SA MAZA GUDU littafi na daya(1) Na Abdul Aziz Sani madakin gini.. A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a cikin daular larabawa a zamanin da babu wata huldar kasuwanci wacce tafi cinikin bayi, anyi wani babban birni mai suna Madinatul Zauwara. Birnin Madinatul Zauwara na karkashin mulkin wani gawurtaccen sarki ne ma'abocin jarumtaka wanda ya zamo gwarzon mayaki kuma dodo ga dukkan sarakunan dake nahiyar,ana kiran wannan sarki da suna Sharkuf bin Aufan. Duk wani abu najin dadin duniya Allah yabawa sarki Sharkuf,yanada 'ya'ya guda tara amma dukkaninsu mazane,sai mace guda daya.Babban dansa kuwa shekararsa talatin da takwas,ana kiransa da Lahaman. Lahaman ya gado maifinsa a sadaukantaka da jarumta kuma shine yake jagorantakar dakarun sarki a duk sa'adda za'a fita FARAUTAR BAYI. A tarihin fitarsa farautar bayi sau sittin da uku bai taba dawowa gida cikin rashin nasara ba,kuma duk sa'adda ya fita baya dawowa da kasa da bayi dubu uku,sau tari idan yarima Lahaman ya fita farautar bayi baya dawowa sai bayan wata biyu ko wata uku. Kashi daya cikin kaso uku na ribar bayin idan an siyar na yarima Lahaman ne,ragowar kason biyun kuwa na sarki Sharkuf ne.Saidai duk dakarun da aka fita wannan farauta dasu akan basu kyautar bayi bibbiyu. Bisa wannan dalili ne a gaba dayan 'ya'yan sarki Sharkuf babu mai kudin Lahaman,kuma wanda wanda mutane ke sa ran cewa za'a bashi gadon KARAGAR sarki to amma shi sarki Sharkuf yaki fadar wanda zai gajeshi. A gaba daya 'ya'yan sarki Sharkuf su tara babu wanda yafi soyuwa a cikin zuciyarsa sama da gimbiya Malika,duk abinda gimbiya Malika ta furta tanaso indai akwai shi anan duniyar sai sarki Sharkuf ya bata,kuma babu wata alfarma da zata nema wajensa ta rasa.Kai saboda tsananin kaunar da Sarki Sharkuf ke yiwa gimbiya Malika ko Fada zaije tare da ita yake zuwa,su zauna tare bisa KARAGAR MULKI,kuma duk taro mai mahimmanci idan bazai samu damar halartar ba,ita yake turawa ta wakilceshi.Sukan su ragowar 'ya'yan sarki idan suna son wani abu a wajen mahaifinsu saidai suyi kamun kafa da Malika,in ba haka ba kuwa bazasu samuba.Wannan dalili ne yasa dukkanninsu suke yi mata biyayyar dole duk da cewa sun girmeta. Yarima Lahaman ne kadai baya saurarenta kuma sai kiyayya da hassada ta shiga tsakaninsu,sabo da ganin kamar sarki zai iya hanashi karagar mulki ya bata. In badon Yarima Lahaman yana matukar tsoron sarki Sharkuf ba,da tuni yasa an hallaka Malika a asirrance,domin ya huta da fargabar dake zuciyarsa da kuma tsananin kiyayyar dake tsakaninsu,babban abinda yake kara baiwa Yarima Lahaman haushi shine duk abinda yake iyayi da kudi itama Malika tanayi,har ma tana iyayin abinda shi ba zai iyaba,saboda komai tsadat abu tana iya sayansa,saboda tanayin kasuwanci a boye ba tareda dashi kansa sarki ya sani na. Saida ya zamana cewa fiye ta rabin fataken birnin nata ne,kuma saida ya kasance a nahiyar gaba daya babu 'yar kasuwar da tafi Malika safarar kayan abinci da makaman yaki Bisa wannan dalili ne tayi sabo ainun da sarakuna da kuma manyan attajirai,ababan misalai.Da yawa daga cikin sarakunan da attajiran basa ganinta sai a karshen shekara.a wannan lokacine take kai ziyara kasa kasa tana karban cinikin da aka tara a hannun wakilanta dake tapiyar mata da kasuwancinta.Sarki Sharkuf duk bai san wannan kasuwancin da take yiba,abinda yasani kawai shine duk karshen shekara tana shirya tafiya ta kai ziyara izuwa manyan kasashe hudu,don ziyartar manyan dakunan bauta dake birnin Kisra,Farisa,Yemen da kuma Misra. A wannan lokacin ba'a barin kowa ya shiga cikin wadannan dakunan bauta face sarakai,manyan attajirai,manyan jarumai,da kuma kasaitattun bokaye.Duk sa'adda gimbiya Malika zata fita izuwa wannan gagaruman tafiya sarkin yakin birnin Madinatul zauwara ne yake yi mata rakiya tare da dakaru dubu uku domin tsaron lafiyarta,dama babban boka na kasar wanda ake kira Muzambil bin Samrad. Wannan gawurtaccen shiri da ake yiwa Gimbiya Malika na tsautsauran matakan tsaro,shi yasa Yarima Lahaman ya kasa kai mata hari,saboda ya tabbatar da cewar shi kadaine zai iya tarar sarkin yakin nasu da kuma bokansu kuma in dai ya tare su sai sun gane shi tunda sun san irin yanayin yakinsa da irin sihirn tsafinsa,idan kuma yaransa ya tura sai asirinsa ya tonu an gane shi ya tura su. Burin Yarima Lahaman shine sarki ya mutu ya gaje karagarsa,to abinda ya aiyana a ransa shine a ranar zaisa a kama Gimbiya Malika da uwarta a kaisu kurkuku,bisa hukuncin daurin rai batare da sun aikata laifin komaiba,sauran kannensa kuwa zai tursasasu suyi masa biyayya,duk wanda yaki dole ne cikon biyu abu guda ya sameshi,kodai