AISHAH-SIDDIQAH 4 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com TUNASARWA/JAN HANKALI Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba. Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa. Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu. Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde. In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi Atqaakum”. Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna. Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada. –Takori Sumayyah AbdulQadir. SADAUKARWA Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI’S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki. KIYAYEWA Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali. GODIYA DA JINJINA Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa. Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira. In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH. KAFIN MU FARA INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. -Takorinku AISHA SIDDIQAH 4 H aseenah na ganin fitowarsa ta mike tsaye with great excitement a kan fuskarta. A take sai Aisha taga Hamma ya wani irin daure fuska. Gabadaya ya koma babu annuri. Ya fito a basarakensa sosai. Yau sai taga ma Hamma yafi mata kama da yarbawa akan Fulani. Fuskar nan ba rahma ko kadan ko kankani. Yace cikin wata irin murya. “What are you doing here?” Haseenah tace “kayi hakuri Prince, just give me few minutes of your time. Ta’aziyya ce nazo nayi maka na Emir. Aunty Taiwo ta gaya min kana Argentina, nikuma na zo yin wani project daga office dinmu, nace zan zo har gida in yi maka ta’aziyya kuma in yi amfani da wannan damar in baka hakuri Prince. Am sure she told you sakon dana bata gareka”. Sai Hamma ya zauna gefen Aisha yana kokarin cooling anger dinsa, ita kuma Aisha taji kamar an kada mata kararrawa a cikin kanta, domin nan take ta ayyana itace tsohuwar budurwarsa Haseenah Ambursa, wadda Kiki ta bata labari. Don haka nan take sai ta mike, amma sai Hamma ya rike hannunta, ya saka idanunsa cikin nata yace “ina zaki mu da zamu fita kuma?” tace “naga kayi bakuwa ne Hamma, zan kawo mata ruwa da lemo ne in baku wuri”. Sai Prince yace mata “zauna, ba shan ruwa ya kawota ba, yanzu zata tafi”. Ya mayar da ita zaune inda ta tashin, zuciyar Aisha tayi mata nauyi, ba don komai ba sai don tuno soyayyar da ake bata labarin Hamma ya yiwa Haseenah, har shine silar da yaki aure shekaru goma sha uku, a zuciyarta tace ita daman matar cushe ce a gareshi, kila yanzu Haseenah ta dawo rayuwarsa kenan, dan bond din da suka fara developing ita dashi zai bi iska. Zai tashi a banza. Mai wuri ya zo mai tabarma sai ya nade kayarsa. Sabon takaici ya lullubeshi na yadda akayi Haseenah ta samu address dinsa na Argentina gun Taiwo, ta shigo gidansa na Sunnah bada izninsa ba. A ran sa yana ayyana yadda zai ci uwar Pareto ciki da waje, da yake budewa kowane kare da kowanne doki gidansa ba tareda ya masa izni ba. Haseenah ta roki samun privacy na tanaso suyi magana ita da shi, wani asararren kallo yayi mata yace. “I have got nothing to hide from my wife”. Nan duk Haseenah tabi ta sha jinin jikinta, cewa wannan sabon Prince Kehinde Abdulrasheed ne, ba wanda ta dade da sani ba. Jikinta yayi mugun sanyi. Ala dole ta fara fadin abinda ya kawota akan idon Aisha. Na farko ta bashi hakuri, kan abinda ya faru shekaru sha uku a baya, tace babu ranar da bazata wayi gari ta kuma wuni tana nadama ba, amma bata da excuse, bata ma son kawo shi. Ta yarda kaddararsu ce tazo a haka amma ba don rashin so tayi masa abinda tayi ba”. Sai Haseenah tayi shiru, sannan ta kalli idanunsa tace “Kehinde, you will always be the one that has got my heart, and I am so sorry for being the reason you stayed this long without a wife. Na tabbata nima hakkinka keta bina na kasa aure sai yanzu, ina ji a raina kullum in har ba na nemi gafararka ba zan fara rayuwa ne akan karya. Ka yafemin. Yarinta ce da shaidan suka taka rawarsu gareni a lokacin. Amma na maka alkawarin cewa na dau darasi na domin Tokumbo bai aure nib a bai kuma kara waiwayata ba bayan ya gama kwasar rabonsa a tare dani”. Prince ya kalleta sai yaga tana share hawaye, a zuciyarsa yaga zallar nadama a tare da ita da talalar Ubangiji bayyananniya. Haseenah duk ta tsofe, wannan kyan duk ya dushe. Ba dai cikin wahala take ba, amma kuma duk kyannan na kuruciya babu shi a tareda ita. Sai kawai ya daga kai ya kalli Aisha, a take sai yaji duk wani bakin cikinnan na Haseenah yana ‘melting’, har ya zamo babu shi babu sauransa ko kadan a tare dashi. Yayi duba ga irin kyawun da Aisha tayi a gabansa, tana sanye cikin shirin atamfa ‘super exclusive, looking beautiful and innocent, yaga cewa in bai yafewa Haseenah bama kamar ya yiwa Allah butulci ne. Saboda ya bashi abinda ya fita sau dari. Wannan shi ake kira “blessing in disguise”. Da wannan tunanin sai kawai Prince ya dubi Haseenah yace. “Haseenah Allah ya yafe mana bakidaya, yes I was hurt, amman in gaya miki gaskiya I have no ill feelings towards you now, Allah ya wanke min zuciya yayimin sakayya da AISHAH-SIDDIQAH...”. Ya dan kalli Aisha da itama shi take kallo, yace “na yafe miki Haseenah ko don albarkacin Aishah. Saboda ba don kinyi abinda kika yi din ba, da ban hadu da ita Aisha ba, so in this way, I must say a big THANK YOU! Allah kuma yasa ku zauna lafiya keda mijinki din”. Prince sai yaga Haseenah tana kallonsa kawai, ta sake share hawaye tace “thank you”. A ranta tana mai kissima babban rashin datayi na Prince Kehinde, wanda ta tabbata ko shugaban kasar Ingila taaura bazata maida kamarsa ba. Prince ya mike ya dubi Aisha yace “muje ko?” Sai Haseenanma ta tashi tace “to na barku lafiya, Madam Aisha bye, till next time”. Prince yace “a’ah Haseenah babu next time, please, kamar yadda nace “I have no ill feelings towards you, haka babu alaqa, na yafe miki, but please don’t show up in our house again”. Tace “in sha Allah. You really deserve to be happy, Aisha congrats to you, you don’t know what God did to you!”. Daga haka sai tayi wani murmushi mai daci ta tafi. Aisha a ranta taji dadin yadda Hamma ya hanata tafiya, ya girmamata a idon Haseenah, amma duk da haka wani irin kishin Haseenah take, ta hau ayyana irin mugun son da Prince yayi mata, data tuna hakan sai taji wani bala’in haushi a makogaronta. Ta koma tana cewa a ranta meyasa ma take jin haushin? Itada ba son Hamma take ba. wata zuciyar tace “ai dai mijinkine da so ko babu SO. Haka dai, duk ta zama confused, taga cewa ko Ishaq da take ikirarin ta so, bata jin wannan zafin zuciyar a kansa da wata. Haseenah na fita, Aisha ta zame hannunta daga na Hamma, ya kalleta yace “muje” tace “nidai na fasa zuwa ko’ina, sai ka dawo kawai, I don’t feel like going out any more” Hamma yace, “Why?” tace “hakanan, ban jin dadi sai wani lokacin”. Ta soma warware daurin kallabin data yi. Nan Hamma yaso ya gane meke faruwa. Ya tuna ranar da yaji tana maganar Ishaq, abinda yaji a ransa, balle ita yau dungurungum Haseenar ce tazo. Sai yace. “Aisha listen to me, Haseenah wata long chapter ce a rayuwata da bani ko son tunawa, don Allah ki fahimta, don’t read too much into it”. “Bakomai” inji Aisha. “Ba sai ka min bayani ba Hamma, matar so ce tazo ban hakuri, love of your life akace ko…. so don’t owe me any explanation. Ni daman ai matar huce haushi ce, so me zai kai nima jin zafin zuwanta? Har zaka tsaya bayanai. Ba komi Hamma bari in yo sallah”. Ta wuce. Prince yana kiran sunanta “Aisha, Siddiqah…Aishah…” tace “ba komai Uncle”. A ransa yayi tsaki yace shi dai Allah ya isa tsakaninsa da Taiwo, ya samu sun fahimci juna yana zaman zamansa ta kwanto masa kura. Yace to wai ita Aisha yanzu har ta san kishi? Ko dai itama ta fara sonsa ne? sai yace “shima fa haka yaji ranar da tayi maganar Ishaq. Haka Hamma ya zauna yanata tsaki buhu-buhu shikadai. Yaje dakinsa yayi sallah ya dawo dakinta yayi knocking, tun kafin ta bashi iznin shiga yasa kai. Yana shigowa tana fitowa wanka daga ita sai tawul, ta juya a firgice zata yi baya ta koma tace “Subhanallah Uncle lafiya?” A ransa yace “wato Haseenah ta zo, kalmar Uncle ta dawo, kai! Taiwo Allah ya isa!”. Ashe a fili Hamma ya fada, yana bude ido sai ya ga Aisha bata nan ashe ta koma toilet din ta rufe ta bar shi a wurin. A wunin ranar bakidaya abun duk ya dameshi, gashi Aisha taki yarda ta tsaya ma yayi mata bayani. Ta zama wata sumu-sumu a gidan. Ta takure kanta, abin duk yabi ya addabeshi. In ya tuno kalmar nan ta “Haseenah matar so” da tace sai yace “Omooo!” Daga ranar da Haseenah tazo, dan taya shi kwanan da ya samu ana yi duk an daina. Ta koma dakinta bakidaya. Yau Hamma ya dawo can dare, ya zo ya sameta a falo tana barci a kujera, ya tasheta yace “Aisha tashi muje daki ki kwanta mana” Aisha ta bude ido fal barci, tace “yau dai ka kwana a gadonka Uncle”. Ya rasa yadda zaiyi da ita dole ya wuce ya kyaleta, don ta kwashe dankwalinta ta koma nata dakin. Washegari Nenne ta kirata Aisha ta amsa suna gaisawa, Nenne ta ji ta wani iri, da ta matsa da tambayar meke damunta? Aisha tace bata jin dadi ne. Hajiya Nenne mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki, nan da nan ta dauka ciki ne keda Aisha ta soma murna baka da zuci. Ta kira Prince tace “Hammansu ashe Aisha bata jin dadi?” Sai kawai yace “eh” sai gata ta fito falon domin ta dora abinci, yana kallonta lokacinda take fitowa suna wayar shi da Nenne. Sai yace da Nenne gatanan ma ta fito, ina jin girki zata yi”. Sai Nenne ta hau fada “itada batada lafiya zaka sa girki? A barta ta huta. Naji muryarta tayi kasa sosai. Kai da zakayi ta lallabata Hammansu, kasan me juna biyu hutu takeso”. A ransa Prince yace “me Nenne ke nufi ne?” Ita Aisha bata ji ba, yace “juna kuma Nenne? What’s that?” tace “kunje asibiti?” yace Nenne daga kwana uku ne zuwa yau fa” Sai Nenne ta hau fada tana cewa “har kwana uku tana fama da ciwo baku je asibiti ba? Ina Aishar? Bani ita” yace “gata” yana karasawa kusa da ita da wayar a kunnensa. Nan Prince ya mikawa Aisha wayar, Nenne ta hadasu su duka tana surfesu da fada, “Aisha ki ajje sokoncin nan kuje a dubaki, haka zaki zauna da ciwo? To dai ciki ba’a masa haka, Allah ya raba ku lafiya”. Ai jin ciki sai Aisha ta yanke da kakkaifar wukar hannunta bata sani ba, tayi maza ta jefar da wukar, tsabar firgici, shima Hammah yace “ciki kuma Nenne?” tace “eh mana. Ba shine ba?” Sai yayiwa Aisha wani kallo, ya kece da dariya. Yace “Nenne yaushe tace miki ciki ne da ita?” Sai Nenne tayi shiru, sai kawai Hamma ya sake fashewa da dariya ya kashe wayar. Aisha itama abin ya dan bata dariya, ta dan dara ba shiri, ta kalli Hamma yana kara kyalkyacewa (he looks amazing), kamar bai ma san kalar kyan da far’a take yi masa ba. A wannan dan dakikan da take kallon Hamma Prince, sai taji (her whole world feels complete). Wannan din mijinta ne da ya hada komai da dan adam ke burin samu, kyau da nagarta, nasaba, ilmi da arziki da kuma kyan hali. Sai kawai zuciyarta ta hasaso mata haka yayi rayuwar soyayya da Haseenah, ita to da aka cusa masa ma ya sake yanzu yake kula da it aba karamin dadi take ji ba, to wannan wane irin dadi Haseenah tayi ta ji a ranta sanda suke tare suke soyayyah yana kula da ita? Sai kawai far’arta ta koma, Siddiqah ta mayar da annurin fuskarta ta sake dinkewa tsaf. Ganin haka sai ya kashe gass din data kunna, ya kama hannunta suka wuce (sitting room). A tare suka zauna a two seater, Hamma yace “Aishah, bana son mu gina rayuwarmu akan zargi da rashin communication. Ko me nayi miki banso kina fushi dani, just tell me. Kina ji na?” Aisha tace “yes” don taga ya kawar da wasa, he is serious now. Yace “menene yake damunki tun ranar can kike ta attitudes?” tace “babu komai” “ko ki fada min ko in kira Nenne, ita in ta tambaya na tabbatar zaki gaya mata” tayi shiru dai, da ya matsa sai tace “Uncle ko ka kira Nenne ni ba abinda kayi min, hakannan dai kawai ban jin surutu”. Hamma yayi shiru, daga bisani ya sunkuyar da kai, yace “kan zuwan Haseenah ne ko?” Sai Aisha ta mike tace “bari in karasa girki na”. Sai kawai ya janyota ta fado cinyarsa duk ta daburce tana kokarin tashi kawai sai taji yayi hugging dinta ta baya gabadaya. “Don Allah Uncle ka sake ni….” yai shiru, jin baida niyya itama ta share tayi shiru, baka jin komai sai bugun zuciyoyinsu. Can kuma Hamma yace (in a cool tone). “Yes, Haseenah was my girlfriend, naso aurenta, amma (she did something bad) da ya raba mu. The worst thing da kika sani za’a yiwa masoyin gaskiya. Kuma a kanta ne na rufe babin mata a rayuwata, wanda hakan yasa I feel Kaman duka daya suke, dalilin ma kenan da yasa ban kuma neman wata ba, kuma ko an bani cikin ‘ya’yan ‘yan uwana a family sai ince banaso…. Toh Aisha har saida Nenne ta nemomin aurenki da kanta, aka yi ban sani ba, don ta san inna sani bazan yarda ba, amma tun ranar dana je asibiti duba Nenne, na ganki, na yaba dake a raina Aisha, har na gayawa Nenne, nace wacece wannan yarinyar mai hankali haka…. Kinga dai kudin goro na yiwa mata, but you stood out, I was impressed with you”. Long story short, tun a lokacinma da bansan ke matata bace, naji kin burgeni da attributes dinki, kuma zama dake da nayi na dan lokaci na sake ganin me Nenne ta ganin min. Aisha naga meyasa iyayena suka nemo min aurenki suka aura min. Kamar yadda kikace addu’ar Nenne a filin Arfah ce ta fado a kanki wannan haka ne. don haka ke zabin Allah ce a gare ni. You are a light in my life and I am telling you you are shining so bright. Kinga duk ciwon dana ji na rashin Haseenah? To yanzu godiya nakewa Allah da nayi wannan rashin nata, don I wouldn’t have met you… So don Allah ki cire maganar Haseenah a kanki, babu abun fushi a wurin, You my Dear kin zama ‘ife mi, orun mi, iyawo mi’ kinji Aisha?” Sai ta daga kai. A zuciyarta wani sanyi na zuba, ashe haka ake ji in mijinka ya fifita ka kan kowa? That’s the Yoruba husband in action. Sai taji haushinnan yanata tsiyayewa… yana bin rariya, ta gyara zata tashi ya kara riketa, yace, “kin fahimceni yanzu?” Tace “yes Uncle” yace “Uncle ya dawo dai? Don Allah ya koma. Ni ina murna kina ce min Hamma, daga nan in zama honey, watarana in dawo Sweetie, shine kuma za’a koma Uncle dinnan, haba babyn Nenne da Dade”. Sai kawai Aisha ta saki murmushi. Tace “naji Ya Hamma” yace “ko kefa?” Sai tace “me kace dazu da yarbanci?” Sai yace “ashe kina ji? To ki koya ki fassara mana”. Aisha tayi dariya, sai lokacin Hamma yaji sanyi a zuciyarshi har da ajiyar zuciya. Bakinsa daidai saitin kunnenta yace “Babyn Nenne da Dade kuma Babyn Hamma ko?” Prince ya fada yana jin wani cool feelings for her, sai ta tashi da karfi zata wuce kitchen don kunya sosai ta lullubeta, tana ‘yar dariya. Hamma yayi maza ya dawo da ita jikinsa. Yaji dadin yadda yana mata bayani ta sauka, kuma da gani har ranta abin ya wuce. She’s a very understanding person. Sai Prince ya sake rungumeta sosai ta bayanta, yayinda take zaune a kan cinyar sa. Itama Siddiqah sai tayi mukus…. Hamma ya kwantar da kansa bisa masangalin wuyanta… yana sunsunar kasan wuyanta, duk sunyi shiruuuu na wani lokaci, kamar ruwa ya cinyesu. Bugun zuciyoyinsu kawai kake ji wadanda ke bugawa a lokaci guda. Murya a sanyaye Aisha tace "Hamma, thank you for the explanation, nasan ba dole bane kayi min bayaninnan, amman naji dadi da kayi min din, domin ya wanke min zuciya. In sha Allahu kuma nima bazan qara fushi ba kan maganar nan". Prince yayi murmushi, voice dinta yana caressing din sa, gabadaya wata kasala ce ma ta sauko masa, yana ta kokarin dannewa. Ya dai kasa magana yai shiru, ya rufe ido, listening to her soft sound, tana masa wannan maganar cikin lumana da gamsuwa da abinda yace mata, and the softness of her skin dake kwance a jikinsa yana kara tasiri a tare dashi. Sai Hamma ya samu kansa da dan murza hannunta …. jin shirunsa yayi yawa bai amsa ta ba, sai Aisha ta juyo kadan haka ta dubeshi. Sai ta ga Hamma da ido a lumshe, kamar mai jin barci. A tsanake tayi kokarin tashi daga cinyarsa, ya kuwa rike ta gam, ya dan bude idon yace "ina zaki?" Aisha tace "abincin zan qarasa" yace "kashe gass din, we will eat out today, just stay here…". Aisha tayi shiru, ta koma jikin Prince ta kwanta tayi lamoo! Yace "please Aisha..... muje outing din?" Tace "toh ai bacci kake ji naga", Hamma yace "bacci? Did i say so?" Ta ce. "To ai Hamma idonka rufe yake fa tun dazu, ina ta maka magana bakaji ba, gashi ma muryar bacci kake yimin". Prince bai san sanda wani kasaitaccen murmushi ya kufce masa ba, he so much loves her naivety. And she is observant, but totally ignorant ga halin da yake ciki. Yes, yanayin sa gaba daya ya canza, wata muguwar sha’awa ce ta saukar mashi. It seems with every word she says kara yayyafa ma wutarsa petrol take, amman babyn Nennen bata gane ba. Wannan childishness dinnata yana kara burge shi. Hamma yace "Ayshaaaaa…" tace "na'am Hamma" yace "ba bacci nake ba, I am just in a mood!" Ya fada yana mata wata kallo, mai shiga rai da sanya kasala. Har sai da Aisha ta tsargu don ya kara jawo ta jikin sa sosai, this time around juyo da ita yayi tana facing dinsa gabagadi. Aisha tayi shiru, yace "baza ki tambayeni what mood ba?" Tace "toh Hamma bacci kake ji, kuma ka kafe kai baka ji" ta dan turo bakin ta gaba, tana fada cikin shagwaba 'yar gaske. Ai kuwa Prince ya sa ido yana kallon bakin da take turowa so soft and luscious, bai san sanda yace "I really really want to kiss you saddiqa… "ya matso dab da fuskar ta, har suna jin numfashin juna, ya kalle ta, cikin idonsa kadai ta ga tsantsar al'amuran dake cin zuciyarsa da gangar jikinsa. An yi sa’a itama ta juyo kenan sai kawai Hamma ya hade bakinsu wurin guda ya soma kissing Aisha-Siddiqah in a serious tone and passionate manner. Da kyar Aisha ta samu ta zame daga Hammah, ta mike jikinta yana rawa a daburce tayi hanyar kitchenette. Hamma da kyar ya iya mikewa yanakokarinsaita kansa. Yabi bayanta yana cewa cikin basarwa, “you know what? Jeki shirya kawai ki bar girkinnan, we are going out, ma ci a waje”. Tace “toh”, sai ga Nenne ta sake kira. Tace “ni Hammansu dazu maganar bikinsu Princesses na kira zan maka na manta, an saka rana, kwanaki goma masu zuwa. Don Allah ka taho da Aisha, kuma kuzo da wuri. Asabar ne daurin aure wato ranar addu’ar arba’in din Sarki”. Prince ya ce “toh Nenne, in sha Allah”. Itama Aisha sai murna lokacin da Hamma ya gaya mata zasu tafi gida Lagos sati mai zuwa, tace “bikinsu Firdausi za’a yi?” Yace “eh, za’a hada da addu’ar arba’in na Emir. Shine babban burinsa kafin rasuwarsa wato auren twins din gidanmu”. Siddiqah tayi ta murna har ‘yar rawa ta shiga takawa a wajen, ta manta shaf a gabansa take, irin murnar zata gida dinnan, after a long while. Hutun Prince ya dade da karewa, zuwan Siddiqah ne yasa ya kai har wannan lokacin a Argentina. Sun fita a daren sun shakata, suka ci abincin dare a wani Arabian Cuisine sannan suka dawo gida. Aisha ta nufi dakinta tayi wanka ta sha rigar barci mai dan kauri purple ta fesa turarukanta masu dadin kamshi ta nufi dakin Prince. Nan ta tadda shi daga shi sai short nicker akan sofa yana shan ‘chamomile tea’ kafin ya kwanta. Ta na shiga Hamma ya dago yana dubanta da wani kallo da bai taba yi mata ba, domin sha'awar matarsa ce zallah yau cikin idanunsa da duk abinda yake yi. Aisha ta juya da sauri zata koma ganin ba suttura a jikin Hamma sai gajeren wando, ga kunya data kamata sai ya aje kofin hannunsa, yace Aisha wait, ya taso ya isa gareta ya kamo hannunta ya shigo da ita cikin dakin yana cewa. "Ya kinzo turakar miji neman albarka kuma zaki koma?" Aisha duk ta daburce ta rikice tarude, sabida yanayin da Hamma ke mata magana yau ya sha banban dana koyaushe. Ba don ta kasance mai karfin ji bama, da bazata ji shi ba. "Dama-dama... zuwa nayi ince maka Hamma saida safe". Hamma ya dora hannuwansa biyu bisa kafadun Aisha hagu da dama yana murzawa. Ya dan mutstsuka jijiyar wuyanta cikin wani salo na tasowar muguwar sha'awar da baisan akwai a tareda shi ba, saida Aisha ta runtse ido sabida tasowar tata sha'awar ta diya mace, kafin hannunsa ya kai kansa saman kirjinta. Yace "saida safe dinma ai irin haka ake fadarsa Ayshahhh, ba da fatar baki ba. You my dear I want to kiss you again today!". Hamma ya fada admiringly idanunsa akan siraran lips din Aisha, yana musu wani inviting looks. Aisha ta kusa narkewa bakidayanta domin a lokacin Hamma ya matsota sosai ne a jikinsa, ya isa cikin nutsuwa ya hade bakinsu wurin guda ya soma sumbatar Aisha a tsanake, sannan ya koma kissing hungrily. Ashe namiji duk dadewar sa babu aure, ba sai an koya masa sumba ta auratayya ba? Ko da kuwa ya fidda rai da ita, ko bashi da sha'awar ta, sanda zata sameshi zai ji tane tana sarrafashi. To hakan ce ta faru da Prince Abdulrasheed yau. Da ya samu kissable lips din Aisha yau ya dinga tsotso tamkar Allah ya aikoshi, saida ya ajiye kishirwar shekaru masu yawa na kuruciya dana shiga girma. Aisha kyale Prince tayi ya yi yadda duk yake so yau, ya jagwalgwala ta iya son ransa a duk ta inda yake so. Ya tsotse duk abinda yake so. Kuma shi da kansa yayiwa kansa limit. Don yana ganin in ya kauda budurcinta any moment zata iya conceiving, shikuma yana ganin kamar bata yi kwarin da zata haihu ba. Tunda har ya samu wannan access din zai iya karawa Aisha lokaci. A kwanaki goma da suka biyo bayan wannan ranar, wata wawuyar shakuwa ce ta shiga tsakanin Hamma da Aisha. Suna kwana a gado guda, Hamma saida ya san yadda yayi ya fara raba Aisha da dukkan sittirun jikinta in zasu kwanta, yana rabar Aisha da dabara da wayau da simple hugs, da light kiss masu sawa ta saki jiki da shi, su yi barci manne da juna. Tun Aisha matukar jin nauyi da tsoro har ta soma sakewa da Hamma sosai. Don ta lura ba shi da nufin abinda take tsoro. Kusan sati biyu kenan irin rayuwar da suke yi a cikin gidan kenan, full of understanding, intimacy and love, Hamma ya zama baya iya barci bai raba jikinsa dana Aisha ba, bai sumbaci bakinta da kirjinta yadda yake so ba amma bai taba wuce hakan ba yake takawa kansa birki, don a ganinsa har lokacin Aisha bata yi girman data isa ya dora mata hidimar dake cikin aure yanzu ba kada tazo haihuwa ta samu matsala. Amma me? A na I gobe zasu tafi Lagos komai kwace masa yayi, ya kasa controlling kansa yadda ya saba duk kuwa da yana tausayawa Aisha, da kyar da roko da magiya harda kuka Aisha ta kwaci kanta a hannun Prince domin kuwa gani take duk ranar da hakan ta faru ba wata wata mutuwa zatayi, in tayi la'akari da irin yanayin da Prince ke shiga a irin wadannan lokutan akanta. A satin dasu Prince zasu dawo Lagos Dade yasa aka je aka shirya gidan Prince na Banana Island, wanda ke daura da gidan mahaifinsa, Prince ya jima da sayen gidan bai taba amfani dashi ba, tun kafin saukarsu Dade ya gayawa Nenne in sun zo a gidansu zasu sauka. Yasa aka gyara gidan aka shigar komai da zasu bukata. Tun saura kwana uku daurin aure suka sauka a Lagos. Gidan ya debi murnar zuwan su ba babba ba yaro, kowa murnar zuwan Hamma yake yi, ga ‘yan biki sun soma isowa daga sauran jihohi. Kiki ce kawai bata samu zuwa bikin Aunties dinta Princesses ba, don tana shirin rubuta jarrabawarta ta karshe a Informatics a lokacin. Aunty Murjanatu Taiwo tana Ilorin, sai bayan addu’a zata taho Lagos tare dasu Nenne in sun je. Dade yace su Hamma su fara sauka a Lagos su huta kwana biyu, in yaso sai su dunguma duk gidan zuwa Ilorin su samu adddu’ar Sarki ranar asabar, wadda ta kasance kuma ranar daurin auren su Fatima. Nenne ta rasa ina taka saka ina taka aje da surukarta Aisha, wata sabuwar kauna da soyayya Nenne take yiwa Siddiqah musamman data gane suna zaman lafiya itada Hamma, Aisha ta samo kansa shima ya samo nutsuwarta, Nenne bata taba jin Hamma cikin farin ciki da nishadin data ji shi ciki ranar da suka yi waya itada su, tana tsammanin Siddiqah ciki gareta ba. don haka tun kafin saukarsu a Lagos yau Nenne da kanta ta