[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: GIRMA YA FADI ! 3 Na zauna dum, naki ko motsi, har ya gama fiddo jakunkunan da yazo da su a but din motarsa, ya zagayo ya bude min kofa ya ce "you are welcome to gwauro's house…" na hadiyi miyau da kyar nace “zai fi kyautuw ka fara shiga, ka yiwa mutanen gidan bayani na, ba wai kawai su ganni a kansu ba, idan sun yarda da bakuntana falillahil hamdu, idan basu yarda bama babu damuwa, sai muje ka kama mun (Guest House) wannan ma ba karamin taimaka ne kayi mun ba and I really appreciate”. Ya sarke 'yan yatsun shi cikin na juna,yayi baya dasu suka bada kara, kas. Yana murmushi yace "you seem lacking confidence in everyone' kina da gaskiya, Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro ne. Allah ya kiyayeki da kwana a (Guest House), domin da jin muryarki an ji 'yar mutunci, wanda ta san ciwon kanta. Ki yarda da ni, bani da niyyar cutarki, hanyace ta hadamu kuma Allah ya kulla zumuncin mu. Yadda kowanne dan uwa na jinni, ba zai ci amanar 'yar uwarsa da suka fito ciki daya ba, haka ba zanci amanar ki ba. Feel free with me, am not that type of person, don haka fito ki biyo ni, nayi miki alkawarin ba zaki yi nadamar bina ba”. Sai kawai nayi kundumbala na bude motar na fito, muka jera zuwa ciki, yayin da maigadi ya biyo mu da kayan sa. Tun daga falo ya daga murya yana cewa (Manma na dawo), daga can kuryar daki ta amsa “mon fils tu ed rtour (sannu da zuwa dana)” kafin ta dogaro sandarta ta fito tana laluben bango. Idanuwanta a bude farare tar-tar amma na fahimci bata gani. Da sauri ya karasa ta lalubi kanshi ta rungume suna magana cikin harshen su. Na yi tsaye tamkar an kafeni, ina kallon dattijuwar da nan take wani abu ya tsirga min a cikin kirji, a dalilin kamanninta da Innata. Ya ce “bani kadai bane Manma, ina tare da bakuwa ne, har da ita 'yan fashin suka tare mu, gashi bakuwa ce a Nijar shi yasa na taho da ita, ta sauka a wajen mu kada ta fada mugun hannu" tace “ina fata kasa an kamesu duka? Tunda ka tafi nake maka addu'ar Allah ya kara daukakaka akan aikinka” da alama bai ji dadin hakan da tace a kunnena ba, ya basar ta hanyar kamo hannunta zuwa kujerar da nake. Tasa hannu tana lalubani sai kyalle take ji. Na zare niqabin ta shafa fuskata sosai, sai kuma tayi murmushi tace “budurwa ce ko? Da alama zatayi kyau, tunda ga dogon hanci ina ji, gashi kace ba daga alkaryarmu take ba". Na daga ido na dubeshi yana kallona, da baki a bude, amma ya kasa magana. Ta ce "kawo mata ruwa mana? Ko sai na buge maka kai da sandata?” Ya hadiye mayataccen kallon mamaki da tsoron da yake mani, ya nufi kofar da jikina ya bani kitchen ne, ya dawo da gorar ruwan (Ragolis) da lemon (Don Simon) masu sanyi, sai raba suke, yake ya ja tebur ya aje mani har yanzu idonsa akaina, ya ce “Laliya bata zo ta dafa miki abinci bane Manma?” Ta lalubi kujera ta koma ta zauna ta ce "bar Laliya da son kudI, yanzu haka wai ta tafi karBo zakkane gidan KANGIWA, bayan albashinda ka bari na bata jiya-jiyannan". Ya hade rai sosai yana cewa "ni kam zan sallameta, ya zan dauko yarinya ina biyanta, domin ta kula da cikin uwata amma ta fita ta bar min uwa da yunwa, Allah bata isa ba tayi kadan, ko ita 'yar Uban wane ne” daga ni har gyatumar dariya muka yi, ya soma tattare hannun rigarsa da alama kitchen din zai shiga da kansa, ta ce "dadi na dakai kenan Mon Amour (masoyina), babu hakuri. Mutumin dake yi maka hidima kullum ranar Allah, rana daya da bai samu yayi ba sai ka yi masa uzuri". Ya ce “nayi uzurin Manma, me kike so na dafa miki cikin mintuna goma sha biyar?” Ta ce “dafa mun kabeji, bakuwarka kuma ka tambayeta abinda take so" ya juyo gareni "bakuwata ke kuma mai kike so?” Tsohuwar tace "au ko sunanta baka sani ba?” Kunya ta kamani, domin ban kyauta ba, na ce “sunana Zaynab, shine bai fada min sunan sa ba Mama, shi yasa nima ban fada masa ba". Yayi murmushi, amma bai dago daga abinda yake yi ba, wato zuba lemu a tambulan ya kai bakinsa, ta soma laluben sa wai zata dake shi, ta ci karo da bango kamin ta kai kas yayi maza ya cafo ta, ya kwantar da ita akan doguwar kujera, ya ce "dukkan ku kuyi hakuri, sunana mai tsada ne. Ina fadarsa ne kawai ga matar da nake matukar so, don haka Manma ki tambayamin bakuwata, shin ta shirya amsa na a matsayin mijin aurenta, in gaya mata sunana?” Kafin gyatumar ta amsa na yi hanzarin tarar numfashinta da cewa "ban shirya ba, ba kuma zan amsa ba, don haka ka rike sunanka mai tsada, bana son ji”. Ya russuna ya kwantara da kansa a cinyar gyatumarsa, cikin matsananciyar nadama yace "ina fatan ba fushi kikayi da tsokanata ba?” Nace “ta yaya zanyi fushi da mutumin da ya karBi bakuncina, alhalin bai san ko ni wace ce ba, bai ji tsoron kada in cutar da gyatumarsa dake da lalaru ba? Bai sani ba mutum ce ni koko ina daga jinsin jinnu? Bana daga cikin mutanen dake yin fushi da wanda yayi musu alheri, komai kankantarsa. Daga baya kuma ya bata musu, sai iny masa uzuri. Jeka dafowa Mamarmu abincinta, mon amour, ko ba haka ne sunan da na ji Mama na kiranka ba?” Ya mike yana dariya yace "inda kinsan menene ma'anar Mon-amour, da baki kirani da shi ba". Daga kwance tace “rabu dashi diyata, ko kin rasa masoyi me zakiyi da wannan tsololon?” Daga can (kitchin) ya amsa “lala Manma, amman kin yanke ni. Na rantse, duk fadin garinnan, kafin a samu saurayi mai kiba ta aiki ne ja" ta ce "a inda babu masu kibar ba". Haka sukayi tayi tana tana yankansa yana kare kansa, kamar wasu kaka da jika. Akwai alamun shakuwa da matsananciyar kaunar juna a tsakaninsu. Yana ji da ita, tana ji da shi, sun fahimci juna, don haka ne bata wani tsaurara magana a kaina ba, don tasan ba zai kawo mai cutar ta ba. Cikin mintuna goma sha biyar din da ya ambata, sai wani irin kamshi ya game gidan gabadaya. Ya iso rike da kwanon silver mai fadi, dafadukan kabeji ne da aka dafa ruwa-ruwa, an kuma yanka kabejin manya-manya. Ban taBa ganin irin wannan abincin ba, kamar in tambaya amma ina tsoron gwasalen da ya yi min dana nuna ina son jin sunan sa. Don haka naja bakina na yi tsit. Ya koma ya shiryo min farin kuskus da aka dafa da koren wake da karas sunyi shar a ciki da miyar hanta, da aka yanka hantar kanana-kanana, a gefe kuma soyayyen nama ne irin wanda ake soyawa a ajiye, domin bukatar gaggawa da lemun (7-alive) ya ce “to Zaynabu, aci da hakuri kinsan girkin gwauro ne" Maman ta ce "gwauro, ko tuzuru?” Ya koma gabanta yana bata kabejin a baki da cokali, yace "duk wanda kuka ga ya dace da ni, dai-dai ne." Maman ta ture lomar da zai sanya mata a baki, ta ce "nidai don Allah ka daure kayi aure Babana, na gaji da wannan wahalar da kake da ni bata dace da kai ba, da wane zaka ji? Da wannan aikin mai hatsari koda kula da gyatumarka, alhalin kai baka da mai kula da kai?” Ya sunkuyar da kai kasa bai ce mata komi ba. Da lama bai so tayi maganar a gabana ba. Na sauko daga kujera na dawo gabanta na karbi silvern a hannunsa, nace “ni idan na baki zaki ci? Ki yi masa hakuri Mama aure ai lokaci ne" na cigaba da bata tana karba tana ci bata ce komai ba. Ban juya na kalle shi ba amma jikina ya bani kallona kawai yake yi. Sai data koshi na bata ruwa tasha, sannan na karasa cin nawa, na lura har zuwa lokacin zaune yake a inda yake, bai tashi ba. Na daga ido na dubeshi, don ganin abinda ya hana shi Magana, fararen idanunsa har yanzun akaina suke, cikin kollon da ba yau na fara ganinsa a idanun maza ba. Na ce cikin basarwa “kai baka ci abincin ba" ya lumshe ido a hankali, maimakon ya masa min abinda na tambaye shi, sai ya mike yana cewa “idan kin gama kiyi amfani da wannan dakin, (ya nuna dakin da dan-alinsa) duk abinda zaki bukata akwai a ciki, domin kanwata ke yin hutu a dakin idan tazo daga makaranta, duk abinda babu kiyiwa Mamana Magana, zata fada miki inda yake". Ya fita daga falon ba tare da ya waiwayo ba tace "yarinya jeki kiyi sallar azuhur, ki kwanta ki huta zuwa la’asur, ai kinga duniya nidai wannan aiki bana sonshi, to ya kafe ne, amma wannan sai da rai dame yai kama?” Na so in tambayeta kowa ne irin aiki yake wanda bata so? Naga wannan ba damuwa na ba ne. Damuwa na shine in samu masauki, in gabatar da abinda ya kawo ni, sannan in nemi dangin Innata. Kenan abinda ya kawoni daban, suma rayuwarsu daban. Saidai babu shakka tsarin rayuwar su shi da mahaifiyarshi ya burgeni. Cikin 'yan awannin da nayi tare dashi, na fahimci abubuwa da dama game da shi. Duk matar da tayi sa'ar aurensa ta yi babbar sa'a, domin zata zauna lafiya. Kasancewarsa mutum mai saukin kai da duk wasu qualities da ake nema daga da namiji, uwa-uba irin mazannan ne da albarkar Uwa ke bibiyarsu, saboda tsananin biyayyar da suke mata da nuna jin kai a gareta, tamkar zasu kwanta mata. Karfe tara na dare muna falo tare dashi muna kallon labarun Jiha, duk da cewa ba abinda suke fada nake ji ba, kasancewar faransanci ake yi amma ai ina ganin hotuna, aka nuno 'yan fashinmu da aka kama daren jiya, ina kallonsa yana ta murmushi ko me ya tuna? Oho can kuma ya dubeni ya ce "wai don Allah menene a katuwar jakar nan ne da kika riketa kamar rai?” Na harareshi, Maman tace "yau naji ikon Allah, wannan shine kaka uwarka ta haifeka, wai naci abinci acikin cikina ace in amayar da shi aga kalarsa. Akan me zata gaya maka abinda ke cikin jakarta? Kana binta bashi ne?” Ya yi dariya yace "Allah Manma, in da kinga irin rikon da ta yiwa jakar, duk karfin dan fashinnan kasa kwatarta yayi a hannunta, sai babbansu yace "ku miko min ita in rage dare da ita, tunda ta hanamu jaka, ta bamu abinda yafi jaka" ta wawuri filon kujera ta saita inda yake azaune ta maka masa, bata san cewa ni ta makawa ba. Ya dinga yi mata dariya ya tashi ya fita ba tare da ya lura da (wallet) dinsa data fado daga aljihun gaban rigarsa ba. Na kai hannu na dauka na bude, don tsabar neman magana irinnawa, kudi ne irin nasu (Saifa) a jere gwanin ban sha’awa. ina zaro ID card kamin in duba sai gashi kamar an jeho shi yayi wuf ya karBe yace "Eye, bin kwaf, na tambayi menene a cikin jakarki, ance nayi miki tambar kaka Mamanki ta haifeki, shine ni zaki yi mun tsirara?” Na fiddo ido nace "ka fassara wane irin tsirara kake nufi, kada Mama ta dauka ‘nakedness' wannan kazafi ne," ta wawuro kofin dana cika mata da ruwa ta kwara masa ta ce “fita ka bawa mutane wuri, kasa yarinya agaba da magana kamar Aku? Ni ban san ma yaushe ne bakinka ya bude ba". Yana kokarin hada kwayan idonsa da nawa, yayi murmushi “nima ban san sanda ya bude ba, Manma, ba mamaki sabida zuwan Zaynab ne". 'Yar tsohuwar taji kunya, tayi gum, da bakinta, ta kurawa allon talabijin ido kai kace tana ganinsu, ta koma sauraron abinda ake cewa, can kuma tace "kaga bana cikin shirmen ku, karo min sautin, naji kamar ana ambaton diyata”. Kyakkyawar fuskarta ta cika akwatin talbijin din, kamar ta fito tayi magana. Kasancewar (t.v)n katuwar gaske ma’abociyar kyakkyawan hoto (flat-screen). Tana gabatar da jawabi cikin faransanci da accent din Paris mai burgewa, a wani taron bude makarantar yaki da jahilci a babban birni Niamey, Nuratu Mainasara ce. Ni kadai naji ina gwama numfashi, domin yakar burgenin data yi da matsananciyar kiyayya. To amma ko (hasidin iza hasada), dole Nuratu ta burgeshi. Hutu da jin dadi sun Boye zahirin shekarunta, sun maidata kamar wata matshiya 'yar shekara ashirin da biyar, ko ni da nake budurwa in my tenth ba zan nuna mata komai ba, sai a zaBe ta da gudu a barni. In kuwa aka koma ta fannin gyaran jiki sai ka dauka tana ‘modeling’ ne. Duk wannan kallon kurullar da nake mata, da hanci da nake hurawa, ashe yana hankalce da ni. Ya fice bai kuma dawowa ba. Gaba dayan hankalin Maman yana kan akwatun talbijin, na matsa jikinta sosai nace "Mama a ina gidan talbijin din garin nan ya ke ne?” Tana fadamin ina daukewa da biro cikin ‘jotter’ na, nace “baku da gidan Radio ne?” Ta dauko fankon idonta ta daura mini, ta ce cikin zargi “me ya hadaki da gidan radiyo da talbijin?” Nayi murmushi mai wanke zargi nace “lah! Ba wani abu, cigiya nake so in bayar a kan dan uwana da ya Bata, shine kuma dalilin barowata gida, ance ana kyautata zaton an ganshi a cikin garin nan." Jikinta yayi sanyi tace "amma da kin gayawa Mon amour, wannan karamin aiki ne a gareshi, cikin kwana daya in har yana cikin garin nan zai nemo miki shi." Na yi shiru ina tunani, wannan na nufin shi dan sandan ciki, ko kuwa Security na jiha (SS). Gaskiya kam biri ya yi kama da mutum. Kenan shine yayi cunen da aka kama 'yan fashin mu? Dole in yi taka-tsan-tsan dashi kenan kada ya zamo silar rugujewar cikar burina. Gaskiya mana bai tsaurara tambaya akaina ba, me nazo yi, wa nake nema da sauransu; a tafin hannunsa kawai yake kallona. Jin nayi shiru tsohuwar tasha jinin jikinta, tayi nadamar sakin bakinta da katoBarar da tayi, sai ta yi hanzarin gyara zancenta da cewa “Ina nufin zai iya sawa a nemo miki shi, tunda shi dan gari ne kuma namiji. Amma mace kamarki tace zata yi neman wani cikin babban gari irin Damagaran, ai ta hada kanta da aiki ". Na yi murmushi nace "wai ai cigiya kawai zan bayar" ta fada mini kwatancen nan ma na dauke da birona ba tareda ta san ina yi ba. Washegari mai aikinta Liliya ta dawo, sai muka hadu ni da ita muka shirya abin karin kumallo, cikin dan lokaci na saba da ita domin 'yar kauye ce ta sosai mai shegen surutun tsiya. Cikin dabara muna hira da ita na sako zancen Mainasara, nace “na ji ace jiya kinje karBar zakka, ke nan Mainasara tana garin nan?” Ta kama baki ta ce "tabdI, bafa ita ce take rabon zakkar ba, aikowa take yi, ita tafi zama Niamey sabida acan mijinta da 'yan uwanta suke. A gidan kakanta ne ake rabon zakkar cikin (Kangiwa Estate). Gabadaya tushen su arziki ne domin marigayi Kangiwa Mainasara, kakanta kenan, yayi shugaban kasar nan shekaru ishirin a baya. Babanta Alhaji Sani Kangiwa, yayi ministan kudi anan Damagaram. Bayan ya sauka ya nemi kujerar Gwamnatin mu, gab da zai lashe zaBen ya je Nijeriya kai diyarshi neman magani sukayi hatsari shi da ita suka mutu, Nuratu kadai ta tsira. Saida ta yi shekaru masu yawa a Nigeria, rana daya sai gata ta dawo, shinefa tun daga lokacin ta rungumi siyasar mahaifinta, ta kuma sami nasara a kowanne fanni na rayuwarta, duk a dalilin kyakkywar zuciyarta da taimakon talakawa. Ba don neman kudi take siyasa ba, sai don daukaka tushenta a tsakanin sauran jihohi tsararrakin ta. Idan nace zan gaya miki abinda wannan baiwar Allah ta mallaka a kasar nan, cewa zakiyi karya ne domin babu wata mace cikin kasarnan gabadaya data mallaki rabin-rabin abinda ta mallaka, to amma ita kanta gada ta yi. Tana da rijiyar man fetur nata na kanta, don haka gidan mai wannan tanada akalla guda goma na kashin kanta” ta sunkuya ta tube takalmanta, irinnasu ne tafka-tafka na fata “hatta wadannan takalman da muke sawa, da jakunkuna da muke ratayawa da sauran kayan amfanin cikin gida da ake sarrafawa da fata kamar su tuntu, filallika da sauran su da akafi amu gidan manya duka daga fatar Mainasara ne. kasurgumar 'yar kasuwar fata ce da take baiwa kasashen Italiya, Farisa da Tailan (Thailand) suna sarrafawa zuwa takalman kwalisa, da ake shigo mana da su. Nuratu nada bankuna na kashin kanta, wadanda mafi yawa dukiyarta ce kadai a ciki, wadanda duka ta gaje su ne daga Kangiwa, kada ki dauka mahaifinta ne kadai dan sa, a’ah, yana da wasu 'ya'yan duk suna Niamey, suma suna da gadon arzikin su dai-dai da nata. Abinda yasa ta zarce su kuma ya kara mata arziki fiye dasu shine kasuwancin fata data fi maida hankali akai. Kiyi fatan Allah ya hadaku watarana a cikin gidannan, zakiyi bankwana da talauci…..". A razane na daga ido na dubeta “a cikin gidannan?” Na fada cikin raina, amma a zahiri murmushi nayi. Cikin raina nace ko a mafarki kada Allah ya hada ni da ita balle a zahiri. A fili kuwa sai na ce "nan gidan kuma?” [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Dana tabbatar Yaya Halima ta yi nisa a barcinta, sai na dora mata a gefen filonta dai-dai inda tana bude ido zatayi tozali da ita. Na mike na dauro cikakkiyar alwana na shimfida darduma a tsakar gida, na dasa Sallah, yi nake kamar bazan daina ba, ina rokon Allah ya yi min jagora, ya kareni daga sharrin abin hawa dana mutum da aljan, a cikin wannan tafiyar da zanyi. Har aka yi kiran assalatu. Na samau jam'in sallar asubahi ina idarwa na koma dakin na canza kayan jikina, na fara da sanya ‘vest’ Kaman yadda yake a al’adata kana na daura atamfa (Super Holland) shudiya mai ratsin ruwan hoda da kore, na fiddo sarkarnan na daura a wuyana, kunne da hannayena gudun kada wani ya kwace jakar, na kawo bakar abaya (after dress) mai kauri na dora, na kawo niqab na rufe fuskata ruf, sai kwayar idanuna kawai, na rataya jakar hannuna wadda take mai girma sosai da takalminta marassa tudun dunduniya, (suna cikin kyayyakin da iyalin V.C suka hada min a dawowata), hatta abayar da ke jikina sabuwa ce dal a ledarta, Hajiyar Imran ce ta bani, a matsayin sallamrta, ban dauki kaya ko kala daya ba sai na jikina, komi ina yinsa ne cikin takatsantsan, yadda na tabbatar motsina ba zai tada ta daga nauyayyan barcinta ba. Har na fito na sake komawa ina kallon Yaya Halima, dake barci cikin nutsuwa, amma ga busassan hawaye nan like a idonta. Tausayinta ya kamani, na tabbata nayi sallama da mai kaunata. Ji nake kamar ina yi mta kallon karshe ne. Na juya da baya da baya na fito daga dakin sakamako wata zuciyar dake neman raunana min gwiwa, da tunanin anya abinda kike shirin yiwa Faruq da Halima kin kyauta? Da gudu-gudu na karasa soro na zare sakatar, a lokacin da na jiyo motsin fitowar malam Harisu mijin Yaya yana fitowa daga bandaki, da yake yau ba'a dakin Yayar yake ba, yana dakin amaryarta Hadiza ne. Na soma taku a hankali a gefen titi, garin babu haske sosai domin ga dukkan alamu alfijir bai gama ketowa ba, misalin karfe biyar da rabi na asubahin safiyar litinin. Idan ka ganni a lokacin sai na baka tsoro, saboda shigar bakaken kaya da niqab dake fuskata, hatta takalman kafata bakake ne kirin. Ina tunanin yaushe zan kai tasha da wannan tafiya da nake yi mai kama da ta mai ciwon cinya, sai na kara sauri. Gab da zan shiga tashar garin Gwarzo wata bakar mulmulalliyar mota mai walkiya (pg 406) dana tabbatar ta Ya Faruq ne da muka dawo cikin ta jiya, ta zo ta gilma ta gabana, na yi saurin boyewa a bayan wata Daf da tayi lodin shanu zuwa Lagos, cike da mamakin me ya fito da Ya Faruq cikin wannan duhun asubahin, kuma ina zai je? Domin in banyi kuskure ba, zance hanyar fita gari ya dauka, ko dai Kana ko kuma Sokoto. Na yi ajiyar zuciya cike da wani matsanancin tausayinshi daya tsirga mini, shin ko yaushe Allah zai kuma yin saduwar fuskokinmu? Shin ko yaya zai ji a ransa, idan ya sami wasika ta? Abubuwa ne da idan na tsaya tunanin amsar su, zai sani fasa kuduri na in zauna tare da su, wanda zaman ba wani amfani ke gareshi ba, illa in shirya nadar bakin cikin rayuwar shegantaka cikin garin Gwarzo da dangin Faruq . Kada Allah ya nuna min wannan auren. Na karasa cikin tashar wani dan kamasho yana ta tambayata "Hajiya Kano, Kaduna, Lagos ko Abuja?” Hawayen ne dai suka kara ciko idona, ban san sanda bakina ya furta ba a hankali "Nijar”. Yyace babu motar kasar Nijar a nan, sai dai ki hau ta Katsina ki sauka a Jibia, daganan sai ki hau ta Nijar din” bani da zabi banda na ce masa “to", ya yi min jagora zuwa wata (Peugeot Station Wagon) mai zuwa garin Jibia, na biya kudin da suka cajeni na nufi can ‘seat’ din baya na zauna a jikin taga, ina ta kalle-kalle na tunda nasan babu mai gane ni, balle a kaiwa Malam labari. Sai da muka Bata a kalla rabin awa har na fara tunanin sauya mota, kada Yaya Halima ta tashi tasa mijinta ya biyo bayana, ni ko na rantse ko zan dinga kwana a kango, ba zan kara kwana a cikin garin Gwarzo. Sai Allah ya kawo pasinja hudu ris a lokaci daya motar ta cika, muka daga zuwa garin Jibia. Sha biyu da rabi na rana muna cikin tashar garin Jibia. Ba da wani Bata lokaci ba direbanmu ya sanya ni a motar Niger ita ma peogeut ce, wani yaro ya zuro min tallar gorar Yoghurt din (Mai dabino) mai sanyin gaske, sai a lokacin na tuna rabona da abinci tun kokon da muka sha kwanaki biyu da suka wuce da marigayiya INNA TA. Na karBa na biya tare da ledar ruwan (pure water) guda biyu, kafin minti daya duk na zuke su. Na fiddo (Al'ma'asurat) cikin jikata na soma karantawa har motar ta cika, muka tasamma Jamhuriyar Niger. Da aka zo (boarder) wato iyakar Nijeriya da kasar Nijer ne muka samu mukai sallahn azuhur da la'asar (kasaru), bayan gama bincike-binciken su suka daga mana kafa muka wuce. Tafiya ake babu cin zango akalla awanni biyu, sannan ne na soma hango Dogayen RAKUMA da rairayin SAHARA. Wata