a batar dashi ko kuma shima a kaishi kurkuku ya karasa rayuwarsa a can. A ranar da ya rage sauran kwana uku kacal Gimbiya Malika ta tafi ziyartar da ta sabayi a karshen shekara ne,yarima Lahaman ya dawo daga farautar bayi.A wannan karon wata nahiya daban suka je suka riski wata karamar kasa kawai sai suka afkawa kasar da tsakiyar dare sukayi mummunar barna. A daren ne sarkin garin yayi sabon aure yana tare da amaryasa suna shirin more amarcinsu kenan Lahaman ya bayyana tsulum a gabansu.Nan take aka kama sarkin aka daure shi a gaban idanunsa yanaji yana gani kuma yana kuka Yarima Lahaman ya yiwa matarsa Fyade kuma yana gamawa da ita ya zare wuka ya lumamata a ciki,take ta sulale kasa matacciya.Koda sarki Hilairu yaga na kashe masoyiyarsa sai shima ya sulale kasa sumamme,Lahaman ya bushe da dariya,ya dubi yaransa yace"ku kama shi ku saka masa sarka ya zama bawana,nine bakin dare mai mayar da sarki nawa. idan baku mantaba kwanakin baya mun fara littafin sai muka tsaya kasancewar sa incomplete ne. Banaso sai ya dauko dadi kuma a katse shi babu dadi shiyasama na daina post din sa. Ammana yanxu alhamdulillahi yasani complete din sa har karshe yadda zamuji dadin sa. Nafara post ne daga farko saboda nasan mostly ba'a karanta ba saboda daukan lokaci. Da fatan littafin yayi... Suleiman zidane Kd Whatsapp no 08161272634 SA MAZA GUDU littafi na daya(1) Part B Lahaman ya dubi yaransa yace "ku kamashi kusaka masa sarka ya zama bawana,nine bakin dare mai mayar da sarki bawa,kuma nine GUGUWAR ANNOBA mai zuwa babu sallama.Haka dai yarima Lahaman yayita yiwa kansa kirari,har suka gama kama bayin dasuke bukata kimanin dubu hudu maza da mata a cikin wannan karamin gari,bayan sun kone gidaje da yawa sun kwashe dukiyoyi da yawa,nan take suka tusa keyar bayin harda sarki Hilairu suka fice daga birnin mai suna Baitul Laharas suka juyi suka nufi kasar Madinatul Zauwara. Bisa al'adar yarima Lahaman duk macen da yayiwa fyade take yake kasheta,har a birnin Madinatul Zaurawa kowa ya sanshi da wannan muguwar dabi'a.Saida sarki Sharkuf ya kafawa Yarima Lahaman doka cewa idan ya sake yiwa wata 'ya mace fyade ko ya kasheta zai cireshi daga matsayin yarima kuma ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai a kurkuki,sannan matan birnin suka samu nutsuwa da kwanciyar hankali.Bakomai ne yasa Yarima Lahaman ya tsani mata ba yake yi musu fyade kuma ya kashe su ba,sai saboda kiyayyarsa da da 'yar uwarsa gimbiya Malika itama tasan hakan kuma yin hakan da yake yi ne yasa taji ta dada tsanarsa fiye da kowa a duniya. Da yammaci ne sakaliya Yarima Lahaman ya shigo cikin birnin madinatul zauwara tare da rundunarsa ta mayaka da kuma bayin daya kama a daure cikin sarka nan bugunsu da bulala ana ingiza su,kai da ganin bayin kasan cewa sunja bakar wahala,domin duksun rame akwai alamun sunsha yunwa a wanannar doguwar tafiya da sukayi,shi kuwa sarki Hilairu sau uku yana yunkurun kashe kansa saboda bakin ciki amma dakarun Lahaman na hanshi da karfin tsiya su tattakashi cikin wulakanci da muzantawa ,duk sa'adda sarki Hilairu ya tuna cewa an kashe masa matarsa Zailat wacce yake matukar SO DA KAUNA,kuma ya tuna cewa an rabashi da mulkinsa,dukiyarsa,kuma shi da jama'arsa da yawa an maishe dasu nayi,dakarunsa na yaki kuwa kusan gaba dayansu aka kashe.ko ina a cikin birnin nasa gawarwakine da jini,sai ya fashe da matsanancin kuka yaji ya tsani kansa da rayuwarsa gaba daya. Sarki Hilairu ya kasance Kyakkyawan saurayi abin kwantance mai kwarjini da haiba irin ta sadaukai amma ko kadan bai kasance jarumi ba,kuma bai taba yin yakiba a rayuwarsa,sarautar ma tsintarta yayi a sama ba gado yayi ba.Sarkinsu na da bashi da 'da ko jika,kuma bashi da wani dan'uwa face Hilairu.Mahaifiyar Hilairu ta kasance Kuyangar Sarkin da ya mutu,don haka shi dan baiwane,ba dan wata 'yantacciya ba,ta haka ne ya gaji wannan sarauta. A daidai wannan lokaci yarima Lahaman ya shigo cikin birnin madinatul zauwara sai akayi akasi gimbiya Malika ta fito rangadi zata fita izuwa bayan gari domin yin parauta a daji.A wannan lokaci tana tare da tsirarun dakaru wandan basu fi su arba'in ba.A daidai kofar shiga cikin birnin sukayi kicibus.A wannan lokaci yarima Lahaman na cikin tsananin farinciki bisa ganin dinbin dukiyar daya samo wacce baitaba samun kamartaba,gami da lafiyayyun bayin da yasan cewa zai siyar dasu da darajar gaske.Koda yarima Lahaman da gimbiya Malika suka hadu sai kowannensu ya murtuke fuska suka bata rai kamar an aiko musu da sakon mutuwa,da ko magana basayi da juna.Koda Gimbiya Malika ta dubi tarin dukiyar da Yarima Lahaman ya samo gami da tarin bayi,sai