shiga kitchen ta shirya abincin tarbar Hamma da Aisha, ta hada dana Dade, girki tayi masa na musamman data tabbatar Hamma ya dade bai samu irinsa ba, wato (Locust Beans Stew) da suke kira Dindin da (Ofada Rice). Bayan saukarsu da kadan Dade yace ma Prince a gidansu zasu tare, yasa an shirya musu komai da zasu bukata. Don haka ana gama cin abincin dare Dade yace Firdausi ta dauko keys din gidan ta baiwa Hamma, ta yiwa Aisha rakiya kuma. Anan Nenne tace “a’ah Dade, ita kam Aisha ta zauna ta huta anan, a bari sai bayan biki sannan ayi tarewar. Ta jima bata nan akwai bukatar ta huta tukunna”. Ai kuwa nan da nan Prince ya canza fuska. Domin a yau kam yayi niyyar angwancewa da amaryarsa Siddiqah babu daga kafa. In yaso idan ciki ya samu ya tayata nakudar. Yanzu kuma Nenne tana wani zance wanda zuciyarsa ta gaza dauka, wai Aisha ta zauna da ita har bayan biki, duk kokarinsa na rainon da yayi tayi wata da watanni ba’a gani ba, sai rana daya da ya saka ran hutawa. Har dai rashin jin dadin hakan ya gaza boyuwa a fuskarsa, ‘yar damuwa ta nuna a fuskar Prince, amma dai bai yi magana ba. saidai tuni Dade da yake shi namiji ne ya ramfo shi. Lura da yanayinsa da Dade yayi, sai yace. “Kehinde kodai kafi so ku tafi tare yanzu ne?” Zuruf! Aisha tayi tace “Dade ayi hakuri don Allah ni nan zan zauna gun Nenne har a gama biki, nayi kewar Nenne for long”. Taki dago ido balle Prince ya kalli kwayar idanunta. Domin ta riga ta san Prince ya gama kaiwa kul a a dalcinsa. Daren tahowarsu da yaya ta tsira? Balle yanzu a gidansa na gado? Takaicin abinda Ausha tace yasa shima ya hadiye, yace “a’ah Dade, ba wata matsala a kyaleta ta sha zamanta”. Amma Kai da ji kasan shagube ne yayi. Ya ajje spoon ba don ya koshi ba, sai don bazai iya cigaba da ci ba’a gane ransa ya baci ba, da abinda Aisha tayi masa a gaban kowa ta nuna bata damu dashi ba, ya mike yace zai je gidansa ya huta. Bai sake kallon inda Aisha take ba ya nufi hanyar fita falon. Anan ne Nenne ta dubi Aisha tace “raka shi zuwa mota mana Aisha” Hamma, wanda a lokacin har ya kai bakin kofa cikin matukar kulewa zai fice, yace. “A’ah Nenne na yafe, ta zauna kawai, na gode”. Wannan gwasalen da Hamma yayiwa rakiyar Aisha, duk ya faru akan idon amare Princess Fatima da Princess Firdausi, don tare aka zauna cin abincin har dasu gabadaya. Abin yayi matukar yiwa Fatima dadi, na yadda Prince ya nuna bai damu da Aisha a gaban kowa ba. ita bata fahimci haushi yaji don Aisha tace da bakinta bazata bishi ba. Har ta samu abin adarwa a gaba. Fatima na komawa dakinta ta kira Aunty Taiwo, tana mayar mata da yadda aka yi, da irin gwasale tayin binsa gidansa da Prince yayi ga Nenne da Aisha, sai Taiwo tace da Fatima, “ewo, to dama nifa na san Kehinde sarai, nafi kowa saninsa, saninda ko Nenne bata yi masa ba, ba son zama da yarinyar nan yake ba, biyayya yake yi musu don a rabu lafiya da kafaffun iyayenmu da basa shawara, su Nenne ke faman cusa masa ita kamar dusa, kamar ance lafiyayyun mata ‘yan asali na manyan gida sun gama karewa a duniya. Na rantse idona idonta a Lagos ko Ilorin in ta sake tazo, sai nayi mata wulakanci da kaskancin da bazata kara kuskuren zuro jiki cikin zuri’ar Akanni ba, balle ta wani kwashi siraran kafafunta tazo mana biki irin wannan na girma”. A dakinta na baya wato dakin Kiki aka sauketa, kafin ta kwanta saida ta kira Ummanta ta gaya mata saukarsu lafiya a Lagos, sannan ta kira Hamma don tayi masa saida safe ta kuma bashi hakuri da kalamai, amma sai ta samu ya kashe dukka wayoyinsa. Haka ta kwana da tunani da damuwar Hamma a ranta. Washegari da safe ita da Nenne ne suka shirya abin karin Dade da Hamma, sai wajen karfe goma na safe Prince yazo gidan kuma a gurguje suka karya shida Dade zasu fita, bayan yabi Nenne dakinta sun gaisa, yanaso ya tambayi Aisha amma ya dake. Sai gata tana shigowa dakin Nennen dauke da lemun tuffah da sassanyar madarada tanbulan na tangaran akan karamin tray, ta gefensa ta wuce zuwa ciki, taci ado har ta gaji gabadaya ta saje da ‘yammatan amarya da suka cika gidan tun jiya. Ta ajiye a gabansa, don tun safe take dakon shigowarsa duk ta damu, tace a ladabce “Hamma ina kwana?” Yayi mata wani kallo yace “lafiya kalau, yaya gajiyarki?” Nenne aka kirata a waya sai ta fita daga dakin tana amsa wayar. Aisha bata yi aune ba taji Prince ya kamata ya mikar daga durkuson data yi a gabansa ya jata zuwa kusurwar dakin ya matseta sosai a jikinsa, sannan ya manne ta a kirjinsa da wata zazzafar hug, ya rage tsaho ya sumbaci lips dinta lightly, yace, “Aisha jiya banyi barci ba isashshe saboda rashin ki a gadona Aisha, I missed you and your sweet lips, me yasa kika yimin hakane wai?” Ya yi mata wani kallo na so da sha'awar da baisan yaushe ya fito daga idanunsa zuwa nata ba, saida Aisha taji tasirin kallonnan har spine dinta, tsigar jikinta saida ya tashi yarrr, Hamma ganin haka ya sake manne bakunansu wuri guda yana kissing lips dinta hungrily, wannan karon zazzafar kiss yake extending Wanda ya rikita Aisha bakidayanta. Duk da haka tunanin a inda suke ya hanata nutsuwa ta amshi sakonnin nasa. Aisha ta soma kokarin kwatar kanta tana fadin. “Please don Allah Hamma ka bari, ka sakeni kada Nenne ta dawo. Dakin Nenne ne fa!”. Hamma yace “I don’t care, ai gara ta gani ta san yadda kuka taru kuka kwareni jiya, I missed your warmth, shine jiya kika ce nan zaki zauna ko? Don kawai kinga ina shirin angwancewa? Wannan ai mugunta ne Aisha. Hummm! Ni na manta ma I am pissed at you na tsaya Ina romancing dinki”. Aisha tayi wani murmushi kawai ta kalleshi “ni dai don Allah Hamma ka sakeni kunya nake ji” ya sake mata kiss a kasan wuyanta sannan ya saketa jin kamar motsi a bayansu. Ashe Firdausi ce ta shigo neman Aisha, ganin abinda ke faruwa tayi maza tayi excusing kanta da gaggawa ta juya tana murmushi. Firdausi na fita Nenne ta dawo, sai Aisha ta gusa ta basu wuri. Har Hamma ya gama gaisawa da Nenne ya fita daga gidan, wanda ya soma dinkewa da baki musamman kawayen amarya dana Nenne, bai kara ganinta ba. Kuma a washegarin ranar first flight ya tashi dasu zuwa Ilorin, shida Dade, Nenne, Aisha da amaren domin su samu addu’ar arba’in kuma a dauro auren a fadar Ilorin. Da hantsin ranar suka shiga Ilorin Emirate, Aisha tana like da Nenne duk inda tasa kafa nan take mayaswa. A yanayin kalar fatar jikinsu da kamanninsu na Fulani sai suka fita dabam a gidan, kamar ‘ya da uwarta. Wadanda basu san matar da aka aurawa Prince bama a gidan a ranar suka ganta, masu yabawa nayi haka masu gatsinen yarbawa na kankantar Aisha. Amma maganar rashin wayewa ya fara barin jikin Aisha ta yi fes da ita ta kara cikowa ta fara cika idanun mai kallonta. Prince yana can fada tareda Uncles dinsa do a ranar ne ake shawarar wanda za’a bawa sarauta a cikin ‘ya’yan Emir. Idris Akanni y ace a’ah, ko dama Emir ya dade yana gaya musu su cire Idris da dan sa daga sha’anin sarauta. Basu kara yarda da hakan ba sai yau da Dade ya fitittike yace bazai karba ba, baida ra’ayin sarauta ko kankani, don haka ya barwa kaninsa mai bi masa wato Abdulyaqeen Akanni wanda shine Turaki of Ilorin. Da wannan aka bar zancen cewa washegari bayan addu’a arba’in din za’a zarce da bikin nadin sarautar da daurin aure. Da farko a dakin da Nenne ta sauka Siddiqah take amma da Aunty Taiwo tashigo yiwa Nenne barka da zuwa, suka gaisa, ta tambayeta Hakeem tace yana fada, tana kallon Siddiqah a kaikaice, taga alamar a dakin Nenne take nufin zata sauka sai tace da Nenne cikin yarbanci da tayi tsammanin Siddiqah bata ji sam. “Nenne keda surukar taki daki daya zakuyi sharing ne? Ai ba’a yin haka a gidannan, ta tashi ta koma cikin matan ‘ya’ya, haba Nenne don Allah ki dinga jan ajinki akan yarinyar nan”. Nenne tayi sakatoto tana duban ‘yarta Taiwo kafin ta samu abin cewa Aunty Taiwo tace da wata baiwa dake gefe ta dauko kayan Aisha ta kai dakin da ta sauka. Jin tace a kai dakin da take yasa Nenne tayi shiru bata tanka ba, koba komai zata so a samu shakuwa da fahimta tsakanin Murjantu da Aisha, bata son yadda Taiwo ke treating matar kanin nata. Taiwo tace Aisha ta biyo ta, kamar kada ta mike don ba tun yau ba jikinta ya gama bata Aunty Taiwo bata sonta ko kowa bai gaya mata ba. Amma jin Nenne bata ce a’ah ba, kuma Taiwo dinnan diyar Nenne ne da bata da maraba da Hamma, sannan Maman Kikinta sai kawai ta zari hand bag din ta da mayafinta tabi ta nata dakin. Babban bedroom ne a wani sashe na cikin gidan sarautar, dakuna ne a jere wasu na fuskantar juna duk iri daya, yawanci matan Uncles din Abdulrasheed da matan ‘ya’yansu in suka zo sha’ani duk anan suke sauka, dakin da suka shiga da Aunty Taiwo ya ji kayan alatun rayuwa na gargajiyar sarauta dana zamani, ga iya kwandishin mai ni’ma nata aiki, akwai tafkeken gado da wardrove, Aunty Bola matar wani Cousin dinsu da Aunty Iyabo matar Turaki da Fatima da Firdausi ne a dakin suna hira lokacin da suka shiga dakin. Jikin Aisha a sanyaye matuka don yarbanci kawai kake ji yana tashi a gidan da sauran dakunan, koda suka shigo ma duk ta tsangwami kanta duk da Firdausi na tsokanarta da fulatanci tana cewa duk ta wani takure, tafi son koyaushe gta like da Nenne, tace ta saki jikinta nan duk iyayen Hamma ne sai su kannensa. Fatima ta Harari Firdausi tace da turanci don kowa yaji “in taga dama ta daure jikin don Allah, kinsan bata son shiga cikin yarbawa kada su cinyeta, ba abin raini a wurin yarinyar nan irin Bayerabe. I wonder yadda na jita shiru kamar an aiki bawa garinsu tun isarta gidan Hamma kuma”. Ifedayo ta zaro ido tace “kamar yaya bata son yarbawa? Ewoo! Bata son kabila ta auri dan su, dan ma babban jikan sarkin Ilorin da muke fatan ta zama uwa ga kowa namu watarana?” Aunty Bola tace “ke ko Ifedayo! Ai ‘yammatan hausawa ba don so suke aure ba, kwadayin su ba inda baya kaisu. Balle taji sarauta zam, taji Prince na kasashen turai ai nan ‘yammatan hausawa dana fulani suka fi kauri. Sai an yi auren kiga ba soyayyar da zata dauwamar da farin ciki a cikinsa”. Kamar an yiwa Aunty Taiwo kunni, ko kuwa allura akan gyambon ta, ta dubi Aisha ta kyabe baki, tace “ku bar ganin laifinta, iyayenta ne manyan kwadayayyu da basu san darajar kansu ba balle na abinda suka haifa, amma ba ita ba, tunda ita batama san shi ba ko kafin a auro ta, su da suka dauki wannnan teenager suka aurawa Kehinde wanda a haife ya haifeta sune suka fiddo kwadayinsu da zalamarsu fili, ta yaya zaka aurawa danka wanda baka ko taba gani a zahiri ko a hoto ba? Sai kawai don jin su waye iyayensa. Wai daga haduwar kan hanya aka baiwa Nenne sadaqarta ta aurawa danta saboda an ga mamora a jikinta. Ni tunda nake ban taba jin aure na rashin mutunci irin haka ba, ban taba ganin auren rashin sanin darajar Da irin naki ba, ai a al’adarku ana lefe, ana yiwa amarya kayan hana gori, amma ke ko lefen bana jin an yi miki, ke suturar da zaki saka ma a gidanmu mu muka yi miki, da tsummokara kikazo, ko wanka babu, aka bi aka asirce mana uwa, bata zance sai naki, amma ku duba kuga daga shan jar miyar Ewedu har ta fara washewa, ku kuke kayan daki amma ke haka aka daukoki zikau! Aka kawo mana. Mun miki komai domin mu suturtaki, mai nuna sadaqarki suka baima Nenne ta likawa Kehinde ta karfi da yaji. Kuma shi ba so yake ba, ya fada ya kara bashi da lokacin soyayyah, bazai taba son ki ba saboda ya dade da gama soyayya tun a kuruciyarsa, akwai wadda yayi shekara da shekaru yana so tun samartakarsa har girmansa bai aureta ba. kuma har gobe ita zuciyarsa ke so. Ni nasan Kehinde wallahi, babu kuma wanda zai gaya min waye Kehinde, ko a kafa aka daura masa ke nan gaba kadan zai kwance ya yar. Kawai kun ga arziki da sarauta kun nace, watakila ma kuna tunanin Kehinde zai yi sarauta ne, to in gaya miki gaskiya inma wanan kukewa keda iyayenki to kije ki gaya musu Kehinde bazai yi ba. Da aka aura masa ke aka kawoki guidanmu saida ya jingineki kusan shekara guda, saida su Nenne suka gaji da ajiyarki a daki ne suka tattara ki suka danna masa ganin wankin hula zai kaisu dare. Da zuwanki gidansa na fahimci kun soma juya masa kai, iyayenki nata surkulle ga dukkan alamu, har wani dora ki yayi a status baya ko jin faduwa a ganshi dake a matsayin mata. Nayi rantsuwa ni Taiwo abokiyar tagwaitakarsa, inma asirinku ne ya fara cinsa ko zan daina barci sai na warwareshi da karfin addu’a, in asiri kuke shiga jeji kuna jefa masa mu addu’a muke kwana yi, yadda kuka ganshi haka zaku kyaleshi. Kakan kakanmu Shehu Alimi, ya dade da tofe zuri’ar shi da kul’aquzai, daga duk wani sharri na masu nufin Kehinde da wani surkulle na magauta da irinku makwadaita”. Duk maganar nan Taiwo na yinta ne cikin sassaukan turanci da fulatanci ziryan, don ma Aisha ta fahimta sosai. Siddiqah dai tana zaune banda kallon bakin Taiwo ba abinda take yi. Kirjinta yana harbawa zuciyarta na matsewa. Fuskarta na rinewa daga yellow zuwa jazir. Saida Aunty Taiwo ta gama cin mutuncinta tas, su kansu su Fatima da Firdausi wadannan maganganu na Yayarsu Taiwo sun san firgitasu domin sunji sun yi zafi da tsauri sosai. Firdausi jikinta rawa ya fara yi ta soma cewa “haba-haba Aunty Taiwo? Haba ke kuwa don Allah Maman Kiki? Wannanba girmanki bane”. Ganin yanayin da Aisha ta shiga ya firgitasu. Babu ko digon hawaye a fuskarta amma tsigar jikinta duk ta tashi yarr, tsokar fatar bakin ta har raurawa takeyi amma ba kuka ba. Taiwo zata wuce toilet ta bar su a wurin suka ga gabadaya jikin Aisha ya dauki kyarma, idon nan ya koma kamar garwashin wuta ya kada yayi jazur… Ga dukkan mamakinsu Aisha ta mike da hanzari ta sha gaban Aunty Taiwo dake neman wucewa toilet wato ta gama zagin banza, ta sha lafiya zata wuce harkokin gabanta. Aisha ta tsaya gaban Aunty Taiwo, gabadaya ta koma Aisha-Siddiqarta fitinanniya, masifaffiya, ta Billiri ikon Allah! Gang leader mara tsoron kowa, sannan mara kara wato mai keke - da kekenta da kowa ya sani, ta kalli Aunty Taiwo cikin ido ta soma magana cikin sarkewar numfashi. “Na rantse yau kinci albarkacin haihuwa, kin ci albarkacin Kiki a wajeana, kinci albarkacin dimbin qaunar da ‘yar ki ta nuna min.Sannan kinci albarkacin girma da shekaru. Sannan kinci albarkacin Nenne, mafi girma kuma kinci albarkacin tarbiyar da iyaye na suka bani akan wanda ya girmeni!!! Kinci zarafin dattako da tarbiya da kamalar da Nenne take dashi kuma ta baku ku ‘ya’yanta, kin ci amanar tarbiyyar data baki!!! Aunty Taiwo ta saki baki galala! Tana kallon yarinya karama haka kamar diyarta Kiki, ta tsaya a gabanta tana maida mata da martani, yarinyar da bata wuce second born dinta Kiki ba, duka mutanen dakin ma su Ifedayo da Aunty Bola sun sha mamaki domin basu zaci zata iya tankawa Taiwo ba sam, da yake cikin turanci take maida mata martanin duk suna ji, kallonta suke, shock duk ya kamasu. Firdausi ta soma bata hakuri daman tunda Taiwo ta fara zuba rashin mutuncin Firdausi tana ta cewa “haba aunty Taiwo, ki bari bai kamata ba” Taiwo ta ce mata “shut up malama! Kada ki kara saka min baki in ina magana”. Ganin haka gudun kada akai ga duka sai Princess Firdausi ta dauki wayarta jikinta nata kyarma ta yiwa Hamma text, tace maza ya bar duk abinda yake yi yazo don Allah ga Aunty Taiwo na cin mutuncin Aisha tana neman wulakantata a gaban dangi”. A take Hamma ya kira Firdausi immediately, ai kuwa Firdausi ta saka masa a handsfree, yana iya jin muryar Taiwo na karasa wassafa ma Aisha… “ki dake ni mana ‘yar Mallam Shehu! Shine zan san kinyi fushi na zagi makwadaitan iyayenki da suka yi miki auren sadaqah. An zagi iyayen naki, wata tsiya ne su? Ko zaki rama eh? Ke a karan kanki da dan hankalinki kinga dacewar ki auri Kehinde? Banda kankanba irin ta talakawa da kai kai inda Allah bai kai ka ba, ina ke ina zuri’ar Akanni? Ai da kin tafi kin auri mai kora shanu a kauye shine daidai ke…. Amma ba dan Sarki babban jikan Sarki ba…”. Hamma be kashe wayar ba a haka ya karaso hankalin sa a matukar tashe. Aisha ta wuce ta gaban Taiwo a zuciye, ko ganin gabanta bata yi. Wani irin tafasa zuciyarta keyi. Babu kuka ko digo a idonta zuciyarta ta bushe. Bata so ta kara wata kalma bayan wannan don zuciyarta na iya bugawa a lokacin. Firdausi ta kula da hakan ta taso ta biyo bayanta da sauri tana Siddiqah tsaya don Allah…. ko jinta batayi ba ta bude kofa, sai karaf! Tayi karo da mutum tsaye a bakin kofar. Data daga kai ta kalle shi da idanunta kamar gauta sai ta kawar da kai, ta sake juyowa tana kallon Taiwo data biyo bayanta…. ganin Kehinde yasa Taiwo tsayawa standstill. Wani irin bayyanannen bacın rai ne a fuskar sa, zata iya rantsewa tunda take da shi bata ta a ganin wannan yanayin a tare dashi ba. Ya bude baki zai yi magana sai jin Aisha yayi ta juya tana cewa da Auty Taiwo…. “Kuma kamar yadda kike ta tutiya kan cewa baya sona, haka zalika nima baya cikin lissafina balle na irin mazan da nake so, ki tambayeshi kiji biyayya duk mukayiwa iyayen mu, saboda sun isa da mu. Daga yau na bar miki shi. Gashinan ki jika shi ki shanye….”. Tana gama fadin hakan ta wuce ta bar musu dakin, ga dukkan mamakin Taiwo sai taga Prince ya bi bayanta yana “Aishah Please wait…Don Allah tsaya…” ko kallonsa Aisha bata yi ba ta kara sauri, ta kara da gudu-gudu, shima ya daga kafa ya bita yana “please listen to me Aisha….”. Yayi sa’ar riko gefen gyalenta, Aisha ta juyo a fusace tace “cikani, daga yau na gama wannan auren”. A lokacin sun kawo kofar dakin data baro Nenne. Kalaman Aisha na karshe a kunnen Nenne suka sauka, inda tace. “na gama auren nan, na barwa Aunty Taiwo dan uwanta Kehinde ta jika ta sha, har abada baa auren!” Da sauri Nenne ta taso suka game ita dasu a bakin kofar, ganin yanayin da Aisha ke ciki da rudewar dake fuskar Hamma saida gaban Nenne ya fadi. Ta kama hannun Aisha suka shiga cikin dakin Prince da hanzari ya rufa musu baya. Nenne na jin irin numfarfashi da ajiyar zuciyar da Siddiqah ke sassaukewa a jejjere, ta durkushe a gabanta, ta hada hannayenta wuri guda cikin roko tace. “Nenne ke uwace mai adalci a wurina, babu abinda zaki sani in ki yi, amma don Allah ki barni naje gun Ummata. Nayi rantsuwa a gidanmu zan kwana yau. Kar kisa nayi kaffara. Ni Nenne wallahi Allah tun ranar da kika kawoni Lagos da niyyar zaki kaini asibiti, har aka kai ga maganar aure, aka yi aka dawo, duk da banaso har raina, ban taba jin zan iya yi muku gardama ba. kuma na karbi kaddarar auren a haka, nima ai da wanda yake so na din nake kuma son shi aka raba mu amma ban yi bore ba. Amma Nenne yau Maman Kiki ta tabo martabar wadanda ba’a iya taba su in hakura, inna hakura ma ji zan yi kamar nayi gagarumin laifi ga iyayena, don haka Nenne don Allah zan tafi, na rantse bazan kwana garin nan ba”. Jikin Nenne yayi sanyi kalau, at the same time she is so proud of Aisha, domin ta haifu, ta cika diya. Prince na kallon Nenne da dukkan hope na cewa zata lallashi Aisha ta shawo masa kanta ta saurareshi. Shi meye laifinsa a ciki? Amma sai gani yayi Nenne ta dauki wayarta tayi kira. Bai dai san wa ta kira ba yaji tana “lallai-lallai a nemo jirgin zuwa Gombe yanzu, idan ma babu direct a nemi na Abuja daga nan sai ta kara shiga wani”. Sai Prince ya dubi Nenne a firgice, yace “Nenne me kike nufi? Gidan zata tafi da gaske? Ta gama auren fa tace, ni kuma fa Nenne?” Gabadayansa a daburce yake, kansa da duk wani lissafinsa ya kwance, duk wani azanci da tsinkaye da kunyar idanun mahaifiyar tasa sun kwace daga hannunsa. Nenne bata ko bashi amsa ba tace “Aisha dauki kayanki kinji, muje driver da Dade suna waje suna jira zasu saka ki a jirgin Gombe”. Dadi sosai ya kama Aisha sai lokacin ta samu hawaye suka zubo, tafe da wata sassanyar ajiyar zuciya, tace “nagode da uzuriki, amma ni Nenne yadda nazo haka zan koma Gombe, ko tsinke bazan dauka ba”. Ta dauko wayarsa da ya bata daga jakarta ta russuna ta ajiye a gabansa ba tare data kalli yanayinsa ba. Saura kadan Prince yayi hauka a cikin kansa, musamman ganin Nenne tasa hijab ta kama hannunta suka fice suka barshi tsaye a wurin. Sai kawai ya fito daga dakin shima a matukar fusace, ya san yayi kadan ya dakatar da Nenne yanzu, a yadda yaga fushinta da bacin ranta irin wanda bai taba gani ba, to balle kuma Dade mijin tace din Nenne, wanda sai abinda Nenne tace yake amfani dashi. Don haka maimakon yabi bayansu, dakin su Taiwo ya nufa. Yana tafe da sassarfa yana tambayar ransa me zai yiwa Taiwo ya huce? Ance ba’a raba hanta da jini, ance blood is thicker than water… wai ba’a batawa da ‘yan uwa saboda mace, komin son da ake yi mata. Amma shi yadda yake jin matukar bacin rai da soyayyar Aisha data bijiro masa yanzunnan, mai raba shi da Taiwo dinsa yau sai Allah. **** **** **** Tun kafin su Nenne su karaso jikin motar daya daga cikin direbobin Emirate da Dade ya kira ya bude musu kofar gidan bayan wata jibgegiyar mota baka wuluk suka shiga har Aisha wadda hannunta ke cikin na Nenne. Direban ya ja motar cikin nutsuwa suka bar fada. Har sai da suka dauki hanyar airport din Ilorin sosai, suka yi nisa fintinkau da masarautar ta Ilorin, sannan ne Aisha ta ji ta (at ease) kuma bugun kirjinta ya soma lafawa, Aisha ta yi ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali, saboda abinda take so Nenne ta yi mata nan take, Nenne ta dubi halarci, kauna da amana ta yi mata kan ta rufe baki. Me za ta ce da Nenne Sappa? Ban da Allah ya ja kwananta? Tana jin Nenne da Dade suna magana amma da harshen Yoruba suke yi, (which means) ba su so ta fahimta sosai, don kuwa yarbancin mai zafi da sauri da sauri sosai suke yi. Amma a cikin dan abinda take tsinta yanzu a harshen ta fahimci kamar Dade na rokon Nenne ne akan ta bari a yi komai a hankali kada ta biyewa fushin Siddiqah, ta bata hakuri su wuce Lagos don yana so ya fahimci meye matsalarta data sa aka taso tafiya Gombe haka bagatatan, suna tsaka da sabgar biki, kuma daga ina matsalar take?” Sai taji Nenne na cewa, “A’ah Dade, yi hakuri ka barta ta tafi, ni a wurina tafiyar Siddiqah Gombe yau ba makawa sai wani babban ikon Allah mai karfi da ya gagari iyawata, matsalar daga Taiwo take, zaka fahimci komai daga baya don ba yau matsalar Maman Kiki ta fara akan Siddiqah ba, na yau din na fahimci yayi tsamari ne tunda har kaga Siddiqah tayi fushi, amma a halin yanzu bazan iya yarda da komai ba banda cikawa Siddiqah burinta”. Ta Lawanti International Airport. Dade ya yi ma Siddiqa tikiti, babu ko waya a hannunta haka ta shiga jirgin, Nenne ta gaya mata tana sauka Malam Buhari direban Nani Oummana zai zo ya dauke ta daga gidan Sarki. Ya kaita har zuwa nasu gidan. In kaga idanun Siddiqah a lokacin a soye suke kamar gyada marau-marau, babu ko kyallin hawaye a cikinsu. Na Nenne ne fal kwalla, suka yi sallama ta shiga jirgin Mangal. Dade dai yana gefe yana kallonsu ya rasa abin da ke masa dadi, don Nenne har zuwa lokacin ba ta yi masa wani cikakken bayani da zai gamsu da tafiyar Siddiqah Gombe kuma ita kadai ba, don ta ce ita ma ba ta gama fahimtar matsalar ba kawai ta yi wa Siddiqah abin da ta ke so ne kada hawan jini ya kama yarinyar, a yanayin da ta ganta kamar mai tashin iskokai sanda ta ke rokonta ta maida ta gida. Hakika Nenne ta tsorata, kuma ta dauki laifin duka ta dora a kan Abdulrasheed, duk da a hargitsatstsen bayanin Aisha ta fahimci ita dasu Taiwo ne. Siddiqah na sauka a Gombe ta tarar da direban Nani Oummana watau Buhari ya dade yana jiranta, wanda dama ta sanshi, duk zuwan da suke yi Gombe da ma shi yake daukarsu zuwa gida haka in zasu koma Lagos shi yake kaisu airport. Suna tafe a hanya Siddiqa banda ajiyar zuciya ba abin da ta ke yi. Wata irin ajiyar zuciya mai tafe da numfashin fushi da bacin rai. Ji ta ke a ranta, daga yau aurenta ya gama karewa da Prince Abdulrasheed ko za’a mutu ko za’ayi rai. Nenne kuma a sanyaye ta kira Hajiya Zainab, bayan tasowar Siddiqah sukuma suna hanyar komawa Emirate, ta gaya mata komai a sakaye. Inda ta ce (murya ba karsashi) “Zaynaba ga Siddiqah nan zuwa, ki yi wa Mallam Yunus bayani, Siddiqah ce ta daga hankalinta sai ta taho gida, muna