*MUJARRABI* ( Age is just a number) A 2024 novel By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 The writer of Wa ya fi so na? ❤️ Ƴar gwoggo RUƊIN ZUCIYA 💔 2024 And now *MUJARRABI* (A destiny love story) _Wannan littafin ƙirƙirarren labari ne, banyisa dan muzantawa kowa ba in dai yazo daidai da labarin rayuwar mutum amin afuwa, nayi shine SBD mu fahimci irin kalubalen da sauran ƴan uwan mu mata wanda suka faɗa a jarrabawa ta jinkirin aure suke fuskanta hakan bayin kansu bane, haka irin tasu MUJARRABIN yake, Allah ya kawo musu abokan zama nagari sannan mu sani wani jinkirin alkhairi ne, na SADAUKAR da dukkanin littafin gare su._ *Godiya da jinjina da kuma ban girma ga shugabar Kungiyar mu ta MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Nimcy luv much love for you.* PG 1 & 2 _MAIDUGURI OLD GRA_ ________ Katafaren flat House ne mai ɗauke da babban gate baki, Ɗaɗaɗɗen gini ne duk painting jikin gidan ya koɗe, ga dukkan alamu gidane na tsohon ma'aikacin gwamnati wanda yayi ritaya, tsarin gidan na da burgewa musamman yanda jerarrun flower's suke da koren ganye duk da daɗaɗɗu ne, flat ne ɗaya mai ɗauke da ɗakuna masu yawa da babban palour ɗaya mai ɗauke da maroon lader sit wanda ya gama koɗewa da kuma fara yayyagewa, akwai tsoffin standard fridge guda biyu kusa da corido, da kuma babban plasma TV. Turo ƙofar toilet tayi ta fito cikin nutsuwa ga dukkan alamu watsa ruwa tayi saboda yadda jikinta ke tashi da ƙamshin pawpaw and ALOE vera soap and gel. Ɗaure take da farin towel daga saman ƙirjinta zuwa tsalatsalan cinyoyinta, cikin takun ta kamar mai tausayin shimfiɗaɗɗen blue Black carpet dake ɗakin ta iso gaban mirror mai ɗauke da mayyukan jiki da kuma na gashin kai, da kuma turaruka masu ƙamshin gaske. A hankali ta zauna bisa ɗan madaidaicin standard chair tare da ƙurawa kanta idanu ta cikin mirror na tsawon 5minit sannan ta sauke ajiyar zuciya, tana mai jin tausayin kanta ganin irin kyau da kuma tsura ta masha Allah da Ubangiji ya yi mata amma kuma har tsawon wannan shekarun nata batayi aure ba. Hannu ta saka ta warware tulin gashin kanta wanda ta yi masa naɗin rawanin buzu sbd tsawon sa, in ba hakan ta yi ba zai dinga takura mata, a hankali ta sakesa ya zubo tare da rufe dukkanin bayan ta, ya sauko har kan tudun mazaunanta. Hannu tasa ta buɗe JET oil da kuma man gurguwa sai pink oil ta ɗebo ta haɗa waje ɗaya ta kwaɓa tare da shafe dukkanin gashin kanta sannan ta taje shi ta sake tufke shi da ribon ta ɗaure sannan ta sake naɗe shi, tissue ta ɗauka ta goge hannun ta, sannan ta janyo normal versilene ta shafa a farar skin nata mai sheƙi da laushi, bata shafa man da zai sa ta hasken skin sbd irin skin nan ne da duk wuya duk rintse yana nan yadda yake. Fashe jikinta ta yi da body's spray, sannan ta miƙe ta sanya doguwar riga wacce ta yi daidai da coca cola shape nata ta yane jikin ta da veil na rigar sannan ta ɗau wayar ta tana shirin fitowa, turuss tayi ta tsaya sbd ganin sa da tayi yana tsaye bakin kofan ɗakin ta, ta haɗe fuska. Murmushi ya sakar mata daman ya zaci hakan daga gare ta, ya sauke ajiyar zuciya a hankali yayi magana ciki silent voice na shi "HAMRA (Farar mace) yau baki da duty ne a hospital?" Sauke numfashi ta yi ta ƙaraso kusa dashi, ta ɗago kanta tana kallon sa ba tare da ta sake fuskarta ba, yana da tsawo ya fita sosai kamar shine gaba da ita ta ce AMMAR ( UMAR) for how long, zan yi ta maimaita maka cewa you have to say salam and get permission before ka shigo min ɗaki, ba ka san yanzu ka girma bane?. Murmushi ya sake sakar mata sbd a kullum ce masa take yaro, yau kuma ta ce ya girma a hankali ya kwantar da kai ya ce "Yau ni ki ke cewa na girma lallai a bin da mamaki, ba ki bani amsa ta ba Hospital za ki tafi ne?" Ta sauke numfashi a hankali ta ce Yau night duty nake dashi, a bin da yasa na ke cewa kai yaro ne sbd kana kasa dani. Daidai ta tsayawar sa ya yi ya ce "I'm sorry, ban jima da shigowa ba, ina shirin tafiya ne and na shigo ne ko kina da sakon da zan karɓo miki, in na tashi dawowa gida anjima" No, babu but in ma akwai we'll talk through phone. Ya yi murmushi yana mamakin irin son girma na HAMRA so tari ana cewa ƙanwarsa ce sbd yadda yake da girman jiki da tsawo amma ita har kullum kallon yaro ta ke masa, ba abu mai wuya bane a wajenta ta kira shi ta aike shi, raɓewa tayi ta gefen shi ta fito main palour ba tare da ta sake cewa komai ba. Hayaniyar da taji ne ya tabbatar mata da baƙi cikin gidan ta wuce side na Mommynta, ganin su Ayshe (A'isha) ne ya sa cikin farin ciki ta ce Shine ba sanarwa kawai sai gaku nan. Murmushi Ayshe ta yi ta ce "Ai na san da zaran na ce dake ina hanya za ki ce za ki ɗaura girki shiyasa ma na taho da abinci ba sai kin wahala ba" Murmushi HAMRA ta yi ta ce Ayya habibty na gode, but ina yaran nawa ne yau? "Uhm suna gidan kakarsu wai sai next weekend zasu biyo ni" "Yaya HAMRA barka da gida?" Ta maida kallon ta ga Zeenat wacce ke zaune dirsham kan carpet da katon ciki, cikin kulawa ta ce Alhamdulillah Zeenat, ya karfin jikin?. "Sai godiya na ƙagu ma na haihu" Da yardan Ubangiji kamar yau ne ai. "Hakane" Cewar Ayshe, HAMRA ta maida kallon ta ga Waleed wanda yake kan bed yana ta dukan bayan mahaifiyar sa a kan ta tashi, ta ce Wannan sarkin baccin an fara sana'ar kenan, ke Maryama ki tashi, kina jin yaro yana kuka ki tashi ki ba shi abincin shi yasha mana. Amma ta yi kamar bata jita ba sai da ta maimaita sannan ta tashi ta zauna ta kalli Waleed sannan kuma ta ɗago ta kalli HAMRA cikin ɓacin rai ta ce "Wai ke menene haka HAMRA a duk lokacin da kika ga na taho gida ina hutawa sai kin shiga cikin rayuwa ta, nazo gida sbd na samu na huta amma anan ɗin ma baza a barni ba, ina ni na haife shi kuma ni na san zafin haihuwar shi to kinga ai na fiki sanin darajar shi" Deep kowa ya ɗauke wuta sbd furucin da ta yi. HAMRA ita ce babbar su baki ɗaya amma Maryama ta ke faɗa mata bakaken maganganun da basu dace ba tana ƙanwarta ta huɗu... Kalaman ta sun yiwa HAMRA zafi amma SBD yadda take da juriya ta ɗauke kai Ayshe ce cikin ɓacin rai ta ce "Maryama, baki da hankali ne wa Yaya HAMRA ki ke faɗin waɗannan kalaman, to ki sani ko ni ban isa na faɗa mata ba ballantana ke, me kike takama.... Saurin dakatar da ita HAMRA tayi ta ce, Ayshe ki bar zancen, ina sbd na faɗi gaskiya shiyasa ranta ya ɓaci ba laifin ta bane, ni ne da laifi in dai ni ce ba zan sake yin magana ga mai da ɗanki ba.... Maryama dake baiwa Waleed nono tayi saurin maida martani "Uhm kada kiyi ai sbd baki san zafin haihuwa ba ne shiyasa, in fisari banza ne kaza tayi mana" Wannan karon zancen yasaka HAMRA tayi shock dayawa what, abinda wasu suke faɗa mata shine yau ƙanwarta ta huɗu ke faɗa mata, take ranta ya matsanancin ɓaci, ana faɗamata hakan amma bai damun ta sai dai jin hakan daga bakin Maryama ya matukar taɓa ta... Sauƙar mari suka jiyo tasss, a lokaci guda suka ɗago ganin AMMAR ne ya ɗauke Maryama da mari yasa Ayshe da Zeenat cewa "Kayi daidai, tun da ta ce ta zaɓi tayi mata rashin kunya" Duk da Maryama tayi mata rashin kunya amma marin da AMMAR ya yi bata ji daɗin sa ba ta kallesa duk jikin ta ya yi sanyi ta ce AMMAR, why did you slap her?, because of... "Yeah, Hamrah I'll do more than that ma in dai ta ci gaba da yi miki rashin kunya" Sauke numfashi HAMRA tayi ta san hakan ba zayyi musu kyau ba..... Saukar muryar mahaifiyar su suka ji tana magana daga bakin ƙofar ɗakin, "Wai meke faruwa ne na ke jin hayaniya tun ɗazu?" A hankali Hamrah ta ɗago ta kalli mahaifiyar su da su ke kira da AMMIE kuma sai ta lumshe idanuwanta, AMMAR ne ya ce "AMMIE, Maryama baki ɗaya ta kanza dabi'un ta a ƴan watannin nan, wlh muddin bata daina ba to.... "Stop it AMMAR, you knows nothing and slap her while she's a married woman, kada ka sake" Cewar AMMIE cikin ɓacin rai, duk jikin HAMRA yayi sanyi a hankali ta miƙe ta fice, ta iso ta zauna ƙarƙashin bishiryar darbejiya dake sakiyar gidan ba tare da ta shimfiɗa komai ba ta kishingiɗe jikin ta tare da zaunawa kan jijiyarta, ta lumshe idanuwanta a hankali take sauke numfashi tana karanta addu'ar innalillahi wa inna ilaihi rajiun....... "Yaya HAMRA" Ta buɗe idanuwan ta a hankali ta zuba su ga Ayshe wacce take tsaye hannun ta ɗauke da babban darduma da kuma basket mai ɗauke da food flask babba da karami sai plate da spoun, da kuma goran swan water a hankali ta ajiye basket ɗin ta shimfiɗa dardumar sannan ta zauna tare da sake cewa "Ki zauna mana kan darduma ai yadda kika zauna jikin bishiyar nan sai jikin ki yayi ciwo" Sauke numfashi HAMRA tayi tare da sakar mata da murmushin da shi ba na farin ciki ba kuma shi bana baƙin ciki ba, ta sauko ta zauna kusa da ita... "Yaya HAMRA, kiyi hakuri da abin da Maryama..... Kada ki damu Ayshe ba komi. Ga dukkan alamu ya nuna akwai abinda ki ke son sanar dani yau, sbd da naga hakan kan fuskar ki. Cewar HAMRA tana kallon ta, buɗe food flask babban Ayshe tayi ta ɗauko mulmulan semo biyu ta buɗe ta ajiye sa kan plate ɗin sannan ta buɗe ƙaramin food flask ta zuba miyan Agushi wanda yaji manja da kayan haɗi, ta ajiye gaban HAMRA ta ce "Eh hakane, nazo ne mu tattauna kan matsalata kin san bani da wacce ta wuce ki da ki ke sharemin hawaye na, yanzu dai ki fara cin abinci tukuna" Hannu HAMRA ta kai cikin basket ɗin ta ɗauko spoun da kuma roban swan water ta buɗe ta ɗauraye sa ta soma cin abinci a hankali yau tun da ta tashi bata sa komai a cikin ta ba, ta ce Ina jinki Ayshe. Gyara zama Ayshe ta yi, take ranta ya ɓaci da ta tuno da abin da ke damun ta, ta ce "Uhm BUKAR ne yake son ƙara aure" Waye BUKAR?. HAMRA ta tambaya tana ci gaba da cin abincin ta, numfasawa Ayshe ta yi tasan HAMRA tasan me take nufi amma kuma so take ta gyara sunan ta ce "Alay BUKAR mijina" Murmushi sosai Hamra tayi ta ce Yanzu Ayshe sbd zai ƙara aure shine kike kiransa da sunan sa na yanka, ina soyayyar da kike masa ne, ina har choculety kike kiran sa dashi. "That was then yaya Hamra, ban taɓa tunanin zai juna min baya ba balle kuma ya munafunce ni, wlh ya matukar bani mamaki, uhmm na miji ba ɗan goyo bane, da yaji kanjin naira sai ya juyawa mace baya" HAMRA ta kammala cin abincin daman mulmulan kanana ne, ta juyo ta kalli Ayshe wacce ke zubar da hawaye ta ce Daman ita rayuwa haka ta gada, yau in kaine da farin ciki watarana ba kai bane, ki sani shi na miji ba a iya hana sa aure kuma ba a saka shi, in yayi niyya babu mai hana sa, amma wane hukunci kika ɗauka tsawon kwanakin da yace zayyi auren?. "Na daina kulasa na fita hanyar sa, shima yana ganin haka ya watsar dani shine nayi tunanin kawai na dawo gida na hakura da zaman auren" A hankali HAMRA ta ɗaura hannunta kan na Ayshe ta ce Maimakon ki gyara Ayshe amma kika sake lalata a bin, wannan a bin da kikayi zunubi kike ta ɗebar wa kanki, dan mijin ki zayyi aure bai kamata ki sauke duk wani abin da ya wajaba a kan ki ba koda baya yi ki daure ki sauke naki hakkin. "Yaya HAMRA abinda ya fi bani haushi fa har yau bai buɗi baki ya faɗamin zai ƙara ba nima a bakin ƙannensa na ke ji, shine kawai na ce zan bar masa gidan" A'a Ayshe ke ce baki basa wannan damar ba, da kinyi hakuri baki nuna masa kin sani ba ta hanyar ƙaurace masa da zai sanar dake komai. Ba ina goyon bayan sa ba ne kuma bance yayi daidai ba, amma kuma duk inda kika je shi bashi da laifi ke za a ɗaurawa laifi, yanzu yaushe ne ranar bikin?. "Uhm wai nan da 2weeks" To shawarar da zan baki shine, kiyi hakuri ki koma ɗakin ki, sannan duk wani ɗawainiyar sa da yake kanki ki sauke kuma kada ki nuna auren ya dame ki. Ki saki ranki kamar yadda ki keyi a cen baya. Sauke numfashi Ayshe ta yi tana jinjina zancen Hamra anya zata iya jurewa..... Ayshe, kin haifa masa yara har kusan biyar ina kike ganin zaki tafi kibar su, wa kishiyar ki ko wa dangin sa, dan haka kiyi hakuri, ƴan mata da yawa suna neman irin rayuwar gidan ki basu samu ba, kuma ma yanzu in kika fito sai kizo mu haɗa sawu a gida, ni ba aure ba ke kuma kin yi kin fito. Jikin Ayshe yayi sanyi da jin kalaman Hamra cikin sanyin murya ta ce "To ni ba a bin da nayi fa haka nake zaune, jiyama ƙanwarsa harda goranta min wai ban kanza set nawa ba gashi aure ya matso" Sauke numfashi Hamrah ta yi ta ce, Wannan ba a bin damuwa bane, ki yiwa Sulaiman furniture magana nawa zaki ƙara masa akan naki set ɗin, duk yadda ku kayi sai ki faɗamin zan turamasa kuɗin. Rungumar Hamrah ta yi tana godiya tare da share hawayenta a daidai lokacin kuma Zeenat ta fito da ƙyar take iya takowa ta ƙaraso ta zauna tare da cewa "Wacce wainar ake toyawa ban dani a ciki? HAMRA ta ce aiko wannan wainar daɗi gare ta kuma babu ta wuce ki. Nan suka saka dariya. Anan sukai sallah azahar har la'asar, suka soma shirin tafiya, itama HAMRA zata je wajen aiki, suna shirin tashi sai ga Maryama ta fito ɗauke da Waleed ko kulasu batayi ba tayi hanyar waje da alamu mijin ta yazo ɗaukanta, dogon tsoki Zeenat tayi ta ce "Ni wai me wannan yarinyar take takama da shi ne, sbd ƴan canji da mijinta ya samu shine take wani ji da kai, munanan sai tazo ta neme mu" Murmushi HAMRA tayi ta ce a'a Zeenat kada ki faɗi hakan ita ɗin ƴar uwar ki ce, kuma ai yarinya ce, da sauran ta... "Wacece yarinya, Maryama ce yarinya tasan namiji ma shine zaki ce yarinya kawai rashin kunya ce, ni zan sauke mata shi" Dariya sukai suka wuce ciki, ko wacce ta shirya suka fito suka tafi, HAMRA ta dawo ɗakinta duk a bin da take buƙata ta ɗauka ta shirya ta fito, ɗakin Ammie ta shige ta tadda ta zaune kan dardumar tana azkhar na yammaci ta ce Ammie zan wuce wajen aiki, sai da safe. Ta miƙe ta fito dan ta san ba amsa mata za tayi ba, kawai ta sauke hakkin ta ne a matsayin ta na ɗiyar ta. Ta fito kenan alokacin kuma AMMAR ke shirin fita cike da mamaki ta ce Wait, daman baka fita bane?. A hankali ya juyo yana kallon ta, ya ce "Bacci nayi sai yanzu zan fice, aiki zaki wuce ko, to mu fita nima ta hanyar ki zanbi" Ta sauke numfashi tare suka fito a motar shi suka shiga ya fice daga gidan, kai tsaye ya wuce da ita AL'UMMA SPECIALIST HOSPITAL, ya sauke ta ta shiga shi kuma ya wuce, a nutse ta shigo cikin Hospital ɗin cikin fara'a suke gaisawa da mutan wajen ta wuce office nata, a hankali ta zauna ta buɗe drower ta fito da duk a bin da za tayi amfani dashi ta ajiye shi kan table, sannan ta sanya white coat da kuma white eyes glass nata ta kunna system nata, turo ƙofar Dr Aliyu yayi tare da sallama ta amsa ya karaso ya ce "Dr HAMRA, akwai patients yau a VIP rooms kuma mutanen MD ne ya ce a basu kulawa a maida hankali gare su abar duk wani patients da ake dubawa daren.... Hannu ta ɗagawa Dr Aliyu alamun ya isa, ta ce Bazan duba ba, ba haka aiki ya ce ba, sai na duba patients nawa tukuna zan duba nasa. Sauke numfashi Dr Aliyu ya yi yasan tabbas hakan zai faru HAMRA ba zata taɓa yarda ba, aikin ta cikin gaskiya ta keyi amma ya ce "Sako ne daga MD kuma kinsa... Na sani, kada ka damu jeka abin ka. Ya fice yana mamakin ta, ta kammala duk abinda ta keyi ta wuce general room (ward) da patients ke ciki suna ganin ta, cikin farin ciki suna ɗaga mata hannu sbd tana basu kulawa sosai kuma tana ɓata lokacin ta wajen jin a bin da yake damun su ganin yau ita ke da duty yasa suke murna, bayan sun gaisa sannan ta dawo officer sbd gabatar da sallah magrib a nan ta zauna har ishai sannan ta fito ta ci gaba da duba patients nata a tare da ita a kwai Dr Zalihat, anfi ji da ita ne sbd ta ƙware wajen iya aiki kuma ta dalilin ta suke samun yawan patients sbd ta iya kulawa dasu. HAMRA bata da cusa kai a kan a bin da bai shafe ta ba, iya abin da zata iya ta ke yi kuma bata so taga ana rashin adalci. Sai kusan 11:00pm sannan ta wuce v.i.p rooms tana bi one by one tana duba su sannan ta dawo officer ta ɗan kishingiɗa sbd huta gajiya. A hankali ya turo ƙofar ya shigo babu ko sallama bata buɗe idanuwan ta ba balle kuma ta ɗago amma taji motsin shigowa, ya tura kofar ya rufe ya iso inda ta ke ya zauna kusa da ita yana kallon ta "Har kin kammala duba patients ɗin ne?" Shine a bin da ya faɗa, a hankali ta buɗe idanuwanta da su kayi mata nawi ta kallesa shima ita yake kallo, sauke numfashi tayi ta ce Dr Mahmoud are you not a Muslim, da za ka shigo babu sallama? Murmushi ya yi ya kurawa ƙirjinta idanu yana wani zazzare su yana jan numfashi. Ta haɗe rai matuka, ta tashi ta gyara zaman ta, ya sosa keyarsa ya ce "I did but maybe you didn't hear it amma Assalamu alaikum" Bata amsa ba ta jefa masa tambaya Do you need something?. Kai tsaye ya ce "Of course, i need you?" Tayi shock dajin maganar amma ta dake kamar bata san me ya ce ba. Ganin haka ya taso ya kai hannunsa zai rike nata ta yi saurin tashi tsaye ta ce Baka da hankali ne, meya haka kuma?. Kurawa coca cola shape nata idanu yayi ya sauke numfashi ya ce "Eh a yanzun bani da hankali amma in kin bani abin da nake nema zan dawo cikin hankalina" Galala take kallon shi babu kunya babu tsoron Allah yake magana idanun nan a bushe suke, ta miƙe da niyyar ficewa ya yi sauri ya kai hannun ya riƙo ta ya janyo ta tare da haɗe ta da jikin garu tayi saurin hankaɗesa tare da ɗauke sa da wani gigitaccen mari cikin ɓacin rai da tashin hankali ta ce Dr Mahmoud, ina maka kallon mutumin arziki sbd wannan gemun da ka ajiye shi a she dai na banza ne, to kasani in kana cin ƙasa ka kiyayi tashuri, get out. Ko ɗar bayi ba ya kafe ta da jajayen idanuwan sa yana sauke numfashi ya ce "Ni zan baki kulawa fiye da wanda Dr Aliyu yake baki, in dai iya tsarrafa mace ne na iya kuma zakiji daɗin wannan harkar" Zuwa wannan lokacin abin ya fara bata soro what?. He thinks that, she slept with Dr Aliyu, ta ɗago da idanuwan ta da suka sauya kala sbd ɓacin rai ta ce Think whatever you want, and God forbid na haɗa jiki da kai, ƙazami mai ƙamamin rayuwa. Tana faɗin hakan ta ɗau wayarta, ta fice ta yi harabar Hospital ɗin tana huci, ta jima da son ajiye wannan aikin amma yau ya fi ko wacce rana fita cikin ranta, kenan zuwan da Dr Aliyu yake yi neman taimakon ta wajen sake wayar masa da kai ta wasu fannin aikin su, shine Dr Mahmoud yake tunanin ƙazamar alaka ce a sakanin su, tana nan tsaye yazo ya gifta ya wuce ko ajikin sa, ta dawo officer ta sanya key ta rufe ta koma kan resting chair ta kwanta, tana jin duk rayuwar ta fice daga ranta, bacci ya ɗauke ta. Washegari tunda ta tashi da matsanancin ciwon kai ta tashi, tun asuba take fama dashi, haɗa kayayyakin ta tayi ta fito har ƴan morning duty sun iso suka gaisa sannan ta fito, ta dawo gida, ganin motar Daddyn ta ya tabbatar mata da yana gida, ta shigo gidan sittt babu motsin kowa, daman ita da AMMAR ne a gidan shiyasa gidan ya ke da shuru dayawa, a hankali ta tako ta iso kofar ɗakin ta har zata murɗa handle door muryar Ammie taji ta kira sunan ta "HAMRA" Jiki a sanyaye ta juyo tare da cewa ina kwana Ammie. Bata amsa ba ta ce "Yanzu wannan rayuwar kika zaɓarwa kanki, to ki sani kiji tsoron Allah ki fidda miji kiyi aure in kina so mu shirya a cikin wannan gidan, dubi kannenki duk sun yi aure sun rufawa kansu asiri amma ke kin tona wa kanbki da kuma mu asiri kina duk abinda ki kaga dama, to ki sani ba zan zuba ido naga kina yin haka ba, na baki nan da karshen wata ki fidda miji in kuma ba haka ba daga ni har ke ba zamu ji daɗin abin da zai faru ba, kin sa sai zancen ki a keyi a family da kuma unguwa kin tsaya zaɓe SBD kyawunki na ruɗan ki to ni ba zan lamun ta ba" Numfashin HAMRA sama² ya keyi hankalin ta ya matukar tashi dajin waɗannan kalaman daga bakin mahaifiyar ta, daman shine dalilin da ya sa take fushi da ita.... "Hajjiya BATULA ba na hana a dinga wa HAMRA irin wannan zancen ba, ina mun riga da munyi magana akan hakan, mesa kuma yau ki ke tada zancen, lokaci ne bayyi ba in yayi za ayi shi kamar yadda a kayi na sauran" Cewan Daddyn su, ya ƙaraso wajen tare da isowa wajen HAMRA cikin kulawa ya ce "HAMRA ki shige ciki ki huta, nasan kin kwana aiki duk kin gaji Allah ya bada ladan taimakon da ki ke badawa" Ameen. Ta ce, ya juya ya fice, Ammie ma ta shige ciki, HAMRA ta juyo tana hawaye zata shige ciki sai ganin AMMAR tayi yana tsaye cikin damuwa yana kallonta da alamu ya ɗan jima a tsaye saurin buɗe ɗakinta tayi ta shige, a hankali ta ajiye kayan hannunta, ta fashe da matsanancin kukan da bata taɓa yin irin saba, daga jiya zuwa yau ta shiga tsananin tashin hankali sbd abinda taji kuma ta gani, fushin Ammie da kuma kalaman ta sun fi ɗaga mata hankali ina zata waiga taji sanyi ne, mahaifiyar ta ma ta juya mata baya..... Alhamdulillah ala kulli halin. Ina godiya ga Ubangiji da ya sake bani damar sake rubuta wani littafin, ina rokon shi kamar yadda na fara ya bani ikon kammalawa lfy. Tafiyar wannan littafin mai rai ce, kuma ba za kuyi nadamar karanta shi ba. Ƙunshe yake da darussa da dama, kuma zaku ƙaru da su. Zan dinga skipping rana ɗaya na posting sbd na sami nutsuwar typing. Comments and share[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 3 & 4 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _______Ƙirjinta yana mata raɗaɗi da zugi kamar zai fito, a hankali take sauke numfashi tana zubda hawaye, tana tuna irin rayuwa ta farin ciki da gata da ta ta yi tare da Iyayenta da ƴan uwa ta. Taso cikin gata da kulawa bata taɓa sammanin zata riski irin wannan rayuwar ba, ta ƙunci da tashin hankali. Basu taɓa ganin iyayen su sun sami saɓani da juna ba sai akanta, kuma wannan duk yana faruwa ne saboda rashin auren da batayi ba, da farko anyi ribibin fitowa neman aurenta amma sai kuma daga baya shuru babu wanda ya ce yana ma sonta balle kuma a je ga zancen aure, har aka aurar da ƙannenta.... "HAMRA" A hankali ta ɗago ta kalle shi, damuwa ce kan fuskar shi sosai kamar zai taya ta kuka, yana mai jin tausayin ta sosai kuma baya son ganin ta tana cikin damuwa, shi ya zame mata abokin kukan ta kuma abokin shawaranta, ganin tana kallon sa kuma tana zubda kwallah yasa ya miƙa mata roban swan water tare da glass cup, ta karɓa ta siyaya ruwan ta sha, sannan tayi ajiyar zuciya a hankali furta Thanks. Sauke numfashi yayi ya ce "Kuka baya miki kyau, kin san me ki ke komawa in kina kuka?" Ba tayi magana ba tayi shuru tana kallon sa ya ce "Kamar shrunk" Murmushi tayi ta share hawayenta daman abin da yake son gani kenan, ta ce Baka fita bane?. "Uhm sai zuwa anjima, shima saboda ana neman mu ne zamu yi meeting akan tafiya training na sojojin da muka sa gaba" Ta sauke numfashi tare da sake zuba ruwan ta sha sannan ta sake cewa Wacce ƙasar ma zaku je? "ABGANISTAN" ya faɗa yana kallon ta tare da murmushi akan fuskar sa. Uhm ya yi kyau, Allah ya taimake ku. Ta faɗa tana ajiye roban swan water da kuma glass cup ɗin "Ameen" Sosai ya juyo yana kallon ta ya ce "HAMRA, ke ki ke cewa mu koyi jure wa ko wacce irin damuwa, mu rufe idanuwan mu kamar bamu gani ba sannan mu toshe kunnuwan mu kamar ba muji ba, amma mesa ke ki ka kasa yin haka, though a baya ki nayi but this time around kuma kin saduda, kin manta cewa duk tsanani yana tare da sauki, in shaa Allahu nan bada jimawa ba komai zai zama tarihi, za ki yi rayuwar farin ciki kamar yanda kowa ke yi, Please kada ki damu da yanayin da Ammie ke nuna miki ita ma zuwa wani lokaci za ta daina" Ta sauke numfashi a hankali ta sake cewa Thank you AMMAR. Ya miƙe ya fice, ita kuma ta tashi ta shige toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nawi, ta hau kan bed tana jin yunwa ga kuma bacci da ciwon kai da take ji... Da sallama ya shigo ya ajiye basket dake hannun shi ya ce "Tashi ki yi breakfast, nasan ba abinda kika ci". A hankali ta sauko tare da cewa Kamar kasan yunwa nake ji, shiyasa nake kara son ka ɗan KANINA. Murmushi yayi ya ce "A'a ya kamata zuwa wannan lokacin ki barmin girman nan daman cewa a ke yi ke ƙanwarta ce" Murmushi tayi ta ce Ai koda girgiza kurna tafi magarya girma. Yayi murmushi ya ce "Ba haka karin maganar take ba, cewa a ke yi ko da girgiza magarya tafi kurna zaƙi" Uhm nawa ne daidai. Suna fira tana cin indomie da kwai da ya soya mata, har ta kammala sannan ya mata sai anjima ya fice, ta ɗan zauna jim kaɗan sannan ta kwanta bacci sai azahar ta farka bayan ta idar ta sake komawa bacci sai bayan la'asar ta tashi ta idar sannan ta wuce kitchen tare da duba menene akwai, gannin Uwale ta kammala haɗa stew yasa ta fere doya ta dafa sa fari sannan ta zuba a plate tare da zuba stew akai ta dawo ɗakin ta, nan ta ci tare da haɗa tea na ruwan zafi ta sha sannan ta tashi ta shirya ta fito. Ɗakin Ammie ta shige tayi mata sai da safe amma bata kulata ba, hakan yasa ta fito cikin sanyin jiki, ta tadda Daddyn su na zaune a farfajiyar gida ta iso cikin girmamawa ta ce Daddy zan wuce wajen aiki. Cikin kulawa ya ce "Likita Allah ya taimaka sai kin dawo, ayi ta hakuri da sha'anin rayuwa" To Daddy in shaa Allahu, nagode. Nan ta fito, ta tari ɗan sahu ta wuce wajen aiki. Tana shiga cikin Hospital ɗin ta wuce office nata, ta kimtsa duk abin da zata buƙata anjima da daddare sai ga Dr Aliyu ya shigo cikin sallama, ta amsa ya ce da ita "Special Doctor an fito ko?" Tayi murmushi tare da cewa Yau kuma harda zolaya? "Ai gaskiya ce kuma kowa ya shaida ke ƙwararriya ce ta fannin aikin ki" Uhm to ina godiya. Ta faɗa idonta a kan system nata, ya ce "MD ya ce akwai zaman ku dashi bayan magrib" Ta sauke numfashi tare da ɗagowa ta kallesa ta ce Badamuwa Allah ya kaimu. Matukar burge shi take SBD jarumtarta duk cikin Hospital ɗin nan tsoron MD ake amma ban da ita, ya sake cewa "Amma bakya tunanin ko abin ya shafe abin da ya ce kiyi jiya da daddare kuma... Dr Aliyu ni in dai a kan gaskiya ta ce ko ina a kaini, meyasa kuke tsoron sa shifa ɗan Adam ne kamar kowa sannan kuma kowa yana da right na kare kan shi so, banga wani abin tada hankali ba, I'm waiting for the hours. Ya sauke numfashi ya ce "Well don special Doctor till we meet later, an fara kiran sallah sai zuwa anjima" Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi tana mamaki sauran likitoci da suke neman gindin zama a wajen MD shi da ba wani aiki yakeyi ba kawai dai yana zagoyowa ne yana taking information akan wasu abubuwan amma duk da haka suke ɓata ta a wajen sa a cen baya tayi tunanin Dr Aliyu ne amma da tayi bincike ta tabbatar likitoci mata ne ke kai masa gulmanta shiyasa ta share su baki ɗaya indai ba sha'anin aiki bane ya haɗasu to bata shiga tsabgarsu, jin ana kiran sallah yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗaura alwala ta fito ta idar sannan ta wuce office na MD tana isowa ta tadda sa yana waya a waje ta shige ciki ta zauna har ya kammala ya shigo cikin girmamawa ta ce Afternoon sir, an ce kana nemana. Ya cire white eyes glass dake idonsa ya ajiye sa kan tebur dake gaban sa ya kuramata jajayen idanuwan sa na wani lokaci sannan ya ce "Jiya saƙo na ya iso ki ko bai riske ki ba" Kai tsaye ta ce ya riskeni. Ya sauke numfashi ya ce "Kinyi yadda na ce ko kuma kinyi abin gaban ki?" Ta sauke numfashi tasan yaji labarin komai kawai yana so ta tabbatar masa ne ita kuma baza ta yi ƙarya dan ta kare kanta ba ta ce Ina da patients waɗanda na ke kulawa dasu, kuma na yi musu alkawarin cewa zan basu kulawa har su sami lfy, shiyasa na fara duba su sannan na duba..... "Who the hell you are da zakiyi abin da ki ka ga dama dake da patients ɗin ai duk a karkashina kuke, daga yau muddin na ce ayi abu kika sauya to ki sani dole ki bar wannan Hospital ɗin, kina ganin tafiyar ki zai sauya komai ne, we'll work even without you, sai me dan kinga OG yana yabon ki shine ki ke wani ganin kan ki kin fi kowa, to ki sani banga wanda ya isa na saka doka ya karya ta ba a duk faɗin duniyar nan" Sosai ta rumtse idanuwanta SBD tsawar da ya daka mata, ta tsani ayi shouting mata akai, nan take take gigicewa, hankalinta ya tashi kuma ranta ya ɓace bata san lokacin da ta miƙe tsaye ta nunasa da yatsa ba ta ce I'm not a young girl, kada ka sake min ihu, a kan wane dalili kake faɗa min waɗannan maganganun? da kake cewa zaka koreni ɗin ai ba kai ka bani wannan aikin ba sai dai OG ya koreni ko da kuwa zan bar wanna aikin, to ka sani ba ta dalilin ka ba, kai kan ka kasan abin da kayi bai dace ma, ta yaya muna aiki domin ceto rayukan al'umma zaka ce a barsu su sha wahala kai a duba naka, wannan ba adalci bane. Tana kaiwa nan ta fito tabarsa baki sake yana mamakin ta, lallai HAMRA bata san waye shi ba, tana dai jin labarin shi ne, amma soon za ta sani. Tana shiga office kanta ya soma tsara mata saboda ihun da yayi mata, maisa MD bashi da imani ne, kowa yana complain na shi a bayan idon sa akan irin zaluntar mutane da yakeyi. Ta sauke numfashi ta shige toilet ta ɗaura alwala ta idar da sallah ishai sannan ta wuce duba marasa lafiya yau kam ta daɗe a wajen su, mutanen MD kuma Dr zalihat ce ta duba su, HAMRA sai kusan 1:00am ta dawo office ta saka key ta rufe kofar sannan ta kwanta. Da safe ta tashi a makare ta gaggauta isar da sallah ta ɗau jakarta ta fito har ƴan morning duty sun iso, bayan sun gaisa ne ta fice kasancewar safiya ce ana wahalar abin hawa saboda kai yara makaranta, hakan yasa HAMRA takowa zuwa bakin titi, tana tsaye tana jiran abin hawa amma duk wanda yazo wuce wa sai taga cike yake da mutane. Har ta gaji da tsayuwa ta yanke shawarar ko ta sake yin gaba ne sai taga wata bak'ar mota jeeb mai liƙe da bakin glass ta tsaya kusa da ita, kau da kai gefe tayi kuma take shirin barin wajen taji an ce "Wa nake gani haka kamar HAMRA pretty kece?" Jin muryar mace ce yasa ta tsaya tare da juyowa ta kalle ta cike da mamaki ita ma ta ce Hauwa'u Jibrin! Kina wannan duniyan?. Aiko ba shiri ta fito daga cikin motar ta tana cewa "Wata sabon gani inji Hausa people, HAMRA pretty ashe zan sake ganin ki, rabo na da saki cikin idanu na tun a secondary School fa, from where?" Uhm Hauwa'u daga wajen aiki nake. "What?. Ta faɗa tana koƙarin gyara parking na motar ta fito sannan ta ci gaba da cewa "Aiki daman ana aiki ne a wannan zamanin ai zuwa aiki ɓata lokaci ne, yanzu da wannan kyawun naki ki ke aiki" Uhm kina nan kamar yanda na sanki, daman an ce in dai ka jima baka haɗu da mutum ba to kada ka tambayi halinsa saboda hali zanen dutse ne baya taɓa kanza wa, to in ba abin ki ba Hauwa'u in dai banyi aiki ba me kike so nayi?" "Shigo cikin mota na ƙarasa dake gida sai mu ƙarasa gaisawa". A tare suka shige cikin mota da mamaki HAMRA ke kallon ta, ganin ita kaɗai ce a cikin motar yasa ta ce Kin kai kids naki skul ne?. Dariya Hauwa'u tayi sosai tana tuki ta ce "Ki jiki wai na kai yara makaranta, ni da ko auren ban yi ba, ina na ga yaran?" Cike da mamaki da kuma tausayawa HAMRA take kallon ta ce Ayya ki ce duk jirgi ɗaya muke. "Don't tell me HAMRA pretty wai da gaske ba kiyi aure ba duk da wannan kyaun naki, to ina ga mu kuma munana" Uhm Hauwa'u ai shi aure ba wai kyau ko rashin sa yake dubawa ba lokaci ne, abin da yasa na tambaye ki ko yara ki ka kai skul shine ganin ki da nayi da wannan motar. Murmushi Hauwa'u tayi sosai ta ce "Har yanzu a gidan ku na da ku ke?" Eh a nan ne. Cewar HAMRA tana kare mata kallo, sanye take da doguwar riga ta habaya baƙa ta yane gashin kanta da gyallen duk da ma tulin kitson Attachment da tayi duk ya baje mata a baya hakan yasa gyallen habayar kasa rufe kanta, farcen yatsun hannayen ta sun sha janfarce, da kuma zobe, ga kuma bleaching da tayi sosai duk fuskar ta fita hayyacinta. Sauke numfashi HAMRA tayi a daidai lokacin da suka shigo layin su Hauwa'u ta ce "Ni ina Shatu, What i mean Aishatu Muktar?" HAMRA ta buɗe kofar motan ta fito saboda parking ɗin da Hauwa'u tayi a daidai kofan gidan su ta ce Shatu tana nan fah amma yanzun tayi tafiya. "Ikon God kai rayuwa! SUCH IS Life, did she get married?" No, ita ma har yanzu like us. Kurawa HAMRA idanu Hauwa'u tayi na wani lokaci sannan ta ce "To a zaman ki yanzu haka me kike yi ne bayan aikin nan, i mean kina da wanda yake ɗebe miki kewa ne ko kuma in ce masu ɗebe miki kewa" HAMRA bata fahimci zancenta ba ta ce, I didn't get you, what do you mean by that, though zan iya cewa aikina kaɗai yana ɗebe min kewa. Murmushi Hauwa'u tayi kai tsaye ta ce "Zaki ce bakya harka da namiji duk tsawon wannan shekarun naki, kina wane ɓoye zancen ai yanzu komai a fili ake yinsa, ba a ɓoyewa saboda abin ya zama ruwan dare gama duniya, kuma rayuwar yanzu kowa nemawa kansa mafita yake, kowa ta kansa yake dan haka feel free muyi magana" Tsayuwa da kyau HAMRA ta yi tana sake karewa Hauwa'u kallo sai yanzu ta fahimce ta, ta ce Hauwa'u kenan, wannan kwatakwata baya daga cikin tsarin rayuwata, dan banyi aure ba shine zan zubar da mutuncina, ina har abada ko da zan dauwama a hakan ba zan taɓa zubar da tarbiya ta ba da kuma darajan gidan mu ba kuma bazan saɓawa mahaliccina ba, to ita kanta rayuwar yanzu kayi daidai ma ya ka kare ballantana bakayi ba, kin ganni nan ko saurayi bani dashi. Dariya sosai Hauwa'u tayi tare da ɗaukan goran faro water ta kai baki ta sha sannan ta ce "HAMRA pretty kada ki mai da karuwa ƴar iska mana, yanzu zaki ce dani ke VIRGIN ce ina, bazan taɓa yarda ba" Ran HAMRA zuwa yanzu ya fara ɓaci ta fara tantama kan Hauwa'u Jibrin anya ba ƙazamar rayuwa ta keyi ba da take cewa ita ba cikakkiyar mace ba ce, ta san dai duk macen da zata faɗi hakan akan ƴar uwar ta mace to hakan yana nuni da ita ba mutuniyar kwarai ba ce gani ta ke yi abin da ta keyi ne kowa ma nayi, cike da mamaki HAMRA ta ce Hauwa'u, ni na yarda da kaina, dan haka bana tsoro ko shakka dan wani zaya min mummunan fahimta kuma naji haushi, to ke kuma fa kina nufin ke ba cikakkiyar mace ba ce?. Murmushi Hauwa'u tayi ta fito da bunch na dubu ɗari guda biyar ta nunawa HAMRA tare da ce mata "Ɗazo kin tambaye ni akan wannan motar da nake cikinta, ita dai wannan motar ɗaya ce daga cikin motaci na wanda ALHAJI GONI ya bani, sannan yanzu ma daga wajensa nake a hotel muka kwana shine ya bani wannan 500k ɗin nasha ruwa a hanya bayan ban da wanda ya turamin ta account, ire-iren su suna da yawa ke har outside muna fita tare da shi, kai da duk wanda ya nemi yin hakan ina shanawa ta, duk abinda matar aure take yi nima ina yinsa to naga ai wannan normal ne, damu da matan auren duk ɗaya muke. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, shine abinda HAMRA ke furtawa cikin tashin hankali ta ce Amma ko Hauwa'u ba kiyiwa rayuwar ki adalci ba, kin cuci rayuwar ki, babu haɗe sakanin kwaɗan rama da zogale, ko ni nan wahala na fiki sau dubu ballanta kuma matar aure. Kiran da zan miki shine har yanzu da sauran lokaci za ki iya tuba ki dawo cikin rayuwa mai kyau ki tsafta ce zuciyar ki..... "Heeeee HAMRA pretty, do you mean za ki ce min baki san namiji ba har yanzu, bazan taɓa yarda ba. To ki sani wannan rayuwar da nake yi bata karewa bace haka kurum ina cin duniya ta da tsinke baza ki kamin cikas ba, in kina so hanya buɗe take zan iya haɗaki da irin namijin da kike burin samu a rayuwar ki, haka kurum ba zaki sa nayi 2 zero ba, ni banyi aure ba kuma ban san na miji ba har na mutu kai ba zayyu ba, kinga tafiya ta" Ta shige mota ta yi tafiyarta, HAMRA sabar kaɗuwa da abinda taji yasa ta juyo cikin tashin hankali ta shigo gida nan tayi kicibis da AMMAR dake shirin fitowa, ta daidaita nutsuwar ta dan kada ya fahimci wani abin tasan da ya sani zai dameta da tambayoyi da SBD ganin tana cikin damuwa, ta kwakulo murmushi ta ce Ina zuwa da safen nan?. Yayi murmushi cikin kulawa ya ce "Kin manta ne ina shirye shiryen barin Nigeria, ko da shike tsufa ya fara kamaki, ba dole ki tuna ba" Tayi dariya ta ɗan bugesa a kafaɗar sa ta ce Kai kasani, girma dai na fika, to Allah ya taimake ku, zan shige ciki na huta. Yayi dariya ya fice yana mai farin cikin ganin ta, cikin farin ciki. HAMRA na shiga ta wuce ɗakin Ammie ta taddata tana breakfast ta duka har ƙasa ta gaidata, amma Ammie ko kallon ta ba tayi ba balle kuma ta amsa mata, HAMRA ta miƙe ta fito sai taji muryar Daddyn su yanawa Ammie magana a lokacin ya fito daga cikin toilet..... "Zamu sami matsala akan wannan abinda kike son haifarwa a cikin wannan gidan, haba hajjiya Batula sai ka ce ba ɗiyar ki ba ce kike mata haka, ya kike so tayi?.So kike taje ta ce da namiji kazo a ɗaura mana aure ko kuma so kike damuwa ta kashe ta, a wannan lokacin ne take buƙatar kulawar ki amma ki ke nuna mata halin ko in kula" "Uhm ALHAJI na kula kai kake ɗaurewa HAMRA gindi take duk abin da taga dama shiyasa taki fidda mijin aure.... "Ya isa haka, na ce ya isa haka, kuma bana so ki sake maimaita abin da ki kayi mata yanzu" Sauri HAMRA tayi ta shige cikin ɗakinta zuciyar ta na harɓawa, ji tayi duniyar ta fice mata a rai, ta saki kuka a hankali, tana tuna abin da Hauwa'u ta faɗa mata da kuma faɗan da iyayen ta sukai akanta, ta jima tana kuka sannan tayi bacci da yunwar da take ji, sai kusan azahar ta tashi ta idar da sallah sannan ta samu ta ci abinci ta koma bacci, har dare tana ɗaki, daman ba inda take zuwa, gidan su Shatu ne take zuwa suyi fira ko kuma ita tazo mata, tunda ta yi tafiya bata fita, daman gidan su kawai take shiga sauran duk ta fisu a shekaru sauran kuma sun yi aure. Ta miƙe ta shige toilet ta watsa ruwa ta sanya doguwar riga mara nawi ta bacci, ta kunna ɗan ƙaramin TV nta plasma dake maƙale jikin garu daman a NTA News yake ta ci gaba da kallon labaran karfe 9:00pm, nocking akayi ta bada izinin shigowa ya shigo tare da sallama ta amsa, sanye yake da jallabiya ruwan ƙasa ƙirar Dubai, ya zauna kan carpet ya ajiye mata ledar da ya shigo da ita ya ce "Ke kam akwai ki da son labarai, ki kanza ki kai MBC max yau akwai raceling" Uhmm kaga Ammar kyale ni na kalli labaran duniya, in kana son kallon wasan dambe koma ɗakin ka, ka kalli duk channel ɗin da kake so, to ba za a zo fada ta ba kuma amin mulki. Dariya ya yi ya ce "Fira nazo taya ki fa shine ki ke korata tam akwai gobe. To gashi na siya miki roasted fish da banana juice" Kai ƙanina kana fa ji dani sosai. Murmushi yayi tasa hannu ta buɗe ladar ta soma ci ta sake cewa Ka jima a waje ashe dai wajen siyayya ka wuce. Ya sauke numfashi yana kallon News ya ce "A'a daga station nake" Cikin sauri ta haɗiye ragowar kifin dake bakinta ta ce Kana nufi police station! Me kuma ya kai ka?. Kai tsaye ya ce "Na raka abokina Abdullahi, saboda case na ƙanin shi Sadiq" A hankali ta kurɓi banana juice ɗin ta ce Iko sai rabbi, me kuma ya sami Sadik ɗin?. "Uhm wai budurwa sa ce da iyayenta suka kai ƙarar shi, shine Abdullahi ya ce na kai shi da mota ta" Budurwa? Yanzu Sadiq har wata budurwa gare shi?. Kai wannan zamanin da abin mamaki yake, in ba karshen zamani ba ina Sadiq da wata soyyayya. Ya juyo ya kalle ta tana cikin kifin ya ce "Eh wai ciki gareta kuma ta ce sam na Sadiq ne".. Aiko kifin da bai wuce mata wuya ba ta ƙware, yayi saurin mika mata robar swan water ta karɓa ta kora sannan ta ɗago ta ce "AMMAR bana son shashanci yanzu wannan yaron Sadiq ne zayiwa budurwa ciki, kai sai dai ko wani cen ya yi mata zata ƙalla masa sharri. Murmushi yayi tare da girgiza kansa ya ce "Shi yayi daga karshe ya amsa, yanzu haka ma sun ce dole sai ya aureta" Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, lallai na tabbata karshen duniya yazo, a ce yaro mai shekaru 20 ya yiwa mace ciki, amma abin da mamaki yake. Ya sauke numfashi ya ce "Waye ne mai shekaru 20, Sadiq fa 25yrs gare shi 5yrs muka ba shi, ai wannan ba abin mamaki bane" Ta kammala cin kifin ta ce Kai Ammar, kai yanzu za kace 30yrs gareka, haba dai sai dai 25yrs. Ta miƙe ta shige toilet ta wanke hannunta sannan ta fito, ta zauna tana jinjina al'amarin kai yaran yanzu da karambani suke.... "HAMRAH kina nufin I'm 25yrs to kenan ke 30yrs" Ta hararesa ta ce Ka jika I'm 35yrs, kana nufin zaka haɗa kanka dani. Yayi murmushi yana kallon ta yace "Shekaru biyar kika bani, kuma suma ai suna ne" Ammar kenan, girman nan dai na fika, kaga bacci zanyi gobe morning duty nake dashi. "To babbar yaya a tashi lafiya" Ya miƙe ya fice ta gyara wajen ta kashe tv sannan ta kwanta saboda kada ta makara wajen tashin safe. Comments and share [1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 7 & 8 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________Tun da na baro gida nake ta sake² cikin raina shin nayi amfani da shawarar da ki ka bani ne ko kawai na watsar nayi sha'anin gaba na. Har na iso gida na ban sami mafita ba, na tadda yaran har sun dawo daga gidan kakarsu ta uba, da akwai Uwale wacce ke taya ni aikace aikacen cikin gida, na tadda ta har ta kammala musu abinci dare kasancewar ni yawanci ban cika cin abinci da daddare ba ko da yamma ma sai dai ko da rana ko kuma da safe haka sai na yi full tank. Na yi shigewata ɗaki sai jin raina na yi yana ɓaci sbd tunowa da na yi za amin kishiya, abin da ya fi tada min hankali shine wai a ce BUKAR zai iya kwanciyar aure da wata mace ba ni ba, kai lallai na miji ba ɗan goyo bane, sai kawai na ji bazan iya kyautata mashi ba, ina nan zaune bakin bed har zuwa lokacin ina ta zancen zuci, daga bisani dai na ɗan sauko na miƙe sbd gabatar da sallah magrib, har zuwa ishai ina kan dardumar sallah sannan na fito palour na zauna. Na jima a zaune ko zanji motsin shigowar shi amma har 9:00pm shuru na dawo ɗakina na faɗa toilet na watsa ruwa kamar yadda na keyi a ko da yaushe in dai zan kwanta, sai na ji alamun tsayuwar motar shi, na sauke numfashi tare da duba agogon da ke manne jikin garun dake cikin ɗakin to 10:00pm. Alay BUKAR kamin ya ɓullo da zancen aure ana idar da sallah isha'i ya ke shigowa gida amma kuma tun da ya tsaro da zancen auren nan sai ya kai 10:00pm to 11:00pm kamin ya shigo kuma ko da ya shigo side nasa ya ke wucewa, yana watsa ruwa yake ɗaukar wayar shi ya kafata a kunne yana fira sai ya kai 2:00am sannan ya ke kwanciya. Wannan yana daga cikin abin da yasa na janye jiki daga gare shi. Jin ya turo kofar palour ya shigo sannan ya maida ta ya rufe ya wuce ɗakin shi, ina jin shi ya saka key, cen kuma na sake jin ya fito, hakan ya sa na fito a hankali dan ganin ina kuma zai je, a zaune a palour na hango shi kan 2setter yana waya, na ce to yau za ka gamu da nawa salon ƙissar, to in ba a abin ita wacce ya ke son auren ta ba magidanci na gidan shi da wannan lokacin ki kira shi ko ya kira ki, ki kuma ɗauka kina jin kan ki wai yana son ki to in dai ki ka yi wa wata to kema wataran za a yi miki. Na koma cikin ɗakina ina ta kai kawo, kawai na sake faɗawa toilet na haɗa ruwan wanka da haɗin ruwan turaruka haɗi na musamman na watsa a jikina na fito sai kamshi na ke, na wuce gaban mirror na shafe dukkanin jikina da man da na haɗa ta coconut oil and carrots, na mulke duk jikina musamman ma mazaunaina da suka fi jan hankalin shi, sannan na shafa haɗin culacham da kuma humra, na iso wajen wardrobe na buɗe ina duba wacce iriyar riga ce zan saka ta tafi da imanin shi, cen na hango wata arniyar riga wacce da ita gwanda babu, milk color ce silk da ita hannun vest ta ɗan sauko kasan mazaunaina kaɗan duk cinyoyina a waje, na sake fashe jikina da turare na cire ribon da na tufke gashin kaina dashi na baza gashin na fito na ce bari yau na yi bariki a cikin gidana, abu na halak. Ina isowa cikin palour na sauya salon tafiyata a hankali na ke tafiya tare da dan jijjiga jikina, ƙirjina da mazaunaina na ke motsa su har na iso sakiyar palour na yi kamar bangan shi zaune ba, cikin yanayi kamar na ɗan yi bacci na farka, na iso kofar palour na sa key na rufe kofar ina cewa Uhm Uwale ko mantawa tayi bata rufe kofar ba yau. Na wuce inda yake kwance nan ne inda makashin wutar palour yake, cikin irin na ɗan ji tsoron nan na ɗan ja da baya tare da furta Subhanallah, ashe da mutum a wajen. Na ɗan wani fari da idanuwana, sannan na juyo cikin sake kanza salon tafiyata na dawo cikin ɗakina, na faɗa kan bed ina sauke numfashi, ina addu'ar Allah yasa wannan tarkon ya kama. Ina cikin wannan tunanin ne naji alamun motsin buɗe ƙofar ɗakin, sai na yi saurin juyawa ƙofar baya na kwanta tare da sake turo da mazaunaina alamun na fara bacci, ya shigo tare da tsuramin idanuwa na wani lokaci a hankali naji ya ce "Oum Ukhty" Na taɓe baki wai tab lallai abin ya yi aiki, sai da ya furta kusan sau biyu na ɗan juyo ina wani motsa jiki tare da murza idanuwana ina Daddyn Ukhty, lafiya da tsohon daren nan?. Ya sauke wani irin gwauron numfashi ya ce "Yunwa nake ji, kamar zan jure sai kuma na tuna in na kwana da yunwa ulcer ta za ta iya tashi min cikin dare, shine na ce ko zan sami abin taɓawa" Kaɗan nayi dariya, kai na miji, Uhmm halin shi sai shi, mutumin da ya kauracewa abincina shine yanzu ya ce wai in baici ba ulcer shi za ta tashi, na ce To yanzu dai ba abinci a ƙasa sai dai ko na ɗan dafa maka indomie na soya kwai akai da kuma tea. Jin hakan ya sa ya matso ya zauna bakin bed ɗin ya ce "Aiko da kin kyauta min beb. Beb! Na furta cikin raina, lallai Alay BUKAR ba shi da dama, ganin ya zauna bakin bed yasa na miƙe cikin rangwaɗa na wuce shi na fito tare da buɗe kofar na fito har ina jin yadda ya ke sauke numfashi, ina fita na sheƙe da dariya na wuce kitchen ina ni za ayi wa iya shege. Cikin mintina kaɗan na kammala haɗa masa na jero kan trey na wuce da shi ɗakina sai dai kuma baya ciki na ajiye masa, jin shuru ya yi yawa yasa na leko ɗakin shi ko yana nufin cen ɗin zan kai mashi ina shiga ko na tadda ya fito daga wanka, cikin sanyin murya na ce Na kawo maka nan ne ko na barshi a cen ɗin?. A hankali ya ke kallona ya ce "Ki kawo min nan ɗin" Har na juyo zan fice ya kira sunana "Ayshe" Na tsaya ba tare da na juyo ba, ina jin shi har ya iso kusa dani yasa hannun shi ya juyo dani tare da ɗago da fuskata ya kuramin idanuwan shi da suka fara kankancewa ya ce "Na gode, na hanaki bacci ko?" Kamar na yi dariya amma na sake haɗe fuska na ce To ai ba komi. Saukar hot kiss naji kan goshina, ya sauke numfashi ya ce "Ki kawo min kin ji" Kai na gyaɗa na fice, ina mamakin wannan al'amarin, na ɗauko na kawo masa na ajiye mashi cikin sanyin murya na ce Gashi nan zan wuce na kwanta. Ya yi saurin isowa ya rike min hannu, ya ce "Please, stay with me har na kammala" Na ɗan wani fari da idanuwana tare da zaunawa, shima ya zauna tare da rike hannuna, ɗayan hannun shi kuma yana cin abinci shi yana kuma ƙurban tea, har ya kammala tare da janyoni jikin shi yana shaƙar kamshin jikina ya ce "Na hana ki bacci ko so sorry beb" Banyi magana ba, na sunkuyar da kaina ya dago da fuska sai ganin hawaye na bin kuncina a hankali ya share min cikin sanyin murya ya ce "Ki yi hakuri Ayshe, i don't meant to hot you, kin fi kowa sanin ina son ki, bazan taɓa cutar da ke ba, ke ta daban ce, kin ji ina son ki" Na sauke numfashi sbd nima na yi kewar shi sosai, sbd Alay BUKAR irin mazan nan ne da suka ƙware wajen iya sarrafa mace. Amma na sake turo baki na miƙe da nufin barin ɗakin ya yi saurin dawo dani ya rungume ni yana sauke numfashi cikin sauri² yana ajiyar zuciya tare da kwantar dani kan bed yana kissing ɗina ta ko ina a jikina, duk ya kiɗime yana "Wlh billahillaza ke ta daban ce, kwal uba.... Nayi saurin manne baki na da nashi sbd ɗakin yaran na kusa da nashi kada su jiyo mu, cikin salo da dabara na ƙiɗimar dashi, yana samun nutsuwa ya koma gefe ya kwanta yana sauke numfashi, ya ɗau tsawon wasu muntuna sannan ya sake janyo ni jikin shi tare da ɗago da fuskata ya kura min idanuwana na wani lokaci sannan ya ce "Ki yi hakuri da kin faɗa miki ƙarin auren da ban yi ba, ban san ya zaki ɗauki abin bane shiyasa nake tsoron faɗa miki, zan ƙara auren ne ba dan kin gaza min komai ba kawai zan yi ne saboda hakan yana cikin ƙaddarata, na miki alkawarin bazan cutar dake ba, kin ji beb so sorry Please" A hankali na lumshe idanuwana na rintse su sosai ina jin zuciya ta tana min zafi, kuma wannan yana da nasaba da irin kishin da Allah ya halicce mu dashi mu mata, na sauke numfashi sannan na buɗe su tare da zuba masa su, ina son Alay BUKAR ba wai auren da zayyi bane bani so, tsoro na ɗaya shine kada wacce zai auro ta shigo ta wargaza min farin cikin gidana, amma ba komi zan na barwa Allah... A hankali na ji saukar hannun shi kan fuskata yana ci gaba da rarrashina har bacci yayi awun gaba damu, washegari bayan mun tashi mun karya ya ce zai je ya dawo. Fitar shi bada jimawa ba ya dawo tare da miƙamin key motar, cike da mamaki nake kallon shi, ya rike hannuna muka fito compound na gidan nan nayi tozali da sabuwar mota, ya ce mani ya siyowa, cikin murna da farin ciki na karɓi key ɗin ina godiya. Da yamma lis ina zaune a palour na ji ana nocking, na miƙe na iso na buɗe sai ganin Sulaiman furniture na yi a tsaye, a lokacin ne ma na tuna da cewa mun yi waya a kan zai zo ganin set na kujeru na, sai muyi magana. Bayan mun gaisa ne ya shigo a lokacin shima Alay BUKAR ya dawo nan ne ya ke tambayar meke faruwa ne?. A nan nayi mishi bayani ya ce kada na damu za suyi magana, to shine fa daga wannan maganar washegari da safe, yau kenan nake nufi aka shigo min da kujeru da tv da kuma show glass, aka ajiye su a ma'ajiyar su, shine ya ce gobe za a kamin set na kayan ɗakina. Sauke numfashi Hamra ta yi cikin farin ciki, ta furta Alhamdulillah, kin ga abin da nake nuna miki ba, da yanzu kin biyewa zuciyar ki da shikenan ta kai ki ta baro ki, hakuri za kiyi, da kuma ki dage da addu'a Allah ya ka miki sauki cikin wannan al'amarin. "Haka ne yaya HAMRA na gode, in shaa Allahu zan ci gaba da hakuri da kuma addu'a" Sun jima suna tattaunawa sannan Hamra ta yi musu sallama ta dawo gida, kasancewar dare ya soma yi ko kuma dare yayi dan a lokacin to 9:00pm unguwar su cike take da majalisar