🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Da sunan Allah mai rahma, mai jinkai. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah!. Dubun salati kuma ga Ma'aikinsa fitilar alkhairi, shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w.)``` *Sallama da fatan alkhairi ga daukacin masoyana. Masu jimiri da kwazon bibiya ta a ko wane littafi da shafukansa. Ina godiya my fans. Sam ban ga laifinku ba, na matsanta min da tambaya a kan ina sabon labarin nan. Ku yi hakuri kun san jiki da jini. Na tsaya in dan huta ne. Yau kam ku motsa, ku mutsutstsuke idonku. Ga labarin 'Yar gwa-gwarmaya nan ya faso. Da iznin Allah zaku ci gaba da samun shi a ko wace rana.* ```Labarin namu ne mata.ku mu je zuwa 😍``` *Jinjinar ban girma, gare ku, zakakurai kuma jarumaina. ZAMANI WRITERS, kuna sanya ni alfahari. Nasmat tana kaunarku sosai da sosai. Allah ya kara daukaka min ku.* 🤝 ```Page 1``` A hankali take tafiyarta cikin isa da iya tako. Babu wanda zai dauka wata take bibiya a yanayin tafiyar tata. Domin ta fi maida hankali ga wayar hannunta, wadda take tafe tana lallatsawa. Sanye take da bakar riga doguwa, sai mayafin rigar da ta yi rolling kanta da shi. Kyakkyawar farar fuskarta ma'abociyar kwarjini ta bayyana. Yanayin lumshin da ake yi a garin shi ne ya karawa lallausar fatarta kala da armashi ga mai kallonta. Fadwa kenan. Ja'jirtacciya, kuma tsayayyar mace. Mai kafiya a kan ra'ayinta. Duk abin nan da take idonta na kan abin harinta, wato Suhaima. Wadda take bibiya ba tare da saninta ba. Wannan karon ta gama yanke shawara. Mai kan-kat, take so ta yiwa babban makiyinta Alh. Habib. Wanda duk duniya bata da makiyi kamar sa. Bata da burin da ya wuce ganin iyakarsa, da shi da mummunar harkallarsa. Ta sadaukar da rayuwa da duk wani jin dadinta. Ba dan komai ba sai dan shi. Dan ganin ta kawo karshen abinda shi ne silar rugujewar ta'ta rayuwar. Ta yi amanna cewa ita ce zata yi gyara a wannan fannin. Ta dade da tattara duk wasu bayanai game da Alh. Habib, amma aka yi watsi da su. Daga karshe aka maida ta rikakkiyar mai laifi kuma abar nema ga hukumomi. Saboda rashin cikakkiyar shaida kuma bayyananniya, ga kokarinta na bayyana ma duniya boyayyiyar fuskarsa da mummunan halinsa, da kuma tarin ta'asar da yake tafkawa da shi da ire-irensa a rayukan bayin Allah 'yan kasarsu. Wannan ne yasa hankalinta ya koma kan Suhaima. Babbar yarinya mai tashe a kasuwarshi ta yanzu. Kuma ta hannun daman shi. Ta tabbata muddin ta sami hadin kan Suhaima, ta shawo kanta har ta fito fili ta bada shaidar gaskiyar abinda yake aikatawa, to ba makawa duniya zata yarda. Saboda sanin kusancinta da shi. Ta dade tana jiran wannan ranar, da zata sami Suhaima ta fito ita kadai. Amma bata samu ba sai yau. Wannan ne yasa gaba daya hankalinta ya tafi gareta. Ta ma manta da tarin jami'an tsaro da 'yan barandar da aka baza suna farautar ta.. Bangare daya kuma Dodonta ne, a's'p Sauwam yake bin sawayenta daga nesa yana murmushi, zuciyarsa cike da farin ciki. Yana mamakin wannan wace irin nasara ce Allah ya bashi haka cikin sauki? Yau ga shi ga gagararriya Fadwa. Ya tabbata a wannan karon kamar ma ta shiga hannu ne. Dan kuwa babu abinda zai sa ya rasa ta kamar sauran lokuta. Ganin ta shiga kofar Hotel na sharaton. Yasa ya dan tsaya daga nesa, sannan ya ciro wayarsa ya danna kiran lambar ofishinsu. "Hello! Yallabai, Abbas ke magana." Aka fada daga can inda ya kira din. "Gud Abbas maza ka debo jami'an tsaro, ku same ni a Sharaton Hotel. Ku yi da jikinku, Fadwa ce na rutsa, kuma na tabbata wannan karon sam ba zata sha ba." "To yallabai." Abbas ya fada yana sarawa mai gidan nashi, kamar yana kallon shi. Duk wannan wainar da ake toyawa Fadwa bata sani ba. Ita kam, kanta tsaye take bin Suhaima. Bata da burin da ya wuce ta riske ta a wani lungu na wajen, kafin ta fada dakin da zata shiga. Ita kuwa Suhaima ko alama bata san ana bibiyar ta ba. Tana isa cikin Hotel din ta hau lifta ta danna lambar hawa na shida. Da isarta ta fita, ta fara tafiya a duguwar hanyar da zata sada ta da dakin da ta zo. Cikin azama Fadwa dake bayanta ta sha gabanta. Turus ta tsaya, suka shiga yiwa juna kallon-kallo. Ita dai Suhaima kallon rashin sani take mata. Da kuma mamakin yadda ta tare ta kai tsaye. Ita kuwa Fadwa kallon kyau da tsarin Suhaima take, da kuma tsan-tsan tausayinta. Domin a yadda take sam rayuwar da take bata kamace ta ba. "Baiwar Allah lafiya?". Suhaima ta tambaye ta fuska a daure. Har ta budi baki zata yi magana suka ji maganar 'yan sandan dake waje. Ta cikin lasifika suna cewa "Fadwa! Fadwa!! Na san kina ji na, kar ki yi taurin kai. Ki fito kawai ki mika kanki ga hukuma. Wannan wajen duka a zagaye yake da ma'aikatanmu. Baki da wata hanyar guduwa. Ki mika kanki kawai 'yar gwa-gwarmaya." Murmushin nan nata na musamman ta yi. Tare da lumshe ido. Wannan ne ya tabbatar wa Suhaima cewa da ita ake maganar. "Yar gwa-gwarmaya?". Ta mai-maita sunan tana kara karewa Fadwa kallo. Hannu ta daga ta nuna ta da shi "dama ke ce 'yar gwa-wagwarmaya? me yasa kike bibiyata nima? Wai me muka tare miki ne kike neman raba mu da jin dadinmu?". Fadwa bata kai ga yin magana ba, jami'an tsaron suka fito daga cikin lifta suka nuna ta da bindigoginsu. "Kar ki motsa Fadwa! Kin shiga hannun ma'aikata." Ta ji muryar a's'p Sauwam ta fada cike da gadara. Idonta a kansa. Sai murmushi yake yana tunkaro ta da inkwa. Da kallo daya zaka gane irin farin cikin da yake ciki. Fadwa ta kuma lumshe ido a karo na biyu, ta yi murmushi. "Kai babban jami'i ne Sauwam, amma me yasa kake goyon bayan rashin gaskiya? Na sha gaya maka ni Fadwa a kan gaskiya ta nake. Ba kuma zan daina gwa-gwarmaya ba har sai burina ya cika." "Gaskiyarki da rashinta ba ni ko ke ne zamu fada ba. Shari'a ce zata bayyana." Yana maganar yana dada tunkararta. "Ka yi gaskiya Sauwam. Tabbas kotu ita take bayyana mai gaskiya. Amma ba irin wadannan kotunan da muke da su yanzu ba. Hujjoji a kan makiyana suna da wahala. Amma ni tuni kun gama hada hujjoji a kaina. Wannan ne yasa ba zan taba baku damar kamani ba." Ta fashe da dariyar nan ta'ta da suke kira ta 'yan iska. Tace "Sai wani ganin a's'p Sauwam." Ganin haka da kuma sanin wace ce ita yasa a's'p ya fara sakar mata harbi. Sai dai kash! Fadwa kam ta bace bat!. Ta bar shi da harbin iska... *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Ina tare da ku masoyana. Sakonninku na fatan alkhairi na zuwa gareni. Na gode! Na gode!! Na gode!!!. Ubangiji ya bar so da kauna su yi karko. 🙏* ```page 2``` Sauwam ya ja wani tsaki. Ya daki goshinsa da tafin hannunsa na dama. Zuciyarsa na masa wani zafi. "Ka kuma rasa ta Sauwam". Ya ji sautin daga kasan zuciyarsa. Ya maida kallonsa ga Suhaima, wadda take tsaye tamkar dasa ta aka yi. Mummunar shigar da tayi ne, yasa ya yi gaggawar kawar da idonsa a kanta. Bai ce komai ba, ya juya ya bar wajen yana furzar da wani iska mai zafi. Haka yaransa ma suka rufa masa baya cikin takaicin rashin samun nasara. Sun rasa gagarumar kyautar makudan kudin nan da aka saka ga duk wanda ya samu nasarar kamo Fadwa. Bangaren Fadwa kuwa. Gidanta na mai-tama ta koma. Zuciyarta cike da kunci. Tun da Sauwam yake bibiyarta bai taba bata mata rai kamar na yau ba. Ya bata mata shiri, gashi ta rasa Suhaima. Bata kuma san yaushe zata koma samun dama irin wannan ba. Ta koma jan tsaki a karo na barkatai. Ta dauki kwalin sigari dake ajiye a gefenta ta zaro daya ta cinna mata wuta. Ta hau zuka tana fesarwa. Sai a lokacin ta fara jin kanta dai-dai. Ta jinginar da kanta jikin kujerar da take kai. Ta lumshe ido. "Fadwa!". Ta ji kira ta da karfi da muryar Ummynta. Kamar dai yadda ta saba. Ta bude idon tana kallon inda aka kiratan. Ummy ce tsaye cikin fararen kayanta (as usual). Fuskarta a murtuke ta fara magana "Fadwa ashe ban gargadeki kan shan taba ba? A haka kike tunanin samun galaba a kan makiyanki? A'a 'yata. Wannan ba ita ce mafita ba. Maza ki tashi ki tsaftace kanki ki dauro alwala. Salla da salatin ma'aiki sune tsayayyar hanya ta yaye damuwa. Karatun alkur'ani mai girma yana faranta ran mumini. Na hane ki da shan wannan shirmen daga yau. In dai kin yarda ni ce mahaifiyarki." Bata jira me zata ce ba ta bace. Da sauri Fadwa ta kashe tabar dake hannunta cikin ash. Ta mike ta nufi bayi. Ba jimawa ta fito da alwalarta bayan ta yi wanka. Ta fuskanci alkibla ta fara nafilfili da kiran sunayen nan na Allah tsarkaka. Tana gaya masa maysalolinta. Kafin daga bisani ta fara karatun alkur'ani. *A kasar Senegal* Karfe biyar na yammacin ranar. Wayar Alh. Habib ta hau ruri. Bai wani bata lokaci ba ya kai hannunsa ya dauki wayar, tare da dagawa. "Sauwam, Allah yasa in ji labari mai dadi daga gareka." Sauwam ya sauke kansa kasa yana koma tuna yadda ya rasa damar da Allah ya bashi. "A'a Shugaba. Labarin ba mai dadi bane ta wata fuskar, sai dai yana da muhimmaci. Muhimmacinsa shi ne mun samu tabbacin Fadwa tana Najeriya, cikin Jihar Kano. Mun ganta har mun tare ta, sai dai Allah bai sa muka yi nasarar kama ta ba." Shugaba. Habib ya mike tsaye lokaci daya gumi ya shiga yanko masa. "Wane irin sakaci kuka yi haka Sauwam? Ka kuwa san hatsarin dake tattare da Fadwa? Ku taimaka min mana. Yarinyar nan nema take ta bata min suna. Nema take ta wargaza rayuwar siyasata fa." Asp Sauwam yace "kwantar da hankalinka Alh. Fadwa ba zata gagare mu ba. Da iznin Allah nan bada dadewa ba zata shiga hannu. Ka huta gajiya." Ya katse wayar, ya bar Alh. Habib rike da wayar yana saka da war-wara. Kai tsaye ya shiga laluben wata number a cikin wayar tashi, ya danna kira. Ringing biyu a na uku aka daga. "Allah ya kama ma Shugaba." Aka fada a can inda ya kira din. "Amin amin Chaka. Kana ji na. Wannan ja'irar yarinyar tana Najeriya. Tana nan cikin Kano. Abinda nake so da kai maza ka baza yaranka kaima ka kutsa kai. Lungu da sako, ku nemo Fadwa kuma ku kashe ta." Wanda aka kira da Chaka ya amsa da "an gama Alh. Ina gaya maka in dai muka yi arba da Fadwa sai dai gawarta." Alh. Habib ya hangame baki, farin ciki ya lullube shi yace "zan kuwa cika maka burukan rayuwarka Chaka...". Ya kashe wayar sannan ya kira Aysha wadda ya kawo Senegal. Dan a yadda yake ji bai kamata ya koma kwana a kasar ba. Duk da akwai masu bukatar yarinyar da yawa. Saboda muhimmancin maganar Fadwa, yana da kyau ace yana kusa. Har wayar ta yanke bata daga ba. Ya ja tsaki yana fadin "wan-can shegen baya da sauki, har yanzu bai bar yarinyar nan ba?". Haka dai ya yi ta zariyar kiran layin Aysha har dare. Bayan ya kira waya airport an yi musu komai na tafiya zasu bi jirgin sha dayan daren. (Ka ji manya) Karfe tara da rabi, Okeke ya dawo masa da Aysha bayan ya yi mata ragas. Dakyar take tafiya. Ya kalli bakin mutumin yana bata rai yace "amma fa baka kyauta ba. Me yasa zaka yi mata haka? Ka kuwa san asarar da ka yi mini? Yanzu fa sai ta dauki lokaci kafin ta koma aiki." Okeke ya hangame baki "sorry Alh. Yarinyar ce da a kwai sweet. Zan baka kudin jinyarta daban, kuma na yi bunking a dawo min da ita karshen wata mai zuwa." Take a wajen ya tura masa makudan kudi a account dinsa. Alh. Habib ya bashi bannu suka gaisa, sannan Okeken ya fita yana shafa fuskar Aysha. To fa 🤔 *Shin Ina bakin zaren yake? Wane ne Alh. Habib Shugaba? Wace irin kiyayya ce tsakanin shi da Fadwa? Wace ce Fadwa? Mene ne burinta? A kan me take gwa-gwarmaya? Ku biyo Nasmat a shafi na gaba.* *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Ina kaunarki``` Kanwata *Amina Auta.* ```kina raina kema``` *Maryam 'Yar Mama* ```ban manta da ke ba``` *Baby Maryam* love you fiye da tunaninku. 😍 ```Sadaukarwa ga``` *Mom Heebah* ```fatan alkhairi gareki 'yar uwa. Nasmat na tare da ke. Addu'ata a kullum ita ce Allah ya bawa Babynmu lafiya.``` 🙏 ```page 3``` *Alh. Habib Inuwa (Shugaba).* Haifaffen Jihar Kano ne. Cikakken mai kudi, kuma sanannen dan kasuwa. Wanda ake damawa da shi a bangaren siyasar Kasa. Shi ba mai mulki bane, sai dai shi ne yake nada shuwagabanni. A gaba daya kasar girmamashi ake. Ana mutuntashi, duk wanda ya gabatar a matsayin wanda za a zaba, ba makawa shi zai yi mulki. Alh. Habib yana da mata daya Laurat da yaranta uku. Abdul Aziz (Baffa) shi ne babba sai kaninshi Faisal. Sai kuma autarsu Anisa. Wadan-nan yaran 'yan gata ne gaba da baya, wadan-da basa neman abu su rasa. Masu galihu, masu yin abinda suke so. Mahaifinsu ne ya daure musu gindin yin hakan. Domin a cewarsa idan yana da kudi 'ya yansa basu sake ba to babu amfanin kudin kenan. Yana da yawan kyauta da sadaka. Yana yawan dibar talakawa da 'ya yansu ya biya musu Hajji. Su je saudiyayya su sauke farali. Wasu lokutan kuma ya dibi kana-nan 'yan mata wadan-da suka gama sakandire, ya tura su manyan kasashen duniya da sunan ci gaba da karatu. Wadan-nan halayen nashi ba karamin kima da daraja suke kara mishi a idon al'uma ba. Musamman talakawa. Kasancewar duk wadan-da yake yiwa hidimar su da 'ya yansu ne. Sai dai a bangare daya Alh. Habib babban azzalumi ne. Makirin mutum, mai fuska biyu. Maha'inci, wanda ya maida 'ya yan talakawa da marayu jarin kasuwancinsa. Ya yarda da safarar 'yan mata sosai, dan yana saurin kawo kudi. Hakan yasa ya maida abin Sana'a. Yana fidda su manyan kasashe da sunan aiki ko ci gaba da karatu. Amma da an je can sai ya tilasta su yin karuwanci. Kudin wahalarsu kuma su dira a asusun ajiyarsa. Kasashen turawa da larabawa suna matukar so da kwadayin bakaken mata, 'yan afrika. Hakan yasa ya dage da tallata hajarsa a kasashen. Kasuwar kuma tana ci sosai. Yana aikin ne cikin hikima da kwarewa. Sam baya barin wata shaida wadda zata bayyana shi a matsayin mai hannu a cikin wannan badakalar. Hakan ya sa koda zarginsa ba wanda ya taba yi. Sai kwatsam a cikin ja'jibe-ja'jibensa ya ja'jibo ruwan dafa kansa. *Fadwa!* Marainiya Fadwa!!. Tun daga lokacin rayuwar shi ta shiga rudu. Sirrin da ya shafe shekaru yana binnewa yake neman fallasa. Mutuncin da kasarsa da talakawanta suke ganin shi da shi yake neman zubewa. Ya tabbata idan burin Fadwa ya cika ta fallasa shi, rayuwarsa ma ba lallai bane ya tsira da ita. Wannan kenan. *Wace ce Fadwa?* Itama dai a Kano aka haife ta. Kuma ta zo ne a jerin 'ya yan nan wadan-da basu da takamai-man wanda zasu kira da nasu. A gidan marayu ta tsinci kanta, bayan an reneta tun daga jarintaka. Da aka tsince ta yashe a gefen hanya. Uwar rikonta ita ce Amina wadda take kira Ummy ita ce ta rene ta tun daga kurciya har girma. Amina macen kirki, mai fara'a da nutsuwa. A karkashin kulawarta Fadwa ta sami cikakkiyar tarbiyya. Wadda ko wadan-da suke gaban iyayensu ba kasafai suke samun irinta ba. Soyayyar dake tsakanin Fadwa da Ummynta soyayya ce kwatankwacin wadda ke tsakanin 'ya ya, da iyayensu. Nagartacciyar yarinya mai kaifin basira da kwazon karatu. Cikin nasara da saka rai ga ci gaba, ta kammala jarrabawarta ta karshe a babbar sakandire ta gwamnati. A shekarar ma kamar yanda ya saba yaudarar mutane Alh. Habib Inuwa Shugaba, ya sanar da daukar nauyin karatun dalibai mata goma a kasar waje. Marayu da 'ya yan talakawa marasa karfi. A cikinsu ne hukumar makarantar suka saka sunan Fadwa, saboda kwazo da dagewarta ga karatu. Bayan fitowar sakamako aka fara shirye-shiryen tafiyar 'yan makaranta kasar waje. Allah sarki Fadwa a lokacin duk abokanin tafiyarta farin ciki suke, amma ita kuka take yi. Ba dan ta san wani abu game da tafiyar ba, a'a kukanta na rabuwa da Uwa ne. Wadda take ji kamar mahaifiya, Ummy. Ita ce wadda ta kara karfafa mata guiwa ga tafiyar. Ba dan ta so ba, ranar wata jumu'a jirginsu ya tashi zuwa kasar England. A inda aka ce an gama yi musu bunking na komai game da karatunsu. Satinsu biyu a wani Hotel ana basu horo game da yadda zasu rika saka kayan turawa da kuma amfani da kayan kwalliya. Al'amarin da ya yi matukar daure kan daliban. Basu kara tsurewa ba sai lokacin da aka tilasta su yin ado, suka saka wasu dangalallun kaya masu kama da tsirara. Aka dauke su hotuna. Da wadan-nan hotunan aka tallata su a kasuwar kana-nan 'yan mata masu budurci a jiki. Nan da nan aka fara zuba daloli a kan su. Basuda labari ana can ana cinikinsu kamar wata haja. Bayan an karbi kudadensu ne aka debo su, aka danka ko wace a hannun wanda ya biya kudi mafi daraja a kanta. Nan fa hankulan 'yan matan suka yi mummunan tashi. Babu yadda suka iya, a wannan ranar aka raba dukkaninsu da rigunan budurcinsu. Bala'i wanda ba a sa mishi rana. Tabbas wannan ranar ta zama bakar rana wadda har abada ba zata kau daga idon Fadwa ba. Wasu a matsayin karuwai aka bada su haya, wasun su kuma duka aka siye su kamar bayi. Fadwa tana cikin wadanda aka siyar duka. An kuma saida ta ne ga wani busashshen bature mai suna James. James bisa manufa biyu ya sayi Fadwa, wato ya biya bukatar kansa kuma ya yi kasuwanci da ita. Wannan ne yasa ta sha wahala sosai a wannan takin. Ta zama baiwa ta gasken-gaske. James yana cikin jinsin jarababbin mazajen nan da basa gajiya da mata. Kusan ko wane lokaci yana tare da ita. Zai iya amfani da ita sau biyar ko shida a rana daya. A hakan kuma zai tura ta biyawa wasu tasu bukatar ya karbi kudi. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Gare ki 'yar Uwa ta gari``` *Ama Alh. Kabir* ```Nasmat tana yin ki sweet Sis Allah ya raya mana zuri'a``` ```page 4``` Rayuwa ta yi wa Fadwa zafi, ko kadan bata samun hutu. Sun maida ita tamkar sex machine. Nan da nan ta ra-rake ta dawo kamar wata babbar mace. *Bayan shekaru Uku* Tun tana cikin firgici da tsoro har ta gaji ta bada kai. Ta zama cikakkiyar karuwa, wadda take ji babu wata macen da zata iya yi mata tunkaho game da juriyar aiki. Ta zama kwararriya wajen sarrafa maza da iya amfani da kwayoyin kara kuzari, da magun-gunan mata na karin ni'ima da juriyar sex. Haka turawa suka ci gaba da jagwal-gwalo da ita. Ta sake sosai har ma tana karawa da gyaran jiki. Kamar yadda yake kasancewa ga sauran wadan-da ake kaiwa irin wannan wajen. Ta fara fadawa shaye-shaye dan ragewa kanta damuwa da yawan tunanin Ummynta. Wadda kullum take kwana take tashi da tunaninta. Babu shakka Fadwa ta bautu ta kuma ci kwa-kwarta kafin ta saba din. Daga baya kuma ta fara kasawa. *Bayan wasu hekarun uku.* Sai ta tsinci kanta a wani yanayi na yawan yin mafarki da Ummynta. Tana yi mata fada da gargadi a kan ta gaggauta barin rayuwar da take. Koda zata mutu ne to ta mutu a kan hanyarta ta komawa gida Najeri. Nan fa hankali Fadwa ya fara komawa gida. Ta fara shiri cikin sirri da kwarewarta. Satar hanya ta fara yiwa mai gidanta James tana kula wasu mazan ta gefe tana karbar kudin. Ta bude asu-sun ajiya (bank account). Ta fara ajiye kudinta, kafin ka ce me Fadwa ta tara biliyoyin kudi. To a hankali kuma a sirrance ta yi passport (visa) ta fara shirin biyan kudin jirgi zuwa Najeriya. Cikin wannan yunkurin ne asirinta ya tonu. James ya gano shirinta na son guje masa. Nan fa ya rikice ya kuma sauya mata. Ba imani balle tausayi ya shiga azabtar da ita. Ya hanata fita ko'ina. Daga gidanshi sai gidanshi. Ya saka ta aiki ya kuma yi amfani da ita. Duk lokacin da zai fita kuma sai ya kulle ta a gida. Haka ta shafe watanni biyu babu mafita. Ga mafarkin Ummynta sai kara matsanta mata yake. Ta matsa mata ta je gareta ko ta halin ya'ya. Rayuwa ta yi tsanani, ta fara tunanin bin umarnin Ummy ta fita ko da James zai kashe ta. Wata ranar lahadi da safe James ya tafi Church wajen ibadarsa kamar yanda ya saba. Ita kuwa sai ta fara shirin barin gidan kafin lokacin dawowarsa duk da gidan yana kulle ne. Tana cikin tunanin ne Jack ya bude gidan ya shigo. Jack abokin James ne na kud da kud. Shi kadai yake da makullan gidan James saboda amintar su, kuma shima ba aure ne da shi ba. Ya kan yi amfani da wadan-nan ranakun ya zo gurin Fadwa a wasu lokutan. Ya biya bukatarsa da ita. Fadwa na ganinsa ta shiga farin ciki sabanin sauran lokuta da yake zuwa gareta. Ta tarbi Jack cikin murna ta bashi hadin kai, irin yadda bai taba samu ba. Sosai ta gajiyar da Jack sannan ta zare jikinta, ta bar shi zube a kan gado ta fada bayi na sashenta ta yo wanka. Sauri-sauri ta gama shirinta, ta tattaro kayan da take bukata, ciki hadda passport dinta. Da sanda ta lallaba ta yi ficewarta. Ta bar Jack can zube kamar kayan wanki. Lokaci mai tsayin gaske ta dauka wajen fafutukar tafiyar ta'ta. Kasancewar bata shirya komai ba. Jirgin ma sai a lokacin ta nema. Hakan ya sa bata tafi ba sai karfe shida na yamma jirgin ya tashi. Wohoho wannan ranar kam ku zo ku ga yadda murna da bakin ciki suke haduwa wa mutum daya a lokaci daya. Murmushi take a cikin jirgin kuma tana kuka. Cikin dare suka sauka birnin Kano. Bayan cire rai na shekaru shida, gashi ta dawo garin haihuwarta. Ta lumshe ido a hankali ta shaki daddadar iskar mahaifarta. Ta taki kasar da dukkan karfinta, zuciya cike da bururruka dabam-daban. Babban abinda ya tashi hankalinta shi ne ganin Shugaba Habib a sahun masu jiran jirgin zuwa Holland. Yana tare da wasu 'yan mata goma sha daya. Sai murna suke suna zumudin barin kasarsu da nufin samo ci gaba. A take abubuwan da suka shude suka fara dawo mata. Ta tuna da wan-can ranar. Ranar da ta kusa zamar mata ganin karshe ga Jihar Kano. Ranar da ta zamo sila ga tarwatsewar shiryayyar rayuwarta. Ga kuma wannan azzalumin tsohon da ya yi mummunar illa ga maraicinta. A lokacin ta fahimci wannan ita ce sana'arsa. Fataucin mata, saka su karuwanci da kuma saida su tamkar bayi. A ranar ta sha kuka bayan ta yi kokarin boye kanta ga Alh. Habib tana kallo har jirginsu ya tashi. Inda ita kuma ta nemi taxi ta shiga zuwa babban gidan marayun, inda ya zama gida gareta. Kuka take sosai a cikin taxi din, tana takaicin yadda ta bar gidan tana cikakkiyar mace, yau gashi ta dawo cikakkiyar karuwa. Tausayin kanta ya kara kama ta. Ta tuna nasihohi da jan kunnen da Ummynta ta yi mata kafin tafiyar. Sai ta koma rushewa da kuka. Haka dai ta kasance har zuwa lokacin da mai taxi din ya shaida mata ya kawo ta inda ta bukata. Ta sauka ta kuma fidda kayanta. A lokacin babu kudin Najeriya a hannunta, dollars ta cire ta bashi ya karba yana murna ya tafi. Ita kuwa ta ja akwatin tana taku dakyar kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi gate din gidan nasu cikin matsanancin kuka... *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Godiya ta musamman ga masu nuna so da kokarin bibiyar labarin 'YAR GWA-WAGWARMAYA babu shakka kulawarku ita take karawa Nasmat kwarin guiwa a dukakkanin al'amuranta. Na yarda babu kamar MASOYI a rayuwa. Ku ci gaba da so na, nima nan mai son ku ce* ```one love``` 😍 ```page 5``` Tana da'da nufar kofar kukanta na kara tsananta. Wannan ne yasa mai gadin gidan fitowa da torchlight dinsa mai dogon haske. Ya dalla mata ita daga nesa tun kafin ta karaso inda yake, ya tambaye ta "wace ce wannan?". Cikin kukan ta bashi amsa, dan ta shaidi dattijon tace "Baba nice. 