💑 *AUREN FARI*💑 0⃣0⃣1⃣ *NA SADAUKAR DA LABARIN GA AUNTY RABI TAH ( HAJIA RABI BADAWI MAMAN IBRAHIM )* Sauri takeyi kamar zata tashi sama, hannun ta rike da kwanon miyar manja, tun dazun aka aketa asibiti kai abinci amma don shiriri ta miyar ta baro gida shine ta dawo dauka. Fakam fakam fakam tafiya takeyi ba ko jinkirtawa saboda tsoron kada Yaya Abba ya dawo masallaci a fada mishi yau kuma ga abinda tayi. Ji kakeyi rikichaaaa,!! Karam karam....... Ta antaya jikin mai tahowa da miyar da ita duk suka afka mishi yayi baya da karfi tare da riketa gamm bayansa ya bigi bango da karfi miyar ta karasa wanke mishi gaban farar gizna din sa, ya runtse ido da karfi lokacin da yajin miyar ya watsa mishi a ido yaji wani irin azaba ya ingije ta silbin miyar ya kwashe ta ta fadi duk ta nade miyar a hijabinta. Ta mike a harzuke malam wannan wane irin wulakanci ne baka gani zaka jefani cikin miya in bata sabuwar hijab dita ta islamiya? Bayan asarar da ka janyo mun kai baka iya tafiya kana duban gaban ka? Bala'i take zazzagawa yana kokarin goge yajin da ke idon sa. Sam bata lura da mutanen dake bin bayan sa ba, sai da wani ya finciko ta karfi zai kwada mata mari yayi saurin daga mishi hannu alamar ya kyaleta. Ta ja baya tare da rike kugu iyyyeee cewa zakayi tafe kake da masu tare ma fada to wallahi yau sai kun biyani miyata da hijabi na..... Sai lokacin ne ya kalleta idanun sa jawur ga bacin rai ga radadin yaji ya da ka mata tsawa ke gidan ku ba a koya miki tarbiyya ba? Wannan tsummar hijabin da banzar miyar manjar ki kike wa mutane rashin kunya akai? Kin San darajar kayan da kika bata? Ya zaro ido ya na nuna jikinsa. Kai ka sani ni kasan miyar nawa aka kashe akayi ta? Ko kuwa kasan kudin wannan hijabin.....shut up!!! Ya daka mata tsawa tare da damko ta. Lokacin ne hankalin mutane ya dawo kan su. Wani yayi saurin dafa kafadar sa yallabai ba girman ka bane don Allah ka kar ka biye mata. Ya hakade ta ya gitta zai wuce sai ta chafko hannun sa da karfi kamar wani zaki ya dubeta da karfi ya kalli siririn hannun ta sannan ya kalleta ita din dukan ta zai iya hadiyewa. Wallahi duk mazuran ka sai ka biyani zaka bar wurin nan yama rasa me zai mata ya chafki hannun ya kudundune ta ya jefar suka wuce yabarta kwance tana ihu duk ta tara mutane kanta asibitin. Abba da ya fito masallaci ya hango mutane taruru ya tukaro wurin yaga lafiya sai kawai yaga *umaimah* wani takaici ya turnuke shi ya figeta da karfi sukayi dakin jinyar, tunda tagan shi jikin ta ya fara kyarma. Suna shiga ya fara wanka mata mari biyu sannan ya tambayi ba asi, tana gama fada mishi kuwa yasa mata charger ya bata kashi sai da goggo ta karbeta. Abincin sai dai aka siyo mai da yaji. Umaimah marainiya ce, gaba da baya tana hannun wan babanta gidan banda gallaza mata babu abinda akeyi ko karatu sun hana a sanyata da tsiya sun kangarar da ita. Matar marikin nata ce aka kwantar duk da nisan da ke tsakanin su da asibitin kullum itace ke kai abincin safe, rana da kuma dare. Kamar mahaukaciya haka ta fito kacha kacha ta nufi gida tana takaicin wulakancewar hijabin islamiyar data samu da kyar aka yi mata. Haka ta koma gida ta shiga wanke kayan da manjan ya kasa fita abinda ya kara harzukata tana addu'ar Allah ya kara hada ta wannan dan rainin wayon. Sati daya, sati biyu....har an share kusan sati biyar basu kara haduwa ba gashi an sallamo goggo sai ta fita batun sa. Umaima bata da kiwa ko Kadan shi yasa take cin gajiyar mutane da yawa cikin unguwar ana yawan kiranta gidaje mai shara, wanke wanke dan wankin yara haka dai idan ta gama abinci, sabulai mai da tsumma. Gidan su Sam babu Wanda ya damu domin sun dauki hakan kaskanci da bayar dakai wani lokacin ma sai suyi ta mata dariya tare da habaici. Ita kuwa tafi jin dadin bautar da takeyi wa mutanen gari suna godewa ba nan da kullum wulakncin safe da rana daban ba. Duk satin nan bata zama gida tana gidan Alhaji yakuba tana taya su aikin biki, musamman gyaran daki domin sun yarda da ita matuka.Har yau ransa a 6ace yake, yarinya karama talaka kuchaka ta dizgashi, zuwansa asibitin biyu bai ganta ba inama lokacin ya kakkaryata lallai da ya huce bai zauna cikin bacin rai irin haka ba, ya ringa hasko ta cikin kuchakan kayanta da shegen yadin da take ikirari da sabuwar hijabi Wanda ko kyallen goge takalman sa yafishi daraja. Ya buga tsaki ina jiye wayarinyar nan haduwar mu nan gaba....... Au wai baka shirya ba? Don Allah malam hanzarta kowa ya hallara kai kadai muke jira. Ya kara hade rai ya mike okay ina zuwa. Yauma cikin rantsattsiyar gizna yake fara tasha aiki na alfarma tafe yake yana kasaita ran nan nasa a 6ace. Yanda yake saukowa a benen yasa abokan duk bushewa da dariya baibi ta Kansu ba kawai yayi gaba abinsa. Mustapha ya yi nuni da baki ji yanda yake hura hanci kamar shine angon duk suka kara kwashewa da dariya. Hajia ta kira umaima lokacin da ake ta faman tafiya party tace ke bazaki je bane? Murmushi tayi ta ce eh hajia. Dalili? Maza zo nan ta kama hannun ta tayi ciki da ita wata durowa ta bude kinga duk wadannan kayan Asma'u cewa tayi a bayar don haka ki zabi Wanda zaki zaka yanzu kije ayi dake idan kin dawo ko zuwa gobe sai ki zo ki kwashe sauran don ke na ajiye wa....ta zaro ido ni hajia. Eh ke fa.. Maza shirya kada motocin su kare, wani paper lace ne milk dinkin riga da skirt ta dauka. Har zata fita taga hajiyar ta shigo da sauri ta miko mata takalma ungo wurin amarya na roko miki wannan kuma gyale ne sanya maza ki wuce. Ko hoda bata shafa ba. Tana zuwa ta fada mota. Ko da a ka sauke su. Fiddausi kanwar amarya na ganin ta tace yauwa umaima zo Ku shiga da kayan nan. Ta ce to ta shiga aiki. Dai dai lokacin da sukayi tsaya da mota kamar ance ya daga kai kawai ya hango ta rungume da lemuka. Da sauri ya fito sai kuma ya yi turus daya tuna inda yazo. Muje ko? Ya rungume hannu a kirji tare da jingina da mota ya ce kuje ina zuwa ...duk suka kalleshi sai kawai yayi sauri ya fiddo waya yasa a kunne hakan yasa suka fahimci waya zaiyi. Suna wucewa ya mayar da ita aljihu, ta fito tana ta faman kakkabe kakkaben kaya yayi murmushi watau yau bata son abinda ka taba kayan jikin ta. Sam bata lura dashi ba ta zo zata wuce sai kawai taji an fizgeta anyi bayan motoci, ta dago da karfi sai kawai ta ganshi. Ta fizge hannun ta tare da ingijeshi kana hauka ne zaka kama ni? Zai yi magana ta juya abinta kayan data fasa dauka kenan ta shiga ciki duk an zazzauna ta hango kujera can tsakiya ta isa ta janyo zata zauna ashe biye yake da ita kawai ya harbar da kujerar ji kakeyi *timmm* ya wuce abinsa duk aka juyo hankalin kowa ya dawo kanta ta wunkura da karfi zata isa gunsa fiddausi ta gani gaban ta. Sannu umaima ke nake nema zo muje ki taya my serving wani takaici ya turnuke ta ta bishi da kallo dai dai lokacin da ya hau gun anguna ya zauna ya juyo yana hararar ta. Kunya duk ta baibaiye ta. Shine ya bude tàro da addu'a ya bada tarihin ango don haka bata nan suna can suna shirya abinci. Fiddausi tace kamata yayi mu fara kaiwa haka . Umaimah tayi karaf Anty fiddausi kawo in faro daga sama wurin angwaye. Yawwa Allah ya yi miki albarka umaimah dama kowa baison zuwa saman cen, ta dauki ture ta fara shiryawa. Zuwa na uku da zatayi ta debi cocktail juice da farfesun kayan ciki ta tafi tana isa kamar zata ajiye bisa yanda ta faro daga farko kawai sai ta antaya mishi duka ajiki har turen jikake rikichaaaa ...... Duk Wanda ke high table din tsaye ya mike hankali tashe........ *MAMAN ABDALLAH* CE😃💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣0⃣2⃣ Kamar da gaske ta dan razana laaaaa ban gani ba taja baya zata gudu Ya chafko hannun ta, Asma'u ta daka mata tsawa haba umaimah baki gani ne? Tayi ta kicin kicin ta kwace hannunta amma ya ruke su tamau, ba komi ya fada yasa dayan hannun sa ya fizgen gyalen ta ya fara kwashe plates din dake bisa jikin sa sannan ya ya ci gaba da gogewa, duk illahirin jikin sa ya baci, yarinyar nan na janyo mun asara amma zan maganin ta a yau. Biki ya tsaya chak! Yaga kowa ya mai da hankalin kansa abinda ya tsana kenan ransa ya kara baci. Ki kwashe kwanukan kikayi tsaye, ta kalli kanta ta yaya zata ratsa dubun mutane ba gyale? Wannan wulakanci dame ya yi kama? Ga kayan duk sun matse ta....ta daka mata tsawa ko ba kyaji? Ta duka tana kwashe kayan ya yi fit! Da kallabin ta kananan kalaban da ke kanta suka watso mata ko ina ta mike da sauri zata zazzaga mishi bala'i ya ce yafa gyalen don naga baya daukar miyar sosai gashi ba towel da zan goge kayan naki sun kama da bargo. Ji tayi an fizgeta da karfi, tana juyawa taga fiddausi, haba umaimah kinsan waye kika batawa kaya? Zo muje ki karbo towel mota kikai mishi. Figai figai babu gyale ko kallabi nake binta zarai zarai idanuna sun kawo wani ruwan bala'i. Anyi anyi ya tashi yaje ya sauyo kaya yakiya wai zai jira a gama. Ransa kuna kawai yakeyi amma ya kasa nuna wa duk da fuskar tasa kullum tamau. Don Allah Anty fiddausi ko kallabinki ne bani in yafa kada in kuma ratsa mutane haka. Har zata yi musu sai kuma ta kwanto ta bata kowa head ya saka amma wani ikon Allah ita fiddausi ba ta sanya ba. Tun kafin ta hau saman ta hango kallabin da gyalen a kasan kafar sa yana goge sauran miyan da suka zuba. Tuni an ci gaba da sha'anin biki amma ganin ta hawo saman sai hankalin amarya ya dawo kanta, ta mika mishi towel din tare da banka mishi harara. Baki iya goge masa wai yau meke damunki *UMAIMAH*? Ya maimaita sunan cikin takaici a zuciyar sa *umaimah* ta duka ta fara gogewa shi kuma ya kara shan mur, dataga hankalin asma'un ya koma can sai ta fara dangwalo wata miyar dake ajiye ta na kara yaba mishi a inda bai samu miyar ba. Hada hannu. Ya kura mata ido yana wani irin mamaki wai yarinyar nan tasan waye shi? Yaci gaba da kallon ikon Allah tasha mur sai kwaso miya takeyi tana kwaba mishi sai tasanya towel din ta dalaye. Tana gamawa zata mike ya dankwafar da ita ta koma da karfi ta zukunne, ya kalli abokin sa yace idan bazaka sha wannan naman ba kaban, ya miko mishi bai ko kalleshi ba yaci gaba da kallon yan rawa, sai kokarin dagowa takeyi shi kuma ya danne kafadarta da hannu, ya dan waiga yaga kowa hankalin sa yana gun yan rawa ya sa hannu ya bude gaban rigar ta ya kwarara mata duka miyar cikin breast ware sannan ya sake ta tafadi ta baya dabas! Ya kawar da kai kamar baisan komai ba. Na kusa dashi ya kalleta easy! Tashi mana. Ta mike a wahale miya na zurarowa cikin rigarta duk ta bata ta nama cike cikin brezia. Kwalla suka shatato mata wannan wulakanci da me yayi kama? Ganin tana kuka yasa yaji wani sanyi a ransa hakika yanzu ya fahimci 6acin ranta. Ta fita farfajiyar tana faman zubda hawaye fiddausi ta tareta tare da daka tsawa haba umaima ji yanda kika batan kallabi, ta dubi kallabin Wanda ya zamo tamkar makwararin juyewar miyar. Zatayi magana ta fizge abinta tayi gaba. Ta koma bayan hall din ta duke tana kuka, kukan takaici ba gyale ba kallabi. Tayi mai isarta, har duhu ya fara nan da nan taga mutane na fitowa alamar an gama ta kara lafewa jikin bango. *zan jira a gama fitowa in koma in dauko gyalena da kallabi cikin miya in yafa hakanan amma bana iya ratsa mutanen can haka* ta fada cikin muryar kuka. Wallahi ko waye ubansa a garin nan sai na rama wulakanci na ta buga tsoki. Acikin hall abokan gewaye dashi suna faman ya taso amma ya kasa ko motsi. Baya iya ratsa dubun mutanen nan haka yanda aka sanshi a gari irin daraja da kimar sa. Ya kara hade rai na fada muku kuje zan taho nayi waya za a kawo mun mota kuyi amfani da wacce mukazo ciki key na hannun.... Gashi nan daya ya fada. Ya tabe baki okay you can go zan taho, zasu kuma magana ya ce please Ku kyaleni wallahi kuna dada sani damuwa. Dole suka fita, a rude amarya da ango suka iso zasuyi magana kenan ya yi murmushi karku damu bazan iya fita haka ba idan kowa ya gama tafiya zanje ya kalli Asma'u karki damu da abinda kanwar ki tayi mun......... Ba kanwata bace yallabai diyar makwabta ce amma tana shigowa gidan mu kama aiki........'yar aiki? Ya maimaita a rai. ......what ever ba komi kuje nayi waya za a zo a daukeni. San in ko waye yasa sukayi gaba. Umaimah kuwa lekowar da zatayi sai taga motar karshe ta fice yayin da wata ke shigowa ta zuro a guje sai taga sojoji biyu sun fito cikin wacce ta shigo din, tayi cikin hall din a rude, dai dai zai mike ya hangota ranshi ya bashi lallai gyalen ta biyo, ya kwashesu duk ya cusa aljihu duk da suke sharkaf da miya. Ganin shi bai wani daga mata hankalin ba domin ta gama rikicewa da dare gashi kowa ya watse, duddube duddube takeyi tana zare idanu shi kuwa yayi tsaye yaji ko zata tanka mishi sai kawai tayi hanyar fita ya zabura ya damko ta, kamar tana jira ta harzuka wai kai *maye* ne? To kurwata tafi karfin ka, meye hadina dakai yauni naga bala'i.... Ina kika ga bala'i wallahi yau sai nayi maganin ki ya figeta sukayi waje yana dube dube yana faman zare ido, kawai sai taga jelar gyalen a aljihunsa. Ta kalleshi taga lallai ya fara rasa hankalinshi don fushi, to me zai Mani? Ganin sojojin nan na tunkaro su yasa ta gantsara mishi cizo a yatsa kamar zata cire ya fasa kara *kaiiiiii* yana sakin ta tayi wajen *gate* din a dari da sittin. Daya daga cikin sojojin ya yunkura zai kamota yayi saurin tsayar dashi. Allah ya taimaketa tana fita ta samu adaidaita da kamar bazai dauketa ba tace party tazo bata gari suka biyota. A kofar gidansu ya ajiyeta, ta karbi dari gurin sham'unu mai manja ta bashi, ta shige gida ana babban falo ana kallo ta sadada taje ta sauyo kayan. Washe gari wunin biki taki lekawa hajia tayi aiken duniya sai ma tabar gidan. Karfe bakwai na safiyar walima hajiyar ta aiko kanwarta ba halin kara wata dabarar saboda ta ce kafarta kafar umaimah. Ko kalaci batayi ba. Tana shiga tasanya ta gyaran daki tana fada kin San idan bake kika gyara man dakin nan ba bana jin dadi amma hiratan jiya kika ki lekowa to yau ai kyasha aiki ko fidda dattin tayil dinan kadai ya isheki. Ga kayan ki can na kulle miki amma ina gyalena dana ara miki? Gabanta ya fadi tayi dan kasake kafin tace, yana gida zan wanke ne, to ba komi tayi waje. Ta shiga gyaran dakin tayi mishi fes cikin yan mintoci saboda bata da nawa, anata shirin walima ta ce umaimah maza shirya ku tafi walima, A'a yau bana jin dadin jikina hajia kuma idan na tafi wazai gyara baranda? Ki bari su tafi sai in karasa gyara miki gidan. Allah yayi miki albarka ya zaba miki miji na gari, ta washe baki amin hajiyar mu. Tayi waje da wasu kwanuka ta ce ina zanje mu kara haduwa da mugun nan? Inba rigima irin tau ba inani ina haye ma irin su? Su hudu suka shigo tana ta faman hada kayan wanke wanke, kafar dattijuwar ta murguda tayi kichaaaaa zata fadi umaimah ta saki kwano tayo kanta ta tare sai ta fada jikin umaimah amma duk da hakan kana jin karar da kafar tayi kat! Subhanallahi sannu mamah ta fada yayin da dattijuwar tace washhh! Sai kawai cikin Matan nan wata ta ingije umaimah move... Ta tallabo matar. Cikin fushi umaimah ta kalleta ta ce *move*? To anki ayi move din ta hankade ta ta tallabo matar duk suka zaburo kan umaimah, kada wacce ta matso, matar ta fadi a hankali. Sorry mama suka fada suna ja baya, Au da taron dangi zasuyi mun? Ashe kuna sonta zaku barta ta fadi? Data kai kasa ai da kun ce *move* da hujja aikin banza. Ta juya sannu mamah ita kuwa sai bin umaimah take da kallo bayan *Umar* ashe akwai Wanda zai iya fada kan lafiyar ta haka? Kukayi kototo ku kamota mukaita daki ta daka musu tsawa. Qalu innalillahi hajiya bilkisu lafiya? Sai bayan da suka ajiye ta saman kujerar sannan ta ce wallahi turjewa nayi. Tana faman runtse ido saboda azaba. Umaimah tayi saurin zuwa gidan su cikin kayanta ta dauko kwankwalaton Robb tana shigowa hajiya ta ce yanzu nake Neman ki jekira sadi a kira mai kamu ya duba kafar, ta ce to bari in shafa mata Robb na dauko gida tukun saboda zogi. Bata jira sun kuma magana ba ta tallabo kafar tana shafa Robb din a hankali mamaki ya cika hajiya bilkisu kallonta kawai takeyi, ita kuwa umaimah tana son gyara kafar data dago sai taga ita take kallo, hajiya na ajiye plate din nama umaimar ta zabura kamar wani abu, suna duban wurin ta mayar da kafar kowa yaji ta ce kas!!! Tare da karar da hajiya bilkisu ta saki. Sama akayi da umaimah ita dai taga anyi hanyar waje da ita..... ❤ *Maman Abdallah*❤ 💑 *AUREN FARI*💑 0⃣0⃣3⃣ Tsawa ta daka musu, ina zaku kaita? Ga kafar ta gyaru ta jujjuyata, suka dire ta, hajiya ta ce ikon Allah umaimah ikon Allah karambanin naki hada gyara rauni? Ta dawo sannu mama haka akeyi idan anyi tirjiya baban mu yana gyarawa...... Na sani tabbas na san haka. Ta dalla musu harara kuje waje Ku jira, tsiraran mutanen da ke dakin suka ci gaba da yi mata sannu, umaimah ta duka tana kara shafa mata Robb. Na gode nagode sannu na gode, bakin ta ya kasa dainawa har sai da ta kalleta tana yar dariya haba ai kece da sannu. Tabar dakin ta tafi tana gyara kitchen. Wannan yarinya da hankali take hajiya suwaiba wallahi na yaba da kulawar ta sosai. Hmmm umaimah kenan yarinya ce mai himma wallahi. 'Ya ce ko jika? Ko daya marainiya ce iyayen duk sun rassu, tana nan makwabcin mu dan uwan mahaifin ta ya dauko riko, shine take shigowa tana dan kama mana aiki. Bata da kiwa ko kadan yarinyar nada dadin zama ga kazar kazar. Allah sarki. Ta ce Tana can baya tana hado kwanukan wanke wanke idan an wanke tana kaiwa kitchen dattijuwar da hajiya suka isko ta. Umaimah hajiya ta kwala mata kira Da sauri takaraso tana murmushi. Ganin su biyu sai ta ce Aaaaaa kafa ta taku, ta karasa maganar tana yar dariya duk suka bushe da dariya hajiya ta ce to uwar iyeshege keda baki bar kowa ba. Tafiya zatayi tace a kira ki rike mata kaya zuwa mota. Tayi hanzarin warware hijabin da tayi damara dashi tace au to tare da karbar kayan. Har get hajiya ta raka ta suka fita tare suna magana, Ina ne gidan naku? Umaimah ta daga kai kin hango jarkokin manja gasu can.... Ta daga ido inda baranda take? Kwarai nan ne gidan mu. Allah sarki. Yaushe zaki zo Mani ziyara? Umaimah ta zaro ido a ina? Sai tayi yar dariya a gidana mana nima ki gyare man daki ki saman dan tsintsiyar kamshi. Ta kwashe da dariya kai wannan hajiya ce ta fada miki ko? Tayi murmushi ai naji dadin yanda kika nunan kulawa yanzu idan za a barki gobe kizo don Allah uwani? Umaimah nake ba uwani ba. Na sani sunan mahaifiyata gareki. Ashe diyata na taimaka duk suka kwashe da dariya. Dai dai sun kawo inda motar, mutanen ta sunyi cirko cirko, lokacin umaimah ta gane watan yan tsaro ne, duk ta bisu da harara tana rike da ledojin. Ta fiddo waya suka dauki hotuna tare , Ta kalleta bayan ta zauna zaki zo goben? In shaa Allah zanzo mama da karfe nawa? Bani no. Ki sai in kiraki. Woooo bani da waya ina ne gidan kiyi man kwatancen da zan fadawa dan adaidaita, tayi murmushi, kice a kaiki lamido crescent dai dai gidan *Umar madaki* Umar madaki nasu hajiya bilkisu? Nasan gidan muna wucewa ai sananne ne daga nan ina zan tambaya? Au kin San gidan? To ana da kinzo bakin kofa ki bada wannan katin......... Hannunta ya sagale ta zaro ido gidannnnn???? Ta fada da karfi. Wannan karon dariya tayi ta ce karki damu ni mahaifiyar sa ce goben kizo don Allah. Ta kalli matan nan a tsorace ta kawar da kai to hajiya zan zo ta fada a sanyaye. Ta miko mata dubu dubu dunkule bata san ko nawa bane ta ce ungo ki hawo dan sahun, A'a haba wallahi bazan karba ba , tayi gaba abinta. Tunani ya baibayeta, umar madaki yaro matashi mai tashen mahaukatan kudi Wanda babansa ya mutu yabar masa kamfanoni da tarin dukiya yaron da gwamnati ke tsoron sa labarin sa kaf ta sani abakin su hajiya. Baima cika zama Nigeria ba yana yawon kasashe anyi anyi yayi aure yakiya. Shi kadai mahaifin sa ya haifa kuma matarsa daya, tsohon mai kudi ne, bada labarin sa bata lokaci ne sai gaba za a ringa fahimta. Tana isa gida ta tara ma aikatan gate ta Nuna musu hoto tace gobe zata zo kunji? Wallahi kada Wanda ya tsorata ta. Yana kishin gide ta shigo kallo daya yayi mata ya fahimci ba daidai take takawa ba, ya wuntsulo har ya tsoratata mamee lafiya? Me ya sami kafar kike dingishi. Yanzu har kaga ina dingishi? Menene ya faru? Ya bukata rude, Tuzgunewa nayi amma da sauki ai motsuwa ce ba rauni..... Eh doctor maza kazo da sauri, ta kalleshi uwar wa zaimun doctor din na ce lafiya ko? Amma bai yarda ba sai da doctor yace ba rauni. Haka yayi ta sunturi, tace haka fa yarinyar nan uwani ta damu wallahi bacin ita ai da ina asibiti...... Wacece uwani? Ta bashi labarin abinda ya faru yanda ta dunga zabga wa masu tsaronta masifa. That's very good amma she is very intelligence. Wannan shine fada mai dalili ba na wasu yan iskan yaran marar tarbiyya ba. Ya kara sa maganar yana tunano partyn jiya. To wai yarinyar ko a billboard bata lura da hotunan sa da labaru,jaridu? To wai waye baisan *Umar madaki* ba don ubanta?..... Ka rage wannan zafin ran ai komai ya wuce tunda gashi Alhamdulillah kafar ba rauni. Nan sukayi fira sai goma ya haye sama, Umaimah kuwa hajiya ta samu ta fada mata yanda sukayi. Ke umaimah kada fa ta kwace man ke don bazan bata ba, kinga Asma'u tayi aure su fiddausi kuma makaranta. Tayi murmushi hajiya ba wannan ma ba kina ganin inje ba matsala? Kwarai kuwa babu kije ai duk gida ne nan da can nida ita ai kusan daya ne, gidan su idan zata kai sha biyun dare babu mai cigiya, washe gari ta shirya cikin kayan Asma'u ta saka wani material ruwan hoda taci gayun ta tace ta tafi gidan Alhaji yakuba. Yan kudaden da hajiya ta bata tayi amfani dasu, misalin karfe sha daya na rana, ga mamakin ta kowa ya ganeta akayi mata iso. Ta ware ido tayi ta kallo tana mamakin gidan, saboda tafiya har ta fara tsorata, tana shiga falon yana hayewa sama, yaji motsin shigowa amma bai waigo ba yana rufe kofa ta kalla. Murna tsalle, duk bakin umaimah sai ya mutu har hajiyar tayi mamaki tace yau uwani kinyi shiru. Tayi murmushi kawai, nan da nan ta fahimceta ke saki jikin ki don Allah ta fara janta da labari, nan da nan ta washe har ana kyalkyatar dariya, dambun nama, kilishi, farfesun yan ciki, kaji, tsoka, peppe chicken shinkafa da miya, shawarma. Kai abinci barkatai umaimah ta kalle su mamah wannan gara haka sai dai kin manta da abu daya, da sauri tace menene? Ja da yellow maganin zawo. Me zatayi ba dariya ba dariya takeyi har tana kwanciya. Umaimah ta na murmushi tace yo toh. Wayarta tayi kara tasa hands free mamee ke dawa kike dariya haka? Kada fa kiyi ciwon ciki. AF zo ka gaisa da uwani nayi tunanin ko kana barci ne, Ina zuwa zan dauki wata waya mamee ya kashe, suka ci gaba da cin abincin. Tana gamawa tace zata tafi. Tayi tayi ta jira ayi la'asar tace karfe uku zataje islamiya, ance umar baya da mata to ina aka samo yaran da keta guje guje? Umaimah zata bar tambaya babu amsa? Tabbb Mamah yaran waye wadannan wai? 'Ya ya nane kin San akwai kanne na biyu dake zaune da matayen su anan gidan. Ta girgiza kai. Ta kwaso mata kaya lesussuka atamfofi , turaruka da kudi masu yawa, aka bata bokitin dambun nama ta kira daya daga cikin yan aikin tace akirawo direba. A'a hajiya zan hau adaidai ta kin San halin mutane yanzu aga mota ta ajiye ni unguwar mu sai a fara surutu kibarshi kawai. Ta kara yabawa da hankalin yarinyar. Ta na fita ya fito sorry mamee ina bakuwar zanje meeting Lagos ya fada yana sauri sauri. Ta tafi , a dawo lafiya. Ta bashi amsa a takaice, ya wuce da sauri, gaba daya layin gidan gewaye yake da sojoji, ta raba can gaba tana jiran adaidaita. Motocin suka raba ta suka wuce wani mugun birki aka ci ba tare da sunyo baya ba taga mutum ya fito yau sanye yake da suite ruwan toka duk da gabanta yau sai da ya fadi amma bata yarda ya gane ba. Ubanwa ya baki ikon tsayawa layin nan? Ta kalleshi a wulakance ta tabe baki kayya dai, ga mutum har mutum amma *fanko* yanzu kai baka jin kunyar zagi? Ke ya daka mata tsawa tare da shako wuyanta ita ma tace kai..... Ko an fada ma wadancen jerin gwanon abokan ka naka zasu firgitani. Tuni nasan baka iya tare fada da kanka sai kayi gayya ga katti can majiya karfi a waje ka kasa biye musu sai ni to gaba da gabanta wallahi sojojin gidanmu zansa yau suyi maka mugun duka. Ya kalleta sakaka sojoji? Ko kana wasa inyi waya? Yasa kafa ya harbar da bokitin dambun ya tarwatse a titi ya ce sojojin gidan ubanwa? Ta harzuka na gidan *yaya umar madaki*........... *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣0⃣4⃣ ......... Ya sharara mata wani kwakkwaran mari. Ta gigice ta kidime ta runtse ido kanta na juyawa ta rasa duniyar da take, tana jin hancin ta na tsiyaya amma bata San shin majina ce, ruwa ne ko jini ba, sama sama take jiyo amon muryar sa. Wallahi wallahi ranar da kika kara ambaton sunan nan da wannan shegen bakin naki sai kin gane kurenki. Ya ingizata tayi baya ta fadi saman bokitin da ya harbar. Kin ga layin nan? Idan kika kara biyoshi na rantse da Allah sai na batar dake Nigeria ko kuwa waye ubanki...... Ya sa kafa ya shuri dambun naman dake baje kasa ya watsa mata ga jiki. Hazo hazo take ganin tafiyar sa har ya isa inda motocin suke, tafi mintuna ashirin kafin kanta ya fara saisaita, ganin jini face face a jikin hijabin ta yasa ta kara kidimewa. Tayi saurin toshe hancin da sauri cike da tsoron irin jinin dake zuba. Ta rushe da wani irin kuka wannan masifa dame tayi kama ni umaimah? Yau mashin ta hawo ba inda tayi ma tsinke sai gidan Alhaji yakuba. Hankalin hajiya ya tashi amma sai tayi mata karya da hatsari sukayi a hanya, barin fuskarta kumbure. Wallahi sai na zubda mishi jini nima ta fada a hankali. Hajiya ki dauki kayan nan na baki idan naje dasu gida kin tabbar masifar da zasu janyo mun. A a zan dai ajiye miki, babu abinda zanyi dasu nikam, Wallahi na baki, ai ba roko na kikayi ba hasali ma duka daga ciki ba abinda zan iya amfani dashi. Shiru kawai tayi mata. Tana shiga gida ta iske su lubabatu sun fiddo jakar kayan ta suna ta rububin rabawa, tana shigowa rayya tayi saurin tarar ta ina son na jikin ta wallahi na riga. Ko kadan bataji komai ba domin idan da sabo ta saba tana yin magana iyayen zasu ce tabar musu tunda gobe ma wasu zata samo. Su kuma sai su duba tsofaffi da suka gaji dasu cikin nasu su bata, kai kawai ta girgiza ta wuce tana cewa qala za a fadawa yaya Abba karya da gaskiya ace ta zagi iyayen ta ya lakada mata tsinannen duka da waya. Ta dauki naira goma ta siyo reza sabuwa ta daure a habar kallabi. Baban su idan ya fita shidda na safe baya dawowa sai shabiyun dare kasuwa kullum. Mamar umar kuwa waya ta dauka ta kira hajiya, bayan sun gaisa ta ce bakuwa ta dawo lafiya? Wane lafiya dan adaidaita ya tandarata da kasa duk ta jeme fuska, subhanallahi tana ina? Ta tafi gida ai da sauki na bata magani nan. Duk sai ta kidime, kwantar da hankalinki wallahi da sauki, to shi kenan ta ajiye waya, amma ta kasa daurewa sai kawai tace azo a kaita, tana kwance daki suka shigo da goggo, zumbur ta mike, ohh uwani ashe haduwa kikayi da tsautsayi haka? Tayi zuru zuru mutanen gidan chirko chirko....... Mamah da hajiya ta aikeni gidan ki wajen dawowa muka fadi da adaidaita ai da sauki ta karasa maganar tana satar kallon su goggo. Zata kara magana tayi saurin cewa gasu goggo da yan uwana hajiya. Ai mun gaisa, ya jikin? Alhamdulillah, Zaki shiga wurin hajiyar? Data zo zatayi magana sai umaimar ta kakalo wata har hajiyar ta fahimta tunda ba yarinya bace, Allah ya bada lafiya ta mike, Don Allah idan mahaifinta yazo ina neman alfarma a bani umaimah tana zuwa tana kama mun aiki ni din yar uwar hajiya....umaimah tayi karaf gidan Alhaji yakuba hajiyar su fiddausi , ta balle jaka ta damtso yan dari biyar biyar ta bawa goggo jummai ga wannan a rabawa yara. Wufff goggo hansatu ta wafce too too Allah ya biya hajiya za a fada mishi ai duk an zama daya, sukayi daki umaimah ta rakata har mota sannan ta dawo, bata bi ta Kansu ba domin tasan naira babu ita ciki, Suna isa ta tarar dashi falo a tsaye, yana safa da marwa, mamee ya tunkaro ta rai bace lillahi wa rasuluhi wannan dame yayi kama yaya zaki ringa fita any how na dawo kowa yace baisan Ina... Gidan uwaka naje, wai har yaushe zakayi hankali umar don iyayenka nice na haifeka ko kaine ka haifeni? Yarinya tazo guna girma da arziki ta yi hatsari sai in ki zuwa dubo ta? Mamee kuma ko waya bazakiyi man ba kin San sarai abubuwan dake faruwa....bazan kiraka ba din na ce anki a kiraka ya wuce cikin fushi sai kuma ya yi sukuku ya bita mamee nifa duk abin nan lafiyar ki nake ji .... Ta juyo a hasale ni kuma lafiyar uwani nake ji.... Sai ya rungumota ta baya wai wacece wannan uwani dake Neman kwace man mamee? Na fara kishi fa ya saketa tare da tirjewa kamar karamin yaro yanda yakeyi mata ta ingijeshi kai tafi can ta shige daki,bya bita yayi ta lallashi har sai da ta washe, na dauko uwani aiki zaka ringa biyanta albashi, yayi murmushi an gama nawa kika yanka mata? Dubu talatin.....talatin mamee hada bangwayen gidan zata ringa wankewa? Idan baka iyawa ni na biyata..... Inji waye ko miliyan kika ce air dole a biya mamee duk sukayi dariya, Karfe biyar goggo ta tasheta, Ke tashi Alhaji ya amince da zuwa aikin ki maza kiyi man wanke wanke don ki tafi da wuri, bata ce komai ba ta tashi bayan ta gama sallah ta hau gyarawa bakwai tabar gidan ta sami hajiya ta fada mata komai har ta na kwallah. Nasan za a rina kawai raina yaban sai ta amsheki , ki kyalesu Kansu suke wulakantawa umaimah kedai ki ci gaba da tsare gaskiyar ki baki sata na shaide ki kada ki yarda ki wulakanta kanki kinji? Tun daga farkon layi tace a ajiyeta ta fiddo reza ta damtse a hannu ya Allah ka hada ni da mugun nan azzalumi, tafe take amma layin kamar anyi Shara shigowa farkon layin sojoji ne tsare da ba kowa suke bari ya ratso ba itama ansan da zuwanta tun jiya, ta fara hango tsiraran sojoji na kara kaina data fara dumfarar gidan kamar ance ta waiga baya kawai taga mutum na sassarfa da kayan gudu. Ta ware ido wallahi shine tafe kawai sai ta tsaya chak! Daya, biyu, uku,..... Tara...... Kawai yazo zai gifta ta kunnen sa da ear piece ko alama bai lura da mutum ba hanakalin sa na can hannu tasa ta damko cinyar hannun sa ya dawo baya da sauri kafin ya hankalta ta farde mishi tsakiyar hannu ta kwasa a guje. Jini ya fartso ya dafe hannun innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ya bita da kallo har ta kule, nan ta kwana? Yarinyar nan ko aljana ce ni umar? Jini ke tarara kamar fanfo haka ya kara gidan yace maza a tado doctor, sai da akayi mishi dinki, azabar duniya ta addabeshi yazanyi da yarinyar nan kada tasa inyi abinda ban da niyya anya bazan kashe ta ba kuwa? Idanun sa jawur kamar yayi ta kurma ihu, a kidime mamee ta shigo umar rauni kaji? Wallahi mamee Yankewa nayi, Dami? Yayi shiru... Kai dami ka yanke? Ina jin ko wuka ce? Kana jin? Baka da tabbas ne? Yayi dabur dabur wuka ce mamee ya ballo magunguna ya sha ta bishi da kallo umar menene ya faru? Ya kakaro murmushi is okay mamee bari in watsa ruwa ya mike zuwa toilet ta bishi da ido kawai, ya hada kai da bango ya dafe kansa kashe ta zanyi tabbas wani yayi hayar yarinyar nan don ta shigo rayuwa ta negatively I must kill her..... Mama lafiya? Umaimah ta riketa, kaini yau naga masifa wallahi umar ne yayi mugun rauni, wannan zafin rai na wannan yaro ya Allah ka rage mishi. Ta zaunar da ita Amin mamah ungo tea kisha ko in kwaso miki kalacin nan? A a barshi ya shiga wanka daya fito zamu karya. Mama karfe sha daya fa bakyajin yunwa? Ko ina ji dole in jirashi in ba haka ba to bazai ci komai ba zai fita, gashi baya cin abincin ko ina sai nan. To shi kenan yanzu ni meye aikina, eh wallahi har yanzu tunani ma nakeyi Ikon Allah umaimah tace a hankali ta mike muje bisa table kafin ya fito. Kema dauko plate ki ajiye nan ta nuna mata kujera jeri jeri haka ake ta zarya zuwa gaida ta ma'aikatan gidan da matan kannen ta, duk Wanda yazo sai tace ga uwani itama daga yau a gidan nan zata ringa zama...... karar rufewar kofar ya antayo wani mugun da dadden kamshi tayi saurin kallon inda karar ta fito zumbur ta mike akayi rashin sa'a kujerar tayi baya a wuntsula tayi saurin tashi tana baya baya a firgice, ke uwani lafiya kai rike man ita mamee ta fada ganin tana niyyar kwasawa da gudu duk ta fita hayyacinta. Step din karshe idanun sa suka sauka kanta ya kara bude ido ko mafarki yakeyi................ *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣0⃣5⃣ .....Mafarki yakeyi ko me? Da gudu ya karasa saukowa ganin ta kwasa guje, karku bari ta fita...... Ya fada da karfi damka daya kawu karami yayi mata sai kawai ta sulale kasa tare da kurma ihu wayyo na shiga uku......... Mamee ta rikice ganin umar ya finciko 'yar mutane ubanwa kika zo yi anan....kai dakata, ta finciko ta da karfi ta kuwa makalkaleta ki dubi Allah da manzon sa ki ceceni na tuba mugu ne...... Ya zagayo zai damko ta yana huci duk suka juya tare da mameee kai wai meye haka, wallahi yau sai naga bayan yarinyar nan na amince idan ta mutu nima a kasheni. Hankalin mamee ya tashi matuka don haihuwar danayi maka umar ka saurara man..... Umaimah ta hadiye wani mugun miyau tana tuno maganar sa, *wallahi wallahi ko layin gidan nan kika kara biyowa sai na sanya an batar dake......* Ta zaro ido abubuwan da suka dunga faruwa suna dawo mata. Na shiga uku na jefa kaina masifa ni umaimah cikin ta ya dunga wani irin rugugi. Yunkuri yakeyi mamee na karewa, mamee ki dubi Allah ki matsa, bazan matsa ba kayi aika aika, to kyale yarinyar nan tabar gidan nan kada in saba umarnin ki yau. Sai dai in bita mu tafi tare,......ya zaro ido what?? Eh wallahi fitar uwani gidan nan fita fita yau, ya dafe kai wayyoooo mamee kar kija in saba miki yau ki kori yarinyar nan kada inyi kisa.....kisa???? Umaimah tayi sama da numfashi wayyo na shiga uku so takeyi ta kwace mamee ta riketa gamm, ya runtse ido da karfi, Me ye ya hada ka da ita? Duk barin miyar da nake zuwa miki dashi 'yar iskar yarinyar nan ce, ita ce.......dazun.... Umaimah ta zaro ido jin zai fadi ta yanka shi tace wallahi mamee shine ya fara watsa man ajiki ni bansan wanene shi ba.... Don ubanki sai kinsan wanene ni zaki mutuntani? Ta juyo ta bayan mamee ta motsa baki yana kallo *badai ubana ba* sarai ya karanto me ta fada ya zaro ido ya yunkuro ubanme kike cewa? Kai tsaya yaushe tayi magana? Wai mamee menene haka yarinyar nan munafuka ce yau sai naji Wanda ya turo ta wurina.... Wazai turo ta umar? Jikin mamee har ya fara ciwo wannan rigima, kawai sai dubara ta fado mata. Ta fara layi da kai. Mamee calm down ki zauna karki shiga abinda babu ruwanki. Na fita ciki kayi abinda kaga dama tunda baza ka saurari abinda zan fada maka ba, kuruciya ce kayi hakuri........ Kawai sai ya yashi fuuuu yayi sama. Umaimah na ganin haka ta shiga neman takalmi, ina zaki je? Kiyi hakuri mamah amma bani iya wannan aikin. Saboda baki kaunata uwani? Don kinga na kwallafa rai akanki bani da 'ya mace ganin ki nake tamkar diyata. Ni na haifi umar kina ganin duk sabanin da kuka samu zan yarda ya cuta miki ina kallo? Duk zuciyar sa dole yabi umarnin maganata. Ki dubi girman Allah ki zauna dani kina debe mani kewa. Idan aka wayi gari kuma na 6ace wa zai nemo ni? Ta fada a zuci, a zahiri sai kawai ta fashe da kuka wallahi mama kuskure ne. Na sani uwani nice shaida. Ki kwantar da hankalin ki zan lallashe shi. Haka dai ta wuni sukuku, karfe biyar zata tafi tana ta dube duben takalmi dagowar da zatayi daga mutum tsaye kanta. Tayi saurin ja da baya, ya dalla mata harara, zuwa nayi in gargade ki , na rantse da Allah zakiyi ma mamee aiki gidan nan kamar yanda ta bukata idan kika saki ko da gigi na ganki kusa dani sai dai uwarki ta haifi wata haka zalika Qala idan kika ce dani sai kin raina kanki banson ganin ki banson jin maganar ki......ta na gama ji taci gaba da dube dube. Ya fincikota ko bakiji ina magana? Ta kalleshi shekeke ikon Allah ina ce kunne keji ko? Ka ce baka son in maka magana to amsar me zan baka. Ka fada naji sai ka shafan lafiya. Ko kuwa yanzu da kazo kiranka nayi nida kai waya tarad da wani..... Ya makaro wuyanta gidana kike hattara....... Yi maza kasheni inyi shahada kai kuma ka karawa kanka bala'i gata dukiya gata kisan kai... Ya ingijeta ta fadi tana tari *mugu kawai* Wanda bai iya fada da katti sai yarinya..... Ya zaburo...kai kai...... Wai umar menene haka? Zaiyi magana umaimah ta rigashi ina duba takalmi kawai yazo yana ta zagina hada makuremun wuya ya faffalla mun mari....ban mareki ba amma yanzu..... Ina ce mun gama maganar nan da kai ko? Na lura kafi kaunar bacin raina fiye da farin ciki don haka tunda ka nunawa duniya ban isa dakai ba kaje kayi abinda kaga dama. Ta na fadar ta juya. Umaimah na ganin ta shige ciki ta buga tsalle ahayye a taba ni asha tsinuwar uwa ta yi mishi gwalo ta ruga. Duk iyakar bincike yayi ya kuma sanya an mishi akan umaimah amma tabbas babu alamar abinda takeyi wani ne ya aiko ta hasali ma tatihin yarinyar mamaki ya bashi ganin wauta da kasada yarinya marar galihu haka take da *gut* na ja dashi. Satinsa uku baya zama kullum yana yawon meeting wani ma cikin jirgi akeyin sa. Hakan yasa umaimah ta saki jiki sosai da mamee ita kadai ke gyara mata bed room da toilet sai ta hana kowa shiga, idan ta gama malamin dake kara ta karatu yazo sai Suyi tare umaimar tafi ganewa don haka idan ya tafi ita ce ke dagewa har sai taga mamee din ta haddace, sannan suci abinci tare kafin a zauna ana labari umaimar na basu dariya da iyashegen ta. Kowa ya fara sabawa da ita. Mamee ta kalleta wannan sarkin rashin yardan da zaki je ki gyara mishi daki kafin ya dawo tunda ya tafi da mika'ilu ina da spare mukulli a hannu na tunda bazai gane ba sai muyi shiru da bakin mu saboda cikin sharudan da ya kindaya man ciki hada kada ki kuskura ko matattakalan benen sa kije. Mamah tunda har yace haka yanzu idan ya dawo kwatsam fa? Daga saman zai tulloni kafin ki zo na zama gari. Mamee ta tuntsure da dariya kai uwani hoo wai gari. Tayi murmushi Allah kuwa. Ki barshi da kayanshi idan yazo sa gyara abinsa. Bazaiji dadin zama nan din ba don mafi yawa idan yayi kwanaki haka to anan yake sauka baya hawa saman sai an gama gyarawa. Da zaki fara yau zuwa gobe duk kin kammala, shiru kawai tayi ta rasa yanda zata nuna rashin amincewar ta, ungo mukullin ta karba kawai. Dukan tara tara kirjinta ya ringa yi. Makeken falo ta tarar daga gefen sa matattakala ce tana lekawa taga swimming pool ne zata kaika da wurin shakatawa wurin kansa abin kallo ne kujeru kala kala group group group. Ta duba dama tabi wata hanya daki ne karo kamar hall da kujeru ta tabe baki meeting akeyi anan ko? Ta dawo baya ta shiga wani daki makeken bedroom yasha kayan alatuta hango kofa ta bude tayi ma kewayen wani kallo ganin jaridu da TV ta zaro ido iyayi..... Watan idan ana kashi ana karatu ko kallo ta tuntsure da dariya tabar dakin, ai wallahi sai naga kwaf kwaf, ta fada wata hanya kayan motsa jiki ta gani ta kale wani keke Tabb ai sai nasha banza Ashe auto ne taji ankwasa da ita guje ana jijjigawa timmmm ta wuntsulo tana haki cike da tsoro ta baro wurin. Sai kuma ta kama dariya, Umm bari dai inyi abinda ya kawo ni. Ta shiga gyara ta dunga canza tsarin komi tana kimtsawa gyaran da ya kaita har magariba abinda ya bata tsoro bedroom dinsa durowowi ta ringa gani da kudi shirye , kasan kafet kudi wasu jakunkuna data bude kudi, tana shirin fadawa kitchen taji kiran sallah tayo kasa da sauri. Mama kada dare yayi Gobe na karasa, tana tsaya tsaya amma ina tayi gida. Washe gari sauri sauri ta gama aikin mamee ta haye saman don ta gama da wuri, ta gyara sosai ko ina ta na yi tana korafi. Musamman kitchen da gani mugun ci gareshi ko ina ka gani kitchen da kewaye an ci ai dole ayi kashi ta bushe da dariya ta gama tsaf ta sa abin kamshi kenan hanne ta hawo da gudu uwani kiyi Sauri ga Alhaji nan inji hajiya........nan tabarta tsaye ta watsa da gudu. Tana isa gaban hajiya yana turo kofa tayi ciki da sauri bai ganta ba, hanne yabi da ido tana saukowa ya daka mata tsawa ke ubanwa kikayo sama? Ni na aiketa mamee ta katse shi. Ya dade falon har mika'il yagama hawa da kayan ya dawo yallabai an gama. Har ka kimtsa ko ina? Ai na tarar da kamar ma yanzu aka gama gyara wurin, Ya watsa hannuwa mamee kenan ya haye sama, gyaran yasha ban ban da Wanda ake masa. Yayi suka bisa gado ya runtse ido yana shakar kamshin dake tashi, Umaimah kuwa sauri sauri ta bar gidan mamee na tsaya ki taya ni kwance tsaraba tana gobe na gani har takai bakin kofa tace af ke gafa waya dazun na bada aka siyo miki saboda tsaren lalura ta buga tsalle toh tayi waje. Tana fita ya sauko mamee wa kika sanya yayi mun gyara haka? Ta zaro ido an maka barna ne? Da a makaranta ne yanda nayi tambayar nan kika tambayeni punishing din ki za ayi. Kai sai kayi yanzu don kaniyarka, ya kyalkyace da dariya ban isa ba my love. Yayi kyau kwarai naga abin wani sabo an kara gyara man dressing mirror an shirya flowers an canza ma komai tsari yayi kyau. To madallah zan ringa sa Wanda nasa yau tunda ya maka. Ya tuno hanne tana saukowa watan ita mamee tasanya. Ta sauya zancen da ina maganar matar da mukayi kace sai karshen watan nan? To ai yau sha hudu ga, zata kara magana wayarsa tayi kara yace ina zuwa ya haye sama. Yau ta makara sakamakon wanki da tayi zaune suke bisa table suna kalaci ta shigo gabanta yayi mugun faduwa, ta shigo sukuku mamah ina kwana..... Ya daka mata tsawa mamar ubanwa baki ce mata hajiya yanda kowa ke fadi? .....ina ruwanka da ita? Mamee ta katse shi rai bace, ta balla mishi harara ta wuce, ya mike wakike yiwa wannan kallo? Tayi ciki da gudu......... *UWAR ABDALLAH* 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣0⃣6⃣ Assshhha dai, mamee ta kalleshi wannan fa abin kunya kake zubdawa kana kaskantar da kanka, ka fita harkar ta ka kyaleta ka daina biye mata, ka ce ko magana babu tsakanin ku meye na tanka mata? Na lura dai kinfi kaunar yarinyar can dani ko? To ki zauna da ita........ Fuuuuu ya haye sama. Ikon Allah ta fada tare da binshi da kallo ga mamakinta taga yana janye da jaka, ina zuwa? Ya mata banza ya fice! Uwani....... Ta kwala mata kira, tana labe jikin kofa tana kallon komai tasan mamee bata taba barin ya cimma mata ta fito da sauri *na'am* Zo zauna, gabanta ya fadi ganin seriousness din mamee din. Kin San zaki mutu ki dubi girman Allah me ya hada ki da umar gashi can ya mun yaji yabar gidan. Kinyi shiru tsakanin ki da Allah na tambaya kiji tsoron Allah bani ba domin wannan kiyayya ta isa, Ta kwance biri har wutsiya bata boye komai ba, ta fara rafka salati tana tafa hannuwa. Kwallah suka zubo mata nasan nayi kuskure wallahi bazan kara ba......shima yayi kuskuren da ya biye miki ke idan yarinya ce shi yaro ne? Ohhh ni jikar Sarakai. To ina kika sami rezar? Ta kara tambaya cike da mamaki. Ta zumburo baki siya nayi ta goma, Sai kawai tayi murmushi kurucchi dangin hauka, shi duk tunanin sa turoki akayi nasan ba Wanda zai turoki ashe ke baki ma san wanene ba. Ta rushe da kuka kuma yace zai 6atar dani. Bazai yi hakan ba. Zaki yi man abu daya? Idan ya dawo zamu je ki roki ya yafe miki ki bashi hakuri zakiyi? Ehh zanyi wallahi. Tayi murmushi ina amfanin rigima irin haka shi yasa naki amincewa da soja saboda zuciyar sa ta banza kullum mutum baya canzawa? .......Burum ya shigo yana ta mazurai alamar mantuwa yayi ya haye sama da Sauri......taso maza muje , taho taho ta figeta sukayi saman fitsari ne kawai umaimah bata saki ba. Dai dai zai sauko rike da wani *file* ya zaro ido mamee wai ya kike so dani ne kina son kureni ko? Sai kawai umaimah ta zube kasa, Don girman Allah kayi hakuri duk abinda ya faru kuskure ne na tuba bazan kara ba........ Da kika ga dukiya zaki saduda? Wai mamee ke bakisan talaka idan yana son abinka ba komai zai iyayi? Haba umar ka fahimci yarinyar nan ku daidaita,.......da wa? Wallahi badon kudi nake baka hakuri ba na rantse bazan kara ba. Mtseww zai wuce mamee tasha gabansa... Wallahi zan harba yarinyar nan kasa mamee ko ki matsa na tsani gidan nan ya fada cikin karaji. Umaimah ta kankame jikin ta cikin firgici. Ban isa dakai ba ko? To karka tafi ni zan tafi kawai yaga hawaye sharrr...... Kuka????? Ni kike zubdawa hawaye mamee kan wannan yar iskar yarinyar? Ya dafe kai ya fasa wata kara umaimah ta zabura ya damko ta gidan ubanwa zakije kina neman jefani *wuta* kawai yaga mamee ta juya tana sauka, ya saketa ya ruga ya riketa, mamee .....ta fizge kuka takeyi sosai hankalinsa ya gama tashi, ta tafi zata fadi shida umaimah sukayi rige rigen tallabo ta, ta ingijeshi ta rike umaimah. Mamee me kike shirin yi? Ta zaunar da ita bisa kujera, ya durkusa kiyi hakuri na tuba ki daina zubda hawaye saboda ni sai kawai shima ya fara kwallah, tsoro ya kama umaimah ita kam ta gama shiga uku, Duk illahirin jikin ta rawa yakeyi kamar mazari, Zan barma gidan ka, kaki yarda dani yarinyar nan ba macuciya bace kayi bincike nayi, na tambayeta, na ce ta baka hakuri tamun biyayya badon ranta yaso ba tayi shin haihuwar ta nayi? Sai kai dana haifa umar ina fada kana mun tsawa...... Ya haye cinyar ta yana kuka zanyi wallahi zanyi mamee na tuba. Na kuma hakura wallahi na miki alkawari. Kuka yakeyi kamar karamin yaro, umaimah kam jingine take da bango tana sharbar Nata, ta dago shi tana goge mishi hawaye kayi alkawari? Nayi wallahi. Tayi murmushi shima yasa hannu yana goge mata kwallah , Allah yayi maka albarka. Can kasan zuciyar sa wata muguwar tsana ce da kiyayyar umaimah ji yakeyi kamar ya hadiye zuciya, simi simi tayi ciki. Washe gari tunda safe yace ya tafi office mamee tasa a gyara mishi daki saboda mika'ilu yaje ganin babansa baya lafiya, Umaimah jinta takeyi kamar sallah tunanin ta tunda anyi haka shikenan sun daidaita da *madaki* Tana shiga mamee ta fada mata sakon sa, amma sai bata fada mata cewar ba garin ya bari ba. Sai kusan hudu ta nufi gyaran saman ta gama da ko'ina sannan ta shiga bedroom dinsa. Yana ta sauri ya shigo yana saurin ya watsa ruwa kada a kira magrib, dabi'ar sa ce da ya hawo sama zai fara balle maballin riga yana isa falo zai cire yanda daya shiga daki ya jefar a gado, Ta yaye zanin gadon ta bude drawer inda ta dauko sabo rannan kenan taji motsin an murda kofa da sauri ta duba dai dai ya shigo ya ce what????? In my bedroom?? In ina ta kama kafin tace mameee ce tace inzo in gyara. Ta tunkaro shi zatayi waje ya maida kofa da karfi yasa key............. *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣0⃣8⃣ *UWA MAI BADA MAMA YOU ARE THE BEST MOM EVER AUNTY HADIZA YAHAYA TUKUR MAMAN AMINA I LOVE YOU SO MUCH YA ALLAH YA KARA DAN KON KAUNA TSAKANIN KI DA UNCLE YA SHIRYA MIKI ZURI'A* Mamee idanun ta nakan waya bata lura da kidimewar da umaimah tayi ta. Tana ci gaba da latsa wayar cikin laluben wata number ta ce maza kije ki karbo babu ruwanki da shi da kin karbo ki sauko abinki. Ta karasa maganar tare da juyowa ta kalleta. Tsayi tsaye tana zare ido mamee ko dai muje tare dake.......... Bani hawa sama yanzu don kaniyarki. Kije ki karbo idan kuma kin yafene to. Tayi sukutii......kafin dabara ta fado mata, ta shige can kuryar dakin mamee ta dauko wayar ta don koda yana kara kulleta ta kirata, tasanya cikin zani bisa ciki taja riga, ta bude wata durowa inda take ajiye kayan gyaran kumba ta Ciro reza ta damtse a hannu, ta fito mamee na zolayar ta *yau uwani baki har ummarun kunne ta lissafi ta kare za'a sha kudi* Duk sukayi dariya ta haye saman, baya ko ina ta duba, gabanta ya kara faduwa, kilibabbe yana daki kwance kamar mace duk ya shirya kayan mata cikin daki shi ga mai kudi ta yatsina fuska da ta6e baki sannan ta banka kofar, ya zabura zaune. Yana ganin ta ya daka mata tsawa, *Are you mad*? ke baki iya sallama ba kuma bazakiyi knocking ba a baki izini zaki fado man daki haka gatsal idan kika tarar dani cikin wani hali fa? Wane hali bayan wannan dana sanka dashi na masifa? Daga bude kofa ka hayayyako mani da bala'i kamar ka haifeni....... *are you serious?* ya fada tare da dirkowa . koma kiyi sallama. Ta rike kugu bazan koma ba yau dai kam sai kuma a tari wani jikon ya tunkaro ta a hasale ta fara kwana, suka fara zagayen dakin yana son tsafko ta taki tsayawa, kaban kudina in fita ni yau naga jaraba kai kullum kamar kana jirana? Jiranki nake don ubanki ya yunkoro zai kamata ta haye gado tayi tsaye. Ni kike takawa gado? Ya zaro ido naje na taka kaban hakki na mana in tafi ko zan tsaya ne ka gana man azaba? Yayi tsalle ya haye gadon ta dirko kasa hannunta ya kado wata robar mai da bai rufe dai dai ba a dressing mirror ya fara zuba. Rezar da ke hannunta ta yanketa Sam ta manta da ta dauko reza tayi saurin wurgi da ita jini ya fara zuba ya zaro ido muguwaaaa yau ma zuwa kikayi ki yanka ni? Ta balla mishi harara hannunta dafe, haka nan zaka kirani inzo ne ta kai duba ga hannun ta, Rannan ma mamata kayi..... Ya mameta ya dirko gabanta tare da damko ta amma sai sulbin mai ya kwasheshi dashi din da itan suka fadi rikichaaaaa tayi baya ya haye ruwan cikin ta. Na shiga uku ta fada da karfi. Jikinsa ya wani bada tsammmm... Tunda yake a rayuwarsa bai taba rike hannun mace ba, ko gaisawa ba yayi dasu a duk inda suka hadu kuma ko wace kasa yaje, kallabin ta ya cire an mata sabuwar kalaba kana duk ta rufe mata fuska, ya kura mata ido *Me yasa yarinyar nan bata tsoro na ne?* Tayi kichin kichin malam dalla daga ni kada ka karya ni. Ko motsi baiyi ba ya kura mata ido ta samu da kyar ta zaro hannun da ta danne. Tayi tayi ta tureshi ta kasa, Kai dai mugu ne wallahi ta fada da kyar, da azaba ta isheta sai ta wawuro kuncinsa da karfi ta cije, ya wuntsila a wahale yana fadin kai kai kai ni kika ciza? Ta dauki kallabinta zata kwasa a guje ya riko hannunta da karfi, ta fado bisa shi sai kawai ta rushe da kuka. Ya kura mata ido kawai yana kallon ta. Kuka takeyi tsakanin ta da Allah, sai ya saki hannun a hankali ya tashi itama ta mike, ya kalleta zan baki kudin ki ne karki gudu ya fada a hankali kawai ya rasa menene yasa jikinsa yin sanyi. Yana juyawa ta kwasa da gudu zata bar dakin ya bita ya riko, ke me yasa kike da kafiya? Ya daka mata tsawa tare da sanya ma dakin key, ya saketa ya juya ina zakije hannunki da ciwo haka ko baki ga yanda kika bata man jiki da daki da jini ba? Hello gaya nan ya kulle daki zai dakeni......... Ya waigo da sauri yaganta tsaye tana waya, sai kawai ya juya yaci gaba da abinda yakeyi, first aid box ya dauko...... Zo in miki dressing. Bana so, Yayi mata wani kallo cike da takaici don zan taimaka miki? Bana so da in baka hannun nan ka taimakeni na gwammace in tsaya haka jinin ya tsiyaye. Zai yi magana yaji bugun kofa *madaki* bude kada ranka ya baci........ Ya kalleta rai a bace kawai ya wuce. Da sauri ta shigo me ta maka zaka dake ta? Karya takeyi gashi nan yankewa tayi zan taimaka mata take man rashin kunya zata fita na rufe kofar shine fa naji tana kiranki a waya, Ya akayi ta yanke daga karbar kudi? Ta daga mishi tsawa, zaiyi magana kana hauka ne? Menene ke damunka wai? Ganin ranta yayi mugun baci yasa yayi shiru kawai ta ci gaba da fada sosai ya kura ma umaimah ido ko zatayi bayani amma tayi shiru, Mamee tambayar ta ina ta sami reza wallahi da abinta ta tazo, na rantse da Allah babu ruwana. Ya daga hannuwa sama yanda yara keyi. Uwani ina kika sami reza ya akayi kuma kika yanke? Gabanta ya fadi. Anya zata fada wa mamee wurin guje guje ne? To me yasa su hakan rashin sallamar da tayi kuma ta bishi da rashin kunya....... Wallahi babu ruwana ai kinji tayi shiru, kai wannan wauta taki uwani Allah ya rabaki da ita. Ka hanzarta daure mata hannun na baro baki ciki. Ta juya har ta kai bakin kofa ta tsaya ganin ta biyota, ta ruko kunnenta ina zaki bini haka je ya daure miki hannun ki sauko ina jiranki zaki raka ni unguwa. Taja kofar. Ta isa gun dan akwatin ta fiddo bandeji ya rike mata hannu. Sakarni zan yi da kaina. Ya kura mata ido wallahi mamaki take bashi ba za a saki ba ya damke hannun tayi tayi ta kasa kwacewa, ya da dauko auduga da spirit ya goge jinin da hannu daya hannu daya rike da ita, Mtseww na tsani shisshigi wallahi, na ce bani so bani so kamar dole, ya kalleta har zaiyi magana sai kawai ta bashi dariya . yayi Dan murmushi kadan yaci gaba, ya daure wurin. To ka sakeni tunda ka kare malam........idan kika kara magana zan dauko rezar can da kika yar in farfade hannun kin San kuwa zan iya...... Kut ta hadiye wani miyau a tsorace. Ya kusa sakin dariya ga tsinannen tsoro ga jan fada ya fada a zuci. Yasa hannun aljihu ya dauko daurin kudi na dari biyar biyar ya wurga mata a jiki sannan ya saki hannun *kilgi dubu talatin kudin aikin ki* Ta yi saurin kallon sa Koni yaron ki ne da zan kilga in baki?. Ta kalli kudin ai duk kwara biyu dubu daya kenan kada ya fahimci bata iya lissafi ba ya kara rainata sai kawai ta kwance, ya kura mata ido ta daddage tsakanin ta da Allah tana hada biyu biyu tana cewa *daya, biyu, uku, hudu....* ke yi a zuci kin cika mun kunne. Ta balla mishi harara Da Allah ni ka rudani. Ta kara lalowa sai kawai ya bushe da dariya. Ta kara hararar sa taci gaba sai da ta kai sha takwas ya ce malama kina batan lokaci kilga kamar kina lissafin gero...... Innalillahi ta rafka salati ta watsa mishi kudin ungo kilga tunda bazaka iya yin shiru in kilga ba. Ya daure fuska ya watsa mata kudin itama wallahi sai kin kilgi kudin ki yau ko ki rasa. Mtsew ta buga tsaki. Mamee ta gaji da jira ta kirata a waya ya fige wayar yasa hands free uwani ko in tafi? Tafi mamee ta na gyaran daki ne. Zatayi magana ya to she mata baki, Saboda rashin imani zaka sanya ta aiki ga yankewa, ya kalli umaimar ita ce ta ce zatayi..... Sai ka biye mata...... Hello hello mamee ba 'aji ya latse wayar. Yaudaraaaaa to wallahi sai na fada mata karya....... Ya buge bakin idan kika zageni sai kin wahala kilgi kudin ki kiban wuri. Ta zumburo baki mugu. Ta fada ciki ciki, Me kika ce? Ban sani ba ta fada tare da fara kilga . Kallonta yakeyi tsakani da Allah. Tana da kyau yarinya ce karama. Ya danyi jimm may be tayi 14-15. She's preety and crazy. Yarinya karama amma ta raina shi. Wai me yasa bata tsorona? Kawai sai yaji yana son Sanin amsar dalilin da yasa ba ta tsoron sa........... Qala kus kaci kanka ta tofa mishi miyau. Yayi firgigi ke kina hauka ne? Ni ce kai, tun dazun ina cewa na gama ka kuran ido. Ta watsa mishi ragowar dubu ashirin dinsa, ga ragowarka ta damtse nata zata mike. Ya janyo ta ina zaki? Zaki fidda mun dubu goma wacce zaki ringa biyana kayana da kika 6ata a baya ko zan dauki asara ne sabbin shaddoji na ko wane kin wulakantar? Zaki fidda dubu uku kudin mai na dana kaiki gida ranar da kikayi dare, zaki fidda dubu biyar Wanda shima zan ringa cirewa yankan da kikayi mun nayi asarar jini na, sai dubu biyu kudin energy na dana yi waste yau kika sanya ni gudu a dakin nan. Sannan Zan fidda dubu biyar bisa ga alfarmar baki San dokar ba daga yau zata fara, duk rashin kunya da maganganun da zakiyi man nan gaba zan fitar da kudin su sai ki ware dubu biyar kiban sauran................... *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘 [1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣0⃣9⃣ *KO KUN SAN INA DA WATA BOYAYYAR MASOYIYA A SOKOTO? DON ALLAH KU SA MATA ALBARKA SUNAN TA BILKISU ABDULLAHI GADA INA MATUKAR GODIYA BILKY WALLAHI TA NA GYARA AURE SOSAI.* *AI KUN SAN ME NAKE NUFI TUNDA NA AMBACI SOKOTO DA GYARA KUMA*😉 Jikin ta yayi mugun sanyi, zuciyarta ta ringa tukuki, a yanda taji tarihin biyan ma'aikatan gidan a dubu talatin ita ce mai karamin albashi ma kamar yanda tafi kowa karancin aiki, dalilin biyan ma'aikata albashi mai tsoka shine don a fidda musu kwadayin sata a gidan, yana daya daga cikin gargadin da akeyi ma duk wata mai aiki banda sata. Amma ga mamakin umaimah sai dai taji labari ita kam ba a mata ba, wannan wane irin rashin tausayi ne? Ko yaya Abba ya ce ta ware mishi dubu cikin albashinta. Ta runtse ido *Ya Allah duk sharrin da ke cikin wadannan kudin ka fidda mun shi, ka kuma kareni da duk wata fitina* Ya kura mata ido jikin sa yayi mugun sanyi wani tausayi ya diri zuciyar sa bai daya, Ya kalleta *sharri?* wane sharri kuddin ke dasu? Yanayin muryar da yakeyi ma mamee idan yayi laifi ya bada hakuri yayi mata. Ta kara tsanar sa a zuciya ko kallon sa bata kaunar yi. Ta mike tsaye ya daga hannu zai kara fizgota ta fincike ta watsa mishi dubu ashirin da da biyar jikin sa. Wannan kudin tattare suke da sharri don ba da zuciya daya kaban ba yau ka tabbatar mun da kai din mugu ne baka kuma da tausayi.....ya yunkura zai kamota tayi baya, ka lissafa ka ajiye magana yanzu na fara, kasan dukiyar taka bata gama isar ka ba ka kawo ma'aikatan da suka fi karfin ka? Can kudi, can kudi can kudi duk basu isheka ba sai ka ci hakkina? To kayi a banza wallahi dukiyar ka bata dada ni da kasa ba aiki ne ba kai nakewa ba wallahi kasan wacce ta kawo ni to darajar ta ko naira daya ka bani zan karba haka kuma zan iya mata aikin kyauta amma wallahi kai ko zaka biyani miliyan dari inshigo gidan nan kawai in fita kasan kayi kadan......wuf ya chafko ta..shut up!!!!!!! Ya daka mata tsawa. Ko gezau batayi ba, ji hargagi to cinyeni damisa ka tsaya ga yar cikinka kana wannan kurarin duk bai isheka ba aikin da nake kuma su ka sanya wa ido.......waje ya bankada ta ya janyo kofa ya rufe, Ya dafe kansa hannuwa biyu biyu ya runtse ido *Why why why????* kalmar da yake maimaitawa kenan. Ya kife bisa gado look at maganganun da yarinyar nan ke fada man me ta dauke ni wai? Ya runtse ido why all this rainin? Tafe takeyi tana rokon Allah ya kubutar da ita daga sharrin mutanen gidan amma abin mamaki gidan ba kowa yara duk sun tafi islamiya, goggo jummai kuma taje suna, goggo hansatu ce kadai zaune a tabarma tana jin redio, tayi sallama ta shigo, ko da ta dago taga umaimah sai ta kawar, ko ajikinta domin ta saba da hakan da kuma rashin bata abinci a gidan tun da ta fara aiki kullum ta dawo bata da kwano. Ta zukunna can karshen tabarma goggo barka da yammaci. Ta dalla mata harara an dawo? Eh, gashi anbiyani yau ta mika mata dubu biyar jikin ta na rawa, tana ganin kudi ta wangale baki, haba? Nawa suka Baki? Tayi shiru don ta gani da kanta sai kawai taga ta mike tsaye ta makure jikin ta taji ta inda dukan zai fara, sai kawai taga goggo na tikar rawa. Ta zaro ido ta bude baki. Wane gidan arziki ne kike aiki haka? Umaimah tayi shiruuu au kai gidan fa ba'asan ina aiki gidan *Umar madaki* ba fa kawai sun tsaya a ina aiki gidan matar tazo 'yar uwar hajiya basu san wacece ba. Da na kawo dubu talatin din nan goggo yau sai ta goya ni. Mugu ya mun bakin ciki....... Ta dafa ta sauraranni ungo dubu boye taki ce, idan kowa ya dawo kice dubu biyu ne albashin ki gata na ware har babanku kice haka ake biyan ki idan za a raba kuma damu ciki idan sun dawo. Duk wata zan ringa baki dubu ina daukar dubu biyu ina Sana'a kinga nice matsayin uwarki idan kin tashi aure 'yan siyayyar uwa ni zanyi. To goggo umaimah ta fada tana washe baki da ajiyar zuciya. Bari in shiga wurin hajiya in dawo....jeki maza adawo lafiya. Ohhh ji goggo anga abin duniya, ta tabe baki ta fice zuciyarta fes! Ta biya shago ta siyo jikkar klin babba ta dari uku ta kaima hajiyar. Ta ce kisa albarka an bani albashi ko kewaye kya wanke. Ta dunga sa mata albarka, akwai kudin ki fa wurina. Hajiya kiyi amfani dasu. A a wallahi ai na rantse bazan taba ba. Tayi murmushi ajiye mun tsaron lalura, kayan ma na dauki atamfa daya sauran da zaran naji zakuyi wani abu zan dunka miki ince ni na miki ko kuma can gidan *madakin* na sansu da shagali. Tayi godiya ta tafi ta siyo lalle na dari biyu. Ta fito kenan ta hadu da yaya Abba. Ta kwala mishi kira ta mika mishi dari biyar ba zato ya buga tsalle don yanzu ya gama maular hamsin. Ta ce albashi na dubu biyu ne nawa aka raba aka bani na baka kasan bazaka sami dubu.....ke share na gode ya watsa da gudu. Ta bishi da kallo wani abin sai aikin shaye shaye, Kai kace gidan biki ake ko suna tun a kofar gida take jiyo hayaniya na rabon kudi. Ina ma yaban kudina chif, yau da nasha dadi gidan nan ta buga tsaki mugu kawai, Dari biyu ta samu cikin kasafin da akayi tana karba ta yi daki ta kwaso tulin wankinta ta hau yi. *Madaki* kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye abubuwan da suka faru yau ke dawo mishi daya bayan daya, ko abinci ya kasa ci da ya zauna ko ya kwanta sai ya tuno gashi nan bisa umaimah ya haye ta da suka fadi, Ya fada kewaye ya sakar ma kansa shower amma da ya runtse ido hakan yake gani. Da ya bude sai maganganunta su dunga tariyo mishi. Ya dunkule hannu ya hada kanshi da bango ya fasa kara *wai tunanin na uban meye* Ya ga wannan bata fissheshi ya fito ya koma falon mamee amma bata dawo ba, ya dauki waya Mamee wai kina ina? Gani a hanya lafiya? Ni kadai ne fa a gida......ina tafe ai nace kayi aure kakiya da kana da matarka yanzu wane kewa? Ya tsinke wayar kawai ya runtse ido *she won't understand* Yan aiki keta kara kaina ya kalli wannan ya kalli waccen Sam ita bata wannan safa da marwan aikin ta tafiyin na zaune ko tsaye bata yawan motsa jikin ta .......ya buga tsaki kuma fa da yarinyar nan ce da yanzu mun gwabza fada, to wai meke sanya mu fadan? duk sai suka bashi haushi ya daka musu tsawa *kar wacce ta kuma fitowa idan ta shiga wacce ta fita kuma karta dawo* Zuwa yayi falon don ya sarara da tunanin umaimah amma suna Neman rikita shi. Me yasa na hanata kudin ta duka? Ranta fa ya sosu, da alama bakinta yaso furta wani abu na lura da hakan, gobe me zata fadawa mamee? Nasan tabbas sai ta tambayeta. Ba karamin 6aci ranta zaiyi ba kuma yarinyar nan tunda ta kirani da mugu babu dalilin da zaisa ta 6oye mata shaida zatayi man. Ya danna abin kiran yan aiki, agurguje suka karaso don basuji dawowar mamee ba . Waye ke da number uwani? Duk suka ce babu. Ya ce su tafi. Mamee na shigowa ya karbi wayarta, ya kuwa yi sa'a uwanin tayi saving da no. Ya na dauka yayi sama da sauri. Ta bishi da kallo. Ta girgiza kai agogo sarkin aiki wani abun ya tuna baiyi ba tayi ciki. Gidan yau gaba daya cikin nishadi ake. Umaimah tsumu tsumu ana fira da ita hada su dariya. Abin kara armashi kowa ya karbi number ta sun sa mata nasu. Mamaki kawai takeyi gidan ya zame mata sabo. Wayarta tayi kara har sau biyu taga number kawai ba sunan. Mamee kadai ke kiranta tayi tunanin ita ce, duk akayi tsit, hankalin kowa ya dawo kanta, tana dauka ta ce mamah biki kikaje halan naji shiru shiru....... Ke natsu magana zanyi dake ya daka mata tsawa, tayi jimm Gabanta ya fadi . Kowa ita yake kallo Gobe idan kinzo.....eh mama..To sannu da zuwa ba komi goben da wuri zanzo.... Ke saurareni madaki....ta latse wayar. Ya hasala *What?* ya zaro ido yana kallon wayar. Ya kara kira zata fara ringing kenan yaga *number busy* Ransa yayi mugun baci ya kara kira a hasale *the mtn number you are trying to call is currently.......* yayi wurgi da tasa wayar.............. *maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘 [1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣0⃣ *INA JIN SAKON NIN KU MASOYANA INA GODIYA SOSAI ALLAH YA YABAR SO DA YARDA LOVE YOU WITH ALL MY HEART*😘😘😘 .....iPhone X ta tarwatse tayi rugu rugu amma ko ajikin sa, me yarinyar nan ke nufi lallai bazan dauki salon wulakncin ta ba. Ya mike ya fara sintiri a daki. Umaimah ta hade rai tana maganar zuci, yau ni naga jaraba, shin mutumin nan bazai kyale ni haka ba. Ina amfanin abinda baya taba wucewa duniya ya dameni ya addabeni bana son hada shi da mahaifiyar shi amma tabbas ya ci gaba da takura man zan fada mata. Haba! Saboda bala'i har ya samo nomba na? Abin nan duk ya isheni kawai ina dagewa ina rama abinda yakeyi ne amma har cikin zuciyana ina jin babu dadi abu yaki ci yaki cinyewa. Mtseww ta doka tsaki....kowa ya kalleta. Nan da nan ta hankara tayi murmushi kawai tana Sosa kunne. Tun karfe bakwai ya sauko ya zauna falon mamee ya kunna computer kana latse latsen bogi yama rasa me zai latsa, kadan kadan ya duba agogo, da ya ji motsi kuma yayi saurin daga kai. Mafi yawan yan aikin gidan anan suke kwana da sun fito suka ganshi zaune duk wacce ta wuce bata kara dawowa. Ya buga tsaki, me ya tsayar da ita ne yau har takwas ta kusa? Ya fada yana kallon agogon hannunsa. Ya runtse ido wai me yasa na damu da tunanin yarinyar nan? Tun jiya na kasa sukuni. Ya kara buga tsaki kai wallahi bata isa inyi tunanin ta ba, kawai ina tsoron takai karana ga namee.....lafiya kake faman doka tsaki *madaki?* me kakeyi kasa da sassafe haka. Ba komi mamee kawai ina wani aikine. Antashi lafiya? Lafiya lau yaushe ne tafiyar ka Germany? Ya kalli a gogo *yeah am preparing for it* Ya bata fuska, ta kawar da kai da alama yau miskilancin yakeji ta fada a zuci. Ina maganar mu karshen wata yayi. Kar ki damu mamee ina kai 'I'll let......burum aka turo kofa maganar tashi ta tsaya chak! ya bita da kallo...... Ta wangale baki kamar kullum tayo kan mameee tana yar dariya, itama tuni hankalinta ya koma kanta tunda ta shigo. Ta zukunna gabanta tare da dafa cinyoyin ta, ina kwana? Lafiya lau uwani yau ma kasan kika taho duk da ansha kudi jiya? Ta kyalkyace da dariya tabb yau hayar dan adaidaita nayi ni kadai na wataya. Ta bude jaka ga salalar ki na siyo miki lalle da tsamiyar biri mutuniyar ki. Mameee ta kyalkyace da dariya sosai *Uwani tawa* Lalle dai kika siyo mun tsamiyar biri ai daman kece kike shanye mun ita. Allah yasaka da alkhairi uwani na gode na gode, ta kalleta tana yar dariya tare da mikewa tsaye lallen ake ma godiya? Yayi sakakaka.... Yana wani irin mamaki wannan wace irin mayaudariyar yarinya ce, duk waftar da nayi ma kudin shine hada siyo wa mamee tsaraba? Ko kallon shi batayi ba tayi ciki abinta, tana zuwa bakin kofa ya daka mata tsawa ke!! Tayi ciki sarai tana jinsa. Ya mike....kutumee... Kai madaki ina zaka? Mamee yarinyar nan tafi karfin ta gaisheni? Zauna ya hakuri in don uwani kilan ma bata ankara dakai bai. Ta daga baki *Uwani*.... Na'am ta fito da sauri. Ki gayar da *Madaki*......ta barshi bana so, ya fada a hasale Ina kwana, ta ce tare da juyawa Ya kara kulewa mamee baki son gaskiya bazan dauki raini bafa, Ka faya daukar komi da zafi na rasa wannan fitina *madaki* ina CE ta gayar da kai ko? Amma kina ganin na kirata tana jina tayi ciki ko? Kayi hakuri zan mata fada. Umaimah na jinsu ta tabe baki *sunana ke* da zan amsa. Ai bazai kyaleni ba ko? To wallahi sai dai ya hanani albashi amma da ya mun zan mishi. Aka hada kalaci kamar kullum mamee tayi tayi umaimah ta fito suyi kamar yanda sukeyi idan yayi tafiya ta ce ta koshi. Ya kara kulewa kawai ya tashi fuuuu yayi sama. Ta bishi da kallo tun yana karami yake da wannan muguwar zuciyar har yau. Saman ma ya kasa zama, menene dalilin yarinyar nan nakin daukar wayata jiya? Zaune take tana guyiguyar kashi gaban mamee cikin kalacin da suka rage suna labari mamee nata dariya, ya sauko cikin kananan kaya tana ganin saukowar sa tunda tayi kasa da kai bata dago ba kada ma yace ko ta harareshi. Saukowa yakeyi idonsa na kanta tana ta cin namanta, Mamee zan fita office. Adawo lafiya. Ta ce dashi har lokacin bata gama yar dariya ba. Muje in baka sako. Sukayi daki, umaimah na gamawa tayi baya, ko da ya fito bai ganta ba yabi wurin da harara ya wuce. Sama sama yakeyin aikin duk motsin da zaiyi sai yaganshi kwance bisa umaimah. Ya mike tsaye shi kadai a office. Umaimah kuwa tana can ita da mamee suna ta labarin su na nishadi a bedroom babu ko hijabi kanta daga zani sai wata yar shamudaddar riga mai kama jiki. Ke bari in shiga kewaye kinji kada kisa inkai ga na saki fitsari. Sauri kawai yakeyi baya son ya tarar har ta tafi gida, ya shigo ransa ya baci ganin ba kowa falo ya wuce dakin mamee ita kuma mamee na shiga ta mike ta shawo ruwa. Tana bude kofa shima ya kawo da sauri suka afka ma juna tayi taga taga zata fadi ya tallabo kugunta ta dawo jikinsa ta daki kirjin sa sai kawai ya maida hannuwansa bayanta tare da runtse ido...... Ta ingijeshi ya kalleta ido jawur, ke me yasa baki da natsuwa idan kina tafiya? Maimakon ta bashi amsa kamar yanda yayi tunani sai kawai ta raba shi zata wuce, ya finciko ta magana nakeyi miki. Ta kalleshi sake ni. Bazan saki ba jiya na kira kin katse mun waya ke ga marar kunya ko?.........Uwani. Mamee ta kwala mata kira, Yayi saurin sakinta dayaji motsin bude kofa, ta kallesu a tuhume, yaushe ka shigo? Yanzu, Gani mamah, ina kika je? Ruwa zan shawo shine........ Yunwa nakeji mamee aban abinci. Ya datse mata maganar. Uwani dauko Qur'an din nan ki kara maimata mun. Ta wuce ya bi bayanta tare da juyowa ya na hararar umaimah itama ta rama ta wuce. Yana gama cin abincin ya hau sama, ita kuma tana gama biya wa mamee sauri sauri tabar gidan. Ya sauko da sauri please mamee sa agyaran bedroom please yanata waige waige. Ta tafi gida kuwa uwani . Ko a sa mansura? A'a , ya ce a takaice Ya tashi kawai. Abin mamaki yau umaimah tare da lubabatu sukaci tuwo kwano daya. Gidan an rage tsangwamar ta. Gidan Alhaji yakuba tayi fira yau sai goma ta wuce ma ta shiga gida. Karfe takwas ta isa yau, a bakin gate take jin mamee ta fita zuwa asibiti. Daman duk sati takanje ziyarar marassa lafiya. Haka shima madaki. Nan ta fahimci farkon haduwar su dubiyar ce yaje. Ta shiga gidan tana dan tsalle irin na yara murna fal acikinta madaki baya nan. A kitchen ta tarar da mansura . Suka gaisa ta ce da ita, hajiya ta ce a fada miki ta tafi asibiti ki gyara mata kayanta kuma ki hau sama ki gyara ma 'Yallabai. Ta ce juya toh bari in gyaro saman kafin su dawo nan duk mai sauki ne..... Ta bita da kallo kamar ta ce mata bai sauko ba sai kuma ta kyaleta. Ta dauko mukulli inda mamin ke ajiyewa tayi saman da sauri tana bambami ai bazan kara yarda mu hadu ba har ya haye man in kasa hakuri, Ko ina karara kamar kana cikin fridge ta tabe baki shi kam sanyin nan bai masa lahani ta murguda baki tijararre, ta bude kofar ta afka abinta, duk ya zubdo kaya cikin wodrop din sa ta isa tana linkewa tana kara shirya masa..... Taji burumm an bude kofa a tsorace ta duba. Daga shi sai towel gabanta yayi mummunan faduwa idan ta ce ta fito rikota zaiyi a hakan, tunda tayi mishi kallo daya tayi cikin wodrop din da fuskarta , tana jin takun sa bayanta jikinta ya dauki rawa, A gidan Ku ba 'a koya miki tarbiyya ba? Ina kika sami mukulli kika shigo man daki? Um..um.. Wallahi nayi tunanin tare kuka tafi ta fada kamar zatayi kuka , Ya juyo ta karfi ta fuskance shi jikinsa sharkaf da ruwa. Ta kalleshi cike da takaici ta mayar da kai kasa idanun ta sun kawo ruwa, ke baki da biyayya ko kin raina ni baki ganin kimata da mutunci na, ya daka mata tsawa ta zabura tayi baya ya bita jiya dama cike nake dake ina ke har kin isa 'yar abun nan dake zaki kashe man waya? Yanzu kuma kin dauko key kin shigo man daki ........ A hasale ta dago, in ba cin hajiya ta bar sallahun inzo in gyara ma daki me zai hawo dani sama an fada ma ina sha'awar nan bangaren ne? Ya dan ja da baya ganin fuskar su dab da juna, ka fiye neman rigima da rashin son a zauna lafiya, ka kwashe mun albashi na kyaleka me zaka ce dani da ka kira waya? Ina ruwan ka dani da zaka kirani a waya ko kai nake ma aiki? Ka fito na maka rantsuwa akan bansan kana nan ba amma baka yarda ba tsoron ka nake ji da zan ma karya? Ka isheni da masifa da bala'i ka haifeni ne? Ta buga tsaki ta raba shi zata wuce wuf...ya chafko hannunta tare da murdota ta dawo da karfi bisa kirjinsa, ya hada da hannuwan nata ya matseta a kirji. Wa kikeyi ma tsoki? Ya matseta kwalla suka shararo mata ta fara shasshhekar kuka.....tambayar ki nake ya sha mur. Ka..ka..ka..kyaleni in yafi ta fada cikin kuka muryar ta a sarke ya tsareta da ido yaki sakin ta. Komi ya gani? Sai ya ingijeta tayi baya dai dai lokacin mamee ta turo kofa. .......... *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣1⃣ .....wallahi nasan za ayi haka duk laifin na mansura ne. Umar baka da hakuri ko kadan...... Ta shigo tana bambami, Naji jiya kana son a gyara ma daki shine nabar sallahu amma bazata kara hawowa saman ba daman ni ke tilasta mata muje uwani.... Mamee yarinyar nan fa rashin kunya takeyi mani ina fada tana fada dubi jikina kawai ina fitowa naganta ciki ba halin in tambayeta? Na fada mishi kece kika turo ni har rantsuwa nayi mishi amma bai yarda ba....anki a yarda din. Mamee ta banka mishi harara, umaimah tayi gaba abinta, ai bazata kuma zuwa ba sai kayi hakuri da gyaran su mansuran ganin kana yabawa da natan ne yasa nake tilasta mata..... Au ni yanzu laifi na kika gani? Don me zanga laifin ka tunda kai ta tarar?... Mamee....ta nuna shi da yatsa rai a 6ace tunda ka nuna ban isa da kai ba kaje madaki abinda duk ka iya kayi. Yarinya marainiya ba uwa ba uwa, inda take bataji dadi ba nan din ma ka takura ta ka hana yar mutane shan ruwa? Kai haka akayi maka! To wallahi kaji tsoron Allah na fada maka.....ta fice jikin sa yayi mugun sanyi Tabbas yau yarinyar nan batayi niyyar biye mishi ba kureta yayi. To ai kuma ni shirun nata ke ban iya jurewa. A gurguje ya shirya ya sauko sai mazurai yakeyi ta inda zai ganta, Simi simi ta fito tana goge kwalla fuskarta duk tayi ja. Kawai sai yaji wani iri alamar rashin yin daidai. Ta saci kallonsa kawai ta gittashi ya bita da kallo.... Yasan ko yabi ta wurin mamee shareshi zatayi sai kawai ya fice..... Duk tayi sukuku ranar har yanzu gabanta bai daina faduwa ba. Ita bata taba ganin babban mutum ba kaya ba sai yau. *madaki nada kyau amma ba shi da kirki* matarsa ta gama shiga uku ta fada a fili. Mansura ta sameta ta bata hakuri ta ce ba komi. Tunda na gama mamah zan tafi gida. Ta kalleta a nutse zo nan uwani ta kamo hannunta tare da zaunar da ita bisa kujera kusa da ita. Kinyi sukuku idan kika biyewa madaki ko ruwa bazaki sha ba, haka yake kwanaki da ya taso wata mai aikina dole ta hakura da aikin wai kazama ce, Ke kuwa yayi ya gama muna nan tare in shaa Allah aure ka rabamu, Tayi murmushi kawai. Duka fa yanzu karfe biyu ki yi zamanki kinji? Zatayi magana ta ce af! Ke dauko mana tsamiyar birin nan mu birirriketa sai ta kwashe da dariya. Shi kenan ta wasanshe Suna sha suna raha kamar kullum, ya shigo rike da jakar *system* din sa. Tana ganin sa jikin ta yayi sanyi. Aaaaaaa mamee kurmusun me akeyi? Ya fada idonsa na kan umaimah yana kallon yanayin yanda take tsotsar abin a bakin ta. Murmushi mamee tayi kurmusun tsamiyar biri, A bani in shaa... Ta dubeshi da sauri ganin ya miko hannu, ta ce uwani mika mishi ta fada tana yar dariya. Af kinga ina zuwa inji mamee ta mike ta shiga ciki da hanzari alamar wani abu ta tuna. Ta dauko ledar ta ajiye mishi kasan kafafun sa ta barshi da hannu sake, A hannu zaki ban. Ta dauko ta mika mishi, tare da mikewa zata bar wurin yayi saurin riko hannun ta, Wai kai idan ba ka taba jikina ba baka jin dadi? Ya yi sauri ya saketa to ki koma ki zauna sannan kidaina gigin matsawa ko ki tashi daga inda kike matukar ina miki magana..... Yanzu magana kake mun? Ka ce in baka na baka sai me? Ya sha mur sai ki zauna ki ringa barewa kina miko mun yanda kikeyi wa mamee.... Bazan ba ko kai mamee ne?.....ya fincikota ta fada jikin sa. Ke bakinki bai mutuwa ko? Ya matseta.... Sakarni malam ko gantsara maka cizo......mansura ta fito uwani kizo inji...... Maganar ta tsaya ganin madaki, ta yunkura ya kara riketa, jeki ce tana zuwa, tayi baya da sauri, Kwalla suka shatato mata, ya bisu da kallo duk tsiwarta bata da wuyar kuka, ya hade hannayenta dauko kiban sannan ki tafi. Taga ba sarki sai Allah ta dauko ga hannuwansa duka rike da ita, sai ya bude baki, ta balla mishi harara sannan ta watsa mishi. Ya saketa barkanki yarinya da....... Tuni ta shige ciki da gudu yabi bayanta da kallo. Gani mamah, Zo nan ki tayani gyaran sarka, Ya tashi yayi sama cikin nishadi yana tsotsa. Cewa nayi a kira mun ke kada ya miki wata muguntar. Ai cikin satin nan dai zai tafi Germany ki huta. Murmushi kawai umaimah tayi. Mamee bazata bar yarinyar nan ta zo ba kona kira. Ya dauki waya hello mamee don girman Allah kibar yarinyar nan tazo ta gyara man daki wallahi kinji nayi rantsuwa bazan kuma sata kuka ba. Na daina biye mata please. Ka tabbatar? Wallahi eh kinji nayi rantsuwa. Shi kenan ta ajiye, Uwani jeki gyara mishi dakin ki sauko. Bata San lokacin da ta ce innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ba. Ta kalleta zuwa saman keda wannan salatin? To bazaki ba wallahi ina dalili. Kyaleshi ai shi ya jiyo. Ta langwabar da kai don Allah mamah tunda na gama in tafi? Tausayinta ya kamata yanzu har tafi sha'awar tafiya gida da zama da ita saboda masifar madaki. Tashi ki tafi kinji. Zumbur ta mike tana murna ta bita da kallo. Shiru shiru sai kawai ya sauko, baisan ko wacece ba zata wuce ya ce ke ina yariyar mamee? Yanzu kuwa ta tafi gida..... *what* ? Da daka tsawa har ta dan firgita. Yayi ciki mamee! mamee!! Ya na bude kofa ya fara masifa, Kinga abinda na ke fada miki ko? Yarinyar nan fa gida ta tafi.....eh ina sane da hakan. Yayi turus! Ka firgita 'yar mutane kwata kwata yanzu bata sha'awar zama gidan nan duk ta tsorata ka hanata sakewa wannan masifar taka ta yi yawa. Shine kika bata dama ta tafi? Fine! Kawai ya juya yayi sama. Gashi ya rarratsa wayar da yake da numberta don bai wani tsaya saving ba, mtsewww yaja dogon tsaki sai kawai ya fara hada jakunkuna. Umaimah kuwa tana fita gidan ta mance komai cikin sa'a tana zuwa ta tarar an maido wuta ta kwashi kayanta ta nufi gidan Alhaji yakuba guga. Karfe shida na safe tana lazimi ya shigo, mamee zan tafi Germany sai Allah ya mana dawowa. Yau ne? Ina ce sai jibi, Eh akwai shirye shiryen da zanyi ne. Ya mike. Tabishi da kallo a dawo lafiya..... Ya wuce yana fushi, tunanin umaimah zai zautashi mamee kuma na babbakewa gara yayi nisa da gidan wata kila zai mance dasu din. Abinda madaki bai sani ba zaman sa gidan a haka ne saukin sa, domin da ya tafi sai da ya gwammace kida da karatu kusan zaucewa yayi hatta matan kasar sai suka ringa rikidewa suna koma mishi umaimah, Kam