mata sa da kuma ta dattawa, a hankali take takowa saboda ɗan sahu a bakin layin unguwar su ya ajiye ta, har tazo giftawa ta ce ɗaya daga cikin waɗanda suke zaune a majalisar dattawa ya ce "Kai ina mamakin rayuwar yanzu, ka duba fa wannan yarinyar tana iskanci ƙarara ubanta na gani, yanzu fisabilillahi a wannan lokacin ya dace a ce ƴa mace na waje, kai da wannan ɗiyata ce wlh ko sadaka zan bada ita" Ci gaba da tafiyarta ta ke, kasancewar bata da saurin tafiya shi ya sa ta ke jiyo abin da suke faɗa, murmushi ta yi tare da girgiza kanta a ranta ta ce shi fa zato zunubi ne, yanzu basu san daga inda ta ke ba suka ƙaƙaba mata sharri in ta ce bata yafe ba ma ya zauna amma ba komi ta barsu da halin su. Ɗaya daga cikin su ya tari numfashin wanda ya yi magana ya ce "Ka taɓo min in da yake min ciwo, abin takaici ma wai akin asibiti ta ke, a ce ƴa budurwa tana aikin asibiti kuma wai har da wani night duty, kai kaji shashanci Bature wato su suna night a na kuma night dasu" Suka kwashe da dariya, ita abin da ya bata haushi ma shine sa'annin mahaifinta ne amma suke faɗin haka akanta, ta ji saukar muryar mutum na uku ya na cewa "Ai ni ban ga laifin ta ba, na ubanta nake gani, shi fa ko a jikin shi tana sheke ayar ta a gaban sa amma bai iya cewa kala, irin waɗannan ai auren dole ya dace ayi musu dan in dai ta su ne su shekara saba'in babu aure" Tayi sauri ta wuce su, ranta bai ɓaci ba tausayin su ma ta ke saboda yi da mutum haramun ne, ta turo kofar gida ta shige, har ta iso kofar shiga palour ta ji muryar AMMAR na cewa "Likita" A hankali ta jiyo ta kalle shi ta ce Ammar, kaima shigowar ka ko?. "A'a tun ɗazu na dawo jin baki gidan ya sa na ji babu daɗi kuma na kira ki baya shiga" Ta sauke numfashi ta ce Ji ka sai ka ce dan yaye, dan bana nan shine ka ke jin babu daɗi to ina kuma ga nayi aure, sai kuma ka yi yaya. Murmushi ya yi sosai ganin yadda ta ke wani zazzare idanuwan ta na faɗa, Hamra kenan akwai hakuri da saurin hawa ta ce "To me a ciki ba sai na biki cen gidan ki ba, mu tare a bani ɗaki, ko ya ki ke gani babbar yaya" Ya faɗa yana dariya, ta hararesa ta juyo tare da buɗe kofar ta shigo ya bi bayanta, ɗakin Ammie ta nufa, ganin haka ya sa AMMAR wucewa ɗakin sa. Ta shiga tare da sallama, Ammie na zaune tana kallo a ɗan karamin tv ta, ta amsa mata, HAMRA ta zauna tare da cewa Ammie na dawo, jikokanki suna gaida ki, Ayshe ma ta ce na miƙa mata sakon gaisuwa. Sauke numfashi Ammie ta ɗago sosai tana kallon Hamra, ganin haka yasa ta yi saurin sudda kai kasa, Ammie ta ce "Da fatan baki mance da abin da na faɗa miki ba, akan cewa na baki nan da ƙarshen wata ki fidda miji?" Jikin Hamra ya yi matukar sanyi ta ce Eh Ammie ban mance ba, sai dai Ammie har zuwa wannan lokacin bani da sayayye..... "Na gama magana ta, shawara ta rage gareki, bazan zuba idanu ina kallon ki ba, sannan ki sani kasancewar ba ki da aure ba zayyu ki dinga zuwa gidan ƙannenki ba, yin hakan ba tsari bane, kema ki yi ƙokari ki mallaki na ki gidan" Sauke numfashi Hamra ta yi ba abin ta yi kuka ba, da yau ko mahaukaci ne ya fito neman aurenta zata amince ayi in dai hakan shine farin cikin Ammie, jiki a sanyaye ta ce In shaa Allahu. Ta mike ta iso ɗakinta, zama ta yi bakin bed tare da riƙe kanta sosai tana ji yana tsara mata, ita kanta zamanta babu aure yana damun ta amma ya za tayi, dole tayi hakuri zuwa lokacin da Allah ya yi za ta yi auren.... "Kuka ki ke yi?" Saurin ɗagowa ta yi ta kalli Ammar dake zaune kan carpet ya tsura mata idanu, bata ma ji shigowar shi ba, girgiza kai ta yi ta ce Shikenan bani da abin yi sai kuka. Murmushi ya yi ya miƙe ya kunna tv tare da kaiwa channel na MBC ACTION, ya dawo ya zauna ya ce "Ba haka na ke nufi ba, na san kin shiga ɗakin Ammie kuma na san da zaran kin fito ki ke kuka, sbd ba ta son kulaki" Ta sauke numfashi a hankali ta ce Mun yi magana da ita yau. Cike da mamaki ya ce "Abu ya fara yin kyau, to me ta ce da ke?" Hamra bata ɓoyewa Ammar damuwarta wani abin ma sai su yi shawara tari kuma ta sami mafita ba tare da kowa ya sani ba ta ce Ammie ta ba ni nan da end of the month na cire mijin aure. Jikin sa ya yi sanyi ya ce "To in ba abin Ammie ba, menene abin gaggawa har da yanke lokaci, kuma ma abin damuwar shine babu tsayayyo balle ki zaɓa, amma ba komai zan yi magana da Daddy..... A'a Ammar mafita zamu nema ba wai sanar da Daddy ba, faɗa masa ba abin da zai haifar sai rashin hankali dan tunkarar Ammie zayyi da maganar kuma kasan baya son wannan magana, mu dai nemo wata hanyar. "Okay, ba damuwa ban nan da zuwa gobe zan samo mafita" Sun jima suna fira sannan ya tashi ya fice zuwa ɗakin shi, ta miƙe ta faɗa toilet ta watsa ruwa ta yi shirin kwanciya sbd fita aikin safe, bayan ta kammala addu'ar bacci ta shafe dukkanin jikinta, ta kwanta. WASHEGARI ____ A nutse ta kammala shirin tafiya wajen aiki, bayan ta gaida Ammie kuma ta sanar da ita zata wajen aiki ta fito, ɗan sahu ta hau dan Ammar na bacci, tana isowa ƴan night na shirin tafiya, ta shigo office na ta, ta ciro duk abin da za ta buƙace shi anjima ta ajjiye kan teburin, sannan ta kunna system ɗinta, sai jin ƙarar abu kamar ya faɗo daga waje, da kuma hayaniyar tafiyan ƙafafuwan mutane, ikon Allah duk da bata da shiga abin da bai shafe ta ba, amma sai ta tsinci kanta da son ganin meyasa ake wannan sintirin, a hankali ta buɗe ƙofar ganin ana fidda kaya daga cikin office na Dr Aliyu yasa ta yi mamakin hakan, me hakan yake nufi Dr Aliyu zai bar office ɗin,...... "Dr Hamrah" Ta juyo ta kalli nurse Laraba iyayen gulsy, ta ce Ya aiki. Nurse Laraba ta ce "Sai godiya woo, yau mun tashi da wani lamari mara daɗi, kin ga wai Dr Aliyu za ayi wa transfer" Cike da mamaki Hamra ta ɗago ta kalli Laraba tare da cewa Transfer kuma?. "Eh haka na ji MD ke faɗi" Sauke numfashi Hamra ta yi, wato ta wannan hanyar MD ya ɓullo amma ba damuwa, she knows what to do......... Comments and share [1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 5 & 6 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _______ Buɗe idanuwanta tayi a hankali a daidai lokacin da ake kiran assalatu ta asubar farko a nan masallacin dake layin unguwar su, da ƙyar ta sauko daga kan bed duk tsawon baccin da tayi amma ji take bai isheta ba duk jikinta yana mata ciwo, sbd gajiyar tafiya da dawowa ta wajen aiki da take yi. Tana shiga cikin toilet ta watsa ruwa bayan ta yi brush ta ɗauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga da dogon hijabi ta idar da raka'a biyu na nafila sannan tayi raka'a biyu na farillah, ta jima tana miƙa kukanta ga Ubangiji sannan tayi azkhar na safe ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sannan ta shigo kitchen, ta tadda Ammie na kitchen tana haɗa karin kumallo hakan ya tabbatar mata cewa Daddyn su zai yi fitan safe saboda a duk lokacin da Ammie in dai da kanta ta shigo kitchen to hakan na tabbatar wa da breakfast zata haɗawa Daddyn su dan shi in ba dole ba baya cin abinci masu aiki sai dai ko su yaran su dafa shima sama² yake ci, HAMRA na taimakon amma tun ranar da wannan al'amarin ya faru a sakanin su Ammie ta dakatar da ita daga duk abin da take yi, HAMRA na da gudun ɓacin ran Ammie shiyasa ta ke taka tsantsan da abin da zai jawo ta bata mata rai. Ƙarasowa ta yi kusa da ita cikin girmamawa ta ce Ammie, ina kwana?. "Alhamdulillah" Kawai abin da ta faɗa ta ci gaba da haɗa souce ɗin kayan ciki, hamrah jiki a sanyaye ta wuce cikin store dan dubo ko da akwai abin da zata girka cikin sauki, mutum ta tayi tozali da shi jirge a gefe guda a store ɗin da alamu jiya da daddare mai kawowa Daddyn ya kawo musu, kai fitanta aiki yasa bata sanin wasu abubuwan saɓanin a da ita ke duba ƙarewar abin store ta sanar, ɗauko ɗaya ta yi ta maida hankali ta fere doyar ta sannan tafasa shi ta soya da kwai ba tare da tayi souce ba ta zuba yaji akan plate ɗin da ta zuba soyayyar doyar ta fito, dan tasan bata isa ta taɓa wanda Ammie ta girka ba, to ina ma fuskar balle ta taɓa haka ta tattaro ta dawo ɗakinta ta haɗa black tea ta sha tare da cin doyar sannan ta shirya ta fito tafiya kada ta makara. Ta shige ɗakin Ammie ta tadda Daddyn su ya shirya yana breakfast da alamu fita zayyi da ya kammala ta gaida shi ya amsa cikin kulawa Good morning Daddy. "Morning likita, har an fito, to Allah ya taimaka" Ameen Daddy, eh na fito ina sauri ma kada na makara. "Gaskiya kam yanzu lokacin gudu yake kan ka ankare ka makara" Eh fah Daddy, Ammie anjima da na tashi zan wuce gidan Ayshe. "To" Kawai Ammie ta ce, taci gaba da cin abincinta, Daddy ne ma ya ce "Ah madallah ki gaida min da jikokai na, ko zaki jira na sauke ki ne?" Zasu ji, a'a Daddy zan wuce ... Ammar ne ya shigo tare da sallama bayan ya gaida Daddy da Ammie ya ce "Ah na manta ashe kin koma morning, to tashi na sauke ki, nima fita zan yi" HAMRA ta sauke numfashi SBD rashin sakin fuskar da Ammie ba tayi mata ba, kuma amsawar da ta yi shima saboda Daddyn su dake wajen ne a hankali ta kalli AMMAR ta ce To tashi mu tafi kada na makara. A tare suka fito, sun ɗanyi tafiya jim kaɗan ya ce "Afwan bari na kira a amshi sako minti biyu Please" HAMRAH ta soke fuska ta ja numfashi ta sauke ta ce Kaga irinta ko, ni dama bari na kayi na hau ɗan sahu hankali na kwance, amma kawai kasa mutum ya makara. Murmushi yayi ya ɗau waya ya yi ƙira, ya sanar da mai shi ya iso. ya juyo ya ce "Ayi hakuri likita, ban yi bayani ba tun farko" Bata ce komai ba ta maida kallon ga bakin titi tana kallon yadda mutane ke sintiri. Suna nan zaune cikin motar Hamrah taji muryar mace tana "Young Roheet how fah" Ta ɗago ta kalleta, fara ce sol ƙirar Yaruba, tana ganin HAMRA ta ce "Is she your sister, kuna kama sosai, hey barka da safiya?" Hamra ta sake fuskantar ta amsa da Yauwa, barka dai. Ammar ya ce "Yeah, uhm Furera ga sakon ki, tun jiya fa nake son kawo miki amma abubuwa sun sha min kaina. Ya mika mata ta karɓa tayi masa sai anjima ta tafi ya tada motar su kayo hanyar Hospital, Hamra ta ce Young Roheet, yaushe kayi sabon suna?. Murmushi ya yi ya ce "Tun sunan da suka saka min jss, shine har ya bini" To, ikon Allah wato kai fans na Roheet ne na India shine suke kiran ka da sunan shi. "Uhm wai muna kama suke cewa" Ta taɓe baki ta ce Uhm ya yi kyau. To AMMAR da alamu bikin Yaruba zamu yi kenan?. Ya sauke numfashi a daidai lokacin da yayi parking bakin gate na Hospital ɗin ya ce "Ni bani da wata budurwa wannan itama tana cikin waɗanda zamu tafi training ne kuma tare muka kammala secondary skul namu" Uhm to waya san muku yaran yanzu. Murmushi yayi ya ce "To babbar yaya sai kin dawo" Thanks. Ta faɗa ta shige ciki a daidai lokacin da MD shima yake parking. Kai tsaye office nata ta nufa ta buɗe ta shirya duk abin da zata buƙata sannan ta sanya white coat ta fito, taci karo da Nurse Laraba cikin sauri ta iso kusa da ita ta ce "Dr HAMRAH, yau kina morning kenan?" Kallon ta HAMRAH tayi sam bata son shishigi da kwainene irin da abokan aikinta to in ma ba abin Laraba ba, da bata morning duty ai ba zata ganta ba, ta ce Eh Laraba, da akwai wani abu ne?. "No, ba wani abu bane, daman tun jiya nake son yi miki magana ashe kina night duty shine na bari yanzu kuma na ga hango ki shine na ce bari mu gaisa kuma naji ana cewa kun sami matsala da MD wai akan ya ce..... Sauke numfashi HAMRA ta yi cikin takaici ta ce Laraba, mind your business. Wannan ba hali bane to menene naki a ciki in ma ya faru ai sakanina da shine. Tana faɗin haka ta shige cikin general ward, tana mamakin gulmar ma'aikatan wannan Hospital ɗin musamman ita wannan Nurse mai suna Laraba akwai kai kawo sakanin ma'aikata. A nutse take gaisawa da patients ɗin ta jima a wajen su, sannan ta dawo office nata, Dr Aliyu ya shigo tare da sallama yana "Good morning special Doctor" Cikin sakin fuska ta ce Morning doctor Aliyu, ya ƙoƙari?. "Sai godiya kam" Da akwai abin da kake buƙata ne?. "Eh Dr Hamrah akwai patients nawa taƙi na duba ta shine na ce ko zaki duɓa min ita, kin san yawanci mata in ba a dole ba ba sa son maza su duba su, ita ma wannan haka taƙi" A hankali ta katse abin da take yi a system nata ta ɗago, ta ce A wane ward take?. "Tana vip 3" Ok ba matsala a tare suka fito, Dr Mahmoud yana daga bakin ƙofar office na shi ya kura musu idanu ganin su tare kuma su biyu yasa ya haɗe rai har suka ɓace wa ganin sa. Dr Hamrah ta wuce vip shi kuma ya wuce wani bangaren, tana shiga ta tadda patient ɗin ta dubata sannan ta fito ta iso office nata. Dr Mahmoud da kuma MD suna tsaye suna tattaunawa har ta iso ba tare da tayi magana ba ta buɗe office ta shige ta zauna, ta kunna system nata ta ci gaba da aikin ta. Taji an turo kofar a hankali ta ɗago MD ne ya ƙaraso ya tsaya yana karewa cikin office ɗin kallo cike da mamaki ta kallon shi mutum ko sallama ba zayyi ba da girmansa.... "Hamrah who are you?" Ta sauke numfashi, bata yi mamakin wannan tambayar ba dan indai bak'ar magana ce ya iya yinta kuma duk yanda yaso haka yake yinta ta ce I'm human like everyone. "Saboda jiya nayi miki magana shine kika ɗau gaba dani?" Ta sake kashe system nata ta ce Subhanallah gaba kuma MD, a'a ni bana riƙe kowa a raina kuma mema zai sa na yi gaba da kai?. Eh wato duk iya shegen sa akwai wacce ta fi shi, murmushi yayi har jajayen hakwaransa suka bayyana ya cire glass na idon shi ya ce "To me yasa da kika ganni da Dr Mahmoud ki ka wuce ko gaishe ni bakiyi ba?" Ta sauke numfashi ta ce Oh i got it, nayi tunanin kuna tattaunawa ne shiyasa bana son katse ku. Nan ma ya ce "Hamrah i need to know more about you" This time murmushi ta yi ta ce I'm nobody but I'm somebody. "What that means" Uhm sir, nothing. Mamaki yake yi tabbas akwai abin da take takama da shi, koma menene zai bincika ya gani sannan kuma nan da kwanaki biyu zata gane kuren ta. Ya juyo ya fice ta ci gaba da aikin ta. Ita sam taki jinin yawan magana musamman ma akan abin da bai da muhimmanci shiyasa sai suke ganin kamar girman kai gareta, amma she's so simple sai dai ba zata juri wulakanci ba, sannan tana girmama duk wanda ya kama girman shi. 5:00pm nayi ta fito, bayan ta kulle office nata, cikin nutuwa ta iso bakin gate na Hospital ta samu ɗan sahu ta mai kwatancen unguwar Ayshe amma ta ce dashi ya tsaya tayi shopping a bakin babban titi. Nan tayi siyayyar tsaraban yaran sannan ya kaita ta sallame sa.Turo gate ɗin tayi ta shigo ta hango yaran suna wasa a compound na gidan hankalin su kwance sai wasan su suke jin ƙarar turo ƙofar ne yasa suka juyo aiko suna ganin ta su kayo inda take suna "Oyoyo Mommy Hamrah" Cikin farin ciki ta rungume su tana cewa Oyoyo, ya kuke? Nazeer, shine ɗan fari a wajen ƙanwarta Ayshe ya ce "Mommy Hamrah muna lafiya, ina grandma and pa?" Tayi murmushi ta dafa kan nazeer ta ce Suna lafiya kalau suka ce a gaida ku. Cikin murna suka rakota ciki, a hanyar ta shigowa ciki ne ta hango sabuwar mota dal anyi parking nata a area park. Suka shigo ciki tana sallama tayi trus ganin an kanza komai na palour, tana ƙarewa wajen kallo yaran kuma su kayi ciki da gudu suna kiran sunan maman su cewa Mommy Hamrah ta shigo. Mamaki take ya a kayi Ayshe ta samu ta kanza set nata bayan sunyi magana da ita, ta ce bata da halin kanzawa. Zubawa sabon show glass din idanu tayi yadda aka jera kwalaben turaren wuta da humaira da culacham a ciki yayi tsari, ikon Allah duk wannan a 2days a kayi shi, sai kuma babban plasma ta dake kan tv stand saɓanin nata da kwanaki ƙarami dake manne jikin garu, tabi kujerun da kallo sunyi kyau cikin yadi golden color.... "Yaya Hamrah" Ta ɗago ta kalli Ayshe dake ɗauke da murmushi kan fuskar ta, ga dukkan alamu tana cikin farin ciki, itama murmushin ta yi ta ce Bakuwa babu sanarwa ko?. Murmushi Ayshe ta yi ta ce "A'a ai nan gidan ki ne zaki iya shigowa a duk lokacin da ki ka ga dama" Murmushi HAMRA tayi taji daɗin abinda Ayshe ta faɗa mata ko ba komai ta mutunta ta shiyasa tasu tafi zuwa ɗaya ta ce Nayi kewar yarana ne naga a weekend amin rowar su. "Uhum kin ganni nan kwana biyu ban zauna ba yanzu hake ke nake bi a raina, ina ta son na kiraki kuma ina tunanin kina Hospital shine na bari in kin koma gida muyi waya, sai ko gaki ƴar halak" Nima haka fa, tun jiya nake son kiranki amman ban samu na kira ba na ce kawai inna tashi wajen aiki sai na biyo na duba ki na shigo kuma naga abin duniya. Dariya Ayshe ta yi ta ce "Uhmm ke dai bari ƴar'uwa, bari na fara baki ruwa ki sha" Ayshe ta shige ciki, yaran kuma suka fito suna sake mata sannu da zuwa so biyar ne ƙaramar cikin ita ce takwarar HAMRA suna kiranta da UKHTY ( ƴar'uwa), HAMRA ta rike hannunta tare da zaunar da namecynta kan cinyarta tare da ciro musu da tsara ta basu sai murna suke, ta ce da namecynta Takwarata, how was skul?. "So good" Ta faɗa cikin siririyar muryar ta, yarinyar ce ƴar shekara 3 kyakkyawa da ita kamar HAMRA ce ta haife ta saboda kamanninta ta ɗauko, HAMRA ta sake ce mata Da anyi hutu zan aiko Uncle AMMAR yazo ya taho dake kinji?. Cikin murna ta ce "To" Suka shige ciki tare da tsarabar su suna murna, Ayshe ta shirya abincin kan Dining table dake Dining area ta dawo palour wajen yayar ta. Zama tayi ta ce to kinga an fara kiraye² sallah magrib mu idar tukuna" Murmushi HAMRA ta yi sosai rabonta da taga ƙanwarta cikin wannan farin cikin har ta manta, ta ce Ayshe na kagu naji menene dalilin wannan farin ciki haka. Itama Ayshe tayi dariya ta ce "Aiko zaki ji, muje bedroom mu idar da sallah tukuna" A tare suka shige cikin, Ayshe ta ce da ita ta shige toilet ta ɗauro alwala, HAMRA ta shige ta ɗauro ta fito itama Ayshe ta shiga. Kusan lokaci guda suka idar, amma Ayshe taki bata labarin ta ce su ci abinci tukuna, HAMRA dai ta taɓe baki suka fito tana ganin mulki, sun kammala cin abinci su ne suka dawo palour suka zauna, a lokacin mijin Ayshe ya shigo tare da sallama ganin Hamra zaune yasa jikin shi sanyi ya ɗan tsaya jim kamar ya koma kuma sai ya yi wani tunani ya karaso ya zauna, murmushi Hamra ta yi da taga abin da ya yi, ta san ya san cewa ta sami labarin ƙarin auren da zayyi shine yake jin nauyinta, ta ce Ina wuni Babana?. Daman sunan da take kiran shi da shi tun ranar da ya saka mata takwara. "Lafiya kalau, ya kwana biyu, na ke tambayar mamar ta ki kin ɓuya kwana biyu, ta ke ce min aiki ne ya ɓoye ki" Sauke numfashi ta yi ta ce Eh fah ai Sunday ne kaɗai nake hutawa, shiyasa fita unguwar ma bana samun yi yanzun ma na ce zan yi sqwizing time nawa na biyu na duba yaran. Ah aiko kin kyauta, ai sha'anin aiki sai an jure abin ba a cewa komai, yana magana yana sunkuyar da kanshi ƙasa, ita dai sai murmushi take to menene yake wani abu so gulty to dan zayyi aure ai babu mai hana shi. Abin da yasa yake jin nauyinta sbd ya sha wahala kamin aka ba shi Ayshe kusan hauka ya dinga yi musu, HAMRA ce ta shige ma shi gaba wajen Daddyn su aka ba shi hakan ma sai da ta haɗa da wani aminin Daddyn su sannan Daddyn na su ya amince saboda shi Daddyn a lokacin akwai wanda babu ya ya kawo kuɗin aure sannan a zo da wani zance ya ce baza a mai dashi ƙaramin mutum ba, to haka dai Hamra ta yi ta rokon sa da ƙyar ya maida musu kuɗin auren da suka kawo, saboda shima yaga tijarar da Alay Bukar yayi har fa kwana yayi a ƙofar gidan su, kuma anyi ruwa a wancan daren yayi mishi duka har sai da ya kwanta a Hospital, daga karshe dai aka bashi ita sosai ya riƙe sunyi soyayyar da sai da kaf familyn su suka sani suke sha'awar su, har ta kaiga ya saka mata takwara, saboda sake kulla zumunci, ranar suna ko anyi bidirin da ba a taɓa yin irin sa ba dan hamra tayi wasan Naira. Sauke numfashi Hamra ta yi ta ce Amma a hutu zan aiko da Ammar ya ɗauko min takwarata. "Babu komai ai, sai yazo ɗin in ma bai samu zuwa ba da kaina zan kai miki ita" Ta sauke numfashi tare da cewa Na gode. Cikin sanyin murya ya ce "Yaya HAMRA" Sunan da yake kiranta dashi a lokacin da yake cikin giyar son ƙanwarta duk da ya girme ta amma yake bata girma a matsayinta ta yar matar sa, cikin sanyin murya ta ce Na'am Alay Bukar. Daman Allah ya ƙaddara zan sake wani auren, kin san rabo babu yadda ka iya dashi, wai aka ce rabo ajali, to a takaice dai next week za a ɗaura min aure" HAMRA ta so tayi dariya da wannan dogon zancen da ya ɗebo tun da dai aure ba fashi ai ba wani ɓoye² ta ce Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya baka ikon yin adalci a sakanin su. Ya washe baki yana "Ameen wlh Daughter" Uhm maza kenan halin su sai su. Wato fa in sun ce sai sun yi to sai sun yi ɗin. Ya miƙe ya shige ciki ya bata da zancen zuci, sai da suka idar da sallah ishai sannan ya fice ya basu waje Hamra daman a ɗaki suke HAMRA ta ce ta bata labarin wannan farin cikin, murmushi Ayshe ta yi ta ce "To yanzu ko zaki ji........ (Sakanin mata da miji sai Allah) To sai ku biyo ni dan jin wasu hanyoyi Ayshe ta bi har wannan Alay Bukar nata ya kanza mata set. To uwar gida taho, biyo ni da gudu zuwa next pg dan jin wannan sirrin. Na san wata zata harare ni ta ce ba set ba koma menene za a kanza ba zata yarda a yi mata kishiya ba💃🤣 Allah yasa dai ana fahimtar littafin MUJARRABI 😃 Comments and share [1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA PG 9 & 10 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ Tana tsaye har zuwa wannan lokacin tana kallon yanda ake fidda da kayayyakin dake office na Dr Aliyu, cikin wulakanci suke fiddawa shiyasa ma sauran kayan suke faɗuwa suke da farfashewa, lallai MD ya cika mara imani, duk da bata fahimci manufar shi ta yin hakan ba amma tasan da wata a ƙasa. Ba abu ne mai wuya ba ya ɗauke duk wanda yaga dama ya kaishi wani bangaren yanzun ma tasan wani ɓangare na daban zai kashi, shiyasa ake kiran shi da transfer master sbd yadda yake juya Nurses kamar waina, a ce ba zaya bar ma'aikata su yi aiki cikin kwanciyar hankali ba kullum cikin farga suke. Ta sauke numfashi kamar zata juyo ta komo cikin office nata sai ta hango shi yana tahowa ya turo ƙaton tumbi sai bubbuɗawa yake yana hura hanci yana taunar goro ya iso ko kallon inda ta ke bayyi ba ya wuce cikin office na Dr Mahmoud, ta juyo ta shigo ta ɗau white coat nata ta sanya tare da sanya white eyes glass nata, ta fito tare da sawa office nata key, ta wuce general ward, a nutse ta ke duba patient na ta wacce ke fama da jiki, sai da ta kammala duba ta sannan ta juyo zata fice Dr zalihat ta ce "Dr Hamrah, neman ki ma nake, jira nake ki kammala ashe har kin kammalan kina shirin fita" A hankali ta juyo tare da cire glass dake maƙale kan idanuwanta tana kallon Dr zalihat tare da murmushi ta ce Dr zalihat, sannu da aiki ya ƙoƙari, nema ta ki ke yi, to Allah yasa ba laifi nayi ba. Murmushi Dr zalihat ta yi daman akwai wasa a sakanin su ta ce "A'a Dr Hamrah, ni a suwa, ai ku bakwa laifi, daman akan zancen ɗauke Dr Aliyu da a ka yi ne a wannan ɓangaren naga abin ba daɗi, sbd yana taimakawa sosai sannan babu ruwan shi harkar gaban shi ya ke y kuma nan ɗin ya fi dacewa dashi amma a ce MD ya dawo kusa da office naki, abin bai wani tsari ba" Cike da mamaki Hamrah ke duban Dr zalihat, MD zai dawo office na Dr Aliyu akan wane dalili kenan, to menene amfanin shi wancan office nashi tabbas ruwa baya tsami banza amma ba zata yanke hukunci ba sbd zato zunubi ne ta ce To ikon Allah, shi kuma Dr ALIYU ina aka kaishi?. Eh to ɗazu nake jin nurse Laraba tana cewa wai cen bangaren yara aka kaishi kuma an yi mashi iyaka da wannan bangaren" Sauke numfashi Hamrah tayi, tana jinjina maganar, iyaka da wannan bangaren akan menene kenan there must be something under, ta ce To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. "Ameen" Ta fito ta tadda sauran nurses ɗin suna ta zance tayi wucewar ta, ta iso office na ta, a lokacin ake shigowa da sabbin kayayyakin MD, sai ganin Dr Mahmoud ta yi ya tsura mata idanuwa yana kallon ta ko kifta su baya yi, ta ɗauke kanta ta shige ciki. Tana ciki har azahar, sai da ta gabatar da sallah sannan ta fito a lokacin babu har an kammala shigar da kayayyakin cikin office na MD an jera su sai ganin Dr Mahmoud ta sake yi yi ya fito daga cikin office ɗin bata kulashi ba ta wuce cen wajen patients ta zauna sai la'asar ta dawo ta idar, tana zaune kan dardumar sallah ta ji alamun shigowar mutum tare da sallama cike da mamaki ta shafa addu'ar da take yi ta juyo sbd ta sake tabbatarwa shi ne ko kuma wani ne daban, ganin shi ɗinne yasa ta ɗauke kanta, murmushi ya yi da yake ɗan duniya ne ya yi kamar ba abin da ya haɗa su, kamar bayyi mata laifi ba, ya rage tsawon shi cikin sanyin murya ya ce "Hamrah, meyasa ki ke son zama ke kaɗai cikin..... Dr Mahmoud, faɗi damuwar ka sbd ina da abin yi. Murmushi yayi ya ce "HAMRA kenan, kamar kina gudu na.... Eh ina gudun ka, sbd dabi'un ka ba masu kyau ba ne, sannan ina sake gargaɗin ka a karo na ƙarshe ka fita cikin rayuwata kuma kada ka sake shigo min office is better for you to stay a side. "Uhmm HAMRA da an ganki za a ɗauka ke wata wayayya ce amma kuma da an bincika za a famin ci duhun kai gare ki, meyasa ba zaki bari na shigo cikin rayuwar ki ba na wani lokaci kinga za... Tsawa daka masa cikin ɓacin rai ta ce Mahmoud, get out. I said get out, tun kan naya maka rashin mutunci ka fita harka ta, wlh hawainiyar ka ta kiyayi ramata and this should be the last time da zaka shigo min office. Kafeta ya yi da jajayen idanuwan shi, yana kallon ta yana kuma sakar mata da murmushi tare da kurawa coca cola shape nata idanun ba abin da yake muraɗi irin jikin ta, cikin sanyin murya ya ce "This is the beginning, yanzu ma na fara, kuma ban taɓa neman abu na rasa ba dan haka ina da tabbacin cewa sai na biya bukata dake, ki ka baiwa wasu gajoji ma ballantana handsome iri na, wanda mata ke mararin so amma nake kin kulasu shine ni zaki wulakanta to ki sani shi saurayin ki ma mun kaishi ƙasa balle ke da ki ke mace, ni zuba ido ki gani" Yana gama faɗin haka ya yi ƙofar fita cikin ɓacin rai da tashin hankali ta ce Kun cika marasa imani, sai Allah ya saka mashi akan zaluncin da ku kayi mishi, amma kuma sai dai kun manta akwai Ubangiji kuma ya fiku shi zai ƙwato mashi hakkin shi. Sannan kasani ni Hamrah na fi karfin ka nesa ba kusa ba kuma ba zaka taɓa cin galaba a kai na ba, it will be the last not the beginning. Murmushi ya juyo ya sakar mata irin na zancen ki ke so, sannan ya fice, ta daki teburin dake kusa da ita zuciyar ta nayi mata raɗaɗi, wannan wacce iyar rayuwa ce, meyasa duk inda take ake samun matsala, meyasa bata samun farin ciki sai bakin ciki, to yaushe zata jita cikin farin ciki kamar yadda kowa ke yi?. Ta sauke numfashi tare da rumtse idanuwanta wani tunani ne ya faɗo mata akan to ta bar wannan aikin mana, sai kuma ta sake sauya tunanin da cewa in kuma ta bari me zata yi, zaman gidan da Ammie bata so kuma tayi ta tunani ko kuma fita shan iska waje ƴan unguwarsu su sami abin faɗa a hankali ta furta Nothing will happen in shaa Allahu. Ganin time yaja yasa ta sauke nauyin ajiyar zuciya ciki sanyin jiki ta kammala shirya ko manta ta fito sbd tafiya gida ta tadda duk office na su a kulle ta fice ta iso bakin titi ta tari ɗan sahu ya kawo ta layin unguwar su, ta sauka tare da takowa zuwa cikin layin, jin tsayuwar mota tayi an parker ta sannan aka fito bata kawo komai cikin ranta ba, ta cigaba da tafiyar ta..... "Assalamu alaikum" Kamar ba zata juyo ba amma dan jin anyi mata sallama yasa ta ɗan juyo tare da amsawa ganin babban mutum ne kuma sanye yake da tufafi ta mutunci yasa ta ɗan saki ranta ta furta Amin wa alaikassalam. "Tambaya nake son yi miki in dai babu damuwa" Ta ɗago tana kare masa kallo cike da mamaki, yana da tsawo sannan shi ba baki cen ba yayi shiga ta babbar riga wacce ake kira da gare, da kuma hula, shaddar dark green ce, ta sauke numfashi tare da cewa To ina jin ka Allah yasa na sani. Ya sauke numfashi da yasa ta sake ɗagowa ta kalle shi, ganin haka ya ce Ba ƙone ni sauka ta kenan daga airport nayo nan, wani gida nake nema gidan Alay SHAREEF wani ɗan siyasa mai neman takar house of reps, to na shigo ne kuma nake ta tantama kamar ba wannan ne layin ba, shine ganin ki yasa na ce da driver ya tsaya na tambaye ki" Ta sauke numfashi ta juyo tana karewa layin su kallo ganin ga majalisu ga kuma shaguna a buɗe ana ta siyyayya bai tambayi kowa ba sai ita da mamaki ta sake juyowa tana kallon shi, dressing nashi sak na garin Maiduguri amma kuma baya shige ko kama da mutanen nan da alamu yarene, to meyasa ya zaɓi da ita yake son tambaya..... Ajiyar zuciya da ya sauke ne yasa ta sudda kai kasa, ya ce "Menene, kina mamaki ne sbd na tambaye ban tambayi mutan da suke layin ba" Ta yi saurin ɗagowa tana mamakin ya aka yi yasan abin da take tunani kenan... "Abin da yasa na tambaye ki shine, bana son shiga cikin mutane sbd wani dalili na, amma da fatan hakan bai bata miki rai ba" Ta sauke numfashi ta ɗago tare da cewa Gidan Alay SHAREEF ba a wannan layin yake ba yana layin baya gida na biyar kofa milk color painting jikin gidan coffee brown ne. "Na gode sosai, kin san yawanci old GRA layin na kama shiyasa kuma ni bako ne ma'ana mata fiyi, da wannan zuwana na uku kenan garin Maiduguri, ina jin labarin karamcin ku ban taɓa yarda ba sai da ki ka nuna min" This time ta yi murmushi ta ce Wannan ba komai bane. Ta juya ta soma tafiya ta ji ya ce "Ko zan iya sannin sunar mallamar, saboda ko wata rana zamu iya haɗuwa na sake gode miki" Hamrah na ke. "Masha Allah, HAMRAH, nice name, i Alhaji Sama'ila by name from Abuja state" Ta sauke numfashi tare da jinjina kai tayi wucewar ta sbd na mujiya da ƴan majalisan matasa da suka zuba mata shikenan yau da chapter ta za a kare zama, ta iso kofar gida ba tare da ta juyo ba, bata san ko mutum ya tafi ba ko kuma yana tsaye ba sai ta taji horn na mota, ta juyo sai ganin motar Ammar ce ke mata horn ya ɗaga mata hannu alamun ta buɗe masa, ta ce Kai da wannan motar ta ka one door ka ke min mulki, to baza a buɗe ba. Dariya ya yi sbd yana jin abin da ta ta ce, wani yaro ne da gudu ya yi cikin gida ya boɗe mashi ya shiga ya yi parking ya fito yana "Likita kada ki damu da zaran na dawo daga ABGANISTAN za ki ga na siyo dan kareriyar mota" Uhm Ammar kenan ce maka a kayi da ga dawowa za kayi kuɗi ai sai ka ci kwakwa tukuna. Ya yi murmushi ya ce "Ai ni da kafar dama na shiga kin san ina da babban kwali kuma certificate biyu gare ni na nan da kuma na out side kada ki yi mamaki na samu genaral" Dariya ta yi tana nufo kofar palour tana Su genaral manya. Ya yi murmushi ya biyo bayan ta yana "In shaa Allahu, duk abin da aka ce Allah an gama komai" To Allah ya sa. "Ameen" ta wuce ɗakin Ammie, shi kuma ya wuce dakin shi. Tana shiga ta tadda Daddyn su na zaune ta gaida shi yake tambayar ta wajen aikin su ta ce dashi Alhamdulillah, ya ce "Kamar na ji tsayuwar motar Ammar" Eh Daddy ya dawo yana ɗakin shi. To madalla ya yi kyau, shima yanzu fama yake da jama'a kin san kasuwanci sai an jure saboda har ka ce ta mutane amma kuma yana complain a kan su" Uhm hakane Daddy sai anyi hakuri, to in ma ba abin UMAR ai harkar jama'a sai an yi hakuri balle kuma customers sai da lallaɓa" Daddyn su ya yi dariya ya ce "Wa Ammar ne zai lallaɓa customers ai ko cewa ya ke in dai tsari ka zo yi ka sara ko kuma kayi gaba, baya ɗukan nonsense" Uhm gashi kuma sun kusa tafiya training. "Eh na kammala haɗa masa duk abin da zai bukata kuɗin shi ma yana account" Masha Allah Daddyn mun gode. Ba damuwa ai.... Ammie ce ta shigo ta zauna Hamra ta gaidata ta amsa sannan ta wuce ɗakin ta. Faɗawa toilet ta yi ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito ta shiryar ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah ta na lazimi aka kira ishai ta tashi ta idar yunwa ta ke ji, ta fito ta shige kitchen yau ko ruwan zafin haɗa tea ɗin ma nata dashi tana kan ɗaura ruwan zafi cikin electric cattle ne AMMAR ya shigo, ta juyo tana duba me zata dafa cikin ƴan mintina ta rasa ya ce "Likita nima yunwa na ke ji a dafa dani" Ba tare da ta juyo ba ta ce To ai abin da zan girka ne ma ban sani ba. "To ki dafa indomie mana" Kai baya raina, kuma dole ke sa na ci, bari na duba cikin store ko na samu abin da zai kwanta min a rai sai na dafa shi. Ta shige cikin store ta duba ganin tayi kwana biyu bata ci macaroni ba yasa ta dauko shi ta dawo dashi nan ta soma haɗashi jollof na shi, ta soma pa_boilling nashi ta zuba shi cikin matsiyaya sbd ruwan jikin ya tsami sannan ta soma haɗa souce ya ɗan ji wuta sannan ta zuba kifi da nama a ciki sannan ta juyi macaroni a kai ta yi ta juya shi komai ya haɗe ta kashe gas tana kammala shi ta juye ruwan zafin cikin tea flask ta miƙawa Ammar wanda ke tsaye yana ta santi tun kan ya ci ta abin cikin cikin food flask su ka dawo ɗakin ta, nan ya zauna suka soma ci, yana santi ya ce "Kai da zayyu da sai ki bini mu tafi ABGANISTAN wlh" Dariya ta yi ta ce Kai Ammar naje nayi menene a cen. "Uhm ki yi ta dafa min irin wannan" Tayi murmushi, ta ce Uhm Ammar kenan, yanzu akan abinci sai na bika cen da yake ni ce ƴar fari ko. Dariya ya yi sosai ya ce "Yes babbar yaya" Ya haɗa musu tea suna sha suna fira ya tashi ya kunna tv sai suka ji ana nocking, Ammar ne ya miƙe ya buɗe, ganin ƙawar Hamra yasa shi cewa "Shatu ki shigo mana" Ta shigo Hamra na ganinta ta sakar mata da murmushin nayi kewar ki, ta ƙaraso ta zauna nan Ammar ya fice bayan sun gaisa. Hamra ta haɗa mata tea tare da zuba mata abinci tana Ƙawata saukar yaushe haka, shiru babu labarin ki. "Yau na dawo, na tambayi Nura mai shago ko yaga giftawar zuwa wajen aiki ya ce eh kin fice, shine na ce sai zuwa dare zan shigo, ji na shuru da kika yi wata ce ta sami matsala shiyasa na rasa number ki" Ayya Shatu so sorry, ya Mama?. "Tana nan tare muka dawo ai, da bazan zo ba ma da ƙyar aka shawo kaina" Subhanallah! Me kuma ya faru?. "Uhm pretty ke dai bari, abubuwa a kullum sake taɓarɓare min suke, wlh da wannan rayuwar ƙuncin da nake ciki gwamma na mutu, i hate this life, menene daɗin duniyar ma..... Shatu. Cewar Hamrah, tare da dafa ta ce In dai akan jinkirin auren ki ke irin waɗannan kalaman to ki sani wannan babu kyau, kina ja ne da jarrawabar da Ubangiji ya yi miki, kuma ba a so bawa sbd yana cikin tsanani ya dinga furta irin wannan kalaman, sannan irin su ke cire mutum cikin musulunci, musulmi an fiso ya yarda da KADDARAR mai kyau ko mara kyau, sannan Ubangiji yana jarraba bawan shi ne sbd ya gwada imanin shi, amma da addu'a, hakuri da juriya sai ki ga ya yaye mana damuwar mu kamar ba a taɓa yi ba, abin da nake so dake shine ki daure ki ci gaba da addu'a Allah zai kawo mafita. "Hamrah pretty na gode da karfafa min gwiwa, wlh matsalar da nake cikin ta, tafi ƙarfin kai na, abin ya wuce tunanin mai tunani, in taƙaita miki saura ƙiris na sami matsalar brain, sbd tunani da kuma tashin hankali" Jikin Hamra ya yi matukar sanyi ta gyara zaman ta cikin sanyin murya ta ce Shatu kina nufin bayan matsalar da na sani kina fama da ita akwai wacce ta fita?. "Eh hakana nake nufi akwai wacce ta fita amma kuma kusan ita wancan ɗin ta rashin auren ce ta haifar da wannan ɗin, zan faɗa miki komai amma sai ranar da baki da aikin wuni zan shigo na sanar dake" Sauke numfashi Hamrah tayi cikin sanyin murya ta ce To shikenan ƙawata gobe ma night duty gareni, babu inda zan je sai kin shigo. Sun ɗan taɓa fira sannan Shatu ta tafi, Hamrah ta dawo ta rufe ƙofarta, ta haye kan bed ta yi addu'an bacci sannan ta kwanta. Ina godiya da addu'oin ku, jina da ku kayi kwana biyu banyi Update ba na shiga rubibi ne amma Alhamdulillah yanzu ina free. Comments and share [1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 11 & 12 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _WASHEGARI_ _______ Da ƙyar ta iya buɗe idanuwan ta da suka yi mata nawi sbd bacci da kuma gajiya dake tattare da ita, a hankali ta karanta addu'ar farkawa daga bacci, ta yi miƙa ta sauko daga bed ta shige toilet a daidai lokacin ake kiran assalatu ta asubar fari, ta ɗauro alwala ta idar da raka'atainil farjir, raka biyu ta na fila sannan ta idar da ta farillah, ta bima tana addu'oi nta sannan ta yi azkar na safe ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sann ta koma bed ta ci gaba da bacci sbd night duty gareta. Sosai ta sha bacci sai kusan 11:00am ta tashi, ta shige toilet nan ta watsa ruwa ta fito daure da towel ta shafe jikinta da mai da kuma turare sannan ta gyara gashin kanta, ba laifi yau kam har da shafa powder da lipstick ta shirya cikin riga da skart wacce ta sake fito da coca cola shape nata, tayi normal ɗauri sannan ta fito ta wuce ɗakin Ammie, ta tadda tana kwance cikin sanyin murya ta gaida ta, ta amsa tare da ce mata yau bata jin daɗin jikinta, ta taimakawa mai'aikinsu su gyara gidan tare da girki, ta amsa da to Allah ya baki lfy sannan ta fito, ta wuce kitchen ta tadda ta har ta soma aikin nan Hamra ta ce da ita ta bari ita zata girka abinci ta je ta gyara palour, nan ta wuce, Hamrah gwanan son girki ta fara sharyawa musu abinci tam kala biyu zata yi, Daddyn su ya fi cin biski da miyar ganye Mommyn su kuma ta fi cikin cin tuken shinkafa da miyar ganye, sbd girkin na rana ne yasa suke da fa abinci mai nawi ita hamra ba kasafai ta ke ƙaryawa ba shiyasa breakfast bai dame ta ba, ta daura ruwan farar shinkafa sannan ta daura ruwan biski (tsaki) a cikin ruwan ta zuba gishiri da mai ta barshi ya tafaso, sannan ta zuba biskin a hankali har ya haɗe kanshi sannan ta rufe shi, ta komawa ruwan shinkafar ganin ya tafaso yasa ta wanke farar shinkafa ( ɗanya) ta zuba ta rufe ta barshi, ta buɗe fridge ta fito da nama da kayan miya nan ta soma haɗa miyar ganyen ta wacce tasha gyaɗa sannan ta koma ta bude tukunyar shinkafa ta tuƙa shi, ta kashe gas ta dawo wajen biskin ta da yayi warawara sbd mai da ta zuba mashi ta kwashe ta zuba cikin food flask, ganin miyar ta dahu yasa ta juye ta, tare da sauke shinkafar ta mulmulata cikin, leda nan ta kammala..... "Wow, what a nice delicious!" Ta juyo ganin Ammar ya sa ta ce Yauwa zo ka taimaka min ka kaiwa Ammie nata sannan wannan zan kai dining area sbd anjima. "To na ji kin ce na Ammie da Daddy ina nawa kuma?" Kashe nan sai ka ɗiba, ai nayi mai wuyan tun da na girka. "Nasan zayyi daɗi duk ƙamshi ya baje gidan" To ɗauka dai sojo. Dariya yayi ya ɗau basket da ta jerawa Ammie duk abin da zata buƙata ya kai mata, ita kuma ta dawo palour ta ajiye, ta koma ta ɗauko nata ta fito dashi, shima Ammar ɗin ya wuce ya ɗauko plate ta zuba mashi tare da ɗauko goran ruwa ya ajiye musu, suna ci suna fira yana santi ya ce "Kai zan yi missing na girkin ki da na tafi" Murmushi ta yi ta ce To ka zauna mana. "Uhm ai ba zayyu ba, kema rigima ta ki ke nema tafiya babu fashi" Ah to ashe kana da sense. Murmushi yayi yana kallonta, ganin ta yi kwalliya ya sa shi cewa "Unguwa za ki tafi?" A'a meka gani?. Naga kinyi kwalliya ne. To ai sai kace bana kwalliya sai zani unguwa, shikenan na fahimta. Ya yi murmushi ya ce "To ai naga baki cika yin shi ba ne shiyasa" To yau nayi is that okay. "Uhm Allah baki hakuri" Wayarta ta yi ringing ganin sunan Ayshe yasa ta ɗauka suka gaisa Ayshe ta ce "Shuru tun da ki ka baro mu, na so kiranki amma ban samu na kira ki ba, ya mutan gida ina Ya Ammar?" Uhm uwargida a gidan Alay Bukar, kowa yana lafiya ga nan Ammar ma. "Umm uwar gidan dole ba an kama an mai dani babba, to na ƙarba ya zan yi, ki baiwa ya Ammar mu gaisa" Hamrah ta miƙawa Ammar wayar ya karɓa suka gaisa ta ke masa ƙorafin ya ƙi gidan ta yaran ma na tambayar shi, ya sauke numfashi tare da cewa Ba haka bane Ayshe abubuwan ne sun min yawa, na ji kuna batun uwar gida, ki na nufin Alay Bukar zai ƙara aure?" "Eh ya Ammar zai ƙara nan da upper Saturday" "Ok ina gari ma, zan shigo kamin lokacin" "To Ya Ammar thank you" Ya miƙawa Hamrah wayar suka ci gaba da firar su, Ayshe ta ce "Yaya Hamrah ankawo min set na ɗaki fah" Barakallah na taya ki murna. "Na gode, jiya aka kawo" To asufar lafiya. "Na gode" Ya su namecy ta? "Suna nan lafiya, sun tafi skul" My regards to them. "Zasu ji" Sukai sallama. HAMRA ta sauke numfashi ta kalli Ammar da ya kammala cin abinci shi yana ƙoƙarin tashi ta ce Har ka kammala sai ina kuma?. "Eh fah office na Daddy zan je yau akwai waɗanda za suzo su ɗauki kaya" To ya yi kyau. Ya fice hamra ta dawo cikin ɗakinta, ta kwanta ɗaya saura amma ta ɗan kwanta zuwa da rabi sai ta tashi. Ta ɗan sami bacci ta farka, ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar da sallah azahar, ta miƙe ta fito ƙarƙashin bishiyar darbejiya ta zauna, sai taji duk gajiyar babu, tana nan zaune ne sai ga Shatu ta shigo, da sallamarta ta ƙaraso ta zauna, daman anan suke wuni su sha firar su sannan ta tafi, ta ce "Tun ɗazu fa nake ta son na shigo amma kuma aiki ya shige min gaba" Sai a hankali ƙawata nima sai bacci bai jima ba na farka, kin san akwai gajiya kema haka daga tafiya ki ke sai kin sami hutu na ƴan kwanaki. "Hakane ƙawata to ni ina naga wani hutu ai hutu ba na irin mu bane" Murmushi Hamrah ta yi ta ce Shatu you have to say Alhamdulillah, tun da kina da rai da kuma lafiya kin fi dubi. "Alhamdulillah ala kulli hali, hakane kam Allah yasa mu dace" Ameen. "Na shigo ne akan maganar da na ce zamu yi jiya, ƙawata ina cikin damuwa duk hankalina a tashe" Sauke numfashi Hamrah ta yi sannan ta ce Ina jin ki Shatu, Allah ya bamu mafita. "Ameen ƙawata, to cikin matsalolina wanne da wannene ki ka san su ina yaso na san yadda zan miƙi bayani ki fahimta har ki bani shawara" Shatu mun jima tare tun muna yara ke mace ce mai juriya da kuma zurfin ciki hakan yasa ba komai ake iya sani naki ba ko a fahimta amma abin da na sani shine, kina fama da matsalar rashin aure da wuri hakan har ya kai ga mijin mahaifiyar ki takure ki, ya kai ga ko ya yi cefanen gida baya so ki taɓa, kai har ya kai ga kwanan gidan ma yana so ya hanaki, wai kina takure shi. Sauke numfashi Shatu ta yi a hankali hawaye ke zubo mata cikin sanyi murya ta ce "Ƙawata, duk abin da ki ka faɗa haka ne amma kuma kusan akwai asalin abin da yasa hakan ya ke faruwa, mijin mahaifiya ba mutumin ƙirƙi bane fatsiki ne, kuma so yake ya lala tamin rayuwata ƙin amincewa da hakan ya sa yake takure min ba tare da kowa yasan dalili ba, ake ganin laifina ne sbd ƙin gaishe sa da na keyi kuma bazan taɓa yarda da shi ba a matsayin uba ba har abada ko da hakan zai zame silar rabuwata da mahaifiyata" Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ya hayyu Ya Qayyum, Shatu me ki ke shirin sanar dani, dan Allah ce min mafarki nake, what Alhaji Yusuf mijin mahaifiyar ki shine ke son lalata miki rayuwa, Shatu Please kada ki ce dani gaskiya ne. "Uhm kin fi kowa sanin yanda nake son mahaifiyata kuma kin san irin shaƙuwa da kuma soyayyar dake sakanin mu, bayan rasuwar mahaifina kowa ya juya mata baya amma ban dani, sannan kin san irin gwagwarmayar da aka sha kamin ta aure Alhaji Yusuf, to kuwa yakamata ki sani ba zan taɓa yi masa ƙazafi ba, abin da na ke shirin sanar dake gaskiya ne" Jikin Hamrah ya matukar sanyi, lallai rayuwa ba tabbas kuma duk irin damuwar da ka ke ciki akwai wanda na shi ya fi naka, wai duk irin nata damuwar ga wacce ta dameta.... "Hamrah, bayan Alhaji Yusuf ya auri mahaifiyata ya ci gaba da kulawa damu tamkar ƴaƴan da ya haifa, ya jamu jikin shi, har muke ji kamar ma bamu rasa mahaifin mu ba, barin ma ni wacce duk abin da zayyi sai ya shawarce ni, hatta abinci ni ke girka mashi, hakan nayiwa mahaifiyar ta daɗi sbd ganin na saki raina daga tunanin rashin mahaifina saboda shaƙuwar da mu kayi. Da farko ban fahimci manufar shi ba yana kirana a duk inda ya ke ina zuwa kamawa office nashi zuwa guest House nashi Ina kai mashi saƙo ko abinci sannan ko yana gida ma haka sai ya kira ni ɗakin shi wai na haɗa mashi tea, ban taɓa zato ko sammanin yana ɗauke da FUSKA BIYU ba kuma har ga Allah kallon uba na ke yi mashi. Wata rana da bazan taɓa manta da ita ba wacce tasa na yi da na sanin haiho ni a duniya, wata safiyar Laraba mahaifiyarta ta sanar damu zata tafi cen Cameroon anyi mata rasuwa cikin dare aka sanar da ita, mu kayi ban kwana ta tafi Alhaji Yusuf ne ya yi mata rakiya zuwa Airport, ba dawo ba sai kusan 10:00pm ya dawo ya kirani a waya a lokacin har na fara bacci, na ɗauka ya ce na same shi a side nashi, na taso na fito duk ƙannena ƙananun sun yi bacci ni kaɗaice ban yi ba, shuru gidan nayi nocking ya bani izinin shigowa na shigo sai dai ganin yanayin shigar shi yasa na juya zan fice ya ce "Shatu ba damuwa ai ki ƙaraso mana, tea zaki haɗa min" Jikina ya matukar sanyi babu riga a jikin shi gajeren wondo ne da shi, kai na a ƙasa na wuce inda food flask na ruwan zafi ya ke na soma haɗa mashi, na kammala sannan na kawo mashi, kai na har yanzu still a ƙasa ya ke na miƙa mishi, sai da abin da naji ne yasa na ɗago cikin sauri na kalle shi hannuna ya haɗa da cup ɗin ya rike yana jifata da wani mayen kallon da ya sanya zuciya ta harɓawa, jikina ya soma rawa ganin yanda idanuwan shi ya kanza kala yana fidda numfashi na yi saurin ja da baya ina mai mashi kallon me ka ke nufi ne, ya yi saurin riƙe mun hannu ya dawo dani tare da zaunar dani bakin bed ya yi saurin cewa "Magana zamu yi, meyasa naga kina jan jiki dani yau Shatu ni ne fah Daddyn ki" Na sauke numfashi har zuwa wannan lokacin na kasa sakin jiki dashi ina waro idanuwa waje cikin tsoro, ina jin shi yana ƙurɓan tea na shi bayan ya kammala ne ya ajiye tare da riƙe mun hannu yana murza su a hankali jikina ya soma rawa ina tunanin anya Daddyn mu ne ko dai wani ne mai kama dashi, na ɗago kaina sbd na tabbatar da cewa shine ko kuma ba shi ɗin bane sai naga shine yana min wani irin kallo, na yi sauri zan miƙe da niyyar na bar ɗakin ya dawo dani tare da janyo ni jikin shi yana shafa ni tare da sauke numfashi cikin sauri² jikina na rawa na hankaɗe shi na miƙe duk ƙafafuwana sun shanye tafiyar ma neman gagarata take nayi bakin kofa ya yi sauri ya biyo ni, na tsaya tare da juyowa na nuna shi da yatsa na ce "Daddy kada ka iso in da nake, wlh zan yi maka abin da ba zaka tabaɓa mantawa dashi ba, wlh ka bani mamaki i have never imagine you'll do this to me, har a kullum ina yi maka kallon uba ne wanda ya zai tarbiyyar ta damu ya ɗaura mun a kan hanya madaidaiciya shine ka ke so ka rusamin rayuwata. Ajiyar zuciya ya sauke ya yi magana a hankali yadda kada wani ma ya jisu, ya ce "Be wise please Shatu, I'm not your real father, it I'll never be, nothing will ever change from that, I'm only the husband of your mom, don't be confused about our new relationship. It's normally happening in our nowdays so this is nothing....... Wani ihu na yi da ya sanya shi ya yi baya cikin tashin hankali, yana kallona kamar wata sabuwar shafar aljanu, na nuna shi da yatsa sannan na ce Ka cuce mahaifiyata, sai Allah ya saka mata sbd cin amanar ta da ka ke yi bata sani ba, tana farin cikin samun ka a matsayin miji, a kullum ƙara alfahari ta ke da kai ashe bata sani ba 2 face gare ka, you showed me your true color and don't ever let her knows, you will regret everything. Ta sowa ya yi ya iso dab da ni babu kunya babu tsoron Allah ya ce "Do you mean za ki faɗa mata komai" Ai ya zama dole tasan wa ta ke aure. Murmushi ya yi ya ce "Na sani ba zaki iya ba, kuma in kina ganin za ki iya to bismillah" Na buɗe ƙofar na fito ina kuka na iso ɗakina cikin tashin hankali, na so a ce wannan abin mafarki ne amma kuma duk inda na waiga ganin a zahiri ne ya faru ina ta juyi har gari ya waye, na tashi da ciwon kai, ban fito ba har yara suka tafi skul ina jin yana tambayar su ina na ke su ka ce dashi ciwon kai na ke yi, sai bayan ya fice daga cikin gidan na samu na fito, haka mu kayi wasan ɓoya na tsawon kwanaki uku, a rana ta huɗe ce ina zaune a palour gidan shuru yara duk suna skul naji sallamar shi, ganin ina zaune a palour yasa ya iso ya zauna kusa dani na yi saurin miƙewa ya dawo dani ta hanyar janjoni ya kwantar bisa kujera ina ta kiciniyar kwace kaina abin ya gagara sbd yadda yake da ƙarfi, ya yi magana "Shatu bana jin daɗin irin gujemin da ki ke yi kin san yanda na ke son ki kuwa amma ki ke wulakanta ni" Sabar baƙin ciki da takaici ma kasa magana na yi sau hawaye, jin ya ɗaura hannun shi bisa gashin kaina yana shafa ya sa na ce dashi Allah ya isa sakanina da kai, ka rusa mana farin cikin gidan mu, sai Allah ya saka mana. "Uhm Shatu kina bani wahala menene a ciki ina kin ja shekaru baki yi aure ba, kuma a kullum cikin son yi ki ke yi to tunda babu mashinshin ki saki jiki dani zan baki kuɗaɗe daga dubu ɗaya zuwa 100 million, zan miki gatan da ba zaki taɓa da kin sanin aikata hakan ba kuma za kiji daɗin rayuwar..... Ya Allah ga bawan ka nan yana son cutar da ni da kuma mahaifiyata, Allah ya shiga sakanina dashi, Allah ka maida mashi sharrin sa kan shi. Cikin ƙarfi na hankaɗe shi na tashi a guje na shige ɗaki na kulle, na fashe da kuka kamar raina zai fita, what anya kuwa Daddy ne wannan, to akan ta zai fara ko kuma daman halin shi ne, tun daga wannan lokacin na tsiri zaman ɗaki har Mommy ta dawo, aranar da ta dawo ta fahimci duk na sauya na rame kuma bana son zama a palour, ta ke tambaya ta ganin tana cikin farin ciki yasa na ki faɗa mata na danne ko ganin idonta zai sauya tunani, amma kuma sai ya nemo wata hanyar da yana bukatar abu sai ya kwalla min ƙira ganin bata san komai ba sai na fito ya ce na dafa mashi abu kaza ko na haɗa mashi tea, amman bana sake mashi, rannan ta fita unguwar ina kwance cikin ɗakina ya shigo tare da sakawa ƙofar key, na miƙe cikin tashin hankali zan sauko daga kan katifata ya yi saurin riƙe ni ya danne ni, tare da rufe min baki ina, na kasa magana ma ballantana na ihu, ya jima yana kallona nima shi nake kallo ina jiran naga ta inda zai fara sai kuma naga kawai kallona ya ke, a hankali ya yi magana "Shatu ba zan daina bibiyar ki ba har sai kin amince da ƙudirina kuma a nan zamu dinga haɗuwa ba a cen guest House nawa zamu dinga haɗuwa, ina son ki.... Ƙarfi ne ya zo min na hankaɗe shi ya faɗi na tashi zan gudu ya janyo ni na faɗi ƙasa har naji ciwo, ganin na ji ciwo yasa ya buɗe ƙofar a lokacin kuma Mommy ta dawo jin ihu na yasa ta iso ɗakin ganin mu biyu bata ce komai ba sai ma tambayar shi da take akan meyasa meni, cikin kwanciyar hankali ya ce da ita wai faɗuwa nayi ya ji ihu na shiyasa ya iso ƙofata, nan tayi ta masifa ta fice na kalleshi cikin ɓacin rai ya sakar min murmushi ya fice. Tun daga wannan ranar na daina gaidashi na fita harkar shi ko ya kirani bana amsawar, abin ya yiwa mahaifiyar ta ciwo har da marina wai ina raina mata miji ta ya zan je bazan gaida shi ba, ai shima ubane gareni dole na yi mishi biyayya kuma ai da amincewar mu ta aure shi to maisa ni zan fara raina shi, na rasa ta inda zan fara faɗa mata shine na fara gaishe sa, to amma kuma na ƙudirin niyyar faɗa mata komai na shigo ɗakinta na tadda ta zaune ina shigowa ta ce "Kamar kin san neman ki nake, to menene kuma naga fuskar a dame, wai ma meyake damun ki ne duk kin rame?" Na sauke numfashi cikin sanyin murya na ce Mommy magana na ke so muyi akan Daddy. "To naji kamin ki fara na ki maganar bari na faɗi nawa" Fito min ta yi da key motar ta ce wai ya bata kyautar ta a ranar hankalina ya matukar tashi kenan babu yadda zan faɗa mata kuma ta amince kawai na ce da ita zan tafi cen Cameroon na zauna, nan ko ta tashi hankali tana ta masifa wai tasani sbd mijinta na ke haka, dan haka bazan je ko ina ba kuma na cire miji na yi aure sannan ya zama dole na girmama shi, kuma na bashi hakuri. Cikin sanyin jiki na dawo ɗakina, kawai na barwa Ubangiji komai na saduda, shikenan mijin mahaifiya ta zai ci galaba a kaina. Bayan ya dawo da daddare ne ta tisani gaba wai na bashi hakuri na bashi. Tun daga wannan lokacin na ɗan sauko ganin kamar ya sauya kwasam ranar Mommy ta ce na ɗau abinci shi na kai mashi guest House nashi zayyi baƙi driver ya kaini, bana son ja in ja da ita na shirya na fito a lokacin kuma babu ita da Rahama sun jera manya manyan kuloli cikin Boot na motar na shiga driver ya kai ni guest House na Alhaji Yusuf mijin mahaifiya ta.......... Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 13 & 14 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ Muna isowa ya taimaka min muka sauke kulolin abincin, sun kai kala 7 kuma ko wannensu da irin abincin da ya ke ciki duk kuma babu na ƙi, Mommyna gwana ce ta fannin girki, shiyasa Alhaji Yusuf ba ya shakkar gayyatan baƙi cin abinci guest House nashi, ko kala nawa ne Mommy zata girka mashi. Driver ya kalleni ya ce "Zan iya tafiya ne ko na jiraki?" A'a ka tsaya mu koma tare.... "Ah har kun iso to sannunku da ƙoƙari" Banyi mashi magana ba, na juya zan shige motar ya ce "Shatu taimaka min mu shigar mana" Ban ƙi ba na taimaka muka shigar sai dai a lokacin da na fito babu driver na dube na ce Ina driver kuma ya tafi. "Oh na aike shi ba zai jima ba zai dawo" Na sauke numfashi na ɗau rogowar kula na shige dashi ciki, sai dai ina ƙoƙarin fitowa kuma na ji ƙofar a kulle, na yi na yi na buɗe abin ya gagara, sai jin takun shi naji na bayana, na juyo ganin babu kaya a jikin shi yasa na ja da baya na haɗe da jikin ƙofar ina waro idanuwa waje, ya matso kusa dani daga shi sai gajeren wondo ya kai hannunsa zai taɓa ni nayi ƙasa tare da matsawa gefe guda na haɗe jikina waje guda ina addu'ar Allah ya kamin ɗauki, daga inda yake tsaye ya kuramin idanuwan shi da suka sauya kala soka koma red da su ya ce "Ki amince mana ko da na wannan ranar ce, ni kuma zan baki abin da zaki shekaru 10 kina amfanuwa dashi, Shatu ki yarda dani babu wanda zai ji wannan sirrin daga ni sai ke" Ya matso kusa dani yana lallaɓani akan na amince, rufe idanuna na yi na kwalla ƙara wanda yasa shi yin baya ya kuramin idanuwan shi wanda suka kaɗa su kayi jajir, numfashi na ke sauke shi on on na ce Alhaji Yusuf, ka buɗe min ƙofa na fice ko kuma dagani har kai duk muyi mutuwar kasko yanzu wlh yanda na ke ji kamar na kashe ka.... Ji na yi ya danƙo ni ya yi min riƙon mutuwa tare da janyo ni ya yi cikin ɗaki dani ya wanke ni da mara, tare da sa hannu zai yage min riga, na samu na ja da baya ina nishi, na ɗauko gwalbar wine da na gani a ajiye na yunƙura zan maƙa mashi ya saurin riƙe hannuna tare da sake jefani kan bed ya danne dukkanin hannayena ya kura min idanuwa yana sauke numfashi, cikin wata iriyar murya ya ce "Kin aikata babban kuskure wajen ƙirana da Alhaji Yusuf ba Daddy ba, kada kiga ina lallaɓa ki yi tunanin tsoron ki na ke ji, to ki sani ko kusa, kawai ni na fi son muyi alaƙar cikin kwanciyar hankali hakan zai fi faranta min, amma na kula ba zan taɓa samun hakan ba cikin kwanciyar hankali da lallami sai na nuna miƙi karfi na" Eh na faɗa Alhaji Yusuf, kai da bakin ka ka ce kai ba asalin mahaifina bane kuma ba zaka taɓa zama ba, to gwamma na kira ka da sunan ka.... Shaƙo ni ya yi tare da ɗauke ni da mari ya ce "Yau sai kinyi da kin sanin zuwanki duniya" Nan ya soma cire min kayana, na samu na kai mashi cizo, na miƙe tare da ɗaukan kwalbar na makamashi a kai na fice da gudu jiri na ɗibana ta window na samu na fito sbd kulle ƙofar da ya yi, da ƙyar na iya kawo kaina gida ina shiga ciki na tadda Mommy bata nan na tattara duk abin da zan buƙata na ajiye ta dawo da yamma na sanar da ita gobe zan tafi Cameroon nan hankalin ta ya tashi wai sam sai na gaya mata dalilin yin hakan, cewa na yi kawai zan tafi haka muka kwana wai bazan tafi ba, ban samu na tafi a ranan ba sai washegari shine har na shigo na ke sanar da ke. To bayan na tafi da wasu satika ne Mommy ta biyo ni wai Daddy ne ya ce ta je ta taho dani, nan fa na ce ba zan dawo ba, sun yi² na faɗa musu dalili amma naƙi daga ƙarshe dai muka zauna akan a shiga sakanina da mijin mahaifiya ta nan aka ce to na yi harka ta ya yi nashi. To bayan na dawo kuma zaman ya koma babu daɗi yanzu haka Mommy fushi ta ke dani wai bana girmama mijinta har ta kaiga ko gaishe ta na yi bata amsawa abinci ma sai dai ni na girka iya cikina ita ta keyiwa ƙannena, shikuma bai fasa bibiyata ba shine nazo wajenki ki bani shawara na sanar da ita ne ko kuma na yi shiru mu" Sauke ajiyar zuciya Hamrah ta yi da ƙarfi tare da share hawayen dake bin ƙuncinta, ta matukar kaɗuwa da abin da Shatu ta sanar da ita, what mijin uwa ya ke bibiyar ɗiya, wannan wane irin tashin hankali ne, wane irin zamani aka zo ne, tabbas ƙarshen duniya yazo, a hankali ta ɗago ta kalli Shatu da ta ƙura mata jajayen idanuwan ta, ta ce Shatu na tausaya miki akan wannan al'amarin tabbas wannan babban tashin hankali amma da yardan Ubangiji komai zai wuce, sanar da mahaifiyar ki kai tsaye zai sake haifar da wani tashin hankalin ne abin da ya dace shine ta ganshi yana yunkurin aikata hakan shine kawai zai sa ta amince sbd na fahimci ta miƙa masa dukkanin yardan ta babu yadda za ayi ta fahimce ki. "Kina nufin na bari har sai ya yi yunkurin aikata hakan, to ta yaya kenan in kuma ya aikata ba daidai ba fah yazama too late kenan?" A'a Shatu zamu ɓullo masa ta inda ya ɓullo miki sannan kada ki manta ba ke kaɗai ce yake yiwa hakan ba tayu akwai waɗanda ya yi musu kammin ke, to yanzu abin da na ke so dake shine ki koma gida ki sami Mommyki ki bata hakuri ki ce kin fahimci ke ce da kuskure kuma kin gane dan haka ta yi hakuri shima Daddy ki bashi hakuri a gaban ta ku koma yadda ku ke a cen baya daga wannan lokacin mu kuma zamu fara namu plan ɗin dan ina da tabbacin bazai taɓa ja da baya ba zai sake gwada sa'ar shi, abin godiya ma shine baya haihu dashi ba. "Zan yi in shaa Allahu sai dai sai na kai zuciya nesa wlh bana son ganin shi kwata kwata" Ƙawata kada ki damu komai zai wuce, ke dai ki aikata abin da na ce in shaa Allahu, Allah zai bamu mafita. Hamrah ta yi ta kwantar mata da hankali har aka kira la'asar suka tashi suka shige ciki suka isar tare da cin abinci, Hamrah ta shirya kar fe 5:00pm suka fito, Hamrah ta shige ɗakin Ammie ta tadda zaune ta sake yi mata ya jikin sannan ta fito zuwa wajen aiki. A hankali suke takowa a layin unguwar su suna ci gaba da fira, Shatu ta ce "Ni kam ƙawata yakama muje shopping gobe tun da kina gida mun jima fa bamu yi siyayya ba" Uhm gaskiya kam dan nima ina son abun da dama amma kuma ba time haka nake hakura. "Ai sha'anin aikin ku sai an jure, shiyasa ki ka ga gwamma business da na ke yi bazan iya aikin Hospital ba" Murmushi Hamrah ta yi ta ce Ni kuma gaskiya ina sha'awar aikin ko sbd ceton rayukan al'umma, yauwa ban faɗa miki ba kwanakin baya fa na haɗu da Hauwa'u. "Wacce ce kuma hauwa'u?" Hauwa'u Jibrin ƴar kyale² wacce muka yi secondary School mana, tana ma tambayar ki. "Wai ki ce ƴar goal kai naso ganin ta ko ya ta koma" Aiko tana nan yadda take. Suna fira har suka iso bakin titi Hamrah ta hau ɗan sahu ta wuce wajen aiki ita kuma ta dawo gida. Akwai shaƙuwa sosai sakanin su tun suna yara haka suke basa rabuwa har suka girma suna tare kuma dukkanninsu ba su yi aure ba. Hamrah ta iso cikin Hospital ta wuce office na ta kai tsaye office na MD a kulle na Dr Mahmoud ne a buɗe ta shige ciki, a nutse ta fiddo da duk abin da zata buƙata sannan ta kunna system ɗinta ta jima tana aiki a ciki sannan ta rufe tare da lumshe idanuwan ta, sai ta ji babu daɗi da bata sanya Dr ALIYU cikin idanuwan ta ba cikin kwanaki biyun nan sai ta ke jin kamar ba lafiya ba, shigowar shi ko da babu komai tana ƙaruwa da shi kamar yadda yake ƙaruwa da ita sannan akwashi da zolaya. Ta sauke numfashi zata je cen bangaren yaran ko zata samu ta ganshi su yi magana ko ba komai anyi zaman tare. Ta fito ta wuce general ward nan ta ci gaba da duba patients ɗin ta ta jima a ce jin ana kiran sallah magrib ne ya sa ta fito ta dawo office na ta sai bayan ta idar da sallah ishai sannan ta fito ta wuce bangaren yara, bata sha wahala ba ta sami office na shi, cikin sanyin jiki ta turo ƙofar ta shige tare da sallama sai dai kan ta ƙarashe sallamar taga abin da ya firgita ta, wani irin tsawa Dr Aliyu ya daka mata cikin ɓacin rai "Me ya kawo ki nan, ko nan ɗin ma kin zo ne shima ki rushe min shi kamar yadda ki kayi min a wancan bangaren" Cike da mamaki ta ke duban shi what, ita yau Dr Aliyu ke dakawa tsawa akan wane dalili kenan sannan kuma meyake nufi da cewa wai ita ta saka aka kora shi daga wancan bangaren, ta danne zuciya tare da cewa Dr Aliyu, yau ni ka ke wa tsawa sannan ka ke neman ɗauramin laifin da ban aikata ba, ka fi kowa sanin na tsani wannan abu biyun da ka yi min, tsawa da kuma ɗauramin laifin da ban aikata ba ya fi komai ɓata min rai da shiga kunci, sannan ka sani ni ban san abin da ka ke cewa ba dan haka kada ka kuskura ka daura min laifi. Ta faɗa tana sauke numfashi cikin ɓacin rai. Ido cikin ido ya ke dubanta cikin ɓacin rai idanuwan shi sun kanza sunyi jajir kamar ya yi marisa ya fito mata a asalin ALIYU HAIDAR zaki, ya ce "Dr Hamrah kada ki mai dani sakarai nasan abin da na ke yi kuma na ke faɗi, kina da sanya hannu zundum cikin abin da a kayi min sannan kuma ke ce silar faruwar komai, dan haka you have stopped acting like a good to everyone bcoz nasan komai yanzu kin bani mamaki ina kallon ki da daraja da mutumci ashe ..... Ya isa! Na ce ya isa Dr Aliyu ka fara wuce gona da iri, ka gyara kalaman ka, kasan me ka ke faɗi ya zaka dunga ɗunkule zance kana jifata da munanan kalamai akan wane dalili?. "A kan alaƙar da ke sakanin ki da Dr Mahmoud daman can kuna mummunar alaƙa ki ke nuna min bakya yi baki ma son shiga sabgarshi ashe ba gaskiyar bane to ki sani na san koma nasan asalin fuskar ki, dan haka ba za ki ci gaba da raina min hankali ba sbd nasan ke fasuƙa........ Saukan lafiyayyen mari ya ji kan fuskar shi sai da shatin zarazaran yatsun ta suka kwanta kan fuskar shi cikin ɓacin rai ta nuna shi da yatsa Dr Aliyu mind your tongue, ka wuce gona da iri amman ka bani, na yi tunanin in da wani ne ya faɗi hakan a kaina you are the first person da zaka kareni shine yau ka buɗe baki har ka ke kirana da ƙazamin suna, lallai ɗan Adam na iya ƙanzawa i won't prove my self but abin da na sani shine you'll regret and be shame at the last. Tana kaiwa nan ta fice cikin ɓacin rai ta nufo bangaren su kai tsaye ta wuce office nata ta shige tare da dukan teburin dake gabanta tana huce, ansha yi mata irin haka amma kuma jin hakan daga bakin Dr Aliyu ya dameta sai ta ji tana so yasan gaskiyan lamarin ya zama dole ta nemo hanyar da za ta yi exposing halin Dr Mahmoud da MD ta yadda zata kawar da zargi da shakka da kuma kokonton da Dr Aliyu ke yi akanta kuma ta sa a dawo dashi wannan bangaren, ta jima tana sake² cikin ranta sannan ta wuce general ward ta ci gaba da kula da patients nata, sai kusan to 1:00am ta dawo office ta ɗan kwanta sai bacci ya ɗauke ta. Da asubah ta farka ta hau shirya kayanta bayan ta idar da sallah sannan ta fito ta ɗau hanyar gida, ta shigo gidan shuru babu motsin kowa ta nufi ƙofar ɗakinta jin miryar Ammie ta yi ta kira sunanta "Hamrah" A hankali ta juyi, cikin sanyin murya ta ce Barka da safiya Ammie ya ƙarfin jikin?. "Hamrah da na buɗe ido na ganki nake jin bakin ciki da takaici bani da damuwa a duk fadin duniyar nan irin na ki, bana iya bacci bana iya cin abinci cikin kwanciyar hankali in na tuna kin ɗabi shekaru a gabana babu aure shin ki sanar dani da akwai abin da ki ke aikatawa ne da ya sanya baki son aure na sani na kuma san irin matakin da zan ɗauka ko kuma kawai so ki ke na mutu da bakin cikin ki" Kanta a kasa tana kwalla tana jin zuciyar ta na yi mata zafi, to in dai mahaifiyar ta bata yarda da ita ba kuma ba zata iya shaidan ta ba kenan duk wanda ya yi mata hakan bai kamata ta ji babu daɗi a hankali ta furta Ki yi hakuri. "Hakuri a cikin shi nake kawai na fahimci ni ɗin ce baki son farin ciki na kin fi son ayi ta zance na cikin dangi da ƴan unguwar ace na ajiye ki naƙi aurer da ke kina duk abinda da ki ka ga dama, to ki sani ina gab da ɗaukan hukunci akan ki ko ni ba bar miki gidan ko ke ki bar min gidan sai ki je in da zaki ji daɗin ci gaba da abin da ki ka ga dama" Jikin Hamrah ya soma rawa ta ɗago tana kallon Ammie anya waɗannan maganganun daga bakin Ammie suke fitowa, meyasa Ammie ke faɗin haka da tana da yadda za tayi da ko ta yi ko dan ganin farin cikin ta, meyasa Ammie ta tsaneta sosai ne, anya kuwa ba wani abin da bata sani ba ...... "Na faɗa miki har yanzu ina kan bakata zuwa ƙarshen wannan watan komai zaizo ƙarshe" Ta juyo ta fice, da ƙyar Hamrah ta iya ɗaukar kafarta ta shigo ɗakinta, ta zaune daka ƙasan bed ta saki wani maraitaccen kuka wanda da ƙyar ta ke iya yin shi cikin tashin hankali a wajen aiki babu sauki a gida ma kuma babu sauki ina zata sanya ranta taji sanyi me, shasheƙar kuka take yi da tana ajiyar zuciya....... "A'a Hamrah Please stop crying, kuka zai haifar miki da matsala.... Ture shi ta yi ta juya mashi baya tana ci gaba da kuka, hankalin Ammar ya matukar tashi ganin ta cikin wannan yanayin ya sake matsowa kusa da ita cikin muryar rarrashi ya ce "Ki yi hakuri Hamrah, kada hakan ya dameki ni na yarda dake kuma ko da duk duniya zasu juya miki baya ni ba zan yi ba, ke mutuniyar kirki ce Ammie na gulma da segumin mutane ne ya yi mata tasiri, amma itama a hankali zata daina, kin ji I'm with you" Sauke numfashi ta ɗago tana kallon shi duk ya tashi hankalin shi jikin shi har rawa yake idanuwan shi sunyi ja, ta ƙirƙiro murmushin dole ta ce Ba kukan abin da Ammie ta faɗa ba nake kaina ke min ciwo. Ajiyar zuciya ya sauke ai ko mahaukaci ne yaga abin da ya faru zai fahimci komai balle kuma shi da ya ke da cikakken hankali, ya ce "To na ji, faɗamin me ki ke son ci?" Duk abin da akwai. "To ina zuwa" Ya tashi ya fice, bai jima ba ya shigo ɗauke da trey ya ajiye a gaban ta ya haɗa mata tea ya miƙa mata ta soma ƙurɓa a hankali ya buɗe pepper soup na jan nama ya ɗeba mata cikin plate ya miƙa mata ta ƙarɓa ta soma sha, ta ya kura mata idanuwa a hankali tace Kai fa ba zaka sha bane?. Ya sauke numfashi a hankali ya ce Zanje na watsa ruwa sai na nayi breakfast sannan na tafi office na Daddy. Okay, thanks. Ya miƙe ya fice, ta kammala ta buɗe drower ta ɗauko da emzor ta haɗiye sannan ta kwanta bacci ta jima tana bacci sannan ta farka, ta watsa ruwa ta ƙarashe shan raguwar pepe soup ɗin ta ji ana kiran sallah azahar ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta idar kenan ta ji sallamar Shatu ta ɗago ta kalleta Shatu ta ce "Ba dai kin mance fitan da zamu yi ba?" Sauke numfashi Hamrah ta yi ta ce Na manta fa amma a shirye nake zamu iya tafiya. Daman ta gaji da kwanciyar suka fito ta shige ɗakin Ammie ta shaida mata zata siyayya bata ce da ita komai ba ta fice jiki a sanyaye, a daidai layin unguwar su suka tadda ɗan sahu, suka hau ya kai su GUMALTI nan suka kammala shopping sun fito da lader niƙi² a hannu sai suka ji ance "Hamrah" A lokaci guda suka juyo cike da mamaki Hamrah ke binshi da kallo mutumin nan ne da ya taɓa tambayar ta a layin unguwar su, cikin sakin fuska ta ce Barka da yamma ci. "Yauwa barka dai ranki shidaɗe da fatan dai baki bance fuska ta ba?" Murmushi ta yi amma bata mance fuskar ma sai dai sunan shi da ba zata iya tunawa ba.... "Alhaji Sama'ila" Murmushi tayi, Shatu ta ce "Bari na nemi ɗan sahu kamin nan sai ku gaisa" "Sannun ki" Ya ce da Shatu. Ta amsa da "Yauwa sannunka kaima" Ya yi murmushi ya ce Ba sai kin nemi ɗan sahu ba nima arean ku zan bi sai nayi dropping na ku ko" A'a ba komai Alhaji zamu ƙarasa ai. Cewar Hamrah, amma ya dage sai da yasa drivern shi ya shigar musu da kayayyakin su sannan ya buɗewa Hamrah gidan baya, ta juya ta kalli Shatu ta yi mata alamun ki shiga, sannan ta shiga itama Shatu ta shiga ta zauna a mazaunin gaba ita da driver, Hamrah da Alhaji Sama'ila a bayan mota suka ɗau hanyar dawowa gida. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 17 & 18 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ Ajiyar zuciya ya sauke da ƙarfi, idanuwan shi sun sauya kala, duk duniya ya tsani ganin yayar shi cikin tashin hankali ko cikin damuwa baya son ganin ɓacin rainta, shiyasa ya ɗau wa kanshi alkawarin samo mata farin ciki, ita ma taji daɗin rayuwa kamar yadda kowa keyi ta daina zubda ƙwalla, shi dai kawai hankalin shi bai kwanta da wannan mutumin ba, amma zai yi zurfi bincike akanshi, a hankali ya ɗago yana kallon ta ganin duk hankalin ta a tashe ya ce "I'm sorry" Ta sauke numfashi jikin ta ya yi sanyi ganin lokaci guda kuma ya dawo cikin hayyacin sa ta ce Bana so, kada ka sake yi min haka, sannan ko ba komai shi babban mutum ne ya kamata ka girmama shi. "Ina yin hakanne don farin cikin ki, bana so ki aure shi dan farin cikin Ammie na fi son ki yi aure cikin so da kuma ƙauna" Ta sauke numfashi, na ji kuma na gode amma kasani dan kaina zan yi ba dan Ammie ba, dan haka ka maida hankali ga shirye shiryen tafiyan ka. Ya sauke numfashi ya ce "To shikenan" Ta fice ta fito compound na gidan ta tadda Alhaji Sama'ila har ya shige cikin mota, ta iso ya buɗe mata ta ciki ta shiga, a hankali ya tada motar sbd shi kaɗai yazo, shuru ya ratsa har suka fito daga layin unguwar su, mamaki ta ke irin na mujiyar da ƴan layinsu suka zubawa motar har suka ɓace. Sauke numfashi Alheri Sama'ila ya yi tare da cewa "A wacce Hospital ki ke aiki?" AL'UMMA SPECIALIST HOSPITAL. "Ok, kin san ba wani sanin kan garin na yi ba, sai kin taimakamin da kwatance" Suna tafe tana nuna mishi hanyar da zai bi, har suka iso nan ya sauke ta cikin girmamawa ta mai godiya ta shige ciki. Office ta sanyawa key ta buɗe ta shige a nutse ta shirya komanta kamar yadda ta saba. Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya shigo tare da sallama, ta amsa ya zauna tare da cewa "Yau kam kin makara, in ce dai lafiya?" Alhamdulillah. Kawai ta ce, ta ɗauko white eyes glass nata ta saka tare da buɗe system nata tana duddubawa, ya yi murmushi ya ce "Can we be friends?" Ɗagowa tayi ta kalle shi tare da girgiza kanta ta ce Friend's, how was that be possible, ni fa mace ce kai kuma na miji ta ya ya za muyi abota. Ya yi murmushi ya ce "Ana yi ai, shi ya fi komai sauki" Uhmm, ni bana yi. Ya yi murmushi ya fice sbd ƙiran sallah da ake yi. Ta sauke numfashi ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar sannan ta fito ta wuce general ward, ta jima a cen sannan ta dawo. Tana zaune ita kaɗai ta ji wayar ta na ringing ta duba Abuja ne suka gaisa nan suka taɓa fira sannan sukayi sallama. Sai ƙiran OG ya shigo ta ɗauka cikin girmamawa ta ce Barka da hutawa OG. "Yauwa barka dai Dr Hamrah, ya ƙoƙari?" Alhamdulillah. Yauwa haɗamin file ɗin da ki ke haɗamin da sauran document ɗin zan shigo on Monday around 10:00am akwai abubuwan da zan yi" In shaa Allahu, zan haɗa su OG Allah ya nuna mana jibin. "Good, ameen" Su kayi sallama. Ta miƙe ta fara haɗa su, daman haka ta keyi duk record yana office nata, shiyasa ido yake kanta, kuma akwai sirri a sskaninta da OG shiyasa yake ɗaura ta kan ragamar komai, bata da yawan magana, kuma bata wasa da aikinta, ta kammala haɗasu ta ajiye su cikin loker ta sanya key, sannan ta kwanta. WASHEGARI a nutse ta haɗa kayanta ta fito babu mutane da yawa sbd Sunday ne yawan ci ƴan visiting ne a farfajiyar Hospital ɗin ta fito ta tari ɗan sahu ta dawo gida, a filin gida ta tadda Daddyn su ta iso gareshi, cikin girmamawa ta duka ƙasa ta gaida shi Barka da safiya Daddy Ya ɗago daga danna wayar shi da ya keyi da alama sako yake son turawa ya ce "Likita barka dai, kin dawo?" Eh Daddy na dawo. "To madalla a huta gajiya" Na gode Daddy. "Yauwa likita Ammie ta faɗa min da akwai wanda yazo jiya kuma yana son ya turo magabatan shi, to anjima da daddare ki sameni sai mu yi magana" Jikin Hamrah ya yi sanyi, anya Ammie bata yi saurin sanar da Daddy ba, da ta bari sun ɗan fahimci juna dashi, amma daga zuwan farko. Ta sauke numfashi tare da cewa To Daddy Allah ya kai mu. "Ameen" Ta miƙe ta shigo ta wuce side na Ammie ta taddata kwance nan ta gaidata ta amsa "Lafiya" Har zata miƙe kuma ta ji muryar ta "Nayi magana da Daddyn ku ya ce za ki iya ce masa ya turo magabatan shi" To. Shine abin da ta ce sannan ta fito ta tadda Ammar yana shirin fitowa cikin sanyin jiki ya kalleta tare da cewa "Kin dawo?" Eh na dawo, fita za kayi?" "Uhm magana Daddy ke son yi dani akan tafiyar mu, an matso dashi nan da satin sama zamu tafi" Ta ɗan yi murmushi ganin yana magana yana kallon gefe ta ce Ina so zamu yi magana anjima ni da kai. Ya sauke numfashi tare da cewa To. Ya fice ta dawo ɗakinta duk jikinta a mace ta watsa ruwa ta sanya riga da wondo na material sannan ta hau kan bed nata ta kwanta, bata jima ba bacci ya ɗauke ta, ta jima tana bacci ta ji alamun an taɓata buɗe idanuwan da tayi ne ta sauke su kan namecynta ta sakar mata da murmushi tare da miƙa mata hannu, ta riƙe ta janyota kan bed suka kwanta, Little Hamrah ta ce "Good morning" Hamrah ta shafa kanta tare da cewa Morning cutie, da Mom ki kazo?. Ta gyaɗa kai alamun eh. Suka ji sallaman su Nazeer suka shigo suna gaidata ta amsa musu nan ta hau raba musu choculate daman bata rabuwa dashi, suna murna suka fita itama ta fito ta dawo ɗakin da suke sauka, tana shiga ko duk suna nan, ta zauna Maryama na ganin ta shigo ta fice Zeenat ce ta ce "Yaya Hamrah duk da ina fushi dake amma bazan ƙi gaida ki ba, ina kwana" Murmushi Hamrah ta yi ta ce Amin afuwa duk da bansan laifin da na yi ba, lafiya ta kalau. "Kin ƙini baƙi ɗaya, ko ƙira ballantana ziyara gani da tsohon ciki ƙafata ɗaya a duniya ɗaya a lahira" Oh sorry Zeenatu na, kin san Allah kina raina tun last week na ke son biya ta gidan ki amma Allah bai nufah ba, ya kuke ina uwar gidan ki?. "Ni dai bazan hakura ba har sai kin je min, uwar gida tana nan fah, sai abin da ya ƙaru a halinta yau ma nazo ki bani shawara" Hamrah ta sauke numfashi tare da cewa Ikon Allah, ita bata sanin ta girma, to Allah shi kyauta. Ameen. Ayshe ta ce "Zeenat ki yi wa Yaya Hamrah uzuri ko dan irin aikin ta, Yaya Hamrah barka da safiya?. Bata ma bari mun gaisa ba" Lafiya ta lau uwar gida, ya shirye shirye?. "Alhamdulillah suna yi, dan ni ko kallo basu isheni ba" Hamrah ta yi murmushi kishi ya motsa ta ce Kuna yi dai ba suna yi ba. "Uhm ke dai bari ashe haka ake ji in za ayi wa mutum kishiya kai abin sai an daure, fisabilillahi duk yadda muke da ƴan uwan shi amma suka juya min baya suka koma gindin Amaryar tun basu shigo ba" Ayshe ki nutsu ki kwantar da hankalin duk wannan ɗokin na wani lokaci ne amma da kansu zasu dawo gare ki. "Kai ki bari a wannan satin kam sai na durza bakin ƙanwarshe fiddausi" Ayshe har yanzu hakuri zan baki, ina nan ina kan shiri nan da kwana biyu zan je na zauna miki in ba danna ƙirji nayi miki ba abin ba zayyi kyau ba. Zeenat ta ce "Gaskiya kin kyauta ki je cen ɗin yanzu ma da na biya ta gidan ta ƙadan ta mari Yayar shi, muna zaune ta shigo wai ko anƙi ko anso sai ankawo Amaryar mubi duk bokan da muka daman bi, tamu ba ta Allah ba" Uhm gwada da baku tanka musu ba, ina yaran ne?. Ayshe ta sauke numfashi tare da cewa "Sunbi Yaya Ammar zuwa waje, ni fah nazo da Abinci ko ci ban nutsu nayi ba muje ɗakin ki Yaya Hamrah mu ci na kwanta ko naji sanyi" A tare suka fito zuwa ɗakin Hamrah, suna shiga suka mimmiƙe Hamrah ta fito zuwa kitchen anan aka ajiye abincin, ta tadda Maryama tana zuba abinci Hamrah ta soma zuba nasu a babban trey jollof rice ne wacce ta ji kayan spices, sai dandarun jan nama, ganin irin rainin dake kan Maryama yasa ta ce Maryama, kina bani mamaki ta yadda rayuwar duniya ke rud'an ki, wannan halin da kika ɗaurawa kanki wallahi babu inda zai kai ki, bansan meyake sanya ki fuzgar kai ba, amma ina mai baki shawara ki bi duniya a sannu. Turo baki da kuma ɗaga hanci tayi ta ce "Ai kinfi kowa sanin dalilin da yasa nake haka in kema baki sauya daga ƙiyayyar da ki ke nunawa habibina nima bazan daina abin da na keyi ba, kin nuna banbanci sakanina da Zeenat bacci ni dake mun fi kusanci.... Ya isa, Maryama kada kiga ina biye miki ki ɗauka tsoron ki nake ji, a'a tausayi ki ke bani sbd kin ɗauki dala ba gamo ne, shi Alay Shatteema ne ya ce dake bana son shi ko kuma ke ce ki ke ganin hakan? To ki sani shi rashin mutunci riga ce kowa ma yana iya arota ya sanya ta kuma ya yi, amma kuma ganin rigar ba mai kyau bace shiyasa ake gudun sanya ta, amma in ba haka ba Maryama kin yi kaɗan kimin na ɗauka. "Ai ko shi Alay Shatteema bai faɗa ba ni ai kin min na gani, kina ɗaya daga cikin waɗanda basu son aurena dashi ko kin manta ne da abin da ya faru a wancan lokacin, sannan haka still ya sake faruwa a ranar sunan Waleed, dan haka duk wanda ya ce baya son mijina to nima bazan yi dashi ba" Murmushi Hamrah ta yi su sai ta ce Au sai yanzu na fahimta wato dai kin fi son mijin ki da danginki to ya yi amma ki sani ba a takama da gidan miji amma anayi da na uba, ki yi indai zai miki kyau Allah bada sa'a. Tana kaiwa nan ta ɗauko abincin ta nufi dakinta dashi tana jinjina lamarin, lallai Maryama ta na dab da zubar da hawayen dana sani in dai akan Alay Shatteema ne. Allah shi kyauta. Nan suka zauna suka soma ci, yaran sun dawo ma ɗakin Ammar suka wuce dan fita ya yi dasu su kayo siyayya. Bayan sun kammala cin abinci ne Zeenat ta kalli Hamrah tare da cewa "Yaya Hamrah na rasa gane kan uwar gida ta, ta hanani sakat a gidan ke numfashi ma so ta ke ta hanani, shima kanshi Alay Gana kamar tsoronta yake da ta ƙirashi har rawar jiki yake duk ya kiɗime" Uhm Zeenat, daman duk wacce tazo a mace ta biyu a gidan miji sai tayi hakuri, duk abin da za tayi ki kau da kai in kince sai kinyi magana babu wanda zai goya miki baya cewa za ayi kin sameta a gidan dole kice za kiyi hakuri. Zeenat ta sauke numfashi ta ce To ai Allah ne ya ƙaddara sai na auri mijinta, dan meyasa zata ja da hukuncin Ubangiji abin da ma zai baki haushi shine tana da ɗiya a gidan miji yadda na ji ma ta kusa haihuwa amma ta ke takuramin" Ayshe da tayi shiru tun ɗazu ta ke jin nata takaicin ta ce "Ai ya zame muku dole ki bi tsarin da muka ɗaura mazajen mu akai ta yaya zaku shigo ku mulke mu, ai ba zayyu ba wallahi" To fah sun rabawa Hamrah kai abin ya koma kowa so ta ke a goyi bayan ta da ƙyar Hamrah ta shawo kan zancen aka sauyata zuwa kayan da zasu ɗinka na fitar bikin nan da kwanaki biyar, sun zazzaɓa akan Ayshe zata karɓo sai ta kaiwa telan ta, nan Hamrah ta sanar dasu zuwan Alhaji Sama'ila, ai ko suka saka murna suna Alhamdulillah Allah ya ƙarɓi addu'ar su, su kayi ta bata shawa akan ta amince mashi su sha biki. Fira ta sauya an koma na bikin hamrah, ita dai bata ce komai ba sai binsu ta ke da kallo, a haka har suka wuni sai yamma lis suka tafi da yaran baƙi ɗaya aka bar Hamrah da kaɗaici, ta dawo ta zauna jin ana kiran sallah magrib yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta idar ta jima tana addu'a akan in Alhaji Sama'ila alkhairi ne gareta Allah ya tabbatar in kuma ba alkhairi bane Allah ya sauya mata da mafificin alkhairi har aka kira sallah ishai ta idar sannan ta fito zuwa wajen Daddyn ta dake zaune a farfajiyar gida tana isowa ta zauna kusa dashi tare da yi mashi barka da dare, ya amsa tare da cewa "Da man akan batun wannan mutumin ne, wanda Mommyn ku ta faɗa min akan shi ne zaɓinki a matsayin wanda zai aure ki, shin ɗan ina ne kuma a wacce unguwar ya ke menene sana'ar shi, waye iyayen shi?" Jikin Hamrah ya yi sanyi sosai ta rasa ta inda zata fara amsa tambayoyin nan ita kanta bata san a salin labarin shi ba kawai dai Ammie ta yi saurin sanar da shi ne , a hankali ta ce Sunan shi Alhaji Sama'ila, ba mazaunin nan garin Maiduguri bane wasu ayyuka ne suke kawo shi, a Abuja state yake da zama. Sauke numfashi Daddyn su ya yi tare da cewa "To ke likita ya za kiyi ki aure mutumin da baki san asalin shi ba, shin ma har tsawon yaushe haka ku ke tare har yasa baki san sana'ar shi ba?" Kanta na ƙasa a hankali ta ce Daddy bamu jima da haɗuwa ba baifi sati biyu ba jiyane dai yazo nan ya ke sanar dani cewa yana so ya turo magabatan shi. "Kayya! Wannan ai bai nuna ba har yanzu zancen danyene ace daga zuwan shi na dauke ki na bashi ce mashi akayi ke kaya ce, ko ko mun gaji da ke a'a ba zayyu ba sai nayi bincike kanshi, kada ki yi gaggawa kema kin ji ko in shi ba zai jira ba ya tafi Allah zai kawo miki wani" Sauke numfashi Hamrah ta yi to yanzu Ammie zata ce bakin ta ɗaya da Daddyn ta ya zata yi kenan, a hankali ta ce To Daddy na gode. Ta miƙe ta shigo ciki nan ta tadda Mommyn ta a tsaye tana jiran shigowar ta, aiko tana ganinta ta jeho mata da tambayar ya suka yi nan Hamrah ta sanar da ita amma ina ranta ya matukar ɓaci ta ce "Ban gane ba sai kun fahimci juna yanzu mutum ya taso daga wata uwa duniya yazo shine za a ce ba mutumin kirki ba sai anyi bincike to shikenan sai ki zauna muyi ta gogan kafaɗar juna cikin gidan" Ita dai Hamrah bata ce komai ba kanta a kasa sai ga Daddyn su ya shigo ya tare shi da zancen ya kalleta ya ce "Hajjiya Batula ni kam me wannan yarinyar ta tare miki ne, yarinya da ko magana bata yi kuma da ta fita tun safe sai yamma ta ke dawowa ko kuma ta fita da yamma ta dawo da safe, to wai ma sbd ta jima bata yi aure ba shikenan daga zuwan shi sai mu bashi ita ba tare da mun san shi ba, ni na faɗa bazan mata auren gaggawa ba, in zai jira zuwa wani lokaci sai a sanya ranar amma daga zuwa ya ce wai har ya yanke lokaci ba tare da ya zauna dani ba ko mun zauna da mutanen shi ba" Ammie ta birƙice musu lokaci guda da ya sanya Hamrah sorata ta miƙe da sauri zata bar wajen ta ji ta ce "Na gaji Alhaji, na gaji ka fito kawai ka faɗamin cewa akwai wata manufa a ƙasa shiyasa, yarinya shekaru sun ja manema sun fito amma kuma kace sai ka zaɓa ka ɗirce is she a diamond, ina itama kamar sauran ta ke haihuwar ta akayi, to muddin tana son mu zauna lafiya ta fidda miji ta yi aure, in dai ba wata manufa ta daban cen ba.... "Hajjiya Batula, meya kawo wannan zancen, me ki ke nufi da wannan Hamrah ɗiyata ce ba zan taɓa barin a cutar min da ita ba shiyasa na ke son na aura mata mutumin da zai riƙemin ita da amana, dan haka sai na duba na tantance kuma magana ta zauna, in kuma kin shirya son rashin zaman lafiya cikin gidan to shikenan" Sauri Hamrah ta yi ta faɗa kan bed ta fashe da kuka me Ammie ke nufi ne... In ba wata manufa ba, to me hakan ya ke nufi kenan? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun...... Comments and share MUJARRABI By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 15 & 16 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ tsit babu mai magana cikin motar, sai ƙamshi da sanyin AC dake ratsa dukkanin jikin su, ko da bata ɗago ta kalli inda yake ba ta san yana kallon ta sbd yadda ta jita bata cikin nutsuwa, haka kawai take jin mutumin na yi mata ƙwarji. A daidai ƙofar gidan su ya yi driver parking hakan ya dawo da Hamrah daga tunanin da ta keyi. Shatu ce ta fara fitowa driver ya taimaka mata suka sauke kayan, Hamrah na ƙoƙarin fitowa sai ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa "Umm bani time na ki mana kaɗan muyi magana" Ta sauke numfashi a hankali ta yi magana ba tare da ta kalleshi ba ta ce Yamma tayi gashi sallah la'asar ma ta wuce mu, zamu je mu gabatar, amma ba ƙin tsayawa nayi ba. Murmushi ya yi yana jinjina kanshi ya ce "To ki ce da Malama nake tare to shikenan amma let's exchange our number" Ta sauke numfashi tare da amsar wayar shi ta sanya number ta sannan ta fito ya ƙira ta yi saving da Abuja, sukai sallama suka shigo cikin gida shi kuma driver ya jashi suka tafi. Suna shiga ciki Shatu ta daka tsalle tana murna, daman gulma na cinta ta rasa yadda zatai tun ɗazu ta kagu ya tafi ta ce "Wayyo ƙawata sanar dani good news Allah ya sa ya ce yana son ki" Murmushi ta yi ta ce Ke to bai faɗa ba, ya so muyi magana amma kuma na ce dashi munyi missing lokacin sallah la'asar za mu je mu gabatar, to shine fah ya karɓi number ta. "Yeee Allah yasa ya ƙira muji alkhairi" To in kuma wani zancen na dabanne fah. "Kai ƙawata ai ga dukkan alamu ma ya kamu" Dariya su kayi suka shige ciki, kasancewar Hamrah tana da night duty yasa suna idar da sallah ta hau shirin tafiya. Bayan sun fito ne Shatu ta wuce gida sbd kayan dake hannunta bata yiwa ƙawarta rakiya ba zuwa bakin titi. Hamrah ta iso bakin titi ta tari ɗan sahu ya kaita bakin Hospital ta shige ciki, kamar yadda ta saba ta ƙimtsa komanta kan teburi sannan ta kunna system ɗinta yau kam ta ɗan makara bata iso da wuri ba taji ana kiraye² sallah magrib ta tashi ta idar tana kan dardumar aka ƙira ishai nan ma ta idar sannan ta fito da niyyar tafiya general ward sai taji muryar Dr Mahmoud yana "MD na neman ki yana cikin office nashi" Kamar ba zata juyo ba amma jin MD yana nemanta shiyasa ta juyo ta dawo ƙofar office nashi har lokacin bai daina kallonta ba, ita kam ko kallon inda yake ba tayi ba tayi nocking ya bata izinin shigowa ta shiga, ta tadda shi zaune ya ɗaura ƙafarshi kan ɗaya ya kishingiɗe jikin kujera ya lumshe idanuwan shi. Afternoon sir. Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata su ya ce "Have a sit" Ta zauna ta maida kallon ta gefe, mutum a gaida shi ba zai amsa ba wannan wane irin hali ne ya jima yana kallon ta sannan ya ce "Dr Aliyu an mai dashi bangaren yara sbd ana bukatar irin shi gogagge ta fannin aiki a wajen, shine naga ya dace da ke da Dr Mahmoud kuyi aiki tare shine yanzu zai zamo messenger na sannan kuma PA nki ina so ku haɗa kai kuyi aiki tare, kamar yadda ku keyi da Dr Aliyu, Please i don't want to see or hear anything from both of you da ya shafi ƙoraf, muna bukatar ku haɗe kanku" Sauke numfashi Hamrah ta yi ta juyo ta kalleshi kamar yadda yake kallon ta tace Amma sir, in dai da mutunci ai yakamata ayi shawara dani akan wannan kafin a yanke hukunci, sannan ni na fi son aiki da Dr Aliyu ba a shawar ce ni ba aka ɗauke shi sannan kuma Dr zalihat ce wacce ta dace a haɗa mu ba wai Mahmoud ba, kai ma kasan aikin mu ba zai taɓa tafiya daidai ba kuma kasan halin shi sarai ba son zuwa aiki yake ba shine za a haɗani dashi sbd ni na ɗau nawin aikin shi, Please a kanza shi da Dr zalihat. Shuru ya yi na wani lokaci sannan ya ce "HAMRAH, you always challenged me at anything, kina nufin ban san me nake yi bane ke kin fini sani, kada kiga OG ya baki office ki ɗauka dani da ke kanmu ɗaya I'm bigger than you in everything yanzu ma na kiraki ne sbd na sanar dake ba wai shawarar ki nake nema ba..... Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya shigo, yana ganin su ya tabbatar hali ya motsa, duk girman kai ne dasu ko wannensu yana son girma, shiyasa basa jituwa cikin tashi salon munafunci yace "Ranka shidaɗe, an kammala duba patients ɗin ka" MD ya washe baki ya ce "Weldon Dr you are trying fa, thank you" "Noted sir, ai in dai kai ne komai ma zan iya yi maka shi" "Yauwa zauna ga Dr Hamrah nan muna magana akan aikin ku ne ku haɗe kai kuyi aiki tare" "Ai ba komai ai in shaa Allahu..... Akwai, ni ba zan yi shiru na cuci kaina ba, bana son aiki da kai Dr Mahmoud dan haka a sauya min shi da wata. "Haba Dr Hamrah, i have changed fah wlh na kanza ba zaki sami matsala dani ba" Uhm. Kawai abin da ta ce, sai tayi maganin shi tun da ya ɓata mata suna a wajen Dr Aliyu sai ta sa ya yi regretting, ta miƙe tare da kallon wayar hannu ta lokaci ya ja gashi yau babu patients ɗin da ta duba, ta yi musu sai anjima ta fice, kai tsaye ta wuce general ward nan ta duba su sannan ta dawo ta kwanta, ta jima tana ta tunani kan rayuwa sannan ta kwanta. Gari na wayewa ta dawo gida. _Bayan kwanaki biyu_ Kasancewar yau morning gareta hakan yasa tana dawowa daga wajen aiki ta faɗa toilet ta watsa ruwa ta shirya cikin doguwar riga mara nawi ta zauna Jin ana kiran sallah magrib yasa ta tashi ta idar har da ishai sannan ta kunna tv tana kallo Ammar ya shigo ya tadda ta zaune tayi zurfi cikin tunani har ya ajiye mata leda ya ɗauki remote ya kanza channel zuwa MBC Bollywood, ana film ɗin student of the year. Ya juyo tare da dan taɓa ƙafarta ta sauke numfashi tare da kallon shi, ya yi mata alamun na tane ta ɗauka. Ta dauko leder ta buɗe ta, roasted fish ne ya kawo mata da moltina sai kuma choculate kala biyu, ta kalleshi tare da cewa Na gode Ammar yau kuma har da choculate sai ka ce yarinya. Murmushi ya yi kai Hamrah akwai son girma, ya ce "Yarinya ce ke mana" Hararar shi tayi, ya yi dariya sbd ta tsani wannan kalmar ta yarinya ta ce Kada kasa na fasa cin abin da ka siyo. Ya yi murmushi ya ce "Allah baki hakuri babbar yaya" Nan ta yi murmushi ta soma ci sai ta ji wayar ta na ringing tana dubawa ta ga mutumin da tayi saving da Abuja ne, sai da ta sinke ya sake ƙira ta ɗauka cikin sanyayar muryar ta tayi sallama, har tana jin yadda yake suke numfashi ya amsa tare da cewa "Ranki shidaɗe, Allah yasa ba bacci ki keyi ba na tada ki" Ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce A'a na kusa amma. "To ashe dai ban yi laifi ba, daman na ƙirane mu gaisa kuma na nemi alfarmar ko zuwa gobe ne nazo sai muyi magana" Ta sauke numfashi tare da cewa Eh to da yake ina fita aiki kuma gobe ina da morning duty sai yamma zan tashi. "Wow, fantastic! Do you mean ke likita ce?" Yes of course. "Masha Allah, that's good, ki ce nima ina dab da warkewa" Baka da lafiya ne?. Eh. Ya faɗa, sannan ya ce "To zuwa yaushe ki ke gida sai nazo" Jibi. "Ok Allah ya kaimu" Ameen. Sukai sallama, ta sauke wayar ta ɗan ɗago ta kalli Ammar wanda ya zuba mata na mujiya tun da yaji da na miji ta ke wayar ta sauke numfashi tare da cewa Menene? "Waye ne?" Me ka ke nufi. Kai tsaye ya ce "Wa ya ƙiraki, me yake nufi da wannan kiran?" All questions for me, ban isa a ƙirani bane yaya Ammar?. "Da gaske nake fah, kamar da na miji ki ke magana, kuma kina ce dashi yazo jibi me zai kawo shi?" Ta tattare ledan ta saka a dustben sannan ta wuce toilet ta wanke hannunta ta fito, ta sameshi ya yi tagumi a hankali ta ce Sunan shi Alhaji Sama'ila daga Abuja yake, to mun haɗu ne ranan na yi mishi kwatancen gidan Alay SHAREEF mai nema takaran House of reps, shine kuma kwanaki biyu da suka wuce muka haɗu a wajen shopping shine ya kawo ni gida, yanzu kuma cewa ya yi yana so yazo akwai abin da ya ke son muyi magana akai. Sauke numfashi Ammar ya yi ya ce "To yazo muji da me yake tafe, amma kuma daga jin sunan shi tsoho ne, in kuma da gaske hakan ne gaskiya ya yi gaba" Murmushi tayi ta ce To cewa fa ya yi magana zamu yi, ba wai so na yake ba. Bayyi magana ba ya ci gaba da kollon shi, ta yi murmushi ta ce To ai naga son na yi aure kowa ya ke to menene kuma na waɗannan tambayoyin?. Ya sauke numfashi tare da cewa "Haka ne muna so ki yi aure amma kuma mun fi son kiyi auren kwanciyar hankali, shiyasa sai mun tantance wanda zaki aura" Dariya ta yi ta ce Ƙanina na kaina, kada ka damu da yardan Ubangiji zan yi dace. Sun jima suna fira sannan ya yi mata sai da safe ya fice, ta yi addu'an bacci ta kwanta. Washegari bayan ta kammala shirinta, ta fito tayiwa Ammie sai ta dawo bata kulata ba ta fice zuwa wajen aiki, tana isowa sai ga motar Dr Aliyu ta shigo har ya yi parking ya fito yana kallon ta, ta shige ciki ta buɗe, bayan ta kammala jera komata ta zauna tare da sauke numfashi, turo ƙofar ya yi tare da sallama yana isowa ya zauna tare da cewa "Good morning my partner" Bata ɗago ba ta ci gaba da danne² wayar ta, ya ce "Nazo ne mu tattauna akan abubuwan da zamu gudanar wunin yau" Ai ni tun kan na fito na ke gama daily plan ɗina. Murmushi ya yi ya ce "Amma kin san yanzu ni PA kine so, we will work together, kuma dole nasan duk wani abin da za kiyi" Ta juyo tana kallon shi, shima ita yanke kallo, ta ce Bai zama dole kasan komai na ba, do you work. Ya sauke numfashi ya ce "Dr Hamrah let's work together, bazan sake yi miki abin da baki so ba, na canja fa" To Allah yasa ba tuban muzuru ka yi ba. Ya yi murmushi ya ce "To dame zamu fara?" Akwai patients a VIP rooms dukkanin su maza ne kai za kaji dasu yau, nima kuma zan duba mata a general ward. Dariya ya yi sosai ya ce "What that means?" Kawai. Ya jima yana kallon ta sannan ya yi murmushi ya fice, ta yi ajiyar zuciya, shi Dr Mahmoud ya yi amfani da Dr Aliyu wajen neman kusanci da ita shi kuma MD yana so ya yi amfani da Dr Mahmoud wajen tattaro bayana daga wajenta, uhmm tayi ajiyar zuciya. 