a had'u ba" Yousuf ne ya kalle ta ya had'e gira sannan ya shafa gemun shi da ya ke tsaye a saman fuskar shi, sannan ya ce, "Wai ke waya baki izini ne har ki ke lissafin fita? Tabbas kin tambaya amma ban fa ce na yarda ba," Cike da shagwab'a ta kalli Umman tasu da ke bin su da kallon burgewa ta ce, " Ummaaa," Ta tura baki gaba ta na jiran taimakon Rasheedahn, cikin Murmushi Mai sauti ta ce, "A'a Yousuf, ka barsu su sada zumunci mana ni Rasheedah na ga illar rashin son zumunci a rayuwa ta Wanda bana fatan daidai da daqiqa d'aya Allah ya sa Wani a zuri'a ta ya yi irin wannan halin, ko da wasa kar kana son raba abinda Allah ya riga ya had'a yake son kuma a dabbaqa shi," Cike da ladabi ya amince masu da tafiyar, Umman su na fita Atiyyaerh ta haye cinyar shi ta na murna,dan ita fa a kullum Jin ta take kamar wata qaramar yarinya bata Jin ta girma Sam sam, "Dole ne a baka tukuicin barin mu zuwa unguwa da ka yi Mijin Ablaerh," Tini Atiyyaerh ta hau birkita masa lissafin kan shi, cikin in Ina ya ce, "Daga yau ki dinga tambayar unguwa dik qarshen wata zan dinga barin ki indai wannan ne tukuici na" Ta bangaren Rasheedah da amaryar ta kuwa komai ya wuce kamar Wani saba'ni be tab'a shiga tsakanin su ba, girmamawa sosai Khadeejah ke Yi w [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼  WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH *Ina masu tambayar yaushe za a gama Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA?   To ina mai yi maku albishir da samuwar Littafin KYAKKYAWAR FAHIMTA dan kuwa ya kammalu ya zama ready, ga masu so su mallaki nasu ku yi min magana ta 09031416423 idan an yi payment ɗin #500 ta wannan account ɗin 0006366584 Ja'iz bank, Hamida Sanusi Ahmad,zan tura wa mutum nashi da yardar Allah...kar ku bari labarin Muid'o da Jiddah ya wuce ku💃🏻❤️* *Duk mai son ta koyi yanda zata haɗa kayan gyaran jiki domin  sana'a ta neme ni a 09031416423 Dan ta mallaki LITTAFIN MAIDA TSOHUWA YARINYA A FARASHIN #1000 kacal* Page 32: Yau kwana hud'u kenan da dawowar Adnan daga Dubai,tin sanda ya je balcony d'in shi ya ga me kama da marigayiya be sake komawa ba, saboda ya na so ya gujewa hana ta fita nata balcony d'in dan Shan iska, idan ya ji ya na buqatar fresh air sai ya ja glass door d'in ya bud'e ya ja labulayen a haka iska zata shiga ta na kad'awa gwanin dad'i, ita kuwa Fauziyya zuwa balcony d'in ta ta tsaya ya zame mata kamar ibada,kullum sai ta je balcony d'in nata ta tsaya ko zata ga bawan Allahn nan me kyau da ta gani rannan, takan Sanya kaya masu mutunci wani lokacin harda mayafi dan bata so ya sake ganin ta a yanayin da ya gan ta a baya,to her biggest disappointment Adnan ya dena zuwa wajen,a kullum ta je bata gan shi ba tana shiga matsananciyar damuwa,a ranar sai ta zama wata iriyar shiru shiru bata son kula kowa bata son Kuma a kula ta. Adnan ne sanye cikin qananan kayan da suka matuqar karbar jikin shi rigar shi ruwan chakulan wando Kuma baqi, sai qamshi ke tashi a jikin shi