takaici ya kamata saboda tasan ce Allah ne kadai yasan irin mugun zaluncin da akayi wajen samosu, Kwatsam sai idanun Malika suka kai kan sarki Hilairu,tana hada ido dashi sai zuciyar ta ta buga da karfi nan take a karon farko a rayuwarta taji ta kamu da tsananin son 'da namiji don haka batasan sa'adda ta kura masa idanuba har suka gifta juna tana waigensa.Abinda ya kara mata sonsa mashi ne shima ya kura mata idanu,cikinalamun tsananin kaduwa da mamaki,har ya tsaya cak ya daina tafiya sai da aka buga masa kulki aka hankadashi gaba yana turjewa na dada bugunsa sannan ya janye.Ashe ba wani abu ne yasa Sarki Hilairu ya kura mata idanu ba face kamanninta yazo iri daya sak da matarsa wacce yarima Lahaman ya kashe tamkar an tsaga kara.Dama tun acan birinin na sarki Hilairu yaran Lahaman suka yita tsegumin suna cewa matar sarki Hilairu tana kama da Gimbiya Malika.Yana daga cikin dalilin ma da ysa Yarima Lahaman ya kasheta,tun da ya tsani Malika,Ya tsani duk mai kama da ita.Har su yarima Lahaman suke kule gimbiya Malika bata daina waigensu ba,kuma zuciyarta bata daina bugawa ba,da zafi,nan dai ta kudurci aranta cewar ta kowanne hali sai ta mallaki wancan bawa wanda ita yanzu ta kamu da tsananin son sa farat daya a farkon haduwa.Babban tashin hankalin ta shine tasan cewa ko nawa zata siyeshi yarima Lahaman bazai siyar mata ba,saboda kiyayyar dake tsakaninsu. Al'amarin Yarima Lahaman kuwa lokacin da yaga gimbiya Malika ta fito rangadi daga cikin gari tare da tsirarun dakaru,sai wani abu ya fado masa a rai.Nan take yayi tunanin ya batar da kamanninsa ya dawo cikin dajin ya afkawa masu tsaronta,amma sai wata zuciyar tace dashi a'a,yin hakan abune mai matukar hadari,domin idan asirinsa ya tonu ba zatayi masa kyauba.Domin akwai lokacin da kwatankwacin hakan ta faru da kyar ya samu kubuta daga zargin sarki. Al'amarin ya faru ne wata rana sa'adda ana zaune a fada,duk su biyun shida Gimbiya Malika suna zaune a fadar tare da sarki,Malika na daman Sarki shi kuwa yana hagunsa,sai ga wani mai gadin kofar gari ya shigo cikin fadar a guje cikin gigita,da zuwansa sai ya zube kasa gaban sarki ya kwashi gaisuwa,muryarsa na rawa kuma kansa a sunkuye ya bude baki yace,"Ya shugabana,kayi sani cewa muna kan aikinmun na gadin kofar gari kawai sai muka hango ...... By Suleiman zidane kd Whatsapp 08161272634 SA MAZA GUDU Littafi na Daya(1) Part C Yace,ya shugabana kayi sani cewa muna kan aikinmun na gadin kofar gari kawai sai muka hango wadansu bakin dakaru acikin shigar bakaken kaya,bisa dawakai sun rufe fuskokinsu sun nufo kofar gari,koda muka hango su muka yunkura zamu busa kahon yaki,sai suka ja baya suka nausa cikin daji suka bace bat tamkat basu taba wanzuwa ba.Bisa wannan dalili ne yasa muka kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali,shi yasa muka ga ya dace muzo mu sanar da kai domin kasan matakin da ya kamata a dauka.Kodajin labarin,sai sarki Sharkuf ya bushe da dariya,sannan yace,ai kuwa tasan gidan mai babbar sanda,tsoro suka ji shi yasa suka juya da baya.To amma akwai wani boyayyan al'amari a tare dasu,domin ko da wasa ba'a taba samun 'yan fashi ko 'yan harin da suka taba kusantar kusa da kofar garin nan ba,saidai suyi shawagi a can wajen gari ciki dazuzzuka,lallai ruwa baya tsamin banza,kuma da dan gari akanci gari.Akwai wani munafuncin da ake shiryawa tare da waninmu.Koda gama fadin haka,sai sarki ya dubi yarima Lahaman yace,ya kai yarima,maza ka dibi dakari dubu kuje ku bi sawun wadannan dakarun sumame,idan sun fice daga yankin kasata ku kyalesu,idan kuma suna ciki ku yakesu ku kashe su,kada kubar mutum daya ya tsira da rayuwarsa.Koda jin wannan umarni,sai yarima Lahaman ya mike tsaye zumbur da nufin yaje yayi shiri,amma sai Gimbiya Malika ma ta mike zumbur tasha Gabansa tace,ya akai da'uwana ina rokonka ka tafi tare dani,domin idanuna suna son ganin ko suwaye wadannan marasa kunya da rashin tsoro har suke tunanin zasu iya kawo mana hari.Koda jin haka,sai kowa ya cika da mamaki a fadar musamman ma sarki Sharkuf wanda a saninsa ko magana Yarima da Gimbiya basayi,amma yau wai itace ke rokonsa akan ya tafi da ita wajen gari don yakar abokan gaba.Lokacin da yarima Lahaman yaji bukatar gimbiya,sai ya dubi sarki domin yaji ta bakinsa ko zai amince ya tafi da itan,Bisa ga mamaki sai gashi sarki ya Amince.Abin ya baiwa kowa mamaki a fadar,soboda ansan cewa a duniya babu abinda sarki Sharkuf ke so sama da gimbiya Malika,kuma baya yarda taje wani wuri mai hadari,kuma yasan irin kiyayyar dake tsakaninta da dan'uwanta Yarima Lahaman,to amma me yasa yanzu ya amince ya tafi tare da ita izuwa yaki?Ita kanta