nutsuwa da ni'ima sauka a zuciyata, muka shiga cikin Maradi. Sai na daga niqab dina ina kallon mutane irin INNATA; farare sol, masu fararen idanu, dogaye masu lange-langen jiki da yalolon bakin gashin kai. Na maida nikab dina na rufe a sanda muka shiga cikin tashar da za'a sauke mu. Na fito daga mota nayi mika sosai, kasusuwana suka ce kakas, na matsa ga direban daya kawo mu nayi masa sallama, ya amsa nace "don Allah Yayana Damagaran zani" ya ce "Wai, ashe kuwa kina da sauran tafiya, bus zaki hau koko fijo in hadaki da wasu direbobin?” Na ce “gara bus din, saboda bana son irin wannan gudun saida rai da kuke, yayi yawa” yayi dariya yace "da bama gudun, da yanzu baki shigo Jamhuriyar Niger ba. Amma in gaya miki gaskiya zakiyi dare, ki kuma yi saukar dare, domin tafiyace ta awanni uku a gabanki kafin ki kai Damagaram tunda kince a bus zaki. Ga kuma motar can ina hangowa fasinja biyu ne kacal a cikinta, don haka babu lokacin tashinta koda za’a kwana ne kuwa sai sun cika zasu tashi. Don haka ina baki shawarar ki nemi wajen saukar bakI, ki kwana, gobe in Allah ya kaimu kiyi sammako domin hanyar bata da kyau" na yi tsuru-tsuru a raina nace na shiga uku ni Zaynab! Ina zani in kwana ina 'Ya mace? Kai gara duk abinda zai faru ya faru amma ba zan yarda da kowa ba, mutum abin tsoro ne, kuma mugun mutum bashi da kama a fuska. Na nisa nace indai akwai motar to ka taimaka ka sani, saboda ban san kowa a garinnan ba, kuma kasancewata mace, kana ganin ya kyautu inje Hotel in kwana ni kadai?” Ya girgiza kai “a’ah bai kyautu ba kam, kinyi tunani yarinya, shige muje, waccan (J5) din Damagaram zata je, Allah ya tsare ya kaiku lafiya". Nice a kujerar karshe cikin mota J5 mai zuwa garin Dagamaran daga MaradI, gajiyar mota gami da duhun mangariba daya fara shigowa suka saukar min da kasalar data sanyani gyangyadi a hankali, daga nan kuma sai barci na sosai, na kwanaki biyu cif da ban samu nayi ba. Bani na farkaba sai da naji rurin motar ta soma tafiya wato pasinja sun cika, na duba agogon hannuna misalign karfe shabiyu na dare. Naji zuciyata ta buga, nayi dakacen karbar shawarar direbannan. Tafiya ta mika duhun dare ya shigo sosai muna ta wuce bukkokin buzaye wani lokacin kurar sahara ta turnike sabida rashin kyawun birjin ta yadda direban ke kasa ganin abinda yake gabansa duk da fitilar motar mai hasken gaskece. Na maida kai na kwanta jikin kujerar gabana. Barci na yayi nisa cike da mafarkai barkatai, masu dadi da marasa dadi duk a game da abinda zan tarar a tafiyar da nake yi. Wanda ya fi daukar hankalina shine na Innata, cikin korayen kaya ciki wani wawakeken koren lambu, zaune bisa wata kujerar azurfa sai murmushi take, fuskarta cike da annuri. Dana karaso kusa da ita sai ta ce dani "na gode Kyauta, da cika min burina na shekara da shekaru da zakiyi, wato neman Nuratu. Sai dai bana farin ciki da kudurinki akan mahaifiyarki, domin iyaye duk yadda suke, duk lalacewar su, sunfi karfin ayi ramuwar gayya a kansu…” Daga haka ta shige cikin koren lambun nan, ba ko waiwaye, ta barni anan ina cizon yatsa, ina son ta tsaya in yi mata bayanin dalilina na daukar fansa akan 'yar uwarta? Sai bata bani wannan damar ba. Ta juyo tana mai daura hannu bisa bakaken laBBanta ta ce "Shhhhh! Nuratu mai kirki ce". Daga haka ta shige abinta, ko waiwaye bata sake yi min ba…… kuuuuuuuuu! karar wani irin cin taya da neman hantsilawa da motar ta yi, tare da ficewa da tayar baya tayi ta nufi jeji, motar ta tsaya cikin kudurar Ubangiji a tsakiyar titi tamkar wani kututture ya tokareta, shi ya farkara dani daga dogon barcina cikin matsanancin firigici da tashin hankali. Mutanen motar nata kwarara salati cikin saddakarwa da mutuwa, direba ya fita tare da wasu fasinja daga cikin motar suna dubawa inda suka fahimci wani karfe ne mai tsini aka ajiye a tsakiyar titin da gangan, wanda in bai Bula taya ba, to ya jawo hatsarin da zai yi sanadiyar rasa rayukan al'ummar da ke cikin motar duk da tazo wucewa. Ganin wannan karfen yasa cikin gabadaya matafiyan ya duri ruwa, don alama ce dake nuna akwai 'yan fashi a kan titin, wadanda suka sassauka suka dawo cikin motar da gudu sai direban motar da karen motar ne kadai suka yi ta maza suna kici-kicin zaro safayar taya su daura. Sai gasu suna fitowa cikin bakar shiga, daya- bayan daya, fuskar kowanne sunke cikin bakin kyalle, jibga jibgan da su ko a lahira bana fatan kara tuna wadannan fuskokin, da suka yi sanadiyar zubowar fitsarin daya kulle min mara, 'ya'yan hanjina suka hautsina bansan ya akayi nayi hankalin cizgo sarkar wuyana na cusa cikin (brazier) ba, karkarwar jiki ya sani kasa taBuka komai bayan hakan sai Innalillahi wa Inna ilahi raji'un nake ta ambato, ba aya ba wakafi. Suka yi magana cikin wata irin murya mai kama da karar saukar aradu cewa kowa da ke cikin motar ya fito ya kwanta a kasa, ko kamin su rufe baki duk mun aikata yadda suka ce. Amma fa ni ina makale da jakata, ban barota a motar ba kamar yadda sauran jama'ar sukayi. Tsayin minti goma sai kwashe kayan motar suke suna shigewa dasu maBoyar su cikin wani irin zafin nama cikin mintuna uku kacal sun kwashe komi kamin babbansu ya umarci a caje mu duka, a kwaso abinda ke jikin mu. Suka dinga bin mu daya bayan daya suna lalubewa har aka zo kaina, suka daka min tsawa na ciro masu zobunan hannuna da 'yan kunnayena, duka haka na zube musu jikina babu inda baya karkarwa, idanuna a rufe gam don ganin munanan fuskokinsu shine babban tashin hankali ga dan adam ba wai abinda zasu kwace masa ba. Daya daga cikinsu ne ya haska da tocilan ya kyalla ido akan bakar jakar dake makale a kafaduna wadda da fari ta saje da kayan jikina, ya fizgota naki saki, ya-ja na-ja don ina ganin babban tashin hankalina to shine rabuwana da wannan jaka, a kasar da ban san kowa ba, ban kuma san in da zani ba. Daga can gefe babbansu ya hango mu muna kici-kici da jaka, karfin halina ya bashi mamaki, ya daga murya yace "kai Fetso, sakar mata jakar ka daukota aka ka kawo min ita nan in rage dare da ita, Allah yasa ba tsohuwa bace" ya kuwa kinkimeni aka ya direwa Ogansa, yasa hannu yana kokarin cizge niqabin nawa yana cewa "idan bazaki bamu jaka ba, kya bamu abinda yafi jaka" ya cizge nikabin ya cillar, yasa hannu ya salube abayar jikina cikin wani irin gwaninta ya cillarta gefe, ya keta rigar atamfar dake jikina tat sage gida biyu tun daga sama har kasa, na kwala ihu na kamo yagaggiyar rigar na kankame da dukkan karfina, yace "wow! What a sweet voice!” Tare da dallare fuskata da tocilan dinsa yana cewa "…may be the face may be as sweet as the sweet voice…….." Ragowar maganar kakarewa tayi a makoshinsa, shima ya kwala wani irin ihun tare da cillar da tocilan din yace "Her Execellency, Mainasara….” Gabadaya yaran suka hau gudu cikn daji, shima cikamin rigar yayi yana ja da baya tamkar bai yarda da kansa ba. Wata zuciyar kuma na ce masa in ita dince sai me? Ka tsaya ka kwashi rabonka… Allah ne ya kawo ma tsuntsu daga sama gashashshe……. Wata kuma tana cewa a’ah, kama ce kawai, me zai kawo Mainasara motar kasuwa? Ya za’ai ta fita haka sakaka batare da shamaki ba? Ai ita mai jiki ce, kuma zatafi wanan shekaru…….. to bai dai samu hakikanin matsaya ga tunaninsa ba, karar motocin 'yan sanda da harbin bindiga gami da watsuwar su cikin jejin ya sashi rantayawa ana kare domin tserar da rayuwarsa. Ina ji wani matashi a bayana, wanda tun tahowar mu a kusa dani yake zaune sai dai ban juyo na kalli fuskarsa ba ko sau daya, ya yi tsaki yace "Wadannan kananan ‘yan fashi ne, sun ci mu da buguzum, ko bindiga basu da ita" ni dai saboda tashin hankali, tuni na shide, numfashina ya yi sama, na durkushe akan kafafuna kankame da jikina. Wannan matashin ya daukomin abaya, jakata da niqabina dake yashe a kasa, ya matso ya mikomin yanayi min magana a hankali "ki kwantar da hankalinki, Allah ya tserar da mu, ungo kallabinki daura, ga jakar ki ma basu dauka ba". Hausarshi bata fita sosai, na mika hannu na karBa amma naki dagowa, shi kuma durkushe yake a gabana cike da zakuwar son ganin fuskar da aka kira da ta (Mainasara) kamar ya sanya hannu ya dago kan nawa. Ya sake cewa "nan da dan lokaci za'a gyara tayoyin motar mu, mu karasa cikin Damagaram" nan ma ban ce komai ba, kamar da dutse yake magana, rokon Allah nake ya kyaleni in samu in daure igiyar abayata sosai, duk da cewa akwai doguwar shimi (vest) a cikin jikina. Shi da kansa ya gane tsugunonsa ya takura ni, ya ja tsumman rayuwarsa ya kara gaba. Na yi ajiyar zuciya na daura igiyar sosai na rataya jakata na doshi sauran abokan tafiyar mu, ashe duk abin nan da nike yana biye dani a baya kamar tsohon maye. Mutanen motar tare da 'yan sandar dake tare damu suna yi musu tambayoyi suka shiga yi min barka da arziki, wata dattijuwa ce ta bani dariya da tace "bude rigar in gani, ince ko basu cire miki rigar mama ba?” Na daga mata kai cikin matsananciyar kunya, ta ce "ita ce kadai ce mai gwal a cikin mu, kuma sun kwace” sukace "Allah ya biyaki da alheri nace "amin". Wani daga bayan mu yace “a’ah ‘yan sandannan zasu dubo su baki abinki in har sunyi nasarar damko su”. Har karfe hudu na asuba ana abu daya, domin gabadaya tayoyin motar sun yi faci, ‘yan sandan kuma wasu na tare damu wasu sunyi ciki sun watsu a dajin har Allah ya basu nasarar kamo wasu daga cikin ‘yan fashin da jibgin kayan al’umma, suka dannasu a mota suka yi gaba, ragowar guda biyar kuma sun tsaya suna ware mana kayan mu kowa yana fadar nashi amma ni ‘yankunne na ba’a maganar su, sabida kankantarsu babu wanda ya gansu sai sunga tashin mu tukunna. Daga can gefe cikin hasken farin wata na hangi saurayinnan tare da 'yan sanda suna ta magana ta tsayin awa guda, ban san me suke cewa ba kasancewar da harshen faransanci suke magana. Daga baya ne da motar ta gyaru muka mika yana zaune a Barin dama na kujerar da nake, ni kuma ina Baryar hagu, sai wasu mutum biyu a tsakanin mu. Ba muyi tafiyar awa daya ba muka tsaya wani masallacin kauye muka yi sallar asubahi daga nan muka mika. Karfe shidda na safe muka soma shiga yankin Damagaram. Dam-dam-dam! Na ji bugun zuciyata ya karu, wani irin dummm! Na ji a cikin kaina, haka idanuna sunyi min nauyi saboda wani irin kwarjini da Allah yai mata. Na daga kai ga kototon (advertisement board) wato irin allonnan da ake amfani da shi wurin yin kamfen ko talla a manyan tituna da manyan hanyoyi, wanda shine ya janwo min faduwar gaba. Na kura mata ido, bata da maraba da Innata, sai dai ta fita haske da kyakkyawan jiki. Ko’ina postarta ce a ciki da wajen garin Damagaram, masu nuna goyon baya a gareta ne zarcewa da gwamnatinta wanda aka rubuta da harshen faransanci. Nayi tir, na yi Allah wadai a zuciyata, nace a raina, shin idan sun san cewa ta aje shigiyar diya a kuruciyarta, ta gudo ta barta, ta sanya 'yar uwarta cikin bakin cikin da yayi sanadiyyar danganarta da kushewarta, zasu yarda su kara zaBarta a matsayin gwamniyar su a karo na biyu? Idan har mutum mai tabo a rayuwarshi baya shugabanci, na rantse, NURATU MAINASARA, ba zata kuma hawa kujerar Gwamniya ba! Sai na lalata siyasarta, sai na lalata sunanta, sai na dauki fansar bakin cikin rayuwar da ta jefa Innata na taraddadin inda take, da halin data ke ciki tsayin shekaru goma sha takwas har ta mutu da shi a zuciyarta. Sai na daukarwa kaina fansar rabani da duk wani farin cikin rayuwa da ta yi, sai na dauki fansar dan uwana Imran a kanta….. Ban san sanda na soma sheshshekar kuka ba, tun inayi a hankali har ya fito cikin motar mutanen motar suka ji shi, su a tsammanin su har yanzu tunanin abinda 'yan fashinnan suka yi min nake, shine har ya sani kuka. Wannan dattijuwar tace "yarinya ai kin auka arziki, ki godewa Allah ba kuka zaki yi ba. Keta haddin da akewa al'ummar mu a wannan hanyar a shekarun baya, ai ba zaki so ki ji shi ba, banda yanzu da muke cikin gwamnatin “mace tamkar da maza Hajiya Nuratu Mainasara”, ai da wannan tallafin da kika samu baki same shi ba. A gaba dayan gwamnatocin da mukayi a baya, bamu samu gwamnatin da tayi tsaye akan harkar tsaro da yaki da miyagun dabi'u kamar ta Mainasara ba. Ruwa ya wadace mu, wuta kuwa bamu da matsalarta, idan kuwa aka koma ta fannin lafiya a garuruwan kasar Nijer baki daya ba zaki samu nagartattun asibitocin gwamnati kamar namu ba, duk a cikin shekaru ukun da Mainasara tayi tana aikinta. Ta fannin ilimi kuwa, fensir wannan bamu san nawa ake sayawa 'ya'yan mu ba, duk ita ce take basu har littafin rubutu. In kuma aka koma ta fannin albashin ma'aikata da malam makaranta, duka Nuratu ta ninkashi. Farin rashin abincin da akayi kuwa akasar nan shekarar baya, mu mutanen Dagamaram bamu san da shi ba. Ta yi mana ayyukan da maza da dama, suka kasa, ta cika dukkan alkawurran data daukar mana, ta cikawa jihar mu burinta na shekara da shekaru. Don haka kuri'armu duk na wannan karon ma mun tabbatar mata nata ne, mu al’ummar Damagaram! Tunda ai munyi Gwamnatin mazan shekara da shekaru bamu ga me suka kulla mana ba, sai zalinci, sata, cin hanci, da rashawa, amma a gwamnatin MAINASARA babu wannan". Daga can gidan gaba wani magidanci ya karBe, “kin manta da inganta tituna da hanyoyin sadarwa, kafin Nuratu, ina muka samu wannan gatan?” Wani ma ya cafke, "kwarai kuwa, ga dakakkiyar zuciya da rashin tsoro, don duk barazanar abokan adawa baya sata fasa kudurinta na alheri. Duk girman buzu da rawaninsa baya bata tsoro, balle ya sata cin amanar talakawan Jihar ta. Ni kam da ana tazarce sau goma, da na cigaba da jefawa Nuratu kuri'ata har a nade birnin Damgaran. Babu abinda zamu ce akan Mainasara sai Allah ya karya makiyanta, ya tabbatar da kujerarta ta gaba, ya zama jagoranta a rayuwa, kada ya bawa makiya da mai nufinta da sharri iko a kanta…." na yi murmushi, a raina nace "irin mu ke nan, amma yabin da ake miki ba zai sa ni yin kasa a gwiwa ga fiddo musu ainahin your real colour ba, sheep in a wolf clothing. A dai-dai lokacin da motar ta tsaya cikin babbar tashar Damagaram, kowa ya fito ya kama gabansa, anan ne idanuna suka raina fata, don ban san inda zani ba. Na tsaya ina ta raba ido har a cikin tashar hotunan ta ne a ko ina. Garin cike yake da hayaniyar siyasa data kacame a lokacin da bana fahimta, domin yarurruka ne sukeyi daban-daban, ko kuwa nawa kunnen ne, oho! Duk da cewa mafi yawa hausa suke yi amma wata irin gurbatacciya ce da wadda na taso a cikinta. Na matsa ga wani mutum mai sai da shayi a irin dogayen butocinnan nasu masu garwashi a kasa, nayi msa sallama, kallona kawai yake bai ce min komai ba, bai kuma amsa sallamata ba. Na dangata hakan da rashin yarda dani sabida yanayin shigata data ban-banta data sauran matan dake wucewa, ga nikab dana maka kamar matar limamin masallacin Makkah. Na tambayeshi ko ina ne gidan saukar baki mafi kusa? Yayi magana cikin harshe faransanci mai nuna baya jin yare na, na canza na koma turanci, nan ma ya gyada kai, bai gane ba, to fa! Na matsa ga na kusa da shi wani mai saida taba shima duka yarukan nawa ba jin su yake ba, dukkan su buzayene na sosai nade cikin bakin rawani, sai idanun su da dogon karan hancin su kawai kake gani. Sai na koma kwatanta musu gidan saukar baki (Guest House) nake nufi, sai ya yi gaba abinsa ya rabu dani, a ransa nasan cewa yake in gaskiya ne abun naki, ki bude fuskarki mana. Ni kuwa tun daga kan dan fashinnan, dana fahimci fuskar nan ta zaga ko'ina a Niger, ba zan kara yin saken da zan budeta ba. Don bansan me hakan zai kuma jawomin ba. Sai na tafi bakin hanya na tsaya ina kallon giftawar motoci akan titi jefi-jefi, don bansan wace iri ce tasi ba. Cikina in banda kiran ciroma babu abinda yake, nayi wujiga-wujiga da yunwa, gajiya rashin kwanciyar hankali da rashin barci. Daga baya na naji wani zazzakan horn din mota irin na YA IM, watau mara gigita mutum, mara karar dake gundurar mai jinta. Naki juyawa na cigaba da tafiya cikin nutsuwa, domin bana daya daga cikin mutanen da ‘horn’ din mota ke sa su waiwaya. Ya wuce ni yayi parking tsaleliyar farar motarsa mai kofa daya (hemi) can gaba da ni kadan, kamin ya fito ya kulle ya doso inda nake tsaye. Saurayi ne ba'abzinen usli jajur da shi, mai lallusa kuma suma nannadaddiyar suma baka wuluk kaman ya hada jinsi da larabawa. Ganin da nai mishi cikin hasken farin wata da duhun dare, shi ya hanani gane hakan a daren jiya. Sanye yake cikin (dark green) shadda ‘yar Mali dinkin tazarce sai daukar ido take, abinka da farin mutum, kada ki so kiga yadda kalar shaddar ta fito da shi, kansa ba hula, wadda na lura ba al'adar mazan garin ba ce. Matashinnan ne da muka shigo mota tare dashi daga MaradI, ban san daga ina kuma yaje ya dauko mota cikin mintuna ashirin ba, ban san dalilin sa na son yi min shishshigi, cikin rayuwa ba, bayan a zahiri ko fuskana bai gani ba. Sai murmushi yake mun tun daga nesa kamar gonar auduga, daya ga ina shirin wuceshi batare da niyyar tsayawa ba, sai ya fiddo hannunsa wanda ke cikin aljihun damansa, yana mun kwalele da sarka ta. Nayi hanzarin kai hannu zuwa inda na ajiyeta, watau cikin ‘bra’ dina, babu ita babu dalilinta, watau ban san sanda ta fadi ba, ba mamaki sanda dan fashinnan ya wancakalar da ni ne. Na bude baki ina murmushin jinjinawa kokarinsa, wane ne a wannan zamanin zai tsinci zinare (White-Gold) yayi tunanin maidawa mai shi? Sai dai-daiku, masu tsananin tsoron Allah. Na ja burki a gaban sa, na mika hannu da nufin ya bani, sai ya maidata cikin aljihunsa ya ce "idan kece kika tsinci abun mutum, kamin ki mika masa, ai ya kamata ki tabbatar cewa nasa ne, ko ba nasa bane?” Na yi murmushi "idan baka yarda cewa tawa ba ce, meye dalilinka na tsayar dani ka nuna min?” Yace "from your voice, I guessed you are a girl in tender age, me ya kaiki yin tafiya irin wannan cikin dare, ba tare da mijinki ko dan uwanki ba?” Na tsuke fuska, don a fahimtar dana yi, yana son kai tsayuwar tamu da tsawo, nace "baka yi mun kama da mutanen dake shiga abinda babu ruwansu ba, this is my personal world, don haka in zaka bani sarkata, ka bani, in ba zaka bani ba, in kara gaba" yace a tausashe "me yayi zafi, gyara kayanka, ba sauke mu raba bane, ina zaka? Ba zo mu tafi tare bane, don haka maida wukar, ga sarkar ki” nayi murmushi na karBa nayi gaba ina cewa "ban taBa jin irin wannan hausar ba. Tsaya a inda kafi wayau, kada ka shiga gonar da ba taka ba, in hausawa suka ji sai suyi maka dariya, don kuwa ba bahaushe bane, Badamagare ne". Ya sha gabana yace "a kasar nan, ni cikakken baushe ne kuwa, kamin ki samu wanda zai miki kyakkyawar hausa haka, zaki dade. Don haka inma ki tsaya ki nemi taimakon da kike nema daga gareni, ko kuwa kiyi gaba ki sha wuya, mutum nawa kika samu da irin tawa hausar da kike rainawa?" A raina nace "kwarai babu” amma a zahiri sai nace "turanci na zai fidda ni a ko‘ina cikin duniyar nan". Dariya yayi, data fiddo jerarrnn fararen hakoransa reras kamar shi ya shiryawa kansa, yace "Mu ba rainon Ingila ba ne, rainon Farisa ne, don haka dauki turancinki ki jefa a wannan katuwar jakar taki data kusan janyo miki salalon tsiya, ki koma dashi inda kika fito, ki dauko faransanci, sannan ne zaki shiga ko'ina a cikin mu. We need no your Engilish…" ban san sanda na murmusa ba, hakannan naji ina kaunarshi, ban san dalili ba, ban jin zan gaza da sauraron tattausar hausarshi koda zamu kwana ne a hakan kuwa. Koma wane ne, farat daya naji jini na ya hadu da nashi. Daga fatar jikinshi, sutturarshi zuwa motar da yake ciki kadai ya isar maka kimanta daga inda ya fito, bi ma'ana, da gani babu tambaya cewa shi wani ne, ko kuma dan wani ne a Damagaram. Don haka nayi gaba, domin baya daga cikin ire-iren mutanen da nake jin zan amincewa cikin garin, nafi son in nemi gidan talakawa 'yan uwana in fara sauka, in ga kamun ludayin mazauna garin, kafin in nemi dangin Innata. Bai hakura ba dai ya sake shan gabana, ya mairairairce kaman wani kan karamin yaro yace “in kin amince ‘I would like to be your host’ (zan so zama mai masaukin ki) don na fahimci ke bakuwa ce, baki kuma san kowa ba". Na yi hamzarin dubansa saboda mamakin yadda yasan hakan, ya dagan kyakkyawar girarshi yace "yes, kuma ba kowa ke karBar bakon da bai sani ba a garinnan” . Nace “shine kai zaka yi kasadar karBar bakuncin nawa, bayan ko fuskana baka sani ba? Idan kuma dodanniya ce fa ko aljanace?” Ya ce yana mai murmushi "na yarda na amince ta cinye ni har hanji na". Tunda muka soma tafiya a motar babu wanda a kara ce da dan uwansa uffan, sanyin A/C ne ya kara sani samun nutsuwa da warwarer gajiya, nake jin shirun namu ne bai yi masa dadi ba, don haka ya mika hannu ya sanya kaset na faifan mawakan 'soulsquad music' sautin na tashi a hankali har muka iso wata keBantacciyar anguwa da tafi mun kama da iri-iren gidajennan namu na GRA, domin dukacin ginin gidajen iri daya ne, kansu daya haka tsarin su ma daya. Ya karya motar a kofar shiga flat na ashirin da biyu, yayi (horn) mai gadi ya bude muka shiga. Korran (Grass Carpet) ne malale a gabadayan harabar gidan banda sauran shuke-shuke kala-kala da suka kawata gidan saosai. ka ramin gida ne hawa daya, da aka yi gininshi da jan dutse kaman a kasar China. Daga kofar shigowa gidan bazaka taba tsammanin haka cikin gidan yake ba. Babban abinda yafi burge ni da tsarin wannan gida shine kacokam ginin gidan a tsakiyar gidan yake, sannan hanyar da zaka bi zuwa cikin gidan duka (grass carpet) ne mai taushi. Na zauna cikin motar na kasa fitowa cike da tunanin a wane matsayi zanje wajen matarsa? In kuma babu matar aure a gidan haka zan zauna da gardin namiji, a irin wannan gidan ihunka banza? Kai da sake, wai an baiwa mai kaza kai. Mu kammala a littafi na 3. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Duk wasu kalami na kwantar da hankali Ya Faruq ya gaya min su a wannan rana, tamkar yawun bakinsa ya kafe, tamkar ya fido zuciyarsa ya nuna min, tamkar harshensa ya tsinke don tabbatar min da abinda yake fadI, jinsa kawai nake, amma hawayena basu bar kwarara ba, wanda na tabbata har abada ba zasu daina ba, haka zuciyata ko daya bata russuna ba ga kudirinta akan NURATU da BABA SA'IDU. In Allah ya yarda sai sun zubar da hawaye, fiye da wanda na zubar. Fiye da wanda Inna ta kwashe shekaru goma sha takwas tana zubarwa akan su. Tare dashi muka kamo hanyar Gwarzo, cikin masiffafar motar da ya iso da ita daga asibitin AKTH dake Kano, yana ta kara kwantar min, da hankali, da kalami masu taushi da kara imani. Akwai inda yace “Zaynab in nine ke, babu abinda zai sa inta zubar da hawaye na har haka, tunda da Allah yayo fitowana a hakan bai barni haka ba. Sai ya sanya matsananciyar kaunata zuciyar iyayen nawa, yayi mun gata irin wanda baiyiwa sauran 'ya'ya irina ba. Kina ina iyayen da suka haifi 'ya'ya kamar ki, suka kai su bola suka zubar, don gudun abin kunya? Kina ina ake tsinto 'ya'ya irin ki ana kaisu gidan marayu, ana kyamar su ana zuwa kallon su? Ke kuwa Babanki sonki ya ke fiye da sauran 'ya'yan da ya haifa ta hanyar auren. Son ki yake fiye da komai na rayuwar duniya, son ki yake ta yadda da da hali, daya mallaka miki duk abinda ya mallaka a duniya. So yake ki zo kusa da shi, saBanin 'ya’ya irin ki da ake neman maraba da su. Kina ina uwar da ta haifi 'ya ta irin hanyar data haifeki, ta kasheta da hannunta, ta tura ta a masai tayi ‘flushing?’ Ke kuwa na tabbata duk inda mahaifiyarki take, cike take da kaunarki da tausayinki, domin soyayyar gaskiya ce tsakaninta da mahaifinki, illa makiya da sharrin Shaidan, gami da kaddara da suka tarammusu. Ki godewa Allah, domin yace “in baku godewa Rahmata ba, hakika zaku godewa azabata”. Ki yafewa iyayenki, ki taya su rokon Allah ya yafe musu, domin babu wanda yake sama da aikata ‘kuskure’ cikin rayuwarsa. Dukkan mu masu saBo ne in one way or the other, amma Ubangijin mu hakuri yake da mu, yana yi mana afuwa har zuwa ranar da kowanen mu zai karBi sakamakon sa, sai ki dage wajen kyautata lahirar ki, ki gani idan zaki taBe. Wannnan shi ne gata na karshe da zakiyiwa rayuwarki, amma ba kuka ba. Kuka babu abinda zai sa babu abinda zai hana, saidai ya kara dagula zuciya, ya raunana imaninta. Muminai na hakika basa kuka akan komai, sai akan tsoron Allah, wannan shine lokaci na karshe da zaki nunawa Innarki kaunar da kike ikirarin kina yi mata, ta hanyar yi mata addu'a da nema mata gafara. Ina yi mana ta'aziyya Zaynab domin bake kadai aka yiwa mutuwa ba, mu biyu ne Zaynab, nima nayi rashin uwa abokiyar shawara kuma mai kaunata…….." Yasa hankici ya share hawayen idanunsa, ya miko mini da hannunsa na dama, ayayin da yayi amfani dana hagun wurin tukin motar "maza share su Zaynab, Inna bata cancanci mu dinga yi mata kuka ba." Na mika hannu na karBa, amma ban san sanda kukan ya kara subuce min ba jin kalaman sa. Na kifa kaina a cinyoyina nayi ta yi ba kakkautawa, don ni har yanzu na kasa amincewa raina wai Innana, ta rasu! To ni in haka ne wa nake da shi a yanzun? Zaman wa zanyi? Ina zani? Tunda mutumin da na rika a matsayin mahaifina, an ce ba shi ya haife ni ba. Mutumin da nake kauna fiye da kowa a duniya, nake ganin GIRMANSA da kimarsa fiye data kowa, a yau bani da wanda na tsana a duniya tamkar shi. A yau kam na daina ganin beken Innata, dana kwashe shekaru goma sha takwas ina gani. Baba Sa'idu ya cuce mu, ya ci amanarta. Ya barmu da tabo da bakin cikin da har abada ba zai gogu daga jikin mu da zuciyar mu ba. Wai ni Zaynab ce 'yar zina? Gaskiya mana! Biri ya yi kama da mutum!! Yadda na tsinci kaina da tsananin son aikata zina, tun 'yar ficiciyata ashe ban yar a kas ba, tsotsa nayi a nono, ba don kariyar Ubangiji da kokarin dan uwana Imran ba. Da ashe bakin cikin yafi haka.. Da tuni nima na aje shagen…… wayyo Allah! Inama ba'a halicce ni ba…….!!” Magana nake cikin zuciyata, ban sani ba tsabar bakin-ciki ashe a fili nake yi. Ya Faruq ya kaashe motar a gefen titi, shima ya kifa kai akan sitiyarin ban san a halin da yake ciki ba. Na sani da da hali, da ya jawo ni jikinsa yayi min lallashin da ba'a taBa yi min ba, yayi min lallashin da wani da namiji bai taBa yiwa diya mace ba, domin nuna mata matsayin da take dashi a zuciyarsa, da yadda damuwarta ta zamo tashi. Ya kasa ce min komai illa tsinkayar numfashinsa da nake, wanda ke fita da sauri-da-sauri kamar na mai ciwon asma. He really lack a word to express his feelings, his sympathy and how much he cares. Gane hakan dana yi ne ya sani yin karfin zuciyar dagowa in share hawayena, na kuma rasa hanyar da zanbi in ganar da shi na daina kukan domin idanunsa a rufe suke ruf. Sai na kai hannu ga ‘horn’ din motar na danna a hankali. Ya bude idanunsa da suka kada suka yi jawur ya dubeni very pale. Sai na samu kaina cikin wani sabon al'amari, wato abubuwa da dama dana gano cikin kwayar idon Ya Faruq, su suka tuna mani da Imran. Bai ce komai ba, ya ja motar muka ci gaba da tafiya, gab da sallar magariba muka iso gida, sai a can bakin hanya ya kashe motar domin gabadayan unguwar babu masaka tsinke, ana yiwa Malam Ali ta'aziyyar mai dakinsa. Zuciyata ta kara tsinkewa, hawayen suka kara malalowa. Na tabbatar Inna ta a yau ta wuni a makwancinta. Ni kadai zan kwana a wannan gadon karfen namu, ni kadai zan rufe da katon bargon mu, ni kadai zan cigaba da rayuwar hakannan ni kadai zan cigaba da dandanar bakin-cikin Nuratu da Baba Sa'idu, ita kam Allahu Arrahmanu ya hutar da ita, wata shari’ar, sai a lahira! Tafiya nake tamkar akan kaya, ina keta daruruwan jama'ar da suka zubo min ido, ina cewa a raina suna ta kallon SHEGIYA, wadda bata da Uba, wadda aka haifa ta hanyar zina. Na yi murmushi, sabida kuna da suyar da zuciyata take yafi gaban kuka. Lallai wata mutuwar Rahmace, inama nice Inna! Koda yake burin Innata ya cika. Ko ba komai na tayata farin cikin cikar burinta, tunda kuwa sai bayan ranta…… na dandani bakin cikin ‘illegitimacy’. Sai bayan ranta wani ya tabbatar min da cwa ni shegiya ce, haka sai bayan ranta na samu amsoshin tambayoyin da suka addabi kwakwalwata, suke banbantani da sauran 'ya’ya, suka tabbatar min da cewa ni 'yar gaba da fatiha ce. Na daga kaina sama a hankali, ina karanto rayuwata ta baya, dana tabbatar na yi sallama da ita. Yanzu ne zan shiga rayuwata ta hakika (ta marassa galihu, marassa ‘identity’). Inna ce galihu na, Malam ne ‘identity’ dina, duka a yau na rabu dasu (ita ta tafi, shikuma zan rabu da shi). Ba zan iya rayuwa cikin kasar ba tare da Innata ba. Na sanya kafata cikin gidan, cinkoson mata ya kara tayar min da hankali, tamkar in ce da kasar ta tsage in shige. Tsoro nake kada wata cikinsu ta kirani da 'shegiya' babu mai kare a min a yau, tunda babu Innata cikin gidan. Ala dole na ja baya zan juya da gudu. Yaya Halima ta ratso cikin mutane itama da gudunta ta kamo ni, ta kankame ni tana kuka haka daga bayana naji nayi karo da mutum ashe Malam ne ya sawo kai, Ya Faruq na biye da shi, sai kallon su nake a tsorace, don gani nake kamar korata zasu yi daga gidan su. Sai makyarkyata nake yi kamar mazari. Malam ya shiga tofa min addu'o’i iri-iri a tsakar kaina. Ya Faruq ya kama hannuwana duka biyu hawaye cike da idonsa, yace "Baba Malam, don Allah Halima ta tafi da Abu gidanta bazata iya nutsuwa cikin taron matan nan ba, ina gudun kada ta samu matsala a kwakwlwarta, ka yi hakuri don Allah tabi Halima tunda kace baka yarda in kaita gidan Baba Sa'idu ba…." na gwalo ido da karfi jin abinda yace, na ce "nima bazani ba Malam dukana zasu yi, kora ta zasuyi, ba zasu barni in zauna musu a gida ba. Ni da gidan Baba Sa'idu har abada…. har shi Baban….. Babu ni, babu shi har abada……." Na fashe da kuka shima Faruq sai ya shiga share hawaye da hankicinsa duk irin dauriyar da yake yi kuwa. Ban taBa ganin Ya Faruq yana kuka ba, tunda nake. Don haka nayi saurin tsayar da nawa, ba don na zuciyar ya kafe ba. Malam ya ce "bude mata dakinsu ta dauki abinda za tayi amfani da shi, ki kula min da Zaynabu amana Halima, kafin zuwa ranar sadakar uku in daura auren ta da Umar Faruq…” Cikin tsananin firgici, mamaki da zargi, na daga ido na dubi Malam Ali, cike da mamakin wane Uba ne na kwarai, zai aurawa dansa dan halak 'SHEGIYA?' Ba mamaki mutuwar matarsa ta samar masa motsuwa a kwakwalwa, domin ni kaina shaida ce kan matsanancin son da yake mata. Ban ce komi ba, na sunkuyar da kaina kasa, domin idanuna sun gano min abubuwa saBani ga tunanina, sun gano min Malam ragas yake, ragagasgas kuwa, sai dai in nice ban ji sosai ba. Amma kwayar idanunsa na tabbatar da abinda yake fadI, haka yake har zuciyarsa. Na maida dubana ga Faruq, don ganin wace irin karBa ya yiwa zancen mahaifinsa? Idanunsa akaina suke, cike da tarin abubuwa da dama, wanda a lokacin rashin kwanciyar hankali bai barni na tsaya ga son tantance ma'anar su ba. Ya lumshe idonsa cikin nawa, ya jefa ni da wani irin 'loving smile’ da har yasa 'ya'yan hanjina sai da suka karkada, domin babu tantama al'amuransa a yanzun, sun juye sun rikide na IMRAN ne sak. Sai naki gasganta hakan da gangan, domin ni ban yarda da abinda ake kira (love at first sight) ba, sai dai tausayi da ceton rai. A ganina ni ba abin tausayi bace, tunda ina da lafiya zan nemawa kaina madogra, in daukarwa kaina da Inna ta, fansa, wanda ba zasu yiyuwa ba, in har da aure a kaina. Ko zanyi aure ai Faruq yafi karfina; shi dan gatane, dan halal ne, mai dangi, sai dai in je duniya in nemo shege dan uwana, wanda ba zai taBa goranta min (illegitimacy) ba. Na shige dakin Inna na da zummar dauko kayana, to amma me? Duk inda na juya ita nake gani a kowacce kusurwar dakin tana 'yan hidimdimunta da basa karewa. Na zauna a gefen gadon karfenta, na dauki bargonta da muka kwana a cikin sa daren jiya na rungume a kirjina, hawaye na malalo mini. Nayi kuka na yi kuka har hawayena suka kafe, sai dai kukan zuci, wanda akace ya fi na zahiri radadi a zuci. Yaya Halima ce ta shigo ta soma hada min 'yan komatsaina, cikin ka tuwar akwatina da na zo da su daga gidan Baba Sa'idu, ta daurawa Zilkiflu ya tafi da shi gidanta, ta kamo hannuna muka fito daga dakin tasa kuba ta rufe. Idanun matan nan dai har yanzu suna kaina, suna ta kus-kus din dake kara daga min hankali. Daga can dakin Inna Dubu Hafsisi ta fito, ta dubeni shekeke, daga ni har Yaya Halima dakatawa muka yi muna kallonta, domin daga ganin irin tsayuwar da tayi, hannu a kugu, ta kuma tare min hanyar wucewa. Kasan bata arziki bace. Cikin daga murya yadda duk wanda ke gidan zai ji, ta ce "to Abu, burin ki ya cika, naji ana zaki auri Faruq ba ni ba. Dadin abun dai ni ba ‘shegiya’ bace 'yar sunna ce. Igiyoyi uku kwarara na aure suka samar dani kuma kowa ya shaida. Kenan ba sai an rufa asiri za'a aureni ba. Ashe dama duk wannan kumbiya-kumbiyar da mahaukaciyar ki Innarki ke yi dake, don kar mu san ke SHEGIYA CE? To ai gara ma da ta mutun, da bazamu sani ba, sai a cigaba da dinke mu a bai-bai. Don haka ba Faruq ba, in ma ALHAJI SA'IDU, dadironki zaki aura, ki je na bar miki, nafi karfin in hada kishi da shege wall….”. Ganin Hafsisi mu kai tayi sama ta kuma fado tik, a kasa. Ya Faruq dake shigowa yayi kwallon ‘tennis’ da ita da kafarsa ta dama, sai jini ta hanci ta baka. Ta kwala ihu iya karfinta shi kuwa ya sake bin ta yana tumurmusa da kafa a tsakar gidan, duk cikin matan an rasa mai kataBus din kwatar ta sabida irin mugun dukan fitar hankalin da yake mata da kafafaunsa, sai mahaifiyarta Goggo Lantana data dora hannu aka ta kwarara ihu, tace "Dubu kawo dauki, zai kashe min 'yar akan 'yar gaba da fatiha…… Karya ake ba shegiyar bace? Ka dauka yau aka haifemu a garinnan bamu san 'yar Nuratu ba ce karuwar Sa'idu.....?" Idanun Yaya Faruq suka rufe ruf, baya ko ganin gabansa, ya fizgo Inna Lanto ya maka da bango, ta kuma kurma ihu data fadi tim, akan kwankwasonta. Ya dunkule hannu ya nausa mata a bakin sai ga hakora biyu, wanda dama lallabasu ake sun biyo jini da yawu sun zubo akan cinyarta. Malam ne da Inna Dubu suka shigo da gudu daga can dakin soro inda suke karBar gaisuwar Hakimin Gwarzo da tawagarsa, suka kwaci Hafisisi da Innarta da kyar, bayan ya hada musu jini da majina, ya fita yana huci ya dauki motar sa a guje ya bar garin kwata-kwata. Rungume Yaya Halima na yi, ina ta kukan fitar hankali ko uffan ban ce ba, haka muka baro gidan zuwa gidanta. A ranar ne labarin da jama'ar garin Gwarzo suka dade suna kokontonsa, ya bayyana gare su. Abinka da dan karamin gari, cikin daren labari ya bazu a ciki da wajen kauyen Gwarzo, cewa ashe Abu diyar Malam Ali, ba 'yar sa ba ce, SHEGIYA CE. A daren daga ni har Halima bamu rintsa ba, ita cin kuka take saboda tausayin raywata ni ko a lokacin idanuna sun bushe, zuciyata ta kekashe. Kalamin Hafsisi sun kyafar da hawayena. Babu shakka abinda ta fadi haka yake babu kuskure a ciki, domin ta fini kusanci da Faruq, ta fini sanin ciwonsa ta fini sanin muhimmancinsa, don Innarta kanwar Inna Dubu ce uwa daya uba daya, dole ta taya dan uwanta jimamin kakaba mishi 'yar zina da za'a yi, ko ni na jajanta masa, haka duk wani mai kaunar sa dole ya jajanta masa. Maganar ta daya ce ta taBa zuciyata kuma ta sani fidda hawaye, (dadironki Alhaji Sa'idu), me wannan kalmar ke nufi? Tana nufin…. zaman da kikayi kina karatu gidan Baba Sa'idu, zama ne na karuwanci, na zina, irin wanda mahaifiyarki, NURATU, ta yi tare da shi har suka sameki…….. Ban san sanda ba na ce "Ya Allah, ka dauki raina in huta da wannan rayuwar, Ya Allah kada ka barni in kara kwana cikin duniyar nan, Ya Allah ka bi mun hakkina akan Nuratu da Baba Sa'idu…" Yaya Halima tasa dankwalinta ta toshe min baki, cikin kuka ta ce “Abu kada bakin ciki ya fidda ke a addininki, kada Bacin rai da maganar mutane ya raunana imaninki, kada bacin zuciya ya kaiki ga aikata dana sani. Naji dadin yanda kika karBi al'amarinki da farko, amma kina nemn lalata ladan da kika samu na yarda da kaddara da fawwalawa Ubangiji komai da kika yi. Wannan ba zai hanaki shiga Aljanna ba, idan har kin kyautata ayyukanki sai ki wuce cikin aljannar mu 'ya'yan halal din bamu wuce ba. Rayuwar duniya duka guda nawa take? Kada ki manta, bafa zama muka zo yi a cikinta ba, to na meye zamu damu kanmu da kaluben dake cikinta? Ki yi saurin yin Istigfari ga kalamunki, tun mala'iku basu rubuta ba………." Na share hawayen da suka yanko mini, na daga kai sama nayi duba ga al'arshin Subhana, wadda ya kawata da wata da taurari, ya maye duhun dare da hasken su. Na saukar da idanuna akan yatsaun kafata nace "Mutane suka koma bani tsoro Yaya Halima”. Itama ta share hawayenta ta ce “Ba kiyi tuban da nace kiyi ba har yanzu Zaynabu-Abu". Na daga kai sama a hankali, tsigar jikina na tashi, kana na sunkuyar. A hankali nace “Astagfirullah!” Ta kamo ni ta rungume a kirjinta, hawayena na sauka a gadon bayanta, nace "ni yanzu ina zan dosa ne Yaya Halima? Ba Uwa ba Uba balle dangi. Ga tabon da duk inda na shiga baza’a goge min shi ba, bayan ba ni na dorawa kaina ba. Ko zan rika kwana a titi, ba zan doshi hanyar gidan Baba Sa'idu ba, ba kuma zan kara kwana gidan Baba Malam ba, sai dai gaisuwar neman albarka daga gareshi da Inna Dubu, haka ko zan mutu ba aure, ba zan auri Ya Faruq ba. Idan nayi hakan na tauye shi, domin shi cikakken mutum ne mai cikakken hali da cikakken usuli, bai cancanci auren mai gurBataccen usuli kamana ba…" ta katseni cikin daga murya “ki daina fadar haka Abu, Faruq na sonki a tun ranar da aka haife ki, shekaru dai-dai yau kusan goma sha takwas….” A razane na dago ido na dubeta, tunanin maganganun Inna na ya zo mani. Wannan na nufin Faruq shine mutum na hudu, cikin masu tabon bakin-cikin BABA SA’IDU, shine ma’abocin soyayyar shekaru goma sha takwas, amma bazai bayyana ba sabida Baba Sa’idu?” Ta lura da yadda maganarta ta taba zuciyata, ta daga min kai (in affirmation), “kwarai ni na sani, Innarki Allah ya jikan rai ta sani, haka Malam da Inna Dubu. Sai dai ya rantse zai iya hakuri har illah masha Allahu, don ba zai taBa ba bari ki gane ba Baba Malam ne ya haife ki ba. Wannan zai dagula rayuwar ki ne, ya jefa ki a wani hali na tsanar duniya da abinda ke cikinta, hadi da ke kanki. Ga kalamunsa a yau sun tabbata. Haba Abu! Sai kace ba musulma ba? Me hakan zai kara ga rayuwar ki me hakan zai rage? Wannan ba shine karshen rayuwar ki ba, idan har kin kyautata zuciyar ki. Ya dawo a dai-dai lokacin da kika suma, da girgizar mutuwar Innarki, da abinda kika tsinkaya su Malam suna fadi, shine ya daukeki ya kaiki asibiti. Ki bar cewa ina zaki Abu, in har kin yarda da ni, kin yarda ni din mai kaunar ki ce, ki zauna tare da ni. Ki bar cewa bazaki ki auri Faruq ba, domin kaunar da yake maki da wadda Baba malam ke maki bata shafi abinda ke kike tunani ba. Wallahi-wallahi Abu saboda ke ne Faruq ya tafi Singapore, saboda lura da yayi cewa kin fada a kaunar dan uwanki, shima Imran din yana son ki, yace shiyasa ya tafi, don a cewarsa ba zai iya jure ganin wannan abin takaicin ba, ya san dai ko yaya ne su Baba Malam ba zasu taBa bari ku auri juna ba”. Na ja gefe na hade kaina cikin gwiwoyina, cikin kuka na ce "kema kinyi mun laifi Yaya Halima. Don me yasa tun a sanda muka zo miki nan ni da Imran, a matsayin muna son juna, baki gaya min ba? Wannan kaunata kike yi ko neman jefani a halaka? Daga ke har Faruq baku da abinda zaku gaya min a yanzu, har da ku aka hada baki aka lalata rayuwata ni da dan uwana. Ko kin san Imran ya tafi inda ba’a san inda yake ba, ba’a kuma san a halin da yake ciki ba? Na hada ku duka na tattara cikin littafin su Baba Sa'idu, har daku aka nakasta rayuwar mu…" Na mike ina kuka sosai kamar raina zai fita, na yi cikin daki, ta kamo gefen zani na, na fizge "Abu kada ki ce min haka, ta yaya kike tunanin zance dake Imran dan uwanki ne, abinda duk duniya babu wanda ya taba tarar ki ya gaya miki? Kina son Innarki tayi karata ne, ko nima ta tsaneni? Wace irin dauka kike tunanin Malam da Faruq zasu yi mini idan zancen ya fito daga bakina, munafuka ko maciya amana……?”