[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  *MAZAUNA GIDA*  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE :1 Garin Kano gari ne wanda Allah ya cika shi da albarka kala-kala wadda baza ta qirgu ba, kamar yanda ake ma kano kirari da Kano tumbin giwa koda me kaje an fika to tabbas fa haka maganar take, in da ustazanci kaje zaka samu wanda ya fika, in kuma da akasin haka ka je nan ma zaka tadda wanda ya fi ka a fagen. Jameelah yarinya ce kyakkyawa ta bugawa a jarida, ta na da kyau mai ɗaukan hankalin mai kallo,fara ce tasss irin farin nan da kowacce mace zata yi fatan ace da ma haka jikin ta yake,ita ba 'yar kowa bace a garin Kano amma Fatar ta kamar gilashi dan ɗaukan idanun mai kallo,unguwar da Jamila take unguwa ce da ke tsakiyar garin Kano, unguwa ce da ta amsa sunan ta ta fannoni da dama musamman kasuwanci, kusan za a iya kiran unguwar da cibiyar kano, gidan su Jameela gidane na haya wanda yake ɗauke da d'akuna kimanin bakwai, band'aki ɗaya, sai tsakargidan da ba wani girma ta cika ba zaure biyu, zauren dake tsakiya anan matan gidan ke sana'o'in su,musamman masu abincin siyarwa da abun sha na siyarwa, tare da saide-saiden 'yan kayan abin amfani na yau da gobe. Zaure na biyu masu ɗaukan talla da kuma 'yammatan dake kaiwa maza abinci dik nan suke zama tare da qalilan ɗin mazan da aka saba da su a unguwa,wasun su ma sukan shiga har zaure na biyu. Iyayen Jameela ba masu qarfi bane, mahaifin ta dattijon kirki ne mai suna Malam Jameel, sai mahaifiyar ta mai suna Ramatu suna kiran ta da Ramai,Jameelah na da qani guda ɗaya mai suna Abubakar suna kiran shi da Bukar, Abubakar irin yaran nan ne marasa tarbiyya baya jin maganar kowa sai wanda zai bashi 'yan canji, su biyu ne yaran da Allah ya azurta Ramai da Malam Jameel. Malam Jameel yana aikin gyaran babura ne a nan unguwar ta su Jameelah,nesa sosai da gidan shi, ba laifi yana iya qoqarin shi dan ganin ya aje ma iyalin shi dik abinda Allah ya hore masa na kuɗi ko abinci kafin ya fita, sannan yana kawo masu na rana da kuma dare ko da babu yawa, Ramai da mijin ta suna zaune lafiya cike da so da qauna tare da kulawa, abu ɗaya ke haɗa su faɗa a Koda yaushe, wannan abun kuwa shine tarbiyyar yaran su, wanda Malam Jameel ba k'aramin qoqari yake yi ba dan ganin yaran  shi sun zama masu tarbiyya, amma ina ba shi da ikon tsawatar masu face Ramai ta shiga ta fita ta hana shi ko ta rusa abinda ya koyar da su, da sun yi laifi ya yi magana zata nuna masa yana ma yara faɗa a gaban maqiyan su za a yi masu dariya, in sun shiga ciki kuma yana yi masu nasiha nan ma tace ba a matsawa yaran yanzu sai su lalace. A haka yake haɗawa har ita ya mata nasiha,ranar haka zata wuni ta na zumb'ura baki da murgud'e-murgud'en baki ita a dole an ci mutuncin ta, dayaa fita zata hau faɗa tana rushe dik abinda ya koyar da yaran shi. Ramai na yin wake da shinkafa na siyarwa ne a gidan,suna yi ne da rana zuwa dare, dan haka Jameela bata zuwa makarantar boko sai ta islamiyyar safe wadda ake tashi sha biyu na rana, in ta dawo tayi wanka ta sha adon ta wuce zauren gidan su wajen talla,a nan zata zubar da dik wani karatu da aka koyar mata a islamiyya dik da cewa kuwa hadda ake yi a makarantar, ita kam kullum sai an dake ta dan kuwa bata iyawa, ko kuma ta gudu bayan aji har sai an gama dukan sannan ta shiga. Kamar yanda kuka karanta tun a farkon labari Jameela yarinya ce data amsa sunan ta Jameelar wato (mai kyau) a shekarun ta sha biyar Jameela ta mallaki dik wani abu da 'yar shekara sha takwas ta ke ɗauke da shi har ma za  a iya cewa ta fi wasu masu shekara sha takwas ɗin zama budurwa, Jameela na ji da wannan kyauwu nata ainun, kusan dan ita yawancin mazan dake zuwa gidan siyan abinci suke zuwa, mutanen gidan dake sai da abinci na matuqar jin kishin Jameela da mahaifiyar ta, dan a ganin su sun kwashe masu masu siyan abincin su baki ɗaya sai na su Jameelah ya qare sannan a sayi nasu. Makarantar su Jameela ba qaramin karatu ake yi ba, wannan shine dalilin da yasa ake kawo yara daga mabambantan unguwanni dake garin Kano, makarantar ta yaye manyan mutane da suka zama wasu a Kano da ma Nigeria baki ɗaya. Umaimah yarinya ce da suke sa'annin juna ita da Jameela ajin su ɗaya hatta da wajen zaman su ɗaya ne da Jameelah ,Umaimah sabanin Jameela ce a halaye da dabi'u da  kuma matsayi, dan kuwa iyayen Umaimah suna da rufin asiri dai-dai misali,mahaifin Umaimah Malam Ibraheem Ayyub aikin gwamnati yake yi,inda mahaifiyar ta Hauwa'u ke aiki a asibiti a matsayin Nurse, tana da babban yaya mai suna Umar, sai da Umar ya shekara goma sha ɗaya a duniya Allah ya azurta Iyayen su da samun haihuwar Umaimah, dan haka akwai tazara sosai na shekaru a tsakanin su. Gidan su gidane abin sha'awa da alfaharin kowanne musulmi, domin kuwa gida ne da ya jiqu da tarbiyya irin ta addinin islama, ga soyayyar junan su da kulawa da lamuran junan su, Yah Umar kamar yanda Umaimah ke kiran shi mahaddacin qur'ani ne shima makarantar da Umaimah take zuwa can ya gama a yanzu yana karatu a jami'ar bayero ta kano, yana karantar medicine  bai da buri sama da ya ga ya zama likitan mata,a yanzu yana shekarar shi ta biyu ne a jami'ar, Umar na da matuqar qoqari kasancewar shi ya samu tubalin karatu mai kyau na haddar qur'ani da sauran littattafan musulinci kafin ya shiga makarantar boko, umar na matuqar son qanwar shi Umaimah baya son dik wani abu da zai taɓa ta in dai ba alkhairi bane,abun cutarwa kuwa Umar na kare qanwar shi daga riskar shi a zarar hankali da tunanin shi ya kai kan shi tun kafin ya kai gare ta. **************************** Kamar koda yaushe , yau ma Jameela ce ta fito daga ita sai daurin qirji daga wanka ta tattare gashin ta cikin hular wankan ta, kasancewar tana da matuqar son rayuwar hutu da gayu shi yasa komai nata take yin shi kamar na wata 'yar hamshaqan mutane ,Jameelah na yawan tunani da jin cewar dama ba a wannan gidan aka haife ta ba kyawun jiki ta kamata ya yi ace ita  'yar masu kuɗi ce,haka ne zai bata damar cin karen ta babu babbaka,duk da ta san cewar akwai masu kuɗin da ke zaune a gidan haya Itama za ta so ace ko za suyi haya zataso ace a irin gidajen nan ne manya masu kyau ba irin wannan gidan yawan ba,rayuwa ta zo mata ba a yanda ta so ta kasance ba,gata duk gayu da kyan ta ta qare rayuwa a cikin gida kamar wannan quntatacce na talakawa, tsaki ta ja da qarfi kamar bakin ta zai tsinke sakamakon ganin baban qawar ta da ke cikin gidan na ta kallon ta kamar zai kife, har wani lashe baki yake yi kamar wani maye,cikin hasala Jameelah ta ce, "Aikin banza aikin wofi ma malam,mutum gemai-gemai da shi ya tsaya yana qurawa 'ya'yan cikin shi ido, Allah ya wadaran naka ya lalace," Matar Malam Buba ce ta fito wadda ake kira da Larai,ganin abinda ke faru wa ne ya sa ta sanya baki cikin maganar dan ba yau mijin nata da sauran mazan gidan suka saba daukar ma matan su magana ba wajen kallon Jameelah, cikin qunar rai ta kalli mijin nata ta ce masa, "Kai dai ka ji kunya da kai da mazan gidan nan marasa kamun kai, ke kuma ba babbar 'yar iska sama da ke ai, daba dan baban ku ya fita ba ai baki isa fito wa wanka daga ke sai wannan tawul ɗin ba iya guwowin ki, ga qwaurin ki nan dik a Waje, dibi d'aurin qirjin ma da an gani an san da gayya ki ka yi shi, in ba rashin tarbiyya ba wace yarinya baliga kamar ki ce a gidan haya  zata yi hakan?  Allah wadaran halin ki Jameelah" Jameela kuwa murgudawa Larai da Buba baki ta yi, sannan ta shige d'aki, ba tare da ta amsa Larai ba,ta na shiga Ramai ta hau yi mata kirarin da ke sanya ta jin cewa ita ɗin wata ce. "Farar mace alkyabbar mata (dik da dai wasu sunce baqar mace) Jameela jarin Ramai, Allah ya kare min ke daga idon maqiya mahassada'yan sa ido, Ameen ya Allah," Tsakargidan Ramai ta qarasa fitowa ta fara tattare kayayyakin wajen, tana yi ta na masifa tana habaice-habaice, ta yi da matan gidan ta had'a da mazan su. Sai da Jameela ta d'auki wajen minti talatin da biyar tana kwalliya da shirin tafiya makaranta, kasancewar yau asabar za a bada hadda shi yasa bata damu da zuwa da wuri ba, dan in ba izu uku daga qasa ba ba zata iya bada izu ashirin da takwas da suke ba, ganin ba za ta iya hadda bane ya sanya ta dagewa  ta iya baqi dan haɗa harufa da wasula ta karanta karatun ta. Sai qamshi take zabgawa ta fito daga d'aki fuskar nan tasha kwalliya gwanin burgewa kamar ba makarantar islamiyya zata je ba. "Larai Mamalo ta shirya ne? Ko nai tafiya ta?" "Ban sani ba nima, nan kika gama zage mata uba da ni kai na, ke da uwar ki da baku son a fada maku gaskiya to ta yi gaba, ai itan ba shegiya bace da zata tsaya jiran ki," "Ta yi wa kan ta, ni na ke d'aga ajin ta ko a makaranta, dan ba ta jirani ba sai me?" Tsaki ta yi ta sa kai ta wuce makaranta, tin daga vakin gate take jin karatun yara, gwanin dadi, jan hijabin ta tayi har zuwa fuskar ta, ta samu ta yi zaman ta a bayan ajin su akan dutsen da ta saba zama har zuwa sanda za  ayi break sai ta shige da sauran dalibai. Ta dad'e zaune tana jira a gama karb'ar hadda, dik ranta ya gama baci, ba ta san ta inda ya biyo ba sai jin bulalai tayi suna kewaye ta, ihu ta zunduma tana qoqarin yaye hijabin data rufe fuska da shi, malam isyaku ya riqe hijabin ta fuskar ya ci gaba da kewaye ta da bulalai. "Wayyo na shiga uku dan Allah malam Isyaku kayi hakuri, kaina ne yake ciwo shine na fito waje na sha iska, wayyooo Baba Wayyoo Ramai ki taimake ni, zai kashe ni," Sake mata hijabin yayi, ya sa hannu a leben shi yana zaro mata ido,cikin takaicin halayen ta ya ke magana, "Shiiii rufe min bakin ki, mara d'a'a kawai, yarinya kamar mai aljanu, dik makarantar nan kin fi kowa rashin ji, wai ciwon kai, a haka da wannan uwar kwalliyar kamar qanwar aljani kike kiran ciwon kai ko? Bari na maki dukan tsiya in yaso ciwon kan gaske ya kama ki da kyau," Wani zillo tayi ta kwace hijabin ta ta keta cikin makarantar da gudu tana zunduma ihu, malamai na jin haka sun san ita ce, ba mara kamun kan da ke wannan abun sai ita. Umaimah na ta karatun ta ta ji an fado mata da qarfi an duqunqune ta, tabbas ta san in ta yi haka ta tsira dan malam Isyaku ba zai dake ta ba gudun kar ya samu Umaimah, best student din shi. Nuna ta ya yi da bulalar fatar yana ta yi mata faɗa, sannan yace ta je gaban allo ta bada haddar ta ko ya sake yi mata wani sabon dukan. Mamalo ke ta dariya qasa-qasa, wani irin ashar din tasha ta lailayo ta maka mata a gaban malamin nasu,wanda hakan  ya jawo sai da yaran ajin suka tsorata da jin zagin, Malam Isyaku gani ya yi idan ya biye mata haka zata yi ta halin rashin tarbiyyar ta da d'a'a a makaranta baki ɗaya, sai ya koma mazaunin shi, tare da yi mata alqawarin mugun duka. Lokacin yin break na yi bayan ta gama cin abincin Umaimah wanda kullum sai tayi santin shi da fatan Allah itama ya kaita matsayin da zata na cin irin wannan abincin mai daɗi kullum. Suna kammala cin abincin ne Umaimah ta juya gefe dan wanke hannu, tana wankewa tana yi wa qawar ta ta nasiha akan abubuwan da take aikatawa marasa kyau,sai ta waiga dan ta miqawa Jameela ruwa itama ta wanke nata hannun ta,amma wayam ta ga ba kowa a wajen, daga kwanon abincin nasu sai ledar awara da Jameelan ta siyo dan su qara, ba su samu damar ci ba dan sun qoshi ainun, dubawa ta hau yi, ko ina dan neman qawar ta ta, cike da mamaki ta buɗe baki tana kallon ikon Allah............. *Jameela 'yan matan zamani, ko me Umaimah ta hango kuma? Ku dakace ni a shafi na gaba inshaa Allahu* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 2: Jameelah ce ke tafe tana ta surutu dan kuwa bata son abinda Umaimah take yi mata sam,cikin quluwa take fad'in , "Ita da an zauna da ita sai ta dinga yi wa mutum nasiha kamar ta maida mutum jahili, a qalla dai nafi wasu sanin Allah karatun nan in dai qur'ani aka ban ba inda ba zan kawo ba indai an yi mana wajen, hadda ce kawai matsalata,kuma itama haddar in an min uziri ai kai na ne baya ja, ita da take ja ba gashi har boko take zuwa ba, haba malam, ni bana san kinibibi a bi a ishe ka." Ji ta yi an bangaji kafad'ar ta da qarfi,cikin sauri ta dafe wajen tare da ayyano wadda zata yi mata wannan ɗanyen aikin a saman titi,cikin masifa ta juya suka yi ido huɗu da Mamalo kuwa nan take ta ce, "Mamalo kina da hankali kuwa? A fa kan hanya muke, shi yasa fa wataran bana son jerawa da ke sai a dinga ganin mutum mara aji, ki bari muje gida, ɗazu ina gani harda ke akai min dariya a aji da malam na duka na, kin san ai zan rama ne indai ni ce baki yi dariya a banza ba sai ta zame maki kuka watarana," Magana take yi cike da yanga, ba mai gane masifa take yi saboda yanda take kare ajin ta wajen samarin unguwar su,jikin Mamalo ne ya yi sanyi saboda tsoron abinda Jameelar zata aikata mata dan ɗaukan fansa,sarai ta san halin Jameela ba a yi mata bata rama ba, sannan bata ɗaukan rainin wayo. Mazan qofar gidan su dake zaune zaman jiran dawowar ta daga makaranta na nan zaune ana ta hira,sun riga da sun san halin ta bata zama har a tashi da ta yi wani laifin ko ta ga za a bada hadda sai ta gudo gida abinta, wasan banza suka tsaya yi kamar ba ita ta gama d'agun kai ba a hanya ta na jan aji,cikin yanga ta ce, "Dan Allah kayi hakuri Babawo, yau na maka alqawarin kai zan fara kawo wa abinci, na ji ma qamshin girkin kamar an gama, kasan girkin Ramai daban ne dana kowa a gidan nan," Wata sabuwar rarumar ya sake kaiwa hannun ta,ita ko tana ta dariya tare da sakar masa hannun yana ta latsawa. "Allah in ki ka min irin na jiya na kama ki zaki san dani ki kayi ," Wani kallo suka yi wa junan su wanda ban gama gane wanne iri bane, dan a iya sani na mata da miji ko wasu masoyan da suka shaqu matuqa ne kawai ke yi ma junan su irin shi. "To ka sakar min hannu na manaaa," "Na sake ki yanzu amma anjima bayan magariba zan zo idan na kama ki ba zan sake ki ba sai na maki hukuncin hana ni zubin farko da ki ka yi jiya sannan na kyale ki, yanzu ki je in an gama ki kawon naci na koma wajen aiki, baban ki daya duba yaga bai ganni ba kamar makaho haka zai hau kirana," "Kaga abinda ke haɗa ni da kai ko Babawo? ka mugun raina baba na," Murgud'a bakin ta ta d'anyi sannan ta fizge hannun ta ta shige gida. Tin daga soron farko masu ɗaukan talla ne ana ta jera abinci a babban faranti da kwali, matan gidan  suna zazzaune a qananan kujeru su na taya su lissafi da jerawa, wasu sun kunna kid'a a wayar su ana saurara ana ayyuka, wasu nata hira da shewa tare da 'yan gulmammaki irin na gidan haya,wata waqa dake tashe a wannan lokaci ta mutanen kudu Jameelah ta ji an kunna, nan take kuwa ta d'age hijabin ta ta baya ta yab'a shi a kafad'a ta hau rawar zamanin da ake yayi, yanayin yanda take rawar sai ya ba wa mai karatu mamaki da tsoron ko aljanu ke motsa mata sassan jikin ta, ihu wajen ya ɗauka da tafi,ita ko sai tiqar rawa take tana bin waqar cike da nishadi da jin daɗi. Sai da waqar ta qare sannan ta faɗa gidan babu ko sallama, buta ta ɗauka ta yi band'aki babu ko addu'a a bakin ta, haka tayi abinda zata yi ta fito.Bayan ta ajiye butar ne ta kalli Lantai dake dafa nata abincin, tace, "Lantai, Mamalo tayi wanka kuwa?" Wani kallo ta bi ta dashi na qasqanci sannan ta ce, "Ina na sani ina nan ina aiki na ni, ki duba mana da kan ki," Ganin irin kallo da amsar da ta samu ne daga Lantai yasa ta saki tsaki mai qarfi cike da rashin kunya ta doka qafa ta d'age labulen d'akin su babu ko sallama ta shige, tana masifar Lantai na yi mata abinda ta ga dama a gidan nan dan ma ta samu ta na neman 'yar ta? Ita fa ke d'aga ajin ta a dik fad'in layin nasu,to daga yau ta daina suje can su qarata da 'yar ta su zata ga kalar qawayen da za ta yi a unguwar, ta na gama masifa ta kalli kwanon da ke gaban ta ta sa qafa ta tura shi gefe sannan ta ce, "Ramai wannan abinci na ne? In dai nawa ne na qoshi ni nan da ki ka ganni sai da nayi nak sannan na dawo gida, baki ga dukan dana sha ba yau a makaranta, amma yayi ta banzar tinda na ci abincn gidan masu kuɗi, ya Allah ka nuna min na shiga daula irin ta su Umaimah," "Ameeen yarinyar kirki in Allah ya yarda maqiyan ki sai sun zama fadawan ki, har shi malam Isyakun dake dukar min ke kamar nace masa jaka na aika masa, ko kallon kalar fatar jikin ki ba zai yi ba ya san ke ba kalar duka bace,so ya ke wataran na wanke qafa na je na masa rashin mutunci, amma ya ci gaba kar ya fasa, watarana ko da miliyoyi aka bashi bulala aka ce ya dungure maki kai ma ba zai iya ba, wuce ki shirya abin ki," Ɗan qaramin towel ɗin ta ta dakko ta daura sannan ta saka wani dan qaramin hijab daya manne mata a jiki, ta dauki soson wankan ta da ruwa a bokiti ta fito tsakar gida nan ta wuce mazan dake diban abinci da abubuwan da suke saidawa a kasuwanni sai bin ta suke yi da kallo wasu ma har leqowa suke yi dan su qare mata kallo da kyau. Ba ta wani dad'e ba a band'akin ta fito, tana ta mita da surutu akan qazantar bandakin nasu na gidan yawa tare da roqon Allah ya nuna mata ta bar wannan gidan gandun ta huta da bala'i.Tana addu'ar Ramai na amsa mata da Ameen. Kwalliyar da ake yayi a wannan zamani ta sheqa ta yi masifar kyau kamar ba 'yar talla ba, daga bisani ta samu wani riga da skirt masu kyau na wani yadin material kalar sky blue, ta daura dankwalin ta a gaban goshi ya zauna dasss kamar hula,skirt d'in da ta sanya kuwa ya matse mata qugu da kyau irin yanda take so ya zauna das a jikin ta ko alamar space babu, ga rigar qarama ce sosai itama a d'ame da fatar jikin ta,qirjin ta kamar zasu fasa ihu su fashe saboda yanda ta matso su, turaren ta ta dauka ta hau fesawa kamar bata so,sai tauna cingam take yi yana qara, yar qaramar lalitar ta ta d'aura wadda ta samo a gwanjo mai hoton biri a jiki mai laushi ta na kammala shirin ta ta fito tsakar gida ta na hura hanci sai ka rantse wani wajen zata mai mahimmanci ba wai tallan abinci ba, ta na fitowa kuwa nan da nan kallo ya dawo kan ta, tin tana fesa turare kowa ke Allah-Allah ta fito, mazan zauren can waje har leqowa suke saboda sun san ta kusan fitowa. Da wani irin taku dai-dai ta qarasa fitowa tsakiyar tsakar gidan, sabon takalmin roba daya dace da kayan ta Ramai ta cire a leda ta watsa mata gaban ta ta na murmushin jin daɗi tare da alfaharin wannan kyakkyawar 'yar ta ta ce, aiko cike da murna Jameelah ta saka takalman tana murmushi Itama. Abincin da take saidawa a soro na biyu an riga an girke mata shi ita kawai ake jira, maza kuwa sai layi suke yi suna ta yi wa junan su rashin mutunci duk saboda ita, masu hankalin su wanda da gaske siyan abinci ke kawo su ci  su tafi ne ke masu nasiha akan su bar yin faɗa kowa zai samu tunda ba su kaɗai ke saida abinci a gidan ba. Tana zuwa ta wani d'aure fuska ta zauna a kujerar da in ta zauna akai take jin kan ta kamar a office take, nan take ta kalli Babawo ta sakar masa murmushi, shima murmushi ya sakar mata da kyakkyawan haqoran shi da suka rine da hayaqin sigari,gira ya daga mata ta sake sakin wani sabon murmushin. Nan da nan ta fara zuba masa abincin sa, wanda baya bata kud'in a wajen sai da dare in ya zo zance a nan ya cake mata kudin ta,banza tayi ma masu kiran sunan ta ta je har gaban shi ta aje masa, sannan ta juya tana kad'a mazaunan ta Babawo ji yayi kamar ya ture mutanen dake wajen ya riqe ta tsam a jikin shi,wani ihu ya kurma sannan ya ce, "Allah ya kaimu dare,bu.....ub....nan kayyasa" Abincin ya ja gaban shi ya dau spoon yana ci yana santi tare da kallon ta, haka tai ta zuba abinci tare da masu taimaka mata tana masifa kamar wadda take basu kyauta,wasu kuma da ta san suna bar mata canji in sun sai abinci sai ta washe masu baki har da fari, su na sane suke bada dubu ɗaya  su ce a yi masu had'in ɗari biyu ko uku su bar mata canji, wasu ma dubu biyu zasu dunqule su bayar ta zuba masu na dari uku suce ta riqe sauran tsabar rashin sanin ciwon kai dan kuwa da damar su ma masu aure ne sun baro gida ba na cefane amma suna kashe wa wadda bata da lokacin su kuɗi. (Sun baro halal din su sun taho su na yaba haramun,matan su da yara a gida kuwa ko za su wanke kan su a inji ba sa burge su, wannan ta wajen da ba halalin su bace shaid'an ya qawata masu ita su na ganin ta ma fi matan su na aure kyau,sannan ita ta fi cancanta su yi wa kyautar kud'in da zai iya ci da iyalan su.) Baban ta ne ya zo zai shige gida yana takaicin yanda d'iyar cikin shi ke wannan sana'a da ya hana ya hana amma anqi ji, ya tabbata tinda ya ganta da wuri haka, ko dai bata je makaranta ba ko kuma ta gudo, dole dai akwai dalilin dawowar ta ta da wuri. Rasa hanyar wucewa ya yi dan kuwa cikin gidan ma kan shi maza da mata ne a cakud'e ana ta hada-hada, ji yayi ba zai iya zaman awa ɗaya bama a gidan, dan haka sai ya fidda dubu ɗaya ya bawa Ramai yace ta qulle masa abincin sa a leda zai koma can wajen aikin shi yaci, aiko ba godi bare na gode ta amshe,haka rayuwar ta take sam bata san meye godiya ba ita, dan haka baya ganewa idan ya kyautata mata shin ta ji daɗin abu ko akasin hakan Zuba masa tayi a ledar ko arziqin kwano bai samu ba a matsayin sa na mai gidan ta miqa masa, ya ko sa kai ya bar gidan yana zuwa soron ya jiyo muryar Jameelah ta na ihun sai an cake mata kudin ta casss ba za ta yarda ba,sai wani fari take yi tana zaro idanu waje. Ganin yanda ta cukuikuye ɗan barno yasa Baban ta daka mata tsawa, sannan yace masa ya tafi ba tare da ya biya kuɗin ba, Cike da rashin kunya haɗe da tsoro-tsoro tace wa Ɗan borno, "Zaka dawo zaka ga ni indai a waje na ne ba zaka sake cin abinci ba, kuma dik inda na ga kuɗi a wajen ka sai na k'wace," "Allah ya shirya min ke jameela," Shi ne kawai abinda Malam Jameel ya iya furtawa cikin takaici ya wuce wajen sana'ar shi, ita kuwa haka ta ci gaba da banbamin faɗa tana bada abincin ta. Sai wajen huɗu na yamma suka tashi daga wajen saida abincin, da wuri abincin ta ya ke qarewa amma bata shiga gida da wuri anan zata zauna har huɗun ko biyar na yamma,zama take su yi ta wasa da mazan wajen da ita da Mamalo da sauran yaran matan gidan da sunan amso kwanuka da kud'in abincin su. Wata ma direct a mazaunan ta namiji zai d'aka mata duka sannan a bata kud'in tana dariya tana fad'in "kaaabaaariiii" wanda bai kai zuci ba. Bayan sun gama sai su ka shiga wajen iyayen nasu suka miqa kudin da su ka yo a ranar,gidan ya yi dan dama duk an tattafi sai masu naci da masu siyan kwantan abinci wajen wanda suka yi kwantai, Mamalo da Jameela ne zaune suna  tatauna yanda za su yi wankan yau. "Kin san me? Yau mu qure wa wanka laya, yaran layin can wai har damu suke takara, atampar da kika saka rannan ta wajen Babawo shi wai Saudatun qasan layi ta sa itama shekaran jiya,ya kamata mu shiga kasuwa fa saboda gaskiya kayan mu sunyi qasa. "Dan Allah fa? Rabu da 'yan wahala kin ji Mamalo duk abin su ba za su taɓa kamo ni gayu ba sai na wuce su biyo baya na ni ce zan dinga raba wa 'yan hassada aiki ba biyan albashi, amma rabu da ita yau zata sha mamaki ,dan kuwa kayan da zan saka kowa bai sanni da su ba ma, zata san dani take gasa a layin nan, sai na gasa ta sosai kamar aya," "Shi yasa kike burgeni tawan, ni kam ko aramin wanda ki ka saka waccan juma'ar kiyi dan Allah, sai na shirya a d'akin ku, kin san Lantai matsala ne da ita ba zata barni ba(kun ji 'yar zamani mai zamammiyar qeya ko?) "Kar ki damu Mamalo kema leshi zan ara maki ki saka yau,ni wannan da zan saka yau kuɗi na tara na siya na kai ɗinki jiya na amso, yau kuma zan buga abuna na ji shegiyar da zata faɗan maganar banza," Su na gama tattaunawa suka sallami juna kowa ta wuce d'akin su, ta na shiga ta cire kayan jikin ta dan ta na so ta huta kafin magariba a yi shirin fita zance kuma,ta na nan kwance ba tare da ta tuna bata yi azahar ko la'asar ba ta hau rera dik wata waqa da ta zo mata a kan ta, (kanta baya ja wajen hadda amma yana ja wajen waqa Jameelah ta daban ce) A haka bacci mai daɗin gaske ya sace ta, kamar wadda aka kwad'awa mari haka ta miqe a firgice a zato na ma tunawa ta yi da bata yi sallah ba sai na ga ta miqe tsaye ta hau sauya doguwar rigar da ta saka kafin ta kwanta zuwa wani lace ruwan zuma farar saqa mai guntun hannu da fad'in qirji, rigar guntuwa ce dan kuwa  da zata ɗan d'aga hannun ta sama ba abinda zai hana a ga cibiyar ta,skirt ɗin rigar ta saka matsattse sosai,sai ta qasa ya bude sosai,ta kafe kan nan da d'auri mai kyau,ga kwalliyar ta nan bata goge ba, Jameelah saboda son gayu na musamman ta sai kayan kwalliya masu tsada irin wanda ake amfani da su a saloon,ta yi hakan ne dan ta nuna wa sa'annin ta ba ɗaya suke ba, da ta yi kwalliya za ka gane da kayan kwalliya masu tsada ta ke amfani, lokuta da dama idan za a yi aure ma har baiwa qawaye aro take yi dan ta nuna masu sune a qasan ta ita ta wuce ajin su. Mayafi siriri ta yafa a kafad'a ɗaya ta saka takalmin ta kalar mayafin, tana wani shan qamshi tare da tauna mutumin nata wato cingam, kudi ta Karb'a wajen Ramai tace zata siyo abinda zata ci yunwa take ji, cike da washe baki Ramai ta ce, "Ga shi, mai nemowa ai in baya ci yana qoshi wataran sai an nemo shi, sai kin dawo," Jameelah na fita tsakar gida ta ɗauki buta ta kurkure bakin ta sannan ta hau kwala wa Mamalo kira, "MAMALOOO ! idan baki fito ba zan wucewa ta fa," Karkad'a jiki take yi ita a dole ta makara kamar wata wadda zata je wata ma'aikatar. Can sai ga Mamalo ta fito sanye da wata shadda da ta ɗan sha wanki, amma ta amshe ta ba laifi tayi kyau sosai itama dai-dai kyaun ta, "Kin ari kaya a waje na me yasa baki saka su ba? ko 'yan baqin cikin iyayen naki sun hana ki sakawa ne? Dama ni dan ki kankaro wa kan ki mutunci ne yasa nake ara maki, ki qure wanka kema a gan mu ba raini amma tunda sun hana sai mu jera kowa ya kalle ki kamar wata mai aiki na,muje ya na iya," Mamalo ta muzanta sosai dan bata ji daɗin abinda Jameelah ta yi mata a tsakar gida ba kowa na ji da gani, amma haka suka ɗauki hanyar zuwa shagunan da ake saida kayan kwalama irin su shawarma da gasasshen kifi da meat pie da sauran su. Su na isa Jameelah ta shiga wani sanannen shago a wajen haka ta hau nuna abinci kala-kala sai ta yi wani fariiii farrrr da idanu tare da lanqwasa harshe tana kad'a qirjin da ba ta gama rufewa dika ba tare da  yatsina ta tambayi farashi,a haka suka gama siyayyar su a wajen suka faɗa wani shago da ake saida qananan kaya nan ma ta sai abinda za ta siya suka ɗauki hanyar komawa gida mai nisa, dan bata so su isa gida da wuri,ta hanyar makarantar su suka bi har an tashi yara kowa ya wuce gidan su sai qalilan da ɗaukan su ake yi su na zaune a waje ɗaya su na jiran iyayen su dan kuwa magariba ta gabato, su na isa layin su ta qarasa cire siririn mayafin da ke kafadar ta ta hau jujjuya shi a hannun ta ta na wani juyi da jikin ta ta na lilo da ledar hannun ta,a dai-dai inda suke zama su yi zance ta ga Babawo babu b'ata lokaci kuwa ta tsaya a wajen suka zauna, Baban ta kuwa na tsaye a qofar gida dan bai jima da dawowa ba ya ga qofar gidan da duhu wanda ya san ya saka k'wan fitila shekaran jiya da safe amma gashi yau ma har an samu wanda ya fashe shi, sai duba wajen k'wan lantarkin gidan yake yi yana mamakin kusan koda yaushe in ya saka k'wai a wajen sai an samu mai fashe shi, amma har yau ba a kama me aikatawa ba ya na gama dubawa ya shige gida ba tare da ya san ya baro 'yar shi a bayan shi ba. Zaune suke su na ta hirar soyayya abun su Mamalo ma na tsaye tana masu hira itama, anan suka cinye abinda suka siyo ta duba sabuwar shimi da panties ɗin da ta siyo a gaban Babawo ko kunya bata ji shi kuwa sai yabawa yake yi tare da fatan watarana ya siyo mata wanda suka fisu kyau ta saka a gaban shi ya gani,suna gama ganin kayan Babawo ya fiddo naman daya siyo mata suka hau ci. Kafin a kira sallar isha'i naga 'yan mata na ta fitowa cikin wanka da kwalliya kamar ana wani kwarya-kwaryan biki a layin cike da mamaki na buɗe baki ina bin su da kallo.......... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻. MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 4: kamar kullum yauwa da safe haka Jameelah ta tashi ta kammala dik wani shiri data saba yi ta shirya dan zuwa makaranta, tare da qudirin yau zata sai dik abinda take so a lokacin break,idan ya so daga baya sai ta sanar ma da Umaimah tana son ta bita gidan su ranar juma'a, so take dai sai ta ga gidan su Umaimah hankalin ta zai iya kwanciya, babbar motar da ake kawo ta ake ɗaukan ta na matuqar girgiza ma Jameela zuciya, ga irin cimar da take kawo masu makaranta kullum kala-kala na sake tabbatar mata da su Umaimah masu kuɗi ne,dan kuwa haka take zuwa musu da kaji a cikin abincin su suci har su qoshi, sannan wataran ruwan roba take zuwa da su gora biyu zuwa uku, ga kudi da bai gaza dari biyu ba ita ko hamsin in ba ta zara a na abinci ba ba mai bata. Karatu ake ta zabgawa a ajin nasu ko da ta isa,kowa ya maida hankalin akan abinda ake koyarwa banda Umaimah wadda ta tattara hankalin ta gaba ɗaya akan qirjin Jameela, wanda a ran ta take matuqar mamakin cikar su, a iya tinanin ta shekarun su daya amma ita da tafi Jameelah girman jiki bata da cikar girji irin na Jameelan, ikon Allah kawai take ta kalla. Kamar daga sama ta ji muryar Jameelan, cikin kare baki dan kar a gan su ta ce; "Yaushe wai zaki kai ni gidan ku ne? Ko dai baki son naje cin arziqi nima? Lallai Umaimah ban taba sanin ke marowaciya bace sai yau, ashe dik abinda ki ke ban a iya nan ne ba zaki iya gayyata ta gidan ku ba? Himmm duniya kenan, yau da ace nima 'yar wani ce da tini kin gayyace ni, shike nan, na gane irin zaman da zan nayi dake daga yau," Cike da mamakin yanke hukuncin da Jameela tayi a kan ta take kallon ta, "Kinyi kid'an ki kin yi rawar ki,kin taɓa ji nace bana son na kai ki gidan mu, Kawai daga fara magana sai ki qarasa ta da kan ki? Ni ba wai bana son kai ki gidan mu bane,halayen da kike yi ne bana so,haka kawai na je na kai ki gidan mu ki jamin faɗa, gaskiya shine dai matsala ta dake" "Indai wannan ne matsalar ki an kauda ita,yanzu yaushe zaki kai ni?" "Ko rannn.... wayyoo Allah malam," Saukar bulala ce da ihun Jameelah ya karad'e wajen, nan da nan kuwa Umaimah ta nutsu ta shiga hankalin ta saboda tasan dukan akan ta zai qare daga qarshe, dan kuwa Jameelah ta riga da ta jawo mata duka, shirun da ta ji ne ya tabbatar mata ita ba za a dake ta ba. Qunquni Jameela take tayi ta na fad'in, "Yarinya ba dan ina son naje gidan ku ba ko dan na bada labari kuma na ci daɗi nima da sai na fanshe dukan nan a jikin ki yau," Bayan an tashi break, Mamalo ta ce ma Jameela, "Qawa zo muje ki ji, ki yi sauri akwai labari, na jira ki mu taho aka ce ai kin yi gaba," "Ban na sha mutuniya ta, nima ki ji nawa," Nan kowaccen su ta faɗa  ma 'yar uwarta yanda suka yi da saurayin ta, cike da zumud'in jin qarshen yanda Babawo ke ma Jameela wasanni Mamalo ke kallon ta, sai da ta gama ji ta d'akko dubun ta ta nuna wa Jameelah, aiko Jameela na gani ta ce, "Yauwaaa ya kamata ki fara tarin kudin ankon Furairah, kinga kar azo baki dashi, dan ke ba kullum kike samu ba," "Waya fada maki? Ai yanzu Sadeeq yace ina fada masa komai nake so, kuma zai dinga ban dubu daya kullum, amma kin san meke damuna? Ni nafi son muna irin soyayyar ku, amma shi kwata-kwata ya qi ya na abu kamar wani baqauye" "Wai me kuke ta tattaunawa ne haka? Kunyi shiru, ko kuna bitar karatun dazu ne," Wata harara Mamalo ta watsa wa Umaimah da ta matsa kusa da su, Mamalo na jin kishin yanda yanzu Jameela ke qawance da Umaimah sosai,cikin washe baki Jameelah ta ce wa Umaimah, "Babu komai zauna muyi hirar dake," Bayan sun gama hirar su suka hau cin abincin su Umaimah, daga nan suka je wajen yin break suka dinga siye-siyen kayan kwalama da abinci, a wannan ranar sai da suka ci suka yi nak sannan suka koma aji. Lokacin da aka tashi kowa sai ya tafi gida,cike da zumud'in zuwa gidan su Umaimah Jameelah ta koma gida, dan haka tin a ranar ta ware kayan da zata saka dik randa zata je gidan su Umaimahn, kaya ne masu kyau da tsada ta ɗauka ta ajiye a saman jakar kayan ta,dama ita ta na tanadin irin kayan fita unguwa na ba raini ɗin nan da kud'in talla ko na samari take siyan irin kayayyakin, tare da taimakon Ramai za a mata dinkin na garari dan kuwa watarana ma Ramai ce da kan ta zata kai mata tace wa tela ayi mata dinkin 'yammata da ake yayi dan kuwa 'yar ta ta 'yar zamani ce, haka za a yi mata dinki ko a auna ta dik Ramai na gani, matsattsen dinki daya bayyana kowacce surar ta amma sai Ramai tana jin daɗi har cikin ran ta ta na jin cewar diyar ta kyakkyawa ce da ba kamar ta a layin har ma da layin dake kusa dasu. Cikin ja da baya ta ke kallon kayan da ta fitar dan zuwa gidan su Umaimah Jameelah ta ce, "Toooo yanzuuuu ina zan samu hijab babba, mai dan kyau da zai shiga da kayan nan, ina da takalmi da jakar da zan saka 'yar qaramar can dana siyo a gwanjo, kaiii Allah yayiwa gwanjo albarka, gaba daya sai ka siya kai luf a bayan shi, a zaci dama abu na ka ne tin fil azal,Allah dai ya biya masu gwanjoooo, Ramaiiii!" Ta k'wala wa mahaifiyar ta kira da ke tsakar gida, babu b'ata lokaci kuwa ta amsa kamar ita ce 'yar ba uwa ba. "Na'ammm 'ya guda ɗaya tamkar zinare ya aka yi?" Cikin shagwaba da bubbuga qafa da wani yauqi da tasan yana qara mata kyau ta burge dik mai kallon ta take maganar, hakan kuwa na tasiri a zuciyar Ramai sai tana ganin ohhhh ni nake da wannan kyakkyawar d'iya, domin Ramai in ba fari ba gaskiya sai a hankali ce, amma kyau da hasken fata na wajen Baban Jameelah, dik da dai yanayin aikinsa ya sa ya yi duhu. "Ramaiiii ! kinga wannan qawar tawa Umaimah ce ta gayyacen gidan su ranar juma'a kuma banda hijabin sakawa, dan gidan su gidan Ustazai ne bana son zuwa da mayafi hijabi nake so na saka dan Allah ki ban kuɗi na d'inka hijabiiii, tayi tayi naje gidan su saboda rashin hijabi yasa ban je ba har yau," "Me yayi zafi ina da kuɗi kuma kece me nemowar muje ciki na baki" Da murna a ran ta tabi Ramai suka koma dakin, amma a fuska sai ta nuna kalar shagwab'a da tausayi kar ace dama son amshar  kuɗi kawai take yi tunda Ramai ta san halin ta sarai, ba zato babu tsammani suka ji muryar Bukar na fad'in, "Ni ma Yasin sai an ban wani abu, kullum sai a dinga bata dik abinda take so ni ba me bani, inna sata ace min b'arawo, ai in ba a son yaro ya ɗau abin da ba na shi ba a dinga bashi abu in yace yana so," "Sannu ubana, nace sannu ubana, ga ta nan, dube ta daga sama har qasa wa ka taɓa gani me kyau a dik layin nan sama da ita? Amma ba talla take yi ba dan a rufa wa kai asiri? Nan take sai da abinci ta sama mana wannan kud'ad'en da ka sa wa ido, kai ruwan piyawata nace zan dinga baka kaima kana zama qofar gida,da aka yi sau ɗaya ka tattara kud'in kai gaba kasha maro abin ka,to tsoron ka nake yi da zan sake baka kid'i na? Ka fita daga ido na in rufe Bukar, ka iya faɗan min abinda ya zama wajibi iyaye su wa yaran su amma baka iya aikata wanda yara zasu ma iyaye dan suna sama masu kudi ba ko,bar nan kan na ma rotse dan uban ka," "Habaa Ramai ko hamsin ki bashi mana ya sai wani abun ko ɗari ce ma haka," Dan bata fuska ta yi kafin daga baya ta d'au wata tsohuwar ɗari ta wurga masa, da murna ya dauke yana mata kirari, sai ga baki an washe, ana cewa "Ja'iri ! sauran a sai sigari kuma, da kudina dai aka sai sigari ban yafe ba," Ficewa yayi yana mata dariya, har sholi an sha da kudin ta dan sigari, yafiyar ta ba abinda zata yi masa a ganin shi. (Ina fatan ko da ban sharhi ba kun fahimci saqon wannan kalaman nata, ta kira shi ja'iri, da damar mutane suna ce ma yara ja'irai wanda ya na nufin 'yan wuta kenan, da wasa ba a sani ba ana kiran yara 'yan wuta, sannan tace ma yaro mara jin magana bata yafe ba, ko sanin amfanin ta bai ba balle yafiyar ta a gare shi, bare har ya kiyaye me tace kar ya halaka,kenan in ya aikata abinda tace masa din Allah zai iya sawa ya qara lalacewa, tinda tace bata yafe ba? Mu kiyaye mu kula da bakunan mu akan yaran mu) Hijabi mai kyau Jameela ta siyo kalar ja mai shiga sosai, dan kalar atampar ta kenan, so take ta burge sosai, amma dole sai ta nuna ma iyayen Umaimah su talakawa ne dan a tausaya mata, sosai. ****************************** Rana bata qarya sai dai Uwar d'iya taji kunya, yau juma'a kuma yaune ranar da Jameela zata je gidan su Umaimah, da kayan ta ta tafi a jaka, fuskar ta yau ba kwalliya, asalin kyaun ta ya bayyana, sai qamshi take zubawa, haka ta saka uniform ta tafi makaranta sai taunar cingam take yi. Ta tinama Umaimah zancen binta gidan su da za ta yi yafi sau bakwai, Umaimah dariya tai ta yi mata, daga baya tace, "Ina sane da wannan ranar Jameela dan kuwa na sanar ma da Mum din mu, ta san da zuwan ki, yau kina da sa'a dan kuwa Dad na nan shi ma, Yah Umar ne ban da tabbas din zaman shi a gida, amma ina fatan ya ga babbar qawa ta shima a yau," Tsaki mamalo ta yi dan jin ance ma Jameela itace babbar qawar, cikin jin haushi Jameelah ta kalli Mamalo ta ce, "Dalla meye na yi wa mutane tsaki? In ba za ki ji hirar mu ba ki bar nan ba wanda ya ajiye ki," Washe baki Mamalo tayi ta dafa kafad'ar Jameela, Jameela ta zame hannun Mamalo da ke kafad'ar ta, umaimah kuwa ta gama gano mamalo, dan haka kawai sai ta buɗe Hadith ɗin ta tana bita ta yi masu shiru, Mamalo sai hirar gida take yi masu tana ta zuba qarya, anyi kaza da kaza a d'akin su, Jameela kuwa bata son ai ta bada labarin gida a makaranta yara su gane talaucin su, ana mata kallon babbar yarinya,cikin hasala ta sake cewa Mamalo, "Dalla ki yi mana shiru, kamar a gidan ku ne kawai ake cin biredi da bota," Dariya aka dinga yi wa Mamalo ta yi abin tausayi, ta d'au jakar ta ta koma nesa da su ta fara karatu, Jameela sai kuma ta ji babu daɗi, amma haka ta basar ta ci gaba da manne ma Umaimah. Drivern su Umaimah ne yazo daukan su ta buɗe mota ta shiga, Jameela data sauya kaya a aji bayan kowa ya fita ta buɗe ɗayan side d'in ta shige, Mamalo na tsaye zuciyar ta baqqirin ji tayi dama ace itama iyayen ta na da kuɗi dan kawai ta burge Jameela, tana son ta da abota sosai, haka ma jameelan amma tafi son umaimah domin kud'in su. Suna tafe tana ta ganin unguwannin masu kudi tana ta santin gidajen a ran ta, amma a fuska ba zaka taba gane irin son abin duniyar da qaramar yarinya irin ta take ɗauke da shi ba. Wani qaton gida taga an nufa, iska ta shaqa mai daɗi ba mai warin kwata da sigari da hammata ba na unguwar su, wata kwallar kwad'ayi ce ta taru a idon ta a zuci take roqar Allah daya fito da su daga wancan lungun nasu ya kawo su sarari irin wannan. "Jameela menene Ko baki son zuwa ne? Ko wani abu ke damun ki," Cikin sauri ta buɗe baki tace, "Ni ce bana son zuwa nan din? Hauka nake da zan ce bana son zuwa irin wannan wajen? Shiga gaba muje ki gani," Da sauri ta bi Umaimah, tana sake qarewa kyakkyawan gidan Kallo. Bayan sun shiga cikin gidan ne Jameelah ta samu qasa gefe da inda Iyayen umaimah suke ta zauna kan ta a qasa take gaida su, sun yi matuqar yabawa da tarbiyyar ta, sun ji daɗi da 'yar su ke da qawa irin Jameelah mai kamun kai da matsuwa, sunyi sunyi ta zauna a kujera amma taqi. Kayan motsa baki aka kawo mata kala-kala dakin Umaimah saboda ta qi shan ko ruwa a gaban iyayen Umaimahn, tana shiga taga gado babba da kayan alatu irin wanda take mafarkin mallaka a d'akin ta a matsayin ta na budurwa me tashe, ji tayi kamar kar ta koma gidan su, zama ta yi a kan gado, ta yi juyi ta sake juyawa, can kuma ta kwanta ta yi lamooo, daga baya ta miqe da sauri ta sauka qasa ta hau cin abubuwan da aka kawo mata ba qaqqautawa, Umaimah na ta yi mata dariya. Allah Allah take Umaimah ta dan fita ta kwashi lemukan ta sa a jaka, amma umaimah ta gano ta sai tace, "Kar ki damu qawata kici wannan, in zaki tafi gida zan baki wasu," "Dan Allah? Yanzu kuna da irin wannan da yawa kenan? Ai kuwa zan din ga kawo maku ziyara akai akai," Dariya Umaimah ta dinga kwasa wajen Jameela. Suna zaune mai aiki tayi kiran su akan suje a ci abinci cike da zukud'i Jameelah ta miqe, sai bayan ta yi gaba sai ta tsaya sai da Umaimah ta wuce sannan ta bi bayan ta, a table ta gan su zaune, kasa qarasa wa ta yi saboda sumar da tayi a tsaye a wajen, jiri ne taji yana d'iban ta, hankalin ta ya kai qololuwa wajen karkata wajen table din da abinda ke tattare da shi, Umaimah na taba ta dan su yi gaba taji ta taho mata gaba ɗaya kamar zata faɗi, da kyar ta tsaida kan ta ta samarwa kan ta natsuwa, qafa ta daga zata yi tafiya amma taji ta mata nauyi, idon ta kuwa ko qiftashi bata yi dan gani take kamar da ta qifta shikenan ta daina ganin abinda ke gaban ta da ya fi komai kyau a idanun ta da zuciyar ta............ [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 3: Wasu 'yan matan tabarmi na ga suna shimfidawa wasu kuma sallaya, wasu kuwa kujerun zaman gida('yar tsugunno) suka dasa guda biyu su ka zauna da samarin nasu, Mamalo na ɗaya daga cikin wanda suka shimfid'a tabarmi domin kuwa saurayin ta Sadeeq mutumin kirki ne yana matuqar son ta auren ta yake son yi, dan ma iyayen ta sun tsaya masu wala-wala da tini ya turo, daya sako maganar aure sai Lantai tace nawa ma Mamalon take? dika-dika shekarar ta sha biyar, me zai tsinta a wajen ta? Dole haka Sadeeq ke hakura ya bar maganar ya yi ta fata da addu'ar Allah ya kai su lokacin da zata qara girma ta kai aure ya aure ta su yi zaman aure. Qarfe 9: 45 na dare baka jin maganar kowa sai mutsu-mutsu da 'yan dareraiku sama-sama a wajen 'yan mata da samarin layin su Jameelah, soyayyar shan minti kawai ake zubawa a lungun nasu, Jameela da Babawo kamar zasu shige cikin junan su tsabar mannuwa da suka yi da juna,ba qaramin jin daɗin rigar da tasaka mai faɗi wadda ake kira da ziro hannun ka masoyi Babawo ya ji ba, hannun sa ya zura ya na ta zare idanu kamar ya biya sadakin ta. Mamalo kuwa ran ta in yayi dubu ya baci saboda Sadeeq ba abinda yake yi mata da ya wuce wa'azi akan abubuwan da ya ke ganin matan layin na su na aikatawa, juya kai tayi ta yi fari farrr da ido sannan ta murguda baki tare da sakin siririn tsaki sannan ta ce, "Wai kai dan Allah Sadeeq yaushe zaka waye ne? Ka duba fa ka gani kowa sai jin daɗin shi yake yi, amma kai ka wani qame a gefe wai kai ustaz, ka mori quriciyar ka tin kafin tsufa ya riske ka,haba malam ! A yi mutum gaba ɗaya shi bai san mene ne soyayya ba? ko dan kalaman nan na soyayya ni baka jiqa ni da su, ko irin yanda saurayi ke fad'awa budurwa yanda yake ji game da ita da yanda zai mata bayan sunyi aure kai baka iya ba, gaskiya ni da sake,ba zan dauka ba, ka waye kawai mu mori rayuwar mu," Sadeeq baki sake yake kallon ta a qalla ya bata kyawawan shekaru takwas amma yarinyar nan bata ji nauyin sa ba ta rufe ido tana fada masa yanda zai gudanar da soyayya, lallai wannan zamanin namu na cikin rud'ani, wa'azi ake yi akan yanda lamura suka tab'arb'are, fadakarwa ake yi amma kamar ba a yi. "Yanzu dan Allah Fateema abinda kika faɗa bai maki nauyi a bakin ki ba? Ko kunyar faɗa min waɗannan kalaman baki yi ba? Iyayen ki cewa fa suka yi na basu nan da shekara biyu ko uku, ke har yanzu yarinya ce amma shine....." "A ganin su ba ! ni fa da ka ganni nan ba abinda ban sani ba, in zaka sake jiki muci soyayya ka sake, ba dan ma ina son ka ba ko bi ta kan ka zan yi ne? ina son ka fiye da yanda nake son kaina, kuma bazan iya rayuwa ba kai ba, shi yasa ma kaji ina fada maka me nake so a yanzu, banda haka aje ka zan yi a gefe na nemi wani," "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un ! me kk ce Fateemah ? Kamar ke ki ka iya fad'in zaki aje ni ki nemi wani saboda ba na yi maki muguwar soyayya? Yo muguwar soyayya mana wannan ai ba soyayyar gaskiya ake gudanarwa ba sam,Wai me ki ka dau soyayya ne ma tukunna? Soyayya fa shine na kare maki mutuncin ki ba na zubda maki mutunci ba kafin aure, inna gama tattabe ki a waje me na tanadarwa kai na a gidan? In muka gama soyayya a waje in mun je gidan meye sabo da za mu yi dan debewa kan mu kewar shekarun rayuwar mu da zamu yi a tare? Kiyi tinani, ni kam anyaaaa Fateema.... anyaaaaa?" "Anyaaa me? Nace Anyaaaa me? Kana kokwanto akaina ne? Bari ka ji ita soyayyar nan dana ke fada maka ba fa wai wani iskanci za mu yi ba,kawai dan simba da runguma ne, ka dubi yanda Jameela suke yi ita da Babawo mana abun nasu gwanin sha'awa, ji dan Allah in muka jera da ita qirjin ta taff da dukiyar fulani, amma ni sai kace allo, gaskiya ni baka kyautamin sai da safe, ba zan zauna in sha sanyin banza da sauro ba ban amfana da komai ba sai shegen wa'azi , sai da safe," Cikin fushi ta shige gida bazar bazar, da matuqar mamaki Sadeeq yabi bayan ta da kallo, kanshi yayi mugun d'aurewa da abinda ya faru yanzu, sai tunani yake yi anya sanda bai samu zuwa ba ba wasu samarin dake zuwa su lallatse ta kuwa? " Aiko da sakel, daga yanzu kullum zan dinga zuwa zance dan ba zan bar wasu banzayen su lalata min ita ba tunda ta na so na kamar yanda nake son ta," Tina sanda suka fara haɗuwa da ita yayi, a lokacin sun taso daga islamiyya ita da Jameelah, kula da rashin kamun kai irin na Jameela ne ya sanya bai ce ita yake so ba dik kuwa da kyaun da take dashi, amma yanzu Mamalo na so ta goge masa haddar kan shi, k'wafa ya yi sannan ya ce, "Dik laifin wannan Jameelan ne, dan komai take yi shi Fateemana take son daukewa, zan yi qoqarin raba su kuwa inshaa Allahu dan na more wa soyayya ta cikin tsafta," Muryar Mamalo ya ji cike da tsiwa ta na kad'a qugu a saman kan shi ta ce, "Wai malam baka tafi bane? Ni to ka tashi zan shiga da tabarma ta," Tana wani jijjiga, kallon ta yayi yayi murmushi kawai, hannu ya sa a aljihun shi ya na d'akko abinda zai bata, tana ganin haka jijjigar ta koma rausaya,tana wani abu kamar mai jin kunya, kuɗi ya d'akko a aljihun shi dubu ɗaya sabuwa fill ya miqa mata,cikin sauri kamar zata haɗa da hannun shi ta amshe ta hau godiya, "Dan Allah ki min alqawarin daina kula dik wani saurayi in ba ni ba," "In dai kayi alqawarin kawon kalar wannan kullumm ba wani qato da zan dinga kulawa wannan alqawarin mamalo ne, kasan kuwa bana karya alqawari inna dauke shi," "Indai wannan ne kin samu, sai da safe abar qauna ta," D'aga masa hannu tayi suka yi sallama ta nad'e tabarmar ta, zata shige gida kenan ta kalli dai-dai inda su Jameelah suke a duhun, dariya ta ji suna yi qasa-qasa, hankalin ta ta tattara gaba ɗaya tare da qura ido qurr, Jameela ce kaɗai take iya hangota, Babawo kam bata ga ina yake ba ma a wajen sai dai tabbas ta san su biyu ne a wajen,haka ta dinga gwale ido ko zata iya ganin shi amma bata gan shi ba, a zaton ta ko ya tafi ma, dan haka kawai sai ta ɗauki hanyar yin wajen  Jameelan, da sauri Babawo ya miqe daga qasan Jameela daya shige, ita kuma taja skirt ɗin ta ta rufe qafar ta ta na b'ata rai,cikin masifa ta ce wa Mamalo, "Meye zaki zo ki wani tsaya mana akai," "Wayyoo kuyi hakuri dama da ban ga Babawo ba na zaci ya tafi ne, sai da safe a ci soyayya lafiya, na baki labarin gobe," Can qasan maqoshin ta Jameela ta amsa ta, tana tafiya Babawo ya maida kan shi inda ya fito. Sai da ya kai wajen minti goma sannan ya fito suna ta dariyar jin daɗi, kudi ya debo canji-canji kimanin dubu biyu, ta tsaya tana kallon shi a ranta tace, 'matsiyacin banza kawai kullum sai dai ya zo ya ji daɗi dani amma ba wani kudin arziqi da yake bani' A zahiri kuwa sai ta kyab'e baki ta ce, "Nawa ne nan kuma? Kasan na tsani canji-canjin nan ko?" "Sorry babyna dubu biyu ne fa shine kike bata rai? canjin ne kawai amma ai yafi na kullum yawa yau ko?" Ɗan sake fuska tayi ta zaci yauma dubun ce, ahhh lallai dole ne ta d'agawa Mamalo kai dan a da kullum ya zo dubu ce ko dubu da dari biyar, to yau gashi an samu ci gaba. Haske ne ya bayyana ya haske masu idanu daga ita har Babawon,daga baya hasken ya tsaya akan Jameela, mahaifin ta baya son ya daga murya aji yana magana da d'iyar ta shi,dan haka sai ya dinga haska ta yana kada fitilar. Cike da zumb'ura baki ta tashi tana doka qafa, Babawo kuwa da sauri ya bar wajen yana kare fuskar shi. Kewaye baban ta tayi ta shige gidan nasu wanda Soron cike yake da yaran gidan samari, suna ta bacci, haskawa yayi ko zai ga Bukar a wajen kwanciyar shi amma ba Bukar ba labarin shi, kad'a kai yayi yana nemawa yaran shi shiriya a wajen Allah, baya taba zagin su ko tsine masu, shi dai fatan shi su shiryu. Har ya sa qafa zai shige dakin su, yaji hayaniya, ana fad'in, "Dalla kar ka fad'o min a ka ni, kayi can ga shimfidar ka can Ramai ta yi maka," Bukar kuwa sai hayaniya yake yi irin na 'yan shaye-shaye, dan kuwa ba mai gane me yake faɗa, fari tasss aka haife shi kamar Jameela, amma saboda shaye-shaye ya koma baqi, musamman bakin shi da hannayen shi. Dika-dika shekarar Bukar sha Uku amma ba irin iskanci da dabar su basu saka shi yi, dan yana qarami da shi suke amfani ya je ya masu 'yan qananun sata,sannan ya yi masu aiken siyan kayan maye, daga nan har ya fara sha shima. Kad'a kai Baban su jameela yayi ya qarasa shigewa d'akin su dan kuwa ba zai je kallon takaici ba, tinda ya dawo gida to Alhamdu lilLAAH. Ya na shiga ya doki qafar ta ta tashi tana gantsaro girji tare da yin hamma, "Malam lafiya ka ke tashi na da wannan tsohon daren? Kasan nayi aiki na gaji fa gashi gobe ma zan ci gaba da aiki kamar kullum, in ban bacci da wuri ba kasan bana samun jin daɗin yin aiki na," "Yi hakuri dan tashi ki duban lokaci a agogon nan," Wani haushi ne ya kama ta, agogon ne bai iya ba ko me? Cikin fushi ta kalla tace. "Qarfe sha daya da rabi na dare mana baka iya agogon bane ko me?" "Yauwaaa alhamdulillah kema kin faɗa da tsohon daren nan, sannan kin ce qarshe 11 na dare,to a tsohon daren sai yanzu yaran ki ke dawowa daga waje daga macen har namijin, ya kamata kenan? Haba Ramai, yarannan fa amana ce Allah ya bamu a hannun mu fa, Allah ya aminta damu fa kenan tunda har ya azurta mu da yara dan mu kula da su mu basu tarbiyya mai kyau, amma shine ke kike sakaci da basu tarbiyyar,ni dai Allah ya sani ina yin iya bakin qoqari na amma ba ki bani had'in kai, kin kyauta min kenan tsakani da Allah," Tin da ya fara maganar ta ji farkon amma qarshen bata san me yake faɗa ba, dan kuwa baccin ta ta koma a zaunen, dan indai ta shi ne kar suyi bacci ayi ta magana akan yaran wanda ita kuwa bata ga abinda suke yi mara kyau ba,ba zata iya matsawa yaran ta ba ta hana su sakewa sammm. Malam Jameel yaji haushi kuwa matuqa amma haka ya danne, ya bi gadon nasu tare da yin addu'ar bacci ya kwanta sannan ya tofa mata itama, dan bai taba gani tayi ba shi kuma baya gajiya wajen yi mata kafin ya kwanta, cikin dakiya da jure ɓacin ran da yake ji ya ce wa Jameelah, "Ki rama sallolin da ake bin ki kan ki kwanta dan bana jin ko azahar kin yi, in Allah ya so ya amsa, in bai so ba ya barki da abun ki, Allah ya shirye ku, kuma kiyi addu'ar bacci kafin ki kwanta," Cike da zumbura baki ta amsa shi.Fita tayi tayo alwala ta yi zaman ta a kan sallaya tana ta tinanin abin da ya faru ɗazu da Babawo yazo sai murmushi ta ke ta zabgawa tanashafo dik wani sashe na jikin ta daya taba. 'Gaskiya Babawo ya iya soyayya sai kace a indiyan fim' Sai da ta dad'e a wajen sannan ta miqe ta ninke abin sallan, ta sauya kayan jikin ta zuwa na baccin data siyo a gwanjo, dan ita tana son harkar hutu, ta yi kwanciyar ta a dan bargon da take shimfidawa kalar pink, a rayuwar ta tana son ya zamana tana da d'akin ta na kan ta, ta yi masa ado irin yanda take gani a wayar Babawo a films. Tsaki ta doka ta sake gyara filon ta mai mugun tauri sannan ta juya wa dakin baya, nan da nan kuwa bacci ya dauke ta...... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 5: Da sauri Jameelah ta ja Umaimah baya cike da in-ina take magana tare da yin nuni da yatsan hannun ta tana Kyafkyafta ido tace, "Wwaaa... nnee... ne wan can???" Murmushi Umaimah tayi mai kyau kafin ta bata amsa da cewa, "Yah Umar kenan dama ina son na nuna masa babbar qawa ta, muje na gabatar dake wajen shi," Cikin sauri Jameelah ta hau goge fuskar ta da bayan hijab dinta ta gyara sosai dik Umaimah na kallon ta bata ce komai ba sai murmushi da take yi,cikin wani sabon ladabi daya matuqar bawa Umaimah mamaki suka jera suna tafiya. "Me yasa kuka koma ne? Ku fa ake jira" "Mum wai...." "Na yi fitsari ne," Jameelah ta yi saurin katse Umaimah dan kar ta faɗi gaskiyar abinda ya faru,kallon Jameela Umaimah ta yi da sauri itama dan kuwa a gidan nan ba ta tab'a tina sanda taji wani ya yi qarya  ba, waje suka samu a saman jerin kujerun dinning table ɗin nasu, kan Jameela a qasa ta sake gaida iyayen Umaimah, cikin jin daɗin tarbiyyar da take da ita suka amsa, Umar sai zabgawa qanwarshi murmushi yake yi, tare da langab'ar da kai gefe irin na masu shagwab'a Umar ya ce, "Lallai ma Umynaa wato kin yi sabuwar qawa ne ashe shi yasa ki ka dai na so na ko? Ta kwace min ke," Sunkuyar da kai Jameela tayi tare da lumshe kyawawan idon ta dan jin daɗin muryar Umar,cikin ran ta ta ayyana, 'Wayyooo Allah na yau gani ga jarumin maza kenan,Allah kasa sanadin haduwa da wannan gwarzon ne ya kawo ni gidannan' Ɗan taba ta Umaimah tayi dan kwata-kwata bama ta san me ake yi ba ta tafi duniyar tinani. "Nanna'am" "Yah Umr na yi miki magana," Kallon shi tayi ta sunkuyar da kai qasa, wani iri yaji azuciyar shi game da ita dan kuwa ta yi matuqar yi masa kyau ba kaɗan ba, a zuciyar shi ya furta, 'Masha'Allah' Shine abinda Umar yace, a zahiri kuma ya sake maimaita mata tambayar shi inda ya ce mata, "Cewa nayi meye sunan ki,Umaimah na son riga ki sanar dani sunan naki," "Jameelaahhh" Cikin salo mai ɗaukan hankali tayi magnar, a zahiri ta nuna kamar bata san ma ta yi magana dan jan ra'ayinsa ba. "Wooow masha Allah Jameelaah nice name, u deserve to be called Jameelaah, naji tace ajin ku daya ko? ashe kema hafiza ce kamar Umynaa....naji daɗin haɗuwa da babbar qawar Umynaa Allah ya sanya albarka a qawancen ku," "Ameen" Itace kalmar da kowa ya fada a wajen, bismilla suka yi kowa ya fara cin abinci, Jameelaa a ran ta sai surutu take yi cikin mita take ayyana. 'Matsalar masu kudi kenan a tashi a hada ku cin abinci a babban teburi tsabar rowa, in ba rowa ba dan kar naci na qoshi da ba sai a bamu mu je can d'akin mu ci hankali kwance ba? ji kaji ma malam yanzu a banza zan barsu' Ɗan juya ido tayi ta d'ibi shinkafa kadan a spoon ta kai bakin ta, tana taunawa a hankali, kowa a tinanin shi tsabar kamun kai ne ya sa take yin hakan,ganin haka sai Mum ta kiran mai aikin gidan ta ce, "Kin ga haɗa masu abinci ki kai masu d'akin Umaimah su ci a can, baquwar tamu ta kasa sakewa ta ci abinci da mu" 'Alhamdu lilLAAH kaiii babar su Umaimah na da hangen nesa,yanzu ba sai na ci kaji acan na gyatse abuna ba? habaa da an wani hadani da wannan mai kalar mutanen boyen ta ya abinci zai shigen' Bayan an kammala haɗa masu abincin an kai masu Umaimah ta kama hannun ta akan su shiga daki su ci, cikin jin kunya ta miqe  basu qarasa shiga ba taji Umar na cewa, "Gaskiya na ji daɗin ganin qawar Umynaa, tana da hankali da nutsuwa ga kuma kunya, " "Gaskiya nima na yaba da hankalin yarinyar, ana fadin yaran unguwar basu da tarbiyya gaskiya naga sab'anin hakan akan ta, yarinya kintsattsiya haka? Lallai iyayen ta sun bata kykkyawar tarbiyya," "Kwarai kuwa, Allah ya musu albarka to," "Ameen dai" Ai wato suna shiga d'akin Jameela ta yi arba da abincin nan ga lemuka kala biyu kowa da nashi ga nama ga shinkafa da miya da salad, wayyooo ji ta yi kamar bata taba cin kowanne a cikin su ba, zama ta yi ta aje hijabin ta a gefe ta duma hannu ta hau yagar naman tana ci tana santi, tasss ta tashi da abincin bayan Umaimah tace ta qoshi, wata gyatsa ta sake ta hau yi wa Umaimah surutu, "A gaskiya kuna jin daɗin ku Umaimah, kullum wai haka kuke cin abinci mai daɗi a gidan nan?" Murmushi kawai Umaimah tayi wa Jameelah,kafin ta yi magana kawai sai Jameela ta fara share hawaye cikin kuka ta ce, "Allah sarki Ramai na da Babana, na zauna na cika cikina da mai daɗi irin wannan, ko su me suka samu suka ci da rana? Wataqila abincin siyarwar da Ramai ke dan dorawa dan siyarwa shi zasu ci yau, Allah kenan mai yarda ya so, mu muna nema ku kuma kun gama samu," Tausayin ta ne mai qarfin gaske ya kama Umaimah da sauri ta rungume ta tana lallashin ta, tare da yi mata alqawarin zata ɗebar mata abincin da taci ta kaiwa iyayen ta, "In aka gani a gidan ku fa ba za a maki faɗa ba? ai sai su ce na zama makwadaiciya Umaimah,basshi kawai kin san soyayyar dake tsakani na da su ne ya sa na ji sha'awar na gan mu muna ci tare, amma ban fada maki dan ki debar min ba," "Na sani kar ki damu, inshaa Allah sai sunci nima hankali na zai kwanta, tashi muje parlour," "To ai ni tafiya zan yi ma, da kin barshi kawai," A hanyar su ta tafiya parlour suka rabu, Jameelah ta yi parlour Umaimah ta yi hanyar kitchen sanye da zumbulelen hijabi...... *A yi hakuri da wannan na yi busy ne thank you mutanen kwarai da hakuri da ni.* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 7: Sosa kai tayi sannan tace, "Baba na jima ina so in gyara dik wani halayen da nake yi marasa kyau malamin mu ya yi mana wa'azin daya shigi jikina kuma ya tsoratar dani, sannan Allah ya amsa addu'ar ka akan nema mana shiriya da ka ke yi a kullum ba ka gajiyawa,ana haka shine na nemi izinin Ramai na je gidan wata qawata dan muyi karatun qur'ani ina so na gyara hadda ta,dayake ita qawar tawa tana da hadda sosai dan kuwa ita ke yin na ɗaya cikin mu arba'in da wani abu a ajin mu, muna zuwa sai na ga ashe masu kuɗi ne, shine mukai karatu da zan tafi iyayen ta da ita kan ta suka haɗa min abin arziqi, na qi Karb'a maman ta tace ai dik abokiyar d'iyar ta d'iyar ta ce, shine na amsa yayan ta ya dawo dani gida, kuma maman ta ta qara mana k'warin guiwar yin karatu tare" Nazari sosai Baban nata yayi ma maganar ta, amma sam bai gano qarya a ciki ba, dan haka fara'a ta bayyana a kyakkyawar fuskar dattijon har ya samu kan shi da fad'in, "Alhamdu lilLAAH, na gode Allah dana ga wannan rana,Allah ya shirya min dan uwan ki shima ya gyara rayuwar daya tsindima kan shi a ciki yaro qarami amma haka za ki ga yana layi a titi dan lalacewa, Allah ya dawwamar dake cikin farin ciki da kuma shiriya," "Ameeen Babana," A haka suka kashe bakin shi, ta dage ta dinga yin duk wani abu da zai tabbatar masa da cewa ta shiryu da gaske kamar yanda ta ce ɗin, shi kuwa baba haka ya saka mata ido dan ya ga ko wani makircin suke qullawa amma har dare bai ga ta je zance ba, dik kuwa da naci irin na Babawo da ya zo har leqawa tsakar gidan ya yi ya hau kiran ta, tana nan rungume da qur'ani ta na jin shi amma ta qi fita. Washegari da assuba bayan tayi sallahta sai ta d'auki qur'anin ta ta hau karatunta ta nata muraji'a, Baba kam daɗi kamar ya d'aga shi sama haka ya dinga sakin murmushi. Bayan ta gama karatun ta ta shirya dan zuwa wanka sai ta saka hijab daya rufe mata jiki gaba ɗaya taje tayi yi wankan ta ta dawo tayi shirin zuwa makaranta,a hanya suka hadu da Mamalo,cikin ɗauke kai irin na masu kishin qawancen nan Mamalo ta ce, "Wai ina ki ka shiga jiya daga zuwa gidan su Umaimah kamar wadda ta yi tafiya wani gari?" "Ba zaki gane baaa yarinya,nace ba zaki gane baaaaa, amma nan da wani lokaci kaɗan zaki gane komai, yah kin tara kud'in anko muje mu siyo ko ki na nan ba ki da ko sisi?" "Eh na tara dubu uku da dari biyu," "Ba laifi in an tashi muje.mu siya,ke ni har na sai takalmin da zan saka ma jiya," "Habaa dai ! lallai ke babba ce qawata," Murmushi tayi saboda ita wannan yabon da take samu daga qawayen ta na lungun su yana mugun d'aga mata aji ainun, sai ta dinga jin kamar ita ɗin wata Zahrah Buhari ce. Bayan sun isa makaranta ne ta samu waje ta zauna a nutse, yi tayi kamar bata ga Umaimah ba ma dan kar ace ita take manne mata, Umaimah bata damu ba ita sai ta zira hannu ta tabo ta, murmushi suka sakar ma juna, sanan suka miqawa muna hannu suka gaisa a mutunce, Umaimah ta ce, "Ya ki ka je gida jiya? Dik da na san lafiya qlou zaki isa tunda Yah Umar ne ya maida ki," "Kwarai kuwa, lafiya qlou na isa gida, dan kuwa Yah umar akwai mutunci," "Sosai ma kuwa, sai ma kun saba zaki ga hakan," Jameelah murna ce ta kama ta da jin kalmar sabo a tsakanin ta da Umar a ranta ta ke ayyana, 'Wayyyoo Allah ka matso da ranar sabawar mu nan kusa' A zahiri kuwa sai ta dafe qirji ta zaro idanu waje ta ce, "Ni Jameelah ni me zai kaini sabawa da namiji kamar Yah Umar? Ai ni din ba ajin shi bace, ko ke ɗin ma dan kina qanwar shi ne amma da sai nace yafi qarfin kula ki bare ni 'yar talaka jikar talakawa" Murmushi Umaimah ta yi sannan ta ce, "Mu ba haka muka dauki rayuwar mu ba Jameelah, kuma na tabbata a jiya kin gane hakan da idanun ki,ko Mum sai da tace na gaida ki da safen nan kafin na taho saboda kin burge su, kin shiga ran Mum sosai" A cikin zuciyar ta ta buga ihu tare da murna ta ayyana, 'Alhamdu lilLAAH uwar mijina na sona' A zahiri kuwa sai ta ce, "Allah sarki Mum ba ruwan ta itama, ki gaidan ita sosai in kin koma, kinga karbi haddata kiji min," Mamaki ne ya kama Umaimah da Mamalo dake manne da su tana jin tattaunawar tasu,amma dole suka shanye mamakin su dan kuwa gimbiya Jameelah ko a jikin ta sai ta fara zubo karatun qur'anin da ya sake tsunduma duk wani mai sauraron ta a cikin duniyar mamaki,daga qarshe dole Umaimah ta shanye nata mamakin ta kasa kunne ta na sauraran haddar Jameelah wadda ke zubo karatun da murya mai dadin sauraro, sabon malamin su da ya shigo ya ji karatun da take zubawa nan take ya kira ta ya tambayi sunan ta saboda ta burge shi sosai. Bayan ta sanar da shi ne ya ce ta je ta zauna sannan ya gabatar masu da kanshi a matsayin Malam Haroon, sannan ya nad'a ta matsayin Monitan ajin,nan da nan 'yan aji kuwa akai ta ihu suna kiran ba sa so, wasu daga qawayen ta gudun kar ta ce harda su aka ce ba a son ta su kai ta cewa suna so. Ko bi ta kan su baiyi ba aka fara karatu, ganin haka yasa Jameela dagewa sosai dan kar ta ji kunya. Malam Haroon baqi ne kyakkyawa kuma Ustaz dan kuwa wandon shi ma a dage yake ga gemu mai kyau daya kwanta a fuskar shi, yana da gira cikakkiya kamar an zana ta, yana da tsananin tsafta, da kuma ilimin addini, yayi boko amma iyakar shi secondary, daga nan ya ci gaba da maida hankali akan kasuwanci da neman ilimin islama. Iyayen shi sun rasu daga shi sai yayan shi mai suna Ishaq,Haroon yana zaune ne a gidan yayan na shi wanda ke da mata guda ɗaya, Yah Ishaq yana da kuɗi sosai shi ɗin babban ɗan kasuwa ne, ana saida manyan laces, dogayen riguna, atampopi shaddodi da mayafai a shagunan shi, matar shi Hauwa'u mace ce irin 'yan duniyan nan masu yin abinda suka so a gidan miji ba tare da ya sani ba, Haroon ya san dik wani iskancin da take aikatawa na zuwa wajen bokaye dan mallake ɗan uwan na shi,Hauwa'u na matuqar son Haroon fiye da yanda take son mijin ta Ishaq, a cewar ta Haroon ne mai jini a jika yayan shi dik ya zama sauran basir, yanzu haka Haroon a cikin matsalar matar Yayan nashi Hauwa'u yake, dan kuwa ta ɗana masa tarko akan dole sai ya kusance ta, in ba haka ba zata masa sharrin da sai yayan shi ya kore shi daga gidan, dan haka zaɓi ya na wajen shi yanzu. Bayan kammala karatu sai ya sa yaran su yi masa addu'a akan Allah ya tseratar da shi daga sharrin dikkan mai sharri ya bashi nasarar tsallake dikkan tarkon maqiya, suna kammala addu'ar Haroon ya raba masu sweet, da zai fita ne ya kira Jameela. Cikin yanga irin ta ta wadda ta zame mata jiki ta durqusa a gaban shi, kallon ta yake daga tsayen gashin idon ta sun kwanta a fuskar ta, ga wani kwantaccen gashi a saman girar ta mai kyau,cikin muryar shi mai daɗin sauraro ya ce mata, "Jameela ko?" "Eh malam," "Ko zaki faɗan me yasa 'yan ajin ku basu son a nad'a ki monita?" Wata a jiyar zuciya ta sauke tare da dafe kan ta, alamar ciwo yake yi mata, ganin haka yasa shi cikin kulawa yace ta miqe tsaye, da sauri kuwa ta miqe, dan durquso ba dabi'ar ta bane. "Kan ki na ciwo ne," "Eh malam" "Subhanallah, maza to je ki amshi magani a office din malamai, sai ki koma aji, mayi maganar watarana," Ta bayan shi ta wuce dafe da goshi, kamar mai tsananin jin ciwon kai, A ranta kuwa sai masifa take yi... 'Kaji min mutum, kawai dan dai hauka akaina ya qare sai na hau faɗa masa ni ɗin ba marajin magana a kaf makarantar sama dani? ka ji a bakin wasu ni kuma na qarya ta su da aiki na,' Murmushin mugunta tayi, ta zagaye office din malamai ta koma ajin su, zaman ta tayi bata sake kula kowa ba dan kuwa a qufule take da kowa, 'yan zuwa surutu wajen zaman su sun taru,suna jiran su ji me zata ce game da wannan sabon salon da suka gani a wajen ta,banza tai da su ta d'au qur'ani ta fara hadda,dan kuwa Jameelah bata da aikin yi sai hadda yanzu, tana fatan ta kamo 'yan ajin,lokacin shashashanci ya qare. ********************** A cikin wata shida Jameela ta gama haddace dik inda aka barta abaya, a yanzu ta iya karatun ta sosai da sosai duk inda aka tab'o a qur'ani da hadith da duk wasu littafan da ake yi masu zata karanto wa mutum tsaf ba kuskure,data zauna a waje sai dai kaji karatu na zuba kamar ruwa, daɗin muryar ta ke qara ma mutane qaimin sauraron ta, gidan su Umaimah kuwa ta je shi yafi ba iyaka. Yau ma sun gama shiri akan zasu je gidan su umaimah yin karatu,driver na zuwa ta faɗa motar kamar tasu,suna ta hira a haka har suka isa gidan. Da sallama ta shiga, bakin ta ta washe data ga Mum. "Mum din mu ina wuni? ya aiki?" "Lafiya qlou Jameelan Mum, ya maman ki da Baba da Bukar" "Suna Lafiya qlou alhamdulillahi, Mum akwai wani aikin da zan taya ki ne? Ina Dad?" Umaimah dake murmushi ta wuce su zuwa d'akin ta dan sabon da Jameela tayi da mum ɗin ta na bata mamaki. "Daddyn ku ya fita, amma na san suna hanyar dawowa yanzu," 'Anzo wajen, na tabbata da Yah Umar aka fita yau,' Abinci ta taya ta suka qarasa dafawa, umaimah ma bayan tayi wanka ta sauya kaya suka qarasa shirya table tare, suna kammalawa kuwa su yah Umar na dawowa,a gajiye suka shiga gidan direct kujera ya samu ya zauna ya na qarewa yarinyar da ke yawan faɗo masa a rai a kome yake yi. Sake kallon Jameela ya yi wadda kullum yake kasa gane a uniform tafi yin kyau ko kuma a kayan gida ne tafi kyau, itama shi ta ke kallo tana masa murmushin da ta kula yana matuqar qayatar da shi. "Yaahh Umarr ina yini?" Sai da ya ji tsigar jikin shi ta miqe, tsabar yanda ta karya murya wajen kiran sunan nashi, "Lafiya Qanwa ta," Wucewa tayi ta koma d'akin su Umaimah, kamar yanda take yi in tazo ta taya Mum aiki sai ta shige ta d'auki karatun ta tayi tayi,hakan ke qara mata babban matsayi a wajen su dika mutanen gidan dan kuwa ko abinci bata ci sai ta kammala haddar ta, dik da mugun kwad'ayin da takan ji dan ganin ta ci abinci kan ta yi karatun, amma tinda akwai motive din yin hakan bata damuwa. A bakin qofar dakin ya tsaya yana bin ta da kallo, yanda ta cire hijab ta rufe kan ta da shi, ta gaba a bude hakan ya yi masa kyau, Umar kasa ɗauke kan shi yayi daga kallon qirjin ta yana mamakin cikar su, Umaimah ko bra bata sawa saboda ba su da wani girma, amma ita sun cika bra din ta sannan sun cika rigar ta har ana ganin su ta saman V neck din ta, Wani abu ke masa yawo a jinin jikin shi game da ita, dan haka komawa baya yayi yana sauke numfashi da sauri da sauri. Sai yamma Jameelah ta kammala isar da saqon zuciyar ta a gidan su Umaimah sannan tace zata tafi, kamar kullum Mum ta bata dubu biyu kudin mota suka yi sallama ta fito dan tafiya gida. A waje ta gan shi cikin motar shi yana zaune kamar mai jiran wani, yana ganin ta ya fita ya buɗe mata gefen mai zaman banza. Kallo ta bishi da shi mai matuqar daukan hankalin mai kallon ta, shagala yayi da kallon ta ta shagwabe fuska sannan ta ce, "Yahhhh Umarrr kallon fa?ko dama dan kayi ta kallona ya sa zaka taimaka ka maida ni?" Murmushi yayi ya sosa qeyar shi ya zauna a mazaunin driver sannan ya tada motar suka fice daga gidan, a hanya ya samu wani wajen bishiya mai iska ya tsaya, juyawa yayi yana fuskantar ta sannan yace, "Ina son na maki wata tambaya, tsakani da Allah nake son ki bani amsoshin su," "Inshaa Allahu zaka sameni mai gaskiya a dikkn abinda zan amsa maka," Umar gyaran murya yayi fuskar shi ba wasa a cikin ta, sannan yace............................ *Allah ya maimaita mana Sallah ta badi mai albarka, Hppy sallah to u all,amin hakuri aikin sallah kun san yanda yake akwai wahala, a ajen naman sallah na zan zo na amsa, sai muyi hakuri da wannan gobe ko dik sanda dai na samu dama mun ji me Yah umar zai tambayaq* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 6: Kitchen Umaimah  ta shiga sanye da zumbulelen hijab ɗin ta dogo,tafe take tana istigifari saboda tasan abinda zata yi bashi da kyau,sai dai wata zuciyar na ce mata, 'Ai ba komai abinda zaki yi ba laifi bane taimako ne, kuma ko su iyayen naki ai sun koyar da ke taimakawa marasa shi dan haka kar ki wani damu, je ki d'eba mata kawai' Da wannan shawarar ta yi amanna ta qarasa kitchen ɗin, tayi sa'a kuwa ba kowa a ciki, mai aikin su na d'akin ta tana cin abinci, nan ta buɗe kowanne abinci ta d'ibarwa Jameelah a leda mai kyau sannan ta ninka ledar sau uku ta yanda ko qamshi ba za a ji ba, ta saka a cikin Hijab din ta ta fice zuwa d'akin ta, a jakar Jameela ta saka wannan ledar ta rataya sannan ta bi bayan Jameelah parlour ,a tsaye ta ha Jameelah ba kowa a parlour sai kalle kalle take yi,raka ta wajen Mum ɗin su tayi dan yi mata sallama, Jameela a bakin qofa ta coge taqi shiga wai ita mai ladabi, kar ta fada masu daki ba tare da an yi mata izini ba,a  nan ma ta samu nasarar samun yarda da amincin Mum ɗin su Umaimah, cikin murmushi Mum ta ce, "Come in my dear, don't feel shy nan ai gidn ku ne kema" Zazzaro ido ta yi waje dan jin Mum ta yi mata turanci, yaren da ko a cikin mafarkin ta ganin shi take yi kamar mutum mai qafa yana mata yawo a kwanya, ba qaramin son ta ji tana yara turanci take ba, "Ammm ban san mee kike ce ba Mum,kiyi hakuri," Baki sake Mum take kallon ta,yarinya budurwa kamar Jameela amma ace bata san me ta fada ba da turanci,? kodai bata da qoqari a makarantar boko ne? Umaimah ce ta ce, "Mum Jameelah bata zuwa boko iyakar ta islamiyya, saboda wasu dalilai daya ke a cikin gidan, so ina ga kawai kuyi sallama zata koma gidan su yamma na yi," "Ya salam ! kiyi hakuri, indai da rabon ki zaki yi boko Jameelah, kin ji," Cikin wani ladabin mage mai kwanciyar ɗaukan rai Jameelah ke kad'a kai, tare da matse kwallar da babu ita a idanun ta, sai nan d nan Mum ta ji kamar ta zage ta ne, inda ta san bata iya turanci ba bata zuwa school da bazata yi mata turanci ba. Tashi ta yi daga kan abun sallah ta isa gaban Jameela ta kama hannun ta, Jameela ta qanqame jakar ta da kyau a hammata dan kar aji qamshin abinci a gane zata tafi da wani gida kamar abincin gidan biki, wato aci ayi guzuri. "My dear, kar ki damu kin ji? ki kwantar da hankalin ki na yi maki alqawarin indai ina raye zaki yi karatu mai yawa har sai kince kin qoshi zaki zama kamar umaimah, sai dai ina so ki yi min alqawarin kare mutuncin ki da kuma maida hankali akan karatun?" Cike da zumud'i da kuka mai hawaye Jameelah ke godiya,dan kuwa bata taɓa zatan wadannan kalaman daga bakin Maman Umaimah ba, durqusawa tayi tana kuka sosai dan jin daɗin kalaman nata. "Shshhhhiiii, ba kuka zaki yi ba Jameelah godewa Allah ya kamata ki yi kin ji? sannan ki bari zan samu lokaci mu ziyarci gidan ku na yi magana da iyayen naki ,babu bata hana karatu tunda ba kan ku farau ba, wani ma baki san da ya ya samu arziqin shi ba, dan haka ki godewa Allah with the little u have, ohhhh sorry, da kaɗan  ɗin da ki ke dashi komai qanqantar shi kuwa,watarana sai labari kin ji?" "Na gode Allah ya qara girma ya jiqan mahaifa, Allah ya saka maku da alkhairi mara yankewa," "Ameeen.....ga wannan ki sha alawa, dan da da akwai da na loda maki ita,dan na kula ke din ma kamar Umaimah ce wajen son zaqi," Dariya suka yi dikan su Jameela ta sunkuyar da kai ta na murmushi, ta ajiye kud'in da aka bata a gefen ta tana wani nuna ita an hana ta amsar kudi a waje, kar Maman ta ta dake ta. Da kyar aka samu ta riqe kud'in,cikin dabara ta qirga su a hijabi dubu biyar Mum ta bata cif-cif,ta na gama qirgawa ta danna abunta a jaka,cikin ranta ko sai gode masu take yi dan kuwa bata taɓa riqe kyautar kuɗi tsababa haka ba a lokaci ɗaya ba a wajen saida abinci ba, a ran ta ta ayyana, 'Kaga masu yi dan Allah, in za ayi za ayi kawai alaji in ba za ayi ba a bari kawai, haka nake so yanzu da wasu ne dana ce bana so zasu danna a aljihu ko jaka shikenan na rasa' "Ga Yah Umar din nan ma...Yah ga qawata zata koma," "Da wuri haka? Ki bari na aje ta gida to dama zan fita ne zan siyo wasu abubuwa, saboda karatu muje na aje ta ko?" "Ba dan zan yi hadda ba dana biku, na gode sosai Jameelaa sai mun haɗu gobe a makaranta," Dad ma dubu biyar ya bata kyauta, nan da nan Jameelah ta ji kan ta na neman buɗe wa, dan kuwa ji tai kamar ta haukace dan murna bata taba riqe kuɗi nata na kanta ba  a dunqule a hannun ta ba irin haka. Tin da suka shiga motar ta sunkuyar da kai tana ta muimui da baki kamar mai tasbihi ga Allah, Umar kuwa a ranshi yace, 'Yarinyar nan tana da hankali matuqa, da dikkan alama tasbihi take yi ko kuma karatun qur'ani' Cikin wata iriyar murya Umar ya ce wa Jameelah, "Kar na katse ki, amma ina son na tambaye ki," "Allah ya sa na sani," Murmushi ya yi kafin ya ce mata, "Kin ma sani Malama Jameelah, meye sunan unguwar ku? Sannan ki yi min kwatancen inda zan ajiye ki kinga ni ban sani ba, kuma baku faɗa min ba, in kuma so kike mu b'ata to shikenan ba zan damu ba dan na b'ata da ke a garin kano" Kama baki ta yi tana murmushi, ita a dole ta ji kunya,cikin murya mai cike da salo ta ce, "Na manta ai, na zaci Umaimah ta sanar da kai inda za muje" "Ta dai sanar dani sunan unguwar ku kuma na manta,sannan bata faɗan inda zan ajiye ki ba," "In mun shiga unguwar mu zan nuna maka waje, ba boyayyan wuri bane, saboda hada-hadar saida abinci da sha da ake yi a wajen musamman saboda masu kasuwanci da matafiya," Jinjina kai yayi, da yabawa yanda take magana cikin tsari da hikima kamar ta wuce shekarun ta. Shiru ba wanda ya sake magana har suka isa, lokaci zuwa lokaci ta kan ji alamar yana kallon ta, dan haka dik wani yanda zata yi ta matso kyau yi take yi ta yanda ba zai gane tasan yana kallon ta ba, ga bakin ta na rasa me take faɗa amma tabbas na san ba tasbihi bane sai dai wani salo irin na yaudarar ta shi ya jawo motsa shi da take yi. Lokacin da suka isa unguwar tasu ne ta hau yi masa nuni da hannun ta inda zai shiga, salon yanda take nuna masa waje ne yasa ya dinga bin yatsun ta da kallo, tare da yaba kyawun halittar su a zuciyar shi. 