Gimbiya Malikan saida ta yiwa kanta wannan tambayar a cikin zuciyarta,nan dai Malika tabi Yarima Lahaman a bya cikin farinciki suke fice daga cikin fadar.Suna fita Lahaman yayi shigar yaki ya tara dakaru dubu sukayi hawa itama Malika sai aka kawo mata nata dokin ta hau suka fice daga cikin gidan sarautar suka nausa cikin dajin suna masu bin sawun dawakan da suka gani.Koda suka iso wani wuri inda hanya ta rabu biyu,sai Lahaman yaja limzamin dokinsa ya tsaya cak yayi nazarin hanyoyin sannan ya juya ya dubi gimbiya Malika yace,Daki tsaya anan ke da rabin dakaruna dan tabbar da tsaron lafiyarki,ni kuma da sauran dakarun zamu shiga ciki harsai mun isa inda wadannan abokan gaba suka buya.Kodajin wannan batu,sai Malika ta ce a'a ba haka za'ayiba,ai yanzu baka da tabbacin cewa hanyar da zakabi can abokan gabar suke,saidai muma mubi daya hanyar idan muka riske su,sai mu yakesu,in kuma kaine ka riskesu ka yakesu.Sa'adda yarima Lahaman yaji wannan batu,sai yayi murmushi yace ,idan wani tsautsayi ya sameki kada kiga laifina tunda dai ni ga inda nace ki tsaya kuma kika ki.Malika ta maidawa Lahaman martanin Murmushin tace,Saki ranka tamkar tsumma a randa domin shi kansa tsautsayin baya zuwa kusa da Malika,in kuwa yazo saidai ya shafi waninta amma ba ita ba.Anyi gumurzu a cikin dajin an kashe gaba dayan dakarun dake tare da Malika amma ita ta tsira da rayuwarta da lafiyarta,aka dawo gida da kyar yarima ya kubuta daga zargin sarki,bayan yasa tambayoyi har yana hada gumi duk da yarima yayi wannan tunanin sai ya kudirce a ransa sai ya dawo cikin dajin ya kashesu farat daya,sannan itama ya kasheta,kuma ya alakanta mutuwarta da 'yanfashi ko miyagun dabbobin daji. Abu na biyu kuma da ya fado masa a rai shine koda bai kasheta ba,to lallai bazai bari ta mallaki wannan bawa nasa ba wato sarki Hilairu saboda ya lura da irin kallon da take masa ya gane cewa ta kamu da sonsa.Lokacin da yarima Lahaman ya isa gida sai ya ware bayi maza guda saba'in mata guda talatin wadanda sune mafi lafiya,da kwarjin da kyawu.Yasa aka kaisu can wani gida nasa na musamman wanda ba kowa bane yasan da shi,aka boye su a can da zummar cewa baza'a sake fitowa dasuba sai ranar da babbar kasuwar birnin take ci,domin ya sayar dasu da daraja ga manyan attajirai.Daga cikin bayin gudu darin kuwa harda sarki Hilairu. Sa'adda aka kai su Hilairu wannan gida aka watsa su izuwa cikin daki,sai suka ga an kawo musu abinci da abin sha lafiyayye,wanda rabonsa da su ci irinsa yafi kwana arba'in tun kafin akawowa birninsu Hari.Nan fa bayin suka rude suka kama wawason abincin suna ci kamar dabbobi,mazansu da matansu har suna kokawa.Shi kuwa sarki Hilairu sai ya zuba musu idanuwa kawai yana kallonsu shashashu.Ya rike kimarsa ta sarki kuma yaki neman abincin dukda yunwar yakeji.Kawai sai ya koma gefe daya ya zauna ya daga kansa sama yana tunani.Ba komai yake tunowa ba face fuskar gimbiya Malika.Take ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa yace,wai shin matata bata mutu ba ko kuwa wacce na gani dazu aljanace,da har zata biyo ni tana dada yaudarata?Ashe yarima Lahaman yasa dakarunsa su zuba ido sosai akan sarki Hilairu saboda kada ya kashe kansa ko yayi yunkurin guduwa ko kuma a turo a sace shi.Sarki Hilairu na zaune cikin wannan hali na tunani sai daya daga cikin bayin wani katon matashi mai...... By Suleiman zidane kd Whatsapp 08161272634 #SAS SA MAZA GUDU Littafi na daya(1) part D Sarki yasan wannan takobi sosai tunda shi ne ya baka ita da hannunsa lokacin daya raba mana takubba gaba dayanmu mu tara.Ko ka manta ne,shaidata ta biyu shine raunmin dake jikin mu ni dakai,idan na fadawa sarki cewar mun fafata kayimin rauni a hannu ni kuma nayi maka a kafada.Za'a duba aga raunin namu kaga kenan dole ya gamsu cewa kayi kokarin hallakani.Idan haka ta faru kuwa kasan cewa sarki zai cire ka daga matsayinka na Yarima kuma sai ka tafi kurkuku.Koda Malika tazo daidai nan a zancenta,sai hankalin Lahaman ya dugunzuma ainun gashi a wannan lokaci jiri ya fara dibarsa sakamakon jinin da ke zuba a jikinsa.Ita kuwa nata raunin karami ne jinin da ya zuba kadanne don haka ya tabbatar cewa idan suka cigaba da yakin cikin kankanin lokaci zata sami nasara akansa.cikin mugun Takaici Lahaman ya dubi Malika yace,mene me abinda kike bukata a wajena?Malika tayi murmushi a karo na biyu tace,A cikin bayin daka zo dasu akwai wani saurayi wanda babu kamarsa a kyau da kwarjini yana da siffa irin ta sarauta.Ina son ka siyar mini da wannan bawa,idan kayi haka zan rufe asirinka bisa wadannan dakarun da ka kashe,nace 'yan fashi ne suka kawo mana hari na fatattakesu.Koda Malika tazo