sakamakon feshe jikin shi da ya yi da turarukan shi masu dadin qamshi da tsada, se ya qawata kyakkyawar qafar shi da baqin takalmi, ya d'auki wayar shi ya fita, balconyn shi,da niyyar shan iska, ( Daddyyyy da niyyar dai ganin Fauzy🤣) yana zuwa da minti kamar 4 sai gata, ta fito, sanye cikin riga da wando, sai ta yafe kanta da mayafi, fuskar ta ba walwala ta fito ta tsaya ,dan a zaton ta yauma bazata gan shi ba, amma bata cire rai ba, kallon wajen shi ta yi cikin yanayin da ke nuna saddaqarwa akan ba ganin shi za ta yi ba yau ma, amma mamakin ganin shi da farin cikin ganin shi ya sa ta kusa sake wayar ta a qasa, wani murmushi ta saki mai nuna tsantsar farin cikin ta, d'aga masa hannu ta yi ba tare da ta sani ba, sai da ta kula da abinda ta aikata ta yi saurin saka d'aya hannun ta sauke wancan, dariya ya yi irin ta manya,ya d'aga mata hannu shima, alamar gaisuwa ta masa, da kai da hannu, shima ya amsa, nuni ya yi mata da yana son ya zo wajen ta,itama ta masa alamar amincewa, cikin kunya ta juya tai dakin ta da gudu,tana shiga ta haye saman gadon ta tana tsallen murna, a haka maman ta da take kira Mum ta shigo, tana ganin Mum d'in ta ta tafi da gudu ta maqalqale ta tana murna,cikin 'yar dariya mahaifiyar ta ta ce, " Meye haka Baby zaki balla ni fa," "Mum ya zo yau, har munyi magana, ya ce zai zo anjima,na amince masa da ya zo, mom I can't wait to see him, I want to hear his voice, I want to know him mommy," Cike da fara'a mahaifiyar ta ta ce, "To Alhamdu lilLAAH na maki murna Baby, fatana Allah ya sa ya zama alkairi a rayuwar ki, ya sa SHI NE JARUMIN KI da ki ke Jira, lallai a cikin kaff Wanda suka nemi auren ki ki ka qi su to wannan ya yi sa'a dan da alama da za a bar ki ke Zaki je neman auren shi da kan ki," Cike da shagwaba ta ce, "Mommyyyyy!  Ko da yake gaskiyar ki ne fa,nice na yi sa'a in kk ganshi tabbas zaki fi gane dalilin da ya sa na shiga wannan yanayin akan shi, he is so handsome and gentle, ya hadu Mum, i think i am deeply in love with him, Ya Rabby Allah kasa shine alkairi na,in ba alkairi bane a rayuwata da addini na, Allah ka min sauyi cikin sauqi ba tare da na wahala ba," A sanyaye ta qarasa addu'ar ta, Mahaifiyar ta ce ta shafa kanta, tare da sumbatar goshin ta ta ce, " Allah ya amsa baby, ki kwantar da hankalin ki, rabon ka baya tab'a wuce ka,sannan abinda ba rabon ka ba baya tab'a samun ka,in Allah ya yarda alkhairi ne a gare ki shi yasa Allah ya had'a ku a airport Kuma ya Sanya kuka zama maqota" D'aga kai ta yi ta na Murmushi da Kuma gasgata maganar mahaifiyar ta,suna tsaka da hira ta zabura ta ruga toilet tare da fad'in, "Mum i have to look beautiful Ina zuwa na yi wanka na zo ki min kwalliya," Dariya maman ta ta yi tace, "Baby ai ke dama can kyakkyawa ce baki buqatar makeup, sannan ma ke me Zaki da Kwalliyar tsofaffin, ki gama ki dai zo ki yi da kan ki tinda kin fini iyawa nima watarana ke kike mini," Tashi ta yi ta shiga duba ma yarinyar ta ta kayan da ya kamata ta saka,wata