. Na toshe kunnuwanada ‘yan yatsuna nayi ciki ina cewa "Ba wani malam da Faruq, amma ai kya dan nuna bakya ‘supporting’ al'amarin, amma har wani cewa kike zaki saya mani Banbar aurena da dan uwana…?” Wani abu yazo ya tokare a makoshina “kai Yaya Halima kema kin cuceni…" na cigaba da kuka. A lokacin ne Halima ta harzuka, ta ce “shikenan Abu, kome kike tunani kije ki yi, nagane da gangan kike kin fahimtana. Tunda kuma kince bana sonki, to na gode, amma kar ki sake cewa ba zaki auri Faruq ba, in kinyi haka kinyi butulci kuma ko Allah ba zai barki ba". Ta haura tabarmarta ta shiga daki ta hau gado ta kwanta, ban sake kulata ba jakar hannuna na dauko na dauki (jotter) nayi wa Faruq 'yar gajeriyar wasika, na kirga kudina dake cikin jakar dana dawo da su daga gidan Baba Sa'idu, kudi ne masu yawa ire-iren kudin da shi Baban yake bamu ne da wanda bakki masu zuwa da abokan su Ya Em ke bamu lokaci zuwa lokaci. Na dauki 'yan kananan abubuwan amfanina da bazasu fi karfin jakar ba na zuba, na zuge. Na jawo akwatina ina binciken sarkar da Mama (Hajiya Azumi) ta bani randa zan taho daga Sokoto, wato sarka da dan kunne gami da zobe da abin hannu guda daya (English Gold) da kyar na ganta, a kasan 'DIARY dina. Jikina na rawa na dauko shi domin na fidda rai da tsammanin inda yake, rabona da ganinsa tun ranar da mukayi maganganun dana rubuta da Inna na. A yau dana bude shafukansa, tun daga farko har karshe na irin al'amuran da nake rubutawa, sai naga na samu cikakken ma'ana na abubuwan da suka shige min duhu, na samu amsoshin tambayoyinda suka dade suna addabar kwakwalwata. Wato dai ya tabbata gareni, Inna ta tsani Baba Sa'idu ne ta kuma kasa yafe masa a dalilin ita ta dauki amanar rayuwarsa, tamkar danta na cikinta, inda shi kuma ya sakamata da yiwa kanwarta ciki na bata hanyar aure ba. Ta ce “zata yafe masa ne kadai ranar dana yafe masa" wato ranar dana gane ni 'yar shi ce, da ya samar dani ta hanyar zina. Na kuma yafe masa. Ta kasa komawa cikin danginta ne domin batasan me zata ce dasu ba a game da Nuratu, da bata san in da take ba. Amma a duk ranar da ta ganta, to a ranar ne zata dawo garesu. "GIRMAN su Hajiya Sa'a yana hannunta." Wanda ke nufin, a duk ranar data fadawa duniya Sa'idun nada shegiyar diya, GIRMAN SU ZAI FADI! "Ita Hajiya Sa'ar ce kece dani SADAKA YALLAH? Bata fadin babban? Wato (Bata fadin ni shegiya ce?)” Wannan na nufin Hajiya Sa'a, tasan tsakanin Abba Baba Sa'idu da mahaifiyata, Nuratu, ta kuma san rayuwar su ta baya. To amma abinda ban sani ba shine shin Hajiyar ta san cewa sun haifeni? Kai babu kama, sai dai ya zamanto cewa ta san soyayyar tasu, amma bata sanda suka kai ga yin cikina, har suka haife ni ba. Tabbas da bata dinga aibatani akan su Hassan ba. Da bata dinga yin fariyar "su da gidan Uban su ba". In haka ne akwai sauran kallo a gaba. Domin kuwa ko ba-dade, ko ba-jima, sai na je na tsaya a gaban Hajiya Sa'a, na gaya mata ko ni WACE CE? In tabbatar mata da cewa BARAROJI kuma SADAKA YALLAH 'yace ga V.C Professor Sa'idu Bindawa. Na kai hannu na shafe hawayena. Idanuna ya kai ga shafin karshe, wanda ya warware min rudanin da zuciyata ke ciki, na kokonto da tunanin ina zan dosa? Wa nake da shi a halin yanzu da ya wuce Baba Sa'idu? Wani farin ciki ya ziyarci zuciyata, ban san sanda fatar bakina ta suBule da murmushi ba, naji kamar an dauke min wani nauyayyan dutse ne aka. To amma ina da tabbacin in sun san ta hanyar da 'yar tasu ta haifeni, zasu yarda su karBeni a matsayin JININ SU har su bari in zauna a cikin su? Inada tabbacin in sun san cewa ita kanta 'yar tasu, gudu tayi ta barni, tun ranar data haifeni don tsira da mutuncinta, zasu yarda su karBeni? Wata zuciyar tace " na Allah basa karewa Zaynab, a ko'ina ba'a rasa na Allah, irinsu Ya Faruq da Yaya Halima, wadanda tunanin su ya sha banban dana sauran mutane, ra'ayin su ya banbanta dana sauran al'umma. Su irin wadannan mutanen kamar wasu mala'ikun Rahma ne da Allah ke saukarwa bayinsa masu matsala irin nawa. ‘They are just like angels in the midst of people' wadanda suke a shirye da sadaukar da kansu domin farin cikin wani. Wannan ne ya kara sani dubar rubutun da nayi shekara daya da wata daya da ya wuce, daga bakin Inna ta; "Kyauta mu ba baroroji bane, sune 'yan kasarmu dake daji, mu 'yan kasar Nijar ne, 'yan usulin wani gari Damagaram, amma iyayen mu da 'yan uwan mu a babban birni Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can”. “In kika shiga Niamey, kika ce kina neman wani daya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan.." Don haka na cusa littafin cikin jakata, na kishingida ina jiran garin Allah ya waye in kama hanyar kasar Nijar neman dangin Innata, in gaya masu rasuwar ta, in rokesu alfarmar su barni in zauna tare dasu, ta hanyar cewa ni ‘yar ta ce. Kamin a hankali in nemo Imran, inyi masa aure da Adda Mami, daga nan nasan ina da Uban da zai rikeni ya kuma cigaba da yi min addu'a ko bayan raina. Wato in zauna tare da shi da iyalinsa muddin rayuwata. Na dauko wasikar da na rubutawa Ya Faruq, na sake binta a nutse, ko akwai wani gyara a ciki? Na tabbatar, babu. Ga abinda na rubutawa dan uwana rabin jiki UMAR FARUQ; "Ya Faruq . Zuciyata ta kasa amincewa da wai in cigaba da zama da Yaya Halima, bayan sanin ko ni wace ce? Gangar jikina ta kasa amincewa da kai wai a matsayin miji, domin tana ganin baka cancanci hada jiki da kazamtacciya kamata ba; You are pure as a clean glass, and I'm a green, but rotten leaf. Har ila yau, zuciyar ta takasa yafewa Nuratu da V.C Sa'idu, don ni ba zan taBa kuma kiran sa ‘Baba’ ba, ba zan taBa iya kiranta ‘Inna’ ba. Don haka na tafi, inda a hankali nake tunanin zan samu labarinta. In tambayeta dalilin shegantani da tayi, ta kuma nemo min dan uwana a duk inda yake cikin duniya a dalilin bakin cikinta. ‘I know it will hurt, but you donno how deeply it hurts the victim’. Faruq ka yafe mani, ka yi mun godiya ga Innarmu, ina nufin (Inna Dubu). Ina fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa". [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Ta ce “eyi mana, baki san makauniyar matarnan tana da alaka ta jini da ita ba? Amma da yake mai bakin kashi ce bata tara komai daga gareta ba, sai dai ita ta dauki nata takai mata" nayi dariya a raina ina kara jin tsoron mutane, dubi yadda Maman keta kareta daren jiya a wurin danta, kada ya koreta, amma ita yanzu gashi tana zaginta. Tace "unh, bari dai inyi shiru da bakina, don kema dai naga kina yanayi da su, ko dai 'yan uwanki ne? Kada inje ko shuka ke nake a idon makwarwa”. Nayi murmushi nace "mutane da yawa sun fadi haka tun shigowata Damagaram, kin san akan samu haka, baka san mutum ba amma sai kayi kama da shi, ni daga Nijeriya na ke". Ta jinjina kai cikin amincewa. Can an jima na sake tambayarta "ko 'ya'yan Nuratu nawa?" Ta sake jinjina kai cikin jimami tace "abin tausayi da wannan baiwar Allah, bata taBa haihuwa ba. An je turai anje Paris an dawo jiya I yau. An kwakwale mahaifa an tsageta an wanke, ko kan 'yar tsana, bata haifa ba. Yanzu kam ta dangana, sai dai tana rikon 'ya'yan kannen mahaifinta, kuma duk ita keyiwa ‘yanmatan zuri’ar su aure, ko kwannan ta aurar da guda biyu a Chadi. Gidansu babban gidane mai dadadden tarihi a Damagaram, don haka ba zaki taBa gane bata haihu ba". Wasu zafafen hawaye suka zubo min, na yi saurin dauke su da 'yan yatsuna, a raina ina cewa su masu abin kunya ai haka suke, da sanya rigar mutanen kirki, son kai da rashin tunawa da wanda ya zame masu dole, balle halin da yake ciki. Sai wanda ba dolen su ba. Inna na yanzu tana can ta zama kasa da turbaya, da tunanin inda take, da halinda take ciki. Itako tana nan tana cin mulki, wasu na can cikin bakin-ciki da kuncin rayuwa duk a dalilinta. Danadam kenan, mai ban mamaki. Muna karya kumallo amma hankalina sam-sam baya tareda ni, yana ga tunanin labarin dana samu ayau na Nuratun Inna Rabi, ganinki yafi jinki. Ya janye ido ga jaridar da yake karantawa, wadda ke rubuce da harshen faransanci yana kallona. Na kurawa kyakkyawan hotonta wanda ya zamo (cover) na jaridar idanu ta baya, bana ko kiftawa. Tana magana akan (racial discrimination) na farare da bakaden abzinawa, tana nasiha akan su rungumi juna su daina wariyar launin fata a tsakaninsu. Duk yadda naso ta daina burgeni, na kasa, amma hakan baya nufin zan fasa kudirina a kanta. Ya ajje jaridar ya tashi kamar mai dauko wani abu cikin madafi (kitchen), wannan ya bani damar daukar jaridar na rubuce adireshin gidan jaridar dake jiki cikin (address book) dina da lambar waya. Ya dawo a dai-dai lokacin da na aje jaridar inda take, na kuma zuge katuwar jakata bayan na jefa dan littafin. Ya dubeni yayi murmushi yace "Hajiya babba da jaka, me zamu ne a cikin jakar?” Nima na mayar mai da murmushin yake na ce "kawunan Damagarawa ne nake tarawa a ciki” ya yi dariya ya buga kafarsa daya a carpet yace "kin san Allah, kawunan mu ba (common) bane sabida GIRMAN su, kyawunsu da ingancinsu sunfi karfin shiga jakar bako" na ce "sai ta dan gari?” Ya basar da zancen yace “in na fita yau sai asubah zan dawo, ko kina bukatar wani abu in taho miki da shi?” Nace “babu abinda nake bukata, sai kudina da zan baka kayo min canjinsu da saifa" yace "to ni in baki mana? Ki bar naki in kin koma Nijeriyarku, jaga-jaga, su yi miki amfani?” Na ce “zan yi godiya kuwa, idan har kayi hakan". Bai fita ba sai da ya aje min damin Niger-Saifa. Bai dade da fita ba na dauko bakin niqabina na maka, na fito rataye da jakata. Laliya na gani na ta zura kitchen da gudu wai na bata tosoro, meye wannan? Na wuceta zuwa dakin Mama na gaya mata zani gidan Radio in sa cigiyar amma ba dadewa zan yi ba, ta yi addu'ar fatan alkairi ta ce in dauki Liliya muje tare kada in bata, na nuna mata babu damuwa ai shata zan dauka daga nan bakin titi da zai kaini ya dawo da ni har gida. Na tari Taxi na nuna masa dukkan adiressikan da zai kai ni, daya bayan daya, ya jira ni in fito sannan ya maidoni, in mun dawo sai muyi balance. Da haka ya ja motar muka mika gidan talbijin na jihar Damagaram, ban sha wahalar samun ganin shugaban gidan talbijin din ba kuma da yake yana jin turanci sosai na gaggaya masa abinda naga dama. Karya da gaskiya harda shaci fadi, har da cewa a gidan marayu na tashi. Da fari ya nunamin ba zai yarda ba, domin bani da hujja. Na daga nikab dina muka yi ido hudu nace “ga hujja ta". Ya dade yana kallo na, ya tabbtar wannan (photocopy) na Nuratu ne a gaban sa, wadda duk duniya ta yarda bata da kwan haihuwa a doron kasa, ai sai ya dauki camera ya dora min ina turancina tiryan-tiryan, wani ma'aikacin gidan talbijin din a gefena na fassarawa. Suka sallameni na fito muka karasa babban gidan Radion kasa wanda keda reshe daga babban birni Niamey. Gidan jarida kuwa da naje ai abin nema ne ya samu, wai matar dan sanda ta haifi Barawo, labari da dumi-duminsa; "Mainasara ta haifi 'ya ba aure a Nijeriya, shekaru goma sha takwas a baya. Ta guda ta barota da rayuwa gidan marayu duk wannan tarin arziki da Allah yayi mata. A yau ga yarinyar tazo da kafafunta, tana neman mafaka a inuwar Gwamnatin Damagaram domin daga can inda take aure a Nijeriya an koreta, a sabili da ganewa da iyayen mijin suka yi ita shegiya ce…. Ga kuma wanda ya karyata, to yazo ofisoshinmu mu hadashi da yarinyar suyi Magana baki-da-baki, budurwa 'yar kimanin shekaru sha takwas, wadda a kamanni da zubin halitta bata da maraba da Mainasara…”. Na dawo gida a gajiye likis, da yamma lis. 'Yar gyatuma tana zaune a gaban allon talbijin ta bude kunnuwa tana saurare, na yi mata sallama amma bata amsa ba, bakinta sai kumfa yake tana masifa cikin abzinanci, da zage-zage cikin harshen hausa, tare da mikewa ta laluba ta angazo talbijin din daga mazauninta jikake taratsatsatsa…! Talabijin din ta soma fidda wani irin hayaki. Laliya dani muka zura da gudu muka zare soket din daya soma cin wuta, ta fadi kasa tana kuka tana birgima tana cewa "duk wanda yayiwa Nuratu wannan sharrin sai Allah ya saka mata, siyasar banza, in banda siyasa mai bankadar da mutunci, wa ya isa ya yi mata haka…?” Haka muka kwana a kanta ba yadda take, gabadaya ta birkice mana kamar mai tashin jinnu, tanata jan Allah ya isa da Li'ilafi ga wadda aka hada baki da ita akayiwa Nuratu sharri, ba zata taBa yafewa ba' Da asubahin fari ya shigo gidan, ya tadda gyatumar sa cikin wannan hali. A kidime ya dagota daga gado ya rungumeta yana tambayarta abinda ya faru, sai cewa take ita dai ya kaita Niamey. Ya dubeni cikin tashin hankali "wai don Allah me ke faruwa ne Zaynab?” Na jinjina kai kamar gaske "tana magana ne cikin French, bansan me take cewa ba”, ya dauketa muka tafi asibiti aka bata gado. Aka zurkuda mata allura ta samu barci sannan ne muka kamo hanyar dawowa don tafiya da abin bukata. Akan hanyarmu ta dawowa daga dauko kayan amfani ne ya kunna radiyon mota, abinda ya fara ji shine, an dakatar da Nuratu Mainasara daga takarar gwamnatin Damagaram a karo na biyu. Tare da koro bayanai dalla-dalla, daki-daki, wannan kuma Oda ce daga kotun kasa (Federal High Court) a turance, har sai sunyi kyakkyawan bincike akan al’amarinta, daga tsarin mulki ne littafi kaza, shafi na kaza sakin layi na kaza. Mai tabbatar da haramcin mutum mai tsohon laifi daga shugabanci. A nutse yake sauraro, babu alamun razana a tare dashi, niko wani gefen daban nake kallo gabana na dakan tara-tara ba uku-uku ba. A hankali naga bakaken gilassai suna maye gurbin farare a cikin motar. Ya fiddo bakin gilashi mai duhu sosai ya saya fararen kwayan idanunsa. Da na juyo na dube shi don neman karin bayani, game da canzawar glassai, sai da nayi nadamar juyowar. Gabadaya ya rikide zuwa wani irin mutum mara imani, mara kyawun gani, tamkar bai taBa dariya ba. Hatta kalar fatarsa sauyawa tayi, daga ja zuwa ‘yellow’, a hankali cikina ke bada sauti “Kululuuu…!” Ya sauke motar a gefen titi tsayin mintina biyu kansa na sunkuye bai ce komi ba, ni kuwa tuni na cure na dunkule wuri guda kamar kashin awaki. Na ji wani abu yana zungurina a wuya, juyawar nan da zanyi sai na yi arba da hancin 'yar karamar bindiga da nake gani cikin fina-finan Amurka ‘revolver' a dokin wuyana. Ya rausayar da kai gefe yace "hmh, tell me, who are you?” Nayi narai-narai da ido, ina yi masa kallon (ka tuna alkawarin daka yi mun kafin in bika cikin gidan ku? Ka tuna alkawarin da kayi mun na ba cuta ba cutarwa a tsakanin mu? Ka tuna alkawarin da kayi mun na zamowa dan uwana na jinni?) Ya gyada kai sama, tamkar ya san me nake tunani yace "imagine you ‘ve never set eyes on me, let us draw to my profession….. " ya fiddo katin shaida (ID card) ya manna min a ido "State Security, Qassim Mainasara". Maimakon inji tsoro, in amsa masa tambayarsa, kamar yadda yayi tsammani, sai na yi murmushi na dubeshi cikin bakin (dark-glass) dinsa, na ce “ai ba tun yau ba, na san kai (SS) ne, kaine dai baka san ko ni wace ce ba. Duk da kasancewar naka mai binciken kwakkwafin dake alfahari da aikin sa”. Ya ce cikin muryar razanarwa "shine nake tambayarki who are you? Ko kinsan wadda kika zo kika yiwa sharri, kika bata mata suna wace ce a gareni?” Na taBe baki nace "tarwatsa kwakwalwata kawai ka daukar mata fansa, ban san wace ce dinka ba, ba kuma na son in sani. Burin da nazo da shi kasarku a yau, ya cika, don haka ko a yau rayuwata ta kare ALHAMDULILLAH!” Yace “kin isa ki mutu, ba'a tagayyaraki an tara maki gajiya a Damagaram ba? Shirmen banza kike, kin dauka wannan shirmen ne zai cika burin naki? Sai ince kuruciya na dibar ki, amma Aunty Nuratu ba sa'ar yin ki ba ce, ke har wadanda suka kulla miki karyar su ta sha karya su ja da Mainasara, domin ita dashen Allah ce, ba dashen mutum ba." Na ce "shine nace ka tarwatsa kwakwalwata da harshashin bindigarka, sannan ne zan yarda da kaunar daka ke mata. Suna kam na riga na Bata mata, wadanda ma basu yarda ba in na fito a gidan talbijin suka ganni a zahiri zasu yarda, sannan kotun kasa dake shirin yin bincike don tabbatar da zahirin maganata zanje su debi jinni na su auna…” yace “…. over my dead body! A bayan raina ba, amma in har ina raye, bazaki kuma zuwa wani gidan talbijin ba, masu diban karya da gaskiya sabida su jahilai ne irin ki, sai dai in mika ki ga al'ummar gari su jefe ki, su kacaccala wannan fuskar da kike tinkaho da ita mai kama data Aunty na…." Nayi murmushi cikin komawa kallon wautarsa, ga gaskiya kiri-kiri yasa kafa yana takewa da gangan don son Auntynsa, nace “kai ni tsakiyar gari Qassim, a yagalgala fuskana mai kama data Auntynka" ya ce “ai idan na yi hakan kuma ban kyauta mata ba, don na tabbata zata so ganin wace jarumace ce ta aikata mata wannan sharrin? Don haka daga nan, Niamey zan kaiki, koda akan iska ne. Ki je gabanta ki maimaita abinda kika fadi, in har kin cika mai tsaurin ido da jarumtaka….” Ya figi motar da gudu sai filin jirgi, ya kulle ni a cikin motar ta ko’ina yadda ko ihu zan yi ba mai ji na, ya fita. Bai san cewa ko a bude ya bar kofar bau inda zan je ba. Nidai tunda burina ya cika, ina maraba da kowacce irin rayuwa ce ta sameni a gaba. To don ya daukeni ya kaini gabanta sai me? Iyakaci tasani a inji, ta markade, ko jama'arta su harbeni da bindiga sai me? Bani da wai sauran ‘hope’ a rayuwa sai na fatan cikawa da imani. Haka kawai kuma naji hankalina ya tashi, bugun zuciyata ya tsananta, wasu irin hawaye kuma da bana ce ga dalilin su ba, suka zubo mini, na nadama ne koko na dakacen me kenan na yi? Me yasa nayi haka? Ban kyautawa Innata ba. Nasan duk inda take a yau tana cike da Bacin raina, ban ji maganarta ba, banyi amfani da gargadinta ba ko daya. Ramuwar gayya bata dace da dan musulmi ba, musulmin kwarai afuwa yake da rangwame cikin al'amarinsa. Ramuwar gayya da daukar fansa aiki ne na yahudu da nasara, wadanda basu yarda Allah ke shiryawa bawa rayuwa ta duk yadda ya so ba. Gaskiyar Yaya Halima ne bacin rai zai sani fita a imani na, zai rauna imanin da nayi da Allah guda daya, shine mai sakamako, da bin hakikin wanda aka zalunta. Babban abin takaicin ma ga UWA, wadda ta dauki nauyina cikin mahaifarta wata tara ras, ta haifeni bayan mawuyanciyar nakuda da Allah kadai yasan adadin azabar dake cikinta. Idan kuma an bi salsala Nuratu bata yi min laifi ba, Ubangijinta ta yiwa. Idan kuma ta rokeshi ya yafe mata, ni ba komai ba ce. Babu wadda zata so ta haife Da babu aure, sai dole, sai tsananin rabo da kaddara. Babu kuma wanda ya isa ya kaucewa kaddarar duk da Allah ya rubuta masa. Sai kuma wani hukunci na Ubangijin mu da yake son nunawa na baya darasi. Amma al'umma bazamu taBa hankalta ba. Laifinta daya gareni, shine na biris din da tayi da Innata, abar ma ta ni kaina, alhalin tana sane da wahalar data barta da ita, da bakin-ciki gami da abin kunyar data jawo mata wanda fadar sa ma bata baki ne, musamman a cikin karkara. Duk da haka 'yar uwarta bata taba budar baki ta fadi kalami na Allah wadai agareta ba. Duk wasu kalamanta akan Nuratu na kauna da alheri ne. Ta ce dole ce ta sa ta gudu ta barta, amma Nuratu mutuniyar kirki ce. To ko bayan Innar, wane ne ya budi baki ya fadi wani abu wanda bana yabo da kauna gami da fatan alkairi a gareta bane? Ko Ya Faruq wanda zai kasance karamin yaro a lokacin da ya santa, yace ba halinta bane, kaddara ce ta afka mata. Hakika halin mutum da makomarsa ana gane su ne daga shaidar da ya samu daga mutanen dake tare da shi. Kamar yadda yace; dukkannin mu masu saBo ne in one way or the other, na wani ma idan kaji sai kaji kamar ka roki Allah ya kifar da duniyar, domin babu komi cikinta sai saBo, kalilan ne suke yin saBon suna kuma tuba. To idan Nuratu ta tuba, Ubangiji ya amshi tubanta, ni menene makomata? Abin nufi, meye makomar dan da ya bankada mutuncin Uwarsa a duniya? Ya tozartata a idon al’ummar dake matukar ganin GIRMA da kimar ta? Abar ta zancen hukuncin rashin yarda da kaddara da fawwala komai a gareshi, wanda ke daga cikin rukunan musulunci, a koma ta hukuncin mai daukar fansa, wanda bai yarda da hukuncin da Allah ya zartar a kansa ba. Ubangiji (S.W.T) yace "kuyi hakuri, hakika Ubangiji yana tare da masu hakuri” ya kuma ce “kuyi afuwa (ga wanda ya saba muku) hakika Ubangiji mai afuwa ne". To ni banyi hakuri ba, banyi afuwa ba kamar yadda Faruq da Halima suka Bata muhimmin lokacinsu suna nuna mini. Mafi tashin hankalin ma daukar fansar tawa akan UWA, wadda sai ta daga min diga-diganta ne zan wuce aljannah, wadda Bacin ranta zai kaini wuta, hawayen ta ya turani jahannama. Wadda (S.A.W) yace “a bita, abita, ya kuma cewa a bita, kamin yace abi Uba….”