tsaka da bikin twins a Ilorin. Ta ce ba ta bi ba’asin maganar ba tukunna sai sun koma gida daga raka Siddiqah, ta dai biye wa Siddiqa ne don kada ta yiwa kanta illah, in ta koma gida daga airport din zata bincika ko me yake faruwa kuma za ta dauki matakin da ya dace, insha Allahu. Nenne tace ma Umman Siddiqah. “For now Zaynaba, ba don ni ba ina so ku taimakeni, ku tausasawa bakuncin na Siddiqah zuwa gareku, ku karbeta babu tambaya babu tuhuma, naga kamar tana da iskokai idan ranta ya baci, ku karbeta da hannu bibbiyu kada ku ce mata don me, yanzu zan koma gidan Kakannin nasu Hammansu, in binciki Taiwo da Firdausi inji me ya faru, saboda na tara al’umma ciki da waje suna jirana da ni da kaina zan rakota, in yaso idan an gama biki an kai amare dakunansu zamu san kwakkwaran matakin dauka. Tun daga nan Hajiya Zainab ta san cewa ba lafiya ba. Bata san Siddiqah da wasu iskokai ba amma tana da fushi in an kaita bango mai wuyar sauka. Don a saninta Siddiqah ta gama kwantar da hankalinta da auren Prince. Kullum ta kira ta sai ta ce “Hamma na gaisheta, Hamma kaza da kaza. Ko kwanaki biyun bayannan sun yi waya ita da Siddiqah tana farin ciki tana dariya ta ce mata sun sauka a Lagos ita da Hamma Prince. Bikin kannensa Princesses. Amma bata jin zasu biyo ta Gombe in an gama, don yace daga gama bikin immediately Qatar zasu wuce bakin aikinsa don hutunsa ya dade da karewa. Har tace ma Umman da zata yarda da ta sa Hamma ya kawo mata Umma har Qatar taga muhallinta. Umman tace mata a lokacin “ashe ni Zaynaba kenan na zama ba bafullatana bace tunda zan biki gidan miji”. Siddiqah tayi ta dariya tana fadin “Umma fulani fa sun waye, sun daina irin wannan yanzu, balle ni Petel dinki wadda ni ce ta fari nice auta, bakiga yadda Nenne take kula da Hamma ba shi da yake babban dan ta ma, bata iya wuni guda bata san me yake ciki ba”. Haka kawai kuma ba za ta zo lokaci guda suna tsaka da biki mai muhimmanci irin wannan ta dagawa Nenne hankali ta ce lallai a maido ta gida ba. Ruwa dai baya tsami banza. Koma dai mene ne za ta jira isowar Siddiqah lafiya, ta gaya mata me akayi mata ta ji. Mallam Buhari direban Oummana yana kashe motar a kofar gidan su Siddiqah, tayi wuf ta bude kofa ta fice. Siddiqah ko sallama ba ta tsaya yi wa Malam Buhari ba ta shige gidansu ba godi bare an gode. Shi kansa Malam Buhari yayi mamaki don ya san ba haka yasan yarinyar ba. A tsakar gida suka yi kacibus da Ummanta, wadda jin dirin tsayuwar mota ya sa ta tasowa da sauri har tana tuntube. Da wata irin azama Siddiqah ta shiga gida tayi karo da Umma, ai kuwa ta rungume Ummanta sosai, Umman ma ta rungumeta tana hamdallah na saukarta lafiya. Sai a lokacin Aisha ta samu kuka dan gaske ya balle mata. Umma na cewa cikin fillanci, “Petel dina, mi ya hwaru? In ji dai lafiya lau kike, ba wasu iskokai, kuma kin zo lafiya baki samu matsalar komai a hanya ba?” Aisha babu baki sai na kuka, wanda tun a Ilorin ya tokare mata a makogaro, sai yanzu da ta ji ta a kirjin Ummanta, ta samu ‘yanci da sukunin fitar da shi, ko ta ji sakayau da sanyi a kirjinta. A haka suka karasa cikin falon Umma, Hajiya Zainab na rike da ita ta zaunar da ita a doguwar kujera, itama ta zauna a gefenta. Siddiqah an samu abinda ake so, wato anzo inda za’a yi shagwaba son rai, a kuma biye mata, nan ta yi ta rusawa Haj. Zainab kuka, tana cewa auren ta da Hamma ya kare, Umma ko za’a yankani ba zan koma ba. Ita gara a ce ita aka taba aka ciwa mutunci basu ba, da ko daga ido bazata yi ba kuma abin ba zai dame ta haka ba. Hajiya zainab ta ce, “Yi shiru Petel ki gaya min Abdulrasheed din ne ya yi miki laifi ko waye? Me yayi miki haka? Mutumin da na lura yana da kirki sosai”. “Babu abin da ya yi min Nenne sai kyautatawa ta alkhairi da mutuntawa cikin alfarmarsa”. Umma ta kara shiga duhu tace “to Petel din Umma, gayamin menene ko wanene?” Daidai lokacin Malam Yunus ya shigo gidan, yana ta sauri kamar ya tashi sama, don har ya fita wajen aiki Prince Abdulrasheed ya kira shi a waya, yana tambaya cikin jin nauyi da murya mara amo da karsashi, bayan ya gaisheshi yadda ya saba kira lokaci-lokaci ya gaisheshi tun bayan rasuwar Emir da suka hadu a wajen makoki a Ilorin, sai ya tambayi Malam Yunus din, “ko Aisha ta iso gida lafiya?” Abban Aisha ya ce masa, “Siddiqah kuma? Ba dazu aka ce min kuna Ilorin ba? Ita da wa tazo? Kai ban san komai ba, amma bari inyi hanzari in karasa gidan in duba”. Sallamar Malam Yunus ta sa Aisha tashi zaune daga jikin Umma. Ta sauko kasa tana gaida Babanta shikuma ya zauna a kusa da ita. In ta tuna irin kalaman Aunty Taiwo a kansa bata sanin sanda ta ke jin sababbin hawaye sun bulbulo mata. Ta durkushe gaban Malam Yunus tana ta sabon kuka. “Petel in ki ka yi haka ba ki kyauta mana ba, ba ki kyauta wa Hajiya Sappa ba, in wani laifi mijinki ya yi miki ai tsakaninki da shi sulhu ne, bai kamata ki daga musu hankali ki ce komai dare sai kin taho gida ba, zo mu zauna zo mu saba shi ne aure. Ina ta yabonki sallah kinyi zamanki kin kwantar da hankalin ki a gidan aurenki kada ki kasa alwala mana Siddiqahrmu Petel ‘yar Ummanta. Yanzu dai gaya mana me ya faru? Don Abdulrasheed bai gaya min komai na dalilin tahowarki ba, ya dai kira ni don jin saukarki lafiya? Kuma daga ji yana cikin damuwa a kan tahowarki. Ya ce ayi hakuri yana tafe gobe insha Allah bayan daurin auren kannensa”. Aisha ta kara sautin kukanta, har da zambarwa tana cewa, “ko Hamma ya zo yayi a banza, don ba zan bi shi ba, na dawo gaban talakawan iyayena kenan, na gama wannan auren tunda a kansa aka ci mutuncin Babana da Ummata da bana hada su da kowa. Aka yi muku zagin da ba zan iya hakura ba a bainar jama’a. Aka yimin gorin suttura harda na lefe, wallahi ko Hamma shi ya saura da namiji a duniya na bar wa Aunty Taiwo dan uwanta”. Ta kwashe komai ta gaya musu, jikinta har tsuma yake da tana fadi, ko kalma daya ba ta cire ba cikin muggan maganganun Aunty Taiwo. Shi kansa Malam Yunus sai da jikinsa da zuciyarsa suka raurawa. Abinki da bafullatanin usuli, sanin kowa ne Bafullacen mutum baya daukar kaskanci da raini ko kankani amma ya kanyi kara da alkunya. Malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Yunus duka jikkkunansu sunyi mugun sanyi, kuma rayukansu sun yi karshen baci don basu taba jin abinda ya taba mutuncinsu irin wannan ba. Kuma wai daga wadda tafi kowa kusanci da Abdulrasheed din. Amma kokari suke su shanye hakan akan fuskokinsu daga idon Petel, don kar su kara dugunzuma ta. Sanin kansu ne Petel bata iya bacin rai ba, bahagon hukunci take yi in aka kaita makura, sannan bata da rufi akan komai, bata boye abinda bai mata ba wai don ta faranta maka wannan halinta ne na tun asali keke-da-keke, kuma bata da kara bata kuma damu itama ayi mata ba. Murya a sanyaye Malam Yunus ya ce. “Haka abin ya zama? Ashe ana maida manufar alkhairi zuwa ta sharri da wulakanci da tozarci? Sha zamanki Petel, duk da cewa aure rai ne da shi to ina rokon Allah ya kawo karshen wannan daga yau. Allah shi ne shaidata na bada aurenki gare su ne darajar mutuncin Hajiya Sappa, ban yi la’akari da dukiya, sarauta ko wani abu nasu ba, karewar ma da na ji hakikanin ko su waye Akanni, a tambayi Yaya Barau cewa nayi ban yarda ba, ba kuma zan yarda ba. Na yi tattaki na tafi wajen Malam Hassan a kan maganar ki da Ishaqa shi kuma ya kwance min zani a kasuwa. A dalilin haka Yaya Barau ya fusata ya ce a basu, ba Yarbawa ba ko Ijaw ne, saboda dalilai masu karfi akan Haj. Sappa. Amma ban da haka wallahi-wallahi na fi karfin kwadayi a wurin kowa, nafi karfin kwadayin sarauta ko mulki ko neman suna, ita ma Hajiya Sappa ta sani, banida wata manufa a kan auren nan sai ta tunanin zasu rike min ke da mutunci da martaba tunda su suka zo suka ce suna so cikin mutunci. Amma tunda haka suka ce, to Petel share dakinki ki zauna, su kawo min takardar sakinki, dama Ishaqa ya dawo Gombe, ki gama iddah ki auri daidai ke. Petel ke kadai muke da, ke kadai Allah ya bar mana, bayan ‘wabi’ na ‘ya’ya goma! Ta yaya za mu yarda ki wulakanta a gidan aure ko a duniya? Bayan ba wai bamu da abinda zaki ci ki sha ki suturta bane? Aure ne kawai wanda ya zama dole akan diya mace? Ko da muke talakawa a kansu, su masu mulki da dukiya wallahi bazasu kira matsiyata ba, ba kwadayayyu bane mu da zuri’ar mu duk fadin garin Gombe kowa ya san masu wadatar zuci ne, masu sana’ar da zasu dogaro da Allah da kuma kansu”. Ran bafillacen ya baci, yana fulatanci yana gamutsawa da Hausa. Umma dai kasa magana ta yi, don ta tsorata sosai da yadda Malam Yunus ya fusata, ya sa Petel a gaban motarsa nan take suka dauki hanyar gidan Baba Barau suka bar Hajiya Zainab ta rasa abinda ke mata dadi. Ba ta so a ce Petel dinta ta zama bazawara, at a very tender age ko a kirata sauta ga wawa, kuma bata so ya zama su Mallam Yunus sun yanke hukunci kawai daga bakin Petel gabanin jiran Dade da Nenne, da shi kansa Abdulrasheed din yace zai zo gobe. Sun samu Baba Barau a gidansa a turakarsa yana cin abinci, ya yi mamakin ganin Aisha. Amma fuskarsu kadai ya kalla ya san ba zuwan ziyara ta yi ba, ba kuma na dadin rai ba. sai ya ture kwanukan abincinsa gefe yana cewa “Indon Legas saukar yaushe?” Wajen zama ya bai wa kaninsa, sannan Aisha ta tsugunna gabansa ta gaida shi, ya ce, “In ce ko lafiya na ga Indo kamar daga sama? Ba ance min kun bar kasar ba zuwa turai?” “Yanzu dai Petel ki fada masa komai da bakinki ya ji”. Aisha ta maimaita wa Baba Barau kalaman Murjanatu kakaf. Da yadda ta tada bori sai ta taho. Baba Barau ya sunkuyar da kai na ‘yan dakikai, kafin ya dago ya ce, “Na ji, kuma sun yi da dan halak. Kin haifu Indo, daya tamkar da dubu ga iyayenta, kuma mun gode da wannan karramawa da kika yi mana. Allah yayi miki albarka tunda arziki, mulki da daular da kika samu kanki ciki rana daya basu sa kin sarayar da mutunci da martabar mu ba. Ni kuma na yi miki alkawarin yadda na hada wannan auren haka zan tsaya in kwato miki martabarki. Taiwo ta ke ko Tuwo, sai ta san ba’a cin zarafin bafillace a kwana lafiya don ko sune Qaruna da Fir’auna don mulki da dukiya kin gama auren dan su”. Ya ce, “Kuma a gidana za ki ci gaba da zama, don Zainaba tsaf kawarta za ta kalallameta ta zugeta su maida ki. Tunda uwarsa da ubansa kadai ke son auren. Shi dinma nataba ganin kafarsa a gidannanya zo gaishemu? Kullum saidai ace baya nan kamar wani tsuntsu. Don Zaynaba kam sanyin halinta bazai bari ta kwato miki ‘yanci ba, kuma kin san kawancennan nasu itada Sappa sai Allah”. Farin-cikin goyon bayan da ta samu kadai daga iyayenta dattawan kwarai ya wanke mata zuciya ta saki numfashi na samun kwanciyar hakali. Ta san da wasu iyayen ne cewa zasuyi zasu maida ta kada sarauta da mulki ta wuce ta kansu. Baba Barau ya sa murya ya kira matarsa Furera, ta shigo ya ce, “Maza Furera share wa Aisha dakin can na kusa da naki, ki kuma kama kaji a yanka ki mata farfesu yanzun nan. In kuma gashi take so sai a kaiwa Ayuba ya gasa mata. Ko me ta ke son ci a yi mata (baba Barau na kiwon kajin gidan gona masu yawan gaske a wani bangare na gidansa)”. Sai bayan fitar Baba Furera ya tambayi Aisha, “bani wayarki kada ma ya kiraki. Shin kina da iddarsa a kanki??” Kunya sosai ta kama Aisha. Ta sunkuyar da kai ta kasa amsawa. Baba Barau ya ce, “Magana nake yi da ke Indo”. Aisha ta girgiza kai a hankali, wato babu iddar Prince akanta. Wayarta kuma tace ai a wurin ta aje masa abarsa. Ba waya a hannunta yanzu. Baba Barau ya kara fusata ninkin ta baya, yayi kuta ya ce, “Allah ne shaidata, ni ban yi la’akari da komai nasu ba na yarda na ba su aurenki, amma in suna ganin akwai wata manufa daga gare mu, ko in hankali bai kwanta ba gara da suka maido ki gabanmu da wurwuri. Amma miji ya jingine mace mai lafiya har watanni tara babu sunna, kuma da sunan aure, sannan suna tare a gida daya ai wannan auren ma da alamar gurbacewarsa. Babu inda zaki koma kin zo gida kenan inyaso su biyo ki da takardarki ni za’ayiwa iya shege da wulakanci?. Idan kuma sun ki, na rantse ko da shari’a sai na raba auren nan. Mu za a wulakanta? Mu ake wa kallon kwadayayyu matsiyata?” Baba Barau har ya fi Malam Yunus daukar zafi. Nan ya tafi ya bar Aisha a gidan Baba Barau yana ta ja wa Furera kunne kan lallai kullum ta kama kaza da zabuwa ta yi wa Aisha farfesunsu da suya ko gashi. Nenne ta kira mahifiyarta ta ta gaya mata Aisha ta taho Gombe, sakamakon abinda Taiwo ta yi mata, da abinda ya biyo baya, wato tahowar Aisha gida. Nenne ta nuna ma Oummana damuwarta sosai kan abinda ya faru a bikin na Princesses dinta, ga jama’a sun gayyato daga ko’ina ba damar ta barsu ta taho, sai an kai amare, shi ne Nani Oummana ta tace ta kwantar da hankalinta su gama bikin twins lafiya. **** **** **** Siddiqah ta wayi gari lafiya a gidan babanta Barau Hamza, amma zuciyarta ta ki yin dadi yadda ya kamata duk da gatan da ake gwada mata kamar ana goyonta, ta kowanne bangare zuciyarta ta rasa sukuni don da dazun da safe ma Ummanta ta yi danmalele mai rai da motsi ta aiko Sunusi ya kawo mata har gidan baba Barau. Danmalelen ya sha manja an shirbineshi da yajin tafarnuwa yadda Petel keso, ga salad da tumatur an yanka masa da albasa da cocumber. Siddiqah wadda rabonta da danmalele har ta manta, watakila tun farkon zuwanta Lagos. Tayi matukar jin dadin samunsa, musamman da Umma ce tazauna ta yi mata shi da hannunta. Furera matar Baba Barau kuma tana ta cika umarnin Baba Barau na fige kaji da zabbi har sun ginshi sha’awar Siddiqah. Washegarin rana ta biyu ma cikinta baci ya yi saboda canjin cima da ta samu, ta saba da cin abincinsu na yarbawa fresh veggies. Don haka Danmalelennan sai da ya saka ta zagayawa toilet har sau uku tana saukeshi, sabida uban yajinsa. Aisha data zo barci sai ta kasa koda runtsawa, saboda tunanin magananun Taiwo. Suka zo suna ta sukarta a kirji kamar allura. Hamma da rashinsa a gefenta, sabonsu ita dashi, na wasu watanni bai yi yawan da za ta kasa barci saboda rashinsa ba, amma abin mamaki barcin baya samuwa saboda tunani da damuwa akan halin data baro Hamma a dakin da Nenne ga sauka. Ita ta san bai mata laifin komai ba, Prince ya darajata ya mutunta yana kuma kan daga darajarta da soyayya abinda kowa baiyi zato ba, Amma a ranta ta yanke ba ita babu komawa aurensa, duk da yadda can wani nesattaccen sako na zuciyarta ke bala'in kewarsa. **** **** **** THE PRINCE Har ya dauki hanyar dakin da ya baro Taiwo wato inda ta sauka sai kuma ya fasa, ya juya da baya-da-baya ya koma masaukinsa na gidan Kakan nasu. Wani tunani ne ya shige shi wato kada ya kulata sai a gaban Nenne da Dade, ba zai so su raba abin fada a cikin dangi ba, ya san dakin da su Taiwo suke ciki akwai sauran matan family dinsu a cikinsa ba Firdausi ce kadai a dakin tare da ita ba, alhalin ana musu kallon wadanda suka fi kowa hadin kai, kyakkyawar rayuwa, kaunar juna da kwanciyar hakali a kafatanin zurri’arsu ta Sarki Abdulrasheed dan Abdullateef Akanni. Don a yadda zuciyarsa ke tafarfasa dinnan bai san hukuncin da zai yankewa Taiwo yau ba, he is afraid ya kai hanu jikinta da sunan duka, in ya yi ido hudu da Taiwo a lokacin yana iya marinta, kuma abinda zai biyo bayan hakan sai wani ikon Allah ne zai sanyaya shi. Don haka Prince yayi koyi da maganar Annabi (S.A.W) ne, da ya ce, kada, kar ka yi hukunci a lokacin tsananin fushi. In kana tsaye ne abun fushin ya sameka ka zauna, in kana zaune ne ka koma ka kwanta. That was why he decided not to talk at the moment. Amma ya kudurce sai a gaban Dade da Nenne. Su Nenne na dawowa dakin da Prince yake suka nufa kai tsaye. Nenne ta same shi a kwance, ya rufe fuskarsa da zara-zaran tafukan hannunsa, shi ya tabbata Taiwo ‘yar uwarsa ce, kuma makusanciya mafi girma a gare shi. Amma wannan attitudes din data ke yi wa iyalinsa na mene ne? ya kasa fahimtar Taiwo. Mene ne haka wai a zuciyar Taiwo a kan matarsa? In haka ne kawai Taiwo ba ta sonsa da rayuwar iyali kome? Tafi son shi da zama a gwauronsa har gobe, saboda ita tana aure har ta aje masu yi mata addu’a kome da shi zata kashe masa nasa auren? Don in banda haka ai in bata godewa Aisha-Siddiqah ba wadda iyayenta suka lankwasata har ta yarda ta yi biyayya ta aure shi da girmansa ita da yarintarta, bai kamata ta saka mata da zagin iyaye da gori mai tsinka zuciya ba. Ya rasa me ke damun Taiwo a kansa sai ka ce a kanta aka fara tagwaitaka. Duk da cewa, tun asali halin Maman Kiki wani iri ne da shi kadai yake iya tolarating, amma shi ma yanzu ya yarda Taiwo annamimiya ce. Halinta bai da kyau, she’s full of pride and arrogance, watakila shi ya sa hatta mijinta uban ‘ya’yanta Toafeeq ba ya iya zama inuwa daya da ita na lokaci mai tsaho zai gudu, ya gwammace ya yi nesa da ita. Ya dinga ganinta lokaci-lokaci tunda ta zame masa dole. In da ya bi hudubobin Taiwo na tuntuni kadan-kadan a kan Aisha, kafin ya gama fahimtar manufarta akan Siddiqah din gabadaya yanzu, da tuni ba su samu fahimtar junan da suka samu shida Siddiqah yanzu ba, da bai samu farin cikin da ya soma dandana da canjin rayuwar da ya soma samu ba. Shi Aisha ce daidai da rayuwarsa. Ta ishe shi, ta masa daidai, more than enough, tayi kunnen doki da duk wani burinsa a kan macen kwarai. Ba ya so ya yi wa Taiwo hukuncin da a gaba za yi nadama, shi ya sa ya dawo daki, ya jira dawowar iyayensu. Sai ga Nenne ta shigo dakin nasa fuskarta kamar hadari. Prince ya yunkura ya tashi zaune da kyar, idanunsa sun kada sun yi jazir sun kuma kankance. Nenne ta dube shi idanunta fal takaici da zallar bacin rai, ta ce, “Hammansu yau na maida Aisha ga iyayenta, kamar yadda na dauko amanarta, tunda haka ku ke so kai da abokiyar tagwaitakarka. Tunda tsoron Murjanatu ka ke, to shi ke nan, ta kashe maka aure, na amince na kuma yarda ta auro maka Haseenah da uku bayan Haseenah. Tunda itace uwarka ita ta haife ka. Amma kada ka sake ka saka ni a maganar bikon Aisha, bazani ba, saboda ina tattalin mutuncina a idon masu ganina da kima, ba kaida Taiwo dinka da baku daukeni a bakin komai ba, inaso iyayen Aisha wato Zainaba da Malam Yunusa su yanke duk irin hukuncin da yafi musu daidai”. Daga bayan Nenne Dade shi ma ya shigo, ya dora daga inda Nenne ta tsaya, ya ce. “Ni kuma Dade dinku ka riga ka san cewa mijin ta ce din Nenne ne, tunda ta cire hannunta ni ma babu nawa, ko Gombe ba zan leka ba, wai ido da kunya. Sai ka je ka gyara barakar da ka yi sake ta faru da kanka, amma kada ka sake ka saka mu a ciki nida Nenne”. Daga haka Dade da Nenne suka juya sua fice, suka bar Abdulrasheed na zufa daga zaune, yana tambayar kansa “me zai yi wa Taiwo ya huce?” ‘Yar halak din sai gata ta shigo minti goma da fitarsu Nenne, tana tafe da irin tafiyar nan tata ta kasaita da mulki tamkar dawisuwa cikin basarakiyar tafiyarta. Murjanatu Taiwo Akanni, ta shigo dakin ta tsaya a gabansa babu alamun ta yi wani abu da ba daidai ba a kan fuskarta. Ta ce, “Kehinde, wai don mun yi magana a kan yarinyar nan ni da su Ifedayo da Aunty Bola shi ne ta bar gidan? To don ubanta sai me? Sai aka ce da ita mata sun kare? Da ma ni ai so nake ku rabun, tun kafin ta haifa mana jikokin Malam Shehu a hada iri da talauci cikin gidannan. In dai mace ce ni zan samo maka daidai da kai, ko ba Haseenah ba tunda tayi aure ita, za ta sha mamaki don kuwa saidai ta dawo ta ganka da mace, wa za ta nuna wa zafin kai da rashin kunya?” Prince kansa na sunkuye, ya kasa dagowa ya dubi Taiwo domin zuciyarsa cewa ta ke yi ya yi kwallo da ita a dakin, ya dauketa ya nunawa sama ita ya nana da kasa, wata na tuna masa Taiwo dinsa ce fa cikin wani halina ajizanci da batan basira, Taiwo ce wadda ta haifa masa Kiki. Wadda ta tsaya masa a kan komai nasa tun zuwansa duniya, ta yi sharing farin cikinsa da bakin cikinsa, ta tsaya da shi a lokutan rauni, ta bashi farin ciki a sanda duniyar da yake ciki ta yi masa kunci. Waccan kuwa matarsa ce, barin jikinsa da yake fatan ta zama uwar y'a'yansa nan bada jimawa ba, wadda ko shekara ba ta cika da shigowa rayuwarsa ba. A yanayin da ake ciki kuwa yanzu dole ya zabi dayarsu ya bar daya, don ba za su taba kara zama karkashin inuwa daya ba, in aka yi la’akari da muggan kalaman Taiwo a gare ta, musmaman da ya bayyana gare shi cewa ita din mai sanin darajar iyayenta ce da kiyaye martabar kanta. A hankali Kehinde ya dago kai ya dubi Taiwo da rinannun idanunsa da suka kada ‘yan hanjinta. Ya ce, “Maman Kiki, please get out of here before I lose my temper!” Taiwo ta zaro ido, ta ce, “Kehinde, ni Taiwo ka ke wa tsawa yau?” Da karfi Prince ya ce, “Get out of my sight please Maman Kiki. I don’t want to touch you da sunan duka. I am disappointed in you, ki daina zuwa inda nake, in ba ni na neme ki ba”. Taiwo ta bude ido da baki cikin mamaki da razana , shi kuma Prince ya ce. “Karyar so ki ke min Taiwo, karyar ‘yan uwantaka ki ke min. Karyar tagwaitaka ki ke domin babu ita a ranki. Da kina sona a matsayin dan uwanki da kin so ni da farin ciki da cikar rayuwa kamar kowa, ko yaya ne da kin barni na tsira da farin cikin dana soma samu. Ki zauna ki laluba zuciyarki Taiwo, zaki tarar babu kaunar Kehinde ko kadan a cikinta yanzu, ko tu daga sanda aka yi masa aure. Wannan yarinyar da ki ka raina don basu da arziki da sarauta, ki ke kushewa a kunnena da idona dare da rana da zagi da aibantawa da gorin bata isa ba, ita ce din dai matar da Allah ya ga damar bani a matsayin kyautarsa, na ladan hakurina da gujewa saba masa ta hanyar zina, a tsahon shekarun kuruciyata. Ni kuma tunda ta jure wa tsufana, nima zan jure wa yarintarta da ki ke rainawa, ita ce uwar ‘ya’yana, uwargidana har a gidan aljannah insha Allahu. Sannan daga yau sai yau kada ki kara yi min zancen iyalina, tunda ba za ki taya ni sonsu ba, kamar yadda nake taya ki kaunar naki, to na shata babban layi tsakaninku har abin da zan haifa. Tunda da bakinki kin ce bazaki taba kaunarsu ba. Mu yi zumunci wanda ya shafe mu, wanda shi ne dolenmu, ba ruwanki da Aisha-Siddiqah, for your information ki sani “ina matukar son MATATA! Banida kowa da ya fiyemin ke sai iyayena sai kuma twins da ‘ya’yanki, kune duniyata komai nawa ya kamata ya zama naku ne. Daga yau kisa a ranki tunda kin kashe min aure zan rayu a yadda kike son ganina, kada ki kara ambata min kalmar aure tunda ba ke kika haife ni ba, ba ki da sauran haske a idanuna amma har gobe kina nan a ‘yar uwata sai ranar da ki ka gyara barnar da ki ka yi min”. (Duka wannan maganar Prince ya furtata cikin harshen turanci ne). Daga haka ya fice ya barta a dakin idanunsa sun kada zuciyarsa ta tabu. In duniya da amana Taiwo bazata zame masa cikas ga cikar farin ciki ba. Komai nashi nata ne da ‘ya’yanta haka komai yake yi a duniya su yake tunawa da samun farin cikinsu. Bashida wani buri da ya wuce itada ‘ya’yanta amma ace wai abu guda daya da ya nuna yanaso, Taiwo ta gagara son shi. Dakin Nenne ya nufa, sai ya tarar ta rufe da key ta ciki, don ta san dole zai biyo bayanta da lallashi akan batun biko ita kuma so take ya dau mataki da kansa, tafi son ya gane da kansa Taiwo fitinanniya ce abinda bai taba yarda a baya ko za’a shekara ana fadin cewa Murjantunsa tana da hali. Itada ta haifesu ma ta kwana da sanin hakan amma shi bai taba yarda. Haka ya bi bayan Dade shima a nasa masaukin, Dade ya ki ganinsa a daren don har ya kwanta, dan lekowa yayi kadan ta tsakanin kofar bai bashi hanyar shiga masa dakin ba, ya ce. “Please Kehinde, ka yi duk abin da ya dace da kanka, but count us out akan maganar Siddiqah da Taiwo, duukansu naka ne, ba wadda zaka zaba ka bar daya, amma akan maganar aurenka mu mun gama sauke nauyin duk da Allah ya dora mana a kanka, don haka duk wanui kalubale na rayuwar iyali sai ka nemi hanyar managing dinsa da kanka”. Auren Princess Fatima da Princess Firdausi kenan bai zo wa kowa a iyalin Engr. Idris Akanni da dadi ba. Taiwo ta bata musu armashin komai don events na al’ada har uku Nenne ta soke, ta ce za ta koma Lagos. In yaso dangi su kai amaren gidajensu haka, tunda an gama mai wuyar daurin aure, sa