[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼 RUBUTAWA: HAERMERBRAERH MUTANEN KWARAI MASU ALBARKA GA EDITING DIN TSOFAFFIN NOVELS DINA NAN ZAN DINGA KAWO MAKU A HANKALI HAR NA KAMMALA, DAGA NAN SAI MU FAD'A SABO DA YARDAR ALLAH...A KARANTA DA HANKURI.....😆 Page 1: "Eamaan kin san ba wadda na ke so a fad'in duniyar nan da aure in ba ke ba, kema kuma na sani duk samarin da Allah ya azurta ki da su ba wanda kike so kike kulawa sai ni, to mai zai sa ki bari a raba mu?ki sani in bake ba zan iya rayuwa me dad'i ba, ba macen da zata zama madadin ki a waje na" Cike da qunar rai Anwar ke magana ya na kallon Eamaan da ke tsiyayar da hawaye saboda baqin cikin rabuwa da babban masoyin ta,a hankali cikin natsuwa ta bud'e baki ta ce , " Anwar kai ma ka san maganar iyaye tana sama da ta kowa ko? ba zai yu iyayena su ce ga abinda zan aikata ba ni kuma saboda son zuciya ta na qi aikata abinda suka umarce ni akai ba, kai ne kullum kake fada min yanda zan qara kyautata tsakanin mu'amalata dasu, me yasa yanzu kake son canjawa? ina kallon yanda kake yi ma iyayen ka biyayya,na tabbata da kai ne suka umarce ka da ka rabu da ni zakai hakan, me yasa ka me so ni na qi bin umarnin iyaye na? Ina zaton mun wuce wannan lokacin dani da kai, ka riga da ka sani kai nake so, duk duniya ma ta san hakan, kuma ba zan sake son kowa ba,na gama so a rayuwa ta, na gama mallaka maka soyayya ta, ba abinda yayi saura a rayuwa ta na soyayya da zan iya yi wa wani namijin, fatana kawai Allah yasa yanda nai karatun nan kar su tauye ni wajen yin aiki, domin yana ɗaya daga burina na rayuwa anan gaba," Eamaan ta qarasa zancenta tana share hawayen dake zuba mata masu zafi a fuskar ta, kallon ta Anwar yayi da girmama wa, sannan yayi mata fatan alkairi ya tafi, kuka suke sosai gaba ɗayan su, a haka ta shiga gidan ta faɗa gadon ta madaidaici da yake kusa da gadon yayar ta Hafsat, gaba ɗaya rayuwar gidan su take tinani, anya ba a qwarar su ita da mahaifiyar ta kuwa? sun taso suna masu son junan su tin yarinta ita da Anwar domin kuwa maqota ne su, iyayen su abokan juna ne, mahaifin Eamaan cikakken dan boko ne, mai ra'ayin kan shi, ba wanda ya isa ko da shawara a canja mai abinda yaso aikatawa, matan shi biyu,Kareema ita ce babba yaran ta biyu mata sun aurar da babbar mai suna Fa'iza,a nan cikin garin kano ga wani hamshaqin dan siyasa, sai ta biyun wato Hafsat ita kuma tana ci gaba da karatun ta a bangaren Law, Eaman d'iyar khadija ce,itace matar Alhaji Muhammad Kabeer ta biyu,mace ce mai biyayyar aure,halayyar su ta sha banban da uwar gidan ta dan kuwa ita Kareema bata yarda a na bata umarni ba sam, sai dai in ma za a bata umarnin to fa ya zama ba zai takura ta da yaran ta ba, saba'nin Khadeeja wadda ko me za a ce tayi indai bai zama haramun ba ko zai tauye haqqin ta da na d'iyar ta tilo to fa zata yarda. Hakane ke shirin faruwa yanzun ma a gidan na su Eamaan ,domin kuwa duk dad'ewar Anwar da Eamaan a soyayyan gashi Daddyn ta na neman raba su, sakamakon wani ra'ayin shi na son zuciya, domin kuwa wanda yake son bawa Eamaan sa'an shi ne mai shekaru kusan 55, a duniya, ita kuma ba zata wuce shekara 24 ba, a cikin wannan shekarar ta gama school of nursing ta fita a matsayin midwife, ba qaramin son aikin take yi ba, tayi wannan karatun ne dan taimakawa mata 'yan uwan ta, bata son taji labarin maza ko arna ke karb'ar haihuwa a asibiti,ranta na matuqar baci da hakan, tin a shekarar da zata gama secondary school suka yanke shawara ita da qawar ta A'ishaa zasu yi karatu a b'angaren ungozomanci, sai gashi Allah ya cika masu burin su, ita A'ishaa har ta fara aiki a wani asibiti mai zaman kan shi a unguwar da ta yi aure, kuma da taimakon mijin ta hakan ya samu, Eamaan ta taya ta murna sosai, itama taiwa kan ta fatan samun hakan, amma da dikkan alamu ba zai samu ba, na farko dai mijin da zata aura ba yaro bane, da gani zai yi ra'ayi irin na mahaifin ta, na biyu kuma dan siyasa ne shima, tasan kuwa da wahala ya barta zuwa aiki, ajiyar zuciya ta yi ta kalli sama " Allah gare ka nake neman zaɓin alkairi ba son zuciya ta ba, na sani duk abinda ka zab'a min dai-dai ne, aslamtu nafsi ilaika ya rahman," Hawaye ne masu zafi ke gangara ta gefen idon ta, shigowa aka yi dakin sai tai saurin goge su ta zauna, tare da sakin murmushin yaqe "Me kike yi anan tin ɗazu banga alamar kin je kin ci abinci ba yau? ɗazu naga kin je parlorn baqi Anwar ya zo ne?" Mahaifiyar ta da take kira da Ammaah ce ta ke mata wannan tambayar, " Eh Ammaah ya zo kuma har ya tafi, na yi mai bayanin komai akan auren da Daddy ke son yi min," Ta qarasa maganar ta cike da kyab'e baki irin na mai son yin kuka, hannu mahaifiyar ta ta sa ta jawo ta jikin ta sosai, ta kwantar da ita a qirjin ta,ta na shafa kanta zuwa fuskar ta, " Shiiiii my baby kar ki sa ka damuwa a zuciyar ki har ki zo kina samun ciwo kina qaramar ki, damuwa ba taki bace bayan kin san dama ba ke kika halicci kan ki ba ba kuma ke kika haifi kan ki ba,kina da iyaye kina da wanda zaki bautawa ya baki lada, dan haka in kika bi iyayen ki sai wanda zaki bautawa wato Allah ya baki lada mara yankewa, ko kina son saɓawa iyayen ki ki shiga fushin Allah?" Girgiza mata kai Eamaan ta yi alamar A'a, " Yauwa yarinyar kirki ki zama mai BIYAYYAH ga iyayen ki zaki zamo mai riba a rayuwar ki, beside Alhaji Abdullahi mai Nasara yana son ki, ba zai bar duk wani abu ya cutar da ke ba, matan shi ne kawai da mahaifiyar shi a gidan,suma kuma in kika zama good girl ba zasu zama matsala a gare ki ba kinji?" D'aga kai ta yi kawai,amma tasan Ammaahn ta na magana ne dan ta kwantar mata da hankali, sarai ta san gidan Alhaji Abdullahi, ba qaramin gidan da ake kwasar shokin tashin hankali bane, musamman da surukar su, ta tsufa tukuf amma sai rashin M, ga sa ido matan shi kuma kishin bala'i ne da su su biyu ne, Hajiya A'i itace babba ba ta da yara,saboda idan ta haihu komawa suke, sai Hajiya Rabi itace ta biyu, yaran ta qanana ne guda biyu dika mata, Ilham da Sabeerah, akan yaran nan sharrin ta ba qarami bane ga duk wanda ya masu kallon banza, amma in kaso su to fa zaku zauna lafiya da ita, wannan dalilin ne yasa ake dambace wa a gidan, dan kuwa Hajiya A'i bata son yaran nan sam, a cewar ta ma waya sani ko 'yan kwaroro ne, dan dai Hajiya Rabi akwai son zuwa unguwa, duk kullen Alhaji Abdullahi sai ta saci jiki ta fice, in tai sati bata fita ba to tabbas ya tsanan ta tsaro, in ko taje ta dawo sai Iya ta tona, daya gama fad'an da zai ya fita zata je ɓangaren Iya ta zazzage mata kwandon tijara. Miqewa Eamaan ta yi ta bi bayan Ammaahn ta domin cin abinci, a zaune ta tarar da Daddyn ta a parlour riqe da jarida ya na karantawa, ganin su ne ya Sanya shi cire gilashin idon shi ya nannade takardar ya ajiye gefe, cike da kulawa yake kallon su, nuni yayi mata da wajen zama a gefen shi, kafin ya yi magana ta bud'e baki ta ce, " Daddy na amince da zaɓin ka a gare ni, ina fatan ya zame mana alkairi gaba ɗayan mu," " Yauwa Mamana Allah ya albarkace ku ke da mahaifiyar ki, domin nasan akwai sa hannun ta a yardar ki,kinga wadancan 'yanneman masu kama da mutane dana roqi alfarmar ai qi suka yi, wai za a tauye mata karatun ta waye-waye, to taje ta auri biro ma qarewar karatu, nan da wata ɗaya za ai komai a gama, game da Anwar kuma kar ki damu, nama mahaifin shi bayani ya kuma gamsu, shima yaron mun yi magana dashi d'azu bayan kun gama, na kwantar masa da hankali ya kuma fahimce ni, duk da cewar yana cikin damuwa, Allah yayi muku albarka ya baku ladan BIYAYYAH," Murmushin yaqe ta yi masa tare da faɗin, "Ameen Daddyna," Miqewa ta yi ta shige d'akinta ta kwanta ta manta da Wani maganar cin abinci, haka hawaye suka dinga zuba daga idanun ta wani na korar wani a hankali take fitar da shassheqar kuka, kamar saukar aradu ta ji maganar 'yar uwar ta Hafsat a saman Kanta ta na fad'in, " ke kika sani wai ke me BIYAYYAH  zaki kai kan ki inda zaki wahala,na farko ma dai ba zaki more rayuwar aure ba, dan wannan tsohon bana jin zai ita tab'uka maki komai, na biyu kuma matan shi kaɗai jarabar su ta ishe ki, sannan ga mahaifiyar shi da qanin shi, dan ma dai qanin zuwa yake yi ya tafi, ke wahalar gidan bata qirguwa ko da girkin su aka bar ki kin wahala, ni ba zan taɓa yarda a min wannann aiki ba a tauye ni, kuma keda cika burin ki na aiki sai in wa'adin wannan tsohon ne ya cika kika gama takaba kin yi aikin inda rabon ki," Toshe kunnuwan ta Eamaan ta yi bayan Yayar ta ta ta gama zayyana mata abin da ta riga ta sani, kuka take yi sosai ga soyayyar Anwar da take jin kamar qara mata ita ake a zuciyar ta, ina zata sa kanta, " Ya Allah ka kawon komai da sauqi," " Ameen" shine abinda Hafsat ta faɗa cike da tausayin qanwar ta ta,da tana da iko da ta hana wannan auren, Yayar su ma auren ɗan siyasa ta yi, amma ita ta nace kuma shima abokin Abban su ne, fatan ta Allah karya qaddara mata irin wannan auren na 'yan siyasa, ita tafi son auren da zata sakata ta wala, ba wani surutai na masu mulki a cikin shi,juyawa tai ta kwanta tare da dora pillo a kanta, dan ba zata iya hana qanwar ta koka takaicin dake ran ta ba, Kuma ba za ta iya jure sauraron kukan nata ba. A cikin wannan satikan gaba ɗaya duk wanda ya san Eamaan sai ya tausaya mata domin kuwa tayi rama sosai,Eamaan yarinyace mai cikar halitta, ta na da cikar qirji da mazaunai fatar ta gogaggiya ce irin ta matan da ke kula da Kan su, Eamaan kuwa haka Allah ya yi mata tata fatar me sulbi da sheqi, ta na da duk Wani abu da za a gani a Kira ta da Mai kyau,Eamaan ta haɗu sosai, ga ilimi both western education and islamic education, dan saukar qur'anin da ta yi ma haddane, kusan dik littafin addinin da akai masu ta shanye shi akan ta, Alhaji Abdullahi yana son ta ne saboda kyawun ta, ba qaramin manemin matan tsiya bane, in ya shallake ya fita Abuja, sai sanda ya ga dama ya shigo gari, sarai Daddyn ta ya san hakan dan tin kafin zancen auren su shi ke ma Alhajin faɗa akan wannan mummunar dabi'a tashi, zancen auren su ya samo asali ne ta dalilin alqawari da Alhaji Abdullahi ya yi na in Daddyn Eamaan ya aura masa ita ko Hafsat ba zai sake neman matan banza ba, jin haka Daddyn ya ce zai aura mai Hafsat, amma ita da Maman ta suka qeqasa qasa suka ce sam ba da su ba gad'a a kushewa, kar Allah ya sa ya daina neman matan, hakura ya yi da maganar ta bangaren su, ya nemi alfarma wajen Ammaah, ita kuma ta tabbatar mai da ba komai, ai Eamaan mallakin shi ne, dan haka bazata taɓa hana shi iko da ita ba, wannan shine dalilin auren Eamaan da Alhaji Abdullahi........ *Wannan hadi anya zai haifar da d'a mai ido kuwa?* [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼 WRITTEN BY: HAERMEEBRAERH page 2: Hidimar biki ta kankama ka'in da na'in,komai da ya Kamata a sai wa amarya Kuma a Yi wa amarya an Yi wa Eamaan, tasha gyara wajen Ammaan ta sosai, gyara kuma bana wasa ba, duk wanda ya kalle ta sai ya qara,Ammaa  ta yi iya yin ta dan ganin Eamaan ta dawo da jikin ta amma abun ya faskara, dik da kuwa sanya mata abincin da  take a gaba ta tsare ta sai ta cinye, amma hakan bai taimaka da komai ba Eamaan na nan a rame saboda damuwa,ita dai  ga ta nan ne dai kawai, 'yan uwa da abokan arziqi sun hallara domin gudanar da shagulgulan bikin da aka tanadar, wasu da suka san ta da Anwar sun yi matuqar tausaya mata, amma ba mai jajantawa saboda yanda kullum take cikin kuka ko a fuska da ka kalle ta zaka ganta kamar mai shirin fasa ihu, haka take a Koda yaushe  cikin quncin zuciya, Hafsat kullum sai ta taushi zuciyar ta amma bata samun wani sauqi, se dai ta na samu ta kwanta a jikin Hafsat d'in da Ammaanta ta Yi ta kuka a jikin su. Daga lefen da aka kawo kowa yasan gidan da za a kaita ba na wasa bane, wasu a unguwa ma cewa suke yi Daddy ya saida ita ne ga ɗan siyasar, wasu suce kwad'ayi ne irin na masu kuɗin yanzu suna da shi ammasai sun qara saboda babu wadatar zuci, masu fahimta ne suka san qaddara ce ta sauka akan ta, kuma sukai mata fatan wanyewa lfy,( ko ina ruwan masu cece kuce ɗin oho).  An daura auren Eamaan da Alhaji Abdullahi a ranar laraba tabawa ranar samu,taron daurin auren da ya qunshi manyan mutanen qasar mu ta Nigeria, motoci kuwa a layin su Eamaan har rasa wajen tsaiwa suka dinga yi, Daddy kam bakin shi yaqi rufuwa dan murna yake da aurar da d'iyar shi ma  ɗan siyasa a karo na biyu. Da dare bayan an kammala  dinner lafiya,an ci an sha an yi watsi da nera, sai aka koma gida aka hau shirin kai amarya d'akin ta,da misalin 9:30pm aka gama shirya amarya dan kai ta d'akin ta,Eamaan dama tunda aka fara maganar auren take kuka, dan haka a yau sai kukan nata ya tsananta,amma babu wanda ya bi ta kan kukan ta haka aka sanya ta a luntsumemiyar motar da ango ya aiko ɗaukan ta aka nufi gidan ta da ita,sauran motocin masu rakiya na take musu baya. ' Yan kai amarya na gano baki sake suna kallon gidan da aka kai Eamaan kowa sai san barka yake yi saboda ganin kyau da tsaruwar gidan, qawayen Hafsat ne ke mata tsiya da cewar, "Babe yanzu da kin yarda da tini muna zuwa ganin wannan makeken gidan, muci arziqi mu bar shi inda yake," "Hhmm baku da hankali, itama fatan Allah ya kub'utar da ita daga sharrin dake tattare da wannan gidan nake yi," A haka kowa ya dinga watsewa ana ma amarya fatan alkairi, bangaren ta ya rage ba kowa sai ita kadai, kafin su tafi saida suka qara gyare mata gidan tass ko ina sai daukan ido yake yi, komai na gidan pink ne da ratsin fari, gidan ya mata kyau sosai,rufe idon ta ta yi wasu hawaye suka zubo mata, wannan rana sun dad'e suna tsara ta ita da Anwar, gashi zata yi ta a wani gidan, gidan da bata tab'a mafarkin aure a cikin shi ba, " Ya Allah na roqe ka dan kyawawan sunayen ka tsarkaka,Allah ka ciren damuwar komai a raina, ka bani iko da juriyar yiwa mijina biyayya da mahaifiyar shi, Allah ka bamu zaman lafiya da abokan zamana, sharrin dake tattare da cikin gidan nan Allah ka kare ni da shi, ka haɗa ni da alkairin dake cikin gidannan ya raheem," Fashewa ta yi da kukan da ya taso mata na kadaici, ji take duk duniyar ita ɗaya ce bata da kowa,tinda ta rasa Anwar to fa ta rasa kowa nata, Anwar shine kowa nata, tabbas rabuwa da masoyi akwai ciwo akwai azaba, gashi tana d'and'anar hakan, gani tai har sha ɗaya angon nata bai shigo ba,sai ta miqe taje ta yi wanka tai brush ta gyare gashin ta, sannan ta fito, dan kuwa tana fashin sallah shi yasa ta yi alwala kawai ba tare da ta yi sallah ba, zuwa ta yi ta tofe qofar shigowar da addu'a ta dawo d'akin ta ta zauna a bakin gadon ta,se ta yi addu'ar bacci ta shafe jikin ta ta ja abun rufa har zuwa qirjinta ta kwanta, bata jima da kwanciya ba kuwa bacci ya ɗauke ta irin mai daɗin nan, bacci ne mai cike da mafarkai barkatai wanda ba zata iya tantance su ba, cikin baccin taji ana shafa ta, firgigit ta miqe tana tsilla idanu kamar mara gaskiya, Alhaji ta gani cikin qananan kaya ya fitso tsaf da shi kamar be kai shekarun da aka faɗa mata ba, dan kuwa tsufannan ya boye a qananan kayan da ya sanya,sai sheqin angonci yake yi abun shi, komawa ta yi ta ja abun rufan jikin ta sosai dan ganin sai kallon ta yake yana had'iye yawu, duqar da Kanta tayi ta gaida shi ya amsa, kanta na nan a qasa bata qara cewa komai ba tana jiran taji daga gare shi, ledar dake hannun shi ya miqa mata yace taci kan ta kwanta, dan ya ga alamar bacci take ji,ya hakura sai Wani lokacin kuma. Sanar da ita ya Yi cewar sun yi magana da sauran matan a babban parlorn gidan za a taru in safiya ta yi, parlourn ya na ta can bangaren mahaifiyar shi ne,dan haka itama ta shirya tare za su je in safiya ta yi, d'aga masa kai tayi sannan ta furta, " Allah ya kaimu safiyar...mu kwana lafiya sai da safe" Takalman qafar sa taga ya cire ya d'ale gadon ya janye abin rufar ajikin ta ya kwanta ya rufuda shi shi kaɗai ba tare da ya kula da abinda ya yi ba, a hankali shima yace mata " Sai da safe," Zare ido ta yi a hankali ta furta, "Anan zaka kwana Daddy?" 'Did she just call me Daddy? Oh my God noo,' Alhaji Abdullahi ya ayyana hakan a cikin zuciyar shi ya, tashi ya Yi ya juya ya d'an kalle ta sannan ya ce, "Me kika kira ni da shi?,"  A hankali ta furta, " Daddy," "No pls don't call me Daddy, i am ur husband not ur Daddy, call me with any sweet name.... like honey, sweetheart, baby and so on," Sake zare ido ta yi ta kame baki tana mamakin wannan tsoho mai budurwar zuciya, dan haka d'aga masa kai kawai ta yi, dan bata son komai ya yi nisa a tsakanin su, ledar dake hannun ta ya Karb'a ya jawo ta jikin shi ya zaunar zumbur ta yi ta miqe ya hannu ya sake maida ita jikin shi yace, " Ammaan ki da Daddyn ki basu ce maki banda yima miji musu ko gardama ba?" D'aga masa kai tayi, alamar sun fada mata banda yi wa miji gardama,sai Alhaji yace da Eamaan, "Oya zauna na baki abinci naji qarar da cikin ki ke yi irin na masu jin yunwa, ni gidana bana son ana zama da yunwa kin gane?," Sake  d'aga kai ta yi bakin ta na rawa jikin ta ma nayi, a baki ya dinga bata kazar tana ci da kyar a haka ya ciyar da ita ta qoshi ya bata fresh milk, sannan ta miqe taje ta yi brush ta dawo, shima hannun shi ya wanko ya koma gado ya kwanta, can qarshe taje ta takure saboda bata yi zaton zai kwana anan ba duba da cewa akwai wasu d'akunan a sashen nata, murmushi ya yi daya ga tayi haka, sai ya hau gadon ya jawo ta jikin shi yace, "Ba abinda zan yi miki bacci zamu yi,dan d'azu dana d'auke ki sai naji alamar baki sallah ko?" D'aga kai ta yi da sauri, dariya yayi mara sauti yace, " To yanzu yaushe zaki gama?"   Nuni ta mai da hannu alamar kwana biyar, " OK ba damuwa Allah ya kaimu, mu yi bacci kenan yanzu ba? naga kin gaji kema," Nan ma d'aga masa kai ta yi kawai, gani ta yi kawai ya rufe ido zai bacci ba addu'a ,se ta miqe ta fara addu'a a tafin hannun ta, tana gamawa ta fara shafawa, binta ya yi da kallon sha'awa dan gaba daya yanda take shafawar ya tafi da shi, ita kuma sam bada niyyar tada Masa sha'awa take yi ba, "Ni ma ko zaki min addu'ar ne," 'Daga masa kai ta Yi ta fara karantowa , tana gamawa ta hura masa iskar bakin ta, Cike da kasala ya ce " A'a ni kenan ba za a shafa min ba?" Kauda kai ta Yi cike da kunya ta koma makwancin da taiwa kan ta ta rufa, murmushi ya yi, ya matsa jikin ta ya ja ta na shi ya rungume ta yace, "Haka zamuna bacci bana son kina nisa dani kin ji ko?," D'aga kai ta yi cike da tsoro a ran ta sai wurga ido take yi kamar mara gaskiya, ga bacci tana ji gashi kuma ta kasa yi, hawaye ne ke zuba mata daga idanun ta zuwa kuncin ta, yana jin haka ya sake ta ya juya baya dan ya kula ya takura ta da yawa, yana juyawa ta sa pillo tsakanin su ta koma can qarshen gadon ta takure kanta, da jin haka sai Alhaji ya yi murmushi, a haka suka kwanta har bacci ya ɗauke su. Qarfe 3:30am nayi ta farka tai addu'ar tashi daga bacci, kallon shi ta yi ta ganshi shame-shame yana ta kwasar bacci,miqewa ta yi taje tai alwala ta fara karanta qur'ani da ka saboda mahaddaciya ce ita, daga qarshe ta kai kukan ta wajen Allah, lokacin sallar subh nayi ta kalle shi duk kiran sallar da ake a masallacin gidan bata ga ya motsa ba sam, sai da aka idar ne ma taga yai wani juyi tare da munshari ya qara jan bargo abun shi, tana so ta tada shi dan ya yi sallah amma tana tsoro, a haka tai shahada taje ta tada shi,ai kuwa haka ya juyo fuskar nan kamar jar wuta babu walwala a cikin ta,ita kuwa gata tsaye zulum a hijab, cikin wata iriyar murya yace mata, " Ko dayake ke baquwa ce a gidannan baki san qa'idoji na da dokoki na ba,amma idan ina bacci ba a tada ni daga yau ki sani kuma ki kiyaye," Juyawa zai ya kwanta yaji tace masa, " Wayyo ban sani ba ka yi hakuri inshaa Allahu zan kiyaye, wai dama na jiye maka tsoron fitar lokaci ne, tinda Allah yace azaba ta tabbata ga waɗanda basa sallah akan lokaci, naga in kai sallar zaka iya kwanciyar ka ka huta,amma tinda haka ne zan kiyaye daga yau," Duk bayanan da take yi masa sun dira a kunne da zuciyar shi, tsaki yaja ya miqe tsaye ya shige toilet,saida yai brush sannan ya yi alwala ya fito, Sallah ya tada ya burbura ta ya sallame ya haye gado ya koma baccin shi, mamaki ne fal cikin ta, dama haka masu kuɗi suke ko dai shi ke hakan? Kafin ya tashi da safe ta yi wanka gudu-gudu sauri -sauri a ɗayan d'akin, dan bata son ya tadda ita tana wanka, tana gamawa sai ta sanya sabbin kayan da ta tafi da su d'akin, ta yi kwalliya sassauqa mai kyau, sannan ta koma d'akin nasu ,zaune ta tadda shi ya dafe kai yana murzawa a hankali,durqusawa ta yi ta gaida shi, ya amsa cikin ɗan sakin fuska, kallo ya bita da shi kamar zau had'iye ta, dan kuwa ba qaramin sha'awar yarinyar yake ba, dalilin da ya sa ya aure ta kenan, ba wai dan yana son ta ba, a hankali ya miqe ya shiga toilet yana saqa abubuwa da dama akan ta, wanka shima ya yi ya shirya sannan ya kama hannun ta suka fita dan zuwa sashen mahaifiyar shi, tana ganin sunyi hanyar waje tace, "Bari na d'akko hijab," kallo ya bita da shi, sannan yace "A cikin gidan ma sai kin saka hijab?" "Dama naga kamar sai munbi ta wajen masu aiki ne, kar na haɗu da wani daga cikin masu aikin ba mayafi jikina kuma shi yasa," kad'a kai ya yi ya jingine yana jiran ta, koda ta dawo sai ya bita da kallo,dan kuwa da ta saka hijab din ma ba qaramin kyau yaga ta qara yiba a idon shi, "Lallai Eamaan komai naki mai kyau ne," Murmushi ta yi tace Masa " Na gode," Hajiya A'i dake tsaye jikin window ce ta hango su suna murmushi sai taji zuciyar ta kamar ta fito waje saboda kishi, "Dubi dan Allah dan tsabar ya siya  mana raini ya rasa wadda zai auro sai d'iyar cikin mu,hmmm ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, dan wannan irin su auren kuɗi ke kawo su, Allah ka azurtani da tsayyen d'an da nima za a dama da ni a cikin gidan nan," Sakin labulen ta yi taje d'aki ta saka d'ankwali, dan ita ba mace ce mai son d'aura d'ankwali ba a koda yaushe,tana gamawa sai ta fito tana takun qasaita, a babban parlour ta tadda Hajiya Rabi da yaran ta Sabeerah da Ilham suna ta shagwab'a a jikin Daddyn su, Eamaan ce ta shafa kan Ilham tace, "Meye sunan ki?" Tana mata murmushin dake nuna tsananin shiga ranta da yaran suka yi,Ilham tace, " Suna na Ilham, amma Sabeerah na kirana da Elly, ni kuma ina kiran ta Saby," murmushi ta yi tace, "Oh kenan wannan itace Sabeerah? Can i call u saby ?" " Yeh u can, and let me tell you u a scret," Sai ta kai bakin ta dai-dai kunnen Eamaan tace mata, " I like u, don't tell anyone," D'aga mata kai Eamaan ta yi cike da jin dariya,itama ta kai bakin ta kunnen Sabeeran tace mata, "I like u too, u ar beautiful Maa shaa Allah," wani fari ta yi sosai tai tsallen murna, Daddyn su da Hajiya Rabi ba qaramin burge su Eamaan tai ba, Ilham ce ta b'ata rai,Eamaan na ganin haka sai ta kama hannun ta tace, " Elly me ya faru," "Ba ku bane kuke gulmata," Daddyn ne ya fara dariya sannan Hajiya Rabi, "Ba qulmar ki muka yi ba zo kiji wata magana kema," sanar da ita tai itama tana son ta, yaran sukai ta murna, suka rungume ta . " Mtsssss aikin banza da asubar fari za a cika ma na kunnuwa, sai kace ku kad'ai ne yara a unguwar nan," "A'a fa Hajiya Babba, ba zai yu kawai ke baki so yarana ba Allah ya kawo mai son su kuma suma suna son ta ki zo ki kina qananan maganganun da kika saba, " Habaaa ai akamar Jira Hajiya Babba take yi sai suka kacame da zage-zage sukai ta faɗa da junan su,nan da nan idon Eamaan ya kawo hawaye dan kuwa ita bata saba ganin wannan ba a gidan su, dik da cewa kuwa itama gidan su mata biyu ne. "To kaji kun fara ko? kut kut kut kut, ga hatsi to kuzo ku tsattsaga, jarababbu, baku da aiki sai jaraba akan miji da 'ya'ya, ke wani ya hana ki yi  cikin ki haifi naki? Ke kuma da kike jaraba akan yara naga dai yaran ba naki bane ke ɗaya, da anyi magana sai iko akan yara, wannan kuma yar afiruwar wace ce ita take zaune kuturinta dana Audu waje  d'aya?" Hajiya Iya kenan wato mahaifiyar Alhaji Abdullahi ke wannan maganganun tana kanne idanu tana nuni da yatsun ta da suka sha jan lalle irin na tsofaffi....... *Iya jaraba kamar yanda Su Saby ke kiran ta ta fito fa*😱 [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼   RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH Page 3: Cike da ladabi Eamaan ta zube a gaban Iya sannan ta ce, " Barka da safiya Iya," Cikin isa da ɗauke kai ta amsa da, " Lafiya ! baku ban amsa ta ba ai kan a kai ga gaishe-gaishen," Alhaji ne ya duqar da kai cike da biyayya yace, " Iya amarya ta ce mai suna Eamaan, jiya ban shigo gida ba sai wajen 12am, shiyasa ban kawo maku ita ba ta gaishe ku,sannan nayi zaton ko dangin ta da suka kawo ta jiya sun kawo maki ita ta gaishe ki," " Eh sun kai ta, amma ai a qunshe ta ke waya gan ta? Miqe ka zauna abun ka," Miqewa yayi ya zauna kowa ya yi shiru,amma Hajiya A'i da Hajiya Rabi sai harare-hararen juna suke yi, Ilham ce ta gaida kakar tasu, cike da fara'a ta amsa mata, sannan Sabeerah ta gaida ta itama, amsawa tai sannan tace, "Shin yau babu mai bamu abinci ne a gidan sai mun roqa?" Kallon kallo suka fara yi a tsakanin su domin kowaccen su tana qyashin ace ita ce zatai directing masu aiki suyi girki bayan mijin na wajen amaryar shi, Hajiya Qarama ce wato Hajiya Rabi ta miqe ta fice hanyar da zata sada mutum da kitchen ɗin gidan,ma'aikata sun yi abinci kala-kala suna jira a kitchen ɗin suna zazzaune suna jiran me zai je ya zo tinda ba a basu umarnin kaiwa ba, tsoron masifar Iya kuma ya sa sun kasa yi wa kowa magana, a tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru ta iske su, dan kusan suna jiyo tashin muryar ta koda basu fahimtar komai sin san masifar take saukewa, umarnin kawo abubuwan da suka dafa ta yi masu, suka ko biyo bayan ta da abincin kala-kala suka ajiye suka yi waje, a qaton carpet d'in  da suke haɗuwa kowa yaci abincin  suka baje, dan Iya bata son hawa dining table,dan haka dole kowa nan qaa zai zube in dai tare za a ci da ita, kowa na zaune yana kwasar girki banzda Eamaan, jita take yi duk a takure,saboda bata saba da su ba,Iyace ta kalle ta a yatsine cikin masifa tace, " Malama idan za kici abinci ki kama ki ci,kina wani sunne kai kamar ta kwarai," Cike da jin tsoron Iya ta fara cin abincin, Alhaji kuma sai ya ji tausayin ta ya kama shi saboda ba haka ya san jikin ta ba duk ta rame, sai ya ji kamar ya bata a baki, gaba ɗaya ya kula a tsorace take da Iyan tashi, a haka aka ci aka gama, kowa ya tashi ya nufi sashen shi masu aiki suka ɗauke komai suka gyara wajen. A hanyar su ta komawa sashen nata ne Alhaji ya kula da damuwar da ke tattare da Eamaan din, kafin ya gama nazarin ta ya ji ta na yi masa tambaya cike da damuwa. " Alhaji kullum a babban parlor zamu dinga cin abinci?" " A'a na yau ne kawai dama ina so ne na haɗa ki da sauran abokan zaman ki ku ga juna, to na zata Iya zata yi mana nasiha ne, amma na ga yau faɗan ta kamar yafi na kullum zan je na ji me ke damun ta yau ɗin, sannan kuma zamu haɗu a bangaren Hajiya Babba mu yi magana zuwa Wani lokacin," D'aga masa kai ta yi alamar gamsuwa da bayanan shi ,dan kuwa bata fatan sake zuwa wajen wannan tsohuwa mai faɗan tsiya. Suna shiga d'aki ta cire hijabin ta ta ninke shi ta zauna waje d'aya a gefen gadon ta, kallo ya bita da shi yaga kamar har wannan lokacin a tsorace take, jan ta ya yi jikin shi ya fara lallashin ta,yanayin yanda yake yi mata ne ya sanya ta mamakin shi, da alama dai Alhaji baya tunawa da shekarun shi idan yana wasu abubuwan, luf ta yi a jikin shi tana zubar da hawaye a hankali dan bata son ya gane kuka take yi,sai kawai ta ja baya ta gyara kwanciyar ta kamar wadda ke yin bacci, murmushi ya yi dan a zaton shi wasannin da yayi mata ne suka sa mata kasala har ta yi bacci, miqewa ya yi yaje ya yi wanka ya fito tare da sanya kaya masu kyau, sannan ya dauki key na motar shi ya fice ya bar gidan dan zuwa wajen shaqatawar shi, wanda da fari ya zaci zai iya hakuri da ci gaba da neman matan banza, amma zuwan Eamaan da lamarin da ta zo da shi na baƙon wata na mata ba zai iya jurewa har ya jira ta gama ba,tana kallon shi ya gama duk abinda zai yi amma bata motsa ba, sai da ya fita ne taje ta rufe qofar ta jingina da murfin qofar ta hau kuka da qarfi, tabbas bata qaunar bawan Allah'n nan, gaba daya ba sa'an yin rayuwar auren ta bane, a ganin ta ko da cikin tsarki take yazo mata ai ganin shi zata yi kamar Daddyn ta, babban mutum haka ya dinga sauke buqatar shi akan ta da qananun shekarun ta? kaiii akwai takura sosai da jin nauyi gaskiya. A haka tana kuka taje toilet dan ta gyara jikin ta, yatsina fuska ta yi ta cire rigar ta ta aje ta a cikin washing machine ta kunna ya shiga wankewa, saida ta gama wanka sannan ta fita ta shirya cikin shadda mai matuqar kyau kalar purple aikin jiki an yi shi da pink ɗin zare,ba qaramin kyau ta yi ba a cikin kayan,tirare gidan tai da tiraran wuta, sannann ta samu waje ta hau rera karatun qur'ani idanun ta lumshe, ta windown parlourn taji kamar ana motsi, aikuwa sai ta miqe a tsorace sannan bata daina karatun da take yi ba, tana leqawa bayan ta kai qarshen aya ta ce "Waye a nan," Juyawa su ka yi za su gudu, a dai-dai lokacin Eamaan ta leqa taga ashe yaran ne, ajiyar zuciya ta sauke da qarfi sannan ta kira su ciki, a hankali suka je kamar masu jin tsoron ta, buɗe masu qoqafar ta yi suka shiga ciki suka tsaya suna jiran su ji ko zata yi musu faɗa. Ba tare da sun san cewa Eamaan taji dad'in zuwan su ba suka hau bata hakuri,ita kuwa murmushi tayi dan dama a cikin kaɗaici take, nan da nan ta rungume su ta hau yi musu wasa har suka saki jikin su da ita. Kafin minti goma sun sake da ita sosai sai wasa suke yi abun su, kan su ta kalla taga gaba ɗaya ya tsufa har tsagar ta haɗe waje ɗaya baka banbancewa tsakanin kitso da tsaga,ga gashi har gashi amma duk a cukurkude yake, kayan su ta cire masu ta wanke masu kan su tass, ta samu bands ɗin ta da take amfani da shi ta gyara masu kan bayan ta yi drying gashin ta yi oiling ɗin shi yana sheqi,kan su ya yi matuqar yin kyau sai sheqi yake yi, cike da murna suka kwasa suka yi wajen maman su dan su nuna mata,a lokacin kuwa Iya tana wajen tana zazzaga mata masifa akan ita zata kula da abinci har Alhaji ya gama angwanci ya raba masu kwana, ranta a haɗe sai qunquni take yi suka shiga,Iya ce tace, "In kika zagen kin zagi ta gida 'yar nema kawai masu abun kunya, gaku nan rid'a-rid'an mata amma kuna zaune miji na neman matan banza a waje, ga shinan ai kun ja an kawo maku yar cikin ku se ku zauna ku yi ta goga kishin da ita," " A'a fa Iya kar ki ɗora mana laifin da ba namu ba ah toh,neman matan shi ba laifin mu bane tinda ba mu muka haife shi ba balle mu bashi tarbiyya," Ta fada tana murguda baki, " Iyyee to me kike nufi tijararriya? Wato ni ce ban bashi tarbiyya ba ko? To a cikin tarbiyyar dana ba shi ne lokacin har ake cewa na yi mai auren wuri, ganin yana bin matan kar ya lalace da yawa ne ya sa na yi masa auren, amma aka kawo ku aka zuba gaku nan kun zama kamar hoto a gidan, shashashai kawai, ita waccan ta yi wani d'irim da ita da anyi magana ta ce ita tayi ta gaji ba zata kashe kan ta ba, amma ai bata gaji da tatse masa arziqi ba ko? Ke kuma da na ke gani a waye kike ashe kallon kitse nake wa ro,......"  Yaran ne suka gaji da jin faɗan da ba gane inda aka dosa suke yi ba suka katse iya da faɗin, "Mum kin ga kan mu," cike da murna suka haɗa baki suka fada, " Wow kun yi kyau,waya kai ku saloon ba a faɗan ba na bada kud'in gyarn kai?" "Mum ba saloon bane ba fa, Aunty Eamaan ce ta yi mana," Tin daga wannan lokacin Eamaan ta samu matsayi a zuciyar Hajiya Rabi, amma a wajen Iya kuwa cewa ta yi na neman gindin zama ne, sam ba a yi mata gwaninta ita, ko kwanta mata za ka yi tabi ta kai ta wuce sai ta kushe maka. A haka Eamaan ta yi kwana shidda a gidan, a cikin waɗannan kwanaki Eamaan ta ga halayen mutanen gidan kala-kala, yau ne kwana na bakwai da kawo ta wanda daga shine Alhaji zai tattara ya tafi wajen Uwargida wato Hajiya Babbah. Idar da sallahr ta  kenan ta cire doguwar riga da hijab ɗin ta na sallah tana ninkewa sai ta mayar inda take ajiye su, ta dauki qur'anin ta da littafin addu'o'in ta tana dubawa,daga qarshe sai ta d'akko wayarta ta kunna data suka hau chatting da Aunty Fa'iza dake qasar waje, sunje shaqatawa ne da Alhajin ta,shawarwarin yanda zata zauna da mijin ta da surukar ta har da kishiyoyin ta lafiya take ta bata, hakan kuwa yasanya mata mutuwar jiki sosai ashe aiki ne babba a gaban ta bata sani ba wanda take ganin anya zata iya kuwa? In ko haka za ta yi ba qaramar wuya zata sha ba kenan a gidan? Suna cikin hira taji shigowar shi gidan ,a ranta ta qudiri niyyar yin dukkan abubuwan da Auntyn ta ta faɗa mata dan samun zaman lafiyar zuciyar ta da gangar jikin ta ko da ran ta baya son Alhajin, wannan dalilin ne yasa ta miqe duk da dukan da zuciyar ta ke yi ta je gare shi dan tarbon shi, amsar kayan hannun shi ta yi,wanda ta kula kitchen ya Kamata ta yi da su dika,godiya ta yi masa tare da sannu da zuwa,shi kuwa cikin kashe murya kamar ba dattijo ba yace, " Godiyar me kike yi min daga dawowa ta kuma? Ki jira mana anjima idan na yi maki babbar kyauta kin yi min godiyar ko?" Murmushi ta yi kawai ta wuce dan ba ta gane abinda yake nufi ba, tana tafe take faɗin, " Ai dole mace ta zama mai yiwa mijin ta godiya a kullum ko dan saka ta a cikin sutura da killace ta da yayi ya bata wajen kwana, balle kuma ya bata abinda zata ci ta sha ina ga ya gama mata komai," Murmusawa ya yi har saida haqoran shi suka bayyana, lallai yarinyar nan ta tarbiyyantu wajen iyayen ta, " Ba komai Eamaan dolena ne biya maki dukkan buqatun ki, indai ina da hali da iko," Godiyar ta sake yi mai da fatan Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin ta da matan shi, kitchen taje ta cire komai ta mai mahallin da ya dace sannan ta fito,zaune ta gan shi a saman kijera sai ta duqa ta cire masa takalmi da safa, Alhaji kuwa sai ya bi qirjin ta da kallo, wani yawu ya hadiya, hula da agogon shi ta cire ta yi d'aki ta ajiye ta dawo. Kitchen taje ta d'ebo masa drinks data haɗa da kanta na pineapple da ginger da lemon, sai flavor da sugar data saka dan d'and'ano, yana sha ya lumshe idanun sa saboda yanda  dad'in abun ke ratsa shi ,nan da nan kuwa ya shanye,ita kuwa sai ta qara masa wani, ya qara shanyewa, cikin dakewa da fad'uwar gaba ta fara qoqarin gwada abinda Auntyn ta ta koya mata, " Sweet kar ka sha ka kasa cin komai,na yi girki me dad'i saboda kai gashi can ajiye a saman dining table kai kaɗai yake jira" Sai da ya kusa k'warewa saboda yanda ya ji kalmar Sweet a bakin ta babu zato babu tsammani, tabbas a kunyace take itama amma tana son ta gwada abubuwan da aka koya mata,domin ba zata manta dalilin da ya sa aka aura mata shi ba dan haka zata yi iya bakin qoqarin ta dan ganin ta samu wannan ladan na tsamo shi daga halakar da ya jefa kan shi ciki ta neman matan banza, cike da jin daɗin maganar ta ya ajiye glass cup d'in ya fuskance ta yace, " Eamaan me kika kirani da shi? Please kirani da sunan again,i want to hear it from your beautiful voice," Murmushi ta yi cike da jin kunya ta rufe fuskar ta, hakan da ta yi sai ya qara jefa shi cikin qaunar ta,murmushin ta kaɗai ya tashi kanshi ya jefa shi a wani hali, cike da jin kunya ta sake maimaitawa tace, " Cewa na yi Sweet kar ka sha ka cika cikin ka..." Wata dariya Alhaji ya b'arke da ita ta Jin dad'i, a kunyace ta miqe tana tafiya ta daukar magana ta wuce dining table,tabbas ta san ta tarowa kan ta babban aiki ,amma ba damuwa indai kwalliya zata biya kud'in sabulu akan BIYAYYAHr iyaye ba abinda ba za tai ba se dai idan abun ya sab'awa Allah ne dole zata guje shi, abincin taje ta d'akko ta jere a gaban shi, sannan ta d'akko qaramin carpet ta shimfid'a,dan ta kula a gidan sun fi son cin abinci a qasa, tana bud'ewa Alhaji ya yi karo da alkubus ɗin flour da ta haɗa da alkama tayi masa miyar gyad'a wadda ta sha naman qaramar dabba, yaji kayan qamshi ba kadan ba sai tashin qamshi miyar take yi, gefe kuma ga kunun aya mai had'in dabino, kayan qamshi, da sugar sai zuma kaɗan da ta saka dan ya qara gard'i a baki da amfani a jiki, gefe kuma farfesun kan rago ne, daya umarci ayi mishi kan ya fita,baje ciki ya yi ya kwashi girkin nan da kyau,dan kuwa tin da ya fara ci ya kasa yin magana, tinani yake yi wannan girkin ko a hotels ɗin da ya sha zuwa Abuja da sauran wuraren 'yan gayu bai taɓa cin irin shi ba, wa yayi girkin nan ne? Daɗi da santi ya sanya ya kasa tambaya, zurawa kawai yake yi, ganin ya ci har ya wuce geji ne yasa ta saka hannu ta riqe hannun shi tace, " Ka yi hakuri ka bar abincin nan haka,in  ka ci da yawa ka qoshi bacci zai gagare ka mai dad'i yau ,ka San Annabi ya ce a raba ciki gida uku, Ɗaya na abincin, Ɗaya na ruwa, Ɗaya kuma na iska, da alama ka cika dika gurbin baka bar komai ba," Cike da jin daɗin kalaman ta masu yanga a ciki ya tashi tsaye bayan ya wanke hannu a robar data zubo ruwan wanke hannun, "A gaskiya duk wadda tai girkin nan sai na bata kyauta mai tsoka,sai abinda ta zaba zan bata," Murmushi ta yi tace, "Ni ce na dafa da kaina dan faranta maka,kuma albarkar ka kawai nake nema bana son komai bayan haka" "In dai albarka ta ki ke nema kin samu, Allah ya albarkace ki, ya baki abinda kike so duniya da lahira," Jin hakan da ya fad'a sai da gaban ta ya faɗi dan kuwa Anwar ne zaɓin ran ta, shine abun son ta, yana yi mata wannan addu'ar shi ne ya gilma a idanun ta, dakewa ta yi ta miqe ta shige kitchen da kayyakin da ta kwashe bayan ya gama, zuciyar ta na saqa mata abubuwa da dama, tabbas bata jin son shi a ranta, a can cikin qasan ran ta a akwai Wanda take so, amma ba amfanin riqo da wannan soyayyar har ta b'ata rayuwar da Allah ne kad'ai ya San qarshen ta,dole ne ta yi hakuri, dole ne ta Yi BIYAYYAH, dole ne ta danne komai ta binne shi a qasan ran nata, dan ta samu farin ciki a gidan auren ta,takun da take yi ne dan zuwa d'aki ya sanya Alhaji Abdullah bin bayan ta ba tare da ya San ma ya na biye da itan ba........ Anya kuwa wannan BIYAYYAHr taki zata haifar maki da d'a mai ido kuwa Eamaan sai na ji ra'ayoyin ku makaranta? [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼   RUBUTAWA :HAERMEEBRAERH Page 4: Suna shiga ciki Eamaan taji alamar yana biye da ita a baya, nan take zuciyarta kama rawa tana tsalle dan tsoro kamar zata fito waje,duk da cewa tasan yau ta ta qare, hawaye taji na son zubo mata amma ta yi saurin maida shi ciki, yaqe ta yi ta juyo shi kuma ya yi mata murmushi,juyawa ta yi da nufin shiga bathroom,hannun ta ya kama ya na bin ta da kallon tuhumar Ina zata je? Cikin yaqe dan kuwa murmushin be kai har zuci ba tace masa, "Ruwa zan ɗan watsa, yanzun nan zan fito" A qa'ida yanzu kam ai ba wani wanka da ze yi shi kam kawai baccin shi zai yi, amma da alama Shima yau ze gwada yin wankan daren, kafin ya gama tinanin da ya ke yi ya ji rufe qofar ta, fad'awa ta yi ciki da sauri ta rufe gam ta fara wanka, tana gamawa ta yi brush tai alwala, samun brush din shi ta yi ta saka masa toothpast a jiki ta ajiye sannan ta fito, ta yi masa nuni da toilet din tana murmushi mai cike da jin nauyin sa, shima cire kaya ya yi a gaban ta ko kunya baya ji, Eamaan kuwa da sauri ta ɗauke idon ta ta kalli gefe, cikin ranta tace, 'shifa wannan tsohon sam naga kamar bai san kunya ba, ko dan yaga ina mai haka ne? Shi bai san daurewa nake yi bane? Haka kawai yau yanda ya wuni baya gida zan barshi ya hau min gado ba wanka,ai bazan iya bacci ba,gashi ya ci abinci kuma be yi brush ba zai kwanta,aiko yau dana shiga uku in yayi min irin abun d'azu da safe kafin ya fita,amai zan yi na tabbata' Tana maganar zuci take gyara jikin ta,wata rigar bacci ta saka mai ɗan kauri kuma ba wata mai nuna jiki ba, amma duk da haka ta yi mata kyau,rigar fara ce sol, sai ta hannu da wuyan ne aka yi musu ratsin blue me haske, zani ta daura a saman kayan ta ɗora hijab, ta shimfid'a masu sallaya ta zauna zaman jiran shi, sai tashin qamshi take yi, yana fitowa ya gan ta a zaune a sallaya sai ya kauda kai, ya shirya cikin kayan bacci riga da wando kalar fari shima, kallon ta ya sake yi yaga abun salla biyu ta shimfid'a, sai yace mata, "Me zaki yi ne na gan ki anan a zaune? daman baki yi salla bane?" Kad'a ido ta yi ta kifkifta su sannan tace, " A'a na zaci zaka ce muyi nafila ne irin na sabon aure da na ji ana yi tinda na ga ba mu yi  ba mu,bana son sai ka fito ne sannan kace na shinfida abun sallah, nafi son na dinga yin abu mai kyau kafin ka bada umarnin yin shi," shi dai bai ce komai ba ya nufi inda take zaune,amma shi bai san wata sallar sabon aure ba, abinda ya sani baya wuce kawai akai masa mata ya kwanta bacci ya biya buqata ya miqe shikenan, "To miqe muyi sallar raka'a nawa zamu yi babyn Alhaji?" Sanar da shi tayi komai tayi a lokaci ɗaya dan ta yi saving kanta da tambaye-tambayen da zai ta yi mata, sallar suka yi,bayan sun idar ne yayi mata addu'a yanda ta koyar da shi da Hausa,dan ta kula se su kwana be riqe larabcin ba,sannan suka miqe suka hau gado, kashe fitila za ta yi,yace sam bai san zance ba, tsoron duhu yake yi, dariya tayi ta masa yanda ya nuna da gaske tsoron duhun yake, dama tin da ta zo sai sun yi wannan dramar kashe fitilar da dare, komawa ta yi ta kwanta ya matsa ya dauke ta cak ya dora a jikin shi, daga haka Alhaji Audu ya sauya salon tsokanar da Eamaan ke yi masa...... Kafin ya gama abinda yake yi idon ta da zuciyar ta sun kumbura kamar su fashe ,ba dan komai ba sai dan kukan zahiri da badini da take yi, ga kunya da ke addabar zuciyar ta da wanne ido zata kalle shi da safe kuma? Mutumin nan fa sa'an Daddyn tane,amma ya zauna ya baje basirar shi a kan ta. wayyooo ina zata sa kanta da wannan lamari yau? Alhaji Audu kuwa lallashin ta yake tayi sosai, tare da mata alqawurran jin daɗin rayuwa kala-kala, shi a zaton shi kayan more rayuwa sune a gaban kowacce mace, bata ce masa komai ba, ta miqe da kyar ta yi bayi,ruwa mai d'umi ta shiga ta zauna,sai da ta ji jikin ta ya yi mata dai-dai sannan ta bari, tai wankan tsarki ta fito d'aure da alwala,lokacin qarfe 2 na dare ne, nawafil tai tayi tana kumawa, a sujjadar qarshe ta samu tai addu'a akan neman zaman lafiyar su, da roqon Allah ya bata jimirin yi mai biyayya,sannan ya yaye mata soyayyar Anwar a ranta ko za ta ji dad'in zaman gidan mijin ta, tana haka taji ya saki wani wawan minshari, addu'a ta ci gaba da yi ta na kuka a cikin sujjadar ta, ta sauke babban nauyin da Auntyn ta take ta mata nuni akai d'azu, ta tabbata a yanzu Anwar yayi mata nisa,dan haka dole ne ta yi hakuri ta rungumi mijin ta da auren ta tin kafin lokaci ya qure mata, Wani shiga damuwa da tashin hankali ba nata bane,a hankali ta miqe ta haye gado ta kwanta ta rintse ido da fatan bacci ya ɗauke ta dena jin rad'ad'in da zuciyar ta ke yi mata. Asubar fari ta tashi tai sallah amma Alhaji Abdullah yana nan kwance yana bacci, dabara ce ta faɗo mata a ran ta,wayar ta ta sa ta kunna karatu ta ajiye a gefen kan shi, karatun ne ya tada shi,nan take kuwa ya buɗe ido yana guntun tsaki, ita ya gani kusa da shi tana yi masa murmushi tare da sunne kai qasa alamar jin nauyin shi, nan da nan abinda ya faru a daren jiya ya bijiro wa ƙwaƙwalwar shi, shima murmushi ya saki wanda be shirya wa, a can qasan ranta kuwa tana jin haushin shi saboda barin ta da ya yi tayi jinyar kan ta, shi Kuma ya baza ciki da baki yana bacci, sake murmusawa ta yi ta sunne kai qasa sosai, cikin murya cike da shagwab'a tace, "My Sweet yau ma zaka makara sallah fa, ni bana son kowa na samun lada ana wuce mijina gaskiya," Sai juya baya irin na shagwab'ab'b'un nan, bacci ne fal idon shi amma baya Jin zai iya jure wannan salon nata, ga wata iriyar shagwab'a da juya jiki da take yi wanda be saba ganin hakan ba a wajen matan shi da sauran karuwan da yake mu'amala da su saboda ya gama yarda Eamaan ta daban ce a cikin mata, tashi ya yi bai kula ta ba ya shige bathroom ya yi  wanka sannan ya zo ya yi sallah,ko addu'a be tsaya yi ba  ya koma gado abin shi tare da Janta jikin shi dan su koma bacci,shafa fuskar ta ya yi a hankali sannan yace , "To na yi sallah lada be wuce mijin ki ba , mu koma bacci dan ni bacci nake ji," Ba tare da ta musa masa ba kuwa suka koma baccin su. Tin daga ranar Eamaan ta zama kwararriya wajen yi ma Alhaji wayo na sa shi yin duk wani abun da ba yayi a da musamman ta bangaren ibada, wajen wanka da brush ɗin dare dana asuba kuwa yanzu shi da kan shi in bai yiba ma zai ji ba daɗi, matan shi ma sun ga sauyi sosai a tattare da shi, Iya ma uwar sa ido sai da ta ga ɗan nata gaba ɗaya ya sauya, har masjid yana fita yanzu, amma taurin kai na tsohuwar nan ba abinda ke haɗa su kuma ya raba su da Eamaan sai zagi, da kyara,ita ko bata nuna mata wata alamar ta ji haushi dangane da yanda take mata a gidan, iyaka in ta mata abinda ya mata zafi sosai,sai ta dawo sashenta ta sha kukanta ta bawa Kan ta hakuri, sannan ta Kuma tina wa Kanta cewar dama zaman BIYAYYAH take yi a gidan ba zaman soyayya ba,Dan haka zata jure komai watarana sai labari. Babban abin da ke damun ta yanzu be wuce matsalar neman matan shi ba da ya dawo da shi, dan kuwa har yanzu bai dena ba, tana yawan ganin condom a kayan shi, rannan ma da yaje Abuja girki ya fad'o ta wajen ta used condom ta gani a aljihun sa na babbar riga,abun na matuqar bata mamaki wai shin wannan jaraba har ina, kuka take yi sosai in ta ga hakan, ace mata har uku amma ba zaka daina neman mata ba? ta qudurta indai ita mace ce da yardar Allah sai ya daina bin matan banza. A cikin wata na uku da auren su Eamaan bata taɓa zuwa gida ba dan ganin iyayen ta da ta yi kewa sosai, dan haka yau ta roqi Alhaji da ya barta taje ganin Ammaahn ta, kullum sai dai su yi waya ta gaji da hakurin rashin ganin mahaifiyar ta,Mama Kareema ma ta matsu ta gan ta tana son zuwa amma basa shiri yanzu da matan Alhaji shi yasa bata zo ba,sunce da munafurcin ta aka haɗa baki aka yi masu kishiya da d'iyar su, da kyar ya yarda dan Alhaji ba dai kulle ba. To fa dama kunsan mai aikata zina ko wani mugun hali, kullum tsoron shi kar nashi su fita ayi da su, bai san in dai kana yi ba sai an yi da naka komai kullen ka, sai dai in ka tuba ka bi Allah, Allah ya yafe maka ya kuma kare zuri'ar ka. Gaye tasha sosai na zuwa gida tana gamawa ta rufe wajen ta ta bi wajen Iya dan yi mata sallama, bayan ta gaida ta ne ta sanar da ita cewar Alhaji ya bata izinin zuwa gaida Ammaahn ta. "To in ya baki izini ni ban bayar ba ba zaki je ba,kina ganin ai gidana ya yi datti amma ba zaki taya a gyara ba, maza jeki d'akko kayan gyara ki gyara min sashe na dika, zan je wancan ɗan filin kan ki gama sabida qura," Sake baki Eamaan tayi idon ta fal hawaye tana kallon tsohuwar,tin da tazo ita fa ke gyara ma Iyan bangaren ta, ba kuma wanda ya saka ta, ita ta saka kanta da kanta,amma yau da zata je gida ace ba zata ba saboda mugunta?wata zuciyar na cewa ki ajiye mata kar ta share ta kwana a dattin, wata zuciyar kuma na cewa ki yi hakuri ki gama mata sai ki tafi,duk wanda ya girmama uwar wani za a girmama tashi, balle ma wannan kaka ce a wajen ki ba iyawar zatai ba kiyi ki samu lada, umarnin ta kamar na Ammaahn ki ne, dan kuwa uwar miji itama uwa ce, "Zaman me kike yi har yanzu baki tashi daga gaba na ba? Ko amsa kike ban akan ba zaki yi ba Na saka mijin ki yayi min?" Da sauri ta girgiza kai ta miqe tsaye ta yi hanyar waje inda kayan shara da goge-goge suke, hawaye wani na korar wani haka suka dinga zuba daga idanun ta, haka Eamaan ta fara shara ta gama ta hau goge-goge sannan ta yi mopping,kan ta gama ta gaji sosai, bangaren Iya ɗaki biyu ne sai babban Parlorn nan da suke taruwa su ci abinci ko a zauna hira a duk sanda ta so, sai toilet a kowanne d'aki, duk haka ta gyara ta wanke su, sai qarfe biyu da rabi na rana ta gama tinda dama bata fita da wuri ba, ganin gida zata je shi yasa bata sani damu da fita da sassafe ba sab'anin wasu matan dake doka wa iyayen su sammako kamar wanda gidan su ya gundire su ko ake yi musu wani abun, sallama ta yi mata zata tafi Iya tace, "Ina kuma zaki je kamar mai daukar wuta, shin wai ni saurin na meye haka, ba dai Audun bane ya barki? Na sa shi ya qara barin ki watarana yau Sahabee zai zo ke nake so ki yi mai abincin nan naki mai dad'i, dan taryar shi," Fashewa Eamaan tayi da kukan da take ta dannewa, dan ba qaramin baqanta mata rai Iya ta yi ba, ace duk ta san da wannan, bata faɗa mata ba tin jiya da ta zo ta gyara mata gidan sai yau da take d'okin zuwa gida? amma gaskiya ba a kyauta mata ba sam,Iya na ganin haka sai ta qanqance ido tace, "kuka fa naga kina yi tsohuwar ki na zaga ko tsohon ki? Ko salon munafurci wani ya shigo yace na sa matar d'a a gaba da baqin hali ko, to baza ki jazan masifa ba, miqe kije tinda bazaki yi ba na saka masu aiki suyi masa girkin,ko na kira Audun na faɗa mai banda ikon sawa ko hanawa agidan shi," Da sauri Eamaan ta share hawayen ta har yanzu ta kasa furta komai, kitchen taje ta fara aikace-aikacen da za ta yi, ba ita ta gama komai ba sai wajen huɗu da kwata na yamma, direct bayan ta jera komai jakar ta ta dauka da mayafin ta tai bangarenta ta bude ta shige, daki ta shiga da gudu ta faɗa gado tai ta kuka tin qarfin ta, sai da ta yi mai isarta sannan ta miqe taje tai wanka ta sauya kaya, ta saka dan gajeren wandon ta mai kama qugun ta da kyau ya fidda mazaunan ta yanda ya kamata da half vest,sai ta d'aure gashinta ta nade shi,kitchen taje ta d'akko ice creem ta zauna a kujerar parlour tana sha tana ajiyar zuciya, Ihun yara ta jiyo sai ta miqe kaɗan ta leqa window,daga nan ta hango shi yana fitowa daga motar shi,lallai sun yi kama sosai da Alhaji dan kuwa ba laifi kyakkyawa ne,amma Alhajin su ya fi shi kyau, fari ne dogo sosai har ranqwafawa yake saboda tsaho da siranta, sakin labulen ta yi ta koma ta zauna tana ci gaba da ajiyar zuciyar kukan da ta sha, da robar ice cream a hannunta tai bacci a doguwar kujera,bata san iya lokacin da ta ɗauke a haka ba, taji kamar kallon ta ake yi, tana bude ido suka sauka a saman fuskar shi da ta firgita ta......... *wane na yasshigo mana gida babu ko sallama jama'a?