'Ikon Allah ! yarinya qarama amma masha Allah she is so beautiful' Motar ce ta tsaya a dai-dai inda ta nuna masa nan ne gidan su,wanda daga nan inda suke tsaye da motar ta nuna masa gidan nasu, ya tausaya mata matuqa ace kamar ta anan take rayuwa, sauke kai tayi qasa tana ziraro hawayen munafurci, ga masu shaye-shaye nan suna ta zuqar sigari, wasu ma wiwi ce suke sha, ga mata nan na fiddo da abinci suna ta wasanni da maza, abun dai sai wanda ya gani ba kyawun gani a wajen mai tarbiyya. "Me ya faru kike kuka? Dan Allah ki bar kukan nan, habaa don't cry mana is ok," A ɗan daburce ta kalle shi dan bata gane me yace ba,nan da nan Umar ya tuna yaji ɗazu suna magana akan bata yi boko ba, sai kawai ya yi shiru bai sake magana ba,miqa mata tissue yayi dan ta goge hawayen ta, tare da lallashin ta iyakar iyawar shi,da a kyar ya samu tayi shiru,dan haka cikin muryar lallashi ya ce mata, "So tell me, sorry, yanzu faɗa min me yasa ki kuka haka ke da na dawo dake gidan ku lafiya ba cizo ba yaqushi?" "Dan Allah kar ka hana Umaimah qawance dani saboda yanayin unguwar mu, bamu da zaɓin daya wuce zama anan, arziqin da iyaye na suke da shi kenan, kuma ni......" Ɗora hannun sa yayi kan leban shi yana nuna mata ta yi shiru, "Habaaa Jameelaah ! akan me zan raba ku qawacen ku da Umaimah dan na ga kalar unguwar da ki ka taso a cikin ta? Ki na tunanin ku kadai ne Allah ya ajiye a haka? Shin baki san rayuwar wasu ma  tafi taku babu ba? Babu abinda zai sa na raba ku ke da qawar ki, kina da qima da daraja a idon ahali na, ke din a cikin waɗannan mutanen kamar audigar da aka bata saman ta ne, sama datti ciki fari, kar ki damu kan ki akan qaddarar ki watarana sai labari," Jameelah kuwa cikin ranta ta ayyana, 'Ohhh Allah ya kawo labarin nan kusa, kawai ina cikin AC da carpet an dawo dani nan,yau na shiga uku ni Jameela talauci ba yi ba a rayuwa' A zahiri kuwa wani kukan ta sake saki, a zaton shi wani abun ta sake tinawa,cikin kuka ta furta, "Na gode, na gode sosai, Allah ya saka ma da alkhairi Yah Umarrr kai din mutumin kirki ne, wanda bai da girman kai da kuma kyamar talaka," Murmushi yayi, yaji daɗin yabon da ta yi masa, haka nan yake jin nishad'i kamar kar su rabu. Buɗe motar ta yi tare da juyawa suka haɗa ido, lumshe idon ta tayi cikin wani salon sace zuciyar shi, amma sai tayi saurin kauda ido ta fice wai ita a dole mai kunya. Kallon kuwa ya daki zuciyar shi matuqa, amma sai shima ya kauda kai, nan take ya sa a ran shi itama qanwar shi ce ai inda kara. Sai da ta ga fitar shi a lungin sannan ta fara tafiya gida, a guje ta shige gidan ta ja hannun Ramai zuwa daki. Suna shiga tayi tsalle ta fada jikin ta tana murna,  Ramai baki sake take kallon ta, daga baya itama ta hau murmushi tana tambayar Jameelah ko lafiya take murna haka? Cikin farin ciki Jameelah ta ce, "Ramai daga yau na daina talla ki samu mai zubawa mazan nan abinci, sannan zan maida hankali na dinga iya hadda ta sosai ke har ta baya sai na tisa ta zauna a kwanya ta tasss, Ramai hijabai za ki nemo min na daina saka mayafai, sannan kema daga yau kina saka hijab in zaki fita girki, Ramai dole ne mu gyara indai muna son kuɗi da jin daɗi su zauna mana zama na har abada, in yaso a bayan fage kome muke son yi muyi abun mu,taho mazo Ramaitaaa duba nan ki gani," Kud'in data samo ta d'akko mata da ledar abincin da aka qullo mata, ta ajiye a gaban Ramai ta na kallon reaction ɗin ta,gefe ɗaya kuma ga ledar 'yan tsarabe tsaraben da Mum ta hada mata. Sake baki Ramai ta yi tana jinjina yawan kudin, ai wannan kud'in yafi kud'in hayan su na wajen watanni ma, dan kuwa a wata dubu ɗaya suke biya kudin d'aki d'ayan da suke ciki, da dari biyar ne ma daga baya aka qara dubu ɗayan. (Na san halin wasu makarantan da yanke hukunci akan rashin sanin abu, amma kuyi bincike dan Allah kafin ku ce ba d'aki a cikin garin kano da ake bada haya akan nera dari biyar tabbas akwai su wasu ma wallahi sai dai a hakura a bar su su zauna dan ba su iya ci da kan su ma balle su bada na hayar,wasu kuma sabo da jimawa da aka yi ana tare idan suka samu mai gidan na da kirki sai ya bar su su ci gaba da zama a kyauta musamman idan basu da shi, dan haka in Allah ya maki/ka ni'ima ka/ki gode masa, Allah ya bama kowa yanda zai yi a rayuwar shi) "Ina kk samo kuɗi masu yawa haka Jameelah? Zo nan na duba ki ban yarje maki kwanciya da kowanne qato ba Jameelah, ban qi ba idan irin soyayyar wannan zamanin da ake yi zakuyi ba a baki 'yan kud'in da za a baki, amma kwanciya da namiji inaaa ba zan taba yarda ba Jameelah, ban shirya karb'ar jikan waje ba dan uban ki, kar ki ga ina sake maki ki je ki d'akkon magana," "Dan Allah ni sake ni meye haka zaki wani hau ciren zani, ko kin manta da inda nace maki zani ne? Gidan su Umaimah na je fa, iyayen ta ne suka ban kudin nan kyauta da wannan abubuwan dika, wajen wane qato zani na kwanta a wnanan unguwar kaff ya ban wannan maqudan kudin? Ni bana son haka gaskiya Ramai," Washe baki Ramai tayi tana bawa Jameela hakuri, tare da buɗe ledojin da tazo da su, ta bude qamshin abinci mai daɗin gaske ne ya ziyarci hancin ta,gefe kuma ga lemuka kala-kala har guda hudu, dik da ba wasu manyan kwali da gora bane amma taji matsanancin daɗin ganin su. Nama ta ɗauka ta kai baki tare da lumshe ido, tabbas mutanen nan wataqila da inji suke dafa nasu abincin, saboda daɗin ba irin nasu bane. Zama tayi sosai ta fara ci kamar mayya, kud'in kuwa ta raba biyu ta bawa Jameela rabi  Jameela na ta bata labarin gidan su Umaimah da abubuwan da tayi a gidan na munafurci dan kar su gane asalin halin ta, sannan ta sanar da Ramai alqawarin Mum din Umaimah na son saka ta a makarantar Boko, "Nan fa ɗaya Jameelah kin san halin baban ki sarai ba zai bari ba, kin san yana da wani ra'ayi, na rashin son kowa yana yi masa abu da iyalan shi, yafi son yana komai da kan shi, yanzu dole mu fitar da dabarar da zai yarda ya amince da maganar, yanzu ya ki ke  ganin zamuyi?" "Barni da shi kedai Ramai, ki rage masa abincin nan ki daina tsince naman dan Allah Ramai," Cikin faɗa ta yi maganar qarshen kamar ta na magana da qanwar ta,ita kuwa Ramai cikin wata dariya ta ajiye sauranta na side hannu ta ce, "Bari na koma kan abincin nawa, ki shirya in kika saida na yau sai a yau ɗin na nemi mai zuba min, dole na rage dahuwa kuwa, dan na san masu siya zasu ragu,indai ba zuwa zaki na yi gefe  kina zama ba har a gama, kin san dai wasu dan ganin ki suke zuwa dama," "Kar ki damu Ramai ai saboda sanin halin mutane da gulma na faɗa masu muna saida abincin, zan na zama a wajen tunda wasu ba dan su kauda yunwar cikin su suke zuwa ba dan su kauda yunwar idanun su suke zuwa, amma fa dole na koyi yin hadda Ramai, dan kuwa sun dauke ni mai ilimi sosai da tarbiyya," A ranar dik suka gama wani sabon abu da suke son gabatarwa. Jameelah ta shiga kasuwa da nata kudin tayo hijabai sabbi, sannan ta amshi kudi wajen Ramai ta sai ma baban su sabon jug da mazubin abinci, da sabon zanin gado, Bukar ma ta sai masa kayan gwanjo masu kyau da kuma takalma biyu na roba. Taji daɗin yin sayayyar sosai, haka ta dawo gida suka baje kayan suna gani kowa ya dauki nashi, suka gyara dakin a tare suka sanya sabon zanin gadon, nan da nan d'akin ya d'au kyalli, Bukar kuwa ya sha faɗa akan shaye-shaye da sace-sace da yake yi, sannan sun masa barazana akan in ya sake zuwa majalisar 'yan shaye-shayen zasu kai shi ga hukumar masu kama masu shan kwaya da miyagun kayan maye, ya kuwa yi matuqar tsorata dan haka ya yi masu alqawarin rage  shaye-shaye har Allah ya sa ya daina dika. (Ba a gyara dan Allah ba ana son a gyara dan a cuci wasu ) Ranar da Baban su Jameela ya dawo yaga an gyara komai ya yi fes har da sabbin kwanuka da zanin gado, sake fitowa yayi ya koma waje dan a zaton shi d'akin wata ya fada, cikin d'aga murya ya ke kiran, "Ramai ! Ramaiii !!" "Baba bata kusa ta shiga bayi dannta yi wanka, sannu da zuwa Baba ga abinci nan ka zauna, " Cikin ladabi Jameela ke yi masa magana, wanda hakan ya d'aurewa Baban nasu kai ainun. Zama tayi da mafici a hannu yana cin abincin tana yi masa firfita,a kunnen shi ne yaji wasu abubuwa na yi mai yawo tsabar daɗin abincin, sake kallon abincin ya yi da kyau nan take ya gane wannan abincin ba irin nasu bane, yau in bai manta ba ma dari biyar ya bayar kan ya fita, d'aga kai yayi ya kalli Jameela, yace, "Daga ina aka samu kudin dafa wannan da sauye sauyen da na gani?"........................... *Toooo readers Allah ya sa mutuniyar ku kar ta gilla qarya dan bata mata kaɗan a baki* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH *Sanarwa !* *Dan Allah masu nema daga farko ku yi haƙuri ku na duba groups ɗin da muke ciki tare,saboda sake turawa a private gaskiya na ci min tuwo a ƙwarya, wannan dalilin ne ya sa nakan ce ko bai baka sha'awa ba da fari ana tarawa maybe daga baya ya baka sha'awa, a yi min haƙuri adinga tambaya a group dan Allah maybe mutum ya dace da mai shi a tura nasa ko a dinga komawa sama a duba za a samu da yardar Allah....na gode.* PAGE 8: "Shin kina da saurayi? Ko nace kin taba yin saurayi?" Wata iriyar faduwa gaban Jameelah yayi, amma sai ta maida hakan wani irin salo na yaran da ba su san komai ba ɗin nan. "Yah Umar saurayi kuma? Ni Jameelah da yin saurayi a shekarun nan nawa? Tabdi jam, ai ni da ka ganni ban taɓa yin saurayi ba ban qi ba idan ka ce ki na da masu son ki? Sai in ce maka akwai masu so na da aure da yawa, amma ni ko zance ma ban taɓa fita ba dan kuwa ba a bari na a gida, yaran lungun mu na zuwa dai amma ni kam Baba baya bari ni kaina ma bana so balle nayi," Kamar ta ɗauki ruwa mai tsafta ta wanke masa zuciyar shi haka Umar ya ji, sai ya gyad'a kai kawai ba tare da yace mata komai ba, cikin matsuwar taji meye ra'yin shi akan ta har ya mata wannan tambaya ta kalle shi cikin wasa tace, "Yah Umar kai fa? Ko mun kusa shan biki ne?" Sosa kai yayi tare da yin murmushi sannan ya nuna ta da yatsa yana kad'awa ya ce, "Jameelaah, Jameelaah, kin cika tambaya ba a wajen karatu ba, ba wajen surutu ba," Dariya tayi zuciyar ta na zillo dan kuwa ta gama gane menene a ran shi game da ita,gyarawa ya umarce ta da tayi dan su wuce ya ajiye ta a gida. Ba haka ta so ba ta so ya bayyana mata matsayin da ya bata a zuciyar shi,ta na so ta ji ya furta mata kalma mai tsada wato kalmar so,dan kuwa ta san tabbas akwai wani abu a game da ita a ran shi. Ramai na zaune tana kwashe tuwo a zauren girki,Baban su Jameelah kuma na d'aki yana shafa mai dan bai jima da ya fito daga wanka ba, Bukar kuwa na qofar gida yana ta uban musu da matasan gidan akan ball lokacin sallah ya qarato ko a jikin su, iyayen su na ta hada-hadar haɗa abincin dare, kowa dai yana ta harkokin gaban shi. Jameelah ta shiga gidan ba sallama ta faɗa d'akin su a gaggauce ta gaida Baban su da ke shiryawa, nan da nan wasu a gidan suka hau gulmar ta, wasu kuwa suna taya iyayen ta murnar gyaruwar ta cikin ɗan qanqanin lokaci,kaya ta sauya dan ta riga tayi wanka a gidan su Umaimah sai ta fito tsakar gida suka hau hira da Ramai,anan ne Ramai ke tambayar ta a kwasa tuwo da ita,Jameelah sai ta yatsina fuska ta ce, "Habaa Ramai ni nan da ki ka ganni a qoshe nake, haka kawai sai yanzu na wani ci tuwo da dare? Gaskiya ni Ramai bana son irin cimar da ake yi a gidannan, gaba ɗaya gidannan ma ya fita akai na, yanzu na dawo daga gida me rab'a AC iya AC alaji,kamata ya yi yanzu ace koda haya muke yi na samu na koma gidan mu mu kaɗai ba wai na dawo nan gidan ba kamar wata kasuwa," Baban ta dake d'aki yana saka riga ne ya saki baki dan jin kalaman ta a ran shi yake fad'in, 'Biri yayi kama da mutum, wato saboda tana zuwa gidan masu hali shine take raina gidan nan, lallai zan d'au mataki babba akan hakan, tinda take su basu taɓa zuwa ba gidan nan ba sai itace ke liqe da su, saboda ɗan banzan kwad'ayi' cikin ɓacin rai ya hau k'wala mata kira kuwa, "Jameelah ! Jameelaah ! Zo nan," Miqewa ta yi tana wata iriyar tafiya ita a dole ranta b'ace yake ta isa wajen shi ta tsaya qiqam,cikin mamakin yarinyar ya ce mata, "Me naji kina fada? Wato ke gaki kina da gida biyu maganin gobara ko? kije can ki wuni ki zo nan ki kwana sannan mu iyayen ki da muka haife ki ki zage mu, daɗin abun naga anan aka haife ki tin farkon auren mu nan na zauna, ko kina da inda yafi nan ne?" "Bab...." "Yi min shiru 'yar wofi kawai, to bari kiji wani albishir da zan yi maki yanzu, Jameela kar na sake ganin ki kin je masu gida in ba su zo nan ba ki tsahirta da zuwa gidan mutane ya isa haka, ke baki san meye kamun kai ba kina mace? Haba Jameelaah a zato na fa kin sauya halin ki ne tsakanin ki da Allah ashe abun ba haka bane,dan Allah ki dinga tsayawa a inda Allah ya aje ki," "Baba kana jin fa yanda yanzu na iya karatu sosai a wajen Umaimah nake koya, inna daina zuwa ya zanyi to?" "In kika roqe ta ta dinga koya maki a makaranta zata dinga yi maki, ko ki roqi malaman ku su koyar da ke ba dole sai ita ba, ko ki jira na dawo saina dora maki," Dariya ta kwashe da shi ta na kallon shi a karkace wai shi zai koya mata karatu, da karatun makarantar allon zata yi karatun da zai birge Umar da iyalan shi? "Habaa Baba, Allah ya kiyaye na zauna a koya min karatun zaure kaga ana ta kiran sallah bari na zuba maka ruwan alwala a tafi a sauke faralin sallah," Ficewa ta yi tana ta surutai akan ba zata daina zuwa gidan su Umaimah ba har sai ta samu nasarar samun Umar a hannun ta, sai da yayi alwala sannan ya tafi masjid take sanar da Ramai yanda suka yi, dariya sukai tayi suna gulmar shi. Da dare ya yi Babawo ya aiko mata da gasasshiyar kaza da kuma Viju guda biyar sai dan lemo da ayaba, ya sha wanka da gayu yana jiran ta a waje, dan yayi tinanin wannan 'yar son abin duniyar da Babar ta in bai sake kuɗi ba ba zai dinga samun hutawa da ita ba. Aiko ba laifi ranar Babawo ya samu abinda yake nema a wajen Jameelah a ranar,dan kuwa sai da ta ci kazar nan ta gyatse Ramai na ta zagin ta akan ta yi sauri taje kar ya gaji da jira,tana gamawa ta wanke baki da brush ta fesa turaruka sannan ta fice, zaune yake kan bencin su da suka saba zama. Wani shan qamshi ta isa ta na yi tare da ɗauke kai, nan take tana zama Babawo ya zura hannayen shi bibbiyu a cikin rigar ta tare da sakin ajiyar zuciya mai qarfi sosai itan ma ajiyar zuciya ta sauke,Babawo ya yi kewar ta sosai haka zalika itama. Sun dad'e suna abun su da suka saba yi idan sun haɗu, kafin daga qarshe su samu nutsuwar rabuwa da junan su, bayan ta sallami Babawo ta kama hanya za ta shiga gida a bakin qofa ta haɗu da Mamalo sanye da kaya masu nuna surar jikin ta, dariya ta fashe da ita dan kuwa Mamalo na nan kan bakar ta ta na so Sadeeq ya samu yana yi mata irin soyayyar zamanin nan, shi ko kan shi a qasa ya kasa kallon ta a haka yake bata labarin gari da abinda garin ke ciki, daga qarshe ya hau roqon ta dan ta sa baki iyayen ta su bashi izini ya turo maganar auren su. Cike da tsokana Jameela tace, "Washhhh Allah ! bawa ya ji daɗin shi bari ya je ya miqe ya yi bacci da saleb'a, Babawo ya hadu a rayuwa ...... Ahhh Mamalo kece a nan ?sannun ku ya na gan ku a tsaye haka, Ko ku naku salon a tsaye ne?" Cike da takaici Mamalo ta buɗe baki zata fara zubawa Jameelah surutu sai Jameelah ta shige ciki tana ta dariya, ta na shiga ciki ta dawo baya ta tsaya tare da leqa kan ta waje,nan taga matan layin nasu na zuba soyayya yanda suka ga dama kowa da irin zaman da suke yi da masoyin ta, da kuma irin soyayyar da ake zubawa a wajen,murmushi ta yi ta ce, " MAZAUNA GIDA kenan, na bariki na can ana buga harkar arziqi" Dik wani iskanci da Jameela take aikatawa bata san tayi wankan tsarki ba,iyaka ta wanke gaban ta tayi zaman ta a haka, a cewar ta ba wanda ya taba saduwa da ita, dan haka ba wankan da ya kamata,koda kuwa ta fidda abinda ke wajabta wanka wato (maniyyi) kunji aikin jahilci, sannan ba zata je yin wanka ba a gane abinda ta aikata. Matasa masu soyayyar zamani in baku yin wankan tsarki kuna cikin azaba da gararin rayuwa, ga sabon Allah an aikata sannan ga zama babu tsarki, tayaya zaku yi ibada to ba tsarki? ******************* "Mum tinda yau alkhamis ko zamu je gidan su Jameela? Bamu taba zuwa ba ina matuqar son naje," "kar ki damu zamu je ne kamar kin shiga zuciya ta, inshaa Allahu zamu je amma sai anjima in yayan ki ya dawo sai ya kaimu," "Ok Mum Allah ya kaimu," "Ameen" "Mum me zamu kai masu?" "D'aga ni to na je na ɗan dudduba me zan kai ma ita mahaifiyar ta ta," 'Yan kayan sawa sabbi, guda biyu, da kayan ciye ciye da shaye shaye(bana maye ba😂) ta haɗa masu, sannan ta d'au turare wanda za ta ba wa mahaifin Jameelah guda biyu. Da yamma liss Umar ya dawo daga makaranta bayan ya ci abinci ya yi wanka yana hutawa Umaimah ta shiga d'akin shi ta zauna a gefen shi ta ce, "Yah na zo maka da saqo daga wajen Mum,sai dai naga kamar ka gaji bari na barka ka huta zuwa anjima sai na sanar da kai,dan na kula karatun ku na son hutu, in ka huta zan dawo na baka labari," "Ai kuwa dai na gaji kamar an min duka haka nake ji na, amma ina zaku da yamman nan haka na ga kun ci kwalliya?" "Gidan su Jameela zam....." Kan ta qarasa ya miqe zaune daga kwancen da yake ya ɗauki Key ɗin motar shi, da kallo Umaimah ta bishi ta na tuhimar sa da idanun ta shin ina gajiyar da ta gani a tattare da shi ɗazu? Lallai ma yayan nan, me yake nufi akan Jameelah ne? "Muje," Umar yace ya na sosa kan shi da hannun sa na hagu ya na murmushi. Bata yi masa maganar komai ba ta wuce d'akin ta bayan ta sanar da Mum Yah Umar ɗin zai kai su,hijab ɗin ta ta saka taje ta taya Mum d'iban kayan dake cikin ledar da zasu tafi da shi. Sun isa layin nasu da yamma liss, 'yan mata an sha kwalliya an fara fitowa qofar gida, yau Jameela bata jin zuwa ko ina dan haka kwance take a d'akin su tana ta zabga tsaki lokaci zuwa lokaci, kyaun ta ace ita yar wani hamshaqin ce, yanda gari yayi kyau ɗin nan ta tafi shopping da Dad ɗin ta ko Mum ko kuma ita ɗaya a mota, amma dan rashin sa'a a rayuwar ta gata kwance gidan yawa ana ta hayaniya. Juyi tayi tare da sakin sabon tsakin dayafi na da ,da sauri ta miqe zaune dan jin shigowar Ramai tare da ɗaukan mayafin ta da ke rataye a jikin qusar d'akin mayafin yayi maqal maqal da datti. "Ke tashi ga wata hajiya nan da diyar ta sun zo ina kyautata zaton sune su Umaimah," Wata iriyar sufa tayi ta d'akko qur'anin ta ta buɗe ta ajiye a gaban ta ta na motsa baki, sannan ta yane kan ta da hijab kamar yanda ta saba idan ta na karatu a gidan su Umaimah. Ramai ce tayi ma su Mum iso su kuwa suka shiga cikin d'akin da ke da duhu sai Mum ta yi amfani da wayar hannun ta ta kunna haske dan su dinga ganin ina suke jefa qafar su, ba laifi d'akin a share yake sosai, amma ba wani wajen zama sai ledar d'akin da ta ji jiki d'akin cike yake da tarkacen kayan su ko ta ina a qulle a zani. Cike da jin kunya Jameelah ta tsaya kallon qur'anin tana murmushi alamar na gan ku amma sai na kai aya zan yi magana. Shafa kan ta Mum tayi tare da sanya mata albarka, tana jin daɗin kamun kan Jameela, waje suka samu a gefen tabarmar da Jameelah ke shimfid'a ta kwata idan dare ya yi suka zauna, ta na gama muimui da bakin nata ta washe baki ta na fad'in, "Mum sannun ku da zuwa, Umaimah shine baki faɗan zaku zo ba yau?" "Ta ina zan sanar dake baki da waya, an baki kuma kin qi Karb'a, yanzu dai gamu mun yi maki zuwan bazata, na karya surutun ki na bana zuwa gidan ku gashi mun zo har da Mum da yah Umar ya na can waje duk na kawo maki su" "Aka dai kawo ki, ka ji bakin ta a wajen" Dariya suka yi baki ɗayan su Ramai ta kawo masu kunun aya da zobo, dibulan da kilishi, ashe dik dad'ewar da ta yi aikan data karkasa yara a sayo mata kenan, Mum taji daɗin karamcin Ramai kwarai ainun. "Mama ! bari na kai wa Yah Umar shima tare suke yana waje," Ramai ke ta zazzare ido jin an kira ta da Mama, taji matuqar daɗi kuwa a ran ta. Ɗaukan gora ɗaya na zob'o ɗaya na kunun aya tayi ta saka cup ta sa hijab ta tafi kai masa a waje. Yana zaune cikin motar ya qurawa hanya ido yana jin kamar ya fada gidan ya gan ta ko zai samu sauqin abinda yake ji game da ita a qoqon zuciyar shi ta fito......... *Wai ni Umarrrr what do u mean? Iyyee? Nace what is ur nufi ne akan Jameelaa?* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 9: Bai san sanda wani qayatattacen murmushi ya kub'uce masa ba a kyakkyawar fuskar shi,sai ya sa hannayen shi biyu ya gyara zaman rigar shi a jikin shi, sannan ya bude qofa ya fita waje tare da kafe ta da idanun shi da yake wani lumshewa, yauce rana ta farko da Jameelah ta ji kunya wai dan namiji yana kallon ta. Buɗe mata mota yayi ta zauna tare da zuba masa kunun ayar ta miqa masa, shanye wa yayi bayan yayi bismillah ya na ci gaba da kallon ta ya miqa mata cup din ta sake cika masa ya shanye, cike da murmushi da jin kunya ta ce, "Yah Umar ya qare fa" "Auu ai ban kula ba ma ni" Dariya suka yi tare, sannan ya kafe ta da ido ya ce, "Kin san wani abu kuwa Jameelahhh?" "Sai ka fada Yah Umar" "Kina da kyau mai ban mamaki Jameelah, the more mutum yana kallon ki, the more yana ganin kyaun ki na qara fitowa," Cike da jin nauyin shi ta ce, "Yah Umar kenan, ai dik wani mai kyau a zamanin nan namu ya bi bayan ka, in ana neman mutum     kyakkyawa aka same ka an gama nema an hutadda kowa," Umar ya ji daɗin kalaman ta,dan kuwa yau ce rana ta farko da wata mace ta taɓa zama ta yi masa irin wannan kalaman duk da cewa ya na samun mata masu nuna suna son shi sosai, babu wadda ta taɓa yi masa irin kalaman Jameelah, kashe murya ya sake yi sannan ya ce, "Da gaske kike yi ko wasa?" "Da gaske nake Yah Umar ba na biyun ka wajen kyau," "Kice in muka yi aure yaran mu za su fi kowanne yara kyau tinda mu ɗin kyawawa ne," Sakin baki tayi ta na kallon shi qirjin ta na d'agawa da sauri da sauri dan tsabar farin cikin jin kalaman shi, wata kwallar farin ciki ce ta taru mata ta sauke ƙwayar idanun ta qasa ta na wasa da robar kunun ayar da ya qare, matsawa ya ɗan yi kusa da kunnen ta cikin murya mai ɗaukan hankali ya ce, "Ko ba zaki iya auren namiji kyakkyawa wa ba Jameelaaahhh?" Da sauri ta fita daga motar tana dariya ta tsaya a jikin motar ta na sauke numfashi, ita a dole wai taji kunya, murmushi Umar yayi ya shafo kwantaccen sajen shi wanda ke haɗe da dogon gemu mai cika da tsaho irin na matasan da ke ji da k'walisa,a hankali take tafiya zuwa cikin gida ta na ji a jikin ta Umar na bin ta da kallo dan kuwa idanun mutane bai taɓa sanya ta jin kamar za ta faɗi ba ta riga ta saba da idanun maza na bin surar jikin ta da kallo, ta tabbata Umar ne kawai ke da wannan damar da ya sanya jikin ta sauyawa,ta na shiga ta tarar da Ramai a tsakar gida da alama leqawa za ta yi kiran ta suka haɗu a hanya,cikin yin qasa da murya Ramai ta ce, "Daga kai ruwa kin je kin yi zaman ki,ai da kiran ki zan je na yi," "Ai gani na dawo, bari su tafi na baki labari," Mamalo da Umaimah na ta hira ta qarasa dakin, zama tayi suka sake gaisawa da Mum sannan Mum ta miqa mata abubuwan data kawo masu,daga bisani ta ce zasu tafi,Ramai ce ta shiga ta na neman waje a bakin gado ta zauna ta ce, "Ku ɗan jira kaɗan yanzu zaki ga baban nasu ya dawo, sai ki yi masa maganar da muka yi dake ɗazu da kan ki, dan zaifi ɗaukan abun da mahimmanci," "To shikenan bari mu yi alwala muyi sallah kafin yazo," Ko rufe baki mum bata gama yi ba Baba yayi sallama ya shiga gidan, a bakin qofa ya tsaya suka gaisa sannan Ramai ta masa bayanin ko su ɗin su waye, cike da fara'a Baba ya ce, "Allah sarki, barkan ku da zuwa muna fa godiya sosai yanda ake kula mana da Jameelah Allah ya qara zumunci," Anan su Jameelah da Mamalo da Umaimah suka koma d'akin su Mamalo dan su ba wa iyayen nasu waje su tattauna akan abinda ya kawo su Mum,sannan Mum ta ci gaba da magana ta ce, "Babu komai Malam, dama yanzu nake faɗawa Maman Jameelahn ni da mahaifin su Umaimah muna neman izinin ka akan ka bamu Jameelah ta koma wajen mu dan mu haɗa ta da Umaimah su dinga zuwa makarantar boko, dan kuwa na taɓa tambayar ta ko tana zuwa makarantar boko amma sai ta sanar dani cewar baka da ra'ayin ilimin boko,ilimin zamani na da matuqar amfani ga rayuwar 'ya mace Malam, domin kuwa yana taimakawa al'ummar Annabi Muhammad sosai ta fannoni da dama, misali kuwa shine aikin asibiti,mace na iya zama lauya ta tsaya wajen kare wa mata 'yan uwan ta hakkin su akan fyad'e ko wata cutarwa da ake masu a rayuwar zaman aure ko zamantakewar yau da gobe, in mace na da ilimin boko ko yawan gulmace-gulmace da dambace-dambace da kuma rashin abinyi yana raguwa a unguwanni da cikin al'umma baki ɗaya,dan kuwa za ka samu irin matan da suka yi ilimin boko da na addini da aji,sannan yawan gasa da sa miji yayi abinda bai da ikon yi yana raguwa,dan Allah ka min wannan alfarmar ka bamu ita mu taimaka ma rayuwar ta itama ta taimaki al'ummar annabi kamar yanda nake yi, dan ni din ma'aikaciyar jinya ce," Tinda ta fara magana Baba ke nazarin maganganun ta,tabbas tana da hujjoji masu qarfi, amma ba zai iya bada Jameela mai son abin duniya ta tafi gidan masu hali ba, shi in so samu ne da da tsayayye ma aurar da ita zai yi ya huta, amma kuma kunyar matar yake ji baya so ya yi mata musu,amma duk da haka Baba ya rufe ido ya ce, "To baiwar Allah na ji bayanan ki kuma na gode da soyayyar da kuke yiwa jini na, Allah ya kare maku zuri'a daga tab'ewa, amma gaskiya Jameelah dai bana da ra'ayin sanya ta a boko, ni da ina da tsayayyen miji ma aure zan yi mata, dan haka ki yi hakuri a bawa Alhajin shima haƙuri, a hakan ma zumuncin da ake mana ina jin daɗin shi sosai," Dik yanda aka kad'a aka raya Baba yaqi aminta ya bada Jameelah daga qarshe haka Mum ta hakura da suka tashi tafiya sai aka kira Umaimah da ga d'akin su Mamalo suka wuce, suna tafiya Jameelah ta shiga d'akin nasu da murna dan jin hukuncin da Baban nata ya yanke akan komawar ta gidan su Umaimah,nan Ramai ta zauna ta rattab'a mata bayani sala-sala, jin yace bazata koma gidan su Umaimah ba sai kawai ta saka uban kuka, kuka ta yi tayi mai sauti tana sambatun Baba baya son ta huta a rayuwa yafi son ta yi ta zama cikin talauci da quncin rayuwa. Yah Umar ya matsu ya ji me iyayen Jameelah suka yanke akan wannan lamari da Mum ɗin shi ke bashi labari amma Mum ta qi qarasa maganar ta saboda fad'awa duniyar tunani da ta yi,ta yi nisa cikin nazarin kalaman Baban Jameelah suka isa gida, tabbas mutum ne shi talaka amma ya na riqe da k'imar sa da martabar sa baya son mutuncin shi ya tab'u, lallai gidan su Jameela akwai tarbiyya da sanin ya kamata. Bayan sun je gida sunyi sallah sunci abinci ne Dad na zaune yana shan tea Mum ta faɗa masa yanda suka yi da mahaifin Jameelah, Yah Umar na d'akin shi yana karatu Umaimah ma na nata d'akin itama. Dad ne ya ajiye mug ɗin da yake hannun sa ya ce, "Lallai na dad'e ban ga talaka mai kamun kai kamar wannan ba, amma kina ganin in har Umar zai amince ya aure ta ba zamu haɗa su aure ba? Ta haka ne zamu sanya ta makarantar boko dan ta sake samun ilimi sosai da zai amfane ta, a yanayin tarbiyyar dana kula tana da shi musulunci zai alfahari da samun yarinya kamar ta dan kuwa zata yi amfani da ilimin ta wajen taimakon mata har ma da mazan ma," "Wannan gaskiya ne Daddyn Umaimah,na ji daɗin maganar ka sosai dan kuwa ni kaina nayi wannan tinanin, tinda yana son ta yi aure ai sai ta zama surukar mu, amma kuma kana ganin Umar zai yarda? karatun shi fa?" "Babu komai zamu iya mu kai komai na aure, ya zamana dai an san yaron mu ne zai aure ta, in yaso sai mu sanya ta makarantar bokon a can gidan su ta fara zuwa,tare da amincewar mahaifin ta amma, daga sanda Umar ya kammala karatun shi sai a daura masu aure ta tare ko ya kika gani?" "Gaskiya Honey shawarar ka tayi kyau sosai, Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi," "Ameen" Da wannan shawarar suka tashi zuwa makwancin su. ********************** Har ranar asabar ta yi Jameelah bata daina kuka da roqon Baba akan ya barta ta koma gidan su Umaimah ba, a ranar da safe Jameela ta tashi idanun ta sun yi mata qanana saboda kuka da ta kwanayi, haka ta shirya zuwa makaranta dan samun sauqin rad'ad'in da take ji a zuciyarta, a hanya ko ci kan ki bata ce wa  Mamalo ba da ke ta yi mata surutu, ko kanzil Jameelah bata ce mata ba,Mamalo da ta kula oganniyar bata da niyyar yin magana sai taja bakin ta ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka isa makaranta. Koda Malam Haroon ya shigo ajin su ya kira Jameelar shiru ta yi kamar bata ji shi ba, wadda ke zaune kusa da ita ce ta maimaita mata mai yace nan ta fara masifa ta na fad'in ai ta ji shi dan ita ɗin ba kurma bace bata ga damar amsawa bane sai yaya? Umaimah ce ta kama hannun ta ta na lallashin ta akan ta yi hakuri ta daina fushin da basu san dalilin yin shi ba, Nan take Haroon ya ji dik ta fita a ranshi, a da yana yi mata kallon mai hankali ashe ba wani hankali a tare da ita, fita yayi yana tina yanda malamai ke masa bayanin halin ta tare da ganin wautar shi na bata monitan ajin, ko shi yasa yaran suka yi ta nuna basu son ta ranar saboda bata  da kirki? A cikin satin sai da Haroon ya gane wace ce Jameela, a satin ya kwace muqamin monitan da ya bata ya miqa shi ga Umaimah. Jameela ko a jikin ta kuwa dan dama ta gaji da playing good girl da take faman yi ba riba,a haka Haroon ya fara sabawa da Umaimah har shaquwa mai qarfi ta shiga tsakanin su. In an tashi break ya kan yi wa Umaimah karatu na musamman, nan da nan Umaimah ta wuce sauran 'yan ajin su a karatu. *********************** Cikin wata iriyar murya da ke nuna tsananin matsuwa da buqatuwa take magana, "Haba Haroon, in baka biya min buqata ta ba wajen wa ka ke so naje? Ko so ka ke na fara kawo maza gidan yayan naka?" "Amma dai Aunty baki da tsoron Allah kwata-kwata a rayuwar ki, mata da dama mazan su na tafiye-tafiye na tsahon shekaru ma ba iya sati biyu ba ko wata ɗaya, kuma suyi hakuri su riqe amanar auren su, amma ke ba zaki iya yin hakan ba? ke kenan chatting ɗin banza da wasu mazan da auren ki, sannan babban abin takaicin wai qanin mijin ki uwa ɗaya uba ɗaya kike neman ya biya maki buk'atar sha'awar ki wannan wace iriyar musiba ce haka fisabilillahi?" "Kai ka san wannan Haroon ni ban san haka ba, laifin waye dan na nemi qanin mijin nawa? Kana da masaniyar cewa yayan ka ba irin yanda ban dashi ba akan ya dinga tafiya dani wajen kasuwancin shi amma yaqi, ba zan taba iya hakuri har na tsahon sati biyu ba babu shi a kusa da ni, ya na da kud'in da zai yi duk wata zirga-zirga da ni amma ya ki yin hakan,ai ni din ba dutse bace ina da bukatar miji na a kusa kuma na sanar da shi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma ya k'i ji" "Aunty fita ! Fita min a d'aki bacci zanyi bana son abinda ki ke yi min," "Sai dai ka rife ina ciki, ba inda zani" Takawa tayi kusa da shi tare da cire doguwar rigar da ta dora akan wasu tallatattun kayan bacci da ta saka, wani irin qamshi ne mai sanyi ya ziyarci hancin Haroon, kafe ta yayi da ido idanun shi sun sauya kala zuwa jawur saboda ɓacin rai dan kuwa kwata-kwata bata bashi sha'awa ba duba da yanda ya tsani zina da dikkan dangogin ta kuma cewar ya na yawan yi wa kan shi addu'ar Allah ya tsare shi daga zina da dikkan abinda ya shafi zina har qarshen rayuwar sa, shi yasa Allah yake kare shi da jin sha'awar Aunty Hauwa'un a duk sanda ta zo masa da buqatar ta,kafin yayi wani yunquri ta fada jikin shi qirjin ta ya na gogar nashi,a kid'ime Haroon ya furta kalmar, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musib....." Da sauri ta rufe bakin ta da nashi, ta fara sumbatar shi,wata iriyar bangaza ya yi mata ta bugu da jikin ginin d'akin nashi, nan da nan goshin ta kuwa ya kumbura ya tashi ɗaukan rigar ta yayi ya wurga mata, tare da d'aga murya cikin tsananin bacin rai ya ce mata, "Allah ya saka mini abinda ki ka yi min ba zan taɓa yafe maki ba azzaluma mai cin amanar auren ta, Allah ya shirye ki ya yaye maki wannan jaraba da musiba da take tare da ke, wannan wanne irin zamani ne lalatacce haka ni namiji ban neme ki ba ke mace ki ke nema na? Ki bar min daki ko na illa taki yanzun nan mara hankali da tunani kawai," "Ni ka wulaqanta haka ko Haroon? Ni ka tozarta Haroon? Tabbas sai na wulaqanta ka kamar yanda ka wulaqanta ni, zaman gidannan sai ya gagare ka Haroon, mu zuba mu gani ni da kai wa ye mai nasara," "Nasara tana a wajen Allah kuma a wajen shi nake neman tsari da ke da dikkan sharrin da ke tattare da ke, komai zaki min zan barshi akan qaddara ta ce a hakan kuma ba zan yi fushi ba, zan godewa Allah a dik yanda yaso ya ganni, kuma ta Allah ba taki ba," "Mu zuba mu gani, mara rabo kawai," "Gaki nan babbar mara rabo, kina da aure ki ke neman qanin mijin ki," Ɗaukan rigar ta tayi ta saka tare da ficewa a d'akin nashi ta daki qofar a yayin futar ta. Rintse ido yayi yana sauke numfashi mai zafin gaske, ya zai yi da wannan jarababbiyar mata, gata bata fushi da duk abinda zai yi mata gobe ma sake dawowa zata yi, dik yanda ya so ya mata rashin mutunci sai dai in yayan shi bai yi tafiya ba amma sai ta sake fito masa da wani sabon salon, har abin key ɗin d'akin shi sai da ta sa aka cire gaba ɗaya saboda rufewa da yake yi ta ciki. Hango sanda ta ke masa kiss yayi a idanun sa cikin sauri ya sa hannun sa na dama yana ta goge bakin shi tare da zubar da hawaye gami da yi mata Allah ya isa. "Ya Allah ka kare ni daga sharrin wannan baiwa taka, kar tayi galaba akaina, Allah ka kare ni daga aikata zina har qarshen rayuwa ta" Kad'e wajen kwanciyar shi yayi sau uku tare da bismillah ya yi addu'ar bacci ya rufe ido ko bacci zai ɗauke shi ya manta da abinda ya faru,amma sai bacci ya qi zuwa masa sam a wannan daren, shin me zai yi ya taimaki rayuwar shi ne? 'Ina ganin maida hankali zan yi akan kasuwanci na, na daina dawowa gidannan ko a shago sai ina kwana musamman sanda Yah Ishaq yayi tafiya, in ba haka ba zuciya bata da qashi ban san sanda matar nan zata iya ribata ta ba, ya Allah ka agaza ma rayuwar maraya' Da wannan tinanin bacci ya ɗauke shi cike da mafarkai kala-kala wanda suka sanya shi tashi cikin mamaki. "Me zai sa nayi mafarkin ta kuma? Bayan ba wata alaqa ta soyayya a tsakanin mu?....... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 10: Tunda ya farka yake ta qoqarin kawar da tinanin mafarkin da yayi akan ta amma ya kasa mantawa, har ya gama shiryawa dan zuwa makaranta bai bar tunanin ta ba, daga qarshe sai ya sakar wa zuciyar shi ragamar ci gaba da tunanin ta dan yin hakan shine kawai mafita a gare shi a wannan lokacin. Yau Aunty Hauwaa har qarfe takwas na safiya ta yi ta na d'aki bata fito ba,saboda kai ya kumbura mata ya yi him ta gaban goshin ta, ga wani azabbben ciwon kai da take ji ta rasa inda za ta saka kan ta ta ji daɗi a ran ta,cikin ran ta take ayyana, 'Ni yaron nan ya tozarta haka,ai kuwa daga daren jiya yayi na qarshe, ko ya biya min buqata ta ko kuma na rusa masu kyakkyawar alaqar dake tsakanin shi da dan uwan shi dani yake zancen in ya san wata bai san wata ba' Bangaren Haroon kuwa yana zuwa makaranta da ita ya fara tozali, murmushi tayi masa sannan ta sauke kan ta qasa tana kallon qur'anin ta, kafe ta yayi da ido yana tuno mafarkin da yayi da ita, da sauri ya fara korar shaid'an sannan ya buɗe murya ya fara karatun qur'ani, nan da nan kowa ya nutsu suka bashi hankalin su, Jameela ce take tab'o Umaimah wadda hankalin ta gaba ɗaya na kan karatun da ake yi masu. "Ke Umaimah, dallah tambayar ki zan yi," "Dan Allah ki bari a gama mana qari in ya fita sai muyi maganar," "Yana da matuqar amfani a wajena" "Menene haka da ba zai iya jiran malam ya fita ba?" "Da wannan surutun da kike yi da amsa ki ka bani tini da an wuce wajen," Malam Haroon ne ya ce, "Jameela fito nan," "Me nayi?" Wasu daga daliban ne da sauri suka riqe baki dan jin tambayar da ta yi ma Malam Haroon, malamin da kowa ke girmamawa saboda ba shi da takura kwata-kwata, cike da Mamaki ya kalle ta ya ce, "Tambaya ta ma me ki ke yi meyasa? OK fito nan in yaso sai na maki bayani," Cikin gantsaro girji ta fita gaba ɗaya na shanun ta sai kad'awa suke yi dan ta nuna masa ita fa ta girma tafi qarfin a na wani kiran ta gaban aji ana dizga ta, ɗauke kai yayi daga kallon ta, shaid'an na sake maida idon shi wajen kallon qirjin nata, da sauri ya ɗauke kan shi tare da a'uziyya a cikin ran shi,cikin ranshi yake ayyana, 'Tin jiya na fara jin wannan baqon lamarin akan mata, meke damuna ne haka?' Ganin ta zo kan shi ta tsaya qerere ne ya sanya shi saurin dakatar da ita ya ce, "Tsaya can malama, ko kin ji na ce ki zo daf dani kamar zaki fado min akai ne? Ke wai me ya sa baki da tarbiyya ko kaɗan ne? Amma babu komai Zanyi maganin ki yau, faɗa min a wacce sura muke sannan aya ta nawa muka tsaya?" Tinani ta hau yi ta rasa ina suke kwata-kwata, sai wani qiqqifta ido take ta na d'aga kai sama ita a dole tuna inda suke take son yi,ta kalli wajen su Mamalo da Umaimah dan a taimaka mata da amsa sai motsa baki suke yi ana faɗa mata amma ta kasa ganewa saboda tun asali bata maida hankali ta gane a ina ake ba balle ana faɗa ta gane ta iya furtawa,ganin ta kasa faɗa ne ya sanya ta murgud'a masa baki sannan ta ce, "To ai ba ni kadai bace nake surutun ai harda Umaimah, ai da ita muke magana sanda ka ganni," Umaimah ce ta d'aga kai da sauri tana zaro ido waje jin Jameelah na so ta ja mata duka,dan ita ba a taɓa ma fidda ta gaban allo ba da sunan laifi, tasan ta yi surutu amma bata fatan a hukunta ta akan hakan dan ba da niyya ta yi ba,malam Haroon da ya kalli sashen Umaimah ya ganta a tsorace sannan ya gane Jameelah so take kawai a yi mutuwar kasko dan haka sai ya ce mata, "Ban gan ta ba ke na gani, ki karanta min surar da muke yanzu ko na saɓa maki," In-ina ta fara yi kawai daga qarshe ta hau yi masa wata surar daban, sai da ya bari ta kai qarshe sannan yace a mata kabbara, ya yafe mata tinda a qalla ta iya karatu in yaso sai ya maimaita dan ta gane wajen da suke, sannan ya yi mata warning akan surutun daya ga tana yi, Ko irin godiyar nan bata yi masa ba haka tai komawar ta wajen zaman ta,Kad'a kai yayi tare da furta. "Allah ya shirya ki Jameela" Da break kuwa Umaimah yau sai ta haɗe fuska sosai, dan kuwa bata ji daɗin yanda Jameela ta tona mata asiri ba, da an dake ta fa? "Haba qawalliya rabin duwais, me ne ne wai? Ke baki san wasa ba, na san ba zai taɓa fidda ki ba kawai na fada ne amma kiyi hakuri" "Kin san dai bana son abinda zai zubda mutunci na ko ya yake,ke kika fara magana bani ba, amma kike son dole sai kin manna min laifin, yanzu to me kike son tambaya ta ɗazu a ajin da ki ke neman ja mana duka a banza?" "Yauwaaaa, yanzu kuwa zan zayyano maki tambaya ta," Zama tayi daf da Umaimah sannan ta ce, "Dan Allah wace shawara kika ji Mum ta yanke akan komawa ta gidan ku?dan kuwa ina da tsananin sha'awar karatun boko yanzu musamman ma ina so na ji ni ina turanci, kyau na ba zai taɓa haskawa ba in ban waye ba, ba mai kud'in da zai auren a haka na san ga talauci ga jahilci ,habaaa abun sai yayi yawa kuma," Baki sake Umaimah ke sauraren ta sai da ta kai aya sannan Umaimah ta ce mata, "Yan zu ke Jameela har hango ki ki ke yi da aure a wannan shekarun namu? Har hango wanda zaki aura ma kike a idanun ki? Ikon Allah ni kuwa kin ganni ban taɓa hango ni da saurayi ba ma balle aure, ni ban san me ta yanke ba akan maganar gaskiya, sai in na je na tambayar maki ita," "Yauwa Ta'umancyna na gode sosai, ke in banda abinki ma yanzu fa muna kusan shekara ta 16 ne fa, sannan ace ba zamuyi tinanin aure ba? ki kalli zubina ki kalli naki mana, kina nan qirji a manne a bra kanar allo ki duba cika ta kin san........" "In ki naiwa Allah mu bar wannan maganar, shekarun mu basu kai ba," Dariya mai qarfi Jameela ke yi wa Umaimah, Mamalo ce ta iso gaban su da awara a leda tana dame ta, zama tayi tare da yi masu bismillah, dan ta san ba me ci a cikin su,musamman Jameela data raina ta. Cikin dariya Jameela ke yi wa Mamalo bayani, aiko dariya su kai ta yi mata suna nuna mata ita din bata waye ba kuma muguwar baqauyi ya ce sannan yarinya ce qarama, wasu manyan kalamai sukai ta fitowa da su daga bakin su suna faɗi, Umaimah tsoro da mamakin me suke faɗa dik ya kama ta, dan ta kula ba abin alkhairi suke faɗi ba, duba da yanayin da suke yi in zasu faɗa ɗin su maqale murya su kare baki da hijab. Tashi tayi ta bar masu wajen tana mamakin su, anya ba zasu tabka kuskure ba kuwa ta hanyar gayyatar Jameelah zuwa gidan su? Kaiii da sakel. *********************** Kusan wata biyu kenan da zuwan Mum dan roqon Baba akan yabar Jameela ta koma wajen su da zama, har yanzu ba su gajiya ba wajen roqon Baban, Jameelah na yi Mum nayi har ma da Dad ɗin su Umaimahn,kowa ya yi amma Baba ya qi amincewa. Ramai ma tayi masifar har ta gaji tayi lallashin nan ma ya kafe, Jameelah ma ta yi fushi har ta gaji ta sauko, har da yajin cin abinci ta yi a gidan, Baba ko a jikin shi bai ma san ta na yi ba, hakan da take yi ma shi ke qara nesanta zuciyar shi da amince mata ta koma gidan su Umaimahn da zama tunda ba dangin iya balle na baba,kuma shi ba bokon ne baya so ba, ah ah komawar ta can ta ci jar miya anjima tace ba sune iyayen ta ba shine matsalar shi. "Gaskiya ina ganin Daddyn su Umar ya kamata kawai a gudanar da gabatarwar aure a tsakanin Jameela da Umar, tinda ya nuna min yana tsananin son ta shima, amma bai furta mata kalmar so ba har yanzu saboda ganin makaranta yake yi ita kuma kamar ta yi qanqanta da soyayya, kaga shikenan ya hutar da mu tunanin kar mu tursasa shi yin abinda bai da niyya akai" "Kwarai da gaske, ina jin ba sai an wani jira Umar ya kammala karatu ba, a auro masa ita kawai  mun sa masu ido mu kula da su, in yaso sai ta fara makaranta kawai anan ai shi ma ba zai bar karatun shi da yake matuqar so ba akan mace," Dariya Mum tayi ta shafa qirjin shi,tare da kafe shi da kallon qauna ta ce, "Daddyn Umar kenan, shin soyayyar ka raina ko macen?" Shima cikin nishad'i ya kalle ta tare da murmusawa ya ce, "Ni na isa na raina ɗaya a cikin su, bayan ina amfana da kowaccen su," Dariya suka yi cikin jin daɗin yanda dik da girman su suna nuna ma juna soyayya mai kyau da tsafta. ***************** Mata ne dattijai masu shiga ta alfarma suka nufi gidan su Jameelaah dan kai dukiyar auren ta,sai kuma maza guda uku wanda sune a matsayin wakilan mahaifin Umar, tafe suke motocin su jere da na juna sun yi layi suna  ta hirar su ta zumunci, Umar dake tuqa mazan bakin shi yaqi rufuwa saboda ya san auren gata za a yi masa. Yamma ce liss matan layin su Jameelaa an firfito ana ta zance da samari, kun dai san ya zancen na su yake gudana. Jameelaa na manne mattt da Babawo ko masaka tsinke babu a tsakanin su hannun shi na cikin rigar ta,yana yin abinda ya saba a cikin rigar ta ta idan ya shiga, motar su Umar ce ta yanko ta shiga layin ta haske gaban gidan, nan da nan samari da 'yan mata suka h[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMMAERH PAGE 11: Mamalo ce ta rugo da gudu ta tsaya a gaban su Jameelah, a qoqarin ta na kare Jameelar dan kuwa ta gane motar Umar a cikin jerin gwanon motoci guda uku da suka shiga layin nasu. Cikin hasala Jameelah ta ce wa Mamalo "Mamalo wai me yasa baki da hankali ne,ke sai muna cikin hirar soyayya mai daɗi ki wani zo....." "Kin kirani mara hankali idan Yah Umar ya gan ki a haka, ga shi nan harda mutanen gidan su suka zo," Da gudu Jameelah ta durqusa can qasan bencin wajen da suke zaune tana gyara zaman bra din ta da kyau a jikin ta,wata iriyar zufa ce ke karyo mata,cikin rawar murya ta ce, "Mamalo banda kamar ki dik duniyar nan, dan Allah je ki boyo littafi a rigar ki ki zo min dashi nan, ko qur'ani ko hadithi, ko ishmawee, ke ko sirah ce ko iziyya ki dakkon yi gudu," Aiko da sauri Mamalo ta nufi gidan su, inda ta tadda mazan zaune a tabarma, matan kuma Ramai ta yi masu shimfid'a da tabarma babba a tsakar gida sun zauna ɗan d'akin nasu ba dai tarkace da duhu ba,Umar kuwa yana cikin Mota yana ta washe baki yana kallon qofar gidan, ya bar motar a bude  fitila na haska shi  a hankali take d'aga kai tana kallon shi, Babawo sai tambayar ta yake yi waye wancan ɗin da ta rud'e dan ta ji an ce ya zo amma Jameelah taqi amsa shi, saboda kar ya ji ta na son shi ya tada mata da hayaniya, gajiya ta yi da tambayoyin Babawon a qufule ta ce masa, "'Yan uwan Ramai ne na Abuja suka zo, sun zo zasu dauken a maidani can dan na yi karatun boko, amma ba zan iya tafiya na barka ba, yanzu ka taimaka ka tafi gobe da rana kazo mu tattauna akan wannan matsalar,  kaga babban ɗan Yayan Ramai can kar ya gan mu ya fad'awa Baban shi, dukan tsiya za a yi min, ba zan samu damar basu hakuri ba ma kar su tafi da ni, dan Allah kaje sai gobe kazo," Kad'a kai kawai yake kamar wani qadangare alamun yana fahimta, daga qarshe ya roqe ta akan ta musu qoqari kar a raba su, bai san yana mugun son ta ba sai yanzu da yaji zancen rabuwa. Har zai tafi ta riqo wandon shi ta ce masa, "Ina kudina na yau? Ko kana nufin kaci bulus ne?" "Ke dai mayyar kudi ce, gashi nan, ana cikin wannan halin tashin hankalin amma ki na zancen kuɗi" Miqa mata dubu ɗaya yayi ya wuce, tana nan zaune sai zagin Mamalo take yi da bata kai mata komai ba, ta kai minti huɗu duqe, sannan Mamalo ta kawo mata iziyya ta miqa mata tace, "Wannan na samu ana can ana bada dukiyar auren ki, akwatunan nan da kika ga an shige da su cikin gida to dika naki ne,wato kayan lefen ki idan kin gane hausata, yanzu haka na baro su naji ana saka ranar auren ki, ban gama ji ba dai na fito, dama aure za a maki ko labari babu? Gaskiya baki da mutunci," Wani irin daɗi ne ya kama Jameelah har sai da ta saki kukan murna mai karfi sai da tayi mai isar ta sannan ta leqa dan ganin ina Yah Umar ke kallo, ganin yana kallon qofar gidan su ne yasa ta miqe ta gyara  hijabin ta,ta ja skirt din ta qasa da kyau, sannan ta fita riqe da littafin ta a hannu kamar wata mutuniyar kirki, cikin wani irin yanayi na wadda ta samu nasara akan cikar burin ta ta ce wa Mamalo, "Mamalo amsoshin tambayoyin ki sai gobe zan baki su," Kanta a qasa ta zo wucewa cikin gidan da sauri Yah Umar ya buɗe mota ya hau kwalla  mata kira, cikin sunne kai ta kalli wajen da yake tsaye, cike da nutsuwa ta taka zuwa inda yake, Mamalo na tsaye tana ganin ikon Allah. Gaisawa suka yi, ya ke tambayar ta daga ina take, "Yah Umar na ɗan je gidan wata qawata ne can layin qasa da mu kaɗan dan ta sake koya min qarin da aka yi mana, saboda bana son a wuce ni ban iya ba kuma na yi shiru,ga shi ko sallahr isha'i ban samu nayi ba ina ta sauri na dawo gida," "Allah sarki Jameelaah tawa, Allah dai ya nuna min ranar da zaki zama mallaki na, lallai zan kwashi ilimin addini a wajen ki ba kaɗan ba, nima taho min da ruwan alwala nayi anan," Amsawa tayi ta shige ciki, a qofa ta durqusa har qasa ta gaida baqin da ke zaune a tabarma da Baban ta da 'yan uwan Baban ta da ke kusa da aka kira su dan karb'ar dukiyar auren ta,ganin littafin dake hannun ta ne ya sanya su suka dinga jin daɗin zata kasance surukar su a nan gaba, da gani daga makarantar dare take, ga Mata nan MAZAUNA GIDA ba abinda suke sai iskance-iskance a lungun, amma ita ta maida hankali wajen neman ilimi. Haka matan ma ta bisu da gaisuwa kafin ta ajiye littafin ta koma dakin su Lantai ta zauna,sukan su matan gidan mamakin sauyawar Jameela suke yi,ta na abu kamar wata wahainiya, yau lafiya qalaou zaka gan ta, gobe kamar 'yar tasha. Ruwa ta d'iba a buta ta fita waje ta kai ma Umar ta koma cikin gida, alwala tayi ta koma d'aki ta tada sallah a lungun d'akin su, matan da aka ma shimfida a tsakar gida suna kallon yanda take sallah a nutse suna ta sha'awar ta, sun tabbata Jameelah ta fita daban a cikin yaran unguwar tunda sun ga yanda yaran unguwar suke basu da tarbiyya amma ita ta fita daban. Matan gidan suna ta kallon kaya suna yabawa, wasu kuma na ta kyab'e baki da yada magana, wanda matan basu fahimta ba sam, dan a iya ganin su Jameelah mutuniyar kirki ce,dan haka karin maganar da wasu daga matan suke bai shafe ta ba. An saka ranar aure wata biyu masu zuwa wanda Jameela ji ta yi dama sati biyu aka saka ba wata biyu ba, me zata yi a wata biyu a wannan gidan nasu? Ai wata biyu yayi yawa. Lefen Ramai ta roqa su koma da shi dan kuwa su ba su yin bidi'a, Jameelah na d'aki tari ya sarqe ta jin wani karambani a wajen Ramai. Ramai ruwa ta ɗauka a cup dan ta kai mata kuma su tattauna game da abinda ta ce kar Jameelar ta saki baki ta yi mata wauta a gaban baqi,tana bata ruwan Jameelah ta damqi hannun ta, ta ci gaba da tari, can kuma sai ta yi qasa da murya sosai sannan tace, "Ramai in kk bari aka koma da kayan nan ko na je gidan sisi ba zaki ga na kawo maki ba, wanne irin kuskure kk qoqarin tafkawa ne haka?" "Baki da wayo, ki tsaya ki ji me zai biyo baya," Tari ta ci gaba da yi a hankali alamar data sha ruwa tarin ya lafa. "A gaskiya ba sai kun bar mana wannan uwar dukiyar ba, saboda mu ba wasu masu qarfi bane, mun godewa Allah da abinda ya azurtamu da shi, in ta koma hannun ku zaku iya mata komai da kuke so," "A gaskiya Yaron mu yayi dacen samun mace ta gari, kud'in abin alfahari ne gaskiya duba da irin society da kuke ciki, to amma ku tsaya ba za a yi haka ba, zamu koma da su kamar yanda kk buqata sai dai zamu ajiye mata a wajen mu, dik sanda aka kai ta gidan ta sai ta d'inga amfani da su, dama kayan ta ne ai," "To wannan kuma ba zan hana ku yi ma diyar ku abinda kuke so ba, amma anan kam mahaifin ta ma na san ba zai bari ayi ta kashe dukiya haka ba," Da haka akai sallama akan matan su fita zasu koma, cike da godiya da jajanta bata basu komai ba dan basu san da zuwan su ba. Baban Jameela bakin shi har kunne dan kuwa ya ji daɗin yanda suka zo neman aure a lokaci ɗaya aka sa rana da komai, ina ma zai iya da yace su dawo gobe a d'aura aure, amma dole ya sama wa diyar shi qima a idanun su kar su ga kamar neman kai yake yi da ita, ko da dai sun ce basu son a kaita da komai na kayan d'aki dole ko gara mai rai da lafiya yayi wa 'yar shi ya fidda ta kunya, dan haka zai yi amfani da kud'in kayan d'akin da za a yi mata ya narka mata su a gara. Umar yaso ya zanta da Jameelaah amma hakan ba zai yu wu ba tinda ba shi ɗaya ya zo ba. Kuka Jameela ta fashe da shi a cikin hijab ganin ana ta ficewa da kayan lefen ta, bata ko duba su ta gani ba. Aiko suna tafiya ta fara masifa tana kuka ta na fad'in, "Gaskiya Ramai kin cuceni, wataran sai na dinga tinanin anya kina son ci gaba na ma kuwa? an kawo kaya masu uban yawa da tsada haka dik da sun ce ba su yi wani shiri babba ba amma kin sa an maida su, haba Ramai haba Ramai," "Dalla kiyiwa mutane shiru ki ji dalilina,nayi hakan ne ba dan komai ba sai dan gudun b'arayin cikin gida da na waje, yanzu baki san a cikin garin nan satar kayan lefe ake ba ko? Ko a yan ganin kaya ko barayin dare, ba ki da wayo sam, kuma da na yi hakan baki ji yanda mutuncin mu da qimar mu ta qaru a idon su ba, suna mana ganin wasu salihai, marasa son abin duniya" Muryar Baba ce ta katse masu hirar da suke yi, cikin baqin ciki ya ce, "Allah ya shirya ku Ramai ke da 'yar ki wato ba dan Allah ki ka yi abinda ki ka yi ba, gaskiya kuna bani mamaki matuqa, mutanen nan domin Allah suke son ku fa, amma ku zuciyar ku ba Allah, sai ku shirya watannin da suka rage nayi na aurar da ita ta bar min gida ko na huta nima," "Baba kaima madadin kasa sati biyu ko uku amma sai ka kai abun har tsahon wata biyu," Duka ya kai mata ta goce Mamalo ce ta yi sallama a d'akin dan karb'ar littafin ta, sannan kuma taji gulma, miqa mata littafin Jameelah ta yi ta komawar ta ciki ta yi banza da Mamalon. Ran Mamalo kuwa idan ya yi dubu to ya ɓaci, a qalla ai ta taimaka mata ta rufa nata asiri amma Jameelah bata gani ba, amma ba komai gobe ma rana ce. ******************** Umar ya maida hankali sosai wajen karatun shi, domin yanzu haka a shekarar shi ta uku yake, yana da sauran shekaru a gaba dan zama kwararren likitan mata. Umaimah na ta jin daɗi Jameelah zata zama matar Yayan ta, dan kuwa tana qaunar ta tsakani da Allah sai dai tsoron halayen ta da ba kowa ya sani ba ke dakushe farin cikin ta, sai kawai ta maida hankali wajen yi wa qawar ta ta addu'ar Allah ya shirya ta. Jameelah ta ci gaba da zuwa makarantar islamiyyah inda Ramai ta dage da shiga kasuwanni wajen nemawa Jameelah maganin matsi dana qara ni'ima tare da na mallaka. Ba abinda magungunan nan ke qarawa Jameelah in ba sha'awa ba,gashi Ramai tayi tsayin daka dan hana ta zuwa wajen Babawo, Bukar kuwa sai amshe ma Babawo kuɗi yake da sunan zai san ya zai ya fito da Jameelah ko a boye ne. Ramai ashe zata iya hana Jameelaah fita tun da ba ta hana ta ba har ta zama abinda ta zama a yanzu, sai yanzu ne take iya hana ta dan kar a tambad'ar da maganin mallaka da na qarin ni'ima a waje, ya ilahi wannan Rayuwa ce muke ciki? A haka aka ci gaba da shirye-shiryen biki domin lokaci ya na ta qaratowa,duk wani gyaran jiki ciki da waje Ramai ta dage ta na ta yi wa Jameelah saboda ta kai ta gidan miji da kwaskwarimar da suke yi na b'oye yanayin da 'yar su take ciki..... *Godiya mai tarin Yawa zuwa ga makaranta MAZAUNA GIDA ina jin daɗin sharhin ku matuqa...sharhi shi ne takin marubuci mai zaburar da shi ya qara qaimi akan rubutun sa .keep on commenting guys za ku ji daɗin labarin anan gaba fiye da yanda kuke ji a yanzu...wanda aka bari a baya basu karanta previous pages ba su yi hakuri a kammala a haɗa document.* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 12: Ansha bikin Umar da Jameelaah cikin wadata da walwala dan kuwa biki ne daya samu halartar mutane sosai, 'yan cikin unguwar su Jameelah an zazzo kamar an yi ruwan jama'a saboda yawa, anko kuwa sai da Jameelaah ta fidda kala biyar, saboda a cewar ta kowa ya riqe gudummawar shi a kece raini kawai wajen fidda ta kunyar saka ankon bikin ta, wasu sun samu sunyi dika dan kar su ji kunya, wasu kuwa sun samu yin wasu basu samu yin dika ba, wasu kuwa ko ɗaya ma ba su samu damar yi ba saboda ta abinda za a ci ake ba ta anko kala biyar ba,ai kuwa wanda basu yi ba sun sha gori da habaici wajen Mamalo babbar qawar amarya, wadda itama amarya ce ta agaza mata da wasu ankon dan kar ta ji kunya a ce babbar qawar ta ma bata yi anko dika ba. Sadakin Jameelaah ya sa qawayen ta sake girmama ta a cikin layin dan kuwa dubu hamsin cif haka aka bata, a tarihin layin su kuwa mace bata wuce dubu goma ko a shirin,tayi wuta shine ake bata ashirin din. Anci ansha da kud'ad'en da Ramai ke ta tari dama saboda bikin d'iyar ta tilo, gara kuwa Baba ya aje ba laifi a qalla a layin su ba a taba yin ya su ba,buhun shinkafa biyu na gwamnati, taliya kwali biyu silver, sugar buhu ɗaya, maggi kwali ɗaya, gishiri qaramin buhu,manja da man gyada manyan jarkoki, kowanne ɗaya-d'aya, sannan ya ɗora dubu goma wai na cefane, mutanen unguwar wasu cewa suka yi ma surukan ne suka bayar dan su fidda su Jameela kunya, da magana ta dawo kunnen Jameelaa, kuwa ta yada nata maganar dan a sake watsa ta kowa ya san iyayen ta ne suka yi wahala da gumin su. Babawo daya ji maganar bikin a qurarren lokaci ɗan qaramin hauka ya yi masu, Jameela kuwa ba kunya ta tsefe shi tasss ta wanke shi da zagin rashin mutunci, dan kuwa ta sanar dashi dik kud'in da ya bayar ya fanshe abin shi dan haka ba mai binta bashi a dik fad'in unguwar nan. Kowacce amarya in za a kaita d'akin mijin ta tana kokawa amma banda Jameela, ganin haka ne ya sa Ramai ta nemi kub'ewa da 'yar ta ta, suna shiga d'aki kowa ya fita ya basu waje ana ta tausayin rabuwar su dan an san akwai shaquwa a tsakanin su irin tasu da ta banbanta da ta mutanen kwarai, abun lura dai kawai shine shaquwar 'ya da uwa shaquwa ce kawai,cikin faɗa Ramai ta ce wa Jameelah "Wai ke wace iriyar sokuwar yarinya ce ne Jameelah? ko kin manta shirin da muka haɗa ne? Naga idon ki gyamas ba hawayen komai, dan Allah kar ki rusa mana shiri Jameelah ki fara kuka tun yanzu ko na ci uban ki, ki yi ta turjewa ki na ihu,amma dan iskanci kin tsaya kina abu kamar wata bazawara Allah-Allah ki ke ki je gidan miji, to ko zawarawan yanzu suna kuka in za a kai su gidan miji balle ke budurwa" "Ah ah fa Ramai yaushe kuka zai samu mahalli a idanu da zuciya ta a wannan dare mai tarin farin ciki a waje na? Allah ya d'auken wahala meye kuma na yin kukan? Kin san kuwa yanda nake jin tsananin farin cikin rabuwa da gidannan ? Dan haka banga baqin cikin da zai sa na zubda hawaye ba, dan Allah kar ki sake danganta ni da bazawara kuma bana so, dan ba wanda ya sanni a matsayin 'ya mace ni," "Dallah rufe min baki shashasha kawai, an faɗa maki lallai sai an kwanta da mace ne budurci ke ɓaci? ke dai jeki ko na qarya ne kiyi," Suna zuwa zasu fita daga d'akin, Ramai taga Jameelah bata da niyyar yin kuka,ai kuwa sai ta maida ta baya ta wanke ta da wani had'ad'd'en mari mai mugun zafi, nan take kuwa Jameelah ta saki ihun kuka, Ramai tace, "Yauwaaa irin wannan kukan nake so naji, maza riqen riga a b'anb'are ki da kyar a jiki na," Jameelaah kuka take saboda zafin mari ga kuma takaici a ranar da zata bar gidan su an falla mata gigitaccen mari wanda tunda take tunb'elan ta a gidan ba wanda ya taɓa kafa mata shi a kunci,wannan wace iriyar muguwar al'ada ce ta kuka haka. Dan haka bata da zaɓin da ya wuce na tayi abinda Ramai tace mata, qanqame Ramai tayi kuwa da mugun qarfi dan har sai da Ramai ta saki 'yar qara dan kuwa ba qaramin ruqo ta yi mata ba, sai zunduma kuka take yi, 'yan daukan amarya da suka zo kuwa suna ta tausaya mata, harda Umaimah aka zo ɗaukan amarya dan kuwa ta ce ba za a barta a baya ba sai ta zo,ita tai ta lallashin qawar ta ta, tausayin ta ne mai yawa a ruhin ta, ganin za a raba Jameelah da gidan su sai ta fara hango ta itama an fidda ta a gidan su watara za a kaita inda bata sani ba, nan da nan ta fara kukan tausayawa qawar ta ta, Ramai kuwa sai da ta yi dana sanin yima Jameela hud'ubar ta riqe ta a b'anb'are ta da kyar a jikin ta, dan kuwa hannun ta sai da ya sauya kala ya koma ja, to abinka da farar mace, da kyar din kuwa aka b'anb'are Jameelar a jikin ta. Ko da aka sanya ta a mota mai sanyin AC ga qamshi sai Jameelah ta saki wata ajiyar zuciya mai qrifin gaske saboda daɗin da taji ya ratsa ta, yau dai gata a babbar mota mai AC za a kai ta gidan miji. Kuka ta sake fashewa da shi dan tina plan ɗin su da Ramai,anyi anyi tayi shiru amma inaaa ta qi sam. A haka suka isa gidan nasu Umaimah inda amarya zata tare da surukan ta, Jameelaa kan ta a qasa suka shiga da dangin iyayen ta dika bangaren Baba da Ramai,Mum sai kwarara mata addu'a take yi ita da angon cikin tsananin so da qauna, sannan qannen Ramai biyu da suka rako ta suka d'aga ta dan kai ta d'akin Umar dake gidan, Daddyn su yace sai ya kammala makaranta kafin su tare a sabon gidan shi da suke gina masu shi da Mum. Ta haka ne har zata fara zuwa makaranta ita da Umaimah ta fara karatun ta babu takura,shi ma kuma ya samu damar yin karatun shi a nutse. Umar da abokan shi na makaranta suna waje suna jiran 'yan kai amarya su tafi su raka ango wajen amarya kamar yanda ake yi a al'ada, can qasan ran shi kuwa baya son kowa ya shiga masa d'akin mata, dan yana da kishi ainun kuma a yanayin kamun kai irin na Jameelaah ya san ba zata so wani ya shigar masu d'aki ba. Iyayen Jameelaah da suka kawo ta sun yi mata nasiha sosai dan sun san halin ta sarai, sun bata shawara akan ta aje dik wani makaman rashin tarbiyyar ta dan kuwa da alama gidan masu tarbiyya ne wannan, jin su kawai take yi ko d'aga kan ma basu samu arzqi ba balle ta amsa masu. Haka suka gama suka tafi, 'yan unguwar su da suka zo ganin kwakwaf suka yi ta shiga suna ganin d'aki suna yabawa, dik da ba wani ɓangare guda aka ware mata ba ba kuma parlour, d'akin su babba a haɗe yake da parlourn gidan,cikin d'akin ta ya sha kayan gado da kujeru masu kyau, doguwar kujera ɗaya aka saka sai qarama ɗaya, da tafkeken gado wanda ya sha babban zanin gado mai tsadar gaske, ga labulaye masu tsada suma an baza sai suka qayata d'akin abun sai wanda ya gani kawai, akwatunan lefen ta ga su nan a aje a d'akin, kowa sai kalla yake yi daga nesa, Jameelaa Allah-Allah take yi kowa ya watse dan ta kalli d'akin nata da kyau. Ba su suka gama kalle kallen su ba sai wajen 10 na dare, ta cika ta yi famm kuwa a wannan lokacin, Umar ma dake waje yana jiran kowa ya tafi dik ya qagu kowa ya watse ɗin. Lokacin da kowa ya tafi, Umaimah ce a wajen ta, da wayo da dabara ta kora Umaimah, dan kuwa cewa tayi kan ta na tsananin ciwo so take ta huta, magani Umaimah ta ajiye mata da ruwa ta fita, tana tausaya ma qawar ta, a zaton ta kewar barin gida ne ke damun ta. Koda Umar ya shiga da abokan shi a parlour ya barsu, dan bai yarda da shigar masu d'aki ba,wasun su sun ji haushi kuwa, amma da d'aya daga cikin su ya yi musu bayanin illar shiga d'akin ma'aurata da sunan rakiyar ango sai suka fahimce shi, suka masu fatan alkhairi tare da tsokana irin ta abokai suka miqe dan tafiya, ledar da suka siyo masu kazar siyan baki suka miqa masa suka tafi, dakin Mum yaje dan yi mata sallama ya ji a kulle alamun tana d'akin Dad ɗin su, dan haka sai ya leqa d'akin Umaimah ya yi mata sai da safe tare da aje mata ledar ice cream ya fita. Ko da ya shiga luf take a gado, tana shaqar qamshin turaren da aka saka ma gadon, ga AC na ratsa ta, wani irin daɗi take ji har cikin qoqon ranta yau gata a dakin aure itama. Umar ya shiga ya tsaya yana ta kallon ta, godewa Allah kawai yake yi a zuciyar shi, domin kuwa yau burin shi na biyu ya cika a rayuwar shi sauran ɗaya. Zama yayi a gefen gadon tare da yi mata sallama, tana jin muryar shi ta zabura ta koma gefe a tsorace tana zaro ido waje ita a dole a tsorace take da shi. Murmushi yayi sannan ya sake godewa Allah, dan kuwa ya san shi zai koyar da matar shi komai, ba abinda ta sani. "Relax dear, ba abinda zan yi maki, taso kici abinci dan nasan yunwa kike ji, Umaimah ta sanar dani irin kukan da kika sha ta waya yau, taso kin ji inshaa Allahu ba zaki yi kewar  gida ba zan dinga kai ki akai-akai ,sannan dikan mu zamu haɗu mu kawar maki da tinanin gida, taso nan kin ji ," Tashi tayi cikin sand'a kamar wadda za a kama, Umar kam dariya kawai yake yi mata qasa-qasa. Zama tayi nesa da shi, a haka suka ci kazar nan, sai hawayen murna take yi, Umar kuwa ya yi zato na tinanin gida ne. Sai da suka gama suka yi alwala suka yi sallah, tare da gabatar da nafila, sannan ya yi mata addu'ar da angwaye ke yi wa amare, suka yi shirin bacci. Umar ganin yanda take a tsorace dashi ne kuma shima bai shirya yin komai da ita ba a yanzu, zai riqe alqawarin da ya yi ma Mum na sai sanda ya kammala karatun shi zai bari wani abu ya shiga tsakanin su, sai ja pillow daga gefen inda take a zaune ya yada a qasan carpet ya ɗauki wani bargo a saman gadon. A qasa yayi shimfid'a ya kwanta, yana danne abinda yake taso masa na son kusantar amaryar tashi, ganin haka yasa ta ji daɗi dan plan din su zai tafi dai-dai yanda suka tsara. Cannn cikin dare, suna bacci Jameelaa ta fara kuka tana ihu tare da buge-buge da cizge-cizge.......... *Makaranta zaku ga na yanke wasu abubuwan na tafi aure direct, nayi hakan ne saboda bana son tsawaita labarin, ina son na kammala da wuri saboda wasu uziri nawa da suka taso ba zato ba tsammani, ina fatan hakan bai rage maku daɗin novel din ba* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 13: "Dan Allah kuyi hakuri, kar ku taba ni, wayyooo Allah na, kar ku taɓa ni, bana so......bana so.....kuji tsoron Allah kar ku taɓa ni.......wayyooo Baba ka zo ka cece ni,innalillahi wa inna ilaihirraji'un, lahaulawala quwwata illa billah, wayyoo Allah na...." Sai kokowa Umar da Jameelah suke tafkawa a d'akin a qoqarin shi na ganin ta samu natsuwa, amma hakan bai samu ba, sai da Mum ta shigo d'akin a guje dan babu inda ihun Jameelah bai shiga ba a gidan, Mum sanye take da doguwar riga ta bacci mai santsi kalar blue, rungume Jameelaah tayi tana ta karanto ayoyin qur'ani tana tofa mata, Jameelaah kuwa dik ta haɗa zufa saboda dambe da suka sha da Umar, shi kan shi gwama nunfashi yake yi dan kuwa ya gaji ainun. Kallon yanda ta ke sauke ajiyar zuciya ya yi cikin tausayawa ya ke ayyana 'Haka yarinyar nan take da qarfi? Me ke damun ta to?ko dai ta na da aljanu ne bamu sani ba?' Amsar da Umar ke ta son samu kenan, wani mugun kallo Mum ta zuba masa Jameelaa na kwance tayi luf jikin Mum, tana shaqar qamshin turaren ta mai daɗi, bacci ya ɗauke ta, bacci ne mai nauyi na huce gajiyar biki, gyara mata kwanciya tayi ta rufe ta, sannan ta tofa mata addu'a, da hannu ta yafice shi,suka fice a tare. "Mum na ga kina ta harara ta lafiya kuwa? Ban taɓa ganin kina min irin wannan kallon ba" "Dole na yi maka wannan kallon mana Umar, ina alqawarin da ka ɗaukar min? Ashe ba zaka iya hakuri ba har ka kammala karatun ka? Shikenan ba zan tauye ka ba, dan kuwa matar ka ce halal ɗin ka ce ita,amma haushi na ɗaya da ka yi min alqawarin barin ta har ta sake yin hankali, kai ma ka gama karatu a lokacin cikin kun saba da juna kuma ta qara wayo da hankali amma ka kasa cika min alqawarin da ka dauka," Nan da nan ya gano me take nufi, wata iriyar kunya ce mai nauyin gaske ta kama shi, cikin tattaro dikkan gaskiyar shi ya fara magana, da bayyana mata komai da ya faru tsakanin shi da Jameelah. "Mum yanda kika ji ihun ta haka nima naji shi, na kwanta a qasa ita tana gado kenan, bayan mun gabatar da komai daya dace dan kwantawa, har ma na fara bacci kawai naji kukan ta kaɗan kaɗan cikin baccina, daga baya da na farka kuma naga tafara bige-,bige tana qanqame jikin ta, sannan kuma tana surutai kamar wadda ake so a yi wa wani mugun abun, nayi qoqarin na tsaida ta, amma na kasa, shine fa kk shigo," Ta gamsu da bayanin shi, dan haka tace, "Ikon Allah, kome ke damun ta? Amma kamar jinnu, kamar kuma mummunan mafarki, gaskiya yafi kama da mummunan mafarki," "Nima haka nake zargi, Allah ya kyauta," "Ameen ya Allah, haka ne kuma muje mu kwanta ka kula da ita sosai, inda buqatar taimakona ka tada ni, in na ji ku ma zan zo," "OK Mum, sai da safe," "Allah ya kai mu" Jameelah bata tashi ba sai da gari ya waye tangararau, shima bai tashe ta ba dan bai san a ya zata tashi ba, abinda tai jiyan ya matuqar tsorata shi. Taji daɗin yanda ya barta ta sha bacci a gadon nasu mai laushi da daɗi. Tsabar makirci irin na Jameelaah sai ta miqe tana salati da nuna tashin hankali na ta makara yin asuba akan lokacin ta ga shi gari ya gama waye wa batai sallah ba, harda kwalla. "Sorry love yi komai a hankali kin ji? jeki kiyo alwala sai kiyi sallah abin ki, kizo mu ci abinci har an kawo mana," D'aga kai tayi tana jin daɗin yanda yake lallaba ta. Alwala tayo tayi sallah, tare da yin azkar abinda bata taba yi ba dik tsawon rayuwar ta,ta na gamawa sai ta fara rera karatun qur'ani da ka, Umar dan daɗi har wani lumshe ido yake yi, sai da ta kai qarshe sannan ta yi addu'a ta kwantar da kan ta jikin gado, hawaye na zuba daga gefen idon ta, Umar ne ya buɗe ido ya gan ta a haka, da sauri ya tashi ya zauna a gaban ta tare da lankwashe qafafun shi, yana mai tambayar ta dalilin kukan nata. "Yah Umar ka yi hakuri, dan Allah ka yafe min ni na yarda kuma zan hakura sannan zan jure ko da zaka rabu dani a wannan ranar ne, amma ba zan taba iya haɗa shimfida da kai ba," "Innalillahi Jameelaah kina da hankali kuwa? Me ya shiga kan ki ki ke kiran kalmar rabuwa a tsakanin mu? ni ne fa Umar naki, me ya same ki? Akan me kike kira mana rabuwa, jiya jiya Allah ya hada mu a bainar jama'a Allah ya mallaka min ke sannan ki so rabuwar mu a yau da na tashi cikin farin cikin kin zama mallaki na," Kuka ne ya k'wace mata mai tsanani har tana shessheka, Umar hankalin shi ya tashi ainun, dan haka ya matsa ya jata jikin shi sosai ya na lallashi,aikuwa sai ta shige jikin shi tayi luf tana ci gaba da kukan,cikin zuciyar ta tana ayyana daɗi da laushin jikin shi. "Dan Allah ki sanar dani me ke damun ki kar zuciya ta ta buga," "Yah Umar inna ce maka ni ɗin ba budurwa bace zaka iya ci gaba da zama dani? Na san ba zaka iya ba, kuma babban kuskuren da muka yi kenan nida Mamana, wanda har Babana bai sani ba har yau, dan Allah ka rufa min asiri kan kowa ya ji ka sallame ni na tafi gidan mu, na yi dana sanin rufewa wanda zuciyata ke matuqar so wannan babban sirrin saboda tsoron kar ka rabu da ni tun kafin ka aure ni, zan iya mutuwa akan son ka amma ba zan iya jure ha'intar ka ba," Kuka take sosai kamar an aiko mata Ramai ta fece qiyama. Ji yayi kamar an doka masa guduma a tsakiyar kan sa, amma ganin yanayin da take ciki sai ya sanya shi nutsuwa dan jin me ya faru har ta rasa budurcin ta. "Zan iya hakuri da dik wani abu a duniya, amma ba zan iya hakuri na rasa soyayyar ki ba, ba zan iya ci gaba da rayuwa in bake a cikin tawa rayuwar ba sanar da ni me ya faru ki ke waɗannan kalaman masu tada hankalin mai sauraro," 'Wayyooo dadi,lallai maganin mallakar nan na aiki, tin yanzu ya fara ji na kamar wani sashe na jikin shi,' Cikin tsananin kuka da kauda kai wai ita kunyar bashi labarin da zata faɗa yanzu take yi ta soma magana. "Yah Umar........... *A dandana wannan, da babu gwanda ba daɗi, na san wasu zasuce yayi kaɗan, ayi hakuri da ban yi niyyar typing ba ma yau dan babu appetite ɗin taifin ɗin sammmmm* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 14: "Yah Umar tin....tin....tin inaaa yyyarinya ne.....aka yi min fyad'eeee" Kuka take mai tsananin ratsa zuciyar wanda bai san wace ce Jameelaa ba, Umar sakin ta yayi ya kafe ta da ido, a hankali idanun shi suke rinewa daga haske zuwa jawur, yawun bakin shi ya qafe kukan Jameelaa ne ya qaru, a hankali ta miqe ta hau ɗaukan akwati ta juye kayan kwalliyar dake ciki ta fara haɗa kayan ta da aka zuba mata na sakawa, tana ninke kayan tana sawa a akwatin tana kuka, sosai hawaye da majina na haɗewa a waje ɗaya a fuskar ta kamar wadda aka yi wa shegen duka, zuciyar ta kuwa nata bugawa saboda tsananin tsoron amsar da zata fito daga bakin Umar, 'Allah ka sa qaryar nan tawa ta karbu, in Yah Umar ya qi Karb'a ta na mutu na lalace, ga samu ga rashi, wannan daula bana fatan barin ta, wayyooo Ramai na wayyooo Babana,' Ji ta yi an riqe mata hannu an qanqame ta, fadawa tayi jikin shi ta sake fashewa da sabon kuka cike da son a tausaya mata, ta kuwa samu abinda take nema ɗin a wajen Umar, dan kuwa Umar ya tausaya mata matuqa, zaunar da ita yayi a bakin gado, sannan yace, "Habaa Jameelaa, ya zaki haɗa kayan ki? Ina zaki je to?" "Ttttaattfiiiyaa zan yiii, na san mun zalince kaa....bamu sanar da kai wannan mummunan abun ba, Mamana bata son ana d'aga maganar......abun ya faru ina da shekaru bakwai a duniyaaa....." Wani irin kuka ta saki har tana shidewa ga tari da ya sarqe ta, Umar ya rikice ya rasa me zai bata na taimakon gaggawa, da gudu ya fita ya deb'o mata ruwa a cup ya bata, shanyewa ta yi tasss dan kuwa tana da buqatar shi, qoqarin ci gaba da bashi labarin qaryar ta yi ya katse ta, dan zuciyar shi ba zata iya jure ɗaukan labarin fyaden da akai ma matar shi ba,qanqame ta yayi yana sauke wani wahalallen numfashi, tare da jama dik wanda ya mata fyad'e Allah ya isa a zuciyar shi. "Ya isa haka, ya isa, come on ki daina kukan haka, ina son wannan maganar ta zama sirri a tsakanin mu, kamar yanda maman ki tace bata son kowa ya sani to ki daina tinawa ki daina maimaita maganar, game da mafarkin da kike yi kuma inshaa Allahu zaki daina, ki dage da yin addu'a da azkar, sannan in zaki yi bacci bayan kin gama addu'a ki yi ta tasbihi ga Allah har bacci ya ɗauke ki inshaa Allah zaki daina mummunan mafarkin nan, zo zo ki daina kukan nace ya isa haka, Allah zai saka mana dik wanda ya yi wannan abun," A hankali take sauke ajiyar zuciya, ranta fari kwal kamar audiga,hankalin ta kwance zuciyar ta zaune a ta Umar take narkewa a jikin shi,ta tabbata lallai wannan labari zai wa Ramai daɗi. Gyara dakin suka yi a tare suna yi suna hira sama-sama, dan kuwa zuciyar Umar cike take da takaicin jin wannan mummunan labari, ya ci burin yin aure mai tsafta amma sai gashi zai b'ige da daukan ragowar wani, gwanda da Allah yasa ma fyad'e aka yi mata ba wai da son ranta bane kuma tana qarama hakan ta faru, ta kula da yanayin shi, sai ta saka fuskar tausayi. Ganin haka ne ya sa Umar ya saki tashi fuskar dan baya son taji wani abu na muzanta tinda ba laifin ta bane. "Yi sauri mu gama muje gaida su Dad kafin ya fita," "Ok to !.... Yah Umar" "Na'am My love," Sunkuyar da kai tayi cike da jin daɗi, sannan tace, "Yah Umar ka yi hakuri, nima ba a son raina ba ne na kula kamar zuciyar ka har yanzu tana maka zafi akan labarin dana baka, dan Allah....." Da sauri ya ja ta a jikin shi ya rungume ta, tare da shafa bayan ta, wani iri take ji a jikin ta tinda take hulda da samarin layin su ba wanda tab'in shi ke shigar dikkan wani sashi na jikin ta kamar Umar, lallai rasa shi a wajen ta babbar asara ce, kuma ba zata bari hakan ya samu wajen zama ba. Sun dad'e a haka sai da Umar ya ji nutsuwa ta gama baibaye shi sannan ya sake ta, kama hannun ta yayi ya sanya mata hijab, sannan ya riqe hannun ta suka fita,suna zuwa tsakiyar parlour taga Mum zaune da Umaimah suna karyawa, Mum da shirin fita asibiti Umaimah kuma da shirin makaranta, Dad ne ya fito ɗauke da jakar shi a hannu yana manna glass din shi a idon shi,zama shima yayi ya dauki mug ya yi bismillah sannan ya kai bakin shi. Hannun ta ta yi saurin zarewa a na shi  ta sunkiyar da kan ta qasa, ta matsa daga gefen shi, Mum ce tayi murmushi dan ganin abinda ya faru, "Ku zo ku karya mana, ko kunci wanda na sa akai maku ne?" "Mum Ina kwana? Dad barka da safiya" "Barka dai Yaron Mummy, ohhh ashe fa yanzu ka fita daga sahun yara,ina fatan kun tashi lafiya? Jameelaa kin tashi lfy ko? Ya kewar gida? Ki saki jikin ki kin dai san nan gidan kune tin da balle yanzu," In ji Dad da ke kallon su cike da sha'awar yanda ya ga kamala a fuskar ɗan nashi. "Lafiya qlou 'yan albarka, ku zauna ku karya," "Mum ni na qoshi tea kawai zan sha," "Dad nima yau zan koma school fa, ka san ba wani hutu indai ba so nake a wuce ni ba," "Hakan yayi dai-dai, yau inna kai Umaimah zan gama ma Jameela shirye-shiryen kaita makarantar bokon itama inshaa Allahu, dan banga abin bata lokaci ba, sai dai kiyi hakuri da dik ajin da aka kai ki, zan samo maki mai maki darasi a gida dan ki samu gogewa sosai, fatana ki maida hankali ki bawa mara d'a kunya, kema ki zama wani abu a rayuwar ki," "Na gode sosai Allah ya saka maku da alkhairi, kun taimaka ma rayuwa ta ta kowanne bangare, bani da bakin gode maku," Wasu munafukan hawaye take matsewa, Mum ta shafa kan ta, sannan ta fara lallashin ta, "Haba Jameelaah ! Ai ke da Umaimah dik daya ne a wajena, kin san dai ina son ki a matsayin d'iya ta, to menene abin kuka da godiya kuma? Muma muna taimaka wa dik wanda Allah ya bamu ikon taimaka wane da abinda muke da shi komai qanqantar shi, shi yasa kika ga muma Allah yake qara bud'a mana kullum, dan haka ki cire komai a ran ki kinji?" D'aga kai tayi sannan mum ta miqa mata mug din da Umaimah ta haɗa mata tea a ciki, ta hada mata da soyayya. dankalin turawa da ya ji uban kwai yaji kayan qamshi da attaruhu, sai qamshi ke tashi, ga farfesun naman rago, wani mugun yawu Jameelaah ta hadiya, 'Ya Allah kasa wannan ne abin da zamu na karyawa da shi kullum, jar uban nan kayyasa, daɗi kan daɗi kenan,' "Jameelaa bismillah," "Ni dai daga yau Yaya Jameelaah zan dinga ce maki, tinda dai kin zama matar yaya," "Kar ma ki soma 'yan aji su ce na tsufa, tinda dai ba wani girman ki nai ba ehe," Dariya iyayen nasu suka sanya har Umar, "Ai ina ga kawai kin daina zuwa Islamiyyar nan Jameelah, zamu samu malami yana koyar da ku a gida zai fi, ko da daga islamiyyar ne ma sai a nemo zamu roqa mu samu ko asabar da lahadi ne sai ana maku a gida da safe ko da yamma," "Dad ai kuwa in haka ne akwai wani sabon malamin mu, indai hakan ba zai zama matsala ba ko za a tuntube shi sai yana koya mana a gida, dan shi ke koya min karatu in an fita break dama, ya iya koyarwa," Jameelaah bata son a kawo Haroon gidan dan kullum faɗa suke, gashi kusan kullum sai ya dake ta a 'yan kwanakin can saboda rashin kunya da take yi masa,dan haka sai ta yi shiru bata ce komai ba, Dad ne ya kalle ta ya ce, "Jameelaa yaya dai ko baki son shi yana yi maku karatun ne? Naga yanayin ki ya sauya," "Ah ah ba komai, ina tinanin Mamana ne kawai," Dikkan su sai ta basu tausayi, kewar gida dole ne dama wajen sabon aure,amma a hankali zata saba watarana, Mum ce ta miqe dan ganin tayi latti, da sauri ta yi masu sallama, ta fita a motar ta, Dad da Umaimah ne suka tashi dan tafiya makaranta, Umar ya raka su har gaban Mota ya koma ciki. Yana zuwa ya ga har ta cinye abincin ta ta qara wani, murmushi ya yi ya san ɗazu kunya ta ji kowa na wajen shi yasa bata ci ba, in ko haka ne a hankali zata saba cin abinci da su, komawa d'aki yayi kar ya katse ta, dan da alama ta na jin yunwa sosai , wataqila tinda aka fara biki bata samu damar cin abinci sosai ba. Sai da ta kusan cinye komai sannan ta tattara wajen tana ta sakin gyatsa mai qarfi kuwa,ta qoshi to tayi nak. Mai aiki ce ta taya ta kwashe kayan wajen sannan ta gyara wajen,Jameelaa bata koma dakin ba sai ta hau goge goge, Umar cikin shirin tafiya makaranta ya fito, da alama wanka ma yayi duba da yanayin shi, ya saka kaya masu matuqar kyau, wani yadi ne mai laushi kalar blue dark, ya amshi jikin shi sosai sai qamshi yake zubawa kafad'ar shi rataye da jakar makarantar shi sai lab coat ɗin shi riqe a hannun sa na dama. Jameelah ta shagala da kallon shi remote ya faɗo mata a qafa, da sauri ta duqa dan ta d'aga, Umar ya isa gaban ta Shima ya duqa ya kama qafar ta ta yana murza inda remote din ya buge ta. Lumshe ido tayi tana amsar saqon da hannayen shi ke aikawa qafar ta. Bata san sanda ta dafa kan shi da babu hula ba ta fara murza gashin kan shi a hankali, da sauri ya kalle ta murmushi ta yi shi kuma ya yi kissing qafar ya miqe tsaye,a hankali ta bude idanun ta ta kafe shi da kallo, can kuma kamar wadda aka mintsina ta fara kame-kame ta d'au tsumman, ta aje gefe ta juya ta ɗauki remote ta aje a qasa dik ta rikice, sumbatar goshin ta ya yi,Jameelah ta qanqame idon ta, cikin murya mai sanyi ya ce. "Sai na dawo ki kula min da kan ki banda bigewa, ni Umar naki ne ke ɗaya har abada inna dawo sai ki ci gaba da kallo na ko?" Murmushi ta yi mai sauti ta gudu d'aki ita a dole taji kunya,Umar ma cike da nishadi ya fita. Har ya bude qaramar motar shi da Dad ya sai masa saboda zuwa makaranta, zai shiga ta fito da gudu-gudu, ɗauke da hula a hannun ta kalar kayan shi, "Kayi mantuwa saboda tsabar kallo na da ka ke yi" Tana fada ta miqa masa ta koma gida da gudu, bin inda ta wuce yayi da kallo zuciyar shi na tsananin son matar ta shi , tinawa yayi da abinda ta fada masa, nan take gaba ɗaya daya annurin zuciyar shi ya kau. A haka ya isa makaranta ya na tunani, ya na shiga aji ya ajiye tunanin komai ya maida hankali sosai ya yi karatun shi, abu ɗaya ke d'aga hankalin shi wanda bai wuce na Kalaman Jameelaah da ta ce anyi mata Fyad'e ba. ********************** Cike da kulawa ya d'aga hab'ar ta ya na kallon fuskar ta ya ce, "Hauwaa me ya samu goshin ki haka? Me zan gani ni Ishaq Subhanallahi," "Sannu da dawowa Yah Ishaaq," "Yauwa Haroon, barayi sun shigo ne?" Da sauri Aunty Hauwaa ta ce, "Ba barayi bane, bugewa nayi," Ta yi hakan ne dan qoqarin hana Harooon yin magana akan abinda ya faru, dan ta ga ɓacin rai a fuskar shi a lokacin da yake magana kar reshe ya juye da mujiya, dan indai ta bari Haroon ya faɗi abinda ya faru tsakanin au yayan shi yarda zai yi ba makawa, saboda ya yarda da dan uwan nashi matuqa, barazana ce dama take yi masa dan kurum ya amince mata. "Ke dai kina da matsala Hauwaa, watarana sai kin rasa wani sashe a jikin ki, dubi dan Allah goshi kamar an saka maki goribar talatin a cikin shi, haka fa kwanaki na yi tafiya na dawo na ga leben ki a kumbure kamar gandar nera ashirin, wai ke yaushe zaki dinga tattalin jikin ki ne?" Kuka ta fashe da shi ta fara bubbuga qafa,sannan ta wani harare shi, goshin nan ya yi gaba idon ya yi ciki, "Yanzu ka ga na ji irin wannan mummunan ciwon amma ka tsaya ka na min faɗa akan ciwon kuma ko irin ɗan lallashin nan kai baka iya ba irin na maza, kayi tafiya kusan wata kenan amma ka dawo ka tirkeni da faɗa," Kuka ta sa ta shige d'akin su ta bar su a wajen suna bin ta da kallo, sai ya ji bai kyauta ba tabbas amma ta ya zata dinga  zama tana bari bini-bini taji ciwo kamar wata me koyon tafiya ko kuma makauniya da bata kallon gaban ta in tana tafiya, Kallon Haroon yayi, yace, "Kai kuma kana ina ta ji wannan mummunan ciwo baka kai ta asibiti ba," "Yanda ka gan ta haka na gan ta nima," "Baka gidan ne?" "Ina nan, inna je makaranta na dawo kasuwa nake wucewa abuna, inna dawo daga