yi dinner washegarin tarewa a gidan mazajensu. Shi kuma Prince ta ki yarda ma ta ganshi har washegari tana doje masa da uzurin mutane sun mata yawa bata da lokacin kebewa dashi, shirin komawa Lagos suke yi itada Dade. Don haka Hamma Abdulrasheed Prince ya zama wani sukuku da shi a gidan, don Taiwo da zai samu ya kara hucewa a kanta da sassafe ta fice ba wanda ya san ina ta yi, kamar ta san ya ci alwashin sake cin ubanta da cin mutuncinta in style, ganin ta jawo hatta iyayensa sun daina sauraronsa akan laifin da ba nasa ba balle Siddiqah data dangwarar masa da wayarsa a inda yake tsaye, balle ya samu damar communicating da ita ya lallasheta kafin iyayensa su yarda su saurareshi asan abinyi a kanta. Ba da sanin Prince ba Dade da Nenne da safiyar washegari suka kira Taiwo ta waya cewa tazo masaukin Dade suna kiranta. Ba ta dade da dawowa gidanta ba don ta zame musu, ta yi sammako ta taho gidan ta, shigowarta kenan daga main house din kiran Dade ya sameta, kuma as usual Toafeeq ba ya kasar. Daga ita sai babban danta Hakeem a gaban motarta lokacin da dade ya kira ta. Tare suka zo da Hakeem, tana sane ta taho dashi wai ko sa ga girman danta da yawan shekarunsa su raga mata, don ta san dai tatsuniyar gizo bata wuce koki ita kuma tunda Kehinde ya ce ya daina ganin haskenta akan Aisha, to kowa ma yayi kadan yasa ta so Aisha (she is very sorry to say) hatta Nenne da Dade saidai suyi mata fada irin wanda suka saba ya bi ta bayan kunnenta a wuce wurin. Dade ya ce da Hakeem ya je ciki za su yi magana da Murjanatu, don haka Hakeem ya tashi a falon yayi musu sallama ya barsu, ya koma mota ya tafi gida. Taiwo ta shigo masaukin mahaifinta, a zuciyarta ta rasa abinda ke mata dadi da abinda Kehinde yayi mata akan Aisha, wato ya zabi Aisha a kanta, a kan wata banzar yarinya ‘yar talakawa da bata ko kai matsayin house girl dinta ba Kehinde ya gaggaya mata magana haka. Ta kara tsanar Aisha Siddiqah, ta kara tsanar duk wasu ‘ya’yan malam Shehu irinta. Tana wannan tunanin ta yi sallama a kofar dakin Dade ta isa ga kofar falon ta bude. Taiwo ta ga uwa da ubanta fuskokinsu kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, ta tuna when last ta ga Dade ya hade fuska irin haka, Taiwo duk ta tsargu, don ta san ba banza ce ta sa suka kirawo ta ba, ko daga fuskokinsu, Dade ne ya fara magana inda ya ce “da gaske ne abinda akace kin yiwa matar Kehinde? In haka ne kuwa baki yi halin Nenne Sappa ba Taiwo. Balle me sunanki Olori Murjanatu. An yi asarar kudin tara dai, kin zama babbar banza da wofi”. Yana fade cewa cikin fushi mai tsanani da harshen yarbanci. “Mu ba mu gaji cin zarafin dan Adam ba, saboda kawai Allah ya ba mu sarauta, ya ba mu aron ni’imar rayuwa daga cikin arzikinsa. Allah da kansa da ya halicci dan Adam ya karrama shi, ke wace ce da za ki wulakanta dan Adam mai daraja a wurin Ubangijinsa?” Dade yarbanci kawai yake saki tamkar ya fasa kunnen Taiwo, irin zazzafan yarbancin nan mara dadin ji da razanar da wanda ake yi mawa. Nenne da bata taba ganin bacin ran Dade irin na yau ba, ba ta sanshi da fushi irin wannan ba, don hak ita kanta ta tsorata da temper din da ta gani tare da shi, Taiwo tana durkushe a gabansa, jikinta na rawa da bari, Nenne kuma ta ce cikin daga murya, “in duniya da halacci har Taiwo ce za ta zagi matar Kehinde? Ko kunya baki ji ba? Iya kara a rayuwa Kehinde yayi miki, keda ‘ya’yanki da zurri’arki. Murjanatu baki kyauta ba sam, kin ci amanar tagwaitaka da zumunci. Haba! ai inda alkawari ko na munafurci ne ya kamata kiso Aisha, tunda kince kina son abunda yake so, ko ba kya son ta bazaki nuna ba ablle gaba da gaba haka, hakan shine adalci ga dan uwanki kuma da abinda kadai zaki saka masa dawainiya da soyayyarsa gareki da Kiki. Wato kiso iyalinsa. Taiwo a shekarunki sama da arba’in kin san hakan, bakya bukatar sai an tuna miki, amma mun tuna miki, a matsayinmu na iyayenki, ya rage naki ki dauki tunasarwar ko a’ah a wannan gabar, in kuma halin tsiya halinki ne ki yi ta yi duniya ce. Amma ko Kiki duk wautarta ai ba ta rashin hankalin dake uwarta Taiwo ki ke yi”. Dade kuma yace “Afuwa daya zan yi miki Taiwo shi ne, in kin je kin gurfana gaban Malam Yunusa, kin mayar da kalaman da ki ka jefe su da su daga bakinki mara saiti, kin dawowa Kehinde da matarsa dakinsa”. Daga haka suka fice. Suka bar Taiwo a durkushe a wurin. Taiwo sai kuka ta ke tana tsine wa wadanda suka kawo Siddiqah duniya. Ba su jima da fita ba, Taiwo ta mike ta koma gidanta, nan ta hau hada kayanta. Bari kawai ta hakura da aikin asibiti daga yau, ta koma wajen mijinta dindindin. Za ta wuce gidanta na Lagos, daga can ta yi shirin wucewa UK. Ba ta jin nan kusa za ta zo Ilorin balle gidan iyayenta a Lagos, tunda sun sallame ta a kan Siddiqah. Ba wani biko da za ta je wa Kehinde, tunda shima yace bata da haske yanzu a idonsa. Yo da aurensa da wannan yarinyar ai gara mata zamansa yadda yake shi kadai a baya, da Dawakansa da soyayarsa da da kulawarsa gareta. “Shin me ke damun Murjanatu-Taiwo exactly?” Tambayar da iyayenta ke yi wa zukatansu kenan a ranar har suka koma Lagos, Kuma a washegarin ranar da suka koma suka ji labarin Taiwo ta baro Ilorin itama zuwa Lagos, kuma wai tayi resigning daga aikinta na asibiti, ba tareda ta yi shawara da kowa nata ba, sannan bata yiwa kowa sallama daga masarauta ba ta baro Ilorin. Su dai sun san daidai gwargwado sun bata tarbiyya daya da Kehinde, sun mata nuni da sanin darajar kowanne dan adam, hali ne kawai, wato halayen dan Adam mabanbanta na halitta da dabi'a wanda bai da alaka da tarbiyyar da ta samu daga garesu. Ko bahaushe kan ce hali zanen dutse ne. In ka shekara ba ka ga mutum ba tambaye shi wani abun daban amma banda halinsa. Tun tana yarinya suka fuskanci tana da nakasu a halayya da dabi’a. Nenne a zuciyarta sai ta koma addu’a tunda nasiha da tunasarwa bazasu yi ba, ta soma addu’a tana rokawa Taiwo gyaruwar hali da saukin kai da halin tawali’u, da daukar duniya da sauki. Don haka Taiwo ko kai amare gidajensu ba ta je ba, ta wuce gidanta na Lagos ta bar Hakeem a Ilorin. *** *** *** An wuce kai amare Lagos Prince ya samu ya sulale ya wuce Gombe. Don ya gama yarda daga Nenne har Dade babu mai saka hannu ya lallashi Siddiqa ta dawo. Balle su je masa biko har gaban iyayenta. Ga shi ta ajiye masa wayarsa barin ma ya samu damar communicating da ita. Ya sauka a Gombe yamma lis, kuma dama tun kafin ya taso ya gaya wa Malam Buhari direban Nani Oummana tasowarsa, don haka yana sauka ya tarar da shi yana jiransa. Malam Buhari akwai wannan kokarin ga iyalin Oummana sabida yadda suma suke kyautata masa. Yasa baya gajiya da hidimar zirga-zirgarsu a duk lokacin da suka bukata. Prince na da gida wani madaidaicin gida flat a mahaifar Nennensa wato Gombe daya dade da saya tuntuni a GRA. Ba zai manta ba, Nani Oummana ce silar sayen gidan da yayi, a wani zuwa da yayi shekarun baya. Domin ta ce in yana so ya faranta mata dole ya sayi gida wanda iyalinsa za su ke sauka a Gombe, bazata yarda ta barwa Akannis shi bakidayansa ba, dole sai sun raba shi gida biyu an baiwa kowanne bangare hakkinsa, ko don ‘ya’yansa in sun taso su basu nasu muhimmancin na dangin Uwa domin kuwa lokacin da suka bada auren Nenne Sappa ga Akannis, sun ce, ‘ya’yanta dole su zo Arewa. A wurin Uncle Abdulmajid ya sayi gidan da jimawa, kasancewar likita Abdulmajid din kafin komawarsa Morocco yana taba sana’ar ginin gidaje yana sayarwa tsakanin Gombe da Bauchi. Duk da haka Malam Buhari bai wuce dashu gidannasa ba, ya wuce da shi kai tsaye fadar Gombe bisa umarninsa, yayiwa maigadin gidan a waya da yaron gidan yace a yi masa gyara yana iya zuwa yau ko gobe. Kai tsaye wajen Oummana ya sauka. A sassan Uwar gari Hajiya Ummana, Prince ne zaune a gefen damanta, tanata zuba mishi hira cikin fulatanci. Sannan tana kokarin saka mishi abinci da fura, wadda ta ji kindirmo ga kananan kankara an zuba a ciki, amma Prince duk sonsa da fura, wadda yake yiwa shan gani kasheni idan ya zo Gombe, yau ko rabin kofi bai sha ba. Nani ta ce, “Ai na san da zuwan nata, Nennenka ta gaya min komai. In shaAllahu za’a gyara komai”. Prince ya ji dadi sosai, iyayensa da kakanninsa ba dai sanin yakamata ba da halin dattaku, duk abin da ya kamata su yi don saya wa ‘ya’yansu mutunci sun sani, bai san inda Taiwo ta debo bakin hali na rashin sanin darajar Dan Adam ba. Shi abin da ke daure masa kai da lamarin Taiwo, ta so Haseenah ma da bata da kowa, bata da nasaba, amma wai duk da haka ta kasa son Aisha. Aishar da saidai a nuna mata gadon mulki da sarauta kawai. Ya nisa a hankali yana cewa cikin ransa, “Murjanatu baki kyauta min ba. Saida kika ga na samu sabon hope, wanda ya farfado dani daga suma na, na fada a wata korama da zaqinta yafi na zuma, gardinta yafi na madara, wadda ban taba fadawa ba a tsayin rayuwata, sannan ne zaki kore min wannan farin cikin dana nema na rasa (for over a decade), bisa wasu hujjojinki akan Aisha marasa ma’ana marasa makama. Aisha ki yafe mu!”. Nani Oummana da yake ta san hakikanin matsalar da ta kawo Aisha Gombe. Nenne ta yi mata cikakken bayani a waya. Amma Oummana ta so ta tambayi Nenne me ya sa ta taho ita kadai? Ta tuna ana tsaka da bikinsu Fatima ne. Ita ma ciwon kafa ne ya hana ta zuwa Ilorin, amma duk haularta da na Uban kasa wato yayan Nenne Sarki Ahmadu Jalloh ‘ya’ya da jikoki sun tafi suna can don yiwa Nenne kara. Da su aka yi komai, don haka Prince Malam Buhari ya sa a gaba ya yi masa jagora zuwa Jeka da fari. Zuwan Prince na farko kenan gidan iyayen Aisha tun auren su. Yana daga cikin mota mai duhun gilassai (tinted) yana nazarin gidan su Aisha da Malam Buhari ya yi parking a kofar gidan. Gidan karami ne, ko kuwa madaidaici, ya sha farin fenti mai santsi, sannan harabar gidan a share take tas. Soron gidan tsaf-tsaf da shi, tsafta ta zauna masa, ba dai gida ne na talakkawa can ba, don ko a layin gidansu Aisha ya fi kowanne fita da haske, kuma fentin da aka yi bai shekara ba, lokacin aurenta aka yi shi watanni tara kenan. Buhari ya bude masa kofa ya fito, Prince yana sanye da yadin filtex sky blue, ya lankwasa hularsu ta yarbawa a kansa. A fuskarsa yau ya dora farin glass, wanda ya dora a saman dogon hancinsa, Kamshin turarensa na ‘Baccarat’ tun daga soron farko sai da ya kai tsakar gidansuAisha. Malam Buhari ne ya zagaya ya bude masa kofa ya fito ya yi ta rafka sallama don bai ga yaron da zai aika ba. Wani matashin yaro ne ya fito daga gidan, wato Sunusi yaron da ke ma Umma aike. Buhari ya ce masa, “Ko Malam na gida?” Sunusi ya ce, “Eh Malam na nan”. Yace “to don Allah ka gaya masa Abdulrasheed ne yazo daga Lagos”, Sunusi yace “toh, bari in gaya masa”. Sunusi ya gayawa Malam Yunus zuwan bakon nasa. Malam Yunus ya dubi Umma itama ta dubeshi sai yace Sunusi ya shigo dashi. Prince ya shigo ya tsugunna ya fara gaishesu, Umma da Malam Yunus suka karbi Prince hannu bibbiyu, fuskarsu ba yabo ba fallasa, Malam ya tambayeshi ya hanya da gajiyar biki da yadda ya baro su Nenne. Malam Yunus na cewa a ransa Prince baiwa Aisha laifin komai ba kuma ba shi ya zageta ba. ya gaya masa Aisha tana gidan Yaya Barau don shine waliyyinta daman, yace babu komai amman dai ka je ka samu Baba Barau magana tana hannunsa. In don ta ni ne ma Abdulrasheed nasan har yanzu akwai kuruciya a tare da Taiwo mace duk shekarunta ai baka rabata da halin yara. Kuma iyayenka su sun san su waye mu, ba don haka ba da bazasu matsa wajen nema maka auren Aisha ba. Amman dai ina baka shawarar kaje ka samu Yaya Barau. Zan sa a raka ka yanzu”. Prince yaji dadi sosai ya kara yabawa da dattakun iyayen Aisha. Ya sunkuya yana kara baiwa Ummanta hakuri, Umma tace “aibabu komai, banda rigimar Aisha ma in nice bazan kula ba”. nan Abdulrasheed yace “a’ah Umma, gara da tayiwa Taiwo haka, ni kaina bansan yaushe Taiwo ta zama mai wannan baudadden halin ba sai yanzu, kuma wallahi na mata iyaka da iyali na, koda wasa abinda ya faru bazai kara faruwa ba in sha Allah. Iyaye ai na kowa ne, wannan ba tarbiyyar da aka bamu bane, don Allah kuma ina kara bada hakuri”. Malam Yunus yaji dadi sosai a ransa, ya tabbatar ya kuma kara yarda bai aurawa Aisha mijin banza ba tunda gashinan hakikanin gaskiyarsa yake basu hakuri, yake kuma Allah wadai da halin ‘yar uwarsa wanda shi kansa Malam Yunusya san tabbas wulakanci ba halinsu bane. Amma still he is so proud da Aisha ta nuna musu iyayenta ba abin wasa bane don haka bazata dau wulakanci ba. Sannan kuma ya ga girma da soyayyar Aishaa idon YarimaAbdulrasheed wanda yasa ya kara jin dadi, amma duk da haka yace bazai shiga maganarsu da Baba Barau ba. gara yaje Baba Barau ya kara wana shi amma zancen kashe aure yanzu babu shi in sha Allahu. Baban Aisha nan take yace da Sunusi ya raka su gidan Baba Barau din. Sunusi ya saka takalmansa ya shiga gaban mota, Prince na owner’s side, Malam Buhari yaja motar suka tafi, don gidan Baba Barau ba nisa sosai, layi biyu ne tsakaninsa da dan uwansa. A zaure suka tadda Baba Barau yana cin abinci, ga fura mai sanyi a gefe an ajiye masa a kwanon silba a gefe. A nutse Prince ya yi sallama a zauren. Baba Barau ya amsa duk da bai taba ganinsa ba, don haka da fara’a sosai Baba Barau yake wa hamshakin bakon nasa da bai san ko waye ba barka da zuwa, ya ce. “Zo nan bisa buzuna ka zauna”. Prince har da cire hula bayan ya cire takalmansa ya ki hawa buzun ya zauna a kan kafafunsa tankwashe a gabansa. Ya fara gaishe shi da hausarshi da ba ta da kwari. Baba Barau ya ce, “Ban gane dan nawa ba, daga ina kenan?” Nan Prince ya gabatar masa da kansa da cewa shine Abdulrasheed daga Lagos. Baba Barau ya kara neman karin haske, don har lokacin bai gane ba, Prince ya kasa magana sai da kyar ya iya cewa “Mijin Aisha-Siddiqah”. Ai nan da nan Baba Barau ya hadiye duk wani annuri da ke fuskarsa, Prince ya kara gaishe shi a ladabce, ya bashi hakuri akan zuwan Aisha. don yana da labarin Baba Barau a bakin Aisha, wani Yayan babanta da ba ya daukar wargi kuma ba ya yarda ko Babanta ya bata mata rai. Yadda Baba Barau ya maida walwalar fuskarsa ne ya sa Prince jin wata irin shakkarsa. Amma hakan bai hana shi fadan abin da ke gabansa ba, ya fara da bada hakuri sannan ya ce masa wallahil azeem shi Aysha tafi karfin wulakanci a garesa. Dalilin ma da ya bari sai yau ya taho kada cece-kuce yayi yawa ne cikin taron bikin. Ya kuma tabbatarwa Baba Barau ya magance matsalar Taiwo. Kuma yayi alkawarin baza’a kara ba. a wannnan gabar Baba Barau kansa ya yaba da hankalin Prince. Ya ce “naji, amma dai a hakura kawai da aurennan, kaima daman ba so kake ba itama haka, to kuma kaga akwai mutunci tsakanin iyayenku mata kada auren nan ya zama silar matsalarsa”. Murya na rawa Prince yace “Baba ni ia son Aisha…” Baba Barau ya dakatar dashi yace “Abduulrasheed maganar gaskiya yaranmu basa auren wulakanci, munada hakuri amman banda wulakanci, kuma abinda yasa Aisha dawowa gida haka to babba ne, inda duk za’a taba maka iyaye bazakaso zama ba. so ina bayan Aisha kan duk abinda ta yanke, kaje zan neme ka zanyi shawara”. Jiki a sanyaye Abdulrashid yace “toh Baba, nagode, zan iya ganinAisha yanzu?” Baba Barau yace “a’ah”. Sai yayi shiru na dan lokaci cikin damuwa daga bisani yace “to shikenan Baba zan tafi nagode”. Suka koma gida, ya kwashe komai na yadda sukayi da Baba Barau ya gayawa Nani Oummana. Da kyar Nani ta rarrashe shi ya dan ci abinci ya yi mata sallama ya wuce gidansa. Nani sai ta dau waya ta kira Nenne suka gaisa, Nani ta yi mata ban gajiyar biki da ta hidima, Nenne ta ce, ai har sun dawo Legos, ta kansile da yawan events din bikin da ba su zama dole ba saboda Taiwo data bata ciwon kai. Tana son kashe auren Hammansu babu gaira babu dalili. Nani ta ce, “Amma Dadensu ya kyauta min da ya wanke ja’ira mai halinsu na yarbawa, mu dai kam Murja ba ta dauko mu ba, can musu cikin Akannin”. Nenne ta ce, “Ai ko a Akanni babu irin Taiwo. Ita kadai ce da halinta, mijinta ma hakuri yake da nature dinta ba tun yau ba. Tun yana kawo kararta ana sulhu har ya gaji ya yi nesa da ita, sai ya yi watanni uku bai waiwayo ta ba”. Nani ta ce, “Addu’a za ku dinga yi mata da nasiha ba fushi da ita ba. A shekarunta dai ta yi girman banza”. Sun dade suna tattaunawa a kan sha’anin Taiwo, har Nenne ta ce, “Ban da abin Murja ma Aisha ba ta ki Hammansu ba saboda ratar shekarun da ke a tsakaninsu sai shi ne zai ki Aisha? Aisha son kowa kin wanda bai samu ba, na bi sarauta da kudi da gudu, na kama wa Hamma Aisha ne saboda nagarta da iyaye na gari, idan kuwa har Aisha ta fada wa iyayenta abin da Murja ta yi mata, to abu ya baci. Don ba kowa zai yarda a taba mutuncinsa a wanye lafiya ba, shi ya sa daga ni har Dade muka ce babu mu a 'yan biko wai ido da kunya. Shi da ya bar Murja ta ke taka rawa cikin rayuwarsa sai ya nemo ta ta yi masa biko”. Nani kuma ta ce, “Hamma meye laifinsa? Ana hora shi ne kawai da laifin da ba nashi ba. Ya je bikon ai ga shi ya dawo ba nasara, ya yi min shame-shame a falo kamar gawa. Duk sonsa da fura tunda ya zo bai sha ba”. Nenne ta ce, mu kyale shi ya yi ta bikonsa shi kadai, ya fi sanin darajar wahalar da aka yi masa aka yi masa aurenta babu ko kobonsa”. Nani kuma ta ce, “A’a za ta sa uban kasa ya shiga maganar, idan Abdulrasheed ya kasa. Kwanan sa biyu a Gombe. Rana ta farko da yaje ga yadda suka kwashe da Baba Barau, don haka ya sake kwana a Gombe. Washegari ya sake komawa wajen Baban Aisha da Umman ta, ya gaya musu yadda sukayi shi da Baba Barau, ya Kuma roki Abban Aisha don Allah ya taya shi baiwa Baba Barau haquri. Malam Yunus ya lallashe shi ya ce ya koma gida zai ma Yayansa magana, dan har ga Allah yaji tausayin sa. Prince ya saki jiki da iyayen Aisha kamar ba jiya ya fara zuwa ba. Sukayi developing good bond. He is open minded, ga kuma hankali. Amman kana ganin sa kaga damuwa. Abban Aisha yace masa kar ya damu yaje gida zai saka baki. Kuma kada yaje gidan baba Barau yau tunda jiya ya je, zai neme shi da kansa, yace yayi haq9uri har ya neme shi din. Prince ba yadda ya iya haka ya dawo Lagos bai san makomar aurensa ba. A daren ranar yana tareda iyayen sa a falon gidansu. Dade ya tambaye shi "toh ya akayi a gomben?" Nan Prince ya fada masa komai, yace murya ba kuzari "nidai Dade ba don Taiwo yar uwata bace da na mata Allah ya isa, finally i have a glimpse of happiness, ta lalata min shi, wannan wani irin rashin sa’a ne?" Prince ya fadawa Babansa in a heartbreaking manner. Yasa hannu ya dafe kan sa. Sai ya ba Dade tausayi matuka. Suna haka aka kira shi daga Qatar, Dade yana jin sa yace musu bashi da lafiya su qara mashi 2 weeks. Sai bayan ya aje wayar ne Dade yace masa "toh ka koma mana sai ka dawo daga baya? By then itama ta huce Aysha din". Prince yace "Dade ko na koma bani da nitsuwar yin aikin, gara dai inyi ta fama ko zata haqura. in kuma taqi haqura sai na koma din. It seems that’s the life my own twin thinks i deserve, a lonely, sad life, unworthy of pure happiness… and apparently you and Nenne too....". Prince ya furzar da numfashi me daci a kasalance ya tashi zai wuce gidansa. Dade yace "why will u say that?" A marairaice Prince yace "toh ba cewa kukai ba ruwanku ba Dade? Ni iyayen aysha basu sanni ba ku suka sani. And if we are being honest I am nothing but good to Aysha. Ita in yarinta ya debe ta ba se a duba ni ba. Ni da ba ni nayi laifin nan ba and also ba ni nasa Taiwo ba. Amman duk laifin ya dawo kaina kuma kunyi shiru kunce ba ruwanku. Gaskiya i won't forgive Taiwo for this Dade she really did hurt me…." ya tashi zai tafi ya juya kenan sai kuwa sukayi ido hudu da ita. Taiwo. Jikinta yai sanyi, tazo ne immediately don Dade ya aika a kirata dazu. Ko kallonta Prince baiyi ba ya fita ya tafi gidan sa. Nan iyayen sukayi mata tatasss, don Nenne ma taji me yace ma Dade tana daga dakin Dade din, kamar yadda Taiwo taji itama tana shigowa. A ranta ta fara nadama. Ga nasihar da iyayen ke mata suna kuma nuna mata ta butulcewa son da Kehinde yake mata in har itace zata saka shi a wannan halin. To duk wannan ya taru yasa Taiwo ta damu, a lokacin ta baiwa iyayensu haquri ta koma gida ta wuce ta sai tiket din tafiya UK. Bayan fitarta ne Dade da Nenne suka kara tattauna maganar, suka aje lallai Friday zasu je Gombe takanas suyi bikon nan da kansu. Alamu sun nuna fa Hamma yana ta iyo a kogin soyayya. Babansa kuma yasan basu iya so ba, gara ya taimaki magajin sa. Nenne har sallahr nafila tayi ranar ta godiya ga Allah ganewa data gama yi Hamma Abdulrasheed yana son Aisha, ga kuma irin matakin da ya dauka kan Twin dinshi Taiwo da cikinsu da ita kanta Taiwo din babu wanda ya zaci zai iya hakan akan Taiwo. Ta san ko da wasa bazai kara barin wani ya taba Aisha ba, dan haka zasu shirya nan da kwana uku suje Gombe, yau talata, toh ranar Friday ko Saturday zasu je gombe. Shi Prince bai sani ba ya tafi gidansa haka ya kwana zuciya ba dadi. Sai asubahi ma bacci ya dauke shi, yana tashi yaga ba amfanin zaman Lagos. Bari kawai ya koma Gombe din sai yayi jiran hukuncin Baba Barau a can. Nan Hamma ya hada 'yar akwatin tafiyarsa ya kira nenne a waya yace zai koma Gombe. Nenne tace ko lafiya ince ko? Prince yace "toh Nenne ai gara ina can in yi ta matsa musu kawai Nenne. Idan Kuma har lokacin basu yarda ba zan tafi inyi reporting wurin aiki… Tawakkaltu Alallah… na fawwala wa Allah". Nenne sai taji ta kuma jin tausayinsa masa je ka Hammansu Allah ya ba da sa’a kaji, Allah kuma yai albarka albarka Annabijo". Prince yace amin Nenne". Ya tafi a ranar ya hau jirgin Gombe. Oummana sai gani tayi baqon shekaranjiya ya dawo. Tace "yaya dai Abdulrasheed?" Sai yace "nan zan zauna, sai an bani matata" Ommana sai ta fashe da dariya tace, "ah lallai Indo ta murza kambu, sarauta ta fadi" Prince yace "ai Oummana warwasss! Sarautar nan ta fadi. Aisharku itace mai mulkin". Me Oummana zatayi ba dariya ba. Tace "sai ka shirya kaje ai" Prince yace "dole ai Oummana… ki mun addu'a ni ko ganinta ma na samu nayi yau". Zuciyar Oummana fessss! Yau ace Abdulrasheed yasan martabar mata a gare shima babbar nasararsu ce. Prince yana fita tasa ai mata kiran uban kasa. Da Uban kasa ya tashi fada sai ya zarto sassan mahaifiyar tasa, nan Oummana ta fada masa komi da ya faru har dawowar Hamma Gombe yau. Uban kasa yace "wannan ai abu ne me sauki Oummana, ai dan nasan abinda ya faru kenan dana aika tun ranar da tazo. Wulaqanci ba dadi amman sai ayi la'akari da ba laifin sa bane. Ayi masa afuwa". Oummana tace "ai ina sane da ban fada maka ba. So nake shima yaji a jikin sa, kuma inga gudun ruwan iyayen sa, in har zuwa karshen mako naga babu wani canji se kuje da auta (Abdulmajeed) dan Allah ayi mana bikon Aisha". Uban kasa yace "bakomi Oummana ". Shi kuma ya tafi ya sake daukar wanka, yau ma cikin brown filtex yadi, ya daura hular manyan matasa na zamani wato 'Tonak' kalar kayan, ya yi fes cikin shiga ta kamala, zati, haiba, kwarjini da kamala duk sun bayyana tare dashi, ko makiyin sa ya ganshi a wannan lokacin sai yace "fatabarakallahu ahsanil khaliqeen". Domin yau Hamma a ruwa biyunsa ya fito, Malam Buhari ya daukoshi zuwa Jeka da fari. Prince yai sallama a gidan su Aysha Baba yunus ya fito yace "laaa Abdulrasheed kai ne tafe?" Yai murmushi yana dukar da Kai, suka gaisa da Baban Aisha, yai masa iso zuwa ciki, Abba ya tambayi su Dade. yace "inace shekaranjiya ka tafi ko baka tafin bane?" Yace na tafi Baba. dazu na dawo". Yace ina Ummanmu?" Abban Aisha yace ta je gidan Baba Barau bikin 'yar sa Maryamu akeyi. Jibi Jumaah za'a daura auren bayan sallar Jumaah. Sun tafi jere wai. Malam ya dubeshi Yana murmushi ya ce "ka san mata da hidima". Prince yayi shiru. Cikin damuwa. Malam Yunus yace "Abdulrasheed ba nace zan kira ka ba?". Yace "Babanmu kayi haquri wallahi ko na zauna Lagos bani da nitsuwa, gara dai in dawo Gomben in zauna jiran hukuncin Baba Barau". Malam Yunus yace "ba ance ana ta kiran ka wurin aiki ba?" Yace "na basu excuse sun qara min sati biyu, shiyasa nace gara na dawo nan din". Sai yayi shiru. Malam Yunus ma duk sai yaji wani iri, yace ba damuwa in an jima zani gidan nasa daman, zan masa magana kaji?" Prince yace "toh Baba. Nima wai da zuwa zan yi in gaishe shi". Yace "toh babu laifi". Yana barin nan yace wa Buhari ya kai shi gidan Baba Barau. Ai kuwa ya samu gida makil da jamaa ana ta hidimar jere yau da kawo lefe. 