*😱 [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼        RUBUTAWA:HAERMEEBRAERH Page 5: "A'udhubillahi minasshaid'anirrajeem,waye kai? Meye haka zaka shigo ba ko sallama, ko an faɗa maka nan ɗin gidan arna ne, dalla malami fita daga nan,Kuma  koma waye kai baka da d'a'a, FITA MANA NACE NA SUTURCE JIKI NA" Da fari Ido ya zuba mata ya na Jin sautin muryar ta kamar busar sarewa a kunnuwan shi,tinda yake tsalle-tsallen shi daga gida Nigeria har waje be tab'a gamo da mace kamar Eamaan ba, a zaton shi ko baquwa amaryar sashen ta yi kyakkyawa haka, dan be tab'a ganin makamanciyar shigar qananan kaya a jikin kowacce mace a gidan ba sai yau,tsawar ta ta qarshe ce ta bashi tsoro ya dawo cikin hayyacin shi,kallon idanun ta ya yi ya tabbatar da wannan fuskar ba alamar wasa a cikin ta, fita ya yi salalo-salalo da dogon wuya ya koma bangaren Iya,yana shiga ya zauna dabar yana dogon nazari, Iya kuwa bin shi kawai ta yi da ido, tinani ya hau yi shin wai wannan 'yar yarinyar ce ta daka mai tsawa kuma ya bi umarnin ta kamar Wani soko? Lallai sai ya koya mata hankali ko ita wacece, sai ya nuna mata bariki fa sune iyayen ta, dan ta yi shigar 'yan bariki take zaton ita wata ce? Lallai rashin sani ya fi dare duhu in ji bahaushe, kwafa ya yi ya janyo jug ɗin da ke cike da juice ya tsiyaya ya sha,wani gard'i ne ya buge masa kunne sai ya d'aga glass cup ɗin yana kallo, duk abinda yake Iya na kallon shi sai kawai tayi murmushi tace, " Labartan abinda ya faru daga fitar ka zuwa dawowar ka yanzu," kwafa ya sake yi a karo na ba adadi tin shigar shi parlourn sannan ya zayyana mata haɗuwar shi da budurwar sashen amarya, ya qara da cewa, "Har ni zata kora da kakkausar murya, wai  na bar mata waje ta suturce jikin ta? Ni wanne kalar jiki ne ban gani ba kuma ban taɓa ba,daga na turawa har larabawa zuwa baqaqen fata namu na nan,ni zata faɗawa jikin ta?" "Dole ta faɗa maka jikin ta mana d'anneman lalatacce( ita take lalata shi kenan tin da ga sunan da ta faɗa masa wai lalatacce)kai da ko kunyar faɗin kai mazinaci ne ba ka yi, a gabana kakr faɗan wacce kalar mace ce baka taɓa ba ko?,saboda ka gawurta, na rasa me yake damun ku Kai da d'an uwan ka, kamar Waɗanda na tsugunna na haife su a gidan magajiya,mtsss maza d'auki abinci kaci soko kawai,Kuma ka sani wannan yarinyar da ka ke magana akai matar Yayan ka ce,dan haka ka kula" Tashi ta yi ta na ta surutai har ta shige d'akin ta. Abincin shi ya ɗauka ya na ci siffar Eamaan da surar jikin ta da ya gani a kashingid'e a kujera nayi masa yawo a kwanya da zuciyar shi, ba wai tsananin kyau ne da ita ba, ah ah kyau ne wanda yake da ɗaukar hankali, sura ce da ita ta daban me ban mamaki ,da tinanin ta ya kammala cin abincin shi da yake Jin dad'in shi har tsakiyar Kan shi. Eamaan kuwa bayan fitar shi ne ta tashi ta sako doguwar riga akan kayan,ta yafa dankwalin rigar ta d'akko wayar ta ta duba lokaci ta ga lokacin da ta saba yin Chatting da qawar ta ne saboda yanayin aikin ta bata so tana shiga lokacin aikin ta tafi so sai ta tashi daga aiki su sha hirar su a nutse,cikin sa'a kuwa ta ga Aishan online sai kawai suka hau hira. Eamaan :'Assalamu alaikum Babe y kk' Aisha :'Gud..sarkin qa'ida tin dazu nake jiran ki hawo online mu sha hira sai in ga time din hawan ki be ba, ni ki na bani mamaki fa sosai Eamaan, a wannan zamanin wa ya damu da wani amfani da lokaci irin haka? Ko ni da nake aikin ma na ce miki ki dinga hawa online zaki same ni a kowanne lokaci amma se ki qi kice sai na taso aiki,', Eamaan : 'Hmmmm Ayshaa kenan, kiyaye lokaci kuwa na da matuqar mahimmanci a wajen d'an Adam, a kalla ko ba ka zama me tsananin kula da lokaci ba ka zama ka San me ka yi da lokacin ka, kar ya zo ya wuce a banza baka mora ba ba a more ka ba, sannan in bama kula da shi sai ajalin mu ya riske mu bamu tab'uka komai ba, bamu Samar wa kammu mazauni me kyau ba a aljannah,ke ni raina ne ma a b'ace' Aisha : Haka ne kuma...amarya da b'acin rai? meke faruwa?😱' Eamaan: 'Allah wani wawa ne kawai ina zaune ya fad'on min cikin parlour ba ko  sallama, gashi ba wata suturar azziqi a jiki na, daga ni sai qananan kaya, dadikkan alamu Qanin Alhaji ne da ake fad'ar zai dawo, Dan kuwa  yanzu da nake tuna  fuskar shi a raina na ga kamannin shi da Alhaji,akan shi aka hana ni zuwa ganin Ammaahna,in Alhaji ya dawo zan Sanar da shi me ya faru' Kamar Aysha na gaban ta haka take magana, cike da shagwab'a. Aisha: 'Babe kar ki damu,kar ki sakar mai fuska ko da wasa,ki yi hakuri kuma kar ki fad'awa kowa ya shigo maki Kai tsaye Kuma ki gyara yanayin Sanya suturar ki a gidan, tinda kin ga yanzu ba ku kad'ai bane, ko Kuma in kin san kin yi irin shigar nan ki na kulle sashen ki' Eamaan : 'Eh na gane na kuma gode, dan da har na fara tinanin sanar da Alhjin,' Aisha: Kar ki fara, daga zuwa ki fara Kai qarar qanin miji ba tare da kin san matsayin shi wajen mijin ba, ke dai kawai kar kina sakar masa fuska ko ki bashi damar zuwa bangaren ki ma kwata kwata, sannan ma baki da tabbas ko qanin shi ne ko ba qanin shi bane" Eamaan: To na gode sai anjima bari mu je mu gana da ubangijin mu,dan an Kira sallah, kin san gwanda komai kana yi kana kula kar ka shiga haqqin Allah" (ba dan chatting aka halicce mu ba dan bautar Allah aka halicce mu, ya kamata 'yar uwa ki ribaci lokacin ki, kar ya lalace a banza, ya zamana kina da lokacin yin komai, ko da a online kike kullum kuma ko wanne lokaci, to ya zamana aikin da zaki samu lada wajen Allah kike yi, balle akwai Application na Qur'ani a waya zaki iya kunnawa ko ki bude ki karanta, in baki karanta shi kina tasbihi, in baki tasbihi kina fad'akarwa akan aikin Allah, banda zaman banza sisters) Miqewa ta yi tayo alwala, tai sallar magrib, ta zauna a nan inda tayi sallar tai azkar,tana nan zaune har aka kira isha'i ta dora sannan ta ninke kayan sallar ta, wanka ta sake yi na dare, sannan ta saka kayan bacci, ta haye gado in da sabo ta saba dad'ewar Alhaji a waje, cikin ranta ba qaramin qyamar shi take ba saboda sai yaje wasu sun gama jagwalgwala shi ya dawo ya sauke masu dattin zina a jiki, hawaye ne suka zubo mata. " Yah Allah ka sani ban kasance daga cikin mazinata ba, Allah ka shiryar da mijina, ka yaye mishi neman matan waje qazamai da yake yi, Allah ka sa ya zamo daga cikin bayin ka tsarkaka masu tsoron ka a duk inda suka sami kan su, su dinga tunawa da cewa kana ganin su idan su basu ganin ka," Alhaji Abdullah ba qaramin jin kunyar addu'ar da ya riske ta tana yi da qarfi yayi ba, a hankali ya koma baya dan a zaton shi ta yi bacci a wannan lokacin, zama ya yi a kujerar parlorn ya dafe kai, yau ce rana ta farko daya taɓa jin nadamar wata aba wai ita zina, dan kuwa a baya shi bai ɗauke ta a komai ba, a hankali ya miqe yayi sallama a d'akin dan ta san da dawowar shi ya shiga, da sauri ta goge idon ta ta rintse Ido  kamar me bacci,bai ga laifin ta ba dan tana ma qoqari a shekarun ta, direct band'aki ya shiga,dan a halin janaba ya shigo gidan, yana wanka yana saqe-saqe a zuciyar shi, bayan ya gama ne ya yi brush ya fito, kaya ya saka ya ɗan shafa mai da turaruka sannan ya hau gadon, janyo ta ya yi yanda ya saba akan su yi bacci ta juya fuskar ta jikin shi, idon ta fall hawaye, a hankali ta rintse Idanun ta suka zubo,kallon ta yake da so da qauna tare da girmamawa, dan ba wanda ya taɓa jin yayi mai addu'a irin haka,ko da mahaifiyar shi ce kuwa, a kullum sai dai ta zage shi ta sake aibanta shi akan halin nashi mara kyau. " Na San idon ki biyu i am very sorry for everything, inshaa Allah zan dena ne, ba lokaci ɗaya na zama mazinaci ba, amma da yardar Allah ina sa ran dainawa wata rana, but i need ur help," Cikin kukan da take riqewa tace, "And i promise to help u in any way possible, ni dai fatana ka dinga qoqarin bari, kan ka bar zina sai ka bar sabab ɗin ta, sabab ɗin ta kuwa sun haɗa da daina halattar wajen da ake yin ta, daina kula abokan yin zinar, da abokan da suke saka ka aikata ta,sannan sai ka kiyaye jin ka da ganin ka ma'ana,sauraron duk abinda zai ja hankalin ka zuwa aika ta zina,kamar misali hirar banza da waɗanda ba muharraman ka ba ,da kuma kallon surar macen da ba muharramar ka ba,ina fatan zaka qoqarta yin wadannan abubuwan,kaga ba ma wasu yawa ne da su ba" D'aga mata kai ya yi kamar yaro, tallafe fuskar shi ta yi ta sumbace shi tare da murmusawa , hawayen ta ya share mata, sannan ya mannata da qirjin shi, a haka suka yi bacci. Da safe kuwa bayan kammala duk Wani abu na al'ada da suka saba, Eamaan shiri ta yi me kyau, suka jera zuwa sashen Hajiya Iya, dan yace da kan shi zai kai ta gida yau tinda jiya bata je ba, sannan shi zai je ya dawo da ita, ta yi matuqar jin dad'in hakan da ya faɗa, suna shiga sashen Iya suka ga mutum ya baje daga shi sai gajeren wando, duk jikin shi a waje sai latse-latsen waya yake yi, da sauri Alhaji ya maida Eaamaan baya ya ce, " kai tashi kaje ka saka kaya, meye haka zaka zauna tsirara," Miqewa ya yi ya na sosa qeya ya fad'a  dakin shi,Iya ce ta d'ingiso ta fito, yau ciwon qafar ta ya motsa, Alhaji ne ya matsa Eamaan ta bayyana bayan shi, "Toooo 'yar jakar Audu, ina kuma zaku da sanyin safiyar nan, qarfe sha daya?," " Iya barka da safiya," "Baka amsan tambaya ta ba, nace ina zaku," "Iya zan kai ta gida ne, jiya na ji bata je ba," "Ohhhh bayan tijarar da ki kai wa Sahabee jiya, shine kenan yau ki ka tasan d'a  gaba sai ya kai ki gida ko?" Da sauri Alhaji ya d'aga kai daga duqen da yake  a gaban Iya yace, "Me ki ka yi wa Sahabeen jiya?" Idon ta fal hawaye ta kasa magana, dan dai ta san ita tsakanin ta da wannan zalb'en ba komai sai alkairi, dan qarewa ma ita ta gyara mai d'akin da zai kwanta, sannan ta yi mai girki, amma shi ya shigo ya nuna mata rashin tarbiyyar shi har ta yi masa tsawa. "Ina zata iya faɗa maka, ya je wajen ta ya gaishe ta amma ta koro min shi," kallon ta Alhaji ya yi,nan take  ya gane tabbas akwai wani al'amarin da ya faru da zai sa ta koro shin,shiru ya yi daga baya yace, "Za mu haɗu dake ne,"  Alhaji Abdullahi ya ce wa Eamaan rai a bace, Iya da Sahabee da ya fito sanye da jallabiyya ne suka kalli juna suka yi murmushi, a zaton su wani rashin mutuncin zai yi mata, ( kar ki zaci wai kyautatawar ki zai sa dangin miji su soki,sam ba lallai bane,haka kawai wani zai tsane ka,baka ci mai komai ba balle ka sha mai,) gaida Iya ta yi, Iya kuwa tana d'ad'd'aukewa ta amsa, Sahabee ne ya gaida Yayan shi, sannan itama ya gaida ta yana shan qamshi, Alhaji ya kula da hakan, sannan ya kula da kallon maitar da qanin shi ke wa matar tashi, " Iya ni zan je na sauke ta, na tafi Office in na dawo na d'akko ta, a yi min addu'a," "To Allah ya kare ka yayi maka albarka," Miqewa su ka yi ta na gaba yana baya, suna zuwa mota ya buɗe mata ta shiga a ranta tana mamakin hakan da yayi,ta zaci zai b'ata rai ya yi ta masifa ne, bayan sun fita daga gidan ne sun ɗauki hanya ne yace, " Me ya haɗa ku da Sahabee bana son ki boye min komai gaskiya nake son ji," "Dama jiya ne da zan je gida na je sanar da Iya, sai ta ce na yi mai girki na gyara mai daki,to nayi hakan na gama kenan sai na ga lokaci ya tafi ba zai yu naje gida ba, ina shigowa kawai sai na yi wanka, na shirya cikin qananan kaya, wanan dana saka irin shi da weekend ɗin can da ya gabata,shine Ina zaune bacci ya fara ɗauka ta sai naji kamar ana kallona ,ina buɗe idona na ganshi a gabana ya kafe ni da kallo shine na kore shi, shine ya tafi, sannan ni ban san ko shi waye ba,kuma koda na sani dole na kore shi saboda mutuncina yafi min komai," Bayan ya saurare ta ne tas yace, "Abinda ki ka yi kinyi dai-dai,sai dai zan faɗa maki kome zaki yi ki na yi ki na kiyaye wa kar ran Iya ya na ɓaci, dan kika b'ata mata rai sai ta b'ata maki ko ina nan ko bana nan,kuma nima bazan so ran mahaifiyata yana ɓaci ba kin ji?" D'aga masa kai ta yi ta bashi hakuri kuma, bai ce komai ba ya kama hannunnta ya riqe,a haka suka isa gidan nasu, suna zuwa gate ɗin gidan ya tsaida mota ya ja ta jikin shi ya sumbace ta, ji ta yi kamar ta saka ihu,ga mutane can gefen wani babban gida a zaune suna shan hantsi,ko da dai sun yi nisa amma wani zai iya ganin su ai, yaqe tai ta d'aga masa hannu bayan ta buɗe motar ta fita sai ta duqa ta dakko jakar ta, ta kulle masa motar tai gaba, tana shiga gida ta ji kamar ta taka a guje ta gan ta gaban Ammaahn ta, ta baya ta ji an dafa ta, tana juyawa kuwa sai taga Ammaahn ta,ai cike da ihun murna ta saki jakar ta a qasa ta d'ale ta,Hajiya kareema dake gefe ta saki dariyar jin daɗin ganin d'iyar tasu tace, "kar ki b'allan 'yar uwa fa, ku har yanzu yarannan baku girma, Yayar ku ma haka take wannan shirmen in ta zo gida," Sakin Ammaahn ta ta yi ta je ga Hajiya Kareema ta rungume ta sosai tace, "Mama na yi missing din ku ne sosai, wata uku faaaa ban gan ku ba," Ta qarasa maganar ta cike da shagwab'ar da take halittar tace hakan, takawa suka yi suka shige ciki gaba d'ayan su suka bar aikace-aikacen da suke a backyard ɗin nasu, ranar Eamaan ji tai kamar kar yamma tayi dan murna, iyayen nata kuwa sun sa ta a gaba da cima kala-kala irin wadda take matiqar so, ga hirar bayan rabuwa ana ta sha, tambayar ta su ka yi komai dai lafiya yake a gidan nasu ko? Nan take ta tabbatar masu da komai, lafiya babu wata matsala, Hajiya kareema ce tace, " A'a Eamaan na san halin ki irin na uwarki ga ta nan da zurfin cikin tsiya, kar ki je kice zaki yi zurfin ciki a gida mai iyali irin wannan, in dai akwai matsalar da zamu iya baki shawara ki faɗa mana tin yanzu," " Allah Mama ba komai, kawai dai rikicin su ne da suka saba tin kan naje kullum sai anyi, in yau ba ai ba gobe za ai,sai dai in yaran na school ne abun ke sauqi tinda akan su aka fi yin faɗan,ni da su kuwa muna shiri sosai har maman su,kawai dai bata nuna min ne a fili koda yaushe,amma kuma bata yi min baqin hali,sai Iya da Sahabee, su ma banda matsala da su, iyaka na je gaida ta na koma sashe na, ita kuma Hajiya babba kishi take dani sosai,amma itama iyakar mu gaisuwa,bana shiga harkar kowa," ( in baki iya rufe sirrin gidan ki gaban iyayen ki ba,topa tabbas mata kika rako, domin kuwa faɗan matsalar da kike ciki ma iyayen ki indai ba wadda ta ta'azzara sai sun sani ba zai ja ma iyayen ki tsanar mijin ki da dangin shi, daga nan zaman lafiya zai yi maki qaura, mijin ki yazo yana jin haushin iyayen ki, su suna jin haushin shi da dangin shi, in kuma aka samu kuka shirya duk yanda zaki dawo kina son su so shi ba zasu so shi ba,sai dai kawai suna sharewa sabo da ke) Su Mama sun gamsu da bayanan ta, sannan ta nuna masu ita da Alhaji suna zaune lafiya dan kuwa yanda yake yi mata kamar wani wanda zai na goyata kullum dan gata, wannan kuma dama haka abun yake, a haka har yamma ta yi Daddyn ta ya dawo yayi mata nasiha, Alhaji yazo ya ci abincin dare anan sannan suka kama hanyar gida, ba tare da sun san Iya na can tana masifa ba, faɗi take tana kumawa, "Ku banni da su wato ga 'yan iska an bari a gida,tasan itace da girki ta tafi ganin gida mu nemi abinda zamu sa abaka ko? Dan masifa irin ta Iya duk masu aikin da ke gidan amma babu me bata abincin se Eamaan, ko da wake bata abincin ta ci kafin zuwan Eamaan ɗin oho. Su Eamaan ana can ana shan soyayya a mota ba su san meke faruwa a gidan Hajiya Iya ba............ [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   BIYAYYAH  💅🏼 RUBUTAWA:HAERMEEBRAERH Page 6: Saida ya biya da su supaer market ta sai kayan kwalama sosai son ranta, shi da kan shi ya qara mata bayan ta gama ɗaukan Wanda take so sannan suka dawo gida,a tsaye a bakin qofar shiga wajen Eamaan suka tadda tsohuwar a coge tana kad'a qafa, Sahabee na ta bata baki akan su koma iska nata kad'a ta amma ta qi, dan ya ga alamar ba da wuri za su dawo ba, ya juya ya fara tafiya kenan suka Jiyo qarar motar Alhaji, me gadi ya isa qofa babu b'ata lokaci ya wangale gate, gyara tsayuwarta ta sake yi ta cuno baki gaba, Hajiya A'i kuwa na tsaye tana leqen su ta window dan taga ya za a qare, itama Hajiya Qarama tana leqawa lokaci zuwa lokaci ta na jinjina masifa irin ta Iya da bata qarewa,Alhaji kuwa zagayawa ya yi gefen Eamaan ya bud'e mata qofa, bayan ya buɗe mata motar ne ta fito ya dakko mata jakar ta da ledojin suka jero su na takawa cikin nutsuwa, Alhaji se santin abincin da ya ci d'azu a gidan su yake yi mata, ita Kuma ta na ui masa dariya tare da tsokanar shi, haushin ganin su cikin nishad'i ya kama kowacce daga cikin matan Alhaji har da Iyan ma da take uwar shi, Sahabee kuwa na can ya lula wani tinani na daban a qasan ran shi,cikin masifa Iya tace musu, " Sannu riqaqqu wato sai yanzu kuka ga damar dawowa ko? Na zaci a titi zaku kwana ai,Kun kama hanya Kun tafi Kun bar ni da yunwa,bayan kin san sarai yau girkin ki ne, tin da ki ka zo gidan nan ki ke azabtar da ni da yunwa ban san me na yi miki ba, to bari ki ji ba zan mutu ba se lokaci na ya yi, Dan haka wuce muje ki tuqan tuwon alkama miyar kub'ewa, dan nasan shi ne kawai ze raba ni da yunwar da na wuni zubur da ita," Mamaki ne fal cikin Eamaan, ita Iya wai ko girman Alhaji bata gani ne take yi masa irin waɗannan abubuwan, koda cewa ita ta haife shi amma ai akwai jin nauyi a tsakanin yara da iyayen su idan an kai wani minzali kuma,da ace Alhaji ya samu haihuwa da wuri da yanzu Yana da jikoki fa, Amma ba ruwan ta in ta tashi yi masa fad'a kamar ta na magana da qaramin yaron goye haka take yi kuma ko a jikin ta. Iya kuwa sa kai ta yi gaba abun ta ta na ta sambatun fad'a,su Hajiya babba na jin haka farin ciki ya kama su dan sun san yau Eamaan sai ta ci uban aiki kan ta kwanta,yana son ya yi magana ko ya bawa Iya hakuri amma sai Eamaan ta kad'a masa kai, cike da murmushin da zai nuna masa kar ya damu zata je tayi aikin take kallon shi, kad'a mata kai ya yi alamar ta bari yaje ya bada hakuri,sai tace, " A'a sweet ka bari kawai yanzu zan dawo ai, abinda ba zai wuce awa ɗaya ba an gama, kaga kan na dawo kaima na saka aiki, ka saka min ice cream ɗina da chocolates d'ina ga fridge, kuma kar a sha min sweet ta wuce biyu, inna dawo zan qirga abuna," kamo ta ya yi cike da so da qaunar halayen ta tare da tsantsan girmamawa a tsakanin su, ya sumbace ta sannan ya raka ta har side ɗin Iya sannan ya juya  ya koma sashen ta, a wannan lokacin ne Sahabee dake gefe yana kallon komai ya cika ya yi fam kamar an tab'a matar shi, ganin yanda Alhaji ya sumbaci Eamaan abun ya Sosa ran shi ainun,qara lab'ewa ya yi jikin gini ya na bin bayan Eamaan da kallo har ta shige ciki. "Shegen kaya Yaya sai kwasar dad'i yake ni ina nan na qare a hannun qadangarun bariki, ni da zan samu kamar wannan ai ba zan yi irin taka ba,da daga ranar na bar bariki," k'wafa ya yi sannan ya kad'a kai tare da yin murmushin da shi kaɗai ya san ma'anar shi, ya kad'a yatsa ya sa a bakin shi ya gatsa sannan ya shige ciki shima, kitchen ta tafi direct,ta fara hada-hadar hada tuwon alkamar,ba jimawa ta ɗora ruwa ya tafasa, garin niqagge ne wanda yake zuwa a tankad'e, ta d'iba tai rude, a ruden ta zuba kanwa kadan ta rufe, tukunya mai kyau ta ɗora ta kunna ɗaya bangaren na gas ɗin, ta zuba manja ta yanka albasa a ciki ta bari ya soyu, dama ta daka daddawa da kayan miya kafin ruwan tuwo ya tafasa, haɗa su tai ta zuba, suka dan fara soyuwa, sannan ta dakko tafasasshen naman da takan aje a fridge da ruwan naman,ta zuba a kan soyayyan kayan miyar nan,albasa ta yanka qanana-qanana,se ta zuba kayan qamshi da na dandano ta rufe dan ya dahu, sai da ya tafasa kamar na minti 5 sannan ta qara ruwa ta sake rufewa, nan da nan gidan ya ɗauki qamshi, Sahabee ne ya shiga kitchen ɗin yana tafiya a ranqwafe yanda ya saba,direct hanyar sink ya nufa zai ɗauki cup, a yau ya ɗauki aniyar taba qirjin ta dake tsone masa idanu ko ta halin qaqa ne, dai-dai zata juyo kenan da nufin d'akko food flask dan zuba tuwo a ciki kawai taji gaba ɗaya qirjin ta ya daki nashi. Numfashi me tsaho ya ja saboda wani irin abu da yaji ya ratsa dikkan jikin shi, da farko dai ta dauka bai sani bane, har ta yi qoqarin bashi hakuri ta kauce zata wuce,amma sai taga ya ajiye cup ɗin yana matso ta ya na bin ta da Wani irin kallon sha'awa irin na kwararrun 'yan duniyar nan, hannun shi ya d'aga da Wani irin salo ya nufi qirjin ta direct zai cafko,bai ankara ba yaji ta ɗauke shi da wasu gigitattun maruka guda uku, fuskar ta kamar ba ta ta ba dariya ba take kallon shi da mugun kallo,Sahabee kuwa yayi matuqar kid'ima dan be taba zaton haka daga gare ta ba,duk ya gigice saboda zafin marin da ta mai ga kuma mamakin ganin qanqanuwar yarinya kamar ta wanke shi da maruka kyawawa har uku,can qasan ran shi kuma ya tsorata da yanayin fuskar ta. Eamaan ta gigita shi ko ta Ina, gaba d'aya ya manta da dad'in da ya ji na daqiqu kaɗan da suka gabata sakamakon marin da ya sha,cikin ɓacin rai ta nuna shi da yatsa tace masa, " kai dabban ina ne kuma ɗan akuyan wane gari ne kai? To bari kaji ko a qasar jakai ban taba jin labarin mai son aikata abinda kake da quduri akai na ba, na ɗauka ba da sanen ka bane ka buge ni, amma yanzu na fuskanci duk inda ka dosa, to bari kaji, ni Eamaan nafi qarfin ɗan iska da izinin Allah, kuma in ka kallen da kyau ba ragowar qadanqarun bariki bace ni balle ka tsammaci wani abu daga waje na, ka kula ko dan gaba! " Cike da mamaki Sahabee ya bar kitchen din ba tare da yace kanzil ba, dan kuwa bashi da abun fade,ita kuwa Eamaan yana fita ta yi kwafa ta koma wajen miyar da ta dora, ta hau qoqarin kad'awa, dan yau ko bata dahu ba haka za a ci ta, d'ebo busasshiyar kub'ewa ta yi ta zuba, dan da d'anyar zata wanke ta goga amma ta fasa,juyawa tayi ta tuqa tuwo,5mnts kawai yai ta kwashe, fuskar nan ba walwala haka ta gama ta zuba a food flask ta leqa ta ga Iya ta riga ta yi bacci, ja mata qofar ta yi ta kama hanyar sashen ta, tana fita farfajiyar gidan ta saki wani kuka mai d'aci, ta kame cinyoyin ta ta duqar da kai tana ta rera kukan ta ,anya zata iya jure wannan sabon halin da take qoqarin shiga da Sahabee kuwa? wannan wanne irin ɗan akuya ne shi da bai san matar wanshi bace ita ko me? Ya na tsaye a d'akin shi kamar Wanda aka dasa ya Jiyo motsin fitar ta,na farko ya qudurta niyyar ko zata mutu sai ya d'ana jikin ta, sai ya amfana da albarkatun jikin ta, sannan sai ya rama marukan da ta watsa masa, amma wata zuciyar tana tsorata shi da yanayin ta, itan ba kamar sauran mata bace da suke son ma ya kula su,amma ko ba jima ko ba dad'e shima sai ya cimma burin shi akan ta. Goge fuskar ta ta yi ta leqa pampon da suke ban ruwa ta wanke fuskarta ta goge da mayafin ta,sannan ta tafi side din ta, kwance ta ganshi ya yi wanka bacci ya ɗauke shi ga sweet leda biyu yasha ya riqe sauran, sai 'yar takarda a jiki da ya rubuta mata.. 'Gashi nan biyu na sha as promised, I love u with all my heart Eamaan,' Ninkewa ta yi ta qurawa fuskar shi ido kawai, ba wani emotion a fuskar ta, ba zaka iya tantance me take ciki ba, ta dad'e a haka a tsaye tana kallon shi daga baya ta wuce bayi ta yi wanka ta fito, mai ta shafa sannan ta fesa turarukan ta masu sanyin qamshi, sai ta saka kaya ta yi sallah,tana idarwa ta kwanta a jikin shi kamar yanda ya sabar mata, dan tana buqatar lallashi ko ba mai bata hakuri a qalla ta jingina da wani,zuciyar ta cike take da kewa, amma bata son tina baya, a Koda yaushe qoqari take yi ta manta Anwar,Amma ina ya na nan manne a zuciyar ta,ta kasa matsar da soyayyar shi ta Sanya ta Alhaji, abinda ta sani shine ba zata tab'a ba wa Alhaji damar ganin rashin son shi a tattare da ita ba, za Kuma ta ci gaba da addu'a Allah ya sauqaqa mata son Anwar ya dasa mata son mijin ta,  hawaye ne suka zubo mata tasa hannu ta share ta yi ta qoqarin shanye kukan ta amma ta kasa, miqewa ta yi ta fita kitchen ta buɗe fridge ta saka kanta ciki ta yi ta kuka, sai da ta yi mai isar ta ta d'akko ice cream ta fita, a tsaye ta ganshi ya jingina da gini yana yi mata kallo cike da so da tausayawa. kar ku manta fa alhaji ya tsani tashin dare,in ya kwanta shifa sai safe, amma sai gashi yau sanadin soyayyar Eamaan ya farka har ya fito waje,cikin sanyin murya yace mata, " Me akai maki.... Waya taban ke? Zo nan ki faɗa min me ya faru," Cikin qoqarin kawar da damuwar ta ta Isa gare shi, ta riga da ta koka damuwar ta dan haka ta samu salama, ido kawai ta zuba masa tare da shanye su, yanda ta San ya na so,ɗora Kanta ta yi a gefen kafad'ar shi ta dama,shi Kuma ya kama qugun ta suka fara tafiya, a hankali ta furta "Ni ba abinda aka yi min kaina ne yake ciwo, kuma na kwanta na kasa baccin shine na fito na ɗauki Ice cream ɗina dana duqa na ji bayana ya yi zafi shine nake kuka," "Assha sannu Eamaanina tashi muje na yi miki tausa, sai ki ji dad'in wajen ko? sannu kinji? Allah ya sawaqa, bari na baki maganin ciwon jiki," D'aga kai ta yi suka tafi daki cike da shagwab'a take takawa, ɗaukan ta ya duqa ya yi kamar irin ɗaukan yara in sunyi bacci,Eamaan kuwa sai ta saqala qafafun ta a gefen jikin shi ta kwantar da kanta, ta bude robar Ice cream tafara sha,sai da suka je d'akin ta zuba masa kaɗan a bayan shi tana sane, gantsarewa ya yi tare da sakin wata siririyar qara,ta kuwa saka dariya, tace, "Na warke aje ni qasa zan iya takawa da kaina, amma ka yi hakuri kar ka rama, na san ma baza ka rama ba ko? Su manya Allah ya zuba masu haquri ba kamar Yara suke ba," Dariya yake yi sosai dan ganin yarinya qarama na son ta yi mai wayo dan kar ya rama abinda tayi masa, a hankali ya rage dariyar shi cikin murmushi yace "Juya to na yi maki tausar na yafe miki ba zan rama ba na san baki sani ba ai,sannan aike baki laifi a wajena," Juyawa ta yi ta kwanta ya fara yi mata tausa tana shan Ice cream ɗin ta, a haka har bacci ya ɗauke ta, robar na kan gadon miqewa ya yi ya dauke robar, ya ajiye a gefe,ya gyara mata kwanciyar ya kwanta a gefen ta ya rufe su. ************* Washe gari da safe Sahabee ya shirya ya koma Ibadan, dan baya son kowa yaga shatin yatsun Eamaan a fuskar shi, a tambaye shi dalili,tabbas za a gane shi ne yaje neman ta ta watsa masa maruka, Iya kuwa sa da ta tashi daga barci tayi sallah kitchen ta shiga ta duba, taga tuwon har lokacin da zafin shi sosai, dan flask din akwai riqe zafi, miyar na tukunya ba qaramin son ci take ba,amma kar dai ta bar Eamaan ta huta sai ta danna waya ta kira Alhaji dan ya tura mata Eamaan ta haɗa mata abin karyawa, " To Iya zata zo ,amma kuma bacci take yi yanzu,jiya bata samu bacci ba sosai saboda gajiya da ta yi mata yawa, in ta tashi zan turo ta,ko masu aiki su ɗan yi maki mana kin ji Iya ta ita kuma ta yi maki na rana da dare ko? " " Iyeeeaaa ashe kai zaka nuna mata ta raina ni da Kan ka Audu? Tin da kaga ina cin abincin masu aiki ne ni? Ba sauran matan ka ke yi min ba, duk da ba wadda ta iya komai cikin su, sai yanzu dana samu wadda zata na yi min mai dad'i shine zaka hana, to shikenan ni bari naje na dafa da kaina in hawan jinin nawa ya tashi na mutu ka huta ai," Cikin sauri yace, " Aaaa aaa Iya nifa ba haka nake nufi ba ga ta nan zuwa," Da sauri ya miqa hannu ya na tashin Eamaan, cikin ranshi yana mamakin hali irin na Iya, dan kuwa ko a da matan sa sai dai su fad'awa masu aiki abinda za a dafa ba su ke yi ba, kawai samun waje ne irin na Iya. "Tashi maza je kiwa Iya a bin karyawa,gata can wai zata shiga kitchen da Kan ta in Baki je ba,kin san ta na da hawan jini, Dan Allah daure ki yi sauri" Dik da ran ta be so ba amma bata nuna komai ba, ta amsa da "to" nan da nan kuma sai yaji ba dadi, yarinya mai biyayya kamar wannan amma ana ta muzguna mata, wai shin ya zai yi ne da halin Iya? Iyan ta ce kullum ita zata na yi mata abinci dan ta iya girki, yana nan zaune ya na tinani har ta gama komai ta shirya zata tafi, ya Kira sunan ta, juya wa  ta yi tare da sakar masa faffad'an murmushi, " Eamaan ki qara hakuri, ba yanda zan na hana hakan faruwa, mahaifi.....," Da sauri ta katse shi da tacewa, "Dan Allah ka bari ai ba wani abu bane hakan, ni a gidan mu bana kai wa haka ina bacci,in muka yi asuba ba mai komawa bacci,da sassafe nake haɗawa Daddy abinci har na tafiya Office, yanzu ba ga shi ba inna je ina jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya ba, zan yi mata nata girkin kaima kuma zan yi maka wanda zaka tafi da shi, duk da dai kana wani qi wai kai babba da tafiya da abinci ko? to yunwa ba ruwan ta da girman ka,kuma ai dole macen kirki tai tarayya da mijin ta wajen kyautata wa mahaifan shi in dai tana son ya shiga aljanna, tinda shi na miji bayan Allah da manzon sa, iyayen shi kawai zai bi ya samu aljanna, dan haka ka daina ban hakuri daga yau dan Allah, in ba haka ba gobe da botle water irin na su Ilham zaka je Office da irin lunch box ɗin su" Ta qarasa maganar ta cike da wasa, dariya ya yi ita kuma ta fita ta bar shi yana mamakin halaye irin nata, ta iya b'oye damuwar ta, dan tabbas yasan kukan jiya ma wani abu ne ya same ta a can amma ba wai abinda ta fada masa ba, kad'a kai yayi ya miqe cike da girmama ta a ranshi. Tana zuwa bayan ta gaida Iya ta bata umarnin ta d'umama mata tuwon ta, sannan ta yi mata farfesun kifi, da kunun shinkafa, amsawa ta yi da "To Iya"ta shiga ta haɗa mata duk abinda take so ta kawo mata parlour ta ajiye a inda take karyawa,cikin mamaki babu godiya Iya tace, " Oh ni ji yarinya kamar wata inji, ke baki gajiya da aiki ke ? Ko dake in ma kin gaji za dai kiyi dolen ki,sai ki tashi ai ki tafi uwar son miji, yarinya qarama dake sai jaraba,wani har yana gaya min jiya baki yi bacci ba, Oh ni yaran yanzu akwai jarabar tsiya," Eamaan Kan ta na qasa idon ta ya kawo kwalla ta yi sauri maida su, ta d'aga kai ta kalli Iya da ke bin ta da harara,tace, " Iya me za a dafa maki an jima?" " Oh ho, ko dambun shinkafa zaki min ma de waya sani, sai anjiman dai in kinzo na ga me za a dafa," Miqewa Eamaan ta yi zata tafi,har  ta kusa fita Iya tace mata " ke zo nan, dubamin dakin Saheebee ya taso ya karya, ki tambaye shi me zai ci se ki haɗa masa" Cike da kasala ta nufi hanyar d'akin nashi........... *Hhhhh Sahabee ai by now ya kusa isa garin yarbawa wallah*😆😆 [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 7: Dab zata k'wank'wasa qofar d'akin ne ta tsaya ta haɗe fuskar ta tamau kamar bata taɓa dariya ba, ta sa hannun dama ta fara k'wank'wasa qofar, shiru-shiru ba a amsa mata ba kuma bata ji motsin kowa ba,ta nan tsaye tsawon minti uku bai buɗe ba, murda hannun qofar  ta yi ta leqa sai taga ba kowa,in fact ba kayan shi ma kwata-kwata a d'akin kamar yanda ya Saba baza su duk inda ya so, kwankwasa toilet ta yi nan ma taji shiru, budewa ta yi a kasada ta leqa sai taga wayam babu kowa, komawa ta yi parlourn ta sanar da Iya bata ga kowa ba, kallo Iya ta bita da shi can tace ta tashi ta tafi kawai, " Allah ya shiryi yaronnan, barikin tashi ta motsa kenan shiyasa ya tafi babu ko sallama," Eamaan na fita kai tsaye bangaren Hajiya babba ta shiga da yake kusa dana Iya, a zaune ta gan ta tana karyawa da bread da kwai, ta hada tea mai kauri tana korawa sai baza hanci take yi, kanta babu dankwali kamar ko yaushe, ga shi kan nata babu wani gashin arziqi, kitson duk ya haɗe , amma fuskar nan tata tasha kwalliya, an damb'ara jagira an saka jan baki a saman idon,sannan a bakin ma ta saka jambaki an ja baqi a saman janbakin, jagirar ta ja ta doguwa sosai, gashi ta lafta mai a saman ta,sai yauqi take tana gatsa biredin cikin yanga ita a dole ta yi kyau, tana ganin Eaamaan ta d'aure fuska tamau, gaida ita Eamaan ta yi Hajiya Babba ta amsa a shaqe, Eamaan na ganin haka ta miqe ta fita,tana jiyo sanda Hajiya Babba ta ja tsaki ta hau zagin ta ko juyawa ba ta yi ba ta faɗa ɓangaren Hajiya Qarama, tana shiga suka yi Ido hud'u da Sabeerah da ta Sanya uniform dan zuwa makaranta, da gudu Sabeerah ta isa gare ta ta d'ale ta,Eamaan kuwa sama ta d'aga ta tana yi mata wasa,suna a haka Ilham ta tako da yanga itama ta je kusa da Eamaan ta dan duqa ta gaida ta, amsawa ta yi cike da jin daɗi a sannan ne Sabeerah ma ta gaida ta, " Ina Mum?" " Tana d'aki tana d'akko mana hijabs ɗin mu," "Ok" zama ta yi dan ta jira sai gata ta fito fuskar ta babu yabo babu fallasa suka gaisa, Eamaan ce tace masu su biyo ta ta basu wani abu su tafi da shi makaranta ihun murna su ka sanya suka haɗa baki wajen faɗin, " U ar the best Aunty Eamaan," "Thank you ba komai sai kun shigo, ina jiran ku," Shafa Kan Sabeerah ta yi kafin ta wuce sashen ta,d'an murmushi Hajiya Qarama ta yi dan kuwa tana jin dad'in yanda take kula da yaran ta, bayan ta koma ne ta ga har Alhaji ya shirya ita yake jira, a gaggauce ta koma kitchen ta d'akko abinda ta bada umarni masu aiki su haɗa mata sai ta kawo masa ya karya ta haɗa masa wanda zai tafi da shi, tana haɗawa tana tsokanar shi, sallamar su Ilham ce ta katse su,  sweets da suka siyo jiya da chocolates ta d'ebo ta basu,sukai mata godiya suka tafi, Alhaji shi ma yana jin daɗin yanda take son yaran shi ba kaɗan ba,a ranshi yana ayyana gaskiya Eamaan ta daban ce. Kusan wata biyu kenan ba labarin Sahabee ba waya ba saqo, hankalin Iya ya yi matuqar tashi da rashin shi,musamman da ya zama baya koda kiran tane a waya, samun Alhaji ta yi da maganar ya kwantar mata da hankali, ya nuna mata zai bincika ya ji ko lafiya yake, a ranshi ko yana ayyana, 'Dan ɗan bariki ya yi nesa da gida haka ai ba abin mamaki bane duk inda yaje zai dawo ne' Iya ta yi matuqar zurfi a tinanin ta tajiyo qamshin girki,da jin yanayin qamshin girkin ta tabbatar da cewa Eamaan ce ta shigo,miqewa ta yi ta nufi kitchen ɗin cikin zafin rai, Eamaan na ganin ta ta durqusa ta fara gaida ita, bata amsa ba ta fara magana cikin fushi kamar za ta Kai wa Eamaan duka "Ke ! me ki kai wa d'ana ya bar gida? Me kika mai ya bar gidannan ba waya ba saqo? Tinda yake ko ya tafi kullum sai ya min waya amma wanan karon ba ko pilasha,(Flashing) kuma dan tsabar munafirci da kika zo ba ki je kin gaida ni ba sai yanzu ne da kika gannj zaki wani zube kina gaida ni?" "Iya ki yi hakuri naje na gaida ki na ji shiru da alama kinyi nisa cikin abinda kike tinawa,bana son katse maki ne yasa na taho dan nayi aikina, Iya ban yi mashi komai ba, ko ganin shi ban yi ba ma lokacin da zai tafi, inshaa Allah Iya zai dawo gida lafiya ki daina sa tinani da yawa a ranki, saboda lafiyar ki,"  Ta dan ji daɗin maganarta Eamaan ta qarshe, ko ba komai a qalla ta samu wanda ya tina mata ba ta da isasshiyar lafiyar sa tinani aranta,a hankali ta ja jiki ta bar kitchen din, tana matuqar son Sahabee fiye da kan ta, dan ko wanne laifi zai aikata a wajen ta bai komai ba, d'akin shi ta shiga direct, ta hau dudduba kayan shi, ba abinda take gani sai kayan shaye-shaye da wata leda doguwa, mai kamar madara ce a ciki ko me oho, ledar nada kyalli da ɗaukan ido,(condom) ajewa ta yi ta ci gaba da dudduba d'akin, a gefen gado ta zauna tana ta tinani kan wani lokaci kan ta ya fara ciwo a wajen ta kwanta bacci ya dauke ta. Eamaan na gama girki ta je d'akin Iya ta duba koina har toilet bata gan ta ba? D'akin Sahabee taje ta duba acan tagan ta kwance tana bacci, ta cika d'akin da munshari, zata ja qofar kenan Iyan ta farka kiran ta tayi haka Eamaan ta koma ciki ta kama ta suka bar d'akin suka koma nata. magungunan ta ta yi umarnin Eamaan ta d'akko mata zata sha dan bata jin daɗin jikin ta,fita ta yi ta fara debo mata abincin da ta dafa, jellop din taliya data ji kayan ciki da kayan lambu ta zubo mata sai tashin qamshi take yi, ga tea data haɗa mata dan ta kula ko karyawa bata yi ba, sannan ta d'akko mata ruwan roba,ta na shiga ta ja qaramin Table dake d'akin gaban Iya ta dora mata abincin sannan ta binciko mata magungunan, Iya abinci ta nad'a sosai, dan kuwa abincin Eamaan ko baka jin yunwa ka fara ci zakaji kamar kar ka daina ci saboda daɗin shi, balle da 'yar Gusau din dama, tas ta share plate din ta kora shayin sannan ta sha maganin, a hankali ta fara jin nutsiwa na zuwa mata, ruwan wanka Eamaan ta haɗa mata sannan ta yi mata sallama ta fice, Hajiya Qarama ce ke girki a ranar,dan haka Alhaji yana ɓangaren ta,da dare Eamaan ta dafa ruwan tea kawai sai ta soya kwai da ta saka ma timatir mai yawa da albasa, ta soya ruwa-ruwa bayan ta saka kayan qamshi da ɗan maggi ta zauna ta ci sannan ta sha tea, wanka ta yi tai brush ta saka kayan bacci riga ce qarama iya cinyar ta, sai wandon rigar shima iya cinyar ta, sai ta saka hula kalar kayan jikin ta, ba qaramin kyau ta yi ba a wannan daren, tana zama a bakin gadon ta sai ta yi addu'a ta shafe jikin ta da shi sannan ta bi lafiyar gado, kwanciyar ta kenan Alhaji ya shigo yi mata sallama, ya jima a sashen ta yana faɗa mata yanda ya yi missing ɗin ta ya kuma matsu jibi tayi ya dawo gare ta, and he wish a nan zai kwana yanda tai kyau ɗin nan ya yi matuqar yabawa, cike da shauqin son kasancewa da ita ya tafi bayan ta raka shi har bakin qofa, yana fita ta koma ta kwanta,zuciyar ta cike da tinani kala-kala ita tata jarabawar kenan numfasawa tayi sannan tace, "Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin," Bayan Alhaji yaga rufe qofar ta sai yayi bismilla ya topa a qofar sashen nata sannan ya wuce ɓangaren Hajiya Qarama,samun ta yayi tana zaune babu kwalliya kamar yanda ta sabar mashi,sannan babu wankan dare, ba qamshi ita a tattare da ita sam babu komai, kuma wai a haka jiran miji take yi ,mijin da ya je sallama da sauran matan shi ya isko Hajiya Babba ta cab'a adonnan nata na kwalli da jan jambaki, an sha lace an sha d'auri ya kalli kudu maso gabas, duk da cika kwalliyar da ta yi a hakan ya ji ta burge shi,a qalla bata yin wari kuma ta yi kwalliyar ne domin shi,ta ɓangaren Eamaan kam ba a magana dan kuwa ta haɗu ta kowanne fanni sai godiya kawai, tsaki yaja ya kwanta, can kuma kamar wanda aka mintsina ya miqe ya saka kayan shi ya ɗauki key ɗin motar shi ya bar gidan sai tashin mota mutan gidan suka ji, ko da me gadi ya fito daga bayi sai ya manta da zuwa ya jaddada rufe gate ɗin gidan, fitar Alhaji da kamar mintuna sha takwas, Mai machine ya ajiye Sahabee a qofar gidan,sallamar Mai machine ya yi ya tura qofar gate ya shiga gidan ,dan kuwa yaga a ɗan bud'e qofar take, yana shiga har ya nufi hanyar bangaren su wata zuciyar ta kad'a shi ya nufi bangaren Eamaan, dan ba qaramin kewar ta ya yi ba a wannan watannin, ko neman matan na shi yake yana kwance da mace zai ta ayyana Eamaan ce, amma inaa dik da haka baya wani samun gamsuwa, haka zai ta abu ɗaya cikin jin haushi ya tashi ya bar mace kwance da takaici, yayi iya qoqarin shi na cire ta a rai, amma ya kasa, musamman in ya tina da deadly look ɗin ta da a yanzu yake matuqar burge shi,nan take ya tuna da marukan da ya Karb'a wajen ta hankalin shi ya dawo jikin shi,anya kuwa zai samu nasara akan Emaan a haka dai ya leqa sashen ta ta window, kwance ya ganta ta kifa cikin ta ta d'age qafafu sama tana kad'a su da ice cream a hannun ta tana sha, hannun ta ɗaya kuma da wani littafi na su na school of nursing tana dubawa,ya dad'e yana kallon ta anan ya gane yau Alhaji ba a bangareta yake ba,wani dariyar mugunta ya saki, ya tattaka a hankali ya murda hannun qofar, a bude ya ji ta,murmushin shine ya qaru ya sa kai ciki, ya mayar da qofar ya rufe,kashe fitilar yayi, ya hau laluben hanya, yana kaiwa bakin qofar shiga d'akin ya ga duhu ya mamaye ko ina, alamar ta kashe fitila itama, ta bangaren Eamaan kuwa tinda ta ji kashe fitilar parlor ta san ba lafiya ba, sannan ta ji ana taku a hankali, tinanin ta ya bata kawai b'arayi ne suka shigo, wayar ta ta laluba ta kira Alhaji,sai dai tana ta ringing bai d'aga ba, ajewa ta yi ta miqe, ta d'akko tiraren ta, ta lab'e a bayan qofa bayan ta kashe wutar, hasken waje ke ratso labulayen yana shigowa cikin d'akin nata ,zuciyar ta kamar zata fito waje dan tsoro, hawaye ta fara yi dan kuwa hankalin ta ya yi matuqar tashi, qirjin ta sai d'agawa yake saboda shiga damuwar da ta yi, a hankali ya murd'a qofar ya qarasa shiga ciki d'akin nata............... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 8: Qafa ta saka masa ya kife a qasa, cikin zafin nama ya yunqura zai tashi ta fesa masa turaren  da ta d'akko a fuskar shi, sannan ta sa bayan hannunta ta buga masa a baya, gwangwanin turaren ta d'aga sama ta kwad'a masa a kafad'a da qarfi, yana son ya yi ihu dan azabar da yake sha hannun Eamaan amma babu dama,saboda baya son asirin shi ya tonu, da lalibe ta kunna fitilar d'akin,Sahabee ya bayyana duqe a gaban ta, haɗe hannayen shi d'aya cikin d'aya yayi yana zubda hawaye a idanun shi ya hau bata hakuri, mamakin ganin wai Sahabee ne ashe ya ke wannan iskancin a cikin wannan daren me ya zo yi to a d'akin nata Sata Ko fyad'e? Sahabee ya gama cika mata ciki wannan karon dan haka haushin shi take bala'in ji, ta tabbata ba shi da cikakkiyar tarbiyya ko kaɗan, d'aga hannunta ta yi da nufin yin magana sai dai kalma d'aya ta kasa fita daga bakin ta,takaicin shi ya tokare mata kowacce kafa da amon sauti zai fita a wuyan ta,cije leb'en ta na qasa ta yi cike da takaici,yawo ta fara yi a d'akin ta kai ta dawo ta Kai ta dawo a gaban shi,qoqarin tashi ya yi zai gudu,Eamaan na ganin haka kuwa ta yunqura itama cike da wani irin zafin nama da bata san ta na da shi bama ta fizge shi ya yi baya, hannunta ta d'aga ta wanke shi da Mari sannan tace masa, "Guduwa za ka yi? Ai ba inda zaka je se ka Sanar da ni me ya kawo ka sashe na a wannan Daren har da kashe min fitila, kashe ni za ka yi ko me?" Sahabee ya tabbata in ya Sanar da ita gaskiyar abinda ya je yi a sashen ta har maganar ta Kai wajen Yayan shi kashin shi ya bushe,ya san dikkan wasu sirrikan shi manya da qanana za su bayyana, dan haka cikin kuka irin na 'yan bariki ya zube a gaban Eamaan ya na bata hakuri, tare da fad'in  tsautsayi ne ya kawo shi,amma ba shi da wani qudiri mummuna a ran shi. Yanda yake bata hakuri ya fara karyar da zuciyarta ta yarda ba shi da wata manufa da ya je, dan haka cikin dakewa ta ce Masa "Zan rufa maka asiri dan kuwa wannan abun kunya ne ace wai qanin miji na ke bibiya ta,sannan dan rashin lafiyar Iya bazan so maganar nan ta fita ba,sannan ba zan so b'ata zumuntar dake tsakanin ka da ɗan uwan ka ba, amma ka sani duk sanda ganganci ya sa ka qara kallona ka bari muka haɗa ido da kai a cikin gidannan ma, Hmmmmm," Wata dariyar da ta matuqar tsorata shi Eamaan ta saki, dariyar da ya kasa gane ma'anar ta,wai yau shi da yake bariki me lasisi a qasar masu kwale shi ake yiwa haka,shi ɗin uban bariki reshe ya juye da mujiya. A yau ya gane ashe barikin ma suna ta tara, lallai yau ya tabbatar da cewa mace sai ta so duk wani iskanci zai wakana tsakanin ta da namiji,murmushi kaɗai ya isa ya ja ragamar afkawa zina balle har a kai ga yin magana da juna. Yau ya gane cewar ashe ba kowacce mace bace yar iska,Sahabee kuka yake yi sosai na baqin cikin ganin shi qasqance gaban yarinya qarama kamar Eamaan ta na yanka masa gargad'i bayan ya yi masa duka,qasan ran shi kuma yana kukan takaicin rasa babbar damar kashe qishin ruwan shi akan Eamaan, gefen idon shi ya yi jawur inda turaren yayi nasarar shiga ciki, umartar shi ta yi daya fice maya daga waje kafin ta sake sanya masa turaren a idanun shi,ai kuwa da gudu-gudu ya miqe zai fice daga sashen nata, Eamaan ta daka masa tsawa ya dakata tace, "Wannann jakar taka da takalmin ka d'aya da ka bar min anan uban wa zai ɗaukar maka," "Bbbaaaabaaa kowwaaa, niiii zannnn d'auuuke abu na" Wurga masa ta yi ya ɗebe su da hanzari ita Kuma  ta danna qofar ta rufe da makulli, kuka ta zauna a wajen tana yi sosai,zuciyarta ta yi mata kunci, wannan shine babban misalin in kayi zina da 'yar wani ko matar wani ko qanwar wani ko mahaifiyar wani kaima za a yi da naka,ficewar motar Alhaji da taji ne ya sanya ta je ta dakko Ice cream ta sha ko ranta zai yi sanyi amma ina bata samu abinda take so ba, nan take taje ta dauki qur'aninta ta fara karantawa ko zai ɗauke mata damuwar dake ran ta, ta fara kenan ta ji shigowar mutum ashe qanin mijin ta ne,ajiyar zuciya ta yi ta goge hancin ta dake d'igar da hawaye da majina,ta tabbata Alhajin na su sai gobe a ganshi tinda ya tafi wajen matan banzan shi, kuka ta ci gaba da yi sosai zuciyar ta kamar ta fito waje dan qunci, wannan wace irin rayuwa ce,Allah ya sani a rayuwar ta bata tab'a hango ta zaune da kishiya ba ita da Anwar d'in ta sai gata a gidan me mata biyu ya qara masu da wasu matan banzan a waje lallai bahaushe ya yi gaskiya da yace qaddara ta riga fata,a yanzu Allah kaɗai yasan iya adadin matan da Alhaji ke bi da wanda ya lalata ba tare da amincewar su ba, cikin kukan da take yi ta kalli sama tace, " Yah Allah ka qaramin hakuri da juriya, Allah ka sani daga bayin ka masu godiya," Sai ta miqe ta share hawayen ta duk ta hada zufa sosai kamar wadda ta yi dambe, ko yake ai qanin damben tayi ma, wanka ta dad'a shiga ta yo tare da d'aura alwala ta zo ta saka doguwar riga, tirarukan ta masu sanyin qamshi ta fesa,ta zira dogon hijabin ta a saman kayan ta sannan ta fara nawafil, ba ta San iya adadin raka'a nawa ta gabatar ba saboda yawan sallolin da ta yi,lokacin da taji ta gaji sai ta sallame ta zauna ta ta fara karanta 'Qur'ani tana idarwa, ta yi addu'o'i ta shafa, tasha kuka a wajen addu'ar sosai, kanta jingine da jikin gado bacci mai daɗi da nauyi ya ɗauke ta. Sahabee kuwa yana fita ya hau waige-waige baiga kowa ba sai da yaje dab zai shiga bangaren su mai gadi ya fito daga d'akin shi ya gan shi, Hajiya Qarama da ta ji motsi ce ta leqa tace waye nan, muryar shi na rawa yace, " Ni ne Sahabee," Sake labulen ta yi tare da sake tsakin ta koma,me gadi ne ya dalle shi da fitila, yana ganin shine ya sauke ya fad'a d'akin shi, dan ya san rashin mutuncin Sahabee kala-kala tinda ya sha yi masa, dan haka ya na iya masa rashin mutunci akan haska shin da ya yi da safe,shi kuwa Sahabee yau ba wannan ne a gaban shi ba, tinani yake yi kala-kala  ga wani mugun tsoron Eamaan da ya ke ji na qara shigar shi a duk sanda ta faɗo masa a rai, bud'ewa ya yi ya shige sashen Iya direct d'akin shi ya je ya aje jakar shi ya faɗa toilet, wanka ya yi ya fito ya wanke kayan da ta fesawa tirare a jiki, dan gaba daya qamshi yake yi irin na Eamaan ɗin,a cikin toilet ɗin ya shanya su ya fito d'aure da towel,kallon kanshi ya yi a mirror yaga irin kyaun qirar da yake da ita 'yammata na mutuwa akan ya kwanta da su amma Eamaan ta yi masa wannan gagarumin wulaqancin da tozarcin,duk kyawun jiki da kyawun fuskar shi amma matar tsoho ke gudun shi take wulaqanta shi. Murmushi ya yi ya tabbatar wa kan shi lallai bahaushe ya yi gaskiya da yace abincin wani gubar wani, ashe ba kowacce mace bace zata zauna ta ci amanar mijin ta da wani a wannan zamanin kamar yanda yayi zato? Sannan ba kowacce mace bace ballagaza mara kamun kai,ashe akwai sauran matan kirki da ke kare daraja da qimar aure komai kyau da kud'in namiji ba za su bishi ba? Matan dake jiran sakamakon su na alkairi a wajen Allah, yau ya tabbatar da cewa komai rashin samun yanda mace take so a wajen mijin ta akwai na k'warai da suke jiran ladan su na haƙuri a wajen Allah ba su kaucewa hanyar gaskiya saboda bin son zuciyar su, rigar shi ya ɗauka a wardrobe ɗin shi ya saka ya haye gado, sai dai Sahabee ya kasa bacci sam, a kowanne second qara ganin girman Eamaan yake, sannan wani irin kwarjinin ta na cika qirjin shi, Hajiya Babba ya tina da ta ke yi mai waya a koda yaushe sannan take manne masa akan tana so ya dinga neman ta, rintse ido ya yi ya toshe kunnen shi, dan kuwa wata iriyar nadama yake jin tana son shigar shi wadda be shirya mata ba a yanzu sam,gani yake yi kamar akwai sauran nasara ko ta ɓangaren Hajiya Babba zaina ci gaba da rage zafi, tinda in yana nan ba ya zuwa wani waje sosai saboda Iya tafi son ganin shi a gida. Tun da asubar fari Eamaan ta farka daga bacci duk jikin ta na yi mata ciwo,bayan ta yi sallah ta kammala duk wata ibada da ta saba yi bayan sallar asuba sai shirya ta fito zuwa wajen Iya,a hanyarta ne taga motar Alhaji na shigowa gidan,sai ta tsaya ta ɗan kalle shi fuskar ta tayi kicin-kicin saboda tsabar ɓacin rai, sai da idon shi ya shiga nata ta sa kai ta yi gaba, gaba ɗaya ta zare masa laka da kallon da ta watsa masa,dan haka da kyar ya qarasa shigowa, ya fita ya yi bangaren Hajiya Qarama, wadda ya tarar itama ta yi kicin-kicin da rai,ko kula ta bai yi ba ya wuce d'aki ya yi wankan tsarki, ya fito sanye da towel iya qugun shi, Hajiya Qarama ce ta hau bin shi da kallon buqatar mijin nata amma kuma wata zuciyar na qissima mata Jin haushin shi. Bayan ta manta itama ta na da nata laifin wajen fitar shi yawon banzan, saboda qazantar ta da rashin kula da miji. Goge jikin sa yayi ya shafa mai da tiraruka ya zira jallabiya da dogon wandon ta ya nufi ɓangaren Iya, a kitchen ya Jiyo motsin Eamaan,ita kuwa tana can tana so ta markad'a waken da tasa tin jiya mai aiki ta sirfa mata dan ta yi qosai da safe da shi,sai ta sake wankewa albasa da attaruhu ta saka ta markad'e sannan ta juye  markad'add'en waken a wani bowl mai fad'i, ta saka zallan gishiri sai dan farin maggi kaɗan da onga green ɗin, saboda in ta saka maggi dunqule yana watsewa a mai, baya haɗe jikin shi ya tashi yanda take so,bugawa ta hau yi sosai kafin nan ta fara soyawa,tana yi ta na duba kunun gyad'an da ta ɗora, bayan ta gama ne ta zuba ma kunun nono irin asalin kindirmo ɗin nan, nan da nan kunun gyad'ar ya qara yin fari tass, ta zuba su a flask ta saka plate ɗaya cup ɗaya, dan bata son ta saka biyu a san ta san da dawowar Sahabee, tana jiyo Alhaji na gaida Iya suna hira sai ta ja ta tsaya dan kuwa bata son ganin shi sam. Wani irin kyankyamin shi take ji yanzu, amma haka danne ɓacin ran ta ta ɗauka  ta shiga da sallama, Iya na ganin ta yawun ta ya tsinke dan ta san zata ci mai daɗi ,amma dan mugun rai sai ta b'ata rai, Sahabee ne ya buɗe qofa zai fito daga d'akin shi saboda yunwar da yake ji,ya na Jin Eamaan a parlour ya yi  maza ya koma d'akin shi ya danna lock ɗin qofar ya rufe yana haki,ba wanda ya san da yana ciki sai qarar danna qofar shi suka ji, bin hanyar su ka yi da kallo baki d'ayan su, Eamaan kuwa da ta San ko waye a dakin  ba ta juya ba ajiye abincin ta yi zata bar wajen. Iya kuwa umarni ta bawa Alhaji dan ya leqa yaga waye a d'akin Sahabee bayan Sahabee baya nan lokaci ɗaya kuma tana dagawa Eamaan hannu ta dakatar da ita, cike da tsoro Iya ke kallon wajen, Eamaan da taga hankalin su ya yi wajen, se kawai ta yi murmushi ta fice daga ɓangaren gaba ɗaya ba tare da ta bi ta kan umarnin Iya dake tsaida ita ba, sashen  sauran matan ta je ta gaida su kamar yanda ta saba sannan ta  wuce nata wajen. Alhaji na leqawa ya ga Sahabee a tsaye sai wurga ido yake yi, a zaton shi Eamaan zuwa ta yi ta faɗa musu me ya faru tsakanin su a daren jiya,ko da ba qarar shi ta kai ba baya son su sake had'uwa da Eamaan idanun ta na rikita shi kwarai da gaske. Eamaan na da wata baiwa da be tab'a had'uwa da mace kamar ta ba, kasa cewa komai ya yi da Alhaji ya nuna farin cikin ganin shi sai ya hau yashe haqora yana yaqe. "Yaushe ka dawo?" Qeya ya sosa kafin yace, "Jiya da daddare na dawo na isko kowa ya yi bacci, kawai sai ban tada kowa ba nima na kwanta, ina kwana Yaya?" Gaisawa suka yi sannan suka qarasa wajen Iya,tana ganin shi ta tashi tsaye tana washe baki murna a wajen ta kamar wanda ya b'ata aka  ganshi, sosai ta ji dad'in dawowar tashi, waya ta ɗauka tace bari na kira Eamaan ta zo ta haɗa maka abin karyawa, wata sufa ya yi ya damqe wayar yana in ina yace , " Baattaa kawaiii zan ci ko me aka dafa maki, ni daga yanzu ma ana haɗa mana abinci kawai ba sai an yi wa kowa nashi daban ba," Daga jin yanda yake maganar kasan akwai wata a qasa duk zufa ta tsattsafo a goshin shi kamar wanda ya yi gudu,mamaki ne fal a cikin ran su bama ya Alhaji wanda ya san halin Sahabee na son takurawa Eamaan ɗin ,nan take ya d'iga wa Sahabee alamar tambaya, tabbas akwai wani abu a qasa, yana ganin irin kallon da Alhaji ke bin shi da shi sai ya hau yaqe yana faɗin, "Ya naga duk kunyi shiru kuna kallo na? Na yi tunani ne saboda rashin lafiyar Iya na daina duk wani rashin da'a ko BIYAYYAH danake yi a baya,daga yanzu na dena qasqantar da na qasa dani," Murna ce ta cika zuciyar Iya a lokacin da ta ji kalaman autan nata, abinci Iya tai ta d'ura masa, shiko sai kwashewa yake yana ci dan kuwa ya yi kewar abincin Eamaan sosai. Eamaan na isa sashen ta ta rufe bangaren ta ta fara gyara gidan, ta goge shi tsaf, sannan ta haɗawa kanta oatmeal dan ta sha,zaune take saman dinning table ta na  wasa da spoon ɗin a cikin qaramin bowl ɗin da ta had'a oatmeal, wani tunani ya faɗo mata a rai, yau mijin ta ya je neman mata ya ci nasara a neman matan nashi,ita kuma qanin shi ya je neman ta Allah ya tsare ta wanda hakan baya rasa nasaba da kullum cikin sallolin ta na farillah da nafila tana neman tsarin Allah akan zina da dik abinda zai kusantar da ita wajen aikata zinar, musamman ma a wannan zamanin da zinar ta yi katutu a zuqatan mutane, ya zata yi a lokacin da jarabawa ta afka mata qanin shi ya ci nasara akan ta? kwallar ta ta share sannan ta kawar da wannan tunanin a ranta da addu'ar Allah ya ci gaba da bata kariya, sannan ta qarasa abincin ta ta wanke bowl din ta ajiye a inda ya dace ta fita daga kitchen ɗin, d'aki ta shiga ta fad'a bathroom ta yi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba balle wata kwalliya ta zira riga ta  kwanta baccin safe, nan take kuwa wani bacci mai dad'i ya ɗauke ta, Alhaji yazo ya yi ta bugun qofar ta  shiru ba ta bud'e ba, gashi ya San ba ta saba rufewa ba, kad'a kan shi yayi ya koma ɓangaren Hajiya qarama, wadda har a lokacin bata yi wanka ba, d'aki ya nufa shima ya rufe ya kwanta, wayar shi ya duba yaga missed calls din Eamaan a jiyan nan da nan yaji tashin hankali da damuwa sun mamaye shi, dan ya tabbata hakan ne ya sata fushi har ta qi buɗe masa qofa,ya qudurta kome zai faru zai shawo babyn shi tinda shi yayi mata laifi, kuma zai qoqarin daina bin mata kamar yanda take buri. Alhaji ya samu nasarar shawo Kan Eamaan ta hanyar yi mata alqawarin dena bin matan banza a waje, ita kuwa sai ta sanya shi ya yi alqawari tsakanin shi da Allah ta nuna masa cewar Allah yake sab'awa ba ita ba,sannan ba Iya ba ba matan sa ba, Allah shi ke da wuta ya ke da aljannah, idan ya tuba ya dena cikin Rahamar Allah sai ya Sanya shi a aljannah, idan ya qi tuba ya ci gaba da aikata zina se ubangiji ya azabtar da shi da wutar shi, kar ya manta wutar duniya ma ba ya iyawa da ita balle ta lahira, da wannan nasihar Eamaan ta samu nasarar hana Alhaji Abdullahi yawon dare, ya kame kan shi ya ke qoqari wajen danne buqatar shi ta bin matan banza a duk sanda be samu yanda yake so ba a wajen sauran matan nashi,a haka yake hakuri ya Jira har ranar girkin Eamaan ɗin ya zagayo ko girkin Hajiya Babba, ita Kuma Eamaan sai take hakuri da danne duk Wani rashin so da qin kusantar ta da yake ta na nuna masa ta na so, Kuma ta na Jin dad'in kasancewar su tare a koda yaushe. A kwana a tashi Eamaan da Alhaji suna ta samun kusanci da junan sj da shaquwa,sai dai har yanzu babu wata soyayyar shi a ran ta sai girmamawa, komai nashi ta sani Kuma yana yin shawara da ita sosai. kwatsam watarana Alhaji Abdullah ya tashi da ciwon baya se yake sanar da ita, Eamaan tayi masa sannu sannan ta bashi maganin ciwon jiki ya sha, abu kamar wasa ciwo kullum na gaba har dai watarana suka shirya dan zuwa ganin likita game da ciwon bayan nashi fatan ta Allah ya sa ba wata mummunar cuta bace ta kama Alhajin nata......