bala'i kada fa ace son yarinyar nan nakeyi? Innalillahi ya Allah kada kayi mun wannan jarabawar . Umaimah kuwa gida yazamo mata gwanin dadi ta warware, ga kwanciyar hankali ba fitinar madaki ga cimar dadi nan da nan jikin ta ya canza duk inda yake a dame ya taso, gida kuma ta kulle ita da lubabatu saboda hasafin da takeyi mata a boye, ko kayanta ma ta daina tabawa, ta karbi kudi gun hajiya ta yanko wasu yan material masu arha kala kala akayi mata dogayen rigunakala uku wasu kuma tayi da skirt kala biyu. Sannan ta yanko hijabai ita da mamee kala kala har ta baiwa lubabatu biyu ciki. Umaimah na da kokari har ta shiga hizif na talatin ta kuma gama hadisai biyu *haqqul mubeen* 1&2 ta shiga *bulugul maram* Duk yaran gidan yanzu ita ke masu kari. Cikin sati uku ta canza sosai girma yazo mata lokaci daya kirjinta ya cika sosai. Duk bayan kwana biyu take hawa sama tana gyara masa, haka zata kunna gwanja tayi ta tikar rawa tana aiki sannan idan ta gama tayi mai isarta sannan ta sauko, Ko sunan madaki bata son taji an ambata ta gama tsanar sa a zuci yar ta bata kaunar kara gajinsa. Gareshi kuwa a bin ba haka yake ba, ya kagara ya dawo wani lokacin yana jin hayaniyarta idan suna waya da mamee kamar yace mata bani ita. Ko tambayarta ya kasa yi ina uwaninki. Ya dankaro mata tsaraba, dogayen riguna, kayan shafa da turaruka, tunda ya siyi kayan yake tunani idan zai bata me zai ce ko kuwa yaba mamee ta bata kara taki karba? Haka dai ake kullum ba canji oga umar madaki. Sanye take da doguwar rigar material fari da flowers pink dinkin ya kame mata kugu ta kaso kallabi tana faman gyara mishi gado..... Mamee na falo taga mutum kamar daga sama, Ta washe baki saukar bazata...??? Yayi yar dariya suka gaisa, ya fara dube dube, Kamar uwani tasan da zuwanka wallahi, tana ta cewa sai gobe zata gyara ma sama kome ta gani? Kuma dai ta tafi, yanzu ma ai ta kusa gamawa.....zumbur ya mike ku hau man da jakunkuna sama yabi bayan su mamee bari nadan watsa ruwa na gaji. Ai dole da gajiya kam, Daya ke dakin bude yake sai kawai taga ana shigowa da jakunkuna...... Ta zaro ido, tayo tsalle ta dirko *ya dawo ne*? *Ga ma shaida*...... Ya fada lokacin da ya kunno kai........... *maman Abdallah* 😘😘😘😘😘 [1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣3⃣ ..... Yau ni naga bala'i ni umaimah, wannan jaraba har ina? Nikam na debo ruwan dafa kaina. Kullum abu daya yaki ci yaki cinyewa, kai ina amfanin abinda baya wucewa a rayuwa? Ikon Allah ashe ya san sunana tsabar wulaknci ne da gadara yasa yake kirana da *ke* ko *wannan yarinyar* Mi zanyi da wata jaka? Nasan menene a ciki? Duk girman jakar nan ya ce in dauka. Tabb da alamar tambaya. Bacin daukata sakarai da yayi ina jin hada rashin wayau ma duk babu yake tunani. Allah gani gareka, Allah kadai yasan gobe me zan tarar ni umaimah. Ka hana kanka zaman lafiya ka hana kowa? Ta tuna idan mamee ta aike ta gidan su kawu yanda take tarar dasu cikin nishadi da walwala amma idan suka shigo bangaren sa kowa jinin sa kan akaifa. Tana son fita harabar gidan amma shaggun ma'aikatan nan zasu ringa mata dan kira suna *fine girl* masu jin hausan kuma *yar Fulani*... Kiri kiri gida ya koma mani kamar wani sansani, kullum zan tafi ina zullumin me zan tarar ga madaki idan yana gari. Wani lokacin kamar yana da tausayi amma wani lokacin ya zamo mugun karfi da yaji shin ko dai yana shaye shaye? Amma kuma ai baya layi da magagin dasu yaya Abba keyi ko kuwa tasu kwayar ta masu kudi kwalwa kawai take tarwatsawa?. *NI KAM UMAIMAH NA SHIGA UKU* Da gudu kowa ya fito masu aiki da mamee. Yayi tsaye yana faman kallon kofa. Duk sukayi turus! Kai lafiya? Mamee ta bukata, Ya kalli yan aikin kuyi *clearing* ya haye sama. Mi ke damun yaron nan ni jikar buzaye? Abinda madaki kullum kara hauhawa yakeyi fa. Yarinyar nan ta maidani sakarai ko? Lallai bazan dauki iskanci ba. Wai tana nufin zanyi asara ne? Ya kalli jakar tabb... Duk yau ya kasa cin abinci. Wannan masifa da me tayi kama, yarinya karama ta hanani sukuni? Tunda Allah yasa yarinyar nan ta shigo rayuwata zuciyata ba kara samun sukuni ba. Wai duk me ke haddasa mana wannan rashin fahimtar? Nida ita wake da laifi? Ya buga tsaki ita ce , Tana fama da rashin kunya ni kuma bana daukar raini. Zan saisaita mata zama, ya tashi yayi alwala ya nufi masallaci nan cikin gidan sa. Takwas da rabi ya shigo zaune take da baki bai ko kalli inda suke ba yayi hanyar sama. Kai nake jira, mamee ta fada , Ya waigo cike da kulawa fuskar nan tashi murtuk, ta mike tayi ciki alamar ya biyota. Yan mata ne su uku ya kara kawar dakai duk suka bishi da kallo. *Yaro matashi mai tashen naira*. Kirarin sa kenan a gari. *madaki nada kyau* shi ba fari ne ba amma saboda hutu, kudi da kuma jin dadi yasa farat daya baka iya gane hakan. Irin kalar nan gareshi ta bakake mai kyau watan mai haske kamar chakuleti. Amma yana da sumar kai mai laushi da tsawo. Kullum tana kwance luf luf tana sheki da kamshi. Dan gayu ne na karshe kuma miskili na kin karawa. Ya kasa yin budurwa saboda mugun miskilancin sa ya ce babu macen da zai yi wa bauta ko ya bita yana lallashi bare uwa uba har ya mata laifi ya bata hakuri. Duk Wanda ke tare dashi yasan haka, Mamee ta kalleshi cikin ido. Gaban sa yayi mugun faduwa yasan doka ce zata saka mishi ko umarni ko kuma wani gargadi mai amfani. Kaga yara falo? Kaje ciki ka ga wacce tayi ma duk na san halin ko wace ciki da mahaifanta, tunda ka ce baka son auren zumunci. Sannan na baka dama har kishi uku kana *failing* Ya kalleta namee ....wallahi bazan kuma sauraron ka ba, kaje kayi abinda nace kada ka hadu da fushi na. Haba madaki ya zaka maidani sakarai kana nufin baka aure ko me? Ko kuwa matan banza kake bi namiji cikakke kamar ka bai yiwuwa ace har yau bakaji son ko wace mace ba........ai kinyi sauri ne mamee. Ta daka mishi tsawa nayi saurin don iyayenka, kaje kayi abinda na umarceka kada ranka ya 6aci....... Ba kince kin san halin ko wace ba? Kije duk wacce tayi miki cikin su shi kenan......yasa kai ya fice kamar ya kurma ihu don takaici. Tayi kasaké...!!! Wannan taurin kai na madaki ya zanyi dashi? Ransa ya gama kara jagulewa, tayi wayar duniya ya sauko yaci abinci yace ya koshi. Haka ya kwanta ga azababben tunani ta ko'ina ga yunwa. Haka ya kwanta har safe ga cook din sa baya nan yayi tafiya, Karfe takwas ta iso, mamee tayi kiran duniya yazo ya yi kalaci amma yaki daga waya, Duk tunanin ta fushi yakeyi, har karfe goma bai sauko ba, Ta kwala ma umaimah kira, tazo. Hau sama ki kira man umar. Hmmm kawai ta fada ta juya. Don bata san me zata fadawa namee ba. Shin ai duk masifar sa bazai dauki raina ba ko? Wata rana sai labari. Ita kadai ke sabbatu, tana tafiya, gabanta na dada faduwa. Ta kwankwasa har kusan sau shida ba ayi magana ba. Tayi tsaye tana tunani kada ta shiga a kara yar gidan jiya, har zata juya sai taji wani irin kakari daga ciki. Ta saurara da kunne tabbas shine. To lafiya? kakarin amai taji ta Murza kofar taji ta a datse, ta sauka da gudu ta nufi dakin mamee tana kwala mata kira mamah! Mamah!! Mansura ta tareta ta zagaya baya fa. Tana jin haka ta yi hanzarin zuwa ta dauko mukulli ta kara hawa saman da gudu. Kwance yake saman kafet cikin amai ko in ce kumallo, gashi yana fama da ulcer. Ya duke yana ta murkususu ya dafe cikinsa. Ta doka salati ta nufi inda yake ta dago shi *baka lafiya?* da kyar ya daga kai *Bani wani abu in ci please* Ta sakeshi da sauri ta kara yin kasa, duk an shirya kalaci a table ta hado tea da madara ta zubo farfesun koda ta hanzarta. Yana inda ta barshi. Ta ajiye kayan ta kamashi zaka iya tashi? Ya girgiza kai alamar a'a. Ya hakuri ka daure bana iya dagaka ta yaya zakaci abinci cikin amai? Ya daddage ya dafata zai mike ta durkushe duk suka fadi gefe. Ta ce wash! Ungo sha tea din. Ya kasa motsawa. Ta lura tabbas ya gama galabaita sai kawai ta ringa diba tana bashi. Yaushe rabon da ya sha tea da madara? Ta dunga dura mishi da spoon yana sha yaji dadin da ya rabu da ji a rayuwar sa. Tana bashi tana faman sannu. Ya shanye duka, ta dauko naman shima ta fara bashi, ganin ya fara farfadowa ta kalleshi kamar hada yunwa ma ciwon. Ita ce ma ba ( kamar ). Jiya banci komai ba gashi ina da ulcer.....ulcer? Ai wannan wauta ce ta fara bambami, gashi ka garkame daki ai da kayi mussai yau. Ya kalleta sai ta bashi dariya, yayi murmushi kawai. Wai me ma ya kawo ki dakina? Ta dalla mishi harara nazo *ceton ka* ya dan tureta zai tashi yayi luuuu ta taroshi da sauri ya fizge ta bishi da kallo. Me ya kawoki dakina? Mamee ke kiranka.... Kada ki fada mata abinda ya faru. Naji ta fada tare da mikewa. Ya tashi da kyar ya dauko magani yasha. Ta tafi ta mayar da kayan . ya sauko ya nufi dakin mamee yaji kiran. Umaimah kuwa tana kai kayan ta koma saman ta goge aman ta gyara mishi dakin tasanya mishi freshener ta canza mishi bedsheet sannan ta shiga kewaye ta wanke mishi. Tana gamawa ta tabe baki. Allah yasa yau ya zame mishi ishara ya rage zafin rai. Tana sauka shi kuma yana hawowa, ya kalleta sama da kasa, ina kuma kika je? Me kike mun a sama. Ta kalleshi ci ke da takaici, abar hali aci me? Gama rasa me zata ce mishi kawai ta raba shi ya fincikota ya hada da bango. Bana hanaki ina magana ki gudu ba? Ta kalleshi kai wane irin mutum ne? Irin ki ne. Ta girgiza kai ni ba haka nake ba........ Ke bakinki bai mutuwa ko? Ikon Allah, ta fada. Saboda bana son maganar zan tafi ka dawo dani shin me kake so? Jiya kin mayar dani sakarai kin pretending na shiga ciki kin gudu ko? Kin gwammace in rike albashin naki da ki dauki jakar can ko? Kwarai kuwa na hakura da albashin. Don haka bani wuri in wuce.... Ta ingijeshi ya daki karfen bene ta baya. Tana yin step daya ya murdo hannunta ya maidota da karfi jikin sa ya maida hannuwan sa duka bayanta. Wani takaici ya diran mata sai kawai ta dora kanta a kirjinsa tana kuka. Jikin sa yayi mugun sanyi, yayi shiru!!!... Tayi mai isarta tukun, ta dago, yayi saurin sakin ta, ta kalleshi idanu jawur, na rasa yanda zanyi da masifar ka, munzo na baka hakuri na daina shiga sha'anin ka, kullum da abinda kake tokalowa. Bana son hadaka da mahaifiyar ka amma ka kasa ganewa. Kwallah suka shatato mata. Na gaji na gaji. Wallahi zakayi dana sanin wulakancin da kayi man yanzu. Bani kwadayin kudin ku. Ina yiwa mutuncin mahaifiyar ka ne.... Kuka yaci karfinta da gudu ta sauka. Ya bita da kallo kaman ya kamota ya bata hakuri amma baya iyawa. A sanyaye ya hau sama, turus yayi ganin yanda dakin ya koma, ya zaro ido innalillahi yarinyar nan ashe gyarawa tazo tayi. Ya dafe kai *ohhhh my God* jikin sa ya kara yin sanyi, Umaimah kuwa tana baya ta lafe tana ruzgar kuka, tayi mai isarta, sannan ta goge fuska, *In shaa Allah bazai kara ganina ba* ko mamah ta aikeni zan San dabara amma wallahi bazan yarda ya kara sanya ni a ido ba. Kuma na rantse da Allah sai ya bani hakuri akan wannan wulakancin.............. Turkashi. *MAMAN ABDALLAH* MU KWAN LAFIYA😘😘😘 [1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣2⃣ Gabanta yayi wani mugun faduwa, ya kura mata ido ta bala'in canza mishi, ya fara taku zuwa inda take tsaye tana yar kyarma, Ta fara yin baya baya yana biyota har sai da ta kure ma bango, ya sa hannuwan sa duka ya dafa bangon yayi mata katanga tare da sunkuyo wa dai dai fuskarsa fuskarsa murtuk..... Ke baki iya gaisuwa ba? Ko kinfi karfin kiyi man sannu da zuwa? Ta dago kai aiken ka nayi? Me yasa kake da neman dalili? Ta ingijeshi ai fa ka dawo,....ya fizgota da karfi ya buga bayanta a bango. Ai fa na dawo? Ni da gidana kike fadan aifa na dawo watan baki so na dawo ba ko? Kwarai ban.....wata muguwar matsa yayi mata tayi shiru sai kawai ta fara kwalla...ya kura mata ido sannan ya saketa a hankali ya dan ja baya ta kwasa da gudu ya bita da kallo. Kafin ta sauka kasa tayi saurin gyara fuskar ta, mamee na ganin ta ta ce yawwa je kikai man wadannan fridge, waccen ledar kuma ki juye mana a tray kizo da wuka, Suna ci ya sauko janye da jaka.... Wai mamee keda yar nan taki baku da aiki sai ci? Dariya tayi, barakallah da lafiya akeci ai, Yayi murmushi Allah yarinyar nan ta koya miki ci duk gashi nan kunyi yan kumatu..... Kai bani son sa ido, Apple din ne ci? Uwani ma da ta tsani abinci kullum nan cikin mata fada nake, Ta mike zata bar wurin duk ta hade rai, ya daka mata tsawa ke! Wallahi kika bar wurin nan bazan biyaki albashi ba wannan watan, To azabau ka dawo zaka hana ta shan ruwa ,hada wallahi? Uwani zo ki zauna, yasha mur kawai. Ta bishi da harara ta zauna. Yarinyar nan ta gama rainani mamee ita tafi karfin ta gaisheni ne? Ko sannu da zuwa fa. Kana mata wannan hayagagar zata gaisheka? Ya kamata ki ringa nuna mata kuskurenta zata sha wahala tamm.. Ta kalleshi kai wane irin yaro ne mai taurin kan tsiya? Shin nayi shiru, ya fada yana watsa hannu, ga tsarabar ki sauran na sama. A a a uwani buda mu gani, mazga mazgan riguna ne irin wadanda mamin ke sawa da mayafai . Ta kalleshi banga abinda zaiyi wa uwani anan ba, Ai daman naki ne, ya mike kawai yayi sama abinsa, Ta kalleta ke bishi kice yaban sauran wata kila acan ciki kya samu, Gabanta ya fadi, in dai don ni wallahi na yafe mama haba.....ni ban yafe ba, ko dan turare ai kya samu gasu mansura can kowa da ledar sa danaji babu taki a ciki nayi tunanin tare zai hado man. Jeki maza ki karbo ta fada tare da shigewa ciki. Tayi tsayeeee!!! Allah gani gareka, me kuma zan tarar? Kamar wacce kwai ya fashewa take tafiya, zan bi duk wata dokar sa in shaa Allah. Sai da ta hadiye wani tsinkakken miyau tare da sakin ajiyar zuciya sannan ta kwankwasa, *come in*... Ya ce daga ciki, Ta murda a hankali *Assalamu alaikum,*..... Allah kasa amsa sallamar yayi *he wasn't expect her now* ya tashi zumbur dama ya dan kishin gida ne, Ta dan sati kallon sa, kwanciya dai kwanciya mtseww kamar mace, amma a fili sai ta ce, Hajiya ce ta aiko wai ka bata sauran kayan. Ya mayar da kai kawai ya runtse ido, yafi mintuna biyu, ta dai yi tsaye tana wasa da hannunta cikin hijab kanta kasa, Ya dago ga su can a Leda.... Ba bata lokaci ta dauka tayi hanyar fita........ Tsaya! Yace, Gabanta ya fadi tayi chak tare da runtse ido, *to wace masifar ce kuma?* Ta kasa juyowa, Ki miko mun jaka gata can...lokacin ta juyo da sauri, tayi hanyar inda yake nunawa, Ta ajiye mishi kawai zata juya, *idan kina so ki dauka idan kuma bakya so kibarta nan*......sai kawai ta juya abinta ya daka mata tsawa cikinta ya murda ya dirko gabanta *bakiji me na fada ba?* Ta kalleshi a wulakance ni kuwa na jika, ka ce idan ina so in dauka idan kuma bana so in barsu nan, haka ne? Ta bukata tana hararar sa sama da kasa tayi kicin kicin da rai, shine kaga na barsu din *domin bani bukata*......ya yi mata wata irin chafka har zaiyi magana kuma sai ya fasa ya bankada ta tayi baya baya taga taga zata fadi. Ko kallon sa batayi ba tayi fice warta, Dan rainin wayo wannan uwar jakar zaice in dauka to duk meye aciki watan in dauka ya gana man wata azabar, kai *madaki ya shiga uku da masifa* INA dalili. Ledar magungunan mamee din ne da take sha na hawan jini tare da sauran maganin da take shafawa a kafafu. Mtseww ta buga tsaki, kyaleshi uwani ai zan tafi umara nima tsaraba sai kin ture. Ta yi yar dariya kwarai kuwa mama. Wai tana nufin zanyi asara ne? Tabb ya zabura sai wayarsa tayi kara. *Yeah Ku shigo ina sama* ya kashe Abokansa ne wadanda ke kula da wasu kamfanonin sa zasuyi meeting. Ya kira mamee, a kawo mana abincin mutum goma . Yayi ta zuba ido yaga umaimah amma bata ciki, abinci ma baici ba don takaici, da la'asar ya sauko, tana ta faman gyara wasu duwatsu kaman na sarka, Ya kura mata ido yana kallo, babu abinda yake kwantar masa da hankali yanzu irin kallon ta, Ta dago kai kawai taga ita yake kallo ya sakar mata murmushi ta balla mishi harara kawai taci gaba da aikin ta. Kai ni kike harara? Yarinyar nan kin rainani ko? Tayi mishi banza Kije ki dauko jakar nan ko kuma wannan watan baki da albashi......ta dago zatayi magana yace wallahi zan hanaki kudinki kin San zan iya ko? Ta mike ta shiga ciki, sallama tayo wa mamee kawai ta fito tayi hanyar waje, Ya yunkuro ya kamota da karfi *me yasa kin fiye taurin kai?* ta lumshe ido tare da dafe kanta tana magagi kamar me shirin somewa, ya kara matsarta ya daga murya, kina ganin zaki iya ja dani........luuu ta tafi ya tareta a kirjinsa tare da zaro ido *UMAIMAH*...Ya firgice ya rikice ya waiga ya waiga ba kowa, ya sungumeta yayi bisa kujera ya kwantar yayi ciki da gudu ya dauko ruwa..... Ta bude ido a hankali koda taga ya shige sai ta mike tare da kwasawa da gudu. Ya fito da kofin ruwa a rude.....kawai yaga wayam. Ya kwala kira umaimah...garam yaji anja kofa. Nan da nan ya fahimci me tayi ya yi wurgi da kofin da ruwa ji kakeyi ratsatsatsa.............. *Maman Abdallah* Good morning to you all😘😘 [1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣4⃣ *A rubutu na idan kuka ga MZ to ina nufin MOTHER a hausan ce ina cewa MOZA* *Ba kowa ke da sunan ba sai Babbar masoyiyata SALAMATU DAHIRU wasu na kiranta SALAME DAHIRU kamar yanda kuke son wannan labarin to tabbatas ita ce jagoran siya mun data ba tare da tayi shawara da kowa ba don in muku rubutun AUREN FARI ku nishadantu ku kuma ilimantar. Zata sami addu'a daga gareku? To ina bara domin nima na ce ALLAH YA KARA DAUKAKA SANA'AR TA YA SHIRYA MATA ZURI'A YA RABATA DA IYAYE DA DUNIYA LAFIYA SANNAN YA KARA FAHIMTA ITA DA MAI GIDA AMIN.* KE MI KIKA CE???😊 ....Yayi tagumi, anya ba nine ke rikita yarinyar nan ba? Ya dunga tariyo yanayin da ta shiga ganin sa a galabaice. Mtseww, talaka ba abinda bazaiyi ba idan yana son abinka. Washe gari tana zuwa tabi ta baya, ko mamee bata ga shigowarta ba, taci gaba da aikinta, ya gama zamansa falo har kusan sha daya baiga tazo ba dole ya hakura ya tafi office, umaimah ta gama lakantar gidan duk inda tasan CCTV zata hasko ta sai ta daina zama wurin, Tana daki zaune ta fiddo mamee kaf tana kara gyarawa mameen ta shigo, Au kina nan wai? Ke bakya gajiya da shirya kaya a durowa? Ga gidan kawu can ana cigiyar ki zaki taya su shirye shirye baffa ke birthday jibi. Ta yi zumbur ashe zamu sha shagali bari in hanzarta ai ina son bazide din nan saboda kek din nan mai yar madara madara. Mamee ta kwashe da dariya, ai nan kika fi auki in da kwadayi to karki yamutsan kaya wurin sauri. Koda ta gama tabi ta baya tayi can. Tana zuwa ta tarar ana ta hura balloons ita ma ta hau yi. Aunty kune ke hadawa da kanku? Ta tambaya Wannan karon daine zamu hada saboda a saman benen *madaki* zayayi kin San baffa da iyaye gashi na gaban goshi ne baya laifi. To sanin ka'ida irin ta madaki gara muyi da kanmu kar ayi mishi ba dai dai ba. Uhumm, kawai ta ce jikin ta yayi sanyi lallai bata ciki. A kulla wannan a kwance wancen haka sukayi tayi sai shidda ta tafi gida. Ko sallama sai dai ta waya tayi wa mamee. Tun biyar ya dawo yana falon mamee a zaune ya latsa wannan tasha ya maida wannan, daya ji motsi sai yayi firgigi, wasa wasa har akayi magrib ya kira cikin yan aikin ke ina uwani? Ta kame hannu tana yar kyarma, ta tafi gida.......sai kawai ya mike yayi sama, Washe gari ma haka tana gaisawa da mamee ta ce ta tafi gidan su kawu aikin birthday. A dawo lafiya kai uwani akwai son shagali ta bita da dariya. Ya fito yana yan dube dube bai ganta ba, kawai ya nufi dakin mamee tana bi ta baya yana shigowa, ya fara dube dube ta kalleshi me kake nema? Ya kara kallon dakin ba komi ya fice, Aiki ya rikeshi office shidda ya iso gida yana ta hanzari yana shiga ya tarar mamee da baki a falon sama sama ya gaishesu yayi cikin dakin mamee yana zuwa wayam! Ya fito ya leka kitchen ke ina uwani? Ta tafi........mtseww ya buga tsaki ya juya. Wai meke tsakanin Alhaji da uwani? Mansura ta bukata, laraba ta ce ya tsaneta ne ita kuma ta nace yarinyar ta fiye shisshigi ke gaki 'yar aiki amma kina acting kamar diyar gida? Hajiya ce take lalata yarinyar. Bilkisu ta dago kai amma bata da raini duk tana bamu girma..... Tabb billahil azim ta raina oga bata tsoron sa ko Kadan....duk suka zaro ido bakin ki aka ji kowa ya watse. Umaimah kuwa tana can ana shagalin toye toye da soye soye abin na matukar bata mamaki birthday kamar shagalin biki? Kai masu kudi na yarda suke so. Ta zage ta dunga aiki tana kwasar ilimi duk abinda akayi gabanta to ba sai an maimaita ba, kowa yaba mata yakeyi yanda ta nuna rashin son jiki kuma komi akace tayi bata gardama ko bata fuska, Sai karfe tara tabar gidan aka dibar mata naman kaji, snacks da lemuka ta tafi gida ko mamee tayi tunanin tun marece ta tafi. Wasu na can sashen mamee da saman madaki ana kulla balloons da kayan kwalliya Sam taki zuwa aikin ta manne wurin abinci duk don ta gujewa haduwa dashi. Hankali madaki ya gama tashi ya sami mamee na lazimi bayan isha'i. Yarinyar nan bata aikin ta yanda yakamata ko? Kwana biyu bana ganin ta...... To fitina'u kwana biyun nan ma tafi aiki bana son neman rigima, yaushe zaka basu kudin su ne? Gobe ya fada da Sauri kowa yaje sama da safe ya karbo don zan danyi aiki bazan sauko ba. Allah ya kaimu, amma kasan gobe ne shagalin baffa nasan kuma ire iren wadannan shiriritun kamar yanda kake fada gidan kake bari tunda wuri gashi a saman zasuyi komai eh zan fita zuwa goma ina nufin suje kafin lokacin. Oho to na gane, Ya fito yana cewa ai shegen son kudi gareta gobe na ganta ba shiri. Zata manta duk wani laifi da akayi mata akan kudi. Murna tsalle gida ya rikice ana lashe lashe da tande tande. Goggo hansatu ta lumba wata tsoka ta cika mata baki, to gobe kwana zakiyi kenan saboda shagalin ko? Ta dago kai da sauri kwana goggo? Eh mana kya taho ba a gama ba? Tayi murmushin takaici. A a dawo wa gida zanyi komin dare. Suka ci gaba da ci. Tunda safe mamee ta tafi Kaduna an aiko ciwon babbar yayar su ya tashi na ciwon sugar. Ta kira umaimah ta shaida mata don haka koda tazo bata iske ta ba, Kawai sai ta wuce sashen su kawu, babu Wanda yaga zuwanta. Ko wace ta karbo kudin ta amma bai ganta ba, ta karshen na zuwa yace ke ina uwani? Wallahi ban ganta ba amma bari in nemo ta, ta karba ta fita da hanzari, ya dauki waya, hello mamee ya mai jikin? Da yake a jirgi ta tafi, Ta ce gata da sauki amma ina tunanin sai na kai gobe gaskiya, asshha zan shigo anjima a gaishe ta. Yarinyar nan taki zuwa ta karbi kudin fa ya kamata ki kirata a waya ko ki turon number ta. Tayi murmushi uwani sarkin hidima kiri kiri taki zama tunda taji za ayi party. Bari in kirata, Eh kirata amma still mamee nima turo man number ta please. Ta ce to ta kashe wayar. Ashe kina nan? Kizo inji Alhaji ki karbi kudin ki..... Na ji. Ta fada a takaice. Zata kara magana wayar umaimar tayi kara, Hello mama kun isa lafiya ya mai jikin? Da sauki uwani, kije ki karbo kudin ki zai fita ke kadai yake jira. To mamah ta fada kamar da gaske. Tana kashewa wayar ta kuma yin kara, ta dauka mamah yanzu fa zanje......... Sai kin gama bata man loka...... Tayi saurin dauke wayar daga kunnen ta, tana ganin number tayi saurin lace wayar sannan ta kashe ta gaba daya. Kutumeee..... Dai dai shigowar nafisa yallabai gata nan zuwa. Umaimah ta bata fuska, Wallahi na yafe kudin, ai shi da ganina sai dai wani tsautsayin wallahi. Ke da wa kike sabbatu? Aunty ta gani gabanta tana dariya. Ta danyi murmushi kawai. Uwani tunda mun gama hada jakun kunan da take away kije gida ki shiryo ki dawo da ke da nafisa, mansura da kuma bilkisu ku ba baki abinci da rabon kayan kuma. Ta ce to, ta tafi amma azuciyarta bata da niyyar dawowa.sai da taje gida tukun ta kunna waya ya kirata yafi sau goma bata daga ba. Ya sauko a harzuke ya gamu da bilkisu ke ina uwani? Tana sashen kawu babba bari na kira..... Ban aikeki ba ya wuce fuuu..... Kamar daga sama Aunty ta Ganshi bai taba shigowa sashen ba ko sau daya, ko haihuwa tayi sai dai akai mishi yaron . Ina *uwani*? Abinda ya ce kenan da shigar sa. Yanzu kuwa ta tafi gida..... *what*???? Ya juya kamar mahaukaci, wai laifi nayi sosai ne? Lallai na gane fushi takeyi yarinyar nan. Mtsewww yeah I know ban kyauta ba but at least won't she give me a little bit chance? I regret and ready to show my appreciation..... Ohh my God ya dafe kai. Tana zaune daki tana gyara jakar kayanta wurin karfe biyar mamee tayi kiranta, Ta dauka tana fargabar ko ya fada mata bata karbi kudin ba. Hello, mamee ina wuni, Lafiya lau uwani kada ki manta ki ringa barmun daki a kulle kinga gidan yau Allah kadai yasan wa zasu shigo gashi bani gari.......gabanta ya fadi ta ce toh. Tana ajiye wayar ta mike na shiga uku, tabar gidan a gaje. Tana rufo dakin ta fito kenan tayi kucibis da baffa, yawwa uwani ungo muje sama, ya tasa keyar ta. Kowa gidan yana can an kawata wurin swimming pool ana ta shagali, nan da nan umaimah ta sake aka fara hada hada. Khausar ta yafito ta da hannu, jeki dauko ledar tissue na can falon mamee. Ta ce toh, tana dawowa kenan zata wuce shi kuma ya fito bai taba tsammanin ta ba, yaja wani uban birki, kallo daya tayi mishi ta wuce ya ware murya... *umaimah* amma ina sai ma ta ruga. Ya salam ya fada wai me yarinyar nan ke nufi kawai sai yabi bayanta. Yayi saurin dawowa da hanzarin ganin me yake shirin yi, yarinyar nan tsab zata yarfa ni gaban mutanen nan babu ruwan ta yaran da ke ganin kima da mutunci na duk ya zube. Yana nan tsaye ya rasa me zaiyi. Ita kuwa tunda taga haka sai ta fara bobboyewa tana neman yanda zata sulale tabar gidan. Haka kuwa tayi sa'a ana shiga sallar magriba ta fito a hanzarce bayan wasu ita ce taji wuf an fizgeta da karfi, zata kwala ihu saboda firgita ya to she mata baki, Ke wai me kike nufi? Ta fizge hannunsa daga bakin ta abinda duk kake nufi shi nake nufi. Na gaji da fitinar ka wallahi wallahi na gama biye maka na gaji da wulakancin ka.......zuwa ki karbi hakkin ki ne wulakanci? Yaya ina ta binki kina neman hasala ni? Na kira wayar ki kinki dagawa nasan ai ban kyauta ba amma bazaki jira in...... Ta kalleshi au kasan baka kyauta ba da gaske? To kaban hakuri na rantse da Allah idan baka ban hakuri ba yanda dai nayi takima da aman ka na bata lokaci na ceto rayuwaraka amma......amma me? Ya ingijeta ke awa zan baki hakuri? Ya nuna ta da yatsa ranar duk da kika kara furta wannan kalmar na rantse da Allah sai na barki kwance. Ta kalleshi shekeke haka kace? To ga sharadi kada ka kuskura koda wasa ka kara tanka mun. Bani da wata alaka tsakanina dakai na rantse ko kallo baka isheni ba bana kaunar ganinka ma bare magana ko wani abu ya kara hada ni da kai idankuwa ka kuskura........ya shako wuyanta me zakiyi? Kina da taurin kai ko? Ta ingijeshi da karfi, *Zan hada ka da mahaifiyar ka* ko baba ai da babanshi. Ni yau naga bala'i ta hada hannuwanta duka alamar rokon sa, kayi wa Allah da manzon sa da kuma darajar mahaifiyarka kasa kan mara inyi fitsari, hanyar duk da nasan kana wurin zan kiyaye binta bana son ko kallo ya hada ni da kai bare magana ta fatar baki......ta juya abinta .....ya mika hannu zai kamota ta kwasa a guje ..... *Umaimah*...... Amma inaaa tayi wajen get da gudu..... *Ni din dai ce taku mai son ku mamar Abdallah diya ga Aunty rabi* 😃😘😘😘😘😘😘😘😘😘 [1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣5⃣ Ya dunkule hannu ya kai ma wani icce duka. Taurin kan yarinyar nan yayi yawa. Amma banga laifin ta ba nine na damu da kucaka *let me snub idiot* ya juya ya wuce. Ka dauki tsanar duniya ka daura mun wannan jaraba har ina? Karar sa zan kai wallahi ya kuma takura mun. Dole in sanar da mamee idan bata dauki mataki ba zan hakura da aikin. Ta je gun hajiya cikin kudin ta takarbo dubu biyar takai ma goggo hansatu ta ce ga albashinta. Ta ware dubu ta bata ta boye dubu biyu, Ta ajiye biyun idan baban nasu yazo ta bashi. Washe gari ma taki yarda su hadu, shima ya dan share abin na can cinsa a zuciya amma ya daure. Kausar tunda akayi dan shagalin nan sai jinin ta ya hadu da umaimah taji kaunarta a zuciya gasu kusan sa'anni amma yanda komi ta ce umaimar tayi bata musantawa, ta shigo suka sha fira abin su umaimar ta ce don Allah idan ta sami lokaci tana so ta dan ringa koya mata boko don ta gane baki, tun a lokacin kuwa suka fara. Sai dare suka dawo tare da mamee, jiyan bai sami zuwa ba sai yau. Tuni umaimah ta dade da tafiya gida. Madaki sam yaki yarda ya kuma amince da cewar zuciyarsa ta kamu da kaunar umaimah ba tare da ta tsaya shawara da kwalwar sa ba, ya rasa inda zai sa ransa don kuna. Ya kwanta ruf da ciki, ya runtse ido wallahi *So bai mun adalci ba* in rasa son da zan fada sai na wannan banzar yarinyar?.....kai ba so bane. To meye? Haka ya dunga kai gauro da mari, kafin kace me ya sami attack na ulcer don zubewa yayi yana firowa sallar asubah. Hankalin kowa ya tashi gidan masu kuka nayi masu kyarma nayi don bai taba irin haka ba. Akayi sama dashi likitanshi ya fara aune aune, nan da nan ya gano damuwa ce ta yado mishi ulcer. Mamee tayi ta jinjina abun a ranta damuwa? Ko dai don ta kawo mishi yaran nan? Nan da nan hankalin ta ya tashi. Umaimah tun a gate ta fahimci kowa yayi zugum, saboda kullum kafin ta shigo sukan dan mata 'yar raha. Ta iske mamee zaune idanu sunyi luhu luhu. Ta isa da gudu har ta kusa faduwa, mamah meya faru ko mai jikin ce? Ta girgiza kai..... *madaki* ne...... Gabanta yayi wani mugun faduwa . ta zaro ido yayi me? Baya lafiya.....ta saki ajiyar zuciya har mamin ta kalle ta, kai na firgita mamah , Allah ya raba mu da mugun ji, mugun gani da mugun aike shi kuma Allah ya bashi lafiya......ta mike . Aaammmeeenn uwani. Ta danyi murmushi rashin lafiyar ne kika sha kuka haka? Ta Dalla mata harara. Ana kakkabe mishi file ne yayi kura ba inda zai tafi sai munga jikalle....... Bata San lokacin data kwashe da dariya ba. Tayi ciki itama tana dariyar ko kefa amma kinyi kicin kicin da rai ni duk kin kadan yan hanji. Ta bita tana murmushi, barkwancin yarinyar yasa ta shiga ranta fiye da kima. Abokansa lodi lodi , zandi zandi da ma'aikatan sa haka ake wuni zarya gaisheshi. Ta tabe baki, kodan kudin sa ai mutane sa soshi. Marassa zuciya biye ake.... Kwana biyu kowa ya hau yayi mishi sannu banda umaimah, yaga da gaske mutuwa fa zaiyi kawai ya yanke zuwa ya bata hakuri, a wuce wurin, Ya sauko daddafe tana ta faman gyarawa mamee akaifa, basu ji saukowar sa ba, har sai da yazo daf dasu yace mamee....... Da dagowar kanta da faduwar gabanta duk suka wanzu lokaci guda. Idanun sa an kanta, suka hada ido tayi saurin maida kai kasa, *kai wallahi ya rame da yawa* ......bazakayi waya akawo ma abinda kake bukata ba ka sauko? Idanun sa har lokacin na kan umaimah ya ce *Abinda nake bukata bai dauko ta waya mamee*..... Me? Yayi firgigi to ina son dan mike kafa ta ne na gaji da kwanciya kamar ruwa ya karasa maganar yana dan murmushi yana duban mamin...... Umaimah ta mike zata bar wurin, ya ce, kowa ya je ya mun sannu yarinyar ki ta kasa zuwa saboda girman kai..... Ya salam, mutumin nan sai fita harka ta kuwa? Subhanallah uwani, Saboda me? Zo nan amma baki kyauta ba..... Ta dan zukunna naje sau biyu yana barci.....karya kikeyi......kai jira, tsaya na ce. Koma dai menene ki gausheshi yanzu ina ji shi kenan ko? Ta dan kaikaita *Allah ya kara lafiya* kawai tabar falon tayi ciki. Ya bita da wani kallo...... Sai kawai ya maida bayansa ya kwantar tare da rufe ido. Ya rasa ya zaiyi duk ta inda ya bullo sai umaimah ta zulle, kwatsam bayan kwana biyu mamee taje asibiti ya rutsa ta a daki, ta ganshi sarai sai ta basar, *Ina son magana dake* kawai ya juya. Tabi bayan shi da harara *Ai sai ganina kam* taci gaba da aikinta. Kusan mintuna biyar ya kara shigowa, *Da ke nake fa* ta dai yi shiru. Ya nufo ta a hasale, ta makure jikin gado sai kawai tasa mishi kuka. Duk illahirin tsikar jikin sa ta tashi yaji wani *yarrr* ga wata kasala. Yafi mintuna uku yana tsaye yana kallon ta. Ta dan sassauta kukan abinka dama da *sharbe* Ya rasa ta in da zai fara. Motsa baki kawai yakeyi ya rasa me zai ce mata? Ya dan kwantar da murya, banyi tunanin abin zai miki zafi haka ba, har ga Allah bana yi da mummunan manufa ba......ya danyi shiru. Sautin kukanta ya tsaya chak! Na rasa ta inda zan bullo miki ki fahimceni kin fiye taurin kai, na mini tsaraba kanki ki karba, albashin ki ma kin yafe, na kira waya kinyi rejecting. *You wrongly and negatively understood me* yanda duk kika daukeni ba haka nake ba. Yayi shiru!!!!....... Ko zata ce wani abu amma motse taki motsawa, Duk jikinta ya dauki wani sauti,ya zukunna gabanta *Umaimah*..... Saura kadan ta saki fitsari tsikar jikinta ta yi *yarrr* gabanta yayi wani irin faduwa da bata ta ba irin sa ba ta kara makurewa tana kyarma. Wani irin abu takeji da bata ta ba jinsa ba...... Ya ruko hannunta zo muje sama inyi magana dake a nutse bana son mamee tazo ta tarar dani nan ke kuma kina kuka......ta kankame jikinta, ya kura mata ido cikin tashin hankali kada fa yarinyar nan bacin kiyayyar da takeyi mun hada tsoro na ta fara.....? Tabbas yarinya ce karama kamar yanda mamee ke fadi, to wai nima wane rashin hankali ya shigeni na biyewa mitsitsiyar yarinya kamar wannan muna *Scandal*? Ya kara sassauta murya yanzu ya kike so ayi? .......ka tafi kaban wuri, Ta fada tana shassheka, Taurin kanki keja muna fitina, yaya ina lallashin ki kina dada rikicewa? Ikon Allah ta ce a zuci, To bazan tafi ba idan kin ga na tashi anan to kin biyoni zuwa sama. Bata kara magana ba yayi yayi amma tayi shiru, Ina son ki fada man abinda duk bakya so daga gareni na miki alkwarin zan daina kuma zan baki hakuri.....lokacin ta dago ido, fuskar duk tayi ja abinka ga farar mace, Ina so ka fita hanya ta ka kyaleni bana son ........ Ke kina hauka ne? Ya daka mata tsawa sai kawai ta kara fashewa da kuka. *Yau na shiga uku* bai San lokacin da yace haka ba. Ya matsa hannuwanta murya kasa kasa *Umaimah ki dubi girman Allah kizo muje sama kada mamee ta shigo, kin San Allah yau sai mun gama maganar nan koda kuwa zaki kwana gidan nan...... Na gama magana dakai na hakura kayi wa Allah ka kyaleni haka. Kamar zaiyi kuka kinfi so kullum muna fitina kamar kaji bakya so mu daidaita? Tayi shiruuu!!!.... Idan ke abin baya damunki ni yana damuna ina so kiban lokaci muyi maganar nan.......mamee oyoyo yara suka fara ihu daga haraba. Ya zaro ido kawai sai ya mike ya sureta kamar jaririya yayi sama a guje...... Zatayi ihu ya hada fuskarta ta kirjinsa ya toshe da kyar take numfashi. Ya dire ta a tsakar dakinsa ya maida kofa ya rufe da key, kana hauka ne zaka kasheni? Da'allah yi mana shiru fanko, Ashe baki da nauyi kamar na dauko karmami ke 'Har abun nan kike ja da *madaki*. Ke nake sauraro ki fada man abinda kike so da Wanda bakya so ko ma daidaita mu daina fada.......ina son yanzu ka bude in fita, sannan bana son ka kara Shiga sabga ta. Dalili? Ban sani ba... Ki fada man dalili ni kuma daga yau zan kyaleki zan kuma baki hakuri, Saboda na tsani inganka kusa dani. Ta fada a hasale, Maganar ta daki zuciyar sa ya matso daf da ita , tayi saurin ja da baya yaci gaba da binta har ta kai ma bango, ta runtse ido tana jiran ya shako ta Lamar kullum ya sunkuyo daf da fuskar ta ...... *Am very sorry* kiyi hakuri. Jikin ta yayi tsammm!!!!! Ya ja baya a hankali ya nuna mata kofa da hannu......... *MAMAN ABDALLAH* 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣6⃣ *KINA RAINA MARYAM ALIYU YAR ADUWA. M. ALI* 😘 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH ....Ta kalleshi sosai, ya nutsar da nashi idon cikin nata yana aika mata sakonni, tayi saurin kawar dasu ta wuce kamar wacce kwai ya fashewa. Ya bita da kallo kamar ya kamo ta amma ya daure ya barta ta tafi, dole in danyi baya baya da yarinyar nan in dan fita harkarta kadan kuma na daina damunta da hayagaga matukar ina son shawo kanta mu daina fada, in ba haka ba zan rikita ta in gigitata ina ji ina gani ta tsorace ni ta kuma kini, kiyayya mai tsanani. Ya zauna gefen gado, amma me yasa na damu da yarinyar nan haka?, saboda me bana hakurin rashin ganin ta ko yaya ne duk da kullum haduwar tamu bata arziki ba ce? A duk lokacin da na ganta kusa dani ko nesa dani burina kawai najita bisa jikina, shin me yasa hakan? Komin yanda na hasala da ita tana fara kwalla zuciyata zata karaya *Why?* Mtsewww ya ja guntun tsaki, Nasan dalili, duk duniya babu wanda ko wacce ta taba yi mun abinda yarinyar nan tayi mun ba, ban taba ganin Wanda baya tsoro na ko shakka ta ba irin ta. To wai saboda me? Me yasa bata tsoro na? A baya babu abinda ya tsana irin zama falon mamee saboda hayaniyar yan aikin ta, amma yanzu duk fadin gidan nan kawai yake sha'awar zama. Kullum burin sa ya tokali umaimah suyi sa'in sa ko da kuwa zuciyar sa zata yi kuna, *to me yasa?* Umaimah kuwa har sai da mamee ta kare ta tambayeta ko bata lafiya? Lafiya ta lau mamah ta fada tana dan murmushi, Ta kai hannu a wuyanta don ta tabbatar sannan ta ce, duk kinyi sukuku kamar wacce tayi karya lafiya dai ko? Ohh mamah, lafiya lau fa. Ta dungureta ganin har ta kosa da maganar, karya kikeyi da abinda ke damunki ko kun kara fada da *madaki*? Sunan sa kawai da taji sai da ga banta ya buga, ta ce *ni ina ma ya ganni?* Ina so in baki labari mamah, tayi saurin janza maganar, jiya khausar aikin da ta bani duk na cinye sa, Au haba? , Uwani Allah ne yasa bazakiyi ilimi mai tsawo ba amma maganar kokari kina dashi sosai. Tayi murmushi. Ko karatun nan fa ji nisan da kikayi wa kowa gidan nan. Da zamuyi sirri da ke da na nemi alfarmar ki, Alfarma? Ta bukata, Eh, Ta me?, Kija bakin ki kiyi shiru amma, Mamah wa zan fada mawa? Tayi murmushi, nasan baki da surutu kam, Zan lallaba *madaki* ya sanya ki makaranta........ Wani tsalle ta buga tare da fadawa jikinta ta kankameta tana ihu. Ke karki karya ni don kaniyar ki. Amma ina tumurmuzarta takeyi tana tsalle dai dai shi kuma yana saukowa daga sama, yayi turus yana kallon su. Ta dago fuskarta zaki dagan kafafu ko sai kin sha kulli? Ta yi saurin tashi ta juya mata bayan *dunkule hannu ki tuma min* duk suka kyalkyace da dariya ta kara kankameta. Ya lumshe ido yana wani irin nishadi, fuskarsa kunshe da murmushi, yarinyar nan ta maida mun uwa kamar ta ta ko? Shin ko dai shagwababbiya ce? Amma ita da take marainiyaniya wa zata yi ma shagwaba? Ya daure fuska tamau ya sauko *ke* daga mun uwa ko sai kin karya kafafun da nake faman *treating?* Zumbur ta mike ta zauna nan da nan annurin fuskarta ya 6ace, Ya kalli mamee *murnar me ta keyi ne?*.....ina ruwan ka sirri ne ko uwani? Ta dubeta tana murmushi. Sirri? Har akwai sirrin da zakiyi da wannan yarinyar da ba zan ji ba? Ta daure fuska kadan gashi ma kaga zahiri. Ya kalli umaimah *ke fada mun tsallen me kikeyi?* Sai kawai ta yunkura zata tashi....ya fizgota da karfi ta fada jikin sa ya harde kafafun sa ta baya ya kange ta, ta zaro ido wata kunya ta dirar mata tsikar jikin ta tabada *yarrr* ... a gaban mamee? .....mameen kuwa tsawa ta daka mishi tana cewa wallahi ka daketa sai ranka ya baci sakar ta. Yarinyar nan fa ta gama yi mun shiga hanci da kudundune mamee nema takeyi ta kwacen fada wajen ki......bazaka saketa ba? Ta daka mushi tsawa. Ya warware kafafun sa ta yunkura sai ya kara tabiyota yanda ta fada mishin sai da fuskar su ta hadu. Ta mike da sauri shi kuma ya dafe hanci kai kai kai ni kika bige? Ya yunkuro zai chafko ta mamee ta janyeta da karfi ta boyeta bayanta. Wai kai wane irin maketacin yaro ne *madaki?