'Yan uwan mijin sun tafi kenan Prince yai sallama, dan Baba Barau ya fito yaje ya fada masa mijin Aisha yazo. Nan aka masa iso zuwa ciki. Wato duk hayaniyar da ake a gidan Malam Barau Hamza, jikake kamar anyi ruwa an dauke tsit!!!!! akayi. Lokacinda Prince ya keto jamaa ya ya wuce zuwa falon Baba Barau, kwarjinin nan na masu sarauta, gashi dai ba girman kai, amman ana ganin sa an ga basarake, haiba, mulki ado, kai komai ma!!! Hamma yayi tsugunno a gaban su Baba Furera yai masu gaisuwa jama’u (in general). Auwalu babban Dan Baba Barau da ya shigo dashi yace dasu "mijin Saddiqah ne"". Ga dangin Aisha gabadayansu sun hadu, nan aka sake gaisawa, ya miqe zuwa cikin falon Baba Barau. Nan aka bar 'yammatan family dinsu Aisha da kawayen amarya da santi da lashe miyau, Saddiqah na tsaye jikin window taji muryar sa, ta juyo tana kallon sa ta tagar, har wata rama taga Hamman nasu Firausi yayi, amman ya zuba kyau Masha Allah. Tana ganin yadda 'yan banzan cousins dinta sai kallon sa suke tace kamar mayu, a ranta ta ce "mayu kawai, mtsw". Da taji ya Auwalu yace mijin SIDDIQAH ne she was proud!!!! Sai daga baya ta tuna tace fa ta gama auren. Sai ta koma ta zauna a gefen gado, ta fara tunani. Prince ya isa palon Baba Barau ya zauna a kasa ya gaishe shi cikin girmamawa, shima ya amsa. Ya tambayi su Nenne yace suna lafiya suna gaishe shi ya sunkai da kai. Baba Barau ya dauka zai masa maganar Aisha yaga bai ce komi ba. Yace "Babanmu ashe biki ake yi". yace "eh wallahi, wa ya fadi maka?" Yace "Baba ne ya fada min dazu. Allah ya basu zaman lafiya. Yaushe ne daurin auren?" Baba Barau yace "jumaa ne in sha Allah". Prince yace "toh Allah ya kaimu. Allah yasa ayi damu", Baba yace "Amin". Zuwa can kuma Prince yace "Baba inzo daurin auren?" yace "ah me zai hana in kana nan kazo". yace "ai ina nan ma in sha Allah". Baba yace "toh Allah ya kaimu". Yai shiru dai, can kuma yace "Baba zan tafi kuma dan Allah ina kara baka hakuri. Waman gaddarallahu hakka qadrihi…. Allah ne ya qadarta faruwar abinda ya faru kuma wallahil azim bazan yi kaffara ba, bazai kara faruwa ba. A gafarce ni don Allah. Baba kar kayi min hukunci da laifin yar uwata. Allah ya Kara hakuri Baba sai jibin in sha Allah". Ya tashi zai tafi, Baba Barau sai yaji duk ya daure shi da jijiyoyinsa, yayi murmushi yace "Abdulrasheed kenan, ni zaka daure ko?" Yayi murmushi shima yace "ah ah Baba". Su duka biyun suna murmushi suka rabu. **** **** ***** TAIWO Ta sauka gidan mijinta a Lancaster da yamma lis, ta isa ga kofar shiga tana ringing bell. Ana bude kofa taga wata kyakkyawar bafullatana da mijinta Toufeeq a bayanta, ga yaranta biyu dasu, da wani kyakkyawan Baby din dauke a hannunta. Wani irin shock ne ya kama Aunty Taiwo, tace "Toufeeq what is this?" Yayi mata kallon rashin tsoro ya ce mata "matata ce itama. Sunanta Hauwa-Maijidda". Ya dubi Maijiddar yace mata "Maijidda this is Taiwo, Maman Kiki da Abdulhakeem". "What???" Sai ga Murjanatu ta sulale ta zauna a dandaryar kasa a bakin kofa. Ta daga ido ta kallo matar, sannan yaran, in zata tuna ta taba ganin hoton yaran yace mata yaran abokin sa ne, wanda suka je auren sa a Yola…. A nan komai ya dawo mata, zuwan sa Yola auren aboki, ashe nasa auren ne. A cikin ranta sai tana ayyana alhakin aisha ke bin ta…. Taiwo tace "hasbunallahu wa ni'mal wakil… Toufeeq......". Sai kuka wiwi. Toufeeq ya soma yi mata bayani cewa "he doesn't want to hurt her ne, shi yasa yai aure bata sani ba, don yasan ta da bala'i. He needs peace in his life da matar da zata damu dashi. Yace ta dawo UK tace baza ta bar aikin asibiti ba, toh shikuma he needs someone close to him, wadda baza ta ke bashi ciwon kai ba. Taiwo ta kara jin muguwar nadama, nadama mara misaltuwa, tace komawa zatayi, Toufeeq yayi ya lallashinta ya kuma fada mata in zata kwantar da hankali ta zauna toh, if not zabi ya rage nata, amman aurensa da Maijiddar sa ba fashi. Taiwo a cikin satin ta dawo Nigeria. Koda ta sauka. Gidanta na Lagos ma kasa shiga ta yi tunda dai Toufeeq ne mamallakinsa. Dole gidan iyayentan dai ta dosa da tarin nadama a tare da ita, don ta kira wayar Kehinde ya ki dauka, ta je gidansa maigadi ya ce mata ya yi tafiya Gombe. Zuciyar Taiwo bugawa ne kawai ba ta yi ba, da abinda Toufeeq ya yi mata, ta zama tamkar zararriya, har magana zaka ga taan yi ita kadai, tana ta gaya wa kanta alhakin Aisha da Abdulrasheed ne ya hana ta kwanciyar hankalin zaman aure, ya tagayyara nata farin cikin auren. Domin don wulakanci irin na Baban Kiki ma cewa ya yi saura ta je ta hada masa bomb a gida, don ba wanda ya san ya yi 'secret marriage', ko a nashi family din kuwa, don yarinyar zuri’arshi bazasu barshi ya aureta ba, kasancewar diyar talakkawa ce sosai a garin Yola ya aurota, shekarun baya yaje yin wani project daga European Union ya ganta tana talln fura da nono ya aura. Babanta ma baduku ne. Don haka daga Nenne har Dade babu wanda ya san dalilin zuwan Taiwo gida rana daya, a taurin zuciya irin nata, da rashin tsoro ko shakkar kowa da kowa ya sani, suka ganta duk ta sauke kai, ta zubda izza, yanayin da suka ganta a ciki ya basu mamaki sosai. Kuma tana zuwa gida ranar Friday da sassafe taga ana ta shiri su Nenne zasu Gombe. Taiwo ta fashe da kuka ta roki su Nenne suyi hakuri tun ba'a je ko'ina ba taga me tagani. Nan ta fada ma Nenne komi tas, ai kuwa Nenne batayi mamaki ba don yasan Toufeeq yayi hakuri da Taiwo ba kadan ba, nan ta sake yi mata nasiha mai kashe jiki da huda zuciya. Tace zasu je ne su yi bikon Aisha, Taiwo tace zata bisu tunda itace tai laifin zata je ta basu hakuri. Su Nenne suka ce "toh". Da hantsin ranar jirgin DANA Air ya tashi dasu Gombe. A gidan Oummana aka sauka. Oummana se ganin su tayi daga sama dukkansu, tace "daga ina haka?" Nenne tace "sunzo biko" Oummana tace "ai ni daman ido na saka muku, da baku zo ba daman anjima zanje gidansu Aisha da kaina inyi ban hakuri". Nan Oummana ta hangi Taiwo, aiko Oummana ta ciwa Taiwo mutunci son ranta, tace "Ashe tareda tabbatacciyar kuke tafe?" Oummana tayi Mata tatas. Uban kasa ma da ya shigo ya ci wa Taiwo nasa. Taiwo tai kuka har ta gode Allah idon nan sun kumbura pummm. Sai ga Prince nan ya shigo around 11am, yana zuba wani irin kasaitaccen kamshi, ya sha fararen kaya, yana riqe da babbar rigarsa a hannu, da hular sa Tonak ash colour, wato kalar zaren da akai aikin kayan, gabadaya suka juyo suna kallon sa. Surprise yaga Nenne da Dade bai ma kula da TAIWO ba. Nan ya shigo ya gaishe su, har suna hada baki sukace, "ina zaka je haka?" Prince yace daurin aure zai je, uban kasa yace "a ina?" Hamma yace "Baba Barau ke aurar da diyar shi" Oummana tace kace "biko kake tayı. Wannan ado haka Hammansu ai dole a baka Aisha Indo yau!". Prince ya saki wani kasaitaccen murmushi yace "Allah ya amsa bakin ki Oummana" duk suka ce "amin". Dade yace "muma biko muka zo ai, amman tunda biki ake yau zamu bari sai gobe sai muje, Prince yace "ah ah Dade, yaya kunyi niyyar alhairi zaku fasa kuje kawai yanzu" duk suka hau dariya, uban kasa yace ban san ka da gaggawa ba, yau da gobe ai duk daya ne. Yana juyawa sai yaga Taiwo duk tayi zuru-zuru. Sai yaji ba dadi, yace "lafiya ke kuma haka?" Sai kuwa Taiwo tasa kuka, tazo ta rungume shi tace I am sooo soo soo sorry Kehinde. I love u so much, I became selfish and possessive ban ma sani ba. I am extremely regretful of what I did, and i will do anything to make it right. Kayi hakuri. Iyayen na kallon su da Kakar su, da zuciya daya ya riko hannunta, yace "Allah ya yafe mana bakidaya Taiwo, Allah yasa kin canza hali kenan har abada", duk aka ce Amin. Sai suka baiwa kowa tausayi musamman Prince, don yana son yar uwarshi. Kehinde akwai yi wa mutane uzuri. it was an emotional moment tsakaninshi da Taiwo dinsa yau. Yana yi mata murmushin afuwa itama tana masa na godiya. Daga bisani ya kalli agogo yaga lokaci ya tafi, yace "kai bari in tafi kar nayi latti". Ya saka hula yana musu sallama. Uban kasa yace "ah ah, ai baza ka tafi haka ba, yace da Kawunka zaka tafi ya raka ka. Yau a basaraken ka zaka je musu, ko Baban Aisha Indo ya daina ja maka rai". Sarki Ahmadu Jallo Umar yayi gyaran murya sarkin dogarai daga bakin kofa ya ce "Ran sarki ya dade, ina kusa", Sarki yace "a kira azo a daura masa rawani, a hada mota, kuma a kira Galadima da Waziri Abdulrashid ya wakilce ni a daurin auren da zashi yau, a hada convoy, a hada dogarawa!!!". Sarkin dogarai cewa yake "an gama Uban kasar Gombe, maganarka doka ce!". Nan ya buga babbar riga ya wuce zuwa cika aikin Sarkin sa, jikinsa na zikiri. Hamma ya bata fuska ya dubi Kawunsa Uban kasa yace "is it necessary? Kar ma suce ‘show off’ ake masu, su sake boye ta a daki?" Nenne da Oummana me zasuyi ba dariya ba. Uban kasa ma da Dade sai da suka dara. Wato duk Taiwo ta jawo ya zama a darare yake da duk abinda zai sa a ce ya raina azikin su Siddiqah. Uban kasa yace "ai dai an gayyace ka daurin aure ko?" Hamma yace "eh" Uban kasa yace "toh ni nace ka wakilce ni. Gara yau dai a gan ka a ainahin gaskiyar ka. Sarauta ai ba karya bace Abdulrasheed". Prince yayi murmushi. Nenne tace "gaskiya kam. Allah dai ya bada sa’a, in an gama daurin aure ka shiga ciki ku gaisa da su Umman Aysha, kace ina gaishe ta". Hamma ya ce "toh Nenne". Daman Kuma karfe 12:45 ne daurin auren, da an idar da sallar Juma’a za a daura. Ai kuwa kan kace meye wannan sarkin dogarai ya cika aiki, an sanar da maganar zuwa daurin auren, Galadima da Waziri sun shirya, ga dogarawa da motoci na alfarma nan uku an ware, sai motar Uban kasa itama an fito da ita. Cikin ta Prince zai shiga. A gefe ga masu algaita. Daga cikin gida kuwa Prince ne zaune za'a nada masa rawani, sai kira yake "shi fa baya son rawani, zafi ne dashi Oummana". Nani Oummana tace "ai kuwa dole kaso rawani, don kuwa kayi gadonsa hawa biyu". Hakanan Hamma ya zauna aka nada masa farin rawani, an masa irin rufin bakinnan, ya dau 'black Gucci shades' kalar dark brown' ya saka, ga hannun nan na dama yana juyawa yana sheki. 'Patek Philippe Grandmaster Chime' ya saka, not extravagant but extremely classy. Yau sai jinin fulatancin gabadaya ya fito. Masha Allahu kawai za'a ce saboda Nenne tana zaune tana kallon sa ya tashi zasu wuce bata san sanda tace "fa tabarakallahu ahsanal khaleqeen. U'izu bi kalimatillahi tammat min sharri ma khalaq". Ta tashi ta tofa ta shafa mashi. Wallahi tama manta basu kadai bane. Oummana tace, "je ka Allah ya tsare" yace "amin Nani". Suka fito tare da Uncle Abdulmajeed shima yasa rawani. Amman Kehinde ya haska. Dogarawa an samu abin so, shi dama gashi miskili kuma rawanin ba so yake ba, ai sai shan kunun da yayi yasa komi looks more regal. Suka hau kirari kamar makoshin su ze fita aka shige mota. Hamma yace don Allah a rage convoy din. Sarkin dogarai yace "ai yayi hakuri tunda sarki yake wakilta baza su fita qasa da haka ba. Ya shige motar Uban kasa shi da Uncle Abdulmajeed sai sarkin dogarai a gaba. daya motar kuma Galadima dayar Turaki da Waziri. Sai ambulance da kuma bus ta dogarai da masu algaita. Aka wuce tiryan_ tiryan zuwa Jeka da fari. A hanya Prince ya kira Baba Yunus, yace “yazo zai fito Uban kasa yace lallai ya wakilce shi a daurin aure, to dai gashi nan a hanya Allah yasa kar yayi wa Baba Barau laifi”. Ashe a ‘hands free’ yake, Baba Barau na kusa da Yunus yana jinsu, sai Baba Barau yayi masa gyaran murya yace "wato Abdulrashid kallon sarkin bala'i kake mani ko?" Prince ya zaro ido yace "subhanallahi, ko kadan Baba. Na dai fada ne kada muzo baku sani ba". Yace "to wa ya taba mayar da wakilcin Uban kasa? Wato don na rike maka Indo, shine kake so ni a kore ni daga kasar Gombe ko?" Yace "ah Baba, tsaya kaji.....". Ai kuwa Baba Barau ya fashe da dariya, Mal Yunus yace "wasa yake maka ka ji! Sai kun iso". Du duk a tunanin su shi da wani aka turo. They have no idea it’s the whole convoy. Nan aka fito aka shiga rumfuman canopy da aka kakkafa a gaban gidan. Aka zazzauna, aka ce sarki yayi wakilci, wa zai daura aure wakilin Sarki bai iso ba?” Haka nan aka dan tsaya aka dan ware wuri kamar na mutum hudu da zasu zauna. Ba jimawa saiga ga jiniya, motar escort na wi-wi-wi-wi. Mata ma daga cikin gida jin jiniya sai aka hau leke, sai ga Bus din dogarai ta tsaya a gefe, suka fice. Baba Barau sai da ya dan firgita. Ya mike tsaye shi da malam Yunus da Malam Hassan wato Baban tsohon saurayin Aisha Ishaq, don shima Mal. Hassan yazo daurin auren. Bakidayansu suka tashi don sun dauka sarki ne yazo. Kafin su tantance komai sai tashin algaita duk inda ka hanga police ne da dogarai, sai ga motar Uban kasa har gaban ‘tent’ din da iyayen amarya ke ciki, dogarai suka zagaye ta ana kirari “Barka da sauka magajin garin Ilorin, barka dai sarki dan sarki jikan sarakuna. Gaba salamun baya salamun. Abdulrashid dan Idrisu jikan Akanni. Jikan Ummaru Jalloh Uban kasar Gombe…”. Abdulrashid yana mota jin ana masa wannan kwakwazon ji yayi kamar ya nitse, cewa yake “don Allah sarkin dogarai kace su bari” yace masa “toh kawai”. Sai ya yunkuro zai fita, dogarawa suka baje riga aka bude kofar, ya fito. Uncle Abdulmajid ma ya fita, yara ‘yan unguwa da matasa sai ihu ake …. kyau kam iya kyau Hamma Prince ya sheka shi. Baba Barau da Baba Yunus suna inda suke zaune kowa yana tasbihi ga Allah a zuciyar su, dan lallai ya bawa diyar su miji nagari, wanda bashi da makusa. Ga nasaba ga addini. Kuma Allah ya mallaka mata zuciyar sa. Sai kawai Baba barau yaji sanyi a zafin sa da yake ji. Ya tashi suka wuce suna nuna masu wurin zama. Sarkin dogarai ya wage baki da murya yace “mai martaba Uban kasar Gombe ne ya wakilta dan sa yazo ya wakilce shi a wannan daurin aure na Maryama. Ya kuma bayar da auren a madadin sa”. Da ya kai aya sai dogarawa suka wuce dasu goro da dabino alawa ana ta jibgewa. Ashe a cikin gida ma ana ta sauke su lemu da ruwa da dai kayan daurin aure. Baba Barau ya tabbatar cewa lallai an karrama shi, an karrama autarsa Maryam. Nan aka zauna Abdulrashid ya gaishe su, zai duqa kenan Sarkin dogarai ya tare shi, ya ce “Yallabai Uban kasa fa kake wakilta, kai ne sarki yau”. Baba Barau yace kul ka tsugunna, muje”. Aka wuce ciki aka bashi waje duk suka zauna. Sarkin dogarai a ran sa yace. “wannan Yarima na zamani, ba abinda ya sani a kan sarautar gidansu”. Nan dai aka fara shirin sallar Jumma’a. Liman yace gudun kada yayi laifi, ko Galadima zai yi limanci? Sai Uncle Abdulmajid yace da Prince yayi. Nan kuwa Prince ya tashi yayi huduba mai ratsa jiki, sannan ya tayar da sallar jumma’a. Da aka idar aka daura auren Maryam da Angonta Yusuf, Kehinde yayi walicci aka bayar da Maryam bisa sadaki naira dubu dari lakadan. Sai fatan Allah ya basu zaman lafiya Ana gamawa kowa yana so ya gaisa dashi, nan duk ya tsaya aka gaisa akayi hotuna, Prince ya matsu su wuce gida saboda cikowar jama’a irin wadda bai zaba a ciki ba, ga rawanin nan ya ishe shi da zafi, duk ya gaji kamar yasa kuka. Zasu shiga mota kenan sarkin dogarai yace wa Mal. Yunus zasu shiga su gaishe da Umman Aisha da matar Baba Barau. Malam Yunus yace “toh ba matsala”. Su mata acan cikin gida al’ajabi ya ishe su, ance sarki yazo daurin auren Maryam, toh ta yaya? Ita dai Aisha jikin ta duk yayi la’asar. tun da taji ana “jikan Akanni” kuma ta jiyo muryarshi yana khutbah…Mal. Yunus ne ya shigo yace da matar Baba Barau da manyan Aunties din Aisha su kimtsa Uban kasa ya turo ai musu Allah sanya alheri. Ai sai suka yafa mayafai, aka taho falon. Suna shiga ya koma yayi musu iso, masu algaita zasu fara kirari Hamma ya daga hannu sai suka yi shiru, da algaitar suka shigo gidan. Amman babu wanda bai ce masha Allah ba, wanda suka gansa shekaranjiya ma basu gane shi bane, suka shiga falo dasu Galadima aka gaisa, da su Baba Barau duka, aka kuma sake fatan alkhairi, sannan suka ce zasu wuce. An karramasu, sun gode. Karaf! Hamma sai ji yayi Waziri yace “toh a bisa al’ada, in sarki ya bada aure, komi na gararauren shi zaiyi, dan haka ga kayan gara nan na Maryama Uban Kasa yace a kawo….”. A dari da sittin Abdulrashid ya kalli Waziri, sannan ya kalli Baba Barau, sai kawai ya rufe ido, a ransa yace “shikenan, daman can Taiwo tayi masu gorin arziki, toh yanzu Baba Barau cewa zai yi shi da kansa yayi musu, amma dai ba’a kyauta masa ba…”. Prince yana cikin wannan tashin hankalin sai ya ji Mal. Yunus ya ce, “sun gode”, ya kara da cewa ayiwa Uban kasa godiya, Allah ya kara girma, ya saka da alkhairi”. Ya kuma kallon Baba Barau, sai yaga dai fuskarsa normal. Suka mike daganan aka tashi za’a shiga mota. Suna gaba sun fito kenan kamar ance ya kalli gaban sa, sai ya hango Aisha da wasu ‘yammata biyu suna dawowa. Cak! Hamma ya tsaya ya dan kalle ta, duk da hijab ne jikin ta amman abinka da farar fata lallen nan ya fito, yatsun nan sunyi jajawur kamar jini, ita ashe tunda taji muryar sa ta fice ta tafi gidansu, tace taje dauko wasu kaya. Shine Furairah matar Baba Barau tayi waya tace ace Aisha ta dawo bakin sun tafi. Tsayawa sallama da mutane yasa har suka dawo suka cimmasu a kofar gida. Ba wanda ya lura ita yake kallo, don tana daga nesa. Amman Prince ya ganta, itama kuma ta ganshi. Da kyar ya shige mota dai suka wuce Hamma yana shiga mota yace ma Kawunsa Abdulmajeed bazai yarda a qara saka shi wakilci ba, Uncle Abdulmajeed da Sarkin dogarai suka yi ta dariya. Da suka koma gida Prince ya kwabe Rawanin a falon Oumana ya shige nasa dakin dake sassanta yayi wanka ya kwanta. Zuciyar sa na hasko masa Aisha. Shi a idonsa kamar ma kiba yaga ta kara. Yace a ransa wato yarinyar nan babu ma abin da ya shalle ta dani, gashi nan tana ta shan lalle tana yawo a unguwa, shi kadai ake yi wa boyon ta. Takaici hana shi hutawar da yayi niyya. Yadda tayi kyau dinnan haka nan take ta yawo a cikin unguwa da gari kowa na kallon lalle ya masa kyau kowanne gardi yana kyasawa a ransa. Ai sai ya mike ya saka jallabiya ya wuce parlon Nani Oummana. Nan ya samu Nenne da Oummana sun idar da isha kenan. Tace “yaya dai Hamman su? Ko a kawo fura? Na ga ko abinci baka ci ba. Yace “Oummana yaushe zaku gidansu Aisha ne?” ta ce “ba ance sai gobe ba yau biki suke tayi?” Yace “ai na ganta tayi lalle sai yawo take a gari kowa na kallonta”. Nani da Nenne suka hada baki suka ce “kayi hakuri, gobe sai aje, in sha Allah. Amman kar ka fada masu za’a zo”. Washegari sauran yan yinin biki duk suka watse. Kafin la’asar gidan ya zama ba kowa sai ‘yan tsirarun mutane. Nenne ma ta kira Umman Siddiqah suka gaisa amman bata ce mata tazo Gombe ba. Tayi masu Allah ya sanya alkhairi a uren Maryam, suka gaisa da matar Baba Barau ma. Nan tace “anata yinin biki” Furairah tace “ai tun jiya suka kai amarya. Yau can gidan ta zasu yi yini, nan dai an gama komi. Nenne tayi masu fatan alkhairi sukayi sallama. Nan take ce ma Oummana ga yadda sukayi da Haj. Zainab da matar wan Baban na Aisha. Suka ce toh a bari zuwa bayan isha tunda Uban kasa yace dashi za’a je. Da aka yi magriba, Hamma ya kira Mal. Yunus suka gaisa, yace “ya gajiyar jiya?” Yace “ai baba akwai ta, saida nayi ciwon kai na rawanin nan, ai nace baza’a qara wakilta ni komai ba” Mal. Yunus yai dariya yace “ayi haka kuwa Abdulrashid?” Yayi murmushi. yace “baba kana gida ne?” Yace “eh, ina gida amman yanzu zani gidan Yaya Barau yace in zo”. Prince yace “toh shikenan Baba a dawo lafiya”. Ana idar da sallahr isha Uban kasa yayi badda kama dashi da Dade a mota daya da sarkin dogarai sai driver Malam Buhari. Nenne da da Hamma da Uncle Abdulmajid mota daya suma suka shiga sa Jeka da Fari. Gabadaya Abdulrasheed ya bade su da sassanyar kamshin turarensa Boss Intense. Yau dai jallabiya ce jikinsa coffee, da hula irin ta saudi dinnan. Ya saka slippers din ‘LV’ da ‘counter’ haka a hannun sa. Sai ya fito yaro sosai, yau kamar ba shine basaraken jiya ba. Shi yayi sallama gidan Baba Barau. Ai kuwa Auwal ya fito ya ganshi, ya shiga ya fadawa Baba Barau. Baba Barau yace “kai wannan yaro ya cika naci. In ba bashi yarinyar nan nayi ba cinye ni zaiyi, haba!” Auwal ya rike dariyar sa shi da Malam Yunus. Yace “amman yau sai naci masa kan wannan naci da yake yi min, je ka shigo dashi”. Baba Barau yana zaune ya bata fuska, yana jiran shigowar Prince, sai ko gashi nan ya ga ya shigo, sai ga Uncle Abdulmajid ma, yace “ah ah, kai ya sake dauko…” kafin ya kai aya sai ganin Uban kasa yayi da Nenne. Yace “la’ila ha illahu…” suka tashi su dukkansu, yace “dan Allah ku zauna. Ai yau ba maganar sarauta, biko nazo wa Da na wurin Baba Barau, ayi mana afuwa”. Baba Barau kamar ya nitse, kunya duk ta kama shi, wato gabadaya kowa kallon bala’e’e yake masa. Yunusa ya zame kansa ya barsa da kunya, yace “Allah ya taimake ka”. Suka zauna dukkansu aka gaisa, Mal. Yunus yace Auwalu yaje ya dauko Umman Aisha. Auwalu ya tashi ya tafi, sai matar Baba Barau ma ta shigo suka gaisa, suna ta jinjina saukin kai na wannan sarki, da kuma irin son da suke ma Aisha da Kehinde. Umma tazo, akai rungume-rungume ita da Nenne, tace “baki ce min kinzo ba dazu da mukayi waya”, Nenne tace ai tun jiya muka zo, da naji ana biki nace sai kun gama. Nan Uban kasa ya basu hakuri yace ayi wa Prince uzuri. Yace kuma yara ne ka haife su baka haifi halin su ba, amman tun ba’a je ko’ina ba itama tayi dana sani, gashi da ita suka zo. Taiwo ta basu hakuri, tace sharrin shedan ne ayi hakuri. Nan dai akayi sulhu, Aisha ma tace ta haqura. Zuciyar Hamma wasai yau. Mutuniyar dai ko kallon sa batayi ba. Saida aka gama Baba Barau yace “toh Aisha dai an siya mata jamb form, zata yi anan Gombe sati mai zuwa”. Nenne tace “ba komai, tayi abinta a nitse, bayan jamb din sai ta koma”. Kehinde dai yayi shiru. Sai Mal. Yunus ne yace Aisha ko zaki hakura kiyi a can, dan nasan Abdulrashid kamar sati biyun da aka debar masa zai kare cikın satin nan mai zuwa”. Nan Siddiqah tayi maza tace “ah ah Malam don Allah, inaso nayi, dan in samu cigaba da karatu na”. Nenne ma tabi bayanta. Baba Barau ya kallo Hamma, sai ya bashi tausayi, yace “kuyi shawara dai”. Koda Hamma ya kalle ta yaga tana wani cin magani yau shiru bai ce komi ba. A haka aka gama hirar. Baba Barau yace sunga sakon jiya an gode. Uban kasa yace ai diyar shi ce, an zama daya yanzu. Akayi ta hira ta dattaku kafin akayi sallama, duk suka shige motocinsu suka koma. Kowa tashi zuciyar fessssss. Aisha ta dauka Hamma zai tsaya ya lallashi ta sai shiru taji ya ware tareda iyayensa. Prince ya dan ji haushin yadda Aisha ta kafe ita sam sai tayi jamb zata koma. Shi kuma yasan dole ya koma Alhamis sabida Argentina zai fara tsayawa, akwai abinda dole zai dauka ya manta gidan su, inyaso Friday ya wuce Qatar ya dan huta, Monday ya koma aiki. Yanzu Aisha naso ta jiqa masa aiki. shi kuma (he wouldn’t beg….) don ya ma lura har wani kiba tayi ta kara haske, ba abin da ya dame ta…. Prince ya shiga damuwa, kada fa yarinyar nan ita (nothing has changed in her feelings towards him, shin shi kadai ke rawar sa da tsalle or what….? Ire-iren tunanin da yayi tayi kenan yau, sai ji yayu ana kiran assalatu. Yayi sallah ya godewa Allah, kuma ya rokar musu dukkan alkhairinSa. Da safe sai wajen 11:30 ya tashi. Yayi wanka ya sa kananan kaya ya shigo falon Oummana, ya gaishe su ita da Nenne, sai Taiwo dake zaune itama sun gaisa. Oummana na tsokanar sa wai daga sulhu sai yau ya qara zama yaro. Prince yayi dariya kawai yace “ai Oummana Aishan tace ita sai tayi jamb zata koma don neman magana. Su Nenne kuma sun bi bayanta ni kamar bani da mai bin bayana sai Babanta”. Nani Oummana tace “ai jan aji ake maka, ka san Indo Aisha ba daga nan ba”. Hamma ya girgiza kai yace “ai na shaida. Ayi jarrabawa lafiya.” Tace kai dai yau ka shirya kaje zance, daga nan ka gwada sa’ar ka, yace “uhm….”