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 9:  Gaba ɗaya rayuwar Alhaji ta zama sai a hankali saboda yawan jin kasala a jikin shi da yake fama da ita,haka tafukan hannayen shi da qafafun shi suke kumbura,kai hatta da fuskar shi ma ta hau ta yi haske, uwa uba yawan jin qaiqayi da yake a jikin shi duk yafi damun shi saboda yawan susa da yake yi ba ya jin sauqin qaiqayin, sai dai ma da ya gama susar wasu quraje ne suke fito masa qanana a jikin shi,idan kuwa ya je yin fitsari to fa da kyar yake iya yi, rabon shi da Kashi kuwa ya kwana biyu, abubuwa dai sun taru sun yi mai yawa. Randa zasu je asibitin ya kama ranar girkin Hajiya Babba ne, ta sha kwalliyar ta kamar yanda ta saba suka shiga mota ita da Alhaji suka zauna a baya Sahabee da driver kuma na zaune a gaba, suna zuwa aka bashi gado, likita ya rubuta wa Alhajin gwaje-gwajen da ya Kamata a masa dan danin makamar ta inda za a yi masa magani, dik da cewa already akwai ciwon da yake zargi shi ke damun Alhajin duba da symptoms ɗin da suka bayyana a jikin shi. Ai kuwa gwajin  farko suka gano gaba ɗaya qodar shi sun samu matsala, d'aya ce kawai me ɗan sauqi-sauqi, akwai yiwuwar in ya sha magunguna aka wanke masa ita zai iya samun sauqi, hankalin Hajiya Babba da Sahabee ba qaramin tashi ya yi ba da jin wannan mummunan labarin,sanda suka yi waya suka sanar a gida kuwa kowa ya shiga  damuwa, a haka likitan ya bashi duk wata kulawa da ya Kamata a bawa mai irin ciwon. Iyalan Alhaji Abdullahi su na iya bakin qoqarin su dan bashi magani akan lokaci da bashi kulawar da likita ya umarta a bashi, duk da sun so matuqa a fita waje da shi amma likitan ya musu alqawarin za su bashi kulawa kamar ya na qasar waje,abokan shi na siyasa sun shiga damuwa Suma duba cewa kusan shi ne jigon jam'iyyar tasu, gashi mutane na son shi da girmama shi, addu'a suke tayi da fatan Allah ya tashi kafad'un shi. Matan Alhaji kuwa shifting ɗin zama a wajen shi suka fara yi kamar ma'aikatan gwamnati, in girkin wannan ya fita wannan ta zo, duk ranar da ta kasance ranar girkin Eamaan ne tofa ranar sahabee ba shi a zuwa asibiti, dan tinda abunnan ya faru yake toshe duk wata kafa da zata had'a su a waje guda. Wata rana Iya ta kira Eamaan sashen ta, duk da cewar washe gari ne zata karbi girki, kimtsawa ta yi ta saka hijab din ta ta fita zuwa wajen Iya, tana zuwa ta tadda ta da himilin rake a gaban ta,Eamaan zama ta yi ta tankwashe qafa a gaban Iya ta gaida Iyar,cikin tsuke fuska Iya tace wa Eamaan. " Ni ba gaishe-gaishe ne ya sa na kira ki nan wajen ba, ammmm kina jina ko wannan raken nake son ki samu ki markad'en shi ki tacen ruwan sa kamar yanda na ji ki a waya rannan kina gayawa wata,jarababbiya kamar ki wai har kin san hada maganin mata da rake, to ni na lafiya zaki haɗawa d'ana yanzu ba na kayan jarabar taki ba, dan haka ki kama ki markad'e shi kar ki sa masa wani kayan qamshi da madara, kawai zallan ruwan nake so a tace a saka a jug a kai masa ya shanye, dan naji ance ruwan raken yana wanke qoda," kanta a qasa cike da takaicin abubuwan da Iya ke yi mata ta ke ta gyad'a kai alamar amsawa,a zahiri dai gashi ita ake mora amma ita ce sharar gidan, fuskar ta cike da murmushi da annuri ta d'ago kanta ta kalli Iya tace, "To Iya yanda kika ce haka za a yi Allah ya bawa Alhaji lafiya," Cike da mamaki Iya take bin Eamaan da kallo, cikin taɓe baki da harara yace wa Eamaan ɗin, " Wai ke bakya fushi ne?" " Iya dawa zan yi fushin, da ke? Allah ya sawaqa na yi fushi dake,Allah kuma kar ya nuna min ranar da zan yi fushi da ke ,domin kuwa ke uwa ce a wajena d'an kirki kuwa baya fushi da iyayen sa sai ya zama marar rabo duniya da lahira, kuma ni na tabbata ba wai so na ne baki yi ba, wataqila wasu daga halaye na ne baki so, inshaa Allah kuma zan yi qoqarin gyarawa na zama d'iya ta gari me neman albarkar ki a koda yaushe, in kuma abubuwan da kike man dan kawai ki baqanta min ne kina son ganin fushina.... Hmmmmmm Iya kar Allah ya nuna maki fushina,"  Ta qarashe maganar ta cikin wani murmushin da ya sa Iya shan Jinin jikin ta,nan take ta ji yarinyar tayi mata kwarjini matuqa, a cikin kalamanta akwai hikima kuma a kwai tsantsar gaskiyar abinda ke ran ta, had'iye yawu Iya ta yi makwattt ta jingina da jikin kujera tabi bayan Eamaan da ke cike da mazaunai da kallo, nan take ta hau karantar wasu abubuwa daga halittar ta,kauda tinanin ta yi daga ranta ta miqe ta shige d'aki. Eamaan na gama had'a ruwan raken a jug ta yi sallama d'akin Iya ta  faɗa mata ta gama, Iya kuwa cewa ta yi ta bawa Sahabee ya kai asibitin sai ta amsa da "To" ta fita, har yanzu jikin Iya a sanyaye yake da kalaman da Eamaan tayi mata,dan haka shakkar yi mata rashin mutunci direct take yi kamar yanda ta saba yi a baya, dan kuwa  da dane sai ta yada mata da baqar magana kafin ta bata izinin tafiya. Eamaan kuwa fita ta yi farfajiyar gidan riqe da jug a hannu wanda ta saka cikin wata leda babba mai kauri,tafe take tana leqa wurare ta na neman Sahabee, tinda koda ta duba d'akin shi bata gan shi a can ba,hanyar backyard ta yi dan da damar lokuta yana zama wajen ya ɗan yi bushe-bushen kayan mayen shi ya sha iska, dai-dai zata gilma ta bangaren Hajiya Babba ta jiyo nishi irin na nishad'i ɗin nan,mamaki ne ya kama ta dan tasan dai Alhaji na asibiti bashi da lafiya,sai dai kuma kamar muryar shi take jiyowa, ɗaya muryar kuwa tabbas ta hajiya Babba ce shin meke faruwa ne a gidan? Qara matsawa ta yi sosai ta jikin window ta ji ana magana cike da nishad'i ana faɗin, "Wai yau Hajiyata me kika sha ne haka gaba ɗaya kin sa tin d'azu na kasa hakura dake? gaskiya Yayah yana morewa da yawa, amma tsabar rashin rabo yake tafiya yawon neman mata," Hajiya ma sambatu take yi tana faɗin, "Sahabeena bana so ka gaji kaga yau 'yar sa idon tamu tana asibiti da yara, waccan kuwa in ta kulle kan ta a d'aka ba fita take yi ba, balle kuma Iya da ta tsani zuwa sashe na, yau ai kaga sai mu kwana muna morar juna,mun dad'e bamu samu dama irin haka ba," Wata razana Eamaan ta yi ta ja da baya hannun ta sai rawa yake yi saboda tsoron da ya kamata, hankalin ta ba qaramin tashi ya yi ba,nan da nan idanu ta suka kawo ruwa suka fara zuba, bakin ta na rawa ta furta, " Sahabee da  Hajiya Babba?" A hankali ta fara takawa jiki babu k'wari ta lallab'a ta bar wajen, wajen mai gadi ta je ta damqa masa Jug ya kai asibitin, dan kuwa bata Jin zata iya komawa ta jira Sahabee ya gama tambad'ewar shi ta bashi saqon, a hankali ta ce ya bawa driver in ya dawo daga kai Hajiya Qarama asibiti ya koma ya kai asibitin ko kuma shi ya hau abun hawa ya kai, in kuma yana da no shi ya kira shi yanzunnan ya dawo ya Karb'a ya kai musu a bawa Alhaji, tana tafiya mai gadi ya tsaya yana kallon ta,sai yaga gaba ɗaya kamar hankalin ta a tashe yake, tausayin ta ne ya kama shi,dan yasan wataqila hajiya masifa ce ta sata a gaba, ko kuma Alhaji qarami(Sahabee) addu'a yayi mata a ran shi na samun sauqi akan komai dake faruwa a gidan, (wannan shine ya dace da kowanne musulmi, yi wa dan uwan ka addu'a a zuciyar ka a yayin da ka fuskanci yana cikin damuwa, in kana da hali ka taimaka masa ya fita a damuwar, in kuma babu,ka yi mai addu'a, ko ka hada dika biyun).   Direct ɓangaren Hajiya Babba ta nufa cikin ɓacin rai da qunar zuciya,cikin sa'a kuwa ta samu qofar farko ba a rufe take da key ba, murd'a wa ta yi a hankali ta shiga,nishin su kawai ke tashi a d'akin wanda hakan da Eamaan ke ji qara mata radadi a ranta yake. Hajiya babba ta girme wa Sahabee nesa ba kusa ba, amma ta bude masa jikin ta yake amfani da ita kamar matar shi,fuskar ta sharkaf da hawaye ta samu waje ta zauna ta ci kukan ta ta share hawayen ta tass, Eamaan ta koma kamar wata wadda bata taba sanin ya ake yin murmushi ko dariya, duk wanda ya kalli cikin idon ta mai baiwar tsorata duk wani mara gaskiya sai ya kusa sakin fitsari a jikin shi, tankad'a qofar tayi nan take suka zabura suka juyo cike da kid'ima da tashin hankali,kwance suke a rufe cikin bargo,hajiya babba ce a sama da wasu sakakkun qirjin ta da suka yamushe, in ba ma bariki ba dai da son aikata sab'on Allah yana saurayi me zai da mace kamar hajiya? Ido suka zaro cike da tsoro, wanda Sahabeee ya fi Hajiya shiga tashin hankali dan kuwa ya san wacece Eamaan a yanzu, rufe qofar ta yi ta koma ta zauna a kujera doguwa tana girgiza jikin ta tana jiran fitowar su, a sukwane Sahabee ya ture Hajiya daga saman shi ta kuwa faɗo qasa timm kamar buhun masara a saman hannun daman ta, wata iriyar qarar azaba ta saki ta fashe da kuka saboda azabar da ta ji ta ratsa ta, bata raba ɗayan biyu ko ta samu karaya ko kuma targad'e ,a haka ta miqe ta kama hannun ta tana nishin wahala dan kuwa da ke gaban ta yafi wannan tashin hankali, a haka ta zura kayan ta itama ta bi bayan Sahabee da ya yi waje daga shi sai gajeran wando, riga da dogon wando da hular shi a hannu ya riqo su ya fito kamar kwarto. A zaune suka tadda ita ta kura masu ido kawai tana kallon su ba tare da tace komai ba, shiru suka yi suma se zufa ke karyo musu,kowa kai duqe a qasa kamar suna gaban magabatan su, Hajiya Babba da Sahabee kuwa na jin yanda zuciyoyin su ke ta bugawa kamar ta bar qirjin su saboda damuwa, Sahabee ya fi Hajiya shiga tashin hankali idon shi ya kad'a ya yi jawur,Hajiya Babba kuwa jikin ta banda rawa ba abinda yake yi,ga azabar da hannun ta ke yi ta mata yana zogi da rad'ad'i,ta rasa ina zata saka kanta. A wajen su kuwa da wannan kallon da Eamaan ke bin su da shi gwanda ko duka ne ta rufe su da shi, sai da ta kai wajen minti goma tana kallon su sannan ta miqe kawai ta yi waje ba tare da ta ce musu ku ci kan ku ba, cike da d'imuwa suka kalli juna shin me hakan ke nufi? "Wani zata gaya wa Ko me?" Hajiya Babba da ta gigice ta kalli Sahabee ta yi masa wannan tambayar. Shima cikin damuwar ya amsa ta da cewar. "Indai Eamaan ce ba zata fad'awa kowa ba, sai dai zamu azabtu da ganin ta a cikin gidan nan Hajiya, duk sanda kika ganta ko kika ji muryar ta sai hankalin ki ya fi na yan gidan yari tashi," " Ya akai kasan ba zata faɗa wa kowa ba? Ta kama mu tirmi da tab'aryar kace bazata fad'awa kowa ba? Ka ko san me hakan ke nufi? Baka da hankali Sahabee, tabbas yarinyar nan ta zama masifa a cikin gidannan, ban taɓa ganin irin wannan kallon kashe wanda ake kallo ba sai a wajen ta, lallai gaskiyar bahaushe ne da yace Ido guba Kuma kallo zai iya kisa, yarinyar nan da ta zuba mana Ido ji na yi kamar zan had'iyi zuciya na mutu, rasa inda zan saka Kai na na yi" " Hmmm nina faɗa maki ba zata sanar da kowa ba, amma kam a wajen ta bamu isa koda gilmawa ba," Se a lokacin ya kula da hannun Hajiya Babba ya kumbura, cikin tsoron ganin yanda hannun ya haye yace, "Hajiya meye wannan naga hannun ki ya kumbura?"   Harara ta maka masa ta miqe daga duqen da Eamaan ta sa su yi na dole, ta fara takawa tana faɗin, " Ba kai ka wurga ni qasa ba na fada ta hannun," zuwa yayi ya kama ta suka zauna ya ja mata hannun dan kuwa baya jin zai iya binta ake wajen masu gyara, tana ihu tana komai ya gyara mata hannun ashe targad'e ne,kafin ya fita sai da suka jaddadawa kan su dole su hakura da juna na wani lokaci kafin su san abun yi. Eamaan kuwa da ta koma d'akin ta ba qaramin kuka ta sha ba, yanzu da Anwar ɗin ta ta aura duk ba zata ga waɗannan abubuwan ba tashin hankalin ba. " Allah kai ne masanin abinda ke b'oye da wanda ke fili Allah ka kawo min mafita, ka ban ikon cinye wannan jarabawar ,shi Kan shi ganin mutane na aikata zunubai irin wannan jarabawa ne,ya hayyu ya qayyum kar ka jarabce ni da aikata Zina da duk Wani abinda baka so" Hawayen ta ta goge ta kwanta tana ta tinani har bacci ya yi gaba da ita. ********************* Washe gari ta shirya zuwa asibiti bayan ta yi wa alhaji girki mai daɗin data saba,ta leqa wajen Iya ta gaishe ta sannan ta fita driver ya kaita, a ranar ne su Amman ta suka je duba Alhajin suma har da Hafsat da Mama aka je, tana ganin su ta fara murna fadawa ta yi jikin Ammahn ta, cike da shagwab'a take magana, " Ammah baku taɓa zuwa ganina ba sai ta dalilin rashin lafiyar Alhaji kuka zo asibiti,gobe fa za a sallame mu da bari ma kuka yi kuka je gidan kawai," Alhaji ne yace, "Gaskiya dai kam Hajiya ya akamata ku yi wa Eamaan zuwa na musamman, kullum sai ta yi maganar rashin zuwan ku gidan ta," " Inshaa Allahu Alhaji za mu zo gaba ɗayan mu har Daddyn su mu gaida Iya sai a gaggaisa baki ɗaya,dan dama muna da niyyar zuwa ɗin," " Allah ya sa to" In ji Eamaan dake murnar jin kalaman Mama. Gaishe gaishe aka shiga yi,tare da tambayar me jiki, anan zauna har a zahar kafin suka tafi,Eamaan ta ji dad'in ganin su sosai. Washegari aka sallame Alhaji ya koma gida,a bangaren Eamaan ya sauka ya ji sauqi sosai kamar be tab'a ciwon ba, tinda an cire masa qodar da ta lalace dika, d'ayar Kuma ta yi sauqi ,sannan likitoci sun dora shi akan abinci da abubuwan da ya kamata ya kiyaye, Iya se murnar samun sauqin shi ta ke yi, har lokacin nan Alhaji bai ga Sahabee da Hajiya babba sun je duba shi ba, ya yi tambaya amma ba wanda yasan dalilin rashin zuwan su, Alhaji bai bar bangaren Eamaan ba sai da yai kwana uku ya qara samu sauqi sosai,sannan ya koma bakin aikin shi. Bayan sati ɗaya yayi shirin komawa Abuja, taro ya kira a sashen Iya kowa ya taru amma banda Hajiya da Sahabee, Eamaan ce ta ce bari taje ta kira su, tashi ta yi taje d'akin Sahabee ta leqa ta ganshi sai safaa da marwa yake yi, a razane ya juyo yana kallon ta,cikin d'aure fuska Eamaan tace masa, "Na tabbata kai ba kurma ko bebe bane,kana jin neman ka da ake yi maka ko? ka na tinanin qin zuwan ka shi zai sa na fasa fad'in abinda na gani idan na yi niyya? To bari ka ji hakan da kake yi ne zai sa naji haushi na fad'awa kowa abinda ku ka yi," Daga nan ta ja dogon tsaki ta fice daga d'akin ,shi kuwa Sahabee ya hada gumi gaba ɗaya jikin shi har d'iga zufa take yi qasa daga hancin shi, ji yake yi anya ba zai fad'i meke faruwa ba da kan shi ya huta, gaba d'aya yarinyar nan na d'aga masa hankali in ya gan ta,ya tabbata da za a gwada jinin shi za a gano ya hau. A hankali ya sa hannu ya goge zufar da yake yi, bud'e qofar ya yi ya fita ya samu waje ya zauna a gefen Iya. Eamaan na shiga ɓangaren hajiya babba ta tarar da ita ta yi tagumi ga hannun ta ɗaya dake a kumbure ya ɗan fara sakewa idon ta ya yi jawur, dan tinda Sabeerahn Hajiya Qarama ta zo ta sanar da ita akwai taro a parlourn Iya hankalin ta ya tashi, ta rasa sukuni, tana ganin Eamaan kuwa sai ta miqe ta hau jan dankwali zata rife cinyayyen kanta da bata son d'aura masa d'ankwali, cikin yaqe tace, "Dama yanzu nake shirin fitowa na ji Alhaji na kira ko," Eamaan ce ta kalle ta ta kauda kai, dan jin tsanar matar take sosai da gaske a ranta " Hajiya wannan abubuwan da kuke yi ke da Sahabee su zasu sa kowa ya fahimci akwai wani abu, ni na wuce tsayawa ina faɗan abinda ku ka yi, tabbas kowanne ɗan Adam yana aikata zunubi, amma mafi alkairin bayin Allah shine wanda yake aikata sab'o kuma ya tuba, dan haka in kin tuba kin  huta, kin wa kan ki daidai,ki je Alhaji na jiran ku kar ya yi missing flight ɗin shi" Ta na gama fad'a mata haka ta sa kai ta fita, Hajiya kuwa ji ta yi kawai gwanda su faɗi me ya faru a tsakanin ta da Sahabeen su huta, musamman in aka tambaye ta game da hannun ta ba ta isa yin qarya a gaban Eamaan ba. Tana shiga sashen Iya................ *Eamaan tawa kin gagara.....tabbas gaskiya da ruqon amana tare da hakuri na saiwa mutum girma qima da kwarjini a idon kowa* [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   BIYAYYAH   💅🏼    WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 10: Shigar Hajiya Babba ke da wuya ta samu waje ta zauna a gefen Hajiya Qarama da ta bi hannun ta da kallo,harara Iya ta banka mata saboda dad'ewar da tayi bata zo ba, daga baya kuma sai ta gyara zama ta fara da godewa Allah da ya bawa Alhaji Abdullahi lafiya ya kuma dawo mata da shi gida lafiya, daga nan ta hau qorafe-qorafen ta na babu gaira babu dalili kafin ta bawa Alhaji Abdullah damar ya yi magana shima. Shima ya fara ne da godewa Allah da ya bashi lafiya ya dawo cikin iyalan shi lafiya daga qarshe ya godewa matan nashi akan qoqarin su a gare shi da dikkan d'awainiya da hidimar da suka yi tayi da shi a lokacin da yana kwance a asibiti,bayan nan ne ya sanar da su zai koma Abuja ana da buqatar shi a wajen hidindimun siyasar su. Kuɗi ya d'akko ya miqa wa kowa nashi kamar yanda ya saba, sannan ya jawa Sahabee kunne akan dad'ewar dare da yake yi. Niko nace wai kura ce za tace da kare maye,hannun Hajiya Babba ya kalla cikin mamaki ya ce, " Hajiya me ya samu hannun ki na ga kamar ya kumbura?" A ɗan razane ta kalli Eamaan da ta kauda kan ta daga kallon ta ta yi kamar ma ba ta ji tambayar da akai wa Hajiya Babba ba, nan da nan zuciyar dake shawartar Hajiyan akan ta faɗi me suka yi ta taso mata,cikin sauri Eamaan tace, " Alhaji ka gafarce ni d'azu na je gaishe  ta ne na buɗe qofar shiga tana wajen ban sani ba na buge ta," "Subhanallahi Allah ya kiyaye gaba, ke kuma kina k'wank'wasa qofa kan ki shiga waje gudun faruwar irin  hakan," Amsawa ta yi da zata kiyaye gaba sannan ta sake kauda kan ta daga barin kallon kowa a wajen, Sahabee da Hajiya kuwa zuciyoyin su babu dad'i dan hakan na qara sanya su a dogon nazari da jin tsoron me zai je yazo game da shirun Eamaan ɗin,muryar Alhaji suka ji yana faɗin, " Sahabee ka kai Hajiya Babba asibiti a duban hannun nata," " To Yayah," yace yana wani sunne kai qasa kamar na Allah. Daga haka sai Alhaji ya miqe ya fice zuwa ɓangaren Eamaan yana fita ba jimawa itama ta bi bayan shi, idanu suka zuba mata gaba ɗayan su har Iya, tana fita Hajiya qarama tace, "Ni fa ina ganin wani al'amari a wajen yarinyar nan, ban sani ba ko kun kula da hakan kuma?" Hankalin Sahabee da Hajiya Babba ne ya qara kid'ima suka faɗa tashin hankalin Allah yasa ba gano abinda suka aikata Hajiya Qarama tayi ba,cikin zumud'i Hajiya Babba tace, "Me kike nufi da maganar ki?" Iya ce ta karɓe maganar da cewa, "Tana nufin Eamaanii na ɗauke da juna biyu na haihuwa," A zabure Hajiya Babba da Sahabee suka had'a baki wajen faɗin, "Cikiii kuma?" Hajiya Babba ce ta dafe qirji da hannun ta me lafiya ta kalli Iya tace, " Iya ciki fa kika ce, yaushe ma tazo gidan har da zata yi ciki ni ina nan ina fama shekara da shekaru ban taɓa koda bari bane?to gwanda ma Hajiya Qarama ta ajiye waɗannan gajiyayyun yaran marasa jin magana, ni yanzu ina na kama babu d'a babu jika?" "Ya ko me zaki yi banda ki zubawa sarautar Allah idanu a yi abinda kike gudu babu ke? Ke kam yanzu in ba wani ikon Allahn ba ba wata haihuwa da zaki yi nan gaba tsufa ya riga da ya riske ki, dan haka kawai ki barmu masu sauran jini a jika mu yi ta haihuwar," Nan fa fad'a ya kaure a tsakanin su dama sun dad'e ba su yi ba,Iya data gaji da jin su ta daka masu tsawa, ta ce "To kaji kun fara ko? kai tashi ka d'ebo hatsin nan na watsa masu, ku tashi ku ban waje shashashan banza kawai,kuda bazaku taɓa zama ku samawa kan ku mafita akan komai ba sai faɗa da hauragiyar banza," Miqewa suka yi suka tafi sashen su kowa na harar 'yar uwar ta, Sahabee ne yabi Hajiya Babba ya ce mata zasu asibiti anjima ta shirya daga qarshe sai ya kashe mata ido ɗaya, d'aga masa kai kawai tayi sannan suka rabu, cike da murna ya shiga d'akin shi ya shirya don zuwan nasu asibiti, tin daga murnar da Sahabee yake yi mutum zai gane duk wanda ya Saba da bariki tana yi masa wuyar bari, har ya manta tashin hankalin da suka shiga lokacin da Eamaan ta kama su dumu-dumu suna aikata masha'a. Eamaan kuwa bayan sun koma ɓangaren ta da Alhaji ne ta samu akwatin da take haɗawa Alhajin kaya in zai yi tafiya Abuja, ta saka kayan duk da zai buqata wanda suka had'a da; manyan kaya da qanana,sai boxers da vest, man shafawa,brush, sai ta samu wani qaramin qur'ani Izu biyu ta saka a aljihun jakar,sannan ta saka turatuka, hula da dai duk abinda zai buqata, wata yar takarda na ga ta yaga guda biyu ta faki idon shi ta zauna ta yi rubutu a cikin su sannan ta saka ɗaya a tsakiyar wata babbar rigar shi, sai ta sa ka wata a wandon qananan kayan shi,bayan ta gama ne ta zauna ta kamo hanun shi ta zaunar da shi a bakin gadon su da ya sha gyara yana fitar da qamshi na musamman. Domin kuwa yanda take turara kayan ta da turaren wuta a kabbasa haka take turara zanin gadon ta da towels ɗin su na wanka shi yasa a koda yaushe qamshin su na musamman ne,kallon fuskar shi ta yi shima ya kalle ta cikin murmushi yace, " Eamaanii na wai meye sirrin ne kullum sai wani irin kyau kike qarawa,shin wai ma ni yaushe rabon ki da ki ga al'adar ki ne?" Gaban ta ne yayi wata muguwar fad'uwa saboda jin tambayar da yayi mata, nan take ta tuna cewar rabon ta da period yanzu ta kai wata uku, tana son ta faɗa masa amma sai ta fasa saboda halin da yake ciki, hankalin ta be taɓa kawo mata maganar ciki ba duba da tana yawan jin ciwon mara sai kawai ta sa a ranta maybe ta ɗan samu tsaiko ne amma zai zo, haka wata zai wuce ciwon marar ya lafa kuma jinin be zo ba, a sanyaye ta bashi amsa da, " Watana na uku kenan," Jan ta yayi jikin shi sannan ya ɗora ta a kan cinyar shi yana shinshinar wuyan ta da alamar murna ya zira hannun shi a rigar ta yana shafa cikin ta ba tare da ya ce komai ba, yana so ya more wannan yanayin da suke ciki me daɗi kafin Allah ya dawo dashi daga tafiyar da zai yi ya kaita a gwada ta a ga me yake faruwa da ita, a hankali Eamaan tace masa, " Sweet ! ina son nayi maka wata magana amma bana son ka ɗauki hakan ta fuskar na raina ka ko kuma ni na yi qanqanta na yi maka irin wannan maganar, dan Allah ka yi hakuri in a maganar da zan yi maka ka samu wata kalma da zata b'ata ran ka, sannan ina son ka dauka shawara ce ke fitowa daga bakin masoyiya zuwa ga masoyin ta," Gyara mata zama ya yi a cinyar shi yana kallon ta da wani irin kallon so da qauna, kenan tana nufin tana son shi a yanzu kenan tinda ta kira kanta da masoyiyar shi? Cikin farin cikin da maganar ta ta sanya shi yace, "Ina jin ki Eamaanii na," "Dan Allah don son Annabin Allah ka taimake mu ka daina aikata neman matan waje, ka ji tsoron Allah domin shi yana ganin ka idan kai baka ganin shi, sannan ka sani Allah ne ya baka rai da lafiya dan ka bauta masa, baka sani ba kana cikin aikata sab'on Allah se Allah ya zare rayuwar ka kaje gare shi kana mai aikata sab'on da ya hana, kaga ka mutu a cikin yan wuta kenan,za kuma a tada kai ne a cikin 'yan wuta, Sweet Haerbeebee ka ji tausayin mu a matsayin mu na matan ka,ka tausaya ma Iya a matsayin ta na mahaifiyar ka,sannan ka tausayawa yaran ka domin kai Uba ne na yara mata kar abinda kake yi da matan wasu ko yaran wasu a yi da naka, nasan ba zaka so haka ta faru akan zuri'ar ka ba to dan Allah ka dena taɓa zuri'ar kowa kaima,ka sani ita zina bashi ce dole idan kayi sai ka biya, ko da ranka ko babu ranka wani zai kusanci zuri'ar ka ta inda baka zata ba,dan haka Ina so ka tuba ga Allah sai Allah ya yafe maka ya kare zuri'ar mu, a qarshe ina yi maka fata da addu'ar Allah ya shiryar min da kai masoyi na Allah kuma ya bada sa'a ya dawo mana da Kai lafiya, wannan shi ne abinda nake so in fad'a maka dama idan na b'ata maka dan Allah ka yafe wa Eamaaniin ka kaji?" Gaba ɗaya kalaman yarinyar sun yi mugun kashe masa jiki, ga hawayen da take sharewa masu zafi a lokacin da take yi masa maganar wanda alamu ne na yanda zuciyar ta ke quna akan abinda yake aikatawa,wata kunya da nauyin ta ne suka dirar masa a lokaci d'aya, ga wani irin baqin ciki daya turniqe shi jin za a yiwa yaran shi abinda yayi wa na wasu saboda keta gonar da ba tashi ba da yake yi. Kalmar godiya kawai ya iya furtawa sannan ya yi wa goshin ta kiss ya share mata hawaye ya tashi tsaye tare da daukar jakar shi da akwatin shi ya fita, hijab ta saka dogo ta bi bayan shi ta amshi qaramar jakar tabishi zuwa waje,gaba ɗaya ji yake ba shi da laka a jikin shi, shagwab'a ta fara yi masa tana buga qafa a qasa ta dakata da bin shi da take yi, juyowa ya yi ya kalle ta cike da sha'awar yanda take masa shagwab'ar yace, " Eamaaniii na ya aka yi ne,ko rikicin ne ya motsa kuma a lokacin da kika san tafiya zan yi?" Fad'awa ta yi gefen qirjin shi ta fara murza jikin ta a nashi tana ci gaba da shagwab'ar ta son ranta,cikin kuka kamar na qananan yara take nuna masa yanda ta fara jin kewar shi tin yanzu,Eamaan kuwa a cikin ranta har mamaki take baiwa kanta idan ta aikata wani abun, a hankali ta sake furta, "Kuma ai kai ne naga kana ta b'ata rai kamar maganata ta ɗazu ta b'ata ranka, kuma gashi ka na fushi da ni za ka yi tafiya salon ka manta da ni idan ka tafi kace ka huta da mitar da nake yi maka kullum shi yasa baka amsa min magana ta ba d'azun," Dariya ta bashi sosai har yaji yana son kasancewa da ita a wannan yanayin da take zuba masa shagwab'ar dake matuqar burge shi, tinani ya yi akan maganganun ta sai ya quduri ko sau d'aya ne zai je ya dawo ba tare da ya taɓa diyar kowa ba, dan haka dole ya sauke wannan buqatar tashi da ta taso masa babu shiri. Janta ya yi suka koma sashen ta cikin yanayi na tsantsar buqatuwa Alhaji ya fara aika mata da zazzafan saqon da take jin zuciyar ta na cunkushewa saboda bata jin sha'awar hakan aranta, amma dole ta hakura ta taya shi sauke masa wannan buqatar,aiko nan da nan tai wurgi da hijab ɗin dake jikin ta ta fara aika masa da nata kalar saqon da take fatan ya mantar da shi aikata zina da dikkan abinda ya danganceta, Eamaan ta baiwa Alhajin mamaki sosai ba kaɗan ba, domin kuwa sai da ya yi mamakin dama Eamaan ɗin ta kware a harkar nan take qin baje basirar ta a baya su mori juna sai yau? Da ba a budurwa ya same ta ba tabbas da sai yace dama can ta san ya ake yin komai tin kafin aure, Eamaan kuwa bata bar Alhaji ba har sai da ta tabbatar da ta cire wa Alhaji hankalin shi ta aje a gefe, ta sa ya ji tinda yake bariki bai taɓa haɗuwa da mace mai iya salon ɗauke hankalin namiji a aza room ba irin ta, da kyar ya hakura ya barta saboda kar yayi dare,maganar bin jirgi ma tini ta tashi dan kuwa yasan yayi missing flight ɗin shi,dan haka dole mota zai bi, wanka suka shiga tare wanda a wajen wankan ma saida suka dad'a shan wata sabuwar soyayyar sannan ya fito ya sauya kaya, itama ta saka wasu qananan kayan sannan suka fito a tare suna sakar wa Junan su murmushin da su kaɗai suka san ma'anar shi,fuskar ta ta yi kyau a cikin dark green din hijabin da ta sanya,bata barshi ba sai da ta raka shi har jikin mota,shiga ta yi ta zauna a gefen shi kafin driver ya shiga, a jikin shi ta zauna ta hau sumbatar shi, kasancewar motar nada baqin gilashi ya sanya babu mai hango su ta waje,bata barshi ba sai da ta tabbatar ta dasa masa tunanin ta wanda zai ɗauke shi tsahon lokaci yana yi har yaje ya dawo daga tafiyar da zai yi,a hankali ta sauka daga jikin shi tana marairacewa ta furta, " I am going to miss u my Sweet baby," wayyoo Alhaji ji ya yi kamar zai suma saboda farin ciki da jin daɗi,yau kuma wai shine baby... Wohohooo lallai babu abinda yafi rayuwar aure daɗi da sanya farin ciki,cikin yaqe baki da nuna tsantsar farin cikin da Eamaan ta sanya shi yace, "Kar ki damu My dear inshaa Allahu da na gama abubuwan da zanyi zan dawo, ga waya zamuna yi kullum ke har video call ma sai muyi abun mu tinda yanzu Eamaanii na ta rage jin kunya ta," D'aga kai ta yi ta sake sumbatar shi a kuncin shi sannan ta fita tana d'aga masa hannu har suka bar gidan shi da driver, komawa ta yi bangaren ta kan ta shiga tana hango kishiyoyin ta na kallon ta ta window,ita kuwa ko nuna alamar ta gansu ma batayi ba ta shige,gaba d'aya yanzu haushi suke bata dikan su, ayi mata basu da aikin yi sai sa idon tsiya, su ɗin ma haushin ta suke ji dan sun kula ta gama janye hankalin Alhaji akan ta ita ɗaya. ************************* Tinda Alhaji ya tafi baida wani aikin da ya wuce na tinanin Eamaan, matan banzan da suka saba huld'a da shi a baya dik ya qi kula su tinda ya isa dan kuwa be kira kowa ba a cikin su kuma sun ji labarin shigar shi Abujan, gaba ɗaya haushi suke ji saboda ya qi sauraron kowa a cikin su,a yanzu ya saba da soyayyar da Eamaan ke yi masa da zaqin ta, ya saba da irin salon kulawar da Eamaaniin shi take bashi sosai, ga shi wannan karon kafin su rabu ta bashi soyayya mai tsayawa a rai, dan haka baya jin akwai wadda zata iya bashi wannan abinda ya samu a wajen Eamaan ɗin, ko da kuwa a cikin matan shi ne kuwa. Yau ya gama aikin da zai yi da wuri ya dawo gidan shi dake nan Abujan gaba ɗaya buqatuwar kasancewa da matan shi ta dame shi, ya rasa yanda zaiyi da ran shi a qoqarin shi na kare kan shi daga afkawa zina. Daga qarshe dai abun ya gagare shi sai ya yanke shawarar leqawa hotel ɗin da ya saba shanawar shi, dan yau d'aya dai ai Eamaan ba ganewa zata yi ba, sannan kwanan shi nawa da zuwa bai kwan da mace ba ai ya yi qoqari sosai ma. Dan haka wanka kawai yayi ya tsane jikin shi da towel ya shafa mayukan shi ya feshe jikin shi da tirare, sannan ya d'akko wata rigar shi daga cikin qananan kayan shi dan ya saka,kawai sai yaga takarda ta fad'o a cikin wandon kayan, buɗe wa ya yi ya ga an rubuta *MY SWEET BABY* murmushi ya yi ya zauna ya fara ware takardar gaba ɗayan ta dan ya karanta abinda ta qunsa.............[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH  💅🏼   WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 11: *My one and only husband, ina roqon ka da kuma sake yi maka tini akan kaji tsoron Allah,ka sani indan kai baka ganin shi to shi yana ganin ka, ka kare mana mutuncin mu ta hanyar adana kan ka har sai ka dawo gare mu, zamu tarbe ka da tarbar da baka tab'a zato ba mijin mu, muna son ka,Allah ya dawo mana da kai lafiya..In kewa ta dame ka ka Kira d'aya daga cikin mu video call ko voice call za mu yi qoqarin taimaka Maka ta kowacce hanya da ta dace*          *Eamaaniin Alhaji shi kaɗai* Nan take Alhaji ji ya ji gaba d'aya an zare masa lakar jikin shi,tini ya nemi sha'awar shi ya rasa, miqewa ya yi ya je ya yo alwala ya yi ta nafilfulu,kamar yanda ya ji Eamaan tana yawan faɗa yin nafila yana kawar da mugun tunani da damuwa. Haqiqa Eamaan tayi gaskiya a maganganun ta domin kuwa Alhaji be gushe yana nafila ba face sai da ya ji wani qarfin imani na shigar shi, tsoron Allah da kunyar Allah ta kama shi, a nan ya zauna yana ta kuka yana neman gafarar Allah akan abubuwan da yayi a baya,sannan ya roqi Allah daya kare shi da zuri'ar shi daga zina,a haka ya fara gyangyadi sai kawai ya miqe ya yi shirin bacci, da asubar fari ya farka ya yi brush ya yi alwala ya yi sallah, tinani ne yazo masa na komawa gida ko kuma kiran Eamaan ta sama masa natsuwar da ta alqawarta masa, domin kuwa tinda ya tashi da safe yake jin shi wani iri. Nasihar Eamaan ce ta yin azumin nafila ta sake fad'o masa a rai a karo na babu adadi,tinda ya iso garin Abuja a komai zai yi sai ya tuna da ita da nasihar da take yi masa,kawai sai ya d'aura niyyar zarcewa da azumi. 'Yana da kyau wanda ba ya iya riqe sha'awarsa ya dinga yin azumin nafila akai akai,kuma ya gujewa dikkan abinda zai tada masa da sha'awa idan yayi haka zai kauce fad'awa sharrin zina' Yana gama tinawa da kalaman yarinyar sai ya saki murmushi mai kyau ya ce, " Da dikkan alamu an sanar da yarinyar nan dalilin aure na da ita shiyasa take yi min wa'azi cikin hikima da ladabi tare da girmamawa dik da ban cancanta da hakan ba,Yah Allah ka yi mata albarka ka bani iKon sauya halaye na domin ka ko iyali na za su samu natsuwa da kwanciyar hankali da ni," Tabbas yana tsananin jin kunyar yarinyar da ya San zai iya haifar wanda suka girme mata ma, akwai wani lokaci da Eamaan ta taɓa ce masa, 'Haqiqa Allah shine mafi cancanta kowanne bawa ya ji kunya ya bar aikata sab'on Allah ba mutane ba, domin kuwa Allah shine yake da wuta kuma yake da aljannah, shi yayi hani da zina da shirka,ya bada umarni a tsaida sallah a bi iyaye, kaga kuwa shi ne zai sanya wanda ya kyautata a aljannah ya jefa wanda ya munana a wuta, dan haka kar ka bar aikata zunubi domin mutane ka bar aikata zunubi domin Allah kawai sai ka rabauta duniya da lahira,' Hawaye ne suke gangara a kuncin Alhaji na tsananin tsoron Allah da yake jin yana shigar shi a lokaci ɗaya, yana cikin wannan halin wayar shi ta yi qara, yana dubawa sai yaga sunan *My Babee* na yawo a saman screen ɗin wayar,murmushi ya yi cikin hawayen da ke zuba a idanun shi ya d'aga wayar,kafin yayi sallama yaji zazzaqar muryar ta na faɗin, "I miss u so so very much my love, na kasa zaune na kasa tsaye saboda tsananin kewar mijina," Dad'i ne ya kama Alhaji tinda ya zo Abuja kusan a rana sai ta kira shi sama da sau biyar, a baya kuwa tinda yake a cikin matan shi babu wadda ta damu da ta kira ta ji ma ya ya isa lafiya balle a kai ga wai ta kira shi haka nan dan jin ya yake, sai dai shi ya kira su yaji ya suke,soyayya suka sha ta waya sosai, da ya ji muryar ta na kashe masa jiki kuwa sai ya ce mata yana ɗan gabatar da wasu ayyuka ne, kamar irin bayan magrib dinnan zai kirata suyi waya, addu'a ta yi masa  tare da fatan samun nasara akan ayyukan shi suka yi sallama suka kashe wayar. ************************** Hajiya Babba ce zaune tana shirya kayan ta na magungunan mata tana aje su inda ta saba, kawai ta ji an bude qofar shigowa bangaren ta, miqewa ta yi dan zuwa ta  ga waye,dik da cewa tinanin ta ya gama bata Sahabee ne ya zo, domin kuwa ta kwana biyu rabon ta da shi,tin sanda Alhaji yace suje asibiti a duba hannun ta bayan sun dawo daga asibitin sai suka je hotel suka yini suna abu ɗaya, da suka dawo ya ajiye ta ya sake fita to tin daga nan bata sake sanya shi a idanun ta ba, a 'yan kwanakin nan duk ta damu tana kuma kewar shi sosai, cikin k'warin guiwa ta buɗe baki tace, "Saha......," Maganar ta ce ta maqale saboda ganin Hajiya Qarama a sashen nata, "Ke kuma me ya faru zaki shigo min gida babu sallama? dan dai ke ba zuwa kike yi ba sai da kwakkwaran dalili," "Tabbas haka yake bana zuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili,to yanzun ma da kika ganni wani abu ne ya kawo ni mai mahimmanci, zuwa na yi ki tashi muje mu yi wa yarinyar can magana akan karuwancin da ta ɓullo mana da shi a gidan nan har ta janye hankalin Alhaji daga kammu," Yawu hajiya babba ta had'iya mai d'aci domin kuwa dik masifa da tijarar ta bata da qwarin guiwar tinkarar Eamaan da maganar komai,cikin jinjina kai Hajiya Babba tace wa Hajiya qarama, "Lallai baki san wace ce Eamaan ba ashe ke har yanzu,to bari kiji ba dani za ai wannan abun ba, amma in kin dage nima abun na ci min tuwo a kwarya na dai kasa magana ne kawai sai na raka ki ina gefe ki yi mata tatas ɗin mu dawo," " Eh na yarda muje ki rakanin ni zan yi mata Magana,haka kawai muna zaune yarinya qarama tazo ta janye mana hankalin miji? Ke ni fa na kula dake da Sahabee wani tsoron ta ma kuke ji, Iya ma kwana biyu ta yi sanyi akan yanda take yi mata masifa a da, to ni ba na tsoron ta, dama ina d'aga mata qafa ne saboda tana son yara na, amma yanzu ba wannan maganar," Tashi suka yi suka nufi hanyar sashen Eamaan,sun same ta ta na zaune ta ɗora qafafun ta a kan center table tana kad'a su a hankali tare da miqar da su ta kuma komawa ta lanqwashe su cikin salo,zaune take daga ita sai guntun wando pink da rigar wandon,wadda iyakar qirjin ta ta rufe sai dogon hannu da hula da take da shi,cikin ta da bayan ta duk a waje suke gwanin burge mai kallon ta,gashin ta kuwa ta d'aure shi wasu sun fito sun zuba a gefen fuskar ta suna reto gwanin sha'awa,dik wannan karairayar da take yi da kashe muryar ashe waya take yi da Alhaji, dan kuwa yanzu ko bata kira shi ba shi zai kira ta su sha soyayyar su. Wata iriyar mutuwar tsaye suka yi dan jin maganganun da take yi wa Alhajin na qarshe, shagala suka yi da kallon shigar da tayi da kuma kyakkyawar surar ta da yanda ta iya sarrafa jikin ta naturally ba wani iyayi da gwalangwaso, ashe haka Alhaji yake shan kallo a jikin wannan halittar mai tsananin kyawun diri? Lallai kishi ko faɗa da Eamaan abu ne mai matuqar wahala a wajen su dan kuwa sun kwana biyu ita kuwa a ganiyar quruciyar ta take,Eamaan kuwa tana ganin su sai ta kashe wayar ta duqa kaɗan ta na gaishe su,Hajiya Babba kam gefe ta yi dan har yanzu tana shakkar Eamaan,ba ma zata iya buɗe baki ta amsa gaisuwar da take yi mata ba balle tayi mata faɗa,Hajiya Qarama ce ta kalli Eamaan a sheqe cikin kishi da b'acin rai tace, " ke karuwar gida hawainiyar ki ta kiyayi ramar mu,kina daga cikin gida kina zabga karuwanci kina son karb'ar mana miji daga zuwan ki, yanzu gaba ɗaya hankalin shi ya tattara ya koma wajen ki, to bari kiji da kyau, ahir ɗin ki da shiga gona ta dan kuwa ni ɗin nan da kika ganni bani da kyau bani da mutunci, ki tambaya ki ji ba ragowa tsakani na da duk wadda zatai qoqarin rabani da Alhaji," Murmushi Eamaan take ta zabgawa, na ganin tsantsar haukan su da wautar su,cikin murmushin ta miqe daga durquson da tayi dan gaida su tace, " Hajiya Qarama kenan amma gaskiya na yi matiqar mamakin zuwan ku nan dan yi min gargad'i akan wai ina qoqarin mallake maku miji, na farko dai ma ku kunsan ni da Alhaji auren had'i ne ba wai son shi ne yasa nake duk abinda nake yi ba, ina yi ne dan taimakon ku da kare mutunci na,yau ace kamar ni Eamaan a ga mijina yana yawo yana raba jikin shi ma kowacce jaka da god'iya ni ina zaune a gida kamar hoto to na faɗi,dan haka dole na kare masa mutuncin shi wanda shine namu, ke hajiya qarama kina ɗaya daga mu'assasin yawon Alhaji, domin kuwa ko a yanzu kin isa misali,dan Allah dubi kayan jikin ki tinda ya tafi baki yi wanka ba da alama balle canja su,kuma a haka kike rayuwa koda yana nan, kin kasa gane cewar Alhaji mai tsafta ne, ta ya kike tsammanin ya kusance ki da datti haka? Ai dole tinda shi mai ra'ayin bin mata ne ya fita ko qarfe nawan dare ne akwai masu saidawa a waje yaje ya biya buqatar shi ya dawo. Sannan da kike kirana karuwar gida Allah ya kiyaye kalmar karuwa ta rab'e ni, dan kuwa ni na fi qarfin karuwa, domin kuwa su zina suke yi ni kuwa jima'i nake yi da mijina halas d'ina babu tsoro sai nutsuwa,ba zunubi sai lada,dan haka kar ki sake kirana da karuwa tinda ni na fita gata da matsayi na fita sanin me mijina yake so menene idan na yi yake rikita shi, na fita bashi abinda ya dace,in kuma baki yarda ba zaki gani zai ci gaba da bin wasu qadangarun barikin ko zai daina? In kuka bani had'in kai sai mu haɗu mu riqe mijin mu mu zauna lafiya,in baku bani had'in kai ba na riqe shi ni kaɗai. Sannan masu zuwa su yi ciki a waje su na qifad'in yaran su yaran cikin gida ne ina sane da su suma,su kuma masu zina a cikin gida su ci gaba kar su fasa" Wata irin faduwar gaba ce ta kama Hajiya Qarama, bata san sanda ta zauna a bakin kujera ba saboda jiri da Wani duhu da ta fara gani,Eamaan kuwa ta kalle ta ta qura mata ido yanda take yiwa dik wani mara gaskiya, gaba ɗaya jikin Hajiya Qarama ya kama rawa,shin a ina yarinyar nan ta san sirrin ta? Yau ta shiga uku ta lalace sirrin boye ya fito fili,kullum suka yi faɗa da Hajiya Babba idan tana yi mata gorin haihuwa sai dai Hajiya Babbar ta zarge ta akan yaran ba yaran Alhaji bane amma ba dan ta san asalin gaskiya ba,murmushi mai sauti Eamaan ta yi ta kalle su dika tace, " ku kiyayi Eamaan dikan ku,ni ina aiki da hankali da hangen nesa ne ba da wawanci ba, sanda Alhaji yasan abubuwan da kuke aikatawa tabbas bai isa ya ce komai ba dan shine sanadi,shi ya jawo kuka lalace a qarqashin ikon sa domin kuwa zina bashi ce,kunga kenan bashi ya biya da ku,indan Kun gama abinda ya kawo ku ku rufe min qofa saboda sauraye ni na yi ciki dan banda lokacin ku" Eamaan sai ta yi shigewar ta uwar d'aka ta barsu zaune cike da tsoro da mamakin ta, da kyar suka ja tsumman rayuwar su suka bar wajen,Hajiya Babba ce tabi bayan Hajiya Qarama suka shiga bangaren ta,cikin jimanta abinda ya faru Hajiya Babba tace wa Hajiya qarama, "Me na faɗa maki game da yarinyar nan? Ai duk inda kike zaton ta ta wuce nan, yanzu sai ki bani labarin ya akai kika haifi yaran nan dan mu san mafita,saboda in bamu ɗauki mataki akan ta ba asirin mu zai tonu gaba ɗayan mu," kallon Hajiya Babba ta yi ɗauke da alamar tambaya, kenan itama nata asirin ya tonu Eamaan tasan sirrin ta,cikin sanyin murya Hajiya qarama tace, " A gaskiyar magana Hajiya yaran nan bana Alhaji bane, Yaran abokin shi ne d'an majalisa dake a Abuja da zama, in ya shigo Kano sai ya min waya na je mu had'u,ni kuma sai na faɗa maku na tafi gidan mu," A razane hajiya Babba ta miqe tana bin ta da kallo, ita kuma sai kuka take yi, cikin kukan tace, "Dan Allah ki rufa min asiri kar wani ya san maganar nan, ba wanda ya san zancen nan sai ku biyu,dan ko Alhaji Saminun ban sanar wa ba, in Alhaji yaji na shiga uku, na yi miki alqawarin zan riqe maku amanar ku ke da Sahabee," Hajiya Babba qara rikicewa ta yi da jin kalaman Hajiya qarama, kenan itama tana sane da neman juna da suke yi ita da Sahabee amma bata taɓa magana ba dan tasan itama tana fita nata yawon, dafe kan ta ta yi bata ce komai ba ta fice daga sashen Hajiya qarama, abun yayi mata yawa a zuciyar ta,shin meke faruwa ne a gidan nasu se kace ana annobar zina a gidan ? wanne irin shaid'anin ne ya shigo masu gida wai ace matan mutum ɗaya na yawon banza, suna mu'amalar aure ba da mijin su ba? Hajiya Babba na cikin tinanin nan Sahabee ya same ta, ya na shigowa hannun shi ya sa a qirjin ta da ta daure cikin bra ya matsa ya kai bakin shi jiki kamar mijin ta na halal ya hau sha, a hankali ta saki ajiyar zuciya ta kalle shi, nan da nan kewar shi da ta yi na kwanaki ta taso mata har tayi sanadiyyar jan shi suka fara tattab'a junan su,tashi tayi ta nufi qofa ta rufe da key gudun afkuwar matsala sannan suka fara masha'ar tasu, ba kaɗan ba Sahabee ke yin dik abinda yaso da Hajiya Babba,nishin ta kawai ke tashi a d'akin hankalin ta kwance babu wata fargaba a tare da ita,da sauri Sahabee ya danne bakin ta da nashi, a haka yake yi mata rad'a kan ta yi ahankali kar ta jawo masu mutane, d'aga mai kai ta yi suka ci gaba da abinda suke yi, basu suka rabu da juna ba sai da aka yi isha'i sannan ya d'aga ta, duk ta yi laushi har ma ta fara bacci ya lallab'a ya sa kayan shi ya fice. A ranshi yake ayyana, 'Ohh ka ji ikon Allah malam mace sai d'anneman muni amma gata nan zam zam da ita,' Yana shiga ɓangaren su ya tadda Eamaan ta gama had'a wa Iya abinci ta d'aga kai ta kalle shi,nan take gaban shi ya yanke ya faɗi dan kuwa a zaton shi yau ma ta gan su,hankalin shi a tashe ya durqusa gaban ta zai fara magana ta bashi wani kallon kar ka kuskura, miqewa ya yi ya had'iye maganar shi sai kyarma yake yi,cikin dakewa Eamaan tace masa, "Me ka yi min da zaka wani durqusa min haka salon Iya ta fito tace na yi maka wani abu? Kar ka kuskura ka sake yi min haka ni babu komai tsakanina da kai da ya wuce fatan shiriya, ba ni na halicce ka ba, dan me zaka ji tsoro na sama da wanda ya baka lafiyar da zaka bauta masa amma kake saɓa masa da lafiyar? Kar ka kuskura ka sake ganina ka nuna kana shakkata, domin ni din ban da wuta banda aljanna, ka qi bin dokar mai wuta da aljanna kaga sai ya saka ka a inda yaga dama," Rab'awa tai ta gefen shi ta shige ta je ta sanar da Iya ta gama haɗa abun kari sannann ta ja mata qofar ta tafi, ba laka a jikin shi ya wuce dakin shi ya rufe, Iya kuwa da ta fito sai da ta biya ta d'akin shi tai bugun duniya shiru yaqi bud'ewa,yana can kwance a gado maganganun Eamaan ke ratsa shi sosai,Iya ce ta harari qofar d'akin nashi tace, " Jarababbe yau baqin halin naka ya motsa kenan, sai ka ci kan ka ai bari naje na kwashi girkina ni,naga yanzu kowa a gidan yayi sanyi, kowa ka taba kamar a firgice yake ku kuka sani 'yan wahala," Tinqis-tinqis ta wuce ta fara cin abincin ta hankali kwance Alhaji ya kira ta suka gaisa, ta sanar da shi yanzu Eamaan ma ta tafi ta gama yi mata abinci,wani dad'i ne ya kama shi,sai ya sanyawa Eamaan albarka,ya sanar da ita gobe zai dawo, sannan kuma yana son ta sa Sahabee ya kai Eamaan asibiti yanzu dan tana can yanzu ta kira shi cikin ta na ciwo sosai, amsawa ta yi sannan ta miqe ta je d'akin Sahabee ta hau bugawa amma duk bugu da kiran da take mai yaqi bud'ewa, waje tai ta kira driver dan ya je ya tada mota zai kai su asibiti da Eamaan, haka nan sai ta ji tana fatan Allah ya sa Ciki ne da Eamaan ɗin ,dan ko ita ta jima tana zargin su Sabeerah ba yaran ɗan ta bane duba da yawan yawon Hajiya Qarama da kuma rashin kama da yaran suke yi da Alhaji da ma zuri'ar su baki ɗaya, bata jin wani kusanci na musamman a tare da su iyaka dai ta na son su saboda yaran akwai shiga rai, tana qarasawa bangaren Eamaan ta tadda ta ta saka kaya da hijab, sai murqususu take yi sannu ta yi ta jera mata, sannan tace ta fita ta shiga mota bari ta koma ta d'akko mayafin ta,da kyar Eamaan ta iya qarasawa ta je wajen motar ta shiga, Iya kuwa ta dakko mayafi ta shiga mota driver ya tada suka bar gidan. Asibiti suka je bayan bayanan da ta yi wa likitar se likita ta baiwa Eamaan gwajin jini,suka tafi lab aka ɗauki jinin ta aka gwada, bayan sakamako ya fito aka bata ta koma wajen likita, likita ta taya ta murnar samun qaruwa da tayi sannan daga baya ta yi wa Iya izinin shiga Office ɗin nata ta Sanar da Iya Eamaan na d'auke da cikin wata uku da sati biyu,sai dai kuma cikin ya na barazanar b'arewa saboda yawan ayyuka da take yi da damuwa, hankalin Iya a tashe ta dinga roqon su su taimaka mata kar ta rasa jikan nan nata tana son abunta, hakuri likitan ta bata ta  sanar da ita za su yi iyakar qoqarin su dan suga sun kula da ita, tana buqatar hutu ne kawai. washe gari da Alhaji ya iso kano ko gida bai bari an kai shi ba ya yi asibitin wajen ganin Eamaan,yana shiga d'akin da aka kwantar da ita yayi ido biyu da ita duk ta rame ta yi fari sosai, tabbas ga alama nan komai ya fito cikin wata uku ya kusa rifa na hudu ya d'ago kaɗan ana iya ganin alamun shi, kwallar dad'i da farin ciki ne ta ziraro wa Alhaji a fuska, Iya ta kalle shi itama da murmushi a fuskar ta tace, "kai ma kaji dad'in ganin matar ka da ciki ko? ABDULLAHI ina son in mun koma gida ka tsannan ta bincike akan su Ilham," "Iya ban gane ba? Kamar ya na tsananta bincike akan yarana wani laifi suka yi?" "Ina nufin ka nemo wane ne uban su, domin ni ka sani ba wai ina tsananin son yarinyar nan Eamaan bane,amma ina jin tana da cikin nan na ji wata qaunar ta ta kama ni, wanda duk son Hajiya Qarama danake ban taba jin haka ba in tana da ciki, hasali ma zargin ta nake yi da yawon banza ni, sannan ba wai dan wannan alaqar da bana ji game da ita idan tana da ciki ba nake zurfafa zargi na, ka San dai Qarama da shegen son yawo, yanda ka ke saka qafa ka fice ba da sanin mu ba itama haka take sa qafa ta fice, ta sha yin qaryar gidan su ta tafi ka Kira ace bata je ba ko ka manta? To Ina take zuwa? Ko da da farcen qafa ne yaran nan ba sa kama da Kai ko ni ko Wani naka, to dole ne ka tsananta bincike akan su" wani irin duka qirjin Alhaji yake yi a dik fitar kalma ɗaya daga bakin Iya, nan take ya hadiyi wani yawun wahala,ya sassauta wa jikin shi ta hanyar cire babbar rigar shi ya riqe a hannu, tabbas maganar hajiya akwai qamshin gaskiya a cikin ta, amma in yaran nan ba nashi ba ne to na waye? Waye yake masa d'anyen aiki haka?............ *Hahaiiiii cassssss wanzami fa baya son jarfa* [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 12: Gaba ɗaya hankalin Alhaji ya kasa kwanciya da matan nashi da ya kamata ace a wajen su ya sauka, dan haka a  wajen Eamaan ya kwana ranar ,dik da cewa Iya tayi-tayi dashi ya tafi gida ya huta amma qi, baya son ya tafi ya bar ta a nan daga ita se Iya dan a ganin shi akwai abinda dole shi zai yi mata Iya baza ta iya ba. Har suka yi kwana uku a asibitin babu wanda yazo duba Eamaan ding a cikin mutanen gidan Alhajin kama daga kan Hajiya Babba har zuwa Hajiya Qaramar balle kuma Sahabee dake a cikin damuwa, qarshe dai dole Alhaji ya yi waya gidan su Eamaan ya Sanar da su halin da Eamaan ke ciki, Hafsat aka umarta data zo ta zauna da ita har ta samu k'warin jikin ta tinda ita ta yi graduating yanzu haka tana aiki a camber din ta na kanta ne, sannan an kawo kuɗin auren ta har an saka ranar auren da wani abokin aikin ta mai suna Kamal, Iya da cewa ta yi a bar ta ba sai tazo ba tinda ga masu aikin gidan cikin su an samu mai zuwa ta zauna da ita, amma Eamaan ta ce a mata alfarmar barin yayar ta tazo wajen ta in zai samu, kan Iya tace komai Alhaji yace ba komai zai je da kan shi ya d'akko mata Hafsar,ita kanta Hafsar ta ji dad'in hakan dan tana son baiwa wa qanwar ta ta kulawa ta musamman. Ammaah da Mama sun tausaya ma Eamaan dan sun tabbatar aiki take shaqa har hakan ta faru da ita, amma babu yanda za suyi da ya wuce suyi mata addu'ar samun sassauci,dama kowacce mace da qaddarar gidan auren ta,Daddy ma ranshi ya baci da jin cewa wai zata yi b'ari saboda yawan aiki da stress amma sai ya danne saboda baya son ya karya wa d'iyar shi mai BIYAYYAH qwarin guiwar ci gaba da yin BIYAYYAH a gidan mijin ta, sai kawai ya bi ta da addu'a da fatan alkhairi shima. Wani irin haɗin kai ne yake wanzuwa a tsakanin matan na Alhaji da Sahabee wanda kai da ka gani kasan ba na Allah da Annabi bane akwai wata a qasa,dan kuwa kowa na nan na jin haushin 'yar uwar ta a qasan ran ta. Tin bayan da aka kwantar da Eamaan sukan haɗu a sashen junan su suyi ta tattaunawa akan matsalar da suke ganin tana tunkaro su a gidan, dan haka yau ma zaune suke a sashen Hajiya Babba suna hira, cike da b'acin rai Hajiyan ta nisa tace, " Hmmm wai baku san cewar an tabbatar da Eamaan na ɗauke da cikin watanni 3 zuwa 4 ba? Meye plan din mu akan hakan ne dan dai gaba d'ayan mu yanzu mu masu laifi ne a wajen Alhaji da ya san me muke aikatawa a bayan idanun shi kashin mu ya bushe,  Qarama kin dai san baki da gadon yaran nan a gidannan dan ko in Alhaji ya fad'i ya mutu ni ko Sahabee ba bari zamu yi a raba da shegu ba tin da mun san komai," Wani mugun kallo Hajiya Qarama tai wa Hajiya Babba, sannan tace, " Yo me zamu yi banda mu qoqarta zubda cikin tin kan yazo duniya? Ko dake na kula ku tsoron ta kuke ji har yanzu," Sahabee ne yayi mata kallon baki da hankali, " ke kan ki tsoron ta kike yi balle mu,akan me ba zamu ji tsoron mace kamar Eamaan ba, macen da ta san me take yi, tasan ta kan tafi da abokin gaba ba tare da tada jijiyoyin wuya ba ko hargowa,tasan yanda zata saka duk wani wanda basa shiri da ita cikin fargaba da tashin hankali, dan haka ni ina ganin kar wadda ta yi yunqurin taba abinda ke cikin ta,koma dai menene Yayah dan uwana ne, dan haka zan so ace yau ko da d'a d'aya ne ya ga jinin shi shima a duniya ,dan haka ku kiyaye kar na ji labarin wani abu ya sami cikin nan," shiru suka yi, kowacce da abinda take saqawa,Hajiya Qarama ce ta buɗe baki tayi magana cikin fargaba da tsoro tace, "Ni yanzu ku ban shawara dan Allah, ya zan yi na sanar da Alhaji Saminu ina ɗauke da yaran shi guda biyu ba tare da ya qi karb'ar su ba?" " Kar kiji tsoron komai ki sanar da shi komai a wannan dawowar da zai yi in ya sani shikenan fargabar ki ta qare,idan yaso kina faɗa masa ki bashi sharuda biyu, na farko dai ko ya Karb'a cewa yara nashi ne ko ki masa barazanar tona maku asiri, ki nuna mai ke baki damu ba dan wani ya sani shi kike jiyewa," Gaba ɗayan su sunyi na'am da shawarar Sahabee, sannan suka shiga hirarrakin duniya daga qarshe suka tashi da fadan nasu na jaraba akan yara, Sabeerah ce ta shigo da gudu ta sanar da su dawowar su Eamaan da yayar ta,a sanadin gudun da tayi ne ta take Hajiya Babba a rashin sani,nan take tako ɗauke ta da mari, aiko nan fada ya rincab'e, Sahabee ya zame jikin shi ya fice,dan shi baya son wannan fadace2n nasu kamar kaji. Gyara gidan Hafsat ta  shiga yi dik da babu sani dattin a zo a ganj sai qura,Alhaji na shiga kuwa ya duba abubuwan da babu sai ya yi wa driver waya yace ya zo Eamaan ta zayyana masa abubuwan da take so, nan da nan aka bashi kuɗi ya tafi siyowa, Alhaji na manne da ita kamar za a kwace ta, sai faman sannu yake mata tare da shafa marar ta yana yin wani irin farin ciki na ratsa zuciyar shi. Hafsat dake kallon yanda yake yi wa Eamaan dai ya sa take jin kunyar shi sosai, a ganin ta tsaf zai yi sa'an Daddyn su amma ya samu yarinya sai wani soyayya yake zubawa kamar saurayi,a haka ta kammala gyara wajen ta koma d'akin dakin da yake nan zata na zama, Alhaji ji yake kamar ya yi ta zama a wajen ta kar ya je wajen sauran matan, dan yaso matuqa da ya dawo ace girkin ta ne, kuma lafiyar ta qalaou yasan tabbas zata cika mai alqawurran da ta yi masa, amma ba yanda zai haka yayi mata kiss sannan ya ɗauki jakar shi ya yi ɓangaren hajiya Babba wadda ba jimawa su sahabee suka koma bangaren su suka barta ta hau 'yan gyare-gyaren da ya kamata mace tayi dan tarbon mijin da ya dawo daga tafiya,fuskar nan ta sha fenti kamar kullum sai tashin qamshi take yi,cikin ranshi yaji daɗin samun ta a haka, dan kuwa gwanda masa ita sau dubu akan Hajiya Qarama, abincin da masu aiki suka yi na gida ta yi masu izinin kawoma,a haka yaci saboda bashi da zaɓi,yana gamawa ya yi wanka ya kwanta nan take bacci mai daɗi ya ɗauke shi saboda tinda ya dawo daga asibiti yake kwana wajen Eamaan to baccin ba wani sosai yake. yi ba. Hajiya Babba na ganin haka ta kulu sosai,wato ya dawo ma bai zo gare su ba sai da matar so ta bashi izini shine ya wani baje yana kwasar munshari kamar shekararren jakin dawa,qwafa ta yi ta cire kayan ta ta kwanta gefen shi, ai kuwa Hajiya bata hakura ba sai da ta san yanda ta yi ta tada shi daga baccin nan mai daɗi da ya samu, dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, nan take ya biye mata suka raya wannan daren, mamaki take yi na yanda Alhajin nasu sam baya tsufa,ko Sahabee da yake saurayi Alhaji ya fishi komai, amma dan jaraba da rud'in shaid'an bazata hakura a kan mijin ta ba sai ta qara da qanin shi. Washe gari yana idar da sallar asuba ya ɗauki hanyar ɓangaren Eamaan dan yaga ya ta kwana da jikin nata,a parlour a kwance ya ganta a saman abun sallah ta yi lamo tana azkar,gaba daya jin jikin ta take yi babu k'wari shi yasa ta kwanta a wajen, zama ya yi a gefen ta ya janyo ta ya ɗora ta a cinyar shi yana shafa bayan ta,sake mannewa tayi a jikin shi kamar wata mage, a hankali ta buɗe idon ta ta kalle shi, tausayin ta ta gani kwance akan fuskar shi, murmushi tayi masa sannan ta gaida shi, bai amsa ba sai kawai ya haɗe bakin su waje ɗaya yana sumbatar ta a hankali, a hankali ya zame bakin nashi daga nata, sannan ya amsa da, " Babeen Alhaji sannu kinji Allah ya baki lafiya, ya sa maki kaffara, Inshaa Allah zaki samu sauqi da wuri kin ji?" D'aga masa kai ta yi idon ta fal hawaye dan kuwa tana jin jiki, Hafsat ce ta fito daga kitchen ɗauke da plate data dafa mata taliya irin jellop ɗin nan na manja da attaruhu sai naman qaramar dabba, dan sha'awar manjan take sosai shi yasa tace a yi mata me manja, tana shigowa taga Alhajin da Eamaan a rungume da juna sai ta rikice  tace, " I...I.... ammm sorry ban san ka shigo ba," " Barka da safiya Hafsat, ya aiki? sannun ki Allah ya baki lada ya sa ai bikin ki a sa'a," Ta ji dad'in addu'ar shi sosai amma fa yana matuqar bata kunya ita kam,a kunyace tace, "Ameeen na gode," Murmushi Alhaji yayi yace mata, " ki daina jin kunyata fa dan kuwa kin dinga ganin irin wannan abubuwan in dai kina gidannan," Dariya ta ɗan yi kaɗan sannan ta ajiye masu abincin zata koma ya ce ta hada mata tea, komawa ta yi ta had'o mata tea ta kawo mata,Alhaji ne ya Karb'a tare da yi wa Hafsat godiya ya fara bata a baki,Eamaan buɗe baki tayi ta dinga Karb'a har sai da ta ci abincin sosai tinda tana so dama,tea ɗin ne kawai bata sha sosai ba, wanka ya ɗauke ta yaje yayi mata, ya sa mata kaya marasa nauyi a jikin ta dan ta sha iska ya kamo hannun ta suka fito zuwa bedroom ɗin ta, taje mata kai ya yi ta d'aure da kanta,ya taimaka mata ta kwanta, yana shafa kan ta zuwa bayan ta a hankali nan take ta yi bacci, miqewa ya yi ya ja qofar a hankali ya fita, yace ma Hafsat kar ta tashe ta ta samu bacci idan ta tashi a bata maganin rana,sanan ya qara yi mata godiya sosai ,Hafsat ta ji dad'in ganin yanda yake kula da qanwar ta sosai,sai dai tana mamakin duk ba wanda yazo duba qanwar ta ta kaf gidan, daga Iya se  Alhajin suke jinyar ta kamar mutan gidan basu san bata da lafiya ba, kyab'e bakin ta ta yi ta dan buɗe d'akin Eamaan ɗin a hankali ta leqa ta,sai tagan ta kwance ya tare ta da pillo kamar wata jaririya, sannan ga shi alamar yanda ya shafa mata gashi duk ya tarwatse, murmushi ta yi ta rife qofar ta koma d'akin ta suka hau waya da Kamal din ta suna ta shan soyayyar su. Alhaji kuwa na komawa sashen Hajiya Babba ya tarar da ita a cikin dakin ta ta cika tayi famm kamar flour da aka sanya wa yisssss, cikin faɗa ta hau cewa, "Dan me zaka dinga yi mana rashin adalci a gidannan ne eye? Akan me zaka tattare komai naka  ka damqawa yarinya qarama baka da lokacin mu sai nata ,yanzu duba tin asuba sai qarfe 8 ka dawo sashe na akan me? Ko girkin tane? gaskiya ba zan dau wannan rashin adalcin ba daga gare ka akan 'yar cikin ka ka zauna kana rawar jiki," Cikin sanyin murya ya furta, " Hajiya ki yi hakuri mana, kina ganin yarinya ce kuma ciki gare ta tana buqatar kulawa ta sosai a wannan gab'ar," "Yarinya? Yarinya fa kace, Eamaan ɗin ce yarinya? Yarinya ce tasan ya zata sami ciki da tsoho kamar ka? To bari kaji na faɗa maka Allah yasa a zanin goyo take bata fara haqora ba tsabar yarinta dole ka tsaida mana adalci,in ba haka ba gaskiya akwai abu mara dad'i da zai faru a gidan nan wanda ba zaka so faruwar shi ba," Tana kaiwa nan ta faɗa band'aki ta bar shi a wajen, shi kuwa Alhaji zama ya yi kawai yana nazarin maganganun ta yana so ya gano laifin shi, buɗe qofar uwar d'akin nasu akai babu sallama ba komai aka shiga, Alhaji na d'aga kai idanun su ya sarqe da na juna.......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH    💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 13: "Me ya shigo da kai har cikin bedroom ɗin  mu Sahabee?" " Ah Yayah dama kana nan, ai na yi ta sallama a can parlour na ji shiru kuma da fari na ji kamar hayaniya sanda na shigo ana daga muryoyi,to da nai ta sallama na ji shiru shi ne yasa na zaci ko wani abu ne ya faru kawai na shigo kai tsaye," wani irin kallon ka raina min hankali Alhaji ya yi masa sannan yace, "Babu komai to je ka kawai," Hajiya Babba ce ta fito daure da towel, tana ganin Sahabee ta daburce bakin ta ya hau rawa tana son tayi magana ta kasa, nan da nan Alhaji ya sak'awani zargi cikin zuciyar shi game da abinda ya faru,shin me ya sanya qanin nashi shigowa kai tsaye ba tare da neman izini ba? Me yasa Hajiya rikicewa daga ganin Sahabeen a d'akin tin kafin ta san dalilin zuwan shi?  Ɗauke kallon shi ya yi daga na ta, ya yada jikin shi kan gadon ya rufe idon shi yana tinani, a gaggauce ta saka riga ta fita waje, a farfajiyar gidan ta ga Sahabeen ya na ta Kai wa da komowa, cikin faɗa Hajiya tace masa, " kai wanne irin soko ne Sahabee, me ya kai ka zuwa yanzu?" "Ina zaune a d'aki ne kika fad'o min a rai sai na ji ina buqatar ki ko na minti gomane,to da yake d'azu na ga shigar shi wajen waccan yarinyar na san zai dad'e, Iya na can ta sani a gaba da zance bana ma gane ina ta dosa,to shine yanzu da ta shiga ciki ta kwanta dan ta huta kawai na yo nan, ban zaci ya dawo ba," Hararar shi ta yi,Sannan ta ce, " kai wane irin shiriritacce ne, amma dai kasan a qa'ida in yana nan baka zuwa ko so kake yi asirin mu ya tonu ne," Sosa qeyya ya yi ya sunkuyar da kai ,ita kuwa sai ta buga tsaki ta juya ta yi ciki, Alhaji duk yana kallon su ta window yana ayyana abubuwa da dama akan su, tana shiga sashen nata ya koma ya kwanta, duk da baya jin hirar su saboda tazarar dake tsakani,kallo ɗaya zaka yi musu ka gano akwai wani abu dake wakana a tsakanin su, Idon shi ya rufe kamar yanda ta bar shi, ta koma ta ɗauki mai ta fara shafawa a jikin ta da ya bushe. Hajiya Qarama ce kwance a gado tayi ruf da ciki tana waya cike da Jin dad'i kamar wata budurwar da ke  yin hira da saurayin ta. " Yanzu kana ganin za ka kai wani satin a gari ne?" " A'a gaskiya ina jin jibi ma zan koma, akwai matsala ne, ko kina son ganina ne?" " kwarai da gaske ina son ganin ka, dan akwai magana mai matuqar mahimmanci da za mu yi da kai," "To shikenan sai ki samu lokaci ki fito mu gana ko," Sai da suka  taba zantukan su na lalacewa kafin daga baya su yi sallama da juna, cike da fargabar me zai je ya zo ta yanke shawarar yanda za ta fita, ita zata karbi girki da dare dan haka ran ta kwal tana ta murna zata samu damar tambayar fita unguwa, Alhaji kuwa fatan shi bai wuce ace tayi wanka ta yi brush kafin dare, ga mace har mace amma ba gyara, dan gaskiya Hajiya Qarama bata da muni ga jikin ta mai kyau sai baqar qazanta da wari. A haka lokacin komawa sashen ta yayi sai ya tattara ya dawo bangaren ta, ba laifi tayi wanka tayi brush harda su sabon kitso,amma fa gaba ɗaya bata qamshi gata nan ne dai kawai a lallab'a auren zamani,a wannan karon Alhaji ya sha karairaya da gata dai-dai iyawar ta, har suka yi shirin kwaciya bacci,sai da komai ya gama kan kama ana soyayya warin hammatar ta duk ya cika masa ciki saboda sai ya zamana kamar tana aikin qarfi ne tana haɗa zufa warin na fitowa, cikin fada ya fara yi mata magana, "Wai ke sau nawa zan yi maki magana ne akan kina amfani da turaruka a jikin ki ne ? Ga su nan da yawa har ban san iya adadin su ba saboda naki ma na musamman nake siyo maki amma ke sam baki san meye amfani da tirare ba ko saka abun da zai ɗauke warin hammatar ki kamar Alimun ko lemon tsami, sai dai ki zauna kina wari malam meye hakan?" Tsaki ya yi ya zare jikin shi daga nata ya sauka daga gadon,da gudu ta bi shi zata maqale shi ya fizge ya bar inda take, kayan shi ya saka ya fice daga dakin,direct ban garen Eamaan ya je ya kwankwasa, Hafsat ce ta buɗe masa qofar idanun ta dauke da bacci, dik da haka sai da ta gane yana cikin damuwa, gefe ta koma ya shige ciki ko kula ta bai yi ba, direct d'akin Eamaan ya nufa,can ya hango ta tana zaune kan sallaya tana karanta qur'ani idanun ta ƙyamas bata jin bacci, agogo ya kalla yaga sha biyun dare ya ɗan gota, d'aga kai ta yi ta kalli cikin idanun shi,nan take yanayin fuskar shi da ya shigo da shi kamar mayaqi ta koma kamar ta qaramin yaron da kallon mahaifiyar shi ya saukar masa da natsuwa,kallon juna suka sake yi yaji farin ciki ya mamaye baqin cikin da ya zo da shi,cikin sanyin murya ya furta, " Tabbas Eamaan ke alkhairi ce a gare ni, ko raina ne ya ɓaci na gan ki hankali na sai ya kwanta,may i spend the night here with you please? Dan in baki barni ba yanda nake jina ɗin nan waje zan tafi," Ya qarasa Maganar cikin muryar tausayi, qur'anin ta ta rufe ta ajiye a gefe sannan ta yi masa nuni da hannu ya je gare ta,kamar qaramin yaro haka ya isa gare ta ya kwantar da kan shi a cinyar ta, ita kuwa nan take ta sanya lallausan hannun ta tana shafawa a hankali "Eamaan ina jin tsoro, ina matuqar jin tsoro, bana son abinda zuciya ta ke zargi game da matana ya zama gaskiya, in hakan ta kasance tabbas zuciya ta bugawa za ta yi na mutu, " Hawaye ne ke gangara daga idanun shi zuwa fuskar shi daga nan sai su yi masauki a cinyar ta,itan ma hawayen take share wa dan kar ya gani, amma inaa ya riga da ya gan su, " Eamaan kema kina zargin su akan cin amanar aure na ko? Please Eamaan tell me what you think maybe  going on in this house, coz i am going insane na rasa me yake faruwa na san cewa tabbas something is fishy in this house amma na kasa gano menene," Kama kan shi ta yi sosai ta manna da qirjin ta tana ci gaba da shafa bayan shi bata ce komai ba domin kuwa bata da abin fad'e ɗin,sai da ya yi kukan shi ya qoshi sannan ya gyara kwanciyar shi har a wannan lokacin bashi da walwala, babyn su ne yai first kick din shi aiko dukkan su suka zabura,cike da murna suke shafa cikin, "Alhamdu lilLAAH kaga baby tana baka hakuri ko, tace Daddy ya yi hakuri akan koma me ke faruwa dashi ya barwa Allah lamuran shi,abinda ake so kowanne bawan Allah yayi shine ya kiyaye dokokin Allah, to sai Allah ya kiyaye shi, sannan tace na sanar da kai ka zama mutum mai kare kanshi daga zina Allah zai kare masa iyalan shi da zuri'ar shi baki d'aya daga zinar, dan haka ina ganin saqon d'iyar ka ya isa ya sanya ka daidaita lamuran ka, ka rabu da zunubai ka yawaita istigifari, Allah mai yawan gafara ne ga bayin shi da suka nemi yafiyar shi, Allah Al-haleem ne, mai yawan kauda kai akan zunuban mu, bana son kana tada hankalin ka akan abunda bai zama gaskiya ba ka ji Babyna?" Maganganun ta sun samu kyakkyawan mazauni a ran shi, a cikin zuciyar shi ya qudirta yau kam ya yi alqawari tsakanin shi da Allah ya daina neman mata har abada, kalmar ta ta qarshe ce ta sa shi murmusawa wai baby,rungume ta ya yi yana ta yi mata godiya, ita kuma ta ci gaba da shafa kan shi, a haka ya yi bacci yana jin kamar an dauke masa wani qaton dutse akan shi,miqa hannu ta yi ta dau qur'anin ta ta ci gaba da karantawa, shi kuma yana ta baccin shi k'wance da kan shi sannan cinyar ta,daga qarshe itama baccin ne ya dame ta ta miqa hannu ta d'akko masu pillo ta saka masu a wajen suka kwanta, bacci suka yi har asuba, sannan suka tashi suka yi brush su ka yi sallah, azkar ta yi ta taba karatu wanda shima ya qoqarta kwatantawa yin hakan, bayan sun gama ne ya miqe yayi mata sallama ya tafi, Hafsat ce ta shigo suka gaisa da qanwar ta ta tace, " Akwai wani abu da kike sha'awar ci ne yau?" " Eh dan Allah ki soyan chips ki baɗe shi da mai da yaji, amma kar ki soyan kwai bana son qarnin, kuma banda tea kawai zallan ruwan randar sanyinnan dana ce driver ya siyo jiya ya ishe ni, ina ce kin zuban ruwa a ciki," "Oh ni Hafsat wannan kwad'ayi na bani mamaki, eh na zuba maki ruwan maman biyu," Dariya suka yi sannan Hafsat ta qarasa shiga ta zauna a gaban Eamaan, " Eamaanii meke faruwa ne ke da Alhaji? Kar fa ki zama kina bashi had'in kai kuna shiga haqqin sauran matan shi dan na ga yana yawan zuwa nan ko ba lokacin girkin ki ba, kinsan shiga haqqin wani haramun ne ko?" Ta fuskanci inda yayar tata ta dosa,dan haka sau ta zauna ta sanar da ita dik abinda yake faruwa a gidan, Hafsat ta yi matuqar jinjinawa qanwar ta domin tayi qoqari ainun wajen cika dalilin da ya sa aka aura mata Alhajin, miqewa ta yi bayan ta yi addu'ar Allah ya kyauta, taje ta yi mata abinda take so taci ta kawo mata. Bayan komawar Alhaji sashen Hajiya Qarama wanka ya shiga ya sake yi sannan ya shirya cikin manyan kayan da suka fito da quruciyar da ta yi masa saura a tare da shi,yana tsaka da fesa turaruka Hajiya Qarama tace, " Alhaji ina son zuwa gidan mu na dad'e ban je ba Mama nata yin waya akan yaushe zan kai su Sabeerah, kaga week end ne zata ji daɗi idan na kai su yau, kai kan ka ka jima baka je gaida Mamana ba idan ka kai mu kuka gaisa sai ka tafi in yaso inna gama na kira driver ya dakko mu," "OK to ki shirya mu je na aje ku din," Cike da murnar samun nasara ta fara shiri ita da yaran, kwana biyu yaran na son zuwa gaida Aunty Eamaan amma an hana su sam,haka suka gama shirin su suka fita harabar gidan, Alhaji sai da ya sake leqa Eamaan suka gaisa again sannan ya fita,kan ya dawo Hajiya Qarama ta cika ta yi famm, a duniya ta tsani wannan mahimmancin da Alhaji ke baiwa Eamaan,kwafa ta yi tace muzuba mu gani idan tusa zata hura wuta kuma a juri zuwa rafi da tulu dan kuwa watarana zai tarwatse a qasa,shiga ya yi motar ya ja su sai gidan su hajiya qarama, maman ta ta ji dad'in ganin ta sosai,nan take sai Alhaji ya cire zargin komai da ke ran shi a ada game da yawan fitar ta, bayan sun gaisa ne kawai yayi masu sallama ya tafi,a can qasan layin su Hajiya Qaramar ne ya ga wani abokin shi nan ya tsayar fa mota a gefen titi suka tsaya gaisawa saboda an dad'e ba a haɗu ba. " Mama bari na je kasuwa na dawo, zan d'an sai wa abokiyar zamana wasu abubuwan da take kwad'ayi kin san me ciki," "  To shikenan Amma fa kar ki dad'e," Shine abinda maman ta ta ce ita kuma ta sa kai ta bar gidan,tana fita soron gidan su ta fesa turaruka masu daɗin qamshi sannan ta dauki sweet mai qamshi a jakarta ta saka a bakin ta( kun ji dai Hajiya Qaraman shagali abinda take yi ko? ta iya yi ma wani qato shiri mai kyau amma banda mijin ta) mai adaidaita sahu ta tare ta hau ta fad'a masa inda zai kai ta, babu b'ata lokaci ya yi hanyar gidan Alhaji Saminu na shaqatawa da ita, gilmawar ta Alhaji Abdullahi ya gani a cikin adaidaita sahu, cikin hanzari ya yi wa wannan abokin nashi sallama ya bi bayan su, daidai qofar gidan  ta tsaya ta sallami mutumin ta fad'a gate d'in da yake a bud'e ,dan ya san da zuwan ta yana ciki yana jiran ta, gidan ko mai gadi babu saboda baya son sa ido,tana shiga Alhaji ya qaraso da motar shi, ya shige ciki shima.......... *Chaiiiii shift let me faint i beg, dan na san Alhaji sai ya suma sau tara, na yi masa karar ɗaya ya cike goma*😱😱😭 [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 14 : Tana shiga ta yi sallama Alhaji Saminu ya fito daga shi sai gajeren wando, yana ganin ta ya buɗe mata hannu alamar ta je gare shi, babu b'ata lokaci ta cire mayafi ta yar a qasa ta nufe shi da sassarfa zata rungume shi taji an daka mata wata gigitacciyar tsawa,Alhaji Abdullah ne yace, "Idan kika kuskura kika taɓa shi a gaban idona sai na kashe ku gaba ɗayan ku," Cike da fushi da d'acin rai yake yin maganar dake nuni akan zai iya aikata abinda ya furta akan nasu, kallon shi ta yi a kidime da tsantsar tashin hankali dan kuwa shine mutum na qarshe da take son gani a yanzu a kuma wannan halin da suke ciki,Alhaji  Saminu ne ya qarasa takowa gaban Hajiya Qarama ya sunkuyar da kan shi ya yi kissing ɗin lips d'in ta,ganin haka ne ya sanya Alhaji Abdullahi jingina da kujerar kusa da shi saboda ganin qarfin halin Alhaji Saminu, gaba ɗaya ji ya yi jiri na diban shi, Hajiya Qarama d'an baya ta ja daga jikin Alhaji Saminun idon ta sai zubda hawaye yake yi, haƙuri take son ta bud'e baki ta bashi amma inaa ta kasa, "Na san me ya kawo ki waje na Hajiya, kuma wannan ranar nake ta jira sai dai to my biggest suprise sai ga shi kin zo min da babban gift na zuwa da Alhaji" Ya juya ya kalli Alhaji Abdullahi da isa da ta qama sannan yace, "Ban fada maka ba?  I vow to destroy your life and family from the day you destroy mine, Alhamdu lilLAAH i have succeeded in destroying your family, yanzu sauran abunda ka mallaka ka jira ni ina nan tafe kan dukiyar ka,maza ka tarkata matar ka ku bar min gida kafin na sakar maku durwan kare na, yayi maku fata-fata," Komawa d'aki yayi ya dakko rigar shi ya saka,Hajiya Qarama ce tayi qarfin halin cewa, "Me ke faruwa ne a tsakanin ku mara daɗi har haka?me yayi maka kake fadan hakan?" Dariya Alhaji Saminu ya yi sosai sannan yace, "Lallai ne ashe fa ke baki san tarihi ba, to bari kiji me mijin ki yayi min har na fara neman ki dan baqanta ran shi, a shekaru masu yawa da suka wuce, lokacin mijin ki na tsakiyar akuyancin shi daga zuwa gidana mu ci abinci, ya qyalla ido akan qanwata kuma amana ta da iyayen mu suka rasu suka bar min, amma haka wannan d'an akuyan ya sata a gaba, sai da yayi mata ciki har sau uku yana kai ta ana zubarwa babu wanda ya sani, a na huɗun ne basu samu nasarar zubarwar ba, jini ya ɓalle mata sakamakon ji mata ciwo a mahaifa da aka yi, " Share hawaye suka yi kusan a tare shi da Alhaji Abdullahi wanda tin da Alhaji Saminu ya fara bada labarin ya hau tina yanda abubuwa suka kasance a tsakanin su a shekarun baya wanda har yanzu idan ya tuna kuka yake yi na tsantsan nadamar lalata kamilar yarinya da ya yi, Alhaji Saminu ne ya ci gaba da cewa, "Tin daga wannan aikin da aka yi mata ta dinga zubda jini kuma taqi fadawa kowa sai a ranar da zata koma ga Allah ne take neman gafarar mu ni da mata ta,a nan ne ta faɗa mana komai da ya faru tsakanin ta da kai, a dai-dai lokacin da qanwata ta mutu wannan bunsurun ya sake ɗaukan wata d'iyar abokin mu ya fita da ita qasar waje yana sheqe ayar shi da ita, duk sai da qanwata ta zo rasuwa ta faɗi abinda ke faruwa, domin kuwa qawar ta ce, a haka ta mutu bai zo ba daya dawo, sanda na je na same shi da zancen lokacin ya fini komai a rayuwa, kuɗi suna, mulki da iko sai yayi min korar kare, tin daga lokacin na quduri niyyar sanadin komai na farin cikin ka, ina fatan ɗaya tarkon dana d'ana a cikin gidan ka shima ya tashi bayan na dukiyar ka dana d'ana maka nan da wasu kwanaki ko watanni, Allah ne kawai masanin sanda zai tashi bummmm,se dai ka ga dukiyar ka ta zama tarihi" Maganganun shi sun yi matuqar tsorata Alhaji Abdullahi da Hajiya Qarama , Hajiya Qarama kuwa ji ta ke kamar ta kashe Kan ta ta huta dan takaici, Alhaji Saminu ne ya daka masu tsawa gaba ɗayan su yace su tashi su fitar masa a gida, " Ohhh na manta Hajiya ko zaki ɗan tsaya ne mu ɗan yi na yau kan ki tafi?" Sai ya isa wajen ta yana shafata cikin wani irin yanayi na duniyanci,janyewa take tana kuka sosai Alhaji ya rintse idon shi, ya miqe da kyar yana hada hanya ya fita daga gidan direct mota ya faɗa hankalin shi a tashe,da taimakon Allah ya isa gida, ita kuma gidan su ta koma ta d'ebi yaranta ta yi gidan Alhaji da su, kowa ya tambaye ta meya sa ta kuka taqi kulawa, ganin haka yasa suma yaran kawai suka fara kuka, a haka suka isa gida yara kuka Hajiya kuka, yana zaune cikin mota yana ta rusa kuka dan ya kasa fita balle ya shiga ciki be san wa zai tinkara da wannan musibar da ta same shi ba, a haka ta shiga gidan ita da yaran,d'aga rinannun idanun shi ya yi ya kalli hanyar da take son bi yace, "Ashe matar nan bata da kunya? Me kuma ya dawo da ita gidana bayan ta ji na san komai? Maybe ta na da death wish ne ya sa ta dawo," Cike da fishi ya ɓalle murfin motar ya nufe ta,wasu kyawawan maruka ya tintsira mata sai da ta kifa qasa, ya bita ya take mata qafa ihu ta zabga wanda ya sanya Sahabee da Hajiya Babba dake tsaka da holewar su suka miqe tsaye a firgice a gigice,nan take suka ɗauki kayan su suka mayar, Sahabee ne ya fara fitowa waje sannan Hajiya Babba, ball suka ga Alhaji na yi da Hajiya qarama yaran ta na ta ihu suna kiran Daddy kar ka kashe Mum din mu, ihun su ne ya fiddi Iya da Eamaan da Hafsat farfajiyar gidan suma, sai masu aikin gidan dake lab'e suna kallo ikon Allah Ita kuwa hakuri kawai take bashi amma yaqi ma yin magana, dan wani abu yake ji ya tokare masa maqoshin shi,Eamaan ce ta tako a hankali cikin ɗan cije lebe dan yanzu ciwon kai ke damun ta,yana ganin Eamaan ya nufe ta da sauri kamar qaramin yaro, ya fada jikin ta, saurin tsaida jikin ta ta yi saboda kar su faɗi,hannun ta dika biyun ta sanya ta zagaye jikin shi da su, kuka ya saki mai qarfi yana ta yi ba qaqqautawa, ita kuma bata hana shi ba sai buga bayan shi da take yi, Iya abun nan ya d'aure mata kai matuqa dan kuwa bata gane komai ba, cike da Umarni ta kira sunan shi, ya d'ago sai ajiyar zuciya yake yi ya kalle ta Iya tace, "Abdullahi sanar dani meke faruwa ne haka a gidan yau kuma?" Eamaan ce ta kama hannun shi ta ce ma Iya, "Iya mu shiga daga wajen ki ko kinga kowa na kallo har da masu aiki, ina ganin in ya zauna ma zuciyar shi zata fi sanyi ya ji dad'in sanar da ke komai," kallon Eamaan d'in Iya ta yi ta kad'a kai sannan ta yi gaba,dikkanin su d'iba suka yi zuwa part din Iya,kamar Sahabee ya gudu haka yake ji saboda kar asirin shi ya tonu, dan tabbas ya san asirin Hajiya Qarama ne ya tonu, suna isa kowa ya zauna Iya ta maimaita tambayar ta, Alhaji cikin kuka ya sanar da ita su Sabeerah ba yaran shi bane, ya qara da Sanar da ita wanene uban su, Salati Iya ta ɗauka,nan da nan ciwon ta ya tashi, da gudu suka nemo maganin ta suka hau dura mata, ana jera mata sannu, Eamaan ce tace a kaita daki ta kwanta ta huta in ta samu bacci tinda dana bacci ciki zata samu sauqi inshaa Allah, d'aki Sahabee ya kaita hankalin shi a matuqar tashe, qin komawa parloun ya yi ya zauna nan wajen Iya, Alhaji Abdullahi kuwa miqewa tsaye ya yi ya nunawa Hajiya Qarama hanya ya sanar da ita ya sake ta saki uku, kuma ko tsinke ba zata ɗauka a gidan ba tinda shi ya siyo mata dik abinda take taqama da shi dan haka ta fitar masa a gida yanda ta shigo, kuka take kamar ranta zai bar jikin ta amma ba wanda da ya tausaya mata,kowa ta kan shi yake yi a wajen, musamman Hajiya Babba da ta sa a ranta in dai aka kori Qarama zata tona masu asiri, nan ko bata san hankalin Hajiya qarama yayi tashin da ta manta da rayuwar su balle ta tona masu asiri, tankad'a ta Alhaji ya yi waje sannan ya yakice yaran dake ta kuka suna kiran Daddy kayi hakuri bazata sake ba, muma ba zamu sake ba, Eamaan ce ke kuka dan sabo da yaran da ta yi,yana ganin hawayen ta kuwa ya haukace da faɗin, "ku tafi nace shegu tsinannu kuna saka min mata kuka, tankad'a kan su ya yi, ya  kira masu aikin gidan maza tare da basu Umarnin a fitar Masa da su daga gidan,ya miqe ya nufi bangaren Eamaan,dan tinda ta ga ya haukace da korar yaran da mahaifiyar su ta bar wajen tsabar tausayi, tadda ita ya yi tana ta kuka bai hana ta ba,dan ya san ko giya ya sha ba zai dawo da Qarama ba ta tafi kenan, sai da ta yi mai isar ta sannan ta miqe ta yi toilet ta gyara fuskar ta ta fito, tana fitowa ta gan shi kwance sai hawaye ke tsiyaya daga idanun shi, "Dama abun da na aikata a baya na nan na bina ban sani ba? neman lokaci irin wannan yake ya d'aid'ai ta ni? to me ne ne Saminu yace sauran ɗaya bomb din? Me zai faru kuma bayan wannan cin amanar da Qarama tayi min?" "Ba abinda zai fatu sai alkairi, dan haka ka kwantar da hankalin ka ka ji," Da wannan ta ɗauke hankalin shi da salon ta da ya yi kewa. Ba dan k'warewar da Eamaan ta nuna masa ba da kuma son da yake yi mata baya jin akwai abunda zai ɗauke masa takaicin wannan ranar, ranar dai Hafsat barin bangaren su Eamaan tayi ta koma na Iya, dan gaba ɗaya Alhaji ya haukace a kan Eamaan, idan Alhaji yana gaban Eamaan jin shi yake yi kamar jaririn ta, zai iya yin komai gaban ta. A kwana a tashi cikin Eamaan ya kai wata bakwai kullum Alhaji cikin nasiha yake mata akan ta kula da abinda ke cikin ta,dan yasan ko bayan ba shi babu mai kula masa da abinda suka haifa a dangin shi,ba masu son shi domin Allah sai dan abinda ya mallaka,a kullum takan nuna masa ta fahimtce shi ya daina saka damuwa a ranshi. Watan da zai kama ne za a yi bikin Hafsat dan haka ta koma gida dan fara shirin biki,ranar da zata tafi Eamaan kuka ta dinga yi domin kuwa ba ta son rabuwa da yayarta ta,lokacin da aka fara gudanar da bikin kuwa Alhaji ya sakar masu kuɗi sosai da su suka qarasa yin siyayyar da basu yi ba, angon Hafsat kuwa idan suna waya Eamaan dariya take yi musu sosai, dan da ganin yanda yake abubuwa zai yi naci,Iya ko yanzu jikin ta ya qara yin sanyi, ba safai take zagewa ta yi ta yiwa Eamaan masifa ba,Eamaan ta dawo da yi mata abinci kamar yanda take yi ada dan tace albarka take nema. Tin safe Eamaan ke shirin tafiya gida saboda gobe za a fara bikin Hafsat, Alhaji bai so ba amma babu yanda zai yi haka ya barta ta tafi,shi kuma ya sanar da ita zai koma Abuja dan bai ga abinda zai zauna yayi ba a gidan bata nan. Hajiya Babba da Sahabee kuwa sak hakan yayi musu daɗi saboda sun samu freedom ɗin yin abinda suka ga dama a gidan babu mai sanya musu ido, fatan su ma shine idan ya tafi ya dad'e wannan karon bai dawoba. Alhaji ba qaramin warning din Hafsat yayi ba akan ta kular masa da Eamaan da abinda ke cikin ta kar a wahalar masa da mata da aikace-aikacen biki sannan ya qara da cewa, "A kuma dinga bata abinci akan lokaci, kar kuna damun ta idan tana bacci, banda yawan sata aiki Hafsat, kinga dai bata jin dadi,i don't want to lose my baby pls" Cike da tausayawa Eamaan ta kama hannun shi ɗaya ta kwantar da kan ta a gefen jikin shi tace, " Ba zaka rasa komai ba Alhajina, kwana biyar kawai zanyi ko ka dawo ko baka dawo ba zan dawo gida ni, ka sa wa ranka salama kar wani ciwon ya zo yana damun ka ka ji?" D'aga mata kai ya yi tare da manne ta a jikin shi ya na sumbatar ta, Hafsat rufe fuska ta yi da hannu d'aya tana fad'in, "Oh ni Hafsat ina ganin rayuwa a wajen bayin nan na Allah ! Thank god na baro gidan ku na dena ganin wannan rayuwa da kuke bani kunya da ita," Alhaji ne ya kalle ta yace, " kinyi magana  ne ?" 'Aaa'aa ni ban ce komai ba," Dariya suka yi gaba d'ayan su, sannan  Hafsat ta taya Eamaan shigar da kayan ta cikin gidan. Aqofar masallacin gidan su ta gan shi yana saka takalmin shi, suna haɗa ido suka ji wani abu daga kan su zuwa qafar su mai nauyi qarshe ya danne zuciyoyin su, saurin kauda kai ta yi tare da yin a'u'ziyya tai maza ta shige gidan su, shi ko tsayawa ya yi kyam ya bi hanyar da ta shige gidan nasu da kallo,gaba ɗaya ya can ja yayi kyau yayi fresh da shi ya aje gemu irin na samarin yanzu, sai dai duk wannan kyawun da yayi be hana a gane irin ramar da yayi ba...... *Eamaan na gayyatar ku auren Hafsat, zamu ci rangyam💃🏻💃🏻💃🏻 who is going with me ? zan maku kuɗin mota*💃🏻 [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 15: Shigewa suka yi da hanzari nan suka tadda gidan a cike da mutane maqil, kowa ya ga Eamaan sai ya yi sha'awar ta ya yaba saboda ta yi kyau ta qara cika dumdum da ita, ga dan cikin ta daya fito gwanin sha'awa, sai yalwataccen gashin ta da bai boyuwa a dik shigar da zata yi, gaishe da 'yan uwa da abokan arziqi Eamaan ta dinga yi suna amsa mata cikin sakin fuska da raha, wasu qannen Mama na ganin Hafsat suka saki gud'a har wata a cikin su tace to ai amaren biyu ne tinda Eamaan ma bata gama cin nata amarcin ba gud'a suka sake saki akai ta shewa ana raha. An sha biki lafiya an gama inda aka kai Hafsat garin Bauchin Yakubu gidan ta madaidaici daidai rayuwar da take sha'awa, ba qaramin godiya ga Allah ta yi ba na samun gida mai kyau haka, Hafsat da Eamaan sun sha kukan rabuwa da junan su,sai bayan kwana biyu Babbar yayar su zata zo ganin gida dan kuwa ta yi missing bikin ba da ita aka yi ba, a haka suka taho suka bar amarya da kewar 'yan uwan ta, direct gida Ammaah tace a ajiye Eamaan, dan ba ta ga me zata koma ta yi masu ba tinda mijin ta ya dawo daga Abuja ya na gari sai waya yake faman yi yana tambayar an gama bikin kuwa?Eamaan taci kuka sosai haushin Alhajin take ji da yayi mata haka, dan bata taɓa yi masa musu ko rashin da'a ba amma zai hana ta ɗan zama a gidan su ta huta gajiyar biki,dika-dika kwanan ta nawa a gidan nema da zai damu da rashin ta shi ba tafiya yake yi ya bar ta ba,a gaskiya be kyauta mata ba ta so ta d'an huta a gidan su itama kafin ta koma, cike take famm da haushin shi aka ajiye ta a wajen gate ɗin gidan nasu,a zaton su mai gadi ne zai buɗe gidan tinda aikin shi kenan sai ganin Alhaji suka yi da kan shi, ya fito ya buɗe yana ta washe baki, kananan kaya ya sanya kan shi ya sha aski ya yi kyau sosai kamar wani matashi, tsabar gayun Alhaji yawancin mutane basu yarda da cewar ya haura shekaru hamsin a duniya, cike da murna ya gyra zaman farin gilashin idanun shi a fuskar shi ya tinkare ta, su kuma 'yan uwan Eamaan suka yi mata sallama aka tada mota suka wuce kowa na sha'awar dacewa da miji dan k'walisa da tayi,a hankali ta ɗan sassauta fushin ta ta gaida shi, daga nan bata qara cewa komai ba ta wuce shi ta shige cikin gidan haka Alhaji ya bi bayan ta riqe da akwatin ta a hannun shi sai surutu yake yi mata ita kuwa ko A bata ce masa ba, suna shiga ya janyo ta ta fada jikin shi, cikin kashe murya yace mata, " Wai me ya faru ne my baby naga kina fushi fa ni," kuka ta sake masa sosai tana buga qafa a qasa cike da shagwab'a tace, "Yau fa aka gama biki zaka matsa se na dawo, na so na je gida na kwana da Ammaahna yau d'aya dai shine za kai ta waya kace a dawo da ni gida," kukan ta ci gaba da yi shi kuma yana aikin lallashi, can qasan ran shi kuma yana dariya, gashi dai kuka take yi amma duk ta bi ta manne masa a jiki tana wani shaqar qamshin jikin shi da take so tin bayan da ta samu cikin jikin ta,dik da bata taɓa faɗa masa ba saboda kunya da tazarar shekaru da ke tsakanin su ya gane da kan shi tana tsananin son qamshin jikin shi, wanda a zaton shi turaren da yake sanya wa take so sai ya siyo mata irin shi sak, qarshe cewa tayi ita ya ɗauke ya dinga shafawa kawai ba irin shi take son shafawa ba, har ta kai ta kawo da kanta take fesa masa ta zauna a jikin shi tana shaqar qamshin, d'aga ta a jikin shi ya yi yace mata, "Wash Allah baya na baby kin ji nauyin da ki ka yi kuwa? Washhh kar ki karya wa Iya yaron ta fa ki haɗu da ita dan naga kwana biyu tana ji dake kun dena faɗa..... to shikenan zo na maida ki gidan ki kwana kin san dik abinda kike so shi nake so nima" Narke wa ta sake yi a jikin shi tana shinshina qirjin shi tace, " A'a sai da na dawo gida kuma zaka wani ce na koma na kwana,wato salon ka ja amin faɗa a wajen Ammaah ko" Dariya ya yi sosai ya ci gaba da lallashin amaryar shi cike da kulawa,su na qarasa shiga sashen ta ya nufi d'aki da ita ya ajiye ta a gado ya hau cire mata mayafin jikin ta da riga da d'ankwalin ta dan ta sha iska, ita kuma tsananin gajiya ya sa ta fara hamma, juyi tai zata gyara kwanciya,yana ganin haka ya san bacci take ji sosai dan haka sai ya kunce mata zanin jikin ta dan ta samu sakewa sosai d'ago ta yayi suna fuskantar juna yace, " A'aa sai fa anyi wanka za ai baccin nan, na san halin ki cikin dare sai ki tada ni kice min zaki yi wanka, muje na yi maki in kin gaji ne," Cike da shagwaba ta ce "Ni dai ka barni na yi bacci na,bacci nake ji sosai idona har yaji yake yi min," D'aga ta ya yi cak ya nufi toilet da ita,cikin nishi yace "Wai Eamaanii na ba dai nauyi ba,kinji nauyin da ki ka qara kuwa, sai ki karyawa ɗan tsohon mijin naki baya ai," Dariya ta yi masa sannan ta qara sake mishi nauyin ta, dan kuwa ta gaji da rakin da yake yi mata kullum akan nauyin da ta qara kamar ita ta sa shi d'aukan ta, da baya amfana da d'aukar ai ta San ba zai yi ba,a haka ya mata wanka da ruwa mai zafi, ta gasu kuwa sosai ana gamawa ta d'aura towel ta tako wajen sink tayi brush, sannan suka fito a tare, mai ya shafa mata tace, "Sweet nima yau ka shafa min irin tiraren ka na dinga qamshin ka ka ji," D'akkowa ya yi ya fesa mata yana mamakin hali irin na masu ciki tinda da dai ita tace bata so yau kuma gashi tace a fesa mata, yana fesa mata taji kamar ba turaren ba taso yin qorafi akan qamshin ta dai daure,kayan bacci ya d'akko mata ya saka mata rigar zai saka mata wandon tace ita fa ba zai saka mata ba zata takura a barta haka ta sha iska ai kuwa a haka suka kwanta, ganin yanda ta gaji yasa bai damu da sai ya nemi haqqin shi ba a wajen ta, ita kuma ta saddaqar in ya nema ba zata yi masa rashin BIYAYYAH ba zata bashi haqqin shi, da ta ji shiru kawai sai ta yi baccin ta cikin natsuwa da kwanciyar hankali. Hajiya Babba dai likkafa ta ci gaba, dan kuwa yanzu Sahabee har kwana yake yi a wajen ta, tin da Eamaan da Alhaji suka yi tafiya ya daina kwana wajen Iya, sai ya shirya kamar zai fice yawon shi sai ya zame ya yi bangaren Hajiya, a haka Sahabee ya maye gurbin Alhaji a wajen Hajiya, yau ma Alhaji na wajen Eamaan shi kuma yana wajen Hajiya, ga su kamar inji ba sa gajiya da yin abu ɗaya. Iya kuwa kullum haka zata yi ta faɗa akan yawon da Sahabee yake yi a bayan idon shi,amma a gaban shi ba ta iya yi masa maganar,sai dai in shi ne ya yi wani zancen barikancin a gaban ta,sai tace masa kai yanzu baka jin kunyar fad'amin kai dan iskane ko? Ita sam bata san ya ake tarbiyya ba sai shegen son nuna ita fa wannan d'anta ne, ko 'ya'yan ta ne, amma tarbiyya kuwa wala. Eamaan ta riga Alhaji tashi kamar kullum sai ta yi wanka ta wanke baki ta saka doguwar riga da d'ankwalin kayan, ganin yanda qirjin ta ya fito sosai a cikin rigar ne ya sanya ta saka qaramin hijab da ya wuce qirjin ta, gyara wajen ta dan yi dan ba datti sai qura, sannan ta fice wajen Iya, daga bangaren Hajiya Babba ta gan shi yana fitowa, ta bishi da kallon ta mai kid'ima shi, daga baya ta ɗauke kan ta irin ko a jikinta din nan rayuwar ku ce, ta shigewar ta wajen Iya,rasa ina zai koma ya yi, in ya koma wajen Hajiya Babba Alhaji ya shigo fa? In ya shiga wajen Iya su kacame a hanya da Eamaan kuma, salin alim ya wuce wajen driver ya karb'i key ɗin mota ya bar gidan abun shi, ita kuma mamakin qarfin halin su take gani sosai, dan ta tabbata a wajen Hajiyar ya kwana, aikace-aikacen ta ta fara yi har ta gama be dawo gidan ba, sai ta je d'akin Iya ta tarar ta farka daga bacci har tayi wanka tana zaune tana sauraren redio,durqusawa tayi ta gaida ita sannan ta sanar da ita abincin karyawa ya kammalu,Iya kuwa fuska babu yabo babu fallasa ta tambayi Eamaan ya gajiyar biki sannan ta yi fatan alkairi. Qarshe dai Iya har da godiya domin yanzu ko ba komai ta gano wacece Eamaan ba kamar sauran matan Alhaji bane ita, yarinya ce data ɗauke ta a matsayin Uwa ba suruka ba, dan haka itama zata qoqarta ta d'auke ta a matsayin d'iyar ta,tashi ta yi taje ta wanke hannu a band'akin dake d'akin ta ta fito parlour, anan ta tadda Eamaan tana haɗa mata kokon da ta dama mata,koko yayi fari qal saboda ya sha madara da pineapple flavour da kayan qamshi sai qamshi yake yi, gefe kuma ga qosai ta yi mata,dan Iya na son wannan haɗin matuqa, sai dan farfesun naman rago da ya ji kayan qamshi da albasa,cikin yatsina fuska Iya tace, " Wai ni ina Sahabee ne? Rabona da shi tin jiya kafin isha'i da yai wanka ya fita ban sake ganin shi ba,duban d'akin shi ki kiran shi, d'annema mai kan buta kawai," Eamaan da ta riga ta san inda yake kawai sai ta tashi ta leqa d'akin ta dawo tace baya nan,Iya sallamar ta ta yi tace taje ta daukar masu nasu ta tafi kawai, shi ya sani, ( Iya ba ta iya yiwa yaran ta addu'ar shiriya ba sai zagi da kiran su da sunayen da in suka bi yaro sai ya qara lalacewa) Eamaan ta tarar da Alhajin ta ya gama shirin shi tsaf na zaman gida da yake yi idan yana gida ba fita zai yi ba,dan kuwa shi mutum ne me yawan gayu a cikin gida dan kawai iyalin shi su gani su ji dad'i, abinda ke baqanta masa rai kenan a baya da Hajiya Qarama, ta na gani shi da yake namiji zai yi wanka ya yi gayu, amma ita ba wannan a tattare da ita sam, ya na Kuma da qoqarin taya matan shi aiki, musamman Eamaan da itama ke yi masa komai da yake so Kan jiki Kan qarfin ta, shi yasa ma da ya tashi be gan ta ba ya ga Kuma ta gyara ko Ina se ya gyara gadon daya tashi akai, yana riqe da cup da ya hada coffee yana sha ta shigo, "Wai ke ba zaki daina wahal da kan ki ba ko a wannan yanayin da kike ciki ko? yanzu na je na hana ki Iya taga laifi na, bakiga kina dauke da ciki ba ne, so kike ki ja mana matsala ne," Cikin murmushi ta ce masa, " Inshaa Allahu bama tare da matsala,wanda basu kyautatawa iyayen su ma basa tare da ita balle ni da nake yi wa uwata aikin lada, ai sai dai na ga alkairi ba dai matsala ba, so kake na zo na jibge kamar kayan wankin da suka rasa mawanki su jiki na ya yi ta ciwo ba dalili?" Kad'a kai ya yi alamar Ah ah tace " To ka gani... ai yi ma Iya abun karyawa ba wani aiki bane mai yawa nima yana sawwaqe min sake zuwa na yi maka naka na daban, tinda bana so kana cin na masu aiki kana da mata,nima kuma dama ba son cin nasu nake ba ,tinda ba zuwa ko ina nake yi ba kaga girkin zai taimaka min na samu k'warin jiki na,dan haka kar kana damun kan ka akai na," Ya gamsu da bayanan ta amma da kam gani yake yi kawai wahala take yi. A kwana a tashi Eamaan ciki ya shiga watan haihuwar shi, komai Alhaji ya fita ya gani na jarirai zai siyo ya kawo mata, murna yake yi sosai saboda za a haifa masa ɗan shi na halal mallakin sa, in yana wa Hajiya Babba karad'i da zumud'in haihuwar sai ranta ya na ɓaci kishin ta ya bayyana ta kauda kai, a haka ya gane itama ba son babyn take ba, Sahabee ma bai wani damu ba ko a haihu ko kar a haihu oho,Iya ce kawai ke taya shi murna kusan kamar tafi Alhaji son wannan abinda za a haifa d'in ma, duk shekarun ta ace bata taba ganin jikan ta ba ai dole ta yi ta d'okin ganin wannan da za a samu yanzu. Eamaan girki take yi a kitchen din Iya hankali kwance, juyawa tayi ta d'aga qafa zata dakko muciya ta tuqa tuwon shinkafa da take yi ta ji qafar ta riqe ta kasa gaba da ita ko baya, abu kamar wasa sai da ta kwalawa mai aiki kira, da kyar ta taimaka mata suka shigo parlourn Iya ta zaunar da ita a kujera, zaune Iya take ita da Alhaji suna hira suka ga an zaunar da Eamaan a kujera, miqewa suka yi da sauri suka isa wajen ta suna tambayar lafiya? Ita kuwa babu abinda take yi da ya wuce kiran sunayen Allah, Alhaji ne ya kama ta suka fita sai wajen mota, da kan shi ya ja su suka tafi asibiti, ba a jima ba kuwa Allah ya sauke ta lafiya, ta samu yarinya kyakkyawa qatuwar gaske ga ta fara fat kamar iyayen ta, se kuka take zabgawa, da fari Iya ta ma zaci namiji ne saboda kukan da take tsalawa saida aka bata jinjirar taga ashe mace ce sai tace, " Sannu ci mu ci acici kajin binni,to bismillahi daga zuwa duniyar mu an fara wage mana baki ana son a ci abinci dan wannan kukan da ji na yunwa ne" Nurses ɗin da suka miqo musu jinjirar kuwa dariya suka Sanya, Iya kuwa tace, " Yo Allah yarinya sai d'anneman cin tsiya,Kai da gani wannan se an aje wa uwar ta buhunan gero da farar shinkafa da gyad'a dan yin kunu kawai" Dariya suka sake sanyawa suna tsokanar Iya da kishi ne kawai ke damun ta. Suna nan zaune ana duba lafiyar baby da Eamaan dan haka ba a sallame su da wuri ba sai dare,asibiti kamar zata tsage dan mutane dake zuwa taya su murna,ba a bar Ammaah da Mama wajen bayyana farin cikin su,har da kukan farin ciki Ammaah ta yi sanda labarin haihuwar ya riske su, likitoci ne sika yanke zasu sallame ta kawai tinda an haihu lafiya. Sun dawo gida cike da murna da farin ciki, Sahabee da ya ga yarinyar sai da ya yi tasbihi ga Allah dan ganin kyaun ta, a zuciyar shi ya nema mata tsari da haɗuwa da maza irin su shi da uban ta, yarinyar ta kwanta masa a rai sosai. An yi suna yarinya taci suna Fateema suna kiran ta da Fatee, yarinyar da alama za ta yi wayo da wuri duk wanda ya wuce sai ta bi shi da ido. Gaba ɗayan ahalin gidan na zaune a sashen Iya har Baby Fatee suna ta hirar duniya suka ji an k'wank'wasa qofa, Sahabee ne ya je ya buɗe qofar, abinda ya gani da mutanen da ya gani sun firgita shi ba kadan ba hankalin shi ya tashi, dan yasan yau kam ta Alhaj ta qare, da baya-baya ya koma parlourn yana nuna masu hanya da hannun shi, Alhaji fad'a ya fara yi masa yace, " Meye haka ne ka dawo kana abu kamar wanda ya yi gamo? Su waye ne suka zo? Matsa ni na ga ko su waye zasu shigo man gida kai tsaye cikin iyali su rikita ka ha.........." Maganar shi ce ta maqale da ya yi arba da su, har wani dan tintsirawa ya yi kamar an hankada shi ya yi baya kamar zai faɗi....... *Hahaiiii casssss gamo ya yi da mutan boye hala*🤣🤣🤣 [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼     BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 16: Ganin hukumar EFCC a gidan Alhaji ba qaramin tada wa kowa hankali yayi ba, jikin shi har rawa yake yi a lokacin da ya koma ya zauna,suna shiga suka samu waje suka zauna suma kamar gidan su tare da gabatar da kawunan su da kuma abinda ya kawo su,babu b'ata lokaci suka fara binciken Alhaji daga fatari har fataari, duk wata dukiyar shi sai da aka karɓe da sunan za a yi bincike akai idan haqqin shi ce za a dawo masa da ita, idan kuma ta gwamnati ce to fa gwamnatin zata karɓe wataqila har hukunci ma ya biyo baya,ganin yanda suke yi masa abubuwa cikin cin zarafi da wulaqanci ne ya koma tunanin anya wannan hukumar EFCC ne ma kuwa? Amshe dikkan kadarorin shi da hukumar tayi