. Nasan inda duk take a yanzu tana can tana zubar da hawaye, ba don bakin-cikin hanata sisaya ba, sai don bakin-cikin FADUWAR GIRMAN ta, bacin suna da zubewar mutunci, duk a sanadiyyar diyar data tsugunna ta haifa a cikinta. Ni ban gyara lahirata ba, gashi dama duniyar tawa gurBatacciya ce. Na kuma kara gurBatata. Idan da na yi tunani, ai kirari ne nayi na zurmawa kaina wuka, ko babu komai na baro inda aka sanni, saboda gudun kar a kirani da ‘shegiya’. Maimakon da nazo inda ba a sanni ba, in rufawa kaina asiri, in nemi dangin uwata da ita kanta, mu taru mu rufawa juna asiri, a'ah, suma na kawo musu guzurin Bacin suna da abin gori har 'ya'ya da jikokin su…. Numfashi na naji yayi sama, kamin ya gagareni fesarwa, kirjina ya shiga wani irin zafi da radadi, kwakwalwata ta shiga bugawa dam-dam saboda zazzafan tunanin dana takurata da shi. Idona ya shiga lumshewa yana budewa a hankali, ban kara tsinkayar abinda yake faruwa da ni ba, illa jin hannun Qassim daya taroni ina shirin zamewa cikin seat dina, yana cewa "Ayya Zaynab! Me yayi zafi haka?” Na lalubo shi na kamo kansa dai-dai kunne na, muryata ta dushe gabadaya, nace "ko bayan raina… ka roka min gafararta, ka gaya mata nima bada son raia na aikata mata hakan ba, zuciya ce tafi karfina……, na-nayi in lankwasata, na kasa, na yi kuskure babba da bani da inda zan sa kayan nadamar shi…." yace “Insha Allahu Zaynabu, ko zaki mutu sai a kirjin mahaifiyar ki. Ko wannan shine abu na karshe da zanyi a rayuwata, zan yi iya kokarina in sadaki da ita…”. Bayan wannan, ban kuma tsinkayar meke faruwa a duniyar ba. *** *** *** A NIAMEY “Aunty Zaynab, muna yi miki barka da zuwa cikin (family) dinmu na MAINASARA KANGIWA". Zazzakar muryar wata matashiyar yarinya da bata fi shekaru sha hudu ba, na ji a cikin kaina kamar a mafarki. Wadda ta kitsa mata fadin hakan ta kara ce da ita “ki gaya mata dama mun san ko ba-dade, ko-bajima zata zo ne, in har tana raye”. A hankali na bude idanuna da suke a rufe, a baryar da sassanyar muryar matar ke fitowa. Fara ce sol, doguwa mai ginannen jiki. Fatar jikinta sumul-sumul jawur, kamar kana tabawa jini zai yi tsartuwa. Sumar kanta yalwatacciya baka kirin, nannade a gadon bayanta. Hancinta a mike kamar biro, sai murmushi take tamkar furen fulawa, hakoranta farare tas kamar kankara, yatsunta na kafa da hannu sun sha adon bakin lalle sunyi shar, santala-santala dasu jajawur kamar na jariri sabuwar haihuwa. Mayuwanci ne ka kimanta shekarunta a lokacin daya, za dai ka kirata babbar mace, mai babban al'amari. Idanunta dara-dara farare sol da kwayar ido mai sheki kamar an diga zyl, sun sha (kohl) sun fito dara-dara cike da barazana da rashin son waigi. Sanye take da ruwan hodar lesi (Cotton) watau (dark-pink) mara nauyi, shara-shara, shafal-shafal kuma mai saukin ado. Wuyanta da kunnenta ya dauki siraran ‘pearls’ na farin dutse, riga da zane ne a jikinta, daurin kallabin ya zauna sosai a kanta kamar nadin inji. Gabadayanta sai kace sabon kwai ne da Dawisu ya nasa yanzu-yanzun nan, domin haka take very delicate. A Bangaren jinsin dan adam (personality) tana cikin rukunin 'phlegmatic people’ watau mutanennan masu fara'a, rashin kuzari da wadatar jini a jika. Mahaifiyatace, Hajiya Nuratu. Kallonta nake cike da mamakin yadda za'a ce matashiya kamar ta, ta haifi katuwar budurwa kamana. Zai fi dacewa idan akace ni kanwarta ce, mai bi mata a haihuwa. Lokaci guda wata irin kauna ta UWA (maternal love) irin ta da da mahaifi, wadda Ubangiji kadai yasan adadinta, ta rika keta zuciyata. Ba abinda zan so a lokacin kamar ta rungumeni a cikin jikinta, inji me 'ya'ya suke a dumin jikin uwa? Amma batayi hakan ba, baya ta juya min tana abinda yafi mun kama da sharar hawaye. kofar dakin ta bude, mata ne suka rika shigowa farare tas-tas manya da kanana, tsofaffi da masu tsaka-tsakin shekaru. Kallon sittirun dake jikinsu da yanayin fatar jikinsu kadai ya isheki kimanta sune iyalin Kangiwa. Tambaya suke ta yi “ina Zaynabu din? Ku matsa na ganta………. Ku gafara mu ganta. Kauce nan na hangota. Zaynabu ina Yaya Rabi? Zaynabu wa ya kawoki Niger? Ina kika baro Yaya Rabi, ba tare kuke ba…?” Na maida idanuna na lumshe, wasu irin hawaye na fita suna shiga cikin kunnuwana. Cancarakas suka dagani suka tsayar da ni akan kafafuna. Daga masu rungumata sai masu kama hanuna da masu tube dankwalina don ganin kalar gashin kaina. Kowanne na fadar albarkacin bakinsa game da kamannu na da mahaifiyata da 'yar uwarta Rabi. Wata gyatuma tukuf a durkushe tana dogara sandarta ta dogaro ta shigo tana "gafara nan ku gani in bugi shashasha…” ta daga sandarta ta muka min a baya, wata mace mai tsaka-tsakin shekaru daga cikin wadanda suka zagayeni ta rufeni ruf da bayanta tace “sai dai ki bugemu tare Yadudu, amma Zaynab kuruciyarta ke dibarta, ta kuma gaya mata miki abinda take tunanin shine dai-dai da ita, ko ni ce hakan zanyi. Kuskurenta daya bata fara tunkarar Nuratu ta ji bayani daga gareta ba. Zaynabu Allah baya ramurar gayya ba kuma ya son masu yinta. Idan kece hakan ta faru dake, zaki so 'yar ki ta yi miki abinda kika yi mata?” Ni dai sai kuka nake na rasa ta cewa. Ganin al'amarin nake kamar a mafarki, na kasa gasganta wannan rana. Wai wadannan duka dangin Inna ta ne jinin ta ne, tsatsonta ne. Na daga kai domin hango karshen su, iyakar ganina banga adadin su ba, da alamama akwai wasu a waje, wadanda duk girman da dakin ke da shi, basu samu wurin tsayar da kafafunsu ba. Na jinjinawa zuciya irin ta Innata, da ta iya rayuwa ‘lonely’ cikin karkara, shekaru ashirin da doriya ba tare da kuwa nata ba, duk da wannan bataliya da Allah yayi mata, ba kowadanne mutane ne masu zuciyar Inna ta ba. A cikin su dai na ci gaba da hange, don karin ganin fuskar dake yawo in my imaginations, kwana da kwanaki, wata da watannni, shekara da shekaru; Nuratun Inna Rabi. Muka yi ido hudu, kallona take babu ko kiftawa, fararen idanunta cike da tarin kaunar da biro ba zai iya rubutawa ba. Duk da haka hawaye basu bar ambaliya daga idanunta ba. Ta tako a hankali suna darewa suna bata hanya, zuwa gadon da nake zaune, na tura 'yan yatsuna guda biyu cikin bakina, domin toshe kukan dake son suBuce mini, ta tsaya a kaina ta ce “ina Yaya Rabi?” Da karfi kukan ya kufce, na yi ta yi babu sassautawa, cikinsu babu wanda ta katseni amma jikkunan su sunyi sanyi, har na yi mai isata ya isheni. Cikin dusashshiyar murya nace “Allah yayi mata rasuwa sati biyu da suka wuce……..” Gabadaya falon ya rude da kururuwar mata da tsofaffi, barin tsohuwar da naji an kira da Yadudu, faduwa tayi tana tana makyarkyata tace "ashe rabon zamu sake ganawa dake ba Rabi? Cikin wannan satin muke shirin tafiya gabadaya gareki, wayyo Rabi baiwar Allah bamu rike amanar mahaifinki ba….." hankalin su duka ya koma kanta, suka cicciBeta suka dora akan gado suna yi mata fifita da bakin mayafan laffayansu, daga baya na fahimci ita wannan dattijuwa kaka ce ga Innata domin ita ta haifi mahaifinsu Alhaji Sani. Ita kadai ta saura cikin matan marigayi Kangiwa. Bana son tuna irin halin da Nuratu ta shiga da jin mutuwar 'yar uwarta. Ta zama jawur kamar jinni, tana kuka da hawaye da majinarta, ta fita daga dakin ta hau matattakala zuwa sama, har dare bata kara saukowa ba. A lokacin ne iyaye maza suka iso daga sammacin da 'yar uwarsu tayi musu. Suka tarar da wannan labari sukace "Allahu Akbar, haka Allah ya so bamu da rabon ganawa dake Rabi sai a Darusallamu, ki yafe mana ki yi mana aikin gafara, bamu sauke hakkokinki dake kanmu ba. Tunda Alhaji ya rasu babu wanda ya bi sawunki, tunda 'yar uwarki ta iso ta ce mana kina lafiya zaman aure kikeyi, babu wanda ya kara bi ta kanki. Hakika idan baki yafe mana ba akwai hisabi a tsakaninmu, ga gadonki muna ta ajiye da shi har yau ba wanda ya ci, don haka zai zamo sadakatul jariya a gareki…". Dacin mutuwar 'yar uwarsu ya shafe nawa al'amarin, suka taru kaf a babban dakin ‘meeting' dinsu dake cikin gidan Nuratu, suka bude al'qur'ani mai tsarki suka yi ta sassauke mata, aka kada Rakuma, shanu da raguna aka yi ta sadaka. Tun daga ranar garar abinci kawai ake fitarwa daga (Estate) na Kangiwa nau'i-nau'I zuwa ga kushewarta, har tsayin kwanaki (7). Ni da Qasism sai dai hange daga nesa a dakin addu'a, ya yi min murmushi in maida masa, sai ranr bakwai Liliya ta kawo Innarsa daya manto a asibiti. Jin abinda ke akwai ai sai ta kara faduwa ta suma, ban taBa ganin rarraunar tsohowa irin wannan ba. Hibbani cousin din Innata wadda ke kareni da Hajiya Yadudu na duka, ita ke gaya min Goggo Azzo, kanwa ce ga kakan mahifiyata watau Kangiwa Mainasara. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Da na tattago radiyon Rabi, na sauke masa a baki, sai ga haBo ya biyo baya, na guda-gudan jinni, suna sauka akan hannayensa nace "kadan kenan daga abinda zaka gani, a duk ranar daka sake gigin shiga harkata". Yadda duk ya dauki abin da sauki, to ba haka yake agareni ba. Ya dauka wannan karon ma zai sake samun kaina da irin kalaman yaudararsa, bai sani ba, kishi yana maida soyayyah, kiyayya, sannan, zama da kishiya is not the type of life I planned for. Rabi kam ta yi tsalle gefe tace babu ruwanta da shirgin mu, tunda sanda muka kulla soyayyar, ai boyewa muke bama so ta sani, saboda mun maida ita 'yar bukulu, saida ta kwaBe masa zaizo ya isheta da 'yar murya. Haka nace da Malam Ali, muddin ya daura min aure da Sa'idu, to zan guda kasar mu, cikin dangina, ya samo mai zama da matarsa. Na kara gasgata rashin tabbas, karya, yaudara, da ha'inci irin na da namiji. Wai zai dubi Sa'idu a haka yace ya taBa yin aure ma balle ya haihu? Wa zai ce ya taba yin soyayya ba a kaina ba? Na rokI Allah ya saka min akan wannan yaudara da Sa'idu ya yi min, ba kuma don komai ba yayi min hakan ba, sai don ganina da yake yarinya karama, mara wayo, domin da yayi aure da wuri tabbas da ya haife kamata. Wai ma ashe tare da matar tasa suke, ya taho da ita ganin gida da kuma bikin auren mu. Ban san haka ba sai da yamma da tazo ana take mata baya, cikin atamfa English marun kala, ta yafo wani dan yalolon gyale, kamar na tatar koko, tana tafe kai a sama, kamar kada ta shaki iskar kauyen, ita a dole ga baturiya. Ta zo har cikin dakinmu yaronta Imran na biye da ita yana ta kuka, ta coge a bakin kofa don dakin bai isa ta taka baturiyar kafarta a cikin sa ba, ta ce "zuwa nayi inga BARAROJIN data kanainaye min miji, zuwa nayi inga SADAKA-YALLAR dake shirin aure min miji? Ba dai wannan berar bace mai kama da dorawa?” Muka daubi juna ni da Yaya Rabi, cikin mamaki, dimuwa da rashin abin cewa, ta cigaba da cewa "Bararoji Nijar babu abinci, kun gudo daga jeji, domin BARA da KARUWANCI, ai da kun tsaya a karuwancin, amma mijina? Yafi karfin auren sadakar-yallah, koko ince, naïf karfin yin kishi da sadaka-yallah". Ta Balle bakin jaka ta debo (pounds) na kasar Ingila curi guda ta watso min a fuska tace Yallah, ga sadaka nan, don Allah a kara gaba. Sa'idu sai Sa’a, sai gani sai hange, ance dake ana yin mata biyu a Ingila ne? karya yake miki baskwata ya gyara miki, duk kuma mai zaune a baskwata, 'yar wanke-wanke ce. Kenan gara miki zamanki cikin kauye, yafiye miki rufin asiri, ko kuma a koma Niger ayi tallan cukui, a kora Rakuma sahara. Muddin kika sake kika biyo shi, wallahi 'yar wanke-wanke na samu, amma nafi karfi in yi ‘sharing’ miji da sadakar-yalla da tsafta ma bata ishe su ba". Ta juya tana kada mazauna ta fice abinta, daga ni har Yaya Rabi, gudun jini ya daskare a jikinmu. Ba'a taBa yi mana wulakanci irin wannan ba a tsayin rayuwar mu. Duuiya mai yayi! Wai mu jikokin Kangiwa ne yau ake kira mayunwata, karuwai, sadakar yallah! Allah sarki! Mukai ta kuka har muka ji babu dadI, nace "wallahi ko zan mutu babu aure, bazan auri Sa'idu ba" Rabi tace “shirmen banza, bazaki aure shi ba kawai idan bakya son shi, amma ba don wannan busashshiyar da aka bashi sadaka ba. Da ta isa ta yi mana wannan zagin a gaban sa, wallahi saki uku zata karBa babu nadama!” Nace “kayya Yaya Rabi, son ma na daina, indai na Sa’idu ne, koda kuwa shine autan maza. Yau mu ake kira karuwai Rabi, har ke da kike a dakin mijinki? Allah ya isa tsakanina da wannan matar dana bari ta fita ban tara mata gajiya ba….” Rabi sai ta koma yi min dariya, ta ce “a hakan? Da dai kanwar ta kar tsami". Na fada jikinta ina kuka nace "Allah sai na rama akan wanda ya janyo miki zagi a rayuwarki". Sa'idu kam da gaske yake, ya cigaba da shirye-shiyen aure batare da ya kara bi ta kaina ba. Dana ga dai da gaske Malam zai daura auren nan, sai na hada kayana da asuba na fice da niyyar in tafi tasha in hau motar Niger, ko yaya Rabi bata ga fitata ba tana barci. A lokacin kuma Malam da Sa'idu suka fito daga masallacin dake daura da gidan mu daga sallar asubahi, suka hango ni ina ta nikar sauri da akwati rindimeme aka kamar wata zararriya. Gabadayan su suka biyo ni, Malam Ali ya sha gabana, ya ce "Nuratu me yayi zafi, kawo akwatun ya daukar miki, kin san dai bazan taBa yi miki auren dole ba, domin kuwa ke amana ce a hannuna da idan naci sai Allah ya tozartani duniya da lahira". Jikin Sa'idu ya yi sanyi, ya tabbatar wannan karon da gaske nake. Babu komai cikin kwayar idona sai kiyayyar shi tsagwaronta. Shi ya dauko akwatin muka dawo, Malam yana ta fada wa Yaya Rabi, kan sakacinta har na fita bata sani ba, yanzu da Allah bai sa sun ganni ba wa yasan inda zan fada? Nikaina fada kawai nake, amma in za'a kasheni bana ce ga hanyar da zan bi inje Nijer din ba a lokacin. Ta dinga salati ta ce “haka kike da taurin kai Nuratu ? To shikenan Sa’idu ya fasa aurenki, ko kece autar mata don Allah ki zuba ruwa a kasa ki sha”. Sabida haushin dana bashi daga ranar bai sake shiga sabgata ba, suka soma shirye-shiryen komawa. A dan tsukin kwata-kwata bana cikin nutsuwata sakamakon mafarke-mafarken da nake masu ban tsoro da Sa'a, kullum sai na ganta cikin barcina dauke da jariri tana miko min ina kin karBa, sai tace “karbi abinki, kiyi gaba, in dai don wannan ne aka ce dole sai kin auri mijina”. Ni kuma sai in yi ta gudu tana bina da shi, da taga ta kasa cimmani, sai ta wurgo min shi. Yana fadowa jikina, kafin in rungumeshi, sai ya mike da kafafunsa ya bita da gudu ya rike kafafunta gam-gam tayi ta kurma ihu. Jariri fa sabuwar haihuwa don haka wannan firgicin ya maidani wata karamar zautacciya. Babu kuma ranar da zan kwanta in tashi, ban yi wannan mafarkin ba, idan na farka cikin dare sai in zauna a tsakiyar gado, inyi ta gursheken kuka. Rannan kuka na ya tayar da Rabi, hankalinta yayi matukar tashi ta rika lallashina akan in fada mata abinda yake damuna, in dai auren Sa'idu ne wallahi an fasa, ba zata taBa yi min abinda bana so ba. Na ce da ita ni mafarkin da nake yi da Sa'a da jariri ne yake bani tsoro. A hankali ta matso jikina ta ce cikin karamar murya "wane irin mafarki ne Nuratu?” Na fada mata tiryan-tiryan, ta yi shiru tana kallona cikin nutsuwa can ta ce "in dai zaki ji shawarata Nuratu, kin san dai bazan taBa kaiki ga abinda nasan zaki cutu ba. Sa'idu yana matukar son ki, Sa'a Malam ne ya bashi sadakarta bada son ransa ba. Ya gaya mun don bazai iya yiwa Malam musu bane amma wallahi baya sonta. Ki kwantar da hankalinki ki fidda ita a lissafin ki, ki auri Sa'idu ina tsammanin akwai rantsatstsen rabo a tsakaninku, wanda Sa'a ke son yin sanadin salwantar dashi. Ni ban san wane irin kishi ne dake ba, ni bakya ganin kishiyoyi biyu nake zaune dasu me ya sameni? Wa kika ga ana so cikinsu yadda ake so na? In gaya miki abinda baki sani ba, matan abzinawa basa boranci ko kankani". Nace “wallahi Ya Rabi ni ba kishin Sa’a nake ba, kawai dai auren da Sa’idu ne nake jin ko za’a tsige min rai, bazan taBa yi ba. Na gwammace in shiga duniya. Amma don so har gobe babu wanda zan so tamkar sa". Sai tayi tsai da ranta tana kallona cikin tunani, tace “Nuratu kwanta kiyi barci, lamarinki na bukatar addu'a, ina tsammanin ba haka Sa'a ta barki ba. To idan ita asiri take, ni kwana nake sallah! Aurenki da Sa'idu bazai yiyuwa ba kadai idan dama ba rubutacce bane". Ta bani addu'oi irin wadanda Malam ke bata, tace kullum kafin in yi barci in karanta in shafe jikina. Washegari da safe ta bani karin kumallon Sa'idu tace na kai masa, duk dai a kokarinta na son ganin mun shirya kan mu. A yau ban san me yasa kwata-kwata ban yi musu ba, karewa ma cike nake da dokin ganin sa, dana azabtu kwarai da rashin yi har tsayin sati biyu. Dama na shirya koda bata aike ni ba, ni din zan je da kaina idan ta fita, domin tun jiya take shirye-shiryen tafiya Bindawa dubo Uwar Sa'idu da bata ji dadi ba, tace zata kai dare. Shatar mota guda Sa'idu yayi mata ya biya zuwa da dawowa tun daga Gwarzo har Katsina. Tun safe nake jin wani irin motsi-motsi a cikin kwakwalwata, kamar ana yi min kida, haka komai nake yi ji nake kamar umartana akeyi da yin hakan. Hatta kokon dana duka zan dauka, sai naji kamar ance dani “baki zuba masa sukari ba”. Na kuwa dauko sukari wurin gongoni hudu na antaya a kwanon koko. Na sunguma na tafi idanuna na wani irin juyawa ko hanyar dakin Sa'idun na manta, amma sai na ji kamar an kama hannuna, ana yi min jagora. Ina shiga shi kuma kamar dama jirana yake yi, sai ya taso ya karBi kokon daga hannuna. Cikin mu babu mai iya kallon fuskar dan uwansa, ya mika hannunsa ya rungumoni ya ce "Nuratu mai-dogon-gashi yaya? Har yanzu kina nan nan akan bakanki, na bazaki aure ni ba? To 'ya'yan da kikayi alkawarin haifa mani fa? Wallahi bazan iya rayuwa mai kyau agaba ba, in kin guje mani Nuratu...." Daga haka ya soma rabani da duk wasu suttirun jikina. Ban yi wani yunkurin ba ko kankani na hanashi hakan. Sai ma kara armasa mishi al’amarin da nayi. Don haka ba zan kirayi al'amarin da sunan ‘raping’ ba illa ‘cooperation’ na dukkannin mu”. Ta sunkuyar da kai daga kallona, tana wasa da kyawawan yatsunta da suka sha adon lalle. Bata yarda mun hada idanu ba. Ta kai yatsunta ta dauke wasu makalallun hawaye daga idanunta. Ni kuma sai na kai hannuna biyu na rufe fuskata da karfi, na kwantar da kaina a cinyoyinta. Domin yanzu na fara fuskantar abinda ada, ban fahimta ba. Na kuma fara gane Hajiya Sa'a mahaifiyar Ya Em, itace silar shigar mahaifiyata cikin halin da ada, nayi alkwarin har abada bazan yafe mata ba. Bata saurari sheshshekar kukan da nake yi mata ba kasa-kasa, ta cigaba da cewa “koda Ya Rabi ta dawo ranar, ta so ta fuskanci wasu sauyuka a tare da ni. Domin na koma daga kwanciya, sai kwanciya, daga daki sai daki. Data matsa min da tambaya na sanar da ita ciwon marana ke matsa min. Da yake kuma ta san yadda nake fama da shi duk wata, wani zubin har suma nake, sai bata wani tsaurara bincike ba. Illa ta hadani da kwayoyin felgin. Wannan shine ya zamo mafari. Daga ranar kullum da kafafuna nake fakar idon kowa in tafi dakin Sa'idu, kullum ta Allah babu fashi kamar masu ibada. A lokacin Sa'a bata gari, taje Gombe can wajen dangin mahaifiyarta. Wata irin kazamar soyayya muke aiwatarwa wadda a duk ranar dana tuna, na kan ji na tsani kaina Zaynab, inyi kuka inyi istigfari, in yi nadama in la'anci soyayyah, domin komi dai mene ne, akwai sharrin soyayya a ciki. Na samu kaina a wata irin sabuwar rayuwa, da ban taBa mafarkin tsintar kaina ba. Sa'idu ya koyar dani wata irin soyayya mai wuyar bari. Yayin da ni kuma na bada hadin kai da zuciya, gangar jiki da ruhina duka. Kaka-tsara kaka! Kwanakin da zasu yi suka kare, suka yi shirin tashi washegarin wata litinin. Zuwa lokacin ya lallasheni na hakura da zancen auren mu, to ma idan ban hakura ba, ina zan iya barin wannan rayuwar mai gardi daya jefa ni a ciki.? Ya samu Malam Ali suka gama magana kan cewa bayan watanni uku zai sake neman sarari ya dawo a daura mana aure mu tafi. Hatta kudin auren da wanda za'a yi min kayan aure ya barsu a hannun Malam. Ita kuwa Inna Dubu ya bata na sayen kayan sa rana. Faruq yafi kowa murna da jin za’a yi mana aure da Yaya Sa'idu, ya ce "Nuratu mai dogon gashi nine dan zamana dakin ki" na ce “to dan dukusuru, in ba kai ba dama waye?” Sai Rabi ta bige min baki, wai bani da kunya, da kaina nake zancen aure na. Tun komawar su Sa'idu, ban sake ganin al'ada ta ba. Ban damu ba don a wautata ai na huta da shegen ciwon dake naman hallakani duk wata. Koda yaushe muna waya da Sa'idu muna sanarwa da junan mu kewar da muke ciki. Ya kan ce “kiyi hakuri Nuratu, wallahi karatu ne yayi min zafi, ga (financial difficulty) dan kudin da gwamnati take bamu na tallafin karatu ya tasamma karewa. Dama wani bature nake yiwa aikin gidan gona yana biyana kuma a komawar nan da nayi na taras Allah yayi mishi rasuwa shiyasa abubuwan suka cude mini. Ita kuma Sa'a shegen kashe kudi ne da ita, bata barina in tara komai balle in kama maki wani gidan hayan, wannnan da muke ciki daki daya ne sai kitchen da toilet. Ga rayuwar London mai tsada sosai, ko abinci zaman kansa yake. Amma alhamdulillahi idan na hada wadannan takardun ne Masters da nike yi, Jami'ar mu sun yi alkawarin zasu bani ‘lecturing’ daganan komai zai dai-daita, don haka ni da zuwa ina jin sai farkon sabuwar shekara”. Ko ciwon kai ban taBa yi ba, bana amai bana tofe-tofen miyau, sai dai na ji cikina yana wani tamkewa da kumbura kadan kamar sabuwar kwarya. Abinki da dagowar mace sambal. Ga kuma manyan riguna dinkin Nijar na shadda su nake zurmawa, hankali na a kwance, don ni har zuwa lokacin ban taBa kawowa a raina wai ciki ne dani ba, har tsayin watanni biyar ris. A lokacin ne jarrabawar mu ta fito, na fito da (credentials) bakwai cif. Na yiwa malam Ali maganar inason cigaba da karatu kamin Allah ya dawo da Sa'idu, ya ce sam ba zai barni in tafi Kano ni kadai ba, inyi hakuri in Sa'idu ya dawo shi da kansa zai samar min gurbin karatu kamar yadda ya samarwa Sa'a a Ingila. Kwanaki suka shura har watanni bakwai a bayan tafiyar Sa'idu. To a wannan lokacinne fa ciki ya soma bayyana kansa. Kafafuna suka kumbura, kumatu na sukayi sutu-sutu da yake irin cikinnan ne na samu mai bin jiki. Na bude na zama wata ingarmar mace danya shakaf. Yaya Rabi mamakinta ya kasa Boyuwa, rannan ta ce “Nuratu maganin kiba kika hadiya ne?” Da yake ita bata taBa haihuwa ba, bata san wasu alamomin ciki ba. Na yi dariya na ce “hutu ne kawai Yaya Rabi, tunda babu zullumin karatu”. Ta ce “haka ne fa, Allah dai yayi gaggawar dawo da Sa’idu mu sha biki”. Nayi murmushi. Duk wasu al'amuran gidan na daina shiga, na koma kullum ina kuryar daki, manne da hoton abin kaunata. Shiga bandaki