Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO:+2349030159301 [14:47, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM* GODIYA ```Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki mai kowa mai komai da ya bani ikon fara wannan littafin Allah ya bani ikon isar da sak'o me amfani kuskuren da ke ciki Allah ubangiji ya yafe min SAK'O GAISUWA GA Haneefah Usman Jiddah Ja'o Yar_ficika Ramalurv Kausar Lurv Ummiey Big Fatiey Azland Amnoor Meelart AHK Ayusha Iliasu Asy Khaleel Billy Sarki Sweery Deejah Jahun Deejah Wazeeri Aunty Jiddah Musa CwtJiddah Mr's Fawwaz Umma yahya Mommy sulti First Lady Memxiey Maryam Abdool MSB Duduwa PML Wanna Littafin tukwici ne ga each and every member of ``` ```PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S Up! Up!! together we stand divided we fall ,we rock even in the heart of our enemies # one ❤ ``` 1-5 SHIMFID'A Jami'ar Umaru Musa Yar Adu'a Jami'a ce da ke d'auke da mutane daga sassan Nigeria daban-daban kama daga Gabashin Nigeria zuwa yammaci,kudanci da Arewaci. a cikin d'aliban da ke wannan Jami'ar ya had'a da wasu Kyawawan 'yan mata guda biyu AYUSHA DA ANEESERH. AYUSHA yarinya ce kyakkyawa ta ajin farko tana da shape me kyau me d'auke hankali,ba fara bace amma kuma baz'a a kirata bak'a ba tana da gashi har gadon baya sai dai matsalanta d'aya Allah bai hore mata yalwataccen dukiyar Fulani ba asalin ta yar garin katsina ce. ANEESERH ma kyakyawa ce ta ajin farko bambancin su Ayusha kad'an ne ita fara ce sol sannan tana da wadataccen dukiyar fulani sai dai gashi ya mata yawa domin dakyar ake samun na parking.asalinta yar Jigawa ce wani gari da ake kira Dangyatin karatu ne ya kawota katsina har Allah ya had'ata da Ayusha suka fara k'awance ita a campus take zama sab'anin k'awarta da cikin gari. *GUNDARIN LABARIN* A nutse suke taku kamar basa son taka k'asa Aneesa ta dubi Aminiyarta tace " 'yan mata ya kamata mu d'aga k'afa fa dan wanna tafiyar tamu ba inda zata kaimu kuma kin san Mr Ojokolo ba mutunci gareshi yana riga mu shiga sai dai muji a slow last week ma bamu samu munyi attending lecture nasa ba" "Hmmm!!k'awata kenan wallah baza ki gane bane, Yau tunda garin Allah ya waye nake jin jikina very week dak'yar na iya tashi na shirya har na samu na shigo school" "subhanallah,me ke damun ki haka" "Wallahi nima ban sani ba nasan dai yau am abnormal, zai yi wuya idan ba wani mummunan aika aika ke shirin faruwa dani ba" sai ta fashe da kuka. Aneeserh tayi saurin rufe mata baki tana fad'in "please sistor ki daina fad'an haka falyak'ul khairan Auliyasmut (ki fad'i alkhairi ko kiyi shiru) in shaa Allahu babu abinda zai faru dake sai alkhairi" itama sai ta fashe da kukan,waje suka samu suka zauna suka ci gaba da kukansu sai da sukayi me isarsu sannan suka bari a k'alla sun d'au minti talatin a zaune ba wacca tace da yar uwarta k'ala daga bisani Ayusha tai k'arfin hali tace "Sistor tashi mu tafi hostel tunda munyi missing period din idan yaso da yamma sai mutafi gida muyi weekend a can dama Mummy na complain wai kwana biyu kin daina zuwa" Aneeserh zatayi magana tai saurin rufe mata baki " bana son jin unnecessary excuse naki dole sai kinyi weekend a gida" Murmushi tai sannan tace "Al-masifatu your wish is my command" dariya sukayi gaba d'ayansu suka nufi hanyar hostel. ```A dai-dai lokacin alk'alamina ya tsaya for today ku biyoni gaba dan bibiyar labarin wad'an nan yammatan da fatan wannan soman tab'in ya k'ayatar da ku``` *ROOKIEY D BEST* [14:48, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_A short_ REMINDER* *_It is normal to see a boat floating on the water but to see water fill up inside the boat is considered dangerous, in that same way you can live in the heart❤of world but you must not let the world enter you heart_* *_This page goes to my one & only Besty KABEER SKT thanks for the Love,care and un endless Support #1Lurv❤_* 6-10 Suna shiga hostel Ayusha tace "wallahi sistor yunwa nake ji yau ko breakfast banyi ba na fito" Aneeserh tayi dariya tace " to dama ke wani cin abinci kikeyi yanzun ma dan dai yunwar ta rinjayeki ne amma breakfast baya daga tsarin ki" "ke dai Kika jiyo,yanzu dai tashi ki dafa min indomie as usual" wani harara Aneeserh ta sakar mata " lalle baza kici indomie ba in dai ni zan dafa miki" "Haba my chef kin san dai ban iya cin indomie kowa idan ba naki ba girkin ki daban yake a cikin mata you are the best among the equals" da sauri ta mik'e tana dariya tace "wannan Ayushan kinfi k'arfin bil'adama idan kika sa naci a abu ko mutum baiyi niyya ba sai yayi" Murmushi tayi tace "k'awata idan baki kula dani ba anan zai kula dani" "dole kice haka munafukfuk ina gama dafa miki zaki fara min iskanci" a haka da wasa da dariya suka dafa indomin bayan sunci sun huta sukayi sallan azahar Sanan Suka nufi library don yin karatu. Misalin 3:45pm suka fito masallaci suka wuce don gabatar da sallan la'asar, bayan sun idar suka koma hostel Aneeserh ta d'auko duk abubuwan da tasan zata buk'ata sannan suka nufi student parking lodge suka dauki mota suka nufi gida. 5:45pm suka isa tun kafin su k'arasa k'ofa Ayusha ta fara suburbud'a hon da sauri Mallam Ayuba Mai gadi yazo ya bud'e get domin yasan halin uwar d'akin nasa idan ta dad'e bai zo ya bud'e ba zata sauke masa masifar guntun gajiyar school, shi kanshi yasan Ayusha tana da kirki ga ba rowa ko kadan bata k'yamar talaka ya rab'eta amma bata da hakuri ko kad'an sab'anin k'awarta Aneeserh bata fad'a ko hayaniya in fact she's totally cool. Yana ganinsu tare ya fara washe baki "Hajjaju makkatu yau kece a gidan namu gaskiya kin bamu rani dayawa dazu fa kamar in ce da Hajia Shatu(haka yake kiran Ayusha) ta ce miki yaushe zaki kawo mana ziyara" "Allah Sarki Baba nima nayi missing naku kwanannan Ina busy sosai shiyasa ban samu na lek'o ku ba" "Ayyah barkanki da zuwa" "Yawwa Baba" Ayusha ta kallesu tace "Baba na Aneesha idan kun had'u baku san rabuwa dan surutu yanxu dai ayi hak'uri magarba ta doso anjima kwa cigaba da gaisawar" dariya sukayi dukkansu sannan suka shige ciki. Tun daga falon k'asa suka fara cin karo da wani had'ad'd'en k'amshin girki na tashi hakan ya tabbatar musu da cewa Mummy na kitchen da sauri Ayusha ta haye sama da gudu tana fad'in "am home Mummy na i miss you today so much" ta fad'a jikin Mummy da sauri Mummy tayi hugging nata tana fad'in "miss you more darling, ya school I hope baki tattare da wata matsala ko damuwa" "yeah! Mummy na bani da damuwan komai" "Alhamdulillah haka nake son ji My Daughter" Da sauri Ayusha tace "au na manta fa ashe nazo miki da surprise a k'asa,bani two minutes yanxu zan dawo" da sauri ta fice ta bar Mummy da tunanin wani irin surprise ne wannan. bata gama tunani ba baji ana fad'in "Mummy close your eye's before i show the surprise" idan da sabo ta saba da shirmen Ayusha ta sani idan bata rufe idon ba ba nuna mata zatayi ba so she has no decision rather than to close her eye's. Tana rufe idon taji ance "Mum open your eye's and see the surprise" tana bud'e idon ta gansu a tsaye suna mata dariya b'ata rai tayi tace"da nasan wannan na surprise d'in da ban rufe idona ba" rau rau sukayi da fuska abin tausayi a tare suka had'a baki wajen ce "Mummy why?" hararan su tayi in a cool way ta Nina Aneeserh "sai yau Kika gadaman zuwa waje na to ku koma inda kuka fito nayi fushi da dukanku" marairaicewa sukayi da face fad'in "we are sorry Mommah" Murmushi sannan tace dasu "your apology is accepted" da tsalle sukayi hugging nata suna fad'in "thanks for accepting our apology Mommah" murmushi tayi tace amma "next time" da sauri suka ce "better" tace " to maza kuje ku watsa ruwa a jikin ku ku huta domin nasan akwai gajiya a tattare daku" "OK Mum" shine kad'ai abinda suka iya fad'a suka nufi ciki. ```Nima Rakiya a dai-dai lokacin na bisu d'akin ina ganin Ayusha ta shiga Toilet Aneeserh d'ora towel nace bari na basu waje letter naci gaba da d'auko muku rahoton.``` *ROOKIEY D BRST* [14:50, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_MY SPECIALPAGE IT ALSO GOES TO MY SPECIAL ONE❤❤❤_* *_A gift sent to me from Almighty, he showed me love lyk no other "LIKE A BLOOD BRO" his shoulders were alwaiz there for me to carry on when I was in a deep sorrow. he's someone i will cherish forever❤he care's so much about me and lend me a helping hands and never get tired of my endless demands._* ❤ *_WHO IS THIS ANGEL??? OF COURSE YOU ARE THE ONE���� UNCLE SULTAN MY PRIDE MY EVERYTHING IN LYF_* ❤ 11-15 Ayusha na fitowa daga wanka tace da Aneeserh " 'yan mata sai a tashi a shiga a watsa ruwa, wai mutum idan ya shiga wanka sai kace me canza fata,wallahi idan na gama shirya wa baki fito ba sauk'a zanyi na barki tunda dama ke ba bak'uwar gidan bace" "Mtswww!!! kin san ni ba bak'uwa bace zaki bi ki addabeni da mita,kuma da kike cewa ina dad'ewa a wanka ke d'in awa nawa kike d'auka kafin ki gama kwalliya lazy girl kawai" tana gama fad'in haka ta fad'a toilet da gudu dan tasan halin mutumiyar yanzu sai ta d'uma mata dundu dan ta tsani a ce mata lazy and she's lazy a reality. Murmushi Ayusha tayi tace "karki damu 'yan mata zanyi cin tuwon kishiya ramako ne" taci gaba da shiryawanta, minti goma sha biyar kacal ta d'auka wajen shiryawa har zuwa wannan lokacin Aneeserh bata fito ba murmushi tayi ta sauk'a k'asa wajen Mummy. tana fita da minti biyu kacal Aneeserh ta fito tana murmushi "Oh su masifatu an sauk'a k'asa za'a je a sauk'ewa Mummy rigima" wato a gaskiya yanayin closeness d'in Ayusha da iyayenta na birgeta sau tari ta kanji dama ace itace take samun wannan kulawar daga wajen iyayenta da taji dad'in rayuwarta,take wasu zafafan hawaye suka fara gangarowa daga kumatunta. Ayusha na isa falon k'asa ta taradda Mum & Dad na zaune suna hirarrakin sun irin na tsofaffin masoyan da suka shak'u da juna,da sauri ta k'arasa da gudu ta fad'a kan Daddy tana fad'in "Oyoyo Daddy na yau nayi missing naka a lot" had'e rai yad'anyi kad'an yace "gashi ni kuma banyi missing d'inki ba asali ma fushi nake dake" zaro ido waje tayi ta marairaice tace "yanxu Daddy da Autan naka kake fushi shi kenan" sai tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka shi abin ma dariya ya bashi yace "idan Auta tayi ba dai-dai ba sai a hukuntata, dan haka tashi daga jiki na, kuma na baki assignment ki binciko laifin da kikayi min daga wayewar safiya zuwa yanxu" shiru tayi na d'an wani lokaci tana tunanin irin laifin da ta aikata, a iya tunaninta dai tasan through out yau basu had'u da Dad ba to ko shi ne laifin da tayi? Yes!!! shi ne ma tasan yadda zata shawo kan Dad yanzu-yanzun nan. Sauk'a tayi daga jikinshi ta zuba gwiwowinta a k'asa tana fad'in "dan Allah Sweetheart kayi hak'uri na gano laifin da na aikata kuma na tabbata girman laifin na can-can ci a hukuntani haka amma duk da haka ina neman rangwamen horon da ake shirin yimin, Dad wallahi ba intentionally na tafi ba tare da mun gaisa ba,sanin cewa jiya ka kwana da ciwon kai yasa da na shiga wajenka ban tashe ka munyi sallama ba sannan aka sake samun akasin na manta wayana a gida,yanzu shigowa na gidan ban fi 30 minutes ba Afuwan Daddyn Auta" Murmushi yayi ya d'agota sama ya zaunar da ita kan cinyarshi sannan yace "shi yasa a kullum nake alfahari dake Auta a duk lokacin da kika b'ata min rai kina k'ok'arin tausasa ta da kalamai masu dad'i da zasu sanya ni cikin farin ciki Ina miki albishir cewa Daddyn ki ya sauk'o daga fushin da yake dake". Murmushi tayi tace "that's why i am always proud of you my Dad Allah ya bar min kai har k'arshen rayuwata" a dai-dai lokacin Anerserh ta shigo falon tana ganin k'awarta kan cinya ta tuntsire da dariya tana fad'in " Daddy sannu da zuwa, k'atuwa a kan cinya ko kunya bata ji, wallahi Daddy ka sauk'e ta zata tsufar mana da kai" murmushi yayi yace " yauwa Aneeserh ai in da sabo na saba da shagwab'an Auta Ina ganin ita da ta daina hawa kan cinyata sai na Aurar da ta barwa 'ya'yanta,ina ga ma kwanan nan zan Aurar da ita" dariyar mugunta Aneeserh ta Saki domin ta sani sarai Ayusha babu abinda ta tsana a yanxu sama da aure domin ita a cewar ko ta gama university sai tayi masters da PHD zatayi aure,so da hazak'a tace "wallahi Daddy a mata auren ko zata shiryu" tana gama fad'in haka ta gudu bayan Mummy dan ta sani sarai ta taro match, take hawaye ya fara zuba a fuskar Ayusha sauk'a yayi daga cinyar Daddy taje gaban Mummy ta zube "Mummy dan Allah dan Annanbi karki bari Daddy yamin aure wallahi har yanxu ni k'arama ce duka-duka fah am just 18yrs,wallahi ni aure baya daga tsarina a yanzu har sai nayi PHD " sai ta fashe da kuka. gaba d'ayansu sai suka kwashe mata da dariya Mummy tace "dai na kuka Auta babu wanda zai miki aure yanzu, shima Daddyn naki wasa yake miki ba yanzu zai aurar dake ba sai lokacin da kika samu saurayin da kike so, amma Ina so ki sani shi aure lokaci ne idan lokacin mutum yayi ko ya shirya ko bai shirya ba sai yayi babbar sunna ce mai k'arfi,sunnar Annabinmu Muhammad Sallallahu Alaihi wa'alihi wasallam saboda haka kar na sake ji kince baki shirya aure yanxu ba". Jikinta yayi matuk"ar yin sanyi sosai a sanyaye tace "na gode Mummy da kika tuna sar dani abinda ban gane ba in shaa Allahu daga yanxu na janye burina na cewa bazan yi aure yanxu ba amma Mummy Daddy bazai min auren dole ba ko" dariya abin ya basu Daddy ya kamo hannunta yace "zo nan Auta ni bazan tab'a miki Auren dole ba na baki dama ki kawo duk wanda kike so in dai ya cika sharud'an da addinin mu ya tsara shikenan" murmushi tayi tace "na gode Daddy na Allah ya barmin ku in rayu da ku" dariya Mummy tayi tace "Auta ko dai kin fara soyayya ne ban sani ba naga fuskarki d'auke da farin ciki mara misaltuwa" rufe ido tayi alamun kunya sannan tace "Daddy kaga matarka ko" murmushi yayi yace "a 'a Mummy karki takurawa Auta ta kuje can ku k'arata da d'iyarki" ya nuna Aneeserh. Aneeserh da ke rakub'e a gefe tana ganin ikon Allah a zuciyarta tanaiwa iyayenta addu'ar "Allah ya shiryesu ya ganar dasu gaskiya su fara nunawa 'ya'yansu so da k'auna" kamar daga sama taji Mummy na cewa "ai d'iyata wayayya ce ko gobe ta kawo miji aurar da ita zanyi,ko ba haka ba Aneeserh" murmushin k'arfin hali tayi ta sukuyar da kai k'asa. Ayusha ta tuntsire da dariya tace "dama ai ita aure take so yanzu haka tanada saurayi" da sauri Mummy ta katseta da cewa "in fitsari banza ne kaza tayi mana" dalilin da yasa haka ta fahimci cewa Aneeserh ta shiga matsanan cin kunya sakamakon katob'arar da Ayusha tayi. Daddy ma ya fahimci hakan shiyasa ya mik'e yana fad'in "ni zan wuce masallaci naji kamar anata kiraye-kirayen sallah saboda haku kuma kuje kuyi" kai tsaye dak'in shi ya wuce ya d'oro alwala ya wuce masallaci,suma saman suka hanye dan gabatar da tasu sallar. daga nan kuma suka ci gaba da gudanar da activities d'insu ,iyayen Ayusha mutane ne masu mutunci,karamci da sannin hak'k'in d'an Adam yabawa da nutsuwar Aneeserh yasu su barin yarsu yin mu'amala da ita tun suna 100level suka so ta zauna a gidan amma tak'i coz she don't want to be a boarding to them,shiyasa once idan tazo weekend sai ta bari sun nemeta saboda tsaro. Normally idan tazo weekend zata koma suna had'a ta shaa tara ya arziki to wanna karon ma haka, yau ta kama monday bayan sun tashi daga bacci sukayi sallah, wanka sannan suka shirya,d'akin Mummy suka nufa suka gaisheta sannan suka d'unguma wajen Daddy nan ma gaisuwar suka kwasa aka d'an tab'a barkwanci na minti biyar dayake Dad mutum ne me son barkwanci, ya bud'e side drower ya zato 20K ya bawa Aneeserh yana fad'in " 'yata ga wanna ba yawa kiyi managing" hannu biyu tasa ta k'arba tace "na gode Abba, Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i" "Ameen di'yar albarka" ya juyo da dubansa ga Auta yaga ta marairaice yace " ya akayi ne autar Babanta" k'ara shagwab'ewa tayi tace "Daddy ni baza a bani kud'in shaa mai ba" murmushi yayi yace "Auta kiji tsoron Allah jiya-jiyan nan fa kikayi full tank" sosa keya tayi tace "to a k'ara min pocket money Daddy" murmushi yayi yace "Auta dai ta rantse sai ta caje ni yau,any ga 5k nan ki rik'e" hannu biyu tasa ta karb'a tana godiya. a gaggauce sukayi breakfast sukayi sallama da Mummy suka fita suna isa school direct lecture hall suka wuce. A haka rayuwa taci gaba da tafiya har suka fara second semester exams,a ranar da suka gama Aneeserh ta wuce gidansu Ayusha kwanan su uku sannan ta tattara ta koma d'angyatin. ```To masu karatu Ku biyo Rakiya dan ganin inda ALLURA ZATA TONO GARMA....this is just the Beginning of the story. ``` *ROOKIEY DBEST* [14:51, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_This page goes to MUFEEN , AREEF (MY SON) ,MAIMUNA (Maman Fatiey) & Fatiey❤❤❤na gode da K'aunar ku Allah ya barmu tare_* 16-20 Rayuwa taci gaba da tafiya yau fari gobe bak'i,a haka har suka gama hutun su suka dawo 300level new session,abubuwa da dama sun faru sai godiyar Allah. wata rana sun fito daga lecture Ayusha ta kalli Aneeserh tace "k'awata kin bamu rani