YAKANAH!-1 Agogon ‘alarm’ da ke gefen makeken gadon ya buga karfe shidda dai-dai na safe, Dr. Hadizah wadda ke kwance a gadon doguwa ce ba can ba, irin tsayin nan gare ta mai tsari da ban sha'awa. Tana sanye cikin rigar barci mai santsi fara sol. Ta yi mika a hankali tare da koro addu'ar (Alhamdulillahil lazee ahyana, ba'ada ma amatana wa ilaihin nushour). Ta mika hannu side din da maigidanta ke kwance, wayam! Tayi hanzarin mikewa daga kwanciyar don a zatonta, ta makara. Daga can kitchen ta jiyo motsin mai aikinsu Goggo Alti tana karakaina da kwanuka. Tana shirin mikewa ta ji motsin maigidanta Sulayman a shower, don haka ta yi ajiyar zuciya mai sanyi, a kalla ko ta makara kadan ne. Ita ma ta fada bandakin don ta taimaka mishi wajen wanka kamar yadda yake a al’adarsu. Wasu ma’aurata ne wadanda samun masoyan da suka shaqu da juna suka kuma yarda da juna, suka aminta da juna, suke matukar kaunar junansu kamarsu a wannan zamanin zai yi wuya. Suka fito kowane daure da towell, shi iya kugun shi ita iya cinyoyin ta. Jiki ne da ita lukui-lukui kamar atafa. Jiki ne da shi na MANYA, kuma kasaitattun maza, wadanda suka dama, suka kutsa cikin manyan ilimummuka daban-daban. Yana da duhu, amma duhun mazan Marocco ne. Dogo ne sosai ma'abocin karfi da kyawun sura ta ko’ina. Idan baka san asalin shi ba, za ka yi tsammanin ya fito ne daga Sirreleone, amma a zahiri Bakatsine ne dan asalin garin Bakori. Wanda Bakorin ta bi sunan shi, ta boye Sulayman-Sulayman din, ake kiran shi Dr. Bakori. Ta bude wardrove ta dauko mishi bakaken Spanish-Suit mai hade da farin tie mai santsi. Ita kuma ta fiddo wata atamfa super shudiya mai ratsin rowan hoda da hasken sararin samaniya, riga, zane da kallabin su, ta dora da farar rigar su ta likitoci. Tuni ta fito a Dr. Hadizarta. Tana tsuke mishi tie ya ja zankalelen dogon karan hancinta in appreciation din (cike da jin dadin) irin kulawar da take mishi. Ya ce "Allah ya bar min ke Dr. D.Z". Ta ce "….Ya bar min kai nima, likitan zuciyata…..". Ta manna mishi kyakkyawar sumba a kirji, kasancewar ya kere ta a tsaho, ita iya kirjin shi ce. Ta dauko tashi rigar likitocin ta zagaya ta bayan shi ta rufa mishi, ya zura hannun shi kana a hankali ya janyo ta ya rungume ta. Sun dau tsawon lokaci a hakan, suna sakin ajiyar zuciya mai sanyi cike da matsananciyar kauna wadda biro ba zai iya rubutawa ba, kamin su saki juna ba don sun so ba, sai don tunanin dimbin al'umma masu larura da suka yi sammako suke jiran su. Sai da suka gama kammalawa tsaf sannan suka fito, tana rike da gilashin idonta a hannu, yayin da shi yake rike da jakarta da brief case din shi. Kai tsaye dakin yaransu suka nufa, inda suka tarar tuni Alti ta shirya su tsaf, kasancewar yau garin an tashi da lullumin sanyi mai tsanani ya sanya ta sanya musu rigar sanyi mai kauri a ciki, ta sanya musu fararen socks ta rufe musu kafafu cikin farin cambas. Yaran su biyu ne mace da namiji, namijin dan kimanin shekaru hudu, macen 'yar kimanin shekaru biyu da kadan. Dole in ka gansu sai ka sake marmarin kallon su, sun kuma baka sha'awa. Munib sak Babansa, yayin da Muniba komi nata na Dr, Hadiza ne. To ba Mamin ba, ba Daddyn ba, kowanne ji yake da kyau tamkar shi ya yi kansa. Akwai shakuwa, fahimta da soyayya mai yawa a tsakanin wannan family. Hadiza ta rage tsawo ta russuna ta rungume diyarta Muniba, "Gud morning my dear......." "Morning Mummy….". Munib ma ya ce "Gud morning Daddy…..". Ya amsa da "Morning my Munib, an tashi lafiya?" Su dukka suka nufi tebir domin yin kalaci. Goggo Alti ta fito daga kitchen za ta wuce bangaren ta, daga Hadiza har Sulayman suka gaishe ta, kamin ita ta gaida su. Wannan dabi'arsu ce da ke karawa dattijuwar jin dadin zama dasu, saboda yadda suke ba ta girma kamar ba a karkashin su take ci ba. Hakan ne yake kara mata himmar kula musu da yaransu saboda Allah. Hadiza ta bude ma'adanan abincin ta soma serving kowannen su da abinda yake so. Sinasir ne da miyar ganye, sai farfesun kayan ciki, sai kuma soyayyen dankali da kwai domin su Munib da bazasu iya cin mai nauyin ba. Ga al'adarsu sun fi cin abinci mai nauyi da safe, don ba za su kara ci ba sai dare in sun dawo aiki, sai 'yan ciye-ciye da ba a rasa ba a office. Hankalin Dr. Sulaiman yana kan 'ya'yan shi, sai da ya tabbatar sun koshi sannan ya ci nasa. Zuwa bakwai da rabi sun gama komai sun fito, suka yiwa Goggo Alti sallama suka wuce rumfar adana motocin su. Akwai motoci har guda uku, daya ta Sulaiman, daya ta Hadiza, daya ta amfanin gida. Sai da suka aje yaran a makarantar su (Maitama Sule) da ke dab da asibitin da suke, wato (AKTH) sannan suka karasa cikin asibiti, kowanne ya nufi bangaren sa. Dr. SULAIMAN-SULAIMAN BAKORI shi ne consultant na (cardiology), yayin da Dr. Hadiza Ja'afar Mai-Yadi take likitar mata wato (gynaec) a labour ward take. Sai da ya fara sauke ta sannan ya wuce ofishinsa, ya soma attending dimbin cases din da ke gabansa. Karfe sha biyu na rana ya zame ya je ya debo yara ya kai ma Goggo Alti, sannan ya dawo. Wannan shi ne tsarin rayuwar su a kullum. *** Shekarun su biyar kenan da aure, amma har zuwa inda yau ke motsi, babu abinda ya canza na daga soyayyar da suke yiwa juna, sai ma abin da ya karu. Hadiza dalibar shi ce irin yaran likitocin nan da ake koyarwa a (teaching hospital). Ya fahimce ta yarinya ce mai matukar kwazo a tsakanin tsararrakin ta. Wani abin mamaki da ya fara bincike a kanta 'yar talakawa ce likis, amma iyayenta sun tsaya tsayin daka wajen daukar nauyin karatun ta, duk da tsadar shi kuwa, da dukkan iyawarsu. Soyayya ce mai tsabta irin ta wadanda suka wadata da ilimi suka gudanar kamin aure. Ga Hadizah ba karamar sa'a ba ce, kuma ba karamin abin alfahari bane samun mutun kaman Sulayman (as a husband). To haka shi ma. Hadiza ta tara duk wasu qualities da yake nema ga diya mace, ga dai kyau ga kyan hali, ga addini da kyakkyawar zuciya, sannan uwa uba ta samu ingantacciyar tarbiyya daga iyayen kwarai. Iyayenta suna nan a unguwar Karkasara dake cikin birnin Kano, sana'ar mahaifinta shi ne yadiddika yake sayarwa, yana da shago a nan kantin Kwari. Hadiza ita ce ta biyu a cikin 'ya'yan gidansu, akwai Yayanta Mukhtar wanda ke aiki da (Zenith Bank) a Kaduna, kusan da tallafin shi ne Hadiza ta samu ta kammala karatun ta. Duk da haka shi ma mahaifinsu a tsaye yake a kan karatun su, don yaga amfanin da karatun yayiwa Mukhtar. Sai kanwar ta Fati, budurwa ce 'yar kimanin shekaru sha bakwai, a bana ne ta kammala karatun sakandire. Sai Hamza da Yusuf, da dan autan su Abdulyassar. Duk cikin kannenta Hadiza ta fi son Fati, wata irin yarinya ce mai sanyin hali, sanyin kyau da sassanyar zuciya. Akwai wata irin shakuwa ta musamman tsakanin Hadiza da 'yar uwarta Fati. Jininsu ya hadu sosai ta yadda Hadiza ba ta iya shawara da kowa kan al'amuranta kamar Fati saboda hankalin ta. Fati yarinya ce mai tsananin son addini da nutsuwa, ba ta da rawar kai ko kadan irin na 'yammatan zamanin nan, komi nata cikin hankali da nutsuwa yake. Ita da Hadiza kamar an tsaga kara, sai dai Hadiza fara ce sol, yayin da Fati ta kasance wankan tarwada. Amma hatta yanayin tafiyar su da murmushin su iri daya ne. **** Sulaiman – Sulayman Bakori, mutumin garin Bakori ne ta jihar Katsina, daga kallo na farko mawuyaci ne ka bambance daga kabilar da ya fito, wani mutum ma'abocin cikar zati da kamala da duk wani nau'in daidaito na rayuwa, ga dimbin ilimi a cikin fannonin kiwon lafiya daban-daban. Ya ci sunan mahaifinshi ne don haka a gidan su ake kiran shi mai sunan Malam. Mahaifin shi Malam Sulaiman, Malami ne mai karantarwa, yana baiwa magidanta anguwar su karatun buzu. Duk wani da ya kwana ya tashi a garin Bakori ya san Malam Sulaiman Mai-Gafaka. Mutum ne da al'ummarsa ke matukar ganin girman sa, kuma ya yi fice a garin Bakori baki daya saboda ilimin da Allah ya ba shi, kowa yana daraja shi. Shi ne da na biyu a gidansu, yayar shi Jummai ta rasu wajen haihuwar fari, sai kannen shi Ramatu, Saude da Ruma, duk suna gidan aure. Sai Khalid wanda ke karatun sakandire a halin yanzu. Sulaiman ya yi dukkan karatun shi ne da taimakon gwamnati da mahaifiyar shi Inna Halima, wadda duk lokacin da hidimar karatun ta tashi take fitar da kadararta ta siyar ta yi masa. In dan ta Malam ne sakandire ma kawai ta isa. Burinsa Sulayman ya zauna a gida ya tallafa mishi kasuwancin shi na fata, ya yi aure ya haifa mishi jikoki shi kuma zai yi masa komai. Amma Sulaiman ya ki, ya dage ga son cimma burinsa na son zama likita. Ba abin da yake so a rayuwar shi irin yau a ce ya zama likita yana yiwa mutane allura. Irin yaran nan ne gifted tun suna kanana, wato 'yan baiwa. Wata irin kwakwalwa gare shi da ba duk mutane Allah yake baiwa ba, duk inda yayi karatu malaman shi sai sun san shi, sun kuma ja shi a jiki, sun so shi saboda hazakar shi. Ya yi gaba dayan karatun shi daga jami'ar Najeriya (NSUKKA). Bayan ya kammala MBBS din shi ya yi nasarar samun scholarship zuwa jami'ar (Manchester) inda ya yi specializing a kan zuciya da duk abin da ya shafe ta. Bayan kammalawar shi da dawowar shi ya soma aiki da federal Government, hakan ne ya sa ake yawan canza mishi wajen aiki. Daga wannan gari zuwa wancan cikin jihohin Najeriya. Ya fara ne da aiki a babbn asibitin koyarwa na Ibadan, daga baya suka mai da shi ABU Teaching Hospital. Nan din bai dade ba suka dawo da shi nan AKTH na Kano, inda Allah ya hada shi da Hadizah. HADUWAR SULAIMAN DA HADIZA Haduwar su haduwa ce special kuma haduwa ba ta dadi ba. Yana tare da patient da ya yiwa aiki satin da ya wuce, Hadizah Ja'afar, da wasu abokan karatun ta suka shigo domin daukar lacca kamar yadda suka saba. A matsayinsa na consultant dinsu, basu samu kallo daga gareshi ba, balle ya tantance kamannin su, kasancewar Allah bai dora mishi lalurar yiwa mata kallon kurilla ba. Tsakanin shi da kowacce diya mace, kallo daya ne, da kau da kai. Wannan a jinin Sulaiman yake. Suka samu kujeru suka zauna, kowacce da jotter din ta da biro a hannu. Yana ta yi musu bayani cikin lafiyayyen turancinshi na Birtaniya mara surki, wani zubin ya yiwa mara lafiyar tambaya ta ba shi amsa. Wata amsa da patient din ta bayar ta sanya su murmushi dukkanin su (ban da Hadiza), cikin kalaman ta za ka fahimci kwakwalwarta ta tabu sakamakon bacin zuciya da damuwa. Ta ce, "Likita nifa 'yar sarauta ce ba mara lafiya ba!". (Wannan ne ya sanya su yin murmushi). Ya ce, "Wacce sarauta gare ki don mu fara girmama ki?" Gaba daya daliban suka yi dariya don yadda yake biye ma shirmen matar dole ya baka dariya. Ta ce, "Sarautar Kano gare ni". Ya ce, "Wacce ke nan?" Ta ce, "Nice 'yar ruwatan Kano". Gaba daya suka yi murmushi, wannan karon ma ban da Hadizah, wadda a lokacin hankalinta baya tare dasu, yana ga halin da ta baro Mamansu a ciki na rashin lafiya mai tsanani. Ba zato Dr. Bakori ya jefo tambaya, "Mene ne delusion?" Ya kuma nuna Hadiza da ya lura hankalinta ba ya tare da shi matsayin wadda za ta amsa mishi tambayar shi. Ya yi mata magana ya kai sau uku ba ta san yana yi ba. Hadiza ta damu da Mamanta sosai, kasancewar ta jarumar Uwa mai hidimtawa rayuwar su, tun daga yarinta har a girman su. Yaya, (Sa'adatu), ba ta huta da dawainiyar su ba. Don haka jin ciwon ta suke tamkar a gangar jikin su. Duka kawayen ta babu wadda ta zungure ta, don sun san da ta ji za ta ba da amsa a yabe ta kamar yadda manyan likitoci suke yabon ta a kullum saboda kokarin ta. Ya buga tebir din gaban shi da karfi har ta razana, ya nuna mata hanyar waje ya ce, 'You can go out..... in kin gama tunanin kya dawo". Ta mike sumi-sumi ta fita, murna gun su Hafsat kamar su yi yaya, yau Allah ya nuna musu likitan da ya yi maganin 'yar gaban goshin likitoci. Ya yi (referring patient) din zuwa psychiatric, su kuma ya sallame su. Ya koma gida a wannan ranar, bayan ya gama duk abubuwan da ya saba na al'adar rayuwar shi kamin ya kwanta, kamar shan fruits da exercise saboda shi da daddare yake exercise din sa kasancewar da safe ba shi da lokaci. Amma abin mamaki ya kasa runtsa idonsa, tunanin fuskar dalibar da ya kora a yau ke gilma mishi, ya hana shi sakat, ya hana shi sukuni, ya yi duk kokarin da zai yi don ya samu barci amma hakan ya faskara. Ya ko kasa runtsa idon sa, wani bakon al'amari ne mai takura zuciya da bai taba tsintar kansa a ciki ba. Hadiza ba wata muguwar kyakkyawa ba ce cancan, tana da kyau dai-dai nata, sai dai kuma yarinya ce mai aji na karshe. Fuskarta zagayayya mai dauke da dara-daran fararen idanu masu sheki da walainiya, hancinta kamar an sanya ruler an ja shi an daidaita shi a kan (oval -shaped) fuskarta. Bakinta dan karami kamar cokali baya shige ba. A kan tsinin hancinta tawwadar Allah ce da aka haife ta da ita, fara ce sol! Irin farin nan da wadataccen ilimin boko ke taimakawa wajen zahharar sa. Bai taba ganin yarinyar da (lab-coat) ta yi ma kyau kamar Hadizah ba. Ba sai ya tsaya wahalar da kanshi wajen tunanin abin da ke faruwa da shi ba, ya tabbata son Hadiza ne ke ratsa kowanne sako a jikinsa. Abin haushin ko sunan ta bai sani ba, zuciya ta kwashe shi ya yi abin da ya zo ya dame shi. Bai taba tsintar kansa a kwatankwacin irin wannan yanayin ba, a kan diya mace. Sai dai shi a ce ana son sa yana hura hanci, kada hakan ya janyo raini, baya fatan hakan ya kasance sakayya ce Allah ya yiwa dimbin matan da ke binsa agindi-agindi don ya so su yana yakice su. Tare da yi musu wulakancin da ko a hanya suka ganshi bazasu yi fatan ace sun san shi ba. Ya fahimci dalibar (obstetric and gynaecology) ce, daga (ID Card) din ta. Yadda ya ga rana haka ya ga dare, ko na second daya bai runtsa ba. So da kaunar student (daliba) Hadiza na narkar mai da zuciya. Abin kamar sihiri, daga ranar bai kara ganin Hadiza ba, bai kuma san ya zai yi ya tambaya ba, tunda ko sunanta bai sani ba. A matsayinsa na babban likita, mai juya sauran likitocin bangaren su, ba karamin zub da kima bane a ji shi yana tambayar wata yarinya cikin masu daukar darasi a wurin su. Duk da haka bai fidda rai ba, yana da yakinin watarana Allah zai sake hada shi da yarinyar ko da a mafarki ne. Ita kuwa Hadiza ba ta dawo TH ba sai bayan sati uku, tana gida tana jinyar Maman su da suke kira Yaya, da ke fama da ciwon hanta. Tana ganin likita a Murtala, har suka kwantar da ita sati guda. Kawarta Surayya ke daukar musu lacca tana kuma sanar da ita duk abin da ke faruwa ta waya. Ranar monday Maman su ta ji sauki sosai, don haka ta shirya ta dawo. Ba zato babu tsammanin shi, yana ganawa da wata patient din suka shigo ita da Surayyah, ya zare gilashin idonsa a hankali, ya saki wata sassanyar ajiyar zuciya irin ta wanda ke neman abu, ya wahala ya dade, kamin ya samu. Duk hankalin sa da attention din sa sai ya koma kanta, ya manta abin da ke gabansa, ya samu kansa da rudewa. Abin da bai taba yi ba a kan diya mace, akwai wani sassanyan kallo cikin kwayar idon Hadizah, da ba duk mata Allah ya mallakawa ba. Suka gaishe shi cike da girmamawa, sannan suka samu kujeru suka zauna. Hadiza dai a darare take, ko kanta ba ta dago ba. Daga gefe-gefen idon ta take satar kallon likitan da ya hargitsa mata tunani 'yan kwanakin nan. Tunda ya kore ta ba ta kara samun nutsuwar zuciyarta ba, har zuwa yau da ta sake tozali da shi a karo na biyu. Ta tambayi kanta, shin ko mutane nawa ne a duniya masu ilhamomin Dr. Bakori? Yana da wasu ilhamomi na musamman a tare da shi da ba ta taba ganin su a da namiji ba, ko yadda yake duban mutane daban ne da na sauran likitocin da ta sani. Tsarin maganar sa cikin seriousness shi ne babban abinda ke burge ta da shi, ga kamun kai da sanin mutuncin kai, hadi da rashin son wasa ta ko’ina. Dr. Sulayman Bakori, ya shiga cikin rukunin wasu mutane da take ganin matukar kima da mutuncin su, sannan kuma ya bi ya manne a zuciyarta, ta yadda dai-dai da minti daya ta kasa manta shi cikin satittikan da ta yi tana jinyar Mamanta. A gurguje ya basu laccar ya kuma sallami mara lafiyar da suke tare da ita. Suka mike da nufin su tafi, baya fatan wannan damar da kubuce masa, don haka bai yi kwauron baki ba, ya yi ta maza (in ji mata) ya ce da Hadiza cikin wata irin lallausar murya da ya kasa yarda cewa tashi ce. "Wato fushi kika yi? Kika daina halartar karatun ki sabida na kore ki a kan kin yi min laifi?" Ta yi ajiyar zuciya a hankali ba tare da ta juyo ba, ta ce, "A haba Doctor! Wane ni in yi fushi? Mum dina aka kwantar a asibiti kuma ni nake jinyar ta sai jiya aka sallame mu". Ya nuna tausayi tsantsa a kan kyakkyawar fuskarsa, a fili kuma ya ce, " Am sorry….!" Ta juyo don ta yi mishi murmushi, suka yi ido hudu da dan Inna Halima, wani chemistry yayi aiki cikin 'yan dakikai, ya kimsa wani al'amari mai GIRMA a zuciyoyinsu mai wuyar bayyanawa. Gwiwoyinta suka yi sanyi, zuciyarta ta karye, duk wata soyayya da Allah ya halitta a zuciyarta ta hadu ta tattare ta dunkule a waje daya. To haka shi ma. Jikin shi ya ba shi wannan ita ce matar auren shi, wadda za ta samar mishi da 'ya'yan da zai yi alfaharin fitowar su daga tsatson ta. Ya ce. "A bani address zan zo in duba Mamar mu". Muryar Dr. Sulaiman har tsakar kan Hadiza. Daga ita har Surayyah sai suka yi mutuwar tsaye, domin abune da ko da wasa basu taba kawowa ba. Kowa ya san shi da halin ko in kula da yake nunawa a kan mata, musamman dalibansa, wanda ke burge kowa. Don haka sun sha mamaki. Ita Hadiza ta kasa magana, sai Surayyah ce ta rairayo mishi adireshin Hadiza. Ya ce, "Idan na zo wa zan ce?" Ta ce, "Hadizah!". Ya ce, "Hadizahh, am I welcome?" Ta yi murmushi ta ce, " You are welcome, our humble consultant!!". (The beginning of everything kenan ). Tun daga wannan ranar kakkarfar soyayya ta kullu tsakanin Malamin da dalibarsa, kullum suna tare, a gida ne ko a ofis. Abin ya soma bayyana ga abokan aikin shi da abokan karatun ta, da manyan likitoci mata na bangarensa da ke yi mishi asirtacciyar soyayya. Wannan ya janyo ma Hadiza hassada karara a wajen mafi yawan abokan karatun ta, to ita ma sai ta share su, saboda ta san Surayyah kadai ke kaunar ta saboda Allah. ***Auren su, wani abu ne da ya bar dimbin tarihi a asibitin Malam Aminu Kano, domin mafi akasarin likitocin cardiology department kabilu da Hausawa sun halarta. Ba a taba ganin daurin auren da ya tara 'yan boko tsantsa, manyan likitoci ziryan a unguwar Karkasara irin na Hadiza ba. Suka tare a gidan Sulaiman da ke cikin asibiti, cikin wata irin soyayya mai wuyar fassarawa. Aure ne auren soyayya mai tsabta, wanda babu ha'inci, yaudara ko karya a cikin ta. Kar-ta-san kar, kowa ya san asalin kowa. Dr. Sulaiman ya sha mamakin samun Hadizah a cikakkiyar mace (virgin) wani abu da bai taba zuwa cikin hasashen sa ba, musamman in aka yi la'akari da matakin karatun ta. Ba gaskiya bane zargin da ake yiwa da yawan 'yammatan (medicine), kawai dan iska dan iskan kansa ne, amma da yawa abin da ya kai su shi ne a gabansu. Cikin shekaru uku da auren su ta yi mishi tukuicin kauna da Munib da Muniba, wannan ya kara sayowa Hadiza matsiyaciyar kauna a zuciyar Sulaiman. Daga baya ne da ya kammala ginin da yake yi a Janbulo suka bar cikin asibiti suka koma, daga nan ne likitocin aka rufe bakin mahaifa ruf, aka fuskanci cigaba. Hadiza ta kare karatun ta cikin nasara, da taimakon mijinta. Ita ce (overall) a year din su. Da gudu aka rike ta a (labour room) wato dakin haihuwa. Sannan ba ta tsaya a nan ba, ta ci gaba da halartar kwasai-kwasai a kan bangaren ta. Har kawo matakin da ta ke kai a yau, na cikakkiyar likitar mata. **** Karfe hudu na yammacin ranar litinin aiki ya tsagaitawa Dr. Hadiza, babu yawan marasa lafiya, don haka ta soma hada 'yan komatsanta don barin asibitin. Tun safe yau kanta ke damun ta da ciwo, gida kawai take so ta je ta huta. Amma dole sai ta fara ganin Sulaiman tukunna, akwai wasu kudi da take son karba a wajen sa za ta biya ta kai ma Fati tayi (registration). Ta bude motar ta kenan ta zuba shirgin hannun ta, wata Nurse ta karaso da gudu tana haki tana kiran ta, "Dr. Hadizah!" Ta juya tana kallon ta har ta karaso. "…….Don Allah ki taimaka, wata ce aka kawo yanzun nan da alama ba za ta iya haihuwa da kanta ba, sai bleeding (zubar jini) take". Ta kama kanta dake sarawa ta ce, "Lokacin tashina ya yi, yanzu Dr. Surayyah za ta zo.........” Nurse din ta katse ta, "Ki ceci rai kamar yadda kika saba, sakayyar ki na wajen Allah! Daga matar har Babyn suna cikin hadari, ga shi babu likita ko daya duk sun shiga meeting. Sannan Surayyah babu wanda ya san lokacin da za ta karaso". Hadizah mai sanyin zuciya, matar ta kashe mata gwiwa da tausasan kalamanta. A take ta manta da ciwon kanta, ta rufe motar ta koma gun mai haihuwa. Wannan halayyar ta ce da ta sha banbam da ta sauran likitocin labour room da kowa ke kuka dasu. Zuciyarta mai laushi ce, shi ya sa daga likitocin har Nurses zuwa labourers ke son ta, suke jin dadin aiki da ita. Hadiza is simple, komi nata a saukake yake. Da gaske ne matar ba za ta iya haihuwa ba. Ta kai matuka wajen galabaita, ta soma ba ta dukkan taimakon da ya dace. Tana cikin aikin Dr. Surayyah ta iso, suka tsaya tare a kan matar nan. Cikin dan lokaci sun yi nasarar fitar da jaririn amma ba rai. To alhamdulillahi an samu uwar. Tana zare safar hannunta ta ce da Surayyah, "Ko da ban zo gobe ba, don Allah ki kular min da matar nan, haka kawai nake jin tausayin ta, dube ta yarinya karama, ga dukkan alamu ba ta isa auren ba suka yi mata. Allah ne ya taimake ta sun zo asibiti da wuri, da babu mamaki VVF ya same ta, wannan stitches da me yayi kama!". Surayyah ta ce, "Matsalar mutanen karkararmu kenan, ban san yaushe za su hankalta ba. A kullum fadakarwa ake a radio da talabijin, amma kamar ana kara zuga su. Allah ya kyauta. Balle ma me zai hana ki zuwa idan da rai da lafiya?" Ta girgiza kai ta yi dan tsaki, ta ce, "Bana jin dadi ne". Surayyah ta ce, "To Allah ya kawo sauki, a shafa min kan Munib": Da haka suka yi sallama ta fita. Da yake yau kowa a motar shi ya zo, wato itada Sulaiman, kasancewar lokutan ayyukan nasu sun banbanta. Akwai tazara sosai daga inda ta yi parking zuwa cardiology. Tana tukin tana duba agogon ‘gucci’ da ke daure a damtsen hannun ta na hagu. Yau Dr. Sulaiman aikin kwana gare shi, kudin Fati sun tsaya mata a rai, ga shi jakarta (is empty). Sannan is too late ta je banki ta fitar da kudi (lokacin ba ATM). Ba al'adar ta ba ce tambayar Sulaiman kudi ba, saboda duk wata yana cika mata account ba tare da la'akari da albashin ta ba. Ita da kudin ta sai dai ta yiwa iyayen ta da 'yan uwanta hidima, amma duk wani nauyin rayuwar ta Sulaiman ya dauke shi. Sau tari, ta kan ji kawayen ta da ba suyi aure ba irin su Dr. Surayyah, na tattaunawa a kan abinda ya hana su yin aure, su kan ce da ka yi aure shi ke nan ka shiga matsalar da namiji (wulakanci, rashin tsayawa ga mace daya, rowa da sauran su). To ita dai yau shekaru biyar cif, ba ta ga ta inda nata da namijin ya kuskuro ta ba; Matakin iliminsa bai sa shi ya zamo cikin kowanne irin aikin ashsha ba. Bai sa shi ya zamo mai tauye mata hakki ba, bai sa shi ya zamo mai girman kai a gare ta ba. Kullum tambayar shi, "No problem Haddizah (babu matsala Hadiza)?" Ta kan tambayi kanta, yadda neman mata ya zamo ado ga akasarin mazan wannan zamanin, masu matakin rayuwa irin nashi, mai ya sa ban da Sulaiman? Duk da kasancewar shi cikin rukunin mazan data ke da tabbacin suna bukatar mace fiye da daya. Ta yadda duk juriyar ta wani lokacin har ta kan nuna gazawar ta. Allah ya halicce ta da rauni a fannin auratayya. Ta taba tambayar shi a wani dare cewar, "Don me ba zai kara aure ba?" Sai ya kankame ta. Ya ce, "Haddizah you are okey for me, in dai ba za ki yi min rowar ni'imtaccen jikin ki ba........." Ta ce, "Baban Munib gani nake ina kwarar ka, you seem not o.k........" A hanzarce ya ce, "Ni na gaya miki?" Ta girgiza kai. Ya ce, "To kar ki kara yi min wannan zancen, silly girl kawai". Ta yi murmushi, da tunanin ta ya zo nan. Dai-dai lokacin da ta iso cardiology, ta yi parking a inda aka tanada don adana motoci ta fito rike da jakarta. A nutse ta karasa (male ward) inda office din Sulaiman yake, ta tura kofar bayan ta murda tare da sallama. Da alama aiki ya kacame masa, yana ta rubutu cikin file-file dake gabansa, ya daga kai yana duban ta duba na so da kauna, kuma na nutsuwa kamar yana son karanto ainihin damuwar da ke fuskarta. Ya mike ya baro kujerar sa ya zauna a masangalin kujerar da ta zauna, wato ta ganawa da patients, ya zare mata gilashi, ya goge gumin dake tsakanin hancinta yace, "Ya ya ne Dr. Hadiza, you look exhausted!" (Da alama kin gaji likis). Ta lumshe zara-zaran gashin idonta ta ce, "Migraine ke damuna (ciwon kan barin kai guda)". Ya kai lallausar tafin hannun shi goshinta, har sai da ta ji wani shock kamar yau ya fara taba ta. Ta yi saurin ture hannun sa, za ta yi magan Dr. Abdullahi ya turo kofar ya shigo, da sauri ya koma yana “excuse me plzzz.......!" Duk suka yi murmushi. Ya ce, "Kin sha magani?" Ta girgiza kai, "Ina so in je Karkasara ne". "Amma lafiya na gaba da komai ko?' Ta ce, "Zan biya emergency in amsa kamin in wuce". Ya kai hannu cikin rigarta wai zai ji temperature na jikin, ta yi saurin rike hannun ta ce, "Haba Sulaiman......." Shi ma ya ce, "Haba Hadizahhh….! Ni kadai zan kwana fa, babu dumin jikin ki Hadizah…..?" Ta yi murmushi ta rusunar da kwayar idon ta cikin jin kunyar furucinsa, domin dai ita mace ce mai tsananin kamun kai a gaban mijinta da jin kunyar sa, kai ka ce basu haihu tare ba. Kullum girmansa da kunyarsa da kimarsa karuwa suke a idanun ta. Yace. "Ke kwanta in duba ki, ban yarda dake ba, har yanzu ba ki cire wannan loop din bane (IUCD)". Ya soma laluben ta. Ta rike hannun shi ta marairaice tace, "Wallahi na cire".Ya ce, "To ko ke fa? 'Ya'ya nake so Haddizah, ki yi ta cika min gida dasu. Bamu da wani sauran abinyi a gaba banda rainonsu da tara su. Bani da harshen da zai iya bayyana hakikanin son da nake miki, you are my life Hadizah….., kada Allah ya rabamu.......". Ya shiga nuna mata son, practically (a aikace) irin yadda bai taba yi ba. Murmushi tayi. Ta ce, "Sulaiman naka son ka sani, amma baka san nawa ba. Sannan ban san yaya zan yi in fassara ba. All I can say (abinda zan iya cewa shine) ina son ka Sulaiman, son da nake yiwa raina......”