* ta fada a hassale, Haba mamee baki ga ketar da ta yi mun ba? Kana ganin don iyayenka banga lokacin da ka tabiyeta da kafa ba? Allah ya kara, alhakinta ne. Umaimah dai tayi sukutiii...kamar ta bude kasa ta shige, yau kawai ta tsinci kanta da wannan kunya, ko don bani da hijabi? Amma sau nawa muna hakan babu hijab kuma banji komai ba, kawai don a gaban mamah ne, Ya bita da wani mugun kallo amma ta sigar harara ta kara soke kai bayan mamee. Tashi ki dauko hijabi ki tafi gida shidda ta kusa, ki dauki sauran naman ki tafi dashi tunda baki ci ba.... Ya mike nima fita zanyi.... Zauna! Ta nuna shi da yatsa. Allah mamee....wallahi ba in da zaka je har sai ta tafi, muguntar ka ke ban sani ba? Wallahi babu abinda zan mata mamee....... Allah bazaka fita ba na ma rantse. Ya zauna rai a bace, Ta fito simi simi ta wuce ya bita da kallo idon mamee na kansa. Ta buga tsoki, Allah ya raba ka da wannan mugun hali. Ka fitina wa yarinya saboda shegen son zuciya kai da abun duniya bai taba wucewa wurin ka.... Mameee... Kawai ta mike tayi ciki tana fadin halinka ne ban sani ba ko kuwa mugun rikon ka ke ban sani ba? Ya tabe baki yana 'yar dariya mamee masu 'ya duk ta hakikance. Bayan isha'i ne mameen ke fada mishi dalilin murnar umaimah, wani dadi ya ziyarce shi ya ce *anzo gurin* sannan yayi murmushi lallai tana son karatu amma *Mr samuel* ya fara mata *lesson* kona wata biyu ne tukun tunda kin ce tana da ganewa. Baki mamee ta bude tana kallon sa bata taba tunanin abin zai zo da sauki haka ba, ta shirya taro mishi ta inda duk ya bullo. Ya zungurota mamee.....yana murmushi. Ta kara kallon shi, tsakanin ka da Allah har azuciyarka haka maganar nan taka take ba wasa? Yau na bani wai daukar me kikeyi man ne don Allah? Kina tunanin duk abinda kike so zan kishi ne mamee? Yau kuma? Ta bukata tana ci gaba da kallon sa. Ya dafa kafadarta mamee *I mean it please* bacin amincewa ma hada shawara na bayar. Ta fara shi mishi albarka yayi sokoko yana kallon ta yanda ta dage tana nuna tsantsar farin ciki. A zuciyar sa kuwa kagare yake gobe ta yi yaga kalar murnar da umaima zata yi idan taji ya amince. Don wacce ta yi marar dalili ce yayi murmushi. *Gobe zata yi mai dalilin kam* daga ni sai ita bata taba mun dariya ba ko ta mugunta kuwa, sai dai na gani a sace ita da mamee shima tana ganina zata gintse... Yaja guntun tsoki. Su goggo nata shagalin nama umaimah na daki ta makure, ohh ni umaimah na shiga uku da wannan mutume. Tsikar jikinta ta kara tashi *yarrrrrrrr* tana hasko ta bisa jikin sa kwance, ta kudundune kai a cinya lokacin da amon muryarsa yazo mata, *am very sorry kiyi hakuri* yau ni madaki ke ba hakuri. Ya ce yana so mu daina fada gashi a gaban mamee ya mun abinda bai taba ba, ko ya daina jin tsoron ta? Jikinta ya kara sanyi ta tuno sungumar da yayi mata ya kaita sama, *ohh ni ina na kai kaina ni marainiyar Allah* Ta dago kai, nima ina so mu daina fada, idan ba masifa yakeyi ba muryar sa na da dadin sauraro, yana da masifar kyau gashi dan gayu, da yawa ina son kallon sa amma ina tsoro. Jijiyoyinta suka kara tsinkewa da ta tuno shi zukunne gabanta yana magana a tausashe. *ohh ni umaimah* mai kudi kamar *madaki* ta ce *Hmmmm* Haka ta susuce ta kwana tunanin sa. Ta kagara gari ya waye, daren yayi mata tsawo juyi kawai takeyi. Karfe uku yau ta yi wanke wanke da duk abinda ta saba, lokacin da aka kira sallah tana shafa mai har tayi wanka, Ta yi tagumi gaban jakar kayanta, wane zan saka? Ta fiddo wannan ta mayar, sai da ta kare kaf, ta yi tsoki tafi mintuna ashirin da a haka, da kyar ta amince da wata atamfa roba wacce ta siyo dari tara lokacin bikin *Asma'u* dinkin riga da skirt ba kwalliya amma kayan na mata kyau. Ta rangada kwalliya saboda gwana ce sosai karambanin ta yasa ta iya kwalliya sosai da daurin kallabi, idan ana sabga ita ke wa mutane da dama. Abinda ke hanata yi karancin kayan shafan. Ba ta hauka tayi ba, bayan ta gyara gira yar hoda kawai ta shafa da dan Jan baki sai kuwa kwalli data zizara, abinka da ba sabanba umaimah ta yi wani fayau. Shidda da rabi tabar gidan, bakwai da kwata ta isa. A gurguje ta gama aikin ta baro mamee ciki ta dawo falo. Kadan kadan ta kalli sama shiru bai sauko ba, tayi zugumm!!!! Haka kawai yau ganin sa take son yi. Mamee ta fito uwani shirya mana break yunwa ta gargado ni, ta tashi da hanzari, tanayi tana waige amma shiru bai sauko ba, Mamee na zama ta dauko flask kenan zata zuba ruwan zafi ya fito *a slow motion* ta rinka ganin takun sa, sanye yake cikin wani farin boyel mai zanen kwallo kwallo ya kashe hula har goshi kansa sunkuye yana faman daura agogo duk falon ya dauka da kamshin turaren sa. Kirjin ta ya shiga harbawa ta fara yar kyarma ta sunkuyar da kai tana zuba ruwan zafin, Idanun sa yakai kanta har ya iso bai daina kallonta ba ita kuma taki dagowa, *Morning mamee! Ina sauri zanje office for an urgent meeting* A aika mun da break by 11:30am. Ta dago da sauri har ya kusa kai kofa. Wani abu ya tuko mata, *Allah ya bada sa'a* inji mamee Daga can waje ya ce amin ya kara gaba. Na shiga uku wai me ke damuna? Ke lafiya? Ta yi firgigi, Menene? Ta kara Bukata, Ta danyi *pretending* cikina ya dan katsa, ta sa hannuwa a cikin. Yunwa ce maza hada kalaci, ta tsareta. Haka nan take cusawa amma Sam ko dandano bata ji. Ta fada mata zata fara *lesson ** daga litinin din nan. Ta danyi murna mamin bata damuba tunanin ta ko cikin ne ya dameta. Shiru shiru har Biyar da rabi bai dawo ba, hankalin umaimah ya tashi *kadai fa son madaki nake na shiga uku?* Ta dauko kayanta ta yi sallama, tana Jan kofa yana budewa yayi Saurin rabewa jikin bango ya bata wuri alamar ta wuce fuskar sa ba yabo ba fallasa. Ta dan kalleshi kadan ta wuce, Ta na bada baya, ya bita da kallo kamar ya janyo ta amma ya sha alwashin daga mata kafa har sai zuciyarta ta dan saki dashi sannan yana gudun kada ya takura mata ta botsare ta ce karatun ma bata so. Wannan shine rashin sani.... Ta dan waigo har ya turo kofa. Na shiga uku ya fita harka ta? Ta juya sukuku. Abu kamar wasa ya ma rage zama gidan, kullum sai ya ce a bishi da kalaci, abin ya dameshi amma ya daure, musamman da yaji ta fara lesson. Ga umaimah kuwa ta gama rikicewa, yanzu labewa ta keyi tana kallon sa ba tare da ya sani ba, wani karin takaici da ya hau sama ya ganta tana gyara sai ya koma falon mamee. Haka zata leko shi tayi ta kallo, Umaimah fa hada yan kwalla ta rasa in da zata sa kanta mamee tayi tambayar duniya amma tayi shiru har ta sa mata ido. Har an yi sati a haka duk susuce, ya dan fara zama akai akai. Amma ba abinda ke hada shi da ita. Bayan kwana biyu yana zaune falo shida mamee suna magana, ta koma can gefe ta tsare shi da ido yana cikin magana ya dan waiga ya hangota ta glass. Gaban sa ya fadi ya kalla sosai shi din take kallo. Tun daga ranar sai ya sa mata ido aikuwa ya gano irin kallon kurullar da ta keyi mishi a boye. A gajiye ya dawo aiki, tana sama tana mishi gyara, koda taji shigowar sa ta watsar da gyaran ta rugo tare da lafewa in da take boyewa, yana kallon ta don yanzu duk wani maboya nata ya sani, suna ta labari da mamee tana ta lekowa tana kallon sa da taga zai juyo sai ta koma, Ta koma kenan ya tashi yayi saman tana lekowa zata kalla ......kwatsam taga mutum gabanta...... *godiya ta musamman ga*:- 1. Agamcy 2. Rahama nahaja 3. Maryam Yusuf. *MAMAN ABDALLAH* 😘😘😘😘😘😘😘😘😘 [1/25, 7:39 PM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣7⃣ ....... Ta tsorata matuka, ga wata masifaffiyar kunya data addabeta. Ya sha mur, wa kike leke? Ta yi dabur dabur..... Ta dan ja baya, ya bita, ta kara baya ya bita, table ya to kareta ta yi baya zata fadi ya tallobota abinda yake so kenan, ta koma jikin sa da karfi ya mata wani riko, Wa kike leke ina tambayar ki? Ta daddage ta cije cikin karfin hali ta motsa jikin ta amma rikon da yayi mata bata iya ko taki daya sai ma ya kara hada ta da kirjin sa sosai, Allah sai kinyi magana zan kyaleki, waye kike leke? Ta dago kadan amma ta kasa kallon fuskar sa, ta saki harara *yo ni kai nake kallo*? Na ce kina kallo nane? Leken me kikeyi? Malam ni ba leke nake ba zan dauko bokiti ne na taho na ganka gaba na. Duk nan sama ba bucket sai kin sauka? Jiya fa da zan fita wacece na hango bayan labule tana kunno kai???...... Kirjin ta ya harba da Sauri na shiga uku, idan ina magana da mamee sai ki koma bayana kina mun kallon kurulla ko shima duk zaki dauko bucket ne? Cikin ta ya kada, lallai ya gano ni, sai gara in nannade kunyar nan da hauka. Ta tattakura ta ingijeshi yayi taga taga.... Idan kai baka kalleni ba ta yaya zaka San ina kallon ka? Allah ya sawake ni banga abin kallo jikin ka ba, wata kila kuma kallon tausayi nake ma babban mutum kamar ka amma kullum ka tsaya *sa'in sa* da diyar cikin ka, ka kasa fita harka ta........ Shut up. Ya hayayyako mata karya kikeyi wallahi kallo na kikeyi kullum ina lura dake, shekaran jiya da kika fita da gudu kika boye bayan flowers kina lekena zan fita ko shima duk tausayin ne? Ya fizgo hannuwan ta ya rike gam, idan kina da wani abu a ranki ki fidda *kada ki jefa kanki ga wahala, masifa, da tashin hankali*....... Gaban ta yayi wani mummunan faduwa na shiga uku. Duk illahirin jijiyoyin jikin ta suka saki. Ke 'yar abun nan har kin isa kiji tausayi na? Yanzu dai cika ni!.ta fada a sanyaye. Ya kalleta sosai shima sai jikin sa yayi sanyi, Ranta yayi mugun baci gashi yana gani a fuskarta amma ta kasa magana. ....bazan cika ki din ba ki kwaci kanki idan kina da karfi.... Sai kawai tasa mishi kuka. Ya tsare ta da ido shi kadai yasan azabar da kukan ta ke haddasa mishi. Ya ci gaba da kallon ta jira kawai yake ta motsa zata gudu ya rungumeta. Yaga dai bata da halin motsawa ya cire bandir din dubu dari aljihun sa ya birkito tafin hannun ta ya saka *ga cikon kudin ki da albashin ki* Yana dorawa ya saketa, tayi kasa da gudu, ta fada toilet din falon don ta gyara fuskarta. Ya bita da kallo, *Wai ita din nan ta iya boye abu a rai* mtseww yayi tsoki. Zukunne tayi ta dora hannu a ka *na shiga uku ni umaimah* sai kuka. Sai da tayi mai isarta tukun ta wanke fuskar ta tafito. Har lokacin yana inda ta barshi, tana fitowa ya gangaro da sauri, ita kuma tana ganin sa tayi ciki da gudu. *Au na kuma yin laifi?* turkashi sai kawai ya koma sama cikin damuwa. Mamee na baya, sai kawai tayi kwance bisa gado. *kada ki jefa kanki ga wahala, masifa, da tashin hankali* maganar sa ke dawo mata ta mata amsa kuwwa. Har yaushe ni umaimah? Ai na gama janyowa kaina duk abinda ka zayyano. Ta tashi zaune, waya aikeni? Wannan wace irin masifa ce? Da kwalla sun taho sai ta hadiye. Zuciyarta tayi mata nauyi. Qalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta daga hannu sama *ya Allah kada ka jarabeni da wannan masifa. Allah ka tausaya mun ba don halina da maraicina ba sai don darajar annabin ka SAW* Kwalla suka shatato mata. Tayi saurin gogewa ta tafi kewaye tayo alwala kawai sai ta hau kwalliya kada mamee ta gane taci kuka. *Madaki* kuwa yana hawa sama ya fada wanka shirin kananan kaya yayi . (Basai na misalta ba kun San dai ruwan designers ne ). Shiri yakeyi yana Sabbatu. Na gaji da rigimar yarinyar nan *Wallahi so na ta keyi* amma Girman kan ta zai wahalar da zukatan mu. Ko kuwa ni zan ce ina son ta don ta daukeni sakarai? Ni da zata furta sai in fake ta nan koda tana kawo man raini in ce taimakon ta nayi. Amma ina bada kaina gareta wallahi *sunana sorry* Yayi guntun tsaki *ina!!! This will never happened* Yana gama salla ya zo ya zauna yana barazanar karatun jarida. Biyar da rabi ta wuce ta fito, hannunta cikin hijab ta rungumo kudin da ya bata cikin bakar ledar data saka su. Har lokacin mamee na baya gun yan aiki. Ya bita da kallo, tana fita ya mike yabi bayanta. *Ke tsaya*! Ta yi chak ba tare da ta juyo ba ya sha gabanta. Meye kike kuminiya dashi cikin hijab? *ko ya fara mun zargin sata?* ta dago da sauri tare da fiddo kudin ta warware ranta a bace. *kudin da kaban ne* ko kana tunanin ina sata ne? Ya zaro ido....... Ta daga mishi hannu, billahil azim ban taba daukar abin wani....... Shut up joo... Ke me yasa kin fiye fassara mun magana bai bai? Daga tambaya, ai nasan kudin ne ..... Au kasan ma sune ka biyo neman magana? Ke malama taimaka miki zanyi in kaiki gida ko kina tunanin duk da wannan kuminiyar da kikeyi dasu cikin jikin ki baza'a gane kudi bane? Kin San hadarin tafiya da su a haka? Ina abinda ya dameka? Koma menene ni kai sama ba kaiba meye zai dameka?..... Ya cumumiyo ta dole ya dameni mana saboda......yayi saurin kulle bakin sa. Taja baya da sauri, kar ka kuskura ka kara taba ni zan..... Me zakiyi ya fizgota. Ka duba ka hango yanda masu tsaronka ke kallan mu.... Ya waiga da sauri tare da sakinta, karki kara zuwa gidan nan ba jaka daga yau. Ta balls mishi harara wani mugun haushin sa takeji, a da ina da niyyar siyan ta amma wannan dokar taka yasa na fasa. Kawai ta juya ta tafi. Ya nufi bakar jeep din sa da sauri ya tayar, body guards dinsa na ganin haka suka shiga tasu ya daga masu hannu alamar kar Wanda ya biyo shi. Ta na ta sauri har an fara Koran sallah yasha gabanta, Shigo in taimaka miki in ajiyeki gida. Bana son taimakon ko Kaine ..... Ya fito da sauri ya fizgi hannun ta yayi mota, ta tokare bafa zan shiga motar ka ba malam... Kawai ya sungumeta yayi ciki ya datse sannan ya zagaya. Kin fiye taurin kan tsiya ya fada tare da zama, an ce za a taimakeki.... Yau naga ikon Allah na ce bana son taimakon ana dole ne? Kwarai kuwa gashi an miki? Ya fada tare da kallon ta yana harara. Ta yi mishi banza. Tuki yakeyi amma hankalin sa na kanta. Duk ta hasala tun dazun, ko baya lokacin ma da suke fitinar gadan gadan yanayin fuskarta baya canzawa haka. Sai wani fushi kikeyi kina turo baki an fada miki gaskiya, bari a kyaleki kiyi *mussai*...... Ya rama fadin kalmar da tayi mishi baya. Kan ka akeji dai. Ta fada. Me kika ce? Ban sani ba ta fada tana murguda baki. Kilibabba, dadi ya gama wulakanta ki kin shiga *motar madaki* amma saboda feleke har......... Allah ya tsareni ai ni napep ko mashin ya fiye mun sau dubu da wannan motar, ya dauko waya, *hello,..... Yeah fine,.... Okay .... Yeah only 10-15 minutes no only .... Thanks* Ta tabe baki *yeah* ta kwaikwayeshi ba tare da ya gani ba sannan ta banka mishi harara. Ya kashe tare da juyowa *ke me kike fada*...Sai naji zafin makara in maimaita... Ya ci wani uban birki, ta kankame jikin ta tasan *shaka ce* Sai taga ya bude ya fita. Ya zagayo in da take ya bude, fito mu je....... Ta kwalalo ido *na rantse da Allah kana tabani zan kwarara maka ihu* ko ka kaini gida ko....ya maida kofar ya rufe Sai yayi locking din ta kawai ya wuce, tabi wurin da kallo. Taga an rubuta, *shop rite* Gidan uwar wa ya kawo ni na bani? Yana nufin Sai ya karaci gantalin sa zai mayar dani gida? Wannan salon wulakanci da me yayi kama anya mutumen nan bai gama karto ni ba? Allah ya karto ni gashi abinda yace dani. Idanun ta suka kawo kwalla *Tawa ta sameni ni umaimah* Dole in danne zuciyata ko zan mutu.... Duk layin jikunan ba kowa saboda wayar da yayi aka dauko mishi designers kala kala ya ce wacece *latest?* Haka aka zabo mishi ta *N250k golden brown* ya biya. Sannan yasa aka kawo mishi katon bokitin ice cream ya fito yaron na dauke dasu. Burun taji ya shigo har ta dan tsorata tayi zumbur, Ya kalleta *ke ar can matsoraciya* Ya bude bayan motar aka saka. Ya dankwashi kanta *ke me yasa baki iya sannu ba?* Ta Dalla mishi harara, wai kai idan hannun ka bai taba jiki na ba baka jin dadi ne? Kwarai kuwa, kin san ni ko ina yaro bani da abokin fada yanzu da na sameki ne abun ke mun dadi. Ta yi mishi banza. Sannun bazata samu bane? Eh ta fada rai a bace, ko aiken ka nayi? Ya girgiza kai ko daya. Nesa da layin gidan su ya ajiyeta ta kalleshi cike da takaici zata yi magana saboda mashin ko napep har bakin kofa,.... Ya ce idan na shiga da motar nan akaga kin fito za a tuhumeki a fara miki surutai ko in karasa? Ta yi shiru... Tabbas haka ne. Ta bude kofar taji gam ta yi saurin kallon sa. Ai ban gama ba ya sa hannu ya janyo jakar, idan kinayi wa Allah karbi jakar nan ba don ni ba *for your safety* Ta dan harareshi menene safety? *ki tambayi Samuel* Kamar bazata karba ba sai kuma ta sa hannuta fizge. Ya kalleta kawai ya basar don yasan *kyas* zata jefeshi da jakar taki karba. Sai ka bude mun ko malam? Ya fita da sauri ya fara fiddo *ice cream* din sannan ya bude mata, ta duro da karfi saura kadan ya kwashe da dariya amma ya kara tamke fuska, ..... Ungo ki kaiwa yan gidan ku tsaraba..... Ta yi saurin ja da baya... Tabb in ce ina na sameshi? Ki ce ubangidanki ya ji Kansu ya siyo..... Wai kai idan baka nemi ci mun fuska ba Baka jin dadi? Kaji Kansu kamar yaya?/na rokeka ne? Sai kin roka? Ko an fada miki bana sane da ta'asar da kikeyi wa mamee idan an kawo mata? Nasan suma haka suke da shegen kwadayi kamar ki. To bazan karba ba bama bukata, kawai ta juya ya yunkuro zai dankota ta kwasa guje. A zaure ta boye kudin cikin zani. Sannan ta shiga. Kamar kullum kowa na tsakar gida ana zazzaune har an fara kiran isha'i. Fitila ta haske ko ina abinka ga karamin gida.... Ko zama batayi ba taga mutum ya fado... *KE NI ZAKI BARI DA BOKITI A HANNU BAKIN TITI?* Ta zabura, tare kwalalo idanu........... *maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘😘 [1/26, 9:14 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣8⃣ *Godiya ta musamman ga Bollywood addict members na gode da addu'o'i da kaunar Ku. Kamar su Rumaisa, sanah, secret writers, Hanan, khadycute da duk wadanda ban ambata ba ina yinku*😘😘 .... Ta zaro ido, yau na gama shiga uku ni umaimah, ya ajiye ice cream din da karfi ya tunkareta tayi baya baya ya hada da bango hannuwansa duka a kafadunta, Duk illahirin gidan kowa ya mike kamar an tsira mishi allura kusan mutum hudu zuwa shidda suka hada baki..... *Alhaji umar madaki*???? Me yasa kike da taurin kan tsiya, Ke bakya tausayin kanki ko? Tayi shiru tana kyarma. Ya daki bango *ki kiyaye ni zan wahalar da ke matukar baki sauya hali ba.* Har ya juya ya dawo da sauri, bakwai idan ta wuce miki da minti daya gobe baki je aiki ba sai na 6atar dake sannan idan kin cika ke din mai taurin kai ce ki ajiye jakar nan kada kiyi amfani da ita, wallahi ko da kuskure baki dauketa ba sai na baki mamaki. Ya juya ya fice yana huci. Goggo hansatu ta kai mata wani uban duka *don ubanki bishi ki bashi hakuri kar ki janyo mana masifa matsiyaciya mai halin munafukai* ta ingizata da karfi, ashe bai fita ba zaure ya lafe tana zuwa ya fizgota tare da toshe mata baki yana magana rada rada. Wannan dogon layin naku zaki bi? Ke me yasa baki da tunani ko kin manta motata nacan farkon layin. Idan kin bini wazai maidoki? Ohh ni dai na bani. Wannan masifa har ina? Tayi tayi ya saketa ya kiya, kwallan da take faman hadiyewa suka shatato. Ya banka mata harara inda kikafi auki kenan ya juyata ta kalli kofar shiga gidan sai kawai ya ingizata *shiga maza* ya fice da sauri. Tabi bayan shi da kallo, duk yau bai bata haushi ba, amma tana tausayin kanta. Lokacin da tashiga an kachame rabon ice cream, Kowa ya bita da harara, goggo jummai ta ce ke kuwa meye hadinki da *madaki*? Tayi narai narai gidan sa nake aiki, matar data zo kwanaki mahaifiyarsa ce........duk suka zaburo *gidan sa*??? Ta ce eh, yanzu ma ita ce tasa ya rage mun hanya shine....... Shine don ubanki kikayi mishi mugun halin naki ko? Tsinanniya mai mugun hali. Wallahi goggo ban san bokitin.....ke ar can munafuka ko baki akayi ki kawo mana mugun halinki zai barki ne? Shi mai kudi an fada miki yana da wannan mugun kudurin ai sai talaka irin ki jakka. To kin daiji sharuddan shi idan kikayi wasa halaka ki zaiyi sakarai kuma wallahi ko cigiya. Mai bakin jini ke duk inda kika raba sai an tsane ki anji ba a kaunarki. Kai ina ma amfanin yarinya irin ki shegiya, Goggo tayi karaf, ai idan ina fadi bekena ake gani. Irin su shatu ne munafukai, idan an kirasu cin arziki sai su zake Suna nuna isa kuma ta banza tunda baka dashi. Luba dake zaune tana ma ice cream cin tuwo da hannu ta ce, Kun tuna mun wata munafukar yar ajin mu. Usaina 'Yar gidan kansila kawar mabaruka ce tare suke komai, to labuda kuma kawar mabaruka ce ta janyo ta itama taci arziki. Kawai sai ta fara kiran ta da *mamana* ai kuwa usaina ta ringa jin dadi tana zabga mata abin arziki, shi kenan tana ganin wuri sai ta fara ma labuda bakin ciki tana gaba da ita, idan gaban usaina ce faran faran da sun kebe tayi mata magana sai ta kyaleta, ai kuwa kowa ya karto tsinanniya aka fara bincike sai gashi an gano ba sunan *uwarta usaina* ba makirci ne da kwadayi irin na munafukan mutane. Kinji ko? Goggo ta fada, muma Allah kadai yasan abinda ake bamu bata kawowa munafuka. Ice cream din da umaimah bata sha ba kenan ta nufi salloli. Tana gamawa ta tafi gidan Alhaji yakuba. Hajiya na ganinta ta ce me akayi miki kamar kinyi kuka? Ta kakaro murmushi tayi tayi amma ta kasa sai kawai ta fashe da kuka, hankalinta ya tashi kwarai, Umaimah ya akayi? Ta dago fuska sharkaf, wallahi na rasa in da zan sa kaina inji sanyi. Ya akayi? Kin san nazo na karbi dubu biyar ko? Abinda ya faru....ta fada mata. To shine yau ya bani da cikon wancen dana wannan watan kin gansu amma INA tsoron kai kudin nan gidan mu sunyi yawa, idan suka saba ina kai kudi da yawa ranar da ban kai ba na shiga uku saboda wani irin birkitatten mutum ne. Ikon Allah, yaro ba mutum ba sai ya girma, duk abubuwan naku yazo da yarinta umaimah, kuma wallahi kin mun Kyan kai tabbas *da* da mahaifi sai Allah kinyi zurfin tunani da baki fada mata ba, maganar kudin nan ma wallahi naga hankalinki, Shi kam yayi wauta da yarinta a matsayin sa bai kamata ya biye miki ba, ina shi in ke? Ta ce *Hmmmm* kawai Ta fiddo kudin ta mika mata shine na ce bari in zo duk abinda kika gani. Ta karba *Au yo ai ke lissafin naki hada riba ya dora* nake ga dubu Dari ne. Tabb wallahi baki basu sarka zan siya miki dasu. Sarka? To ke kuma fa me zaki dauka? Tayi murmushi wallahi bani taba miki kudi kinji na rantse. Wadancen ma suna nan zamu ajiye tsaron lalura. Daga wannan watan idan ya baki zan fara miki siyayyar kayan kitchen ina ajiyewa, ki ringa basu dubu biyar din. Allah yana tare da maraya. Kuma kayanki nacan duk na bayar dunki saura leshi da atamfa na ajiye zuwa gaba.... Wallahi nabarwa farida nima na rantse bazan karba ba. Ta rasa me zata ce mata . Tayi saurin canza zancen *kuma Hajiya zata sanyani makaranta.* ta kamota ki bari don Allah, Allah har an fara mun lesson ma Dana gama fahimta zan fara zuwa. Amma tace inyi shiru , Nima abinda zance kenan. To Alhamdulillah ai kyawawan dabi'un ki umaimah bazaki taba wulakanta ba. Suka sha fira, umaimah ta fito zuciyarta fes! Duk wata damuwa ta rageta. Lokacin da ta shiga kowa ya kwanta, itama tabi lafiya, amma jiya wayau, barci sama sama tunani ya hanata runtsawa. Goggo ce ta tada ta karfe biyar da rabi, *Barcin ubanwa kikeyi* ta kai mata duka tayi firgigi, shegiya kafaffiya duk gargadin da yayi miki shine yau ma kika gyara kwanciya? Idan ke zaki janyo wa kanki da sauki muma tana iya shafar mu ja'ira mai taurin kan tsiya. Ki tashi kiyi man wanke wanke da shara. Haka ta yi sallah ta hanzarta kada ta makara, Daga bakin gate ya hango shigowarta tana ta uban sauri rataye da jaka, yana tsaye sama yana kallon ta har ta shige ciki. Yayi murmushi ya koma daki ya kwanta. Ko da ta shiga babu kowa falon tayi ciki tana gunani, masifa ce kawai ko nazo ko banzo da wuri ba ina abinda ya dameshi tunda ba jirana yakeyi ba. Idan ta gaskiya ne ya zauna falo mana. Mtsew taja tsoki. Tana shiga mamee ta tashi zaune 'yar halak kinki ambato wallahi yanzu nake shirin kiranki a waya. Tayi murmushi gani ta samu ne? *Dan kifin nan* zaki siyo mana irin na rannan kiyi mun faten dankalin ki......hahahaha lallai kinji dadin sa. Kuma kamar wasa na kwatanta dana gani a *Arewa 24* A a da dadi kam, ki siyo mun tumatur irin manyan nan. Tayi murmushi kwadon ne ko? Kin tuna mun da *lansir* ....ai fa ta fada tana laluben inda kudin suke, ta dan juyo nawa zan dauka don zan siyo kwakwa da danyar citta...... Dauki dubu biyar ai lissafi yanzu kika fara. Duk sukayi dariya, kifin na nawa? Dubu daya ko yayi kadan? Kuma zan dauki har dubu biyar? *lansir* din da na hamsin ma mugun wajiba akeyi dashi? Ta yi yar dariya kedai dauki hakan nasan yalo, soyayyar aya duk suna can suna jiranki, suka kara dariya. Yi sauri ko kya dawo. Saboda duk kasuwan kowa na sammakon siyayya saboda juma'a ce sai goma saura ta dawo, tana shigowa ta tarar dashi zaune ya hada gabas da yamma. Simi simi zata wuce ya daka mata tsawa... *Daga ina kike?* Ta yi chak! Ko ba kya ji? Kasuwa, ta fada kai sunkuye Ya banka mata harara tare da yamutsa fuska *kasuwa?* Ya mike , ta yi sauri ta bude jaka wallahi kaga mama ta aikeni na siyo kifi, tumatur, lansir ta fara fiddo kaya ruwan kifin duk sun bata jakar da na tumatur. Ya zaro ido *What?* *Umaimah kina hauka ne jakar *200+ kika sako wannan shits din*???? Barkan mu da rana *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘 [1/26, 9:59 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣1⃣9⃣ ...... Kayi hakuri ledojin ne sukayi mun yawa shine naga meye amfanin jakar.... Ya finciko ta baki fahimci me nace ba? Kin San kudin jakar nan kika sako mata wannan tarkacen? Ya girgizata *dubu dari biyu da hamsin* Ta zaro ido na shiga uku, ta zazzage kayan da sukayi ragowa tana kyarma, *dubu dari biyu da hamsin* kudin kawai take maimaitawa duk ta gigice sai kawai ya rungume hannu yana kallon ta cike da takaici, Tabar jakar nan ta shiga kwashe kayan tana kaiwa kitchen, sannan ta dawo ta dauki jakar tana dan sayar kallon sa, Ta tarar komai an hada mata har dankalin an fere, ta shiga hadawa, Koda ta gama ta kawo musu bisa table bata tsaya ba sai tayi ciki. Ya bita da kallo, *yarinyar nan muguwar bagidajiya ce mtseww* Mamee ta kalleshi cike da kulawa lafiya? Ya ce ba komai, Ta zuba faten zata fara sha, ya kalleta Meye ke kamshi haka? Faten dankali ko zaka sha? Ya danyi jimm, eh kamar hakan. Tayi murmushi kilibabbe, Wasa wasa sai da ya share plate biyu, a lomar karshe ya kalleta mamee dama shi kika mun tayi last time na bar dadi haka? Tayi yar dariya au kajiye ma bakin ka kenan. Gaskiya ya mun dadi ayi. 'Yan aikin nan naki na bada wuta kwanannan. Na lura masu kalacin safe sunfi sauran iya abinci fa, last week ma na ci wani Dan bread da SOS ya mun dadi a office kamar na kuma waya. Ai uwani na kokari kam don yanzu kalaci inba ita ta hada mun ba bana jin dadin sa saboda yan makulashen nan. Uwani? Ya bukata, Uwani fa ai karambanin ta ya wuce inda duk kake tunani, duk abinda ta ga wani yayi sai ta kwatanta. Ga tambaya, ai tana da kwalwa. Lallai idan akwai saura zanci da dare a ajiye mun. Ta kalleshi da sauri *a ajiye ma Kana nufin a *dumama*? Yayi murmishi haka na ce mamee, Umaimah kuwa tana baya ta debo uban *klin* ta zuba a katuwar roba tana ta gurzar jaka, mamee ta kwala mata kira, Ta antayo da gudu hannun ta duk kumfa, Ya bita da kallo duk ta jike hijab dinta, Naga hannunki kumfa me kikeyi agogo? Mamee ta bukata tana kallon ta cike da kulawa. Tadan murza hannun kumfan ya fado kasa tana satar kallon sa, jaka nake wankewa...... Ya dago *what a ruwa kika saka ta?* Mamee yar nan taki wallahi duk abinda nayi mata kar kiyi magana. *Da tayi maka me?* Ki tambayeta gata nan, ya nuna ta da yatsa, Uwani me kika mishi? Ta dan kara kame jikin ta tana dan in ina....... Uwani matso nan saki jikin ki. Ta kalleshi wallahi bani son takurawa yarinyar nan da kake yi madaki tsoron ka takeyi kamar me dubi yanda jikin ta duk ya rikice da kyarma ina dalilin wannan azaba? Ta kamota me kikayi mishi? Jiya ne ya ban jaka ban san cewar mai tsada bace shine....... Ki faro mata daga farko.... Ya katseta. Kai bana son shiga uku kai ka fada man mana. Mamee yarinyar jiya zan tafi stadium na hadu da ita hanya zata je gida na taimaka mata na rage mata hanya na ganta da kudi a hannu na ce bata sawa jaka ta ce bata da ita, na biya na siya mata mai tsada shine yau ta yo cefane da ita duk kifi da karikitan data siyo ciki ta zubo shine......... Shine me? Ina ruwanka idan wuta ta saka ta Ina ce kai dai ka bata ko?, zai yi magana ta daga mishi hannu kai bani son rashin gaskiya, daman ka siya ne don ka uzzura mata, duk tsadar ta ina ita zata san haka? Ta kalleta kin rage dan faten? A a duka na juyo shi sai Wanda na diba a plate...... Sai ki ajiye mun shi kar ki taba. Mamee ta bishi da kallon takaici, Ko bakiji ba? Ta ce to zata juya, mamee ta kamota je ki ci fita batun sa,..... Haba mamee ....... Zakayi mata kurulla ne? Sai kawai ya mike ya nufi kitchen din ya dauko. Wai madaki meke damunka? Ai mamee idan na zauna gidan nan wata rana ma cewa zakiyi ba ki haifeni ba sai uwani ya wuce sama da plate din. Ungo wannan je karasa cinyewa kyaleshi. Kullum ganin kansa yakeyi yaro karami shi yasa nake burin yayi *Aure* gaban umaimah ya fadi *wai ya zanyi naga madaki da wata?* Tayi ciki tana karasa wanke jakar, Ta ringa jiyo hayaniyar mutane, ta sami mamee daki ta ce, kamar baki nakeji falo. Wannan fitinannen ke meeting ai shirin zuwan su ne jiya na wuni baya ina gargadin su mansurah, manya manyan manajojin sa ne, Au, ta fada a takaice. Firatan ya ki hawa sama duk ya takura kowa. Madaki kuwa yasan yau wuni zaiyi tare dasu gashi baya son umaimah ta tafi bai sani akwai maganar da zaiyi da ita. Karfe uku aka fara shirya musu abinci kamar yanda ya tsara, umaimah an dage aiki baji ba gani, magana yakeyi amma hankalin sa na gunta idan ya hangota ta fito. Ashe shima cikin manajojin shi daya ya hangota nan da nan hanakalin sa ya dauku. Ya dan juyo yana sosa keya, 'Yallabai ni fa na hango iri. Ya maida hankalin sa gareshi sosai saboda shine babban manager da yake ji dashi a Lagos yake, Iri na me? Dai dai ta fito ya ce waccen yarinyar....... Ya sha mur *Bana son maganar banza* abinda ya kawo ka kenan? Nan da nan ya kame kansa saboda suna bala'in tsoron sa. Suka tafi zuwa dining, Sun fara cin abinci kenan sai gata da tray an nado kaji gasassu. Rashin sani ta ajiye gaban manager ya dago kai tare da dan murmushi ita ma ta mayar mishi, ya ce sannu....... Wata fizga yayi mata sukayi ciki ya kaita har kofar dakin mamee ya ingizata *wallahi kika kara fitowa sai na bata miki rai* ya juya. Ta bishi da kallon takaici, su manager na ganin haka jikin kowa yayi la'asar ya dawo yanata mazurai ya nuna ma kowa plate *serve your self* Kowa sukuku ana ci ana tattaunawa. Yana sauraron kowa yana kurbar lemu yaki cin komai. Umaimah kuwa tana shiga ta ce mamah mun gama bari na dan huta , suka fara fira, Bayan sunyi sallah suka dauko gyada mai bawo soyayya data siyo kasuwa ta juyo ta a tray suna ci. Gashi an rufe kofar baya ya ce kada Wanda ya bude, ga shidda ta wuce tana son tafiya gida, ta rasa yanda zatayi. Kamar mamee ta karance ta, Uwani yau ko fira za a mun naga baki fara wannan saurin naki ba gudu gudu. Ta danyi murmushi, na ga har yanzu suna falo kada ya ce ina mishi sintiri.... Ke kama hanya ki tafi gida kinji gobe kin san akwai lesson kuma na safe. Taji wani kwarin guywa ta fito simi simi *ya daka mata tsawa bana ce karki fito*.......tayi baya guje Mamee ta ganta kamar an jefo ta. Ke lafiya waya biyoki? Tayi shiru tana kallon kofa. Ya mike tsaye, kowa na iya tafiya gobe ma karasa by 8:00am. Yana gama fada ya haye sama da sauri. Mamee ta ce muje ta taso ta a gaba. Ba kowa falon umaimah tayi turus. Kama hanya ki tafi gida yanzu kyaji kiran sallah. Ta ringa hada kafafu don sauri gudu gudu ta fito tana rufo kofa taga mutum tsaye. Ya figeta sukayi wata hanya, me yasa ke kullum kin fi so kiga ina miki hayagaga? Ta sunkuyar da kai. Ya bita da kallo wai yarinyar nan yanzu bata biye mun? Da ke nake magana . tayi shiru, idan kika kara fitowa nayi baki sai ranki ya baci daga yau. Ta ce toh a hankali. Ya kalleta sosai, ko bakiji ba? Naji, ta ce kanta a kasa. Ya dan saketa ga jakar ki can da kika ki karba ta tsaraba na ce maikudi ya kaiki gida kije yana jiranki...... Ta kalleshi da sauri maikudi drivern sa da baya tuka kowa? Ta girgiza kai bana shiga. Dalili? Haka nan, Idan na ce dole fa? Malam bafa zan shiga motar ka ba, kawai sai aga cewar waccen motar ta ajiyeni wane kallo za ayi mani? Zai kara magana ta hada hannuwa don Allah ka kyaleni haka nan na kai makura..... Har jakar bazaki dauka ba? Ko na karba zan raba ka da su ne ba tare da nima na amfana dasu ba to meye amfamin amsar? Ya kalleta har zaiyi magana ya ingijeta ya wuce.... Ta bishi da kallo ohh wannan akwai bahagon mutum ta wuce tana yan tunane tunane. Ya wuce masallaci yana magana kasa kasa cikin fada, gidan nasu zan je in kyare masu warning duk shegen da ya yi amfani da kayan inci uwashi. Ai na karanci matsiyata tun jiya....... *Mukwana lafiya* 😘😘😘😘😘😘😘😘 [1/26, 9:18 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣0⃣ ....... Tana shiga ko zama batayi ba goggo jummai ta nuna mata tulin kayan wankin ta ita da yara, Ko sallar magriba batayi ba ta shiga yi don ko hijabi ta nufi cirewa ta tabbatar sai ta daketa, Karfe takwas da rabi taci dunin wankin sosai, duk suna bisa tabarma ana ta shewa ita ta basu baya. Tsit taji gidan yayi kamar wuta ta dauke ta juyo da sauri, katti ta gani ko wane da bakaken kaya tadan ware ido nan da nan ta gane ko su waye, ta mike zumbur dai dai shi ma ya shigo wasu na binsa a baya. Duk su goggo suka makure sun kasa ko motsi ganin ko wane da bindiga, *Sannu da zuwa*..... Ta fada hannunta jage jage da kumfa, ya kalleta Tun daga sama har kasa sannan ya fara waiwaye ya hango tulun wankin da ke ajiye da kuma Wanda ke a robobi manya. Ya sha mur *Zuwa na yi in miki gargadi na karshe* Tunda mamee ta na ce sai kin mata aiki to babu yanda zanyi domin duk abinda takeso bana kin sa matsalar bazan taba daukar *Kazanta ba* duk yan aikin gidana babu kazama irin ki, ya nufeta kamar zai shaketa tayi baya ya dan bita, *Kinga wannan jakar?* kaya ne a ciki Su zaki ringa sakawa kina zuwa aiki na san ko kala nawa ne don ni na siyo, ko wane turare, sabulu, mai da duk abinda ke ciki nasan kamshin sa da adadin da zaiyi. Ya fizgota na sanki da *Taurin kai* ki bada ko toothpaste ne kiga yanda zan *halaka ki da Wanda kika ba din* Su goggo kowane ya zaro ido tare da hadiye wani dunkulallen miyau. Ya kalli lubabatu dake bakin tabar ma *Ina ne take kwana?* ya daka mata tsawa. Ta tsira hannu *Gashi can*! Ba tare da yayi magana ba cikin kattin wani ya yi ciki da jakar. Ta kalleshi cike da takaici wannan mutum akwai wulakantacce ni zai kira *kazama*? Ji yanda yazo yana mun hayagaga har gidan mu ban tsira ba. Kai ohh ni umaimah na jefa kaina a jafa'i. Ya kalleta sosai *Ki rufawa kanki asiri ki bi doka ta* ya juya kawai duk suka bi bayansa. Ta bishi da harara ta wuce wurin wankin ta. Lubabatu ta saki ajiyar zuciya, goggo jummai ta ce yau naga masifa, wannan matsiyaciyar yarinya zata janyo mana bala'i. Kowa na tofa albarkacin bakin sa amma goggo hansatu ko motsi sai da luba ta lura sannan ta tabo ta *inna*..... Tayi firgigi ta ce *Wayyo mun shiga uku*....... Duk aka kwashe da dariya ta mike da gudu ta suri buta tayi kewaye. Umaimah me zatayi ba dariya ba. Ta ce su goggo manya wannan 'yar barazanar ta firgitata da sune yake ma wujijjigawar da nakesha wataran mussai zasuyi. Ta kara tuntsirewa da dariya sai kawai ta ganta tsaye gabanta tana nishi idanu duk sun fito, kyayi dariya don ubanki hankalin ki ya kwanta ki kawo mana ajalinmu har gida. Ta shiga bambami kowa ya dunga zagin umaimah. Ta waigo goggo haka fa yake da wannan masifar ta babu gaira, saboda Allah luba bana tsafta idan zan tafi? Duk suka kwalalo ido *Anya yarinyar nan bata tare da aljannu?* firar yau batayi tsawo ba kowa ya shige daki. Sai goma saura ta gama tayi salloli, ta kura ma jakar ido gabanta ya fadi *Ohh ni umaimah* Ta juya luba kinyi barci? A a ido na biyu. Au, kuma kikayi lamo? Tashi mu danyi fira bana jin barci wallahi. Ta janyo jakar ta bude sai kawai ta dafe kirji *Na shiga uku* wasu irin kayana ta gani ta ce luba zo ki gani. Mi? Tabb um um , sai kawai ta bata baya kada ma ta hango wani abin ya birgeta. Tayi murmushi ta dauka wasa takeyi sai ma tayi mata banza. Duk sai taji babu dadi *wannan ai mugun hali ne* ta fada a hankali. Kiri kiri yazo ya firgita jama'a. Dogayen riguna masu kyau wasu matsattsu wasu budaddu, turaruka, Mayan shafa wani abin ma bata San ya ake amfani dashi ba,Gyaluluwa kai kaya barkatai , kunya ta kamata ganin brezias mtsew ta buga tsoki ta rufe jakar. Luba dai na jinta tayi lamo. *Madaki* kuwa suna fita yaji kamar ya koma ya dauko umaimah su tafi gida. Yarinyar nan tana wahala gidan can. Wanki hada na yara? Amma mutanen nan akwai matsiyata, zasuci ubansu, ya kuta. Sai na gama ci masu uwa sannan in dauketa in mayar da ita gidana zan fara nemo waye uban tukun shima dayan *shashashan* Yayi dan murmushi Matsoratan banza duk sun rikice ganin bindiga. Sai na mayar dasu ma'aikatan ta a gidan *nasu wasa ne* Da safe ta fito da shirin ta normal zata tafi , tayi karo da goggo lami, ta kalleta sama da kasa Sai kawai ta fizgota ta fara bugu, duk mutanen gidan suka fito lafiya? Ta kallesu tana nishi Ku dubi duk gargadin da yarinyar nan tasha jiya a haka zata tafi. Kowa ya dauki salati nan suka yo kanta mai kulli nayi mai kwanya nayi, suka tasa ta a gaba tana ta kwalla har gaban jakar , goggo tasa hannu ta fiddo wata bakar riga tasha ado da duwatsu rigar ta yi kyau matuka da dan gyalenta karami, suka tsareta ta saka, sanan suka dauko turaruka suna feffesawa suna ci gaba da dankwasar ta *Shegiya mai kunnen kashi* baki gudun wahala baki gudar ma wani. Ta kalli kanta ta kallesu tana kuka goggo haka zan fita da wannan dan mayafin in ratsa gari?........ Gam goggo hansatu ta buge bakin , wannan shegen bakin zai yi shiru ne? Idan ba da shi da uwaki zaki tafi? Ta jefa mata wasu golden brown din takalma maza kisa ki tafi suka rufe jakar, duk tulin kayan babu wanda ma yabi ta kansu har su birgesu. Karfe bakwai da rabi ta shigo tayi sama da gudu cikin bacin rai don kagare take ta iso gidan, yana kwance daki bisa gado yana ta sharar barci, haka kawai yau yaji barci kamar me, Ta dunga bugun kofar da karfi ya tashi firgigi da jallabiya tunda ya dawo sallar asubah. Ya kasa magana ya taso da sauri ya bude a hasale, yana ganin ta yayi turus yaja baya tayo kansa tana bala'i, me kake nufi dani ne, ya dunga baya baya tana binshi, ka firgita man iyaye ka rikitatsu ka kara jefa ni masifa, *Why are u increasing my problems?