doguwar riga ce,Fara sol,da ratsin golden color a jiki,ta sha aiki ta wajen wuyan ta da hannu, ta tsuke ta sama sai ta yi fad'i sosai ta qasan ta, sai mayafin rigar shima kamar rigar ya sha ado ta d'akko mata, ta feshe mata rigar da turaruka masu sanyin qamshi, ta d'akko mata wani golden color takalmi, mai dan tsini amma ba can ba,ta aje mata,sannan ta yi murmushi tace, " Allah ya bada sa'a Baby bari na je na had'a maku abun motsa baki kafin ki kammala, na fi so na yi da kaina kar mu fara da bashi abincin masu aiki ko" Tana gama magana ta fita,Fauziyya kuwa ta na can tana qalqale fata, kamar ance mata tabawa zai yi ya ji ta fita ko da datti, bayan ta gama ta fito d'aure da towel tana ganin kayan da Mom d'in ta ta fiddo mata sai ta yi murmushi tace, "Thanks Mum," Gaban mirror ta je,ta hau gayu, kwalliya ta yi sama2,wadda ta qara fitar da sirrin kyan ta, gyara gashin ta ta yi, sannan ta saka kayan ta, Masha Allah, duk wanda ya kalle ta dole ya yi marmarin qara wa,tana zira takalmi, Daddyn ta ya kwankwasa d'akin nata tare da sallama ya bud'e qofar ya shiga, kallon ta ya yi daga sama har qasa ya ga yanda ta yi masifar kyau, sai kawai ya tsaya a kan qafar shi d'aya ya na bin ta da kallon tuhuma,hannun shi d'aya a qugun shi sannan ya ce, "Wannan gayun fa, ko dama can kina da masaniyar zuwan baqo wajen ki ne?" Cike da jin kunya ta rufe fuskar ta, murmushi ya yi ya bata hannu akan ta je gare shi, miqa masa hannun ta yi, suka fita a tare, sai da suka je babban parlourn nasu sannan ya zaunar da ita kujerar dake d'an nesa da ta Adnan,da Auwal, dan ya sanar dashi zasu zance,Auwal ya yi ta tsokanar shi, daga qarshe yace in sun gama da nan shima zashi yaga tashi budurwar, kallon ta kawai suke,kamar sunga sabuwar halitta, Daddyn ta ne ya zauna kusa da ita suka qara gaisawa da su, itama ta gaida su, sannan Daddyn ta ya fara magana kamar haka, " Alhaji Adnan, da Alhaji Auwal,naji dad'in zuwan ku matuqa, da kuma abinda ke tafe da ku,kamar yanda na sanar da ku d'azu in dai ta b'angare na ne ban da matsala akan hakan, sai ma fatan alkairi da zan yi a gare ku,amma ina son ku san wani abu d'aya,dik yanda zan baka goyon baya in baka  nemi soyayyar ta ba lamarin ba zai yuwu ba dan ba zan yi mata dole ba,duk duniya bayan mahaifiyar ta, ita nake gani na ji dad'i, itace sanyin idaniya ta, ka ga kuwa duk yanda na kai da son ka in Fauziyya ba ta yi na'am da Kai ba gaskiya sai dai na baku hakuri, ina fatan zaka riqen amanar ta, kuma bazaka tirsasa min ita ba?" " Inshaa Allah Alhaji  ba zaka samu sabanin abinda kk so ba daga wajen mu,kamar yanda na Sanar da Kai nima ina da Yara ka ga ba zan so na yi wa taka ba daidai ba, Allah ya shige mana gaba a wannan lamarin," "Ameen, to ni bari na shiga daga ciki" Sallama ya musu ya basu waje, kunya a wajen Fauziyya kuwa kamar tace qasa bude na shige,duk jin ta take a takure, ta saba zama gaban maza ayi hira ayi karatu amma wannan karon sai take jin ta wani iri,gaishe su ta sake yi suka amsa