. Ya kai hannu ya toshe mata baki, wayar shi ta yi kara ya juya yana amsa call din amma bai saki hannunta ba. Ya gama ya kashe ya maida aljihun shi, yana yi mata wani sassanyan kallo ya ce, "Ki yi min alfarma ki taya ni kwana ko hira ce ki dinga yi min ina aikin". Ta ce, "Ka yi min afuwa Baban Munib, Fati zan kai ma kudi za ta yi registration gobe". Da sauri Ya ce, "Registration din Fati ya fini?" Ta bude baki ta rufe da hannun ta, ta kasa cewa komai. Ya tsare ta da sexy eyes din sa, masu kassara ta, ba shiri ta sunkuyar da kai, don ba ta iya jure kallon idanuwan nan na Sulaiman din ta, masu rikirkita kowacce lafiyayyar diya mace, balle ita matarshi ta sunnah, data fi kowa sanin sirrinsa na zahiri da badini. A raunane ta ce, "Ban so ka yi min wannan fahimtar ba". "Sai wacce kike so in miki?" "Irin wadda ka saba, understandable (ta fahimta)". Ya yi murmushi ya mike daga kujerar ya koma mazaunin shi, duk ya shafa mata mayataccen kamshinsa na turaren ‘Chris Adams’. Nutsuwar matarshi da haibarta na burge shi, magana take cikin nutsuwa da haiba, kamar ba daga bakinta furucin ke fitowa ba, dauke da matsananciyar kauna a cikin kwayar idanun ta. Son ta da kaunar ta na kara kwarara a zuciyarsa, ya rasa inda zai sa kansa. Ya kama kanshi da hannuwan shi biyu.Ya ce, "Hadiza bana so ki tafi ne, sai in ji ni lonely kamar maraya........!" Ta ce, "Alfarma za ka yi min Sulaiman, muna tare muddin rayuwar mu". Ya mika mata hannu ta kama, ta isa gare shi. Ya miko mata kumatun shi ya ce, "Kiss me plzzzz……???". Ta ji kunya sosai, ta boye kanta a kafadun shi, ita ba ta iya wannan keke-da-keken ba. Ta ce, "Kudin da zan kai mata za ka bani Sulaiman, ba kudi a waje na". Ji yake in zai iya ba ta ranshi, to zai ba ta. Balle duniyar da abin da ke cikinta. Bai tambaye ta me za ta yi dasu ba, ko adadin da take so, ya kwaso duk abin da ke cikin aljihun shi ya zuba a jakar ta. Allah sarki! Kamar ba za su rabu ba, a lokacin har duhun dare ya shigo, likitoci uku ne da ke karkashin sa suka kwankwasa suka turo kofar suka shigo. Dole Hadiza ta dau jakarta da lab-coat hadi da gilashinta ta fita, yana kara jaddada mata ta yi tuki da kula. Dan banzan go slow ne ya tare ta a titi, ba ta isa gidansu ba sai tara da rabi, Maman su da suke kira Yaya, tana zaune a tsakar gida da rediyo a hannun ta tana sauraron Jakar Magori. Autan su Abdulyassar yana gefe yana hada motar kara. Yaya Babar su Hadiza ba wata tsohuwa ba ce cancan, don irin auren wurin nan aka yi mata, shekarun ta arba'in kenan. Hadiza ta yi sallama Yaya ta amsa, Abdulyassar ya watsar da kayan wasan shi da gudun shi ya kwaso ya rungume 'yar uwar shi, kasancewar ta mai jan su a jiki tare da nuna musu kauna. Yana tambayar ta ina Munib? Daga can dakinta na 'yammatanci, wanda a yanzu ya zan mallakin Fati, sautin Abdurrahaman Sudais ke tashi a hankali cikin suratul Al-Imran, wannan ya tabbatar mata Hafiza FATIMA JA’AFAR na gida. Ta samu gefen Yaya ta zauna, Yaya ta mike daga kwanciyar da ta yi bisa tabarma. Kai da ganin kyakkyawar fuskarta ka san ta ji dadin ganin diyar tata, ta ce, "Da daddaren nan Hadiza? Shin ba Sulaiman ya hanaki tukin dare ba?” Ta ce, "Wallahi Yaya, Dr. ne ya tare ni da magana, tun dazu na tashi, aikin kwana zaiyi shiyasa bamu zo tare ba, na kawo ma Fati kudin ne". Ta ce, "Amma kin kyauta, don da ta yi ma Yayan ku maganar ta waya ya ce ba zai samu zuwa Kano wannan satin ba, ga shi baban ku kwanan nan kasuwar ta ja baya, kuma ta ce daga wannan satin za a rufe". Ta ce, "Baba bai dawo bane?" Yaya ta ce, "Ya dawo tun yamma, ya tafi dubiyar dan gidan Malam Abdu ne babur ya buge shi dazu". Ta ce, "Allah ya sauwake, Fati na ciki ko". Yaya ta ce, "Yanzu ta gama cin abinci ta shige ciki tana rehearsal, jibi za su yi musabakar jiha kuma ita za ta wakilci jihar Kano, kin san Fati ba daga nan ba". Cikin alfahari da kanwar tata a zuciyarta, Hadiza ta tura kofar dakin cikin sallama ta danna kai, Fati ta diro daga gado ta rungume 'yar uwarta tana yi mata oyoyo. Hadiza ta dubi Fati sama da kasa, yau sai ta ga ta zame mata cikakkiyar budurwa sosai. Ta kama baki. "Fati girma haka?" Fati ta yi murmushi, kumatunta duka suka lotsa gwanin sha'awa, wushiryarta ta fito siririya da ita. Hadiza ta ce, "Wane course aka samu?" Ta ce, "Course din da na nema ne (B.A Islamic Studies)". Ta ce, "Masha Allah, da an je kuma sai a samo saurayi, irin wannan girma haka Fati?" Ta ji kunya, ta boye fuskarta cikin tafukanta, ta ce, "Ai hijabi zan ke zumbulawa irin mai hannun nan, kada a ce ana so na". Hadiza ta ce me za ta yi ba dariya ba, duk girman Fati baka raba ta da wauta. Ta kirgo kudi a jakarta naira dubu ishirin ta ba ta, Fati ta yi godiya ta ce, "Allah Yaya Hadiza kwana biyu ba’a kawo su Munib ba". Ta ce, "Makaranta ta boye su, amma da anyi hutu suna nan tafe insha-Allah". Sai sannan ne ta ga hakoran Fati. Ita shaida ce kan cewa ba abinda Fati ke so a duniya irin ‘ya’yanta Munib da Muniba. Ta ce, "Ashe kuma musabaka za a yi Fati ba labari? To Allah Ya ba da sa'a". Ta yi murmushi ta ce, "Ameen". Tana shirin fita Baban su na shigowa, ya ce, "A'ah, manyan likitoci ne yau a gidan namu? Ina matas da abokin?" Ta yi murmushi ta tsuguna har kasa ta gaida tsohon ta, ta ce, "Suna nan lafiya basu samu hutu bane, da sun samu za su zo". Ya ce, "Kinga kafar nan tawa kwanan nan bana jin dadin ta, har na gaji da hadiyar magani". Ta ce, "Wane magani ne Baba? Likita ne ya rubuta?" Ya ce, "A'a, maganin ciwon kashi ne kawai nake saya a wajen masu talla". Ta kama baki cikin gigicewa, "Baba irin wadannan magungunan ba masu kyau bane, yawanci ma sun yi expiry don Allah ka daina sha. Baba meye amfanin mu nida Sulayman? Da har zaka sayawa kanka magani? Yanzu bari in rubuta maganin in bawa Fati ko Hamza su je su siyo". Ya ce, "To na gode". Ta baro Karkasara karfe goma dai-dai na dare, dauke da tazbihi a bakinta domin ba abu ne da ta ke so ko ta saba ba, abu ne da mijinta ke matukar ki, wato (night driving) tukin dare. Ta biyo ta titin Court Road ta hawo titin Gandu, ta yi kwana ta hau titin B.U.K Road. Ta iso Kabuga ta dau titin sabuwar jami'ar Bayero, wanda zai sadata da Janbulo. Babu wadatar motoci a titin. Daga gefen ta wayarta ta yi kara, sunan Sweetypie ya soma yawo a screen din. Ta yi murmushi ta mika hannun damanta ta dauka, ta rike sitiyari da hannun hagu cikin sanyin sauti ya ce, "Yaya dai D.Z? Hope for now kina gida???" Ta yi ajiyar zuciya cikin karyayyar murya ta ce, "Na kusa dai, ina kan hanya.........". Iya abin da ya ji ke nan sai wata irin kara da ta fi kama da fashewar taya, ya yi kira "Hello!.....Hello....Hadddizah!" Amma ba amsa. Motar ta hantsila ta shige karkashin wata trailer da ke cike da buhunhunan abinci, duk da kokarin da direban ya yi wajen kauce mata hakan bai samu ba, motocin da ke gabansu da bayan su duk suka yi birki cikin salati, tsirarun mutanen da ke gefen titi suka runtumo don kawo agaji. *******Ta hanyar katin shaida (ID Card) jami'an tsaro suka gano ko wacece Hadiza. Don haka ba su sha wahalar samun nombar wayar mijinta ba, wanda ke can cikin gigicewa. Nan asibitin aka taho da ita cikin jinni kaca-kaca, rai a hannun Allah. Likitoci biyar ne a kan Hadiza, sai Sulaiman cikon na shida, wanda ya manta wani abu wai shi karatun likita, komawa ya yi tamkar bai taba halarta aji ba. Shi da Hadiza da ke kwance babu maraba, illa shi a tsaye yake, sai dai jingine da garu (bango), wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa. A lokacin da za ka tsaga ba za ka samu ko digon jini a cikin jikinsa ba. Tashin hankali ba a sa maka rana! Haka wannan mummunan labari ya iske iyayen Hadiza da 'yan uwanta ta hanyar Dr. Surayyah. A daren Mukhtar ya baro Kaduna zuwa Kano, a daren suka dungumo baki dayan su suka taho, sai dai basu samu ganin Hadiza ba. Har zuwa lokacin likitoci na tsananta bincike a kanta, haka suka kwana a barandar asibiti cikin tsananin sanyi. Amma babu mai jinsa. Fati sai kuka take kamar ranta zai fita tunda suka taho, Yaya na lallashin ta. Sai washegari da safe result din Hadiza ya iske Sulaiman da iyayen ta, bayan raunuka da ba za su kirgu ba, babu karaya ko daya a jikinta. Babban tashin hankalin wanda ya girgiza kowa shi ne, jijiyar bayanta wadda ta hada daga wuya zuwa bayan ta (spinal cord) ta tsinke, wanda ke nufin Hadiza ba za ta kara iya mikewa ba, ba za ta kara iya tafiya ba a gaba daya sauran rayuwar ta. Dr. Sulaiman ya mike tsaye ya nuna Dr. Samson da dan yatsa, "Ka san abin da kake fada, ban san cewa baka san aikin ka ba sai yau. Kuma shi ke nan daga yin accident sai ka nakasta min mata? Uwarka ce ba za ta kara iya mikewa ba, amma ba Hadiza ba......" Kai da ganin yadda yake maganar, kwayar idanun shi a juye, ka san ba a hayyacin sa yake wannan furucin ba. Samson ya sunkuyar da kai, duka likitocin babu wanda ya kara magana. Tausayi ne fal a zukatan su. Dr. Hadiza abar so ce ga kowa, suna jin dadin tarayya da ita, marasa lafiyan ta na yaba kokarin ta. Wannan accident da ya yi mata karan tsaye da kuruciyar ta, ya zamo nakasu ga dimbin taimakon da take bai ma al'umma. Malam Ja'afar mahaifin Hadiza da ke gefe shi ya soma tausar Sulaiman da kalami masu dadi da sanya imani, yana tuna masa muhimmancin yarda da kaddara. Sulaiman ya yi shiru, ya koma ya zauna a kujerar sa. Ya kifa kai cikin cinyoyin sa, amma har yanzu ya kasa yarda da abin da kunnuwan sa suka jiye masa. Wai Hadiza ta zama sai dai a kwantar a tayar ba za ta kara amfanuwa ba, ba za ta kara moruwa ba. Balle ta amfanawa kanta komai. Ita da 'ya'yanta da mijinta sai dai gani da ido. Abin da suke gani kullum yana faruwa da al'umma yau Allah As-Samadu ya juyo da shi kansu. Dimbin ilimin su, karfin aljihunsu da tunanin su babu abin da zai iya a kai, domin ita wannan jijiya ba ta doruwa. Sai ya fashe da kuka. Malam Ja'afar ya mike daga kujerar sa ya isa ga Sulaiman, ya mikar da shi tsaye ya rungume a jikinsa. "Haba Sule! Kamar ba namiji ba? Namijin ma, likitan likitoci. Ba ka yi kuka a kan sauran al'umma da kuke kwana da yini kuna fama dasu ba sai a kan matar ka kadai? Su Allah ba ya son su ne yake dora musu lalura? Allah da ya halicci Hadiza ya fi mu son ta, shi kadai ya san dalilin sa na hukunta hakan a gare ta. Yau in Hadiza mutuwa ta yi me zamu iya ban da mu yi mata addu'a? Amma tana raye, a kalla muna ganin ta muna jin dadi, ka yi tawakkali ka barwa Allah, ka zamo mai YAKANAH, sai ya yi maka tukuici da abin da baka zata ba. Kai za ka ba ta kwarin gwiwa, ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata. Amma idan ka fita karaya, wane ne zai karfafa wani?" Ya mika hannu yana share masa hawayen da suka kasa daina ambaliya daga kyawawan idanun sa. Dr. Ruth ta yi gyaran murya, ta dubi Dr. Sulaiman ta sunkuyar da kanta, kana ta dago ta ce, "Ina ganin idan Dr. Hadiza ta ji sauki, raunikan jikinta sun warke, za ta iya ci gaba da aikinta ta hanyar amfani da wheel chair, idan har za’a samu wanda zai juri kawo ta da mai da ita". Kiris! Ya rage ya lailayo ashar ya antaya mata, ko ya faska mata mari, amma da ya tuna Malam na wajen sai ya balla mata harara, a zuciyar shi ya ce, "Uwar ki za a sa a wheel chair ba uwar Munib ba!!!". Samson ya ce, "Shawarar Ruth abar dubawa ce, hakan zai debe mata kewa fiye da ta zauna a gida ba abin da take yi. Ko ba don zuwa aiki ba dole za a nema mata wheel chair ko da a gida ne". Ba shi da abin cewa, don duk likitocin abin da suke cewa kenan. (They cannot afford to lose HADIZA in the Nigerian medical practition). Malam dai baya ji saboda cikin harshen turanci suke maganar. Shikadai ne ba likita ba a ofishin. Wannan na jefo tasa wannan na jefo tasa kai kace a gaban ofishin Barrack Obama kake. Da zancen ya ishi Sulaiman sai ya tashi ya fita cike da jin zafinsu. Ta amfanin ta ga Nigeria da asibitin su suke, bata gurguncewar rayuwarta bakidaya ba. Ya nufi ICU inda aka kwantar da Hadizah. A bayan kofa ya tsaya ya rabe, yana leken ta, ya kasa karasawa, ya kura mata ido yana ta'ajjibin yadda kwana daya rak! Allah ya jirkitar da kyakkyawar fuskar Hadiza, ko ina a jikinta rauni ne, nan plasta can plasta. Barci take sadidan, sai dai da gani ba na Allah da Annabi bane (na karfin allurai ne). Rabin fuskarta nade cikin bandeji, wadda ta kumbura ta yi sumtum kamar an hura (baloon). A hankali ya soma taku ya isa ga gadon da take kwance, ya ja kujera ya zauna dai-dai fuskarta yana fuskantar ta. Ya kai hannu bisa goshin ta wanda ke nade cikin bandeji, kamar an ce da ita bude idon ki. Suka yi ido hudu da Sulaiman din ta, ta dubi dakin ta dubi kanta, ta tabbatar a kwance take a gadon asibiti. Ta maido duban ta ga Sulaiman wanda ke binta da ido da zuciya, ta ce cikin kankanuwar murya, "Sulayman Accident na yi ko?" Ya daga mata kai. Ta dora hannunta mai rangwamen raunika bisa nashi dake goshin ta, ta sauke, don ji take kamar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse. Ta yunkura da niyyar ta tashi zaune amma ta ji kamar ba jikinta ba, ya mike ya kama ta ya mikar da ita zaune. Ya janyo pillow ya tusa mata don ta ji dadin jinginar, ya tabbatar dai da gaske ne Hadizar shi ta zama disabled (nakasasshiya), sai jikinsa ya soma kyarma. Duk dauriyar da yake yi abin ya ci tura, da sauri ya rungume ta, cikin shesshekar kuka ya ce, "Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!" Kuka suke dukkanin su babu mai rarrashin wani, don ita Hadiza ta tabbatar abin da zai sa Sulaiman kuka, to tabbata ba karamin abu bane, wannan shi ya gigita ta, ita ma ta fashe da kuka. Fati a gaba, Yaya, Malam, Hamza da babban Yayan su Mukhtar suka shigo, daga Hadiza har Sulaiman babu wanda ya san da shigowar su, shessehekar kukan Fati ne ya ankarar da Sulaiman cewa akwai mutane a dakin. A hankali ya zare jikinsa daga na Hadiza ya juya ya fita daga dakin ba tare da ya iya hada ido da surukansa ba. Malam Ja'afar ya karasa jikin gadon Hadiza ya kama hannun ta inda babu ciwo, ya ce, "Ki yi tawakkali Hadiza, ki zamo mai YAKANAH a dukkanin al'amuran ki, ki zamo mai godiya ga Allah a duk yanayin da kika tsinci kanki. Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba, yarda da kaddara dole ne ga duk musulmin kwarai". Cikin kuka mai tsanani ta ce, "Na ji Baba, amma don Allah ku fada min me ke faruwa dani? Sulaiman bai gaya min komi ba, sai kuka yake yi, kukan shi ya daga min hankali, ku fidda ni a duhu. Wani abu ne ya faru dani?" Malam ya sa habar babbar rigar sa ya share hawayen da suka ciko mishi ido cikin dabara wai kada Hadiza ta ga shi ma kukan yake kamar Sulayman din, amma ta ganin. Hadiza ta musamman ce ko a cikin 'ya'yansa, yana son ta son da bai yiwa su Mukhtar, ta kama duka hidimar gidansa ta rungume, kafin Yayanta Muktar ya Kawo sau daya ta kawo sau goma. Ta sha cewa don su take aiki. Ganin Babanta yana kuka wiwi sai ta kara tsananta kukan ta. Cikin tausasawa Mukhtar ya ce, "Cool down Hadiza, take it easy......." Ya shiga rattabo mata al'amarin da ya samu rayuwarta, ya kare da cewa, "Wannan shi ne ya dagawa Sulaiman hankali, amma kamar yadda Baba ya ce ne, ki yi tawakkali, ki zamo mai YAKANAH! Wannan ba shi ne karshen rayuwar ba!" A matsayinta na cikakkiyar likita, ma’abociyar sani a fannonin kiwon lafiya, tuni ta hararo mummunan nakasun da ya samu rayuwarta rana tsaka wanda babu wani likitan duniya da zai iya maganin shi. Ta nemi hawaye a kwayar idonta ta rasa, ta nemi miyau don ta hadiya a kan harshen ta ya kafe karaf! Kamar bai taba gudana a cikin bakinta ba. Ta runtse idonta da karfi, tsawon mintuna biyar ba ta bude ba. Ita kadai ta san radadin da take ji a zuciyarta, ita kadai ta san azabtuwar da ruhinta ke yi, al'amarin ya shallake tunanin ta. Ba ta yi tsammanin al'amarin ya yi kamarin haka ba, bata taba kawowa ba, spinal cord injury! A gareta ita Hadiza. Lallai dan adam ba a bakin komai yake ba. Yau ne kake mai rai, gobe ne kake gawa. Yau ne kake da amfani, idan Ubangiji ya so, gobe ne ka zama tarihi. A rayuwar Hadiza ba ta taba tsammanin wata kaddara makamanciyar wannan za ta taba shafar rayuwar ta ba. To ina ruwan Allah! Ta bude idon a hankali daga runtsewar data yi musu, tana kallon iyayen ta da 'yan uwanta wadanda dukkanin su ke sharar hawaye, sai ta soma lallashin su cikin muryar ban mamaki, tamkar ba ita ba. Ta fi su karfin zuciya, ta fi su tawakkali, ta fi su YAKANAH. Ta karbi kaddarar ta da hannu bibbiyu, tana fatan Allah ya sa hakan ya zamo kaffara a gare ta, in kuma jarrabawa ce ya sa ta cinye jarrabawar ta. **** Dole kanwar naki, Sulaiman yana ji yana gani, da hannusa da kudinsa ya sayo ma Hadiza wheel chair ana i gobe za a sallame su daga asibiti. Wani bigire na karshe da ko makiyinsa baya yiwa fatan ya hau. Don duk raunin dake jikinta ya kame sai karfin jiki da dan abin da ba a rasa ba. Yaya ta so Sulaiman ya ba ta Hadiza ta wuce da ita gida inda za ta fi samun kulawar iyaye da 'yan uwa, amma sai ya sa musu kuka. Da me zai ji ne? Da lalurar da ta kashe masa rayuwa, ko da rashin Hadiza a cikin gidan, wadda ta zamo wani bangare na rayuwar sa, kundin farin cikin sa, sannan barin jikinsa? Dole suka kyale shi da matar shi, amma sun ce Fati ta koma gidan ta zauna tare dasu, don ta dinga taimaka masa kula da Hadiza, musamman kasancewar sa ba mazauni ba. Sulaiman bai so ba, don shi tun fil'azal Allah bai sa mishi son Fati ba, saboda son da Hadiza ke mata. Yana kishin Fati, a ganin sa Hadiza ta fi son Fati a kanshi. Sannan zubin ta na zuhudu (gudun duniya) ya yi yawa, bai fiya son mutane irin ta ba, kasancewar shi (sociable). A tsarin halittar dan adam (personality), tana cikin rukunin al'ummar da ake kira (introvert). Ba ta iya hada ido da shi, kai da kowa ma, saboda kunya. Da wuya ka ga hakoranta, sai dai in guri ya kure ta yi murmushi, ‘dimple’ din da ‘cleft’ su lotsa, wanda shi ne muhimmin al'amarin da ke daukar hankalin dubban maza a kanta, sai dai kuma bai isa ya tsallake hukuncin da Yaya ta yanke ba. Haka Fati ta hado kayan ta tsaf, ta dawo gidan 'yar uwarta da zuciyar 'yan uwantaka. Zuciyarta cike fal da so da kaunar 'yar'uwar ta da tausayinta, karatun da ta taso shekara da shekaru da burin yin sa, gashi ta samu, amma a yau ta sallama shi, ta jingine shi ta sadaukar da rayuwarta kacokam da lokacinta ga rayuwar, 'yar uwarta Hadiza. Sulaiman ya ciccibo Hadiza ya fito da ita daga mota, Fati ta bude (boot) ta fiddo wheel chair a nade, cikin sauri ta warware, Sulaiman ya sanya ta a ciki ya tura a hankali zuwa cikin gida. Fati ta fiddo kayansu daga cikin motar ta rufe motar, ta soma diban kayan daya bayan daya tana shiga dasu cikin gida. Malam Ilu maigadi, ya yi sallama a falon, a lokacin Sulaiman na kici-kicin aza Hadiza a daya daga cikin kujerun falon, ba tare da ya juyo ba ya amsa masa. Ya zube har kasa yana jajantawa iyayen gidansa kaddarar da ta same su. Yana magana yana sharar hawaye, saboda yadda yake matukar kaunar Hadiza, saboda karamci da kyautatawar ta gare shi. Haka Goggo Alti ta fito daga kitchen, ganin Hadiza yau nade cikin kujera sai ta fashe da kuka, Sulaiman ya yi saurin ficewa a falon ya dau mota ya fita don dauko yara a makaranta. Hadiza ta dubi Alti ta yi dan murmushi, "Alti wane ne ya halicce mu?" Ta ce, "Allah (S.W.A)". Ta ce, "To kinga in haka ne ke nan bamu da iko da kanmu sai abin da ya ga damar hukuntawa a gare mu, mu kuma dole ne mu zamto masu godiya idan har muna so imanin mu ya cika". Alti ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na uwargijiyarta. Hadiza ta juya ga Fati ta ce ta kai kayanta dakin ta, kasancewar a tsarin gidan likitocin babu wani extra room, ita za ta yi amfani da na Sulaiman. Fati ta ce atafau ita dakin su Muniba za ta zauna tare dasu, ta kada ta raya amma ta ki, ta ciccibi jakarta ta yi dakin su Muniba d ita. Fitar ta daga falon ke nan su Munib suka dira a falon, Baban su na biye dasu yana rike da jakunkunan su da food flasks din su. Suka tafi da gudu suka rungume Mamarsu, Munib da yake shine mai wayo ya ce, "Mummy yaya jikin ki? Daddy ya gaya mana kin yi accident kin ji ciwo kina asibiti ana yi miki allura?" Ya kai hannu ga tabon ciwon goshinta, "Sannu Mummy, kin ji?". Ta shafa kansa ta yi masa murmushi bata ce komai ba. Ita kuwa Muniba bin jikin Mummyn ta yi ta lafe kamar mage, dama ita ba ta fiya magana ba. Zuciyarta kal da ganin mahaifiyarta da ta jima ba ta gani ba. Munib ya soma jan hannunta wai ta taso suje su yi kwallo (ball) kamar yadda suka saba, Sulaiman ya kau da kai, bai son ganin wannan abin tausayi, ya mai da hankali ga lallatsa wayar sa, baya son su ga hawayen sa. To ita ma Hadizar duk dauriyar ta sai da hawayen suka tsatstsafo, ta sa yatsun ta biyu ta dauke su, ta kama dukkan 'ya'yan biyu ta rungume a kirjinta. Kukan zuci take wanda ya fi na fili soya zuciya. Ta ce, "Ku tafi wurin Anti Fati tana dakinku ku yi kwallon tare, har yanzu bani da lafiya". Da gudu suka mike daga jikinta suka nufi dakin su suna murnar zuwan Antin su da suke tsananin so. Alti ta yi sallama dauke da tray kanta a sunkuye, idonta cike fal da hawaye, muryarta a sanyaye tace da Hadiza, "Na ce sai na daina daura abinci a tebir?” Hadiza ta yi murmushi mai hade da wani irin radadi a zuci, ta ce, "Idan maigidan yana son hawa tebir din fa?" Ta fada tana kallon Sulaiman. Bai dago ya kalle su ba, haka bai tofa musu ba, duk da ya lura ta bakinsa suke son ji. Alti ta ajiye katon tray a gaban Hadiza ta juya ta fita. Tana ba da baya ya suri Hadiza a kafadar shi sai dakin barcin su. A hankali ya sauke ta a makeken ‘family bed’ din su, ya koma toilet ya cika baf da ruwa mai dumi, ya zuba dettol kadan ya dawo ya soma warwarewa Hadiza kayan jikinta, ya nade ta cikin towel ya sake sungumar ta ya yi toilet ya sanya ta cikin ruwan da ya hada. Ita karfin Sulaiman mamaki yake bata. Ya yi mata kyakkyawan wanka da kamsassan sabulun Zest, ya nado ta ya fito da ita. Yawancin kayanta a dakin suke dama, don haka ya shirya ta cikin riga da wandon pakistan ruwan goro (orange), ya dauki (kumb) ya soma sharce mata gashin kanta da ya wanke da (head&shoulder) wanda rashin gyara kwana biyu ya sa shi duk ya cukurkude. Ta ce, "Da ka bari Sulaiman Fati za ta yi min gyaran kan". Bai saurare ta ba ya ci gaba da abin da yake, amma da a ce ta kalli fuskarshi a lokacin, data lura da yadda ya dan hada rai, saboda ambatar Fati da ta yi, wato ta fi son Fati ta kula da ita fiye da shi. Ta yi murmushi ta ce, "Amma tunda ka hada ruwan wanka ka yi mai wuyar, zan iya wanka da kaina, sai Fati ta shirya ni koda yake ma zan iya shiryawa da kaina.......". A hassle yace . "Is o.k Hadizah, very o.k, ba tun yau ba na san kin fi son kanwar ki fiye dani. In ba haka ba ni amfanin me ke gare ni? Da ba zan kula dake ba a lokacin da kike cikin lalura?" Ta kama baki, don ba ta ji dadin maganar shi ta farko ba, amma sai ta share ta ce, "Yau da gobe ne sai Allah Sulaiman…….". Can kuma ta yi rau-rau da ido kamar hawaye za su zubo, "Me ya kawo maganar na fi son Fati a kanka? Ban ji dadin nagetive response din ka ba". Ya ce, "To ai ke ce Hadiza da wani irin batu, amma ina so ki yarda da cewa, idan zan gaji da hidimar ki Hadiza, to zan gaji da hidimar kaina……". Ta ce, "Amma Sulaiman......" Ya kai hannu ya toshe mata baki, "Kina shakka da abin da na ce miki?" Ba ta son jan zancen da nisa, har ya yi tsayin da zai zamo bacin rai, sai ta ce, "Bana shakka Sulaiman, Allah ya bamu rai da lafiya". Ya turo ta cikin kujerar ta suka dawo falon don cin abinci. Munib da Muniba suka shigo, fes dasu cikin kaya 'yan kanti (pink colour) har Fati tayi musu wanka ta shirya su ta feshe su da turare. Suka saki baki cikin mamaki, ganin Daddy yana tura Mummy cikin kujera mai tayoyi, abin ki da yaro, sai ba su kawo ma ransu komai ba, ko wani abu ne ya faru da Maman nasu, sun dauka haka nan dai yake tura ta don bata da lafiya. Sai suka sa rigimar ta tashi suma Daddy ya tura su. Haka Sulaiman ya sauke Hadiza a seater, ya dauke su su duka biyun ya aza a kujerar, ya yi ta zagaya falon dasu suna jin dadi, sai kyalkyatar dariya suke. Hadiza ta juya ta dube su, ganin abin nasu ba na kare bane ta ce, "Oya! Food is ready, maza ku zo ku ci kafin malamin lesson ya zo, ko kuna so ku yi latti ya yi muku bulala?" Suka diro daga kujerar suka nufo abincin, Sulaiman ya zauna tsakanin Hadiza da Muniba, kafadun su na gugar na juna. Ta sa murya ta ce, "Fati!" Ta fito sanye da hijab, da alama sallah ta idar, kallo daya Sulaiman ya yi mata ya dauke kansa, ya ci gaba da cin abincinsa. Daga can bakin kofa ta tsaya ba ta karaso cikin falon ba, son addini irin na Fati yana matukar burge Hadiza ba kadan ba. Ta ce, "Taho mu ci abinci in kin idar da sallar". Ta yatsina fuska ta ce, "Na ci tun dazu, Alti ta zuba mini". Don jikinta ya yi sanyi da hararar da Sulaiman ke zabga mata, bayan ita ko da gida da mota aka hada ta dama ba za ta ci abinci da shi ba, don ta ki jinin mutum mai halin GIRMAN KAI. To a ganin ta halin Sulaiman kenan, babu wanda ke ganin walwalar shi sai 'ya'yan shi da matarshi, duk ilimin da ya ke takama da shi a ganin ta girman kai ba hali ne da ya dace da likita ba. Ba ta san cewa shi ma bekenta yake gani ba. Hadiza ta ce, "Don me ba za ki bari mu ci tare ba? Kada ki sake yin haka". Fati ta ce, "Haka nan na saba, ba zan iya cin abinci da mutane ba". Sulaiman ya balla mata harara, ya dago a sukwane. "Su waye mutanen? Bakauya kawai, saboda ni ne ba za ki ci ba. Na yi kama da rubabben saurayin ki ne? Dube ta da Allah kullum da zumbulelen hijabi kamar takari, gara ma ki rage wannan zuhudun ko kya samu mashinshini, don duk mijin d aka bawa ke ko da sadaka ne an cuceshi wallahi wallahi, ko mata sun kare a duniya". Fati ta harare shi ta zumbura baki kamar ta yi kuka, ta ce da Hadiza, "Kina jin shi ko?" Hadiza ta yi dariya ta ce, "Rabu da shi Fati na, ko shi din me zakiyi dashi? Allah na tuba ko mutuwa nayi ai ya yi miki tsufa, me za ki ci da dan late thirty? Sai yaro sabon jini kamar ki". Daga Fati har Sulaiman, kalmar “mutuwa” da Hadiza ta ambatawa kanta, ta taba zuciyar su. Sulaiman ya tsame cokali daga plate ya aje gefe yana bin Hadiza da wata irin harara da ita kadai ta san ma'anar ta. Ita kuwa Fati ba ta kara tofawa ba, ta koma daki tana cewa cikin ranta; “kada Allah ya nuna min wannan ranar…., Yaya Hadiza sai dai ki yi min makoki, ba dai in yi miki ba”. Kwana bakwai cif Sulaiman yana gida cikin iyalinsa bai je ofis ba, yana kula da lafiyar Hadizar sa. Ta fuskar shan magungunan ta a kan lokaci, hidimar ta da walwalar ta, tare da ba ta karfin gwiwa na karbar rayuwa a duk yadda tazo, yana nuna mata kaddarar da ta same ta ba ta shafi ko kankani na daga soyayyar da yake yi mata ba. Ta yarda, ta amince Sulaiman mai son ta ne, kuma irin mazan da da wuya a samu kamar su a wannan zamanin wajen rike alkawarin soyayya da sanin darajar diya mace. A 'yan kwanakin ta kara samun karfin jikinta, don haka ta kirkirowa kanta abubuwan debe kewa da dama, wadanda a da ba ta da lokacin su, kamar karatun jaridu da mujallu, ‘Internet browsing’ da kuma kasancewa full-time house-wife da 'ya'yanta suka kara shakuwa. Abu na hudu da take ganin zai taimaka ainun wajen debe mata kewa shi ne, rubuta tarihin rayuwar ta a matsayin story-writing cikin harshen Hausa. Wanda take so ta sanyawa suna “YAKANAH!” Da Sulaiman ya fahimci damuwar Hadiza ta ragu da 80%, sai ya samu kwarin gwiwa da jarumtakar fuskantar aikin sa. Ya koma aiki ranar monday cike da tausayin Hadiza, yana mai tuno lokutan zirga-zirgar su cikin asibitin don ceton rayukan al'umma, da matsalar ta mai magantuwa ce ba ya tsammanin in zai rasa duk abin da ya mallaka zai gaza wajen nema mata magani. A wani bangaren kuma yana tunanin shawarar su Dr. Ruth ne da suka ce Hadiza za ta iya komawa aikin ta a haka. Da ya tuntube ta, ta nuna ba ta yi na'am da wannan shawarar ba, don ba ta yanke kauna da rahmar Ubangiji ba, za ta zauna a gida ta yi zaman aure, wanda a da ba ta yi ba. Ta ga shi kuma yaya yake? Wace irin riba ce a cikin sa, tunda ta yi aikin, ta ga ribarsa da rashin ribar sa? A wautar Hadiza, tunda wannan lalura ta same ta shikenan Sulaiman ya daina sha'awar ta, wato ya daina mu'amalar aure da ita, tunda ta nakasa, ba ta da abin da za ta ja hankalin sa. Ba ta yi la'akari da cewa soyayyar ta a cikin jinin Sulaiman take ba, ba’a abun jan hankali ba. Kwata-kwata sati biyu cur da fitowar ta daga asibiti, sai labari ya sauya, Sulaiman soyayya har ta fi ta baya, kamar wanda ya je ya kara yin course a kan (love-making) ga masu lalura. Watakila da da hali da ya tsaga kirjinsa ya sanya ta a ciki, mai yiwuwa sannan ne zai zamo (contented). Sai da komai ya lafa ya fahimci Hadiza kuka take, ba kuma kukan komi take ba, ….kukan rashin yarda da kai ne. Amma shi duk sai ya rikice, kukanta da hawayen ta ba karamin daga mai hankali ya yi ba. Ya tarairayo ta ya dora a kan kirjin shi yna mai shafar bayanta, cikin sassanyar murya yake tambayar dalilin kukan, "Did I hurt you Hadizahh?'” Ta girgiza kai, cikin shesshekar kuka ta ce, "Sulaiman kai ne???" "In bani bane wane ne?" Sai ta yarfar da hawaye da hannun daman ta, ta ce. "Ni dai don Allah na rokeka, kayi min alfarma ka kara AURE!" Sai ya janye jiki daga jikinta a hankali cikin mutuwar jiki da sagewar gwiwa, "Kafin in baki amsa Hadiza, ko in bi umarnin ki, ina so in san mene ne dalilin ki na cewa hakan?" Kai tsaye ta amsa. "Saboda Hadizar da, ba ita ce yanzu ba, wannan nakasasshiya ce, ba ta cancanci wannan dimbin soyayyar ba". Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskarta a dan hasken asubahi da ya soma keto shara-sharan farin labulen dakin, kamin ya yi murmushin takaici ya zauna sosai ya bata baya. "Hadiza tafiyar ki ce ta sa na aure ki? Ko ko yanga da kwarkwasa kika yi min na ji ina son ki?" Ta girgiza kai, wasu tawagar hawaye na biyo idanunta. "Babu ko daya. Amma son da nake maka Sulaiman, ba zai barni in kware ka ba, idan ka ci gaba da zama dani ni kadai, na kware ka; a matsayin ka na lafiyayye kuma cikakken namiji. Idan ka kara aure zan ji dadi, zuciyata za ta sake. Akalla ina da tabbacin baka cikin kwaruwa, amma yanzu sai nake ganin, na kware ka........ I'm nothing but a burden to you.....". Ya daga mata hannu ya ce, "Ya isa, ya isa Hadiza...." Ya ma rasa me zai ce don takaici, sai ya karkada kai ya fita ya bar mata dakin. Kwanaki uku suna kan wannan takaddamar. Hadiza ta dage ta ja tunga a kan bakanta, in ya yi fushi sai kuma ya sauko ya yi dariya don mamaki. Yau Hadiza ke neman kai dashi. Hadizar da ko kallonsa bata so mata su yi in ba bisa dole ba. Ba ya son duk wani abu da zai bata ranta a dai wannan lokacin da yake angwancewa bayan shan jinya ta lokaci mai tsaho, da kuma yin la'akari da halin da take ciki. Don haka a rana ta biyar da ya ga ba zai iya jure wannan horon da ta tsiri yi mishi ba, don ba shi da juriyar a wannan fannin ta inda take samun weakness din sa kenan. Sai ya kama hannayen ta ya langabar da kai kamar karamin yaro, idanuwan nan sun juye sun rikide zuwa damuwa tsantsa. Ya ce, "Hadiza na baki wuka da nama, ke ce mijin ke ce matar, ki zabo min duk yarinyar da kika ga ta dace dani, don bani da idon kallon wata diya mace, tun daga lokacin da Allah ya mallaka min ke......". Ta cira kai a hankali ta dube shi, sai ya bata tausayi, don numfashi kanshi a wahale yake furzar da shi da sauri da sauri. Ganin yadda jidalin ta ya ramar da shi kwanaki biyar kacal, sai ta kara jin tausayin sa. Amma jan ajin mu na mata, sai ta balla masa harara wadda in ka lura ba komi ne cikin ta ba face tsananin son mijinta da matsanancin kishin sa, ganin daga karshe din kuma ya sauko ya bi ra'ayinta kamar yadda take so. Kamar ta yi kuka ta ce, "Nice ma zan nemo maka matar? Ashe you are not serious…!" Ta juyar da kai, sai ga hawaye sharrr! Sun zubo a kan kundukukin ta. Kiris ya rage dariya ta kubce masa, amma ya danne kada ya kara laifi. A gicciye ba tare da ya dube ta ba ya ce, "Wai ko a cikin student din ward din ku, irin 'yan yara-yaran 'yammatan nan? Ko rikakkun 'yammatan likitoci irin su Dr. Surayyah". Haushi ya kama Hadiza, don ta lura ya mai da abin zolaya. Ta yi shiru ba ta ba shi amsa ba. Ya rungumota ta baya, ya dora kan shi a kafadun ta, yana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. A sanyaye ya ce, "Ko kin daina sona ne Hadizahh? Kike neman kai dani? A da ko kallo na wata ta yi, kallon da bai yi miki ba, sai kin kwana bakya yi min magana, amma yanzu duk kin daga hankalin ki wai in yi aure. Which means...... na gundire ki…. kina neman mataimakiya don ki huta….. Ni ina ruwana da wasu kafafun ki tunda ba su nake aure ba? Inda nake aure zam-zam yake. Da aka yi accident din ma, kamar an kara masa armashi. Kafafu? Ni ba ina da su ba? Kuma ba ina daukar ki dasu ba? To meye damuwar ki? In gaya miki gaskiya, ba zan iya sharing kaina ba, saboda ina da kyama, ba kowacce mace zan iya hada jiki da ita ba. Babu, ban taba ba, bana fata, kada ki tursasa ni, don ba zan iya ba, ba zan iya adalci ba. An ce kuma in ba za ku iya adalci ba, to ku zauna da daya. Amma in kin gwammace ranar kiyama in tashi da shanyayyen barin jiki, all the same, sai in auri Surayyah! Kinga daga nan sai ku kara dankon zumunci........". Ta ture shi da sauri, duk da jikinta ya yi sanyi da maganganun sa, ta tabbatar iya gaskiyar shi yake fadi, don shi bai fadin abin da ba haka bane a zuciyar shi. Don kaji dadi, ko don ya faranta maka. “In haka ne kenan Sulaiman da gaske za ka iya auren Dr. Surayyah?" Sai hawaye suka zubo. Magana take a zuci, ba ta san cewa a fili ta yi ba. Ya sauka daga gadon ya zauna dabas a kan kafet a gabanta, ya dauki hannu ya rafka uban tagumi, "Ni Sulaiman na shige su, duk yadda na yi, ban iya ba. Duk yadda nayi ban fita ba. To ki fadi yadda kike so, ni kuma mijin ta ce ne!" Idon ta fal hawaye ta dube shi cikin ido, abin da bata yi sai rana ta kure, "Ka gaya min gaskiya Sulaiman, Surayyah kake so?" Ya yi murmushi ya shafi siraran lebbansa, "Ya ya ba zan so ta ba tunda tana son ki, tana son 'ya'yana?" "Ni ba wannan son nake nufi ba........". Ya mike tsaye ya bata baya zai fice, "Koma wanne kike nufi shi ne, yarinyar nan rikicinki ya ishe ni, son ta nake na soyayya, soyet. Kin gane yanzu ko? Ki yi kuli-kulin kubura dani, ko ki yi ta kuka, har hawayenki ya kare........!!! " Duk da kuka take ba ta san sanda ta yi dariya ba, ganin kuma ya dawo ya cafko ta yana son a sauya hirar da irin wacce ya fi so ayi, mai ma'ana da tsayawa a zuci, hadi da dimbin lada. Ba ta da zabi (she have no choice) ban da ta rungumi mijinta, mai son ta, mai kaunar ta da gaskiya. Ta nuna mishi nashi son kawai ya sani, bai san nata ba. Duk abubuwan da take yi kan ya kara aure hasashe take, dauriya take don kada ta zamo mai son kanta, amma ita ma ta san ba za ta iya raba Sulaiman din ta da kowa ba. ***Da wannan Sulaiman ya kashe bakin Hadiza da maganar ya kara aure, saboda ita ta nakasa. Don ta san cewa zai yi zai auri Dr. Surayyah, ita kuma in da abin da ta tsana ya fito daga bakin sa, to bai wuce wannan furucin ba. Surayyar ba ta watsar da Hadiza ba, ta kan zo in ta samu sararin aiki kuma suna yawan yin waya. Tayi-tayi Hadiza ta koma aiki in ya so sai Fati ta dinga kula da zirga-zirgar ta amma ta ki. A ganin ta ita Fatin zaman ta kenan ba za ta yi nata auren ba? Ko ko haka za ta karar da rayuwar ta wajen hidimar ta alhalin bata kai ga cimma komai a rayuwa ba? Gara ita ta kai ga matakin da duk dan adam ke burin samu; tayi ilmi, tanada kwali, tayi aure, ta hayayyafa. Don ta zauna gida a halin yanzu babu komi. Amma Fati fa? Ta ce, "Surayyah mune bamu gane ba, ko da yake mu namu aikin mai tushe ne daga addini. Amma ba abin da ya kai mace ta zauna a dakin mijinta ta yi biyayyar aure dadi da kwanciyar hankali, amma ina amfanin da auren ki da mijin ki da 'ya'yan ki amma kin watsar dasu kin barwa mai aiki kullum kina titi, bayan mijin ya tsare miki dukkan bukatun ki na rayuwa?" Surayyah ta ce, "Ke din ce dai kawai kin yi sa'a Hadiza, amma ba ko wadanne maza ne irin Dr. Sulaiman ba". Kishi ya motsawa Hadiza ta hadiye shi mukut, amma ta san Surayya gaskiya ta fada, Sulaiman is unique, akwai wani simpleness a tare da shi wanda maza da yawa basu da shi. Hadiza ba ta samu kwanciyar hankali ba sai da Dr. Surayyah Yahya ta kawo mata katin auren ta da Dr. Bashir Bunza, cike da shakiyanci ta nunawa Sulaiman. Ya karanta ya ciji yatsa, "Shege Bunza, ya kasa ni!". Ta kyalkyace da dariya ta ce, "Eh, to kai ne ka tsaya sanya". Ya harare ta da idanun kauna, "Haka ma za ki ce? Bayan ke kika kashe min gwiwa, ai da tuni na karkata hula nasa kai, wallahi da ni zan kasa shi". Ta sake yin dariya ta ce, "Oho dai, sai abi wani sarkin ba Ado ba". **** Asabar ce sassanya mai dauke da wani irin lullumi mai sanya nishadi a zukatan dan adam, ana saura kwana biyar a kama azumin watan Ramadan, kamar kowacce asabar din karshen wata. Dr. Sulaiman ya zuba 'ya'yan shi a mota suka nufi Bakori ainihin gidan iyayen shi kamar yadda suka saba, can za su wuni, wani zubin har yamma ko dare. To yau ma hakan. Gidan ya rage daga Hadiza sai Fati, don Alti ta je kauyen su Kukawa ganin gida za ta yi sati biyu tunda yaran ma cikin hutu suke. Fati ta tura Hadiza kitchen kamar yadda ta bukata, ita tana girki Hadiza na mata hira. Ta ce, "Fati yau shekara guda cur da faruwar al'amarin nan, nayi-nayi ki kara neman wani admission din amma kin ki, kina nufin haka za ki yi ta zama kina yi min bauta ni da iyali na ba karatu ba aure? In don nice wallahi bana cikin matsala a halin yanzu I can take a good care of myself (zan iya kula da kaina) ko da a ce ni kadai ce a cikin gidan nan". Fati ta sauke tukunya ta dora wata, ta yarfar da hannu don zafi. Sannan ta dubi 'yar uwarta, "Yaya Hadiza ba zan iya barin ki ke kadai in tafi makaranta ba, ko na tafi tunanin halin da kike ciki ba zai barni in mai da hankali a kan karatun ba". Ta yi murmushi, "Cewa nake watarana aure za ki yi Fati?" Nan da nan Fati ta yi kicin-kicin da fuska, ta juya mata baya ba ta ce komi ba. Hadiza ta ce, "Ko baki ji ni ba? Aure za ki yi Fati dole ba da jimawa ba, don haka ki tsaya ki gina rayuwar ki kamar yadda muka gina tamu, bana so saboda amfanin kaina ke in tauye ki. Don haka na baki kwana biyu ki yi tunani, an fara sai da JAMB na wannan shekarar, don haka ki nutsu ki kama abin da zai taimake ki ranar da bani. Duk wata kauna da dan uwa na gari zai nuna wa dan uwansa kin nuna min ita, sakayyar ki na wajen Allah. Sai dai ba zan bari ki kari rayuwar ki baki dandani zakin ilimin ko auren da na dandana ba, dole in samar miki future kafin Allah ya yi hukuncin da ya so a kaina....". Fati ta yi saurin juyowa ta dubi Hadiza, domin a da ta bata baya ne. Ba ta gane abinda take nufi ba. Hadiza ta yi murmushin karfin hali ta ce, "Fati zan gaya miki wani abu, amma bana so ki daga hankalin ki. Bani da lafiya Fati, amma don Allah ko Yaya ban yarda ki gayawa ba balle Sulaiman. Fati na dade ina fama da ciwon kai wanda nake yi lokaci-lokaci, Sulaiman ya sani ina yawan fama da (migrain) amma bai taba zurfafa bincike ba, don ban taba gaya masa tsananin zahirin yadda nake jinsa ba. Ba tare da sanin sa ba na je wajen Dr. Bunza mijin Surayyah, da ke likitan kwakwalwa ne, cikin sirri ya yi min bincike mai zurfi inda ya sanar dani ina fama da kansar kwakwalwa (brain cancer)". Fati ta zazzaro ido ta sulale ta zauna a kasa, ta kai hannu ta dafe kirjinta, sai ga hawaye suna shatata! Hadiza ta yi murmushi ta matso da kujerar ta inda Fati take, ta dora hannu a kanta. "A'a, Fati kada mu yi haka da ke, amanar rayuwata nake gaya miki, wadda bani da wanda zan bawa sai ke. Ba wanda zan iya gayama wa sai ke, ciwon bai yi tsanani ba, kuma ina shan magani a boye, ko Surayya ba ta sani ba. Fati abin da ya sa na gaya miki don ki tallafa min ne, Sulaiman likita ne wanda ke bukatar kwanciyar hankali don samun (confidance) wajen gudanar da aikinsa na ceton rayuwar al'umma, idan ya ji wannan maganar ba zai taba samun kwanciyar hankali ba. Fati Sulaiman yana sona, sosai, irin son da zai iya bani rayuwar shi, bana son abin da zai dagula masa lissafi, ki rike min amanata, ki rike min 'ya'yana, ki basu tarbiyya irin taki kada ki bari Sulaiman ya tagayyara a bayana. Ina son shi yadda yake so na, na so in ci gaba da rayuwa tare da shi, in ci gaba da haifa mishi 'ya'ya kamar yadda yake so, amma ban san ya ya Allah zai yi dani da rayuwata ba. Ki rike min Sulaiman Fati... bana so rashi na ya tagayyara shi........". Zuwa wannan lokacin duka 'yan uwan biyu sharbe suke, na hawaye da majina. Girki yana ta kauri, amma ba su kula ba. Fati ta rage sautin kukanta, ta ce, "Shi brain cancer ba’a warkewa?" Hadiza ta ce, "Ba a warkewa gaba daya, ko ya lafa zai tashi, amma ina kula da shan magani". Fati ta yarfe hawaye ta ce, "Wannan ba abun boyewa bane Yaya Hadiza, ki daina fidda rai da rayuwa saboda ciwo. Insha Allah ke za ki aurar da Munib da Muniba, ya kamata ki sanar da Dr. domin ya taimaka miki da addu'a, duk wani hali da zai shiga ai shi musulmi ne ya san duk son da yake miki ya san bai kai wanda Ubangijin ki yake miki ba. If the condition become worse, ba tareda saninsa ba ba zai taba yafe miki ba.......!" Hadiza ta yi shiru tana mamakin zurfin hankali irin na Fati, yarinya karama sai tunanin manya. Ta ce, "Zan duba shawarar ki Fati, Allah ya kara min YAKANAH, ya bawa 'ya'yana tarbiyya irin taki. Ai dai za ki kula min dasu ko Fati?" Cikin kuka ta ce, "Yaya Hadiza ki daina yi min wannan maganar, bani da jarumtakar sauraron ta……". Ta ce, "Na rantse da Allah idan baki yi min wannan alkawarin ba nima ba zan bi shawarar ki ba". Cikin makyarkyatar murya ta ce, "Eh.......eh......na yi alkawarin zan kula dasu!!". Ta ce, "To nima zan bi shawarar ki, amma ba yanzu ba. Tashi sauke tukunyar can tana kauri". Ta share idonta ta mike ta sauke, ilahirin jikinta sai rawa yake. Ta kashe komi ta maido Hadiza falo, ta yi dakin su ta rufe ta fada kan gadon su ta soma girka kuka. Ta ga kukan ba zai amfane ta da komai ba, sai ta je bandaki ta dauro alwala, ta shimfida sallaya ta soma sallah, a kowacce sujjadarta tana yiwa Hadiza addu'ar Allah ya ba ta lafiya. Wayar Hadiza ta yi kara, a lokacin tana bisa sallaya tana azkar, don haka ba ta daga ba har ta tsinke. Sai ya yo text, ta dauka ta duba. Sulaiman ne yake gaya mata suna bisa hanya har da Inna Halima za ta zo ta duba ta kuma za ta ga likita, don haka a gyara mata daki don za ta kwana biyu. Hadiza ta ji dadin zuwan Inna, domin Innar Sulaiman mutum ce har mutum, ma'abociyar raha da sanin mutunci. Don haka ta kira Fati a waya ta ce ta kara yawan abinci da ta aje a falo, ta kuma canza shimfidar gadon dakinta, don kullum a gyare yake Fati ba ta wasa da tsabtarsa. Tara na dare dai-dai suka shigo, Inna dauke da Muniba da tayi barci a kafadunta. Hadiza da Fati suka yi mata sauka ta ban girma. Sai lokacin kwanciya ne aka kai ruwa rana da Inna, don ta ce ba za ta zaunawa Hadiza a daki ba, sai tare da 'yan jikokinta, dole suka kyale ta. Duk juyin da Inna Halima ta yi a wannan dare, Fati take gani a kan sallaya, ta yi sallah, ta yi lazimi. Da asubahi kuwa ta soma rero (Suratul Yaseen) da sauti irin na Abdurrahman Sudaith. Kai ka ce daga masallacin Madinah aka kunno karatun. Saida tayi sallar asubah sannan ne ta dan samu barci. Karfe shida ta fada kitchen ta soma aikace-aikace, Inna na hankalce da damuwar da yarinyar ke ciki, ta rasa abin da ke damun ta kankanuwa da ita haka. Bata uhm bata umhumh. Lokaci lokaci tana sanya gefen hijabinta tana dauke hawaye. To haka a washegari ma, har cikin kitchen wannan yarinya ba ta rabo da hijabi da carbi, tun tana burge ta har ta koma bata tausayi. Washegari litinin bayan sun yi kalaci, Inna da Sulaiman suka wuce asibiti in da za ta ga likitan ido (ophthalmologist), ba su dawo ba sai da rana ta take, yana sauke Inna ya juya ya koma ofis. Sun fara cin abinci ita da Hadiza a kan darduma irin traditional carpet din nan na fata, an kuma shimfida ledar cin abinci. Don Fati ba ta cin abinci cikin mutane, loma ta farko, ta biyu, ta uku Hadiza ta soma kelayo amai kamar ta amayar da 'yan hanjinta. Da sauri Fati ta shigo, Inna na rike da Hadiza, ita kuma ta kawo ruwa da roba Hadiza ta kuskure bakin ta. Fati ta sa moper ta gyare wajen, ta koma kitchen don hidimar abincin dare. Ko me take yi cikin kitchen bakinta ba ya rabo da ambaton Allah, duk a kan lafiyar 'yar uwarta. Ita dai Inna haka nan ta ji Fati tana burge ta, tana bata sha'awa. Zahidah ce, babu duniya a gabanta, gata da dan banzan kyau da fata lafiyayya, amma ba sa gabanta, lahira take nema da harshen ta da goshin ta da gwiwoyin ta, ba ta furuci sai wanda ya zame mata dole, ko in an tambaye ta. Amma a kwanaki bakwai da ta yi, Inna Halima babba ce mai cikakken hankali, ta lura Sulaiman ko ganin Fati a gidan shi ba ya son yi, don dai ba yadda zai yi ne, kuma bai son abin da zai bata ran Hadiza. Suna falo ita da Sulaiman misalin karfe sha daya na dare suna hira a nutse irin ta da da mahaifi, ta ce, "Wai ni mai sunan Malam me yarinyar nan kanwar Hadiza ta yi maka ko kallon ta ba ka yi? Dazu da safe ina kallo tana gayas da kai ka dauke kai ka fita, haka tun zuwana ban taba ganin ka yi mata magana ba, balle wasan nan irin na mijin ya da kanwarta. In kana wuri ta shigo sai ka tashi, in kana falo ta ganka sai ta koma ta yi ta zaman daki. Ita da ganin 'yar uwarta sai in baka nan, mene ne manufar hakan?" Ya juyo yana kallon Inna kasa-kasa, yace, "Wacce yarinya kike magana?" Ta ce, "Fatima". Ya ce, "Fati wai?" "Eh, ita". Ya yi shiru kamar bazaiyi magana ba yayinda Inna ta kura masa ido cikin tsananin son jin amsarsa, ya rausayar da kai ya ce, "Raini ne bana so, kuma ni ban iya wani wasan kanin miji ko kanin mata ba". Ta yi sakale tana jin sa, ta ce, "Hala wani laifi ta yi maka? Har Hadiza na lura ranta yana baci da irin halin ko in kulan da kake yiwa 'yar uwarta. Ban san ka da bakar zuciya ba, kada ka a fara a kan FATIMA, domin mutum ce cikin 'yammatan da babu irin su a yanzu, wannan yarinyar tana da halayen 'yan aljanna, ka yi a hankali baka sani ba ko waliyya ce". Shi abin ma sai ya ba shi dariya, ya ce, "A wannan kalatacciyar duniyar tamu dama akwai sauran waliyyai Inna?" Ta harare shi ganin ya bagarar da zancen cikin wata siga ta daban, ta cigaba da magana cikin kakkausar murya. "Dariya ma kake min?” Ya yi saurin cewa, "A'a, yi hakuri Inna ba dariya nayi ba". Ta ce, "To ka gyara ma'amalar ku, zai fi kyau a ce akwai kyakkyawar alaka a tsakanin ku ko saboda Hadiza, in ta gaishe ka ka dinga amsawa cikin walwala da sakin fuska, wanda ya rike ibada ba ya wulakanta a duniya da lahira Ubangiji kansa girmama shi yake. Baka sani ba ko ta fi ka matsayi a wajen Allah, ka canza takun ka a kanta, rayuwa baa yi mata haka, don sauyawa take kamar WAHAINIYA ta inda bama tsammani. Ai ba haka na ga kana yiwa su Ruma ba, to matsayin ta daya dasu a gare ka, ka ji na gaya maka". Bai ce komi ba ya jawo wata hirar, don dai a sauya wannan. He is not interested at all (Fati is not the kind of person he wanted to relate with), wato ba ta daga cikin irin mutanen da yake son yin mu'amala dasu akan dalilai masu yawa. Wadanda in aka ce ya zano akan karan- kansa sai ya ji su masu rauni da rangwamen muhimmanci (null and invalid ). Amma daga ciki ya san akwai gudun RAINI da rashin son sa da WASAN KANIN MIJI. Sauran hujjojinsa kuma ai a sarari suke; jinin su bai hadu ba, don yana son Ya, ba dole sai ya yi wata kakkarfar alaka da kanwar ta ba, bayan wadda musulunci ya ce, don haka ne baya damuwa ba ‘hypothesis’ din kowa akan ma'amalar sa da Fati, ai ba abokiyar wasan shi ba ce, kanwar shi ce. **** Kwana bakwai din da Inna Halima ta yi jinyar Hadiza suke ita da Fati, komai ta ci sai ta amayar, ga zazzabi da ciwon kai mai zafi, sai ta rike kanta idan ciwon ya motsa mata tana wani irin kuka mai keta zuciyar duk mai imani. Sulaiman da farko bai sani ba, don ya dauka laulayin ciki ne irin wanda ta saba, kuma ciwon baya tasar mata da daddare lokacin da suke tare kenan. Ita ma Inna ta lura ta san laulayi ne na sabon ciki, amma wannan buga kan da Hadiza take yi a jikin bango da kukan da take yi na azaba ta fahimci akwai dai wani abun, amma tana ganin dukkan su likitoci ne sun san abin da ke damun ta, kuma ta ga Hadiza tana shan magani, sai ba ta yi magana ba, amma dai ba ta taba ganin irin wannan laulayin cikin ba. Don haka ta kara sati saboda lafiyar Hadiza wadda ta daina cin komai sai ruwan bakin lipton da ruwan tsamiya. Gaba daya ta rame ta fita hayyacin ta, ba ta taba yin cikin da yake wahalar da ita irin wannan ba. Tun Sulaiman bai gane ba har ya fahimci Hadiza ba ta da lafiya sosai, wannan ya wuce laulayi kuma wannan (migrain) yana bukatar bincike. A daren ya fito daga wanka yana tsane kanshi da dan kankanin towell, tana kwance rigingine a gefen gado, cikin doguwar rigar barci mai santsi mara hannu ruwan madara, kyawawan kafafunta da cinyoyin ta a mike sambal, a haka sai ka rantse lafiyar ta kalau ba ta tare da wata lalura. Son matarshi da kaunar ta na kara girgiza zuciyar sa, yana hargitsa gangar jikinsa. Ta kure fanka da A.C amma ba ta daina zufa (gumi) ba. Da sauri ya karasa zarga igiyar pyjamas din shi ya yiwa kanshi kyakkyawan matsuguni a bayan ta, ya daura hannu a kan goshin ta, zafi rau! Dole ya hadiye nashi bukatan ya soma ba ta kyakkyawar kulawa ta hanyar sanya karamin towell a ruwa yana goge mata kanta don zafin kan ya ragu. Sannan ya soma bin gabban jikinta da message don ta ji dadin kasusuwan ta. Ya juyo ta ya rungume ta ganin wani irin gumi na tsatsafowa daga cikin kanta, a yau ma ya sake cewa, "Cikin kowanne hali, INA SON KI HADIZAH!" Ta bude idanunta a hankali, wadanda suka kankance suka yi jawur don azabar data ke dandana, tana kallon abin son ta, shi ma kallon ta yake kallon yaya zan yi da raina? Me zanyi in sama miki lafiya? Ya ce a galabaice, "Gobe zan dauko Dr. Bunza ya duba ki". Gabanta ya yi wani irin faduwa, ta runtse idon ta da karfi ta ce, "Bana so, kada ka dauko shi, idan kuma har ka dage sai ka dauko shi to zan koma Karkasara". Ya girgiza ta da karfi ya ce, "What do you mean (me kike nufi)? In barki a gida kina ciwo ban nema miki magani ba? Bansan hakikanin me ke damunki ba? Allah sai ya tambaye ni, iyayen ki da suka danka min amanar rayuwarki su tuhume ni. Wannan ciwon kan bana wasa bane yana bukatar bincike". Ta ce, "Ai ba yau na fara ba ka sani, kuma da na sha magani shi ke nan yake lafawa". "Ina maganin? Dauko min in gani". Ta ce, "Ya kare dazu, da safe nake shirin in aiki Fati ta siyo wasu". Ya ce, "Wane magani ne?" Ta yi shiru. "Tambayar ki nake yi, ina maganin? Ya ya sunan sa?' Ta ce, "Panadol". A mamakance ya maimaita "Panadol?" 'Eh". Ya ce, "You are silly, ko in ce you are a nonsense Doctor! I did not trust you.........". (kina shirme, ke shashashar likita ce, ban yarda dake ba). Ya tashi a fusace ya fizgi waya ya kira Dr. Bashir, ‘consultant’ na ‘neurology’, Surayya ce ta dauka, bai ko amsa gaisuwar da take mishi ba ya ce, "Ina mijin ki?' A ladabce ta amsa. "An kira shi a ‘emergency’ kuma ‘he is on call’ yanzu ya fita, ya manta wayar". Ya kashe wayar ya cillar ya zauna a gefen gado ya dafe kai, Hadiza na kuka a hankali tana kara hargitsa shi, ya ce a fusace, "Enough.......is enough Hadizah! Ki gaya min fisabilillahi mene ne babbar matsalar ki?" Ta ce, "Nifa na gaya maka laulayin ciki ne, sai migraine wanda ba yau na fara ba, kuma ka san shi dama ina da magungunan da nake sha a kan shi, wannan zazzabin da haraswa laulayin ciki ne irin wanda na saba, zan gaya maka karya ne? Yau da bakin ka Sulaiman kake cewa baka yarda dani ba?" Jikinsa ya dan yi sanyi, ya rage sauti ya ce, "To ta ya ya zan ce zan kira likita da ya san matsalar ki ya duba ki ki ce a'a? Sai in dauka wani abu ne daban kike boye mini". Ya yi mata wani irin murmushi da har abada ba zai gushe daga zuciyarta ba, ta dauke kai alamar ta yi fushi. Ya bi bayan ta a hankali ya kwanta, suna raba zazzabin tare. Akwai wani abu wai shi 'hot kiss' da Hadiza ba ta sani ba daga Sulaiman sai a yau, ya mantar da ita rashin lafiyar ta, ya dauke ta ya jefa a duniyar soyayya, ta manta cewa ita nakasasshiya ce, ta manta damuwar ta na cewa lafiyarta na hannun Allah, ta dauka cewa, tana a matsayinta nna Dr. Hadiza ne ta baya. Ba za ta mance da wannan ranar da Sulaiman ya zubar da hawayen shi a karo na biyu a kanta ba. Na farko saboda ta nakasa, na biyu na dimbin soyayyar da yake yi mata. To wanne ne zai kasance na uku??? ******** Inna ba ta koma Bakori ba sai bayan watanni biyu, lokacin laulayin Hadiza ya ragu, tana yi mata dabaru irin na manya har ta samu sauki. A lokacin cikin ya shiga wata hudu, sannan ne laulayin ya tsaya. Sannan ciwon kanta ya jima bai tashi ba, saboda Dr. Bunza ya sauya mata magani, Fati ce ke zuwa ta karbo ba tare da sanin Sulaiman ba. Ganin ciwon ya dade bai tashi ba sai Hadiza ta watsar da shawarar Fati ba ta gayawa Yaya ba, shi dama Sulaiman tuni ta binne shi ya kuma yarda cewa migraine take. Cikin Hadiza wata bakwai, ya fito ya yi tororo kamar watanni tara. Haka za ka ganta fus! A cikin wheel chair tasa cikin a gaba tana kallo tana mamakin sarautar Allah, wanda ya ga damar ta haihu a cikin halin da take ciki. So da kulawa wurin Sulaiman kamar ya yi mata nakuda. Watan Aprilu ya kama, wanda ya yi dai-dai da EDD din ta, cikin dare wani azababben ciwon kai ya tashe ta, ta soma bubbuga kanta a jikin gado, kafin a yi haka ta yi dogo suma jini ya kece kamar da bakin kwarya. Duk wani kokari da zai iya shi ne kiran Dr. Abdullahi ko Dr. Surayyah a waya, amma hannun shi ya kasa kama wayar saboda dimaucewa. Sannan shi ya manta kansa balle ya yi tunanin wane irin taimako zai iya ba ta komai kankantarsa, a matsayin shi na cardiologist wanda kuma ke da general knowledge a kan komai. Sai ya sunkuto ta ya nufo harabar gidan, ya shimfidar a bayan mota. Malam Ilu ya wangale mishi ‘gate’ ya fita, cikin ranshi yana cewa kai wannan yarinya kina cikin jarrabawa kala-kala, Allah ya baki lafiya. Da taimakon innalillahi........ da yake ta ambato ya samu nutsuwar da har ya iso AKTH, aka karbe ta a bangaren ta wato dakin haihuwa, su Dr. Surayyah, Dr. Abdullahi suka rufu a kanta, ba ta san inda kanta yake ba. Suka soma ba ta duk wani taimako da ya dace don ta haihu da kanta kamin su yi bincike a kan wata matsala daban da suka hango wadda da alama dadaddiya ce. Amma duk iya kokarin su sun tabbatar da ba za ta iya haihuwa da kanta ba, don haka suka miko mishi takardu don ya sanya hannu a shiga da ita tiyata. Da kyar yake iya sarrafa 'yan yatsun shi a lokacin da yake rattaba hannun, zuciyar shi ta riga ta bushe da tashin hankali. Yana tsaye aka turo ta a kan gadon daukar marassa lafiya zuwa dakin tiyata, bai yi tunanin gayawa kowa ba sai da safe, kasancewar ba shi da nutsuwar yin hakan. Da ya ga wannan ba za ta yi mishi ba, sai ya nufi ofishinsa ya murda kofar ya shiga, ya jingina da kofar ya soma tunanin wasu al'amura da ya lura Hadiza na boye mishi, da yawan waya da take yi da Dr. Bunza na mene ne? Sannan da kwayoyin maganin da ya gani a leda babu suna babu takardar su a karkashin gadon su. Ya yi wani irin huci mai zafi, "Akwai wata matsala wadda da alama dadaddiya ce". Ya tuno furucin Dr. Abdullahi. A sukwane ya bude kofar ya fita ya nufi ofishin Dr. Bunza a Neurolgy. Dr. Bunza na rubuce-rdubuce a file suna hira da Dr. Karaye, Dr. Sulaiman ya bankada kofar ofishin ba tare da ya yi sallama ko neman izinin shigowa ba, ya kai wa Dr. Bunza shaka ya ce, "Gara in kashe ka, kafin ka kashe ni….". Dr. Karaye ya soma kokarin kwatar Dr. Bunza wanda ya sha shaka matuka, duk idanun sun yo waje. Ya ce, "Ba zan cika shi ba, sai ya gaya min abin da ke damun matata, da magungunan mene ne yake dirka mata?" Dr. Bunza ya ce, "Ka yi hakuri Dr. Sulaiman mu yi maganar cikin nutsuwa". Ya samu ya sake shi da kyar ya koma kujerar sa yana gyara wuyan rigarshi, yayin da Sulaiman ya yi mishi kerere a kai, idanun shi a jujjuye, shi dai kawai so yake ya ji mene ne matsalar Hadiza? Dr. Karaye ya ce, "Ka yi hakuri ka zauna Dr. Bakori, Dr. Bashir ba zai cuce ka ba……". Ya juyar da juyayyun idanunsa a kan Karaye, "Akwai wata cuta wadda ta wuce wadda ya yi min? Matata na dauke da cuta shekara guda amma bai taba gaya min ba? Ya biye mata suke yi min rainin hankali, na yi kama da wanda bai je makaranta bane Dr. Karaye?" Dr. Bunza ya ce, "Ba haka bane Dr. Bakori, ina bisa aikina ne, akwai sirri tsakanin likita da petient din sa, wannan shi ne hujja ta. Sannan Dr. Hadiza na da tata hujjar, ta boye maka cewa tana da (brain cancer) don samar maka da kwanciyar hankali, ta ce idan ka ji babu kai babu sauran kwanciyar hankali, kuma nima na yarda you are not taking things easy (ba ka daukan abubuwa da sauki). Ka bini a hankali in maka bayani". Ya kunna computer inda (record) din Hadiza yake yana nuna masa yadda ciwon ya ci karfin ta a yanzu, da irin taimakon da ya ba ta. Shi kan sa Bunza sai da ya yi hawaye balle gogan, wanda gudun jini ya katse a jijiyoyin jikinsa. **** Karfe shida na safe Dr. Surayyah ta fito da jaririyar da aka cirowa Hadiza, kamar ta daya da Baban ta kamar ya yi kaki ya tofar, har duhun kalar nashi ne. A lokacin ne jama'ar gidan su Hadiza suka iso, Dr. Surayyah ta sanar da su. Fati karfe bakwai na safe ta iso asibitin, ta baro yaran da Alti ta zo a (keke-napep). Dai-dai lokacin da aka turo Hadiza za a mai da ita ICU, ya yi dai-dai da sanda Surayyah ta mika mishi jaririyar ya ki amsa, sai Fati ce ta amsa. Za a wuce da Hadiza ta rike hannun sister Magajiya ta rada mata cikin nishi, "Ina son yin magana da su…..". Don haka sister ta dakata. Sulaiman da Fati suka garzayo gareta, kowanne ya fita hayyacinsa. Fati rungume da jaririya tsantsan tana ta tsala ihu. Itama Fatin Kukan take. Hadiza ta runtse ido hawaye na zirara, ta ce, "Fati ina alkawarin mu?" Cikin Kuka ta ce, "Yana nan Yaya Hadiza". Ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, duk su Malam Ja'afar na kallo, ta ce, "Fati har da shi a alkawarin fa.........." Ta yi sharbe ta yarfar da majina da hawaye ta ce, "In kula da shi kika ce? Yaya Hadiza ai shi babba ne?” "Babba ba ya bukatar kulawa Fati……?" Ta ce, "Ban sani ba". Ta ce, "To yana bukata, shi ma kamar Munib ne, bambancinsu shine shi Munib kulawar UWA yake nema, shi kuwa Sulaiman kulawar MATA yake nema..........". Ta yi murmushi ta runtse idonta, cikin azabar da take dandana a kwakwalwarta. Sulaiman ya russuna ya sumbaci goshinta, hancinta, bakinta da idanunta. "You will get well soon Hadizah……, bana bukatar kulawar kowa sai taki, in ba taki ba na yafe, zafin ciwo yake sa ki yin irin wannan magana.........". Ta girgiza kai tana kara manne hannun su cikin nata ta ce, "Sulaiman-Fati............". Dr. Bunza ya karaso ya tura gadon da kanshi yana ta yiwa sister Magajiya fada. Yaya ta karaso ta karbi 'yar da ke hannun Fati ganin tana neman kwala ta da kasa. Dr. Sulaiman ya mai da hannun shi cikin aljihu, yana so ya yi kuka amma idanun sun bushe kamar soyayyar gyada marau-marau. Sai Malam Ja'afar ya iso gare shi ya kamo hannun sa suka zauna tare, yana cewa, "Karbi 'yar ka sa mata albarka". Amma Sulaiman ya ki, sai kirjin shi da ke ta kai kawo kamar zuciyar ta ballo allon kirjinsa ta fito. Ana shigar da ita cikin computer don a yi hoton kwakwalwar ta kamin likitocin su san me za su yi a kai, ta soma wata irin jijjiga mai ban tsoro, kamin ta yi salati rai bakon duniya ya yi halinsa. "Allah ya ji kan Dr. Hadizah!" Abin da dukkanin likitocin suka furta kenan, a lokaci guda suna share ambaliyar hawaye daga idanuwan su, tare da kai hannu su rufe mata idanun ta. ****An bawa Malam Ja'afar da Sulaiman gawar Hadiza cikin mota ambulance, zuwa nan unguwar Karkasara. Inda daruruwar jama'a suka yi jana'izar ta. Mijinta da Mahaifinta suka sanya ta a kabarin ta, suna masu yi mata addu'ar fatan alheri, yafiya, afuwa da addu'ar Allah ya yi mata masauki da aljanna, Annabi ya san da zuwan ta. Su kuma ya basu imanin jurewa. Sulaiman ya baiwa kowa mamaki, saboda yadda ya tsaya a kan jana'izar Hadizah, babu ko digon hawaye a idanunsa. Ba su san shi kansa kukan na zuwa ne idan an san abin da ake yi ba. To bai san me yake yi ba, bai san halin da kwakwalwarshi ke ciki ba. Ya san dai kawai Hadizar sa ta rasu, sun kaita makwancin ta na gaskiya, bayan wannan bai san komi ba, bai san kansa ba, bai san a ina yake ba. Ya dai bude ido ya gan shi a gidan su Hadizah, dakin Mukhtar, ba ya rintsawa, yadda ya ga rana haka yake ganin dare, ya wuni yana karbar ta'aziyyar 'yan uwa da abokan arziki. Tun a ranar Inna Halima, Malam Sulaiman da sauran kannen shi suka zo Kano, da su ake karbar gaisuwa har zuwa kwana uku. Ranar lahadi suka juya Bakori cike da juyayin halin da Sulaiman ke ciki. Malam ya ce zai dinga aiko mishi da rubutu tsayin kwana bakwai. Ya ce, "To". Wadda ta zama kalma mafi saukin fada a bakinsa, sai kuma bin kowa da ido, amma abinci da ruwa wannan kwanan shi uku bai dandana su ba. Alti ma tana gidan ita da yara wadanda suka damu kowa da tambayar ina Momin su? Alhamis aka yi sadakar uku, Alti ta koma kauyen su tana kuka da hawayen ta, ta ce sai ranar sadakar arba'in za ta dawo. Tambaye ni ina baiwar Allah Fatima Ja'afar Mai-Yadi? Tana can dakinta tana kuka, inna ce kuka ina nufin kuka, mai futa daga karkashin zuciya da ruhi, tana kuma fama da jaririya, bini-bini ta hada madarar (SMA) ta dura mata, ta ba ta ruwan zam-zam. Ba ta barin ta tayi kuka, idan ta bata madarar da ruwan sai ta sa ta a baya ta goye, ta zauna ta yi ta jijjiga ta, har sai ta samu barci, ta sakko ta ta sanya ta a gadon ta, ta zauna a gabanta ta yi ta girka kuka. Idan kukan ya ishe ta sai ta bude littattafan addu'o'in ta, ta yi ta karantawa tana rokon Allah ya kai ladan makwancin rabin jikin ta Dr. Hadiza Ja'afar Mai-Yadi. Mutuwar Hadiza ta girgiza kowa a gidan nan, haka duk wanda ya santa ya koka ya gode Allah. Kada Dr. Surayyah ta ji labari, to ina ga wanda farin cikin rayuwar sa ya ta'allaka ne kacokam a wuyan ta? Ya ke kwana da ita yake tashi da ita, yake yi mata son da ko iyayen ta sai dai su ce su suka haife ta? Don haka Doctor Sulaiman-Sulaiman Bakori, yana cikin wani irin hali da duk masoyinsa dole ya koka masa, in har yana da imani, ya bishi da addu'ar Allah ya ba shi dangana da YAKANAH! Tuni Mukhtar ya koma Kaduna, ranar da aka yi bakwai shi ma Malam Ja'afar ya ce ya koma bakin aikin sa. Ya bishi da "To". Kamar yadda yake bin kowa da ita. Ya tattara ya koma gidansa, shi kadai kwal kamar maye. Sai da ya gwammace da bai dawo ba, a lokacin da ya ci karo da wheel chair din Hadiza da kayan ta dake watse a dakin barcin su, a nan ne komi ya dawo masa danye, karo na uku da ya soma kukan da ya tabbatar har abada ba zai daina ba. Haka ya kulle kansa, ba shi da abinci sai ruwan lipton wanda yake dafawa a kettle ya dura a flask ya wuni yana sha, babu ko tunanin sa sukari. Cikin kwanaki ashirin da mutuwar Hadiza ya zama babu kyawun gani, kasumba ta cika fuskar sa. Duk wannan gayun ya daina shi, wanka ma ba kullum yake yi ba sai ya ji alamar jikin shi na dan wari-wari, ya kashe wayoyinsa gaba daya, ya yi sallama da aikin sa, amma bai fasa kwana yana yiwa Hadiza addu'a ba. Uwa, mahaifiya, duk ta rasa sukuni, tana can Bakori, hankalinta na Kano, ta san cikin kowanne hali Sulaiman yake yana cikin halin da yake neman matallafi. Kuma cikin halin da yake bukatar mai tausar sa, da nuna masa kauna da kulawa. Don haka yau ta tambayi Malam Sulaiman cewa za ta taho Kano wajen Sulaiman. Ya ce hakan ya yi. Yana zaune a falo, daga shi sai wata dukunkunanniyar jallabiya ruwan makuba, da kofin ‘tea’ a hannun shi da ‘remote’ yana kallon tashar Saudiyyah, inda suke gabatar da sallar magariba. Aka danna kararrawa wajen sau biyar kamin ya yunkura ya aje kofin a kan side table ya bude kofar. Inna Halima ce tsaye cikin atamfa holland ta sha lullubi da koren mayafi kalar atamfar ta, har ranshi ya ji dadin ganin ta, ya ba ta hanya ta wuce cikin falon, ya tsuguna ya gaishe ta. Ba ta amsa ba sai kallon shi take cikin al'ajabi, "Haka ka lalata kanka Sulaimanu saboda Allah? To wannan rashin tawakkalin da kake shi zai dawo da Hadiza duniya ko me? Ka sani Hadiza ta riga ta koma ga mahaliccin ta, ba za ta taba dawowa ba, ka fuskanci rayuwar da take jiran ka a gaba, ka zamo mai YAKANAH cikin duk halin da ka tsinci kanka. Tsakanin ka da Hadiza yanzu addu'a ce, ba wannan lalata rayuwar ba. Idan Hadiza tana raye, ba za ta so ganin ka haka ba, ka yi hakuri mai sunan Malam. Shin yaushe rabon ka da cin abinci?' Ya sunkuyar da kai bai yi magana ba. Ta jawo ledar da ta shigo da ita ta fiddo ma'adanan abinci guda biyu, ta bude ta tura masa, tuwon shinkafa ne lafiyayye da miyar taushe ta ji nama zuku-zuku, ta ce, "Cinye maza ka bani kwanon". Ba musu ya dauka ya soma ci kamar Allah ya aiko shi. Inna ta mike ta soma tattare bolar falon, ta share shi tsaf, ta shiga dakunan ta gyare ko ina, ta wanke masa toilet. Sanda ta gama ya dade da yin barci a carpet, ta zauna a gefen kansa tana tofa masa addu'a. Yana tashi ta ba shi rubutun da ta zo da shi cikin jarka ya sha, ya mai da kai kan tuntun ya koma barci. Bai tashi ba sai la'asar, ta je bandaki ta hada mishi ruwan wanka cikin kwami, ta dawo falon ta same shi ya idar da sallar la'asar, ya mike kafa yana kallon ceiling, ta tsuguna a gabansa ta ce, "Tashi ka je ka yi wanka, ka shirya muje mu ga mai sunan Hadiza". Wannan karon ma bai yi musu ba, ya mike ya je ya yi wankan, ya zubo farar shadda dinkin Mohammed, ya dora hula fara sol amma bai fesa turare ba, ya fito ya tadda Inna ta idar da sallah tana lazimi. Ta yi addu'a ta shafa, ta mike suka fito harabar adana motoci, duk motocin sun yi kura futuk! Alamar an dade ba a taba su ba. Ya sa key ya fiddo motar dai-dai inda Inna take, Malam Ilu ya karaso da sauri ya gaida Inna, ya sa ‘duster’ ya karkade motar cike da jin dadin ganin yau Ubangidansa ya fito, wanda yake kwana cikin wannan gida shi kadai ransa, sai dai yana tausaya masa, don ya san rashin matar kwarai kamar Dr. Hadiza ba karamin abu bane. Inna na baya shi kuma yana tukin suka nufi unguwar Karkasara. A dai-dai titin asibitin AKTH kamar an ce da Inna ta juya, ta hango Fati rike da hannun Munib da Muniba cikin kayan makaranta tana tare tasi, da alama ta dauko su ne daga makaranta. Da sauri Inna ta ce, "Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su". Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, "Baka ji ni bane? 'Ya'yan ka fa ta dauko daga makaranta!". Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, "Ai sun shiga mota ma hadu a can". Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba. Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata. Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta. Ta ce, "Me nake gani haka ni Sa'adatu? Sulaiman me ya yi zafi? Hadiza ba ta yi gaggawa ba, muma jiran namu wa'adin muke. Karbi 'yarka tunda ta zo duniya baka taba daukar ta ba, ita kuma laifin me ta yi? Ka zamo mai YAKANAH, wannan ba shi ne karshen rayuwar ka ba!!". Inna ta mika mishi yarinyar, ya fi karafin mintuna uku kamin ya karbe ta, ya kura mata ido yana mamakin kamannin shi da ita har sun fi nashi da Munib. Dai-dai sanda Fati da yaran suka shigo cikin sallama, tana sanye da katon hijabin ta har kasa mai hannaye, rike da lunch box din yara da jakunkunan su. Cikin nutsuwa ta tsuguna har kasa ta gaida Inna, ba tare da ta kalli Sulaiman ba ta ce, "Ina wuni?' Bai amsa ba, ita ma ba ta tsaya sauraron ya amsa ba ta wuce ciki. Ai Munib da Muniba suna ganin Baban su suka fada mishi suna ta tsallen murna, ya mikawa Inna Baby ya zaunar dasu duka a cinyoyin sa, suka soma ba shi labari iri-iri, duka rabi ‘AUNTY FATI’ ta yi mana kaza, ta yi mana kaza. Yana jinsu bai ce komi ba. Malam Ja'afar ya shigo hannayen shi rike da manyan ledoji yayo cefane ciki har da madarar SMA da Nana ke sha, ya kwalawa Fati kira ta fito ya bata. Sai a sannan ya lura da bakin takalma har da na namiji a kofar dakin Yaya, ya ce da Fati, "Waccan madarar ta kare ne?" Ta ce, "Eh, saura kadan". Ya ce, "To ki dinga gaya min kafin ta kare ba sai ta kare kaf a barta tana kuka ba". Ta ce, "Ai masassara take shi ne take kuka, amma dama gobe zan kaita asibiti". Ya ce, "To Allah ya sauwake, ke kuma Allah ya ba ki ladan hidimar da kike yi da 'ya'yan ki, ya sa suji kan ki kamar yadda kika ji kan su, ya kai rahama kabarin mahaifiyar su". Ta ce, "Amin Baba". Shi ma Sulaiman da ke can daki yana jin su ya ce "Amin". A zuciyar shi. Malam ya daga labulen ya ce, "A'a! Ashe Inna ce, barka da zuwa kin sha hanya, ya ya aka baro Malam?" Ta amsa, suka ci gaba da gaisawa suna hirar 'yan jikokin su, tare da kara yiwa juna ta'aziyya. Malam Ja'afar ya dubi Sulaiman sosai ya ce, "Ina maganar aiki ta kwana?" Ya yi shiru kanshi a sunkuye, can kuma ya ce, "Zan koma gobe insha Allahu". Malam ya ji dadi, ya kara mishi da nasiha mai sanyaya zuciya. Ba su baro gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan Inna da Yaya sun yanke shawarar yaran za su ci gaba da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantar su. Har za su tafi ya dubi Yaya fuska ba walwala ya ce, "Duk abin da ake bukata Yaya, don Allah a gaya min". Yaya ta yi murmushi ta ce, "Me ake bukata ban da madara? Bayan ita babu abin da zai gagara da izinin Allah". Ya ce, "Duk da haka ina son sanin sauran abubuwan da ake bukata, ai ragi-ragi ne". Ta ce, "To ka tambayi Fati". Ba don ranshi ya so ba ya nufi kofar dakin nata. Ta goya Nanah tana jijjiga ta, wannan karon babu hijabin a jikinta, kwayar idanun su ta hadu, ya yi saurin dauke kansa don gani ya yi kamar Hadiza, hatta digon tauwadar Allah da ke kan tsinin hancin Hadiza akwai shi a tsinin hancin Fati. Zuciyar shi ta yi wani irin mummunan bugu, don gani ya yi tana rikide mishi Hadiza sak, kasancewar bai taba ganin ta babu hijabi ba. Ya tsaya daga bakin kofar hannun shi duka biyu zube cikin aljihu. Da kyar yake magana kamar an tilasta mishi, ba tare da ya kara kallon ta ba. "Na tambayi Yaya abubuwan da yara suke bukata, ta ce in tambaye ki?" Kanta a kasa ta ce, "Sai ko pampers da madara". Ya ce, "Bayan su ba wani abu?" Ta ce, "Eh, amma malamar su ta ce akwai prize giving day ranar asabar kuma ana son iyayen yara su je". Sannan ta dauko report card na yaran na wannan zangon ta mika masa. Garin karba hannayen su suka gogi juna, sannan suka kara hada ido a lokaci daya babu wanda bai ji a jikin sa ba. Ita tsoro ta ji, shi kuma ji ya yi kamar hannun Hadiza. Bai ce komi ba ya karba ya sanya a aljihun shi ba tare da ya duba ba, bai kuma ba ta amsar zai je ko ba zai je ba ya fita. Ya tadda Inna har ta fito suka tafi, ya bar Fati cikin tunani. Ta zauna a gefen gadon ta, ta sauko Nanah wadda ta samu barci ta rungume cikin hannayen ta, tana tunanin me Hadiza ke nufi da ta ce ta kula da Baban Munib??? "…..Munib kulawar Uwa yake nema, Sulaiman kulawar MATA yake nema….". Ta tuno kalaman Hadiza. To ai ita ba matar shi ba ce, ba gidansu daya ba, ta ina za ta kula da shin kada rashin Hadiza ya tagayyara shi? Wannan baudadden mijin nata dake yi mata kiyayya maras dalili? In har Hadiza na nufin ta auri mijinta ne wanda ba ta fito baro-baro ta fada ba, sai hannunka mai sanda da ta yi mata, ta hada ta da wani al'amari da ba zai taba yiwuwa ba. Ba ta fata, kuma kada Allah ya tabbatar ta yi tarayya da Hadiza a kan abin da take so, ta tafi ta bari ba don ba ta so ba, sai don hukuncin Allah wanda ya fi karfin dan adam ya yi jayayya da shi. Hakika ta dauki alkawarin da ba ta san yadda za ta yi ta sauke shi ba. ****Washegari da yamma sai ga Inna ta kara dawowa, Dr. Sulaiman ya kawo ta, Hamza da Abdulyassar suka shigowa Fati da katon na madarar SMA, katon na diapers da himilin shopping na kayan masarufi da kayan biskit da choculate da su Indomie wanda su Munib ke zuwa makaranta da su. Ta adana kowanne a inda ya dace, Inna ta ce ya je sai dare ya zo ya dauke ta. A lokacin Malam Ja'afar ya iso da shi da Inna da Yaya suka kule a daki, suka sakayo kofa, me suka ce me suka ce oho, sun dai dade suna magana kafin ya dawo ya dauki Inna su wuce, kasancewar a gobe zata koma Bakori, ya biya ta Jifatu ya yi mata sayayya mai yawa kamar yadda ya saba, ita da Malam da sauran kannen shi, suka wuce gidan sa. Inna ta tuka mishi tuwon semovita da miyar ganye ya ci, ta takura mishi ya bude wayoyinsa. Yana budewa sakonnin ta'aziyya daga likitoci 'yan uwansa da sauran abokan arziki ya soma tittidowa cikin wayar. Sannan ana neman shi a ofishin (Chief Medical Director) na AKTH ranar litinin. Don haka yana kai Inna Bakori suka gaisa da mahaifin shi bai tsaya ba. Da zai tafi Inna ta ce, "Ni kuwa akwai wata magana muhimmiya da nake so mu yi, ga shi na ga alamar kana sauri". Ya ce, "Gaskiya kam ina cikin sauri, sai ko idan na dawo". Ta ce, "Shi ke nan Allah ya kiyaye hanya, ya kara maka hakuri da YAKANAH, ya shige maka gaba a kan al'amuran ka, ya yi maka musayan alheri". Har ransa ya ji dadin addu'o'in Inna, wata nutsuwa ta kara shigar shi, son mahaifiyar shi ya kara shigar shi. Ta ce, "Ina so zuwa sanda za ka dawo in ga canji, kamar yadda ka yi min alkawari, in ganka a likitanka ba mai sunan Malam ba". Murmushi ya yi, wanda rabon shi da yin shi tun wani karni can da ya shude. **** Litinin, ya isa ofishin CMD, sun dade suna tattunawa a kan wani aiki na dashen zuciya da za a yiwa ministan lafiya. Yana daya daga cikin likitocin da zasu gabatar da aikin. Ya koma office dinsa ya daidaita komai ya ci gaba da aikin sa, cikin karfin zuciya da neman rinjaye a kanta. Sai ya zamto yana jin dadin aikin sosai, don yana debe mishi kewa, yana hana shi zama shiru har maraicin matarsa ya gallabe shi. Ya tarar da tulin ayyuka da yawa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya. Ranar alhamis ya saci jiki ya je yayowa 'ya'yan shi siyayya ya biya ta makarantar su ya gansu, lokacin da aka fito cin abinci, a karkashin wani benci ya zauna ya rungume su suna ta labari, ya bude ‘kit-kat’ yana basu suna ci suna yi mishi hira. Tun suna damuwa da rashin Momin su har sun hakura sun dangana sun daina tambayar ta. Munib ya ce, "Daddy ba ka zo (prize giving) din mu ba, kowa Baban shi ya zo banda mu". Ya kama kunnen shi cikin nunawa yaron amsa laifin sa, ya ce, "I am very very sorry..... aiki ne ya yi min yawa. To wa ya kawo ku?" Suka ce, "Aunty Fati, ta yi mana kwalliya ta kawo mu". Ya ce, "Aunty Fati ta kyauta!". Suka yi murmushi. Ya ce, "Next year ba zan sake ba". Aka kada kararrawar komawa aji, suka fella da gudu suka nufi ajinsu, ya bisu da kallo yana murmushi cike da kewar su. Hakan yake yi duk sanda ya samu sararin aiki, ya daina zuwa gidan don kar ya ga Fati, tana tuno mishi da wasu al'amura msu yawa a kan Hadiza. Sannan ba ya son wata alaka take shiga tsakanin su, shi ma kuma bai san mai ya sa ba, ya danganta hakan da rashin haduwar jininsu na tuntuni. Ita kuma ta danganta hakan da wulakanci da raina mata wayo, yana ganin ta kamar ba ta san abin da take yi ba, bayan in da wanda ya san ciwon kansa a duniya to ita ce. Sai dai tsarin rayuwar su da ya banbanta, kowa da irin nashi tsarin rayuwar, sun dauki rayuwar bature mai zafi sun yafa shi da Hadiza, ita kuwa Lahira ta sani ita take wa tanadi, shiyasa yake mata wani gani-gani, don haka ita ma ta yi kamar ba ta san yana zuwa makarantar yaran ba, bayan kuma suna gaya mata.Ana i gobe sadakar arba'in din Hadizah, Malam Sulaiman, Inna Halima da Baffanin Sulaiman guda biyu, Malam Surajo da Alhaji Umar suka iso gidan Sulaiman a Kano, a daren suka bukaci ya kai su Karkasara. In da ya ajiye su da daddare ya wuce asibiti, da cewar zai dawo ya dauke su. Manya sun kule a falon Baban Hadiza, wato Malam Ja'afar suna magana ta gemu-da-gemu har da Yaya da Inna. Yaya ta ce, "Ni bana jin Fati sai shi Sulaiman, anya zai yi na'am da al'amarin nan?" Malam Sulaiman ya yi murmushi ya ce, "Kune baku san Sule ba har yanzu, yana da wani hali tun yana yaro, abin da zai so sai ya fara kin shi tukunna. Ga yadda mahaifiyar shi take bani labari, babu jituwa ko ya ya tsakanin sa da Fati, ita kuma ta kama kanta ba ta shiga shirgin shi. Mu dai burin mu ku bamu hadin kai, Allah ya gani muna son zuri'ar gidan nan, muna son zumunci ya ci gaba da gudana kamar yadda aka faro. Fati ita ta fi cancanta da ta rike 'ya'yan 'yar uwar ta, don a wannan zamanin da wuya a samu macen da za ta rike maka 'ya'ya har uku duk son da take maka. Sannan mun yaba da hankali da tsarin rayuwar Fati, muna sa ran yara za su tashi da kyakkyawar tarbiyya har zuwa girman su. Fati ba za ta dauwama a gida tana bautar 'ya'yan 'yar uwarta ba, dole watarana za ta yi aure. Ranar da hakan ta faru ya ya Sulaiman zai yi da yaran nan? Ga shi suna karatun su mai kyau a nan balle mu tafi dasu Bakori. Fati ita ta fi cancanta da ta maye gurbin 'yar uwarta a zuciyar Sulaiman. Don haka muna neman hadin kanku, yardar ku da amincewar ku Malam Ja'afar. Shin an bamu Fati? Da karfin mu muka zo, da sadakin mu a hannu, gobe muke so bayan an shafa addu'ar Hadiza a daura auren Sulaiman da Fatima". Malam Ja'afar ya ce, "Tun kafin ku yi wannan tunanin na riga ku yin sa, kun dai riga ni furtawa ne. Tabbas duk matar da Sule zai aura nan gaba ta rike mishi marayun shi ba kamar Fati ba, wadda ta san ciwon su, tasan ciwon 'yar uwarta. Sannan Hadizah ta yi wani abu a ranar da za ta koma ga mahaliccinta, wanda ya tsaya min a rai kwarai, ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, sai dai ban ji me suke cewa ba. Fati yarinya ce mai biyayya, ba za ta tsallake umarnin mu ba, amma kamar yadda Sa'adatu ta ce ne, da kyar idan shi Sulaiman din zai amince. Sannan ya wuce matsayin da za a ce za a yi mishi aure ba tare da sanin shi ba". Alhaji Umar ya ce, "Ku bar wannan a hannun mu, kamar yadda Fati take mai biyayya, shi ma Sulaiman mai biyayya ne, iyayen shi basu taba saka mishi kara ya tsallake ba. Ina da yakinin zai yi biyayya ga mahaifin shi, kuma a daren nan zamu sanar da shi ba sai gobe ba. Ga sadaki naira dubu ishirin ga goro, daga aljihuna ni waliyyin sa. Jikina ya bani alheri ne zamu kulla, don irin wannan auren na son zuciyar iyaye ba karamar falala ake samu a cikin shi ba". Kowa ya jinjina kai. Yaya ta ce, "Nima a daren nan zan sanar da ita insha Allahu". Da haka taron ya tashi, ya yi dai-dai da sallamar Sulaiman a falon, dukkanin su suka amsa fuskar kowannen su cike da walwala da annuri. Malam ya ce, "Faduwa ta zo dai-dai da zama kenan, ita ma Fatiman a kirawo ta". Yaya ta tashi ta fita don kiran Fati. Tana yiwa su Munib shimfidar kwanciya goye da Nana, Yaya ta yane labulen dakin ta ce, "Fati kin kwanta ne?" "A'a, ina harama dai". "To biyo ni dakin Malam yana son magana da ke". Ta sauke goyon ta zurma hijabin ta, ta bi bayan Yaya har dakin Malam. Ta sha mamakin ganin taron dakin har da Baban Munib, wanda ke can sunkuye da kai a gefe. Ta yi sallama cikin sassanyar muryar ta dukkan su suka amsa, ban da Sulaiman wanda ya fara shan jinin jikinsa kan wannan taron domin shi aka yi. Jikinsa ya yi sanyi, gaban shi ya soma faduwa, haka nan gwiwoyinsa ya jisu kamar an rarrade su da murfin kwano. Ta samu gefen Inna ta zauna, ita ma jikinta ya soma kyarma don ba ta son a tirke ta a cikin mutane. Iyayen dai na duban su suna nazarin kowannen su, sun fahimci dukkan su a firgice suke, amma firgitar ta fi karfi ga Sulaiman. Wannan taro na mene ne? Malam Sulaiman baya shiga kankanuwar magana. Sai da suka tabbatar sun dan samu nutsuwa sannan Malam Sulaiman ya dubi dansa ya ce, "Mai sunana wani abin alheri ne za mu yi maka, da fatan za ka karba hannu bibbiyu". Bai yi magana ba, amma ya dago ya dubi mahaifin sa. Ya ci gaba da cewa, "Muna kara yi muku ta'aziyya, sannan muna so ku sani cewa, duk abin da Allah ya tsara akwai hikimar yin hakan a cikin sa. Mun zauna mun yi tunani, mun yi shawara mun yanke cewa, Fati za ta maye gurbin 'yar uwarta a gare ka, ku ci gaba da raino da tarbiyyar 'ya'yanku kamar yadda mahaifiyar su ta fara yi musu, kuma 'yar uwarta ta karbe ta. Allah ya riga ya hada mu, zuri'a ta hada mu. Don haka Sulaiman bana son ka da wani aure in dai ba jinin gidan nan ne ya kare ba. Za mu yi alfahari daku idan kuka taushi zuciyoyin ku kuka yi mana biyayya. Allah zai nunawa Hadiza har cikin kabarin ta cewa, ke Fati kin rungumi iyalinta, kin rungumi mijinta baki bar rashin ta a rayuwa ya tagayyara su ba. Sannan kai Sulaiman Hadiza za ta yi farin ciki idan har ya zamto ka rungumi amanar rayuwar 'yar uwarta ta hanyar aure, wadda kowa shaida ne kan bata da kamarta, muna neman hadin kan ku, shin za mu samu Fatima da Sulaimanu?" Da a ce Malam Sulaiman ya lura, da ya ga irin jibin (zufar) da ke ambaliya a fuska da jikin Sulaiman, yayin da gudun jini ya katse a jikin Fati, idanuwanta suka juye suka kada suka yi jazur, hanjin cikinta ya dunkule waje daya ko dan yatsanta ta kasa dagawa balle ta motsa bakinta. Tana addu'a cikin zuciyarta idan mafarki take Ubangiji Allah subhana ya yi gaggawar farkar da ita. Sai dai a bangaren shi Sulaiman, ya so a ce shi da iyayen shi ne kadai su kai wannan maganar, da a take zai ce dasu idan kasa da sama za ta hadu bai amince ba. To an ce wai ko mutuwa tana kunyar iyaye, balle iyayen Hadiza? Ya zai yi ya iya ya budi baki a gabansu ya ce baya son jinin Hadiza? Shi tunda ya rasa Hadiza bai kara tunanin nan gaba zai kara yin aure ba, bai kara tunanin wai yana da future ba, balle ya yi tunanin yin aure. Kuma a rasa wadda za a aura masa sai wannan yarinyar da bai san a matsayin da ya ajiye ta a zuciyar sa ba. Duk da yadda take hidima da 'ya'yansa, Fati ba ta taba burge shi ba, Allah bai sa masa kaunar ta a zuciyar sa ba, sannan kuma wai auren ma daga yin arba'in din Hadiza? Sannan da shakikiyar ta? Fati ba ta taba burge shi ba balle ya so ta, bai taba tunanin irin ta a matsayin matar shi ba. Ya ya ma za ai wannan kidahumar yarinyar 'yar sakandire ta maye gurbin Hadiza? Ta ya ya mahaifan shi suke tunanin zai iya rayuwa da kanwar Hadiza? Ya yada girman sa ya yi mu'amalar aure da ita? Kwarai ya fahimci abin da Hadiza ke nufi tsakanin shi da Fati a ranar da Allah zai dauki ranta, amma (he is sorry to say) ba zai iya cikawa Hadiza burinta ba. In don 'ya'yan shi ne a ba shi abinsa ya rike ko ya bai wa Inna, karatun nasu a birnin Kano ba dole bane, ba sai an makala mishi auren da bai san ya ya zai yi da shi ba. Malam Ja'afar ya ce, "Duk kun yi shiru, ko da yake shirun alamar amincewa ne, To ku tashi ku je Allah ya yi muku albarka, dama mun sanar daku ne kada sai gobe ku ji an daura aure ku ce ba a sanar daku ba. In kuma akwai mai magana to ya yi, a shirye muke da mu bai wa kowannen ku hakkin sa". Inna tana murmushi ta dubi Sulaiman ta ce, "Ni na san mai sunan Malam ba zai ki abin da muke so ba". Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya nemi duk wata hujja da zai bayar ya neme ta ya rasa. Zuwa lokacin Fati ta mike za ta fita, juwa na kwasar ta, da dafa bango ta samu ta bar falon. Ta yi dakinta ta dauki 'yar jaririyar ta wadda ke ta tsala kuka a dalilin ta manta ba ta sa mata gidan sauro ba ta fita, sauro ya hana mata barci. Shi ma bai yi magana ba yana jin su suna ta kida suna rawar su na addu'o'i, sa albarka da fatan alheri a gare shi. Gwiwa a salube ya fito jikin mota ya baro su suna ta sallama.YAKANAH!