nan a zancenta,sai Yarima Lahaman yayi shiru yana tunani da nazari,ba komai yake tunani ba face hanyar da zai bi ya yaudari Malika ya nuna ya amince amma yabi hanyar da a karshe zai hanata mallakar wannan bawa,amma sai ya kasa samun mafita.Kawai sai ya dago kai ya dubi Malika a karon farko a rayuwarsa yayi mata murmushi yace,To kanwata yau kinyi nasara akaina amma ki saurari ranar da zan dauki fansa.Ki sameni a gidana na can bayan gari da yammaci muyi cinikin wannan bawa ki biya ki tafi dashi.Koda jin wannan batu,sai Farinciki ya kama Malika ta ruga ta kama wani doki ta zabureshi da gudu ta nufi cikin gari. A can kuma gidan sarauta kuwa,koda sarki Sharkuf yaga lokacin da Malika ta saba dawo gida daga farauta ya wuce sosai,sai Hankalinsa ya tashi,nan take ya tura aka kirawo sarkin yaki,ya tambayeshi yace dakaru na wane suka yiwa gimbiya rakiya izuwa farautar?Cikin Alamun damuwa sarkin yaki ya sunkui da kansa kasa yacemya Shugaba ai dakaru Arba'in ne kacal.Koda jin haka sai sarki sharkuf ya dakawa sarkin yaki tsawa,ya rufe shi da fada,yana mai cewa ai wannan ganganci ne kabar gimbiya ta tafi daji farauta tare da dakaru Arba'in kacal.Alhalin kasan cewa wasu lokutan 'yan fashi na iya kawo harin sumame.Cikin tsananin fishi sarki sharkuf ya dubi wani hadiminsa yace,yaje ya dauko masa kayan yakinsa da dokinsa da kansa zaije ya dubo gimbiya.Koda jin haka sai sarkin yaki ya zube kasa bisa guiwowinsa ya kama tuba yana mai rokon sarki ya hakura shi zaije ya dubota yanzu.Gama fadin hakan ke da wuya sai sukaji sukuwar doki,suna waigawa suka hango gimbiya Malika ce ta shigo cikin gidan sarautar ita kadai bisa doki kuma ga rauni akan damtsen ta na hagu.Cikin firgici sarki sharkuf ya ruga gareta ya ruke mata dokin ta sauko ya rungumeta sannan ya goyata a bayansa ya ruga da ita zuwa cikin gidansa yana mai kwalawa likitansa kira,kai kace wani mugun raunine a jikin nata.Sarki sharkuf bai sauke Malika a ko ina sai akan gadonsa cikin kuryar turakarsa,nan take likitansa yazo ya duba raunin nata,ya dubi sarki yace,ya shugabana ai raunin ma karamine ba sai anmata dinkin ba,mahani za'a samata.Nan take likitan ya gama aikinsa ya fice.Fitarsa ke da wuya Sarki yasa aka kawowa gimbiya abinci da ababan sha na alfarma.Da hannunsa ya shiga ciyar da ita har ta koshi,sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace,yake 'yata bani labari mene ya faru gareki har kika sami wannan raunin kuma ina dakarun dake tsaron lafiyarki,su arba'in?Koda jin wannan tambaya,sai Gimbiya Malika tayi Murmushi tace,kwantar da hankalin yakai abbana,kayi sani cewa duk irin hadarin da zan shiga zan iya kare kaina koda kuwa bana tare da dakaru.Koda jin haka,sai mamaki ya kama sarki yace,tayaya zaki iya kare kanki alhalin baki iya yaki ba?Dajin haka,sai Malika ta mike tsaye taje ta zaro wadansu takubba guda biyu dake jikin bango a rataye ta jefawa sarki guda ya cafe,tace,tashi ka jarraba jarumtakar 'yarka yau kasha mamaki.Koda jin haka,sai sarki Sharkuf ya mike tsaye yana murmushi gami da yi mata kallon mara hankali yace,haba 'yata wai shin anya kuwa yau ba Aljanu bane suka shafeki acikin daji?Ta yaya kike tunanin zaki iya tarata da yaki alhalin ko yayanki Yarima Lahaman da yazamo jarumin da babu kamarsa a wannan nahiyar,ya kara dani baiji dadi ba.Malika ta maidawa masa da Martanin murmushin tace,ai sarko goma zamani goma,ni yanzu karfina ya kawo kuma na dade ina yiwa kaina tanadi.Tana gama fadin haka sai ta juya tayi tafiya gaba daku goma da yake turakace mai girma da fadin gaske.Daga inda ta tsaya sai kawai sarki yaga Malika ta dako tsalle a sama tamkar an harbata daga cikin baka,kafin ya ankara ta kawo masa wawan sara aka.Cikin bakin zafin nama sarki sharkuf ya yunkura ya daga takobinsa dake hannunsa ya kare saran amma saboda karfin saran da nauyinsa sai da ya dan durkushe kasa rawaninsa ya tuje.Al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan ya mike tsaye ya koma gefe daya yana mai motsa dukkan gabban jikinsa domin shirin fara yakarta.Nan take murmushi ya subucewa sarki sharkuf ya juya ya fuskanci malika yace,yaya akayi kika koyi yaki amma bansani ba?Kabari sai mun gama motswa jikin na baka labari.Kawai sai Malika ta sake rugowa izuwa kan sarki suka sake ruguntsumewa da masifaffan yaki tamkar sun kasance tsofaffin abokan gaba ya zamana cewa suna kaiwa junansu SARA DA SUKA cikin zafin nama,juriya,bajinta da jarumta.Nan da nan suka fara lalata duk kayan kawar dake cikin turakar.Karar takubbansu kuwa ya firgita dakaru,suka rugo da gudu izuwa cikin turakar rike da makamai tsirara domin zatonsu wasu 'yan simame ne suka hauro cikin