'Yarka ce Fadwan Ummy". "Fadwa?!". Baba Ilu ya tambaya cikin tsananin firgici. "Fadwa mutum ko fatalwa? Domin mu dai wadda muke da ita a nan Allah ya yi mata rasuwa." Fadwa ta koma fashewa da kuka "Baba nice fa, yaushe kuka sami wata Fadwa bayan ni? Yaushe kuka maida ni matacciya?". Ta yi masa tambayoyin da karfi cikin matukar mamaki. Dattijon ya karasa fitowa daga gate din ya nufo ta, cikin tsananin mamaki. Yana mai kara haska fuskarta da fitilar hannunsa. Tabbas Fadwa ce. "Ya Allah!". Baba Ilu ya fada kana damki hannunta ya ruga cikin gidan, yana kwalla kiran sunayen iyaye da shugabannin gidan yana cewa "ku fito! Ku fito ga 'yar Amina ta dawo bata mutu ba. Ku zo, ku ga abin al ajabi ga Fadwa ta dawo a raye, wallahi bata mutu ba." Maganganun Baba sun kara ma Fadwa duhun kai. Kenan ce musu aka yi ta mutu? Kafin kace me mutane sun cika tsakar gidan, yara da manya. Tsofaffi da ma'aikata. Cikin masu son yin arba da Fadwa hadda Ummynta wadda ta kwashe fiye da shekara tana fama da ciwo, na hakurin rashin Fadwa da ta kasa yi. Tun bayan lokacin da labarin mutuwarta ya riske su. Saboda hasken da yake kewaye da tsakar gidan kowa na iya ganinta, wanda babu makawa sun tabbata ita ce. Sai ko canji na jiki da girma da ta kara yi. Ummy ta fashe da kuka ta ruga ga Fadwa ta rungume ta. "Fadwa 'yata. Dama kina nan baki mutuba? Meya same ki 'yata? Sun ce mana kin mutu. Fadwa sun saka ni kukan da ban taba yi ba. Ashe baki mutu ba 'yata." Ta koma fashe da kuka ta kankame ta jikinta. Haka iyayen suka yi ta shafa fuskar Fadwa suna mamakin ganinta a raye. Daga karshe suka zarce zuwa ofishin shugaban gidan, wanda dama yana cikin ayarin da suka taru ganinta. Shi kuma ya bukaci su bishi zuwa ofishinsa. A can ne bayan kowa ya nutsu suka bawa Fadwa labarin yadda suka sami labarin mutuwarta a bakin Shugaba, Alh. Habib kenan. Wanda suke yiwa kallon Uba ga marayu da marasa karfi. Har ma suka dora mata da gagarumin tallafin da ya basu. Bayan shugaban gidan ya kai aya ne, ita kuma ta fara basu labarinta tun daga tafiya har dawowarta bata boye musu komai ba. Ciki har da karuwanci da aka tilasta su yi, da kuma shaye-shayen da ta fada yi. Hayaniya da koke-koke suka kaure a ofishin. Masu kuka na yi, masu jifar Alh. Habib da tsinuwa suna yi. Tsananin tausayin marainiyar ya kara kama su. A ranar su kam suka yarda da duk bayananta, suka sanya Alh. Habib a layin azzalumai masu ha'intar kasarsu da rigar karya. Ta kuma shaida musu har yanzu bai daina dibar 'ya yan talakawa yana kaiwa kasashen ketare ba. Ta gaya musu ta ganshi yau din-nan ya fita da wasu zuwa kasar Holland. Ranar kam kowa a gidan sai da ya yi kwanan bakin ciki. Washe gari suka maka Alh. Habib kotu dan nemawa 'ya ya mata 'yanci da kuma nufin dakatar da shi daga wannan kazamar harkallar. Tsoro da firgici suka dirarwa Alh. Habib a lokacin da ya sami labarin wai wata daga cikin 'yan matan da ya fitar waje ta dawo har ma jagororin gidan marayun da take sun saka shi kotu. Sun ce asirinsa ya tonu yarinyar da ya ce musu ta mutu ta dawo gida bayan shekaru shida. Ta bar gida tana nutsatstsiyar budurwa ta dawo musu a rikakkiyar karuwa. Hankalinsa ya yi mummunan tashi a ranar, sam bai tsaya yin cinikin yaran da ya tafi da su ba. Ajiye su kawai ya yi ya dawo Najeriya. Da saukarsa ya gayyato manya kuma kwararrun lauyoyinsa suka hadu a wani gidan gonarsa. Ya gaya musu cewa shi bai san komai ba game da zargin da suke masa, ba mamaki 'yan siyasa ne suka sayi yarinyar dan ta bata masa suna. Ya umarce su da su yi, duk abinda ya kamata su lalata wannan case din. Dukkansu sun yarda da zancensa kasancewar duk kusancinsu da shi basu taba ji ko ganin wata alama da ta kusanta shi da wannan ba. Haka aka fara gwa-gwarmayar shari'a. Shari'ar da ta dauki hankulan dubannin 'yan kasa. Wadan-da da yawan su sun fi yarda da maganar lauyoyin Alh. Da suka ce 'yan siyasa ne suka sayi yarinyar don ganin sun bata mishi suna. Shari'a ta yi zafi, shaidannu sun bayyana cewa duk abinda Fadwa ta fada karya ne. Burinta daya, shi ne ta batawa taddijon suna. A cikin shedannunsu kuwa hadda ragowar 'yan matan nan da aka dauke su tare da Fadwa. An zo da su kasar, sun kuma bada shaida kan cewa tun da suka tafi su kam karatu suke. Ga takardunsu nan na ko-wane mataki. Sannan suka bayyana Fadwa a matsayin wadda ta gudu daga inda aka ajiye su, ta tare a wani club ta fara rawa da wokoki. A can ta koyi shaye-shayen miyagun kwayoyi ta kuma kware a fannin karuwanci. Suka ce lokacin da aka fara nemanta kuma sai labari ya zo daga gun da take zaune wai ta mutu. Domin kwantarwa iyayen rikonta da hankali yasa ba a gaya musu cikakkiyar gaskiyar halinda ta jefa kanta a ciki ba. Wannan shi ne abinda suka sani game da ita. Duba ga ire-iren wadan-nan shaidannun ne aka yi watsi da karar, tare da wanke wanda ake zargi. A karshe kotu ta daure Fadwa na shekaru uku a gidan kaso, bisa laifin batawa babban mutum kamar Alh. Habib suna. Wannan shi ne rashin adalcin da ya fara fusata Fadwa, ya fara sauya tunaninta. Ta fara nazari a kan neman mafita. A rayuwarta ta gidan kaso kuwa ta kara samun wayewar rayuwa a cikin masu manyan laifuka. Mata ne daga Jihohi dabam-daban. Wasu laifukansu na kisan kai ne, wasu kuma na ta'addanci a ciki ma har da 'yan fashi da makami. Sune suka kara tunzura ta, suka hure mata kunne kan ta yi duk yadda zata yi wajen ganin ta tona asirin Alh. Habib. Fadwa ta yarda, ta kuma karbi shawarwarin da abokanin zamanta na gidan kaso suke bata. A haka rayuwarta ta yi ta tafiya a can. Yayin da bakin ciki da kunci suka cika gidan marayu. Har zuwa lokacin da aka yankewa Fadwa ya kare ta fito daga gidan kaso. Zuwa lokacin ciwon Ummynta ya kara tsananta har ta kai bata iya tashi. Saboda bakin cikin da take ciki na halin da Fadwa ta shiga. Jikin kowa a gidan ya yi sanyi. Sun ja'janta mata, a karshe suka ce ta fita hanyar Alh. Habib ta maida hankali ga gyaran ragowar rayuwar da ta rage mata. Sun tsoratar da ita game da abinda zai iya yi mata idan ta ci gaba da neman tona asirinsa. Ranar bacci gagarar idonta ya yi. Ga tsananin ciwon Ummy ga bala'in matsin da zuciyarta take mata kan kar ta yarda ta bar maganar nan, ta ci gaba da bibiyarta, har lokacin da zata yi dacen yin nasara a kansa. Da dai tunanukan suka hadu suka yi mata yawa sai ta saka kuka. A lokacin tana zaune gaban Ummynta wadda take tunanin ta dade da yin bacci. Cikin kukan ta fara magana "yanzu shikenan muna ji muna gani zai ci gaba da bautar da rayuwar 'ya yan bayin Allah marasa karfi? Iyayen da suke samun abinda zasu ci dakyar. Su ciyar da 'ya yansu, su kuma tarbiyantar da su. Su tattare duk abinda suke da shi su basu ilmi. Duk wannan kokarin suna yin shi ne dan buri da fatan ganin yaran nasu sun zama na gari. Su sami ingantacciyar rayuwa. Amma a karshe sune ake maida 'ya yansu karuwai. Ababen kasuwanci? Tir! Ya Allah dubi halin da Ummynna take ciki, duk saboda bakin cikin gurbatacciyar rayuwar da aka jefa ni a ciki. Yanzu haka iyaye zasu kare a wannan kuncin? Allah ka amshi raina, ni dai ba zan iya rayuwa ina kallon wannan azzalumin mutum da ire-irensa a cikin kasata ba tare da na dauki wani mataki a kansu ba. Ba zan iya ba." Ta kara tsananta kukanta... Ummy wadda ke sauraren maganganun 'yar ta'ta, ta juyo da dakyar. Ta lalubi hannunta ta damke. Sannan ta kakaro kalmomin sunanta ta hada ta kira ta. Ta amsa murya na rawa, saboda tsabar kukan da take. Ummyn tace "Fadwa ni kaina ban goyi da bayan hakan ta ci gaba da kasancewa ba... *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```page 6``` Ta ci gaba da cewa.. " 'Yata ke nake jiyewa, bana so wani abu ya same ki. Amma tunda har kika yi wannan tunanin na tabbata zaki zama mai juriya, na san zaki ja'jirce. Na baki dama 'yata. Ki dakatar da Shugaba Habib da masu sana'a irin tasa in dai zaki iya. Ni kuma zan zamana mai sa miki albarka ko bayan raina. Fadwa kin fadi gaskiya iyayen irin wadan-nan yaran bakin ciki ne zai ci gaba da kashe su kamar yanda yake daf da kashe ni. Ba zan boye miki ba 'yata, bana ji wannan ciwon zai bar ni. Saboda haka na baki dukkanin goyon bayana. Ina goyon bayan manufarki, na kuma baki dama ki fara gwa-gwarmaya. Ki tunkari duk wani azzalumi ki toni asirinsa. Kar ki barsu, kar ki sassauta musu. Rike wannan..." Ta karashe maganar tana damka mata wata karamar laya a hannunta na dama. Tace "wannan layar ta bata ce. Gudummawa ta farko da zan baki, saboda na san wadan-nan maha'intan zasu fara farautar rayuwarki. A duk lokacin da kika matsu, aka rutsa ki. Sai ki matsa ta da bismillah. Da iznin Allah zaki bacewa ganinsu, zaki bayyana a duk inda kika yi ra'ayi. Sannan abu na gaba da zan gaya miki shi ne, ki tsarkake kanki da zuciyarki, ki yi watsi darayuwar da kika yi a England ki buda wata sabuwa a nan. Ki zama mai yawan ibada da kaiwa Allah kukanki. Ki dage da bincike a kan abinda kika sa gaba. Ina kaunarki Fadwa. Ina jinki kamar 'yar da na haifa a cikina. Na gama magana da shugaban gidan nan, duk wasu kudade da na shafe shekaru ina tarawa, na aiki da ma na gudumawa da ake bamu, na mallaka miki su. Ki yi amfani da su wajen tafiyar da aikinki. Ina da wani karamin gida a mai-tama na san kin gane gidan da nake nufi. Shima na mallaka miki shi. Domin ya zama dole ki bar gidan nan, ki nisanta kanki da wadanda suka san ki. Kar ki yarda da kowa sai kanki. Kar kuma ki nemi taimakon kowa sai na Allah. Ke ta daban ce, ni na rene ki. Na sani zuciyarki ta musamman ce. Zaki iya duk abinda kika sa a gaba. Ina miki fatan alkhairi 'yata. Zan zama mai alfahari da ke, idan kika zama *fitilar 'yan-cin mata.* Fadwa ta rungume Ummy cikin tsananin murna da farin cikin goyon bayan da ta samu daga gareta. Ta fara kwarara mata godiya da kyawawan adduo'i. Haka suka kasance har zuwa asuba. Inda ta tashi ta shiga bayi ta dauro alwala, ta fito ta tashi salla bayan da ta lura cewa Ummynta ta samu yin bacci. Ta dade da kammala salla da adduo'inta, amma Ummy ko motsawa bata yi ba. Tunaninta ya bata ramakon bacci take yi, tun da jiya duk basu yi baccin ba. Karfe bakwai dai-dai ta yanke shawarar tashin ta dan ta yi salla a yadda take lallabawa tana yi kullum. Amma inaa. Abinda bata sani ba shi ne Ummynta ta dade da amsa kiran buwayi. Ta tafi inda ba a tafiya a dawo. Tayi bacci ne irin wanda ba a farkawa a doron kasa. Allahu Akbar! Fadwa ta da'da shiga kunci, ta yi kuka kamar ranta zai fita. A karshe aka kai Ummy Amina gidanta na gaskiya. A lokacin ne Fadwa ta san maraici, a lokacin ta san zafin rabuwa da iyaye. Bayan lokaci mai tsayi ta aiwatar da duk abubuwan da Ummy ta bar mata wasiyyar ta yi. Ta karbi makudan kudaden ta loda su a account dinta. Ta hada su da nata. Sannan ta tattare ta bar gidan marayu ba tare da sanin kowa a gidan ba. Kamar yadda Ummy ta bukata bata yarda ta sanarwa kowa shirinta ba. Kawai dai an wayi gari aka ga babu ita a gidan. Hukumar gidan da marayun da suke gidan har zanga-zanga suka yi, saboda batan dabon da Fadwa ta yi. A tunaninsu Shugaba ne ya tura aka sace ta. Ganin haka yasa ta aika musu wasika a rubuce, cewa su kwantar da hankalinsu bata hannun kowa. Kuma a inda take tana cikin koshin lafiya. Daga wannan lokacin ne ta fara binciken sirri, da bibiyar duk wasu ayukka da Shugaba Habib yake aiwatarwa. Daga lokacin ta daura damarar *gwa-gwarmaya* da yakar azzaluman mutane irinsa a cikin kasarta. Zuwa lokacin kuma al'amarin shugaban ya kara habaka. Ya ma daina dibar dalibai da 'ya yan talakawa, ya koma kan karuwan gari. Irin wadan-da suke samun matsalar Auren dole da iyayensu, su baro gidajensu. Da masu haduwa da kaddarar cikin banza, iyayen su kore su. Kasancewar zuwa lokacin sun yawaita sun cika ko-ina. Suna neman mafaka da abinda zasu ci su biya bukatunsu. Sai ya zamana aikin ya daina bashi wahala. Yarje-jeniya yake kullawa da su yana kai su kasashe suna karuwanci. Idan aka dawo sai ya basu dan ihsani a cikin abinda ya samu da su din. A haka yake kara bude musu idon. An fara hawa jirgi ana harka da turawa. Sai suke jin kansu kamar wasu hamshakai. Hakan yasa ya tara karuwai yarurruka dabam-daban. Ya rarraba su a wasu gidajensa na sirri. Sai dai wannan duk a cikin sirri ne. Amma ita Fadwa duka ta san komai game da shi. Wannan shi ne tarihin rayuwar *'Yar gwa-gwarmaya Fadwa* da musabbabin 'yar tsamar dake tsakaninta da shugaba Habib. Mutumin da al'uma suke wa kallon Uba, adali, mai so da tausayin talakawa. Hakan yasa duk garin suka tsani *'yar gwa-gwarmaya* a ganinsu abinda aka fada game da ita gaskiya ne. Wato wasu'yan siyasa ne suke amfani da ita wajen ganin sun shafa masa bakin fenti. Lokacin da ayyukanta suka fara bayyana kuma, sai suka dawo yi mata kallon 'yar ta'adda. *Ci gaban labari...* Washe gari da safe Fadwa ta koma daura damarar shiga gari neman wata damar. Kamar yanda a can ma Chaka (dan ta'addan Shugaba) da yaransa suka shirya tsab dan nemanta bisa umarnin Shugaba. A cikin garin Kano. Haka bangaren Asp Sauwam ma ya tashi da tsare-tsaren gudanar da bincike na musamman a cikin garin dan nemanta. Tun da ya samu tabbacin tana garin. Hotel din nan na sharaton ta kuma komawa, saboda hasashenta ya bata Suhaima kwana zata yi a can. A bangaren cin abinci ta tsaya, inda ta yo odar abin karyawa ta fara ci. Hankalinta na kan mashigar wurin, kasancewar wajen gilas. Daga inda take zaune tana iya ganin duk wanda zai shiga ko zai fita harabar hotel din. Wasa-wasa har karfe sha biyun rana ba labarin ta. Sai ta fara tunanin ko dai tun jiya ta bar hotel din ne? Da wannan tunanin ta mike ta biya kudin abincin da ta ci, sannan ta kama hanyar ficewa. Ranta ya sosu, sam bata ji dadin rashi ganin Suhaima ba. Domin shirinta na yanzu duk a kan karuwansa ne. Tafe take tana sake-sake a ranta. Karaf! Ta ji ta yi karo da mutum wanda bata ma san daga ina yake zuwa ba... *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Wannan shafin tukuici ne ga babbar masoyiyar wannan labarin na``` *'yar gwa-gwarmaya* ```na gode sosai``` *Ikram* ```sakonni da yawan comment dinki sun nuna karara irin so da kikewa labarin. Ba ke kadai bace Iki, nima ina yinki sosai. Ina son mai sona. Allah dai ya bar so da kauna.``` ```page 7``` Babu tsoro ko alamarshi a tattare da ita, ta dago. Sabanin wanda ta yi karon da shi. Alamu sun nuna ya tsorata matuka. Suka kafe juna da ido kowannen su na kokarin tuna inda ya san daya. Ita ce ta fara tunawa, cikin abinda bai fi sakanni ba ta tuno da Ab'ha, (Abba kenan.) Mahaukacin masoyin class mate dinta Hamida a makarantar sakandiren government collage da suka gama. Duk da ya kara darjewa ya zama cikakken saurayi. "Abba kai ne?". Ta tambaya tana nuna shi da yatsa. Ya gyada mata kai kawai ba dan ya gano wace ce ita ba. Sai kuma ya tuna da abinda yake tattalin da suka zube yayin karon da suka yi. Da sauri ya rankwafa ya fara tattare takardu da wasu hotuna da suka fadi a hannunsa. Hakan yasa ita ma hankalinta ya koma kansu. Sai dai kafin ganinta ya sauka garesu ya riga ya gama tattarewa, daya kawai ta gani wanda ya dauko a karshe kafin ya saka a file. Ta girgiza, ta kuma cika da mamakin ganin hoton tsohuwar budurwarsa Hamida daga ita sai pant da bra, tare da wani ba'amurke dake sanye da gajeren wando a bakin ruwa. Ta tabbata ba a dade da daukar wannan hoton ba. Ta kuma kallonsa da mamaki tace "Abba har yanzu baka rabu da Hamida ba?" Wanda ta yiwa tambayar ya kuma zare ido. Duk da alamu sun nuna ya tsorata da tambayar sai dai karfin soyayyarsa ga budurwar tasa babba ne. Ya kalle ta cikin ido yace "in dai ni zaki kira to ki hada sunana da nata. Kamar yadda yake tun farko, ki kirani Ab'ha, bani da sunan da ya wuce shi. Rabuwa da Ha'ab kuma sai dai bayan rai. Na rantse ko zan mutu sai na rabota da wannan kasar da kuma wannan rayuwar. Ba zan daina sonta ba. Still ina sonta a haka". Yana gama fadin haka ya figi jiki ya yi gaba, kamar a fusace. Da sauri Fadwa ta sha gabansa "Ab'ha wai baka gane ni bane?" Ya kuma kallonta irin kallon da ya mata dazu. Tabbas yana ji ya san fuskar amma gogewarta ta hana shi gano ta farat daya. Ta mari kuncinsa da wasa tace "kai mahaukaci Fadwa ce fa. Class mate din Ha'ab dinka a Government collage". Ab'ha ya saki dukkan fara'arsa yace "Fadwa?! Dama kina raye?". Bata tsaya bashi amsa ba ta kama hannunsa, ta ja zuwa hanyar fita hotel din, domin ta tabbata abinda yake bibiya nada alaka da bincikenta. Yana da muhimmanci gareta da bincikenta a yanzu. A karamin nazarinta ta lura har yanzu yana bibiyar tsohuwar budurwarsa. Wadda aka fitar da su tare zuwa kasar England. Tabbas zai mata amfan... Tirjewar da ta ji Ab'ha ya yi ne ta katse mata tunani. Ta kalleshi da mamaki "ya dai?". "Ba zan fita wajen nan yanzu ba Fadwa. Bibiyata ake. Yanzun ma gudowa na yi daga harin wasu 'yan ta'adda". Kafin tace wani abu sai ganinsu suka yi a gabansu. Wasu tsagerun 'yan ta'adda ne kusan su bakwai. Hannayensu rike da adduna. Ab'ha ya juya da zummar guduwa, Fadwa ta kara damke hannunshi dake cikin nata. Idonta cikin a kan masu bibiyarsa. Hakika ta shaide su, kamar yadda su ma suka shaide ta. Yaran Shugaba ne. Ta san su farin sani, domin sun sha kai mata farmaki bisa umarnins... Kafin ta kai karshe ga tunaninta babbansu ya karaso wajen cike da izza. A lokacin kuma suka fara magana "kai Oga. Ka ga wata sa'a, wlh ga Fadwa nan Yar gwa-gwarmayar nan". Jin hakan yasa Chaka ya fito da karamar bindigarsa, tare da saita ta da ita. Yau kin gamu da ajalinki Fadwa, kwanankinki sun kare abin farauta'ta". Gaba daya suka saka dariya, kafin ta katse su cikin daga murya. "Karya kake banza kare, ko da Fadwa zata mutu to ba dai a hannun karnuka irin ku ba". Kafin dukansu su yi wani yunkurin sai suka ji wucewar harsashi da karfi ta kansu. Ya wuce ya daki gilashin kofar shiga sashe na biyu na Hotel din. Asp Sauwan ne da tawagarsa. A take yaran Chaka ma suka fiddo nasu bindigogin, suka fara maidawa jami'an tsaron martani. Suna kokarin ficewa daga wajen. Sai ko aka shiga musayar wuta. Ganin haka yasa Fadwa jan hannun Ab'ha suka kauce a gurin. Cikin sauki suka fice daga Hotel din. Suka bar su nan suna aikawa junansu harsa-sai. Zan ci gaba... *Nasmat* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Slm masoya, ma biya labarin 'yar gwa-gwarmaya. Hakika shafina na yau zai kasance na musamman domin zan sadaukar da shi ne ga wata ta musamman. FATIMA USMAN kanwata. Ina alfahari dake da kuma kwazonki. Fatana shi ne Allah ya kara haskaka min haska-kakkiyar kwakwalwarki amin. Ana matukar tare. 🤝* ```page 8``` Lokaci mai tsayi suka dauka suna musayar wutar, kafin daga bisani 'yan ta'addar su sami nasarar bindige police daya. Su kuma 'yan sandan suka kashe musu mutum biyu suka kama wasu biyun. Hudunsu kuma suka sha dakyar. Bayan Fadwa da Ab'ha sun fita wajen, bata nufi gidanta da shi ba. Wani Hotel din ta samu suka shiga. Ab'ha wanda gaba daya hankalinsa yake a tashe ya kalleta bayan sun zauna yace "wai dama ke ce 'yar gwa-gwarmayar da nake jin labarinta?." Ta sakar masa murmushin nan nata tace "ni ce." A takaice. Tana kurba lemun da suka saya. Mamakinsa ya kara bayyana yace "kaina yana cikin duhu dan Allah ki bani labarin rayuwarki. Kin san bana kasar ina can ina bibiyar ruhina a kasashen duniya." Ta yi murmushi mai bayyana sigar tausayawa ga wanda aka yi wa shi. Tace "Abba kana bani tausayi sosai. Hakika so ya yi maka mugun dabaibayi. Yayin da kaddara ta yi wa rayuwarka karan tsaye. Na tabbata ba zaka iya barin ta ba. Amma ta yaya kake ganin zaka iya samunta a wannan rayuwar?". Ya sauke numfashi kansa yana sunkuye a kasa. Hakika yana cikin damuwa da manyan hadarurruka game da wannan burin, amma giyar so sam, bata nuna mishi zai rasa. A kullum zai samu cikar buri yake gani. Bayan gajeren nazarin maganganunta ya dago kansa cikin sanyin jiki yace "bani da zabi Fadwa. Kaddarata kenan. Ba sai na gaya miki ba, abu ne da kika dade da sani. Son Ha'ab a cikin jinin jikina yake, ba zan iya hakura da ita ba. Ki sani saboda ita na rasa kowa. Abbanmu ne kawai yake tare da ni yanzu. Amma Umma da kannena duk sun tsane ni saboda son ta, da nace matan da nayi. Fadwa na sha yin addu'a, amma son ta bai taba raguwa a zuciyata ba. Kullum hauhawa yake. Bacin sabani da familyna kin ga halin da rayuwata take ciki. Farauta ta ake tamkar nama. Rayuwata ake nema ruwa a jallo." Ya sarara yana shafa file din gabansa. Bata ce komai ba sai kallo da kara nazarinsa da take yi. Ya ci gaba. "Bayan dogon bincike na gano gaskiya. Da gaske ne Ha'ab karuwanci take yi a can. Sabanin karatun da shugaba yace suna yi. Koda ba ke ce 'yar gwa-gwarmaya ba ina da burin nemanta a matsayina na mutum na farko da ya gano gaskiyarta kuma ya yarda da ita. Wlh Fadwa wannan Shugaban azzalumi ne, fataucin yaran mutane shi ya mayar sana'a. Kin ga Ha'ab yanzu ta manta da kowa. Bata tuna kowa, ta mance da shakuwa da zurfin soyayyarmu. Ta manta Abba mahaukacinta. Kaina ya gama kullewa, na rasa mafita, ina son ta har yau ina kaunarta. Na kasa nisanta kaina da ita. Na kasa ficewa daga lamarinta, duk da an nuna karara za'a kashe ni saboda bibiyarta. Ki kalli hotunan nan, rayuwarta take cikin kwanciyar hankali. Shekara daya ina bin rayuwarta ba da saninta ba. Rana daya kuma ta farko da na bayyana kaina gareta cike da yakinin zata saduda saboda ni. Tar-bar da ta yi min shi ne sanar da shugaba ina bibiyarta. Tun a England aka fara neman raina. Dakyar na dawo Najeriya, gashi nan din ma ban tsira ba. Kamar yadda kika kudurta nima na kudurta. Koda zan mutu sai na tona asirin munafikin tsohon nan. Sai na sa shi dana sani. Na fara hada gagga-gaggan hujjoji a kansa. Na kuma ji dadin haduwa dake." Ya dasa aya idonsa a kanta. Murmushi ta yi sannan ta ja hotunan gabanta ta fara budawa. Sai da ta gama sannan ta dago ta kalle shi. "Aiki mai kyu. Kai ka dauki hotunan?". "Eh ni na dauka duka". Ta gyada kai. Takardun bayanai ne a kan yadda suke tafiyar da rayuwarsu a can. Sai hotunan da ya dauka na ita Hamidan a wuraren da take harkokinta da maza dabam-daban. Ta kalli Ab'ha da ya zuba mata ido yana jiran jin me zata ce. Tace "na yarda da kai. Na kuma yarda zaka iya. Kamar yadda ka so, nima na amince mu yi aiki tare matukar rai. Babu sauyin ra'ayi, babu ganin wahala ko wuya a karaya. Mu yi aiki bisa burukanmu babu makawa zamu yi nasara". Ya saki murmushi "na ji dadin haduwa dake Fadwa". Ta masa hararan wasa tace "Yar gwa-gwarmaya dai". Gaba daya suka yi dariya sannan suka hada hannayensu waje daya suka damke tare da fadin "alaka ta fara, aiki zai kankama". *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Wannan shafin naka ne Autanmu, KING BOY ISAH. Zamanawa da daukacin makaranta litattafan hausa online suna matukar alfahari da kai... Kai din na daban ne. Ubangiji ya kara girma da daukaka Allah yasa ka fi haka amin* ```page 10``` Daurewa ya yi ya lalubo nutsuwarsa. Sai da ya fara da gyara murya tukunna yace "ina jinka Sauwam, lafiya dai ko?". Asp ya amsa "lafiya kalau. Dama zan sanar maka ne mun koma karo da Fadwa, a wannan karon ma Allah bai bamu ikon kama ta ba. Amma a tare da ita mun samu wasu 'yan ta'adda. Ga dukkanin alamu babu jituwa a tsakaninsu. Mun yi nasarar kama biyu daga cikinsu. Insha Allah zamu tsananta bincike a kansu, ta nan ne nake sa ran zamu kara gano wace ce ita, su waye suka tsaya mata? Da kuma manufarta. Alamu sun nuna da akwai 'yar tsama sosai tsakaninsu. Da wannan zamu binciki wadan-nan da suke hannunmu dan gano meke tsakaninsu da ita." Ya dasa aya, yana jiran abinda Shugaban zai fada. Shugaba daya zama kamar mutum-mutumi ya fara tsuma. Cikin rawar murya ya fara magana. "Haba dai Sauwam ta yaya wadan-nan 'yan ta'addan zasu amfane mu cikin wannan case? Gwara ma ka sake su su tafi, Fadwa nake son jin ka kama, ba wasu tsageru ba. Batawa kanka lokaci ne kawai zaka yi. Ka sani sarai mugu baya tona aibun mugu. Ba mamaki ma wasu kudin ne suka hada su. Ka yi watsi da wannan kawai ku nemo Fadwa ita ce abar farauta." Ya takaita yana sauke numfashi kamar wanda ya yi gudun mitoci. Mamakinsa ya kama Asp. Kasancewarsa kwararren ma'aikacin tsaro da bincike, ya tsinci alamomi na tsoro da rashin gaskiya a cikin kalaman Shugaba. Bai koma cewa komai ba ya katse wayar. Shugaba ya sauke numfashi yana godewa Allah. Dan shi a zatonsa har an gudanar da binciken ne, sun bayyana sunansa a matsayin wanda ya tura su yin kisa. Ab'ha ya kalli Fadwa dake kallon hotunan manya da kana-nan karuwan da Shugaba yake aiki da su yanzu. A cikin karamin falon hidanta da ya zame musu gurin zama. Yace Fadwa ni kuwa da zaki karbi shawarata da na baki ita. Na tabbata kuma muddin muka yi amfani da wannan shawarar ba karamin girgiza wan-can tsohon zamu yi ba". Ta sauke numfashi zuciyarta na mata tafasa, kamar ko wane lokaci idan tana kallon hotunan. Tana ganin yadda ya kara jefa rayukan 'yayan jama'a cikin bala'i. Ta sauke manyan idanuwanta a kansa tare da cewa "ina jinka". Ya dan shafi gefen kansa. Yana al'ajabin yadda Fadwa ta zama marar fara'a kuma mara son yawan magana. Yace "abinda ya kamata mu yi yanzu shi ne, mu fara sato 'yan matan nan da yake amfani da su wajen bunkasa kasuwancinsa a nan. Mu tanadi waje na musamman inda zamu tara su. Na san wannan ba karamin tashin hankali zai haifar masa ba. Tsakaninmu da 'yan matan kuwa ba cuta ba cutarwa a hankali muna nuna musu illar abinda suke yi, ga rayuwarsu da ta iyayensu har Allah yasa su dawo hanya. Kin ga babu mamaki hakan ya zamo mana wata sauka-kakkiyar hanya ta tona asirinsa." Ya kare maganar idonsa a kanta. Fadwa ta yi shiru tana nazari, a ranta cewa take babu shakka duk kaifin basira da tunanin mace, ba zata taba zama dai-dai da namiji ba. Wannan ita ce hanya mafi sauki da zasu bi su girgiza Shugaba kuma su tashi hankalinsa. Duk da cewa bata da burin da ya wuce jefa shi a tashin hankalin amma sam bata taba kawo wannan ba. Ab'ha kuwa har ya fara cire rai da zata yi magana. Domin ya fara sabawa da wasu halayenta. Sai kawai ya ga ta saki wani lallausa kuma kakkyawan murmushi, wanda tun da suka hadu bai taba ganin irinsa a fuskarta ba. Ta kama hannunsa ta rike gam a cikin nata. Cike da farin ciki tace "har yanzu basirarka tana nan Abba. Hakika wannan ita ce shawara mafi dadi da muhimmanci da na taba ji tun bayan da na fara gwa-gwarmaya. Na gode Ab'ha. Babu shakka tarayyarmu zata zamo makamin tarwatsa zalumcin Shugaba." Ab'ha ya ji dadi sosai. Yadda ta karbi shawarar tashi, har ma ta nuna jin dadinta a fili. "Babu filin godiya tsakaninmu Fadwa, kin manta duk tafiyar daya ce?". Ta yi dariya. Abu mafi tsada a rayuwar Fadwa. Tace "haka ne, sai mu fara shiri. Domin na dade da sanin gidajen da yake tara su". Ta dauko hotunan nan da list na sunayensu suka fara dubawa. Yana budawa tana gaya masa guraren da suke zaune. *01:30am* Karfe daya da rabi na daren ranar. Kamar yadda suka shirya suka fito cikin shirinsu. Ita din tana sanye da bakaken kaya na roba, riga da wando. Sun bi jikinta sun shafe, kai kace a nan aka kirkire su. Sai bakar hular sanyi da ta saka bayan ta tufke gashin kanta waje daya. Takalmin kafarta ma bakake ne irin masu shegen tsinin nan. Sai glass da ta rufe idonta da shi wanda shima dai bakin ne. Wannan ita ce shigar Fadwa a duk lokacin da aiki irin wannan na fitar dare ya same ta. Ab'ha yana cikin kayan sanyi up and down. White in colour. Ya rufe kansa da hular sanyi ita ma fara. Sai takalminsa cover farare. Bai saka wani glass a fuskarsa ba. Haka suka jero cikin takun nuna isa da izza har suka isa gaban wata mota kirar boss dake ajiye a garejin dake ciki matsakaicin gidan suka tsaya. Ba wanda ya yi magana a cikinsu. Suka kalli juna na 'yan dakiku kafin daga bisani suka yi shaking hand, sannan ko wanne ya zaga ya zauna a mazaunin gidan gaba. Ab'ha ne mai tukin ya tada motar a hankali ya silalata suka fice... *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Keep following...