-2 Karfe goma sha dayan dare garin Kano ya yi tsit, sai iskar hunturu da ke kadawa. Malam Ja'afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida. Zai gifta ta dakin Fati ya jiyo shesshekar kukan ta, ya dakata ya daga labulen yana kallon ta, tana zaune a kan darduma ta kunshe fuskar ta cikin hijabi sai kuka take. Ya karasa shigowa cikin dakin ya ce, "Fadimatu kukan me kike yi?" A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur, sun yi luhu-luhu alamar ta yi kuka har ta gode Allah. Malam Ja'afar ya zauna a wata 'yar kujera da ke dakin yana fuskantar diyar sa. Nanah ta soma motsi alamun za ta tashi daga barcinta, ta soma rirriga ta. Ya jima bai yi magana ba sai da Nana ta koma barcin ta ya ce, "Gaya min damuwar ki Fadimatu, ni mahaifin ki ne". Ta share idon ta da hankici, ta ja shessheka kafin ta ce, "Baba babu komi". Ya jima yana kallon ta, sannan ya yi murmushi ya ce, "Kina tuhumar mu da yi miki auren da baki so, auren mijin 'yar uwar ki. Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba za ku gane ba sai nan gaba, idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwar ku". Fati ta yi shiru tana sauraron Baban su, ta ga cewa wannan ita ce damarta ta karshe, daga gobe za a zarga mata igiyoyin wanda ta tabbatar ba ya son ta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai, ta ce, "Ku yi min alfarma Baba, Baba baka taba sani in yi wani abu na shallake maganar ka ba, amma a wannan karon, ina so ka duba hujjojina. Baba Dr. Sulaiman ba ya sona, Baba Dr. Sulaiman ya fi karfina, bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba Sulaiman ba zai taba son wata ba, bayan son da yake yiwa Yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma Dr. Sulaiman tun fil azal ya tsane ni, ban san laifin da na yi masa ba. Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka bai taba duba na a matsayin jinin Hadiza ba, balle ya yi la'akari da wannan ya kaunace ni. In dai don 'ya'yan shi ne ai nima 'ya'yana ne, zan ci gaba da rike su ba sai na zama matarsa ba". Ya ce, "Amma za ki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aure ki da zugar 'ya'yan Yayar ki? Da ‘yar uwarki ta damka miki amanarsu? Na ji hujjojin ki Fati, na kuma yarda bazaki yi mun karya ba, amma nima ina so in tambaye ki. Wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar babban likita irin Sulaiman? Tana 'yar talakawa kuma mace kamar ki?" Babu dogon tunani ta ce, "Ilimi". Ya ce, "A ina ta samu?" Ta ce, "Fita ta yi ta nema". Ya ce, "In haka ne ke mai zai hana kema ki fita ki nema?' Ta ce, "Ba zan iya irin nata ba!" Ya yi murmushi ya ce, "Duk ilimi sunan sa ilimi, balle ilimin ki ya fi na kowa, yafi na komai, ilimin Alkur'ani ne da ke wanda ya kunshi dukkan rayuwar duniya da lahira baki dayan ta, ke din nan ba abar wulakantawa ba ce 'yar baiwa ce, mahaddaciyar Alkur'ani, wallahi-wallahi a rayuwar duniya da lahira ba za ki tozarta ba. Sannan don kina gaishe shi bai amsa ba, sai ki ce ba ya son ki? Me kika yi masa? Mutum ne mai kyakkyawar zuciya, shekaru dai-dai har bakwai da nayi tare da shi ban taba ganin wata halayya ta banza a tare da shi ba. Tunda ya auri 'yar uwar ki ba’a taba jin kansu ba, ba ta taba yin yaji ba, ba ta taba kawo karar shi ba. Sai ki yi tunanin me Hadiza ta yi ta samu wannan mafificiyar soyayya a zuciyar mijinta, tunda kin zauna da ita, kema ki kwatanta ko ba duka ba, ki gani idan ba za ki samu ba?". Ta share ido ta ce, "Baba ai ni gani na yake 'yar kauye, ga shi ni kuma ba zan iya yin irin rayuwar su ba. Mai ya sa ba za ka gane ba? Banida abinda zan burge shi da shi. Don Allah Baba ka aura min ko wane ne, komi yawan matansa da yawan shekarun sa, na rantse zan zauna da shi, amma kada ka kai ni inda ba zan yi kwarjini ba, inda za a wulakanta ni, inda ba za a so ni ba….". Ya yi murmushi ya ce, "Babu inda zan kai ki sai gidan SULAIMAN! Na kuma tabbatar miki ko a yanzu bai son ki, watarana na zuwa da za ya so ki. Kamar, ko ma fiye da yadda yake son 'yar uwarki. Daina kukan nan kada ya haddasa miki ciwo, a duk sanda ki kai sujjada cikin sallolin farilla ki ce, "Allah ka sanya soyayyata a zuciyar mijina". Za ki sha mamaki Fadima, ki sanyawa zuciyar ki salama, shi da yake namiji bai bijirewa iyayen shi ba sai ke? A'a kada mu yi haka da ke Fadimatu, na san ki, na san halin ki, na tabbata ba za ki bani kunya ba. Ki yi min alkawarin za ki zauna lafiya da mijin ki, ki yi min alkawarin za ki yi mishi biyayya, ki yi min alkawarin za ki ba shi soyayya irin wadda shakikiyar ki ke ba shi, ki yi min alkawarin ba za ki taba kai karar shi wani waje ba, ke ko mu din nan ban yarda ki kawo karar shi gare mu ba, balle iyayen shi. Duk abin da ya yi miki na rashin dadi ki yi hakuri, ki yafe mishi cikin zuciyar ki, ki yi mishi uzuri. Wannan halin YAKANAH kenan! Sakayyar ki na wurin Allah!!". Tana kuka sosai ta ce, "Na ji Baba, kuma na yi maka alkawari". Ya dora hannu a kanta, "To Allah ya yi miki albarka, ya ba ki juriyar rike 'ya'yan ki, ya sa suma mahaddata alkur'ani ne kamar ki. Tashi ki dauro alwala ki ci gaba da neman yardar Allah da yardar mijin ki". **** Dr.Sulaiman yana tuki amma hankalinsa ba ya jikinsa, in banda tafasa babu abin da zuciyarsa ke yi, amma kamar wanda aka dinkewa baki ya kasa ce da iyayen shi komi wadanda ke ta hirarrakin su a kan karamcin iyayen Hadiza. Har suka iso gida ya kai su bangaren da ya tanada don bakin kwana, wanda ke daga wajen gidan. Inna kuma ta wuce dakin da yake na Hadiza. Ya fada toilet ya yo wanka, yana alwala cikin sink sai jini ya balle mishi ta hanci. Haka ya tsaya yai ta kwararar da habon (nasal bleeding), yana bin shi da ruwa yana wucewa. A duk lokacin da yake cikin takurar zuciya habo yake yi, ya soma yiwa kanshi taimakon gaggawa har jinin ya tsaya. Ya fito ‘bed room’ din su wanda ya zama kaca-kaca saboda rashin gyara, ya dauko wata rigar barcin Hadiza ya kwanta rigingine, ya dora rigar a kan fuskar shi yana shakar kamshin Hadizah na dindindin na turaren 'escada-sentiment'. So da kaunar matar shi ke dawainiya da shi. Ya lumshe ido ya shafo makwancin ta, katon fili ya yi mishi sallama, wasu irin dumammun hawaye, suka mirgino ta gefen idon sa. A sannan ne tunanin shirmamman auran da za a yi mishi a gobe ya dawo mishi cikin kwanya, Eh! Shirmamme mana, don bai dauki wannan auren da sunan aure ba. Amma a yadda Inna da Malam suka sanya ransu da zuciyar su a auren nan in ya ce baya yi ya tabbata zai bata goma ne daya ba ta gyaru ba, don za su yi fushi da shi, sannan kuma ba za su fasa ba. Don Malam bai yin magana biyu, sannan ransu za ya baci, kuma ba za su taba shiryawa da shi ba. Don haka maganar ya je ya ce da Inna bai yarda ba, ko bai amince ba, kamar yadda zuciyar shi ke ta kimsa mishi ba ta ma taso ba. Illa ya zuba musu ido su yi yadda suke so. Sai dai ya san yadda suka kawo yarinya, haka za su zo su dauki abar su. Shi mijin mace daya ne a duniya da lahira (Hadizah). Bayan ita bashi da sauran bukatar komi daga kowacce diya mace, balle kanwarta duk da Allah ya halarta, amma ai da kunya, ya hada rayuwa da kanwar Hadiza, balle wannan yarinyar da bai san irin ta ba, sannan Allah subhana bai halicci zuciyar sa da kaunar ta ba. Ba kilin (clean) ba isasshen wanka a jikinta, balle aje ga ado irin na 'ya'ya mata. Kullum cikin tsummokara! Yo tsummokara mana? Kyawun surar ta ya tashi a banza tunda ba ta san yadda za ta yi ta gyara kanta ba. Shi duk ma ba wannan ya dame shi ba, kawai ranshi baya son Fatima Ja'afar, duk da kasancewar ta kanwar Hadiza. Jikinsa ya sha ba shi akwai wani al'amari mai GIRMA tsakanin shi da yarinyar, tun daga sanda ya fara ganin ta, cikin kwayar idanunsu wani ‘chemistry’ mai girma ya afku rana ta farko da ya ganta matsayin kanwar Hadiza, amma bai taba kawowa cewa aure ne ba. Yadda Fati ta kwana ido biyu, haka Dr. Sulaiman ya kwana ido biyu, kowannen su zuciya na zugi. Sai dai ita Fati ba ta kin al'amarin musamman in ta tuna da alkawarin da ta daukar wa 'yar uwarta. Damuwar ta shi ne Sulaiman ba ya son ta, da dan karen tsoron zama dashi dankare a zuciyar ta. Shi kuwa tunanin yadda zai yi ya tsallake auren yake ba tare da ya batawa iyayen shi ba, ya san a sake dai bai isa ya ce ya saki ba. Daga karshe ya yanke wa kansa shawarar da yake ganin ita ce za ta fissheshi. Don haka ya dan samu sa'idar da ya kwanta ya runtsa idon sa. Kwanciyar sa ke da wuya aka soma kiraye-kirayen sallar asubahi. Ya dauro alwala ya gabatar da raka'atainil fijri, kamin ya dora da farillar. Ya yi addu'o'in shi ya koma ya kwanta. Zuwa bakwai ya tashi ya feso wanka ya debi koriyar Getzner sabuwa kar sai sheki take, ya fesa turare ya zuba hular kube, ya fito kamar saurayi dan shekaru ashirin da bakwai, ba za ka ce shi ne ya aje su Munib ba, zuciyar shi wasai da hukuncin da ya yankewa zuciyar shi. Ya fito ya janyo kofar ya iso falo, nan ya tarar da Inna ta hada musu kalaci, kunun gyada da dafadukan taliya, kasancewar a gurguje ta yi don dai ya samu ya ci wani abu kafin ya fita. Ya je ya shigo da su Malam suka yi kalacin gaba daya. Daga nan suka nufo Karkasara. Kofar gidan Malam Ja'afar ya cika makil da jama'a wadanda suka zo addu'ar arba'in din Dr. Hadiza, aka rarraba pieces *na alkur'ani aka yi mata sauka, aka yi addu'o'i na musamman. Daga nan kafin mutane su watse, waliyyai suka gabatar da daurin auren Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, da Fatima Ja'afar Mai-Yadi, a kan sadaki naira dubu ishirin kacal. Mutane suka yi ta mamaki tare da sanya albarka, domin an yi koyi da fadar ma'aiki (S.A.W). Malam Ja'afar ya dubi Inna Halima ya ce, "Babu bukatar wata bidi'a, gobe Sulaiman ya zo ya dau matarsa da 'ya'yan shi su tafi, Allah ya yi musu albarka". Fati da ke uwar dakin Yaya tana jin duk abin da ke faruwa a gidan, ta takure a bayan labule sai gursheken kuka take, goye da 'yarta sai makyarkyata take. Ta rasa inda za ta sa ranta ta ji dadi, shin rayuwarta da wadda za ta je ta tarar wace irin rayuwa ce? Shin meye makomar rayuwar ta? Ta tabbata, kuma a ko’ina za ta yi rantsuwa a kan cewa Sulaiman bai son ta. Takura mishi aka yi. Yaya Hadiza ta dora mata nauyi, da kananan shekarun ta ba za su iya saukewa ba. Amma in ta tuno nasihar da Baban su ya yi mata a daren jiya, sai ta ji sanyi a ranta. Jin Inna na neman ta, ta yi saurin shigewa toilet. Inna ta daga labule ba ta ganta ba, ta ce da Yaya “bata nan, watakil ta shiga bayi”. Daga nan suka ci gaba da hira ita da Yaya a kan maganar lefe, ta ce za ta sa su Ruma su hado ko gidanta ne a kai mata. Yaya ta kafe a kan cewa wallahi sun yafe, ko tsinken Sulaiman ba za su karba ba. An riga an zama daya sai dai su bi yara da addu'a. Amma Inna ta kudire a ranta sai an yiwa Fati lefe irin wanda ake yiwa kowacce yarinya budurwa. Sai da su Inna suka bar gidan sannan Fati ta fito daga maboyar ta, makota na ta shigowa suna yiwa Yaya ta'aziyya da Allah ya sanya alheri. Ta nufi dakinta ta shimfidar da Nana, sannan ta kwanta a gefen ta ba laka a jikinta. Yaya ta shigo rike da kwanon silba da damammiyar fura mai sanyi, ta zauna a gefen ta tana kallon yadda duk ta zuge kwana daya kacal. Ta ce, "Ungo fura tashi shanye ki bani kwanon". Ta girgiza kai, "Bana son cin komi". Yaya ta ce, "Haka za ki daure ki dura, zama da yunwa da bacin rai ba naki bane, tunda dai auren nan an riga an daura ya kuma dauru, sai ki saki ranki ki watsar da duk wani tunani wanda zai hana miki kwanciyar hankali. Karbi na ce". Ta tashi zaune ta amsa, ta kafa kai tana sha tare da kokarin maida kukan da ya taho mata a dalilin furucin Yaya, "Aure ne an riga an daura kuma ya dauru….". Wato dai da gaske ta zama matar Dr. Sulaiman mijin Yayarta. Sai da ta shanye furar ta share hawaye da 'yan yatsunta, Yaya ta ce, "Kukan dai? Sai ki yi ta yi tunda kin ga shi zai fisshe ki. Haba, ayi yarinya da shegen kuka kamar Muniba? Yanzu ki tashi ki je ki yi wanka, ki sa kaya masu kyau ki je a wanke miki wannan dankararren gashin naki da yau kwana arba'in ba ki tsefe shi ba. Ko ni uwar Hadiza ban takura rayuwata yadda kika takura taki ba. Gobe za su zo su dauke ki, don Allah ki dan gyara kanki yadda za ki yi kyan gani, ki aje hijabin nan haka ki yiwa mijinki kwalliya.......". Ai kuwa sai ta balle da kuka, "Ni wallahi ba inda za ni, ni wallahi bana son sa...........". Yaya ta bige mata baki ta ce, "Don Allah in an kaiki ki sha poison kema ki mutu, ba zan kasa rayuwa ba!!!". Ta juya ta fita. Ta tabbatar ran Yaya yai matukar baci tunda har ta yi wannan furucin, tana kuka ta taso ta biyo ta dakinta, tana zaune a kujera ta yi tagumi. Ta zube a gabanta ta kama kafarta cikin rishin kuka ta ce, "Don Allah Yaya ki yi hakuri ki yafe min, wallahi ba zan kara ba". Ta ce, "Ni me ki kai min da za ki bani hakuri? Ke aka yiwa laifi ke za a bawa hakuri. Me kika fishi ko me kike takama da shi da za ki ce bakya son sa? Ban da Allah ya kashe ya baki ai Sulaiman ba tsaran ki bane, ba za ki gano gatan da aka yi muku dukkanin ku ba sai nan gaba. Wannan shi ne karshen kauna da za ki nunawa Hadizah, ki rungumi iyalinta a bayanta, sai dai in dama ba son ta kike yi ba........!" Ta kara sautin kukan ta, "Na tuba Yaya, na bi Allah na bi ku, na yarda zan zauna da Baban Munib ko ba ya so na.......". "Shi ya ce miki ba ya son ki? Bana son mummunar fahimta, ko bai miki son soyayya ta aure ba, yana yi miki son 'yan'uwantaka, wadda a hankali in kin sadaukar da kanki gare shi za ta rikide ta koma soyayyah!. Sanda aka aura min mahaifin ku ban san shi ba, ban taba ganin sa ba. Haka aka lullube ni aka kawo ni, ko sunana bai sani ba nima ban san nashi ba. Amma kyautatawa da sadaukar da kai ya sa a yau ba abin da muke so da kauna sama da junan mu, har muka kai ga haifar ku daya bayan daya. Kina gani har yau bai taba yi min kishiya ba, bai taba bata min rai ba sai bisa kuskure. Bacin raina na nufin tashin hankalinsa, fushina na nufin tabarbarewar al'amuransa. Ki yi auren BIYAYYA ba SOYAYYA ba ki ga wacce irin riba za ki samu a cikin sa? Idan mun san babu riba ba zamu ba ki jarin ba". Fati ta share hawayen ta, cikin zuciyar ta tana cewa, mazan da dana yanzu ai ba daya bane Yaya! Balle wadannan da suka hantse cikin ilmummukan zamani masu gigitarwa, suka saba ganin mata iri-iri dai-dai da tsarin rayuwar su. Ina zan iya burge shi balle har ya kaunace ni? Ina zan iya mai da kaina irin Yaya Hadiza?Yaya ta yi murmushi irin na manya wadanda suka san cewa ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, sarai ta gane abin da Fati ke nufi; Hadiza 'yar gayu ce, kuma wadda ta gogu cikin zuzzurfan ilimin boko, ita kuwa 'yar Islamiyyah ce, wadda Allah da Annabi sune kawai a gabanta, wato dai ita 'yar Arabiyyah ce wadda ta horu ta goge cikin ilmummukan addini daban-daban da fadin Allah da manzonsa. Wadanda 'yan bokon irin su Sulaiman ke wa kallon 'yan kauye, wannan banbancin a farrake yake. Ta ce, "Fati kowacce mace da kika gani da kissarta aka haife ta, sannan kowacce da yadda Allah ya halicce ta. Sai dai ra'ayi da akida sun banbanta. Amma fa duk sunan su daya (MACE), kuma abin da ke jikin wannan shi ne a jikin waccan, ba wadda ta fi wata a matantakar sai dai ko kazama da mai tsafta. Fati ke mai tsafta ce, har a makaranta tun daga firamare har sakandire an fahimci tsaftar ki an kuma sha baki kyauta a kanta. Wannan kadai kika rike jigo ne a gidan aure, kuma ya ishe ki ki yaki zuciyar kowanne da namiji ba Sulaiman kadai ba. Kamar yadda kika ce baki da abin da za ki burge Sulaiman sai in ce a'a, Fati kina da shi, HANKALI da sanin CIWON KAI sune manyan halayen da ke burge namijin da ya san ciwon kansa irin Sulaiman ba kyale-kyalen mace ba.........". Fati ta dago ido tana kallon mahaifiyar ta, "Yaya kina nufin Baban Munib bai fi karfina ba?" Yaya ta yi murmushi a karo na uku, ta ce, "A doke kam idan za ku gabza ai ya fi karfin ki, amma a zaman aure bai fi karfin ki ba. Tunda kema mace ce kamar Hadiza, kuma a hakan da kike ba sai kin yi wata kwarkwasa ko kwalisa Sulaiman zai so ki ba. A'a, maintain your own qualities (rike taki sigar) kada ki aro wadda ba taki ba don ki burge. Kwalisa, kwarkwasa da yanga ba sa burge namijin da ya san ciwon kansa, sai hankali, nutsuwa, kamewa, ilimi da sanin ciwon kai. Wadanda dasu ne Hadiza ta samo zuciyar Sulaiman ba appearance (kamantuwar ta ba). Saboda haka Fati ki kwantar da hankalin ki, ki yi biyayya ga mahaifin ki, Alqur’anin ki, ba zai bari ki tozarta a rayuwa ba…..!!". Ta mike ta na murmushi cike da jin dadin kalaman mahaifiyarta, ko ba komi ta bata kwarin gwiwa cewa, itama mace ce kamar sauran mata ba mata ta rako duniya ba kamar yadda Sulaiman ke cewa. Ta cire mata inferiority complex din da ya bi ya addabe ta, har ta ji za ita iya jure duk wani hali da za ta tsinci kanta ko da a ce hasashen Yaya ba su zamo gaskiya a kan nata al'amarin rayuwar ba. Da kanta Yaya ta zaunar da ita a gabanta, ta sa kibiya ta tsefe mata gashin kanta da ya yi masifar dauda ya duddunkule saboda rashin gyara har tsayin kwanaki arba'in da biyar. Fati sai yawan gashi amma babu tsayi irin na asalin Kanawa, sannan ga shi da karfi kamar reza, sabida ba ta taba shafa mishi relaxer ba, da za ta shafa mishi din da ya mike ya zama mai ban sha'awa. Fa'iza ta yi sallama ta shigo tana cewa, "Wai da gaske ne abin da nake ji?" Ta tsuguna ta gaida Yaya ta amsa. Fati na hararar ta ta sake cewa, "Don Allah Yaya da gaske ne? Yau an daurawa Fati aure?" Yaya ta yi murmushi ta ce, "Eh, haka Allah ya nufa". Ta ce, "To, Allah ya sanya alheri". Yaya ta ce, "Amin". Fa'izah kawar Fati ce, tare suka yi makarantar kwana a G.G.C Kano, kuma gidansu nan cikin layinsu yake babu nisa zuwa gidan su Fati. Yaya ta ce dama yanzu zan tura Abdulyassar ya kirawo ki, ki zo ki raka ta wajen wankin kai, na san in na bar ta a haka za ta tafi gidan mijin. Daga nan ku biya ayi mata kunshi". Fa'iza ta ce, "Gaskiya kam, kawo in karasa mata tsifar". A daren sai ga kannen Dr. Sulaiman da wata kanwar Inna sun kawo akwatuna hudu shake da kaya, ga shi ba su gayawa Yaya za su kawo ba balle ta tara masu karba. Ta kama baki ta ce, "Yanzu Allah sai da aka takura Sulaiman da yin lefen nan yana fama da halin da yake ciki?" Ruma ta ce, "Ai babu komi, abune da idan ba mu yi ba, ba zamu ji dadi ba". Yaya ta ce, "To Allah ya amfana, ya sa an yi a sa'a, ya kuma tabbatar da alherin da aka kulla, amin". Fati kwana ta yi sallah, in 'yar ta yi kuka sai ta dakata ta kula da ita har ta koma barci, sannan ta ci gaba, Cikin sujjadarta tana mai rokon Allah koma mene ne zai zo cikin rayuwar ta ya zo mata da sauki. Washegari ko tsakar gida ba ta leko ba, don gidan ya cika da 'yan uwan Yaya da dangin Malam, saboda kowa da Hadiza a zuciyar sa babu wanda yake yin hayaniya. Karfe uku na rana Fa'iza ta kawo mata kayan da za ta sanya, wani leshi mai taushi ruwan zuma da kananun stones da ta kai Diallo (Zoo Road) aka yi mata dinki express, amma ya yi kyau sosai, ya amshi dan karamin jikinta. Fati siririya ce, kuma ba ta kai tsayin Hadiza ba, komi na halittar ta (natural) kamar fata, gashi da hakora yiri-yiri, kuma farare kal wadanda ba ta wasa da kuskure su da listerine (mouth wash) a duk lokacin da ta goge su. Shiyasa suke farare tas, kamar kankara A can gidan Sulaiman shi ma cike yake da nashi 'yan uwan, suna ta gyare-gyare, suka gyara gidan tsaf, dama tuni an kwashe kayan Hadiza har gadaje da (wardrove) an balle an fitar dasu an kai gidansu. Malam Ja'afar ya ba da daki guda aka kulle su, Inna tasa aka sayo katuwar katifa aka aje a dakin da a yanzu ya zama mallakin Fati kamin a yi mata jere. Kai! Rayuwa!! Ran dan adam ba a bakin komai ba, kowa ganin al'amarin yake kamar almara, masu yiwa Hadiza addu'a na yi, masu kokawa na yi, masu korafin anyi gaggawar yiwa Sulaiman wani aure na yi. Amma a bayan idon Inna, don kowa ya san irin son da Sulaiman yake yiwa Hadiza. Shi kam bai ma gidan yana asibiti tun safe, ya kama wayoyin shi ya kulle kada Inna ta neme shi. Don a daren jiya ta shaida mishi wai shi zai je da kanshi Karkasara ya dauko Fati da yara, shi kuma ya kudire in har shi zai yi hakan, to wallahi sai dai idan ba za ta zo gidan ba. Zuwa karfe hudu ran Inna ya soma baci da rashin samun Sulaiman a waya, sai dai ta yi mishi uzri. Ta sani sarai sun takura shi, wanda su sun tabbatar abin alheri suka yi, sun gyara zumuncin su da iyayen Hadiza, sun kawo wadda za ta rike 'yan jikokin su da gaskiya, sannan sun aura mishi mai kama da Hadiza, kuma shakikiyarta. Akwai gatan da za su yi mishi da ya wuce wannan? Ta kudurce a ranta za ta tsayawa Fati da addu'a da yakin zuciyar Sulaiman har sai ya so ta kamar yadda yake son 'yar uwarta. Don haka sai Inna Talatuwa kanwar Malam da su Ramatu ne suka taho dauko amaryar a motar mijin Ruma, don motar shi da ita ya fita, ta Hadiza tuni an sayar sai ta amfanin gida rufe cikin tampol. Cikin girma da mutuntawa aka basu amarya. Yaya ta ce a bar mata yaran bayan sati daya za a kawo su. Ruma ta ce, "Yaya baki yiwa Fati nasiha ba". Ta yi murmushi ta ce, "Duk nasihar da zan yi mata na yi mata jiya, Allah ya sa ta je a sa'a". A dakin Malam Ja'afar kowa ya fita ya bar su, ganin irin kukan da Fati ke yi kamar ana zare mata rai sai zuciyar shi ta motsa. Ya ce,. "Fadimatul-Zahra'u, ki daina kuka, ban aurar da ke ba sai a hannu na gari, hannun dana san cewa ba zan taba yin dana sani ba". Har aka iso gidan, wanda ba bakonta ba ne tana tauna maganar Babanta, me ya sa Yaya da Baba suke son Dr. Sulaiman har haka? Me ya sa kowa ya budi baki kyakkyawan kalami yake yi a kanshi? Me ya sa ita ba ta ganin kirkin nashi da nagartar tashi? Kenan ita kadai yake yiwa rashin kirki, to laifin me ta yi masa? Babu wanda zai ba ta amsar sai Sulaiman din kansa, wanda ta tabbatar har abada ba za ta ji amsar ba in har sai shi din ne zai amsa mata. Inna ta tarbe su ta rungume ta, ta kama hannun ta har dakin da a yanzu ya zan mallakin ta, ta aje ta a bakin katifa. Fa'iza da Karima kawayenta na gefen ta, wannan ya shigo wannan ya fita, amma ita tunanin ta ya tafi ga Baby Nanah wadda ta baro a wajen Yaya, ta shaku da yarinyar sosai ta yadda har take mantawa cewa ba ita ta haife ta ba, ta alkawartawa ranta za ta roki Inna ta karbo mata ita gobe ba za ta iya yin kwanaki bakwai ba tare da ita ba. Zuwa karfe goma na dare gidan ya yi shiru, masu tafiya sun tafi, masu gajiya sun kwanta barci. Su Fa'izah duk sun tafi, Inna ta shigo dakin rike da kulolin abinci guda biyu, ta ce, "Kin yi barci ne Fati?' Ta mike zaune rike da carbi a hannun ta, ta ce, "A'ah". "To tashi ga abinci ki ci, tun dazu na so in kawo miki na san ba za ki iya ci cikin mutane ba". Ta mike zaune ta karba, jellop din cous-cous ne wanda ya ji kayan lambu a filas din farko, sai farfesun kayan ciki da ya ji kayan kamshin gargajiya a daya filas din. Inna da kanta ta zuba mata ta soma ci. Inna na kallon ta cikin tausayi, ganin yadda take cin abincin hannu baka hannu kwarya. Allah kadai ya san tun yaushe rabon ta da abinci, mai yiwuwa tunda aka yi mata zancen aure da mijin Yayarta. Ta gama ci ta kora da gwangwanin fanta, ta koma ta kishingida Inna ta yi mata sai da safe ta kwashe kulolin da plate din da gwangwanin fantar ta fita. Karfe daya na dare Dr. Sulaiman ya shigo gidan, ya tabbatar zuwa yanzu dai kowa ya kwanta balle a dame shi. Yana shiga dakinsa ya danno kofa ya murza key, hoton Hadiza cikin dan kankanin ‘frame’ da ke kan ‘side drower’ na gefen gadon shi ya yi mishi sallama, tana murmushin ta ni'imtacce cikin farar shirt din calvin-klien wato C.K. Ya zare falmaran din suit din shi ya zare tie ya fada a kan gadon, ba tareda ya cire takalmi da safar kafarshi ba, ya fizgo hoton ya rungume a kirjin shi, ya yi magana cikin muryar kuka, "Why do you leave me Hadizahh….??? Mai ya sa kika boye min cewa kina da brain cancer? Likitancin ki bai gaya miki cewa babu ciwon da ba shi da magani ba? Hatta kanjamau ana nan ana kokarin nemo maganin ta. Mai ya sa baki jira ni mun tafi tare ba? You left me incomplete, shattered….!" Ya mirgina ya kara rungume hoton ya feso wani irin huci mai zafi. “Da gaske Allah ba ya barin wani don wani, na tabbata da ba zai dauke ki ya barni ba. Ya za ai a ce na zama mijin kanwar ki? Wannan cin fuska da cin amanar soyayya har ina? Ba za a yi ta dani ba! I am for Hadizah only….!! Zan jira wa'adina Hadiza in iske ki acan mu ci gaba da rayuwar mu a inda babu mutuwa…. balle ta sake raba mu……". Ya lumshe ido, hawaye suka mirgino, ya budesu a hankali ya kai ‘frame’ din ga siraran lebban sa, ya yi masa sumba mai tsayi da zurfi, kafin ya yi masa murmushi ya ce, "I love you HADIZAH….Cikin kowanne hali INA SONKI HADDIZAHH!!!" **** Masoyan Hadizar na da yawa, domin ita ma a can, Fadima, a dai-dai wannan lokacin, goshinta na gaban mahalicci, cewa take. "Ya Allah! Ka yi rahma ga baiwar ka Hadiza, ka yalwata kabarinta da haske da kamshi, ka yaye mata duhun kabari, ka shayar da ita ruwan Alkhausara, ka bani juriyar cika alkawarin ta duk da na san ba abu ne mai sauki ba……….". Kafin gari ya yi haske tuni Dr. Sulaiman ya fice, sai karar motar shi Inna da ke lazimi ta jiyo. Ranta ya baci sosai, ta dauki waya ta yi kiran sa, anyi sa'a wayar na bude ba shi kuma da hujjar kin amsa kiran Inna. Yana amsawa ta ce, "Dabbobin da ke cikin gidanka za su koma makyankyasar su, sai in ce Allah ya hada mu da alheri". Kafin ya yi magana ta kashe. Ya juya wayar a hannun sa, "Dabbobi? Dabbobi? Su waye dabbobin? Eh, dole ta kira kanta dabba a gidansa, tunda har za ka iya fita tana cikin gidan ba ka gaishe ta ba". Jikinsa ya yi sanyi, a hankali ya yi round ya juyo. Lokacin da ya iso gidan har sun faka kayan su suna sawa a motar Jibril mijin Ruma, tana kokarin fitowa yana kokarin shigowa suka yi karo, karaf, ya yi saurin ja da baya. Ya ce, "Inna ki yi hakuri in je in yi signing yanzu sai in dawo in kai ku". Ta harare shi ta ce, "Ai ba kai kadai ke da mota ba, tunda ka iya ka kwana cikin gidan ka wayi gari ka fice ba tare da ka binciki halin da muke ciki ba ai dabbobi ka dauke mu. Ni matsa ka bani hanya bana son motar taka". Ya soma magiya, "Ki yi hakuri Inna, mu koma ciki mu yi magana, wallahi dama ban yi niyyar dadewa ba zan je ne in dawo kuma ban san yau za ku koma ba". Ta balla masa harara sai kuma ya ba ta tausayi. Wanda ya san Dr. Sulaiman a baya, ya kuma ganshi a yanzu, zai yi wuya ya shaida shi in ba ya yi masa farin sani ba. Duk da ya aske kasumbar da ta cika mishi fuska, hakan bai voye muguwar ramar da ya yi ba. Ita kanta muryar shi ta canza ta zama mara amo, kamar ta mai fama da mura. Dara-daran idanunsa sun zurma ciki. Kallo daya za ka yi mishi ka tabbatar da cewa har yanzu mutuwar matar shi ba ta gama dukan shi ba. Ta juya suka koma ciki, suka zauna a falo. Ta ce, "Ka kara YAKANAH Sulaiman, a kan wadda kake da ita. Ka rike Fatima da amana, domin amanar ce a hannun ka. Jiya baka je ka ga ya take ba, ya ta zo, meye matsalar ta balle lafiyar ta. Sannan yanzu ma ka fita ba tare da ka neme ta ba”. Ya yi shiru kansa a kasa, a gaskiya! An takura rayuwar sa, an kakaba masa abin da bai san ya zai yi da shi ba. Ba ya jin ko sautin shi zai iya bai ma Fati. Amma Inna gaskiya ta fadi, dole ya dinga bincikar lafiyar ta. A