da yawa fa rabon da kizo gida weekend yaka 3 weeks fa" "k'awata ban da sharri fa duka-duka rabona da gidan two weeks kuma in shaa Allah this coming weekend a gida zanyi" "yauwa ko ke fah wallahi Mum &Dad ma suna missing naki kin san ni kad'ai ce a gidan nai ta musu rigima" "shegiya ba k'atuwa dake baki dai na hawa kan cinya ba wallahi ya kamata kiyiwa kanki fad'a na tabbata ko yanzu aka aurar da ke tsaf zaki zauna a gidan miji amma tsabar iya shege kiyi ta abu kamar yarinyar da ba'a yaye ba" dundu Ayusha ta d'uma mata sannan tace "shegiya sai ki aurar dani ai,idan ke idon ki ya rufe da soyayyah ni nawa a bud'e yake so allow me to shana,ni da aure sai nai PHD" "lalle baki da hankali k'awata har kin manta nasihan da Mummy ta miki akan aure ko, to wallahi ki nutsu ki farka daga nan nauyan baccin da kike aure shine mutunci d'iya mace saboda haka daga yanzu ki ma sanya aure cikin budget naki kafin grads" "Allahu akbar ya Al-sheik Allarammiya Aneeeserh matar Allaramma Mujaheed,any way naji magan ganunki may be Zan yi thinking a kai" " ke kika sani dai in kin ga dama kiyi dreaming ma" Dariya Ayusha tayi tace "dreaming d'in ma zanyi kuma duk abinda na gani in my dreams zanyi believing dashi" dundu Aneeserh ta d'uma mata tace "shegiya jaka Allah yasa ki gano aure a kwana kusa Ameen" "Hegiya muguwa ba Ameen ba,sai dai na gano aurenki da Mujaheed, yauwa k'awata wai me ya faru ne kwana biyu bana jin d'uriyarki da Mujaheed ne ina fata ba sab'ani kuka samu ba" " eh to k'awata zan iya cewa mun samu misunderstanding dashi" "kamar ya fa!!!?" "kin san tun last year yake bina akan yana so ya tura magabatan sa gidan mu iyaye na su san dashi nace ba yanzu ba, shine shekaran jiya ya sake tayar min da zance wai a gidansu an takura mishi ya fitar da mata idan ba haka ba zasu bashi duk wacca suka ga dama nayi-nayi na fahintar dashi matsalan ya kasa fahimta ta ni yanzu i'm totally lost and i don't know how to fix it" tana gama fad'in haka sai ta fashe da kuka. Da sauri Ayusha ta kamo ta, ta zaunar da ita kan wani resting chair itama ta zauna sannan ta sassauta murya tace "k'awata ki kwantar da hankalinki, komai yayi tsanani maganin sa Allah, ni banga laifin Mujaheed ba dan yace yana so ya turo magabatan sa ke ce fa nan kike min wa'azin aure,yanzu dai ba wannan ba ina so ki fad'amin mene ne damuwarki ni kuma na miki alk'awari in shaa Allahu sai zan taimaka miki wajen ganin kin cimma burinki" shiru tayi na d'an wani lokaci sannan tace "ki gafar ce ni k'awata,na san zaki iya yin komai dan ki sanya ni cikin farin ciki, bawai bana so na fad'a miki damuwa ta bane no I'm waiting for the right time,please ki gafar ce ni wallahi in time yayi zan sanar da ke" Shiru Ayusha tayi tana observing nata daga bisani tace " ba komai k'awata Allah ya kaimu lokacin" jikin Aneeserh yayi matuk'ar yin sanyi jin kalaman k'awarta ita kanta tasan bata kyautawa Ayusha bata tab'a boye mata damuwanta ko ya yake amma ita dai-dai da lokaci d'aya bata tab'a fad'a mata na ta ba,ba komai wannan karon dai ya zama dole ta sanar da ita duk da tasan cewa babu taimakon da Ayusha zata iya, in shaa Allahu in tazo weekend zata sanar da ita komai. Ayusha yarinya ce mai zurfin tunani da hangen nesa, ta dad'e da observing Aneeserh na facing problem and bata son kowa ya sani shi yasa batai insisting ta fad'a mata ba ta bar ta har zuwa lokacin da tayi niyar fad'a mata.suna a zaune a wajen wasu course mate's nasu suka zo sukayi joining nasu Fateema da Safiyyah sun dad'e suna hira daga bisani suka watse suka nufi parking lodge Ayusha ta d'auko mota tace da su Teema su tsaya tayi dropping nasu, ba musu suka shige motar a k'ofar hostel ta sauk'e Aneeserh sannan ta juyar da kan motar zuwa waje a dai-dai bak'in gate wani matashin saurayi wanda a k'alla zai kai 30yrs ya gobza mota, wani wawan birki taci ta tsaya,shi kuwa gogan zaune yake cikin motar sa ko kad'an bai da niyan fitowa rai b'ace ta fito daga nata motan ta k'araso tai masa knocking, a hankali ya bud'e k'ofar yana mai sauk'ar mata da mayatattun idanu wansa a kan ta kallon up and down tai masa sannan tace "Mallam kai makahon ina ne,ka buga min mota and you still have the gouts to seat kana nufin ni zan biyo ka" shiru yayi bai ce ko uffan ba har ta gama bal-ba-lin bala'in ta ta tafi. Da sauri ya bud'e motar ya biyo ta a baya yana fad'in "pretty wait!!! dan Allah kar ki tafi ki barni" manna mishi bajon mahaukata tayi ta shiga mota. Safiyyah ce ta kalleta tace "Beb i like your action,kin min dai-dai da baki saurareshi ba irin banzayen samarin nan ne da basu san me sukeyi ba" "Hmm!!! ni daman bani da lokacin shi ai yaci sa'a yau a Shatu nake wallahi da a Indo nake da yaga tsantsar wulak'anci" k'yalk'yalewa da dariya sukayi Teema tace "wallahi guy d'in A1 ya had'u over,wallahi ban gaji da kallon sa ba muka baro gun" wani dogon tsak'i Aysha taja sannan tace "ke wallahi banza ce a haka zaki k'are da kallon maza ina hud'uwar take anan, ni ban ma yadda yana da cikakken hankali ba domin abinda yayi mai hankali ba zai aikata ba" har suka isa inda zata sauk'e su basu dai na discussing issue d'inta, tana aje su ta pigi mota sai gida. Tun daga nesa take ta faman buga mai gadi da kansa yasan yau ba lafiya duk lokacin da yaji tayi irin wannan hon d'in yasan akwai matsala,da sauri yazo ya bud'e mata gate ya doka mata kirarin da ya saba ko kallo bai ishe ta ba ta shige ciki. a falon k'asa ta iske Mum & Dad daga musu hannu kawai tai ta haye sama baki suka sake suna kallonta, sai da ta kusa hayewa gaba d'aya Dad yayi gyaran murya yace "zo nan d'iyata,waya tab'a min haka kike cic-cin magani" Da gudu ta sauk'o ta fad'a mishi sai ta fashe da kukan shagwab'a Daddy yayi murmushin su na manya yace "kukan ya isa haka Auta fad'a min damuwarki" nan ta kwashe mishi da duk abinda ya faru from A-Z bayan ta gama koro bayani yace "yanzu saboda d'an wannan abin kika tada hankalinki, ki godewa Allah ma da abin ya tsaya a kan motar yanzu haka wani mugun abin ya tare, sannan cin mutuncin da kika masa bai dace ba ba irin tarbiyyar da muka baki ba kenan saboda haka kar na sake jin kin ci mutuncin wani, bari na k'ira Nazeer electrition yazo ya tafi da motar garage" "na gode Daddy in shaa Allah bazan sake ba" "good, ko ke fa" tunda aka fara show d'in Mummy bata ce komai ba sai da aka gama sannan tace "duk abinda ya kamata na fad'a Abbanki ya fad'a saboda haka ki jiyaye" "to Mummy in shaa Allahu zan kiyaye" "yayi kyau Allah yai miki albarka, tunda yau kin dawo da wuri shiga ciki ki huta anjima zan aike ki gidan Hajiya Zainab zata baki sak'o ki kawo min" "to Mummy bari na shiga cikin" ```To masu karatu anan na dakata for today kuci gaba da bina har zuwa lokacin da Allura zata tono garma``` *ROOKIEY D BEST* [14:51, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_Wannan shafin d'ungurugum d'inshi na sadaukar dashi ga k'awar Arziki FATEEMERH MUKTHAR D'AN-MALLAM (Yarmal) Amaryar December In Shaa Allah, Allah ya barku tare da Hubby❤❤❤yan LAKER'S Ku shirya akwai bikin bud'e madara @ KT lols��������_* 21-21 Misalin k'arfe biyar Ayusha ta shirya tsaf cikin wani maroon gawn me d'auke da milk Stone's a jiki simple make up tayi tai rolling kanta da milk vail ta d'auko milk jaka and shoe's ta sanya, wajen mirror ta nufa ta kalli kanta tsaf sannan ta murmusa tace "Masha Allah ashe ni d'in kyakkyawa ce" sannan ta fice daga d'akin, direct d'akin Mummy ta nufa. Tana shiga d'akin Mummy ta kalleta tace "Wow My Daughter kin gan ki kuwa irin wannan kyau haka Masha Allah, Allah ya sa a fita a sa'a" murmushi tai tace " na gode Sweet Mum,amma ban gane sa'ar da kike nufi ba" murmshi Mum tayi tace "yaro man kaza ai nasan baza ki tab'a ganewa ba so a bar zance kawai coz idan nace zan tsaya miki explaining tym zai tafi" "ok,Mum bani da kirki wallahi, rabona da gidan Aunty Zainab har na manta, kullum tazo nan sai tamin gori amma a banza" "Hmm....ke kika jiyo dai ba kullum in nace miki kije ki gaishe ta sai kina kawo min wasu unnecessary excuses naki ba idan kin je kya mata bayani ai" murmushi Ayusha tayi tace "Aunty Zainab tawa ce nasan yadda zan shawo kanta, so yanzu fad'a min sak'on kar na makara kin sa ba mota a hannu na" "je ki d'auki keyn mota ta ki tafi da ita" "no Mummy bar shi kawai ban jin zan iya driving yanzu zan hau adai-daita kawai" "shikenan Auta, idan kin je kice ina gaishe ta, sannan ki ce da ita ya labarin sak'on nan ne na jita shiru bata motsi, idan sak'on ya samu ta baki ki kawo min, sannan dan Allah ki kula da kanki Auta". "OK Mum in sha Allah zan kula" "good Allah yai Albarka" "Ameen Sweet Mum" Da yake gidansu ba nisa da bakin titi tana fita ta samu NAPEP me NAPEP yace da ita "Hajia wani unguwa za'a kaiki" "SARDAUNA ESTATE zaka kaini San nan ni kad'ai zaka d'auka ban san gayya" "Angama Hajjaju in dai masu gidan rana na aiki to babu inda baza a kaiki ke kad'ai ba" tunda ta shiga ta manna mishi bata kula shi ba saboda taga alama yana da rawar kai. Suna isa estate d'in yace "Hajiya ina muka nufa" directing nashi tayi zuwa k'ofar gidan Aunty Zainab tana sauk'a tace dashi nawa ne kud'in ka" "300 ne Hajjaju" 500 ta ciro a jaka ta bashi, ta juya zata tafi yace"Hajiya tsaya ki karb'i can jin ki" murmushi tayi tace "no ka bar shi kawai" "godiya nake Hajjaju Allah ya baki miji na gari me k'aunar ki" ta amsa mishi da "Ameen" ta wuce. Knocking k'ofar falon tayi, wata yarinya yar kimanin 7yrs ce ta bud'e k'ofan tana ganin Ayusha tayi murmushi tace "sannu da zuwa Anty kyakkyawa" dariya tayi tace"yawwa Cutie coz kema kyakkyawar ce" dariya yarinyar tai tace "na gode Anty, wajen wa kika zo Mummy ko umma, ko Mami?" murmushi tayi tace " yammata kai ni wajen Mummy" kamo hannun Ayusha tayi tace "muje" suna shiga falon ta taradda da Amaryar su Anty Zee Fatima wacca suke k'ira Mami wani kallon raini ta fara watsa wa Ayusha "sannunki" shine kalmar da ta iya fitowa daga bakin Ayusha "ke kuma daga ina" shine abinda tace da ita manna mata Ayusha tayi ta shige ciki ba tare da ta tsaya bata amsa ba "iyeh, lalle wannan yarinyar tacacciyar mara mutunci ce ki tako har gidan nawa sannan ki kawo min iskanci, hmmm zaki gane baki da wayo" ita kad'ai take bambamin ta domin Ayusha bata san ma tana yi ba, falon Anty Zainab yarinyar ta kai ta sannan tace da ita "Anty zauna anan,bari na miki magana da ita tana kitchen" "OK 'yan mata" zama tayi kan kujera ta tsurawa falon idon tana kallo komai na falon d'os da shi gwanin ban sha'awa a zuciyar tana fad'in, " Anty Zainab sarkin gayu komai nata na 'yan gayu ne jibi falon ta kamar na sabuwar Amarya, Allah sarki rayuwa kamar ban zauna a gidan nan ba nida nake shafe wata da watan ni anan amma yanzu a k'alla na kai kimanin shekara goma ban zo ba, rayuwa kenan" Tana cikin tunani taji an dafa ta ana fad'in "Aunty Me kyau ga ga drinks kisha Mummy na zuwa" firgita tayi tace "oh Cutie har kin bani tsoro" "Sorry Anty Mekyau nai ta sallama shiru baki amsa ba shine nace bari na dafa ki ko zaki jini" " oh!!! haka ne fah na shiga duniyar tuna ni ne" "tuna nin me Anty" "Ba komai Cutie" "to Anty wani drink zan mik'o miki HAPPY HOUR KO MULT" "bani Happy hour dan ban cika sha Maltina empty ba" Happy Hour ta tsiyaya mata a tumbler, sannan ta matso mata da center table gaban ta tace "Anty na zuba miki drink d'in gashi ki had'a da snack's" "wow Cutie wanna duk nawa ne ni kad'ai, thank you very much, amma bani kad'ai zan ci so kema d'auko cup kiyi joining d'ina" ba musu tace "to" ta wuce d'auko cup tare da Anty Zainab suka shigo tare tana shigowa tace "Lalle kam Anty Mekyau ,Afrah ta shigo ta same ni wai in zo Anty Mekyau tazo, na rasa gane wace ce Anty Mekyau ashe ke ta ke nufi, ko da yake bata san ki ba domin rabonki da gidannan tun kafin a auro mahaifiyar ta" zaro ido waje tayi tace "Amma ba yar matar da nagani a babban falo bane" "dariya Anty Zainab tayi tace "no mamarta bata nan ta fita unguwa ban ce ta dawo yanzu ba saboda bata dad'e da fita ba may be Sumayyah kika gani" "OK" Nan dai suka shiga gaisawa da junan su Anty Zainab tai mata tatas sannan tace "nasan wannan zuwan ma ba zuwan kanki bane aiko ki akayi gobe nake shirin aika mata sak'on sai gashi kinzo" dariya tayi tace "kimin afuwa Aunty abubuwa ne yamin yawa shiyasa bana samun damar zuwa amma In Shaa Allah daga yanzu zan dinga zuwa ko dan Cutie ma" "a lalle wato kema da sunan da kika sa mata kenan to shike nan idan zakiyi aure zamu baki ita" gaba d'ayan su suka kwashe da dariya.k'iran sallan magrib akayi Aunty Zee tace "Ayusha shiga ciki kiyi sallah,naji an fara k'iran sallah" "to Aunty" ```Masu karatu kuyi hak'uri da wannan ku ci gaba da bibiyar Allura ta tono garma``` [14:52, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_Wannan shafin naki ne HAUWA BASHIR ISA (MEKWI A.K.A EXCLUSIVE) The most shortest girl among the giant set of LAKER'S 2011 @ HIGSS lols������ ni kaina na san kin fi kowa K'aunar ALLURA TA TONO GARMA��i heart you Beb❤Allah ya barmu tare_* *_NOTE:_*```Ku min Afuwa masu karatu nayi Making mistake wajen numbering page maimakon 21-25 nasa 21-21 so zan cigaba da 26-30 hope you will not be confused ❤ ``` 26-30 Ayusha na shiga ciki ta nufi toilet ta d'oro alwala tayi sallah, bayan ta idar da sallah Anty Zainab ta shigo fuskar ta d'auke da murmushi tace "sorry Ayusha tunda kika zo bamu zauna sosai ba yau nice a kitchen shi kuma babansu baya cin abincin mai aiki, so ban samu na d'aura girkin da wuri ba har magrib tayi, yanzu na gama abinci,Allah-Allah nake kar yazo ya samu ban gama ba" "wallahi ba komai Anty, miyan me zakiyi na shiga na miki tunda nayi sallan" "la ki bar shi kawai kar na wahalar dake, nasan baki dad'e da dawowa daga school ba, gajiya bai gama barin ki ba, so idan na idar nayi kawai miyan alayyaho ne bai da wahala na gama yanka komai da na idar zan had'a" "walahi yau da wuri na dawo so bari naje nayi kawai" "to shi kenan Allah yayi albarka" "Ameen" Ayusha kitchen d'in taga komai neat kamar ba girki ake a ciki ba, murmushi tayi a fili tace "Aunty Zee kenan gidan tsafta da gayu wai a hakan girki take amma komai tsaf dashi, ni kitchen d'in ne ma ya birgeni komai orange" Bayan ta gama sumbatun ta ta nufi gas ta kunna, tukunya ta d'aura ta zuba mai ta soya da albasa, da yake man gyad'a ne soyuwan sama-sama tai masa, sannan ta d'auko sulallen nama ta zuba, shima ta d'an razana shi sannan ta zuba ruwan sulale kad'an ta sa taruhu da spices ta rufe tukunyar, kafin tukunyar ta tafasa ta wanke kwanu kan da tayi using bayan taga wankewa ta bud'e ta zuba Alayyaho da albasa mai tarin yawa ta d'auko sardine guda biyu ta bud'e ta zuba ciki ta rufe. A take kitchen d'in ya turnik'e da k'amshi nan take ta kuma d'auraye sauran kayan aikin,5 minutes kacal allayahon yayi ta sauk'e, wasu zafafan warmers ta hango a gefe take ta nufi inda suke ta d'auko k'aramin ta juye miyan a ciki sannan ta mai da shi inda ta d'auko, bud'e babban tayi taga wani irin abinci Anty Zee ta girka, tana bud'ewa taci karo da had'add'en cous-cous anyi ganishing nashi da carrots & peace gashi yayi wasar-wasar gwanin ban sha'awa,rufewa tayi ta k'ara tattare komai sannan ta nufi fridge ta bud'e fruits ta gani a ciki sai yoghurt . Banana ta d'auko ta b'are guda shida ta yanka su dai-dai misali sannan ta d'auko yoghurt roba biyu,banana ta fara sawa a blander sannan ta zuba yoghurt d'in a cikin tai blending, sai da ta tabbata ya nik'u sannan ta tace da rariya cikin bowl ganin yayi yadda take so yasa ta juye a Jug ta maida fridge, sannan ta dawo ta sake saftace kitchen d'in ta d'auki abincin ta shiga da shi ciki tana shiga parlor ta nufi dinning area ta shirya komai tsaf sannan ta wuce ciki wajen Anty Zee. Tana shiga ta taradda Anty Zee ta idar da sallan isha tana lazimi toilet ta shiga ta sake d'auro alwala ta tada sallah. Bayan ta idar da sallah Anty Zee tace "sannu da k'ok'ari 'yata na je naga miyan ki sai yayi dad'i in yanzu haka falon ya turnik'e da k'amshin d'adi,Allah dai yayi albarka d'iyar arziki, badan kina da lectures gobe ba da kin kwana gobe ki tafi" "karki damu Anty in shaa Allah upper week zanzo nayi weekend anan" da sauri tace "why not next week Ayusha" murmushi tayi tace "wallahi next week ina da visitor,Aneeserh zata zo min weekend" "okay, wace Ayusha kuma?" " baza ki santa ba Anty wata course mate d'ita ce takan zo tai mana weekend a gida" "to why not kuzo tare" "Hmm.....ai Mummy baza ta bari ba tana son zama da Aneeserh sosai so ki bari upper d'in in shaa Allahu zan zo" "to shi kenan ba komai Allah ya kaimu" "Ameen" Kamar daga sama suka ji ance "Hajia Zainabu Abu mai dad'in tuwa, yau kuma wani daddad'an kikai mana ne tun daga bak'in gate k'amshin girkin ki ya bigi hanci na murmushi tayi tace "Alhaji kenan kai kullum baka rabo da zolaya to yau ba ni na girka abincin ba d'iyar ka ce ta girka" sai a sannan ya lura da mutum a d'akin kallon farko da ya mata yaji bugun zuciya take yaji gabanshi yayi mummunar fad'uwa take ya fara furta