* ```page 9``` Bangaren Shugaba kuwa hankalinsa ne ya yi masifar tashi a lokacin da Chaka yake gaya masa police sun kashe masa yara biyu, sun kuma kama wasu biyun. Domin in da akwai abinda yafi tsoro a duniya bai fi tonuwar asirinsa ba. Zaune yake shi kadai a tafke-ken falonsa yana zare ido. Ya rasa yadda zai yi. Ga wani wahalallen gumi dake tsatstsafo masa a duk kofofin gashin dake jikinsa. A haka ya fara jin karar wayarsa alamar kiransa ake. Saboda halin da yake ciki sam bai yi tunanin duba lamba ko sunan mai kiransa ba. Ya daga wayar da guntuwar sallama. Karar tashin dariyar da ya ji ne ya saka shi saurin cire wayar daga kunnensa, ya duba number. (Unknown) ya gani. wannan ya tabbatar masa da mai kiran "Fadwa ce". Ya fada a cikin zuciyarsa. Dan kuwa ya sani ita kadai ce mai kiransa da boyayyiyar number. Kamar zai katse kiran, sai kuma ya kasa. Yana so ya ji me zata ce masa. Ya mayar da wayar a kunnensa ba tare da yace komai ba. Fadwa kam dariyarta ta yi mai isarta sannan ta takaita ta fara magana. "Alh. Habib Shugaba. Gaskiya kana da matukar wayau. Sosai nake yabawa zummarka ta son ganin ka kawar da duk wanda ya fara gano gaskiyarka. To ba ma wannan ba. Na kira ka ne dan tayaka murna na ji an kama karnukan farautarka biyu, bayan da aka aika biyu barzahu. Ba shakka 'yan sandanmu na aiki tukuru wajen ganin sun kawar da ta'addanci a kasarnan. Sosai na jin-jinawa aikinsu. Sai kuma ka bani tausayi..." Mai makon ta karasa maganar sai ta koma kecewa da wata dariyar. Nan ma sai da ta yi mai isarta, sannan ta ci gaba da magana. "Ka san inda kake bani tausayi? Duk da cewa ka sani amma bari in kara tuna maka." Ta yi shiru kamar ba zata yi magana ba. Sai can tace "gaskiya ka bata wayonka wajen barin karnukan nan su san cewa kai suke yi wa aiki. ka san fa tsagerun yanzu sam basu da juriya. Ya kake tunani idan suka ji horo suka bayyanaka a matsayin uban-gidansu? Kai inaaa gaskiya abin ba zai maka kyau ba. Fatan alkhairi Shugaba..". Sai ta karashe cikin dariyar nan tata. Sannan ta katse wayar. Shugaba da ya gama tafiya duniyar mutuwar sassan jiki ya tattara dan ragowar kuzarin da ya rage masa ya motsa hannunsa dakyar ya sauke wayar daga kunnensa. Ya zuba mata ido, kamar mai neman mafita a jikinta. Ya tabbata abinda yarinyar nan ta fada duka zai iya kasancewa. Nan ma ya koma shiga wani sabon rudu, hankalinsa ya kara tashi. Ya mike daga zaune ya fara zarya a falon, yana kai da komo kamar wanda aka saka matarsa labor. Ya rasa inda zai fara. Tun da yake harkokinsa bai taba haduwa da matsala kamar Fadwa ba. Gashi babu hali ya kira jami'an tsaro game da wadanda aka kaman. Yana cikin wannan halin ne wayarsa ta koma daukar ruri. Ya dagota yana kallon sunan mai kiran. A take 'yan hanjin cikinsa suka kada. Gumin da yake yi ya ninku. Ya tattara yawun bakinsa dakyar ya yi musu wata hadiya, ji kake "mukut". Tamkar wanda aka shaki wuyansa kafin ya hadiyi yawun. Ya shafi fuskarsa da tafin hannunsa sannan ya koma bude ido ya kalli sunan mai kiran dan tabbatarwa. Shakka babu Asp Sauwam ne mai kiran. Hannunsa ya shiga kyarma ya kasa daga wayar har ta yanke. Ba jimawa kiran ya sake shigowa, bai san ya aka yi ya dauki kiran ba. Sai kawai ya ji muryar Asp yana kiran sunansa ba ko sallama. "Shugaba kana ji na kuwa?". Da ace da wani a dakin to babu abinda zai hana shi jin kukan 'yan cikin Shugaba... *Ku yi hakuri da wannan, na san ya yi kadan. Ina cikin uzuri ne shi yasa.* Insha Allah gobe zan ci gaba. Kuma in muku da yawa 😜 *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Domin ki kawa ta gari ASIYA ISAH (MAMAN NANA FIDDAUSI) Ubangiji ya raya mana baby rayuwa mai albarka. Sannan ya kara dankon so da kauna da Oga.* ```page 11``` Sannu a hankali yake tukin kamar wanda baya son tafiya. Duk da akwai tsaro sosai a lunguna da sakon garin hakan, hakan bai kawo musu cikas a tafiyar tasu ba. Har Allah yasa suka isa GRA. layi na uku, gida mai lamba ashirin da biyu. Dai-dai nan suka tsayar da motar suka fito. Gabansu gadi duka nufi gate din gidan kamar masu gida. Da sauri ta jiyo ta kifta masa ido, alamar ya koma mota. Bai tsaya komai ba ya juya zuwa mazauninsa. Da zuwa ta kwan-kwasa gate din gidan bayan ta cire hular kanta ta baje gashin a gadon bayanta da gefe-gefen fuskarta. Ta gyara tsayuwa. Shiru ba amsa, sai da ta koma kwan-kwasawa a karo na biyu sannan tsumakakken buzun ya taso yana tambayar "wane ne a cikin daren nan?". Karamar kofar ya bude yana haska ta da fitila. Cikin gurbatacciyar hausarsa yake tambayarta "waye ne kai?". Ta sakar masa murmushi "sannu Audu. Ni ce Bintu kawar Shakira. Wani fati na zo dare ya yi min kusan nan, shi ne nace bari kawai in zo in kwana a nan." Ya kara gyara tsayuwa yana nazarinta. Da ganin yanayin shigarta dai ya san duk sune da masu gidan. Sai dai yanayin tsaro sam ba a bashi damar barin wani ko wata ya shigo gidan bayan mazaunanshi ba. Yace "aa kayi hankuri, wallahi bai bari wani siga". Ta bata fuska "haba Abdu kar ka min haka mana, yanzu in ka hana ni ina zan je in kwana kenan?". Duk ya tabbatar ta san su tunda har sunansa take fadi. Amma fir ya hana ta shiga, saboda tsoro da gudun ya rasa aikinsa kamar yadda aka gindaya masa sharadin. "Kai hankuri yarinya. Wallahi ba laifinmu, laifin masu gida ne". Ya ja baya yana shirin rufo kofar. Ganin zai bata musu aiki, Fadwa ta yi wuf ta shako wuyansa. Kafin ya yi wani yunkurin tuni ta rufe bakinsa da naushi, hade da hular nan tata. Hakan ne ya hana shi yin ihu duk kuwa da cewa ya ji zafin dukan. Ta kai shi gefe ta zaro wata siririyar igiya ta daure hannayensa ta baya ta koma kai masa wani naushin a fuska, wanda ya yi sanadin dakatawar numfashinsa. (Ya suma) ta jefar da shi gefe ta budewa Ab'ha gate din ya shigo da motar ya fito, suka nufi cikin gidan a tare. Daya bayan daya suka fara bude kofofin da suka tarar suna shiga kafin daga bisani suka tsinci kansu a cikin gidan. Gida mai tarin dakuna da kofofi, dole suka shiga bin dakunan daya bayan daya. Duk inda suka shiga sai sun ci karo da 'yan mata uku ko hudu a gado daya suna sharar bacci. A ko wane daki Ab'ha ne yake fesa musu wani sinadarin saka bacci mai nauyi, sai su buge. Su kuma su ja su ratai-ratai su kai su mota. Haka suka dinga yi har Allah ya basu iko suka kwashe duka matan dake gidan-nan su goma sha bakwai. Sannan suka tayar da motar suka tafi. A hanyar su ta komawa kam kamar an share babu kowa a kan titunan, kasancewar dare ya kara tsalawa. Cikin sa'a da nasara suka isa gida, nan ma daya bayan daya suka jido su zuwa cikin babban dakin dake gidan, wanda ba komai a cikinsa sai Capet. Kamar matattu haka suka jere su, sai baccinsu suke a natse, sannan suka fice suka rufe dakin da kye. Ko-wannensu ya nufi dakinsa fuskokinsu dauke da farin cikin samun nasara. Washe gari da safe, kamar ko wane lokaci haka ta fito ta shirya musu abin karyawa, Ab'ha bai tashi da wuri ba, saboda rashin sabo. Bayan sun kammala karin ne suka fara sabon shiri yadda zasu sato ragowar matan da suke a daya gidansa dake Maagana. Kamar dai wan-can haka shima suka tsara yadda aikin zai tafi. Sannan ko-wannensu ya mike suka koma dakunansu dan kara samun hutu. *02:30pm* Labari ya gama baje ko-ina cewa "a daren jiya an sace wasu mata masu zaman kansu guda goma sha bakwai a cikin garin Kano". Tashin hankali! Lokacin da wannan mummunan labarin ya riski Shugaba, sam kasa tsayuwa da kafafunsa ya yi. Al'amarin da ya tashin hankalin uwargidansa Hajiya Laurat da yaranta duk da basu san takamai-man dalilin hakan ba. Kawai dai suna kallon labarun rana a tashar BBC ne suka ga ya fara kyarma daga tsaye yana neman faduwa. Nan da nan su Baffa suka kinkime shi suka kai shi dakinsa, da hanzari aka kira likitansa Dr. Yakub. Ba jimawa ya bayyana a gidan, ya kuwa dukufa wajen ganin ya shawo kan matsalar domin Shugaba abu sai sama yake yi. Jiki na karkarwa. Likitan ya samu nasarar samo dai-daituwar numfashinsa. Sai dai yana cikin mawuyacin hali kamar yadda yace. Ya korawa iyalan nashi jawabin musabbabin ciwon na shi wato, damuwa. Domin kuwa jininsa ne ya hau. Irin mummunan hawan nan da ba a cika so ba. Wanda yake yi a lokaci daya. Ya kare da cewa "a irin haka ne in ba sa'a ba sai kuga mutum ya kamu da mutuwar barin jiki farat daya." Hankulan yaran da matarsa suka kara tashi. Auta Anisa sai kuka take. Likitan yace "ba kuka zaku yi ba addu'ar samun sauki zaku yi masa. Insha Allah nan da dan wani lokaci zai tashi." Ya bukaci daya daga cikinsu ya biyo shi asibiti ya karbowa Alh. Magani. Auta ta mike tana share hawaye. Faisal yace "ki zauna kanwata barin je in karbo". Ta girgiza masa kai alamar aa ita zata je. Baffa ya share mata ragowar hawayen yace "to ku je". Likita ya fice ta rufa masa baya. Sauran kuwa sun kasa fita dakin uban na su. Sun yi cirko-cirko suna kallon yanayin fitar numfashinsa domin ya dan jima da yin bacci. A asibitin Mai jama'a private hospital. Likita ya faka motarsa ya fito. Anisa ma ta faka tata ta fito ta bi bayansa zuwa ofishinsa. Jikinta kana-nan kaya ne riga da wando. Pink in colour. Rigar iya guiwa wandon kuma pencil ne sai siririn mayafin dake sakale a kafadarta, kamar ba 'yar musulmi ba. Likita ya tura aka kawo masa maganin ya bata tare da addu'ar Allah ya bawa mahaifinta lafiya. Ta amsa da "amin". Ta fita. Ta shiga motarta ta tayar ta kama hanyar komawa gida. Ta dan yi nisa sosai har ta sauka daga babban titi, ta kama kebabbiyar hanyar unguwarsu. Sai ta ji muryar mutum a motar yana cewa "ki tsayar da motar nan". A razane ta taka birki a tsakiyar hanyar ko gefe bata iya sauka ba saboda tsorata da ta yi. An gode Allah hanyar ba ababen hawa. Ta juyo da sauri dan ganin mai magana a bayan motarta. Juyowarta ke da wuya aka fesa mata wani abu a fuska, daga nan kuma bata koma gane komai ba. Wanda ya yi mata hakan din ya gaggauta fitowa daga baya ya zauna a mazaunin direba ita kuma ya tura ta a bari daya. Ya tashi motar ya yi ribas ya fice daga unguwar. Ab'ha kenan. Tun shigowarta asibitin ya ci karo ita, a lokacin shi kuma ya zo siyen sinadarin nan mai saka nannauyan bacci da suke amfani da shi ne a asibitin. Ganin haka yasa ya siyi abin da gaggawa ya fito ya yi wa kansa masauki a motarta, kasancewar hankalinta a tashe bata tsaya kulle motar ba. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```page 12``` *Gidan Shugaba* Abu wasa-wasa har dare babu Anisa babu labarinta. 'Yan uwa sai kiran wayarta suke bata tafiya. Hankula sun tashi saboda an kira lokita ya kuma tabbatar musu da cewa tun da suka je ya sallame ta ta tafi. Zuwa lokacin Shugaba ya farka amma babu kwarin jiki. Uwar ce ta gargadi yaran da kar su sanar da shi halin da ake ciki na batan'yarsa saboda ganin halin da yake ciki. Hakan kuwa aka yi. Can tsakaninsu suke ta bulayin bin gidaje na 'yan uwa da abokaninta har karfe dayan dare ba wani labari mai kama da samunta. Sai suka juya akalar neman zuwa asibitoci da police station. Nan ma shiru a ranar Momy Baffa da Faisal ba wanda ya iya rumtsawa. Gaba daya layukanta a kashe sai kuna suke. *Mai tama* Mamaki ne ya kame bakin Fadwa a lokacin da Ab'ha ya isa gidan da Anisa. Farin ciki ya tirnike ta, ta rasa bakin magana ta rasa kalmar furta masa. Wannan wace irin nasara ta fara samu haka? Sai kawai ta rungume shi lokacin da idonta suka kawo kwalla. "Abba kai din na daban ne, wannan wace irin sa'a ce? 'Yar Shugaba a hannunmu? Babu shakka lokaci ya yi da zai dan-dana zafi irin wanda iyaye suke ji game da 'yayan da yake bautar musu ta hanyar safara. Ab'ha ka gama min komai. Fadwa ta jinjina maka. Hakika tarena da kai haske ne, kai fitila e mai haska hanya ga 'yar gwa-gwarmaya. Na gode Abba." Ab'ha wanda ya kusa fita hayyacinsa yace cikin duburburcewa "bab...ba..komai Fadwa ai yi..wa...kai ne." Yanayin da ta ji shi ne yasa ta yi hanzarin raba jikinta da na shi. Tana murmushi ta dauki cup na tea ta shige dakinta. Ya zubawa kofar da ta shiga ido, domin har zuwa lokacin bai gama dawowa hayyacinsa ba. Tun da yake a duniya mace bata taba rungumarsa ba. Haka shima bai taba ba. Amma duk da haka sai ya ji Fadwa daban. Bai taba jin kansa a yanayi kamar yadda ya ji shi yau ba. Wannan ne ya kara tabbatar masa hakikanin mazantakarsa. Ya lumshe ido yana kokarin kawar da abin a ransa. Ya juya shima ya shige dakinsa zuciya dauke da abubuwa. *washe garin* Hajiya Laurat da yaranta sun kasa jurewa lokacin da suka hadu a gurin cin abinci babu Anisa. Tunanin halin da take ciki yasa kuka ya kwacewa dukansu. Uwar da 'ya yan ba mai rarrashin wani. Shugaba kam ido ya zuba musu cike da rashin fahimta yana tambayarsu "lafiya?". Hajiya ce ta yi masa bayani cikin kuka. "Innalillahi wa inna ilaihi raji-un." Haka ya dinga fada kamar wani mutumin kirki. Jikinsa na bari ya lalubo lambar commissioner of police ya fara rattafa masa. Ya katse ya kira Sauwam shima ya gaya masa. Ya kashe ya nemi gidajen TV nashi da na kasuwa ya gaggaya musu. Nan da nan labari ya bazu cewa "an sace Anisa 'yar gidan Shugaba." Talakawa da al'umar gari suka shiga taya su da addu'ar Allah ya bayyana musu ita. Sai raba hotunanta ake a ko ina. Wanda bai san ta ba ma yau ya san ta. Shugaba ciwo ya dawo sabo kwanciyar gida ta gagara dole sai asibiti aka kwantar da shi. *Bayan sati daya* Faifan video mai ban al'ajabi ya bayyana ya kuma yawaita a Jihar kano da kewayenta. 'Yar gwa-gwarmaya ce ta bayyana kanta a matsayin wadda ta sace matan nan masu zaman kansu, wadanda ta bayyana a matsayin ajiyar Shugaba. A ciki ta nuno fuskokinsu duka inda suke ta kuka suna neman ceto. Sai kum maganar Anisa tace su hutar da kansu da wahalar neman ta domin tana hannunta. Tana kuma yi wa Shugaba albishir da cewa ya shirya kallon videon dillancin 'yarsa nan da sati daya. Inda za'a yi cinikinta a sayar kamar yadda yake saida'ya yan al'uma. Daga karshe a lalata rayuwarta kan idonsa. Duk a cikin video na gaba. Wannan videon ya haifar da rudani ga dangi da iyayen Anisa. Haka kuma ya haifar da tace nace tsakanin jama'ar gari. Inda wasu daga cikinsu suka fara yarda da gaskiyar Fadwa, wasu kuwa har yau gani suke wasu makiyansa ne suke dauke da nauyinta. Mafi yawan al'uma dai su kan ce Allah ya taimaki mai gaskiya. To fa an jangwalo masu gari. An baza jami'an tsaro a ko-wani filin jirgi da tashoshin mota. Haka a kan tituna awanni ashirin da hudu suke suna binciken duk wanda zai shiga ko zai fita garin Kano, babu kakkautawa. *Bangaren Fadwa da Ab'ha kuwa* Zan ci gaba. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Keep following...* ```page 13``` *Bangaren Fadwa da Ab'ha kuwa* Abinda masu neman nasu basu sani ba shi ne kwanaki hudu kenan da suka fitar da Anisa daga kasar. Fadwa ce ta tafi da ita ta ganyar kasa suka tsallaka ta kasar Niger. Ab'ha kuwa ya tsaya yana kula da matan da suka kamo din nan. *A kasar Morocco* Zuciyar Fadwa ta gama dakewa duk wani tausayi na 'ya ya mata bata jinsa a kan Anisa, saboda mugun hali da mummunan aikin mahaifinta. Zaune take bisa wata kasaitacciyar kujera, manyan mutane da suka saba da harkar ta dade da saninsu. Sune ta gayyato mutum uku sai Anisa dake tsugune a tsakiyar su tana rusar kuka. A hankali Fadwa ta fara magana da harshen turancin England da ya shiga bakinta ya zauna kamar a nan aka yi shi. Tace "budurwa ce fil a leda ba a taba saduwa da ita ba. Ina uzuri maza ku fara tayi. Ba kuma na son tayin wulakanci. Da akwai sharadi kan wannan danyar yarinyar. Duk wanda ya siye ta zai bani dama na daukar video na saduwar farko da za'a yi da ita. Wannan sharadin wanda ya yarda da shi ne kadai zan saidawa hajata." Ta saka aya tana sararonsu. Abinka da turawa sai duka suka amince. Aka fara ciniki. Kukan Anisa sai kara tsananta yake. Wannan wane irin tashin hankali ne? Ta yaya hakan zata kasance da ita?. Tana ji tana gani aka kammala cinikinta a gabanta aka zubewa Fadwa kudinta kasa ba check ba. Ta dago da narkakkun idanunta ta zuba su bisa yarinyar, ta fara magana a hankali da harshen hausa. "Tun da nake a duniyata ta farko ban taba yarda da ana safarar mata ba, balle kuma in kai ga yin ta da kaina. Amma sanadin mahaifinki na sani. Kamar yadda kike jin kanki yanzu haka na ji a lokacin da ya saida ni ya karbi kudi. Gashi yau nima na yi. Kuma bana fatan kuma aikatawa, sai dai dakatarwa. Idan Allah ya yi miki tsawon ran da kika koma hannun shi sai ki tambaye shi me yasa ya rasa sana'ar yi sai ta raba 'yaya mata da abinda suka fi so? Wannan shi ne raddina farko ga mahaifinki. Yanzu ne zai fara jin asalin dafin saran 'Yar gwa-gwarmaya". Tana gama fadin hakan ta mike tace su tafi. Mutumin yayi gaba hannunsa rike da Anisa, wadda jikinta ya yi sanyi mutuka, yayin da tsoro da tashin hankali suka kara kanainaye ta. 'Yar gwa-gwarmaya! Ta mai-maita sunan a ranta, sai kawai ta fashe da kuka. Domin kuwa ta san ta'ta ta kare. Wani mugun murmushi Fadwa ta saki, sannan ta mike ta bi bayan wanda ya siye tan wato Mr. Mike. Wanda ya tabbatar mata cewa "yanzu-yanzu zai kauda budurcin yarinyar." Tausayi da imani ranar a gefe Fadwa ta ajiye su. Inda ta saita wayar hannunta tana daukar video yadda Mike ya raba Anisa da budurcinta ta karfi. Tana kuka tana fizge-fizge har ta sume ta fita daga hayyacinta. A nan Fadwa ta takaita ta bar musu dakin zuciyarta cike da farin cikin da bata taba tsintar kanta a cikinsa ba tun da ta fara gwa-gwarmaya. Hankalinta kwance ta nufo Najeriya inda ta samu ana nemanta ruwa a jallo. Daga boda ta danna layarta ta bata tare da bismilla. Ta kuwa bace bat! Bata bayyana ko ina ba sai a cikin gidanta. Lokacin dare ne sosai Ab'ha ya yi bacci ta leka dakin da matan nan suke suma ta same su suna bacci. Ga abincin darensu nan wanda wasu sun ci wasu kuma basu ci ba. Ta yi murmushi ta rufe su. Sannan ta nufi dakinta. A daren ta tace video nan ta gyara shi ta maida shi faifan CD. Inda ta ci gaba da yin copy-copy nasa tana tarawa har gari ya waye. Ab'ha ya yi mamakin ganinta ba tare da sanin lokacin da ta shigo ba. Murmushi kawai ta masa ta tambaye shi ya gidan? Ya amsa da "lafiya lau komai normal". Cikin zakuwa ya tambayeta labarin tafiyarta. Ta kwashe duk yadda abubuwa suka tafi fa gaya masa. Kafin ta kama hannunsa suka nufi dakin sarrafe-sarrafensu. Ta kunna video suka fara kallo. Sai a lokacin Fadwa ta dan ji tausayin yarinyar. Sannan a bangare daya zuciyarta ta rage zafi da zogin ciwon abinda wannan azzalumin mutumin ya yi mata. Ta mike ta nufi dakinta tana tuna Ummynta. Da yadda ciwon abinda ya aikata mata ya zama silar tafiyarta. "Ka shirya mutuwa Shugaba." Ta fada a kausashe lokacin da ta hau media ta fara yada videon. Sannan ta tashi ta fita da sauran CD nan ta watsar a kan hanya, kamar yadda ta yiwa wadan-can. Ta koma gida zuciyarta wasai. Zuwa yanzu ta fara shiryawa mutuwa. Ta san ko da yau Allah ya amshi ranta ta fanshe abinda Alh Habib ya yi mata. *06:00pm* Zuwa lokacin ba iya jihar Kano ba, ga baki daya al'umar Najeriya har ma da wajenta sun kalli mummunan videon batsa wanda aka aikata da 'yar Alhaji Habib Inuwa (Shugaba). A ranar gaba daya familyn sai da suka kwana a asibiti. Ranga ranga aka kwashe su a lokacin da suke tsaka da kallon video ko-wannensu ya yake jiki ya fadi sumamme banda Baffa ya rufe kayan kallon nasu da duka har sai da hannayensa suka farfashe. Shugabanni da masu mukamin gwamnati sun shiga rudu. Sun nunka kudade ga duk wanda ya zo musu da Fadwa ko labarin inda take. Ba dan sun san gaskiyarta ba, kawai dan ta cutar da jigonsu, wanda suke wa kallon adali uban nakasassu. Alhaji Habib kwanansa uku a asibiti bai san inda kansa yake ba. Sabanin Matarsa da 'yayansa maza da tun a ranar suka farfado. Ga 'yan jarida sai zarya suke a asibitocin suna son yin magana da shi. Hankula sun tashi tunani ya jigata. Kwakwalwa ta dauki rudu. Abdul Aziz (Baffa) babban yayan Anisa ya yi magana da 'yan jarida cikin kuka da kunan rai inda ya yi rantsuwa ko za'a kashe shi ne, sai ya kashe Fadwa. Wannan 'yar gwa-gwarmayar yace shi ne ajalinta. Faisal kam banda kuka ba abunda yake tun da ya dawo hayyacinsa. Tun a ranar Baffa ya mallaki bindiga da harsasai ba adadi. Ya hana kansa sukuni ya koma kamar wani zararre. Ba abinda yake sai yawo a cikin garin ko-wane bangare bi yake, ba tare da ya san inda zai ganta ba. Haka dare ya riske shi, dole ba dan ya so ba ya kama hanyar asibitin da Abbansu yake. Sai dai kafin ya kai ga isa asibitin shima ya fada tarkon 'yar gwa-gwarmaya. Fadwa cikin shigar nan tata ta dare as usual. Ta tare hanya a matsayin jami'ar tsaro ta cafke shi da laifin mallakar makami ba bisa ka'ida ba. Sannan ta nufi gidanta da shi a madadin ofishin 'yan sanda. A ransa yana mamakin wannan jami'ar tsaron da ba a iya ganin fuskarta. Bangare daya kuma cewa yake ko ma wace ce su je. Ya san ai dole za'a sake shi ne. 🤔 Babbar magana. *Keep following...