* ya zaro ido jin tayi turanci, yana kaiwa ta bango Sai ya daga hannuwan sa sama *am sorry* ta daki kirjin sa bazan yi ba wallahi na gaji da halayen ka ...... Ya ce, Ammmmm.... Ta kura mishi ido. Kayan nan sun miki kyau. Ya bita da kallo tun daga sama har kasa yana dan murmushi, taja tsaki tare da juyawa ya fincikota ya maida ga bangon fuskarsa daf da tata ya sunkuyo, ya zaki tayar dani barci ki gudu ai yau muna nan. Ta zaro ido..... Ya balla mata harara kilibabba an kwana tunanina zaki wani taho a 360 kina wani borin kunya.... Ya buge bakin zatayi magana naji ba haka bane kwalliya aka zo nuna mun in yaba ko? Ta ture shi da karfi zata gudu ya maidota tabaya a jikin sa ya leko da kansa ta wuyanta, *Ke bakya godiya idan an miki abin arziki ko?* tsikar jikin ta ya tashi ta rasa in da zata sa kanta, ya lumshe ido yana shakar kamshin jikin ta. Duk sukayi shiruuu kowa najin abin da yakeji a zuciya. Shine mai karfin hali ya dan saketa amma Sai ya ruko hannunwan ta muje can kasan ya dan fizgeta..... Ta jiyo muryar mamee ta yi saurin turjewa ya kalleta *ya dai?* Kai ni dai sakeni don Allah. Ya kara fizgarta bazan saki ba haka zamu sauka sai kawai ta zukunne *Na tuba wallahi ga mamee can*!!!! ...... Shi ma ya zukunna kina jin kunyar ta ne?.......... Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣1⃣ https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH ....... Ya kyalkyace da dariya ta bishi da wani irin kallo. Mamaki ya baibayeta wai meke damun *madaki sometimes?* Ta langabe don girman Allah kayi hakuri ba don ni ba wallahi bazan kara ba... Baza ki kara me ba? Ta yi shiru, kinji? Don Allah ni dai kayi hakuri. Okay naji zanyi amma da sharadi kullum da kinzo zaki wuce sama ki fara gayar dani kafin ki shiga inda mamee take kin amince? Eh na amince duk ta kagara ta sauka, Ya kalleta idan kika saba menene hukuncin ki?....ka rike albashina na amince, No! Banda wannan... Ta kalleshi cikin kosawa duk abinda kaga dama na amince kayi man.... Ko menene? Ta daga kai eh na amince bama zan saba maka ba kayi hakuri , Kiyi man alkawari duk abinda nayi miki zaki rama. Ta kalleshi ya daga kai *yes*! Idan na mareki kema zaki dalla man mari. Ta sunkuyar da kai na amince, no! Kiyi rantsuwa Kice wallahi zan rama. Ta dan kalleshi kaikaice *wallahi zan rama* Ya danyi yar dariya *Good girl* ya maida hannuwan sa baya yadan kishingida kin ce ko menene fa? Haka na ce ta fada tare da yin hanyar falon mamee. Ya bita da kallo yana yar dariya. Saukowa takeyi mamee ta bita da kallo har ta kusa karasowa kusa da ita, sai mamee ta dauki salati..... La'ilaha ilallahu mahammadu rasulullah tana tafa hannuwa *Uwani?* gabanta ya yi wani mummunan faduwa.... Kallon ki kawai nakeyi ina tunanin ina muka sami 'yar balarabiyar budurwa tun da sassafe kuma daga saman bene? Ta karasa maganar tana yar dariya. Ta zumburo baki kai *Mamah* ta kyalkyace da dariya wallahi da gaske nake waya baki tsarabar makka ko kudin naki ne kika kwashe kika siyo..... Kai mamah wai ya akayi? Ta karasa gunta tana yar dariya. Ta dago fuskar ta anya *Uwani na ce yau*? Kai wallahi kinyi kyau. Ko kefa don Allah ki ringa sauya shiga amma kullum cikin kodaddun kaya kamar almajira kina fama da hijabi balam balam kai kace matar liman. Duk suka kwashe da dariya. Allah kullum ina son miki magana amma bana son kiji babu dadi tun da ban san tanadin naki ba. Ta mike zuwa ciki tana yar dariya ta bita da kallo ohh uwani yarinya ce har yarinya talauci babu abinda baya boyewa kuma sai ta zamo tana da hakuri da rashin kwadayi. Kamar kullum *Mr Samuel* yazo ta fita lesson. Yana bala'in jin dadin koya mata saboda bai taba tambayarta sau biyu ba, ya dade baiga mai kokarin umaimah ba. Ya kalleta da yake bayajin hausa ko kadan wata biyu ta gama kwarewa da turancin sa tana ganewa kawai wajen maidawa ne wani lokacin take samun matsala amma yana gyara mata to an wuce wurin. Ya kalleta yana murmushi *primary certificate din ki ya kammala* zan bawa oga shawara ya sanyaki js 3 kawai ina da tabbacin zaki iya. Kinga da kin je SS2 kawai kiyi WAEC. Ta washe baki haba? Lallai naji dadi. To wane school zasu amince? Ta bukata , yayi murmushi *Madaki international school* ta zaro ido yana da makaranta? Makarantu dai ai duk kasar nan babu inda baida branch. Yanzu haka private university yake ginawa, kano, Kaduna, Abuja, Lagos da katsina. Zaiyi lunching a lokaci daya. Tabb lallai ta fada. Ya kalleta ke ai kilan anan cikin gida zakiyi ta ki. Ta kyalkyace da dariya sai kawai taga mutum kamar an jefo shi ya kalleshi *koya mata kakeyi ko maganganun banza?* Ya mike yana kyarma no sir is part of our lesson...... Shut up, ya kalleta 6ace man da gani kada in miki rauni...tayi ciki da gudu. Ya nuna shi da yatsa *Ka shiga hankalinka* Ya fara bashi hakuri. Lesson din da ba a kara ba ya hana. Washe gari kamar yanda tayi alkawari ta wuce sama direct yau idonsa biyu, kwankwasawa daya tayi ya ce *Shigo* Tana bude kofa ta durkusa ina kwana? Ya dan harareta da Allah malama shigo ciki. Ai kaji matsalar, nasan bazai taba amsa gaisuwa ta ba. Ta fada a zuci tare da shigewa ta rabe a bago. Kinga leda can da jaka ki dauko, uniform din ki ne da school bag. Ta washe fuska ta nufi wurin da sauri. Monday zaki fara zuwa idan kika saki kika kasa maida hankali sai na miki bugun kudina don bazan yi asara ba. *Ta durkusa guywa biyu* na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara arziki mai amfani. Ya dade yana kallonta har ta ji ba dadi tunda kanta a kasa yake. Ya ce amin. Magana ta karshe makarantar *mix* ce wallahi kika kula wani namiji kin gama karatun daga ranar..... Ta banka mishi harara ya zaburo *Au baki dauka ba?* Ta kwashi kayan tayi waje da gudu tana fadin *Nima so kake in tsofe irin ka ba aure*? Ya biyota da gudu yana iyye yarinyar nan kin gama rainani ji kakeyi daf daf daf....da da da.... Karar gudu dai dai mamee na fitowa tayi bayanta wayyo mamah ..wayyo zai dakeni. Ta tattare kai tsaya wallahi ka taba ta sai ranka ya baci. Me ta maka? Umaimah daga bayanta ta ce uniform ya bani zan fara zuwa makaranta litinin wai idan na kula maza na gama daga ranar. Don na ce so yake in tsofe kamarshi ba aure shine ya biyoni zai daka...... Mamee ta zaro ido ta kalleshi sai wani mazuran borin kunya yakeyi. Sai kawai tayi murmushi, kayi hakuri toh bazata kara ba. Mamee yarinyar nan fa ..... Na ce kayi hakuri *uwani shige ciki* ta ruga da gudu kuwa. Ya bita da kallo kamar yanda mamee itama ta tsareshi da idanu. Fakam fakam yayi sama. Ta koma ta zauna bisa kujera *Haba wallahi koda naji* fitinar nan ta uwani da madaki ta isa watan *Son ta yakeyi shi ne yaketa wannan haukan* Wani sanyi ya diri zuciyarta bani da matsala da uwani wallahi. Ta rike haba *ohh*.... Ta yi ciki ta tarar da ita zaune. Ta na ta nishi. Ta kalleta taji ta kara sonta fiye da *da* wannan kauna da nakeyi ma uwani ta isa, ashe surukuta zanyi da ita. Ta zauna kusa da ita, uwani?. Ta kalleta kawai, ki daina biye mishi kina wannan mugun gudun wata rana sai kinyi wa kanki rauni. Idan ya taso ki tsaya kiga zai kasheki? Duk sharuddan da ya kindaya miki to kibi su babu kuskure matukar kina son Ku zauna lafiya ya daina wahalar da ke. Ta ce toh, ta kalleta wai rigunan da yawa kika siya haka naga ta yau tafi ta jiya kyawu. Ta yi murmushi mamah wadannan kayan fa *Madaki* ya kawo mun ta zaro ido *madaki* ta kwashe duk yanda akayi ta fada mata sai kawai ta hau dariya *Au har mutanen gidan naku ma basu tsira ba?* Lallai abun nashi azimun ne. Shawara daya zan baki ki daina hawa sama idan yana nan in ba wani kwakkwaran dalili ba ko gyara idan zakiyi ki bari sai ya fita office ranar da duk bai fita ba to ki kyaleshi. Ta ce toh. Ranar litinin tunda safe ta iso a falo ta tarar da shi nan suka gaisa tayi ciki don shirin makaranta. Ta dora hannu a kai *Na shiga uku* dan skirt ne bai karasa kai guywa ba hade da karamin wandon sa sai farar riga yar shirt mai karamin hannu tare da neck tie. Ta zaro ido wai makarantar su Khausar zanje? Irin kayan su ne ta shirya tsaf, da doguwar safa sai farin takalmi *camp bus* sai yar hula karama daman tayi sabuwar kalaba kanana amma duk ta hadeta wuri gida ta kulle, shiru shiru ta fito mamee ta shiga ta ganta tsaye. Ke fa kadai bus ke jira gasu can suna *oda* Mamah haka zanje? Ta zaro ido babu ruwansu da ke makarantar duk turawa ke koyawa..... Kirjinta ya harba. Mamee ta kamo hannunta ta sagalo jakar sai rinjayarta takeyi saboda nauyin litattafai. Ya bita da kallo wani kishi ya turnukeshi ya daga murya. Mamee.... Ta juyo da sauri Sai kawai yasha mur ya kalli umaimah *Ke jeki sanyo doguwar hijabi idan kinje makarantar kya cire* Mamee ta dankara mishi harara ke muje ta fizgeta. Ya taso da sauri suna fita ya hango su baffa cike a motar suna jiranta. *Cikin gardawan can zata tafi?* Wuf, ya fizgota hannun mamee ya daga murya *kai isma'ila tafi kawai zan kawo ta*...........Ya yi ciki da ita yana zuwa falo yayi sama ya dauko key din *private car* din sa. Mamee na waje tayi tsaye tana dariya kamar me? *Ta gama tabbatar ma zargin ta* farinciki kamar me tana jin motsin fitowar su tayi baya da sauri. Umaimah dai simi simi ta rasa inda zata kanta don kunya tayi shiru kanta kasa. Tuki yakeyi yana faman tsaki duk karatun nata ya bashi haushi. Kadan kadan yayi tsoki yana ta sake sake, Mamee ta ce tohh abin haka yake ashe ina ta wahalar da kaina a waje ashe rabon na tare dani. In na haukan madaki ba an taba so da *Masifa*? Ta kyalkyace da dariya yau naga ikon Allah ni jikar buzaye. Ya kaita har bakin kofar office din principal ya ce ki shiga zasu kaiki class idan an tashi kuma ki jira zan aiko..... Ta fita da sauri ta kyaleshi. Ya bita da harara kawai ya juya a guje. A class din su khausar aka kaita SS1 wurin zaman su daya. Hankalin kowa ya dawo kanta. Khausar ta gabatar da ita amatsayin yar uwa hakan yayi mata dadi sosai. Umaimah na cikin matsala da farko don bata ganewa sosai saboda ta riga tasa tsoro a ranta bata taba zama aji ba. Sai da khausar da wata kawar khausar da suke kira *Yar gata* sukayi ta karfafa mata guywa. Cikin sati biyu sai ta ware. Tun da ta shiga makaranta bata da lokacin kanta ga azumi ya kusa, Idan ta dawo makaranta karfe biyu kafin ta gama wa mamee kintse kintse hudu tayi ta tafi karatun islamiya shidda tana yi gudu gudu zata bar gidan. Ranar wata asabar tazo karfe takwas ta tarar mamee da baki falo ta shiga musu hidima yi wancen dauko wannan. Har ya shirya ya fita ransa a jagule. Washe gari tana zuwa ta tarar har ya yi wanka yana faman daura agogo ta durkusa kenan ya ce *ta shi kawai* yau ranar punishment ce , tasan za ayi haka gabanta ya fadi ganin yanda ya 6ata rai. Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. Ya tako zuwa inda take kin tuna da alkawarin da kikayi cewar zaki rama duk abinda nayi miki ko? Ta daiyi shiru ya fizgota ta fada jikinsa ...... Jikinta ya fara kyarma ya kai bakin sa kunnen ta *Kinyi alkawari*..... Tsikar jikin ta ya tashi ta yi baya zata zulle ya maidota da sauri wannan karon fuskarta ya tallabo kawai taji ya mata *kiss*............. *Barkan mu da juma'a* 😉 *MAMAN ABDULLAHI*😘😘😘 [1/26, 10:04 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣2⃣ *INA YABAWA DA KE AKODA YAUSHE 'YAR UWATA , MAI AIKINA KUMA BAIWA TA . ZALIHA SHEHU SHEMA*( ZALIN 😜) ..... Fiddo duka idanun ta *Na shiga uku* ta fada cikin rai, sumar tsaye tayi yadan ja baya... Yaushe zaki...... Ta kwasa a guje tabar dakin. Ya bita da wani wahalallen kallo. Ta zukunna *Ni yau na bani kawai* ta kudundune jikinta tana wata irin kyarma. Data tuna sai ta tusa kanta cikin cinyoyi ta ce *wayyo Allah* tsikar jikinta *Yarr* Ta kasa motsi duk ta rikice. Mamee har sha daya taji shiru ta kirata a waya tana jin ringing ta kara makurewa *ta boye fuskar ta kamar mamin ce a gabanta* ta ce Wallahi gida zan gudu. Ta fara bin bango zata gudu mansurah ta hangota laaaahhhh *Uwani* ta kwala mata kira. Mamee najin haka ta fito taga ko lafiya? Ba arziki ta koma duk tunanin su lokacin ta zo. Magana ake mata amma sai sumke sumke takeyi tana kyafta idanu. Mamee ta rikota uwani lafiyan ki qalau yau?...... Sai kawai ta fashe da kuka ita kanta bata san kukan ko na menene ba. Hankalin mamee ya tashi ta jata sukayi daki, tambayar duniya ta kasa magana. Mamin tayi shiruu zuwa can ta ce *Gida zani bani lafiya* Uwani baki lafiya kuma zakiyi ta kuka haka? Menene ke damunki? Zazzabi. Ko dai akaiki asibiti? A a gida zanje ta durkusa *don Allah mama zanje gida* Jikin mamee yayi sanyi anya lafiyan uwani qalau? Ta dafa kafadar ta, kiyi hakuri kiyi kalaci tukun bayan kin sha magani sai ki tafi..... A a zan ci a gida. Tashi ki tafi amma jira a zubo miki ki tafi dashi. Duk ta rikice bata son ya dawo tana gidan don taji fitar sa dazun. Ta wuni daki kwance data tuna sai ta kankame jikin ta. *Mi hakan yake nufi?* wai ni me ya daukeni? Ta wuni tambayoyi amma ba amsa. Shi kuwa wuni yayi kamar an mishi bushara a office yau yaba kowa mamaki yanda yake ta murmushi. Karfe biyu ya dawo cin abinci yana ta waige waige mamee na dai kallon sa. Mansurah ta fito ya ce *ke kirawa mamee uwani* yanda yasha mur din yaba mamee dariya amma ta sumke, Uwani ta tafi gida tun dazun, ya kalli mamee gida, lafiya? To nidai ta zo mun duk a harmutse yau na kasa gane kanta wai bata lafiya..... Sai kawai ya kyalkyace da dariya. Mamee tasha mur kamar da gaske ko kaine ka mata hakin? Me na mata? Wannan yar taki mamee muguwar bagidajiya ce. Kawai ya haye sama. Guduwa tayi? Tabb gidan zanje anjima. Bakauya ta kasa furtawa an bata satar amsa duk tayi failing *Na gaji da wahala* Kwanciyar ta isheta ana sallame isha'i ta fito zuwa gidan Alhaji yakuba wata kila ta ji dama dama, ga yunwa bataci wani abin kirki ba. Tana kunno kai shima yana zuwa daf da kofar , numfashin ta yayi sama Zata ruga ya kamo hannunta ya hakuri zo muje in baki hakuri na yi laifi.... Ta kankame jikin ta bani zuwa sakeni *wayyo* yaga da gaske zata rikice mishi ya shigar da ita soron gidan. *ya daka mata tsawa don ta nutsu* kizo muje inyi magana da ke tafiya zanyi ya fizgi hannunta kamar ranar da ya kawota farkon layin ya ajiye mota. Suna tafe yana cewa ko agida kike yau zuwa nayi in fiddoki waje. Ta fara kuka, Yana zuwa ya sakata mota sannan ya zagaya shima ya zauna sai kawai ya tayar da motar ta kalleshi *Ka rufa man asiri na shiga uku ina zaka kaini?* Ya kalli agogo yanzu fa bakwai da kwata malama har mu dawo. Ta durkushe karkashin mota tana kuka don girman Allah ka tsaya, ya ci uban birki. To ki tashi inyi magana da ke. Ta zauna, Umaimah? Ta kasa amsawa, Yayi shiru.... Kiyi hakuri da abinda ya faru dazun kada ya dameki kinji? Ta daga kai, Ya danyi murmushi to zaki iya ramawa? Ta kudundune jikin ta, Kunya kike ji? Tayi shiru. Ke ki tashi tambayar ki zanyi naji bana son ki rama na yafe kije can kiji da alkawarinki. Tambayar ki zanyi saboda Allah zaki bani amsa? Tayi shiru, ya saisaita murya kamar yanda yake mata magana a da, *Ki zauna sosai ina so ki fahimceni* Kina jina? Ta daga kai, Kina so in daina takura miki na fita harkarki? Tayi saurin daga kai alamar eh Yayi murmushi *TO ZAKI AURENI???* Taji wani tsammmm! *Ni ina son ki* na lura zakifi gane wannan yaren. Gashi *Na ta ko* har in da kike da *Kokon barata* Ya dan karkato *ni umar madaki ina son umaimah* Ko ban miki ba nayi tsufa da yawa? Ya koma ya kwanta , kin hanani sakat umaimah tun ina boyewa har na fara *loosing control* idan naci gaba da shiru *Any thing can happen* ina matukar kaunar ki. Ya dan waigo malama ki bude baki kiyi man magana. Ta kudundune jikinta kunya kamar ta narke wurin. Ya ce *Tabb aiki ja* karki dorawa kanki wahala don yanda na galabaita din nan kin san ina bukatar kula. Ko muyi waya anjima? Tayi saurin daga kai *ohh yauni umaimah ke ma rowar magana* ya fada kamar mace. To baza ayi wayar ba yanzu zaki ban amsa na miki ko ban miki ba? Na san dai kwanaki anyi ta labewa ana kallona, rannan kuma na ajiyeki school naga kina hararar yar kawar ki don mun gaisa. Kema kuma kinga yanda nakewa maza idan sun koda kalleki, ga dokoki , ya kyalkkyace da dariya *Umaimah kin kusa haukatani* Ya dan waigo don Allah kina sona? Ta daiyi shiru tana murmushi taki yarda ma ta dago kai, ina wayar ki? Ga ta nan ta fada da kyar. Zan kiraki anjima ki daga kinji? Ta ce toh. Gaskiya bana son tafiya gashi har tara ta kusa, ta daiyi shiru.. Ya kalleta bani number babanki. Ta fiddo wayar ta sunga mishi, ya harere ta *Ke bani son gidadanci fa* da Allah malama karanto man. A hankali take karantowa kadan kadan. Ya ja dogon tsoki wallahi abinda nake gudu kenan tun farko shi yasa na gwammace muyi ta fadan kamar kaji. Ya dan kalleta yau saura kwana uku azumi guda nawa zakiyi? Bata San lokacin data harareshi ba daman idanun sa na kanta, tayi saurin dukewa bata san yana kallonta ba. *Kilibabba* malama ki bar wani sunkewa na dade da ganin kaunata a idanun ki. Wannan kallo haka sai ki sanya dana koma in tada wa mamee zaune tsaye. An ce man duk CA din ki basuyi kyau ba har 2/20 kike ci. Tayi murmushi yo turawa ne fa kaji turancin su wani *Rara ra ra ra ra* ya tuntsure da dariya ta zumburo baki. Duk turancin da Samuel ke Dan kara miki? Tabb wallahi ba irin shi sukeyi ba. To ai kema laifin ki ne kin dage banga me zaki tsinta ba nidai bazan taba barinki kiyi aiki ba, kawai abinda rai keso. Tabb ni dai ina so .....ta fada can ciki. Me kika ce? Tayi shiru Yayi dan murmushi kin san dai ban iya jira har ki gama gara ma kisan dabarar da zakiyi wa mamee don ita kadai zata ban matsala. Ta dago da sauri *Gaskiya ni dai sai na gama* Ya yi sa'ar hada ido da ita, *Kin amince kenan zaki aure ni?* Ta kara dukewa, ya kyalkyace da dariya *ni wallahi ban son gulma* *Da zaki amince sai naje gidan ku na fada masu zaki kwana a gidana* Ta dago da sauri *me*? Ya sha mur ai nasan bazaki amince ba. Ina wayar ki? Ta kara fiddo wa, Ya mika mata sabuwar waya irin tasa *iPhone X8* Me zanyi da wayar ka? Ta fada a hankali. Ba ita ba ce kin ga tawa ya fiddo, kawo in mayar miki da *Sim* Ta mika mishi yayi charaf da hannun. Ko kiban amsa ko in fizgoki ki dawo nan *sit* din. Kin san karamin aiki nane. A tsorace ta ce wace amsa? Ki ce kina sona, *Nima ina son ka* Ya saketa yana murmushi ya ci gaba da sanya mata sim din. Ya duba agogo goma da rabi, ya mika mata wayoyin duka ya ce wannan kya ba wani. Ya zakulo wata leda wurin kafar sa ga mutumin *ice cream* ta mika hannu na gode. Naji amma gobe zance zanzo dashi musha tare. Bata san lokacin da tayi dariya ba . Ya rike mata suka fito. Ta fara sauri ya maidota baya *Malama yanga akeyi idan anjera da saurayi ba tafiya buzum buzum ba* Kunya ta kamata wallahi madaki ya iya dizgi ta fada a zuci............ *Good morning* *Maman abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘 [1/26, 10:06 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣3⃣ ........ Luba ta fara barci takai hannu luba tashi. Ta murtsuke fuska ya akayi? Ta fara bude leda tashi Musha..... Zumbur tayi, ashe ba ice cream kadai bane hada biscuit biscuit masu tsada da gasassar kaza. Ta zaro ido ina kika sameshi? Don Allah kedai kiyi shiru muci. Ta wuntsilo suna ci suna yar fira. Ta mika mata tsohuwar wayar ta ungo na baki. Ta kara fiddo idanu ke umaimah da gaske? Na taba miki wasa? Allah na bar miki. Amma ina so karki fadawa kowa ga abinda muka ci yau. Ki debi biscuit din Wanda kike so saura kisa mun jaka ta. Ta wawusa da sauri kai wallahi na gode. Amma umaimah waya canza miki waya? Zatayi magana kenan wayar tayi kara. Ta ce *Ai fa na bani* Luba ta bita da kallo. Ta dauka hello. Malama da kika ji shiru ba sai ki kira ba? Ta yi murmushi, ina gun baba ne zan kira. Kawai ta kashe. Luba ta bita da kallo *Wanene*? Ke kyale shi ni nasan ma ko waye? Madaki kuwa ya bi wayar sa da kallo cike da takaici *Haka zamuyi da yarinyar nan*? Ya mike tsaye *ni zata jama aji?* Yana kira yaji wayar a kashe. Kasusuwan luba taje can kasan bola ta tusa ledar. Sukayi kwanciyar su da kyar umaimah ta sami barci ya sace ta. Zullumin zuwa gidan kawai takeyi, salon soyayyar madaki na bata tsoro gaskiya. Shi kuwa tunda ya tashi yake faman zarya mamee na kula dashi tayi kamar bata san yanayi ba ko kalaci yakiyi gashi sai waya ake mishi office yaki tafiya. Ransa ya baci matuka, ya zauna tare da dafe kai yayi shiru.... Goma saura ta shigo yana ganin ta ya mike kawai yayi sama. Ta gayar da mamee tana ta sunne kai ta wuce ciki. Ta bita ta ido tana 'yar dariya *Wannan soyayya ni dai an mini kancal* Ya sauko yana ta fushi mamee sai na dawo..... Ta kalleshi *Kalacin fa ko zaka aiko?* na koshi ya wuce, ta bishi da kallo. Koda umaimah ta gama yan gyare gyaren ta sai tayi baya gurin su mansura. Har ta tafi bai dawo ba. Da daddare taci gayu ta ce zata je gidan Alhaji yakuba amma tayi tsaye zaure tana jiransa amma shiru ta fita waje tafi kusan awa daya amma bashi. Duk sai ta shiga damuwa ta kwanta sukuku, Washe gari karfe shidda yabar gidan, mamee ta rutsata daki tana janta da labari har ta dan saki. Ni uwani kwanakin nan duk bana jin dadin yanda nake ganin ki ko kin fara gajiya dani? A a mamah ta fada tana yar dariya, Allah kuwa, sai nake gane kamar kin gaji dani in ba haka bane to ki saki jikin ki kamar farko. Kin ji ko? Ta ce toh, tana murmushi, Ta danyi shiru, uwani na daukeki tamkar 'yar da na haifa don haka ki saki jikin ki kada abinda ya shiga tsakanina da ke kinji? Ta ce toh, Idan kika ga mutum ya bata rai da ke ko ya ce kin mishi laifi kada kiyi girman kai ki bashi hakuri kinji? Ta ce toh mamah kiyi hakuri. Tayi murmushi bani ba ina nufin abokan zama kinji? Ta ce toh. Lallai mamee ta iya siyasa ta gama karto cewar *madaki* fushi yakeyi da umaimar. Duk da bata san dalilin Fushin ba, zaman falo dai ya gagari umaimah yanzu saboda kunya , mamee na zaune ya shigo da sauri ya haye sama tayi saurin kwadawa umaimah kira ta zo da gudu saboda yanayin kiran. Ta ce maza hau sama ki dauko mun kwalin ruwa. Ta ce to ta wuce domin tasan bai gidan. Ta na hawa shi kuma zai sauko saura kadan su hade yayi baya da sauri, har zaiyi magana sai kuma ya fasa kawai ya raba ta ya wuce. Ta bishi da kallo *Wai fushi yakeyi dani?* Me na mishi? Sai kawai taji itama ranta ya baci. Mamee na hangoshi ya taho tasan bai kula ta ba. Gaban ta ya fadi ko uwani ba ta karbi soyayyar tasa bane. Ita ma umaimar ta sauko rai a bace ta ajiye mata ruwan ta shige ciki. *Ikon Allah ta kame baki* Ta rasa me ke mata dadi, duniya ta yi ta zumbure zumburen baki. Mamee ta shige kewaye ta ringa dariya sosai. Har bayan magriba umaimah taki tafiya gida, Uwani yau bakya gudun dare? Mamee ta isketa daki zaune ta rabka uban tagumi, Ta mike yanzu zan tafi cikina ne bana jin dadin sa, ta sumke dariya, assshhha cikin ne yau ma? Tayi shiru ta dauki hijab ta wuce kawai. Tana zuwa gida ta bude waya ta tura mishi sako da turanci saboda bata iya rubutun Hausa ba, *Pls what did I do?* Ya na ganin message din ya tashi zumbur dama kishingide yake. *good kin fahimci kinyi wani abu kenan* Wani ya kara shigowa , *Sorry* Ya bi wayar da kallo yana murmushi *naki wasa ne yarinya* Tafi mintuna talatin rike da wayar amma bai maido amsa ba ta kara tura mishi:, *I know whatever happened, Should not have happened the way it did, But, I am really sorry on my part, My intention was not this from the start, So please forgive me!* Tsalle ya buga yana wani irin ihu. *Billahil azim ta kamu* Ya koma ya kwanta *Sai kin fada da bakin ki yarinya* Tayi shiru, kai jama'a wannan da me yayi kama nifa bana son yawan fushi. Anya zanji dadin zama da *madaki* a matsayin miji? Ta yi saurin sauya zancen *tabb duniya akwai namijin da zai taba birgeni bayan shi?* Ta kara tura mishi sako, *Please forgive me for what I did, My intention was pure I admit, I did not want to hurt you a bit, I am really sorry for what I did!* Ya kara tashi zaune yana kara kallon rubutun , yarinyar nan yaushe ta iya turanci haka? Wani sakon ya shigo har kyarma yakeyi, *Madaki , Things are not the same without your company, I am missing you a lot, and I told you sorry, Please forgive me and start a new chapter, This won't ever happen again!* Ai sai yayi mutuwar zaune, motsi ya kasayi duk illahirin jikin sa kasala ne, Da ta kara jin shiru sai kawai kwalla suka zubo mata ta kashe wayar, Lokacin da hankalin sa ya dawo sai kawai ya nemi kiranta yaji *Switched off* Ya dora hannu aka ya ce *na gama banuwa*......Ya ziri makulli kamar mahaukaci ya fito, yana zuwa falo agogo na bugawa karfe sha biyun dare, ya koma da karfi bayansa ya daki bango ya runtse ido cikin wani irin radadi. Dukkansu babu Wanda ya sami damar runtsawa, Karfe shidda tayi sammako, shi kuwa tun biyar ya gama shiri ko da ya fito sallar asubah bai shiga ciki ba yana zaune bisa dan dakalin kofar shiga. Daga nesa ta hangoshi zaune, Sam baiyi tsammanin ta ba yasan zata kai takwas zuwa tara, kansa duke yana lazimi ta iso, Yaga alamun tsayuwar mutum ya dago da sauri , Ta rike kugu idanun ta sun kawo ruwa *Wai me na maka?* Saura kadan dariya ta kufce mishi. Ya sha mur *laifi* *bana baka hakuri ba?* Ya dan dukar da akai don gaf yake da ya kwafsa, Yaushe? Tayi shiru tana kokarin maida kwallan bata so su zubo kafin ta ce, jiya na maka text. Ya tabe baki ya dan watsa hannuwa ban gani ba. Meye kika ce a text din? Ta fiddo waya a hasale ta budo page din *Duk gashi* duba gashi kuma yaje na tabbatar tana faman scrolling. Ya kyalkyace da dariya. Ta bishi da kallo nan da nan ta tsargu kunya duk ta baibayeta ta balla mishi harara ta wuce ya janyo ta ta fada jikin sa. Lallai ana kauna ta *kut* Ta fara kokarin zamewa ya ce *ke kilibabba* dadi na san zai halaka ki ne abinda kikayi missing kenan duk kin rikice. Ya kamo hannun ta zo muje in baki labari nima ai na wahala....ya rike hannun ta sukayi ciki yana dariya. Suna shiga ya tarar da mamee zaune tayi tayi ta fizge ya riketa gam, Ta yi sukutii... Kamar da gaske sai mamee tasha mur *ina zaka je da ita?* Ya jata da karfi zasu wuce ya ce gyara zata mun sama. Ta daka mishi tsawa zaka saketa ko kuwa? Bana hanaka yi mata wannan zillar ba? Har yaushe zaka kyale yarinyar nan ta sarara? Uwani wuce ciki daga yau na sa miki doka baki kara hawa sama........... 😃😃😃😃 *maman Abdallah* 😘😘😘😘 [1/26, 10:10 AM] ‪+234 813 180 9991‬: 💑 AUREN FARI 💑 0⃣2⃣4⃣ DAFATAN ZAKU SAKA TA ADDU'A AKODA YAUSHE HAJIYA RABI BADAWI MAMAN IBRAHIM DA NURY .............. Ke tsaya ya daka ma umaimah tsawa, ya isa gun mamee da sauri , kiyi hakuri mana. Na ce kamun laifi ne? Tunda ka rainani to bazata kara rabarka ba har ka gana mata azaba......wace azaba mamee ya marairaice, gyaran da zatayi mun shine azaba? Ta kalli umaimah Na ce ki shiga ciki ko? Ya mike tsaye ke kina hauka ne? ya kara daka mata tsawa ......wai mamee menene haka? Ya kalli umaimah dake niyyar shigewa ya ce wallahi kika shiga zan fiddo ki .......wai mamee menene haka? Duk ya rikice, ya kalli umaimah dake makale a bango Malama kiyi mata bayani ...ya juya mamee wallahi bazan mata komai ba gata nan tambayar ta. Kinyi shiru mamee....me zance tunda ka rainani ka nuna ban isa ba? Duk lokacin da ta hau saman da kuka take saukowa ka zageta tsaf ka gama.......Qalu innalillahi mamee ki sassautan mana. Ya maka wa umaimah harara Wai bazakiyi magana ba? Ta ce me? Mamee na tuba dakin can yayi kura....... Shin naji na amince gyara kake so? Zauna ga kujera Uwani je ki gyaro ki dawo Simi simi zata wuce ya mike Ta koma kawai bana so......fuuu yayi sama. Uwani jeki ciki abinki kinji ko? Tana juyawa wayar ta tayi kara tayi ciki da hanzari. Hello Sato ki taho don Allah Tabb wallahi mamee na falo.......ke da waye a waya? Tayi saurin latsewa......ni... Nida luba ta juya tana kakkabe gado. Ya zaro ido Wayar ma hanawa zatayi? Ya sauko da gudu gudu yayi sa'a ta fito falon , tana hangoshi ta kara tsuke fuska. Ya zauna kusa da ita, wallahi mamee yarinyar nan ki tambayeta yanzu bama fada ko kadan. Da zakayi hakuri mu bar maganar nan..... Saboda me? Ko magana ta fatar baki idan ta sake hadaku sai na...... Tsaya mamee ki rufa man asiri na tuba. Ta hasala Sam baka bin magana ta nayi nayi ka fiddo mata kakiya ka zauna kana tokalo fitina da yar cikin ka...... Ya mike yana murmushi Aure Aure this is your only problem. To ai UWANIN TAKI NAKE SO NA AURA Ya koma ya durkusa ita na ke so! Duk bakin mamee ya kulle farin ciki ya baibayeta. Yayi hanyar dakin ta yana fadin Yanzu ai kya taimaka kiban ita inyi magana ko? Tana duke tana share carpet ya shigo tare da janyo hannunta....tayi saurin turjewa, ya kalleta wallahi daukar ki zanyi matukar kika man gardama. Ta bishi yaci gaba da bambami kuna neman haukatani ku rikitani ke da mamee..... Ya na zuwa falo wayam babu mamee, ashe shigarshi tayi baya da sauri don tabbas Madaki sai dai taji kunya shi da gaske yake. Suna zuwa babban falon sa ya zauna bisa kujera two sitter , ta tokare tsaye shi kuma yaki sakin hannunta, ya kalleta ta zumburo baki tana fushi. Me akayi? Ya bukata yana hararar ta, Gaskiya abin nan zai dameni yanzu mamee tace kada in zo gashi ka kawo ni ta yaya zan sauka saboda Allah? Ya ficikota ta zauna cinyar sa da karfi, ke kwantas na fada mata mun jone ya karasa maganar yana murmushi tare da kashe ido daya. Mun shiga uku ta zabura me ka ce mata? Ke ban son rashinin wayewa baki lura yanda za... Read more [1/27, 7:42 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣5⃣ Ya fi mintuna ashirin bai ce qala ba kafin Ya dago kai yana murmushi, ko alokacin jahiliyya ranka shi dade ban taba jin anyi haka ba. Hasali ma idan son yarinyar kakeyi kaine zaka tarar da iyayenta komin kudin ka komin mulkin ka ba iyayen yarinyar zasu kawo kansu ba kamar yanda mukayi yanzu. Aure rahama ne yana daya daga cikin dokokin Allah da manzon sa cewar a girmama aure a kuma daratta shi, umaimah marainiya ce ni na saki nono mahaifin ta ya kama. Wallahi matukar nayi mata haka ba la'antar Allah kadai ba tsinuwar dangi da mutanen gari bazasu taba sanya ni in zauna lafiya ba. Amma ina mai baka hakuri idan abin da na fada bai ma dai dai ba. Ya juya Allah shi gafarta malam ga maganata akwai gyara? Ba liman yayi magana ba *madaki* ne yayi Hakika babu gyara ga maganar ka baba. Kuma naji dadin maganganun ka . kafin in sanar da kai dalilina ina son ka amsa mun tambayoyi biyu zuwa uku, Na farko me yasa kabar gidan ka sakaka babu kula?, ya akayi duk yaranka na makaranta banda umaimah?, sannan minene ka gwammace tabi gidaje aiki akan zaman gida bata aikin komai. Saboda ko kafin umaimah ta fara aiki gidana ta dade da fara bauta gidajen unguwar mu? Yayi shiruuuu.... Kafin ya nisa, idan ma na boye muku to bazan boyewa mahalicci na ba. Na farko ina iya kacin bakin kokarina a kan gida matsala daya aka sami da na karo mata ta uku shine cin mutunci ya fara shiga har matan nawa suna zagina ko su sanya 'ya'yansu manya su nemi sa'in sa dani. Sai na yanke shawarar idan na fita kasuwa tun bayan fitowata sallar asubah sai talatainin dare sannan zan dawo. Umaimah kuwa, gaba daya daukota ma da nayi shi ne ya kara jagula duk wata matsala, ko na fita na barta zata tafi makaranta to bata zuwa, tsinke wannan idan na siyo da sunan ta tabbas ranar na janyo mata masifa da ni kaina shi yasa na tattara na watsar. Aiki gidaje kuwa shi ne in da tafi ko ina samun natsuwa, zata ci zata sha zasu bata tsumma ta daura. Wannan shine dalilina na barinta tana yi don kada yunwa ta kassarata. Ya juya gun su liman Malam kunji da kunnen Ku? Hakika munji yallabai. Suka fada. Ya ce good, Baba, kayi hakuri amma maganar gaskiya dalilin da yasa na kiraka anan shine da ka kuskura an daura Aure na da umaimah wallahi da sai na sa an daureka don ka tabbata baka San *Hakkin Dan Adam* ba, idan kuma baka amince ba to shi yasa na kira malamai don kamar yanda na ji bayanin ka na tabbatar akwai rashi ko karancin ilimi sai Suyi maka wa'azi. Ina Neman afuwar ka baba....... Ya sunkuyar da kai haba haba babu komai, babu komai. Liman yayi gyaran murya, to Alhamdulillah, shi musulunci sauki gareshi kuma Aure kamar yanda ka fada ne babba. Namiji ga gidan sa shi *Linzami* ne, shi yasa Allah SWA ya ce *ARRIJALU QAWWAMUNA ALAN NISA'I....* a wurin Allah wannan ba hujja ba ce, Suka fara mishi wa'azi daki daki hakkin iyali, hukuncin Wanda ya zalunci maraya da sauran wa'azi. Iyakar kunya malam bawa yaji ta, sannan ya tausaya ma kansa akan saken da yayi. Ya sallami su liman sanna ya ce wadannan kudin baba ka dauki dauri biyu ka ba aminin ka daya, Ku kara jari. Zamu je da kai can gida kaga inda umaimar take domin hankalin ka ya kwanta....... Babu damuwa. Malam nasidi ya ce nikam zan koma rumfa mun baro yaro marar wayau. Mansurah ta dunga tuntsurar dariyar keta, Wai ke ya akayi ne? Sai da tayi mai isarta sannan ta fada masu. Bilki ta zaro ido anya kina cikin hankalin ki kuwa? Kin manta duka gidan ko ina akwai kamara da yallabai ke ganin komai? Kina tunanin zaiyi shiru bazai bincika ba?..... Bata rufe baki ba mansura ta baza da gudu tana zuwa ta tarar da kawar khausar ita kadai, daman ta wuto su a kitchen. Ta ce kije inji khausar tana fita tayi saurin bude jakar ta mayar da kayan dai dai lokacin da dayar ta fito toilet. Tayi waje da Sauri, ta bita da kallo cikin tsarguwa. Suka fara mata dariyar har taji babu dadi, ke kin fiye sauri irin gidan nan an fada miki haka kawai zaka bigi gaba kayi tuggu? Ko kuwa duk wannan feleken da daukakar da uwani ta samu an fada miki haka kawai ta shigo zikau bata shirya ba? Bilky cikin dariya ta ce, ai idan baki fitar da ita ba ke kya fita saurin me kikeyi? Suna gama cin abincin suka tafi. Ita kuma ta kabbara sallah, raka'ar karshe mamee ta fara kwala mata kira, tana karasawa ko addu'a batayi ba ta ruga sanye da hijab din mamin domin ita da gyale tazo, Gani mamah, Aunty murja ta kalleta Tun daga sama har kasa *Ina kika sami gadararriyar yar aiki?* Aunty jamila ta yamutsa fuska, yaya mai mutane.... Saboda samun wuri yar aikin ce da hijab dinki? Ashe jita jitan da mukeji da gaske ne tabdi. Lallai zamu kowa Aunty yaya da bayani....... Au har kunji labarin uwanin? Kwarai kuwa ance ta raina kowa ke da madaki ma tsoron ta kukeyi to........ What? Aunty jamila kuna hauka ne?...... Mamee ta daga mishi hannu. Sam bata yarda ya raina mata yan uwa ko Kadan. Babu Wanda yaga shigowar sa. Sukayi sukutiii don tsoron sa sukeyi kamar me. Baba bisimillah ya daga murya. Umaimah ta zaro ido baba ta tareshi tana yar dariya. Mamee ta kalleshi alamar tambaya *Baban ta ne* ya fada tare da zama bisa kujera. Mamee ta washe baki kai maraba maraba. Ya nuna mishi kujera ya dago suka hada ido da aunty murja, kawai ta mike ita ma jamilar tabi bayanta. Munafukan banza ya fada cikin rai. Bayan gaisuwa da mutunta juna. Mamee ta kalli sadauki wallahi kayi kokari kayi Kyan kai. Wanin uwani bai taba zuwa gidan nan ba. Ta mike tsaye sannu baba. Mamee zama zakiyi na sameshi ne akan umaimah ta zauna anan zuwa bayan sallah kada zaryar tayi mata yawa ga azumi. Mamee ta fadada fara'ar to ya amince da hakan? Umaimah dake kusa dashi ta taunkulo cinyar sa tare da girgiza mishi kai wai yace A'a . sai ya kwashe da dariya ya kai mata duka aka, kaniyar ki da mintsili na....... Mintsili????? Me zasuyi ba dariya ba. Wallahi mintsili na tayi wai in ce A'a. Mamee ta kasa magana don dariya, madaki ya kalleta *Yanzu baban kike mintsili?* ta zumburo baki ta noke kai, Uwani hoo, mamee ta fada Ba zaki zauna ba kenan? Baba ya amince kyaleta mamee ita tana tausayin kanta ne? Ta bishi da harara, Inji waye uwani zaki zauna ko kuwa...... Haba hajiya shawara za ayi da ita? Ya mike tayi zamanta can din me takeyi daman ai barci ne kawai ke maida ta. *Madaki* ya buga kafa *Good papa* mamee ta baka mishi harara. Malam bawa dai kansa kasa yana ta murmushi. Su Aunty murja na labe, anya wurin can babu alamar tambaya? Hmmm ai muna ganin ikon Allah ni jamila. Ya mike zan tafi Allah ya kara arziki. Ta mike ai nima lokacin tafiya ta yayi gobe na dawo da kayana duka, Madaki zaiyi magana mamee ta daga mishi hannu dole yanaji yana gani tabi baban ta. Suna zuwa suka tarar da himilin kayan abinci buhu buhu da jarkunan mai banda kayan shayi ba abinda babu. Matan suka tare shi, suna mishi bayani. Ya ce eh na san dasu daga gidan aikin umaimah ne suka bamu zakka...... Ya wuce ciki. Umaimar ce ta tsaya yi musu bayanin gidan zatayi azumi. Luba kuwa ta dunga kuka saboda dan kurmusun da sukeyi cikin dare. A gidan Alhaji yakuba tayi sallar magriba. Ba karamin dadi taji ba amma har yau kunya ta hana umaimah fada mata cewar madaki na son ta. Tana gidan ya kirata a waya yana jiranta a mota. Bata yarda hajiyar ta ga wayar ba tana soke cikin zane, lokacin da ya kira kuma ta dan fita, ta ce zata koma gida ta shirya kaya. Ta fiddo mata sunkunan ta ta ce ungo tafi da su. Yana hangota ya fito tare da bude mata kofar mota, *Barka da isowa ranki shi dade* ta dan bata fuska *Ya kake*? Yayi murmushi ya rufe yana shiga ya ce lafiya garas tunda gani gabanki. Ta ce *Good*....... Malama wai lafiya kike wani basarwa ko nayi wani laifin ne? Ta girgiza kai ko daya naga dai *Kaima haka kake wulakanci da rai* idan ana baka girma..... Dariya yakeyi har yana kwanciya, *Kai umaimah ke karshe ce* watan wulakanci nake da rai. Tayi murmushi eh mana suyi ta kyarma suna tsoron ka....... Ya kara yin dariya ai ke bakya tsoro na ko? Tayi yar dariya Allah ina tsoron ka..... Ko maganar ka naji sai gabana ya fadi. Ki ce Allah! Allah kuwa, Tabb wallahi nima haka, Ta kalleshi da sauri yayi murmushi, da gaske nake wallahi dana tunkaro gida sai gabana yayi ta faduwa. More especially idan fararen kaya ne jikina, a office wani lokacin har zabura nakeyi ina firgita idan na tuno masifar ki. Ba wani nan, kullum kai ne ke tokala ta, Ai matsalar da na ganki sai inji kawai mu kafsa, saboda ko gardama ba'a taba yi dani ba ko bakiga yanda nake *wulakanci da rai ba*? Tayi yar dariya na gani kuwa. Ya kai mata duka,...... Da an canza ma suna yau. Ai nasan hannunka sai ya taba ni. Ya tuntsire da dariya kin San kuwa dana fara son ki burina kawai mu hadu kina bala'i ni kuma ina rungumrki......laaaaaa ta ce tana hararar sa. Meye kika kawo mun a leda? Ba komai dun kuna ne...... Allah? Cewa zakiyi gayu zan sha, ta dan harareshi *Wai ma*...... Wayar sa ta fara ringing ya duba kamar ba zai dauka ba ta tsareshi da ido, yana dagawa ya saisaita murya kamar bashi ne ne raha yanzu ba. Hellooo..... Lafiya, zan kiraki zuwa anjima ya kashe wayar.... Umaimah ta bude marfin mota yayi saurin fizgota ke ina zuwa? Ta murtuke fuska zan baka wuri ne don ka sami halin kiran nata ba ma sai anjima ba.......ya kyalkyace da dariya yanzu dai rufo kofar kafin sauro ya halakamu. *kut*.....kishi umaimah ki ce na shiga uku. Tayi kicin kicin ita dole fushi takeyi ya kwanto jikin ta ya janyo kofar tare da locking kawai ya baje bisa kafafunta....... Malam daga ni banda kwari kada ka karya ni. Ya mata banza ya latso lambar da aka kirashi, yasa hands free, hello sir, Yawwa ina jinki menene? Dama jirgin nan ne da zai sauka lagos da kaya yazo, na port Harcourt kuma munyi waya in the next two hours zai iso. Okay yayi kyau sai ki kira *BASHIR* Suyi magana da Agents. Okay sir, ya kashe yana kallon umaimah, *What next?