kalmar "innalillahi wa'inna ilaihi raj'un, Allahumma ajirni fii nusibatihi wa aklifni khairan minha" sannan ya tattaro dukkanin nutsuwar sa yace "Hajjaju wace ce wan nan d'in ban wayeta ba wallahi" murmushi Anty Zee tayi tace "baza ka gane ta ba ai d'iyata Ayusha ce yar wajen Aminiyata" "Oh!!! kina nufin wannan Ayusha 'yar wajen Hajiya Fatima ce?" "kwarai kuwa" "Allah mai ikon wallahi ko a hanya na ganta bazan shaida ta ba, yarinyar da take k'arama bata da wajen zuwa hutu sai nan,idan ban manta ba rabonta da gidannan tun tana da shekara takwas" "kwarai kuwa Alhaji coz yanzu haka tana da 10yrs which means shekararta goma bata zo ba" Shiru Ayusha tayi tana sauraron su sai da suka gama lissafe-lissafen su ta tsugunna har k'asa tace "Abba ina yini" "lafiya lau Ayusha, ya kike ya bayan rabuwa, yanzu kina JSS nawa" murmushi tayi tace "300level nake" da sauri yace "ikon Allah girman d'an mutum ba wuya ni ina miki batun JS ashe ke har kin shiga jami'a, to Allah ya taimaka Allah yayi jagora" "Ameen" Aunty Zee tace "gaskiya yallab'ai ka ragewa d'iya ta classa dayawa yarinya da a 16yrs tayi candy" "sorry Hajjaju, a min afuwa naga alama so kike ki hana ni cin girkin d'iyar ki shiyasa kike son maida gobe tomorrow" "ina ni ina hana ka kwasar gara, yakamata muje muci saboda dare nayi Ayusha zata tafi gida kuma ba motor a hannun ta" "au dama ba kwana ta kawo mana ba, shi ke nan muje muci in yaso sai na kaita dan bai kamata a barta ta tafi ita kad'ai ba" gaba d'ayansu suka d'unguma sukayi falo don yin dunner. ```Nima Rakiya na kwashi tsumman legs d'ina na basu waje domin k'amshin miyan Ayusha ya tsuma ni dayake daukan rahoto nazo ba kwad'ayi ba and nasan muddin Ayusha ta hangoni zatamin bismillah lols�� na barku lafiya dearies kuci gaba da bibiyar labarin akwai disaster a next page ``` [14:53, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *QUOTE: Doing Good for a good done to you is simply repayment, whereas doing good for an evil done to you is a tremendous virtue. _THIS PAGE IS SPECIAL IT ALSO GOES TO MY SPECIAL ONE Auwal Shanu (MY ROSE��)_* 31-35 Alhaji ne a gaba Aunty Zee da Ayusha na biye dashi a baya suna isa dining Alhaji ya zauna sannan Anty Zee ta zauna, Alhaji ya kalleta yace "Hajjaju ya banga d'iyar tamu ba ko kunya take ji ba zata iya cin abinci a gaba na ba" "Hmm!! in dai Ayusha ce zata iya amma fa tare muka fito da ita daga d'aki, bari kawai nayi serving naka sai naje wajen ta muci tare" mik'ewa tayi ta fara serving nashi sai ga Ayushu ta fito daga kitchen ta shigo da tire a hannun ta me d'auke da Jug & cups. Anty Zee tace "Ayusha ke dama kitchen kika shiga har mun fara tunanin ko kunya kike ji baza ki iya cin abinci da Abban ku ba" murmushi tayi tace "ba haka bane dazu da na gama girkin na had'a wani local drink shine nasa shi a fridge dan yayi sanyi " da sauri Alhaji yace gaskiya "Ayusha kina ji da iyayen nan naki har wani drink kika yi preserving that's good Allah ya miki albarka" "Ameen" tace sannan taci ci gaba da serving nasu. suna cikin ci Alhaji yace "Hajiaya a ina zan samu irin cous-cous na shuka saboda b'aci wan rana kar a zo wata rana a rasa a kasuwa, na godewa Allah da yasa na shuka Alayyaho tun tuni kin ga bani da case da wannan" Hajiya tace "Hak'k'un gaskiya ya kamata mu bin ciko irin amma ka d'an kurb'i lemon kad'an ko Allah zai sa a tuno inda za'a samu irin" Alhaji dai bai ce ko k'ala ba ya d'auki cup ya kai baki bashi ya sauk'e wannan kofin ba sai da ya shanye lemon da ke ciki tass sannan yace "Hajjaju k'aro, wato a hausawa sunyi gaskiya da suka ce wanda ya bar gida gida ya bar shi, ni fa dama can nafi son natural drinks akan artificial, dan Allah Ayusha ki zo mana hutu kinga zaki taimakawa Hajjaju sosai wajen sarrafa drinks" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, Anty Zee tace "lalle Ayusha yau kin ciri tuta tunda Abban Fahad yayi santin girkin ki, shi fa ba girkin ko wace mace bane yake birgeshi, saboda haka Alhaji a bamu tukwici" "an gama uwargida sarautar mata" haka dai suka d'an tab'a barkwan ci daga bisani Hajiya taja Ayusha ciki ta bata sak'on Mummy suka fito, a falo suka tarad da Alhaji, hannu yasa a aljihu ya ciro 20K ya bawa Hajia yace "ga tukwi cin d'iyar ki" hannu biyu tasa ta karb'a tai masa godiya sannan ta mik'awa Ayusha tace " ga tukwicin ki nan d'iyar kar ki kuskura kimin gardama dama" hannu biyu tasa ta karb'a sannan tace "na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya k'ara bud'i" yaji dad'in addu'ar da tai mishi so da sauri yace "Ameen, muje in kaiki da wuri kar dare yayi sosai" "Gaskiya kam, yanzun nan ma Hajia Fatima ta k'irani nace da ita yanzu zata zo" cewar Anty Zee Kenna da sauri Alhaji ya suri makullin mota ya yi waje suka biyoshi a baya,Anty Zee da kanta ta bud'ewa Ayusha mota tace "na gode d'iyata, idan kin je kice da Aminiya ina gaisheta" "zata ji" Malam Iliya mai gadi ne yayi saurin bud'e gate saka makon hon din Fahad da yaji, yana shigowa su kuma suna fita hannu ya d'agawa Abba shima ya d'aga masa yayi ya shi ge. Tun da suka fara tafiya babu wanda yace da d'an uwansa k'ala har suka isa gida, yana sauk'eta tace "na gode' yace "ba komai idan kin shiga ki gaida min iyayen naki" Anty Zee na zaune a falon Fahad ya shigo sallama yayi ta amsa sannan ya samu waje ya zauna yace "Mum barkan ki da gida, wallahi yau d'innan some how nake jina na rasa me ke min dad'i wallahi" "dole kaji ka some how mana Fahad,tun safe ka fita baka dawo ba na tabbata yunwa da gajiya ne suka maka rubdugu" murmushi yayi yace "wallahi rabo na da abinci tun breakfast, kuma yanzu haka bana jin zan iya cin abinci wallahi" " subhanallah!!! me ke damun ka haka har ya hana ka cin abinci, kasan fa kana da chronic ulcer kuma sannin kanka ne Doctor ya hanaka wasa da cin abinci,dan haka bari na tashi na kawo maka kaci yanzu-yanzun nan a gaba na" tana gama fad'in haka ta nufi kitchen murmushi yayi yace "Mama na ta kaina bata tab'a barina na zauna da yunwa,Allah ya bar min ke tawan" Afrah ce ta shigo falon,da gudu ta d'ane cinyar Fahad tana fad'in "Yaya sannu da zuwa,yau tun safe da ka fita baka dawo ba har Anty Mekyau tazo ta tafi" "yawwa Little,wace ce kuma Anty Mekyau?" a dai-dai lokacin Anty Zee ta shigo hannun ta d'auke da tire ta zubo mishi abincin a plate da jug &cup sai da ta ajiye tiren sannan tace "Afrah uwar surutu,ba fa kowa ce kyakkyar da take nufi ba illa k'anwar ka Ayusha yar gidan Hajiya Fatima" "oh!!! Mummy dama yarinyar tana duniya wallahi na ma manta da ita da yake mun dad'e bamu had'u ba" "ai idan ka ganta a hanya ma baka shaida ta ba dan ta girma ta zama 'yammata,yanzun nan Abban ku ya ya kaita gida, karma ka biye surutun Afrah ga abinci na kawo maka kaci" Duk da cewa ba wani yunwa yake ji ba ya zama dole ya d'and'ana wannan domin kuwa tunda ta shigo da abincin k'amshin ya mamaye shi. jawo plate d'in yayi ya kalli Afrah yace "Little je ki d'auko spoon muci tare" "na k'oshi tun d'azu Anty Mekyau ta samun nawa naci" "gaskiya kina ji da wannan Antyn naki" Anty Zee dai shiru tayi tana kallon shi, tun yana d'eban abincin a hankali har ya fara rushing bai tsaya ba sai da ya cinye tas ya kora da drink sannan yace "Alhamdulillah, Allah na gode maka da ka bani mahaifiyar da tafi ko wace mace iya girki a duniya, Mummy tun da nake a duniya ban tab'a shan drink me dad'in wannan ba, Mum wannan miyan Zogale ne ko me? gaskiya idan da saura ki ajiye min na d'umame" Dariya sosai Anty Zee tayi sannan tace "oh!! ni Zainabu Abu yau d'iyata ta sace min zuciyar d'a da uba da girki, Abban ku ma haka yayi ta santin abincin nan kai ma kazo kana buga naka santin" "Mum kina nufin ba kece kika girka abincin nan ba?" "cous-cous kawai na dafa sauran kuma Ayusha ce tayi" "wow!!! gaskiya tayi k'ok'ari sosai dama a ce yadda ta iya girkin nan haka pretty ma ta iya" "pretty kuma!!!,wace ita?," Anty Zee ta fad'a in shock domin tun da take da Fahad bana shekarar shi 30 amma bai tab'a mata zan cen budurwa ba" Sosa kai ya fara yi yace " wallahi M..u..m d'azu ne na shiga University wajen Sa'eed shine accidentally na buga mata motar ta, to bata tsaya ta saurare ni ba tayi tafiyar ta shine abin yake ta damuna, ban san ina zan sake ganin ta ba" Murmushi Mum tayi tace "kwantar da hankalin ka My Son in shaa Allahu zaka sake ganin pretty,ka bata hak'uri,ina ce daga ka bata hak'urin shike nan?" girgiza kai yayi yace "No! Mum ba shike nan ba" "OK! then what next!!!" ta fad'a tana kallonshi mik'ewa tsaye yace "good nyt Mum a bar zan cen kawai"yayi gaba a bin shi murmushi tayi a zuciyar ta tace "wato My Son ya fara fad'awa tarkon so, ya Allah ka bashi sa'an abin da yake nema, Allah ka bayyana mishi pretty" Ayusha na shiga ciki ta tarar da Mum &,Dad a falo suna hira,da gudu ta fad'awa Dad tana fad'in "Oyoyo Sweet Papa yau nayi missing naka sosai, i hope kai ma kayi missing" "nayi missing naki sosai Auta, tun d'azu nake jin gidan some how saboda baki nan" "Allah sarki My Love yanzu kam na dawo zaka ji ka normal" "tabbas Auta na naji normal yanzu" dariya tayi tace "Alhamdulillah tunda kaji garau bara naje na kwashi gaisuwa wajen Sweet Momma na" "Hmm....dama kin rik'e gaisuwar ki tun da Daddyn ki kad'ai kika sani kuma kike missing" "haba Sweetheart baki gane bane shi fa Dad rabona dashi tun da na dawo daga school while ke kuma bamu wani dad'e da rabuwa haba Habibty kar kiyi fushi da Autar ki mana" "to shike nan Auta na karb'i uzurin ki, ya kika baro min Aminiyar tawa" lafiyan ta k'alau tana gaishe ki" nan dai Ayusha tai ta basu labarin gidan tare da kud'in da Abba ya bata, su Mummy harda d'aukan ta k'ira Anty Zee tai musu godiya. 10:00pm nayi Ayusha tai musu sallama ta haye d'akinta tana shiga ta rage kayan jikin ta ta fad'a wanka tai shirin kwanciya, tun da ta kwanta ta nemi bacci sama da k'asa yak'i zuwa babu abinda idanun ta ke hasko mata sai fuskarsa, kunnuwanta na d'auko mata sautin Zazzak'ar muryar sa me kama da busar sarewa a yayin da yake fad'in.............. ```To fah masu karatu nawa kunnen ya kasa jiyo mana sautin muryar tasa kuyi min afuwan haka amma in shaa Allah zan ci gaba da bibbiyar Ayusha dan gano cewa wani me sa'an ne yayi tattaki ya ziyarci zuciyar ta a wannan daren ``` *ROOKIEY D BEST* [14:53, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *_This page is for you FATTY AXLAND (Mrs Lameed'o) Happy Birthday to you my special friend WLLNP❤Hip��Hip��Hip��Hurray_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* 41-45 Tunda suka shiga lecture ba abin da take ganewa, attention d'inta complete ya karkata ga tunanin guy d'in da ya buga mata mota, burin ta shine ta ganshi ta bashi hak'uri ko ta samu relief. Kamar daga sama taji an tab'a ta ance "Baby in love tashi mu tafi kowa ya watse ya barmu" a firgice ta juyo ta juyo da kallon ta ga Aneeserh sannan ta sauk'e wani zazzafan ajiyan zuciya tace "wallahi har kin bani tsoro" ta kalli hall d'in wayam sannan ta sake cewa "yaushe aka watse aka barmu mu kad'ai" " dama ina zaki sani kin tsunduma cikin kogin so" mik'ewa Ayusha tayi tace "kin ga malama bana son sharri, kefa dama baki iya samun abu ba daga baki labari sai ki canza akalar zancen, dan haka bana so zancen ya tsaya a haka" murmushi Aneeserh tayi tace " 'yanmata stop deceiving your self frankly speaking you are in love dan haka zan taimaka miki da addu'a Allah ya had'aki da lucky guy d'innan da ya sace miki zuciya " murmushi Ayusha tayi tace "ni na dad'e da gano cewa kina da mental problem so na miki uzuri lets go " Fitowa sukayi daga hall Aneeserh ta rakata bakin gate ta tari Napep bcoz na cikin school d'in is occupied with people, sallama sukayi da junan su sannan suka rabu. A b'angaren Fahad kuwa yana fitowa daga Fatie Shema estate ya karkata akallar motar shi zuwa hanyar da zata kai shi main road na 'Yar_adua University, agogon hanunshi ya duba yaga time 3: 45pm waje ya Samu yayi parking a kusa da wani masallaci, alwala yayi yai sallan la'asar yana mai addu'an Allah ya had'ashi da pretty d'insa. 4:05pm sharp ya fito daga masallacin motarsa ya nufa gaggawa saboda kar ya makara wajen neman pretty, tuk'i yake a nutse zuciyar sa na mararin kallon ta yana zuwa dai -dai da wajen wani road division d'aga idon da zai yi ya kalli right caraf yayi arbada da side view d'in ta, kokwanto yake kamar ita kamar ba ita ba, bai yi aune ba yaga ta karkato da fuskarta zuwa side d'in da yake, ba shiri ya karkata akalar motarsa daga left zuwa right dan ya cimma su amma unfortunately sun mishi nisa, wani wawan tsaki yaja yace "pretty me yasa zaki min haka, kin san baza ki bari muyi magana ba me yasa zaki bayyana gare ni, dan Allah ki tausaya wa rayuwa ta, ki tsamo zuciya ta daga kogin son ki " haka dai yayi ta sumbatun sa shi kadai kamar wani tab'ab'b'e, da yaga babu sarki sai Allah sai ya hak'ura ya koma gida. A b'angaren Ayusha kuwa tana zaune cikin Napep tana ta sak'a da warwara ta yadda za'ayi ta had'u da wannan guy d'in, ji kamar wani abu ta mitsine ta, da sauri ta dawo daga duniyar tunani juyawan da zata tayi arba da kyakkyawar fuskarsa yana k'ok'arin juya kan motar sa da sauri tace da mai Napep d'in "Malam yi sauri ka k'ara speed uzurin gaggawa ya taso min" shi ko kamar jira yake da sauri ya zaburi Napep a 90. Yana sauk'e ta a k'ofar gida ta zaro 1K ta bashi ta nufi k'ofar shiga gida "Hajiya tsaya ga can jinki " "No ma rik'e na barma" "Godiya nake ranki shi dad'e Allah ya saka miki da alkgairi" "Ameen" tace sannan ta shige gida. As usual Mum & Dad ta tarar a folo gaishe su tayi ta nufi upstairs Mum ce ta dakatar da ita "Auta dawo nan, akwai maganar da muke son yi da ke yanzu" dawo wa tayi ta samu guri ta zauna a k'asa. Dad ne ya fara magana kamar haka "haba Autar Mum &Dad me ke damunki ne kwana biyu naga kin canza, idan wani abu kike da buk'ata ai sai ki sanar mana ba kisa kanki a damuwa ba, ke kanki kin sani farin cikin ki shine namu babu abin da zaki nema mu kasa miki face yafi k'arfin mu, saboda haka feel free ki fad'i buk'atarki in shaa Allahu zamu miki gwargwadon iyakar mu" k'ak'alo murmushin dole tayi tace " babu abunda nake buk'ata Dad, kawai dai boko ne ke gara ni, assignment sun min yawa ga thesis dake gaban mu that's all" "Ayusha yaushe kika fara b'oye mana damuwar ki, wannan maganar da kika fad'a ba gaskiya bace, ni na haifeki nafi kowa sanin halinki saboda haka fito fili ki fad'i mana damuwar ki"cewar Mummy kenan. Shiru tayi for some seconds sannan ta sauk'e ajiyar zuciya tace "Mum & Dad ina alfahari daku kun kasance nagartattun iyaye masu kula da sauk'e nayin da Allah ya d'aura musu, na gode sosai da kulawar ku gareni Allah ya barmin ku, ina so ku kwantar da hankalin ku, ku yarda cewa babu abinda ke damuna face boko stress kun manta 300level nake yanzu komai k'ara zafi yake" To shi kenan "Auta Allah ya tabbatar mana da alkhairi" "Ameen thumma Ameen iyayen k'warai " zama tayi suka sha hira da iyayen ta har dare suna tare, da lokacin bacci yayi tayi sallama dasu ta nufi makwanci ta sai bacci ya gagara tunanin shi ya sake dawo mata, wani zazzafan hawaye ne ya fara gangarowa daga idonta. Zuciyar ta ce ta fara tariyo mata abinda ya faru d'azu take tace "Ayusha why!!! me yasa zakiyi haka, ke da kike nemansa ruwa a jallo ki bashi hak'uri amma zaki guje masa, kina da tabbacin zaki sake had'uwa dashi nan gaba!?" sai ta fashe da kuka "wayyo ni Shatu na cuci kaina idan na mutu da hakkin mutumin nan me zan cewa mahalicci na, na tabbata cin mutuncin da nai masa ne ke addabar zuciya ta da zaran na bashi hak'uri komai zaiyi normal. ```to masu karatu Ayusha dai ta kasa amincewa tana son Fahad all what she knows is that tana bashi hak'uri shike nan zata ci gaba da normal life nata. Shin haka abin yake ko yaya ina,idan kuma akwai wani solution da kuke gani Ayusha zata bi tunanin Fahad ya bar zuciyar ta ta ko da basu had'u ba to sai ku bata ina jiran comments naku kafin nayi typing next page NA BARKU LAFIYA taku har kullum``` *ROOKIEY D BEST* [14:54, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_Kindness Indeed Is Kindness I will never ever forget you in My life, you are more than a friend to me, My love for you is parmanent no wala-wala no algus I really appreciate your kindness, love,care and concern, you always put me in the right part when I'm wrong, you make sure i succeed before we depart i really miss you My Mentor HANEEFAH USMAN the whole page is your's������i heart you Beb❤ keep on rocking dear you rock even in the heart of your enemies LONG LIVE MY HANNEE_* 36-40 Babu abin da kunnuwan ta ke d'auko mata sai sautin zazzak'ar muryar sa me kama da busan sarewa a sa'ilin da yake ce mata "pretty wait!!!" a fili ta furta kalmar "OMG!!,wallahi ni d'in nan banza ce me yasa na wulak'anta shi ban tsaya na saurare shi ba, to wai ma ina ruwa na dashi ne da zan tsaya ina tunanin shi may be ma ya manta da existence d'ina yana can yana harkokin gaban sa ya barni da tunani!" tana ta tunane-tunen sa har