* *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```page 14``` Ranar litinin da sassafe aka tashi da rudanin rashin ganin Baffa. "Wannan wane irin al'amari ne? Alhaji me ka tarewa yarinyar nan ne? Don Allah ka taimake ni ban ga Baffa ba. Kar ace shima ta raba ni da shi". Hajiya Laurat ce mai wadannan maganganun cikin kuka tana zune gaban gadon da Alhaji Habib yake kai. Hankalinsa ya koma tashi, kamar wanda aka tsikara haka ya mike zumbur ya tashi daga gadon asibitin yana mai fiz-fizge robar karin ruwa dake makale a hannunsa. "Wace irin magana kike haka, ina Baffan ya tafi?". Cikin matsanancin kuka tace "ban sani ba, shima dai fita yayi tun safiyar jiya bamu koma sa shi a ido ba". "Haba inah! Abin ya isa haka kuma, wallahi ba wanda ya isa ya ga bayana ni Habib, sai dai mu ga bayan juna. Kamar ni za..." Karar wayarsa dake ajiye a gefen gadon da ya tashi, ita ce ta katse shi. Hajiya Laurat ta dauko da sauri ta duba ko zata ga sunan danta. Amma sai ta ga (null) boyayyiyar lamba. Hannunta na rawa ta mika masa. Ya karba yana ganin number ya gaggauta danna receive. Kaifin ta yi magana shi ne ya fara. "Ke "yar gidan marasa mutunci, ina dana yake?". Fadwa ta lumshe lumsassun idonta fuskarta dauke da murmushi. Amma a kasan zuciyarta ta ji zafin zagin da ya dannawa iyayenta. Sai dai yanayin tashin hankalin da ta ji shi a ciki ya fi mata komai dadi a duniyar nan. Ta bude idanunta a hankali sannan ta fara magana "gud Alhajina. Na ji dadin da ka yi saurin gano danka yana hannuna. Na tabbata daga yau zaka fara killace kayanka saboda tsoron Fadwa. Ina so ka haddace daga yau duk abinda ka nema baka gani ba ka neme shi a gurin Fadwa. Daga karshe ina maka albishir Shugaba. Lokacin bakin cikinka ya soma. Wutar 'Yar gwa-gwarmaya ta fara cin abinda ka mallaka kenan har zuwa lokacin da zaka bayyanawa duniya asalin gaskiyarka. Dole mutanen nan su san boyayyiyar fuskarka. Na barka lafiya Shugaba... Am... Ka ga na manta fa, danka yace yana gaisheka, ni kuma har yanzu ina kan tunani ne. Idan na gama yanke yaddda zan yi da shi zan gaya maka". Tana kokarin yanke wayar Hajiya Laurat dake sauraronsu tayi wuf ta fizge wayar ta kanga a kunnenta. Muryarta har rawa take ta fara magana cikin kuka. "Dakata mana 'yar nan, dan Allah ki yi min rai ki dawo min da dana. Na san kema 'ya ce kuma uwa a wata rana, ki tuna abinda ke tsakanin'yaya da iyayensu 'yar nan..." Sai kuka ya kwace mata. Jin matar na neman karyar mata da zuciya yasa ta katse wayar, sannan ta zube bisa kujerar dake kusa da ita. Ruf! Ta rufe idonta tana maida numfashi. "Hakika duk wanda ya san darajar iya da abinda ke tsakaninsu da 'ya yensu a bayana yake Hajiya. Ki sani saboda wannan kaunar ta iyaye nake fafutuka. Domin sharewa iyayen da ake fandarar musu da 'ya yansu hawaye. Na sani ke uwa ce. Amma mijinki azzalumin uba ne. Kuma na rantse ba zan bar shi ba". A fili take maganar cikin zafi kamar tana gaban Hajiyar ne. "Mene ne Fadwa?". Ab'ha ya dake gefenta ya tambaya. Bata ce komai ba ta mike ta nufi dakin da ta kulle Baffa a daren jiya. Shugaba da ya zama kamar zararre ya kalli matarsa dake rike da waya a hannu tana rusa kuka. Yace "ki kwantar da hankalin...". Bai karasa ba ta katse shi "a a, kar ka bata bakinka da lokacinka, ka sani babu wata kalmar rarrashi da zata isarwa uwar da ta rasa danta muddun ba mutuwar Allah ce ta dauke shi ba. Ba zan iya hakura ba Alhaji, kuma hankalina ba zai taba kwanciya a wannan takin ba". Shugaba kam ya fara rasa tunaninsa sai zare ido yake, ya ma rasa wata kalma da zai koma furta mata. Can ya tsinkayo muryarta ta ci gaba da magana cikin kuka "Ni wallahi na ma fara zarginka, ina ji a raina wanda aka cuta ne kadai zai iya aikata wadan-nan abubuwa da yarinyar nan take. In ko da laifinka a sanadin lalata rayuwar 'yata ba zan taba yafe maka b..." Saukar wani mahaukacin mari da ta ji a kuncinta, shi ya hana ta cikata kalmominta. Ta dafe kunci tana kallonsa cike da mamaki da tsoro. Cikin karfin hali da 'korewa irin ta mai son faranta kansa, ya fara magana cikin masifa. "Lauratu ashe baki da hankali ban sani ba? Ashe za'a wayi gari ki zarge ni da kanki? Tabbas kuwa mace ba adila bace. Duk duniyar nan babu wanda ya san sirrina sama da ke. Babu wanda ya fi ki kusanci da ni. Amma yau da bakinki kike neman yarda da buyagin makiyana. Kike cewa kina zargina... Ya jijjiga kai, cike da alamar tsabar takaici. Sannan ya dora ...to ke da duk mai bi na da sharri Allah ya fi ku". Ya fizgi jiki ya fice daga dakin a fusace. Hajiya Laurat jikinta ya yi sanyi sosai. Sai a lokacin take jin lallai bata kyauta ba, soyayyar 'yaya ce kai ta ga barin hayyaci har take kokarin saka zargi ga adalin mijinta. Nan da nan ta shiga istigfari tana tubarwa Allah. Shugaba kuwa wayar ma a hannunta ya bar ta balle ta yi yunkurin kiransa. Sannu a hankali ta kai hannunta ga handle na kofar ta mirda bayan ta murza key. Jin an bude kofar yasa ya dago da idanunsa da suka gama rinewa ya zuba ma mai shigowar. Ras! Ya ji gabansa ya yi wani mugun faduwa a lokacin da suka yi ido biyu da ita. Sanye take da doguwar riga dikin gown, ta wani lallausan yadi ja mai ratsin fari. Ba dan-kwali a kanta sai lallausan gashin kanta da ya sha gyara irin na turawa. Kana-nan 'yankunne ne makali a jikin fari kuma kakkyawan kunnenta. Kalar fatarta chocolate ce mai dauke da sirruka. Duk da cewa babu wata kwalliya a fuskar nan ta'ta, amma ba abinda take sai sheki da daukar ido. Ya kasa kauda idonsa ga barin kallonta, tun da ya mallaki hankalinsa bai taba ganin macen da komai nata ya burge shi farat daya kamar na wannan dake gabansa ba. A ransa yace "tsarki ta tabbata ga mahaliccin wannan kakkyawar halittar". Ya dauke kansa dakyar, zuciyarsa na raya masa ya samu abinda shi da iyayensa suka dade suna nema wato matar aure. Babu shakka wannan 'yar sanda ta tafi da imaninsa... Bai kai karshe ga maganar zucinsa ba ta katse shi. "Kai karamin mara kunya, shin ka san inda kake kuwa?". Baffa cikin sanyin muryar da shi kansa bai san yana da shi ba yace "ranki ya dade, na san ina hannun jami'an tsaro ne". Fadwa ta fashe da muguwar dariyar nan ta'ta mai ban haushi ga wanda ya san manufarta tace "shakka babu uban da 'yayan duka kwakwalen jakai ne da su". Maganar ta tunzura Baffa kasancewarsa mai saurin daukar zafi. Sai dai sanin muhimmancin wadda yake maganar da ita a zuciyarsa yasa ya danne "ban gane me kike nufi ba". Ya bukaci karin bayani. Ta girgiza kai "yaro, yaro ne. A yadda naga zafinka a gidan TV sam ban kawo haka zaka yi sanyi a gaban abin nemanka 'yar gwa-gwarmaya ba". Maganar ta saukar masa kamar almara. Kansa ya buga da karfi, lokaci daya tare da ziciyarsa. Ya kura mata ido yana neman gasgata abinda ta fada. Kasancewar duka video da ta sake babu fuskarta sai dai murya. Tabbas ita ce. Yanzu muryar take dawo mishi. Cikin karaji da matsanancin zafin bacin rai ya zaburo mata... Zan ci gaba. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Alhamdulillah na ji dadi na kuma gode da yawan comments da privete test naku a kan wannan labarin. Hakika kuna karawa Nasmat kwarin guiwa matuka. Ku ci gaba da bibiya ni kuma cikin farin ciki zan ci gaba da antayo muku shi.* ~The great gift in this life is a *love* and *care*. U guys give all those to me. I hav no one like u my fans keep following~ 🤝 ```page 15``` Jin ya kasa mikewa daga kan kujerar ne ya tuna masa a daure yake. Ya zubawa sarkar da ta daure shi da ita ido, yayin da bakin ciki ya mamaye zuciyarsa. Ya sake dago da jajayen idonsa ya kalleta yana cewa "banza karamar tsagera. Wannan daurin da kika min ya tabbatar min kina jin tsorona ne, in ba haka ba ki kwance ni ki tsaya a gabana mana. Wallahi kisan da zan miki shi zai zama kisa mafi muni da aka taba yi a cikin duniyar nan". Ya saka aya yana ciccika kamar wani mayunwacin Zaki. Fadwa ranta ya yi masifar baci, ita ma a take launin idonta ya canza. Jikinta har bari yake ta fara magana "lallai kai jahili ne. Kallon me kake min ne? Ka dauka 'yar gwa-gwarmaya kamar ko-wace mace take? To bari a kwance ka din ka yi abinda zaka iya". Ta fice daga dakin a matukar fusace ta nufi nata dakin a ranta cewa take lallai yau ko bata kashe wannan yaron ba sai ta hada masa jini da majina. Ba jimawa ta fito tana huci hannunta rike da daurin makkulansu. Ab'ha dake zaune a falo yana kallon shige da ficenta ya miki ya rufa mata baya, saboda ganin yanayinta. Da isarta dakin kai tsaye ta isa gaban kujerar tana kokarin kwance shi. Tsabar yadda ya kagu ya kashe ta, tun kan ta gama kwance hannunsa daya ya yi amfani da kansa ya buga a nata. Ji kake gum! Dai-dai da shigowar Ab'ha kenan. Ta tsaida abinda take ta dago ta wanke kuncinshi da wani rikitaccen mari, wanda ya sa idanunsa suka fara gani bibbiyu. "Banza mai karamin tunani, ka bari na kwance ka mana. In yaso sai ka fito da dukkan karfin da kake da shi ka kashe ni". Ta koma dukawa da nufin ci gaba da kwance shin. Ab'ha ne ya yi wuf ya rike hannunta tare da mikar da ita tsaye. "Me kike shirin aikatawa haka Fadwa? Ta ya kike tunanin hada karfinki da na namiji? Wannan kuskure ne karki soma pls". Wani kululun bakin ciki ya taso ya tokare mata a makogwaro, wai me maza suka dauki mata ne? Bata san lokacin da ta kai wa Ab'ha wani mugun naushi a fuska ba. Ya yi baya taga-taga ya fadi kasa. Daga lokacin ya daina ganinta sai maganganun da take cikin fushi, da yake ji sama-sama. "Ina namijin yake? Wannan ne namijin? Me kake tunanin samu a jikin da aka gina shi da haramun? Dole in ganar da wannan kuskurensa. Dole ya san ni din ba kamar ko-wace mace bace, burin ramuwa bai bar ni sakankancewa na san dadin jikina ba". Ta juya ta ci gaba da kwance shi. Baffa ya zuba mata ido yadda take zuba masifa. Bangaren zuciyarsa na kokarin yabon yadda fadan ya yi mata kyau. Bangare mafi rinjaye kuwa Allah Allah yake tagama kwance shi ya yi mata kisan gilla. Hakika yau zai kawar da abinda ya hana mahaifinsa da duka familynsa sukuni da walwala, abinda ya jefa rayukansu a cikin bakin ciki. Sai da ta gama kwance shi sannan ta ja da baya ta yi wani irin juyi, lokaci daya rigar nan dake jikinta ta nadi-diye. Ta sa hannu ta daure ta a inda ta taru. Ta daure gashin kanta waje daya ta zuba masa ido tana cewa. "To me kake jira? Bismillah man zo ka kashe Fadwa". Baffa ya yi saurin kauda yabon yadda ta kara kyawu a zuciyarsa. Tsana da kiyayyarta suka mamaye a lokacin da ya tuna video da ta dauka na yadda ake lalata rayuwar gudar kanwarsu Anisa, wadda a sanadinta har yau basu san inda take ba. Ya yi wani rin karaji ya nufe ta da gudu zuciyarsa dauke da mugun nufi. Haka itama ta tare shi cike da burin jiyar da shi asalin karfinta. Nan fa aka kaure da fada babu ji babu gani. Ba wanda yake rike da wani makami a cikinsu, sai dai ko-wannensu na kokarin nuna asalin karfi da kuma kwarewarsa. Burin ko-wanne ya illata abokin fadansa. Naushi da yakuci suke kaiwa junansu ta hannu da kafa, kafin kace me Baffa ya fara jigata. Duk abinda ake dukansa daya bai sami taba Fadwa ba. Da kwarewarta take kare harinsa kuma ta dake shi. Tun yana taga-taga har ya kai ga faduwa, baki da hancinsa duka jini suke fitarwa. Ga wasu manyan gurare uku da ta kumbura masa a ka. Sai a lokacin idon Ab'ha suka dawo da ganinsu dai-dai. Saboda mugun naushin da Fadwa ta masa. Ganin Baffa a kasa tana ball da shi yasa shi hanzarin mikewa. Wannan karon da rarrashi ya je mata. "Dan Allah ki dakata Fadwa, hakan ai kashe shi zaki yi. Ya isa haka pls". Ya rike ta yana jijjigata. Bata ce da shi komai ba ta fizge jikinta ta fice daga dakin, ta bar shi da Baffa ranga-ranga. Ab'ha ya tallafa masa ya mikar da shi ya maida kan kujerar da yake kai ya zaunar da shi. Ya yi laushi sosai har baya gane komai. Kansa ma ya kasa tsayuwa sai lilo yake kamar dan mashalo. Da gudu Ab'ha ya nufi dakin Fadwa. Ya tura kofar ya shiga yana kiran sunanta. A lokacin tana tsaye gaban karamar freezer dake dakin tana kora ruwan sanyi. Sai goge gumi take da wani karamin kyalle dake hannunta. Ta juyo ta zuba masa ido kawai. Shi kuwa cikin rawar murya yake mata bayani. "Guy din nan fa zai iya mutuwa, bai san inda kansa yake ba. Ga baki da hancinsa na zubda jini". Sam bata ji wani tausayinsa ba, amma sai ta ji sam bata so ya mutu ko dan saboda mahaifiyarsa. "Ka je ina zuwa". Iya abinda tace da shi kenan. Ta shige toilet dinta. Shi ko ya koma gurin Baffa da sauri. Ta dauki mintuna goma kafin ta fito a hakan ma ta hanzarta saboda tausayin uwar yaron ba dan shi ko ubansa ba. Ta shigo dakin cikin wata sabuwar shigar. Hakan ya nuna wanka ta yi ta sauya kayanta zuwa wasu kana-nan kaya riga da wando pink colour. Da flat shoe su ma pink. Ta tattare gashin kanta ta daure shi guri daya bayan ta taje shi. Wannan wata baiwa ce da Allah ya yi mata, wato a duk lokacin da ta sauya shiga sai mai kallonta ya ga tafi ta dazu kyau. Karamin akwatin agaji ne a hannunta, ta zuba masa ido cikin wani yanayi. Ita kanta bata san ta illata shi hakan ba. A yadda yake kam babu mamaki zai iya mutuwa. Sai ta ji faduwar gaba ta riski zuciyarta, dan tun da take bata taba yin kisan kai ba. Ga tausayin halinda mahaifiyarsa zata shiga idan shima ta rasa shi. Sai ta ji tana tsoron ta zama wannan mugun sanadi. A dan tsorace tace da Ab'ha "na shiga uku Ab'ha, mahaifiyarsa ba zata yafe min ba in na kashe shi. Pls ka yi wani abu". Ganin ta bashi dama yasa ya dauko Baffa daga kan kujerar nan ya kwantar da shi bisa dogon bancin dake ajiye a tsakiyar dakin. Sannan ya dauko akwatin ya dire. Wani tunani ne ya zo wa Fadwa kasancewar bata da wani makiyi sama da Shugaba a kullum burinta ta saka shi bakin ciki. "Dakata Ab'ha kar ka masa komai, ina zuwa". Ta fada tana mai ficewa daga dakin. Ab'ha ya bita da kallon mamaki al'amarinta ya fara bashi tsoro. Sai kace mai al'janu? Ya tambayi kansa. Bisa dole ya dakatar da aniyarsa yana kallon mawuyacin halin da Baffa yake ciki na rai ko mutuwa. Ba jimawa ta dawo da wayar hannunta ta dauki hotunan guy din guda biyu sannan ta yi murmushi. "Ka yi duk yadda zaka yi ka ceto shi, bana so ya mutu". Tana gama fadin hakan ta juya ta fice. Dan tana da yakinin in dai ba lokacinsa ne ya yi ba Abba zai iya dawo da shi. Tana zuwa da hotunan sai ta dora su kan media kawai a groups na Facebook da whatsapp tare da bayanin ga dan gidan shugaba da ya bata yana hannun 'yar gwa-gwarmaya tana azabtar da shi. Abinka da 'yan social net basa sanya wajen yada ire-iren wannan post din, sai nan da nan labari ya game ko-ina, hotuna suka bazu. Yau ne ranar shiga kotu da sanannun 'yan ta'addan nan da Asp Sauwam ya kama wadanda suka bindige dan sanda daya kuma suka yi musayar wuta da jami'an tsaron. Bayan dogon bincike da azabtarwa sun sanar wa Asp cewa basu da wata alaka da Fadwa basu santa ba sai ta dalilin Shugaba Habib, domin shi suke yi wa aiki. Shi ne ya basu umarnin su kashe ta. Jikin Asp ya yi sanyi sosai, hankalinsa in ya yi dubu ya tashi. Yayinda zuciyarsa ta kasa raba daya biyu. Shin da gaske Shugaba mai laifi ne, ko dan tana neman bata masa suna ne ya yanke wannan hukuncin?. Domin bayan wannan ba abinda 'yan ta'addan suka sani game da shi. Kawai dai yace su kashe masa ita. Wannan ne yasa ya kasa sanarwa kowa sakamakon bincikensa duk kuwa da matsin tambayoyi da yake samu daga 'yan jarida. Baban kotun ta gama cika da batsewa da lauyoyi da kuma masu son jin ta bakin 'yan ta'addan a kotu tunda sun kasa samu a gurin jami'an tsaro. Tuni 'yan jaridu daga bangarori dabam-daban suka hallara. Hilix biyu aka ciko da ma'aikata tare da masu laifin suka faka a kofar kotun. Asp Sauwam ne kan gaba, sai yaransa dake rirrike da masu laifin suna rufa masa baya. Fitowarsu ke da wuya 'yan jarida suka yo musu caa da tambayoyi. Sai dai tun a can headcoter Ogan ya gaya musu kada wanda ya zanta da su. Hakan yasa ragowar 'yan sandan suka shiga ture mutanen suna buda musu hanya har suka shiga kotun. Aka tsayar da masu laifin a inda ya dace kowa ya sami guri ya zauna. Kotu kam ta cika makil, ba masaka tsintsiya. Sahun 'yan jaridu dabam na 'yan sanda da masu kallon shari'a dabam. Kowa da abinda yake cewa, hakan yasa dakin kotun ya kaure da surutu. Ana cikin haka aka buga kofar karamin dakin alkali dake bangare daya a cikin kotun. Tsit! Kake ji ba wanda ya koma magana. Ba jimawa sai ga alkalin ya fito "kooot!".cewar rajistara dake zaune a gaban kotun. Gabaki daya mutanen suka mike dan girmamawa ga alkali. Sai bayan da ya zauna, sannan kowa ya koma mazauninsa. Rajistara ya mike ya karanto karar dake kan layi. Karar dake tsakanin hukumar 'yan sanda ta Jiha da 'yan ta'adda biyu Nura tero, da Hali maiki. Shiru ya biyo baya. Sai da alkalin ya gama duba wasu takardu dake gabansa sannan ya dago ya kalli masu laifin. Dukkansu sanannu ne, kuma rikakkun 'yan ta'adda masu kisa. Ya sauke kansa ya yi dan rubutu sannan ya dago ya bada dama ga wakilin 'yan sandan wato furoskito domin ya karanto yadda al'amarin yake. Furokiton ya mike bayan ya russuna ga mai shari'a ya fara magana kamar haka:.. *Ku ci gaba da bibiyana* *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 16``` "Ya mai girma mai shari'a, hukumar 'yan sanda ta Jiha tana tuhumar, Nura (tero) da Hali (maiki) da laifin ta'addanci. Karya dokar kasa, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, musayar wuta da jami'an tsaro. Har ma da bindige jami'in dan sanda guda daya Abbas Malik. A lokacin da suka zo kashe wata mai suna Fadwa. ma aikatanmu kuma suna kan kokarinsu na kama ta, kasancewarta mai laifi da ake nema ruwa a jallo, wato Fadwa 'yar gwa-gwarmaya." Ya dasa aya a nan ya koma mazauninsa. Alkali ya ci gaba da rubutun da yake tun lokacin da furoskiton ya fara magana. Bayan ya kammala ne ya dago ya kalli masu laifin yace "kun ji abun da mai gabatar da kara yake tuhumarku a kai?". Suka ce "eh". Yace "to kun yarda kun aikata duka abinda ake tuhumarku da aikatawa?". Nan ma ba musu suka amsa da "eh". Nan kana-nun maganganu suka fara tashi kasa-kasa. Kafin alkalin ya dago daga rubutun da yake sai kowa ya kama bakinsa. Ya koma kallonsu yace "me yasa kuke son kashe mai laifi kamar Fadwa?". Hali ya yi shiru, hakan yasa Nura ya fara magana. "Muma saka mu aka yi". Alkalin ya yi dan gajeren rubutu kana ya dago "wa ya saka ku yin kisan kai?". Kansa tsaye ba ko shakka yace "Shugaba ne". "Wane Shugaba?". "Alhaji Habib Inuwa Shugaba". Kotu ta kaure da hayaniyar 'yan kallon shari'a inda a nan a take wasu suke fadin "karya ne! Karya ne!". Har sai da alkalin ya buga gudumarsa sannan nutsuwar kotun ta dawo. Ya yi rubutu a takardar dake gabansa ya koma dagowa. "Mene ne alakarku da shi Shugaban?". "Bamu da wata alaka da shi, kawai dai ya kawo mana aiki ne". "Ku din baku da wani aiki sai kisan kai?". Suka yi shiru suna muzurai. Alkalin ya tattara takardun gabansa sannan ya dago ya kalli jama'ar dake kotun yace "an daga sauraren wannan karar zuwa ranar litinin mai zuwa uku ga watan bakwai kenan. Sannan kotu ta bawa hukumar 'yan sanda ta jiha damar zuwa da Shugaba a zama na gaba". Yana gama fadin haka ya mike ya fice. Ya bar kotu da hayaniyar jama'a. A ranar kam duk jaridun Jihar kusan abinda suka wuni bugawa kenan. "Kutu ta bada damar kamo Shugaba a zo da shi a zamanta na ranar litinin, bisa tuhumar aika 'yan ta'adda su kashe mai laifin nan Fadwa 'yar gwa-gwarmaya. Wanda ya yi sanadiyayyar kashe dan sanda daya". Wannan al'amarin ya razana kowa, inda wasu mutanen suke cewa duk sharri ne. Wasu kuma su ce zai aikata ko dan yadda ta wulakanta 'yarsa, ta yada tsiraicinta a idon duniya bayan ta sace ta. Haka dai mutane suke ta musayar ra'ayi. Da yawansu sun kagu ranar ta zo, su ji me Shugaban zai ce?. *Gidan Shugaba* Gidan ya zama tamakar wurin zaman makoki. Su da suka saba da yin rayuwa mai dadi da yin abinda suke so. Yau gasu an tarwatsa su. An dai-daita su. Gidan daga Hajiya Laurat sai Faisal, dukkansu kuma ba wanda yake iya magana zaune kawai suke jugum bakin ciki na cin su. Yau ga su a gida babu Anisa ba Baffa. Babu kuma wanda ya san inda suke. Alhaji Habib kuwa rabonsu da shi tun da ya fita a fusace daga asibiti. Suna cikin haka wayarsa da ya bari a hannunta ta koma yin kara. Mr. Suwat. Shi ne sunan da ya bayyana, wannan kiran kuma shi ne kira na ashirin da biyu da aka yi da layin. Lambar kasar Rasha ce. Hakan yasa ta yanke shawarar daga wayar ta sanar masa mai wayar baya nan. Ta kai hannunta ta yi receive tare da kangawa a kunnenta. Sai dai kafin ta yi magana aka fara daga dayan bangaren a dan fusace a cikin harshen turanci. "Haba, haba mana Abib. Har yaushe zaka saka ni in yi ta jira? Shi ne ina kiran wayar ma baka dagawa ko? Kaga in dai babu yarinyar nan a kasa kawai ka dawo min da kudina, na gaji da jira". Hajiya Laurat da zuciyarta ke neman bugawa ta daure tayi magana, ita ma da harshen turancin tace "mai wayar baya gida". Mr. Suwat ba kunya yace "idan ya zo ki gaya masa in ba kaya ya bani kudina". Ya kashe wayar ransa a bace. Hankalinta ya yi masifar tashi amma ganin Faisal a gurin yasa ta daure ta hadiye abun. Hakan kuwa bai hanawa gumi ci gaba da tsatstsafo mata ba. Ta mike ta nufi dakinta. Da shigarta dakin ta fara binciken wayar tashi tun daga bangaren test message har zuwa email. Amma bata samu komai mai kama da wannan ba. Hawaye kuwa sai zariya suke a fuskarta jiki na bari. Kar dai zargin yarinyar nan ya tabbata. Kar ace da gaske mijinta safarar mata yake. To in ba haka ba wace yarinya ce ya karbi kudinta da har ake cewa in babu ita ya dawo da kudin?. Bata da amsar tambayoyinta, amma dukkanin alamu sun nuna mijinta na safarar mata ne. "Innalillahi wa inna ilaihi raji-un". Kalmomin da bakinta ke ta nanatawa kenan, a kokarinta na ganin ta samun nutsuwar zuciya. Ta kasa zama ta kasa kwanciya bata toilet bata dakin nata cikinta sai juyi yake. Tana cikin haka Alhajin ya shigo ransa a matukar bace, saboda sakonni biyu na tashin hankali da ya samu. Na farko hoton gawar dansa da ya gani Fadwa ta yada, dan shi a tunaninsa babu rai a jikinsa. Ga kuma labarin kiran da kotu take masa ya wanke kansa a ranar litinin, da ya riske shi. Hajiya Laurat ta yi iya kokarinta wajen ganin ta boye tashin hankalinta. Ta masa sannu da zuwa bai amsa ba. Tace cikin sanyin jiki "an yi ta kiranka a waya baka nan, musamman wani Mr. Suwat da ya maka kira sun fi ashirin. Shi kam saboda yawan kira ma sai da nasa aka daga aka ce masa baka nan". Da sauri ya kalleta "wa ya daga wayar?". Tace "Faisal ne. Yace mutumin yace in babu kayan ka mayar masa da kudinsa man". Wani gwauron numfashi ya sauke cike da godiyar Allah a ransa. Sannan yace a diririce "su turawan nan sam basu da hakuri, da zarar abu ya hada ku sai su yi ta matsa maka". Yana kokarin fita ta jefa masa tambaya "kasuwanci ka fara Alhaji?". Tambayar ta zo masa a ban-barakwai ya kalleta da mamaki "au da baki san ina kasuwanci ba?". tace "wallahi ban sani ba, Allah ya sanya alkhairi" yace "amin" yana danna kiran wayar tare da ficewa. Dakinsa ya nufa kai tsaye. Da sauri ta mike ta bi bayansa da sanda. Saboda zuciyarta ta kasa hakuri lallai tana son sanin gaskiyar mijinta. Ya murda kofar ya shiga yana magana kasa-kasa a wayar. Dai-dai kofar dakin ta tsaya. Dukda bata jin me yake cewa sosai amma ta tabbatar da Suwat din ne yake magana, dan taji yana bashi hakuri. Ko matsowa ya yi oho, ta dai ji muryarsa ta fito sosai yana cewa "kai matsalarka kenan wlh. Na gaya maka yarinyar nan an sace ta tare damatan nan da aka sace min. Amma ka nace sai ita. Ka bari in kawo maka wata ka gwada ta, na tabbata zata fi maka waccan ma. Domin wannan mai zafi ce bata dade da farawa ba". Bata ji me aka ce masa a cikin wayar ba, ta dai ji yace "to ko kai fa, gobe zan turo maka ita ka tare ta airport. Saboda ni banida lokaci yanzu, ina cikin wata damuwar". Duk a cikin harshen turanci yake maganar. Jin kafufuwanta na rawa yasa ta yi gaggawar barin wajen tun basu kasa daukarta ba. Da taimakon Allah ta isa dakinta saboda duhu-duhu da idonta ke gani. Addu'a kam duk wadda ta zo bakinta yi take. Wannan wace irin masifa ce? Ashe dama haka Alhaji yake? Ashe yarinyar nan mai gwa-gwarmaya a kan gaskiyarta take? Innalillahi wa inna ilaihi raji-un. Sai ta fashe da kuka. Nan da nan zazzafan zazzabi ya rufe ta, jikinta sai kyarma yake yana ciccira. *Maitama* Bayan dogon lokacin da matashin likitan ya shafe a kansa. Baffa ya dawo hayyacinsa, har ma ya shiga baccin dole. Da dare misalin karfe takwas ta shirya zama da matan nan da suka sato, wadan-da tun da suka zo gidan basu taba ganinta ba. Suna zaune cirko-cirko aka budo kofar aka shigo. Gaba daya suka dago tare dan jin wani lafiyayyen kamshi da ya cika dakin, sabanin kullum idan mai shigowar ya zo. Ganin mace ya basu mamaki matuka. Hakan yasa suka kara maida hankali gareta. Kujerar robar da ta shigo da ita ta ajiye ta zauna tana fuskantar su. "Sannunku 'yan uwa, kuyi hakuri fa, na tara ku nan amma ban samu muka hadu ba. Na san ba wadda ta san ni a cikinku. Sai dai na san zaku san sunana. Fadwa nake 'yar gwa-gwarmaya. Na kawo ku nan ne domin ganar da ku asalin batan da kuke kai. Ku mata ne, amma har yau baku san daraja da martabar da 'ya mace take da ita ba. Mafi yawan mata sun kare kansu da mutuncinsu. Amma saboda ire-irenku matan titi, ana yi musu kallon wulakanci. Irinku mata masu zaman kansu ku kuke karya darajar 'ya mace a idon duniya. Shin ku bakwa kishin jinsinku ne?". Ta takaita tana kallon fuskokinsu da suka yi la'asar. Ganin ba wadda ta yi magana yasa ta ci gaba. Nan da kuke gani na, na tsinci kaina a kuncin rayuwar da ya nunka wanda ko-waccenku ta taba shiga. Na rasa mutuncina, alfaharina. A lokacin da yake daf da amfana ta. Ni marainiya ce, wadda ta taso da burin yin karatu mai zurfi don inganta rayuwarta. Hakan yasa na tilastawa kaina karatu, ba dare ba rana. Kwazona yasa makaranta da iyayen rikona suke alfahari da ni. Ni kuwa ina yin wannan fafutukar ne dan samawa kaina kima a idon duniya, na taso da burin gwadawa 'yan uwana marayu cewa babu maraya sai rago. Amma kafin cimma wannan burin Uban-gidanku ya ruguza rayuwata. Ya yiwa burukana kisan gilla. Kutsen da ya yi a cikin rayuwata da nufin taimako shi ya maida ni yadda kuka ganin nan. Shugaba Habib ba karamin makiyi bane ga mata. Ku sani gatan da yake yi muku ba so bane, ba kuma taimako bane, kasuwancinsa kawai yake ingantawa da ku. Yayin da ku kuma a kullum kuke dada nisanta kanku daga rahmar Allah. Kuke fama da bakar addu'ar matan kirki bisa bata musu suna da kuke. A kan karamin laifin da bai kai komai ba ku baro gidajen iyayenku. Ku bar duka danginku dan kuna jin da akwai abin kudi a jikinku. Kun manta wannan abin na dan lokaci ne? Kun manta kuruciya ke karuwanci?". Ta koma sararawa tana kallonsu. Ba wadda ta yi magana jikinsu kuma ya yi sanyi sosai. Ta jijjiga kai tace "ni mai son ku ce, mai matukakar kaunar ku. A rayuwar da ta rage min bani da burin da ya wuce inga na samawa mata 'yanci. Burina a wayi gari babu karuwa a kasar hausa. Ya zamana duka matan duniya sun san matsayi da darajarsu. Ko-wane namiji ya wahala ya biya sadakinki kafin ya mallake ki. Wannan shi ne cikar kimar mace. Ba wai ta zama bola abin zuba sharar ko-wane fasiki ba Yanzu ku kalli nan". Ta danna musu play ga TV dake dakin wanda ta riga ta gama saita komai. Hoton video ya bayyana yadda aka keta haddin Anisa 'yar Shugaba. Duka sun gane ta, suka shiga kallon-kallo. Fadwa ta kashe TV ta koma fuskantarsu. "Da gan-gan nasa aka yi mata haka. Domin shi ma ya ji yadda iyaye suke ji, a lokacin da yake dora musu 'yaya a kan turbar karuwanci. Saboda wannan da kuka gani kwanakinsa uku a asibiti bai san kansa ba. Kun san saboda meye? Saboda ita tashi ce, ya san darajarta, yana son mutuncinta. Ku kuma ya dauke ku dabbobi wadanda basu da iyayen da zasu cutu kan rayuwar da suke. Da yawa a cikinku nan bakin cikinku zai kashe iyayenku..." Tun bata karasa ba wata a cikinsu ta fashe da kuka. Sannan ta taso daga inda take zaune ta nufo inda Fadwa take. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Godiya mai tarin albarka gareki MAMAN ISLAM na gode da yabo, da tarin adduo'inki gare ni. Fatana shi ne Allah ya bar zumunci da kaunar juna* ```Ki sani ina sane dake a cikin jerin masoyana, ana matukar tare``` 🤝 ```Page 17``` Da zuwa ta zube a gabanta, tare da kama kafafuwanta ta soma magana cikin kukan... "Hakika Anti ke mace ce da kika san darajar mata. Da ace duka mata zamu yi koyi dake, da duniya ta tsarkaka, da masifun da muke ciki sun takaita, da bala'in da ake saukar mana ya ragu. Domin a yau a halin da muke ciki babu abinda aka mayarwa hankali kamar zinace-zinace. Wallahi Anti safarar nan ta mata da ake kar ki so ki ga yadda ake yi da su. Da yawa daga cikin mu ma ba ta inda Allah ya halatta ake amfani da mu ba. Kazantar ta girmama, babban tashin hankalin ma shi ne, ki ji, ko ki ga masu daukar nauyin matan suna tura su yin karuwancin. Da yawa a cikinsu manyan mutane ne, masu kima da daraja a idon al'uma. Wadanda ko sunansu aka kira a cikin masu laifin ba zaki yarda ba. A yau su ne suke bautar da 'yayan talakawa masu karamin karfi. Wadanda 'yayansu ke barin gidajensu a sanadin yin cikin shege, ko auren da basa so (auren dole). Da kuma masu samun wani sabanin daban tsakaninsu da iyaye. Wanda wannan kuskuren namu ne mu da iyayenmu. Wasu iyayen su suke korarsu suce sai sun bar gidan, wasu kuwa ba ma da sanin iyayenba suke lallabawa su baro gidajen saboda gudun auren wanda ba shi suke so ba. Anti da haka rayuwar 'yaya mata take fara lalacewa, a farkon fitowarmu wahala muke sha sosai, domin ko abinda zamu ci wahala yake mana. A haka ne muke samun masu neman mu fasikanci, tun muna jin tsoron yi har mu fara. Sannu a hankli mu samu muhalli, kudi da ababen more rayuwa. A cikin haka ne muke haduwa da irin su shugaba. Wadanda ke kwadaita mana duniya da kyale-kyalinta. Sai muga ai da wanda muke a nan da wanda zamu yi a can duk karuwanci sunansa. Wannan ne yasa bama shayi ko shakkar amsa kiransu. Ya zamana har ma dadi muke ji idan aka zabe mu, domin kudaden da muke samu a can sai mu shekara a nan bamu same su ba. Wannan ne yake sawa muke biyewa masu yin safara, da saninmu muke bada kanmu gare su. Amma a yau Allah ya kawo mana ke, babu shakka ke *fitilar 'yan-cin mata* ce. Kin haska ni, na kuma ga tarin kazanta da koma bayan da nake ciki. Anti Fadwa na bada kaina gareki, daga yau an daina amfani da ni wajen yada zina a doron kasa. Na yi niyyar tubarwa mai duka. Tare da neman gafararsa bisa laifukana na baya". Ta karashe maganar tana tsananta kukanta, tare da kankame kafafuwan Fadwa da take rungume da su. Kafin Fadwa ta ce wani abu, ta kusa da ita ta fara magana... "Babu shaka a maganar Zainab, iyayenmu ma suna da rawar da zasu taka, domin rage yaduwar karuwanci a kasarmu. Wannan rawar ko ita ce: su guji korar 'yayansu mata daga gidajensu don kaddara ta afka musu, ko don sun ki bin zabinsu ga aure. Idan aka samu haka hakika za'a rage masifu. Sannan kuma mu mata mu kiyaye, kurciya ta daina fizgarmu muna yin abinda muke so. Wlh mata muna cikin hatsari. Nima daga yau na tuba, ina bayanki. Ki ci gaba da haska muna hanya, yake wannan *fitilar*". Ta miko hannayenta ga Fadwa. Fadwa ta amsa ta rike ta gam. Haka dai da guda-guda suka yi ta bada kansu gareta. Duka su goma sha bakwai din-nan babu wadda ta juya bawa. Allah ya yi musu rabo sun yarda har cikin ransu cewa karuwanci koma baya ne, kuma masifa ne ga rayukan mutane, har wadanda basu ji ba, basu gani ba. Domin ita masifa idan zata sauka ba kan iya masu laifin take tsayawa ba. (Shiyasa a kullum idan kaga laifi ba a so ka kauda kai dan kai baka aikatawa, an fi so ka tsaya ka yi iya kokarinka wajen ganin ka dakatar da shi. To ko da abin yafi karfinka ka riga ka samu ladar. To balle kuma ka yi nasarar dakushe shi. Allah yasa mu dace amin.) Farin ciki mara misaltuwa ya kama Fadwa, har ta rasa bakin magana, sai wasu siraran hawaye dake bin kuncinta. Ta kalle su, kallo na jin dadi tace "alhamdulillahi dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, madaukaki. A yau ina cikin farin cikin mara misali, dalilin wannan goyon bayan naku. Domin da gudumawarku ne zamu samu dukkanin hujjojin da mahukunta suke bukata domin gurfanar da Shugaba a gaban kuliya. Ta ware hannayenta aiko duk suka yanyame ta, ko-wannensu na cike da farin ciki. A wurin ta ware guda takwas daga cikinsu, wadanda tauraruwarsu ke haskawa, kuma su ne Shugaba yafi ji da su a kasuwar tashi ta sake su. Saboda ta san muddin ta sake su duka zai gano shirinta a kansa. Bayan ta gama shirya musu yadda zasu dauko mata sirrukansa irin na harkarsu, ta bawa ko-wacce daga cikinsu kayan aiki, sannan ta dora su a hanya. *3:56pm* Wayar Shugaba Habib ta fara ruri. Kishingide kawai yake yana saka da warwara. Tunanin 'yarsa Anisa da halin da take ciki ya addabe shi. Sai juyi yake yana neman abin yi. Hakan yasa bai yi wani jinkiri wurin daga wayar ba. Lambar Umaima ya gani. Daya daga cikin matan nan da Fadwa ta sace masa. Da sauri ya daga wayar yana kiran sunanta. Ta amsa da kyar ta fara magana cikin yanayin galabaita. "Shugaba ka taimake mu, gamu nan mun gudo daga hannun azzalumar nan, amma bamu san inda muke ba. Muna cikin wani hali dan Allah a kawo mana dauki". *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ _Alhamdulillah ala kulli halin_ *Assalamu alaikum masoyana, masoya wannan labarin na 'YAR GWA-GWARMAYA. Babu shakka na san kun nuna so da kauna kuma kun jira. Ku sani ba dan ciwo ba da babu abinda zai tsayar da ni. Da wannan shafin nake muku albishir cewa na dawo bakin fama. Da iznin Allah zaku ci gaba da samun labarin kullum, kamar yadda aka saba. Na riga na gamsu cewa abinda kuke nuna min shi ne asalin abinda ake kira kauna. Ku sani, ku kara sani, nima nan ina kaunar ku duka. Allah ya bar zumunci ya yi karko amin.* _Nasmat ta gode!_ ```Page 18``` Shiru ya yi, yana nazarin maganarta, kafin daga bisani tunani ya zo masa da mafita. "Umaima." Ya kira sunanta a dan gajarce. "Kin sani sarai cewa ba zan iya zuwa ko turo wani daga bangarena ya taimake ku ba saboda gudun zargi. Amma ki jira yanzu zan turo muku lambar jami'an tsaro, ku neme su, su zasu zo duk inda kuke su dauko ku a saukake". Yana gama maganar ya kashe wayar, sannan ya tura mata test mai dauke da number Asp Sauwam. Ba bata lokaci ta kira lambar. Shima dai a galabaice ta yi mishi bayanin halin da suke ciki. Nan da nan kuwa ya tashi ma'aikatansu ya tura su inda ya gano a can suke ta hanyar yin (tracking) din number da ta kira shi da ita. Shugaba ya kasa zaune ya kasa tsaye. Sai kai komo yake yana jiran jin yadda zata kaya. A haka dansa Faisal ya same shi. "Kai lafiya ka fado min daki ba ko sallama?". Ya tambaya yana kallon yanayinsa. Shi kuwa cikin rudu da tashin hankalin da yake ciki yace "Dady ka taimake mu. Momy ce ba lafiya, gata can kamar zata mutu". Ya waro ido da alamar al'ajabi. Bai koma cewa komai ba ya nufi dakinta da sauri-sauri, gudu-gudu. Faisal din ya rufa masa baya yana sharar kwalla. Halin da ya same ta ciki ya yi matukar razana shi, bata iya magana, ga wani jijjiga da jikinta ke yi. Sam bata san waye a kanta ba. A take ya ajiye mamakinsa gefe Faisal ya taimaka masa suka kinkime ta zuwa mota. Driver ya ja su suka nufi asibiti. *Police station* Linda da Zainab, da sauran 'yan matan nan ne durkushe a gaban Dpo bayan da jami'an 'yan sandan suka ceto su a cikin wani babban jeji. Bayan ya gama rubutu a file din dake gabansa ya dago ya kalle su. "Wacce ta yi garkuwa da ku tace ku ajiyar shugaba Habib ne, shin ya wannan zargin yake?". Wata mai suna Aysha ta amsa "karya take yallabai, mu bamu da wata alaka da shi". Ya jijjiga kai. "To yanzu ina ragowarku suke, a wane hali kuka baro su?". "Suna can hannunta yallabai, kuma a gaskiya suna cikin wahala. Mu kanmu yin Allah ne kawai ya tsiratar da mu". "Shikenan duka zaku koma muhalkanku, hukuma kuma zata ci gaba da bincike domin gano inda ragowar suke. Zaku iya tafiya." Suka yi masa godiya suka fita. Hankalin Shugaba ya rabu kashi-kashi. Ga matarsa kwance a asibiti bata san inda kanta yake ba, ga zuciyarsa ta kasa hakura da tunanin halin da 'yarsa Anisa da Baffa suke ciki. Ga kiraye-kirayen turawa a bangare daya, wadan-da dayawa a cikinsu ya karbi kudadensu ne kan cewa zai turo musu yara. Duk ya furgice ya yi wani zuru-zuru da shi. A lokacin ya sami sakon Umaima cewa sun koma gida su takwas da suka gudo, ragowarsu kuwa suna hannun 'yar gwa-gwarmaya. Yana goge sakon likitan dake kula da ita ya fito ya kira nurse suka koma ciki da sauri. Faisal kam banda kuka ba abinda yake. Jimawa kadan likitan ya fito yana sanar musu ta sami bacci. Ya kuma bukaci ganin Alhajin a ofishinsa. Bayan sun je ne yake sanar masa damuwa ce silar ciwon matarsa. Hakan bai bashi mamaki ko yasa yayi wani tunani ba saboda sanin halin damuwar da dukkaninsu suke ciki na batan 'ya yansu. Addu'ar samun sauki suka yi mata shi da likitan, sannan ya yi masa sallama ya fita. Daga asibitin ya wuce gida ya yi wanka ya canza kaya, sannan ya dan sami nutsuwa ya kira wayar gidan da 'yan matanshi suke dan raba musu aiki. Amina ce ta daga wayar, wayar da take kan recording. Ta gaishe shi cikin girmamawa ya amsa. Kana yace "ki gayawa Aysha ta shirya yau da yamma zata tafi Mexico, Umaima kuma da sassafe zata wuce Rasha. Zainab ta tafi Dubai, ke kuma Canada. Sauran su jira zuwan kasuwa. Zan turo wa ko-waccen ku lambar wanda zata hadu da shi. Ku kasance cikin shiri bamu da lokaci sai kirana suke". Ta amsa da "to". Suka ajiye wayoyin. Ta isar da sakonsa ga duk wadanda ya abmbata. Nan da nan suka hau shiri cike da murnar samun dama. Dukkaninsu sun sani wannan shi ne aikin karuwancinsu na karshe dan tsaida shaidu da manyan hujjoji kamar yadda suka tsara da Auntynsu Fadwa. To fa 🤔 *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 19``` *Barka dai masoya makaranta wannan labarin. Ina yi wa kowa da kowa barka da wannan lokaci. Har yau dai hakuri nake bawa masoya kan tsaiko da ake ta samu ga wannan labarin. Wanda dukansu suna samuwa ne bisa manyan dalilai. Na farko na hadu da matsalar rashin lfy, bayan dawowana kuma sai matsalar waya. Wadannan abubuwan su ne suka yi mini katanga da ku da wannan labarin. Gabadayanku ina sonku kamar yadda kuke so na. Babu shakka masoya abin alfari ne ga ko-wane tauraro. Ina alfari da ku duka. Nasmat ta dawo, labarinku ma ya dawo ku mu je zuwa. 😎* Washe gari dukkaninsu suna kasashen da aka bukaci su je. Aysha ce ta fara kammalawa a kwana dayan. Bayan ta gama maida rigarta ta kalli tsumakakken baturen da ya gama amfani da ita yake saka kaya tace cikin turancinta da bai gama kama bakinta ba "wai tafiya zaka yi, kudin aikina fa?". Busashshen baturen ya kalleta da mamaki yace cikin ingantaccen turanci "wannan wace irin magana kike kamar wata bakuwa? Kudinki kam tun kafin ki zo suka sauka a asusun mai gidanki Alaji Abib". Yadda suke kiransa kenan. Aysha ta wayance da cewa "Oh! Yi hakuri, na manta ne saboda uzuri na bukatar kudin da nake ciki". Baturen mai suna Michale ya daga kafada irin ko a jikinsa din nan ya fice yana mata sallama. Ta sauke numfashi tana mai kashe camera da ta kunna tana daukar maganganun da suke. Ta mike cike da murna tana hada kayanta dan komawa gida Najeriya. *Ranar assabar a maitama* Bayan ta gama motsa jiki ta fito da nufi komawa dakinta, sai ta tsinci kanta da son ganinshi da halin da yake ciki. Duk da Ab'ha ya sanar mata cewa guy din ya warke sumul. Kawai ta ji ne tana son ganinsa ne. A hankali ta nufi kofar dakin da yake cikin takunta na cikakkiyar mace mai ji da kanta. Ta mirda kofar bayan ta murza key, ta tura ta shiga. Baffa da idonsa suke kan kofar tun da ya ji ana taba key ya zubawa mai shigowar ido. Shi a zatonsa Ab'ha ne domin rabonsa da ganin Fadwa tun ranar da wannan tsautsayin ya gifta ta masa dukan kawo wuka. Amma Ab'ha kam kullum suna tare, shi yake kula da abincinsa. Sun saba da shi sosai fiye da kima. Ita da shi duka ba wanda ya yi magana, sai dai dukkaninsu sun zurfafa ga kallon junansu cikin wani irin yanayi. Ita ce ta fara yin jarumtar kauda kanta ga barin kallonsa tana mai jin haushin zuciyarta kan yadda take yabawa da kebance kyan zubi da halittar Baffa a kan duk wani da namiji da ta taba gani a rayuwarta. Bata san shi ba sai a kan wannan abin na ubansa, amma zuciyarta tana nuna shi daban ne da ko-wane namiji. Take haushin kanta ya fara kamata, sai ta ga kamar yana ganin halin da take ciki. Da sauri ta juya da nufin barin dakin ba tare da tace komai ba. Har ta kama handle na kofa zata murda ta ji sautin muryarsa cikin sanyi da tausasawa yana cewa "dakata mana Fadwa, ba dan ni da nasabata ba ki tsaya ki saurare ni domin Allah". Cak! Ta ja ta tsaya, tare da dakatar da bude kofar da ta yi niyya. Babu wani kwakkwaran dalili kawai sai ta ji jikinta ya yi sanyi. Ko dan yanayin yadda ya fitar da maganar ne?.. Ci gaba da maganar da ya yi ne ya katse mata tunani. "Ki yi hakuri Fadwa. Hakika na sani idan kika kalle mu ta fuskar nasaba da tushe sam ba mu can-canci ki yi mana afwa ko rangwame ba. Amma ina so ki kawar da duk wadannan. Ki kallemu a matsayin al'uma, 'yaya marayu wadanda basu da uba a duniyar nan. Fadwa ki dubi Allah da darajar Annabinsa ki dawo mana da Anisa. Da can a baya ina miki kallon azzaluma mara imani wadda ake biya kudi tana cutar da mahaifina. Amma a yanzu da Allah yasa aka yi walkiya ta haska idona na ga komai Fadwa. Abokin aikinki ya gaya min komai ya kuma nuna min tsayayyin hujjojin da suka saka na yarda da ku, na ji bayanai dabam-daban a bakin 'yan matan nan da suke nan. Fadwa na gano mahaifina da halayyarsa su suka saka kike yin duk wani abu da kike. Har ga Allah ban ga laifinki ba, mutumin da aka zalumta kamar ke babu abinda ba zai iya yi ba. A yanzu na san waye mahaifina, na san cikakkiyar gurbatacciyar sana'arsa. Na tsane shi, na tsani halayyarsa. Bana fata ko burin a koma kiransa ubana, bana son ko-wace alaka ta koma hadani da shi na tsane shi." Ya matse idonsa da karfi wasu zafafan hawaye suka silalo zuciyarsa cike da nadama da dana sanin zamowa daya daga cikin 'yayan Alhaji Habib. "Ban san ya kike ji ba a matsayin ki na wadda aka batawa rayuwa, aka raba ta da mutuncinta ta karfi. Amma na san yadda ni nake ji a matsayina nan yaya, kuma dan uwa ga wadda irin hakan ya faru da ita. Uwa ce kawai ban san yadda ita kuma zata ji ba." Ya koma matse idonsa domin rage musu nauyin hawayen dake ta turereniya da juna a cikin su. "Fadwa ki dubi Allah ki dubi halinda mu da Momynmu muke ciki ki dawo mana da Anisa. Wallahi na rantse miki a yanzu bana ganin laifinki. Mahaifina shi ne ya assasa komai kuma shi ne mai laifin. Na roke ki da Allah ki dawo da wannan 'yar ga mahaifiyarta." Ya karashe maganar cikin rishin kuka. Take ta ji wani iri ba dadi. Bata juyo ba, kuma bata ce komai ba. Ta bude komai da sauri ta fita. Baffa kuwa kansa ya daga sama ya ci gaba da kuka cikin kuna da zafin zuciya. Kukan da yake jin yinsa zai iya rage masa wannan zafi da nauyin da yake ji bisa kirjinsa. Da zuwa ta fada kan faffadan gafonta, mai laushi da kyan shimfida. Ta lumshe manyan idanuwanta tana tariyo abinda ya faru, sam bata yi tsammanin yaron nan zai fahimta kuma ya sauko cikin sanyi haka ba. Mamakinta shi ne yaushe ma Ab'ha ya iya wannan jawabin da kokari na ganar da da laifin ubansa? Tunawa da maganganunsa yasa wasu siraran hawaye zariya kan kyakkawar fuskarta. Sosai kalamansa suka fama mata raunin zuciyarta, wanda ya fara bushewa. Tunawa ta yi da Ummynta uwar riko ba ma wadda ta yi dawainiyar kawota duniya ba. Ta amsa sunan uwa domin har ta koma ga Allah da tabo na ciwon abinda aka yiwa 'yarta duk da cewa ta dawo gabanta. Sai tausayin mahaifiyar su Baffa ya kamata, hakika zata fi Ummy bakin ciki, domin kuwa ita Ummy bata ma gani da idonta ba. Ita kuwa ta gani, yadda aka keta haddin 'yarta gudan jininta sannan kuma aka badda ta ta inda basu san inda take a duniya ba. Kunkanta ya kara tsananta, tasayinsu yasa ta ga bata kyauta ba. Ta san duka abinda take tana yi ne domin ramuwa ga Shugaba, amma wannan hukuncin ya yi tsauri ga ahli. Domin kuwa shi uba ne kawai, ba zai taba jin kwatankwacin yadda uwa zata ji ba. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​ _*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 20``` Ranar kam kwanan bakin ciki da tausayin mahaifiyarsu Baffa ta yi. A ranta tana ganin rashin kyautarwarta, domin a ganinta hukunci na mai laifi ne. Su kuma basu san komai ba. Washe gari tun da asuba ta bar gidan bayan ta yiwa Ab'ha sallama da kara jaddada masa ya kula da gida. Shi kansa bai san inda ta nufa ba. Sai dai bayan fitarta ta kira waya ta umarce shi da ya kwance Baffa ya bude shi, shima ya sake cikin gidan kamar ragowar 'yan matan nan. Duk da ya ji mamakinta na yin hakan amma abun ba karamin dadi ya yi masa ba, domin kuwa yana jin dadin zama da Baffan. Guy din yana da saukin kai da saurin fahimta. *Washe gari da dare* Suna cikin yin kalacin dare suka ji an budo kofa an shigo. Fadwa ce ta shigo cikin wata shiga ta atamfa England dinkin zamani, na riga da sket. Kanta yane da wani karamin gyale sky blue kalar kayan jikinta. Hannunta rike da na Anisa wadda ta sha jinin jikinta tana jiran ganin inda aka kawo ta da kuma abinda zai koma biyowa baya. Ab'ha da Baffa suna kan danning suna cin abinci. Yayin da su kuma 'yan matan suke baje a kan Capet din falon suna gabatar da nasu kalacin. Ganin Fadwa da wadda ke tare da ita yasa ko-wannensu dakatawa da abinda yake yi suka zuba musu ido cike da mamaki da al'ajabin wannan ba zata. Anisa kuwa ganin babu idon sani a gurin ya saka idonta suka fara cikowa da kwalla. Daya bayan daya take kallonsu, ai kuwa karaf idonta suka suka kan dan'uwanta gudan jininta Baffa. Wani uban tsalle ta daka ta kwace hannunta daga cikin na Fadwa ta nufe shi da gudu tana mai kiran sunansa da karfi. "Yaya Baffa!". Ta rungume shi tare da sakin wani irin kuka mai taba zuciya da sanya ta nutsuwa. Baffa da ya gama sandarewa idonsa kyar a kan Fadwa, ya kasa dauke su a kanta ya kuma rasa kalmar da zai furta mata a matsayin godiya ko nuna farin ciki bisa wannan gagarumin taimakon da ta yi masa. Hannayensa ya daga dakyar ya rufe Anisa dake kankame da kirjinsa, ya damke ta tsam, yana ji kamar mafarki yake yau ga kanwarsa a gabansa. "Anisa..." Ya kira sunan cikin wata raunanniyar murya da ta fito can karkashin makogwaronsa, yana shafa kanta. Kukanta ya tsananta ta kankame shi tana son magana bakinta na rawa, a hakan ta daure ta fara maganar. "Yaya nan kuma ina ne? Me kake yi a nan? Yaya dan Allah ka dauke ni mu je gida, wannan da kake gani azzaluma ce yaya itace ta..." Hannun da ya dora a kan lebenta shi ya dakatar da kalaman dake fita bakinta. Ta dago kai ta kalle shi, sai ta ga yana girgiza mata kai idonsa cike da kwalla. Yasa hannu ya janye ta daga gabansa ya fara takawa daga inda yake zuwa inda Fadwa take tsaye tana kallonsu. Har a zuwa lokacin babu wata kalma da ya ji ta zo masa wadda ta can-canta ya yi amfani da ita wajen godewa Fadwa. Sai da ya zo daf da ita sannan ya tsaya ya zamana ko-wannensu na iya jin numfashin dan'uwansa. Rashin sanin abin yi yasa ya sauke girmansa da ji da kansa ya tankwashe kafarsa ya gurfana a gaban Fadwa cikin matukar girmamawa da darajawa ya kama kafufuwanta yana son furta mata kalmar godiya amma ya gagara. Wani irin shokin ta ji ya shige ta tun daga kan yatsun kafar tata har cikin gashin kanta. Da sauri ta ja da baya tana mai girgiza masa kai alamar ya bari. Bata yi magana ba ta raba shi ta wuce da sauri ta shige dakinta kana ta rufo kofar. Anisa kuwa tsaye kawai ta yi tana kallon ikon Allah. 