gidan sarautar.Amma duk wanda ya shigo cikin turakar sai yaga ashe sarki ne da Malika suke yaki.Sai ya kamu da tsananin Mamaki ya koma gefe daya ya rakube yana kallon ikon Allah,amma da yakin ya sake nutsuwa sai kallon ma ya gagara ,kuma hankali ya dugunzuma domin tun suna gumurzu a cikin kuryar daki saida suka dawo babban falo,daga nan suka fito waje,sai gasu a cikin harabar.Ba komai ne ya dugunzuma hankalin gaba daya jama'ar dake cikin gidan sarautar ba face ganin yadda sarki da Malika ke kaiwa junansu mugayen hare hare irin na abokan gabar dake son hallaka juna farat daya.Lokacin da aka shafe rabin sa'a ana wannan dauki na dadi,sai sai salon fadan ya sauya domin a sannan ne gimbiya Malika ta gane cewa ruwa ba sa'an kwando bane saboda ji tayi alamun ta fara gajiya har takai cewa da kyar take iya tare saran sarki saboda Karfinsa da nauyinsa.Duk sa'adda ya kawo mata saran ta tare sai taji kamar katon dutse ya kwado mata.Amma saboda bakin naci da muguwar juriya taki yarda ya fadi kasa kuma bata daina yunkurin maida martani ba.Duk da cewa wani lokacin har durkushewa kasa take bisa guiwarta amma sai kaga ta mike zumbur a haka.Saida suka sake shafe wata rabin sa'ar bataje kasa ba,amma kuma ta gaji likis.Ana cikin haka ne sarki ya shammaci Malika ya kwarfi kafafunta a tayi sama da baya taje ta gwara bayanta a jikin katangar gidan sarautar ta fado kasa a mutukar galabaice ta kasa tashi.Koda faruwar hakan,sai sarki Sharkud ya sauke takobinsa kasa yayi jifa da ita sannan ya kama yiwa Malika tafi.Nan fa gaba dayan Jama'ar gidan sarautar suka kama yiwa Malika tafi.Sarki Sharkuf ya nufo Malika fuskarsa cike da murmushi yazo daf da ita ya mika mata hannu ta kama,ya tashe ta tsaye suka rungume juna,sannan ya janye jikinsa daga cikin nata ya dubeta yace,Ina tayaki murna saboda kece jaruma ta farko wacce ta iya jure yin gumurzu dani har tsawon sa'a guda.Hatta yayanki Yarima Lahaman da kyar ya jure tsawon rabin sa'a.Bani labari yake 'yata yaya akayi kika iya yaki haka da jarumtaka?Koda jin wannan tambaya,sai Malika tayi Murmushi sannan ta zaiyana masa a wuraren da ta koyo yaki kamar yadda ta gayawa Yarima Lahaman,lokutan da take fita ziyara kasashe.A karshe ta kara da dace batun Jarumtaka kuwa ai kaima kasan cewa barewa batayi gudu ba danta yayi rarrafe.Na gaji sadaukantaka ne a wajenka da wajen kakana na uwa.Koda jin wannan batu,sai Sarki Sharkuf ya kyalkyale da dariya yace,Tabbas maganarki dutse ce,to naji wannan yaya kuma batun wannan rauni dake hannunki da kuma batun dakarun da suka yi miki rakiya izuwa farautar?Koda jin wannan tambaya,sai Malika tayi ajiyar zuciya tace,'yan fashi ne suka kawo mana harin bazato kafin muyi wani yunkuri sun kashe gaba daya dakarun nawa.Ni kuwa saina afka musu muka ruguntsume da azababban yaki.Da suka ga nafi karinsu,sai suka girgiza suka bace bat na nemesu na rasa.Lokacin da Malika tazo nan a zancenta,sai taga sarki yayi mata wani irin kallo na rashin yarda sannan yace,yake 'yata ta yadda naga irin jarumtakarki a yanzu babu wasu 'yanfashi a wannan nahiyar da zasu tareki da yaki batare da kin samu nasarar kashe koda mutum dayaba daga cikinsu a cikin dakiku kadan bare harma wani daga cikinsu ya sami nasarar yi miki wannan raunin.Shin yanzu idan akaje wajen da kukayi gumurzun za'a sami gawar koda mutum daya daga cikinsu?koda wannan tambaya sai Malika ta gyada kai tace,Ai muna fara yakin suka bace kawai sa'a ce tasa shugabansu yayi nasarar yimini wannan rauni.Sarki Sharkuf yayi dan guntun murmushi mai nuna alamun rashin yarda,sannan ya dubi Malika yace,A nahiyar nan gaba daya mutum daya ne zai iya fafatawa dake ya samu nasarar yi miki wannan rauni,kuma ba wani bane face dan'uwanki Yarima Lahaman.Fada min gaskiya shine Lahaman yakai miki harin bazato ne?Malika ta girgiza kai tace, Ina mai tabbatar maka da cewa a nahiyar nan tamu kaf babu wata bafatakiya data kaini arziki da kayan abinci da makaman yaki fiye da harkar fataucin bayi.Ka sani cewa a yanzu na gano cewa fataucin bayi wahala ce kawai.Kudi na cikin fataucin abinci da makaman yaki,duk inda naji labarin ana yin yaki a duniya to fa nan nake ratsawa da karfin tsiya nakai tallan hajata izuwa ga kasashen dake yakar juna kuma bani da bangare kowa na wane.Ka sani cewa a halin yanzu ina da rijiyar dinare masu zurfin RIJIYA GABA DUBU guda dari bakwai.Guda dubu uku kuma inada rijiyoyin dinare masu zurfin gaba dubu cike da lu'u lu'u,guda cikin kogon na bude rijiyoyin da wadansu mukullai na musamman wadanda dole saida su za'a iya budewa komai jarumtakar mutum da aljan kuwa,ka sani cewa ban tara dukiya domin komai ba sai domin na