sarkin iya sata ya sace ta, a b'angaren Fahad ma haka abin yake tunda ya shiga d'aki ya watsa ruwa ya haye gado bai sake sanin halin da yake ciki ba dan ya tafi duniyar tunanin pretty bai samu ya rintsa ba har asuba. Tunda bacci yayi awon gaba da ita bata farka ba sai 6:30 a firgice ta tashi tana salati, tana ganin time tace "ya salaam!!!, yau nice na makara banyi sallar asuba a kan lokaci ba" da sauri ta sauk'o ta nufi toilet ta d'auro alwala ta gabatar sallah da azkar sannan ta fad'a toilet tayi wanka, a gaggauce ta shirya cikin wani material gown rose pink, light make up tayi sannan ta d'auko milk veil tai rolling takalmi da jaka ma milk sannan ta feshe jikinta da designer perfume na FARASHA ta fito daga d'akin ta nufi wajen Mummy. Tana shiga d'akin Mummy taga wayam da alama bata ciki so direct kitchen ta nufa ta taradda ita tana had'a musu breakfast, " Morning sweet Momma da fatan kin tashi lafiya!" "lafiya lau Auta,har kin fito, to maza je ku gaisa da Daddyn ki a falo kiyi break" "Mum ni fa bana jin zan ma iya cin abincin nan ba yau nayi latti sosai" tana gama fad'in haka tayi saurin ficewa daga kitchen d'in dan tasan halin Mummy yanzu zata sata a gaba tace sai tace and ita kwata-kwata ma bata buk'atar cin komai. A falo ta iske Dad d'urk'usawa tayi har k'asa tace "Morning Dad da fatan ka tashi lafiya" "lafiya na lau Auta an shirya boko kenan, yana da kyau a dinga bada himma, Allah ya miki albarka, ya sanya albarka a rayuwar ki ya baki sa'an abinda kika je nema" "Ameen Thumma Ameen Sweet Papa, ni zan wuce school" "ki tsaya muyi breakfast sai nayi dropping naki tun da ba motor a hannunki" "A'a dadi ka bari zan tafi a NAPEP coz idan na tsaya break zanyi latti" "ok ba damuwa ga 5k ki rik'e a hannunki ko zaki buk'aci wani abu" "No Dad ka bar shi akwai kud'i a hannu na wanda mijin Anty Zee ya bani jiya" "to shi kenan Auta a dawo lafiya Allah ya kare" " Ameen" Tana fita k'ofar gida ta samu NAPEP ta shiga, a cikin gida kuwa Mum & Dad na breakfast Daddy ya kalli Mummy yace "Fatima wai baki fahimci wani changes a tattare da Auta ba ne?, naga yau d'in a bai-bai take" "wallahi Alhaji rigani furtawa kayi amma tun jiya da daddare na fahimci hakan,amma koma miye ne anjima idan ta dawo sai mu tambaye ta" "to shi kenan Allah ya kaimu anjiman dan ni sam bana son ganin Auta ta cikin damuwa" haka dai sukayi ta tattauna wa game da batun Ayusha. Tana shiga school ta k'ira Aneeserh a waya, ringing biyu yayi tayi picking "Hello K'awata wai kina ina ne tun d'azu ina ta trying layinki ban samu ba yanzu har Mr Patrick yayi lecture baki nan" "wallahi yau makara nayi ban tashi da wuri ba yanzu haka na shigo school d'in kina ina" "ok ki zo ina zaune a bayan library" "ok to ganin nan zuwa" Tana zuwa bayan Library ta hango Aneeserh a zaune waje ta samu kusa da ita ta zauna sannan suka gaisa kallo d'aya Aneeserh tai mata ta gane tana cikin damuwa sassauta murya k'asa tayi sannan tace "k'awata me ke damun ki dan naga damuwa k'arara a fuskar ki" "ba komai kawai dai bana jin dad'i ne" " Hmm... K'awata kenan to ai baki san wani abu ba duk wanda yasan ki a jiya ya ganki yau ya san kina cikin damuwa balle kuma ni da muke tare da ke kullum ya za'ayi dan naga changes a tattare da ke na kasa fahimta kawai Malama ki fad'a min matsalar idan da taumakon da zan iya sai nayi" shiru tayi na d'an wani lokaci sannan daga baya ta sauk'e wani dogon ajiyan zuciya sannan tace "jiya bayan mun sauk'e a hostel mun juyo", nan dai ta zayyane mata labarin Fahad hatta baccin da ta kasa saboda shi bata b'oye mata ba daga bisani tace "wallahi ni babban damuwa ta ma shine bai wuci ina zan ganshi na bashi hak'uri ba" Aneeserh tayi shiru tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata in sha Allahu Allah zai bayyana miki shi and also na fahimci cewa zuciyar ki tana k'ok'arin fad'awa tarkon so ko ma in ce ta fad'a ciki tsundum" "lalle yarinyar nan baki da hankali dan nace miki ina son ganin shi na bashi hak'uri sai kice na kamu!!! ce miki akayi na shirya yin soyayya yanzu" " ko kuma kece babbar mara hankali ba yaya kike k'ok'arin hana zuciyar ki a bin da take so, Ayusha ki saurare ni da kyau kin san dai na girmeki a k'alla na baki shekara d'aya me kyau so wajen hankalin ma da bambanci,ke da kanki kin san na fiki sanin me duniya take ciki must especially ma ta b'angaren soyayyah!!" tana gama fad'in haka ta tuntsire da dariya dundu Ayusha ta d'aka mata sannan tace "shegiya yar iska ai dama anan kika fi k'wari ko Romeo and Juliet haka suka ganki suka barki " sosa wurin dundun tayi tace "Allah ya isa daga fad'an gaskiya sai ki dake ni" haka dai sukayi ta shirmen su har next period yayi suka koma lecture hall. A b'an garen Fahad kuwa tun bayan da ya idar da sallan asuba ya kwanta bai farka ba sai 12:pm shima da k'yar ya iya tashi yayi wanka yaje gaida Mum a falo ya sameta tana kallo waje ya samu ya zauna sannan yace "ina kwana Mum, da fatan kina lafiya" tun da ya shigo falon take kallon shi har zuwa lokacin da yake gaisheta bata sauk'e idonta a kan sa ba har ta amsa masa da "lafiya My Son, sai yanzu ka tashi daga baccin Abban ku ya bar sallahu cewa idan kayi ka biya office ka same shi " "ok" shine kad'ai abinda ya fad'a ya mik'e tsaye sannan yace "Mum ni na tafi amma dan Allah kimin addu'a Allah ya had'ani da pretty na bata hak'uri" murmushi tayi tace "dawo ka zauna My Son akwai wata muhimmiyar magana da zamuyi da kai" Waje ya samu ya zauna yana kallon ta sai da ta tabbata yayi paying attention nashi sosai sannan ta ce " yi maka addu'a ya zama wajibi a gareni My Son, amma dan Allah ina so ka nutsu ka kwantar da hankalin ka idan Allah yayi zaka had'u da pretty ka bata hak'uri zaku had'u dan haka ka cire damuwa a ranka ka dawo normal yadda kowa ya sanka daga jiya zuwa yau duk kabi ka susuce ka sukurkuce, ko breakfast bakayi ba ka kama hanya zaka fita kuma na tabbata idan ka fita ma ba abincin zaka nema ba kuma kasan matsalar da kake fama da ita, dan haka bari na d'auko maka d'umanen ka na jiya" shiru yayi yana kallonta dan yasan tunda ta zaunar dashi to sai yaci abincin. Tashi tayi ta shiga kitchen ta d'auko masa abincin ba tayi tsammanin zai ci na kirki ba saboda yanayin damuwar da ke bayyane k'arara a fuskar shi amma ga mamakin ta sai taga ya cinye tas. "Yawwa ko kai fa da kaci abin cin ai zaka fi samun kuzari a jikin ka" "wallahi Mum yarinyar nan A ce a girki Allah yasa pretty ma ta iya girki haka" "Ameen My Son, yanzu dai ka tashi ka tafi wajen Abban naku" " ok Mum sai na dawo" "to a dawo lafiya Allah ya had'a ka da pretty" "Ameen Sweetheart" ya fad'a yana dariya sannan ya fice. Bin shi tayi da ido tana mamakin yadda akayi d'anta ya sukurkuce one time " ya Allah ka bayyana mishi wannan yarinyar idan har alheri ce a rayuwarshi" ta fad'a a fili. Yana fitowa daga gida ya shiga motor Mai gadi ya bud'e masa gate ya kama hanyar office d'in Abba, a zuciyar sa sai sak'a da warwaran hanyar da zai bi yaga pretty yake, "ya zama dole ina barin wajen Abba na shiga Yar-adua neman pretty na" wanna shine kalmar da yake ta maimai tawa har ya isa office d'in. Yana zuwa ya tarad da Abba da wasu bak'i seat ya samu ya zauna sannan ya gai da su a ladabce da fara'arsu suka amsa mishi sannan Abba yace "Fahad har ka iso kenan, to ya ka baro mutanen gidan" "lafiyan su lau Abba" d'aya daga cikin mutanen ne yace "au Alhaji Umar kana nufin Fahad d'an wajen ka ne ya zama haka" Abba yace "k'warai kuwa" "ikon Allah gaskiya girman d'an mutum ba wuya nifa rabona dashi ina jin tun yana secondary, Masha Allah" Abba yace "lalle kun dad'e baku had'u ba, Fahad wannan fa Alhaji Nafi'u ne Abban Su Muneer,wan can kuma baka san shi ba abokin mu ne Alhaji Hussain daga Niger yazo" Fahad ya sunkuyar da kai k'asa "Allah Sarki Abba sannu da zuwa ya Niger d'in da fatan ka barota lafiya, Abba ya gida ya su Muneer shima mun dad'e bamu had'u ba" Alhaji Nafi'u yace "Muneer lafiyan shi lau yana India next month zai kammala masters nashi ya dawo" "Masha Allah" cewar Fahad sannan Alhaji Hussain yace "Niger lafiya lau take, yaushe zaka kawo mana ziyara" murmushi yayi yace "next week zan koma school amma in shaa Allahu ida na dawo next year zan je, domin akwai friends d'ina da nake son kai wa ziyara can" "Masha Allah ai ziyara na da kyau sosai" Abban Muneer yace "kai yanzu a ina kake karatu ka kammala degree d'in ne ko yanzu kake yi" Murmushi Abba yayi yace "ai yaron naka da zafin shi ya taho ya gama Degree &Masters nashi yanzu haka yana PHD a U.K next year in sha Allah zai gama" "wow!!! lalle yaron nawa babba ne wani course yake studying" "International relationship" cewar Abba gaba d'ayansu suka ce "gaskiya abu yayi kyau Allah yayi Albarka" "Ameen" ya amsa musu dashi sannan Abba yace "dama ba komai bane yasa nai k'iranka,illa ina so kaje ka gano min sabon gidan da na siya last week a FATI SHEMA ESTATE ka gano irin gyara-gyaren da ya dace ayi sai ka sanar dani" " ok Abba in shaa Allahu yanzu zan je" "yayi kyau Allah yayi albarka,yauwa ina fatan ka fara shirye-yen komawa school d'in dai ko?" "Ameen Abba na gama komai" "yayi kyau" sallama ya musu ya bar office d'in. Direct FATI SHEMA ESTATE ya wuce bayan ya duba yana yin gidan da komai da za'a buk'ata sannan ya kama hanyar Umar Musa Yar'adua University. ```masu karatu kuci gaba da bibiyar yar Mutan yobe dan ganin me zai faru a gaba da fatan Allura ta tono garma na baku feelings. Na barku lafiya ni ce dai har kullum``` [14:53, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_Wannan Shafin naki ne FEEDO DEEDO YAR-FICIKA My Aminiya A.K.A Mosoyiyar amma fa a daa bcoz yanzu kin zama 'yar AIR (Lols)Allah ya barmu tare, Allah ya nuna mama ranar Aurenku da Ahmadie muje KT mu kwashi shoki_* 51-55 Alhaji ne yayi ta maza ya fara magana kamar haka " dama ba komai ke damuna ba illa...." sai kuma yayi shiru "illa me?, dan Allah ka daure kayi magana mana" "Hmm!!! bawai maganan bane bana so abin da zai je ya dawo nake gudu" "kar ka damu in sha Allahu babu abinda zai faru sai alkhairi, saboda haka feel free and say out your mind " "emm... to dama de tun ranar da na fara kallon ta Allah ya dasa min k'aunar ta a raina, da tunanin ta nake kwana dashi nake nake tashi, duk hanyar da zanbi naga na yak'i zuciya ta nayi amma abin ya gagara dan Allah dan Annabi ki taimaka min na same ta wallahi idan ban mallake ta ba komai zai iya faruwa" yana kai wa nan ya fashe da kuka. Da sauri ta matsa kusa dashi sannan ta rungumo shi jikin ta tana bubbuga bayan shi kamar wani k'aramin yaro sannan tace "ka kwantar da hankalin ka My Love kai kanka kasan bani da wata matsala akan kishiya, fatana shine Allah yasa sauran matan naka su yarda" wani sassanyan ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Alhamdulillah! amincewar ki kawai nake nema Hajjaju sauran nasu mai sauk'i ne" "To amma me yasa kafi buk'atar amincewa ta fiye da na sauran matan?, ina so ka sani dukan mu matan ka ne matsayin mu d'aya ne a wajen ka so suma suna da hak'k'in ka sanar dasu" "haka ne amma kusancin da ke tsakanin ki da ita nake dubawa shi yasa nafi bid'ar taimakon ki" "Hmm!!! kusanci ya wuce Wanda ke tsakani na da Muneerah amma ka rufe ido ka aureta to yanzu me zai sa na tada hankali dan zaka auri wata" "Hajjaju kenan dan Allah ki daina tuna abinda ya faru a baya" "Abban Fahad kenan ai tuna baya ya zama dole, ehm! wai ni wace kake son aura ne haka da kake cewa akwai kusanci tsakani na da ita?" Take yaji wani wawan fad'uwan gaba saboda yasan yanzu game d'in zai fara" "kai fa nake tambaya kamin shiru?" ta sake jefo masa wata tambayar unexpected , dakewa yayi yai ta maza a zuciyar sa ya k'udirta cewa ya zama dole yayi jahadi ya fad'a mata ko ma wace ce !!! sai da ya gama tattaro nutsuwar sa baki d'aya sannan yace "d'iyar ki AYUSHA 'yar Hajia Fateema nake so,kin ga idan nayi haka na raya sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam" ni Rukayyatuwa nace "Sunnah me k'arfi ma kuwa" "Innalillahi wa'inna ilaihi raj'un, Alhaji me kake so ka zama a duniya, yanzu budurwar zuciyar taka har takai ka son d'iyar cikin ka, no wanda kake ta kwana-kwana ashe kasan me ka tab'uka tsabar idon ka ya rufe zuciyar ka ta k'ek'ashe ka kasa tuna matsayin Ayusha a waje na, to idan ka manta bari na tuna maka Ayusha 'ya ce wajen Aminiyata da muka tashi tun muna yara saboda haka idan kai baka d'auke ta a matsayin 'ya ba ni 'ya take a guna kuma kai ma ya zama dole ka yarda da hakan, ko da yake bazan yi mamaki ba tunda ka Auri Muneerah waye baza ka aura ba, ina so kasan wani abu guda nasan tunda ka furta kana sonta ban isa na fidda maka ita daga zuciyarka ba amma ka sani k'arshen zamana da kai yazo, saboda bazan tab'a iya had'a shimfid'ar aure da d'iyar ciki na ba, ina!!! wallahi never,over my dead body" tana gama fad'in haka ta fashe da kuka sannan ta mik'e ta nufi hanyar fita. Tana zuwa bakin k'ofa yayi saurin zuwa ya sha gabanta, zuba gwiwowin sa yayi a k'asa ya dafa k'afafun ta da hannayen sa sannan yace "Hajia dan girman Allah kiyi hak'uri ki fahimce ni, wallahi banyi hakan da niyar CIN AMANA KO CIN ZARAFI a gareki ba illa dan zuciyata ta samu sukuni daga tarkon da ta afka, nima ba yin kaina bane, kin san shi SO ba ruwansa da cancanta, ba ruwansa da dangantaka,please kiyi hak'uri ki taimaka ki cetoni, ki fidda ni cikin halin da nake ciki, wallahi tallahi ba yin kaina bane" sai ya fashe da kuka, bangaje shi tayi tace "dakata malam ni fa ban hanaka auran abinda zuciyar ka ke so ba, idan ka ga dama ba Ayusha ba ka had'ada Hafsat da Maryam ma ka auro ba damuwata bane amma ka sani ni Zainab bazan iya zama da kai a matsayin miji ba, mai budurwar zuciya kawai mtswww...." ta fice ta barshi a d'akin. Tunda ta shiga d'akin take ta faman Safah da Marwa, can ta tuna ashe fa ta manta wayan ta a d'akin shi da sauri ta nufi hanyar d'akin nasa domin tana da buk'atar wayan a kusa da ita, tana shiga d'akin ta tarar dashi kwance shame-shame a k'asa dak'yar yake numfashi, da sauri ta nufi inda yake "na shiga uku Alhaji lafiya!!! , me ya sameka" a dai-dai lokacin ta k'arasa wajen da yake kwance, wani nishi me k'arfi taji ya sake sai numfashin sa ya d'auke d'if!!! wani mahaukacin k'ara ta saki "wayyo Allah jama'a kuzo ku taimakeni Alhaji ya mutu" da gudu mutanen gidan suka hallara, basu tsaya wata -wata sukayi rushing nashi zuwa AUTOPEDIC HOSPITAL dake nan katsina. ```TAKU HAR KULLUM``` *ROOKIEY D BEST* [14:54, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_Wannan Shafin naku ne_!!!