sanyaye ya ce, "Ki yi hakuri Inna, insha Allah, zan kula". Ta ce, "To Allah ya yi maka albarka". Ya ji dadi har kokon ransa, ya ce, "Za ku jiranin in je in dawo in kai ku?" Ta ce, "A'a, ka maida hankali kan aikin ka. Ga Jibril zai kai mu, sai mun yi waya, Allah ya hada mu da alheri". Ya zaro kudi cikin aljihun sa ba tare da ya kirga ba ya mika mata, "Sai a ba Jibril ya sha mai". Ya sake zaro wasu, "Wannan kuma sai a rabawa su Ruma, karshen watan nan zan zo insha Allah in abin da nake jira ya fito". Ta ce, "Meye abin da kake jira?" Ya yi murmushi kadan, "Sai na zo din dai Inna". Bayan fitar sa ta shiga dakin Fati, ta tarar da ita ta yi wanka ta sauya kaya, cikin doguwar riga kirar Omman ruwan makuba, ta makala dan kankanin hijabi fari iya wuyanta, fuskarta sumul babu ko tabon pimples ko daya, sannan babu wani make-up amma ta yi kyau sosai. Akwai wata boyayyar kauna da Inna Halima ke yiwa Fati, wadda ta dasu a ranta tun daga lokacin da ta fara zama da ita daki daya, ta fahimce ta, ta fahimci akidar ta. A wancan lokacin ta ce a ranta, ina ma ina da wani babban da in aura mishi Fati ko ya samu tabarrakin da ke tattare da ita, Khalid bai isa aure ba. To ashe dukkan su rabon Sulaiman ne, haka Allah ya tsara. Ta zamo daga gadon ta russuna tana gai da Inna, ta kama hannun ta suka zauna a gefen gadon tare, ta ce, "Mun kwana lafiya Fatima?" Ta ce, "Lafiya kalau Inna, ya ya gajiyar ku?" Ta ce, "Gajiya ta bi lafiya Fatima, mu za mu wuce Bakori, sai kuma Allah ya hada mu cikin alherin sa". Idanun ta suka yi rau-rau kamar za ta yi kuka, Inna ta ce, "A'a, kada mu yi haka da ke, mun yi waya da Alti tana nan dawowa karshen wannan satin, ba za ki zauna cikin kadaici ba. Sannan ungo wannan".Ta mika mata kwalin karamar waya kirar Nokia, ta ce "A hade take da caji da komai har layi an sanya, jiya na aika Jibril mijin Ruma ya siyo, duk wata matsalar ki kada ki nemi kowa ki neme ni. Sannan kada ki ji shayin gaya min komai wai don ina uwar Sulaiman, dukkanin ku 'ya’yana ne, baki da wata damuwa?" Cikin nishin kukan da ke son ya balle ta ce, "Dama........dama ina so a karbo min Nana ne". Inna ta yi shiru kamar tana tunanin wani abu, can kuma ta ce, "Ki dai yi hakuri zuwa rana ‘i ta yau din, ko kin manta ke AMARYA ce? Ki huta kwana bakwai, ki kula da mijin ki. Rana ita yau za a kawo miki 'ya'yan ki dukkan su. Allah ya yi muku albarka kan biyayyar da ku kai mana, kuma ya sa 'ya'yan ku su yi muku fiye da ita. Kada ki yi wasa da GIRKI Fati, domin shi ne mafi saukin hanyar isa ga zuciyar miji. Na barku lafiya". "AMARYA! AMARYA!!" Fati ta maimaita kalmar Inna. Bayan fitar Innar. Sannan ta koma ta kwanta rub da ciki a kan katifar ta “I'm not a bride Inna (ni ba amarya ba ce Inna). Ita amarya cikin farin ciki take, cikin sa take kwana, cikin sa take wayar gari, cike da soyayyar mijinta. Amma ni yaya na kwana? Kwana na yi cikin suyar zuciya da tunanin 'yar uwata abar sona, wadda take min soyayyar da babu mai yi min ita a duniya, in ka cire iyayena. Bana kin sa shi yake kina, a kan laifin da ban sani ba. Ban san so ba balle in ce bana son sa. Amma ni meye laifina a kan auren da nima ba so nake ba? "Kulawar MATA yake nema…..". Ta tuno furucin karshe na Hadizah. To ga ni na zama matar tasa Yaya Hadiza, wace irin kulawa kike nufi in ba shi? He is old enough ya kula da kansa, wanka zan mishi ko pampers zan cire masa? Goyon shi zan yi ko feader zan ba shi? Ban san wacce irin kulawa kike nufi ba. Ta kai bayan hannu ta shafe hawayen ta, banda GIRKI kamar yadda Inna ta ce, in za a kashe ta ba ta san wata extra kulawa ta daban da mace ke yiwa miji ba. Sannan ba ta iya shisshigi da cusa kai a inda ba za ta yi kwarjini ba. Bayan tafiyar su Inna gidan sai ya yi shiru, babu sauran wani mahaluki in ka dauke Malam Ilu dake can bakin ‘gate’ yana gadi, an bar ta daga ita sai halinta. Ji ta yi kamar an kawo ta kabarin ta, ta yi kuka ta yi kuka har ta gode Allah. A karshe ta tattara komi ta mikawa Allah, ta jawo kular da Inna ta ajiye mata ta debi abinci tana ci. Ai ba ta tashi jin tsoro ba, sai da karfe tara na dare ya yi, Fati ba ta taba kwana a gidan da babu mutane ba, ta tabbatar ita kadai za ta kwana a wannan katon gida, don tuni ta san Dr. Sulaiman ya saba aikin kwana. Jikinta ya soma mazari kamar ana kada mata gangi, ta daddage ta takure a can karshen katifa ta kudundune cikin bargo tana dakacen ina ma ita ce ta tafi, Hadiza ta zauna, ko babu komai Hadiza ta fita bukatar rayuwar. Na farko tana aikin lada, ta hanyar ceton rayuwar mata ‘yan uwanta. Na biyu tana da 'ya'ya tana kula da tarbiyyar su da rayuwar su, na uku tana da mijin da ke son ta suke rayuwa cikin so da kaunar juna. To amma ita fa? Babu sidi babu sadada. Ba ta kai karshen tunanin ta ba ta ji karar fashewar tangaran a kitchen, wannan ya tabbatar mata ba ita kadai ce a gidan ba, to wane ne? Ta san dai ba maigidan bane, don shi in ya dawo karfe shida ba ya kara fita sai takwas, ba kuma zai dawo ba sai past ten sai dai in yana da aikin kwana. Ta ji dan tsoron ya ragu, ko ba komi tana da confidence na cewa akwai mutum cikin gidan ba ita kadai ba ce. Ta mike ta fito ta nufi kitchen, wanda ba ta zata ba shi din ta gani, ya tara hannu cikin famfon sink yana wanke jinin da ke bulbula daga hannun sa, ga kuma kwai yana ta kauri a kan cooker. Ta karasa da sauri ta sauke, ta kashe gass din. Ta dauki tsintsiyar laushi ta soma tattare fasashshen tangaran din, kafin ta farga ya fice a kitchen din yana ta disar da jini a kan tiles. A take ta hada wani kwan ta soya masa, ta juye a farantin tangaran ta debi ‘cake’ samosa da spring roll cikin firji ta dumama a microwave , ta tafasa ruwa nan da nan ta juye a karamin tea flask ta kwasa ta yo falo don ta bashi. Ya tada kai da karamin filo yana kwance a tsakiyar kilishi, sanye da fararen riga da wando na barci marasa nauyi, har yanzu dan yatsansa bulbular da jinni yake, amma bai damu ba, kamar ba jikinsa ba, ta zo gaban shi ta russuna ta aje mishi, sannan ta sanyaya murya ta ce, "I'm sorry!". Bai kalle ta ba, haka bai amsa ba kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta a gun ba. Kai bangaren data ke ma bai kalla ba. Ta mike za ta koma daki cike da tunanin hannun shi da ke ta kwararar da jini, amma matsayin shi na likita bai yi wani kokari ba ko yaya ne don dakatar da gudun jinin ba. Ta san da Hadiza tana nan Allah kadai ya san irin gigicewar da za ta yi, sannan za ta sa mishi magani ne ta daure, sannan ta yi ta jinyar ciwon har sai ya warke. Hakan ya taba faruwa da ya sharce babban dan yatsan sa garin ferar tuffaha, irin wannan kulawar kenan Hadiza ke nufi ta yiwa mijinta? Da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Aka ce wargi ma wuri shika samu; ko fuska babu, ba ta son tuno yadda ya yi da fuska kaman an aiko mishi da manzon mutuwa lokacin da ta shiga kitchen din. Ba ta kai ga shiga daki ba ya yi mata wata irin tsawa wadda ta gigita ta, ya ce, "Ke!" Ta juyo da sauri. Ya ce, "Zo ki batar min da wannan shirgin naki a nan, na ce da ke ina bukatar taimako ne?" Jiki na rawa ta dawo ta russuna za ta dauke, ya kama fatar kunnuwan ta da riko mai karfi, ta sa kuka don azaba. Ya ce, "Daga yau sai yau kada ki kara shiga shirgina, ko me za ki ji na yi kada ki zo inda nake, tunda ban neme ki ba. Na yi kama da saurayin ki ne? Be careful ni Yayanki ne, mijin Yayarki, Hadiza. Idan kin manta in tuna miki. Tun da kin yarda a kawo ki ki yi zaman 'ya'ya ki lalata kuruciyar ki a banza, to ki yi ta yi. Ranar da kika gaji, ki gaya min in maida ke gida, kina ji na?' Cikin kuka ta daga mishi kai, ya saki kunnen ta ya ce, "To kwashe su a nan tun ban yi ball dasu ba, kema in babballaki". (Yana nuna wa da hannayen shi irin yadda zai babballa ta din). Jikinta na kyarma ta kwashe ta yi kitchen dasu, ya ja tsaki "Tsuu…." A ranshi ya ce, "Kai! Inna da Malam sun takaice ni wallahi, me zan diba a jikin wannan fingi-fingin?" Ya yi ball da filon da yake kwance ya mike ya nufi (exercise area) din sa. Fati bata daddara ba, washegari tunda ta tashi da asuba ba ta koma ba, kitchen ta shiga ta shirya kalacin funkason alkama da miyar agushi. Wanda ta kwaba tun daren jiya. Ta kara da Quaker oat da plantain soyayya ta aza a ‘master dining’ din shi kamar yadda ta ga Hadiza na yi. Da gudu ta koma daki ta kulle, yana fitowa zai fita rike da ‘brief case’ ya yi tozali da sabbin warmers, sai kamshi ke tashi bisa dining din shi. Da gaske yunwa ta gallabe shi, hanjin cikinsa har rawa yake. Sai dai yana ganin idan ya ci ya zama sakarai tunda ga abin da ya ce da ita jiya, kuma raini zai gitta. Don haka ya hadiye azababbiyar yunwar shi ya fice. yana shiga AKTH ya nufi gun cin abincin manyan likitoci na asibitin, can ya yi kalacin sa. Sai dai a bakinsa babu dandano, don Hadiza ta riga ta sangarta shi da cimar Fati mai dadin da ba ya misaltuwa, ya kuma fi na Goggo Alti wadda a da yake ganin babu wadda ta kaita iya sarrafa abinci, musamman na Hausawa wanda ya fi kama mishi ciki kasancewar shi ma'abocin tara yunwa kafin ya yi quenching din ta. Da ta tabbatar ya fita, ta fito ta bude ma’adanan abincin, babu abin da aka taba. Bata ji haushi ba, ta tattara ta mikawa Malam Ilu bayan ta dibi iya wanda take ganin za ta iya ci, ta koma daki ta yi wanka sannan ta zauna cin abinci. Tana kammalawa wayarta da ta sa a caji ta yi kara, ta amsa cikin kamilalliyar muryar ta, Inna ce. Suka gaisa, sannan ta mikawa Malam Sulaiman shima suka gaisa. Ya yi mata addu’a sosai, ya kara da cewa, ta jure duk wani rashin jin dadi da za ta fuskanta daga mai sunan shi, nature (halittar shi) kenan, fara nuna kiyayya ga abu kamin ya so shi. Da yardar Allah watarana za ta tashi da riba. Ranta ya yi fari, zuciyarta ta yi haske, a kalla ta san ta samu surukai na gari da ke son ta. Ta kara jin karfin gwiwar son ci gaba da kyautatawa Sulaiman, ba don ya yabe ta ko ya so ta ba. Ita ma ba son na shi take yi ba, sai dai ba za ta iya yin watsi da al’amarin shi kamar yadda ya bukata ba, saboda alkawarin da ta daukar wa Hadiza, ta tabbata sakayyar ta na wurin Allah. Don haka ta mike ta nufi dakin shi don ganin ko akwai gyararrakin da za ta iya, cikin sa’a rufe kofar kawai ya yi amma bai sa key ba. Ta murda ta shiga cikin sallama duk da babu kowa, wannan tarbiyya ce mai kyau sabida mala’ikun rahma. Dakin babu kintsi, ko ina takardu baja-baja, gado a yamutse, kayan wanki a toilet fal cikin kwando. A jikin bed side ta yi tozali da ‘yar uwarta tana murmushi. Ta karasa ta dauki ‘frame’ din hoton tana shafawa a hankali tana murmushi itama, hawaye fal idanun ta. Ta maida shi mazaunin shi ta nade hannun riga ta soma gyara komai neatly, ta cire bed sheet ta canza wani. Ta kunna A.C don dakin ya yi sanyi. Ta koma toilet ta hau wankin da ya dauke ta har zuwa azahar, ta fito da kayan inda suke shanya ta shanya, ta wanke bandakin sosai da parazone, sai daukar ido yake, ta jawo kofofin ta fito ta soma aikin falo wanda babu datti sosai don su Inna sun tsaftace ko ina kamin su tafi. Zuwa la’asar kayan sun bushe, sai tashin kamshin Dr. Sulaiman suke kamar yanzu aka fesa turaren gidan (Chris Adams) ba’a sanya su a omo ba. Ta yi shimfida a falo ta soma goge su da dutsen guga, ta kammala cikin dan lokaci, ta je ta jera mishi a wardrove ta kunna burner ta turare dakin da bandakin da touch me, sannan ta fita ta koma dakinta ta yi wanka ta kwanta tana hutawa. Bai dawo gidan ba sai goma na dare, nan ya soma shakar daddadan kamshin amarcin da gidan ke yi, ya kara cin karo da sakon Fati a kan dining cikin wasu flasks din asu zabar kyau ba na dazu ba. “Wato yarinyar nan ba ta jin magana”. Ya fadi a zuci. Ya danna kai dakin shi, kamar ya sume don daddadan kamshin da dakin ke yi, da wata ni’ima ta musamman dake fita, wanda ya gauraye da rabar split mai sanyaya zuciya da kasalantar da gangar jiki. Ya bude wardrove don ya sauya kaya, nan ma ya cimma sakon Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Ya girgiza kai ya ce, “Na san maganin ki tunda baki da zuciya”. Washegari ma Fati ta kara yin kalacin kunun tsamiya dan leda, da poncake ta aza dining. Yau ma da ya gani wucewa yayi yana girgiza kai, cikin ransa yake fadin. “Lafiya ce ta yi miki yawa kike losing energy din ki a banza!”. ‘Surely’ yana bukatar abincin, amma girman sa da yake tattali a idanun ta ya hana shi. In ya ci girkin ta ashe tana da amfani cikin gidan kenan, shi kuma so yake ya nuna mata da ita da babu duk daya. Babu wani amfani da mace za ta yi masa tunda ya rasa wadda yake so, ya jure rashin Hadiza ma balle rashin cin abincin da yake so? Haka suke ta gangarawa har tsayin sati guda. Ranar lahadi yana gida, Mukhtar ya yi sallama ta hanyar danna kararrawa. Ya tashi daga kan computer ya je ya bude, Mukhtar Ja’afar ne rungume da Baby Nanah, Munib da Muniba na biye da shi, suka rangada da gudu suka rungume mahaifin su. Shi ma ya rungume su yana bin kowannen su da sumba, idon shi a lumshe. Suka karasa cikin falon shi da Mukhtar, Mukhtar ya mika mishi Nana, ya karbe ta ya rungume yana sunsunar ta. Sannan ya tsaya yana kallon ta, kamannin shi da ita har sun yi yawa. Suka yi musabiha da Mukhtar, yake gaya mishi Inna ce ta yi waya ta ce a kawo su wajen babar su. “Ina Fatin ne? Ko barci take?” Cikin dauriya ya ce, “Bari in duba”. Ta fito daga wanka ke nan tana rufe kofar bandaki, karamin towell ne ta daura daga kirji zuwa cinyoyin ta, kanta cikin hular wanka, tana jona hand dryer don busar da gashin kanta da ya jike. Ya turo kofar ya shigo, idanun shi suka yi kyakkyawan gani, shi kadai ya san abin da ya tsirga daga yatsar kafa zuwa zuciya da kwakwalwar sa, ashe model yarinya ce a cikin HIJABI? Kallon second biyu ya yi mata ya dauke kansa, sannan ya juya da sauri cikin kakkausar murya ya ce, “Mukhtar ke kiran ki”. Ta zubo doguwar rigar shadda ‘dark-bluesenegalese’ ta dora da matsakaicin hijabi, ta tadda su a falon. Ai kuwa su Munib suka yo tsalle suka yo kanta, har suna kokarin kada ita. Itama ta rungume su, suka soma jero mata tambayoyi. “Anti Fati, Mummy ba ta dawo ba har yanzu? Ina kika tafi muka daina ganin ki? Nana tana ta kuka idan bakya nan, don Allah kar ki kara tafiya ki barmu…..”. Ta ce, “Ba zan kara ba”. Ta kamo hannun Muniba, “Ba inda zan je muna tare kun ji my kids?” Suka yi murmushi sannan ta karasa ta russuna ta gai da Yayanta, wanda suke ta hirar su shi da Sulaiman, ta nufi firjin kitchen ta kawo mishi lemon (Donsimon) da gorar ruwan (Eva) mai rangwamen sanyi. Mukhtar bai dade ba ya yi musu sallama ya tafi. Bayan ya karbi lambar Fati. Tana so ta karbi Nana amma tana bisa cinyoyin sa, ta fara kuka don ta dade ba ta sha madara ba. Dole ya mika mata ita, hannuwan su suka saka kara gogewa dana juna. Wasu irin hannuwa gareta masu bala’in taushi kamar auduga, wadanda suka tada tsigogin jikinsa. Ita kuma suka haifar mata da kasala irin wadda ta ji a ranar da hannun ta ya fara shafar nasa. A hanzarce ya mike, “Oya kids! Muje mu sha (Ice-cream)”. Suka yi tsalle suka dane kafadun shi, Munib ya ce, “Amma har da Anti Fati za mu je?” Ya yi kamar bai ji shi ba, ita dai jakar kayan su ta dauka ta yi ciki da Nana a hannun ta. Ya sunkuci yaran shi duka biyun a kowanne hannu daya du girmansu, suka yi waje. Dama tana da tafasasshen ruwa cikin filas a kitchen, nan da nan ta dama madara ta soma baiwa Nana bayan ta sha iska. ****Kayan cefanen su sun kare, ba ta san ya za tai ta gaya mishi ba, saboda irin yadda yake bi ya daure fuska kamar wani soja idan ya ganta. Fati na mamakin wannan wace irin kiyayya ce Sulaiman yake mata ta babu gaira babu dalili? Kamar ita ce ta kashe Hadiza? Yana da wata kima a idon ta kasancewar shi wanda ya auri ‘yar uwarta da ba ta da ya ita a duniya, ya zauna da ita, ya rayu da ita cikin so da kauna da kyautatawa har ta koma ga mahaliccin ta, ba ta taba fadan laifin sa ko aibunsa ba, ko wani abu da ya yi mata na rashin dadi. Sannan da kasancewar shi Baban ‘ya’yan da take so sama da komi a duniya. Idan ba zai so ta ba ai ta ci albarkacin Hadiza. Amma yadda yake nunawa kamar ko a hanya basu taba hada wata alaka ba, idan ta biyewa wulakancin da yake mata ta ce za ta dinga bata ranta a banza, ita ce za ta cutu, ta dorawa kanta ciwon zuciya da hawan jinin da ko duba ta ba zai yi ba, balle ya rubuta mata magani. Don haka ta debe tsoro da shakku, bayan sun dawo yana kwance a falo yaran shi sun baibaye shi suna ta yi mishi tadi, shi kuma yana aiki cikin kwamfutar da ke bisa ruwan cikin sa. Ta lallabo ta fito uwa munafuka, tana goye da Nana ta rabe a gefe, Muniba ta taho ta zauna a cinyar ta. Sai a lokacin ya ankara da shigowar ta falon, ya juyo da sauri kamin ta yi magana ya mike, ya aje computer a fusace. Ta runtse ido tana jiran saukar mari a lallausan kumatun ta, ya ce, “Don’t I warned you? Idan ban neme ki ba ki daina zuwa inda nake?” Cikin makyarkyatar murya da gigicewa ta ce, “Ka yi hakuri, kayan cefane ne suka kare, sannan babu kayan abincin makarantar su Munib”. Ya yi tsaki “Tsuuu!” Kamar ya tsinke harshen sa, ya ce, “Na ji shikenan ko?” Ta mike a salube gwiwa babu karfi ta koma daki, don ita ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata tsawa. Su kansu yaran sun tsorata da tsawar da Baban su ya yiwa Antin su, sun yi zuru-zuru, suma ya nuna musu hanya ya ce su bita. Da gudu suka tafi har suna faduwa, ya kashe komai ya fice daga gidan. Washegari Alti ta dawo, ba karamin jin dadin dawowar ta Fati da yara suka yi ba, ko ba komai ta samu mai taimaka mata da debe mata kewa, don Goggo Alti mutum ce mai barkwanci da ban dariya. Sai ga Malam Ilu yana shigowa da kayan abinci nau’i-nau’i. Suka zaun ita da Alti suka gyara komai suka adana na adanawa a firij, suka markada na markadawa suka adana a ‘freezer’ Washegari ta tashi da wuri da taimakon Alti suka kammala komi da wuri, suka shirya yaran da abincin su, karfe bakwai da rabi Babansu ya kwashe su ya wuce dasu, sannan ya dangana ga ofishinsa. Kuma ranar ne su Yaya Haulatu kanwar Yaya da wasu daga aminan arzikin ta suka zo suka yi mata jeren kayan gado dai-dai karfin iyayen ta da dan uwanta Mukhtar. Falon ba ya bukatar komi, masu gidan sun riga sun tsara abin su dai-dai da rayuwar su ta masu murza tsinin biro, sai ba’a taba komi ba, iyakacin su dakinta. A kwanaki bakwai da Alti ta yi tare dasu, ta fahimci irin zaman kare da kyanwar da ake tsakanin Fati da maigidanta Dr. Sulaiman. A ranta ta ce, “Yarinya kyakkyawa kamar Hadiza, ga hankali da addini, ko meye nakasunta da Dr. Sulaiman ya kasa son ta?” Ta ce, “Ko da yake so ba’a nan yake ba, abune wanda ke faruwa kawai a duk sanda ya so, ga duk wanda ya so, cikin iko da kudurar Allah. A yau suna yankar alayyahu ita da Alti, domin yin miyar wainar masar dare. Suka jiyo motsin shi yana shigowa kitchen din, tuni Fati ta soma makyarkyatar jiki, kan ka ce meye wannan wuka kakkaifa ta shiga cikin naman hannun ta. Don ita ko gyaran muryar shi ta ji gigicewa take ta fita hayyacinta kada ya yi mata tsawar nan tashi mai dimauta ta. Jini ya soma bulbula a dai-dai lokacin da ya idasa shigowa kitchen din. Alti ta ce, “Ya salam! Kin gani kin yanke, na yi na yi ki daina amfani da wannan wukar kin ki, ta fiye kaifi da yawa, sannan gaki da saurin gigicewa”. Ya ji hankalinsa ya tashi ganin yadda jini ke gudu amma ba ta dago ba. Ta dukar da kai ko motsi ta ki yi. Ya basar Ya ce, “Babu sauran ruwan roba ne Baba Alti? Firjina babu komai, sannan ina jin kishi”. Ta mike zuwa store ta dauko mishi katon na FARO ta dawo, ta kama hannun Fati ta ce, “Babu kananzir balle in sanya miki, bari a daure da tsumma”. Ta tsaga zanin ta tana kokarin daure mata. Ya kalle ta a kaikaice ta kasan ido ya fita, zuciyar shi babu dadi, don ya tuno yadda ta nuna damuwa ranar da ya yanke nashi hannun. Mamaki ya kama Alti, ashe Baban Munib ba shi da kirki? Matarka ta yi irin wannan yanka amma ko kallo ba ta ishe ka ba? Tana daure mata Fati ta fara kuka yankar ta fi karfin daurewa da tsumma. Alti ta biyo shi, ba ya falon yana dakin sa. Ta tura Munib wanda ke ta wasan game cikin computer ta ce ya kirawo Baban shi. Jim kadan suka fito tare shi da Munib, yana rike da gorar ruwan yana sha. Cikin takaici ta ce, “Zan kai Fati asibiti ne”. Ya sunkuyar da kai duk jikin shi ya yi sanyi, ganin bacin rai kwance a fuskar tsohuwar da bai taba ganin bacin ran ta ba tsayin shekaru shida da suka yi tare da ita, ya dukar da kai sosai ya ce, “Bari in diba ciwon nata”. Ya koma daki ya dauko first aid box ya same su a kitchen din, jinin na ta zuba har yanzu. Sanye yake da brown getzner ta sha dinkin Mohammed wanda shi ne dinkin sa kawai, ya russuna dai-dai inda take sunkuye, ya kama hannun ta. Wani sanyi ya tsirga a zuciyar ta. Dago idon nan da za ta yi sai idanun su cikin na juna, wadannan kwayan idon na Sulaiman suka birkita ta, kamar yadda suke birkita zuciyar duk wata lafiyayyar macen da ta san cewa akwai tsokar zuciya a tare da ita. Amma ga shi Sulaiman, gani yai ta rikide mishi ta koma Dr. Hadizah…… “Wannan yankar sai an yi dinki”. Ya fadawa Alti. Cikin sanyin murya ta ce, “Ai shi ya sa na ce muje asibitin”. Ya ce, “Ba damuwa bari in dinke mata”. Ya fara da yi mata allurar ‘anaesthesia’, sannan ya fara dinkewa. Idanunta a rufe ba ta bude ba har ya gama. Bayan ya gama ci gaba ya yi da rike hannun bai saki ba, ita kuma ba ta sani ba cewa ya gama ko bai gama ba. Alti ta yi saurin fita ta bar kitchen din. Ya soma samun wani sassanyan sauyi a tare da shi, ya dinga hango rashin kyautatawar sa na tsanar jinin Hadiza da ba ta tsare mishi komai a rayuwa ba. Auren su da aka yi ya tabbata ita ma ba da son ranta a kai ba, soyayyar Hadiza da ta yi mishi yawa, ita tasa yake kin kowacce mace. Ita kuwa Fati ba zai ce ga dalili ba. Ya danganta hakan da rashin haduwar jini kawai, ina ruwan shi da tsarin rayuwar ta? Tunda ba a goshi zai lika ta ba? Ya soma kokarin goge muguwar kiyayyar da yake yi mata ta hanyar baiwa zuciyar shi uzuri iri daban-daban ga duk muguwar hujjar da ta kawo. Sai dai muhimmin abin da iyayensu suka hada wato AURE da mu’amalan auratayya, baya jin zai taba iya yin shi da wadda ta zamo kanwa ga Hadiza. Duk da ba haramun bane shi kam ya haramtawa kansa, an halicce shi kadai don Hadiza, kuma har ya koma inda Hadiza take ba zai kara mallakawa wata diya mace soyayyar shi ba, babu gurbin da zai iya jogana son wata. Sai dai shi kansa yana mai kalubalantar tunanin sa na cewa zai iya dauwama a haka ba tare da mace ba, kasancewar ta wani bangare na rayuwar dan adam, da kuma ganin tun ba a je ko ina ba ya fara kwana cikin halin ha’ula’i. Dole ya dau matakin da zai kawo karshen duk wannan, wato ya yi nisa da Fati, tun YAKANAR ta, kyautatawar ta, hakurin ta da juriyar ta basu ciwo galabar tattaurar zuciyar sa ba. Jin ya yi shiru ba ya dinkin kuma bai saki hannun ta ba, Fati tayi saurin bude idon ta, suka yi ido hudu da Sulaiman dan Sulaiman da Inna Halima. Ashe haka Baban Munib yake da kyau? Ban taba sani ba? Fati ta ce a zuciyarta. “Ina ma a ce yanda yake da kyan nan haka zuciyar shi take da kyau?”. Zuciyar ta kara tambayarta. Ta samu kanta cikin wani sabon yanayi da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba. A wannan daren mai dimbin tarihi a rayuwar kowannen su, daga Fati har Sulaiman babu wanda ya runtsa, soyayyar junan su ke neman samun muhalli a zuciyar kowannen su. Amma sun sa kafa suna fatali da ita da gan-gan, don a ganin kowannen su bai dace ba. Sannan ita Fati ta riga ta yiwa Dr. Sulaiman mummunar fassara zuwa na makiyinta, mai nuna mata kiyayya karara, kiyayyar da babu wani mahaluki da ya taba nuna mata a rayuwar ta. Don haka a kan me za ta so shi in ban da sharrin zuciya, don haka take ta ciccijewa, ita lallai karya zuciyar ta take yi ba son shi take yi ba. Shi kuma a can nashi bangaren, Sulaiman, ya kasa sukuni, ya kasa runtsawa ne a dalilin abubuwa da dama na yarinyar a yau da suka fizge shi. Ga dai kamannin Hadiza, sannan ga wasu (extraordinary qualities) da ya lura dasu a dan zaman watannin da ya yi tare da yarinyar. Don haka ya kwana cikin yiwa kai da zuciya hisabi, don tantance al’amarin da ke shirin faruwa da shi a kan Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Sakamakon ba mai saukin fadi bane a gare shi, halayen ta da yakanar ta da juriyar ta wajen yin abubuwan ta don Allah ba don ya yabe ta ko ta burge shi ba, sun taimaka kwarai wajen sayo mata soyayyar dole, wanda ke nufin Fati ta yi nasara kenan a kansa? Shi kuma ya fadi game din da suke bugawa. (He is the loser, and she is the winner! Idan ya yi sake hakan ya bayyana gare ta shikenan za ta raina shi, GIRMA YA FADI! Ya manta cewa a magana ta aure babu raini tsakanin mace da mijinta. To amma ina zai kai jin kan? Na tunanin kankanuwar yarinyar da yake rainawa ta yi winning a kansa? Don haka tunanin sa na ya yi nisa da Fati, don gudun RAINI ya kara kamari a tare da shi. A kwanakin da suka biyo baya, duk hanyar da ya san za ta hada shi da Fati a gidan yana kauce mata. Ita ma Fatin hakan, tun daga ranar da ta yanke hannu, ga shi har ciwo ya kame. **** Basu Kano ba su Abuja shi da wasu daga cikin likitoci ‘yan uwansa, suna fafutukar ‘visa’ zuwa jami’ar Chicago domin halartar wani kwas na shekaru biyu a kan dashen zuciya (heart transplantation) da ‘federal government’ ta tura su. Ko Inna ba ta sani ba, sai da ya gama dukkan shirye-shiryen sa, shi lallai dole yana yaki ne da zama da Fati kada soyayyarta ta rinjaye shi, shi ya sanya ya sanya kanshi cikin ‘yan tafiyar, don da babu yadda shugaban su bai yi ba ya shiga cikin tawagar amma ya ce a’a, duk da matukar bukatar shi da kwas din da asibitin ke yi, don haka da ya zo da kansa ya ce zai tafi, ba karamin jin dadi shugaban su ya yi ba. Suka fara shirye-shirye, har zuwa yau da Allah ya nufa suka kammala, sai tafiya kwanaki uku masu zuwa. Ya cimma su ita da Alti a kicin don su nan ne ofishin su, suna ta suyar dambun nama. Ya hada giran nan sama da kasa lokacin da idanuwansa su kai arba da na Fati, ita ma ta hade tai murtuk kamar ta ga mala’ikan daukar ranta, wannan gigicewar da take yi in ta gan shi yau ba ta yi ba, sakamakon jimawa da ta yi ba ta sanya shi a idon ta ba. A can wani gefe daga karkashin zuciyar ta, wani sanyi ne ya sauka a zuciyar ta wanda ba ta san dalilin shi ba. Hakika ta azabtu da rashin ganinsa a dan tsakanin, saboda yadda ganin sa ya zame mata SANYIN IDANIYA, yake gusar da duk wani bacin ranta, yake rage mata zugin rashin ‘yar uwarta da ke cin zuciyar ta, duk da rashin alherinsa gare ta kuwa. Babu ko tantama ta fada a ‘soyayya,’ a inda take da yakinin cewa ba za a taba son ta ba, in haka ne zuciyar ta ta gingimo mata babban aikin da ba ta san ya za ta yi da shi ba. Yana duban sashin da Fati take kasa-kasa ya gaida Alti, sannan ya dauke kanshi a sashin Fatin, ganin yadda ta yi murtuk da fuska. Ya yi murmushi ya ce da Alti, “Ku yi shiri zan je in watsa ruwa mu wuce Bakori yanzun nan”. Alti ta ce, “Allah ya sa lafiya?” Ya yi murmushi ya ce, “Lafiya kalau Goggo Alti, yara sun kwana biyu basu ga Inna ba, suna ta tambaya ta”. Ta ce, “To bari mu yi sauri mu karasa”. Taso ta ce da shi, “Har da Fati?” Ta ga wannan ba abin da ya shafe ta bane sun fi kusa, wai harshe da hakori. Ita ma Fatin da ba a ce da ita ba kawai sai ta hau shiri, domin tana son ganin Inna ainun. Ta zuba Abaya kirar Kuwait, ta kawo katon hijabin