kare mutuncina dana jama'ar kasar nan saboda nasan cewa duk ranar da babu kai ya zamana cewa Yarima Lahaman ne sarki zai iya yunkurin wulakantani ko cutar dani da sauran talakawa.Amma a yanzu nayi wannan gagarumin shiri nafi karfin wulakancinsa,kuma zan iya kare kaina da jama'a idan naso ma zan iya fita wajen gari nasa a gina mini fada ta musamman inda zamu zauna cikin kwanciyar hankali tare da mahaifiya da sauran masoyana har izuwa karshen rayuwa.Sa'adda Malika tazo nan wa jawabinta,sai mamaki ya turnuke sarki Sharkuf kuma ya kamu da tsananin farin ciki ya kama kafadunta ya ruke yace,Yake 'yata na rantse da gemun ubana tunda ake haihuwa acikin zuri'ar wannan gidan sarautar nami ba'a taba samun mai basira da hangen nesa kamarki ba.Wannan shirin da kikayi yayi daidai amma kisani cewa akwai sauran rina a kaba,duk wannan dukiyar dakika tara wacce kike ganin cewa tana da yawa to bata kai kaso daya ba cikin kaso goman wacce ni na tara,kuma na boyeta a inda babu wanda ya sani,kuma babu wanda ya taba jin labarinta sai ke a yau,idan na mutu sai kowa yasan wannan dukiya da kuma inda take.Kuma idan har dan'uwanki Yarima Lahaman ya riga ki sanin inda take yaje ya mallake ta,kashinki ya bushe,domin ya sami damar da zai iya ganin bayanki,babban bakin ciki na a doron kasa shine ko a bayan raina ace dayanku ya kashe dan'uwansa wannan abin gori ne dazai ta bibiyar zuri'armu har abada,duk abinda Lahaman zai miki kada kiyi yunkurin kashe shi,saidai kiyi duk yadda zakiyi ki kare kanki daga dukkan sharrinsa.Abu na karshe dana keso ki sani shine har a cikin zuciyata bani da zabi a tsakaninku bisa wanda zai gajeni na barwa kaddara ta riga fatar wannan.Koda jin wannan batu,sai idanun suka ciko ta kwalla tace,haba ya kai abbana ko yanzu idan babu kai kuma baka bar wasiyar wanda zai gajeka ba a tsakaninmu yaya za'ayi kenan?Sarki Sharkuf yayi shiru yana mai ajiyar zuciya sannan ya dago kai ya dubeta da yanayi mai nuna tsantsar damuwa,yace ko a yau na fadi na mutu yan majalisata sun san yadda zasu yi su fitar da wanda ya dace ya zama ya gajeni daga cikinku.Sau daya irin haka ta faru a wannan gidan sarauta a zamanin mahaifina wato su biyu ne wadanda suka cancanci sarautar kuma acikinsu aka fitar da gwani ya zamana cewa mahaifin nawa ne ya zama sarki..Malika ta kama hannun sarki Sharkuf tace,to baka sanar dani yadda aka warware wannan matsalar ba tunda da akwai alamun cewa nima zan tsinci kaina a cikin hakan? Sarki Sharkuf ya gyada kai yace,kamar yadda bazan iya sanar da dan'uwanki ba haka kema bazan iya sanar dake ba,saboda an bar al'amarin sirri a cikin wannan gidan sarauta,in kuwa na gaya miki tamkar na gaya miki sirrina da zaki sami nasarar zama sarauniya ne alhalin so ake kowannenku cancantarsa akeso ta kaishi ga matsayin.Aikin dake gabanku da yarima Lahaman ba karami bane,yanzu dai mu manta da wannan batu mu koma kan batun tafiyar dake gabanki nan da cikar kwana uku.Shin tunda yanzu nasan dalilin yin wannan tafiya taki bazaki hakura ba ki zauna tare dani in yaso ki tura amintattun yaranki su wakilceki?Koda jin wannan batu sai Malika ta dubi sarki Sharkuf cikin alamun mamaki tace,me yasa baka son nayi wannan tafiya alhalin na saba yinta kuma baka taba hanani ba sai yau?Koda jin haka,sai sarki Sharkuf ya mik By Suleiman zidane kd Whatsapp 08161272634 SA MAZA GUDU LITTAFI NA DAYA 1 Ina mai tabbatar maka da cewa a nahiyar nan tamu kaf babu wata bafatakiya data kaini arziki da kayan abinci da makaman yaki fiye da harkar fataucin bayi.Ka sani cewa a yanzu na gano cewa fataucin bayi wahala ce kawai.Kudi na cikin fataucin abinci da makaman yaki,duk inda naji labarin ana yin yaki a duniya to fa nan nake ratsawa da karfin tsiya nakai tallan hajata izuwa ga kasashen dake yakar juna kuma bani da bangare kowa na wane.Ka sani cewa a halin yanzu ina da rijiyar dinare masu zurfin RIJIYA GABA DUBU guda dari bakwai.Guda dubu uku kuma inada rijiyoyin dinare masu zurfin gaba dubu cike da lu'u lu'u,guda cikin kogon na bude rijiyoyin da wadansu mukullai na musamman wadanda dole saida su za'a iya budewa komai jarumtakar mutum da aljan kuwa,ka sani cewa ban tara dukiya domin komai ba sai domin na kare mutuncina dana jama'ar kasar nan saboda nasan cewa duk ranar da babu kai ya zamana cewa Yarima Lahaman ne sarki zai iya yunkurin wulakantani ko cutar dani da sauran talakawa.Amma a yanzu nayi wannan gagarumin shiri nafi karfin wulakancinsa,kuma zan iya kare kaina da jama'a idan naso ma zan iya fita wajen gari nasa a gina mini fada ta musamman inda zamu zauna cikin kwanciyar hankali tare da mahaifiya da sauran masoyana har izuwa karshen