5:00pm na yi ta tattaro yanata² ta yo hanyar gidan, sai dai kuma wani tunani ya bata ta shiga gidan su Shatu su gaisa a tsai tsaye ko ba komai ita tana zuwa mata amma ita bata da time na kanta ma ballantana ziyara, tana shiga a daidai lokacin kuma Alhaji Yusuf yana ƙoƙarin fitowa Mommyn shatu tana yi mai rakiya cikin girmamawa ta gaidasu ya yiwa Hamrah kuri da idanu har ta shige ta girgiza kai a ranta ta ce Allah ya shirya. A palour ta tadda shatu aiko tana ganinta cikin murna ta ce "Ƙawata kamar kin san ko kina raina daman cewa na yi koman dare zan shigo" Murmushi Hamrah ta yi tare da cewa, Aiko ba zan ma jima ba a gajiye na ke zan wuce, daman mu gaisa ne. "Duk da haka sai na shafa miki labarin" A lokacin Mommyn ta tashigo tare da cewa "Hamrah ki zauna mana" A'a Mommy daga wajen aiki na ke zan wuce ma. To Shatu yi mata rakiya ko. Shatu ta miƙe suka fito, Hamrah ta ce Kamar Mommy ta sauko kin yi yadda muka tsara ne?. "Eh na yi tun washegarin ranar na baiwa Mommyn hakuri dashi kuma Daddyn sai dai jikin shiya yi sanyi amma bai fahimci komai ba" Ai ba zai fahimta ba sai nan gaba. Dariya sukai suna fira har ta rako Hamrah kusan gidan su Hamrah ta ce Yauwa ƙawata wannan mutumin na Abuja mun yi dashi gobe zaizo. "Kai amma na ji daɗi ki ce na shigo mu haɗa beta na taran baƙo" Ke rufani ki sayani, a da ma da nayi yarinta ke ɗibata yanzu kam ba wanda zan mai wata beta in ya yi mutunci na bashi ruwa, ballema shi wani abun ne zai kawo shi innayi beta ma sai yaga rashin hankalina. Nan sukai dariya sannan suka rabu, Hamrah ta shigo gida a lokacin ma Ammar ya dawo yana tsaye yana waya ganinta yasa ya kashe ya ce "Ashe baki shigo ba sai yanzu, na yi tunanin kina ciki ai" Murmushi ta yi ta ce Gidan su Shatu na shiga, me akwai ne naga kamar da labari. Murmushi ya yi ya ce Muje ki girka mana abincin ki mai daɗi. Ta ɗan buge shi a kadaɗa tare da cewa A gajiye na ke yau sai dai ka siyo mana a bin taɓawa a waje. "To ƙanwata kada ki damu harda choculate ma zan siyo" Hararar shi ta yi ta ce Ko mutum zayyi ya ya dai girma an fi shi. Ta yi hanyar ciki ya yi dariya ya bi bayanta. Ɗakin Ammie ta shige ta gaidata amma bata kulata ba ta wuce ɗakin ta har dare tana kwance, Ammar ya shigo masu da kayan ciye² ya ajiye tare da kunna tv suka soma ci sai suna fira sai da suka kammala sannan ya tafi ɗakin shi. Wannan ɗabi an tun suna yara su keyinta har suka girma basu daina ta ba, shiyasa akwai kyakkyawar fahimta a sakaninsu kuma basa ɓoyewa junan su sirrin su. _WASHEGARI_ A hankali ta buɗe idanuwan ta tare da ƙurawa farin slink ido, tunowa da tayi yau Friday ne yasa ta sauke numfashi ta miƙe ta gabatar da sallah asubah ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sannan ta koma bacci bata farga ba sai wajen 10:00am da ƙyar ta iya tashi ta ƙimtsa dakinta sannan ta wuce kitchen ta dafa indomie ta zauna a kitchen ta ci, ta wuce ɗakin Ammie ta zauna a lokacin Daddyn su yana shirin fita, suka gaisa ya fice ta kalli Ammie a hankali ta ce Ammie, anjima akwai baƙon da zaizo ya ce yana son magana dani. Ga mamakinta sai taga Ammie ta saki fuskar har da ƴar murmushinta ta ce "To saura ki yi sake kamar yadda ki ka yiwa sauran suka tafi" Kanta a ƙasa ta ce Ammie ba saurayina bane, haɗuwa mu kayi ya ce yana so muyi magana. "Ah in ba abinki ba haka kurum ai bazai ce zaizo ba, ni dai na faɗa miki kisan irin tarɓar da zaki yi mashi" To Ammie na gode. _____ cikin nutsuwa ta ke shiryawa ta sanya riga da skart ta lace mai background pitch da kuma ratsi blue ya yi dai dai da shape nata ta yi normal ɗauri ta fashe Jikinta da turaruka masu ƙamsha tare da yane jikinta da gyalle ta dau wayarta dake ruri ta yi sallama ya ce "Na iso" Ok ka shigo ba damuwa. To. Ya faɗa ya kashe wayar. Ta juyo zata fito sai ganin Ammar ta yi a tsaye yana kallon ta, ta ƙaraso ta ce Meyasa ba kayi sallama ba, kuma kasan bana son hakan. Haɗe fuska ya yi ya ce "Ya yi tsufa da yawa, please kada ki bashi fuska wannan kwalliyar ma ki sauyata" Sosai ta ke kallon shi cikin ɓacin rai ta ce Ina ruwan ka da sufan shi sannan ma ce maka ya yi yana so na ne?. Sauke numfashi ya yi ya ce "Da gaske na ke ni kwata kwata bai kwanta min ba" Ta raɓe ta gefen shi ta wuce ɗakin Ammie ta sanar da ita yazo, sannan ta fito. Tun da ta fito Alhaji Sama'ila ya saki baki da hanci yana kallonta har ta iso cikin sanyayar muryarta ta ce Sorry, na jima ba. "A'a ai girman kujerar ki ne" Ya faɗa yana tsosa keyar shi, ta janyo farar kujerar zama ta ajiye mashi ya zauna sannan ta ce ina zuwa, ta shige ciki, ta ɗauko mashi gorar swan water ta fito ganin Ammar ta yi yana yi mashi magana bata ƙaraso ba ta ɗanyi jim kaɗan sannan ta ƙaraso ya bar wajen ta ajiye mashi tare da cewa Sannunka da zuwa. "Yauwa" Duk jikin shi ya yi sanyi ba kamar ɗazu ba ya ce "Waye wannan wanda yanzu ya fice" Ta sauke numfashi a hankali ta ce Ƙanina ne shi. "Ƙani" Ya faɗa yana kare mata kallo, ya sauke numfashi, ta ce "Eh girman jiki gareshi amma yaro ne" Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Hamrah bazan ɓoye miki, ina son ki kuma da aure, tun a ranar da na hango ki har na tsayar dake muka gaisa na kamo da sonki, in har kin amince min nan da karshen wata zan turo magabata na a sanya ranar biki, kin san ni ba mazaunin nan bane wasu abubuwan ne suke kawo ni amma kuma hakan ba zai hana na tsaya ayi komai dani ba" Jikin Hamrah ya yi matukar sanyi ta ɗago ta kalleshi kwarjinin shi yasa zuciyar ta harɓawa, bashi da wani abin da za a koshe shi sai dai girma da kuma girman jikin da yake dashi ne ba kowacce mace bace zata amince ya aureta. Ta sauke numfashi ta ce To zan yi shawara tukuna, bani nan da kwanaki biyu. Murmushi ya yi ya ce "Ko dai ganin na fara tsufa ne?" Ta yi murmushi tare da cewa A'a. Ya ce "To ba matsala zan jira amma kada ki ja lokacin ya yi tsawo" To. Sun ɗan taɓa fira ta ce dashi zata wuce wajen aiki, ya ce ta fito ya sauke ta, taƙi amma ya dage hakan yasa ta shige ciki ganin Ammie ta yi zaune a palour tana ganin Hamrah ta ce "Da me yazo" Jikin Hamrah ya yi sanyi kuma amma yadda Ammie ta sake fuskarta yasa taji sanyi ta ce Ammie cewa ya yi da aure ya ke so na. "Alhamdulillah me ki ka ce dashi?" A hankali ta ce Na ce zan yi shawara. "Ba ga irinta ba hamrah wannan halin naki shine ya sanya saura gudawa, wacce shawara da ta wuce ki amince" Eh Ammie daman wai muyi magana ne..... "Ammie gaskiya basu dace ba, kin gan shi kuwa sai ka ce Daddyn... "Ammar ka ci gidanku, manya na magana kana saka baki, tshoholo ko shi ya kawa tsufa duniya tunda ya ce yana so angama" Ya turo baki ya shige cikin ɗakin shi. Hamrah ta ce Ammie zan shirya na wuce wajen aiki. "To Hamrah a dawo lafiya" Ta ɗago ta kalli Ammie sbd rabonta da taji ta faɗi hakan a kanta ta manta, ta wuce dakinta ta dauko jakarta ta fito ta shige ɗakin Ammar ta taddashi ya cika sai batsewa ya ke a dole Alhaji Sama'ila bayi mishi ba ta ce AMMAR. Ya kalleta da jajayen idanuwan shi bai ce komai ba ya ɗauke kanshi. Ta yi murmushi a ranta tace su Umar hali ya motsa ta zauna kusa dashi tare da cewa Ammar, dama ce ta sameni bai kamata mu bari ta kubuce min ba, baka ga yadda Ammie ta saki fuska muna magana ba, sannan menene in na aure shi ai ba wani matsala ni ma ai na tsufa. Ya sauke numfashi ya fisgar da iska ya ce "Na yi mai tambayoyi daga dukkanin alamu bashi da gaskiya.... Kai Ammar, shiyasa ya ke tambaya ta wanene kai a gareni ashe da abin da ka faɗa mashi, Please tell me me ka faɗa mishi?. Ban ce komai ba kawai tambayar shi na yi waye shi, menene sana'ar shi sannan menene taka mammen abin da ya keyi anan... Ammar wannan ba hurumin ka bane, kabar manya su yi magana, stay out of this, abin da ka keyiwa sauran suke gujemin shine abin da ka ke so kayiwa wannan ko kana tunanin ban sani bane, to kasani muddin ka zama dalilin tafiyar wannan mutumin to babu ni babu kai......... Comments and share. *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 21 & 22 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* ________ Bankaɗo ƙofar ya yi ya shigo kamar wanda kura ya biyo shi yana huci tare da zazzare idanuwan shi da su kayi jajir yana kallon ta cikin ɓacin rai, ba a taɓa mashi irin abin da ta yi ba, ta zubar mashi da mutunci a idon ma'aikatan da suke shakkan shi, who is she da za ta ja dashi, tsayawa ya yi a kanta yana sauke numfashi ya nuna ta da yatsa, zuba masa idanu ta yi tana kallon shi duk ya fita hayyacin shi ya ce "Ke Hamrah ki ke ko what so ever, ki fita cikin idanuwana na rufe har kin isa ki tuɓe min rigan mutunci a bainan nasi, har ma jina haɗa kai da ni to ki sani kin taro match sai kin yi regretting abin da ki ka aika yau sai kin yi kuka da ba a haiho ki duniya ba" Yana ajiyar zuciya, Hamrah ta miƙe cikin nutsuwa ta ke ƙare mashi kallo sbd su ta ke ta tabbatar da cewa shin a hayyacin shi ya ke ko kuma ya yi marisa dan ba abin mamaki bane zai iya aikatawa ta ce MD ni bana ja da kai kuma bana haɗa kaina da kai, amma kuma wasan da ka fara ne na ƙarashe shi sannan duk abin da za kuyi ku aikata babu ni a ciki..... "Hold on Hamrah, mu me ki ke nufi da mu ni da waye kenan?" Ta sauke numfashi ta ce MD I have told you, ka aikata duk abin da ka ke so amma kada ka sanya sunana a ci, sbd I hate sharri, ba nayi kuma ban so amin dan haka do what ever you want amma kada ka sanya ni a ciki. Murmushi ya yi yana zazzare idanuwana yana bin office nata da kallo ya ce "Na fahimta takamar ki wannan office ɗin ne to ki sani kina ji kina gani sai kin barshi, sai kin zubar da kwallah kina begging ɗina akan na dawo dake amma kash a lokacin kin makaro sbd bakin alkalami zai bushe" Murmushi ta yi ta ce MD shi sharri ɗan sako ne, zaka iya aikashi duk inda ka keso amma kasani zai je ne kuma ya dawo, da Allah na dogara babu abin da bawa zai iya yiwa bawa ɗan uwanshi fa ce da izinin Ubangiji, kuma Allah ya haramta zalunci bisa kanshi kuma ya hana ayi shi dan haka ba zai bari ka yi galaba a kaina ba sbd bani da hakkin ka, kuma God forbid na roke ka akan wani abin dunya kai wannan aikin ya dama dan haka kai za kayi ta daga hankalin ka. Girgiza kai ya yi alamun za ki sani, ki jira lokacin sannan ya fice, ta zauna tare da sauke numfashi ta lumshe idanuwanta kanta ya fara yi mata ciwo sbd tsawar da ya daka mata, ta mike ta wuce general ward ta jima acen sai bayan la'asar sannan ta dawo office nata. Bayan ta idar da sallah ta sake komawa genaral ward har da vip sannan ta dawo nan ta tadda OG da MD suna magana ta shige cikin office nata ta hau tattare kayayyakin ta kammala kimtsasu OG ya shigo cikin girmamawa ta ke welcoming nashi ya zauna tare da duban ta ya ce "Dr Hamrah lokacin tashi ya yi ko?" Ta sauke numfashi tare da cewa Eh sir, da akwai abin da zan yi maka shine?. "No, babu kawai na fahimta kamar akwai matsala a wannan Hospital ɗin ne shine na ke so mu zauna nan da kwanaki biyu mu samu mu gano matsalar sai mu san yadda zamu gyara" Ta sauke numfashi cikin farin ciki ta ce Ok sir, as you do. To shikenan, ina son bayanai na wannan Hospital ɗin da kuma ya patients suke ji da abincin da ake girkawa har zuwa kan fitan kuɗi da kuma shigowar shi sannan da sabon list na staff's da matsayin su" Ta jima tana so ayi irin wannan zaman dan haka abin ya yi mata daɗi ta ce Ok sir, zan shirya komai yaushe ne zaman?. "Eh to ko zuwa Thursday haka" Ta sauke numfashi tare da cewa Thursday. Ya kalleta ya ce "Ko da matsala ne?" Akwai biki shine daman zan karɓi hutu na kwanaki biyu zuwa uku sai Monday na fito bakin aiki. Shuru ya yi na wani lokaci sannan ya ce "Kamar yaushe kenan?" Thursday zuwa Saturday, tunda Sunday weekend ne sai na fito Monday. "Ok ba matsala sai ki yi magana da partner nki na office da kuma na duty" Na gode sir. Ya miƙe ya fice itama ta ɗau jakarta ta fito ta sanyawa ƙofar key ta hango MD yana yi mata mugun kallo bata bi ta kanshi ba tayi tafiyarta har ta iso ƙofar fita ta ji muryar Dr Aliyu yana cewa "Dr Hamrah shigo na kaiki gida" Ta juyo ta ɗan kalleshi sai kuma ta ɗauke kai ta fice yana kallonta ta hau a daidaita ta wuce. Ta iso gida ta tadda Daddyn su zaune a farfajiyar gidan ta gaida shi sannan ta wuce ciki ta iso ɗakin Ammie nan ta gaidata bata ko amsa ba da safen ma albarkacin Daddyn su yana ɗakin ne har ta miƙe zata fice ta ce da ita "Hamrah da fatan baki mance da abin da na faɗa miki ba ga me da fidda miji, nan da karshen wata kuma kinga lokacin matsowa ya dan haka ki je ki yi shawara tun kan lokacin yazo" Kan Hamrah na ƙasa ta ce To Ammie. Sannan ta fice jiki a sanyaye ta shige ɗakinta. Ajiye jakarta ta yi ta faɗa toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nawi ta zauna a bakin bed ta yi tagumi tana tunanin abin da Ammie ta ce, to ko dai kawai ta faɗawa Alhaji Sama'ila ta amince ya turo ɗin ba tare da ɓata lokaci ba, wata zuciyar ta ce to ya za ki yi da Daddyn da ya ce sai ya yi bincike.... Ƙirana sallah magrib yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar tana kan dardumar sallah tana ta lazimi har lokacin sallah ishai ya yi ta idar, tana jin yunwa kuma bazata iya tashi ta ɗaura komai ba akan gas duk ta gaji, dabara ta faɗo mata ta ɗau waya ta kira Ammar ya ɗauka tare da cewa "Yanzu zan iso gida.... In ba kayi nesa ba kazo min da abin taɓawa yunwa nake ji. "Babu na siyo ma, zan ƙaraso yanzun nan" Ta katse wayar, Alhaji Sama'ila ya ƙira da ta yi saving da Abuja ta ɗauka tare da sallama ya ce "Na yi fushi ba a kira anmin ya gajiya ba" Murmushi ta yi ta ce Ayi hakuri ina niyya. Ya sauke numfashi ya ce "To ya zanyi in ba hakurin zan yin ba, da fatan kina lafiya?" Alhamdulillah, ka sauka lafiya?. "Alhamdulillah, lafiya lau, da fatan da zaran na dawo zan ji amsa daga gareki?" Ta sauke numfashi tare da cewa Eh Allah ya dawo da kai lafiya. "Yauwa likita na gode, zan huta sai zuwa gobe" Su kayi sallama. Ammar ya shigo yana sauke numfashi ya ajiye ledar tare da cewa "zan je na watsa ruwa ki ci ki ajiye min nawa" Tab aiko in ka jima sai dai biri ya ganka. Ya yi murmushi ya ce "Yanzu zan fito ki ci iya cin ki" Ya wuce, ta buɗe ladar chibs ne da roasted fish sai kuma banana juice ta miƙe ta wanko hannu ta soma ci, ya jima sannan ya shigo sanye yake da bak'ar jallabiya wacce ta hasko fatarsa, kunna tv ya yi ya ce "Yanzu kallon news ɗin ma ba kiyi" Ya zauna ta ce Kayya abin kaina ma ya sha min kai, ni mantawa ma nake da kallo. Hannu ya sanya suke ci a nutse suna fira shikuma yana kallon Ball, ta zame hannunta ta miƙe ta shige toilet ta wanke ta fito ta zauna bakin bed tana kallon shi ta ce Ammar ranar yaushe ne specific time or day na tafiyanka?. Ya sauke numfashi tare da cewa "Next Tuesday by the grace of God" To Allah ya nuna mana. "Ameen, me ki ke shirya min ne?" Don't know amma sai na yi tunani tukuna. Ya miƙe ya shige toilet na ta ya wanke hannu shi ya fito ya ce "This coming Saturday ne ko auren mijin Ayshe?" Ta sauke numfashi tare da cewa Eh fah, zuwa jibi ma zan koma cen amma gobe na keso muyi magana da Ammie da kuma Daddy akan batun. "To hakuri za tayi haka Allah ya ƙaddara, in ba abin Bukar ba me zayyi da mata har biyu wannan ai ɗaurawa kai pressure ne" Murmushi ta yi ta ce Baza ka gane bane Ammar you are still young, kai ma da ka kai irin age nasu haka za kayi ku maza ai sai a hankali. Ɓata fuska ya yi ya ɗago ya kalleta tare da cewa Ki daina faɗamin ni yaro ne, zuwa yanzu na girma kuma zan iya aure kawai dai baya agenda na ne amma ni nasan ba yaro bane" Dariya ta yi tare da hararar shi ta ce Do you know what you are saying Ammar, aure fa kace, ce maka akayi auren abin wasa ne, umm kai yaro ne mana da sauran ka. Ya sauke numfashi cikin ɓacin rai ya ce "Wallahi ki daina ce min yaro, zan baki mamaki ai ina dawowa na yi aure ko dan ki tantance ni yaro ne ko kuma na girma, ina su Ayshe ƙanne na ne to ai babba ne ni" Murmushi ta yi ta ce Kai da aure sai nan da 10 yrs. Ya miƙe cikin kulewa ya wuce ɗakin shi, wai me Hamrah ta ɗauke shine da zata ce mashi yaro, zai je ya dawo sai ya bata mamaki, itako ko a jikin ta tayi addu'ar bacci ta kwanta tana mamaki yanda yara maza ke aure a wannan zamanin. _After 2days_ Zaune ta ke a office ɗinta tana ƴan rubuce-rubuce, sbd so ta ke ta yi arranging komai kamin ta tafi huta da zata yi na 2 days kasancewar daren Thursday night duty ne da ita, ta samu ta kammala ta miƙe ta sanya su cikin loker ta rufe sannan ta ƙimsa kan teburin. Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya iso tare da sallama ta amsa ba tare da ta kalleshi ba ya matso inda ta ke zaune ya zauna kusa da ita har tana iya jiyo bugun zuciyar shi, cike da mamaki ta ɗago ta dubeshi ya zuba mata ƙananun idanuwan shi da suka sauya kala, ta ce What these means, ka sakani gaba kana kare min kallo?. Ya sauke numfashi tare da damƙo hannunta ya riƙe shi gam cikin nashi yana fidda numfashi on on ya ce "Bazan iya jure sha'awar da na ke ji a kanki ba, ina son kasancewa dake kuma a daren yau kuma ya zama dole ki bani haɗin kai" Zuciyarta ta buga cike da tashin hankali ta ke kallon shi, tana tantama abu yasha baya cikin hayyacin shi, tayi saurin ƙwace hannun ta amma ya haɗa duka biyu ya damƙe su cikin hannu ɗaya, ta yadda bazata iya kwacewa ba, hannu ɗayan kuma ya kai ƙan botton na rigar da ya soma cirewa, zara idanuwana ta yi a lokacin da taga ya ɓalle bottonan idanuwan shi sun yi jajir dasu jikin shi ya soma rawa cikin rawar murya ya ce "Ke kaɗai na ke muraɗi, kuma ke ce wacce zata kashe min ƙishirwar da nake ji yanzu, please kada kimin gaddama nasan kin san komai kawai ni ne ba ki so amma ina mai tabbatar miki cewa sauran samarinki suna suka tara da ƙin ji salona zaki...... Jikin Hamrah na rawa tsoro ya rufe ta sbd bata taɓa kasancewa da namiji ba cikin wannan yanayin, da ƙyar ta tattaro karfinta ta hankaɗe shi ta miƙe tare da nufo ƙofar hannunta na rawa tana ƙoƙarin buɗewa ya yi saurin isowa ya rike ta tare da janyo ta ya haɗata da jikin garu yana sauke numfashi ya ce "You do like baki san na miji ba alhalin kin san komai kuma.... Tasssss, ta wanke shi da mari da ya sanya shi saurin dafe wajen ta nuna shi da yatsa ta ce Kayi kaɗan Mahmoud, kuma ka yi ƙarya ɗan iska ka kawai mara mutunci, think whatever you want amma ba zaka taɓa samuna ba. Duk da jakircewar ta ya tsorata ta, ta dau wayar ta tayi sauri zata bar wajen ya biyota zai chapke ta aka turo ƙofar cikin sauri ta yi hanyar fita Dr Aliyu ganin hakan yasa ya matsa mata ta fice Mahmoud kuma ya tsaya suna kallon juna yana sauke numfashi, cike da mamaki Dr Aliyu ke kallon shi ya jefa nashi da tambayar "Me ka ke shirin aikatawa?. Are you out of your mind, fyaɗe za ka yi mata" Dariya Dr Mahmoud ya ce "Rape, with who?. Bayan kuna sheƙe ayar ku tare shine za kace zan yi mata fyaɗe, gwada sa a ta naƙe" Hankali Dr Aliyu ya matukar tashi ya ce "Gwada sa'ah, hakan yana nufin ƙarya kamin ranan da ka ke cewa kasanta, kenan sharri kayi mata?" Ya isa. Ku fice min daga cikin office, kada ku ƙara shigo min. Cewar Hamrah tana tsaye daga bakin ƙofar, saka botton na rigar shi ya yi cikin sanyi jiki ya fice, ta sauke numfashi tare da dafe kanta bayan ta zauna Special Doctor, ki yi hakuri da abin da na faɗa miki ranan nan, ban san cewa sharri ya yi miki ba..... Please Dr Aliyu ka tashi ka fice, bana son jin komai da kai dashi duk halinku daya ne, tunda kunyi tunani iri ɗaya a kaina. "A'a Dr Hamrah kada ki haɗani da wancan fasukin, na yi miki hakanne a rashin sani ki ya fe min" Ta sauke numfashi tare da cewa I need to be alone, please go back to your office. Ya miƙe tare da sauke numfashi ya fice. Hamrah ta girgiza da abin da ya faru sakanin ta da Dr Mahmoud tabbas yana cikin maye ne amma za tayi maganin shi da zaran ya dawo hayyacin shi, har ta kwanta bacci ya ɗauke ta. Gari na wayewa ta shirya ta fito sbd da tafiya ta rufe office nata ta wuce office na Dr Aliyu wanda MD ya kwace kuma ya maida mashi abin shi, ta turo ƙofar ta shige ta tadda shi zaune shima ya kammala shirin tafiya ganinta yasa ta muƙe tare da cewa "Barka da safiya?" Barka dai, zan tafi sai Monday zan shigo. "To likita Allah ya nuna mana, amma lafiya ko?" Lafiya. Kawai ta faɗa tare da ajiye mashi wasu document ɗin ta fice. Kai tsaye ta dawo gida ta shige ɗakin Ammie ta gaidata a lokacin ma Daddy ya shigo suka gaida ya ke ce mata "Likita yau za ki tafi gidan Ayshe ko, to ayi ta hakuri fa kada kuyi abin da za ayi ta magana akai, Allah ya yi albarka" Amen Daddyn, mun gode. Ta miƙe ta dawo ɗakinta ta faɗa toilet ta shirya sannan ta fito daman kayanta a haɗe ta ɗauko tana ƙoƙarin fitowa Ammar ya shigo ganin haka yasa ya ce "Zuwa ina kuma naga ko hutawa ba kiyi ba?" Ta sauke numfashi tare da cewa Yauwa taimaka ka fitar min, sai ka nema min ɗan sahu ina sauri jirana suke. Kallonta ya yi sbd ganin yadda ta ke magana kamar da ɗan 15 yrs wai ya je ya kira mata ɗan sahu, ya ɗauki kayan ya fita dashi ta bi bayan shi sai gani ta yi ya sanya cikin motar shi, ta ce Kai ni za kayi da ka kiramin dan ɗan sahu, kai kam Allah ya shirya kana na miji baka son wahala. Bai ce komai ba ya koma ya dauko kayan dake ɗakin Ammie daman ta ce zai kai anjima kawai zai haɗa su tafi tare. Ya fito ya tada motar ya kalleta tare da girgiza kai ta ce Me kuma?. "Ba komai, nima daman ina son zuwa gidan Ayshe" To sai muje ai. Ya ɗan juyo ya kalleta itama ta ɗago ta kalleshi ya sakar mata da murmushi ya ce "Kamar kina cikin damuwa, akwai abin da ya faru ne a wajen aiki?" Daram ƙirjinta ya buga da ta tuna da abin da ya faru da ita daren jiya. Bazata sanar dashi ba dan kuwa zai aikata mashi abin da ya taɓa aikatawa shekarun baya dan haka ta ce Ba komai, ciwon kai ne. Ya sauke numfashi ya ce Ciwon kai, ciwon kai always shine amsa, anyway bakomi. Sai da suka biya suka yi wa yaran siyayya sannan kai tsaye suka wuce gidan Ayshe....... Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 19 & 20 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* __________ Da ƙyar ta ke iya fidda numfashi tana sauke ajiyar zuciya on on zuciyarta na yi mata zafi sai gumi ta ke haɗawa, tana jin kanta na tsara mata zazzaɓi na neman rufe ta cikin ƙanƙanin lokaci. Ta juya tare da jan blanket ta rufe jikin ta tare da rumtse idanuwanta waɗanda suka kasa fidda kwallah sbd damuwa, a kullum sai tayi tunanin meyasa hakan ke faruwa cikin rayuwarta, yaushe zata ji ta cikin farin ciki kamar yanda kowa ke ji, yaushe iyayenta zasu daina faɗa a kanta, yaushe za a koma cikin farin ciki irin na rayuwar baya, yaushe, yaushe, yaushe?. Amma da ta tuna cewa ko wane bawa da irin ta sa jarrabawar sai taji sanyi cikin ranta, duk abin da ya yi farko yana da ƙarshe kuma duk tsanani yana tare da sauki kamar yadda bata taɓa zaton zata riski wannan lokacin ba haka bazata cire sammanin samun sauki nan gaba ba. "Hamrah" A hankali ta buɗe idanuwanta sbd jin muryar Ammar da ya ƙira sunanta, ta haɗiye damuwar ta tare da sauke numfashi ta fito da fuskar ta tare da ɗan kishingiɗe jikin bed ta ce Ammar, na yi tunanin ka kwanta ai, shiyasa nima na kwanta sbd gobe Monday kuma morning duty gareni. Ya sauke numfashi sosai ya ke kallonta, duk da tana ɓoye damuwarta kada ya gane amma tun shigowan shi ya riga da ya gane sannan yaji abin da iyayensu suke cewa, ko shi kanshi baya son irin yadda su keyi, sun daina jituwa da juna zaman lafiyar ma yanzu ba sosai suke yin ta ba, abin damuwar ma shine yanda Ammie ta ke ɗauka hot akan maganar, babban tashin hankalin shi shine tafiyar da zayyi ya bar Hamrah, yasan za tayi ta shiga damuwa gashi kuma zayyi nesa da ita babu mai kwantar mata da hankali. Ya sauke numfashi a hankali ya ce "Ban kwanta ba ina chatting ne muna online meeting, muna gamawa ne na ce bari nazo sbd ɗazu kin ce kina son magana dani" Ta kwakulo murmushi dole tare da cewa Ammar, shin menene laifina akan zaɓar Alhaji Sama'ila da nayi, meyasa ka ke ganin bai dace na zaɓe shi ba, shin akwai abin da ya faɗa maka ne?. Ajiyar zuciya ya sauke tare da kura mata idanuwa na wani lokaci yana jin tausayinta yasan tana yin wannan ne saboda ta sami kulawar Ammie ta samu ta sauko su koma daidai kamar yadda suke a cen baya har ake ƙiransu da ba a shiga sskaninsu sbd yadda suke shawara da juna koman Ammie Hamrah. Sai dai ya fi sha'awan ta aure saurayi ko da wanda ya ja shekaru ne amma Alhaji Sama'ila girma ya gama bayyana a gareshi yasan dududu ba zai ƙara shekaru goma kan nashi ba a duniya, a hankali ya yi magana cikin sanyin jiki "Hamrah, farin cikin mu shine kiyi aure, kema ki sami farin ciki kamar kowa, ba wai bamu son Alhaji Sama'ila bane a'a ba haka bane, kamar yadda Daddyn ya ce babu wanda yasan asalin shi, sannan ba a san sana'ar shi ba, ba zayyu a dauke ki a bashi ke ba, ba tare da anyi bincike akan shi ba, bai ce min komai ba sannan bai bani amsar tambayoyin da na yi mashi ba kawai ya girgiza kai ne wanda i don't know what that means shine na ji shakku akan shi, amma kuma in dai zai aure ki ya baki farin ciki muna maraba dashi" Ta sauke numfashi tare da tashi ta zauna ta naɗe ƙafafuwanta ta ce Ga dukkan alamu mutumin kirƙi ne, sannan in kayi duba da lokaci guda ya ce yana so na da aure hakan ya nuna kamilalle ne, sannan next time idan ya zo zan tambaye shi labarin shi kaga zamu sami duk amshoshin mu. Ya sauke numfashi ya ce "Allah shi kyauta, me ki ke so na kawo miki zan fita bakin hanya na dawo" Ta fahimci baya son maganar ne shine ya sauyata, ta ce Ni bana ma sha'awar komi duk abin da ka siyo ka kawo ina so sai dai amma abin ya zamto mara nawi. "To shikenan sai na dawo" Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi ta shiga zancen zuci daman haka sha'anin aure yake da zaran an fara zancen yin sa sai an sami tangarɗa amma baza ta bari wannan damar ta wuce ta ba ta ɗau tsawon shekaru tana jiran irinta, ai kuma duk wanda ya ce yana son ka kuma yana son haɗa zuri'a da kai to ya fi wanda zai ce ba ya son ka..... Ringing wayar ta tayi tana duba ba sai ganin Abuja ta yi yana ƙira ta ɗauka tare da sallama ya amsa tare da cewa "Likita bokan turai in ban nemeki ba ke baza ki neme ni ba, shariyar ta yi yawa" Ta yi murmushi ta ce Yau na wuni da ɓaki shiyasa ban samu sukuni ba sai yanzu shi ɗin ma kwanciya na yi sbd na samu na miƙe. Ya sauke numfashi ya ce "Ni dai nasan har yanzu ban sami gurɓi cikin zuciyar ki ba" Murmushi tayi ta ce A'a ba haka bane, na faɗa maka uzuri na. "To shikenan ranki shidaɗe, da fatan kina lafiya?" Alhamdulillah. Suna fira Ammar ya shigo jin da Alhaji Sama'ila ta ke wayar yasa ya ajiye mata ledar bai ko waiwayo ya sake kallon inda ta ke ba ya fice abinshi, ta yi murmushi tare da girgiza kanta suka ci gaba da firar su, yake sanar da ita gobe zai wuce Abuja zayyi kwana biyu kafin nan ya dawo ta ce dashi Allah ya kiyaye hanya su kayi sallama ta buɗe ledar ta ci gashashiyar kazar da ya siyo da fresh milk sannan ta kwanta. Tun da ta farka sallah asubah bata koma ba ta hau shirin tafiya wajen aiki tea da bread tasha ta ɗau jakarta ta fito ɗakin Ammar ta yi nocking jin shuru yasa ta turo kofar ta shiga sai ganin shi ta yi yana Sallah ta duba a gogo a lokacin 7:00am, ya sallame tare da juyowa ya kalleta tana zaune bakin bed ya ƙarashe addu'o'in shi sannan ya ce "Good morning likita?" Ta sauke numfashi ta ce Ammar yaushe ka daina sallah asubah kasan kuwa karfe nawa yanzu?. Ya sauke numfashi tare da cewa "Makara na yi jiya ban kwanta da wuri ba" Ammar ai ya kamata ka sanya Alarm, Kai ba yaro bane da za kayi ta bacci sai lokacin da kaga dama ka tashi ka idar, sannan ko yaro ma an fi son ya dinga yinta har ta shige jikin shi amma gaskiya ka gyara hakan ba daidai bane. Ya sauke numfashi ya tashi ya iso kusa da ita ya zauna ya ce "Na gaidake baki amsa ba" Lafiya ta kalau, Please ka dinga tashi da asubah kana sallah akan lokaci. "Na faɗa miki makara nayi amma zan gyara" Wannan ba hujja ba ce kace ka makara amma tunda kace zaka gyara that's good. Sallar asubah itace mafi alkhairi fiye da Bacci, ka rage bacci don ka ribanta da goben ka. Bacci amsawar zuciya ne ita Kuwa sallah amsawar kiran Ubangiji ne. Shi bacci mutuwa ne ita kuwa sallah rayuwa ce. Shi bacci hutu ne na gangar jiki sallah kuwa hutu ne na ruhi. Bacci da mumini da kafiri duk suna yinsa ita kuwa sallah musulman kwarai sune kadai ke yinta. Masu tashi lokacin ketowar alfijiri sun rabauta, fuskarsu kuma ta haskaka, goshinsu kuma yayi Haske da Kyalli, lokacinsu kuma yayi albarka, idan kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka roki ALLAH Ya saka Cikin su. Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya da abinda ke cikin ta. Ita sallar asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'iku masu aikin safe duka suna halartar ta, kasani duk wanda ya rayu akan wani aiki toh akansa zai mutu, wanda ya Mutu kan wani aiki kuma akansa za'a tashe shi. Jikin Ammar ya yi matukar sanyi, ko shi bai ji daɗi ba da ya tashi a makare amma ba ɗabi'ar shi bace ya ce "Na gode da tunatar dani da ki kayi, har kin shirya ko?" Eh bari ma na wuce kada na makara. Ya miƙe tare da yi mata rakiya suka fito, ya koma ita ta wuce ɗakin Ammie ta same su da Daddy suna faisa sannan ta fito ta wuce wajen aiki, baya ta ɗan a daidaita ya sauke ne tashigo ganin yanda ake kai kawo yasa ta tabbatar da sun ji labarin OG zai shigo tayi murmushi a ranta ta ce duniya ba gaskiya ba zasu yi aiki sakanin su da Allah ba sai dai suyi dan mutum, Allah shi kyauta. Ta buɗe office ta shige tare da fito da duk wasu abubuwan da zata buƙata tana cikin hakan ne Dr Mahmoud ya shigo. Ɗauko white coat nata ta yi tare da sanya white eyes glass ta ɗau wayar ta tare da sanyata cikin aljuhun rigar tana ƙoƙarin fitowa ya yi saurin riƙe ƙofar ya hanata fitowa ya ce "Amma ai kin ga shigowa ta shine zaki fice wannan bai dace ba" Ɗagowa ta yi tana kallon shi da fararen idanuwanta ta ɗan waro su ta ce Dr Mahmoud i think you have nothing to do, so bani hanya na je na duba patients ɗina lokaci na tafiya. Ya sauke numfashi yana kallon pretty face nata ya ce "Yaushe zaki daina min wulakanci, sbd kinga na damu a kanki ne ki ke min haka, to ki sani badan MD ya haɗa mu muyi aiki tare ba, ba ki isa ki wulakanta ni ba" Murmushi Hamrah tayi ta ce I need to go. Ya ɗan matsa ta buɗe kofar ta fito tare da ce mashi Zan kulle ƙofar. Ya fito ta rufe ta kama hanyar tafiya general ward shi kuma yana biye da ita har suka shigo tare suka duba so ya rigata barin wajen ita kam ta jima sannan ta dawo, zata shige ciki ne taji muryar MD ya kirata ta shigo tare da gaidashi ya amsa ya ce "OG zai shigo nan da 30 minutes so, you should get ready with the all records, if possible ma i have to see them before ki kai mashi ko ki faɗa min me da me yake buƙatar" Ta sauke numfashi a ranta ta ce, tasan wannan abin ne ya kai Dr Mahmoud office nata ɗazu ganin basu sami wani kwakkwaran dalili bane yasa ya yi kiranta da kanshi ta ce Sir, akwai abubuwan da zan sake dubawa bari na tafi. Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata ya ce "In kin kammala ki kawo na gani" To. Ta faɗa sannan ta dawo office nata, a nutse ta fiddo su ta shiga dubasu kamar yadda ta keyi nan ta shirya komai ta kammala tsarawa ta ji ana nocking ta bada izinin shigowa Dr Laraba ce ta ke shaida mata OG ya iso an hallara a ɗakin meeting ta fito in ji MD, ta ce da ita tana fitowa. A nutse ta fito ganin office na Dr Mahmoud da MD a kulle yasa ta sauke numfashi tare da furtawa Thank God. Ta iso a lokacin OG ma ya shigo ana gaisawa ta gaida shi, sanye yake da suit baƙi koman shi baki hatta eyes glass dake idanun shi ma baƙi ne, yana da haske ba cen ba ya cire glass ɗin ya ce "Dr Hamrah lafiya kalau ya kokari" Alhamdulillah sir. Ta ajiye mashi komai ta ɗan kalli MD shima ita yake kallo sabar haushi kamar ya shaƙo ta badan OG ne ya ƙirashi ba da ko sai ya karɓi document ɗin ya sauya komai ya tafi daidai da na office nashi kada ya banbanta. Ya sakar mata da harara ta yi kamar bata ganshi ba ta yi murmushi ƙasa² ta ce cikin ranta da saura jira akwai wasan da baka san dashi ba yanzu za a fara buga shi..... "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yake bamu ikon akan komai, ina mai farin ciki da jin daɗin yanda ku ke gudanar da aikace-aikace a wannan asibitin kuma ina jin yadda jami'a ke yaba ku, Alhamdulillah, musamman ma Dr Hamrah tana na mijin ƙoƙari kuma ina alfahari da ita" Cewa OG sai da ya kai aya ya yi shuru yana duban su sannan ya kai hannu ya fara duba document dake gaban shi a nutsu ya ke dubawa sai da yazo kan list na staff da partner su sai yaga na list da kuma office dake cikin document da MD ya bashi daban ya ke da wanda ya ke wajen Dr Hamrah, cike da mamaki ya ce "Ya naga banbanci sakanin list of staff's and there duty's partners ya banbanta me yasa haka?" Saurin miƙewa MD ya yi ya ce "With do respect sir, ni ne na sauya sbd ci gaban wannan Hospital ɗin naga ƙanzawa shine zaifi kuma zai kawo cigaba" Sauke numfashi OG ya yi ya ce "To ya aka yi yasha banban da na Dr Hamrah, sannan kuma meyasa ka yanke hukunci ba tare da neman izinina ba" Nan wuta ta ɗaukewa MD ya juyo da jajayen idanuwan sa yana kallon Hamrah ganin haka ta ɗauke kai kamar bata san yana yi ba ya sauke numfashi tare da cewa in kin san wata baki san wata ba, cikin ranshi ya faɗa a fili ya ce "Eh na manta ne banyi comparing da nata ba but all this ya faru ne sbd rashin bada haɗin kai da bata yi ba" Sosai OG ya ke kallon shi sannan ya ce "For what reasons ta ki bada haɗin kai?" Kai tsaye MD ya ce "I don't know kawai bata girmama ni ne" Murmushi Hamrah ta yi bata ce komai ba sai da OG ya kalleta ya ce "Hamrah meyake faruwa ne, shin gaskiya ne MD ya ke faɗi?" Cikin girmamawa ta ce Eh sir amma ina da dalilina na yin hakan. Ya kalleta tare da cewa "Menene dalilin?" Yana da ikon yanke hukunci amma kuma duk da haka ya kamata ya shawarce ni wajen kanza min partner kawai kwasam sai dai jin na yi ya ɗauke Dr Aliyu ya kaishi bangaren yara, sannan kuma ya sauke mishi albashin sa, a kullum neman ci gaba ake ba wai baya ba sannan hakan da ya yi takura ce da kuma jefa shi cikin damuwa shine naga hakan bai dace ba wannan ne dalilin da yasa naƙi bashi goyon baya. Shiru wajen ya yi ya kalli MD tare da cewa "Haka ne abin da ta faɗa?" Ya tsosa keyarsa ya ce "Haka ne amma..... "Ya isa haka, na yi cansel na wannan transfer from office to another office dan haka kowa ya koma nashi office ɗin na da sai mun zauna zamu sauya" Yana gama faɗin haka ya fice, MD ya daki teburin dake wajen yana huce wai always Hamrah, Hamrah, Hamrah. Ya fice a wajen ya wuce office nashi yana huce Dr Mahmoud ya shigo amma ya ɗaga masa hannu alamun ya fita, ya fice ya ci gaba da tunani zuci ya akayi ya faɗi a wannan lokacin amma yasan yanda zai bollowa al'amarin. Hamrah cikin farin ciki ta dawo office nata, ko ba komai Dr Aliyu zai dawo office nashi ya ci gaba da aikin shi, tana so ta wanke kanta daga ganin cewa da ita aka haɗa baki aka cire shi daga cikin office nashi.... Turo ƙofar Dr Aliyu ya yi ya shigo cikin sanyin jiki, bata ɗago ba jin turo ƙofar yasa ta ke tunanin Dr Mahmoud ne ko MD har yanzu idanuwanta a lumshe suke .... "Dr Hamrah" Jin muryar Dr Aliyu ne yasa ta buɗe idanuwanta ta kalle shi, bata yi mamakin zuwan shi ba dan tasan zaizo amma kuma bata yi farin cikin ganin shi ba, har ya ƙaraso kusa da teburin ya zauna tare da cewa "Dr Hamrah.... Dr Aliyu i don't need any word from you, please step out. Sauke numfashi ya yi kamar zayyi kuka yana bukatar ta saurare shi amma yasan abu ne mai wuya sbd irin ci mata mutunci da ya yi, cikin sanyin jiki ya miƙe a hankali ya fice da nufin da ta sauko zai sake dawowa. (Ji na da ku kayi shuru 2days rasuwa aka min naje na dawo. Masu addu'oi da kuma waɗanda suka ƙirani da waɗanda su ka yimin magana duk ina godiya, Allah ya bada ladan ta'aziya) littafin MUJARRABI labari ne mai ɗauke da sakonni daban daban ta ko wanne fanni kuma tafiya ce mai ɗan tsawo sai dai ina tabbatar muku cewa baza kuyi nadamar bibiyar labarin ba. Har yanzu muna cikin shinfiɗa asalin labarin na nan zuwa. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 19 & 20 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* __________ Da ƙyar ta ke iya fidda numfashi tana sauke ajiyar zuciya on on zuciyarta na yi mata zafi sai gumi ta ke haɗawa, tana jin kanta na tsara mata zazzaɓi na neman rufe ta cikin ƙanƙanin lokaci. Ta juya tare da jan blanket ta rufe jikin ta tare da rumtse idanuwanta waɗanda suka kasa fidda kwallah sbd damuwa, a kullum sai tayi tunanin meyasa hakan ke faruwa cikin rayuwarta, yaushe zata ji ta cikin farin ciki kamar yanda kowa ke ji, yaushe iyayenta zasu daina faɗa a kanta, yaushe za a koma cikin farin ciki irin na rayuwar baya, yaushe, yaushe, yaushe?. Amma da ta tuna cewa ko wane bawa da irin ta sa jarrabawar sai taji sanyi cikin ranta, duk abin da ya yi farko yana da ƙarshe kuma duk tsanani yana tare da sauki kamar yadda bata taɓa zaton zata riski wannan lokacin ba haka bazata cire sammanin samun sauki nan gaba ba. "Hamrah" A hankali ta buɗe idanuwanta sbd jin muryar Ammar da ya ƙira sunanta, ta haɗiye damuwar ta tare da sauke numfashi ta fito da fuskar ta tare da ɗan kishingiɗe jikin bed ta ce Ammar, na yi tunanin ka kwanta ai, shiyasa nima na kwanta sbd gobe Monday kuma morning duty gareni. Ya sauke numfashi sosai ya ke kallonta, duk da tana ɓoye damuwarta kada ya gane amma tun shigowan shi ya riga da ya gane sannan yaji abin da iyayensu suke cewa, ko shi kanshi baya son irin yadda su keyi, sun daina jituwa da juna zaman lafiyar ma yanzu ba sosai suke yin ta ba, abin damuwar ma shine yanda Ammie ta ke ɗauka hot akan maganar, babban tashin hankalin shi shine tafiyar da zayyi ya bar Hamrah, yasan za tayi ta shiga damuwa gashi kuma zayyi nesa da ita babu mai kwantar mata da hankali. Ya sauke numfashi a hankali ya ce "Ban kwanta ba ina chatting ne muna online meeting, muna gamawa ne na ce bari nazo sbd ɗazu kin ce kina son magana dani" Ta kwakulo murmushi dole tare da cewa Ammar, shin menene laifina akan zaɓar Alhaji Sama'ila da nayi, meyasa ka ke ganin bai dace na zaɓe shi ba, shin akwai abin da ya faɗa maka ne?. Ajiyar zuciya ya sauke tare da kura mata idanuwa na wani lokaci yana jin tausayinta yasan tana yin wannan ne saboda ta sami kulawar Ammie ta samu ta sauko su koma daidai kamar yadda suke a cen baya har ake ƙiransu da ba a shiga sskaninsu sbd yadda suke shawara da juna koman Ammie Hamrah. Sai dai ya fi sha'awan ta aure saurayi ko da wanda ya ja shekaru ne amma Alhaji Sama'ila girma ya gama bayyana a gareshi yasan dududu ba zai ƙara shekaru goma kan nashi ba a duniya, a hankali ya yi magana cikin sanyin jiki "Hamrah, farin cikin mu shine kiyi aure, kema ki sami farin ciki kamar kowa, ba wai bamu son Alhaji Sama'ila bane a'a ba haka bane, kamar yadda Daddyn ya ce babu wanda yasan asalin shi, sannan ba a san sana'ar shi ba, ba zayyu a dauke ki a bashi ke ba, ba tare da anyi bincike akan shi ba, bai ce min komai ba sannan bai bani amsar tambayoyin da na yi mashi ba kawai ya girgiza kai ne wanda i don't know what that means shine na ji shakku akan shi, amma kuma in dai zai aure ki ya baki farin ciki muna maraba dashi" Ta sauke numfashi tare da tashi ta zauna ta naɗe ƙafafuwanta ta ce Ga dukkan alamu mutumin kirƙi ne, sannan in kayi duba da lokaci guda ya ce yana so na da aure hakan ya nuna kamilalle ne, sannan next time idan ya zo zan tambaye shi labarin shi kaga zamu sami duk amshoshin mu. Ya sauke numfashi ya ce "Allah shi kyauta, me ki ke so na kawo miki zan fita bakin hanya na dawo" Ta fahimci baya son maganar ne shine ya sauyata, ta ce Ni bana ma sha'awar komi duk abin da ka siyo ka kawo ina so sai dai amma abin ya zamto mara nawi. "To shikenan sai na dawo" Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi ta shiga zancen zuci daman haka sha'anin aure yake da zaran an fara zancen yin sa sai an sami tangarɗa amma baza ta bari wannan damar ta wuce ta ba ta ɗau tsawon shekaru tana jiran irinta, ai kuma duk wanda ya ce yana son ka kuma yana son haɗa zuri'a da kai to ya fi wanda zai ce ba ya son ka..... Ringing wayar ta tayi tana duba ba sai ganin Abuja ta yi yana ƙira ta ɗauka tare da sallama ya amsa tare da cewa "Likita bokan turai in ban nemeki ba ke baza ki neme ni ba, shariyar ta yi yawa" Ta yi murmushi ta ce Yau na wuni da ɓaki shiyasa ban samu sukuni ba sai yanzu shi ɗin ma kwanciya na yi sbd na samu na miƙe. Ya sauke numfashi ya ce "Ni dai nasan har yanzu ban sami gurɓi cikin zuciyar ki ba" Murmushi tayi ta ce A'a ba haka bane, na faɗa maka uzuri na. "To shikenan ranki shidaɗe, da fatan kina lafiya?" Alhamdulillah. Suna fira Ammar ya shigo jin da Alhaji Sama'ila ta ke wayar yasa ya ajiye mata ledar bai ko waiwayo ya sake kallon inda ta ke ba ya fice abinshi, ta yi murmushi tare da girgiza kanta suka ci gaba da firar su, yake sanar da ita gobe zai wuce Abuja zayyi kwana biyu kafin nan ya dawo ta ce dashi Allah ya kiyaye hanya su kayi sallama ta buɗe ledar ta ci gashashiyar kazar da ya siyo da fresh milk sannan ta kwanta. Tun da ta farka sallah asubah bata koma ba ta hau shirin tafiya wajen aiki tea da bread tasha ta ɗau jakarta ta fito ɗakin Ammar ta yi nocking jin shuru yasa ta turo kofar ta shiga sai ganin shi ta yi yana Sallah ta duba a gogo a lokacin 7:00am, ya sallame tare da juyowa ya kalleta tana zaune bakin bed ya ƙarashe addu'o'in shi sannan ya ce "Good morning likita?" Ta sauke numfashi ta ce Ammar yaushe ka daina sallah asubah kasan kuwa karfe nawa yanzu?. Ya sauke numfashi tare da cewa "Makara na yi jiya ban kwanta da wuri ba" Ammar ai ya kamata ka sanya Alarm, Kai ba yaro bane da za kayi ta bacci sai lokacin da kaga dama ka tashi ka idar, sannan ko yaro ma an fi son ya dinga yinta har ta shige jikin shi amma gaskiya ka gyara hakan ba daidai bane. Ya sauke numfashi ya tashi ya iso kusa da ita ya zauna ya ce "Na gaidake baki amsa ba" Lafiya ta kalau, Please ka dinga tashi da asubah kana sallah akan lokaci. "Na faɗa miki makara nayi amma zan gyara" Wannan ba hujja ba ce kace ka makara amma tunda kace zaka gyara that's good. Sallar asubah itace mafi alkhairi fiye da Bacci, ka rage bacci don ka ribanta da goben ka. Bacci amsawar zuciya ne ita Kuwa sallah amsawar kiran Ubangiji ne. Shi bacci mutuwa ne ita kuwa sallah rayuwa ce. Shi bacci hutu ne na gangar jiki sallah kuwa hutu ne na ruhi. Bacci da mumini da kafiri duk suna yinsa ita kuwa sallah musulman kwarai sune kadai ke yinta. Masu tashi lokacin ketowar alfijiri sun rabauta, fuskarsu kuma ta haskaka, goshinsu kuma yayi Haske da Kyalli, lokacinsu kuma yayi albarka, idan kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka roki ALLAH Ya saka Cikin su. Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya da abinda ke cikin ta. Ita sallar asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'iku masu aikin safe duka suna halartar ta, kasani duk wanda ya rayu akan wani aiki toh akansa zai mutu, wanda ya Mutu kan wani aiki kuma akansa za'a tashe shi. Jikin Ammar ya yi matukar sanyi, ko shi bai ji daɗi ba da ya tashi a makare amma ba ɗabi'ar shi bace ya ce "Na gode da tunatar dani da ki kayi, har kin shirya ko?" Eh bari ma na wuce kada na makara. Ya miƙe tare da yi mata rakiya suka fito, ya koma ita ta wuce ɗakin Ammie ta same su da Daddy suna faisa sannan ta fito ta wuce wajen aiki, baya ta ɗan a daidaita ya sauke ne tashigo ganin yanda ake kai kawo yasa ta tabbatar da sun ji labarin OG zai shigo tayi murmushi a ranta ta ce duniya ba gaskiya ba zasu yi aiki sakanin su da Allah ba sai dai suyi dan mutum, Allah shi kyauta. Ta buɗe office ta shige tare da fito da duk wasu abubuwan da zata buƙata tana cikin hakan ne Dr Mahmoud ya shigo. Ɗauko white coat nata ta yi tare da sanya white eyes glass ta ɗau wayar ta tare da sanyata cikin aljuhun rigar tana ƙoƙarin fitowa ya yi saurin riƙe ƙofar ya hanata fitowa ya ce "Amma ai kin ga shigowa ta shine zaki fice wannan bai dace ba" Ɗagowa ta yi tana kallon shi da fararen idanuwanta ta ɗan waro su ta ce Dr Mahmoud i think you have nothing to do, so bani hanya na je na duba patients ɗina lokaci na tafiya. Ya sauke numfashi yana kallon pretty face nata ya ce "Yaushe zaki daina min wulakanci, sbd kinga na damu a kanki ne ki ke min haka, to ki sani badan MD ya haɗa mu muyi aiki tare ba, ba ki isa ki wulakanta ni ba" Murmushi Hamrah tayi ta ce I need to go. Ya ɗan matsa ta buɗe kofar ta fito tare da ce mashi Zan kulle ƙofar. Ya fito ta rufe ta kama hanyar tafiya general ward shi kuma yana biye da ita har suka shigo tare suka duba so ya rigata barin wajen ita kam ta jima sannan ta dawo, zata shige ciki ne taji muryar MD ya kirata ta shigo tare da gaidashi ya amsa ya ce "OG zai shigo nan da 30 minutes so, you should get ready with the all records, if possible ma i have to see them before ki kai mashi ko ki faɗa min me da me yake buƙatar" Ta sauke numfashi a ranta ta ce, tasan wannan abin ne ya kai Dr Mahmoud office nata ɗazu ganin basu sami wani kwakkwaran dalili bane yasa ya yi kiranta da kanshi ta ce Sir, akwai abubuwan da zan sake dubawa bari na tafi. Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata ya ce "In kin kammala ki kawo na gani" To. Ta faɗa sannan ta dawo office nata, a nutse ta fiddo su ta shiga dubasu kamar yadda ta keyi nan ta shirya komai ta kammala tsarawa ta ji ana nocking ta bada izinin shigowa Dr Laraba ce ta ke shaida mata OG ya iso an hallara a ɗakin meeting ta fito in ji MD, ta ce da ita tana fitowa. A nutse ta fito ganin office na Dr Mahmoud da MD a kulle yasa ta sauke numfashi tare da furtawa Thank God. Ta iso a lokacin OG ma ya shigo ana gaisawa ta gaida shi, sanye yake da suit baƙi koman shi baki hatta eyes glass dake idanun shi ma baƙi ne, yana da haske ba cen ba ya cire glass ɗin ya ce "Dr Hamrah lafiya kalau ya kokari" Alhamdulillah sir. Ta ajiye mashi komai ta ɗan kalli MD shima ita yake kallo sabar haushi kamar ya shaƙo ta badan OG ne ya ƙirashi ba da ko sai ya karɓi document ɗin ya sauya komai ya tafi daidai da na office nashi kada ya banbanta. Ya sakar mata da harara ta yi kamar bata ganshi ba ta yi murmushi ƙasa² ta ce cikin ranta da saura jira akwai wasan da baka san dashi ba yanzu za a fara buga shi..... "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yake bamu ikon akan komai, ina mai farin ciki da jin daɗin yanda ku ke gudanar da aikace-aikace a wannan asibitin kuma ina jin yadda jami'a ke yaba ku, Alhamdulillah, musamman ma Dr Hamrah tana na mijin ƙoƙari kuma ina alfahari da ita" Cewa OG sai da ya kai aya ya yi shuru yana duban su sannan ya kai hannu ya fara duba document dake gaban shi a nutsu ya ke dubawa sai da yazo kan list na staff da partner su sai yaga na list da kuma office dake cikin document da MD ya bashi daban ya ke da wanda ya ke wajen Dr Hamrah, cike da mamaki ya ce "Ya naga banbanci sakanin list of staff's and there duty's partners ya banbanta me yasa haka?" Saurin miƙewa MD ya yi ya ce "With do respect sir, ni ne na sauya sbd ci gaban wannan Hospital ɗin naga ƙanzawa shine zaifi kuma zai kawo cigaba" Sauke numfashi OG ya yi ya ce "To ya aka yi yasha banban da na Dr Hamrah, sannan kuma meyasa ka yanke hukunci ba tare da neman izinina ba" Nan wuta ta ɗaukewa MD ya juyo da jajayen idanuwan sa yana kallon Hamrah ganin haka ta ɗauke kai kamar bata san yana yi ba ya sauke numfashi tare da cewa in kin san wata baki san wata ba, cikin ranshi ya faɗa a fili ya ce "Eh na manta ne banyi comparing da nata ba but all this ya faru ne sbd rashin bada haɗin kai da bata yi ba" Sosai OG ya ke kallon shi sannan ya ce "For what reasons ta ki bada haɗin kai?" Kai tsaye MD ya ce "I don't know kawai bata girmama ni ne" Murmushi Hamrah ta yi bata ce komai ba sai da OG ya kalleta ya ce "Hamrah meyake faruwa ne, shin gaskiya ne MD ya ke faɗi?" Cikin girmamawa ta ce Eh sir amma ina da dalilina na yin hakan. Ya kalleta tare da cewa "Menene dalilin?" Yana da ikon yanke hukunci amma kuma duk da haka ya kamata ya shawarce ni wajen kanza min partner kawai kwasam sai dai jin na yi ya ɗauke Dr Aliyu ya kaishi bangaren yara, sannan kuma ya sauke mishi albashin sa, a kullum neman ci gaba ake ba wai baya ba sannan hakan da ya yi takura ce da kuma jefa shi cikin damuwa shine naga hakan bai dace ba wannan ne dalilin da yasa naƙi bashi goyon baya. Shiru wajen ya yi ya kalli MD tare da cewa "Haka ne abin da ta faɗa?" Ya tsosa keyarsa ya ce "Haka ne amma..... "Ya isa haka, na yi cansel na wannan transfer from office to another office dan haka kowa ya koma nashi office ɗin na da sai mun zauna zamu sauya" Yana gama faɗin haka ya fice, MD ya daki teburin dake wajen yana huce wai always Hamrah, Hamrah, Hamrah. Ya fice a wajen ya wuce office nashi yana huce Dr Mahmoud ya shigo amma ya ɗaga masa hannu alamun ya fita, ya fice ya ci gaba da tunani zuci ya akayi ya faɗi a wannan lokacin amma yasan yanda zai bollowa al'amarin. Hamrah cikin farin ciki ta dawo office nata, ko ba komai Dr Aliyu zai dawo office nashi ya ci gaba da aikin shi, tana so ta wanke kanta daga ganin cewa da ita aka haɗa baki aka cire shi daga cikin office nashi.... Turo ƙofar Dr Aliyu ya yi ya shigo cikin sanyin jiki, bata ɗago ba jin turo ƙofar yasa ta ke tunanin Dr Mahmoud ne ko MD har yanzu idanuwanta a lumshe suke .... "Dr Hamrah" Jin muryar Dr Aliyu ne yasa ta buɗe idanuwanta ta kalle shi, bata yi mamakin zuwan shi ba dan tasan zaizo amma kuma bata yi farin cikin ganin shi ba, har ya ƙaraso kusa da teburin ya zauna tare da cewa "Dr Hamrah.... Dr Aliyu i don't need any word from you, please step out. Sauke numfashi ya yi kamar zayyi kuka yana bukatar ta saurare shi amma yasan abu ne mai wuya sbd irin ci mata mutunci da ya yi, cikin sanyin jiki ya miƙe a hankali ya fice da nufin da ta sauko zai sake dawowa. (Ji na da ku kayi shuru 2days rasuwa aka min naje na dawo. Masu addu'oi da kuma waɗanda suka ƙirani da waɗanda su ka yimin magana duk ina godiya, Allah ya bada ladan ta'aziya) littafin MUJARRABI labari ne mai ɗauke da sakonni daban daban ta ko wanne fanni kuma tafiya ce mai ɗan tsawo sai dai ina tabbatar muku cewa baza kuyi nadamar bibiyar labarin ba. Har yanzu muna cikin shinfiɗa asalin labarin na nan zuwa. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 25 & 26 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* ________Ganin ya rufe min baki yasa na waro idanuwana ina kallon sa sbd farga da tashin hankali cikin kankani lokaci na haɗa uban gumi a lokacin da na yi la'akari da ganin babu kaya a jikin shi sai gajeren wondo, ya sake janyo ni jikin shi na haɗe da ƙaton tumbi shi ya yi magana cikin dashesheyar murya tare da zaro min idanuwan shi alamun gargaɗi da kuma tsoratarwa ya ce "Kada ki kuskura kimin gardama dan za ki sha baƙar wahala kuma ba kyaleki zanyi ba, dan haka is better for to accept me for the hours, bazamu jima ba amma kin kin bini yadda na ke so in kuma ba haka ba zan aikata miki abin da har ki mutu ba zaki dawo daidai ba" Zuciyata taci gaba da bugawa na tsorata at the time na saduda dan na sadaukar babu mai ceto na a wancan ranar, jikina na rawa, sai zazzaro idanuwana nake sbd rufemin baki da ya yi babu yadda zanyi nayi magana balle kuma nayi mashi magiya, ganin babu sarki sai Allah na soma karanta duk adduar da tazo cikin zuciyata, ina neman tsari daga azzalumin mijin mahaifiyata..... Fincikoni ya yi ya tadani zaune tare da yaga min rigar dake jikina daman doguwar riga ce, ganin haka yasa na kurma ihu ina rokon sa da ya kyaleni amma kuma sai ya yi kamar baijiba ya hankaɗe ni na faɗi ta baya kan bed ɗin ya danneni yana huce ya ce "Kinci sa'a kina period ni kuma ina ƙyanƙyamin mace wacce ta ke cikin al'ada, amma ba komai zamu gamu nan da kwanaki" Ya miƙe ya fice, na sauke numfashi na sake fashewa da kuka cikin ƙuna da takaici ace mijin mahaifiyata yaga jikina, wannan wane irin ƙazamin mutum ne mara imani da tsoron Ubangiji, sam ya manta da cewa akwai mutuwa. Na jima ina kuka sannan na miƙe na faɗa toilet na watsa ruwa na sauya kaya a daidai lokacin Mommy ta dawo gida, na fito palour duk na ka sa nutsuwa, ya fito ya tadda mu a zaune ya dubeni tare da cewa na kawo mashi tea na saka suger kaɗan a ciki. Da farko na ƙi amma kuma ganin Mommy ta bata fuska sbd ganin naƙi tashi yasa na miƙe na wuce kitchen na haɗa, tun daga wannan ranar ya sanya min ido duk motsina a kan idanuwan shi ko me yake dubawa oho, sai dai kuma indai ya aike ni ɗakinshi bana zuwa, da ya fuskanci hakan shine ya ƙirƙiro cewa yana meeting a guest House nashi dan haka Mommy ta dinga aika mashi abinci, a tunanin sa ni zata dinga aika amma kuma sai yaga driver ne yake kaiwa, ranan ya yi waya akan ta turoni da kulolin abincin akan na zanyi serving baƙin, da farko naƙi amma ganin Mommy ta ɓata fuska yasa nabi driver na tafi, a lokacin da muka iso sai ya sallame driver ya rage daga cikin sai shi, rarrabe idanuwa nakeyi ko zanga baƙin amma kuma babu kowa, shuru banji motsin shi ba na soma tafiya, na iso kofar palour na murɗa handle door amma sai najisa gam a rufe, nayi² na buɗe yaƙi sai naji motsin fitowa na juya muka haɗa 4eyes da da daddy ɗaure yake da towel a kugun shi, cikin tsoro da firgice na fiddo ita waje ganin yana yimin murmushin mugunta, a tsorace na ci gaba da murɗa handle door ko zai buɗe dan na fahimci plan ya hada amma yaƙi, cikin sauri ya finciko ni na faɗai kasan tyles na buga kaina nan ta ke ya fashe bai ko tausaya min ba ya janyoni a hakan ina zubda jini yana jana har ta kusa ƙofar ɗakin shi muka jiyo an danna door bell, cike da mamaki yake dubana ina cikin mawuyacin hali bazan iya tashi ba balle kuma nayi magana, ya wuce baƙin ƙofar ya leƙa ta maleƙa ganin wacce ya gano ne yasa ya yo kaina a guje cikin tashin hankali ya yi cikin ɗakinshi tare da ɗauko wani kyalle ya ɗaure min bakina baibi ta jinin dake malale kan fuskata ba ya buɗe ɗan wani karamin ƙofar ya sakani cikin sannan ya wrgani ya fice bayan ya ɗaure min hannayena, ina jin motsin shigewar sa ɗakinsa da kuma goge inda jinin ya ɓata, sannan ya buɗe ƙofar palour sai jin muryar Mommy nayi tana "Ikon Allah, ya naga gidan shiru ina ɓakin ne?" Da ƙyar na miƙe ina bin jikin garu na leƙa ta wani rami ina hango su, gani nayi ya tsosa keyarsa ya ce "Ai cewa su kayi sai yamma zasu iso" "To ina kuma Shatu tayi gashi bata nan ɗin ma?" "Ai bai jima ba ta tafi gida" "No driver kaɗai na gani na tambaye shi yace ya barota anan, to daman miyar kuɓewar ce ta tuwan shinkafar suka manta shine na fito dashi daman unguwa zan wuce" "Ai Shatu bai jima ba ta fice, nayi mamaki ma da baku haɗu ba" "To daman wucewa zanyi ga miyar nan" Ta ajiye ta juya da niyyar tafiya kuma ta tsaya tare da cewa "Jini........ Ringing na wayar Hamrah ce ta katse labarin da Shatu ke bata, ta kalleta tare dayi mata alamun bari na ɗaga, Daddyn su ne ta ɗauka cikin girmamawa ta gaida shi ya amsa yake tambayar ta, ya su kayi bikin, ta amsa da komai lafiya sannan su kayi sallama, ta kalli Shatu dake zaune dirsham kan carpet sai a wannan lokacin tayi la'akari da ciwon dake goshinta ta sauke numfashi tare da riƙe hannun Shatu ta ce So sorry bestie ashe kina cikin mawuyacin hali banne meki ba, meyafaru bayan Mommyn ki ta kalli jini?. Sauke numfashi Shatu tayi tare da share hawayen dake kan fuskar zatayi magana sai suka jiyo an turo ƙofa an shigo, Zeenat ce suka gaisa ta ce "Yaya Hamrah dangin mijin Ayshe sun shigo injita wai ki tarɓesu" Ajiyar zuciya Hamrah tayi tare da cewa Ina fitowa. Zeenat ta fice, Hamrah ta ce da Shatu Ƙawata ina zuwa ɗan bani muntuna bazan..... Wayar Shatu ta hau ruri ta ɗauka tare da cewa "An gama kenan zan iya tahowa?" Ba tare da Hamrah taji mai aka ce ba sai jin Shatu tayi ta ce "Ok on my way" Ta katse wayar tare da kallon Hamrah wacce itama ita ta ke kallo ta ce "Lawyer na ne ya ƙirani, zan tafi, zuwa gobe zan tafi gidan ku na ƙarashe miki labarin" Lawyer kuma?. Cewar Hamrah tana takewa Shatu baya suka fito ganin jama'ar dake palour yasa Shatu ficewa ba tare da sunyi sallama ba, Hamrah ta hau hidima dasu sai bayan la'asar ta huta shima a lokacin ake shirye shiryen shigowa da Amarya wajen uwar gida ta shige ɗaki ta kwanta sbd kanta dake tsara mata, lallai Shatu na cikin bala'i wannan wane irin tashin hankali ne, sai 4:30pm aka shigo da Amarya sukayi buɗan kai sannan aka watse. 