kasuwa na koma makaranta ta yamma, so banda lokaci, dazu ma baban wata d'aliba ta ya nemi dana dinga zuwa gida ina yi wa yaran shi karatu, za a na biyana dubu biyar a wata, sannan da yamma zan dinga zuwa dik weekend ko da safe, yanda dai naga ya min," "To masha Allah, Haroon Allah ya yi maka albarka, ya kare min kai daga dikkan sharri na mutum da aljan, ina jin daɗin yanda ka sadaukar da rayuwar ka wajen bautawa Allah, Allah ya barka a bawan shi na gari har abada, lallai matashin da ya tafiyar da rayuwar shi wajen bin tafarkin Allah ya hakura da soye soyen zuciya da rud'in duniya da na shaid'an ya na da babban tanadi na lada da jin daɗi a wajen Allah ranar gobe qiyama," "Ameen Yaya na, nima ina maka fatan alkhairi a rayuwar ka, Allah ya kawar maka da dikkan wani abu maicutarwa a rayuwar ka ko me ne shi," "Ameen Haroon" A dai-dai nan Hauwaa ta fito daga d'aki kuma ta ji sarai addu'ar da Haroon yake yi wa Yayan nashi,kuma ta san akan ta yayi ta, banza ta yi da shi sannan tace, "Nima a sanya ni a addu'a, Allah ya cikan burina akan abinda nake nema," "Ameen idan na alkhairi ne" Hararar Haroon tayi, ta ja hannun mijin ta, suka shige d'aki daki. Haroon ya shirya tsaf dan zuwa gidan su Umaimah a matsayin malamin da zai na koyar da su karatu a weekend,littafin da ya rubuta adireshin su ya ɗauka ya duba, ya qara karantawa  ya ninke ya sanya a aljihun shi, sannan ya fita,kallon kan shi yayi a jikin windown dake waje komai ya yi kyau acan acan,haka kawai yaji yana son ya yi kyau kafin ya je gidan su Umaimah dan koyar da su karatu...... *Ni kam ban yarda haka kawai bane d'annan, rabani da kitifin yaran zamani ka ji* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 15: Ya dad'e yana buga qofar gidan kafin mai gadi ya buɗe masa, a zaune ya gan su akan tabarma kowacce riqe da littafan ta suna hira, sanye ya ga Jameelaa da babban hijab, mamaki ne ya kama shi dama gidan su daya? Suna ganin shi suka gyara zama. "Assalamu alaikum," "Wa'alaikumussalam" Bayan sun gaisa ya fara masu karatu, suna maimaitawa. Sai da ya tabbatar sun iya kowanne karatu da ya masu sannan Jameelaa ta masa sallama ta shiga gida. "Shin dama gidan ku daya da wannan mara kunyar?" "Ehh ah ah ! da dai ba gidan mu ɗaya ba, amma yanzu gidan mu ɗaya, dan kuwa yayana ke auren ta," "Aure? Jameelar?" "Eh mana ba ta isa aure bane? Sa'ata ce fa" "To ke ɗin wata babbace? Ke ɗin ma ai baki fi a kira ki da 'yar baby ba," "Habaa Malam baby fa,gaskiya ni na fi qarfin a kira ni da baby, Jameelah ta ce masu shekarun mu da yawa an yi masu aure ka ga kuwa mu ɗin ba yara bane" "Ke kike ganin kan ki wata babba, amma na san dika-dika ba za ki wuce shekaru sha takwas ba," "Tabbb ai ka qaramin shekarun ma da yawa, 16 muke, mundai shiga 17 yanzu" "Ahaff ashe ma cika min ido ki ka yi har naga kamar kin kai 18 years" "In kun gama hirar ki je Mum na neman ki," Da sauri suka kalli inda Jameelah take tsaye hannun ta a qugun ta tana harar Haroon, kad'a kai ya yi saboda Jameelaa ba zata sauya ba sai addu'a kawai. Sallama ya yi musu ya tafi gida, Umaimah kuwa haka nan take jin daɗin hirar da suka ɗan yi a yau da malam Haroon dik da ba wani abu aka ce ba mai mahimmanci a hirar. Haka bangaren Haroon ma ba qaramin daɗi hirar tasu ta yi masa ba,a qafa yayi rabin tafiyar shi zuwa gida yana tafe yana hango murmushin ta da kunyar ta tare da kamun kan ta, gaskiya zuciyar shi na son fad'awa cikin damuwa, domin kuwa shi da Umaimah akwai banbancin rayuwa mai tazara,iyayen ta na da hali sosai, shi kuwa dukiya ta yayan sa ce yau idan aka ce me ka mallaka abinda zai nuna bai taka kara ya karya ba idan an haɗa da abinda iyayen ta suka mallaka,kowa kuma ya san mutumin kirki baya taqama da abun wani sai nashi, sannan gashi ba shi da wani zurfin ilimin boko, anya abinda yake ji game da Umaimah zai je mataki na gaba kuwa? Ko da ya isa gida Hauwaa na zaune a kujera ta ɗora qanqara a goshin ta tana jinya, sanye take da wata iriyar riga ta atampa an yi mata dinkin qananan kaya, gaba ɗaya qirjin ta kusan rabi a waje yake, cinyoyin ta buɗe, ta kuma tattare rigar sama dik da rashin tsaho da take da ita, sai kiran "Washhhh Allah na.....washhhh zafi..wayyooo Allah na" take. Kauda kai Haroon ya yi tare da sakin tsaki mai qarfin gaske, da sauri ta juya ta ga shine, itan ma tsaki ta saki sannan ta ce masa, "Soko mara rabo kawai," Shima cike da rashin kunya ya amsa mata da, "Rabon wahala? Allah ya min tsari da rabon wahala duniya da lahira, in baki sauya hali ba wannan azabar duniya kenan ki ke sha, ta lahira sai kin gwmamace baki san namiji ba ma a rayuwar ki gaba ɗaya," "Ah kuna nan kenan,ina can ina duba ki ashe ke kina nan kuna hira abun ku," Da sauri ta juya tare da sauke ajiyar zuciya saboda bai ji me suke magana akai ba. "Yah na dawo daga gidan dana faɗa maka zan dinga yi masu karatu....gaskiya Yah ina ganin ya kamata na koma makaranta ko bangaren kasuwanci ne na karanta," "Woww ! yau kuma kai ne ke maganar karatu? Me yasa? Ina ce karatun mahammadiyya ya ishe ka kawai? Meye dalilin son komawar ka makaranta yanzu kuma?" "Ba komai Yah Ishaq, kawai na ga ya dace ne na koma tun lokaci bai qure min ba, sannan yaran danake koyawa karatu su na da ilimin boko sosai, ina gudun kar a zo a yo min wani turancin ban iya ba na ji kunya," Dariya sukai ta yi shi da yayan nashi, can yayan nashi ya kafe shi da ido ya na murmushi ya ce, "Akwai budurwar ka cikin su ko?" Zaro ido Haroon yayi sannan ya ce, "Nii kuma Yaya da budurwa? Habaaaa ni dai kawai ina son makaranta ne yanzu," Wani yawu Hauwaa ta had'iya dan sauraro take ta ji ko budurwar ce zata sanya shi komawa makaranta, (ko meye nata a ciki oho?) Haka sukayi ta hira, Hauwa na zaune kusan tsirara amma ko a jikin Ishaaq, haka tai ta gilmawa a tsakanin su Haroon gajiya yayi da kallon da take jifan shi da shi ya yi ma yayan shi sallama ya shige d'aki, cike da takaicin yanda Yayan nashi sam baya kula da iyalin shi ya bar wajen. *********************** Rayuwa na ta juyawa yana yi na sauyawa ci gaba ya samu a gidaje da dama, gidan su Umaimah na ɗaya daga cikin gidajen da suka samu nasarori masu yawa, nasara ta farko shine kammala karatun Umar tare da kasancewar shi cikakken likitan mata har ya fara aiki a asibitin Aminu kano, a ta bayan asibitin Aminu Kanon Mum da Dad suka maka mashi ginin gidan shi mai kyau madaidaici, d'aki uku ne da parlour ɗaya mai haɗe da dinning area,sai kitchen a tsakar gida,da toilete ɗaya a tsakar gida saboda baqi, dakin mai gida na da na shi toilet a ciki,ginin ya qayatar matuqa dan kuwa an fitar da fasali mai kyau, ga wasu fulawowi da aka shuka sai suka qarawa gidan kyau matuqa,kowa ya ga gidan sai ya yaba tare da santin ginin,wata na sama ake saka ran tarewar su Umar da Jameelah a sabon gidan nasu. Umaimah ta kammala secondary school tana zaune a gida, Mum tace ko zata ci gaba da karatu sai a gidan miji, dan haka su na jiran manemin aure ya bayyana kullum addu'ar su Allah ya bata miji na gari mumini salihi. Ta bangaren su Ishaq kuwa Haroon ya samu nasarar shiga makarantar Bayero dake cikin garin Kano,a bangaren Kasuwanci ya samu gurbin karatu yana cikin shekarar shi ta biyu kenan, sauran shi shekara biyu ya kammala. Haroon yana son ya bayyana wa Umaimah son daya ke yi mata amma sai yaji nauyi da tsoro sun mamaye shi, Umaimah ji take yi kamar ta furta masa irin son da take yi masa tunda shi ya kasa bayyanawa, amma kunya irin ta 'ya mace ta hana ta, gefe ɗaya kuma wani haushin shi ta ke ji saboda ya kasa furta mata abinda kowa ya fuskanta game da shi akan ta, dan kuwa har Dad ya gane yana son ta. Yah Ishaaq yayi yayi ya je ya bayyana qudirin shi akan Umaimah ko an san da zaman shi, shi kuma a matsayin sa na babban wan shi makwafin uba a gare shi ya je ya nema masa auren Umaimahn amma sai ya qaryata son da yake yi mata yace shaquwa ce kawai irin ta malami da d'alibar shi mai k'wazo. A can gidan Malam Jameel kuwa Ramai kullum naci take yi ma Jameelaa akan ta qoqarta masu ta sama masu gida a wajen da 'yan gayu suke ko da na haya ne,dan kuwa ita ta gaji da rayuwar lungun nasu ta cakud'ed'eniya, ta san Jameela bata da kud'in da zata sai masu gida amma a qalla ko hayar ce su samu su bar wannan gidan, Jameelah kuwa sai dojewa take yi duba da cewa dika-dika auren nasu bai wuce shekara biyu ba amma ace zata fara tatsar miji manyan kuɗi irin haka,wanda har a wannan lokacin ba abinda ya shiga tsakanin su ta bangaren auratayya. Yau ma kamar kowanne lokaci in zata je gidan nasu takan ci ado ta sa kaya irin na ba raini ɗin nan, yau kuwa adon da ta yi ya fi na kowacce rana qayatuwa da tsada domin kuwa bikin Mamalo ake yi, kuma har yanzu qawancen su na nan ba abinda ya sauya a tsakanin su, wata leda ce a hannun ta wadda ta d'ebi kayan abinci dan kai wa Ramai ta ɗauki atampa da takalmin da zai shiga da atampar ta lullub'e abincin ta yanda ba za a gane ba, dan kuwa ta riga ta sanar da Umar za ta ɗaukar wa Mamalo kaya a nata tinda ba a wani saka mata kaya ba sosai a lefen ta ba, har yanzu iya abinda take aikatawa kenan mara kyau a gidan, wato satar abinci in zata je gida, Mum ta gane amma bata cewa komai saboda ta yi zaton babu ce ta sanya Jameelan d'iban kayan abinci ta kai gidan su ba tare da an bata ba,duk da cewa Mum taga wautar Jameelar ta nan in ta tambaya za su iya bata mafiyin wanda take satar ma amma ta gwammace ta ɗauka ba a bata ba. Jameelah kuwa jira take yi su koma gidan su ta buɗe asalin rayuwar ta da take son zubawa ta more, ga wata iriyar buqatar mijin ta dake addabar ta a iya tsahon lokacin nan daurewa kawai take yi matuqa dan kar Umar ya gane labarin da ta faɗa qarya ne,ta bangaren Umar kuwa ya kasa sauke haqqin auren dake kan shi ba dan komai ba sai dan alqawarin da ya ɗaukar wa Mum, da kuma ya gama makarantar sai tsoron idan ya kusanceta me zai tarar ya shige shi saboda tunanin fyaden da tace an yi mata a baya,lokuta da dama sai ya fara romancing ɗin ta da zafi-zafi kamar zai zarce sai kawai ya ji wata iriyar fad'uwar gaba ta kama shi ya dakata duk da yanda Jameelar ke maqale masa watarana har kuka take yi amma haka zai qi ci gaba ya bar ta. Umar na son ya san waye ya yi mata fyad'e ta na qarama yana kuma tsoron me zai ji da zai tarwatsa tunanin shi, a qarshe ya yanke shawarar sai ya kaita asibiti an gwada ta in bata ɗauke da wani mugun ciwon to a sannan ne zai kusance ta, ba zai bari kowa ma ya sani ba sai sun koma gidan su sannan zai keb'anta da ita. Jameelaah kuwa ta yi duk yanda zata yi ya neme ta abun ya ci tura basirar ta har neman qarewa take yi, shi kan shi ya na buqatar kasancewa da ita amma tsoron mai zai tarar ke dakatar da shi, a yanzu dai ya yanke shawarar kafin lokacin komawar su ya cika zai ce su koma kawai dan ba zai iya qara sati ɗaya ba ba tare da ya san matsayin Jameelaah ba a likitance shin ta na da lafiya ko bata lafiya. Umar ne ya kai ta gidan bikin bayan ya bata kuɗi da zata yi liqi da su da wanda zata riqe ko da za a buqaci wani abun ta taimaka da shi a wajen bikin kamar yanda ta ke ta yi tunda aka fara shirin bikin,gaba ɗaya hankalin matasa da 'yan matan da ke qofar gidan duk ya tattare ya koma kan Jameelah da Umar tare da motar su dabuwa dal da aka ajiye ta a cikin ta, ko da ya ajiye ta sai da suka ɗan taɓa hirar su ta soyayya sannan ta ja ledar da ta boyo ta ajiye a gefen qafar ta ta busa masa sumba sannan ta fita suna murmushi tare da d'aga wa juna hannu ta shige cikin gidan su ta na taku kamar wata sarauniyar mata, ta na shiga ta tadda qawayen ta da su Mamalo ana zaune a tsakar gida, ihu wajen ya ɗauka Mamalo ta ce, "Heeeeeeeee shegiya qawata ! kina wutaaaa hajiya ta ina bin ki da fetur, dan Allah ku matsa ku bata waccan kujerar ta zauna qawata ba ta zama a tabarma bace, kuna ganin ta kun ga matar manya," Jameelaah kuwa nan da nan ta hau jin kan ta kamar zai fasa gini dan girma,har wani d'age gira guda ɗaya take yi, zama tayi ta harɗe qafa, sannan ta zaro gudummawar wata atampa mai mugun tsada dan neman suna a gaban qawayen su na layin ta bawa Mamalo, "Ga gudunmawa ta nan na kawo maki,ko yau ki ke so a d'inka maki ita a layin nan sai an d'inka ta saboda tsadar ta na ga dacewar na kawo maki ita a kai ki gidan miji da ita dangin sa sun san basu saka maki kamar ta ba a lefe dan haka kin ga ba raini zaki kankaro wa kan ki aji, ga wannan a kai ɗinki yanzun nan a kawo mana ita an jima a dinke," Shewa wajen ya ɗauka da shi ana yabawa da jinjina wa babbar qawar amarya, wasu kuma suka hau fad'in, "Ji baqauyiya kamar wadda tazo zanen suna, meye na kawo atampa ana bikin aure a matsayin gudummawa? Ko dan a nuna mana an kawo babbar atampa ne oho? Aikin banza kawai lalle a mazaunai,ai dama shi ɗan talaka bai iya samun arziqi ba sai ya nuna daga geto ya fito," Cikin turancin ta na 'yan qaramar sakandire Jameelah ta fara magana ta na yatsina hantsi ta ce. "What say? Say it loudly mana to hear u, ashe ma kuna jin tsoro na har yanzu, ni yanzu kun san i am not ur mate, dan kun samu ma mun gayyace ku bikin ne amma ba laifin ku bane, qazamai kawai" Tsit wajen ya yi, saboda da damar su gayu iya gayu an sha shi amma ba boko, ga kyau da iya ɗaukan wanka, amma wasu ko arabin ma babu,ba dan ba su zuwa ba ah ah sai dai kawai idan an je ba a maida hankali a yi karatun da ya kamata har a iya turancin. (Wasu daga yaran cikin gari haka suke,i repeat wasu ba dika ba, kar a ce na zagi 'yan cikin gari nima ita ce, da damar su sunan an je makaranta ne kawai an b'ata lokaci da kud'in makarantar amma ba a maida hankali a koyi abinda ya dace, haka zaka ga yarinya ta gama secodary school amma ba zata iya yin sentence ɗaya kwakkwara ba da kalmar turanci, na sani turanci ba shi ne ilimi ba amma yana daga cikin abinda idan mutum ya na fahimtar shi to an san ba asarar kud'in makaranta aka yi ba a kan shi,tunda karatun namu na Nigeria da turancin ake yin sa idan baka ji ta ya zaka fahimta? Dole sai an fassara maka zuwa yaren ka sannan ka gane me ake koyarwar, gashi da damar maza ba su cika son zuwa islamiyya ba da sun je na ɗan shekaru kafin su balaga shikenan suna balaga ake neman wasun su a rasa a islamiyya, dan haka mata musamman na cikin gari dan Allah mu dage da neman ilimi mu karya record ɗin da aka yi mana mara kyau mu bawa mutane mamaki da kunya akan tambarin da akai mana na rashin ilimin addini da zamani) Ta na gama zuba masu rashin kirkin da ta ga dama ta miqe ta shiga d'akin su suka gaisa da Ramai, ta bata kayan da ta deb'o mata da kuɗi, sannan ta bata na baban su ta kuma jaddada wa Ramai akan ta bawa Baban nasu dan ta san halin ta, in ma bata bashi ba zata kira shi ta faɗa masa ta bata kuɗi ta bashi, tsaki Ramai ta yi ta hau masifar dan za a bata abu shine sai an yi mata rashin mutunci,Jameelah bata bi ta kan ta ba ta yakice mayafi da jakar ta ta shige cikin 'yan biki aka ci gaba da shagali da ita. Biki ake ta sha ana tiqar rawa a ɗan tsukukun lungun su Jameelah duk da cewar ango ya hana amma sai da Jameelaa tai uwa tai makarb'iya tasa yaran layin suka samo redio da sipiku manya aka dasa, Bukar da abokan sa ne suke kula da kid'an har magariba ana nan ana abu ɗaya,inda Hajiya Jameelah ta dinga liqa kuɗi ta na taka rawa fili ya zama kamar dan ita aka buɗe shi. Wayar Jameelaah ce ta fara ruri tana dubawa taga Umar ne, da sauri ta fita daga filin rawar ta faɗa soron gidan su ta amsa wayar, umarni ya bata akan ta fito za suje wani waje daga nan sai su wuce gida, in yaso gobe ta dawo a ci gaba da bikin da ita zai ma raka ta har kai amarya. Ta ji dad'in hakan kuwa sosai dan kuwa zai qara d'aga ajin ta a wajen mutanen layin su, qawayen ta zasu ga mijin ta kyakkyawa na nuna wa sa'a ga kuma kuɗi ya na da su masu gidan rana,gida ta shiga a guje ta hau tattara kayan ta, cikin sauri ta ce wa Ramai, "Ramai zan tafi yazo yana jirana a waje," "Wai yanzu yarinyar nan ba zaki duba roqona ba da nake ta yi maki na tsahon shekara biyu, dibe ki ki ga yanda kika sauya kin yi jajawur dake kin yi bulbul gwanin sha'awa amma mu muna nan muna ci gaba da dirzar wahala, kin kasa koda sama mana gidan haya ne mu tashi anan mu koma can mu huta da wannan muguwar rayuwa?" Shigowar Baba kenan daga wajen aikin sa, duk da be so dawowa gidan ba a wannan lokacin duba da yanayi ne na biki mata za su cika wajen to amma yunwa yake ji ba shi da kud'in siyan abincin sayarwa a waje Ramai kuma bata yi hankalin aika masa koda abincin biki bane balle wanda ya bayar a dafa da gumin sa,cikin takaicin jin maganar Ramai ya ce, "Wai Ramai yaushe zaki yi hankali ne dan Allah? Haqqin ta ne nema mana gidan haya dama ko kuma haqqi na ne a matsayina na mijin ki kuma uban yaran ki?nace banda niyyar tashi anan yanzu saboda banda halin kama wani da ya fi wannan dole ne sai kin yi rayuwar jin daɗi a lokacin da Allah bai nufa ba?" Cikin d'aure fuska Ramai tace, "A gaskiya kana shiga haqqina da yawa malam to ni na gaji da irin wannan muguwar rayuwar hakuri na ya gaza, haba ! gida sai kace na gado, tin kan a haife ta muke nan kowa a nan ya sanni, ba zamu samu mu sauya rayuwa ba, ana ta mutuwa sai mu zauna bamu mori duniya ba, qiyamar ma baka da tabbas," "In har kina bauta ma Allah da gaskiya, kina kuma kwadayin rahamar shi Allah zai baki aljanna dan ya yi ma wanda ya yi kwadayin rahamar shi alqawarin samun rahamar," "Kai ka san wannan ni dai na gaji ehe, nace na gaji a dau mataki akan wannan muguwar rayuwar da muke ciki ko kuma na dauka da kaina,habaa sai kace akan mu talauci ya ƙare?" Juyawa ta yi dan ta yiwa Jameelaah magana taga wayam ba ita ba labarin ta,haka tai ta masifa tana gwada layin Jameelaah da 'yar qwabirar wayar ta amma ana yi mata turanci, soke wayar ta yi tana fadin zasu gamu ne goben. Hanyar asibiti ya ɗauka da su, dan kuwa a yau zai kaita a dau jinin ta a gwada ta in result ya fito ya ga lafiya take to a washegari zasu koma gidan su, dan kuwa komai na more rayuwa an zuba a gidan su kawai yake jira ......... *Allah ya kaimu goben muji meye sakamakon gwajin jinin da za a yi wa Jamcy baby, shin makaranta Umar ya kyauta kuwa da zai je ayi gwajin jini bayan Jameelaa bata da masaniyar me za ayi?* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 16: Ana gama d'iban jinin ta ya ce wa masu gwajin su yi mashi gwajin da suka yi magana za a yi akan wannan jinin yau zai je ya dawo,daga nan parking space suka wuce suka shiga motar su ya ajiye ta a gida, ta yi masa tambaya gwajin me za a yi mata yafi sau a qirga amma bai bata amsa ba, qarshe sai ce mata ya yi gwajin malaria ya kai ta a yi mata,mamaki take ta yi dan dai bata ce masa bata da lafiya ba ita rabon ta da ciwo ma musamman wanda zai kwantar da ita har ta manta, daya ga bata yarda da shi ba sai ya kama hannun ta yace. "My love tinanin me ki ke yi ne haka? Ko baki yarda da abinda na faɗa maki bane?" "Kawai ina mamaki ne Yah Umar akan gwajin da ka kawo ni a yi min naga ni dai lafiya ta qalaou," "Kin san yanda nake matuqar son ki ba zan so ki shiga cikin lissafin masu malaria na duniya ba a shekarar nan da za mu shiga, ko baki da masaniyar yanda malaria ke kisa ne kuma duk shekara ana tara data na iya adadin mutanen da ke ɗauke da cutar malaria na duniya? Qungiyar Wold health organization na fitar da wannan qididdiga duk shekara ki bincika zaki tabbatar da hakan,Baby dik abinda zai zama barazana ga rayuwar ki inshaa Allahu in ina da iko zan kawar da shi tun kafin ya riske ki, yanzu yayin mace-mace ake yi saboda wannan mummunan ciwo na malaria dan haka dole na kula dake," Jameelah ta ji daɗin kalaman shi sosai, saboda irin wannan kulawar da ya ke bata tana qara sanya mata hakuri da juriya akan qin kusantar ta da bai ba har na tsawon wannan lokacin,amma a qashin gaskiya ta fara gajiya akan rashin kulawar aure da yake bata,ita ai ba dutse bace in shi dutse ne, tana wanan tinanin ta ji buɗe qofar motar shi ya fita, nan ko bata san yana ta yi mata magana ba ma,itama fita ta yi suka shiga gidan a tare,cikin sauri ya juya ya gaishe da Mum da ke zaune a parlour ta na kallo,tambayar shi ta yi, "Saurin me ka ke yi haka Umar?" "Mum ina son naje na amso wani abu ne, yanzu nan zan dawo da yardar Allah akwai wani abu ne?" "No ba wata damuwa dama ina son na sanar da kai ne ko zaku bar komawar ku gidan ku sai ranar juma'a ɗin anan mai zuwa? Saboda akwai gyare-gyare da nake son na yi wa Jameelaah, domin so nake ku koma gidan ku kamar ranar aka yi auren ku, tabbas kun yi min biyayya dole ne nima na kyautata maku, fatana Allah ya yi muku albarka, ya baku masu yi maku biyayya fiye da yanda kuka yi min,ba kowanne ɗa bane zai yi abinda kuka yi, na sani ban kyauta ba dokar da na sanya maku ta yi tsauri, sai gashi kun bani mamaki har bayan kammala karatun ka Umar kuna riqe da kan ku kuna jiran umarni na da amincewa ta,ko da ace kun saɓawa doka ta ba ku yi laifi ba, amma riqe alqawarin da ka yi ya qaramin ganin qimar ka da son ka da kuma son na ga na qara kyautata maku dika a matsayina na uwa a gare ku," "Muuuummm, zaki sa na yi hawaye amma na farin ciki, na ji daɗin addu'ar ki sosai a gare mu Allah ya amsa, bari na yi sauri na dawo ana jirana" Kyab'e baki Jameelah ta yi ta wuce d'aki,cikin ranta ta na ayyana yanda zata muzgunawa Mum a duk sanda ta samu dama itama dan kuwa wannan ba qaramin zalunci aka aikata mata ba, mum kuwa ta zaci tsabar kunya ce ta hana ta tsayuwa a wajen ta gudu d'aki sai ta yi murmushi ta maida hankalin ta akan Umar ta ce masa, "To sai ka dawo," Da hanzari ya koma asibitin, sai da ya tsaya ya yi sallar Isha'i a masallacin da ke cikin asibitin sannan ya qarasa lab din, ana miqa masa result ɗin ya damqe shi tare da yin godiya mai yawa ya fita yana yi musu sai da safe. Zaune yake a mazaunin driver ya kasa buɗe takardar saboda fargaba,da kyar ya samu ya buɗe sakamakon da ya gani ya yi matuqar sanyaya zuciyar shi, wata hamdala ya dinga saukewa, sannan ya hau tasbihi ga Allah cikin farin ciki ya ke fad'in, "Na yafe ma dik wanda ya yi maki fyaden nan tinda bai goga maki ciwon da zaki haramta a gareni ba, na yafe masa duniya da lahira, na yafe masa duniya da lahira, na yafe masa," Nannad'e takardar yayi ya yagata ya zubar, shopping yaje ya yi wa Jameelah na kayan kwalama sosai da kayayyakin shafawa da turaruka masu kyau da tsada, sannan ya yi ma Mum da Umaimah siyayya suma, Dad ma ya sai mashi turarukan da yasan yana so. Gida ya wuce cikin farin ciki lokacin kowa yayi bacci banda Jameelaa, idon ta biyu ta na ta tinanin ina Umar ya shiga gashi har ta yi wanka ta shirya cikin kayan bacci jikin nan ta mulke shi da lotion mai gyara fata gashin ta ya sha gyara sai sheqi yake,sweet ce mai qamshi a bakin ta ta na ta tsotsa saboda tun tana gida ta tsani wani ya ji warin bakin ta balle kuma Umar da take mugun so. Da kaya niqi-niqi ya shiga gidan, d'akin Umaimah ya leqa ya ajiye mata ledar ta a gefen gadon ta, sannan ya aje na Mum a d'akin ta itama, dan kuwa bata d'akin ta na d'akin Dad,duk abinda yake yi akan idon Jameelaah yake aikatawa, tsaki taja mai qarfi sannan ta ce, "Dik bari mu koma sabon gidan mu za ku sha bakin mamaki ko ganin shi sai ya yi maku wahala, komai wai sai an yi raba dai-dai da ku, sai kace mijin su aikin banza," Ta na nan ta na surutu da baƙin ciki ya koma parlourn bata sani ba sai jin muryar shi tayi ya na fad'in, "My love ke da wa ki ke magana? To ayi hakuri indai ni ne gani na dawo, muje ciki ko?" Washe baki ta yi tare da amsar leda ɗaya dake hannun shi suka shiga d'akin su,suna shiga ya baje kayan a gaban ta tare da d'aga ta tsaye, ya manna ta da qirjin shi, cikin farin ciki ya ce, "Love na amso sakamakon  gwajin da aka yi maki kin samu nasara baki dauke da ciwon qa.....mammmamalaria," Cikin sauri ya sauya akalar maganar tashi kallo ta bishi da shi dan son gano me yake boyewa,idon shi tsilli-tsilli kamar na munafukin da aka turke ya na tsaka da gulma, sakin ta ya yi da sauri ya fara d'aga rigunan bacci  dogaye biyu daya siyo mata masu mugun kyau, chocolates da sweets gasu nan barbaje a qasa, nan da nan kuwa uwar kwad'ayin ta basar itama kamar yanda ya yi ta hau duba kayan da ya kawo mata, wata leda ya janye gefe idon ta na sauka akan ledar ta miqa hannu da sauri ta ɗauke ta na dariya, "Wannan turarukan na waye?" "Na Dad ne gobe zan bashi tinda sunyi bacci yanzu," Ranta bai so ba sam duba da yanda ta ga ya yi wa Mum da Umaimah ma siyayyar amma ta maze ta ce, "Ohhhh d'a da daɗi kaga ka sai ma Dad turare dan neman albarkar shi, Allah ka ban iko na kammala karatun nan na samu makarantar gaba da sakandire na gama ta nima na fara aiki na dinga sai ma iyayena abubuwan more rayuwa ko zan dinga samun lada kamar yanda ka ke samu a koda yaushe ,gaskiya Yah Umar in mutum na zaune da kai sai ya iya abubuwan alkhairi kala-kala," Ya ji daɗin yabon da ta yi masa, amma kuma sai ya ji bai kyauta ba da bai sai ma mahaifan ta komai ba, shi ya sai abubuwa ma nashi iyayen amma baya tunawa da nata sam,wayancewa yayi ya ce, "Ai wannan ma harda Baba na siyo, nafi son na bashi da kaina ne, saboda ya samin albarka," Kauda kai tayi ta murgud'a baki, taso ya kawo ledar da ya kaiwa Mum d'akin ta dan ta samu na daukar ma Ramai, amma ba komai zata fanshe ne a wani wajen watarana. Godiya ta yi ta masa har sai da ya rufe mata baki da nashi su Jameelaah an samu abin nema, ai kuwa ta qanqame shi ta hau shafa sassan jikin shi, Umar ya jiqu matuqa da salon Jameelaah, da kyar yake fidda numfashi tsabar yanda ta kannad'e shi kamar an ce mata guduwa zai yi. Ganin yanda ta kai qirjin ta saman fuskar shi ne ya sanya shi saurin janye ta a jikin shi, yana neman iska dan ya shaqa, hawa saman gado yayi ya kwanta ya yi shiru ya na qoqarin daidaita kanshi,Jameelah kuwa tana nan kwance a aqasan carpet tana maida nata numfashin cike da matsanancin takaici, wannan wace irin rayuwa ce suna zaune gida ɗaya daki ɗaya da mijin ta amma saboda wata dokar banza ba zasu iya jiyar da junan su daɗin zaman aure ba, wasu hawaye ne masu zafi suka gangaro mata. Umar idon shi lumshe suke yana sauke numfashi a hankali, gaskiya hakurin shi ya qare ba zai iya bari har juma'a ba kafin ya keb'e da matar shi inaaa ba zai iya ba hakurin shi ya qare, ya ma yi qoqari ai,a da fargaba da tsoron kamuwa da ciwon qanjamau na tsaida shi tare da dokar Mum ta ya bari ya kammala karatu,to a yanzu menene ke tsaida shi kuma? Babu komai, dan haka gaskiya gobe zai sama wa kan shi da matar shi mafita. Jameelaah a nan ta fara yin bacci Umar ya yi bakam kamar wanda yayi bacci, sai cikin dare ya tashi ya je d'akin Mum din shi ya duba keys ɗin gidan su ya zari biyu ya fice, d'akin su ya koma ya kwanta. Da safe Jameelaah ta gama dik wani shirye-shiryen tafiya gida yau za a kai amarya, daga yau an gama biki, Mum ta bata kuɗi mai ɗan yawa da atampa da sabulai na wanka da wanki da babban ledar omo ta ce ta kaima Ramai, daf zata fita ta hanyar kitchen Mum ta bita, dan bata son surukar ta ta taci gaba da satar abinci, dan haka tace "Jameelah bari na d'eba maki ɗan dankalin nan ki kaiwa Maman ki, ki ce ina gaida ta" Cikin kame-kamen ko dai an gano ta ne ta tsaya cak, sai zaro idon ta da yasha kwalliya take waje. Tana nan tsaye mum ta ɗebar mata dik wani abu data ga ya dace ta bata, Drivern dake kaisu makaranta shi ya kai ta, Umar yace tayi gaba taje gidan su, in ya gama abinda yake zai je ya ɗauke ta ya kai ta gidan amaryar. Koda sika isa gidan ta tarar da gidan cike yake ana ta hada-hadar biki, masu biki na nan na ta hidimar su gefe ɗaya masu sana'ar abinci na kullum na nan basu fasa ba, dan kuwa Ramai ma tayi nata yana can qofar gida ana ta saidawa, lungun shaqe yake da mutane kala-kala, can daga nesa ta hango yaran gidan nasu wasu na wasa wasu na zaune kawai suna kallon masu shige da fice, sai ta kira su ta sa suka d'ibar mata kaya suka nufi cikin gidan da shi, sai wani shan qamshi take yi ita a dole driver ne ya kawo ta, ga kaya nan niqi-niqi ta kawo gidan su, ai kuwa ta yaqi 'yan matan dake zaune a waje ana ta budiri da samari,nan da nan suka hau gaishe ta suna haɗa baki wajen fad'in, "Jameelaah kin iso kenan, sannu da zuwa.....Jameelaa sannu da zuwa.....jameelaa tare zamu tafi gidan amarya anjima...." Sai da suka gama surutan su ta d'aga masu hannu ta ce, "Sannun ku," Ta yi shigewar ta cikin gidan su ta bar su nan tsaye baki sake, ai kuwa samarin wajen me za suyi in ba dariya ba, nan aka dinga yi ma matan da Jameelaa ta wulaqanta dariya, tin suna iya kare kan su har suka kasa. Ramai na ganin an fara shiga da kaya ta hau gud'a tana yiwa Jameelah kirari har sai da ta shige d'aki tana wani nuna Kyankyamin zama a dakin,cikin yatsina fuska ta ce, "Ramai ina kud'in ledar d'akin dana baki ne dan Allah?" "Na cinye dan uban ki,ke bari ki ji fa ba yanda za ai na saka ledar d'aki anan wajen dik a lalace, in kina son in kin zo ki zauna a waje me kyau na sanar dake ki sa mijin ki ya kama mana haya amma kin qi, kamar ke ɗaya kike son hutun" Shiru tayi dan ba ta son su ja maganar ta yi nisa, Ramai ta kasa ganewa so take sai sun koma gidan su zata fara baza mulki son ran ta,tafi Ramai son ta gyara su su fito tsaf dan kuwa ta jima ta na yanka wa qawayen ta na makaranta qaryar iyayen ta masu azziqi ne, tinda gaba ɗaya yaran masu hannu da shuni take tare da su a makaranta a yanzu. Kayan da ta zo da su Ramai ke ta fitowa da su tana gani tana murna, kuɗi Jameelaah ta qirga dubu uku ta bata sannan ta sake qirga dubu uku tace na baban tane wannan, sannan ta aje ma Bukar dubu daya. Turaruka biyu ta bawa Ramai tace na Baban tane, Ramai dik amsa tayi tana ta godiya,a ranta kuwa ta na fad'in, 'Shashasha an faɗa maki kowa soko ne irin ki? taya ma zan bawa baban ku wannan turarukan masu tsada? ai saidawa zan yi na manne kud'in, tinda shi ko an bashi ba wani amfani yake da su ba, kullum ana fama da man babur da na keke yaushe yake da lokacin fesa turare irin wannan?' Waya ta tsinkayo Jameelah na yi da Umar, "Na'am Kana waje? Ka manta sai qarfe shida na yamma nace maka za a kai amarya?......k to gani nan zuwa," Jakar ta ta buɗe ta fesa turarukan ta masu qamshi, ta sake shafa hoda ta saka janbaki sannan ta jefa sweet mai qamshi a bakin ta ta yi saurin tattaunewa ta shanye, Jameelaah ta qara gogewa ta yi kyau sosai ta iya gayu na musamman saboda zama da yaran masu kuɗi,ta zama cikakkiyar budurwa 'yar sha takwas, jakar ta ta ɗauka ta yi ma Ramai sallama Ramai sai jinjina kyau irin na d'iyar ta ta take yi kamar ba ita ta haife ta ba. A mota ta gan shi zaune ya sha gayu da manyan kaya, ya yi kyau ainun matan layin su da 'yan biki kamar su janyo shi tsakiyar su tsabar yanda suke kallon shi duk ya qosa Jameelah ta fito su bar wajen, wanda suka san Mijin tane sai gulma suke yi suna fad'in, 'kyau da kyau an haɗu',wanda basu sani ba kuma sai suka hau tambayar waye shi, har ta zo qofa ta tina bata ma Mamalo magana ba ma tunda ta shiga gidan, da sauri ta koma ta ce mata Umar yazo zasu fita, in za a kai amarya zata zo. Da wani irin taku ta fita kamar wata matar wani qusan a gwamnati sai wani hura hanci take yi,nan da nan kuwa ido ya koma kan ta har ta kusa isa wajen Umar ɗin da ya fita dan buɗe mata motar, ta na ganin haka ta sakar masa murmushi shima ya mayar mata, da ta shiga motar sai ya rufe ya zagaya ya shiga shima sallama ya yi ma samarin wajen sannan ya ja suka fice daga layin, wani ihun daɗi ta sake tana ta dariya,umar cikin murmushi ya kalle ta ya ce, "Lafiya ki ke wannan ihun haka?" "Yah Umar ka gama biyana yau, ka gama kashe gayun layin mu yau, kaga yanda kowa ke kallon mu,ka gama min komai Yah Umar,me kake so a duniyar nan na baka ko na yi maka dan kuwa ka fiddani kunya a lungun mu yau, kaiiii wani abu sai ma anjima a wajen kai amarya malam, har wasu kayan nazo da su dan sake kashe kala," Rage gudun motar shi yayi ya kalle ta ya ce mata, "Kin tabbata komai nake so zaki yi min? Kuma kin yi alqawari?" "Sosai ma na yi alqawari, in dai abun da ka ke so a waje na bai saɓawa addini ba zan yi maka shi, sab'on Allah ne kawai ba zan ba akan ka Yah Umar, amma indai ni Jameela ina da iko akan abu tambayi zan yi maka ko meye," "Kina ma da shi muje ki gani, zan faɗa maki me nake so," Wata hanya ya ɗauka da su wadda ta kula hanyar asibitin su ne da suka je rannan, me kuma za su sake yi a asibitin, tsoro ne ya kama ta kar dai allura za a sake yi mata yau ma a deb'i jinin ta?..... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 17: A k'ofar gidan nasu mai matuqar kyau da ɗaukan hankali ya ajiye motar shi,har ya buɗe mata qofar motar bata sani ba saboda yanda ta saki baki ta na kallon fasalin ginin gidan da ya tsaru ya gaji da kyau,sai da ya yi mata magana sannan ta fito tana ganin ya fara bude gidan ta fahimci inda Umar ya dosa da kawo ta wannan tsararren gidan dan ita ɗin dai kun san ba sabon hannu bace, amma saboda makirci irin na Jameelah sai ta daburce ta kalle shi a ɗan tsorace ta ce, "Me muke yi anan kuma Yah Umar? wai ina ne ma nan ɗin?dan Allah ka maida ni gidan mu a kai amarya dani," Jikin ta har wani karkarwar munafunci yake yi,ganin haka sai Umar ya saki murmushin da bai kai zuci ba,a qasan ran shi yana tausaya mata ta bangarori da dama,labarin da ta bashi na fyad'en da aka yi mata ne ya bijiro masa ya qara dasa masa sabon tausayin ta a ran shi, sannan ga shi an aura masa ita har tsahon wasu shekarun bata san menene jin daɗin rayuwar auratayya ba, dole ne yau ya bata dikkan haqqin ta da yake a kan shi,dan kuwa Jameelah ta cancanci hakan a wajen shi. Hannun ta ya kama ya shigar da ita gidan ya rufe gofar ba tare da ya yi tunanin sanya key ba,  tsakar gidan ya yi bala'in ɗaukan hankalin ta har ta manta da me ke faruwa a wannan lokacin, madaidaicin gida ne ya sha adon fulawowi gefe da gefe da saman katangar gidan sun yi kore shar ga furanni nan sun fito jajaye da kalar pink,ga kuma wata babbar qofa ta shiga a salin cikin gidan wadda aka qawata ta da ado wajen gera ta, juyawa tayi ta kalli kitchen da toilet da ke tsakar gidan ta ga yanda aka yi su cikin tsari duk da cewa a rufe suke bata ga ciki ba ta yaba da fasalin su,a hankali ta taka ta murd'a handle ɗin ta leqa ta ga yanda cikin ya tsaru, murmushi ta saki a lokacin da Umar ya ke taya ta exploring gidan. Nan da nan wani irin farin ciki ya lullube ta lallai wannan gidan dik da ba irin qaton nan bane ya yi mata matuqa gaya dan kuwa gida ne na ba raini daga wajen masu kuɗi har talakawan ma. Koda suka shiga parlour baki ta saki ta na kallon ko ina da ko ina na wajen,komai an saka a parlourn banda kayan kallo, saboda ba a saka wuta ba a gidan, kujeru ne d'uma-d'uma masu numfashi irin royal chairs ɗin nan kalar blue dark da golden, carpet ɗin da aka malala musu kalar blue ne da adon flawowi baqi, ga manyan flower vase masu tsada da aka girke a parlourn sai frames masu kyau, qanqame hannun shi tayi shi kuma ya bita da kallo yana murmushi. "Yah Umar dik wannan gidan na waye?" "Gidan Jameelah da Umar da yaran da Jameelah za ta haifa wa Umar ne, ko baki san dama a ta nan area ɗin su Dad suka yi mana gini ba? Komai na gidannan mallakin mu ne da duk abinda za a karo anan gaba,dan kuwa kusan kullum Mum akwai abinda zata siya ta ajiye saboda mu,duk tanadin ta ita da Dad akanmu ne ni da Umaimah yanzu da an gama jan wuta a gidan da wasu gyare-gyare a kitchen da na ji tana magana akai zamu dawo ranar juma'a, kinga kafin nan sai mu riga su kawo kan mu, ko ya kika ce tawan?" Ya qarasa maganar shi tare da kashe masa ido ɗaya ya na murza hannun ta a cikin nashi,cikin ran Jameelah kuwa ihu take ta na murna tare da ayyana, 'Wayyooo Allah na, Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana finally dai ɗan gidan Mummy zai karya alqawarin da ya yi wa Mummyn shi,waiii Allah na Jameelaa kin sha wahala, kin kuma yi qoqarin zama ba harka har na wannan tsahon lokacin mai tsaho na jinjina maki' A zahiri kuwa sai ta fara matsawa baya ita a dole tsoro take ji, wasu marayun hawaye ta fara matsowa tana kad'a masa kai,cikin sigar lallashi Umar ya nufe ta ya na fad'in, "Haba Love please kar ki yi min haka, ni fa mijin ki ne kar ki guje ni, in dai kina son ki halarci kai amarya ki bani had'in kai mu yi mu gama yanzu na maida ki da wuri, ga samun lada sannan ga shi ni da kaina zan kai ki kamar yanda kike so," Cikin ranta ta ce, 'U fool abinda nake jira kenan ka tsaya surutu,to wai surutun na meye kawai ka jani muje ciki, ko so kake na bika zoqal zoqal kamar wawuya' Maqe kafad'a ta yi tana buga qafa irin na shagwab'ar nan wanda ta san dole ya sake jan ra'ayinsa gare ta, Jameelah ta san duk wani salon dake jefa maza cikin rud'ani, da ganin yanda ko ina na jikin ta ke motsawa Umar ya ja ta ciki, ni ko ganin idanun shi a tsaitsaye ba kunya ya sa na jira su a waje,tinda Jameelaah ma A-Z ce. Na jima zaune ina jiran su, ga ba kayan kallo bare na kalla sai kawai na d'akko waya ta na fara Chatte wa da qawaye na na rai da rai, muna ta shewa a HAERMEEBRAEH NOVEL GROUP na ji bude qofar shiga gidan tare da fadin, "Yauwa ku shigar da kayan cikin nan kitchen din, bari na duba shi na san wataqila ko daga Office ya shigo dan ya ɗan huta,ko gajen hakuri ne ya kawo shi gama kalle gidan yaje ya ba amaryar tashi labari," Ya zan yi ne? Shin zuwa zan na kira Umar nace a tashi haka daga....ko na bar Mum ta shiga ta yi gamo da kan ta? Kafin na gama tunani na ashe Mum har ta shige sai ji nayi ta rafka salati an buga qofa da qarfin gaske, Mum dau ta shiga ta yi wa idanun ta mummunan gamo ta rufo musu qofar ta baro d'akin, cike da jin matsananciyar kunya ta dafe kan ta ta na salati,Umar ne sanye da gajeran wando ya na qoqarin sanya riga ya biyo sahun ta da sauri ya na kiran sunan ta, kafin ya iso Mum ta kora mutanen da suka zo tare da su waje. Da sauri ya kama hannun ta ta tsaya cak ya kasa cewa komai saboda kunyar ta da ta mamaye shi,ita kan ta Mum kunyar ɗan nata ta gama baibaye ta, ina zata kai wannan kunyar da alhakin yaran da ta ɗauka na tsahon wannan lokacin? Gaskiya ta tafka babban kuskure na hana su kasancewa tare,yaran ma sun yi hakuri ainun kuma sun yi biyayya matuqa,dan haka ba zata ga laifin su ba sai ma dai ta ga laifin ta. Cikin zubda hawaye Umar ya fara magana, "Mum dan Allah ki yafe min ina tsananin buqayar iyalina kusa dani, kuma ban taba yi ba sai yau, ki yarda dani, ban taba yi ba sai yau, yau din ma bana nufin kwana a anan yanzu dama nake son mu koma na maida ta bikin qawar tata, bata da laifi sai da taqi ni na tursasa ta," "Umar Allah ya yi maku albarka, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba saliha kuma mumina, Allah ya baka masu yi maka biyayya fiye da yanda kamin a rayuwar ka, Umar baku min laifin komai ba, nice dai nake neman gafarar ku, saboda hana ku kasancewa a inuwa ɗaya da nayi, bayan kun halatta ga junan ku, ka yafe ni Umar, sannan ku yi zaman ku, zamu had'o maku sauran kayan ku da dik abinda ya dace, yau za a zo a ja wuta a gidan dama na riga na gama magana da masu haɗa wutar,dan haka a yau za a saka wutar da yardar Allah, Allah ya yi muku albarka," Dik maganar nan da take yi ta kasa haɗa idanu da ɗan nata kan ta na kallon waje take maganar nan, dan kunyar Umar da Jameelaah yanzu da take ji ko surukan ta bata jin kunyar su haka,da wanne ido zata sake kallon su? Ta shiga tagan su a tube? A manne da juna ɗan ta na qoqarin kaiwa ga buqatar shi? Wannan abu ba zai taba goguwa a zuciyar ta ba, da shi zata koma lahira tabbas, tayi dana sanin zuwan ta gidan a wannan lokacin, tayi dana sanin hana ɗan ta kasancewa da iyalin shi tun farko da bata yi wannan mummunan gamon ba, aure nawa aka yi shi ana karatu har aka haihu lafiya ? Aure nawa aka yi yarinya na da qarancin shekarun Jameelah kuma ta haihu lafiya? Tabbas bata yi lissafi ba, bata yi dogon nazari ba kafin yanke hukunci a baya, yanzu gashi ta jawowa kan ta ganin abinda ba zai gogu a kwanyar ta ba har abada. Jameelaa da ta gama jin komai tayi tsallen murna ta faɗa gadon ta ta yi birgima ta sake yin birgima, da kuwa dik ranta a b'ace yake da zuwan Mum ɗin ta katse masu jin daɗin su, tin da take bata taɓa sanin haka rayuwar aure take da daɗi ba,ashe rayuwar zina bata da wani armashi shaid'an ne kawai ke qayata masu ita,rayuwar zina ana yin ta ne komai babu nutsuwa ba sakewa ga uwar fargabar kar a kama mutum, gwanda da aka basu damar kasancewa tare,tashi ta yi ta leqa su ta ga yanda suke ta tattaunawa Umar ya saki ran shi daga tashin hankalin da ya shiga da fari,ta nanan tsaye a bakin kofar ta ji sun fara sallama Mum za ta tafi,cikin sauri ta bar bakin qofar ta koma ciki ta zauna a bakin gado ta hau kukan munafurci. Umar ya dad'e zaune a parlour kafin ya iya shiga d'akin, kunyar Jameelan yake ji sosai Mum din shi ta gan ta a yanayin da ko Mahaifiyar ta bai kamata ta gan ta a ciki ba kuma shi ne silar faruwar hakan, a hankali ya qarasa gaban ta ya durqusa a saman guiwowin sa tare da kama hannayen ta ya ce, "My love dan Allah dan son Annabi ki yafewa Mum d'ina, kiyi hakuri ki yafe min nima, ni na janyo maki wannan abun kunyar, na san zaki dad'e kina jin kunyar Mum saboda yanda ta ganmu, amma ba zamu koma ba har sai sanda kika ji zaki iya zuwa gidan," Da sauri ta faɗa jikin shi tana kukan qarya tare da goga dikkan jikin ta a nashi, Umar kasa daurewa yayi suka koma ruwa. Jameelaah ta hana Umar sakat a ranar kuma taqi ta nuna masa da gayya take nane masa,komai take yi cikin taka tsantsan takeyi da dabara yanda ba zai fahimci ita ke son abun ba. Shi ko ya ɗauka naturally haka mata suke jikin su na qara sa namiji jin sha'awa ko da bai yi niyya ba. A ranar dai Jameelaa bata je kai amarya ba a gidan su suka yi zaman su, masu gyaran wuta sun zo bayan la'asar lokacin su kuma suna sallah, dan sun makara yin azahar. Bayan sun idar aka fara sanya masu abubuwan da suka dace, daukan ta yayi suka tafi siyan abinci, dan kuwa tace masa yunwa ta ke ji sosai. Umar jin shi yake kamar a yau aka d'aura masa aure, koda suka je wajen siyan abincin farfesun kaji tace a siyo, sannan a siyo gasasshen nama irin mai ruwa-ruwan nan, daga nan suka sa yi freshyo da fruits masu yawa,shi kuwa harda tuwo ya siya dan ya saba cin tuwo da dare. Gida suka koma a d'aki suka zauna har an gama da master bedroom , d'akin yayi kyau sosai hasken wutar kalar blue mai duhu da haske aka sanya masu,sai AC da fan dik an kunna dan su tabbatar suna yi, sanyin yayi yawa dan haka Umar ya kashe fan din ya rage sanyin ACn, suka zauna suka fara cin abincin, ya yi mamakin ganin yawan abincin da Jameelaa ta ci, dan kuwa ta tashi da kaza ɗaya tass ita ɗayan ta sannan ta qara da naman, ga fruits da ta sha sosai suma, gyatsa tayi ta jingina da gado, suna haɗa ido da Umar ta sauke nata idon dan tsabar kunya da ta kamata, turo baki tayi sannan tace, "Yah umar dole fa naci abinci sosai kasan ka wahalar dani ba kaɗan ba, ba zaka gane irin yasar da naji anyi min a cikina ba," Dariya suka yi a tare masu sanya wuta sai bayan magrib suka kammala suka tafi, ya so ya sallame su suka tabbatar masa da Mum ta biya komai, duk da haka bai barsu haka ba sai da ya basu wani abu na ihsani suka yi masa godiya sosai suka tafi. Umar wanka ya sake yi sannan yace bari ya ɗan leqa asibiti yanzu zai dawo, qanqame shi tayi wai ita tsoro take ji,ya kula da hakan dan kuwa da gaske tsoro take ji bata saba zama gida ita ɗaya ba, to mutumin da ya taso a gidan yawa? Gashi kuma gidan sabo ne,hawaye ya ga ta na zubarwa dan haka sai ya kama ta suka zauna ya ce mata, "Jameelaa bari na faɗa maki gaskiyar inda zan je yanzu, dama zan dan leqa asibiti ne akwai wani yaro dani nake kula da shi ya karye a qafa, mummunar  karaya yaron ya yi kuma yaron basu da hali, nakan kai masu abinci da dai abinda suke da buqata haka sannan daga nan zanje gida na d'akko maki uniform ɗin ki saboda gobe akwai makaranta ko kuwa har kin manta da makaranta?" "Yah Umar ni dai muje tare ba zan iya zama ni kaɗai ba," "Zaki iya ganin Mum ba matsala?" "Ai ba sai na shiga ba, ni dai ba zan zauna ni ɗaya ba," Haka Umar ya sa ta a gaba suka tafi yana ta tsokanar ta tare da kiran ta matsoraciya,sun tafi asibiti kenan Umaimah da mai aikin Mum suka je gidan dan  kai kayan su musamman na sawa da na toilet suka tarar da gidan a kulle, mota suka koma ta dakko waya ta kira Umar ta sanar dashi zuwan su, sanar da ita ya yi su ɗan jira yanzu zai juyo ya dawo, sun ɗan fita ne,a tsorace Jameelah ta ce, "Yah Umar wacece ta je gidan, na shiga uku na ni Jameelah Mum ce?" "Ba ita bace Umaimah ce ta je kuma kaya suka kawo mana, sun hutar damu shan kunya" Koda suka koma Jameelaa ta sha tsokana wajen su Umaimah, haɗuwa suka yi da me aikin Mum suna ta tsokanar ta wai amarya ta gudu d'akin miji ba 'yan rakiya,ita kuma ta yi ta shagwab'a, Umar kuma ya hau yi ma Umaimah faɗa akan ta kyale masa matar shi kar ta takura mata. Cikin raha da nishad'i suka rabu, a ranar umar dai bai samu zuwa asibiti ba, sai wani abokin aikin shi ya bawa saqon yin komai. Washegari da safe bayan sun yi sallah da asuba sun shirya dan fita malama Jameelaah da kyar ta kyale Umar dan kuwa dik ta wani maqalqale shi, Umar kuwa sai wani lallab'a ta yake yi yana matuqar qara jin son ta da wani shauqin kasancewa da ita na qara shigar shi, ji yayi kamar ma ta ajiye karatun ya isa haka, wani irin kishin ta yake ji fiye da da, anya ba daga secondary zata aje karatun nasaran nan ba kuwa? Tinda ta na da na muhammadiyya dai-dai gwargwado. *********************** Zaune ya ke a d'akin shi tunanin duniya ya dame shi, yau Yah Ishaaq yayi tafiya zuwa Dubai dan shigo da wasu sabbin dogayen riguna da ake yayi. Waya ya d'akko ya kira No shi da yake amfani da ita a can. Sai da ta katse ba a d'aga ba, furzar da iskar bakin shi yayi sannan ya shafi gefen sajen shi, kira ne ya shigo, da sauri hannu na masa rawa ya dauka. "Hello qanina har ka fara missing d'ina ne? Dan da alama lissafa awanni kake ta yi shi yasa ka daidaici lokacin da na sauka ka kira ni," Ɗan murmushi Haroon yayi mai sauti sannan yace, "Ina fatan ka isa lafiya Yayana?" "Lafiya qlaou muka sauka alhamdulillah, akwai damuwa ne naji yanayin ka wani iri?" "Yah gaskiya ni dai yau na saddaqar ina son Umaimah, Yah Ina matuqar son ta, qirji na har wani zafi yake yi min da nauyi yau na rasa dalilin faruwar hakan Yah dan Allah ka yi ka dawo ka nema min auren ta kar na mutu, ban san haka so yake ba, a da na zaci shaquwa ce kawai a tsakanin mu, dan Allah Yah ka yi ka dawo, kar a bawa wani ita, zan iya mutuwa idan na rasa ta," Hawaye ke zuba a idon Haroon kamar wanda aka ce masa Umaimah tayi sabon saurayi za a d'aura masu aure a yau ɗin. Ishaaq tsayawa ya yi tsak ya dena tafiyar da yake yi a lokacin da ake duba shi dan fita daga filin jirgin,tunda yake bai taɓa jin qanin shi a cikin wannan halin ba, kuma da alama kuka ma yake yi. Ji yayi zai iya aje komai ya koma dan biyan buqatar qanin nashi, dan haka yace, "Haroon kar ka damu, ka ban kwana uku zan dawo zan je kuma na nema maka auren Umaimah, kuma zan mallaka maka in da zaka zauna da ita kuyi rayuwar aure inshaa Allahu, ka daina kuka ka ji qanina, haba namijin duniya, ban taba zaton mace zata karya maka zuciya da izza irin haka ba," "Kaiii Yaya ba wata izza da mazantaka, kawai sai ka dawo din,Allah ya bada sa'a ya sa ka dawo lafiya," Dariya sosai Ishaaq yayi, yaro kenan da baka san mene ne soyayya ba, yanzu ka san ta ka gane ya ake ji a cikin ta. Kiran Hauwaa Ishaq yayi yace ta kula da Haroon, yana buqatar kulawa a yanzu haka, ai kuwa tayi masa alqawarin kula da Haroon din cikin wani yanayin da shi bai fahimta ba . Suna gama wayar ta ɗauki turarukan ta ta fesa a dik inda ya kamata, sannan ta cire komai na jikin ta ta saka qaton hijab, fita tayi dan zuwa wajen Haroon, tinda yayan shi ya bata Umarnin kula da shi, za kuwa ta kula da shi ainun.......................... *Casssssssss, hope u like this page? dan ni dai i no like am, ya ni b'arin hannu* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 19: Sallamar Ramai ce ta daki kunnuwan su Umar ne ya isa ya qarasa buɗe mata qofar ta shiga, kwance Jameelaa take ko motsawa bata yi ba daga inda take. "Ke lafiya na gan ki kwance haka? Ince dai ba wata matsalar bace," Tana magana tana harar Umar kamar ta na zargin shi da ci mata zalin 'ya. Da sauri kuwa ya buɗe baki dan kare kan shi, amma Jameelaa ta katse shi ta hanyar cewa, "Wuce kaje ka qarasa abinda kake yi," "To" Yace ya na dauk'ar da kai ƙasa,dan kuwa ya so ya kare kan shi wajen surukar ta shi, "Ramai na faɗa maki kar ki dinga shiga lamarin mu, ina ruwan ki zaki na tuhumar shi kamar ya maki sata? Ni ba abinda ya yi min kaina ke ciwo, kuma Ramai yaushe yaushe muka dawo gidannan, amma kusan kullum sai kin zo," Juyawa ta yi tana murgud'a baki da fari da ido, ranta a mugun bace, "Dan uban ki da ba na zuwan zaki samu maganin da zaki maida mijin naki haka? Ko uban ki ban taɓa nemawa maganin mallaka ba sai ke,saboda uban naki bai tara abinda zan mallake shin ba, ya ji da talaucin shi ma, kin samu ina kawo maki ne bari na koma da wanda na zo naga ɗan iskan da zai na kawo maki," Da sauri Jameelaa ta cafke hannun Ramai ta kwanta a jikin ta, tana dariya ta ce, "Habaaa Ramai na, kin san idan bana jin daɗi dama haka nake masifa, dan Allah ki yi hakuri kawo na gani," "'Yar kwal uba kai, hanni zaki nunawa kin yi kud'in da ba zan zo gidan ki ba? Innai niyya ke kan ki sai na mallake ki naga ta tsiya," "Haba Ramaiinaaa bai kai na haka ba, muga wannan miqo min na fara amfani da shi, kin san shi da yawan ibada, sai abun ya damqe shi anjima kuma ki ji ya fara lalacewa," "Matsalar da malam (malamin dhibbu) yace kenan yana fama da ita akan wannan tattauran mijin naki, shi bai da aiki sai karya masa sihiri, ina kyautata zaton fa wannan biyayyar da yake maki ba wai naganin kaɗai ke aiki ba dan dai kawai yana son ki ne, amma ba dan sihirin mu ya kama shi da kyau ba," "Koh?" "K'warai kuwa, yanzu dai kawon abinci na ci na ɗan sha jusi na tafi sannan ki ɗan haɗan kayan abinci, na gida ya kusan qarewa," "Ramaiii hooo,ba wani qarewa wannan uban abincin da kika kwasa shekaran jiya ne za a ce ya kusan qarewa? Ai na san zai kai ku sati ma aci a wadace,ke dai kawai ki ce sai kin sake diban wani," " 'Yannema mai kan kwando je ki deb'o kawai bar tone-tone" "Yah Umarr ! Yah Umarr !" "Na'am my love," "Dan Allah zuba mana abincin nan yunwaa nake ji,kaga ga Mamana ma tazo," "Na gama zubawa ma, dama naga kuna ta hira ne shi yasa ban yi magana ba," Da sauri ya tafi yaje ya kawo abincin a babban faranti da lemu da cups da dik wani abu da zasu buqata dai ya ajiye masu ya koma kitchen, a tsaye ya cinye nashi ya dau jaka dan komawa bakin aikin shi, kuɗi masu ɗan kauri ya miqawa Ramai, Jameelaa ta amshe ta raka shi, a hanyar dawowa ta rage wani ta soke, Ramai da tinda suka fita take leqen ta, ta kasa hango wajen saboda window irin na glass ɗin nan ne kuma rufe yake da labule jibga jibga ga kujera ta rufe ta dai-dai wajen ta kasa janyewa, ido ya sha hayaqin dafa wake da shinkafa ba wani gani take sosai ba, k'wafa ta yi ta ce, 'Zaki ci uban ki ne, ba dai ni ke kawo maganin ba, har aban abu ki wafce? Naga shegen da zai dinga maki wahala kina samu kina ci ke ɗaya,' Jameelaa ce ta shigo ranta b'ace dan ma kar Ramai tai maganar abinda ya faru ɗazu, aiko batai maganar ba abinci suka ci sukai nak, sannan Jameelaa ta shiga kitchen dan debarwa Ramai kayan abinci, sai da ta loda mata sosai sannan ta kira ta dan ta ɗauka, ita kam tace ba zata iya d'ibar kaya ba a gajiye ta ke. Ramai kuwa haka ta shiga dan tsabar kwad'ayi ta kwashe komai da aka d'iba domin ta, ta tsare mai napep ta shige sai gida. Jameelaa bacci ta kwanta tayi, sai da ta farka ta yi sallah gaba daya wato ta haɗe Azahar da la'asar dika sannan ta yi wanka ta shiga maqotan ta ta samu garwashin wuta ta turare gidan da mix din turaren wuta da maganin mallaka da aka kawo mata,ba a jima ba kuwa Umar ya dawo. Da ganin shi ka san a gajiye yake wanka ya shiga yayi sannan ya fito, kan shi yake ji yana juya masa, dan haka ya zauna ya dafe kan nashi, nauyi ya masa kamar an d6ora masa abu mai nauyi, tasbihi yake tayi ga Allah, yana istigifari, tare da hailala da hauqala, nan take ya ji ya fara jin sauqin jirin da yake gani. Zama tayi kusa da shi tana ta nazarin yanayin shi. "Yaushe ka dawo? Naga ma har kayi wanka," "Ban wani jima ba da dawowa ba na shigo na ji ki shiru,kawai sai na shiga na watsa ruwa na ɗan zauna na huta," Shagwab'a ta fara yi tare da d'alewa cinyar shi, ta zagaye hannayen ta a wuyan sa sannan ta manna qirjin ta dake rud'ar da shi a fuskar shi tare da kukan shagwaba, "My love menene shin me ki ke so?" "Ni gaskiya yau bana son ayi girkin dare a gidan nan,sha'awar naman rago nake irin gasasshen nan da ka ke siyo min da freshyo sai fruits," "To bari kuka dan dai wannan kawai? tashi ki sa kaya muje a siyo," Tsalle tayi ta qara faɗa masa gaba ɗaya a jikin shi kyakkyawar runguma ta samu a wajen shi, sai da suka dan taba soyayyar su sannan taje ta saka kaya suka fice, yawo ta sa yayi tayi da su tana shaqar iska, magrib ta wuce amma bata ji su koma gida ba daga nan su yi can, sai da ta sa Umar kashe kuɗi sosai,har yana tinanin anya za a samu kud'in su kai shi qarshen wata kafin wani albashin ma kuwa? Bayan magrib liss suka koma gida, bata b'ata lokaci ba wajen baje kayan a nan parlour, ta fara cin na ci,tana ware na iyayen ta, da nasu da alwala ya zo ya tsaya a gaban ta yana tambayar tayi alwala ne ta kalle shi tare da harara "Yanzu fa muka dawo, habaa ai ka bari ma na dan ci na qoshi tinda ka san yunwa nake ji," "Nayi sallah ta kenan tinda ba zaki zo muyi jam'i ki samu ladan bin liman nima na samu ba," "Yi taka sallar ni na haɗa da isha'i" Kad'a kai yayi ya je ya tada sallar shi, cikin sujjadar qarshe yake roqon Allah daya sa jameelaa kar ta sauya daga kyakkyawa zuwa mummuna,dan ya fara ganin wasu halayen da sam bai taba sanin tana da su ba. Da weekend ya so yaje ya gaida Mum amma sai yaji gaba ɗaya baya son shiga gidan nasu, ba wai iyayen nashi ne bai son gani ba ah ah gidan nasu ne kawai yake jin qiwar zuwa. Suna zaune suna shan soyayyar su, dan Jameelaa ba abinda ta fi so irin ya zauna yana wasa da ita, tare da yi mata irin soyayyar da ta saba da ita tin asali. Wayar shi ke ta ringing, amma bai gani ba saboda ta sa masa wayar a silent, tana ganin wayar na haske taqi yi masa magana, cikin dabara ta haye cinyoyin shi ta kwanta a jikin shi ta leqa wayar, sunan Mum ta gani a jiki,  hannu ta sa zata sake tura wayar qasan kujera suka hada ido da shi, sai ta wayance ta d'akko ta miqa masa. Karawa yayi a kunne bayan ya amsa, sallamar Mum ya amsa tare da gaida ita. "Ok Mum inshaa Allah zan zo anjima, ko yanzu zasu zo?........ok to ga ni nan zuwa" Kashe wayar yayi, da hanzari ya miqe yana murna, "Kin san me? Maneman auren Umaimahn ki ce zasu zo, shine Mum ke kirana ya kamata naje ayi komai dani," Dan yatsina fuska tayi, sannan tace, "Kuma zuwa za ka yi ɗin?" Dan haɗe fuska yayi ya kalle ta da alamar ban gane ba? Wayancewa tayi ta fara kame-kame sannan tace, "Nima gaskiya sai kaje da ni, dan kuwa ba za a yi maganar auren qawata kuma qanwata ba bana nan," D'aga ta ya  yi sannan ya saki fuska ya ce, "Muje maza mu shirya ana jiran mu," A tare sukai wanka suka shirya, cikin jallabiyya kalar blue wadda ta sha aiki ya saka wandon rigar, turaruka masu qamshi ya sanya, itama doguwar riga ce a jikin ta, dark blue, mai ratsin pink a jiki, ta yafa mayafin rigar tare da sanya takalmi mai tsini kalar pink da jakar shi suka fita zuwa gidan su Umar.   Koda suka isa an gama komai sun tadda kayan saka rana da Daddy da Mum tare da Umaimahn suna ta hirar bikin Umaimah, shigar su ce ta sa suka maida hankali kan su, Mum cike da jin nauyin su ta gyara zama. Dad ne ya fara yi masu barka da zuwa, Umaimah ta tafi da sauri ta rungume Jameelaah ta ce, "Gaskiya nayi kewar ki sosai,  da alama ke kam hankalin ki kwance yake, ji har wata qiba ki kai sati biyu kawai da tafiya," Wank irin haushin Umaimah ne ya kama Jameelah cikin ranta take fad'in, 'Ji dalla yanda ta wani cukuikuye ni kamar ta samu flour tana curawa,mtsssww' Yaqe ta yi mata suka samu waje suka zauna, suna gaida iyayen nasu. Bayan gaishe gaishe ne Daddy ya yi masu bayanin sanya ranar auren Umaimah da aka yi watanni biyar masu zuwa da Haroon,Jameelah ce ta ce, "Dama na san malamin nan na son ta, itama kuma tana son shi, amma dana tambayi yarinyar nan sai ta musa min," Rufe fuska Umaimah tayi ta tafi d'akin ta tana dariya, Jameelaa na nan a zaune taqi tashi, sab'anin da da take nuna jin kunyar Iyayen mijin bata son zama da su su dad'e a waje ɗaya,yanzu kuwa idon ta fess akan su, Allah Allah take ya tashi su wuce ta gaji da zama a gidan. Sun kula da sauyawar ta ta amma basu ɗauke ta ta wata mummunan hanya ba, a zaton su shaquwa ce ta ke tasiri a tsakanin ma'auratan. Message ta masa akan su wuce ta gaji kuma kanta na ciwo, sai ya mayar mata da ta ɗan jira kaɗan sai su tafi, aiko nan da nan ta b'ata rai, Umaimah na can d'akin ta tana jiran Jameelah ta je su ɗan yi hirar yaushe gamo amma ba ita ba alamar ta,shirun da taji yayi yawa ne ya sa ta leqa ta ce mata, "Qawata muje ciki mana ki sha labari, naji ance anyi bikin mamalo ko?" Wani kallo tai ma Umaimahn sheqeqe,sannan ta ce mata, "Lallai Umaimah baki da kunya, ni kike ce wa qawar ki? Ko kin manta ni matar Yah Umar ce yanzu? Dole yanzu suna na ya sauya a bakin ki, sannan ni kaina ma ciwo yake yi so nake mu tafi gida," Kowa a wajen har Umar kallon ta yake cike da mamaki, me ya same ta ne haka? Jameelaa mai kunya da hankali tare da sanin ya kamata ita ke magana kamar wata babbar mata mara tarbiyya, Umar ne zai yi magana, Mum ta kula da bacin ran shi, nan da nan ta tari numfashin shi ta ce, "Subhanallahi ! ciwon kai kuma Jameelah? Ya kamata kam ki sha magani ki kwanta ki huta, Umar tashi maza ka kaita gida, ka kula da matar ka sosai," Bai musa ba kuwa ya amsa mata da toh, kafin ya miqe Jameelaa ta tashi ta saɓa jaka a kafad'a ta kai qofa? Ba magana ba komai balle ta yi wa surukan nata sallama. Har suka isa gida ba wanda yayi magana, suna shiga ta fara cire kayan ta a parlour Umar yayi yayi dan ya ɗauke kai akan abinda take yi da gayya dan jan ra'ayinsa amma ya kasa jin idon shi yake yi kamar an manna a jikin ta, sai da ta gama cire komai tsaf na jikin ta sannan ta d'ebi kayan a hannu ta shige d'aki, kamar raqumi da akala haka ya bi bayan ta har ciki, bata ce masa ci kan ka ba ta sake fita dan shiga d'akin shi tayi wanka, dan nan ne kaɗai ke da band'aki a cikin d'akunan dika,manna ta yayi da jikin qofar bayan ya mayar ya rufe qofar, na so na ga me zai mata dan tana buqatar a zane ta ta dawo hayyacin ta haka na fita ina ta murna dan kuwa abinda tai ta cancanci a hukunta ta. Na kai awa ɗaya a waje ina jiran na ji kukan Jameelaah abun mamaki sai kawai na ga sun fito riqe da junan su suna ta sheqa dariya, ta na dukan shi cikin sigar wasa cizon yatsa na na yi na bar gidan gaba ɗaya ba zan iya kallon abin duka ba sanda ba. ********************** Haroon kuwa hankalin shi ya kwanta da aka bashi Umaimah, dan haka yanzu ya maida hankali kan karatun shi da kuma kasuwancin shi, sai chatting da waya da Umaimah da yake yi a koda yaushe dan sake kafa gwamnatin sa a wajen ta, kusan kullum suna tare da junan su a waya, hirar su rabi bata wuce akan qara mata junan su ilimin addini, rabi kuma ta soyayya. Yah Ishaaq ne ya dawo daga kasuwa tare da Haroon, suna cin abincin dare Ishaaq ke sanar da su za shi india dan saro wasu kayan. Hauwaa ce ta kalle shi cikin ɗauki tace, "Dan Allah kaje dani, ina son india sosai," "Kin dai san me kike tare da shi a yanzu ko? Kina ɗauke da ciki na wata ɗaya zan ɗauke ki tafiya wata qasa? Ba inda zaki je gaskiya," Haroon bai ce komai ba yana ta kallon su, tayi magiyar tayi roqon amma shiru ya qi yarda daga qarshe tana hawaye ta bar wajen. "Yah dan Allah ina son na maka wata magana a matsayina na qanin ka amma ina tsoro da tinanin ya zaka d'auki magana ta,dan Allah ka fahimci abinda zan sanar da kai, kar ka min mummunar fahimta, sannan ka gyara abinda zan maka magana akai, ba tare da ka bi diddigin ya akai na sani ba," "Haroon wannan bayani naka ya sa naji mutuwar jiki,me nake aikatawa mara kyau haka?" "Yah a gaskiyar magana ina son shawartar ka ne dama akan matar ka, mace na da matuqar rauni, mace tana da son a tattala ta, tana son ta zama dik inda take mijin ta na nan, yana bata soyayya da kulawa tare da girmamawa, Yah na san zaka ce me Hauwaa ta rasa? Komai tana ci ta sha ta sanya tayi ma wani ma, amma a gaskiyar magana ta rasa soyayyar ka, ba ina nufin baka son ta ba, a iya sani na bayan ni Hauwaa ce mafi soyuwa a gare ka, amma baka bata soyayyar da ke ɗauke cikin ran ka, in zan iya faɗan wannan kalmar ba tare da kaji haushi ba ina nufin u ar not romantic, gaba daya baka nuna mata kai ɗin dan soyayya ne, ba irin gifts ɗin nan na masoya tsakanin ka da ita, ba wata soyayya, kuma kwanaki na ji tana magana a waya akan baka biya mata buqata sosai, i am sorry to say amma kaga wannan babbar matsala ce da zata iya jefa ta neman wasu mazan musamman tinda baka nan, kuma baka tafiye-tafiye da ita,kuma Hauwaa mace ce da take very sensitive, abu kadan yana tasiri a ran ta me kyau ko mara kyau," Shiru Ishaq yayi cike da jin kunya yau wai qanin shi ke nuna masa me ya kamata yayi, "Me kake ganin ya dace nayi mata yanzu Haroon?" "Naji daɗi da ka fahimce ni, ina roqon Allah daya baka ikon sake siyan soyayyar ta da yarda ta a karo na biyu a rayuwar auren ku, shawara ta na farko shine ka je da ita wannan tafiyar, amma kai suprising ɗin ta, in yaso sanda zaka faɗa mata sai kace ka ce bazaka da ita bane yau dan kar ta rusa maka plan ne dama, ka dai lallashe ta in yaso in kun je su ta can ba ruwan su suna saida magungunan maza da na matan ma dika sai ka siya abun ka, sannan ka daure ka ɗan dinga ɗan wasanni da ita da zuwa wajen shaqatawa haka," "Lallai ba banza ba kake so a yi maka aure yaro ba abinda baka sani ba, na gode to na gode sosai, Allah ya yi maka albarka, gaskiya naji daɗin shawarwarin ka a gareni,ina godiya sosai qanina, ina godiyar yanda ka zauna ka bani shawara sosai wanda ba kowa ne zai iya ban shawarar yanda zan zauna da iyalina lafiya irin haka ba," "Yah ai kaima abin a gode maka ne ba dika mutane ke son a nuna masu gazawar su ba musamman ta ɓangaren rashin qarfi a wajen mu'amalar auratayya,sai ka ga namiji har na miji amma a d'aki babu fus, mata suyi ta haƙuri da shi, yana gani kamar shi ya gama yi masu komai dan ya mallaka masu dukiya," Haka dai sukai ta tattaunawa a kan matsalar ma'aurata Haroon na ci gaba da wayar ma da yayan shi kai a harkar aure a musulunci. ********************* A qofar gidan Mamalo umar ya aje Jameelaa, glass din idon ta ta cire tana kallon gidan cike da d'agun kai................... [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 18: Babu inda Hauwaa bata duba ba  a gidan amma bata ga Haroon ba,babu ma alamar yana cikin gidan,cike da takaici ta koma parlour ta zauna, wayar ta ta kunna ta nemo No Haroon ɗin ta hau kira, tayi ringing yafi a qirga amma bai d'aga ba. Har ta cire ran zai ɗauka ta ji sallamar shi,cikin muryar bacci, "Ina kaje?" "Ke meye naki na nema na a wannan lokacin?" "Ina son sanin inda kake ne, saboda yayan ka ya kirani ya ce na kula da kai," "Jariri ne ni? Ai ba jariri bane ni da za a ce ki kula da ni, ke in ba dan tsaurin ido ba da kuma kina auren yayana har kin kai wadda zata kula dani? Ke koda kin girmen ma, ni namiji ne da ace kina da halin kirki ni zan kula da ke amma ba ke za ki kula da ni ba, zan kashe wayata kar ki sake kirana dan ban ga abinda zan yi maki ba," Kuka ta saka mai ban tausayi sannan ta ce, "Dan Allah kar ka kashe tsaya kaji, dan Allah ni dai ko dan wasa ne ka dawo muyi, yayan ka kwata-kwata bai iya komai ba, bana samun abinda nake nema a wajen shi, da na san yana da qani kamar ka da ba zan taɓa auren shi ba kai zan aura,.....hello....hello...Haroon?" Shirun da ta ji ne ya tabbatar mata da cewa Haroon ya kashe wayar shi, kuka ta sa mai qarfi tana dukan kan ta da hannun ta, gaskiya ba zata iya zama gida ɗaya da Haroon ba, ko a sauya masa wajen zama, ko ita Ishaaq ya sake ta habaa, ga namiji tana gani amma bai iya tab'uka komai ba ya dinga abu sai kace ba namiji ba, Haroon yafi Ishaaq cikar mazantaka a ido ma. 'Zuciya ta baki yi min adalci ba, yaushe ma kika kamu da sha'awar qanin mijin ki haka? Ko miji na ban taba sha'awa kamar yanda nake ma Haroon ba,ina buqatar taimako indai ina son cimma buri na' Tinani ta yi tayi har bacci ya kwashe ta a wajen. Da safe wajen qarfe tara na safe Haroon ya shiga gidan, ta gyara ko ina kamar yanda ta saba, ta sha kwalliya da qananan kaya matsattsu, wandon iya cinyoyin ta sai qaramar vest mai bayyana baya da qirji, bra din data saka ita ce ta rufe mata qirjin sosai, tare da dago su,tin da ya kalle ta mistakenly bai sake kallon inda take ba, wani kallo ta kafe shi da shi kamar itace miji shine macen tace, "Ga abincin ka nan sanyin idaniya ta" "Really? Wai ke Hauwaa baki da hankali ne?" "Hauwaa? Ina ka baro aunty Hauwaan?" "Mata da dama suke samar wa kan su mutunci, sannan da daman mata suke saida wa kan su mutunci, ke baki da mutuncin da zan kira ki da girmamawa, matsa in ba haka ba dik abinda na maki ke kika jawo, dan kuwa zan maki dukan da Yah ba zai iya gane ki ba" Abincin da ya kai hannu zai ɗauka ta dauke, sam ita bata yi fushi da kalaman shi ba, ta ɗauka da niyyar ya bita daga nan suyi ta zagaye wajen dan ya k'wata, shaidan kuwa daga nan ba abinda ba zai iya kimsa masu ba baki ɗayan su, sai Haroon ya bata mamaki kamar koda yaushe. Tsaki ya ja mai qarfi ya shiga d'akin shi ya barta riqe da abincin ta a hannu, kayan shi ya d'iba masu ɗan yawa ya saka dik wani abu da zai buqata a jakar ya fita, a bakin qofar d'akin shi suka yi karo da Hauwaa, yi ta yi kamar zata faɗi, a zaton ta ya taro ta amma ko kula ta Haroon bai yi ba, aiko sai ji ya yi ta faɗa jikin shi, zuciya ta kai masa ko ina saboda haushi ji yake yi kamar ya zage damtse ya naɗa mata na jaki, amma ya hakura yawurga ta gefe ya fice daga gidan, Hauwaa kuka ta saka mai cin rai, a ranta ta na ayyana, 'Na zaci hakan da na yi zai taimaka min amma inaa, sai ma nesanta ni da yayi da shi, ina zashi oho? Gaskiya ba zan iya rayuwar quncinnan ba, dole ne Ishaaq yayi abu ɗaya acikin biyu, ko ya nemi maganin da zai zama cikakken namiji kuma ya iya soyayya da faranta min rai, ko kuma ya sakeni,gaskiya ba zan iya zama da shi a haka ba,' Sosai take kuka kamar wadda akai ma mutuwa, bata san iya lokacin da ta dauka ba a wajen,   da kyar ta tashi ta shiga d'aki ta kwanta tana jin wani zazzaɓi na shigar ta. Kwanan Ishaaq uku kamar yanda ya faɗa wa Haroon zai yi ya dawo ya dawo kuwa, Hauwaa shadda ce a jikin ta ta sha aiki daga sama har qasa kalar purple, an mata aiki da baqin zare da golden,ta kafe dauri mai ban sha'awa, abinci ta dafa kala-kala masu daɗi da kyau a idanun mai kallo, ta san dolen Haroon ya dawo gidan a yau. Shigo wa yayi cikin qananan kaya wandon nan a d'age kamar ko da yaushe ga gemun nan ya sha taja sai kyalli yake yi, baqin shi mai kyau na ta haskawa da annuri, sallama yayi ya zauna a cikin ɗaya daga kujerun parlourn, Ishaaq ya kalle shi cikin kulawa yace, "An ce min baka kwana a gida ko zan iya sanin dalili?" "Barka da safiya Yayah, ai ka bari a gaisa ko?: "Barka dai," "Ya kasuwa? Ina fatan ka gama komai lafiya? Yaushe kayan za su iso?" Nan da nan hirar kasuwa ta kan kama a tsakanin su, suna cin abinci suna hirar irin riba da kuma ci gaban da kasuwar tasu ke samu,Hauwaa takaici dik ya ishe ta ita taso a yi magana akan Haroon da inda yake tafiya ya kwan yanzu, amma sun tsaya suna wani zancen kasuwancin banza,da qarfi ta aje spoon din ta akan dinning din ta shige d'aki fuuuuu. Kallo suka bita da shi Ishaaq a tinanin shi ko dan ya share ta ne ya maida hankali akan qanin nashi. Haroon ne ya ke tinani a ran shi. 'Ta ya zan yi wa Yah magana akan rayuwar auren su? Bana son zargin wani abu ya shiga tsakanin su ya gano me matar shi ke aikatawa akaina,' Ishaaq ne ya tashi dan tafiya d'aki wajen Hauwaa, Haroon ya tsaida shi. "Yah ina son dama na yi maka wata magana mai matuqar mahimmanci..." "Haroon ko za ka iya barin maganar zuwa gobe? Iyali na na da buqata ta yanzu," Da sauri-sauri Ishaaq ya wuce ya bi bayan Hauwaa. "Kashhh da ka tsaya kaji ma me zan ce maka, ko kaje ba burge wannan mara godiyar Allahn za kai ba," Ci gaba yayi da shan juice ɗin da ya zuba a glass cup, daga baya ya fita zuwa gidan su Umaimah. Umaimah ce kwance tana danna wayar ta,dana leqa sai naga ashe karatun qur'ani take abun ta, labban ta da suke ta walqiya sai motsawa suke cikin nutsuwa, kira ne ya shiga wayar, ta qarasa ayar da take sannan ta dauka cike da murmushi, 'Ko me zai ce min oho? ' Sallama sukai ma juna tare da gaisuwa, sannan ya sanar da ita yana qofar gidan su, in ba damuwa yana son magana da ita, "Magana? Akan menene haka?" "Magana ce akan zuciya ta da taki," Nan da nan kuwa zuciyar ta ta ta fara tsallen murna, dan kuwa ji tayi kamar ta gan ta a gaban shi, amma ta dake, "Indai akan zuqatan mu ne ka makaro dan kuwa wani ya riga ka ya ɗauke tawa, ma'assalam" Kit ta kashe wayar tana ta dariya , cike da d'imaucewa da gigicewa Haroon ya sake kiran ta, qin ɗauka tayi tana ta yi masa dariya, 'Zaka gane kuren ka ne sai ka nemi Dad da kan ka,dan ko arziqin sanar da kai ka neme shi ba zan yi ba,yanda ka wahal da zuciya ta kaima sai taka ta jikkata,' Qin d'aga wayar shi da ta yi ya sake tabbatar masa da gaskiyar maganar ta, a wajen ya tsugunna sai ga hawaye na fita daga idanun shi. Dafa shi ya ji anyi ya miqe da sauri yana goge hawayen shi, kiran sallar da yaji ne ya tabbatar masa da lokacin daya ɗauka duqe a wajen ya na zubar hawaye domin kuwa sallar la'asar ake kira, "Barka da Yamma Alhaji," "Barka dai, Malam ya dai ka zauna anan cikin damuwa," Sosa kai yayi tare da maida hannun shi ɗaya bayan shi kai da ganin murmushin da yake yi kasan na dole ne, ji suka yi za a shiga sallah, da sauri suka nufi masallacin, "In an idar ka sameni a gida," "Inshaa Allahu," Bayan anyi sallah ya je gidan su Umaimah, yana zaune a kujera a harabar gidan Daddyn su ya dawo, katse azkar din da ya keyi ya yi, ya bi bayan shi zuwa ciki, Sai da Daddy ya shiga ya zauna bai ga Haroon ba ya kwala masa kira, ya tabbata bai shiga bane saboda yana ganin bai kamata ya faɗa gidan mutane ba kai tsaye ba tare da an yi masa izini ba. Da sallama ya shiga ya samu qasan kujera ya zauna,Daddy yayi yayi ya hau sama amma yaqi saboda girmamawa. "Malam Haroonaa me ya faru da kai ka tsaya a gate din gidannan kana hawaye? Ina fatan zaka sanar dani ko meye matsalar ka in ina da halin taimakawa na taimaka," Haroon ya dad'e yana kame-kame kafin ya bayyana ma Daddy abinda ya sanya shi kuka, murmushi irin na manya yayi, sannan yace, "Wannan wasan yara ne a tsakanin ku, amma ni dai ban san na yi ma Umaimah miji ba, kar ka damu kaje gida, zan yi magana da ita, in akwai wanda take so mun ji daga wajen ta, in babu zan baka umarnin ku fito inshaa Allahu," Zuciyar Haroon tana a tsakanin murna da kuma damuwa,what if tana da wanda take so ba shi ba? What if ba zai samu auren ta ba. Godiya yayi, sanan yace zai tafi gida, Daddy ya yi ta roqon shi akan ya tsaya ya ci abinci amma yaqi, zuciyar shi gaba ɗaya ba daɗi. Umaimah na maqale a jikin kitchen tana leqen shi, sai ta ji bata so yanda ta gan shi ba, sannan bata ji daɗi ba data ji Daddy yace ya gan shi yana kuka, ita bata zaci abun zai sanya shi baqin ciki har haka ba, kamar ta d'au waya ta faɗa masa dalilin ta na fad'in hakan amma taqi, iyaka in an tambaye ta ta tabbatar ma da iyayen ta shi take so, shine zaɓin ta ba wani ba. *********************** Gidan Mamalo gidan haya ne mai ɗauke da d'aki biyu sai band'aki da kitchen, d'aki ɗaya aka sanya mata kayan gado, d'ayan d'akin kuma sai aka sanya kujeru da 'yan kayan kitchen ɗin ta na gayu, sai ledar d'akin ta mai kyau. Ba laifi dan bata zaci ma zata samu hakan ba Sadeeq shima yayi qoqari ainun, tinda aka kai mamalo Sadeeq yaqi d'aga mata qafa, dan kuwa a daren ya angwance, Mamalo an kai budurci gidam miji lafiya, ansha kukan shagwab'a kala-kala wanda ya ke burge Sadeeq tsabar jin daɗin hakan ya dage sai lallashin ta yake amma taqi daina kukan, cike da nishad'i Sadeeq ya ce, "Haba masoyiyar Abubakar mai gaskiya, dan Allah ki daina kukan haka ya isa, har fa maqota na iya jiyo ki, taso muje na taya ki ki gyara jikin ki kin ji? Sai muyi bacci inshaa Allahu gobe kika tashi ba zaki ji ciwon komai ba," Cikin kuka da shagwab'a tare da wani irin jin kai da taqama da kuma alfaharin ta kai mutuncin ta gidan aure take magana, "Ni ba zan iya tashi ba,bayan ka gama min abinda kaga dama, tinda su Jameelaa suke zance da Babawo ban taɓa jin ta koka ba, in ba daɗi da take ce min taji ba, amma kai rana ɗaya ka gama yi min rauni, dubi har da jini fa tsabar mugunta," Har cikin ranta take jin daɗin kai budurcin ta da ta yi gidan aurenta dan haka take magana kai tsaye hankalin ta kwance zuciyar ta zaune a qirjin ta. Sadeeq ji ya ke kamar ya tsaga qirjin shi ya saka ta dan tsabar so, shi talaka ne ba shi da kyautar da zai yi mata irin yanda yake jin ana yi wa  wasu matan da suka kai budircin su gidan miji,amma yasan abu ɗaya da zai yi mata zuwa biyu. Kama ta yayi ya ɗora ta a jikin shi yana shafa bayan ta da sigar lallashi ya ce, "Fateemana ! ba abinda zan ce maki sai dai nace Allah ya yi miki albarka, Allah ya qara min son ki sama da wanda nake maki a yanzu Allah kuma ya biya maki dikkan buqatun ki na alkhairi, dole zaki ji zafi kuma dole na ne na maki dik abinda zai sauqaqa maki, kiyi hakuri kin ji? Na maki alqawarin dik abinda kike so indai bai fi qarfi na ba zan maki shi, zan kula dake, zan kare maki dikkan mutuncin ki, kinga amfanin qin amincewa da na yi muyi soyayyar shashanci ko? Yanzu gashi munyi komai cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankali, ba tsoro ba fargaba, ba tinanin wani zai gan mu, babban ribar kuma babu zunubi sai tarin lada," Dik abinda yake faɗa yana mata ma'ana a kwakwalwa da zuciyar ta, yanzu ta fahimci dik abinda yake faɗa mata abaya take ganin rashin wayewa ne, sai gashi a dare ɗaya ya gwada mata shi ɗin kwararren ɗan soyayya ne, ba dan zafin da ta ji ba ai irin soyayyar daya gwada mata bata jin ko a india akwai wanda ya fishi iyawa. Sun dad'e suna ta hira a tsakanin su, yana mata alqawurran jin daɗin da zai bata wanda har cikin ranshi yake faɗan su, dan kuwa bai ɗaukar wa kan shi qarya ba shi a rayuwar shi, iyakar gaskiyar shi yake fada mata. Daga qarshe ya fita ya kunna risho ya ɗora ruwan zafi ya juye a bokiti, sai da ya tara wanda zai ishe su sannan ya kai masu dana sirkawa band'akin,wanka ya taya ta tayi ya gasa mata jikin ta sosai, sannan ya riqo ta suka koma d'akin su, zama tayi a saman sallaya ya gyara masu gadon su, sannan ya sa suka sake yin nafila, kafin suka yi bacci, Mamalo dik hakan sabon abu ne a wajen ta, in tai sallahr farilla bata ta nafila sai gashi zama da mutumin kirki ta san ta yi nafila a dare ɗaya. Bayan kwana huɗu da auren su tana ta bacci ya tashi ya yi masu abin karyawa k'wai ne ya soya sai shayi ya dakko bread din daya shigo da shi a daren jiya ya kai d'akin, ragowar kilishin da basu cinye ba ya juye a plate ya rufe, zama yayi a gadon ya tashe ta, tare da mammatsa mata qafafun ta. Bude ido tayi tana qoqarin komawa baccin ta dan kuwa tunda aka kawo ta Sadeeq yake nuna mata shi fa ɗan soyayya ne dama lokaci yake jira. "Yi hakuri ki tashi haka, ki wanke bakin ki mu ci abinci, " Tana jin abinci ta dire a qasa, zama ta yi zata fara ci ya kad'a kai, tare da kama hannun ta ya ce, "Sai kin wanke baki kinyi sallah sannan mu ci abinci dan kuwa  kin makara, na so tashin ki amma na kyale ki ganin irin gajiyar da ki ka yi , taso muje ki yi alwala ko kina so na wanke maki bakin da kaina ne irin na rannan?" Tinawa ta yi da daren jiya sai kunya ta kama ta ta miqe ba musu, ya ko bi ta da tsokana har waje, shagwab'a ta fara yi masa tana son yin kuka sannan ya yi shiru ya kyale ta, kujera ya ajiye  'yar tsugunno guda biyu, ɗaya tata ɗaya tashi, toothpast ya sa mata a brush yana jiran ta fito ya bata, Mamalo na ciki ta rasa yanda zata yi tace ya tashi daga wajen, dan kuwa tutu take ji sai kaiwa da kawowa take a cikin band'akin, jin motsin da take yi kamar mai tafiya ne ya sa ya buɗe ya leqa ta,gani ya yi ta haɗa zufa sharkaf, sai matse hawaye take yi da sauri ya isa gaban ta ya riqe ta, a tinanin shi can wajen ne ke yi mata zafi har yanzu. "Sannu kin ji Fateemaa, bari na sanya maki ruwan d'umi,sai ki kama ruwan dashi,ki yafe ni da na san zaki ji zafi haka da ban yi ba dana hakura" Wata majinar wahala ta sharce, ko kwakkwaran motsi ta kasa yi,fita yake son yi yaji wani irin mugun warin bala'i, Mamalo ta saki wata tusa mai d'anneman wari, kasa shaqa yayi ya fice da sauri daga band'akin yana fita ya shaqi iska mai kyau ya kalli hanyar band'akin, sai a sannan ne ya gane me ke damun ta. D'aki ya shiga  ya zauna, tanaleqawa taga baya nan kuwa ta zage ta dinga zazzage cikin ta, sai da ta gama tass ta fita ta wanke bakinta ta yi alwala, kunya ta hana ta shiga d'akin, tsaye ta yi a bakin qofar, ganin inuwar ta yayi ya kwashe da dariya, "Fatee na shigo abin ki kowa ma yana yi, nima dana tashi sai da nayi sannan nai alwala nai sallah wai ke yanzu a yanda muka riga muka zama ɗaya har akwai abinda zaki ji kunya ta akai irin haka? Habaa ai an riga da an zama ɗaya Mamalonaaa," Kukan shagwab'a ta fara yi har da hawaye, ita bata san wanne irin mutum Allah ya haɗa ta da shi ba, komai daga zuciyar shi yake faɗan shi ba wani boye-boye, ita dai gaskiya yana bata kunya. Haka rayuwar su mamalo ta ci gaba cikin girmamawa da qauna tare da soyayyar junan su,yanzu ta fahimci menene darajar kai budurci gidan aure lafiya, da kuma me ake kira da asalin soyayya, dan kuwa Sadeeq A ne har ma zuwa Z, a cikin sati ɗaya da kwanaki da suka yi yanzu da shi ta tabbatar da cewa soyayyar aure ita ce dahir. *********************** Daga makaranta ta dawo ko abinci bata yi ba kan ta fita, tinda ta saba in ta koma daga school ko kafin ta fita mai aiki ke masu abinci acan shi yasa a cikin kwanakin nan da suka yi da Umar a sabon gidan su ko gas bata taɓa kunnawa ba duk abinda take so koda ruwan zafi ne kuwa shi zai dafa mata ya kawo mata har inda take da buqatar shi, jikin ta dik ciwo yake yi mata sai kawai ta zube a kujera bacci mai daɗi ya ɗauke ta, Umar ne ya shiga da sallama yaji shiru gidan,  ya na qarasawa parlour ya ganta a zube a kujera da alama a gajiye take, kuma yunwa na damun ta. Bai tsaya b'ata lokaci ba wajen tub'e kayan shi ya shiga dafa masu abinci, yana cikin girkin ta tashi ko da ta jiyo shi a kitchen kwala masa kira tayi, da sauri Umar ya fito  cikin wani ladabin da ban taba ganin ya yi ma mahaifan shi ba, ta ce, "Kawon ruwa da maganin ciwon kai, kaina ciwo yake yi," "Ina dafa mana abinci yanzu ko zaki bari ki ci abinci sai ki sha maganin, kin san magani ba abinci baya ci," Harara ta watsa masa kafin ta ce, "Kai zaka faɗan me zan yi? Ni ban ruwa da maganin ciwon kai dalla na sha" Ai kuwa cikin sauri ya je ya kawo mata abinda take buqata kamar wani bawa da uwar gidan shi haka Umar yake bin umarnin Jameelah cikin ɗan qanqanin lokaci................ *Shin wa zai sanar dani meke faruwa a gidan Umar da Jameelaa ne?* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 20: Cikin taqama da izza ta shiga gidan tana sallama,Mamalo ce goye a bayan Sadeeq sai tiqar dariyar ta take yi duniya ta yi musu daɗi,cikin nishi Sadeeq ya ce, "Kin san me babe? Ba qaramin nauyi ne da ke ba, bayana kamar zai balle nidai yanzu na tuba ki yafe ni ba zan qara ba sakko haka kar ki b'urma min bayan," "Sai ka yi minti ɗaya kana zunkud'a ni zan sauka, gobe ba ka qara leqani in ina wanka ba, " "In banda abin ki dan na leqa ki me ne? Ni fa mijin ki ne, dan ma ban maki wankan ba gaba ɗaya, ko baki da labarin Annabi yana wanka da matan shi? Suna wanka a mazubi daya hannayen shi na gogar na Nana Aishaa, irin soyayyar nan nake so muna yi,ba soyayyar da ta wuce ta gidan Rasulullah daɗi da wayewa ko baki son na jiyar dake daɗin da ke cikin gidan aure ne?" "Kaiiii ni ko nake so," "To inshaa Allah na maki alqawarin jiyar dake daɗi ko wanne iri ne in dai ina da hali da ikon yin hakan" Mamalo dan jin daɗin maganar shi bata san ta sauka ba ta rungume shi, sai ji ta yi yana qoqarin yi sumbatar ta ai ko tsayawa tayi tare da lumshe ido, jira take taji saukar sumbar shi sai taji saukar cizo a kumatun ta, ai kuwa da qara da zare ido ta buɗe idon ta, tana ganin yana mata dariya ta bishi da gudu, suka fara zagaye gidan, gajiya Jameelaah tayi da ganin shirmen nasu (inji ta fa ba ni na fada ba) ta buga qofar kitchen da qarfi. "Ana ta maku sallama kuna nan kuna wasan yara," Kallon ta Sadeeq yayi, ya yi murmushi, "Habaa qawar mu ba dai wasan yara ba sai dai wasan masoya  bismillah," Mamalo kallon ta tayi ta ɗauke kai, dan kuwa fushi take da ita parlour ta shige abun ta ta zauna,Sadeeq ne ya yi magana qasa qasa ya ce, "Sai ki shiga ki bawa qawar taki hakuri, kin san har yau fushi take akan rashin zuwan ki kai amarya? Kusan kullum sai tayi maganar," Tinawa da me ya faru ranar ta yi sai ta yi murmushi sannan tace. "Kar ka damu zan shawo kan ta yazun nan qawata akwai son jin gulumsy" Shiga ta yi ta faɗa jikin Mamalo da ke ta zumb'ura baki, dan yanzu Sadeeq ya shagwab'a ta,kowa ma yi masa shagwaba take yi, sun shaqu da shi fiye da tinanin mai karatu, kamar sunyi shekaru a zaman auren su. "Keeee qawata bari b'ata rai in kika ji gulumcyn daya hana ni zuwa kai amarya ai sai kin ji daɗi kema" Mamalo na jin maganar gulma ta fara washe baki ta na fad'in, "Fesa min ! fesa min da sauri na ji," Sadeeq ne ya shigo ɗauke da plate mai dubulan da alkaki na kayan gara, sai pure water a wani plate din ya sha gayun shi ya yi kyau da alama fita ya ke son yi, ajiye musu yayi, sannan ya kashewa Mamalo ido ita kuwa ta kafe shi da idanu kamar ranar ta fara ganin shi. "Yah ne amarya ta, ko akwai magana ne? Fita zanyi na barku dan in dai kuna tare na san ba za a kula ni ba,gwanda naje waje nima," Tashi Mamalo tayi tace, "Muje na raka ka, dan kuwa ba kai qarya ba, yau akwai hira, mun gode fa naga ka riga ni kawo mata abin tab'awa" "Anything for u my Fatee" Dariya tayi suka je daga waje, suna fita Jameelaa ta kad'a ido sama ta na ayyana, 'Wai su masoya dibi yanda yake wani mammane mata, Mamalo har kin isa miji ya tattala ni kema a wani tattala ki? Mu zuba ni da ke' (Wasu haka nan suke a rayuwar su ba su son suga zaman lafiya da soyayya na wakana a tsakanin masoyan da suka shaqu kai ko ba ma soyayya mai qarfi indai da zaman lafiya haka kawai sai wata taji bata son ganin wadannan mutane zaune lafiya da junan su, sai ta yi dik yanda zatai ta raba zaman lafiyar nan, ya Allah ka nesanta idon maqiya akan dikkan ma'aurata da masu niyyar aure) Sai da Sadeeq ya tsotse lips din Mamalo da kyau sannan ta koma tana ta nishadi da jin daɗin irin salon soyayyar Sadeeq da bata gajiyawa da kallon sabuwar ta a  kullum. "Ban labari qawata," Nan kuwa Jameelaa ta zayyana mata kooomaiii, da ya faru a ranar, hatta da yanda suka kwanta bata boye ko sakaya ba, ga qarya da ta haɗa labarin nata da shi dan ta bawa Mamalo haushi, Mamalo kuwa sai taya ta murna take da samun miji kamar Umar, bayan kuɗi ashe mutumin kirki ne haka, faɗa ma Mamalo Jameelaa ta yi wai ya sai mata fili a unguwar iyayen shi, saboda first nyt ɗin su,Mamalo bata san wani first nyt ba, kawai ta make,dan ita ko bata ji abu ba bata ragewa gulma daɗi sai ta kai aya a sauraro. "Gaskiya na mana murna da samun mazan da bamu taɓa tsammani ba, tsakanin Yah Umar ɗin ki da Sadeeq ban san wa ya fi zama mutumin kirki ba,Allah ya bar qauna dai," "Ameen," Hira sukai tayi Jameelaah na cin kayan gara, Mamalo ta sa mata tabarma da pilo a waje, dan zata ɗora girki tinda ga baquwa sun yi kuma kar Sadeeq ya dawo ba abinci, taliya da miya tayi da ɗan kifi tayi daɗi sosai, amma data kawo ma Jameela sai Jameelaa ta yatsina fuska ta ce, "Yanzu kina amarya zaki dafa taliya da miya da kifi? Ina nama? Ko kaza? Sanan ba ganye dibi ɗazu ma fa ruwa kuka ban ba wani ɗan lemu haka babu kayan marmari, gaskiya ni kam sai naje gida naci abinci," (Kun san taliya akwai tsinka yawu, koda baka cin taliya ina da yaqinin ka ga an baɗe ta da miya sai kaji yawun ka ya tsinke, ko da mai da yaji, yanda kuka san lemon tsami haka take da tsinka yawu) Jameelaa ma ba a barta a baya ba wajen tsinkewar yawu, sai tayi sauri ta wawuri cincin ta danna a baki, tana ci tana kallon Mamalo da jikin ta yayi sanyi, saboda kalaman Jameelaa, kuma itama sai yanzu ta kula a matsayin ta na amarya kuma wadda ta kai budurcin ta ba wata kyauta da ya bata, ta dai san ya yi mata addu'a, amma kyauta ai ko ta goro ce tana da daɗi, sannan gashi ko wata basuyi ba wanne ma wata ko sati biyu basu rufa ba amma abinci ba nama sai kifi, kifin ma na rufin asiri. Jan plate ɗin ta yi rai ba daɗi, ta fara d'ibar taliyar zata kai baki, wani yawu jameelaa ta had'iya maqwatt,dan ganin kyaun taliyar a ido, kuma ta san girkin su Mamalo akwai daɗi, (Girki na ɗaya daga cikin qualities na matan kano tabbas ba qarya) "Yi hakuri qawata naga kamar ran ki ya ɓaci, bari na ci ko kaɗan ne, matso dan Allah ki saki ran ki," Taliya Jameelaa ta fara d'iba ta kai bakin ta, ta na taunawa kuwa kunnen ta ya riqe qauuuu dan daɗi, amma haka ta basar ta sosa cikin dabara, sai da suka cinye taliya tass sannan ta sud'e hannu, dan kuwa ajiye cokali tayi tsabar bata son b'ata lokaci. Hira sukai tayi  Jameelaa na ba Mamalo labarin 'yan uwan mijin ta masu kudi, da irin zaman da tayi gidan surukan ta yanda ake ji da ita ake lallab'a ta, da yanda take zuba mulki, sai abinda tace ayi wai shi ake yi a gidan, da qaryar wai da shekarar data wuce Baban mijin yaso ya kai ta Hajji amma Allah bai nufa ba, yace dai tayi ta addu'a Allah ya kira ta, bana da ita za a je. Mamalo murna kamar zata zauce, tsakani da Allah take taya Jameelaa murna, amma Jameelaa gani take kamar Mamalo irin murnar qarya take yi ɗin nan amma a qasan zuciyar ta haushi take ji, nan mamalo ta bata labarin irin jin daɗin da Sadeeq ke bata, da alqawarin da ya yi mata kala-kala, Jameelaa ta so Mamalo ta bata labarin daren farkon su, amma tai ta nuna mata kunya take ji, bazata iya fadan sirrin auren su ba. Sai dai ta bata labarin yanda Sadeeq ke son ta yake ririta ta da kulawa da ita. Wajejen la'asar Umar yayi wa Jameelaah waya akan gashi nan zai zo ɗaukan ta, amsa masa tai da wata murya mai daɗi da rausaya, sai ta juya ta hau magana da turanci, Mamalo kam kallon ta take da sha'awa da burgewa, sannan da taya ta farin ciki. Sai da suka gama magana ta tura masa saqo akan ya siyo fruits leda biyu da kayan kwalama dai in ya zo ya ba Mamalo ɗaya, wai suna cikin babu, ta tausaya masu. Umar sarkin tausayi da son taimako haka kuwa ya tsaya ya siyi fruits masu yawa da cimar zaqi, ya qarasa gidan su Mamalo, sun gama shiri ta d'ebarwa Jameelaa kayan garar ta danna a jaka, dan kuwa tana son kayan gara sosai kamar bata dauki komai ba haka ta fita dan bata so umar ya gani sai ta b'oye,Mamalo ta saka mayafi ta raka ta har waje. Bayan sun gaisa da Umar ne ya d'akko ledar ya miqa mata, aiko ta sake baki ta na kallon shi cike da mamaki kafin daga baya ta hau yi masa godiya, sai Jameelaa ta kwab'e fuska irin na tausayawa dinnan, Umar sai yaji Jameelaa ta burge shi yanda ta tausayawa qawar ta har take son a taimaka mata. Mamalo da murna ta koma cikin gida, tana jin daɗin kayan da aka kawo mata,gyara su tai ta saka wasu a qaramin fridge din ta dake parlourn su, sannan ta yanka wasu ta zauna ta fara sha. Bayan su Jameelaa sun koma gida ba irin qaryar da bata zabga ba akan Mamalo, wai mijin ta baida kuɗi,na abincin da suka ci ma da rana ita ta zara a jakar ta ta bayar, ta hau matse kwalla wai ita zatana yawan zuwa dan ganin qawar ta bata sha wahalar gidan miji ba ko dame ta samu ta taimaka masu da shi. Da kyar Umar ya lallashe ta,yana jin son ta na yawo a jikin shi, mace mai tausayi mara son kan ta ai tayi a rayuwa. Tana a rungume da shi take murguda baki dan ta san dole zai dinga bata kuɗi dan ta bawa mamalon daga nan zata na sokewa. *********************** Hauwaa na zaune tana chatting da wani saurayi da ta yi sabo a whatsapp, suna ta exchanging pics na batsa sai juye-juye take tsabar yanda take jin sha'awa na motsa mata, ta rasa yanda zata saka ranta,taji budewar qofa da sauri ta rife wayar ta gyara kwanciyar ta,tare da b'ata rai, daga baya kuma kawai ta sai washe baki kamar gonar audiga............... *Ban taɓa tunanin wasu groups ɗin suna karanta novel ɗin nan ba turawa kawai nake yi sai da na ga masu tambayar page 20 within awa ɗaya da tura page 21-22...a min afuwa na yi mantuwa ne na zaci a page 20 ɗin aka tsaya....i beg of you to pray for my wellbeing and dacewa da samun kyakkyawan qarshe na yafe comments ɗin*😔au rab'ewa, ana kame-kame....................[11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 21: Kame-kame ta hau yi tana qoqarin boye wayar ta sai dai ta yi rashin sa'a dan kuwa a qasa wayar ta faɗi a kife, har rige-rige suke yi ita da Ishaq wajen d'aga wayar daga qasa, cike da tashin hankali ta amshe wayar a hannun shi ta na zazzaro ido wata iriyar zufar tashin hankali na tsattsafowa daga saman baki da hancin ta,yanda take lamuran ta ne ya sanya Ishaq son ganin meye a wayar ta shiga tashin hankali irin haka, da sauri Hauwaa ta faɗa jikin shi ta ajiye wayar a gefen su ta hau kissing ɗin shi sosai, tare da yunqurin cire masa rigar jikin shi, Ishaaq ma a yau ya shirya tsaf dan ganin ya gwadawa matar tashi soyayya kamar yanda qanin shi ya shawarce shi da ya yi, wasu had'e-had'en magunguna na gargajiya ya sha ya yi tatul wanda wani abokin shi ya bashi bayan ya yi masa bayanin matsalar shi dan haka tuni ya manta da batun waya ya biye mata. Sai da ta ga ta mantar da shi maganar wayar ta sake shi zata wuce ta kwanta, shi kuwa janta yayi ta baya ya fara yi mata wasanni, mutuwar tsaye tayi saboda abinda Ishaaq bai taɓa yi ba kenan, da sauri ta juya ta tura shi baya, idon ta taf hawaye saboda bata son ya fara abinda ba zai iya qarasawa ba, haka rayuwar su take tun farko sai an d'akko abu rumi-rumi kamar gaske sai ya rigata ya barta da abu ajiki tai ta fama da wahala. Qara matsawa yayi ya rungume ta, cikin kuka ta sake qoqarin janye jikin ta amma bai bata dama ba, cikin wata iriyar muryar da Hauwaa bata taɓa jin mijin nata da irin ta ba ya ce, "Dan Allah kar ki guje ni ki bani dama na nuna maki jiya ba yau bace sannan goben mu ba zata ci gaba da zama kamar jiya ba za ta ci gaba da zuwa da kyawawan sauyi na alkhairi har abada" Kuka ta fashe da shi tare da sake k'wace jikin ta a nashi ta ce, "Please Ishaq let go of my hands, kar ka min haka na gaji, ba zan iya ba kullum kai kenan ka gama jagwalgwalani ka biya taka buqatar ni ka barni ko mutuwa zan na mutu baka da asara? Dan Allah ka barni, na gaji da wahalar dani da ka ke yi ba zan iya ci gaba da irin wannan rayuwar ba Ishaq," Ishaaq bai san sanda wani tausayin ta ya shigi ranshi ba,nan take ya fara zubda hawaye, da qarfi ya riqe ta gam a jikin shi ya ce, "I am so so sorry Hauwaa ki yafe min ,yanzu ne na san ina cutar da ke wanda hakan bai taɓa zuwa a tunani na ba balle na yi yunqurin gyarawa,amma inshaa Allahu daga yau an wuce wannan wajen, daga yau zaki samu dik wata kulawa daga wajena da ke da abinda ke cikin ki, ina son ki shirya tafiyar nan da zamuyi dake zanyi ta, in naje can zan sake samo wasu magungunan, yau na samu wani na sha kiyi hakuri mu gwada mu gani in yaso in ba a dace ba sai in munje can naga kwararren likita, ina fatan zaki yafe min?" Da sauri ta faɗa jikin shi tana kuka sosai mai ban tausayi, a hankali ya fara aika mata da saqonnin da ada ita ke yi masa irin su shi sai dai ya tsaya mata kamar gunki, cike da shauqi da son abinda yake yi mata take miqa masa ragamar jikin ta........... Hauwaa ta sha mamaki ainun ashe mijin ta gwarzo ne haka dama bata sani ba? shine yake son ya kashe ta da yarintar ta ya jefa ta a halaka (ki jefa kan ki dai,ita zina zaɓin rai ce ai,idan ka so sai ka aikata ta, idan baka so ba ka bi hanyoyin da musulunci ya ce ka kare kan ka daga gare ta ga lada ga biyan buqata) baccin shi yake hankali kwance, dan kuwa shi kan shi ya yaba ma kan shi qoqarin da yayi a yau, tashi tayi a hankali ta shiga toilet da wayar ta a hannu. For the first time ayau taji tsana da kyamar hotunan batsan da take zama ta kalla,wata iriyar nadama da kunyar Allah ne ya fara ziyartar zuciyar ta, da sauri sauri hannun ta da bakinta na rawa hawaye na gudu a idon ta ta fara da goge dik wasu hotuna dake kan wayar ta, har masu amfani ma sai da ta goge su tass gaba daya ta cire Sim card ɗin ta ta sa a toilete ta kora ruwa, No mazan da take waya dasu dan rage dare dake kan phone dik tabi ta goge, zama ta yi a saman toilet  tana ta kuka, tare da qanqame jikin ta kunnuwan ta ta toshe, tare da rintse idanun ta dan hango abubwan da ta kalla take kamar a film, da kalaman maza da ta dinga saurara ta na jin daɗi tare da amfani da muryoyin mazan da ba muharraman ta ba ta na biya wa kan ta da kanta buqatar sha'awar ta, labb'an ta ta ciza da qarfi sai da taji d'umi alamar ya fashe saboda da su ta ke yi wa mazan banza kalaman da mijinta ne kawai ya cancanta ya ji su,tattaune harshen ta ta soma yi can ta tuna in ta yi masu haka bata tuba ma Allah ba ai aikin banza tayi, da sauri ta fara karanto istigifari a zuci har ta soma a saman bakin ta, alwala tayi ta fito ta fara jero nafilfilu, tana kuka a dik sujjadar da tayi, sai ta dad'e tana neman gafarar Allah kafin ta d'ago, Ishaaq na ta sheqa bacci amma Hauwaa ta kasa rintsawa, kusan akan sallaya ta kwana ranar saboda nadama da neman gafarar Allah mahaliccin ta, bacci ma tsoron Hauwaa yaji a daren nan, dan ji yayi gaba ɗaya ta firgita shi ba zai iya ɗaukar ta ba. Da safe idon ta ya kumbura ainun saboda kukan da ta sha,abinci ta haɗa masu ta koma tayi wanka, ta saka atampar ta da ta aje can qasan akwatin ta, tana da irin su d'inkakku sunfi akwati biyu cike da kayan mutunci, amma bata sawa sai qanana dan kawai jan ra'ayin Haroon. Riga da zani ne ɗinkin mai kyau ya yi matuqar karb'ar kyakkyawan jikin ta mai shape mai kyau,ya rufe ko ina da ya dace a rufe a jikin ta, mayafi kalar kayan ta saka ta koma dan su karya, jirgin su zai tashi zuwa India da yamma. Kallon plate kawai take tana d'iban abincin tana maidawa cikin plate ɗin ta kasa cin koda loma ɗaya ne, Ishaq ya kula tinda suka tashi yaqe kawai take yi masa, shi kuma a tinanin shi yanda ya baje mata basirar kan shi jiya a jikin ta zai same tane yau cikin farin ciki, dan kuwa ta yaba ta koka sosai saboda haduwar tashi ta yi mata,amma kuma me yasa yau ta tashi fuskar ta babu annuri sam. Gyaran murya yayi ya taɓa ta, ganin haka Haroon ya tashi da plate ɗin shi yayi d'aki, Ishaq bai tsaida shi ba dan yana buqayar jin meke damin matar shi. "Meke damun ki ne Baby? Dan Allah kar ki min qarya ki sanar dani ko mene ne, inshaa Allahu na maki alqawarin sama maki mafita akai," Sauke ajiyar zuciya tayi ta kalle shi, hawaye ya zubo mata a kuncin ta,ta sa hannu ta share, sannan ta miqe ta ce masa, "Muje ciki na faɗa maka," Kamar raqumi ta riqe masa akala haka suka shiga ciki.Sai da suka zauna a bakin gado, kan ta a qasa tace masa, "Dan Allah da son Annabi Ishaq ka yafe min dik abinda na yi maka wanda ka sani da wanda baka sani ba, ka tausaya min ka yafe min na san bana kyauta maka a gidan nan, amma inshaa Allahu daga yau zan gyara rayuwa ta, zan sake sabon zubin alkhairi a zaman mu," Bata bayyana masa laifin ta bane saboda ita zina zunubi ne tsakanin bawa da ubangijin shi, wajen Allah zata maida hankali ta yi ta neman gafara da afuwa har ya yafe mata,sannan ta gujewa duk wani abu da zai sa ta komawa wannan zunubin,ta kuma gyara tsakanin ta da Allah,neman yafiyar mijin nata kuma zata yi shi ne saboda ta cutar da rayuwar auren su ta yanda idan har ta faɗa masa ainahin mai ya faru to duk son da yake yi mata zai tafi,idan kuma be daina son ta ba to za su yi ta zama da zargi ne da tsana da jin haushin ta har abada wannan tabon ba zai taɓa gogewa ba a ran shi, madadin ta gyara sai ta b'ata wataqila ya qara nesanta da ita, ko ya qara aure ya kuma sanar da kishiyar ta me ta aikata abun ya zama abun gori a yi ta yaɗa maganar har yara da jikoki,wataqila ta dalilin nisantar ta da zai yi ta koma ruwa. To rufewar ba tare da ta bayyana asalin laifin nata ba ya na da nashi amfanin. Ji yayi kamar ranar ya fara ganin ta, wani irin kyau ya ga ta qara yi masa sai ya ga qima girma da darajar ta ta qaru a idanun sa duk da bai san me ta aikata ba, saboda wanda yake neman gafara irin haka tabbas ya san ya yi laifi kuma a shirye yake da ya gyara laifin nasa,cikin murya mai nuna farin ciki ya ce mata, "Na yafe maki kome ki ka yi min a tsahon zaman mu da ke Hauwaa komai girman shi indai zaki kasance cikin farin ciki na yafe maki, murmushin ki kawai nake son gani a yanzu," Ai kuwa murmushi ta fara yi na tsantsar farin ciki tare da share hawayen dake zuba mata, can ta sake saka fuskar tausayi ta na so ta yi magana ya riga ta da cewa, "Subhanallah menene kuma?" "Dan Allah ina son ka siyo min hijabbai dan ban da hijabi babba ko ɗaya, in zamu tafi su nake son sanyawa," Wata raruma ya kai mata yana sumbatarta ta ko ta ina ya na dariyar farin ciki, sakin ta yayi ya ɗauki key ɗin mota dan bai ga ta zama ba sai ya je shagon su ya buɗe sabbin hijaban da suka shigo da su, ya dakko mata iya yanda zata buqata hankalin shi zai kwanta,sai kiran shi take amma ya fita yana ta doka murmushi, murmushin da ya sa ta murmusawa itama. Haroon ne ya fito dan aje plate ɗin shi da ya gama cin abicin safe da shi ya na ajiyewa zai fito suka haɗa ido Hauwaa, sai taji kunya da nauyin sake haɗa ido dashi,  shi kuwa sauyin da ya gani a tare da ita ne kawai ya sanya shi kasa ci gaba da kafe ta da ido,a hankali ya ce mata, "Godiya muke da abinci mai daɗi Aunty Hauwaa," Da sauri ta zube a kan guiwowon ta, ta fara hawayen nadama da kunyar abinda ta aikata masa a baya. "Haroon dan Allah ka yafe min na san....." "Shiiiii ya isa Aunty Hauwaa tashi dan Allah, tashi da sauri kafin wani ya gan ki a haka ya zaci wani abu ne na daban, ni Haroon na yafe maki ki ɗauka komai bai faru ba na goge shi a kwanya ta da zuciya ta, kema ina fatan zaki manta da komai ki riqe Allah kiji tsoron shi iyakar iyawar ki kuma ki bi mijin ki ki yi masa biyayya," "Nayi nadama Haroon, na tuba nabi Allah nabi ma'aiki, " "Yauwaa Aunty naa, yanzu ki zauna kafin Yah ya dawo, kema ki fara shirya kayan tafiyar ku, ki je ni kuma zan je na dakko takardar da jiya na kasa bacci sai da na rubuta ta,wato takardar list ɗin kayan danake son a sanya a lefen matata" Murmushi suka yi wa juna a hankali ta fara sakewa da shi, d'aki ya je ya d'akko mata list ya miqa mata, sai ta hau dubawa ta ga ya rubuta kusan komai da komai da ya kamata da kuma wanda shi yake so a sanya wa matar shi a lefen nata. Ishaaq ne ya dawo da ledoji manya masu ɗauke da tambarin shagon su da adireshin shagon, hijabs ne manya da dogayen riguna da qananan hijabs din su, da socks sai niqab, ya baje mata su a gaban ta dariyar farin ciki ta dinga yi, ta na godiya da yi masa addu'a. Wata leda ya d'akko sarqoqi ne a ciki guda uku, masu ɗauke da abin hannu harda sarqar qafa da zobunan su da d'ankunne daga india suke shigo da irin su. Murna ta farayi sosai ta dinga godiya sabanin da kome zai aje mata a wulaqance take kallon shi, tinda ya gaza a gado, raini ne sosai a tsakanin su. "Ni fa gaskiya sai an cinye abincin can, in baku cinye ba ba za ai tafiyar nan ba," "Tabbb ai bari ka ji daga can ma gaba mukai yaro, ba dan ka qi ba ma ai da tare da kai zamu je ka haɗa lefen ka da kan ka mu kuma mu sha honeymoon din mu da bamu yi ba ada" Rufe fuska Hauwaa tayi ta shige d'aki tana dariya dan kuwa yanzu kunyar su take ji gaba ɗayan su kwarai da gaske, ta na tafiya Ishaq ya rungume Haroon yana murna da farin ciki tare da yi masa godiya, cikin washe baki ya ce, "Wai qanina me ka keso na yi maka ne dan kaji daɗi kaima a duniya?" "Ka auramin Umaimah, ka zauna da matar ka lafiya cikin so da qauna, shikenan ka biya ni," "Ka kuwa samu, auren ka za a yi shagali na gani na faɗa inshaa Allahu" Haroon ne ya kai su filin jirgi bai bar wajen ba sai da jirgin su ya tashi ya koma gida cike da godiyar Allah, nan ya kira Umaimah sukai ta hirar soyayya tana ta mamakin shi, kamar ba Haroon da ta sani ba, dik sai yana bata tsoro ma wani lokacin idan ya yi magana, irin su ne ustazan da idan ka aure su ka ke shan soyayya kamar a turai. *Tooooo ayi hakuri da wanga zuwa gobe mu leqa mutan india mu ga soyayya🙊😂* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 22: Jirgin su na sauka a airport ɗin dake babban birnin Delhi ta india aka zo ɗaukan su a motar hotel ɗin da zasu zauna a ciki,Ishaq ya shiryawa wannan tafiya da gaske, dan haka suna gamawa da filin jirgin drivern ya loda kayan su cikin mota sai ya ɗauki hanyar hotel ɗin nasu mai suna Cartel palace wanda ke cikin garin na Delhi. Waje ne mai kyau da ban sha'awa, iya kudin ka iya shagalin ka,daki ne madaidaici wanda ya qumshi kayan more rayuwa, Ishaaq na aje kayan shi ya sumbaci goshin ta ya fita sai tambayar shi take yi ina zashi amma sauri yake ya je ya kammala komai sannan ya nutsu ya sha amarcin da bai sha ba ada. Kallon wajen ta tsaya yi taɓa wancan ta gama ta duba wancan haka tai tayi sai da ta kashe qyayar idon ta sannan ta yi shirin wanka, wanka tai sosai da ruwa mai zafi, ta gasa jikin ta da kyau dan ba qaramin tsami ya yi mata ba, toilete ɗin ya tsaru sosai dan haka bata san iya lokacin da ta ɗauka ba wajen gyara jikin ta da kayayyakin wanka da na gashi, sai duba sunayen abubuwan take yi dan tana sha'awar itama ta siya ta dinga gyara jikin ta dan mijin ta ya ji daɗi shima. Wata rigar bacci ta saka mai musulmin kyau kalar kore, kun dai san Hauwaa wajen sanya qananan kaya oganniya ce dama, dan haka zan taqaita maku ince sai wanda ya ga wannan riga kawai. Yunwa take ji amma tana tinanin ya zata yi tai magana akawo mata abincin ita bata taɓa zuwa hotel ba dan haka bata san ya ake yi ba, tinanin yanda ta gani ana yi a film tayi, dan haka kawai ta dauki salular d'akin ta danna kira, da turancin su irin na indiawa suka tambaye ta ko zasu iya taimakon ta da wani abu? Kafin tayi magana aka qwanqwasa qofar d'akin ajiye wayar tayi ta sanya hijab domin buɗe qofar dan taga waye, tana bud'ewa taga ma'aikatan hotel din ɗauke da abinci kala-kala an turo a teburin da suke aza abinci na qarfe, matsawa ta yi suka shiga ciki suka ajiye mata, 'yan mata ne kyawawa sun saka kaya irin na indians amma kala ɗaya sun nannad'e gashin kan su sun sanya qarshen a cikin wata baqar hula hakan da ta gani ne ya bata tabbacin wannan shine uniform ɗin su kowacce da sunan ta rubuce a wani golden qarfe a gaban mayafin ta. Murmushi suka yi mata tare da yi mata barka da zuwa hotel din  Cartel palace, ajiye abincin sukai sannan suka fita. 'Ishaq' Shine abinda zuciyarta ta raya mata dan ta tabbata shine zai bada umarnin a yi mata hakan tunda ita bata yi magana a kawo ba, bud'e abincin ta fara yi yawun ta na tsinkewa, abinci ne kala-kala masu tsinka yawu,sai juice kala uku, da babban bowl mai dauke da fuit salad, fruits din ciki wasu ma bata taba ganin irin su ba, sai shayi a wani qaramin kofi,murmushi ta yi dan kuwa da a gida ne ai sai ta kandama shi a babban kofi ta sha ta koshi. Zama tayi akan kujerar da ke kusa da table ɗin da suka aje mata abincin, ta dauki bowl din fruit salad ta hau sha, sai da taji ta kusan qoshi ta ajiye ta tattab'a sauran abincin hamdala tayi ta jingina bayan ta a kujerar tare da lumshe ido ta ce, "Wannan itace irin rayuwar danake mafarki kullum, da na tsaya zan zalunci kaina na kai kai na da kai na wuta da mugayen ayyuka na" A haka bacci mai daɗi ya ɗauke ta, ta ko duqunqune kan ta saboda sanyin ACn dake ratsa ta. Ishaaq sai da ya gama auna kayan shi zuwa gida Nija ya tabbatar komai ya kammala, sannan ya fara neman inda zai samu ɗan maganin da zai yi amfani da shi a daren duk da ma ya ga dare ya yi sosai an kusa kiran sallar asuba, kafin gobe ya je ga likita. Wani ba'indiye ne mai kamala ya zo wucewa ta gaban shi, sai yaji kawai bari ya tambye shi wataqila ya san inda zai samu irin magungunan, da harshen turanci ya fara yi masa magana dan yawan zuwan da yake yi qasar be sa ya iya yaren su ba, sai dai da alama turancin ba'indiyen ba sosai bane, sai da Ishaq yayi da gaske sannan mutumin ya gane me yake nufi, dan kuwa qarshe ta kurame ya yi masa. Yana ko ganowa ya washe baki, ya fara yi masa yare, Ishaaq dai kad'a kai kawai yake yanda yaga sukan yi da kai suma idan suna magana. Jan Ishaaq yayi suka hau adaidaita sahun irin nasu suka isa wata kasuwa, wasu shagunan ma dik an rufe su saboda gabatowar asuba, wani babban shago suka shiga sai da Ishaaq yaji kunya dan ganin magungunan gyara na maza da mata birjik, mutumin yana gama nuna masa waje ya yi haramar tafiya, Ishaq ya bi shi ya ɗauki kuɗi irin nasu ya ba ma mutumin, amma yaqi Karb'a, can nesa da shagon Ishaq yaga mutumin ya nufa, da alama ko ya san wajen sosai ko dama a ta nan ɗin yake. Yaron shagon ne ya nufo shi yana masa bayani yana nuna masa kayan wajen, A Ishaaq bai ce ba saboda jin nauyin magungunan, hamdala ya yi da Allah ya sa a wata qasar ya zo siyan irin maganin nan da kan shi ba a Nigeria ba,nan take ya dinga mamakin abokin shi da ya bashi maganin da ya sha rannan yanzu haka suke zuwa shaguna ana ganin su suna siyan waɗannan abubuwan? ganin yanda Ishaq ya yi gum ya na nuna alamun jin kunya ne ya sanya wani babba a cikin su ya taso, ya fara yi wa Ishaq bayani da turanci nan da nan suka fara ciniki Ishaq ya deb'i na ɗiba ya bar na bari, ba shi da burin da ya wuce ya kyautata mu'amalar auren shi da Hauwaa dan haka dole ya jure ya daure ya ajiye kunya a gefe a take a wajen ya sha wasu ya kora da ruwa. Ishaq sai huɗu da rabi na dare ya koma Hotel ɗin nasu, a hankali ya bude qofar, dubawa yayi saman gadon bai ganta ba, cann saman kujera ya gan ta kwanukan abincin da ya sa akawo mata kan ya fita a barbaje a gaban ta alamar taci ta yi nak. Murmushi yayi ya isa gaban ta ya rufe ta da bargo sannan ya yi waya dan a zo a ɗauke kwanukan sannan a taho masa da Tea da chips, dan kuwa shima yunwar yake ji sosai tinda ya fita bai ci abincin kirki ba, ba a jima ba kuwa namiji ɗaya da mace suka je. Dik a qofa Ishaaq ya bar su suka tsaya, shi yayi ta miqa masu kayan, ya amshi wanda suka kai masa ya koma ciki. Sai da ya sha tea ya qoshi da chips sannan ya sha ruwa ya shige toilet, wanka yayi sosai,yayi brush shima harda shinshina bakin yayi tayi ta hanyar hura iska a hannun shi ya shaqa, sannan ya dawo ya b'oye kayan da ya siyo a jakar shi, ya ɗauki na bacci ya saka. Turarukan shi masu tsada da qamshi ya fesa, jin kan shi ya ke kamar ba shi ba,yana jin shi kamar wani sabon angon da ya yi sabuwar amarya dal a leda,duqawa yayi ya fara sosa mata kuncin ta a hankali tare da fad'in, "Sleeping beauty a tashi haka, a tashi a yi sallah, dan na san da kyar in kinyi isha'i ki ka b'ingire," Bude ido tayi a hankali suka sakar ma juna murmushi, kunya kunya nauyi nauyi da wani irin sabon feelings ke mamaye da su, tashi tayi dan shiga toilet dan kuwa tana buqatar sake wanke baki tunda ta sha bacci, Ishaaq kuwa qoqari yake ya manna ta da qirjin shi, zamewa tayi da gudu ta faɗa band'akin da murmushi ya bi ta, ya zauna zaman jiran ta, daga baya ya bi bayan ta, alwala suka yi bayan ta gama brush suka koma. "Ka dad'e gaskiya baby, ina fatan ka gama komai kamar yanda ka tsara?" "Na kammala komai na waje kin san dake mun gama siyan komai dama amfanin zuwan dan mutum ya ga yanda komai zai tafi kamar yanda yake so ne, sannan ya sake duba quality ɗin abinda ya siya kar sai an kawo ka ga ba abinda ka siya ba aka baka,tooo yanzu tunda na gama da waje sauran aikin ciki ko?" Murmushi suka yi wa juna sannan ta dan harare shi, tace, "Ka yi tafiyar ka ka barni ni kaɗai ina ta jiran ka,ba dan munyi sauran sallolin mu a jirgi ba ai da tini ina zaune da salloli akai banyi ba, na rasa gabas ni kuma na kasa tambayar su," "Sorry my dear, muyi sallah lokaci na wucewa amma da kin sani kin yi sallar a haka saboda gudun fitar lokaci ballantana a harka ta addini ba a kunya ko jin nauyi, ga lokacin sallar asuba ma ya gabato mu jira mu yi kawai saboda kar mu makara" Bayan sun yi sallah suka ɗora da nafila,dan kuwa Hauwaa har yanzu ji take kamar tana tattare da tarin zunubai domin bawa bai da tabbas akan ko Allah ya karb'i tuban shi, sai dai kawai ka kiyaye aikata sab'on ka kuma tsananta wajen neman gafarar Allah, sannan kayi wa Allah kyakkyawan zato. Suna idarwa suka zauna suna addu'o'i lokacin asuba na yi suka maida sallar asubahi suna idarwa Ishaaq ya ja ta zuwa jikin shi, ya fara aika mata da saqon da yake ɗauke dashi, Hauwaa tashi tayi ta gudu zuwa kan gadon su, a tsakiyar gadon ta zauna, tare da cire jallabiyar da ta yi sallah da ita, rigar baccin da ta sanya ta bayyana, kafe shi tayi da ido da kallon so da qauna tare da shauqin son kasancewa da shi, har na samu kujera na make kawai naga duhu ya bayyana, sai hasken fitilar gefen gadon mai kalar ja, kun san idon nawa sai da gilashi kuma na manta shi a Nijaaaa, dan haka kawai na kulle idona na hau bacci, nabar Hauwaa amarya da Ishaaq tsohon hango su amarce. Washe gari Hauwaa tashi tayi da wani irin annashuwa da annurin fuska haka ma Ishaaq, bai taba zaton rayuwar aure na da daɗi irin haka ba, bai qi ya dawwama a tare da Hauwaa ba a yanayin da suka kasance da asubar ba har qarshen rayuwar shi. Sai wani nan nan suke da junan su, yanzu Hauwaa in Ishaaq ya ga Alif yace Baa ce itama hakan take kawai a wajen ta,sai da suka sha bacci suka qoshi sannan suka tashi suka yi wanka suka yi azahar suka fita kasuwa. Shopping ɗin lefe Haroon da Umaimah suka fara yi basu suka gama komai ba sai sha ɗaya na dare suka koma hotel din nasu a gajiye, dan kuwa bayan sun gama komai aika kayan gida 9ja suka yi, suka kutsa cikin garin dan kashe qyayar idon su. Ishaaq yayi booking ganin likita a gobe, sannan a goben ne yake son ya kai ta Taaj Mahaal, shi ko sanin inane ma wajen bai ba, ita kuwa saboda kallo ta matsu ta je ta bada labari. Yau ma Ishaaq ya qara ma Hauwaa karatu akan na jiya, Hauwaa fa ta gama gane halal tafi haram alfanu, Ishaaq kuwa ya gama gane ashe da cutar kan shi ya dinga yi bayan cutar da Hauwaan. Ishaq ne gaban likita yana masa bayanin komai, likita na rubucewa, daga baya ya rubuta masa magunguna da shawarwarin abubuwan da suka kamata ya dinga yi. A reception ya same ta tana ta danna waya, tana buɗe sabbin account na social net, dan ta rufe na da ta kuma sauya suna daga sunan da aka santa da shi a da,  tana ganin shi ta tashi suka tafi, Hauwaa ta dau hotuna kala-kala a Taaj Mahal, taji daɗi sosai, Ishaaq sai kallon farin cikin ta yake, bai taɓa jin daɗin tafiya irin wannan ba, ashe da tauye kan shi yake yi. Yau su Hauwaa zasu bar India a wuce qasa mai tsarki dan yin umra. Hauwaa sai kuka take dan bata zaci zata wannan qasa nan kusa ba duba da yanda mijin nata bai taba zuwa da ita ko ina ba. Sai lallashin ta yake yana jin ba daɗi a ranshi dan ya san shine silar cire mata ran zuwa duk da cewa ya fi qarfin kud'in da zai kai ta makkan. Sanda ta ganta gata ga d'akin Allah kuwa a guje ta qarasa ta qanqame ka'aba kamar za a hana ta tab'awa, tayi kuka ta kuma har sai da taji ta kasa kokawa bayan ta gama umarar tadika ta samu waje ta yi nafila raka'a biyu kamar yanda ake yi bayan kammala umara ta hau addu'a sosai tin ina iya saurara a tsaye har sai da na zauna,basu jima a makka ba suka wuce madina sai da suka yi sati ɗaya sannan suka tattara nasu ya nasu dan komawa zuwa gida. Haroon sai tsokanar su yake yi wai sun sauya gaba ɗaya kamar wasu turawa. ********************** "Ba zai taba yu wa na bar wannan cikin ba ina fama da karatu, ga shi da na haihu na san dik wannan kyaun jikin nawa sai dai ya zama labari," "Me kike nufin zaki yi to?" "Ina nifin ka taimaka ka zubar min da cikin nan inna kammala karatu sai na haifa maka kantin kwari ma in kana so, dan Allah yah Umar ka tausaya min," Kawai sai ta sanya masa kuka, Umar jikin shi dik ya mutu, ya rasa ma tinanin da zai, shin biye mata zai yi ko kuma ya zai yi mata? Ga kukan da take yi masa ya na jin shi har tsakiyar zuciyar shi, baya son ganin koda ɓacin ran ta ne balle hawayen ta. Ganin halin da ya shiga ne ya sanya ta sake rikicewa da sabon kuka, har tana tari da k'warewa, tare da dafe gefen zuciyar ta ta durqushe a gaban shi tsabar makirci irin na Jameelah. Umar cikin damuwa mai tsanani ya d'ago ta ya rungume idon shi na zubda hawaye ya ce............ *Thanks to every parson that commented on this novel,ina jin daɗi, ina jin daɗi, ina jin daɗi sosai idan ina karanta comments ɗin ku, Allah ya sa saqona na isa inda ya dace fiye da abinda na ji kuma nake gani a comments din ku, Allah ya shiryar damu dika ya tabbatar damu akan daidai,Allah ya yafe mana kurakuren mu, Ameen* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 23: "My love me kike faɗa ne haka? Bari in tambaye ki, shin waye namijin da ki ke son kasancewa da shi har qarshen rayuwar ki?" "Kaine😏" "To me yasa dan kina ɗauke da cikin da nine sanadin samuwar shi kike son zubar dashi? Kin taɓa jin na yi wa halittar ki kushe? " "A'a" "To yanzu zan maki wani alqawari, ni Umar na yi maki alqawari ba zan taɓa rabuwa da ke ba saboda lalacewar halittar ki ko kuma rashin ilimin boko mai zurfi ko wata nakasa ko tawaya da zata same ki anan gaba ke har abada ma,ni Umar ina tare da ke ne saboda Allah da son da nake yi maki, dik randa kika ga na rabu da ke to kin saɓawa Allah ne, ko kin yi abinda yake mummuma ainun, wanda na san ba zaki taɓa yin hakan ba," Nan da nan idon ta ya yi qifi-qifi ta hau sosa hanci, sai taji bata son a ja maganar ma saboda kar kuma a fara 'yar tone-tone. Lallab'a ta Umar yayi tayi, tana masa shagwab'ar iya shege har daga qarshe ta nuna masa magana ta wuce ba zata sake tado ta ba. ********************** Kwanci tashi asarar mai rai, yanzu cikin Jameelaa ya kai wata huɗu,a cikin watannin nan huɗu sau ɗaya ta yarda ta haɗu da Mum, Umaimah ba yanda bata yi da Jameelah ba akan su yi jigilar bikin ta tare amma taqi, ko sanda su Aunty Hauwaa suka kai lefe qememe taqi zuwa, wai bata da lafiya  labarin cikin ta ya baza 'yan uwa da abokan arziqi, tanadi kuwa tini ta fara yi dan yin suna na gararin da ba a taɓa irin shi ba a lungun su,Mum kuwa na ta murna zata samu jika dik tinanin ta ya bata cewa Jameelaa kunyar ta take ji ta ganta da ciki shi yake hanata zuwa inda suke, in tayi wannan tinanin sai tayi murmushi ta ji daɗin yin dace da surukar kirki irin Jameelah da ta yi. Mamalo kuwa na ganin fi'ili kala-kala dan kuwa kusan koda yaushe Jameelah na hanyar zuwa gidan ta,qaryar kuwa da ta d'ingimo za a yi da sunan nan ba qarama bace, qawayen ta na social media dik sun san tana ɗauke da ciki ta kuma sanar da su irin shirin sunan da zata yi, dan haka dik wanda suke a garin Kano sun yi mata alqawarin zuwa sunan, qawayen ta na makaranta yaran masu kuɗi da 'yan qaryar makaranta dik sai d'igimin zuwan jariri ko Jaririya suke yi. Bikin Umaimah da Haroon ya taso gadan-gadan, dan kuwa Jibi ne d'aurin aure, Jameelaah uwar bidi'a tinda taji ance ba za ai partyn komai ba ranta yake a b'ace, dan haka ta gama shirya qaryar da zata yi ba zata je bikin ba sai ran kai amarya, ranar kuwa zata kasance kusa da Umaimah dan a bata kud'in siyan bakin amarya. Motar Umar ce ta tsaya a qofar gidan nasu, tana jin qarar kuwa ta d'iba da gudu zuwa d'aki ta kwanta tare da qaqalo kuka ta hau rerawa, tana ta murqususu kamar me jin naquda, sallama ya dinga yi bai ga kowa ba a parlour ba, kwanon da taci soyayyar kaza da lemun da ta tsiyayo a cup na nan ajiye a saman center table, d'ankwalin ta na yashe a qasa, murmushi yayi dan ya san maybe tana d'aki tana bacci, tinda cikin nan ya shiga wata biyar ta daina laulayi sosai sai bacci da yawan cin abinci. Yana dosar qofar d'akin nashi ya jiyo kukan ta da sauri ya qarasa ciki, ganin ta kwance tana murqususu ne ya sanya shi shiga damuwa duqawa ya yi a gaban ta ya na shafa ta ya ce, "Subhanallah My love me ke damun ki?" "Wayyooo Yah Umar zan mutu ciki na ! innalillahi wa inna'ilaihirraji'una ka kiramin Mamana da Babana ka ce su yafe ni ni tawa ta zo qarshe," "Plsss my love ki daina irin wannan maganar tell me, me kk ji a jikin naki yanzu haka?" Nan ta rasa me zata ce masa saboda sam bata yi wannan tunanin ba ma ta fara wannan iya shegen ta jima bata amsa shi ba sai cann cikin kuka ta hau kiran, "Wayyoo cikina sai motsawa yake yi da qarfi, Yah Umar ɗan nan so  yake ya fasa min ciki na ya fito," "Dan Allah ki daina fad'ar haka, baby ne ke juyawa, ba tin rannan na fada maki ba haka zata faru sanda ya fara girma a cikin ki ko kin manta ne?" "To ni zafi yake yi min, dan Allah na ce a cire ka qi, inna mutu wajen haihuwa fa?" Kawai sai kukan gaske yazo mata, dan tana tsoron haihuwar da gaske har cikin ran ta, "Yah Umar please do something" Umar gaba ɗaya ma ya kasa cewa komai tsabar yanda ta kid'ima shi, a duniya baya qaunar abinda zai ji ance ya rabu da ita ko menene shi,dan haka ya qanqame ta yana shafa bayan ta, yana ajiyar zuciya,ganin haka yasa ta ji daɗi sosai a ran ta hankalin ta ya kwanta ta san ta gama da shi ya gama matowa akan ta ba abinda ba zata aikata masa ba ya shanye,daga baya ya sa ta kwanta a bayan ta ya hau duba cikin nata da kan shi,ya na gamawa ya tabbatar mata da ba ta da wata matsala ita da babyn suna nan cikin qoshin lafiya motsi ya fara yi shiyasa take jin abinda take ji. Umar ko tsinke bai barta ta taɓa ba sai abinda ya zama dole, sai nan nan yake yi da ita, ga shi a matse take da buqatar shi, amma dan kar ya ce qalaou take haka ta hakura, sai dai taqi sam ya rab'e ta, dan in ya taba ta tana iya aje ciwon nan a gefe ta mamaye shi. *********************** Tin da safe ta ke shirin zuwa gidan Mum, dan kuwa ta ci aniyar sai an bata kud'in siyan bakin amarya, ta qara a na sunan da ta d'ingimowa kan ta kamar amaryar ce ta sa ta yin sunan kece raini. "Wai shirin me kike yi ne haka ke da baki gama warkewa ba? inace jiya da yamma nan ki kai ta birgima a qasa kina kuka, sai da na samu ki kai bacci kika samu sauqi" "Zan je kai amarya ne mana, da ba zan iya ba ai ba zan ce zani ba ko? Ko baka ga alamar na samu sauqi bane?" Umar shiru yayi saboda ya kula da wani rashin kunya-kunya take yin maganar, ya na tsoron tanka ta cibi ya zama qari. Waya yayi ma Mum ya ce mata ga Jameelaah nan zuwa a kula da ita dan bata da ishasshiyar lafiya kwana biyu, ta bashi tabbacin zata kula da ita sosai, dan itama bata son ta wahal da ita din. Sai da ta gama shirin ta tsaf ta fito,ba qaramin kyau tayi ba kuwa kun dai san mutuniyar taku wajen kyau, sai qamshi take zabgawa kanta daya sha gyara sai walqiya yake yi. Umar na biye da ita da ɗan qaramin mazubin da take zuba ruwan sanyi da jakar ta, ita kuma tana tsaye tana yafa mayafin ta, yafin mayafin da ta yi irin na 'yan mata ta yi, a zuciyar shi baya son hakan amma yasan in yayi magana yanzu cibi zai zama qari dan haka sai ya kulle bakin sa ya yi gum ya kyale ta . (Irin wannan soyayyar sai ta kai mijin da matar ma dika wuta) Suna tsaka da kulle gidan suka ji maganar Ramai a bayan su. "Ikon Allah Jameelaa ina zaku haka? Ko bikin zaki je da wannan zungurin cikin naki?" "Ramai me ya kawo ki gidana da sassafe haka?" "Habaa Jameelaa ya zaki na yima mahaifiyar ki tambayar me ya kawo ta gidan ki da sassafe?" In ji Umar da ya ji maganar tata ta yi masa girma a kunnen shi. Yaqe tayi ta sosa hancin ta, sai dai ɓacin rai ne kwance a zuciyar ta game da Ramai da ke son rusa mata shirin ta,washe baki ta yi sannan ta ce, "Ba nufina ke nan ba, ina nufin naji daɗin ganin ta sai dai na yi mamakin ganin tane dan kuwa kamar ta san tana raina," "Allah sarki d'iyar albarka, zuwa na yi dama danna sanar dake mahaifin ki ba lafiya gashi can kwance, ruwan batirin babur ya taɓa masa qafa wajen yayi mummunan rauni, kin san kuma yanayin gidan namu a matse d'aki daya, ga band'aki na gidan gandu jiya da yamma ya shiga band'akin dan kama ruwa ya faɗi, shine ciwon ya sake kwab'ewa, nayi ta kiran wayar ki kuma bana samu, shine nace bari na zo na sanar dake abinda ke faruwa a can gida" "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un," Umar da Jameelah suka haɗa baki wajen faɗa, sannan Jameelaa ta fara magana cikin damuwa, dan kuwa uban ta na da matsayi mai girma a wajen ta, yanda take son shi bata son Ramai ma haka, soyayya mai tsafta take yi masa, matsala ɗaya zuwa biyu ne ya sa take jin haushin sa wato bai wuce tsananta mata da yake yi ba wajen bata tarbiyya, da kuma rashin wadata su da dukiya da bai yi ba kamar an faɗa mata shi ke azurtawa,wannan dalilan sune suka jawo take jin haushin shi. "Muje Yah Umar ka kaini na ga babana, na shiga uku ni Jameelah ya Allah ka hore mana iyaye na su samu muhallin k'warai," Umar cikin tausayawa ya ɗauke ta ita da Ramai sai gidan su Jameelaah ,Ramai na ta zayyana masu yanda abun ya faru a hanya. Koda suka isa gidan Baban Jameelaa na qofar gida a zaune a tabarma, ciwon dik ya kwakkwab'o abin tausayi, da alama yana jin jiki, Bukar na gaban shi ya dawo daga makaranta dan kula da shi, dan tinda Jameelaa ta sashi a makaranta, dan ta kare yawa kar a zagi qanin ta da ita kan ta shi kuma ya ji daɗin makarantar sai ya riqe ta da hannu bibbiyu,Bukar ne ya ce, "Sannu Baba Allah ya baka lafiya Ramai na nan zuwa da Jameelaah taje ta fada mata," Murmushin takaici Baban su Jameelah ya yi sannan ya ce, "In ba rashin hankali ba irin na Ramai ina wannan halin zata tafi fad'awa Jameelah da kan ta ba zata aika ka ba,ta kuwa san yanda zafin abunnan yake? Ji nake kamar ana yankan nama na, zuwa asibiti ba shine yafi mahimmanci ba? Amma saboda bani da kud'in zuwa shi yasa ba zata kai ni ba bayan ta na da kuɗi ta kuma san na san ta na da kud'in,Kaii Allah ka shirya min iyali na," Motar su Umar ce ta parker, Jameelaah ta bude ta fita da sauri, ganin qafar Baban nata ya sa ta saki kuka mai qarfi ta je wajen shi da gudu ta tsugguna tare da fad'in, "Sannu Babana Allah ya baka lafiya, Bukar Yah Umar ku kama shi mu wuce asibiti yanzun nan dan Allah," Bayan Umar ya gaishe shi ya yi masa sannu ne shi da Bukar sai suka saka shi a mota, sai sannu umar yake yi masa shi kuma Baban Jameelah yana amsawa, cike da jin nauyin surukin nashi,dan a ganin shi bai dace ya shiga motar Umar ba, babban takaici da mamakin sa bai wuce na yanda Ramai ke qunshe da kuɗi a qugun ta ba amma ta kasa kai shi asibiti har sai ta kirawo taimako,ina soyayyar da take yi masa a matsayin ta na matar shi? Ina tausayi irin na miji da mata da kuma na musulunci? A hanyar su ta zuwa asibitin kowa ya yi shiru ba ka jin komai sai tashin kukan Jameelaah, Baban ta ne ya kula da Umar kukan Jameelaah na damun shi, Murmushi yayi dan kuwa ya san yanda Umar ke tsananin son Jameelaah baya son ganin damuwar ta, dan haka sai ya ce mata, " 'Yar baba ke da bakya kuka ai be kamata ki yi kuka mijin ki na gani ba sai ya tsokane ki bayan na warke, ko ki na so ya dinga tsokanar ki da me kukan banza ne? Rabon ki ma da kuka fa ni har na manta, me zai saki kuka kamar wanda na rasa qafa gaba ɗaya? Dan Allah kwantar da hankalin ki, ki yi min addu'a kawai kin ji?" D'aga kai tayi, Umar kuwa cikin sauri ya ce, "Dan Allah ki daina kukan nan haka, zaki iya samun ciwon kai, kina jin dai Baba yace he is fine,so please stop crying kin ji?" Sai jan majina take yi Bukar kuwa na ta qoqarin taya baba riqe qafar kar ya fama ta. Ramai kuwa sam bata so aka barta a gida ba, taso aje da ita ta ci gaba da cusa qoqon barar ta na  a sai masu gida ko a kama masu wani su ci gaba da hayar, dan kuwa ta matsu su rabu da wannan gidan da ya zame masu kamar na gado. Tin da aka shiga da Baban wani daki likita da nurses suka hau duba shi, Jameelaa ta lafe a jikin Umar sai matse hawaye take yi, ganin jini da azabar da Baban ta ke sha ya sa ta jin ba daɗi a ran ta sosai, Mum ce tayo wa Umar waya dan tana son ta ji ya taji su shiru basu je ba kamar yanda suka ce,Jameelah ce ta karb'i wayar ta d'aga ta sanya kuka, Umar ne ya amshe wayar shi ya kanga a kunnen shi ya yi sallama, cikin damuwa mum ke tambayar shi ko lafiya ta ji Jameelah na kuka? "Mahaifin ta ne ya samu hatsari a qafar shi da ruwan batirin babur, shine muka kawo shi asibiti, dan ya fama ciwon wajen ya samu rauni sama da na da, gamu a asibitin ku ma yanzu haka," "Subhanallahi, Allah ya sawaqa inshaa Allahu zamu zo duba shi in aka kai amarya, dan ka san yanz ba a kaiwa da dare zuwa 4 zasu iso su d'au amarya daga nan zamu zo da Daddyn ku inshaa Allahu a gaida mai jikin" Jameelaah dake manne da Umar tana jin maganar kai Amarya ta kid'ime ta raba hankalin ta gida biyu, ga mahaifin ta a asibiti sannan ga kai amarya, wanne zata ɗauka yanzu? ************************ Mamalo ce jingine da Sadeeq sanda ya gama buɗe masu qofa suka shiga gidan nasu sai sannu yake jera mata, a qasan ledar d'akin su ta zube, shima binta yayi ya kwanta a kusa da ita ya dora ta a jikin shi, hannun shi a cikin zanin ta saman marar ta, sai shafawa yake yana murmushi, "Sannu maman biyu, Allah ya qara lafiya, ya sauke ki lafiya kin ji Fateena?" Cike da shagwab'a ta ke murje murje a jikin shi, shi kuwa daɗin hakan yake ji, cikin sassauqar murya irin ta marasa lafiya Mamalo ta ce, "Ni dai gaskiya ka bar tsokana ta bana so ba wani ciki da nake da shi ni, likitocin nan shegiyar qarya gare su, Jameelaaah nan haka rannan tace min wai ina abu kamar me ciki, ko kuma dai itama har ta zama likitan da gaske kamar yanda tace min, dama haka ake yi daga fara boko sai mutum ya zama likita?" Dariya Sadeeq yayi sosai, sannan ya juya da ita suna fuskantar junan su ya ce, "Likita bincikawa yayi ya tabbatar da samuwar cikin naki Jameelaa kuwa kinga tana da ciki itama, in taga wadda sukai anko kuwa kin ga ai dole ta gane ba wai dan ita ɗin ta zama likita bane, zama likita ba abu bane mai sauqi ba dan ina nufin ba zata iya zama likitan ba ko da anan gaba ne kin fahimta?" Kad'a kai tayi,sannan ta saka kan ta a qirjin shi ta ce, "Ni kunya ma nake ji, yanzu su Lantai sai kawai su ji ina da ciki?" "Ke ce ai baki sani ba, wancan maganin da ta aiko kina sha tace na shawara ne, ai maganin masu ciki ne yana qara lfy," "Wayyoo Allah na na shiga uku na, da gaske kake yi Masoyi? Kenan likitan yayi gaskiya daya ce cikina wata uku yanzu? Tinda dai tin kwanaki da nai rashin lafiyar nan da tazo ta ganni take kawon maganin nan ina sha," Sadeeq dariya ya dinga yi saboda shi a duniya yarintar Mamalon nashi na tafiya da shi, haka ya dinga kwasar ta yana shan dariyar wautar ta. ********************** Gidan dake manne da na su Ishaaq ya sha gyara iri daya ne sak dana Ishaaq, nan Haroon zai zauna da Umaimah, Ishaaq bai taɓa nuna ma Haroon cikin gidan ba, dan kuwa Haroon bai ma san mallakin su bane, tin da suka dawo Unguwar yau shekara sama da goma bai taɓa ganin wani ya shiga gidan ba, shi kuwa Ishaaq bai taɓa gangancin barin Haroon ya gan shi ya shiga gidan ba,dan baya son mallaka ma matashi mara aure gida ba tare da iyali ba, tinda aka fara auren su Haroon ke son a nuna masa inda zai zauna da iyalin shi amma yana jin nauyin ya tambayi yayan nashi, daya tambayi Hauwaa sai tace itama bata sani ba tana dariya kawai, sai tace masa ya jira yayan shi zai nun masa in lokaci yayi. Sai gyara gidan ake yi ana sabunta abubuwa Haroon ya zaci maqocin nasu yana son dawowa ne shi yasa ake gyare-gyare,dake ana hidimar bikin shi ma sai bai wani damu da sanin abinda masu gidan ke ciki ba, hankalin shi na kan bikin shi,ya tabbata dai tunda yayan nashi ya ce ya na da gidan da zai zauna da matar shi kar ya damu to fa akwai ɗin yayan sa bai taba bashi kunya ba, ya tsaya masa a kan abubuwa da dama na rayuwar shi. Abokan shi na makaranta da Islamiyya sun hallara anyi walima, suma su umaimah ana can ana walima kafin a gama mata suje d'akko masa amaryar shi. Wayar shi ce ta fara ruri, dubawa yayi yaga sunan yayan shi. "Yayan ango kayi wuyar gani," "Gaskiya kam, ai dole tinda qanina yace shima auren nan yake so,  ka shigo gidan nan na maqotan mu ina ciki," Buɗe baki Haroon yayi ya na tunanin lallai yayan shi akwai cusa kai ba kwarjini, daga fara gyara gida har ya yi abota da masu gida har ya shige? "Hello kana jina kuwa," "Ehhh... ehh ina jin ka, me kake yi a gidan mutane?" "In ka shigo zaka gani," Murmushi Ishaq yayi kawai dan kuwa ya san zai sha mamakin ganin gidan, ta ciki komai iri ɗaya ne dana shi ta fannin tsarin gini, kuma shi ya zuba kayan d'aki da komai, dan islam bai ce dole dangin  amarya ne za suyi kayan d'aki ba,dan haka duk yanda iyayen Umaimah suka so su yi kayan d'aki sai Yah Ishaq ya hana, ya nemi alfarma wajen Dad akan a barshi ya yi komai saboda qanin nashi shi kaɗai yake da shi Allah ya hore masa dukiya dan haka hakan da zai yi ya san zai faranta ran ɗan uwan nashi, da kyar dai ya samu Dad ya amince ya yi komai. Gate d'in Haroon ya ja ya bude ya shiga da kyar dan shi wannan irin gate mai jan wahalar buɗe wa yake bashi, gate ɗin gidan Yah Ishaq mai qofa biyu ne, baki ya bude dan mamaki a lokacin da ya yi arba da asalin cikin gidan,ganin gidan ya yi sak irin na Yah Ishaq a hankali yake shiga gidan, karatun qur'ani ke tashi a ciki,Ishaaq na bakin qofar shiga cikin gidan yana ma Haroon dariya, cikin buɗe hannayen shi dika da farin ciki ya ce wa Haroon, "Supriseeee"  Keys ɗin gidan ya kad'a ma Haroon da ya isa baki sake ya na kallon ikon Allah,cikin dariya Ishaq ya ce masa, "Riqe nan ango ga gidan Amarya nan, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka," "Dama kai ne ka kunna karatu jiya da dare nake zaton ko masu gidan ne suka dawo?" Dariya Ishaaq yayi ya damqa masa keys ya fice ya bar shi cikin ta'ajibi, ba inda haroon bai leqa ba a gidan tsabar daɗi da murna bai san hawaye na bin kuncin shi ba sai da yaji gishirin su a bakin shi, zama yayi a kujera riqe da remote yana kallon makka tare da sauraran qur'anin dake fita daga bakin Shaik alfasee, kuka sosai ya saki, Yayan shi ya zama uwa ya zama uba a gare shi, ba shi da wanda ya fishi a rayuwar shi, Allah bai ɗauke iyayen su ba sai da ya masa arziqin ɗan uwa mai riqo da zumunci fiye da abin duniya. "Ya Allah ka farantawa ɗan uwana, ka qara masa arziqi mara yankewa, ya Allah ka bashi zuri'a mumina saliha," "Ameen 'yar budurwa me kuka, shin ko kaine amaryar ne banda labari? Sai ka tashi dan kuwa ga shi can an tafi d'akko amarya, na leqo na ga ko akwai abinda za a sake gyarawa kawai na gan ka zaune ka na kuka," In ji cewar Hauwaa da ta shiga a daidai wannan lokacin da Haroon ke kuka da addu'a, kallon ta ya yi ya na share hawayen shi ya ce, "Yanzu dama har da ke aka yi min rufa-rufa dama wannan gidan namu ne? kullum nake cewa maqotan nan namu ba zasu shiga gidan ba sai aljanu sun gama samun muhalli, rana tsaka a d'aga su azo ana fama da matsalolin jinnu ashe namu ne," "Naka ne dai, kai ne mallakin gidan ai,tin kafin muyi aure ya siye filin dika biyun, sai da ya tabbata ya gama gin muka baro na haya muka dawo wancan aka kulle wannan yanzu da lokacin shiga yayi ba gashi za a shiga ba? Komai lokaci ne dashi ai dama a rayuwar nan, yanzu ka tashi na san ba wani jimawa za ai ba amarya zata iso, qannena biyu Safna da Safiyya ma sun zo za aje dasu d'akko ta," "Masha Allah na tafi nima na shirya dan tarbar amarya ta," "Ina zaka je? Kayan ka na can d'akin ai, ko baka kula zubin ginin mu ɗaya bane, Yayan ka ya tattaro maka komai ɗazu ai," "A gaishe da yaya wato ya ma sallame ni, ni ban taɓa ganin ango irina ba ana ta hidimta min ba tare da na sani ba," Hauwaa duba ko ina tai taga tsaf yake ba abinda zata gyara, dan haka ta fita tana ta godewa Allah, in zuciyar bawa babu tunanin sabawa Allah a cikin ta sai bawa ya ji ta wasai,sai ka ji ka baka da abin boyewa daga duniya har lahira, sai kaji ka kamar wani leda dan rashin nauyi. ********************** A can asibiti kuwa tinda Jameelaa taga an fiddo Baban ta qafa ta sha gyaran likita bokan turai, Baban ta ma bacci yake yi ta saka borin sai an kai ta gidan Mum an kai amarya da ita, dan kuwa ba zata bari a karbi kudin siyen baki ba ita ba. Dik yanda Umar ya so nuna mata ba komai ba sai taje ba qi tayi, daga qarshe yace ma Bukar ya zauna zai kaita ya je gida ya d'akko Ramai, sai su dawo tare, shi ya kula da Baban yanzu kan su dawo.......... *Wacce addu'a zaku ma Jamee, akan kudin siyan bakin nan data sawa ido kamar bakin ta za a siya...kar ku manta fa bata je bikin ba amma zata je dan kud'in siyan baki?* 😂😂😂😂😂😂😂😂 [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 25: Ko da ta koma gidan ta direct parlour ta shiga ta zauna a kan kujerar da ke kallon duk mai shiga da fita, tagumi ta zabga ta na ta tunanin yanda zata tara kuɗi Itama ayi suna mai qayatarwa idan ta haihu, har Sadeeq ya shiga gidan bata sani ba, a gaban ta ya tsugunna tare da qare mata kallo cikin yanayin damuwa ya ga fuskar ta,to meye ke damun Fateen nashi ne ko dai watace ta b'ata mata rai? Cikin yanayi na kulawa ya ce, "My Teemaa meke damun kine har na shigo baki kula da dawowa ta ba?" A dan tsorace ta kalle shi sannan ta yi ajiyar zuciya, tura baki tayi gaba ta maida kan ta dayan bangaren bata kula shi ba,cikin damuwa kuwa Sadeeq ya ce, "Subhanallahi me aka yi maki ne fateena? Ni dai in dai ni na b'ata maki rai ki yafe ni sannan ki sanar dani laifi na saboda na kiyaye gaba, ko kuma Baban Jameelaan ne wani abu ya same shi?" "Ina fa ! Ba abinda ya same shi kuma ni ba wanda ya b'ata min rai kawai so nake tinda sallah ta gabato mutane na ga sun fara kawo ɗinkunan su, wannan ɗinkin da za ka yi na shekarar nan ka dage ka tara kuɗi sosai, sannan albashin ka na makarantar boko in an baka muna rage wani abu mai yawa a ciki, a samu babban asusu ko ka kai banki ka ajiye, kaii ni koma ya za ai kawai ka tara kuɗi mai yawa kafn na haihu, dan kuwa ina son inna haihu ayi suna mai ban mamaki, sunan da tinda ake aurar da yaran layin mu su haihu ba a taba irin shi ba," Baki sake yake kallon ta sanda take masa wannan bayanin me kama da wadda aljanu suka taɓa ko suka bawa shawara,tashi yayi daga durquson daya yi kamar wani me neman gafara, cikin qanqance ido ya ce wa Mamalo, "Ke da wa kuka tattauna kuka yi wannan shawarar?" Yanda ya yi magana cikin d'aure fuska itama haka ta mayar masa da amsa cikin daure tata fuskar ta ce, "Ni ban yi shawara da kowa ba, wato ka maida ni mara wayon da sai nayi shawara da wani sannan zan faɗi abinda nake so a yi min da suna na?" "Hummmmm Allah to ya hore mana abinda zamu yi sunan idan kin haihu lafiya," "Ameen Allah ai yana taimkon wanda ya taimaki kan shi ne" Ta fada a sanda ta ke tashi dan shigewa d'akin su, a gaskiya ta gaji da zama Jameelaah na fin ta a komai na rayuwa, bayan layin su ɗaya kuma gidan su ɗaya, wannn karon ko bashi zataci sai taci itama an buga suna na ban mamaki. Sadeeq yana zaune yana mamakin sauyawar Mamalo cikin qanqanin lokaci, qarshe mamakin sa ya kau da ya tuna cewa da dikkan alama Jameeelaa ta zigo masa ita ne dan ba haka matar shi take ba, ba tun yau ba  ya kula da yanda Jameelaah ke taka mahimmiyar rawar dake gurɓata tunanin Mamalon shi, dan dik abinda Mamalo tayi mara kyau in aka bincika sai an gano da sa hannun Jameelaah a ciki,in ko haka ne zuwan ta wajen Jameelaah ya zo qarshe,dan ba zai dinga gini ana rusa masa ba, dama ba wata cikakkiyar tarbiyya gare ta ba lallab'a wa yake yi ta dalilin soyayyar da take masa ne yasa take jin maganar sa, sai yake amfani da hakan yake bata tarbiyya mai kyau da inganci musamman yanzu da take ɗauke da gudan jinin shi,dan haka dole ya sa ido kar yazo yana tufka wata na warware wa. Kitchen ya shiga ya dau abincin shi, dan ko arziqin a kai masa ma yau bai samu ba. *********************** Yau aka sallami Malam Jameel mahaifin Jameelaa daga asbiti yaji sauqi sosai qafa tawarke sai abinda ba arasa ba, tin da safen dama Umar ya ɗauki Bukar suka fita basu dawo ba sai yamma,lokacin da aka sallame su ɗin kenan,bakin Bukar yaqi rufuwa da alama akwai abinda yake son faɗa amma ya kasa,Ramai da Jameelaah ko sun yi tambayar duniya ya qi magana har sun gaji sun kyale shi, Umar kuwa sai kallon shi yake yi yana kad'a masa kai, da dikkan alamu akwai wata a qasa amma za su barsu idan ta yi wari sun ji. Sun gama kwashe komai nasu da suka yi kwanciyar asibitin da shi suka yi sallama da maqotan su da ke asibitin Ramai na gaba ita da Jameelah suna hira Umar da Malam Jameel na baya Bukar kuwa har ya isa gaban mota ya ajiye kayan su kawai yake jira su tafi, bayan sun shiga Umar ya tada mota suka kama tafiya,sai Malam Jameel yaga ba hanyar gidan su aka ɗauka ba,sai kallon wajen yake yi yana son ya tambaya, amma yasan surukin nashi bazai yi wani abu dan cutar da su ba da alama wani wajen za su biya kafin ya kai su gida, dan haka ya ja bakin shi yayi shiru,Hajiya Ramai kuwa ta gaza hakuri dan kuwa gaba ɗaya bata gane hanyar da aka dosa ba sam dan haka sai ta ce, "Ni fa ban gane nan hanyar ba, ohhh ni Ramatu Kano kenan tinjimin bajimin gari, Kano ta dabo timbin giwa jalla babbar husa, wato wani wajen dik girman ka a Kano har ka mace baza ka san da shi ba, nan kuma inane muke tafiya?" Bukar ne ya kalli Ramai dake ta zuba ya kwashe da dariya sannan ya ce mata, "Gidan Yanka kan mutane zamu je Ramai," "A kul nakuma ji dan Uban ka, dika-dika shekara ta arba'in da 'yan kai, ban shirya ma mutuwa ba sai na mori alatun duniyar nan nima" Cike da jin kunyar kalaman ta Malam Jameel ya yi tsaki ya kauda kai,Jameelah ce ta ce, "Balle kuma ni dana fara jin daɗin rayuwa ta ba, wataqila dai akwai inda zai kai mu," "To gamu mun iso sai kowa ya fito," "Mun iso ina?" "Gidan ku da zaku dawo da zama, in yaso Mama gobe sai kuje ku deb'o kayan ku da kuke da buqata a can tsohon gidan, za akawo mota ta kai ku ku kwaso, wanda baku so zaku iya kyautarwa, dan kuwa daidai gwargwado an saka abubuwan buqatar ku anan ɗin, nan gidan mallakin mahaifi na ne wanda ya mallaka min shi a jiya dana roqe shi, dik da ba wani girma ne da shi ba ina fatan zai ishe ku, nan daki biyu ne da parlour sai kitchen da madafin gargajiya,  dan Allah da son Annabi ba dan ni ba domin Allah Baba kar kace komai, kawai kamin addu'a ka sanya min albrka, shikenan ka biya ni kai uba ne a waje na baka buqatar yi min godiya sai dai addu'a da sanya albarka," Malam Jameel hawayen farin ciki ne ya ɓalle masa, Ramai kuwa zubewa tayi a qasan wajen ta hau zabga godiya, Umar har kunya yaji ta kama shi dan kuwa abun nata yayi yawa. "Ku shiga ciki ina zuwa," Kafin ya gama rufe baki ta kai hannu ta amshe keys ɗin gidan a hannun Umar ɗin, Baban su Jameelaaah kuwa gaba ɗaya kunyar duniya ta gama baibaye shi akan abinda Ramai ke ta yi kamar dama tana jiran hakan ta same su. Budewa sukai suka shiga wata uwar gud'a suka ji an rafka, Malam Jameel na ji ya san daga ina ta fito, kad'a kai yayi ya kalli Umar ya ce, "Ummaru Allah ya saka maku da mafificin alkhairi kai da iyayen ka, gaskiya ba dan roqon da kayi min ba da ba zan amshi kyautar nan mai girma ba,akwai kunyar ka mai yawa a ido na na san halayen d'iyata da naka sun sha bam-bam ta ko ina, amma a haka ka hakura kake zaune da ita cikin so da qauna,Ummaru ba abinda zan ce maka sai dai nace Allah ya yi maka albarka,ya haɗa ka da alkhairi a rayuwar ka a dik inda yake, ya nesanta ka da sharri a dik inda yake, muna godiya kwarai da gaske, kuma ka sanar dani sanda ake samun mahaifin ka agari sai naje na miqa godiya ta, kyauta irin wannan ta wuci saqo" "Baba ni ne da godiya ni da aka yi ma kyautar mutum, dik soyayya irin ta iyaye da yaran su kuka hakura kuka auramin Jameelaa ai komai nai ban biya ba,kuma bana jin zan iya biya ba," Wani irin nauyi kafadun Baban Jameelaa suka yi sai yaji matsananciyar kunyar Umar ta kama shi, sun aura masa yarinya wadda ba kintsattsiya ba amma shi godiya ma yake musu, share k'wallar data gangaro masayayi yace, "To bismillah muje ciki," "Ai Baba da ka turo ta kawai mun wuce gida kaga magrib tayi,bai kamata muna yawo da magrib ba musamman dake tayi nauyin nan," Sosa kai yayi daya kula dame ya faɗa nan take ya juyar da kan shi yana murmushin jin kunya, Baban ma murmushi yayi sannan ya shige gidan dan kiran gimbiyar. Sai santin wajen suke yi tinda yau sune har da parlour nasu na kansu mai dauke da kujeru, ga carpet blue dark irin na gidan Jameelah kujerun kuma light blue, labulayen ma kalar dark blue kamar carpet ɗin sai qaramar TV ta bango dakin su Baban an saka gado da katifa da ledar daki, sai kitchen ɗin da aka saka risho da kananzir a cikk sai indomie k'wali ɗaya da kayan shayi, da sabbin tukwane a kwali shikenan, d'aki d'ayan kuma katifa ce babba sai leda, murna suka dinga yi kamar wanda aka ma albishir da gidan gwamna,ko da Baban Jameelah ya sanar da ita ta shirya mijin ta na waje yana jiran ta su wuce sai ta hau turje-turje ta na fad'in, "Haba Baba ka bari ayi isha'i mana," "Nace ki wuce yana jiran ki ko? Me zaki yi mana in kin zauna ɗin?" Cike da zumburar baki ta shuri takalman ta tafice, Ramai na ta sa mata albrka. A mota ta same shi zaune itama sai ta buɗe ta zauna bakin nan an cuno shi gaba kamar cokali, ganin haka sai yaji kamar yace ta koma anjima ya dawo ɗaukan ta,amma inaa bazai iya ba. Tada motar yayi yana tinanin yanda yau zai lallab'a ta ko ya sha jaraba. Ko da suka isa gida ma haka tai ta turo baki, kuɗi ya zaro dubu uku ya miqa mata ya ce, "Ga sauran canjin katifa a sa a susu," Washe baki tayi nan tafara yi masa shagwab'a,shi kuma ya yi ta bata hakuri kamar ya yi mata laifi, duk abin alkhairin da ya yi mata da iyayen ta bata san ta buɗe baki ta yi godiya ba qarshe ma sai da ya bata cin hancin dubu uku ta baje baki ta na yi masa bayanin kud'ad'en da take tara wa,in ta saka wannan dubu ukun da ya bata tana lissafi ta sa ya kusan dubu talatin da wani abu kenan, Umar yayi mamakin yanda aka yi  kud'in ya kai haka amma sai ya basar, sam bai taɓa kula da ɗauke-d'auken da take yi masa ba,tsabar iya taku wajen sibaren na bayye, in ta ɗauka baya taɓa gane ta zara. *********************** Jameelaa fa yau kwanan ta biyu tana naquda a tsaitsaye dik ta fige tayi zuru zuru tsabar wahala, sai zuwa duba ta ake yi kamar wadda ta riga ta haihun, kowa hankalin shi ya tashi da yanayin da take ciki cikin ya yi girma da yawa gashi haihuwar fari, umar ya kasa ya tsare da shi ake yin komai watarana idan yaga ta na shan wahala zama yake yi ya yi ta kuka kamar ba likita ba,a rana ta uku ne midwife ɗin da Mum ta roqa a asibitin su tazo duba Jameelah anan ne ta yi masu albishir ɗin ta kusan haihuwa inshaa Allahu, ai kuwa nan ta sa Umar dole ya fita, dik da yaso ayi komai da shi tinda shi likitan mata ne, raunin sa akan Jameelan ne ya sanya Mum saka baki a lamarin dan haka ganin Mum na wajen ya sa yaji nauyi ya fita ɗin kamar yanda aka buqata, Mum ma a parlour ta zauna duk da cewa itama cikakkiyar Nurse ce amma ta kasa shiga, ta gan su sau ɗaya a halin da bai kamata ta gan su ba dan haka ba zata sake maimaita wannan gangancin ba ,Ramai kuwa tunda ta zo gidan take ta doka tagumi daga wannan bangaren zuwa wancan , ta kasa ta tsare tace ba mai kai mata yarinya asibiti, ta sha gani a layin su in an kai mace asibiti suna dawowa da qorafe-qorafen midwifes, musamman akan farke ma mata gaban su da suke ba tausayi dan su huta da jiran mai haihuwa, ba zata yarda Jameelaa ta rasa jarin ta ba ah atoh, ranar Mum taga jahilci tsabar shi a waje Ramai, dan kuwa dik bayanin da ake wa Ramai baya shiga kunnen ta, har mamaki ta dinga yi a ranta ta na ayyana ashe dama jahila ce mahaifiyar Jameelaa ,tinda har wa'azi ta yi mata akan maganganun da ta dinga furtawa dik akan haihuwar amma ko ratsa ta basu yi ba. Suna nan zaune suka ji ihun Jameelaa tare da kukan Baby mai qarfi ya daki kunnuwan su a lokaci ɗaya ,nan take Umar ya zube dan yin sujjadar godiya ga Allah. Yana dagowa kuwa ya afka dakin, Jameelaa na kwance... *My FiFul barka-barka Jamcy kala ta haihu* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 24: Zuwan su ke da wuya Jameelaah taga motocin kai amarya na qoqarin tafiya kuma idan ta fita ba zata samu shiga ba dan babu mai jiran ta tinda basu san da ita ba, kwab'e fuska tayi zata yi kuka, Umar kuwa na ganin motocin sun tafi ya kalli Jameelah ya ga zata yi masa kuka sai ya juya motar shi suka bi bayan motocin kai amarya, ai kuwa cike da murna ta zabaro masa wuya ta manna masa kiss a kuncin shi, murmushi yayi dan ganin ya burge ta. "My love akwai ki da rigima,sai ki dinga abu kamar wata yarinyar goye," "Ni ce me rigima kooo?" Ta faɗi hakan cike da shagwab'a,a wajen Umar hakan ma wani abun burge wa ne daga wajen Jameelar shi, sai ya ga ta qara yi mishi kyau, kad'a kai yayi ya d'age hannayen shi daga kan motar tare da zaro ido waje ya ce, "Nii na isa nace dake nake?" Dariya suka yi atare suna ta hirar su gwanin sha'awa ,Umar kuwa ya qi barin ko wacce mota ta shiga tsakanin motar su da ta ɗaukan amarya, a ran shi kuwa yana ta ayyana, ' Yau dai ga yayan kwabo an samu a gari da shi za a kai qanwar shi d'akin miji.' Ko da suka isa qarfe shida na yamma yayi, cike da kid'a sauran motocin suka tsaya aka buɗe kowa ta fito,amma motar da amarya ke ciki ba a kunna kid'a ba dan kuwa tace bata so, albarkar aure take nema ba tab'ewar shi ba. Sai da aka fara shigar da ita wajen aunty Hauwaa aka gabatar da ita tare da yi masu nasiha akan zaman tare da hakuri da juna,a nan 'yan uwan Mum da Dad suka miqa ta amana wajen Aunty Hauwaa, Aunty Hauwaa kuwa wadda bakin ta yaqi rufuwa saboda murna sai maimaita fad'in, "Na Karb'a, na Karb'a da babban hannu,da hannu bibbiyu ya Allah ka taya ni riqewa da gaskiya da amana," take yi. "Ameen ya Allah," mutanen wajen suka amsa. Nan aka rankaya har aunty Hauwaan zuwa gidan Amarya,Amarya Umaimah kuwa na cikin mayafi tana kuka Jameelaah ta kutsa cikin mutane ta na so ta isa wajen ta ganin ta ɗauke da ciki ya sa mutane suka dinga bata waje, dan kuwa har wani sake turo shi gaba take yi,dangin Mum da basu san ta bane suka fara kallon isa da mallaka irin na Jameelaa. Wata daga qannen Daddy ce tace ai matar Umar ce wannan,nan wasu suka washe baki aka hau gaggaisawa, wasu kuma suka d'aure fuska, a ganin farko suka gano bata da mutunci, gaida su ta hau yi tare da qoqarin durqusawa amma suka hana ta, a cewar su sun yafe durquson, bata kusa da Umaimah suka yi aka qarasa shigewa da ita gidan na ta, Karatun qur'anin da aka saka ne tin kwana da kwanaki ke ta tashi, dan kuwa Haroon da Ishaaq sun ce gidan na buqatar karatun da wasu addu'o'in ma duba da cewar gidan yayi shekara da shemaru a rufe ba a san meke zaune a ciki ba. Jameelaah sai walqita ido take yi dan ganin ta inda zata ga abokan ango sun bayyana tana ta washe baki,Umaimah ce ta ja ta kusa da ita sosai ta yi mata rad'a, "Ya jikin Baba? Mum tace bai ji daɗi ba? Ya naki jikin," "Da sauqi dika sai da na tabbatar likita ya kula da shi na taho,yanzu ke ba lokacin tambaya bane banga angwayen ba fa Ina suke ne?" "Ni ina zan sani? Ki daina yi min maganar angwaye gabana faɗuwa yake yi," Dariyar yaqe tayi kawai ta ci gaba da zaro idanuwa waje,cikin ran ta ta ce, 'Akan me zan daina zancen angwaye in basu wa zai bamu kud'in siyan baki gashi na ji an ce masu kuɗi ne? Kenan zuwa na ya tashi a banza?' Qawayen su na islamiyya ne suka iso, suna ta yafito Jameelaah dan an ce kar ai hayaniya tinda an saka karatun qur'ani,sai dai an rage volume sosai, ta na ganin su ta ɗauke kai ta qi zuwa,kallon marasa hankali ma take yi musu dan kuwa a ganin ta ta kere musu nesa ba kusa ba amma suke abu kamar makafi,ganin ta qi kula su ne ya sanya suma suka ɗauke kai suka share ta. Zama suka yi suka yi da'ira a tsakiyar parlourn, nan da nan suka fara karanta qur'ani daga bakunan su cikin suratul Rahman, basu tsaya ba sai da suka yi shafi biyu, sannan qanwar Hauwaa mai suna Safnah ta fara yin addu'u'o'i masu matuqar ratsa zuqata saboda da hausa take yin su, tana nema wa ango da amarya zaman lafiya da kwanciyar hankali, da zuri'a d'ayyiba,sannan Safiyya ta amshe itama ta fara zubo kalar nata addu'o'in kusan kowa dai a wajen sai da ya yi masu addu'a sai abun ya basu sha'awa su kan su,Jameelaa ta kula sun maida gidan kai amaryar islamiyya, ana zuwa kan ta tace, "Allah ya bada zaman lafiya ya kawo qazantar daki," Ta ja baki ta gume shi gum dan ita bata ga amfanin waɗannan abubuwan ba gidan kai amarya an maida shi kamar wata islamiyya meye hakan?ai kyawun ta a baza masu kid'a irin na soyayyar nan me ratsa zuciya amma sun wani tsaya karatu kamar qauyawa ta na can ta na zancen zuci bata ma san kowa a wajen ya bi ta da kallo ba, saboda a qalla kowa yayi addu'ar da tafi haka balle ita babbar qawar amarya, kiraye-kirayen sallar magrib aka fara yi, nan 'yan uwa da qawayen Umaimah su kai ta yi mata Allah ya sanya alkhairi suka hau fita dan tafiya gida ,sai d'akin ya zama daga Jameelaa sai Safnah da Safiyya da kuma amaryar, Umaimah ta ɗan saba da su dan tin da aka fara bikin sun haɗu ya fi sau biyu dan haka da ta ga zasu fita sai tace da su, "Dan Allah kar ku barni ni ɗaya mana," Cannn dai Safiyya tace bari muje muyi sallah zamu dawo in mijin ki bai shigo ba kenan, dariya suke tayi qasa-qasa dan sun shirya guduwa ne dama. Safiyya ce ta fara fita sai da Safna zata fita ta gane wayo suke son yi mata, da gudu Safnah ta amshe mayafin ta ta fita tana dariya, riga da skirt ne jikin ta sun amshi jikin ta sosai saboda safna akwai ta da diri mai kyau, ɗan acuci mazan ta da ta yi da gashin ta mai uban yawa ba tsaho ya qarawa d'aurin d'ankwalin ta kyau, tafe take tana ɗan gudu tana dariya suka ci karo da Umar dake jingine a bakin motar shi ya b'ata rai ganin yanda 'Yan matan wajen ke ta kallon shi suna qusqus, yana nan kafe kamar an kafa shi yana jiran hajiyar tashi ta fito su tafi,dan kuwa tunda ta shiga yake zaman jiran ta sallah kawai yayi ya dawo ,a tsayen yake ta azkar din shi. Bata kula da tsaiwar shi a wajen ba sai ji tayi ta bangaje mutum, da sauri ta juya dan bashi hakuri, sai taga yana yi mata kama da Umaimah sosai, sai ta rage dariyar da take yi tace, "Dan Allah kai Yayan umaimah ne?" Cikin d'aure fuska Umar ya ce mata, "Eh ni yayan ta ne meye?" Sai kawai ta ja mayafin ta da ya zame tin a gidan Umaimah ta qarasa yafe jikin ta da shi sannan tace, "Ga qanwar ka can tana yi ma mutane kuka dan an kawo ta gidan miji bayan ita tace tana so,ka shiga ka bata hakuri ko taa sako maka matar ka, dan kuwa tana can ta qanqame ta ta hana ta fita," Kawai sai ya fara dariya ya san halin Umaimah sarai da shagwab'a, girgiza kai kawai yayi ya na dariyar shima can qasan ran shi kuwa tausayin qanwar tashi ne fal ran shi a hankali ya ce, "Yanzu in banda abinki baiwar Allah ina ni ina shiga gidan surukai? Zata fito ne na san Jameelaah da ta gaza hakuri zata mata wayo ta gudo," "Ashe ma baka san Umaimah ba har yanzu, a iya ganin da na mata na gano wayo ne da ita itama,ko yanzu da kyar na kwaci kai na plan muka haɗa na guduwa amma Safiyya na fita ta gano mu ta damqe ni da kyar na kwace na gudo," Daga haka fa Safnah da Umar sukai ta hira, daga baya tace ta shiga ciki bata yi sallah ba sai watarana. A cikin hirar su ne ya ji cewar ita ɗin qanwar matar wan mijin Umaimah ce sun zo bikin ne suma, amma tana makaranta a Zari'a tana karantar mass com. Umar yana tsaye yana ta murmushin hirar su da Safnah Jameelaa ta fito, lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar isha'i ranta a mugun b'ace ta taddashi,ba ango ba abokan ango ba alamar ma za ta ga ango a wannan lokacin,sam ba haka suke biki ba su a cikin gari,ta yaya za a kawo maka amarya tin biyar na yamma har takwas na dare amma baka zo ba to sai yaushe za ka zo? (An yi karatun qur'ani ta ce su qauyawa ne amma an zo bangaren kuɗi ta ce su ba haka suke yi ba a cikin gari,komai dama akwai lokaci na musamman da aka qirqire shi) Ga wata muguwar yunwa da take ji har ta na jin kamar za ta yi amai saboda rabon ta da abincin kirki tin safe, sai uban ruwa da tai ta d'irka da Lacasera. "Muje gida" Ta ce masa ta na hura hanci ta na b'ata rai kamar zata kai masa duka, umar kuwa da sauri ya kalle ta ya ce, "Gida ko asibiti?" "Ni ka kai ni dik inda zan samu abinci yunwa nake ji marowatan banza kawai ku tara mutane amma ko wannan shegiya shinkafa babu balle mutum ya saka ran samun nama ko wani abu makamancin hakan," Ta qarasa maganar cikin datse haqorin ta dan haka baiji me ta ce ba, kawai dai ya ga tana b'ata rai ta zauna a kujerar me zaman banza (as she is) ta na qunquni. Gidan Mum ya ɗauki hanya zai kai ta ya san a can za ta ci abinci kuma ko Allah ya sanya alkhairi ta yi musu duba da cewar tinda aka fara bikin bata je ba, bata yi masa musa ba amma ta d'aure fuskar nan kamar hadari, suna isa suka tarar da gate a bude yake, sa kan motar yayi ciki ya parker suka shiga riqe yake da jakar ta da abun ruwan ta dan kuwa ta yi gaba a yunwace take, suna shiga kowa ya bisu da kallo, cikin sauri ta zauna yaraf tana maida numfashi, ganin kallon da ake yi mata ne ya sa ta wayance ta ce, "Yau na ga shagwab'ar Autan Mum, Mum Kinga yanda Umaimah ta dinga kuka kuwa tana qanqame ni dik jikina ciwo yake yi sosai, ga yunwa da nake ji, da kyar na k'waci kaina na taho," Dariya sosai wasu suka hau yi ana maida zance kowa na fad'in abinda ya gani da abinda ya faru, wata daga cikin qannen Mum ce tace, "Ai gwanda kukan ta akan naki fa Jameelahh ke da ki kai ta kuka kamar zaki shid'e sanda za a kawo ki?" Rufe fuska ta yi alamar wai kunya take ji, Mum ce ta shigar mata tace, "Kinga rabu da su taso muje ki ci abincin ki kin ji 'yar albarkan Mum," Da kyar ta bi bayan Mum ita a dole wai kunya take ji, kitchen suka je da Mum sai da ta zaɓi abinci tsabar gashi nan kala-kala anan kitchen ɗin aka zuba mata taci ta yi nak,sannan tace zata wuce asibiti daga nan ta ga Baban ta a kunyace tace, "Mum yah Umar fa shima yunwa yake ji bai ci abinci ba tun da safe da muka baro gida," Murmushi Mum tayi tace, "Ai muna parlour ana hirar nan ya shiga ya d'iba ya wuce d'aki, bari na zuba maki ki kai asibitin ki gaida mai jiki idan kun je gobe inshaa Allahu zan shigo, sai na duba shi," "Allah ya kaimu Mum, ai da kin bari naje gida na yi masu girki tinda naga kamar akwai baqi sosai kar na kwashe kuma yazo bai isa ba," Mum bata kula ta ba ta ci gaba da ɗebar mata abincin dan kuwa tana cike da fara'a da jin daɗin samun suruka mai kirki a ran ta,haka ta