ne ya sanya jikin Alhaji ɗaukan rawar sanyi, Eamaan kam ta dad'e da fara kuka saboda matsanancin tausayin mijin nata da ya kama ta,abubuwan da suke samun shi akai-akai na musibu sun yi yawa. Eamaan da Iya sai kuka suke zabgawa babu mai lallashin wani a cikin su,Alhaji kuwa yana zaune shiru banda karkarwa babu abinda jikin shi ke yi, ma'aikatan hukumar da kansu suka dinga shiga lungu da saqon gidan suna ɗaukan takardu da dik abinda yayi musu, Hajiya Babba kuwa takaicin kwashe mata sarqoqin zinaren ta dik shi yafi damun ta har ya sanya ta kasa yin kukan ma, shi kuwa Sahabee baqin cikin yanda aka k'wace komai ba tare da ya samu wani abu daga wajen yayan nashi ba shi ya sanya shi zabga tagumi yana bin kowa da kallo,daga gidan da suke ciki sai motoci biyu kawai aka bar musu. Suna cikin wannan halin na jimami aka sake k'wank'wasa qofar parlourn Iya,nan take Alhaji yaji k'wank'wasawar har cikin tsokar zuciyar shi,gani yake yi kamar wata musibar ce ta sake tinkaro shi da iyalan shi,babu wanda yayi jarumtar amsawa mai k'wank'wasawar daga qarshe dai da kan shi ya buɗe ya shiga parlourn cike da isa da taqama, Alhaji Saminu ne yake ta zabga murmushin da yafi dacewa a kira shi da sassanyar dariyar samun nasara kafin yace, " Alhaji Abdullahi kenan a zaton ka zaka samu kuɗin gwamnati ka sace ka killace dan ka mora kai da iyalan ka ba tare da gwamnati ta k'wace abinta ba? to bari kaji wani sabon albishir da zan yi maka dan na kula baka kalli news ba jiya kana nan kana shanawa da wannan kyakkyawar matar taka ko? Albishir ɗin shine majalisa ta sauke ka daga muqaminka yanzu haka ana can ana jefa quri'ar samun madadin ka,kai kuma kana nan a nade wajen mata," Ya na gama faɗin maganganun nashi dake kama da shaqiyanci ya kwashe da dariyar mugunta harda tafa hannayen shi,a harzuqe Alhaji yayi kan shi da niyyar yi masa dukan tsiya,kafin ya qarasa gaban Alhaji Saminu ya yanke jiki ya fad'i a qasa yana ta wani abu kamar mai bugun iska. Ihu Eamaan ta sanya ta ajiye Fatee ta nufe shi tana jijjigawa, Iya kuwa jinin ta ya jima da hayewa ganin ta gaba ɗaya yayi rauni jinta take yi kamar ba zata kai gobe ba saboda tsananin ciwon kai da bugawa da zuciyar ta keyi dan haka ko yunqurin zuwa wajen Alhaji bata yi ba,dan kuwa ta riga ta san da ta miqe se dai a yi biyu,sunan Allah kawai take ambata dan shine mafitar ta a wannan halin da suke ciki. Eamaan kuka take tayi sosai ta na yima Sahabee magana akan ya rabu da Alhaji Saminu daya dunqunqunewa wuya ya zo akai Alhaji asibiti,amma ya qi sai naushin Alhaji Saminu yake yi yana zagin shi, shi kuma yana dariya kamar ba jikin shi ake duka ba. Jikin Alhaji Abdullah ne ya saki ya daina motsi Eamaan kuwa sai ta fasa ihu da qarfi wanda ya ja hankulan Hajiya Babba da Sahabee,Waje Sahabee yaje ya hau kiran masu gadi da driver akan su zo su taimaka masa, suna zuwa kuwa suka hau ciccibar Alhajin suka fita dashi suka sanya shi a mota . Asibiti suka kai Alhaji nan da nan likitoci suka duqufa akan shi dan duba lafiyar shi, ba shi ya farfado ba kuwa sai da asubar washegarin ranar da suka kaishi asibitin, Eamaan ta ci kuka ta gode Allah har ta hakura ta barwa Allah komai, Fatee kuwa sai kallo take bin kowa da shi,lokacin da likitoci suka sanar da iyalan Alhaji samun cutar barin jikin da ya yi ba qaramin shiga cikin damuwa suka yi ba, likitocin kansu sai da suka tausaya ma su saboda sun san shi farin sani ma kuwa yana daga cikin masu kuɗin dake taimakawa asibitin nasu, ga Alhaji nan kwance samb'al babu imm ba umm umm sai ido,yawu ma baya iya hadiye shi gaba ɗaya sai wani ya zubo,Eaamaan kamar zata haukace haka take jin kan ta, saboda shiga damuwa da tashin hankali,tashiga wani irin yanayi na tsantsan tausaya ma mijin nata,nan take ta hau yi masa addu'ar Allah yasa ta hanyar jinyar nan da ta same shi ya samu gafarar Allah,Allah ya yafe masa dukkan abinda ya aikata. Bayan kwana biyu likitoci suka basu shawarar kawai a maida shi gida a ci gaba da jinyar shi,idan yaso sai su dinga kawo shi gashi akai-akai, dan kuwa ciwon ba mai warkewar bane yanzu, kuma gashi kuɗin zaman asibitin ma yana neman ya gagare su, haka aka basu kujerar tura marasa lafiya da magunguna aka d'oro Alhaji suka dawo gida. Duk ran girkin kowaccen su sai a tura shi akai shi bangaren ta,masu aiki kuwa Iya ta sa aka tara mata su dika ta basu hakuri ta sallame su, cikin kuka da fatan samun lafiyar Alhaji Abdullah suka bar gidan, tinda suke a gidan basu taba zama da yunwa ba haka ma yaran su dake gida kullum a qoshe suke,masu kirkin cikin su ma har maqotan su suke yi wa alkhairi,sutura kuwa sai dai su baiwa wasu saboda basu da talaucin ta ga albashin su mai tsoka suna Karb'a akan lokaci babu fashi ko yankewa, masifar Iya da Sahabee ce kawai dama ke sanya su jin sun gaji da zaman gidan watarana. Bayan tafiyar masu aiki sai gidan ya zama shiru kamar babu mutane a cikin shi, a hankali Sahabee da Hajiya Babba suka dai na tausayawa Alhaji halin da ya shiga, har ta kai idan ya dawo ɓangaren Hajiya Babba ta dinga masifa kenan idan yayi fitsari a jikin shi ko ba haya, yawun shi kuwa ganin shi take yi kamar wata najasa idan ya zuba a qasan carpet ɗin ta ta dinga zuwa ruwa tana wankewa tana masifa kenan,qarshe dai idan baya nan tafi samun kwanciyar hankali ta yanda ita da Sahabee sai su kwana aikata masha'ar su a natse,a hankali suka buɗe sabuwar rayuwa ta jin daɗi babu kama hannun yaro, daga baya ma duk da sun kula Alhajin ya sani ba ya iya komai baya iya magana sai idon shi da zai ta zubar da hawaye ba su damu ba, harkar su kawai suke yi ko yana sashen Hajiya Babbar. Iya kam kullum ta na kan abun sallah tana kai kukan ta ga Allah ya kawo musu sassauci ya baiwa Abdullahn ta lafiya,a kwana a tashi kula da Alhaji da komai nashi ya koma wajen Eamaan,ita ke kula da kashi da fitsarin shi, itace ke qoqarin d'aga shi duk nauyin shi ta wanke shi ta gyara shi, Ammaahn ta kullum kukan tausayin d'iyarta ta take yi game da halin da take ciki, haka ma Daddy da Mama suna tsananin tausaya mata, duk wanda yaji rayuwar da gidan Alhaji Abdullahi ta koma sai ya tausaya masu. Yau Eamaan ta fita a girki Hajiya Babba zata ɗauka dan haka tin kafin lokacin komawar shi sashen Hajiya Babban yayi Eamaan ta bashi abinci yaci ya qoshi ta yi masa wanka ta gyara masa jikin shi sannan ta gangara shi zuwa sashen Hajiya Babba, koda taje sai ta k'wank'wasa qofar sashen Hajiya Babbar, ita kuwa tana zaune ta sha kwalliya sai zabga qamshi take yi tana taunar chewing gum kamar wata qaramar yarinya,cike da rashin mutunci ta buɗe qofar ta tsaya ta kalli Alhajin ta maida kallon ta kan Eamaan da ta rame tayi duhu saboda wahala sannan tace, "Wai ni meye ne na wannan gangare-gangaren ne ? Ni ki je na yafe maki girkin nawa ki haɗa dika ki riqe,dan banga dalilin da zai sa ana kawo min aikin kashi da fitsari ba kullum, naji da nawa ma mana haba ! ke da kika ga zaki iya kije kiyi ta fama amma ni kam ba zan iya wankin kashin qato ko na ce tsoho kamar wannan ba, in kuma zancen auren ne sai ya sallamen na qara gaba dan bashi da wata mamora yanzu a waje na," Hannun Alhaji na dama dake motsawa kaɗan kaɗan ya d'aga yayi nuni da yatsun shi guda uku,nan take Eamaan ta durqusa a gaban shi tana ta cankar abubuwa amma yana kad'a mata yatsa alamar basu yake nufi ba, qarshe dai Hajiya Babba ce ta ce masa, "Wai tsaya ko dai masakin mijin naki yana nufin ya sake ni saki uku ne?" Nan take Alhaji yayi saurin daga yatsan shi qarami alamar eh,salati Eamaan ta sanya tace, "Ah ah ba haka yake nufi ba,ai kin ga bashi da lafiya ma be san me yake faɗa ba," A rikice Eamaan take yin maganar saboda bata so ta gasgata abinda Alhajin yayi,ita kuwa Hajiya Babba shewa ta sanya ta buga cinya tace, "Tafi nono haske Abdullahi,me zan ci gaba da zama nayi a cikin wannan qaddararren aure dama ni? ko da can ba zaman ka kai kada'i nake yi ba a gidannan zaman qanin ka da dukiyar ka nake yi, shi yasa kaga na kafe har ina jin tsoron kar asirin mu ya tonu, na godewa Allah da bana haihuwa da tini ka samu abinda zaka sarqafe ni na zauna da kai dan dole a wannan halin babun da ya same ka,shi kanshi wanda nake zaune domin shi yanzu ya zama lagwani, ba sosai yake iya min aikin danake so ba,dan haka sai dai nace Allah qara sauqi," Ta kad'a jikin ta ta shige bangaren nata, akwatunan ta ta d'akko ta loda kayayyakin ta sannan ta ɗauki dik wani abu da ta san yana da daraja a sashen nata,sai da ta gama tana qoqarin fitowa sanye da mayafi ta tarar da Eamaan a bakin qofar ta tsaye cikin ɓacin rai tace mata, " kin san Allah kika kuskura kika ce zaki deb'i wani abu ki bar gidannan da shi sai kin fita a nakashe kema, in kuma kin musa abinda zan iya aikatawa bismillah saboda in zan iya tinawa randa Hajiya Qarama zata bar gidannan bata ɗauki komai ba Itama har murna kika dinga yi a ranar,ina da labarin ke ɗin auren cushe aka yi masa dake kuma ya hakura ya zauna dake babu ko tsinken iyayen ki a siyan kayan d'aki, dan haka kama hanya ki fita kafin na nuna maki d'anyen aikin da zan iya aikatawa," Hajiya Babba tayi matuqar tsorata da yanda Eamaan ta canja cikin qanqanin lokaci ta koma kamar wata mahaukaciya sabon kamu. " To ai dai a barni na ɗauki jakar hannu ko," Hajiya Babba ta faɗi hakan cike da tsoro da fargabar abinda Eamaan zata yi mata, Eamaan hanya kawai ta nuna mata ta na bin ta da gigitaccen kallon nan nata mai rikitarwa, sumi-sumi Hajiya Babba ta rab'e ta ta fice tana maganganu qasa-qasa kamar wata qaramar yarinya,sai da taje bakin gate din fita kuma ido ya raina fata, gaba ɗaya tinanin rayuwar su ta baya ya dawo cikin kanta kamar a film ta hau tina farkon haduwar ta da Alhaji har ta sanar da mahaifiyar ta tana son shi aka sanya Iya a tsakanin magana ta bashi umarni ya aure ta, ita ce matar shi tin ta saurayi da budurwa,nan take ta hau tina irin jin dad'i da gatanta ta da yayi. kuka ne ya zo mata mai d'aci a wuyan ta da bakin ta, kuka ne irin na nadama da tunanin yanzu gashi ta tsufa ta girma amma zata koma zaman gaban iyayen ta,gashi ba wani arziqi gare su ba,Alhajin ne dama ke taimaka masu duk wata. "Yanzu ina ji ina gani zan bar wannan gidan na koma na qasa na barwa wannan yarinyar ita kaɗai," Hawaye ne ya dinga zubowa a idanun ta babu qaqqautawa, ba dan ta so ba dole ta fara takawa ta bar gidan tana waiwayen shi,ta sha tafiyar qafa kafin ta fita daga unguwar ta samu abun hawa  ta yi gidan su, ba qaramar zufa ta had'a ba saboda rashin sabo da tafiyar qasa da tayi, a baya kuwa dik inda zata je komai rashin nisan shi sai dai driver ya kai ta,yanzu gata itace zaune a adaidaita sahu. Ta na isa gidan nasu ta sauka ta ce wa me adaidaitan ya Jira ta karɓo Masa kud'in shi, da kyar ta samu a wajen qanin ta takai masa, labarin abinda ya faru na rasa dukiyar Alhaji ya riski kunnen mutanen gidan nasu baki ɗaya,dan haka qannen ta da a baya ita ke taimaka masu suka fara fatan kar shegen son abin duniyar ta da kowa ya santa da shi ya rabo ta daga gidan mijin ta da suka yi shekaru sama da ashirin a tare, idan ko ta kuskura tayi hakan ba qaramin takura musu za ta yi ba, zawarawan ai se su yi yawa a gidan nasu, sai dai cikin rashin nasarar amsa roqon su Hajiya Babba ta kaso auren ta gotai-gotai da ita ta dawo gida . Lokacin da Sahabee ya dawo aka sanar da shi abinda ya faru ba qaramin baqin ciki ya yi da faruwar hakan ba, haushin yayan nashi ne ya kama shi sosai saboda sakin Hajiya Babba da yayi, ba qaramin dad'in mu'amala da Hajiya Babban yake ji ba a gidan, d'aki ya shige ya na masifa kamar wanda ya biya sadakin auren ta, "Mutum ba lafiyar ma ba zai hutawa ran shi da shegen sake-saken mata ba, da tana nan yanzu da baka huta da wasu abubuwan ba Kai bawa? Ka kama ka saki mace saki uku da tsufan ta da komai ai sai ka zauna da wannan afiruwar ku qarata can," Iya binshi kawai take yi da kallo dan ganin yanda yake ta faɗa kamar shine babba ba Alhaji Abdullah ba, nan take ta hau zargin shin ko dai Sahabee ne wanda Hajiya Babba ke magana akai? gaban ta ne yayi wata iriyar faɗuwa data tina wasu abubuwan dake faruwa a tsakanin su wanda a baya bata kawo komai ba ta zaci tsananin shaquwa ce kawai ta matar wa da qanin miji, lallai kuwa biri yayi kama da mutum ashe dai an jima ana cin amanar d'an nata a cikin gidan shi? Kuka ne mai qarfi ya k'wace mata, nan take nadamar irin mummunar tarbiyyar da ta baiwa yaran nata ta baibaye ta. Daga qarshe da ta ga kukan ba zai kaita ko ina ba sai dai ma ya tada mata da ciwon da bata da maganin shi a yanzu sai kawai ta fara addu'a tana nemawa d'an nata gafarar Allah akan zunuban da ya kwasa na zina, ga illar da zina ta janyo masu a rayuwa, dan kuwa dik halin da suke ciki ta tabbata sakamakon zinace-zinacen da yaran nata suka aikata ne. ( yan uwa mu sani zina babbar musiba ce ta kowacce fanni a rayuwar me aikata ta,zina na wakana a wannan lokaci da zamani namu ta hanyoyi kala kala, a kullum sabon salo ake fitowa da shi Wanda yake qara qawata wa masu yin ta ita, yake Kuma sauqaqa wa masu yin ta ita, a komai da muke na yau da gobe an qawata ta kuma an kutsa ta cikin shi ta yanda ko ka sani ko baka da masaniya kana aikata Wani sashe na zinar, misali kallon tsiraicin mata da maza a waya ko films da muke ganin ai kallo muke yi ba wani abu ake yi ba mara kyau, to shi kallon tsiraicin fa me za a kirawo shi? Ka zauna kana kallon gashin Kan macen da ba muharramar ka ba har ka yi sha'awa, ke kuma kin qurawa qirjin namijin da ba muharramin ki ba ko cinyoyin shi har ki yi sha'awa, ko sauraron muryar Wanda ba muharramin ki/ka ba har sha'awar muryar ta gifta ma mutum a zuciya,sai wanda yai tsantsar nazari ya fuskance ta kuma Allah ya kare shi shine zai fahimci ta Ina ta kutsa masa/ta a daqile ta,dan haka mu zama masu kula,da yawaita istighfar dan musibun zina ba su da iyaka,ba kuma su da adadi, Allah ya kare mu daga sharrin zina da dikkan dangogin ta). Gidan Alhaji Abdullah ya koma abun tausayi saboda yanda iyalan shi ke cikin halin ni 'yasu,lokuta da dama haka za su tashi basu da ƙwayar hatsi a gidan,gashi babu wasu kuɗi da suka rage da Eamaan zata yi amfani da shi koda kuwa ta fannin samun wata guntuwar sana'ar ne da zata riqe su,qarshe dai aikin da Alhaji ya samarwa Sahabee ada ya raina shi ya koma yi dole wanda da kyar suka karɓe shi, albashin nashi kuma qarshe dai rabi mata ke cinyewa rabi ya sammasu ba wani isa yake yi ba, ba laifi yanzu Alhaji tinda yana ganin likitoci ana ba shi kulawar data dace ya fara magana saidai ba ta fita sosai,sannan yana samu ya d'aga hannun shi na dama sosai, bangaren hagun shi kuwa yana ta lallab'awa da qoqarin motsa shi. Motocin da suka rage musu guda biyu a gidan ne Iya ta bada shawarar a bada ɗaya haya sai ana kawo masu kuɗin a kullum suna samun na cefane ɗaya kuma su barta dan ci gaba da amfani da ita a gidan,haka ko aka yi sai suka kirawo asalin drivern su na da suka yi masa bayanin komai ya amince zai yi aikin dama tinda ya bar gidan bai samu wani aikin ba. Tinda ya fara kuwa kullum yana kawo masu balance din dubu biyu wanda ba ta kai su ko ina,hakan ta faru ne sakamakon sabo da kashe kuɗi da suka yi a baya, Eamaan kuwa ta yi alqawarin ba zata ɗauki matsalar gidan ta ta kai wa iyayen ta ba zata yi dik iya qoqarin da zata yi dan taga ta wadata su da abincin da za su ci da sauran buqatun su. **************************** Zaune suke a saman dinning table zasu karya Ammaah ta hau yiwa Daddy kukan ya taimaka wa Eamaan da iyalan ta dan kuwa ta tabbata suna cikin matsin rayuwa duba da abubuwan da suka faru da su,tana so ita dai ya barta ta je ta ga d'iyarta ta, Daddy kuwa yace sam ba zata je ba saboda idan taje ma d'agawa Eamaan hankali zata yi su yi ta koke-koke Mama ma ta sanya baki amma yaqi amincewa sam, suna cikin maganar ne Eamaan ta yi Sallama ta shiga parlourn nasu goye da Fatee......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 17 : D'aga kai suka Yi gaba d'ayan su suka kai duban su kan Eamaan da ke shiga parlourn nasu, Ammaah ce ta yi saurin goge hawayen ta ta miqe ta nufi Eamaan da sauri ta rungumeta,Eamaan cikin fara'a ta sakko mata da Fatee dake ta kuka, baya Ammaah ta ja kaɗan ta karbe ta ta rungume ta tana lallashi, gaba d'aya yarinyar ta sauya ta koma kamar wadda ruwan nono baya isar ta, ita kan ta Eamaan ɗin duk ta sauya,'yar qibar nan da tayi duk ta sauka,to damuwa tayi mata yawa kuma ga gidan miji komai ya ja baya ba kamar da ba, gaida su ta yi cikin natsuwar ta da ladabi da biyayyar ta Daddy cikin sakewa da tausayawa ya amsa mata,Ammaah kam da Mama cikin share hawaye suka amsa mata dan sun kasa b'oye damuwar su akan halin da suka ganta, itan ma idon ta ya cika da kwalla amma sai ta sanya hannunta ta share, tambayar ta suka yi mai jiki ta amsa musu da cewa, "Da sauqi alhamdulillahi dama abin da ya kawo ni kenan akan Maganar Baban Fateen ne, muna son muje gashi wannan satin amma bamu da kud'in mota, ga kud'ad'en da ya biya na asibitin da muke zuwa sunce ya qare an kuma rubuto wasu magunguna,yanzu haka daga wajen sayar da gwalai-gwalai na dawo na sayar da nawa kud'in dana had'a naga akwai sauran cikon 20k kafin su isa na maida shi asibitin shine nace bari na zo dan Allah Dad......," kan ta qarasa maganar ta yayi sauri ya katse ta da faɗin "Kar ki roqe ni dan Allah Mamana, fad'a min buqatar ki yanzu na biya maki ita in dai bai fi qarfina ba, kome kike so ni zan yi maki shi a duniyar nan, in dai bai sab'awa Allah ba,wanda na san ma ba za ki taɓa bijiro da sabon Allah wajen mu ba, dan haka taso ki karb'a ki yi sauri ki je a kai shi asibitin, Allah ya qarawa rayuwar ki albarka ya baki ladan biyayyar da kika kasance kina yi mana a koda yaushe, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka,domin babu addu'ar da zaka yiwa ɗan uwan ka musulmi data wuce ka nema masa albarka a wajen ubangiji,albarka ta qunshi komai na duniya da lahira da bawa zai samu na alkairi, Allah yayi miki albarka da zuri'ar ki baki ɗaya Mamana," Cikin tsananin kuka da jin dad'in kalaman mahaifin nata ta je gare shi ya miqe tsaye ya rungume ta tsam a qirjin shi tare da sumbatar goshin ta,ya sa hannu a aljihun shi,ya zaro kuɗin da shi kan shi bai san ma iyakar su ba ya bata, Ammaah ce ta koma ɗakin ta ita da Mama suka d'akko mata kuɗi,kayan abinci da sauran su suka bata suna sanya mata albarka tare da yi mata fatan samun sassauci a rayuwar da take fuskanta, godiya tayi masu sosai ta tattare komai zata tafi, Daddy ya sa driver ya maida ita gida. Cike da murna ta shiga sashen Iya da ta kai shi ajiya dan kar ta barshi shi kaɗai, nan ta same shi kwance a kujerar shi ya yi kashi a jikin shi yana ta kuka ,dan kuwa Iya ta kasa koda motsa qafar shi ce balle ta d'aga shi ta gyara masa,fuskar shi tayi jawur har ajiyar zuciya yake saukewa sabida kukan da yayi, da sauri ta qarasa wajen shi tana tambayar shi lafiya yake kuka haka? Tana qarasawa inda yake ta ji wari, kauda kan shi yayi gefe saboda nauyin ta da yaji ya kama shi,ita kuwa sai tayi murmushi ta sauke Fatee da ta yi bacci a wajen Iya ta tura shi suka koma sashen ta ta fara gyara masa jikin shi,sai da ta gama yi masa tsarki da wanka tass sannan ta canja masa wajen kwanciya, ta dauki kayan daya b'ata ta je ta wanke su ta shanya ta koma ta d'akko tiraren wuta ta kunna a dakin ta fesa na fesawa, daga nan ta koma ta d'akko Fatee da ke bacci ta kwantar da ita a gado ta koma ta yi wanka,cikin shirin doguwar riga ta fito ta zauna kusa da shi ta kama hannun shi tace, "Sweet na sha gaya maka ka daina damuwa dan ka yi bayan gida,ba ga ni ba zan wanke maka ko akwai wani abu dake damun kane da baka sanar dani ba? Ko kuma dai ladan da nake samu ne baka soooo" Ta fad'a cike da shagwab'a,hawayen shi ne ya sake sakkowa saman kuncin shi cikin maganar shi da kamar koya yake yi ya labarta mata abinda ya faru da bata nan, " Iya ce na ce ta wanke min jiki na sai ta hau toshe hanci tana fad'a akan me yasa da girma na zan yi kashi a jiki na, sai dai na bari ke ko sahabee ku dawo ku gyara min ita bazata ci kashina sau biyu ba a rayuwa,Sahabee ma daya dawo ta saka shi ya gyara min shima cewa yayi saidai na bari ki dawo Allah ya kiyaye ya wanke min kashi, tin da kika fita na yi shi sai da kika dawo na samu kika wanke min, Eamaanii na Allah yayi miki albarka,Allah ya sa ki gama da duniya lafiya Allah kar ya gajiyar dake hidima dani, a yanzu ne na qara tabbatar da cewa Iya da Sahabee ba zasu riqe min jinina ba ko bayan babu ni a raye, ki tabbatar ba wanda ya raba ki da Fateema ko bayan babi ni Eamaan ki jajirce wajen kula da ita da tarbiyyar ta, na roqe ki Eamaan kar ki rabu da Fateema a hannun Iya da Sahabee ko bayan babu ni a raye," Ya qarasa maganar shi cikin matsanancin kukan da ita kam tini ta ke yin shi, kwantar da jikin ta ta yi a gefen na shi tace, " Sweet ka daina kuka, ka daina saka damuwa a ranka indai kana son ciwon nan ya barka, kasan damuwar ka zata hana ka samun sauqi akan kari ko? yanzu dai gashi alhamdulillah muna ta samun ci gaba,yauwaa har zan manta ma ban faɗa maka ba ɗazu da na fita gida  naje gaida su Ammaah da zan tafi Daddy ya bani wannan,da naqi karb'a ma nace muna da kuɗi sai suka dage sai na Karb'a shine na amso," Eamaan tayi haka ne dan kar ya ji ba dad'i a ran shi ,yaji cewar ta je wajen iyayen ta ta roqo kuɗin da zata kula da shi da mahaifiyar shi da sokon ɗan uwan shi, godiya yayi tayi mata da iyayen ta dan kuwa ya ji dad'in kuɗin da suka bata sosai,yace to ta yi wa drivern su waya in yana kusa sai ya zo ya kai su asibitin, wayar ta ta d'akko ta kira shi yace zai iso nan da awa ɗaya da 'yan mintuna. Dai-dai lokacin daya ambata ya iso gidan nasu sai suka d'unguma zuwa asibiti, Eamaan cikin ranta ta qudirta daina barin Alhaji da Iya tinda dan taga yanzu basu da shi shine ta ke nuna masu halin ko in kula ita da Sahabee, in ta je gaida Iyan ma takan same su suna cin dad'in su sun manta da su da rayuwar su, basu damuwa da su ji ko sun ci abinci a ranar ko basu ci ba. Basu samu dawowa a ranar da suka je asibitin ba saboda wasu gwaje-gwajen da aka yi wa Alhajin,koda suka kammala da asibiti sai ta kirawo driver yazo ya maida su gida, suna shiga ciki ta kwantar da Fatee dake ta bacci sannan ta dawo ta kai Alhaji band'aki ta cire masa kaya itama ta cire nata, wanka tayi masu gaba d'ayan su,da taimakon kujerar da yake hawa ta je ta saka shi a kwamin wanka dan ta gasa masa jiki da ruwan d'umi a cewar ta zai ji daɗin jikin shi sosai tana gama saka shi ciki itama ta shiga, sukai wankan su a tare kamar yanda suke yi ada, Alhaji ya ji dad'in hakan sosai,Eamaan kuwa sai qoqarin yi masa abubuwan da zasu faranta ran shi take yi musamman ta bangaren bashi labarai na ban dariya, kukan Fatee ne ya fito da ita da sauri daga band'akin tana daura towel, ɗauke ta gan ta hannun Sahabee yana zare mata ido tare da ce mata, "Ke shiiiiiii ! Ki yi min shiru nace me shegen kukan tsiya," Eamaan na ganin haka sai ta koma da baya ta sako hijabin ta da ta cire,dik da haka Sahabee da ya ganta sai da ya haɗiyi wani mugun yawu,tana isa gaban shi ta sa hannu ta kwace 'yar ta tace masa, " ka kiyaye ni fa Sahabee har yanzu ba ka gama sanin abinda zan iya aikatawa ba idan ka takura min na ga alama," Zata juya ta ajiye Fatee kenan ya janyo hijab ɗin ta ta baya, tana juyowa kuwa ta yanka masa wani irin mugun mari,cikin tsananin mamaki da kad'uwa Sahabee ya dafe kuncin shi yana kallon ta, cike da b'acin rai Eamaan ta nuna shi tace masa, "kai ɗan akuya ka ajiye tsalle-tsallen ka a waje kar ka shigo min dashi cikin gidan nan,idan ba haka ba kuwa watarana zan illata ka," Cikin zafin nama ya damqo ta ta ko ajiye yarinyar dake ta kuka a kujera ta damqe wuyan shi shima ko alamar tsoro babu a idanun ta, Alhaji na can yana jiyo dik abinda ke faruwa sai kwala mata kira yake yi,Sahabee kuwa jan ta ya yi zuwa gaban Alhajin yace, "ke har kin isa dan ina son tarayya da ke ki dinga mari na kamar kin samu ɗan ki,kin zaci qarfi na ki ka fi da nake kyale ki ko me? tin zuwan ki gidan nan nake maitar kusantar ki na sha gwadawa bana dacewa, to yau se na fanshe marukan da ki ka jima ki na zabga min da jikin nan naki da ki ka d'auke shi kamar zinare,ko da da kika ga na yi atempting kusantar ki kin min waɗannan abubuwan na ji tsoro na kyale ki saboda wannan nakasasshen mijin naki na da lafiya ne,in ya ji zai iya hukunta ni akan abinda nayi miki, amma yanzu ai baki isa ki sa ni na fasa abinda na yi niyya ba, zan kusance ki a gaban shi tinda in ban manta ba ka tina d'iyar Sabi'u, da ka sa aka d'akko ta uban ta ya bika har gidan shaqatawar ka amma baka fasa fasa masa budurwar 'yar shi ba a gaban shi, dan haka a yanzu nima zan yi abinda naso da matar ka na ji d'ad'anon zumar ta ko mad'acin ta a gaban ka, yau dai nima zan ji meye ke cikin wannan kyakkyawar surarar da ake b'oye mana," Sahabee na magana yana qoqarin cire wa Eamaan hijab ɗin dake jikin ta tare da k'wace wuyan shi da ta shaqe ya banqare mata hannayen ta ya zame towel ɗin jikin ta surar ta ta bayyana a fili, Alhaji ne ya rintse ido da qarfi cike da azabar da zuciyar shi ke yi masa yake baiwa Sahabee hakuri da karyayyen harshen shi da baya fita sosai. Zuciyar Eamaan kuwa a dai-dai wannan lokacin babu komai cikin ta sai wani d'aci da take yi mata dik zafin da take ji na matsar da ya yi wa hannun ta amma a haka ta qoqarta ta juyo cikin hikima da kwarewa a qoqarin ta na son kare kan ta,gwara masa kan ta ta yi a hancin shi nan da nan kuwa ya fara tsiyayar da jini, ta dunqule hannayen ta ta buga masa a dokin wuyan shi, ta sanya guiwar qafar ta ta daki gaban shi da qarfin gaske,nan take ya zube a qasa yana murqususu. Cikin sauri ta ɗauki towel ɗin ta ta d'aura,ta maida hijab ɗin ta jikin ta, Fatee da ke ta kukan fitar rai ta je ta d'akko, ta ajiye ta a tsakiyar palour dan ta kusa fad'owa daga kujera, Sahabee na duqe cikin azaba sai murgina kai yake yi idanun shi sun yi jawur, jini na ta fita a hancin shi, muciya taje kitcen ta d'akko ta dawo inda yake idon ta ya rufe da b'acin rai ta dinga muqa masa a jikin shi tana faɗin, "In a zina yau aka haife ka qarewar bariki sai na fidda maka sha'awar ta kai ko da matar ka ce ta sunna ba matar wani ba bazata qara baka sha'awa ba,shege mara imani, mara tausayi, wanda bai san mene ne dokar Allah ba balle ya bita, yanzu d'an uwan ka na cikin halin jinya ka ke so ka qara masa damuwa? butulu kawai masu manta alkhairi,komai zunubin shi in ya tuba ga Allah Allah zai yafe masa,Kai wane ne da ka ke so ka hukunta shi akan abinda ya aikata a baya? Yau se na nakasa ka kaima" Duka tayi masa sosai kamar wanda 'yan sanda suka kama da mugun laifi,da kyar ya samu ya fita da gudu, ta ko bi shi a guje tana fita tayi karo da Iya a hanya,Sahabee ne ya qanqame ta yana ihu, cikin tsananin mamaki Iya tace, "Me zan gani haka? Na shiga ukuna yanzu kashen min d'an zaki yi Eamaan? Jama'a ku taimaka min zata kashe min yaro," Sai ta saka kuka tana duba fuskar Sahabee da ta daku sai fitar da jini take yi, dik maganganun da Iya ke yi Eamaan bata kula ta ba saboda gudun kar tayi mata rashin kunya, dan yanda take jin zuciyar ta zata iya zagin Iya tsaf, dan haka sai kawai ta koma sashen ta ta kulle qofar da makulli ta wuce ta dauki fatee ta saka mata abincin ta a baki,ai kuwa fir yarinyar taqi kamawa tana ta ci gaba da tsala kuka, itan ma kuka ta fashe da shi, daga can band'aki kuwa Alhaji ta jiyo ya yi wani nishi mai qarfi, da gudu ta aje Fatee ta je wajen shi, tana isa ta duqa gaban shi tana faɗin, " Alhaji ! Alhaji !Alhaji ! dan Allah ka buɗe idon ka ka kalle ni kar ka yi min irin wannan wasan bana so, bari na saka maka kaya mu je asibiti, please Alhajina stay with me dear i will be right back," Da gudu ta je ta d'akko kayan su ita da shi dan ta sanya musu, gaba d'aya gambal habaru ta d'akko bata kula ba tsabar tashin hankalin da take ciki, a haka ta hau saka masa nashi da kyar saboda yanda taji jikin shi ya saki sosai fiye da da,da kyar ta iya dora shi akan kujerar shi ta saka nata kayan ta maida hijab din ta,parlour ta koma ta goya Fatee da ta gaji da kuka ta yi bacci,a guje ta sake d'iba tayi d'akin ta ta d'akko wayarta ta kira drivern su,tayi sa'a kuwa yace mata dama gashi ya kawo balance, tace ya kawo motar daf da side din ta yazo ya taimaka mata su saka Alhaji a mota bashi da lafiya,kafin ya iso ta tattare yan kud'ad'en da suka rage a wajen ta ta saka a jaka ta rataya a kafad'ar ta tana jiran shi,yana zuwa suka ɗauke shi sika saka a motar, Iya da Sahabee na hango su amma basu je ba. Gaban Iya ne yayi wata mummunar fad'uwa sai dai tana tinawa da me Eamaan ta yi wa Sahabee a qaryar da ya zuba mata sai kawai ta kauda kan ta ta bisu da harara,a guje drivern ya nufi asibiti da su, ita ko Eamaan sai addu'a take yi tana kumawa akan Allah ya ba wa Alhajin ta lafiya, hankalin ta gaba ɗaya ya gama fita a jikin ta, tabbas ko ba so akwai shaquwa a tsakanin su sannan akwai qauna ta musamman da take yi mishi a matsayin shi na mijin ta, zuciyar ta na tsananin tausayin shi, tana fatan ya warke ko dan ya ci gaba da zama uba ga yarinyar ta k'walli ɗaya da suka mallaka ita da shi Eamaan ta fuskanci Alhaji fa baya numfashi dan haka cikin kuka tace, " ka qara gudu dan Allah kar na rasa shi," kuka ne ya qara sarqe ta ta kuwa toshe baki ta dinga rero shi kamar waqa. Suna isa likitoci suka rufu kan shi sai shige da fice ake akan shi, daga qarshe dai wani daga cikin su wanda ta kula kamar shine babban su a wajen ya je yace mata.......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 18: Umartar ta ya yi da ta bishi office din shi yana son magana da ita, suna isa ya mata nuni da wajen zama, ta zauna hankalin ta gaba daya a tashe yake, kallon shi take ko qiftawa bata yi, gyaran murya ya yi yace, " Hajiya a gaskiya Alhaji yana cikin matsala sosai, domin kuwa ada mun samu ci gaba sosai, yanzu komai ya koma mana baya, na sha fada maki kuna qoqarta kauda shi daga abinda zai b'ata ran shi, amma yanzu ki duba ki gani yanda gaba d'aya komai ya koma mana baya, a gaskiya banji dad'i ba sam, kuma a yanzu kam sai dai na baku shawarar akan ku fidda shi waje, domin a samu ya samu sauqi da wuri, in ba haka ba a gaskiya ina jiye maku tsoro sosai," kukan ta ne ya qaru sosai, a hankali ta share hawayen ta ta yi masa godiya sannan ta fita, direct gidan su ta tafi, ta je ta samu Iya da Sahabee a palour suna tattauna wa akan Eamaan, yana qara fada mata qarya da gaskiya akan abinda ya faru, Sallama yi ta musu ta shiga, a tare suka daga kai suka kalle ta, Sahabee kuwa a matuqar razane ya kalle ta, Iya ta kula da hakan nan take ranta ya qara ɓaci, wato har Eamaan na da wannan effect din akan d'an nata " Meya kawo ki nan kuma?" Kallon Iyan ta yi da tsantsar tsana tace, "A da na zaci zan kyautata maki har Allah ya ganar da ke ki so ni, na jure duk qunci da wahalar ki, na kasance ban taba kwana da abinda kika yi min a raina ba,a lokacin da kika batamin rai a lokacin nake mantawa kuma na yafe maki, dan haka yanzu ina son gaya maki ni ban riqe ki da komai ba na yafe maki dik abinda kika yi min ko da baki nemi yafiyata ba, amma ku sani wannann gidan akwai mai shi, kuma mai shi d'in nada buqatar gidan shi, kamar yanda baku damu da shi da lfiyar shi ba haka nima ba zan damu wajen sanar daku daga yau zuwa ko wanne lokaci gidannan da abinda ke cikin shi zai zama mallakin wani ba, ruwan ku ne ku samu wani wajen fakewar kuma ruwan ku ne ku zauna har masu siyan gidan su zo su fidda ku," Tana kaiwa nan ta sa kai ta fice, gaba d'ayan su baki suka buɗe suna kallon ta har ta b'ace wa ganin su,nan take wani irin fargaba da tsoro suka shige su yanzu ina za su je?  lallai lamarin Eamaan a bin tsoro da firgitarwa ne, to yanzu ya zasu yi?shin me ma ya sake samun d'an nata, sai a yanzu wannann tinanin ya zo mata,cikin hanzari kuwa ta yinqura ta tashi tana dingisa qafar ta da ta ke ciwo zata fita,Sahabee ne ya kalle ta yace, " Iya ina zaki je kuma bayan ta gama fad'a mana saqon rashin mutuncin data ga dama ta tafi?" "Kai da Allah ja can, daga dikkan alama Audu bai da lafiya sosai, shine dalilin da yasa za ta saida gidan a yi masa magani da kud'in ,ko kuma so take yi ta cinye kud'in gidan dan taga bai da lafiya bai san ina kan shi yake ba," Tana fita ta tarar da Eamaan da wasu mutane tsaye suna magana har da drivern Alhaji,shi kan shi drivern haushin su Iya ya ke ji, yana ganin Iyar ya d'auke kai gefe ya haɗe rai sosai, buɗe sauran bangaren su Hajiya Babba da Qarama su Eamaan ke yi, komai na nan kamar yanda suka bar shi, sai da suka bud'e ne ma suka ga akwai sarqoqi da wasu abubuwan masu amfani har da kuɗi a sashen Hajiya Qarama, d'iba Eamaan ta yi ta damqa a hannun drivern tace yaje ya siyar ya dawo, duk da ta San ta yi a kasada amma gwanda shi ya nuna damuwar shi akan mijin ta sama da mahaifiyar shi da ɗan uwan shi da ya wahaltawa a rayuwa. Masu siyan gidan sun shiga ko ina sun gani, gida yayi musu fiye ma da yanda suke so kuma yayi musu za su siya, sun tsaida magana akan za su fara bayarda rabin kud'in zuwa wata uku masu zuwa su cike sauran,Eamaan kuwa ta yi na'am da hakan, dan haka Kiran lauyan Alhaji ta yi aka yi komai a gaban shi. Driver kuwa  direct wajen saida gwala-gwalai ya nufa ya siyar ya dawo mata da kud'ad'en ta cass ko sisi bai rage ba,ko da ta duba sai taga ta samu kimanin million biyu da rabi, nan take ta wari dubu d'ari ta baiwa driver, qin karb'a ya yi  ya na hawaye yace mata a qara a maganin Alhaji baida komai da zai taimaka da shi dan haka ba zai karb'i ko sisi ba,cikin kukan tausayin su ta yi masa godiya amma ta bashi 20k ta matsa masa dole ya karba. Shiryawa ta yi ta koma asibiti wajen mijin ta dan ta ga ya jikin nashi yake, a daren masu siyan gidan suka dawo dan nuna wa ma'aikatan da suka d'akko inda za a yi musu gyare-gyare,Iya ta rasa ya zata yi da ranta dangane da lamarin saida gida da son jin ya lafiyar ɗan ta take,Eamaan kuwa sam taqi kula ta balle tayi mata bayanin halin da ake ciki. A cikin satin aka gama had'a masu komai na tafiya qasar India domin duba lafiyar shi wanda har likitan da zai duba ta ya san da zuwan su an gama arranging komai su kawai ake jira,tafiyar tasu ta zamto babu namiji a ciki daga ita sai Hafsat da Fatee. Hafsat na ta bata kwarin guiwa akan zasu iya ba dole sai da namiji ba kar ta damu, tinda  Sahabee ba namijin arziqi bane ba dole su za su yi komai,  a asibitin NARAYANA HOSPITAL suka sauka, asibiti ne babba mai matuqar girma da d'aukaka a fadin qasar ta India dama wasu qasashen, domin asibiti ne daya had'ar da likitoci kala-kala masu aiki akan kowacce cuta,sai dai sunfi k'warewa wajen dashen zuciya da masu ciwo irin na Alhaji,ai ko cikin hikima ta ubangiji suna zuwa likitoci suka amshe su,babban doctor din su ne ya zo da kan shi ya duba shi, yana ganin yanda Alhaji yake ya san sai Wani hukunci na ubangiji zai tashi,amma dole zasu gwada su gani ko da abinda zasu iya yi akan shi, sun fi awa bakwai  suna abu ɗaya akan Alhaji. Eamaan idon ta ya yi baqi ta qasa alamar rashin hutu da bacci duk yanda Hafsat taso ta huta amma inaaa ta qi sam, hankalin ta a tashe yake wanne bacci za ta yi kuma, washe gari wajejen qarfe 12:36pm Dr. Maheer Shatty ya fito dauke da rigar shi a hannu, cike da rauni da tausayawa ya kalli su Hafsat ya wuce Office din shi ya jima a zaune kafin ya aika a yi masu iso wajen shi, suna shiga ya deb'o ruwa a cup ya tsiyaya ma Eamaan, da Hafsat a glass cup d'in shima ya sha, Eamaan ce ta tambaye shi cikin harshen turanci, take sanar da shi ya fada mata me ke faruwa dan ita ba ta ruwa take ba, kallon ta ya yi da tausayawa yace, mata sai dai su yi hakuri amma sun yi iya bakin qoqarin su amma sai da suka rasa Alhaji, qamewa ta yi a kujerar ta na fidda wani nunfashi mai zafi daga baki da hancin ta, yanda ta tsorata ya sa likitan tashi daga kujerar shi ya je gaban ta ya dafa kafad'ar ta ɗaya yace, " Madam take it easy please,breath in and out everything will be ok" " Everything will be ok? When my husband is dead? Everything will be ok when i don't have anyone to take care of my daughter? Don't tell me everything will be ok, u have no right to tell me everything will be ok,just take me to him, i want to see my husband, i wanto to talk to him, i know he is doing fine, u just don't want to tell me, pls take me to my husband," kuka take sosai wanda ya sa Dr. Da  Hafsat kwalla ,Fatee ma kukan take kamar ta san me ke faruwa,a hankali ya miqe ya kai ta d'akin da gawar Alhaji ke kwance, kamar ba shine majinyacin da ya ke cikin jinya da wahala ba, kamar ba shine yake kashi awando magana ta gagare shi ba, fuskar shi cike take da annuri da murmuhi a saman ta, magana Eamaan ta fara yi masa kamar wanda yake jin ta,shi kuwa bai san tana yi ba saboda babu ruhi a jikin shi kwance kawai yake a miqe samb'al , Eamaan bata san ta shaqu da Alhaji ba sai a yau, ganin tane ya fara yi mata hazo a hankali ta yanke jiki ta faɗi a wajen. Alhaji ya nuna mata so mara adadi, ya zama kamar raqumi da akala a wajen ta , ya daina munanan dabi'un shi ta dalilin son da yake yi mata da shawarwari da wa'azin da take yi masa, Alhaji ya zama wani bangare na jikin ta. Bayan sun samu ta farfado ne Hafsat ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah,ita kuwa kwance take a gado bata imm bata umm umm, sai dai hawaye da yake zuba ta gefen idon ta kawai, shirye-shiryen komawar su Hafsat ta hau yi, a wannann lokacin dole akaiwa Fatee yayen dole, dan ko ruwan nonon babu ma a tattare da ita ya ɗauke kan shi,saboda rabon ta da abinci tun a jirgi da za su zo, in an zaunar da ita sai dai ta qurawa waje ido,in ta dad'e a haka daga baya sai ta fashe da kuka,a haka suka dawo Nigeria d'auke da gawar Alhaji, drivern sune yaje ɗaukan du wanda direct gidan su Eamaan ya yi da su, don yanzu Iya da Sahabee sun canja unguwa wanda suka sayi gidan su sun tashe su,tinda suka je gidan Eamaan bata ce komai ba sai da taga kowa ya hallara sannan tace, "Duk wanda ya sanar da su Iya mutuwar Alhaji kan akai shi bai kyauta min ba, ya ci amanar tarayyata da shi ko wanene," Tana gama faɗin haka ta shige dakin su na da ta kife a gado ta yi ta kuka tana nemawa Alhaji gafarar Allah tare da rahamar shi da kuma sauqin kwanciyar qabari, daga wannan addu'o'in da take masa ta samu nutsuwa ta rage kuka,a haka aka haɗa ruwan wankan da za a yi masa aka kira ta, dan kuwa ta ce ita za ta yi masa, d'akin da zata yi masa wankan Ammaah ta raka ta ta shiga sai ta ja mata qofar ta rufe,tsarki ta fara sannan ta yi masa alwala ta soma yi masa wankan tana yi tana hawaye tare da yi masa addu'a, qamshi ne kawai ke tashi a ɗakin saboda turarukan da tayi masa amfani dasu, har a wannan lokacin murmushin dake saman fuskar shi bai gushe ba, a haka ta gama ta yi masa addu'a sosai sannan ta buɗe ta fita daga ɗakin, qarasa hada shi aka yi , sannan aka dauke shi sai gidan shi na gaskiya gidan da kowa zai je, gidan da ke jiran wanda ba a haifa ba ma, gidan da ba ruwan shi da matsayin ka ko na iyayen ka, kawai kaje masa da aiki mai kyau kaji daɗin kwanciya a cikin shi,kaje da mummuna kuma zaman ka ya munana. ( Kun taɓa aikata zina a rayuwar ku? Tuba kawai zaku yi tuba na gaskiya sai Allah ya karb'i tuban ku ya kyautata qarshen ku,idan kuma mutum bai yi tuba na gaskiya ba, to fa tabbas yana cikin tashin hankali nan duniya da qiyama, Allah ka tsare mu da dikkan musulmi daga aikata zina da abinda ya dangance ta,) Dik da cewar Eamaan bata zamo daga cikin mutane masu yawan surutu ba tin farkon rayuwar ta, sai mutuwar Alhaji ta sa ta sake zama shiru-shiru,a koda yaushe cikin yi wa Alhaji addu'a take yi da kuma neman itama Allah yayi mata kyakkyawan qarshe, dan kuwa mutuwar Alhaji babbar aya ce da Allah ya saukar, tana nan kwance tana hawaye Ammaahn ta ta shiga ɗakin ta samu gefen gado ta zauna,hannun Eamaan ta kama tace, "Eamaan na san kin yi hakuri tin daga farkon haɗa auren ki da Alhaji har zamantakewar auren ku da shi, sannan na san irin hakurin da kike yi a yanzu da ya rasu, amma dik da haka ina mai qara baki hakuri tare da yi maki nasiha akan ki ci gaba da hakuri, Allah ya jiqan shi ya sada shi da rahamar shi, ki taso muje palour kin yi baqi, amma ina son ki tausasa zuciyar ki ki sanyawa kan ki hakurin nan da na san ki dashi" D'aga mata kai kawai Eamaan ta yi, ta sa hannu ta share hawayen ta sannan ta zira hijab ɗin ta dogo har qasa suka fita,ba ta tab'a tsammanin ganin su yanzu ba dan haka ganin su zaune sai ya sanya ta jin kamar ta koma d'aki amma haka ta daure ta qarasa cikin parlourn.... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 19: Sahabee ne da Iya zaune suke ta zabga kukan rashin Alhaji Abdullahi da aka yi, gaba d'aya parlourn kallon su kawai ake yi babu wanda ya tausaya masu sai ma haushin su da kowa ke ji a wajen, amma saboda karamci irin na su Ammaah ko a fuska ba su nuna masu ba, daga Daddy har mama kowa ya gaishe da Iya yayi mata ta'aziyyar rashin ɗan ta da tayi,Eamaan na ganin su wani tuquqin baqin ciki ya taso mata, kawai sai ta nemi waje ta zauna tana bin su da kallo, dan kuwa ita gani take yi ta sanadin abinda Sahabee yayi ne ta rasa mijin ta,Iya kawai ta gaida saboda kasancewar ta mahaifiya ga Alhajin ba dan haka ba ko kallo bata ishe ta ba, " Ina wuni," Ta furta tare da komawa gefe ta zauna a kujera idon ta rufe dan ko ganin su ba ta son yi, amsawa Iya ta yi tana ta zuba tana fad'an a inda suka ji rasuwar,shiru wajen ya ɗauka babu wanda ya ce mata ci kan ki,kalma ɗaya kowa ke amsa masu da Ameeen idan suka furta Allah ya jiqan Alhaji. Eamaan kam ma ko kula su bata yi ba balle ta amsa Ameen ɗin ,tana kyautata wa Allah zato ya gafarta wa Alhaji kuma zai yi masa rahama da yalwatacciyar rahamar shi,suna nan zaune banda maganganu da kukan Iya dake tashi baka jin komai a haka aka kawo Fatee tana ta kuka, Eamaan ce ta karɓe ta tana ta jijjiga ta a hankali ta samu ta yi shiru, Ammaah ce ta kawo mata abinci ta ɗauke ta tana bata, can a cikin surutan Sahabee  su ka ji yana fad'in " Allah ya jiqan Yayah, tin da abubuwa sun zo a haka kuma Fatee ita kad'ai ta rage mana a dangi da zamu kalla muji dad'i, sai a had'a mana kayan ta mu tafi da ita," Cikin sauri Ammaah ta ajiye Fateema a cinyar Mama ta yi kan Eamaan ta riqe ta tana yi mata magana cikin sanyin murya,Ammaah ta tsorata da yanayin da taga 'yarta ta ta shiga cikin qanqanin lokaci, yanayi ne da tinda ta haife ta bata taɓa gani a tattare da ita ba, jikin ta sai rawa yake yi, idonta kuwa ya yi jawur kamar jan yadi, tashi tayi tsaye Ammaah na riqe da ita ta fara takawa tana bin Sahabee da wannan deadly look din nata, cikin sauri Sahabee ya ja gefe kusa da Iyaa yana zaro idanu, bata ce wa kowa komai ba ta shiga ɗakin ta, Ammaah ce ta basu hakuri tana qoqarin bin bayan Eamaan ɗin sai gata ta fito ɗauke da leda a hannun ta ta wurga ta a fuskar Sahabee, abinda ke cikin ledar ne ya leqo,nan fa sahabee yayi arba da kuɗi sai ya hau zare ido yana washe baki, " ku tashi ku fita da ragowar abinda ya yi saura na ɗan uwan ku a wajena, na yafe gadon shi bana so ku haɗe ku cinye dika dan shine dama ya fiye maku ɗan ku, d'iyata in ta girma kun bata nata a hannun ta in kuma kun cinye kun bata a lahira,ni ba zan karb'i gadon ta ba ba kuma za ku bar shi a hannun dangina ba, marasa hankali da imani kawai, kutashi ku fice nace !!!!" Cike da wata gigitacciyar tsawar da ko iyayen ta basu taba jin ta yi irin ta ba ta qarasa maganar ta,ai kuwa tayi matuqar kid'ima kowa a wajen, ba shiri Sahabee ya tattare kud'ad'en ya mayar ledar ya kama Iya suka bar gidan hankalin su a tashe, daf zasu fita ne ya juyo yace, "ko ba jima ko ba dad'e sai Fatee ta dawo hannun mu," "Naga dan iskan da zai ɗaukar min yarinya ya kaita gidan tsohuwar da bata san ya zata baiwa kanta tarbiyya ba balle yaran ta su tashi cikin son junan su ɗaya bai yi sanadin rasuwar ɗaya ba, har ta samu damar yi wa jikar ta tarbiyya ta zama yarinyar kirki bata sanya ta zama karuwa ba kamar yaran ta," A kunyace Iya ta sa kai tsakar gida ta ja hannun Sahabee dan su bar gidan,shiru gidan ya ɗauka dan kuwa babu mai bakin magana Eamaan ta baiwa iyayen ta da suka haife ta suka raine ta mamaki ma balle kuma wanda suka same ta da girman ta, shi yasa bahaushe ke cewa a kiyayi fushin mai hakuri. Direct gidan hayan da suka kama a cikin gari suka nufa dikkannin su babu mai cewa kowa komai a hanya,bayan tafiyar su kuwa Eamaan ta zauna dab'as a qasa tana ta kuka,cikin kuka ta ke faɗin, "Na rantse ba wanda ya isa ya ɗauki Yarinyar nan a cikin azzaluman can, Ammaah dan Allah ku yi min alqawarin ko me zai faru ba zaku bada Fatee ga wad'ancan marasa Imanin ba, gwanda akai ta gidan marayu wasu su ɗauka su raine ta dana basu ita, Ammaah baku san halin mutanen nan bane,Sahabee shine ya yi sanadin da ciwon Alhaji ya tashi har ya kai shi ga mutuwa, a gaban Alhaji ya so keta min haddi Allah ya bani iko na yi masa duka da muciya,Sahabeen nan da kuke gani shine ke neman matar alhaji tin da ran shi, Iya ta sani amma bata d'auki mataki ba,Iya ta san Alhaji bashi da lafiya amma ko ta nuna damuwar ta akai, kaiiii wadannan ba mutane bane, they are monsters, they don't deserve to be called humans, ba su da humanity kwata-kwata a tare dasu Ammaaaaah," kuka take yi tin qarfin ta tana wata iriyar jijjiga,Ammaahn ta na gefe tana share hawayen ta itama,Mama ce ta zo ta rungume ta ta d'aga ta a wajen ta kaita d'aki ta kwantar da ita tana shafa kan ta a hankali da sigar lallashi,tana nan zaune da Eamaan har Eamaan tai bacci, Fatee ma dake kuka ma ta yi nata baccin Ammaah ta shiga ta kwantar da ita a gefen mahaifiyar ta da ke sauke ajiyar zuciya,ta ja masu qofar suka fita. Parlour suka koma dukkan su suka zauna jigum-jigum suna jimanta abinda ya faru a zuciyoyin su, Daddy dake zaune bai ce qala ba tinda su Iya suka zo ya sake dafe kan shi dake sara masa ya fashe da wani matsanancin kuka,kukane na dana sani da nadamar sanya 'yar shi cikin damuwa da rud'anin rayuwa, ashe haka d'iyar shi ta qunshi baqin ciki kala-kala a gidan da yayi zaton tana zaune cikin farin ciki? Yayi zaton labarin kulawar da Alhaji ke baiwa Eamaan da yaji a wajen Hafsat shine asalin labarin rayuwar da 'yar shi ke fuskanta a gidan auren ta, ashe akwai wani qullalen qulli da take fuskanta wanda tsananin Biyayyar ta ya sanya bata taɓa kokawa ba, tabbas bai wa d'iyar shi adalcin haɗa ta aure da Alhaji ba,farin cikin shi ɗaya yanda abokin nashi ya daina neman mata kafin rasuwar shi, yasan inshaa Allah ya samu rahamar Allah, amma ta wani ɓangaren yayi sanadin samun tabo a zuciyar 'yar shi mai wuyar warkewa, dole ne ya bata hakuri ya nemi gafarar ta kada haqqin ta ya kama shi. Ammaah da Mama ne suka zauna a kusa da shi suka dafa shi a hankali suke bashi baki dan ya kwantar da hankalin shi kar ciwon shi na hawan jini ya tashi,Ammaah ce tace, "Ba ka da laifi akan dik abinda ya faru Alhaji,dan haka ka kwantar da hankalin ka kayi wa abokin ka addu'ar Allah ya jiqan shi, ka sanyawa 'yar ka da jikar ka albarka kayi musu fatan alkhairi a rayuwar su, Allah ya kyautata rayuwar su ya baiwa Eamaan ladan biyayyar da tayi mana,kar ka manta mahaifa suna da hakkin samarwa 'yar su budurwa miji dan haka babu laifin da ka aikata balle ka damu," Share hawayen shi ya yi ya murmusa yayi masu godiya ya shige d'aki ya rufe kan shi. Bayan kwana biyu Sahabee ya haɗe kud'in da Eamaan ta basu da wanda ya sace na Hajiya Babba, wanda shi kaɗai yasan tana ajiya a kitchen cabinet ɗin ta,yayi mamaki shi kanshi da ya duba ya same su dan yayi zaton ta kwashe su da zata bar gidan,ana bashi albashi ya haɗe ya biya kudin gidan qasar da suke haya a ciki ya siye masu shi,abinda ya yi saura wanda bai wuce dubu saba'in ba kuma sai ya b'oye yana da wani quduri akan su wanda baya son sanar da Iya sai komai ya kankama. Iya kuwa tinda ya haɗa ta da dubu talatin ta rufe bakin ta tayi shiru tana ganin ai ta samu kuɗi mai yawa duba da dama ba wani abune ya rage ba na Alhajin da suka gada da ya wuce wannan kuɗin da Emaan ta basu. *************** Sauran kwana takwas Eamaan ta kammala takabar ta, wanda a cikin wannan kwanakin da tayi tana takaba ta fara maida jikin ta ta hakura ta dangana da rashin Alhaji ta barwa Allah komai,a yanzu tana zama a yi hira da ita sosai , a duk sanda ta tina da rashin Alhaji sai ta kaɗaici tai ta kuka, Fatee ta girma tana takawa ga wayo da take dashi bakin ta ya buɗe in tana magana sai kowa yayi mamaki saboda qarancin shekarun ta, kyawun yarinyar sai qara fitowa yake yi tare da kamannin da take yi da Alhaji. Watarana Eamaan suna zaune ita da Yayar su da ta zo ganin gida ita da Hafsat,hira suke tayi har musu ya qarke tsakanin su kowa na cewa wajen shi Eamaan da Fatee zasu je dan su huta,Hafsa ce tace, "Yayah ke fa kin ga baku rabuwa ke da ɗan tsohon mijin ki kullum kuna manne kamar chewing gum,sannan ba zama kuke ba a waje ɗaya, yau kuna wannan qasar gobe kuna waccan qasar ta ina zata ji daɗin zama da ku?dan Allah ki bar ta taje wajena idan yaso sanda kuka natsu waje ɗaya ta je maku, " Hararar ta yayar sun ta yi tace, " Lallai ma yarinyar nan baki da ta ido, to ni da ke ai anga mai mannewa miji, ke da har yanzu ba ku daina d'okin sabon aure ba yaushe zata je ta zauna da ku kuyi ta bata kunya? kinga in tana waje na ma zata fi sakewa in ba ma nan , she will have the house to her self sai abinda taga dama zata yi, pls just go with me dear ki rabu da Hafsy," Ta qarasa maganar ta cike da roqon Eamaan da idanun ta, dariya kawai Eamaan take yi musu tana kuma jin dad'in yanda yayun nata ke son ta, amma a can qasan ranta ta fi son taje wajen Hafsat,tinda sun fi shaquwa d'akin su d'aya sanda suna 'yammata, kusan komai a tare su keyi kamar wasu sa'annin juna, Hafsar ba ta da son girma, duk da ta baiwa Eamaan shekaru biyu da watanni amma kamar qawar ta ta dauke ta,shi yasa suka zauna lafiya tinda Eamaan ba ta da rashin kunya,a na haka Fatee ta zo sai Hafsat tace, " Yauwa Yayah in kin yarda a baiwa Fatee zaɓin ina zasu je hutu," " Tab dan ku min wayo,na riga da na san ke za ta yi choosing in a minute or second ma, ban yarda ba gaskiya," "To Yayah ya kike so ayi kin san