8:00pm ta kammala shirin tafiya gida suka fito ita da Zeenat da kuma Maryama, Ayshe tayi² su sake kwana amma suka ce zasu tafi Hamrah kuma tana da morning duty gobe kuma Monday ne sai ta koma gida ta shirya Ba zayyu ta kwana anan ba da safe ta wuce, a haka ta hakura suka fito Maryama mijinta ne yazo ɗaukanta ita kuma Zeenat driver ya tura, Hamrah na ƙoƙarin fitowa bakin layin unguwar su Ayshe taga call na Abuja kamar bazata dauka ba ta ɗauka cikin sanyayyar tayi sallama ya amsa tare da cewa "Baby nah, kwatantamin unguwar da kike yanzu zan iso" Ta sauke numfashi tare da cewa Oh yanzu haka na fito zan koma gida. "Ba damuwa gani nama iso faɗa min layin?" Ta sanar dashi, aiko babu jimawa sai gashi ya iso da kansa yake tuka motar yayi parking a kusa da ita ya fito tare da sanya mata kayanta cikin boot na motar ya buɗe mata ta shige ta zauna, sanyi da ƙamshin dake cikin motar yasa ta lumshe idanuwanta tare da sauke numfashi, ya shigo ya tada motar suka fito daga layin sai dai kuma sai taga ya ɗau wata hanyar ba inda ta ke tunanin za taje ba, cikin sauri ta kallesa ya sakar mata da murmushi ya ce "Yi hakuri baby zan bada saƙo ne sai na maidaki gida" Ta ɗan sauke numfashi ba ta ce komai ba suka wuce Hotel ya yi parking a bakin gate ɗin ya kalleta tare da cewa "Baby nah yi min rakiya na bada saƙo sai mu fito" Kai tsaye ta ce A'a ka shiga ka fito. Ya yi murmushi ya ce "Kamar kina shakka a kaina, na yi tunanin yadda na yarda dake haka kema ki ka yarda dani, amma ba komai jirani na shiga na fito" Ya fice, tana zaune tana kallon yadda ake shigowa da ƴan mata da kuma fita dasu tana mamakin meyasa Alhaji Sama'ila ya sauka a hotel, kuma ace duk faɗin garin Maiduguri yarasa masauki.... "Sorry baby na jima ko?" Ta kalleshi bata ce komai ba har ya tada motar ya kawo ta ƙofar gida, zata fito ya yi saurin cewa "Baby nah kamar kina fushi dani, Please faɗamin laifina sai na bada hakuri" Tayi ajiyar zuciya tare da cewa Ina so muyi magana amma ba yanzu ba duk na gaji ina so na huta, sai dai ko gobe. Murmushi ya yi yana mamakin irin kaifin brain nata ya ce "Ba damuwa gobe zan zo da yamma ko kuma bayan ishai sai muyi magana" To Allah ya kaimu. "Amen" Ya faɗa tare da saukowa ya cire mata kayayyakin ta sai ganin Ammar ya yi ya zuba masa na mujiya ya ɗaga masa hannu tare da cewa "Ɗan saurayi taho mana ka taimakawa yayarka" Ammar ya cika ya yi tam kamar ya haɗiyi zuciya, kut lallai wannan mutumin..... Ammar zo ka taimaka min kaji. Ba zaiƙi taimakawa yayar shi ba ya iso ba tare da ya kalli inda Alhaji Sama'ila yake ba ya ja luggage na Hamrah ya yi ciki dashi, ta bi bayansa yana ganin ta shigo ya kalleta ya ce "Hamrah ki jawa wannan tsohon kunne ya fita cikin harkata ya kuma iya bakin sa dan kin bashi dama bazayyu ya yi duk yadda yake so ba damu" Murmushi tayi ta ce Ammar mijin da zan aurane so yana da daman ya aiki ƙanina sanan kaima ai ƙanine gareshi. "Kai ina wannan tsohon ya yi ɗa dani wallahi, kina gani duk ya kusa sheƙewa" Bata kulashi ba ta wuce ciki ta barshi yana ta huci, ɗakin Ammie ta shige ta ajiye mata sakon da Ayshe ta ce a bata, ta amsa tare da yi mata tambaya akan komai ya tafi daidai ta bata amsa da eh Alhamdulillah, sannan ta wuce ɗakinta tadda Ammar zaune ya kunna tv yana kallo ta ajiye jakar hannunta ta faɗa toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya ta zauna bakin bed ta kalli Ammar ta yi murmushi ta ce Ammar jibi warhaka baka nan. "In shaa Allahu, ina cen ABGANISTAN ina shan snow" Murmushi tayi ta ce Zanyi kewarka zan kasance ni kaɗai cikin gidan nan. Jikin shi ya yi sanyi ya juyo ya ce Ai zan dawo, kuma zamu dinga waya. Hakane kam. Sun jima suna fira ya tashi ta fice ita kuma ta kwanta bacci. Washegari tunda ta tashi ta shirya ta fice kada ta makara, ta iso a daidai lokacin ƴan night duty sun fara tafiya ta buɗe office nata ta shige ta shirya komanta ta sanya white coat nata da kuma white eyes glass nata tana ƙoƙarin fitowa Dr Aliyu ya shigo ya gaidata babu yabo babu fallasa ta amsa ta ce zata wuce general ward nan ya bi bayanta, sun jima acen yana taimaka mata sannan suka dawo. 5:00pm na yi ta shirya ya fito ta dawo gida, ta wuce ɗakin Ammie ta gaidata tare da sanar da ita akan Alhaji Sama'ila zaizo anjima, amma harda murmushi ta ce "To sai kije ki shirya mashi snacks ko, to Allah yayi albarka" Amen. Hamrah ta miƙe cikin farin cikin ganin Ammie ta saki fuska, ta faɗa toilet ta watsa ruwa kamar yadda ta saba ta shirya ta gabatar da sallah tana kan dardumar sallah har aka kira ishai ta idar Alhaji Sama'ila ya kirata akan ya iso ta sanya hijabinta ta fito taci karo da Ammar dake ƙoƙarin shigowa ɗauke da niƙe² kaya ya ce "Ya kamata yau muyi fira dan gobe zan tafi" To Ammar na yi baƙo sai na shigo. Ya haɗe fuska ya wuce ciki, ta fito ta taddashi zaune, ta yi masa sannu da zuwa ya amsa tare da kura mata idanuwa ko ruwa bata kawo mashi ba ballantana snack tasan ba ci zayyi ba ya ce "Ranki shidaɗe na iso ina sauraronki, da fatan ba laifi na yi ba?" Ta sauke numfashi tare da cewa A'a ko kusa ba laifi kayi ba, daman so nake nasan waye kai, tunda kasan ba zayyu mu gina rayuwa cikin duhu ba. "Alhamdulillah hakan yana nufin kin amince dani, to na gode da wannan karamcin. Sunana Alhaji Sama'ila kamar yadda ki ka sani, mazaunin garin Abuja kuma ni ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoni nan Maiduguri, ina da mata ɗaya da kuma ƴaƴar 7 ina so ne na aureki sbd na yaba da hankalinki kuma naji inason na haɗa zuria dake" Ganin ya yi shuru yasa ta ɗago, ya sakar mata da murmushi ya ce "Is that enough?" Ta sauke numfashi ta ce Eh. Daddyn ta ne ya shigo ya yi parking, ganin haka yasa Hamrah miƙewa tsaye tana sudda kai, ya iso inda suke cikin girmamawa Alhaji Sama'ila ya gaida shi nan ya ce ta shiga ciki za suyi magana, ta wuce ciki, sai ganin Ammie ta yi a tsaye a palour ta ce da ita "Ya na ganshi da Daddyn ku?" Eh Ammie magana zasu yi. "To madalla abu ya yi kyau" Umm Ammie ina so muyi magana. "To bismillah zauna mana" Hamrah ta zauna tare da cewa Daman akan Alhaji Sama'ila ne, bakon nawa akwai abin da ya ɗaure min kai game da shi. "To menene kuma?" Ammie a hotel ya sauka kuma ya ce dani yana da mata ɗaya da ƴaƴa 7 sannan shi ɗan siyasa ne, to amma ni zaman hotel ɗin ne bai kwanta min ba.... "To sannu ƴar iya, tun da mu bamu sani ba ke ce masaniyar komai ko to ki sani aure babu fashi bari Daddyn ku ya shigo naji ya su kayi zan sake tabbatar mashi da cewa wannan karon dole sai anyi in yaso da kunyi aure ya dafa ki ya cinye ki, mutum ya tako ya bar iyalin shi ya taho domin neman aurenki amma ki ce wai kina tantama shi baice yana tantama a kanki ba da ki ke kwana wajen aiki sai ke. To ki sani wannan karon ba zan lamunta ba, ya zama dole ki amince" Jikin Hamrah ya yi sanyi ta ce "Ki yi hakuri Ammie" Ammie ta shige ciki, cikin fushi Hamrah na zaune ta shiga zurfin tunani ta ji muryar Daddyn su na cewa "Hamrah jeki baƙonƙi na jiranki kuyi sallama" Jiki a sanyaye tare da jin kunya ta miƙe ta fito ta tadda shi yana tsaye ta ce Zaka wuce ko? "Au korata ma ki ke to ki sani yanzu na zama ɗan wannan ahalin ne" Murmushi ta yi ta ce To da wuri haka. "Yes Daddy ya ce na turo da manyana" Daddyn kenan, to ya yi kyau. Ta mai rakiya ya tafi ta dawo ciki ta wuce ɗakin Ammar, yana zaune yana shirya katanshi ya ki kallonta, ta fahimci fushi ya ke ta zauna kusa dashi tare da sanya hannu tana maimaka mashi suna shiryawa tare ta ce Fushi ka keyi? "Eh kinsan daga gobe ba zamu sake zama muyi fira ba har sai na je na dawo shine ki ka jima" Murmushi tayi ta ce Daddy yazo ya tadda ni da Alhaji Sama'ila sun tattauna kuma ya ce ya turo magabatan shi..... "What?" Cewar Ammar yana zaro idanuwana waje.......... Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 23 & 24 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _______ Horn ya yi a daidai ƙofar gidan Ayshe bai fi 2 minutes ba gate man ya buɗe suka shige ya yi parking a area park/ parking space sannan ya kashe motar Hamrah ce ta fara fitowa tare da ƙoƙarin sauke kayan dake boot na motar, ya matso ya taimaka mata, sbd nawinsu da kuma yawansu, kasancewar gidan yana da gate 1 and 2, one ɗin shine side na Ayshe two ɗin kuma na patients na mijinta, dan haka gate 2 abuɗe yake sai kaiwa da komowa mutane keyi, Ammar ya dauki kayan ya yi bangaren Ayshe dashi gate man ya taimawa Hamrah su kayi ciki da ragowar. Da sallama Ammar ya shiga ta bi yansa yaran na ganin su su kayo kansu suna oyoyo Mommy Hamrah and Uncle Ammar, ya ajiye kayan ya rungume su, suna dariya ya ɗaga little Hamrah yana cillata sama tana dariya sauran suka je ga Hamrah sukayi mata barka da zuwa, ta wuce ciki bayan sun ta amsa ya tsaya suna ta yi mashi fira, ya riko hannun little Hamrah dake ƙoƙarin bin namecynta, itako Hamrah a gajiye ta ke tashige ciki ta tadda ɗakin da akwai baƙi ta shiga ƙawayen Ayshe ne da kuma wasu daga cikin dangin mijinta, suka gaisa a lokacin Ammar ya ƙaraso ganin da baƙi yasa ya koma ɗauke da little Hamrah sauran yaran ma suka bishi waje, Hamrah ta dawo palour ta zauna Ayshe da Zeenat suka fito, murmushi Hamrah ta yi bayan ta karewa Ayshe kallo ta yi kyau tayi kitso da ƙunshi, uwar gida... "Yaya Hamrah barka da zuwa, nayi tunanin sai zuwa yamma za ki shigo in kin tashi a wajen aiki, tun ɗazu zaman kaɗaici nake" Cewar Zeenat tana ƙoƙarin zama da ƙoton cikin ta, murmushi Hamrah ta yi ta ce Night duty na yi da safen nan na dawo shine na shirya na taho nan, ya ƙarfin jiki?. "Hmm kedai bari gashi dai abu yaƙi fashewa duk na gaji" Da alamu baza ki wuce next week ba in shaa Allahu, ke dai ki dage da addu'a. "Allah ya karɓi addu'ar ki" "Yaya Hamrah, sannunki da gajiya?" Cewar Ayshe, Hamrah ta ce Lafiya kalau uwar gida, ya shirye shiryen bikin?. Turo baki Ayshe ta yi ta ce "Na kula fa kina goyon bayan babanki a wannan abin" Dariya Hamrah ta yi ta ce To in ban taya Daddyna ba wazan taya, in kuma ta fiki kulawa da Daddyna sai na so ta fiye da ke?. Miƙewa Ayshe tayi ta wuce ciki wai a dole zancen ya ɓata mata rai. Murmushi Hamrah ta yi ta juya suna fira da Zeenat Ammar ya shigo ɗauke da little Hamrah ta taho wajen namecynta ta kwanta jikinta Hamrah ta shafa kanta tare da cewa Namcy yau kam zamu sha fira ko?. Little Hamrah ta gyaɗa kai alamun eh. Ayshe ta fito ta tadda Ammar zaune suna gaisawa da Zeenat ta ce "Lahh ya Ammar kai da kanka lallai yau gidana ya yi farin jini" Murmushi ya yi ya kalleta tare da cewa "Na sameku lafiya?" "Lafiyanmu kalau, ya shirye shiryen tafiya?" "Alhamdulillah, week ɗin da zamu shiga ma zan tafi" "Kai Ya Ammar ka ce tafiyar tazo?" Cewar Zeenat tana gingina kai, ya ce "Eh fah Zeenat kuyi ta sanya ni cikin addu'o'in ku" "Zamuyi da yardan Ubangiji" Ayshe da Zeenat suka faɗa lokaci guda, sun jima suna fira Ammar ya yi musu sallama ya tafi baima jira abinci ba, har dare ana hidima ƙafa bai yanke ba mutane sai shigowa suke kamar yau ne ranar bikin, ko da shike Ayshe akwai ta da zumunci. Hamrah tana zaune a palour tana shan fruit salad Zeenat ta fito itama ta zauna an watse baifi mutum biyu zuwa uku bane a ɗakin Ayshe, suna fira Alay Bukar ya shigo ya tadda su, zama shima yayi suna gaisawa ya ke tambayar Hamrah ya aiki ta amsa mashi da Alhamdulillah, ta tambaye shi ya shirye shiryen bikin ya ɗan tsosa keyar shi ya ce "Daughter ya ƙoƙari?" Murmushi ta yi ganin ya dawo mata da tambayar ta ce Alhamdulillah. Ayshe ce ta fito ganin ya shigo yasa ta fice daga palour duk sai ya ƙiɗime yabita da kallo, ya miƙe ya shige cikin ɗakin shi bai jima ba ya fito ya fice a lokacin ta shige ciki, Hamrah ta girgiza kai tana mamakin irin kishi na Ayshe ta miƙe ta shige ciki ta samesu nan su kai ta fira har lokacin kwanciya ya yi suka kwanta. _The next day_ Washegari kasancewar Friday ne short day yasa tunda suka tashi basu kwanta ba suka hau hidiman biki, gida ya cika da mutane musamman side na parents nashi sai shige da fice ake, Ayshe duk jiki ya yi sanyi ganin fa abin yazo sai wawwaro idanuwana ta ke tana kallon mutane Hamrah na danne ta tare da bata addu'oin, har yamma kafin nan Hamrah ta samu ta ɗan zauna, da shigar ta ɗaki wayarta ta hau ringing ta ɗauka sbd ganin sunan Bestie a jiki tayi murmushi tare da ɗaukawa ta ce Shatu kamar kinsan ko kina raina. "Nazo gida na tadda Ammie ita kaɗai ta ke sanar dani wai kina gidan Ayshe kuna bikin?" Sauke numfashi Hamrah ta yi tare da cewa Uhm kiyi hakuri ƙawata Alay BUKAR ne ya ke ƙara aure, na sha'afa ban sanar da ke ba gobe ne ma ranar taron in kin samu sai ki biyo. "A'a ba zan zo gayyar soɗi ba sai da na kira shine ake sanar dani, in kin dawo nazo mu tattauna" Sauke numfashi Hamrah ta yi ta san bata kyauta mata ba, ta ce I'm really sorry bestie abubuwa sun min yawa shiyasa ban sanar da ke ba amma ki zo goben. Ajiyar zuciya Shatu ta yi ta ce "Gobe zani wani bikin sai jibi zan je miki" To bestie godiya nake, da akwai labari ne?. "Sosai ma" Okay sai kinzo. Sukai sallama tana tsinke ƙirana sai ga kiran Abuja ya shigo nan ta ɗauka tare da sallama ya ce "Busy tun ɗazu da wa ake waya haka Baby?" Sauke numfashi Hamrah ta yi tace Uhm da ƙawata ce, ina wuni?. "Ok lafiya kalau, daman ƙira na yi na ji muryar ki da fatan kina lafiya?" Alhamdulillah. "To maybe gobe na shigo Maiduguri" To Allah ya dawo da kai lafiya. "Ameen baby" Sukai sallama tana mamakin yawan tafiyanshi da kuma zuwan shi bayan kuma ya ce bai san kowa ba anan Maiduguri... "Yaya Hamrah, Alay BUKAR yana neman ki yana waje" Ta ɗago tana kallon Zeenat da ta shigo bayan ta fita tattaki sai haki ta ke da alamu tana jin labour ne, ta ce da ita To gani fitowa. Ta miƙe ta fice, ta tadda shi yana rakuɓe jikin garu yana jiran fitowar ta, ta iske shi tare da gaida shi ya amsa ya ce "Daughter faɗamin me da me ku ke buƙatar gobe baya tampol da su carpet abin da ya shafi abinci da abinsha" Ta sauke numfashi tare da cewa Daddyna ba mu buƙatar komai ai duk abin da mu ke so ka siyo su sai dai Allah ya bada zaman lafiya. Ya sauke numfashi tare da ɗagowa ya kalleta shiyasa ta ke matukar burge shi akwai ta da zurfin tunani ya ce "To na gode, amma kuma ina so na yi magana da Ayshe ta ki saurara ta Please ko za ki yi mata magana ta samu ta fito mu gaisa" Murmushi Hamrah ta yi ta ce To Daddy na. Ta shige ciki Ayshe na zaune cikin ƙawayenta ta yi mata magana, ta miƙe tare da isowa inda ta ke Hamrah ta riƙe hannunta ta ce Zo nan Ayshe. Suka shige ɗaki ta ce "Menene yaya Hamrah?" Ayshe kenan duk nasiha da kuma ban baki da mu kayi miki ya tashi a banza to naga babu amfanin zaman mu anan dan haka mu watse kowa ya san inda dare ya yi masa tunda baki bukatar mu. Hankalin Ayshe ya matuƙa tashi ganin yadda Hamrah ta kanza lokaci guda ta riƙe hannunta tare da cewa "Yaya Hamrah me kuma na aikata da ya sanya ki ke irin wannan maganganun?" Ayshe come to your sense, ai koda tunani ya gushe hankali baya gushewa, ke ba yarinya bace da za ayi ta maimaita miki abu guda ɗaya, maisa sai da akazo dab da gaɓar kogi za ki sare, kuma ina mai tabbatar miki wannan sarewar da ki ke shirin yi zai sa ki aikata da kin sanin da ba za ki taɓa mantawa dashi ba, kuma hanyar da ki ke ƙoƙarin bi ba mai bullewa ba ce, kaurace masa da kin tsayawa ki saurare shi da ki keyi tamkar sake rushe alakarku da kuma zubar da kimarki ki keyi, tunda ya yi magana ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba to me ki ke so ya yi miki, ya fasa auren ne, bayan ya tara dubban jama'a ko kuma ya ki ke so ya yi?. Sauke numfashi Ayshe tayi tare da cewa "Meyasa kowa ya kasa fahimta ta, sai ganin laifi na ake bayan kuma andakeni sannan kuma ace za a hanani kuka kuma ai abin sai ya taru ya yi min yawa, sannan kuma ai munyi magana na faɗa mashi yaje shi wajen ta na bar mata shi" Ayshe kina cikin hankali kuwa, kin san me ki ke cewa, kada kishi ya rufe miki ido ki kauce hanya fa, to wlh kiyi gaggawar tuba sbd da Allah ki ke jayayya ba da Bukar ba kenan kin karyata ayar ubangiji da ya halatta aure ya basu damar su yi daga ɗaya har zuwa huɗu shine ki ke cewa baki so, to ma a kanki aka fara kishiya da za ki ɗaga hankalinki?" Kuka Ayshe ta soma yi ta ce "Ni bana jayayya da ayar ubangiji, kawai ina jin zafi ne tamkar ci min mutunci yake son yi" Ayshe, qu'rani zancen Allah ne kuma maganar sa ce dan haka kuma shi ya basu damar yin hakan amma ya ce in zasu iya adalci to kinga Bukar ya shirya zai kuma iya yin adalci sannan da ki ke cewa cin mutuncin ki zayyi ya yi ne ai bai aikata ba sai ki bari ya aikata shi tukuna. Shuru Hamrah ta yi sbd ganin Ayshe tana kuka ta zauna kusa da ita tare da ɗaura hannun ta kan kafadarta ta tausasa murya tasan Ayshe na da zafin kishi tun tana ƙarama, a hankali ta ce Ayshe gobe ne ɗaurin auren kiyi hakuri ki daure daga yau zuwa gobe zuwa jibi komai zai wuce ki yi ta karanta addu'oin da na rubuta miki za kiji sauke, da ace Bukar yana bin mata a waje ana yawo dashi ai gwamma ace ya yi aure ana daraja shi sannan hakuri da kuma juriyar ki sa kawaicin ki ne zaisa kiyi kima da daraja a idanuwan dangin shi da kuma shi kanshi, kuma zai kawo muku kwanciyar hankali. "To yaya Hamrah me ki ke so na yi yanzu?" Yauwa ko kefa, tashi ki wanke fuskarki ki shafa powder sai ki je ki compound na gida mijin ki na jiranki yana son magana dake, kada ki nuna mashi damuwar komai ki yi mashi addu'a da kuma kalamai masu daɗi da zai sanya ya yi farin ciki gobe cikin jama'a. "To" Cewar Ayshe ta miƙe ta yi yadda Hamrah ta sanar da ita sannan ta fito ta wuce inda mijinta ne tsaye ta hango shi ya rakuɓe jikin garu yana jiran isowarta, Hamrah na tsaye daga window tana kallon su ta ji tausayin Ayshe, duk wanda yaga irin soyayya da kuma shukwar da su kayi sannan bata son auren ƙanwar ta ya mutu dan haka za tayi komai taga sun zauna a gidajen su. Ayshe na isowa Alay BUKAR ya rungume kamar zayyi kuka, jin tayi magana ba yadda ya saba ji ba tunda ya sako zanjen ƙarin aure yasa ya ɗago ganin tana murmushi yasa ya yi matukar mamaki ta ce "Honey, ya Hamrah ta ce kana nemana shin kana bukatar wani abin ne?" Saurin rungume ta ya sake yi yana sauke numfashi tare da shigewa cikin jikinta yana shaƙar kamshin ta, jikinta ya yi sanyi taji tausayin shi to meyasa yake son ƙara aure in dai yana sonta to me yake buƙatar ne haka?. Ta daure ta ce "Do you need something Honey" Ya ɗago da ita tare da ɗan lumshe idanuwan shi yana sauke numfashi ya ce "Kawai ina so naga wannan kyakkyawar fuskar ta ki" Ta yi murmushi, sun jima a tsaye yana kwantar mata da hankali tare da yi mata tambayoyi ko da abin da ake bukata ta faɗa masa suna da komai sannan su kayi sallama, ta dawo ciki a lokacin kowa ya kwanta, sai Hamrah ce kaɗai tana shiga ta kwantar da kanta kan kafadar Hamrah tana kuka ta yi ta rarrashin ta daga bisani suka shige ciki suka kwanta. Washegari ranar ɗaurin aure suka tashi da hidimar biki 10:00am aka ɗaura aure Ayshe ba karamin jarumta ta yi ba har suka wuni. Da daddare aka kawo amarya around 8:00pm Hamrah na zaune kusa da kanwarta ganin ta saki ranta yasa ta miƙe ta fito wayarta ta yi ringing ta ɗauka Alhaji Sama'ila ne bayan sun gaisa ya ce da ita "Baby na shigo gari fah tun 3:00pm shuru ba ki kirani ba ko ƴar sannu da zuwa ma ki min" Ta sauke numfashi duk ta gaji ta ce So sorry, muna hidiman biki ne duk bani da nutsuwa, ka dawo lafiya?. "Ok ayya ya yi kyau, Alhamdulillah. A ina kuke bikin?" Nan unguwar jiddari polo. "Ko zan iya zuwa?" Eh to gaskiya yanzun a gajiye na ke sai dai ko zuwa gobe. Ya sauke numfashi tare da cewa "Gashi kuma ina son ganin ki, ko za ki zo inda na ke mu gaisa ne?" Cike da mamaki ta ce Ina kenan?. "Hotel, Dujuma hotel" Ta sauke numfashi ta ce A'a. "To shikenan gobe zan zo" To. Nan sukai sallama. Sunday, shine ranar wunin bikin humaira na kwance bayan sun kammala dukkanin hidima ta gaji ta shige ɗakin Alay BUKAR ta kwanta kasan carpet bata son hayaniya wayar ta ta yi ringing ta ɗauka sbd ganin suna bestie dake jikin, Shatu ta sanar da ita ta iso tana ina nan ta faɗa mata inda ta ke, ta ɗan jima sannan ta shigo Hamrah ta ce A ina kuma ki ka tsaya?. "Ina ɗakin Ayshe muna gaisawa" Bari nasa a kawo miki abinci. "A'a barshi zuwa anjima yanzu dai na zo muyi magana ne" Hamrah ta tashi ta zauna ganin Shatu na hawaye yasa ta ce Ƙawata meyafaru?. "Daman akan plan ɗin da muka yi ne na aiwata amma kuma an sami matsala" Subhanallah wacce irin matsala kenan?. Gyara zama Shatu ta yi ta ce "Kamar yadda ki ka ce na baiwa Mommy hakuri da kuma shi mijinta a gabanta na yi, kuma ta sauko, muka koma normal kamar yadda muke, da farko Daddy baya shiga harkata amma kuma bayan an ɗau wasu kwanaki sai ya tsiro da hanyar da zaisa na dinga zuwa inda ya ke, ganin a gaban Mommy ya ke aike na yasa nake zuwa, har ya kaiga ko bata nan yana kirana ɗakin shi kamar yadda ya keyi a baya nake haɗa masa tea. Ranan ina kwance babu kowa a gida duk sun tafi skul Mommyn ta tafi gidan bikin suna naga ni kaɗai ce yasa na shige cikin ɗaki na kwanta bacci ya ɗauke ni, cikin bacci naji hannu na yawo a jikina a hankali na buɗe idanuwa na sai ganin Daddy ne kwance gefena ya zubamin manya manyan idanuwansa waɗan da suka sauya kala lokaci guda su kayi jajir dasu yana fuzgar numfashi yana kallona, zanyi magana yasa hannu ya rufe min baki............ Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 31 & 32 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _______ Kura mata fararen idanuwanta tayi tana kallonta cike da mamaki da kuma al'ajabi tabbas tayi nesa, kuma nesan da bazata taɓa jin kira ba, ko baza su taɓa jin kira bata yi mamakin yadda sauran matan suka basu haɗin kai lokaci guda. Matsalar mace ita ce, rabin rayuwar mace duk a kuɗi suke tafi, rayuwar mace na tare da kuɗi sbd mace ƴar kyalkeli ce da za iyaye ko miji zai daure ya ɗauke kaɗan daga cikin bukatur mace da ɓarnan bazata yi yawa ba, da kuɗi ƙalilan ake siyan zuciyarta, sbd duk bukatarta da ta ke so duk suna da alaka da kuɗi. Matan aure da suke zina a waje alhali suna da miji shima yana da alaka da son zuciya da kuma rashin basu kulawa100% ba dole ta sami 100% ba amma aƙalla ta sami 50 to 70 percent ɓarnan zata ragu. Da wannan hanyar Hauwa'u Jibrin da Zee sukayi amfani dashi suka ci galaba akansu sannan su karan kansu daliline ya sanya su cikin wannan harkar dan haka bazata gaza ba har sai ta sanya sun janye wannan tallafin sun ganu gaskiya sun dawo kan daidai. Zata fara ta kansu manya sannan kuma ta hanyar su za a samu su idda sako...... "Ku keda duhun kai, kune dai baku san me kuke yi ba, tir da wannan harkar taku in dai ta wannan hanyar ce zanyi arziki Allah ya tsareni, yanzu har wani abin alfahari ne da yaye ɗalibanku har kuna wani kuri da kuma farin ciki. To ki sani ko ince ku sani kun aikata babban kuskure kuma kuna kan aikatashi, kun cuci ƴan'uwanku mata shawarar da zan baku shine Ubangiji gafururrahim ne duk girman laifi zai yafe muku muddin kuka nemi yafiyarsa ku ka kuma watsar da wannan harkar ta iskanci" Cewar Shatu cikin ɓacin rai ta katse Hamrah daga tunanin da ta ke yi. Mun amince da abin da kuka zo mana dashi Hauwa'u Jibrin ƴar gold amma zaku amfana dani ne na wata ɗaya kacal kuma muna roƙon Ubangiji ya bamu nasara...... "Bestie, are you out of your mind, kin kuwa san me kike cewa kin amince da buƙatar su kina nufin za ki sanya hannu a yaɗa alfasha. Come to your mind and wake up from your deeply sleeping, a tunani na za kiyi musu nasiha amma shine ki ke so ki jefa rayuwar ki dumu² a ciki never, that'll never ever happen" Dariya Zee ta yi ta kalli hauwa'u Jibrin suka tafa suna farin cikin samun nasa tabbas sun kusa mallakar makuɗan kuɗaɗe, Hamrah zata zame musu mukullin arzikin su. Murmushi Hamrah tayi ta dubi a gogon dake ɗaure a hannunta ta kalli Hauwa'u Jibrin tare da cewa Da kaina zan nemeku yanzu zan tashi na wuce ciki na shirya zan wuce wajen aiki ina da night duty. "To pretty mungode da bamu haɗin kai sai mun jiki Please kada ki ɗauki lokaci mai tsawo wajen yin tunani" Cewar Hauwa'u cikin farin ciki, murmushi Hamrah tayi ta ce I promise you za ki jini nan da kwanaki. Cikin farin ciki suka tafi, Shatu cikin ɓacin rai ta ce "Bestie me ki ke nufi da hakan?" Murmushi Hamrah tayi ta ce I want to help. "Which kind of helping is that, kina so dai ki sanya rayuwar ki cikin hatsari wajen taimakon wasu Please let them do whatever they want and ke ma ki yi rayuwar ki" Shatu yin hakan da ake yi ne yake sanya bamu taimakawa, taimako yayi ƙaranta kuma hakan shine ke jefa yawancin mutane cikin wani hali. I'll do my best naga na ceto wasu daga cikin matan. "May Allah be with you bestie, amma gaskiya ina tsoro. Allah ya taimake mu dai dan tare zamu gudanar. Tare suka shige ciki Hamrah ta shirya suka fito ta wuce wajen aikinta. Bayan ta idar da sallah ishai ne tana zaune kan dardumar sallah tana addu'a taji wayarta na ringing ta shafa addu'ar ta ɗauka sbd ganin Zeenat ke kira sai dai kuma da tayi sallama sai taji muryan mijin Zeenat yayi magana cikin sauri "Dr Hamrah kina cikin Hospital ne?" Ta amsa masa cikin sauri da Eh, lafiya?. "Zeenat ce jikin babu daɗi maybe haihuwa ce" Ok to sai kun iso. Ya katse wayar ta mike ta sanya white coat nata ta fito ta wuce labour room ta sa a shirya bed ɗin kafin su iso suna ko isowa aka shigar da ita baifi 30 minutes ba ta haihuwa cikin murna da farin ciki Hamrah ta shirya baby boy ɗin ta kwantar dashi babu jimawa yayi bacci. Zeenat jiki da sauki ta tashi ta zauna kamar ba itace wacce ta haihu ba, Hamrah na ta tsokanarta har Aunty maimuna ta shigo suka gaisa Hamrah na mamakin waya sanar da ita nan ta ke faɗa mata mijin Zeenat ne, babu jimawa Ammie ma ta iso nan Ayshe ma ta iso sai kusan 10:00pm suka koma gida amma Aunty maimuna yayar Zeenat wacce suka fito ciki ɗaya sune suke kanta har gari ya waye. Gari na wayewa Zeenat ta ce a bata sallama tunda bata jin komai da ƙyar Hamrah ta bata sallama suka wuce gidanta, nan ko baƙi suka dinga zuwa wunin ranar Hamrah a nan ta wuni sannan ta wuce hospital ta kwana. Sai da ta jera kwana biyu tana sintiri sakanin gidan Zeenat da kuma hospital da gidansu duk sai ta gaji. _Bayan kwanaki biyu_ Tana kwance a ɗakinta kasancewar bata da aikin safe shiyasa ta kwanta tana hutawa, sai da tasha bacci sannan ta miƙe ta watsa ruwa ta shige kitchen ta haɗa breakfast mai sauki ta fito tana ci kuma tana chatting sai ga kiran Ammar ya shigo ta voice call ta ɗauka cikin sanyin muryar ya ce "Nayi fushi tunda an daina kulani" Murmushi tayi ta ce Ammar iyayen rigima ina ni ina kiranka ai sai a zuƙemin kuɗina, da fatan kana lafiya?. "Au ta kuɗinki kike bata ni ba shikenan na gode" Uhm da wasa nake Ammar aikine ya sani gaba ga kuma Zeenat ta haihu shiyasa ka jini shiru. "Masha Allah, ta sauka lafiya?" Alhamdulillah, lafiya kalau, ta sami baby boy. "Wow kice soja ta haihu to saura taki sanya min takwara tun haihuwar ta na fari ta ke min alkawari" Kama cire rai ba zaka samu ba. Nan ko yayi tayi mata fira daga bisani sukai sallama ta sauka a online ta miƙe ta maida plate ɗin kitchen ta dawo taji wayarta na ringing ta ɗauka cikin sanyin murya tayi sallama ya amsa tare da cewa "Ina kofar gidanku ki fito" Ok to Alhaji Sama'ila amma kashigo cikin gida. "To" Ta miƙe ta yafa gyalle ta fito ta taddashi zaune ya sakar mata da murmushi ganin yadda tayi kyau cikin shigar da tayi ta doguwar riga ta atamfa cikin sanyin murya ta ce Sannu da zuwa. "Yauwa likita, na kula yanzu ba a yina" A'a ba haka bane aikin ne. "To ai ko kirata a waya za ki iya yi ai mu gaisa" To na amshi laifina zan gyara. Murmushi yayi tare da cewa "Ai bakya laifi, nazo ne na sanar dake next week on Friday zan turo magabatana suzo su saida ranar biki, naga gwanda ayi a wuce wajen kawai kada ina ji ina gani a kwace min ke" Murmushi tayi ta ce Allah ya nuna mana. Ameen. Sun jima suna fira sannan ya miƙe yace zai wuce nan ya ajiye mata envolope cike da kuɗi ta ce bazata ansa ba amma ya dage sai ta ƙarɓa haka ta karba sai dai yawansu yasa ta kasa kirgawa ta shigo ta ajiye ta shirya ta wuce hospital. jiki a sanyaye ta shige office nata ta ajiye komai kamar yadda ta saba ta zauna ta kunna system ɗinta tana dubawa Dr Aliyu yayi sallama ya shigo bata ɗago ba ta amsa ya ƙaraso cikin kusa da ita ya ajiye mata leda tare da cewa "Special Doctor ki sanya min albarka ga snacks da kolanut and sweet na sanya ranar bikina" Cikin farin ciki ta ɗago ta kallesa ta ce Na tayaka murna Allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna mana lokacin. Cikin farin ciki ya ce "Amin thanks" Samun wajen zama yayi ya zauna nan suka shiga tattaunawa akan aikin da zasu gudanar a daren yau kiran magrib ne yasa ya miƙe ya fice. 11:00pm ta dawo office nata ta cire white coat ta rataye sa ta dawo kan resting chair ta zauna tare da cewa Wosh na gaji, ba a gama wancan wani sai ya biyo baya gashi jibi sunan Zeenat kuma morning gareta ko ya zatayi.... Ya turo ƙofar ya shigo cikin sanyin jiki ya ƙaraso tare da yi mata sallama ta amsa ta ɗaure fuska ya zauna kan kujera yana kallonta itama shi take kallo ya sakar mata da murmushi ya ce "Wai damman babu wata alaƙa soyyayya a sakaninki da Dr Aliyu, niyi tunanin saurayinki ne sai gashi ya kawo min chewing gum da auren sa shine nace bari na shigo na sake tabbatar da cewa ba to yaudararki yayi ba" Murmushi tayi ta ce In kuma yaudara ta yayi fa what are going to do?. Murmushi yayi ya ce "Sai na mai dukan cin amanar ki da yayi har sai ta gane kuskuren sa sannan na kyalesa" Ah lallai naga alama, da fatan dai ba kwayar kasha ba kashigo min office. Dariya yayi yace "A'a ai yanzu ban cika shanye² ba kuma ina so na daina ko zaki dinga ganin mutunci na" Uhm Dr Mahmoud Allah yasa ba tuban muzuru kayi ba, Allah ya kara shiryarwa. "Amin Dr Hamrah bari na tafi ko" To Dr Mahmoud. Ya fice tana mamakin sa lallai wannan mutumin to Allah ya sake shiryar dashi. Washegari da safe ta tattaro ta dawo gida ɗakinta ta shige saboda jin shuru gidan kamar bacci suke basu tashi ba tana shiga ta faɗa kan bed ta kwanta dan ta huta bacci ya ɗauke ta sai 10:30am ta farka ta miƙe ta watsa ruwa sannan ta fito ta shige ɗakin Ammie nan ta taddata cikin sanyin jiki ta sanar da ita sakon Alhaji Sama'ila akan zai turo da magabatan shi nan ta ce da ita taje ɗakin Daddynsu ta sanar da shi. Ta shigo ta riskesa yana danne² cikin laptop nasa ta duka har ƙasa ta gaida shi ya amsa cikin kulawa yake dubanta cikin sanyin murya ta ce Daddy, daman wancan mutumin ne yace zai turo magabatan shi nan da next Friday. "Wane mutumin kenan likita?" Ya tambaye ta ba tare da ya ɗago ba yaci gaba da abin da yake yi. Ta sudda kai dan kunya abin da ya dace Ammie tayi shine ita zata yi kuma nawin hakan take ji, jiki a sanyaye ta ce Alhaji Sama'ila na Abuja. Yayi murmushi tare da sauke numfashi yace "Allah ya nuna mana" Amin. Ta faɗa ta sake duban sa a hankali ta furta Uhm Daddy. "Na'am likita, da akwai damuwa ne?" A'a daman tambaya ce nake so nayi daga cikin babanninmu mata. "To likita ina jinki" Daddy wacece Baba Hajara?. Chak ya dakatar da abin da yake yi cikin sauri ya ɗago ya kalleta yana mamakin meyasa ta tambaye shi, yace "Hamrah a ina ki kaji ana ambaton wannan sunan kuma menene dalilin ki na tambaya" Ajiyar zuciya ganin yadda ya tashi hankalin sa lokaci guda sanan ya jima bai kirata da sunanta kai tsaye ba sai yau cikin sanyin murya ta ce A'a Daddy kawai na tambaya ne. "A'a Hamrah haka kurum bazaki tambaya ba sai da dalili" Ta ɗago ta kallesa kamar yadda yake kallon ta tace Da gaske Daddy na komai. Ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa Wannan maganar ki barta anan kada kowa yaji sannan kada ki faɗawa Umar ma ya sani kuma ki cire ta cikin zuciyar ki, kin ji" To Daddy. "Tashi ki tafi" Ta miƙe ta fice, jiki a sanyaye ta wuce ɗakinta tana mamaki meyasa Daddy baya so tasan wannan matar Hajara, meyasa da ta ambaci sunanta taga tashin hankali a tare da shi, ta sauke numfashi ta faɗa kan bed, tare da rumtse idanuwanta ta jima tana bacci sai yamma lis ta shirya ta wuce wajen aiki. Zaune suke ana ta hayaniyar gidan bikin suna iya danginsu ma kaɗai sun cika gidan balle kuma ace da sauran ƴan uwa da ake zumunci, kasancewar ba wani aiki mai yawa suke yi ba sbd contract na komai sun bada ayi musu. Hamrah ta fito daga ɗakin mai jego ta nufo inda sauran ƴan uwan su ke zaune suna yanka cabeji da dai ƙananun abin da ba a rasa ba. Sanye ta ke da riga da skart ta farin lace tayi normal ɗauri tayi matukar kyau, komanta fari ne hatta sarka da ɗankenne da ta sanya masu duwatsu suma dare ne, plat shoe ɗinma fari sai kuma ɗan karamin jaka dake hannunta ma fari ta zauna kusa da Ayshe tare da ɗauro wuka tana kankare carrots tana gaisawa da ƴan uwanta da suka shigo, Maryama ma ta fito ta zauna Aunty maimuna ta kalli Hamrah tare da cewa "To Hamrah sai a dage a fidda miji abar zaɓe tunda kinga ƙannenki girma ya fara kamasu Ayshe ta zama uwar gida Zeenat kuma ta fara tara yara Maryama ma a ɗakinta Ammar ma yana dawowa zamu aurar dashi, kinga zaki rage ke kaɗai ce" Hamrah batayi magana ba sai ma murmushi da tayi taci gaba da kankare carrots ɗin, ba wannan bane karon farko da take fuskantar irin wannan daga familyn su dan haka baya damunta. Maryama ce tayi caraf ta ce "To da wani auren ba gwamma ta shekara dubu a gidan su ba, wasu da su suke ci da kansu da kuma ƴaƴansu kai harda mijin ma, wlh ba zan taɓa ci da gardi ba sai dai ko kasannayi" Sittt.... Aunty maimuna tayi tasan da ita take mara kunya kawai Indai Maryama ce zata faɗi fiye da hakan, dan kaf gidan itace zakka... "Ke Maryama babu son rashin kunya da fusara dan tayi wa yayar ki magana akan ta fidda miji itama ta samu rahamar Ubangiji ta dalilin aure aɗaga gawarta sama tayi daraja shine ki ke faɗin haka to kul ki iya bakin ki, ai takai shine take faɗa mata haka me yafi daɗi a duniya bayan aure. Cewar wata daga cikin dangin Ammie, caraf ko Maryama ta turo baki ta ce "Oh ni Maryama har dasu kaza a da cin danko in ana magana ta aure da masu jini a wuya ake yi, ba wai waɗanda mazajen su suke tatil da giya ba su lakaɗa musu na jaki kuma su zauna ba, da irin wannan auren ai gwamma batayi saba" Sittt......... Akayi bakin kowa ya mutu suna kallon Maryama cikin ɓacin rai da ta kuncewa Innarta zani a kasuwa kowa kuma yasan halin da ta ke ciki da ta sani batayi magana ba...... Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 27 & 28 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* ______Kallon shi ta tsaya yi sbd yanda ya wani firgita da jin zancen yana wani waro idanuwa waje, ta yi murmushi, tana mamakin meyasa Ammar yaƙi jinin Alhaji Sama'ila ne, mutumin bashi da makusa da farko tana jin fargaba a kanshi amma kuma tunda ya faɗa mata wanene shi taji sanyi a ranta, zata aure shi ko dan hankalin Ammie ya kwanta ta daina fushin da ta keyi da ita duk da ba laifin ta bane ƙaddararta ce jinkirin aure, amma tunda Ubangiji ya nufa ta samu mijin aure zata rufawa kanta asiri ta zauna dashi..... "Wai kina nufin tsohon nan za ki aura da gaske, look Hamrah kada kiyi gaggawar yanke hukunci ki nutsu ki sake fahimtar shi kada kalaman bakin shi su yaudareki" Ammar munyi magana ya faɗamin cewa yana da mata da kuma yara 7 shi ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoshi Maiduguri so no need na sake damun kaina akan sai na sake tambayar shi wannan bazayyi making sense ba, kuma ga shi babban mutum ne. Sauke numfashi Ammar ya yi ya ce "Bana ƙinshi ni kawai na fi son ki aure mutumin kirki sannan wanda shekarun shi bai ja ba, amma kuma tunda kin ce ya yi magana da Daddyn mu that's okay, to amma kwa bari ai na dawo daga training ko?" Eh to maybe. Ya haɗe fuska ya ce "What do you mean by maybe kamar ma ɗauki ki ke" Murmushi ta yi ta ce Ai ya zama dole ƙanina ya halarci taron bikina, za a jira ka dawo. "Yanzu naji batu, to me za ki bani na tafiya?" To mai kuwa zan baka da ya wuce na yi maka addu'ar Allah ya kai ku lafiya ya kuma bada sa'a a bisa abinda aka je nema, a kula da ibada ayi riƙo da gaskiya ban da kanza dabi'a ko tarbiyya. Ya yi murmushi ya ce "Na gode babbar yaya amma kuma amin kyauta ta musamman " Ok, na fahimce ka kace na haɗa maka snacks kamar yadda na keyi in dai za kayi tafiya. Dariya ya yi ya ce "Yes, kin gano ashe kin san kuwa daɗin cake ɗin ki na keji kuma yana ɗauke min yunwa" To zan yi maka sbd kace dani babbar yaya amma badan haka ba, bazan yi ba. Sosai ya ke mata dariya wato dai wannan son girman ba zai taɓa ƙanzawa ba amma yana son ganin ranar da zata dauki girman ta bada ta dauki ƙanƙanta. Bayan sun kammala shirya kayan ne suka wuce kitchen ta shiga shirya masa caka, donot greba sun jima suna yi sannan ta samu ta kammala dare ya yi sosai gashi duk sun gaji kuma tana so ta tashi da wuri ta yi mashi rakiya airport sannan ta wuce office a adaddafe ta shige dakinta ta kwanta bayan ta kammala shirya mashi ta bashi ya wuce dashi ɗakin sa. _WASHEGARI_ Da ƙyar ta iya tashi daga bacci ta watsa ruwa tare da ɗauro alwala ta idar bayan ta shirya ne ta fito ta tadda Ammar, Daddy da Ammie suna zaune a palour suna yi masa nasiha ta gaidasu, sannan suka fito ita da shi da kuma Daddy a tare suka yi mashi rakiya airport Daddy ke driving nasu. Bayan ya yi parking a parking space na airport ne ya fito tare da ce musu yana zuwa ta ɗau waya ta kira Dr Aliyu cikin rawar jiki ya ɗauka ta sanar dashi bazata iso da wuri ba duk abin da ya dace ya yi, su kayi sallama. Ammar ya kalli yayarshi tare da cewa "Na gode yaya Hamrah da ƙoƙarin ki na jiya i really appreciate it, kuma in dai ina dasu to bana zama da yunwa. Zanyi kewarka ku" Murmushi ta yi ta ce Muma zamuyi kewarka, ka kula kaji banda soyayya da masu jan kunne. Dariya ya yi sosai ya ce "Ni abin da ya kaini shi zanyi ba wata sabuwar alaƙa ba, burina shine na yi nasara" To Allah ya dafa muku. "Ameen" Suna cikin fira Daddy yazo Ammar ya fito ya wuce suna gani har jirgin ya tashi sama sannan suka juyo Daddy ya sauketa wajen aiki sannan ya wuce nashi office ɗin yau ba Ammar dake taimaka mash. Kai tsaye office nata ta shige ta fidda duk abin da zata buƙata ta sanya white coat nata tunanin ta baki ɗaya yana general ward, turo ƙofar Dr Aliyu ya yi tare da sallama ya shigo ta juyo ta kallesa ta ce Dr Aliyu sannu da kokari, na yi rakiya ne da safen nan. "Lah ai babu komai Dr Hamrah, na kammala duba patients ɗin ma sai dai ko zuwa anjima sai ki sake duba su" Ok na gode. Ya fice yana jin daɗi, Hamrah na da saurin fushi kuma bata da riƙo gashi duk abin da ya yi mata ta yafe masa, sai ya ji jikin shi ya yi sanyi. Tunda Dr Aliyu ya ce ya kammala duba patients ɗin sai ta miƙe kan resting chair sbd hutawa gashi daren jiya bata kwanta da wuri ba kuma ta tashi da wuri. Baccin 10 minute ta duk jikinta yayi mata nawi bata sami isasshen bacci ba a hankali ta tashi ta zauna sai kuma taja da baya ta haɗe da jikin kujera tare da waro idanuwa alamun mamaki da kuma tunanin me yake nufi da yi mata sanɗa, lallai wannan mutumin yana wuce iyakar shi, ba laifin shi bane amma za tayiwa tufkar hanci, ta nuna shi da yatsa ta ce Kai Dr Mahmoud abin naka har yakai kashigo sbd ina bacci, ka aiwatar da nufin ka a kaina to ƙaryarka ta ci ƙarya, to bari na takaita maka kada kaga kana kwalɓewa ana yi maka uzuri wai baka cikin hayyacinka to kasani ba ƙwaya ka ke haɗiyaba ko durum na giya ka ke sha to wallahi baka isa kaci galaba a kaina, tashi ka fice min tun kan na tara maka ma'aikatan cikin wannan Hospital ɗin. Ta ƙarashe maganar cikin ɓacin rai da kuma tsantsan tsana da kuma ƙyamatar shi, sauke numfashi ya yi tare da kura mata idanuwan shi ya ce "Ba abin da nasha I'm in my normal sense, ni bana shaye shaye..... Ka fice min daga office Dr Mahmoud or should I call OG and tell him that, you always interrupting me. Jin haka yasa ya miƙe sbd yasan zata aikata, ya fice. Ta sauke numfashi tare da lumshe idanuwa ta buɗe ta miƙe ta shige toilet ta ɗaura alwala ta idar da sallah azahar sannan ta wuce general ward. Bayan ta tashi daga wajen aiki ta dawo gida tana shiga kuma sai jikinta yayi sanyi da ta tuna Ammar bayanan, ɗakin Ammie ta shige ta gaidata sannan ta wuce ɗakinta ta faɗa kan bed ta ɗan miƙe tana washh sbd gajiya, ta ɗan jima a kwance sannan ta tashi ta faɗa toilet ta watsa ruwa ta fito ta shirya ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah har aka kira ishai sannan ta miƙe ta hau kan bed sbd kaɗaici ta hau online ta yi kwana biyu batayi chatting ba, tana hawa ko message ta ko ina tana reply a nutse tazo kan na Ammar video ya tura mata tun da suka shiga ABGANISTAN har zuwa masaukinsu tana ta dariyar abin daga bisani ta kwanta bacci. Washegari kasancewar bata da morning duty sai night duty yasa ta jima tana baccin safe sai kusa 11:00am ta tashi ta shirya ta fito kitchen ta nufa, breakfast mai sauki ta haɗa ta fito ta ci sannan ta wuce ɗakin Ammie ta shaida mata cewa zataje gidan su Shatu, ta fito ta wuce sai dai kuma wayam babu kowa gidan ma da alamun babu kaya a ciki, ta fito ta komo gida tana mamakin abin ko gate man ma bayanan, tana isowa gida ta zauna a ƙarƙashin bishiyar darbejiya ta kishingiɗe jikinta duk sai taji kaɗaici ba shatu babu Ammar ta ɗau waya ta kira number ta bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa "Bestie kina wajen aiki ne ko kina gida" Ina gida Shatu yanzun nan ma daga gidanku na taho. Cewar Hamrah tana sauke numfashi. "Gani shigowa" To. Sukai sallama, babu jimawa sai gata ta iso Hamrah ta shige ciki ta ɗauko darduma suka zauna ta ce Ƙawata meyafaru ne naje gidanku babu kowa. "Uhmm ƙawata ki bari, muna nan muna ta rigima da mijin Mommy na, yanzu haka muna zaune ne a asalin gidan mahaifina" Ƙawata kin fara bani labarin bamu ƙarashe ba ki ka tafi to ki ƙarashe mun na fahimci komai duk ina cikin damuwa hankalina yaƙi kwanciya. "Haka ne ban ƙarashe miki ba a ranar sbd ƙirana da lawyer ya yi. A wancan ranar da Mommyna taga jini a guest House har ta tambayi Daddy na sai ya bata amsa cikin tsoro da kuma tashin hankali da firgici dan shi a tunanin shi ya goge komai jin ta ambaci jini yasa ya ƙiɗime da ƙyar ya tattaro nutsuwar sa ya ce "Jini kuma hajjiya, abu ne ya zube mai kama da haka nasa a goge amma kuma basu gyara mai kyau ba" Ta sauke numfashi sosai ta ke karewa palour kallo sannan ta ce "To na wuce sai na dawo" Har ta kusa isowa ƙofar fita kuma sai ta tsaya sbd ƙarar bugun ƙofar da taji ana yi, ta juyo ta kalleshi sai taga duk ya haɗa gumi, ni kuma ganin haka yasa naci gaba da bugawa da gwiwata, cike da mamaki ta sake dawowa sakiyar palour ta ce "Alhaji kamar ina jin ana buga ƙofar cen, shin wayene a wajen?" "Babu komai a cikin store ɗin kayane da kuma ɓeraye" Zuba masa idanuwana tayi tana karantar shi ya ganin uban gumin da ya haɗa da kuma yadda jikinshi yake ɓari yasa ta fara fahimtar akwai abin da yake ɓoye mata, takowa ta yi zuwa inda yake tsaye ta ce "Alhaji lafiya mai yasa you are so gulty, meyake faruwa ne... Jin bugun ƙofar da na keyi yayi yawa yasa, ta iso bakin ƙofar tare da saka hannu ta murɗa handle door amma kuma sai taji ta a rufe, ta juyo ta kalleshi tare da cewa "Ina key na wannan ɗakin?" Zuwa wannan lokacin Alhaji ya fara ruɗewa cikin tashin hankali ya iso inda ta ke ta ce "Na faɗa miki babu kowa a ciki, tunda wucewa za kiyi to ki tafi mana kada ki makara" "Alhaji akwai abin da ka ke ɓoyemin shin budurwa ce a ciki ka ke ɓoyemin baka so na gani ko kuma wani abin ne na daban" "Babu dukkan abin da ki ke tunani.... Na sake buga ƙofar tare da cewa Ummmmm. Alamun ina neman taimako, cikin ɓacin rai ta ce Alamun jin kamar muryar mace da taji ne yasa tace "Da alamun macece, ka buɗe naga wacece a ciki" Duk ya ƙiɗime ta shige ciki ya ɗauko key ya fito sai dai ganinta riƙe da jakata tana kare mata kallo, ina kallon sa ta wannan ramin ya dafe kanshi tare da jujjuya sa cikin tashin hankali. Mommy ta iso inda yake tsaye ta nuna mashi jakar tare da cewa "Wannan jakar Shatu ce, ina Shatu, ina ta ke?. Shin itace a cikin nan ɗin" Bai bata amsa ba, ya sauke numfashi duk ya gigice, tasa hannu ta warci key ɗin ta wuce ƙofar kai tsaye ta buɗe da ɗauri da kuma jinin da ya gama ɓata min jiki na faɗo jikinta, baifi 2mint ba da faɗawa jikinta na tsume ban tashi fargawa ba na ganni kwance kan bed na hospital mommy na a kusa dani tana ganin na farka ta fashe da matsanancin kuka ta kasa magana, ni kam kukan ma na kasayi sai bin ɗakin da kallo nake. Nurse ce ta shigo ta tadda kukan da Mommy ta keyi, nan ta fidda ta waje sbd kada hankalin na ya tashi kuma jikin babu daɗi duk da ba wata rashin lafiya nayi ba amma a wuni ɗaya na kanza kamar nayi jinyan 1week. Kwanana biyu a hospital aka bamu sallama muka dawo gida na tadda ana fita da kayayyakin mu, na kalli Mommy tare da tambayar ta Mommy ya naga ana fidda kayayyakin mu ina zamu je?. Bata kalleni ba kuma bata ce komai ba har aka fidda komai aka zuba su cikin manya manyan motoci na ɗeban kaya ta ce "To Shatu kama ƙannenki ku shige motar" Na ce da ita To mommy. Na tattara su muna shirin fitowa ne Daddy ya shigo ganin abin da yake faruwa yasa hankalin shi sake tashi ya iso inda muke tsaye ya ce "Babu inda zaku tafi ku wuce ciki ku zauna.... "Ku fice ku shige motar Shatu, bai isa ya dakatar da ku ba" Cewar Mommy ranta a matukar ɓace, ya iso inda ta ke zayyi magana ta ce "Alhaji keep you words sbd baza suyi maka amfani anan ba ka jira zuwanmu court maybe suyi amfani acen amma kuma baka isa ka hana mu tafiya ba" Tana faɗin haka ta hanyar fita amma yayi saurin shan gabanta ya tare ƙofar fita ya ce "Na faɗa muku babu inda za kuje, ko kin manta ne da aurena akanki in ki ka fita bada izinina ba ban yafe ba" Dariya Mommy tayi wanda ya fi kuka ciwo ta ce "Kacika ɗan ta'addan da baya riƙe tokobi, irinka annubane cikin al'umma zama daku bazai haifar da ɗa mai ido ba rabuwa dakai shine mafi alkhairi a garemu, a tunaninka ban san me kake aikatawa bane to ka sani tun ranar da Shatu ta ɗibi ƙafa tabar wannan gidan zuwa Cameroon na san da akwai dalili, kiyayyar da ta ke nuna maka ma ta sake tabbatar min da akwai wani abun amma kuma bani da hujjar da zan tuhume ka, sannan kuma miyar ƙuɓewar da gangan na wareta daga cikin sauran kulolin na ajiye ta ina jiran zata dawo ne tare da driver ko kuma shi kaɗai zai dawo, ganin shi kaɗai ya dawo yasa zargina ya fara tabbata, na fahimci duk sanda ka ce kana da meeting a guest House to a wannan ranar driver da Shatu dawowarsu na banbanta, sai kuma da shatun ta dawo nake kasa gane kanta. Ganin komai a zahiri yasa na sake tabbatar da zargina shine kake ganin zan zauna dakai a matsayin miji to wlh ba zai taɓa yuwa ba sbd kai ba uba bane gare su ko zan shekara da auren ka a kaina gwamma in zauna dashi ba tare da ina ganin ka ba, ka cuceni ka cuci ƴaƴana bazan taɓa yafe maka ba da ka yaudareni da fuska biyu, dan haka na tafi kuma ina jiran takarda ta nan da kwana biyu in kuma ba haka ba na fito na sanar da duniya irin ɓoyayyen halin ka da danginka da kuma ƴaƴanka na sauran matan su sani" Tana faɗin haka ta tisamu gaba muka tafi, tun daga wannan lokacin yake ta bibiyarta ta yafe mashi amma ta ƙi da dai yaka ta shirya tsaf zata tona masa asiri shine ya tura mata ta kardan saki ta hannun lawyer na wanda da yayi gardama bai aika ba Court zata makashi. Babban damuwata itace BP Mommy ya tashi sbd wannan abin kullum cikin tunani bata cin abinci duk hankalin mu a tashi yanzu haka dai likita ya ɗaurata kan magani tana sha jikin dai za a ce da sauki" Sauke numfashi Shatu tayi da ta ƙarashewa Hamrah labarin tare da sake fashewa da kuka, ita kuka Hamrah kuka aka rasa mai rarrashinsu sai suka jiyo muryar Ammie daga bayansu tana cewa "Kuka ba shine mafita ba, ku cire mazan aure kuyi aure shine mafita kuma wannan ne kaɗai hanyar da zaku tsira da mutuncinku kuma kuyi daraja" Juyowa sukai suna kallonta lokaci guda cike da mamaki kenan Ammie taji duk abin da suke tattaunawa.......... _________________________ Assalamu alaikum fan's jina da ku kayi shiru 2days banyi Update ba kuma nace daku nasami hutu zan dinga yi on on to yau da gobe na hannun Ubangiji, baƙi nayi sun zo min hutu shiyasa bana na samun time na zauna nayi typing amma in shaa Allahu zan dinga squeezing lokaci ina typing. Ayi hakuri da typing errors bana samun daman yin editing ne. Sannan ina godiya da fan's masu ƙirana da kuma masu tambayata, thanks habibaties 💕 😘 love you all❤️. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 29 & 30 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ Ƙarasowa ta yi dab dasu ta tsaya tana kare musu kallo suka sudda kai ƙasa suna share hawayen dake kan fuskar su. Ɗagowa Hamrah ta yi ta kalli Ammie da ke kallon su cikin sanyin jiki ta ce Ammie barka da fitowa da abin da zan yi miki ne? Sauke numfashi Ammie ta yi ta ci gaba da cewa "Ku zaman ku gabanmu ma ko gunduranku baya yi, fisabilillahi ku duba ƙannen ƙannenku ma sunyi aure sun rufawa kansu asiri sun zauna a gidajen su kuma muma sun rufa mana asiri, amma ku sai dai kuyi ta janyo mana zagi da abin faɗa abin haushin ma ku ko a jikinku baima dameku ba, kuji tsoron Allah ku fidda mijin aure kuyi aure ku tafi cen gidajenku ku zauna, ku kuhuta muma mu huta da gori da kuma nuna mu da ake yi wlh a ta dalilin ki Hamrah na janye jikina daga shiga cikin dangina da kuma dangin Daddyn ku to cewa ake ni ce na hanaki aure alhalin ina bakin ƙoƙarina wajen ganin kinyi amma kuma ke a koda yaushe sai zuba min ƙasa a ido ki ke to bari kuji na faɗa muku kuka da kuke yi yanzu kuka fara indai kun zaɓi zaman gaban iyayenku to ke shatu ba dole mijin uwar ta ƙi ya faɗa a sha'awar ki ba kin kai aure har kin wuce kuma kina gaban shi kina giftawa, duk abin da ya sameku ku kuka ja wa kanku, kun tsaya zaɓi ko to zakuga zaɓe" Shiru sukai babu wanda yace ƙala mamaki ne ƙarara a fuskar Shatu tana duban Hamrah da ta sudda kai ƙasa tana watsa da zoben dake hannun ta jiki a sanyaye da alamu ba wannan ne karon farko da ta ke fuskantar wannan matsalar ba sai taji Hamrah ta ce Za muyi in shaa Allahu. "Haka dai ko da yaushe kuke cewa amma kuma ni banga alama ba to in kuma wani abin ake kullawa to ba a isa ba kuma anyi kaɗan" Ammie na gama faɗin hakan tayi ciki abinta. Ikon Allah, cewar Hamrah cikin zuciyata bata ji daɗin faɗin hakan da Ammie tayi a gaban Shatu ba, ai ko ba komai akwai girmamawa da alkunya a sakanin su sannan kuma bata so kowa yasan halin da ta ke ciki bayan ƴan gidansu, sannan kuma abin Ammie kullum ƙaruwa yake kalaman yau sun ɗaure mata kai wane abu kenan ake ƙullawa ko za a kulla.... "Bestie meyake faruwa dake wanda bansan dashi ba ko ince me yake shirin faruwa me kuma Ammie ta ke cewa ban fahimta ba yaushe kuka fara ƴar haka da ita me take cewa ne dake da kuma waye kuke kulla wani abin?" Sauke numfashi Hamrah tayi ta kwakulo murmushi cikin sanyin jiki ta kalli Shatu ta ce Babu komai Shatu kawai dai tana son nayi aurene shiyasa ki kaji ta ke faɗin hakan.... "Look Hamrah kada ki ɓoyemin komai kamar yadda nima bana ɓoye miki nawa, har tsawon yaushe hakan ke faruwa dake kike ɓoyewa?" Shatu Ammie mahaifiya ce ban isa naja da ita ko nayi fushi da ita ba ko kuma na tuhumeta da wani abun balle kuma na tambayeta wannan dalilin yasa bana magana akan batun. Sauke numfashi Shatu tayi ta ce "Hamrah cewa na yi yaushe hakan ya fara kuma menene dalilin?" Shatu bana ce ga dalili ba amma kuma rashin aure da banyi ba shine dalilin, zan iya cewa hakan ya fara faruwa ne a lokacin da aka sanya ranar bikina da Deeny akan za a haɗa dana Maryama to wannan abin ya farune ranar bikin da kuma a lokacin suka sami matsala da dangin Daddy a haka aka watse ko rakiyar Maryama basu yi ba suka bar gidan sai dai kuma naji suna ambaton sunan wata acikin musayar kalaman da suke yi wai ita HAJARA ban fahimci komai ba har aka watse aka barni da tashin hankali na fashin aurena da akayi bayan na kammala dukkanin shirina to zan iya ce miki tun daga wannan lokacin Ammie ta ɗauke min wuta bata shiga tsabgata, sannan kuma sakaninta da Daddy ma babu jituwa sai kuma kalaman da suke fitowa daga bakinta masu ɗauremin kai amma kuma abin da bansani ba shine dalilin da yasa Daddy ke cewa in ma akan wancan batun ne to tama daina tunanin zai faru. Nayi² na haɗa dukkanin maganganun waje guda na sami amsar su amma na kasa shiyasa ki kaga bansanar da ke ba. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Shatu tayi tana kallon Hamrah tana nazari akan kalaman ta sannan ta ce "Wacece Hajara?" Ban santa ba. Cewar Hamrah. "Bestie duk abin da ya faru dake mukaddari ne babu kuma wanda ya isa ya kanza hakan, Ammie uwace amma kuma zan iya cewa bata miki adalci ba sbd kowa yasan asalin abin da ya faru ranar bikinki ba laifin ki bane daman cen Allah ya yi ke ba matar Deeny bace. To amma meyasa ta ɗau zafi cikin kwanakin nan" Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce Eh to wannan yana da nasaba da fitowar Alhaji Sama'ila neman aurena, da farko Daddy bai amince ba amma kuma yanzu ya amince sai dai ni ce hankalina bai kwanta dashi ba kuma matsalar na faɗa mata shine take ganin kamar ko auren ne banaso to shine ta ke faɗan waɗannan kalaman dan kada naja da baya dan yin hakan zaisa Daddyn ƙin amincewa da Alhaji Sama'ila ita kuma Ammie bata so ya sani. Jikin Shatu ya yi sanyi tana jinjina lamarin ta ce "To ke bestie meyasa baki son shi?" Ƙawata ba wai bana son shi bane, kinga masaukinsa shine hotel kuma yace dani shi ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoshi Maiduguri sannan yana da mata ɗaya da kuma yara to duk irin wa'yannan mutanen baza su rasa wajen zama ba amma zama a hotel ba girmansa bane, rannan fah cewa ya yi naje na samesa a cen to ni bansan me haka yake nufi ba. Sauke numfashi Shatu tayi ta ce "Bestie shawarar da zan baki shine yadda kika ga Ammie ta ɗau zafi wannan karon ki amince ki auri Sama'ila, tunda da zancen aure yazo tunda niyyar sa mai kyau ce ki yarda ayi kawai a wuce wajen sannan kuma you have to find out who is that Hajara bcoz Ina da tabbacin tana da dangantaka da wannan matsalar da kike tare da ita maybe muji wani abin daga wajenta" Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce To nagode ƙawata na amince zan auri Sama'ila sbd hankalin kowa ma ya kwanta to amma batun nemo wannan matar Hajara bansan wa zan fara tambaya ba Daddy ko Ammie dake fushi sani?. "Daddy za ki tambaya ko ki tambayi Zeenat tunda kinga maybe ta sani dan suna tare da dangin Daddy" To zan yi. Suna fira tare da baiwa junansu shawa suka jiyo sallama daga bakin gate suka ɗago cike da mamaki suke kallon su tare da amsa sallama suka ƙaraso. "Hauwa'u Jibrin!" Cewar Shatu ceke da mamaki ganin ɗayar yasa tace "Wai tab in ba a mutu ba za a haɗu, Zainabu Abu mai tagwayen suna" Dariya sukayi suka haɗa baki wajen cewa "Aishatu muktar ashe rai kanga rai, to har yanzu ana nan ana ƙawancen kenan ya yi kyau" "Uhm ai ni da Hamrah aminya mutu ka raba ne" Dariya sukai Hamrah tayi musu barka da zuwa tare da ce musu su shige ciki amma suka ce anan ɗin zasu zauna ta basu kujerun roba suka zauna, nan aka shiga gaisawa Hamrah ta ce Zainab Ayuba kina nan a gari ikon Allah ko matsin ku ba a ji. "Uhm pretty kenen ina nan fah harkoki ke riƙe ni" Ikon Allah, ya yaran naki da mai gidan?. Dariya Hauwa'u da Zainab sukayi lokaci guda sanan Zainab ta ce "Ai banyi aure ba har yanzu" Cike da mamaki Shatu ta ce "Kai da mamaki kenan yawancin ƴan set namu da muka kammala secondary School bamu yi aure ba ikon Allah" "Uhm fah shine ma abin da ya kawomu sbd mu tattauna akai though we have already talked about it me and Hamrah Amma kuma she didn't respond to me, maybe bata fahimce ni bane shine muka zauna dani da kuma Zainab muka sake shawarar zuwa mata da zancen sai kuma gaki to hakan ma yayi kyau sai mu tattauna kan batun" Hamrah ta miƙe tare da cewa Let me find you some water. "Ai daga Restaurant meke bamu da yunwa da kuma ƙishirwa, ki zauna muyi magana wannan karon da babban batu mu kazo" Sauke numfashi Hamrah tayi ta zauna tare da ƙurawa Hauwa'u idanu wacce ke cewa daga Restaurant suke sanye take da riga da wondo tashi kitson Attachment mai colour hulace wacce bata rufe gashin kan ba. Ta juya ta kalli Zainab wacce ta ke sanye da doguwar riga itama tasha cikon gashin Attachment ta yafa ɗan ƙaramin mayafi duk sun sha mai kamar ba ƴaƴan Musulmai ba, tayi ajiyar zuciya ta ce Hauwa'u muna jinki. "Da farko dai kamar yadda kuka sani ni ce hauwa'u ƴar goal mai lakaɓi da bini a hankali in kayi gardama kasha ƙasa, ina da kungiyoyina na kaina sun kai 7 amma kuma uku ne suke tashe wato ina da fannin ƴan mata waɗanda basu taɓa aure ba sannnan ina da na zaurawa da kuma matan aure. Zainab shugaba ce a ƙungiyata ta ƴan matan da suka jima basu yi aure ba to ita ke riƙe da duk yadda za ayi kuma adace akwai Rahama ita kuma ke riƙe da na zaurawa, ni kuma ina riƙe da na matan aure, sannan akwai masu tallafa mana manya manyan ƴan siya da nan gida Nigeria da kuma wasu daga cikin shahararrun ƴan kasuwa sai kuma ƴan outside..... Tayi shiru ta sauke numfashi tana dubansu suma sun zuba mata na mujiya suna kallonta cike da mamaki da kuma son sanin shin wane irin kungiya ce wannan mai dubban mutane. Kamar tasan me suke tunani tasa ta cigaba da cewa "Bari na tafi kai tsaye kan batun so muke mu haɗa kai daku wajen sake bunƙasa wannan kungiyoyi guda ukun musamman ma ke Hamrah pretty ba ƙaramin ƙaruwa zamu yi dake ba ina tabbatar miki karon farko ma Saudi Arabia zaki tafi acen za ku fara shan iskar ku" Shiru da ta yi ne yasa Hamrah cewa "Ƴar goal har yanzu ban fahimce ki ba wacce irin kungiya ce wannan wacce kuke taimakon ƴan mata, zaurawa da kuma matan aure kuma wane irin tallafi kuke bada har da kuna da masu taimakon ku" Sauke numfashi Zainab ta ce "Haba Hamrah pretty kada ki ce min kina da duhun kai mana, harkar ce baki sani ba zaki ce min ko kuma gwadamu ki ke son yi, to naga ita ɗinma taimako ce tunda tamkar business ta ke do me i do you ne, harka ce ta ƙaruwa da wannan zaman da kuke yi a gida ana matsa muku duk da ba sai kun faɗa ba nasan haka abin yake kuna cikin damuwa to duk wacce ke cikin irin wannan matsalar muke warware ta, yanzu waɗanda suka samu abin yi ta hannun mu suna da yawa dan zan iya cewa last 3month mun ya yi mutane dubu ɗari biyar daga cikin su akwai ƴan mata wasun su kuma akwai zaurawa sannan mata masu jinkirin aure yanzu haka suna da manya manyan shops su ke riƙe da kansu wasu ke riƙe da iyayensu, shine muka zo kema ko ince kuma ku shiga wannan harkar sbd mu faɗaɗa abin musamman ma ke Hamrah pretty da ki keyi... Ya isa na ce ya isheku ƴar goal da Zee, lallai kun cika ƴan ta'adda masu cutar da al'umma amma to ku sani ko bamu da komai ko da yunwa meke kwana baza mu taɓa shiga cikin kungiyar ta ku ba Allah wadaran da da ƙungiyar ta ku. Cewar Hamrah cikin ɓacin rai da tashin hankali. Shatu ko tsuman zaune ta yi tana kallonsu kamar mutum butumi cen ta numfasa ta ce "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah yasa mafarki na keyi" "Uhmm meyasa kuke bada mata ne abu kun sani mun sani amma kuna son wahalar damu, in zaku saki jiki muci arziki mu barshi a inda yake to ku amince kawai ba wai ku tsaya kuna wani nuƙunuƙu ba" Cewar Hauwa'u Jibrin tana murmushi sbd ganin wannan karon za tayi nasara akansu....... Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 33 & 34 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* ______ Ajiyar zuciya ta sauke a hankali taci gaba da kankare carrots ɗin cikin sanyin jiki ko kaɗan bata ji daɗin abin da Maryama ta ce ba, bai dace ta zubar musu da mutunci ba a bainan nasi ko ba komai iyayenta ta. Su faɗi duk abin da suke so su faɗa akanta bazata damu ba sbd tasan watarana zai zamo tarihi. Ayshe dake zaune gefen ta taci gaba da yanka cabeji tayi murmushi bayan taji abin da kanwarta su ta faɗa sun santa sarai ba a gasa mata baki ba duk abin da yazo bakinta faɗa take kuma ba wannan ne karonta na farko da take musu hakan ba duk cikin su anayi musu abu suna shanyewa amma banda ita, sam bata barin takwana kanayi take maida maka, murɗaɗɗiya ce ba a iya gane mata yanzu zakaga kamar mutuniyar kirki ba a wuce wasu lokuta kuma ta sauya kamar mai juju take, cikin sanyin jiki Ayshe ta ce "Uhm Maryama ko za ki duba abin da na bari akan wuta a cen cikin kitchen please" Tasan sarai korarta Ayshe ke son yi shiyasa ta faɗi hakan.... "Ke Maryama kada kiga kina tsula tsiyarki uwarki na ɗaure miki gindi ko kuma kina takama da wani guntun arzikin da mijinki ke dashi kina cin mutuncin ƴan'uwanki yau ko uwarki Ammie bata raye su zasu rike ki amma shine kike buɗe baki kike faɗa musu haka waye baisan rayuwar yanzu ba kowa lallaɓa gidansa yake yi yaga ya rufawa kansa asiri in batayiwa ƴaƴanta ba wa zataiwa naga kayi hidima a gidan ka ai ba laifi bane, kuma ai gaskiya ta faɗa dubi fah kiga yadda shekarun ta suka ja she has almost 35yr mai kuma ya rage mata na jin daɗi yanzu bayan tabar kuruciyarta. To ki sani ba abu mai wahala bane na dirza bakinki da jikin garu yanzun nan yayi jini mara kunya kawai" Cewar Baba Uwani tana huce takaici taƙi jinin Maryama duk ƴaƴan Ammie itace ta fito mara kunya ba a isa a faɗa mata taji ba..... "Kai duniya ina zaki damu, oh ni Maryamu Daso yau naga ta kaina, yaushe akayi dare da har garin ya waye, tab wai kura ce tace da kare maye. To ke Baba Uwani yaushe kikayi auren ina dududu 2yrs ne da yin aurenki kuma kema kina da shekaru 45 kafin kika samu tsoho yayi wuff dake ai gwamma ita Hamrah 35 ne kuma tana da kyaun jiki da kuma baby face, ina kema lallɓa zaman ki ke shi kanshi Alhaji Audu ba zuwa miki yake ba ke kike binsa cen Kaduna da ya gaji ya koroki, mun san komai kawai bamu son magana ne sbd sanin mutumci amma tunda kunki rike girmanku to me yasa mu zamu baku" Ayshe ce ganin abin na neman girmama ta ce da Maryama "Maman Waleed ki tashi kijeki ki duba abin da na faɗa miki yana kan wuta" "Barta Ayshe, barta muci uwar ta Batula tunda bata bata tarbiyya ba batasan ta girmama manyanta ba mara kunya fusararriya kawai dan kinga kinayi ana kyalikine shiyasa ki keyi to ki sani ko shi ubanku bai isa ba ballantana ke karamar alhaki" Cewar cewar Sa'ade wacce suka tashi gida ɗaya da Daddyn su Hamrah, Hamrah tayi saurin cewa Maryama kiyi shuru manyanmu ne bai dace kiyi sa'insa dasu ba ki tashi ki shige ciki. Maryama ta cika tayi fal daman zafin rai gareta an zagi uwar ta da kuma ubanta dan haka bazata kyalesu ba sbd duk taro sai sun tada husuma haka lokacin bikinta sai da suka tada rigimar da yasa aka watse cikin ɓacin rai babu wanda yayi mata rakiya daga dangin Daddynsu dan haka yau zata sauke musu ta kalli Baba Sa'ade ta ce "Kai mutane na bani mamaki kowa da guntun kashi a suliyarsa baya gani amma yana leka na wani, ke baba Sa'ade har kina da bakin magana keda da haduwarki da walakiri a kabari ba zatai miki kyau ba, ina zaman zina ki keyi a gidanki baki da aure ki ke zaune da mijinki sbd ya yi miki saki yafi dubu amma kika rufe ido kika ce wai cikin ɓacin rai yayi sa kika zauna kike ta haifan shegu, shine har kike wani kuri kina cika kina batsewa to sai ki dakan na gani da yake ni ɗin shukakkiyar bishiyace ai dole na tsaya ki dakeni" Aiko nan aka hauta da faɗa sunayi tana maida musu da ƙyar Hamrah tasa tayi shuru, a hankali ta ce Ayi hakuri da abin da Maryama ta faɗi kuruciya ke ɗibarta in kukayi la'akari da cewa har yanzu bata gama mallakan hankalinta ba. Ku ma ku rike girmanku kuja darajarku ku daina biye mata. Babu macen da zata so ta zauna bata da aure har karshen rayuwarta, kyan mace shine ɗakin mijinta, nima burina shine nayi aure na zauna a ɗakina kamar ko wacce mace amma kuma hakan baya yuwa sai da izinin Ubangiji. Bana cire rai wataran nima zanyi, amma zancen da ake yi wai ina zaɓi ne shiyasa naƙi yin aure ba gaskiya bane kowa yasanni ni macece wacce bata da dogon buri sannan ina da rufin asiri na dan haka ba zan ɗaurawa kaina cewa sai mai kuɗi zan aura ba. Babu wacce zata so ta auri mijin da bashi da sana'a ko wace mace tana so tana kuma muraɗi ta shiga gidan da zata sami kwanciyar hankali in ta tsaya ta dirje ta nemi mijin da zatafi samun nutsuwa da kuma kwanciyar hankali ba laifi bane. Ni kawai na ɗauki jinkirin aure a matsayin jarrabawa ce a gareni kuma Allah yana sane yayi haka shine mafi sani akan komai maybe yayi hakanne sbd ya gwada imani na sbd Ubangiji baya ɗaurawa bawansa abin da yafi karfinsa sai dai bawa ya ɗaurawa kansa, Allah shine ke jarabta kuma shike yayiwa sannan hakan yasa na maida dukkanin al'amurana gare shi kuma na ɗauki hakan a matsayin MUJARRABI na. Sauke numfashi Hamrah tayi ta ɗago tana kallon su kamar yadda suma suka zuba mata na mujiya suna kallonta duk jikinsu yayi sanyi da bata maida musu da martani mai zafi ba cikin ruwan sanyi take magana, ta cigaba da cewa "Na rike mutunci na, masu ce ina bin maza ko ina karuwanci shiyasa naƙi fidda mijin aure to ba haka abin yake ba, ban taɓa sanin wani ɗa namiji ba, na kiyaye mutunci na da kuma martaban gidanmu, bazance ban yafe wa masu faɗin hakan ba amma har ga Allah ina jin zafin mummunar shaidar da ake yi min, amma babu komai duk a rashin sani ne. Yin aure da kuma rashin sa duk daga Ubangiji ne, kamar yadda yayi dare haka kuma yayi rana, haka zalika kamar yadda yayi safiya haka yayi yammaci, yayi rayuwa kuma yayi mutuwa yayi mace ya kuma yi namiji, yayi fari ya kuma yi baƙi yayi duhu kuma yayi haske, yayi samu kuma yayi rashi, yayi zafi kuma yayi sanyi, dan haka bazan ɗaga hankalina ba. Shine aure nufi ne na Ubangiji da yanufa za ayi, ba wai dabararmu bace ko wayonmu zaisa ayi aure shi karan kansa menene aure me ake nufi da wannan kalma ta aure? ___.....shin menene ma Auren? Aure shine haɗa wata irin alaƙa tsakanin mace da namiji, wannan yana nufin haɗe rayuwarsu ta zama ɗaya hakan nan kuma makomarsu ta kasance guda ɗaya. Allah (Subhanahu wata'ala) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu kamar yadda ya gaya mana a Alkur'ani mai tsarki. Wannan yana nuna mana cewar alaƙa tsakanin mace da namiji Allah ya kullata tun fil azal. Sai dai kuma duk da wannan alaƙa Allah bai halatta Aure ba sai Aure ya zamo Sunnah ce ta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama Dan mace ko namiji bai yi aure ba wannan baya nuni da cewar mutumin banza ne ko wani laifi yai wa Allah shi yasa har yanzu bai auruba ko bata auruba. Aure Sunnah ce ta ma'aiki rashin yinsa kuma ba zai hana bawa shiga aljanna ba matuƙar ya kame kansa, tunda muna da sanin cewar daga cikin Sahabbaima akwai wadanda basu yi aure ba kuma muna da tabbacin ƴan aljanna ne kenan aure baya hana shiga aljanna hasali ma wani aure da yinshi gara rashinsa in muka yi la'akari da irin matan da su ke da aure kuma suke aikata zinna wasu ma maɗugo su ke yi da auren su Wa'iyazubillah mace ta mutu a wannan gabar ai itama ta san makomarta Da yawan mutane suna daukar rashin yin aure ƴan'mace wata tawayace a gare ta basu sani ba jarrabace daga Allah kuma shi Allah yana jarraba bawansa ta yadda ya so kuma ba zai daurawa bawansa abinda ya san bazai iyaba ƙaddara ce kowa da irin ta sa, nawa ake auren amma kuma ana tsaɓawa mahalli nawa kuma ba a auren kuma ake samun rahamar Ubangiji sannan abu mafi ɓacin rai da kuma takaice shine mafi yawan masu gorantawa ƴaƴan wasu suma suna da ƴaƴan basa tunani suma daga cikin ƴaƴansu hakan zai iya faruwa dasu. To ku sani yin hakan tamkar shishigi ga al'amuran Ubangiji ne kuma jayayya da ikonsa kuke yi in kunne yaji to gangan jiki ya tsiri. Hamrah na gama faɗi haka ta miƙe ta shige ɗakin Zeenat. Har yamma suna shagalin suna sai bayan magrib suka tattaro inasu ina su ko wacce ta watse. _After 1week_ Kamar yadda Alhaji Sama'ila yayi musu alkawarin zai turo magabatan shi ranar Friday ya tabbata dan haka suka hau shirye shiryen tarɓansu, aladan Maiduguri shine ranar yanke lokacin biki ko sanya rana ko tambaya ana ɗan karamin hidima wa abokan manemin dan haka kusan kowa ya hallara banda Zeenat mai jego, an haɗa musu roban papare dosen biyu kusan rabin da kwatan dosen ɗin kaji ne a ciki sai kuma sauran aka zuba snacks, dibla, cake, donot, greba, garabiya, alkaki da kuma drinks sabar murna da kuma farin ciki karamar biki sukai ita dai Hamrah na daga gefe tana kallon su duk jikinta yayi sanyi gani take kamar ba da gaske bane abin kamar a mafarki, sai kuma da ta tuna da abin da ya faru ranar bikin ta da Deeny sai gabanta ya faɗi tana tsoro kada hakan ya sake faruwa. Sai yamma suka iso aka sanya rana sunce sati biyu suke so amma Daddy yace a'a sai dai a sanya 2month da ƙyar aka bari akan 1month aka watse Alhaji Sama'ila ya bada sadakin Hamrah a ɗunkule lokacin guda akan 15 million Daddy ya ɗauke dubu ɗare biyar sannan ya maida sauran amma ina dashi da kuma sauran mutanen da suka zo suka ce a'a rabonta ne baza su ansa ba a riƙe ai wannan ba komai bane, da labari ya iso cikin gida kuma nan aka hau guɗa Hamrah najin haka tsoro ya kamata what, menene dalilin sa na yin hakan kai ita abin tsoro ya bata. Daddy yace da Ammie gaskiya ya tsorata da wannan mutumin amma Ammie ta tashi ta dire ta ce ba zayyu ba sai anyi in kuma a abin da danginsa ne suka faɗa shi yake so ya aiwatar to ya faɗa mata tasan nayi amma kuma sai ya hau rarrashin ta ya karɓa ya ajiye to abinda ya sake ɗaure musu kai shine cewa da yayi baya bukatar ko kwandalarsu shi matarsa kawai yake so dan haka komai zayyi mata a cen Abuja inda zasu zauna nan ma hankalin Daddy ya tashi amma da ya tuna aure za ayi sai hankalinsa ya kwanta. An watse lafiya an bar Hamrah ita kaɗai a ɗaki ta ɗau waya ta kira Alhaji Sama'ila bugu ɗaya ya ɗauka yana cewa "Matata ya kike da gajiya da kuma ɗawainiya, kai gaskiya abokaina sunyi farin ciki da wannan tarban" Uhm, ba komai, kuma ai kunyi ɗawainiya amma kuma kuɗin sadakin da ka bada yayi yawa sannan kuma kace kada amin komai a kaini daga ni sai kayana shine ya ɗaure min kai meyasa kayi hakan, meyasa ka ɗaurawa kanka wannan ɗawainiyar shin taimako na ka keyi ko tausayi na ka keji?. Ajiyar zuciya yayi cikin sanyin murya ya ce "Hamrah aurenki fah na fito nema dan nayi hakan ba laifi bane kuma ai ko nawa na kashe a kanki ai kaina nayiwa ba ba dawata manufa nayi ba, ki ɗauki hakan a matsayin ƙauna ce da nake yi miki" Sauke numfashi tayi ta ce Duk da haka ai sai ka bari in na shigo gidan ka sai kayi min amma ba a gidanmu ba. Murmushi yayi sosai sannan ya ce "To ranki shidaɗe daga wannan bazan sake yi ba" Uhm shikenan nagode. Sukai sallama akan gobe zaizo su gaisa. Kiran Ammar ya shigo ta ɗau wayar cikin sanyin murya ta ce Yanzu ko nake son kiranka sai ko gashi kaki rani..... "Eh Hamrah yayi miki kyau da kika zaɓi wannan tsohon a matsayin wanda zaki zauna dashi kuma har an yanka lokacin biki shine baki faɗa min za ayi ba shikenan kawai ko kinyi aure babu ruwana dake" Cewar Ammar ya katse ta yana magana cikin damuwa. Haba Ammar kaima kasan bazan taɓa aikata hakan ba kawai muma mukaji an sanya rana daman tambaya ce za ayi to shine aka haɗa kawai aka sanya lokacin amma ai an sanya shi daidai da dawowarka. "Ni dai kawai anyi hakan ne dan bana nan" Uhm Ammar ai ko kana nan ko baka nan dole zanyi aure so, banga wani abin damuwa ba, abu sai kadawo ma za a ɗaura. "To shikenan sai anjima" Ya katse wayar, tabi wayar da idanu ikon Allah menene kuma abin fushi ko da shike an fara musu alluran sojoji ai sai a hankali. Har ta kwanta bata ga Ammar ya hau online ba haka ta hakura tayi bacci. Washegari, tana tashi ta shirya ta fito sbd tafiya wajen aiki ta shige ɗakin Ammie ta taddata zaune hannunta riƙe da takarda da kuma biro tana ta rubuce rubuce, ganin Hamrah ta saki murmushi tare da cewa "Yauwa kamar ko kin san ke nake jira amma ba dai wajen aiki zaki ba?" Cike da mamaki take bin Ammie da kallo ta ce Eh Ammie zan wuce wajen aiki. "To wannan sai kin dawo sai mu cigaba da lissafin abubuwan da za a siyo to in ba abin surkin nawa ba yaushe zamu ɗauki yarinya mu bada babu kayan ɗaki ai ba zayyu ba sai munyi" Galala take kallon Ammie rabonta da taga tana fara'a yau kusan 2yrs kenan........... Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 35 & 36 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________Sauke ajiyar zuciya Hamrah tayi tare da gyara zamanta ta kalli Ammie wacce ke cikin farin ciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan Aljanna, mamaki take ganin lokaci guda ta sauko daga fushin da take yi da ita, daman rashin mijin aure ne tunda ko ta samu komai ya wuce. Ta dau alkawarin zama a ɗakinta koman yaya ta tadda zata jurewa duk rayuwar da zata sinci kanta a gidanta indai hakan zaisa Ammie farin ciki, a hankali ta ce Ammie ba sai mun zauna munyi list na komai tare ba kiyi duk abinda ya dace nima yamin. "A'a jeki wajen aiki kin tunda da yamma zaki dawo in yaso zuwa dare sai muyi magana, ai wani abin sai anji ra'ayinki kowa da irin zaɓin sa ballantana ku ƴan zamani da son kyalele ai sai ku kuka san abinku" Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce To Ammie sai na dawon sai mu tattauna. "A dawo lafiya" Hamrah ta miƙe ta fito, tunowa da tayi da ta manta da snacks ɗin da zata kai wajen aikinsu na sanya ranan bikinta yasa ta koma ɗakinta ta ɗauko su kamar yadda ta kulle na kowanne su cikin lada. Ta iso kamar yadda ta saba batayi late ba yasa ta wuce cikin office nata ta ajiye jakarta ta ɗauko white coat nata ta sanya sannan ta ɗau wayarta da kuma ledan snacks ɗin ta fito ta riski Nurse ta bata nata ta faɗa mata an sanya ranar bikinta, aiko da jin haka ta karɓa ta dinga bin office by office tana rabawa nan da nan zancen sanya auren Hamrah ya karaɗa Hospital masu mata fatan alkhairi nayi masu zancen ƙasa² ma nayi, tana zaune a office nata Dr zalihat ta shigo ta tadda ta zaune tana danne dannen wayarta ta ɗago sbd sallaman da tayi ta amsa tare da sakar mata murmushi ta ce Dr zalihat ke da kanki sannunki da zuwa. Murmushi tayi ta ce "Eh fah na ce wannan abin farin cikin yakamata na taho takanas ta Kano nazo na sanya alkhairi. Na tayaki murna Allah ya nuna mana lokacin" Murmushi Hamrah tayi ta ce Nagode sosai Dr zalihat. "Ba komai, amma dai da fatan bazaki bar aiki anan ba ko da bayan kinyi aure" Murmushi Hamrah ta sake yi ta ce Yanzu dai bana ce komai ba, dan babu tabbacin anan garin Maiduguri zan zauna amma da zan ci gaba da aikina da yafi amma sai yanda yayu. "To masha Allah, Ubangiji yayi maki zaɓi na gari, muma da zaki zauna da munyi farin ciki" Sun jima suna fira sannan ta tafi, Dr Hamrah na zaune Dr Aliyu ya turo kofar ya shigo cikin farin ciki ya ce "Special Doctor sai naji labari mai daɗi, kai na tayaki murna sai ko gashi dani dake duk a sanya lokacin bikinmu" Murmushi tayi ta ce Eh fah haka Allah yake al'amuran sa nima lokaci yayi. "To Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin" Amen. Sun ɗan tattauna akan aikinsu da zasu gudanar a ranar sannan ya fice. Yamma nayi Hamrah ta soma shirin tafiya gida amma kuma sai tunani ya faɗo mata zata biya gidan Zeenat ta dubata sannan ta wuce gida. Turo ƙofar Dr Mahmoud yayi ya shigo cikin sanyin jiki yayi sallama ta amsa ba tare da ta juyo ba tana ƙimsa files ɗin da suke kan teburin taji ya ce "Da gaske ne abin da naji ake cewa akan an sanya ranar bikinki?" Barin abin da take yi tayi ta juyo tana kallonsa yadda yayi maganar cikin sanyin murya kamar ba shi ba ganin duk tashin hankali ya bayyana akan fuskar yasa tayi mamaki ta ce Dr Mahmoud, nurse Laraba bata baka snacks ɗin bane?. Takowa yayi dab da ita ya zuba mata jajayen idanuwansa yana kallon fararen idanuwanta yana sauke numfashi akai akai ya ce "Ba abin da nake son ji ba amsa kawai zaki bani eh ko a'a?" Eh. "Dan meyasa sbd kinga an sanya ranar Dr Aliyu shine ke ma ki kayi hakan sbd ki huce haushin cin amanar ki da yayi ko ko yaya?" Murmushi tayi sosai tana kare masa kallo anya Dr Mahmoud yana kalau kuwa, ta sauke numfashi ta ce Dr Mahmoud ba zaka taɓa ƙanzawa ba, sannan ni banga dalilin da zan tsaya inayi maka bayani ba sbd ba zaka taɓa fahimtar komai ba, kawai abin da zan iya cewa think whatever you want. Ta ɗau jakarta tana ƙoƙarin fitowa yayi saurin tare ta ya tsaya yana huci ya ce "Dr Hamrah amma kinsan ina sonki kuma ina son na aureki kawai ina so na baki time ne zuwa wani lokaci na faɗa miki, amma ban san kina son kiyi aure yanzu ba da na fito cikin manema ki" Uhm Dr Mahmoud, i need to go Please mu bar wannan maganar bata da amfani yanzu. "Dr Hamrah please don't leave me, i really love you" Ganin Dr Mahmoud da gaske yake kuma ya dage sai ta fahimce shi yasa ta ajiye jakarta akan resting chair ta ɗago tana kallon sa, duk da bata san so ba, bata san raɗaɗinsa ba amma kuma ganin yanayin da Dr Mahmoud ke ciki ta tabbatar yana sonta, a hankali tayi magana cikin rage muryar ta ce Dr Mahmoud ai ban san kana so na ba kuma kaima kayi jinkirin sanar dani kuma kaga babu an sanya ranar bikina kuma kasan nema cikin nema haramun ne, dan haka inayi maka fatan ka sami wata kaima kayi aure. Kamar zayyi kuka, idanuwan sa sunyi ja dasu, shi kanshi bai tashi sannin soyyayyar ta tayi nesa cikin zuciyar sa ba sai cikin kwanakin nan yana jin sha'awar ta ne a cen baya amma bai taɓa tunanin zai faɗa a tarkon sonta ba, to yanzu ya zayyi dole ya hakura amma yasan zaiji jiki..... Dr Mahmoud bye, till tomorrow morning. Ta fice ta barshi nan tsaye ta tsaya a ƙofar office ɗin ya jima sannan ya fito ya wuce office nashi ta rufe office nata har zata juya sai taji muryar MD yana kiranta. Ta iso cikin office nashi cikin girmamawa ta ce Evening sir. Ya sauke numfashi ya ƙarashe tauna ragowar goron dake bakinsa ya ce "I heard you are going to be a Bride, what was the month" Uhm, yes sir at the end of this month. "Uhmm so good, amma dai ba irin na wankan karon za ayi ba a taramu kuma a watse ba tare da an ɗaura ba, ki sake dawowa bakin aiki bayan kinyi sallama da kowa" Ɗagowa tayi ta kallesa bata ce komai ba, ya cigaba da cewa "Za ki cigaba da aikin ne bayan kin yi auren ko kuma za ki sauya wani aikin?" I don't know. Ta bashi amsa a takaice ta ɗaura da cewa Zan wuce. "Okay" Ta fito tana mamakin MD da son abin duniya ya kwallafa rai akan wannan aikin kamar ba zai mutu ba. Tana fita ta iso gidan Zeenat cikin murna ta tare ta suka gaisa ita kaɗai ce a gidan ta kawo mata baby ta bata suna ta fira sai da aka kira magrib sannan ta miƙe ta shirya ta ce zata tafi gida. Kallon Zeenat tayi cikin sanyin jiki ta ce Zeenat tambayar ki nake son yi?. "Yaya Hamrah ina jinki" Sauke numfashi tayi ta ce Wacece baaba Hajara?" Cikin sauri Zeenat ta dago tana kallon Hamrah bakin ta na rawa ta maimaita "Baaba Hajara?" Eh ita, shin kinsan inda zan sameta ne?. "Uhm amma meyasa ki ke son saninta, kuma ina ki kaji ana ambaton sunanta?" Zeenat tayi mata tambayar da Daddynta yayi mata to hakan na nufin Zeenat tasan wacece Baaba Hajara dan haka ta ce Zeenat kada ki ɓoyemin komai tare muka taso cikin gida ɗaya kinsanni na sanki kinsan bazanyi abinda ba zai zamo daidai ba Please tell me ina zan ganta?. "Uhmm yaya Hamrah baaba Hajara ta jima da rasuwa nima a bakin Aunty maimuna naji suna firar amma maganar gaskiya basan dangantakar da take da ita damu ba amma kuma yadda naji suna firar ta na tabba tana da mahimmanci cikin wannan familyn" Sauke numfashi Hamrah tayi tana jinjina lamarin to baaba Hajara ta rasu to meyasa da ta ambaci sunan ta gaban Daddy hankalinsa ya tashi kuma meyasa bai sanar da ita ta rasun ba, ta kalli Zeenat ta ce Please do me a favor, i need to know more about her. Ta sauke numfashi ta jinjinawa Hamrah kai alamun to. Sukai sallama Hamrah ta fito ta dawo gida ta shiga ta tadda Ammie na sallah ishai ta wuce ɗakinta sai bayan ta idar da sallah ta fito ta wuce ɗakin Ammie ta tadda tana cin abinci nan ko Ammie ta sata saida ta ci suna fira suna ci sai da suka kammala sannan ta dawo ɗakinta tana jinta wasai cikin farin ciki, a hankali ta furta Alhamdulillah. Bacci yayi awun gaba da ita cikin farin ciki komai ya kusa zamowa karshe, itama tayi aure ta zauna a ɗakinta kamar yadda sauran yan'uwanta suke. _After 1week_ Auren Hamrah saura 3 weeks, sai shirye shirye ake yi su Ayshe da Zeenat kam ba zama duk rabi da kwatan siyayya su sukai mata su ce ta sayi abu kaza yana da kyau ita dai sai dai ta basu ATM nata suyi duk abin da ya kamata, tana fita aiki kamar yadda take yi Alhaji Sama'ila ma na zuwa zance ya koma. Kasancewar yau weekend ne ta shirya cikin doguwar riga ta habaya ƴar Dubai ta matukar yin kyau a cikin ta, royal blue ne ta fito bayan tayi sallama da Ammie ta wuce gidan su Shatu inda suke da zama ahalin yanzu daga nan suka wuce address ɗin da ƴar gold ta basu. Suna isowa suka kirata a waya ta ce su shigo aiko baki da hanci suka sake suna kallon cikin gidan a lokacin da gate man ya buɗe musu karamar kofa ta shigowa. Wannan shine aljannar duniya, danƙararren benine mai hawa uku wanda yaji ginin zamani, faɗi tsarin gidan da kuma kyaun sa ɓata lokaci wata ce ta fito cikin shiga ta mini skirt tayi musu jagora ciki, jikin Hamrah yayi sanya tun kafin ta ƙarasa ciki ta tabbatar wa kanta cewa faɗa da aljani baya sauki, lallai sai ta dage sannan ta samu ta showa kansu dan kam sunyi nesan da baza suji kiraba giyar kuɗi ta gama mamaye jinin jikinsu.... "Pretty barkanku da isowa bismillah ku ƙaraso cike" Cewar Hauwa'u Jibrin, sauke numfashi Hamrah tayi daga zurfin tunanin da ta shiga, suka hau makalan da Hauwa'u ta bi suka yi tattaki har zuwa babban palour dake sama, suka zauna Zainab ta fito cikin farin ciki ta rungumi Hamrah zata rungumi Shatu amma ta ƙi ko kallon ta Shatu ba tayi mai kyau ba ta ɗauke idanuwan ta, ita ko Zee ko ajikinta ta zauna nan ta bada umurnin akawo musu abin taɓawa. Rahma ma ta fito suka gaisa ta zauna nan suka taɓa fira suna basu labarin yadda kungiyar su ta sami ci gaba, daga bisani ko wacce tayi ciki ya rage daga Hamrah sai Shatu da kuma Hauwa'u Jibrin, Shatu ta miƙe ta sauko sbd ta baiwa Hamrah damar shawo kan ƴar gold, sai ke numfashi Hamrah tayi ta ce Ƴar gold wannan arziki haka na innalillahi wa inna ilaihi rajiun, daga ina ki ka samu sa kuma gidan nan na waye ne?. Murmushi ƴar gold tayi tare da tashi daga inda take zaune ta zauna kusa da Hamrah ta ce Ai wannan ƙaramin gidane daga cikin gidajena na nan Maiduguri ina dasu sunfi biyar sai kuma waɗanda nake dasu a wasu garuruwan, a jinki kuɗin da nake samu almubazzaranci nakeyi dashi a'a kadara nake ajiyewa sbd tsaro basan me zai faru nan gaba ba" Murmushi Hamrah tayi ta sake cewa To Hauwa'u batun aure fah?. "Uhm aure ai na wuce age na aure wa zai aureni kawai cigaba da harkan nan zan yi zuwa wani lokaci naga ya hali zayyi" A hankali Hamrah ta ɗaura hannunta kan na hauwa'u ta ce Hauwa'u Jibrin aure baya taɓa wucewa kuma bai kamata ki cire rai ga aure ba domin shi lokaci ne da lokacin yayi za ayi amma batun shekaru age is just a number, ko kin kai shekaru 50 za ki iya aura indai lokacin sa yayi, amma kuma menene dalilin ki na buɗe wannan kungiyar kuma nasan kina da tabbacin cewa abinda ki ke aikatawa kuskure ne.... "Hamrah kin zo muyi harkan nan tare ne ko kuma kinzo bincike" Murmushi Hamrah tayi cikin kulawa ta ce I need to know more about the ƙungiyar sbd nasan ta yadda zan fara. "Uhm yanzu naji batu. First and foremost, i came from the poor background family, we don't have anything, infact sometimes or somedays zan iya cewa muna wuni bamu ci abinci ba, ke ma shaidace sai nayi sati ina zuwa skul ba tare da na kashe ko 5naira ne ku ne ma kuke taimaka min na ɗan saka wani abin a bakina, muna cikin wannan rayuwar ce muka zana jarabawa ta zuwa senior set, da ƙyar na na wuce kuma a lokacin ne mahaifiya ta rasu, na sake sintar kaina cikin tashin hankali ga ƙannena mata har su uku kuma dukkanninmu mata ne, kawai sai Abbanmu ya ƙara aure, da farko muna zaman lafiya har na kammala secondary School nawa a lokacin ƙannena duka uku suka sami mijin aure, ya saura ni kaɗai na rage nan fah babu mashinshini gashi bani da kuɗin da zan ci gaba da karatuna, nan fah nake fuskar fitina kala daban daban na matar ubana har ta kaiga ta shiga sakanina da mahaifina tsam ya tsaneni, damuwa tamin yawa na nemi shawarar wata ƙawata da muke kawanci irin na unguwa haka tana da aure an unguwar tamu, shine ta bani shawara muje wajen mallamin da yayi mata aiki har ta sami mijin aure. To zuwanmu karon farko yace bakin iska gareni kuma ya aureni bazai bari nayi aure ba dan haka ni da aure har abada. Da farko na karaya amma kuma daga baya na sake ce mata inda wani takaini shine ta kaini wajen wani shi kuma ya ce matar ubana ne ta tura min iskar, kuma ya ce zan auro amma ba nan kusa ba. Na hakura na zauna na zubawa sarautar Allah ido, ga tashin hankali da nake fuskata a gidanmu ta wajen Abban da kuma matarsa har ta kaiga bata bani abinci gashi ba wata kwakkwaran sana'a ce dani ba, na lalace kamar wacce tayi jinya ta shekaru 2 haka dai na dinga lallaɓa rayuwa ta kwasam watarana da bazan manta da ita ba, ina zaune a gida akace ana sallama dani, na fito sai ganin wani mutum ne a tsaye muka gaisa nan take sanar dani yana so ne nayi masa hanya na haɗashi da wata ƙawata da take gaba da layinmu to ban san komai ba a tunanina neman aurenta yake nayi mishi hanya suka fara soyyayya kawai tashin farko ya bani kyautar 100k na kiɗime sbd ganin kuɗin, na boyesu ban nunawa kowa ba na dinga amfani dashi a hankali ina cefanena wasa² sai ko abin ya fara girma sai sumin magana da abokan sa ni kuma na haɗasu suna bani kuɗi daganan abin ya koma sana'a lokaci guda nayi kuɗi ni ke juya gidan da Abbana da matarsa suka koma yimin biyayya nan na sake musu bakin aljuhu daga nan kuma sai ko na daina zama a gida ni ma na faɗa a harkar sbd shi wannan mutumin ne ya fara lalata min rayuwa ya buɗe min ido nasan me duniya take cike, to daga lokacin na fara fita outside anan na haɗu da Zee muka sake kulla abotar da muka fara a secondary School shine muka buɗe wannan kungiyar ta taimakon mata da suke fama da irin tamu matsar minti nesa cikin wannan harkar sannan muka haɗu da Rahama muka sake habbaka abin amma ita Rahama matar aure ce" Shuru Hamrah tayi tana kallo da kuma saurari abin da ƴar gold ke faɗi, itama Hamrah take kallo ganin ta zuba uban ta gumi ta cire tare da cewa "A wannan yanayin ki ke tunanin zan sami mijin aure tab da wuya shiyasa ban taɓa tunani ba balle kuma na saka yuwar hakan cikin raina" Sauke numfashi Hamrah tayi tare da ɗaura hannunta kan na Hauwa'u ta ce Hauwa'u waye ne ya halicce ki?. Cike da mamaki ta ce " Allah mana" To waye kuma ya halicci su mallamai ko ince bokayen da ki kabi suka ɓatar dake, dole nace bokaye mallamai magadar annabawa ba zasu taɓa faɗin hakan ba sai dai su dauraki kan hanya mai kyau ta yadda zaki bi har ki rabo da dukkanin cutar da take damunki amma ace ba zaki taɓa aure ba har abada bacin akwai aya cikin Alqur'ani da take cewa Allah bai saukar da cuta ba sai da ya saukar da maganin ta. Babu cutar da bata da magani, ɗaukan su waɗannan bokayen da ki kayi a matsayin kin yarda da su shine ki ke ganin ba daidai ba sbd Allah baya ɗaurawa bawansa abin da ba zai iya ba da kin jure kin miƙa al'amuran ki gareshi da kinga kyakkyawar ƙarshen KADDARAR ki........... ________________________ Ina matukar godiya da addu'oin ku. Kada ku manta har yanzu muna cikin shimfiɗa ne na wannan littafin mai suna MUJARRABI (Age is just a number) asalin labarin na gaba ku dai ku biyoni dan jin abubuwan da ya kunsa. Littafin book 1&2 ne muna dab da ƙarashe book 1 in shaa Allahu. A dinga hakuri da typing errors, bana samun time na gyarawa. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 37 & 38 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* __________ sauke numfashi Hamrah tayi ta kalli Hauwa'u cikin damuwa da kuma tausayawa labarin rayuwar ta itama shaidace na ganin irin rayuwar wahala da kuma tashin hankali da Hauwa'u ta fuskanta a lokacin da suke secondary School, duk da a makarantar kuɗi suke wato private skul dan a lokacin marigayiya ummanta ke biyan kuɗin makarantar, tana da tabbacin bayan mutuwar uwar ne ta faɗa cikin ƙuncin rayuwa mai tsanani har ya kaita ga faɗawa cikin wannan yanayin. Amma bazata nuna mata cewa tana tausayin ta ba yin hakan zai sake jefa rayuwar ta cikin son ci gaba da wannan harkan kuma ita gani take tana kan daidai bata da laifi yana yi ne ya jefa ta cika. Tabbas akwai yanayin da yakan zo wa mutum yarasa mafita ya rasa masu goya masa baya wajen janyo sa jiki dan a gano matsala a taimake sa wajen bashi shawara da kuma kwantar masa da hankali amma anzo zamanin ko in kula kowa kansa ya sani babu ruwan wani da wani babu taimakekeniya a sakaninsu.... "Amma pretty kinsan su mallamai ma suna faɗin gaskiya kuma cewa da akayi bakin aljani ya aureni gaskiya ne ina kallon shi cikin bacci na kuma muna mu'amala kamar mata da miji sannan kuma gashi na kasa auruwa to kinga maganar su gaskiya ce. Allah shine ya halicci mallamai kuma ya basu sani shine suke taimakon ire-iren mu matsu matsala. Mu da kike gani irin tamu kaddarar ce da man tun farko a rubuce yake sai munyi irin wannan rayuwar dan haka ki daina ɗaura mana laifi" Ajiyar zuciya ta sauke ta sake gyara zamanta ta kalli ƴar gold sosai na wani lokaci sannan ta ce Ƴar gold ki dawo cikin hayyacinki, tabbas faɗin bakin aljani ko bakin iska gaskiya ne, amma cewa da mallamanki su kayi akan cewa ba zaki taɓa auruwa shine kuskure sun shiga lamarin Ubangiji sun yanke hukunci, shine kaɗai yasan da cewa zaki auro ko bazaki auruba, duk tsanani yana tare da sauki duk mai hakuri yana tare da nasara. Tabbas tun kafin a haifi kowa wane bawa an rubuta kaddarar sa amma ki sani Allah na duba zukatanmu taka niyyar mu kuma ya kawo mana sauki, da bakiyi garajen yarda da abin da su Mallam suka faɗa miki ba da duk hakan bai faru ba sannan kuma ƴar gold akwai ƙarancin addu'a a tare dake da kuma tawakkali, da kin je Islamic medicine kinyi musu bayani ba zasu ce sai sunyi duba ba kawai zasu haɗa miki magunguna na ko wanne fanne kiyi amfani dashi kuma ki dace, bance na gargajiya haramun bane amma da yawa daga cikin su na kai mutum halaka kamar yadda kema yanzu kina cikin halaka, sannan ma indai har kina da wannan laruri na bakin iska hakan na nufin babu wani ɗa namiji da zai kusance ki to ya akayi su na bariki suke taraiya dake mesa bai hana su ba, kinga da ayar tambaya anan so, Please don't ever believe on that...... "Pretty kenan baza ki taɓa fahimtar hakan ba sbd baki fama da larurar ce amma ba komai bari na kawo muku abinci yanzu kam Laure ta kammala" Murmushi Hamrah tayi ta ce Uhm Hauwa'u ai nima ina da wannan matsalar ta jinkirin aure amma kuma rashin bibiyar diddigi da banyi ba Alhamdulillah I'm safe daga rabamin kai da za a dinga yi. To ba damuwa ina Shatun ne?. Shatu na cen kasa tana ta kaiwa da komowa duk gidan ya gundureta tana mamakin yadda mutanen yanzu sun manta da mutuwa da kuma gamuwarsu da Ubangiji da yawa sun manta cewa akwai tsayuwar kiyama.... Shatu ki hau mana tun ɗazu nake raba ido ko zan ganki ashe kina nan kasa. "Kun gamane mu tafi, hankalina na gida" Murmushi Hamrah tayi ta ce Ƙaraso mana Bestie. Shatu ta hauro ba dan taso ba suka haura sama suka zauna a palour ta kalli Hamrah ta ce "Da fatan an dace?" Uhm tukuna. "Na faɗa miki ai sunyi nesa babu wanda ya isa ya kira su waigo ɓata lokacin mu kawai mu keyi" Bestie babu abin da tafi ƙarfin addu'a da kuma nasiha yau da gobe tafi ƙarfin wasa, kyamatarsu da zamuyi sake tunkuɗasu cikin halaka ne zamu yi, na faɗa miki ki barmin komai a hannu na. I'll handle it. Ƴar gold, Rahama da Zee suka fito tare da ɗauke da niƙe niƙen food flask na abinci suka ajiye akan Dining area sukayi musu su taso su ci Hamrah ce ta miƙe ta iso wajen amma Shatu ko kallo basu isheta ba, Hamrah tayi hakan ne dan su saki jiki da ita, juice kawai ta shafa sannan su masu aikata irin wannan abin ba najasa bane su kawai ɓatan kai ne ya samesu da kuma rashin neman sani. Wunin ranar a gidan Hauwa'u Jibrin su kayi ta, Hamrah ta miƙe ta shige kitchen tana kallon yadda tsarin kitchen ɗin yayi matukar kyau sai ga Rahman ta shigo ɗauke da tea cups wanda su kayi amfani dasu shine ta kawo ganin Hamrah a tsaye ta ce "Pretty ashe kina nan, da akwai abin da ki ke so ne?" Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce A'a Rahama, amma nayi mamaki da akace kina da aure kuma kina cikin wannan harkar abin da ɗaure kai to menene amfanin aurenki in dai kina son wannan harkar kamata yayi ki sauke nawin auren da kuma darajar sai ki shigo amma yin hakan kuskure ne babba. Murmushi sosai Rahama tayi ta ƙurawa Hamrah manya manyan idanunta ta ce "Uhm da aurena gwamma babu shi, babu macen da bazata so zama a ɗakin aurenta, rufin asirinmu mu mata shine ɗakin mazajen mu to amma kuma wani lokacin sune ke sanya mu muke aikata wasu abubuwan duk canji da za ki gani daga mace to babu tantama miji ne ya sauyata, wasu mazan suke rugurguzawa mata rayuwar su. Pretty na tsani rayuwar aure babu komai cikin sa sai tashin hankali da kuka da takaici..... Subhanallah! Bai kamata ki faɗi hakan ba sbd aure ba abin wasa bane ta hanyar aure ne hanya mafi sauki samun shiga aljannar mace, sannan duk abin da ki kaci karo dashi a gidan aurenki jarrabawa ce da kinyi hakuri kin jure sai kiga daga karshe kece da riba amma batun munanan kalamai ga aure kuskure ne sbd aure turɓane ta bautar Ubangiji. Amma menene dalilinki na faɗin haka meyasa ki ka zaɓi wannan hanyar baki nemi wata ba shin ina mijinki da kuma ƴaƴanki?. Jan ɗaya daga cikin kujerun dining table dake kitchen Rahama tayi ta zauna tare da cewa "Have a sit pretty, amma kuwa kinsan yadda ki ke da kyau su ƴar gold naji suna faɗi sai da nagani kuma naga ya wuce tunani na, kai gaskiya Masha Allah" Murmushi Hamrah tayi ta ce Rahama bani amshoshin tambayoyi na. Sauke numfashi Rahama tayi ta ce "Ni haifaffiyar Kaduna state ce, ban taɓa zuwa Maiduguri ba ban san ya take ba aure ne ya kawo ni zan iya cewa sanadiyyar aure ce na san Maiduguri. Soyayya ce mai karfi sakanina da Ahmad yana matukar kaunata sai dai a lokacin bashi da sana'a tsayayya a shogon wani yake ma'ana a karkashin wani yake aiki, haɗuwarmu a sali a facebook ce kuma karon farko da soyayya ya tunkare ni kamar da wasa yaje garin Kaduna muka haɗu, to tun daga lokacin muka sake kulla dankon soyyayya mai karfi, sai kuma maganar aure ta taso amma iyayena suka ce ba zayyu na aure shi ba nayi nesa da gida sunyi sunyi su rabamu abin yaƙi. Daga karshe dai suka amince amma da sukaji a karkashin wani yake suka sake cewa ba zayyu ba, ina ƴar gidan masu kuɗi na auri talaka kuma wanda bashi da tsayayyen sana'a dan haka ya ƙara gaba. Kuka na dinga yi musu har suka amince aka ɗaura aure da ƙyar aka samu aka kawo ni dakina shima ni na biya kuɗin kawowa dan na rufa masa asiri, ɗaki ɗaya ya kamamin sauran kayana aka koma dasu dan sun fi karfin gidan, ban damu ba haka na hakura har na haihu diyata ta fari ni nayi suna to haihuwa mai albarka albarkacin haihuwa ya samu shima ya buɗe shago a kasuwa ya dogara da kansa har ya kaiga muka samu muka tashi daga wannan daki dayan muka koma ciki da palour ya samu ya canja min kaya, muna lallaɓa rayuwar mu har muka sami ƴaƴa hudu. Alhamdulillah hankalina ya kwanta zuwa wancan lokacin aka daina goranta min. Kasuwarsa ta sake habbaka har ya gina mana dankareren gida flat, a lokacin da muka koma na haifi ɗiyata ta biyar. Daga nan rayuwa ta sauya na daina gane kan Ahmad kwata kwata baya son ganina na sha matukar wahala wajen hakuri da kuma janyo hankalinsa kaina, da ƙyar na samu nayi hakan. Sauke numfashi Rahama tayi tare da zubda ƙwalla a lokacin da ta tuno da tashin hankalin da ya faru da ita ta ce "Watarana da yammaci ya shigo min da luggage riƙe a hannunsa na miƙe cikin girmamawa na karɓa ina ƙoƙarin shigewa dashi ciki sai nayi la'akari da wacce ke shigowa ta ƙaraso tare da gaidani na amsa tare da cewa bakuwa mu kayi, ya ce eh "bakuwa ce" nayi mata isowa ciki na bata ruwan sha ta sha ya bata ɗakin da yake bama amfani dashi, sai cikin dare yake sanar dani cewa ƴar baffansa ce sunyi hutun skul tana karatu a unimaid za tayi kwana biyu sai ta wuce Ummah sa ta sani. Nan na hau hidima da ita har tsawon 1week to ganin yadda take sakin jiki dani yasa nima na saki raina tana taimaka min sosai. To bayan kwanaki biyu sai naga Ahmad na yawan tashi daga bacci cikin dare ya fice tun hakan bai damuna har ya fara kwasam rannan sai nace zanga me yake yi, yana fita na tashi nabi bayan shi abin da ya bani mamaki shine ganin ya doshi ɗakin wannan yarinyar da ake kira da Fateemah, kamar zan bi bayan sa kuma na fasa na dawo ɗakina na kwanta cike da mamakin me ya kaishi ɗakinta ina cikin tunanin naji ya shigo a lokacin awansa 1 da rabi, kamar zan tambaye sa amma nayi shuru. Gari ya waye na fara observing nasu sai kuma nake fahimtar wani abu na daban yana yawan kallonta su sakarwa juna murmushi, a daren ranar na ce kai sai naga me suke nufi ne kuma me suke ƙullawa na, yana fita da 10 minute's nabi bayansu. A hankali na tura kofar abin da naci karo dashi ne ya gigitani kusan 5 minutes brain nawa ya daina aiki jikina da a lokacin za a saga dako ba za a sami ko da ɗigon jinine na matukar kaɗuwa, ina karanta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sannan na fara dawowa daidai. Mijina kwance kan ruwan cikin Fateemah suna aikata zina a gidana a kuma ɗakina da kuma gadona, wata zuciyar ta ce na watsa musu ruwan zafi. Wata kuma ta ce na kashe su na huta, amma kuma da ikon Allah na sake daurewa na fito cikin tashin hankali na komo ɗakina ina ta sake² cikin raina na irin matakin da zan ɗauka, sai kuma wani tunani ya faɗo min na cewa in kuma sun san nasan me suke aikatawa suka kasheni fah suke ɓarayi ne suka shigo, to in dai Ahmad zai shigo da dadironsa cikin gidana babu abin da zai hanashi kasheni... Ina cikin wannan tunanin ne ya shigo ya wuce toilet ya watsa ruwa ya shirya ya dawo ya kwanta ganin idanuwana biyu yake tambaya ta me ya hanani bacci kamar na shake sa ya mutu amma na daure na bashi amsa da eh. Washegari na shirya na ce ta rakani muje gidan iyayensa amma fir ya ce bazata je ba sai dai ni kaɗai na tafi, nan na gama fahimtar komai sai na shiryawa mahaifiyarsa da ƙannensa waleema na ce suzo ba tare da ya sani ba, kawai kwasam sai yaga sun diro cikin gidan ...... "Hamrah magrib ya kawo kai ya kamata mu tafi" Cewar Shatu ta katse Rahama da labarin da take baiwa Hamrah wacce tayi suman zaune da jin wannan labari, ta sauke numfashi cikin sanyin jiki ta kalli Shatu ta ce Gani fitowa. Shafu ta koma Hamrah ta ce da Rahama Zan dawo nan da kwanaki biyu sai ki ƙarashe min. "Ba komai a gaida gida" Hamrah ta amsa sannan ta fice zuwa palour. Nan su kayi musu sallama suka fice akan sai zuwa nan da kwana biyu zasu dawo Hamrah suka dawo Shatu ta wuce gida. _Bayan kwanaki biyu_ Hamrah ce tsaye bakin titi tana jiran ɗan sahu zata shopping na mayyukan gashin kanta, daman sunyi waya da Shatu akan zata biya mata su wuce, har ta tari ɗan sahu kuma sai ga kiran Abuja ya shigo tayiwa mai a daidai yayi hakuri ya tafi da hannu tayi masa alama, ta koma gefen hanya ta ɗauka tare da sallama ya amsa ya ce gashi zuwa gidansu ta sanar dashi tana hanyar tafiya shopping ya ce ta jirashi nan ta sake sanar dashi ya bari zuwa gobe zata wuce gidan ƙawarta Shatu amma ya nace sai yazo haka ta hakura yazo ya ɗauke ta suka wuce gidan su Shatu, ta kallesa ta ce Bari na shiga sai mu fito ko?. Kai ya gyaɗa mata alamun to. Ta shige ciki suka fito da Shatu cikin girmamawa shatun ta gaida shi ya amsa cikin fara'a tare da cewa "Yauwa yau na haɗu da kawar matata wacce zamu dinga shawara game da bikin" Murmushi Hamrah da Shatu suka yi shatun ta ce "Aiko nima nayi farin cikin haɗuwa da mijin bestie nah" Suka shige motar ya tada ta yake tambayar su wane shop suke son zuwa nan Shatu ta sanar dashi amma kuma sai ya kaisu wani babban shop a tare suka shigo sukai siyayya ya dinga jido musu kaya kamar babu gobe, suka fito bayan ya biya ya riga su fitowa tare da wani ma'aikacin wajen ya taimaka masa ya fito musu da sauran kayayyakin. Shatu da Hamrah na ƙoƙarin fitowa sai su kayi kicibus da su yar gold, cike da mamaki Zee ta ce "Aminai an fito siyayya kenan?" "Uhm fah Zee kuma ku kayi balle kuma mu" Bata fahimci abinda Shatu ke nufi ba Hamrah ta ce Da mutum muke tafe kada ya jiramu yaga mun daɗe. Juyowa suka yi lokaci guda, suna kallon motar cike da mamaki ƴar gold ta ce Kamar nasan wannan motar............ Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 41 & 42 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ Kallonta Hamrah keyi tun da ta shigo ta ganta ta soma bala'i bata ce komai ba sai dai tayi mamaki a ina taji zancen za tayi aure ita Hamrah ba wasu kawaye ne da ita ba ballantana zancen aure ya bayyana kuma ba wasu ƙannene da ita ba waɗanda za a ce su suka yaɗa sbd yarinta, ƙannenta duk sunyi aure kuma ba masu yawan yawace² bane. Bata so ƴar gold ta san da zancen aurenta ba tafi son ayi sa cikin sirri har ta kammala abin da take so cikin kwanaki kaɗan amma ba komai ko a hakan ma tasan za tayi nasa ko bajima ba zasu gano gaskiya su dawo kan turɓa madaidaiciya. Ta sauke numfashi a daidai lokacin da ƴar gold ta ƙaraso ta zauna ta tsareta da idanuwanta ita a dole anci amanar ta, murmushi Hamrah tayi ta ce Ƴar gold, sannun ki da gajiya ban ma jima ba da shigowa, Rahama ke faɗa min kina hanya.... "Dakata Hamrah ki fara bani amsar tambaya ta wai shin da gaske this week za a Daura aurenki?" Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce Eh Hauwa'u abin da ma ya kawo ni kenan... "Ba wani pretty daman cen da wata manufa a ƙasa, yaudarar mu ki ke son yi, in ma ita ce to ki sani ko da aurenkinne ma za ki ci gaba da wannan harkar" Uhm. Cewar Hamrah, Zee ta ce "To ai daman tasan da hakan kawai dai auren da za tayi a matsayin kariya ce daga idon al'umma" Rahama zaune duk jikin ta yayi mata sanyi da abinda Hamrah ta faɗi mata, a hankali ta ce "Ai aure ba matsala bane muma ai yana kanmu kuma muke harkar, zata iya fitowa ayi da ita kawai a bata sati kan cin amanar ci tana gamawa sai ta fito" "To na ji wannan shawarar amma tunda taji sirrin mu ya zama dole ta zauna ayi harkar tare amma cewa zata bari bazata ga daidai ba" Cewar Hauwa'u Jibrin, ita dai Hamrah bata ce komai ba, bata jima ba ta fito ta dawo gida, a ƙofar gida ta tadda Alhaji Sama'ila a tsaye a kofar gida yana gingine cike da mamaki ta iso inda yake yana ganinta ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce "Wayar ki bata shiga duk na damu, tun ɗazu nake nan na rasa wanda zan aika shi cikin gidan ya kiramin ke" Ajiyar zuciya Hamrah ta sauke tare da ciro wayar ganin network ne ya ɗauke ta ce Wayar a kunne take service ne ya ɗauke. "Ok shigo mota" Ta zagaya ta shiga suka zauna jikinta duk yayi sanyi ta zauna cikin sanyin murya ta ce Amma lafiya ko?. Ya juyo sosai yana kallon ta na wani lokaci sannan ya ce "Em nazo ne na baki kuɗaɗen da zasu isheki, sannan kuma kinsan ba a garin nan zamu zauna ba a cen Abuja ne, dan haka bana son ƴan rakiya dake kaɗai zamu tafi kuma bana son tarkacen kaya ina da komai cikin gidana" Ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce To zanje muyi shawara da yan'uwana duk yadda mu kayi sai na sanar maka.... "A'a Hamrah bana son hakan shiyasa tun farko na faɗawa maneman auren cewa bana bukatar komai daga wajenku sbd bana son yawan magana ne kawai muyi maganar nan a sakanin mu, ke ba yarinya bace da zamu tsaya muna cece kuce kawai maganar ta zauna a haka" Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce Gaskiya, maganar gaskiya wannan ba al'adar Maiduguri bace kamar yaya zan yanke hukunci da kaina, bayan bani ce zan aurar da kaina ba, zancen akaini babu kayama bai taso ba dole sai amin duk abinda ake yiwa ko wacce amarya. In yaso ko daga baya ne sai akai min cen ɗin. Amma menene dalilinka na son na tafi babu kaya kuma babu ƴan rakiya?. Ganin ranta ya tsoma ɓaci yasa ya rage murya ya ce "Shikenan ayi miki kayan, amma daga baya sai a kawo miki, bani account number ki sai na tura miki kuɗi" To. Ta faɗa ta bashi sannan ta shigo cikin gida bayan sunyi sallama, mai Alhaji Sama'ila ke nufi ne. Har ta shigo cikin nan ta tadda Ammie a palour tana zaune tana ta shirya kayayyakin da tasa a kawo. Zama Hamrah tayi cikin sanyin murya ta gaida ta Ammie barka da yammaci?. "Barka dai Hamrah kinga yanzu babanninki suka tafi kalli abin arziki da suka kawo min nan, kai amma sunyi ƙoƙari sosai" Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce Ammie, yanzu Alhaji Sama'ila ya tafi. "Ah to madalla. Amma fah ya ce wai baya son a haɗani da kayayyaki komai akwai acen, kuma babu ƴan rakiya, Ammie na fara jin tsoro. Murmushi Ammie tayi tare da cewa "Ke zolaya ce, giyar wake muke sha da za ace a kaiki babu komai shima kawai faɗa yayi ai sai anje anga masaukinki" A hankali Hamrah ta sauke numfashi jin abin da Ammie ta ce, dan haka ta miƙe ta shige cikin ɗakinta, ta watsa ruwa ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah har aka kira ishai ta idar ta kwanta. Cikin dare ta farka duk tayi gumi taba sauke numfashi zuciyar ta nata harɓawa sbd mummunar mafarkin da tayi, ganinta tayi cikin daji ita kaɗai dajin naci da wuta babu kowa tana ta neman masu cetonta amma babu har wutar ta kusa dab da isowa inda take shine ta farka ta sauke nauyin ajiyar zuciya. A hankali ta furta Mafarki ba gaskiya bane. Ta tashi ta ɗaura alwala tayi addu'ar bacci ta kwanta. Washegari tun da ta tashi ta idar da sallah asubah ta koma bacci. cikin bacci taji ana tattaɓata ta buɗe ido little Hamrah ce ke zaune kusa da ita da murmushi ta rike hannunta tare da cewa Namesake saukar yaushe?. Turo baki little Hamrah tayi ta ce "Da Mommy na muka zo tana ɗakin granny" Turo ƙofar da sallama Ayshe tayi ta shigo ganin little Hamrah ta ce "Au nan ki ka shigo ina ta duba ki" Hamrah dake kwance ta miƙe ta zauna cikin sanyin murya ta ce Aiko ita ta tadani da ko yanzu ina ta bacci. "Kema ki shirya yaya Hamrah ki fito mai gyaran jiki ta iso zaku fara tun kan rana tayi zafi" Uhm kai Ayshe wane gyaran jiki kuma, ai bikin da saura. "Wane da saura this coming Saturday nefa yau kuma Sunday please get ready, muna cen baya sai kin fito" Ayshe ta ɗauki little Hamrah suka fice. Hamrah ta shige toilet ta yi brush sannan ta fito tayi inda suke. Anan suka wuni akaiwa Hamrah gyaran jiki wuni daya tayi matukar kyau sai sokanata suke tana murmushi har suka watse. Biki saura kwanaki uku duk ƙannena ta suka tare a gida, gida kam cike yake da baki kamar aranar ce za a daura ƴan kauye ma duk sun hallara. Hamrah tayi matukar kyau kamar ba ita ba Ayshe ce tayi mata rakiya zuwa saloon aka gyara mata gashin kanta sbd ba zai kitsu ba yana da yawa da tsawo da kuma tsantsi. Ana washe gari biki akayi mata kunshi da kuma lalle tayi matukar kyau. Zaune suke bayan sallar la'asar suna fira su Ayshe sai sokananta suke wai ta Alhajin Abuja mai komai dozen, ita dai sai murmushi take yi, suka ji daga waje ana marhaban mutanen ABGANISTAN. Aiko su Ayshe, Zeenat da Maryama suka fice daga ɗakin Hamrah sbd yiwa yayansu oyoyo sai da da fitarsu suka dakata tare da tsayawa kallon shi, sbd yadda yayi wani haske da kiɓa kamar wani Balarabe ko ba India ya koma tamkar jarumannan na indiawa masu faffaɗan ƙirji da shanyeyen ciki, sanye yake da riga read da kuma ba Black trouser sai kuma bakin agogo, fuskar nan ta fito rau da kwantaccen saje da size box, gashin kannan yasha gyara kamar na larabawa. Murmushi ya sakarwa kannensa ganin yadda suka tsura masa idanuwa suna tantama shine ko ba shi ɗin bane. A hankali cikin silent voice ya ce "Ina amaryarmu take?" Suka ƙaraso tare da cewa "Ya Ammar tana ciki" Suna tayi masa sannu da zuwa kai tsaye ya shige ɗakin Hamrah ya tadda tana zaune kasan carpet ganin shigowar sa yasa ta sake baki tana kallon sa irin kallon nan na saukar yaushe. Murmushi yayi ya iso ya zauna kan kujerar gaban mirror ya ce "A jinki ba zanzo bikinki bane ai ko in bana nan baza a ma daura ba sai na zo" Dariya tayi ta ce To alwalina, tunda kazo barka. Ya hanya?. "Alhamdulillah, ya shirye shiryen biki kuma?" Anayi. Sun ɗan taɓa fira ya miƙe ya wuce ɗakin sa ya watsa ruwa sannan ya fito ya wuce wajen Daddyn shi sbd tattaunawa kan yadda zasu tsara gidan sbd taron da za ayi na ɗaurin auren. Har dare su Ayshe na ta sokanar Hamrah abin da ya basu mamaki shine yadda gidan ya cika makil da mutane har da wasu ƴan uwan su da basu taɓa gani ba, Hamrah tun tana gaisawa dasu har ta gaji duk tayi laushi, ta zame jikinta ta dawo ɗakinta ta zauna. Ammar ne ya turo ƙofar ya shigo ganin sa yasa ta tashi ta zauna. Zama yayi bakin bed tare da cewa "Baki kwanta ba ashe, nima sai yanzu na shigo ina cen wajen Daddy wani abu naji wai meke faruwa ne me wannan Alhaji yake nufi da wai baya buƙata ƴan rakiya ya turo wani dattijo wai gobe da yamma za a tafi dake masaukinsa kuma wai baya buƙata ƴan rakiya a ina aka taɓa yin hakan?" Sauke numfashi Hamrah tayi tare da cewa Ya turo da wani kuma Ammar?. "Eh Hamrah, ba kuyi magana bane" Ta sauke numfashi ta rasa gane kan Alhaji Sama'ila meyasa baya bukatar ƴan rakiya me kuma na cewa ita kaɗai zata je masaukinsa wane masaukin kenan yake nufi shin ya tanada mata inda zai ajiye tane ko kuma menene... "Ya kinyi shiru?" Ammar munyi magana amma na ce dashi ba zayyu ace babu ƴan rakiya ba shine ina ga ya tura wani. "Gobe zan yi mashi magana kamin a ɗaura auren" Sun jima suna fira sannan ya fice zuwa ɗakin shi. _WASHEGARI_ Gida ya kauraye da hayaniyar hidiman biki sai kaiwa da komowa ake yi su Ayshe kam sai rawar jiki suke ana auren babbar yaya, an kashe Naira iya Naira bikine wanda ba a taɓayi ba Daddy ya buɗe bakin aljihunsa yana zubda Naira karfe 11:00 am aka ɗaura auren Hamrah da kuma Alhaji Sama'ila, akan sadaki 15 million, wuni akayi ana hidima har 4:00 pm aka kawo kayan akwatin Hamrah dozen biyu dukkanin su cike da kayayyaki na gani na faɗa da key mota a cikin kid na dankunnayen gold nan akayi ta murna ana ta sanya albarka. Sai dab magrib motar tazo kwalli ɗaya wai anzo ɗaukan amarya nan hankalin kowa ya tashi akace ba zayyu ba sai anga inda zai ajiye ta, aka kirasa ya ce a hotel zasu kwana da safe zasu hau jirgi su wuce Abuja amma akace ba zayyu ba da ƙyar aka amince masa shima sbd yace da safe masu rakiya su shirya sai azo a ɗauke su. Hamrah kuka kaman ranta zai fita Ammie ce ke rarrashinta tare da banbaki, ganin Ammie ta sanya baki yasa ta ɗan sagaita kuka ta shirya aka fito da ita aka sanyata cikin motar abin da ta bata mamaki shine babu kowa a cikin motar sai driver kawai tana shiga ya tada motar kai tsaye sai a hotel ya direta ta baya yayi mata jagora suka shige ta tadda Alhaji Sama'ila zaune cikin manyan kaya sai ƙamshi yake yana ganin ta ya miƙe ya riko hannun ta zuwa bakin bed ta sudda kai ƙasa tana wasa da zoben gold ɗin dake hannunta ya rike hannunta tare da ɗago dashi ya ƙurawa lallen ido yana jujjuya tare da shafawa. Ta sauke numfashi a lokacin da ya janyo ta cikin jikin shi tare da ɗago da habarta ya kura mata idanuwa, a hankali ta sauke nata idanun sbd ba zata iya jure ganin nashi jajayen nan ba duk a tsorace take. Babban yatsan hannun sa yakai kan bakinta yana shafawa a hankali, ta ɗago ta kallesa zuciyarta na harbawa, idanuwanta sun ciko da kwallah kamar zatai kuka murmushi ya sakar mata tare da cewa "I'm sorry dear" Bata fahimci mai yake nufi da kalmar ba a hankali tana kokarin zamewa daga jikinsa ya sake riketa gam tare da zame mata ɗankwalin lace ɗin kanta, bayyanar gashin ganta da yayi yasa ya sauke numfashi tare da bin gashin yana shafawa hannunsa ya soma rawa abin da bai taɓa yi masa ba. Gaskiya wannan lady special ce, kokari zuge mata zip na rigar ta da yake yi ne yasa ta rike hannun sa tare da yin magana muryarta na rawa ta ce Ba muyi sallah ba kamar yadda ake yi. Lumshe idanuwan sa yayi ya buɗe tare da sakar mata da murmushi ya shafi gefen fuskar ta yayi jin laushinsa yasa ya sauke numfashi tare da cewa "Yanzu na idar da sallah kuma na sanya ki cikin addu'a so no need sai mun sake yi" Daram ƙirjinta ya buga me yake nufi, ita dai tasan ana yin raka'a biyu na godewa Ubangiji kafin a kwanta amma meyasa Alhaji Sama'ila yaƙi suyi, ba tayi aune ba taji ya zuge zif na rigar ta tare da sanya hannu ya cire mata rigar da kuma kunce zanin. Jikinta ya tsoma rawa yayi saurin kai bakinsa kan labbanta ya soma tsosa kamar tsohon maye. Tsoro da fargaba yasa jikinta rawa, ga yunwar dake addabar ta wunin ranar ba abinda ta saka abaki anyi² taci abinci ta kasa ci. Sosai yake sarrafa ta ita dai banda rawar da jikinta keyi ba abinda tayi. Ya miƙe ya barta kwance ya cire dukkanin kayan jikinsa ya tsaya yana kallon ta duk ta tashi hankalin ta ganin ƙaton tumbinsa da kuma manyan nonuwansa kamar mai shayarwa yasa ta fara zubda ƙwalla a tunanin ta zai kashe wutar ɗakin ne amma taga ya hayo kan bed ɗin ya kai mata danƙa kamar a old hungry Lion, a hankali bakinta na rawa ta ce Dan Allah, kayi min a hankali ban taɓa yi ba wallahi tsoro nake..... Kan ta karasa ya rufe bakinsa da nata yana masa shan rake a tunaninta horo man ne yana so ya zuƙi jininta. Nan ta fara kokarin kwatar kanta a hankali ya zame bakinsa ya kalleta da jajayen idanuwan sa ya ce Hamrah wai meye haka ne?. kinsan dogon lokaci da na naɗauka ina jiran wannan ranar, bana son haka ki barni na dirji kuɗina in kuma ki kayi kaddama ke jikinki zai gayawa" Bakinta na rawa ta ce Dan Allah... Amma yaki saurara mata, yana dab da shigar ta kuma hakan yazo daidai da kusan ta shiɗe sai taji ya dakata ya ɗanyi shuru na wani lokaci sannan ya dago da fuskar ta yana mata kallon mamaki tare da yin magana cikin rawar murya ya ce "Are a virgin?" Kirjinta ya kara bugawa daman me ya ɗauketa cikin sanyin jiki tare da rawar murya ta kaɗa masa kai alamun eh. Ya sauke numfashi tare da cewa "I'm really sorry" Daga nan bata sake sanin inda take ba sbd sumar da tayi. 10:00am, a hankali taji kamar ana tattaɓata ta buɗe idanuwanta da su kayi mata nawa da ƙyar tana bin inda take da kollo a hankali komai ya dawo mata, ta ɗan juyo taga Alhajin da yake ƙoƙarin tada ta kuma sai taga akasin haka, ta sauke idanuwan ta kan wata ƴar budurwa sanye take da jan riga polo da kuma bakin skit sai face cap. Da alamu ma'aikacinya ce a wannan hotel ɗin a hankali tayi magana sbd yadda zazzaɓi ya rufe ta da kuma ciwon kai da yunwa ta ce "Kina son abu ne?" "A'a turoni akayi na gyara wannan room ɗin sbd akwai wanda ya kama zuwa yamma zai iso" Cewar wannan ma'aikaciyar. Cike da mamaki Hamrah ta sake waro idanuwanta tana kallonta ta ce Inaga ba nan bane, dan da mijina nake, ki bari ya shigo inaga ya ɗan fita ne in yazo sai kuyi magana. Gyara tsayuwar ta ma'aikaciyar tayi cike da mamaki ta ce "Baiwar Allah miji kuma, ai wanda ya kama ɗakin tun safe ya sake daman kuɗin dare ɗaya ya bada, yanzu ma manager ne ya turoni na gyara ganin ki kwance kuma yasa nayi mamaki......... _________________________ Alhamdulillah yanzu aka fara wasan. Daman nace tun daga farkon PG ɗin zuwa PG kafin wannan shimfida ne to yanzu labarin ya soma. Ayi hakuri da typing errors bana samun time na gyarawa ne. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 39 & 40 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* ____________ Da mamakin su suka bi inda ƴar gold ke kallo, ƙurawa motar Alhaji Sama'ila idanu tayi tana rarrabe su, tana so ta san a inda ta taɓa sanin motar, Hamrah ta sauke numfashi tana mamakin ina kuma ƴar gold ta san shi, Shatu ce tayi magana cikin sauri tare da yin gaba ta ce "Ah to kisawa ranki cewa ba wanda kika sani bane wannan special man ne" Tayi gaba abin ta, Hamrah tabi bayanta bayan ta ce da yar gold Sai nazo ko zuwa nan da kwanaki biyu. Sukai sallama ta wuce cikin motar Alhaji Sama'ila ta tadda sai fira suke shida Shatu, ta sauke numfashi da ya sanya ya juyo ya kalleta itama ta ɗago ya ce "Ya dai gajiya ne?" Uhm to dashi ɗinma, 2 days ban huta ba. "Kin kusa ki huta ma ai daga fita aikin, let it be next week, kawai kiyi bankwana da aikin kinga za ki sami hutu kamin ki fara hidimar bikin" Ta sauke numfashi ko ita daman haka take son tayi zuwa next week ta sami OG suyi magana akan zata sake aikin, a hankali ta ce Inna samu na kammala wasu abubuwan zan sake aikin. "Ok it's better kam" Shuru ya ratsa har suka iso ƙofar gidan su Shatu yayi parking tare da cewa "A'isha mun iso bari na buɗe boot ki ɗauki kayanki ko" "A'a duk siyyan Amaryar ka ce babu nawa a ciki" Cewar Shatu tana kokarin fitowa Hamrah ma ta fito tana cewa Akwai wani white lada naki ne ki ɗauka. Alhaji Sama'ila ya fito mata da kayayyakin ta, da ƙyar ta amsa tana godiya ta shige ciki bayan sunyi sallama da Hamrah. A nutse ta shigo cikin motar ya tada ta suka nufo gida, shuru babu mai magana a sakaninsu daman ita Hamrah bamai yawan magana bace har suka iso kofar gida yayi parking, juyowa tayi zata mai godiya taga ya kafeta da idanuwansa masu kwarjini sai ta kasa magana, shiru suna kallon junansu cikin sanyi jiki ta janye nata idanun tare da sauke numfashi, shima ajiyar zuciya yayi ya ce "Kina bukatar wasu abubuwane da suka shafi biki nan kusa?" Kai ta gyaɗa alamun a'a, murmushi yayi ya ce "A'a buɗe baki za kiyi muyi magana ai yanzu mun zama ɗaya, babu batun ma wata kunya ko jin nawi na" A'a yanzun dai gaskiya bana buƙata komai. Ta faɗa cikin sanyin murya ta sake ɗagowa a karo na biyu ta kallesa har yanzu shina idanuwan sa na kanta yana kare masa kallo duk sai taji ta takura ta ce Ɗazu a bakin shop mun haɗu da wasu ƙawayena ɗaya daga cikin su ta ce ta sanka. Murmushi ya sakar mata sosai yana yinsa ya ce "Menene sunanta?" Ƴar gold, Hauwa'u Jibrin. "Ƴar gold" Ya maimaita yana jinjina sunan, a hankali ya kai hannunsa zuwa kan nata hannun dake kan ciyarta ya rike tare da matsesa cikinta, ya sauke numfashi tare da kiran sunanta "Hamrah" Hannunta ne ya tsoma rawa, ta sudda kai ƙasa tana kokarin kwato hannun amma yaki sakewa cikin sanyi murya ya ce "Are you doubting me" Ta ɗago cikin sanyin jiki tana kallon sa sai kuma taji kunyar abinda ta faɗa ta girgiza kanta alamun a'a, murmushi ya sakar mata ya ce "I don't know her, did you agree" Ta sake gyaɗa masa kai, ya sake hannun nata ya fito ya buɗe boot cikin sanyin jiki ta fito ya kira yara su shigar mata da kayayyakin ciki, nan suka soma jidansu suna kaiwa cikin. Da mamaki take kallon yadda suke shigar da kayan ita dai siyayya kaɗan tayi yana nufin duk waɗannan kayayyakin nata ne, ta kallesa tare da cewa Wannan ai ɗawainiyar tayi yawa bansan mani kayiwa waɗannan shopping ɗin ba da ban bari ba. Murmushi yayi ya ce "To ikon Allah, laifine dan nayiwa matata siyya, ai kin wuce hakan ma" Thank you. Ta faɗa, tana kokarin shigewa ciki ya ce "Ba komai ki huta gajiya" Ya shige motar ya tada ta ya tafi, ta dawo ciki ta tadda yaran sun ajiye kayayyakin a palour Ammie na tambayar su waya aiko su, ta ce Ni ce fah Ammie, ta sallami yaran Ammie ta ce "To ashe tare kuke tun yau kika fara siyayya haka?" A'a Ammie Alhaji Sama'ila ne ya min siyayya. "Yazo kenan, to yayi kyau" Eh. Ta faɗa shige ciki itama Hamrah ta wuce ɗakin ta da sauran kayayyakin sannan ta sake fitowa ta jidosu zuwa cikin ɗakin. *Bayan 1 week* A nutse ta shigo cikin hospital kamar yadda ta saba ta iso office nata ta buɗe ta shiga, duk jikin ta a mace a hankali take tattara duk abin da ya dace. Dr Mahmoud ya turo ƙofar ya shigo cikin sanyin jiki ya ƙaraso kusa da ya jin gina da jikin garu a hankali ya ce "Good morning Dr Hamrah" A hankali ta ɗago ta kallesa cikin sakin fuska ta ce Morning too Dr Mahmoud, how was your morning?. "Not good at all" Uhm but why?. "You are going to leave us" Ta dakatar da abin da take yi, jikinta yayi sanyi tunowa da yau za tayi handle off na aikinta, bata so ba tana son aikinta da Alhaji Sama'ila zai amince da ya barta anan garin Maiduguri sai ta dinga fitowa, amma ina last zuwan sa da yayi wajenta sunyi magana amma ya nuna sam a wannan ranar ta bar aikin, sbd shirye shiryen bikin, a hankali ta sauke numfashi ta ɗago ta kallesa tare da kwakulo murmushi ta ce Dr Mahmoud ai indai ana raye wataran za a haɗe, ai ba a rabu ba. "Uhmm baki san yadda zamu ji bane indai baki nan, we are going to missed you, much our special Doctor" Murmushi tayi ta ce Nima ina jin duk wanda yake cikin wannan hospital ɗin tamkar ƴan uwana na jikina nima zan yi kewar ku. "Humm a bar zancen haka kawai, karfe nawa OG zai shigo?" Ya ce 10:30. Ya jinjina kai tare da sauke numfashi yana ci gaba da kallon ta har ta kammala tattara duk abin da ya dace ta ɗauke ta ajiye su cikin drower nata kuma ta maida shi gefe ta ajiye ta juyo ganin Dr Mahmoud kusa da ita yana tsaye ta tsaya tare da ɗan jada baya yayi saurin cewa "Dr Hamrah ke mace ce wacce ke da kyawun zuciya da kuma kyaun hali da kuma kyaun fuskar maybe all this be the last in you, you are so special, duk wanda ya mallake ki yayi dace, ina miki fatan zama a ɗakin aurenki ya albarkaci rayuwar ki da ƴaƴa na gari. Because of the zan zamu mutumin kaina zan dawo cikin hankalina, you changed me thanks for that. Daga karshe ina neman ki yafe min duk abinda nayi miki a baya" Sauke numfashi tayi ta Nagode da yabona da kayi, kuma nayi farin ciki da sauyawan da kayi. Ni ban taɓa ko da kwana da kai ba ban iya ba bansan yadda ake yi ba, Allah ya shige mana gaba. "Ameen, thank you for the understanding till we meet at the meeting room" Ya fice kamar zayyi kuka, ta shirya ta fito ta wuce general ward nan tayi sallama da wasu patients nata wasu har da kuka, cikin Doctor's da kuma Nurses ɗin ma sun zubda ƙwalla wasu kuma na farin cikin tafiyarta, dan Adam sai Allah. Ta dawo zata shige office MD ya kirata, ta juyo ta shigo ya washe jajayen hakwaran sa da zata iya cewa wannan fara'ar tun farkon dawowar aiki cikin Hospital ɗin dan haka batayi mamaki ba ta gaida shi ya amsa tare da cewa "Komai yayi farko zayyi karshe yau zaki bar Hospital, to sai a yayyafe mana zaman tare ban sani ba ko na ɓata miki" Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba kanta na kallon gefe shi kaɗai yana ta surutan sa, ta ce "Ba komai" Ta miƙe ta fice, ta dawo office nata ta ɗan kishingiɗe jikin kujera tana sauke numfashi, Dr Aliyu ya shigo cikin sanyin murya yayi sallama ta amsa ya zauna tare da cewa "Our special Doctor tun yanzu muka fara kewarki" Uhm Dr Aliyu ya za ayi ai kuma bazaku so ku ganni cikin wannan yanayin na rashin aure ba, tun da yanzu Ubangiji ya nufa sai muyi masa godiya. "Haka ne amma kinsan sabo akewa kuka, mun zauna dake lafiyar kamar kema kin zauna da kowa da zuciya ɗaya baki damu ba duk abin da za ace you still help people, masu irin wannan halin kaɗanne basu da yawa. Ina miki fatan zama a ɗakinki na har abada. Allah ya albarkace da zuriya ɗayyiba" Amin Dr Hamrah much appreciated with your dua. Thanks. Kiran OG ya shigo a tare suka tafi meeting hall nan yayi dogon jawabi ya fara da yabonta da kuma irin cigaban da ta samar a wannan Hospital ɗin sannan yayi mata kyauta ta musamman na kuɗaɗe masu yawa bayan ya bata award na special Doctor kamar yadda yaji ake cewa kuma ya tabbatar, anan tayi handling aikin tare da bashi files da ya taɓa cewa ta haɗa masa na ci gaban wannan Hospital ɗin, bayan ya dubasu ya ce nan gaba duk kuɗaɗen da zasu shigo ta account nashi zasu shigo, aiko nan hankalin MD ya tashi what OG da kansa ya koma accounter shikenan ta kare masa yana murna bayan tafiyan Hamrah zai ci karensa babu babba ashe ma gwamma tana nan ɗin ma. A haka dai har aka fito daga meeting Dr Zalihat da kuma Nurse Laraba sukayi mata rakiya har bakin titi, tana fita sai ga Alhaji Sama'ila yayi parking ya fito ya buɗe mata alamun ta shigo duk jikin ta a sanyaye tana masa kallon mamaki bata ce komai ba ta shiga ta zauna ya shigo ya tada motar suka dawo gida a kofar gidan yayi parking bata ce komai ba, duk sai taji ta wani iri da tabar aikin duk da ta taɓa yin hakan a baya amma bata taɓa jin irin wannan ba, cikin sanyin murya ya ce "Baby nah ya dai ko dai baki jin daɗi ne muje muga likita" A'a, I'm doing well. "To ki shige ki kwanta zuwa anjima sai muyi waya" To. Ta fito ta shige gida, ta tadda Ayshe da Zeenat sun iso suna ganin ta suka saka murna suna sukananta amarya, murmushi kawai tayi ta zauna a kan kujerun da suke palourn ta sauke numfashi tana bin kayan da ke jibge a zube ta ce Na menene kuma waɗannan?" Ayshe ta ce "Wannan kayayyakin da za ayimiki gyaran jiki na aurenki da abubuwan da zaki amfani su, wadannan kuma ankon biki ne na family anko tunda kince ba zaki cire na kawaye ba shine mu mun siya yanzu haka mutane 70 muka sayawa ga kuma kuɗin mutum 40 ta dangin Daddy. Yanzu ma munzo ne zauna muga su me dame ya kamata a shirya" Uhm ga Atm nawa kuyi duk abinda ya dace Please ku barni zanje na ɗan kwanta. Cike da mamaki suka bita da kallo har ta shige ciki ta kwanta abin ta, duk sai take jinta wani abu haka to ita dai ba murna ba bakuma bakin ciki ba har bacci yayi awun gaba da ita. Sai bayan la'asar ta farka ta watsa ruwa ta fito ta tadda har sun kammala duk abinda suke so suna shirin tafiya su kayi sallama. Biki saura 1week Hamrah ta shirya ta tafi gidansu ƴar gold ita kaɗai wannan karon, ta tadda rahama ce ita kaɗai a zaune a palour ƙasa da alamu shigowar ta kenan, tana ko ganin Hamrah ta saki murmushi tare da yi mata sannu da zuwa ta kawo mata ruwa, sun taɓa fira take tambayar su ƴar gold ta ce da ita ai suma suna hanya ba zai jima ba zasu dawo. Shuru ne ya ratsa sakaninsu a hankali Hamrah ta ɗago ta kalli Rahama dake ta danne dannen wayarta ta ce Rahama da son jin karashin labarin ki na tafi kuma ina tabi a rai, in zayyu ko zaki ƙarashemin ne meya faru ne a lokacin da iyayen mijinki Ahmad suka shigo suka tadda Fateemah wacce mijinki ya kawo ta a matsayin ƴar uwarsa. Ɗagowa Rahman tayi ta kalli Hamrah tare da cewa "Uhmm ki bari kawai pretty, ai Ahmad ya cuceni ko ince ya cuce kanshi, a lokacin da mahaifiyar sa da kuma ƙannensa suka shigo duk sai ya ruɗe jikinsa har rawa yake yana musu barka da shigowa, Fateemah bata palour suka zauna har suka sha ruwa sannan ta fito cikin shiri zata fita cike da mamaki suke binta da kallo tare da cewa "Ah bakuwa ki kayi Rahama ya mutun Kaduna?" "Uhm daman jira nake so aje wajen na ce Ah Ummah ai Fateemah ce ko baki ganeta ba. "Fateemah ta ina kuma?" Ahmad dake sugune duk ya jike da gumi ya ce "Kuci abinci zuwa anjima sai a tsaya tambaye² teemah ki gaidasu mama" Mamah?. Na faɗa a fili tare da miƙewa na tare ta na ce Zo kiyi musu bayani daga gidan uban wa ki ke munafuka, kin ɗauka mahaukaciyar ce ni ko bansan me nake yi ba. Ummah Ahmad ce ta miƙe take cewa "Wai meke faruwa ne Ahmadu, me nake gani wacece kuma wannan?" Tsilli² yake yi da idanuwa ya rasa abin cewa, na ce "Ummah cewa yayi ƙanwarsa ce ƴar baffansa ce satin ta biyu a nan gidan" Wawan mari umman sa ta ɗauke da dashi ya rage tsawo yana hawaye nan yake sanar da ita marainiyace an korota daga gida matar ubanta ce ta koreta sbd babu uwar ta.... Kan ya karasa ta sake wanke shi da mari ta ce "Ah ka manta a kanta aka fara maraici, meyasa ka ɓoyewa matarka sai da ta bincika ta sani to ka sani ta tattara ta fice ta koma gidan ubanta" Aiko Ummah bata tafi ba sai da ta tabbatar Fateemah ta tafi sannan ta fice cikin ɓacin rai ta ce kada Ahmad ya sake zuwa inda take. To sbd wannan abin da ya faru yasa ya ce tunda na haɗa sa da iyayensa babu shi babu ni kuma ba zai sakeni ba sai ya gana min azaba kuma ko ƙwandalansa ba zai kashe min a matsayin kayan abinci ba. Na jikata ya fice yayi tafiyarsa sai da ya ɗebi 3 month kafin nan ya dawo daman ba sana'a ce dani ba, nayi complain a gida suka ce ina tunda naji na kuma gani na zaɓesa bayan sun ce a'a na eh to na zauna dashi ko a wane irin hali nake ciki ni na sani. Shine na faɗa cikin wannan harkar har zuwa wannan lokacin" Sauke numfashi Hamrah tayi ta kalli Rahama da take zubda ƙwalla. Lallai akwai darussa da dama cikin labarinta, a hankali ta ce Mu matsalarmu mu mata munayin abu ne da dawo mana dashi, akwai mu da hakuri da kuma juriya da kwallafa rai akan abu, duk da cewa shi yaba kyauta tukuici ne, amma bai dace a dinga kwallafa rai akan kinyi sai anmiki. kuskuren ki na faro shine bijirewa iyayenki da ki kayi tun farko akan cewa ke Ahmad ki ke so in ba a baki shi ba sai dai a rasaki, su iyaye suke da hangen nesa akan ƴaƴansu suna nema miki farin ciki ne na har abada amma ki kayi kunnen uwar shegu wai ke ga mai miji, to shine Allah ya barki da Ahmad ɗin kuma ai kinga aya. Sai kuma kin rufa masa a siri kina tunanin ba zai taɓa cutar dake ba kin miƙa masa dukkanin yardan ki sbd abinda ki kayi masa ya wadatar ba zai kyalla ido yaga wata ba sai kuma gashi yayi shine hakan ya sanya ki cikin depression. Nan gaba in zakiyi abu ki yi dan Allah bance Ahmad yayi daidai ba, yayi kuskure amma da yake shi na miji duk abinda yayi ado ne, nashi ya ɓoya naki kuma duniya ta sani, bakya tunanin makomar ƴaƴanki ko kina nufin ba zasu taɓa yin aure ba, sannan ma da wane irin idanuwana zaki kallesu a lokacin da suka mallaki hankalin su suka fahimci irin abin da ki ke aikatawa. Shawarata anan shine ki goma gida ki zauna kiyi nazari ki nemi mafita tun kan lokaci ya kure miki, sannan ki nemi mijinki ku sasanta da yanzu dake dashi kun zama daya tunda da kin aikata ma fiye da abinda ya aikata....... "Hamrah pretty daman nemanki nake, mu zaki rainawa hankali ki ce zaki shigo cikin kungiyar mu ashe kina cen kina shirin yin aure to ki sani wallahi baki isa ba kinyi kaɗan" Cewar ƴar gold a lokacin da ta shigo ta tadda Hamrah a zaune a palour nsu daman nemanta take ruwa a jallo.......... . Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 43 & 44 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ A hankali ta maida rinannun idanuwanta masu yi mata zafi da zugi ta rufe jinsu take kamar an zuba mata ruwan borkono a ciki take ji, zazzaɓi mai zafi ya ratsa dukkanin jikinta, yunwa ciwon kai rashin karfin jiki suka haddasa mata jin jiri duk da tana kwance ne kan bed amma tana jin duniyar na juyawa da ita. A hankali tayi yunkurin tashi ta gagara ta koma ta kwanta ba tare da ta buɗe idanuwanta ba, sbd jin raɗaɗin da kasanta ke mata, buɗe idanuwanta tayi ta sake duban wannan ma'aikaciyar da take sanar da ita cewa mutumin da ya kama ɗakin ya rigada ya sake tun safe, to wa take nufi ne, cikin rashin fahimta ta yi magana a hankali da ƙyar muryarta ke fitowa ta ce Inaga ba wannan ɗakin bane aka turoki, wannan ɗakin mijina ne ya kamma, ki duba maybe next room ne ko kuma room kafin wannan. Sauke numfashi wannan ma'aikaciyar tayi tana mamakin abin da take cewa, ita dai tasan babu wasu mata da miji da suka shigo wannan hotel ɗin dan cin amarci, an kwan biyu gaskiya. Tayi magana tana mai sake kallon Hamrah ta ce "Baiwar Allah ba ɓatan kai nayi ba wannan room ɗin ne aka sake wani ya kama har anbiya kuɗin ma, manager ne ma da kanshi ya ce nazo na kimtsa shi. To amma ki kace da mijinki kuka shigo ina mijinki yake?" Sai a lokacin kuma ta tuna rabonta da Alhaji Sama'ila tun daren jiya, to ina kuma ya tafi ba tare da ya sanar mata ba ko dai ya tafi sallaman bakinsa ne ya dawo su tafi cen Abujan. Ta dubeta cikin sanyin murya ta ce What the time now?. "To 11:00am" Cewar ma'aikaciyar, daram ƙirjin Hamrah ya buga har 11:00am yayi basu tafi ba to ina ya shiga ne?. A hankali ta sake cewa Please miƙamin wayata. Ta nuna da hannu kan bed side. Nan ma'aikaciyar ta nufo wajen ta sa hannu zata ɗauka sai tayi arba da wasiku guda biyu, ta dauki wayar tare da cewa "Kinga wasiku biyu a ajiye a kan bedside" Wasiku kuma?. Miko min su. Ta miƙawa hamrah su, ƙaramar Hamrah ta buɗe arɓa da abin da ta gani ne a rubuce yasa ta saki kara a wajen ta sume nan take kan bed ɗin. _3 hours left_ Da ƙyar ta buɗe dishashun idanuwanta a hankali tana bin ɗakin da kallo, idanuwanta suka sauka kan drip ɗin dake makare jikin window dake kusa da bed ɗin zuwa hannunta, tana son tuno maisa aka sanya mata drip ne, mai kuma ya faru da ita?. ... "Kin tashi sannu kinji" Muryar da taji ne yasa ta juyo ta ɗayan bangaren ta kaleta, ma'aikaciyar hotel ɗin ne zaune kusa da ita tana kallon ta cikin tausayawa ta sake cewa "Just rest you'll feel better soon" A hankali ta fara tuna abin da ya faru da ita wasu zafaffun hawaye ne suka zubo mata, ta sauke nauyeyyen ajiyar zuciya tare da rumtse idanuwanta tana addu'ar Allah yasa mafarki takeyi, duk wannan abin ba a zahiri ne yake faruwa ba a hankali ta buɗe idanuwanta ganin a zahiri ne yasa tabi jikinta da kallo ganin doguwar rigar ce irin na marasa lafiya a jikinta yasa tayi saurin kallon wannan ma'aikaciyar ta ce Bayan na suma mai ya faru dani? Sauke numfashi wannan ma'aikaciyar tayi ta ɗan dafe jikin bed ɗin da dukkanin hannunyenta cikin tausayawa tace "Sunana Hadiza Aliyu, ma'aikaciyar a nan hotel ɗin na jima ina aiki cikin wannan hotel ɗin, nasan duk wani shige da fice na wannan hotel ɗin, nasha cin karo da ire-iren abin da ya same ki sai dai banbancin naki da nasu shine ke da aurenki akayi miki hakan, na tausaya miki fiye da yadda ki ke tunani, mutumin da ki ke magana akan shi shine wanda ya kama wannan room ɗin sbd bayan kin suma ne na fita da gudu zuwa reception na tadda manager nan nayi masa bayani cikin tashin hankali, cikin sauri ya biyo ni muka shigo yaga abin da yake faruwa he feel so bad. Hankalin shi ya tashi nan ya kira wata likita ya mata bayanin abin da yake faruwa kuma da alama kamar an sadu dake, jin haka yasa tace mu fita muka fita. Nan ta duba ki ita da kanta ta shirya ki da ta fito ne take sanar damu cewa kin sami buɗewa ta kasanki tayi miki ɗinki, amma kina bukatar drip, aka turani na siyo na kawo ta sanya miki, sannan ta tafi. Abin da nake so dake yanzu shine kiyi hakuri ki kira gidanku ki sanar dasu ga abin da yake faruwa dake sai suzo su tafi dake gida amma maganar gaskiya ya sake ɗakin dan mun duba sunan wanda ya kama ɗakin kuma mun samu shine wanda ya sake kuma yayi tafiyar sa shi da wasu mutane ne ma suka fice" Tunda ta fara magana Hamrah ke kallonta bata ko kifta su ba, jin ta take kamar ma bata cikin duniyar baki ɗaya anya itace kuwa, to me yake shirin faruwa da ita ne me wannan Alhajin ke nufi da yin hakan ne, meyasa ya kashe mata kuɗaɗe in dai sbd ya kwanta da ita na dare ɗaya meyasa yayi mata haka menene tayi masa shin daman ba aurenta yake son yi bane tun asali?. Rashin samun amshoshin wanɗanan tambayoyin da tayiwa kanta ne yasa tasa hannu ta cire drip a hankali ta tashi da ƙyar ta zauna cikin tashin hankali take bin ɗakin da kallo idanuwanta suka sauka kan wayarta ta ɗauka missed calls ya kai 50 ta gani cikin sanyin ciki ta kunna wayar tana kallon waɗanda suka kirata, Ammie 20 missed calls, Daddyn 10 missed, Ammar 15 missed calls, Ayshe 3 missed calls Zeenat 2 miss calls ta sauke nauyeyyen ajiyar zuciya tayi tare da kumshe idanuwanata da suka ciko da kwallah rumtse su da tayi ne yasa suka karasa zubewa, zuciyar ta nayi mata zugi da kuma ƙona, ta yaya zata koma cikin gida ta sanar dasu abin da ke faruwa, mema zata ce dasu tace Alhaji Sama'ila da aka ɗaura aurenta dashi jiya j ya gudu ya barta, ta ina ma wannan maganar zata shige su. Sannan tayi yaya da mutanen dake gidan innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine kaɗai abin da take ita faɗi cikin ranta.... "Kiyi hakuri ƴar'uwa ki kuma kwantar da hankalinki ki sami nutsuwa ki bar zubar da kwallah" Cewar Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin, a lokacin da ta dafata Uhm. Shine kaɗai a bin da Hamrah ta iya cewa dan wannan tashin hankalin bata san da meyayi kama ba ita ko a tarihi bata taɓa jin abin da ya faru da ita ya faru da wata ba, sannan duk cikin labaran da ta jisu daga bakin waɗanda suka faɗa cikin jarrabawa ma bata ji makamancin irin nata ba, komawa tayi ta kwanta tana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ta jima a kwance ta rasa mafita a hankali ta sake duban wayarta ta shiga contacts ta rasa wa zata fara kira, wani tunani ya faɗo mata ta kira Shatu mana suyi magana ko zata sami mafita, wata zuciyar kuma ta ta bari ba yanzu ba. Cen kuma ta ce ko ta kira Ayshe ne ta sanar da ita hanlin da take ciki, cen kuma ta ce ko Ammie ko kuma Daddyn su, tana ta wannan tunanin ne Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ta sake cewa "Ki tashi ki gabatar da sallah azahar lokacin ma ya wuce la'asar ma ta kawo kai" Sauke numfashi tayi tare da juyowa ta kalleta ita sabar tashin hankali ma ta ma manta da ita a zaune. Ba tare da tayi magana ba ta mike ta shige toilet da ƙyar take iya takawa ta tadda akwai na'urar dafa ruwan zafi ta kunna ta dumama ruwa ta shiga ciki ta jima a cikin sai da taji ta ɗan dama² sannan ta ɗaura alwala ta fito ta sanya kayanta na lace da ke jikinta jiya ta yafa mayafin ta gabatar da sallah. Ma'aikaciyar ta fice dan haka tana sallame wa ta dawo kan bed ɗin ta zauna ganin message ya shigo ne ta duba kuɗi ne daga Alhaji Sama'ila Naira miliyan 10, sai da ta sake dubawa da kyau ta kula ashe tun safe ya tura mata. Tayi saurin kiran layinshi kuma a kashe, ta sauke numfashi ta kira number Ayshe kira na farko ta ɗauka tare da cewa "Amarya ran gida tun jiya nake ta kewar ki aure ya rabamu, amma meyasa ake ta kiran number ki baki ɗaukawa duk hankalin mu ya tashi musamman ma Daddy tun jiya ya kasa cin abinci, haka ma yaya Ammar" Sauke numfashi hamrah tayi ta haɗiye abu mai zafi cikin ranta tare da haɗiye kukanta ta ce Ayshe bacci ne ya kwashe mu, bayan na farka kuma na koma sai yanzu na tashi, ina Ammie?" Dariya Ayshe tayi ta ce "Madallah yaya Hamrah kin shiga system ɗin, ai daga yanzu ko zaki fara rama bacci. Ammie tana nan, tun safe duk ta damu ƴan rakiyar ki sun shirya amma kuma shuru ba a ji komai daga gareku ba" Daram ƙirjinta ya buga, wai tashin hankali yanzu ya za tayi kuma ta san dole sai ƴan rakiyar nan sun rakata hasbunallahu wa ni'imal waƙil, Allah yakawu mata mafita shine abin da take faɗi cikin ranta, a hankali ta ce Ki hau online muyi video call. "To yaya Hamrah yanzu ma ko" Dukkanin su suka hau online Hamrah sosai ta ɓoye damuwarta ta kirkiro murmushi amma ana iya hango damuwa ƙarara kan fuskar da dakuma idanuwanta, cewa Ayshe tayi ta dinga yawo da wayar tana son ganin mutan gida, Ayshe ko ta dinga yawo dashi gida ko cike yake maƙil da mutane, sai kaiwa da komowa suke, wasu a zaune wasu kuma a kwance ana ta fira ana raha ta iso inda Ammie take tana tsaye tana haɗa kayan Hamrah wanda za a tafi dasu ta mota katse video call ɗin tayi ta fashe da kuka, sosai taci kuka jin ringing da wayarta keyi ne yasa ta share hawayenta ta ɗauka ganin sunan Zeenat ta kara a kunne tare da sallama Zeenat ta amsa ta ce "Yaya Hamrah barka da rana, yanzu Ayshe ke sanar dani kunyi waya na ce bari na kiraki mu gaisa" Da ƙyar Hamrah ta ita iya yin magana Eh hakane inna shirin kiranki ma kika kira ya gajiyanku?. "Sai godiya, amma ya kamar kina kuka?" Uhm a'a Zeenat ba kuka nake yi ba. "Kai yaya Hamrah gashi naji har muryarki ta dishe, kada ki damu kaɗaici ne ke damunki kuma zai wuce kewace muma duk munyi irinta kina kaiwa sati ɗaya za ki saba da rashinmu" Haka ne Zeenat thank you. "Yauwa ga Ammie nan ku gaisa tana ma son magana dake" Ta sauke numfashi ta ce To ki bata. Ta mikawa Ammie cikin masifa Ammie ta ce "Haba Hamrah abin da ki kayi bai dace ba yaya za ku shanya mutane tun safe suna jiran ku a ɗau hanya amma sai ku sharesu haka ake yi ne, wallahi banji daɗin hakan ba, yanzu ya za ayi ne goben ne tafiya tun da yau an ɗaga ko kuma kun tafi ne?" Wani kuka ne ya zuwa Hamrah kamar ta ɗaura hannu a kai ta saka ihu amma ta jure ta danne ta ce "Ammie ya gajiya eh tafiyan sai gobe in Allah ya kaimu da man sunyi magana da wasu ne akan ɗiban kayayyakin to ban san ya abin zai kasance ba, bari muga goben. "To ki kira ki sanar dani da wuri dan ko da ƙyar na tsaida babanninki wai zasu tafi, to in kinga tafiya ba ta gobe bace sai su tafi kada mu ɓata musu lokaci ba" To Ammie. Shine abin da Hamrah ta iya furtawa. Ammie ta kashe wayar nan Hamrah ta rushe da kuka kamar ranta zai fita ta soma furta kalmar Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ya Allah ka kawo min ɗauki Allah na tuba ka yafe mini, Allah ina cikin tashin hankali na rasa mafita Ubangiji kai dayane zaka taimakeni Allah ka dubi lamurana ka rufa min asiri ka taimaka min taimako ka kaɗai nake nema. Sosai take kuka, har lokacin da Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin ta shigo ta taddata tare da Manager suka shigo, nan ta dinga rarrashinta tare da ban baki da ƙyar Hamrah tayi shiru sannan manager yayi magana "Ba abin da zan iya cewa akan wannan abin da ya faru ya riga da ya faru sai dai na baki hakuri, ki ɗauki hakan a matsayin kaddararki Allah shine MUJARRABI yana jarabtan bawansa ta ko wacce siga musamman irin sigar da bawan ke yaƙi da ita yaga ko in abin ya samesa zai jure ne kamar yadda yake son wasu su jure to ban sani ba ko kina ɗaya daga cikin su. Yanzu dai duba da halin da ki ke ciki yasa na dauke miki kwana ɗaya zuwa biyu a nan dakin sbd wanda yake da niyyar kamawan ma na sauya masa da wani dan haka zaki iya zama nan da zuwa jibi in kin sami lafiya da kuma nutsuwa sai ki koma gida ki sanar dasu halin da ki ke ciki" Hamrah dai kanta a ƙasa ta rasa bakin magana sai zubda ƙwalla take tabbas maganar wannan manager abin dubawa ne tayu sbd da tana wayar da kan wasu akan kada su kaucewa tsarin musulunci su jure wa duk wani halin da suka sinci kansu a ciki shine Ubangiji ya jarrabe ta yaga ko ya ita za tayi a hankali ta furta Astagfirullah. Manager da Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin suka fita basu jima da fita ba ta shigowa Hamra da abin da zata sanya a cikin ta, ta ajiye wa Hamrah ganin ko kallon abinci batayi ba yasa ta haɗa mata tea mai kauri ta bata tasha, kaɗan ta sha ta ajiye ta kwanta. Har dare tana kwance ta rasa mafita tayi tunanin duniyar nan ta rasa mafita ta rasa wanda zata kira suyi shawara ya taimaka mata cen sai wata zuciyar ta ce AMMAR nan ko sai hankalinta ya kwanta da ta tuna dashi a hankali ta ɗauki wayar kira ɗaya ya ɗauka tare da cewa "Ni har nayi fushi dan kinyi aure shine har kika manta dani na kira baki ɗauka ba na ce to su amarsu" Uhm Ammar, ai ban isa na manta da kai ba, bana jin daɗin jikina ne yasa na kasa amsar wayar. "Subhanallahi, meke damunki, ya naji muryar ki haka ince dai lafiya?" A hankali ta ce Zan tura maka address na hotel ɗin da nake Please be hurry ina jiranka. "Hamrah is something wrong, are you alright?" Uhm just come now Ammar. Ta kashe wayar. Ta tura masa address na hotel ɗin da take ta kuma faɗa masa room number da kuma sunan wacce zai je wajenta Hadiza Aliyu tayi masa jagora zuwa inda take. Ta miƙe ta daura alwala ta idar da sallah ishai tana kan dardumar sallah taji turowar kofar ta shafa addu'ar da take yi ta juyo ta kalli bakin kofar Ammar ta gani a tsaye yana karewa ɗakin kallo idanuwansa suka sauka kan roban drip ɗin dake bedside da kuma tulin magungunan dake wajen, ya sake juyowa ya kalleta cikin sanyin jiki ya ƙaraso inda take kallo ɗaya yayi mata ya fahimci akwai matsala ya rage tsawonsa ya zuba mata idanuwan shi yana sake karantar yanayi ta, a hankali yayi magana "Kada ki ɓoyemin komai Hamrah idanuwanki sun nuna min akwai abin da ya faru, kuma yanayin ki ma ya nuna? Ina Alhaji Sama'ila?" A hankali hawaye ya zubo mata ganin Ammar yasa ta danji sanyi a hankali ta ce Nima ban san inda yake ba. A take numfashi sa ya soma hawa yana kallon ta irin kallon nan na me ki ke nufi, bakin ta na rawa ta ce Tun da na farka da safe ban sake ganin shi ba har yanzu. "Ah bangane ba ina ya tafi baki kira number shi ba ne?" Na kira baya shiga, amma manager hotel ɗin ya ce wai tun safe ya sake ɗakin ya basu key ya fice. A take idanuwan Ammar suka kaɗa su kayi jajir numfashin sa ma na sizin, ya ce "Ya sake ɗakin ya tafi gidan ubanwa ya tafi ya barki me yake nufi da mu ne?. Yaudarar mu zayyi ko kuma yaya. Ita dai sai hawaye ta rasa abin cewa ta nuna mashi wasikun da ya bari da hannu, ya miƙe ya iso wajen ya buɗe karamar nan take jikinsa ya soma rawa shatin jijiyoyin jikinsa suka bayyaa tun daga kansa zuwa hannayen sa ya dunkula hannu ya daki jikin garu take hannunsa ya fidda jini yana fuzgar da iska ya ce "What?. Mu za a yaudara, to in ya saba yiwa wasu mu ba zayyi mana mu kyaleshi ba, yana nufin taron da mu kayi ya tashi a banza ya maida mu shashashu kenan taron iska mu kayi, to bai isa ba yayi kaɗan kuma sai ya gane kurensa yayi kuskure da yayi AUREN HARAMCI dake......... _________________________ Alhamdulillah ala kulli halin. Masu min addu'oi ina godiya matukar. Akwai masu cewa labarin ya sauya ban sauya labarin ba asali ma PG kafin wannan shine PG 1 wannan kuma PG 2 to duba da yadda nake son sakon ya isa kafin abin da ya sami ita Hamrah ta cikin labarin shine na kawo labaran wadanda suke dauke da jarrabawa daban daban SBD in tata jarrabawar tazo a fahimci abin. Ayi hakuri da typing errors. Akwai waɗanda suka tura min kyauta ina godiya Allah ya saka da alheri, nayi farin ciki kuma ban sanmaci zan sami haka ba a wannan littafin. Nayi Updating WhatsApp ɗina ɗan Allah su min magana in har sunyi arɓa da wannan PG ɗin su min magana ta pc dan basa ɗaya daga cikin group nawa. Akwai wata kuma Fa'izi something dai please su min magana kada kuga nayi shuru kamar ko girman kai ne. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 45 & 46 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* ________ zuciyar shi nayi masa tsuya da raɗaɗi, ji yake tamakar zata tsago ta fito sabar tashin hankali da kaɗuwar da yayi sbd jin abin da Hamrah ta sanar dashi da kuma ganin wannan wasikar da Alhaji Sama'ila na Abuja ya rubuta ya bari. Kaiwa da komowa yake yi yana safa da kuma marwa, jikinsa naci gaba ɗa ɓari ji yake ina ma gashi ga Alhaji Sama'ila na Abuja da ko sai ya yabawa aya zaƙinta. Isowa yayi gaban window ɗakin ya ɗan yaye labulen yana ya ƙurawa fitulun dake haske wajen, kallon farfajiyar hotel ɗin yake yi yana kaɗa ƙafarsa ɗaya yana kallon shige da ficen da mutane ke yi. A hankali kuma ya sauke numfashi tare da juyowa yana kallon Hamrah dake kuka a zaune wuni guda duk ta fita hayyacinta ta faɗa sosai ta rame duk ta kuma yi sanyi. Ya maida idanuwansa kan tulin magungunan dake kan bedside yasa hannu ya ɗauko su tare da roban drip ɗin ya zube su gabanta ya duka har ƙasa ya zuba mata jajayen idanuwansa yana fitar da iska ya ce "Yayi miki wani abun ne da yasa aka sanya miki ruwa ko kuma sabar kiɗimewa ce da abin da ya aikata miki?" Jin wannan tambayar da Ammar yayi mata ne yasa gabanta faɗuwa ta sake ruɗewa, tabbas Alhaji Sama'ila ya cuceta ya rabata da budurcinta ya saka kafa ya sallaketa yayi tafiyarsa abinsa bai damu da ita ba ko ta mutu ko ta rayuwa. A hankali ta ɗago ta kallesa ganin yanayin sa da kuma yadda idanuwansa suka sauya launi zuwa ja hatta farar fuskar sa sai da ta koma ja sabar baƙin ciki da takaici, tana ganin yadda faffaɗan ƙirji kai sheking kamar ana jijjiga shi. Kasa ci gaba da kallon sa tayi ta maida idanuwanta kan tulin magungunan da ya kwaso ya zube su gabanta. Tunowa da abin da ya faru tsakaninta da Alhaji Sama'ila ya dawo mata kunya ce kuma ta lulluɓe ta me Ammar yake nufi da wannan tambayar ta yaya kuma zata iya faɗa masa alhalin tana yarsa yana ƙaninta ai hakan bai dace ba a hankali tayi magana da ƙyar ma ta iya furtawa Uhmmm daman suma nayi ne shiyasa aka sanya min drip. Ya sauke numfashi da karfi har sai da tayi saurin ɗagowa ta kallesa, kai tsaye ya ce Ya kwanta dake ne?. Kirjinta ya bada rasss.... Eh. Ta furta a kunya ce to bata san me zata ce ba sai kawai taga ya miƙe ya daki jikin garu ya kuma ɗauko light dake kan wani madaidaicin stool ya makesa da ƙasa yana huci a tsorace ta miƙe ta sa hannu ta rikesa tare da rike hannunsa sa dake zubda jini jikinta na rawa ta zaunar dashi da ƙyar ya dago da jajayen idanuwansa yana kallon ta itama shi take kallo, lallai yau zuciyar su UMAR Soja ta tashi a hankali ta ce Please Ammar calm down, kana ji wa kanka ciwo. Sauke numfashi yayi tare da kau da kansa gefe ya fuzgar da iska ya ce "Me yasa kika amince masa bayan kinsan cewa mayaudarine, meyasa baki kirani tun a daren jiya kin sanar dani ba, ai sai daga baya nake jin wai a hotel zaku kwana to dan ubansa ce masa akayi saboda wannan dalilin ne aka basa ke. Yayi kaɗan ya raina mana hankali sai na tabbatar masa cewa ke macece wacce ba dare ɗaya ake bukatar ta ba, har abada ake sonta kuma ake so ayi rayuwa da ita kuma a zauna da ita" Ita kunya ma duk ya rufe ta, da jin abin da Ammar ke cewa, batayi auni ba taji ya miƙe cikin ɓacin rai ya sake make jerarrun pot flower's da akayi decorating dasu daga gefe ji kake rassss suka faɗo ƙasa warwas. Saurin boɗe kofa akayi wani maaikaci ne yashigo sanye da uniform na ma'aikatan cikin hotel ɗin yayi magana ciki ɓacin rai "Kai baka da hankali ne ya zaka shigo mana hotel ka lalata mana ɗaki, to wallahi kaji na rantse sai ka biya mu zaka nunawa zuciya... Aiko bai kai ga rufe mouth nashi ba yaji saukar naushi, Ammar ya shaƙo sa daman me neman kukane aka jefesa da kashin shanu aiko ya haɗesa da jikin garu har sai da idanunsa suka fito waje. Ammar yayi magana cikin ɗaga murya kamar ya haɗiyesa ya huta ya ce "Kayanku na banza na wofi, da asarar su da su da babu duk ɗaya suke, an farfasa su kaima kanka sai nayi gunduwa gunduwa da part na jikinka kayi wasa, kun gina waje kun baiwa katti daman cin zarafin mata shine har kake alfahari da wajen kana na fasa muku kaya to an fasa baza a biya ba kada ma kasa na rushe hotel ɗin baki ɗayansa" Da ƙyar Hamrah ta kwace wannan ma'aikacin daga shaƙan da Ammar yayi masa, aiko ya ari ma kare ya fice a guje dan shi bai yarda kan Ammar ɗin daya bane duk a tunanin sa Ammar dukan Hamrah yake sbd yasha jin ana hakan. Hamrah ta zaunar da Ammar bakin bed ta zauna kusa dashi ta juyo da fuskarsa suna facing juna ta ce Ammar bai dace kayi hakan ba, nima da akayi min na jure na danne balle kai, kayi hakuri muna cikin Hotel ne kada ka tara mana mutane, please. Maida idanuwansa yayi ya rufe a daidai lokacin manager ya shigo ganin Ammar da baisan da shigowar sa ba da kuma ganin yadda aka farfasa musu kayayyakin da sukaiwa ɗakin ado yasa yayi magana "Haba bawan Allah ya zaka shigo cikin Hotel kana mana hayaniyar bayan kasan nan wajen hutawa ne da mutane a ciki, sannan kuma wa yace ka fasa mana kaya kasan nawa aka siyesu" Ammar ya zabura zai tashi Hamrah ta riƙe shi ta hanashi tashi ta juyo tayi magana Haba manager ka dubi halin da muke ciki dan Allah abar maganar na ɗauki nawin biyan duk abinda ya fasa yaro ne kada ka maida hankali irin nasa ka rike girmanka. "Manager kake ko waye, sai na kai karanta court da duk wanda yake da hannu cikin buɗe wannan hotel ɗin sai kun yi bayani, tunda daman ba wajen Allah da Annabi bane kun tara katti suna sheƙe ayarsu kuce ana hutawa" Please Ammar kayi shuru dan Allah. Da ƙyar ta fidda manager dan cewa yayi ya sauke kwanan da ya bata a ɗakin gwanma ya bata kuɗi taje ta kama wani hotel ɗin, Ammar kam ko kaɗan hakan bai damesa ba shi haushin ma bai samu ya shaƙo manager bane yake jin zafi. Bayan fitan manager ne ta dawo rarrashi ita da zai bawa baki ta ya dawo ita ke bashi ba ki da ƙyar ya sauko ya ciro wayarsa yana ƙoƙarin kira tayi saurin rike wayar tare da cewa Wa zaka kira? Ya tsareta da idanuwan sa ya ce "Daddyn zan kira, yasan halin da muke ciki sai mu koma gida tare, ba zan bari ki kara koda minti ɗaya ne cikin wannan hotel ɗin ba" Dan Allah kada ka sanar da kowa halin da nake ciki wannan dalilin ne ma yasa na kirata mu tattauna akai. "Ban gane ba, me kike nufi bazaki koma gida ba, a ina zaki zauna anan hotel ɗin ki keso ki zauna hakan ba zayyu ba mu koma gida asan irin matakin da za a ɗauka" A hankali ta sauke numfashi, hawaye suka biyu kuncinta ganin haka yasa jikin Ammar sanyi ya ɗan sassauta murya ya yi magana "To Hamrah ya ki ke so ayi baki son na faɗawa Daddy to akan wane dalili?" Ammar farin cikin iyayenmu shine suga nayi aure, kuma gashi hakan ya faru anyi bikin nawa, na sani daga jiya zuwa yau suna cikin farin cikin sosai saboda nayi aure kuma suna da burin na zauna lafiya a gidana, kada ka manta irin abubuwan da nayi facing a gida akan rashin aure ba irin kuka, damuwa, rashin hankalin da ban gani ba, kafini sannin irin zaman da nake yi a gida, to yanzu kwasam sai na ce dasu AUREN HARAMCI Alhaji Sama'ila yayi dani ba na halak ba, ta yaya zasu ɗauki abin nasan dole hankalin su ya tashi, sannan ga mutane nan cike da gida duk kuma sbd wannan auren suka zo idan suka ji wannan labarin basan dole ransu ya ɓaci suga kamar anɓata musu time ne. Ɗazu mu kayi waya da Ammie take sanar dani cewa ƴan rakiya suna jirana kuma ta gama haɗa min kayayyakina na tafiya sannan kuma yaushe ne zamu tafin na ce da ita gobe ba tare da nayi tunanin komai ba yanzu kuma na rasa mafita shine na kira muyi shawara ya zanyi da gobe da na ce da ita nasan zuwa goben dole ne su kaimin kayana inda zan zauna, shine nayi nazari na ce ko kaje ka sanar dasu cewa anan garin Maiduguri zan zauna zuwa wani lokaci sai na koma Abuja, sbd Alhaji Sama'ila ne ya sauya tunani yace na zai kamamin gida. In yaso gobe sai ka biyo tanan ka sanar dani yadda ku kayi sai kasa a bincika min flat house sai akaimin kayana cen a jera min su kaga daga nan sai mu zauna mu tsara muga yadda abin zayyu sai na sanar dasu halin da nake ciki. Ta sauke numfashi bayan ta kora masa dogon jawabin tana kallon yadda yake karɓan shawarar. Sauke numfashi yayi yayi shiru yana nazarin maganganun ta a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce "To naji Hamrah amma why not mu sanar da Daddy komai in yaso sai bayan an watse sai a zauna a tattauna kan batun kinga komai zaizo da sauki" A'a Ammar in muka sanar dashi yanzu zai shiga tashin hankali sosai kuma kasan Daddy ba zai ɓoye bacin ranba sai kowa ya sani, kawai kayi yadda nace in shaa Allahu zamu sami mafita. "To ba komai a daren yau ɗin nan zan saka a nemo min dillali zuwa gobe komai zai yi kamar yadda ki keso, shikenan hakan yayi miki" Kai ta gyaɗa ganin lokacin ya tafi kusan 10:00pm yasa ta ce ya tafi da ƙyar Ammar ya tafi, ta sanyawa ɗakin key ta dawo ta kwanta tana ta tunanin ko ya su Daddy zasu ɗauki wannan lamarin har bacci ya ɗauketa. _WASHEGARI_ A hankali ta buɗe idanuwanta da sukayi mata nawi da zafi sbd kukan da tasha, bin ɗakin da kallo tayi tasa hannu ta janyo wayarta ganin lokacin sallah asubah tayi yasa ta sauko da ƙyar ta iya kai kanta toilet jiri ne ke neman ɗibanta sbd yunwa da damuwar da take ciki ta ɗaura alwala ta fito ta idar da sallah anan kan dardumar sallah ta kwanta bacci ya sake yin awun gaba da ita..... Cikin bacci taji alamun ana tashinta jim kaɗan tayi ta buɗe idanuwan ta ganin Ammar sugunne kanta duk ya tashi hankalin sa yasa ta tashi ta zauna tare da sauke numfashi ta ce Ammar yaushe ka shigo?. Ajiyar zuciya yayi da karfi ganin ta buɗe idanuwanta ya ce "Kin matukar bani tsoro, tun ina gida nake ta kiran number ki amma baki ɗaukawa har na iso bayan nazo ne na tadda kofar a kulle nayi tunanin wani abu ne ya sameki shine na koma na sanar da ma'aikatan wajen suka zo suka buɗe ganin ki anan nayi tunanin baki numfashi wallahi na tsorata" Ta sauke numfashi, a hankali ta ce Bacci ne ya ɗibeni. Ya ku kayi?. A hankali ya janyo ledar dake kusa dashi ya ajiye gabanta tare da wani cup mai murfi ya buɗe haɗaɗɗen tea ne mai kauri ya ajiye gabanta tare da buɗe ledar ya ajiye mata gashashiyar kaza ce da kuma cheaps sai egg souce ya ce "Ki ci sai na faɗa miki yadda mu kayi" Kai t girgiza masa tana jin yunwa amma bata sha'awar komi, ganin bata da niyyar ci yasa ya sake cewa "To shikenan zanje na sanar dasu Daddy gaskiyar lamarin indai zaki hukunta kanki da yunwa" Tasan sarai zai aikata, kuma in bata ci ba zai tayi mata rigima yasa ta sanya hannu tana ci kaɗan kaɗan ci take yi amma bata jin ɗanɗanon komai ɗaci ma take ji cikin makokaronta da ƙyar take iya haɗiye ya zuba mata idanu kamar wata karamar yarinya sai da ta ci mai ɗan yawa sannan ya sauke numfashi, ya ce "Jiya ina shiga gida na tadda Daddy a farfajiyan gida, na sanar dashi abin da ki kace na faɗa ya ce bakomai zai sanar da Ammie to kinsan gidan da jama'a har na fito bamu haɗu da Ammie ba amma na haɗu da Daddy ya ce inji Ammie in an samu a sanar dasu, shine na biya ta wajen abokaina nayi ta cigiyar gida sun haɗani da wani dillali yanzu dai mun gama a cen new GRA mun sami gidan kuma ya haɗu sai dai yayi kuɗi kuma bansan iya kwanakin da zaki zauna aciki ba shine na ce bari na zo muyi shawara" Alhamdulillah. Shine abin da ta furta taji sanyi cikin ranta shikenan komai zaizo cikin sauki ta ce Thank you Ammar Allah ya baka mace ta gari ka gama min komai. Tunda ka ce gidan na da kyau ba sai an tsaya jayayya ba ko nawa ne zan bada amma nasan baza su karɓa kuɗin kwanaki ko sati ba sai watanni zan kama na 1yrs a faɗi kenan in komai ya daidaita a wannan watan ma falillahil hamdu sai na koma gida kai kuma ka zauna acen na wani lokaci sai mu sake ko ya ka gani. Murmushi kawai tayi yabi ra'ayinta ne kawai dan yaga tana cikin damuwa kuma baya so ta tashi hankalinta ne amma bayan an watse zai sanar da iyayensu sbd a samu mafita. Ciro wayarsa yayi ya kira wannan mutumin bugu ɗaya ya ɗauka ya sanar mashi cewa za a bada kuɗin nan suka gama su kayi sallama. Ya dawo da kallon shi kanta ya ce "Sai kuma menene ya rage yanzu?" Ta sauke numfashi ta ce "Let me inform Ammie about the house, sai zuwa yamma in yaso akai kayan" Yana kallon cikin tausayawa wai yaushe Hamrah zata sami farin cikin ne kullum cikin damuwa, kuka, tashin hankali. Ɗauko wayar tayi ta kira Ammie ta ɗauka tare da gaidata Ina kwana Ammie. "Lafiya Hamrah, yauwa naji komai daga bakin Daddynku ya sanar dani, kuma hakan ma yafi duk ƴan'uwanki na nesa suga ɗakinki su sanya miki albarka" Uhm. Ammie an sami gidan ma cewa ma yayi za'a tura motar da zata kwashi kayan sai aje gidan a jira. "Ah to madalla babu damuwa mu ai mun haɗa komai a shirye yake sai sunzo kawai" To. Ka katse wayar ta fashe da kuka, da ƙyar Ammar ya rarrasheta tayi shuru ta ce dashi Ina zamu sami motar da zaikai kaya da kuma mutane anjima da wanda zai kaini. Kamar yayi kuka ya ce "Barmin komai a hannuna" Ammar ya fice ya bar Hamrah zaune jigum kamar wacce akayiwa mutuwa ko da shike babu maraba da mutuwar hawaye ke fitowa babu kuka ita dai ganin abin take tamkar a mafarki. Ta ɗau waya ta kira Shatu bugu ɗaya ta ɗauka cikin zolaya ta ce "Amarya ran gida, amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida" Haɗiye damuwarta tayi ta ce Shatu ya gajiyanki naso kiranki tun jiya amma ban samu damar kiran ba, yauwa ki je gidanmu ki tadda Ayshe da Zeenat za a kai kayana a jera kin san mun sauya shawara zan zauna anan zuwa wasu watanni sai na koma Abuja da zama. "Kai ƙawata nayi matukar farin ciki dajin wannan batu daman ina ta jimamin tafiyanki tun jiya kamar mara lafiya nake, aiko yanzu zan shirya na tafi cen gidanku" Uhm nagode bestie. "Ba komai" Su kayi sallama. Ta kira Ayshe da Zeenat suke ta shawara da juna har Ammar ya samu babbar motar da ta kwashe kayan Hamrah aka kai wunin ranar kam a cen akayi duk an jikkata, sun shirya mata gida. Shatu da Ayshe suka kawo mata kayan da zata saka har cikin hotel ɗin suna ta sokanar ta wai tayi kyau a kwana biyu ita dai dariyar yake kawai take yi har Ammar ya hayo mutanen da zasu zo a matsayin abokan Alhaji Sama'ila suka ɗauki Hamrah bayan tayiwa manager hotel ɗin godiya ba tare da Shatu da Ayshe sun fahimci komai ba. Sai da aka biya ta gidansu aka kwashi ƴan rakiya sannan aka wuce gidan amarya, a lokacin da suka iso kofar gidan su kamar ta ruga da gudu ta shiga haka take ji tayi ta kuka har suka iso gidanta. _________________________ Abin da ya samu kenan a yau, ina fita aiki shiyasa bana samun isasshen lokacin yin typing kun san sha'anin aiki ga kuma hidimar gida. Amma in shaa Allahu a weekend zanyi readmore fiye da haka. Godiya gareki A'isha Allah ya bar ƙauna 🥰 Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 47 & 48 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* __________ Da isowarsu unguwar new GRA suka yi parking a gaban katafaren gida mai ɗauke da babban gate milk color, sun ɗan yi jim kaɗan da yin parking ɗin aka buɗe gate ɗin, wani dattijo ne ya buɗe musu ganin haka dukkanin su suka dunguma cikin gidan a farfajiyar gidan su kayi parking aka fara fitowa. Tun daga farfajiyar gidan suke yaba gidan har suka shige ciki a nan babban palourn duka yada zango. Hamrah dake zaune cikin motar ta rabka uban tagumi ta zubawa sarautar Allah ido dan ta miƙa masa dukkanin al'amuranta, duk sai tayi sanyi ganin abin take tamkar a mafarki sai al'ajabin abin dake faruwa da ita take yi ace yau ake rakiyarta ɗakin aurenta amma babu miji, bata taɓa kawo irin wannan ranar zata risketa ba. Ganin yanda ƴan'uwanta ke farin cikin rakota da suke yi ne ma yasa ta ɗan ji sanyi cikin ranta ko ba komai ta faranta musu, musamman ma Ammie. Tana cikin wannan tunanin ne taji muryar babarsu dake zaune a gefenta ta ce da ita "To mun iso menene kuma abin kin fitowa" A hankali ta sauke numfashi dan ita tayi nesa cikin tunanin zuci bata ma san anayi mata magana ba, ganin an buɗe ƙofar motar da suke cikin ne babarta da kuma Innarta sun fice yasa ta saka kafa ta fito, suna rike da ita har cikin palour nan ko sai guɗa ake ita dai tayi shuru bata ce komai ba, har aka shigar da ita ɗakinta. Kaya kam Masha Allah Daddy yayi mata dan kaf gidansu ta fiso kyaun kaya tun daga na palour, ɗaki zuwa kitchen ba abin da aka saya da farashi mai sauki duk kayan masu sadane. A bakin bed ta zauna tana jin yadda suke yaba gidan suna ta sanyawa Alhaji Sama'ila albarka suna ta musu fatan alkhairi har lokacin tafiyarsu yayi. Nan ko Hamrah sabon kuka ita tama rasa na menene na tafiyarsu ne ko na bakin cikin da take ciki ne da ƙyar Ayshe da Shatu suka yi ta rarrashin ta tayi shuru har suka fice. Ta rabka tagumi a karo na biyu, oh yanzu kuma ko wacce iriyar rayuwa za tayi ita kaɗai a wannan kata faren gidan dan tasan kan ta sanar dasu Daddy sai an dau tsawon wasu watanni dan zuwa wancan lokacin babu sun mance komai hankalin su ya kwanta sai ta sanar dasu. Ta miƙe tsaye tare da yaye gyallen dake jikinta tana bin ɗakin da kallo ganin set na ɗakinta wanda yaji uban kuɗi da kuma kyau sbd ba a Nigeria Daddy ya siya ba order sa akayi a lokacin da za a shigo masa da kayayyakin business na sa. Sauke numfashi tayi gashi anyi mata hidima kuma ace suji wannan mummunar labarin ai dole hankalinsu ya tashi, ta fito ta wuce palour nan ma haka ya matukar haɗuwa da kuma tsaruwa musamman Dining area ya matukar kayatu, ga standard fridge nata haɗaɗɗe da kuma babban plasma. Hawaye ne take ya wanke mata fuskar sai a lokacin taji wani irin kuka ya taho mata nan take ta zube a wajen ta saki kukan tana jujjuya kanta tana kuma tausayawa rayuwarta shikenan ta rabu da farin ciki na har abada kuma ta ɗaukarwa kanta alkawarin babu ita babu aure har aba kawai za tayi ta bautawa Ubangiji in ta kama ma ta zauna a wannan gidan ta karashi rayuwarta..... Jin an taɓata ne yasa ta ɗago a hankali tana sauke idanuwanta kan Ammar dake zaune kusa da ita ya dafata yana girgiza mata kansa alamun ta daina kuka sai dai kuma ina shi kansa ya kasa jurewa nan hawaye suka zubo masa, ji yake da yana da halin ɗaukewa Hamrah damuwar da take ciki da ko ya ɗauke mata ya dawo kansa. Hamrah ganin Ammar na ƙwalla yasa ta tsagaita nata kukan tare da share hawayenta cikin sanyin murya ta ce You have to go back Ammar, dare ya soma yi babu daɗi kana waje kuma... Hannun sa yasa ya riƙe nata da ƙyar ya buɗe baki yayi magana dan zuciyarsa nayi masa tsuya da raɗaɗi ga kuma tausayinta da yake ji a hankali ya ce "Do you think, i can go and leave you hear?. No, I can't" Uhm Ammar, ni ce ya zame mun dole na zauna ana cos i don't have a choice amma kai ba zayyu ka bar gida ba, kuma nasan Daddy zai nemeka. Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya ɗauko ledar da ya shigo da ita wacce bata ma san da ita ba ya ajiye gabanta shima ya zauna kamar yadda take zaune bisa ƙafafuwanta ya ce "Kin manta lokacin da muke yara in zaki kwana bikin kawarki in Daddy ya hanaki Ammie kuma ta barki sai mu haɗa plan sai Daddy ya shigo na taimaka miki ta saman garu ki fice a tunanin Daddy kina gida to irinsa nayi yau ma. Ya shigo mun gaisa mu kayiwa juna sai da safe shine na biyo ta baya na hawo garu na wuce nayi miki siyayya dan nasan tun abin da ki ka saka a baki tun safe baki ci komai ba" Murmushi tayi duk da yanayin da take ciki sai taji zuciyarta tayi mata sanyi, tuno mata da rayuwar kuruciyarta da Ammar yayi ne yasa tayi murmushi. Ganin tayi murmushi yasa ya buɗe ledar ya fiddo da roasted fish and chicken with souce ya matso dashi kusa da ita ya buɗe mata fresh milk mai sanyi ya ce "To kici abinci ba a fushi da abinci" Uhm Ammar i don't feel to eat anything at all this time.... "Ki daure ki ce kin cin da ki keyi shine ki ke jin kamar baki da lafiya shi wanda ya jefaki cikin wannan halin fah yana cen yana wantayawarsa ko a jikinsa to ke meyasa zaki tashi hankalinki, ki daure ki" A hankali take yanka tana ci kamar ta amayar take ji amma ta daure gaskiya ne bai kamata ta na fushi da ƙaddararta ba, duk da akwai ciwo amma ya zama dole ta yarda da ƙaddarar da ta sameta. Ba laifi ta ɗan sha fresh milk ta koma da baya ta jingine jinjina kujera tana sauke numfashi... "Ga magungunan ki nan ki sha sai ki kwanta" Da mamaki ta kallesa ita ta ma manta tana kan magangana an ɗaurata akan su shiyasa ma ta mance bata dauka ba to amma yaushe Ammar ya ɗauko bata sani ba. Ba tare da ta ce komai ba ta buɗe su ta haɗiye ya mika mata wani sachet ɗin ya ce tasha ba tare da tasan na menene ba ta karɓa ta haɗiye sa, nan da nan ta fara jin bacci ta miƙe ta shige ciki sabar baccin yayi nawi da kayan jikinta ta faɗa kan bed nan take ta bacci yayi awun gaba da ita. _WASHEGARI_ Buɗe idanuwanta tayi ta ƙurawa roba slink, ganin haske ya gauraye ɗakin yasa tayi mamaki wane irin bacci ne tayi har gari yayi haske bata farka ba, a hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta tashi ta zauna tare da karanta addu'ar tashi daga bacci. Tayi miƙa ta sauko daga kan bed ta shige toilet ta haɗa ruwan ɗumi ta watsa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa ta shimfiɗa dardumar sallah ta gabatar da sallah asubah duk da ta makara amma ta jima tana ta addu'oin. Jin ana nocking kuma tasan Ammar ne sbd babu kowa cikin gidan bayan ita sai shi yasa ta miƙe ta buɗe. Murmushi ya sakar mata ya ce "The breakfast is ready" Sauke numfashi tayi tare da cewa Uhm sai zuwa anjima zanci kaci naka. "Kin manta ne kina kan shan magunguna kuma ba zaiyu ki shasu ba tare da kinci abinci ba, kuma ai ya kamata kimin kara ko dan tashi da wuri da nayi na haɗa miki delicious" Fitowa tayi ta wuce Dining area tare da cewa To muje na gani. Ya bi bayanta, ya matukar sharya Dining table ɗin ya matukar burgeta harda wasu flower's da light a jiki suna kawowa su kuma ɗauke tayi murmushi Allah sarki Ammar a dole yana son ta mance komai. Ta iso ta zauna shima ya iso a nutse ya soma buɗe rufaffun plate ɗin da ya jerosu kan Dining ɗin yana nuna mata, murmushi tayi a kan ko wanne plate yayi decorating da abincin wani aresh ne wani kuma fried yam sai kuma ma ɗauke da souce na hanta. Abu dai kala daban daban kuma ba masu yawa ba, ko wanne ya ɗiba ya zuba mata kan plate dake gabanta ya haɗa mata hot tea mai kauri ya bata sannan ya zuba ma kanta. Ta ɗan dauko spoun tana ci kaɗan kaɗan ba laifi ta ɗan ci ya bata magungunan ta ma tasha sai kuma bacci a nan palour kan kujera ta kwanta tayi bacci ganin haka ya fice ya koma gida. Kusan wunin ranar tayi tane a kwance sbd bacci da ta dinga yi babu tantama Ammar maganin bacci ya bata tasha. Bayan ta idar da sallah la'asar ne taji tsayuwar motar ta leka Ammar ne da wani mutum a tsaye ta fito sbd ganin da sabuwar motar ta wacce Alhaji Sama'ila ya siya mata shi ya taho. Tana nan tsaye ya sallami mutumin ya iso inda take ya ce "Ga mukullin motar ki Daddy ya ce na taho muki dashi yana kuma gaidaku" Uhm Ammar, na bar maka motar in ma saida ita za kayi kaje kayi ni bana sonta. Murmushi yayi ganin ta juya ta shige ciki ba tare da ta karɓi kin motar ba, yabi bayanta, ya taddata zaune kan 1sitter shima ya zauna daga gefe ya ce "Babbar yaya fushi ba naki bane sbd duk wannan abin tafe yake da plan naki dole ki amshi motar kiyi amfani da ita har zuwa lokacin da zaki sanar dasu Daddy komai" Ta sauke numfashi tasa hannu ta amshi key ɗin motar tare da cewa Ya mutan gida?. "Yau duk yawanci sun tafi ina ji zuwa gobe zuwa jibi za a ma watse" Alhamdulillah, kaga komai yana tafi kan tsari. Allah ya kaisu lafiya. "Ameen" Sun jima suna fira kusan magrib ya fice, sai 8:00pm ya dawo ya kawo mata abin taɓawa ta ci suna fira ta shige ciki ta kwanta dan shi yace ba zai tafi gida ya barta ita kaɗai ba. Haka rayuwar Hamrah ta kasance har tsawo sati biyu, sai dai zuwa wannan lokacin ba kullum bane Ammar ke kwana a gidanta, sbd kada Daddy ya fahimci wani abin. Hankalin Hamrah ya fara dawowa jikinta ta ɗan sami nutsuwa Zeenat da Ayshe suna kawo mata wuni su koma bata taɓa barin sun fahimci komai ba, haka bestie nta Shatu ita ma tana kawo mata wuni su sha firar su da ƙyar suke rabuwa. _After 1month_ Cikin sauri ta fito ta faɗa cikin motar ta tadata ta fito tayi parking a waje ta koma ta rufe gate ɗin dan har zuwa wannan lokacin basu nemi gateman ba tun bayan sallamar wanda suka tadda yana gadin wajen, sunyi hakanne sbd kada sirrin abin da suke ɓoyewa ya tonu, ta shige motar ta figeta cikin gudu ta hau titi kai tsaye sai Na kowa hospital tayi parking a farfajiyar Hospital ɗin ta shige ciki bata ma ganin gabanta duk ta fita hayyacinta. Tana isowa ta shige cikin office ɗin da zata gamu da ko wacce iriyar likitace, tana shiga ta tadda Doctor da ta duba ta a hotel na washegarin aurenta cikin sauke numfashi ta iso kusa da ita suka gaisa bata shaida Hamrah ba sai da Hamrah tayi mata kwatankwacin wancan ranar ta ganeta cikin sanyin murya ta ce da Hamrah "Kina bukatar wani abu ne?" Ganin office ɗin da mutane ta ce Eh likita amma a sirrance. Ta sauke numfashi suka shige wani karamin room dake cikin office ɗin, Hamrah cikin kuka ta ce Nayi farin ciki da yasa dake na haɗu a yau kuma nasan kin san duk abin da ya faru dani a hotel kwanakin baya, to yanzun ma kusan matsalar tare suke, likita a takaice dai ina ɗauke da ciki sakamakon abin da ya faru, bana son cikin wallahi bana so ba haife shege ko shegiya dan Allah ki rabani dashi. Sosai Hamrah ke kuka kamar ranta zai fita, da ƙyar likitar ta iya rarrashinta ta, ta ce "Abin da ki ke shirin aiwatar wa babu kyau shawarar dan zan baki ita ce ki yi hakuri ki amshi babyn maybe alkhairi ne amma zubda cikin hatsari ne ga rayuwar ki kuma zaki aikata laifi, sannan menene laifin abin da ke cikin shi bai san komai ba kada ki sanya shi cikin abin da ubansa ya aikata miki" Har kasa Hamrah ta duka tana kuka ta haɗe hannayenta biyu ta ce Ni da ki ke gani nima likitace kuma kwararriya nasan illar yin hakan amma kuma hakan shine hanya mafi sauki daga gareni ki taimaka ki zubar barin shi tamkar ruguza rayuwata ce, yau nake fatan komawa gida na sanar dasu abin da ya sameni a ranar bikina na, daga kuma rana irinta yau na sage gina sabon rayuwa sai kuma wannan abin ya sameni dan Allah likita ki zubar min shi..... Kuka take yi kanta na ƙasa, jin shuru da likita tayi ne yasa ta ɗago tana hawaye idanuwanta suka sauka kan Ammar dake zaune a gabanta ya kura mata idanuwansa da suka kaɗa su kayi jajir, baya tayi cikin sauri tana mamakin yaushe ya iso nan ɗin kuma ya akayi yasan tayo nan ɗin?. "Ba zaki zubar da cikin ba Hamrah yin hakan kuskure ne ya zama dole ki haifeshi, the baby was innocent bai san komai ba" Miƙewa tsaye tayi ta nuna shi da yatsa kamar wata zararriya ta ce Bai zama min dole na haifi cikin shege ba Ammar dole ne a fidda min shi ko ana so ko ba aso bazan taɓa haɗa jini da azzalumi ba kuma fasuki ba, in kuma aka dage sai na haifeshi to zan kashe kaina kowa ma ya huta. Hankalin Ammar ya matukar tashi tunda suka taso shi da ita bai taɓa ganin ta shiga cikin ɓacin rai ba irin wannan, duk da yasani da ciwo to amma ba zai bari ta zubda ba. Ya miƙe tsaye shima tare da kai hannu zai riƙe ta sbd ganin kamar nema take ta faɗi ƙasa tasa hannu ta bugesa. Ajiyar zuciya yayi ya ce "Hamrah everything is a matter of time, we should be more patient. If Allah wills, everything will be right. All things must come to an end. Kamar yadda ki ka jure zama da agida na wani lokaci ki kayi hukuri ki ka kau da kai har Allah ya nufa ki kayi aure washegarin bikinki mijinki ya gudu ya barki kika jure hakan to haka ma wannan karon hakuri za kiyi ki kuma jure ki amshi kyautar da Ubangiji ya baki da hannu bibbiyu, dayawa na neman hakan basu samu ba. Kuma bamu sani ba ko da wane irin alkhairi wannan babyn zai zo mana so, Please Hamrah accept it as your destiny" A hankali ta sulale kasa ta zauna kamar wacce aka cirewa laka, hawaye na ci gaba da zubo mata, ta rumtse idanuwanta a hankali take furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Abin ya fara fin karfinta, kuma ya wuce tunaninta tabbas Allah ne mai iyawa bawa ba ya iyawa sai da iyawar Ubangiji, a tunaninta a yau ranar farin ciki ne dan tana murna zata koma gida gaban iyayenta bayan rabuwa da tayi dasu na tsawon wata ɗaya a matsayin tana gidan mijinta ashe abin ba haka bane, kana naka Allah na nashi nasa ne kuma shine dai-dai. To yanzu ya za tayi?. Sunkuyowa Ammar yayi tare da share mata hawayen dake fuskarta cikin tausayawa ya tausasa murya ya ce Tashi mu koma gida. Rike hannunta yayi suka fito a tare har cikin motarta ya sakata ya zaunar da ita a mazaunin gaba, ya koma ya sanyawa motarsa key a inda ya bakata sannan ya dawo shige cikin motarta ya zauna a mazaunin driver yaja ya fice daga cikin Hospital ɗin suka dawo gida yayi parking ya taimaka mata suka fito, ya zaunar da ita a palour. Ita kam ta koma mutum butumi sai ido babu bakin magana ji take sam kamar ba ita bace. Ammar ya fice babu jimawa ya dawo da alamun ba da motarta ya fita ba amma jin shigowar motar yasa ta tabbatar da cewa Hospital ya koma ya ɗauko tasa motar. Shigowa cikin palourn yayi yanda ya barta zaune haka ya taddata, hawaye da bin gefen fuskar ya zauna kusa da ita cikin kulawa ya ce "Ko kina ganin yau mu sanar dasu Daddy abin da ke faruwa in yaso musan irin matakin da zasu ɗauka" A'a. Kawai abin da ta ce. Ya sauke numfashi ganin yanayin da take ciki yasa ya kyaleta ya koma kan 3setter ya kwanta tare da lumshe idanuwansa. Ya akayi kasan Hospital na tafi?. A hankali ya buɗe idanuwansa ya juyo ya kalleta ya ce Nazo ne da niyyar ɗaukanki na kaiki gida kamar yadda mu kayi sbd sanar da iyayenmu gaskiya akan aurenki da Alhaji Sama'ila shine naga kin figi motar kin fice daga layin a daidai lokacin kuma ni ina ƙoƙarin shigowa nayi mamaki ma da baki ganni ba, ganin haka yasa na fahimci ba lafiya ba nabi bayanki sai dai abin da ya bani mamaki shine shigar ki cikin Hospital ɗin me ya kawo ki, kawai nayi parking na biyo ki ciki shine na tadda abinda ki ke sanar da likitar" Ajiyar zuciya tayi a hankali ta sake cewa To ya zanyi da abin da ke cikina shin bayan na haifeshi ina zan kaishi rikesa zanyi ko kuma zan nemo ubansa?. Tashi yayi ya zauna ya kura mata idanuwa na wasu lokuta, sauke numfashi yayi a hankali ya ce "Ai ba zamu baiwa Alhaji Sama'ila abin da zaki haifan ba ya zama namu mu zamu rikesa ko riketa har zuwa lokacin da Ubangiji ya kayyade mana, kuma nasan iyayenmu zasu amshi abin da ƴarsu ta haifa..... Ni bani son abin da zan haifa, dole ne in na haihu a kaiwa ubansa. "A ina kenan?" Abuja. Murmushi mai ciwo Ammar yayi ya ce "Kina da tabbacin a Abujan yake ina da tantama ma bashi da asali. Ni na amince in kin haifa ki bani babyn zan zame masa uwa da uba in kuma lokacin Allah ya ƙaddara nayi aure sai na tafi da babyn gidana mu renesa" A hankali ta ɗago ta kallesa da jajayen idanuwanta ta ce Na mallaka maka tun yanzu ko na mutu ko kuma ina raye na baka babyn ni kuma bayan na haihu, I'll to go far na fara sabon rayuwa. Comments and share*MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 49 & 50 _end of book 1_ *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _MIKIYA mai hangen nesa, mai kuma farin jini wajen al'umma, mai ɗauke da tarin marubuta hazikai kuma fasahai. Kungiyar masu haɗin kai da fahimtar juna. Godiya ban girma ga shuwagabannin kungiyar da kuma members ɗin ta kun nuna min kauna wajen sharing, shawara da kuma ƙwarin gwiwa, i dey with you till.....🤣 You showed me love 💕😘. Much love for you._ _Bana taɓa mantawa dake habibty Bilkisu S fari. Much love for you 😘_ __________ Laulayi sosai cikin ya sanya mata bata iya cin koma sai amai da tofar da yawu duk ta fita hayyacinta, ta rame ga yawan tunani da take yi, bata iya komai daga kwanciya sai zama duk ayyukan gidan Ammar ke yinsa. Kwance take a wannan lokacin ma idanuwanta biyu tana kallon jikin garu kamar me nazarin painting dake jikin mai ɗauke da kyalli² lokaci zuwa lokaci take sauke numfashi. A hankali ya turo kofar ɗakin ya shigo ya zauna kusa da ita ya kura mata idanuwa cikin tausayawa yayi mata magana "Hamrah ki tashi ki sanya abu a cikin ki rashin cin abinci zai haifar miki matsala tare da abinda ke cikin ki, ko bakyaso ki daure ki ci Please" Kamar zayyi kuka yake rarrashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi ta zauna da ƙyar ta kallesa kuma sai ta kau da kai gefe, saukowa tayi ta nufi toilet tana shiga kuma sai kwara amai tun tana iya yinsa har ta gagara sbd babu komai cikin cikinta daman ruwa ne gashi kuma ta amayar, nan take ta faɗi sumammiya. Cikin hanzari Ammar ya iso cikin toilet ɗin sbd jin karan faduwar da tayi yasa ya taso dan ganin abin da ke faruwa. Ganin ta kwance a ƙasa yasa ya dinga jijjigata yana tashin ta amma ko motsi bata yi ba yasa ya ɗauke ta chak kamar wata jiririya yayi waje da ita ya sanyata cikin mota ya kwantar da ita a sit na baya, sannan ya wuce ya buɗe gate ya dawo ya shiga ya tada motar ya tukata zuwa kofa yayi parking daga gefe ya fito ya rufe gate ɗin sannan ya koma cikin motar ya tada ta kai tsaye sai Hospital. Da taimakon Allah dana likitoci Hamrah ta farfaɗo aka sanya mata drip bata san inda take ba sai da ta kai kwanaki uku a hospital, ta farka taga ƴan gidansu a kanta binsu take da kallo su kuma suna mata ya jiki, da kai take iya amsa musu, jikin dai tana jin sa da sauke da taimakon karin ruwan da akayi mata. Sai da tayi 1week a hospital sannan aka bata sallama sai dai wannan karon Ammar sam yaki goya mata baya akan ta koma gidanta duk da bai sanar dasu komai ba amma ya ce mijinta baya nan dan haka a tafi da ita main house ta ɗan huta. Haka ko akayi gida aka tafi da ita sai da tayi 3 weeks sannan ta dawo gidanta. Zuwa wannan lokacin kam jikin dama² dan tana iya komai da kanta Ammar ma ya fara fita office nashi na soja sbd kwazonsa tashi guda aka basa matsayi, yakan zuwa da safe sai ya fice sai kuma dare yazo ya ganta wani lokacin ya kwana wani lokacin kuma ya tafi. ************************ Cikin sauri akayi labour room da ita duk hankalin su a tashe sbd bleeding ɗin da take yi, ganin haihuwa ce ta kamata kadan² yasa likitoci mai da hankali akanta sai da aka dau 1hour 30munute sannan ta haifu baby girl nan ko murna da farin ciki a gun ƴan'uwanta ba a magana, ita dai tun da taji babyn ta faɗo ta kama bacci bata san wainar da ake toyawa sai da ta farka ta ganta a side room an shiryata saf kamar ba mai jego ba, ita kaɗai a ɗakin shuru babu motsin kowa. Jin motsin turo ƙofar ne yasa ta ɗan juya ta kalli ƙofar. Amma ta gani a tsaye hannunsa rike da handle door kamar bazai ƙaraso ba a tunanin sa bacci take, ganin idanunta biyu yasa ya ƙaraso ya zauna kan kujerar dake kusa da bed ɗin ya sakar mata da murmushi a hankali yana ci gaba da kallonta sauke numfashi tayi a hankali ta ce Did you tell them the secret?. Kai ya girgiza mata alamun a'a, sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce "No. I won't, until you agree" Sauke numfashi tayi ta maida idanuwanta ta rufe.... "The baby is pretty like you" A hankali ta buɗe idanuwanta ta kallesa, sai kuma ƙirjinta ya bada rasss, to yanzu kuma ta haihu ko wacce iriyar rayuwa zata sake sintar kanta cikin ta dan wannan karon ba zata iya ɓoye komai ba zata bayyanawa iyayenta komai sbd itama ta samu taji sanyi cikin ranta ta rabu da fargaba, bata ce dashi komai ba shima ganin bata son yin magana yasa yayi shuru har Ammie ta shigo da babyn tana cewa "Lah ashe uwar taki ma ta farka, to taho meje ta baki mamman naki kisha" Hamrah dake kwance ta kalli Ammie dake ƙoƙarin ƙarasowa da babyn, ta sauke numfashi tare da tashi ta ɗan kishingiɗe da jikin bed ɗin, Ammie ta mika mata babyn tana "ki bata tasha yunwa sai addabar take tun da ta taho duniya bata sha nono na sai ruwan zamzam da dabino" Sudda kai ƙasa tayi tasa hannu ta amshi yarinyar ta kura mata idanuwa tana kallon yadda ta sanya babban yatsar ta cikin bakinta tana sosa alamun yunwa take ji, fara ce kal wanke hannu ka taɓa duk da jaririya ce kyawunta bai buya ba wasu kwantantun gashi ne saman goshinta, idanuwanta farare tas da su roung face gareta hanci ɗil dashi da ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da jan laɓɓe, sai wusili wusili take da idanu. A hankali Hamrah ta sauke numfashi tana jin tausayin yarinyar na shigar ta sosai tana jin ƙaunarta... "Oh ni yaran zamani, ki bata tasha shine ki ka zuba mata idanu yunwa fa take ji" Cike da kunya Hamrah ta buɗe rigarta ta fidda nono ta sanyawa yarinyar a baki nan da nan ta kama sosa tana sha, a hankali ta ɗaura hannunta saman kan yarinyar tana shafa gashin kanta mai laushi da tsantsi baki wuluk dashi. Jin ajiyar zuciya da Ammar yayi ne yasa ta ɗago ta kallesa kura musu idanuwana yayi yana kallon su ko kiftasu baya yi, sun matukar burgesa mamaki yake Hamrah na feeding baby lallai rayuwa kenen. Harararsa tayi da ya sanya ya saki murmushin da ya fito da boyayyun dimples nasa fararen hakwaransa suka bayyana ya girgiza kansa ya miƙe tare da yiwa Ammie sai anjima ya fice. Baby kam daga shan nono tayi baccinta nan Hamrah ta kwantar da ita a daidai lokacin kuma ƙannenta suka shigo Ayshe, Zeenat da Maryama suna mata sannu tana amsawa. Anan suke wuni da yamma su tafi har aka sallameta suka dawo gidan Hamrah saboda shirye shiryen bikin suna. Shirye shiryen bikin suna ake yi babu kakkautawa Daddy kam kamar akan Hamrah ya fara samun jika sai hidima yake musu musamman da yaji cewa Alhaji Sama'ila na cen Umrah yana ibada Daddy yace ko yana nan ko bayanan hidima sai anyi nan Hamrah ta kwantar da hankalinta suka sha suna bidia kala kala, gift kam ba a magana kowa yazo taron sunan nan zai koma da goma ta arziki anyi wasan Naira yarinya taci sunan kakarta Fateematul Batula wato Ammie aiko ranar Ammie wuni tayi tana washe hakwara. Washegarin suna ne Ammie ta ce za a tafi wankan jego babu musu suka tafi dan Hamrah cewa ma tayi Alhaji Sama'ila ya amince ya ce ta zauna a gida har sai ya dawo. Satin Hamrah 3 da haihuwa jikinta yayi sumul kamar ba ita ba, sai dai kuma yawan shuru da take yi ne da kuma yawan keɓance kanta ke sanya Ammie mamaki kamar ba Hamrah ba duk da daman bata da yawan hayani amma wannan karon shurun yayi yawa. Ammie ta shigo ɗakin Hamrah ta taddata tana nan zaune tana aikin tunani ta zauna kusa da ita sosai take kallonta cikin kulawa ta kira sunanta "Hamrah" A hankali ta ɗago ganin Ammie yasa ta gyara zama tare da cewa Na'am Ammie, yaushe ki ka shigo?. "Ai baza ki sani ba tun da ki zaɓi ki dinga zama ke kaɗai kina tunani, wai meke faruwa dake ne shin gidanki da matsala ne ko kuma akwai abin da ke faruwa sakaninki da mijinki ne?" Jikin Hamrah yayi sanyi tayi ajiyar zuciya a hankali ta ce A'a Ammie babu komai fah kawai babu ƴan tayani firane shiyasa. Sauke numfashi Ammie tayi ta tsurawa Hamrah idanu tabbas akwai abin da ke damunta, a hankali ta ce "Hamrah akwai abin da ke faruwa sakaninki da mijinki dan na kula tun ranar da kika haihu har zuwa yau baki sake yin maganar da ta danganta dashi ba sannan ko waya ma bana ji ko ganin kuna yi. In dai da matsala ki faɗeta tun kan ya dawo mu sami bakin zaren mu warware ki koma ɗakinki lafiya" Ƙirjin Hamrah ya bada rasss, tab ai abin da ke faruwa ya wuce matsala ai da zata sanar da Ammie dako tafi kowa shiga tashin hankali, sauke numfashi tayi tare da ƙirƙiro murmushi ta ce Lah Ammie ba komai yawancin wayar dare muke yi sbd inda yake ba lallai ne na sameshi a waya ba. Ammie na kallonta jikinta ya bata da matsala kawai Hamrah taki sanar da ita ne amma zata bincika ta gano koma menene. ************************* Ɗauke take da little Ammie ƴar lukuta kwana arba'in da haihuwarta amma kamar ƴar wata 2, yarinya barakallah sai wayyon tsiya ga kuma yawan dariya kamar tasan me ake yi, bata da rigama da ta ƙoshi sai wasa da ƙafafunta. Yanzun ma wanka Hamrah tayi mata ta sanya mata doguwar riga pink color har da headband shima pink gashin nan yasha gyara daman ba ayi haski ba. Daman da pampers a jikinta ta dauko ta suka yi ɗakin Ammar, turo ƙofar tayi tare da sallama ya amsa yana tsaye ne gaban mirror yana shiryawa da alamu fita wajen aiki zayyi sbd kakin uniform na sojas dake jikinsa, iya wandon ne da farar riga ta ciki a jikinsa yayi zanzaro da balt na sojoji, yana taje bakar sumarsa mai sheƙi da laushi kuma kwantacce ganin shigowar ta yasa ya juyo yana sakarwa little Ammie murmushi aiko tana ganinsa ta saki dariya ta wangale baki bubu hakuri, ya bar abin da yake yi ya taho ya karɓeta ya soma cillata kamar yadda yake yi sama da ita yana yi mata wasa. Hamrah ta zauna kan bedside tare da rabka tagumi ganin haka yasa ya zauna bakin bed ɗin ya kalleta ya ce "In ce dai lafiya kinyi tagumi kamar wacce ke cikin damuwa" Sauke numfashi tayi cikin sanyin jiki ta ce Ammar damuwa kam ai ina cikin ta sundum kuma bansan ranar da zan rabu da ita ba. Kaga jiya mu kayi arba'in kuma kasan dole yanzu na koma gidana dan zamana anan ba zayyu ba kuma nasan Ammie ba zata bari ba zata ce na koma ɗakina tunda dai na gama wankan jego shine nake tunanin bansan ya zanyi ina son zama agida bana son tafiya cen ɗin duk kaɗaici zai dameni. Ajiyar zuciya Ammar ya sauke a hankali ya ce "Ni a shawarce kawai ki sanar dasu halin da ki ke ciki in kuma ba zaki iya ba ki bari na zanyi magana dasu in yaso muji ta bakinsu kinga sai kiyi zaman ki anan ɗin" Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi tare da ginginewa jikin garu ta ce Ammar ta yaya zan fuskanci Ammie da kuma Daddy na sanar dasu cewa AUREN HARAMCI Alhaji Sama'ila yayi dani kuma tun washegarin bikin ya tsallake kafa yayi tafiyarsa daga irin ta wankan ranar har zuwa yau ɗinnan ban sanya shi cikin idanuwana duk wannan zaman da nayi a gidana ni kaɗai ke rayuwa. Ai abin da ciwo zasu ji........ "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, lahaula wala kuwwata illabillah. Me nake ji haka, me kunnuwa na ke ji haka?. Daman nasan da akwai abin da kuke ɓoyemin amma bansan abin na da girma haka ba girman da kunnuwana ba zasu iya ɗaukansu ba Hamrah me kika aikata haka?" Daga Ammar har Hamrah sai da hanjin cikin su suka kaɗa sbd unexpected suka ga Ammie a tsaya akansu tana rabka salati kuma sun tabbatar taji komai. Hamrah jiki na rawa ta iso inda Ammie ke tsaye, hawaye na zuba ta ce Ammie ki fahimce ni..... Ba abin da zaki gaya min Hamrah naji komai daman irin wannan rayuwar ki keyi kika kuma ɓoye sa a matsayin menene kenan saboda kina son mijinki ko kuma kina son ganin farin cikin mu to ki sani ni ba zan ɗauki wannan abin ba dole Daddyn ku ya san halin da ki ke ciki, kai kuma Ammar yayi maka kyau da ka goyi bayan tayi haka yayi maka kyau sosai" Daga jin yadda Ammie ke magana ya tabbatar musu ta fita hayyacinta dan bata san ma me take cewa ba abin ya matukar kiɗimata basu yi aune ba suka ga ta fice cikin ɓacin rai, Hamrah ta zube kasa ta fashe da kuka shikenan ta faru ta kare yau da bakin ciki iyayenta zasu wuni da kuma bakin ciki zasu kwana. Amma na ganin haka cikin tashin hankali ya kwantar da little Ammie kan bed yabi bayan Ammie sai kuma yaga ta wuce ɗakin Daddynsu kamin ya iso kuma babu ta shige ya dafe kanshi da hannu ya sauke numfashi shikenan Ammie zata sanar da Daddy Kai ko yaya Daddy zai ɗauki batun, har zai juya kuma sai ya fasa ya nufi ɗakin Daddyn su sai dai jin furucin da ke fita daga bakin mahaifinsu yasa Ammar daskarewa waje guda take zufa ta karyo masa hankalin sa in yayi dubu to yau ya tashi what me Daddy yake cewa ne wai me ke faruwa ne, har tsawon shekarun nan basu san wannan sirrin ba, anya kuwa kunnuwansa sun jiye masa, aiko yana nan tsaye duk ya ruɗe nan Daddy ya sake maimaita abin da ya faɗawa Ammie cikin ɓacin rai da tashin hankali sosai Daddy ke faɗan duk maganganun da suka fito bakinshi a kalmarsa ta karshe ne da ya yita yasa Ammar dafe ƙirji ya zube kasan gwiwowinsa yana karanta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Lallai allura ta tono garma yau yaji abinda aka jima ana ɓoyewa to daman sbd wannan dalilin ne yasa Ammie ta dinga ɗaga hankalinta akan sai Hamrah tayi aure tabbas kuskure kan kuskure suka aikata lallai Ammie taso kanta dayawa. Yana nan sugunne ne yaji alamun Daddy zai fito yasa ya miƙe ya dawo ɗakinsa cikin tashin hankali. Bai tadda Hamrah a ciki ba dan haka ya soma safa da marwa yana jan numfashi yana sake tuno da abinda Daddynsa yake faɗawa Ammie. Ya soma zancen zuci why all this is happening, why from this to that?. Wai to daman babu wata alaƙa ta jini a sakaninsu ashe kuka yanzu Hamrah ta fara yinsa ashe damuwa bata kare ba, to ta yaya ma zata dauki abin kai anya kuwa ba mafarki ya keyi ba, wai shin da gaske ne tsawon waɗannan shekarun Ammie na kullatan Hamrah duk sbd da wannan dalilin ne gaskiya in har hakanne Ammie ba tayiwa Hamrah a dalci ba to WACECE HAMRAH?. Kamar wani sabon zautacce yake magana cen kuma ya dauki duk abinda ya gani ko yayi arɓa dashi yake makewa da ƙasa yana furta "Why, why, why?. Cikin sauri hamrah ta ƙaraso cikin dakin sbd jin ihun da yake yi yana maganganu duk ya kauraye side nasu da karan fashe fashe yasa ta kwantar da little Ammie dake bacci ta fito ta shigo. Ganinta kuma hankalinsa ya sake tashi yana kallon ta cikin tausayawa ya koma bakin bed ya zauna cikin tashin hankali yake sauke numfashi. A hankali ta rage tsawo ta duka kan gwiwowinta ta ɗaura hannunta kan kafadarta cikin sanyin murya ta ce Ammar kada ka tashi hankalinka please take heart, nima fah nayi shuru kuma na ɗauki dangana kuma duk fushin da Daddy zayyi nasan zai sauko kuma ya fahimce mu kaima ka nutsu kabar zubda ƙwalla. Zuba mata jajayen idanuwansa yayi yana kallon ta yana jin tausayinta har cikin ransa da ko tasan abin da hakan ya haifar da ta gwanmaci tun wuri bata ɓoye musu komai ba gashi garin haka allura ta tono garma. Cikin sauri ya janyo ta ya rungume ta ya sanyata cikin faffaɗan ƙirjinsa ya rike ta gam kamar za a ɗauketa daga gareshi cikin tashin hankali yake cewa "Bazan bari ki tafi ba, ba zayyu araba wannan alakar ba, babu inda zaki je mu ɗin jini dayane dukkanin mu ahali ne babu wanda zai bar cikin gidan nan kamawa daga kanki har zuwa kan Maryama ba zan bari hakan ta faru ba. Dan Allah kada a rabamu" Hamrah cikin rashin fahimta zancen da Ammar keyi yasa ta kwace jikinta da karfi tana kallon sa, ganin yanayin da yake ciki yanzu har yafi wanda ta tafi ta barshi a cikin ha a mai yake cewa ne, ai itama yanzu babu inda zata je tunda Ammie ta san komai abinda suke ɓoyewa ya fito fili dan haka a hankali tayi magana Ammar babu inda zanje ina nan cikin gidan kuma babu wanda zai rabamu tabbas mu ahali ne. Ka kwantar da hankalinka zanyiwa su Ammie bayanin komai kuma zasu fahimce mu. "Mun shiga uku meyake faruwa ne, menene haka cen Ammie kuka Daddy na zubda ƙwalla munzo nan ma haka yaya Hamrah kuka kaima yaya Ammar kuka ya kuke so muyi ne?" Lokaci guda suka dago dan jin muryar da basu yi sammanin ji ba a wannan lokacin, Ayshe ne da Zeenat a tsaya daga bakin kofar ɗakin Ammar sai kuma Maryama wacce ke tsaya daga baya kaɗan. Cike da mamaki Hamrah ta miƙe tana kallon su ta ce Ayshe, Zeenat daga ina haka?. Ƙarasowa ciki su kayi Ayshe ta ce Daddy ne ya kiramu a waya yace duk abinda mu keyi mu bari mu taho gida shine muka taho ganin halin da suke ciki ne yasa hankalinmu tashi sai kuma yace muzo mu ƙiraki ke da Ammar. To shine muka shigo kuma muka tadda kuma cikin tashin hankali shine duk muka sorata, wai meke faruwa ne?" Sauke numfashi Hamrah tayi hankalinta take ya sake tashi duk sai ta kiɗime jikinta ya soma rawa tunda Daddy yasa a kira su to fah abin ba kyau. Bata sanar dasu komai ba har suka fito suka wuce palour inda Daddy da Ammie suke zaune, Ammie rakuɓe gefe guda hankalin ta a tashi daga gani anyi ba daɗi kuma yau ta kure mijinta dan fah a yau ya fito tamkar ba shine ba mai daukan duk shirmenta. Yana ganin su Hamrah ya miƙe yana kaiwa da komowa wa ya juyo ya kalli Hamrah wacce ke zaune duk ta rasa yadda za tayi bata so abin yazo a haka ba, ganin yadda idanuwan Daddyn su suka sauya kala zuwa ja yasa tayi saurin sudda kai ƙasa, ya jima yana kallon Hamrah sannan ya ce "Saki nawa yayi miji?" Jikin Hamrah ya fara rawa muryarta ma na sheking ta ce Kayi hakuri.... Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu tare da cewa Ba zancen ki bani hakuri bane cewa nayi saki nawa yayi miki? Ba...ba...bab... Daman tun farko babu auren. Hankalin kowa ya tashi cikin faro aka jero salati cikin bacin rai Daddy ya ce "Babu aure, sadaki da kuma sanya rana da kuma ranar ɗaurin auren da aka tara dubban jama'a aka ɗaura shi kuma menene?. Ba aure bane ko kuma rufe ido yayi mana. Cikin kuka tashi Daddy matansa huɗu nice ta biyar. Haka ya rubuta a wasika ya ajiye min washegarin bikina ya fice. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Dukkanin ƙannenta suka haɗa baki wajen furtawa tare da kaɗuwa da abin da Hamrah ta faɗa. Sauke numfashi Daddy yayi cikin ɓacin rai ya ce "Ina wasikar?" A hankali Ammar ya ce "The letter is with me" Cikin daka tsawa Daddy ya ce "Go and bring it" Jikin tashin hankali ya miƙe ya shige cikin ɗakin sa ya ɗauko duka biyu ya kawo Daddy ya warware ya karanta a fili _Da farko ina mai baki hakuri da abin da zan sanar miki, kuma nasan zuwa lokacin da zaki yi arɓa da wannan wasikar na riga da nayi nesa dake. Sorry to say, i have 4 wives and haven't, not any single child. Ban taɓa haihuwa ba, ma'ana bana haihuwa. Abin da nayi miki ba shine na farko ba a kanki, daman ina yinsa amma nasan ke hakan zai damaki sbd ke ƴar gidan mutunci ne._ _I'm really sorry dear. Take the gift._ Cikin zafin nama Daddyn su ya danƙo wuyar rigar Ammar ya ɗagosa sama ya daidaita tsayuwar su suna facing juna, ji yake tamkar ya sami Alhaji Sama'ila ne, ya wanke sa da wani irin gigitancen mari........ ************************* _Niko Sayyada ganin haka yasa na ari na kare na fice a guje daga palour dan kada a haɗa dani ko ta kalmi ban tsaya sakawa ba, nayi waje road 🤣🤣🤣🤣_ Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen book 1 na littafin MUJARRABI, tare suke da book 2 amma zanyi rowarsa paid book ne ga me buƙatar ta ci gaba da karantawa sai tayi payment. On Monday 20th January zan fara sake book 2 in shaa Allahu sbd na ƙarashe sa kafin mu shiga watan Ramadan. Abin da na rubuta cikin book 1 mai Amfani Allah ya bani ladansa kuskuren dake ciki kuma Allah ya yafe min. Allah yasa sako ya isa inda nake son ya iso. Ko iya book 1 nasan ya faɗar amma fah book 2 duniya ne kada ku bari a baku labarin hot love dake cikin. Wai shin ya makomar su ƴar gold ne, ya kuma Labarin Alhaji Sama'ila ne shin zai dawo ne ko kuma ba zai dawo ba. Cewa fah yayi baya haihu to ya akayi Hamrah ta haihu dashi. Menene sirrin da Daddy da Ammie suke ɓoyewa. Shin ya kuke ganin rayuwar Hamrah ta gaba. Wai shin wane irin shaƙuwa ce sakanin Hamrah da Ammar?????Duk amshoshin suna cikin book 2. *Jan kunne zuwa ga iyaye mata, dan Allah a daina matsawa ƴaƴa mata akan sai sun fidda mijin aure ko ta halin ƙaƙa SBD jinkirin yin aure da su kayi, yin hakan kuskure ne kuma shike jefa yawancin ƴan mata cikin mummunar rayuwa. Daga karshe abin yazo yana damin ku da kuma su kansu ƴaƴan. Shi aure lokacine da lokacin yayi za ayi sa mace bata tsufa Age is just a number. Allah to be sincerely ƴan mata na kokawa da iyayensu akan wannan al'amarin, Please a jasu jiki, a kuma kwantar musu da hankali wajen basu shawararwari da kuma yawaita addua.* Duk wacce tayi payment tamin magana na bata link na paid group da kuma comments section. Already daman akwai SBD tun a first pg aka fara payment. Thanks fan's. MUJARRABI 500 only inji Bature, complete document kuma 1k ne. In dai ba zaki siya ba kada kimin raddi mara daɗi dan ko a jiya wata ta turo 5k ire-irenta na da yawa ko da basu kai nata ba amma sun kamanta. *Name: Hadiza Saleh Abba* *Account number 1399826356* *Bank name access Bank* Shaidar biya 09021706569 Sai mun haɗe a paid group. Thanks fan's much love for you 🥰❤️😍👌🙏 Comments and share.