'Yan matan nan sun zagaye ta suna mata barka da dawowa gida amma ko jin su bata yi. Idonta na kan yayanta da abinda ta ga yana kokarin yi ga wadda ta ruguza mata rayuwa. Kuka ta fashe da shi ta karasa gareshi "yaya kanka daya kuwa? Ka kuwa san wace ce wannan? Fadwa ce fa, wannan 'yar gwa-gwarmayar da ta d'ai-d'aita rayuwata ta maida ni karuwa, kuma abin ki fasik..." Baffa ne ya yi saurin toshe bakinta yana girgiza kai. Ransa a matukar bace ya fara magana bayan ya kama hannayenta. "Aa kanwata, karki ga laifin fadwa bisa abinda ta aikata gareki. Domin kuwa babban mai laifin shi ne Dadynmu. Dady da kike gani shi ne cikakken azzalumi, wanda ya kai makura ga lalatawa da tarwatsa rayuwar 'yayan mutane..." Ya kwashe komai da ya ji game da mahaifinsu da abinda ya yiwa Fadwa ya gaya mata, ya kuma nuna mata hujjojin da shima aka nuna masa, ga uwa uba shaidar kan-kat! Wato wadannan 'yan matan da suke masa kasuwancin karuwanci. Kuka sosai Anisa ta yi, wanda har yasa ta tsani ci gaba rayuwa a matsayin 'yar Alhaji Habib Shugaba. Tsananin son 'yan uwanta da Momynta ne kadai yasa take son ta rayu. Ba dan tana da su ba da yau ta zama daya daga cikin jerin wadanda bakin ciki yasa suka kashe kawunansu. Ta yi kuka, ta yi gumji, har ta dawo babu murya kuma babu hawayen. *Asibiti* Karfe bakwai da rabi na daren, yana zaune a kan kujerar robar dake fuskantar gadon majinyatan. Hannunsa rike da hannunta wanda aka saka mata roba ta karin ruwan jiki. Faisal kenan kanin Baffa kuma yayan Anisa d'a ga Hajiya Laurat matar Alhaji Habib Shugaba. Idonsa a kan uwar tashi dake kwance tamkar babu rai a jikinta. Banda kuka ba abinda yake yi. Addu'a kam bai sai adadin wadanda ya yi ba. Zaune kawai yake amma shi kansa hoto ne kawai ruhinsa ya balle izuwa duniyar tunanin wannan iftila'in da ya afka musu. Ga Momy kwance a asibiti, Baffa ya bata, ita Anisa ba a ma san inda take ba. Wannan wace irin masifa ce. Kofar dakin aka budo aka shigo, ya dago kansa dakyar ya zubawa mai shigowar ido. Mai gadin gidansu ne Izike. Har zai dauke idon nasa ya yi gaggawar komawa da su ga kofar, saboda ganin wadanda ke biye a bayan Izike. "Anisa! Yaya Baffa!!". Ya ambaci sunayen cikin tsananin mamaki da tan-tamar sune ko dai idonsa ne suka fara yi masa gizo? Anisa ce ta tabbatar masa da su din ne. Ta hanyar rugawa da gudu ta kankame shi tana kiran sunansa "yaya Faisal". Firgigit Hajiya Laurat ta farka daga nannauyan baccin da take bayan ta dawo daga suma. Kamar a mafarki ta ji ana kiran sunayen 'yayan nata. Ai kuwa tana yin arba da su ta shiga kiciniyar cire robar dake hannunta ta mike zaune. Gaba daya suka yi kanta suna kokarin kwantar da ita. Ta ja Anisa zuwa jikinta ta rungume ta. Wani kuka mai karfi ya kwace mata a dalilin tunawa da yadda ta ga ana wulakanta 'yar tata a fai-fan video ana keta haddinta. Ta rumtse ido da karfi tana kaico da alawadan kasancewarta matar shi. Bata san lokacin da bakinta ya furta kalmomin ba. "Allah ya isa tsakanina da kai Alhaji, har abada ba zan yafe maka ba. Ka cuce ni ka cuci zuri'armu". *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 21``` Gaba daya yaran suka zuba mata ido cike da mamakin jin abinda take fada musamman Faisal da bai san komai game da mahaifin nashi ba. Su kuwa Baffa da Anisa mamaki suke ta yaya Momy ta san laifin na mahaifinsu ne? Waye ya sanar da ita?... Suna cikin wannan tunanin suka jiyo Faisal yana jerewo Momyn tambayoyi cikin wata rikitacciyar murya mai dauke da dimuwa. "Wane Alhajin kike nufi Momy? Ba dai Dady ba ko? Me Dady ya yi miki wanda har kike cewa ba zaki yafe mishi ba Momy? Shin wace cuta kike ganin ya yi mana a matsayinmu na zuri'rku? Momy kam sai lokacin ta san maganar ciki ta fito fili. Sam bata san a fili ta furta kalaman ba, amma a ganinta laifin Alhaji Habib ba abin boyo bane. Matsalarta daya ita ce ta yaya zata sanar ta kuma fahimtar da yaran laifin mahaifinsu?. Cikin kunci da tsantsar takaici ta jijjiga kai "kwarai kuwa shi, mahaifinku nake nufi Faisal. Babanku mutumin banza ne, azzalumi mai boye aibu da alkhairai. Shi kare ne da fatar kura, fuska biyu ke gare shi. Wannan halin na mahaifinku abin tir! Da Allah wadai ne". Ta kai hannu ta dafe kanta da take ji yana barazanar tarwatsewa. Sannan ta ci gaba "ya zama dole in gaya muku babban aikin mahaifinku shi ne safarar 'yan mata. Kananun yara 'yan kasa da shekara ashirin yake diba yana sayarwa turawa suna yin abinda suke so da su". Ido waje Faisal ya gurfana gaban gadon da Momy take kai yana kallon fuskarta. A lokacin ji yake kamar ta saki murmushi tace duk abinda ta fada wasa ne. Ko kuma ma a ce wata zautuwa ce ta kamata ta fadi hakan a kan amintaccen mijin nata mafi soyuwa ga zuciyarta. "Momy!" Ya kira sunanta a razane yana jijjiga kafarta wai ko Allah zai sa ta dawo hayyacinta ta karyata abinda bakinta ya fada a kan Dadynsu. Ganin babu sauyi ko alamar karaya a fuskarta yasa ya saki kafar tata da sauri ya koma gun yayansa da ya gani zaune daram kamar bai ji abubuwan da Momyn take fada a kan Dadynsu ba. Hannayensa ya kama cikin wani yanayi yake girgiza shi "yaya shin kaima kana jin abinda take fada ko da kunnuwa ne suke gaya min karya?" Ganin yayan nasa bashi da niyyar yin magana yasa ya juya ya koma kan kanwarsa "Anisa, Anisa baby kina ganinsu ko? Ita tana fade-fade shi kuma ya yi shiru. Shin ba zasu yi min magana ba? Kanwata kema kin ji me Momy take fada ne?". Wani matsanancin kuka Anisa ta fashe da shi ta fada jikin Faisal ta rungume shi ta tabbatar a yanzu su ababen tausayi ne. Bakin ciki kuwa su duka sun daura aure da shi. Tsoro da fargaba sun hana shi iya motsa gabban jikinsa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Abinda ya shiga furtawa kenan a lokacin da ya fahimci al'amarin da'iman ne. Kansa ya yi masa nauyi, dakyar ya kai hannunsa ya dafe shi. Ganin zai sami matsala ya sanya Baffa saurin mikewa ya janyo shi jikinshi da shi da Anisa duka ya hada ya rungume su. A ransa yake kwatantawa shikenan sun shiga maraicin rashin uba. Cikin tattausan lafazi yake kara tabbatarwa kanin nasa maganganun mahaifiyarsu. Ya dora masa da wadanda ya ji kuma ya gani. Haka ita ma Momy ta tabbatar musu babu ko shakka halayyarsa ce domin ita ma ta ji da kunnenta yana waya kan zai tura yaran ga wani bature dan kasar rasha. Dukkaninsu kuka suke suna jajantawa kansu. Tsananin tsana ta bakin cikin halin uban nasu ya cika zuciyoyinsu. Momy ce ta yi karfin halin tsayar da nata kukan ta soma rarrashin su. Ta kuma umarce su da su yi hakuri su danne zukatansu su ga karshen gudun ruwansa. A yadda tace bata bukatar ko-wannensu ya nuna a fuska ko a bayyane cewa ya san wani abu game da shi. Tana bukatar karin lokacin da zai yi dai-dai domin tarfa shi. Cikin kunan rai ta karkare zancen da cewa "idan har Alhaji bai fuskanci hukunci kan laifinsa ba to nima ban can-canci in amsa sunan 'ya mace kuma uwa ba". Gaba daya yaran suka jinjina kai cikin jimami. Karfe tara da mintuna ya dawo Asibitin dauke da ledoji masu kunshe kayan marmari da drinks. Mamaki ne ya bayyana karara a fuskarsa na ganin yaransa biyu da suka bata sun dawo a lokaci daya. Bai iya boye farin cikinsa na ganinsu ba duk kuwa da yana cikin damuwa. Haka ya zauna da yaran sama-sama domin hankalinsa ya riga ya kasu kashi-kashi. Kasancewar yau ta kama assabar, washe gari kuma lahadi, yayin da rana ta gaba zata kasance litinin kuma ranar da alkalin babbar kotu yake bukatar ganinsa a gabansa domin ya kare kansa bisa zargin da ake masa. A gefe daya kuma ga babbar barazanarsa Fadwa, wadda ta gagare shi, izuwa yanzu kuma bai san me take shirya mishi ba. Wannan ne yasa ga baki daya ya rasa nutsuwarsa domin kuwa shi mara gaskiya aka ce ko a ruwa gumi yake yi. A daddafe ya samu ya yi musu sallama ya bar Asibitin bisa bada uzurin cewa zai shiga wani zama na gaggawa da shugabannin kananan hukumomi. *Mai tama* Fadwa ce tare da Ab'ha a dakinsu na harhada bayanai da ajiye duk wani abu mai muhimmanci. Sun dukafa sosai ga aikin da suke yi na tattara bayanai da bidiyoyin da suka samu daga wajen 'yan matan nan na Alhaji Habib da ya tura kasashen duniya. Dukkaninsu suna cikin gagarumin farin ciki na samun nasa, wanda akalla sun san ko ba a sami wasu ba wadannan hujjojin kawai sun isa su daure Shugaba. 'Kirrrr...!' Wayar Ab'ha dake ajiye a gefen hannunsa ta dauki ringi, alamar wani yana son magana da shi. Ganin number bakuwa bai bashi mamaki ba kamar yadda ya ganta da alamar kari (+) wato dai number ta kasar waje ce. Shiru na dan lokaci kafin daga bisani ya daga wayar da sallama. Zumbur ya mike tare da dora hannunsa kan kirjinsa, saboda bugawar da ya ji yana yi. Fadwa ta zuba mishi ido kawai tana kallon shi. Shi kuwa muryar Hamidarsa daya ji cikin kuka tana ambaton sunansa yasa gaba daya ya rasa nutsuwarsa. "Ha'ab?!" Ya kira sunanta cike da son tabbatarwa. Ta amsa da sauri tana share hawaye kamar tana gabansa. "Abba ka yafe ni ka yi mini aikin gafara. Hakika na aikata kura-kurai da yawa a rayuwata, amma a cikinsu babu wanda ya kai kin ka da na yi. Na yarda kin masoyi babbar masifa ce, Ab'ha na tuba ka yafe min. Na san zaka yi mamakin ji na a wannan lokacin to ba yadda na iya ne. Alhaji Habib ya cuce ni. Ya maida ni baiwarsa mai bautar da rayuwarta a banza. Duk iya zaman da na yi da shi bai gani ba. A kan wani karamin kuskure da na aikata masa yasa ana farautar rayuwata. Ni yanzu ban damu da kaina ba, damuwata daya ita ce juya maka baya da na yi a lokacin da kake matukar kaunata. Na dauki alkawarin sai na tozarta rayuwarsa kanfin ya cimma nufinsa a kaina. Gobe zan shigo Najeriya, zan kuma zo da gagga-gaggan hujjojin da zasu daure shi iya rayuwarsa. Ka tare ni karfe bakwai dai-dai jirgin safe zan biyo". Duk wannan dogon zancen ta yi shi ne wani na bin wani. Sam bata bada wata dama ga Ab'ha ya yi magana ba har saida ta zo karshe. Cikin sarkewar murya yake amsa mata da "Sikenan Allah ya kai mu goben". Dif! Ya katse wayar ya zauna kan kujerar da ya tashi a kanta. Idonsa a kan fadwa cike da murna yake sanar mata Ha'ab ta yi nadamar abinda take zata kuma dawo gida. Ya gaya mata duk abinda ta fada masa. Fadwa ta jijjaga kai, tana nazarin maganar. Kafin ta kalle shi tace " Allah ya kai mu goben lfy". Iya abinda tace kenan ta ci gaba da aikinta. Washe gari tun da ya yi salla zumudi bai bar shi ya koma kwanciya ba. Shi kansa a wasu lokutan yana mamakin irin yawan so da kaunar da yake yi wa Hameeda. Duk da ya san halin da take ciki dai-dai da rana daya bai taba jin sonta ya ragu a zuciyarsa ba. Yau yana cikin farin cikin da ya debi shekaru bai yi kwatankwacinsa ba. Duk rawar kan da yake yi Fadwa na lura da shi, amma bata tanka shi ba. Haka ya kammala shirinsa karfe bakwai saura kwata ya fita gidan ya nufi airport. Karfe bakwai dai-dai jirgin Dubai mai dauke da fasijoji dari da sittin ya dira a babban filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Kano. A cikin jerin mutanen dake fitowa daga jirgin ya hango ta cikin shigar doguwar riga baka hade da mayafinta. Ta kara kyau ta murje, ta cika bul-bul da ita gwanin sha'awa. Ab'ha ji ya yi kamar ya ruga ya rungume masoyiya abar so da hangen ruhi da gangar jikinsa. Amma sai ya daure ya jira isowarta. Tana ganinsa ta fara sharar kwalla sannan ta saki jakar hannunta ta isa gareshi ta rungume shi tana ambaton sunansa cikin raunin murya. Ab'ha kam kusan rasa ji da ganinsa ya yi a lokacin, saboda wani irin shauki na masoyan da a baya suka cire rai ga samun ababen son nasu. Dakyar ya iya raba jikinshi da nata yana dai-daita tsayuwa ya yi mata barka da isowa. Har zata tari taxi ya dakatar da ita yana sanar mata cewa ai da mota ya zo. Hakan yasa ta bi bayansa zuwa inda motar take a ajiye. Tafiya mai dan tsayi ya yi kafin ya tamyeta game da abinda ya ji ta fada "me yasa kika zabi ki sauka a hotel madadin ki wuce gidan iyayenki kai tsaye?" Hameeda ta marai-raice fuska ta soma magana "ina so ne sai na fara tura wasu dattabai su rarrasar min su, ina so zuciyarsu ta yi sanyi kafin na tunkare su. Ka san suna fushi dani saboda dadewar da nake ban zo gida ba". Ya jinjina kai yana auna kalaman nata. A lokacin kuma sun fara shiga karamar hanyar da zata sada su da karamin hotel din da ta bukaci ya kai ta. Kasancewar lokacin lokaci ne na sanyi kuma da safe, yasa layin ya yi shiru baka ganin giftawar mutum ko wani abin hawa a kan kari. Shiru ya ratsa tsakanin masoyan biyu. Ab'ha ya dukufa kan tukin da yake, ita kuma tana duba jakarta kamar mai neman wani abu. Ta saka salati tare da dan fiddo ido alamar ta rasa wani abu. Da sauri ya taka birkin motar yana kallonta da kuma jiran jin abinda ta yar ko ta manto a can. Cikin wannan yanayin ne ya samu ta shammace shi ta rufe masa fuska da wani karamin kelle. Kafin ya yi wani yunkurin tuni ya rasa kuzari a gabban jikinsa, kafin daga bisani kuma numfashinsa ya tsaya ga fita a kai-a kai ya dawo daya bayan daya. Hameeda ta saki wani shu'umin murmushi na samun nasara, sannan ta dauko wayarta ta fara laluben wata number ta danna kira. Ba jimawa wanda take kiran ya daga wayar kamar dama can ita yake jira. Ba ko sallama ta fara magana. "Da girman kujerarka, aikinka ya kammala. Yanzu ina kake so a kai shi?". Ban san me aka gaya mata ba, ta dai amsa da cewa "an gama". Kawai sai ta katse wayar. Ta fita ta zagaya ta yi wa kanta mazauni a bangaren driver. Ta tashi motar tare da juyar da kanta ta cillata bisa babban titi... Babbar magana. 🤔 Ku ci gaba da bibiya, zan ci gaba. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 22``` Ab'ha yana sunkuye bisa kujerar motar kamar mai bacci. Yayin da Hameeda take ta sharara gudu bisa titin kasancewar babu yawan zirga-zirgar ababen hawa a kan titin. Tafiya mai nisa ta yi kafin ta fara fita garin Kano. A lokacin ta fara hango inda ta nufa da shi, wato tsohon gidan gonar Alhaji Habib Inuwa. Zuciyarta ta fal da farin cikin cika aikin uban gidanta. Wani mahaukacin birki ta taka lokaci daya ta rike motar iya karfinta tana mai kife fuskarta bisa sitiyarin motar a matukar tsorace. A zatonta motar zata kife ne. Hakan kuwa duk ya faru ne a dalilin ganin mutum da ta gani ya diro mata tsudum a tsakiyar hanya ta gabanta, ba tare da sanin ta ina ya fito ba. 'Kuuuuuuuu...' Kake ji karar birki da kokarin tsayar da motar da take tsaka da gudu lokaci daya. Wani irin ihu Hameeda ta saki ganin motar zata bi ta kan wannan bakon mutumin da ya dirar mata a kan hanya sanye da bakaken kaya fuska a rufe. Sai dai kafin ta kai karshe ga tunaninta ta ga ya bace bat! Kamar bai taba wanzuwa a gurin ba. Sannan kuma motar ta tsaya lokaci daya. Hameeda ta shiga waige-waige tana ware ido, ajiyar zuciya take saukewa wata na bin wata. Cikin sauri-sairi ta fara yunkurin yi wa motar key hannunta na rawa. "Wai shin ina ne kike kokarin kai shi Ha'ab?". Ta juyo da kallonta zuwa sit din motar na baya inda ta ji sautin na fitowa a matukar tsorace. "Na shiga ukuna waye kai?...". Ta fada tare da dafe kanta cikin tsantsan tashin hankali da rudewa, saboda ganin wannan mutumin da motar ta bi ta kansa zaune a kan kujerar motar ta baya. Tunda take bata taba jin kanta a yanayin tsoro kwatankwacin wanda take ciki a yau ba. Mai bakin kayan nan ya saka hannu ya yane hular roba dake rufe da ilahirin fuskarsa zuwa wuya. Ga mamakin Hameeda sai ta ga gashi ya zubo ya rufe fuskar mamallakin kayan. Tsoronta ya kara hau hawa zuciyarta ta shiga sake-sake, a yanzu kam ta tabbatar gamo ta yi da aljan. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!". Ta fada cikin matsancin razani tana neman balle motar ta fita. Cikin zafin nama mai bazajje gashin nan ya yunkura ya kife ta da mari. Ji kake tas.! Ta tsandara kara tare da dafe kuncin nata da ta ji kamar zai cire saboda zafi, idonta a kan wannan aljani kamar yadda ta dauka. Mai bazajjen gashin ya saka hannu ya yaye gashin tare da watsa shi bayan kansa. Me zata gani? Fadwa ce tsohuwar class mate abokiyar gaba. " Fadwa?!". Ta kira sunan cike da mamaki kana ta shiga tunanin gaggawa. 'Anya ma Fadwa ce? To idan ita ce ta yaya take bacewa kamar aljana?' Fadwa ta bushe da mahaukaciyar dariyar nan tata. Kana ta dora da cewa "dama na sani, mugu bashi da sabo Hameeda. Yanzu ke rashin arzikin naki har ya kai ki ga iya cutar da Ab'ha? Shin kin manta waye Abba kuwa? Abba fa shi ne mahaukacin masoyin nan naki, Ab'ha shi ne wanda ya bar iyayensa da 'yan uwansa da kuma duk wani jin dadin rayuwa saboda ke. Kin yi kuskure Hameeda kin yi kuskure na cutar masoyi kamar wannan. Duk muguwar hallaya da mummunar dabi'arki bai taba daina sonki ba. Kullum fatansa shi ne ki shiryu ki dawo gida, ki zama ta gari ku ci gaba da soyayyar da kuka fara a baya. Tir dake, da kuma halayyarki Hameeda". Hameeda ta sunkui da kanta kasa cikin tsananin jin kunya da nauyin kalaman na Fadwa. Hakika bata fadi karya ba ita kanta shaida ce, tafi kowa sanin irin son da Abba yake mata. Ita shaida ce game da hakan tunda ya shafe shekaru yana bin bayanta a kasashen duniya... Tunaninta ya katse ne lokacin da ta ji an buda kofar motar dai-dai inda take an fizgo ta waje. Naushi daya fadwa ta yi mata ta nisanta ta da shaka da kuma fitar da numgashi dai-dai. Ta sumar da ita, sannan ta watsa ta bayan motar ta rufe, ita kuma ta shiga mazaunin driver ta tayar da motar ta nufi gidanta da su. A ranar da karfe bakwai da rabi na safiya aka sallami Hajiya Laurat daga asibiti saboda ta sami sauki. Haka suka dunguma ita da yaranta wadanda take ganin su kadai suka rage abinda ke faranta mata a duniya, suka koma gida. Zukatansu dunkule da sabon yanayin kunci da jimamin da ya zame musu abokin rayuwa a 'yan kwanakin. Gidan ma sai ya zame musu wani fanko kamar ba asalin gidansu ba, sai suke kallon komai dake gidan kamar haramtacce ne a garesu. Haka kawai suka tsani gidan da komai dake cikinsa, sun tabbata duk wani jin dadi da suka yi an gina shi ne haramun. Mummunan haram na sayar da mutuncin 'yayan mutane. Alhaji Habib kuwa yana can ya kebance kansa a daki yana jiran kiran Hameeda, domin ta sanar masa ta kai Ab'ha inda ya bukata. Manufarsa a kan hakan kuwa shi ne ya san in dai Ab'ha yana hannunsa to zai san duk wani shiri da Fadwa take yi a kansa, sannan ya wargaza shi. Zai kuma san sirrinta da inda take rayuwarta wanda hatta jami'an tsaro duka suka gagara sani. Ya tabbata idan ya sami duka wadannan zai iya batar da ita, ya shafe tarihinta da duk wasu muradai nata na nemawa mata 'yanci bisa kasuwancin da yake da yi su. Yana cikin wannan dakon ya jiyo kiran ya shigo wayarsa da number tata. Cikin azama da ya daga wayar yana fadin "kin jinkirta da yawa Hameeda, ina nan ina ta zullumi". "Ka ci gaba da zullumin Shugaba, domin ko har yau baka fita a cikinsa ba". Fadwa ta gayar masa a zafafe ta cikin wayar. Alhaji Habib ya zabura kamar tsinke aka saka aka zungure shi. Ya kalli wayar, ya kuma kalli number. Babu shakka number Hameeda ce, amma muryar kam ya fi kowa sanin mamallakiyarta. "Fadwa?!". Ya fada a lokacin da gabansa yake dukan uku-uku, kansa na fitar da gumi. Ya tabbata ya rasa komai, ya rasa Hameeda ya rasa na hannun damanta Abba. Anya wannan mutum ce? Ta yaya ta gano shirinsu? Ya ma aka yi ta kama Hameeda bayan ta tabbatar masa ta kama gayen...?' *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 23``` Cikin tsawa ta katse masa tunani da fadin "ka dakatar da wannan karamin tunanin naka ka saurare ni tukunna. Na san yanzu ta riga ta kare maka kai kanka ka san da hakan, saboda haka nake gargadinka a kan ka tabbatar ka fadawa duniya da kotu gaskiya a tsayuwarka ta gobe gabanta. Ina mai shawartar ka da kar ka yi kokarin yin karya a goben domin ni na riga da na gama shirina. Ko da ka yi karyar na tanadi gaggan hujjojin da zasu tabbatar da gaskiya, saboda haka ka kula. A karshe ina maka albishir cewa gobe ce ranarka ta karshe da duk wani mahaluki zai kalleka da mutunci a ciki da wajen jihar Kano. Karshenka ya zo Shugaba..." Ta kece da dariya tana karasa maganarta "tabbas na fada kuma zan cika burina zai cika." Alhaji Habib a matukar razane ya fara magana "ke tsinanniya 'yar gidan marasa mutunci, goben da kike cewa ta kare min to ke ce ta karewa baki sani ba. Ke har kin manta da yadda jami'an tsaron jihar nan suke nemanki ruwa a jallo? To ki sani har yanzu ni Alhaji Habib Inuwa Shugaba ne. Kina yin kuskuren bayyana kanki a goben kin zama gawa ko da kuwa a cikin kotun ne. Shashasha mara hankali" ya katse wayar a kufule ya shiga kai komo a dakin yana share gumi. Cike da neman mafita game da wannan masifar da ta tunkaro shi. *A maitama* Karfe shida na yamma Ab'ha ya farfado daga nannauyan baccin da ya yi ta dalilin wata fauda dake jikin kyallen da Hameeda da shaka masa. A firgice ya farka yana kokarin tan-tance inda yake. Ganin kansa a cikin dakinsa ya yi matukar girgiza shi. Zumbur ya mike ya bude kofar ya fita yana dube-dube. Babu kowa a falon sai TV dake ta faman aiki ita kadai. Ya dauki remote ya kashe TV sannan ya zarce izuwa dakin Fadwa. Da sallama ya tura kofar dakin ya shiga, tana zaune bisa kujerar gaban madubi tana daure gashin kanta da band. Ya ja ya tsaya a jikin kofa yana tunano abubuwan da suka faru da shi. Ya ma rasa ta inda zai fara magana. Shi dai ya san ya dauki Hameeda amma bai sami kaita inda ta bukata ba, ya kuma san ta yafa mishi wani kyalle a fuska. Daga nan kuma bai koma sanin komai ba sai yanzun da ya farka ya ga kanshi a gida. "Meye ya rage wanda baka gaya min ba kuma Ab'ha? Naga ka yi shiru. Ka fada mana, kana sonta, ka yarda da ita, ba zata iya cutar da kai ba ko?". Tana maganar tana ci gaba da shirin da take. Ya yi kasa da kansa cikin matukar nauyi da jin kunyarta "ki yi hakuri Fadwa ni na dauki so kamar iri daya ne. Ashe abinda ban sani ba shi ne yadda nake ji game da ita daban yadda itama take ji game da ni daban. Na yi nadama Fadwa na kuma bar so bari na har abada. Na yarda soyayyata ta zo a sahu na marasa sa'a a duniya. Domin kuwa shi so daya ne, kuma ita kadai nake yi wa shi. Ta cuce ni ta ci amanata. A yadda ta nuna zata iya kashe ni.." Wasu zafafan hawaye suka biyo bayan kalaman nashi, kafin ya ci gaba "zata iya kashe ni Fadwa, saboda haka yanzu na tsane ta, na tsani duk wani abu da ya shafi so!". Allah sarki Ab'ha tausayinsa ya kama Fadwa shiru ya ratsa na dan lokaci kafin ta nisa tace "shikenan ka manta da ita kawai, ka ga, da ban je da wuri ba da sun lalata duka shirinmu. Nufinsu shi ne su azabtar da kai har sai ka fada musu shirinmu, su san inda nake su kashe mu duka da ni da kai. Amma Allah bai basu iko ba. Ka manta kawai komai ya wuce, na san Allah ba zai taba basu wannan damar ba". Shiru ya koma ratsa tsakaninsu. Ganin haka yasa ya dago kansa dake kasa yace "na gode da ceton rayuwata da kika yi Fadwa". Murmushi kawai ta yi mishi ya juya zai fita. "Ab'ha". Ta kira sunanshi, ya juyo yana dubanta tare da fadin " aa Fadwa ki kirani Abba kawai." Sai da ta dan sarara saboda tausayin shi da yanayin yadda ya yi maganar. Sannan ta kauda kanta tace "sorry Abba. Ka kasance cikin shiri gobe komai zai zo karshe". Ya gyada kai alamar ya gamsu sannan ya fice jikinsa a sanyaye. Bayan ya kammala waya da lauyoyinsa ya koma kan gadonsa ya zauna tare da hada uban tagumi da duka hannayensa biyu, ya ma rasa abin yi. Yana cikin wannan halin wata bakar sakar ta zo masa a rai. Ai ko cikin azama ya daga wayarsa ya kira lambar Acp Sauwam. Har wayar ta yanke ba a daga ba. Ya koma danna kira itama dai kamar zata yanke sannan aka daga da "Hello". " Hello Sauwam kana ji na?". "Ka yi hakuri ba zai sami damar amsa wayar ba yanzu yana meeting". Aka fada da wata kakkaurar murya. "Ok idan ya kammala a sanar masa na kira kuma ina neman shi gidana". "To yallabai". Dukkaninsu suka kashe wayar. Karfe takwas na daren Acp Sauwam ya isa gidan Alhaji Habib domin amsa gayyatar da ya yi masa. Bai sha wata wahala wajen shiga gidan ba, kasancewar shi sananne ga dukkan securitys din. Yanayin da ya ga Alhajin ya tabbatar masa cewa yana cikin damuwa. Bayan gajeruwar gaisuwa aka gabatar masa da abin motsa baki. Sai dai bai ci komai ba idonsa na kan Shugaba. Ya fara magana "yallabai kamar kana cikin damuwa, ka kira ni nan ko lfy?". "Lafiyar kenan Sauwam, na tabbata a irin wannan aikin da kuke sam baku can-canci a kiraku jami'an tsaro ba". Asp cikin rashin fahimta ya kalli Alhajin yana neman karin bayani. Shugaba cikin fada-fada yake magana. "Banda lalacewar aikin dan sanda a yau, ta yaya za'a ce mace daya ta gagari ilahirin 'yan sandan dake jihar Kano? Ta sace min 'yata sannan ta watsa video yadda ake tozaratar da ita. Ta koma sace min dana, shima ta sako video yadda ta wulakanta shi ta kashe shi. Har yanzu ban san inda suke ba. Saboda jin dadin duk wannan abin da ta yi ba a kama ta ba yau ta kira waya tana shaida min gobe a tafiyar da zan yi kotu zata kashe ni a bainar jama'a. Wannan shi ne tsaron da kuke bawa kasa?" Sauwam jikinsa ya yi sanyi, sai yanzu ya fahimci inda maganganun Alhajin suka dosa. Ya gyara zama yana fadin "ka gasgata ni Alhaji har yau muna kan binciki a kan wannan mai laifin. Ina tabbatar maka idonmu-idonta ba zata sha ba. Yaranka kuma da iznin Allah zaka same su cikin koshin lafiya. Ka kwantar da hankalinka babu abinda zai same ka, muna tare da kai. Babu shakka wannan wata dama ce a garemu da zamu sami damar kama ta. Barta ta zo gaben, babu makawa karshen ta'addancinta ne ya zo". Ya mike a fusace ya yi wa Alhajin sallama ya fita, a ransa yana sakawa muddin Fadwa ta bayyana kanta gobe to ko shi ko ita, sai ya tabbata kwato wa 'yan sanda mutuncinsu da take neman zubarwa a idon duniya. Alhaji Habib ya bi bayansa da wani shu'umin murmushi ya tabbata ya kwanto mata kura, ta zo goben. Mikewa ya yi ya shiga cikin gidansa yana umartar Baffa da Anisa a kan kar su yarda su fita gidan nan balle har wani ya gan su ya san sun kubito daga hannun Fadwa. Yana gama maganar ya wuce sashensa ya barsu da kallon juna cikin wani al'ajabin. Mugun shiri 🤔 Keep following, mu ga me suke shirin yi wa jarumarmu? 😒 Zan ci gaba. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ ​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​. _____________________________________ © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 24``` *Daren lahadi* Wannan daren ya kasance mai tsayi kuma mai cike da buruka ga mutane masu yawan gaske. Ilahirin jama'ar jihar Kano sun kagu gari ya waye a je kutu, domin su ji me Shugaba zai fada domin kare kansa a gaban kotu? Musamman 'yan siyasa masu ban-bancin ra'ayi. Haka talakawa da suke masa kallon inuwa kuma mafaka ga irinsu. Sun kagu garin ya waye su ga me ake shirin kulla masa? Abin ya yi kamari a zukatansu domin wasu daga cikinsu ji suke kamar zasu iya bada rayukansu domin kare Shugabansu. Haka bangaren 'yan sanda sun riga sun gama yin kwakkwaran shiri domin ganin sun kauda tarihin wata 'yar gwa-gwarmaya a birnin Dabo. A ganinsu wannan shi kadai zai sa su ci gaba da amsa sunan jami'an tsaro cike da izza. To Fadwa ma ba a barta a baya ba ta gama shirinta tsab, da kuma hada duk wasu ababen da take da tabbacin zata bukata goben a cikin kotu. Duk da cewa abokin aikin nata baya cikin nutsuwarsa, Ab'ha ya kusa rasa tunaninsa duka. Saboda ganin soyayyar da ya shafe shekaru yana tarairaya ta ruguje a rana daya. Ya rasa mafaka ko mafita, shi kansa bai san takamaiman yanayin da zuciyarsa take ciki ba. Ya zama tamkar wani hoto abin jinginewa. Babu um ba um...um. Sai ido da yake binta da su a duk shiga da fitarta. Hajiya Laurat da yaranta ma a ranar basu bari an barsu a baya ba, domin kuwa su ma sun gama yin shiri tsab dan yakar zalumci da son zuciya irin na Alhajin, sun gama yanke hukunci a matsayinsu na al'uma sun tabbata barin mutum irinsa a sarari ba karamin illa bane ga duka kasa. Duk da suna cikin matsanaciyar damuwa hakan bai hana zukatansu son bayyana gaskiya ba. A wannan daren mai sarkakiya Alhaji Habib baccinsa ya tika hadda minshari, domin zamansa gogagge kuma masanin siyasa da tuggunta, ya san ya riga ya hadawa Fadwa kashin da ba zata iya rabe shi ba. Wato ya dana mata tarkon da ba zata taba tsallakawa ba. Bisa wannan dalilin ya tattare duk wata damuwa ya yi watsi da ita gefe. Domin dama Fadwa ita ce babbar damuwarsa. *Washe gari* Kasancewar ranar litinin ce, yasa zirga-zirga da kai komon jama'a da ababen hawa ta yawaita. Duk da cewa ana tsuga sanyi hakan bai dakile al'uma ga fitowa da sanyin safiyar suna nufatar guraren ayyukansu ba. (Monday) litinin kenan aka ce ko Nasara na tsoronta. Karfe takwas dai-dai makeken agogon dake manne a bangon barandar kofar shiga high court din ya buga. Dimbin jama'a maza da mata yara da manya sun gama cika wajen har ba masaka tsintsiya. 