dai Eamaan ba zata zab'a inda zata je hutu a tsakanin mu ba ko," " Oh ok na yarda Fatee ta zab'a but no cheating," Dariya suka yi, sannan Yayah ta fara tambayar Fatee, " My baby zaki je hutu wajena in dinga sai maki ice cream da sweets ko zaki wajen Aunt Hafsat ne?" Kallon su ta yi Hafsat ta ɗauke kan ta tana kallon wani wajen tana dariya saboda in ba haka tayi ba Yaya zata ce tayi cheating, ita ko Yayah fuskar tausayi tasa ma yarinyar ta ci gaba da tambayar ta , gani tayi yarinya ta taka dugu-dugui ta yi wajen hafsat tana qoqarin hayewa cinyar ta cikin gwaranci tace, "Mamaa" (haka take kiran Hafsat) Nan da nan Yayah ta koma wajen zaman ta ta zauna ta dau lemon da take sha ta kurba ta ce, " To kin yi nasara na amince su biki, next time sai su zo min hutu," Dariya suka hau yi suka ci gaba da hirar su, cikin dariya Eamaan ta kalle su cike da so tace, " I love you guys ina alfahari da ku sosai,kuma Yayah kar ki damu dana gama hutawa gidan Hafsy zan zo wajen ki kema, sai na fi ma dad'ewa a wajen ki," Cikin tsamin baki Fatee tace, "Ana sho Mamaa" " To 'yannema mai kan buta naji kina son Mamaan na fasa baki sweet d'ina, dan kin ga ma Ina son ki shine kike min wulaqanci,nasan dan baki ganina ne sosai shi yasa da wacece wata Hafsat a kayan miya" Dariya suka hau yi sosai, Hafsat kuwa sai ta qara rungume yarinyar a qirjin ta tana sumbatar ta,suna nan zaune suna hirar su suka ga ana buɗe gate wata had'ad'd'iyar mota mai kyau tana shigowa, kallon su suka mayar kan motar suna son suga wanene mamallakin ta,sai da yayi parking ya ɗan jima kafin ya fito cikin takun sa na isa da qasaita ya zo gaban su ya yi masu Sallama, Eamaan ba zata taba manta fuskar nan ba har bada, jikin ta nan da nan ya hau rawa ta miqe tsaye, idon ta cike da hawaye.......... *Many many many thanks to u BIYAYYAH FANS GROUP 1&2 tabbas masu son biyayyah daga gani ku masu biyayyah ne, ina jin dad'in yabawar ku a gare ni, musamman group din TAWHID IS THE KEY, a gaskiya sai godiya, sauran groups din na da yawa, ina godiya sosai, dan yabawar ku ke sa ko nai niyyar yin page d'aya na ji bari na qara maku, dan mai son abun ka sai ka taya shi so, na gode ba iyaka* *ME LOVE U ALL❤* [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 20: Wani abu ne da ba zata Iya tantance mene ne ba ya ke taso mata a wuya, maqaqin da take ji baya yi mata dad'i, after all he put them through he have the nerve to show his stupid face a gidan su? lallai yau za a yi ta kenan dan kuwa sai ta nuna masa itama 'yar zamani ce. Wata zuciyar ce ta taushe ta har taji a ranta tana son barin wajen tin kafin ta kasa riqe kanta, tashi tayi tsam daga sama kujerar robar da take kai zata shiga gida ɗauke da Fatee a hannun ta,tana zuwa gefen da yake zata zagaye shi ya sha gaban ta ya tsaida ita,wani kallo ta d'ago ta watsa masa da idanun ta da suka rine suka yi jawur kamar jan yadi,nan take jikin shi yayi sanyi izzar shi ta fara raguwa saboda kallon ya shige shi, sai dai taurin kai irin nashi ya hana shi ya kauce ya bata waje ta samu ta bar wajen,cikin muryar shi mai nuna isa da taqama yace, " Hajiya Eamaan barka da war haka, ya qarin hakurin mu kuma?to Allah ya jiqan Alhaji yayi masa gafara," Haka ya gama gaishe-gaishen shi ba tare da ta ce masa kanzil ba, burin ta kawai ya matsa ya bata waje ta wuce, Hafsat na ganin yanayin da Eamaan ke ciki ta miqe ta isa gaban ta, hannun ta sai wata iriyar rawa yake yi,hannu ta sanya ta amshe Fatee daga wajen Eamaan ɗin ta tsaya a gefen qanwar tata. " Uhum ina jin ka sai me ya kawo ka bayan fake concern din da ka gama nunawa yanzu? In ba ka da abin fad'a ka wuce ka tafi, kafin raina ya yi matuqar baci naka ran yafi nawa baci yanzun nan," " Eamaan na zo ne da magana mai mahimmanci, wanda ina ganin bai kamata muyi ta a tsaye ba," " Dakata min malam, kai har kana da magana mai amfani da zaka zauna ka yi min ne har na saurare ka? Waye kai? me kake taqama da shi da har zaka manta komai da ka aikata dan baka da kunya kazo min ta'aziyya? kayi kaɗan ka ce zaka yi amai ka lashe akaina, ka kama hanya tin bamu shiga wani hali na rashin mutunci da kai ba," " Ina son ki Eamaan kuma auren ki nake so nayi wannan shine muhimmin abinda ya kawo ni wajen ki, ina sane da kin gama......" Wani shahararren mari ta ɗauke tsohon mutane da shi, ta qara yanka masa wani marin, haka ta dinga kifa masa mari tana kuka,  Yayah ce ta iso gare ta da gudu ta riqe ta tace, " Ke Eamaan baki da hankali ne kike marin babban mutum kamar wannan, me yake damun ki ne, kalmar so tana jawo qiyayya ne?" Cikin qara da tsawa ta furta " Eh Yayah ! kalmar so na jawo gaba ma ba qiyayya ba, Yayah wannan ne Alhaji Saminu, da ya shiga cikin taswirar rayuwar mu ya b'ata ta, ya nakasa min miji ta zahiri da bad'ini, sannan a qarshe ya yi sanadiyyar mutuwar shi,waya baka damar zuwa min da shirmen kalmar so waje na? hhhhh idan ka amince zaka aure ni to zan aure ka, amma se dai in ni ce zan zama ajalin ka,shin ka yarda?" Tinda mutanen gidan su suke da Eamaan ba su tab'a ganin ta yi faɗa da kowa ba balle har duka ya shiga tsakani irin haka sai yau, ko da ace bata tab'a son Alhaji Abdullah ba tabbas ya na da Wani babban matsayi a zuciyar ta Wanda ba zai gogu ba, Alhaji Mutum ne da ya so ta sama da yanda take ganin Anwar ma zai so ta, ya kula da ita sama da yanda ta ke tinanin Anwar zai kula da ita, Alhaji Mutum ne da baya son damuwar ta, ya tsare mata dikkan Wani haqqi na aure nata da ke Kan shi, ta ya ba zata ji mutuwar shi ba?shi ne fa uban 'yar ta tilo, Cike da qunci da d'acin zuciya take bin shi da mugun kallo idanun ta na kwarar da hawayen baqin cikin da zuciyar ta ke ciki, 'yan uwan ta da masu aikin gidan har ma da iyayen ta da suka fito kowa sai mamakin yanayin da  Eamaan mai sanyin hali da kunya tare da kawaici ta koma a cikin kankanin lokaci, yau har ta kai ga itace ke ikirarin kashe wani,cikin tsawa ta sake furta, "Ka fita daga gidannan i don't want to see your face ever again, if you ever show your ugly face here i swear to God  i will not hesitate to kill you" Alhaji Saminu tin da ta fara kifa masa tafi ya qame qam a wajen cike da tsoron yarinyar, qasan ranshi kuwa wani ɓacin rai da qiyayyar ta ne ya mamaye zuciyar shi,ya kasa gaba ko baya ballantana yabi umarnin ta ya bar gidan,kallon idanun ta yayi yaga babu komai a cikin su face matsananciyar tsanar shi da qiyayyar shi,tabbas aka bar shi daga shi sai ita zata iya aikata abunda tace akan shi, bai ankara ba da tinanin shi ya hango glass cup na yowa ta wajen shi,alamar jefo masa akai, a qoqarin kauce masa ne ya daki kafadar shi, duk da babbar rigar dake jikin shi sai da ya ji wani zafin saukar shi a jikin shi, kafin yayun ta su kai hannu dan hana ta ta dakko wani zata kwad'a masa,yana ganin haka ya taka a sukwane ya isa gaban motar shi ya buɗe zai shige, Eamaan ta kwasa a guje ta bishi da wani cup ɗin a hannu ta saita shi ta wurga masa a kai, nan take cup ɗin ya fashe ya yanke shi a kan shi, ihu ya kurma yana fad'in, "Ta hauka ku riqe ta kar ta kashe ni," A guje ya take motar shi yayi ribas ya bar gidan, banda zagin shi da tsine masa babu abinda Eamaan keyi, kuka ta durqushe a wajen tana yi mai ban tausayi, Mama ce ta iso wajen ta jata jikinta ta rungume ta tsam a qirjin ta, da fari sai tirjewa take yi tana fad'in a barta ta kashe shi tinda azzalumi ne, a hankali ta fara dawowa nutsuwar ta, sai kukan zuci da take yi hawaye na zuba mata a kuncin ta, cikin gida suka koma mama tayi mata masauki a dakin ta a gefen gadon tana shafa bayan ta a hankali,Eamaan kuwa sai ajiyar zuciya take, fuskar ta kuwa ta yi jawur kamar an kara a wuta,ruwa Ammaah ta kawo mata dan ta sha. Ita kanta Ammaah idanun ta sun kad'a saboda ganin damuwar da Eamaan ke ciki,mamakin Alhaji Saminu kuwa ya kasa barin zuciyar ta, idan bata manta ba shine sanadin da Alhaji Abdullah ya kamu da ciwon shanyewar barin jiki, shine mutumin da ya nemi matar Alhaji Abdullah har suka haifi yara biyu,amma saboda rashin kunya ya lallabo zai ce yana son 'yar ta. Ruwan ta kurb'a sau biyu ta ajiye saboda baya yi mata daɗi,ido ta lumshe kawai ta jingina da jikin gadon hawaye na zuba ta daga idon ta,lallai mutumin nan ya raina mata hankali, bayan duk abubuwan da yayi musu shine zai zo yace yana son ta da aure? Kwantawa ta yi ta dunqule a waje ɗaya sai sauke ajiyar zuciya take yi kamar yaron da ya yi rigima ya gaji ya yi shiru dan Kan shi,Mama da Ammaah na ganin ta kwanta sai suka bata waje suka koma parlour, cikin jimami Hafsat tace, " Mama Ammaah ko zamu yi wa Daddy waya ne a sanar da shi abinda ya faru dan ina jin tsoron wannan mutumin, kuma ni a gani na da kawai mu tafi bauchi yau tinda bamu san me zai iya aikatawa ba, na tabbata a can ma Zata samu nutsuwa sosai," Mama ce tace, " shawarar ki tayi Hafsat kuje ke da yayar ku ku fara parking kayan ku, bari na kira Daddyn ku na sanar dashi abinda yake faruwa," Direct daki ta wuce ta sami Eamaan kwance idanun ta kulle suna zubar da ruwan hawaye, tausayin ta ne ya kama ta, cikin sanyin murya tace mata, " ki shirya mu tafi bauchi yanzu,na tabbata zaki fi jin daɗin zuciyar ki and ko babu komai zaki yi nesa da baqin cikin ki," Bude idonta ta yi da sauri ta bi Hafsat da kallon dan ta gasgata maganar ta,d'aga mata kai ta yi alamar da gaske take yi yanzu zasu tafi, cike da jin dad'i ta tashi zaune ta sauka daga gadon ta shige toilet ruwa ta watsa sannan ta shirya ta fito, Hafsat da Yaya na gama haɗa kayan su suka shirya Fatee, sun gama hada komai nasu kenan Daddyn su ya dawo. Babh b'ata lokaci Mama ta sanar dashi dik abinda ya faru, cikin b'acin rai ya dinga masifa yana fad'in da sun sani tin zuwan shi suka sanar da shi ya dawo, hakuri suka.bashi, suka sanar da shi.plan din su,  Shima ya yi.na'am da hakan, in dai Eamaan din na so, fitowa suka yi, yana ganin ta guiwar shi ta yi sanyi, yana dorawa kan shi laifin komawar ta haka, " Eamaan ki yafe ni, i thought i did the right thing, ashe ba haka bane, dubi yanda kk koma, Eamaan ki kwantar da hankalin ki in kin je can kinji, ba zan qara saki ko wani ma yin abinda ba shi yake so ba," 'Daga rinannun idanun ta ta yi da suka yi jawur ta kalle shi ta ce, " Daddy ba laifin ka bane, haka Allah ya tsaran rayuwa ta,kowa da qaddarar shi, wanda ya yarda da Allah da ranar akhirah, dole ya yarda da qaddara mai kyau da mara kyau, kenan in dai ina son imanina ya cika sai na yarda hakan na cikin qaddara ta, d'ayan mu ba shi da ikon  cutar da wanin shi face abinda Allah ya hukunta zai kasance, kai mahaifina ne in kana jin haka ni ba zan ji dad'i ba, kai min addu'ar samun sauqin abinda nake ji, ban tab'a dana sanin auren Alhaji ba, tinda shi d'in mutum ne da yasan haqqin zaman tare, kuma he gave me the most beautiful gift ever, gata nan Fateema, dan haka bana dana sani kuma har abada ba zan yi danasani ba thank u Daddy, for everything," Rungume ta ya yi sosai, hawayen shi na sauka akan ta, itama kukan take,haka duk wanda ke wajen banda Fatee dake ta wasan ta, a haka ya kai su waje, ya kira driver, " Tinda tafiyar dare ne ka kai su washegari ka dawo a ta haya ka bar wa Eamaan motar ko zata buqace ta," "To ranka ya dade, Allah ya kai mu lfy," " Ameen" kowa ya amsa , Daddy ya damqa wa driver kud'i shi da Hafsat da Eamaan d'in, ko da za su buqaci Wani abu, raka su suka yi har bakin mota, shigar da kayan  su driver ya yi bayan  motar,suka dau hanyar Bauchin Yakubu, ( yan bauchi kuna da babbar baquwa, a dafa mata shinkafa da wake😋🤣) sun dau hanya ba mai cewa komai, har suka yi nisa suka bar gari, Eamaan addu'a ta fara yi, domin ta san Allah na amsa addu'ar matafiyi, dan haka ta hau addu'a tana kokawa a wajen Allah da ya kawo mata komai da sauqi, Hafsat ce ta matsa kusa da ita ta kwantar da Kan Eamaan a jikin ta, Eamaan d'in kuwa ta  kwanta ta yi shiru , Fatee ma bacci take. Sun isa bauchi bayan isha'i, mijin Hafsat ne ya bud'e musu gate ya taya su d'ibar kayan su zuwa cikin parlour, bayan shi suka bi bayan Hafsat ta nuna wa driver d'akin da zai sauka, gidan ba Wani kantameme bane gida ne madaidaici me kyau, farfajiyar gidan bata wuce wajen aje motoci biyu ba,bayan ya ajiye kayan ne  ya kama hannun matar shi ya na bin fuskar ta da kallo alamar ya yi kewar ta sosai, murmushi suka yi wa juna kafin ya saki hannayen ta ya dauki kayan  su ya shigar musu d'aki, already sun yi waya da Hafsat ta Sanar da shi zuwan su tare da Eamaan d'in, d'akin ta bi bayan shi d'auke da Fatee a hannun ta ,ta masa godiya tare da qaramin murmushi, yana fita ta samu ta kwanta a gadon bayan ta kwantar da Fatee, kan ya fita sai da ya sanar da ita in ta gama.akwai abinci ta fito su ci, ta amsa masa da "To na gode"sannan ya fita, murnar dawowar Hafsat ce ta cika shi da zumud'in ganin ta kamar zai taka da gudu ya Isa gare ta yake ji, daki suka shige suka barni tsaye sororooo. Eamaan wanka ta yi wa Fatee itama ta yi, tana ta ma ta  dariya kuwa, da surutu kala kala, shiryawa ta qarasa yi itama ta fita parlour riqe da hannun Fatee,kamar yanda ya fad'a kuwa abinci ne me rai da lafiya kamar ba namiji bane ya dafa shi, zama ta yi a kujera ta kunna TV Dan ta Jira su. Hafsat kuwa da mijin ta suna d'aki ana soye wa, an jima ba a gamu ba, Dan ma Hafsat na ta bashi hakuri ya Jira se an jima, kar Eamaan ta yi ta jiran su da kyar ya hakura ya taya ta wanka, ya bar ta ta qarasa, kafin ta fito ya dakko mata kayan da zata saka marasa nauyi, ya fesa musu turaruka, ya ajiye, ta na fita ya nufe ta ya na sake bin jikin ta da kallo, tare da fad'a mata yanda ya yi kewar ta, itan ma bayyana masa irin yanda ta yi kewar sa ta yi, sannan suka sake tambayar juna bayan rabuwa. Ta na kammala shiri ya saqale hannun ta a nashi  suka fita parlour, Eamaan na ganin su ta miqe ta sake gaishe shi, Yaya da ta kira shi da shi se ya bashi dariya, ya ce Dan Allah kar ta tsufar da shi, dariyar itama ta yi, ta ce dole ta kira shi da Yaya tinda mijin yayar ta ne shi, abinci suka ci har Fateema, suna gamawa ta miqe ta musu sai da safe, ko ba Dan komai ba ma ta gaji, sannan ta na kallon irin kallon zalamar da mijin Hafsat din ke bin Hafsat d'in da shi, be Kamata ta b'ata musu lokaci ba. "Ba Zaki sha tea din naki ba na qa'ida Zaki kwanta Eamaan?" "Na gaji mun had'u da safe" Murmushi kawai Hafsat ta yi, ta kula Eamaan na Allah Allah ta Basu waje ne, Dan haka da Kan ta ta miqe ta kunna gas ta Dora ruwan tea, ya na gama dahuwa ta zuba a mug ta Dora a qaramin trey ta nufi d'akin Eamaan d'in, ta na shiga ta tarar har ta yi bacci, se  surutai take a baccin nata, " Alhaji ka dawo pls, ka zo wajen mu muna kewar ka," Tana ta surutai idon ta na hawaye,tausayin ta ne ya kama hafsat, ta toshe bakin ta dan kukan da take son yi, sai da ta maida kukan ta ta daga Eamaan d'in, wadda tai firgigit ta tashi, tana zaro ido, " Hafsat yanzu naga Alhaji, yana ta mun murmushi, yana min bye bye,ina ta ce masa ya dawo yana kadan kai yana ban hakuri,yace na kwantar da hankali na shine kwanciyar hankalin shi," "You see, hakan na nuna maki kukan da kk yawan masa baya so, addu'ar ki kawai yake so, dan haka ki sawa ran ki hakuri shima ya samu dadin kwanciya, kinji,karbi ki shana hado maki tea din naki," Karb'a ta yi ta shanye sannan ta miqa mata mug d'in, ta koma ta kwanta, "Na gode 'yar uwa ta, Allah ya bar mu tare" Shafa kafad'ar Eamaan Hafsat ta yi, ta ja mata abun rufa ta dauki  Fatee ta wuce da ita q kafad'ar ta, dik da Eamaan ta hana saboda Gani take in ta farka zata Hana su sakewa, Hafsat ta ce mata ba komai zasu kula da hakan, Kan ta koma mijin Hafsat ya Kai wa driver abinci da ruwa, ya nuna masa dik abinda zai buqata sannan ya koma ciki,bayan sun kashe komai na wuta suka kulle gidan suka wuce d'aki kwantar da ita suka yi, bayan Hafsat ta yi mata shimfida da lallausan bargo, ta sa mata pilo, su kuma suka haye gado, kwata kwata mijin Hafsat ko a fuska be nuna Jin haushin dakko Fatee da Hafsan ta yi ba, shi dai fatan shi a zo a bashi haqqin shi. Da safe Eamaan ta riga kowa tashi, ta shiga gyara gidan, dik da bai wani datti ba, ta je ta fara hada abin karyawa, nata ta zuba ta zauna tana ci suka fito, cikin wanka da kwalliya, mijin Hafsat dauke da Fatee Hafsat dauke da jakar shi, suna ma Fatee wasa, tana ta dariya da shirmen labarin da take Basu na yarinta, sai suka bata sha'awa, zama suka yi, ta gaida su, mijib Hafsat na tsokanar ta mai baccin wuri, abinci suka fara ci, Hafsat ta tashi da gudu tai toilete dake cikin palour ta yi ta kwara amai, sai da ta gama ta fito, tana nishi, mijin ta daya ke tsaye bakin qofar ne  ya kama ta yana ta jera mata sannu, " Ya kamata fa a kaita asibiti,tin da taje take amannan da safe, komai ta ci sai ya dawo, in ta yi da safen nan shikenan Bata sake yi se washegari to kuma zata ci komai lfy," Damuwa ce kwance akan fuskar shi, yace to ta gama ya sauke ta a sibitin ya dawo da ita, haka suka yi kuwa, bayan sun je likita ya mata tambayoyi, da gwaje2 suka.gane tana dauke da qaramin cikin, wata biyu,suna dawowa Eamaan taji labari ko sai murnar damun cikin ya mantar da ita damuwar ta, sosai sike godewa Allah da wannan kyauta, ranar kam mijin Hafsa aiki ruwa ta sha, dan bai je ba. Zaune yake a qayataccen gidan nashi, wanda na kula duk kyaun gidannan  ba matar aure cikin shi, yana karanta qur'anin da aka fassara zuwa harshen turanci, gaban shi swimming pool ne,sai dan qaramin table a gefen shi, da ya dora cup da ruwa a gefe, ya sa sun glasses, saboda akwai rana kadan, duk da yana qasan lema ne, kyakkyawan matashin da ya aje gemu irin na ustazan nan, ya gaji da kyau, tsam ya daina karatun ya shiga duniyar tinanin abinda maqocin su Kuma abokin shi ya sanar da shi jiya.......... A karanta da hakuri...Kun San tsohon rubutu ba zai daidai da sabo ba.[24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   BIYAYYAH  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 21: Anwar ne zaune a kujera a parlour yana hutawa,tunani yake yi mai zurfi kafin daga baya ya d'akko wayar shi da ke saman qaramin table ya hau danna digits d'in abokin shi, ringing biyu tayi ya ɗauka , cikin shaqiyanci irin na abokai ya ke tsokanar Anwar, " Yahhhh ustaz ya ne....Ya Bauchin kuma? ina fatan dai by now Ustaz ya samo mana  ustaziya acan da zamu sha biki, kasan fa 'yan bauchi ustazai ne." "To kanya sarkin zuba, ai kama jira in amsa maka gaisuwar taka  ko? dama na kira ka ne akan labarin da ka bani game da Eamaan kwanaki ,tin da ka fada min nake ta tunanin anya gaskiya ne kuwa?" " Man da gaske ne mana, yanzu haka tana garin Bauchi a gidan yayar ta Hafsat,saboda jiya an wangale gate d'in gidan na hango ta tana ta kuka tana masifa ma wani Alhaji, ina nan zaune ina mamaki akan abinda na gani, saboda gaba ɗaya Eamaan ta sauya akan yanda muka santa,na kai minti biyar a wajen bayan Alhajin nan ya tafi,dake qofar buɗe aka barta shi ya bani damar ganin ana saka musu kaya a bayan mota,ana gama loda kayan ne suka yi sallama da mutanen gida suka shige mota driver ya ja suka bar gidan, tafiyar su da mintuna na zauna a qofar gidan su,to dake ka san baba me gadi mutumin mu ne, a wajen shi nake samun labarin dik abinda na fad'a Maka kwanaki har ya min qarin bayanin ai jihar Bauchi suka nufa zata je Bauchin gidan Hafsat dan ta huta da hayaniyar da keta faruwa." Ajiyar zuciya Anwar yayi cikin zuciyar shi yace, 'Lallai wannan babbar dama ce a gare ni ta dawo da soyayya ta sabuwa dal a zuciyar Eamaan.' Abokin shi ne yace, "Man yaa dai na ji ka yi  shiru? Lafiya dai ko?" "Lafiya qalaou kayi min qoqari na gode sosai Allah ya qara mana zumunci, sai mun yi waya, Assalamu alaikum," Sallamar  abokin na shi ya amsa suka kashe wayar, murmushi ne kwance a fuskar shi, da kuma addu'ar da ta zama sirrin shi,domin kuwa dik tsawon waɗannan shekarun bai taɓa mantawa da ita ba, soyayyar ta kuma bata taɓa gushewa daga zuciyar shi ba. Girki take a kitchen su kuma suna zaune a plour da Fatee sai sa su dariya take yi, Kamal ne yace da dan qarfi yanda Eamaan dake kitchen zata iya jiyo shi, " Eamaan ko zaki d'akko takardun ki ne a nema maki aiki ki fara, nema maki aiki ba zai min wuya ba in Allah ya yarda, akwai Wani cousin d'ina da ya bud'e Wani asibiti ko anan se na nema maki,zuwa aikin shima zai taimaka maki wajen rage maki kad'aici ko baby?" "Kwarai da gaske wannan m shawara ce mai kyau." Inji Hafsat,Eamaan kuwa sai da ta kammala abunda take yi,sannan ta dakko abincin  ta fito parlour ta same su, kunun acca ne Hafsat ke so ta yi mata da alala, da rana su kuma tayi masu rice and stew da salad da pepper meat mai cike da veges a ciki,gefe ɗaya kuma Apple drink ta hada masu domin tafi son haɗin gida akan lemon kwali ko na roba,a tsakiyar su ta aje sai kowa ya ja plate suka fara ci,bin ta ya yi da kallo, dan har lokacin bata bashi amsa ba,a hankali ta furta, " Yayah ka d'an bari ba yan zu ba, sai naje gidan Yayah Babba na gama mata hutun ta na dawo, saboda kaga ba lallai bane na ci gaba da zama anan dindindin, wataqila zan koma kano," kallon ta ya yi da harar wasa sannan yace, " kina nufin ba zaki zauna a wajen mu ba har Allah yasa ki samu d'an bauchi ki aura kin ga shikenan Hafsat ta samu 'yar uwa a kusa." murmushi suka yi, "Ohhhh ashe son kai ne abuunn, shi yasa ake son na samu aiki a bauchi ko, to naqi wayon kano ma Mama da Amma na jirana,sannan Hafsat bata da Wani dangi da ya wuce Kai da 'yan uwan ka, mu haka aka koyar da mu a gidan mu, dangin mijin mu su ma 'yan uwammu ne in bamu d'auke su 'yan uwa ba wahala zaman zai yi mana Ina fatan ka gane" Dariya suka yi ya kalli Hafsat tabbas ya kula da hakan, shi yasa Hafsat bata tab'a nuna banbanci tsakanin dangin shi da nata ba, Kuma ya kula dangin shi na son ta sosai kamar dama can a cikin su take, kallon ta ya yi ya marairaice fuska akan ta sa baki, d'aga hannayen ta ta yi tana juya ido da kai, sannan ta dan kyab'e baki tace, "Ba ruwana kai da qanwar ka ne, in ta yarda zan fi kowa farin ciki da hakan, in bata yarda ba faqat,ka lallab'a abarka da Kan ka, kalan in shiga ku kunyata ni ko?"   kauda kan shi ya yi zuwa wajen Fatee yana ma Fateen wasa wai shi irin ya yi fushin ɗin nan, dariya suka hau yi masa, ita kuma Hafsat ta d'an mintsine shi kadan, ya saki qara yana sosa wajen yana kallon ta,cikin dariya Hafsat tace, "A haka ka ke son ta zauna in wani ya kawo mata raini wa zai rama mata, daga d'an wannan mintsinin zaka sake mana ihu se kace Wani budurwa" Ta na ganin alamun ramawa ze yi ta miqe suka yi ta zagaye wajen suna dariya,Eamaan kad'a Kan ta ta yi sannan ta kai cup din lemon da ta d'ebo bakin ta,cike da murmushi da nishad'i take kallon su suna burge ta sosai,tinanin yanda Alhaji ya ke yi mata wasa ne ya  faɗo mata a rai, cikin kasala ta sauke cup din, idon ta ya tara ruwa sosai, a hankali ta miqe zata shiga d'aki,sai a sannan ne suka kula da yanayin ta, ba su hana ta barin wajen ba, waje suka samu suka zauna manne da juna suna maida numfashi, bayan ta shige ne Hafsat tace, "Da alama wasan da muke yi ne ya tina mata Abban Fatee, domin kuwa bawan Allahn nan duk da ya tsufa ya nuna mata irin yanda yake son ta,ya nuna mata shi saurayi ne a zuciya, dan jin dad'in ta ba abinda baya yi mata, haka zai goya ta kamar wata jinjira ya na jijjiga ta, na sha ganin shi ya na mata abubuwan da ko da saurayin ta aura ba lallai ta samu kulawa haka ba, Fatee ce ta hau cinyar Hafsat ta kwantar da kan ta, Hafsat d'in ta  shafa bayan ta da tausayawa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Eamaan na samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da iyayen ta da 'yan'uwan ta keyi mata fata a bauchi,kullum a Sky crown suke siyan bread dan basu da nisa sosai, haka shima gidan Anwar ba nisa da wajen. Wata rana mijin Hafsat ya fita office basu tashi da wuri ba suna ta bacci sai wajen 10am suka farka har Fatee, dan daren ranar sun sha hira ne sosai har lokaci ya ja basu kwanta da wuri ba, shiyasa suka makara basu samu tashi da wuri ba, dubawa suka yi suka ga ya yi sultan chips sannan ya dafa Tea daya sha kayan qamshi, ya rubuta ma matar shi saqon yana son ta ya fita aiki sai ya dawo dan haka ta kula da kan ta da su Eamaan, murmushi ta yi ta aje takardar, ta rufe flask din abincin ta samu waje ta zauna, "Ni yau sky crown bread nake son ci, so nake na ji laushi da dad'in shi a baki na,musamman mai inibi da mai kwakwar nan," Yawu ta hadiya kamar wadda ta gan shi a gaban ta amma an hana ta ci, "To bari na je na siyo maki mana,sauran kuma kafin na dawo ki cinye abincin zaki dafa min wani, dan na kula yanzu kin zama hamburin hayam, ki bari na dawo mu ci tare dan yunwa nake ji nima,in ma bamu qoshi ba sai na yi mana wani ." Dariya Hafsat ta yi tace, "Ni ki ka ban bread dina ma ko kallo baki isheni ba," Dariya suka yi ta ɗauki kudi da hijab ta saka ta fita, tafiya take a qasa don ba wani nisa gare su ba ta ga wata dalleliyar mota ta wuce ta,a hankali kuma sai motar ta fara yowa baya, qin d'aga kai ta yi ta kalli motar sai ta ci gaba da tafiyar ta,tana isa sky crown ta nufi wajen da zata sai bread ɗin ta shi Kuma ya fito daga motar yana son tsallaka wa inda take,Eamaan ta kula da cewar wani na bin ta a baya,cikin sauri ta samu wani lungu a wajen ta boye qirjin ta na bugawa dan tsoro,shi kuwa Anwar dubawa ya hau yi ko ina bai gan ta ba,tsaye yake yana kalle-kalle cikin shigar shi ta qananan kaya ya ɗora hannun shi a qugu dayan kuma a goshin shi,a haka ya fito yana ci gaba da duba ta ko zai samu dacewa ya ganta, tinanin ana jiran shi a asibiti ne ya katse shi daga neman da yake yiwa abar ƙaunar shi da ya gani bayan shekaru ,motar shi ya shiga ya tada ya tafi zuciyar shi na tabbatar masa da Eamaan ya gani. Bayan tafiyar shi ne ta fito daga maɓoyar ta ta wuce wajen siyan bread ɗin ta,har aka gama bata zuciyar ta bata dena tunanin wake bibiyar ta ba,ana bata ta biya kuɗi ta karb'a ta koma gida cike da tsoro,miqawa Hafsat bread ɗin ta yi ta wuce d'aki jikin ta duk ya yi sanyi, dama haka unguwar masu kuɗi take gaba d'aya sai kaga mazan kusan dikkan su masu son matan tsiya ne, kawai ba dama aga mace ta d'an haɗu ta fita ba ruwan su da dare ko rana zasu tsaya su dame ta,tsaki ta ja kawai ta fad'a gado, ta yi lamo, ta rasa ma tinanin me take yi. Muryar Hafsat ce ta dawo da ita cikin hayyacin ta tace, " Eamaan me ya faru ne naga kin dawo kawai kin kwanta baki zo mun karya ba me aka yi maki?" Zama tayi a saman gadon cikin damuwa ta baiwa Hafsat labarin abinda ya faru, murna ta gani kwance akan fuskar Hafsat daga baya kuma ta ce, "Too Allah ya kyauta taso mu je mu karya," Tashi Eamaan ta yi suka je suka ci abinci sama-sama,dan kuwa ba yanda taso ci ta samu taci ɗin ba. Tin da yaje asibiti yake tinanin tabbas ita ya gani ba wata ba,to dama a kusa suke kenan tinda gashi ya ganta a bakery ɗin unguwar su? tabbas in a kusa suke kuwa zai sawa wajen ido yaga daga gidan da take fitowa,a hankali ya furta, "Ba zai yu na qara rasa ki ba a karo na biyu Eamaan d'ina,Zaki zama tawa  wannan karon inshaa Allah." Tiyata suka yi ma wata mata da ta gagara haihuwa da kan ta,bayan ya koma office ɗin shi ne ya buɗe fridge ya dakko gorar ruwa ya ruwa ya tsiyaya ya shanye yana lumshe ido, key d'in motar shi ya ɗauka cikin sauri ya fice daga office ɗin ya wuce wajen da yayi parking motar shi ya shige........... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 22: Direct bakeryn ya koma, yana shiga masu gadi da ma'aikatan wajen suka yi ta gaida shi da fara'a a fuskar su, dan suna matuqar son Anwar sosai,Anwar  akwai mutunci ga kamala, da kyautata wa, yana yawan zuwa wajen siyan abincin shi da na Mai gadin gidan shi da Mai masa share share, in ya zo su na Shan hira kala-kala kan ya tafi,hirar siyasa ne ta ilimi ne da kuma hira akan yanda samari da 'yammata ke gudanar da soyayya a wannan zamanin saboda kasancewar wajen wajen saida kayan kwalam suna ganin abubuwa kala-kala dake faruwa. Tin da yake zuwa wajen basu tab'a ganin ya je da budurwa ba, ko Kuma su ga ya tsayar da budurwa a wajen, dik da cewa waje ne da matasa maza da mata ke zuwa siyan snacks da sauran su. Kwatsam sai su ka ji ya na musu tambayar da ta sa su kallon juna fuskokin su dauke da fara'a da alama bana Anwar ya samu wadda ta sace zuciyar shi, shi ma d'an murmushi ya yi ya gyara tsayiwar shi sannan yace, "Tabbas akwai abinda baku sani ba game da rayuwa ta, wannan da kuka ji ina tambaya itace rayuwata,itace firsr love d'ina, wadda nake sa ran ta zama last, dan in ba ita na aura ba ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba ko soyayyar gaskiya,nan na ga ta shigo d'azu da safe kafin na wuce asibiti, ta na sanye da hijabi kalar pink dogo har qasa, fara ce me matsakaicin tsaho, ta na da kyau Mai d'aukan hankalin me kallon ta,tana da siririyar murya Mai sanyi da zaqin sauraro, girar ta na da cika sannan..." Cikin tausasawa murya d'aya daga cikin securities na wajen  yace, "Ranka ya dade ina roqon Allah daya mallaka maka ita Allah ya sa rabon ka ce, ba sai ka qarasa kwatancen ta ba ma na gane ta, tabbas na ga shigar baiwar Allahn Kuma na ga sanda ta b'uya a can wajen cike da tsoro, da Wani irin yanayi a tattare da ita, sanda ka shigo Ina gaishe ka baka ji ni ba ai, se na ga kana dube dube ka fita cikin damuwa, tafiyar ka ke da wuya baiwar Allahn ta fito ta sai bread ta tafi cikin hanzari, ranka ya dad'e gaskiya ban mata sani na musamman ba amman yan da ka kwatanta ta dai tabbas sun tab'a zuwa nan sau  biyu  su biyu mata da Kuma  namiji  d'aya sai qaramar yarinya sun siyi pizza ranar Sunday da ta gabata,inaga yanda za a yi yanzu shine tinda Ina da lambar ka da na ga  sunzo zan faɗa maka sai ka zo ka riske ta" Cikin rawar hannu Anwar ya miqa masa hannu suka qara gaisawa, ya shiga godiya kamar har ma an had'a shi da Eamaan d'in shi,ya yi masu alherin da ya saba ya tafi gida cike da addu'ar Allah ya sa a kira shi da wuri idan an ganta, zuwa ya yi gida ya yi wanka ya wuce masallacin Juma'a aka yi sallah da shi,ya na dawowa gida sai ya ja qur'anin shi ya karanta suratul Kahfi bayan ya idar ya hau yiwa Annabi salati ,yana cikin yi ne bacci ya dauke shi. 'Baby  pls ka bari, ni bana soooo' 'kina mana so Sweety,to tsaya idan baki son wancan bari na maki wannan' Sai ya fara tickling d'in ta ita Kuma ta na ta dariya, d'an tsaya wa ya yi kad'an ita kuma ta rungume shi,zata kai bakin ta nashi kenan ya ji an jijjiga shi, cike da jin haushi ya miqe tare da addu'ar tashi a bacci. " Kai dalla can galahore kawai, meye haka zaka zo ka tada ni ina bacci na me dad'i," Dariya abokin shi Jamal ya yi yana kallon yanda Anwar yake fushin da bai san shi da shi ba, kwata kwata fushin ma be dace da shi ba tinda ba halin shi bane. " Haba namijin duniya,meye zai d'aga hankalin ka a mafarki haka? To koma mene ne alkhairi ne da yardar Allah success is urs man, Allah zai kare ka daga dikkan Sharrin da mafarkin ya qunsa ya kuma haɗa ka da alkhairin shi, dan haka ka miqe lokacin fara addu'o'i ya yi, tin da ka san dai ba wai mun san sa'ar da aka ce in mutum ya dace da ita a ranar juma'a ya yi addu'a Allah zai amsa bane lalube muke a duhu, Allah ya datar da mu" A hankali ya tashi dik jikin shi a mace ya shiga wanka sannan ya d'aura alwala, sai da suka yi la'asar ya ci abinci sannan ya koma ya ja qur'anin shi suka hau karatun qur'ani, bayan sun idar Kuma kowa ya kama yi wa Annabi Muhammad salati, sannan daga baya naga suna ta addu'o'i wanda na san Anwar kam dole sai ya yi addu'a akan Allah ya had'a shi da  Eamaan,suna idarwa magrib ta yi suka fita masjid, sai da akai isha'i abokin shi ya ce suje suci abinci daga nan ya wuce gida,wajen cin abinci suka je suka ci suka sha,bayan sun gama ne Anwar ya tafi gida shi kuma abokin shi ya tafi nasu gidan, yana isa gida ya gaida Baba Mai gadin shi da  me masa d'an aikace-aikacen gida,ya miqa masu nasu daya taho masu da shi,sannan ya shige cikin gidan wanka ya yi sannan ya sa kayan baccin shi ya kunna karatu a wayar shi ya kwanta, a hankali ya tara hannayen shi a bakin shi ya karanta addu'ar bacci ya shafe jikin shi ya sake kwantawa cike da tinanin ta, sai juyi yake baccin yaqi daukar shi, ya kai wajen qarfe biyun dare a haka yana fatan Allah yasa ranar sunday ya ganta,ganin ya kasa bacci sai ya sakko daga gado yayi alwala, ya tada sallah yana roqon Allah in Eamaan alkairin rayuwar shi ce Allah ya bashi ita, kar ya zo ya yi ta wahala akan ta wannan karon ma ta samu wani, yana gama fad'an haka a addu'ar shi ya kuma tabbatar da me yace a addu'ar ta shi ya zaro ido waje, lallai in Eamaan ta bar shi a karo na biyu ya kad'e, tini ya fara roqon Allah akan ya mallaka masa ita in alkairi ce a gare shi,in ba alkairi duk da dad'in da son ta ya ke yi masa a ran shi da sabon da ya yi da son ta Allah ya yaye masa,a haka ya kai har 3am ya na addu'a kafin ya  miqe ya hau gado, nan da nan bacci mai nauyi kuwa ya yi awon  gaba da shi, 5:35am ya tashi ya ci gaba da ibada. Haka rayuwar Anwar take gudana kullum, daga yaje wajen aiki, sai yayi ibada ya ci abinci ya nemi waje ya kwanta,sam baya daga cikin samari masu shiriritar neman matan banza ko shashancin shaye-shayen zamani, yana matukar k'ok'ari wajen kiyaye hakkin Allah da ya rataya a kan shi. Yau sunday tin safe Anwar bakin shi yaqi rufuwa saboda murna da fatan sake ganin Eamaan, domin rage wa kan shi lokaci sai kawai ya yi ta aikace-aikace,dare na yi kuwa ya gabatar da sallahr  isha'i  a masallaci ya dawo ya yi  wanka, gayu ya yi na d'aukan magana shi Kan shi ya yaba da kyawun da ya yi, ya yi shiga cikin doguwar rigar shadda fara sol kamar wanda ke da yaƙini akan zai ga Eamaan a daren ranar haka Anwar ya sha tiraruka sai qamshi yake zabgawa,agogon shi da takalmin shi masu ruwan hanta daya saka kalar aikin kayan shi da hular shi. Yana nan zaune ya gaji da Jira ba a Kira shi an ce an ga gilmawar ko da me kama da Eamaan bace, dan haka rufe parlour ya yi ya dauki key d'in motar shi ya fita,masu aikin shi sake baki kawai suka yi suna kallon shi dan ganin irin kyan da yayi, ga mota ya sa an wanke masa sai daukan ido take fara qal, me gadi ne ya tsokane shi yace, " Ranka ya dad'e ko za a je wajen surukar tawa ne irin wannan kyau haka?" Dariya yayi sannan ya ce "I hope zan had'u da surukar taka a daren yau Baba,ka taya ni da addu'ar samun nasarar farautar da zan je ko Allah zai sa na samu sa'a" "Allah ya baka sa'a d'ana, kaje lafiya ka dawo lafiya cike da nasara," Cikin jin dad'i ya fice daga gidan, direct Sky crown ya je,ma'aikatan wajen na ganin shi suka hau gaida shi, suna ta yaba kyawun da ya yi,Anwar baya daga cikin maza masu tsananin kyau, za a iya sanya shi a layin matsakaitan mazaje wajen kyau, tsaftar shi da Iya gayun shi ke qara fidda kyan shi,domin ita tsafta da iya gayu na sa mummuna ma a ga kyawun shi, zuwa yayi ya samu wani table da babu kowa ya zauna ta yanda duk wanda ya shigo ko zai fita zai ganshi,kira yayi aka kawo masa coffee da sandwich wanda yaji vegetable a tsakiya da nama,  ko tab'a sandwich d'in bai yi ba dik da yunwar da yake ji zuciyar shi nata bugawa saboda ɗokin ganin Eamaan,shin wai ta ina zata shigo ne? coffeen kawai yake ta kurb'a kadan-kadan. Anwar ya kai wajen minti talatin a wajen amma bai ga mai kama da Eamaan bama ta wuce, kallon hanyar shiga wajen ya sake yi, idon shi ya sauka Kan wani abokin shi Kamal ɗauke da yarinya a hannun shi, kafe yarinyar ya yi da ido ya na so ya tina inda ya tab'a ganin ta amma ya kasa tinawa, Eamaan da Hafsat ne biye a bayan Kamal mijin Hafsat ɗin. Wata iriyar ajiyar zuciya Anwar ya sauke mai qarfi tare da yin hamdala a bayyane, yalwataccen murmushi ya saki wanda ya sake qawata fuskar shi, miqewa ya yi ya na bin Eamaan da ke tafiya kamar d'awisu, fuskar ta se sheqi take yi a cikin hasken ƙwan lantarkin dake wajen,gani yayi ta yi masa wani irin kyau kamar bata tab'a aure ba a rayuwar ta balle a ce ta haihu, Ido kawai ya zuba mata ta baya ya na aje qafa a duk inda ta d'auke ta ta, ya ma manta da ya ga Kamal gaba d'aya ya tattara hankalin shi ya ɗora shi a Kan Eamaan din shi. Qamshin turaren shi ne ya yi wa Eamaan dad'i a hancin ta,nan take ta tina yanda Anwar ke son irin turaren, tsayawa ta yi cak, kamar wadda aka dannawa remote control,lokaci daya ta juya , iskar da take shaqa ce ta ji ta na neman yi mata kad'an sakamakon idanun ta da ta sanya a cikin na Anwar. Kallon ta yake yi baya ko qifta wa saboda ji yake yi kamar in ya qifta zata bace masa, ma'aikatan wajen sun kula da yanda gaba d'ayan su suka qame qam suna aikawa junan su kallo na musamman,nan take suka fara tunanin wannan itace wadda ta sace zuciyar Anwar, a hankali yake takawa dan ya qarasa gaban ta, Eamaan kuwa  da sauri ta juya baya ta na sauri ta bar wajen, tini hawaye sun wanke fuskar ta saboda rashin halin da ta tsinci kanta a ciki da tayi,Eamaan ta rasa me ya Kamata ta ji game da sake had'uwar ta da Anwar ,shin farin cikin ganin Anwar zata ji ko baqin cikin sake ganin shi a wannan lokacin? Shin Kunyar shi take ji ko Kuma kunyar Kan ta a matsayin ta na  bazawara a yanzu? Me ya sa take Jin kamar ta koma wajen shi ta dena gudun da take yi? Anwar kuwa bai b'ata lokaci ba wajen rufa mata baya. Hafsat ce ta tafi da sauri wajen Kamal d'in ta ta fad'a masa me ke faruwa, a tare suka bi bayan Eamaan da Anwar. Da qafa Eamaan ke sauri har ta Isa qofar gidan su, tana zuwa qofar gidan  nasu dole ta tsaya dan a kulle yake kuma babu key a wajen ta,Anwar na haki ya isa inda take tsaye tana share hawayen ta wasu na zuba, duqawa ya d'anyi yace, " Yanzu meye na bamu wannan gwale-gwalen dan Allah, kullum sai fa na tafi gudu da asuba inna gama sallah, abin biyan bashi ya zama dan yau ban je ba ki sani gudu haka," Bata tab'a zaton ta yi kewar muryar shi haka ba sai da sautin muryar shi ya sauka a dodon kunnen ta, Wani irin kuka ne ya kub'uce mata mai nauyi a qirjin ta, ba makawa tsohuwar soyayyar Anwar ke neman yi mata dabaibayi a cikin lokaci ƙanƙani,tabbas tsohuwar soyayyar shi ke son d'aure mata jiki da ruhin ta, ba zata Iya jure wannan feelings d'in ba, abun ya mata nauyi sosai, ba ta San ta ya zata Iya fassara abun ba. Kamal ne ya iso, dauke da Fatee a hannun shi cikin haki ya ce, " Malam kai waye ka ke bin qanwata haka? Meye tsakanin ka da ita da zaka matsa mata, har kasa ta gudu haka a titi," Dan jimmm Kamal ya yi sannan ya ce "Ahhh Anwar dama Kai ne ke bin qanwa ta da sauri haka? Me ya faru?" Murmushi Anwar ya yi ya je gaban shi ya miqa masa hannu suka gaisa, Kamal na bin shi da kallon ina jiran amsar ka, " A zato na Hafsat ta Sanar da Kai ko ni wane ne a wajen Eamaan,koda yake bahaushe ya ce waqa a bakin mai ita ta fi dad'i ni ne zuciyar ta, kuma ita ce zuciya ta, shekarun da suka shud'e ne ta tafi da tawa zuciyar na zama ba zuciya a jikina,tinda da ace akwai zuciya a ƙirji na dana aje son ta na fuskanci rayuwa na samu kowacce kalar mace ce na aura wataqila nima Allah ya bani kamar wannan kyakkyawar yarinyar na haifa na aje na sa mata suna Eamaan in dinga kallo ina jin dad'i, amma ban samu dama ba, shine yanzu dana gan ta na biyo ta in ji dalilin tafiya da ta yi da zuciya ta, ta dawo Kuma bata neme ni dan ta dawo min da abata ba" Mamakin yanda Anwar ya zama me surutu haka ne ya cika Eamaan, Kalaman shi sun Sanya Kamal sassautowa, be tab'a zaton abokin shi Anwar ne Anwar d'in da Hafsat ke bashi labari ba, sake gaisawa suka yi, sannan Anwar ya ce, "Ka na magana da Anwar d'in Eamaan da yardar Allah" " Na ji dad'in cewar Kai ne Anwar d'in Eamaan, amma ni labarin Anwar d'in Eamaan  da aka bani bashi da magana Sam-Sam kamar ka" Dariya suka yi suka tafa,Eamaan kuwa ta gaji da tsayuwa, ta samu gefe ta rakub'e Allah-Allah take a bud'e gidan ta shige abunta dan bata da ta cewa a yanzu, bata jin ma ko ta buɗe baki akwai kalmar da zata iya fita mai ma'ana a bakin nata, Hafsat ta kula da hakan dan haka sai ta ce, "My dear Ina ga a bud'e gidan mu shiga mu zauna, dan kuwa yau mu na da babban baqo ko?" Cikin sauri Eamaan ta ce, "Da wa za a shiga gidan? Me zai je yi mana a cikin gidan?  ni gaskiya ka sallame shi anan kawai,ya tafi sai da safe" Kamal ne ya ce, "Eamaan kin manta na tab'a ce maki zan sama maki aiki a Wani asibiti? To ba asibin kowa bane face wannan bawan Allah'n, kin ga kenan na riga da na San shi ko ba dan ke ba ma ai zai Iya shiga gidan nan ko? Ballantana yanzu da na san cewar shine Anwar ɗin ki dole ne na ƙara ƙarfafa abotar mu." Tura baki ta yi gaba ta kauda kai gefe,sam ba za su gane halin da take ciki ba, ita kad'ai ta San ya take ji game da sake had'uwar ta da Anwar a halin bata da aure a yanzu. Hafsat na bud'e gate d'in  ta sa kai ta shige ciki ba tare da ta ce wa kowa komai ba, qasan zuciyar ta kuwa ba qaramin dad'i ta ji ba da Hafsat ta ce ya shiga, ko ba komai ta na Jin dad'in sake Jin muryar shi. Amma daga ganin shigar shi da yanda Anwar d'in ya koma, sai ta ke Jin Wani fad'uwar gaba, Anya Anwar zai sake kula ta da sunan soyayya kuwa? Ita d'in fa bazawara ce a yanzu,daga Kalaman shi na d'azu ta fahimci cewar be yi aure ba, anya Anwar zai aure ta a yanzu kuwa? Farin cikin me ta fara yi ne tin kafin taga ya rayuwa zata maida ita a yanzu bayan haɗuwar ta da masoyin ta na farko? Dole ta tsawatar wa zuciyar ta kar ta saka tsammanin samun abinda ba lallai ne ya zama nata ba, ko Anwar ya yarda zai aure ta bata jin Hajiyar shi zata yarda, duba da cewa a baya ma ba Wani son ta take da Anwar d'in ba sosai balle yanzu da ta zama bazawara. Daki ta shige ta rufe tana jin su suna ta hira,amo da sautin muryar shi na ratsa kunne da jikin ta, Hafsat ce ta shiga kitchen ta dakko masu kazar da Eamaan ta gasa kan su fita siyo pizza,sai kawai ta aje masu da plates da komai da zasu buqata,Juice din farar shinkafa da pineApple da Eamaan din ta hada nan ma ta dakko masu da cups ta aje ta koma d'akin Eamaan, kwankwasawa take tayi tana jin ta taqi budewa, daga qarshe komawa ta yi wajen su ta zauna,cikin murmushi Anwar yace, " Hafsy kar ki damu ai naga waje, zan ta zuwa yad'a manufata ina fatan ba zaku damu ba da yawan gani na da za ku na yi akai-akai ?tinda da can ba mu Maida hankali mun yi zumunci ba ai kunga yanzu se a fara" Dariya suka yi sannan suka tabbatar masa da  suna maraba da zuwan shi a kowanne lokaci, ya ji dad'in hakan nan take ya d'aga Fatee sama yana mata wasa yana murna yace, " ki ce ma Mum din ki ta tausayawa bawan Allah kin ji," Dariya take kamar ta san me yake nufi da hakan,shi ma biye mata ya yi suka dinga wasa su na dariya sauke ta ya yi bayan ya zaro kud'i ya baiwa Hafsat yace asai mata sweet,godiya suka yi mishi har Fatee d'in daga nan ya masu sallama da saqon a gaida mai zuciyar shi, ya fara taka wa zuwa waje, Hafsat kuwa ta ce, "Ai gashi zaka tafi baka ganta ba, inni ce kai tin da ban gan ta ba sai na ci abinda ta dafa," Hafsat na faɗan haka ya kalli girkin gaban shi ya kalle ta, alama ta masa da Ido na eh Eamaan ce ta dafa,komawa ya yi ya tsiyayi juice din a cup, kurb'a ya yi tare da lumshe ido ya sosa kunne, sai da ya shanye ya yi godiya ya tafi,tana jin tafiyar shi ta bude qofar ta leqo tana sand'a , ji take kamar ta ce masa kar ya tafi, bayan shi ta bi da kallo, Anwar ba dai tsafta da Iya d'ora hula ba, murmushi ne ya kwace mata, ta na tsaye ta na yaba takun shi da yanda ya riqe hannun Fateema ya na mata hira ta Jiyo taku alamun ana fitowa daga kitchen, Hafsat ta gani ta nufo ta fuska ba walwala, ai kuwa ta juya a guje ta koma ɗakin ta ta  danna qofar tana dariya, "Da ki bari na kama ki mana, yar rainin hankali kawai, ai kina sane da cewar dan ke yazo amma kika bar ni da bayani da surutu ko, zan kama ki ne ai, munafuka ana so ana kaiwa kasuwa, kar ki kuskura ki ce Zaki tsaya Wani abu wai shi Jan aji in ganganci ya sa ki ka tsaya shirmen nan Zaki sha mamaki yarinya, wataqila ya samu wata ya aura, tinda zai tabbatar Baki son shi ne kawai," Wata iriyar fad'uwa gaban Eamaan ya yi, ta hau girgiza Kai, ta na Kiran sunan Allah, tare da fatan Allah ya sa kar ya juya mata baya. Hafsat kuwa koma wa parlour ta yi suka je suka fara cin naman kazar  ita da mijin ta tace, "Mu cinye gobe ta gasa wani, Dan na tabbata yau ba zata Iya cin komai ba, ko Kuma in mun gama ka siyo mata pizza din ta ci in ta ji yunwa tinda dama pizza ta fi so, ka San Allah Habibi yau Eamaan ta ban haushi," "Mene na Jin haushin ta? Ni Kuma  ta min dai-dai, so kike daga zuwan shi bai fito yayi jawabi ba sai ta miqa kai? Ai ba haka ake yi ba, ku mata masu aji ne fa,  so kk ya ga tayi arha da yawa?" Gyad'a kai ta yi cikin fahimta,sannan tace, "Kuma fa haka ne Habibi,amma ni a gani na ita da Anwar ai ba wannan a tsakanin su, ka kuwa San yanda suka so junan su a baya? Na tabbata ko da aka aura mata Alhaji bata tab'a dena son shi ba, kawai BIYAYYAH ta yi ta hakura, saboda ita ta daban ce," "Kar ki damu, da yardar Allah wannan karon Eamaan ta Anwar ce" "Allah ya yarda" Abincin su suka ci suka sha lemon farar shinkafar su, sannan Hafsat ta ci gaba da bashi labarin soyayyar Eamaan da Anwar ya na jinjina biyayya irin ta Eamaan,a haka bacci ya fara d'aukar Hafsat, dama Fatee ta jima da yin baccin ta, dan haka sai ya ɗauki Fatee ya tashi Hafsat suka wuce d'aki. Sai da Eamaan ta tabbata sun tafi ta fita parlour ta zauna ta nad'e qafa kan kujera ta kunna kallo,Kamal ne ya fito riqe da Key d'in mota dan ya je siyo mata pizza, kallon shi ta yi ta sunkuyar da Kai qasa ta na murmushi, shi ma murmushin  ya yi ya wuce ta be ce komai ba. Se da ya siyo ya dawo ya miqa mata ne ya samu kujera me cin mutum d'aya ya zauna ya na fuskantar ta ya ce, "Eamaan yau dai na ga Anwar d'in ki Kuma aboki na, danni dai a nan garin na San shi, ban ma San shine  the same Anwar da ake ban labari ba,a iya d'an sanin da na yi masa na San Anwar mutumin kirki ne , Kuma gashi ya had'u ko ta ina, dan haka zan Baki shawara kar ki yi wasa da damar ki, ba safai ake samun irin soyayyar da Anwar yake miki ba a wajen maza, Anwar ya nuna shi masoyin ki ne na gaskiya, to ki daure ki zama masoyiyar shi ta gaskiya kema,Allah ya muku zab'in alkhairi, sai da safe" "Ameen na gode" Ta furta a hankali shi kuma ya shige d'aki ya barta ta na ci gaba da kallon ta, bayan tafiyar shi ne ta hau cin Pizza tare da korawa da lemon ta, can qasan ranta ta take hango murmushin Anwar da sautin muryar shi, zuciyar ta fari kwal kamar farar takadda. Ta na gamawa ta kashe ta shige d'akin ta ta yi brush tayi alwalar da take yi kullum kafin ta kwanta bacci, addu'ar bacci tayi ta shafa a jikin ta sannan ta  kwanta cike da tinanin shi a ranta. Tin daga ranar nan Anwar ya samu wajen zuwa, ga tsaraba da yake yowa Fatee na ci da na wasa duk zai je gidan, a nan yakan ci abincin dare da ya bar gidan sai ya je ya saiwa me gadin shi da me sharar shi a wani wajen, tinda yake zuwa basu taba hira da ita ba, dan ba ta bari su zauna a inuwa ɗaya ,da ta jishi zata miqe ta gudu ko ta yi shiru taqi magana,  abun na matuqar damun shi. Dan haka yau dai ya yi alqawarin sai ya sakata tayi masa magana,ko tana so ko bata so, dan ya san tana son shi she is just playing hard to get. Bayan ya  parker motar shi a waje ne ya kalli Kan shi a gilashin motar ya tabbata ya had'u,murmushi ya wa Kan shi sannan ya bud'e gate din gidan ya shiga bakin shi d'auke da sallama, a bakin qofar shiga cikin parlour ya tsaya ya na kwankwasawa tare da sallama, Hafsat ce ta bud'e masa ya shiga, daga tsayen suka fara gaisawa, shi Kuma ya dauki Fateema ya na d'aga ta sama suna dariya, Fatee na ganin shi, ta fara murna ta na fad'in Daddy , Anwar d'in ne ya ce tana ce masa Daddy,dan kuwa yana son yarinyar sosai. Sanda Eamaan ta ji ya na ce wa Fateema ta na Kiran shi Daddy ta ji dad'i amma Kuma ta ga rashin dacewar hakan, what if hasashen da suke be zama gaskiya ba,ai ai daga baya Yarinyar ta shiga damuwa. Eamaan ce ta fito domin mayar da plate ɗin da ta sha fruits kitchen sai satar kallon su take yi, suna bata sha'awa in ta gan su a tare,kallon Fateema yayi ya ce, " Babyna na zo yau zan maku sallama tin da Mummyn ki ba kula ni za ta yi ba ina ganin na hakura kawai, kar na takurawa zuciyar ta, duk abinda take so shi nake so, na hakura zani a daura auren nawa da waccan da  aka zaba min shekara da shekaru Ina qi, a yan zu na San Eamaan ta dena so na, ni Kuma ba zan takura mata ba har abada" Yanda yake maganar dole mutum ya zata da gaske yake yi, zaro ido Eamaan ta yi sai gata gaban shi kamar ta riqe shi take ji, cikin narkakkiyar murya kamar ta me son yin kuka ta ce, "Please Anwar don't go, Kai ma ka San abinda ka ke fad'i ba haka bane, pls don't marry anyone while i am here beside you, Ina gudun kar na sake shiga halin da na shiga ne a baya akan soyayyar ka,bana so na saki jiki a raba mu." Eamaan ta qarasa maganar ta cike da zubda hawaye, Anwar ji ya yi kamar Allah ya gama amsa masa addu'o'in shi gaba d'aya dan kuwa Yana da yaqinin Eamaan na son shi , amma sai ya saka fuskar tausayi ya ce, "To Eamaan me yasa kika ƙi kula ni all this while, baki ma son ganina, na zama kamar dodo a gare ki," Kwalla ce ta taru a cikin idanun shi,Hafsat na ganin haka ta ja hannun mijin ta suka shige ciki,suna shiga ya k'wace hannun shi yace, "Ke malama da kin bar mu mun ga soyayya, " "Zo na baka soyayya bar su su yi tasu ta yaushe gamo"   Kama qugun ta ya yi suka haye gado suna dariya. Eamaan da hawaye ya wanke wa fuska ce tace, "Na qi kula ka ne sabida bana son karya zuciyoyin mu a karo na biyu, ka sani zai wahala Hajiya ta bari ka aure ni, tinda tin fil'azal ita ɗaya ce bata son tarayyar mu a baya, hakan ne ya bawa Daddy kwarin guiwar aura min Alhaji ko ka manta ne?  