ta ja baki ta yi shiru,masu aiki ne suke shigo da kayan motsa baki, bayan sun gama ajewa sun tafi, Auwal ya gabatar da kan shi sannan ya gabatar da Adnan a matsayin Wanda yake son ta da aure ba da wasa ba, bayan kammala yad'a manufar su da Auwal ya yi Adnan na ya karb'e ya qara jaddada mata manufar shi akan ta sannan suka yi shiru suna jiran jin ra'ayin ta, cike da kunya ta ce, "Na amince da Kai da Kuma abinda ke tafe da Kai waje na,Allah ya tabbatar mana da alkhairi,ya kare dikkan abin qi a lamarin" Ta na gama fad'in haka ta rufe fuska da siraran yatsunta, "Ameen" Shine abinda suka had'a baki suka amsa mata da shi cikin murmushin ganin yarintar ta,hira suka ci gaba da yi a nan ne ta ke Jin taqaitaccen tarihin shi,se dai ya b'oye mata kamannin da yake ganin ta na Yi da marigayiya gudun kar ta yi zaton ko shi yasa ya zab'e ta, ba zata ji dad'i ba, kowacce mace ta na so a so ta dan ita d'in ake so ba dan wata alaqa ba, Fauziyya ta tausaya mashi sosai, dan ta kula akwai soyayyar matar shi sosai a ranshi,ta yi masa ta'aziyya sannan Kuma ta masa uziri rashin masoyi tabbas ba dad'i,daga baya suka mata sallama suka tafi, bayan ya aje mata tsarabar daya kawo mata, na turaruka. Gidan budurwar Auwal suka je daga nan, ta sha kwalliya da atampa kalar red da fari, sai ratsin baqi,ta yi kyau sosai itama ba laifi ba makusa,se ta yafa farin mayafi a saman Kwalliyar ta, ta qawata qafarta da farin takalmi, dan Auwal ya sanar da ita dawowar  Adnan da yake yawan bata labarin shi,dan haka ta san komai game da rayuwar su, bayan sun gaisa itama ta masa ta'aziyyar rashin Sakeenaah, yaji matuqar dad'in hakan,suka taba hira kafin su tafi itama Adnan ya bata ledar da ya yi mata tsarabar turaruka,sannan suka rabu kowa ya yi gidan shi. Rasheeda na zaune ido tarwai bata ko Jin alamun bacci a cikin su, qarfe goma daidai ya yi sallama ya shiga gidan, "Daga ina kk malam? Ohhh daga wajen karuwar da kk son kawo min cikin gida a matsayin kishiya ka ke ko? To bari kaji na fad'a Maka Auwal, ba zan zauna da kishiya ba, sai dai ka zab'a,ko ni ko ita," Ta kame hannu a qirji tana girgiza qafa,sanye take da doguwar rigar bacci mai santsi da ta daurawa zani a saman ta. "Ke dai zaki zab'a zama dani ko tafiya gidan Abbah, ni dai na wa qanwar ki 'yar aljannah da yardar Allah alqawarin ba saki tsakanin mu, amma in kina ganin zaki tafi ko kina son sakin zan iya baki, aure kam kamar na yi na gama, yanzu ne zaki tantance a Ina ake yin kishi Rasheedah,a tsakanin soyayyar zumunci da soyayyar miji, sannan da wasa kk sake ce ma matar da zan aura karuwa tabbas sai na barar maki da haqora, in yaso kin ji dad'in yin kishin da b'ab'urarren baki, sokuwa kawai," Kuka ta d'ora hannu aka ta rusa, yaran su na d'aki suna jiyo su, kowa dariya fal ciki, Afrah da take ita d'aya a d'akin ta kasa jurewa ta yi,ta kuwa hau kwasar dariya abin ta, dan ji take kamar ta matso da ranar auren Abban nasu, Yousuf bai son ya yi dariya saboda Sulaiman ba'a sirri da shi dan