* *_AYUSHA ILIASU MUSA (the eloquent writer of 'YAR BOKO very Interested and Educative Novel) & AMEERAH AMNOOR (Saraku for life)na gode sosai da gudunmawar da kuke bani Allah ya bar zumunci (AMEEN) ina k'aunar ku har cikin raina irin SOSAI d'innan��_* 55-60 Suna zuwa asibiti aka shiga dashi emergency room, likitoci biyu ne a kanshi, take nan suka shiga bashi taimakon gaggawa. Hajia Zee da sauran kishiyoyin ta na zaune a reception sun shiga cikin matsanan cin tashin hakali, kallo d'aya zaka musu su baka tausayi most especially ita da tafi kowa sanin mene ne musabbabin abin, tambayar ta suke me ya sameshi amma ta kasa basu amsar komai saboda tasan zafin kishin Muneerah yanzu sai ta fara musu hauka a asibiti shiyasa suna tambayar ma tace "yanzu bata wannan muke ba, fatan mu dai Allah ya bashi lafiya sai muyi maganar daga baya". *_BAYAN HOUR D'AYA_* Dr' Sa'ad ne ya fito biye dashi wata nurse ce hannun ta d'auke da file, yana k'arasowa suka nufi wajen shi at once suka jefo mishi tambaya "Likita ya jikin nashi, ya farfad'o ne?" "Ku biyo ni office mayi magana can" Suna shiga suka samu waje suka zauna, rubutu yayi a hospital card nashi sannan yace dasu "Hajiya ku kwantar da hankalinku in shaa Allahu zai samu lafiya, dama yana da Asthma ne?" "Eh! Doctor yana dashi " "ok, Allah ya basa lafiya, asthma d'insa ce ta tace due to wani abu na b'acin rai da ya sameshi and bai samu yasha magani ba har k'arfin numfashins sa ya d'auke so hakan yayi leading to doguwar suma, yanzu haka Dr. Ahmad na gudanar da wasu bincike a kansa in shaa Allahu zai farfad'o any moment from now, so ga wannan kuje pharmacy ku siyo da sauri magani ne da allurai, dan yana farkawa za'a mishi alluran " Da sauri Anty ta k'arba tace mun gode Doctor, sannan suka fice daga office d'in zuwa siyan magani, tana zuwa pharmacy aka duba bubu ko d'aya daga cikin so da sauri ta k'ira driver a waya yazo ya sameta su shiga gari ne, ko minti uku batayi da k'iranshi ba ya zo suka tafi.Sun je a k'allah chemist uku basu samu ba sai a na hud'un suka samu complete. Ko 30 minutes basuyi da fita ba alhaji ya farfad'o a dai-dai lokacin Hajia Muneerah da Hajia Rahma sun shigo, "Hajia dan Allah dan Annabi ki barni na aureta, wallahi nayi alk'awarin yin adalci a tsakanin ku" kalmar da ta fara fitowa daga bakin shi kenan. "Tabd'i jam!!! wallahi sai dai ka mutu baka aureta ba, wato dama ciwon SO ne ya kwantar da kai anan duk muka bi muka tada hankalin mu to wallahi baka isa ba" "haba Muneera me yasa sam baki da tausayi ne, ki dubi halin da bawan Allan nan yake ciki amma kizo ki titsiye shi da masifa da wanne zai ji da ciwon da ke jikin shi ko da masifar ki" "Ai dama ke ba hankali ne dake ba Rahma!!! ko da yake kin ci amanata kin aure min miji ai baza ki damu ba dan yace zai k'ara aure" " dakata!!! malam kar ki nemi ki wuce gona da iri dan na auri mijin ki sai me, ke d'in ba mijin wata kika aure ba, idan abin kunyar ne ma ai daga gindin ku ya fara fitowa mtsww!!!" Suna cikin hayaniyar Anty Zee ta shigo d'akin idonta bai sauk'a a ko ina ba sai kan Allahi da yake ta fitar da wani irin numfashi yana kakarin amai, da sauri ta bankad'e su ta nufi wajen shi tana "innalillahi wa'inna ilaihi raj'un!!!"a dai-dai lokacin ya fara amai, wani ihu Anty Zee ta saki "wayyo Allah na shiga uku!!! shi kenan kun k'arasa shi aman jini fa ya keyi" wani mugun tsaki Muneerah ta saki sannan tace "idan k'arasawan ne ma sai dai in ke zaki k'arashi tun da kin k'i amince mishi ya aure wacca yake so, wallahi ki sani duk abinda ya samu mujina to kiyi kuka da kanki" tana gama fad'in haka ta fita ta nufi office d'in Doctor Sa'ad da gudu. Abin bai bawa Anty Zee mamaki ba saboda ta dad'e da fahimtar cewa Muneerah, jaka ce bata hankali, a kan kishi babu abinda bazata iya yi ba.Ita ko Rahma nufowa tayi wurin Anty Zee ta taimaka mata suka d'aga Alhaji dan har ya gangaro daga kan gadon. Doctor Sa'ad ne zaune a office Muneerah ta shigo da gudu Doc!! Doc!! please we need your help Alhaji zai mutu kazo da sauri ka taimake shi kar ya mutu" kawai sai ta fashe da kuka "Sorry Madam,you don't need to cry addu'ar ki yafi buk'ata by now , so muje in ganshi" Suna shiga suka tarar Doctor Ahmad yazo joining nashi Sa'ad yayi suka bashi duk wata kulawa da ya dace, alluran da aka siyo Sa'ad ya mishi sannan ya umarce su da su biyo su office d'in doctor Ahmad. Suna shiga suka basu wajen zama, bayan sun zauna Doctor Ahmad ya fara magana kamar haka "da farko ina so na sanar daku cutar da ke damun mijin ku tare da hanyoyin da za'a bi a shawo kan matsalan, idan har kuna son lafiyar mijin ku ya inganta to sai kun taimaka masa, kun k'arfafa masa gwiwa wajen ganin ya samu abin da yake so, mijin ku ya kamu da Heart Attack wanda akafi sani da ciwon zuciya sakamakon mummunan b'acin rai da ya shiga game da wani abu wanda mu nan bamu sani ba sai ku matansa, rashin wannan abin na iya zama barazana ga rayuwarsa" Doctor Sa'ad kuma ne yace "kamar yadda d'an uwana ya muku bayani zan d'aura nawa akai, mutanen da suke d'auke da irin wannan cutar suna buk'atar kulawa ta musamman, lallab'asu ake kamar k'ananan yara, a guji duk wani abinda zai b'ata musu rai saboda lafiyan su idan ba haka ba komai zai iya faruwa Allah ma ya rufa asiri" gaba d'ayansu suka amsa da "Ameen" Doctor Ahmad yace "kuma dan Allah kar a taru a wajen shi dayawa idan da hali ma mutum d'aya ya zauna a wajen shi" "shi kenan Doctor in shaa Allahu zamu kiyaye duk abinda kuka ce bi'izinillahi rabbi zai samu abinda ya keso" Tun da ta fara maganar Muneerah ta zuba mata eyes jira take takai aya ita kuma ta d'aura daga inda ta tsaya, Anty Zee na rufe baki tace "Ai nasan ke abin bazai tab'a damunki ba, so dole kice zai samu abinda yake so tunda ba ke za'ayi wa kishiyar ba" "to ke da kike tada jijiyoyin wuyan ke za'a yiwa kishiyar?" cewar Rahma kenan. Doctor Sa'ad yace "dan Allah Hajiya kuyi hak'uri ya isa haka, yanzu da lafiyar shi zaku ji ko da batun kishiya" ya nuna Muneerah yace "ke d'in ba yanzu kika zo waje na kina kuka in taimaka miki baki son Alhaji ya mutu ba?, amma gashi kece me tada zaune tsaye, abinda nake so ki sani shine kiyaye lafiyar shi a hunnun ku take sai ki zab'a ko, ki barshi ya samu abinda yake so ko kuma rayuwar shi ta k'are a haka, dan naga alama ke ce me matsalan" yana gama fad'ar haka yayi ficewar sa suma fitowar sukayi daga office d'in suka nufi wajen Alhaji, bacci yake sosai amma kana ganin shi kasan yana fama da jiki. Misalin k'arfe biyar da rabi ya farka, Anty Zee da Rahma ne suka taimaka masa ya zauna, "sannu Alhaji, ya jikin da fatan ka fara jin k'arfin jikin ka" atare suka fad'i hakan, shiru yayi yana kallon su d'aya bayan d'aya "ina Muneerah take" ya fad'a a hankali bud'e k'ofar d'akin da akayi ne yasa su yin shiru basu bashi amsa ba. Da sauri ta k'araso wajen shi tana fad'in "ka kwantar da hankalin ka mijina in shaa Allahu zaka samu abinda kake so dukanmu mun amince ka k auri wacca kake so, ko ba haka ba Anty" da k'yar Anty Zee ta iya d'aga kai ta amsa mata alamar eh!!! haka dai sukayi ta kwantar masa da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya a haka dare tayi suka tattara suka koma gida suka barshi da Anty Zee. Washe gari y'an dubiya sukayi ta zuwa dubashi cikin su harda Mummyn Ayusha da Dad, satin su d'aya a asibiti aka sallame su suka koma gida, kulawa sosai yake samu wajen matan sa a haka har ya wartsake ya dawo normal kamar bashi ne yayi jinya ba. *_BAYAN SATI BIYU_* *_5: 00pm_* Alhaji Umar na zaune a d'aki yana sana'ar tasa wato tunani, Hajia Zee ta shigo d'auke da tea flask da fara'ar ta ta k'araso gurin shi ta ajiye flask d'in a kan center table,mug ta d'auko ta tsiyaya mishi sannan tace "Alhaji ga ruwan zafin nan ka sha" shiru taji yayi bai amsa ba, ajiye mug d'in tayi a gefe ta d'aura hannu ta a saman nashi tace "haba Abban Fahad, dan Allah yaushe zaka daina tunanin nan haka tunda muka dawo daga asibiti nace zan je na sanar da iyayen Ayusha abinda ake ciki ka hana, kuma kai banga kayi yink'urin yin wani abu a kai ba gaskiya ni kam bazan iya jurar ganin ka a irin wannan halin ba saboda haka in shaa Allahu gobe zanje gidansu na sanar da iyayenta halin da ake ciki" "Kina da tabbacin cewa yarinyar da iyayenta zasu yarda? " shine tambayar da ya jefo mata "kwarai kuwa tun da na amince in shaa Allahu suma baza su k'i amincewa ba dama abinda zai hanasu amincewa saboda ni ne" "to naji, idan iyayen ta sun amince yarinyar kuma fa?" "kar ka tada hankalin ka akan wannan Ayusha kamilar yarinya ce, mai tarbiyya da bin umarnin iyaye matuk'ar iyayenta suka yarda da kai to itama zata yarda domin a duniya bata tab'a bijirewa umarnin su, idan kana tunanin cewa ko tana da wani saurayi ne a'a mahaifiyar ta ta shaida min har yanzu bata fara soyayyah ba" "Madallah da matar k'warai irinki, Hajiya Zainab Allah ya saka miki da alkhairi yasa ki gama da duniya lafiya, da ace duka mata zasuyi koyi da irin kyawawan halinki da mata dayawa baza su shiga wuta ba" ```Masu karatu ku jimin Alhaji da sweet mouth... Lols Sai mun had'u a next page dan gani badak'alar da za'a kwasa Bissalam Nice har kullum``` *ROOKIEY D BEST* [14:54, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* 61-65 Haka dai Alhaji yayi ta kalallame Anty Zee da sweet mouth, ranar through out wuni yayi yana farin ciki hatta 'yan office nasu sun fahimci hakan, ko ina sai side talks ake domin rabonsu da suga farin ciki a fuskar sa tun lokacin da ya fara afkawa kogin so, kai hatta matan sa da 'yayan sa sai da abin ya dinga basu mamaki domin sun dad'e basu ga yana sakar musu fuska haka ba yau har zama yayi a falo akayi hira dashi kamar da. Masu karatu kuji Alhaji da zak'ewa sai kace wanda aka ce mishi Ayusha da iyayen ta sun amince (Lols) . Washe gari ya kama Sunday tun safe Anty Zee ta fara shirin tafiya misalin 10: 30am ta gama komai nata d'akin Alhaji ta nufa domin yi masa sallama, tana shiga ta tarar shima ya shirya tsaf cikin wani cuffee brown shaddar shi me d'aukan ido. "Hajiya Hajjaju gidan sammako, wato fa ke da gaske kike sai kin nemowa angon naki mata , to masha Allahu haka ake so ke dai kici gaba da bada himma ladan ki na wajen Ubangiji" Murmushi tayi sannan tace "Yaa Alhaj, sarkin dad'in baki, ni dai kabar fasa min kai na da yawa, irin wannan kwalliya haka sai kace me zuwa zance" shima murmushin yayi sannan yace "kai Hajjaju ta inda kika b'ullo kuma! to ni wajen d'aurin auren wani abokina ma zani, sai ma muje na sauk'eki tunda naji kince motar ki na gareji ko?" "eh wallahi tun jiya Bala Driver ya kai ta yanzu na k'irashi a waya yace ba'a gama gyaran ba so muje ka ajiye ni kawai sai yazo ya d'aukeni" " ok haka za'ayi Uwargida sarautar mata" "Hmmm... kaji dashi dai" Murmushi yayi yace "Hajiya Zainab ikon Allah muje kar na makara sha d'aya da rabi ne d'aurin auren" fita sukayi daga d'akin suna fara'a, key d'in motar ya bata sannan yace "je ki jirani a mota bari nayi sallama dasu Muneerah" "ok" shine abinda tace ta karb'i key d'in ta wuce. Bayan yayi sallama da sauran matan ya dawo mota suka fice daga gidan, hira suke sosai cikin ni shad'i kamar wasu saurayi da budurwa, suna cikin tafiya wayarsa tayi ringing, yace da Anty Zee "Hajjaju angon ne ma yake k'ira sa min wayar a hands free, muji dame yazo" "to" Tana sawa Alhaji yace "Ango kasha k'amshi! ka jini shiru ban iso ba ko wallahi uwargida ce ta rik'e ni amma yanzun nan zan k'ara so" "aboki dama ka zauna a inda kake dan an ma fasa d'aura auren" "what!!!why!!! ya akayi haka ta faru " "kai dai ka bari kawai yanzu haka ma bana gari idan na dawo zamu tattauna batun" "to shikenan Allah ya dawo da kai lafiya yasa hakan shine mafi alkhairi" "Ameen" Bayan ya gama wayan ya kalli Anty Zee yace "uwargida kin ji abin bak'in cikin da ya faru da abokina ko" "wallahi kuwa, Allah ya rufa asiri" "Ameen" haka dai suka ci gaba da hirar su har suka isa k'ofar gidan. "To Hajjaju Allah ya bada sa'an abinda aka zo nema ina nan ina jiran feedback Hajiya ta" "Alhaji akwai wani hanzari ba gudu ba, me zai hana mu shiga tare, ina ganin abin zai fi zuwa mana da sauk'i" "yanzu ke a ganin ki hakan yayi" sosai ma, bari na shiga na sanar dasu zuwan ka " "your wish is my command ranki shidad'e" murmushi tayi ta sauk'a daga motar ta shiga gidan. Da sallama ta shiga gidan a falon k'asa tayi kicib'is da Mum & Dad na breakfast a falo, da sauri Mum ta nufo ta tana fad'in "lalle yau munyi babbar bak'uwa gaskiya k'awata kin shammace ni yanzu nan fa nake cewa Abban Ayusha ya kamata anjima naje na dubo ku tunda aka sallame ku sau d'aya naje, ya me jikin to, ga waje ki zauna" "jiki Alhamdulillah, yanzu haka ma tare muke dashi yana waje" "Haba Abuwa ya zaki baro min aboki a waje sai kace wani bak'o, bari naje na taho dashi" cewar Daddy kenan, yana gama fad'an haka yayi waje. Murmushi Anty Zee tayi tace wato mijin ki bazai daina cemin Abuwa ba ko? ko da yake nasan maganin sa" Mum tace "kun fi kusa me shiga zancen ku shi zai ji kunya" Dad ne suka shuga tare da Alhaji Umar, zama sukayi a kan kujera bayan nan gaisuwa ya biyo baya, bayan an gama gaisawa Mummy ta kawo musu kayan motsa baki, sun kai 30 minutes suna hirar duniya domin sun dad'e basu had'u dukansu a waje d'aya ba. Daga bisani Anty Zee tace "wai ni ina d'iyata ne tunda nazo fa ban ganta ba, kuma ko motsin ta banji ba" "laa Ayusha ai baza ki ganta yanzu tana can tana sana'ar baccin nata da yake jiya munyi dogon hira sosai Aneeserh ce ma ta iya fitowa ta had'a mana breakfast " cewar Mummy kenan. "Yauwa ni kam ina so naga Aneeserh nan da nake ta jin labarin ta rannan da nace Daughter tazo min weekends ma cewa tayi inyi hak'uri sai Aneeserh ta tafi" Daddy yace "ai Aneeserh yarinyar kirki ce sosai" "Allah sarki, yauwa tun d'azu mun tsaya surutu bamu samu mun tattauna abinda ya kawo mu ba" inji Anty Zee, Mummy tace "ai ni nasan ruwa baya tsamin banza yaushe rabon da kuzo gidannan tare to Allah yasa dai lafiya" "Anty Zee ce tace "lafiya lau sai alkhairi, wata muhimmiyar magana ce ta kawo mu, amma bamu san yadda zaku d'auki maganar ba" Sannan taci gaba da cewa "Munzo neman wata alfarma ne a gurin ku da fatan baza ku kasa yi mana wannan alfarman ba" "wallahi k'awata kin bani kunya, ke kanki kin sani tun muna yara d'ayan mu baya tab'a neman abu wajen d'an uwansa ya rasa to me yasa yanzu zakiyi kokwanto wajen tambayata abu har ma kike k'iranshi da alfarma" "ba haka bane k'awata wannan karon abin yasha ban-ban, ni dai fatana ku amince da buk'atar mu" "Kar ku ji komai Abuwa, tun kafin ki fad'i buk'atarki an amsa miki" inji Daddy, shi dai gogan namu shiru yayi yana kallon ikon Allah zuciyan sa sai dukan tara-tara yake da ya tuno kalaman uwargidan sa na jiya da daddare inda take cewa "ka kwantar da hankalin ka My Lurv nace maka muddin na gabatar musu da buk'ata ta zasu amince" take sai yaji relief domin yaga alamun nasara a tattare dasu. Baiyi aune ba yaji tace "wato abin da yake tafe damu shine... " sai ta tsinci kanta da jin nauyin maganar, hankalin Alhaji yayi k'ololuwar tashi take ya fara auro irin halin da zai shiga idan ya rasa Ayusha. "Ci gaba da magana mana Abuwa, lokaci na tafiya fa azahar ma ta gabato" cewar Daddy, Mummy tace "k'yale yar rainin hakali idan taga dama kar ta fad'a d'in" "kwantar da hankalin ki k'awata me kika ci na baka na zuba, yanzun nan zakiji komai , dama akan Ayusha ne tun ranar da Alhaji ya d'aura idonsa a kanta yaji duk duniya babu wanda yake so ya aura sama da ita, nasan zakuyi tunanin abubuwa da dama a kai na, to ni na yarda na amince da hakan shiyasa ma nayi masa jagora zuwa gareku!!!? Dakata Zainabu, kina nufin d'an wajen ki Fahad ne yaga Ayusha ko kuma wa? " tambayar da Daddy ya jefo mata kenan, k'arfin hali tayi tace "ba Fahad nake nufi ba Alhaji Umar baban Fahad ne yaga Ayusha yake so" "wallahi tallahi k'awata kinyi asarar rayuwar ki, sai kace kin rako mata duniya yanzu ke tsabar dak'ik'anci ki rasa wa zaki zo nemawa aure sai mijin ki, auren ma na Ayusha ina hankalin ki da tunanin ki suka je, to idan ma mafarki kike to kiyi saurin farkawa dan wallahi tallahi bazan tab'a amincewa da wannan iskancin ba Mtwww!!! kai ma na dawo gareka babban munafiki wato buduwar zuciyar taka bata tashi sauk'a a kan kowa ba sai a kan d'iyata!!! to ka sani ko zaka mutu baza ka tab'a samun ta ba dan haka ka tashi ka tattare 'yanmatan k'afafun ka bar gidan nan tun kafin nayi maka rashin mutunci, tsohon najadu kawai" duk wannan bala'in Mummy ce keyi..... Ajiyar zuciya me k'arfi Anty Zee tayi sannan tace "dan Allah dan Annabi k'awata ki kwantar da hankalin ki, ki saurari abinda zan fad'a miki" "baki da sauran kalaman da zan saurara daga gareki, kunya dai kin riga kin bani dan haka ki tashi ki bishi kuje wani wajen neman matar ba nan ba tunda de ke kare ya riga da ya lashe zuciyar ki" Ba suyi aune ba sai ganin Alhaji Umar sukayi ya zube a k'asa yana fad'in "dan Allah dan Annabi ku taimaka ku ceto rayuwata daga halin da take ciki wallahi tallahi bazan tab'a iya rayuwa ba tare da Ayusha ba rasa Ayusha dai-dai yake da rasa rayuwata!!!" sai kawai ya fashe da kuka. Mummy tsabar tak'aici ma kasa magana tayi, Allah sarki Daddy da yake shi namiji ne yasan ba k'aramin abu bane zai iya sa gawurtaccen namiji kaman wannan kuka, yace "tashi ka zauna Alhaji muyi magana" A dai-dai lokacin suka jiyo ihun Aneeserh na fad'in "wayyo Allah na shiga uku Mummy kuzo ku taimakeni Ayusha ta.....!!!" ```Masu karatu kuyi manage da wannan sai mun had'u a next page dan ganin me ya samu Ayusha. Bissalam nice dai har kullum``` *ROOKIEY D BEST* [14:55, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* 66-70 Da gudu suka hau sama dan ganin halin da Ayusha take ciki, sun sameta a kwance shame-shame kamar gawa a take hankalin su yayi mugun tashi Dad yace "Aneeserh me ya same ta?" cikin kuka tace "wallahi nima ban sani ba dan muna zaune da ita tace bari taje ta gaishe ku, bayan ta fita ta dawo cikin wani yanayin da ban tab'a ganin ta ba fuskar ta d'auke da hawaye sannan ta rik'e kanta da hannun ta da sauri na nufi inda take sai gani nayi ta fad'i k'asa tana nishi numfashin ta na fita sama-sama lokaci d'aya ya d'auke" sai ta k'ara fashewa da kuka. Dad yace "Tabbas taji maganar da muke tattaunawa da alama suma tayi" kafin ya rufe bakin shi Aunty Zee tayi saurin shiga toilet ta d'ebo ruwa ta watsa mata,Mommy na rik'e da ita sai tofa mata addu'a take, d'ago idon ta tayi sukayi four eyes da Alhaji dogon tsaki taja sannan ta nunashi da yatsa tace "wallahi idan na rasa 'yata kotu ce kad'ai zata rabani da kai" Shi bai ma san tanayi ba balle yaji zafin maganganun ta, tunda ya shigo yaga Ayusha a wannan yanayin hankalin sa ya tashi zuciyar sa ta fara murd'a tana zugi da rad'ad'i. Dogon ajiyar zuciya Ayusha ta saki wanda yayi dragging attention nasu cewa ta farfad'o "Alhamdulillah" shine kamar da ya fito daga bakin Dad, Mummy ta rugunmota jikin ta tana fad'in "sannu Auta, ina ne ke miki ciwo fad'amin kin ji d'iyata" shiru tayi tana binsu da kallon one by one tana k'ok'arin tuno wani abu da ya faru tana kai idon ta kan fuskar Alhaji ta fashe da kuka tana fad'in "me ya kawo ka d'akina ka fita ka bani guri natsane ka na tsani me k'aunar ka, wallahi ko maza sun k'are a duniya bazan tab'a auren ka ba i hate you!!! " Aunty Zee ce tayi saurin matsowa kusa da ita ta, ta kamo hannun ta, zatayi magana kenan.. Ayusha tayi saurin dakatar da ita ta fincike hannun