kawai ke fito dani. Sai dai ni kaina abun yana damuna, sabida nauyin da jiki na yayi da kumburin da kafafuna ke kara yi. Ga wani wutsil-wutsil da nake ji cikin cikina lokaci zuwa lokaci kamar mai macijin ciki. Ni da kaina sai na fara zargin kaina. Al'amarin ya samo asali ne ranar wata talata, na fito domin yin alwalar sallar mgariba. Inna Dubu ma ta fito da butar ta ta zauna a wani kututturen icce kusa dani zata yi alwala, ni kuma na zauna bisa wani dutse. Zamana ke da wuya nepa suka kawo wata wuta mai karfi, ta dago tana yi min magana ganin yadda na gacire kugu ina yamutsa fuska na kasa yin alwalar. Ta yi kasake! Tana dubana kafin idanunta su sauka a kafafuwana. Ta ajiye butar idanunta a jirkice ta mike, har tana tuntuBe da turmi, tayi turakar malam shi a lokacin ma ya fito zai tafi masallaci. Sai ganinsu na yi sun fito tare sunyo dakin Yaya Rabi. Suka kulle kansu me suka ce, me suka ce Allah a’alam. Na kammala alwalata na nufo dakin sai na taras sun sa sakata. Sai na jingina da bango duk nasha jinin jikina, a sannan ne na samo jiyo sheshshekar kukan Malam Ali. Hankalina ya tashi, don ban taBa jin malam yana kuka ba, ko a sanda aka aiko mai rasuwar gyatumarsa da ke Funtua. Ji nayi an zare sakatar, Inna Dubu ta fito ko kallona bata yi ba ta nufi dakinta, nasa kai cikin dakin Malam yana ta kuka, ita kuwa Yaya Rabi sai ta sa min ido kawai tana kallona. Can anjima ta soma wani irin gurnani da huci kamar macijiya. Mika hannun nan da zata yi, sai ta zaro wata sharBeBiyar wuka da suke yankan naman sallah ta yiwo kaina. Ban taBa sanin Rabi nada karfi haka ba sai ranar, don kuwa daga ni ta yi cancakas ta kayar dani dai-dai lokacin da Dubu da Rakiya suka shigo suka rirrikita suna “Subhanallahi. Rabi kada ki yi kisan kai ayi nadama goma da ishirin”. Tuni ta watsar dasu ta yiwo kaina ta dora min wukar a wuya ta ce "Don Ubanki, gidan Uban wa kika je kika yo cikin? Wallahi ko ki gaya min ko in kashe ki, in yaso nima a kashe ni daki jawo min bakin-cikin da zai kaini kushewa…” Idona suka firfito ganin mutuwa muraran. Malam Ali ne yasa karfi ya kwace wukar a hannunta, sai ta sakeni ta soma kuka. Ta ce “Nuratu kin cuce ni, Allah sai ya saka min ya sakawa mahaifinmu. Ki fita daga dakina ki koma wajen wanda yayi miki cikin, bani ba ke ko a lahira kada ki ce kin sanni…. Allah ya gani Malam Ali bashi da hakkinki. Duk wata tarbiyya da ubanki mahaifi zai baki ya baki. Ya baki sani na Alqur'ani, addini dana book. Ya daura dukkan burin sa na samun nagartattun jikoki daga gareki, amma sakamakon da ya samu daga gareki kenan, ki tashi ki fita, ki tafi duk inda zaki bana son ganinki…….” Malam Ali ya tsagaitar da hawayen idanunshi, ya kirayi sunan Allah nutsuwa ta zo mishi, cikin lallashi da kwantar da murya yace "yaki Nuratu!” Jikina in banda tsuma ba abinda yake, hankalina ya tashi, tsigar jikina gabadaya suka tashi. Na soma rokon Allah ya dau raina da wannan abin da nake ji. Na roki Allah ya dau raina kafin furucinsu ya zama gaskiya. Na ja jiki na rarrafa gaban Malam Ali, hawaye ko dis basu diga daga idanuna. Lallai ne da ake ce wani tashin hankalin yafi gaban kuka. Idan ya tabbata cikin ne da gaske a jikina, ni Nuratu yaya zanyi da rayuwata? Cikin zuri'armu kaf, babu wanda ya taBa yin wannan abin kunyar. Abar ma ta kunyar duniya mai sauki, to kunyar lahira fa, da tsaywa gaban Sarki Allah! Sai a lokacin al'amarina da Sa'idu ya soma dawomin tar-tar. Tamkar wadda ta warke daga shafewar kwakwalwa (lose of memory). Shin ya aka yi ma har na bari hakan ta faru da ni? Ya aka yi na bari soyayyar Sa'idu ta rufe min ido har hakan ta faru? Ni Nuratu na yi asara! Haka Sa'idu ya cuce ni!! Duk wata soyayya da nake masa na nemeta na rasa. A karo na farko na ji na tsaneshi, na tsani kaina na kuma tsani soyayya a rayuwata. Malam Ali ya lura na koma kamar mutum mutumi, ya tabbatarwa kansa ni kaina bansan cikin ne dani ba. Dubu da Rakiya duka sun hada tagumi, sai gumi ne yake yanko musu. Yaya Rabi kuwa kuka take kashirBan, irin wanda ban taBa ganin ta yi ba a rayuwarta, har kuwa lokacinda aka anar da ita rasuwar mahiafin mu, kuma ba abinda zai sa, ba abinda zai rage. Ba abinda yafi damunsu a lokacin kamar mutuncin Malam Ali a idanun jama'ar Gwarzo. Ba karamin abun kalubale bane a ce haka ta faru a cikin gidan sa. Malam Ali shahararren malamin Alqur'ani ne, da babu ya shi a garin Gwarzo, haka halayensa da tsoron Allah irinnasa, sun zamo ababen koyi ga duk wani da ya kwana ya tashi a Gwarzo. Su kenan. Ni kuwa tunani na ai rayuwata bata da sauran amfani; 'ya mace nike, wadda wannan tabon bazai taBa goge mata ba, har 'ya'ya da jikoki. Maganar tunanin aure da Sa'idu ma kwata kwata bana yinta, na shafe ta kamar yadda ake shafe mataccen abu a doron kasa. Yo wane aure kuma bayan abinda ake yiwa auren an gama samunsa a titi! Mutunci ya zube, ganin GIRMAN juna YA FADI! Sai a sannan ne na samu wasu hawaye dunkulallu, suka mirgino a kundukukina. Na kai bayan hannu na ina sharewa, a yayin da dan cikina ya shiga wutsil-wutisl! Cikin koshin lafiya, da tuna min yana jin yunwa. Na runtse ido da karfi, wai ni Nuratu ce yau zan haifi SHEGE! Wannan tunanin kadai ya kusa sani in fita a hankalina. Cikin tattausar murya Malam Ali yace "Nuratu cikin jikin ki na wane ne?” Babu musu, babu ja’in’ja, babu jinkirtawa nace "wallahi Malam, Sa'idu ne!". Sai ganin Yaya Rabi mukayi ta yanke jiki ta fadi. Malam ya fita da gudunsa ya debo ruwa yayi bisimillah ya shiga yayyafa mata. Tun daga ranar ta koma wata shiri-shiri, ba mai hankali ba, ba taBaBBiya ba. Kullum sambatu ta ke da Sa'idu, da cin amanar da ya yi mata, da take cewa har abada ba zata yafe masa ba! Tun daga ranar ko nan da can ban kara lekawa ba. Bayan kunyar Malam Ali da sauran mutane, ina jin kunyar Ubangiji na. Abinci sai Dubu tasa ni a gaba da fada kamar ta duke ni, sannan zanci kamar ina taunar madaci. Fassara halin da zuciyata ke ciki ma a wannan lokacin ba zai yiwu ba. Dubu ce ta tsaya tsayin daka wurin ganin cewar na dage da yin istigfari, da kuma Innalillahi… domin samun gafara wurin Ubangiji da sauki acikin kwakwalwata. Ban taBa ganin kishiya irin Inna Dubu ba, har inda nan ke motsi. Zuciyarta me kyau ce, kudurinta na alkairi ne ga kowa. Itace tace abar maganar nan a tsakanin su. Babu maganar zubar da ciki, domin ya shiga wata na shidda, kuma malam Ali yace ko da wata daya ne, shi bazai zubar da halittar Ubangiji ba, da bai ji ba bai gani ba. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Data farfado ne ta fara kuka, ta laluboni ta rungumeni tace "'yar ikon Allah kenan, Allah yasa kece jarrabawa ta karshe da zamu gani cikn zur'armu, Nuratu kam bata kyauta ba, to amma ta tuba taga isharori iri-iri a kanki, sannan kuma wannan al'amari ba yinta bane, kaddarar Allah ce. Mu nan Musulmi ne masu imani da yarda da kaddara don haka bamu bambance ki da sauran jikokinmu duka daya kuke. Allah yayi miki albarka Allah ya sanyaya miki zuciyr ki, Allah ya baki hakuri. Mantawa nayi da al'amarin data bamu labarinsa tun dawowarta, shiyasa nayi tunanin abokan adawa ne suka kulla mata sharri. Ashe ni ina zaune da jinina tsawon sati biyu rashin ido bai sani na gane ba. Sau tari na kanji kamar muryar Nuratu cikin gidan ashe diyarta ce, kai amma (Mon amour) anyi sauna da bai gane ta ba". Ashe yana tsaye a bakin kofar shigowa falon ya tokare hannunsa na dama da kofar yana murmushi yace “wa yace maki ban ganeta ba? Dalilina na takurawa da nacewa ta biyoni ai sabida dan fashin dana ji ya fasa ‘raping’ dinta saboda kamanninta da Gwamna Mainasara….." gaba daya suka hada baki “'yan fashi? Menene kuma raping?" Ya yi musu bayani dalla-dalla suka yi salati ni ko don kunya sai na ruga daki da gudu wurin Haiti diyar Aunty Habbani, da zamuyi tsara da ita, ina gaya mata shi Yaya Qassim baya jin kunyar tsofaffin nan. Daga can fa lo suka ce "shi yasa ake ce ka shuka alkairi, a ko'ina zaka tsinci abinka. Alkairin Nuratu ga al'ummarta, bazai bari a taBa tozarta jininta a duniya ba". Ranar da aka yi addu'ar bakwai ne Alhaji Aliyu Mainasara, Alhaji Kamilu Mainsara, Adam Mainasara, Shettima Mainasara, da mijin mahaifiyata Senator Alhaji Kabiru Bedeggi, wadanda suke masu fada aji ga iyalin Mainasara suka keBe mu ni da ita, daga ni har ita kamar surukai muke, ba mai iya kallon dan uwansa cikin ido sai satar kallon juna kasa-kasa. Nafi sakewa da Hibbani, kome nake son gaya mata sai dai in gayawa Hibbanin ta gaya mata, gashi a ranar ne zata koma can kasar Chadi in da take aure. Haiti kuma zata koma makaranta a Kuala Lampur (Malaysia) dama tazo hutu ne al'amarin ya ritsa da ita. Ita kadai ce budurwa don tace duka tsarrakinta a family dinmu anyi musu aure, itama da sanya ranarta akanta da masoyinta Ahmad yana aiki a Abidjan, watanni biyu ya rage ta kare karatunta ayi bikinsu, cikin kwanaki bakwai ita ta yi min bayanin kowa cikin zuri'ar da matsayinsa gareni. Ita Aunty Hibbani diya ce ga wan Baban Nuratu Alhaji Aliyu Mainasara kuma itace mahaifiyarta. Ta ce mu anan family dinsu tun daga kan labarin Aunty Nuratu, ba'a aje budurwa sama da shekaru sha shidda ba'a yi mata aure ba, nima don ban samu mijin da wuri ba ne, har Baba yace wai sadaka zai bada ni, sai kuma ranan na raka Aunty Nuratu taro Abidjan muka hadu da Ahmed, ma’aikaci ne a ‘airport’ muka kulla. Ada ta ce bata yarda ba wai bare ne, sai dai a hadani da Qassim, shi kuwa yace ko sama da kasa zata hade ba zai aure ni ba". Na ce “me yayi zafi, duk kyannan naki Haiti?” Ta ce “uhm Yaya Zaynab, kece baki san Qassim ba, bai aje kansa anan kusa ba, kema wallahi ba karamin mamaki nake ba da naga yana shiga shirginki, amma kafin ni 'yammata biyar cikin family dinnan duk yaki su, wasu kwailaye yake kallon mu, rannan yace cikin mu har yanzu ba'a haifi matarshi ba”. Dariya nayi sosai. Na ce “ya akai shi kadai naji yana turanci sosai a cikin ku?” Ta ce “oh! Qassim bai yi karatu anan ba, dukkan karatunsa na (Criminlogy) yayi shi a Jami’ar Dundee, U.K”. Jiya da daddare daya leko yi min sai da safe, ni da ita munyi shirin kwanciya muna addu'o’I, tayi murmushi ta dauko filo ta aza a karkashin kanta tace "Allah na lura kamar Qassim na sonki" cikin rashin kulawa nace “don me kikayi tunanin hakan?” Ta ce "his actions…..baki ji an ce idan kada kare na sunsunar takalmi dauka zai yi ba?" Nace "to ki ma bar wannan tunanin, babu wannan cikin rayuwata, duk wani abu da zai sa a binciko mun wannan usulin ina gudun shi ina nesantar shi Haiti…" Idnuna suka ciko da kwalla, duk da munyi ‘light-up’ taga kyallin su cikin idanuna, ta mike ta kunna fitila dakin ya gauraye da haske. Ta dubeni sosai ta ce "in har kuwa zaki cigaba dasa wannan tunanin a zuciyarki, kina tare da Bacin rai kullum. Ki manta da komi ki dauki komai ‘as a bygone’ ki fuskanci sabuwar rayuwar kwanciyar hankali da kika samu kanki a ciki Yaya Zaynab, bazaki dauwama haka ba, dole zakiyi aure ko kinso ko kin ki za'ayi miki bada jimawa ba, in har ke jinin Mainasara ce. Idan har da gaske ne abinda kike gudu kenan, to ki auri Qasim, shine ya da ce da rayuwarki, tunda dan uwanki ne na jini, wanda ba zai taBa goranta miki abinda kike gudu ba, haka duk danginsa. Mu tsintsiyane a madauri daya, da wuya kiji an samu saBanin ra'ayi cikin zuri'ar mu, tunannin su daya, zuciyarsu daya, haka kowa na jin dan uwanshi a cikin jikinshi. Qassim is the right man for you; shine wanda zai rike ki kamar kina a gaban mahaifiyarki, ba tare da ya kaiki inda za'a taBa goranta miki ba, tunda abinda kike gudu kenan, haka zai yi duk iya kokarinsa wurin kare miki martaba da mutuncinki a idon kowa, ko don sabida kaunar dake tsakanin shi da mahaifiyar ki. Baki sani ba, a hannunshi ya daukoki ya kawo ki har gadonta tun daga Damagaran, a sume, bakisan in da kanki yake ba. Yace koda wannan shine aiki na karshe da zai gabatar a rayuwarsa, sai cika maki burinki". Na ce "amma ai a jirgi? Ta ce "eh, a jirgi”. Na yi murmushi nace "to menene abin wahalar anan? Akwai wanda yayi shekaru goma sha takwas yana kaunata, duk da a san ko ni WA CECE? Bai taBa furta min ba, ba don komai ba sai don gujewa rayuwata shiga cikin garari idan na gane matsayina. A sanda na gane ni din wace ce, ya tsaya mani, ya gaya mani cewa koda daga sama na fado he'll continue standing by me, ina kuma da yaqinin abinda ya fadi, haka yake har zuciyar shi. Domin ya nuna min na gani a zahiri”. Ta ce "don Allah waye wannan?” Na yi murmushi, tare da jin wani sabon abu da ya dunkule min a zuci, ya hanani sukuni, game da Ya Faruq. Na kai hannu na latsa makunnin fitilar dake jikin gadon fitilu koraye suka maye gurbi masu haske, na ja bargo na rufe har kaina saboda raBar A/C dake ratsa kasusuwana nace "sai da safe Haiti". Ire-iren hirarrakin da muke da Haiti kenan, gashi a yau zata tafi ta barni da kewa, daga ni sai Nuratun da ko gaisheta bana iya yi, don haka kewar tafiyar su ta addabeni, ta hanani sikit, hakanne yasa da Babannin suka keBe mu a falo, ni da Nuratu, duka raina a jagule yake. Ita kanta na lura bata son tafiyar tasu sai don ba yadda zata yi ne tunda kowannen su zai koma dakin mijin sa/bakin aikinsa tare da iyalansa. Alhaji Aliyu yace “to Nuratu mu zamu wuce, sai mu kara addu’a mu kara Istigfari, wannan wata ishara ce Ubangiji Subhana ya nuna mana, Allah ya jikan Yaya Sani”. Ta share bawayen idonta da kyakkyawan hankicinta, ciki-ciki ta amsa da ‘ameen'. Ya cigaba da cewa "ku kwantar da hankalinku, ke Zaynabu kin zo gida, cikin dangin mahaifiyarki inda ake kaunarta, don haka ko shegu dubu ta haifa ba zamu juya masu baya ba, zamu kaunace su kamar su Haiti, wannan tsakaninta da Rabbil Izzati ne. Sannan ke muna rokonki da ki yafe mata, kiyi mata sassauci ki zamo mai afuwa, ki barta da bakin-cikin da kika kunsa mata. Alas! Ba rikicin sisaya yanzu, Zaynabu ta rabashi, sai ki zauna agida, ki huta, ki cigaba da biyayyar aure, dama mun yanke shawarar bazaki cigaba da kujerar ki ba, su mutane ne suke son ki da hakan, amma Kabiru zai nema a madadinki (mijinta) tunda shima 'tenure’ dinsa a Sanator ya kare daga wannan shekarar. Allah yasa hakan shine mafi alkairi”. Alhaji Badeggi ya amsa "Zaynabu feel free with us, ki saki jikinki da mu, ki dadukeni tamkar Alhaji Sa'idu, inada ‘ya’ya nima don haka nasan ciwon haihuwa, don haka na yiwa Allah godiya daya karo mana da ke rana daya. Na dade ina shawartar mahafiyarki da mu dauko ki, tana ki, sabida a lokacin tana kan kujerarta kinsan yanayi na siyasa mai cike da abokan adawa da bin kwakkwafi. Nida mahaifiyarki kauna ce mai tsabta da yarda da juna a tsakaninmu. Don haka ki dauki kanki tamkar diyar cikina, kada ki kara tunanin wai ke daban ce cikin al'umma, babu wanda ya fi wani, sai wanda ya fi tsoron Allah. Ina fatan daga rana irin ta yau, ba zan sake jin wata kalma wai ita ke "shegiya ce" daga bakin ki ba". Na share hawayena na ce "insha Allahu Baba bazan sake ba" ya ja doguwar addu'a muka shafa, aka rufe taron da raha da dariya. Nasa kai zan fita sai naji Alhaji Aliyu na cewa "Ya kamata mu nemo shi V.C Sa'idu, don yasan tana hannun mu ko hankalinsu ya kwanta”. Mun raka su Haiti filin jirgin saman Yamai (Mano-Dayak) inda zasu tashi zuwa Chadi. Sai da muka ga tashinsu muka dawo ni da Qassim wanda ke jan motar. Muna tafe shiru, babu wanda yayi magana har muka iso unguwar mu inda ‘estate’ din Mainasara yake watau (Plateux), anan ne ya rage gudun motar yayinda hankalina ke ga tsari da kyawun anguwar plateux, na kare nace "da alama babu anguwa mai kyawun wannan a Yamai" ya ce "eh, ai shugaban kasarmu ma a cikinta yake, shima jini ne ga Mainasara. Zaman anguwar mun gaje shi ne tun iyaye da kakanni, kuma a kalla mu muka cinye rabinta, kinga tun daga farkon ‘estate’ dinnan har zuwa karshen sa, gidajen Kangiwa ne" na ce “amma me yasa kuka fi son Damagaram?” Ya yi murmushi yace "kowa ya bar gida…. Zaynab. Duk cikin Niger babu inda nikeso irin Damagaram, donnhaka ne ma zabi da inyi aiki tare da gwamnatinsu, waddannan gyatuman da kika gani duk daga can suke, don ke suka zo, matasa-matsan ke zuane a nan domin itace (capital territory) namu, akwai wadatar (infra-stuructures) fiye da ko'ina. Mijin Aunty Nuratu, Alhaji Badaggi, Sanator ne na Damagaram a nan, don haka ne rabin rayuwarta na nan, ko a sanda take gwamniyar mu. Data sauka kuma kwata-kwata sai ta dawo nan gabadaya, amma duk da haka duk karshen wata tana Damagaran”. Hirarrakin da muke ta yi kenan har muka kawo gida. Tana tsaye a jikin madubin dogon yaro tana kulla sarka a wuyanta, na murda kofar dakin na shiga da sallama. Ta cikin madubin take kallona bata juyo ba, tace "har kun dawo? Jirigin nasu ya tashi?” Kaina a sadde na amsa da "eh" tace "zo nan ki daura min sarkar wuyana” na karasa na amshin sarkar ina sanya mata. Ta cikin mudubin na gane ashe tsawon mu daya, illa ita ta fini kauri da murzajjen jiki. Na sanya mata sarkar na juya zan fito daga dakin, har na kawo bakin kofa ta ce "Zaynabu me zakiyi yanzu?” Nasa hannu na dauke hawayen da suke cike min ido, batare data gani ba, na ce "sallah zan yi" ta ce “to in kinyi sallar kizo kiyi mun kitso, ai kin iya ko?” Na girgiza kai da sauri na ce "a’ah ban iya ba". Daga haka nasa kai na fita. Dakin da muke kwana ni da Haiti, wanda a yanzu ya zamo na kwanana ni daya wanda ke daura da nata na nufa, a bakin gado na zauna. Na kifa kaina cikin tafukana soma girza kuka. Na yi kuka har naji babu dadi tamkar zuciyata ta fashe. Wai uwar data haifeni ne wannan, amma kwakkwarar magana wannan ba zamu iya yi a junan mu ba. Wasu tausasan hannuwa naji sun rungumeni tsan-tsan, dumammun hawaye na sauka a gadon bayana. Na yi hamzarin dagowa na dubeta, Nuratu ce. Nayi wata irin ajiyar zuciya mai karfi, wata rahmah ta sauka a zuciyata, nima na rungumeta sosai mukayi ta kukan mu tare, kuka maras dalili, maras tushe, illa na huce takaicin da zuciya ke ciki, da kuma matsananciyar kauna irin ta da da mahaifi da bazaka iya ganin dayan cikin damuwa ka iya jurewa ba. Akalla mun dauki mitiuna goma a hakan, kamin ta ce cikin sanyin murya "Zaynab kin yafe mani?” Na mike tsaye a hankali na bata baya. Na isa ga taga ina kallon kifayen da ke watsalniya cikin akwatin ‘aquarium’ dake kudu maso gabas na dakin. Tunanin Inna na ya dawo mani. Na bude idanuwa sosai na kalli irin rayuwar daular da take ciki. Girman gidanta da alatun dake cikinsa, fadansa sai ya zama kauyanci. Motocin hawanta da gwalagwalai ba zasu lissafu ba, fadin abinda ta mallaka da nau'in rayuwarta, abu ne da ba zai taBa yiwuba, illa ince samanta da kasanta, hagunta da damanta duka arziki ne. Duk da haka tana sane da irin rayuwar data baro Innata, a cikin karkara, dai-dai da rana daya bata taBa tunanin ya dace ta nemeta ba, ko bata rabi ni'imar da take ciki ba, taji a wane hali take bayan halin kuncin da ta barota cikin shekaru goma sha takwas! A tsayin shekarunnan tsammani take Nuratu na wani wuri daban, Nuratu na cikin mummunan yanayi. Nuratu na cike da kewarta. Har ta dangana da kushewarta hakanne a zuciyarta Allah Sarki! A yau ni na gano mata saBani ga tunaninta. Nuratu ‘have already broke a new ground’ ta manta da ita, ta manta da iskar data debota balle Dan tayin shegen data barota da shi; ya rayu ko ya mace? Idan ya rayu wace irin rayuwa yake ciki? Wannan ba damuwarta bane tunda kuwa ita ta tsira da nata mutuncin, tana nan tana zuba mulki su kuwa ko oho…..! Na shiga girgiza kai da karfi, hawaye na fita min tarara. Ta taso a hankali idanunta jike da hawaye, ta karaso gareni, na bata baya ne don haka ta yi amfani da hannunta daya soma kyarma ta juyo da ni gareta, "wanna na nufin… na nufin baki yafe mini ba Zaynabu Abu. Na rantse da Allah abinda kike tunani ba haka yake ba, labarin mai tsaho ne dana san babu wanda ya taBa gaya miki. Zan kaiki Paris ki sayi duk abinda kike so…. Zan bude miki (account) da duk abinda na mallaka …. Zan cigaba da kula da rayuwarki muddin rayuwata….. zan maido maki farin-cikin da baki samu ba shekaru goma sha takwas a gabadayan tsayin rayuwarki. Zan tsaya tsayin-daka domin inganta rayuwarki da abokin rayuwa nagari… A bayan raina kadai, wani zai kiraki ‘shegiya’ Zaynab…." Na dago idanuna daketa ambaliyar da hawaye, na yi mata duban tsaf. Mace har mace, data baiwa arba'in baya. Amma tana magana irin ta yaran goye. “Baki da arzikin da zaki saye dattin ki dake raina. Ban taso cikin talauci ba, cikin rufin asiri na taso. Ban taBa kwana da yunwa ba, a tun bayan da kika hana mani nononki. Malam Ali yana da shanu, na sha daga nononsu na rayu har na kawo yau. Nayi dogayen kafafun dana zo na nemeki dasu. Banzo nan don rashin sutura ba, da zaki kaini Paris din ki saya mani. Ko da nazo ba tsumma bane a