loda ma Jameelaa abinci,naman da ta zuba mata kuwa kala-kala, akwai na rago, na sa, dana kaza, sannan da miyar masa da aka yi da kayan ciki na rago, Jameelaa tunani take yi yanda zata rage abincin taje da shi gida, saboda ba sai tayi girki ba washegari,in ta sa a fridge sai ta dumama masu kawai su ci, (wannan zarmewa taki na ban mamaki Jameelaa, komai akai maki na gaba kike hangowa, Allah ya shirya ki). Mum kamar ta shiga ran ta sai ta d'ebi wani a leda ta saka mata tace, "Kar ki manta da wannan da kunje gida ki sa a fridge,kin ji ko? gobe da safe kin huta da girki," "Mum dik kin kwashe mana ai, mun gode to Allah ya qara girma, ba dan kin matsa ba ma ba zan Karb'a ba, amma tinda kin matsa bari na Karb'a abinda babba ya hango yaro ba zai hango ba," Mum shiru dai tayi amma ita yaushe ta matsa? Sai da Umar ya taya ta d'iban abincin suka fito za su tafi sai sallama take yi wa mutane, Mum ke ma matan wajen bayani mahaifin ta ne ba lafiya yana asibiti, nan suka fara yi mata ya mai jiki, dan da sun zaci iskanci ne ya sa tin da aka fara bikin bata halarta ba. A hanya sai tinani take yi shin ko bayan tafiyar su Haroon yaje da abokai an ba Umaimah kud'in siyan bakin ko yaya oho? Haka suka isa asibiti Baba ya farka ba ko na abinci suna nan zaune, Ramai da ta je dan kwana da shi tana sane taqi badawa a siyo, saboda so take surukin nata ya ga tsananin babun da suke ciki, Ai kuwa Umar daya ga haka sai yaga bai kyauta ba sam, shi yana cikin yalwa da iyalin shi wadda take 'yar su ce amma iyayen ta na cikin matsatsin rayuwa. Alqawarin sauya masu wannan rayuwar da ya gani da abinda Allah ya hore masa ya dauka a ran shi. *********************** Umaimah na ganin ba kowa kuma magrib da isha'i sun wuce ta bata yi ba, kawai sai ta tashi ta rufe d'akin da key ta shiga band'akin dake cikin d'akin ta yi alwala, band'akin ya haɗu sosai dan bata zaci ma zata samu kamar hakan ba,gashi komai tsaf a jere, ga kayan wanka da gani daga waje aka kawo su saboda haɗuwar su kawai ta isa ta sanar da mutum hakan,kayan wanke baki ta hango kala-kala masu kyau ai kuwa bata b'ata lokaci ba wajen wanke bakin ta tsaff sannan ta fita. Sallah ta yi tana addu'a taji ana murd'a qofar, ji tayi an fara qwanqwasawa a hankali, lullub'in ta ta gyara sosai sannan ta je dan bud'ewa, Haroon ne a tsaye ya ci babbar shadda an baza masa ɗinkin babbar riga sai qamshi ke tashi a jikin shi,sai ta gan shi ya sauya mata kamar ba shi ba kafe shi tayi da ido ta na qare masa kallo, shi ɗin ma ita yake kllo kafin daga baya cikin zolaya ya ce mata, "Shin amaryar nan kuwa zata bawa angon ta damar shiga ciki Ko sai ta gama kalle shi a bakin qofa?" Wayyooo kunyar ta ina za ta shiga ta buya? ji tayi kamar qasa ta bude ta shiga dan kunya,da sauri ta matsa ta koma kan sallaya ta zauna, ta duqunqune kan ta a mayafin ta ta na dariya qasa-qasa. Dariya yake yi mata dan ganin yanda take jin kunya bayan ta gama shagala da kallon shi bata ma san ta yi ba, a hankali ya furta "Sallah kika yi ne?" "Eh" "Ok nima bari na rage rigar nan sai muyi nafila kawai, ina da alwala," Ajiye ledar hannun shi yayi ya rage rigar jikin shi, sannan ya tsaya a gaba tana baya,a haka suka yi raka'a biyu bayan sun idar ya jagoranci yin addu'a, sannan ya yi mata addu'ar da ango ke yima amarya wadda tazo a sunnah,daga baya ya ce mata, "Ke d'aliba ta ce na san kin san farillan sallah da sunnoni da na alwala dana wanka, sai dai abu ɗaya, ban taba ganin kin gwada a gabana ba musamman shi wankan, dan haka yau zaki gwada a gabana na ga ko kin iya," Da sauri ta cire lullub'in da tai har fuskar ta ta kalle shi, taya za ta iya wankan janaba gaban namiji namijin ma da take jin kunya kamar shi? Cikin tura baki gaba ta ce, "Gaskiya ni sai dai na faɗa maka yanda ake yi, kuma in baka yarda na iya ba ka tuna mana ko rannan da ka koya mana a gida nafi Jameelaa iyawa har kyautar hisnul muslim ka bani," "Ni dai ban tabbatar ba dan kuwa da baki ki ka faɗa na ji a kunne na, yanzu tinda kin zama halal d'ina kawai sai ki gwada a gabana na gani," Idon ta ne ya ciko da k'walla tana jin qirjin ta na bugawa saboda shiga damuwa da ta yi a hankali kuma ta gano inda ya dosa da kalaman shi Murmushi yayi ya cire hular kan shi a qalla saqon shi ya isa ta fahimci me yake nufi, janyo ledar da ya zo da ita yayi gaban su ya buɗe gasasshiyar kazar da yaje har Markaz ya siyo musu, qamshin kazar kaɗai ya isa tsinka yawu,balle mutum yayi ido biyu da ita har ya kai baki, hummm (an tadan da tsohon kwadayi na na 1877) Sai da suka ci suka sha sannan suka kora da madara, dan kuwa Umaimah bata tsaya fulako ba irin na su oo, ci ta yi ta qoshi ta yi hamdala daga qarshe ta tashi ta kwashe sauran dan ta adana a fridge ya amsa ya ce, "Yau daren naki ne gimbiya ki huta ba sai kin yi wahala ba bari na taya ki," Sunkuyar da kan ta tayi ta shige toilet, ta wanke bakin ta sannan ta fita, kayan bacci ta ɗauka masu kyau ta saka sannan ta koma ta kwanta, ya dad'e kafin ya koma d'akin ,cikin shirin bacci ya shiga d'akin, ganin ta yayi ta kulle idon ta kamar mai bacci, siririyar dariya ya saki dan ya san idon ta biyu,sai ya kashe fitila a cikin duhun ya taka ya isa inda take. Kuma kenan kashe wutar zaku yi dan ku kore ni tinda ba gani nake ba a duhu, sai da haske nake gani.... Washegari ko da na kalli Umaimah kuka ne kawai ban yi mata ba, saboda kun dai san Ustaz kuma malamin islamiyya yayi karatu sosai, to fa Ustazu ya fassara mata karatun nan sala sala, kuma da alama ta fahimta da kyau, idanun ta sun kumbura sosai saboda kukan da ta sha. Haroon ma idon shi kamar wanda ya yi kukan,tea ne a cup mai zafi da kauri ya had'o mata ya tallabo Umaimah jikin shi yana bata, sai kuka take mai cike da shagwab'a tana zubo da hawaye, a hankali Haroon ya ce, "Dan Allah Mar'atussaliha ki yi hakuri ki sha, in ki ka sha za ki ji daɗin jikin ki, dan Allah ki daina kuka sai in dinga jin kamar zan yi kuka nima, kin ga dai yanda ki ka sani kuka nima jiya saboda kukan da ki ka dinga yi ko?" Karb'a tayi ta na sha a hankali ba jimawa ta shanye tas, ji ta yi tana son qari dan kuwa yunwa take ji kwarai, cake deb'o ya bata ta ci sannan ya bata ruwa ta sha, hamdala ta yi Haroon sai ya aje sauran ya yi kissing din wuyan ta, kwab'e baki ta yi kamar zata yi kuka,qarasa kwantar da ita ya yi a faffad'an qirjin shi ya na lallashi,cikin kunnen ta yake rad'a mata, "Shiiiii ba abinda zan sake yi miki har sai kinji sauqi, sai dai dole ne na faɗa maki cewar tun jiya nake yi maki addu'ar Allah ya saka maki da mafificin alkhairi,kin shayar dani zuma wadda zaqin ta ba zai taɓa gushewa a ƙwaƙwalwa ta da zuciya ta ba, har yanzu ina jin zaqin ta a baki na da gangar jiki na, na san kuma har abada ba zan daina jin zaqin nata ba, ina roqon Allah da ya yi wa iyayen ki albarka ya sanya su a aljanna maɗaukakiya, domin sun reni fulawa mai kyau da qamshi tare da zaqi," "Gentle dan Allah ka daina zuga ni haka, ameen na gode da addu'o'in ka tare da yabawar ka a gare ni,amma daga yau ba zan sake kiran ka da gentle ba saboda ka sauya daga Gentle ka koma wani abu na daban," "Ohhhh Mar'atussaliha, na roqe ki da ki ci gaba da kirana haka, wataqila sunan ya zama linzami ya bini na zama ina maki komai cikin gentleness,ko ya kk ce?" juyawa ta yayi tana kallon shi, daga baya ta kwantar da kan ta, saboda kunyar shi take ji, buga qofar akai da alama sun samu baqin safe ne. Zuwa yayi ya bude gidan aunty Hauwaa ce ɗauke da kulolin abinci, gaisawa suka yi ta bashi zata juya ta tafi ya ce, "Ba zaki shiga ciki bane?" "Niii kaza miji na zakara? In shiga ciki kuma in yi me? Amaryar ka mai raki jiya har gidana muna jin kukan ta, kai kuma da yake ba hakuri a lamarin naka ko ka d'aga mata qafa,tinda nake da kai baka taɓa zuwa inda nake daga kai sai gajeren wando da vest ba amma kalle ka yanzu a gabana, dan haka ban isa shiga gidannan ba nan da wata ɗaya ma albarka" Kunyar duniya ba irin wacca bata kama Haroon ba sai da ya yi danasanin yi mata tayin shiga gidan, shikenan Umaimah ta janyo masu abin magana har gidan yayan shi an ji su, cikin dariya,Aunty Hauwaa ce ta juya tace masa, "Kaii wasa fa bane maka ba abinda muka ji, sai anjima in mijina ya tafi kasuwa zan shigo, ba zan shiga na dad'e ba yana can yana jira na" "Aunty Hauwaa 1-0 zan rama ne" Suna dariya gaba ɗayan su suka bar wajen, aje abincin yayi a parlour yaje ya d'aga ta, sun riga da sun yi wankan su tun safen tsaf suke sai qamshi ke tashi a jikin su, kayan daya sanyawa Umaimah ne ke bata kunya, wata riga ce iya cinyar ta, gashi gashin ta da ya sha kitso qanana ya sake shi zuwa wuyan ta, a da ta dan d'aure abunta da band saboda ba wani tsaho ne da shi sosai ba, amma shi yana sha'awar ganin su a wuyan nata shi yasa ya cire band ɗin. Yayi yayi taci abinci ta kasa saboda ya riga ya bata tea, shine dai ta zuba masa ya fara ci kuwa, sai da ya qoshi ya je ya wanke baki suka koma baccin gajiyar biki. *********************** Mamalo ce taje asibiti dan duba baban Jameelaa, can suka hadu bayan dubiya Mamalo ke fad'awa Jameelaa tana da ciki itama, nan kuwa Jameelaa ta taya ta murna, daga haka ta fara gaya mata irin tanadin da ta yi wa cikin ta in ta haihu, da irin kud'in da za a kashe, sai Mamalo ta ji dik ta muzanta ta dan kuwa ba ta da irin wannan kuɗin da zatai hidimar bikin suna irin na Jameelaah, tinani ne fal ran ta lokacin da take komawa gida na yanda zatai itama ai suna mai qayatarwa irin na Jameelaah.................. *Ikon Allah wai na kwance ya faɗi, in fa baki da gashin wance kar ki ce zaki yi kitson wance, habaa Fatsun Sadeequu* [11/09, 2:28 pm] asiyahabibu93: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMMAERH PAGE 26: Tsabar azaba Jameelah sai da ta suma wanda da kyar aka samu ta farfaɗo, Umar na manne da babyn a qirjin shi yarinya ce kyakkyawa Jameelah ta haifa masu, nan take Umar yaji ya kamu da tsananin qaunar yarinyar da tausayin mahaifiyar ta tare da qauna mai tsanani, ji yake yanzu a duniya bayan iyayen shi ba shi da wasu wanda suka fi soyuwa a rayuwar shi sama da matar shi da diyar shi sai kuma qanwar shi Umaimah, alqawarin tsantsar so da kulawa tare da yi masu dik abinda suke so indai zasuyi farin ciki kuma bai fi qarfin sa ba sannan bai sabawa addini ba ya yi musu tsakanin shi da Allah. A nan take ya sanya mata suna Nana A'i'shaa, yana burin dama sawa abinda ya haifa wannan suna mai albarka idan mace ce,Mum taji daɗin hakan sosai, domin kuwa suna ne mai daraja sunan matar ma'aiki da ya fi so bayan Nana khadeejah. Nan da nan zancen haihuwar Jameelah ya bazu kafin yamma mutane an cika gida sai shiga ake ana daukan jaririyar ana sanya mata albarka, Jameelaah kuwa na nan a kwance idon ta rufe dik jin ta take yi bata da k'wari a jikin ta, tea ne mai yawa da kauri Ramai ta kindimo a babban kofi, tare da farfesun naman rago ta shiga uwar d'akin ta zauna a gefen gadon da Jameelah ke kwance ta ce, "Tashi ki ci ki sha ko kin samu qarfi a jikin ki, kowa ya maida hankali akan jaririya na gode Allah ma daya sa ina nan, da haka za a barki ko ki mace ko ki rayu ba mai asara sai ni da uban ki," Jameelaah da kyar ta iya tashi ta zauna tare da taimakon Ramai, tabbas Mum ta dan ji kunyar abinda suka yi na kyale Jameelah kowa ya maida hankali akan jaririyar, sam sun sha'afa da Jameelaan suna ta yi wa yarinya wasa da ba gane me ake yi take ba, dan haka sai ta hau kame-kame ta na bada hakuri, amma haka Ramai ta d'aure fuska ta ciyar da Jameelaa sosai, sannan ta je waje dan duba ruwan da ta ɗora, se taga bai ba saboda bata jima da sawa ba ta koma ta ci gaba da zama kusa da Jamelaan, yarinyar aka miqa mata ta amsa, wani hawaye ne na tsananin qaunar jikarta ta ya kwaranya a idon ta, cikin jan majina ta ce, "Allah ya raya mana A'i'shaa, ya yi mata albarka, ta yi kama ainun da mahaifiyar ta sanda na haife ta, kamar an tsaga kara," Cike da jin daɗi Umar yace, "Ke nan zata yi kama da ita sak idan ta girma ko Mama," Ai nan fa Ramai ta samu waje ta dinga fad'in qarya da gaskiya akan kyau irin na Jameelaah, Umar kuwa sai jin daɗi yake yi, Mum dik kunya ta kama ta dan kuwa har labarin sanda Jameelaan ta fara al'ada da qirgan dangi sai da ta bawa Umar, ruwa na can ya tafasa ya tafarfashe,  Jameelaah sai sheqa bacci take abun ta. Mum ce ta je ta haɗa ruwan wankan ta aje komai da ake buqata sannan ta shiga dakin cikin sakewar fuska tace, "Umman Jameelaa zaki yi mata wankan ne ko naje na yi mata kawai," "Subhanallahi na manta na ɗora ruwan zafi fa, bari nayi mata kawai ke yi wa jinjirar," Tashin Jameelaah suka yi daga baccin wadda kan ta ya rage ciwo sosai dan kuwa ta ji daɗin abinda taci da kuma hutun da ta samu, ruwan ba mai zafi sosai ba aka haɗa mata aka yi mata wankan da shi, haka ma wanda ta zauna ciki, ba shi da mugun zafin nan shima, (irin wannan ruwan ko hawan jini gari mutum ba zai yi masa illa ba) Mum kuwa ta yi ma jinjira wanka ta shiryata cikin kaya masu taushi da laushi kalar pink na jarirai,Ramai kuma ta shirya mai jego ta yi sharr sai sheqi take yi, Umar komai akan idon shi ake aikatawa yaqi fita sannan bakin shi yaqi rufuwa saboda farin ciki. Da dare Umaimah suka iso da  Haroon Umaimah dake tana da jikin qiba nan da nan ta yi dumurmur da ita gwanin ban sha'awa, tana ganin Mum ta rungume ta itama ɗin tayi kewar ta sosai sai suka rungume juna. "Mum ina mai jegon? A ban babyna na dauka,Allah ya raya mana ya yi albarka," Jameelaa dai sai ido ta haihu ta ga qarshen zance jikin ta qaura yayi mugun yin magariba, ashe haka iyaye suke ji? Haihuwa babban abu ne ashe ta ke raina lamarin, iyaye girman su mai girma ne ainun, dole ne kowa ya girmama iyayen shi, son Ramai da Baban ta sun qaru a ran ta k'warai a wannan lokacin. Cikin mutunci da girmama juna suka gaisa da Umaimah har saida Umaimah ta yi mamakin sauyawar Jameelahn ganin yanda qawar ta ta ta yi laushi da wuri, dariya sosai tai tayi tana tsokanar ta. Har qarfe taran dare ba su tafi ba, mutane sun dan zazzo na kusa da aka sanarwa da haihuwar,qarfe tara da rabi Haroon yace zasu tafi Umaimah tai ta shagwaba ita a barta, dama a kusa da juna suke a zaune, dan haka kawai bai ce komai ba, sai zura hannun shi yayi ta bayan ta ya shafi bayan ta, qafewa tayi da maganar da zata yi tayi, ba wanda ya kula da me ke faruwa, cikin sarqewar murya ta ce, "Mum zamu wuce," "Har kin gama shagwabar?" "Yah ai na yau ne kawai, gobe in nazo sai an gama suna zan koma," Ta kalli Haroon tare da murguda masa baki, cikin salon soyayya,(ba da rashin ta ido ba faaa)    Mum ma tashi tayi dan komawa gida, drivern su ne ya zo dan komawa da ita gida,Ramai anan zata kwana, saboda kula da mai jego. Bayan kowa ya tafi ne Jameelaah da Umar na d'aki sun saka jaririya a gaba suna kallo, kowa na fadin albarkacin bakin shi. Ramai ce ta shiga kitchen ta dumama naman da ta dafama Jameelaah ta ciko kwano da shi, tare da singumemen bread sai ta haɗa tea mai shegen kauri, ta je d'akin da ta sauka ta aje a qasan carpet ta zauna ta na ta lodawa cikin ta, sai santi take tana zuba surutu tana fad'in, "Ina nan daga nan har ayi arba'in ba inda zani, ni inda hali ma sai na dawo nan in ta yi masu reno, Jameelaan ta koma makaranta, irin wannan dabge haka, kullum bawa in zaici nama sai qwarori amma nan gashi ka cika kwano ka ci ba mai ganewa ko ace dan me," Sai da ta tashi da shi tass ta saki gyatsa mai qarfi sannan ta mayar da kwanon ta wanke hannu taje ta kwanta. Washe gari da asussuba ta tashi ta dora ruwan wanka, ta dora abincin kari, farfesun kaza ta yi mata ta saka yan kayayyakin mata a ciki, Dankalin turawa ta fere ta soya shima, irin suyar tsoffi yankan manya manyan gaske, wanda bai saba cin irin yankan ba ba zai ji daɗin shi ba, ta kai ta aje. Bayan ta gama ta je dakin su ta kwankwasa qofar, Umar ne ya fito, dauke da Baby a kafadar shi, Jameelaa na zaune bakin gado tana saka takalmi zata fita dan yin wanka, d'aure take da towel ta yafa wani akan ta,bayan sun gaisa da Umar ne ta cewa Jameelaah cikin fara'a, "A kwana a hantse sai kyakkyawa, maza taso na sille ki ki zo ki karya, ba a son me jego tana zama da yunwa," Wanka ta yi mata sosai, ta sa ta zauna a ruwan da ta dafa da bagaruwa kadan ba da yawa ba sai kuma aloevera da ta wanke ta b'are cikin ta tafasa ya dan huce dai-dai yanda za a iya zama a ciki, sannan ta zauna sai da ya huce sosai sannan ta fita, sai surutu takewa Ramai akan me yasa ba zata bari a gama suna ba sannan ayi wannan wankan na tarkace, "Ke ja can ga kaza can ma ki gama ki cinye tass ai gyara yanzu kiks fara yi ba d'aga qafa har sai kinyi arba'in, gobe ma ruwan da zaki zauna har da qarin ganyen magarya zan saka a ciki danya wanken dattin jikin ki tass," "Ramaiii ni dai gaskiya bana son abu mara daɗi ba zan ci ba dik wani abu me d'aci kar ma ki fara ban dan ba san ci ba ko na sha" "Kar ki damu ba masu d'aci bane muje na samu na wanke jinjirar itama," Jameelaa cikin wani dakken leshi ta shirya dan yana daga cikin burin ta dama daga randa ta haihu har bayan suna ta yi ta sanya kaya masu matuqar kyau da burge dik wanda ya gan ta. Jaririyar ma kaya masu tsada aka sanya mata Ramai ta share gidan ta kunna turaren wuta sannan ta saka na garwashi gidan sai qamshi yake yi. Bayan sun karya ne  Jameelaa ta hau social net ta hau sanar da qawayen ta 'ya'yan masu kuɗi ta haihu an sami mace sai sanya albarka ake ana mata alqawarin zuwa ganin jaririya, kiran Mamalo tayi ta sanar da ita ta sauka fa, itama tana nan da nata tulun, "Wayyooo kin sauka? Masha Allahu, ina nan tafe yau inshaa Allahu, yanzun nan Sadeeq ya fita shago, zan sanar da shi sai na taho," "Sai kin zo to," "Me zan taho maki da shi na ci ?" Wani murmushin rainin hankali tayi sannan ta ce, "Habaaa Mamalo wanne irin me zaki kawon na ci kuwa? Yanzu haka farfesu ne sun kai kala hudu gabana, daga gidan su Umar ma an kawo min ga Ramai da ta yi min wani, kar ki damu, in baki karya ba ma ki zo, sai mu karya tare," Mamalo ji tai kamar an buga mata guduma, dan sarai ta san da yanayin zagi aka mata wannan kalamai,amma bata damu ba tayi murnar haihuwar qawar ta ta, waya tai ma Sadeeq ta nemi izinin shi,nan take ya amince mata kuwa ta je, nan da nan ta gama shiri ta fita, a hanya ta bi ta kai masa keys din gidan nasu, ya amsa ya yi mata Allah ya kiyaye, da gargad'in ta kula da kan ta, in ya samu sararin ɗinkunan zai biyo yaga jaririyar sai su koma gida tare. Adaidaita sahun a qofar gidan su Jameelaa ya tsaya, motoci wajen guda hudu ta gani pake a qofar gidan, a tinanin ta ko dangin mijin Jamelan ne, sai da ta shiga, taga gidan gaba ɗaya ya sauya dan kuwa an sauya labulaye, da wasu daga kayayyakin parlourn, Jameelaa har kujeru taso a sauya, amma hakan bai samu ba, sai ta hakura. Da sallama Mamalo ta shiga lokacin sha ɗaya na safiya ta gota ma,Jameelaa ce zaune ta ci uban ado sai walqiya take yi, ta sha zinaren da Umar ya sai mata as a gift na haihuwar ta,Mamalo idon ta kamar ya faɗi qasq dan tsabar kyaun da taga Jameelaa tayi mata, wasu had'ad'd'un 'yan mata ne zaune da manyan wayoyi a hannun su sai hira suke yi, kowaccen su in ka dubi kayan jikin ta kasan ta sha nera. Gaida su tayi, suka daga mata hannu sai masu cewa "Sannun ki" Zama tayi a kujera Jameelaa ta dawo ɗauke da jaririya a hannu ta miqawa wata da ake kira da Kabeerah, sai santin kyaun yarinyar suke yi suna ɗaukan ta a hotuna, Mamalo gyaran murya tayi tace, "Mejego manya, an samu kai qalaou? ALLAH ya raya mana, ya sanya albarka," "Ameen, ya kike? Ya me gidan?" Ko amsar Mamalo bata jira ba ta ci gaba da hira da qawayen ta masu kudi, qarshe dai Mamalo ta sa ta kwashe kayan da aka ci aka sha a wajen ita da sabbin qawayen ta. Haka ma Ramai aiki tayi ta sanya Mamalo, Mamalo ta gaji sosai saboda a lokacin nan cikin ta ya fara yin nauyi, suna nan zaune har bayan azahar Sadeeq bai zo ba, zama tayi shabar alamar ta gaji,can sai ta miqe ta d'akko jakar ta tare da wayar ta, kiran Sadeeq ta gani da yawa suna zaune a wajen ba wanda ya damu yace ana mata waya, tana ta hidimta masu, Message din shi ta gani yana mata magana akan ya san tana nan ana manne da jaririya sun yi d'iya ta manta da shi, anjima yana nan tafe su wuce. Wata kwallar baqin cikin bai san me ya faru ba ne ta kwaranyar mata a idanun ta, da sauri ta share, ta dauki jakar ta ta danna masa kira, bayan ya dauka yayi sallama ta amsa tace masa, "Ba sai kazo ba, ka je ka bude mana gida gani nan dawowa yanzun nan" Ba wanda tayi wa sallama ta sa kai ta fice, ranta yayi matuqar baci da irin walaqancin da Jameelaa ta yi mata, qawayen ta wannan tazo wannan ta tafi ta ma sa ran ko Umaimah zata samu zuwa amma shiru, tana hanya tana zancen zuci, ta samu abin hawa sai gida. Da kuka ta faɗa jikin Sadeeq, shi kuwa a gigice ya kama ta yana son jin me ya same ta sai da tai kukan baqin cikin daya tokare mata zuciya sannan ta labarta masa dik abinda ya faru, sannan ta qara masa da cewa, "A yanda muka taso da Jameelaa, ni nayi sadaukarwa kala-kala akan ta amma ita a kullum bata da burin da ya wuce ta ga tana muzanta, ni mai iya yin dik wani aiki ne dan ta haihu ba tare da gajiyawa ba, amma duba ka ga yanda take ta wulaqanta ni gaban qawayen ta sabbi masu kudi, ni na tashi a banza kenan, naso umaimah ma taje dana danji sanyi-sanyi araina, amma bata je ba ni Fateemaa nayi alqawarin ko da bashi da saida kayan dana mallaka ne sai na bawa Jameelaa mamakin abin da ta aikata min, sai na nuna mata ba ita kadai bace zata fantama da kuɗi ba a duniya..........[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 28: Haroon ne zaune cikin motar da Ishaaq ya sai masa sabuwa dal yana jiran su Umaimah dan kai su gidan Jameelaah haka nan shi dai bai son Jameelaah har yanzu, dan ganin ta ya ke yi irin mutanen nan masu halayya biyu, amma da alama su ba su gane ta ba, ita ɗin ma ba son shi take yi ba dan ta ga alama ya gama gane ta tsaf, shi yasa bai son Umaimah na rab'ar ta sosai. Sai da suka gama b'ata lokaci sannan suka fito yana ganin shigar Sapna ya b'ata rai, sai da ya bari ta zo daf zata shiga ya d'aga kai yace, "Ince dai ba ni zaki bi a haka ba ko?" "To da wa zan bi? A mota fa muke," "Habaa hajiya, gaskiya ko ki sauya mayafi ko ki sauya kayan jikin ki dika, dibi wata muguwar tsagu da akai ma skirt din ki, dibi saman rigar ki ke a ganin ki wannan shiga ta dace da mace mumina?" "Ya ustaz Attaqwa hahuna anyi nuni da saitin zuciya so a zuci abun yake ba wai a shiga ba, ba kayan da zan sauya nidai sai dai kace kawai ba zaka d'auken a motar ka ba na hakura,ko na hau adaidaita sahu," "Kin manta da ayar da tace a faɗa ma matan annabi da muminai su sanya jalbab? Ba dole sai hijabi ba koda mayafi ne ki saka amma wanda zai rufe ko ina na jiki to Shima jalbab ne, kuma sutura da zata rufe jiki dikkanin shi itama jalbab ce,ke yanzu amma gaba daya kinyi shiga ta tabarruji sannan ga uban turare kin fesa wanda tin kan ki iso na ke jin qamshin jikin ki sannan kice attaqwa hahuna? Kina tinanin in har akwai taqawa cikakka a zuciyar bawa a jikin shi ba za a same ta ba? Tinda a iya sani na zuciya ke juya jiki, ban hana ki dan tozarci ba, na hana ki ne kawai saboda ke kina daga cikin ahalina yanzu, mun zama ɗaya Aunty Hauwaa Yayata na ɗauke ta ta jini ba iya matar wana ba,dole inna ga wani nata ya yi ba dai-dai ba na nusar dashi, last warning ki koma ki sauya kayan jikin ki ko minti nawa zaki ɗauka ina jiran ki," Maganganun shi sun shige ta sosai, amma kunya take ji ta koma ya gan ta musamman tsagar bayan ta, sai yanzu ta ji kunyar fita a haka, "Dan Allah ki je ki sauya muna jiran ki, na san ba zai tafi ba sai dake, mutuncin ki yake kare maki jikin mace na da daraja da qimar da ba kowanne jaki da doki ya kamata ya gani ba sai muharramin ta, jikin mace yana da matuqar qima da daukakar da yafi dukiya da dik wani abu mai mahimmanci, tinda ko gobara akai aka ce komai ya qone zakiji an fara tambayar anyi asarar rai? Ki je ki sauya, baya son jikin ki ya zama makamashin wuta ne, kije...." "Ya isa haka Umaimah say no more please, na fahimce shi tin farko ban san ya zan na wuce ta gaban shi da tsagar skirt dina bane kunya nake ji," "Muje na raka ki, muje wajena na baki hijabi," Jan ta Umaimah ta yi, sukai ciki ta aje mayafin ta, ta bata hijab madaidaici kalar kayan ta, ita kan ta sai tafi jin daɗin da sakewa a cikin hijabin unlike da ta sa mayafi sai tai ta ja dan rufe wani wajen da bata son ya fita. Koda suka dawo Haroon fuskar shi ɗauke da murmushi suka shige suka ja sai gidan mai jego Jameelaah. Ramai na ta haɗa kaya tana sharar kwalla dan kuwa an kawo mai aiki mai suna kulu, da kulun gatsal Jameelaa ke kiran ta, dik da cewa matar ta girmi Ramai, Umar kuma yana ce mata Iya, d'akin da Ramai ta zauna nan aka kai mata dan qullin kayan ta, Kulu ta iya aiki sosai, ga iya girki musamman na gargajiya, Umar yaji daɗin samun ta a matsayin wadda zata na taimaka masu. Jameelaa ta buɗe abubuwan data samu tana gani sai murna take da jin daɗi, dan kuwa ta tara sutura ba kadan ba, daga ita har jaririn ta, ga kudi da ta samu ta biya bashi har da ragowar 30k a sama ta samu, dubu biyar ta bawa Ramai a ciki, Ramai kuwa ranta ya baci k'warai ina laifin ta bata dubu goma? dik aikin data tiqa a suna da kafin sunan ya tashi a banza kenan?  Umar ya bata kudi wanda Jameelaa bata san nawa bane sai son sanin nawa ne aka bata take yi amma Ramai ta damqe abun ta ta kuma kwashi kayan gara, sai da ta haɗa buhu da kayan sawa dana abinci da tarkacen abubuwa dai harda flask. Umar yaso maida ta ta kafe zata tafi ya wuce office kawai, dan haka ya fita bayan ya bata saqon gaida Baba da yi masa godiyar basu ita da ya yi. Motar su Haroon ce ta tsaya, suka fita dikan su shi kuma Haroon sai ya wuce kasuwa, tare da alqawarin komawa qarfe uku dan maida su gida, tinda azumi ake su yi masu abin shan ruwa. Da sallama suka shiga Kulu ce taje ta buɗe qofar, bayan gaishe-gaishe  ta wuce d'akin ta, Jameelaa na zaune bayan fitar Ramai, tana kallo tana bawa baby nono taga su Umaimah sai ta hau murna tana fad'in, "Ahhh lale maraba da Umaimah, sannun ku Aunty hauwaa, barka da zuwa, qawata ammmm???" "Sapnah," Sapnah ta tuna mata da kan ta, sai Jameelah ta qara qashe baki ta ce, "Yauwa mai sunan mutanen can, sannun ku da zuwa bismillah ku zauna" 'Allah ya sa kun zo da kayan barka, ko dake na fi son kuɗi akan kaya na gaji da amsar kaya haka kud'in ne dai ko dubj ɗari zaku bani ba za su yi min yawa ba' Wata leda ta gani a hannun Aunty hauwaa baki ta qara washe masu sosai tana masu maraba, "Gashi azumi ake yi da an kawo abin motsa baki," "Wannan sai ku masu jego miqo ta nan wajen Goggon ta" Miqawa Umaimahn babyn tayi suka dinga ɗaukan ta, wannan ya ɗauka wannan ya aje,hira sukai tayi ta na ba Umaimah labarin yanda sunan ya gudana bayan tafiyar ta. "Kaiii amma nayi missing na kuwa so mu haɗu da Fateemaa, mun jima bamu haɗu ba sosai da sosai, anya tin kafin auren ta ma mun haɗu kuwa?" "Gaskiya bana jin kun hadu, ai ta kusan haihuwa itama a wannan watan inshaa Allahu, kin ga sai kije suna," "Haka ne Allah ya kai mu," "Ameen" Hira suke tayi kamar ba za a daina ba lokacin sallah yayi, Aunty Hauwaa ce ta miqawa Jameelaa ledar hannun ta, aiko kamar jira take yi haka ta cafke tana ta zabga godiya, dik sun zaci a sakin fuskar ta ne da mutunci da take dashi ya ta yi hakan, Aunty hauwaa ce ta tambayi bandaki Jameelah ta nuna mata hanyar waje, dan ba toilete a kowanne daki sai nasu, wajen ta fita Sapnah tace, "Ohhh aunty Hauwa dama ki bari na shiga a matse na ke da fitsari," "Da kina zaune da fitsarin kuma baki yi magana ba? To da ban ce zani ba a zaune zakiyi shi? nima a matsen na ke sai ki jira ni," Matse qafa Sapnah ta yi tace taje ta na jiran ta ta dawo, ganin haka yasa Jameelaa tace ma Sapnah ta shiga na dakin su. Da sauri ta cire hijabin ta ta shige band'akin dake cikin d'akin su ita da Umar dan nan ne kaɗai ke da band'aki dika gidan, sai ko na waje, daga shigar ta d'akin ta ci karo da komai a baje, gadon ba gyara, komai 1-1, ganin haka sai kawai taji ba zata iya shiga bayin ba, dan bata san me zata tarar ba fita tayi, ta wayance tace, "Bari na jira Aunty Hauwa na shiga naga alamar kamar d'akin me gidan ne, d'akin miji ai ba a barin kowa ya shiga zan iya matse shi har ta gama" "Ohhh su Sapnah manya," Haka dai sukai ta mata tsiya tana yaqe dik sai ta raina Jameelaan, dan dai ko mace bata zama mai tsananin tsafta ba ana so a same ta dai ba qazama ba, amma da alama parlourn ma dan mai aiki ta gyara ne da ba zai ganu ba, ai gwanda ta shiga na tsakar gidan ta san mai aikin ta gyara shi. Suna nan Aunty Hauwaa ta dawo, ita ma ta shiga sai da tai fitsarin ta sannan ta yi alwala ta koma suka yi sallah, Umaimah ma tayi sallah suka ci gaba da hira, sun dad'e ba su haɗu sun yi hira haka ba. "Yanzu ya zaki da maganar makaranta?" "Wai yace haka zan koma kulu tana riqen ita, ni dai gaskiya ba zan iya karatu da yarinya ba a bari na yaye ta kawai sai na koma," "Ai yara ba su hana karatu, ki yi hakuri ki ci gaba," "Shikenan zan duba na gani" Suna zaune Umar ya dawo, Sapna na shafa powder, Umaimah na tsokanar ta akan a mota suka zo a mota zasu koma ba mai gani a hanya balle ta damu da powder. "Ke kika sani sai dai na shafa ɗin, kika ishen mijin ki zan aura,' "Aiko da na yi farin ciki da hakan," "Sannu da dawowa Yah umar" "Yauwa yau kune a gidan namu, ance kin zo suna kin tafi da wuri" "Eh Yah kasan shi baya son yawan fita," "Yayi dai-dai ai nima bana son yawan fitan nan" "Sarkin surutu yau me ya sami bakin ki?" "Ina yini?" "Hummm lafiya," "Dama ka san ta ne?" "Mun haɗu randa aka kai ki surutu gare ta kamar redio," Dariya suka yi tayi har Sapnan Jameelaa kuwa ranta ya baci ganin yanda Umar din ya sake da Sapnah ana wani hira jefi-jefi ta dinga sanya baki gaba ɗaya sai ta ji jikin ta ya mutu. Qarfe uku dai-dai Haroon ya iso dan ɗaukar su Umar ne ya shigar da shi gidan da kan shi nan ya ga baby again bayan sun gaisa da Jameelaah kafin su tafi saida ya aje kuɗi yace na baby ne, Jameelaa sai washe baki take yi Haroon kuwa sai b'ata rai yake saboda ya gama gano ta yar son abin duniya ce. Bayan sun tafi Umar ya dami Jameelaa da maganar su Umaimah da Sapah, da yanda suka fara haɗuwa,cikin hasala da b'acin rai ta ce, "Kai ni dan Allah ya ishe ni haka bana son surutun tsiya, sai wani zancen Sapnah kake ma mutane, ko dai son ta kake yi ne?" "So kuma Jameelah Wanne irin so ? dan Allah ki daina wanan maganar tinda baki son maganar su na daina, kawai ina qara yi maki bayani ne akan yanda muka haɗu da ita, dan na kula kin b'ata rai da kika ji na san ta tin da," "To dai magana ta qare haka dan Allah ni, bana son na sake jin zancen wata wai ita Sapa take kowa oho," Umar ne yayi dariya sosai sannan ya kwantar da kan shi a bayan ta, tare sa saqalo qugun ta a hannayen shi ya ce, "Ohhhh mata ta na kishi na ashe har haka? To kar ki damu Umar naki ne ke kaɗai,ba zan taɓa haɗa ki kishi da wata ba," Qara kwantar da jikin ta tayi a jikin shi,tana dariya itama, "To to ya isa haka dagani gwanda ke, nikam inni sa'imun" Bin shi tayi zata yi masa cakulkuli sai ga Kulu zata tambayi me za a dafa, basarwa suka yi Umar ya shige daki ita kuma ta kame kamar ba ita ba. ******************** "Aunty Hauwaa ni kam mutumin nan ya bani tausayi " "Wa kenan?" "Mijin Jameelaa mana matar wan umaimah" "Ke fa kina da matsala sapnah yanzu mene na tausayin nashi? Mutumin da Allah ya azurta da komai na rayuwa dai-dai misali, wata nakasa kika ga yana da ita?" "Kwarai kuwa dan kuwa bai yi sa'ar mata ba, ki duba d'akin ta kiga baqar qazantar dake ciki, wai a ce nan ne dakin miji? Ga wani uban wari daga ji daga toilet yake fita, shi yasa na qi shiga, namiji bai sa'ar mace me tsafta ba ai abun tausayi ne,kuma fa ki ga da alama bata aikin komai, karatun ma ta samu dama miji na son taci gaba amma wai ita bata so, wannan wace irin mace ce, ga son abun duniya, kiga da Haroon ya bata kudi ya ce na baby ne kamar za ta kifa," "Hhhhhhh baki da dama wajen bata lokaci ki karance halayen mutum, to yana baki tausayi ta ya za ki taimaka masa? Dan na san halin ki sarai yanzu sai kice zaki taimaka, wannan dai ba almajiri bane balle ki bashi sadaka," "Shi kam ba abinda zan yi masa dan taimaka masa amma dai kam akwai gyara," Umaimah ce ta aje naman da taje cirowa a freezer ya qanqare da kyar ta ciro ta ji suna hirar yayan ta sai tace, "To ko dai za ki je a ta biyu ne? Kin ga sai ki taimaka masa kawai," "Keeee Umaimah rabani da shiga gidan qazama, ni mijina ni zan fara bare shi a leda kamar yanda zai bareni a leda shi kuma yayan ki second hand ne fa," "Baki abin magana aikin kuke ko surutu?" "Yah Ishaaq sannu da dawowa gaskiya zan fara azumin magana, kowa ya d'aukeni a mai surutu, inna daina magana zanga wanda zaku na kira da me surutun," "Ai shi surutu ko ka daina yana nan maqale da kai, tinda shi kamar ciwon qanjamau ne da ka fara baka iya bari," "Zan baku mamaki kuwa" in ji Sapnah. Ranar haka Umar da Sapnah suka kwana tinanin junan su, ba wai tinani irin na soyayya ba, tinanin umar akan sapanah shine yawan surutun ta, ita kuma tana tausaya masa akan qazantar da yake zaune ciki gashi Kyakkyawa kuma ɗan gayu........... *In ba iyayi ba da kuma wata qullaliya a qasa meye na tinanin juna, Umar ina tausaya maka in Jameelaa tai leqe ta gano da tinanin wata kai bacci😂* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 27: Tin daga wannan ranar Mamalo bata sake komawa gidan Jameelah ba,haka itama Jameelaah bata neme ta ba, duk wata sutura da sarqa da d'ankunne haɗe da takalmi da jaka da ta so sawa sanyawa take yi ta k'wame k'wam abinta, Jameelah tayi yanda take so har ma fiye da hakan dan kuwa Umar ya tsaya mata, komai an kawo na abincin suna Ramai ta rud'e ta kid'ime k'warai dan ganin kala-kalar cimataku na abinci, Bukar daga makaranta kullum nan yake zuwa yaci abinci har zuwa dare sannan ya tafi gida, da a son shi ne ma idan yazo a dinga bashi renon d'iyar tashi saboda qaunar dayake yi mata, Baban Jameelaa ya zo sau ɗaya ya ga jikar shi, daga nan ne suka je gidan su Umar domin yin godiya akan alkhairin da ake ta yi masu kala-kala da shi da iyalin shi, Daddy ya karɓe shi hannu goma ma ba biyu ba saboda mutuntawa, dan kuwa sai da Baban Jameelaa ya gano inda Umar ya gaji arziqi da mutunci, fatan shi Allah ya gwada masa nashi iyalin sun zama mutanen kirki kamar haka, yanzu dai ya samu Bukar ya kintsu, yana yiwa  Ramai da Jameelaah fatan shiriya suma,a tare suka yi sallar Azahar da Daddy sannan suka dunguma dikan su har Daddyn dan ganin jikar su, Daddy ya yi mata addu'a sosai sannan suka yi sallama da  Baba ya koma wajen aikin shi, Daddy kuma ya wuce Abuja domin gabatar da aikin shi shima. Umar akan dole yake zuwa asibiti saboda kula da marasa lafiyar da suka zama dole akan shi, gashi kuma gidan kullum a cike yake da mutane duk yanda ya so zama dole ya basu waje, 'yan uwan Mum da Dad ne yawanci sannan  ga 'yan uwan Ramai da Baban Jameelaah gefe ɗaya ga mutan unguwar su da Jameelah ta dinga shigewa daf lokacin da taga ta kusan haihuwa dan su bata gudummawa kuma babu laifi sun bata kuɗi sosai da kayayyakin jinjira. Ramai har wani ja take a kwanakin nan tsabar yanda ta yi haske ta yi qiba, sai wani bud'a hanci take ita a dole uwar me jego,Jameelaa ta ware mata kaya na musamman tana sauyawa itama dan bata son a raina mahaifiyar ta, ga sarqa da dan kunne masu kyau da takalma duk ta bata ,gaba ɗaya wanda ya san Ramai me shinkafa da wake a da ba lallai ya gane ta ba yanzu, sai a zaci tana da Hassana ko Hussaina ne. Matan gidan su na da da matan layin da suke dan zumunci a da sai gulmammaki ake yi akan su ita da 'yarta, wasu kuwa murna suke taya su na samun ci gaban rayuwa da suka samu. (Allah ka sanya mu a cikin masu taya 'yan uwan mu musulmi murna akan ci gaban su ka kare mu daga cikin bayin ka masu yawan qyashi da hassada) Jameelaah ce zaune ta na doka murmushi saboda kallon kayan da ta baza zata sanya ranar sunan da ya samu halartar manyan mata na dangin su Umar da kuma qawayen ta na social media da yaran masu hannu da shuni na makarantar su ta boko, a wannan rana Jameelah ta yi kuma ta na kan yin yanda ta so dama abinda bata taɓa zaton zata yi shi ba, dan kuwa ko a cikin unguwannin masu kuɗi aka yi sunan da aka yi a nata an kai aya,wani hamshaqin gidan ɗaukan hotuna aka gayyata dan daukan hoton sunan Humairah, duk wanda ya halarci taron nan ya ci ya sha ya yi guzurin abinci. A ranar Mamalo ji ta dinga yi kamar kar ta je, amma haka ta hakura ta shirya da yamma liss, ta sanya dinkin ta mai kyau abunta wanda  Sadeeq ya d'inka mata shi da hannun shi, atampa ce mai kyau ta amshi jikinta ta kafe d'auri mai kyau, koda ta zo mutane dik sun ragu d'aki ɗaya Jameelaah ta ware ta zuba kayan gifts da ta samu, kuɗi kuwa ta same su da yawa wajen qawaye da kuma 'yan uwan mijin ta, sanda Mamalo ta  isa gidan Jameelaa na d'aki tana shayar da Humairah dik ta gaji, amma jira take yi yarinyar tayi bacci ta sanya ta a gadon ta, ta sake wasu kayan ta fita ta qara yin barazana, Mamalo na ta gaisawa da mutanen da ta sani ana ta yi mata fatan itama Allah ya sauke ta lfy, tana masawa da Ameen. Jameelaah ce ta fito ɗauke da Humairah, (sunan da suke kiran A'i'shaa kenan) ta sauya kaya da wata shadda milk da aka zubawa uban aiki ruwan zuma mara duhu, sai ta kafe d'auri mai ban sha'awa ga qamshin turare na tashi, sarqa harda ta qafa sai da ta sanya irin ta mutanen india, qaryar mutum yace bata ratsa shi ba saboda haɗuwar da ta yi. Mamalo baki sake take kallon ta, dan kuwa bata zaci Jameelaah ta shiryawa sunan har haka ba,nan take zuciyar ta ta raunana ta fara waswasin anya kuwa zata iya kamo Jameelah? Wani yawu ta had'iya mai dumi ta fara gaida Jameelan tare da yi mata barka,sai ta d'akko ledar kayan jaririyar da ta zo da shi ta ajiye mata a gaban ta,a cikin ledar kuwa riguna ne guda biyu, da atampa ɗaya sai takalmin yarinya biyu da sabulu sinqi ɗaya. Jameelaah bud'a ledar tayi ta kalla sai tayi murmushi ta ajiye a gefen ta tare da yin godiya. "Ramai ki ce da Khadeejah a kawo ma qawata abinci,a sanya mata komai da komai dan Allah," "To shikenan bari na duba ta ina jin tana can tana gyara kitchen," Ramai ce ta samu Khadeejaa ɗaya daga cikin dangin Umar ne, da sukai ta taimakawa a sunan dan aikin ya yi ma Ramai yawa, Umar har ya yi magana da Mum a sama masu mai aiki babba wadda zatana kula masa da gidan da iyalin shi, sun tsayar bayan suna za a kawo mai aikin, Ramai tayi iya yin ta dan ta hana a kawo kowa amma sunqi hanuwa sunce in bayan suna ta koma wa zai na kula da su? tace ah ah ai ita zata zauna har bayan sunan Mum tace ai ba za a bar Baba shi ɗaya ba, ta dad'e anan ya kamata ta koma gida,ba dan ta so ba ta hakura dole zata koma gidan nasu. Babban trey ne aka doro abinci kala-kala akan shi da abubuwan sha sai wata qatuwar leda da aka ciko da abinci again aka dire gaban Hajiya Mamalo, ganin kayan kwalamar da ke gaban ta ne ya sanya yawun ta ya kai maqura wajen tsinkewa, bata b'ata lokaci ba kuwa ta sa a gaba tai ta ci, Jameelaah na murmushin mugun ta, sai da ta kammala ci ta yi nak sukai ta hira, dan kuwa ta sake mata sosai saboda daga ita sai mamalon ne ba wasu important mutane da take jin kunya , sun sha hira ba kamar wancan zuwan ba, har mamalo taji bata kyauta ba data dinga jin kamar Jameelaa ta wulaqanta ta rannan sannan ta janye qudirin ta na son fin Jameelah a abubuwan more rayuwa na yau da gobe dama ba halin ta bane haushin da aka bata ne yasa ta ɗaukan wannan alwashin,sannan ta kulama ba zata iya yin competition da Jameelah ba. Magrib na gabatowa Mamalo ta ma Jameelaa sallama, Jameelaa ta tashi dan raka ta, a hanyar su ta fita daga gidan ne Mamalo ke tambayar Jameelah Umaimah dan tinda tazo basu haɗu ba. "Tazo da ita akai suna akai komai da safe ta koma dan kuwa kin san Malam kamar wani mayen ta haka yake baya barin ta ta sake ko kaɗan,tun wajejen 11am ya kawo ta ya dawo around 3:30pm ya ɗauke ta" "Ikon Allah Jameelaa ina matuqar tayaki farin cikin yanda rayuwar ki ta kyautatu, dibi har turanci kike yi abun ki, Allah nima ya kaini wannan matsayin kema ya qara maku ɗaukaka," Murmushin qasaita Jameelaa tayi, sannan tace, "Mamalo baki da wayo na baki shawarar yanda zakiyi ki tara kuɗi kema kiyi suna irin nawa amma kin qi, yanzu duba ki ga sunan nan dana yi, da kud'in bashin dana faɗa maki da shi na kashe wata yawar ko Umar be sani ba,gashi yanzu na maida kud'in har da riba, na fita kunya ko ban fita ba?  dik da dai gaskiya Umar ma da mahaifan shi sun taka rawar gani sosai, amma ba dan kud'in dana ranta ba da tini na san ba zan fita kunyar qawaye na gaba ɗayan su ba," Murya qasa qasa sosai suke yin maganar saboda Jameelah bata so aji tana zuga Mamalo, Mamalo ce ta yi ajiyar zuciya sannan tace, "Jameelaa yanzu inna ce zan yi aro wajen wa zani? Wa zai ara min kuɗi masu yawan da zan shiga na fita kamar yanda ki kai,kar ki manta mijina qaramar sana'a da aiki yake da" "Kar ki damu indan wannan ne a inda na aro kema a nan zan aro maki, a ajin mu yaran masu hannu da shuni ke yin adashi, dik wata kowa na saka 20k su goma ne, ta haka suke siyan dik abinda suke so, ni kuma da sukaji waye mijina da surikina shine dana nemi aban d'iba na biyu aka bani, na samu Allah ya taimaken na sai kaya na d'inka tun a lokacin, na sai wasu daga abubuwan da aka raba a sunan nan, Umar ma ya sai min kaya masu kyau da tsada dan haka bai ma san nayi ba a zaton shi na lefe na ne na qara da su, in kina so zan iya shige maki gaba dan na tabbata kin kusan haihuwa dan dai ko ki haihu cikin azumin nan ko bayan azumi da kadan" Tinani sosai Mamalo ta shiga yi, wanne irin yara Jameelaa take tare da su a makaranta da suke adashin kudi masu yawa haka iyayen su basu damu ba? Dan taga dik yaran ta girme su in ba saurin girma irin na yaran masu kuɗi ba. "Kinga na baro mutane na zo nan muna ta tattuanawa amma kin yi shiru kina tunani, in ba dan amintar mu bama kin ji na faɗa maki sirri na in ba kya so ki fada min tun da wuri na sani," "Ina so nima ki nemar min ɗin dik abinda na samu a suna sai na tara na biya, in ma basu cika ba na nema na biya," "To shikenan,ki gaida gida, ya kamata ki samu a bin hawa anan, dan kayan sun yi maki nauyi," (Kayan suna jameelaah ta sa aka d'ibar ma Mamalo masu yawa dan ta sake kwad'aita mata karb'ar bashin itama a fantama a bikin sunan ta) Mamalo sai tunanin hirar su da Jameelaa take yi tunda ta koma gida, zuciyar ta ta gama aminta da shawarar Jameelaa dari bisa dari, ita ta san Mai zaman gida ce bata aikin komai Jameelan ma haka, amma a qallah suna da 'yan uwa da abokan arziqi ta san za suyi mata biki zata samu kuɗi, sai ta biya su in an gama suna, ko da kujerun ta ne ta shirya tsaf bayan suna ta siyar ta cika ta basu kud'in su ,in ta samu daga baya ta sai wasu. Koda ta koma gida gum tayi bata ce ma Sadeeq komai ba akan wannan maganar, yayi tambayar duniya akan me ya sa take yawan tinani taqi magana, dole ya hakura ya qyale ta ya san halin matar shi ba ta da b'oye-b'oye da wani abu ya faru tabbas da ta fada masa. *********************** Azumi ya kan kama Safnah ta zo hutu gidan yayar ta, dan haka koda yaushe suna tare da Umaimah, tare suke yin girki kullum Safnah na koya mata na zamani dan tafi kwarewa wajen su, ita kuma Umaimah tafi gwanancewa ana gargajiya, dan kuwa Haroon su yafi so, amma a saka kaya yafi son na turawa, yana son yaga matar tashi na d'ame ko ina na jikin ta ya dinga  juyawa. Haroon shi kan shi yana mamakin gano yanda yake da tsananin buqatar matar shi bayan ya yi aure wanda a da da ya kame kan shi kafin yayi aure har tinani yake anya lafiyar shi qalaou kuwa? Sai yanzu ya gane ashe zina ma waje ta samu, in kai exposing kan ka a gare ta sai ta mamaye ka, amma in ka kame kan ka daga barin ta sai kaji baka da wata doguwar sha'awa da zata kai ka ga halaka duniya da lahira, idan ka biye wa zina sai ka gama jin daɗin lokaci qalilan saita guje ka,Allah na taimakon bayin shi da suke qoqarin nesanta kan su daga zunubi, amma wanda suke kusanta kan su daga zunubi sai Allah ya barsu da iyawar su tin da sun sauka daga hanyar shi, Umaimah ce taje wucewa ta gaban shi da wasu qananan kaya a jikin ta, Haroon ya kauda kan shi da sauri yace mata, "Dan Allah je ki saka doguwar riga, azumi fa ake yi ni kar ki min targade a azumi na" Dariya sosai Umaimah ke yi masa, saboda rigar doguwa ce amma mara hannu sai ta haɗa ta da dogon wando, sannan akwai hula akan ta kuma bata shafa komai ba a fuskar ta na kwalliya,kawai kayan sun haɗu ne kuma sun karb'i jikin ta sosai,turare ma baya baya ta sanya, wai amma shi a haka yana jin wani abu game da ita, wanne irin abu ke damun mijin nan nata ne haka? "Sai dai kuma in barin gidan zaka yi gaskiya tinda dai naga doguwar riga ce a jikina" "Assalamu alaikum" "Wa'alaikumussalam" "Yauwaa Aunty Hauwaa, thank God u ar here, dan Allah me ye matsalar riga ta?" "As in, ban gane ba ku fahimtar da ni?" "Ba komai rabu da ita,me zaku yi mana ne yau?" Murgud'a baki Umaimah ta yi ita kan ta tana mamakin ina ta koyi rashin kunya haka, daya mata abu sai ta murgud'a masa baki,kallon ta ya yi ya qanqance ido ya ce, "Dani kk?" Ta sake murgud'a bakin tace masa, "Eh din" "Ba matsala na yafe maki yanzu, Allah ya kaimu a sha ruwa Lafiya" "Asha ɗin mana wake tsoron ka?" "Ba komai bari dai a sha ruwan" "Kun ga ku bari in ansha kun lalibo mai tsoron wani a cikin Ku kun ji? yanzu ki tashi muje mu fara shirin yin abin shan ruwa lokaci na tafiya," Aunty hauwaa har yau kunyar Haroon take ji in ana maganar da ta danganci soyayya, shiru ta yi tana murmushin yaqe ta faɗa kitchen ɗin umaimah, dan yau a wajen ta zasuyi aikin. Bayan sun kammala ne suka d'ebi abincin suka baje shi a tsakar gidan, inda suke haɗuwa har Ishaaq a ci, watarana kuma a bangaren su hauwaan suke bazuwa a tsakar gidan su sha ruwa. Umaimah ce tayi wanka ta sanya doguwar riga sannan ta saka qaramin hijabi kalar rigar, ba tare da tayi wata kwalliya ba, mai kawai ta shafa sai turare shima sama-sama, zama ta yi ta dauki qur'ani tana karanta wa tare da jiran dan lokacin daya rage yayi  suje wajen shan ruwa, karatu take ta rerawa cikin muryar ta mai daɗin sauraro, Haroon ya shigo sanye da jallabiyya fara sol da hula itama fara, hade take da wandon ta rigar ya dage shi sama ya fito a ustaz ɗin shi sak. Zama yayi suka ci gaba da karatun a tare suna ta yi aka fara kiran sallah, suma suka kai aya suka ci gaba da bin kiran sallah, bayan sun kammala suka yi addu'ar da ake bayan kiran sallah tare da salatin annabi. Addu'a suka yi tayi wa kan su, kowa da abinda yake roqa na alkhairi akan dan uwan shi. "To baqaqen larabawa kuzo muje mu sha ruwa Allah ya amsa," Tashi sukai suka bi bayan Safnah, Ishaaq na ganin sun fito ya hau kama ciki shi a dole yunwa yake ji, dariya suka yi tayi suka zauna suka fara da dabino, sannan Ishaaq ya sha kunun gyad'a, Haroon kuma baqin shayin da Umaimah ke haɗa masa kamar na ibada ya sha, baya rabuwa da shan shayi matan kuwa da fruit salad suka fara. Bayan sun gama karya azumin suka koma kan sallaya da suka shimfida Haroon ya ja sallah suka yi magrib. Suna idarwa suka ci gaba da cin abincin su suna hira, sosai suke hira ana ta nishadi, can Umaimah tace, "Dan Allah ka barni na koma gidan Yah umar ganin baby, kaga ga Safnah da Aunty Hauwaa ma sunce zasu je, gobe kawai sai muje ko?" Kallon ta yayi ya haɗe fuska ya ci gaba da cin abinci, mugun kishin ta yake ji baya son tana fita, in ta fita ji yake kamar kowa ma kallon ta yake yi. "Ni dai na amince maku ku je amma ban san me gidan naki ba ke Umaimah ko ya amince ko yana jin mulki, dan naga mulkin masu gidan ya motsa," Bai san sanda ya sa dariya ba wai mulki,cikin dariyar ya ce, "Yah ni ban san yawan yawo ne fa," "Ziyara daban yawo daban, in kana so ba sai kawai ka kaisu da kan ka ba, in sun gama su maka waya ka dakko su, ko me kace?" "Allah ya kai mu goben yah,"....... ❤ [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 29: Azumi nada kwana 25 Jameelaa tai wa Mamalo waya dan tabbatar da amincewar ta akan karbar bashin da za su ci bikin suna dashi, a cewar ta gwanda su Karb'a da wuri su sai kayan da zata saka a kai dinki, in yaso daga nan ma sai su sayi duk wasu abubuwan da za a raba abikin suna wanda ba zasu ɓaci da wuri ba. Mamalo ta tabbatar mata da amincewar ta akan karb'ar bashin, a take kuwa ta bugawa qawayen nata waya ta yi masu bayani kuma cikin qanqanin lokaci kowacce a cikin su ta aminta da a sake bata tinda ba ta yi wasa da wancan da aka bata ba ta dawo da shi akan lokaci,kuma ma dai su basu da wata lalura da shi kamar yanda ita mai iyali take da buqatar kud'in. Godiya tayi ta masu sannan ta tura account no da zasu tura mata kuɗin, bata jima a zaune ba kuwa ta ga alert na kimanin dubu dari biyu sun shiga wayar ta,Mamalo ta sake kira dan taji ra'ayin ta akan irin kayan da take so, cikin tsananin farin ciki da nuna godiyar ta Mamalo tace, "Na gode qawata Allah ya saka da alkhairi ya bani ikon biyan wannan bashi,to ni yanzu ai kune idon gari, kin san kayan da ake yayi kawai ki siyo min a kai ɗinkin," "To shike nan zan dinga rubuta komai aka siya na ajiye saboda ki ga nawa aka kashe kuma a ina aka kashe su, zan ajiye a waje na dan kar lissafi ya b'ata watarana, inshaa Allah sai dai ki ji na aiko maki telana ya gwada ki," "Na gode sosai qawar rufin asiri," "In Allah ya kaimu ki ka haihu lafiya kuwa har qawaye na 'yan gayu sai na gayyata dan in d'aga darajar ki kema a wajen matan lungun mu, zaki ga yanda sunan ki kema zai yi aji ya zama abin bada labari a unguwar mu baki ɗayan ta," Mamalo cikin washe baki ta hau godiya,bayan sun yi sallama Jameelaa ta buga tsaki ta ce, "Ke dai za ai suna me kyau yarinya amma ai ke kan ki kin san ba zan bari ayi wanda zai fi nawa ba ko? Tin da ba hauka nake yi ba," Umar ne ya shiga parlourn ya zauna gefen Jameelaah tare da fadin, "Ke da wa kike magana kuma?" "Ba kowa tasbihi nake yi," "My love kina burgeni gaskiya, kina da yawan ibada da tsoron Allah, Allah dai ya qaramin qaunarki," "Ameeen Abban Humairah," "Dan Allah ina son zani asibiti gobe, naga tana yawan kuka naje naji meke damun ta," "Subhanallahi haka kawai take kuka ko sai an taba wani wajen?" Kame-kame ta fara yi dan ganin yanda Umar ya rud'e, ta rasa ma me zata ce masa, daga baya ta ce, "Ina jin kunne ke yi mata ciwo ko kuma ciki kasan shi ke rud'a yara, ana zaune qalaou in ta rikice da kuka rasa inda zan saka raina na ke yi," "Ehh gaskiya ya kamata ki kaita asibiti, goben zan aje ku sai na wuce, in kin gama ki min waya sai na zo na ɗauke ku," "Habaaa kana kula da marasa lafiya zan taso ka? Ka bari kawai zamu dawo nan nan da asibiti ka aje mu kawai kaje zamu dawo, inna dawo zan maka waya na sanar da kai," "To shike nan Allah ya kaimu," "Ameen ya Allah" Har aka sha ruwa Umar bai ga Humairah ta yi kuka ba, na d'aga hankalin da za a ce bata da lafiya, haka dai ya bar maganar yayi tinanin wataqila da baya nan tayi kukan har Jameelaan tayi tinanin ko kunne ke damun ta, bari ya barsu suje saboda kwanciyar hankalin su baki ɗaya. Da sassafe kuwa suka shirya dan  kar ta samu layi a cewar ta,ai kuwa qarfe 8 a asibiti ta yi musu, yana fita ta wuce ta je ATM ta cire kuɗin siyayyar ta tass ta koma asibitin dan cin lokaci, sai da taga likitan yara aka duba su ba abinda ke damun yarinyar aka haɗa su da paracitamol in case in tayi kuka jikin yayi zafi, tinda tace in tana kuka jikin ta har zafi yake yi sai a bata. Godiya tayi ta fita sai kasuwa, siyayya ta yi tayi na dik abinda ya dace, harda su sarqa da dan kunne da abun hannu, takalma da jaka, abubuwan da zasu raba abikin sunan dik sai da ta siya, ta wuce wajen telan ta ta bada ɗinki tace ya yi ɗinki dai-dai nata amma ya rage ta sama saboda Mamalo bata kai ta girman qirji ba. Sai da ta cake masa kud'in ɗinki sannan ta tafi tsohon gidan su ta je ta kai wa Lantai sauran kayan ajiya, tace na Mamalo ne in suna ya zo dasu za ai amfani ta aje mata bata son Mamalo ta san tayi mata wannan siyayyar. Ai kuwa Lantai ta dinga sa mata albarka tana godiya sai addu'a take Allah ya bar masu qawancen su har aljannah. Sai da ta kammala komai ta koma gida ana kiran azahar lokacin da ta isa,sannan ta ɗauki waya ta kira Mamalo ta yi mata bayanin komai, Mamalo harda kuka dan farin ciki a ganin ta bata da masoyi yanzu sama da Jameelaa. Suna yin sallama ta kashe ta kwanta a gefen Humairah da ta yi baccin wuya dan kuwa yarinyar tayi kuka har ta gaji tayi bacci, tinda suka fita bata samu ta shayar da ita ba,sai da suka dawo din tana waya tana bata mama, har bacci yayi gaba da ita. "Mamalo kin gama cin gudummawar ki na suna a wannan wahalar dana sha, ko a nawa ban wahala haka ba," A haka suka yi ta shirye-shiryen suna a boye, daga wannan lokacin Mamalo kuwa dik maqotan ta samu take ta ɗan shiga a gaisa, wai a nata shirmen a haka za a saba har a ɗan samu su yi mata wani abu idan ta haihu (kamar aje su tayi, da can ba ai zumunci dan Allah ba sai dan a bata abun suna, hummmm). Bayan kwana uku da kammala siyayyar komai da suke da buqata Mamalo ta tashi da naquda, naqudar ta zo mata da sauqi sosai dan kuwa bata dad'e tana yi ba Sadeeq ya kai ta asibiti suna shiga d'akin haihuwa da mintoci Mamalo ta haifi yaron ta mai matuqar kama da mahaifin shi, sai dai wani babban abun tashin hankalin Mamalo bata haifi yaron nan a raye ba, dan kuwa ko kuka bai yi ba da aka haife shi, ai kuwa tana farfadowa daga azabar haihuwa ta dinga washe baki tana a miqo mata abinda ta haifa ta gani, kowa a wajen shiru yayi, Midwifes ɗin da suka amshi haihuwar Mamalo ita da wata a d'akin sune suka mata bayanin komawa da ɗan ta yayi, wata qara ta saki ta hau jijjiga idanun ta suka qaqqafe, a guje suka fita dan kiran Dr. Jariri kuwa na hannun Mahaifin shi wanda ke ta kuka saboda rasa babyn shi da yayi, ga kuma halin da Fateeman shi ke ciki. Likita ne ya shige dan duba Mamalo, ko wanne taimako daya dace a bata an bata, sai dai inaaa shi alqawarin Allah in ya cika ba mai hanawa, kowacce mai rai zata dandani d'aci na mutuwa, Mamalo ta koma ga mahaliccin ta sakamakon kid'imewa da ta yi dan jin ɗan ta bai zo da rai ba, komai dawo mata yayi a lokacin ta hau tinanin kuskuren data tafka na amsar bashi mai yawa gashi yaro ya mutu kuma bata sanar da ko da mijin ta bane abinda ta aikata,wanda aka amshi bashin domin shi ko qamshin duniyar ma bai shaqa ba ya koma, hakan ne ya sa zuciyar ta bugawa ta bi bayan ɗan nata. Sadeeq kuwa qaramin hauka ya hau yi masu a asibitin, da kyar aka samu ya nutsu, ya zauna a qasa ya dafe kan shi ya dinga rusa kuka, tabbas yayi rashi, yayi babban rashin abar son shi, ba zai taba samun kamar Fateen shi ba. Da kyar ya iya ɗaukan waya ya kira Malam Buba mahaifin Mamalo ya sanar da shi rasuwar Mamalo da abinda ta haifa, Malam Buba  shima kid'imewa yayi 'yar tashi guda ɗaya tilo yanzu ta zam babu, Lantai kuwa da ya sanar mata suma ta dinga yi. Mahaifan Sadeeq sun samu halartar gidan su Mamalo sun miqa ta'aziyyar su ga iyayen ta,Sadeeq kuwa baya imm baya imm imm yanzu da ya zauna tinanin irin rayuwar jin daɗin da suka gudanar a gidan su yake yi shi da Fateen shi. Jameelaa bata tashi jin rasuwar Mamalo ba sai washegari, kuka ta dinga yi tana kumawa cikin ranta tana fad'in 'Na shiga uku ni Jameelaa na lalace na d'akkowa kaina jaraba da bala'i, yau ya zanyi da bashin waɗannan bayin Allah dana amso ba tare da sanin kowa ba? Ga shi ba wanda ya san ma na amso mata sai mu ya mu kawai balle na kafa shaida, dan Allah Mamalo ki tashi na san baki mutu ba, wayyooo Allah na ta mutu ta barni da bala'i,' Mutane sai riqe ta ake yi sanda ta shiga gidan ta tabbatar da gaske Mamalo mutuwa ta yi, wasu sun zaci tsabar shaquwar dake tsakanin su ce ta janyo ta shiga halin damuwar da take ciki, nan kuwa ba su san me ke cikin ran ta ba na damuwar inda zata samu dubu ɗari biyu ta biya bashin da suka ɗauka take yi. Umaimah ma ta samu zuwa gaisuwar rasuwar Mamalo, mutane sun samu zuwa sosai saboda abun ya girgiza kowa, maqotan ta sai yabon ta suke yi, suna tina yanda take shiga a 'yan kwanakin, (dik da basu san abinda ke kai ta ba amma sun bada shaida mai kyau akan ta) Bayan sallah qarama da sati ɗaya Qawayen Jameelaa suka fara doka waya suna tambayar ya suka ji shiru, qarya ta zabga masu da cewar har yanzu qawar ta ta bata haihu ba, ko da ta kashe wayar tinani ta dinga yi ko sata zatai a wajen Umar ne ta biya su? To ta yaya zata saci har dubu ɗari biyu bai gane ba? Ko da da take sata ma qananan sata take yi ba manya haka ba. Dik wani irin tashin hankali Jameelaa ta shige shi a wannan lokacin,kayan sawar da aka d'inka aka kawo mata a ranar ta fara cigiyar masu siya, haka kuwa aka dinga yi mata tayin walaqanci, a haka ta saida kayan wajen dubu hamsin banda kud'in ɗinki da ta bayar wajen dubu arba'in, kuka kuwa Jameela ta dinga yi wanda ta rasa mai lallashi. Wanka tayi ta fita ta bar Humairah wajen Kulu Umar ma bai san zata fita ba, gidan su Mamalo ta je, da sallama ta shiga suka gaisa da kowa ta nufi d'akin Lantai,Lantai na zaune ta zabga tagumi tana tinanin d'iyar ta hawaye sirara na bin kuncin ta, dan kuwa bata san sanda zata ji sanyin wannan rasuwa a ranta ba, 'yarta ta kenan guda ɗaya bayan sun gaisa da Jameelaah a mutunce ne Jameelahn ta ce, "Lantai ki kara hakuri kin ji?hakurin dai zamuyi baki ɗaya dole, Allah dai ya jiqan ta," "Ameen Jameelaah ba abinda zan ce maki sai godiya, kin gwada min soyayyar da kike wa Mamalo domin Allah ce, Allah ya albarkaci rayuwar auren ki kema," "Ameenn Lantai......immmm.... damaaa.... na zo ne akan kayan dana kawo kwanaki, dama a gaskiyar magana bashi muka ci ni da ita, dan a fita suna lafiya kar a ji kunya, yanzu na zo na amsa na sai da su ko da ba su kai kud'in dana siye su ba na haɗa da kud'in wajena na biya masu kuɗi kud'in su, yanzu dik sauran kud'in ni zan cika na biya gashi banda ko sisi, tinda abunnan ya faru hanyoyin samuna suka toshe gaba ɗaya kamar an datse min su, ko nera dubu Abban Humairah bai sake bani ba" Cike da bacin rai Lantai ta kalli Jameelah ta ce, "Kan uban can ! auuuu ina yabon ki sallah zaki kasa alwala Jameelah? Ina ganin Mamalo bata da masoyi sama dake ashe har yanzu halin ki na nan na son abun duniya? Yarinyar ma ta mutu amma ba zaki bar ta ta huta ba?" Wani irin tashin hankali ne ya rikitowa Jameelah ta ji kamar zata zaga dan tsabar damuwar da take ciki, cikin fitar numfashi sama-sama ta ce, "Ba haka bane Lantai da gaske bashi muka ci wajen qawaye na ni da marigayiya yanzu haka sai waya suke yi min nayi qarya nace bata haihu ba, dan Allah ki rufan asiri ki ban naje na siyar na haɗa dana hannu na na rage wata asarar,ki barni naji da biyan sauran kudin, in baki biya bashin bane ma zata wahala a qabari, dan kuwa tana cikin azaba dan akwai bashin mutane akan....." Gaffff naji qarar duka ya sauka a bakin Jameelah, ai kuwa Jameelaah ta buɗe murya tun qarfinta ta zunduma uban ihu ta dafe bakin ta da ya fashe, tana kallon Lantai a tsorace, Lantai kuwa cikin tsananin fushi da bacin rai ta ke nuna Jameelaa da yatsa ta ce, "In kika kuskura kika sake kira wa yarinya ta azaba a qabari na rantse sai kin kwashe haqoran ki a qasa, dan uwar ki tashi ki bar nan, ki kira kotin qoli ta amsar maki kayan matsiyaciya wadda bata san mene ne mutunci ba," Qofar dakin Lantai kuwa nan da nan aka taru ana son jin me ya faru, Jameelaah kuwa sai tayi gum da bakin ta dan tasan tonuwar asirin Mamalo tonuwar nata asirin ne, Lantai ma ba zata so wannan labarin ya fita ba itama, tankad'a Jameelaa waje ta yi, daga dakin ta, sannan ta ce, "Kar ki bari idona ya sake shiga naki mara mutunci, ki bar nan gidan ko na qarasa maki abinda na fara dan kuwa sai na cire maki haqori" Jameelaah ba baki sai ido haka ta d'au jakarta ta fita a qofar gidan ta sai ruwa ta wanke bakin ta dake fidda jini ta yi gida. Ita dai yau ta shiga uku ina zata nemo dubu ɗari da goma ta biya bashi? Ko wajen Mum zata ta roqa ne? Ko zuwa zata yi ta kai dubu arba'in wajen malamai su juya mata da kan Umar ya mata kyautar wannan maqudan kuɗin a dare ɗaya, ko kuma yau zuwa za ta yi ta sha maganin mata da ake cewa gida ko mota ko kyautar kujerar makka wataqila idan Umar ya gigice zai yi mata kyautar da zata wanke mata takaicin bashin da suka gingimo ba mai biya???? *A cikin shawarwarin nan da take yi, wanne ne kuka zaba?* *Ina ma masoyan Mamalo ta'aziyya rasuwar takuyi hakuri, haka labarin yazo, na san ba za kuji daɗi ba amin afuwa* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 30: Zaune take ta saka sarqar da Umar ya bata ta zinare a gaba  tana ta kallo, tinani take yi ko saidawa za ta yi ne ta fidda kud'in mutane dan rufuwar asirin ta, dik da dama ba son komawa makaranta take yi ba balle a gano maqaryaciya ce ita,dan kuwa  in ta bari magana ta fita ajin ta ya zube a wajen kowa da take huld'a da shi a makarantar,ko a wajen qawayen ma bata isa magana ba sai dai su rabu, dan ba su son harkar qaranta su. Kukan Humairah ne ya dawo da ita daga dogon tinanin da ta tafi, can ta hango ta gefen gado da dikkan alama fad'uwa tayi, sai tsala ihu take yi kuwa kamar zata tsaga gidan, Kulu ce ta shiga dakin tana tambayar lafiya? Ita kanta kulu ta kula da yanda gaba ɗaya yarinyar bata samun isasshiyar kulawa daga wajen mahaifiyar ta sam. Kuka Jameelaah ta fashe da shi dama ta kai iya wuya wajen quluwa da shiga damuwa, a gigice kulu tace, "Subhanallahi uwar d'aki na me ya same ki haka ki ke kuka? Me ya same ta itama naga gefen kan ta yayi ja kamar ta bige? kawo ta nan na gani," Kuka kawai suke tsalawa daga Jameelahn har jinjirar ta, ji take ko zata sanar wa Umar me ya faru ne dan ya biya kuɗin a huta, amma ba zata so ya gane ta amshi bashi da sunan Humairah ba ba zai ji daɗi ba tinda komai ya yi iya yin sa dan yaga ya wadata su da duk abinda suke da buqata,cikin kuka Jameelah tace, "Dan Allah Kulu kin san inda ake saida gwal?" Kallon ta kulu tayi da mamaki tace, "Eh na sani, amma uwar d'aki na me zai kai ki saida kadarar ki?" "Ba ruwan ki ni dai kawai ki nuna min muje yanzu kafin Abban ta ya dawo muje mu dawo," "Ai kuwa sai dai ki bari ya dawo yaci abinci ya koma, sannan muje dan kuwa ya kusan dawowa," Wasu hawaye ne masu zafi suka sake zuba mata, tabbas ta dakkowa kan ta masifa har da bala'i, amma kuma ta san wannan bala'in da take ciki dik Mamalo ce ta jefa ta a cikin shi, da ta sani da bata amsar mata bashin ba, gashi komai nata ya tsaya cak bata samun ko sisi tunda ta karb'i bashin har lokacin mutuwar Mamalon ita da Umar a rana sai ya bata 5k, wataran ma aje kuɗi yake masu yawa yace in tana so ta d'iba ta yi hidimar gaban ta,amma yanzu ko ɗari biyar bata haɗa su tinda abunnan ya faru baya barin sisi ma a gidan dika,hanyoyin samun ta sun qare tasss, rarar 30k data samu a sunan Humairah da ta san haka zai faru data adana bata kashe a banza ba, a qallah ai da ta d'aga dubu saba'in yanzu gashi ɗan abinda ya rage a ciki take ta kuɗin mota shiga can fita can duk dan ta rufawa kan ta asiri. Har Umar ya shiga parlourn bata sani ba tana nan zaune tana tinanin da ba mafita, sallama yayi ta yi kafin daga baya ta tsorata ta miqe tsaye tana amsawa. "Ya akayi ne? My love kwana biyu na kula kamar baki cikin nutsuwar ki me ye matsalar ki ne? Faɗa min na yi maki maganin ta,dan kin san ni a duniya bana son na gan ki cikin damuwa ko ya ya ne ba tare da na kawo maki qarshen ta ba" Hawaye ne ke qoqarin zuba mata ta danne, ba zata yi subul da baka ba, dole ta rufe magana har sai taje ta saida sarqa, in kuɗi bai cika ba ta roqa ya cika mata. "Ba komai kawai na gaji da zaman gidan ne, anjima ina son zuwa gida na gaida Mamana, wataqila naji daɗi," "Indai wannan ne kar ki damu, bari na ci abinci muje na ajiye ku," Bai jira me zata ce ba ya fita parlour ya zauna kan dinning din su madaidaici mai kyau na glass ya fara zubawa kan shi abinci, sauri tayi ta shirya, ba komai indai zata samu ya aminta ta fitan ai tayi satar hanya suje su siyar su koma gidan nasu sai yaje can ya ɗauke ta. Tana gama shiryawa ta d'ebi kayan Humairah ta kaiwa kulu dan ta sauya mata, shiryawa sukai sika karkashe kayan wuta da fitilu na gidan (a dinga kulawa nan gaba kadan sanyi za a shiga, a saba da kashe kayan wuta kan a bar gida, Allah ya kare) Keys din shi ya koma d'aki ya ɗauko suka fita suka shiga mota sai gidan Hajiya Ramai, sarqar da d'ankunne na maqale a jakar ta, har da abun qafar dika ta d'akko. A qofar gida ya ajiye su ya ce in ya dawo ɗaukan su ya gaida Maman ta kafin nan ma Baba ya dawo. A qofar gidan suka maqale sai da suka daidaici ya tafi suka fita a qafa suka tsaida mai adaidata sahu suka haye sai kasuwa, wajen saida gwalagwalai nan kulu ta kai su,suna isa bayan sun tattauna akan saida gwal ɗin nata ta miqa dan a auna, zafi ya dami Humairah sai zanyara kuka take yi amma ko a jikin Jameelaa ita dai ta d'aga ajin ta wajen qawayen ta kar su yi mata terere. Dubawa akai dika sarqa da dan kunne zobe da abin qafar ya kai dubu dari hudu da sittin , wata iriyar shewa ta saki a kasuwar, nan da nan tace ta siyar babu ko ciniki a tsakanin su, ai kuwa da jin haka sai suka lalo kuɗin ta casss suka bata,dubu ɗari da saba'in ta dauka ta miqa sauran tace a bata wata sarqa da dan kunne ko da ba abun qafa da zobe. Nan kuwa suka bata wasu masu shegen kyau har ma da zobe amma bai kai wancan girma ba a haka Jameelah tai ta murna tana godewa Kulu, nan ta ɗauki Humairah a gaban masu saida gwalagwalan ta zaro nono ta fara bata tana ta hira da shewa da murnar samun warakar matsalar ta, Kulu sai kakkare ta take yi dan sai taji wani irin kunyar ganin Jameelaa na shayarwa a gaban kowa, aiko mazan wajen sun ga N*** a arha ba su biya ba, sai kallon ta suke yi suna ta biye mata ana ta hira. Sai da Humairah ta qoshi suka koma gidan Ramai dubu biyu ta zara ta bawa Kulu kyauta dan murna. A nan ne take zayyanewa Ramai dik abinda ya faru suka jajantawa juna, amma Ramai tace Allah ya kashe ta Lantai bata isa taci wannan jakunkuna da takalma da sauran kayan ita ɗaya ba, ko su raba ko ta tona mata asiri, sai da Ramai ta gwammace bata faɗi haka ba, nan Jameelaa ta dinga masifa da bala'i tana wa Raimai warning akan kar taje garin fad'ar ta aro wa mamalo kuɗi a gano ita ma aron kuɗi tayi taci suna ajin ta ya zube. Da kyar Ramai ta hakura itama, tai ta wa Jameelaa faɗa akan wautar da ta yi, "Yanzu akan kare ajin ki shine kika bar ma matar nan kayan kuɗi masu yawa haka," "Na bar mata ɗin Ramai,barta taci da ace ma Bukar har yanzu yana taɓa sace-sace da shi zan aika ya saton amma tinda baya yi yanzu dole na hakura da dai ajina ya zube, kin ko san sai kowa na lungun nan ya sani? Wataqila magana ta bazu har gidan surukaina, inaaa ba zan iya ɗaukan wannan abun kunyar ba batta kawai taci Allah ya isa" "To ni yanzu me zan samu?" "Kamar ya fa? Ke wai Ramai me yasa dik qoqarin da nake baki godewa Allah akai ne? Kina fa jin bala'in dana shiga fa wanda yanzu haka du kuɗin nan wasu qattin zan bawa banci nanin ba ga nanin nan na ci na," "Ko dubu ɗaya ba zan samu ba kenan Jameelah a wajen ki?" Cikin fushi ta buɗe jakar ta ta zaro dubu ɗaya ta miqa mata ranta a mugun bace,ba kunya kuwa Ramai ta amsa ta soke a bra,Kulu kuwa na zaune ta na ganin ikon Allah gaba ɗaya uwar da d'iyar ba tarbiyya. Qarshe da suka tashi hirar wajen malamai sai suka bawa Kulu Humairah wai suje parlour su sha iska. Ita da ba qaramar yarinya ba, sarai ta gane za ai wata maganar rashin gaskiyar ne. Sai da suka kammala tsara yanda za a kai umar gidan wani sabon boka, dan sun gaji da bin malamai ba nasara gwanda yanzu suje wajen tsafi sosai, suna son albashin shi yana damqawa a hannun Jameelaa, yanda ba zasu dinga matsalar kuɗi ba. "Amma fa kema sai kin saki kuɗi aiki zai kankama shegen maqon kuɗi gare ki," "In da ina samu ɗin ai ba sai an kaishi wajen kowa ba, babu ne shi yasa, ɗan wanda yake bari a gida bai wuce dubu goma ko ashirin shikenan fa, tinda ma na shiga matsalar nan ko sisi bai bari yanzu, ke kuma komai sai kice sai an kawo kuɗi, wasu iyayen da kan su suke nemawa yaran su taimako ba sai sun biya ba," "Laaaa kin raina wanda nake yi miki kenan Jameelaah, Allah sarki ashe dik wahalar da nake in shiga tafasa da mazamfari saboda ke baki gani, daɗi na dake rashin godiyar Allah," "Yanzu dai ki yi hakuri, in Allah ya yarda zan sake hannu dan kuwa ina cikin matsalar kuɗi gaskiya" "Shi kenan zako ki ga aiki dan kuwa ana yabon bokan nan sosai," Baba ne ya dawo, ya siyo kayan marmari Ramai ta Karb'a ta yanka ta raba sannan ta kai masa abinci da ruwa, sai da ya gama cin abinci sannan jameelaa ta shiga suka gaisa, yaji daɗin ganin ta sosai itan ma haka, fatan alkhairi yayi mata sannan ya mata nasiha sosai akan komai za ta yi ta dinga jin tsoron Allah, kuma ta bi mijin ta ta yi masa biyayya ta kyautata wa iyayen sa da 'yan uwan sa,ta zauna da maqotan ta lafiya kuma ta maida hankali a karatun ta, ta dinga aikata abubuwan alkhairi saboda yaran yanzu a wajen basu tarbiyya ko ka faɗa masu suna so su ga kana aikatawa kaima kafin su bi,inda Jameelaa wata mai hankalin ce da ta dauka ta zauna lafiya a gidan auren ta ds rayuwar ta ma baki ɗaya, amma yanda ya gama yi mata nasihar  haka ta bar masa nasihar shi a wajen. Umar na tashi wajen aiki gidan su Jameelaa ya je, suka gaisa da iyayen ta sannan suka tafi gida. Washegari da sassafe tai ma qawayen ta waya akan suje su amshi kuɗin su, sun so ta aika ta acc kawai amma tace kash ne itakuma bata son zuwa banki, nan dai suka ce in an tashi daga makaranta zasu je su Karb'a. Kafin su je Jameelaa ta sha wanka ta zuba babbar atampa mai tsadar gaske, ta saka sabon zinaren ta, ta sa Kulu ta qalqale gidan fiye da da, har d'akin Umar yau ya samu arziqin gyara sosai sannan an buga girki mai daɗi da ya ji nama da kayan lambu. Humairah ma an sa mata riga mai kyau da tsada abun dai sai wanda ya gani, ga lemo da zob'o na musamman da ta aka haɗa, tana zaune tana sana'arta ta wato kallo suka shiga mutum uku ne suka samu zuwa, wasun su sunce a Karb'a kawai ba sai sun zo ba. Cikin fara'a ta miqe tana masu sannu da zuwa abinci aka gabatar masu, ai kuwa sun ɗan ci dan daga makaranta suke suna jin yunwa, sannan ta je ta d'akko masu kud'in ta miqa masu cike da izza da taqama tace ko za su qirga ne? "Habaa ai ba komai mun yarda dake, ke din babbar yarinya ce ba kya harkar qaranta," Wayyooo daɗi kashe Jameelaa 'Ajiiiiii kenan Alaji' Ta ayyana a ran ta, zahiri kuwa murmushi tayi tace, "Habaaa ai kune manyan yara, a shekarun ku kuna yin dabarar tara irin wadannan kud'in ai gaskiya ba na biyun ku sannan iyayen ku na ji daku ba qarya" Haka sukai ta yabon juna da faranta ran junan su sannan suka tafi masu ɗaukan su na jira a mota. Umar daya dawo ya ga kwalliyar da Jameelaa ta sha yayi ta yabawa, amma yana mamakin sabuwar sarqar da ya gani a wuyan ta. Qarshe ya gaji ya tambaye ta ya ce, "My love a gaskiya kin yi kyau, na kasa ɗauke ido na daga kallon ki,bayan tsantsar kyau da Allah ya zuba maki ga wata kwalliya da ki ka zuba,kin qawata kwalliyar da sarqar zinare mai ɗaukan ido,ina ki ka samu wannan sabuwar sarqar dan ban san ki da ita ba" Nan take idon Jameelah ya raina fata.......... *Yau na ji daɗin comments ɗin ku gaskiya, Ameen to all ur prayers* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 31: Shiru ya yi yana jiran amsar ta tare da kafe ta da idanun shi, cikin wata jarumta ta tattaro dik hankalin ta waje ɗaya sannan ta yi masa fari da ido, wanda ta san yana jan hankalin shi ta ce, "I am sorry Abban Humairah naso na yi maka suprise ne dama, shi yasa ɗazu nace maka ka kaini gidan mu, dama na je na sauya sabon design ne na sarqar da d'ankunnen yanzu irin wanan ake yayi, kuma kasan mu mata yana da kyau mu dinga sauya abubuwan mu, lokaci zuwa lokaci dan birge ababan qaunar mu" Ta qarasa maganar cikin yi masa wani irin wasan da ya mugun tafiya da shi, lumshe ido yayi tare da sauke numfashi, ya jata jikin shi abun nema ya samu, sai da su kayi romancing junan su sosai sannan ta daga shi,cikin wata iriyar murya Umar yace, "Ina zaki je kuma Ki qarasa binda kika fara mana ko ladan naki ya cika?" Ya qarasa maganar shi yana wani lumshe idanu. "Ina zuwa bari na kaiwa Kulu Humairah na dawo" Tana kai Humairah wajen Kulu ta koma sai da wasa yayi wasa sanan Jameelaa tayi shiruuu, Umar ya matsu ya kammala abinda ya fara amma 'yannan tai mursisi taqi bashi dama. "Come on my love, ya kika tsaya," "Ni ba komai kawai tinani nake yi ne ina son na ɗora ma Mamana jari amma bani da kuɗi, bata son zama ba sana'a" "Indai dan wannn ne zan baki 50k ki kai mata zai isa?" "Anya kuwa kasan fa sai ta sake kayan aiki, ta yi awon dik wani abu da zata yi amfani da shi, sannan...." "Please love ki bar maganar can a gefe ki qarasamin abinda kika fara, i promise to take care of all her needs, i will give her money to start her business again, please love," Jameelaa na jin maganar kuɗi zasu shigo kawai ta ci gaba da gigita Umar hankalin ta kwance bata tsoron Allah bata tsoron cewa mace haramun ne ta amshi kuɗi ko wani abu a dai-dai lokacin da mijin ta ke tsaka da biyan buqtar shi a wajen ta, wallahi dik macen da ke hana mijin ta kan ta sai ta yi ciniki dashi ko sai ta nemi wata biyan buqatar ta ta son zuciya, ko sai ya mata alqawarin wani abu wanda ta san zai cutar da shi to ta sani ko a ina take ko a wanne lokaci za ta koma wajen Allah zata gamu da Allah ta yanda batai tsammani ba, domin kuwa shi zunubi ko wanne iri ne ana son bawa ya bar shi kafin lokaci ya qure masa, mata masu hali irin na Jam Jam a nutsu a ji tsoron Allah, maza masu kuɗi kuna sakewa matan ku su ci arziqin ku, matan ku sune abokan rayuwar ku, masu tara haram ma dan matan su suji daɗi da yaran su suke yi balle kai me tara halal? K akashe kud'in ka ta halal ka more rayuwar duniya da lahira, dan in ka kashe ma mace kud'in ka wallahi at the end kai zaka mora dan kai za ai wa qunshi, kitso, siyan kayan kwalliya, siyan turare, yi ma yaran ka siyayya, rage maka cefane mata muna da tausayi, rashin ganewar ku ne maza yasa kuke mana dik abinda kuke so mara kyau wai dan tsare gida , ka sake zuciyar ka ma mace kaga yanda zata maida kai ɗan lele, sai dai in kaga mace na mugun abu to yar uwar Jameelaa ce,kuma Ramai ita ce maman ta,sannan mata masu karb'ar kuɗi a wajen mazan su dan mazan sun sauke buqatar su ta sha'awa a wajen su su sani da su da karuwai na kan titi 'yan gudu ibinin (Good evening) basu da banbanci. Washe gari Jameelaa ta yi ma Ramai waya akan ta aika Bukar ai kuwa kamar wanda take jira, ta katse wayar ta yi wa Baban Jameelaa qarya da cewa, "Malam Jameelaa ke kira na naji Humairah na ta tsala kuka, wai sun rasa me ke damun ta magani anyi har na asibiti, shine nace bari naje na gwada na gida," Ko d'ago kai Malam Jameel bai yi ba ya ci gaba da yankan farcen hannun sa ya ce, "Yaushe kika zama mai bada maganin gargajiya banda labari Ramai? Da alama kin manta da wayar ki ana iya jiyo qarar mai magana dake tsabar qure mata sauti da ku kai , to ba inda zaki je ki aika Bukar kamar yanda tace ko kuma ki fita ba da izini na ba kamar yanda kika saba,dana gama yanke farce na zan fita anjima zan aiko a kawo cefane, na ga kamar kayan miya sun qare" Cikin jin haushin shi ta amsa da, "A had'o da nama dai ah toh," "Inshaa Allahu za a had'o da shi kuma a daina yi wa jika ta qaryar ciwo irin wannan bana so," "Anyi din" Ta furta a hankali, "Na'am magana ki ke?" "Ince me?😏" Murmushi yayi ya ajiye rezar a saman window ya fita, ya kula har yanzu matar tashi na da halin yara, ji yanda take wani kumbura dan ya yi mata faɗa kuma ya hana ta fita. Bata da zaɓin daya wuce na ta aika Bukar ɗin, dan haka ta faɗa d'akin ta dan ta dan jira ya kammala shirin makaranta ta sanar da shi,in an tashi daga makaranta ya je ya ji meye kiran Jameelaan, Tana nan zaune bacci ya kwashe ta sai zabga munshari take yi Bukar kuwa da yaga tana bacci ya wuce makaranta abun shi, kamar wadda aka maka wa duka haka ta miqe ta hau kiran Bukar, jin shiru ya sa ta sanya mayafi ta rufe gidan ta sa kai zata je gidan Jameelaah da kan ta. Surutu take ta yi ita ɗaya a hanya, akan bari tai sauri ta koma kan wancan jarababben ya koma yaga bata gida,fakam fakam fakam take tafiya cikin sauri,har ta yi nisa sosai tana tafiya amma babu abin hawa, kamar daga sama taji an kwashe ta an watsar a qasa a gefen hanya, wasu matasa ne a kan babur sun yo goyon biyu su na ta yi mata magana dan ba horn a babur ɗin nasu ga qarar babur ga ihun da suke mata amma tana can tana tinanin gidan Jameelaa me za a samu ya sa bata ji su ba har sai da suka iso suka rasa yanda za su yi su kauce mata, qarshe dai suka kwasa ta a saman hanya. A kan qafar ta ta hagu Ramai ta cake ai kuwa nan take ta samu tsagewar qashi,tini ta zube a wajen sumammiya, mutane an taru a kan ta wanda suka buge ta kuwa sun gudu abin su. An duba ta tsaf ba a samu waya ko wani abu da zai nuna daga ina take ba, sabuwar unguwa suke balle a ce wani ya san ta, qafa tayi tsami ta fara kumbura mutane sai video ake yi mata, wasu sun fara rubutun qarya akan videon ta da pictures da suka ɗauka suna turawa social net kamar su facebook, instagram, whatsapp da sauran su, kowa da kalar labarin da yake qirqira akan ta, amma ba masu daɗi bane kaff labaran, an rasa mai taimakawa koda farfadowa ne a samu ma tayi. Wani bawan Allah ne ya kutsa ya hau tura mutane baya yana masifa, "Meke damun ku ne mutanen wannan zamani ? Kun manta da taimako Allah Allah kuke ayi wani abun ku fara qirqirar qarya kuna yaɗawa, yanzu da kuka d'au hotuna da video shine abinda tafi buqata? Ba mai qoqarin kaita asibiti, dubi qafar ta yanda ta kumbura, yanzu da kun tura social net wasu masu qaramin tunanin zasu yi ta sharing, wanda in da wani abun alkhairi aka rubuta da zai amfani al'ummar annabi ba za a yi sharing ba, sai labaran batsa, da videos na batsa, da labarai masu saka shubuha da masu fidda mutum a musulunci ma dika kuji tsoron Allah fa tamm" "Kaii kama min ita mu kaita asibiti daga can sai mu bada cigiyar 'yan uwan ta," "Haka kuwa aka yi nan aka sanya ta a motar bawan Allahn nan ya tuqa suka tafi basu tsaya a ko ina ba sai a asibiti, accident and emergency aka shige da ita nan take likita da nurses suka fara bata taimakon gaggawa da sun ce sai an kawo police, mutumin yace indai basu kula da ita ba ta mutu shi kuma zai maka su kotu. Yana ganin sun amshe ta ya koma gefe ya jira a waje yana hoping ta tashi ta fada masa ita wace ce? a ina take?........ *Hummmm wanda bai ji bari ba zai ji hoho ai, Allah gwai inji Kabawa😂*[08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 32: Koda Baban Jameelaa ya aika da kayan miya gida ɗan aike yafi awa ɗaya bata nan ga kuma gida a kulle, ya gaji da jira ya koma ma Baban Jameelaa ya sanar da shi ba kowa a gidan a rufe ma gida yake,kad'a kai ya yi ya amsa suka ci gaba da aikin su a ran shi yana ayyana, 'Allah ka shirya min iyali na Ramai ba ta jin magana ta dik maganar da na ke mata baya shiga kunnen ta sai da ta tafi hankalin ta ya kwanta' Sai da lokacin tashi daga wajen sana'ar shi yayi ya wuce gida, Bukar na qofar gida zaune yunwa ta gama yi masa illa sai matse hawaye yake kamar ba namiji ba, Baban Jameelaa ne ya dafa shi nan take ya fara shan majina yana d'aga kafad'a tare da share hawaye, "Kayi hakuri Bukar daina kukan haka ya isa, bata dawo ba ko?" "Eh Baba bata dawo ba ni yunwa nake ji, ko karyawar kirki ban ba na fita kuma ban je makaranta da kuɗi ba gashi na dawo tin rana ba kowa, banda kud'in abun hawa balle naje wajen ka ko wajen Jameelaa" "Yi hakuri Allah ya qara maka hakuri akan wanda ka ke dashi Allah ya qara shiryar min da kai, Allah ya yi maka albarka, zo ga dari biyu kaje ka sai wani abun, ga mai soya awara can a bakin titi je kaci, bari na kira wajen Jameelaa nace ta dawo haka tinda ita batai tinanin dawowa ba har yanzu ɗazu na kira wayar ta naji a kashe" Wayar shi ya ɗauka ya fara kiran Jameelaa, Bukar kuwa ya wuce titi dan siyan awara ya ci. Sai da ta kusan tsinkewa sannan Jameelaa ta dauka, "Hello Baba, barka da yamma," "Barka dai Jameelahn Baba babar ku na nan? Ina ta kiran ta baya shiga, tace kina kiran ta ɗazu ko? To kice ta dawo ta bamu ɗan makulli in yaso ta dawo ku kwana anan" "Baba ai nima bata zo ba kuma tin safen nake kiran ta naji Bukar shiru dama nace ta turo shi," "Ah ah, to ina taje kuma?" "Ba ta gida ne?" "Bata gida tin hantsi na aika a kai mata kayan miya bata nan, ina kuma kyautata zaton halin ta data saba ne dana sa qafa na fita itama ta fice, to ina zata je in bata zo nan ba?" "Ikon Allah, bari nayi ma Abban Humairah waya ya faɗa ma 'yan sanda a fara binciken inda taje, na shiga uku," Kuka ta fashe da shi dan kuwa hankalin ta bai kawo komai ba sai ko ta b'ata ne? Ko wajen sabon bokan da tace zata ta tafi ta b'ata a hanya? "Daina kuka ina zuwa naje tsohon gidan mu ko taje masu ziyara," Kashe wayar yayi ya jira saida Bukar ya dawo sannan ya ce ya jira a qofar gidan in yaga ya dad'e bai dawo ba ya je gidan Jameelaa ya kwana, nera dari ya bashi na abun hawa sannan ya tafi. Shi din ma adaidaita sahu ya hau sai unguwar su ta da. Ba binciken da bai ba gida-gida amma kowa sai ya ce ai ta dad'e rabon ta da unguwar ma. Malam Jameel ya fa fara shiga tashin hankali, bai san yana ji da Ramai ba sai yanzu, ada kullum halayyar ta na sa yaji ta fita akan shi, amma rashin ta ya d'aga masa hankali, ko ba komai matar shi ce kuma abar son shi, halayen ta ne abin qi a gare shi. Gidan Jameelaa ya wuce shima dan ya san Bukar baya gida yanzu, koda yaje ya tadda Bukar na cin abinci, shima zuba masa Jameelaa tayi amma haka ya kasa ci, ruwa kawai ya sha ya yi jigum. Umar ne yayi sallama ya dawo daga kai ma 'yan sanda qorafin rashin ganin ta da ba ai ba, Malam Jameel ya shiga matsananciyar damuwa a wannan dare, da kyar sukai ta tausar shi har ya samu ya sha tea kawai, Umar da cewa yayi ya kwana anan gidan amma yace inaa zuwa zasu yi su yanke kwad'on su shiga, in yaso an sai wani. A mota Umar ya maida su shi da Jameelaa wadda sai kuka take tayi, dan bata san wane hali Ramai ke ciki ba. Umar ma dik ya damu ganin habibiyar shi na kuka. Sai da aka buge kwad'on suka shiga sannan suka juya, Malam Jameel bai iya kwantawa ba bayan Bukar yayi bacci ya buɗe qofa ya fita, shiga nan fada can haka yayi ta yawo yana tambayar mutane ko sun ga mace mai kama kaza da kaza. kowa yace masa bai gani ba, zama yayi qofar wani gida yana zubar da hawaye, dare yayi sosai, dan kuwa 12am tayi a lokacin, qoqarin tafiya gida ya ke, wani mutum a babur ya zo shigewa, sauran kadan ya buge shi, kauce masa yayi yana masifa. "Ku dattijan nan sai ku dinga tafiya akan hanya, dazu mai babur ya bankad'e wata dattijuwa yau,sai wahalar neman dangin ta nake ban samu ba, asibitin da na taimaka na kai ta an hana ni tafiya yanzu ma gudowa na yi, kana son na buge ka na koma cikin wahalar dana baro daga taimako," Cikin sauri Malam Jameel ya bi bayan mutumin yana kwala masa kira, "Malam dan Allah tsaya ya kamannin matar yake, ni ma nan da ka ganni neman mata ta nake yi a ina abun ya faru?" Ɗan tsayawa mutumin yayi ya juyo, sannan yayi baya kaɗan inda malam jameel yake tsaye, bayanin yanayin matar da inda abun ya faru ya yi wa Malam Jameel. Sujjada malam Jameel ya koma gefe yayi yana ta godewa Allah,cikin farin ciki ya cewa mutumin, "Bawan Allah na gode Allah ya biya maka dikkan buqatun ka na alkhairi, yanzu faɗan inda uwar 'ya'yana take mata ta ce, tin rana ta bar gida yau kusan gaba ɗaya neman ta muke" Faɗa masa inda ya kai ta yayi sannan ya ce dan Allah yaje gare ta, shi kam ya gama taimakon nasu yau ko wajen nemawa iyalin shi abinci bai je ba, Da sauri Malam Jameel ya dakko wayar shi ya kira no Umar, ya sanar da shi har sun fara bacci a parlour, Jameelaa kwance a jikin shi da Humairah a qirjin ta ta ci kuka har tayi bacci. Ya so sanar ma da Mum din shi amma ta kafe akan bata son kowa ya san ba a ga mahaifiyar ta ba, har sai nan da kawana uku, ko bayan an ganta bata son kowa ya sani, Umar kuwa ko da wasa bai ji yana son sanar ma da kowa ba tunda gimbiyar ta hana. Ai yana faɗa mata an ga maman ta ta miqe a firgice sauran kadan ta kada Humairah ya riqo ta, da sauri ta saka mayafi suka bar gidan basu zame ko ina ba sai asibiti. Ramai ta farfaɗo ciki fal yunwa tin shayin bunu na safe da tasha bata ci komai ba, ta sawa ranta shegen kwad'ai za ta gidan Jameelaa taci me daɗi. Da gudu Jameelaa ta faɗa a jikin ta ta fashe da kuka. "Ramai na me ya same ki haka? Dan Allah kar ki qara yin nisa ki bar ni inna rasa ki mutuwa zanyi," "Gani ai daina kukan kun zo min da abinci? Yunwa nake ji Jameelah tun safe ban ci komai ba" "Ah ah bamu kawo komai ba, tinda bamu tabbatar ke ce ko bake bace, munzo dai muga wace ce,dik da Baba yace yana kyautata zaton ke ɗin ce ma," Kuka Ramai ta fashe da shi, "Ni kuka ya kama Jameelaah kin ganni nan wata iriyar mahaukaciyar yunwa nake ji qirjina har zafi yake min, ban jima sosai da farkawa ba, ban ma san waya kawo ni nan ba, dan Allah ku taimakan da abinci kar ku rasa ni," Umar da Malam Jameel har rige-rige suke dan fita suje shagon dake cikin asibiti su sama mata abin da zata ci. Koda suka kawo mata fresh milk da biscuit ci ta hau yi kamar wadda ta shekara bata ci ba. Tausayin ta Jameelaa tai ta ji Malam Jameel kuwa ba mai gane halin da yake ciki, dan kuwa kallon Ramai kawai yake. Ramai kuwa sai tinanin qaryar da zata shimfid'a masa take tayi amma ta rasa yau dai qaryar ta ta qare. A nan Malam Jameel ya kwana Jameelaa kuwa suka koma gida da mijin ta hankali ya kwanta, dan tsagewar qashi tayi tinda an mata gyara sai a jira ya warke kuma. Ramai ta kasa haɗa ido da Baban Jameela, shi kuma ya qi yi mata magana akan abinda ta yi yana zaune saman kujera a haka yayi bacci. Washe gari Kulu ce ta kawo abinci ita da Umar, Jameelaa ta tashi da ciwon kai saboda rashin ishasshen bacci da bata samu ba, da kuma kukan da tayi. Ramai an kwashi garar da ake so, nama ta dinga tsama tana ci na kaza da dankalin turawa da akai mata farfesun su, Malam Jameel dik kunya ta kama shi, Umar kuwa tinani yake ko dan ta kwan da yunwa ne yasa take cin abincin haka kamar mayunwaciya. Kulu kuwa tsaf ta fara gano halayen su, dan haka ta san tsantsar kwad'ayi ne kawai ba wani abu ba. Satin Ramai biyu a asibitin aka sallame su,randa suka koma kuwa ta sakan kance Baban jameelaa ya manta da abinda tayi, ta sha gayu ta zauna zaman jiran Baban Jameela. Bashi ya dawo ba sai goman dare, lokacin dik kwalliyar ta goge yana cin abinci ya watsa ruwa ya kwanta a qasa, cikin mamaki da gatsali ta ce masa, "Sabon salo, wanne irin abu ne haka zaka kwanta a qasa, na dad'e bana gida yau na dawo shine zaka wani kwanta a qasa?" Ko lashi kan ki bai ce mata ba balle yace ta ci kan ta, tayi maganar tayi surutun ya mata shiru, daga qarshe ma sai minsharin shi ta jiyo yana tashi. Haka Malam Jameel ya qaurace ma Ramai a d'akin su na tsahon sati ɗaya akan sati biyun baya da ta yi tana jinya kamar yanda islam yace in zaka qaurace ma mace ka qaurace mata a daki, ga ka ga ta amma ka hanata kan ka. Ramai fa ta jiga ta matuqa gaya ko hirar da suka saba yi basu yi, bayan sallama da amsa gaisuwar ta baya ce mata ta fasa balle yace sauke. Bukar daga boko yake wucewa islamiyya, dan haka bai wani kula da sauyawar mahaifin nashi ba, musamman da ya zamana shi sukan zauna suyi hira abun su da shi. Yau dai Ramai tayi alqawarin sauke ma kanta wannan hukunci da ake mata, dan haka Bukar na tafiya makarantar boko ta zube gaban shi ta fashe da kuka, tana neman gafara, bai kula ta ba dan kuwa so yake ya ga ko da gaske ta yi na dama, kukan ta na taba shi, amma haka ya kyale ta ya fita wajen aikin shi. Ramai fa har ramewa tayi saboda tsakanin ta da Allah bata son fushin mijin ta, abinda bai taɓa yi mata ba kenan a duk tsawon zaman su, wannan hukuncin na shi ya yi mata tsauri,tun da jajayen sawaye ma ba a hukunta ta haka ba sai yanzu? Da yamma ta dafa masa abincin da ya fi so ta gyara gidan tsaf kamar ba gidan da ta fara b'atawa da qazanta ba, ta saka kayan ta na qarshen adaka, sannan ta kunna turaren wuta a gidan, tana zaune tana jiran dawowar ɗan dattijon mijin ta ko kwantawa yace tayi yau za ta yi ta ba shi hakuri, ba zata iya jure fushin shi na kusan wata biyu ba dan ta horu ainun. Abinda bata sani ba shine shi kan shi Baban jameela ya gaji da wannan hukuncin da yake yi mata, dama nema yake ta bashi hakuri ya huce taurin kai irin nata ya sa ta dad'e bata bada hakurin ba, wajen masu gasassun kaji yaje ya sai masu 'yar guda daya ya wuce gida da ita. Ko da ya shiga sauyin da ya gani a gidan ya sa ya sake samun nutsuwa, daya yi wanka ya koma parlour sai yaga an jera masa abinci a sabbin mazubin da ta zo da su tin sunan Humairah, daya buɗe yaga abincin da yake so ne, ji yayi ya yafewa Ramai dik abin da ta yi masa, ci ya yi ya qoshi ya kora da ruwa mai sanyi. Ramai ce ta shiga da sallama ta durqusa ta fara neman gafara harda kukan ta, dan abun ya gama isar ta ta matsu su daidaita. "Ramatu ni na yafe maki tin tini, ina hukunta ki akan halayen da kike aikata min ne shekara da shekaru, ban niyyar amsa maki ba, nayi niyyar rama shekarun da kikai kina min abinda kika ga dama nima kafin na amsa ki," Zaro ido ta yi ta fara lissafin shekarun auren su, dan in bata manta ba tinda Jameela ta fara girma suka fara samun matsala da shi, in ya hana abu ta kafe shi za ai tsoro taji ya kama ta, "Habaa Baban su ba za ai haka ba, dan girman Allah ka yafe min, in dai ni ce ba zan sake aikata abinda dik ka hana ba," "To shikenan ya wuce ina maki nasiha da kiji tsoron Allah ni ba wai ina hana ki abu bane dan son rai na, ko dan na b'ata maki rai ba, ina hana ki ne dan Allah ya hana ne, Ramatu waye ya halicce ki?" "Allah," "Me yasa in ya hana abu kike yi? Ko kin manta shi ya halicce ki, kuma zai iya ɗaukan ran ki a dik sanda ya so kin manta da hakan ne? Kin manta cewar dik abinda ki kai akwai littafi ana rubuta maki mai kyau ko mara kyau? Dan Allah yanzu ki zauna na baki minti ashirin ki tina a rayuwar ki kaff me kika aikata da in kin je lahira zai tseratar da ke daga fad'awa wuta, sannan me da me kika aikata na haramun da zai kai ki wuta, in kika bawa kan ki amsa, ki zo ki samen a d'aki bayan kin tuba ga Allah, kuma kiyi qoqarin sauya rayuwar ki daga mummuna zuwa kyakkyawa in ba haka ba qarshen zaman mu ya kusa dan ba zan ci gaba da zama da wadda bata ɗauki sabon Allah a abakin komai ba musamman abinda ya haɗa da shirka," K'walalo ido ta sake yi waje ido ya yi mata jawur ga hawaye faca faca, me yake nufi da shirka? "K'warai shirka nace,ko ji kike ban san kina zuwa wajen malamai yan duba ba? Masu sabon Allah na sani Ramatu, komai da kike aikatawa akan idona yake, idona ya rufe da son ki ne a baya amma yanzu in baki gyara rayuwar ki ba kin qoqarta gyara ta Jameelaa ko zan rasa raina gwanda na rasa dana ci gaba da zama dake, kar ki manta ki zauna sai nan da minti ashirin ki biyo ni ki yi tinani," Ko da ya fita ya shiga d'aki, addu'a ya dinga yi Allah ya sa qarshen rashin tarbiyya ne ya zo a gidan shi, Allah ya amsa kukan shi akan shiryuwar matar shi. Ramai kuwa tinda ta fara tinani daga quruciyar ta zuwa yanzu ta d'au sama da awa biyu a wajen bata sani ba ma, kuka ta dinga yi ta na istighfari, da sauri ta d'aura alwala ta shiga d'aki ko ta kan malam bata bi ba ta sa hijabi ta dinga rabka sallolin da bata san iyakar adadin su ba, tin tana yi a tsaye sai da ta ci gaba dayi a zaune, da taji bacci na neman cin qarfin ta ta yi addu'a da neman yafiyar Allah tare da nemawa kan ta shiriya da iyalin ta dika,sannan ta cire kayan adon da ta sha ta kwanta dan kuwa Malam ya dad'e da yin bacci. *********************** Aunty hauwaa da Sapnah ke waya tana bata labarin makaranta sannan ta sanar da ita sauran wata ɗaya ta yi jarabawar qarshe ta dawo gida kwata-kwata "In kin dawo dan Allah ki zauna a nan gidan, kinga wannan cikin nawa shima har ya yi nauyi, na kusan haihuwa, nan da wata biyu inshaa Allahu zan sauka kin san Safiyya mayyar gida ce ba zata zo min ba, ko yanzu inna ce ta dan zo ta taya ni wasu abubuwan ba zuwa take yi ba, ga Umaimah na laulayin qaramin ciki itama kinga ba mun sa matar mutane aiki ba ko?" "Kar kiji komai ai ni ina son zuwa gidan ku,ina wannan matar wan Umaimahn qazamar nan?" "Ohhh ni Hauwaa har yanzu baki manta ta ba watanni nawa yanzu da zuwa gidan nata? Inajin 'yar su ma za ta yi wata biyu yanzu fa," "Allah sarki Aunty ban san me yasa ba haka kawai sai ina yawan tina Yayan Umaimah, ina matuqar son sake sanya shi a ido na,ban san me yasa ba dik da na kula baya kallon kowacce mace da gashi in ba qazamar matar shi ba," "Sapnah kina da hankali kuwa? Kin kuwa san me kike faɗa? Mijin fa wata kike maganar kina son gani?" "Aunty hawauaa ba laifina bane, ni kaina ina mamakin faruwar hakan," "Kinga mu bar maganar nan sai anjima, ki maida hankali akan karatun ki kar ki saka shiririta kin ji ko? Kuma kiji tsoron Allah ki kare mutuncin ki, kar ki biyewa samarin makaranta kin ji," "Eh naji na gode Aunty Hauwaa sai anjima a shafan babyna, ina gaida Umaimahn da Yayana," "Zasu ji" Hauwa shiru tayi tana tinanin Sapnah, Ohhh Allah ya sa ba qalatar son maza qanwar ta take da shi ba kamar yanda tayi a baya.......... *Hummmm Allah shi kaɗai ya san karatun bebe* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 31: Shiru ya yi yana jiran amsar ta tare da kafe ta da idanun shi, cikin wata jarumta ta tattaro dik hankalin ta waje ɗaya sannan ta yi masa fari da ido, wanda ta san yana jan hankalin shi ta ce, "I am sorry Abban Humairah naso na yi maka suprise ne dama, shi yasa ɗazu nace maka ka kaini gidan mu, dama na je na sauya sabon design ne na sarqar da d'ankunnen yanzu irin wanan ake yayi, kuma kasan mu mata yana da kyau mu dinga sauya abubuwan mu, lokaci zuwa lokaci dan birge ababan qaunar mu" Ta qarasa maganar cikin yi masa wani irin wasan da ya mugun tafiya da shi, lumshe ido yayi tare da sauke numfashi, ya jata jikin shi abun nema ya samu, sai da su kayi romancing junan su sosai sannan ta daga shi,cikin wata iriyar murya Umar yace, "Ina zaki je kuma Ki qarasa binda kika fara mana ko ladan naki ya cika?" Ya qarasa maganar shi yana wani lumshe idanu. "Ina zuwa bari na kaiwa Kulu Humairah na dawo" Tana kai Humairah wajen Kulu ta koma sai da wasa yayi wasa sanan Jameelaa tayi shiruuu, Umar ya matsu ya kammala abinda ya fara amma 'yannan tai mursisi taqi bashi dama. "Come on my love, ya kika tsaya," "Ni ba komai kawai tinani nake yi ne ina son na ɗora ma Mamana jari amma bani da kuɗi, bata son zama ba sana'a" "Indai dan wannn ne zan baki 50k ki kai mata zai isa?" "Anya kuwa kasan fa sai ta sake kayan aiki, ta yi awon dik wani abu da zata yi amfani da shi, sannan...." "Please love ki bar maganar can a gefe ki qarasamin abinda kika fara, i promise to take care of all her needs, i will give her money to start her business again, please love," Jameelaa na jin maganar kuɗi zasu shigo kawai ta ci gaba da gigita Umar hankalin ta kwance bata tsoron Allah bata tsoron cewa mace haramun ne ta amshi kuɗi ko wani abu a dai-dai lokacin da mijin ta ke tsaka da biyan buqtar shi a wajen ta, wallahi dik macen da ke hana mijin ta kan ta sai ta yi ciniki dashi ko sai ta nemi wata biyan buqatar ta ta son zuciya, ko sai ya mata alqawarin wani abu wanda ta san zai cutar da shi to ta sani ko a ina take ko a wanne lokaci za ta koma wajen Allah zata gamu da Allah ta yanda batai tsammani ba, domin kuwa shi zunubi ko wanne iri ne ana son bawa ya bar shi kafin lokaci ya qure masa, mata masu hali irin na Jam Jam a nutsu a ji tsoron Allah, maza masu kuɗi kuna sakewa matan ku su ci arziqin ku, matan ku sune abokan rayuwar ku, masu tara haram ma dan matan su suji daɗi da yaran su suke yi balle kai me tara halal? K akashe kud'in ka ta halal ka more rayuwar duniya da lahira, dan in ka kashe ma mace kud'in ka wallahi at the end kai zaka mora dan kai za ai wa qunshi, kitso, siyan kayan kwalliya, siyan turare, yi ma yaran ka siyayya, rage maka cefane mata muna da tausayi, rashin ganewar ku ne maza yasa kuke mana dik abinda kuke so mara kyau wai dan tsare gida , ka sake zuciyar ka ma mace kaga yanda zata maida kai ɗan lele, sai dai in kaga mace na mugun abu to yar uwar Jameelaa ce,kuma Ramai ita ce maman ta,sannan mata masu karb'ar kuɗi a wajen mazan su dan mazan sun sauke buqatar su ta sha'awa a wajen su su sani da su da karuwai na kan titi 'yan gudu ibinin (Good evening) basu da banbanci. Washe gari Jameelaa ta yi ma Ramai waya akan ta aika Bukar ai kuwa kamar wanda take jira, ta katse wayar ta yi wa Baban Jameelaa qarya da cewa, "Malam Jameelaa ke kira na naji Humairah na ta tsala kuka, wai sun rasa me ke damun ta magani anyi har na asibiti, shine nace bari naje na gwada na gida," Ko d'ago kai Malam Jameel bai yi ba ya ci gaba da yankan farcen hannun sa ya ce, "Yaushe kika zama mai bada maganin gargajiya banda labari Ramai? Da alama kin manta da wayar ki ana iya jiyo qarar mai magana dake tsabar qure mata sauti da ku kai , to ba inda zaki je ki aika Bukar kamar yanda tace ko kuma ki fita ba da izini na ba kamar yanda kika saba,dana gama yanke farce na zan fita anjima zan aiko a kawo cefane, na ga kamar kayan miya sun qare" Cikin jin haushin shi ta amsa da, "A had'o da nama dai ah toh," "Inshaa Allahu za a had'o da shi kuma a daina yi wa jika ta qaryar ciwo irin wannan bana so," "Anyi din" Ta furta a hankali, "Na'am magana ki ke?" "Ince me?😏" Murmushi yayi ya ajiye rezar a saman window ya fita, ya kula har yanzu matar tashi na da halin yara, ji yanda take wani kumbura dan ya yi mata faɗa kuma ya hana ta fita. Bata da zaɓin daya wuce na ta aika Bukar ɗin, dan haka ta faɗa d'akin ta dan ta dan jira ya kammala shirin makaranta ta sanar da shi,in an tashi daga makaranta ya je ya ji meye kiran Jameelaan, Tana nan zaune bacci ya kwashe ta sai zabga munshari take yi Bukar kuwa da yaga tana bacci ya wuce makaranta abun shi, kamar wadda aka maka wa duka haka ta miqe ta hau kiran Bukar, jin shiru ya sa ta sanya mayafi ta rufe gidan ta sa kai zata je gidan Jameelaah da kan ta. Surutu take ta yi ita ɗaya a hanya, akan bari tai sauri ta koma kan wancan jarababben ya koma yaga bata gida,fakam fakam fakam take tafiya cikin sauri,har ta yi nisa sosai tana tafiya amma babu abin hawa, kamar daga sama taji an kwashe ta an watsar a qasa a gefen hanya, wasu matasa ne a kan babur sun yo goyon biyu su na ta yi mata magana dan ba horn a babur ɗin nasu ga qarar babur ga ihun da suke mata amma tana can tana tinanin gidan Jameelaa me za a samu ya sa bata ji su ba har sai da suka iso suka rasa yanda za su yi su kauce mata, qarshe dai suka kwasa ta a saman hanya. A kan qafar ta ta hagu Ramai ta cake ai kuwa nan take ta samu tsagewar qashi,tini ta zube a wajen sumammiya, mutane an taru a kan ta wanda suka buge ta kuwa sun gudu abin su. An duba ta tsaf ba a samu waya ko wani abu da zai nuna daga ina take ba, sabuwar unguwa suke balle a ce wani ya san ta, qafa tayi tsami ta fara kumbura mutane sai video ake yi mata, wasu sun fara rubutun qarya akan videon ta da pictures da suka ɗauka suna turawa social net kamar su facebook, instagram, whatsapp da sauran su, kowa da kalar labarin da yake qirqira akan ta, amma ba masu daɗi bane kaff labaran, an rasa mai taimakawa koda farfadowa ne a samu ma tayi. Wani bawan Allah ne ya kutsa ya hau tura mutane baya yana masifa, "Meke damun ku ne mutanen wannan zamani ? Kun manta da taimako Allah Allah kuke ayi wani abun ku fara qirqirar qarya kuna yaɗawa, yanzu da kuka d'au hotuna da video shine abinda tafi buqata? Ba mai qoqarin kaita asibiti, dubi qafar ta yanda ta kumbura, yanzu da kun tura social net wasu masu qaramin tunanin zasu yi ta sharing, wanda in da wani abun alkhairi aka rubuta da zai amfani al'ummar annabi ba za a yi sharing ba, sai labaran batsa, da videos na batsa, da labarai masu saka shubuha da masu fidda mutum a musulunci ma dika kuji tsoron Allah fa tamm" "Kaii kama min ita mu kaita asibiti daga can sai mu bada cigiyar 'yan uwan ta," "Haka kuwa aka yi nan aka sanya ta a motar bawan Allahn nan ya tuqa suka tafi basu tsaya a ko ina ba sai a asibiti, accident and emergency aka shige da ita nan take likita da nurses suka fara bata taimakon gaggawa da sun ce sai an kawo police, mutumin yace indai basu kula da ita ba ta mutu shi kuma zai maka su kotu. Yana ganin sun amshe ta ya koma gefe ya jira a waje yana hoping ta tashi ta fada masa ita wace ce? a ina take?........ *Hummmm wanda bai ji bari ba zai ji hoho ai, Allah gwai inji Kabawa😂* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 33 Mum ce zaune a parlour ita da Umaimah wadda ta kai wa iyayen nata ziyara,suke tattauna wa game da halin Jameelaa. "Umaimah ni fa halayen qawar ki gaba ɗaya sun sauya, rabon ta da ta zo  gidanan har na manta,an ce masu Daddyn ku ba lafiya, Umar yazo yafi sau huɗu amma ita bata zo ba, nima nayi ciwo ko aiki bana zuwa amma yarinyar nan bata zo dubani ba, da na ji sauqi naje dan na ga lafiya suke ko fitowa daga d'aki batai ba, sai da na gaji da zama na tafi, sannan ta min waya wai tana toilet ne, can u imagen, tana toilet for over an hour kenan? Habaa ai dai mai motsuwar kai ma ba zai ɗauka ba balle ni, abinda ya fi ban mamaki jiya na je gidan Kulu ta kawon lemon abarba da suke yi su aje a fridge wai yarinyar nan take tambayar kulu dika ta juyo min? Kulu tace ah ah ba dika bane, sai kulu tace ai yana nan cike da jarka babba. Yau ko dika aka juyo min kuma bata sha ba ai a gani na bai kamata ta yi magana akai ba, kuma tana gama maganar ta shige d'aki ta kwanta tana wasa da yarinya, sai da na gaji da zama bata fito ba na yima kulu sallama na wuce, dan bana son na kai lokacin dawowar Umar ya ji me tamin na haddasa masu rikici," "Hummm Mum ko Malam ma haka yace Jameelah fuska biyu gare ta mune bamu gane ta ba har yanzu, tana da munanan halaye wanda sai mai wayo ne zai gane tana dasu,  nima wataran na kan fuskanci wasu abubuwan a tattare da itan na rashin kyautawa, ga qazantar tsiya, ki duba ki ga lokacin da tana ita ɗaya yanda gidan yake, yanzu da kulu tazo ne aka samu sauqi,amma d'akin baccin su ko dawasa yanda kike da tsafta ba zaki iya shiga ki jima ba," "To ubangiji ya ganar da mu abinda bamu da ilimi akai,ya kawo mana mafita mafi alkhairi," "Mum bari na zo na koma,Malam yace daga kasuwa zai wuce gida, basu da makaranta,gashi har yamma tayi ban kula bama" "Ya kamata ki koma kam,Allah ya maku albarka, ya sauke ki lafiya," "Mummmm, ni dai ban da komai, dan Allah ki daina min irin wannan maganar," "Kinji da gulmar ki,muje na raka ki," "Mum sammin dambun nama da dadaddawa, in kina da kuka a ɗebar min, ina son na yi tuwo yau," "Muje kitchen din, sai na d'eba maki" Komai data lissafa sai da Mum ta d'ibar mata, harda wanda ma bata ce ba driver ya maida ta gidan ta. Haroon ne ke kitchen yana tuqa masu tuwon semo ta yi sallama ta shiga, dariya ta fashe dashi ganin yadda dik ya zubar da garin a qasa, gashi ya shafa wani a gemun shi, sannu da aiki ta yi masa ya maqale kafad'a ya buɗe mata hannayen shi, zuwa tayi ta kwanta a jikin shi, ya maida hannayen shi ya rufe, sannan ya yi mata kiss a wuyan ta lumshe ido tayi, tace "Bari na je na rage kayan jiki na sai na zo mu qarasa girkin tare, da baka wahal da kan ka ba ma babe tinda ga abinci nan na aje maka," "Duba ki ga na tashi da shi tsaf, yau ai a gajiye na dawo kuma da yunwa, kuma na ga ya kamata na taya ki ne, tinda kina yin tuwon nan kullum, na rasa me kike ji a cikin tuwo sam baki gajiya da shi," "Hummm ba zaka gane ba na ma samo kuka da daddawa harda kub'ewa busasshiya, yau ba miyar taushe zan mana ba miyar yauqi zan yi," "Me ciki," "Ni dai bana so, ka daina kirana haka, wani in yaji sai a ce min 'yar....." "Yar me?" "Immm 'yarr...immm shikenan ina zuwa," "Zo nan ba inda zaki je sai kin faɗi me za a kira ki da shi," Matse ta yayi a jikin shi tare da daga mata kai tana kallon shi can ta sauke idon ta tana murmushi tace, "Ɗan sake ni na fada maka ka matse ni da yawa zafi na ke ji," Sassauta mata riqon yayi, ai kuwa ta balle ta ruga daki da gudu tana dariya, "Zan kama ki ne zaki qarasa me za a kira ki dashi," Juyawa yayi ya fara kwashe tuwon dan yayi ba shi da yawa, a leda ya daure ya kashe gas ya fita, bai ɗauke komai ba a wajen ya bar su, sai da ta kammala sauya kaya da wata guntuwar riga mai faɗi daga qasa, daga sama ta kama ta, armless ce rigar kalar baqi da flowrs jajaye, ta saka hula baqa a kan ta. Gyara kitchen ɗin tayi ta zubawa tukunyar ruwa, ta aje a cikin sink, ta ci gaba da haɗa miyar ta tana yi suna hira, shi kuma yana ta mata wasanni, sai kauce wa take amma yaqi barin ta tayi aikin ta da dad'in rai. Sallamar Sapnah ce ta dawo da shi nutsuwar shi ya shige d'aki ya yi zaman shi. "Oyoyoooo Sapnah saukar yaushe? Ba ko waya na tanadar maki abun daɗi?" "Kar ki damu ai gani a yi abun daɗin a gabana naci, me kike yi ne haka, nake ta jin qamshin girkin tsoffi?" "Tuwo nake yi ya karatu?" "Ahhh lallai zamu ci daɗi ashe...karatu sai godiya, mun kammala shi alhamdulillahi yanzu sauran mu jira Allah ya kawo mana miji muyi aure, dan kuwa Abban mu yace sai munyi aure zamu fara aiki," "Masha Allahu, Allah ya taimaka gaskiya na taya ki murna, nima Malam yace inshaa Allahu zan ci gaba da karatu, har sai na ce ya isheni, ina son karatu sosai Sapna," "Yauwa dakata wai dan Allah meye na cewa mijin ki malam? Ki waye mana, ko ɗan sunan zamanin nan ke baki sa masa ba sai wani malam, kamar a makarantar allo, ko bokon yanzu an daina cewa Malam," "Baki da dama Sapnah, Allah ya nuna min mijin ki, na san zai sha gata da tarairaya da kulawa,kuma ni ba Malam nake kiran shi ba ni da shi, a gaban mutane ne nake cewa Malam kawai" "Kwarai da gaske, dan kuwa inna auri mijin da ya iya soyayya shima sai mun fi Lailah majnun soyewa," Dariya suka yi a tare sannan suka tafa,haka sukai ta hira suna qarasa aiki, dan Umaimah ta qara samun wayewa ta zamani tunda ta kula Sapnah na da ita sai ta ce mata, "To yanzu dan Allah bayan Baby wanne suna kike ganin zan dinga kiran shi da shi?" "Ai shi miji ba dole sai suna ɗaya ake kiran shi da shi ba, ya danganta da yanayin da kuke ciki ne kawai,kawai dai ana son ki riqe suna ɗaya da in kin faɗa ko a gaban waye an san shi kike nufi,amma ke da shi ki dinga faɗa masa dik kala-kalan suna masu daɗi da ki ka sani, ki dinga la'akari da yanayin da kuke ciki ke da shi, in kina shagwab'a kina kiran shi da suna kamar Sweet one,zaunjee, mineeee, in kin zo qarshen kina ja cikin shagwab'ar, in ko miji ne ke maki shagwab'a, kina kiran shi da Baby, ko My baby, ko mine, su kuma irin su sweetheart, ko my dear, My love da honey, su misalin sunaye ne da zaki iya kiran shi da shi a ko ina Kuma a koda yaushe. Sannan akwai sunayen da in yana maki abu mai daɗi zaki dinga fad'in su, da yaren da kuke magana dan yafi shigar shi, ke ni fa na matsu nai aure na fara gabatar da dik wani ilimin gidan miji dana sani, nan da kika ganni practical ne kawai ban ba amma komai na sani akai na" "Ohhh ni Umaimah na shiga uku, 'yan matan yanzu sai su tsorata ka " "Dalla rufen baki ban girme ki ba? Amma kike a dakin miji har da result ɗin abinda kuke yi a d'aki, ke yanzu yarinyar primary ma ta san komai balle ni dana gama Jami'a" "Haka ne kuma, Allah dai ya tsare mana imanin mu," "Ameen... ina mijin naki, ko bai dawo daga makaranta ba?" "Yana d'aki ai ya dawo yau ko makarantar ma be je ba," Cike da jin kunya Sapnah ta ce, "Innalillahi Umaimah kin kashe ni, shine baki faɗan ba nake ta zuba kamar kanya? Ba zan sake shigowa wajen ki ba,tinda ni dai bakina baya iya shiru, sai anjima mun b'ata dake," "Dan Allah ki yi hakuri ki zo kici kayan daɗin nan," "Ke wasa nake maki a qoshe nake, ki ci abinki ki qoshi, dambun naman kawai zaki debar min na wice gida," "Ba dai gida zaki koma ba," "Ah ah ina nan sai aunty ta haihu, na ga yau ma tin da ta tashi sai yatsina take,anya ba ta fara naquda ba a tsaitsaye?" "Anyaa? ni dai ɗazu dana shiga normal na gan ta," "Aiko yanzu ta sauya kinga bani na tafi, dan ba zan so haɗuwa da mijin ki yau ba, kullum sai ya kama ni ina shegen surutuna da bana gajiya" Dariya suka yi tayi umaimah ta d'eba mata dambun naman ta tafi. Dakin ta ta shiga wanda a da shine d'akin Haroon, kwantawa tayi ta lumshe idon ta ganin Umaimah da hira da ita ya sanyaya mata zuciyar ta, dik da yayan ta taso gani ba ita ba, amma ta danji daɗin ranta. *********************** Sadeeq mahaifan shi sun aura masa wata bazawara dake maqotaka da gidan su yarinya ce shakaf sakin wawa, yarinyar akwai nutsuwa da hankali sosai, ga ta da kamun kai da tawakkali hakurin ta shi ke sa Sadeeq sake mata fuska, saboda har yanzu soyayyar Mamalo na nan a danqare a ran shi, sai ma kewar ta da yake ji a kullum na qaruwa, yarinyar bata damuwa, dan wataran ma mantawa yake da sunan ta ya kira ta da Fateema haka zata amsa ta masa abinda yake so, a hankali kunyar ta ta fara shigar shi, tin baya damuwa dan ya kira ta da sunan mamalo har ya fara jin nauyin ta, zaune suke cikin girmama juna har yau ba abinda ya shiga tsakanin su na auratayya, saboda ba shi da sha'awar kowacce mace in ba Mamalo ba. (Muje zuwa zama ka ware ne d'annan, indai mace ce ). ********************** Hauwa ke ta naquda dik ta jiga ta tsabar tausayi ya sa Sapnah kuka, dik fuskar ta yayi jawur, dik surutun ta kamar an dinke mata baki a ranar, addu'a kawai take Allah ya sauki yayar ta ta lafiya,midwife din da ke karb'ar haihuwar Hauwaa ce ta fito ta same su a bakin d'akin da aka shigar da ita, tace ma Ishaaq ya miqo kayan haihuwar da suka zo da shi ta kusa yanzu kam. Jiki na rawa ya tafi inda sukai parking ya d'akko kayan kafin ya dawo har ta haihu, yana isowa yaga Sapnah na dariya hawaye na bin fuskar ta cikin wani irin yanayi ya ce, "Sapnah lafiya?" "Yaya ta haihu lafiya kai ake jira ta sauka, sunqi sanar dani me aka samu sai dariya suke yi min" "Alhamdu lilLAAH Allah abin godiya, miqa masu kayan maza maza," Da sauri kuwa ta kai kayan sai da suka gama gyara su sannan suka miqo masu jaririn, yaro ne qaton gaske kamar ba ita ta haife shi ba. Ishaaq sai da ya zubda hawaye dan farin ciki ya manna yaron da qirjin shi, sanan ya masa addu'o'i, Hauwaa sai washe baki take bayan an maida ta wani d'akin dan hutawa. Nan da nan kuwa suka fara bugawa 'yan uwa da abokan arziqi waya ana sanar da su haihuwar, Sapnah sarkin surutu sai faɗa ma mutane take baby da ita yake kama. Umaimah ta sanar da Jameelaa haihuwar matar wan mijin nata, dan haka ta masu alqawarin zuwa in Umar ya dawo. Basu zo ba a ranar sai washegari da aka sallame su zuwa gida, tinda lafiya qlou suke daga ita har jaririn. Har cikin gida su Umar suka shiga Ishaaq ya ji daɗi sosai kuwa, ya na alfahari da yanda zumuncin su yake qara qarfi da su Umaimah tinda suna ziyartar juna. Sapnah ce ta kawo masu abin sha Jameelaa tana zaune ta na yatsina hayaniya tayi yawa wai a fad'ar ta, ta tashi ta yi ta koma ɓangaren Umaimah ita ɗaya kamar mayya, tana ta chatting da qawayen ta masu hannu da maiqo, nan kuwa Umar da Sapnah da umaimah har da mai jegon suka kafa dandalin hira, ba qaramin jin daɗin hirar Umar ya ke yi ba, Sapnah kuwa tafi kowa jin daɗin faruwar hakan, dan yanzu ta riga da ta gama gane cewar son Umar take sosai, kuma ta qudiri niyyar sai ta sanya masa soyayyar ta a tashi zuciyar da yardar Allah............. *Wa me son a yi wa Jam Jam kishiyaaaa??? A daga hannu na qirga ku.....banda mugunta dai ah toh* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻   MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 34: Sai da suka tashi tafiya sannan Jameelaah ta dawo sashen Aunty Hauwaa sai ya tsina take yi ita a dole ga 'yar gayu kyakkyawa ta wuce ajin su Sapnah da za a zauna ana wani hira da ita, Umar yana ganin ta ya tina ashe fa tare suka zo, wannan kuwa shine karo na farko da Umar ya zauna ba tare da tinanin Jameelaah ba tun bayan da suka haɗu da ita a rayuwar shi balle ma har ya manta da ita,cikin yatsina fuska tace, "Abban Humairah ina ganin ya kamata mu wuce gida mu bar mai jego ta huta ko? Surutun ku har gidan Umaimah ana ji" "Ke ba kin gudu ba ai da ke ya kamata ma ayi ta hira, ko dai baki son hira cikin mu ne?" Cikin wasa Sapnah tai mata wannan tambayar, kowa kuwa ya zuba mata ido ya na so yaji amsar da zata bayar, harda Umar a cikin masu jiran amsar ta ta. Kame-kame ta farayi can kuma ta basar ta ɗauki Humairah da key din motar Umar tace ma Umar ɗin, "Ka same ni a mota," Taji haushin yanda Sapnah ta qure ta da tambaya a gaban mutane,ina ruwan ta da qin zaman ta a wajen ko dan salon ta sa Umar ya ga bata son huld'a da qanwar sa?  Tayi tsaki yafi a qirga a dai-dai lokacin da take buɗe motar zata shiga ta zauna ta jira shi, ga wani qarin takaici Umar din ma bai fito ba a haka ta zira masa key ɗin ta gyara zama ta ci gaba da jiran shi,wani tsakin ta sake ja mai tsaho tare da kallon qofar gidan Umar ne da Sapnah suka fito suna ta sheqa dariya, Umar har wani duqawa yake yi, tinda take da shi bata taba ganin irin wannan dariyar ba a tattare da shi he is always calm and gentle, Sapnah ta gani tana tafiya tana turo hannaye gaba tana tafiya kamar wani robbot tana hura kumatu, Umar sake kwashewa da dariya yayi itama ta fara dariya, sannan suka tsaya, "To abokin surutu na sai da safe mun gode sosai da zumunci, Allah ya saka da alkhairi ya raya mana Humairah," Kallon ta Umar yayi cike da kulawa sannan ya saki wani qayatatten murmushin da ya nuna tsantsar jin daɗin addu'ar da ta yi masa da 'yar shi yace, "Ameen abokiyar surutu na,ni surutun ki yafi nawa har mamaki ma kike bani," "Anya kuwa na fika surutu? muje ga Maman Humairah can na jiran ka, kar taga mun dad'e sai wataran zamu tantance wanda yafi wani surutu a tsakanin mu," "OK we shall see then" "Yes Allah ya kaimu ranar tantancewa" D'aga masa hannu tayi shima ya d'aga mata sannan ya tafi, koda zai shiga mota ma sai da ya yi mata murmushi sannan ya buɗe ya shige ya zauna. Jameelaa ta ma rasa me zata yi saboda ganin wannan sabon salon lamarin da ke faruwa a gaban idanun ta, kawai sai ta sake baki da hanci da ido tana ganin ikon Allah, under her own very nose ana soyayya da mijin ta kambala'innan kayyasa, lallai yau za a ci uba kenan a unguwar nan kafin tayi yunqurin fita ta isko ma Sapnah a inda take wa mijin ta murmushi mai cike da tarin so da qauna tini Umar ya ja mota, da sauri ta cire hannun ta daga murfin qofar motar da taso budewa ta maida kallon shi gare ta. "Me na gani ɗazu kenan Umar? Me yake faruwa tsakanin ka da waccan me shegen surutun?" Cikin tsananin mamakin kiran sunan shi da ta yi gatsal ba Yah Umar ɗin ma babu kuma sunan soyayya balle kuma Abbahn Humairah ya biyo baya, ya rufe bakin sa ya shanye mamakin sa ya yi kamar ma bai gane me take nufi ba ya kalle ta sanan ya juya ya ci gaba da tuqin shi yace mata, "My love me kike nufi da maganar ki? Ban gane inda tambayar ki ta dosa ba," "Kana nufin kace min dik a cikin hira ne kake dariya da ita dariyar da baka taɓa min irin ta ba? Ko kuwa kana nufin dik a cikin hirar ne kake magana sosai wanda ko da ni baka taɓa sakewa kayi hakan ba? Ba zan ɗauki rainin hankali ba malam, tin wuri ka san me kake ciki na faɗa maka," Cikin ran shi yake maimaita kalaman ta kamar mai koyon magana, 'Me nake ciki? Ba zata d'au rainin hankali ba? Tin da muke me na taɓa yi mata na rainin hankali? I have to be a man just for today oo in ba haka ba wannan shirmen zai ta tabbata a gidana ,abun nata ya isa haka fa tana son ta tsallake dik wata katanga ta mutunci dana gina mata,' Dan haka cikin d'aure fuskar da bata taɓa ganin ya yi wa kowa irin shi ba balle ma ita ya ce, "Bana son maganar banza ni kike ce ma na san me nake ciki? Aje ni ki kai ko me? Ko kuwa sai na nemi izinin ki ne zan yi dariya ko nayi magana da wasu? Inace nan nan barka muka je amma ke basu ishe ki kallo ba kika tafi kika bar wajen,ni na zauna kuma sannan ya zama abin magana, idan da ki na so na har haka da yawa da baki tafi kin barni a inda zuciyar ki bata nutsu da su ba,kar ki sake min magana kamar kina magana da ɗan ki na faɗa maki ki kiyaye" Shiruuu Jameelaah ta yi kamar ruwa ya ci ta, dama Umar ya iya faɗa haka, 'Ya kamata na je wajen Ramai mu san abin yi, ba zai yu na rasa mijina ba, ɗan girman da yake ban ma yanzu naga yana qoqarin dai nawa gashi nan yanzu har wani faɗa yake min' Haka suka isa kowa ya yi fuska ba mai cewa kowa komai, Humairah ke ta ke 'yan waqe-waqen ta na yara. Yana tsaida motar ta fice ta shige ciki sai kumbura take yi, kwantar da kan shi yayi jikin kujerar ya lumshe idon shi, tunda suke ko zata b'ata masa rai bai taba biye mata ba sai dai ya danne, amma yanzu  ba zai iya ba ya isa haka, in bai taka mata burki ba haka zata mai da shi lusarin namiji. Jameelaa na can na fushi harda kuka, a zaton ta ya bita yayi ta lallashi yanda ya saba yi mata,(in kina ma miji kuka bayan kece baki da gaskiya a kullum,to akwai lokacin da zai juya baya ya daina biye maki,amma kukan shagwab'a da kuka akan kina son wani abu kamar yanda yara keyi, da kuka in kinyi laifi saboda a yafe maki, wannan yana sa miji ya qara son ki, ya kuma tausaya maki, sannan ya yafe maki laifin ki, mata a daina kukan banza akan rashin gaskiya) Haka suka kwana kowa na fushi da ɗan uwan sa, Umar na ta jin ba daɗi kamar ya bata hakuri sai kuma ya fasa, ya kamata ya koya mata respect, dole tana bashi girma a matsayin shi na uban yaran ta, nan gaba haka zata na wulaqanta shi gaban yaran su ko ta na faɗa masa magana a tsaitsaye. Cikin ran ta tana ayyana wulaqancin da zata masa in ya neme ta a daren nan, dan kuwa sai ya gwammace bai nema ba. Komai sai da kwanciyar hankali, dan haka Umar ko sha'awar ma bai ji ba, baccin shi ya fara cikin kwanciyar hankali, saukar numfashin shi taji alamar yayi bacci, cikin takaici kuwa ta buga masa qafa gyara kwanciyar shi yayi ya ci gaba da baccin shi, tsaki taja mai qarfi, sannan ta muskuta jikin ta ta rintse idonta ta so yin bacci sosai a wannan daren amma ta kasa, Umar kawai take hangowa da Sapnah suna ta dariya, a nata wautar ma har hango su take sun yi aure suna cin soyayya da yaran su, qara ta kwalla mai qarfi ta tashi zaune tana maida numfashi, Umar a firgice ya tashi yana tambayar ta menene, duka ta rufe shi da shi tana kiran shi da maci amana, "Ka cuceni ka ci amanata ba zan taba yafe maka ba, ashe dama abinda ke ran ka kenan? Qara aure zaka yi dama? Umar na baka dikkan soyayya ta amma shine kake qoqarin yi min kishiya Allah ya isa tsakani na da kai," Lallashin ta ya fara yi dan abun nata kuma ya fara bashi tausayi, ya kula tsabar kishi ne kawai ke damun ta ba wani abu ba. A haka ya samu tayi bacci bayan ta sha kuka ta qoshi.  Kwantar da ita yayi sosai shima ya kwanta a gefen ta, Humairah na gadon ta tana ta bacci abin ta, kallon fuskar Jameelaa yayi, yana ta mamakin halayen ta da suka sauya, first ya gano yanda ta tsani shiga mutane da kuma qyanqyamin talaka, sannan ya gano kwata-kwata bata son zuwa gaida mahaifan shi, dik ta inda ya ɓullo sai ta toshe dan kar taje, sannan kuma kullum tana  masa maganar qawayen ta masu kuɗi, gashi tana son ya na bata kuɗi, ko ya sai mata abun kuɗi mai tsada, dik a da bai taɓa kula da hakan ba sai baya bayan nan. 'Ko dai ban fahimce ta bane? Wataqila zuciya ta ke son yaudarata dan na zargi iyalina akan wani abu mummuna' Tinanin Sapnah ya fara yi nan da nan fuskar shi ta bayyana wani annurin haske da nishad'i, qanqame Jameelaa ya yi yana ta tina hirar su da Sapnah, in ya tina abun dariya sai ya sa dariya, a haka yana tinanin abokiyar surutun shi bacci ya dauke shi. *Bayan suna* Sapnah ce ke ta wasa da Muhammad sunan yaron Hauwaa kenan, yi take tayi kamar ance mata yana gane me take faɗa,shidai jariri sai bin ta da kallo yake yi,Aunty Hauwaa ce ta zauna a gefen ta tace, "Wai ke dan Allah baki gajiya da surutu ne? Jaririn ma sai kin yi masa magana" "Ehhh mana saboda ya samu ya iya magana da wuri, kinci  abincin kuwa?" "Eh na ci na sha magunguna na dika, thank you qanwata," "Ga shi bari na ɗan shiga wajen Umaimah," "Ok ki gaida ta ki yi mata ban gajiya," " Ok to" Kitchen ta biya ta d'auki farfesun naman kan da ta yi masu da safen ta wuce wa Umaimah da shi. Ta ɗan jima tana buga gate ɗin kafin Umaimah ta buɗe mata,shiga tayi tare da tambayar ta mai gidan na nan? "Baya nan da baki ga motar shi ba, me na samu ne naga kwano a hannun ki har naji yunwata ta motsa yawuna ya tsinke, dan kuwa na san ki gwanar girki ce," "To akwad'ai zaki bari na shiga ciki ko kuwa?" Dariya umaimah tayi ta amshe kwanon hannun Sapnah sannan suka shiga a tare, tin a hanya ta bud'a ta na ganin farfesun naman kan ta ji yawunta ya kawo, da sauri ta qarasa parlourn ta  ta buɗe tare da yin bismillah ta hau ci, "Ohhh wannan babyn naki akwai kwad'ayi," "Ba laifi dan kuwa ana tab'awa" Hira sukai tayi a hirar Sapnah ta dinga wayon jin abubuwan da Umar yafi so da wanda baya so sai hadda take yi ,Umaimah kuwa sai zuba take tana faɗin abubuwan da umar din baya so da irin shaquwar dake tsakanin shi da Mum din su, Sapnah sai taji tana qaunar Mutan gidan baki ɗaya, yanzu kuwa zata fara gabatar da dik wani abu da zai janyo mata soyayyar Umar dan kuwa ba zata bawa kowa dama ba a maneman ta har sai umar ya fara son ta ta tura shi wajen iyayen ta,idan yanda take so bai samu ba to ta san Allah bai nufa zai zama mijin ta ba dole ta hakura da shi. Umaimah ce ta gama cinye farfesun da aka kawo mata tass, ta shiga d'aki ta dan zuwa wanke hannu a toilet,ta na shiga wayar Umaimahn ta fara ringing, Sapnah ce ta d'aga nan ta ga me kiran, mayarwa tayi ta ajiye in Umaimah ta zo ta kira shi, kira yayi tayi Umaimah bata fito ba dan haka sai ta sake miqa hannu ta ɗauki wayar ta amsa sannan ta kara a kunnen ta............ [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 36: A wani qofar gidan qasa mai shago a ta waje suka tsaya, a dai-dai jikin shagon ya tsayar da su, nan take ya fita ya riqe mata Humaira itama ta fita tana ta bin wajen da kallo, Abokin shi na ciki ya yi wata iriyar shiga kamar bokan gaske. Sai surkulle yake ta yi  Jameelaa na ganin shi jikin ta ya hau rawa dan kuwa bata tab'a zuwa gidan boka ba sai yau, yau ɗin ma gata ita ɗaya bata ko san sunan unguwar da suke ba, kukan zuci take tayi da dana sanin zuwan ta ita ɗaya wannan waje mai ban tsoro,amma da ta tino abinda ke gaban ta na son mallakar Umar ita d'ayan ta ba tare da ya haɗa ta da wata mace ba a rayuwar su sai ta samu kan ta da ware wa ta na jin wani farin ciki na shigar ta a hankali ta tabbata yau ta kawo kukan ta gidan mutuwa. "Ta kan tsamiya ta taimaki boka ga baquwa na kawo maka, tana cikin tashin hankali da damuwa akan halin mu na 'yan maza jincewa tana neman taimako ne ya sa na ce bari na kawo ta wajen me kankat dan haka gata nan a taimaka mata," "Firrrrr, tiiiirrrrr, sirrrrrrr, bucaaaaaa.... ke ta shi maza ki fita aikin ki ba mai yuwa bane firrrrrr," "Na shiga uku na lalace ni Jameelaah dan Allah ka taimaka min, ka tsaya na faɗa maka matsala ta na san zaka tausaya min kamin aikin nan, da dikkan alamu ana samun biyan buqata anan, tinda har kawo ma mutane ake yi" "Tiiirrrrr shin wai ba akan kishiya bane matsalar ki? Kuma kina son mallake miji? Ba zai yu baaaaa, tashi tashii kafin ta kan tsamiya ta fusata," Gurfanawa tayi a gaban shi ta fara kuka sosai har da majina, Humairah ce ta farka daga bacci ta fara kuka, Jameelaah ko ta kanta bata bi ba ta duqa gaban matashin nan tana kuka tana bada hakuri akan ya taimake ta,jin kukan Humairah ya yi yawai sai ta sa hannu ta janyo Humairah daga baya ta fara bata nono, nan take ta hau zayyana masa qarya da gaskiya akan matsalar da take ciki, bayani take amma hankalin su na kan nonon ta da take shayarwa da dashi, gani ya yi jan ran ya isa haka ya kamata su fara mata aiki kawai sai ya ce, "Siiirrrrrr, Hajiya aiki na mai sauqi ne ya kan d'au wata ɗaya ko biyu ana yi, ni ban cika karb'ar kuɗi ba ma, saboda aljanar kan tsamiya tafi son ayi mata yanka, fiiirrrrr bucaaaaaa... ga shi abinda muke son ki yi mana ke ba zaki iya ba kina da rauni, akwai imani da Allah kaɗan a ranki,in ance ki yi ba zaki iyaba," Da sauri ta janye nono a bakin Humaira ta aje ta a wajen, ta haɗa ta da yar jakar ta tayi wasa,sannan ta maida hankalin ta kan bokan nata tace, "So kake na rantse maka kan ka yarda zan iya komai akan Umar? In kana son na rantse zan rantse, tinda kaga na taso na zo nan kasan na kai qarshe wajen tijara nima, kawai kome za a yi ayi ni dai na mallaki mijina ni ɗaya shine fatana, ko uwar shi ce a raba shi da ita, ya zama ni ɗaya ce a zuciyar shi," "Angamaaa indai zaki iya yin komai aka ce kiyi, kin aminceee????" "Na amince" "Kaii dan rakiya jeka daga waje za a yi mata aiki, Takan Tsamiya zata kira mazajen aljanu na Nijer su yi mata aiki, je ka wajeeee jeka wajeeee....za dai ki iya jure aikin aljanuuuu kooo?" "Ni wai sau nawa zan ce maka zan iya ne, kaiii je ka waje ayi a min aikin nan na koma gida kar mijina ya koma yaga bana nan," Da sauri kuwa mai a daidaita ya shiga adaidaitan shi yana fita bokan qarya ya miqe yana rawa yana surkulle, dan abin wasa ya bama Humairah, sannan ya dau wani ruwa a cup ya bata, maganin bacci ne mai qarfi a ciki, nan da nan kuwa ba a jima ba ta bingire, Jameelaa ta tsora ta hau kuka tana tambayar me ya ba ma 'yar ta, "Magani ne na kariya daga sihiri dan kuwa 'yar ki an mata mummunan asiri, ita da ya sake ta sai nan da kwana daya, karki damu, tub'e maza aljanu su fara aiki akan ki lokaci na tafiya, suna tsaye suna jiraaaaa, suna da aiki a wani wajen" Wani ruwa ne a bokiti zundumeme, ya dinga yafita a cup yana fesa mata, sai qoqarin kare qirijin ta take yi, amma kun dai san Jameelaa da manyan halittar qirji ba za su karu da hannun ta ba, hakan da tai na dago su sama ne ya sa ya sake fad'awa cikin sha'awar ta, wata yar qara ya saka ya fara jijjiga yana surkulle,shi a dole aljanu sun shige shi zai yi mata aiki, "Dauki ki shaaa... daukiii ... daukiiii shanyeee, mummunan sihiri aka maki maza shanyeeee" Aiko cikin sauri ta shanye ta side cup din saboda zaqi zaqin da taji a ciki, Nan ta fara ganin duhu a hankali ta kwanta bacci, ai kuwa Leqawa yayi ya kira abokin shi, su ka rufe qofa, nan sukai ta hawan Jameelaa wannan yayi ya bawa wannan tsabar ganin banza da arhar ta. Bayan sun kammala ne suka ta shi suka gyara jikin su, suka maida ita gefe suka lulluba mata zani, tsaf suka gyara ta kamar ba abinda ya faru, suka manna mata Humairah a jikin ta, ɗan rakiya ya ce shi ya ware zai je yayi sana'ar shi, shi kuwa d'ayan ya tsaya a bakin shagon yana zuqar sigari, daga baya ya kulle ya shiga gida, ya samu an gama abincin rana yaci ya qoshi ya fice. Bashi ya dawo ba sai bayan la'asar, yana isa shagon ya buɗe, Jameelaa na nan kwance ruwan gishiri da lemon tsami ya d'ura mata ai kuwa cikin minti uku ta fara tari tana kakarin amai, amai tai ta kelayawa na ruwa zallah da wani yalo-yalo a aman saboda ba abinci cikin ta ko karyawa batai ba ta fito yawan gantali. Sai da tai amai ta gode Allah yana zaune yana ta surutai na surkulle, "Da kyauuuu... aiki yayi kyauuu, aljanu sun yaba aikin da suka yi maki, kije gida ba ke ba zancen kishiya, balle takurawa ta uwar miji," Jikin ta taji yana wani irin wari mara daɗi kamar warin jikin maza, sannan can qasan ta kamar an sadu sa ita ganin kayan ta tsaf a jikin ta kuma an rufe ta kif ya sa ta amince wataqila aikin da aljanun suka yi mata ne yasa take jin haka dama ance maza ne. Kuɗi ta zaro tace ga abin sadaka na aljanu, a yi musu yanka, nan da nan ya daka mata tsawa yace, "Keeee ! aje cannnn kusa da aljanar kan Tsamiya, kar ki nufo ni da kuɗiiiii,bana soooo, bana soooo," Can kusa da wata kwarya ta ajiye ta goya Humairah ta fita, saida ta fita ta fara tinanin nan ina ne? Ina zata ce a kai ta? Ohhh yau yawon neman biyan buqata ya kaita dare dan kuwa har biyar na yamma ta gota, yanzu tasan a yanda cunkoson hanyar garin kano yake da yamma sai ta kai magrib kan taje gida. Wani kid'imammen tsoro ne ya shige ta dan tunawa da me Umar zai ce idan yasan bata gidan su kuma bata je gidan iyayen shi ba? Cannn ta buga murmushi sannan tace, "An mallaka min kai Umar na san yanzu sai yanda nace kayi zaka yi, Allah ka kaini gida yau na ga tasirin wannan magani," Tambayar wani yaro tayi tace masa meye sunan unguwar nan ya faɗa mata cikin tsoro ta dafe qirji, tabb ai sai isha'i kan taje gida yau, kallon inda ta fito tayi, ta ga wajen ba wuyar ganewa, da ta ji duku-duku kan Umar ya ɗan warware zata dawo. Da kyar ta samu mai taxi ta hau aka kai ta unguwar su, cikin fargaba ta shiga gida, Umar baya nan ya bazama neman ta, kulu ta yi jigum dan yau ta sha faɗa wajen Umar da ko sunan ta baya iya kira, amma ya zarge ta da sakacin bar masa mata ta fita, Tana shiga ta fara kuka ta zube a qasan tsakar gidan, sai kuka take harda majina da sauri Kulu ta latsa yar qwabirar wayar ta ta kira Umar, tace masa gata ta dawo. Wani irin burki ya ja ya juya ya kama hanyar gidan su ,dan da ya nufi gidan su Jameelaa ne a karo na uku dan ya ji ko ta koma can daga duk inda ma ta je, tunda Ramai ta yi hatsarin nan ya gano akwai su da son satar fita ita da uwar ta, bai dai taɓa ba abun mahimmanci bane kuma bai zaci Jameelaah zata yi masa haka ba. Da sauri ya fice ya rufe marfin motar ya shiga gidan da kukan Jameelaa ya fara cin karo, riqe da Humaira a hannu ta  tana ganin shi ta sake zunduma ihu,a guje ya zube a gaban ta yana faɗin, "My love me ya same ku haka? Kin gan ki kuwa? Kinga yanda kika koma a wuni ɗaya kuwa?" "Umar ka yafe min yau na ga tashin hankali, dik dan akan karna takura maka, " "Menene ya faru ne ki yi min bayani? ki gaggauta sanar dani, me yasami Humairah naga bata motsi," "Tin da ka fita ta fara kuka jikin ta zafi rau ta qi karbar nono, shine....shine...shineee nace ba zan takura maka ba ka fita aiki, bari na kai ta asibiti, shine adaidaita sahun da ya ɗauke mu ya ga taqi daina kuka, sai ya bamu ruwa a roba yace na bata ko qishi ta ke ji, ina bata kuwa ta amsa nima na sha, tin daga nan muka fara bacci,bamu tashi ba sai a wani daji,.....ya duba ya ga ban da kuɗi, ya mammare ni ya maido mu ya yasar ya guduuuu" Kuka sosai take ta yi kamar ranta zai fice duk wanda ya ga yanda take kukan nan sai tsoron Allah ya kama shi ya tabbatar da abinda Allah ya faɗi na Innakaidakunna azeem,da sauri Umar ya ɗauke su ya wuce mota dan kaisu asibitu aga lafiyar su dika. Kulu mamaki ya hana ta motsawa daga inda take dan kuwa tana ganin sanda Jameelaa tayi murmushin mugunta, tabi bayan umar tare da dan tsallen samun nasara, sannan ta ga sanda ta fita da safe lafiya lafiya ta bar gidan amma ta zabga qarya irin wannan anyaaaa???? A asibiti bayan an ɗauki jinin su da ita da Humairah an tabbatar ma da Umar sun sha maganin bacci ne, Umar kuka ya sanya ya qanqame Jameelaah saboda ya tabbata ta wahala ita da yarinyar su, itan ma kukan take amma mamaki fal ran ta, me zai sa a ga maganin bacci a jinin su? Bayan aikin karya sihiri aka yi masu???????? *Jameelaa ina zan sani? Tambayi bokan ki dame ya haɗa maganin* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 35: Karawa tayi a kunne tare da yin sallama cikin sauri tace, "Bata kusa ka kira ta anjima. Kit ta kashe wayar dan ko jiran ya amsa sallamar bata yi ba ma. Sake kira yayi ta sake d'agawa tace, "Nace bat..." "Haba 'yanmata ai kin jira ma na amsa sallamar ki kafin ki katse ko amma ki ka yi saurin katsewa ke a dole gaki 'yar isar da saqo ko?.... wait a minute wai Sapnah ce?" "Ohhh ni Sapnah gaskiya ka fini surutu,eh Sapnah ce," Dariya yayi sosai sannan yace, "Tabbb na fiki surutu a ina? Muna dai da surutu ni da ke da ace gida ɗaya muke sai mun d'aga rufin gidan da surutun mu" Wani iri ta ji a jikin ta dama ace maganar shi ta tabbata ba rufi ba ko katangar gidan ce ta zube ba komai in dai tana tare da shi. "Ya ki kai shiru ne ko yau 'yan maganar basu kusa ne?" "Ammm ba komai kasan akwai gajiyar suna da aka yi, kuma ka kyauta baka bamu aron matar ka tazo mana suna ba," "Ya salam...gaba ɗaya na manta anyi sunan, kuma baku tunamin ba shiyasa," "Ta ina zan tuna maka baka da no ta ban da taka?" "Haka ne kuma fadon min No ki yanzu na maka su a wayata in case  ko za a gayyace mu wani abun," "Ehhh zamu gayyace ku sunan Umaimah mana," "Dan Allah da ta fara naquda ki kira ni ai kar ki bari a ma kai ga haihuwa, in ta haihu banga naqudar auta ba ke zan kama," Sassauta murya tai cikin wani irin salon saye zuciya sannan tace, "In ka kama ni mi zaka min to?" Shiru yayi yana jin muryar ta na tsaga dikkan wani sashe na jikin shi tana shigewa tana kwanciya, kuma da dikkan alama wannan magana ta shige kenan har abada, a hankali shima ya furta, "Inna kama ki zan....." "Amshi wayar ki wannan yayan naki sarkin surutu yana ta kiran ki na taimaka na ɗauka, gashi ku ci gaba da hirar ku zan je gida," Amsa Umaimah tayi ta yi sallama suka fara gaisawa, "Yah Umar lafiya na ji ka haka? Duk sai naji muryar ka dik a sake, ko dai wani abu ne ya faru? Wayyoo Yah Umar me ya faru sanar da ni," Sai da ta faɗi haka ya farfaɗo daga suman da Sapnah ta sa shi yi a zaune, "Ke ke dakata kwantar da hankalin ki ba komai, ba abinda ya faru jikina ne kawai a mace, ina office na ce bari na kira na ji ya kike? Dan ina son na dinga jin ya kike har Allah ya nuna mana kin sauka lafiya, Allah ya raya mana abinda ke cikin ki dake kan ki sai anjima qanwata ina son ki," "Na gode Yah Umar da kulawar ka, baka gajiya wajen jin lafiya ta, ina son ka nima fiye da yanda kake so na, Allah ya bada sa'a ya sauqaqa gajiyar aiki," "Ameen bye" "Bye"  Suna gama waya da Umar, wayar Haroon ta shiga wayarta,cikin murmushi ta furta, "Masoya na kenan," Cike da fara'a ta daga wayar tayi masa sallama ya amsa, "Gaskiya kai da Yah Umar kuna ji da ni sosai dole ne na yi maku kyauta na ga alama,dik wanda na kula yafi ji dani zan bashi kyauta mai tsoka, ba tare dana faɗa ma wani a cikin ku ba," "Haka kika ce? Inshaa Allah ni zan ci kyautar nan, amma sai dai a barni na zaɓi me za a bani," "Waaaayoooo, ni fa nace zan bada kyautar sannan kai zaka zaba?" "Ehhh ni zan zab'a mana kuma dole abani dik abinda nake so, indai an yarda in ba a yarda ba to a bar wannan kyautar," "Na amince to,ina fatan ka isa kasuwa lafiya?" "Lafiya qlou Mahboobatee, ya unborn dinmu? Ya jikin ki?" "Lafiya qlou muke sai dai ni fa bayana na dan yi min ciwo,yanzu sapnah ta kawon ma naman kai naci, ina ta murna naci amma sai da nai amai bayan na gama,  ni dai gaskiya na gaji da aman nan" "Subhanallahi ! kar kice haka lada ne kike samu, kar ki manta a dik sanda bawa ya shiga cikin halin qunci Allah yana bashi lada, balle uwa dake ɗauke da ciki,ki qara hakuri kinji? Lokaci na  nan zuwa da zaki daina aman," "Allah ya kaimu lokacin Mahboob, na gode da kulawar ka a gareni, Allah ya bada sa'a, Allah ya haɗa ku da halal komai qanqantarta, ya kare ku daga haram,komai yawan ta, Allah ya dawo min da kai lafiya, Allah ya sa in 'yan mata sun zo shago siyan kaya kar su gan ka suga Yah Ishaaq shi ɗaya," Dariya ya dinga yi kamar kullum in ta yi irin addu'ar nan, sannan ya dan haɗe fuska yace, "Kashhh network ba kyau bana jin ki sosai me kika ce ne a qarshe? Saqo kike bawa Yah Ishaaq ko me? Ni ban ji ba sosai," Cikin wauta da rashin sani ta sake maimaitawa, "Ba saqo na bashi ba addu'a nayi, nace Allah ya sa in 'yan mata sun zo siyen kaya kar su gan ka, suga Yah Ishaaq" "Tabbb di jamm, amma kuwa Umaimah sai na hada ki da Hauwaa, dama addu'ar son kai kike ma na? To kuwa..... Dif Ishaaq yaji wayar ta katse ya kalla ya yi murmushi ya miqawa qanin na shi dake ta kwasar dariya, "Ashe addu'ar mugunta akewa Hauwaa ko, kamar a kunnen ta kuwa" "Dan Allah ka rufa mana asiri, wasa muke maku, habaa ai daga kan ta babu qari," "Za dai kuji sammaci daga kotun Hawaa'u Autar mata" Haka sukai ta nishad'i abun su suna gudanar da kasuwancin su, har Ishaaq in ya tina da maganar da Umaimah ta yi sai ya yi murmushi saboda ya ji yanda ta tsorata da ta ji muryar shi. Sai yamma da suka kusan dawowa Umaimah ta yi wa Haroon message, *Ni kaiwa haka ko? Zaka dawo ka sameni, sai dai Yah Ishaaq din ya rako ka, amma yau ni da kai ne a gidannan i love u my Mahboob.* Dariya yayi tayi Umaimah salon ta na bashi dad'i sosai shi yasa yake sake jin qaunar ta a koda yaushe, in ya fita zata kira shi ta ji ya isa lafiya? Ko shi ya kira yaji ya take in ita taita kira bai kira ba bata fushi bata qorafi uziri take ba shi akan maybe aiki ne ko karatu ne suka riqe shi. In kuma sukai waya sai ta faɗa masa abinda zai ta tinawa mai daɗi, ko ta bashi dariya. In ya kusan shiga gida zata masa message din addu'ar komawa lafiya mai daɗi, ko kuma in yayi laifi ta masa irin na ɗazu,wanda zai ji ya ma matsu ya koma ta hukunta shi ɗin. Haka rayuwar Umaimah da Haroon take abar so abar kwatance ga kowa, bata raina abinda ya bata sannan bata sanya ido a abinda yake dashi, kuma bata taɓa roqon shi wani abu, sai abinda zai amfane su dika, buqatar ta ta danne ta har sai ya kula ya yi mata tunda bata rasa ci da sha da sutura ba balle wajen zama mai kyau, in bai mata ba bata damuwa dan ta san ba ita ta bashi ajiya ba, kyautatawa ne dama a tsakanin miji da mata,a ranta takan ce in tana son abu zata nema da kud'in ta ko ta yi kasuwanci itama ta ji daɗin cin kud'in ta, amma ba zata yarda da roqar miji ba har tin yanayi yaga dan kud'in shi take zaune da shi, duk abinda bai zama dole wajibun ba bata tambayar shi. A kullum Haroon godewa Allah yake yi akan samun Umaimah da yayi a matsayin matar da ya aura, tindaga sanda ya fara son ta ta sauya masa tinani, gashi yanzu yana makaranta ya kusan kammalawa, ya samu ilimin sake haɓaka masu kasuwancin su, yanzu haka yafi Ishaaq ilimin kasuwanci na zamani. Kasuwancin su ya bunqasa kwarai da gaske abun nasu ya zama sai godiya ga Allah, cikin kasuwa da cikin gari yanzu kusan dik an sassansu, da wahala ka haɗu da wanda bai san shagunan su ba. Shi dai bai taɓa fita waje bane, yace ma Ishaaq sai ya kammala karatu ya amshi kwalin shi a hannu, zai tsindima cikin kasuwancin sosai. *********************** Umar na fita ta goyi Humairah ko wanka basu yi ba ta fice itama, maqudan kuɗin dake hannun ta wanda ta tara a wannan satin ta qara matsewa a jakar ta, Humairah na ta tsala kuka, dan kuwa yunwa take ji sosai yanzu an fara bata abincin yara nono baya isar ta, balle ma yau ko na safe ba a bata ba. Burin Jameelaah bai wuce tagan su gaban boka ba yau, dan ayi komai kwaf ɗaya a raba Umar da kowacce mace koda kuwa Mum ce bata damu ba, akan ya yi mata kishiya. Sai da ta sai k'wai da bread da madara da milo sugar da butter sannan ta wuce a adaidata sahun da ta ke ciki, a gefen qofar gidan su ya aje ta tace ya tsaya zai kaisu unguwa, zata biya ko nawa ne wayar ta ta duba taga takwas ta gota kusan da rabi, ta tabbata baban ta baya nan sai ta faɗa gidan. Tin daga soron gidan taga sauyi gidan ya yi fess qall ko ta ina, ga shi sai tashin qamshin turaren wuta dan tsinke yake yi. 'Sabon salo, kodai Umar ya sama masu mai aiki ne suma?' Sallama ta rabka Ramai ta fito ta amsa, ba wata kwalliya tayi ba amma ba had'in gambiza yanzu sannan kayan ba mugun datti kamar da. "Ramai lafiya kuwa Naga dik gidan ya sauya,me aiki umar ya sama maku?" "Nice nan me aikin kaina shigo daga ciki," "Ni kam kinga ba shigowa zan yi ba, ga waɗannan na ɗan siyo maku na san zai dan maku ko sati ne haka a sa mana albarka, zuwa na yi ki raka ni wajen bokan nan, mai adaidaita sahu yana jirana, dan Allah ki yi sauri," "Jameelaah ni nan da ki ka ganni na tuba nabi Allah,Allah shine mai biyan buqatun bayin shi ba boka ko malam ba ko mai duba, Allah shine ya basu damar ganin komai da aiwatar da komai, dan ya masu talala, talalar ubangiji bata da daɗi in bawa ya faɗa cikin ta, ki kiyayi Allah Jameelaah, ni dai na kiyaye shi ina fatan ya kare ni daga komawa zunibin da na bari a baya, na maki alqawarin dik abinda ya dame ki zan maki addu'a ke sai nai azumin nafila ma dan buqatar ki ta biya sannan na kwana sallar dare, amma ba zan sake kai ki gidan boka ba balle muje tare ina maki nasiha da ki zubar da makaman yaqin ki na zuwa wajen bokaye macuta masu cin kud'in mata a banza kuma su kai su wuta a wofi," Baki sake Jameelaa ke kallon Ramai anyaaa kuwa Ramai ce? "Kinga Ramai ana jirana na gode da nasihar ki, bai san na fito ba sai na nemi izinin shi zan dawo ki min nasihar sosai," Ramai ta ji dad'in yanda tashi ɗaya Jameelaa ta amshi shawarar ta, nan ta fita ta haye adaidaita sahu, Humairah har ta gaji tayi bacci, masifa ta dinga yi tana faɗin "Tinda ke ba za a maki kishiya ba ai kince haka mana, taya za ai ma na zauna ban nemi taimako wajen bokaye ba, ke ni in bori aka ce na hau akan Umar sai na hau shi, keki ka ga zaki daina zuwa wajen boka ni banga hakan ba, daman ban fara ba ke keki ka koyamin sannan yanzu kice kin janye ina tsaka da neman biyan buqata? ba zata sab'u ba," "Ammm malama ba dan kar nai maki karambani ba dana kai ki wani wajen da na sani, ko yanzu sai da na bi can sannan na zo na ɗauke ki, kinga ba dan na je can ba ya min duba da ban sa'a ba har na  haɗu dake ga shi har zaki biyani kuɗi mai yawa, da sai dai nai ta ɗaukan qananun masu tafiya ana ban hamsin sittin," "Bawan Allah ka taimakeni muje mu koma da wuri kan mijina ya koma gida," "An gama" Hanya ya ɗauka d'od'ar sai gidan abokin shi da suke sana'ar kai mata gida da niyyar bokanci, tin a hanya ya danna ma abokin kira, dan haka akan kunnen shi akai maganar, shi kuwa kan su je ya maida gidan da shi kan shi na boka...... *Casssss ana yi ina jin nayis ana bari ina jin kuka* [08/09, 10:18 pm] Aunty Hameeda: 💅🏻   MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 37: Ranar Umar kasa bacci yayi, saboda tausayawa Jameelaa da d'iyar shi, dan tin da ta farka take ta shan nono tsabar yunwa, an bata abincin ta na yara ta shanye tass, da sai da d'ura take sha. 'Da zan kama ɗan adaidaita sahun nan kan na kaishi wajen hukuma sai yaci tsinannen duka a wajena' Washegari da safe Jameelaa ta tashi washar haka ma Humairah, sai wasan ta take yi, Umar sai da ya tabbata lafiyar su qalaou sannan ya fita, dan acewar shi har da sakacin shi, baya kula da lafiyar su yanda ya kamata shi ya jawo hakan ta faru, ya na can ya na kula da lafiyar wasu amma ya yi neglecting ta iyalin shi. Kulu kuwa ta qudiri a niyar sanar da Mum dik abinda ke faruwa a gidan, amma tana shakkar kar Mum taqi yarda dan yadda suka  yarda da Jameelaa abun har abun mamaki. Amma ta ayyana ma ran ta ko ba zasu yarda da ita ba sai ta faɗa masu abubuwan da take gani kuma da wanda akai a gaban idon ta. Jameelaa ce ta sha kwalliya tana zaune gefen ta Humairah ce kwance ta na wasa irin na yara, Kulu ce ta shiga da sallama ta durqusa kamar yanda take yi mata tace, "Barka da hutawa uwar d'aki na," "Barka dai, ya aka yi?" "Dama na gama aikina ne nace bari na zo na nemi izinin ki ina son naje na gaida su hajiya, na kwan biyu ban ji labarin mutan gida ba" "Ki gaishe su," Magana take cikin isa da taqama ita a dole mai gida da mai aikin ta. Kulu ce ta tashi ta sanya hijabin ta dake hannun ta ta dan yi wa Humairah wasa sannan ta tafi. Koda taje gidan Mum ta tarar bata nan, zama tayi suka sha hira da mai aikin Mum taci abinci tayi sallah ta dan kwanta, bata jima da fara bacci ba Mum ta dawo, mai aikin gidan ta sanar da ita, bari suka yi sai da taci abinci ta yi wanka, ta fito parlour sannan Kulu taje suka gaisa tace, "Hajiya dama tin ɗazu nazo ai ni na ma manta yau ranar aiki ce, ina tafe da wata muhimmiyar magana ne Hajiya ina fatan ko baki yarda dani ba zaki yi bincike akai, saboda ki gano gaskiyar lamarin" "Ikon Allah ! wannan wacce iriyar magana ce mai mahimmanci haka? Ina sauraron ki Kulu," "Yauwaa Hajiya.... dama magana ce akan Uwar d'akina Jameelaah da uban d'aki na Ummaru, a gaskiya Hajiya zaman nasu na kasa gane irin shi, yaron nan yana iya qoqarin shi na kyautata ma iyalin shi daga kan ci da sha sutura, lafiyar su, da komai na su da idona ya gani, amma matar shi bata da godewa Allah, kwanaki munje gidan mahaifiyar ta, ana zaune ana hira, sai kawai suka ban Humairah wai na je waje na yi mata wasa, ina fita na tsaya tsakar gida, ina jin suna tattaunawa akan Uwar zata kai ta gidan boka, sannan jiya abinda ya faru ya ban mamaki kuma ya sa ni zargi kala-kala, yarinyar nan tin da ta fita da safe sai dare ta dawo, ta dawo da wani irin salo na makirci, saboda kar Ummaru ya tambayi ina taje, qiri-qiri bata damu ko zan gani ba, bayan ya juya baya ta fara dariyar mugunta harda tsalle, ni ina zargin ma fa ko tana bin wasu maz......" "Dan girman Allah dakata anan kulu, haba kulu da girman ki, da hankalin ki, kike aibata yarinya mai nutsuwa da hankali irin Jameelaah? Taya zaki zayyana waɗannan abubuwa a kan Jameelaa? Sannan har ki yi zargin tana bin wasu mazan bayan Umar mijin ta? Gaskiya ban ji daɗin wannan maganar ba," "Hajiya dama ai ba magana ce mai daɗi ba, magana ce ta kiyi bincike akan abinda na sanar da ke yanzu, ni dama ai bance ki amince da magana ta ba a tashi ɗaya ba tare da kin yi bincike ba, ki bincika ki gani, innai qarya a magana ta sai ki d'au mummunan matakin qazafi akaina na amince, soyayyar ku a raina ta daban ce, ba zan bari Ummar ya cutu ba ina ji kuma ina gani inshaa Allahu," "To kulu zan yi bincike akai, yanzu ki koma gida kar ta neme ki na gode," "Ta san na zo nan dan da izinin ta na zo nan, yana daga cikin laifukan ta shine satar fita, daya fice ta sa qafa ta fice itama," "To yayi haka kulu, zan bincika na gode," Dubu ɗaya ta bata tace ta hau abin hawa ta koma gida, godiya tayi ta koma. La'asar ake kira lokacin da ta isa gida ta tarar da Jameelaa bata gidan, ta kuma tabbata bata fita ba sai da ta tabbatar Umar ya ci abinci ya koma, kad'a kai tayi ta faɗa kitchen dan ɗora abincin dare, ta sake gyara inda aka b'ata. Jameelaa ce ke ta bulayin neman layin da aka kaita jiya, in an shiga layi ta ce ba nan ba, har suka shiga wani layin da ke kusa dana bokan nata, yana zaune cikin abokai ana zuqe-zuqen kayan maye, shi sigari yake ta busawa, yana hango ta cikin adaidaita sahu ya sunkuyar da kai, sai da suka wuce ya bi ta siririyar hanyar ya d'iba da gudu zuwa gida, shagon shi ya maida kamar na boka, yana tsaka da saka rigar bokan cin shi ya ji ana buga qofar, surkulle ya fara yi, yana faɗin a jira shi, yana gamawa da 'yar matumbura. Sai da ya shirya tsaf ya zauna sannan yace a shiga, shiga ta yi tana ta washe baki ta zauna tace, "Ta kan tsamiya ta taimaki boka, boka na zo godiya ne, aiki yayi kyau, shine nace dole na zo na kawo gaisuwa ta musamman" "Tiiirrrrr, sirrrrr, firrrr, bucaaaaa, kin kyautaaa, kin kyautaaa, hakan yayi daidaiiii, Ta kan tsamiya na jin ki, kuma itama ta ji daɗi," "Boka sai dai akwai wani hanzari da nake tafe dashi a yanzu, jiya da kyar yarinya ta ta farka daga baccin nan na karya sihiri, dan saida muka je asibiti aka ce mana maganin bacci ta sha," Dan zazzare ido yayi sannan yace, "Kar ki damuuu, ai su likitoci basu so a ce basu iya aikin su baaaa shine kawai, amma maganin karya sihiri na baku dika, kuma ya karye, sai dai akwai matsala aikin Uwar mijin ki bai yi ba, sai an......." Wayar ta ce ta katse masu hanzari, janyo jakar ta tayi ta duba, no Mum ta gani nan ta nuna masa, ya yi mata izinin d'agawa sai kace wayar shi haka ta bi umarnin shi ta d'aga,bayan gaishe-gaishe ne Mum tace, "Jameelaa lafiya kuke kuwa? Rabon ki da zuwa gidannan har na manta, ko a waya baki kira a gaisa in ba ni na kira ki ba, ko akwai wata matsalar ne ki sanar da ni?" Sai da ta gama rashin kunya da baki da ido sannan tace, "Ni ba komai kawai 'yan zuwan ne basu zo ba, amma dik sanda na so zuwa zan zo" Tirqashi ! Mum ce ta miqe tsaye sakamakon saurarar kalaman Jameelaa da tayi, lallai maganar Kulu akwai qamshin gaskiya aciki, "Jameelaa lafiyar ki kuwa kike yi min magana a haka?" "Qalaou nake ni yanzu bana nan na dan fita unguwa in anjima munyi magana," Kit ta kashe wayar, "Kinji me nake fada makiiii,aikin ta bai yi baaa, sai an sake aiki akan ta, ki tube a yi maki aiki,ki tubeeee, tubeeee, tubeeee" Ai jiki na rawa Jameelaa ta tube, kallon da ya ke binta da shi ne ya fara tsorata ta, gashi yau bashi da maganin da zai sanya mata, dan haka ya hau borin qarya yana faduwa yana miqewa, shi a dole aljanu ne suka zo, "Lale maraba da zuwan ku na Nijer, maraba maraba, yauma ta dawo a yi mata aiki, a raba ta da Uwar mijiiiii, ta dawo a yi mata mai sauqiiiii" Nan ya fara da fesa mata ruwa kamar jiya, daga nan ya fara shafe mata ruwan daya fesa mata, tin tana daurewa har ya fara bata wani yanayi a jikin ta, (kun san dai mutuniyar ku, ba sai anyi ta dogon bayani ba😂) nan da nan cikin sauqi ya same ta, ita da ake ma aiki sai ta dawo tana aiki, nan suka samu suka gama lalacewar su, ta gyara jikin ta tsaf ta tashi, "Dama irin wannan ne aikin? Aini jiya baka sanar dani ba, ga mallakar miji na samu, yau kuwa ina fatan na samu ta uwar miji, aikin ka akwai biyan buqata ta kowanne fanni," Kudi ta laluba ta damqa masa, ta goye Humairah ta fita, a gaskiya ba qaramin nutsuwa ya samu da ita ba, da da yanda zaiyi kullum tana zuwa ai shi bai da case. "Ki daina bani kudiiii bana soooo, bana soooo, aje su cannnn Ta kan tsamiya zata daukaaaa, ki dawo gobeee sai kinyi wata kina zuwa kafin aikin ki yayi kyau, shi irin sihirin nan na dindindin yana buqatar ayi wata ana yin shi, in ya kama jiki har abada ne, sai kin mutu aljanin dake baki kariya zai rabu dakeeee," "Lallai da na zama mai sa'a na mallaki umar da iyayen shi har mutuwa ta,da kuwa na mallaka maka dukiya kaima mai tarin yawa,na yi maka alqawari dik abinda na samu zan raba uku na baka kashi ɗaya," "Bana son kudiiii, bana soooo, bana soooo, sai dai ki kawo na yankan Takan tsamiya," "Shi ɗin dai za a Kawo babban boka mai babban aiki, bari na koma ni kar a neme ni a ga shiru na gode bokan duniya, Ta kan tsamiya ta taimaki babban boka" Nan ta fice tana murna, aikin akwai daɗi kuma akwai biyan buqata. (Wannan shi ake cewa tsafi gaskiyar me shi) Yau ma sai magrib ta koma gida Umar bai koma gida ba,  kulu na kula da dik abinda take yi, wanka ta fesa mai kyau kamar ba abinda ya faru, ta sha kwalliya sosai koda Umar ya dawo ya ganta wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar shi, Humairah ma an mata gayu sai qamshi take zabgawa. Ɗauke take da Humairah ta je yi masa Oyoyo, dikkan su ya haɗa ya d'aga su sai dariya suke yi gaba ɗayan su, kafin daga baya ya ajiye su ya amshi Humairah yana yi mata wasa, ita kuma Jameelah sai ta amshi jakar shi suka shige ciki. 'Kaiiii da na san da wannan boka tin asali da na je, da Umar ya dad'e ashe mallake a hannuna, rashin sani ya fi dare hudu, ba zan kuwa wasa da dama ta ba, sai na ci gaba da zuwa na wata ɗayan nan cirr, na samu a mallakan shi na har abada' Abinci ta zuba masa ya fara ci ya yi masa daɗi sosai abincin amma ba halin yayi santi tinda ba ita ta dafa ba, in yayi santi sai tace yana yabon girkin wata bayan ita ba tai masa ba da kan ta. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya daga baya ma idan zata fita yawon ta sai ta aje ma Kulu Humairah ta fice, dan kar a asirin ta ya tonu sai take raba qafa, taje gidan su sannan ta wuce, ko in ta dawo daga wajen bokan ta je gidan nasu. ************************ Umar na duba marasa lafiya ya bar wayar shi a Office, koda ya koma ya tarar da missed calls da yawa,No Umaimah ce sai ta Mum, yana cikin dubawa Umaimah ta sake kira. "Assalamu alaikum, sweet sis," "Uncle Umar wa'alaikumussalam,albishirin ka" "Sapnah me kike nufi da uncle? Kar ki faɗan umaimah na ta haihu sai yanzu ake sanar da ni?" "Kwarai da gaske Umaimah ta haihu lafiya  mun samu mace tin da ta fara naquda nake ta kiran ka ba ka daga ba ai, Mum ma nan sai kiran ka take yi shiru baka ɗauka ba, so kaga kenan ba laifin mu bane" "Haka ne baku da laifi me muka?" "Mace muka samu," "Masha Allah,Allah ya raya mana, gani nan zuwa na gama abunda nake yi dama kuna ina?" "Muna gida a gida ta haihu," "Ok sai nazo to," Tattara wayoyin shi yayi ya rufe office sai gidan su Umaimah. Murna ta hana shi rufe baki yana matuqar qaunar qanwar shi sosai, gashi ta haifa masu yarinya,Humairah ta samu abokiyar wasa. Jameelaa ya kira ya sanar da ita yace ta kira ta yi wa Umaimah barka. Cikin murna kuwa ta kira qawar ta ta, daga wayar Sapnah tayi dan Umaimah na bacci. "Qawata qanwa ta kuma maman Baby barka... barka.. barka, kin sauka qalaou?" "Lafiya qlou ta sauka, kina magana da Sapnah ne," "Mtsssss me ye naki na amsa wayar mutane ke kuma karere, ke kenan ba zaki zauna gidan yayar ki da kika zo ba sai kin je gidan Umaimah, salon ki kwacewa mutane maza ko? An tsufa gidan tsoho ana neman wajen sakad'a d'uwais ba a samu ba shine ake bin mazan mutane, to kurwar mazan mu kur ba ki isa samun mazauni a zuciyar mijina ba, ni nafi qarfin ki bari kiji na faɗa maki tun yanzu dan ki san na san menene qudirin ki akan Umar d'ina, aikin banzaaa kawai ko da boka kike yawo akan ki baki isa mallake min miji ba,duk ki gama asire-asiren naki munafuka kawai, in ba rashin imani ba har yarinya qarama kike yiwa asiri? To ta Allah ba taki ba,kuma kin kai qarshen iskanci da asiri tinda kin taɓa ni " "Keee malama dakata min! Sapnah ce fa kike magana da ita ba wata ba ni me na yi maki?" "Zaki ga me kika min in na zo gidan, zaki ga hauka ganin idon ki," Sapnah riqe wayar tayi a hannu hawaye na zuba mata cikin tsananin takaici, tinda take ba wanda ya taɓa yi mata rashin mutunci irin haka, harda zargin tana asiri? Akan me zatai asiri bayan tana da Allah. "Me ya faru kike kuka? Ke da wa?" Aunty Hauwaa da Mum ke mata wannan tambayar, bata iya amsa su ba ta aje wayar Umaimah ta fita daga gidan gaba ɗaya, wayar Aunty Hauwa ta ɗauka, ta ga sunan Jameelaa shine last call da aka dauka. "Ikon Allah ! Mummy kiran Jameelaa ta d'aga fa take kuka, ko me ya faru kuma sai Allah," umar yaga shigar ta gidan Ishaaq tana kuka amma bai san dalili ba, ko me ya same ta kuma oho? Sai ya ji ranshi na masa zafi dan ganin kukan ta, amma son ganin umaimah da babyn da aka haifa masu yafi yawa a ran ranshi dan haka sai ya fita ya nufi gidan Umaimah. Mum na ɗauke da jaririyar ya shiga nan suka fara yi wa juna barka, "Ina Umaimahr?" "Tana d'aki bacci take an yi mata wanka, taci abinci sai kuma ta b'ingire da bacci" "Allah sarki ina maqale matan mijin ta yake naga ban gan shi ba?" "Yana kasuwa, ana ta kiran su shi da yayan nashi ba su d'aga ba, sunje store fidda kaya" "Allah sarki na riga shi ganin baby, sai yazo na san ya dame mu akan ba a sanar da shi ba.....Mum me ya faru naga Sapnah ta fita tana kuka?" "Ka gan mu muma tambayar da muke wa kan mu kenan, ana zaune lafiya lafiya, ta na sanar ma da mutane haihuwar sannan tana amsa wayar Umaimah sai matar ka ta kira sukai magana shine ta aje ta fita tana kuka" "Subhanallahi ! to me ya faru? Me tace mata? Bari dai naje na ji daga bakin Sapnah me aka yi mata" Basu babyn yayi ya fita zuwa gidan Ishaaq, ya na zuwa sai ya hau buga gate, ya dad'e yana bugawa kafin Sapnah ta leqa idon ta yayi mugun ja hancin ta ma haka, tana ganin shi ta sake fashewa da kuka, da sauri ya qarasa gaban gate ɗin, ya durqusa kamar yanda tayi, "Sapnah dan Allah ki sanar dani me ya sa ki kuka? Kin dai san dik wanda aka haɗa da Allah an gama komai ko? Ki fad'an meke zuciyar ki tsakanin ki da Allah," Zayyana masa komai daya faru ita da Jameelaah tayi, sannan ta qara da cewa, "Yah Umar tabbas na san zuciyata ta kamu da son ka, kuma ban san sanda hakan ta faru ba, na tabbata saboda kyawawan halayen ka ne ya sanya, amma na hakura na danne a raina ban taɓa yunqurin kai kaina wajen ka ba, dik da a baya na so yin hakan, sai na ga bai kamata ina mace nai ta cusa kaina wajen ka ba na hakura, dan ko no da kace na baka ina sane na hana ka,kawai shine matar ka zata zargeni da yi maka asiri, shirka fa kenan? Akan namiji sai na sab'awa Allah na?" Kuka ta sake fashewa da shi Umar kuwa ji yayi wata iriyar soyayyar Sapnah mai tsafta na fizge shi, kallon ta kawai yake yi bai ma san me zai ce mata ba a wannan yanayin da ya shiga wanda shi kan shi bai san da wanne suna zai kira shi ba, abinda kawai ya sani shine ba zai taɓa bari Sapnah ta kub'uce mashi ba. "Kutum......bur......ubancan kayyasa, yau za a mutu a unguwar nan me nake gani haka?" Ashar din da suka ji ne ya sanya su juyawa gaba ɗayan su a tare sannan suka miqe daga durquson da suka yi, tin kan adaidaita sahun ya tsaya ta dira, kan Humaira kuwa ya buge da qarfen adaidaita sahun, kuka ta fasa mai qarfi da gigicewa, amma Jameelaa ko a jikin ta, Umar ne ya tafi da sauri zai amshi Humairah, Jameelaa ta hankada shi baya, "Kar ka kuskura ka taba mu maci amana, ashe kana nan ma sanda nake mata magana tana nuna min bata san meke faruwa ba, kuna nan kuna cin amana ta, yau sai an mutu, dan uwar ki fito nan munafuka kike b'uya a bayan mijina," Nan da nan kuwa 'yan gulma suka taru ana kallon su, faɗa ba sabon abu bane a wajen Jameelaah dan kuwa sanda tana lungun su har da maza yi take yi, 'yan kallo kuwa ta gan su kala-kala  waɗannan tsirarun ba za su hana ta ci wa Umar da Sapnah mutunci ba,shi kuwa Umar kunya dik ta gama baibaye shi,Sapnah kuma kuka ba baki, ita a duniya tafi son ai ta hira ana darawa ta tsani faɗa da tashin hankali. Umaimah data tashi a bacci ce tace, "Mum hayaniya nake ji a waje, kamar ana faɗa," "Faɗa kuma? Wanne irin faɗa anan unguwar taku?" "Nima dai abun ya ban mamaki, dan bamu saba jin hayaniya haka ba," Nan dai Aunty Hauwa ta aje Muhammad ta sa mayafi ta fita, tana ganin abinda ke faruwa ta koma ta kira Mum, kunyar duniya ta gama kama Mum, jin irin ruwan ashar da rashin mutuncin da Jameelaa ke saukewa Umar da Sapnah, har da kiran su Mazinata. Saphan nata aikin kuka, dan ita kam cin fuska an gama yi mata shi. "Jameelaa muje ciki ayi maganar a ciki saboda kinga mutane na ta kallon ki mutuncin mu kike zubarwa anan fa," Tankad'a Mum tai sai da ta fadi qasa warwas irin fad'uwar nan ta bazata, sannan ta nuna ta da yatsa tace, "Ku har wani mutnci gare ku, d'anki na waje yana zina da wata kuna ciki a zaune yana nan yana cin amana ta, amma kike maganar mutunci, wanne mutunci ya rage maku kuma?" Sapnah ce ta yi saurin d'aga Mum daga qasa, Umar kuwa fuskar shi tayi jawur saboda tsananin ɓacin rai da shiga tashin hankali da baqin ciki akan abinda yake gani a gaban shi,Jameelahn shi mai natsuwa da kamala da hankali ce yau ta tura mahaifiyar shi abar son shi da qaunar shi qasa????........... *Hummmmmm lallai ne Jameelaa, Umar yau ka nuna min ka haihu cikin Mum😡* *Makaranta ina son jin qarin bayani a game da zuwan Jameelaa gidan boka, da nasarar da take samu, akwai wadda ta fahimci abinda na fahimta kuwa? Sai naji amso shin ku zan gane ko akwai mai irin tinani na ko wadda ta fini ganewa* *Haermeen Haermmearh love u XoXo❤* [09/09, 10:32 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 38: Juyawa tayi zata ci gaba da yi ma Umar masifa taji wani gigitaccen mari ya ziyarce ta wanda ya sa ta tafi da baya zata faɗi qasa, da sauri ya tare goyon nata ya kwance 'yar shi cike da fushi mai tsanani ya qarasa turata qasa, zai bi ta ya take Mum ta kira sunan shi da qarfi, juyawa yayi idon shi ya kad'a yayi jawur, Mum bata taɓa ganin ɗan nata a wannan yanayin ba duk da yanda kowa ya san masu sunan Umar da zafi da faɗa nata Umar ɗin nada sauqin hali da sanyin hali, ashe dai ba a taɓa samun wanda ya yi pressing ɗin shi irin haka bane, ita kan ta sai da ta ji shakkar shi ta kama ta , sai ta kasa furta masa komai,Haroon da Ishaaq kusan a tare suka iso gidan, gani suka yi qofar gidan nasu an cika ana ta kallo,haka suka kutsa suma nan suka yi arba da abinda ke faruwa, Haroon ne ya je gaban Umar ya dafa kafad'ar shi yace, "Broth ko me ke faruwa kayi hakuri mu shiga ciki, sai a gama maganar a cikin gida, kaga mutane suna ta kallo" "Da wa za a shiga gidan? Ni Umar ni nake auren Jameelaah Jameel ko? to yau na sawwaqe mata aurena akan ta da igiya ɗaya, ko gidana ban amince ta shiga ba, in kuma zata shiga gidan ku ni zan tafi na bar maku gidan," "Ta shiga ta yi mana mi? Muje ciki " In ji cewar Haroon da tun asali ya washi Jameelaah, tun da ya ga haka ta faru kuwa ya san asirin ta ne ya tonu. Nan suka shige suka rufe gate suka bar Jameelaa tsaye baki sake, ta kasa tantace ita Jameelan aka saka ko wa? Ganin kowa ya watse an barta a wajen, kuma an  shige da Humairah ta kwalla wata qara cike da hargowa ta bi su, ta dinga buga gate tana kuka tana baiwa Umar hakuri, akan ya maida ta d'akin ta ta tuba ba zata sake ba, sai kiran sunan Mum take tana kuka,ba wanda ya kula ta, suka shige ciki,da ta dame su Umar ya zabura zai je ya mata rashin mutunci Mum ta hana shi Umaimah ta tsorata da ganin Umar a wannan yanayin kai har Mum din ma, dan tinda ta haife shi bata taɓa ganin shi cikin irin wannan yanayin ba , Umar mutum ne mai hakuri da son 'yan uwan shi, tare da tausayawa na qasa da shi. Amma yau gaba ɗaya ya sauya,ko kalar fukar shi ta koma jawur kamar qosai. "Umar kaayi saurin yanke hukunci da baka sake ta ba, gata da yarinya tana shayarwa, kishi ne kawi ke damun ta ba wani abu ba," "Mum dan Allah ki bar wannan maganar, kishi hauka ne? Akan ta aka fara zancen kishiya? Ko ta taɓa jin nace zan yi aure, meye bana yi mata dan kawai ta ji daɗi,dik abinda take min kauda kai nake yi dan a zauna lafiya, bata isa ta taɓa mahaifiya ta a wannan yanayin na kyale ta ba, ban haifu ba ma kenan" "Yah wai sakin ta kayi? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" "Ni dama na dad'e da sanin halayen ta, kune baku gane wace ce Jameelaa ba, har bincike sai da na yi akan ta, ba mutanen kirki bane ita da mahaifiyar ta, mahaifin  ta ne mutumin kirki,Allah ya kyauta ya sa hakan shine mafi alkhairi, in da rabon zama a gaba Allah ya shirya ta," "Babu ma rabon zama, ba wadda ta isa ta taban mahaifiya ko mahaifa na kyale ta," "To Allah ya kyauta mana" "Ameen" Kowa ya amsa, sai sannan Haroon ya fara neman jaririyar shi, Ishaaq ya dauke ta ya yi mata addu'a, Haroon ma haka, nan aka fara hira kamar ba abinda ya faru, Umar kuwa ya kulle idon shi yayi shiru, yana jin rad'ad'i a ran shi, wanda ya san na farko dai akwai wulaqanta masa mahaifiya da Jameelaa tayi, na biyu kuma akwai rabuwar shi da macen da yake tsananin so, sannan na uku sanin mummunan halin Jameelaa da yayi, tabbas yayi nadamar fadawa soyayyar ta, Sapnah ke riqe da Humairah, wadda ta lafe a jikin ta kamar mai jin bacci, lokaci zuwa lokaci tana satar kallon Umar, tausayin shi ne fall zuciyar ta, can kamar wanda aka mintsina, ya ɗauki waya ya kira Kulu, tana ringin ta ɗauka tayi sallama, ya amsa sannan yace, "Kulu ki rufen gidana ki kai min keys gidan Mum ki zauna acan ko waye ya je shiga in bani na dawo ba kar ki bari koda kuwa Jameelaah ce, ki rufe har d'akuna da ko ina," Ko amsar ta bai jira ba ya kashe wayar, ya sake kulle idon shi, kowa shiru yayi, Aunty Hauwaa ce ta fara fita, sannan Sapnah ta miqe dan bin bayan ta, ajiye Humairah tayi wajen Mum ai kuwa ta sa kuka, ta riqe mata riga, har qirjin ta na bayyana ta sama, da kyar ta samu ta amshe , Umar ne yace ta miqa masa ita, zuwa tayi ta miqa masa yarinyar, ta tsaya tana kallon shi, sannan ta juya ta kalli sapnah, daga qarshe taje wajen Umar, kowa sai dariyar qiwar ta yake yi, banda Umar da Sapnah, wanda su kadai suka san mene ne a zuqatan su, Umar sai kallon ta yake da yanayi na tsantsar so da qauna, yau ya tabbata ita kaɗai ce zata iya son shi ta haɗa da dangin shi, murmushi ya yi mata a hankali ya furta, "Thank u" "For what?" "For everything" "Ur welcome, and thank u too" "For what?" "For staring" Murmushi sukayi, ya qarasa karbar Humairah sannan ta yi ma Mum sallama, da mai jego ta tafi. A nan Umar da Mum sukai magrib, dan kuwa sai da Mum tai wa Umaimah wanka sannan Haroon ya kira Aunty Hauwaa akan su zauna zai maida Mum ya d'akko Kulu ta ci gaba da kula da Umaimah da babyn su. Haka kuwa aka yi ,Umar ma a gidan su ya kwana ranar, dan kuwa Humairah ba a saba zuwa da ita gidan ba bata saba da Mum ba, kuka ta dinga yi da za a bar ta, dan haka Mum tace ya kwana kawai. ********************** Jameelaa da ɗan sauran dubu ukun dake jakar ta ta yi gidan bokan ta, dan kuwa bata ga ta zuwa gida ba, in bata je an juyo mata da kan Umar ba ya maida ta a daren. Koda taje a kulle taga shagon dan haka ta zauna anan, tana jiran shi dik inda yaje ya dawo ya yi mata aikin ta ta koma d'akin ta,sai bayan isha'i ya koma gidan, yana ta zuqar sigarin shi, shida mai adaidaita sahun daya kawo ta ran farko. Tana ganin su ta miqe ta na hamdala, "Boka ka taimake ni... dan Allah ka taimaken ka sa mijina ya maida ni gidana, ya sakeni ya raba igiyar dake riqe da auren mu,na shiga uku inna rabu da Umar, shine rayuwa ta, dan Ta kan tsamiya ka taimakamin," Kallon juna suka yi da abokin shi, dik da ba wani haske sosai, amma har sun karanci junan su, "Bude qofar muje ciki," Bude qofa mai adaidaita yayi  suka shiga gaba ɗayan su, nan boka ya zaro kayan aiki, kamar sokuwa kanta ya toshe ta kasa gane komai ba gaskiya bane. "Gaskiya kinyi azarb'ab'i, ke da aka ce maki sai anyi wata ana aiki, shine kika kasa hakuri watan yayi? Yanzu haka daga zuwa binne mahaifar karya muke, dan ya zama sai yanda kikai da shi daga qarshen watan nan, gashi nan kin rusa mana komai, dole a sake aiki daga farko, amma yau tinda auren ya qare ki kwana a kwana ana yi maki aiki, shima wannan da kike gani yana taimaka min wataran musamman binne abubuwa a bayan gari, kamar yanda muka je binne wannan mahaifar karyan da shi, maza ki tashi ki tube a fara yi maki aiki, kai jeka daga waje, in za a miqo abu zan kira ka," Mai adaidaita waje ya fita yana ta murna, yau zasu yi till down suna raqashewa, ruwa aka fara fesa mata, zuciyar ta ba daɗi samm, ko sha'awa bata da shi, haka ya fara sarrafa ta, yana cikin sarrafa jikin ta, tinani ya fado mata, me yasa yau bai tuma ba na zuwan aljanun Nijer? Sannan yau kwata-kwata bai zancen Ta kan tsamiya ba, ba wani surkulle yau, ga shi an sake ta, anya kuwa bokan gaske ne wannan? Sai zuciyar ta ta fara qaryata shi sai wata ta gaskgata shi, tace da baya ci ai da kwanaki baki samu nasarori wajen Umar ba harda kud'in da kika tara a dakin ki da baki yi nasarar samun su ba, tinawa da kudin data tara a dakin ta ne yasa ta bangaje shi ta miqe tsaye, Tsawa ya daka mata akan dole ta koma ta kwanta, "Kina da hankali kuwa? Aljanu na maki aiki zaki miqe a zabure haka ba a maki izini ba? So kike yi ki haukace ko?" "Kaiii dakata dalla can, kuɗi na ya saken nayi shirme ban koma na kwashi komai ba na zo nan, ga uban kuɗi can a gida, matsa ka ga, in da da gaske aikin ka naci da ba a saken ba yau, da mijina bai daken ba cikin mutane, aure na ya ɓaci ne saboda kai, nayi dana sanin sanin ku a rayuwa ta, kwalama mai a daidaita sahu kira yayi, aikuwa ba a jima ba ya shiga, rufe qofar sukai, sukayi kan ta, daure mata baki suka fara yi, sannan suka ci gaba da yi mata dik abinda suka so, Jameelaa tin tana kuka ta cikin tsumman dankwalin ta har ta kasa, jikin ta ya mutu murus, ko hannun ta kasa d'agawa take, basu barta ta huta ba sai wajen 1 na dare. Suka wurga mata kayan ta suka fidda ta daga shagon, a adaidaita sahu suka sanya ta, har gida suka kai ta, dan bai manta inda ya kai ta ba ranannan, suna aje ta a qofar gidan suka gudu. Tsoron dare ne ya kama ta ya sa ta fara buga qofar tasu cikin sanyin jiki. Ramai a tsorace ta miqe ta tada Baban Jameelaah dake shaqar baccin gajiya,Bukar ma na d'akin shi ya farka yayi wuqi wuqi da idon amma ya kasa motsawa, tinda suka dawo basu taɓa jin an taɓa qofar gidan su ba bayan 10 na dare balle 1 da kusan rabi na dare. Malam Jameel ne ya kwantar ma da Ramai hankali sannan ya fita, yana ta magana Jameela murya bata fita sai faɗi take tana "Baba ni ce," amma inaa sam baya jin ta. Da addu'a ɗauke a bakin shi ya buɗe qofar numfashin shi kamar zai dauke dan fargaba, to muna cikin zamani na kashe-kashe, gani yayi bai ga kowa ba, ya fara jan A'uzubi kalimatillahi.... a zuciyar shi, wataqila aljanu ne suke musu bugu haka, da sauri ya ja baya zai rufe qofar Jameelaa tana daga kwance ta ja jikin ta ta shiga ta kama qafar Baban nata, ihu ya zunduma ya fara karanta qul'uuhiya. Cikin dasasshiyar murya tace, "Baba ni ce Jameelaa, nice Baba" D'agawa yayi daga faduwar da yayi ya kalle ta, nan da nan ya yi shiru, ya tashi zaune sosai ya sake kallon ta, sannan yace, "Jameelaa? Jameela me ya same ki haka? Kin gan ki kuwa kamar wadda tai artabu da manyan 'yan fashi da makami?" Kamata yayi suka shiga ciki, Ramai ta qule a qasan gado tin da taji ihun gwarzon mijin ta da bashi da tsoro, ta san ko meye yafi qarfin ta. Sai kwala mata kira yake amma haka taqi fitowa, Bukar ne yayi ta maza ya fita, ganin Jameelaa ya sanya ya kwala kiran sunan ta da qarfi, tare da zuwa inda take yana tambayar ta lafiya take ko dai fashi aka yi masu ina Yah Umar da Humairah? Ramai na qasan gado ta ce, "Jameelaa kuma, me zai kawo ta gidannan da tsohon daren nan?" Sai ta hau qoqarin fito wa daga qasan gadon. Da kyar Ramai ta fito, har ta rasa ya akai da fari ta shiga qasan gadon ma,abu kamar wadda aka d'agawa ta shige. "Malam Jameelaa naji kuna kira fa iwar haka, me ya faru" Ganin jameelaa a qasa ne ya sanya ta ruga wa wajen ta itama da gudu,Ramai ce ta kula ma kamar a sume take da sauri ta janyo butar tsakar gidan ta kuza mata ruwa, ai kuwa tana farkawa ta fashe da kuka mara sauti, dan kuwa muryar ta a dashe take. "Dora ruwa mai zafi Ramatu a yi mata wanka, dik jikin ta qasa ne ga shi na kula da wani yanayi a tattare da ita, in ta huta taci abinci, ta samu bacci gobe maji meye matsalar tunda mijin ta be kira ba kuma bai zo ba sannan ba tare suke ba" (Kun ga ko anan hakan ya nuna kyawun halin Umar da kuma yanda ya so Jameelaah ya nuna mata kulawa da tsananin qauna) Ba b'ata lokaci Ramai ta yi yanda mijin ta yace,a nan tsakar gidan ta wanke ta tass, ta tabbata kuma ta gani da idon ta alamar an sadu da Jameelan, lallai Umar mara mutunci ne, sai da ya gama saduwa da d'iyar tasu ya lallasa ta da dikkan alama shine ta gudo gida,ruwa mai kyau ta sa mata tayi wankan tsarki. Tinani Ramai ke ta yi akan,wataqila ma gudowa tayi saboda azabar ta yi yawa, Ramai na gyara ta tana kukan tausayin Jameelaa. Taci abinci sosai dan kuwa tana buqatar shi, koda aka gama mata wankan da kan ta ta iya tsaiwa yau har sallah ta rama tun daga farkon wadda bata yi ba a ranar,bayan ta idar ne ta samu waje ta kwanta, Ramai kuwa bata iya komawa bacci ba ita da Malam Jameel kwana sukai suna sallar dare, dan kaiwa Allah kukan su akan Allah ya bayyana gaskiyar mai gaskiya tsakanin yaran biyu. Washe gari da safe Jameelaa bayan anyi sallah an karya ta zayyana qarya da gaskiya tace Umar dan zai yi mata kishiya ya sake ta harda duka, amma ta b'oye dik wani laifi data aikata masa da mahaifiyar sa, Malam Jameel ne yace, "Kashhh anya Jameelaah abinda ya faru kenan? A halayyar ki dana sani yaron nan ba zai maki haka ba, sai dai ma ya girmama ki , ya karrama ki, sai dai in asiri aka masa aka juya kan shi akan ki," Cikin sauri ta cafe zancen da cewa, "Ehhh Baba asiri aka masa, boka na yace asiri aka yi masa aka rabani da shi," Fadin bokanta da tai ne ya sanya gabanta yin wata iriyar mummunar fad'uwa da tsittsinkewa, abu na farko tinawa da azabar da suka bata jiyan tayi, sannan ta furta boka a gaban baban ta da Ramai dake yawan mata nasiha a kwanakin nan akan ta gujewa sharrin bokaye maqaryata ne, "Jameelaah bokan ki fa ki ka ce? Har boka gare ki ma kenan, tabbas ruwa baya tsami banza, dole muje mu bawa iyayen yaron nan hakuri, sannan in ba shi yayi ra'ayin maida ki ba Jameelaa sai dai ki auri wani ko kiyi ta zama damu. Na maki izini Ramatu kije ki ba mahaifiyar yaron nan hakuri ki jiyo mana asalin me ya faru, ni kuma zan je naji daga wajen mijin nata me ya faru sannan na gana da mahaifin shi Bukar shirya mu tafi yanzu," "Inshaa Allahu zani malam anjima, ke kuma kin wa kan ki, kan ki kika zalinta, wai ace dik irin alkhairin da yaron nan yake mana ya sai mana gida, abin hawa, abinci, abin sha, da komai da muke buqata, amma kika qi hakuri akan rayuwar da kike ciki koda mata uku zai auro a rana ɗaya ,haka ki ka murje ido kika qi godewa Allah da dikkan baiwar da ya maki,  Ni kaina na uwar ki aje makaman jahilci na na koma ga Allah, Malam na koyan karatun addini kuma kullum sai na yi maki nasiha a qoqari na na kawar da tunanin ki akan mummunar turbar da na ɗora ki tun farko,kar ki manta fa Jameelah kin haddace qur'ani da wasu littattafan na islama, dik da ba dan Allah ki kayi hakan ba ya kamata ace sun maki amfani yanzu amma inaa, sai taurin kai da kauce hanya ma ki ka sake yi"   "Ramai na shiga uku na lalace Ramai, ina zan saka kaina, abinda na jawa kaina ba qarami bane Ramai, ki taimaka min Umar ya maida ni d'aki na kodan yarinya ta" Zan ga yanda za ai bari na shirya na je gidan nasu na ji me ya faru dan na san ba zaki taɓa fad'ar gaskiya gaba ɗaya ba ko za a yanka ki.......... *Maji ma gani in tusa zata hura wuta* [09/09, 10:36 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 39: Ramai ce zaune a parlourn su Umar Humairah na ta wasa a jikin ta, Mum sai mamaki take yi dan ganin yanda yarinyar ta sake da Ramai, can ta daina mamaki tabbas dole yarinya tafi shaquwa da Ramai tinda suna je mata akai-akai,  ita aka raina aka raba da jikar ta, dan haka bata san ta ba, shine dalilin yi mata qiwa. Umar ne ya fito cikin shirin tafiya Office, yana ganin Ramai ya isa ya durqusa gaban ta ya gaida ta, amsawa tai cike da jimami. "Umar na zo ne dan na baka hakuri, dan kuwa dik wani abu da Jameelaah take aikatawa koda bani nace tayi ba ina da kamasho a ciki, domin nice Ummul aba'isin lalacewar ta,anfi samun kaso mai tsoka na tarbiyya ne daga wajen uwa, ni ɗin na zama mai son kai, shi yasa Jameelaa bata da tarbiyya, lokacin dana gane gaskiya ina nuna mata hanya lokaci kuma ya qure min gaskiyar ba za ta wa Jameelaa amfani ba sai dai in Allah ne ya so ta da rahama, ta riga ta riqe dik wasu hanyoyi marasa kyau da na koya mata a baya" Hawaye Ramai ta share ta ajiye Humairah a gefe, ta durqusa a qasa, ganin haka Umar ya durqusa shima sosai yana roqon ta akan ta tashi, qin tashi tayi ya juya wajen Mum yana mata alamar ta yi mata magana,Mum ce tace, "Habaa Maman Jameelaah, hakan bai kamata ba, komai kike so wajen Umar kinfi qarfin shi, amma bai kamata ki durqusa masa ba, miqe dan Allah ki zauna," "Dole na durqusa Hajiya, mun maku ba dai-dai ba ne ai, tin daga ranar da akai aure muke rufar ku har yau, na sani Umar baka same ta a budurwa ba amma ka rufe magana kamar yanda tace min baka sanar da kowa ba,wannan ya zama sirrin ku, amma ina son ka sani ni na bata shawarar yanda zatai dan ka ɗauka an yi mata fyade ne, Umar ka yafe min, ni ke karba mata taimako na mallaka, daga nan ta fini zaqewa daga wajen malamai ta koma wajen bokaye, Umar tabbas mun cutar da kai, amma yanzu mun gane kuren mu, mun fayyace maka halayen mu munana a fili ka gani, muna bin ka da sharri kana bin mu da alkhairi, Umar ka yafe mana Mun tuba mun bi Allah , na maka alqawarin ba zamu sake aikata abinda mukai a baya ba,dik da na san bai kamata na tona mana asiri ba wajen neman gafara amma ya zama dole ka sani komai Jameelaa take yi ta sanadi na ne, amma inshaa Allahu ko zaka maida Jameelaa sai ta zama mutuniyar kirki, ba Jameelaar da ka sani a baya ba, ba zan takura maka ko na roqe ka ka maida ta ba, sai dai zan takura da roqo har sai ka yafe mana wannan babban laifi da muka yi maku," "Ballan tana ma aure  ni da ita ya qare, musamman dana ji waɗannan laifukan da kuka aikata akaina, na yafe maku duk abinda kuka yi min amma ba zan sake haɗa wajen zaman aure da d'iyar ku ba har abada, gida da babur da na sai ma mahaifin ta na yafe masa na baku kyauta, amma ba zan baku d'iyata ba zan riqe ta, ku kuma ku riqe ta ku d'iyar, na tafi office majinyata na jira na" Cikin tsananin damuwa ya fita, ashe qarya suka yi masa? Ya ci gaba da kwanciya da ragowar wani? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, wannan wace iriyar rayuwa muke ciki? Ko da ya shiga mota kuka mai quna ya saki saboda tsabar damuwa da tausayin kan shi, he is so innocent bai taɓa b'ata 'yar kowa ba, bai taɓa cewa ma yana son 'yar kowa ba sai akan Jameelah amma sai da aka samu wadda ta cutar da shi, baya nufin kowa da sharri, hasalima soyayyar ta ce fal ran shi, har yanzu da yake jin tsanar ta da halayen ta son ta bai fita a ran shi ba, zai daure zai jure amma ba zai koma mata ba, wannan alqawarin shi ne. Share hawayen shi yayi ya gyara fuskar shi sosai sannan ya kunna motar shi yayi asibiti. Fuskar Mum ma jawur saboda ɓacin ran abinda taji, amma haka ta danne saboda su ɗin mutane ne masu karamci, ta ce ma Ramai sun yafe masu, amma gaskiyar magana basu buqatar mace kamar Jameelaa a zuri'ar su. Ramai na kuka ta fita ta bar gida, ranta ba daɗi akwarai, Humairah ma kukan take dan ta saba da Ramai sosai, tinda kullum sai sun je. Tana zaune tana ta kukan baqin cikin rabuwa da d'iyar ta da mijin ta akan son zuciya ga kuma qasan ta dake ta mata rad'ad'i saboda tsabar azaba,dan ba kaɗan ba suka wahal da ita jiyan, Ramai ce tayi sallama ta shiga, idon ta yayi jawur alamar ta sha kuka, "Ramai lafiya... waye ba lafiya... Ko Humairah ce?me Umar yace zai maida ni ɗin?" "Ashe ma zai koma shan nonon mahaifiyar shi kenan Jameelaah? Ke da Umar kam in ba wani iko na Allah ba ko kuma rabo, na tabbata ba ke ba shi, domin kuwa ya jaddada min hakan da kan shi mahaifiyar shi ma haka, sannan yace ba zai ba da Humairah ba, shine babban abinda ke sanya ni kuka, ina tausaya ma yaron da aka raba da mahaifan shi uwa ko uba wajen rabuwar aure,wasu  yaran na tashi cikin qunci da tsanar kowa tare da lullub'ab'b'en munafurci da mugun hali a qasan zuciyar su, wanda suke aiwatar da shi ba tare da angane su ke yi ba, Jameelaa da yanda na fara koyar dake munanan abubuwa dana aje na fara koya maki mai kyau kin ɗauka da ba haka ba, yanzu wa gari ya waya? ki daina min kuka haushi ke qara kamani ni dan uban ki" Jameelaah har buga kan ta take a jikin bangon da ta jingina da shi tsabar shiga damuwa da tashin hankali, ina zata saka ran ta yanzu Umar ya barta har abada? "Na shiga uku na lalace na banu ni Jameelaa, yau na ga ta kaina, dan Allah ku taimakamin na koma gidan mijina, wayyooo Ramai na shiga uku na" "Dan Allah ni karki taran maqota a zaci mutuwa aka min, ki shiga d'aki ki rufen baki kar ki ja na lallasa ki laifin waye? In ina da laifi a lalacewar tarbiyyar ki ai na yi qoqarin sauya maki halayya dana gano gaskiya ko? amma haka ki ka kafe ki ka munafurce ni ki ka nuna min kin sauya ashe kina can kina qullawa kan ki gadar zare, ni ban girme ki ba amma na aje makaman jahilci na? sai ke kika maqale naki kamar jakar fata, to ga abinda kika jawa kan ki nan, ina bokan naki yau?" Haka Ramai ta yi ta aikin gida tana faɗa bakin ta ya qafe qafff ba yawu a ciki, ranta sai suya yake musamman in ta tuno Humairah, saboda ba da wasa take son yarinyar ba. Jameelaa kuwa daina ci da sha tayi saboda damuwa, abincin ma baya shiga ko ta ci sai ta dawo da shi. *********************** Yarinyar Umaimah ta ci sunan Mahaifiyar su Haroon Ameena sina kiran ta da Ummee, Haroon ji yake dik duniya ba wanda ya kai shi jin daɗin rayuwa, saboda samun iyali nagartacce, Sapnah na matuqar son yarinyar akwai kyau da qiba, futum-futum din kumatun ta mai lotsawa ke burge ta, Muhammad ɗin Hauwaa na son taɓa mata kumatu, Umaimah ta hana tace gani yake kamar balambalam ne hala, haka Sapnah zata haɗa su dika tai yi ta masu wasa, tana yi masu surutu kamar suna ganewa. Humairah yanzu ta fara sabawa da Mum amma ba wani sosai ba kamar yanda ta saba da Ramai, tinda tana zuwa aiki ba koda yaushe take a gida ba. Yau weekend dan haka suka shirya dan zuwa ganin baby Ummee, komai Mum ta haɗa a jaka na Humairah,  ta sanya mata kayan ta kalar nata, abin gwanin sha'awa, Umar ya qure wanka, dan yau yake son ya bayyanawa Sapnah sirrin zuciyar shi, shi ke jan motar suna tafe suna hira. Koda suka isa gidan Umaimah a rufe yake, tinda Ishaaq da Haroon suka fita ta koma wajen Hauwaa, Sapnah sanye take da riga da wando wanda suka yi matuqar amsar shape ɗin ta, sai cilla Muhammad sama take yi sama shi kuma yana dariya, "To zauna ayiwa Ummee itama," "Ah ah Sapnah ban isa ba, bata yi k'warin daza a wurga ta sama haka ba" "Ohhh yaran zamani babu ko kara? Ai itama uwar ta ce, ko an faɗa maki in ta wurga ta ba zata dawo bane?" "Mummm oyoyo," Da gudu ta faɗa jikin Mum Umar ne ya shiga gidan ɗauke da Humairah, Sapnah ta aje Ummee ta amshi jakar hannun Mum, ta durqusa ta gaida ta, sannan ta kama hanyar d'akin ta dan zuwa sanya hijabi, Umar kurrr yayi mata da ido, dik da bata kai Jameelaah shape ba ba ta rasa komai ba itama, ga kalar fatar ta mai kyau. Hararar shi ta yi sanda zata shige dakin tare da murgud'a masa baki, dan ta gama kama shi yana kallon ta,murmushi yayi ya sosa kai da ɗayan hannun nashi, sannan ya qarasa shiga ciki, bayan gaishe-gaishe ya tambayi masu gidan suka sanar da shi basu nan sun je kasuwa. "Ohhhh ashe fa ku 'yan kasuwa ne , ba kuyin weekend," "Muna yi mana ran lahadi amma," Dariya suka yi sannan Umaimah ta ɗauki Humairah, shi kuma ya ɗauki Ummee suna ta hira abun su Sapnah ta fita ta je kitchen ta had'o masu abun sha da na ci, zuwa tayi ta aje ma Mum nata a gefen ta, sannan ta aje ma Umar a nashi gefen, zata tafi yace, "Madam ba gaisuwa ne?" "Ina kwana?" "Bana cin miqe," Kallon gefen Mum tayi ta ga bata ma kallon su, murgud'a masa baki ta sake yi ta shige kitchen, murmushi yayi salon ta na burge shi. Yana sane ya ɗauki lemon ya zuba kaɗan a jikin shi akan idon Umaimah kuwa hakan ta faru, zata yi magana ya sa hannu a bakin shi alamar tai shiru, dariya tayi qasa-qasa, sannan ta kad'a kai alamar ta gano shi. "Kashhh abunnan ya zuba min a kaya, Sapnah ɗan zuban ruwa na wanke," "Ok taso to," Bata kawo komai a ranta ba haka Mum da Aunty Hauwaa ma basu gane komai ba, suna zuwa kitchen ta miqa masa ruwa a cup ɗin da suke amfani dashi wajen d'iban ruwa, qin amsa ya yi ya tsaya ya kafe ta da ido tana ja da baya yana bin ta, sai da bayan ta ya taɓa fridge sannan ta tsaya, kallon ta ya dinga yi, tin tana iya kallon shi har ta kasa, ta sauke idon ta qasa ,daga nan ta fara qoqarin guduwa, dubawa tayi space ɗin daya basu ba wani isasshe bane tana taku daya zasu hada jiki, wato ya mata haka ne dan kar tace zata gudu ko? "Please ni dai ka matsa na wuce kar su ga mun dad'e," "Sai su zaci me ke faruwa kenan," Wani qamshi taji ya fita daga iskar bakin shi nan take ta lumshe idon ta, zuciyar ta na gudu kamar zata fito waje, "Yah Umar dan Allah ka matsa," "Sai kin amsa min wata tambaya kuma da eh nake son ki amsa, in ba haka ba, daukan ki zan cak na maida ki parlour na ajiye ki a  gaban su Mum " Zaro ido waje ta yi ta kama bakin ta,Umar yace mata, "Kin amince?" D'aga kai tayi da sauri, dan ta matsu ya bar wajen, kusancin nasu yayi mata yawa. "Ina son ki, ina qaunar ki domin Allah, ina son ki zama uwa a wajen Humairah da qannen ta da zaki haifa min, ina fatan zaki aure ni?" Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka fara sauka a kuncin ta na tsananin farin ciki, zuciyar ta kuwa na tsananin sauri saboda bugawa, sai wata zufa da ta fara tsattsafo mata ba zato ba tsammani, da gaske kunnuwan ta suke da suka jiyo wannan kalaman ko qarya ne? Da kyar ta buɗe baki, lips din ta na rawa tace........................ *Casssss sai anjima ko gobe maji me zata ce* [09/09, 10:36 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 40: "Matsa baya dan Allah, bana son wani ya gan mu a haka abinda matar ka ta zarge mu ya zama gaskiya a idon mutane," "Subhanallahi haba Sapnah ! inshaa Allah hakan ba zai taɓa faruwa a tsakanin mu ba har abada sai munyi aure" Baya ya ɗan ja, tare da rungume hannayen shi a qirjin shi ya langab'ar da kan shi gefe daya yana jiran yaji me zata ce masa, goge hawayen ta tayi idon ta a qasa, tana buɗe baki zata yi magana wasu hawayen suka zubo mata, "Dan Allah Sapnah kar ki min haka, ki tsaida zuciyar ki a wajen da ta dace, kar ki saka shakku akan abinda ke ran ki, na sani kina so na, nima ina son ki, kawai amsar ki na ke nema ko zaki aure ni?" "Yah Umar a gaskiyar magana ba zan iya auren ka ba, me kake tunani mutane zasu ce? Tinda kusan akaina kuka samu sab'ani da matar ka," "Akan ki aka fara rikicin amma ba dan ke na sake ta ba, saboda abinda tayi wa mahaifiyata ne naga ya kamata na rabu da ita, and yanzu haka da za ki ji abinda ta aikata lallai da ke kan ki kin tinkare ni da maganar aure dan ki sanya ni farin ciki, fuskata dake dauke da dariya bayan ta akwai wani baqin ciki daskararre mai wahalar fita wanda kece ruwan d'umi da soson da zata wanke min su, kiyi jahadi ki amince da aure na ki ceci rayuwa ta Sapnahh," "Please Sapnah domin Allah ki amince ki auri Abban Humairah, dan ki zame mata uwa ta gari, kar ta tashi da tarbiyyar da ba uwa a cikin ta, tarbiyya in ba uwa a ciki bata cika tarbiyya ba, dan akwai abubuwan da dole sai uwa ce ta san zu zata koyar da yaron ta su, ina nema wa yayana alfarma a wajen ki in ba haka ba zan kira Mum itama tazo ta roqe ki, and ku rage sauti an fara jiyo ku a parlour" In ji cewar Umaimah da ta shiga kitchen din, matse sauran hawayen da ke maqale a idon ta Sapnah tayi, sannan tace, "Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi, zanyi shawara da Aunty Hauwaa dik abinda muka yanke zan sanar da kai," Fuskar tausayi ya sanya yaqi amsa ta, ganin haka ne ya sa tayi murmushi, he is so cute..... "Yah ka bari mana is just a matter of time, lokaci na yi komai wayon amarya sai an sha manta," Duka Sapnah ta kai ma Umaimah,tare da harara, Umaimah ta ce, "Dik ni kadai matar yaya? To na gode da kulawa," "Ni gaskiya a kira aunty Hauwan yanzu, so nake a gama komai yau, ko hankali na zai kwanta baki ji yanda nake  jin rad'ad'i a raina ba ne, da ba zaki iya ja min rai ba kema" Idanun shi sun sauya kala, alamar da gaske yana cikin wani hali. Umaimah ce ta leqa parlour da kan ta, ta kira aunty Hauwaa ta yafito ta da hannu, "Umaimah please ki bari mana zuwa gobe,yau da gobe ai dik ɗaya ne," "A wajen ki ba," "Ta samu ne? Me kuke yi ne shiru ba wanda ya koma, da an shigo kitchen sai a laqe ba a komawa?" "Shawara Sapnah ke nema akan ta amince zata auri Yah Umar ko kar ta amince? Ke meye ra'ayin ki akai?" Sapnah da kan ta ke qasa ce ta yi saurin kallon Aunty Hauwaa tana zaro ido, dan jin amsar da zata bayar zuciyar ta sai harbawa take da sauri, Allah ya sa tace ta aure shi, shine fatan da take tayi. Kula da yanayin ta ne ya sa Hauwaa tace, "A gaskiya ni dai Umar bai dace da Sapnah ba....... "Aunty me kike fada ne haka? Waye to ya dace da ni in ba shi ba?" "Ke ce kika dace da shi Sapnah, dan haka shawarata kuyi aure nan ba da jimawa ba," Wani daɗi da kunya ce ta kama ta, dan reaction din ta ya nuna tin da ta amince kenan amma tana neman izinin yayarta tane. Dariya suka fara yi mata ta rufe idon ta zata shige ya tare hanya, "Not so fast 'yan mata, baki faɗa min amsar ki ba, a yau ina son Dad yaji labari mai daɗi irin wannan daga waje na," Cike da shagwab'a ta buɗe fuskar ta ta turo baki gaba kaɗan tana wani langwab'e kai tace, "To wai ba aunty Hauwaa tace maka na dace da kai ba?" "To ke meye ra'yin ki akan hakan? nima na dace dake tinda an gano kin dace dani ko?" "Kaiii Yah Umar, ka iya sanya mutum a tsaka mai wuya," "Ba wata wahala, da tini dana tambaye ki kin amsa ni da ba a kai haka ba," "Eh na amince ka dace dani, na dace da kai, mun dace da juna, Allah ya sanya mana albarka a rayuwar mu" "Ameeennn" Umar jingina yayi da bangon kusa da shi ya lumshe ido yana sake jin sautin kalaman ta masu daɗi na ratsa shi, "Wai shin me ake a nan ɗin ne? Kun aje mu a can kun tattare anan, meke faruwa ne? Umar ya kamata mu wuce Daddyn ku yau zai dawo," Da sauri Sapnah tayi baya ta fice ta qofar kitchin ɗin a guje, ta zaci Mum shiga zata yi, tana fita ta hau dariya tana rufe baki, a hankali ta furta, "Sai kace marasa gaskiya," "Ai shi nagani," Kallon shi tayi, bata san ya na biye da ita ba, buga qafa ta yi a qasa ta ce, "Wai ba kaji me Mum tace bane?tace  Kaje ku tafi, bana baka amsa ba? Me kake jira kuma?" "Ki sake kai min lemon ɗazu da nawa ya zube," "Ni ina zargin ka ma in ba kai ka zubar ba da gangan" Dariya ya sanya ita kuma ta shige, ta haɗa masa wani ta bashi, ya fita fuskar shi cike da annuri, Mum da Umaimah ne suka tafi gidan Umaimah, sun tadda Kulu ta koma daga markad'e ta yi masu abinci, gidan tsaff sai tashin qamshi yake yi Kulu akwai tsafta da iya girki. Umar ne ya yi wa su Sapnah sallama, tare da miqa mata wayar shi dan ta sanya masa No ta, tana gama sa mishi ya kira ta tayi saving tashi, ya dinga leqawa yaga dame ta yi  saving taqi bari ya gani, shi kuwa ya sanya mata  *Hayatee*  tana ganin me ya sa ta yi murmushi, dan kuwa anko suka yi, amma taqi nuna masa. Koda ya shiga gidan Umaimah yaga Mum ta aje mata wasu tarkace a leda da robobi a gaban ta, sai ya hau tambayar mene ne, Mum banza tai da shi kamar bata ji ba, tace ma Umaimah, "Ga su nan zamuyi waya zan maki bayani dallah-dallah kowanne ma na rubuta bayani na saka a ledar amma zan sake maki bayani ta waya, sa idawa sun shigo kuma," "Aikuwa dai Mum kin iya bada suna, Yah Umar akwai sa ido, da tambaya," "Ni kike wa rashin ta ido? Dana ara maki Iya Kulu,Iyaaa! Iyaaa!, .....Yauwa Iyaa, ki shirya na kusa sake aure, zamu koma gida, dan taga na bar mata ke har magana yarinyar nan take faɗa min" Dariya kawai Kulu tayi snnan tace, "To Uban d'aki na an gama, ai ko zuwa nan da izinin ka nayi shi, dan haka tafiya ma da izinin ka zan tafi" Wasa da dariya sukai tayi Mum taji daɗi da ɗan nata ya warware, ya bar ma Allah komai , a hanya suna komawa ya labarta mata yanda suka yi da sapnah bai boye mata komai ba, Mum tayi ta dariya, tace "Yaran zamani salon ku daban ne" Da dare bayan Dad ya huta daga tafiyar da yayi, Umar da Mum suka gabatar masa da maganar Sapnah, fada ya fara yi ba dan bai son Sapnah ba shi a cewar shi a maida Jameelaa, Umar kuwa baya son ya bata ta a idon Mahaifin shi, a bar ta da laifin da tai ita da Allah dan haka yace, "Daddy, ni ke auren Jameelaa, ni nake zaune da ita, ni na san wanne iri ne halayen ta, Daddy dan son Annabi kar ka ce na maida ta, da da halin maida ta dana hakura da komai na maida ta kodan Humairah, amma ba zan iya ba, ba iya wannan ne laifin ta ba, laifin ta babbane a wajena, da wajen ku,da zaka ji daka ban izini ko a hanya kar mu gaisa, amma ba zan so na bata ta a idon ka ba, dan Allah kar ka ce na maida ta," "Kwantar da hankalin ka magana ta wuce , Allah ya sanya albarka a auren naku kaida Sapnah, ita kuma Allah ya sa rabuwar kuce tafi alkhairi," "Ameen Daddy," Daga baya suka ci gaba da hira suna wasa da Humairah. ************************* Lokacin yin period ɗin Jameelaah ya gota sosai amma shiru kake ji ba bayani ta shiga damuwa iya damuwa, a kid'ime ta bazama zuwa asibiti, ko da taje ana mata gwaji aka gano tana ɗauke da ciki wata biyu, dai-dai watannin ta a gidan su kenan, kuka ta sanya tana kiran ta shiga uku ta lalace, ina zata saka ran ta, wannan kalmomi su suka zama mata kamar tasbihi, a iya watannin nan da ta zauna ta tina baya, sai ta hau kiran ta shiga uku ta lalace ina zata saka kanta. Wannan cikin baida laulayi irin na Humairah, shi yasa ma bata gane komai ba, sai shegen ci da take yi. "Likita dan Allah ka markaden cikin nan a zubar, in na  barshi asiri na zai tonu," "In ma na rufa maki asiri anan, a lahira zai bankade, bamu zubda ciki asibitin nan, kinga mun ɗauki report ɗin ki, ki tabbata ba abinda ya samu cikin nan, in kika zubar ko ba anan ba zamu kai ki kotu, dan kuwa zan sa a dinga bibiyar ki a ga me kike aikatawa" "Yau ni Jameelaa na ji jaraba, kai baka taimaka min ba kuma ka hana a taimaka min, wannan wace iriyar masifa ce na jawa kai na," "Bansan kalar ta ba, amma ke kin fini sanin ta tinda ke kika dakko ta," "Ni ba da kai nake ba... , kaga dai ba da kai nake ba, kar ka shiga maganar da ba ruwan ka," "Ke malama fita min anan wasu matan masu hankali na jira na," "Ni waya ce maka hauka nake," 🤷🏻‍♂ kafad'a ya d'aga sannan ya nuna mata hanyar fita, tana tafe tana masifa, da Allah ya isa akan takunkumin da ya sa mata. Gida ta je ta rasa yanda zata yi ta faɗa ma Ramai tana da ciki, in ma ta faɗa ta na da ciki to na waye? UMAR? KO BOKAYEN BOGI??????.......... *TAMBAYA A GAREKU MAKARANTA,SHIN CIKIN WA JAMEELAAH KE ƊAUKE DA SHI?*[09/09, 10:36 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 41: "Wai ni aman me nake ganin kina yi ne haka? Gashi yanayin ki duk ya sauya kamar na mai ciki, " Kuka ta fashe da shi kwuyan ta har yana kumbura dan tokare mata wuya da kukan yayi , ta shiga cikin tsananin tashin hankali, da can kafin aure bata yi cikin shege ba sai yanzu da girman ta da 'yarta, tinda dai ta tabbata wannan ba cikin Umar bane,sun dad'e rabon su da su kaɗai ta da juna. "Daga tambaya sai kuka?" Tattaro nitsuwar ta tayi, tayi gyaran murya sannan ta ce, "Ramai dole na yi kuka mana ciki fa gare ni, kuma gashi uban d'an ya koren daga gidan shi, dan Allah ku maida ni kodan yarana," Zuciyar ta na ta harbawa ta zabga wannan qaryar, a ranta take ayyana. 'Allah ka rufan asiri su yarda su roqi Umar ya maida ni d'aki na' "Alhamdu lilLAAHi, kaiii amma na ji daɗi sosai da samun wannan cikin naki, Allah ya sauke ki lafiya,.....a gaskiya tinda muka samu ya yafe mana,bazan iya cewa ya maida ki ba, iyaka zan sanar da shi kina dauke da ciki, ya rage na shi ya hakura ya maida ke, ko kuma ya barki anan ki haihu ya amshi abin haihuwar shi," "Dan Allah Ramai kar ki ce haka , kimin kyakkyawan fata na koma gidan miji na" "Kyakkyawan fata kam ina yi maki in ban maki ba wa zan yi wa? Allah ya tabbatar mana da alkhairi," Bari mahaifin ku ya dawo, sai na sanar da shi meke faruwa. Da dare bayan Baban Jameelaa ya dawo ya kammala komai, suna zaune yana kallon labarai, Ramai ke sanar da shi abin farin cikin da Jameelaah ke ɗauke da shi. Baban Jameelaah ya ji daɗi shima, yayi mata addu'a da fatan alkhairi, sannan yaci gaba da kallon shi, shiru ne ya biyo baya,bata ji yayi maganar maida ta d'akin ta ba. Kuka ta fara da shan majina,ta tabbata asirin ta ne zai tonu, "Me ya faru kuma?" "Ammmm....Malam wai fa ita so take a sanar da mijin ta, ya maida ta d'akin ta," "Hummmm d'akin ta kuma na ina kenan? Dakin da ta yi wa tofin Allah tsine da ayyukan ta? Ai d'akin nan ina jin kam in ba wani iko na Allah ba ya haramta a gare ta kenan, saboda yanda Mahaifin Umar ya min magana da shi kan shi Umar ɗin na tabbata ba zasu so sake maida ki gidan su ba,ba inda zani, sai dai zan sanar da shi kina ɗauke da gudan jinin shi saboda gaba ya san yana da d'a ko 'ya dake ya rage nashi ya maida ki,ko ya barki anan" Rintse idon ta tayi hawaye masu zafin gaske suna zuba a kuncin ta, kan ta jingine da kujera da kyar ta tashi daga qasan ta yi masu sai da safe ta koma d'akin ta, wayar ta ta jawo, ta danna no Umar ,ta yi ta ringing bai d'aga ba, a zaton ta fushi ya yi ,bata san baya kusa da wayar bane. Haka ta kwanta cikin tsananin damuwa da zubda hawaye. *********************** Ɓangaren Umar kuwa yana zaune gaban Iyayen shi ya kasa ya tsare, shi a dole sai an kai maganar shi gaban manya,ba zai iya zama ba Sapnah ba na tsahon lokaci. "Gwanda ma ka cire soyyar ta mai zafi a ran ka, kar ka manta abinda ya janyo mana fad'awa cikin tashin hankali komai zaka yi kana yin shi baya-baya Umar" "Mum ina son ta, kowa ya san inda suke  inda basu da d'a'a da Ishaaq bai auri yayar taba," "Dole mu san komai daga tushe, mu nemi asalin ta, da na iyayen ta, kai inda hali ma har da dangin ta dika, saboda ba zamu sake kwatanta abinda mukai a baya ba na rashin bincike" "Wannan gaskiya ne, mahaifiyar ka tayi gaskiya, Umar mun yi kuskure a baya na rashin bincika asali da kuma sanin wace ce Jameelaah, munyi hanzarin yarda da ita kasancewar ta boye mana ita din wace ce, so zan yi bincike sosai akan Sapnah kafin mu shigar da magana wajen manya, kuma mahaifiyar ka ta baka shawara mai kyau, ka yi komai a hankali, kar ka zurfafa," Jikin Umar yayi sanyi, tabbas gaskiya suka faɗa masa, amma da soyayya ta so ta sake makantar da shi, Allah ya sa yana da iyayen da suke masu hangen nesa, sun nusar dashi gaskiya saboda kar a maimaita mistake ɗin baya. Haka suka yi ta tattaunawa akan abinda ya kamata su yi, Umar daga baya ya musu sallama, bayan ya shafa kan Humairah da tai bacci a jikin Dad ya koma d'akin sa. Koda ya shiga d'akin ya hango wayar shi na haske, da sauri ya qarasa kiran Jameelaah ya gani,sai ya qi d'agawa, sai da ta katse sannan ya suba wayar sosai anan ya ga ashe ba kiran farko kenan ba, wajen 26 missed calls ta yi masa, yaso d'agawa amma ya sa a silent ya yi addu'ar bacci ya kashe fitila ya kwanta a hannun daman shi, ya ba wayar baya. Jameeelaah na ta kira bata gaji ba sai da bacci ya ɗauke ta a haka. Da asuba da ta tashi ta tura masa message ta sanar dashi ya kamata yaje gidan su akwai wata magana mai matuqar mahimmanci da take son suyi. 'Ko me zata ce min Oho?' Da safe bayan ya gama shirin office ya karya, ya ɗauki Humairah yana ta yi mata wasa, yanzu ta sake sosai da gidan da mutanen cikin shi, in ta fara kewaye gidan da rarrafe sai an kamo ta. Yana mota ya aje jakar shi, zai tada ta, kiran Jameelaa ya shiga wayar shi tsaki yayi, sannan ya d'aga a hasale, dan ya gaji da wannan baqin nacin nata. "Assalamu alaikum" 'Ya Allah! this gurl is going to kill me with her sweet voice' Dakewa yayi kamar muryar ta bata affecting din shi yace, "Wa'alaikumussalam, dan Allah meye ne? Kiie ta kirana kamar na ci maki bashi?" "Da bashi ne dana yafe maka amma abinda ke tattare dani yafi qarfin bashi, dan haka kazo Baba na son ganin ka anjima" "Too meye wannan shi kuma? Meye naci da yafi bashi?" "Sai kazo zaka ji," Bayan ta kashe wayar, Umar bin tashi wayar yayi da kallo, kamar an rubuta me Jameelaah ke son sanar da shi a jiki, can ya tada motar shi ya nufi gidan su Jameelaah, ba zai iya bari sai yamma ba, bai san me zai je ya zo ba, bai san wani abu mai mahimmancin da za a kira shi akai ba a gidan su duba da yanda suka rabu. Kiran ta ya sake yi yace, "Baba na gida? In yana nan gani nan zuwa yanzu" "Eh yana nan, amma kayi sauri kan ya fita," "Ki tsaida shi mana ki faɗa masa gani nan zuwa ba shi yake nema na ba dama?" Cikin faɗa faɗa yake mata maganar, ji tayi kwalla ta taru a idon ta, Umar ya daina son ta, a da ko b'ata rai baya yi da ita, yanzu har faɗa ma yake yi mata. (Ya sake ki ma balle faɗa) Da sauri ta tashi ta sauya riga, ta saka wata mai kyau daga wanda Ramai ta bata, dan har yau Umar bai sake buɗe gidan su ba,balle yace a kwashi kayan ta ko a bar su. A qofar gidan su Jameelaah motar Umar ta tsaya, ya ɗauki wayar shi ya sanar da Jameelaah ya iso, tai sauri ta sanar da Baba yana son ya wuce office, Yana cikin waya da ita ya ga Baban na fidda machine din shi da Umar din ya sai masa. Da sauri Umar ya katse wayar ya isa gare shi, Umar na son dattijon sosai ba kaɗan ba, dan kuwa mutumin kirki ne shi , kama masa yayi suka fidda tare da gaida shi, "Ahhh malam Umar,kaine da safe haka? Lafiya qlou, ya kuke, ya amarya ta me qiwa," "Kowa lafiya Baba, amaryar ka na gaida ka" "Ina amsawa, ai ta ci gaba da qiwa in Maman ta ta haihu kaga shikenan an sake min wata matar ko kuma aboki tayi ta yanga ma Alhaji ni na yafe," "Haihuwa kuma Baba? Wace zata haihu?and Baba kace na zo amma naga kamar fita za kayi," "Ikon Allah, ai na zaci kazo ne kunyi magana da ita Jameelaa ta waya akan abinda ke faruwa, dan yanzu take sanar dani zaka zo," "Ni kuma ce min tai kana nema na, dan haka ban wuce office ba na zo nan naji maqasudin kiran" "Ohhh Allah na gode maka da wannan yarinya, mu je daga ciki, ba za a yi wannan magana a waje ba," Bayan sun zauna a parlour Baban Jameelaah ya bayyana masa komai da ke faruwa, ai kuwa nan da nan ran Umar ya baci, "Ciki dai ba nawa ba ne Baba sai dai a tambaye ta inda ta same shi, amma ni kam indai wata biyu ne ba nawa bane, raboda na da ita yafi wata biyu bai dai cika uku ba amma tabbas yafi biyu, ina take Baba a kira ta tayi bayani da kan ta," Kwala mata kira Baba ya yi ta fita cikin zumud'i da farin ciki, dan ta hango su a waje suna hira suna dariya, ta tabbata komai ya wuce d'akin ta zata koma, Ta bulbulewa Ramai ɗan turaren nata, data fara amfani da shi, ta shafa powder qirjin nan an matso shi a riga, abinda Umar ya fi so kenan, zuwa tayi ta zauna ba ko mayafi balle hijabi, "Jameelaa ashe baki da mutunci, kin rantse sai kin kunyata mu a idon duniya, sai kin sa ɗan mutuncin da ya rage ake ganin mu da shi ya gama qarewa? JAMEELAAH CIKIN WA KIKE ƊAUKE DA SHI, IN BAKI FAƊAN GASKIYA TSAKANIN KI DA ALLAH BA NA YAFE KI MA DUNIYA" Cike da tashin hankali Ramai ta shiga itama, kallon Jameelaah dikkan su suka fara yi, ja da baya ta dinga yi dan ta gudu, sai buge Ramai dan bata san ta shiga ba, da sauri Ramai ta kife ta da wani hatsabibin tafi, sannan ta nuna mata tsakiyar parlourn tace, "Zaki sanar damu gaskiyar wake da cikin jikin ki ko sai na lallasa ki?" "Dan Allah kuyi hakuri zan faɗa, wayyooo Allah na na shiga uku na lalace, ni....ni....niiiimaaa bann sann na...naaawayee baaaaa" Ta saki wani irin kuka mai quna a zuciya, ita kan ta tana cikin rud'ani, "Bamu gane hausar baki san na waye ba, maza dubu ɗari nawa kika bi, Jameelaaaaaah ashe abun naki azimun ne haka?ya rabbi ka gafarta mana laifi na ne komai dake faruwa," Kuka Ramai ta sa sai da ta samu wajen zama saboda takaici, wannan wacce irin rayuwa ce, "Kin dai tabbata ba nawa bane ko? Dan kinfi kowa sanin ba nawa bane ko," D'aga kai tayi ta rushe da sabon kuka, miqewa yayi ranshi a matuqar bace, dole yaje a gwada jinin shi kar yana ɗauke da mummunan ciwo bai sani ba, bai san sanda ta fara neman maza ba da auren shi akan ta. "Baba na wuce office, Allah ya sake sadamu da alkhairi," Baba kunya tasa tinda ya duqa bai d'ago ba, wasu siraran hawaye ne ke sauka a idon shi,da wanne ido zai daga ya kalli yaron? Ta gama zubar masa da qima da mutuncin shi, ganin Umar zai fita ne ya sa ta zabura ta bishi a guje, ta qanqame shi, sai da yaji kamar ya taba wutar lantarki alokacin da jikin shi ke jiqe. Tsayawa yayi cakkk, ya lumshe ido, Jameelaah ce mace ta farko da ya fara sanin auratayya da ita, kuma taɓa ta ne kadai ke sanya shi a hali na buqatuwa da mace, amma yau ji ya yi yana jin matsanaciyar tsana da haushin ta, tura ta baya ya yi da qarfi, ta bugi jikin window, sannan ya nuna ta da yatsan shi manuni ya qanqance ido cike da masifa amma ya kasa furta komai. "Abban Humairah ka rufan asiri ka maida ni d'aki na, dan Allah ina son ka fiye da tinanin ka, ban san ina son ka haka ba sai yanzu, dan Allah ka manta da komai ka maida ni," "Tsakanin ki da Allah zaki iya manta me kika yi min?" Shiru tayi tana zubda hawaye, daga baya ta kad'a kai, alamar ba zata iya mantawa ba, "Balle kuma ni da kika cutar, kar ki sake kirana a waya, kar ki sake neman inda nake, sannan kar ki sake danganta shegen cikin ki da ni," A guje ya bar qofar gidan nasu da motar shi, ita kuma sai ta janyo hijabin dake kan igiya ta saka, qafarta ko takalmi babu ta fice................... *In ka shuka alkhairi zaka girbi alkairi, in ka shuka sharri shi zaka girba* [09/09, 10:38 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA  💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 42: Tafe take a qasa sai yanka zufa take, saboda saurin da take tayi dik ta galabaita, haka ta isa gidan bokan qaryan ta, shagon rufe yake da kwad'o,sai ta zauna dan ta huta kafin nan sun iso. A wajen baccin gajiya ya ɗauke ta, bata tashi farkawa ba sai da aka kira azahar, miqewa tayi ta kade jikin ta ta yi sallama a gidan da shagon yake ta dad'e tana sallama kafin wata dattijuwa ta leqo dogare da sanda, alamar dayar qafar ta na da matsala gaida ta Jameelaa tayi, sannan ta tambaya mai zama a shagon nan yana nan kuwa? "Baiwar Allah wanne daga ciki? Sule ko Bashari?" "Su biyun dik da ban san sunan su ba amma akwai fari akwai baqi, kuma farin gajere ne, baqin dogo,dan Allah ki taimaka min ki sanar dani inda zan gan su tin safe nake zaune ina jiran su ba ko ɗaya a cikin su," "Allah sarki, yarinya ai basa nan, sun tafi Habuja neman kudi, shi Sule ya saida adaidaitan shi suka tafi habuja dan su fara sana'a a can, yau watan su ɗaya da kwana tara da tafiya, ke ɗin wace ce?" Kuka Jameelaa ta fasa mai qarfi, sai shasshekar kuka take tana kumawa, dattijuwar nan ta dogara sandar ta ta dafa kafad'ar Jameelaa? Sannan tace, "Kema wani abun suka yi maki ko? Tafiyar yaran nan an kawo qarar su tafi a qirga, na yi iya qoqarin da zan na raba Bashari da Sule amma abun ya faskara, abotar su tayi qarfi ainun qarfin da dik wani yunquri da nai dan raba su abun ya gagara," Dukan cikin ta ta fara yi tana kallon dattijuwar tana mata bayani, idon ta na tsiyayar da hawaye sinyi jawur kamar garwashi. "Ciki ne da ni kuma nasu ne, ban san waye uban cikin dake jikina ba.....na zo su wanken baqin cikin da nake ɗauke da shi a cikin rashin sanin su ɗin ba bokayen gaske bane, gashi sun ninninkan baqin ciki da azabar da nake ciki, ina zan sa kai na," Kuka mai tsanani ta fashe da shi, dattijuwar ta kama baki tace, "Na shiga uku ni Delu, bokan ci kuma? Me ya haɗa Bashari da bokanci na san wannan dan iskan Sulen ne zai koya masa wannan shegantakar, yarinya kinga tin kan dare ya maki ki san abun yi game da cikin nan, dan kuwa tinda suka sa gaban su gabar ban san ranar dawowar su ba," "Ai ko da ace ba zasu dawo ba har abada tinda na dau cikin su dole na aje maki jika,ko tattab'a kunne,dan kuwa ba inda zan kai abinda ke cikina sai nan,.......kuma karki qara ɗorawa wani laifi na lalacewar ɗan ki ko jikan ki ne oho, saboda shi da kan shi ya fara nema na, Sulen da ki ke ta ambata kawo mai ni yayi, amma shi ya fara nema na, son kai ya hana ki gane d'anki ko jikan ki tantiri ne, kike mannawa wani laifi," Tana kaiwa nan ta fice tabar Delu da masifa, nan da nan ta shige cikin gidan ta fara tinanin yanda zata yi da wannan mata, da ganin idon ta a tsaitsaye yake zata aikata kawo mata jikan shege a gida, yanzu shawara dayia ce, shine ta tattara ta nemi yanda zatai ta saida gidan nan ta sai wani can inda ba za ta san ta koma ba ma, in yaso ta samu wani amintaccen da zai sanar da d'anta inda ta koma in ya dawo daga yawon barbad'ar tashi ya same ta can. Jameelaah na tafe ta na kuka har ta daina kukan ma, ga yunwa na cin ta ga tafiyar qafa data ci, rana ta bude sosai qafar ta sai zafi take yi ta rasa ya zatai da ran ta, ga yawun bakin ta ya qafe, zuciyar ta sai quna take, jiri ne ya fara d'iban ta, daf zata shiga lungun su, nan take kuwa ta faɗi tin tana ganin hasken rana na ratsa idanun ta har ta fara ganin duhu, ihun mutane kuwa kamar qarar redio take jin shi a kunnen ta shuuuuuuu,dan kuwa bata gane komai. Bata tashi farkawa ba sai a asibiti, hannun ta ɗauke da jini ana qara mata, Ramai na gefen ta da Bukar zaune, Bukar yayi kuka har ya godewa Allah, Ramai kuwa tana ganin ta farfado ta fara godewa Allah, cikin kuka da tsantsar tausayin diyar ta ta. "Ramai zan sha ruwaa, yunwa nake ji Ramai, a ina nake?" Sune abinda take ta maimaitawa, ba salati ba addu'ar komai, "Habaa Jameelaa, kin san kuwa kwanan ki nawa anan? Shine zaki farka da zancen abinci da ruwa? Ki godewa Allah mana da kikak sake ganin yau? Allah na tuba ka yafe ni ba laifin kowa bane sai nawa, laifi na ne, laifi na ne, Allah ka ban ikon gyara abinda na b'ata," "Inshaa Allah, Mama zaki gyara abinda kika b'iata, inshaa Allahu Allah zai taimake ki, saboda kinyi niyya mai kyau yanzu," "Allah ya sa Bukar, amma Jameelaa ta yi lalacewar da nake matuqar yin babban dana sani a rayuwa ta," Tea ta haɗa mata ta bata, ta shanye kuwa, sannan suka bata taliya da ta ji kifi, iya abinda suke da ikon bata kenan, sai da taci tayi nak, ta dawo hayyacin ta sannan ta tina da cikin da take ɗauke da shi. Shafa cikin ta ta fara yi, tare da kwarar da hawayen baqin ciki, "Ramai yau yaushe ne? Sannan me ya samen naga ana qaramin jini?" "Yau Juma'a Baban ki yaje masallaci in ya dawo zaki gan shi, yau kwanan ki uku kenan a nan, sannan cikin da kike ɗauke da shi ne ya lalace, kin zubda jini sosai shi yasa ake qara maki jini, an deb'i na mahaifin ki aka sanya maki," Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar Jameelaah, har ta kasa rufe wa saida ta saki ihun murna, sannan ta hau cewa, "Wayyoo Allah na daɗi ana baqin ciki in an yi.j bari ni dai murna nake, dana haifi shege ni jameelaah dana barwa kaina mummunan tabo a rayuwata, daga nan duniya har lahira, wayyooo Allah na gode maka, Ramai zubarwa kika sa ayi?" "Yo wa ya san ya akai ya zube, ba dai mu an zo an kiramu ba muna gida aka ce ga ki a kwance,shine muka tare me tasi aka kawo mu asibiti, likita yace aiki me yawa kikai ko dai wata wahalar kika sha shine ya janyo zubewar cikin,dan kuwa tin a can inda kika faɗi muka same ki cikin jini face-face, dama so nake ki farka naji ina kika je? JAMEELAAH baki san kiyi nadama ba ko? Shine kika je kika zubda cikin? Jameelaah ba dan mahaifin ki ya taushen bama ba zaki ga haqorina ba yanzu" "Ramai ban zubda ciki ba, ban taba sawa a raina zan zubda ba, tabbas wahalar dana sha ne na zuwa na sami waɗanda sukamin cikin shine ya sa ya zube, amma Ramai koda cikin shegene ban sa ma raina zubda shi ba, sai dai na san dik sanda na haifi abinda nake ɗauke dashi qarshen farin ciki ya zo min kenan har abada" "Allah na ganin ki, in ma zubarwa kikai, dan dai ke yanzu ba abar yarda bace," Likita ne ya shiga ya duba ta, sannan ya mata murna da farfaɗo eada tayi, dan Ramai ta sha kuka har ya tausaya mata. Sai da suka yi sati da wasu kwanaki aka sallame su, sannan likita yace ta guji yin aikin wahala nan da wasu watanni, mahaifar ta ta samu rauni sosai. Ramai ta yi iya qoqarin ta na ganin Jameelaah ta gyara lamuran ta ba laifi, rashin Umar kaɗai ya shiga jikin ta ya sa tayi laushi ta koma ga Allah. ************************* Bayan dogon bincike da tabbacin nagartar zuri'ar su Hauwaa, Iyayen Umar sun kai qoqon barar nema wa Umar ɗin auren Sapnah, ba wata ja in ja kuwa iyayen ta suka amince, nan da nan kuwa aka fara shirye-shiryen biki ba kama hannun Yaro, Umar ya yi iya qoqarin shi na ganin Sapnah amma rowar kan ta take yi masa, wataran haka ba zai zo neman ta tana lab'e tana ganin shi amma tace bata nan, Aunty Hauwa da Umaimah sun yi dik iya yin su taqi yarda ya gan ta, kullum sai dai suyi waya da Chatting, Da sadaki da lefe dik gaba ɗaya aka kai tare, Umar Allah Allah yake ranar d'aura auren su tazo. Yau Sapnah na zaune a parlour ita ɗaya, Aunty Hauwaa sun haɗa baki da Umar da Umaimah akan sai ya ga farin cikin shi yau, tana zaune da Muhammad tana sanya masa kaya ta yi mishi wanka, sai qiriniya yake yi, sanye take da doguwar riga mai kyau kalar maroon, da aikin baqi a jikin ta, ta dora gular rigar akan ta, tana miqewa hular ta sauka ta bayyana gashin ta da ya ke ta shan gyara saboda gabatowar auren ta, bata wasa wajen gyara kan ta, dik wanda ya santa watanni biyu baya ba zai gane ta ba yanzu sai ya kalla da kyau. "Muhammad ka nutsu ko na sa maka wando a matsayin riga," Dariya yaron yayi tayi kamar ya na gane me take faɗa. Qamshin turaren shi ta ji , mai sanyi da kwantar da hankali, limshe ido tayi, ta yi murmushi ta tabbata kizo qamshin shi yake yi mata, amma ta san ba Umar bane. Hular ta ta maida saman kan ta, sanan takwashe sauran kayan Muhammad dake qasa, ta juya cike da murmushi zata koma d'aki ta aje kayan. "Ko baki faɗa ba nasan tinani na kike yi," Ihu ta bude baki zata yi ta toshe da hannayen ta biyu da sauri, kayan Muhammad da man da komai suka watse a qasa, Murmushi kawai Umar ke bin ta da shi, hannayen shi zube a aljihun shi,  takawa ya farayi gaban ta tana qanqame idanun ta, sai da ya gama qare mata kallo, sannan ya duqa ya fara kwashe kayan da ta zubar. Bude ido tayi a hankali ta gan shi yana kwasar kaya, da sauri ta duqa itama ta na kwashewa, kallon juna suka tsaya yi, da sauri ta amshe na hannayen shi zata gudu ya tare qofar d'akin, "Ai baki isa ba yarinya, ki dawo kawai mu sha hira, na riga na gama ganin abinda ake min rowar ta shi, a gaskiya ba dan kar na yabi kaina ba da nace kin yi kyau sosai, soyayya ta ta karɓe ki," Hararar wasa ta yi masa, sannan ta dawo gefen shi ta tsaya tace, "Soyayya ta dai ta karɓe ka, kaga yanda kai kyau kuwa? Har wata qiba kayi," "Lallai yarinya kince wani abu, wato ma tsokana ta kike ko? Zaki gane ne dan Allah ki maimaita hakan randa aka kaimin ke in kin cika matsokaniya," "Kai ma ka maimaita kaga in ban maimaita ba, kasan in aka ce min A sai na ce Z" Kad'a kai kawai Umar yayi, yasan bata san dawan garin bane shi yasa, Zama yayi a kujerar dake kusa da shi, ya kama goshi da hannu daya, "Washhhh kaina ciwo yake yi yarinyar nan zaki gane Umar kika ba wa baqar izaya haka, sanda zan damqe ki ina tausaya maki," Bata ce komai ba sabida ta gano me yake nufi sarai, Ruwa ta d'akko masa da juice, sannan da maganin ciwon kai, aje masa ta yi ba tare da ta ce komai ba ta koma kitchen, abincin da ta dafa ta d'eba masa, sannan ta yanka fruits ta kai masa. Zama yayi ba kunya ba musu ya cika tumbin shi, tana ta kallon shi, tana lumshe ido, hango ta kawai take a jikin shi bayan aure suna cin abinci tare, firgigit tayi kamar wadda aka mintsina, ta kalle shi taga ko ya gano irin tinanin da take "Lafiya kike kuwa?" "Qalaou nake,to ya aikin yau? Ina fatan komai normal?" "Ehhhh to gaskiya akan sauran ranaku yau na samu sauqin komai, sai dai na sha wahala kafin mu haɗa plan din ganin gimbiya," "Habaa habaa ai  dama na faɗa da wadannan masu kan mutanen aka haɗa baki ka samu damar sani a kwana haka, ba komai zan rama ne," "Well, hakan na da kyau ai kin san in aka maka abin alkhairi ana son ka maida da alkhairi kaima," "Ya yi maka kyau, ai kai yau kamar sallah haka ke jin kana san," "Kema kuma haka ba, na san kin ga ɗan saurayi kyakkyawa hankalin ki ya kwanta," "Kaine ka ganni yau ni kusan dik zuwan da kake yi ina ganin ka ai" Zama ya gyara ya kalle ta, ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa, ya jinjina kai alamar zamu haɗu ne, dariya ta dinga masa, "Ka ishen da surutu ban tambayi d'iya ta ba, hope tana lafiya ko?" "Kwarai kuwa tana lafiya, sai dai ta na kewar ki fiye da yanda nayi kewar ki," "Ka dai dage sai anyi zancen ka, ni maganar d'iyata nake ba taka ba,ka shafamin kan ta in ka koma, Allah ya yi mata albarka," Sallamar Ishaaq da Hauwaa ce ta katse su, dan har yamma tayi lokacin dawowar su Ishaaq din basu ma kula ba suna ta hira, "Ohhhh Sapnah an boye miji anan ana ta shan hira, aka koramin mata waje," "Yah ni fa bani bace, in fact haɗa ma baki suka yi sai ganin shi kawai nayi anan," "Sapnah ba kyau qarya fa, ke kika min waya kika ce nazo kin kora Aunty hauwaa gidan Umaimah," Kallon shi tai da wani kallon inna kama ka zaka wahala a hannu na, dariya sukai ta yi mata,ta shige d'akin ta, ta kwanta tana murmushn jin daɗin ganin ruhin ta. Bata san sanda ya tafi ba sunyi-sunyi ta fita suyi sallama taqi, Ishaaq yace baya son gulma tana zaune tana kalallame shi da hira sai da ta gan shi shine zata qi fita,tana jin su tayi luf abinta tana dariya qasa-qasa. *********************** "Assalamu alaikum, aban awara ta nera hamsin" "Zauna ka bi layi bari na gama sallamar waɗannan sun riga ka," Jameelaah ce ke ta soya awara a cikin gida sanye da mayafi da riga da zani, dik ta rage haske dan kuwa tin da taji sauqi sosai ya bata sake saka qafarta a waje ba, kullum tana gida, ganin shiru da tinani zai iya sanya mata ciwo ne kawai sai ta maida hankali wajen saida awara a cikin gida, mutane kuwa nan da nan aka fara siya, kun dai san Jameelaa da nasibin talla, wayar ta ce ta fara ringing, ta d'aga ta zaro ta daga jikin ta, no qawar ta ta makaranta ta gani, wadda suka bata bashin kuɗi taci suna. Share majina tayi da gefen mayafin ta ta d'aga kiran tace, "Hello Khadeejah, ya kk?" "Lafiya qlou, kina lafiya kuwa? Kwata-kwata ko a social net an daina ganin ki, tinda kika haihu kika daina zuwa school, qawayen mu ana ta tambayar ki, yaushe zaki dawo na yi masu albishir?" "Dan Allah qarasa zuban awarar," "Ta nawa ma kace? Yi hakuri ina waya," "Ta ɗari zaki samin," "Wake saida awara? A ina kike ne haka?" Shiruuu tayi zuciyar ta na raya mata ta yanka qarya kawai, saboda kare AJIN ta.................. *What do u think guys? A kare aji ko aji down?* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏻  MAZAUNA GIDA   💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 43: Shiruuu ta yi har Khadeejaah tayi zaton ko layin ya tsinke ne, sai taji suna magana. "Shegiyar qarya, ai na je gidan mijin na ga ba ta nan, dana bincika sai naji ance ya mata dukan tsiya ya kore ta, ya mata saki uku, yanzu haka tana gidan su, ko gidan ma mijin ne ya sai masu, sana'ar da Baban ta yake da abin hawan shi dik shi ya basu, amma ta dinga qera mana qarya tana kiran uban ta qusa ne a gwamnati, qusa a gwamnati ko qusa a gyaran machines" Dariya sosai suke yi, Allah kaɗai ya san iya mutum nawa ne suka ji wannan labarin dan kuwa taji dariyar mutane da yawa ba zata iya tantance mutum nawa bane a wajen, ga kida qasa-qasa yana tashi tana jiyowa Allah kaɗai ya san ko ma a gidan biki ko Bd party suke tinda su bini-bini an yi party dan kawai a kashe kuɗi. Hawaye ne ya dinga sauka ta na zuba awara tana miqawa, kuma taqi kashe wayar, dan ta san ko kud'in sun qare suna da na sake sa wasu. Khadeejaah ce ta ɗauki wayar ta dan suyi hotuna,kawai sai taga bata kashe ba ashe, ji tayi gaban ta ya faɗi, (kunsan gulma in kayi ta ko kana sane kayi in aka kama ka ba daɗi) Da sauri ta kashe ta na nuna ma sauran, sune suka dinga nuna mata sai me dan Jameelahn ta ji ai da sun san ma gidan uban nata har can sai sunje sunga kwal uwar daka, (gulma ba a wajen talaka ta tsaya ba fa ooo, masu kud'in ma manyan magulmata ne wasun su, sai dai su gulmar su akan abin duniya ta fi tasiri). Bayan ta kammala saida awarar ranar ne ta ware riba ta ajiye, sauran jarin ta bayar a siyo kayan yinna gobe, dik ta zama wata so silent magana ma wahala take yi mata sai abinda ya zama dole take tankawa ko ta faɗa, haddar qur'anin ta data bari ta zube a banza ta kama tana tisawa, ta nan ta samu zuciyar ta ta fara yin sauqi, amma still soyayyar Umar na nan daram a ranta ta san da shi zata koma ga mahaliccin ta. ********************** Sai da ya gama kwashe komai mai amfani na d'akin nasu wanda zai buqata, sannan ya kai mota ya zube su, dakin ta ya nufa dan dubawa ko akwai wani abu mai amfani da zai cire mata, sauran dik bayarwa zai tinda da kud'in shi ya siya ba da na wani ba, Kamar ance ya bud'a kayan ta, yana bud'awa yaga wata baqar leda Viva zarowa yayi, yaga damin kuɗi a ciki, a qallah sun haura dubu ɗari uku bai tsaya qirgawa ba, yana ganin yanayin su ya san na shi ne wanda yake bata, bai taɓa bata lokaci ba ya saka a aljihun shi, ya ci gaba da duba kayan, sarqoqin ta kayan kwalliyar ta da dikkan kayan sawar ta, ya kwasa ya kai wata motar, yaran da suke taya shi aiki suna ta sanyawa a motar, yana kammalawa, ya bama drivern kwatancen gidan su Jameelaah, ya bashi da ledar aljihun shi ta kuɗin yace su kai mata su dawo a ɗebe kayan gadon a kaiwa Kulu can asalin gidan ta. Kulu harda kukan murna tayi, dinning din shi anan aka bar shi, da manyan fridge guda biyu, sabon fenti za ai ma gidan, a gyara shi, iyayen Sapnah sunce su zasuyi kayan d'akin diyar su basu buqatar komai nashi. Koda saqo ya iske Jameelaah kuka ta sanya sosai tana sake danasanin abinda ta aikata, kuɗi take so da mallaka meye bata samu ba a wajen Umar? Meye Umar bai mallaka mata ba? Ya bata kan shi, ya bata jikin shi zuciyar shi da rushin shi, ya mallaka mata dukiyar shi, ya bata dikkan soyayya da kulawa, wanda da wahala a samu miji mai halin Umar a wannan zamani amma ta yi fatali da komai saboda son zuciya ta na hango fiye da abinda take samu. "Baiwar Allah ki nuna mana inda zamu aje kayan mana ko mu bar maki anan zaki shiga da su ne?" Cikin sanyin jiki ta nuna masu hanya, suka dinga shiga da kayan sawar ta, manyan laces ɗin ta da atampopi dik ba wanda ya taba mata, jakunkuna kamar lefe, ta kalman ta da komai da komai Umar bai taɓa mata su ba, harda sarqa da d'ankunnen ta na zinare sai da ya had'o mata da su da kayan Humairah, ɗaukan kayan humairah tai ta qanqame tana ta rusa kuka. "Dan Allah Yah Umar ka dawon da d'iya ta ka maida kayan ka bana son su, kaico na ni Jameelaah na yi mummunar shukar guba, ga ta tana illata kowacce gaba ta jiki na, ina zan saka raina yau, wayyooo Umarr, dan Allah ka maida ni d'aki na" "Dan Allah kiyi hakuri ki rufen baki, kar ki sa maqota su kasan kunne habaa, kan ki aka fara saki? Ki godewa Allah ma ya maido maki da wannan, wani ne ko tsinke ba zaki gani ba, kuma wannan abin da yayi ya yi dai-dai, na tabbata ba zai qi barin Humairah in tai wayo tana zuwa mana hutu ba, tinda har ya iya aiko kaya, yanzu dole yaji tsoron hana ki d'iyar shi kar a koya mata mummunan hali, Jameelaah ni mahaifiyar ki ce, iyaye kan nemi gafara wajen yaran su musamman in sun san sun cutar da su, a yau ina neman gafarar ki akan cutarwar da na yi miki ta bangaren tarbiyya, ki yafe min, kuma ki ban had'in kai na koyar dake abinda ya dace mai kyau, ki yafe min, ki yafe min Jameelaah," Jameelaah rungume Ramai tayi sukai ta kokawa, har Bukar ya koma da saqon kayan yin awara ajewa yayi ya isa ya zauna yana tambayar waɗannan kayan fa masu tarin yawa daga ina? Nan Ramai ta masa bayani shima ta nemi yafiyar shi, suka yafe wa juna. "Mama (sunan da suka koma kiran Ramai dashi kenan)  ni ina da shawara fa, tinda kin iya girki, mai zai hana ki samu ki dinga yin dambun naman kaza ana siyarwa? A irin robobin nan, a kafa waje anan qofar gidan, tinda kan hanya ne, za a yi kasuwa, sosai" "Kuma kacewani abu fa Bukariri, bari mahifin ku ya shigo ayi maganar in shawara ta tsaya ni da kai na zan dinga yi," Kallon Jameelaah tayi ta ji me zata ce akan hakan amma taji shiru, Jameelaah na can duniyar tinani, ta langwab'e kai gefe hawaye na zubar mata, fatan ta kawai Umar ya maida ta gidan shi. ********************** An d'aura Auren Sapnah da Umar akan sadaki nera dubu ɗari, ba wata hidimar biki da akai in ba wuni da iyayen su suka yi ba, Umaimah da Aunty Hauwaa da Mum sun tsara zasu ɗauki nauyin yi ma ango da amarya walimah bayan an kai amarya gidan ta kamar yanda islam ya tsara, sun gama qayyade iya adadin mutanen da zasu gayyata, sun gayyaci kala-kalan mutane  guda hamsin, a babban wani hall za a haɗu  duk a yi walimar. Sun riga sun yi order na abincin da za a ci a sha, sannan da takeaway da mutane zasu tafi da shi. Ishaaq da Haroon tare da Daddy sun sake ma matan su kuɗi dan cika burin su, dan haka ba zama sun zama busy, hakan ya sa Sapnah damuwa ainun, tana cikin matsanancin buqayar lallashi a wajen Aunty Hauwaa da Umaimah, dan kuwa Umaimah qawar ta ce sosai, sun shaqu matuqa. Daga ita sai Safiyya a d'akin, tana ta kukan rabuwa da iyaye da 'yan uwan ta, Maman ta ta shiga ta same ta kwance saman cinyar Safiyya suna ta kuka. "Ikon Allah ! kuna nan kuna ta kuka ga qawayen ku can a d'akin ku kun baro su kun dawo d'akin Abban ku, wa ya fada maku aure mutuwa ne? Ai ranar farin ciki ce yau, addu'ar neman alkhairin dake cikin shi da neman kariya daga sharrin dake ciki zaki tayi a zuciyar ki amma ba kuka ba, dan ban ga me kukan zai qara maki ko ya rage maki ba, ke kuma da kika zauna kike taya ta kin kai ma mutanen da nace ki kai masu abinci abincin?" "Eh na kai Ummaah, Ummah kukan kewa muke yi ai, yanzu in ta tafi ba zan dinga ganin ta ba akai-akai," "Ban son shashanci, da ɗin akai-akai kike ganin ta? Ina makaranta take yi da a can wani waje, daga baya ta koma wajen Jidda, to yanzun ma in ta koma gidan ta ba wani abu bane sabo in kin so ganin ta zaki je can," "Taso kin ji ta gidan Ummaah, daina kuka, ke dai ki riqe biyayyar aure, bana jin ki ta kowanne fanni,saboda na san baki da dama wajen iya girki, kwalliya, iya tsara kalamai masu daɗi, shagwava kuwa har ta saidawa kina bayarwa, ga shi wajen qamshi a gaskiya ke din abar yabawa ce mutum baya gajiya da shaqar qamshin jikin ki, kina da tattali baki da almubazzaranci, dai-dai misali kina da tsoron Allah da ibada, Sapnah ko ta wanne bangare za a lissafa Kyakkyawan hali kin mallaka, to me ne ne abin kuka? Kuka ya kama wadda bata da dik waɗannan abubuwan da na lissafa amma ba ke ba, share hawayen ki, zuwa qarfe biyar za a zo a kai ki d'akin ki kinji? Dan Allah kar ki bani kunya, kar ki kunyata zuri'ar mu, Allah ya yi maki albarka, ya baku zuri'a d'ayyiba saliha mumina, Allah ka saɓa halayen su, in yayi fushi ke ki sauka,in kinyi fushi shi ya sauka, Allah ya kare ku daga sharrin zamani da rud'in duniya, Allah ya kare ku daga sharrin shaid'an kin ji? Taso maza kije wajen qawayen ki, dan ke suka zo ba dan kowa ba, ba daɗi ki bar su su kaɗai ki dawo nan ki tare" Share hawayen ta tayi suka jera da Umman nasu tana riqe a jikin Umman suka fita, wasu yan uwan su suna ta tsokanar ta akan shagwab'ar ta tayi yawa ko Safiyyah dake qarama bata shagwab'a sai ita, sake lafewa tayi jikin Ummaan nasu, tare da boye kan ta. Daf za su shiga d'akin su suka ji qawayen su na ta hira, wata Ameerah na magana, "Dik irin kurin Sapnah ace bikin ta ko dinner babu, ba wanai casu ba party,  a gaskiya wannan yawa ne, ba aji" Safiyyah ce ta bude qofar cikin fushi zata yi magana Sapnah ta hana ta, nan da nan kuwa ta kafe ta da ido, ranta ya ɓaci, ta danne ɓacin ranta, "Kar ki ce komai Safiyyah, dik kuri na ban taɓa yi wa kowa qarya ba, na godewa Allah ina da surutu na sani amma ban taɓa cewa kowa komai akan aure bama balle nai qaryar za a cashe a bikina, gobe ki zo hall.......... ki ga me za ai inshaa Allahu, ina gayyatar kowa a cikin ku dan ganin me zai wakana goben," Nan da nan kuwa qawayen su sukai ma Ameerah caaa, har wadan da da ace bata zo ba suna da niyyar topa albarkacin bakin su, amma ganin an kama Ameerah ya sa sukai lif suka wayance. Zama Sapnah tayi ta takure, tana jin su bata tanka ba, Safiyyah dataji daɗin amsar da Sapnah ta bayar ta ware sai hira da qawayen su take yi. Umar ke ta kiran ta amma taqi d'agawa, dan sai take jin wani haushin shi dan zai raba ta da iyayen ta da kowa nata, sai take ganin hakan a matsayin son kai. Message ya tura mata ta whatsapp, da kwalliyar da yayi, lokacin daurin aure, murmushi ne ya k'wace mata, dan kuwa ya tafi da numfashin ta, Itama tura masa nata tayi, ya maido mata da qatuwar heart, ~kiyi magana mana babes, ki faɗan yanda kike ji a yanzu, na matsu lokacin kawo ki gare ni yayi, na matsu na nuna maki tsantsar qaunar dake danqare a ruhi na, ina son ki Mrs Umar~ Zaro ido tayi waje fall hawaye, lallai ma Umar dinnan mugu ne, wato ya matsu akai ta ya gwada mata muguntar daya tanadar mata dai, banza tayi da message ɗin ta ci gaba da share hawayen ta, qirjin ta na bugawa da qarfi a dik second ɗin dake qarato da kaita d'akin mijin ta. Kiran sallar la'asar ne ya tada su, wasu kuma suka zauna saboda basu yin sallah, wasu basu tashi ba saboda kar su goge kwalliya, wasu kuma da alwalar su, Aunty hauwaa ce tayi sallama ta shiga d'akin, Sapnah na ganin ta ta kwab'e baki irin na shagwab'ar nan ta miqa mata hannayen ta, kamar wadda za a ɗauka, aunty hauwaa da sauri ta isa gare ta ta fara lallashin ta. "Taso muje kiyi sallah," D'akin Abban su suka shiga, ruwane zundum mai qamshi sosai da lalle aka cika kwamin wanka da shi, (lallen jiqawa ake a tace sai a zuba a ruwan wanka ko bayan anyi wanka sai a wanke jiki da zallan ruwan lallen saboda fata tai santsi da haske). Kayan ta aunty Hauwaa ta fara taya ta cirewa bayan ta mata bayani tayi wanka kafin tayi alwala, tayi sallah su shirya ta ita da Umaimah. Bata musa ba dan ko ta musa ba kyale ta zasu yi ba, taji daɗin ruwan d'umin kuwa sosai, ya dauke mata gajiyar da tayi sai da ta jiqu da ruwan lallen nan qamshin turarukan suka ratsa ta, sannan Aunty Hauwa ta d'akko irin garwashin nan na leda ta turara ta da kayan qamshi,ta bata farin musk mai kyau ta shafa a HQ, ta shafa mata alimun a hammata kadan, bakin ta kuwa sai da tayi brush,wanke da mouth wash ta qara da fesa mouth freshner, sannan ta bata kaninfarin guda ɗaya ta tauna, tai ta yamutsa fuska kuwa wai da yaji, Aunty hauwaa bata kula ta ba ta ci gaba da gyara qanwar ta ta ko ta wanne kusurwa bata bar wani datti ko kafar wari a jikin ta ba, gashin ta kan shi sai da ya sha turaren wuta dana gashi, sannan ta gyara mata shi ta d'aure mata. Wasu fitinannun kaya Aunty Hauwaa ta deb'o ta bawa Sapnah ta saka riga ne da wando, rigar qarama sosai ta manne da cikin ta, hannun bra gare ta, sai wando iya cinya, kalar baby pink, sai ta bata wani skirt dogo mai faɗi sosai har qasa yake ja, da wata riga mai shara-shara itama mai dogon hannu da mannewa a jiki tace tayi sallah sannan suyi kwalliya. Bayan sunyi sallah dika Umaimah ta gama shayar da Ummee, ta je ta tsara mata kwalliya mai kyau,irin simple din nan,nan da nan kuwa ta qara yin kyau, ga turaruka masu kyau da tsada da suka feshe ta da su(inma baki da mai tsada amarya ko ɗan d'ure mai daɗin qamshi da sanyin qamshi asanya abinki, iya kud'in ka iya shagalin ka kar dai a yi tsami) Laffaya kalar baby pink mai ratsin baqi da golden a jiki kamar kayan dake jikin ta suka naɗa mata, takalmanta da qaramar jakar hannun ta golden ta riqe, sai abun hannu kowanne hannu an sa masa awarwaro na zinare, da kudin sadakin ta da wanda Abban ta ya bayar Aunty Hauwaa ta siyo mata a d'azun, kukan murna taji na son ya zo mata, sai qoqarin maidawa take yi kar ta b'ata kwalliyar ta, "Kika sake kika min kuka saii na make qeyar ki" Dariya suka yi tayi dikan su sannan suka raka ta waje inda motocin kai amarya ke tsaye ana jiran ta, a wuce da ita gidan mijin ta abin son ta, dik yanda ta so ta riqe hawayen ta kasawa tayi, ganin qoqarin da take na kar tai kuka kadai sai da yasanya mutane kuka suma, Aunty Hauwaa har sai da Umaimh ta riqe ta saboda kuka take sosai na tausayawa qanwar ta, zata shiga sabuwar rayuwa,rayuwar da ta qunshi komai da komai a cikin ta, abinda ka zata da wanda ba ka zata ba shi zaka gani a ciki,abinda kake son gani da wanda baka son gani duk zaka tarar a cikin ta. *Cassssssss ni dai a radu ina lab'e ko kowa ya kai amarya ya tafi ni gidan nika kwanci yau sai an ci kaza da ni😂* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏻 MAZAUNA GIDA 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 44: 'Yan kai amarya dai jama'a a gidan suka sami ango shi ya yi masu iso zuwa cikin gidan, sai dariya kuwa ake yi masa ana qusqus,shi kuwa ko a jikin shi, ganin haka mutane suka yi ta fita suna komawa mota tinda sun ga gida kuma sun sanya albarka zaman me za su yi? Sai fatan alkhairi da suke yi wa Sapnah da Umar ɗin , Safiyyah sai kuka take da zata tafi, Sapnah ma tsabar kukan da ta sha kan ta sai sarawa yake yi bayan tafiyar kowa Umar ya shiga ya same ta tana ta tsiyayar da hawaye, jingina yayi da gefen gadon da take zaune, ya kafe ta da ido, cikin yanayi na tsokana ya furta, "Ohhhh Allah na, daɗi na da aure yana sa dik wani mara kunya mai surutu yayi ladab,who could have thought wai Sapnah zatai laushi ta yi irin wannan kukan kamar wadda akai wa auren dole? Ah ah ah..... na manta fa, maybe auren dole aka yi mata bata so na wayyooo...abin tausayi ni Umar ..... gaskiya Umar in ka barta ta kwana a gidan ka baka kyauta ba, ya kamata ka maida baiwar Allahn nan wajen Umman ta,...ko dai wajen Aunty Hauwaa zan maida ki?" Tinda ya fara maganar tayi d'if dan ta samu damar jin me yake faɗa da kyau, jin tambayar da yayi mata ne ya sa ta kallon shi, suna haɗa ido kuwa ta zabga masa harara, idon nan kamar zai faɗi qasa, bakin kuwa kamar zai tsinke saboda murgud'a shi da take yi. "Dawa kike?" "Da kai nake" Ta faɗa muryar ta sam bata wani fita sosai, amma yaji me tace sarai, "Kayyaa... na zaci tsiwar taki ta hayaqa ashe iya gida ta tsaya ba a zo da ita gidan miji ba, da ki faɗa mana kice dani kike da qarfi ki ga ya zan maida ke yan zunnan" Shiru tayi dan bata son dik wani abu da zai sa Umar ya kusance ta a yau, a matuqar tsorace take da shi. Sai takalar ta yake yi ita ko ta yi masa banza, daga baya ya fara da cire mata mayafi, nan fa ta qanqame qammm, Umar yayi yayi ya cire ya kasa tabdi jam, ashe bayan surutu Sapnah gwanace wajen qarfi, saki yayi kar yaji kunya, yarinya sai shegen qarfi kamar wadda ake taya wa? "Ina zuwa be a gud girl please yanzu zanje na dawo, na san me yasa kike b'ata rai, ba kiji qamshin mutuniyar taki ba ne ko ? wato kaza, bari na je na siyo na kawo kazar amarci, harda kud'in siyan baki zan had'o miki," B'are baki tayi ta fashe da kuka wai Umar me ya maida ita ne, sai wani tsokanar ta yake yi, tama gama gane ina ya dosa da kalaman shi, son auren take yake nufi ko kuma qin auren take yi kenan oho, sai yayi tufka ya warware. Rungume ta yayi tsam a jikin shi yana shafa bayan ta, tin tana kukan har ta fara sauke ajiyar zuciya, qamshin junan su kawai suke shaqa, Umar ji yake gaba ɗaya sai a hankali, in bai samu yanda yake so ba akwai matsala, dole ya samu had'in kan Sapnah yau, tin da yayi auren farko ya fara kusantar Jameelaah bai taba nesa da matar shi ba sai da Jameelaan ta fara iya shegen ta, da sauri ya sake qanqame Sapnah, zuciyar shi na bugawa da qarfin gaske. 