ya na fasa dariya zata Jiyo su,in kuwa  ta ji su se sun sha jarabar ta akan su zata juye haushin uban su, ai ko suna had'a ido suka fashe da dariya a tare,Sulaiman da ba a sirri da muryar shi har waje, tana ji kamar mahaukaciya sabon kamu ta yi hanyar d'akin tana zage2 ta na fad'in sun raina ta,ba laifin su bane laifin ubansu ne daya sai mata raini a wajen su, kafin ta idasa shiga d'akin Yousuf ya yi tsalle ya datse qofar ya rufe da key, ta gaji da fadan ta a bakin qofa tai gaba, dariya suka ci gaba da yi,suna maida zance. A lokaci d'aya, Adnan ya shigo masu da lefe,har na Atiyyaerh shi ya had'a tinda Allah ya hore masa arziqin yin hakan, sadakin Atiyyaerh da  Sulaiman Auwal ya d'auki nauyi, Adnan ya sanar dasu, dukkan su a gidan shi sabo da ya sa aka gina tin kan ya dawo zasu zauna, har Abbah da Mama duk zai dauke su daga nan tsohon gidan,mijin Afrah ne kawai zai dauki matar shi ya Samar mata muhalli dan kar su ga an musu katsalandan a lamuran su,dik da cewar Adnan ya fara yi wa mijin nata tayin komawa sabon gida amma ya nuna masa ah ah ,ya fi so su zauna a inda ya gina da kan shi,dake yana da zuciyar nema shima, ya ce A'a yana da gida,in dai Afrah zata iya zama, d'aki uku ne, kitchen da toilete a kowanne daki, ga toilet a tsakar gida,sai babba parlor da dinning area, ga parking space, da ba zai wuce wajen zama  mota d'aya ba, ba laifi, gidan ya yi sosai,Afrah ta aminta, inda ta nuna mai ita ko da gidan qasa ne zata zauna da shi,albarkar auren suke nema. Sati biyu da kai lefe aka d'aura auren su, gaba daya, an sha shagalin biki ba kadan ba, nera kam ta koka, kuma sun koka rashin Sakeenaah a wannan rana, wanda Rasheedah ce ta fara kokawa har abun ya ba su mamaki, har ma ta dinga yi mata addu'a, mutane ma akai ta yi mata addu'a, 'yan uwan Adnan ma sun nuna bajinta a wannan gagarumin ruguntsumin bikin aure me dimbin tarihi da aka gudanar na tsahon kwana hud'u,bayan kammala dinner da aka gabatar a rana ta hud'u mutane da dama suka koma gidajen su,Wanda za su Kai amare da Kuma Wanda za su kwana washe gari su wuce suna nan ana ci gaba da harkokin azziqi. Amare da angwaye ne zaune a qasa a gaban Abbah ya tara su a babban parlourn shi dan yi musu nasiha da addu'o'i kowa zaune kusa da matar shi,amare sai 'yan koke koke suke na al'ada, Atiyyaerh kuwa kukan ta ya had'a ma'anoni da yawa, tinawa da auren ta na fari, rashin mahaifiyar ta,da  murnar samun auren zab'in ran ta. Abbah da Mama sun ce za su bar angwaye da amare su gama amarcin su kafin su koma sabon gida, Dan haka ba da su za a tare ba. Rasheedah kuwa kamar zata mutu haka take jin kishin nan na tab'a qoqon ranta,cike da takaici ta shige motar Auwal ta na jiran shi ya je ya ja su ya Maida su gida, a gaba ta qame qam ta na jiran ta ji an ce ta koma baya ta sauke kwandon rashin mutunci, ba Wanda ya kula ta, Auwal ya bud'ewa amaryar shi baya ya Saka ta ya koma mazaunin driver ya ja su suka wuce gidan su. Adnan kuwa da motocin shi akai ta zirga zirgar