'Yan jaridu daga kafafen yada labarai iri-iri sun bayyana har sun fara gudanar da ayyukansu. Duk inda ka gifta ji kake suna fadin "masu kallo da saurarenmu kamar yadda kuke ji kuma kuke gani, wato filin babbar kotu ya gama ciki da batsewa da jama'a, masu son ganin yadda wannan murdaddiyar shari'ar zata kaya. Lauyoyi daga ko-wane bangare sun bayyana, yayin da masu laifin ma tuni aka kawo su cikin kotun. Yanzu ya kasance kowa a nan yana dakon isowar Shugaba Alhaji Habib ne da kuma ainihin babban alkali na wannan jihar tamu mai albarka." Suna cikin wadannan bayanan ne suka jiyo wurin ya kaure da karar jiniya ta motocin jami'an tsaro. Nan da nan mutanen suka fara darewa da kansu suna bada hanya ga jerin gwanon motocin suna wucewa. A filin suka yi farking sannan suka fara dirowa kamar tsinukka suna bin sahu, ko-wannensu dauke da zungureriyar bindiga da hular kwano. Fuskokin nan nasu babu ko annuri. Haka suka yi leshi suka zagaye motar da Alhaji Habib yake cikinta. Acp Sauwam ne a kan gaba cikin gagarumar shiga irinta ma'aikacin da ya shiryawa fita filin daga. Da gudu wani dan sandan ciki ya zo ya bude masa kofar. Cikin mutumcin nan nashi da nuna kamala ya fito daga motar fuskarsa dauke da murmushi. Nan da nan jama'ar dake wajen suka dauki ihu da sowa suna daga mishi hannayensu alamar suna bayansa. Da murmushin nan yake daga musu hannu yana jinjina kai. 'Yan jarudu ko suka yo masa caaa! Da tambayoyi. Ji kake suna "Ranka ya dade me zaka ce game da wannan zargin da ake maka? Dan Allah Alhaji kace wani abu mana. Mutane suna son ji daga gareka". Kowa da irin tambayar da yake jefa masa, sai dai tuni jami'an tsaro suka killace shi ta hanyar saka shi tsakiya suka zagayeshi. Wasu a gaba wasu a baya suna ture mutane suna buda hanya. Bai amsa tambaya ko daya ba har suka shigar da shi cikin kotun. A can ma basu daga suka barshi ba, layi daya aka ware duk na masu bashi tsaro ne, kujerarsa na tsakiya. Basu jima da shiga ba aka sanar da isowar alkali. Mutane kam ko rabi basu sami shiga ba kotun ta cika. Ganin hayaniyar na wajen ta yi yawa yasa aka yi gaggawar samun mafita ta hanyar jona camera da babban majigi dake make a gaban kotun ta waje, yadda duk wanda yake waje zai iya ganin komai da ake gabatarwa a ciki. Sai da aka tabbatar kotu ta sami nutsuwa sannan aka bude karamar kofar, bayan kowa ya mike tsaye ne alkali ya fito ya zauna a mazauninsa. Sannan kowa ya koma ya zauna. Saida aka fara da gabatar da karar sannan aka gabatar da masu laifin su biyu. Shiru kotun ta yi a lokacin da kan alkalin yake kasa yana gabatar da 'yan rubuce-rubuce a kan wata farar takarda. Sai da ya kammala rubutun sannan ya dago ya bukaci lauyoyin dake dakin su gabatar da kansu. Daya bayan daya lauyoyin Alhaji Habib guda biyar suka gabatar da kansu, sannan daga bisani barrister Bashir Bayo. Ya mike ya gabatar da kansa a matsayin lauya mai kare masu laifin. Al'amarin da ya bawa kowa dake wajen mamaki musamman masu laifin da basu san sun dauka ko wani ya daukar musu lauya ba. Amma saboda jin yace zai kare su ya saka basu musa ba suka yi shiru. Ragowar lauyoyin Alhaji Habib kuwa tuni suka fara kus-kus-kus domin duka sun san Barrister BB kamar yadda ake gaya masa. Lauya ne mai kafiya da dagewa kan abinda yasa gaba. Baya shakka ko tsoron case ko na waye, domin shi din lauya ne mai zaman kansa kuma korarre. Wanda zai iya fafatawa da kowane lauya a fadin duniya. Bayan gajeren rubutun da alkalin ya yi kan bayanan gabatar da kai na lauyoyi ya dago ya fara da tambayar masu laifi a kan waccan maganar da suka fada a zama na farko. "Kuka ce saka ku aka yi ku kashe mai laifi Fadwa ko?". Dukkansu suka amsa da "eh". "Wa ya saka ku?". Kai tsaye suka kara mai-maita abinda suka fada a baya. "Alhaji Habib Shugaba". Shugaba da yake gogagge ne ya zuba musu ido, yana kada kai cike da alamar mamaki kamar bai taba ganinsu ba. Alkalin ya koma yin rubutu sannan ya dago yace "kotu na bukatar ganin Alhaji Habib a gabanta yanzu". A tsanake babban mutumin ya mike jami'an tsaro suka rufa masa baya. Cikin takun nan nasa na kasaita da amsa sunansa. Ya isa gaban munbarin tsayuwar ya tsaya yana fuskantar al'umar dake cike da kotun. Kutu ta kaure da maganganun mutanen dake daga mishi hannu. Alkali ya buga gudumarsa domin dawo da nutsuwar kotu. Ai ko duk suka yi tsit! Ya kalli Alhaji Habib yace "Alhaji Habib ko zaka gabatarwa kotu da kanka?". Alhaji Habib ya gyara tsayuwa. "Da fari dai sunana Alhaji Habib Inuwa. Wanda aka fi sani da Shugaba a bakunan al'uma". alkalin ya koma kallonsa bayan ya rubuta bayaninsa yace "ko ka san wadancan mutanen kuma mene ne alakarka da su?". Sai da ya koma kallonsu a lokacin su kansu shi suke kallo. Sannan ya kau da kansa gefe yace "aa, ban san su ba ya mai shari'a". Alkalin ya koma rubutawa sannan ya kalli lauyoyin yace akwai wanda yake da tambaya ga Alhajin? A bangarensa suka ce aa. Amma bar.BB ya daga hannu alamar zai yi tambaya ga Shugaba. Kotu ta bashi damar yin hakan. Ya mike ya isa gaban Alhaji Habib ya kalle shi da guntun murmushi yace "ranka ya dade kace baka san wadannan mutanen ba?" Alhaji Habib ya amsa da "eh, ban san su ba". Yace "haka ne? To in baka san su ba me yasa zasu tsallake kowa dake jihar nan kai katsaye su ambaci sunanka a matsayin wanda ya basu aikin?". Alhaji Habib ya saki fuska a wayance yace "to lauya, ni a ganina wata manufarsu ce kawai ta kokarin ganin sun bata min suna". "Kenan kana zargin suma wani ne ya turo su domin ganin sun bata maka suna?". "Eh haka nake tsammani". "To yanzu kai wa kake zargi game da hakan?". Ya yi shiru alamar yana dan nazari. "A gaskiya ba zan ce ba, dan ban taba rike kowa da mugun nufi ba, balle in yi tunanin shi yake ramako a kaina". "To ko in haka ne me yasa kace kana zargin wani ya saka su?". Tambayar ta zo masa a ba zata, amma kasancewar sa kwararre wajen iya magana ya yi saurin juyeta "to ka san mai hannu cikin lamuran siyasa baya taba rasa 'yan adawa da magauta". Br.BB ya yi murmushi "amma Alhaji na ji ita wannan 'yar gwa-gwarmaya ta zargeka da cewa kana lalata rayuwar yara mata kana dora su bisa turbar karuwanci, sannan ka fara safararsu daga nan zuwa ko-wace kasa turawa na yin badala da su. Ya abin yake?". Nan da nan yanayin shugaba ya canza, ganin dubannin idanu ne a kansa yasa ya yi gaggawar nemo nutsuwarsa "wannan karya ce kawai mara tushe. Ba ni ba, hatta makiyina bana masa fatar kasancewa mai irin wannan dabi'ar". Kotu ta sake kaure da ihun masoyansa, suna fadin "sai Shugaba. Allah ya kare ka". Bayan sun lafa da maganganun Bar.BB ya kalle shi da murmushi yace na gode Alhaji zaka iya komawa ka zauna". Ya fada a lokacin da yake taku zuwa gaban masu laifin nan. Alhaji Habib kuma ya sauka daga inda yake ya koma mazauninsa bayan kotu ta bashi iznin hakan. Bar.BB ya sami iznin tambayoyi ga masu laifin ya fara da tambayar su ayyukansu. Kamar ba zasu fada ba sai kuma suka yanke shawarar su fada kawai su tona asiri a nemo duka ragowarsu kar su wahala su kadai. Hali (maiki) ne ya fara magana. "A wannan al'amarin fa ba mu kadai bane. Muna da yawa, kuma muna da shugaba. Bamu da wani aiki da ya wuce ta'addanci shugaban namu shi ne yaron wancan Alhajin... Ya nuna Alhaji Habib. Sannan ya dora ...Shi yake kira a duk lokacin da yake bukatar mu yi masa wani aiki na ta'addanci kamar kisa ko tsorata wasu mutane dake neman bijire masa. A iya rayuwar shashancinmu bamu taba rika bindiga ba sai da muka fara aiki da shi. Shi ya saya mana makamai a kokarinsa na ganin mun kawar masa da ita wannan 'yar gwa-gwarmayar da yace ta addabi rayuwarsa. Wanda a kokrinmu na yin hakan ne aka kama mu." "Mene ne shaidarka game da hakan?". Bar.BB ya tambaye shi. Abokanen aikina sune shaidana. Zan iya fadawa jami'an tsaro inda suke domin su ma a kamo su a gurfanar da mu tare. Kirjin Alhaji Habib ya buga da sauri ya yi kasa da kansa. Bar.BB ya yi godiya ga alkali sannan ya koma ya zauna yana 'yan rubuce-rubuce kan takardar dake gabansa. Saida alkalin ya gama rubutunsa sannan ya dago yana kallon jama'ar dake cikin kotun yace "bisa yadda zantuka suka gabata daga bakin masu laifi, sun kara tsunduma Alhaji Habib Inawa a cikin wannan shari'ar. A saboda haka kotu ta daga wannan shari'ar zuwa mako mai zuwa, tare da bawa jami'an tsaro iznin kamo ragowar masu laifin domin samun tabbatacciyar shaida a kan wanda ake zargi. Saboda haka... "Wannan Shari'ar ta rana daya ce ya mai girma mai Shari'a". Wata murya da ba a san mamallakiyarta ba ta katse alkalin da fadin haka a cikin wadanda ke zaune bisa jerin kujerun dake cikin kotun. Hakan ya ja hankalin alkali da lauyoyin tare da ilahirin mutanen dake kotun zuwa ga mai maganar. Mace ce zaune bisa kujera, fuskarta yane da karamin mayafi. Cikin 'yan dakiku ta sauwaka ma masu son ganinta ta hanyar mikewa ta tsayu a gaban kotun tare da bude fuskarta gaba daya. Fadwa ce! 'yar gwa-gwarmaya. Tirkashi... Keep following. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​ _*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 25``` Ai kuwa a take kotun ta kaure da hayaniya ciki da waje. Dubbanin mutanen dake jin labarin 'yar gwa-gwarmaya da hatsabibancinta suka marmatso dan ganewa idonsu wace ce ita?. Cikin matsananciyar kaduwa da tashin hankali Alhaji Habib ya mike tsaye yana fadin "Gata nan Fadwa ce ku kama ta kashe ni zata yi". Ya fada cikin bada umarni ga daukacin ma'aikatan dake wajen. Gaba daya suka mike suka nufi inda take suka yi mata kawanya. Kawunan bindigoginsu na fuskantar kwakwalwarta. 'Yan kallo na ciki da waje suka dauki ihu "ga 'yar gwa-gwarmaya, ga 'yar gwa-gwarmaya, yau dubunki ta cika, ku harbe ta! Ku harbe ta!!" Abinda da yawa suke fada kenan. Ganin kotun ta kacame da maganganunsu yasa alkalin buga gudumarsa domin dawo da nutsuwar kotu. Tsit! Kake ji ba wani mai magana ko dogon motsi, jami'an tsaro kuma suna nan zagaye da Fadwa alamar ta shiga hannu. Ita kuwa ko a jikinta ballatana ta nuna wata alama da zata nuna ta ji tsoro. Alkalin ya kara daidaita zaman gilashinsa yana kare mata kallo. Yasha jin labarinta a gidajen radio da tv, jaridu da kuma bakunan al'uma. Amma bai taba tsammanin haka take ba. Yariya ce shar da ita, siririya mai matsakaicin jiki, wankan tarwada mai karamin kyawu da yake tattare da sirruka. Da kallo daya zaka gane hakan a tattare da ita. Kada kai ya yi, ya yi sabon rubutu bisa takardar gabansa sannan ya yi gyaran murya ya fara da bawa jami'an tsaron umarnin su matsa gefe kutu tana son ji daga gareta. Nan fa 'yayan cikin Alhaji Habib Shugaba suka duri ruwa. Ganin 'yan sandan sun matsa bisa umarnin alkali yasa ya mike cikin marairaicewa da kaskantar da kai. "Ya mai girma mai shari'a, a taimake ni a kama wannan mai laifin wallahi guba ce mai bata zukatan al'uma, ta sace min 'yata ta kuma baza video yadda ake keta mata haddi ana wulakanta ta a duniya. Ta kuma sace min babban yarona har yau ban san inda suke ba. Ta kuma sanar cewa nima yau zata kashe ni". Alkalin ya gama kallon Alhaji Habib da kuma nazartar kalamansa ya maida kallonsa ga Fadwa. Yana mamakin Kasancewar wannan yarinya dunkule da wadannan laifukan. Ya tsaida idonsa kan Alhaji Habib kana yace "da kai da ita duka kuna gaban shari'a yanzu. Saboda haka ka kwantar da hankalinka kotu ba zata taba barin mai laifi ya sha ba. Ya juya ga Fadwa dake tsaye a inda take tamkar wadda aka dasa ya jefa mata tambaya "yarinya zamu iya sanin wace ce ke da kuma dalilin sako kanki a cikin wannan shari'ar? Shin mene ne alakarki da su dukan?" Babu wani jinkiri ta daga fuskarta daidai ta fukanci al'umar dake wajen sannan ta fara magana. "Dafari dai sunan Fadwa wadda a yanzu aka fi sani da 'yar gwa-gwarmaya. Kuma ni marainiya ce da ta tashi a gidan marayu na gwamnati mai lamba 3 a nan cikin garin Kano. Tun lokacin da na fara wayon sanin matsayina na tsinci kaina a matsayin marainiya maras asali da tushe. Hakan yasa na kuduri aniyar sayawa kaina kima da nemawa kaina makoma ta gari ta hanyar dagewa in sami nagartaccen ilimin da zai saya mini 'yanci a rayuwata ta gaba. A saboda haka ne na zamo daliba mafi kwazo da maida hankali a makarantar gwamnati ta jeka ka dawo da nake zuwa. Wannan ya saka gaba daya malamai da shugabannin makarantar suke alfahari da ni. A shekarar 2005 na sami nasarar kammala karatuna na sakandire. Inda a wannan lokacin ya zamana nice dalibar da tafi kawacce maki a matakin karshe. Wannan ne ya saka na sami damar kasancewa a cikin dalibai goma da wancan azzalumin yake dauka da sunan tura su kasashen duniya su ci gaba da karatu. Farin ciki sosai iyayen rikona suka yi a lokacin da labarin ya zo garesu. Bayan duk wasu shirye-shirye muka bar Nigeria muka tafi American da zummar ci gaba da karatu. Amma kash rana ta farko da muka shiga kasar ba a barmu mun kwana da mutuncinmu ba. A ranar ya saida mu duka ya karbi kudinsa ya dawo Najeriya. Mutanen nan basu duba karancin shekarunmu da maraicinmu ba a wannan lokacin, haka suka yi ta ci mana zarafi tun muna wahala har muka dawo muka saba. A karshe da na sami kubita na dawo da zummar tona asirinsa karyata ni ya yi. Aka ce biyana aka yi in bata masa suna. A lokacin har ya gabatar da yan matan da ya fidda mu tare a matsayin shaida a kotu da takardun karya masu nuna alamar cewa lallai karatu suke yi a can". Ta sarara tare da matse kwallar idonta. A lokacin duk wanda yake ciki da wajen kotun jikinsa ya fara sanyi. Ta dago da jajayen idonta ta ci gaba. "Bayan wannan lokacin na yi kokarin fita batun maganar in barshi da Allah, amma me? Sai na ga har zuwa lokacin bai daina abinda yake yi ba, bai daina kwasar 'yayan jama'a yana kaiwa turawa suna biyan bukatunsu da su ba. Haka kuma al'uma basu daina kallonsa a matsayin mutumin kirki mai kaunarsu ba. Bakin cikin rayuwar da ya jefani shi ya kashe uwar rikona duk da ba ita ta haifeni ba. Wannan ne yasa na dauki damarar yaki da shi. Saboda tsananin tausayin iyaye duk da ni ban san nawa ba. Babban burina shine ko wace mace ta sami farin ciki ko da ni ban samu ba. Bani da burin da ya wuce in kawar da karuwanci a kasar haihuwata. In kuma dakile ire-iren wannan mugun bawa masu safarar mata domin yin fasikanci, saboda lalacewar abin yanzu har kasa mai tsarki suke kai karuwai suna yin karuwanci. Maganar da ya yi na cewa na sace 'yarsa an keta mata haddi tabbas gaskiya ne. Ni na sace Anisa kuma na saida ta kamar yadda ya sayarda ni aka lalata ni. Amma maganar basu dawo gareshi ba wannan karya ne, a gidansa dukkansu suka kwana. Ina tafe da cikakkun bayanai da hujjoji da zasu tabbatar da laifinshi a fili kowa ya ganshi. Idan kotu ta bani iznin hakan." Ta saka aya idonta a kan alkalin kotun. Zumbur Alhaji Habib ya mike, jikinsa na kyarma ya fara magana da karfi. "Karya take, mai shari'a wallahi karya take. Ban taba saida 'yar kowa ba. Ban san komai game da maganganunta ba.." Maganar alkalin ce ta katse shi. Inda yake cewa "kutu zata baka damar yin magana idan bukatar hakan ta taso. Yin magana ba da izni ba laifi ne, dan haka ka kula". Saboda tsabar rikicewa da fitar hayyaci kasa zama ya yi. A lokacin ji yake kamar ya rufe ido ya ganshi a gidanshi. Wani masifaffen ciwon kai ya ziyarce shi lokaci daya. Idonsa suka fara gani dishi dishi. Wani daya daga cikin lauyoyinsa ne ya mike ya taimaka masa ta hanyar zaunar da shi. Gaba daya ya soma fita hayyacinsa. Alkalin ya maida kallonsa ga Fadwa yace "ina hujjojin naki suke? Kotu na bukatar gani da kuma jin su. Farin ciki ya lullube zuciyarta ganin dukkanin matsalointa sun zo karshe. Hannu ta saka ta sauke jakar hannu dake rataye a kafadarta. A cikinta ta fiddo wani faifan CD ta fara mikawa mai gabatar da kara na kotun wato rajistara ko ince muhutin alkali. Bayan samun izni daga alkalin aka dauki faifan CD aka saka a wata DVD dake ajiye a wurin. Wadda dama an tanade ta ne domin ire iren haka. Jama'ar dake wajen duka sun nutsu, al'ajabi ya cika zukatan wasu. 'Yan jaridu sai kara saura kamarorinsu suke a daidai fuskar TV da suka tabbatar ta cikinta hoton videon zai bayyana. Ni kaina Nasmat tsayar da idona waje daya na yi dan ganin abinda zai fara bayyana a cikin laifukan Alhaji Habib Inuwa. Readers ku ban lokaci zuwa gobe dan jin me aka fara karo da shi. Keep following.😘 *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​ _*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ Na gode! Na gode da kulawa da kuma dimbin comments naku masoyan gaske. 'YAR MUTAN ARKILLA NOVES GROUP KIN BOY ISAH NOVELS UMMYN YUSRAH NOVELS ZAMANI WRITERS FANS WAHALA BATA KISA FANS GROUP Nasmat na matukar godiya gareku mambobi na wadannan groups masu albarka Allah ya bar zumunci ya yi karko, ana matukar tare. ```Page 26``` A karon farko hoton Hameeda ne ya fara bayyana, wanda Ab'ha ya yi daukarta a lokacin da yake bibiyarta. Jikinta sanye da irin tsinannun kayan shan iskan nan na turawa irin na hutun bakin ruwa. Tana kwance ta yi plat bisa kirjin wani bature dake kwance a kan farin yashi yana shafa kirjinta. Daidai nan tace a dakatar. Aka tsayar da CD ta hanyar danna stop. Ta fara magana "wannan da kuke gani wata daya daga cikin takwarorin tafiyata ne. Tare ya fitar da mu america. Amma da yake su suna da ra'ayin karuwancin har yau suna aiki tare da shi. Har yau bata daina yin karuwanci ana bashi kudi ba. Bayan ita yana da 'Yan mata sama da talatin wadanda duk aikin da suke masa kenan." "Ab'ha" ta kira sunan da daga sauti. Ba a ji amsa ba, sai karar bude daya kofar kotun da aka ji, tayayyen matashin ya shigo rike da ita tana ware ido, hannayenta na daure a baya kamar police ya kama mai laifi. Ilahirin jama'ar dake kotun duka hankalinsu ya koma kan Hameeda. A lokacin ne kuma Fadwa ta dora da cewa "wannan ita ce kuka gani a jikin videon nan. Mutane suka kara kafa mata ido cike da son tabbatarwa, "tabbas ita ce, wallahi ita ce". Abinda suka shiga ambato a tare kenan. Suna "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Wasu daga cikin na fadin " subhanallahi". Hameeda ta yi kasa da kanta cike da kunya da bakin cikin ganin wannan rana da bata taba saka ran ganinta nan kusa ba. A take kuka ya kwace mata ta shiga girgiza kai tana fadin "wallahi nima na yi nadama, na yi matukar da na sanin kasancewa haka. A zamana a hannun wannan abokiyar karatun tawa na kwana daya, ta ganar da ni abinda a baya ban sani ba. Ta tunatar da ni abinda na sani kwakwalwata ta yi watsi da shi. Ta ankarar da ni wata daraja da nake da ita wadda ni da sam ban san ina da ita ba". Ta saki kuka wiwi kamar wadda ta rasa uwa da uba lokaci daya. Cikin matsanancin firgicin da bai taba shiga ba ya mike tsaye bakinsa na rawa hannu na karkarwa. Ya rasa wata kalma, ya rasa ko wace kalma da zata karyata wannan abin da Fadwa ke shirin aiwatarwa wato toma masa asiri. " karya suke, gaba dayansu karya suke. Wane ne ya biya ku ku kulla min sharri? Har nawa aka baku da zaku tsaya ku dage wajen tozarta mutum mai mutunci kamata. Ya mai shari'a walla..." Tasawar da mai Shari'a Musa ya daka mishi ita ce ta tsayar da kalominshi. Alhaji Habib kenan da ya yi matukar fita hankalinsa. Jikinsa ya hau tsuma kamar mai shirin kamuwa da ciwon barin jiki. Ya koma ya fada kan kujerar da ya tashi a kai gumi na bin gefen saje da jijiyoyin wuyansa. Daga can wajen kotun kuwa kara da kururuwar wani dattijo ce ta cika mutanen dake wajen har yana kokarin hana su jin abinda ake fada daga cikin kotun. Hakan yasa mutanen dake kusa da shi rufuwa kansa suna tambayar dalilin kukansa. Tsohon cikin sautin kuka ya fara magana "mun shiga uku wallahi 'yar dan uwana ce Hameedatu. Tun da ta bar kasar nan da sunan ci gaba da karatunnan ana murna, bata koma dawowa ba. Iyaye na ta nemanta ta dawo ta yi aure ta ki, babu zaryar da bamu yi a gidan Alhaji Habib ba amma atafau yace sai ta kammala karatu sannan zata dawo. Ashe azzalumin ya san abunda take shukawa a can. Allah ya isa munafiki ba zamu taba yafe maka ba". Kuka sosai Tsohon yake yana doka tafukansa a kasa saboda tsabar bakin ciki da takaici. Ya ciro wayar hannunsa ya fara kiran yayansa wato mahaifin ita Hameedan. Mutanen dake wajen kuwa jikinsu ya yi sanyi, hankulan wadanda suka bada imaninsu ga Alhaji Habib sun fara tashi. Domin kuwa sun fara tabbatarwa duk abinda ake zargin nan gaskiya ne. A cikin kotu kuma mai Shari'a Musa ne ya buga gudumarsa dan neman daidaito da nutsuwarsu. Bayan duka sun tsagaita da maganganunsu ya maida kallon shi ga Hameeda da kanta yake kasa yace "ke yarinya meye gaskiyar abinda wannan ta fada game da ke?". Shiru ta yi hawaye na bin kuncinta, ba tare da tunanin goge su ba ta fara magana cikin nadama marar amfani. "Kwarai haka ne ya mai shari'a, duk abinda ta fada gaskiya ne". Ta kwashe komai game da abinda ya shafi rayuwarta a can ta gaya musu... Tana dasa aya Alhaji Habib ya yi zumbur ya tsallaka kujerun dake bayan nasa, ya kade rigarsa ya zuba da gudu... *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​ _*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ *Na yarda so shi yake kawo kauna. Abinda kuke nuna min kauna ce ziryan masoyana. Ina sonku ina kaunarku ina matukar jin dadin kulawar da kuke nuna min. Ubangiji ya albarkaci zumuncin dake tsakanina da ku gaba daya amin. 