ta har gwiwa ta zuba. Bayan ta shirya yaran dukkanin su, ta fi son ta goya Nana, maimakon ta yi ta rike ta a hannu ko a kafada. Har Sulaiman kan yi mamaki ya ce a ransa, ita wannan ba ta gajiya da goyo ne? Duk sanda zai ganta goye da Nana zai ganta. An ce mai da wawa, kulawar da take yiwa ‘ya’yan shi ya taka rawa ba kadan ba, wajen sayo mata soyayya ta kwarai a zuciyar shi. Kafin wani dan lokaci sun kimtsa tsaf suna falo suna jiran shi, ya fito cikin wagambari shudiya mai hasken sararin samaniya, wato navy blue, hannun shi na hagu daure da agogon RADO na bakar fata, haka takalmin da ke kafar shi wanda ya kasance budadde na fatar damisa. Babu gilashi a idon shi sai fararen idanun shi ke sheki da daddadan kamshin ‘Chris Adams’ da ya baibaye su. Yaran suka nufi jikin shi, ya kama hannun kowannen su suka nufi harabar adana motoci, ita kuma ta koma kitchen ta juye dambun naman da suka yi gaba daya ta taho da shi don ta kai wa Inna. A wajen shiga mota ne ake dirama, yana son ganin in da za ta zaba don zama don son sanin matsayin da ta aje shi, tunda ‘yar gaisuwar da ta ke mishi ma a darare ta hakura ta daina, tunda baya amsawa. Ta bude gidan gaba su Munib suka shiga, sannan ta sunto goyon ta shiga baya ita da Alti. Har suka hau titin Kabuga babu wanda ya yi magana, sai yaran da ke ta rigima a tsakanin su a kan jirgin sama mai batir na Munib da Muniba ta dage sai ta amsa. Ita dai Alti shiru ta yi tana nazarin su, ga dukkan alamu kowannen su ya sauya, ya yi sanyi, amma an rasa wanda zai sauke ya bi dan uwansa. Tana son ganin wanene zai yi jarumtakar tsaga billensa ya bi dan uwansa? Wadannan ma’aurata suna ba ta dariya, ganin har ta cikin mudubi satar kallon juna suke, amma in daya ya kama daya sai a yi maza a fuske, a dauke fuska, wato babu shiri babu alaka. Tafiya ta yi nisa a kan kwalta, barci ya fara daukar Alti, yaran tuni sun yi barci har Nana, ya mika hannu ya rage musu karfin na’urar sanyaya mota. Kawai Sulaiman ya faka motar a tsakiyar daji, ya wani irin juyo ya dube ta, an yi sa’a ita ma a lokacin ta dago daga madara da take bai wa Nana, idanunsu cikin na juna, wani miracle ya yi aiki cikin ‘yan dakikai, ya haifar da wani al’amari mai GIRMA a zuciyoyin su. Ji yake kamar yana yi mata kallon karshe ne, ya tuhumi kanshi da rashin sauke wani nauyi mai girma da Allah ya ce ya yi, ga shi har zai tafi, tafiyar da babu tabbacin zai dawo ko ba zai dawo ba, tunda rayuwar ba a hannunmu take ba. Ya samu kansa da son tausasa mata, ko babu komi yana son goge mugun tabon da ta yi mishi a zuciyar ta. Ya tabbata idan Inna ta san har zuwa yanzu bai kula ta ba, la shakka za ta dauki mataki, duk da ya san da wuya Fatin ta gaya mata, tunda ba ta da magana. Amma in Inna ba ta sani ba ai Allah ya sani, kuma ba zai kyale ba. Ya mika mata hannu, “Kawo ta in taya ki rainon”. Ta galla mishi harara, sannan ta kara kankame ‘yarta. Ya yi murmushi ya ce, “Ko ‘yar gaisuwar da kike min kin daina, why Fati?” Wannan karon ma ba ta yi mishi magana ba, amma ta tsuke baki ta juyar da kai. Ya yarfar da hannu, “Tunda kin ki mu yi hirar bari mu karasa gaban Inna, watakila ita za ki yi mata bayanin dalilin ki na daina gaishe ni a matsayina na mijin ki da kuke kwana gida daya ku wayi gari cikin gida daya, zan gaya mata ‘ya’yan ki kawai kika sani, amma ni kin daina shiga sabgata, kin mai dani saniyar ware, dan gyaran dakin da ake min tun daga ranar da kika yanke hannu kin daina. Haka nan zan iya tunawa cewa, tun daga ranar ne kika daina gaishe ni”. Nan ma shiru, kamar da dutse yake magana. Haushi ya ishe shi ya fizgi motar. Bai kara tsayawa ba sai a kofar gidan su cikin garin Bakori. Malam Sulaiman na alwala a kofar gida lokacin da suka isa, ya soma maraba da ‘yan jikokin shi. Suka dunguma suka shiga gidan tare, Inna na sallah lokacin da suka shiga falon ta, sai da ta idar ta shafa addu’a, sannan ne ta karvi Nana a hanun Fati, tana yi musu sannu da zuwa. Alti tana daga waje, yaran ma Khalid ya shigo sun bishi shagon sa, falon ya rage daga Inna sai Malam, Fati da Dr. Sulaiman, hira ce suke sosai a junan su, ba ta tsoma musu baki ba. Can anjima ya dubi sashen da take ya yi mata wani irin kallo da ya sanyaya gangar jikinta, ya ce, “Na kawo karar Fati Inna, ta daina gaishe ni, ga shi ban san laifin da na yi mata ba, na tambaye ta ta yi min banza”. Kunya ta kama ta, ta mike za ta fita Inna na ganin yadda ya bita da kyawawan idanun shi kamar ya fasa kuka, ta yiwa Allah godiya cikin zuciyar ta, ta tabbata Sulaiman ya fara son matarsa, addu’ar da ta ke kwana da yini tana yi ba ta fadi a banza ba. Ta ce da Fati, “Koma ki zauna”. Ba musu ta koma ta zauna, amma ba ta kara hada ido da kowa ba, ji take dama kasar ta tsage ta shige saboda kunyar da Baban Munib ya bata. Inna ta ce, “Wai haka Fatima?” Malam kuma ya ce, “A’ah! Fatima ba za ta yi haka ba haka kawai, kai dai ka san laifin da ka yi mata”. Bai yi magana ba. Inna ta ce, “Me ya yi miki Fati? Na san ba shi da kirki”. Da kyar ta ce, “Ni bai yi min komai ba, bana ganin sa ne”. Inna ta ce, “Koma ya yi, ki yi hakuri kin ji Fati, komi na duniyar dan hakuri ne da yafiya (afuwa), kowa hakuri yake da abokin zaman sa, ta hakan ne za a ci ribar zama amma ba ta kullaci da rashin afuwa ba”. Sai ta ga kamar Inna ta shiga zuciyar ta, da gaske ta kullaci Dr. Sulaiman kullata mai yawa a kan abin da yake yi mata, duk da ta fahimci shi ma ya sakko yana son a shirya, amma ba za ta yarda a shiryan haka (so easy) ba. Ya kuntata mata, ya cuzguna mata yadda harshenta bazai iya bayyanawa ba. Wanda tun farko ya riga ya ce ba ya son ka, daga baya ya dawo ya ce yana son ka akwai dalilin shi na yin hakan. Change happens only on reasons. Amma ba za ta iya yin musu da Inna ba, don haka ta ce, “Na yi hakuri Inna. Shima Allah ya huci zuciyarsa”Tana ganin sanda sulaiman ya saki wata boyayyar ajiyar zuciya. Inna ta ce, “To Allah ya yi muku albarka”. Ya gyara zamansa cikin nutsuwa yace, “Inna dama na zo in yi muku sallama ne….”. Cikin mamaki ita da Malam suka hada baki suka ce, “Zuwa ina?” Fati kuwa zuciyar ta ce ta buga, irin bugun da ba ta taba yi ba. Ya soma yi musu bayanin course din da aka zabe su su goma shi da abokan aikinsa na shekaru biyu a cikin jami’ar Chicago din Amurka.` “Amma tare za ku tafi da iyalinka bakidaya ko?” Malam ya tambaya. Ya ce a ransa, “An yi ba’a yi ba kenan! Fatin yake gudu, Fati yake son tserewa, Fatin yake so yayi nisa da ita, Fatin yake son yiwa kandagarki daga son kutsowa cikin rayuwarsa da karfin gaske, bai shiryawa hakan ba, bai taba mafarkin kasancewar hakan ba, kada ta rushe masa plan din rayuwa, in ya dauke ta suka tafi me aka yi ke nan? Bonono rufe kofar da barawo? Duk da shi ma ya soma kalubalantar kansa da ganin wautar sa na tsallake abinda rai da zuciya suka soma so da gangan, wai don kada GIRMA YA FADI!”. Ya ce, “A’a, za su zauna ita da Alti saboda yara suna zuwa makaranta”. Malam ya ce, “Kun yi shawara ne ta yarda za ta zauna?” Bai iya karya ba, kai tsaye ya ce, “A’a, bamu yi zancen ba”. Ya ce, “To sai ku yi shawara a tsakanin ku can, in ta yarda za ta zauna din shikenan, mu ‘yan sanya albarka ne”. Ba su taho ba sai yamma lis, kamin su iso gida har an yi kiran isha’i, kasancewar duk a koshe suke, Inna ta cika musu ciki da dambun shinkafar ta mai dadi, basu shiga kicin ba kowacce ta nemi makwancin ta, yaran ma sun nabba’a a dakin su, shi kuma ya juya asibiti. Fati tana shiga daki ta kwanta rub da ciki, da filo a karkashin ta cikin wani mawuyacin hali na soyayyar Baban Munib da ke cin zuciyarta. Ta kai hannu ta dafe kirjin ta wanda ke bugawa da-sauri-da-sauri da haruffan SU-LAI-MAN a kowacce dakika, zai tafi ya barta, bayan ya gama da farauto zuciyarta, ya kimsa mata soyayyar da ba ta san iyakacin ta a zuciyar ta ba. Ya warware duk wata nutsuwa da tunanin da ke tare da ita, ya mamaye 80% na zuciyarta. Ya haifar da wasu al’amura masu girma a gare ta da ba ta san ya ya za ta yi dasu ba. Jin tafiyar shi take har ruhi da bargon jikinta, Fati tace wai maiyasa wasu mazajen suke haka ne? Idan sun san sun kimsa maka soyayyarsu, sai su nemi gudu su barka da jibgin abar ka? Wasu hawaye suka zubo, maimakon ta share sai ta tara hannu tana tarar saukar su a kan tafukan ta. Ba ta ji motsin bude kofa ba sai alamar zaman mutum a gefen ta, kafadunsu suka gogi na juna, ta yi hanzarin juyawa, Dr. Sulaiman ke kallon ta da murmushi. Ya sanya hannu cikin aljihun bakin jeans da ke jikinsa, ya zaro hankicin sa ya mika mata, ta jima ba ta karba ba, daga karshe ta karba ta share ambaliyar hawayen ta. Ya mika mata hannu alamar ta ba shi abinsa, sai ta kalle shi sannan ta sunkuyar da kai ba tareda ta bashi ba. Ya ce, “Bani mana? Ko kukan bai kare bane?” Ta tsuke fuska, ta tsuke baki, ta hade girar sama da ta kasa. Ya yi murmushi ya sa hannu cikin hannunta ya dauke hankicin sa, kadan ya rage ta sume da hucin sassanyan numfashin sa ya doki fuskar ta, kamshin jikin sa na fizgar ta, da wata itin fizga mai karfi, kamin ta farfado daga shidewar da ta yi na wucin gadi ya fice a dakin. Zuwa can kuma ya dawo da takardu a hannun sa, sai dai wannan karon ya janye murmushin da ke kan fuskar shi, ya zauna dab da ita cikin kakkausar murya ya ce, “Me ya sa ki kuka?” Shiru ta yi masa ba ta amsa ba, zuciyarta na ci gaba da azalzala da azabar soyayya, wadda ke linkuwa a bayan kowacce dakika. Jikinta ya soma rawa, tana son cewa ya tashi ya ba ta waje ta samu iska amma ta kasa. Kallon ta yake yana (observing) da ido, da zuciya. Gaba daya yanayin ta ya sauya, ya nuna wata mace da ke azabtuwa da soyayya da sha’awar mijinta mai yawa. Amma kawaici da kau da kai ya rinjayi komi, ya tabbata idan ya tafi ya bar ta cikin wannan halin, Allah ba zai yafe mishi ba, amma tunanin Hadiza ya danne komi. Tattalin girmansa da mutuncinsa a idanun yarinyar ba zai bar shi ya aiwatar da abinda zuciyoyin su da gangar jikin su ke so ba, idanun shi a juye yake kallon ta, gangar jikin shi babu inda bai kaduwa. Ya soma kokarin saisaita kansa, in azabar soyayya ce ai ya fita dandana, ba tun yau ba. Ya janyo brief case ya fiddo daurin kudi masu tudu ‘yan awolawo ya ajiye a gefen ta, sannan ya mika mata form din JAMB Online. Ta dan ware ido tana kallon sa da alamar jin dadin hakan sosai a kwayan idanun ta, ya kawar da fuskar shi gefe ya ce, “Zan bude maku account da skyeBank in Allah ya kai mu gobe, in na wajen ki sun kare kuna da bukata sai ku je ku diba. Akwai sabon direba na aje muku duk inda kuke son zuwa ki kira shi a waya ki gaya masa, ni zan tafi jibi insha Allahu sai Allah ya nufe mu da dawowa. To amma Fati, ba zan samu ko da kalmar Allah kiyaye hanya ba, daga Fatin da ba zan kara gani ba, sai bayan wasu shekaru har guda biyu?” Hawayen ya kara zubo mata, ta yi saurin sharewa da bayan hannun ta. Ya tsura mata ido analytically, can kuma ya ce, “Girl, ina so in san damuwar ki….., Akalla ko ban yi miki maganin ta ba, ina da shekarun da zan ba ki shawara a kanta. Ta bangare na dai duk hanyar da nasan zan bi in gyara kuskure na nabi, amma kin ki bani hadin kai I do not your thoughts. Not even a single word from you, you are indeed a nice person! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi!!” Ta yi hanzarin dagowa ta dube shi, kallon ta yake ta cikin kwayar idon shi, da wani lallausar murmushi makale a gefen bakin shi. “Gaya min mene ne damuwar ki Fatima?” A hankali ta ce, “Babu”. “Ba kya bukatar komai?” Nan ma ta ce, “Eh, Allah ya kai ku lafiya!”. Ya ji dadin addu’ar da ta yi mishi, sai dai ba irin wannan rabuwar yake so su yi ba, ta rashin dadin zuciya. Ta ki sakin jiki dashi ko yaya ne. Ya kama tafin hannun ta ya rike cikin nashi, “Ba za ki gaya min abin da ke sanya ki kukan ba?” Ta ce a ranta, “Za ka yi min magani ne?” Magana ta yi a zuci, ba ta san ta fito, ta shiga kunnuwan sa ba. “Idan ina da shi me zai hana in yi miki?” Ta ce, “Bani da damuwa, ba sai mutum yana da damuwa yake yin kuka ba, wani zubin mutum yana yin kukan, don ya ji dadin ransa”. Ya yi murmushi a kaikaice ya lakaci kuncin ta da dan alinsa, وتتاىاMu kwana lafiya, amma ina rokon ki duk wasu inconveniences ki yafe min su!!!”. Ta lumshe ido kafin ta ce, “Babu wani inconvenience game da kai a tare dani, kada ka manta ka ce ni kanwar ka ce. Idan Yaya Mukhtar ya yi min laifi zan kullace shi ne, ko zan kasa yafe mishi?” Ya yi kirr! Da ido yana duban ta da wani irin sassanyan kallo. Kalmar “Yayan” sai yau bata yi mishi dadi ba kamar ba shi ya jaddada ta ba. Tattausar muryar ta da nutsuwar ta na burge shi har bai son a daina hirar, ita kuma so take a gama, saboda yadda yake kara ruruta wutar son shi a zuciyarta Nana ta yi motsi za ta soma kuka, dukkan su suka juya gare ta, suka mika hannu a tare don su dauke ta, nata hannun ya riga sauka a kan Nana, don haka nashin sai ya sauka a kan nata. Dukkan su babu wanda bai ji a jikin shi ba. Ta yi saurin sakar mishi Babyn, ta dunkule hannun ta. Ya dauke ta ya kai kafadun shi ya mike tsaye yana safa da marwa da ita a dakin don ta koma barci, ya kasa fita a dakin Fati, mai wani irin sihirtaccen kamshi da ba zai ce na kowanne turaren wuta ne ba, haka nan gauraye da rabar A.C mai kwantar da hankali. Dakinta ko tsinke babu saboda masifar tsafta. Bai ki ba su kwana a hakan, yana jin sassanyan sautin ta mai motsa zuciya, ta yi mata rahma ko da ba da son ran mutum ba. Ya kwantar da Nana cikin dan gadon ta dake kan gadon Fati, ya mika mata hannun daman shi, cikin sigar son a yi hannu ya ce, “Can we be friends apart from Yayan?” Murmushi ta yi, ta sarke hannuwan ta a baya, “A’a, ai ka ce ni kanwar ka ce wadda take zaman lalata kuruciya........”. Daga yadda take furta maganar za ka karanci (bitterness) wato dacin da maganar ta yi mata a kan harshen ta da zuciyarta. Ya ce a ransa, “Baki shi ke yanka wuya….”. Yana da tabo mai yawa a zuciyar yarinyar, wanda ke dakusar da karfin soyayyar sa da ta soma shigar ta. Dole ya wanke kanshi, domin karfi da yaj Fati na neman zamowa wani bangare na zuciyar sa cikin dan kankanin lokaci. Ya ce, “Mun yi magana a kan ALL the inconveniences, not SOME of the inconveniences, kin ce kin yafe su, amma why kike maida hannun agogo baya?” Sai ta yi murmushi, ita ma ta mika mishi tattausan hannun daman ta, suka sarke su cikin na juna. Kowanne siririyar fatar bakin shi dauke da murmushi. Dai-dai lokacin da suka ji kiran sallar asubahi a cikin kunnuwan su, a sannan ne suka mike domin haramar sallah cike da mamakin tsayin lokacin da suka bata suna hirar zuciya da zuciya (heart to heart talk). Washegari ma bai samu zama ba, suna ta zirga-zirga a airport na booking jirgin tashin su. Bai dawo ba sai dare, lokacin kafatanin mutanen gidan sun yi barci. Bai nemi kowa ba shi ma ya ci abincin da suka aje masa ya yi wanka ya shirya ya kwanta, amma tunanin Fati ya hana zuciyar shi sukuni, yana so ya san halin da take ciki, yana so ya sake jin sassanyar muryarta da ke yi mishi yawo a kwanya, yana so ya sake jin taushin hannun ta, yana so....... yana so…... Kai yana son komi nata! She is indeed a blessing cikin gidansa da rayuwarsa…. She is also a DARLING (abar so) farin cikin kowanne da namijin da ya san ciwon kansa. Amma ba za a gane hakan ba farat daya, sai wanda ya yi zama da ita na tsayin lokaci ya nazarce ta, amma a fuska za a fassara ta da mutum mara son magana, kidahuma mai takurawa rayuwarta. Sai an fahimce ta a hankali za a fuskanci halitta ce, wato nature. Ya so ya je gare ta a wannan daren da ya zamo na karshe da zai dade bai ganta ba, su raya shi da hira ta fahimta kamar yadda suka raya shi jiya. Wata zuciyar ta ce, “A kul! Kama girman ka ka rike tsam-tsam kada ta ga weakness din ka”. To kamun girman har yaushe ne? Shi ma ya tambayi zuciyar tasa. Tunda dai ba za a dauwama a haka ba, kuma ba zai taba sakin Fati ko ya yi mata kishiya ba, don bai da ra’ayin zama da mace sama da guda daya. In haka ne dole watarana za’a aje girman a gefe a ranar da Allah ya nufa. Shin ko yaushe ce wannan ranar? Bai sani ba! Fati ta riga ta kama zuciyar shi fiye da yadda biro zai iya rubutawa. Tana shirya masa kalaci a dining ya fito, cikin shirin tafiya, duk ta yi sanyi ta zama cool. Kodayake dama haka halittar ta take, amma na yau na daban ne, komai cikin sanyi take yin sa, amma na yau ya fi na kullum. Ya tokare hannun shi jikin kofar dakin shi, dayan na zube cikin aljihu, ya langabar da kai yana kallon ta. Jikinta ne ya ba ta ana kallon ta, don haka ta dago kai ta dube shi, sai ta yi murmushi ta sunkuyar da kanta, “…Morning friend Fatima!!” Ya fada. Tare da miko mata hannu, tana murmushi ta mika masa nata. Ji take kamar in ya tafi shikenan ba za ta kara ganin shi ba. Daga gaisuwar bai cika ta ba ya janyo ta a hankali ya rungume ta, ya sumbaci goshinta sannan ya cika ta. Ta lumshe ido a hankali tana daidaita tunanin ta. Wani abu na zarya a dukkan ilahirin jikinta. Ya iso ga tebir ta karaso da sauri ta yi serving din sa, ya kama kasan hijabinta ya cire ya ajiye a kan daya daga cikin kujerun, ya ce, “A dinga ajiye shi a cikin gida, don a sha iska”. Wata muhimmiyar kunya ta kama ta, saboda ‘yan kananan kayan da ke jikinta. Kukan Nana ne ya cece ta daga kaifafan idon Sulaiman, don haka ta garzaya shi kuma ya fara cin abincin kamar bai taba cin abinci mai dadi irin shi ba. Har karfe goma ya kasa fita, yana tare da ‘ya’yan shi da Nana a cinyar shi suna ta bashi sautun abin da zai sayo musu yana murmushi yana rubutawa. Abokan tafiyar shi sun yi waya har sun gaji, yana cewa, “I am coming….. (gani nan)”. Sai da Dr. Khalil ya biyo bayan shi sannan ya mike, ya mika wa Fati Nana wadda kanta ke sunkuye. Ya dago habarta da hannun sa, ta lumshe ido sai hawaye ya balle. Ba sai ta fada ba ya san ko na mene ne, Fati ta kamu da ciwon da shi ma yake fama da shi, amma kawaici da alkunyar ta ya sa take boyewa. Yatsun shi biyu ya sa yana goge mata hawayen, kararrawar da Dr. Khalil ke dannawa ta sa dole ya amshi brief case din shi a hannun ta. Da sassarfa ya juya ba tare da ya kara waiwayowa ba, da sanyin ido ta bishi har ya fice a falon. Nana da ke hannun ta na ta kuka amma ba ta san tana yi ba, yara na ta yi mata magana, suma ba ta ji me suke cewa ba, ta tafi cikin duniyar kewa, shauki, bege da soyayya…… mai wuyar fassarawa. Idan wannan ita ce soyayya da Sulaiman ya dandana ta Hadiza, sai ba ta ga laifin shi ba na wulakanta ta a farko, don ba ta jin in ita ce ya mutu a yanzu za ta yarda ta kara yin wani aure a rayuwar ta, ko zata kara son wani, kwatankwacin wannan son na Sulaiman da take ji a zuciyarta, ruhi da bargon jikinta. Ta kara tausaya mishi kwarai game da yadda ya jure da rashin Hadiza. Idan haka rabuwa da masoyi yake, tana addu’ar Allah ya sa ita ma ya so ta ko da rabin-rabin yadda yake son Hadiza ne”. **** BAYAN TAFIYAR SULAIMAN Rayuwa ta yi zafi ga Fati, komi na yanayin rayuwarta ya sauya, ta zama calm mai yin komi cikin kokari, juriya, karfin zuciya da dauriya. Soyayyar mijinta ta hana ta sukuni, hatta ‘ya’yanta sun san Auntyn su ta sauya, ta rage zama da su, ta rage walwala, sai dai Nana kullum tana jikinta. Ta sakar ma Alti ragamar komi na gidan, ta fiya kwanciya tsakiyar gado, rigingine da Nana a kan ruwan cikinta. Ta rasa walwala da kazarniyar ta, komi ya fice mata a rai, mijinta kawai take so, wanda kuma ya yi mata nisan da ba za ta kamo shi a nan kusa ba. Ita Alti sai ta yi zaton ciki ne, don haka take bata kulawa ta musamman. Misali da yake ta rage cin abincin gidan, sai lemu da ruwa, sai take tambayar ta ko da wani abu da kike marmari in yi miki? A lokuta da dama cewa take babu, in kuma akwai sai ta fada mata. A daddafe ta zana jarrabawar JAMB. Ba jimawa ta sake samun admission inda za ta karanci fannin da take so, wato Islamic Studies. Idan direban yara ya kai su da motar da Dr. Sulaiman ya bar musu, sai itama ya sauke ta a makaranta. Kullum cikin zumbulelen hijabin ta har kasa, Alti kan zauna a kofar aji ta rike mata Nana, ko su zauna masallacin Ramat su jira ta ta fito lacca. Karatun na taimakawa dari bisa dari wajen debe mata kewa da rage mata tunanin Dr. Sulaiman din da take zaton zuwa lokacin ya manta da ita. Don har yau da ya cika watanni biyar da tafiya, ko sau daya bai kira ta ba. Kai tana jin ma ba shi da nomba din ta. Duk sanda suka yi waya da Inna tana tambayar ta lafiyar ta da ta ‘yan jikokin ta, ba ta yin zancen Sulaiman, tana so ta tambayi Inna ko yana yi musu waya, tana kuma tsoron kada su yana yi musu ita ce ba ya nema, Inna ta yi mishi magana ya ce ta kai karar shi. Don haka ta ci gaba da jurewa ba ta yiwa Inna zancen ba. Shekarar farko ta kare cike da dimbin nasarori a gare ta, domin duk jarrabawar da ta zana ba ta faduwa. Ta kare shekarar da maki mai daraja. Nana ta yi bul tana gudun ta ko ina, ba ta taba sanin ba Fati ce mahaifiyar ta ba. Ta shiga 200 level cike da karfin gwiwa, tun Alti na zuba idon ganin ciki ya bullo mata har ta gaji ta gane ba ciki bane. A yau da suka tashi Karkasara suka wuce domin duba jikin Baban su da bai ji dadi ba. Yaya ta ji dadin ganin su, fes dasu cikin koshin lafiya, wanda ke nuni da cewa babu abin da suka nema suka rasa. Dr. Sulaiman ya tsaya musu a kan komi. Alti na tsakar gida, ita da Yaya suna daki suna hira irin ta da da mahaifi, ta ce, “Dazun nan nake ce da Sulaiman kun kwana biyu baku zo ba, ya ce karatu ne ya yi miki zafi ashe kuna tafe”. Mamaki da haushi suka kama ta, wato yana kiran kowa har ‘ya’yan shi yana kira a makaranta ofishin malaman su su yi hira ya ji lafiyar su, ita ce dai ba ya kira don har yanzu yana kin ta, don rannan Munib yake gaya mata wai Daddy yana gaishe ta. Ta ce, “A ina ka ganshi?” Ya ce, “Waya muka yi a school”. Sannan ga shi yau Yaya ma ta ce yana yi musu waya. Duk inda ranta yake in ya yi dubu to ya baci, har Yaya ta lura kamar ta yi shiru tana tunani. Ta ce, “Lafiya ko?” Ta yi saurin girgiza kai, “Babu komi”. A dakin Baban su bayan sun gaisa, ta tambaye shi jiki ya ce ya ji sauki alhamdulillahi. Sannan ya ce, “Fati har gobe ba zan daina sanya miki albarka ba, saboda yadda ki kai mana biyayya kika zauna lafiya a dakin mijin ki, duk da na san ba da son ranki aka yi auren nan ba. Biyayyar ki da YAKANAH…. ni na gaya miki ba za su tashi a banza ba! Allah ya baki ‘ya’yan da za su yi miki biyayya fiye da yadda ki kai mana”. Idanun ta suka cicciko, kamar ta gaya mishi cewa har yanzu Sulaiman ba ya son ta, da yana son ta da ya damu da lafiyar ta. Amma ko ya take tsayin shekara guda bai taba cewa ba. Idan kuma ta yi tunanin sauyikan da ta gani a tare da shi kafin ya tafi, sai ta samu kanta cikin rudu a kan al’amuran Dr. Sulaiman, ta kasa tantance cewa yanzun yana son ta ko ba ya son ta? “You are darling! Duk wanda ya zauna da ke na lokaci kankani, zai so ci gaba da zama da ke muddin rayuwar shi”. Ta tuno kalaman shi ana i gobe zai tafi. Gaba daya maganganun da suka yi a ranar take tunawa filla-filla, wadanda in aka auna su a ma’auni na hankali da tunani suna nufin Dr. Sulaiman ya sauya muguwar fahimta da akidar shi a kanta. To amma why yake kin neman ta a waya ko common gaisuwa ce su yi? Me hakan ke nufi? Babu wanda zai amsa mata tambayoyin ta sai shi. To ina za ta gan shi? Ta MAIRON HURE da ta ce, “He is far away.....’ (Ya yi nisa). **** Da la’asar sakaliya suka yi shiri suka nufi Bakori dukkannin su, za su yiwa Inna week end (hutun karshen sati). Direba Malam Habu ne ke jan su, zuwa karfe shida na yamma suna cikin garin Bakori. An yi sa’a Saude, Ruma da Anti Ramatu kannen Sulaiman duk suna gidan sun je biki sun dawo suka zarto wajen Inna. Don haka falon Inna yau ya yi albarka, ya kauraye da hira. Ita dai Fati ba ta magana illa in anyi abin dariya ta yi murmushi, suna son yarinyar sosai saboda sanyin ranta. Anti Ramatu da yake sarkin barkwanci ce, ta ce, “Fati sai yaushe za mu zo suna ne? Mun kosa fa Nana ta samu kani ko kanwa”. Kunya ta kama ta, musamman da yake Inna tana wurin. Ta rufe fuska da mayafinta, haka suka yi ta tsokanar ta su lallai suna jiran baby da Yayansu ya dawo. Wayar Inna ta yi kidi tana neman agaji, Inna ta amsa cikin nutsuwa don ta gane lambar ta Sulaiman ce. Bayan sun gaisa ya ce, “Hirarrakin me nake ta ji haka?” Ta ce, “Su Ruma mana, sun sanya Fati gaba duk sun hanata sukuni, gasu nan sun zo dukkannin su baka ga yadda Nana ta yi wayo ba”. Ya lumshe ido yana sauraron Inna, amma bai ce ta ba shi Fati ba sai ‘ya’yansa. Sun dade suna ta shirmen su kamar ba kudi suke narkarwa ba, har gwalantun Nana an sanya mishi ya ji, sannan suka shiga gaisawa da kannen shi. Ya ce, “Ina Khalid?” Inna ta ce ya je Malumfashi ta aike shi wajen Inna Atika kanwar ta. Cike da kewa ya yi sallama da su, ya koma ya kwanta ya ta da kai da hannayen shi a rest chair irin kujerar nan da turawa ke sakawa da zaren roba da katako. Ya mika hannu ga zungureriyar robar coca-cola ya daga, ya tashi zaune yana daddaka. Sanyin lemon da karfin ‘gass’ din shi na soya mishi makoshi, amma bai kula ba. Ga wanda duk ya san Dr. Sulaiman-Sulaiman a da, lokacin Hadiza, ya kuma gan shi a yanzu, to ba zai gane shi ba. Gaba daya ya rame, ya kara yin duhu, sai dai hakan bai boye zahirin kyawun halittar sa ba. Ba abin da ya sa gaba sai abin da ya kawo shi, sai dai hakan bai sa tunanin yarinyar ya barshi ya huta ko na second daya ba, kamar yadda ya yi tsammanin nisa da ita shi ne hanya mafi sauki da zai yaki kutsowar soyayyarta. Ashe hakan tamkar zubawa wuta fetur ne? Tunanin sa na cewa yin nisa da Fati shi ne babban makamin yaki da farmakin data kawowa rayuwarsa ashe ba shi ne maslaha ba. Abinda bai sani ba sai bayan tahowarsa Fati ta riga ta yiwa zuciyar shi kamun kazar kuku, ta yadda dai-dai da rana daya tun tahowar sa zuciyar sa ba ta taba hutawa ko na dakika da tunanin ta ba. Dr. Smith ya iske shi a hakan, ya dade yana magana bai san yana yi ba. Kafin dan lokaci ciwon ciki ya turnike shi, ya kama cikin ya soma juyi, sai ya fado bisa kilishin dake shimfide a farfajiyar wajen. Da sauri Dr. Smith baturen Chicago ne na asali, ya kama shi ya soma binciken abin da ke damun shi, tare da ba shi taimakon gaggawar duk da ya dace. Bai samu kansa ba sai bayan awanni biyu, lokacin ciwon cikin ya lafa. Ya sa ido yana kallon Dr. Smith wanda ke shan lemo a gefen shi, shi ma kallon shi yake amma bai fasa shan lemon sa ba. Ya mike zaune a hankali suna kallon-kallo. Dr. Smith ya dauke kansa ya ce, “A lokuta da dama bakar fata ku kan birge ni wajen rike amanar matan ku, mazanku da matan ku, da wuya daya ya ci amanar daya a cikin aure. Wannan dabi’a ce mai kyau, in ka san ba za ka iya zina ba, me ya hanaka tahowa da matar auren ka? Sai ka zauna kana tara abu har sai ya kashe ka a banza?” Ya aje tambulan din hannunsa ya dubi Dr. Sulaiman sosai, ya ce, “Don me baka taho da matarka ba, alhalin gidan da aka baka yalwatacce ne? Sannan dai-dai gwargwado ba za ka kasa rike ta a nan ba. Tun wancan karon na gaya maka abinnan yana barazanar kwantar da kai, wanda in ka ci gaba da tara shi zuwa wani lokaci sai anyi maka aiki. Duk me ya yi zafi? Ka aika matar ka ta zo, mene ne wahala a ciki?” A sanyaye ya ce da shi, “Hadizah ta rasu!” Dr. Smith ya ce, “Oh dear! Tun yaushe ne?” Ya rausayar da kai ya ce, “For almost a year and a half kenan”. Smith ya ce, “Why not ka kara yin wani auren Dr. Sulaiman?” Ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, har Smith ya kara maimaitawa. Ya dago idanun shi da suka shagide ya dube shi. “Ina da wata matar Smith”. “To me ya sa baka taho da ita ba?” Ya yi murmushi ya ce, “Ba zan iya bane, saboda kanwar mata ta ce, auren hadin iyaye aka yi mana”. “Which means….. baka son ta….?” “Ko ina son ta ba zan iya hada jiki da ita ba! Idan na yi hakan GIRMA NA ZAI FADI A IDANUN TA. Ka gane, ina tattalin mutunci na ne, duk da Hadiza da kanta hakan take so kamin ta rasu, wato ‘yar uwarta ta maye gurbin ta, amma ni ba zan iya ba!” Smith ya ce, “Wannan shirme ne, baka da hujja kwakkwara. Idan har kana son matarka ka aje girman kan nan ka daidaita da ita, domin kana zalintar ta. Kana zalintar kanka. Dubi yadda kake suffering (wahala) baka tunanin ita ma haka take, sai dai ta nuna kawaici? In kuma baka son ta ne ka sahile mata ka ba wa iyayen ku hakuri, ba za ta rasa mai son ta ba, kai ma ba za ka rasa samun wadda za ka so ba.......” Ya yi saurin katse shi da cewa, “Babu saki tsakani na da Fati, har abada, babu. Ko bana son ta balle halayen ta da nagartar ta sun sayo mata soyayya mai yawa a gare ni. Hujjar nan dai da na gaya maka ita ce, wato tana ganin girmana bana so ta raina ni, bana so GIRMA NA YA FADI a idanun ta”. Abin ma sai ya baiwa Smith dariya, ya murmusa ya ce, “Babu zancen raini a harkar aure, ka yarda dani Dr. Sulaiman, ka daidaita da matarka don samun lafiyar ka da nutsuwar dukkanin ku, sannan da albarkatun da ke cikin aure. Poor Fati! Na tausaya mata, aure kusan shekara biyu ba ta san albarkar da ke cikin shi ba. Wallahi ka yi a hankali, tun hakki bai kama ka ba”. Da maganganun Dr. Smith ya kwana, yana cizawa yana busawa. Ta yaya zai doshi Fati da bukatar aure? Gaskiyar Hadiza ne he is not taking things easy (ba ya daukar abubuwa da sauki). Fati yarinya ce mai hankali da zuzzurfan sani a addini, mawuyaci ne ta raina shi don ya gyara rayuwar auren su. Ya juya a hankali ya rungume filo, ya samu kanshi da flashing no Fati, cikin shekara daya da rabi da ya yi bai taba kiran ta ba, don ko abin ya ciyo shi ya dauko wayar zai neme ta fasawa yake yi. Yau dai ya tabbatarwa kanshi Fati ta ci kwallon, ta yi winning a kansa, ta kayar dashi warwas, duk da tana kidahumar ta. Kenan a so mutum, soyayya ta gaskiya ba ya nufin a nuna tsiraici, ko abubuwa na jan hankali. Halin mutum shi ne jarinsa, ‘yammata sai ayi hattara! **** T ana kwance a gadon bonon Inna, lokacin da wasu lambobi rankacau suka shigo cikin wayar ta. Ba a jima ba sako ya shigo. “Ni na san ni mai laifi ne, amm ina neman afuwar ki kamar kullum. Fati, zan samu?” Ta maimaita sakon ya fi sau hamsin, babu wanda ta sani a kasar waje sai mijinta Dr. Sulaiman. Ta mike ta yi sujjada ga Allah da ya karkato mata da zuciyar abin sonta, cikin addu’o’in da take kwana da yini tana yi. Amma ba ta ba shi amsa ba, don ta dade da sanin shi hawainiya ne canza kala yake yi. Tana tsoron kar ta kara sakin jiki da shi ya zo ya sake guje mata kamar baya, bayan ta sakankance da shi ta amshi ban hakurin sa da soyayyar sa. Tun yana sauraron amsa har ya koma ya jingina da balcony na harabar flat din shi. Ya kira wayar har ta gaji ta tsinke ba ta daga ba. Ya san Fati ta yi fushi! Haba!! Ai ko shi ne, shekara guda da rabi ba kwana guda da rabi ba. Sai dai ya san sanyin halinta, da wuya su yi arba ya ba ta hakuri ba ta hakura ba. Hankalin sa ya tashi sosai, “Wallahi ka yi a hankali tun hakki bai kama ka ba”. Ya tuno kalaman Smith, kirista ma kenan, balle shi da yake a cikin musuluncin sa. Inna na tuyar masa, Fati na wankin kayan Nana a jikin famfo, sanye take da riga da zani na atamfa (super) ruwan ganye. Ta makala dan karamin hijabi iya kafadun ta. Babu wani make up a fuskarta, sai tsabar kyawun halittar tsurar sa. Nana na gefe ta yi fes cikin fararen suwaita da (mini skirt) kanta ya sha ribbons da rufaffen takalmi da socks a kafarta, tana ta wasa da Saddika ‘yar Anti Ramatu. Khalid ya soma shigowa da wasu firda-firdan jakunkuna, can kuma sai wani kamshi da ta dade da sani na turaren ‘Chris Adams’ ya bakunci hancinta, kamin ta gama tantance abin da ke faruwa ta jiyo ‘husky’ muryar Dr. na Hadiza suna gaisawa da Malam a soro. Ranta ya yi fari, duk wani kunci da ke cikin zuciyar ta sai ya yaye, ta tabbata ya kasa hakuri ne da yin biris din da ta yi da shi, shi ne ya taho, ba zato ba tsammani. Ba ta fasa aikinta ba amma kar ki so ki tona zuciyar ta, da soyayya ta yiwa illa mai yawa. Ji ta yi kamar an dauke numfashinta, tana shirin faduwa a gindin famfon, ta yi sauri ta kama kan famfon, harshen ta na addu’ar neman nutsuwa daga rabbil izzati. Karasowa ya yi gindin famfon ya yi tsuguno a gaban ta, ya leka fuskar ta yana murmushi. Ta gan shi ya yi kyau, amma ya rame, fatar shi ta kara taushin gani a ido, ya zama cool kamar ba shi ba. Ta yiwa Allah tazbihin kasancewar ta matar Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori, domin ba ba kowadanne maza ne irin Sulaiman ba, ko da ba ya son ta ai ya damu da ita, tunda fushin ta ya tunkudo shi har inda take. Ya mika hannu ya dauki Nana yana sumbatar ta, fuskarta babu fara’a ta ce mashi, “Sannu da zuwa”. Hararar ta ya yi, “Bana son sannun ki, rike abin ki”. Inna ta fito daga cikin kitchen bakinta ya kasa rufo, suka wuce dakin ta yana dauke da Nana wadda ke ta kukan ya sauke ta don ba ta san shi baMunib da Muniba suka shigo, sai suka tsaya saroro suna kallon sa, sannan suka tafi da gudu suka rungume shi suka soma zubo masa hira. Inna ta kawo mishi waina da taushe ta ji tantakwashi da lemukan zobo da na Aya da ta ke siyarwa cikin firjin da ya saya mata. Fati ba ta shigo ba, tana gama wankinta ta shanya ta dau mayafinta jikin igiya ta gudu makota gidan wata makociyar Inna Goggo mai gyada. Ba ta shigo gidan ba sai bayan azahar, lokacin shi da Malam suna kofar gida suna sallah da mutane. Ta zaga ta bayan su ta shiga gidan ta shige uwar dakin Inna. Ya dawo dakin Inna suna hira, shiru-shiru bai ga Fati ba. Ya ce, “Wai yarinyar nan Inna gudu na take yi?’ Ta ce, “Ni ina na sanar muku, ai kun fi kusa”. Ya ce, “Tana ina ne?” Ta nuna mishi uwar dakin ta da dan alinta, ita kuma ta fita don ta dora sanwar dare. Tana jin shi zai shigo ta yi linkim a gadon Inna, ita a dole barci take. Ya karaso ya zauna a saitin kanta yana kallon kyakkyawar fuskarta ta dan hasken tagar Inna da ya ratso, babu wadatar haske a dakin don haka ya fiddo wayar shi yana haskata sosai. Ta soma rikide mashi tana komawa Hadiza! Kanshi ya dinga zagayawa jiri ya soma diban shi, a lokacin da ya soma romancing din ta da fuskar Hadizahh……... Ta yi wani irin juyi ita a dole barci take, kamin wani dan lokaci al’amura suka rikice musu, tun tana pretending har al’amarin yafi karfin kawaicinta da juriyar ta. Jin maganar Inna a falo ya sa ta daddage ta kwaci kanta, jikinta babu inda ba ya rawa saboda firgici da sabon al’amarin da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba. Idanun shi a galabaice ya ce, “Haba Hadizah! Don Allah Hadizahh.....!!” Wani haushi ya kama Fati, karona farko a rayuwarta da kishin Hadiza ya darsu a ranta, wato ma da sunan Hadiza yake alakanta ta, sannan ne zai iya auratayya da ita? Za ta fita ya cafke hannun ta, ta wani irin juyo tana hararar sa. Wai an ce aikin banza, harara a duhu. Don kuwa bai gani ba. Shi ma ya juyo kukan Nana da maganar Inna, don haka ya yi saurin sakin hannun ta, ta fita amma shi bai fito a lokacin ba, sai da ya daidaita kansa tukunna. Sai dai fa shaddar Ghanilla baka wul duk ta yamutse. Yana tsaye a falon Alti ta shigo suka gaisa, ya ce, “Goggo Alti sai ku shirya tafiya zamu yi”. Ta ce, “To ranka ya dade”. Fati ta kwakkwabe fuska ta ce, “Nifa Inna sai gobe zan tafi”. Inna ta ce, “A’a, ga mijin ki ya zo tun daga wata uwa duniya ai wurin ki ya zo, yana bukatar kulawar ki, tashi ku tafi idan ya koma sai ku dawo, mu kullum muna maraba daku”. Ba da son ranta ba ta tattara kayan su suka tafi. Wannan karon ma a baya ta zauna ita da Alti, duk yaran har Nana suna gaba. A ranshi ya ce, “Tunda na rasa Hadiza ai ba abin da ba zan gani ba, ga shi na zama direban Fati ina ji ina gani…..”. Har suka isa gida babu wanda ya ce da dan uwansa uffan, don babu fuska a wurin Fati, fushi take sosai kan biris din da ya yi da ita tsayin shekara guda da doriya. Sai shi da Munib suke ta hirar su, Alti na mamakin wadannan ma’aurata da ba ta san yaushe za su saduda su san Annabi ya faku ba. Ba ta san kuma laifin na wane ne a tsakanin su ba. Suna zuwa gida ta dauko makullin dakin sa ta shiga ta soma gyara, duk da dama a gyare yake, domin duk bayan sati biyu take shiga ta share ta gyara ta wanke toilet. Shi kuma da ya ajiye su fita ya yi, bai dawo ba sai karfe goma na dare. Ya yi wanka ya yi excercise ya zuba pajamas da turaren shi na kullum, amma a yau sai ya samu kansa da karawa da ‘Boss-Intense’, ya cakuda da ‘far away’. Sannan ya kara da ‘Gio-Gio Armani….’ Ango sosai. Mai ji da koshin lafiya da kuruciya, wanda Allah yayiwa duk wata ni’ima ta rayuwa. Ya tadda Fati a dakinta, ita ma lokacin ta yi wanka tana busar da gashin ta da hand dryer, cikin wasu tausasan nighties, masu shara-shara, ya kashe dirayar ya ajiye a gefe, cikin kunnuwan ta yake rada mata. “…..Ki yi hakuri mana Fati…..don Allah ba don ni ba”. Ta ce, “Da aka yi me fa?” Ya ce, “Rashin kiran ki a waya, ba haka kawai bane ina da hujjoji na”. Cikin raunin murya ta ce, “Kana da hujja sosai, hujjar baka damu dani ba, kana kiran kowa ban da ni, ba sai ka yi haka zan san cewa baka so na ba, lika maka ni aka yi. Tuni na kwana da sanin wannan......” Hawaye suka balle mata. Ya juyo ta da sauri suka fuskanci juna, sanyin numfashin su na dukan fuskar kowannen su. Ya ce, “Ni na ce da ke bana son ki?” “Baka fada ba amma ka nuna mini, ka nunawa zuciyata. Tunda har ka iya ka yi shekara baka nemi jin lafiya ta ba, saboda ni kadai ka tsana a duniya, a kan laifin da ban sani ba”. Ya yi murmushi sosai ya ce, “Dole sai ta bakin ki zan ji lafiyar ki? Ina ji a bakunan da ba za su yi min karya ba. Maganar lika min ke aka yi, sai in ce MADALLAH da wadanda suka lika min ke, yaa ke ma’abociyar YAKANAH!. Domin na hadu da alhairori da yawa a tare da auren ki. Ki yi min afuwa Fatima kamar kullum, ban san ki da kullaci ba, saboda ke na jingine komi dake gabana na zo, kada ki sagar min da gwiwa, saboda in gyara zaman mu, in gyara kurakurai na. Na tabbata Hadiza ta tafi; She is my past…... and you are my present.....!!!” Haka ya ci gaba da kalallame ta da kalami masu dadi, har ya samu ya karbi abin nan mai matukar daraja daga gare ta. Ya rungume ta tsantsan yana fadi a ranshi, “Yaya, (Sa’adatu) ta haifi ‘ya’yan baiwa”. Albarka da addu’a, hadi da godiya mara iyaka Fati ta samu daga Dr. Saiman har ta gode Allah. A bisa yanayin daya risketa. Idan aka ce mata wani abu mai kama da MAFARKI to wannan ranar ce. Ranar da bata taba mafarkin gani cikin mafarkanta ba. It’s a dream that comes true. Bata jin akwai wani sauran buri da ya rage mata a rayuwa bayan na cikawa da imani da dorewar wannan ‘indescribable moment’ har karshen rayuwarta. **** Kwanaki biyar din nan da yayi bai zuwa ko’ina sai barzar amarci, har Fati ta saba, duk da tana matukar cin kwakwa, tana galabaita matuka da wannan sabuwar rayuwa data samu kanta. To abin ne an tara shi fal, tsawon shekaru biyu ba kadan. Albarka kam tana shan ta, ya soma tunanin yadda zai iya komawa ya bar Fati, saboda yadda ta zamo wani bangare na gangar jikinsa, zuciyar sa da ruhin sa gabadaya, ga shi suna tsaka da karatu balle ya yi mata visa in ya so yaran a kai su wajen Yaya. A gobe ne zai tashi zuwa Lagos, daga nan ya bi jirgi mai zuwa Chicago. Fati tana hada mishi kaya, duk jikinta ya yi sanyi saboda mugun sabon da suka yi cikin kwanaki shidda kacal, sannan ga wata iri kewa na cin zuciyarta mai wuyar bayyanawa. Ya fito daga wanka yana tsane kanshi da karamin tawul, jin kansa yake wani sabo, fresh, kamar yanzu aka bare shi a leda. Tunda ya samu ya sauke al’amuran da suka takurawa zuciyar shi da lafiyar shi. Inda zai iya maida Fati ciki, da watakila ya yi hakan ya sanya ta cikin ya gudu da ita. Abin alfahari ce ga duk namijin da Allah ya baiwa, ya gode Allah da bai bi son zuciyar shi ya bijirewa iyayen shi ba. Ya tabbata da tuni yazo yana nadama. Nadama mara amfani kuwa. Ta mika mishi wasu kayan barci ‘yan Indonesia marassa nauyi, ta ci gaba da hada sauran. Ashe hawaye take zubarwa shi bai sani ba, ya sanya kayan barcin, ya zauna a gabanta ya janye jakar kayan da ta ke hadawa, ya kamo dukkan hannuwanta biyu ya rike cikin nashi. “Haba Fati! Ai sai ki karya min gwiwa, ku yi shiri ke da Nana ku raka ni har Lagos, sai in sanyo ku a jirgi ku dawo. In kin yi kuka ke da kike da ababen debe kewa (‘ya’ya) ni kuma in yi ya ya? Kamar yau ne za ki ga na je na dawo, mai da hawayen nan maza-maza bana son ganin su”. Ta ja shessheka tana kokarin mai da hawayen, daga nan kuma aka koma aikin lada, mai gigitarwa. Karo na farko da Fati ta taka matattakalar jirgi a rayuwarta. A Lagos sun jima suna tsimayen lokacin tashin jirgi me zuwa Chicago, yana ta tausar ta da kalami masu dadi kamar ba Dr. Sulaiman ba, da cewa; ta kula da kanta, karatunta, da ‘ya’yanta. Suna daga mishi hannu ita da Nana ya bi matattakalar jirgin da sauri, ba tareda waiwaye ba, ya tabbata zai yi kewar su. Karfe biyu na rana nasu jirgin (Bell-View) ya dawo dasu gida (Kano). Malam Habu ya debe su a Airport. Tun tana damuwa da rashin Sulaiman har ta saba, ta sanyawa ranta salama, musamman kuma da yake duk dare suna tare a waya, ta maida hankali kan karatun ta da rainon ‘ya’yan ta. Shekara kwana ga mai yawan rai, Dr. Sulaiman-Sulaiman Bakori, ya gama course din shi cikin nasara da shi da sauran likitoci ‘yan uwansa. Aka yi mishi sauyin aiki da karin girma zuwa babban asibitin koyarwa na Abuja, a lokacin Fati na mataki na uku a jami’a, dauke da tsohon ciki na haihuwa yau ko gobe. Zuwa wannan lokacin Fati ta gama mallake komi na Sulaiman, da da’arta, halayen ta da addinin ta. Ita ce matar shi mafi kusanci da shi, sannan kawar shi abokiyar shawarar shi. A gefe abin so da kaunar shi. Iyayen na matukar alfahari da wannan aure da suka hada a bayan ran marigayiya Hadiza, wadda har gobe, jibi, har gata basu daina yi mata addu’a ba. Kuma tunaninta bai taba gushewa daga zuciyar kowannensu ba. Dr. Sulaiman yana Abuja, sai week end yake zuwa musu, sai ko in duk sun samu hutu suma su ke bin shi Abujan. Ranar wata litinin kwana daya da tafiyar Sulaiman nakuda ta kama Fati, suka nufi asibiti ita da Alti, yaran duk suna Karkasara. Kafin magariba ta haifi sankacecen danta mai kama da Baban shi har farcen kafa. Sai waya Dr. Surayyah ta yi mishi cewa baby ya iso. Sai ga shi a washegari kamar an jefo shi, ya tadda Fati da baby a ‘aminity’, sai dai dakin cike yake da ‘yan uwanta. Sai daga nesa yake jifanta da murmushin ‘bani da abin da zan gode miki’. Ita ma murmushin take masa da su kadai suka san ma’anar abin su. Ba da son ranshi ba Yaya ta wuce da ita gida inda za ta yi wanka, don Alti an aiko mata rasuwar danta a kauyen su Kukawa, don haka za ta tafi a washegari. Dakin ta na da Yaya ta gyara mata suke wankan, Munib dan kankanba ya kasa sukuni saboda ya yi kani namiji dan uwan sa. Bini-bini zai ce a ba shi ya dauke shi, ita kuma Fati ba ta gajiya da mika mishi shi. Kawarta Fa’iza ta zo mata barka wadda ita ma an yi auren ta tuni, suka wuni sur suna hirar bayan rabo, don Fati ta zamewa Fa’iza abin sha’awa ganin yadda ta yi kyau ta kara girma, yanda duk wanda ya dube ta duba daya zai tabbatar tana da kwanciyar hankali a gidanta. Sabanin ita da kishiya ta sa ta gaba, ta hana ta zaman lafiya. Fati na tausar ta tare da ba ta shawarwari na gari. Ranar suna yaro ya ci sunan Malam, wato Ja’afar. Malam ya roke su kar su boye mashi suna su kira shi da Jafarun shi. Juma’a yamma lis, Dr. Sulaiman ya iso Kano daga Abuja, kai tsaye gidan surukan sa ya fara dosa. Bayan motar shi dankare da himilin tsaraba, Yaya ta yi mishi shimfida da sabuwar tabarma, ta sunto baby da ke bayan ta ta mika mishi. A lokacin Fati ta fito daga bandaki, ta yi daurin kirji ta rufu da tawul, ta sha dukan ganye, jikin nan ya kara zama fresh, fatar nan ta kara zama mai taushin gani a ido. Ta kasan ido ya dube ta, sai ya ga duk ta canza mishi, ta kara zama yarinya danya sharaf. Da alama ba ta da damuwa, sun barshi da kadaici, sai fama yake da biro da takarda. Yaya ta shige kitchen ta barsu, ai kamar jira yake ta tashi ya yi ma dakin Fati tsinke. Tana tsane gashin kanta da tawul ya bude mata dukkan hannuwan sa bayan ya aje babyn a cikin katifar sa. Ta rufe ido tana dariya, shima ya san bazata iya ba, har a gobe halayenta na kawaici da alkunya basa canzawa, sai shi ne ya karaso ya rungume ta tsantsan a hankali, yana fada mata kalaman da suka zama sirri ne a tsakanin su tana ta sakin murmushi. Cikin ranta addu’a take Allah ya barta da SULAYMAN dinta, ya dorar da rayuwarsu cikin daukaka da soyayya, kamar yadda ta faro, har zuwa ranar da suka daina numfashi. *** *** SHEKARU GOMA SHA BIYAR A GABA! Taron rantsar da sabbin ministoci da mai girma shugaban kasa President Umaru Musa ‘Yar Aduwa zai gabatar a yau a hotel din NICON NOGA, har da babban likitan zuciya da kasarmu Najeriya ke tanka how da shi, wato Dr. Sulaiman Sulaiman Bakori, wanda aka rantsar a matsayin Ministan Lafiya na kasa baki daya. Ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Maris, na wannan shekarar. Dr. Fatima Ja’afar, H.O.D Islamic, a jami’ar Abuja, cikakkiyar mace ‘yar kimanin shekaru talatin da bakwai da haihuwa, uwar ‘ya’ya biyar a halin yanzu, in ka hada da manyan ‘ya’yan ta Munib, Muniba da Nana Khadija sun zama su takwas kenan. Tana sanye da bakar abaya kirar Bahrain da mayafinta, hannunsu sakale dana juna suka isa ga mazaunin su, daukacin Ministocin da ake shirin rantsar wa suna tare da matansu da rakiyar ‘ya’yansu, to haka suma, Muniba, Nana Khadija, da Ja’afar. Ya yin da suka baro Mufida, Mufid da Ibrahim da dan autan su Abdulhak a gida, cikin kulawaar tsohuwa Alti. Bayan mai girma shugaban kasa ya rantsar da Ministocinsa, aka zarce da gagarumar walima. Ba su baro dakin taron ba sai dare, suna kan hanyar isowa gida wayar Munib ta shigo, wanda ke can kasar ‘Srilanka’ yana karatun harhada magunguna. Munib Ya ce, “Daddy kun manta dani, ko waya an fi sati ba wanda ya yi min. Yanzu nake jin abin alheri a BBC, congratulations Daddy!” Ya ce, “Kwantar da hankalin ka Munib, zirga-zirga ta hana mu neman ka. Ina mai yi maka albishir da cewa, muna tafe dukkanin mu cikin satin nan, sai ka tanadar mana better”. Ya yi ihu ya ce, “Allah Daddy da gaske?” Fati ta amshe wayar ta ce, “Amma sai in point din ka na wannan semester ya kai CGPA 4.00, if not, babu wanda zai zo”. Ya ce, “Wallahi 4.60 ma na samu Mummy”. Ta ce, “Ah, lallai Babban Yaya ka gama min komai, zuwan kowa ya zama dole, tunda duk muna cikin hutu”. Ja’afar ya amshe wayar ya ci gaba da ba shi labarin duk shagulgulan da ake yi a yau. Munib ya ciji yatsa ya ce, “Ayya! Na yi missing….”. Daga nan sai Muniba, ita kuwa Nana ta ce, ba za ta yi magana da shi ba tunda baya yi mata waya sai budurwar sa kawarta Naina. Daddy ya harare ta ya ce, “Bana son sakarci, shi ba shi da wata budurwa dan makaranta ne”. Ta ce, “Amma yake yi mata waya yake yo mata tsaraba in zai zo?”. Ya ce, “Ba kanwar shi ba ce? Ke ba ya yi miki?” Ta ce, “Wallahi Daddy nata ya fi yawa, har da kati an rubuta I LUV YOU”. Fati ta tintsire da dariya, shi kuma Dr. Sulaiman sai ya rasa ta cewa, yaran zamani sai a barsu, da wayonsu ake haifar su. Ya dubi Fati da wani irin sassanyan kallo, “Momin yara, wai da gaske ne Munib yana da budurwa?” Ta rausayar da kai ta ce, “Shirmen Nana ne, Naina Bunza, tana da shiga ran kowa sosai ba Munib kadai ba, suna shiri da Munib sosai sabida kokarinta.”. (Diyar Dr. Surayyah). Ya ce, “Ba zan yi mamaki ba in son nata yake, ai jin kanshi yake matured (balagagge) kamar kowa”. Dariya ta kama Fati, sai da ta murmusa sosai. Sun isa gida yara kowanne ya kama harkar gabansa, ya cacumi Fati su kai sama ana biyan bashin soyayya, wadda hidimar kwana biyu ba ta bari ba. Suka ci gaba da amsa sakonnin taya murna da fatan alheri daga ‘yan uwa da abokan arziki, har tsayin sati daya. Ranar juma’a jirgin MEA International ya tashi dasu zuwa Srilanka, har filin jirgi Munib yaje ya taro su, ya dauki Abdulhaq ya rungume suka karasa zuwa makarantar su bayan sun yi booking din hotel din da za su sauka. Farin cikin Munib ba sai an fada ba, ya rasa inda zai sa iyayen shi da ‘yan uwan shi. Dr. Sulaiman ya yi bincike sosai kan karatun shi, ya yaba sosai da hazakar da yaron ke nunawa. Kwanan su uku suka wuce Saudiyyah suka yi Umarah, sannan suka dawo gida. Da albashinta da ta ke tari, da kuma taimakon Dr. Sulaiman, Dr. Fatima Ja’afar, ta bude makarantar Islamiyya ta yara maza da mata a nan Abuja, da aka sanyawa suna NANA HADIZAH ISLAMIYYAH. Haddar Alkur’ani mai girma ake yi tsantsa, sai sauran littattafan addini irin su Ishmawi, Bulugul Maram, Sirah, Hadith, Al-Akhdari, Fikh da koyar da harshen larabci. Ana zuwa daga karfe biyu na rana zuwa shida na yamma. Ba ta da abin da za ta ce da Dr. kuma Minista, Sulaiman dan Sulaiman, sai godiya da addu’ar alheri, domin ya gama cika mata burinta na son yada ilimin Alkur’ani da hadisi, kamar yadda ta ke buri. Ya lullube ta da duk wasu alhairori na rayuwa, ya lullube ta da so da kauna. Gaskiyar Babanta ne; Alqur’anin ta ba zai bari ta tozarta ba!!! Ta san Sulaiman ba ya son ta ya aure ta, kuma ba zai taba son wata diya mace kamar yadda ya so Hadiza ba, amma tana tantama a halin yanzu, idan son da yake mata baiyi kunnen doki da wanda ya yi wa Yayarta Dr. Hadiza ba. A alfarma ta soyayyah, ta san ba ta cancanci Dr. Sulaiman ya so ta a wancan lokacin ba, amma ya so ta saboda hakuri, juriyar ta da YAKANAR ta. Ya so ta sabida kyawawan halayenta. “Mene ne YAKANAH?” Nayi tattaki har gidan Dr. BAKORI na tambayi Malamarmu, Dr. Fatima Ja’afar Mai-Yadi. Ta yi murmushin ta mai motsa zuciya tace. “Takori ba ki san Yakanah ba?” Na ce, “Ina zan sani Fati? Sai ku malaman addini”. Ta yi murmushi ta ce, “Nima daliba ce SUMAYYAH! Sai dai in sanar da ke dan abin da na sani a dalibtaka ta”. Na ce, “daure ki sanar dani Aunty Fati, komi kankantar sa. Domin al’umma zasu so su san me ita wannan kalma ta YAKANAH take nufi?”. Faty ta yi murmushi tana dubana ; MECE CE YAKANAH??? Ita YAKANAH ba kasaifai ake ganin ta a wajen yawancin mutane ba, YAKANAH ita ce take daukaka darajar mai yin Ibadah, ta kai shi wani matsayi na daukaka a wajen Allah. YAKANAH ita ce tushen dukkanin aiyuka na gari, wato daukacin ayyukan kirki suna fitowa ne daga cikin ta. Mutum mai YAKANAH shi ne mai yin babban jihadi ko gwagwarmaya da kansa wajen watsi da abubuwan da rai da zuciya ke so, saboda neman yardar Ubangiji, da neman dadin falalar sa, tare da nuna biyayya a gare shi. An ambaci irin wadannan mutane a cikin Alkur’ani mai girma, kamar cikin suratul Al-Imran (3:17) Al-Nisa’i (4:25, 127-128), Fussilati (41:34) da sauran su. Irin wannan babban jihadi da kai ana yin sa ne tsakanin mutum da zuciyar sa (Nafs Al-Ammara), domin sauya ta ya zuwa (Nafs Al-Lawwama), sannan ya zuwa zuciya madaukakiya (Nafs Al-Mutma’innah). Saboda haka madallah da ita wannan baiwa ta YAKANAH, domin tana kai masu yin Ibadah zuwa ga matakin shiga cikin rukunin salihai wadanda a koyaushe suna masu yin godiya a kan dukkanin abin da ya zo musu daga Allah. YAKANAH it ce kololiyar taqwa wato tsoron Allah. Takwah kuma ita ce mai kore tsoron haduwa da Allah (wanda ba ya jin kunyar ubangijinsa kuma mai sabon sa, shi ne mai zama cikin fargabar haduwa da Allah). Daya daga cikin ma’anar YAKANAH ita ce, ka dinga kallon kanka a matsayin kai ba kowa bane a cikin jama’a, kuma kowa ya fi ka, saboda haka YAKANAH tana nuni da rashin kasancewar mutum cikin halin GIRMAN KAI! Misalai: Idan ka kasance mutum ne kai mai YAKANAH ta gaske, a duk lokacin da ka gamu da wani mutum wanda baka san shi ba, komi lalacewar sa, sai ka ce da kanka a cikin zuciyar ka. “Watakila matsayin wannan mutum a wajen Allah ya fi nawa”. Idan kuwa ka gamu da yaro kankani, sai ka cewa kanka, “Ka ga wanda ba ya sabon Allah, ni kuwa ina yi”. Idan kuwa ka gamu da wanda ya girme ka, sai ka ce, “Ka ga wanda ya jima yana bautar Ubangiji tuntuni kafin ni”. Idan kuwa ka yi kicibus da mutum mai dimbin ilimi, sai ka ce, “Ga wanda aka yiwa baiwa da abin da ni bani da shi, domin ya fi ni ilimi, kuma yana aiki da ilimin sa, amma ni ko ya ya dai?” Idan kuwa ka yi karo da jahili, sai ka ce, “Dubi wani yana sabon Allah cikin rashin sani, ni kuma ina yi cikin sani. Ga shi kuma ban san yanda karshen sa zai kasance ba, kuma ban san nawa karshen ba. Ko me zai zama a nan gaba? Allah shi ya fi kowa sani”. Idan kuwa ka gamu da kafiri, sai ka ce da kanka, “Wa ya sani? Watakila nan gaba ya musulunta kafin ya mutu, kuma wa ya sani ko ni kuma in mutu a kafirce?” Ire-iren wadannan maganganun gaba daya suna nuni da halin mutumin da YAKANAH da tawali’u suka baibaye shi, yake kuma cikin hali na binciken kansa a koyaushe. Dalilin irin wannan tunani a zuciyar wannan bawan Allah shi ne, yana cikin yanayi na rashin yarda da kansa. Tare da rashin tabbas game da abin da zai abku wajen haduwar sa da Allah. Ire-iren wadannan tunani kuwa suna nuna karfin imani ne da dogaro da Allah madaukakin sarki wanda shi ne tushen kaskantar da kai. A kowanne lokaci idan bawa ya kaskantar da kansa, Allah zai kare shi daga masifu, kuma ya ba shi sirrin “Ikhlasi” Wato nacewa da son bin hakikar gaskiya a dukkannin al’amuransa na yau da kullum. Daga wannan mataki ne mutum zai kasance cikin mutane ‘yan kadan wadanda suka samu yardar Allah tare da kusanci da shi. YAKANAH ita ce kofar da ake bi ta cikinta zuwa wurin da baiwar Allah da rahamar sa suke muhimmancin YAKANAH ga musulmi kamar kwatankwacin bargo ne a cikin kashi. YAKANAH tana a matsayin bargo na Ibadah, kuma sauran ayyuka suna a matsayi na kashi. Bayin Allah wadanda ake kira ‘zahideen’ masu cike da da’a da tsantsenin duniya, tare da ‘nasiqeen’ masu sadaukar da rayuwar su domin bautar Ubangiji, dukkannin su suna ji da wannan baiwa ta YAKANAH. Bayin Allah masu YAKANAH basa yin maganganu barkatai, basa yin tsegumi ko wata muguwar magana a game da wani a bayan idanun sa, su kan fadi abin alheri ne a game da shi. Ba sa shiga sharo ba shanu, kuma zuciyar su fes take. Ta kuma nisanta da miyagun dabi’u, kamar hargowa da JI DA KAI. Wato kirjin irin wadannan bayin Allah garau yake. Duk maganar da irin wadannan bayin Allah masu YAKANAH suka fadi, ta dace dai-dai da abin da suka yi, suka kuma yi imani da shi. Basu da wani abu da za su boye a zuciyar su domin kada wani ya sani, wato basu da wani mummunan abu a tare dasu. Bayin Allah ne masu zallar gaskiya da rikon ta, wanda duk ya yi hulda da irin su zai ga cewa basa fafutukar neman kuskure a kan wani, maimakon haka, a shirye suke wajen neman kuskure daga wajen su, wato a kan kansu. Basa yarda su zauna tare da (marada) (masu kawo tsegumi). Don haka ‘yan uwa musulmi mu yi damara da kokarin kasancewa cikin bayi masu YAKANAH, mu rike addininmu, mu kama Alqur’anin mu, mu suturce jikinmu, mu tsayar da sallah domin samun dacewa a duniya da lahira. Kamar jarumar wannan littafi, Allah ya bamu iko amin summa amin. Takori..