rayuwa.Sa'adda Malika tazo nan wa jawabinta,sai mamaki ya turnuke sarki Sharkuf kuma ya kamu da tsananin farin ciki ya kama kafadunta ya ruke yace,Yake 'yata na rantse da gemun ubana tunda ake haihuwa acikin zuri'ar wannan gidan sarautar nami ba'a taba samun mai basira da hangen nesa kamarki ba.Wannan shirin da kikayi yayi daidai amma kisani cewa akwai sauran rina a kaba,duk wannan dukiyar dakika tara wacce kike ganin cewa tana da yawa to bata kai kaso daya ba cikin kaso goman wacce ni na tara,kuma na boyeta a inda babu wanda ya sani,kuma babu wanda ya taba jin labarinta sai ke a yau,idan na mutu sai kowa yasan wannan dukiya da kuma inda take.Kuma idan har dan'uwanki Yarima Lahaman ya riga ki sanin inda take yaje ya mallake ta,kashinki ya bushe,domin ya sami damar da zai iya ganin bayanki,babban bakin ciki na a doron kasa shine ko a bayan raina ace dayanku ya kashe dan'uwansa wannan abin gori ne dazai ta bibiyar zuri'armu har abada,duk abinda Lahaman zai miki kada kiyi yunkurin kashe shi,saidai kiyi duk yadda zakiyi ki kare kanki daga dukkan sharrinsa.Abu na karshe dana keso ki sani shine har a cikin zuciyata bani da zabi a tsakaninku bisa wanda zai gajeni na barwa kaddara ta riga fatar wannan.Koda jin wannan batu,sai idanun suka ciko ta kwalla tace,haba ya kai abbana ko yanzu idan babu kai kuma baka bar wasiyar wanda zai gajeka ba a tsakaninmu yaya za'ayi kenan?Sarki Sharkuf yayi shiru yana mai ajiyar zuciya sannan ya dago kai ya dubeta da yanayi mai nuna tsantsar damuwa,yace ko a yau na fadi na mutu yan majalisata sun san yadda zasu yi su fitar da wanda ya dace ya zama ya gajeni daga cikinku.Sau daya irin haka ta faru a wannan gidan sarauta a zamanin mahaifina wato su biyu ne wadanda suka cancanci sarautar kuma acikinsu aka fitar da gwani ya zamana cewa mahaifin nawa ne ya zama sarki..Malika ta kama hannun sarki Sharkuf tace,to baka sanar dani yadda aka warware wannan matsalar ba tunda da akwai alamun cewa nima zan tsinci kaina a cikin hakan? Sarki Sharkuf ya gyada kai yace,kamar yadda bazan iya sanar da dan'uwanki ba haka kema bazan iya sanar dake ba,saboda an bar al'amarin sirri a cikin wannan gidan sarauta,in kuwa na gaya miki tamkar na gaya miki sirrina da zaki sami nasarar zama sarauniya ne alhalin so ake kowannenku cancantarsa akeso ta kaishi ga matsayin.Aikin dake gabanku da yarima Lahaman ba karami bane,yanzu dai mu manta da wannan batu mu koma kan batun tafiyar dake gabanki nan da cikar kwana uku.Shin tunda yanzu nasan dalilin yin wannan tafiya taki bazaki hakura ba ki zauna tare dani in yaso ki tura amintattun yaranki su wakilceki?Koda jin wannan batu sai Malika ta dubi sarki Sharkuf cikin alamun mamaki tace,me yasa baka son nayi wannan tafiya alhalin na saba yinta kuma baka taba hanani ba sai yau?Koda jin haka,sai sarki Sharkuf ya mike tsaye yayi tafitaku uku,yana mai juya mata baya,sannan yace yake 'yata kiyi sani cewa ni fa yanzu girma ya fara kamani tunda yanzu shekaruna sunkai sittin da takwas a duniya bana son naga kina yin nisa dani tunda kullum lokacina karewa yake,kuma har yanzu akwai sirrikana da dama wadanda baki sansu ba,asali ma dan'uwanki Yarima Lahaman ya fiki saninsu saboda ya girmeki sosai kuma na jashi a jikina daga kuruciyarsa kawo izuwa girmansa kafin na fahimci cewar shi azzalumine wanda baya kishin talakawansa na gujeshi.Lokacin da Sarki Sharkuf yazo nan a zancensa sai hawaye ya subuto masa gimbiya Malika ta sake dafe hannun sarki akan cinyarta ta dubeshi tace,ya kai abbana kamar yadda bakasan rabuwa dani daidadi da rana daya haka nima na kasance,amma ina rokonka alfarmar nayi wannan tafiya domin itace tafiyata ta karshe akan harkokin kasuwancina kuma acikin tane nake so na cika wani buri nawa wanda bani da kamarsa a raina.Kayi hakuri bazan iya gaya maka wannan sirrin ba kamar yadda kaima bazaka iya gayamin hawa KARAGAR MUKIN kasar nan ba,amma zaka san nawa burin da zarar na dawo kuma nayi maka alqawain cewa bazan fi wata uku ba zan dawo.koda jin wannan batu,sai shima sarki Sharkuf hawaye ya zubo masa ya kamota ya rungumeta a kirjinsa suka dan jima a kankame da juna.Suna cikin wannan hali ne Malika taji an kirawo sunata,a tare suka waiga baya. SHIN WANENE WANDA YA SHIGO MUSU BATARE DA NEMAN IZINI BA? SARKI SHARKUF ZAI BAR GIMBIYA MALIKA TAYI WANNAN TAFIYAR? YARIMA LAHAMAN ZAI BATA WANNAN BAWAN? INA LABARIN BAWAN DA YARIMA LAHAMAN YA KAMO? TSAKANIN GIMBIYA MALIKA DA YARIMA LAHAMAN WAYE ZAI GAJE KARAGAR MULKIN SARKI? MU HADU A CIKIN LITTAFI "SA MAZA GUDU" LITTAFI NA BIYU(2) DON JIN WADANNAN AMSOSHI. AMMA MENE HASASHEN KU?. By Suleiman zidane kd Whatsapp 08161272634