. Aisha ana can gida, tun jiya dama da suka tafi iyayenta suka sake yi mata nasiha ta zaman aure suka ce kuma ta gode Allah ya bata surukai na kwarai da mijin da yake matukar son ta. Dan an gwada shi ta ko’ina kuma yaci gwajin. “Duk wasu experiments da suka dora jikan Akanni bai fadi ko daya ba!”. Dan haka suka ce ta kawar da maganar Taiwo daga ranta ta fuskanci aurenta da mijinta da iyayen mijinta. Ta kyautata musu ta kuma rike su da kyau. Baba Barau yace “tunda naga ya matsa ma Indo ko zaki hakura ki bar jamb din ne? Ban ga amfaninta ba tunda kasar zaku bari fa.” Tace “Baba gara inyi, ko ba komi dole zan koma makaranta, ina so in cigaba”. Baba Barau yace “toh bakomi”. Addar Kumo tace “gara dai ki kara satin kema, sai ayi miki shirin amarya, kamar yadda akayi ma ‘yar uwarki Maryam. Yanzu ne za mu kai diya, dan wancan kaiwar daman dai yin sa kawai akayi”. Ummanta tace “nima zanfi son haka”. Aka ce “toh shikenan. Allah ya masu albarka”. Toh dazu bayan azhar tana tsakar gida sai ga Baban ta ya shigo yace Hamma ya kira shi yace zai zo anjima ya musu sallama sabida gobe daga Litinin ze wuce Lagos, jibi zai tafi Argentina. Aisha tace “toh” tayi ciki. Ta ma rasa me take ji. She is happy, kuma har ranta abin da ya faru ya wuce, amma kuma sai tana jin haushin Hamma yace zai tafi. Wato bai ma damu ba, da tace baza ta bishi ba. Hmmm! Da Haseena ce kila kuka zai yi tayi…mtsw….. Satin nan da tayi a gida, quite sure tasan Hamma bashi da laifi, amman kawai dukansu taji sun bata haushi daga Taiwo din har shi. But daga baya tana dan missing dinshi. Amman jiya yadda taji Baba Barau yana bata labarin nacin da yayi tayi akanta, ya dawo Gombe ma gabadaya duk sai ta ji tausayin shi da so me girma. (She always want to be loved) sosai irin haka, toh gashi itama dai kamar Prince ya fara sonta. Amman wannan cewa da yayi zai koma be matsa su tafi tare ba, ya bata haushi. Ta sake kwana a gidan Baba Barau dai, ta dawo gidansu tayi kwance har akai magrib. Daman tun yau da safe aka fara mata gyaran jiki itama. Ummanta tasa an mata halawa dazu dasu dilka, tace baza a qara ba. Toh yanzu ana ida magrib Umma ta miqa mata diye tace taje ta durje jikinta dashi ta hada mata lalle da khumra kuma tace ta dauraye jikin dashi. Aisha tace “toh”. Ta shige toilet tayi ta gama ta fito. gaba daya dakin har waje kamshi ke tashi. Tace “Umma nidai mura zanyi in kullum zan wannan wankan”. Haj Zainab bata tanka ta ba dai, tace “yi ki shirya ko Hamma yau zai zo zance” tace “kai Umma, ina tsoho ina zance” Umma tace Patel kenan, ana so ana kaiwa kasuwa. Ni je ki shirya kyaji da gulmar ki”. Ta wuce ta barta a wurin. She is so nervous, a haka ta tashi tai sallahr isha. sai ta dauki kulaccen da Ummanta ta bata ta shafa, da tasa undies dinta black ta ma rasa kayan da zata sa, akwai wata abaya da Ummanta tazo mata dashi daga Hajj bata taba sakata ba daman suka tafi Lagos da Nenne. Ita ta dauka tasa, white and silver haka kuma cif-cif jikinta. Sai ya kwanta lubb! A jikinta, kugun nan nata ya fito masha Allah. Tace ta san dai tayi kiba saboda abayan kamar yanaso ya matse ta, karin kibar nata har haka ne? data gama ta dauko ‘yan hannun gold din da Nenne ta bata na Makkah ta saka su, tasa ‘yan kananan ‘yan kunne na gold suma ba sarka. Tayi parking kitson ta tayi gammo da gashi. Sai ta dau gyalen abayar ta yafa. Tana zaune taji ana gaisuwa a tsakar gida, gaban ta ya fadi…. Shi kuma Prince tun da akai magrib ya dau wanka. Ya dai ma kasa cin abinci. Yayi sallah yana zaune da jallabiya har akayi isha, sannan ya shigo cikin sassan Oummana, Nenne tace yazo yaci abinci yace a koshe yake. Bari ya shirya zashi gidansu Aisha zai masu sallama tace “toh” ya shiga ciki ya dauko kananan kaya sai kuma ya mayar, yace gidan surukai ne. Sai ya dauko wata baqar (voile lace) na maza. tana da shara shara haka sai daukan ido kyallin ta yake. Wando da riga irin iya cinya dinnan cip jikin sa dinkin. Sai karamin hannu haka ba dogo ba iya gwiwar hannu. Haka Hamma ya shirya tsab, ya dauko hular sa Tonak ya saka baka itama, da design din silver a jikinta, ya zuba turaren ‘Tomford Oudwood’ ya kuma dauko ‘Francis Kurkdjian Baccarat Rouge’ ya fesa. Wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikin Prince ya dauko ‘black hermes’ ya saka ya daura ‘rolex’ dinsa ya fito. Ai yana fitowa sai Taiwo tasa guda har ma dai yaji kunya, su Nenne duk suka juyo, yace “meye haka Taiwo?”, tace ko dai mu dauko mayafi mu bika naga daukar amarya zaka yau” yace “kash!” Ya wuce. Nenne da tayi murmushi dan tun bai fito ba suke jin kamshi. Lallai Aisha Siddiqa ta ciri tuta. yau Kehinde ke ta wannan rawar kafar haka zai je zance. “Alhamdulillah” Nenne ta gode ma Allah. Yace musu se ya dawo ya fita. ya dau mallam Buhari suka wuce. Prince ya yi sallama gidan su Aisha, Mallam Yunus yana tsakar gida suna zaune da Umma, ya amsa ya ce “shigo mana Abdulrashid”. Ya shigo ya gaishe su. Sun burge shi. Domin sun shimfida katuwar dadduma ga abinci nan a gefe, ga sallayar Umman Aisha da hijabinta akai. Nan tayi sallah kenan. Tana gefen Mal. Yunus suna hira tana dama fura. Shikuma ya kishingida haka kan tuntu. They look so simple and very in love. Masha Allah kawai yace a ransa, ya karaso suka gaisa yace Oummana na gaishe su. Mal. Yunus yace suna amsawa ina Dade? Yace ai ya koma Lagos tun dazu. su Nenne suma jirgin safe zasu bi gobe. Suka ce “toh Allah ya kai su lafiya”. Akayi shiru, Umma tace “shiga palo Hammansu, bari in kira Petel”. “Petel!!!!” Umma ta kwada mata kira, ta amsa daga cikin dakinta tace “na’am” tace ga “Hammanku yazo, ki debo ruwa da abinci ki kai masa. Hammansu akul kayi min fulako” yayi dariya yace “Umma ai daga gida nake, furar kawai zan sha”. Tace “toh bari ta kawo maka” yace “toh”. Ta nuna masa kofar falo ya shiga, ya zauna yana jiran gimbiyar tasa. Can sai gata ta fito, Ummanta tace “dau fura da yamri a fridge da kindirmo duk ki tafi dashi, wanda yafi so sai ki dama masa”. Tace “toh Umma”. Umma duk sai ta ga wani kyau diyarta yau ta tatso, tace “uhm lallai… Aisha dai an girma, masha Allah”. Tayi sallama ta shigo, fuskar dai a gimtse, da dan nisa tsakanin falon Baban nata da cikin gida. Prince ya amsa mata, ta shigo, ya daga ido yana kallon ta. Tashi yayi don ya taya ta da kayan hannunta amman sai ya kasa. Wani kamshi takeyi da ya rasa wane iri ne tun shigowarta, ta qara cika, ga wata abaya nan ta saka ta kwanta jikin ta, gabadaya surarta ta fito waje…. shi yarinyar nan take so ta jiqawa aiki a gaban iyayen ta. Tana shigowa tayi sallama taji ya amsa tunda ta fito tsakar gida take jin wani irin kamshi yanzu da ta shigo kamar tana aljanna…. Prince ya amsa mata ta dan daga kai ta kalle shi, “hasbunallah…” tace a ranta, my husband, yayi kyau. abinki da fari, yasa bakaken kaya, duk ya bar qasumba se ya sake zama yaro dan shekaru 35. Ta karaso, kamshi cool ya cika ko ina… ta ajiye furar da tray din a table din kusa dashi, sannan ta zauna, duk yana binta da ido. Ta zauna kan carpet tace “Hamma ina yini?” Yace “lafiya lau” da kyar… tace “ya su Oummana da Nenne da Maman Kiki?” Yace “they are all fine, how are you?” Tace “Am fine, Alhamdulillah yace “hmm….” don gabadaya kokawa yake da kansa. Domin data duka yanzu don ajje tray dinnan a gabansa kamar ya kamo ta. Tayi kyau, ga lallen nan ashe har kafa aka yi shi. Wadannan siraran abin hannun gold din data saka sai ya kara masu kyau. Ga wani kamshi da take da ya rasa menene. Kai shi kamar ma har canza kala Siddiqah tayi. Ya kafe ta da ido, yana yi wa kansa fada, shi fa ba yaro bane, meye haka yake abu kamar sabon balaga? Zuciyar sa ta ce to meye maraba? Tunda dai tuzurun saurayi ne yayi sa’ar samun sweet 16? Sai duk sukayi shiru, tace a hankali “Hamma a dama furar? Ko yamri za a saka?” Yace “furar dai” tace “to” ta tashi ta dauko sai taga bata dauko bowl ba, sai ta mike zuwa dining din palon, ta duka haka tana neman bowl din tangaran na dama fura, gabadaya shi kuma ya kafe ta da ido, dukawar nan da Aisha tayi kuwa yaga Ali, Ali ya gan sa. Se yaji kamar yasa ihu… Yace waye ya koya ma Aisha seduction haka… Omooo this girl wan kill me…!”. Ta dauko ta qaraso tana zama sai taji tashin motar Baban ta, tace “ah Abba fita yayi? Ina zuwa” sai ta leka waje ta gan shi tace “Abba ina zuwa?” Yace Baba Barau ne ya kira ni” tace “toh a gaishe su, sai ka dawo” (ta dawo like a child), ta zauna tasa fura a gaba tana ta dama masa, duk sun kasa magana. Ta gama zata juye a bowl, yace shi a qwarya zai sha, da fulatanci ya fada, sai tace “toh”. Ta miko masa, sai ya nuna table din gefen sa yace a can zata sa, ta taso zata ajje ya cire hular sa yasa gefe. Ai tana ajje wa yana kama qugun ta, abinki da abaya silky nan ya jiyo jigida fal qugun, ga wata ‘curve besin’ ya fara bi da hannu bayan ya zaunar da ita cinyar sa, Prince yace murya na shaqewa. “Siddiqqqqqaaaaaa, nazo bada haquri ne, kiyi haquri kinji, it will never happen again in sha Allah. Sauri kikai… na gaggawa, da ba sai an kai haka bama zaki ga action da zan dauka”. Tayi shiru, tace “ya wuce Hamma”. Yace “ai ba wanda zai taba ki Aisha inyi shiru, I am not like that. Iyaye sun wuce gaban wasa. So ko ba ke ba, ko wani naga an tabawa iyayen sa, I will make a stop to it, balle ke matata. So again, I am sorry. Tace “wallahi Hamma ya wuce”. Sam Aisha bata da riko. He hugged her, yace “Aisha i missed u so much”. Siddiqah tayi wani lup ta kwanta a jikin shi tana jin kamshi da shauqi, yace “you didn’t miss me ko? Ai naga har wata kiba kikayi, irin ko a jikin ki, ni ko har rama nayi. I don’t know how much I fell for u, sai a week dinnan”, Siddiqah ta daga kai ta kalle shi, yace “yes, I fell soooo hard! Amman ke ina jin har yanzu ni ‘father figure’ ne ko?” Tayi murmushi tace “ashe mita ce da kai Hamma? Tun yaushe akayi maganar nan?” Yace “toh kallo na fa kikayi cikin idona kika ce mun kin gama auren….”. Sai kawai ta rufe ido. Yace “no matter how I am feeling ba abinda zai sa na taba furta haka….” Ta ce “ai fushi nayi”, yace “toh ki daina magana in kikai fushi kin ji Ayshah, sabida kar ki fadi abinda daga baya zaki zo kina nadama. Nan gaba (try and rationalise) kin ji?” Ta ce “toh Hamm…. kan ta karasa sai jin bakin shi tayi cikin nata tare da wata ajiyar zuciya data kwace masa. He kissed her good, se ji yayi ludayin fura dake hannun ta ya fadi kasa, qarar yasa ya kyaleta, don yasan dai a gida suke. Aisha ta sulale daga cinyar sa, ta dau ludayin tayi hanyar dining zata ajiye, har tayi rabin tafiya taji mutum a bayan ta, kan ta juyo ya rungumota ta baya, ya hada ta da bangon dining din a hankali, he is completely a manne da bayanta, he can thoroughly feel her on his body, hannun sa kan flat tummy dinta tace “Hamma…” yace “shhhh…” tace “Umma..” yace “I know…”. Ya sake matse ta yana kissin kasan wuyan ta…a ta a tare suka saki numfashi mai wahala. Al’amarin na Hamma Abdulrasheed (Prince) yafi karfin birona ya rubuta shi, can dai naji yace “Ya ilahi…”. Gaba daya wata kasala Hamma ya saukar mata, basu taba tsintar kansu a irin wannan yanayin ba sai yau… tana cikin wannan halin taji Hamma ya…… bata san sanda tace “Babyyyyy!” Ai babyn nan da Siddiqah tace sai ya kuma kwance masa notika. Ya juyo da ita ta kalle shi ya kalle ta… ba wanda yake hayyacin sa a cikinsu, he started kissing her lips again. French kiss. Duk dan karatun da ya fara koya mata ya zubar yau, gabadaya ya zuba sababbi. Dan Baby brain din nata ya juye shi tassssss…..a kwarya. Ba abinda Prince yake so irin yau ya angwance, gabadaya sha’awar da ya dakile sun zubo, ten folds yau! Siddiqah ita ta fara dawowa tunanin ta, na kada fa Abbanta ya dawo tayi maza ta kwace bakin ta… Hamma yayi lamooo a wuyan ta, ya tsaya a haka yana maida numfashi yana manne da ita. Bai san sanda ajiyar zuciya ta kwace masa ba sosai…. ita kuwa kunya kamar ta nitse. Sai da duk suka nutsu ma kunyar ta sauko mata. “Siddiqah u will not kill me…” ya dago yana kallon ta. Da kyar taji me yace, gabadaya muryar sa ta dashe, ita dai ta rufe fuska da hannun ta… Hamma ya qare mata kallo, ya sake gashin ta daya rike dama dankwalin ya dade da zamewa a kasa, ya duka ya dauko mata dankwalin yace “ouchhhh….” tace “Hamma yaya?” Ta tsugunna itama yace “it’s u….” se gani tayi Hamma…. tayi maza ta dauke kai, ta bar jikinsa ta yafa gyalenta, ta koma ta zauna kan kujera kamar ba ita ta gama cewa “babbyyyyy” ba dazu. Prince ya tsaya ta gyara sannan ya qaraso inda take har wani dingishi taga yana yi, ita dai ta daina kallon sa… he sat close to her, yace “babyyyy!” tayi smiling tace “in miko ma furar?” Yace “ai kin bani fura har da nono” tace “innalillahi….” duk ta daburce. Zata mike Hamma ya janyo ta yana dariya. A ransa yana son kunyar nan tata, amman ya san se ya mayar da ita mara kunyar kwarai. The Prince yayi wani ‘evil smile’. Yace “this baby has no idea what she is in for….. Tace “menene kake dariyar mugunta?” Yace “baby, tausayinki nake ji, you have no idea what is in store for u…. hmmm….”. Gabadaya a lokacin fuskar sa ta canza, ya dawo “Yoruba Demon” dinsa yana mata wani arnen kallo, ita ji tai ma kamar period ta fara a lokacin, sai ga horn din Baban ta ya dawo. Aisha ta zabura ta dauki gyalenta, ta mikawa Hamma hularsa, duk ta rude na rashin gaskiya, shi dai yana kallonta yana murmushi tace “don Allah Hamma ka sha furar nan” ya karba yana sha yana kallonta, sai raba ido take kamar munafuka” tace “Abba ya ce zaka Argentina, ba Qatar kace ba? Ya kalle ta, ya ajje furar bayan ya gama sha, ya goge baki. Yace “kizo mu tafi tare gobe… I need you Babyyyy, kin dai ji irin yadda… it wants u so baaaaddddd…”. Ya ja baaad din, she felt it har ranta, a ranta tace “yanzu Hamma Abdul ne ke abubuwan nan Innalillahi”. Bata sani ba ashe a fili ta fada, yace “baki ga komi ba, Hamma ya samu abinda yake so… life begins at forty!” Siddiqah tayi murmushi. Yace mu tafi din?” Tace “Hamma wallahi inaso nayi jamb din, kuma jiya ma bayan kun tafi Ummana tana ta murna zan kara one week kan mu tafi, gashi kace ka kara hutu. Allah kadai yasan sai yaushe zamu dawo. Kayi hakuri ina gamawa ko Sunday ne na yarda mu tafi”. Prince ya numfasa, ya ce “it’s okay baby…. bakomi. Amman I have to go on Thursday nayi mantuwa a Argentina, its vital kuma. Sai in hada abinda zan dauka Friday na wuce Qatar don in dan huta kafin Monday din, in yaso Monday din sai ki taho”. Ke dai kiyi min addu’a kar in mutu before Monday”. Siddiqah ta bata rai tace “haba Hamma!” Yace “baby you wouln’t understand” ya riko hannunta ya kai bakin sa yayi kissin. Daga nan Hamma ya tashi yace “bari in tafi” tace “toh” suka fito a jere, Siddiqah ta ga dai ya tsaya ya sake kimtsawa. Suka fito tana gaba yana binta a baya har dardumar su Ummanta, ba kowa. Ta leqa dakin Umma tace “Umma ga Hamma zai tafi” Umman ta fito sukayi sallama, Haj. Zainab tace “Baban naku ya shiga wanka”. Yayi masu sai da safe. Ta raka shi har kofar gida tana tafiya lankai-lankai, tana kuma dama masa lissafi. Tace “da safe zaku wuce da Nenne?”. Yace “ai ni sai nazo na sallami amarya ta, so afternoon flight zan bi ko evening”. Tace okay. toh se da safe Hamma”. Yace “ban hannun ki, ta bashi, yasa hannu a aljihunsa ya dauko waya ya saka mata ciki, yace “I will call u tonight, don’t sleep”, tace “okay”, yasa hannu ya dan mata side hug da kiss, ya kalle ta yace “I love you so much Siddiqah. Sai na kira”, tace “okay”. Har ya fita ya kusa shiga mota tace “love u too..” a hankali. Shi kuma Hamma da shegen ji, yace “Ayshah what did u say?” tayi cikin gidansu a guje. Zuciyar ta yau sai “lahaula wala quwatta illa billah….” don farin ciki ne ziryan a ciki. Idan Prince ya tuno abubuwan da suka faru yau sai murmushi ya dawo, ba kowa a Falon Oummana shima bai neme su ba ya yi cikin dakinsa ya fada gadon sa ya kwanta ‘Re-play’ kawai yake na inda tace ‘babyyyyy!” And kissing him back, he don’t know why intensity din yau is different, ko don tana gidansu ne ya san he can’t have her… makes him want her more… Ya ji zai daga ma kansa hankali yayi toilet ya saki cold shower akansa… yace yanzu with what he is feeling, ta ya za’ai satin nan? Bayan ya fito yayi sallah kenan sai ga wayar Kiki. Suka gaisa, tana bashi hakuri kamar zata yi kuka. Antinta Firdausi told her all what happened, yace mata ai ya wuce yanzu ma ya dawo daga wurin Aysha din. Kiki tace tana ta kiranta off, yace zai tura mata sabuwar lambarta, Kiki tace “so you went to do ZANCE!”. Tayi ta yi masa shakiyanci son ranta. Da suka gama hirar su da Kiki, ya kira mutuniyar a waya, sau biyu bata dauka ba sai a na ukun. Siddiqah tace “Hamma!” shikuma yace “babyn Hamma… ba nace kar kiyi bacci ba?” Tace “bansan nayi ba. Gajiya ce”. Hamma yace “me akayi har kika gaji… don’t be a lazy wife ooo, wallahi to gym zan saka ki kina isowa Qatar”. Siddiqah tayi dariya tace “hidimar biki fa… ka manta biki muka gama?” Yace “oh! Na dauka Hamma ne ya miki nauyi”. Siddiqah ta zaro ido tace “good night!” Kit! Ta kashe. Sukayi bacci mai dadi da mafarkan juna masu dadi yau. Da safe su Nenne suka wuce. Shi kuma jirgin sa se karfe shidda na yamma. Yana yin sallar la’asar ya sallami Oummana da Uban kasa, yace daga nan zai biya wajen Aysha daga can ne zai wuce airport, gobe ne jirgin sa na Argentina da dare sha biyu na dare Uban kasa da Nani Oummana suka masa addu’a sukayi masu fatan alkhairi. Oummana tace lallai yace ma Aisha tazo mata. yace “toh, na bata waya zata kira ki”. Yau dai Prince wankan kananan kaya akayi. Duk ya zama dan yaro karami. Da ya iso gidan Abba baya nan sai Umma. Suka gaisa, yace yana so yaje ya sallami Baba Barau. Umma ta ce Aisha ta raka shi. Nan ta saka hijabi Mal. Buhari ya kai su. Suka shiga suka gaishe shi. Hamma yace “anjima kadan ze tafi” Baba Barau yayi masu nasiha. Ya saka masu albarka, yace in ya isa yayi settling ya kira shi sai a shirya mata tafiya ko bayan sati ne, sabida ya kimtsa. Da sauri Prince yace “ai Monday zata taho, Baba ba abin da za a kimtsa”. Baba Barau yayi dariya yayi masu sallama. Suka fito suka dawo gidan su Aisha, a parlon Abban ta. karfe hudu lokacin, 5 ze tafi airport jirgin 6:15 ne. Nan ya lalace a wurin ta, ta kawo masa abinci ya dan tsakura yana hira yana abubuwansa. Itama dai yau Siddiqah sakar masa jiki tayi yana kissing dinta tana mayar masa, abin nasu wane jiya. Ga Abba baya nan so free suke jinsu. Ita Ummanta ma bacci ne ya dauke ta. ta saba bacci tsakanin azhar da la’asar. To dai romance kawai ake a falon nan, can Aysha tace washhhhhhh can kaji Kehinde yana kiran babyyyy….. Malam Buhari daga waje ya duba agogo, yace shikadai, “yaran zamani, sai jirgin ya tashi ya barshi”. Mukuma nida team of editorial board dina muka ce “ko ina girman Prince Kehinde?” Domin gabadaya Prince ya zama yaro mai tashen balaga, a nan duk ya lalace, sai ji yai wayarsa na kara. Mal. Buhari na tuna masa jirgi bazai jira shi ba. Nan dai ya dawo hankalin sa ya nutsu ya dauka. A ladabce Malam Buhari yace “Yallabai, na ga biyar da rabi ne, ba shida bane tashin jirgin? Ka san akwai dan tafiya”. Yace “ina zuwa”, a gajarce yayi maza ya kalli agogon sa. 5:40 yace “Baby kinsa nayi missing flight dina” tace “ba ruwana” ya rungumo ta, ya dau wayar sa yayi dialling wata number, suka gaisa, yace “yanzu zan bar Je ka da fari, zan samu jirgin?” yace “to ba komai, a yankar min wani ticket na morning flight gobe”. Aisha ta zare ido tana kallon sa…. ta tashi ta zauna, yana kallon ta lovingly, tace “Hamma da gaske ka rasa jirgin?” Yace “cewa yayi saidai inyi gudu, ni kuma ban son hanzari shine nace ya yanko min na gobe da safe. Bari in tashi in tafi ina kallon ki haka dinnan bazan iya barin gidan nan ba”. Aisha ta mike, shima Prince haka. Har sunzo kofar gidan Prince yace “ina fa da gida a garin nan, ko muje ki gani?” Yana mata wani kallo ta ce “noooo!” tayi cikin gida ta barshi. Har ta shiga gida sai ga message din sa, yace “anjima zai zo ya kai ta fadar Gombe, Nani Oummana tana son ganin ta”. tace “toh”. Sai ga wayar Mal. Yunus, yace “Abdulrashid an tafi?” Yace “wallahi Abba nayi missing flight dinne, sai da safe. Karfe 6 ne amma nace se 5 zan tafi airport, toh kuma hold up” Abba yace “assha. Allah yasa haka shi yafi alkhairi” Hamma yace “amin”. Yace. “Toh sai ka kaita wajen Oummana din da kan ka kawai. Daman nace zan kai ta anjima”. Prince ya ce “toh shikenan Baba”. Suna tafe a hanyar zuwa fadar Gombe, Malam Buhari na gulmar Prince a ransa. Yana cewa wato jinkirin aure ga namiji ba sauki gareshi ba, ranar duk da ya samu mata ko yaya take komai yarintarta sai Allah, domin kamun kazar kuku mace take musu, dubi dai yadda 'yar yarinya ficiciya ta tashi kan Yallabai Abdulrasheed, yana can ya like mata ya lalace har jirgi ya tashi ya barshi. Yawan shekarun nan nasa, matsayi da girman sarautarsa (mulkinsa na gado gaba da baya), da 'fame' din nasa na Polo (as African Polo Legend) duk an tashi kansu cikin dan lokaci ya dawo yaro daidai ita. Domin tareda shi Malam Buhari din Nenne tayi ta zaryar nemawa Prince auren Aisha. Bata Lagos bata Gombe, har saida ta tabbatar sun daura auren sun daukota Ilorin. Nani Oummana ma sai daga ido tayi taga Prince ya dawo. Bayan sun riga sunyi sallama ta karshe cewa daga can zai wuce airport ya tashi gida Lagos. Ba suyi dashi zai dawo ta nan ba. Oummana tace "Yaya haka Hammansu? Mantuwa kayi?" Ya zauna yana cewa "to ya za'ayi? Jirgin ya tashi ya barni Oummana". Wani miskilin murmushi Oummana tayi masa, tace "garin yaya toh? Kana can kana soyayya ko?" Hamma ya dukar da kai yana ‘yar dariya yace, "kusan haka, ai bakya karya Oummana" Oummana ta sake yin murmushi irin nata, ita tasan watarana za'ayi haka. Domin da alama AISHA INDO SIDDIQAH! Ta shigo rayuwar Yarima da zafinta. Zata murza kambu son ranta, ranar duk da Prince ya shiga komarta. Yarinyar nada tarin baiwa da kullum take tuna mata da auren Nenne da Dade. Kusan tace tarihi ke maimaita kansa akan Abdulrasheed Dan Idris dan Abdulrasheed Akanni. Tana fatan wannan soyayya da Prince yake yiwa Siddiqah ta dore musu har tsufansu, su zama (typical replica) na Sappa da Idrisu. Ganin Oummana bata ce masa komai ba sai murmushi take zabgawa yace cikin basarwa da hadiye kunyar da yaji. "Amma gobe in Sha Allah bazan yi wasa ba Oummana, morning flight dani zai tashi karfe 6am, ko sallama bazan je mata ba". Oummana me zata yi ba dariya ba, tace "to ni me kaji nace ne? Ko nace kayi laifi ne? Haka akeso abubuwa suyi daidai. Saika koma ka daukota ka kawomin ita yau da kanka. Daman nafi so in ganku a gabana tare". Yace "In sha Allahu Oummana, Baba Yunus ma da kansa yace yace inje in daukota in kawo miki, dama na gaya musu kinason ganinta. Da nayi sallahr Isha zan koma na taho miki da ita". Ya wuce zuwa dakinsa na sassan Oummana kai tsaye toilet ya fada don yin wanka, don yasan a yanayin da suka kasance da Aisha yau, bai yiwuwa yayi sallah yanzu bai yi wanka ba. Saida Umma ta tashi daga barci taga Siddiqa a zaune a gefenta, tace "har ya tafi?" Tace "eh Umma, gashi har jirgin Lagos da zai hau ya tashi ya barshi. Dole sai gobe zai tafi gida". Sannan cikin jin kunya ta gayawa Ummanta Hamma yace zai dawo su tafi wurin Oummana anjima, ta aikoshi tana son ganinta. Nan Haj Zainab ta hau tunanin me zata baiwa Aisha ta tafiwa da Oummana, karshe tunaninta ya tsaya a kan turarukan ‘Oud’ da ‘Sandaliyyah’ na jiki dana turaka data sayo a Saudiyyah. Su ta saka a kyakkyawar leda tace Aisha ta kaiwa Oummana tsaraba. Kafin sallahr Isha Siddiqah ta yi wanka ta kara shiryawa cikin wani tattausan cotton lace mai tsananin taushi da adon kananan duwarwatsu, kalarsa Orange ne da adon (milk color) furanni, tun lokacin hajjin bara Ummanta tazo mata dashi daga Jeddah, sannan tayi sallah Maghreb da Isha. Aisha ta dauko turarenta Fahrenheit ta feshe jikinta dashi. Kana iya jiyo sanyin kamshinsa tun