ta a jikin ta, Malama karki kuskura ki k'ara attempting tab'a ni domin a yanzu nafi tsanar ki fiye da kowa, na d'auke ki a matsayin uwa ashe ke ba haka kika d'auke ni ba Allah ya isa tsakani na da ke muguwa azzal... " bata k'arasa maganar ba Dad ya d'auke ta da wawan mari "Ayusha dama baki mutunci ban sani ba? tarbiyyar da muka baki kenan, to ki sani na yanke hukunci ko zaki mutu sai kin aure shi" Rik'e k'uncin ta tayi tana kallon Dad tun da take a rayuwa bai tab'a sa hannu ya duke ta ba sai a dalilin Alhaji Umar a zuciyar ta tayi alk'awari to ko sama da k'asa zata had'e baza ta tab'a yarda ta aure shi ba, wani irin kuka ne ya yunk'uro ta tace "Dad yau nice ka mara saboda wannan mutumin" ta nuna Alhaji, sai kawai ta mik'e tsaye take jiri ya d'ebe ta ta fad'i ak'asa . Mum da Aneeserh sukayi saurin d'agota suka d'aura ta kan gado, a take jikin ta ya d'au zafi ta fara karkarwa tace "Mum kaina zai fashe ciwo yake min d'auko bargo ki rufeni sanyi nake ji" da sauri Aneeserh ta jawo bargo ta rufe ta. Anty Zee tace "na shiga uku na lalace ya zanyi da raina ni Abu Alhaji dan Allah kayi hak'uri ka janye maganar auren nan kaga halin da yarinyar nan ta shiga sanadiyyar mu idan wani abin ya sameta ma Allah bazai barmu haka ba" Kasa magana Alhaji yayi saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga babu abinda idanun sa keyi sai zubda k'walla lura da halin da yake ciki yasa Dad ya rik'o hannun shi yace "kwantar da hankalin ka aboki na muje masallaci an k'ira sallah" ya kama shi suka fita waje. Suna fita Aunty Zee ta k'araso gaban Mum ta zube "dan Allah dan annabi k'awata kiyi hak'uri da abin da ya faru, kar wannan abin ya zamo silar rushewar zumuncin mu ki sani bani da niyar cutar da Ayusha nayi haka ne dan na ceto Alhaji daga halin da ya ke ciki amma ki min afuwa daga yanzu komai zai dawo normal in shaa Allah" wani mugun kallo Mum ta watsa mata sannan tace "baki da abinda zaki ce min, tunda bakiyi la'akari da halin da yarinyar zata shiga ba saboda son zuciya ke dai burin ki kawai ki farantawa mijin ki rai ki b'ata na wasu" Wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga idanunta tace "OMG!!! dan Allah K'awata ki fahimce ni, wallahi ban yi haka dan son zuciya ba illah dan ceton rai!" "Ceton rai kuma!!!? nifa ban gane ina kika dosa ba" cikin kuka Aunty Zee tace "ranar da Alhaji ya tunkare ni da batun Ayusha babu irin haukan da ban mishi ba,ji nayi a duniya ban tab'a tsanar wani d'an adam irishi ba, nayi dana sanin kasancewa tare dashi amma daga baya na tausaya mishi sakamakon halin da ya shiga dalilin k'in amince masa..." nan dai ta kwashe labarin abinda ya faru ta basu da irin shawarwarin da likita ya basu sannan ta k'ara da cewa "yanzu haka Allah ne kad'ai yasan halinda Alhaji yake cikin kamar yadda yace rasa Ayusha dai-dai yake da rasa ransa haka abin yake, dan Allah dan Annabi kin ga laifi na dan nayi k'okarin ceto shi" Duk wannan labarin da Aunty Zee ke bayarwa a kunnen Ayusha da Aneeserh, Aneeserh ta tausaya mishi sosai, ita ko Ayusha ji tayi ta k'ara tsanar shi sannan ta k'ara k'udirta wa bazata tab'a yarda ta aure shi ba, Mummy ma tayi matuk'ar tausaya mishi sannan ta k'udiri niyar cewa in shaa Allahu zata shawo kan Ayusha ta amince ta aure shi domin yana buk'atar taimako, tana ganin abin ma zai zo mata da sauk'i tunda Ayusha bata da saurayi kuma tasan yanzu ma b'acin rai ne ya sata yin hauka dan bata tab'a bijirewa umarnin su. Dafa kafad'ar Aunty Zee Mum tayi tace "ki kwantar da hankalinki k'awata yanzu na fahimce ki kuma na miki alk'awarin in shaa Allahu komai zai dai-daita" a dai-dai lokacin Dad ya shigo a gigice yace "Hajia mik'on makullin mota ta mu tafi asibiti yanzun nan mun fito daga masallaci Alhaji umaru ya fad'i yana ta aman jini" "Innalillahi wa'inna ilaihi raj'un, shike nan Alhaji ya mutu kawai!!! ,dama Doctor yace idan muka bari irin haka ta kuma faruwa zamu iya rasa shi" Dad yace "ki kwantar da hankalin ki Zainabu, bai mutu ba da ranshi addu'ar mu yafi buk'ata yanzu ku zo mu tafi asibitin" Gaba d'ayansu suka fice daga d'akin Ayusha da kawai suka bari ko motsawa tak'i yi daga kan gadon. *_kuci gaba da bibiya ta har yanzu da sauran rina a kaba, domin yanzu labarin ya fara.... mu had'u a shafi na gaba dan ganin ya zata kasance tsakanin Alhaji da Ayusha sannan wani hali Fahad yake ciki. TAKU HAR KULLUM dai_* *_RØØKÏÊY D BEST_* [14:55, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* 71-75 Suna fita waje suka tarar da Mallam Ayuba mai gadi a tsaye a kanshi, kin kimarshi sukayi da Dad suka sashi a motor Aunty Zee a gefen shi Mum a gaba Dad na driving, Mum ta kalli Aneeserh tace "ki koma ki kula da k'awarki sai mun dawo" "to Mummy a dawo lafiya" "Allah yasa" Dad ne ya kalli Aunty Zee yace "Zainabu wani asibiti zamu je!? " cikin muryar kuka tace "Autopedic, a can file d'insa yake" "ok" Aneeserh na shiga ciki ta tarar Ayusha ta fito daga toilet da alama alwala tayi, kallon ta tayi taga gaba d'aya one time ta canza ta birkice ta susuce take taji tausayin ta ya k'ara kamata tace "k'awata alwala kikayi ne, wallahi baki ga halinda bawan Allah nan yake da kin tausaya mishi sai kin ganshi very unconscious wallahi" Tsaki Ayusha taja tace "to ina ruwana da unconsciousness nashi idan ya gadama ya mutu ma ba damuwata bane,nima ku barni naji da abinda ke damuna!!" tana gama fad'in haka ta wuce ta d'auko sallaya ta shimfid'a ta zira hijab ta fara sallah. Girgiza kai Aneeserh tayi tace "Allah ta kyauta" ta wuce ta d'oro alwala ta gabatar da nata sallan, bayan ta idar tace da Ayusha "k'awata na tabbata da kin ganshi sai kin tausaya mishi" "dakata!!! nifa bana so kina min maganan tsohon najadun nan, me yasa ni baza ku tausaya min ba sai shi, wallahi tallahi na tsane shi duniya wa lahira shine mutum na farko da yake k'ok'arin ruguza farin ciki na, tun da na taso a rayuwa ta Dad bai tab'a d'aura hannun shi a jikina da sunan duka ba amma a sanadiyar shi har mari na yayi,ina da wanda nake so a zuciyata amma zuwan mutumin ciki rayuwa ta na shirin rabani da abin k'auna ta abin alfahari na wanda nake fatan kasancewa dashi har abada" sai ta fashe da kuka "mai yasa bazan tsaneshi ba, saboda shi Mummy &Dad suka tafi suka barni ba tare da sun yi la'akari da abinda zai biyo baya ba" Kuka ne yaci k'arfin ta tayi shiru, Aneeserh ta matso kusa da ita tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata na fahimce ki sosai, amma yaushe kika fara soyayya bamu sani ba, sannan wane ne shi saurayin naki a ina yake?" "Na fara soyayya ba tare da ni kaina na san hakan ba sai yanzu, ban san sunan wanda nake so ba, kuma san komai game dashi ba all what i know about him is Love!!! in fact bai ma san inayi ba amma ni dai ina son shi, k'awata ki taimaka ki nemo min shi wallahi i can't live without him" "Innalillahi wa'inna ilaihi raj'un!!! wannan wani soyayya ne k'awata, ta inna zamu fara nemanshi tunda bamu da details akan shi!" "ni dai kawai ki nemo min shi idan kina so nayi alfahari dake a matsayin jajirtacciyar k'awa" "to shike nan, Allah ya shige mana gaba" "Ameen" Haka dai suka zauna sukayi ta tattauna batun ko zasu samu solution amma shiru, daga baya Aneeserh ta tashi ta shiga kitchen ta girka musu abinci ta zuba wanda za'a kai asibiti. *_AUTOPEDIC HOSPITAL KATSINA_* Suna shiga nurses suka zo da wheelchair suka d'auke shi sai emergency room, sun ci sa'a Doctor Sa'ad ne on duty so bai sha wani wahalan binciken me ke damun shi ba, treating nashi yayi based on physical observation. Bayan an shiga dashi ciki Anty Zee ta k'ira sauran matan a waya ta sanar dasu halin da suke ciki, Mummy & Dad ne suke controlling nata domin gaba d'aya tayi loosing hope a kan Alhaji sai faman sumbatu take kamar zararriya. *_30 MINUTES LETTER_* Doctor Sa'ad ne ya fito rai a b'ace daga emergency, wata nurse na biye dashi da files a hannun ta ko k'ala bai ce musu ba ya wuce office Nurse ta kallesu tace "kune patient relatives da aka kai Emergency yanzu ko" "Eh mune" cewar Dad "Ok!!!Doctor na son ganin ku a office" da sauri suka nufi office d'in doctor Sa'ad, suna shiga suka samu seat suka zazzauna. Doctor Sa'ad ya kalle su da kyau yace "Alhaji me yasa kuka bari ya shiga cikin matsananciyar damuwa haka, wallahi badan kunyi gaggawar kawo shi asibiti ba da sai ta Allah kawai yanzu haka mun samu munyi resolving case d'in amma sai mun kai shi ICU (Intensive Care Unit) domin tabbatar da k'wak'awaran bincike a zuciyar sa and also ina shawartar ku da ku nemo masa abinda yake so wanda rashin sa yayi coursing ciwon, domin ganin abin a kusa dashi na iya taimakawa wajen samun lafiyar shi" Dad yace "ba komai in shaa Allahu za'a nemo masa abin, yanzu ya jikin nasa" "jiki Alhamdulillah, yanzu haka mun masa allura da zata taimaka wajen dai-dai ta bugun zuciyar sa, so zai iya kai wa kamar kwana uku bai farka ba, amma in shaa Allahu da zaran ya farka za'a ga changes and idan so samu ne yana farkawa yaga wannan abin a kusa dashi" " ba komai Doctor in shaa Allahu za'ayi yadda kace" *_5: 30pm_* Aneeserh ta kammala komai tace wa Ayusha ta tashi ta shirya su tafi asibiti wajen su mu, tsaki taja tace "kin ga Malama ni fa karki takurawa rayuwa ta, tun d'azu kike damuna da abinda bai shafeni ba, dole ne sai munje tare ki tafi ke kad'ai mana ai ke ba bak'uwar garin bace" Murmushi Aneeserh tayi tace "Allah ya huci zuciyar ki Mr's Unknown, kinga tafiya na barki lafiya" "Allah raka taki gona ba Mr's unknown ba komai ma ki k'irani" A dai-dai ta sahu Aneeserh ta shiga ya kai ta asibitin, bata wani sha wahalan neman su ba bcoz a reception ta hango Dad a zaune, bayan sun gaisa yayyi allocating nata zuwa inda su Mum suke, bayan sallan Magrib suka tattara suka dawo gida. Tun da Aneeserh ta tafi Ayusha take kuka sai da aka k'ira sallan magrib ta hak'ura ta tashi tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta d'auko Al-Qur'ani me girma ta fara karantawa ko zata samu waraka cikin zuciyar ta, tana cikin karatun taji shigowar su amma ta manna musu ta ci gaba abinta. Sun iso gida ana sallan isha so Dad na parking mota ya wuce masallaci, Mum da Aneeserh suka shige ciki, ganin tana karatu yasa Mum bata kulata ba ta wuce nata d'akin dan tayi nata sallan haka abin yake a wajen Aneeserh ma ban d'aki ta shiga ya d'oro alwala. Bayan ta idar da karatun ta tashi ta gabatar da sallan, tana cikin sallah Mum ta shigo tace da Aneeserh "idan Auta ta idar kuzo ku same mu a falo Abban ku na son ganinku!!!" bayan ta idar tayi addu'o inta sannan suka d'unguma zuwa falo, waje suka samu suka zana a k'asa yau ba hawa cinya domin sunyi fad'a da Dad......kallon ta yayi sosai shi kanshi ta bashi tausayi lokaci d'aya ta sauya kamar ba ita ba, yace "Auta ya jikin naki, da fatan kin ji garau yanzu" "Jiki Alhamdulillah" "Masha Allah haka ake so, dama ba komai bane yasa na k'iraki illah.... " *_A dai-dai lokacin alk'alamina ya fad'i k'k'asa!!! Afuwan masu karatu manage with this little page, kuci gaba da bibiyata in shaa Allahu zakzaku gane inda labarin ya dosa.._* *RØØKÏÊY KÆXS* [14:55, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* 76-80 "Dama ba komai bane yasa na k'ira ki illah ina so mu tattauna wata muhimmiyar magana dake, sannan in rok'i wata alfarma a gareki" shiru tayi tana kallon Dad a zuciyar ta kuwa cewa take "kowace irin alfarma kake buk'ata zan maka Dad amma banda na Auren Alhaji Umar " sannan tayi ajiyar zuciya tace "ina jinka Dad". "Yauwa D'iyar kirki, maganar da nake so muyi dake game da cutar da ke damun Alhaji Umar ce, dazu ya fad'i anan yana ta aman jini da muka je asibiti likitoci sun tabbatar mana da cewa yana d'auke da ciwon zuciya, kuma ciwon ya kamu da ita a dalinlin sonki ne, yanzu haka yana kwance shame-shame rai a hannun Allah baya iya ko motsi, ana kyautata zaton nan da kwana uku zai farfad'o in shaa Allah, sannan sun ce idan so samu ne ana so yana farfad'owa ya fara ganin abinda yake so a kusa dashi, shine nake neman alfarma a gareki dan Allah dan Annabi Mamana ki amince muje asibiti ya farfad'o a gabanki, sannan ki dubi girman Allah ki amince da soyayyar shi ko dan ki ceto ranshi, amma ki je kiyi shawara kafin nan da kwana ukun ni bazan miki dole ba, duk hukuncin da kika yanke dai-dai ne amma ki sani amincewa da soyayyar shi tamkar kin ceto ran iyalan shi daga fad'awa maraici ne, tashi ki tafi Allah ya miki Albarka" Maganganun Daddy sun matuk'ar kashe mata jiki amma fa hakan baya nufin ta zubda makaman yak'in ta, domin baza ta tab'a yarda ta auri wanda bata so ba, a hankali ta mik'e ta nufi d'akin ta Aneeserh ma ta mik'e da niyar binta Mummy tace "Aneeserh dawo bamu gama da ke ba". Dawowa tayi ta gyara zama sannan Mum tace " ni haifi Ayusha sannan nafi kowa sanin halinta, tana da taurin kai da kafiya sosai, idan muka ce zamu mata ta k'arfin tsiya to abin zai fi haka b'aci, dan haka muna so ki taimaka wajen bata shawara ko Allah zai sa a dace, kin je asibiti kinga halin da mutumin nan ke ciki amimcewar Ayusha ne kawai zai dawo dashi hayyacin shi, kinga yana da kyau kema ki bada gudummawa wajen ceto rayuwar shi" ta k'arashe maganar tana zubda hawaye. "Ku kwantar da hankalinki Mum&Dad in shaa Allahu nayi alk'awarin shawo kan Ayusha ta amince, zan jure duk wani wulak'anci da zata min dan na cimma buri na" Dad yace "idan kikayi haka kin tabbatar mana da cewa ke 'yar halak ce, saboda haka daga yanzu aikin ki zai fara Allah ya miki albarka ya baki nasara" "Ameen thumma Ameen Dad, bari na shiga na sameta duk yadda mukayi da ita I will let you know" "ok d'iyar albarka Allah ya bada sa'a" inji Mummy. Aneeserh na shiga ta tarar da ita ta had'a kai da gwiwa sai kuka take, da sauri ta k'arasa wajen ta tana fad'in "Subhanallah!!!, haba k'awata bai kamata ki tada hankalin ki akan k'addarar da Allah ya sauk'ar miki ba, addu'a ya kamata kiyi Allah yasa hakan shine mafi alheri" "kar kiyiwa k'addara sharri domin wannan ba k'addara bane son zuciya ne, me yasa Mum &Dad suka canza sun kasa fahimtar halin da nake ciki, abin da ke damun Alhaji Umar shi ke damuna, idan har bazai iya hak'ura da soyayyata ba nima bazan tab'a iya hak'ura da son wanda nake k'auna ba amma gaba d'ayan ku daga ke har su kun kasa fahimtar hakan, to ki sani idan ma aiko ki sukayi ki koma ki sanar dasu cewa nayi making decision ban amince da shi ba kuma bazan tab'a amincewa da shi ba" tana gama fad'an haka ta fad'a kan gado ta fara wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro" "Ayusha bazan tab'a mamakin fitowar wad'annan kalaman daga bakin ba, domin duk wanda soyayya ta rufe masa ido babu abinda bazai iya aikatawa ba... amma ina so kiyi saurin dawowa hayyacin ki k'awata ki sani fa shi bawan Allan da kike hauka a kanshi ma bai san kina yi ba, baki da tabbacin zaki sake ganin shi a rayuwa idan har Allah ya k'addara had'uwar ku dashi ma baki da tabbacin zai so ki ya aure ki" "Ai dama banyi dan yasan inayi ba kuma da kike cewa bai zama lalle ya soni ba ban kai ya soni ba? ko kina nufin bani da qualities d'in macen da ya dace a aura ne!!! wallahi Aneeserh kin bani mamaki ban tab'a tsammanin haka daga gareki ba, Mum &Dad sun juya min baya kema haka" sai ta k'ara fashewa da kuka. Matsowa bakin gadon Aneeserh tayi sannan tace "k'awata ina so ki fahimci wani abu guda d'aya idan kika ce mun juya miki baya sai Allah ma ya tambaya ki, muna k'ok'arin mu nuna miki hanyar da ta dace ne, ki tuna fa tunda kike a rayuwarki baki tab'a neman wani abu wajen iyayen ki kin rasa ba, duk wani abu da suka san zai saki farin ciki shi suke miki sannan suna gudun duk wani abu da zai b'ata miki mai yasa a karo na farko baza ki faranta musu rai ba, kar ki manta Ayusha Dad da bakin sa yace yana so ki mishi alfarma while kin san yana da right d'in da zai iya d'aura miki aure da duk wanda yake so ko kina so ko ba kya so, and another thing da nake so ki sani shine faranta musu rai dai-dai yake da faranta ran mahaliccin ki sannan b'ata musu ma dai-dai yake da b'ata masa ki tuna da hadinsin manzon Allah ( S. A. W) da yake cewa *_"Ridallahi fii Ridal Walidaini Wa Sukhd'ullahi fii Sukhd'ul walidaini "(Yarda Allah yana tare da yardar iyaye kuma fushin Allah yana tare da fushin iyaye)_* saboda haka k'awata ina mai shawartar ki da kiyi gaggawan dawowa hayyacin ki, ki farantawa iyayenki ko kya samu tabaraki a rayuwa" "Baza ki gane bane K'awata, wallahi dai-dai da na second d'aya ban jin zan iya k'aunar Alhaji Umar, domin shi mutum ne mai son kansa da yawa, budurwar zuciya gareshi, kar ki manta Anty Zee aminiyar Mummy ce tun yarinta tare suka tashi komai nasu tare sukeyi har sukayi aure basu daina zumunci ba, Anty Zee ta kasance mace yar k'walisa da gayu ga addini da ibada uwa uba ga san mutane d'anta d'aya a duniya Fahad daga shi bata sake haihuwan wani ba, Allah yayi ta da son jama'a hakan yasa ta d'auko cousin sister nata Muneerah ta dawo wajen ta da zama, Muneerah na primary 3 ta dawo wajen ta da zama tana gama secondary school tsabar rashin