* Ta danyi murmushi yo wani abu na ce? Sai kince wani abu? Gashi zaki gudu kuma wai ni duk ina kokarin baki full time bana son wani issue ya shiga lokacin ki. Wasa fa nake... Ya tallabo fuskarta karya kikeyi wallahi kishi ne. Ta runtse ido *Wayyo Allah* ya tashi da sauri lafiya? Kafafu na sukayi *Yami* Ya kyalkyace da dariya wallahi baki kyautawa yami kamar wani kwanannen abinci? Ya bata labarin yanda sukayi da Babanta, ta ce, Ohh Allah sarki. Ashe Allah yamun *Alam nasharaha* ta banka mishi harara ai wallahi da kauye zan gudu. Ina zullumin gobe wallahi saboda zama kusa da mamee takurani yakeyi banga dalilin da zaisa ka assasa sai na dawo gidan da kwana ba. *Baza ki gane bane yarinya* Gobe zan aiko a daukeki da safen saboda kayanki....... Bana so. Ya yi murmushi to kawo wannan nayi miki gaba dasu. Hmmm kawai ta ce, Sai sha daya saura suka rabu. Karfe tara ta fito gida amma anan waje ta tarar da drivern shi. Babu yanda ta iya dole ta shiga, su lubabatu na ta mamaki. Malam bawa kuma yaki cema kowa komai. Isarta bata tarar dasu Aunty jamila ba madaki ya masu korar kare jiya bayan ya koma ya tarar sun tsare namee suna mata tambayoyi da maganganu akan umaimah. Karfe goma ya sauko zai tafi office mamee ina uwani? Ta na ciki tana shiri, Shiri? Eh zan aiketa cikin gari ne. Okay to tayi sauri na ajiyeta daga nan mu biya office kawai ta dawo miki da sakon, Kwarai kuwa kaga har na manta da munyi maganar. Ta fito cikin atamfa dinkin doguwar riga yasha stones, ta yafo dan gyale batayi tunanin yana falon ba ta fito da gyalen a hannu tana gyara dauri. Mamee ta washe fuska, fara'ar ta ta karu, Uwani ashe kin dinka atamfar nan? Nima kuwa yau tawa zan saka kai amma naji dadi. Ta danyi yar dariya, waya miki dinkin nan? Hajiya ce ta bada mun......au haba? Ya kasa motsi kamar ya rukota yakeji kalacin da bai karasa ba kenan ya ce muje kawai, Ta kalleshi tana harara....... Mamee fada mata kada ta batan lokaci ya fara duba agogo. Zai ajiyeki ne amma zaki karbo mun sako wurin sa. Ta ce toh, suka fita, Yana rufe kofa ya janyo ta *Wai ke yaushe zaki waye?* Me nayi? Ba ko gaisuwa? To sakeni dai ka kalli gabanka, bai saketa ya dan waiga masu gadi ne da jama'an gida suka taho gaisuwa. Ya kara riketa ya sha mur, Haka ya gaisa da kowa duk wanda ya gaidashi sai ya ce *Ranki shi dade barka da safiya* mutum biyu ta amsawa, kunya ta dunga tsunkulin sa ta baya yayi mata banza. Suna shiga mota ya shako wuyanta ke wai *Yar fari ce?* ........ *kuma auta* ta fada. Kina mintsili na gaban mutane. Allah cizonka zanyi. Ya kyalkyace da dariya. Yanzu ni zan gaisheki ko kuwa kece? Wanda duk ka zaba . Yayi murmushi ina kwana, An tashi lafiya? Ya kara yin dariya naga kin fara *Wulakanci da rai* ta yi murmushi *Wai ma* Ya na zuwa office ya tarar da dandazon yan jaridu, yaki fita mota ya ce maza ace su tafi sai karfe biyu su dawo baida appointment da kowa yanzu. Sai da ya tabbatar sun watse sannan suka fito shida umaimah taki jerawa dashi daya Dan waigo sai ta nemi kwasawa da gudu ta rike riga, Ya sha mur meye kikeyi haka? Eh anji wuce dai muje zan bika abaya. Murmushi kawai yayi ya wuce body guards sun baibayeshi sunata mazurai. Dai dai an bude mishi kofa wata matashiyar mata ta iso..... *Yaro matashi*.......ya waigo da sauri yana murmushi tana zuwa ta fada jikinsa sukayi *Hugging* umaimah ta ja baya da sauri tare da fiddo ido kirjinta ya buga da karfi. Tare suka fara shiga office din , umaimah na ganin haka ta yi baya tabar wurin da gudu. Tana fita harabar office din ta tari mashin tare da fadin *TAL'UDU*................ *Good morning all* *Maman Abdallah*😘😘😘 https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣6⃣ ........... Ya waiga bai ga umaimah ba , ya fito da sauri ko tsayawa tayi , babu ita... Ya kira security din sa da suka zo tare yana tambayar sa yayi damama ya fara dube dube ya daka mishi tsawa *Are you mad*??? ....... Hankalin kowa ya dawo wurin duk aka mimmike tsaye, billahil azim idan baka nemo mun ita ba a bakin aikin ka ya yi hanyar waje duk aka rufa mishi baya. Ina yarinyar nan ta tafi? Ya kwadawa securities din bakin gate kira suka kwaso a guje yarinya ta fita yanzu?...…. Eh yallabai ta hau mashin....... *What????* Kuna hauka ne *Don ubanku* Ya dauko waya yayi kiran duniya taki dagawa. Ya kira mamee kamar yayi hauka, Mamee yarinyar nan ta dawo gida? Lafiya, Menene? Ta dawo? A'a me ya.... Kit ya kashe To wai ubanwa yasa kuka bari ta fita.... Ya zaro ido ohh my God *Anya ba ganin samira yasa ta gudu ba?* Kaiii kishi umaimah ke gareta sosai?? Tawa ta sameni ya kara kiran nameee... Ta ce ka ganta? Tana daga wayar. Ina ne kika aiketa? Gidan hajiya bara'atu tal'udu.....kit, ya kashe. Ya kalli driver *Maza dauko mota*..... Kadan kadan yayi tsoki, rigimar yarinyar nan tayi yawa. Daga nesa ya hangota hannuwanta rike da manya manyan ledoji suna rinjayar ta, tana shirin hawan adai daita, ya daka mishi tsawa *Kada ka bari ta shiga* Kawai taga mota gaban ta, tayi saurin fadawa adaidaita ya sauko da sauri... *ke kina hauka ne?* mai adaidaita ya zaro ido ganin *Umar madaki* Ta kalleshi a wulakance daga turu na fito malam muje..... Wallahi ka tayar da mashin din nan zakayi asarar ta. Yasa hannu zai fizgota ta ingijeshi na rantse da Allah ka taba ni zan tara ma jama'a, ta daka wa mai adaidaitan tsawa *Malam na ce muje ko?* Sai kawai ya fado ciki muje malam..... Ta yi saurin fita ta dayar kofar ta barshi ciki kafin ya fito ta haye dan mashin...... Ransa yayi mugun baci, suka bi bayanta. Hon sukeyi amma ta ce wa mai mashin din ko juyawa kada yayi. Ana sauketa bakin gate shima ya fito, umaimah.... Umaimah tayi banza dashi ba halin ya ruga ya rikota duk saurin sa ya kasa cin mata, Falo ta tarar da mamee tana ganinta ta taso uwani me ya faru ne ina kika tafi?...... *Ke kin raina ni ko?* ya shigo kamar an ingizoshi. Ta ajiye ledojin gashi mamee ta ce wadancen lesukan basu iso ba. Tayi ciki abinta ya daka mata tsawa.....amma ko saurarenshi batayi ba tana jin ya biyota koda ta shiga dakin sai tasa makulli. Ya yi bugun duniya taki budewa..... Mamee na jin su tayi zaman ta falo tana fada, *Yara kamar kaji* kullum cikin masifa mtseww. Ya dawo kamar zautacce mamee zan batawa yarinyar nan rai bana son raini, kinga yanda ta wulakanta ni bakin titi tabarni cikin adaidaita, mun shigo ina magana ta mayar dani sakarai, a gaban ki kuma yanzu kinga ta rufe kofa fa.... Me kayi mata?? Ya buga tsoki kawai kishin banza ne na rashin dalili, Samira sardauna ce na tarar office daga gaisuwa ta gudu. Au samirar tazo kasar ne? Nima ganinta kawai nayi. Ya zauna bisa kujera *Gaskiya mamee ki fadawa yarinyar nan* Ta kalleshi me? Tasa ma ranta hakuri saboda yanayin harkokina da ya kunshi kowa jiya fa *Uche* ta kirani a waya wallahi yarinyar nan ta nemi birkicewa. Me ta dauke ni ne? Mtsew... Ni zan fada ma uwanin haka? Tabb lallai kana da sauran aiki. Ta mike ka fidda ni cikin wannan maganar ma can Ku ta shafa. Mamee.... Kawai ta yi ciki. Kiran sa kawai akeyi a waya ya kasa dagawa, banda sakonni. Mamee ta ce bude uwani nice, Mamee na shiga ta nemi maidawa ta rufe ta kalleta tana yar dariya keni tsaya fita ma zanyi kayan da kika dankwarar man dasu falo na kawo. Ta ja baya ta kasa ko murmushi, dadi kamar mamee ta goya ta ganin kishin madaki haikan a wurin ta. Cikin zuciya ta ce lallai uwani kin cika *Diya* zaki gyara man shi da alama. Don zanga inda za Anyi *So* da zafin rai. Har karo yakeyi da namee zata fita yana kokarin shigowa, ta kalleshi kamar ta kyalkyace da dariya amma ta basar, ja'iri hada alhakina don iyayenka, nan na dunga kawo maka yara kana gwasaleni, ta fada a zuci ta wuce , Umaimah na ganin sa ta zauna bakin gado ya karaso zai kamata tayi saurin wawuro wata flower ta glass dake bakin gadon mamee, *Na rantse da Allah ka kuskura ka taba ni zan maka rauni* Ya yi turus, ta kalleshi a wulakance, kallo da yafi tsana a rayuwar sa fiye da duk wata kalmar ta muni da zata furta, Wai kana mun daukar sakarai? Ko kuwa kana mun daukar makwadaiciya wacce zata bika saboda dukiyar ka?...... What are you talking about? Ya daka mata tsawa....ita ma ta hayayyako mishi. Bani son ka wallahi yau na tsaneka bana kaunar ko ganin ka a rayuwata. Mtsewww haba no wander ba da aiki sai ka kai hannun ka jikina ashe halin ka ne ko wace yar iska tabawa ........ *Ke* .....ya daka mata tsawa ..... Ita ma ta tace .. *Enough* tare da mikewa tsaye ko ka fita harka ta ko kuma na bar gidan nan bari na har abada, kasan dai na isa shari'a ko? Yaga da gasken gaske yake sai ya fara rokon ta *Umaimah please let me explain*...... *Explain what?* ta katse shi. Maharramar ka ce? Ni kaina na fada maka bana so kana taba ni ko kuwa ya hallita? Zai yi magana ta daga mishi hannu *Wallahi idan baka fita kaban wuri ba zan bar ma gidan gaba daya* Dole ya fita, Ta buga tsaki, duk ya fita ranta, bata kaunar ko ganin sa. Samira child hood friend din sa ce, sun shaku matuka, yana bala'in shiri da ita yarinya ce natsattsiya a kasar London tayi aure can kuma take da zama mijinta ya rassu amma bata dawo Nigeria ba saboda aiki da takeyi, yaranta biyar, babu wani abu tsakanin su, duk Wanda yasan madaki yasan samira. Mamee bata san fitar shi ba, yana zuwa office ya tarar samira ta bar mishi note na wulakanci saboda ta kira ta kira bai dauka ba kuma ta tura text ba replay. Ya rasa abinda ke mishi dadi a rayuwar sa, komai ya jagule mishi duk Wanda ya tunkare shi sai bala'i. Washe gari aka tashi da azumi. Abu kamar wasa sun kwashe kusan kwana hudu umaimah tayi wuri ta kyaleshi, bata daukar wayar sa bata zama duk inda tasan yana nan. Yana kwance sama ya kira taki dauka, ya ce wannan yarinya da bakin kishi take, tama ki saurara ta taji uzuri na. Mamee taki tasa baki nayi rokon duniya ta ce kar na kuma yi mata maganar ma. Ya runtse ido kawai dabara ta fado mishi ya tura mata text. *I know that there is no forgiveness for the kind of mistakes I do. But if you can forget my mistakes and give me a chance, I'll make everything as good as new. I'd start everything all over again and make you happy.* Tana ganin message din ta kashe wayar ta ya kara tura mata wani yaga pending.. Yana kiran wayar yaji ta kashe, Ta harari wayar *Wallahi sai ka gane kuren ka* kai taba jikin mace baka dauke shi bakin komai ba? Ban iya wannan iskancin. Ko aure na ya yi wannan wata rana ya tabo jikin wata yaji tabshi lokacin nawa ya taurare banza zan zama. Kishin yarinyar nan yayi yawa, daga *Hugging?*...... Kai na gamu da gamona ni madaki, problem din ta gama gane na mutu kanta, Ya tashi zaune, kaii..... Lallai , in ba umaimah ba wace yar iskar yarinya zan ringa bi tana mun wannan wulakancin, wai ni madaki nake ba mace hakuri tana mun tsawa a kai. Mtseww *I hate this condition* ya dafe kansa. Ta tsaneni ko ganina bata son yi? Ga mamee na sane ta zuba ido? Ya kara tsoki, wallahi zuwa zanyi ayita ta Kare na gaji, ita bata da tausayi ne? Ya sauko sai kawai ya hangota ashe mamee ta aiko ta, Tana hangoshi ta juya zata koma ya karaso da gudu ya tari gabanta, ki dubi girman Allah ki saurareni umaimah .....zatayi magana ya katseta, ,,... *Girman Allah na ce* Tayi shiru. Haba umaimah wannan kiyayya haka ko lokacin da muke tsahin hankalin ma bakiyi mun haka ba ballatana yanzu da muke son juna kawai dan kuskure ne da za a iya gyarawa..... Ta kalleshi *Dan kuskure* Yayi saurin daga hannu sama, *Babbar matsala* ce afuwan. Wallahi samira babu wani abu tsakanina da ita, kinji na miki rantsuwa ...... Ni na ga haka tunda ka mance dani ka mamuke ta,... Kamar zaiyi dariya ya dai tsuke, shin ai don na hugging din ta ko? To wallahi bazan kara ba, yanzu haka na rantse da Allah ko clerks dina tsoransu nakeyi. Tayi mishi banza, ya nuna mata kujera don tsoron tabata yakeyi ki zauna ba don ni ba don Allah...... Ta zauna kanta gefe tasha mur, Ya ce kut, cikin rai. Ya fiddo waya duba ki gani text din da tayi mun ko a ranar sannan tabar mun note office hada zagi na rantse da Allah baki bina bashin rantsuwa umaimah ban kulata ba har yau. Ko kirana akayi yanzu naji muryar mace gabana faduwa yakeyi . ya kamata ki sassauta man saboda akwai huldodin da dole dasu nakeyi........ Na fika sanin haka, don yanda ka saba taba jikin mace bazaka iya ko wace hulda bata ba........ Innalillahi sharrin da zakiyi man kenan? ..... Ni na gani da ido na. Ta taba wayar gari nan gidan baka dankeni ba? Haka idan kaje office ka dunga rungumar mata sannan ka dawo nan ka dosa dani ...ta kalleshi na maka kama da *Yar iska?* Ya zaro ido umaimah ki fahimceni.....wallahi ban fahimtar ka, ni bakai man ba. Ta mike tsaye ina rokon ka ka ajiye maganar so mu ringa mutunta juna. Wallahi bani iya auren namiji mai hali irin na ka....... Ya tari gabanta idan na taba rike wata diya mace bayan ke Allah ya tsine mun, sai kuwa samira tun yarinta idan mun hadu zamu........ Zaku kadaddabe juna. Ya langabar da kai, *Kiyi hakuri* in shaa Allah na miki alkawari hakan bazai kara faruwa ba. Zatayi magana ya hada hannuwa *Na tuba* kiyi hakuri na kai karshe wallahi na horu, ba zan kuma na please........ Ta kawar da kai *Ya wuce*... Ya saki wata sanyayyar ajiyar zuciya har sai da ta waigo ta kalleshi ya sakar mata murmushi...ta kara tsuke fuska. Ya zauna taimaka ki kawo mun ko tea ne inyi buda baki, ta kalleshi da sauri...... Kina mamakine? Wallahi bana sahur bana buda baki kullum daga dabino sai madara nake sha. Ya langwabe ai na ga *Bone* kwanakin nan..... Ta wuce shi kawai. Shiru shiru mamee ta fita taga lafiya kawai taji maganar su falo sai kawai ta sadada ta koma, Ta zubo mishi farfesun kaji da fruits salad nan da nan soyayya ta tashi, da ya kawo hannu zai kamota sai ya tuna ya basar ....... Ana tsoron mu nida iya, inji diyar mayya......😃😃😃😃 Suna nan sai dai kawai sukaji liman ya kwala kiran sallah....Allahu akhbar.... *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘 Na gode da addu'o'in Ku. Aunty rabi na godiya matuka🤝🏼😘 [1/27, 7:42 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣7⃣ *Abincin wani gubar wani ina rokon duk Wanda labarin nan bai mishi ba don girman Allah kada a karanta don Anyi shi ne kawai don ilimantarwa da nishadantar wa, duk wani marubuci mai hikima yana kokarin fiddo abinda ya zama ruwan dare a rayuwa ya misaltashi kafin ya nuna illar sa. Maganar runguma da akeyi ai gashi nan a universities 'yayan hausawan mu suna chudanya da maza rike hannu da rungumar basu daukeshi bakin komai ba, mafi yawa kuma sakacin iyaye ne, saboda haka ina sane da abinda nake rubutawa a daina sauri ana zarbabi, masoyana kuma ku sani labarin AUREN FARI wallahi na rubuta shi don girman SOYAYYA saboda haka ni bani raina masoyina duk in da yake kuma ko yaya yake. Ku sani nafi kaunar ku fiye da yanda kuke son labarin AUREN FARI wallahi, Allah yabar so da yarda. Kada a manta don HAJIYA RABI BADAWI MAMAN IBRAHIM DA NURY na rubuta AUREN FARI da duk daukacin masoyana.* ...... Ya kalleta ta kalleshi, suka kwashe da dariya, ni ban taba kwanan zaune ba yau gashi ka janyo mun, Mamee ta fito, me zatayi ba salati ba, anan kuke zaune har assalatu? Umaimah ta buga hamma, Ya kalli mamee to tunda kin sa mun ido zanyi mussai a cikin gida ba dole ni in shawo kan abata ba, Ta wurga mishi harara, mamee tayi yar dariya au ka bayar da hakurin? Dole na ma, Kuma shine ka tsare mun 'ya har assalatu, duk kuna cewa me? Ohh yauni na shigesu da mamee fira mukeyi da begen juna ko bakiga kwanakin da muka kwashe ba tana gudu na, Ya mike samira zata janyo mun ko ma in ce ta janyo mun bala'i. Au wai duk fitinar akan samira ce? Dai dai ya zauna bisa dining wallahi mamee ita ce daga *Hugging* yarinyar nan ta birkice mun, Da kyau......mameee ta fada itama lokacin tana zama. Uwani taso muyi sahur kike ta hamma daga zaune, Da kyau fa kika ce mamee, Eh mana, ta mun dai dai kaga yanzu sai ka fahimci abinda kake aikatawa bashi da kyau lokacin da nake fada ma dariya ma na baka irin ban waye ba to yanzu kaga wayewa zata bi da kai don da alama uwani ba sakarkarun matan nan bane... Ya bata fuska, mamee ban tunanin gidan nan zaki taba ganin laifin yarinyar nan, maimakon kiyi mata fada ta sanyawa ranta hakuri ki kwatanta mata yanayin huldodina da mutanena shine zaki kara zuga ta? Akan me?, ko kadan wallahi, huldodin banza sai aka ce hulda dole da mata za ayi ka kamo hannun waccen ka riko waccen.? Mameee......... Haba wannan wace irin shaidata ce kin mayar dani magnet. Ai na daina ko sunan mace bana son ji yanzu, Ta tuntsure da dariya, da sauranka yaro. Umaimah na gama hada musu ta dauki nata tayi ciki yayi kiran duniya ko waige, da basu yi haka ba kamota zaiyi ya bita da kallon takaici, duba kiga abinda takeyi man mamee tana jina tayi shiru in rikota yau in wuni cikin azaba........ Kaii ni *madaki* naga ta kaina. Me mamee zatayi ba dariya ba. Ai uwani na birgeni wallahi ka sami mata dai dai da halinka. Saboda duk wacce ka aura tana jin tsoronka ko tana binka saboda dukiyar ka bazata taba fada ma gaskiya ba, bazaka taba gane kayi kuskure ba haka zalika baza ka taba gane rayuwar aure ba har abada. Amma a yanzu uwani ta fara bi dakai hanya.......haba mamee, Tayi yar dariya na yi karya ne? Zaiyi magana canza zancen, jiya *Yaya ta kirani* Watan babbar yayarsu ta Kaduna, Ya bata fuska su Aunty jamila sun kai mata gulma ko? Madaki..... Ka dubi girman Allah ka daratta yan uwana bana son kana nuna masu ko ka shiga maganar da ba taka ba. Ya ajiye spoon shi kenan na daina in shaa Allah. Me ta ce miki? Tambayata takeyi da gaske ka sami mata cikin yan aiki? Na ce mata eh amma ba yar aiki ba ce. Kika bata bakin ki? Sai ki bita da eh,tana da abinyi ne? Mamee na fama da yan uwanta, yaya ta kaduna ita ce babba sai ita mamee din sannan anty jamila da aunty murja, Aunty jamila ita ce munafuka duk wani motsi da mamee zatayi ita ce ke kwarmata wa sauran. Mijin yaya yafi madaki kudi nesa ba kusa ba. Amma idan sabga ta tashi mamee ce dawainiyar su da komai, basa tausayin ta ko kadan, yaya bata wata bata fita wata kasa ba, amma ko sabulu bata taba kawo wa mamee ba da sunan tsaraba. Mamee kuwa da yake tafiye tafiyen bai dameta ba sai kamar ko umara daga can su biya kasa daya ko biyu, haka zata bi su da kayayyaki designers su da ya'yen su, idan sallah ta tashi haka zata dunke 'yayansu da tsadaddun kaya. Ta aika mota a dauko su tela ya auna su. Amma sai yayar ta ce ana ma yaranta dunkin banza a ringa kawo mata suna badawa dunki. Kullum dadi sukeji madaki yaki aure har suna gulmar koda kudi ba sai da farin jini ba? Jin ya sami mata yar aiki kuma yanzu surutu ya karu. Ya riko hannunta, mamee ki kwantar da hankalinki kada duk abinda zasuyi ya dameki. Ko kadan kawai ina takaicin uwa daya uba daya amma bakinciki ya shiga zumunci da jin zafi. Cuta ce mamee, hassada sukeyi miki kuma sune a kasa kada ki fasa kyautata masu, kullum ina fada miki daga naira daya zuwa miliyan dubu mamee kada kiji shakkar tambayata koda kina sha'awar kawai in baki kisa masu wuta. Tayi yar dariya Allah yayi Maka albarka umar, Allah ya kara maka arziki mai amfani kaima ya baka yaran da zasu ji kanka su tausaya maka su kula ka kamar yanda kayi mani. Aamminnnn mamee, amin. Ina so daman muyi magana, Tsakanin ki da Allah mamee Umaimah ta miki? I mean uwani, Tayi murmushi, kwarai kuwa, hasali ma ni uwani tayi wa kafin tayi maka......ya kyalkyace da dariya na sani. Ina maganar fa AURE. Ta daga kai tabbas kuwa ta yi mani wallahi bani da matsala ko kadan da uwani, yarinya ce mai hankali, barkwanci, girmama na gaba da ita, tausayi, bata da kwadayi uwani bata sata, na auna yarinyar nan yafi sau dari amma wallahi daga baya ma sai da na ji kunya, Yanda duk baka tunani ina son uwani ummaru. Ya fadada fara'ar sa to ina son kiyi man alfarma in je in nemo auren ta a daura mana aure ranar sallah. Ta zaro ido baiyi sauri ba? Karatun ta fa? Duk ina sane dashi wallahi wallahi bazan taba hanata karatu ba mamee ko PHD take son yi zan kyaleta amma aiki ne bazatayi ba. Maganar sauri kuma zanje Abuja muyi magana da baba Lawal da baba Nura sune zasu sanar da sauran. Zan biya Kaduna da kaina na fadawa...... A a ita dai ka bari na fada masu. Amma ka fara tuntubar uwanin kuyi shawara sannn.....mamee rigimar yarinyar nan nake tsoro kada ta birkice mun kuma, Dariya mamee keyi hada kwalla wai yau *Madaki* ke Shakkar wani abu a rayuwar sa, Yayi murmushi, Allah kuwa rigimammiya ce. To kasan abinda za ayi? Ka je kuyi magana da mahaifin ta komi ya ce shi kenan...... Haka za ayi ya fiddo waya, Kai bani son hauka.....amma ina har ta fara ringing, ya ce to ai yanzu yana sallame sallah zai fita gara in fada mishi ya jira in zo. Hakan kuwa akayi. Yana dawowa sallah ya shirya kawai ya fi ce, Umaimah kuwa tana sallame sallah itama ta kudundune a bargo, mamee na shigowa ta tarar da ita, sai kawai ta rage mata A.C ta ja mata dakin ta koma falo. Malam bawa ya share zaure da kansa ya shinfida tabar ma yana jiran Madaki. Shi kadai yazo, bayan sun gaisa yana ta tsumayen yau kuma da me yazo? Ya dan yi jimm, baba adaiyi hakuri don Allah... Haba haba wallahi babu komai in ce dai lafiya? To kusan lafiyar dai zance, wallahi wata alfarma na zo nema da kuma shawarar ka, Ya kalleshi a mamaki yallabai tami kuma? A gaskiya baba ina son umaimah kuma so na aure hasali ma idan za a taimaka man baba ina son auren kada ya wuce sallar nan idan muna da rabon kaiwa. Yadan yi shiru, jin malam bawa bai ce komai ba ya ci gaba da cewa, Wallahi bana son ko tsinke naku na yafe ita kadai nake so ku bani sannan zan dauki duk wata dawainiya ta bangaren ku. Wannan ita ce alfarmar da nake nema, shawara kuma, Ina zullumin kada umaimar taki amincewa don yanzu haka na sanya ta karatu tanayi kuma na yi alkawarin wallahi zan barta ta karasa duk inda take son kaiwa a matakin karatu. Shin in sanar da ita ko inyi shiru? Ya dan yi shiruuuu!!.... Ya langabe baba don Girman Allah ka taimaka man. Haba yallabai, babu abinda zaka roka in hanaka, matsalar ina da yan uwa kauye zan so na sahawar...... Idan har kana ganin babu damuwa na amince mu je yau ka gabatar dani. Kafin iyayena su koma. Ya danyi murmushi yallabai hakanan zaka wahalar da kanka in shaa Allah zan je da kaina. Baba kayi hakuri don Allah ..... To shi kenan bari na shiga na fito kada rana tayi mana hanyar bata da kyau. To baba maganar umaimah fa in fada mata? Rabu da ja'ira ni zan mata magana da kaina don kada ta ga laifin ka tunda har kana da tabbacin zata iya birkicewa.... Ya shige gida in ba iyeshe na yaran yanzu ba ita har tana da abinda yafi auren a wannan maraicin nata? Sai biyu da rabi suka dawo, Madaki na ta murna yanda aka tarbeshi kai wadannan mutane da mutunci suke, Shima malam bawa yana ta jin dadin yanda madakin ya saki jiki kuma ya girmama yan uwansa ba tare da raini ko nuna kyama ma. Suna zaune falo ita da mamee ya shigo yayi lilis don gajiya, mamee ta kalleshi yanda ya zauna da kyar, Wash wallahi na gaji mistake daya nayi da na tuka mota yau. Ke baki iya cewa sannu da zuwa darling? Mamee ta harareshi ka dawo zaka sa miyon bakina kafewa ina ka tafi yau wayar ka ma bata samuwa? Bari mamee wallahi mutanen nan na dade ban ga masu mutuncin su ba, mota ta nacen cike da buhunnan wake da aka bani. Nan da nan mamee ta dago shi ta kalli umaimah uwani jeki karasa man gyaran durowar kinji....... Kiyi sauri danayi sallah zamuyi zance. Ta yi ciki tana dariya mamee ta bishi da harara, ina sauraron ka ni ra sa kunya..... Ya kwashe duk yanda akayi ya fada mata. To amma kai yanzu ga azumi ya zakayi da wadannan tafiye tafiye ga hada kayan aure, ....ya mike tabbb ni kuwa nasan yanda zanyi mamee ya haye sama ....... Kuyi hakuri wallahi yau school naje. Afuwan 👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼😃 *Maman Abdallah*😘😘😘😘😘😘 [1/27, 7:42 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣8⃣ ........ Daga masallaci ya wuce shi da driver gidan su umaimah, lokacin da suka isa malam bawa ya gama shinfida zaure, Ya tare shi cikin girmamawa amma Madaki sai sumsumkewa akeyi alamar nauyi da kunya. Bayan sun zauna malam bawa ya mika mishi hannu alamar su gaisa Madaki ya zukunna har kasa abinda ya kara daure kan sa kenan. Bayan sun dan zauna jimm, malam bawa ya kalleshi wallahi ranka ya dade tunda naji wayar ka na kasa natsuwa ina ta zullumi da fargabar ko lafiya? Ya danyi murmushi lafiya qalau baba daman ina son rokon wata alfarma ce kuma da neman shawarar ka. Alfarma? Wallahi kafi karfin komai a wurina yallabai. A yanda nake jin labarin ka a gari ban taba tabbatar wa ba sai da naga zahiri. Ka cika *Da* na halas! Na ji dadin yanda ka mun duk mai son ka a rayuwa shi ke fada ma gaskiya...... Baba mubar maganar nan ta wuce! Abinda ya kawo ni ina neman Alfarmar *Auren umaimah*...... Ya dago kai da sauri....... Kada in ce daman furucin ka na farko da gaske kakeyi ko kuwa har yanzu kana da tunanin...... Wallahi baba bani da tunanin komai sai alkhairi. Ina son umaimah saboda Allah kuma ina son ta zamo *Uwar 'ya'ya na* Alfarmar da na ke ka taimaka man da auren ta karamar sallar nan mai zuwa. Baba amincewar ka kawai nake bukata wallahi tsinke bana so daga gareku sai ita kadai. Maganar hidima zan dauke muku komai. Yayi shiruuu...... Kafin yace, Alhamdulillah. Na ji dadi sosai da wannan albishir domin a gareni albishir ne, gareni baka da matsala, amma ka sani ina da yan uwa a kauye wadanda suma suna da hakki akan yarinyar kuma muma muna da iyaye zan so ka bani lokaci....... Baba banyi gaggawa ba amma ina rokon ka da idan babu damuwa yau zan kasance tare dakai matukar zaka jagorance ni garesu in gabatar da kaina kafin in aiko da magabatana. Yayi murmushi wallahi babu wata damuwa sai mu tafi. Sai maganar shawarar ka, agaskiya ina tsoron fadawa umaimah kada ta birkice mun....... Au daman bata amince maka ba? .....wallahi tana so na baba, na sanya ta makaranta ne, to bata son katse karatun nata....... Yayi dan murmushi *Au*, Kuma zan barta ta karasa karartun ta sannan idan ma tana son karawa gaba na amince *Aiki* daine bazan amince ba. Shine na ce in sanar da ita din ko kuwa ana zaku mata bayani? Malam bawa ya mike tsaye kaima ka zama yaron kenan, kyale ja'ira kada Wanda ya ce mata qala, tunda har kana tunanin zata ki amincewa. Bari na sako babbar riga kada muyi rana yayi ciki. Goggo hansatu ce ta fara tarar sa malam kai da wa ye haka tunda safe? Ya fadada murmushin fuskar sa, maneman auran umaimah ne yanzu haka zamuje kauye....... Ta daki kirji *Aure?* Suna fitowa Abba yazo zai wuce fangan fangan... Malam bawa ya daka mishi tsawa ganin zai ingije bako. Yayi yar dariya babu damuwa baba. Kayi hakuri ba natsuwa a hanya yake fada mishi ko waye Abban, ya tausaya masa tare da alkawarin da sun dawo zai daukeshi yakaishi *Rehabilitation* Yayi mishi bayani sosai ya kuma gamsu yana ta godiya. Kauye ne mai cunkusassun gidaje,Abinda yaba malam bawa mamaki shine yanda *Madaki* ya saki jiki bai nuna wata kyama ba ko shimfida akayi mishi sai ya yaye ya zauna yanda kowa ya zauna, babu Wanda baiba girma ba. Wannan abu ya wa malam bawa dadi a rai. Hatta kananan yara sai da ya raba musu kudi. Shi kuma duk gidan da suka je sai an basu ko gero ko wake, haka suka dawo da tumbaye ransa sayau, Yayi yayi malam bawa yabar tumbayen abincin nan amma yakiya. Hakan ya kara sanyaya zuciyar Madaki kaunar umaimah da tausayin iyayenta ya karu cikin ransa. Karfe biyu da rabi ya isa gida suna zaune falo mamee taga ana shigowa da yan buhunna , ya shigo mamee ta kalleshi duk ya gaji..... Daga ina haka? Ya zauna wash! Sannu da zuwa, umaimah ta ce dashi tana satar kallon mamee. Yawwa my dear ya gida? Sannu da gida mamee love.... Kai ban son iyashege kaji ko. Ya tuntsure da dariya umaimah dai tayi ciki. Ya bita da kallo *Ke dawo*....... Amma ina ta shige. Ya kalli mamee yarinyar can dole inyi maganin ta ta raina ni, Naji, ina ka tafi ko wayar ka ba a samu ka shigo da wasu yan buhunna kamar Wanda yaci kasuwar kauye..... Kin canko dai dai. Kauye naje mamee.... Kauye? Wallahi kuwa ya bata labari kaf! Ta rike baki Allah sarki, wayyo Allah kai masha Allah wadannan mutane sunyi bazata.. Kwarai kuwa. Gobe zan tafi Abuja zamuyi magana dasu baba Ibrahim muji me zasu ce. Sai in biya Kaduna ...... A a ka bari zan fa da ma su yaya. Ya dauki waya yawwa kaga missed call dina ko?,......okay ka ganshi? To passport nake so latest jibi don na gama magana da embassy..... Ya kashe. Me zakayi da passport? Na umaimah ne umara zaku tafi kuyo mana addu'a kafin ku dawo na gama wasu gyare gyare. Don Allah? Kai masha Allah. Amma naso ka bari sai karshe...... Mamee kuyi hakuri bana so kuyi sallah can saboda daurin aure ya mike. A ajiye mun kayana kada a taba mun, Ka fada mata? Kiyi shiru sai zaku tafi.... Kai ban son shirme komai ayi shiru komai ayi shiru to sai na fada mata. Ya haye sama kunfi kusa.. Sallah kawai yayi ya kwanta barci. A saman yasha ruwa cook din sa ya hada mishi tea da sandwich. Umaimah taji shiru har ta dawo asham amma bai sauko ba ga mamee zaune tana kunyar ta kirashi sai kawai ta tura mishi text. *I know for sure that you are my life, Since the time you have left today ,i feel so blue and nothing interests me, i think you have taken a part of me ,And I really can't survive without you ..I love you and I miss you , You should know that I truly do ,Please come down soon!* Ya maida mata amsa *When I say thank you, I mean it from my heart, Dear you helped me achieve so much, You were there from the start, A heartfelt thank you to you, am coming dearest* Bata karasa karantawa ba ta hango shi yana saukowa, ya sha wanka cikin kana nan kaya *Kai madaki nada kyau* suka hada ido ya sakar mata wani narkakken murmushi ta mayar mishi tare da sunkuyar da kai. Mamee na lura da ita, sai tayi kamar bata ganshi ba ta mike uwani idan kin gama kallon kya kashe ni kam na gaji...... Mamee barka da shan ruwa ina zuwa kuma? Au ka sauko? Barkan mu juna, zan dan kwanta ne na gaji. Yayi murmushi kawai. Tana wucewa ya ce matso malama ki fassara mun text din ki. Ta danyi murmushi kawai, ansha ruwa lafiya? Qalau, Me kika rage mun? Kosai..... Ya kyalkyace da dariya wallahi banci, sai me? Dan na rogo.... Ya fara dariya. Ta tashi ta dauko mishi yanballs da samosa, sai dan juice din ta na kwakwa da fresh Ginger, mamee ta ce kafi son mai dan nama nama gashi idan zaka iya ci don kai nayi. Ki ce Allah! Allah kuwa, Ya janyo cooler iyye yarinyar nan fa zatayi *Caring* Ta ce hmmmm Ya fara ci yana Santi Cewa zakiyi nabar banza na tsaya cin sandwich saboda kiwa. Gaskiya. Ya dan zaro wani abu gaban aljihun sa kawo hannun ki in baki tukuici. Ta mika mishi, ya zo zai kama tayi baya dashi da sauri tare da 6ata rai, wallahi kaga abinda na tsana a tare dakai. Ohh am sorry please. Ya kamata ka fidda wannan muguwa tabi'ar a ranka gaskiya domin wallahi haramun ne,...... I said sorry woo.. Yeah I know but let me tell you, ka fidda fashion a maganar nan ka sanya addini, taba mace baliga haramun ne , me yasa namiji baligi ko baliga idan sukayi alwala akace shafa ko babu sha'awa alwalar ta warware? Addini fa sauki gareshi wallahi ko musulman mu dake zuwa kasashen turawa suna gaisawa dasu bala'i suke daukar ma Kansu. Haka ma khausar a school sai da na mata magana ita da kawayen ta kawai kana zaune kato zaizo ya kai hannu ya dafa ka ko ya kai duka wai abobota. Ya kamata ka daina bana so na fada ma da arziki, na fada ma cikin fushi to yanzu na fada ma a addinance wallahi next bazatayi mana kyau ba. Wallahi na daina kiyi hakuri ungo zobe ne zan saka miki amma saka da kanki Allah ya bada hakuri ustaziya ta. Ta yi murmushi. Shi yasa na ce wa mamee kuje umara tare kiyo mana addu'a kinga sai ki rungumi ka'aba ki Rokan mun Allah ya yaye man wannan hali....... Umara? In shaa Allah. Jirgi zan hau? Ya kyalkyace da dariya a'a bisa keke zaku tafi. Itama ta yi dariyar. Na gode Allah ya kara arziki. Aminnnnn my love. Yau fa da wuri zan kwanta bazanyi kwanan zaune ba. Ya langabe kiyi hakuri mana haba don Allah. Okay naji sha daya nayi zanje in kwanta. A a na yarda sha biyu dai. Zatayi magana ya canza da cewa, Don Allah kiyi mana dawafi Allah ya tabbatar mana da alkhairin aure na dake, sharrin da ke tare dashi Allah ya karemu kinji. Banda kai za a tafi? Gaskiya, Ta bata fuska, dalili Akwai abubuwan da zanyi ne kafin ku dawo, yanzu haka ma Gobe Abuja zan tafi. Kai baka jin azumi? Ko ina ji ya zanyi mai nema ai baya kwanciya umaimah baki ganin ni maraya ne. Ta balla mishi harara in kaji maraya raggo. Ka ma gode ma Allah kai kana da mamee ni kuma fa..... Ke kuma kina da *Madaki* Hummm Ko baki sona? Ni kuwa ke son ka....... Ta yi saurin tsuke baki, Don Allah karasa tawan. Hahahhaah kaji abinda kaji. Kedai bakauya ce wallahi. Naji wayayye. Ina so in tambayeki, a tsarin gida wannan ya miki? Ta kalleshi, ban gane ba. Ina nufin idan munyi aure zaki zauna anan nida ke muna sama mamee na nan..... Yau na shiga uku ta fada tana tafa hannuwa. Don Allah ka rufa man asiri ni wace amsa zan baka? Zai kara magana ta daga mishi hannu nidai canza magana baka da amsar wannan. Yayi murmushi. To kina iya mun list na abinda kike so batun lefe nake da kamar irin kayan kitchen,....... Ta mike yau firar taka duk kame kame kakeyi sai da safe..... Yayi saurin tarar ta, ya hakuri ki dawo wasa nake. Ta koma tana hararar sa, Yayi murmushi, ke yanzu baki iya fada man abinda kike bukata umaimah? Kinji? To wai me nake bukata saboda Allah, a hakan ma na gode Allah ya kara arziki. Ko muyi chatting? Hummm, Kinji? Ohh ni! Ta fada, Kiyi hakuri mana. Kaini fa bani bukatar komai. To takalma fa kina son masu tsini? Ta mike wallahi kaga tafiya ta yau firar taka tafi karfi na, Yana tunkurawa tayi ciki da gudu............... *Ayi hakuri da kadan*😃😃😃👆🏼 *Maman Abdallah taku ce*😘😘😘😘 [1/27, 7:43 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣2⃣9⃣ ......ya yi murmushi, lallai kina da kawaici da zurfin ciki. Washe gari ya tafi Abuja. Yaya kuwa mamee na kiranta tafada mata sai ta hau zage zage wai har yaushe madakin ya sami mata ba a fada mata ba sai da aure yazo? Bakin ciki da bacin rai ya taso mata, bata taba tunanin zai yi aure haka da wuri ba amma ga mamee ita hakan ma ya jima. Abinda su yaya keso ko motsi mamee zatayi ta sanar dasu, sannan basa iya tsinana mata komai sai magana da gulma. Ga hassada, ita hassada mutane basu gane ba, ciwo ce, uwa daya uba daya ana hassada. Kawai sai dai addu'a Allah ya raba mu da kullihin musulmi da ita. Yana dawowa bayan an sha ruwa ya ce umaimah ta shirya zai kaita gida suyi bankwana . Jikin ta yayi sanyi. Suna fita ya kalleta ko dai bakya son zuwa? Me ka gani? Duk kin wani darare, Ta ce hummm, Kar ki damu kedai kiyo mana addu'a tare da iyayen mu. Wai kina ma su addu'a ma kuwa? Tayi yar dariya kwarai kuwa. Babana fa? Hada shi. Ki ce Allah. Tayi dariya . Yau ma anan zaka tsaya? , ya gyara parking gaskiya, kinsan manzon Allah SAW ya ce idan alheri ya sameku to ku boyeshi har sai idan ya bayyana. Ita kadai ta tafi ya zauna yana jiranta a mota, Sallama tayi duk suka mike ana tsallen zuwan ta, yau ita ce hada dauko kujera wai ta zauna. Dariya tayi kawai ta raba bakin tabarma. Ta kasa boye mamakin ta. Bayan sun gaisa ta fada ma su abinda ya kawo ta kowa ya fara tsalle ana bata saftu. Su goggo ta ciki na ciki, amma basu nuna mata ba. Har zata tafi luba ta ce wai umaimah wanene angon? Ango? Ta bukata, Goggo ta dan dungureta ke ban son surutu...... A a goggo kuma fa kuna taso kusan wanene. Ban gane ba luba. Jiya wanene yazo wurin baba aka kaishi kauye gaida iyaye? Gabanta ya fadi, ta tuno dawowar madaki da yan buhunna. Uhummm kawai ta ce ta tafi. Tana fita goggo ta ce da luba bita kigano mana ko wanene watakila mai gadin gidan ko direba ne ta samu, don duk yanda akayi jikin gidan shima yake yanda naga malam nata fachaka. Ta dawo da sauri anya ita kadai take tama shiga gidan Alhaji yakuba. Duk suka tabe baki. Sauri sauri ta tarar dashi ya dan kishingida yana jin gwanja. Ko zama batayi ba ta ce, jiya kauye kuka je? Duk da yaji faduwar gaba kuma bai san abinda aka fada mata gidan ba sai kawai ya wayance. Eh, ina ta so in fada miki kinga na manta. Jiya na je na sami baba akan ina neman izinin fara nemanki da aure ma'ana ( zance ) kamar yanda addini ya tanadar kada suji wai wai a dauka ko na raina su or something like that, shi ne ya ban shawarar in sami lokaci muje kauye na gaida kowa tunda shima yana da na gaba dashi. A jiyan am free so nayi amfani da daman na ce muje kawai ko nayi laifi? Tayi murmushi ko daya. Ya tayar da mota, when last kika je kauye? Tayi yar dariya gaskiya mun dade. Shi yasa jiyan akayi ta mamaki wai har kinyi girman da zakiyi aure? Tayi dariya kawai. Maimakon gida ya wuce suka siyo ice cream suna tafe suna sha. Zaki sha ice cream saudiyya mai dadi, ta danyi murmushi kawai. Me zaki siyo mun tsaraba? Duk abinda kake so, A a kawai dai kiyo mun tsaraba da choice naki. Okay I'll try my best. Yayi murmushi ya janyo wata leda ungo ga guzurin ki kuyi amfani da dollars sunfi dadin harka..... A a duk ka hada kabawa mamee idan ina bukata zan karba wurinta. Ya kalleta da kyau. *Why*?, nake ga hakan zaifi. To ai itama ga nata nan ya fiddo wata ledar, ta danyi yar dariya yawwa to hade mana wuri daya duk ka bata.......ke ban son rashin wayewa malama. Ta dan harareshi Kaine ba kauye don Wanda ya waye baya gardama kai kuwa kullum sai anyi musu da kai. Ya ma rasa me zai ce mata? Kamar ya janyota ya rungume amma ba hali. Ya dan lumshe ido, Alhamdulillah wani jinkirin alkhairi ne tabbas Allah ya karbi rokona. Ya dan kalleta, Umaimah duk umara ko hajjin da zance wallahi addu'ata ya Allah ya bani mace ta gari wacce zata soni ta kauna ceni badon kudi ko kyawuna ba, sannan yasa ta so mahaifiyata kamar yanda nake sonta, ta tausaya mata fiye da yanda nake tausayinta. Ta danyi murmushi, kaima da wata magana, su iyaye ai na kowa ne, wallahi ko na sona ko baka sona mamee ta dauketa tamkar mahaifiyata, bata kyamace ni ba, bata taba zargina ko guduna da duk wani abu nata ba, ta dauki yardar duniya ta dora mun ta yaya zan taba gudunta ko wani abu ya nemi hadani da ita,? Wallahi ko a lokacin da bama jituwa idan bala'in yayi bala'i naso guduwa sai in tuna yanda ta amince mun sai na gwammace in hakura da takurawar taka in mata halacci. Ya runtse ido tare da danna hon....masu gadi suka rugo ya shige da motar, Na ga irin kulawar da kike bata, naga yanda kuke son junan Ku umaimah wallahi nima na yarda dake 100%, kuma ban taba zargin ki ba. Ya kashe mota lokacin da kike mun gyaran daki baki ga kudade ba? Na gani wallahi. Ya juya ya kalleta sosai, wallahi ko buhun kudi na ajiye aka taba ina ganewa, lokacin da na kunna CCTV ina kallon yanda kike kara gyara man kudin hankalina ya tashi domin Wanda duk kika San ya shiga dakin nan wallahi sai an mun sata, shi yasa na hana kowa. You are different umaimah, cikin dubu da kyar za a sami goma irinki. I love you with all my heart, ni kadai nadan yanda nake feeling, ta danyi murmushi ko? Ni ma haka. Suka fito tare da jerawa, yana fada mata yanda ya kagara ta zama matar shi. Sai dai tayi murmushi ta ce *Uhumm* Mamee na kishin gide falo suka shigo hannuwan sa da ledijin kudin su, ita kuma da dan kingin ice cream, Cewa zakuyi kwadayi kuka biya shi yasa naji shiru. Mamee ta fada tana ta kokarin tashi zaune, Ya dan zauna umaimah kuma ta tafi can kusa da ita, gashi ma na rago miki nayi nayi ya siyo dake yace a a. Ya zaro ido ke..... Mamee ta karba tare da hararar sa na sani uwani nasan babu yanda zaki mance dani. Ta yi mishi gwalo, mamee na satar kallonta. Ya nunata da yatsa nafiki iyawa yarinya. Mamee ta ce kwarai kuwa ka fita iya rowa. Suka yi dariya ita da umaimah ya sha mur ni zaku hade ma kai? Ta kama kunne sowie wasa ne ko mamee? Shi yasan hakan ne, Ya kyalkyace da dariya dole aban hakuri........ Ohhh son girma kamar maruru!! Me umaimah zatayi ba dariya ba kaii mamee wai maruru. Ya mika mata ledojin kudin ga guzurunku, kince kowa na ware mishi gata nan taki karba tace sai dai na hade duka na baki idan tana bukata sai ta karba. Mamee ta kalleta da sauri , dalili,???? Zatayi magana ta sha mur ke bani son iyashege yanda nake fama dake anan ina ciwon baki ki dauki kudi kiyo siyayya haka ma can kike so inyi ta babatu? Maza karba kada ranki ya baci, Ta dan langwabe kai, haba mamee ni fa ce uwani, kin manta ni ke rokon kudin tsamiyar biri......... Ungo ta yi mata dakuwa, naira ashirin hamsin din? Ta turbune fuska tare da mikewa, so kawai kike yayi mana dariya kin gwasaleni ta wuce tana zumburo baki. Ya kyalkyace da dariya na ganku a rana.... Ta harareshi kai tafi can samna, yanzu kai matsayin ka na miji baka iya dabara da lallashi ta karbi kudin ko?. Nasan uwani da kawaici wallahi kunya bazata taba barinta ko taga abu ta nuna tana so ba, in kuwa hannunta suke tafi sakewa. Ya watsa hannuwa kawai kiyi ta zuwa da ita kina nunnuna mata amma kada ki bari ta siyi zinari ko zobe, kuci dadi kusha dadi please. Sai yan kayan kyale kyale sannan kuyo mun tsaraba don ta dawo mun hannu biyu akwai rigima. Mamee ta mike kilibabbe sai ka ce tayo ma ba muyo ma tsaraba ba. Kai Allah yasa maka kunya ni *Rabi'atu* ta wuce ciki.Washe gari karfe sha biyun rana su umaimah aka tantsa kasa mai tsarki a *Madaki airline* an kame first class anata wulakanci da rai, da jirgin zai daga yan cikin ta suka yamutse ta kama mamee gammm tace *Wayyooooooo yan hanjina* Mamee ta tuno umaimah fa bata taba hawa jirgi ba sai ta hau tofa mata ayatul kursiyu. Ta na warwarewa ta kalli mamee *Kut yau na jiyo kamshin lahira* Me mamee zatayi ba dariya ba? Madaki kuwa koda yaga tashin su sai kawai ya koma gida don fara shirye shirye saboda hatta hotel din da zasu sauka madina titi kawai ya raba shi da masallaci daga dakin su idan an kira sallah ma suna ji. Haka garin makka, Ko motoci akwai wadanda zasuyi jigila dasu inda duk zasuje. Cikin kwana uku yasa aka fidda kayan gidan daman yayi order wasu daga *Italy* Sai da aka fente gidan kaf sannan ya mayar da kayan gaba daya tsarin gidan ya canza. Su kawu keta shige da fice da matayen su tare da sauran yan aiki. Aka kara ma gidan securities, Ga kayan da yayi order na lefe daga kasashe daban daban nata zuwa. A saudiyya kuwa, mamee ta zama yar gata, bata taba umara mai dadin wannan ba saboda ko abinci umaimah kamar ta bata a baki. Ga ibada tunda ta gane hanya kullum masallaci karfe ukun dare ta ke tafiya sai asubah sannan mamee ta isketa , haka da suka makka. Duk abinda mamee ta tambayeta me zata siya sai tace turare, ko a madina katuwar jaka tayo. Musamman da mamee ta fada mata cewar ba za a yi masu awo ba. Ta saki jiki duk abinda takeso ta siya. Har sai da ta kare tayi mata magana a wani babban shago dake *Shahara mansir* uwani wai duk shagon da muka je sai kin siyi turare? Anan fa duk Inda kikayi siyayya kina karawa gaba zaki ga mafiyin sa ko wanka zaki ringa yi da turarukan nan sun isheki hakanan jakuna biyu? Haba. Ta kaita wani shago na inner wears sai mameen ta dan fita ta bata wuri tare da ajiye mata makudan kudi nan ne ma ta yi ma kanta siyayya amma duk turarukan nan madaki take kwasar mawa tsaraba. Domin ta rike da turarukan sa wani ko ta mance sunan tana ganin kwalbar zata tuna. Yaya tazo daga Kaduna ta tarar da gida yanda ya koma hatta fitulu an canza su. Ta buga ma jamila waya hankali tashe kinga gida? Wallahi abu sukeyi daga ita sai danta babu shawara don ta daukemu sakarkaru. Haka sukayi mahada suka bude babin tsinewa mamee suna mata mugun alkaba'ai sannan sukayi alkawarin ko kwandalar su gudummuwa kuma bikin ba wani abinda za ayi dasu zasu zuba mata ido. Madaki kuwa bai tsaya gidan shi kadai ba hada gidan malam bawa a lokacin ne su goggo suka san wa umaimah zata aura. Gyara abinda ka gyara yayi masu ko wace ya canza mata kayan daki ga abincin hidima ga kudade azumin nan fa su basa jin sa ko kadan. Jakunkuna set shidda yayi mata ko wane set guda Biyar ne. Kamar lesussuka da shaddoji *Marley* ya bada aka dinko mata, atamfofin ne ya bayar *Ghana* shima wata manager sa ke fada mishi. Bani iya lissafa lefen umaimah kawai a kiyasta ga tunani. ( don kun san wurin akwai wulakanci da rai ). Ya bugo kati, ya fara rabawa iyaye kuma sunje kai kudi dukkan su suka dawo da son barka. Abokan sa ko wa yaji burin sa ya san wacece wannan? Musamman yanda sukaga madakin na rawar kafa kowa sai abin ya daure mishi kai. Tambayar daya ce *Wacece wannan lucky girl?* Kowa kagare yake yaga umaimah. Mamee kuwa ba ita kadai ba mutanen da suke hulda dasu a can babu Wanda baya sanya ma umaimah albarka yanda take kula da mamee wata mata har cewa tayi mamin ta bata ita danta ya aura tace ai itama surukarta ce. Babu Wanda baiyi mamaki ba wurin saboda duk daukar su mahaifiyata ce. Wannan ya kara sa mamee taji ta kaunaceta fiye da baya. Waya kuwa a rana suna iya wayar fin dubu ashirin ita da madaki saboda a can akwai tsadar kira kwarai da gaske ko shi ya kirata sai an debi kudin ta haka itama . sunfi yawan waya bayan azahar da kuma la'asar sauran lokutan baya samunta tana masallaci. Yayi yayi ta tura mishi hotuna takiya, shi kuma yana son amfani dasu ne a bubbugo abubuwa. A kasansu tayi kawa wata barabiya sunan ta *Fatimah* kullum umaimah na gunta bayan isha'i tana koya mata yanda suke yafa gyalen jallabiya a fuska yayi kyau. Ta koya mata kuwa kala kala. Ranar da zasu dawo baiyi barci ba. Da kanshi yaje daukosu airport, jirgin na tsayawa motocin na karawa. Yana ta dube dube, Bai gane umaimah ba tasha wani katon glass baki da wata matsiyaciyar jallabiya ta yane fuskar ta da gyalen tayi nadin larabawa, ya dan kawar da kai yana kara kallon kofa sai kawai mamee ta fito yaga umaimah ta mika hannu ta rikota ya zaro ido tare da hayewa matattakalar........ . *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘 [1/27, 7:43 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣3⃣0⃣ ..... Tana hango shi tayi saurin cire glasses din ta dan ja baya tare da dan bata fuska. Ya dalla mata harara malama ba taba ki zanyi ba kwantas, ta danyi murmushi ganin har ya karanto abinda take nufi ya ruko mamee tayi saurin janye hannunta ganin yana niyyar dan shafowa. Ta harareshi *Ni zakayima wayau?* Zaku fara? .... Zaku fara ko sababbu? Mamee ta fada Yarinyar nan mamee muguwar bagidajiya ce wallahi ji yanda ta yankwana ni, Da ta maka me? Ya kara hararar ta ba sai ta rugo ta dan rikeni ba ko ba arzikin *Hug*....... Tooo lallai kunnenka na kashi ne, to bazatayi hakan ba. Ya kyalkyace da dariya wasa nakeyi...... Bakinsa ya rufe ganin yan jaridu kamar an ingizo su. Ya daga masu hannu da sauri kada su ballo mishi ruwa, *Kada Wanda ya ce wani abu* bani da wannan lokacin suka wuce. mamee ta fara salati da sallallami. Ganin yanda gida ya koma, suna shiga falo ta yi turus!!, daman bai shigo ba ya dan tsaya waje da wasu baki. Aka fara shigowa da jakunkunan su ana wucewa dasu daki. Ya shigo da sauri mamee wai wadannan iyayen jakun kunan na menene kuka kwaso? Ta nuna umaimah gata nan bacin na mata magana kilan da ta rungumo makka ko madina wannan da kake gani. Ya tun tsure da dariya abu yazo ga ma iya. An dawo lafiya? Darling welcome....... Mamee ta wuce ciki tana kwakwazo, wai duk yaushe aka yi aikin?sati ukun da bama nan? Umaimah ta dan zauna ya zo gaban ta ya zukunna. Wallahi kin canza kinyi kyau umaimah anya zan zauna da ke Nigeria? Wannan fatar bata nan kasar ce ba..... Ta danyi murmushi , mun sameku lafiya? Ya mike ya zauna kusa da ita, ke ba lafiya lau ba na galabaita wallahi. Ta danyi dariya, a hakan? Ya harareta kawai. Ina tsarabata? Kai ciwon ciki ..... Ka daiyi hakuri ko ruwa in sha ko? Ya kyalkyace da dariya ni ne ciwon cikin? Gaskiya je ki kawon tsarabata. Ta ce hummm, Kinji? Wai baka bari na in huta? Aikin me kikayi? Wallahi kamar an mun tsinannen duka, Yayi yar dariya wane hutu gareki yanzu? Bani da shi? Ta bukata tana murmushi. Ya mike tsaye don idan ya saki bai tashi ba sai yayi halin, nidai jeki dauko mun ina jiranki sama. Zatayi magana kawai ya wuce yana fadin *Ina jiranki* Kai *Rigimar duniya* ta fada tare da mikewa tayi ciki. Ta iske mamee tsaye, itama tayi turus! Uwani kinga gyara? Ta washe baki, wallahi mamee gidan nan yayi kyau kamar ba shi ba. Kin dai gani, ai idan madaki yasa kansa abu baya shawara, kina tunanin idan ina nan zan bari yayi wannan almubazzarancin, shine ya koramu yayi bikin kansa. Umaimah tayi dariya kuma gyaran ya tsaru, Ta dan kalleta ya yi kyau ma sosai. Ya na ina? Gashi can ya hau sama wai lallai in kai mishi tsarabar sa. Sai ki hanzarta ai, neman rigima ce kawai mamin ta shige toilet. Jakun kuna 3 ne nashi biyu turaruka daya jallabiyoyi da agoguna. Ta kirawo sadisu ya taimaka mata da na turarukan ita kuma taja na jallabiyoyin. Yana zaune falo. Yanzu ya daina bari su hadu bedroom din sa, ya bita da kallo, yana ajiyewa ya juya ta dan karasa dana hannunta gabanshi gasu nan. Ya kalleta lefe kika hado man? Ta kyalkyace da dariya a'a ka manta *Aure* ya tashi da sauri ya janyo jakunkuna ya fara budawa. Yayi shiruuuuu , ya kalleta don Allah zauna umaimah. Sannan ya janyo wacce ta riko ya buda jallabiyoyin ma basu da yawa don basu wuce kwara goma ba agogunan ne suka dauki hankalinsa fiye da turarukan. Ya durkusa gabanta, umaimah: *This gift you gave me was more than perfect in each and every way. Thank you so much for it. I will always preserve and keep it with me forever.* thank you so much my love. Kun ya ta baibayeta ni dai tashi don Allah. Ya akayi kika San duniya nafi kaunar turare da agogo? Na sani mana, ta fada tana wasa da yatsun hannunta. Umaimah ka kira sunanta duk ya rikice, kina azumi? Gabanta ya fadi *Nashiga uku* ko ya gane banayi? Me zai hanani azumi? Ta harareshi, yayi murmushi in tambayeki zaki ban amsa? Um, idan ina da amsar zan baka, ta dan kalleshi kadan duk ya diririce, Ki taimaka man ki aureni umaimah wallahi bani iya hakurin rashin ki, a duk lokacin da kike kusa dani sai inji ina neman fita hayyacina, ranar da duk na wuni ban ganki ba kuwa zan kasa sarrafa kaina in nemi haukacewa....... Haba dai, Allah na amince da kai kasan haka kuma, Ki tausaya man, na miki alkawari wallahi zan barki ki karasa karatun ki believe me, Shi kenan, ta ce a takaice. Ya mike zo muje ki gani..... Ya fara zagayawa da ita tsarin duk ya canza banda dakin sa ya kara gyara wani an zuba sabbin kayan daki masu launin *White and pink* ta dan saci kallon sa taga ya zuba mata ido...... Ta dan sunkuyar da kai. Ko bai miki kyau ba? Ya yi mana!, suka zagaya ta baya dakuna biyu ne na yara daya komai da ke cikin dakin sky blue and white ne, Daya kuma komai na dakin dark and light pupple. Ga dakin yaran mu maza daban....... Ta fice kawai ya biyota kin fito ko bai miki ba a canza tsarin? Ta kalleshi da kyau *Yau me ke damunka ?* Kaunar ki, umaimah sonki me Neman zautani . Ka barni na je na huta na gaji........... Ya langabe kai anya kinyi missing dina umaimah? Tayi murmushi nayi mana........ Maganar mamee yajiyo tana kwala mishi kira itama ta hawk saman. Ta gansu tsaitsaye, kai kuwa akwai fitinannen yaro bazaka barta ta huta ba? Zaiyi magana idanunta suka kai ga jakunkunan tsarabar umaimah.Ta rike baki *Au daman duk kai ta jibgowa wadannan turarukan?* Sai kawai umaimar tayi kasa da gudu. Ta bita da kallo kya gudu ja'ira. Uwani taki ci taki tsinana ma kanta uwar komai kullum ta fita sai ta dawo da turaruka ko agogo. Ya yi murmushi miji ake ma tsaraba mamee, ta dalla mishi harara kai dai wallahi baka San annabi ya faku ba. Ya kyalkyace da dariya, suka fara zagayawa, mamee kamar ta goya shi. Suka dawo falon sa, naga akwatuna dakina set biyu. Ya ce au zo muje kiga lefe. Wancen naki ne...... Nawa ne me? Kana hauka nima lefen zakayi mun? Zata fara fada ya rungumota haba mamee love haka zaki ci bikin ba dinkuna? Ta harareshi kana dai son kara janyo mun zagi gurin su yaya ko? Kin San kuwa tazo..... Ya fada mata wulakancin da ta zazzaga. Tayi murmushi kawai ta ce *Uhumm* Kai Allah ya saka ma da alkhairi *madaki* Allah ya baku zuri'a dayyiba. Wallahi duk abinda kayi ma uwani ta cancanci fiye da haka ta bashi labarin kyautatawar da tayi mata saudiyya tana kara fada mishi kyawawan dabi'un ta. Addu'a takeyi yana ta faman *Amin mamee* Ta kalleshi don Allah na sanka da saurin daukar zafi kamar wutar murhu madaki ka sanya ma ranka hakuri ga zaman aurenku. Har yanzu uwani yarinya ce kada ka biye mata kuyi ta yarinta don Allah ka bada mamaki. Zanyi mamee trust me. Kamata yayi tunda saura sati daya gobe ta shirya ta koma gida saboda suma a basu daman shirye shirye kuma can su sanar da ita. Nidai mamee da kin kyaleta nan sai ana gobe daurin aure? Ta mike saboda kana mahaukaci ko? Ya marairaice don Allah kitaimaka man mamee , ta wuce ma tabarshi wurin tana fadin abin naka ya wuce mizani. Ta iske daki tana da yan gyare gyare , to agogo aikin ne? Ta danyi dariya kai mamee. Ta zauna bakin gado. Na wuto su Mansurah nata tsalle kin cika su da tsaraba. Allah ya biya. Amin mamee, ta fada tana mamakin Yanda suke mata godiya kuma fa duk abinnan daga garesu ya fito. Kaii samun mutane irin su mamee yanzu wallahi sai anyi da gaske, shi madakin duk ya rikice wai saboda tsaraba, shi fa ya biya mana, kaii wadannan mutane hoo. Uwani na ce zuwa gobe sai ki tafi gida ki kai masu tasu tsarabar kidan kwana biyu sai ki dawo ko kuwa? Ta fadada fara'ar ta eh wallahi mamee. Ta kalleta uwani kenan? Duk muzgunawar da ake miki gidan Ku Har yau baki taba gajiya dasu ba baki taba gudun su ba. Kai halinki na da wahalar samu. Ta danyi dariya kai mamee. Kusan yanzu idan suna magana kusan amsarta kenan tace *Kai mamee* Saboda gajiya da wuri ta kwanta shi kuwa har kusan biyu saura yana tare da mamee suna ta tsara yanda za ayi. Da safe ta shirya wajen karfe goma mamee ta kara mata tsaraba sosai. Kamar mamee ta sani ta ce kinga uwani ki sadada *Haruna* ya kaiki kawai don madaki na fitowa wallahi baki tafiya yanzu. Ta mike tana dariya. Har sai da taga sun tafi sannan ta shigo tana tausayin umaimar saboda zata dawo gidan a matsayin *Mata* Tana shiga yana kokarin saukowa ya kalleta cikin zolaya ina aka fito hajiya mamee? Ya dora hannu bisa kai *Qalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un* amma mamee kin gama dani yau. Ya zauna da karfi idanun sa sun kada sunyi jawur, yarinyar tayi sati uku bata nan jiya kiri kiri kika ce na kyaleta ta huta kuma yau tunda safe ki harba ta gida? Au harbata ma nayi? Yayi shiru, ya fiddo waya ya kira Haruna, amma yace mishi har ya ajiyeta ya juyo, ya dafe kai, duk sai jikin mamin yayi sanyi kuma don ransa ya baci sosai. Kai da sati mai zuwa za a maido maka ita a baka har abada? Ya daiyi shiru, Yarinyar nan ta tsargu wallahi bana son ta gane nafi son iyayenta su fada mata..... Na sani mamee amma da sai ki tausaya mun ko kirana kiyi muyi bankwana. Yanzu idan aka sanar da ita ta birkice fa? Ko zan shawo kanta fa sai idan ta zo gidan nan kin sani. In shaa Allah hakan bazata faru ba ka kwantar da hankalinka. Ya mike ya fice yana kumbure kumbure. Abu yazo ga ma'iya ni *Rabi* ta fada tana rike baki. Umaimah kuwa Sam bata gane gidan su ba, hada *Gate* sai da ta kalla sosai ta runtse ido ta bude tabbas ba gizo idanun ke mata ba, Murna tsalle, gida ya rikice yan unguwa kafin kace me, sun cika gida ana kallon umaimah. Ita dai sai dariya takeyi. Abinda yake daure mata kai kowa ya shigo amarya amarya. Sai da komai ya lafa ta fiddo ma kowa tsaraba sannan aka kukkulla ta makota. Malam bawa ya shigo yana ta washe baki ya shige dakin sa ya ce a kira mishi umaimar. Ta dauki ledojin tsarabar sa ta tafi. Suka gaisa ta dan bashi labari da wasu abubuwan da suka faru na kyautatawar. Ya ce Alhamdulillah, Ai Alhajin yazo munje har kauye. Tayi murmushi ai haka naji, ta fada mishi yanda akayi lokacin. Ya danyi dariya ai ya ce yana tsoron kada ki tayar da hankalinki. Kin tabbatar kina son sa umaimah kada kisa kwadayi da son abin duniya ki dubi maraicin ki da mutuncin ki. Kina son sa? Ta danyi murmushi. Ya kara cewa kada kiji kunya ko nauyi idan bai miki ba kiyi magana. Ta kara murmushi. Ya fadada fara'ar sa masha Allah. To abinda nake so da ke don girman Allah ki sanya ma ranki hakuri kada ki tayar da hankalinki, yayi alkawarin zai barki kiyi karatun da kike so...... Gabanta ya fadi . Wai ya akayi ,ne? Ta tambayi zuciyarta. Kamar ya karanto tambayar sai ya ce, Ya turo iyayen sa, munje kauye an yi magana kinga dai dawainiyar da yake tayi kinga gida kinga dakunan iyayenki jibi nawa, don Allah kada ki bamu kunya. Ranar sallah za a daura auren ki dashi.......ta dago ido cikin tsoro baba ranar sallah kuma? Sai ta fashe da kuka. Ya bata fuska to uwaki za a jira? Au na baki hakuri shine zaki tayar da hankalin naki? Ni dai baba a bari sai nan gaba duka nawa nake....... Yaro ba mutum ba . amma umaimah kin tabbata sakarai. Yayi kasa da murya ni zaki kunyata ki tona ma asiri saboda ko habaici ya isheni gidan nan ga shi kinzo kuma zaki kara janyo mun wata maganar. Dama suna fadin asiri akayi daman tallar ki muka kai sun manta lokacin da kika sami aikin ma bakin su na ji. Ta ci gaba da kuka kawai duk hankalinta ya tashi, sallamar hajiya ta jiyo har zata mike ya ce zauna ta shigo nan. Hakan kuwa akayi suka taru suna kwatanta mata tare da kwantar mata da hankali saboda ita kanta hajiyar madakin yaje har gida ya sameta. Ta wuni kwance daki tana kuka saboda shi kanshi dakin an gyara masu shi sosai don yasan zata dan zauna na kwana biyu. Karfe takwas yazo, har ciki ya shigo ta dan tashi zaune kanta kasa, fuskarta tayi jawur tasha kuka har ta bani. Hankalin sa ya tashi ya karasa kusa da ita ya zauna *Umaimah kuka kikayi haka?* ..... Kamar ya zugata wasu hawayen suka zubo *Sharrrrrrrrr*............... *Barkan mu da rana*😃 *Maman Al'Amyn, Amynatu da Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘😘 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣3⃣1⃣ *Dedicated to all auren fari fans group* and you *( DIJA)*😘 ....Hankalin sa ya tashi , umaimah ba ki son auren nan a fasa? Ta yi saurin daga kai alamar eh, Saboda baki sona baki kaunata?, Gabanta ya fadi. Kinji? Tayi shiru, ki ban amsa menene dalilin da baki son auren? Ta goge hawayen *Haka nan* A'a baiyiwuwa ai duk mai hankali baya yin abu babu dalili. Tayi shiru, ya kara kallonta *Baki so na ko?* Ta girgiza kai Alamar ba haka bane, To menene for God sake? Kwalla suka kara zubo mata. Ya runtse ido, umaimah don Allah ki rufa man asiri kada ki raba man hankali biyu. Ga pressure family, gata mutanen gari ga ki ke kuma da zan raba in ji sanyi kin fara kuka . Ki kwantar da hankalin ki wallahi ina sonki yanda baki tunani umaimah kuma bazan taba cin amanar ki ban ko in wulakantaki. Idan kika ci gaba da nuna damuwar nan zan hakura da auren nan kawai har sai kin shirya, amma ki sani duk halin da na fada kada kiyi kuka da kowa sai kanki kin amince? Tayi shiru, Me yasa dazun kuka hada baki da mamee kika taho ban sani ba? Na lura Sam ke baki wani doki na ko? Inyi ta rawar jiki akanki kina *Wulakanci da rai* .......lokacin ne tayi murmushi. Kin tuna *Kalmar?* Ta daga kai. To bani ma'anar ta please. Ta kara murmushi tana goge yan guntun hawaye. Kinji? Kaima kasan ma'anar. Yayi yar dariya Allah ban sani ba. Tayi yar dariya zan fada ma . yaushe? Tayi shiru kawai. Umaimah kina fama da mulki. Wallahi Jan ajin ki ya fara man yawa, kin gama gano cewar Ina matukar kaunar ki shi yasa. Zuwa na yi in tambayeki dame dame kuke bukata keda kawayen ki? Hummm, ta ce, Ai kinji, ke kam ban San lokacin da zaki waye ba, da wata wayayyar ce cewa zatayi , my love ka bamu miliyan daya, ka siyo mana raguna da katon sa sannan ka kawo mana lemuka da ruwa...... Ta kyalkyace da dariya ganin yanda ya dage yana maganar mata. Shima yayi dariyar burin sa ya cika ya sanyata dariya. Ta ce haka mata ke magana? To yaya kukeyi? Ta sunkuyar da kai saboda yanayin kallon da yayi mata. Ni ai bani da kawaye....... Gayyar da khausar tayi fa? Ta amshi kati yafi hamsin wurina. Kawayenta zata gayyata, ke ba naki bane? Um, ta ce ataikaice. Ya mika mata ledar ga naki kema ki gayyato.....Allah banda kawaye. Ya kyalkyace da dariya yauni tawa ta sameni *Card* din ma kunyar su kikeji? Tayi murmushi ganin ya karto ta. Aiki ya dubeni . Ki fada man kudin zan Baku ko kuwa list zakiyi abinda kuke so? Kasan Allah bani son komai. Ko abincin gidan nan da ka kawo ma ina za a kaishi?....yarinyar nan kin fiye gardama. Ya fiddo daurin yan dubu dubu guda uku ya ajiye, sun isa ko a karo? Ta kalleshi wai kai kudi kaikayi sukeyi maka da baka iya hakuri idan ance ba'aso? Yanayin yanda tayi maganar yasa shi kyalkyacewa da dariya. Ai ni duk duniya ke kadai nakeyi ma kyauta kice ba ki so. Ta harareshi ka dauke kudin nan Allah. Haba umaimah ke in ba ke ba, wace mata ce mijinta zai mata kyauta ta ce ya mayar bata so? Au na ma zama matar? Yayi murmushi cewa zakiyi *Thank you my love*...... Ta rafka mishi filo tashi ka tafi na sallameka...... Ya kara yin dariya A'a'a hada *playing love?* Sai kawai ta mike ganin kunya zata kassarata, ni bari in bar maka da kin......ya tare kofa yanzu ina taba ki zaki birkice mun gashi ke kuma zaki karya doka ta, wallahi idan baki sani ba ki sani yau idan kuma kin sani kin manta zan tuna miki. A tarayya ta dake abinda ke saurin hasalani ya bata mun rai shine idan muna magana ki nemi guduwa ki barni a wurin. Jikin ta yayi sanyi ta dawo ta zauna. Ya zauna kasan kafafunta ta zaro ido nidai tashi ka zauna don Allah. Yayi murmushi, umaimah kin kara kyau wallahi umaran nan ta karbeki ana gama biki zan daukeki mu gudu ....... Ya zaro ido nan da nan suka ciko da hawaye, ya tashi da sauri ya zauna kusa da ita, Bari in baki wani labari, lokacin da muke fada kullum na gama matsarki da kin gudu sai inji zuciyata zata fashe don radadi ko kuma naga kin fara kuka, sai inji wani zafi cikin rai. Sai daga baya na gane ashe duk *So* ne. Ya mike bari na tafi sha daya hada rabi, ai mamee ta kwafsa mun wallahi. Ta barmun ke can ta assasa sai kin dawo gida gashi ba abinda kikeyi gidan sai kwanciya kina wani kukan maraicin rashin ganina........ Ta kara dankara mishi harara, Allah ya baki hakuri yi zamanki na yafe rakiyar. Ka ji,?? Ta fada yana shirin fita, ya dawo da sauri ya akayi inyi zamana ko da asubah na tafi....... Ta kara hararar sa, yayi murmushi to menene? Kudin nan wallahi sunyi yawa ka bamu dubu ashirin sun ishemu.........umaimah, wai baki son kyauta daga hannuna ne ko kuwa ni din ke ba ki so? Allah ina so, Ta fada kanta kasa tana wasa da yan yatsu, kyautar taka tana wuce misali, gaskiya sunyi yawa, Yayi shiru yana kallon ta, yarinya karama amma ta saisaita murya tana zaro magana, taci gaba da cewa , shagalin biki kawai ka bamu har dubu dari uku? Yanzu haka a garin nan akwai wadanda suna can sun wuni basuci ba zasu kwana da yunwa, nidai don Allah a kaina ka daina kashe kudi irin haka ko hidimar da kayi gidan nan yayi yawa. Yayi murmushi, to naji ki dauki dubu ashirin din ki ajiye mun sauran zan karba kinji? Ta daga kai, ya kara matsowa *What next*? Tayi murmushi shi kenan, Ya kura mata ido *Ya sunana?* Ta kalleshi da sauri, ya daga kai *Yes what's my name?* Ta danyi dariya. Allah sai kin fadi sunana yau. Kaiji ai ina fada kamar wani dana na fari? Yayi murmushi to ce inji ko kuma wallahi danki na farko in sa mishi umar kuma in hana a boye sunan. Ta kara yin dariya duk kunya ta baibayeta. Ke nake jira ko kuma wallahi yau in kwana dakin nan kin San karamin aikina .......... *Madaki* ta fada da sauri Ya fadada fara'ar sa toooooo kema *Madaki* kike cewa? Lallai. Ya tallabo fuskar ta ya bata kiss *sweet dream* ya fice da sauri, gudu gudu..... Ta zaro ido *innalillahi*...... Tare da rike kunci. Bata kara sanya shi ido ba sai dai waya, ta karaci fushin ta har ta fara begen ganin nasa lokacin sauran kwana uku sallah da kuma daurin auren ta. Gida ya fara cika da baki, dangin su baba da ga kauye da kuma dangin su goggo. Umaimah da tace bata gayya sai ga kati ya kare kaf! Gida dankame da mutane ana zaman jiran kawo lefe, umaimah dai ta hada tarkacenta tayi gidan hajiya, khausar tayo mata waya gobe zasu taho da kawaye duka, ita da farida da wasu kawayen faridar ne suka fara yan shirye shirye, ga azumi ga hidimar biki kai Madaki bala'i ne, Hajiya ta shiga gyara amarya ta dafa mata kaza da auren tantabara sannan ta ringa bata wasu ruwa tana sha, umaimah da ta motsa sai kuka *Gani takeyi ta gama shiga uku* Mata cike da gida har la'asar amma lefe shiru dole kowa ta koma gidanta don hada buda baki. Gashin umaimah har bisa baya yake kadan ne bai karasa hawa kugu ba, ba a gamewa saboda kullum cikin kalaba take sai ta nade shi ta boye, Tana zaune dakin hajiya suna buda ba ki ya kirata yazo gida bata nan, ta mike da sauri ta fito, Ta dai ga motoci amma bata ganshi ciki ba, tana shiga sukayi kicibis a zaure, taja baya, Ya kalleta ke ban son yawo ina kika tafi? Gidan hajiya ai acan zamu kwana saboda gidan ba ki ne, ta jiyo cikin gida an rangada guda, to ki shiga ciki lefen ki ne na kawo. ... Ta kalleshi Kaine ka kawo lefen? In ba ni ba wazai kawo? Ta kama tafa hannu na shiga uku nikam kana janyo mun magana, sai kawai ya kasa ce mata komai don bai san lokacin da zai ma umaimah dai dai ba. Ta juya, ina zaki? Gidan hajiya ni bani iya shiga gidannan gaskiya. Ya kyalkyace da dariya mtseww yarinyar nan gaskiya bata waye ba , eh naji ta wuce, ya bita baba ya kirani dazun sun bani makudan kudi na kayan dakin ki wai bazasu taba mika ki salin alin ba tunda na saka komai to inyi amfani da kudin. Ta ce *Uhumm* Sun yanka mun sadaki dubu talatin amma na ce zan kara........ Ta juyo da sauri wallahi ka kara zan maido ma. Ai karancin sadakin mace albarkar aurenta, kai *Madaki* kudi na maka kaikayi. Ya kyalkyace da dariya to anji ustaziya. Abokaina zasu zo gobe kada ki saki ki fito, dalili? Ya sha mur na dai fada miki saboda wurin yan mata zasu zo. Naji ta fada. Wai ke ba ki Dan kunshin amaren? Ta kyalkyace da dariya zanyi mana ai kwana zanyi dashi irin na tsofaffi zanyi duka hannu duka kafa. Ya zaro ido ki rufaman asiri umaimah na tuba. Me zatayi ba dariya ba. Kai ina ruwanka to. Ya langabe kai kada ki yi man haka bana son sa. Ta Dan sha mur kamar gaske, shi zanyi, ko ka manta laifin da kayi man? Ya hada hannuwa biyu Allah ya baki hakuri na tuba. Kawai kayi hakuri lallan ma na cen na jika shi. Jikin sa duk yayi sanyi ya CE shi kenan ai. Ni zan tafi, okay sai da safe ta wuce ciki. Yarinyar nan ta gama dani , ya rasa inda zai sa Kansa. Bai taba ganin ta yi kunshi ba, gata da kyan hannu da kafa ga ta fara kullum yana kiyasta ya zata kara kyau idan an mata kunshin zane.? Mtseww ya buga tsaki ya wuce. Washe gari tunda asubah mai kunshin ta tazo , kwararriya ce don duk wani mai kudi da ya amsa sunanta burinsa tayi wa yarsa kunshi ga biki. Ta tsantasara ma umaimah kunshi abin da ka kunshi. Na kafar dawisu ta zana kan ya fara daga karamin yatsan kafa bazar ta hau kan kafafun har kusan guiywa.Sai kusan azahar aka gama sannan mai kitsonta ta tazo ta yanyara mata kananan kalabarta. Khausar Tun karfe tara suka zo. Mai kunshin yan mata daban tana ta masu. *Madaki* yayi wa faty mamza waya don zatayi ma umaimah *Make up* ranar daurin aure saboda a ranar za ayi dinner bayan an kai amarya. Bikin umaimah ya bada kala ga murnar sallah ga shagalin biki. Abokan sa har daga kasashen turawa shi kansa hankalin sa ya fara tashi ganin mutanen da ya tara. Duk hotel hotel dinsa da guest house ya zuba ba ki amma har wasu na hada dakuna mutane hudu biyar. Malam bawa ya bada mamaki domin yanda Madaki yayi mishi sai yayi amfani da kudin da ya bashi ya kara yayi hidima yaba hajiya su aka yi ma umaimah gara, ya kuma dibi wasu cikin Wanda madakin ya kawo. Ko mi buhu goma aka kai mishi banda manya manyan bokitan cin cin da dubulan. Manshanu kuwa daga kauye haka akayi ta lodo wa shi yasa ta sami manshanu fiye da tsammani. Sannan aka ware mishi dubu dari biyu za a mishi Karin ango. A kano suke zaune amma samm basubi al'adar su ba yabi yanda sukeyi can kauye. Hajiya kuwa sai ta sami katon Kofi ta cika da fura ta tsare umaimah tana kuka amma sai ta shanye ta banda abinci. Umaimah taga da gaske akeyi, ta fara kukan wiwi ana gobe daurin aure. Tun da ya kirata da rana yaji bai kara samun natsuwa ba sai da yazo da daddare. Kafarta da safa, hannunta cikin hijab, sama sama ya dan bata baki ya tafi saboda wayoyin da aketa doka mishi. Mamee kuwa, mutanen ma da bata tunani su ta gani. Gudummuwa kuwa tama rasa in da zata kudi. Saboda wannan shine bikin ta na farko tun haihuwar Madaki bata kara tara taro ba sai yau. Su yaya kuwa sun ja gefe sunyi zaune banda gulma da hassada babu abinda sukeyi. Ga hidima sunki shiga ciki, sai dai hakan da sukayi bai rage komai ba sai ma kara ma bikin armashi saboda mutanen arziki ne suka tsaya tare da fidda mamee kunya. Sannan aka sami wasu daga cikin aminnnan suka ringa yada masu magana nan da nan sai duk kunya da rashin gaskiya ya kamasu, ko sisi babu Wanda ya ba mamee cikin su amma kullum suka zo gidan zasu taho da ledoji a jaka su kwashi abinci kala kala, ( kai ya Allah ka raba mu da mutuwar zuciya, da karanta, hassada , jin zafi da bakin ciki ). Amin. Gidan sai ya fara gagarar su ganin ko sunzo da zuwan nasu da babu duk daya mutanen arziki ke fidda mamee kunyar *AUREN FARI* Na danta kwaya daya tilo. Karfe goma dai dai aka daura auren *umar madaki da umaimah hamza* a babban masallacin idi. Yan jaridu, gidajen rediyo da talabijin sai binsa sukeyi amma banda dariya babu abinda yakeyi ya kasa cewa komai. Umaimah kuwa da ance fito ga yan jarida sai tayi bisa gadon hajiya ta fashe da kuka . Da kyar suka kwaci kansa shida abokan sa. Ya kallesu, muje daukar amarya ko?....... Ka rufar masa ana dariya don ubanka wa zai baka ita yanzu suna tsakiyar shagli? Ya buga tsaki wallahi sato ta zanyi zaku rufo wata Ku kawo anjima. Duk suka bushe da dariya ana ci gaba da yi mishi tsiya. Duk tunanin su wasa yakeyi sai kawai ya bisu da dariya. Biki yayi biki su umaimah na daki sai kuka akeyi kawaye na waje ana rawar asharalle, Kokari yakeyi ya zille amma mutane sun hana, Da kyar ya samu ya kutto. Nan ma kofar gidan su umaimar yaga mutane da maroka cike, ya tabbatar idan ya fita ya sunan sa sorry, cikin bakar jif dinsa yazo daga shi sai driver yasan ko ya kirata bata dauka ya kira khausar ta fito da sauri. Ya daka mata tsawa malama shigo mota kada ki hada mun *Go slow* tayi saurin shiga. Jeki lallabo mun umaimah ki kawo mun ita don Allah. Ta ce toh. Tayi tsaye gabanta ta rasa wace dabara zata mata, ta zauna kusa da ita, Kizo inji yaya Madaki. Ta harareta cikin kuka, Ina ga fa zuwa yayi ya tambayeki yaushe za a dauki amarya ya ce ya kira wayanki a kashe. Ki tashi kin san halin shi in har baki je ba tabbas yanzu zasu kawo mota amma idan kika je Kice mishi sai zuwa dare ko kuwa? Uwar wa kike fada mata? Hajiya ta shigo, Ta waiga da sauri mama yaya ke kiranta waje, Au to tashi kije umaimah kinji. Ta mike suka wuce. Khausar tayi saurin bude mota ta turata, ita kuma ta shiga daga gaba yaya gata nan. Ya kalli driver kai muje................... *Barkan mu da juma'a* *Maman Al'amyn , Amynatu da Abdallah*😘😘😘😘😘😘 [1/27, 7:43 AM] ‪+234 806 091 7227‬: 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣3⃣2⃣ ..... Ta firgita ta daka ma drivern tsawa *Wallahi ka tayar da motar nan zan shako ka ta baya muyi hatsari.....* ya rikota ke umaimah...... Ta fizge au an daura auran ma bazaka shafan lafiya ba? Wai meke damunka? Kwallah suka shatato mata. Gaban khausar ya buga da karfi yaya madaki umaimah ke ma tsawa? *Kut*....... Umaimah wallahi wallahi idan baka fidda ni motar nan zan bala'in kunya ta ka yau........ Ya bude kofa da sauri *Allah ya baki hakuri*........ Ta fito da gudu tayi cikin gida. Khausar jikin ta yayi mugun sanyi ta bude mota zata fita ya kirata a hankalii, khausar, da sauri ta ce na'am, Ki kulan mu da ita please , taci abinci? Saura kadan tayi dariya ta ce au wai yaya abincin zaka je ka bata yanzu?...... Ya dalla mata wani mugun kallo ke tambayar ki nayi don ubanki. Tayi sukuy sukuy, eh mama na bata tana ci ko bata so. Okay jeki kawai. Ya bita da harara kamar ita ta kashe zomon. Ta murguda baki kaiji yaya zai huce a akaina. Ta kara jinjinawa. *Kut* lallai umaimah *Tabbb*.... Haka ta ringa yi har ta shiga ciki. Yana hawa sama abokai suka yo mishi chaaaaa ya sha mur ya wuce dakin sa. Nan ma cike da mutane, ya ingije *Ibrahim bababa* ya kwanta ruf da ciki. Duk aka kwashe da dariya kuzo *Madaki zai fara kuka*.........nan aka yayyabeshi ana mishi tsiya. Khausar ta shigo ke umaimah haka kike wahalar da yayan namu? Ina ma laifin....... Khausar fita don Allah ta daga mata hannu. *Mamza* tayi tayi umaimah ta tsaya ayi mata kwalliya tace bata so a bari sai anjima idan za aje dinner. Karfe uku aka zo a ka tafi da ita gida anan aka mata fada tun tana kuka ana ji har ya kasance sai dai hawayen kawai ke fita. Karfe hudu aka dauki amarya, akayi akayi *madaki* yazo su bar gidan ya ce wallahi ba in da zai tafi. Haka aka kawo umaimah saman cike da abokansa aka wuce da ita daki, sai leken ta akeyi kowa so yakeyi yaga fuskar matar *Madaki* *Bababa* ya kai mishi duka to don ubanka gata nan mun kawo. Ya balla mishi harara au bata ce *Bata zuwa ba?* ya maida kansa bisa filo *Duk wayon amarya sai ansha man ta* aka dau ihuuu...... Duk saman benen ya amsa. Hankalin umaimah ya kara tashi ta fashe da kuka, Da kyar aka lallasheta bayan magariba aka mata kwalliya shima sai da khausar ta kira mamee ta waya ta mata magana. Takwas dai dai aka fito za aje *Dinner* duk ya rikice kagare yake a fiddo mishi ita. Wani matsiyacin farin boyel ne fari jikin sa kai *Madaki* yayi kyau samira na gefe yake kawai takeyi tana bala'in son *shi* amma inaaa ya mata nisa yau. Yanda yake ta rawar kafa yasa ta kara saduda. Yana zaune cikin mota shida Ibrahim sai faman tsoki yakeyi shi kuma banda dariya babu abinda yakeyi mishi. Ya hango an riko mata riga yan jarida anata binsu da camera ya bude mota.......ya riko hannunsa please *Basar*....... Ya fizge *ubanka ne in basar* kawai ya fice yana zuwa kawai ya dauketa yayi sama da ita...... Yan jarida har gudu sukeyi kofar gidan ya rikice da ihu. Ya shigar da ita mota sannan ya amshi sauran rigar da suke riko ya sanya ya kalli kowa yana yar dariya *Kowa ya shiga mota*......... *Yallabai yallabai*....kawai ya shiga ya ja kofa yana fadin ban taba ganin banzaye irin yan jarida ba yanzu ne lokacin bayani? Gabana kake zagin yan jarida madaki? Ya dafe kai *na tuba* ( mahaifin Ibrahim) tsoron Dan jarida ne. Ta na ta kame hannu idanun sa ya kai visa kunshi ya zaro ido ya fizgon hannuwan *Wawwww* ...... *kaiiiii*...... Ya daga rigar kadan yaga na kafan ta duma mishi kulli ya fasa kara......kai wallahi ban son iskanci zan fita ka nemo driver.......... *Duka na tayi na rantse da Allah* ya fada yana dariya. Ya juya yaci gaba da Yuki yana fadin *Tamun dai dai* Kyan ka dukan ai. Ya kalleta *Wallahi na yi sa'a wurin nan tsantsari*...... Bababa ya tuntsure da dariya. Ya buga mishi harara Allah ya isa ka kara jin firar mu.......... Ta bika, waya hana ka dauko kurman driver.? Ya tallabo fuskarta yana murmushi, yau dai a barni in taba inda nake so....... Ta tureshi da karfi zata ja baya ya fizgota *Wasa na keyi jira* sannan ya Dan saketa,yana dariya. Ka dai firgitataka gani idan........ Allah ba kai zaka maido mu ba don na lura nayi zaben tumin dare don ubanka. Ya kalleta ki ce mun wani abu mana, Ke ko masifa ce yi mun please. Dai dai mota ta tsaya, ya buga tsoki ni dama suyi partyn abarmu anan ko umaimah? Lokacin ne ta harareshi, Yayi Har dariya keni ba harara ba *Say something* Abokan sukayi wajen motar tare da bude su kowa so yakeyi yaga fuskar umaimah, yayi saurin rungumeta ta soke fuskarta kirjinsa, Duk suka hayayyako mishi *Wallahi kai mugun dan iska ne madaki* Kyaleshi ai duk janbakinta zai kare a rigar sa yayi saurin dago fuskar ta hakan kuwa akayi ya tuntsure da dariya ya kalli bababa ka tuna bikin *sadiq* da aka mun barin miya? Duk suka kwashe da dariya yace Allah ya kawota yau ma don ubanka.......ya juya fuskarta *ita ce* .... Duk suka zaro ido aka dau ihu...... Ya kalleta *yau ma kin bata na AUREN ki* Ta sunkuyar da kai *ita kawai tasan yanda takeji* ga kukan ma yaki zuwa. Abokanta suka iso aka fito za a shiga. Sound ya fara tashi na *Because you love me* Ya kalli wata ya ce malama je ciki kice a sa mana gwanja........ Rawa zakayi yau ne? Ya kalli umaimah *To gani dai idan ta amince* Aka kure sautin best wakar sa *Indosa* aka fara taku hannunsa gam cikin na umaimah. Gunguni kawai abokan sa keyi bayan sa. *Tsakani da Allah madaki ya dauko mace* tabbb *Ziza*.....:Bashir ya ce *Kai ai wallahi tana da kyau ko hasadun izaa hasada ya ga waccen yarinyar sai ya ce tayi* Duk aka kyalkyace da dariya. Yan mata an sha ankon leshi blue da head silver suna ta tattaka rawa, ya dan sunkuyo *ki Dan taka please*...... Ta harareshi dai dai lokacin aka basu flasher.... *Dinner* madaki da umaimah ba a taba irinta ba a kano. Da aka yanka *Cake* ya debo ya bata ta mika hannu aka fara dariya sai zumburo baki takeyi tana fushi ya tabe baki ya sanya mata aka dau *sowa*, wurin bashi nan ma sai da akayi daru ya kawo hannun ya kai bakin sa da kansa, ta wurga mishi harara. Abikan sa sukayi ta kyalkyatar dariya *kai madaki yau na shan harara* shamsu ya fada, bashir ya ce ashe duk kun lura. Shagali har kusan biyu sannan aka tashi maganar ciye ciye da liki ba sai an fada ba. Umaimah dai da ance amarya da ango su fito sai tayi tsaye, yayi yayi suyi rawa takiya shi ma sai ya basar. A gida kuwa , su yaya bayan an tafi party suka hau sama ganin dakuna ana tabe baki, Ta kalli jamila duk shi yayi komai 'yar kawai aka bashi. *Hummm* ai ta raina mu kina ganin damu da banza duk daya sai su *maryam hamza* su ne gaba gaba dasu ake komai. Haka suka yi ta gulma da korafi ko *dinner* sai da kowa ya tafi har an fara suka isa, ko wace ta ledojin ta a jaka na kullar abinda duk aka ci. A mota suna zaune anata tafiya da mutane, tayi shiruuu kanta sunkuye gani kawai takeyi tamkar a mafarki.Ya mata rada a kunne *Ko sai na siyi bakin za amun magana?