Kai amare da shi kuwa da kan shi ya ke son ya Kai amaryar shi gidan ta, dan daga wajen Dinner a gidan Abbah dik suka taru har Baffanin shi da Kawunan su akai addu'a da Sanya albarka. Bangaren Rasheedah kuwa ko da suka Isa gidan qin fita ta yi a motar ta na so ta ga kwal uwar daka, Auwal be kula ta ba ya je ya kulle gate ya yi addu'a, sannan ya ja hannun amaryar shi ya ce ta kulle gidan in ta shigo suka shige suka barta a wajen,a tsaye ta tadda Auwal ya qanqame amaryar shi kamar za a kwace ta sai Wani shinshinar ta yake yi, amarya kuwa kunya duk ta hana ta kwakkwaran motsi,bakin shi ya Kai saman nata ya sumbata a hankali narkewa ta yi a jikin shi ta na b'oye Kan ta a qirjin shi, motsin Rasheedah ne ya sa amarya ta janye jikin ta daga nashi,tana kallon Rasheesah da ta cika ta yi fammm, Abba ne ya yi masu magana akan yana son ya yi magana da su, ganin irin kallon da Rasheedah ke wurga wa amarya se ya bawa Amarya haushi, dama ta na da labarin Rasheedah kaff Dan haka sai ta koma ta sake lafewa jikin Auwal cikin shagwab'a ta ce, "Gaskiya ka bari sai gobe ka yi mana  maganar please baby, saboda ni dai ....ni daiiiii Ina buqatar mijina yanzu ka ji baby," Cike da shagwaba ta qarasa maganar kamar wata 'yar qaramar yarinyar da bata gama Iya magana ba, gaba d'aya Auwal ya rud'e, ya susuce, janta ya yi kawai suka fad'a d'akin su, Amarya ce ta rufe qofar, tare da watsawa Rasheedah mugun kallon da ta ga ta na bin ta da shi itama, sannan ta ce mata "Yah dai na ga ki na biyo mu ko da ke za a shiga d'akin amarya da angon ne?" Ta ja guntun tsaki sannan ta doka qofar ta shige,wata qara Rasheedah ta sake, ta durqushe a wajen tana kuka, da kan ta ta rarrashi kan ta ta yi shiru,ji ta yi sun tada sallar su ba Wanda ya kula ta,daga nan taji Auwal na yi wa amarya addu'a suka ci kazar da bata San sanda aka siya ba balle sanda aka Kai ta d'akin,to Ita Ina tata kazar? Amma dai Auwal bai da adalci in dai haka ne,  sai hirar su take ji sama sama, dik da dai Auwal ne ke ta zuba amaryar ta koma Jin kunyar shi, can Rasheedah ta ji  ya sauya salon nishin shi da kalaman shi, da gudu ta bar wajen ta yi daki ta na mugun gunjin kuka tare da fad'in, "Na shiga uku ni Rasheedah, dama wannan ne kishi, kenan da gaske Hassada nake wa qanwata uwa d'aya uba d'aya, a da bana jin wannan qunar zuciyar da na ke ji a yanzu, wayyo zuciyata , Sakeenaah ki yafe min, tabbas kin yi gaskiya,abinda kk so na gani na gane a yanzu na ganshi Kuma na gane wayyoo ni Rasheedah na shiga uku na lalace," kuka take kamar ta had'iyi zuciya take ji, kanta kamar zai cire qasa dan ciwo, a nan qasan ta yi baccin wuya, kamar a mafarki ta ji an bud'e qofar d'akin ta an shiga, dukan qafar ta ta ji ana yi kamar tashin ta ake Daga bacci, bata gasgata ko me ke faruwa ba ita dai zaton ta ya bata mafarki take, muryar Amarya ta ji a kan ta ta na fad'in, " Malama ya ya dai naga har yanzu kina kwance ki na bacci baki soma qoqarin had'a mana abin karyawa ba, ko so kk in ya dawo daga