jikina, kaya ne irin na 'ya'yan gata. Baki da farin-cikin da zaki bani, domin dubun ki sun sadaukar da rayuwarsu domin farin-cikina. Wa yace dake rayuwa nayi cikin kunci? Saboda kin gudo kin barni domin tsira da siyasar ki? Kina kyashin in sha nononki, sabida ni shegiya ce? A gidan Ubana na rayu, wanda sanin ta hanyar daya samar dani, bai sa ya guje ni ba, maimakon haka sai ya tsaya tsayin-daka domin ganin hakan bai takaita rayuwata ba. Ya jani a ciki iyalinsa, duk da dattin dake jikina. Tun ban san kina ba ya mallakamin duk abinda ya mallaka. Ban zo gareki domin raBar inuwar arzikin ki ba, sai don daukar fansa. To amma zuciyar musulunci da kaunar iyaye, ya canza manufata zuwa ta alkhairi agareki. Tunda kika haifeni kika dire, kin kara waiwayana? Kin kara komawa don ganin wace irin rayuwa nake yi? Sannan yanzu don kinganni rana daya, a matsayin cikakkar mutum kice wai zaki kula da ni? To wace irin kulawa? Kashi zaki wanke mini ko tumbidi zaki share mini? Maganar zaki tsaya don ganin ba’a kirani shegiya ba, kin taBa jin an sakewa tuwo suna….???” Kallona kawai take cike da mamaki, dimuwa da ta'ajjibi. Don bata zaci ina magana haka ba. Ta kai dan yatsanta ta saitin kirjinta ta nuna kanta tace “ni kike gayawa haka Zaynab?” Na sunkuyar da kai, ina share hawaye nace "kiyi hakuri, idan maganganuna sun miki ciwo. Ina amayar miki da abinda yake tamkar guba ne a cikin raina. Idan na barshi sai ya kassara ni, in kuma ci gaba da kallonki da shi. Ina kara gaya miki baki da kudin da zaki wanke dattinki da ke raina." Zuciyarta ta karye, jikinta ya mace murus, “ki saurare ni Zaynab, tsayin mintuna goma sha biyar, in gaya miki gaskiyar abinda kike zargi, wanda ba haka bane…" na girgiza kai da sauri "baki da kalmar da zaki gaya mini in yarda kina kaunar Innata yadda take ka unarki. Da kina kaunarta, wallahi da ba kiyi shekaru goma sha takwas bata san inda kike ba, alhalin kina da masaniyar bazata taBa samun kwanciyar hankali akan hakan ba, da baki bari bakin cikin ki ya kaita kabarinta ba…." cikin shesshekar kuka tace "Waye ya gaya miki bansan halin da kuke ciki ba? Waye ya gaya miki bansan a gidan Sa'idu kika taso ba? Waye ya gaya miki ban san har soyayya kun yi da Imran ba?" Nayi hanzarin dagowa na dubeta a rikice, tayi murmushi ta juya min baya tace "Zaynabu ke nan, you are still a baby ina jin sai na sake haifarki. Ina Umar Faruq, ina Imran ina Babanki…..?" Na bude baki hangangan ina kallonta, ta yi murmushi tace "ki rufe bakin kada kuda ya fada” sai na yi murmushin da ban shirya ba, ta sake mamakantar dani da cewa "ina 'yan uwan ki Iftihal da Azizah?” Na kai hannuna duka biyu na rufe baki ina dariya "kina yin maganganu wadanda suke bani tsoro". Ta lakuce min baki tare da kama fatan kunnena ta ja ta da karfi kamar zata tsinke min shi, nayi ‘yar kara bata saki ba tace "kamar yadda kudina ba zasu sayi dattin dake ranki ba, haka zasuyi min amfani ta hanyar samomin labarinki keda Ya Rabi. Abinda yasa ba zanyi fushi dake akan maganganun da kika yaBa min ba, don nasa kina a cikin zargi ne. Sannan na gane kina da hankali, kina kuma kaunar mai kaunarki. Wallahi-wallahi Zaynab, baki fini son Ya Rabi ba". Ta juya da sauri zuwa dakinta, jim kadan ta dawo rike da wata 'yar batta da na soma tunanin ina na san ta? Ta fiddo abinda ke ciki, haskensu ya dallare min ido, na soma kif-kiftawa. Idan har ba gizo idanuwana ke mun ba, sarkar da Baba Sa'idu ya bani ce, shekaru takwas a baya ta dutsen Sapphire, dana baiwa Ya Faruq ajiya. Tana murmushi ta ce “ungo kayanki mai Uban dake sonta. Ba wannan ne abinda ya mallaka mikin ba, tun kina firamare? Ki tambayi wanda kika baiwa ajiyar, kafin ki bashi wannan ajiyar, nawa aka bashi?" Wannan na nufin; Ya Faruq na tareda mahafiyata a duk tsawon shekarunnan? Ya san inda take, kuma ta hanyarsa ne take samun labarina, kai! Nuratu zata fasa mun kai…. Na kai hannu na dafe kaina da ya soma sarawa tamkar ya rabe gida biyu, ni ban karbi sarkar daga hannunta ba, ita bata fasa mikomin ba, nace idanuna a runtse "idan ba so kike kaina ya tsage ba, ki fidda ni duhun da kike sanya ni". Ta kamo ni ta rungume tana dariya tace "ba ke kikace bazaki saurare ni ba? Zaynab ya zan haifeki, kiyi tunanin bana sonki, alhalin soyayyace mai tsanani ta kaimu ga aikata hakan nida mahaifinki, tunda an hanamu aure karfi da yaji, sai kuma sharrin shaidan da bin son zuciya. Shin ko kin san Sa'a, ina nufin matar Sa'idu?" “Ni kuwa na santa". Ta runtse idonta a hankali cikin tunanin al'amarin daya faru shekaru ishirin da biyar a baya, a yau ya shiga dawo mata tar-tar kamar a majigi. Taja hannuna muka koma bakin gadon muka zauna, ta dubeni tayi murmushi ta dauke siraran hawayen da suka cika mata ido da kyawawan yatsunta, yayin da kaunar Uwata ya cigaba da bunkasa a zuciyata, na kasa cigaba da jurar ganin hawayen da take fitaswa, a hankali na matsa na kwantar da kaina a cinyoyinta. Sai naji tamkar Innata. Tana share min hawayen da yatsunta ta soma…… KAUYEN GWARZO (1970) LABARIN NURATU. Kamar yadda kika sani, ko kuma kika fahimta Zaynab mu haifaffun kasar Nijar ne, cikin garin Damagaram. Zaman mu anan Yamai ya samo asali ne tun daga lokacin da Kakana Mainasara Kangiwa ya lashe kujerar shugabancin kasar Nijer. A lokacin su mahaifinmu basu da wayo, su biyar ne 'ya'yansa kuma duk in gansu. Aliyu, Adam, Shettima, Kamilu, da mahaifinmu mai rasuwa. Hajiya Azzo da kika sauka a gurinta kanwarsa ce, cikin su daya, ita ta haifi Hibbani Babar Haiti. Qasim ba danta ba ne, jikanta ne, tunda kuwa da ne ga Baba Aliyu mai bin mahaifinmu. Zamanta tare dashi ya samo asali ne tun daga wajen haihuwa, da mahaifiyarsa ta mutu ta barshi, ita ta daukeshi ta raine shi, har ya zamo tamkar da a gareta. Tun Kangiwa yana da rai ya shaci wannan filin wanda daga baya ya zamo anguwar plateux dinnan da muke ciki, ya assasa ginin wannan ‘estate’ yayiwa su mahaifin mu aure a ciki, wanda aka cigaba da canza ginin yadda zai tafi da zamani har kawo na yau da kika gani, wanda duk fadin kasar Nijar, an tabbata babu gini kamar namu, domin duk bayan shekaru uku magina daga kasar China suke kara sabunta ginin da sabon nau'I na zamani. Wannan gidan da nake ciki shine kason mahaifinmu, wanda ya zamo gadon mu ni da Ya Rabi. Bayan rasuwar Kangiwa, dukkansu sunci gaba da harkar siyasa daban-daban, mahaifinmu ne kadai yafi bada karfi ga kasuwancin fata, wanda ya amshe shi sosai kuma Allah ya sanya mishi Albarka a ciki. Yana fitar da fatar rakuma da sauran dabbobi zuwa masana'antun kasar China da Thailand, daga baya kuma har Nigeria saboda suma akwai sana'ar kayan fata, inda ya san manyan mutane da yawa a Kano ta wannna hanyar. Duk cikin matan Kakanmu, Yadudu Babar mahaifinmu kadai Allah ya yiwa tsawon rai, tazo nan kin ganta, itace tsohuwar data dake ki da sanda, domin inda akwai wanda tafi so duk cikin zuri'arta to ni ce. Wannan ya samo asali ne da kaunar da take yiwa mahaifinmu. Inada shekaru biyar mahaifiyarmu ta rasu ta bar mahaifinmu ta sanadiyar ciwon kansar nono (breast cancer). An ce mahaifin mu hauka ne kadai bai yi ba, saida 'yan uwanshi suka tafi dashi Saudiyyah suka yi tayi masa addu'a, da taimakon su da taimakon Allah ya koma dai-dai, saboda yadda yake kaunar mahaifiyarmu. To bayan rasuwarta sai ya dauki dukkan kaunar nan ya daura akan mu nida ‘yar uwata. Haka ya shafe shekaru biyar bai kara aure ba yanata harkar fatarsa, mu kuma muna hannun Yadudu a Damagaran, inda a can ne Ya Rabi ta gamu da lalurarta ta shafar aljannu, a lokacin kam mahaifinmu ya bunkasa ya tara arziki sosai. Akwai wata rijiya ta Man fetur da Kangiwa ya gadar masu tun yana raye, tana nan a Damagaram, kinsan yanayin kasar mu (sahara) don haka mallakar rijiyar man fetur a cikin kasar nan ba karamin abu bane. Shi kansa Kangiwa an ce ba'a san ta ina ya hako wannan rijiyar ba, kawai an wayi gari ne an ganshi da ita (just a mirage). Ko da akazo rabon gado bayan rasuwar Kangiwa, mahaifinmu shi ya mallaki wannan rijiyar shi daya, bai karbi ko kwandala na daga dukiyar mahaifin su ba. Banda wannan gidan da muke ciki komi ya tafi ga su Baba Shettima. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Kishingide yake a falon alfarma na Baffa Aliyu wanda ke daura da gidan Nuratu. An cika gabanshi da kayan marmari dana ciye-ciye da tsotse-tsotse. A gefe cinyar rakumi ce aka gashe aka kyafe masa ita sai naso take da tashin tiriri. Ga wukar yanka da cokali mai yatsu an soke a jiki, suna hirarsu da Aliyu da Shettima muka yi sallama a tare. Duk da GIRMA daya soma samunshi, da furfura tsilla-tsilla a cikin kanshi, still yananan a BABA SA'IDUna dana sani; Baki ingarman gaske, ma’abocin gargasa, gagara-gasa a cikin maza. Fi-sauran Babanni ( kamar yadda marigayiya Innata ta rada mishi). Ya dago fararen idanunsa ya dube ni, sai na fadi ragwaf, akan gwiwoyina domin sun kasa daukata. Saboda wani irin GIRMA da kwarjini da yayi min, koko ince, Allah ya rigaya yayi masa. Baba Sa'idu dashen Allah ne kuma murucin kan dutse, abin nufi, Allah ya rigaya ya tsayar da shi, babu wanda ya isa/ba abinda ya isa ya FADAR dashi, yayi masa haiba da nasibobi da dama. Irin wadannan mutanen tsiraru ne, a cikin al’ummah. Yayi murmushi yana nunawa Baba Shettima ni da dan alin sa, yace “ZAYNABU kenan, KYAUTAR ALLAH, KYAUTAR INNA RABI, ABUN FARUQ, ABUN BABA SA'ID, BABBAR MACE, MAI BABBAN AL'AMARI! Suka yi dariya sosai ya ce "Allah ba da wasa ba Shettima, Zaynabu tana da babban al'amari irin na NURATU! Ni na gaya maka nan gaba Zaynab wata ce, sai ta zama ZAYNAB MAINASARA…..!!” Da gudu na runtuma na rungume Babana, ina kuka yana sharemin hawaye da hannunsa, ni ke neman afuwar, amma maimakon yayi afuwar, sai tawa afuwar yake nema. Su Iftihal sai suka zama 'yan kallon kauna irin ta da da mahaifi. Ashe ‘YAYA DUKA ‘YA’YA NE, amma abin a zuci GIRMA-GIRMA NE……!!! *** *** *** A ‘family meeting’ din da aka gabatar, wanda dukkan Kangiwa sun halarta. Malam Ali, Alhaji Sa'idu, Nuratu, Azumi, Alhaji Badeggi, Faruq, Imran da Inna Dubu, gami da Yaya Halima, itace kadai mai kananan shekaru a dakin taron bayan su Ya Im. Bayan tattauna duk abinda ya dace, an nemi afuwar juna. Nuratu da Sa'idu sun yi afuwa ga junansu. Imran ya sunkuyar da kai yace "akwai sako daga mahaifiyata ga Nuratu da Baba Sa'idu”. Nuratu da Sa'idun ne kuwa suka juyo suka dube shi. Ya lumshe ido ya cije lebbansa masu sulbi, yana mai kawar da dubanshi daga idanun Nuratu masu kaifi kamar reza, ya mayar ga mahaifinsa, ya ce "Hajiya tace ku yafe mata, domin wai itace silar duk abinda ya faru da rayuwarku data Zaynab, amma baku da kaico!” Falon ya dauki tsit, Inna Dubu tace "ka bude baki kayi magana sosai yadda ta fadi maka”. Yayi ajiyar zuciya yace "A cewarta, sanda Baba yazo mata da maganar auren sa da Nuratu, hankalinta ya tashi sosai, saboda ta san Abba baya sonta, saboda darajar malam kawai ya aureta, yake kuma zaune da ita. A tunaninta muddin ya auri zabin sa, ita kuma tata ta kare, wulakantata zai yi, ko kuma ta kari rayuwarta a zaman boranci, saboda irin tanadin da yake yiwa Nuratu ba kadan bane. Da farko ta dauki Nuratu yarinya karama kuma 'yar kauye mara wayo, ta dauka idan tayi mata barazana kawai zata hakura ta ji tsoro ta fasa auren Abban, sai taga Nuratu da Inna ko a jikinsu. Shima Abban babu abinda ya fasa na shirye-shiryen aurensa da Nuratu. Saboda haka ne ta tafi garinsu can Gombe, a wani kauye, Kumo, ta sami wani hatsabibin malami ta yi masa bayanin matsalarta na a lalata maganar auren Nuratu. Malamin yayi duba yayi mata bayanin cewa yayi bincike yaga akwai rantsatstsen rabo a tsakaninsu. Don haka tayi hakuri ayi auren, in yaso sai su san yadda zasu lalata auren daga baya. Ita kuwa tace da ta ga auren Abba da Nuratu, gara taga karshen rayuwarta. Malamin ya ce to akwai mafita guda daya, zai iya yi musu asirin da zasu haife duk wani rabo dake tsakanin su a titi, daga nan kuma babu maganar aure, zai cusa matsananciyar kiyayyar junansu a zuciyoyinsu. Bata taba sanin cewa Zaynab diyar Abba bace sai ranar da ya fadi musu da bakin shi dukkansu a asibiti. Lokacin ana cuku-cukun fidda shi kasar Jamus. Tun daga lokacin data yanke jiki ta fadI, ta samu (stroke) wanda har yanzu tana nan a kwance”. Ya yi shiru yana maida numfashi a hankali, idanunsa sun kada sun yi jawur. Duk cikar falon an ransa mai magana. Ba Nuratun ba, ba Sa'idun ba, kowanne ya fada a tafkin tunanin al'amarin da ya faru dashi, shekaru goma sha takwas a baya. Sai kuma tausayin junansu ya zo ya lullube su, idanuwan su suka kada suka yi jawur, tsohuwar soyayya ta soma tashi, dama ance wai ita soyayyah, bata tsufa, duk GIRMA, sai dai masoyan su tsufa. Wannan haka yake. Amma Allah bai kaddari suna da rabon aure a tsakanin su ba. Ko sun yafe din ko basu yafe ba Allah masani. *** *** *** A taro na gaba. Nuratu ta mike kokon bararta ga Sa'idu, na nemawa kaninta Faruq auren diyarsa, Aliyu Mainasara ya nemawa nasa dan Qassim auren diyarsa Azeezah, sannan shima Baban ya nemawa Imran dinsa auren Haiti. Jin haka Badeggi shima yace ba za'a barshi a baya ba. Ya matso ya zauna gaban Sa'idu, yace “BABA SA'IDU nima ina yiwa Abdulhakim, kamun Iftihal, yana Parisa, jibi-jibinnan zai dawo a hada shi". Gabadaya falon aka sa dariyar aminci, yarda da GIRMAMA juna. *** *** *** Biki yayi biki! Sha'ani yayi sha'ani!! Ba'a Damagaram ba ba’a Yamai (Niamey) ba, ba Sokoto Birnin Shehu ba, har Gwarzo ta Jihar Kano, inda anan akayi kamun amaren cikin dakin Inna Rabi. Angwaye da Amare sun gaji tulis, har sun soma tunanin shafe wasu ‘acitvities’ don su samu hutu da amarensu da Nuratu ta babbake ta hana masu ko da jin kamshin su. Haiti 'yar hutu tuni ta fara ciwon baya. Azeezah kuwa kullum kara fiddo sababbin ‘programmes’ take wanda zai yi dai-dai da irin burinta, ga mijin Allah ya bata a hannu sai yadda tayi da shi, bai san irin wannan hayaniyar ba, sannan an bashi wata irin mata 'yar giggiwa, mai shirin maida shi waina a tanda. Iftihal da Abdulhakim ko sai shukurah, komai nasu yayi dai-dai. Abdulhakim Kabiru Badeggi (Managin Director na Nuratu's World) watau shagunan Nuratu dake birinin Paris, mutum ne nutsatstse mai sassaukar rayuwa, komai nasa yayi dai-dai da Iftihal wadda dama ita babu karya da nuna isa acikin al'amarinta. To ga Haiti da Imrananta sai ince kusan burin Imran ya cika, na auren farar mace, ba'abziniyar usli mai jinni a jika wadda tafi Zaynab hasken fata da murjewar jiki, kai kace tocilan ce a cikin duhu, sai dai fa kowanne na jin kansa, ita tana jira a fara neman soyayyarta, shi yana jira azo a tsuguna ana lallashinsa tabdi! Baka san Haiti ba malam, don haka in ma mafarki kake ka farka, ko kuwa a dawwama a hakan. A Sokoto ne Faruq ya kira wayar Zaynab yace "kina ina ne? Am almost, nearly to die Zaynab, na gaji, na gaji da wannan takunkumin na Mamie, rabon da in ganki fa tun kafin a daura aure, in ba so kike in mutu ba sai ki ta biye mata. Ita Haiti da yake tana da wayo ba gashi nan ba ta san yadda tayi ta fito ba suka fice da Imran, sannan Azizah da Qassim gasu can cikin lambun Abba kin zauna kullum kina biyewa kauyancin Iftihal" murmushi ta yi mai fidda sauti, “kai Ya Faruq, ba mun gaisa ba ranar daurin aure, ni yanzu dilke ake yi min" ya ce “in ma dinke ki ake ki taso kizo nan dakin Imran, I seriously want to tell you something, Allah ko in shigo ciki in jawo ki wallahi” ta dinga dariya ta ce "to bismillah, ai ga Aunty Hibbani nan itace ma take min dilkan, ga kuma Mamie da Mama nan a bakin kofar shigowa" ya dinga jan tsaki, tsut-tsut a kai-akai yayi cilli da wayar. Ya suri hularshi bisa ‘centre-table’ din Imran yayi cikin gidan fuuuu… kamar guguwa. Da gaske take Mamie da Hajiya Azumi ne a bakin kofar. Don haka daya hango su sai ya rage taku ya koma cikin nutsuwar shi. Ya duka ya kwashi gaisuwa suka bashi hanya ya wuce ba tare da tambayar shi komai ba, hakan ba karamin dadi yayi mishi ba da bai san amsar da zai bayar ba, abinda ya sani kawai shine yan tsananin son ganin matarsa inda hali, har ya ji duminta cikin jikinshi whatever the case! Kai tsaye yasa kai dakin Mama, da gaske dilkan Hibbani ke mata daga ita sai daurin kirji, ya zauna dab da ita yana fuskantar Aunty Hibbani wadda sam bata ji shigowar shi ba ta dukufa tana aikinta tukuru, na lailaya da kalailaitar fatar jikin ‘yarta, sallamar ma a ciki yayi masu, ita Zaynab din dake fuskantar kofar shigowa itace kadai taga shigowarshi, don haka Hibbani sai ganin shi kawai tayi a gabanta kamin ya soma kokarin cire riga. Ya ce “nima ayi mun dilkan, ai nima, ango ne!" Hibbani tayi salati ta yar da wanda ta kunso a hannunta ta mike ta fice tana cewa “ban san baka da kunya ba Faruq sai yau". Duk da abin ya bata dariya amma ta sha mur ta ce “haba don Allah Ya Faruq, zuwa fa zatayi ta gayawa su Mamie…." wani kallo daya watso mata, ba shiri ta kama bakinta ta dinke. Duk da dilkan dake jikinta da karnin danyen kwai da ba’a kai ga wankewa ba. Haka ya tarairairayo kayarshi yana sakin wata irin ajiyar zuciya mai karfi, tare da cigaba da abinda yake ganin shine kadai kwanciyar hankalinsa, cikin ranshi yana yiwa Allah mai girma, godiya mara iyaka. Hibbani ta fito tana ta fada, ta ce "kun san Allah ku ba yarannan matan su hakannan, bikin nan na menene? Tun ana abu cikin marmari ana dariya har ya gundire su. Duk hakuri da kawaici irin na Faruq yau kun kureshi yayi muku keke da keke. To wallahi in baso kuke a maida su mata cikin dakunan ku ba, akan idanun ku, to yau dinnan ku lullube matansu ku kai masu". Hajiya Azumi ta iso bakin kofar tana kwankwasawa da yatsunta, amma bata shigo ba, tace “Faruq” ya ce "shigo mana Mama, dilkan da Hibbani ta ki karasa mata nake karasa mata" ta ce “to hakan yayi kyau, amma fito in shiryota in kawo maka ita gabadayanta yanzunnan”. Daga shi har Zaynab suka sa dariya yace da ita cikin rada "kin ga ai na yi mana maganinsu" ya dago murya yace “Allah Mama ki shigo, ko kwarzane ban yiwa 'yar ki ba, hira kawai muke yi” ta ce "wai ina wasa da kai ne? Nace ka fito ko?” Ya fito yana murmushi, ta daddage ta zuba mishi rankwashi a tsakar ka ta ce "bace min da gani, mara kunyar banza" sai da ya kai bakin kofa ya juyo yayi mata gwalo. Tuni Nuratu ta bace a sama. *** *** *** Acikin gidan-gonar Zaynab da ke garin Gwarzo, walima ce ta musamman Zaynab ta hada musu su takwas kacal. Tana sanye da fararen ‘wedding gown’ dogaye har suna jan kasa, tayi lullubi da farin ‘net’ amarya dai sosai sai walkiya take ta inda duk ta juya, ta matsa jikin bishiyar ‘guava’ ta aje ‘yar karamar (automatic video camera). Bata kai ga dagowa ba Faruq ya karaso ya kwantar da kanshi a bayanta, yace I luv u Zaynab". Qassim ya sakar masu flash din Camera a hakan. Imran dake zaune can gefe kan wani dutse, Haiti na zaune daga gefen kafafunshi, tana yi mishi jan yatsu a hankali, suka juya suna hango abinda ake yi, wato irin soyayyar da ake zubawa tsakanin Zaynab da Faruq dinta, ya lumshe ido yana murmushi yace "kin ga inda ake soyayya can, ba irin tamu ba" ta harareshi, cikin wata siga mai jan hankali tace “au daga gareni ne ma?” Ya dirgo daga kan dutsen ya kwantar da kai a kafafunta, ya rintse ido yace “na yarda daga gareni ne, amman nima daga yau na daina Haiti I luv u, I luv u more than I can say. Don Allah mu rike amanar juna. Ba soyayyah ce ta hadamu ba, iyaye ne, daga baya kauna ta hadamu, in sha Allah bazamu taba ganin ba dai-dai ba a rayuwar auren mu". “Ya Im! Ya Im!!” Zaynab ce ke kira daga nesa, cikin siririyar muryarta "ka taho gashi na yi ‘serving’ dinka” ya ce “to Zaynab dina”. Ya kama hannun Haiti suka nufi inda suke. Makekiyar ledar cin abinci ce aka shinfida, aka shaketa da ‘warmers’, sunkin ‘foil-papers’ da tangarayen abinci. Manyan ‘picinic-coolers’ suma shake suke da nau'i-nau’in kayan abin sha masu dan karen sanyi. A gefe tirkeken rago ne guda aka gashe. Yana tsaye jikin karfe cikin ramin da ake gasa shi sai naso yake ya gasu yayi lugub, mai so sai ya je ya yanko iya yadda yake so ya ci. Suka soma cin abincin suna nishadI, aka ci aka sha akayi hani'an. Ko kafin su gama duhun dare ya fara shigowa, wato an kirayi sallar maghriba. Suka matsa ga (pipe) din da ake ban ruwan shukoki suka dauro alawala. Faruq ya ja su jam'in sallar magriba, sukayi addu'a ta musamman akansu, domin neman zaman lafiya a tsakaninsu da zuri'ar da zasu haifa a gaba. Ko kafin su shafa Inna dubu ta aiko Halima ta kwaso mata amaren za’a kaisu gidajen mazajensu. Faruq da Zaynab suka ce da Halima, ta gayawa Inna Dubu su a cikin gidan gonar-nan zasu kwana cikin (Hut), wato irin bukkar nan ta zamani, da ake yi cikin gidan-gona, tuni sun sa an sanya masu dindimemiyar katifa, gobe zasu tafi nasu gidan da kansu. Halima ta kama baki, cikin dimuwa. Ya daga mata gira yana murmushi yace "Yes, muna son kafa tarihi ne!”