daga dakinta har tsakar gidansu zuwa dakin Ummanta. Daidai lokacin Baba Yunus ya dawo, Siddiqah tayi masa sannu da zuwa ta karbi ledar hannunsa yace mata balangun Ayuba ne ta juye su ci ita da Umma shi sun ci shi da Baba Barau. Ya kuma ce ta shirya Hamma ya kira shi zai zo yanzu su wuce gun Oummana, Mallam Yunus ya gyara zamansa akan kujera yace "toh Indo nasan ba sai na maimaita miki ki kula da kanki ba, kuma ba sai na gaya miki ki zama ambassador din kanki da kanki ba a wurare irin wadannan. Waje ne da yake bukatar nutsuwa da kamewa wadanda bana jinki a kansu Siddiqah. Tunda gidansu mahaifiyar sa ne". Aisha tace "toh in sha Allah Baba". Daidai lokacin Sunusi ya shigo yace "wai mijin Aisha yazo daukarta, suna cikin mota". Siddiqah ta dauki gyalen data tanada wanda yayi matukar shiga da kayan jikinta ta yafa wato off white, nan ta dauki karamar 'hand bag' dinta tun tana gida take amfani da ita, ta dauki ledar sakon Oummana ta yiwa Umma sallama. Haj. Zainab tace, "to sai kun dawo. A gaida Nanin". Prince ya mika hannun damansa ya budewa Aisha kofa barin hagunsa ta shiga. Malam Buhari na kokarin fitowa don ya rufe ya hutasheshi. Shi da kansa ya rufe mata kofar. Saukin kan Prince yana kara masa kima mai yawa a idon dattijon direban. Ya koma ya zauna ya rufe kofa ya jasu a hankali suka bar Jeka da fari, zuwa babban titin da zai kaisu gidan Sarkin Gombe. Saida Prince ya san yadda yayi cikin dabara ya sanya tafin hannunshi cikin na Aisha. Ya sarkesu, sannan ya matsesu cikin nasa hannun. Taushin hannun kowannen su ya ratsa su. Suna tafe yana mata hira kasa-kasa amma ta kasa sakin jikinta dashi kamar dazu, don Ummanta ta jaddada mata ta kama kanta, ta rike kunyarta, don gidan su mahaifiyar shi zata je kuma zuwa na farko. Da yake duhun dare ya shigo ba kowa ya ankara da shigar su sassan Oummana ba. Suka sameta har lokacin akan dardumar sallahrta tun bayan data idar da sallahr Isha tana zaune tana lazimi bata tashi ba. Shigowarsu tasa ta shafa addu’ar da take yi, ta mike tana cewa "Jabbama da Indo Siddiqah, barka da zuwa, Indo Aisha". Aisha tayi kasa ta zube a gaban Oummana zata fara gaisheta cikin girmamawa, tsohuwar ta kamo hannunta ta mikar da ita tsaye, ta jata zuwa kan shimfidar fata irin ‘traditional rug’ dinnan da akeyi da fata wanda akanshi take zama a falon, da Tum-tum a kowanne gefe da gefe manya har guda hudu, Nani Oummana ta zaunar da ita a kusa da ita. Kasancewar Oummana bata zama akan kujera sai wannan shimfidar tata. Prince ne ya zauna a kan two seater, a gabansa akwai karamin centre table dauke da ‘tray’ shake da kayan marmari. Prince ya dauki apple guda daya jawur da ita yana yankawa da karamar wuka kaiwa bakinsa yana ci. Yana kallon Oummana ta rasa ina taka-saka -ina taka-aje da Siddiqah, kaunar da suke mata itada Nenne, ya tabbata daga Allah ne ta dalilin son da suke yi masa. Domin bayan Oummana ta zaunar da Siddiqah a kusa da ita, sawa tayi hadimanta suka cika gabanta da kayan motsa baki na alfarma, wanda ko tabawa da hannunta Siddiqah ta kasa yi, ji take kamar yau ta fara haduwa da Oummana. Daga bisani ta gaida Oummana da fulatanci, Oummana ta amsa ta kuma tanbayeta lafiyar su Ummanta da Babanta da iyalin Baba Barau. Siddiqah ta amsa duka, kanta a sunkuye, murya a ladabce. Anan Oummana tace maqasudin kiran nata dama don tayi mata nasiha ne. Nan tace Hamma ya basu wuri. Hamma yace "Nani abin harda kora?" Tace "ai zan kiraka ne inna gama da ita, akwai abinda ba sai ka ji ba". Prince ya shige dakinsa ya barsu. Oummana ta fara yiwa Aisha fada da nasiha kamar ita ta haifeta. Nasiha ce ta manya sannan mai shiga jikin yaro, inda tace wa Aisha. "Idan kana aure yana nufin ka girma. Abubuwa da yawa zasu iya faruwa a rayuwar auren mace, musamman da dangin miji, to idan irin haka ta faru ba komai ake fadawa iyaye ba Indo, sabida gudun bacin ransu. Sannan shi aure rai ne dashi. In zama bai kare ba mace da mijinta sai su dawo su shirya, su manta komai cikin dan lokaci, amman iyaye basa mantawa. Don haka toh a kiyaye irin haka anan gaba, kuma koda wani abu ya faru to Aysha kizo ki sameni ni Oummana ko Nennen ku, na tabbatar hukuncin da zamuyi wallahi Umman ki baza tayi ba. Kinji ko Indo? Sabida Allah shine shaidata, yadda nake jin Hammansu a raina haka nake son ki babu bambanci a wurina, kinji? Shiyasa nake so nan gaba ba fata ake ba abin Allah ya kiyaye, ko da wani abu irin haka ya faru toh dan Allah Aisha ki koyi magance shi tsakanin ki da mijin ki. Musamman irin wannan da ya faru da Taiwo, mijin ki na matukar son ki, har Taiwo ta isa tasa kice kin bar auren ki? Allah yayi maki albarka ya kawo muku yara masu albarka. Shi wannan da baya son sarautar nan tamu, wato ya gado ubansa, Allah yasa ya haifo min wanda zai so sarauta. A zuciyar Aisha tace "Amin". Sai lokacin ta gane Hamma baya falon ya basu wuri itada Oummana. Da ya tashi fitowa ba kayan da ya fita dasu ne a jikinsa ba, ya canza su zuwa kananan kaya farar shirt LV da bakin wandon Jeans. Yace "toh Oummana dare ya fara zan maidata" Oummana tace "Aisha nagode Allah ya kara albarka" nan Aisha ta mikawa Oummana sakon Ummanta. Ga Oummana da son Sandal da Oud. Nan tayi ta godiya,ta kuma sa aka miko mata babbar jakar data shiryawa Aisha tsarabar da zata tafi dashi gida. A hanyarsu ta dawowa ma Prince na makale da kafadun Aisha Malam Buhari na tuki, ya sassauta murya yace "Ayshah! Kin ce bazaki je gida na ki gani ba ko? Koda akwai abinda bai miki ba a canza don shine gidanki da ‘ya’yanmu anan Gombe". Da sauri Siddiqah tace "Don Allah Hamma Abdul a'ah, ba sai naje ba, zan gani next time". Hammah yace "ai shikenan. Kin dade baki je ba. Wanda ya jure yayi rainon Dan shillansa wajen shekara guda, ai jiran kwana bakwai bazai gagareshi ya fige abinsa ba". Da haka suka kawo kofar gidan su Siddiqah. Taimakon da Allah yayima Siddiqah ta fito nan da nan shine Malam Buhari dake cikin motar nan, wanda ya kure radio yana sauraron wata tsohuwar waqa ta Sani Aliyu Dandawo. Da Prince bazai barta hakannan ba sai ya kara cakudata. Duk da haka cike da damuwa Hammah ya rike hannunta yace. "Babyyyyy. I will miss you kin sani ko?" Siddiqah ta dube shi idanunta narai narai tace dashi cikin harshen yarbanci "I will Miss you more Hamma....". Ba zato taji ya kai hannunta ga bakinsa ya sumbata. Da kyar ta samu ta zare hannunta daga cikin nasa ta shige cikin gida ba ko waiwaye. Don gabadaya Hamma ya saka mata wata irin kasala (by just mere looking into his blurred eyes). Umma da Abba sun sha labarin Nani Oummana, irin kirkinta da karamcinta daga bakin Aisha. Ta fidda kayan da Oummana ta bata har da alkhyabba ta mata da manyan turamen super guda uku da manyan lesika uku. Ga bandir din filtex na Abban Aisha da Baba Barau. A ranar sai can dare Siddiqa ta bar dakin Ummanta zuwa nata dakin, sun raba dare suna hira don ji suke kamar gobe-gobe ne Petel zata tafi ba kwana shidda masu zuwa ba. Don Hamma ya tabbatar ma Abban Aisha in sun tafi zasu jima basu waiwayi gida ba, don hutun shekara ya kammala harda kari mai yawa. Wajejen karfe 12 na dare Siddiqah ta gama komai na shirin kwanciyar ta. Hammah ya kira ta, Siddiqah ta daga hatta muryarta ta canza don barci take ji sosai tace. "Hammah, baka kwanta ba?" Yace "na kasa barci ne Baby.... Ina missing furar kinnan da kindirmo..." Aisha ta rufe ido tana jin kunya kamar Hamma na kallonta, tana kuma tuna incident din na yau da ya kasa bacewa daga idanunta, feelings din kuma sababbi suka kasa barin ranta. Hamma yace "Baby you know what?" Ta girgiza kai kawai kamar Hamma na kallonta. Hamma yace "ban taba jin eagerness a rayuwata irinna ranar da zaki dawo min ba. I will be patiently waiting for you and your annoying Jamb.” Daga ranar da kika dawo ne zamu fara rayuwa. Kinsan rayuwar mu ta Argentina babu komai cikin ta sai introduction na AISHA zuwa cikin lonely and pitiful rayuwar KEHINDE. I reserved the day for you only, as I reserved myself for 43 years waiting for the day. Please Baby, ki bani dukkan go ahead da juriyar ki da zan bukata, kinji?" Kunya kamar ta kashe Aisha. Prince ya cigaba da kashe Aisha da kalamai masu dadi yana gaya mata irin tanadin soyayyar da yayi mata daga ranar data dawo, har zuwa karshen rayuwar su. Ashe dai Ishaq da take ji a ranta akan yana gaya mata kalamai da suke zauna mata a rai bai iya komai ba. Ga inda kalaman fatar baki kadai ke neman narkar da zuciyarta a take. Har hakan ya saka mata (nervousness) akan zuwan ranar tarewarta dinnan da Prince ke ta maimaitawa, ba tareda Prince ya san ya saka mata nervousness din ba. A daren yau Hammah ya gaya mata maganganu masu matukar nauyi. A ciki ya gaya mata cewa throughout the 43 years of his life he had never had a sex with anyone. Waiting for her…. his dream wife. As a hopeless romantic, ya jira zuwan true love dinsa tsayin wannan lokacin, and today, he thank the Exalted Lord Almighty for bringing her to his life. (Duk da Haseenah ta so ta saka Prince ya kauce hanya Kehinde bai taba yin abinda ya wuce kissing na shan minti da ita ba. Wanda a yau, wancan abinda ya dan gitta a tsakaninsu ma regretting dinsa yake yi, yana kara istigfari). Ya yarda ba wata soyayya ta kwanciyar hankali da sakewa da jin dadi mara misaltuwa kamar ta auren Sunnah. Da sanyin muryar Prince dake kasheta da dadadan kalamai cikin kunnenta Aisha tayi barci akan wayar, sai ji yayi numfashin ta ya canza a hankali mai nuna tayi barci ta bar shi da wayarsa, batareda ta san lokacin da barcin ya sace ta ba. Shine dai yaga wayar na cigaba da reading kuma bai kara jinta ba. Dole ya kyaleta ya kwanta shima. Amma kam yau Prince yayi wahalallen barci na azaba wanda ko zamanin samartakarsa dana tashen balagarsa baiyi irinsa ba. Firdaus ta taba gayawa Nenne a cikin gorin da Maman Kiki tayi wa Aisha harda na 'Lefe'. Ashe Nenne bata manta wannan ba abin yana tsaye a ranta. Don haka tun ranar da suka koma Lagos ta kira Hamma Abdulrasheed suka gaisa. Nenne tace "Hammansu akan zancen lefen Aisha ne, na maka aure da dukkan hidimarsa amma lefe na al'adar Hausa Fulani na tuna ba’ayi ba na bar maka kayi da kanka. Zaka fi sanin irin dawainiyar dake cikin aure da wahalar sa". Prince yayi murmushi yace "Nenne kenan, ai da kin fada tuntuni da tuni an yi. Yanzunma bata baci ‘better late than never’. Nawa zan bayar?" Nenne tace "da yawa. Don sawa zanyi a hada komai cikin kwana uku kafin Aisha ta baro Gombe ta dora hannunta akan lefen nan" shi ya san Aisha sarai bata wani damu da abin duniya ba balle wani lefe, kuma ita a wurinta maganganun Taiwo sun dade da wucewa bata kara waiwayarsu, amma yasan Nennensa sarai tunda ta rike shi a ranta to fa sai anyi. Hamma yace, "to Nenne bakomai, ayi amfani da 'Black Card' dina dana baki ajiya kafin na taho, ba limit a cikinsa. In ce ko shikenan?" Nenne tayi murmushi bata yi magana ba. Prince ya sake cewa "in ma kin karar da abinda ke ciki Nenne dana iso zan bada ‘dollar card’ dina a karasa, ince ko hakan yayi miki? Ayi lefe lafiya". Yana sauka a Lagos kuwa gidansu ya zarce. Yace "Nenne yaya an gama lefen?" Tace "an kusa dai". Har ya fita zai tafi gidansa ya dawo. Ya baima Nenne dollar card dinsa yace "in case wancan ya kare" Nenne na dariya a ranta tace Hammansu da Dade dinsa ‘are real Yoruba Demons’ akan son matansu basu da na biyu. Nenne da Taiwo suka hada lefe na gani na fada ranar Friday Taiwo ta taho da lefen Gombe. Sai Nani Oummana tasa wata Aunty dinsu da matar Uncle Abdulmajeed da tazo a lokacin tareda Taiwo suka kawo lefen gidansu Aisha da daddare. Sai ga Taiwo har dakin Aisha yau, tana cike da 'guilt' mai yawa, Don gani take hatta lefen nan sabida ita aka yi shi. Ta kara jin nadama mai yawa. Sai ta bige da yiwa Aisha hirar Kiki, ta gaya mata Kiki na tafe sati biyu masu zuwa, kuma da tazo za'a saka ranar aurenta da Tosin. Nenne kuwa taji dadi da akayi hakan, ko ba komai anyi drawing attention dinsu zuwa ga abinda yake cikon al'adar aure ga Hausa/ Fulani. Taiwo ta sanar da Haj. Zainab sakon Nenne na cewa ita zata wuce Lagos da Aisha idan ta gama jamb dinta ranar asabar, to lahadi sai su tafi. Haj. Zainab dai basu gaya mata zasu kawo lefe ba, don haka duk a dame take da rashin shirya musu komai bisa al'ada su kuma Nenne sun yi haka ne don kada su tasheta tsaye inji Nenne, duk da haka sai ta aika Sunusi ya kira Baba Furaira ta karbi lefen. Suka bada tukuici na kudi Inji Baba Barau. Aka rabu cike da farinciki da godiya ga juna. Don haka Umman Aisha ta dukufa da yiwa Aisha gyaran da tuntuni take son yi mata cikin kwana biyun daya rage musu. Tasa an yiwa Aisha halawa da Dilka mai kunshi kuma tazo har guda ta rangada mata irin black and red henna dinnan. A gefe kwararriyar mai kitso tayi nata aikin, kitso yiri-yiri ta yiwa Aisha kamar da allura ta tsaga shi irin na 'yan Maiduguri. Sai ga Aisha ta fito tas a cikakkiyar amaryarta tana sheki da sparkling. Abubuwa ne da tun wancan lokacin Haj Zainab taso tayi mata bata samu dama ba sai yanzu. Don haka Aisha ba karamin gyaran amarci ta samu ba, ta fito tayi das da ita. Washegari Asabar Malam Yunus da kansa ya kai Aisha yin Jamb a location din da zata zana, Jamb dinda Aisha ta kallafawa rai yau Allah yayi an zana ta. Tun 7:30 suka fita karfe 8 suka shiga kuma kafin 10 Aisha ta gama. Abbanta ya jirata har ta kammala ya dawo da ita gida. A daren Aisha suke sallama dasu Umma. Sun raba dare suna hira, Nenne ma ta bugo taji yaya Shirin tahowar tasu ta gaya mata ta gama shiryawa, sallama suke itada Umma. Aunty Taiwo tace sai 11 zasu zo su dauketa su zarce airport. Hakan kuwa akayi. Malam Buhari da Taiwo a kofar gidan su Siddiqah 11 na safe tayi musu. Aunty Taiwo ta shigo suka gaisa da Umman Aisha, sukayi sallama, Sunusi ya kai kayan Aisha mota, ta rungume Umma, ta sake rungumeta. Har ta fita soro ta dawo ta sake rungume Umma ido fal kwallah. Umma dariya da dauriya duka, tace. "Petel dina, zanyi kewarki! Allah ya tsare yayi albarka mai yawa". **** **** **** Su Aisha sun sauka Lagos da tsakar rana, nan suka tadda tarbar Nenne ta alfarma. Ga abinci (Yoruba traditional food) da fresh juice din kankana da apple Nenne ta shirya musu. Ga yoghurt da ta yiwa Aisha na musamman. Aisha na bude warmers din taga Ewedu ta hau dariyar farin ciki, tasan tayi kewar kalolin abincin Hamma har mafarkinsu take amma ashe Nenne ta fita sanin su take marmarin ci. Nenne kamar tasan me takewa dariyar, tace “shiyasa nayi miki su ai, na san rabonki da Yoruba food tun barinki Lagos”. Prince ya gama yiwa Aisha duk wani shirin tafiyarta Qatar tuntuni, a yadda ya tsara washegari Litinin zata bar Lagos ta sameshi a Qatar. Amma sai Nenne ta ce ta daga tafiyar Aisha Qatar sai alhamis, saboda zasu tafi Umrah ita da Dade alhamis din, kuma Qatar airways zasu bi. So zasu taho da ita kawai su kawota da kansu, dama last time bataso tafiyar Aisha ita kadai ba babu 'yan rakiya don dai umarnin Emir ne. Don haka yanzu da kansu zasu taho da ita su kawota sannan su wuce Umrah. Prince ko kadan bai so hakan ba, amma dai yace "toh Nenne Allah ya kaimu". Wannan daga zuwan na Aisha daga Monday zuwa alhamis da Nenne tayi ya baiwa Prince damar yin settling sosai, bayan komawarsa Qatar, don ashe aiki ne damqam yake jiransa bai sani ba, wanda zaiyi in ba shi ba. A cikin ayyukan da ya tarar akwai zuwa consultation na aiki kasar Singapore sati mai zuwa. Kuma in yaje sai yayi sati biyar acan. Tafiyar ta kama masa sati daya da dawowar Aisha gidansa, tunda sai upper week. Har ila yau, daga zuwan nata da Nenne tayi zuwa alhamis sai ya karawa Prince wani irin dokantuwa da zuwan Aisha fiyeda na baya. Don haka ya shiga gyaran gidansa domin taren Siddiqah. Yasa aka fidda duka furniture din gidan tun daga gado har kujeru ya saka sababbi farare sol. In bai manta ba Kiki ta taba gaya masa ya kamata ya sakawa Aisha sababbin furniture, a wancan zuwan nata Argentina. Tace amarya komai sabo ake saka mata. Ba furniture kadai ba hatta curtains din gidan da rug carpets saida Prince ya canza da samfurin zamani kirar jiya-jiya (latest arrivals). Kayan cefane kuwa ba abinda bai sa an ajiye mata ba, tun daga kan gishiri har tsinken sakace, kai har da wadanda Aisha bazata bukata bama daga zuwanta, duk Prince yasa yaron gidansa na Qatar wato Zaid ya ajiye mata. Wato bayeraben miji in ya tashi soyayya da dukkan zuciyarsa yake yin ta musamman mai shekaru da cikar hankali irin na Hamma Prince, don babu rawar kan kuruciya a tareda shi da zuciya daya yake son Aisha yake kuma hidimtawa soyayyar. Kai lallai shiri ba dan karami ba na hango Kehinde na yiwa Aisha. Sai mu ce amarya Aisha Allah ya kiyaye hanya ya kawo kazantar daki. Ya shirya mata lafiyayyen dakin barci dab da nasa, bayan master bedroom da zasuyi sharing. Babu abin da babu na bukatar mace ‘yar gayu a dakinnan na Petel Siddiqah. Wannan gidan da Prince yake ciki is not a Ranch House, gida ne da Qatar Refinery suka bashi don ya zauna yayi musu aiki. Gidan 'penthouse' ne. Ranch House da Polo Horses dinsa duka suna can Argentina. To dama Qatar wajen da yake aikinsa ne kawai, baya Polo a Qatar sai ya haura kasashen turai ko Argentina yake yin abinsa. **** **** ***** Nenne ta gama ma Aisha duk wani shiri da ake yiwa amare 'yan kabilar Yoruba wadanda za'a kai gidan miji karo na farko, har ciccibin nagge Nenne ta dafa mata ta cinye ba tareda ta san ko menene ba. Aisha ta sha mamakin ganin Aunty Taiwo bata koma gidanta ba tun saukarsu, ta tare ma a dakin Princess Fatima. Kuma da alama zaman gida take. Bata tambayi komai ba amma ta gane akwai matsala a auren Aunty Taiwo yanzu, shiyasa ta dawo gida. Ranar Alhamis kamar yadda suka alqawartama Prince Nenne da Dade da surukarsu Aisha Siddiqah Yunus, suka daga cikin Qatar Airways, daga filin jirgin saman Murtala Mohammed na jihar Lagos. Tun jiya Dade ya gaya masa lokacin tasowarsu da landing time. A cikin jirgin, Dade da Nenne suna a first class Q suites na Qatar Airlines (aisle seats), so sun rufe kofar ya zama kamar daki suna hirarsu, Aisha kuwa na jikin window ta kwantar da kanta akan wuyan seat dinta, tayi shiru cikin tunani, tana tuna waccan tafiyar tata ita kadai zuwa Argentina, da abubuwan tarihi da suka faru cikin tafiyar. Har gobe bata san hikimarsu Dade ta tura ta ita kadai da farko ba a wancan lokacin, saidai da yake Nenne ta gaya mata daga baya cewa Allah ya jikan rai Emir ne yayi umarnin hakan. Ita da kanta daga baya take tunanin watakila hikimar Maimartaba Emir of Ilorin na yin hakan shine basa son tursasashi yayi welcoming dinta, wato ya zamanto ya karbeta karba irin ta ganin idonsu, su tafi ya canza mata zuwa true colour dinsa, sun barshi yayi deciding yadda zai karbeta don radin kansa. Bata san meyasa ba tafi jin dadi da kwarin gwiwa har ma da karin ‘self-confidence’ na isa ga Hamma yau, da fara sabuwar rayuwar meaningful aure tare da shi, da ya zama cewa su Nenne ne suka kawota da kansu yanzu. Har sukayi landing a Qatar, Aisha bata jin me suke cewa cikin hirarsu, wadda suke yi da yarbanci, wani lokacin su cakuda da harshen fulatanci, duk dai suna tattaunawa ne akan sha’anin rayuwar ‘ya’yansu da matsalar auren Taiwo. Da alama a irin wannan trip din kadai suke samun lokaci su tattauna extensively akan ‘ya’yansu irin haka. Ita daga karshe ma barci tayi, bata farka ba saida aka ce cikin bututun magana kowa ya daura belt, jirgi zai sauka a Qatriyyah. Prince daga office dinsa kusan duk bayan minti biyar sai ya duba agogon swatch din dake hannunsa, tun kafin lokacin saukarsu ya cika ya yanke duk abinda yake yi ya taho filin jirgin daukarsu Nenne. Jirgin su Aishah na sauka shima yana shiga reception na tarbar baki, don haka Prince baiyi zaman dogon jiransu ba. Aisha ce ta fara fitowa rike da jakar hannunta data Nenne, kafin su Nenne su biyo bayanta. Prince ya runtse ido ya bude yana kallon beautiful Aishah… tana takowa majestically zuwa gareshi, da wani madaukakin murmushin SO a fuskarta, hamdala yake a zuciyarsa, sai kuma ya hango Nenne daga bayanta itama ta taho, tana taku ita kuma cike da sarauta. Prince ya karasa da hanzari ya fara rungumar Nenne, sannan Dade, kafin ya dawo ga Aisha ya rungumeta itama, yace “Aysha welcome oooo, sai yau Nenne ta gama boyon naki ta kawo min?” Dade yayi dariya, Nenne ta harareshi, Dade yace “yaushe muka boye ta din? Daga cewa zamu yi mata rakiya?” Duk suka yi dariya, nan Hamma ya karba mata jakunkunan hannunta, ya sake rungumota jikinsa yana cewa “welcome Aysha! Welcome oooo!”. Daga haka suka wuce mota. Kasancewar Dade da Nenne duk sunada ‘Entry Visa’ na Qatar kuma zasu yi transit na awanni hudu a Qatar sai suka yi amfani da wannan damar suka rako Aisha har gidanta. Prince na tuki akan hanyarsu ta isa gidansa, amma hankalinsa rabi na kan Aisha wadda jikinta duk ya nuna gajiya da lalaci, ta dauko wayarta daga jakarta ta kunna, ta soma kokarin roaming layinta domin ta samu ta kira Umma da Baba Yunus, ta gaya musu saukarsu lafiya amma ta kasa connecting. Duk wani motsi da Aisha tayi a cikin motar sai taji idon Prince Abdulrasheed a jikinta, kai har a ruhinta, ita kuma ta ki yarda su hada ido da gangan kada taje ya bata kunya, don tun daga rungumar da yake mata a gaban su Nenne ta san komai ma zai iya (that’s his real identity of Yoruba demon), gashi duk dagowar da tayi sai ta hango Nenne ta cikin mudubin gefenta, wadda ke zaune a kujerar bayanta, Nenne waya take yi da Fatima a lokacin bata maida hankali a kansu ba sam. Aisha ce dai duk ta ji ta takura da idanun Prince dake yawo a jikinta. Kuma idanun nasa sun rikitata. Finally, Abdulrasheed ya kashe motar a muhallinta wato ‘parking lot’ na kofar gidansa, yaron dake kula masa da gidan wani baqar fata ne dan Senegal mai suna Zaid, kuma har ila yau, Zaid is a good Chef for him, tun kafin su iso ya gama girki na musamman na larabawa, ya shirya a dining sai jiran isowarsu bisa umarnin Ogansa, tunda safe Zaid ya shiga kitchen yake aiki saboda zuwansu. Zaid ya shirya Lamb mandi, kebabs, fatoush salad, humus, Baba ganoush, ga kuma desserts da bakhlava ga arabic coffee. Duk ya tanadar musu kamar mai hada wata ‘yar kwarya-kwaryar get together. Saidai ba wai yayi da yawa bane daidai cin abincin mutum 4-5. So already table was set before their arrival. Suna shigowa Prince ya budewa Aisha dakinta ya shigar mata da akwatinta ya ce “your room”. Su Nenne ma, ya bude musu wani dakin yace su shiga su yi alwala da sallah, nan ne Nenne ta gane Hammah yayi gyaran gida sosai, ta yaba mashi bisa wannan kokarin ta kuma dan tsokane shi da fulatanci “da angon Aisha ka sha kamshi, na Siddiqah bada kanka a sare”, nan dai duk suka yo alwallah har Aisha, Hamma ya jasu sukayi sallahr jam’i gabadaya, sannan suka fara cin abinci cikin nutsuwa suna yi suna duba agogo. Da suka kammala Nenne tace a bata ‘black tea’ (lipton) ta kara, saboda Nenne bata shan coffee ita. Prince da kansa ya dafo shayin a kettle din dafa ruwan zafi, ya hado ma Nenne a kan tray da mug cup da liptons kala-kala na alfarma da yake ajiyewa don baki don shi in ka cire chamomile da lavender ba shayin da ya ke sha, ya ajiye mata bakidaya liptons din kala kala don ta zabi wanda tafiso cikin su, (and honey instead of sugar) don Prince baya shan sugar sai zuma. Nenne na sipping zazzafan lipton Dade ya hada Prince da Aisha yana musu nasiha a tare. Ya ja hankalinsu kan su hada kansu su zauna lafiya, su zama sirrin juna, su kuma taimaki junansu akan komai. Yace ma Aisha, ko me Prince zai mata na rashin kyautawa ta doshesu kai tsaye. (They are always there for her) muddin suna raye. Ya roketa kada ta kara dosar iyayenta da matsala inba a inda taga sun gaza daukar mataki ba. Shikuma Prince Dade yace dashi “har kullum ka tuna Aisha mace ce, kuma mai kankantar shekaru a kanka. Yadda duk ka mikar da ita a haka zata girma. Don haka sai ka nuna mata abinda kakeso da wanda baka so a hankali. In tayi kuskure ka nuna mata ta lalama da jurewa kuruciyarta. A karshe suka saka musu albarka shida Nenne, a bisa biyayyar da suka yi musu, suka roki Allah ya basu masu yi musu mafiyinta da gaggawa. Ya kuma sa ‘ya’yansu su kasance nagari masu bin iyaye kamarsu”. Dade yace “saura ke Nenne ko?” Tace “ai you have said it all Dade, banida abin cewa, addu’a kawai zanyi musu, wadda kullum bana fasawa. Allah yayi musu albarka da zuri’a dayyiba albarka Annabijo”. Daga haka duk suka mike, Prince ya dauki mukullin mota don ya maida su, yace ma Aisha, “Ayshah ki rufe kofar falon ta ciki, in na dawo zan bude da key dina, idan Zaid ya tattare wajennan ya tafi”. Ya gaya mata akwai yaron gidan, mai suna Zaid, amma baya kwana a gidan, da safe yake zuwa ya tafi karfe 6 na yamma in ya gama masa dinner. Har sun fita tare dasu Dade sai yai excusing dinsu ya dawo kamar yayi mantuwa. Da sassarfa ya isa ga Aisha ya rungumota ta baya tana kokarin rage nauyin laffayar jikinta. Aisha tace cikin ‘yar rawar murya “Hammah, mantuwa kayi? Kada suma kasa jirgi ya tashi ya barsu fa?” Prince kamar bai ji korafinta ba, ya sunkuya ya sumbaci bakinta dake maganar cikin shagwaba so lightly yayi sumbar, sannan a daidai kunnenta yace cikin shauki. “Welcome Ayshah.. welcome to your abode! The lady of my heart, love of my life, mother of my children, the one that has completely changed and shaked my whole universe. I am coming back soon to welcome you Baby, kin ji?” Ya sake kai mata sassanyar sumba a wuyanta da lips dinta, amma Aisha bata barshi yayi nisa ba ta kwace bakinta cikin jin kunya, tace cikin shagwabar da bata zuwar mata sai in tana gaban Hammah Abdulrasheed kadai. “Hamma Abdul mana?! Dade da Nenne, suna bakin mota suna jiranka fah?!”