adalci da son zuciya irin na Alhaji Umar ya aure ta, babu kunya kuma ya ajiyeta a gidan take abin da ta ga dama domin Muneerah bata da kunya sannan bata da mutuci ko kad'an" Daya ke Allah ba azzalumin nawansa bane shekarar Muneerah uku ya auro Rahma, Rahma k'anwar kishiyar Maman Muneerah ce suna zuwa gidan tare da k'anne ta har Allah yasa ya k'yallaro ta ya auro ta sannan ni ma yanzu yace zai aureni, inaa wallahi sai dai ya mutu ya bar duniyar gaba d'aya amma bazan tab'a yarda na aure shi ba, mu uku Iyayen mu suka haifa, Anty Khadeeja da Anty Fareedah sai ni Auta duk kansu auren soyayyah sukayi me yasa sai ni da nake autar su za'a min auren dole a rasa ma wanda za'a aura min ma sai tsoho sa'an Babana mai 55years a d'oron k'asa inaa wallahi da sake sai dai Mum & Dad su tsane ni su daina sona kwata-kwata amma bazan tab'a yadda na aure sa ba" sai ta k'ara fashewa da sabon kuka. ```Wasa Farin girki This is just the beginning of the story kuci gaba da bina dan ganin yadda labarin zai kasance na barku lafiya masoyana ``` *RØØKÎÊY D BEST✍��* [14:56, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* 81-85 Sake matsowa kusa da ita Ayusha tayi tace "ki kwantar da hankalin ki K'awata na fahimce ki sosai da sosai amma ina so ki sani Mum & Dad baza su tab'a cutar dake ba a rayuwa wannan zab'in da suka miki shine dai-dai a wajen su nasan zakiyi tunanin cewa dan ba ni ce cikin wannan situation d'in ba yasa nake fad'in haka, to ki sani ko da nice iyayena suka nemin alfarmar nan a guna zan musu duk da cewa they are not responsible parents basu yi deserving a musu hakan ba amma domin samun rabauta wajen ubangiji zan amince musu" kuka ne yaci k'arfin ta yasa ta yin shiru. D'ago jajeyen idon ta Ayusha tayi sannan tace "what do you mean by they are not responsible, Aneeserh iyayen naki kike fad'awa haka, bai kamata damuwa ta tasa ki fad'an kalaman da basu dace dasu ba, ki tuna fa ke kike min nasiha akan iyaye no matter what they do basu cancanci haka ba" "Ayusha nasan abin da nake fad'a gaskiya ne so no need kiyi tunanin cewa ban kyauta musu ba, idan kika ji labarina zaki san cewa eh lalle basu dace su zama iyaye na ba shiyasa a ko da yaushe iyayenki suke birge ni rayuwar su tayi min A1". "Ban fahimce ki ba k'awata" "yanzun nan zaki fahimce ni in shaa Allah, yaune rana ta farko da zan fara baki labari na so tari ina attempting fad'a miki sai naji kunya ta dabaibaye ni amma ya zama dole na sanar dake ko zaki d'auki darasi a ciki." *_LABARIN ANEESERH_* Da farko dai sunana Aneeserh Adam Muhammad, asalina yar jigawa ce a wani gari ana k'iranshi D'angyatin, Mahaifina ya kansan ce yana kasuwancin fata kuma Alhamdulillah yana samu sosai da sosai gidan mu babban gida ne me kyau da tsari, mahaifiyata Hajia Zainab ita ce uwargida sai kishiyoyin ta Maryam da Halima, mu goma sha biyar ne a wajen mahaifin mu kuma nice babba, mu bakwai wajen Mamar mu, sai biyar na Maryam uku na Halima" Tun da na taso a rayuwata ban san menane parental love ba (soyayyar mahaifa) nayi k'uruciya ta cikin wahala da tashin hankali, bani da ikon yi komai a gidan mu mahaifiyata bata damu dani ba kamar ba ita ta haife ni ba, da nayi abun da bai kai ya kawo ba sai ta hau zagina a gaban k'anne na da kishiyoyin ta kamar "shegiya, mahaukaciya, jaka dabba mara hankali wacca bata san ciwon kanta ba, ke dai a haka zaki k'are". Shiyasa daga kishiyoyin nata har k'annena basu ganin mutunci na yaro sai ya rufe ido ya zage ni son ransa ban isa na tanka ba, shima mahaifin mu ba damuwa yayi da yaja mu a jiki ba, abinci dai baya yanke mana a gidan nan sannan idan sallah ta zagayo zai mana d'inki amma fa sauran responsibilities d'in sai a slow ko wace mata ita take yiwa 'yay'anta banda mahaifiyar mu, gashi tana business sosai yadda bakya tsammani amma dai-dai da pant bata tab'a siya min ba. K'awata na taso cikin tashin hankali yadda bakya tsammani domin tsakanina da mahaifiyata maganana mai dad'i baya shiga sannan kuma ta kafa min takun kumi ban isa na fita ko bakin k'ofa ba ko k'awaye na ne suka zo ban isa na raka su ba, gashi ni kuma Allah ya halicceni me farin jinin jama'a daga manya har yara idan na fita suna sona. Bayan na gama primary school na tafi FGC Gwaram dake nan jigawa state, mahaifina yana min shopping na provision dai-dai gwargwado ya bani pocket money da yasan bazan buk'aci wani ba, to idan naje nakan siya inner waers da sauran necessary things d'in da bani dasu a wajen metron namu. Tunda na shiga secondary school rayuwata ta fara canzawa domin na had'u da friends da yawa masu sona da k'aunata, idan mun zauna suna labari iyayen su sai dai nayi shiru domin bani da abinda zance me dadi game da nawa iyayen idan lokacin visiting yayi sai dai amin aike ko karen gidan mu bazan gani ba har visiting ya k'are. A haka rayuwata taci gaba da tafiya har nakai SS1 a wannan lokacin na fara mallakan hankalin kaina girma yazo, domin a lokacin na ma fara period, ranar da na fara period nayi kuka sosai domin ban san wani abu game dashi ba wata k'awata mai suna Amma na samu na sanar da ita abinda ke faruwa tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata girma ne ya kamaki ai it's normal a wajen ko wace mace, kinga ni a gida na fara so ban wani sha wahalan neman Pad ba Mamana ce ta koya min komai sannan tamin nasiha sosai tace kar na kuskura na diga mu'amala da maza ko da kuwa yayyena ne ko hanuna namiji ya rik'e zanyi ciki da zan dawo ta had'oni da PAD shida dan haka muje na baki idan kin koma gida sai ki sanar da maman ki, nasan zata ji dad'i sosai " muka je ta bani pad ta koya min komai. Tun daga wannan lokacin na fara siyan PAD da kud'ina har na kammala secondary mahaifiya ta bata tab'a attempting tambayana ko na fara period ko ban fara ba balle tayi k'ok'arin siyamin pad, inada 16years na kammala secondary school Samari da dama sun na kawo min hari duk wanda yace yana sona bana bashi fuska domin ina tsoron abinda zai je ya dawo, nayi applying ABU &BUK ban samu ba ina ji ina gani na cinye wannan shekarar a gida. The next year wani Uncle d'ina ya sake biya min kud'i nayi jamb shine na samu admission anan 'YAR'ADUA UNIVERSITY KATSINA kafin na taho warning mai gamma iyayena suka min akan soyayya musamman ma mahaifiyata da tayi ta jifana da kalamai marasa dad'in ji akan maza wanda ko mak'iyinta akai wa baza taji dad'i ba. A sheka da nazo Allah ya had'ani da ke da Mujaheed kun zamo wani babban jigo na rayuwata wanda bazan tab'a iya rayuwa ba tare da ku ba, Mujaheed ya dad'e yana takura min game da ya turo iyayen shi gidan mu nak'i amince mishi badan komai ba illah dan ban san ta yadda zan shawo kan al'amarin ba,Ayusha iyayen ki sun min komai a rayuwa sun maye min gurbin iyayena sun soni kamar d'iyar cikin su bani da abinda zan saka musu dashi sai addu'a saboda haka dan Allah dan Annabi ki daure ki amince da buk'atarsu albarkacin kasancewar su iyayen na gari" Tana gama fad'in haka ta fashe da kuka Rungumota Ayusha tayi suka ci gaba da kukan su. Sai da sukayi mai isarsu sannan Ayusha tace "lalle k'awata kinga jarabawar rayuwa Allah yasa k'arshen wahalar kenan in shaa Allah zanyi k'ok'ari naga na dai-daita tsakanin ki da iyayenki na dawo miki da farin cikin da kika rasa shekara da shekaru" "K'awata na gode da kullawar ki gareni amma ki sani in da sabo na saba da halin iyayena sannan shawo kansu ba abu bane mai sauk'i domin kaf family d'in mu babu wanda bai san halin da nake ciki ba tun ina k'arama wasu ke k'ok'arin sulhuntamu amma abin yak'i so ni yanzu ba wannan bane a gaba na fata na ki amin ce da buk'atun iyayen ki domin sun kai a sadaukar musu" "Aneeserh baza ki gane bane Mum &Dad are more than everything they deserve more than sacrifice from me, the fact is that bazan iya amimcewa da soyayyar tsohon nan ba na tsane yadda bakya tsammani" "Ayusha me yasa kike da taurin kai ne, na san abin da ciwo amma yak'ar zuciyarki ya kamata kiyi bawai kibi umarnin ta ba, ki zauna kiyi nazari sosai a kan batun idan kina da hankali labari na da na baki ya isa ki k'ara tausayawa tare da k'aunar iyauenki" haka dai sukayi ta tattauna batun sai wajen 2: 00am sukayi bacci. *_WASHE GARI DA SAFE_* Sai misalin 10: 00am suka tashi daga bacci already Mum ta had'a musu breakfast, so had'uwa sukayi gaba d'ayan su sukayi break, ko a fuska Ayusha bata ga wani changes a wajen iyayen ta ba, bayan sun gama break tace da Mum & Dad zata shiga ciki ta kwanta domin baccin bai isheta ba. Bayan ta shiga ciki Mum tace da Aneeserh "ya kuka k'are da ita jiya ne" "ke dai ki bari kawai Mum, wallahi ban tab'a sanin Ayusha na da taurin kai haka ba sai jiya duk yadda nayi da ita tak'i amincewa da batun yanzu haka ma bama magana na fita harkarta" Dariya sosai ta basu sannan Dad yace "to in banda abinki d'iyata miye na gaba kuma keda kika ce zaki jure duk wani wulak'anci da zata miki sai ki b'ige da gaba" "Baza ka gane bane Dad gaban ma wani salo ne ai" "ok sai yanzu naje ghana" A kwana a tashi ba wuya, yau ta kasance saura kwana d'aya ranar da Doctor yace Alhaji zai farfad'o yayi, iyayen Ayusha sai zuba ido suke ko zata basu had'in kai zuwa wajen shi asibiti amma shiru ko alamu babu a wajenta, Aneeserh ma da take jiyo musu information tayi shiru. *_RANAR FARFAD'OWAR ALHAJU_* 6: 00am Ayusha da Aneeserh suka tashi suka shiga kitchen suka had'a breakfast sukayi shirin zuwa school bayan sun gama suka zuba a flasks sukayi wa Mum & Dad sallama zasu tafi school dashi domin yau suna da visiting lecturer kuma zasu iya kaiwa yamma lis a can, tsabar takaici basu iya cewa dasu komai ba sai "Allah ya kiyaye hanya". ```To Masu karatu ku biyoni dan ganin me zai faru da Alhaji tunda Ayusha ta rufe ido ta kama gabanta tayi school ``` *RØØKÏÊY D BEST* [14:56, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* *_Assalamu Alaikum Masoya na nayi farin ciki sosai da na dinga cin karo da sak'wanninku tabbas idan ba makaranta barubuta, amma ina so ku fahimci wani abu guda d'aya idan muka ce a rayuwa duk abin da muke so sai mun samu to muna tare da wahala sannan akwai matsala babba domin wani abun ba alheri bane idan mun k'wallafa rai mun same shi daga baya za muzo muna da nasani dan haka dan Allah 'yan-uwana mu kiyaye mu rungumi duk k'addarar da ta zo mana hannu bibbiyu, saboda haka ina so duk abin da ya faru a littafin nan ku d'aukeshi a matsayin K'ADDARA da JARABAWA, Muje Zuwa. sannan wannan Shafin na sadaukar dashi ga duk wani masoyin ALLURA TA TONO GARMA����_* 91-95 Washe gari da safe bayan sun kammala komai na aikin gidan suka yi shirin school sannan suka had'u a dinning dan yin breakfast, Favorite food d'in Ayusha Mummy ta dafa wato D'an wake amma abin mamaki shine kowa yana cin abincin banda ita ta tsaya sai jujjuya fork take. Dad ya dube ta da kyau yace "Auta lafiya bakya cin abincin, tunanin me kikeyi haka?" "ba komai" "da komai mana Auta,tunda kin kasa kai koda gudan d'anwake d'aya ne bakin ki, while kin san cewa saboda ke nayi d'an waken nan" "wallahi Mummy bana jin zan iya cin d'anwaken nan saboda gaba d'aya nayi loosing appetite d'ina, baki na ba taste wallah" Dad yace "Look Auta!!! har yanzu akwai sauran damuwa a tattare da ke so say out your mind ni kuma nayi miki alk'awari zan zame miki garkuwa na miki abinda kike so idan bai fi k'arfina ba" Kallaman Dad sun matuk'ar kashe mata jiki har take jin ba zata iya gabatar musu da buk'arta ba amma wata zuciyar tace da ita "haba Ayusha this is the only opportunity left!!! wallahi idan kikayi wasa da wannan damar shike nan kin rasa Dream Guy d'inki har abada, you better do something to save your love, ki zab'i inda zaki samu farincikin rayuwar ki, me zakiyi da tsoho ai yaro sai yarinya " D'aya zuciyar kuma tace "a gaskiya Ayusha idan kikayi haka baki kyautawa iyayen ki ba ki duba kiga irin damuwar da suka shiga yanzu sakamakon rashin cin abincin ki, har suna ikirarin komai kike buk'ata zasu miki, to idan ki sanar musu canjin ra'ayin da kikayi ya zasuyi feeling and da wani ido zasu kalli su Anty Zee while in public kika furta cewa kin amince da auren Alhaji Umar, ya kamata ki dawo hayyacin ki kisan me kikeyi domin dream guy d'in naki ma bai san da existence naki ba balle ya damu dake" Bata gama deciding wace zuciya zata bi ba taji Mummy ta jefo mata tambaya a k'ufule "wai ke ba magana ake miki bane kikai banza da mutane Ayusha bana son sakarcin banza da wofi fa". wasu hot-hot tears ne suka fara gangarowa daga idon ta a hankali ta bud'i baki zatayi magana sai ta tsinci kanta a mai jin kunyar iyayen ta. Dad yace "kinga Auta idan baza kiyi magana ba shikenan, amma ki sani barin damuwar taki a ciki ba shi zai magance miki ita ba. "Dad dama ba komai bane fa, tun jiya da muka baro asibiti nake ta tunanin halin da Uncle Umar yake ciki shine nake so idan mun tashi daga school mu biya mu duba shi" A take Mum ta fara washe baki "dama wannan ne damuwarki kika tsaya kina wani kwane-kwane, ba komai idan kun tashi daga school d'in sai ku je" nazarin ta sosao Dad yayi sanna yace "kin tabbata abin da kika fad'a mana haka ne?" "Eh haka ne" "to shike nan Allah ya miki albarka ya baki ladan biyayyan da kika mana, shima Alhajin idan yaji sauk'i sai a fara zancen biki dan ba wani dogon lokaci za'a d'auka ba saboda yanayin da ake ciki" Da k'yar da lallami suka shawo kanta taci abincin, bayan sun gama Dad ya basu kud'i yace su Siya fruits da drinks su kai asibitin. Suna fita ta fashe da kuka Aneeserh tace "dan Allah K'awata ki kwantar da hankalin ki mana, naga alama kin kasa karb'ar k'addarar da ta zo miki, saboda haka ni zan koma ciki na sanar da Mum &Dad cewa kin janye maganar auren Alhaji Umar ai abin is understandable " tana gama fad'an haka ta juya da niyyar komawa gida da sauri Ayusha tasha gabanta "dan Allah kiyi hak'uri K'awata wallahi na kasa amincewa zuciyata ta so shi amma daga yanzu na miki alk'awarin zan amince dashi zan karb'e shi a matsayin hannu bibbiyu koda kuwa hakan na shirin barazana ga rayuwata ne saboda haka daga yanzu na sadaukar da soyayya Dream guy zuwa gare shi" Rungumota Aneeserh tayi sukayi ta kuka san ransu sannan suka k'arasa car park Ayusha ta bata key ba musu ta karb'a da yake itama ta iya motan suka nufi boko, da yamma liss suka je asibiti, abubuwa da dama sun faru tsakani Ayusha da A. Umar tayi k'ok'arin danne tsanar sa a fili ta bashi kulawa ta musamman, ita ko Anty Zee sai nan-nan take da Ayusha kar abu kad'an ya faru tace ta faso domin tayi observing cewa dauriya kawai takeyi ba son shi takeyi ba, Allah ya taimaka Muneerah bata nan tun jiya da ta fice bata sake lek'ewo ba, Rahma ma tunda ta tafi da azahar bata dawo ba so abin ya zo da sauk'i, sai da sukayi Magrib sannan suka koma gida. Kusan kullum Ayusha sai taje duba Alhaji Umar amma fa kullum da daddare bata bacci dream guy d'in ta ne ke zuwa mata a mafarki da kalamai masu rikitarwa tun tana damuwa har ya zama jiki. Bayan sati d'aya aka sallami Alhaji Umar daga asibiti Alhamdulillah an samu improvement sosai domin ya dawo normal sai d'an abinda ba'a rasa ba, kwanan shi uku da sallama ya fara zuwa Zance, Ayusha in taje banda Uhm.. da ummm-ummm babu abinda take cewa har a tashi daga hiran idan ta dawo tayi ta kuka domin yanzu Aneeserh mai d'ebe mata kewar ma bata nan ta tattara ta koma school. A kwana a tashi ba wuya har sun fara exams a lokacin ne aka. tsaida lokacin auren ta da Alhaji bayan ta gama exam's da two weeks, ba k'aramin tashin hankali Ayusha ta shiga ba da jin labarin auren, amma saboda tsananin tawakkali irin nata bata tab'a yarda Mum &Dad ko Aneeserh sun gane hakan ba, sannan bata da aikin yi cikin dare sai ibada, (karatun Al-Qur'ani mai girma, Nafilfili da Nagartattun addu'oi) tana sanar da ubangiji damuwar ta. Ranar last paper sukayi sharing IV k'awayen ta mamaki suke domin sun san Ayusha bata son aure yanzu ita da take ikirarin sai tayi Masters da PHD sai gashi 300level d'in ma bata gama ba zata shiga daga ciki, da suka isheta da zolaye tace "kai ku k'yaleni lokaci na ne yayi, daa d'in ma yarinta ne ke damuna, yanzu da na girma ba gashi na rigaku kawo miji ba " Sai suka kwashe da dariya suna tambayar ta event nawa za'ayi a bikin Sai tace dasu "ku kwantar da hankalinku 'yammata, bawani bidia zamuyi a bikin ba domin mijina Ustazu ne, walima ce ran Friday sai yini ran Saturday that's all, batun anko kuma ba siya zakuyi ba Daddy ya mana odar dogayen rugunan da zamu sa a walima shi kuma ango ya siyo mana atamfar da zaku sa ranar d'aurin aure abinda zakuyi kawai d'inki ne fak'at!!!" Nan fa 'yammata suka kacame da hayaniya kowa na tofa albarkacin bakinshi daga masu cewa"gaskiya Dad da Ango sunyi sun rage mana wahala" "gaskiya an kwafsa mana da baza'ayi chasu ba" sai masu cewa "hakan ma yayi dai-dai ai, albarkar aure ake nema ba komai ba" Bayan sun gama exam's da kwana biyu suka shiga raba anko daya yake friends d'in nasu basu da yawa basu wuce 20-25 ba a kwana 3 suka kammala komai domin AYUSHA ba wani gayya