Ina sane da yanda ta dinga murna ta nuna Maka illar soyayya da ni,na samu labarai kala-kala akan yanda ta so ka yi aure Kai Kuma ka qi, ka na ganin yanzu zata amince ka aure ni ne?" Kad'a kai ya yi alamar bai manta ba, " To ka gani, so ka ke sai munje mun shaqu fiye da da muzo rabuwa ta mana wahala? Wannan shi ne dalilin qin kula ka da bana yi, amma ni ba dan bana son ka bane," Ta Kai qarshen maganar ta cike da jin nauyin Kalaman ta, zaunawa suka yi a tare suna ta tattauna matsalar da suke hasashe da yanda zasu yi maganin ta, ba tare da sun kula da lokaci ya ja ba, Kamal ne ya fito ya na hamma ya ce, "Akaramakallahu yau ko a rufe qofar da Kai ne?" Kallon agogon bango suka yi a tare sha biyu saura tayi, da sauri Anwar ya miqe yayi musu sallama ya tafi gida da alqawarin zai dawo washegari su qarasa magana. Raka shi Kamal ya yi daga nan ya rufe gidan ya dawo sai ya tarar ba kowa a parlour, yau Fateema da Eamaan zata kwana, dan dama ita tana ganin  yarinyar na takura musu, su kuwa tsabar yanda suke son ta ne ya sa suke kwana da ita. A daren ranar Eamaan da Anwar sun yi bacci Mai dad'i cike da mafarkai kala kala. washe gari............. [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼  BIYAYYAH.  💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 23: Da sassafe ya shirya dan  zuwa kano, ya matsu ya ga manyan shi dan su shiga maganar auren su da Eamaan, a bari ya huce shi ke kawo rabon Wani in ji bahaushe, sanyin jiki da Jan jikin shi na daga abinda ya ja masa rasa Eamaan a baya,wannan karon kuwa ba zai yi qasa a guiwa ba wajen gabatar da Kan shi da wuri. Bayan ya gama shirin tafiyar shine tsaf, ya dakko jakar shi da zai tafiya da ita ya saka a mota, ya na so ya fara biya wa ta asibiti ya duba marasa lafiyan da ya yi wa aiki shekaran jiya ka fin ya wuce,asibitin shi na da kwararrun likitocin da ko baya nan za su kula da komai magana  ya yi ma Baba mai gadi da mai share share akan su kula da gida, ya musu  sallama tare da damqa masu kud'i a hannun su ko da zasu buqaci Wani abun baya nan, Anwar mutum ne Mai tausayi da kyautayi, ba ruwan shi da Yana biyan su albashi kullum cikin kulawa da su yake baya gajiya. Direct gidan su Hafsat yaje ya tsaya a waje ya yi ma Kamal waya,ya sanar da shi abinda yake shirin yi, Kamal kuwa sai ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari,tare da qarfafa masa guiwa, sannan yace ya shigo su gaisa da Eamaan mana kafin ya wuce, shiga cikin gidan yayi ya jira Kamal ya bud'e masa qofar parlour ya shiga da sallama. Hafsat ce ta fito sanye da babban Hijab, dan cikin ta ya fara girma ba laifi, gaisawa suka yi ta wuce dakin Eamaan dan Kiran ta, karo suka yi a hanya ta miqe hannayen ta ta na miqa, dan ta gama sakankancewa Kamal ya fita tinda takwas ta gota, Anwar dake hango Eamaan da ke miqa wani yawu ya hadiya ya kyafta kyafta idanu, da  saurin  ya dauke idon shi saboda rashin ganin dacewar qura mata Ido da ya yi, a zuciyar shi ya hau istighfar, can shaid'an ya sake bijiro masa da kyawun surar ta, numfashi ya ja ya na tunanin wa zai ga wannan yace ta taba aure ballantana ma a ce har ta Kai ga haihu? Allah mai halitta kenan ,hannu ta d'aga ta daure gashin ta tana kallon Hafsat dake Jan hannun ta dan su koma ciki, ja ta yi ta tsaya sannan ta ce, "ke malama, kamal bai tafi ba fa har yanzu, yau ya makara kin dai gane ai, kuma Anwar ma na palour ya na jiran ki, Allah ya taimake ki kamal na d'aki be gan ki ba, amma dai wataqila Anwar ya ga amaryar shi cikin night wear kafin aureeee" Turo baki ta yi cike da shagwab'a tace, "Me yasa ba ki faɗan duk waɗannan bayanan ba ki na hango ni se da na gama dik Wani shirme ya ganni, sannan shi mijin naki  me ya hana shi tafiya Office da wuri yau,  kuma shi Anwar d'in me ya kawo shi da wuri qarfe takwas gidan mutane?" Dariya sosai Hafsat ta yi ta tura Eamaan toilet dan bata da lokacin amsa tambayoyin ta dika, ta dakko mata kayan da zata saka kan ta fito,Jiranta ta yi dan ta taya ta shiryawa da hanzari, nan tana fitowa kuwa ta saka kayan ta Hafsat ta gyara mata gashin ta tayi kyau sosai, sai tashin sassanyan qamshi take in ba ka matsa kusa sosai da ita oba ba zaka ji ba,( Saboda har yanzu shi din ba muharramin ta bane, dan haka ba zata sake ta saka tirare mai qamshi sosai da zai ja masu fitina ba, musamman yanda suke son juna tirare zai Iya kunna masu wutar fitina a tsakanin su, gare ku mata masu zuwa zance wajen masoya a ci turare Eamaan na magana) yana ganin ta a zuciyar shi yace, ' Yah Allah she is so beuatiful, ko wace shiga ta yi kyau take yi mata' Sai da ta sake maimaita sallamar ta  da qarfi tare da dan dukan table ɗin gaban shi sannan ya dawo daga kallon ta, ɗan murguda baki ta yi kaɗan ta ce, " kallon fa?" Shi Kuma ya ce, " kyawun fa?" Dariya suka yi a tare, sannan ya zama  serious ya ce, "Da gaske nake  kyawun ki ne ya sa na kasa sanin kin iso gare ni har na shagala da kallon ki," kunya ce ta kama ta, ta dan yi murmushi ta ce, "To naji sarkin tsokana kana nan da halin ka ko? Me ke faruwa ne na gan ka da sassafe haka?" Gyara zaman shi yayi sannan yace, " Babu tsokana a tsakanin mu indai ta wajen fad'an gaskiya ne, Eamaan ke me kyau ce, kyan ki na d'aukan Ido Kuma ya na sanyaya zuciya, Allah ya qara kyautata halayen ki su ninka kyawun fuska da jikin ki." Ta ji dad'in Kalaman shi sosai, murmushi kawai tayi bata ce komai ba ya ci gaba da magana, "Ammm abu na gaba shine dama na zo na ne na shaida maki zani Kano dan sanar da magabatan mu batun sake qulla alaqar soyayya a tsakanin mu, Wanda muke fatan ya Kai mu ga aure, tinda kin ga yanzu mu ba yara bane,mun mallaki hankalin mu, kar mu yi shiriritar jinkiri Wani abu ya gifta a tsakani, kar mu zo ina baya-baya wani ya shigen a sake maimaita abinda ya faru ao baya, a toh dan wannan karon sai dai ai yaqin duniya na uku ba yarda zan yi ba ehe," Ya fada cike da abun dariya, sai kace qaramin yaro, dariya ta yi sosai tace, "kai ko, Allah ya bada sa'a ya san ya mana albarka a tarayyar mu,"   cikin murna yace, "kin amince kenan na je neman auren ki da yawun ki? " " sosai ma,na amince" Ta fada tana rufe fuska, miqewa yayi dai-dai Hafsat ta fito dauke da plate da kayan karyawa akai, " A'aa ina kuma zaka je baka karya ba," "Inaaa ai ni yanzu na ma fasa biyawa asibitin waya zan kawai su duban mara lafiyar nan, ba zan zame ko Ina ba Daga nan sai Kano, an ban damar zuwa neman aure ai ban ga ta zama ba," Eamaan ce ta miqe ta je kusa da shi ta dan shagwab'e fuska ta ce, "Yanzu tafiya za ka yi bamu ci abinci ba, da ni fa zamu karya ko baka son cin abinci da ni?" Ta qarasa maganar ta tana kallon shi, ai bai san sanda ya zauna ba ya karb'i babban tray din hannun Hafsat ya na mata godiya ya dire a gaban Eamaan ya na bin ta da kallo fuskar shi cike da annuri, bude plate din gaban shi ya yi, soyayyan kwai ne da chips, sai miyar hanta, da taji kayan lambu, ga tea a flask mai kayan qamshi, zuba masa tea Eamaan ta yi tace ya fara ci bari ta had'o nata Tea din, dan bata shan wannan irin me Madara, in ta dawo bai fara ba ta fasa ci da shi, yana jin haka ya gane so take yaci kawai, amma dama ba tare zasu ci ba, nan take ya yi murmushi dan a koda yaushe yana alfahari da Eamaan din shi, sai da ya gama tass ta dawo,zata kwanukan yace mata, " Ina Fatee na? Ko bacci take ne," "Ban sani ba gaskiya, dan ba dani take kwana ba," Kamal ne ya fito cikin shirin fita shima dauke da Fatee a hannun shi ko nauyin ta baya ji, Hafsat Kuma na  ɗauke da jakar shi kamar kullum, tana ganin Anwar ta hau tsalle-tsalle a jikin Kamal tana faɗin, " Daddy, Daddy oyoyoooo," Tana ta dariya shima cikin so da qaunar yarinyar ya isa ya karɓe ta, an mata wanka sai qamshi take yi, wannan aikin Kamal ne wato feshe ta da turare, da an mata wanka an shirya ta in zai saka tirare itama sai ya feshe ta da shi, har waje suka kai su, Kamal ya bawa Hafsat kiss kad'an a lips d'in ta, Anwar na gani ya radawa Eamaan a kunne, "Kinga gani ko, kin ga yanda ake yi in miji zai fita ko? Haka za mu dinga yi bayan mun yi aure, ni fa su Hafsat na bala'in burge ni,ko dayake muma nan da wasu 'yan watanni zamu fara irin nasu, ko dake namu ma sai yafi nasu ko," Kallon shi ta yi tare da qanqance ido,fuskar ta kuma na dauke da murmushi, dauke kai ya yi alamar yaji tsoron wannan kallon ya miqa mata Fatee wadda ta fara kuka saboda bata son su rabu, lallashin ta ya yi da sweets, ya mata wayo ya tafi, dik da haka sai da ta yi ta kuka sosai kafin ta hakura, addu'a Eamaan ta masa akan Allah ya kiyaye ya Kai shi lafiya ya dawo da shi lafiya,ta d'aga masa  hannu ya tafi, gida suka koma dikan su kowacce na kewar masoyin ta. ****************************** " Ni fa Iya aure zan yi, sai ke ki koma wancan d'akin na saka amaryar anan," "Dan qwal uban ka ni zan koma wancan dan tsukukun d'akin daga gani ma kiwon wani abun akai a ciki, dan kai tantiri ne ko baka san matsayin uwa a wajen ka ba ko?k.8" Sosa qeya ya yi ya gyara tsayuwar shi sannan  ya ce , "Ni fa Iya iya adalcin da zan miki kenan, ai dai gadon ki kin cinye shi a yan kwanakin nan, sannan ni aure zanyi na gaji da bin ƙadangarun bariki, yanzu ke bama zaki min murna ba kenan zan aure na bar yawon bariki" "Yaro duniya ce ka je ta ishe ka riga da wando, sai kai auren ai,ni ba zan hana ka ba, Amma ta ya za a ce ka Maida ni wancan d'akin kamar akurki kai da matar ka ku dawo nan?" Majina ta sharb'a alamun kuka ya zo mata, ta tattaka a hankali ta shiga d'akin ta hau  kwashe yan tarkacen ta tana sharar kwalla,tinawa da Alhaji da ta yi ya sa ta zauna ta saka kuka mai cin rai, shi da ko girki bai yadda ta yi da kan ta ba, miqo d'akko ma na yau da gobe sai da ya aje mata masu yi, matar shi ma sai da ta maida ita mai aiki a gidan mijin ta. A haka ta gama tattare komai ta je ta share d'akin da zata koma da zama Wanda da Gani kiwon tattabaru ko kaji akai a ciki, ba wata  iska Dake ratsawa sosai, haka dai ta tsara kayan ta ciki ta ja qofar ta ciki ta rufe, Bata sake fitowa ba sabida bacin ran Sahabee. Shi kuwa fita ya yi yaje wajen budurewar shi ya sanar da ita komai ya yi normal kamar yanda take so, murna suka dinga yi ta na qara masa pampo akan yanda zai kawar da Iya gefe su sha soyayyar su bayan aure, shi Kuma sokon ya na biye mata kamar be tab'a sanin mace ba se akan ta zai fara. Wata qwanqwararriyar yar bariki ya samo, ta gama barikin ta gida an ce ta fidda miji, kaf maneman nata sun San ita wace ce sosai dan haka sai suka gudu,Sahabee ne ya je sama  ta ka zai soyayya da ita, ta kuwa zage suke Shan soyayya dan tin Kan auren ma ba za a Iya qirga sau nawa su na keb'ewa ba,ko yanzun ma da ya kawo mata wannan labarin me dad'i se da suka  sheqe ayar su son ran su, a kwanaki goma cif cif  akai aure ba istibra'i ba komai aka kawo amarya ta tare a gida d'aya da Iya. Daren ranar Iya ta yi kwanan takaici ,kuka sosai ta sha ta tina sanda take Kiran Eamaan da jarababbiya dan ta ji ta na waya akan  had'in maganin mata da ake da rake da kaninfari da citta, ashe yau ne zata ji jarabar iyakar Jin ta kuwa dan kuwa komai akan kunne ta suke yin shi, amarya babu sirri ta na sane ta ke duk abinda take yi dan Iya taji, Wanda ban San ribar da zata ci ba tinda Iya dai ba kishiyar ta bace uwar miji ce. Wani ihu da ta zabga kuwa se da Iya ta toshe kunnen ta, nan take wani irin nauyi da kunya suka lullube ta,ita kuwa Amarya se sambatu take tana surutai na rashin d'a'a wanda tasan dole surukar ta ta zata ji, shikuwa Sahabee sai fadi yake yana kumawa "Ashe abun nan na aure ya fi daɗi ban sani ba nai ta yawo a titi ban aure da wuri ba? Oda na sani na yi aure tin Ina da sauran qurciya ta, wayyooo Iya kin cuce ni da baki min aure da wuri ba" (niko nace dan ma baku bi yanda tsarin ya ke ba da kun fi morewa) Salati Iya ta zabga ta miqe tsaye Dan zuwa ta buga musu qofa, ko ba su yi shiru dan ita ba, su duba maqota mana, Wani ihu da Sahabee ya saki tare da amaryar shi ne ya Maida ta ta yi zaman 'yan bori ta na zubar da hawaye, lallai kuwa za su yi ajalin ta nan kusa in dai haka rayuwar gidan za ta kasance ...... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼      BIYAYYAH.  💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 24: Anwar ya isa kano bayan azahar, direct unguwar su ya nufa cike da d'oki, sai dai bai san me yasa gaban shi ke ta fad'uwa ba, addu'a ya fara yi akan Allah ya kare shi daga dikkan abun qi ya tabbatar musu da alkhairi, ta gaban gidan su Eamaan ya wuce, aran shi yana ayyana nan da yan kwanaki za a daura auren su da Eamaan din shi anan, Wani qayataccen murmushi ya saki, ya tarar da  mai gadin gidan nasu a qofar gate din gidan tare da abokan shi ya na ta hira,hango motar Anwar ne ya Sanya shi sheqawa a guje dan bud'e gate d'in, sallama ya wa abokan Mai gadin nasu sannan ya danna hancin motar shi compound din gidan su Mai d'auke da motoci kala-kala,daga inda yayi parking d'in motar shi ya na iya hango mahaifiyar shi dake cikin lambun gidan tana ta kaiwa da komowa hannayen ta hard'e a bayan ta cike da isa,da dikkan alama tana cikin wani yanayi ne na damuwa, fuskar ta sam babu walwala a cikin ta kamar kullum, tayi nisa sosai a cikin tinanin da ta ke yi shi yasa bata San shigar Anwar d'in gidan ba ma. Bude motar shi ya  yi sannan ya fita  tare da zagayawa ya  bude bayan motar ya ɗauki ledojin da ya tsaya a hanya ya yo tsaraba ya fara takawa zuwa ga mahaifiyar shi da suke Kira da Hajiyah, yana isa ta d'ago kan ta ta kalle shi tare da murmusawa kaɗan,sannan ta ce, " Sannu da zuwa mutanen bauchi qaya baku san na gida ba," Murmushi Shima ya mayar mata sannan ya ce, " Barka da hutawa Hajiya ta,akwai abinda ke damun ki ne? Na ga kin yi nisa cikin tinanin da kike yi har na shigo baki sani ba," Kama hannun shi ta yi suka fara takawa cikin gidan, " Muje ciki kai wanka ka ci abinci ka huta zamu yi magana mai mahimmanci da kai," 'Daga mata kai ya yi alamar to, amma zuciyar shi sai bugawa take da dikkan alamu abinda za su yi magana akai Mai mahimmanci ne, tinda Hajiyah ta gama nuna hakan a fuskar shi, bayan sun shiga ne ya kammala komai, ya kwanta da niyyar ya dan samu bacci, amma inaaa baccin nan ba zai samu ba, tabbas sai yaji me ke damun Hajiyan shi haka? Tashi yai ya saka qananan kaya marasa nauyi ya fesa tirare ya saka takalmin shi ya fita. A daki ya same ta tana kwance kamar mai bacci amma idon ta biyu, sallama ya yi ta tashi zaune tare da  amsa masa sallamar shi, nuna masa kusa da ita ta yi alamar ya zauna, zama ya yi yana fuskantar ta, ta shafa kan shi tare da murmusawa tace, "Anwar in baka yi wasa ba zaka zama babban tuzuru a layin nan, rashin auren ka na damun mu matiqa ni da Abban ku,shin wai yaushe ne za ka yi aure? Ka sani kai d'aya ne Wanda muke  da shi, ga shi girma ya fara kama mu ba kai aure ba balle mu sa ran samun zuri' daga wajen ka,bama ka da niyyar aure Anwar why? Yarinyar da ka kwallafawa rai ta yi aure mijin ya mutu,zawarci take yi yanzu, kaga ba sa'ar auren ka bace ita sai ka nemi wata, amma Anwar 8inaa ka qi sam, ko an nemo maka sai ka ce basu yi maka ba, ya kake8 so na yi ne Anwar," Ta qarasa maganar ta cikin damuwa sosai, Anwar ya fita shiga damuwa musamman da yaji tana neman condaming auren na su tin kafin ya fad'i me ya kawo shi, zufa kawai yake yi,a hankali ya saka hannu ya share, kallon shi ta yi cikin kulawa ta ce, " Son me ke faruwa ne na ga ka shiga halin damuwa? Ko na faɗi wani abu daya d'aga maka hankali ne haka," " Kwarai kuwa Hajiya ta,domin kuwa yanzu haka har mun daidaita da Eamaan akan maganar auren mu,kuma ta amince da ni nima na amince da ita, yayun ta dika sun yarda na faɗa wa magabatan na wato na fada maku a nemar min auren Eamaan, Hajiya na rasa ta a baya ba....." "Haka wannan karon ma zaka sake rasa ta, wai Kai Anwar wanne irin yaro ne Kai mai kafiya da naci? Ba ka ganin yanda mahaifiyar ta ta mallake mahaifin ta se abinda ta ce, so ka ke Ina zaune wata ta zo ta dinga juya ka se yanda ta yi da Kai ni na sha wahalar banza kenan? Ba zai Yu ba to! can gidan ma da ta bari Ina da labari har mijin ya rasu ita ke juya gidan,me ka ke tunanin zai faru anan gidan in ka aure ta?" Cike da fushi ta miqe tana fad'an hakan,a hankali Anwar yace, " Hajiya ban gane me kike faɗa ba, ina son Eamaan ke shaida ce, ban da macen da zan zauna da ita zaman aure ban cutar da ita ba saboda ba zan iya mata adalci ba tinda bana son ta,iin kk ce ba zan aure ta ba a karo na biyu, na rantse sai dai na zauna ban da aure har abada, don kuwa kowa zaku auran ba zan taba zama da itaba har abada,kai gida daya ma ba zan zauna da ita ba," Idon shi ya yi jawur saboda damuwa yake maganar da bai taɓa yi wa mahaifiyar shi irin ta ba,cike da mamakin maganganun Anwar Hajiya ke kallon shi, lallai Eamaan ta yi nasara, tin kafin ya aure ta ma ta fara juya mata Kan yaro to Ina ga ya aure ta? Anwar da ko kallon-kallo na rashin kunya be tab'a had'a ta da shi ba shi ne ke mayar mata da magana haka, cikin damuwa ta ce " Anwar ni nake fada kake faɗa, akan mace? Lallai dole ne na haramta maka auren yarinyar nan, domin bana jin zai haifar da d'a mai ido a gare mu dika anan gaba," Cikin fushi idon shi ya gama rufe wa da hawaye da jimanta wa zuciyar shi baƙin cikin kalaman Hajiya ya dau hanyar fita Daga d'akin nata, ko gaban shi baya gani saboda tsabar damuwa me Hajiyah ke so daga wajen shi ne wai ? wace iriyar biyayya ce baya yi musu, wasu ma koya musu yanda za su bi iyayen su yake yi balle shi, bai tab'a masu musu ba tinda ya girma ya San matsayin iyaye a wajen d'a,me yasa Hajiyah ke so ta rusa masa farin cikin shi,wannan karon zai tsaya tsayin daka dan ganin ba a raba shi da Eamaan d'in shi ba, Luuu yayi ya fara tafiya qasa sakamakon wani jiri da ya ɗebe shi, ji kake timm ya faɗi qasa, da gudu ta nufe shi, ta na k'walla masa kira tana jijji shi, amma inaaa ya suma be San ma ta na Yi ba, hawaye ta Gani ya na gangarewa ta gefen idon shi, da gudu ta fita waje dan neman taimako,kicibus sukai da Abban shi ya gan ta a gigice, kama kafadun ta ya yi,tana ganin shi ta qanqame shi ta na nuna masa hanyar d'akin ta,da hanzari ya janye ta ya nufi d'akin nata ta bishi a baya, yana shiga yaga gudan jinin shi yashe a qasa, hankali tashe ya d'aga shi, ya kwantar a gadon, Number ɗin likitan su ya danna yayi masa bayanin halin da ya tsinci  Anwar a ciki, likita cewa ya yi su kai shi asibiti kawai. Waje ya je ya samo matasa biyu suka ɗauke shi su ka nufi mota da shi suka saka a ciki, Abban shi da Kan shi ya ja mota suka yi asibiti, suna zuwa aka bashi gado, likita ne ya shiga duba shi da kyar ya samu nunfashin shi ya daidaita ya dawo hayyacin shi, allurar bacci suka masa ya samu bacci, a dan wannan tazarar ko wanda bai san shi ba ya kalle shi ya san yana cikin damuwa, saboda yanda fuskar shi ta koma, "Fada min me ki kayi masa? Kin nuna masa qiyayya akan Eamaan ko kamar yanda kika saba ko? Kin sanar da shi mummunar a qidar ki mara tushe da madafa akan yarinya Mai nutsuwa da kamun Kai tare da BIYAYYAH kamar Eamaan ko? Ke wai me yasa kike da qaramar ƙwaƙwalwa ne watarana? ko mai aka fad'a maki baki d'auka, ko nace kina da son kan ki, in ba son kai ba in kin manta bari na tina maki, Mubaraka qanwar ki, ba a bazawara kuka aurawa saurayi ba wata hud'u da suka wuce, wato ke kece mai d'a ba zaki bar d'an ki ya auri bazawara ba, tinda su ba su da gata ko wata cutar ce a jikin su, ko kuma wani mummunan d'abi'u ne da su da yayi fice, to in wannan kike hangowa da baku ba d'an uwana ya auri qanwar ki ba, mai shegen son kan tsiya,for ur information Hajiya d'azu-d'azu muka gama magana da mahaifin yarinyar akan had'a auren su, tinda ke baki da tarihin Annabin rahama akan ki, waya fara aure a rayuwar shi ne? Bazawara ce Nana Khadeejah mai yara,wadda ba aure ɗaya ma tayi ba kafin auren Annabi ,sannan ta girme shi ma ita,  kuma sun yi zaman da yake yabon ta har saida ya koma ga Allah,sannan ta haifa masa Yara Mafiya daraja a duniya da lahira, to shi Anwar wane ne shi? Wa ya fi da ba zai auri bazawara ba, musamman ma da shi ya kawo ta ya ce ya na so, Anwar ya kuma girmi  yarinyar nan ya bata shekaru d'ai-d'ai har bakwai, sannan ke da kan ki kk yabon halayen ta a baya dik da kina ƙin ta,amma yanzu kike son ki rufe idanun ki dan son zuciya ki ce ba haka ba, to bari ki ji aure babu fashi idan ki ka sake nuna masa qiyayyar auren nan zai zama a bakin naki auren, sannan in Wani abu mummuna ya samu yaro na ko....." Bai qarasa maganar shi ba ya zuba mata Wani mugun kallo ya kade rigar shi ya fice daga asibitin gaba d'aya, ta gama bata ran shi, ai ta magana d'aya amma bata gane komai? Zuciyar ta ta matuqar raunana, musamman na ganin gudan d'an nata a kwance kamar matacce,sai a lokacin ta gane ashe ma ran gaba d'aya shi ba abakin komai yake ba, da mutuwa ya yi da itama mutuwar za ta yi ai tin da ita ce sanadi , hawayen ta ta share ta goge majina da tissue, ta qura masa ido, a nan suka kwan, mai aikin su ta kawo masu abinci, da kayan Tea, Abban shi na son ya dawo amma so yake ya koya mata hankali, ya fita sha'anin ta, dan ya sani zasu wahala saboda ya San in ta shiga damuwa ta na tsananin buqatar tallafin shi, Dan haka dole ya nuna mata kuren ta musamman in bata yarda da maganar auren  ba har yanzu. ************ " Subhanallahi me ya same shi? "OK to shikenan, yanda kace hakan za ai," "Ba damuwa, zuwa goben sai a daura ɗin, Allah ya bashi lafiya, yau zamu zo duba shi da yardar Allah" Aje wayar Daddyn Eamaan ya yi, ya Maida  kallon shi ga matan shi da ke zaune gefen shi suna magana akan auren Eamaan d'in da Anwar. Bayanin Kiran da mahaifin Anwar ya Masa yanzu yayi musu suma, sun jimanta rashin lafiyar da yake sannan suka yi fatan Allah ya Sanya alkhairi da albarka a cikin auren,sun yanke cewar da an yi sallar magrib za su je duba shi,Amma tace ita kam sai dai a tafi da Mama ita za ta yi wasu abubuwan in basa nan, kuma ai ba a bar gida shiru ba sai masu aiki kawai, murmushi suka yi dan sun gano ta, Daddy ne yace, "To fullo ba komai munje da yayar taki Allah ya kaimu," Dariya suka yi dikkkan su, ita kuma kunya ta qara kama ta, dan tana tsananin son d'iyar ta ta, ga shi Allah ya had'a ta da abokiyar zaman da sai dai sabanin harshe da haqori amma Mama ba ta da matsala ta ja girman ta sosai, ita kuma tana bata girman nata,bar Mama dai  da son bin ra'ayin ta, bata yarda a yanke mata hukunci ba tare da an yi shawara da ita ba, ko Kuma ta yi niyyar abun, a wannan kam za a buga da ita sosai. Washe gari da misalin sha d'aya na safe aka daura auren Anwar da Eamaan, kan sadaki dubu hamsin, wanda Abban shi ya so su bada d'ari, Daddy ya qi,yace albarkar suke nema ba yawan ba,lokacin da labari ya iske Anwar tini ya ware ya miqe daga gadon asibitin ya na qoqarin cire qarin ruwan da aka masa,tangararau ya ke tafiya kamar ba shi ne ya sha jinyar love ba,har office ya Sami  likitan ya matsa Masa a sallame shi shi ya ji sauqi, likita ya shaida ya ji sauqin tinda ga shi tsaye rasss,dan haka ba shi da zab'in da ya wuce na ya sallame shi. Tinda suka koma gida Hajiyan shi ta kasa gane Kan shi Dan ko fara'a yake daya ga Hajiyar shi sai fuskar shi ta canja zuwa ba yabo ba fallasa, abun na matuqar damun ta, Abban shi ya tsime shima ya dauke mata wuta,ta rasa inda zata je ta ji dad'i a wajen su, gashi ta nuna musu ita fa ta sakko ta bi Allah ta bi mijin ta da abinda d'an ta ke so. Eamaan ke zaune sai juya cokali take a abinci tana murmusawa, ita d'aya,sabuwar wayar ta na gefe wadda Kamal ya sai mata a  jiya, Hafsat ce ta zauna gefen ta tare da dafa ta ta ce, "Wai ke albishir aka maki da makka ne kk ta murmushi haka? Kin ma qi taba abincin ki a bakin ki sai juya cokali kk, meke faruwa ban San da shi ba, ban labari na sha dear sis," Murmushin ta ne ya fad'ad'a, "Ban san me ke damuna ba Hafsy, kawai ji na nake ina cike da nishadi, tinda na sa qafa na sauka a gado, da  farko dai daren jiya cikin damuwar wani abun da ban san meye ba na kwana, amma yanzu zuciyata cike take da farin ciki kamar ance an mallaka min Anwar," Ta qarasa tare da dafe bakin ta lokacin da ta ji qarar takalmin Kamal na zuwa wajen su, qara gyara mayafin ta ta yi ta rufe jikin ta sosai, tana murmushi, "Kin ji da gulmar ki an jima shi zaki ta yi wa wannan rashin kunyar taki ai," "Albishirin ku, ko dake Eamaan albishir, me zaki ban inna fad'a maki wannan kyakkyawan labarin," Zaro ido ta yi waje cikin wata iriyar  murna kamar ta san me zai ce mata, " Yah Kamal sai abinda kk so zan baka," " kin tabbata?" " Eh na tabbata," "Ok dazu da misalin sha d'aya aka daura auren Anwar da Eamaannnnnn" Ya qarasa maganar shi cikin d'aga murya yana farin ciki,sai kama hannun Hafsat yana juya ta yana kallon Eamaan suna dariya, Idon ta ya cika da hawaye murmushi ɗauke a fuskar ta,daga  baya kawai se suka ga ta fashe da kuka ta miƙe zata bar wajen.......... [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH.   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 25: Kukan murna Eamaan ta yi sosai kan ta ɗago da idanun ta da suka sauya kala daga farare tas zuwa launin ja, haqoran ta farare wanda suke a jere ɗauke da siririyar hushirya sai haskawa suke, Hafsat da ta matsa kusa da ita tana shafa bayan ta da sigar lallashi ta kalla, itama murmushin ta sakar mata Fatee kuwa na ta kallon ta da mamakin dalilin kukan nata, Eamaan ce ta ce, " Yah kamal me kake so a matsayin goron albishir d'in da ka min yanzu?" " Ba abinda nake so illa kafin nan kafin ki tafi ki koya ma Hafsat duk girke-girke  da kike yi mana masu dad'i, sannan kuma a bar mana Fatee har tsawon lokacin da kuka gama cin amarcin ku sannan ku karɓe ta, ke in ma Anwar ba zai d'auke ta ba ni nayi tayin riqe Fateema har abada a matsayin ta ƴata" Farin ciki ne ya qara sanya ta kuka sosai mai cike da murmushi, lallai Yah Kamal na son Hafsat sosai, dan ta kula yana taya Hafsat son duk abin da take so, ko baya son abun nan indai ta na so to fa Shima abun nan ya zama abin son shi,lokuta da dama shi da Eamaan sukan zauna su yi ta gulmar Hafsat d'in, su Kan yi magana da Eamaan akan shi fa baya son kaza a da amma tinda ya kula Hafsat na so ya ji ya fara son abun. " Yah Kamal kome kake so zan yi maka,kai daga yau ma zan fara inshaa Allah, game da Fatee kuma shi fa Anwar cewa ya yi da ita za mu tare duk sanda Allah ya sa muka yi aure, amma dole zan lallab'a shi mu barta ko wata biyu muka yi an maida ta yanda dai ya amince," Kamal ne ya kalli Hafsat da farin ciki ya bayyana a fuskar ta ya matsa jikin ta ya dora kan ta a gefen jikin shi dan itan tana zaune a hannun kujera ne kusa da Eamaan da ke kukan farin ciki sannan yayi kissing goshin ta, a tare suka yiwa Eamaan godiya tare da fatan Allah yasa Anwar ya bar musu Fateema su riƙe ta na tsawon lokaci. ************************** Anwar na qara murmurewa ya sa aka je gidan shi sabo aka gyara shi fes, dan ba abinda bai zuba ba na more rayuwa dai-dai qarfin shi, komai yayi masa yanda yake son shi, gidan na ɗauke da d'aki hud'u ne sai palour biyu, dinning area ɗaya, kowanne d'aki da toilet ɗin shi, sai Kuma toilet guda d'aya a harabar gidan, gidan ya na da  farfajiya mai girman da zata Iya d'aukan a qalla mota uku, a can bayan gidan Kuma ya yi dan garden me d'auke da kayan wasa na yara wanda manya ma zasu iya hawa lillunan wajen, gidan yayi matuƙar haɗuwa gwanin sha'awa,yana tafe ya na kallon  yanda aka tsara gidan ne ya ji qarar saqo a wayar shi, daya duba sai yaga No Kamal ne ta turo mai wata Number waya a qasa an  rubuta *Ur sweetheart No* wani dad'i ne ya kama shi, dan dama yana son ya aika kuɗi yace kamal ya sai mata waya mai kyau amma da alama Kamal d'in ya riga shi, shi kuwa me zai yi ya biya Kamal kyautatawar da yake yi masa, saving ya yi da 'My one' ai ko yana gamawa ya shiga ɗaya daga cikin palourn ya qame a kujera ya danna kiran layin na ta, Eamaan na can na ta faman koyawa Hafsat girki ta ji wayar ta na ringing wanke hannun ta tayi ta d'aga tare da yin sallama a zuciyar ta tana mamakin waye wannan da ya samu No ta sabuwa haka? Iya sanin ta ba kowa ne yasan tana da waya ba. Ajiyar zuciyar da ya sauke ne da ƙarfi ya sanya ta dafe jikin cabinet na kitchen ɗin ta jingina dashi tana murmushi mai sauti, Hafsat na ganin haka ta daki kafadar ta ta ce, "Sarakan soyayya bari na kwab'a na yau na tara  a gaba, na San yanzu ko wuqa zan caka maki ba ji Zaki yi ba," Fita ta yi ma daga kitchen d'in kwatakwata ta tafi d'aki ta kwanta a gado ta mimmiqe ta na sauraron muryar Anwar d'in da ke ratsa dik wata kafa ta jikin ta. "Kin san me?" " A'a sai ka fada" " Ina gidan mu yanzu haka,inda zamu zauna ni da ke da Fateema nake nufi,ina kan doguwar kujera a kwance nace bari na kira ki naji muryar ki,yanzu iwar haka inshaa Allah wani satin kina gefe na a kwance muna hira ko?" Cike da jin kunya kamar yana ganin ta ta rufe idon ta, " Kaii Daddan Fatee, ni dai ba ruwa na, babyn ka na jin ka, gata a kwance tana bacci" Dariya ya yi dan ya san wayon ta,gani yake kamar kunyar ta tama qaru ne akan tada da take budurwa, anya zasu sha amarcin da yake hango masu kuwa da wannan kunyar tata? "Ita ma Fateeman ai ta shaida Daddyn ta na son Mummyn ta sosai, dan in ba ita ba zai iya rayuwa ba, sauran qiris na mutu Abbana ya taimaka ya yi ma Daddyn ku magana aka daura auren mu," Nan ya kwashe komai ya sanar da ita har halin da suke ciki shi da Hajiyan shi, " Allah ya qara maka lafiya Daddan Fatee, amma gaskiya banji dad'in yanda ka yi wa Hajiya magana ba, waya faɗa maka ana jayayya da iyaye ta yanda ka yi? Ko kuma kai fushi da su? Kar ka manta fa dik BIYAYYAHr da na yi wa iyaye na Kai ne sila, tarbiyyar da ka dinga d'ora ni a Kai ta yin BIYAYYAH wa iyaye ita ta Kai ni ga auren Alhaji, gashi yanzu alhamdulillah naga ribar BIYAYYAH Anwar, ko kasan sanadin BIYAYYAH ne yanzu zamu yi aure? So kake in mun samu yara muma in mun musu fada suna fushi da mu? idan baka son haka ta kasance damu ka baiwa Hajya hakuri ka daina mata yanda kake yi mata kaji nawan," duk abinda take fada yana yi yana bata amsa da A'a da eh ne tare da d'aga kai kamar tana ganin shi, "Inshaa Allah yanzu dana koma zan bata hakuri na gode sosai, kuma ki fara shiri nan da sati zaki tare, me kike gani zamu yi na bikin, dinner ko walima?" "Ni gaskiya bana son yin wani bidi'a na fi son auren mu ya yi albarka,domin kuwa auren da aka yi cikin ƙanƙanin kashe kuɗi yafi albarka,sannan auren da ba a sab'awa Allah ba wajen nuna murna Shima ya fi albarka, dinner din yanzu da ake Banda nuna tsiraicin amarya, se rashin kunya da fitsara da ake yi, ga kad'e-,kad'e na mutanen da ba addinin mu d'aya da su ba, ga Raye-Raye da zaka ga mata da maza ana yi, dan haka mu yi walima a cikin gida kawai, yan uwan mu da abokan arziqi su hadu aci a sha kowa ya sa mana albarka shikenan, ko ya kace?" Yaji daɗin maganganun ta sosai dan ta nuna mai tana aiki da ilimi, shiko zai bata mamaki wajen sata ta ji dad'i a rayuwar ta, "Shikenan yanda kk ce haka za ai gimbiya ta, jibi ina hanya," "Ko kazo ba zaka ganni ba,dan kuwa ba zan fito ba, sai sanda aka kaini za ka ganni," Yana kwance ya d'ago ya zaro ido, " lallai da kin azabtar da mu kuwa, habaa ke kuwa kar mu yi haka da ke manaaa," Dariya ta yi ta masa ta jaddada masa ba fa zai gan ta ba,haka ya hakura yace to kuwa ba zai dawo ba, har sai an kai masa ita, haka suka yi ta soyayyar su ta waya, suka ci gaba da tsara yanda zasu yi zaman su in Allah ya kaisu ranar da zasu kammala mallakar junan su. Amarya ta sha gyara sosai, da kan ta take gyararrakin jikin ta, wanda da dama da kayan da muke dasu ne na cikin gida take amfani dasu irin su fruits, madara, baking soda, da sugar gishiri da sauran su( ku duba novel dina na baya 'YAN ABUJA, WATA UWAR,DA KAINE JARUMI, 'YAR RAWA zaku samu kayan gyaran jiki inshaa Allah, ko kuma ku sayi littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA za ku ga yanda ake gyaran jiki da natural abubuwan da muke dasu a tare damu 09031416423) Eamaan ta yi kyau sosai, ba kad'an ba, Kamal kullum sai ya tsokani Anwar ta waya akan irin kyan da yaga Eamaan tayi, shi kuma ya yi ta jin kamar ya yi tsunstu ya zo ya ɗauke ta, wataran in ya ji yabon ya yi yawa, yakan ce masa, "Malam she is my wife oo,ya kamata a dena kallon ta da yawa haka," Kamal ya kan yi dariya sosai sannan sai ya bashi amsa da "Ni da nake da Hafsat me zan da Eamaan?" Anwar da kamal sun zama manyan abokai fiye da yanda sukw a baya,a dik sanda Anwar zai ga kiran kamal to fa zai ɗauka cikin sauri da gaggawa dan yaji yanda Eamaan ɗin shi take. ************************* Wanka Sahabee da amaryar shi suka fito a tare, daure take da towel iya guiwa duk qafar ta da tasha man bleaching ta yi kala biyu nan baqi can fari, sai gwaguis ɗin gashin ta da ya sha relaxer qeyar duk ta cinye, sai kad'a jikin ta da yake a sake shakaf take faman yi ita a dole ga wayayyiya ƴar bariki, sai buɗe gajeren hancin ta mai faɗi take yi kamar salansar babur. Amaryar Sahabee ba kyakkyawa bace, sannan ba za a kira ta da mummuna ba a tashin farko,shi kuwa a wajen shi babu macen da ta kai ta kyau a idanun shi dan haka duƙawa yayi ya dakko bokitin wankan da kwandon wanka ya biyo bayan ta, Iya na ciki bata San ma sun shiga wanka tare ba, zafi dik ya ishe ta ga warin kashin kaji be gama sakin d'akin ba,dan haka sai kawai ta ɗauko tabarma da matashin Kai ta  fito ta shinfida a tsakar gidan dan ta shaƙi iskar ƴanci. Tafe suke Amarya na gaba angon ta na biye da ita riqe da bokoti da kwandon wanka a hannu,tana ganin Iya a tsakar gidan kwance sai ta koma da baya ta rungumo shi tana wani shafa qirjin shi, Iya da ke kwance ce miƙe zaune ta hau tari babu qaqqautawa, amarya kuwa ƙin sakin Sahabee tayi dik da ƙoƙarin da yake na son zuwa wajen Iya,cikin takaici Amarya tace, "Baby meye haka kuma ina zaka je? Ko kana nufin ba zata yi tari ba saboda gata yayi mata yawa? Wuce mu je ka shafa min mai ni kar na bushe." Gaba suka yi abin su suna shiga ta ɗakko mai ta bashi ya shafa mata sannan ya sanya mata kaya, daga karshe sai ta hau yi masa magana cike da kirsa da shagwab'a tana faɗin taso yin wanki gashi ta yi wanka bata so ta b'ata jikin ta, "Kar ki damu zan wanke maki mene a ciki, ai duk a cikin soyayya ne," Tulo masa kayan ta masu datti ta yi dan tinda aka yi auren su ko tsinke bata taɓa wankewa ba,dan haka kayan wanki gare ta masu yawa, aiko ya na ganin su ya zaro ido yana ayyana anya wannan ba tin daga gidan su tazo masa da masu datti ba? Kan dole babu yanda zai yi ya d'ebi kayan ya je yayi ta wankew. Ita kuwa zaman yin kwalliya tayi a d'akin ,bayan ta gama ta fita tsakar gidan ta dasa kujera ta zauna a gefen shi tana yi masa fari da sun haɗa ido,hannun ta riƙe da mafici tana firfita fuskar ta da ta dame da powder da zufa, data ga alamar ya gaji zata zaro zancen batsa ta watsa masa,nan da nan zai qara qaim wajen yin wankin yana washe baki,Iya da ta ga abun na neman fin ƙarfin ta sai ta tattare shimfidar ta koma ɗakin ta,tana shiga d'akin ta zauna a bakin katifa tai ta kukan baƙin ciki da dana-sanin rashin tarbiyyar da bata baiwa yaran ta ba musamman sahabee, nan take zuciyar ta ta tuno mata Eamaan baiwar Allah da irin muzgunawar da ta dinga yi mata dik tsananin biyayyar da ta dinga yi mata. A ɓangaren amarya Eamaan kuwa........ [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼      BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 26: A hankali Amarya ta maida Sahabee tamkar wani bawan ta, domin kuwa dik wani aiki da ya kamata a ce itace take yin shi sai ta mayar masa da shi aikin shi,shine shara, wanke-wanke,girki, d'iban ruwa da wankin kayan su,a dik sanda yayi girki taci taji bai yi mata daɗi ba yanda take so sai ta sa shi ya siyo a waje. Yana matuƙar wahala wata yazo ya wuce bata je biki ba, babban abinda yafi ƙayatar da ita a zuwa biki shine ɗinka anko,wannan shine babban dalilin da yasa ta ƙware wajen yawan roqon kud'i,abinda dik ya bata da shi zata sayi anko tayi ɗinki idan ya ragu ta kaiwa bokan ta ya qara kafe mata shi ta yanda sai abinda tace yayi kawai zai yi, dik kuma abinda bata so to fa bai isa ya aikata shi ba. Wajen shaye-shayen magungunan mata kuwa an bata lambar yabo dan kuwa ƙwararriya ce a wannan fannin tinda ta gama gano lagon sa,indai  zai samu biyan buƙatarsa to fa komai zata yi masa baya gani,kan kuce me Sahabee ya tashi daga d'an gaye ya koma Wani iri da shi kamar d'an aikin gidan dama can shi ba me kaurin jiki bane se ya sake jemewa ya rame sai uban tsawo kamar igiya,gaba ɗaya ya zama wani abin tausayi da shi. Tsakanin uwa da ɗa sai Allah,ganin halin da ya shiga ne ya sanya ciwon Iya yake yawan tashi, Sahabee bai ma san tana yi ba balle ya sai mata magani, watarana har kasa tashi take yi ta fita koda yin alwala ne. Idan abun ya yawaita ne yaga be ga gilmawar ta ba na kwanaki sai ya ɗaga labule daga bakin ƙofa zai yi mata sannu sannan ya kama gaban shi ya shiga sabgogin shi kamar bai ga halin da take ciki ba,matar shi kuwa sai suyi kwanaki bata leqa ta ba balle ta duba ya jikin ta yake, lokacin da ta ga damar gaishe ta kuwa to daga bakin qofa take d'age dan buhun labulen itama ta ce mata sannu ta yi gaba abunta,a cewar ta ai uwar miji ba uwar ta bace. Babban abinda yafi baƙantawa Iya rai bai wuce yanda matar nan zata kalli idanun Iya ta dinga kiran ta da ƙazama wadda bata share ɗakin ta balle tayi wanka taji dad'in jikin ta,Iya ta yi nadamar abubuwan data dinga yiwa Eamaan a baya, gefe ɗaya kuma ta yi nadamar yanda ta dinga yiwa Alhaji Abdullah da yake tsananin tausaya mata da taimaka mata tare da yi mata ladabi da BIYAYYAH,a kullum ba shi da burin da ya wuce na ya ganta cikin walwala da farin ciki, duk dan kar ran ta ya baci da girman shi haka zata sa shi a gaba da fad'a kamar yaro qarami, ga masu aiki wajen uku ya zuba mata ita kaɗai a sashen ta dan su kula da dikkan buƙatun ta, amma dik da haka ta takurawa matar shi mai tsananin BIYAYYAH dik da cewa ba auren soyayya suka yi ba, idan tace masu abu fari ne komai baqin shi basa yi mata musa haka zasu yarda da abinda tace ɗin.kuka shine ya dawo abincin Iya Kuma ya zamto abin Shanta. Idan ana girki a gidan haka hayaƙin zai shiga ta ɗan ƙaramin windown nata tai ta tari tana neman iskar shaƙa mai kyau, dik randa tayi gigin fita dan ta shaƙi iska amaryar sahabee sai ta nuna mata bariki ta hau taɓa shi a gaban idanun ta shi kuwa yana biye mata,tsananin da Iya ke ciki yayi tsanani har ya kai ga yanzu bata gani sosai saboda hawan jini da yayi mata yawa da kuma hayaƙi dake addabar ta kullum. Muryar Amaryar Sahabee ke tashi kamar wata gardi a cikin gidan cikin ɓacin rai take magana. " Yanzu honey kana nufin bashin da na ciwo saboda ankon bikin qawata ba za ka samu biya ba? kai fa ka yi min alqawari kafin auren mu ba zan tab'a neman abu na rasa ba kace min babu ni babu wahala aikin gida da komai ba nawa bane naka ne, sannan ka jaddada min kar na damu da maganar kud'i ko nawa ne baka da matsala akan su zaka dinga bani,ni ba ma abinda ya fi min ciwo ma sama da alqawarin zama a qaton gida bayan d'aura mana aure sai na ga an kawo ni nan, hakuri kawai na yi na rufa Maka asiri wajen dangi na da qawaye na muke zaune a wannan akurkin, domin rufin asirin ka shine nawa,se yanzu na gane duk Kalaman ka a gare ni qanzon kurege ne,tin yanzu gashi ka fara karya alƙawarin ka na bani kud'in anko a duk sanda na buƙata,to ka buɗe kunnen ka da kyau kaji ni,wannan ankon da na ciyo bashi se ka biya ba zaka sa na ji kunya ba,dubun nan talatin da bakwai cassss se ka kawo su,sannan ga kudin ɗinki dubu biyar da aka yo min,dole ne ka biya kud'in takalmi da jaka da mayafi da na sa qanina ya amso bashi a shagon abokin shi, ba zaka sa na ji kunyar qanne na ba a dinga raina ni ana zagin miji na ana kiran ka talaka,sarqa da dan kunne da abun hannu da zan yi amfani dasu Kuma ka siya daga baya kafin ranar bikin tazo. Kai dama zaka godewa Allah na samu bashin?  Yanzu a wannan zamanin bashin ma ai se ka yi da gaske zaka same shi, ni yanzu na gama gane inda ka dosa dik ƙarya ka zuba min lokacin neman aure na,gashi yanzu ka gaza a kula da ni, dama ko a gadon ma hakuri nake da Kai yanzu," fashe wa ta yi da kuka har da shessheƙa kamar shine ya gama yi mata rashin mutunci ba ita ba, duk maganganun da take yi sun shiga kunnen Iya sun zauna a zuciyar ta daram, kad'a kai Iya ta yi alamar muje zuwa yanzu aka fara tinda na hana ka auren ta ka kafe, to ga irin ta nan ai. Sahabee kuwa duqawa ya yi a gaban ta ya na bata hakuri da tabbatar mata ze biya kud'in ko nawa ne, murmushi ta fara yi masa ta na wani kakkama shi, Sahabee na ganin ta sakko ya tallabe kan ta zai yi mata kiss, cikin nuna qyanqyamin shi ta janye jikin ta tace, "Haba my baby ki yi hakuri mana na ce maki inna samu zan baki, kinga a wajen aikin mu ni ke ajiyar kud'i, inna je zan ranta na baki, a albashina sun dinga d'auka a hankali har na gama biya, ba dai dubu tamanin bane dika kud'in? kar ki damu zan baki ni dai ki min murmushin ki me kyau na gani ko naji dad'i a raina" Murmushin ta masa ta rungume shi tana boye fuskar ta a bayan shi tare da murgud'a masa baki da harar shi, shafata ya soma yi cikin b'ata rai ta ture shi tace, "A'a gaskiya ciki na babu komai me zan iya yi maka yanzu? ni yunwa na ke ji kamar banci komai ba nake jina, gaskiya ka samo mana yar kaza yau mu d'an ci a gidan nan mu maida mugun yawu, kaima kasan kullum sai na ci kaji bama kaza ba sanda Ina gidan mu,amma ka duba ka gani sai na yi sati ko kwana hudu ban ganta ba anan gidan." Hawayen munafurci ta share ta fyace majina ita a dole zaman haƙuri take yi a gidan Sahabee, jikin shi na rawa ya fita ya amso bashin qatuwar kaza guda d'aya,wanda da kyar ma aka bashi bashin kazar saboda dama can akwai tsohon bashin kusan dubu bakwai da Mai kajin ke bin shi, yau d'in ma dan ya gilla qaryar a gobe zai kawo masa har na baya ne sannan ya yarda ya bashi, Sahabee ya qudurta a ran shi gobe zai je wajen aikin nasu ya d'akko kud'in ba Wanda ya sani tinda a office ɗin shi suke. Koda ya dawo sai ya baje mata kazar a gaban ta yana murmushi, zama tayi kamar mayya tana washe baki, a tare suka hau cin kaza tana zuba surutu kamar tsohuwar redio, yawun Iya gaba ɗaya ya gama tsinkewa saboda tana jin dik abinda ke faruwa,hawaye take zubarwa tsabar kwad'ayin da ya addabe ta, tinanin gidan Alhaji Abdullah kuwa ya zame mata ibada dan kuwa kullum sai tayi,yanzu da acan ne ko kaji nawa take so se ta sa a gasa mata ta ci,a rayuwar nan dama dik wanda yasaba cin dad'i tofa shi yafi begen dad'in, haka suka gama tass suka sha ruwa basu sammata koda fuffuke ba, da kyar Sahabee ya samu had'in kan ta ya sauke buƙatar shi dik da faranta mata da yake ƙoƙarin yi a kullum. Washe gari da sassafe ya shirya bayan ya gama yi mata aikace-aikacen gidan da ya saba,sai ya leqa Iya ya mata sallama, bai ji ta amsa ba ya wuce dan bai damu daya ga lafiya take ba ko akasin hakan, yana fitowa ya sa kai ya tafi. Lokacin da ya isa office bai tarar da mutane ba sosai sai ya zauna  ya gaggaisa da mutanen da ya tarar,sannan ya tashi zai shiga office ɗin shi d'auke da jakar shi a hannu,sauran ma'aikatan kuwa yana tashi suka hau qulmar shi suna cewa tin da ya yi aure ya rame kuma yake makara,ko kuma ma ya yi fashi gaba d'aya yaƙi zuwa,yana ji bai kula su ba ya wuce, sai da qafa ta d'auke lokacin cin abincin rana ya yi ya buɗe wajen da ake aje kud'in ya kwasa,da har ya dauki dubu d'ari ya rufe, daga baya kawai yace bari ya ɗauki dari biyu zasu masa amfani a gaba, sun dinga zara a albashin sa a hankali har ya gama biya, yana gama d'iba ya rufe ko ina ya tafi gida hankalin shi kwance, yana zuwa gida ya zaro dika kud'in ya zube a gaban ta tin kafin ya cire kaya ya huta, amarya kuwa na ganin wannan uban kud'in sai rawar kai ta tashi, tana ta yi maaa sannu da zuwa harda tashi ta ɗora girki tana faɗin ya gaji ya zauna ya huta zata yi musu abincin. Bayan sun ci abinci sun gama ne ya shiga wanka ya fito yayi alwala saboda gabatowar sallar magariba, koda ya je masallaci yayi sallah ya dawo da isha'i Amarya ta maqale masa,ranar Sahabee ya samu kulawa ta musamman a wajen matar shi har bai san sanda dare yayi nisa ba,bata barshi ba har sai da taga bashi da sauran qarfi a jikin shi, tana ganin ya yi bacci ta ɗauki wayar ta ta kira qawar ta tace mata, "ke shegiyar ga fa kayan ki nan zan dawo maki da su, ni kam na samu kudin da na dan samu zan qara gaba, na gaji da qaddararren auren nan, dama ace yana d'an samu ne  kuma yana da qarfi sosai a gado to da na hakura, amma ba komai daga sama har qasa komai a bushe me zai zaunar da ni? Ina nan tafe yanzu ki saurare ni nan da awa ɗaya, dan haka ki fito bakin hanya na baki kayan ki na ƙara gaba." Dariya kawai waccan take kwasa tana ta hura mata kai, tana ziga ta,cikin shewa tace, "To muguwar sai kinzo, ai ita bariki haka take dama, wanda bai zo bama jiran shi take gashi ya faɗa hannun ki kin kwashi rabon ki zaki arce,ina nan ina jiran ki sai kin zo." Sallama suka yi ta aje yar rakani kashin ta ta fara haɗa kayan ta a hankali,sahabee kuwa na nan washarere jiki a bude dik ya gaji, ta kalle shi ta tofar da yawu a gefe tace, " Allah ya kiyaye na ci gaba da zama da wannan lagwanin, ba kuɗi ba biyan buƙata, ga mazaje can a waje na jira na a biya min buƙata kuma a bani kuɗi  amma ina nan a rakub'e kamar ƴar karo? dama ai dan na zaci har lokacin yana tare da wannan yayan nashi ne mai kuɗin da yake kashe min a baya,wanda shima na ji ana ta rad'e rad'in d'an hannu ne,(Matsalar zina kenan yan uwa, Alhaji dai ya mutu amma ga wata tana tino da labarin shi kuma tana maimaita ai dan hannu ne, wanda ana so in za a tina ka a tina ka da aikin alkairi, Allah ya kyauta ya samu aikata dai-dai, ya yafe mana a inda muka yi kuskure, Allah ya shiryar damu da zuriar mu) tana gama mitar ta ta kwashe kud'in ta d'ure a jaka ta sa kai ta bar gidan, d'akin Iya ta leqa taga yanda ta barta tin safe tana nan kwance a haka har a wannan lokacin, sakin labulen ta yi ta kyab'e baki tai gaba tana mitar sai shegen son jiki kawai tsohuwar ta sani da sa ido, tana fita gidan qawar ta ta nufa ta miqa mata kayan da dubu biyu kamar yanda suka yi alqawari tai gaba. Sahabee kuwa sai da ya kai awa d'aya bayan fitar ta ya na bacci kafin ya farka, kallon d'akin ya yi yaga kamar anyi yasa, shiru ya yi ya ɗauki gajeran wandon shi irin na ƴan ball ya saka,neman ta ya fara yi amma babu ita babu dalilin ta, ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce, "Wataqila tana can tana gasa kan ta, dan yau na more ta sosai ba kad'an ba , yaushe rabon da ta barni nayi irin na yau? Muguwar ai haka zan nayi mata kuwa daga yau." Yana nan har aka kira la'asar yaji shiru bata dawo d'aki ba,sai ya tashi ya leqa band'aki dan yaga me take yi haka, yana shiga yaga wayam, hankalin shi ne ya fara tashi cikin sauri ya koma d'akin ya hau bincike, nan fa yaga babu kud'i babu dalilin su Kuma ba kayan ta na sawa,sai wata dubu buyu da ya gani da takarda a aje an dora kwalbar Mai akai. Buɗewa yayi ya ci karo da mummunan bayanin da ya sanya shi yin zaman ƴan bori a ƙasa,wasu zafafan hawaye ne suka fara tsartuw daga idanun shi,a guje ya fita zuwa d'akin Iya dan sanar da ita mummunan abinda ya same shi,yana zuwa sai ya ganta kwance yanda ya barta tin safe da zai fita aiki. A hankali cikin rawar jiki ya qarasa shiga cikin d'akin ya sa hannu ya taɓa ta ya ji shiru bata motsa ba kuma bata ce komai ba,hannu biyu ya sa ya juyo da ita sai yaga bata motsi,da gudu ya fita tsakar gida ya samo ruwa ya hau yayyafa mata amma shiru Iya bata farka ba. Ɗaukar ta yayi da kyar ya yi waje da ita ya ajiye ta a dakalin ƙofar gidan su ko riga babu a jikin shi, se da ya wahala kafin ya samu abun hawan da zai Kai su asibiti, dubu d'aya me adaidaita ya caje shi, ya ce su je ba komai ze biya, ko da suka Isa asibiti Sahabee kuka ya sa ya na neman a taimaka masa, ganin yanayin da yaje asibitin dashi ne daga shi sai gajeran wando ga Iya a kwance rai kwakwai mutu kwakwai ne yasa likita ya ce a shigar da ita ya duba ta sun kawo kuɗin daga baya. Da kyar aka samu Iya ta farfad'o daga doguwar sumar da ta yi, takarda likita ya bashi me d'auke da magungunan da za a siya wa Iya, likita ya ce daga baya za a yi maganar bill na asibiti Kuma. Likita ya shawarce shi akan ya samo mata abu me ruwa-ruwa da zata sha in ta farka saboda akwai yunwa a tattare da ita sosai, Sahabee tsugunnawa ya yi  a wajen yayi tsuruu yana tunanin inda zai samo kud'ad'en da zai yi wannan hidimar da su. Kamar wanda aka mintsina haka ya miƙe cikin hanzari ya nausa ya nufi ma'aikatar su,dan kuwa ya tabbata yanzu ba kowa dik an tafi gida, zai yi amfani da wannan damar dan ya samo wasu kud'ad'en a can,a guje yake tafiya yana haki duk inda ya wuce mutane sai sun bishi da kallo sai kace wani kwarto,a rayuwar shi kaf bai tab'a tinanin zai shiga damuwa irin haka ba,a yau ya gane ashe uwa uwace,dik duniya bayan Allah da manzon sa baka da kamar ta. Kamar yanda ya zata kuwa ya na zuwa ya tarar da wajen a rufe ba kowa dik an tafi gida sai Mai gadi, zagayawa ya yi ya haura Katanga ya shige ya balle makullin cikin dabara da kwarewa irin ta tsoffin 'yan bariki, (Kun San Wanda ke bariki ba a raba shi da sata) dubu dari da hamsin ya qirga casss, ya zamana ya saci dubu dari uku da hamsin kenan, yana gamawa sai ya barbaza kayan wajen ya koma ya haura Katanga ya koma asibitin,yana zuwa ya biya komai da ya Kamata ya biya har ya samu na abinci da zasu ci, gida ya koma dan ya yi wanka ya d'an huta Kuma tinda Iya bacci take, ko da ya kammala duk abinda zai yi se ya kashingid'a da niyyar zuwa bayan isha'i se ya koma asibitin,bacci ne mai nauyi ya ɗauke shi ba shi ya farka ba se subahi tsabar gajiyar da ya kwasa. Kwanan Iya biyar a asibiti jiki yayi sauƙi ta murmure, dan haka likita yace musu a yau zai sallame su, Iya na Jin maganar Sallama ta hau kuka ta na fad'in ita su bar ta a wajen su kawai kar a bari Sahabee ya Maida ta gida, kowa a wajen ya tausaya mata sosai dik da cewar basu san menene tsakanin su ba, ba yanda za su yi dole hakuri suka bata  Sahabee yazo da yamma suka koma gida. Tinda suka koma gida sai ya rage mugun hali ya ɗan fara kulawa da ita,dan kuwa watarana har yakan sai mata madara ta leda guda d'aya da bread yankan nera ɗari, sai ya dafa mata ruwan lipton ya sa mata sigan ashirin a ciki, shi kuwa kafin ya wuce aiki zai je wajen mai shayi ayi masa had'in kauri yaci ya sha ya ƙoshi. A haka rayuwar Iya da Sahabee ta ci gaba har kud'in ya tasamma qarewa, a wajen aikin shi kuwa da fari sun zaci shiga aka yi akai sata, saboda samun wajen da suka yi a b'alle,sai da bincike yayi bincike suka gane cewar Sahabee ne ya yi satar. Wata ranar talata suna zaune shi da Iya yana ta mata masifar ta yi fitsari a zaune, dan kawai bata jin dad'i ba zata qwarara jikin ta ba ta isa bayi sai ta saki fitsari a zaune? da anyi mata magana kuma tace qafa ke matsa mata,waye qafarshi bata ciwo amma haka yake tafiya bayi sai ita? Hawaye kawai take zubarwa tana jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu dan baƙin cikin sahabee ya ishe ta,yana nan yana sababi aka hau k'wank'wasa ƙofar gidan nasu, Sahabee ne ya miqe dan zuwa ya ga waye yake musu  bugu kamar ya basu ajiya, dan shi ya riga ya cire ran waccan gantalalliyar zata dawo gare shi ma shi yasa ko neman ta baiyi ba, shi se yanzu ma yake danasanin auren ta da yayi dama haɗuwar bariki ta gaji haka,tafe yake ya na ci gaba da masifa har ya isa qofar gidan, a jingine da qofa yaga shugaban wajen aikin su da ƴan sanda biyu,wani tsallen bad'ake ya yi zai juya ciki a guje suka ko yi ram da shi, ihu yake yana fad'in, "Ku yi min rai sharrin talauci ne ya sa na tab'a maku kuɗi amma zan biya ku ba sata nayi ba aro ne, kunga mahaifiyata ita ce ba lafiya na deb'o na ke mata magani dasu." Ba wanda ya kula shi suka tasa ƙeyar shi gaba suka saka a mota, Iya na kuka shima yana yi, hakuri suka bata dan ba zasu iya yafe masa ba,bayan tafiyar su kuwa Iya ta sha kuka kamar babu gobe, ko ba komai mutum rahama ne, sannan hannun ka baya taɓa rub'ewa ka yanke ka yar in ji bahaushe. Kan dole ta hakura ta yi shiru, ga shi ita bata taɓa ma shiga maƙotan ta ba balle su san da zaman ta su taimaka mata, matar Sahabee duk ta gama sawa an tsani gidan nasu ba mai son su a unguwar kaff, haka Iya ta koma rayuwa ita d'aya da safe ta ja jiki ta yi bara a qofar gida har ta samu na siyan abinci, da yamma ma ta fita qofar gida ta zauna, in duhu ya fara ta ja jiki ta kulle gidan ta ci abinda ta samo ta yi sallah ta shige daki se Kuma wata safiyar. *************************** Sauran kwana biyu a kai Amarya Eamaan d'akin ta, wasu daga cikin ƙawayen ta da suka yi makaranta a baya tare ne suka shirya dan zuwa bauchi, ciki har da babbar ƙawar ta Aisha,Yayah ma ta samu zuwa bauchi dan kuwa tace wannan karon ba zata yi missing bikin Eamaan ba.   