👏* ```Page 27``` "Arrest him". Muryar alkali Musa ta ratsa kotun cike da amsakowa. Kafin ya kai ga kofar da zata sada shi da wajen kotun jami'an tsaron da suke tsaitsaye a ciki suka zagaye shi. Cak! Ya ja ya tsaya yana maida numfashi da kokarin daidaita shiga da fitar numfashin nasa, yana zare ido kamar wani bokon duniya. A yadda yake tsayen ji yake kamar a mafarki ne, zuciyarsa ta kissima mishi ina ma ace mafarki yake yi? Da kuwa ya mallakawa duk wanda ya tashe shi abinda yake da shi a duniyar nan. Wannan wace irin bakar rana ce ta zo mishi? Ta yaya hakan zata faru da shi farat daya?' Yana cikin wadannan nazarce nazarcen ya fara jin sautin ihun mutanen dake wajen kotun suna jefo shi da munanan kalamai marasa dadin ji. Tamkar an yagi fatar kirjinsa an murza masa gishiri, haka ya ji wani irin zafi da radadi sun ziyarci zuciyarsa. Ya rumtse idonsa da karfi yana fadin "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku ni Habib na cuci kauna". Ya fada lokacin da yake dafe kansa da hannayensa guda biyu cikin matsananciyar Dana sani. A cikin kotun ma hayaniyar ce ta kaure mutane suka mimmike tsaye suna la'antarsa suna nunashu da hannu kamar zasu rufe shi da duka, a cikinsu hadda manyan abokanansa 'yan siyasa da sanannun 'yan kasuwa. A kokarinsu na ganin sun wanke kansu kar a zarge su kan wannan mummunan laifin nashi da basu ma san yana aikatawa ba. Lokaci mai tsayi aka dauka a hakan, yayin da jami'an tsaro suka dawo kokarin kare Shugaba daga fushin 'yan kallon shari'ar dake cikin kotun. Dakyar alkalin ya samu nasarar tsawatarwa game da hayaniya da rudanin. Alhaji Habib kuwa ya yi tsuru tsuru a gaban jama'ar da a da suke daukarsa a matsayin jigonsu kuma uba, jagira ga ragamar rayuwarsu. Alkalin ya yi gayaran murya, sannan ya maida kallonsa ga lauyoyin Alhaji Habib yace "ko a cikin ku da akwai wani mai ja game da wannan shaida da ta gabata?". Dukkansu suka yi kasa da kansu cike da jin kunyar kasancewarsu masu kariya a gareshi. Suka ce "babu". Alkali Musa ya kalli Fadwa dake tsaye yace "zaki iya ci gaba da gabatar da shaidannunki yarinya". Ta yi godiya ga kotun sannan ta dora da kiran sunayen 'yan matan nan. Wadanda dukansu babu boyayya a cikinsu. Manya ne kuma sanannun karuwai, wadanda mafi yawan mutane suka sani a cikin garin Kano. Daya bayan daya suka gabatar da kansu da ayyukansu, da kuma alakar dake tsakaninsu da Alhaji Habib. A karshe suka rufe da bada gamsassun hujjojinsu masu bada tabbacin abinda suka fada din. Na faro hotuna ne da video wadanda suka yi dauka a sace idan suka hadu da shi Alhaji Habib din. Kamar yadda suka saba. Wato zaman kasafi na kudi da suke yi da shi, inda yake fidda musu nasu ihisani kan ko wace fita da suka yi a karshen wata. Sai voice record da suka dauka na umarnin da yake basu na suje nan, su je can a kan waya. Da kuma wadanda suke dauka na turawan nan da ake turasu wajensu. A karshe ta rufe da cewa "ya mai girma mai shari'a wadannan sune tsayayyun hujjojin da nake da su game da wannan mutumin. Ina kuma rokon kotu da ta taimaka ta duba hujjojina da kuma shaidannun da na gabatar, da kuma halin da mai laifi ya nuna karara a bainar jama'a. A taimaka a yanke masa hukunci daidai da laifinsa". Ta gama tana mai hada hannayenta waje daya tana rokonsa, hawaye na bin kuncinta. Alkalin ya sadda kai kasa yana 'yan rubuce rubuce. Yayin da kotu ta kaure da wata hayaniyar ta 'yan kallo ciki da waje. Alhaji Habib kam kansa ya gagara dagowa, ba zai iya kallon jama'a da wannan zunubin ba. Ya sunkuyar da shi kasa yana zubda hawayen nadama. A daidai lokacin ne kuma Hajiya Laurat da yaranta suka kunno kai cikin kotun. Wata sabuwar haniyar ce ta koma kaurewa ana fadin "ga yaransa nan, ga su nan yace bai san inda suke ba". Hajiya Laurat ta tsaya tangaram a gaban kotun tana karewa mijin nata kallo cikin cunci da kunan rai. Yaransa kuwa gaba dayansu kuka suke suna sharar kwalla. Mai shari'a Musa ya tsawatar ga masu tace nacen dan ci gaba da shari'a. " ke kuwa wace cs ke, kuma mene ne alakarki da wannan case din?". Hajiya Laurat ta share hawayen da suka kasa yankewa daga idonta ta amsa. "Sunana Hajiya Laurat kuma ni matarsa ce. Wadannan dake tare da ni kuma duka yaransa ne". Alkalin ya kalleta shekeke sannan yace "to meke tafe dake ne, ko kina da wata hujja da zata wanke mijin naki daga zargin da ake masa?". Hannayenta na rike da wajen tsayuwar ta sauke idanunuta bisa gare shi, tare da nannauyar ajiyar zuciya. Tana mai kara jin tsantsar tsana da kyamar halinsa tace "na zo nan dan in kara tabbatarwa kotu da abinda ta ji a bakin wannan baiwar Allah. Ta fada tana nuna Fadwa. Babu ko shakka mijina munafikin mutum ne wanda ya dade yana cutar al'uma da fuska biyu. Ni nan shaida ce game da hakan. A karshe ina rokon kotu da ta yaimaka yanke masa hukunci daidai da laifinsa. Domin 'yaya mata su sami salama da nutsuwar rayuwasu. da haka ne kadai zamu iya yakar ta'addanci da wannana safarar yaranmu mata a wannan kasar. Ganin an hukunta wannan mugun bawan ne kadai zai sanya salama ga rayuwata, domin kuwa shi ne sila kuma dalilin lalata rayuwar 'yata". Ta kai karshen maganar hade da kuka mai ban tausayi. Alhaji Habib kuwa ido ya zubawa Hajiya Laurat cikin tsananin mamaki da ya shafe duk abinda ke ransa. Yaushe ta san yana safarar mata, kuma me ta sani game da hakan nan?". Kamar ta san abinda ke ransa ta zayyane masa komai a bainar jama'ar. Tsananin kunya da dana sani sun dada lullube shi. Nadama mara amfani ta baibaye rayuwarsa. Kansa a sunkuye ya amsa tambayar alkali Musa da ya yi masa kan cewa "ya yarda ya aikata wadannan laifuffukan da ake zargin sa da su?". "Eh". Ita ce amsar da ya bayar cikin rishin kuka. Allahu Akbar! Fadwa ta fada lokacin da take dora kanta bisa tsayayyen katakon dake zagaye da ita a inda take tsaye. Godiyar Allah take a zuciyarta inda ta kara tabbatarwa kanta cewa komai na duniyar nan yana da karshe. Ta yarda ikon Allah ne kadai zai dore koma ya dauwama. Tun da take gwa-gwarmaya bata taba kawo wa a ranta zata samu irin wannan gagarumar nasarar a nan kusa ba. Yau gashi Allah ya kawo karshen zalumcin Alhaji Habib. A gaban dubannin jama'a kuma da bakinsa ya amsa laifinsa. Wasu siaran hawaye ta ji suna bin kuncinta ba tare da ta ji fitowarsu daga idonta ba. Ta dago kai tana kallon jama'ar dake cikin kotun wadanda ga baki dayansu suka yi sanyi lakwas kamar wadanda aka zarewa laka. Kotun ya yi shiru, baka jin komai sai kukan Alhaji Habib da na yaransa. Yayin da alkalin ke aikin rubutu bisa farar takardar dake gabansa... *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​ _*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 28 second to the test page``` Ya jima yana rubutun kafin ya kammala ya dago ya fuskanci al'umar dake wajen ya fara magana. "Alhmdulillah, da wadannan shaidannu da kuma amsa laifi ga masu shi muka zo karshen wannan shari'ar. Duba ga yadda mai laifin ya amsa laifinsa ba tare da wahalar da shari'a ba, kotu ta yanke masa hukuncin zama gidan kaso na tsayin shekaru ashirin da biyar, tare da horo mai tsanani. Da kuma tarar kudi Naira miliyan dari uku da dubu dari shida a matsayin diyya ga wadanda ya zalumta". Ko da jama'a suka ji haka sai suka cika da farin ciki suka kaure da ihun murna suna tafi, yayin da wasunsu ke daga murya suna fadin "daidai kenan". Wasu kuwa cewa suke "da ma kashe shi aka yi". Alhaji Habib ya fashe da wani irin kuka mai tsananin kafin ya gurfane a wajen, hannunsa dafe da zuciyarsa, saboda irin masifaffen ciwon da yake ji a cikinta. Yaransa kuwa sai suka kara tsananta kukansu, duk kuwa da yadda suke jin tsanarsa a zukatansu. Domin dai sun riga sun san har gaban abada yana nan a matsayin mahaifinsu duk kuwa irin ta'asar da ya shuka. Hatta hajiya Laurat sai da ta zubda hawayen tausayinsa duk yadda zuciyarta ta bushe. Da kyar alkali Musa ya iya tsayar da hayaniyar mutanen nan sannan ya dora da fadin "su kuma wadancan biyun da suka amsa laifinsu na aikata ta'addanci har ma da kisan jami'in tsaro. Kotu ta yanke musu hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, tare da umartar jami'an tsaro da su gaggauta kamo ragowarsu a gurfanar da su gaban shari'a. Domin su ma su karbi hukunci. Sai magana ta karshe game da ita wannan 'yar gwa-gwarmayar Fadwa. Kotu ta wanke ta bisa zargin da aka dade ana yi mata na batawa wannan mutumin suna. Haka kuma kotu na umartar hukumar kare hakkin mata da kananun yara ta jiha da ma ta kasa baki daya da su karrama wannan yarinyar da ta yi aikin da ya kamata a ce su ne suka yi shi. Sannan daga karshe su yi koyi da ita wajen gudanar da ayukkkansu. Allah ya kara daukaka duk wani mai son taimakon al'uma". Ya dasa aya tare da buga gudumarsa bisa teburin dake gabansa alamar kotu ta tashi. Gaba daya jama'ar suka mike tsaye saboda girmamawa. Sannan ne kuma alkalin ya fice ta karamar kofar da ya shigo, wato kofar ofishinsa. Jama'a suka fara bi gefen Alhaji Habib dake zagaye da jami'an tsaro suna wucewa tare da jefa masa munanan kalamai kamar su "ka dai ji kunya Alhaji". "Alhmdulillahi an yi walkiya mun ganka, Allah ya ci gaba da tonawa ire irenka asiri". "Allah ya isa bamu yafe maka ba azzalumi". "Mugu bakin kumarci". "Allah ya kara bayyana mana duk mai irin halinka". Kowa da abinda yake fada. Haka jama'ar dake cikin kotun suka yi ta fadar albarkacin bakinsu game da shi. Yana nan sunkuye a inda ya gurfana kan guiwoyinsa baya ko motsi. Jami'an tsaron dake tsaye a kansa kuwa ganin zai bata musu lokaci yasa suka kai masa cafka da nufin su mikar da shi tsaye su fita da shi. Luuu... Suka ga ya tafi tim! Ya kife kasa. Sakamokon tabinsa da suka yi. Da sauri suka dago shi suna girgiza shi. Yayin da Baffa da kannensa ma suka yo kansa cikin kaduwa da tashin hankali. Hajiya Laurat na tsaye a inda take duk tsoro ya baibayeta. "Shikenan ma jama'a sun huta da turaddadi da kuma saka ran zaka fito ka koma addabarsu". Cewar wani dan sanda da yake mikewa tsaye bayan ya dafa kirjin Alhajin ya ji shiru. Cikin rashin fahimta Faisal ya cakumo rigarsa yana fadin "me kake nufi?". "Sai hakuri, mahaifinku ya riga da ya mutu. Ba mamaki zuciyarsa ce ta buga". Sai a lokacin Hajiya Laurat ta iya motsawa daga inda take. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Alhaji ya mutu?". Ta tambaya tana dago kansa dake kasa kamar mai shinshinar kasa. Gaba daya jikinsa ya saki, babu alamar rai a tattare da shi. Su duka suka dafe kai suka fara runtuma kuka, daidai lokacin da 'yan jaridun dake waje suka fara kunno kai cikin kotun dan tabbatar da abinda suke gani a waje. Nan fa suka shiga daukar hotunansa da kokarin yin magana da iyalan nasa. Abinda basu samu ba kenan. Domin hankalinsu ya kai kololuwar tashi. Da taimakon 'yan sandan suka kai shi mota dakyar da tura mutane saboda cinkoso dake wajen. Duk wanda ke wajen burinsa ya ga gawar ido da ido. Ko wace gawa ana raka ta da adduo'in neman rahamar Allah, banda ta Alhaji Habib. Dandazon tarin talakawan dake wajen jifarsa suka hau yi da munanan adduo'i suka bi motar da ta dauke shi. Duk abinda ake Fadwa da Abba suna gefe suna kallonsu. Allah Akbar! Illa da kuma matsalar zalumci kenan. Duk yadda ya karbe ka, ka ji dadinsa wata rana karshenka zai zo. Komin girma da tarin alfarmarka Allah ba zai barka da su ba. Karshen ba zata taba yi maka kyau ba. (Ya Allah ka kare mu daga kusanci da zalumci, kar mu yi kuma kar ka bari a yi mana. Amin) Fadwa ta matse guntun kwallar dake idonta, tana shirin juyawa ta ci karo da zungureriyar lasifika a gabanta. Kyakkyawar budurwar dake rike da lasifikar ta fara magana "barka dai Auntynmu 'yar gwa-gwarmaya. Ina taya ki murnar wannan nasarar da kika samu". Ta yi murmushi sannan ta amsa mata da "na gode". 'Yar jaridar ta dora "in ba zaki damuba ina da 'yan tambayoyi ne a gareki". Ta gyada mata kai "ina jinki". "Duba ga yadda kika sami wannan nasarar a cikin wannan abin da kika kira da gwa-gwarmaya, shin yanzu kuma mene ne burinki na gaba?". Sai da ta yi murmushi kafin tace "to alhmdulillah a gaskiya yanzu bani da wani buri da ya wuce in kirkiri wata hanya da zata rika samarwa irin matan nan da matsala ke rabasu da gidajensu kudin biyan bukatunsu. Ina nufin in samar da wata cibiya ta musamman da zata zamo gata ga duk wata macen da take cikin hatsarin karuwanci. Cibiyar da zata fara kafuwa daga gobe. Ina so in yi amfani da wannan damar in isar da wannan sakon ga al'umar jihata. Ta dan yi jim kamar mai wani tunani kafin tace "na yi rayuwar bariki ta dole, na kuma zauna da wadanda suka yi ta son ransu. Na gani na kuma san yadda karuwanci yake. Na tabbata babu wadda take yinsa don dadinsa, sai dai kawai su yi shi don neman abin biyan bukatunsu na dole. A saboda haka kafin in kai ga ganin karshen fitowar mata daga gidajensu yawon duniya sai na fara da samawa wadanda suka fiton mafita da madafa. Na gama yanke hukunci daga gobe kuma zan fara zartarwa. *Fitilar 'yancin mata* sunan karamin kamfanin kuma masarrafin abubuwa masu yawa. Wannan kamfanin shi ne zai zama gata ga ko wace macen da ta rasa gata a jihar Kano. Nice jagorar wannan tafiya. Ma'aikatan kamfanin kuma zasu kasance wadannan matan marasa mafaka da makoma. Wadanda dukkaninsu sun riga sun tuba ga abinda suke yi sun mika wuya gareni sun canja rayuwa. Adireshin kamfanin yana nan unguwar mai tama babban layi. Wannan ita ce lambar da duk wacce ta hadu da wannan kaddarar zata neme ni". Ta karkare tana nuna lambar waya ga 'yar jaridar". Tana gama maganar ta juya ta nufi gun da motocinsu suke, inda Abba da sauran 'yan matan nan suke jiran ta. A cikinsu kuwa hadda Hameeda. Wadda ta gama saduda har ga Allah ta mika wuya ga Fadwa. Abba kuwa kansa na gefe ya tamke fuska ko kalloninda take baya son yi. Murmushi kawai ta yi ta shiga motar tana maidawa jama'ar dake faman daga mata hannu martani. Suka tashi motocin duka uku suka fice daga harabar kotun cikin tsananin farin ciki. *Nasmat* ✍ 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 *'YAR GWA-GWARMAYA.* (Fitilar 'yan-cin mata.) 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​ _*Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร*_ https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation? © 'Yar mutan Arkilla✍ ____________ ```Page 29 last page``` 👐 Da isarsu gida suka fara shirye shirye a matsakaicin wajen nasu da take kokarin mayarwa kamfanin dogaro da kai ga matan hanya. Farin ciki a ranar kam ba a magana. Hameeda ta zama daban a cikinsu domin kuwa su 'yan matan nan tuni sun riga da sun saba da su. Ita kadai ce take jin kanta bakuwa. To dama dai haka rayuwa take aka ce lokacin murnar wasu lokacin kukan wasu. Hakan ce ta kasance a gidan Alhaji Habib Inuwa. Abin duniya ya taru ya yi musu yawa. Shi kuwa Alhaji ya riga ya tafi tafiyar da bata da waige balle dawowa. Bakin cikin iyalansa bai fi mummunan tambarin da ya tafi ya bar musu ba. Domin kuwa duk yadda suka so ko suka ki, shi Uba ne kuma jigo ga rayuwarsu har abada ba za'a taba goge shi a cikin tarihinsu ba. Abin kunya mutane uku ne kacal suka yi jana'izarsa daga limamin gidansu sai 'yayansa biyu Faisal da Baffa. Gidan nasu ma ba dan ana jin kunya da tausayin yaran nasa ba da tuni an ruguza shi. Mutane ko ta ina tofin ala tsine suke ga mamacin. Fadwa kuwa cewa suke Allah ya kara kawo dubunta, Allah ya shi mata albarka, ya taimake ta kan dukkanin al'amuranta. Bayan makonni uku dukiya da kadarori wadanda basu taba sanin ya mallaka ba ake ta kawo musu daga kasashe dabamdaban, a matsayin na shi da ake juya masa a can. Ga wadanda yake da su a nan manyan kamfanoni biyu da gidajen man da ba zasu kirgu ba. Haka suka yi ya tara dukiyar da suke ganin ba su ba har 'yayan da zasu haifa sai 'yayansu sun ci ta. Hajiya Laurat da har cewa ta yi ba zasu ci kudin ba, amma da ta nemi fatawa gun wani malami sai yace a matsayinsu na magada wadannan kudin halal ne a gare su. Wanda ya neme su ta mummunar hanya shi suke haramun a wajensa. Tunda suka ji haka suka fara kamfata daga cikin kudin suna gina masallatai da makarantu. Inda ake wahalar ruwa kuma su gina murtsatse. Cikin dan kankanin lokaci suka wanke bakin fentin da ya shafa musu da alkhairansu. Birni da kauye yabonsu ake kai ka ce wasu sanannun 'yan siyasa ne. Duk wannan abin da suke hankalin Baffa baya jikinsa, a duk wani bugu na zuciyarsa tana yinsa ne tare da tunanin Fadwa. Ya yi juyin duniyar nan amma ya kasa cire tunaninta a zuciyar tashi. Fadwa kuwa tana can aiki ya kankama. Kamfani ya ginu har an fara gudanar da ayyukan sarrafe sarrafe. Domin kuwa bayan kudin diyya da kotu da umarci iyalan Alhaji Habib su basu. Su yaran da kansu suka ware kaso mai tsoka a cikin dukiyar suka mallaka musu. Haka gwamnatin jiha ma a madadinta ta basu ruwan kudi naira miliyan biyar, domin a cewarsu wannan aikin su ya kamata su yi shi. Ta haka ne suka sami wadataccin kudin da suka yo odar manyan injuna da ragowar kayan aiki daga kasashe dabamdaban. Cikin wata daya suka kammala daukar yawan ma'aikatan da suke bukata suka fara aiki babu kama hannun yaro. A wannan kamfanin suna buga zannuwa iri iri wato atamfa. Suna buga takalmi na mata da na maza da jakunkuna. Suna yin mayafai. A bangare daya kuma ayyakan takardu ne. Litattafai ake bugawa manya da kanana. Kafin kace meye kamfanin *FITILAR 'YANCIN MATA* ya bunkasa ya yi fice a fadin najeriya. Ya zamana bayan 'yan kasuwa ma gwamnati da kanta tana yi da su sosai wajen basu kwangila ta buga zannuwa da litattafai a lokutan siyasa suna rarrabawa ga mata da makarantu a matsayin campaign. Madalla da wannan tsarin na Fadwa, hakika maganarta ta bayyana gaskiya ta yi halinta. Mata masu zaman kansu a garin Kano sai kawo kansu suke gare ta manya da kanana har ma da wadanda zasu kai sa'ar hihuwar wasu a wajen. Sun fada sun maimaita cewa wahala da tsananin rashin gata ga masu barin gidajen iyayensu su suke saka su yin karuwanci ba dan suna da ra'ayin yin hakan ba. Sannan kuma babu yarinyar da take barin gidajen iyayenta bisa son ranta sai dai ta barshi dan dole wanda mafi yawa duk ta sanadin auren dole suka fi fitowa, sai kuma wadanda ake korowa idan kaddarar yin cikin banza ta fada musu. Jin wadannan maganganun daga garesu yasa Fadwa ta ware wasu manya daga cikinsu ta hada su a matsyin komitin wayar da kai ga iyayen yara mata. Wadanda suke zagayawa cikin kauyuka da birane suna wayarwa iyaye kansu game da hatsarin dake tattare da korar 'ya mace daga gidansu. Da kuma illar shi kansa auren dole. Ai kuwa da yake abin yinsa ake da gaske kafin wani dan lokaci fadakarwar ta baza ko'ina na birni da kauyukan dake cikin jihar Kano. Fadwa kam tsakaninta da Allah sai godiya, domin kuwa ya gama mata komai a wannan rayuwar burukanta sun cika, rayuwarta ta haska, sunanta ya tumbatsa a cikin duniya. Ta kara gogewa ta yi fresh ta kara haske. Kwanciyar hankali ta samu, jiki ya murje tai bul bul abunta bata da matsala da kowa. 'Yan mata marasa gata da karuwai daga ko wane yanki gargadowa suke zuwa ga wannan rahamar da Allah ya aiko musu. Kuma duk wadda ta zo wannan kamfanin babu ita babu karuwanci har abada, sannan kuma ba zata nemi abu ta rasa shi ba. Fadwa ta zama wata fitila da ta haska rayukan mata da iyayensu. Matsalolin da ake yawan samu na korarar 'yaya mata a gidajensu ta ragu kashi tamanin da biyar bisa dari. Haka kaso cas'in a cikin dari na karuwan da a da suke zube a cikin Kano suna saida kansu sun koma ma'aikatan kamfanin *FITILAR 'YANCIN MATA*. A yanzu karuwanci baya burgesu. Burinsu shi ne su hana masu yi, kuma su dakatar da masu shirin fitowa su yi. Duk wata sabuwar jaridar da zata fita kasuwa sai an sako maganarsu irin shahara da gagarumar nasarar da suka samu farat daya. Babu shakka Fadwa ta yi gwa-gwarmaya kuma ta yi nasara. Sannu a hankali ta fara kokarin sada matan da suke karkashinta da iyayensu. Wasu su koma gidajen nasu wasu kuma iyayen da kansu suke cewa su zauna a nan tare da ita har Allah ya fiddo musu da mazajen aure. Munanan ayyuka sun ragu fiye da kima a cikin garin da ma wajensa. Domin kuwa karuwai sun yi wuyar gani, babu su babu alamarsu a duk guraren da aka saba zuwa a same su. Hakan ya sanya matan aure suka sami sa'ida a gidajen aurensu. Domin da yawan mazan sun watsar da matayen da suke gidajensu sun rungumi karuwai. Amma a yanzu rashin karuwan yasa duka sun maida hankalinsu ga iyalansu. Wannan bun ba karamin dadi yayi wa matayen sunna ba. Kuma sun tabbatar wannan duk ta dalilin 'yar gwa-gwarmaya ne. Hakan kuwa yasa duk wata salla da zasu yi sai sun rokar mata rahamar Allah da kwanciyar hankali ga ilahirin rayuwarta. Baffa ya kasa hakura da Fadwa, zuciyarsa ta Gaza daurewa kan tsananin sonta dake addabarsa na tsayin lokacin da ya santa. Ya isar da bukatarsa gareta kuma alhmdulillahi ta amshi rokonsa. Ta aminta da soyayyarsa dari bisa dari. Ko babu komai tana son ta yi aure domin karawa kanta daraja a duniya da lahirara. Kuma tana son daukacin matan nan da suke tare da ita suma su yi koyi da ita su yi aure tunda ba zasu dauwama a nan ba. Farin ciki ya cika gidan marigayi Alhaji Habib a lokacin da suka ji kulkuwar alaka ta soyayya tsakanin Fadwa da Baffa. Wannan ne yasa ba wani bata lokaci ba aka shiga shirye shiryen biki. Zuwa lokacin kuma Abba da Hameeda sun koma daidaita kansu. Wata sabuwar soyayya suka koma ginawa kansu, idan ka gan su sai ka rantse basu taba samun wata matsala ba. Bayan gwaje gwajen asibiti su ma Fadwa ta fara shirin nasu auren da kokarin sada su iyayensu. Wannan abin kuwa ba karamin taba zukatan ragowar matan nan ya yi ba. Hakan yasa suma wasu shida daga cikinsu suka daidaita da tsofaffin mazajen dake neman su a baya aka fara maganar aurensu. Alhmdulillah wanan abu ba karamin faranta ran Fadwa ya yi ba. A lokaci daya aka saka duka bikin nasu. Daurin aure takwas a rana daya. Daurin auren da ya sami hartar manyan manyan jagororin gwamnati da jigajiganta. Sun kuma sami tallafi daga gwamnati da wasu daidaikun mutane da ma kamfanoni masu zaman kansu. Bayan auren ko wacce ta tare a gidan mijinta. Watanni biyu kuma Fadwa ta koma bakin aiki bisa amincewar mijinta abokin rayuwa, wanda take jin samun kamarsa zai yi wuya a duniyar nan. Baffa da mahaifiyarsa da kannensa sun karbe ta hannu bibbiyu babu wani bambanci babu canjin fuska. Sun kuma nuna goyon bayansu dari bisa dari kan aikin da take na taimakon al'uma. *Bayan shekaru uku.* Kamfanin *FITILAR 'YANCIN MATA* ya kara samun daukaka, sunansa ya tumbatsa a duniya. Duk matan da aka fara kafa kamfanin da su sun yi aure sun tafi gidajensu. A yanzu sai sababbin fuska da aka dauka. Kuma dukkansu Fadwa ce ta yi musu komai da aurensu. Ab'ha da Hameeda na can suna rayuwar aurensu cikin farin ciki. Bayan ta daidaita tsakanin ko wannensu da iyayensa. Yau ta kama ranar week end ne asabar. Fadwa tana gida tare da mai gidanta da kuma karamin Fawad dinta. Yaron da ta haifa a shekaru biyu da suka wuce. Muhammad (Fawad) mai matukar kama da mahaifinsa. Yaro dan shekara biyu a duniya. Ya zama farin ciki kuma sanyin idanunsu. Falon ya yi tsit! Baka jin komai sai dariyar yaron ya yake ta yi yana wasa da teddynsa tare da mai renonsa Hannatu. A dakin Baffa kuma shi ne a kwance ya yi dai dai bisa lallausan gadon, idonsa a lumshe tamkar mai yin bacci. Ta tura kofar dakin ta shiga da salla. Cikin wasu kaya na atamfa dinkin doguwar riga buba. Ta yi matukar kyau kamar a sace ta a gudu. Ta kara cika ta yi bul bul gwanin sha'awa. Hannunta dauke da basket na abinci. Ta isa gaban gadon ta jere komai a kasan tails din inda ta shimfida wani zagayayyen farin kyalle, ta kalle shi da dara daran fararen idanunta tace "sweet husband ur break is ready". A hankali ya bude idonsa ya zube su a kanta kamar yau ya fara ganinta. Shi a kullum Fadwa sabuwa take zamar masa. Duk wata shiga da zata yi sai ta yi mishi kyau. Ya lushe idon ya koma budewa yana fadin "to a zo a dauke ni". Ya yi maganar a shagwabe da sigar wasa. Ya bata dariya sosai ta kuwa dara sannan tace "ai ko Fawad dinka ya wuce dauka yanzu balle kuma kai ubansa". Ya waro ido kadan "au haka ma zaki ce? To shikenan ki ci abincinki ke kadai". Jin hakan yasa ta marairaice fuska "afwan sweet husband tuba nake zo in dauke kan". Ta isa gareshi tana kokarin daga kansa ya tashi zaune. Shi kuwa sai dada narke mata yake yana dandara kansa da filo. "Allah Dadyn Fawad rigimarka ta yi yawa, yanzu ya kake so a yi?". Ta tambayeshi lokacin da take daidaita zamanta bisa gadon. Ido daya ya kashe mata yana daga bargon da yake rufe da shi alamar ta shigo. Ta gane wayonsa da kuma manufarsa saboda haka ta makale kafada "ka bari mu fara yin break to". Ta fada a marairaice. Shi kuwa gogan sai ya saki blanket din ya juya mata baya. Wai a dole ya yi fushi. Da sauri ta kwanta a bayansa ta yi masa kyakkawar runguma tana rada masa a kunnensa "kar ka yi fushi da ni masoyi. Ni da duka abinda nake da shi naka ne hakak malak. Gani gareka hasken raina". Baffa da ya kasa jure salonta da yadda take maganar ya juyo da sauri ya kankame da yana fadin "Fawad zai iya girma a idonki Fadwa amma ni ba zan taba girma gareki ba. Ki sani ni ne asalin Babynki mai matukar bukatar kulawarki. Pls take a Gud care of me kin ji Fadwana?". Ta kanainaye mijinta cike da so da kauna da kuma jin dadin yadda yake gaya mata gaskiyarshi tace "yadda ka so haka Fadwa zata kasance..." Bata karasa ba ya mirginata suka shige blanket aka hau musayar... Nasmat kam na tattare litattafai da birurrukana nace "fatan alkhairi ga ilahirin rayuwarki 'yar gwa-gwarmaya ". Tammat bi hamdillahi. A nan na kawo karshen wannan labarin mai cike da darussa ga rayuwar al'uma. Shakka babu labarin kirkirarre ne, amma abubuwan dake cikinsa asalin zahiri ne. Babu wanda ba a aikatawa a cikinsu. Fatana a kullum shi ne rubutuna ya yi tasirin canza rayuwar koda mutum daya ne daga mummuna zuwa kyakkyawa. Allah ta ala yasa mu dace amin. 🙏 Godiya mai tarin albarka ga daukacin masoya masu kokarin bibiyar wannan labarin wadanda ba zan iya kirga dukkaninku ba. Ina son ku duka kuma ina kaunarku. Fatana shi ne ku amfana da duk abinda na zo da shi. Na san kuna tare da ni, to ku ci gaba da kasancewa da ni zaku yi farin ciki. Ina muku albishir da sabon littafina na gaba mai suna *BAN SAN SHI BA* karamin labari mai dauke da babban sako. Zai fadakar ya wa'azantar, sannan ya nishadantar da ku masoyana. *Jinjina ta musamman ga kungiyar* ZAMANI WRITERS ASSOCIATION. Da daukacin marubutan dake cikinta. Allah ya kara hasken kwakwalwa jarumaina. 👍😇 Na barku lafiya 🙏 *Nasmat* ✍