tayi niyyar yi ba suma wad'annan d'in dalilin da yasa ta basu I.V ba komai bane illa course mates nata ne da kunya suna tare ba'ayi grads ba suji labarin tayi aure ba invitation, da baza tayi inviting nasu ba. Sun gama rabiya da kwana d'aya suka tattara suka nufi D'angyatin garin su Aneeserh tare da Mum & Dad, iyayen Ayusha sun sha wahala sosai wajen shawo kan iyayen Aneeserh akan abin da suke aikata mata, da farko iyayen ta rufa ido sukayi suka fara rashin mutunci "wai su babu wanda ya isa ya koya musu yadda zasu tafi da rayuwar iyalinsu, wato ma dan rashin mutunci ma k'ararsu ta kai ko? to daga yanzu sun soke university d'in ma zaman gida za tayi tunda bata san ciwon kanta ba" da yake Mum &Dad mutane ne wayayyu sun san yadda zasu bi da mutum duk irin bak'aken maganganun da suke fad'a musu bai sa sunyi fushi dasu ba, sai ma gyara zama da sukayi saka fara sanar da su illar abin da girman hak'k'in d'a akan iyayen sa. Jikinsu yayi sanyi sosai sukayi ta kuka suna neman gafarar Aneeserh sannan suka ce ta sanar da Mujaheed idan ya shirya ya turo magabatan sa a d'aura musu aure rana d'aya da Ayusha, nan dai farin ciki ya dawo sabo" Nan fa Dad ya nemi alfarma cewa idan iyayen Mujaheed sun amince da auren yana so a d'aura a katsina tunda can Aneeserh zata zauna, sannan batun kayan d'aki shi zai musu, Abban Aneeserh yace ya amince a d'aura auren a can amma shi zai musu komai da komai domin a karo ma farko ya faranta ran d'iyar sa. Kowa ya amince da hakan domin Wannan alamu ne na cewa ya zubda makaman shi, Ayusha ce tayi wa Mujaheed waya ta sanar dashi abin farin cikin da ya faru, yayi murna sosai da daddare ya k'ira ta ya tabbatar mata da cewa gobe iyayen shi zasu zo, a daren suka sanar da iyayensu. Kamar yadda Mujaheed ya fad'a hakan kuwa akayi domin iyayensa sun zo an tsaida maganar aure, washe gari Mum & Dad suka koma Katsina suka bar su Ayusha a D'angyatin domin Maman Aneeserh tace itama baza a barta a baya ba ita zata gyara 'yammatan ta in yaso ana sauran two days to bikin sai suje gaba d'ayan su. Duk abinda aka sa masa rana sai yazo yau ta kasance ranar walimar Auren Ayusha da Aneeserh inda Angwaye da Amare da sauran 'yan uwa da abokan arziki suke farin cikin wannan ranar banda Ayusha domin ta so ace da dream guy d'in ta akeyi amma haka tayi ta managing rayuwar ta har zuwa ranar d'aurin Auren. Ranar Saturday da misalin 10: 30 am aka shaida d'aurin auren ANEESERH da MUJAHEED, AYUSHA da ALHAJI UMAR muna musu fatan zaman lafiya da farin ciki mai d'orewa. Lokacin da Ayusha taji an d'aura aure haukacewa ne kawai batayi ba domin dak'yar Aneeserh dak'awayen su suka shawo kanta domin tirewa tayi sai an warware auren Allah yaso duk Dramar da akeyi iyayen su basu sani ba so sunyi nasaran shawo kanta amma fa wunin ranar da ba a dad'in rai tayi ba. Da dare yayi su Anty Zee 'yan d'aukar Amarya suka zo nan ma Ayusha tace bata san zance ba da yake normally amare nayin haka sai mutane basu fahimci komai ba, ana cikin show d'in dangin Mujaheed suka zo nan fa aiki ya dawo sabo da k'yar aka raba Ayusha da Aneeserh domin kowa cewa take ba zata tafi ba sai ta raka 'yar-uwarta sai da aka musu da gaske kafin suka rabu. SARDAUNA ESTATE aka kai ANEESERH ita kuma AYUSHA G.R.A daren ranar da zazzab'i ta kwana duk wanda suka kwana a gidan ta basuyi baccin kirki ba domin ta matuk'ar tada musu hankali. Nidai RØØKÌÊY KÆXS nace Allah ya bada zaman Lafiya AYUSHMAR, ya kawo Zuria d'ayyaba. Kuma ANEESMU ban barku a baya ba duk da cewa kuna k'aunar junanku hakan ba shi zai sa na kasa yi muku addu'a da fatan alkhairi ba. *_#TEAM FAHAD kuyi hak'uri da abinda ya faru nima ba da son raina Alhaji ya auri Ayusha ba amma ku sani mutum bai isa ya wuce k'addarar sa ba, kuyi duba ga Aneeserh a lokacin da batayi zato ba rayuwarta ta canza ta dawo dai-dai domin ta tsaya ta jajirce ta mik'a lamuran ta ga Allah. Dan haka kuyi hak'uri kuci gaba da bibiyata domin tsugunno bata k'are ba dan har yanzu ALLURA bata TONO GARMA ba._* *RØØKÎËY D BEST* [14:56, 02/12/2017] ‪+234 703 786 0131‬: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO* *GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED ON FICTION & CONCOCTION_* ® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S *MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_* *BY* *_ROOKIEY KAXS_* *DEDICATED 2* *_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_* 96-100 Washe gari da safe jikin Ayusha ya tsanan ta sosai dan haka ba'ayi wata-wata ba su Aunty Fareeda suka kaita ALHERI SPECIALIST HOSPITAL wani private hospital da ke nan G.R.A. suna zuwa basu tarar da mutane ba kasancewar asibitin private ne dan haka babu b'ata lokaci Doctor yayi diagnosing nata, bayan yayi wasu 'yan rubuce-rubuce ya d'ago ya kalle ta da kyau sannan yace "ke ko 'yammata tunanin mai kike haka kina nema ki illata rayuwar ki,gaskiya tunani bai kamace ki ba at your young age" . Duk da azababben ciwon kan da ke damun ta hakan bai hanata d'agowa ta galla mishi harare ba a zuciyar ta tana fad'in (lalle Doctor d'in nan ya raina min wayo, ina ruwan sa da shekaru na da zaina min kallon yarin ta, yana wani iyayi sai kace shi d'in wani babba ne Mtwss!!!" taja tsaki ashe ya fito fili bata sani ba. Da sauri yace "sorry 'yammata na miki shishigi a lamarin ki ko" kafin tace wani abu Aunty Khadija ta shigo hannu ta rik'e da waya "Doctor sannu da aiki, Ayusha ga Mummy nan zakuyi magana a waya" bayan Ayusha ta karb'i wayan Doctor yace "Bismillah Anty ga waje ki zauna za muyi magana da ke,ku ne kuka kawo wannan patient d'in ko,dan naga kuna kama sosai hala SISTER d'inki ce ko dama ba wani abu bane illa ina so ku mata fad'a ta rage yawan tunani domin yana gab da ya mata mummunan illah" hospital card ya mik'a mata "ga wannan kuje pharmacy ku siyo Magani,Allura da Drip ne aka rubuta zamu bata gado domin za'a d'aura mata drip kuma condition d'in nata is not stable tana buk'atar hutu" "Doctor bazai yiwu mu tafi da ita gida a sa mata a can bane,saboda Amarya ce jiya aka d'aura auren ta, kaga hankalin mutane zai tashi sosai idan suka ji an kwantar da ita anan" "eh to za'a iya sa mata a gidan ma amma dan Allah a keb'eta daga cikin mutane domin hayaniyar su na iya coursing wani ciwon, sannan tana buk'atar kulawar ku domin jinin ta ne ya hau sosai sakamakon wani b'accin rai ko damuwa da tasa a ranta so you need to counsel her because she is in risk at her young age" "Innalilahi wa'ina ilaihi raji'un yaushe Ayusha ta kamu da hawan jini dama ni nasan ba son mijin nan take ba, tunda haka ne wallahi sai an raba auren nan" ta fad'a tana kuka a lokacin ne Aunty Fareeda ta shigo da Ayusha tace "Doctor ga patient d'in ka na dawo maka da ita wai hajijiya take ji sosai" kafin Doctor yayi magana Aunty Khadeeja tace "Ayusha yaushe kika fita bamu sani ba" "ai kina mik'a mata wayar ta fice ina kallon ta, dama zata ji hajijiya mana tana tattare da yunwa cikin ta ba komai ga zazzab'i da sauran su" cewar Doctor kenan. Aunty Fareeda ta kuma cewa "Khadeeja mai ya same ki naga kamar kina kuka" "ba kama bane Aunty kuka nake Ayusha na d'auke da hawan jini saboda rashin adalcin da aka mata na aura mata wanda bata so, wallahi zanyi iya kacin bakin k'ok'ari na naga an raba auren nan" sai ta kuma fashewa da kuka. "Yi shiru Khadeeja wannan ba maganar da zamu tattauna a nan bane saboda haka kiyi hak'uri yanzu ta lafiyar ta muke tukun idan mu koma gida zamu san me zamuyi a kai" Doctor ya tambaye su ko suna da wanda zai mata allura ya sa mata drip ne a gidan Anty Fareeda tace "muna dashi Doctor wannan da kake ganin ta ma Nurse ce so zatayi duk abin da ya dace" "OK!!! tunda haka ne ba damuwa kuje ku siyo sai tai mata abin da ya dace Allah ya bata lafiya" "Ameen Doc." suka fad'a a tare sannan suka fita da ita. Suna fitowa daga office d'in Doctor suka nufi pharmacy, bayan sun gama da komai suka koma gidan Amarya suna isa suka ga gidan ya sake cika da mutane sai faman sannu ake musu, d'akin Ango aka kaita domin nan ne ba hayaniya. Aunty Zara'u Cousin sister d'in su ce ta shigo musu da breakfast tana fad'in "sannun ku da dawowa, ga breakfast nan Aunty Zee ta aiko tun d'azu" "OK sannu da k'ok'ari K'awas had'awa Ayusha tea tasha, sai tasha magani a sa mata drip" cewar Anty Fareeda kenan. "Ok to ba matsala Allah dai ya baki lafiya Amarsu ta Alhaji, wallahi yarinya ki kwantar da hankalin ki ki zauna da mijin ki lafiya" Aunty Zara'u gidan surutu kenan tana had'a tea tana suburbud'a zance bayan ta gama suka sa Ayusha a gaba sai da ta kusan shanye one cup sannan tasha magani Aunty Khady ta d'aura mata drip,a hankali ta samu bacci ya d'auke ta sannan suma suka samu sukayi breakfast. Sun kai kusan minti talatin suna hirar duniya sannan Aunty Khadeeja tace "Sister har yanzu baki ce komai ba game da issue d'in Ayusha da na miki magana d'azu a asibiti ba, nifa gaskiya zan je gida na samu Daddy na mishi bayanin abin da ke faruwa domin wallahi ni bazan iya barin ta cikin halin nan ba" "Matsala ta da ke gajen hak'uri wallahi, yaushe ma muka dawo gidan balle mu tattauna batun, maganar ki akan hanya take amma yanzu mu bari idan Ayusha ta tashi daga baccin sai muji labarin komai kafin musan matakin da zamu d'auka, kar muje mu yanke hukunci kuma ya zama tana son kayan ta" "haba Sister wani irin so kuma wallahi tallahi Ayusha ba Son shi take ba kawai dai an tursasata ne amma in banda k'addara me zatayi da tsoho sa'an baban ta ko ni da nake da 26yrs yamin tsufa balle Ayusha Sweet 18" Murmushi Aunty Zara'u tayi tace "Deeja k'aya baki san na gida ba, idan banda abin ki akwai wanda ya isa ya wuce k'addarar sa ne? Allah ne kad'ai yasan dalilin had'a auren nan ki duba fa kiga yadda Mum suke da Aunty Zee amma gaba d'ayan su suka iya amincewa had'in nan cikin sauk'i ai wannan ma kad'ai ya ishe mu muyi accepting fact d'in dan haka ni a ganina raba auren nan ba shine mafita ba addu'a ya kamata mu bisu dashi dan bamu san me zai faru a gaba ba" "yawwa K'awas fad'a mata dai ko zata gane" cewar Aunty Fareeda kenan "babu abin da zan gane wallahi!!! baza ku gane rad'ad'in da take ji ba tunda ku ba auren dole aka muku ba ni dai gaskiya bazan..." Bata k'arasa maganar ba Ayusha tayi saurin cewa "Dan Allah Aunty Khadija kiyi hak'uri kar a ra ba auren nan wallahi ina son shi na amin ce zan zauna dashi" kawai sai ta fashe da kuka. Da sauri suka koma wajen ta suna lallashin ta "Ayusha karki yaudari kanki da wad'an nan kalaman da baza su miki amfanin komai ba, ni da ke da su duk mun san bakya son shi, to why not mu samo mafitar da zata sama mana kwanciyar hankali baki d'aya, dalilin da yasa kika ga na dage da hakan shine ni auren soyayya nayi nasan dad'in ta na san d'acin ta, idan kana son mutum no matter how hurting d'in ka da zai yi zaka iya resisting kayi controlling kanka albarkacin SO sai kiga zama yayi lasting forever, but idan baka son mutum baza ka iya jure komai ba no matter how little it is baza a je ko ina ba za'a fara facing problems, kin sani mijina barrister ne nasha ganin cases d'in aure k'iyaya a wajen shi and abin ba dad'in ji that's why bana so kema ki shiga irin wannan halin gashi matsalar kina da kishiyoyi ba d'aya ba ba biyu ba har uku, idan ita Anty Zee mun san tana da pure mind are we sure of the rest? dan haka maganin kar ayi ma kar a fara ne just accept the fact that bakya son shi wallahi you will see wonders" duk wannan bayanin Aunty Khady ke zizaro su. Wasu Zafafan hawaye ne suka zubo daga idanun Ayusha tabbas tasan maganganun da Aunty Khady take fad'a gaskiya ne amma baza ta tab'a accepting ba tunda har yanzu bata san matsayin ta a wajen Dream guy ba,da ace ta san inda yake to wallahi babu abin da zai hanata d'aukan shawarar 'yar-uwar ta, kai!!! koda tasan inda yake ma baza ta kashe auren ta ba dan tayi alk'awarin sadaukar da farin cikin ta ga iyayen ta, "kinyi shiru Ayusha baki ce komai ba ko har yanzu kina kan bakan ki ne?" "Tabbas Aunty maganar ki akan hanya take amma bazan iya rabuwa da Uncle Umar ba though ban tab'a jin ko da d'igon son shi a raina ba, nayi alk'awarin sadaukar da soyayyata gareshi domin farantawa iyaye na, nasan duk kan ku baku gane inda zance na ya dosa ba amma Yanzu zan warware muku zare da abawa" Ido suka zuba mata suna kallon ta nan dai ta kwashe musu labarin abinda ya faru from A-Z hatta labarin Dream Guy bata b'oye musu ba, sannan ta k'ara da cewa "Dan Allah Sisters kuyi hak'uri mu yarda da k'addarar da ta same mu sannan kuyi min wata alfarma ko da wasa kar ku bari wani yasan ina da hawan jini nayi alk'awarin kula da kai na zan koma Ayushar da kuka sani , Mum & Dad idan suka san ina da hawan jini zasu shiga damuwa zasuyi zaton na kasa musu biyayya ne" Maganganun Ayusha ya tsuma su sannan ta basu tausayi sosai kaf cikin su babu wacca bata zubar da hawaye ba amma basu da yadda suka iya da ita domin matacciyar soyayya takeyi ,wanda take so d'in ma bata san shi bata san komai game dashi ba kuma bata da tabbacin cewa yana son ta itama ko sun kashe auren ma a banzan domin Allah yafi mu sanin dalilin faruwar hakan. Anty Khady tace "Allahu Akbar Kabeeran!!!,Alhamdulillah Allah shine abin godiya, na gode Allah da bai bari shed'an yayi tasiri a zuciya ta na aikata babban laifi ba Alhamdulillahi ala ni'imatullah" gaba d'ayan su suka amsa da "Allah shine abin godiya" nan da suka din ga jan Ayusha da labaran da zasu sakata nishad'i da walwala, sannu a hankali ta fara warewa kamar ba ita ba. *_10:00am_* K'arfe goma dai-dai taje tayi wanka ta can cad'a kwaliya ta sa kaya ta fito fes a Amaryar ta sak, san nan taje ta gaisa da mutane ta dawo d'akin Oga wajen Anties sunyi ta bata shawarwari masu inganci game da yadda zata tafi da rayuwar auren ta tun da ma gidan su ba d'aya da kishiyoyin ba. *_Bari mu lek'a rayuwar FAHAD (Dream Guy)_* Kamar yadda na fad'a muku a baya ya hak'ura ya fauwalawa Allah komai dangane da pretty yaci gaba da tafi da harkokokin shi dai-dai gwargwado amma a duk lokacin da ya keb'e shi kad'ai bashi da wani aiki sai tunanin ta da imagining irin rayuwar da za suyi da ita idan sunyi aure. Wani abin mamaki shine a 'yan kwanakin nan yana yawan mafarki da ita tazo ta durk'u sa a gaban shi tana kuka tana fad'in "dan Allah dan annabi mijina ka taimakeni rayuwata tana cikin hatsari kai ne zab'i na kai ne farin ciki na,kai kad'ai ne zaka iya taimaka min a halin da nake ciki yanzu" shi kuma sai yaja mata dogon tsaki yana fad'in "tafi can malama ki nemi mijin ki bani ba, ni ba sa'anki bane na miki nisa neman da nake miki ma dan in baki hak'uri ne dan gane da buga miki motor da nayi yanzu da ki hak'ura da kar ki hak'ura duk d'aya a waje na" sai ya tafi ya bar ta a wajen . Da zaran ya farka daga mafarkin sai ya tashi ya d'auro alwala ya gabatar da sallah yana kuka yana rok'on Allah ya masa zab'in da ya dace, idan gari ya waye kuma ya k'ira Mummy ya fad'a mata labarin da mafarki da yayi sai tayi ta mishi nasiha da addu'a wani sa'in har kuka yake mata a wayan. Ana cikin haka ranar Sunday da yamma bayan sallar la'asar yana zaune a kan sallaya yana tilawar Al-Qur'ani mai girma, Suratul Maryam yake karantawa,sai yaji wayar sa tayi ringing bai d'aga ba sai da ya k'arasar da Ayar da yake. Abokin sa Shareeef ne ya k'ira "Assalamu Alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu" shine abin da yace da yake gaskiya shi ba kasafai zai d'aga waya yace "Hello" ba tare da ya fara sallama ba. *_(Yana da kyau yan uwa musulmai idan zamu amsa waya mu fara da sallama domin wani lokacin bamu san wane ne zai k'ira mu ba,bamu san dame yazo ba, yazo da mugun nufi ne ko sab'anin haka wannan sallamar da zamu fara gabatarwa kafin Hello na iya zame mana garkuwa da kariya a garemu ALLAH YASA MU DACE)_* "Wa'alaikumussalam,Aboki na ina ka shiga haka ina ta kira bakayi picking da wuri ba,to ka fito ka bud'e min k'ofa gani a k'ofar gidan ka dan nasan kana gida ba inda kake zuwa kamar matar kulle" "to gani nan zuwa Suda sarkin magana idan ka fara magana no comma no full stop" Yana gama fad'an haka ya kashe wayan dan yasan halin Shareef da surutu ba k'aramin aikin sa bane ya rike shi da magana a wayar ya hana shi bud'e k'ofar da wuri. *_Kafin ya k'arasa bakin k'ofa naji an k'ira sallan magrib a 9ja shine na barsu na taho nayi sallah so ku jira in na idar sai naci gaba da d'ebo muku rahoto da fatan masu karatu kuma idan lokacin da kuke karantawa yayi dai-dai da na sallah zaku ajiye kuje kuyi domin sallah gaba take komai, labarin yana nan a inda yake babu inda zai je amma Sallah idan ya wuce ya wuce kenan sai dai na gobe ga me rabon gani daga ni har ku bamu da tabbacin cewa zamu samu na Goben_.* *_Allah ya bamu ikon kiyaye sallah a kan lokaci wannan itace tunatar wan da nake so na mana ayau kuma Alhamdulillah nasan zai tunatar da wasu Allah ya bamu ikon tsira ranar alk'iyama,Bissalam NICE DAI HAR KULLUM_* *RØØKÍÊY D BÊST✍��* *ROOKIEY D BEST* Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO: +2349030159301