* Kirjinta sai bugawa yakeyi. Dabara ta fado mishi, ya dan kawar da fuska ina so in fada miki jiya da sai dai kiji mamee a asibiti...... Ta juyo da sauri *Me ya sameta?* ya sha mur hayaniyar mutane ce kawai. Muryar ta duk tayi sanyi ta canza ta ce *Amma da sauki yanzu ko?* To ban dai sani ba saboda yau din sau daya ma na ganta...... Ta ce hummm Ya kusa yin dariya. Me na yi kuma? Ko ban kyauta ba dana fada miki? Amma da ka kara komawa ka dubota ...... Ya kyalkyace da dariya. Nan da nan ta gano shi. Ta yi kasa da kai tana murmushi. Ya kalleta duk kin rame kin sa ma kanki damuwa zaki zo gidan *Madaki* Ko kuwa ramar ta an dade ba a kawo ki bane?......... Ya mu ta fi ko? Bababa ya shigo yana kokarin tayar da mota. Ya harareshi yi ka sauke mu na gaji da kai *Disturber*. Suna isa, wani abokin sa ya zo suna magana ta sulale ta gudu............. Bai kara ganin ta ba sai washe gari da yamma an fiddo ta sashen mamee tana gaisawa da mutane ya hangota lullube, har ya juya zai tafi bashir ya fizgeshi sukayi waje............😃 Ba nan na so tsayawa ba na gaji aradu😃 *Maman Abdallah*😘😘😘😘 juma@ mabruk 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣3⃣3⃣ *NURY*😘😘😘😘 *only u!* ........ Duk ka tsorata 'yar mutane don ubanka. Ya kyalkyace da dariya, yarinyar can wallahi bazaku gane ba gwala ni takeyi kamar kwallon kafa. Karya kakeyi kai da kace babu macen da zaka bi, baka ba mace hakuri, baka......Alhaji anji. Suka kwashe da dariya. *waya fada maka barno gabas take* Umaimah nata, kuka mamee sai lallashi takeyi, jamila ta turo baki *Yaya dubi mutanen ki*.... Ta tabe baki sa ji dashi kilibabbu. Kinga sarkar da ta sanya jiya? Murja ta fada tana tabe baki. Jamila ta ce ki duba wuyanta kiga ta yau tafi ta jiya sau hudu. Aikin banza waccen figaggar yarinyar cinye su zatayi har babu. Ai kunji tayi shiru har yau taki cewa da mu komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki. Yaya ta fada tana mazurai. Ku jira Ku gani waccen maryam din data fifita fiye da mu zanci ma uwa munafukan banza..... Yo yaya bakiga kudi ma ita take ba ajiya ba? ( uwa daya uba daya gaskiya basu duba wa mamee ba. Allah ya raba mu da hassada ) Hassada ciwo ce wallahi, uwa daya uba daya akwai ta kawai ta wasu tafi ta wasu fitowa, Mamee ta ringa raba atamfofi super, da barguna masu kyau na kasashen waje, ga wasu robobi, bokitai, glass cups, kai kaya barkatar, su yaya sai tabe baki sukeyi *Karyar banza* ( wai arziki kamar na madaki a kirashi da karya ) Akayi budar kai, kowa na ba umaimah kudi kamar yanda al'ada ta nuna su yaya na zaune turus! Bayan an maida umaimah sama suka baje bisa carpet, yaya ce me korafi *Naga ana wucewa da tuwo mu banda mu?* Hafsat tayi tsagal, tuwo zakuci? Yanzu kuwa, ta lodo masu har sai da yaya ta ce wannan tuwo kamar rugaye? Ta yi dariya tare da yada masu magana ta ce *wai don kuci Ku dauka kamar kullum* Duk sukayi damama ta wuce bata bi ta kansu ba ta ciko wata yar roba da man shanu ta kawo masu da ruwa da lemu sannan ta rike kugu da yake takadara ce ta ce *Sai me?* Yaya cikin yake ta ce tuwon ya mana yawa da akwai leda dana dauki biyu saboda dumame....... Jamila ta yi karaf nima zan dauki biyun nan........ Hafsat ta ce baku da matsala yanzu zaku ga tuwo, ta je ta sami ledoji hada Wanda zataci ta lodo masu sannan ta ciko wasu robobi da miya ta ce duk gashi ai tuwo baya hada fada gidan mamee. Duk abin nan mamee ma bata San wainar da ake toyawa ba. Kawai masu tare fada ne Allah ya kawo mata. Dama hafsat hake take dasu wurin party ance iyaye su fito kawai su yaya suka kalleta suka ce *Sai kuje iyaye* haka kuwa akayi ta tafi ta dunga rawa daman mamee ta bata himilin kudi ta ringa watsama ango da amarya. Ganin yanda hafsat keyi duk sai suka tsargu rashin kyautawa ya dan damesu. Suna gama cin tuwon suka sulale ko bankwana. ( kai Allah ya ganar da masu irin wannan hali ). Karfe tara abokai sukayi sukayi su rakashi ya ce wallahi shi zai kai kansa. Sai da ya sallami kowa sannan. Suka mishi addu'a sosai saboda sunji dadin bikin sa yanda ba a zato ya bada gidan man shi daya duk Wanda zai tafi yaje yayi full tank. Banda kayayyaki da ya raba, generator, spare tire , mashin mashin, kai abubuwa barkatai. Ya shigo karfe goma da kwata, mamee na ciki ita dasu hafsat, ya leka suka gaisa ya fito mamin ta biyoshi, ya zauna falo, mamee na gaji. Ta yi dariya da gajiya *madaki* sannu da kokari wallahi ka cika *Da* na gode Allah ya shirya maka iyalinka ya baka zuri'a dayyiba. Ammkinnnn mamee love, ya kukayi da mutanen ki? Tayi yar dariya kai lafiya qalau, girgiza kai kawai kawai yayi yasan fada mishi ke bata son yi. Uwani duk ta tayar da hankalin ta. Ta fada tare da langabe kai., ya danyi murmushi kawai, Ta kalleshi don Allah ka dubi maraicin yarinyar nan kaji tsoron Allah. Wallahi rikon maraya yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Da mutane zasu gane falala da kuma dunbin rabon da mutum ke samu idan ya kyauta ta wa maraya lallai da wasu sun ringa bi gida gida suna sallamawa duk in da yake su dauko. Mamee zan kwatanta na sani. Ta harareshi na san ka da zafin kai madaki uwani yarinya ce kada ka biye mata don Allah. Kadai ji yan surutan da yan uwana keyi idan ka rike kanka idan kuma ka banzatar wallahi zan dauki mataki....... Zan kiyaye mamee. Jikin sa duk yayi sanyi. Ta mishi nasiha sosai yayi shiru kawai. Ta mike mu kwana lafiya sakonka nacen sama an kai. Ta shige ciki. Ya mike a hankali yana zuwa yaga katon tire cike da gasassun kaji an rufe da foil paper. Gaban sa ya fara faduwa, kamar bazai iya Shiga ba. Tana zaune bisa gado kuka kawai takeyi , kukan maraici na ban tausayi. Ya bude kofar a hankali. Ta hadiye wani miyau dunkulalle cikin ta ya kada ya bada kulululu....... Ya zauna shiruuuuu... Ya dake ya fara magana cikin kakkausar murya . idan kin gama kukan zo nan in magana dake. Tayi shiru ya daka mata wata tsawa..... Ta matso da sauri. Ya yaye gyalen malama ki man shiru kinji. Ta sunkuyar da kai. Yayi kasa da murya, umaimah kamar an miki auren dole? Wannan kukan naki yayi yawa gaskiya, ya kamota ya maidota kusa dashi. Umaimah wallahi ba abinda zan miki kinji har na rantse, zan tafi dakina ma in kwana, amma sai kin mun alakwarin zaki daina wannan kukan kuma zaki ci abinci...... Tayi saurin daga kai. Yayi murmushi good. Sha re hawayen toh, ya fada yana gogewa da hannu. Jeki yo alwala muyi sallah tukun . Ta mike tayo alwala sannan shima ya shiga, bayan sunyi raka'a biyu kamar yanda sunna ta koyar ya dafa kanta yayi mata addu'ar da manzo SAW ya koyar sai ya fita ya dauko naman da ice cream. Tana zaune ta zabga uban tagumi ya dan kalleta, ni zan baki ko zaki...... Tayi saurin kai hannu ta dauko ta fara ci. Yayi yar dariya *Mrs madaki*...... Ta harareshi ya kyalkyace da dariya ba injini ba inji *yan jarida* Da ta janye hannunta sai yace au kin koshi? To kawai in kwana anan......sai ta mayar da hannu haka har taci sosai, ya mika mata ice cream din sha kiban muyi kama kama inji yara. Ta dan harareshi kadan, yayi murmushi. Ya kalli jerin akwatunan lefenta ya ce *umaimah an bani da rowa* haka kika dawo da kayan baki ba dangi ba? Ana rabawa iyaye da yan uwa fa, Ai na basu, ta fada kamar mai koyon magana. Haba? Ya fada ganin ta danyi magana. Ta ce Allah. Su wa kika ba? Ta dan kalli jakunkunan Na ba baba shadda goma, su goggo atamfofi uku uku, itama luba na bata lesuka da kayan shafa, baba ma na bashi turaruka, an dibar ma dangi yankunnaye da atamfofi suma, sannan na bada *Hajiya ta* leshi uku, atamfofi biyar. Cewa zakiyi kin rabar da kaya kaf! Sai kawai Tayi murmushi shi fa ya kirata da mai rowa yanzu kuma ta bayar yace ta rabar. Ya kalleta yaushe rabon da ya ga murmushin ta? Haka ya dan jata da fira har daya saura sannan ya ja mata kofa ya tafi dakin sa. Yana fita ta saki ajiyar zuciya *Ohh madaki ikon Allah* Barci ya dauketa saboda gajiya ga kuma kuka anci. Shi ko sai kusan uku ya samu yayi barci yana ta gyare gyare. Cikin kunnenta aka kira sallah, ta tashi da sauri ta shiga tayo wanka gudu gudu ta sanya wani material ruwan kwaiduwar kwai,sai da ta gama sallah sannan ta dan shafa mai ta zauna lazimi, shidda da rabi ta shiga ta wanke kewaye, sannan ta zo ta gyara gadon ta jera jakun kunan duk ta dan gyara fasalin dakin sannan ta kunna abin turaren kamshi mai kamar kwanon glass ga sanyin A.C, ta dauko wasu turarukan ta na cikin lefe ta feffesa ma labulan daki., nan da nan dakin ya rikice da wani irin kamshi. Ya dan kwankwasa, tayi saurin zama kamar tana lazimi kafin ta ce *Shigo*....Yana sanye da jallabiyar da ta siyo mishi, ya dan turo a hankali sanyi da kamshin dakin ya daki hancin sa, .......ina kwana, ya dan lumshe ido *Morning sweetheart* yayi suka bisa gadon mamee ta ce idan kin gyara gado baki so a bata miki, ta mike tana ninke abin sallah tana murmushi. Shi ne kika bari na makara ko? To Alhaki kanki. Ta dan saci kallon sa kadan, ya tashi zaune miko mun littafin can, tana zuwa ya damko hannunta, kilibabba kina ta wani satar kallon miji kedai umaimah baki waye ba, ta kyalkyace da dariya tana noke fuska, Ya cacumota bari dai in fidda miki kunyar nan ta daina takura mu........ Ta fasa ihu wayyo na shiga uku wallahi na daina wayyo mameee.......... Ke tsaya saurara wasa nakeyi ya tallabo fuskarta, wasa nakeyi ya jaddada mata da kai. Duk illahirin jikin ta ya rikice da kyarma. Ya kwantar da ita bisa kirjinsa yana bubbuga bayanta, ya hakuri wallahi wasa nakeyi. Ya dan runtse ido, lallai yana da babban aiki wannan tsoron na umaimah yayi yawa. Ya dagota, ki saki jikin ki dani ki yarda dani please bana son wannan tsoron da dararewar. Ta danyi murmushi, ya ja hancin ta yar rainin wayo kamar ba matsiwaciyar yarinyar nan ba. Kwanta muyi barci...... Ta zaro ido mamee zan gaido. Ya dan muskuta ya cire jallabiyar daga shi sai vest da dogon wando ta dan basar don tana motsawa zai jata jikin sa. Ya mika mata, malama to lunke tunda cirewar ma kin kasa taimakawa, ke kam kina ban kunya, idan miji zai cire riga sauri akeyi a cire mishi kar ya wahala...... Ta danyi murmushi . ita dai duk bata amince da shi ba. Ya maida kansa bisa filo don Allah kizo mu koma barci....... Bana ji. Ta ce a hankali. Ya fizgota ke bazan dauki wannan gidadancin ba. Na shiga.....yayi saurin rufe mata baki da hannu shiru kiyi barci. Tayi lamoooo kirjinta na harbawa, ya kai hancin sa a wuyanta lallai amaryar nan kina zuba kamshi. Gabanta ya fadi ta fara raba ido. Yana ta faman zolayarta, a hankali a hankali taji ya fara saukar da numfashi alamar barci ya daukeshi. Ta saki ajiyar zuciya ciki ciki a hankali. Ta bashi kamar minti biyar sannan ta zame jikinta a hankali ta maida mishi filo, har zata fita taga yadan ja kafarsa alamar kamar yana jin sanyi, sai ta koma a hankali ta rufe shi da bargo sannan taja kofar ta fice, Ta sauka, dakin mamee tayi ma tsinke, bata ciki ta zagaya dakin baki wadanda basu kai ga tafiya ba su naryam hamza, hafsat, Aunty Aisha, duk dai aminan ta suna nan. Sai kawai ta fada toilet ta wanko shi fes! Sannan ta shiga gyara mata dakin, duk wani sako da loko sai da ta sharo shi, Sa'annan ta goge ta feffesa abun kamshi, ta kusa karasa gyaran wodrop kenan taji mamee ta rafka salati bayanta. Mi zan gani ni *Rabi*, uwani?????? Ta yi sauri ta isa kusa da ita tana murmushi tare da zukunnawa *Mamah* Ina kwana,. Ta kamota ta mike, wanene ya turo ki wannan aika aika? Ina madakin? Ta dan dukar da kai *Yana barci*........koma sama maza ga kalaci can an hau dashi...... Kuji mun yarinya ni jikar buzaye kai *Uwani* al'amarinki sai ke. Ta danyi dariya kai mamah bari in karasa gyaran...... Ke bani son iyashege kinji zaki koma daki ki huta ko sai..... *Kai mamah* ta fada kamar zatayi kuka, ta dauko kwadon zuba shara ji fa abinda na sharo dakin nan in banyi ba waye zaiyi? Su mansurah ta bata amsa. Ta zumbure baki ta juya tana ci gaba da lunkewa. Ta matso kusa da ita, zaki wuce ko sai na kwakkwada miki wannan ludayin da ke hannuna. Maza kije ki tado mun shi kice yazo su Aunty salma zasu tafi dasu Hafsa.... Ta danyi murmushi Allah dawowa zanyi ko na kirashi ta wuce ...... Ta bita da kallo tana yar dariya *Uwani* ....... *Uwani* ikon Allah. Allah dai ya baku zuri'a dayyiba. Wannan kuruciyar taki gara yazo ya daukeki kubar kasar can kya dan natsu kisan kin girma ja'ira. Tana buda kofa ya farka, amma sai yayi shiru cikin bargo. Ta zo tayi tsaye kansa tana alwalar kuda, ya fara dariya saboda tabbas yasan kiransa zatayi. Ta dan juya *Kazo inji mamee*, yayi shiru Ta kara cewa, shima ko motsi, Ta ce *Madaki*........ Ya lumshe ido kamar bakinta sunan ya fara fitowa, Kaji mamee na kira shima yayi shiru, Ta dan sa hannu ta yaye bargo kawai ya fizgota ta fada saman sa, Innalillahi dama kana jina? Ba'a sani ba, ke dai ba kauya ce an fada miki ko a kauye yanzu ana tada miji haka? Ya kara matseta, haka zaki dan hawo sannan ki dan mun kiss kamar haka...... Ya mata a goshi sai ki fara cewa *Honey*......... Kina dan shafani.......ta wuntsula ta sauka ya kyalkyace da dariya. Mikon rigar in saka, tana daukowa ta wulla mishi ta sauka da gudu ya fara dariya. Shi ya kai su Aunty bintar airport da kan sa. Kiri kiri mamee ta hana umaimah saukowa dole ta tafi daki tayi zaune. Ya shigo da sauri rike da kayan kalaci, yarinyar nan abinki akwai son kai shine kika gama cika cikin ki ni ko in gane? To zo muci mamee ta koroni yau. Tayi murmushi nima koroni tayi. Ya kyalkyace da dariya kyaleta gobe kamar yanzu mun bar mata gidan. Ta kalleshi da sauri, Ya kai dankali a baki *Dubai zamu honeymoon*...................... *Good morning* *Maman Abdallah*😘😘😘😘😘 Godiya ta musamman ga *Salamatu dahiru* ( MZ) Ayi mun uzuri yau post daya zanyi. Wannan. 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣3⃣4⃣ *Gareki AYFA ( AYSHER BAITEE )*😍😘😘😘😘 *Mrs Faruq* ......... Ta zumburo baki. Ya kalleta da kyau bazakije ba ne ko kuwa Dubai din ke bakya so?. Ki fadi kasar da kike so umaimah you have that right. Ni ba tafiyar ke bana so ba zolayar nan ta jirgi idan zai tashi nake tsoro wallahi hanjin cikina kamar zasu fito........ Har kwanciya yayi saboda dariya ta yi murmushi wallahi ka fiye mugunta kai kuwa. Sai da yayi mai isar sa sannan ya ce ba irin wancen jirgi zamu hau ba, wannan na daban ne sha kurumin ki wifee. Ta ce *Hmmm* Ki matso muci ko na kamoki yanzu nayi miki dura,..... Ta matso da sauri saboda tasan duk abinda madaki ya ce zai yi to zai iya, suna ci yana janta da fira. Wayar sa tayi kara, gaban sa yayi mummunan faduwa ganin sunan samira, ya dauka idan ta gane mace ce ya shiga uku, ya ki dauka shima matsala. Ta dan saci kallon sa ganin waya nata ringing har tana niyyar katsewa, ya dan bata fuska ya daga yana kallon fuskar ta..... Hello Aunty har kun isa? Samira ta dauke wayar daga kunnen ta tayi saurin kallon screen din tana zargin ko ba *Madaki* ta kira ba, Yaji shiru, yaci gaba da cewa amin na gode Aunty Allah yabar zumunci ya latse wayar. Dai dai ta mayar da ita kunne itama. Toooo faa! Ta fada tana zaro ido, wai ya akayi? Ta mike tsaye, lallai abinsa azimun ne wannan yarinyar tsoron ta yakeyi kamar rai da ajali. Abinda yafi na shafa ma kaina lafiya da *Matashin yaro* idan ya nemeni welcome idan bai nemeni ba kuma umma ta gaida asshhaa ina dalili. Ya kalleta tana ta tura dankalin da kyar sai kawai ya sha mur, ke juyo ki fuskance ni. Gabanta ya dan fadi ta juyo tana kallon sa kanta a kasa, Na lura sai na biyo miki ta bayan gida sannan zamu shirya ko? Kin dai san yanda mukayi jiya da ke ko? Ta daga kai *Eh* To ina nan akan baka na babu abinda zan miki, sai dai dole ki sauarara kin kindaya miki sharudda saboda yanda na ke kokarin tsara zaman namu bazai taba tafiya dai dai ba. Kin dai San yanzu ke matata ce ko? Ta daga kai *Eh* Good to bazan jure wannan makurewar ba wallahi kinji na rantse. Na farko anan zan kwana yau nida ke saman gadon can...... Ta zaro ido wallahi na tuba zan yi yanda kake so.......... Jira da Allah malama, kawo man ke akayi in kalla? Na ce ba abinda zan miki kin kuma San abinda nake nufi da hakan sai dai bazan iya hakurin wannan makurewar ba, idan kin hana in taba ki baya yanzu dai baki da iko. Magana ta biyu zaki ringa bani abinci daga yanzu a baki har in koshi, sannan ba maganar zama nesa dani ko kusa dani kin ga nan? Ya bugi cinyar sa nan ne mazaunin ki Allah. ......zatayi magana ya daga mata hannu *umarni nake baki* ba wai ina neman shawarar ki ba. Tayi narai narai, sai magana ta uku idan ina barci zaki tasheni dole kema ki kwanta kusa dani kina shafani a hankali kina kiran sunana har na farka ko kin gane? Ta daga kai *Eh* Good taso ki dawo nan toh ya janyo hannunta , tayi sukutii ....ya kalleta wallahi ki ware kawai don baki ga komai ba game da dokokina ba. Ta fara debo dankalin zata bashi ya ce hajiya ajiye chokalin da hannu ake ba mai gida abinci........ Na bani kawai.....ta fada azuci. Da ta bashi ta kara debowa sai ya rike hannun ranki ya dade ba a sauri *Slowly*........ Ya kashe mata ido. Ta yi dai sukuy, yana koshi ya gyara zama sannan ya rungumeta kamar jaririya yana bata, ( yau na ga ta kaina ni umaimah ) ta fada kamar ta nutse. Karfe biyu ya shirya ya ce mata zai je cikin gari. Tana fitowa ta kira su bilky ta kwashe bokitan gara duka ta ce a mayar sashen mamee hada manshanu. Tana ciki tana harhada kudin gudunmuwa bata san wainar da suke toyawa ba, umaimar ta shiga . Tana ganinta ta washe fuska 'yar halak yanzu nake tunanin ki a raina. ta zauna tana tayata harhadawar mamah kuma ba sai ki kirani ba? Tayi dariya kawai, ashe gobe zaki kara katari da nutumen? Duk sukayi dariya sannan ta turo baki wallahi bana kaunar abinda ka kara hawa dani jirgi mamah ki ce a bar tafiyar don Allah. Uwani ina ni ina hana tafiyar da an gama komai gobe goben nan?, to ki shirya mu tafi tare don Allah mamah......... Ke bani son iyashege, haka kawai sai in biku? Ta langabe idanunta suka kawo ruwa wallahi zanfi jin dadi idan muka tafi da ke don ni tafiyar gaba daya bana so........ Ta ajiye kudin hannun ta kafin ta kamo hannuwanta duka biyun. Uwani ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru sai alkhairi, idan kuka tsaya garin nan tabbas ke kanki abin sai ya dameki saboda fitar nan da kika ga yayi office ya tafi, wallahi matukar madaki na garin nan bazai huta ba. Kuma kema dama ce gareki da zaki San me mijinki keso meye baya so........ Bata san lokacin da bakinta ya kucce ta ce humm ba. Bata bi ta kanta ba taci gaba da cewa, kuma kya gano gari kiyo kallo tunda naji yawo zakuyi kasashe don jirgi ai sabawa zakiyi wancen ma don karonki ne na farko. Ta fara janta da yar firarraki har ta dan saki. Suna zaune falo ya shigo tara da rabi har ta gota, uwani da mamee ya fada yana murmushi, ina so inji yanda firar ku take kasancewa yanzu su uwani an zama matar madaki, To rasa kunya beran tanka,zaka fara ko? Uwani tashi ki tafi daki kada ya hanaki sakewa kinji, tayi zumbur ta wuce simi simi ya bita da kallo iyye yarinya sama tayi yau bad akin mamee ba…….itama mikewa tayi ta wuce ciki, yana waigowa yaga har ta kusa shigewa y ace mamee ina zuwa? Ko waigowa batayi ba barci nake ji kasan akwai gajiya tayi ciki. Ya danyi murmushi kai mamee karshe ce wallahi. Tana ta kakkabe kakkabe tama rasa me zatayi hankalinta a tashe wai gado daya zata kwana da madaki. Ta yi kasa da murya ba abinda ke cikin aure sai fargaba, takura, zullumi da tsoro. Wallahi kamar in gudu nakeji………….ki tafi ina? Tayi firgigi ko kadan bata ji shigowar sa ba. Ta danyi kasa da kai, ya kamota zo nan meke tayar miki da hankali kike tunanin guduwa? Ya bata rai umaimah dana san baki kaunata da ban aure ki ba…..Allah bah aka bane, to menene? Tayi shiru, ya zauna bakin gado ita kuma ya dorata bisa cinyarsa, umaima wallahi aure da kike ganin sa babu abinda ke ciki sai jin dadi, farin ciki,walwala da nishadi. Shi yasa Allah SWA cikin suratul rum yake cewa : kuma na halitta maku matan aure sannan na sanya soyayya da nutsuwa a tsakanin ku lallai wannan ayar mutane ce masu yin tunani. Saboda haka ki saki jikin ki wallahi zan jiyar da ke dadin da ba’a taba jiyar da wata mace shi ba, zan shagwabaki yanda ake shagwaba yaro daya tilo wanda iyayensa suka samu bayan sun dade suna rokon haihuwa kuma daga shi basu karaba, zan kula da ke yanda duk baki tsammani na jiyar da ke dadin da ba kowa ce zata sameshi ba. Abinda duk kike tsoro sai ya faru yau, gobe , jibi ,next month,next year ke any time but zai zo miki lokacin da baki tsammani lokacin da baki tsorona, lokacin da kika saba dani, lokacin da kika san dadin madaki…….. kawai ki saki jiki dani wannan shine abinda nake bukata umaimah saboda ni mutum ne mai son kula, kuma ina sha’awar taba jikin ki wanda baki isa ki hana ni ba duk tsoron ki duk wata makurewa da zakiyi. Tun kafin in fara gwada miki karfi kawai ki ware hajia, ya tallao fuskar ta. Ya harareta wallahi matukar baki rage wannan kunyar ba tabbas zan gaggawar wancakalar da ita a wuce wurin…. Kinji ko? Ta daga kai tana murmushi. Kilibabba irin ku kunfi jaraba sumimu kasau, ni yanzu gashi dai na karya record yau idan kinji wayoyin abokai dana amsa wani dan iska ma cewa yayi zai zo ya rakani in kaiki asibiti. Basu san cewar ni madaki ba haka nake ba lokacin da ake tunanin da zanyi abu sai na kiyi ko laifi akayi man lojkacin da ake tunanin zan dau mataki sai anyi shiru, wallahi umaimah sai kin zauna zaki fahimceni bani da fitina da kike ganina na mugun miskili ne ni kawai ke baaki gane bane saboda yanayin chakwakiyar mu ko kuwa? Duk suakayi dariya, ta ce wai chakwakiya, eh mana ko kin manta yakin da muka gabza kika farden hannu? Ya kyalkyace da dariya kai naga bala’I ni ummaru. Tayi murmushi, ya mike ya fita sai gashi da gyalen hajia wanda ta bata aro lpkacin da suakyi ma juna wankan miya a fatin asma’u, ta fara tafa hannu tana salati, daman yana hannunaka? Ya yi murmushi ke wannan gyalen ai kusan haukatani yayi lokacin da muna cikin fitinar idan na dauko shi zuciyata har hayaki takeyi don azaba. Da kuwa na kamu da son ki da kin gudu kin barni sai na zo na daukeshi ina bege. Ta kyalkyace da dariya ta ce wai bege. Nan da nan ta sake kawai suka hau fira hada tafawa, sai kusan sha biyu ya watsa ruwa yayi yayi da kyar ta shiga kewaye ta janzo kayan barci wata guntuwar riga iya cinya fitowa ta gagara sai shine ya fiddota da tsiya tana hawa gado tayi saurin yayo bargo ta lullube , ya hawo yana taunar cingam…. Yarinyar nan wallahi da gangan akayi budurwar kauye ai ke sunan ya dace da. Ya janyo ta zo kiga yanda ake barci da miji hancinsa da nata ya haduya matseta ganin zata zulle malama jira haba, ya kura mata ido kaii ya naga hancinci bai kai nawa tsawo ba lallai cewa zakiyi akwai ragi ga abinda na bayar…….. yayi dariya idan kunya kike ji rufe ido in miki kallon tsaf!! Ta rasa in da zata sanya kanta, ya kura ma dan bakinta ido, ALLAH sai nayi kissing…..ya ayyana azuci. Ke bude kiga wani abu ….bude bude bude…….ya fada kamar ga ma abin nan ya taho gadan gadan… tayi saurin budewa ya fiddo cingam din bakinsa ungo kici…..tayi saurin runtse ido gashi ya riketa ta ce nag a ta kaina anya bawayau zai mun ba?......bata karasa tunani ba taji bakin sa cikin nata……wata kunnanniyar wuta ta dauke mata, ta rasa duniyar da take . yafi mintuna goma sai da yaji network na neman dauke mishi ya sa kawai ya zare a hankali. Ta tafi da kanta luuuuu ta soke cikin kirjinsa ya maida hannuwansa bayanta ya rufe su da bargo ………………mu kwan lafiya. Na bakin madaki lallai umaimah anji network. Don sallar asubah ma sai da ya dawo masallaci sannan ya tada ta, Ya tasa ta gaba ya dinga mata dariya wai taji network barci harda minshari. Ta yi ta hararar sa, dai taci gaba da lazimi. Da kansa ya hada masu kayayyakin da zasu tafi daasu cikin yar karamar jaka daya. Cikin ranta tace kilan jibi zamu dawo. Mamee bata koma ciki ba sai da taga fitar su gate, umaimah nata matsen kwalla duk tunaninta airport sukayi sai kawai taga sun dau hanyar gidan su. Wani dadi ya kumeta, musanman da ta hango baban tsaye kofar alamar isowar su yake jira. Kafin ta fito kofar gidan ya cika da jama’a ta dan raba tayi gidan hajiya da sauri, gudu gudu ta fito har ya shiga mota yana jiranta, yana hangota ya fito ya isa wurin ta ya fakaici mutane ya saka mata kudi a jaka y ace bakauya idan mutane sun taru haka don kai alheri ake masu , tayi sukuti daman taga ya yi rabo cikin gida su luba har da rawa da taga umaimah. Ta dan juya ta hango auwalu mai manja ta yahuto shi da hannu ta damka mishi daurin kudi ta ce raba muku tayi mota da sauri, suna dagawa ya kalleta yana dariya ina cewa zakibi kowa ne ki bashi. Tayi yar dariya tabbb! Da sun karya ni kuwa……au ashe kin sani ta harareshi kawai. Suna zuwa jirgi na slow, ko zama basuyi ba ya cacumeta wa kike ma harara dazun, sukayi bisa doguwar kujera rikichaaaaa ya fara mata chakulkulo tun tana zullewa har ta fara kyalkyatar dariya tana zillewa…… ana haka yaji jirgin ya tashi har y agama saisaituwa sararin samaniya…. Ya dan saketa, tayi jimm tana gyara cucukuyar kayanta tana zullumin tashin jirgi sai kawai ta hango hazon gajimare, nan da nan ta fahimceshi. Ya kwantar da ita jikin sa yana fadin dumaman jiki in dan runtsa please………….. Maman Abdallah. INA MUKU BAN GAJIYA NA’IMA AMADU: mun gode da karamci Allah ya kara arziki ya shirya zuri’a. RAKIYA AMADU [ yar baba] HALIMA SHEHU karofi HADIZA SADA nabebe BADIYYA AMADU m/bread ALLAH YA JIKAN SAMIRA ABDULLAHI KANKIYA YA KYAUTATA NAMU ZUWAN. *Maman Abdallah* 😘😘😘😘😘😘😘 💑 *AUREN FARI* 💑 0⃣3⃣5⃣ ..... Mamaki ya kamata ganin da gaske ya fara barci, ta zuba mishi ido yanda yake barcin kamar wani karamin yaro. Matashi Dan gayu mai kyau. Tayi murmushi Allah ya bani gaskiya madaki Nada kyau yana da kuruciya ga kudi, yaro matashi Allah ya bashi arziki na ban mamaki ga mu'ujizar mutane da Allah ya bashi. Ta bi jikinsa da kallo, fatar sa lumuy lumuy Hutu ne kadai da jin dadi, bata lura ya farka ba sai kawai taji kiss a bakin ta. Tayi saurin yin baya, ya yunkura *Almura* ashe kina nan zaki cinyeni da kallo.. Gaskiya dole in warware miki kunyar nan ta na wahalar dake, Ya dauko sandwich da coffee ya ce bisimillah cikan ciki. Tayi murmushi , ya kalleta fadi kar ta kashe ki, ta dunguna mishi katon sandwich a baki ni dai amshi. Ya ci gaba da mata dariya. Suna isa taga yanda ake ta kyarma da madaki, abin ya daure mata kai wai har Dubai an San shi? ( umaimah kenan ), wani makeke gida suka isa, turawa,indiyawa da larabawa ne ma'aikatan gidan kowa yasan sunan sa, gidan har yaso yafi na Nigeria tsaruwa saboda shi bai kai girman wancen ba. Ya kalleta hajiya da kafar dama zaki sha kinzo gidan ki na Dubai. Gabanta ya fadi haka su goggo suka ce da ita lokacin da zata shiga gidan sa. Ya danyi murmushi sukayi ciki. Ta kalleshi ya na kokarin hawa bene, kai wannan mutum da son bene yake kamat tsuntsu. Ba abinda babu gidan. Bani iya misaltashi. Ya fara bubbude drower abin mamaki ta ga kaya tsangare ciki. Tayi shiru ta na kallan ikon Allah. Ya fara watso ruwa sannan ya ce ta shiga tayo. Sai wani basarwa yakeyi yana dan shan kamshi alamar za ayi wulakanci da rai. Ya shirya cikin kananan kaya yana ta faman jiranta, Ita kuwa har ta bushe data leko ta hangoshi sai ta koma ciki. Ya kalli agogo au yarinyar fa kasa fitowa tayi.....mtsew yaja tsoki, ya dauki hijab ya Dan bude kewayen kadan ungo ki saka idan fitowar ne bazaki iyaba....... Ta miko hannu tana karba ya yi saurin bude kofar ya fizgota saura kadan tawul din ya balle ta daddafe....... Ka rufa man asiri kayi hakuri don girman...... Ke bari hada ni da abinda yafi karfi na wallahi sai na fara rage miki kunyar nan ya janyo ta..... Na daina billahil azim bazan karaba amma inaa sai da ya kaita bisa gado yana fadin na ce ki saki jiki dani kin kasa bari kawai a kashe boss madam........ Na daina wayyo na shiga uku ta kankame jikinta zata fara kuka, ya saketa, jeki shirya fita zamuyi....... Ta yunkura da sauri duk ta rikice, ya harareta gulmammiya. Ta shige bayan wodrop ta saka bra da pant tana kokarin sa dogon skirt din kayan da ya fiddo mata kawai taga mutum.....ta hade da bango *Madaki* wai meye haka don Allah na tuba....... Ya tallabo kugunta *Nawa gareki*......zo in koya miki sauri....... Duk iya kokarin da nakeyi? Tayi saurin janyo skirt din ta karasa sanya shi ya juyo ta karfi ke me yasa kike haka? To meye din naga wannan?...... Kawai yakai hannu kirjin ta, .... Ta rikice gashi ya riketa gamm ... Ka dubi girman Allah kayi hakuri sai ta fara kyarma. Tabb wallahi sai na taba....ta zaro ido ka taba me? Wayyo na shiga uku kawai taji yasa hannu ya ballo bra din ta kwalalo ido ni dai bani so wayyo mamee...... Ya kyalkyace da dariya nasan zaki kirata shi yasa na gudo dake nan....... Ya zareta duka..... Ta fada jikinsa ta makalkaleta ka rufa man asiri madaki na tuba....... Ya yi dariya *Good* ko kefa? Ya fara shafan bayan ta zuwa kugu yana mata rada a kunne idan ba kyajin yunwa muyi hakuri da abincin nan zuwa dare ........ Yunwa nakeji nidai mu tafi ta fada tana yan kwallahi. Allah? Ya bukata Wallahi yunwa nakeji don Allah ka kyaleni. Ya yi murmushi ya janye hannun sa to nima sakeni. Tayi shiru, kinji? Ko in ci gaba? To kaban bra ta in mayar . Ya danyi dariya kin ganta nan a kasa sakeni in miko miki. Ni dai tafi zan dauka. Ya kyalkyace da dariya to ki sakeni mana..... Ta Dan ja baya shi kuma ya juya kamar zai tafi. Tayi saurin dukawa ta dauko tashin da zatayi taji duka hannuwansa bisa su............ Ta kurma ihu Qalu innalillahi...... Na shiga uku. Ya maidota ta jikinsa ta baya ai na ce wallahi sai na taba da banyi rantsuwa bane. Yadan murza...... Kin San tun lokacin da nake hadiye masu miyau ........ Duk illahirin jikinta ya mace murus, ta rike hannuwansa shi kuma ya kara luma su. Kafafunta suka kasa daukarta lakkar jikinta tayi sanyi, ba abinda tsikar jikinta keyi sai ta shi. Da kyar ta bude baki don Allah ka yi hakuri na Tu......... Ya juyo ta da karfi kafin tayi wani motsi ya hada bakinsa da nata. Ta karasa rikicewa ta tafi luuuuu zata fadi ya tallabo kugunta kawai ya sureta zuwa gado. Hankalinta ya tashi ta fara kuka *Madaki* ka yi hakuri kuka takeyi sosai musamman da taji bakinsa akan nono........ Ta fasa kara ta ringa ruzgar kuka tana magiya hankali tashe, Ya dade kafin ya dago idanunsa sunyi jawur tayi saurin kawar da fuska don bata iya jure kallonsa haka.......wai meye kike tsoro? Don girman Allah kibarni ki kyaleni.......... Ta fashe da kuka don Allah kayi hakuri ....... Inyi hakuri in zuba miki ido ina kallo? Ke baki son ko ido mu hada ya kara kai hannunsa kiyi hakuri in rabaki da kunyar nan a wuce wurin...... Na bari bani karawa.... Ya kalleta kamar zai yi magana ya buga tsoki ta shi ki shirya mu tafi, ya fice falo. Ta Dan gyara fuskarta yana tsaye har lokacin idanun sa basu washe ba, ta fito simi simi....... Ya wuce. Wani hadadden wurin cin abinci sukaje daganin inda suke, Musamman aka shirya masu, duk ya hade rai, yana satar kallonta, ita kuwa ta kasa dagowa ta kalli ko gefen ta, ya kara buga tsoki, kunya, kunya dai. Wallahi fiddata zanyi. Suka Dan zagaya suna kallon wurare yana rike da hannunta sai sunsunkewa kawai takeyi. Ya kira mamee yace sun sauka lafiya ya karbi wayarta ya kashe. Sai bayan isha'i suka koma gida, gabanta sai faduwa yakeyi ganin yanda yake ta shan mur, Ya gama shirin sa tsaf ya kwanta tana ta yan kame kame, zuwa can taji alamar barci ya daukeshi ta sanyo wasu riga da wando na barci ta lallaba wai kada yaji ta kwanta bayansa, duk yana jinta. Tana gama tofa addu'a ya juyo sai kawai taji mutum ya janyo ta , kirjinta ya buga da karfi. Ya fara shafata a hankali, ta runtse ido da karfi, duk abinda yakeyi tana jinsa tayi shiru yana jin yanda kirjinta ke halbawa, ya ce cikin zuciya tsoron nan na iya haifar miki da matsala. Bata motsa ba sai da taji yana kokarin raba ta da kayanta, ta ksnkame jikinta zata fara magiya yasa bakinsa akunnen ta, kiyi shiru kawai kamar yanda kika fara yi da farko komai zai tafi a hankali......... Ta fashe da kuka kiyi hakuri umaimah wannan tsoron naki yayi yawa bari kawai a wuce wurin, ya yi wurgi da rigar ta fara kuka yana bata hakuri........duk abinda yakeyi bai fasa magana a hankali ba, ina tunanin wata ce ta firgita ki da yawa gara ki san *Duk karya ce* Tun yana magana shima sai wutar sa ta dauke........ Kuka takeyi har muryarta tashake. A hankali tunanin sa ya dawo nan da nan kuma ya fara lallashi, ta ingijeshi ya danyi murmushi *Kut* nayi laifi ya janyo ta ya hakuri bani karawa.....ta kara fashewa da kuka, Da kyar ya samu tayi shiru daya yunkura zai ta shi sai tayi tunanin dawo mata zaiyi sai kawai ta firgita dole ya hakura har barci ya dauketa mai nauyi wajen karfe uku da rabi. Yayi shiruuuuuu zuciyarsa tayi fes! Tausayinta ya baibayeshi. Ya lumshe ido yana tunanin yanda yakeji a zuciyar, ya yayi murmushi gobe akwai daru gidan nan, rigimar umaimah gobe Allah kadai zai kwaceni, a haka shima barawon ya sace shi. Kukanta ya tayar dashi duk jikinta yayi dayi, ta kasa tashi, gaban sa ya fadi kada fa maganar abokan sa ko ya mata rauni. Ya zo zai kamata *Umaimah* ta dan fizge, bata so. Yayi murmushi ya hakuri tare da yaye bargon subhannallahi haka rana ta yi? Ya wuce kewaye, sannan ya fito zo muje in taimaka miki....... Bana so ta fada cikin kuka, yayi yar dariya kawai ya sungumeta ta fara zille zille idan baki tsaya ba wallahi zan kara ....... Ta fashe da kuka. Ya gaggasa mata jiki yana zolayar ta, jiki ne bana wahala ba ba a iya daukar bokitin ruwa amma an dauki madaki....... Ta ci gaba da kwallah shi kuma yana dariya. Ya fi mintuna ashirin yana gargasa ta sannan ya kara sa mata wasu ruwan ya kalleta *Kin dai iya wankan janaba ko?*..... Ta dauko katon sabulu ta kwala mishi..... Yayi hanyar fita lallai karfi ya samu bari inyi ta kaina. Ya fice yana dariya. Dadin ruwan zafin yasa taki fitowa sai da ta shafe kusan awa guda sannan. Tana fitowa bata ganshi ba ya gama gyara dakin ya canza bed sheet amma bai iya shinfidawa ba ya dai dan badada shi kawai. Ta tabe baki ta sanya wata blue gown mai karamin hannu ta Dan shafa mai da turare kawai sannan ta kabbara sallah. Raka'ar karshe ya shigo yana ta uban kamshi cikin farar t-shirt mai karamin hannu da blue jeans. Yana dauke da Dan tray. Ya zauna tare da zabga uban tagumi yana kallonta, ji yakeyi kamar ya hadiye ta, , duk fuskar ta kode saboda kuka amma sai ta kara mishi wani kyau da annuri. Ko kallonsa batayi ba ta ta shi tana ta fushi ta haye gado... Yayi murmushi yasan dole ayi haka. Ya karasa shima ya hau gadon yana fadin Allah yayi miki Albarka kamar kin San nima ban gaji ba ya janyo bargo zai rufe su ta sauka da sauri ta kydundune jiki tana kuka. Ya kyalkyace da dariya *Ke wasa nakeyi* ya zagayo inda take, ya hakuri nima na San nayi laifi umaimah bazan kara ba kiyi hakuri kinji? Ka tafi kaban wuri ...... Yayi murmushi a a ina nan fa. Sai dai kiyi man duk hukuncin da zakiyi man amma fa ba inda zanje. Ga kunya ga takaici ta rasa ya zatayi da shi. Ya fahimci tabarmar kunya takeson nadewa da hauka sai ya janyo ta zo muyi kalaci kinji 'yar amaryata ban karawa jiya ma kuskurene ....... Zo in baki da kaina yana faman lallashi. Ba wani cin da tayi sosai suka koma barci, basu tashi ba sai uku da rabi. Shine ma ya rigata tashi. Tare sukayi jam'i na la'asar sannan ya kamo hannunta suka fito tana ta fushi. Shi kuwa sai wani nishadi yakeyi yana satar kallonta. Abinci kala kala suka tarar an kawo na lunch nan ne yasha mur ya sanya taci sosai sannan ya sungumeta sukayi bayan gidan wurin ruwa. Daga ranar sabuwar rayuwa ta bude ma umaimah da madaki. Bai kara taba ta ba har kusan sati sai dai an fara shakuwa har ana guje guje da yar goyo. Duk wani wasan yan yara umaimah ta kawo mishi hada yar boyo. Umaimah an gama shan kwana tunda hawan jikin madakin ya zama ba komai ba. Sun gama mallaka junan su zuciyoyin su. Da daddare tana kwance bisa cikin sa, ya fara shafar ta yana canza salon firar ba kamar kullum ba nan da nan ta fara rikice mashi cikin matsanancin tsoro. Ya tallabo fuskar ta *yau dadi zakiji* trust me mana. Ta fara kuka ya ce wallahi yau babu zafi kwantar da hankalinki.......... Hankalinta bai kwanta ba sai da ta tabbatar azabar bai kai farko ba. Amma dai an dan wahala. Daga nan ya kyaleta kusan kwana hudu sannan haka ya ringa stepping back na kwanakin yana ragewa kafin a koma kullum. Ma'aikatan gidan Kansu sai da umaimah da madaki suka ringa birgesu. Soyayya akeyi ruwanta watan su biyu Dubai kafin su ka tafi *France* nan ma aka balle bushashar sati biyu suka wuce *Pari* satin su daya umaimah tace kasar batayi mata ba saboda mugun sanyi suka wuce gidan sa da ke London anan labari ya canza umaimah aka fara amaye amaye. Duk wani turare da madaki zai saka bata sonsa. Ta ce bata son warin gidan. Ya ce to ko mu tafi hotel, nida gidana ya gagareni? Wani abokin sa ne yake fada mishi juna biyu gareta, ya kuwa dauketa sai asibiti likita na tabbatar mishi da gaskiya ya kwala wa mamee kira. Yana shaida mata itama ta hau murna. Sai Sabon kulawa ga hajiya umaimah. Ya ce to ke kina ma iya zuwa hajji kuwa? Sai da suka wuce umara sannan suka koma gida. Umaimah ta zama kamar gwal. Amma in da tayi Kyan kai hakan bai taba sawa ta fasa yi wa madaki duk abinda yake so ba wani lokacin ma shine ke tausaya mata. Yaya Abba ya dawo dumur dumur madaki ya bashi manager gidan daya daga cikin gidajen man shi. Hajiya kuwa ko 'yayan cikin ta bata jin dadin su yanda takejin dadin umaimah, umaimah ta bayar da mamaki yanda duk ba'a tunani. Allah ya sauki umaimah lafiya ya bada zuri'a dayyiba. Ayi hakuri labarin ya tsaya daga nan saboda wasu dalilai.Allah ya kara hada mu da masoyan mu. 😃😃😃😃😃😃😃 Kadan mai albarka ........... Ina kara bada hakuri *TAMMAT BI HAMDU LILLAH* SAI KUN KARA JINA GA WANI SABON LABARIN IN SHAA ALLAH. Na gode nagode da kaunar Ku gareni. *SUNANA ZAINAB DAHIRU WOWO DUTSINMA*😃😃😃😃😃😃😃 Maman Al'amyn Amynatu da Abdallah.😘😘😘😘😘😘😘😘 Ina bada shawara don Allah duk Wanda zaka so to ka soshi don Allah.👏🏼👏🏼👏🏼 *THE END* JOIN OUR TELEGRAM CHANNEL 👉 t.me/hausa_novels