masjid ni da nake amarya na fito had'awa? Sarai kin san, ban da lfy, qafafuna ciwo suke,sai na sake shiga ruwan zafi tukunna,zan ji dama dama saboda yanda baby ya hana ni bacci jiya, gaba d'aya gabb'ai na ciwo suke" Hawaye ne ke Malala a idanun Rasheedah da ta gama tabbatar da cewa idon ta biyu ba mafarki take ba, Wani abu ne mulmulalle take ji ya tokare mata wuya tsabar baqin kishin da take ji na dawainiya da ita,gashi wani kwarjini yarinyar ke mata har wani tsoro tsoron ta take ji, Auwal ne ya shigo, amarya na ganin shi se ta yi  kamar miqewa ta yi daga tsugunnon gaida Rasheedah, da sauri ta saki wata 'yar qara, Auwal na ganin haka ya yi sauri ya nufe ta ya qarasa d'aga ta, "Sannu, ni bana ce maki kar ki fito bane, sai kin gama warke wa? Gashi nan zaki qarawa kan ki ciwo ai, wuce mu je na sake sa maki ruwan zafi ki shiga wataqila za ki fi Jin dad'in jikin ki, sannu Allah ya sawaqe," Cike da shagwaba ta fad'a qirjin shi, ya tallabe ta yana shafa bayan ta,cikin kissa da maqale murya ita a dole ga mara lafiya ta ce, "Wai da zuwa na yi mu gaisa da Yaayaah, se na ga kuma kamar sallah ta ke shine na Jira ta idar na gaishe ta," Baki Rasheeda ta saki dan tsananin mamaki, lallai akwai aiki a gaban ta babba ashe?.......... *Woo ke Woo ke  Amaryar Auwal, sha sha'anin ki duniya ce samaaaa*💃🏻💃🏻💃🏻👄👄👄 [07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: Ta bangaren Rasheedah da amaryar ta kuwa komai ya wuce kamar Wani saba'ni be tab'a shiga tsakanin su ba, girmamawa sosai Khadeejah ke Yi wa Rasheedah, yaran amaryar ma gaba d'aya Rasheedah ke kula da su, a kullum bata da aiki, sai yiwa qanwar ta Sakeenaah addu'a da fatan samun rahamar Allah, ta tabbatar da cewa Sakeenah na can ta samu ladan gyara zumuncin da ta yi sanadin shi, ta gode wa Allah da ya bawa Sakeenaah JARUMIN miji kamar Adnan, Wanda ya yi hakuri ya jure rashin 'yar shi a kusa da shi dik da labaran da yake ji na azabtarwa da ta yi mata, ta gode wa Allah da ya sa ta gane halayyar da take na hassada da kyashi da kishi ba abu bane me kyau tin kafin ta mutu, a yanzu rayuwa suke Cike da so da qauna da girmama juna ita da Auwal tabbas Auwal SHINE JARUMIN ta na har abada, ba zata gaji da gode masa ba a bisa hakuri da ya yi da halayen ta marasa kyau. Ahmad kuwa na can ya Maida hankali wajen neman ilimi da kasuwanci, ya na matuqar kewar Atiyyaerh wannan dalilin ne ya sa ya kasa neman mata da kan shi ya aura, sai Hajar ce ta sama mashi mata cikin qannen ta aka aura masa, Yana da Yara biyu Shima mata dika, ta farko ta ci sunan mahaifiyar shi, ta biyu Kuma ya Saka sunan Atiyyaerh, gaba d'aya gidajen ana zumunci da juna daidai misali. *Alhamdulillah....Nan na kawo qarshen novel dina mai suna,KAI NE JARUMI, ina riqon Allah daya gafarta min kuskuren dake ciki,alkairin da ke ciki ya yad'a shi a dika duniya ya bani lada, ya bama makaranta ikon amfani da saqonnin dake ciki na alkairi Ameen.* *A cikin mazajen nan na labarin KAI NE JARUMI wanene Jarumin ki/ka?*