Eamaan tayi wani irin kyau na musamman fatar ta har wani santsi da sheƙi take yi kamar wadda aka wanke da inji, ga wani irin mayen qamshi me kama jiki da take yi, gashin ta kuwa ya sake cika da tsaho kamar wanda ake bawa taki,Eamaan ta maida kayan fruits abincin ta,madarar shanu, zuma,da sauran kayayyaki masu gina jiki,in zata yi wanka sai an saka ruwan lalle a ruwan wankan nata da madarar turare. Ranar kai amarya kuwa Hafsat Yayah da ƙawayen amarya sun shirya angwaye kawai suke jira dan su rankaya garin kano kai amarya ........ [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 27: Yayun amarya da qawar ta Aysha sun  gama shirin su tsaf  dan dawowa da amarya garin kano ta dabo tumbin giwa,tafiyar awanni hud'u da minti arba'in ne ta iso da su har qofar gidan su Eamaan d'in, Wanda ta kula da shige da ficen mutane a gidan nasu,har hakan ya tuna mata da lokacin auren ta na fari, a wancan lokacin ma haka aka yi taron mutane sosai a gidan nasu, wannan karon bata zaci zata ga kowa ba duba da yanda auren nata ya zo da Kuma cewar ita fa yanzu bazawara ce ba budurwa ba, wanne taron mutane Kuma za a yi? Anwar bai san da dawowar su ba, da ace ya sani to fa ba makawa sai ta ganshi a ƙofar gidan nasu,direct d'akin su suka nufa suka yada zango dan huce gajiyar da suka kwaso, sanin cewa amaren na tafe ne ya sa aka tanadar masu abinci da abin sha, Hafsat da ke Jin yunwa ce ta zuba masu ita da Fatee suka fara ci, a can tsakar gidan kuwa cike yake da 'yan biki mata, gaba d'ayan su mamakin taruwar mutane da yawa suka dinga yi, Yaya ce ta katse masu tinanin su ta hanyar cewa, "Kun San yanzu fa aure ne za a yi na soyayya, aure ne za a yi Wanda tin fil azal dangi shi suka zaci zai faru, duba da cewar kowa ya San soyayyar dake tsakanin Eamaan da Anwar d'in to kuma qaddara ta riga fata, dole kuwa yanzu ku ga dangi ko ta Ina" Su Kan su su Ammaah da Maman sun yi mamakin cikar dangin nasu, saboda ba su yi gayyata ba, sun dai Sanar da daurin auren Eamaan da Anwar d'in, saboda dangi su sani, se Kuma suka basu mamaki da zuwa, 'yan uwan Mama sun ce dole ne a yi yinin biki, ba ruwan su da Wani auren bazawara ne, mijin ta ai saurayi ne. Shagalin biki kuwa ya kankama, Eamaan ta yi mamakin ganin uban lefen da aka kawo Daga gidan su Anwar, se Daga baya ta yi murmushi ta tabbata Anwar be tab'a cire ran zai aure ta ba, maqota da abokan arziqi an tsattsaya ganin lefen da ya ba wa kowa mamaki, akwati seti d'aya da rabi kowanne kalar shi daban, Goggon Anwar ce ke musu bayani, seti d'aya ango ne ya yi abun shi tin da jimawa ya aje, Rabin setin kuwa uwar ango ce ta yi shi, kowa ka kalla fuskar shi d'auke take da annashuwa da annuri. Bayan su Eamaan sun huce gajiyar su ne su Kai shiri da yamma dan zuwa gidan Iya,Eamaan Hafsat Yayah da  Fatee ne zaune a mota Yayah na tuqa su, sai da suka tsaya a Wani shago Eamaan ta yi musu tsaraba, duk Wani abu da Iya ke so se da ta siya mata dai-dai misali, sannan ta qara da d'an abubuwan ci da sha suka ci gaba da tafiya,da kwatance da tambaya aka kaisu  har gidan Iya, tana kwance jikin nata ya motsa, maganin ta na hawan jini ya qare, ga ba kud'in siya ko da da kud'in ma wa zai siyo mata sahabee baya nan? Duk tayi kashi da fitsari  a inda take kwancen a tsakar gidan, jikin ta ya yamushe ta rame kamar ba ita ba, cikin ta sai qara yake saboda yunwa Dake addabar ta,kwance kawai take bata san ina kan ta yake ba. Ko da suka yi ta doka sallama suka ji shiru sun so su juya, a tinanin su ko wrong address ne aka basu,wata yarinya ce data nuna musu gidan ta basu tabbacin nan ne gidan, tsohuwar gidan na ciki yau kwata-kwata basu ga ta fito bara ba. "Bara Kuma? Wanne irin bara, Iyan ce ke bara Kuma Ina Sahabeen?" Inji Eamaan da kalmar barar ta gigita ta. "Ai 'yan sanda sun kama shege, ya ishi kowa a unguwar nan da neman matan tsiya, matar shi kuwa bata da mutunci kwata-kwata bata raga wa kowa, to qarshe ma na ji ana cewa ta gudu ta bar shi, shi Kuma 'yan sanda sun tafi da shi shekaran jiya" "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un," Tini hawaye ya fara zarya da rige rige a kuncin Eamaan a hanzarce ta afka gidan, ganin Iya a yashe a qasa cikin Wani mawuyacin hali ne ya Sanya ta qarasawa a guje ta tallabi Kan Iyar ta Dora a cinyar ta ta na kuka ta na Kiran sunan ta, Iya da ke kwance magashiyan bata San wake Kan ta ba, sai qoqarin bude ido take amma ta kasa,  haka dai Yayah da Eamaan suka d'agata daga qasan, Eamaan tana kuka sosai ta ke gyara mata jikin ta, jallabiyar ta data dora akan atampar ta ta cire ta nade Iya a ciki, ta ce ma Hafsar ta taimaka ta siyo mata pure water ,domin kuwa Eamaan ta kula farkon abinda ya Kamata su fara yi wa Iyar maganin shi a wannan lokacin shi ne yunwa, dan yanda cikin ta ke kukan yunwa abun ya ba su matuqar tausayi,yau ko me Sahabee ya yi a ganin Eamaan ya Kamata 'yan sandan da suka kama shi  su tausaya musu, Hafsat na tsaye ta na jinjina irin tausayi na Eamaan. Fita ta yi ta siyo ruwan roba ta kawo ma Eamaan d'in, shayi Eamaan ta had'a mata da ruwan pure watern da Kuma kayan tea din da ta yo mata tsarabar su, Eamaan ta hau d'ura wa Iyan a hankali, Wani ya shige Wani ya dawo, a haka ya qare,sun Kai kusan minti biyar zaune kafin Iya ta fara bude ido, tana juya shi a hankali, Eamaan na zaune a qasa Kan Iya na cinyar ta, cike da tausayawa take kallon Iyar se take ganin Bata kyauta wa Alhaji ba da ta bar mahaifiyar shi a wulaqance haka, to amma ba laifin ta bane, Bata San haka abun yake ba da ta taimaka musu.   Iya na fahimtar a saman cinyar wa take sai ta fashe da Wani irin kukan da ya sa Eamaan ma fashewa da kukan tausayin Iyan, ba komai ke sake Sanya ta kuka ba face ganin wai yau ace mahaifiyar Alhaji Abdullahi ce anan, kuma take  a haka cikin mawuyacin halin jinya da talauci,yanda ya rayu ya na gatan ta mahaifiyar shi da kula da ita, gashi yanzu qanin shi da be San darajar ta ba Yana wulaqanta ta, Allah ya wa Alhaji rahama ko Dan yanda ya rayu ya na kula da mahaifiyar shi. Tun Eamaan na yi wa Alhaji addu'a a zuci har ta fito Fili  yayunta na amsawa da "Ameen" kafin Yayah ta dafa kafad'ar Eamaan d'in ta ce mata "Kukan ya Isa haka dear ,ya kamata mu zo mu tafi dare nayi, mu miqata asibiti,dan wannan da gani ba  yunwa bace kad'ai matsalar ta har da rashin lafiya,in yaso bayan an gama walima goben mun je asan ya za ai da ita,ni na maki alqawarin zan sauya mata gida zan aje mata wadda zata kula da ita,Ina ga ai hakan yayi ko?" Gaba d'ayan su sunyi na'am da shawarar ta, nan suka dauke ta suka ja qyauren gidan, suka tafi da ita asibiti suka damqa a hannun kwararrun likitoci Dan mijin Yayah sanannen d'an siyasa ne da ake damawa da shi, transfer na kud'in da za a kula da Iya ta yi wa asibitin suka fara Shirin komawa gida, Eamaan kuwa  zuciyar ta ta karaya ji take kamar kar ta tafi, zuwa ta yi wajen Dr. ta masa magana akan ya taimaka a ba wannan tsohuwar kulawa ta musamman, tabbaci ya bata akan kar su damu, za a kula da ita kamar yanda ya Kamata, a gaban ta ya kira wata nurse mai kamala ya damqa komai hannun ta sannan suka bar office din Dr. d'in, akan da safe zasu dawo. Jaka Eamaan ta bude ta zaro kudi ta bawa Nurse d'in tace ta sai wa Iya kayan shayi, da Duk abinda zata buqata tana so a bata kulawa sosai, kar a barta da yunwa, ta dinga bata abinci ta ci ta qoshi, sauran canjin ta riqe, godiya ta mata sannan suka tafi, Yayah ce ta ke Jan motar ita ko Eamaan na gefe idon ta a rufe, tana ta tinani kala-kala ,a haka suka isa gida jikin ta ba kwari. Washe gari da sassafe ta je kitchen da kan ta, ta haɗawa Iya kunun gyaɗar da ta saba haɗa mata a da, abokan wasan ta na ta mata tsiya, murmushi kawai take ba ta iya mayar musu,ta na gama kunun  ta mata ferfesun kaza ya ji kayan qamshi ya nuna sosai ya yi luguf ,ta dora mata da bread mai laushi, ta saka a food  flask, se da ta ga ta kammala komai sannan ta shiga wanka ta hau Shirin fita, ta gama shirin tafiya kenan Ammaah ta shigo, "Ni kuwa Baki fad'an ya kuka samu su Iya ba jiya, Kun dawo Ina tare da mutane ban samu na tambaye ku ba" Kwalla ce ta taru a idon Eamaan ta samu waje ta  zauna a gefen gado, Ammaahn ma zama ta yi a gefen gadon tana bin Eamaan da kallon son Jin me ya faru a jiyan. Cikin sharar kwalla ta fad'a mata abinda ya sami Iya, da inda suka  kaita a jiyan, shine yanzu take son ta je ta gan ta, Ammaah ta jinjina wa d'iyarta ta da zuciyar tausayi,rungume ta kawai ta yi da fari bata San ma me zata ce ba kawai se ta hau shafa bayan ta, sun dan jima a haka kafin ta samu bakin magana, " Allah yayi miki albarka Eamaan,ni dai a wannan lamarin zan iya qaryata bahaushe da ke cewa albasa batai halin ruwa ba, dan kuwa ni dai tawa albasar tayi halin ruwa a nan har ma ta fi yanda ake zaton ta,ana fad'in kyawawan halaye na Ina ganin anya haka nake? To Eamaan ke har  kin fini kyawawan halaye ma, Allah ya qara maki imani, da tsoron shi, ina son ki Eamaan,Allah ya miki albarka da ke da zuri'ar ki da sauran yaran musulmi dika" " Ameen Ammaahna nima ina son ki da yawa," Murmushi suka yi a tare sannan Ammaah ta share wa Eamaan hawayen ta,tare da miqa mata hijab din ta, Eamaan komawa kitchen ta yi ta dauki food flask da Kuma flask din ruwan zafi da ta zuba kunun ta zuba su a Wani basket na d'aukan abinci, sannan ta koma dakin su ta zauna tana jiran Hafsat ta dawo daga dakin Mama, dan da ta shiga nan toilet din nasu Dan wanka se  ita da Fatee suka tafi na Mama,kafin su zo ta kira Anwar ta labarta masa komai, sannan ta bashi hakuri jiya ta fita ba da izinin shi ba, gashi yau ma suna Shirin komawa asibitin, nuna mata ya yi Babu komai, in da abinda take buqata ma ta Sanar da shi, in Kuma ya zo ya Kai su ne ma Duk se ya fito, da sauri ta dakatar da shi Dan Bata son abinda za a ga rashin kunyar ta Kuma, ta na zaune bayan ta gama wayar ne su Hafsat suka  shiga suma sun kammala shirya wa se kawai suka fita mota suka wuce asibiti. Suna isa suka tarar da Iya sai kuka take tana ba ma'aikaciyar da Eamaan ta sa ta kula da ita labarin Ƴan sanda sun tafi da Sahabee, jiya wasu suka je gidan ta suka mata wanka, bata san ko su waye ba, da sauri Eamaan taje ta kama hannun ta dika da take ta wurgawa a iska tana bayani, " Iya nice Eamaan kin manta ne jiyan har ki ka kalle ni ki ke kuka, Iya ni ce Eamaaniin ki, ga Fateema ta zo ta gan ki Iya, jiya ita muka je kai miki amma se muka tarar da ke a cikin mawuyacin hali,se muka kawo ki nan," Qanqame hannun Eamaan Iya ta yi, ta fashe da kuka, ta kasa magana sai kuka,hakuri ta dinga bawa Eamaan, Eamaan ta nuna mata ba komai, komai ya wuce, labarin rayuwar da sukai da Sahabee da matar shi Iya ta ba wa Eamaan, da kuma yanda ta na zaune 'yan sanda su ka zo suka tafi da Sahabeen ta,ita kuma tana zuba mata abincin ta na sauraron ta tare da jimanta lamarin,sosai Eamaan ta tausaya wa Iya rayuwar da ta yi ,Sahabee kuwa can ta matse masa ai shi ya ja wa Kan shi rayuwar wahala to se ya ci wahalar shi shi kad'ai d'auke Iya za ta yi Daga wajen shi. Ko sisin ta ba zata saka dan fidda shi ba, in ya dawo yana buqatar tsohuwar shi ga ta nan, amma ita da shi ko a hanya ba ragowa, shida ko mutuncin kanshi bai sani ba balle na wani? baiwa Iya kunu ta fara yi,Iya kuwa cikin sauri ta shanye cup ɗaya, tausayin ta ne ya qara kama Eamaan,  Hafsat kuwa dariya ce ta kama ta ta kauda kai tare da shanye dariyar, naman Eamaan ta dakko ta yi  ta zare mata qashi tana bata a Baki,sai da ta ga Iya ta qoshi ta Kai geji sannan ta kyale ta. Iya da ta ji cikin ta ya d'auka ta kalli Hafsat da ke d'auke da Fatee ta ce, " wannan itace jikallen tawa?  Taho wajen kakar ki Fadhimatu kin ji" Maqale kafad'a Fatee ta yi, Eamaan ta dauke ta zata miqa ma Iya ita ta tsanyara kuka tana kiran Daddyn ta,mamakin ta ne ya kama Eamaan da Hafsat wannan shi ake Kira da sabon salo, sarai sun gane wa take nufi (Anwar) Iya ce ta share kwalla tace, " ku kyale ta banga laifin ta ba, laifin mu ne da tun da bamu neme ta ba, dan yanzu ta qini ba laifi bane," Eamaan ce ta ji tausayin Iya ya ratsa ta, " Iya dan Allah ki dena tuna baya komai ya wuce, sannan ina so in Sanar da ke yanzu in sun sallame ki zamu tafi dake gidan mu, na sake yin aure cikin satin nan, yau ne walima in Allah ya kaimu anjima da yamma da dare Kuma zan tare, in an kwan biyu kuma zamu koma bauchi da zama ni da mijina, ko da ace har aka sallame ki baki qara gani na ba,Iyayena da Yayah Babba zasu kula da ke, dan kuwa ko ba komai ni da Alhaji mun zama d'aya,Kuma mutuwa ce ta raba mu ba Wani tashin hankali ba, sannan kuma ke kakar Fatee ce dole mu girmama ki mu kula da ke" Iya kam kunya ta gama baibaye ta, ta yi kukan har ta gaji, Hafsat ce ta fada ma Eamaan cikin harshen turanci akan taje ta ga likita ta ji ko za a iya Basu sallama a yau d'in se su tafi da ita kawai,haka akai kuwa, aka rubutawa Iya sallama da magunguna na hawan jinin ta suka tafi. ***************************** Sahabee kuwa na can wajen 'yan sanda sun bar shi a cell ba a miƙa shi kotu ba ƴan duniya suna casa shi kamar masara a turmi,ihu kawai yake yana faɗin, "Waaaayyoooo officer dan Allah ku ma wannan qaton magana ya daina kirbata kamar ya samu kub'ewa, wayyo Allah, na wayyoo Allah na," "Ba zaka rufe min baki ba,nace  za kai shiru ko sai ka ci uwar ka, ai dama na gaya maka tin a alaba rago zamu had'e ne watarana, ga shi mun had'u, ka manta yanda kai kutun-kutun ka rabani da dadiro na sannan ka dawo ka aure min yarinyar da na yi niyyar aura, ka min asara Kai ma ai ga shi yanzu ta gudu ta barka kana cin kwakwa," Dariya suka d'auka gaba d'aya 'yan wajen, dan yanzu sun fahimci me yasa ogan nasu da suke Kira da Mugu ke ta jibgar shi tin da aka kawo shi dukan safe daban na dare daban, su kuwa ma'aikatan wajen dama suna tsoron mugu, dan costomer ne an Saba kawo shi, duk jikin Sahabee ba inda baya ciwo ya yi tsami sosai, ga targad'e da ya samu a hannu, ya daku iya dakuwa,Duk  ya Wani bushe ya  qara qobarewa, in an kawo wa mutanen wajen abinci cinyewa suke ba me sammasa,da fari har ya amsa laifin shi da bakin shi, da Jin an ce ya biya kud'in ya dawo ya ce ba shi bane, an kad'a an raya ya ce ba shi bane, a tunanin shi in yace bashi bane za su hakura su kyale shi, in kuwa suka ce ya biya da shekarun shi ze biya? Me ya ajiye ? Wannan ne dalilin da ya sa suka ki miqa shi kotu suka aje shi anan, in ya wahala ze amsa laifin shi,ma'aikatan wajen ba Wani abincin kirki suke bashi ba, in ma an bashi ya na fara ci Oga Mugu da yaran shi ke  amshewa  su cinye,ya yi kuka har ya gajia ya daina, in ya roqa su bashi ya ci, sai su saka masa a qasa su danna kan shi suce ya ci yana haushin kare a haka zai ci yana yi yana kuka, in ruwa ne a gwangwanin da suke kama ruwa suke juye masa ya kafa kai su dangwara kan a ciki haka zai sha ya na hawaye, rayuwa a yan kwanakin nan kawai ta mai qunci, Allah Allah yake a miqa shi kotu, wata qila azabar ta ragu,su kuwa sun gaji da tambayar shi ya amsa laifin shi sun zuba masa ido. ****************************** A gidan su Eamaan kuwa suna nan suna ta shan walima, abinci gashi nan ba a magana kamar an riga da an tsara taron,  Amarya ta sha gayu na daukar magana, ango na can da abokan shi, Kamal, Jamal  da wasu Daga cikin ma'aikatan asibitin Anwar d'in suna tasu walimar,sai kusan magrib aka tashi . Dangi na kusa daga wajen walimar gidajen su suka wuce, 'Yan Kai amarya na nan an yi dandazo ana jiran motocin Kai amarya, ai kuwa ana fara jera motoci a qofar gidan mata sukai ta shigewa ana ta diban su  zuwa gidan amarya, Yayah ce akan komai ita da qawayen ta, kowa ya je ya ga gidan sai ya yaba matuqa Dan kuwa Anwar kusan ba abinda be zuba ba, dik da ba Wani zama za su na yi sosai ana d'in ba. Da misalin goma na dare Yayah da qawayen ta suka dawo gida, ango yazo a motar shi daban, sai abokan shi da suka rako shi, daga nan su wuce shi kuma ya dau matar shi su tafi gidan su, wannan tsarin Hajiya Yaya da qanin ta Anwar ne, shine dalilin tsayawar ta a gama hayaniyar da ganin gidan ya d'au matar shi su je su huta. A qofar gidan suka yi parking motocin su suka firfito, ciki suka dunguma,Daddy ya sa aka fito da Eamaan dake kuka, kamar wadda za aiwa auren dole, kukan nan na matuqar taba zuciyar Anwar, ji yake kamar yaje ya lallashe ta, amma haka ya duqar da kai yana sauraron ajiyar zuciyar da take saukewa, qarasowa ta yi gaban daddy, Daddy ya bud'e mata hannayen shi ta je ta fad'a tana buɗe sabon babin kuka, shima share hawayen shi ya yi,ya kira Anwar ya kama hannun shi ya damqa masa hannun Eamaan,kansu aduqe Daddy yayi masu addu'ar zaman lafiya, sannan ya gyara murya ya ce " Anwar ga amanar princess d'ina nan na damqa maka, bar gani na tsoho, if u ever make her cry zaka gamu da ni, in dai ba kuka ne na farin ciki ba, ina fatan ka gane,Allah ya muku albarka ya baku zaman lafiya da zaman hakuri da juna,Ina so ku San cewa shi aure ko wanne irin ne ko na soyayya ko na had'i hakuri shi ne jigon shi, Dan kuwa ko Mai yanda kuke son juna da mace da an d'aura auren nan Kun zauna gida d'aya to fa hakuri ne zai tafiyar da rayuwar ku, Daga sanda ku ka cire hakuri a lamarin ku to a sannan ne soyayyar ke komawa qiyayya, Allah ya Baku zuri'a muminai salihai,Allah ya muku albarka" "Ameen ya Allah" Shine abinda mutanen wajen suka amsa da shi, Anwar ne ya d'aga Kan shi cikin yanayi na murmushi ya ce, " Daddy na gode, kar ka damu, ba zan tab'a sa Eamaan kukan baqin ciki ba Ina sane cikin hayyaci na da yardar Allah, sai dai ta yi kukan farin ciki, in tai kukan baqin ciki, lallai zuciya ta da ganganr jikina zasu hukun ta ruhina ba sai ka wahala ba Daddy, mun gode akan dik abinda kuka yi mana, Allah ya biya ku ya saka da alkhairi " Rungume su Daddy ya yi a jikin shi a haka suka isa waje, masu sharar kwallar farin ciki na yi, masu dariya nayi, Ammaah da Mama na hango su za su fita Suma suka taho sanye da manyan mayafan  su,har bakin mota suka raka Eamaan d'in wadda ke cikin mayafi bata San da zuwan su ba ma, sai da Daddy ya bud'e mota ze saka ta ne Anwar ya juya ya ga su Mama sai ya nuna wa Daddyn su, sakin su Daddy yayi suka nufi su Mama nan take Eamaan ta fad'a jikin Mama ta na kuka, dik dauriya irin ta Mama se da ta yi hawayen kewar Eamaan d'in, Ammaah kuwa ta yi namijin qoqarin danne hawayen ta, albarka suka Sanya musu kafin Daddy ya kama hannun su ya  saka Eamaan a mota, ya zagaya ya saka Anwar shima, kowa ya hau daga masu hannu, Anwar kuwa ya  tada mota suka tafi, kuka take sosai a hanya, tsaida motar yayi a gefen titin ya dago ta gaba dayan ta ya yi baya da kujerar shi yanda zata ishe su, ya janye mayafin  nata ya na kallon yanda fuskar ta ta yi ja saboda kuka, sannan ya ce " Eamaan, me ke damun ki,ko baki son aure na ne matsa maki na yi?" Da sauri ta bud'e idon ta da suka yi jawur ta zabga masa harara, cikin jin kunyar shi Kuma  ta yi saurin sunne kan ta a qirjin shi, ta ya ma zai ce bata son auren shi, bayan a rayuwa ba wanda take so samada shi......... *Anwar dinnan duk sai ya bata mana lokaci a hanya*🙄🤕 mun matsu mun matsu mu ga an je gidan amarya da angoooooo...casssss [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼   BIYAYYAH    💅🏼 WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH Page 28 : Eamaan ta San kusan dik abinda Anwar ke so, shi ne dalilin da ya sa ta qi yadda a cika mata fuska da kwalliya, ta riga da ta San ba abinda ya fi burge Anwar sama da ya dinga kallon fuskar ta ba wata mashahuriyar kwalliya a jiki,shi a so samun shi ma kar ta shafa komai ta zauna da fuskar ta a haka ya yi ta kallo ya na Jin dad'i, yanzu ma abinda ya mantar da shi cewar a saman hanya suke kenan, ya shagala matuqa wajen kallon fuskar Eamaan Mai d'auke da sirrikan kyau. 'Ga mace har mace, amma na San wannan kunyar ta ta sai ta hana ni sakewa yau d'innan' Anwar ya ayyana hakan cikin ran shi. A hankali ya fara kusantar da fuskar shi gare ta, idanun ta a rufe ta na sauraron bugun zuciyar shi, ba tare da sanarwa ba ta ji saukar labb'an shi masu taushi da Wani irin d'umi a saman nata, Suma ne kawai Eamaan bata yi ba a wannan yanayin da ya jefa ta, cikin rashin qwarewa Anwar ya fara sumbatar ta, murmushi ta yi a cikin bakin nashi, Wanda ya Sanya shi sake Jin kwad'ayin sumbatar ta, tura shi baya ta yi ta kalle shi ta ce,   "Da alama ka na buqatar malama, but this is not the right place,mu je gida" Girar shi ya had'e waje guda fuskar shi still na d'auke da murmushi da Kuma alamar tambaya. "Malama Kuma? karatun me za a koya wa bawan Allah Anwar?" "Idan mun je gida za ka gani" "Ohhhh har na matsu mu Isa" Kafin ta gama rufe bakin ta Anwar ya tada motar cike da zumud'in son sanin me za a koya masa, ko Ina na jikin shi ya na tsananin bege da qaunar kasancewa da Eamaan a daren yau, be tab'a sanin ya yi hakurin zama ba aure ba se a yau da ya gan shi ga shi ga Eamaan a matsayin matar shi ta aure Kuma halaliyar shi ,jiki na bari yake driving Allah Allah ya ke su Isa gidan, yau se ya ga gidan nasu ya Masa Wani irin nisa, murmushi ta sake yi a ranta ta na tabbatar wa Kan ta Anwar d'in ta sabo ne fill a leda ita zata b'are abunta, godiya ta yi wa Allah da bai sa ta zamo daga cikin mata masu zinace zinace ba,hamdala ta sake yi ga Allah a cikin ran ta da ya bata miji kamar Anwar. Yau so take ta bashi mamaki akan kallon da yake mata na ba zai Mori soyayyar shi ba saboda  kunya, d'an murmushi ta sake yi mai sauti, ya juyo ya kalle ta suka hada ido, ta yi saurin sunne kai, ga ni take kamar ya gane ta, a haka suka isa makeken gidan nasu, mai gadi ya bude masu gate,ya sa kai ciki,ko ina fess yake sai tashin qamshen tiraren wuta gidan yake, irin na sudanis dinnan na musamman Yayah ta ba wa wata qawar ta kud'i aka had'o musu tiraren wuta da humra Mai dad'in qamshi su dika ukun, sannan ta zaba mata tiraren wuta na tsinke masu dadin gaske, lumshe ido ya yi ya zagaya bangaren da take ya bud'e mata murfin qofar hannun ta ya kama ya rungume ta tsam a jikin shi suke takawa a tare,Eamaan na sane ta manne fuskar ta a cikin jikin shi take goga wa a hankali tana aika masa da saqon da ita kad'ai ta San kalar shi, bawan Allah Anwar a tunanin shi tsabar kunya ce ta sanya Eamaan rufe fuska a jikin shi, shi dai ya San kunyar nan se ta hana shi sakewa yau. Suna nan rungume da juna suka isa har dakin da ya ke shine a matsayin turakar shi, a bakin gado ya zaunar da ita, ya sunkuya, ya na cire mata takalmin ta, yana shafa lallen da aka zana mata mai kyau a qafar ta mara kaushi balle Faso (qafar matan novel irin Dijeena) kallon shi kawai take Ido  cikin ido, ko qiftawa bata yi, wannan kallon ya qunshi tsantsar so da qauna,da kuma nuna masa yanda ta kwadaitu da shi itama, se da ta tabbatar kallon ya shige shi ta yi saurin saukar da Kan ta qasa ta na murmushin Jin kunya, Eamaan fa ta gama birkitawa Anwar lissafi, a hankali taga yana yo wa inda take, dakatar da shi tayi cikin hanzari tace, " Habaa Daddyn Fateema, kamata yayi ai mu fara gabatar da nafilar gode ma Allah ko, dan ko da ba a nafilar godiya ga Allah, ina jin mu ya Kamata mu yi a daren yau, dan Allah ya gama mana komai daya mallaka mana junan mu," "Wannan gaskiya ne Mommyn Fateema, Alhamdu lilLAAHi ala kulli ni'imatin," Hannu ya miqa mata tare da taimaka mata ta miqe tsaye, sannan ya yi mata nuni da bayi, tambayar shi ta yi shin Ina ne nata d'akin? "Ko Ina d'akin ki ne a gidan nan Gimbiya ta, amma zan nuna maki inda aka ajiye kayan sawar ki" Murmushi ta yi masa Mai kyau, suka taka har qofar d'akin dake kusa da wannan d'in, shiga ta yi zai bita ta tura shi ta rufe qofar suna dariya. Bayan ta yi alwala ta wanke bakin ta, shiri ta yi Mai d'aukan hankali, ga humrah da turaruka da ta shafe jikin ta da su, kallon Kan ta ta yi a madubi ta ga yanda rigar baccin da ta saka ta yi mata kyau, "Hafsat ba dama, wato so take dole a daren nan sai na nuna kwarewa ta ko?" Murmushi ta yi ta lakace wa Kan ta hanci sannan ta dauki qaton hijabin ta ta zira, kafin ta kammala sakawa ya bud'e qofa, da sauri ta qarasa Sanya hijabin ta na Masa hararar wasa tare da tuhumar shi akan shiga ba Neman izini, "Ni da d'akin amarya ta se na nemi izini? Come one yunwa nake ji, taho mu yi sallah" Qanqance Ido ta yi ta na kallon shi, murmushi ya yi, ya miqa hannu zai ja hannun ta saurin janye hannun ta ta yi tai gaba, ya bi ta a baya, Ina zata yarda ta yi alwala ya riqe mata hannu alwalar ta ta yi targad'e. Sallah ya ja su raka'a biyu, su na idarwa ya zauna ya dafa Kan ta ya hau kwarara mata addu'o'in da suka zo a Sunnah ango na yi wa amarya, yanayin yanda yake larabci abun na burge Eamaan ji take har tsigar jikin ta na tashi saboda dad'in muryar shi, ya na idar wa ya kalle ta ya ce ya na zuwa. Waje ya fita wajen Mai gadin shi da ya aika ya karbi saqo ya Masa godiya ya koma ciki, ta na nan zaune inda ya barta ta d'aga hannaye sama ta na addu'a ya dawo, zama ya yi Shima ya nutsu har ta gama ta shafa addu'ar sannan ya mata Bismillah su ci abinci. Cike da Jin kunya suka ci kazar su da aka gasa da dankalin bature ta ji kayan qamshi ga fresh milk nan da juice ya bud'e musu suna korawa, Eamaan se da ta qoshi ta tsame hannun ta, Dan ta kula a yanda Anwar yake Jin Kan shi ganganci ne ta zauna da yunwa, Anwar ma ci ya yi ya qoshi sosai sannan ya tattara wajen ya nufi kitchen. Kafin ya dawo ta tafi d'akin ta ta sake wanke bakin ta ta yi tsarki da ruwan d'umi ta dakko had'in da Yayah ta mata bayani ta saka a wata kwalba ta bud'e, man zaitun ne sai na habbatussauda da Zuma kad'an, sai tiraren musk Mai kyau da qamshi sai ruwan bagaruwar mata da aka matse a ciki da ruwan da aka tafasa kaninfari,dangwalar kadan tayi tayi matsi da shi, nan da nan kuwa ta ji wajen ya sake had'ewa ya yi zam-zam, ga laushin da ya yi ba me cewa Wani abu ta shafa, zato za a yi dama can haka take a matse,ta na gamawa  ta d'aura alwalar bacci da ta Saba ta fito, a bakin qofar bayin suka had'u da Anwar, da alama Shima sai da ya sake gyara jikin shi, kallon ta ya tsaya yi Daga sama har qasa, rigar da ke jikin ta sunan ta fallasa cefane, ba abinda baya hangowa cikin ta, da sauri ta fara kare qirjin ta zata gudu ya kuwa yi ram da ita, mutsu mutsu ta dinga masa Wanda ya sake birkita shi, kafin qiftawa da Bismillah na sheqa waje da gudu, saboda kar a yi abun kunya a gaban idon Ta Hammah. Anwar ya tabbata har abada ba zai tab'a samun Jin dad'in da Eamaan ta jiyar da shi a daren nan ba a wajen kowacce mace,Eamaan d'in shi ita kad'ai ce ba ta da na biyu,daban take ta kowanne fanni, be yi danasanin jimawar shi babu aure ba a rayuwa, ya Kuma gode wa Allah da be yo shi Daga cikin matasa mazinata ba, lallai da ya yi asara da danasanin wannan dare, ba su yi bacci ba sai da suka yi wanka, Wanda da kyar ta yadda suka yi tare se da ya ce mata, "Wace kunya Kuma Zaki ji bayan kin koyan karatun da ya fi qarfin Kai na, dama malintar da ki ke magana akai dazu kenan? Lallai Eamaan ke ba qaramar malama bace Mai fasaha, Allah yayi miki albarka, Allah ya raba ki da baqin cikin duniya da lahira, Allah ya so ki ya aminta da ke, Eamaan ban San irin addu'ar da zan maki ba, Eamaan..." Muryar shi ce ta fara rawa saboda kukan da ya kama shi, Eamaan ta daban ce a a cikin mata, rungume shi ta yi ta na hawayen farin ciki,ya gama yi mata komai a rayuwa, wannan addu'o'in ba kowacce mace bace zata samu a wajen mijin ta, Alhamdulillah ta yi dacen mijin da ya San yabo da godiya , a haka suka yi wanka tare suka sake yin alwala sannan suka yi Shirin bacci. Da asuba bayan sun yi brush suka yi alwala tare da gabatar da raka'atanil fajr, ana kiran asuba Anwar ya ja su suka yi,suka yi azkar din safe se suka yi karatun qur'ani ,suna idarwa sukai addu'o'i. Kwanta wa ta yi a jikin shi ta hau wasa da qirjin shi ta ce, "Ina kwana Abu Fadheemah," Lumshe idanun shi ya yi sannan ya amsa ta da cewar, "Lafiya qalou Ummu Fadheematu, ya Daren jiya?" Murmushi ta yi ta sauka a jikin shi da sauri ta Haye gado, ta rufa ta na ta Dariya, ya na nan Daga zaune ya ke bin ta da kallo ya na murmushi, ci gaba ya yi da karatun shi sanda ya ji alamun ta yi bacci, be Dena ba se da ya ji idon shi na yaji yajin bacci, sannan ya ajiye Shima ya kwanta a gefen ta. Bata farka ba sai goma na safe, Anwar ta gani a gefen ta ya sarqafe qafafun shi a nata, juyawa ta yi a hankali ta na kallon shi,murmushi ta yi sanda ta tina abubuwan da ta masa a Daren jiya, kunya ce ta kama ta, ta ciji leben ta na qasa, ta na tina Shima abubuwan da ya mata, har da kukan shi kamar shi ne macen. 'Wannan shi ne na auri saurayin' Ta ayyana a ran ta. "Me ki ke tinani haka?" Da sauri ta miqe ta shige toilet da gudu ta na dariya, Shima bin bayan ta ya yi ya ji ta rufe ta ciki, komawa gado ya yi ya kwanta ya na murmushin Jin dad'i, lallai Eamaan ta zuba masa karatun da ba zai tab'a mantawa ba har abada. Haka ango da amaryar nan suka yi ta cin duniyar su da tsinke har tsahon sati uku, a cikin sati na hud'u ne suka shirya zasu gidan su Anwar, dan su gaishe da iyayen shi, Wanda Eamaan ce ta matsa Masa a cewar ta be Kamata ba su jima basu je ba,shi a son shi sai za su tafi Bauchin se su je su yi musu sallama, tinda an fara neman shi a asibiti. Abinci ta zauna ta tsara na gani na fad'a,m da drinks, sai fruit salad, ta zuba a mazubi biyu, daya na gidan su daya na gidan su Anwar, ga ado ta ci na musamman da wata atampa, mai tsadar gaske, ta sha dinkin zamani mai kyau, sai sheqi take, gaba daya jin ta take ta gaji sosai kamar wadda ta yi Wani aiki me yawa ga zuciyar ta dake ta tashi a lokacin da take aikin, sai tai tinanin tsabar qamshin girkin ne daya cika mata ciki, a hanya ta kasa hakuri ta juya ta dakko Apple ta fara ci,kallon ta yake tayi,ta gatsa Apple ɗin kenan ta kula da sai kallon ta Anwar yake satar yi, d'aga kafada ta yi, ta wara hannu tare da kafe shi da ido tace, " what?" Girgiza kai yayi da sauri, dan a 'yan kwanakin nan sai ta dinga abu kamar tana son yin fad'a da shi Dan ta na yawan hasala ko da wasa yayi mata se ta mayar da magana kamar ya mata ba dai-dai ba, shi dai gata nan dai be gane me ke damun ta ba,shi fushin nata ma dariya yake bashi, a haka suka isa gidan su Anwar, suka shiga cikin farin ciki, Hajiyan Anwar ta zubar da makaman ƙiyayyar da take yi wa Eamaan ta rungume ta sai nan nan take da ita,basu suka bar gidan ba sai bayan azahar, daga nan sai suka wuce gidan su Eamaan wadda duk ta shanye dan jam bakin da ta shafa tass, su Mama sunyi murnar zuwan su sosai har suka rasa inda zasu saka Eamaan d'in..... Na gajiiiii a Jira zuwa anjima inshaa Allahu. [24/04, 6:02 pm] asiyahabibu93: 💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH Page 29: A babban palourn gidan su Eamaan suka yi masauki,  iyayen su Eamaan har ma da ma'aikatan su sun yi matuqar farin cikin ganin Eamaan d'in,ta  yi irin qibar nan Mai kyau ta sabbin amare ga Wani irin haske Mai ban sha'awa da ta qara, atampar da ta Sanya Mai dinkin doguwar rigan da ta sha stones ta karbe ta, gaishe da Mama suka yi tana murmushin Jin dad'in ganin masoyan da suka yi matuqar dacewa da junan su. "Ai da na ji shirun ya yi yawa na ce wa Ammaahn ku zan je in ga ko 'yata na lafiya, ba zuwa ba waya shiru shiru, se ta ce ai lafiya ke b'uya to shi yasa baku ganni a gidan naku ba " Kunya ce ta kama Eamaan cikin jin kunya ta ce, "Mama muna nan lafiya qlou, kin san dake auren an yi shi cikin hanzari wasu basu sani ba se daga baya to baqi Muka dinga yi, abokan shi da 'yan uwa haka suka yi ta zuwa yau ma cewa mu ka yi bari mu fito da wuri Duk Wanda ya je ya ga bama nan ya yi hakuri se watarana" "Eh to da wannan Dan wannan ma dama haka ne, gidan amare baya rabo da baqi" Ammaah ce ta fito itama ta zauna aka hau gaisawa, Anwar na ganin surukar tashi  yayi saurin duqawa da kyau ya gaishe ta,a kunyace ta amsa, " Ashe kuna tafe, to sannun ku da zuwa Allah yayi muku albarka,gashi Daddyn naku baya nan," "Ai muna nan se dare...ni kam Amma ina Iya ne,ban ji duriyar ta ba," Mama ce ta amsa ta da cewa "Ai Iyan ki ta kafe ba za a sa ta a Wani gidan ba a aje ta anan Kuma  a nan d'in ma a bangaren masu aiki zata zauna, mun yi-mun yi ta zauna a dakin baqi amma taqi, wai tafi son can," "Allah sarki Iya, ai shikenan Allah dai ya qara lafiya, Kuma har yau Sahabee be zo neman ta ba ko?" "Be zo ba, ba Wanda ya zo neman ta, uhmmm ya wajen su Hajiyan taku," Cikin ladabi Anwar ya amsa da, "Suna lafiya, yanzu ma seda mu ka biya ta can suna gaida ku sosai," " Muna amsawa Kuma muna godiya," " Abu Fadheemah muje mu ga Iya kan ka tafi ko? Anjima sai ka zo ka d'auke ni," Tashi suka yi tsaye Eamaan ta Maida mayafin ta,suka fita  dan zagayawa ta kitchen su je wajen Iya, su na shiga kitchen d'in ya ga ba kowa sai ya kama qugun ta, da sauri ta jujjuya ta na kallon kowanne gefe kar Wani ya gan su a haka, buge hannun shi ta yi har da Wani d'an cije lebe "In wani ya gan mu fa," "Sai in ce ke ki ka ce na d'auke ki kin gaji da tafiya...baby ba maganar wasa ba tin a gida nake kula da ke gaba d'aya kin sauya  kamar baki da lafiya ko kin gaji, ina jin zan zo da wuri na maida ki gida dan ki samu ki ware kan gobe tafiya, ko kina ganin mu jinkirta tafiyar sai kin huta? Abubuwa sun maki yawa ko da yaushe cikin aikace-aikace ki ke?" Girgiza masa kai ta yi, alamar a'a, tana matuqar jin dad'in yanda yake kulawa da ita, yake son sata farin ciki a Koda yaushe. "Kar ka damu I am ok, mu je ko?" Suna isa qofar dakin Iya ya duqa ya cire takalmin shi, ita kuma ta shiga ciki, sanan shima ya bi bayan ta,Iya zaune take akan abin sallah, ta yi 'yar qiba abinta a cikin wata d'aya,da yake dama can ita me jikin qiba ce, to komai take so shi take ci dole kuwa ƙiba ta samu muhalli,uwa uba kuma ga kwanciyar hankali ya same ta, banda tinanin halin da Sahabee yake ciki ba abinda ke damun ta a yanzu,su Hajiya Iya se tasbihi ake yi, juyowa ta yi tare da fad'ad'a murmushin ta tana kallon Anwar da Eamaan,addu'a ta yi ta shafa, sannan suka shiga gaisawa, cikin fara'a Iya tace, "Wannan ne sirikin nawa? Tabarakalla Masha Allahu gashi nan kamar Wanda aka haifa larabawa na Kiran ta'ali ta'ali" Sosa kai Anwar yayi ya na dariya qasa-qasa Eamaan ma na dariya ta ji ana tab'a ta, shi kuma amfani yayi da d'ayan  hannun shi ya zura shi ta bayan Eamaan dake zaune  kusa da shi, ya shafa bayan ta, lumshe ido ta yi a hankali ta bud'e su akan shi,  girkiza masa kai ta yi alamun ya dena, murmushi ya yi ya kauda kan shi kamar be gan ta ba, ya ci gaba da shafa bayan ta, kyale shi ta yi da halin shi dan ta San ba denawa ze yi ba, ta kalli Iya da ke nad'e abun sallar ta ta na saka wa a saman hannun kujerar da ta tashi kusan ta ta ce, " Iya me yasa wai baki son komawa cikin gida ne inda kowa yake ki ka zab'i zama a nan wajen ke ɗaya? Ai bai kamata ba hakan a gani na tinda waje ne da aka yi shi Dan masu aiki" Murmushi kawai Iya ta yi sannan tace, " Eamaan kenan baiwar Allah, Eamaan Mai saka alkhairi ko da an mata Sharri,Eamaan 'yar aljannah da yardar Allah,kar ki damu Kan ki Eamaan nan shine ya dace dani, dan ba zan koma cikin gida ba gaskiya nan ma ya Isa Kuma na ga nan din ma ai ba laifi, kalli fa gado da kujerun da ke d'akin, tsohuwa da ni har da fridge,ai ba abinda zan ce maku sai dai Allah ya saka da alkairi," Ta qarashe maganar ta tare da matse ragowar guntun hawayen da bai sauka ba. "To Iya yanzu abinda ki ke so dai shi za ayi maki, amma dik sanda kk ji ki na son komawa ciki ki yi magana, akwai d'aki da Zaki yi zaman ki a ciki" Iya da Anwar har sun Saba saboda hira da suka zage suka sha abun su kamar ba ranar suka fara ganin juna ba, sai labarin yaran ta take bashi, anan ne ya fuskanci irin zaman da Eamaan ta d'an yi da su, dik da ma ta na kauda wasu zantukan na Iya kar ya ji, abinka da tsohon mutum in ya so labari se ya labarta abinda ke cikin shi zai ji dad'i, Anwar ya ji son Eamaan da ganin qimar ta da mutuncin ta sun qaru a idon shi,fatan shi Allah ya bashi zuri'a Mai albarka da ita su zama masu BIYAYYAH kamar ta ko fiye da ita ma. Se da aka kira la'asar sannan yace zai tafi se ya dawo an jima zai sake leqa Iya yayi mata sallama, rako shi Eamaan ta yi har jikin motar su, bud'e masa mazaunin driver ta yi bayan ya buɗe motar tin Kan su Isa, godiya ya mata ya zauna, can Kuma ya fito kamar Wanda ya yi mantuwa ya manna mata kiss a lips d'in ta,ya na dariya ya koma ya zauna ya rufe qofar shi, zaro idanu waje ta yi daga baya ta qanqance su ta had'e haqoran ta tare da kiran sunan shi, gwalo ya yi mata ya d'aga mata hannu, ya fara tafiya a hankali "Sai na dawo da anyi magrib zan zo ki shirya, Love you" "I love you too" Shiga gida ta yi fuskar ta d'auke da annuri da farin ciki, Mama ce ta kalle ta ta miqa mata hannu d'aya, isa ta yi wajen Maman ta zauna gefen ta sannan ta gyara ta kwantar da kan ta a cinyar Maman "Nikam Eamaan dama kin gama al'ada ne akai auren ki ko kuma zaki fara ne aka yi?" Tinani Eamaa ta yi sosai, nan ta gano kamata ya yi ace kwana uku da auren su ta fara amma gashi har yanzu shiru, sanar da Mama ta yi, sai taga Mama na murmushi, "Ko da na ji, yanayin ki se yake tinamin wasu 'yan shekaru kamar uku da suka wuce" cike da tsokana Maman ta yi maganar ta. "Maaa mene ne Dan Allah?" Eamaan ta fada a shagwabe, shafa kan ta Maman ta yi sannan  tace, " Eamaan i think zaki sake zama Mummy ne nan da wasu watanni masu zuwa,ko har kin manta yanda cikin Fateema ya yi miki ne? Ko da yake kowanne ciki yana zuwa da nashi salo,amma shi mijin naki da yake likita be gane komai ba?" Eamaan tashi ta yi ta zauna da kyau, a hankali komai ke dawo mata a kwakwalwar ta, Wani yawan kwad'ayi, saurin hasala, yawan kasala da sauran su, ga uwa uba an yi tsallaken al'ada, kunya ce ta kama ta ta duqunqune a jikin Mama, tana ta dariya, "Me ye haka zaki balla min Yaya? Me ake tattaunawa ba da ni ba," Ammaah ce ta qaraso dauke da fara'a itama ta yi wa Kan ta mazauni a gefen su. " I thing we ar going to become grannies again," Ammaah tayi murna a qasan zuciyar ta sosai ,sai ta dinga yi wa Allah godiya, a zahiri Kuma sai tace, " Lallai wannan angon naki ko amaryar taki da gaske suke, tinda ke kadai ki ka gane samuwar su tin Kan likita ya gano su,ko mijin naki ne ya gwada ki? (Kad'a Kai Eamaan ta yi ta tabbatar mata da ko asibiti ma Basu je ba) amma dai Ina me baku shawara ya kamata ku je asibiti a tabbatar,ko Kuma shi ya duba ki a gida, ba aikin shi bane dama?" Tashi ta yi ta d'akko musu  dambun naman kaza da ta yi da Kan ta a daren jiya da lemon kankana da ta sa Masa ginger da lemo,a hankali Eamaan ta d'iba ta sa a baki, dad'in shi da ya ratsa ta se gata zaune ta tankwashe qafa ta na dumbuza ta na kaiwa baki, se da akai magariba Daddy ya dawo, ya yi matuqar murnar ganin ta itan ma ta yi murnar ganin shi sosai, sannan ta Sanar da shi yanda tayi kewar shi sosai a kwanakin nan, nan fa suka dinga  hira da Daddyn ta, har  da labarin da ba su yi da Ammaah  da Mama ba ta kwashe ta na ba Daddyn ta, Ammaah da Maman ne suka kalli juna suka miqe a tare mama tace, "Toooo lallai ne, uba ya fi uwa se an jiman ku ku sha hira lafiya," Tattara wa Eamaan duk wasu kayayyaki masu amfani da suka San za ta buqata in ta je Bauchin ita da Hafsat suka shiga yi, su Daddawa ne da aka daka da kayan qamshi, su dakakken zogale ne, kayan qamshi ne, su magarya da bagaruwar mata ne, su kuka kub'ewa busasshiya da markad'add'iyar gyad'a ne, abubuwa dai birjik kamar 'yar makarantar boarding haka suka had'a musu ita da 'yar uwar ta Hafsat. ( kar ku manta, matan da ba su da isasshen kud'in siyan turaruka, ko Kuma masu warin zufa da sun yi aiki kad'an za su iya saka Alim a hammatar su bayan sun  fito wanka sai su goga shi alim d'in a hammatar, saboda ya dauke wari, in ka saka tirare ba zai warin zufa ba ko wanne irin aiki za kai, sai dai qamshin tiraren ne zalla zai na tashi,mu kiyaye ba a tsarki da alim, yana da illa Daga baya, ganyen zogale Kuma da aka Maida shi gari  zata na sha da madara da zuma ne Dan qarin ni'ima,sai ganyen magarya za a na tafasa shi  a kama ruwa da shi in ya huce, a wanke HQ da shi, dan dauke wari da qarni da datti, ko ta dafa shi da lalle tai wanka, yana gyara jiki, kayan qamshi kuma musamman mai had'in minannas a ciki na fada maku yana gyara jikin mace, ya bata dumin jiki, da ni'ima, kar muna wasa da aje kayan qamshi, maganin wannan mugun ciwon ne na infection) Kan a kira isha'i sun kammala had'a mata kayan,Mama ta markada cucumber, da kankana, ta matse ta zuba kayan qamshi a ciki,ta matsa lemon zaqi a ciki, sai ta debo zuma ta saka cokali biyu, asalin mai kyau din ba narkakken sugar ba,(shi din ma ba laifi in ba zumar) sannan ta saka mata madarar shanu, ta juya sosai ta bata ta shanye, komai akan idon ta aka yi, Mama na yi ta na fad'a mata wasu had'e had'en da ke qara saukar da ni'ima da gyara wa mace skin. Daddy ya tafi masjid Dan gabatar da sallahr isha'i ana idar wa ya dawo gida,saboda Anwar na nan tafe ya na so su gaisa, kafin Anwar ya zo suna zaune Daddy na ta mata nasiha se  ya bata kudi masu yawa yace ta ajiye ko zata buqace su, sannan ya bata shawarar ta fara sana'a in ta ga yanayin gurin zai kyau da hakan, zama ba sana'a lalura ne sosai, bani bani bai da dad'i, ya nuna mata yanda su Mama ke business din kayan kitchen da abayoyi ta online, Kuma suke da shaguna a kasuwa, godiya tayi sosai suka zauna zaman jiran Anwar ko minti biyar ba a yi ba kuwa suka Jiyo qarar bud'e gate da dirin mota, Eamaan ta gane cewa Anwar d'in ne amma ta yi shiru se da ya yi sallama ya shiga. Kafin su gama gaisawa da tab'a hira Eamaan ta shiga d'akin Mama ta sheqa wanka da irin kayan wankan Mama masu dad'in qamshi da gyara fata, Yayah ke siyo musu Daga qasashen waje in ta je kowa da nashi ita da Ammaah, wata doguwar riga Mai bin jiki Mama ta bawa Eamaan ta Sanya, d'aya daga irin kayan da suke siyarwa kenan a shagunan su ita da Ammaah. Kwalliya Mai sanyi da sanyaya rai Mama ta sa Eamaan yi, Ammaah na ta yi musu dariya, ta na cewa su bar d'an mutane haka Dan Allah ai ya kamu, mama kuwa ta ce inaaa namiji ba a Dena kama shi, yanzu ma suka fara "To Allah ya baku sa'a kenan zan ce ko? " "Ameen" Mama ta amsa da shi, Eamaan kuwa sinne Kai ta yi jikin Mama, turaruka masu sanyin qamshi ta fesa sannan ta Sanya mayafi Mai bayyana komai a jikin ta a saman rigar tinda dare ne, Kuma a motar su suke, sallama suka yi wa mutanen gidan, suka raka su har mota, Anwar ne ya tina da Iya ya ce wa Eamaan su je su yi mata sallama, ai kuwa da suka je Iya kukan farin ciki ta dinga yi, ta na musu addu'a da Sanya albarka, se suka qara burge ta, musamman yanda ta ga Eamaan na cike da annashuwa da annuri Wanda ya dace da ita. Tin a hanya Anwar ke Sanar da ita yanda ya yi missing din ta gaba d'aya ranar, "Kaiiii Abu Fadheemah yaushe yaushe muka rabu ma? Ko Dake Nima fa na yi missing din ka, Anya za mu Iya kwana bama tare da juna kuwa?" Ina Jin maganganun su na gane yau gidan su Eamaan fa za a soye za a qurmushe za a raqashe Kuma gidan ba na shigata bane ba, na lallaba nai baya na koma d'akin Iya mu Kwan tare. Da asuba bayan sun yi wanka sun gabatar da sallahr nafila da farillah suka hau shiri a gurguje, a so samun Anwar su Isa bauchi da qarfe tara ko goma, Dan haka french toast kawai ta musu, da tea suka karya da shi, sannan ta debo dambun naman da ta masu tin kan su fita da su meatpie, da duk dai dan abubuwan da zasu tafi da shi, shi Kuma ya yi ta kaiwa mota, ya na dawowa d'iban wasu kayan, hijab din ta ta saka suka ja qofar suka yi addu'ar fita daga gida suka qara da ta shiga abin hawa, makullan gidan ya damqa a hannun Mai gadin gidan suka masa bankwana suka fita a motar su sai Bauchin Yakubu.   A gidan su da bashi da nisa da na su Hafsat suka sauka, sun tarar Hafsat ta gyara ko Ina ta musu girki sun sha kwalliya gaba d'ayan su ita da Fateema da kamal gwanin sha'awa, sun yi murna sosai da ganin juna, Fatee tafi kowa murna da ganin Daddyn ta Wanda suke waya kullum ba adadi , sanda Hafsat da Kamal suka  zo tafiya qin bin su ta yi,dik nacin da Kamal ya yi sai hakura suka yi suka barta, Anwar ya ce kar su damu ta hutar da shi Jin kunyar tambayar a bar masa ita ne, Kamal ya ce gobe za su kawo kayan ta, Eamaan tai masu godiya sosai, suka raka su bakin gate. *BAYAN SHEKARU TAKWAS* Fatee na gani da wasu yara guda biyu, ta ruqo masu hannu bayan sun fito daga mota, na mijin na ta tsalle-tsalle sun dawo daga school, da gudu namijin ya je ya rungume Mummyn su sannan ya ce, " Mummyyyy" Dariya d'aya yarinyar ta yi ta ce, "Shiyasa 'yan ajin ku suke ce maka Mama's boy, ji yanda kake abu kamar yaro, kowa ya San kai twin d'ina ne amma kana wani sawa ana raina ni," Gashin kanta mai kananan kalba da ya zuba a gaban fuskar ta ta mayar baya ta kada idon ta tana wani yanga, in a matured way ta ce, " Assalamu alaikum Mummy," " Wa'alaikumussalam habibty, ya school ɗin uwar manyance?" " Alhamdu lilLAAH Mummy, kaifal yaum Mummy?" " Alhamdu lilLAAH Subai'a" Fateema ce ta sunkuya ta sumbaci kuncin Eamaan itama ta yi mata sallama, kallo suka nad'e hannaye suna bin qaramin su mai suna Abdullah takwaran Alhaji wanda suke kiran shi da Ameer, cike da tab'ara ya ce musu " Whattt?" " Amir say ur salam to Mummy" in ji Fateema, cikin tura baki shima ya yi sannan suka wuce ciki dan cire uniforms din su da Kuma watsa ruwa. Kafin su fito Eamaan ta haɗa masu abinci, Anwar ne ya shiga kitchen d'in ya same ta ya riqe ta ta baya ya dora wuyan shi a kafadar ta, ya ce " Allah ya miki albarka mata ta, in dai namiji ke d'aga qafa mace ta shiga aljanna ni kam bana fatan na sake tafiya a qasa, Eamaan na gode, kin ban happy and beautiful family, Wanda suke da tarbiyya da BIYAYYAH kamar ki, Eamaan ke ta daban ce, banda qiriniyar ki wanda itan ma Ina so, har yau ban ga abinda zan kushe ki akai ba, Eamaan ki na da kirki ga ki da tsafta, iya kwalliya, girki, tafiya, magana, bani shawara akan komai, kina son iyayena kamar naki, ga uwa uba tsoron Allah, Eamaan ke mai cikakken imani ce, Allah ya qara son shi da tsoron shi a ran ki, Eamaan kin ci sunan naki dama bahaushe ya ce suna linzami ne, me shi yaka wa Zane to tabbas sunan ki ya bi ki Eamaan Ina son ki Eamaaniii na" Ba qaramin dad'i ta ji ba da wannan yabon da mijin ta yayi mata, dan haka kawai sai ta juya ta rungume shi ta na sauke ajiyar zuciyar kwanciyar hankali,takun yaran suka ji suka saki juna su na murmushi, kawai se ya fara taya ta diban kayan abincin zuwa dinning, yaran sai suka koma suka zauna suka nutsu suna jiran a kawo abinci, zuzzuba abincin Fateema ta miqe ta fara yi, dan Eamaan ta koya mata yanda zata dinga taimaka mata da aikace aikace a gidan, shi yasa ko Mai aiki Bata da shi, ko rashin lafiya ce ta kama ta Fateema ke mata ayyuka, bismillah suka yi  suka fara cin abincin shiru wajen ya yi  kamar ba kowa, se Abdullah da ke 'yan maganganun shi in ya ga dama. Hafsat ta haifi 'yar ta mace mai suna, Amal, ta d'an girmi Subai'a kad'an, amma iyayin Subai'a sai ya sa mutum ya zaci ita ce babba,Yayah itama Allah ya bata yara biyu maza, Sudais da Farouq. Malam Sahabee kuwa an jima da sakin shi daga gidan yari,ya so matuƙa wajen aikin shi su yafe masa ya ci gaba da aiki da su,amma sai suka qi sam,se fafutukar neman aiki yake abun ya gagara banda kwakwa ba abinda yake ci a rayuwa, in ya je duba Iya ne ma a gidan su Eamaan yake samu ya ci ya qoshi, har ya tafi da Wani,Iya ta qi bashi fuska Sam balle ma ya ce zai kwaso ya dawo gidan mutane da zama,  gaba ɗaya Sahabee d'an gaye d'an bariki ya sauya, wanda duk ya san shi da se ya wahala Kan ya gane shi yanzu, hannun shi da ya yi targad'e ya samu matsala, ga wani wawan yanka da na gani ya duri ruwa a gefen kumatun shi, ko yaushe yaji shi Oho? Sai dai in ce Sahabee Allah ya shiga lamarin ka ya shirya ka. *Nan na kawo qarshen wannan novel nawa mai suna BIYAYYAH, ina roqon Allah kuskuren da na yi a ciki ya yafe min, alkairin da ke ciki ya min albarka ya jiqan magabatana ya qarawa Mamana lafiya da Imani yayi mata kyakkyawan qarshe, ina roqon Allah da ni da makaranta  ya Sanya mu daga cikin bayin shi muminai salihai.*