'Jameelaah, Ya Allah ka sa wannan ba halin su ɗaya ba, Ya Allah ka sa halin ta yanda yake a fili na b'oye yafi shi kyau,' In Sapnah ta kasance irin Jameelaah zuciyar shi bugawa zata yi, a da ya zaci ba zai sake son wata sama da Jameelaah ba amma a yanzu ji yake ba kamar Sapnah a zuciyar shi dik duniya, d'aga ta yayi daga riqon da ya yi mata yace, "Tashi kiyi alwala muyi sallah dan gode ma ubangijin da ya mallaka mana juna mu, mu roqe shi daya yi mana albarka, ya sa mutuwa ce zata rabamu" Babu musu ta miqe cikin dishewar murya ta ce masa, "Ina da alwala" "Anyaaa kuwa Sapnah? Fadi gaskiya anya bata karye ba?" Dukan wasa ta kai masa a qirjin shi, ya riqe hannun ta a wajen yana shafawa da hannun ta, "Ouchhh,hannun ki na da zafi fa, kar ki karyan haqarqari fa, bari naje nai alwala ki jira ni" Zama tayi tana murmushi haka Umar yake dama, yes ta san yana da magana kamar yanda take da magana, dik da Umaimah tace da ita yake sakewa yayi surutu mai tsaho haka, amma bata taɓa zaton ya zama mai shegen tsokana irin wannan ba. Shimfid'a masu abin sallah tayi ta gyara laffayar ta ta rufe jikin ta sosai, ya jima sosai dan sai da yayi brush ya sake gyaggyarawa ya fita, sallah sukai raka'a biyu sannan ya yi masu addu'a, ya dafa kan ta ya karanto addu'ar da tazo a sunnah ango na yi wa amaryar shi, sannan ya ce, "Taho muyi hira mu rage lokaci, dan yau daren namu zai yi tsaho" Sanya ta yayi a tsakanin qafafun shi, ya fara da yi mata tambayoyin da suka shafi addini, tana amsa masa dai-dai gwargwado, a zaton shi a iya boko ta k'ware kawai, ashe ta bangaren islam ma ba laifi,sauraron ta yake tayi, tana zuba masa bayani akan tambayar da ya yi mata na yanda ake wankan tsarki, ta haɗe dikkan kala-kalan wanka da ake a islam tana yi masa bayani da banbancin su, Umar yayi kasaqeee da kunne yana sauraron ta. "Da kyau, ba zan boye maki ba wasu abubuwan ma yanzu na san su, Allah ya yi miki albarka, zadakillahul ilm wa taufiq wa fatahallahu alaiki" "Ameen ya zaujissalih" "Iyyeee lallai ne yarinyar nan da gaske kina so na, soyayya ta ta rufe maki ido gaskiya ke da kike cika baki in kin zo ko kallo na baza ki yi ba jibe ki yanzu kwance a jikina, kin wani qanqame ni" Da sauri ta d'aga shi ta koma can saman gado tana dariya, tare da rufe fuskar ta, Tashi yayi ya je Allah ya bashi sa'a ya k'wance laffayarta ta sama, adon da tayi ne ya bayyana, tare da wani irin qamshi mai sanyi ya bugi hancin shi qoqarin Karb'a take yi, ya kai hannun shi wuyan ta wani iri ta ji a jikin ta, sai da ta rintse ido hannu ya sa ya cire band din da aka d'aure mata gashi da shi, nan da nan gashin ta mai madaidaicin tsaho ya bazu a kafad'ar ta, d'aga kai tayi ta kalle shi, bata taba ganin shi a wannan yanayin ba, zama yayi daf da ita, yana qare mata kallo, cikin bushewar lips dan tsoro ta zaro harshe ta tsotsi lips din ta, Umar ji yayi kamar da gayya tayi hakan, bai bata lokaci ba wajen kai nashi bakin zuwa nata..... Yana cikin jagwalgwala mata kwalliyar ta da Umaimah ta bata lokaci wajen tsarawa, aka kira sallar magrib, hamdala tayi a cikin ran ta, dan kuwa ta gama zata ta shiga hannu kenan. Bata tashi sanin me Umar ya mata ba sai da ya daga ta zai je masjid taga daga ita sai dan qaramin wandon rigar dake jikin ta, gashin ta dik ya yamutse saboda saka hannun shi daya dinga yi, jikin ta tini ya ɗauki rawa ta ja mayafin ta ta ruje jikin da shi, Umar dariya yayi ta qasan maqoshin shi, dan magana ba zata samu ba a wannan yanayin da yake ciki. Sai da ta tabbata ya tafi sannan ta sake watsa ruwa ta sanya turarukan wanka da ta gani a toilet ɗin, tasan aikin aunty Hauwa da Umaimah ne, murmushi tayi ta masu addu'a a ran ta, ta kammala ta daura alwala, sannan ta fita, doguwar riga ta zira kawai ta tada sallah, Umar a mota ya fita yaje ya yi masu siyayyar abubuwan da zasu buqata, sai ya koma masjid, bayan anyi sallar isha'i ya ɗauki hanyar gida. Itama sai da tayi sallah sannan ta nemi wani riga da wando na bacci masu santsi da kuma kyau ta saka, gani tayi kayan gaba daya qanana ne sosai na bacci a haka wannan ne mai mutunci a kaf lefen nata, shima sunan riga da wando ne amma komai a bayyane yake. Hijab ta ɗora a kai ta haye gado ta rintse ido cikin ta sai kukan yunwa yake, dan ita kan ta bazata iya tina rabon ta da abinci ba, amma ta qudirta ba zata tashi ba sai safiya. Ko da ya shiga yaga an karkashe fitilu ya san ta kwanta kenan, amma ai da kyar in tayi bacci. Shigar da komai yayi ya zuba a inda ya dace, sannan ya zubo masu turkey daya siyo a plate, ya d'oro a babban trey, ga fresh milk a sama da cups biyu sai wuqa da cokali mai yatsu. "Assalaaamuuu alaikummmm, Mrs Umar tashi muci abinci yunwa zata ma Umar din ki lahani, na jima rabona da abinci," "Balle kuma ni da....." Da sauri ta damqe bakin ta, tariga da ta tona kan ta surutun tsiya baida amfani, ohhh Allah yau ta shiga ukun ta wajen Umar da tsokana ta san. Kwalla ce ta taru a idon ta ,tana kwance taji ya yaye bargon da ta rufa da shi, sannan yana qoqarin cire mata hijab din jikin ta ya na tambayar ta da, "Balle ke kuma mi? Taso amaryar qauye, waya ce maki ana wannan yayin kwana da hijabin?" "Ni ba ruwana ban san me ake yayi ba ka barni nayi bacci na gaji," "Sannu kin ji, zan maki tausa bayan kin ci abinci sai ki i baccin ki, taso na san kina jin yunwa" Mammatsa qafarta da hannayen ta yake,ita kuma tana kaucewa, "Ni bana wani jin yunwa, dan Allah ka barni" Cikin ta ne ya qarya ta ta, Umar kuwa ya sake kai kunnen shi cikin nata yana dariya, ɗaukan ta yayi ya dire a qasan carpet, sai mutsu-mutsu take, ita dik a tsorace take dashi, bata son abinda Umar keyi mata sai wani kusanta kanshi da ita yake, alhalin da ba haka yake ba, ('Yannan yanzu kin zama mallakin shi, he has the right to touch every little part of u, ba yanda zaki yi😂 and a gaskiya soyayyar Umar da sapnah ni kaina tana burgeni har gobe, na amince da cewar miji da matan da basu san juna ba kafin auren su auren yafi qarko, Umar da Sapnah kafin aure ba suyi soyayyar zamani ba, amma wallahi wallahi wallahi a wannan zamanin yana wahala a ce budurwa da saurayi suyi wata ɗaya suna soyayya bai lalube ta ba, an dad'e ayi shekara biyu wasu sun gama sanin dik wani part na junan su ta hanyar wayar nan da kuma ido da ido, wasun su kuwa wallahi har saduwa sunayi ba aure, ciki anyi an zubar an kuma an rufe an zubar daga qarshe a yi aure kuma a haka, wace irin rayuwa ce wannan ake gudanarwa kenan? Zai wahala yara su yi shekara da shekaru a tare a wannan zamanin ace ko hannu basu taɓa riqewa ba, masu mutuncin cikin sune suka tsaya a rungume-rungume da kisses, d'aid'aiku ne suke aure salim alim ba lalata, Sapnah da umar na daga cikin qalilan na gari da suka rage da basu yin soyayyar shan minti,'yan uwana mata da maza mu dage sosai dan Allah mu bawa shaid'an kunya mu tsaftace rayuwar auren mu kafin mu shige ta.) Suna ci Umar na tsokanar ta, amma taqi kula shi, dan da ta fara ci taji daɗin na ratsa ta sai yunwar ta motsa bata tsaya fulako ba sai da ta qoshi ta sha madara ta je ta wanke baki da hannu sannan ta koma ta kwanta, "Imm imm imm imm Mrs Umar, this is really bad, ya zaki ci abinci ki kwanta? Ai sai ki yi qaton tumbi, yanzu ki tashi ki zauna, bari na wanko hannu na nazo mu ɗan motsa jiki kin ji," Kashe mata ido ɗaya yayi ita ko ta zare ido tare da shaqar iska, ta toshe bakin ta, dan kuwa ta gane me yake nufi,abun na Umar kuma ya koma sai lahaula,ta bashi award ɗin sarkin surutu ta bar masa sarautar. Umar bai fito ba sai da ya gama shirin bacci, ya kwashe komai ya kai kitchen, ya koma bayan ya kashe komai da ya dace a kashe, ya ma qofar gidan su ayatul kursiyyu sannan ya shiga,addu'ar bacci ya samu tana yi, ya kashe fitila ya kwanta, shima ya fara yin addu'ar tsabar neman magana irin na Umar ya yi addu'ar shi amma yake neman magana, "Ki shafa min addu'a nima please Mrs Umar," "Dan Allah Yah umar kayi bacci ni ma bacci nake ji, kaga in ka damen zan gudu can d'akin na kwanta" "Shikenan tinda ke ba zaki shafamin ba, ni ban da rowa bari ki gani" Ina ganin Umar ya shige bargo ya ja Sapnah jikin shi, nace tooo an gama leqen asiri Haermeen Haermmaerh, an shiga hurumin manya su Sapnahn Umar😂 Washe gari da sassafe Umar ya yi wa Safnah wanka idon ta yayi luhu luhu saboda kuka,muryar ta ta idasa dudashewa, zazzabi take yi sosai, tabbas Umar ya same ta a budurwa,ashe yana da rabon ya d'and'ani zaqin mace budurewa kuma mai dimbin ni'ima a rayuwar shi? jinin da ake ta cewa wai ana kai mace budurwa ake gani a washegarin aure kamar an yanka rago duk bai gan shi ba, a matsayin sa na likitan mata kuwa ya san possibilities ɗin dake sanyawa a rasa wannan jinin, amma ya tabbatar da cewa matar shi Sapnah budurwa ce. Bayan ta gama shiryawa cikin wani farin lace mai matuqar kyau da tsada, an masa adon pink da flowers masu kyau, riga da zani ne buba aka mata, tayi irin shigar yan garin su Oduduwa ta dakko abun hannun ta na zinare ta saka, ta d'akko sarqar ta da d'ankunne irin na Indiya, zata saka ta ji an zagaye mata wuya da sarqa mai ɗan nauyi. Haɗa ido suka yi ta mirrow da Umar ta sauke nata kwayar idon da sauri, dan kuwa wata iriyar kunya Umar ke bata, ba abinda take tinawa sai kukan da ya dinga yi sosai bayan ya gama mata sala sala, ita kuka shi kuka, a zaton ta ko bai gamsu da ita bane, amma sai taga yana bata kulawar da tinda take ba wanda ya taba bata, sai ko da tana yarinya. "Daga idon ki ki kalle ni so much with pride my love i am all urs, and u ar all mine, and i promise to keep us together for rest of our lives, Sapnah Allah ne kaɗai zai sanya ki a irin irin farin. cikin da kk sakani jiya har fiye da haka ma, kuma ina fatan in ya tashi saki a farin cikin ya ninninka maki,ta yanda ba baqin cikin da zai rab'i wanin ki ma ba ke ba, Allah ya saukar da albarkar shi akan ki, wannan kyauta ce ta iya abinda zan iya mallaka maki a yanzu, kafin Allah ta sake hore min, bayan zuciyata da jikina da ruhina dana baki na mallaka maki wannan sarqar, Mum d'ina ce ta bani tace na baki, sarqa ce mai mahimmanci a wajen ta, ta gaje ta wajen mahaifiyar ta,ina fatan zaki so ta kema ki adana ta, har Allah ya kawo mana ɗan da zai girma shima yayi aure ki bashi ya bawa matar shi," Wani irin shauqin son shi ke fizgar ta wanda ada bata ma san tana yi masa kalar wannan son ba, da sauri ta juya ta qanqame shi har d'aurin da ta kafa yana fad'uwa, sun jima a haka kafin ya d'ago ta yace, "To ya isa kar ki goga min wannan hodar da kuke shafawa a farin kaya, ina ustaz na fita ace na rungume mace," Goga fuskar ta ta sake yi a jikin shi, sanna ta d'aga tana hararar shi, har ya isa yayi wata magana akan rungumar mace bayan abinda yayi mata jiya? Ɗan kunnen ya sanya mata da zoben, sannan ya ɗauki dankwalin ta da ya faɗi yana dariya, ta amshe tana nuna shi da yatsa, dan ta san halin tsokanar shi, "Not a word from u,i said not a word!" Qunshe dariyar shi yayi, tare da d'aga hannayen shi sama ya fita, itama dariyar tayi, ta zauna tana kallon kan ta, Umar har ya maida ta basarakiya, dibi yanda take kyalli, d'aurin ta sake yi, ta kalli dakin taga yanda ya gyara masu shi ko ina fess, kamar ba d'akin su ba da ya hautsina jiya tashi tayi da kyar dan dik jikin ta ciwo yake yi mata, taje kitchen dan wanke kayan da suka ci abinci taga ba komai an wanke an gyara, lallai ta dad'e a wajen wanka tinda har yayi aiki haka bata fito ba. 'Yan walima fa sun fara hallara, masu kuɗi da suka ga harda talakawa a wajen wasu ransu ya baci, gani sukai an qasqantar da su, wajen cin abinci an jera mai kuɗi ɗaya talaka ɗaya duk anjera su akan carpet dogaye, wannan na kallon wannan, wancan na gogar jikin wannajn, ga abinci nan mai rai da lafiya an rarraba kowa an zuba masa zama kawai za a yi a fara zubawa uwar hanji wato tumbi............... *Ayi hakuri da wannan, zuwa gobe ko anjima inshaa Allah zan ci gaba, mai son zuwa walima ta shirya a yi walimar bikin su Sapnah da ita💃* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼   *MAZAUNA GIDA*  💅🏼 *WRITTEN BY HAERMEEBRAERH* Page 47: Tagumi ta zuba tana bin shi da kallo shi da tsiren nashi yana ta maganar shi shi ɗaya bata iya ce masa komai ba,rayuwa kenan gajiya tayi da zaman ya cinye nashi ya na buɗe mata nata zai bata a baki, ita kuma tana qoqarin cire nad'in mayafin jikin ta,dan bata ga amfanin lullub'ar nan ba, wace kunya ce zata ji wajen tsoho sa'an Baban ta? "Amarya Jameelaah, ina zuwa haka?" "Zan zaga ne nayo alwala banyi sallar isha'i ba," "Subhanallahi, maza maza kije ki yi sallah,ba a wasa da ibada ko me mutum zai yi kar yayi wasa da ibada," Daga masa kai tayi ta fita sai taga babu buta a waje sai ta dawo dan ta ɗauki butar,taga yana lashe hannu alama ta nunaya ci mata tsiren ta kenan murmushi tayi da taga ya diririce, "Dama na mayar na rufe ne tunda naga baki ci ba kar ya gama shan iska," "Kar ka damu Baba ka ci kawai ni a qoshe nake, in ma inajin yunwa zan ci kayan garan can," "A ina ne da kayan garan? " Cikin nuna tsananin kwad'ayi yake maganar, nuna masa ta yi a bokitan da suke, sannan ta debi ruwa ta sa kai zata fita, kiran ta yayi murya can qasa yace, "Kin ga ki a dana mana wannan, kar ki bari kowa yasan akwai su,a hankali zamu dinga ci har ya qare," D'aga kai kawa tayi ta fice ta san komai game da salon rowar shi, akwai yarinyar shi dake aure a Kazaure suna ce mata Hajjo, sukan haɗu da da Jameelaah jefi jefi, har wajen Ramai mamar ta Uwar gidan take aiken ta a da dan a sammata garin tuwo ko wani abun dai, saboda ba kullum kasuwar ke buɗe masu ba sannan ga shi shi kuma akwai matsi. Jameelaah ta yi alwala tayi sallar ta ta samu ta sauya kayan jikinta ta kwanta, "Amarya ba kin yi gayyataba a taya ki hirar dare?" Washe bakin shi yayi da ya ke fidda warin albasar tsiren da ya gama cinyewa, ga kalar goro data qara ma bakin kyankyami, yana kusantar inda take taji wani mugun warin hammata ya dake ta,ba shiri ta miqe,taso kwarai ta basar ya gama dik abinda zai yi da ita amma inaa  juriyar nan ba zata samu ba,cikin raunin murya tace, "Dan Allah na tambaye ka Baba," "Allah ya sa na sani Amarya, ki daina kirana da baba ina laifin ango? Ko ki kirani da suna na Tsalha  kamar yanda sauran suke yi, ko ki kirani da Baban Hajjo," "To kayi hakuri Baban Hajjo, dama ina son na tambaye kane dan Allah kaji wani wari na fita daga jiki na?" "A'uzubillahi me ya haɗa ki da wari kuma? Irin wannan qamshi dake tashi a jikin ki, kamar wadda ta fito daga kamfanin turare" "Na gode da wannan yabon da ka yi min, amma baka tambaye ni ni ya naji game da kai ba, ko baka son na ji qamshin da kaji a jikina ne ?" Shiru yayi na wani lokaci, can yace, "A gaskiya ba zan b'oye maki ba, rabona da wanka tin shekaran jiya dan haka na san bama na qamshin da kike so," "In kana so ni da kaina zan iya taya ka kayi wanka yanzu na baka sabon brush da abun wanke baki saboda yau daren amarcin mune, kaga dole mu gurji amarci da kyau ko ya ka gani?" Cinyar shi ta shafa ta tsakiya, wani ihun murna ya saki, ya sauka a gadon yana faɗin, "Allah na gode maka ashe da rabon nima zan yi qara'in quruciya ta, muje ki wanke ni tatas,kamar yanda malamai ke faɗa ayi wanka da mata akwai soyayya a ciki, nan ba wadda ta taɓa min haka,tunda jajayen sawayen mu gashi har an jeme" Sauka tayi ta fita ta kai ruwan wanka, sai da ta tsaya ta sha kukan ta ta goge hawayen ta sannan ta sanar dashi ta kai ruwa ya fito, wanka mai kyau Jameelaah ta yi masa, sai ga Tsalha ya fito fess dashi, haqoran nan kuwa tana goge su tana kauda kai,dan kuwa kamar zatayi amai haka take ji. Shi kan shi sai yaji wani irin iska da nutsuwa na ratsa shi,da datti dik ya maqale masa akafar gashin jikin shi. Alwala ya d'aura domin yana son su gabatar da nafila kafin komai ya kankama tsakanin su. Ranar Tsalha ya ba ma Jameelaah kunya, har yasa ta dinga tinanin ya zata kalli matan shi da yaran shi da safe? Tasha sambatu da sanya albarka, ko ta toshe masa baki sai yayi ta surutai a cikin hannun ta, da kyar tasamu ya kammala ya miqe, Jameelaah ta sha mamki, kamar ba dattijo ba, lallai duk yadda zatai zatayi ta gyara shi, su more auren su, tinda Allah ya qaddara mata zama da shi. Yana gama hutawa ya tashi yace ta tashi taje suyi wanka, kar su kwanada janaba, baya da kyau hakan,ita dai yana bata mamaki dan kuwa akwai ibada. Sai da sukayi wanka suka koma d'akin kwantawa suka yi, yana son ya rungume ta yana jin nauyi, ta kula da hakan sai ta kad'a ido sama,a ranta tace, 'Wai kunya yake ji saida ya gama lallashe ni kota ina sannan zai dinga wani sunnekai, indai ina son na samu na mallaki soyayyar shi dole sai na sake masa jiki, nayi amfani da wannan damar na daidaita lamarin shi ko zamu mori rayuwar auren mu' Janyo hannyen shi tayi ta ɗora a saman qirjin ta bayan ta juya masa baya, ma'ana yayi kamar shi ya rungume ta ta baya. Wata ajiyar zuciya ya sauke tare da sake sanya mata albarka, amsawa tayi tayi shiru,hawaye na tsiyaya a idon ta, haka bacci ya dauke su. Da sassafe taji ana ta hayaniya, ga zage-zage ana ta yi sai d'ura ashar ake a tsakanin yaran, manyan kuma na ta bada umarni da hayaniya. Tashi suka yi da sauri dan yin sallah dan ba su san sun makara haka ba, warin yawun bacci Jameelaah taji jikin ta nayi, tako tabbata Tsalha ne ya sa mata shi, rintse ido tayi ta miqe, hijabi ta nema ta saka sannan ta sa masu abun wanke baki dika su biyun ta miqa masa nashi, ta dura masu ruwa a butoci suka fita, duuuuuu idanu suka yo kan su, wasu yaran sun sha mamakin ganin Baban su a rana ta farko zai alwala da rana gatso-gatso, dan sun san da asuba yake sallah ya tada kowa. D'aure fuska yayi tamau anan Jameelaah ta qara gane mugun tsoron shi ake ji a gidan ta kuma fara gane wanene Tsalha angon ta..... [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼   *MAZAUNA GIDA*  💅🏼 *WRITTEN BY HAERMEEBRAERH* Page 45: Walima ta qayatar sosai bayan an kammala cin abinci ne malamai suka yi wa'azi mai matuqar amfani, inda bayan sun yi wa ango da amarya nasiha da addu'a sai kuma suka nuna ma mutanen wajen mahimmancin zama a ci abinci gaba ɗaya kamar yanda a masallaci ba a ware mai kuɗi da talaka haka ko a wajen cin abincin walima ma bai kamata a ce za a ware mai kuɗi da talaka ba saboda dika 'yan uwan juna ne mu, sannan kuma hakan zai ragewa masu kuɗi jiji da kai, sannan a taron wani mai kud'in zai iya samun ladan wani talakan ta hanyar taimaka masa, kuma kowa ya tina cewa da mai kuɗi da talaka dik bayi ne na Allah, ba wanda ya fi wani a wajen Allah sai mai tsoron shi, masu kud'in da ada suke ganin an qasqantar da su sai suka ji dik wannan tinanin ya kau, a nan take da damar marasa shi suka samu alkhairi mai yawa wajen masu hannu da shuni, wasu ma aikin yi suka samu Umar da Sapnah sun sha albarka da addu'a mai kyau a wajen mutane amfanin walima bayan d'aura aure kenan dama mutane su sa wa ma'aurata albarka. (Bikin yanzu ko yawanci kana zuwa zaka gane layin da ka ke, dan masu kud'in kan su ko basu san juna ba sai ku ga sun ware kan su,yanamu yanamu suma suna zuwa ko basu san juna ba dole su ware kan su saboda gudun wulaqanci,ko wajen rabon abinci wai sai an fara sallamar waɗan da sun baro mafiyin wannan abincin da za a basu a wajen biki a gida kafin a baiwa waɗanda sai su fi wata ɗaya ma basu ga nama ba balle lemon roba ko shinkafa,sai a yi ta qarawa mai qarfi qarfi.) Mutane ana ta guzirin abinci ana tafiya dashi bayan wanda suka ci suka sha suka qoshi, Aunty Hauwaa mamaki tai ta yi na yanda abincin yayi albarka haka, addu'a kam Amarya da ango sun sha ta ba kaɗan ba. Amarya dai dik abinnan da ake yi tinda ta sha lullubi ta zauna aka ci abinci da ita ta koma ta zauna a d'akin dake hall ɗin bata sake fita ba saboda zazzaɓi take ji sosai, kanta take ta murzawa a hankali saboda a tunanin ta hakan zai rage mata zafin ciwon da take ji,Umaimah ce ta shiga ganin halin da Sapnah take ciki ne ya sanya ta cewa, "Lafiya kike kuwa Adda Sapnah?" "Dan Allah ni kar ki wani kira ni wata Adda na yafe maki ki kira ni da Sapnah ta habaa,ni kaina ne yake ciwo kuma cinyoyina da nan wajen zafi suke yi min" Murmushi Umaimah tayi lallai Yah Umar ba hakuri jiya-jiya daga kai masa mata har ya gama komai kamar wani wanda yake jira? Ai ya dan d'aga qafa a gama walimar ma mana a basu waje. "Sannu bari na duba jaka ta na ga ko akwai maganin ciwon kai, bana rasawa dana Ulcer, sai ki sha magani, sannan na haɗa maki ruwan zafi ki zauna inshaa Allahu zaki ji sauqi sosai" Haka kuwa aka yi sanda sika gama mutane dik an tattafi,sauran 'yan uwa na jiki sosai a hall ɗin. Material ne a jikin ta mai laushi mai kyau an yi masa ɗinkin riga da skirt na zamani, ya yi mata kyau sosai, Umaimah sai yaba mata take yi, suna cikin hira Haroon ya iso tafiya dasu Aunty Hauwaa, tayi iya qoqarin ta na ganin ta danne hawayen ta amma inaa,aunty hauwaa sai lallashin ta take yi, daga baya ta hakura suka wuce, ko da Umar ya maida ita gida itama abun ya qayatar da ita dan kuwa gidan ya sha gyara sai qamshi ke tashi, bayan Umar ya fita Sapnah ko ina sai da taleqa taga yanda iyayen ta suka kashe mata kudi, tana tsaka da yi masu fatan alkhairi wayar ta ta ɗauki ringing takiran Umman su ta gani amsawa ta yi suka yi ta waya, sapnah kuwa sai wani shagwab'a take yi ,Safiyya ce ta amshe wayar tace, "Ohhhh da alama mijin ki ya fita shi yasa kika tina da mu ko? Jiya tinda kika tafi ko flashing ba a yi mana ba ai se yanzu da muka kira zaki wani ishi mutane da narke murya" Umman su ce ta ɗan daki kafad'ar ta, tayi dariya,Sapnah kam lumshe ido tayi sanda ta tina abubuwan da suka faru daga jiyan zuwa yau a ckin qanqanin lokaci, "Ba zaki gane ba, ki samu kizo kiga abin alkhairin da na samu jiya, yaushe zaki zo?" Kafin Safiyya tayi deciding amsar da zata bata har ta kashe wayar, sakamakon wani abu da taji ya ratsa jikin ta, ba komai bane face hannayen Umar, lumshe idanun ta tayi dan bata san sanda ya shiga gidan ba,sai kawai ta jinginar da kanta a qirjin shi,ya sa hannu biyu ya zagaye ta, yana sunsunar wuyan ta, dake fidda qamshi mai sanyi da daɗi, "Barka da dawowa Zaujissalih," "Barkan ki da gida mar'atussalihah, sorry na bar ki ke ɗaya da kewa ta ko?" "Ba komai yanzu ma waya muka gama da Safiyya da Ummana" "Umman ki ko Ummn mu?" Juyawa tayi tana kallon shi, sai taga ashe yafi kyau in ana kusa da shi daf da daf haka,  "Ya da kallo ko kin qyasa ne?" Kwacewa tayi ta hau inda-indan daukan wani abun, ba komai a wajen da zata ɗauka, d'aki tawuce da sauri-sauri tana dariya, yaushe ta zamame kunya haka ne? Iya sanin ta bata d'agawa kowa qafa, kuma magana ba a biyan ta bashi sai ta maida. "Kinyi dai-dai da kika shigo inda nake son kawo ki, kaiii yarinyar nan gaskiya na yi sa'a, na gama mallake ta" Pillo ta wurga masa ya kama, ya isa gaban ta ya zauna a qasa, ya ɗora kan shi a cinyar ta, tsintar kanta tayi da shafa kan shi a hankali,a shagwab'e Umar yace mata, "Wanka nake so," "OK bari na haɗa maka ruwa," "Ah ah ni kimin wanka," Buɗe baki tayi tana qoqarin magana ta ma rasa me zata ce masa wannan wanne irin sabon salo ne kuma? kawai sai ta ture kan shi ta wuce wajen haɗa masa ruwan, Umar da gaske yake dan haka ya cire kayan shi, yayi shirin wanka, tana qoqarin fita ta gama haɗa masa ruwan ya tare bakin qofar kallon ta yake da wani irin kallo ita kuma tana kad'a masa kai alamar kar ya yi mata abinda yake shirin yi. "Ah ah please Zauj kar ka min haka ni nayi wanka ɗazu kuma banda lafiya, jikina ciwo yake min dan Allah kar ka sa na jiqe kayi hakuri, ba zan iya wanka da babban namiji kamar ka ba," "Ouchhhh, nine babban namijin? Habaa na zaci a irin surutan ki da wayewar ki kin san ana ma miji wanka, anyways in baki sani ba zan koya maki yanda ake ma miji wanka, qarin ilimi ne, ba sai kin biya ni da komai ba, in kin matsa sai kin biya kin biya anjima, yanzu wanka kawai zaki taya ni, in ma bazaki taya ni ba ki jira ni tsoro nake ji," Ya langwab'e kai ya yi ya turo baki irin na shagwab'ar nan, dariya ya bata sosai, tana dariya taji anyi sama da ita, sai cikin kwamin wanka, da kayan jikin ta da komai ya sata a ciki,tana jin ta cikin ruwa ta kuwa bare baki tin qarfin ta ta fara kuka, shima shiga yayi, ya rungume ta, tana ta dukan qirjin shi, harda su yaqushi, sai qara yake amma yaqi sakin ta, daga qarshe ya fara cire mata kayan dake jikin ta, suka fara wanka, ban dai san ya akai ba sai ganin Sapnah nayi ana kyalkyala dariya. Kafin sati ɗaya sun zama abu guda,Sapnah ta aje kunya ta fara qoqarin maida mijin ta nata, kafin sanda zai zama nasu, dan bata taɓa sa ma ran ta mijin da zata aura zai zama nata ita ɗaya ba, tinda Allah bai halicci maza dan mace ɗaya ba. Shaquwar su har abun mamaki,kowa ya gan su zai iya rantsuwa sun yi shekaru da aure, saboda shaquwa. ************************ Sana'ar dambun naman kaji ta kan kama, dan kuwa mutanen unguwar da ma wasu unguwanni suna zuwa siya har da masu sari, abun yafi qarfin Ramai ita ɗaya, sai suka buɗe shagon qofar gidan, guda biyu suna sana'ar a ciki, Jameelaah ta ɗauki ma'aikata biyu suke kula da wajen, dik da ta san Umar yayi aure, bata d'aga wa kan ta hankali ba, ko ta sakawa kan ta damuwa, dan a yanzu ko ita kan ta kunyar sake haɗa ido da Umar take yi, ko zata mutu dan son shi ta haramtawa kan ta Umar, Allah ya raya masu d'iyar su, ko da yaushe ne in ta girma zata neme ta, amma dik da haka in kewar su ta kama ta tana shiga d'akin ta tayi kuka ta godewa Allah. Baban ta da Ramai suna matuqar tausaya mata a yanzun, amma sai ta nuna masu she is Ok, zata iya rayuwa ba Umar, kome ya faru ita ta jawa kan ta, ko batai abinda tayi ba in Allah ya nufa bazata koma gidan umar ba bayan sun rabu ba yanda zata yi, Allah ya zab'a mata abinda yafi dacewa a rayuwar ta. *Bayan shekara Uku* Humairah ba inda bata takawa, ga dan neman surutu a wajen yarinyar,a yanzu ta koma wajen Sapnah da zama Ammi ma take kiran ta da shi, umar kuwa Abbu, in ta fara surutu kamar kanyar da bata da daɗi, Umar yakan ce in batai ba ai sai an tambayi wace maman ta, tinda Sapanh ma haka take da surutun. Har yanzu Sapnah ba ta samu rabo ba, ta damu sosai da hakan kuwa, Umar kuwa a koda yaushe yana kwantar mata da hankali, suna samun taimakon likitocin da suke zuwa wajen su neman magani, Mum tace su kwantar da hankalin su komai lokaci ne. Humairah ce cikin kwalliyar atampa sun yi anko ita da Sapnah, sun yi kyau sosai Umar ya fito yana gyara hular dake kan shi sai qamshi suke bugawa dikan su yawo zai kai su su sha ice cream daga nan yaje da su gidan Zoo, Humairah taga Lion, ita a kayan namun dawa ta riqe shi sosai saboda kallon Cartoon ɗin Simba. Sun fita da la'asar sakaliya, sai goshin magrib suka kama hanyar gida, a titi an tsaida su suna mota Sapnah taga dambun nama a roba sai ta kira mai saidawar wani da ya fita kusa da mai dambun naman ya karɓe ya siye, aiko ta dinga masifa can tayi shiru kamar zata yi kuka dan haushi, ganin haka Umar ya kira mai saidawar yaji a ina ake yi suje ya sai mata, kwatance ya masa na inda yake sari, jin kwatancen yayi sak na gidan su Jameelaah, nan da nan ya b'ata rai. Sapnah da Humairah suna ta murna za a je a sai masu dambun nama, suka ji yace, "Ba inda zamu je, gida zamu wuce in munje kinyi ki ci," Bata fuska tayi ta fara kukan shagwab'a ita da Humairah, wata uwar tsawa ya daka masu, nan da nan kuwa Humairah ta b'are baki da kukan gaske, dik yanda Sapnah ta so tayi shiru qi tayi, shi kuwa bai kula su ba har suka isa gida, da kyar ta d'aga ta ta kai ta ciki, sai kurma ihu take tana kiran dambun nama zata ci, a hasale Umar ya shiga d'akin ya wanke ta da mari sai da yatsun shi suka fita a saman fuskar yarinyar. Cikn fushi mai tsanani Sapnah ta juyo da shi, tare da miqa mashi nata kuncin akan ya mare ta itama, "Nace ka mare ni nima, tinda ni na fara cewa ina so, akan me baka bamu abinda muke so ba zaka dinga fushi bamu san dalilin fushin ka ba kuma, ka sanar damu mana cikin lumana, kace inna dawo zan yi ba shikenan ba me tayi maka?" "Ba zaku ci dambun naman ba, na san daga inda ya fito, kuma ban da ra'ayin sake huld'a da su har abada" Shiruuu Sapnah tayi dan gano ainahin me ya sanya shi fushi, zuciyar ta ke kai kawo akan yi masa magana akan fushin da yake da Jameelaa, wata zuciyar tana kar ki so ma, ai ba ke kk haɗa su ba da, sannan ba ke kika raba su ba.............. *Shin ya kamata Sapnah ta shiga wannan batu kuwa?* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼  *MAZAUNA GIDA*  💅🏼 *WRITTEN BY HAERMEEBRAERH* Page 48: Bayan sun idar da sallah ne taga ya d'akko irin qur'anin nan me falle falle ya na karatu irin na zaure, sai da ya gama yayi azkar, sannan yaran suka dinga zuwa bakin qofar d'akin ta suna gaida shi, a ciki-ciki yake amsawa,matan ma haka suka bi suka gaida shi suka koma tsakar gida ya fita ya kama qugu Yana muzurai yace, "Kuna ina?" Cikin hanzari kowa ya fito suka tsugunna, sai da ya gama qare masu kallo sannan yace, "Wato dan rashin mutunci ni d'ayane a d'akin ko? Ita ba zaku gaida itaba? Ko haka na koya maku qin gaida na gaba da ku?ku kuma saboda ɗan banzan kishi ne ya hana ku tambayar ya Amarya ta ta kwana Ko kuma wanne iskanci?" Uwar gidan ce da ake kira da Baba Abu tace, "Ba fa zaka zo ka samu a gaba da yaran ka damu ka mana kud'in goro ba ehe,amarya ka nuna mana kalar ta balle ma mu san ya ta kwana? Yaran ka dai da basu gaida ta ba ka sa su fara amma banda mu can mata" "Abu ki kiyayen in ina magana ke ce mace ta farko da zata fara mayarmin ko? Ranki zai baci," "Bacin rai na nawa kuma? Wanne kalar bacin ranka ne ban gani ba, shiru shiru ai ba a ce maka tsoro bane kawai gudun magana ne, in Mero na tsoron ka ni kam bana tsoron ka, munga jiya munga yau tare da kai, ka cud'eni na cud'e ka dan haka na daina raga maka" "Kika cud'eni a gidan uban wa? In ba jiya ba ina na san ana cud'ar miji? Gaku nan ba abinda kuka iya sai baqar qazanta da shegen kishin tsiya, ku kuma me kuka tsaya saurara zaku wuce kuje makaranta ko sai na b'alla yaro," "Ka b'alla ka gyara," "Abu ki fa kiyaye ni," Gaban ta ya je ya daga hannu zai zabga mata mari, da sauri Jameelaah dake tsaye jikin labulen d'akinta ta fita ta riqe hannun shi, "Dan Allah kar kayi haka tunda Annabi yake bai taɓa d'aga hannun shi akan matan shi ba da sunan duka,to kai me yasa zaka d'agawa matan ka hannu? Kamar ba da Annabin Rahama naga kana koyi ba? Habaa, kenan nima nan gaba dukana zaka dinga yi?" Gaba daya qamewa yaran da matan suka yi, ji sukai Mero ta fashe da kuka, kowa kuma sai ya maida kallon shi kan ta, "Allah sai ya saka mana, dama an shirya mana kora da hali ne kawai, in ba haka ba ina kai ina auro mace kamar wnnan? Dibe ta ka gani irin wannan sai a talabijin muke ganin irin ta, amma zaka had'amu kishi da ita, nidai ba zan taɓa yafe maka ba, ke Zara'u muje ki dama koko kowa ya sha ya wuce makaranta, na sake faɗa ban yafe ba," Cike da kuka da shan majina ta bar wajen, yaran da suka mallaki hankalin kan su dariya suka dinga yi har da kama ciki, tabbas Jameelaah ta firgita su da kyau da haɗuwar ta, amma Abu ko gezau bata nuna tsoratar ta a fili ba dan ta san Jameelaah tun bata kai haka ba,girma kawai da kyau ta qara akan sanin da ta yi mata,sannan kuma taurin zuciya gare ta, shi yasa ko faɗa sukai da Tsalha ko Mero sai dai su buga su barta, inda yake sata ta yi laushi ɗaya  ne, wato dik sanda yace ta tafi gidan su yanzu zata nutsu. Jameelaah bata kula su ba fatan ta ta saita lamarin gidan, dan kuwa tabbas sai yanzu ta tabbatar da qazantar dake gidan sune mu'assasin ta, qazantar su har abin kallo ne. Jikin su fari fat kamar bai taba ganin mai ba, in ko ya taba wataqila tin na jarirantaka ne, ga kayan jikin su ba mai gane asalin wace kala ne? Ita dai Mero da ganin ta kyakkyawar mace ce, dan dik yaran ta da ita suke kama, kuma kyawawa ne, Abu ma ba laifi, black beauty ce, amma dik ba a gane kamannin su, datti da qazanta sun cinye kyan. 'Ina da qaton aiki a gabana ashe' (Kun ji Jameelah ta koma 'yar agaji) Shiru-shiru ba wadda ta kai masu abin karyawa a gidan, fita Tsalha yayi sai da ya jima ya dawo ɗauke da madara da milo sugar da lipton a aljihun babbar rigar shi, ya shiga madafi da kan shi ya kwaso ruwan zafi a flask ɗin Jameelah, ya wuce d'aki yana jin Abu na masifar an taɓa mata ruwa bata yafe ba, amma gudun kar ya b'atawa Jameelaah sai rai bai kula ta ba, a ran shi ya ayyana, 'Lallai matan nan wato sun samu dama ta yanzu, da wa ta isa ina magana tana mayarwa ko faɗan kishin su zasuyi sai bana nan, amma shine yau suke maida magana a gaba na harda furtan ba su yafe ba, lallai zan d'au mataki mai girma akan ku' Har Jameelaah ta gama haɗa tea bai sani ba yana ta tunani,a hankali tace masa, "Tinanin me kake yi haka? Haba Baban Hajjo kar ka na sawa ranka damuwa, in kana damuwa wani ciwon ya kama min kai ya zan yi da rai na?" Sai ta fara hawayen gulma, nan kuwa dik hawayn takaicin rayuwar da take ciki ne, dama kuma kukan na kusa, ganin hawayen ta ne ya sa ya kid'ime ya rude, ya janye tea ɗin gefe ya fara lallashin ta yana shafa bayan ta, jin ta take kamar wata jaririya saboda yanda yake yi mata, shiru ta farayi a hankali sannan ta miqa masa tea again ta deb'o kayan gara ta aje masa da dambun naman da ta ga an saka a ciki nan kuwa ya washe baki yana murna ci ya farayi sai yaga ita bata ci, ya kalle ta sosai can kuma sai  ya ci gaba da ci, dan shi akan abin da zai ci baya wasa, sai da ya qoshi yaga dai bata ci komai ba, sai a sannan ya kula ma ma shi kadai ta hadawa tea ɗin,cikin nuna kulawa yace mata, "Wai kam Jameelaah me ya faru ne? Naga baki haɗa wa kan ki shayin ba,sannan bakici komai ba kuma, lafiya kike kuwa?" "Lafiya nake sai tsoron wani abu ɗaya danqaren a zuciya ta," Cikin tsananin damuwa ya isa gaban ta ya jata jikin shi, ya dora kan ta a cinyar shi yana shafa bayan ta yace, "Jameelaah me kike tsoro haka da zai hana ki cin abinci, ni da kika ganni nan bana wasa da abinci, dan haka bana son kema kina wasa da abinci, meke damun ki sanar dani inshaa Allahu zan yi maki maganin shi, indai bai fi qarfina ba," Kuka ta fara yi mara sauti,nan da nan Tsalha ya sake rikicewa yace, "Subhanallahi, me kike jin tsoro haka tashi ki nuna min shi, inna kashewa ne a kashe yanzu nan" D'aga ta yayi ya haura da ita saman gado ya na dube dube, hannun shi ta kama ta manna da qirjin ta tana ci gaba da zubda hawaye. "Amarya ta dan Allah ki sanar dani abinda kike so," "Inna fada maka ma na san ba lallai kamin shi ba, shi yasa nake jin tsoro," "Ya Allahu ya rahamanu, dan Allah karki ce na sake ki ba zan iya ci gaba da rayuwa babu ke ba, daga jiya zuwa yau na san daɗin aure a rayuwa ta, in kika barni ina zan saka raina?" Sai ga Tsalha na matsar kwalla, ganin haka yasa Jameelaah, kwantar da jikin ta a nashi, musamman qirjin ta da ta kula yana maita. Ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi,cikin shagwab'a tace, "Ba zan taba cewa ka saken ba ni, ba kuma na fata mu rabu har abada, ni da kai mutuwa ce zata rabamu in Allah ya yarda, ina son ka Baban Hajjo, ko ba komai ka rufa ma rayuwa ta asiri da ka aureni ka killace ni a gidan ka," "To indai kina so na haka me zai sa kiji tsoron sanar dani abinda zai hana ki cin abinci ya sanya min ke kuka?" "Dama....immm... damaa.. gamee daa..., immm ɗazu abinda na gani kayi ne, ina tsoron kar nima wataran kamin haka in ka min haka ina zan sa kaina" Sai ta sake fashewa da wani mummunan kukan,rikicewa yayi sosai da sosai ya manna ta da qirjin shi yana bubbuga bayan ta alamar tayi hakuri ta daina kuka, shiruuu ya biyo baya na wasu mintuna, can ya gyara murya yace, "Yanzu ki sanar dani me kike ganin za ayi akan hakan? Inshaa Allahu zan yi maki," "Indai kayi alqawarin zaka sauya yanayin zaman ka da matan ka da yaran ka, ba abinda zai hana nima na yi maka alqawarin baka da kuma yi maka dik abinda kake so, indai baifi qarfina ba," "Inshaa Allahu na yi maki alqawarin gyarawa, amma yaran ne in ka sake masu raini zai shiga tsakanin ka da su matan ma haka " "In faɗa maka me yasa zasu raina ka ba zaka ji haushi na ba kuna baza ka d'au hakan a matsayin zagi ko cin fuska ba?" "Habaa ai ba wannan a tsakanin mu, na tabbata Jameelaah kin fi qarfin aure na ko ta wacce hanya, amma kika hakura kika aure ni, ni kuwa meye ba zan yarda dashi ba indai bai saɓawa Allah ba," "Kaga na farko d'aure ma yaran ka da kake baka jansu a jiki baka wasa da su shi zai sa su zama suna aikata abubuwa marasa kyau a bayan idon ka kuma su dinga tsoron ka a gaban ka, sannan matan ka da kake sakarwa cefane wataran har da  awo raini zai iya shiga a bayan idon ka su dinga zagin ka, sannan a hankali su daina son ka, na tabbata kuwa kana son su su dikan su, (gyada kai yayi) to ka gani, sannan rashin zama kuyi hira zai dinga nesanta jka da iyalin ka, mu mata muna son ana hira damu, ana jin matsalar mu, ko ba za a biya mana buqatar ba ayi mana alqawarin inshaa Allahu in Allah ya hore za a yi mana, to zaka sami mace tana girmama ka, sanda ka samu in ka mata abu zaka ga girma da qimar ka da kuma darajar ka ta d'agu a wajen ta, ka sani maqo baya daga cikin halin Rasulullah,Annabi yana wadata iyalin shi da abinda yake da shi,abinda bai dashi tinda sun san samun shi da rashn shi basu damuwa, kar na cika ka da surutu dan ni ɗin ba wata malama bace ka fini sani, kawai ka gwada sauyawa akan kan ka zaka ga me nake nufi, sanda iyalin ka suka fara nuna maka so kamar su had'iye ka, sai dai kishi na zai qaru fa in aka janye min kai" Saqala hannayen ta tayi a wuyan shi ta rungume shi, tana murmushi qasa-qasa, shiru yayi yana ta bitar maganganun da ta yi masa, tabbas maganar yarinyar akwai qamshin gaskiya a ciki, yanayin sana'ar su ɗaya da Malam Jameel sai dai shi shago ma gare shi saboda ya fi su samu sosai, wasu masu gyaran ma har suna zuwa wajen shi ana siyan kayan gyara, amma in ya samu kud'in shi sai dai yaci daɗi shi kaɗai, sai sanda akai kasuwa sosai yayi awo su kuma matan su ji dana cefane. In ya qare kuwa baida kuɗi sai dai su nema da kan su, cikin murya mau natsuwa yace mata, "Zan duba maganar ki, ki kwantar da hankalin ki ba mai janye ni, ni naki ne har abada" Sunne kai tayi dan taji kunya, fita yayi ya deb'i ruwan wanka yayi wanka, rabon dayayi wanka sau uku a jere a haka ya manta, tin kafin yayi auren fari. (Matsalar shi kenan daga uwargida aka faro ta, itace bata tafi dashi yanda ya kamata ba har mai bi mata ta ɗora daga inda ta tarar) Yana komawa d'akin ya shirya ya ce mata zai leqa kasuwa akwai abinda zai yi, rakashi tayi har bakin qofa tana d'aga masa hannu ya wuce ita kuma ta koma ciki,a tsakar gida ta tadda mero, "Ohhhni Mero yau naji iyayi iya reto kad'a gado ba miji, ai na zaci tare zasu tafi kasuwar fa Abu,irin wannan kitifi haka?" Murmushi Jameelaah kawai tayi ta wuce d'akin ta,a ranta ta na ayyana, 'Lallai ruwa ya daki tsohon zakara, in ba dan haka ba har kun faɗan rashin kunya ni?' Farantai ta d'iba ta d'ebi kayan gara ta zuba dai-dai, ta kuma d'iban wasu a farantai bibbiyu suma ta zuba dai-dai, ta ɗauka ta fita sallama ta yi masu, idon su akan kayan garan Mero me habaici ji kake ta yi difff bakin nan ya mace murus, durgusawa tayi kaɗan ta gaida Abu, ba yabo ba fallasa ta amsa mata, "Babar Hajjo ga wannan naki ne, wannan na yara su raba ba yawa ayi hakuri da shi," Amsa tayi tace "To an gode, Allah yayi albarka," "Ameen" "Babar Zara'u ga naki gana su Zara'u a basu na sune ba yawa," "An gode," Miqewa tayi ta koma d'aki yaran su da basu zuwa makaranta suka yo caaa a basu kason su, nan suka karkasa aka aje na sauran yaran da basu nan suka boye masu, sai aka bawa wanda suke gida kuma nasu kason. Saida ta gama gyara d'akin ta sannan ta yi shirin wanka, wanke band'akin tayi tass sannan ta shiga wankan ta fito, ta shirya cikin wata shadda da tazo da ita daga gida ,ta ware wasu daga cikin kayan ta da zasuyi wa 'yan matan gidan ta aje a gefe sai sun dawo zata siye su da kyutatawa, ta haka zata siye manyan su kuma su taimaka mata da qannen su. (Wa ya tuna gidan su Umaimah yanda yarinyar nan Jameelah ta dinga zuba mulki? Hummm ka ji tsoron Allah bawa ka zauna lafiya wallahi) Tsakar gida taje ta saka kujerar ta ta zauna sai qamshi take zubawa, ga kuma uban kyaun da ta yi iyayen suna aiki suna kallon ta, "Akwai aikin da zan taya ku da shi ne Babar Hajjo? Zaman shirun ba daɗi," "Kar ki ce baqar magana nake miki wato ina mamakin abubuwan da kika yi yanzu Jameelaah, saboda ni dai kin san na san ki na san kuma wacece Ramai, kuma na san dik ba haka kike ba a da, ko zaman zawarci ne ya koya maki hankali?" Jameelaah bata ji daɗin tambayar nan ba amma ta san ita ta jawa kan ta, tinda ita ta b'ata kan ta tin farko,dan haka cikin bata tabbacin ta shiryu tace, "Lallai a da ban zama daga cikin yaran kirki ba, amma kowa na samun dama ta biyu a rayuwar shi, ruwan mutun ne ya gyara Allah ya dafa masa,in kuma ya samu dama ta biyu ya sake jefa kan shi ga halaka,sai Allah ya barshi da iyawar shi da yake ganin ya iya," Shiru suka yi gaba dayan su nan ta miqa mata gyaran wake tace ta taya ta, tana cikin gyarawa ya Malam Tsalha ya shigo tare da wasu yaran a bayan shi, sai shigo da kayan abinci ake yi, dik da rabi-rabin buhu ne amma ba a taɓa yin hakan ba a gidan,abincin sun haɗa da dangin su ; shinkafa, masara, gero, wake, kwalin taliya, kayan su maggi da barkono da mai, sai sabulan wanka dana wanki da omo. "Wannan fa daga ina Tsalha?" "Naku ne kowa in ranar girkin ta ya zo sai ta d'iba a girka dan Allah banda almubazzaranci, Ke Abu da Mero ku samen a dakin Abu ke kuma ki je ki karya, dan da ganin ki har yanzu baki ci komai ba," Cike da matsanancin mamaki matan ke bin shi da kallo, ledar da ta rage a hannun shi ya miqawa yaran yace, "Ku raba harda 'yan makaranta,Allah yayi muku albarka, ya hore kuma a sanya ku a makaranta" A tsorace suka amsa ya kai hannu zai shafa kan yaron Mero,yaro ya yi saurin kauda kai ya zaci mazge shi za ai, murmushi yayi ya san watarana zasu saba ne amma sai a hankali. Jameelaah kuwa ta ji daɗi sosai da  ya ɗauki gyaran da tayi masa da wuri, sai yanzu take ganin batai gaggawar neman gyara masa iyali ba kuwa, daga zuwa sai gyare-gyare kamar kafinta? Dan ganin ya yi sanyi sai suka wani tsaitsaya a tsaye ba ladabi suna jiran suji me zaice, tinda suke bai taba tara su ba in ba sanadin rabon faɗa ba, "Na kira ku ne saboda ina son na baku haƙuri akan irin zaman da muka yi a baya, ban taba kula ina saɓa maku ba, kuma ina saɓawa Allah ba sai yanzu da yarinyarnan ta nusar dani, bana kyauta maku na sani, ku min hakuri inshaa Allahu daga yau komai ya qare ya kuma wuce, zaman jahilci da muka yi a baya ba za a maimaita shi ba, ina fatan zaku bani had'in kai?" Jikin su ne dik ya mace samun waje sukai suka zauna, suna jin kunyar abubuwan da sukai ta aikatawa. "Ka yafe mana muma Baban Hajjo lallai zuwan yarinyar nan alkhairi ne a wajen mu baki ɗaya Allah ya yafe mana" "Ameen sai ku gyara sosai, in ba haka ba ta kwace maku ni, dan dai kunga yanda take ɗaukan wanka da burushi ga kuma uwa uba qamshi," "Tabdijam ai mu mutu ka raba ne mu da kai takalmin kaza ba,ba wadda zata kwace mana kai" Nan sukai ta raha da hirar da suka dad'e basu yi ba. ********************* Bayan dogon bincike Sapnah ta gano ina ne gidan su Jameelaah, dan haka shiryawa tayi ta d'ebi 'yan kayan Humairah, ta qudurta ko Umar zai yi faɗa sai ta kai ta wajen mahaifiyar ta sun ga juna, itama taji daɗi a ran ta, ta san dik inda take tana kewar d'iyarta rashin ta a gare ta ya na damun ta............... *Na rantse ba ruwana dik abinda Ummaru ya maki no my water insayiz tammm* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼  *MAZAUNA GIDA*  💅🏼 *WRITTEN BY HAERMEEBRAERH* Page 49: Hankalin ta a tashe yake sosai dan bata san me zai je ya zo ba,amma ta riga ta qurdurta ma ran ta yau sai ta kai Humairah wajen Jamewelaah sai dai a yi wadda za a yi haba, koma meye ya faru da su a baya Jameelaah is her biological mother bai kamata ya datse alaqar dake tsakanin ta da 'yarta ba, a qalla ko da hutu ne ana kai ta musamman yanzu da yarinyar tai wayo take jin maganganu wajen yaran maqota da 'yan uwa tinda sunyi zama da mahaifiyar ta. Tinawa tayi da tambayar da  yarinyar ta yi mata a daren jiya bayan ta dawo daga maqotan su kai musu abinci, dan indai suka yi girki sukan kai masu musamman wanda ta san qamshin shi ya karade unguwa sai ta zuba komai kashin shi Humairah ta miqa wa moqota dan fidda haqqin maqotaka. 'Ammi wai dama ashe inada wata Maman Inji su Laure,?' 'Ohhh ni duniya, yanzu daga shigar ki miqa masu abincin nan har sun faɗa mki wannan maganar? Tabbas kina da wata mamar itace ta haife ki kuma, amma ta koma gidan su itama, watarana zan kai ki ku ga juna inshaa Allahu,' 'Da izinin wa za a je ganin nata?" Kama hannun shi tayi dan kar yayi b'arin baki a gaban yarinyar wanda har abada Humirah zata na ganin baqin shi, domin kuwa Uwa Uwace koda kuwa mahaukaciya ce. 'Me yasa zaki hana ni yin magana? Ai gwanda ta san wace irin uwa gare ta' 'Lallai kuwa daka zubar da qima da mutuncin ka gaban d'iyar ka har abada wai ni meke damun ka ne? Kai da mahaifiyar ta ku ka samu sab'ani fa ba da ita ba, ita bata san sanda kuka yi cikin ta kuka haife ta ba, da kun san zaku rabu har ya zamar mata tabo da baku haife ta ba, wannan shine sak abinda d'iyar ka zata iya faɗa maka in kanuna tsanar mahaifiyar ta a gaban ta, kar kace bazata iya ba,itama 'yar zamani ce, sannan kuma kai ɗin kai ne sanadin kawo ta duniyar da matar da ka tsana a yanzu, so ba ruwan ta da matsalar ku, wannan shawarata kenan in kaji ka ɗauka ta yi maka amfani a gaba,' Umar shiru yayi, kamar ba zai ce komai ba,daga baya kuma ya ce, 'Ba za ta je wajen ta ba a yanzu har sai ta mallaki hankalin kan ta,taje da qafar ta a lokacin' 'Yarinyar da ta kai shekara goma ita ce bata mallaki hankalin kan ta ba?yara nawa kamar ta suke zuwa dik inda suka ga dama,ka diba ka gani yanda mutane ke faɗa mata labarai kala-kala na qarya da gaskiya akan mahaifiyar ta baka tunanin lokaci ya yi da za ka manta da baya ka fuskanci gaba? Shekarun fa da yawa ba jiya abun nan ya faru ba ba kuma  shekaran jiya ba,amma a gaskiya Abbahn Humairah ka bani mamaki, ka ban mamaki, ashe kai baka yafiya?' Rintse idon ta tayi a sanda ta tina yanda ta fita tana kuka daga d'akin amma ko bin ta bai yi ba dan ya lallashe ta ko ya bata hakuri,yau kuwa labarin da Humairah ta kai mata ance akan mahaifiyar ta shine dalilin da ya sa zata kaita dan ta tabbatar mata da kwanciyar hankali a ran ta, kuma ta gane me take faɗa mata akan mutane, in dai zaka bi ta maganar su ba zaka yi huld'a da kowa ba, saboda za a kushe mutum ne according to yanda aka tsane shi. A qofar gidan su Jameelaah tayi parking ɗin kyakkyawar motar ta da Umar ya mallaka mata a ranar zagayowar shekarar haihuwar ta, dan kuwa yanzu likafa ta ci gaba ko gidan su ma da suke ciki Umar ya siye filin gefen shi ya qara faɗin shi ya sai mata mota ya kuma sayi wadda za a dinga kai Humairah makaranta da ita, arziqi sai shukran,Sapnah har yanzu bata samu rabo ba, sai b'ari da tayi sau biyu. Buɗe qofar motar suka yi tare da ɗaukan kayan sawa na Humairah da suka deb'o,suka nufi gidan da ya sha fenti sakamakon bikin 'yan matan gidan da akai wata ɗaya daya wuce. Jameelaah na kwashe abinci tana rabawa yaran na miqawa kowa nashi, Abu da Mero na zaune a tabarma babba suna jiran ta gama su ci nasu, kowaccen su ta sha gayun ta dai-dai iyawa da kuma wadatar ta, gaba  ɗaya sun zama 'yan gayu sun sauya rayuwar da suke yi a baya mara kyau mai qazanta. Sallamar su Humairah ne ya sa Jameelaah d'agawa da sauri dan kuwa har abada bazata manta da wannan muryar ba miqewa tayi tsaye sannan ta ambaci sunan ta cikin mamaki, "Sapnah?" "Na'am, Jameelaah," Maida kallon ta tayi gefen Sapnah ta ga 'yar matashiyar yarinyar da take kyautata zaton Humairahn ta ce,dan kuwa ko a ina ne zata iya gane fuskar gudan jinin ta dik da jimawar da suka yi basu haɗu ba, a ganin Jameelah girma kawai tayi amma kamannin ta na nan tun na yarinta, idanun ta ne suka tara kwalla mai mugun zafi, Sapnah ce ta tura Humairah gaban Jameelah da niyyar taje wajen Jameelaahn, amma sai ta koma bayan Sapnah sannan ta kama hanyar fita tace, "Ammi muje kawai na gan ta na fasa yin hutun anan,dama dan saboda gaba kar mu haɗu a hanya na kasa gane wacece ta haife ni ko kuma har ɗayan mu ya mutu bai ga ɗaya ba shi yasa na matsu a kawo ni na gan ta" Da sauri Jameelaah ta tsallake kwanukan dake a gaban ta ta bi Humairah da gudu ta baya ta jata jikin ta ta rungumeta tana kuka sosai, Humairah ma kukan take yi amma taqi yarda ta juya su haɗa ido da mahaifiyar tata da ta nuna halin ko in kula da rayuwar ta,ba dan Allah ya haɗa ta da matar uba mai kirki kamar Sapnah ba da shikenan haka zata watsar da rayuwar ta kamar ba ita ta haife ta ba? Kome ya faru tsakanin ta da mahaifin ta be kamata ta ɗauke qafa a cikin rayuwar ta ba, tana jin son Mahaifiyar ta amma tana jin haushin barin ta da tayi ko sau ɗaya bata taba neman ta ba bata waiwayi rayuwar ta ta ji shin tana lafiya? Ana kyautata mata ko kuma tana zaman qunci a hannun matar uba? Cikin kuka da sarqewar murya Jameeelah ke magana, "Ki yi hakuri ki juyo ki kalli mahaifiyar ki Humairah, na san ban kyauta ba, shekaru masu yawa sun gushe amma na kasa fuskantar ki balle mahaifin ki, ina da babban tabo a zuciya ta, da jiki na, ina jin kunyar fuskantar mahaifin ki na ce ya bani ke ko da sau ɗaya ne mu kasance a tare, sannan naji labarin yanda Sapnah ke kula dake kamar ita ta haife ki, na san baki da maraicin Uwa, beside ko ina nan bana jin ina da cikakkiyar tarbiyyr da zan baki kamar wannan da Sapnah ke baki, na sani na yi ilimin addini mai tarin yawa amma ban tsaya na yi amfani da shi ba ta hanyar da ya dace, dan Allah Humairah ki yafe wa wannan gafalalliya kuma mai tarin zunubin mahaifiyar taki," Da sauri Humairah ta qanqame ta tana kuka,Sapnah kuwa sai lallashin su take yi dan itama sun sanya ta kukan. "Humairah is time to go home indai har ba zaki zauna anan ɗin ba, coz ur dad is on his way back home yanzu bana son ya san mun fita bai sani ba,sanda kika shirya zama anan ɗin watarana sai mu dawo," Da sauri Jameelaah ta kalle Sapnah after all this years bai yafe mata ba dama? Lallai tana da aiki a gaban ta, ko shi yasa har yanzu bata samu rabon aure ba? Allah ya jarabce ta da tsananin son haihuwa, amma bai ba ta ba, dama a kullum tana zargin kan ta akan abubuwan da ta aikata a baya. Share hawayen ta yi sannan ta shiga d'akin ta ta deb'o wa Humairah dik wani abu data ke da shi wanda ta san yarinya kamar ta zata buqata ta miqa masu, zuciyar ta ta dake sosai. "Ga wannan maza ku koma gida, Sapnah kar ki qara fita bada izinin mijin ki ba rayuwata babban darasi ne ga kowacce mace, inshaa Allahu da kaina zan zo na bashi haƙuri, har sai ya yafe min zan daina zuwa, kin san dai illar fita ba da izinin miji ba, ko ni na ishe ki ishara, mu mata MAZAUNA GIDA ne ba masu yawo ba izinin miji bane" Humairah na kuka haka ma Sapnah a haka ta sa yarinyar a mota suka wuce, Jameelaah na soro sai da ta ga wucewar su ta juya a guje zuwa d'akin ta tana kuka, d'akin ta ta shige ta faɗa gado tana ta zubar da hawayen tausayawa kan su. Abu da Mero sun tausaya mata sosai, yaran ma kowa sai ya koma wani sukuku saboda ganin  Jameelaah a cikin damuwa, Jameelaah ta taimaki darayuwar su, miji ya zama abin so agare su yanzu, mijin su na da lokacin su dana yaran su, ga shi yanzu har shagon kekuna gare shi arziqi ya bunqasa sai godiyar Allah, abinci ya wadatu, tsafta ta wadatu a gidan, ga uwa uba tarbiyya, dan ta tsaya tsayin daka dan ganin yaran sun kaucewa rayuwa irin wadda tayi a baya, soyayyar da yaran suke yi mata wata ran har kishi iyayen su suke yi. Sun sani zai yi wahala kuma ta sake fita cin abincin, dan haka suka dakko mazubin Tsalha suka zuba mata nata, sannan Abu ta shiga d'akin nata ta ajiye mata sannan ta zauna a gefen gadon Jameelahn ta dafa bayan ta cike da tausayawa ta ce, "Auntyn yara dan Allah ki daina kuka haka, komai yayi farko zai yi qarshe,duniya dama ta gaji haka, komai kayi a rayuwa kamar jifa ne, in yayi sama dik nisan dad'ewar da yayi a saman zai fad'o qasa, ko ya fad'o maka dai-dai yanda ka jefa, ko ya fad'o maka a tarwatse, ki godewa Allah a kan ni'imomin daya yi maki, dik da irin mugunyar rayuwar da ki kai a baya amma bai bari kin wulaqanta ba, muma ga shi kin taimaka mana da tarbiyyar yaran mu, tinda ke kika san maganin irin halin da matasan yanzu suke fuskan ta,wanda ba dan zuwan ki ba da yaran mu sun lalace, Allah ya taimake mu yanzu ga shi yara bakwai muka kai d'akin miji lafiya, ga mahaifin su yanzu yanda ya sauya dik ke za a godewa akan hakan, ko dan haka bai kamata ki sanya kan ki cikin qunci da damuwa ba, dan Allah ki warware ki fito, mu sha iskar duniya mu warwasa abun mu yanda muka saba,in ma bazaki ci abincin ba yanzu zuwa anjima kunci ke da Baban Hajjo kuna ci kuna soyayya abun ku," Cike da jin kunya ta rufe idon ta sannan ta yi murmushi ta share hawayen ta tace, "Ni ba zan ci da shi ba da ku zan ci," "Gulmamma nan nan ba tare kuke ci ana kaiwa juna a baki ba, ana kalaman qauna, ai ina sane da yanda kike susuta mana ɗan tsohon mijin mu, amma karki damu, muma dik mun koya yanzu duk abinda muka ga kina yi mai kyau yana yabawa muma yi muke koda bai yaba mana kamar yanda yake maki ba a qalla yana nuna mana jin daɗin sa," Dariya sosai Jameelaah take tintsirawa cike kuma da jin nauyin Abu, ashe komai suke yi akan idon su ake yin shi. Abu taji dadin yanda Jameelaah ta saki ranta,dan haka tare suka ci abincin su, suna ci gaba da tsokanar ta, tana ta faɗin dan Allah su bari, yara na ji fa. Koda Tsalha ya dawo sai da yayi wanka ya ci abinci, sannan suna hutawar su ta faɗa masa komai da ya faru da rana, ya ji tausayin ta sosai sannan daga baya ya lallashe ta yayi mata alqawarin har da shi za a je a bawa Umar hakuri, kuskure ba wanda ya wuce ya aikata shi ai, Allah na san bayin shi masu neman tuba da masu yafiya idan an nemi tuban su. Im fada maku gaskiya dana ga tsalhan ku ban gane hyi ba fa, Tsalha har wani ja ja ja ja yake yi, gemun nan ya tsaya carrr, kumatun ya bayyana, daga lob'awar da yayi, jikin shi kamar ba nashi ba, ya koma mijin yarinya, shima ya zama saurayi abun shi yana ta dangwalar romon dimokuraɗiyyar soyayya abinshi. ********************* Bayan Ummee wato Umaimah ta haifi Ibraheem Khaleel ❤️sai Shukrah wadda take shayarwa a yanzu,Aunty Hauwaa kuma bayan Muhammad ta sake haifiar Saifullah. Sadeeq da amaryar shi wadda yake ji da ita a yanzu kamar k'wai, suna da d'iya mai suna Fateemaah wato (Mamalo) dan shi da Mamalo ma ya ke kiran ta, Matar shi ta san ko me zatai da wahala ya so ta kamar Mamalo, dan haka take kyautata ma Fateen nasu, yana jin daɗin hakan kuwa sosai. ************************ "Washhh Allah na gaji Mama akwai dan abin kaiwa bakin salati kuwa? Yunwa nake ji kamar naci babu, na so na leqa shago na karb'i dambun nama kanna tafi amma da yake ina sauri sai na manta," "Da dikkan alama yau ma ba ai nasara ba kenan ko Bukar?" "Kamar kullum kuwa Mama, har yanzu ban samu aikin ba, na rasa meke damun qasata Nijeria, wai a ce ka gama karatu, da k'yar da sid'in goshi, sannan aikin ma da k'yar da sid'in goshi za ka samu ba wani tanadi da gwamnati ta yi wa matasa dan ganin sun samu aikin yi da zarar sun kammala karatun su da kyakkyawan sakamako,yanzu ki duba fa Mama mu da muka kashe lokacin mu, jikin mu, da dik wani arziqin mu bama samun aikin, sai waɗan da zasu jera sati basu je lecture bama, ko jarabawar gama sakandiren ma siyan ta suka yi, sune suna zauna a AC za a kai masu takardar aiki har gida, aikin ma haka za suna zuwan shi sanda suka ga dama, in ba su ga dama ba suyi wa mutum aiki ba dai-dai ba, kayi magana su zage ka, kaiii subhanallahi, talaka na cikin izayar rayuwa Mama, gwanda ma ni ai ban cika shekara ina neman aikin ba, ga wasu abokai na da suka rigani fara makaranta suka rigani gamawa su fa mama akwai masu shekara biyu uku a cikin su ba aiki, in ka nemi sana'a a dinga yi maka kallon jahili bayan da kwalin ka mai kyau na degree, in ka zauna ba aiki k'wandala ta gagare ka, in kai sata a garqame ka, ya ilahi ina talaka zai sa ranshi ne ?" "Oohhh an tab'o me baki yau, yau da gwamnati taji wannan sharhi da sun baka aiki Bukar kowa ya huta," Dariya yayi, sannan ya ja kwanon data kai masa abinci ya fara ci  yana ci gaba da surutai, "Ni kin san ma me nake tunani Mama? Aikin nan aje neman shi zan yi, na kama sana'ar nan tamu na bunqasa ta, ko ina ana kai dambun nan ana siyarwa ta haka ne masu sari da siyan ɗaya za su qaru, in da rabon na samu aiki shikenan, in babu ban dai zauna da jahilci ba ko? To godiya ta tabbata ga Allah" "Baki abun magana kenan Bukariri Allah to ya sanya albarka, mahaifin ka da Malam Tsalha kaga suma Allah ya bud'a yanzu shagunan keke gare su,mahakurci mawadaci aka ce, sana'a maganin rashin aikin office" Kamar yanda ya tsara haka ya gabatar, Bukar na sa hannu a sana'ar dambun nama Allah yasake sanyawa abun nasu albarka da nasibi, yanzu da wahala kaje unguwa a kano baka ji ana da shago ko wajen da ake bada sarin dambun naman su ba, in an samu riba sai su kasa ta uku, Jameelaah na da kashi ɗaya su kuma kashi biyu, da ita suke baiwa Kashi biyun ta ce su yafi cancanta da su riqe kashi biyu ba ita ba. ********************** Umar ne zaune a farfajiyar gidan shi riqe da jarida kasancewar yau weekend ne ba aiki, Sapnah na zaune a gefen shi tana b'are masu lemo shi da Humairah itama tana sha. "Wajen nan qwari sun yi yawa Ammi duk sai cizona suke yi," Cike da shagwab'a take yin maganar, kallon ta Sapnah tayi sannan tace, "Ki shiga ciki mana kin damen da surutu tin ɗazu, kin saka ɗan qaramin wando da yar riga to tsoron ki suke ji da bazasu cije ki ba? Yanzu ga jarabawar JSSCE din ku ta gabato, ya kamata ki maida hankali wajen yin karatu ba wasa ba, in kin ga ina zaune ba abinda nake yi kema ki bi waje ki zauna,ni ɗin nan na sha gaya maki da kwali na na digiri digirgir yarinya,aiki ne dai naqi yi, saboda ina son zama na kula da iyali na," Humairah tashi tayi ta rungume Sapnah, tare da manna mata kiss a kuncin ta sannan ta shige ciki tana faɗin, "Na wuce ciki ni dai tinda dai kin kore ni, karatu kuwa zan baki mamaki Ammi zaki yi alfahari dani watarana,"   "Haka nake so ai dama na sha mamakin sannan ko a yanzu ina alfahari dake Allah ya yi maki albarka," "Ameeen Ammin Humairah,kema Allah ya yi maki albarka" Umar ne ke ta murmushi baya gajiya da jin hirar Sapnah da Humairah, a can qasan ran shi kuma yana jin haushin Jameelaah da taurin kai ya hana ta zuwa ta nemi qafarar shi ta roqe shi ya bata Humairah dan itama ta saba da ita haka, shi kuwa yayi alqawarin in ba ita ta zo ta nemi a bata Humairah ba ba zai taɓa kaita wajen ta ba da kan shi. "Tinanin me kake yi haka Zauj?" Ya buɗe baki zai yi magana kenan, aka buɗe qaramar qofar gate ɗin gidan nasu aka ziro qafa, qurawa qafar ido Umar da Sapnah suka yi dan ganin wanene zai shigo, ko a ina Umar yaga wannan qafar tabbas zai gane qafar da ya sha yi wa tausa da hannayen shi ce, qafar da ya sha shafa mata mai da hannayen shi ce qafar da................... *Casssssss anayi ina jin nice, ana bari ina yin😢* [09/09, 10:39 am] Aunty Hameeda: 💅🏼  *MAZAUNA GIDA*  💅🏼 *WRITTEN BY HAERMEEBRAERH* Page 50: Ajiye jaridar hannun shi ya yi ya miqe tsaye Sapnah da ke riqe da lemon da ta bare masa ta bi qafafun da yake kallo da idanun ta,Jameelaah ce ta shiga sanye da atampa riga da zani sai mayafin daya yi kala da kayan jikin nata, haka ma takalmi da purse ɗin ta iri ɗaya ne, kamala da kwarjini tare da nutsuwa sun bayyana a fuskar ta, lallai dik kyaun mutum in baida kamala bai gama cika mutum ba, yanzu ne Jameelaah take cikkkiyar kyakkyawar. Sapnah ce ta tashi ta je gare ta fuskar ta ɗauke da murmushi mai qayatarwa, ta kama hannun ta tana mata sannu da zuwa, ciki ta shigar da ita, sai da ta zauna suka gaisa sannan Jameelah tace mata, "Ni da maigidana muka zo yana waje," "Ahhh shi ne baki yi magana ba, bawan Allah ya na can waje a tsaye ai da kun shigo tare duk gida ne ai" Zuwa ta yi tayi ma Umar bayani haka nan sai yaji dik wani haushin ta da yake ji ya kau a ran shi, gaba ɗaya yanda yaso ya yi mata rashi mutunci ya farfaɗa mata maganganu marasa daɗi a dik sanda ta zo wajen shi sai ya ji ko kallon banza ba zai iya yi mata ba. Shigar da Tsalha ya yi cikin gidan, Tsalha zama ya yi kusa da matar shi sai ta miqa masa lemon da aka tsiyaya mata,cike da tsokana Sapnah tace, "Ohhhh Maman Humairah wato soyayya daɗi ko, ai gashi zan zuba masa nashi shima," "Ammin Humairah baki da dama, wato har yanzu baki bar surutu ba ya huta shima ko?" Dariya suka yi dikan su harda Umar, Umar kuwa sai kallon Jameelaah yake yi Tsalha ma na kula da kallon da yake ma matar shi,nan da nan kishin 'yan mazan jiya ya motsa,sai ya yi gyaran murya ya fara magana dan suyi suyi abinda ya kawo su su bar gidan, "To da farko dai dalilin zuwan mu shi ne, mun zo ne dan mu bada hakuri akan abubuwan da suka faru a baya,ba sai an maimaita su ba a yanzu,na san duk irin abubuwan da Amaryata Jameelah ta aikata maka marasa daɗi a baya,gamu mun zo tana mai neman gafara akan su, ina fatan zaka dubi girman Allah ka yafe mata su,mun sani dika Allah baya barin haqqin wani akan wani, koda Allah ya yafe mata kaima tana da buqatar ka tausaya mata ka yafe mata," Umar dake kallon yanda take tsiyayar da hawaye ne ya ji jikin shi ya yi sanyi, sai ya ji me yasa ya ɗauki wannan tsahon lokacin bai yafe mata ba ? saboda ko ba komai Jameelaah ta so shi kuma shima ya so ta, ya daukake ta a rayuwar shi, ya girmamata a lokacin da dik bata cancanci hakan ba, me zai hana ya yafe mata a yanzu da ta zama mutuniyar kirki, har ta buɗe baki za ta yi magana Umar ya riga ta da faɗin, "Na yafe mata Allah ya yafe mana baki ɗayan mu,dama ita rayuwa ana son mutum in ya yi laifi ya nemi yafiya, shi kuma wanda akai wa laifin ya yafe, shine cikar mutuntaka, dan haka na yafe mata dik abin da ta yi min wanda na sani da wanda ban sani ba, nayi hakan ne kuma domin Allah, ina fatan nima Allah ya yafe min," Jameelaah ce ke ta shasshekar kukan farin ciki, abubuwan da ta aikata masu muni a baya na ta dawo mata a kwanya da zuciyar ta, kallon gidan ta sake yi taga yanda aka sauya komai, arziqi ya haura na da, Sapnah ce ta miqe ta tafi d'akin Humairah,tana tafiya Jameelaah ta buɗe baki tace, "Na gode Abban Humairah, Allah ya qara girma da daukaka, kaima Allah ya sanya ka farin ciki fiye da yanda ka sanya ni a da da kuma yau, na gode na gode," "Ba komai ya wuce,ina fatan nima ki yafe min in akwai abinda na taɓa yi maki da ya b'ata ran ki," "Ba ka min komai ba Yah Umar innace ga abinda ka yi min yau mara daɗi na maka qazafi, baka rage ni da komai ba, ka bani dikkan kulawa da girmamawa tare da cikakkiyar soyayya, ni ce nai fatali da komai, in ma yi kamin wani abun ko menene shi na yafe maka, Allah ya yafe mana baki ɗaya," "Ameen ya Allah, sai kuma maganar Humairah ga ta can dik sanda suka samu hutu inshaa Allahu zata dinga zuwa, ko kuma da weekends, zata zo har ku saba da juna inshaa Allahu," "Muna godiya malam Umar nima kaga ka koya min wasu darussan na zaman duniya, Allah ya albarkaci rayuwar iyalin ka, muna godiya sosai," "Babu komai, nima na gode" Nan Sapnah ta shigo da Humairah da ta dame ta da tambayar ina zasu je? Sapnah taqi sanar da ita ta dai ce ta saka kaya sosai ta sanya mayafi ko hijabi, dan haka sanye take cikin riga da skirt na leshi, ta ɗora hijabi a saman su sai zaro ido take yi taga suprise ɗin da aka ce zata gani, su na zuwa parlour taga Jameelaah, cike da murna ta isa gaban ta ta rungume ta, Uwa Uwa ce😍 itan ma rungume ta tayi, tana shafa bayan ta, baki yaqi rufuwa, daga baya Humairah cike da jin kunya ta zauna a qasa, ta gaida su suka amsa, Jameelaah na shafa kan ta tace, "Lallai Humairah kema girman jiki gare ki kamar ni," Dariya sukai banda Humairah da ba ta so ana ce mata yar lukuta,tinda a iya shekarun ta jikin ta babba ne,dan har bra take sawa a yanzu. Turo baki tayi tana kallon Umar, alama ce ta ta kai qarar Jameelah wajen shi, "Yi hakuri Daddy's girl wasa na ke yi maki, to jikin ki kamar na Abban ki," Murna ta fara yi, dan kuwa har yanzu Umar kowa ya san shi da suka sake haɗuwa yanzu ba zai ce ya sauya ba, sai dai ma a ce ya qara kyau da haiba. Murna sosai Humairah tayi bayan sun taba hira Tsalha ya ceto su fa zasu tafi, "Habaa ku dan qara zama mana, ga abinci can ya kusan yi," Inji Sapnah da ta yi maganar har cikin ran ta, dan kuwa ba qaramin daɗin samun wannan daidaito a tsakanin Umar da Jameelah ta yi ba ko dan Hunairahn ta ta samu farin ciki mai d'orewa. "Ahhh ba komai kar ku damu, 'yan uwana nacan na jiran mu muci abinci, dan kuwa na ce masu ba jimawa zamuyi ba." Tsalha yaji daɗin maganar ta sosai, saboda ko ba komai zuwan ta gidan shi ya sauya daga gidan qazamai ya koma na masu tsafta, tarbiyya ta wadatu, shi kan shi dik wata furfura da wani rama dik sun zama labari, yi 'yar qiba mai ban sha'awa yayi haske, ba wanda ya damu da furfurar shi, saboda kyaun da ya yi. Umar kuwa d'aki ya shiga ya sanya kaya sosai, ya deb'i wasu shaddoji guda biyu masu tsadar gaske, da turaruka biyu, sai hula ɗaya takalmi ɗaya ya saka tashi hular ya ɗauki makullin mota sannan ya fita yace suje ya sauke su a gida daga nan yaga wajen da suke da zama ma. Ai kuwa basu yi masa musa ba dan yanda Umar yayi magana ba damar musu n ma gashi yayi gaba ya bar su baya alamar su yake jira, sai da suka fita Sapnah ta fito itama ɗauke da ledar ta a hannu, kayan kwalliya ne da turaruka sai wani sabulun wanka da body scrub da skin oil sai hair oil da hair mask duk na kamfanin HAMIBRAH BEAUTY PALACE kaya ne dake gyara fata kuma basa saka bleaching sai dai suyi maganin quraje da qesbi, sannan gashi ya yi kyau ya yi tsawo ya yi daɗin maintaining. Jameelaah tayi ta godiya kamar ba zata daina ba Sapnah har taji kunya ma ta kama ta, sanda zasu tafi Umar yace Humairah ta shiga daga nan sai su dawo tare. Cike da murna kuwa tashige kusa da Jameelaah suka wuce. Har gidan ya kaisu kuwa ya jira dan saida Jameelaah da Humairah suka shiga ciki sannan Umar ya baiwa Tsalha kayan daya d'akko masa, Umar na ganin alamun Tsalha zai qi Karb'a ne ya yi saurin riga shi yin magana ya ce, "Don Allah kar ka qi Karb'a, ga shi nan a yi ma matan gidan kwalliya, yanzu ni da ku ai mun zama daya inshaa Allhu," "Kaiii amma na gode, ba dan ka roqe ni ba da sai nace ka bar su, daga zuwa neman gafara sai a had'o mu da irin wannan kab'akin arziqin haka?" "Alamu ne na an yafe maku kenan ai," Dariya suka yi, Tsalha ya shiga gidan shi a dakin Jameelaah ya aje kayan sannan ya ma matan shi izinin su sa Hijabi su gaisa da Umar, a soron gidan suka tsaya suka gaggaisa,bayan sun koma cikin gida ne sukai ta yaba Kyau da kwarjini tare da kud'in Umar, dan kuwa ko a jikin shi ya nuna shi din ya shaqi nera. Nan da nan suka sake girmama Jameelaah a zuqatan su, ace tai zaman aure da irin wannan zankad'ed'en miji ta dawo ta auri tsoho sa'an baban ta? Sai da suka rungume junan su sannan Humairah ta sake shigewa jikin Jameelaah,Jameelah ce ta bude motar ta sanya ta ciki, tare da sumbatar kuncin ta, sai d'aga masu hannu suke yi bayan sun wuce Jameelaah ta share qaramar k'wallar dake idanun ta, suka koma ciki da mijin ta abin son ta wato Malam Tsalha. Tin daga wannan lokacin Umar yake kai Humairah wajen su Ramai, tayi masu weekend, wani satin kuma wajen su Mum, wani sati kuma gidan Jameelaah, ba qaramin jin daɗin ziyarar da take yi ba take, wataran kuma Sapnah zata kai ta gidan iyayen ta da gidan su Umaimah da Aunty Hauwaa, ganin su take yi suma a matsayin kakannin ta, Humairah da Ummee 'yar gidan Umaimah sun zama best friends kuma best sisters, komai tare suke yi saboda makarantar su ma ɗaya ce,Muhammad ma makarantar su ɗaya ya yi girman jiki shima kamar Humairah, dan tsaurin ido cewa yake shi yayan su ne, saboda dik inda mace take namiji ne gaba da ita, shi ke kula da ita. Bayan shekara biyar Bukar da yayi aure ne suka je gidan Ramai dan kai gaisuwa, matar Bukar fiddausi anan maqotan su ya gan ta ya ji yana son ta har aka yi musu aure tare, ta yo girki mai daɗi guda biyu, ɗaya na gidan su Bukar ɗin ne ɗaya na gidan iyayen ta,dik zubi ɗaya ta yi musu ba bu bambamci, hatta da mazubin dik a abu iri ɗaya ta saka, saboda ba ta son kowa ya zargi ta fifita wani sama da wani. Ramai na alfahari da samun suruka kamar fiddausi, dan bata ɗauke ta a uwar miji ba a uwa ta ɗauke ta, dan haka itama a d'iya ta ɗauke ta,  in taje ta tadda wanki, ko wani aikin Ramai bata yi ba to zata zage suna hira tana yi mata aikin, dik wani abu in bata iya ba bata jin nauyin tambayar Ramai, saboda yanzu ita ce uwa a wajen ta, gane hakan da Ramai tayi ba qaramin jin daɗi take yi ba, ko ba komai itama ta sake samun wata d'iyar. Matar Bukar na ɗauke da ciki wata biyu, Bukar da ya kaita zai gudu, wai kunya yake ji ace matar shi na da ciki, Ramai tace ohhh ji soko ita mace bataji kunya ba sai shi namiji, haihuwa inda rai da rabo ai an fara yi kenan, in Fiddausi ta koma gida kuwa tai ta tsokanar shi, in ya neme ta tace itama kunya take ji, sai yayi ta bata hakuri sannan take yarda. A tsakanin waɗannan shekarun Jameelaah da Sapnah Allah ya azurta su da samun haihuwa, dika maza, Tsalha ya saka sunan Malam Jameel, inda suke kiran shi da Abbah, Umar kuwa ya sanya sunan Baban su Sapnah, dan kuwa zaɓi ya bata ita kuma ta sanya sunan mahaifin ta, Abdulqadeer, suna ce nasa Abdul. Tin daga nan haihuwa ta buɗe masu, in sun ziyarci juna suna hira suyi ta faɗin, ikon Allah sai da d'iyar su ta girma ta isa kaiwa d'akin miji sannan haihuwa ta buɗe masu. Jameelaah tace indai aka aurar da Humairah zata rufe haihuwa, akwai kunya aje sunan nata haihuwar sannan a tafi na d'iyar ta, Sapnah sai tace ai ba komai haka Allah ya qaddara, kar ta bi na mutane, in haihuwa ne bata yi ba zasu ce bata haihu ba, yanzu da ta haihu, kuma zasu sa mata ido, ba a iyawa ɗan Adam, dan haka ta rungumi dik abinda Allah ya bata kawai. ********************** Dr. Aeeshaah Humairah Umar likitan yara ce yanzu a asibitin Ameenu Kano, dake cikin garin Kano burin ta ya gama cika a yanzu ita da Ummee, twins ma wasu mutanen ke kiran su, dik da cewar Ummee tafi Humairah tsaho, ita kuma Humairah tafi Ummee cika, shape din ta irin na Jameelaah ne sak, ta dai qi amincewa ne dan ana ce mata 'yar lukuta, dik da ba wata qiba sai cikar qirji da mazaunai. Ummee ta samu miji daga dangin su Umaimah, wan da ake kira da Abbas, (Ba Abbas din Fauziyya ba fa na littafin MUGUN MIJI NA MASOYIYAR MARUBUCIYAR KU HAERMEEBRAEH) ma aikacin gidan talabijin na NTA ne dake a Lagos, Humairah kuwa ta samu nata ne a nan asibitin su, shi kuma likitan Mata ne kamar mahaifin ta mai suna Imraan, Dr. Imraan iyayen shi ba wasu masu hali bane, kusan shi ke kula ma da su, amma Alhamdu lilLAAH akwai rufin asiri, ya mallaki gidan kan shi da abin hawa. An saka ranar auren su a tare, dan haka Iyayen amare an fara gyaran amare sosai ba kama hannun yaro, lokuta da dama sunfi haɗuwa a gidan su Jameeelaah dan kuwa Jameelaah har yau bata sake da su Mum ba tana jin nauyin abinda ta yi mata a baya, dik kuwa da qoqarin da Mum take akan ta saki jikin ta, amma inaa ta kasa hakan, dan haka wataran gidan su Jameelaahn Ummee da Humairah suke zuwa, ta yi masu gyaran jiki, ko ta koya masu wasu abubuwan da ya dace ace sun iya. An daura auren Ummee da Humairah, akan sadaki daidai aljihun mazajen su, aure ne daya halarci zuri'a kala-kala, ta kowanne ɓangare dangi sun halarta, dangin Ramai dana Malam Jameel, dangin mum dana Dad, ga bangaren su Sapnah, ga wajen angwaye,suma dangin uwa da uba duk sun halarta. Biki dai sai wanda ya gani, rabon da na ga amare sun sha kwalliya mai kyau irin wannan har na manta, doguwar riga ce fara tass mai kyallin stones masu haske, an kama daga qirjin su aka sake ta daga qasa, dogon hannu gare ta sai mayafin ta mai cikar ado, aka yafa masu saman daurin da aka kafa masu da gwaggwaro irin na wannan zamani, da ake yayi, fuskar su ta sha kwalliya, sun sha kwalliya mai qayatarwa ga abinci nan cima kala-kala ko a KFC albarka😂. Ana nan ana ta shan dinner kowa ka gani cikin farin ciki yake, yau ga Ramai ga kaji da snaks, amma ba handama ba had'ama, taci iya cin ta ta kauda kai tai hamdala, tare da sanya albarka a auren jikokon nata. An kai amare gidajen su lafiya,  inda Humairah take zaune anan garin Kano a unguwar Gedi-Gedi, Ita kuma Ummee sun lula ta jirgi sun tafi Lago shine your eyes, suna zaune a unguwar Yaba. Bayan watanni shida Matar Bukar ta haihu, Jameelaah ana ta hidimar suna, Sapnah da su Umaimah da Aunty Hauwaa ana ta aikin d'ura sobo a gorina, Mum da Ramai suna ciki suna ta hira suna ganin yanda 'yan uwa da abokan arziqi ke ta taimaka masu wajen yin abinci da kuma ganin komai ya tafi dai-dai, Humairah ce kwance tana danna waya suna hira da mijin ta, sai shagwab'a take yi masa akan sai ya kawo mata agwaluma, tana jiran shi ya bata hakuri ta bari har ta koma gida taqi, gashi tin safe bata karya ba har 1pm tayi, ganin bai da zaɓin daya wuce na ya je ya nemi dik inda agwaluma take ya kai mata ne yasan shi ya miqe daga office ya ɗauki makullin mota ya fita gefe daya kuma yana nan yana ci gaba da magana da ita ta waya. "To gani nan na tafi, wannan babyn in ta/ya zo duniya sai na mammake shi/ta, wahala iya wuya na sha ta, zanci soyayyan quli quli sabuwar suya, zan ci awara mai yaji, zan sha kankana, ga abinci masu gina jiki sosai ba za a daure a ci ba sai k'walama," "Ni kake yi ma faɗa ko? Bari ka ga na sa kuka a waya in an tambayen na ce cewa kai zaka zo ka d'auken ba za ai suna da ni ba, sai dai su zo sunan naka babyn," Qamewa a inda yake ya hau bata hakuri, dan Humairah na da iya shege in tace zatai abu, to kuwa zata yi ɗin, sai da taji ya yi nadamar faɗan daya mata sannan ta fara dariya tace, "In banda abinka banda hankali ne da zan hau maganar ciki da su," "Yo na sani," "Kace mi??" "Ah ah cewa nayi bari na kashe naje na siyo maki, bye love u," K'wafa tayi tana murmushi, ta san sarai yayi magana da ita, tashi tayi dan zuwa ta taya su aiki, Sapnah ta kira ta ɗauke da kwanon tuwon shinkafa miyar taushe, ya ji naman rago, sai zobon da suka gama qullawa ta bata. Tana ganin kwano ta fara tura baki,ahaka tana qi tana qi Sapnah ta sa ta ci mai yawa, kowa a wajen ta burge su sosai,dan kuwa wanda basu san alaqar su ba ganin ta suke mara kunya tana sangarta d'iyar ta a gaban kowa. (Mutum kenan kayan Allah, ka nuna ma ɗan ka gata ace ka sangarta shi, yayi laifi ka hukuntashi ace ka tsane shi, ka barshi ya lalace ace baku da tarbiyya😂 ya ilahi which one man go do na? Bama ɗan ka tarbiyya iyakar iyawar ka, ka toshe kunnen ka daga surutun mai surutu, as long as kasan akan dai-dai kake, to kowa yaci kan shi ) Rayuwar su haka take ci gaba da tafiya cikin nishad'i da walwala cike kuma da arziqi da wadata,sai dai abinda ba a rasa ba na yau da gobe dan kuwa rayuwar dama yau fari ne gobe tsimma, yau zuma ce gobe kuma mad'aci, yau arziqi gobe talauci,haka rayuwar kowa take tafiya. *Alhamdulillahi dika-dika anan na kawo qarshen novel dinnan mai suna MAZAUNA GIDA, ina fatan Alkhairin dake ciki Allah ya sa mutane su amfana da shi, akasin haka kuma Allah ya shafe shi cikin rubutu na da zuqatan bayin shi. Allah ya sa ka ma dik wanda suka karanta da alkhairi sukai comments masu daɗin karantawa, Allah ka saka ma mutan group dina na HAERMEEBRAERH NOVEL GROUP da alkhairi ka haɗa da GROUP ƊIN GIDAN ƊAN LITI ya Allah ka haɗa da dikkan hausa novel groups ɗin dake karanta wannan labari. Allah ka sanya mu a aljannah ta sanadiyyar karanta abun alkhairi ko wanne iri ne.* *Ya Allah ka sa rubutun nan nawa da nake yi su zame min alkhairi a ranar gobe qiyama,Allah ya sa na kafa hujja da su a gaban ka ya Allah kar su zame min hujja akai na.* *Wadda dik na batawa sanadin wannan novel a yafeni, masu ciki Allah ya sauke ku lafiya,masu yara Allah ya raya ya yi musu albarka, masu neman haihuwa Allah ya bada masu albarka.* *Fidda Allah ya qara maki hakurin rashin da kika yi ya kawo masu albarka, Yaya Barira Allah ya jiqan ki ya yi maki rahama, Allah yaraya abinda kik bari da imani* *HAERMEEBRAEH ❤️CE*