. Prince da kyar ya juya ya fita kuma da baya da baya, yana sumbatar hannunsa yana huro mata iskar, ita abinma sai ya bata kunya da dariya, tasa tafukanta ta rufe fuska tana kallonsa ta tsakanin yatsunta cikin idonsa da wani irin kallon SO, wanda yasa Prince yin tuntube a bakin kofar fita. Da kyar Hamma yakai bakin mota, su Nenne dai tuni sun bude sun shige basu kara bi ta kanshi ba. Bayan fitar Hammah Siddiqah ta yi unpacking ta fada wanka ko ta samu karfin jikinta daga gajiyar data kwaso, ta sille jikinnan tas ta zuba sassanyan turaren humra na “turarewutashop” (crème de la crème), tana gamawa ta dauko ‘lounge wear’ dinta wando da riga ta saka, sai ta dora hijab ta fito falon, tana fitowa taga wayam, Zaid har ya gama tattare wajen ya kunna bakhoor burner ya kwashe kayan abincin da wadanda aka bata, ya bar musu flasks na coffee da tea a dining din, da mugs da desserts harda da dan cup cakes ya tafi, ta kashe turaren don ya kare, sannan ta cire hijabinta ta kunna kallo. Daman Hammah ya mata connecting wifi kafin ya tafi mayar dasu Nenne. Sai kawai ta kira Ummanta ta whatsapp vedio call, suka danyi hira akan saukarsu lafiya sannan Siddiqah ta haska mata wani sashe na gidan ta gani, tace “Umma kinga gidan” Umma tace “na gani Petel” ta sa albarka, bayan sun yi sallama da Umma ta kishingida a three seater din falon tana kallo, daga nan ne barcin gajiya ya dauketa. Kuma ko a cikin barcin nata duk mafarkanta Hamma Prince ne. Saida su Nenne suka wuce priority lounge zasuyi jiran one hour kafin tashinsu Hamma ya juyo gida. Yana tafe a hanya ya kira Zaid, yace kada ya zo masa gobe da safe sai ya neme shi da kansa. They will take care of themselves. A lokacin yana adana motar a muhallinta, ya dauko abubuwan da yake bukata ya fito ya rufe motar. Yasa mukulli ya bude kofar shiga falon. Shiruuu baka jin komai sai hucin AC. Kafin ya ankara da Aisha a three seater tayi dai-dai akan kujerar tana sharar barcinta sadidan. Prince har da sakin ajiyar zuciya don ji yayi tamkar komai na rayuwa yanzu ya gama yi masa daidai (with his wife Siddiqah by his side). Hamma bai tasheta ba don ya ga alama tana jin dadin baccin, dakinsa ya wuce ya fada wanka. Har Prince ya fito yayi sallah yayi changing zuwa kayansa na barci wasu ruwan tokar pajamas Aisha bata farka ba, a hankali Prince ya sunkuya yasa hannunsa biyu ya dauki Aisha, ya soma tafiya da ita a hannunsa, yana sumbatar kasan wuyanta da saman lips dinta softly, jinta dauke a hannun Hammah da wannan sumba da yake mata (soft and light kiss) Aisha ta bude idonta ba shiri, idanun ta suka fada cikin na Hamma Abdulrasheed (Prince). Aisha tace “Hammah…” cikin magagin barci shi kuma yace “shhhh, cigaba da barcinki ban so kika tashi ba Baby”. Sai Aisha ta mayar dasu ta sake lumshewa, ta kuma sunne fuskarta cikin kirjinsa don kunya, katuwa da ita an mata daukar jarirai. Prince ko a jikinsa don bata fice baby din ba a idanunsa. A takiyar dakin Prince ya sauke Aisha, kasancewar ya kashe wutar dakin ga barci a idonta sai bata fahimci a inda suke ba, har sai da Prince ya kunna wutar dakin haske ya gauraye ko’ina ta gane masterbedroom dinsa na. Aisha ta fara bude idonta a hankali cikin nutsuwa tana kallon yadda Prince ya shirya mata ‘special welcome’. A kowacce kusurwa ta dakin kyawawan welcome cards ne na bature, da ‘scented flowers and rose petals’ zube akan gado, wai duk don maraba da saukarta, har saida abin ya so ya sata dariya ya kuma sata jin kunya da farin ciki sosai. Daga bayanta Prince yasa hannu ya rungumota bakidaya zuwa jikinsa. Ya bata ‘fresh red rose bouquet’ a hannunta, bayeraben mijin nan nata yau zai kasheta da soyayya da farin ciki mai yawa, yace. “Welcome my darling Baby! You have no idea how happy I am that you are here!”. Ya sumbaci kasan wuyanta a hankali, Aisha na murmushi tana kara wartsakewa daga barcinta tace “thank you darling!”. Sai ji tayi Hamma ya saka bakinsa a tsanake cikin nata, ya soma sumbatarta, deep gentle and cool kiss, wanda nan da nan ya soma shiga kwanyar Aisha ta soma kyarma. Hamma na iya jin yadda jikin Aisha ya soma rawa din. It obviously shows her nervousness and naivity, ta kuma kasa cewa Hammah komai, domin sosai kisses dinsa ke shigarta. Prince ya kwantar da kan Aisha a kan kirjinsa, wanda hakan yasa dankwalinta ya zame ya fadi ta baya. “Yaa Subhanallah” kawai Hamma ya iya ambato, lokacin da kyakkyawan kitson Aisha akan gashinta mai laushi da baki da sheki ya bayyana, hasken lantarki kuma ya kara masa kyau, siraran jelunan kitson suka kwanto lambam akan wuyanta. Prince kasa jurewa yayi, don bai taba ganin abinda ya masa kyau irin wannan gashin na Aisha ba, sai da ya shafo kitson da hannun damansa tun daga farkonsa har kasan jelunansa don kamar ba mutum ne yayi ba. Wata rahma na sauka a zukatansu su duka. Yace “Aysha…” tace da kyar “na’am Hammah”, alhalin ilahirin jikin ta yana shaking, and he can feel it, wato yana jin irin rawar da jikinta ke yi a nasa jikin. Sai ya soma shafar bayanta a hankali cikin lallashi da son saka mata nutsuwa, ya ce “Aisha are you nervous?” Murya can kasa, ita kanta muryar tata da tasa rawa take, kamar yadda jikinsu ma yake rawa da karkarwa irin nafarin shiga, because she can feel how aroused the Prince is which makes her more frightened. Ta daure tace “a’ah Hamm… am not”, yace “to relax, kin ji Aysha. Ki saki jikinki dani, ba abunda zan miki in har zuciyarki bakya so yau. I will never force you to be with me in this regard. I just want to feel your warmth in me and I feel it, so relax kin ji”. Aisha har da ajiyar zuciya, ta fara nutsuwa. Kehinde yana rungume da Aisharshi kamar mai tsoron kada wani ya kwace masa ita, ko ta kara komawa Gombe ta barshi. Yama rasa inda zai sakata cikin jikinsa da zuciyarsa ya zama contented. Daga bisani ya dora Aisha a laps dinshi suka zauna a gefen gadonsa, ya matseta sosai ya hadata da kirjinsa kamar zai hadiyeta. Bata san meyasa wata irin kasala ta sameta ba a wannan lokacin da Prince yayi shiru kawai yana makale da ita, sai ta samu kanta da kwantar da kai a kirjin Hammah kawai, tana kara samun wata irin muguwar kasala. Hammah kamar ya san halin da Siddiqah take ciki, cikin dabara ya kwantar da ita a tsakiyar gadonsa, ya kuma dora mata dukkan nauyinsa. Prince ya soma yi mata hira, irin hirar masoya mai jan hankali, he’s just trying to make her comfortable with him. A tsakiyar gadon Hamma suke kwance yanzu, yana kallon jan lallenta, ya soma jan yatsun da suka sha lellen yana mata hira mai ban dariya duk don ta saki jikin ta daga barin da yake yi, daga jan yatsu Hammah ya zarce da yiwa Aisha tausa a santala-santalan kafafunta, tausa mai tsada har ya isa ga inda yake son isa. Kafin kace meye wannan gabadaya Abdulrashid ya fara kunna Petel din Umma, rawar da jikinta ke yi maimakon ya ragu sai ma ya karu. Kasala ta karu mata. Don Nenne ta bata abinda bazata iya resisting din Hammah a wannan daren ba; wato ciccibin Naggen yarbawa, ga touches din Hammah na kara shigarta very irresistible, amma duk da haka Aisha bakidaya a tsorace take da Hammah a matsayinta na yarinya budurwa a ranar farkonta, har tsoron da fargabar ya rinjayi sha’awar bakidayanta, don dai kasala ta hanata motsi ne balle ta noke masa. Ya lura sosai da halin kasalar da take ciki, ko yatsanta bata iya dagawa, yace cikin lallashi “Baby please, be comfortable….kinsan nayi hakuri nayi kokari mai yawa tun aurenmu ko?” Siddiqah ta gyada kai, duk don ta boye masa fargabarta da rauninta. Tuni barcin idonta daya daukota tana yi ya ware. Prince ya lura da hakan yace. “Aysha na tashe ki daga barcinki ko? Haven’t you slept on the flight?” Tace “wallahi nayi fa Hammah, ka san tafiya ko yaya sai tasa mutum jin kasala da mutuwar jiki”. Prince yace “yeah, that’s true. Muje ki sha tea dina na barci (chamomile) zai saki barci mai dadi da ‘bakhlava’ sai mu dawo nan in miki massege kinji Baby?” Aishah tace “ai Hamma bacci kawai zanyi, na koshi sosai. Kaga fa naci kebab sosai” ya sakar mata wata harara yace “toh ni zan sha tea din, zo ki raka ni in hado sai mu kwanta”. Aisha tace “okay” (wani irin innocently). In ka ganta a lokacin sai ta baka tausayi she looks pale, Hamma ya tashi ya mika mata hannu ta taso. Ita de ta kawar da idonta daga kallonsa ta daga kai suka fita. Ya kunna wutar falon. He actually looks younger yau, ko kayan jikin sa ne? A duniya ta lura Hammah Abdulrasheed nason wannan ‘pallazo’ wandon ‘grey’ kuma ya lafe a jikin sa sosai, ga rigar ma haka tai masa cippppp! Masha Allah kawai Aisha tace a ranta, wannan sarbadeden saurayi Allah ya bata ita kadai in sha Allah…. sai tayi murmushi. Hammah ya kalle ta yana zuba tea shima, tayi masifar kyau. Yau kuruciyarta ta fito sosai bakidaya, she looks adorable. Ga lallen da Kitson, amarya sakkkk! Sweet 16 mallam, dukiyar fulaninnan so perky…. ya tuno yadda ya samesu ranar nan a Gombe, ranar da yaje zance… “kai! Ya Ilahi!”. Hammah yace bai ma san ya fadi ba. Kawai sai jin zafi yayi a hannun sa, ya kuwa saki flask din kasa, “subhanallahi!” Suka ce a tare. Siddiqah tace “Hammah ka qone? Mu gani?” Ta taso da rawar jiki ta rike hannun nasa, yace “no, I am fine” tace “kai ko Hamma Abdul me kake tunani haka har ka qone?” Yace “U, my darling” tayi smiling tace “ba gani nan ba har sai ka yi tunani na kuma? Gashinan ka kone ai, sannu” ta kama hannun tana hurawa da bakin ta, wani softness yaji kamar ya rike Baby, ga iskar nan da take hura masa kamar petrol take zuba ma wutar sha’awar ta a zuciyar shi. Prince ya mika dayan hannun, ya kamo small waist dinta, sai kissing passionately. He was actually not in control, becoz he is not even trying to control himself, he is in love and he bloody don’t care he want the love to just carry him along. Duk wasu plans na binta a sannu da kama kai sun watse. Zuciyar sa ya sakar ma ragamar, duk yadda tayi daidai ne!!!! Aysha zata matsa ya kuma matso ta sosai yana kissing, yace “I love u baby!”. Aisha cikin tsananin kunya da karamar murya tace “love u too Hammah” tana dan murmushi sheepishly. Prince ya sake ta jin ruwa na diga a kasa daga kan tebir. Yace “bari in dauko towel a kitchen” tace “karasa hada tea din, bari in dauko”. Ta wuce da sauri. Ya fara sipping. Ta shiga kitchen ta dauko mop mai bucket, ta shigo ta iske shi kan kujera yana kallon ‘polo line tv highlights’ yana ‘sipping tea’ din sa, hannunsa daya cikin aljihu. Ta karasa ta koma ta ajiye, sai jin motsin ta yayi, ya juyo yana kallon ta. “Oh, my God!” Prince yace a fili. Ya aje mug din, ya fara taku zuwa hanyar kitchen din, ita aisha taji sanda yace “Oh, my God” din, amman ta dauka kallon da yake yi na tv ne. Tana so ta matse mop din, ta shanya. Shi kuma gogan ashe sura ya gani, yace “Allah yayi halitta”, ashe wani wandon rashin imani ne a jikin Siddiqa, roba ce a baya daidai tsakiya so gabadaya yaiwa kugunta tamkar bra, gashi tana tafiya da sauri so her whole body is shaking, wanda ita halittar tace haka, ba wai yi take da gangan ba. Gaba daya Prince ya nemi nutsuwa da girman sa da kwanciyar rai ya rasa. Wallahi shi bai ma san yana binta a baya ba. Like he said… following zuciyar sa kurum yake yi yau! Wannan view na bayan Aysha ya sake kunna shi fiye da tsammani, kunsan dai bayerabe da son wannan. Aysha na fitowa ta kashe wutar kitchen sai taci karo kawai da mutum kamar mayunwaci ya wawuro ta ya hada da kofar kitchen din… “Hammah what I ….” sai jin bakin sa tayi a nata, this time intensively. Gabadaya his hands are shaking squeezing her whole body, his lips are quivering, yana kissing bayan wuyan ta, sai taji ashe romance din da Hamma yayi mata a Gombe ba komai bane, wannan mai degree da masters ne. Ashe wancan na Gombe waec ne da neco ne. Prince yana magana a hankali kamar bai ma san yana yi ba. Yana fadin baby you are so soft… you smell provocative… my God…!”. Shi wannan breathing din da take heavily in his ears, duk numfashi daya sake kwance masa notikan kai yake bata sani ba. Prince ya sake ta jin yana iya cika aiki bisa dining table… and he know a kan sabon gadon su ya kamata komai ya faru, wannan babban darasin bai kamata ya faru anan ba…. He has no idea na yaya akayi ma dai ya tsaya. Ya dai san ya sake ta yayi baya, ya jingina da bangon wurin, yana kallon ta looking flushed, fuskar nan tayi jawur abinki da farar fata… looking so alluring a hargitse… ganin kallon da yake mata Aysha ta dan ji kunya, ta sunkuyar da kai, ta mike tayi daki yabi bayanta, dab da zatayi dakinta ya cafko hannunta ya karkatata sai masterbedroom, yace. “Ai wannan dakin kuma Ayshah… sai dai kizo kisa kaya in kin so, amman ga dakin mu nan”. Ita kunyar kanta taji, yasa zata gudu, dan har mamaki take baima kanta. Fisabililllahi itace ma kuwa? Gabadaya kamar ba ita ba. Hamma ya mayar da ita spoilt child, matsalar daya ce wallahi da ya taba ta sai ta nemi hankali da kunya a kwanyar ta taji sun kare, she just wants more. He is sooo gentle yet so sexy…. kamar wuta Hammah ke kunna mata. Ta san sunyi wasu abubuwa a Gombe amman gabadaya na yau daban take jinsa. Ita wallahi Umma ce ta janyo mata tunda ta fara bata wannan kayan zakin ta rasa kanta, ga Nenne itama ta zo ta dora da irin nata, tana zancen zucin nan suka iso dakin, ta tuna me sukayi yanzu tayi murmushi, yace “menene?” Tace “babu” yace “tell me”, tace “kawai kayi kyau ne Hammah… kayan nan suna maka kyau” yace “sosai?” tace “yessssss….” yadda ta fadi “yessss” din ma yace “you want to kill me koh?” A matukar sanyaye. Tace “Allah ma ya tsare Hammah, not now….” yace “zo in miki tausar to babyn Hamma…” tace “uhm uhm,” yace “toh ni yi mun” tace “okay”. Sai ganin sa tayi ya cire top din ya ajiye, ya kwanta yace “oya” ta zo ta zauna gefe zata fara yi masa yace “not like this…. zama zaki dirshan a baya na” baiwar Allah tace “okay”, ta zauna ta fara masa tausa shi ji yake kamar ma tafiyar tsutsa take masa ba tausa ba, ya fara sake tsuma, tana yi a zuciyar tana admiring her God given hunk of a husband! “wait” taji muryarsa can kasa, ta tsaya, ya ce “lemmi turn”, ta tashi ya juyo rigingine yace “yadda kika mun a baya haka zaki min yanzuma. kinga inda ke min ciwo…” ya daura hannun ta on his shoulders… ya zamo dasu kar daidai kasan cikinsa yace “nan zaki tausa baby”, ta kuwa sa hannu ta fara da zuciyarta daya (Takori and her crew, muka soma ja da baya, muka ce kai ita dai wannan Petel ta cika ta fari sannan auta, ba wayo ko na kwabo. Dan Yarbawa ya gama da ita, amman zaki sani ne). Petel ana massage Prince na lumlumshe ido, tana yin tausar har kirjinsa, groans din Prince na karuwa, reaction dinsa to her every single touch ke narkar mata da zuciya… har bata san sanda… Prince yace “Ya ilahiiiiiiii….” Daga haka ya janyo ta jikinsa kamar kiftawar ido, yasa hannu ya cire mata top din, yaga bra a kasa ya sa hannu ya ballo shi, tayi maza tasa hannayenta ta rufe tana “Hammmaaaaaa…..”. A hankali Prince yace “Baby plsss don’t deny me to see you, I really… really…. really neeed you tonight, you know wanting you comes in waves a kwanakin nan, but tonight I am drowning… I need you to save me (with each word followed by a kiss, in a part of her upper body). Aisha ta dauka waec da neco akai na romance a Gombe, toh ashe dai primary leaving exams ne, yana wannan bayanai yana daga hannun ta data rufe..”. Toh daga nan ko ya akayi sai ji mukayi Prince yace “get the hell out of my room Takori and your CREW!” (Ashe-ashe Prince ya hango mu ta bayan labulen da muka buya muna dauko muku rahoto). Sauran al’amuran da suka biyo baya masu nauyi da girma ne daya shallake tunanin kowannensu yafi karfin bironmu nida crew dina. A wannan lokacin Abdulrasheed is more than bewildered. Gabadaya ya dauki Aisha ya kaita wata duniyar daban da bata taba mafarkin zuwa ba ko cikin mafarki. Ya mika hannu ya canza musu launin fitila daga mai haske zuwa mai duhu. Daga nan dai daga ni har Crew dina, bamu kara hango me ya faru ba, har zuwa sanda Petel din Umma ta amshi certificate din girma da sallama da kuruciya irinna kowacce ‘ya mace, daga bayeraben mijinta Prince Abdulrasheed (Kehinde). Bamu kara jin duriyar Aisha da Abdulrasheed ba. Mun barwa mai karatu ya kissima abinda zai kasance a wannan muhimmin daren a garesu bakidayansa. Just imagine a 43 year old bachelor yau ya angwance da ‘yar 18 years. A lokacin da soyayyar juna ta kai ta kawo ta tumbatsa a zuciya da gangar jikin kowannensu!. **** **** **** WASHEGARI Prince Abulraheed Idris Kehinde Akanni, da matarsa Aisha Siddiqah Yunus, sun wayi gari cikin farin cikin ma’aurata da bazai misaltu ba. ya sakawa Aisha albarka tafi cikin kwando. A yau ya wayi gari da farin cikin zama cikakken magidanci da farin cikin halin da ya samu Aisha na cikar mutunci da tarbiyyah, ya kuma wayi gari da farin cikin dabbaqa sunnar Ma’aiki SAW. Ya zama cikakken miji a gidansa abin so da alfahari a wuri matarsa. Amma kwarai ya tausayawa Aisha, but he is happy, more than a word can say. Don haka duk wata kalar shagwaba ta Aisha ya jure ta, da kansa ya taimaka mata da dukkan taimakon da zai iya, Aisha ko jariri a wannan ranar nan ya ganta ya barta wajen shagwaba da narkewa miji. Hamma Prince ya rasa irin taimakon da zai bata da farko, domin kwarai yayi aika-aika, wadda shi da kansa saida ya tausayawa Aisha. Luckily to him, sai ga Dr. Taiwo ta kira, Aisha na kwance bisa kirjin Prince tana zuba shagwaba, domin babu inda baya ciwo a jikinta. Prince ya amsa wayar Taiwo alhalin yana shafa bayan Aisha da gashin kanta da dayan hannunsa. Yace “Taiwo, Aisha is sick, ya zanyi? Gashi bazata iya takawa muje asibiti ba” Taiwo na jin haka ta gane Kehinde dinta sai yau ya angwance, tace “take her to bathroom yourself, ka tara ruwan dumi ka sakata a ciki, for some minutes, ta bata pain reliever”. Ta gaya masa duk abinda ya dace yayi mata, a matsayinta na kwararriyar gyneacologist. Da sunan maganin da zai aika a karbo mata a pharmacy. Prince duk yayi yadda Taiwo tace, har Aisha ta fara samuwa. Da kansa ya hada musu light breakfast don ya hana Zaid zuwa yau. Haka yayi ta lallabata tana dada narkewa har ya samu ta ware kafin dare. Soyayya gangariya ‘yar usuli kuma mai tsafta ta cigaba da gudana a gidan Prince Abdulrasheed Kehinde har zuwa zagayowar satin da suka daga zuwa kasar Singapore. A ka’ida Prince aiki ne ya kawoshi Singapore, na tsayin wasu satittika, amma sai ya maida damar ta koma masa ta hutun amarci zallah. Prince baya taba gajiya baya gundura da Aisharsa. Itama kuma kullum son bayeraben mijinta Prince da tsananin kaunarshi karuwa suke, kasancewar kullum sabunta girman son nasa da tasirinsa yake a ranta, da samfur-samfur din soyayyarsa ta bayeraben miji mai tsananin son matarsa. Basu dawo Qatar ba saida Siddiqah ta fahimci samuwar yaron ciki a tareda ita, aka dawo Qatar da guzurin tattaba kunnen Sarkin Ilorin. Dawowarsu Qatar keda wuya, Tosin Abdulnaseer ya kawowa Prince ziyarar ban girma, da gaisuwar rokon iri har Qatar. Shikuma nan da nan ya hadashi da Baban Kiki a waya, a lokacin ne Tofeeq yaji kunya sosai kan abinda yayima Taiwo, yayi tattaki zuwa Lagos ya roki iyayensu Prince a kan a maida masa Maman Kiki, ya tuba. Dade yace da wa ya rike ta? ita tayi fushi ta zauna a gida. Amma kuma ya fito filiya bashi laifin yin aure a boye da yayi. Yace Taiwo ai musulma ce na me zai boye mata? babu mai hana shi aure inda yace zai yi ai su duka musulmai ne masu bin sunnar Annabi SAW. Amma wannan iskanci ne kuma wulakanci ga uwargida, no matter what she deserves to know and consent idan mijinta zai kara aure. Tofeeq yace shi wallahi tsoron bala’in Taiwo yake. Dade yayi masa fada sosai yace ai sun wuce wannan stage din shi da ita. Ya kuma nuna musu su duka sun girma, irin haka ba nasu bane, alhalin suna shirin kai Kiki dakin aure. Tofeeq yayi nadama sosai yayi ta baiwa Taiwo hakuri. Aka lallaba Taiwo da kyar ta yarda ta koma gidanta na Lagos. A satin da Aunty Taiwo ta koma gidanta aka saka auren Kiki da footballer Tosin Abdulnaseer sati biyu masu zuwa. Bayan bikin Kiki ne Aisha ta fara karatun jami’a a Qatar inda take karantar Pastry Art. A lokacin kuma cikinta ya bayyana sosai kamar ya zarta watanninsa, cikin da Kakanni da iyaye keta lelensa kamar ba’a taba haihuwa a zuri’ar Sarki Abdurasheed Akanni ba. sai akan cikin Prince da Aisha. Dangi sun yaba kwarai da rawar da Aisha da Prince suka taka a auren Kiki. Prince yayima Kiki abinda ko Toafeeq bai yi mata ba a lokacin aurenta. Haka Aisha ta taka rawar gani wadda ko Taiwo saidai tace ita ta haifeta. Duk da Aunty Taiwo tayi nadamar abinda tayiwa Aisha, ta kuma koma zaman lafiya da ita, lokuta da damaa tana dan dana halayenta na fada da shiga sharo ba shanu. Sabida shi halin mutum hausawa suka ce zanen dutse ne. baya goguwa gabadaya. Aunty Taiwo is forever Kehinde’s twin (Taiwo). Amma bata yarda koda kuskure ta dana halin nata akan Aisha wai hausawa suka ce wargima wuri shika samu. Wata fuskar tafi gaban mari. Ban taba ganin ‘yar gatan mace a gun miji da iyayensa irin AISHA INDO SIDDIQAH ba!. **** **** **** Haihuwarta ta farko ‘yan biyu ne maza wadanda nan take aka mayar da sunan Sarkin Ilorin da Sarkin Gombe mai rasuwa. Addu’a suke nan gaba Allah ya basu wasu saitin twins din mata a samu mai sunan Nenne da Umma Haj. Zainab. Rayuwar Hamma Abdulrasheed (The Prince of the Ilorin Emirate) kacokam dinta, bakidayanta, is an inspiration ga maza irinsa, sannan darasi ce babba ga mazan da suka samu kansu a yanayi na jinkirin aure, mudubi ce mai nuni da cewa, rashin aure da wuri, matsayin sarauta, mulki, da wadatar arziki ba tikitin zaman namiji “Dan Akuya” bane. Cikar kamalar namiji kuma shine ya zamanto cewa ya iya ‘controlling desires’ din shi. SADAUKARWA NE GA MAZAN DA SUKA SAMU KANSU CIKIN KADDARAR JINKIRIN YIN AURE BA TAREDA SON RAN SU BA!!! SADAUKARWA NE GA DUK BAHAUSHIYA/BAFULLATANAR DATA CIREWA RANTA KABILANCI AKAN KABILAR “YORUBAWA” DA SAURAN KABILUN NAJERIYA TA DALILIN KARANTA LABARIN |AISHA SIDDIQAH YUNUS| -SUMAYYAH ABDULQADIR MAY, 2024 07030137870 LITTAFINNAN NA SAYARWA NE IN KIN TSINTA KIN KARANTA KI JI TSORON ALLAH KI BIYA (1000) TA WANNAN ACCOUNT DIN (2089357770 SUMAYYAH K. ZENITH BANK) INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. -Takorinku