. Ta ce “to Allah ya tashe mu lafiya". Ta juya tabi bayan su Imran. Har ta kusan tadda su sai ta dawo, ta kamo hannun Zaynab ta jata gefe tace “sai kin yi hakuri da Faruq, don na sha gaya miki yana matukar son ki. Wannan rubabben son na shekaru goma sha takwas, duk a yau zai nuna miki shi. Kiyi dauriya ki kiyi juriya ki zama mace tagari Zaynab, kuma in gaya miki Imran ya cika alkawarin da ya daukar min. Bamba goma sha biyu, suna nan ya bani na kai miki dakinki”. Dariya tayi cikin annashuwa, hasken farin wata na kara haskaka kwalliyar amarcinta. Tace “Yaya Halima bani da kalmar da zan gode miki". Ya karaso cikin kaguwa ya kasa kunne yace “wai gulmar me ake yi ne? in ji dai ba gulmata bace. Ke Yaya Halima dadi na dake in baki ki kulla nunkufurci ba bakya jin dadi ('yar mace, da dan namji suke)”. Ta harareshi, ta juya tana cewa "kai nan har ka isa in nunkufurceka? Sai dai in maka kan mai uwa da wabi" (ta zuge Zaynab taki yarda da shi). Yana dariya ya sakalo Zaynab suka shige bukkarsu. *** *** *** Duk wata rawar jiki da karkarwarshi, ZAYNAB ta fishi. Duk wata zakuwa da nuna zalamarshi, ZAYNAB ta fishi. Duk wani kokarinsa da jarumtakarsa da kyar ya iya ya gamsheta. Halittarta na daga cikin halittar matan da turance ake kira ‘nymphomaniac’. To amma shima ai namijin gaske ne. Yayi mamaki amma yai shukurah ga Allah abisa halin da ya risketa. Ya rungumeta sosai tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, hasken farin wata da alfijir daya soma kokarin ketowa, ya haskaka mishi kayatacciyar fuskarta, yace cikin shauki “Zaynab are you O.K?” Gyada mishi kai kawai tayi, kamin wasu irin hawaye su mirgino su jika kundukukinta. Tana fatan Allah ya dorar da soyayyarsu da rayuwar su da Faruq cikin GIRMA da daukaka kamar yadda ta faro. Shi kuwa addu'a yake Allah ya bashi tsawon rai, karfi da lafiyar da zai cigaba da iyawa bukatar gangar jikin ZAYNAB, har zuwa ranar da suka daina numfashi. *** GIRMA YA TASHI! SHEKARU ASHIRIN A GABA. Zaynab Mainasara, na daya daga cikn jami'an majalisar dinkin duniya (United Nations) dake wakiltar Nijeriya, sannan (member) ce a kungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Africa ta yamma da aka fi sani da (ECOWAS). Gabadayan karatun ta har zuwa digiri na kololuwa, ta yi shi ne akan tattalin arziki (Economics) daga Jami'ar Porstsmouth, U.K. Danta na farko data haifa tun a shekarunsu na biyu da aure (Aliyu) ta bada shi ga Mamie Nuratu tun daga shekarun yaye. Ta yi masa aure da Sa'adatu diyar Haiti da Imran, yana da shekaru goma sha takwas. Ta aurar da Rabi'a tun tana da shekaru goma sha hudu, ta aurar da Nuratu (Mamie) tana da shekaru sha biyar. A nan gaba kadan tana shirin aurar da Halima (Dubu), da kanwarta Hibbani, wadanda ke aji uku na sakandire. Sai dan autanta Sa’id, mai kimanin shekaru goma a duniya. Na daga jaridar (New-Nigeria), mai dauke da kanun labaran bikin cikar su shekaru ishirin da aure. Ban taBa ganin fuskokin mata da miji da suka dace da juna irin ZAYNAB da FARUQ ba. A kasan hoton an rubuta “an extraordinary lady, ZAYNAB MAINASARA, in celebrating her 20th wedding anniversary” da aka yi a Niamey, cikin wannan shekarar. Duk da irin runguma mai cike da kauna da maigidanta yayi mata, cikin hoton, tana kuma murmushi, akwai wasu dunkulallun hawaye cikin fararen idanunta. Na samu kaina da maimaita lakabin da akayi mata watau ‘extraordinary’, kwarai sunan ya dace da ita. Ban taBa ganin mace mai ban mamaki irin Zaynab Mainasara ba; mijin da Allah ya nufe ta da samu, dukiyar da Allah ya hore mata, ilimin da Allah ya bata, da daukakar da yayi mata cikin kasar mu mai dinbin albarka, bai goge Bacin ran dake cikin zuciyarta ba, bai shafe Boyayyen bakin cikin dake boye cikin kwayar idanunta ba. Masha Allahu lakuwwata Illa Billah! Masoyana a duk inda kuke cikin duniya, wadanda na sani, da wadanda ban sani ba, na gode da yabo da fatan alkairin da kuke yi min. Kamar Zaynab, nima nake cewa ; "Da fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa!" [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: A kasuwancin fatar shi ya tara duk abinda yau nake da shi, ko in ce muke dashi nida marigayiya Innarki. Duk wannan arziki da Allah ya keta buda masa, hankalinsa ba’a kwance yake ba saboda larurar Ya Rabi, da wani lokaci zasu nannadeta kamar alkaki ko su hana hannaye da kafafunta motsawa. Aka dukufa neman magani har Tumbuktu, Morocco, Mali da Mouritania. Amma mayun sunki rabuwa da ita, ko sun tafi kwana biyu sais u dawo. Mahaifinmu yana da dadadden burin yin Gwamna a Damagaran, ba don komai ba sai don ya kara fito da jiharsa ta tserewa sauran jihohin mu, don haka a dai –dai wannan lokacin ya kacame cikin hayaniyar siyasa Allah kuma ya bashi jama'a magoya baya kamar me, domin al'umma Nijar bakidaya sun yaba da shugabancin Kakanmu Kangiwa, don haka ne duk wani da ya fito takara daga tsatson Mainasara nan da nan yake lashewa, sai dai in bai tsaya ba. Su kance “Mainasara ba don sata kuke mulki ba, sai don kishin mu”. Ana sauran watanni ukku zaBen, a irin tafiye-tafiyen da yake cikin Nigeria, ya jiyo labari Malam Ali Mai Almajirai ta hanyar wani dan kasuwar fata mazaunin garin Kano, shine ya bashi labarin irin wahalar da yake yi na nemawa Rabi magani, inda shi kuma yayi mai hanyar Malam Ali, ya je suka gana yace ya je ya zao mai da Rabin. Da fari Yadudu taki aminewa, inda ta ce sai dai shi Malamin ya biyoshi wato a daukoshi yayi mata maganin a can gidanta, inda ya nuna mata Malam Ali ba malamin ciwon hauka bane kawai makiyayi ne mai nasibobi daga Allah, baya karBar ladar aiki sai sadaka, itama ba ko yaushe ba. Ni kuwa nace kafata kafar 'yar uwa ta, don haka ne mahaifinmu ya dauko mu mu biyu kacal ya taho da mu Kano ta jirgi, muka yi a kalla sati biyu gidan Malam Ali ana yiwa Ya Rabi magani, muna kwana dakin Innar Faruq wato Inna Dubu. A lokacin Faruq bai fi shekaru biyar ba, inda ni kuma nake da goma sha biyu, Yaya Rabi sha biyar. Allah cikin ikonsa yaba Malam Ali sa'a ya rabata dasu cikin 'yan satittika, muka soma shirin tahowa. Lokacin da Babanmu ya tambayi Malam Ali me zai bashi ladar aikinsa? Budar bakina sai cewa ya yi, ya aura masa Rabi, baya karBar ladar aiki sai sadaka. Baban mu bai duba yanayin rayuwar karkara ta malam Ali ba, ko wadata ko waninsu, illa tunanin ya zai yi dani idan ya rabani da 'yar uwata? Alhalin ko barci baya rabamu. Yana tuntuBar Ya Rabi ga mamakinsa sai ta amince farat daya, ni kuwa nace kafata kafar 'yar uwata. Haka ya aurawa Malam Ali Ya Rabi, akan sadaki kalilan. Damuwar sa shine, me zai ce da Yadudu da su Baba Aliyu? Da wannan damuwar ya hawo jirgi, kwata-kwata baya cikin nutsuwarsa, akan hanya ne Allah ya aiko a jalinsa, jirgin su ya kife, babu wanda ya tsira a cikin jirgin. Malam Ali ya samu labarin hatsarin a radio. Hankalin sa ya tashi, don bai san kowa namu ba, sun rabu ne akan bayan zabe zai dawo tare da dangin mu su ga inda take, nikuma su tafi dani in cigaba da makaranta. Ya yiwa mahaifinmu addu'a sosai tare da alkarwarta ma ransa rike mu amana. Shi da bakinsa rannan yace bai tunkari mahaifinmu da neman auren Rabi haka kai tsaye ba, saida ya kwana uku yana Sallah yana rokon Allah a kansu shi da Rabin. Don haka da yaji rasuwar mahaifinmu ya kara kafe Rabi a cikin gidansa kar ta gudu, domin ba karamin so yake yi mata ba. Sai kuma Allah ya hada jinin Rabi da Faruq, kullum yana dakinmu, tare da shi muke zuwa makarantar boko shi yana aji uku ni ina aji biyar. Haka in mun dawo muna tare muke daukar karatun allo sai dai shi ya wuceni nesa ba kusa ba a karatun allo saboda inada tangarda a harshe, har rige-rigen wanke allo muke yi, inda ni kuma na yi masa fintinkau a makarantar boko saboda na samu tushe mai kyau a makaranta mai tsada a Damagaram. Innar Faruq mutuniyar kikice, bata dauki Rabi a matsayin kishiya ba sai kanwa, domin a haife ta haifeta. Rabi shekarunta goma sha biyar kacal a lokacin. Wannan sai Goggo Rakiya (kishin). Sunan da Faruq ke kirana dashi a lokacin shine (Nuratu-mai-dogon-gashi), ni kuwa ince Faruq dan dukurkusu), don ni na fisi tsayi sosai, haka nake kama hannunshi mu tafi makaranta ko in daura hannu a tsakiyar kanshi in tasa shi a gaba, shi kuwa haushin hakan yake ji, domin shi a lallai sa'a na ne, bayan shekaru bakwai rigis na bashi. Idan na dora hannu a kafadunsa sai ya ture, shi sai dai mu jera, bayan kuma rabi na ne. Akwai wani daki a soron gidan Malam, da kullum yake a rufe, tunda muka zo gidan ban taBa ganin an budeshi ba har na kammala karamar sakandire, da yake makarantar kwana nake yi a Garko wato (Garko Science) ban san Sa'idu a gidan yake ba, kuma wannan dakin nasa ne, ban kuma san sanda suka shaku da Ya Rabi ba fiye da Faruq, ya zamanto hatta kwanon sa a dakin Rabi yake, kuma da yake yana da cutar gyambon ciki (ulcer) sai take tsaye sosai akan abincinshi. Rabi ita ce uwar dakin Sa'idu, wanda yake almajiri ne ga Malam, kuma Malam ya sanya shi a makarantar boko cikin Kano, sanda yake zuwa gidan sau tari ina makaranta. Rabi na son Sa'idu sosai fiye da duk 'ya'yan rikon dake gidan da sauran almajiran Malam, har ta kai ta kawo duk wani sirrin shi da Rabi yake yi, idan zai koma makarantar haka take kulla 'yan canjinta ta bashi, haka ko daga can makarantar yana aikowa ta aika masa da abinda yake so ko ta karBa a wurin Malam ta bayar akai masa. Rannan shiryawa tayi ta tafi Bindawa zaman makoki, wai Baban Sa'idunta ne ya mutu. Lokacin da Sa'idun zai zana jarrabawar tafiya kasar waje. Rabi bata yi barci ba, kwana take sallah da addu'ar Allah yaba Sa'idunta sa'a. Har bashi take ci wurin Goggon Dubu ta baiwa Sa'id yayi hidimar karatunsu, inta dauki adashinta ta biyata. Sanda ya soma daukar alawus daga kwalejin horas da malamai ta jihar Kano sai ya sayo mata keken dinki da gabadayan kudin ta soma dinki, amma wallahi duk abinda ta samu a dinkin a wani katon banki take tarawa, idan na tambayeta me zatai da kudin da take ta tarawa a banki, sai tace gudunmawa take tarawa Sa'idu in yazo yin aure. Amincin dake tsakanin Rabi da Sa'idu ba zan iya kwatantashi ba. Ta daukeshi tamkar dan data haifa a cikinta, shi kuma ya dauketa da muhimmancin uwar sa. A haka ya tafi Turai ya soma karatu, amma duk sanda ya samu dama sai ya yo mata aike ita da Malam. Zuwansa hutu na farko daga Turai ma ina makaranta, sai tangamemen hotona a dakin Rabi. Ya dade yana kallon hoton yace "amma nan baki fi shekaru goma sha bakwai ba, aka dauki hoton ko Innata?” Ta yi dariya har taba uku lada, tace "yanzu da gaske Sa'idu baka san kanwarka, Nuratu ba?” Ya cika da mamaki ya ce "itace ta zama budurwa haka? Lallai girman 'ya mace, ba wuya, ba kwanakin baya-bayannan nake ganinta ta kama hannun Faruq sun tafi makarantar firamare ba?” Tace "eh to, gatannan ko yanzu akayi mata aure, gobe zata haihu”. Ya dade yana kallon hoton, cikin wani sabon yanayi atare dashi ya ce "Inna Rabi, Nuratu kyakkyawa ce”. Ta yi murmushi tace “don ma baka ganta tana shekaru biyar ba, sai kace 'yar tsanar roba ce. Da bakin mutane na kama Nuratu, da bata kawo yanzu ba. Hatta kank nin yaro Faruq ya kance Nuratu mai dogon gashi, duk garin nan babu mai kyanta. Da bata fini tsawo ba da na aure ta" suka yi ta dariya. Bai tafi ba sai da ya jona mata kan ‘telephone’ a dakinta domin su rinka gaisawa, ta kuma rika jin halin da yake ciki. Haka ya koma cike da tunanina a ransa. Da na dawo gida na tarar Ya Rabi tayi kan telephone, na cika da mamaki, kafin na kama tambayar dalilin da zai sa Malam yayi haka, wato ya sanya mata bai sanyawa Inna Dubu ba, ya yi dariya yace “bani bane na sanya mata, danta Sa'idu ne”. Ba tun yau nake jin sunan Sa'idu a gidan ba, to amma ban zaci yayi girman da har zai sayi telphone ba, a wancan lokacin kam ba karamin mutun ne zai sanya kan telphone a gidansa ba, sai ya zamanto har makotanmu masu mu'amala da birni, kanzo cin aziki dakin mu, har numbar suke badawa a bugo musu, in je in kira su suzo su amsa. To nima sai na sahiga karbar lambar kawayena na makaranta da suke a nesa, muna gaisawa. Rannan Ya Rabi ta shiga wanka, ni kuma ina sharce kaina dana wanke. (Telfon) ta shiga kira, tayi har ta tsinke ban dauka ba, ina cigaba da abinda nake mai kiran dai bai hakura ba, ya sake kira a karo na biyu, wannan karon ma sai data kusa tsinkewa kamin in aje kum din in amsa da "sallamu alaikum, mai telphone din ce ta shiga wanka" yayi dariya yace "hala kece Nuratu?” Na cika da mamaki bance komai ba, ya sake cewa "ko ba Nuratu bace, Nuratu mai dogon gashi?” Na yi murmushi nace "hala kaine Sa'idun dake England?” Ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi yace "na dade da son jin muryar Nuratu, na dade da son ganin Nuratu a zahiri. Ban zaci muryar Nuratu yayi taushin haka ba, ban zaci ajin Nuratu ya kai har haka ba, ashe Nuratun classic babe ne? Irin wannan JAN AJI haka?” Ban san sanda nayi murmushi mai sauti ba, nace "ina wuni Yaya Sa'idu, yaya sanyin England?” Yace "Sanyin nata har ya kai sanyin muryar Nuratu?” Nikam ban saba jin irin wannan maganganun ba, don haka na ji duk na takura, don ni ban taBa tsayawa wai in saurari wani saurayi ba, tunda nake, ko irin malaman mu na makaranta da ke cewa suna sona, kara nake kaisu a koresu, don a ganina ai iskanci ne ace ana son ka. Don haka da Sa'idu ke min wadannan maganganun da basu dace da wadanda na saba ji a bakin mutane ba, sai naga to me yayi zafi da zan takurawa kaina da cigaba da hira da shi? Na yi hanzarin cewa "ka sake kira in an jima kadan, lokacin ta fito". Ba kuma tare dana bashi damar kara cewa komai ba, na ajiye. Tun daga ranar ne kuma idan na lura Sa'idu ya kira Ya Rabi, sai in fita daga dakin in Buya a bandaki. Kiran duniyar nan zatayi min ba zan amsa ba, sai sun gama yayi mata sallama sai na shigo, ta ce “Sa'idu yana gaisheni, tayi ta kirana mu gaisa bata ganni ba”. In ce “ina amsawa”. Shi kuma ba yadda za’ai ya kira bai ce ta nemoni mu gaisa ba kamar maye. Kai tun bata ganewa da gangan nake fita, har ta gane, sai ta yi min dabara, ban sani ba. Da lokacin kiran nata da yake yi yayi, sai tace dani "au dazu kin fita ke da Halima, kawarki 'yar Hadejia ta yi kiranki, nace bakyanan amma bakiyi nisa ba, ta ce zata sake kira nan da rabin awa". Don haka na zauna bakin waya a kalla awa daya zaman jira kiran Maryam Hadejia, calssmate dina. Kiran yana shigowa kuwa na dauka babu ko sallama nace "shegiya Maryam, kina can mukus a Lagos abinki, kin bar mu da zafin Arewa" daga can Bangaren aka ce "ke kuma kina nan mukus a Gwarzo ba, wai Nuratu ashe daman baki da kirki?” Nayi murmushin gane mai Maganar, a shagwBe nace “kai Yaya Sa'id, amma ka shammace ni…” yace "in tambayeki Nuratu, samari nawa kike jawa aji, irin yadda kike ja min?” Na kyalkyace da dariya nace "Allah ni bani da wasu samari, ka tambaya Ya Rabi ma" ya ce “to don Allah, gani, ko nayi maki tsufa ne in aske furfurar?” Nayi dariya don ni maganarsa a wasa, na dauketa nace "lalle ma Yaya Sa'idu, zolayata kake yi, kai da kake can kana kallon masu jajayen kunnuwa da jan gashi, me zakaci da wata 'yar kuayen Gwarzo?” Yayi murmushi cikin nishadi yace "ai kema jajayen kunnuwan gareki. Allah Nuratu baki san irin aji mai matsayi da muhimmanci da na sakaki bane. A hoto kawai na ganki, kin hana mani barci. A tafe nake, a zaune, a tsaye ko a kwance, tunanin Nuratu nake, mafarkin kasancewarta matar aurena nake kowanne dare. Jiya ma ganinta na yi cikin barci na, rungume da 'yan tagwayena, mace da namiji, tana shayar dasu nono, baki gansu ba jawur dasu kamar Nuratu ………” na katse shi ina dariya da cewa "kai don Allah Yaya Sa'id?” Yace “Allah wallahi da gaske nake Mummy Nuratu" muka yi ta dariya kamar wasu shashashu, ya bini ya maida kansa yaro kamata muka yi tayi. Wallahi tun daga ranar na fara kaunar Sa'idu. Son sa da kaunarsa ya soma bin jinin jikina, domin yana daga cikin irin mazan da nake burin aure ta kowanne fanni. Ina son na auri namiji mara girman kai, karya da nuna isa, barkwanci da nuna kauna hakanan mai ilimi. To Sa'idu duk ya tattara wannan har ya zarta da wasu. Ban taBa ganin shi ba, a waya kawai na soma kaunarsa, a waya ya ginawa kansa babban matsayi a zuciyata da ni kaina ban san iyakarsa ba. A karshen shekarar ya zo hutu, a ranar na samu kaina da yin kwalliya, da ake kira kwalliya, irin wadda ban taBa yi ba. Na yiwa gashina gyara mai suna gyara, irin wanda bai taji ba. Na yiwa kumbana fenti da lalle jawur, kamar wata sabuwar amarya. Yaya Rahi sakin baki tayi galala! Tana kallona kamar a ranar ta fara ganina, ta ce "Nurtu haka kike da kyau kamar aljana? Shin ina zaki ne? Wannan kwalliyar bata dace ki yiwa kowa ba sai mijinki". Domin su kansu kayan jikina masu fidda sura ne, idan a Gwarzo ne ba za'a barni in yi dinkin ba, to Maryam kawata ta kawomin su daga Lagos a dinke, riga da siket ne ‘fitted’, na wani bakin yadi mai santsi da adon jajayen fulawoyi. Ita bata san don Sa'idu na yi wannan kwalliyar ba, don ko a mafarkinta bata kawo wai soyayya muke a waya ba, abinda ta dauka shine hira ce irin ta wa da kanwa, domin bana fadin abinda har zata digama ayar tambaya, shine dai yake ta aman soyayyarshi kamar wani Romeo, ni kuma ina kasancewa cikin nishadi. Na tabbatarwa kaina idan na yi sa'ar auren Sa'idu, na yi babbar sa'a, domin namiji ne mai masiffaffar soyayya da zai iya mai da kansa sakarai akan macen da yake so. Na kan kissimawa raina kamanninsa? Ko yaya yake? Dogo, gajere, baki, ko fari? Mai kiba ko siriri? Oho, koma wada ne, nidai ina son kayana haka, zan kuma cigaba da son shi muddin rayuwata. Sai kawai gashi tsaye tokare da kofar dakinmu, hannun sa daya a jikin kyaure, daya harde a bayansa. Baki ingarman gaske da a turance ake kira 'giant, yafi fadi daga kafadu sannan kafafunsa tsayayyu ne. Baki ne sosai da (weather) din kasar England ya maida ‘cool' kuma bakin shi bai Boye fararen idanunsa ba. A kiyasce yayi shekaru talatin da takwas, a yayin da ni kuma keda sha bakwai. Kenan tsiran mu ba kadan bane. Gashinan dai fes, kamar wankan inji, ban taBa ganin cikakken namiji mai haibar Sa'idu ba har yau. Dole duk wata lafiyayyar mace, tayiwa kanta sha'awar mallakarsa, ba-katsinen usuli, mai tsaka tsakin kyawun sura. Ni da shi tsayawa muka yi cirko-cirko, kamar zakaru muna kallon-kallo. Ba sai an gaya mani ba jikina ya bani he is the Sa'id I'm dreaming of. Ya saki kofar yana murmushi yace “idonki kenan Nuratu?” Na kai yatsuna da suka sha adon lalle, na rufe fuskata ina dariya, cikin wani irin nishadi da soyayya mai tsanani, ya karasa shigowa cikin dakin yayi ido hudu da Yaya Rabi, dake kwance tana sauraron rediyo bata lura da tsayin mintunan daya Bata a tsaye cikin kallon soyayya ba, ta yunkura ta mike ta ce “oyoyo Sa'idu na! Da akwai katon zani da zai goya min katon mutum kamar ka, yau da na goya ka." Ya shiga sosa keya cikin alamun sarakuta, yau kunya sosai yake nunawa ba kamar da ba, ita bata ma san yana yi ba, ta cigaba da oyoyonta. Inda duk ta mika hannu, sai ta zaro mai abin sawa a baka tana cewa "wannnan ma kai na ajiyewa, kaga gyadar nan yau satin ta guda da soya maka, na san ka da son gyada". Tana bada baya domin kawo mashi abinci, ya yi tsalle ya dawo gabana, a yayin da ni nake still a tsaye tamkar an kafeni da kusa, yace "this is not the kind of welcome I expect from you…" Na ja da baya ina dariya, na ce “wacce iri ka tsammana? Duk wannan adon da nayi domin ka?” Ya kuwa bini da ido ‘up to down' ya sauke su a yatsun dana rufe fuska da su, yace "eh, an yi mun kwalliya kam, to amma ai ba'a barni na gani sosai ba an kama an rufe fuskar" ya kai hanu ya sauke hannun daga fuskata, wani irin ‘shock’ daya sameni ya tunasar dani tunda na kawo haka, wani babban namiji bai taBa kama jikina ba. Ya sunkuyo da kuncinsa dai-dai bakina yace "c’mmon! Give me a welcome kiss…." numfashinsa da lallusar kamshin dake tashi jikinsa na dukan hanci na, ya tayar da tsigogin jikina gabadaya, nayi ta maza naja baya da karfi na bugu da bango ina fidda numfashi a wahale. A sannan ne Ya Rabi ta dawo dauke da tray data shako da kayan abinci nau'I-nau'I, yayi hamzarin amsarta yana ta jera mata sannu, nan ya nade hannun riga yana kwasar gara yana zuba santi, tare da gaya mata yadda yayi kewar abincinta. Duk yadda ya so mu keBe a ranar bai samu hakan ba, domin babu hanya. Ya Rabi tana dakin bata je ko'ina ba, to a wanne dalili? Haka ya wuni kame-kame, Nuratu in ga littafinki na makaranta? Nuratu naji Halima ta tsayar da Malam Harisu, ke kuma wa kike tsayar? Duk rabi Yaya Rabi ke bashi amsa, ni dai iyakata murmushi da daga kai, eh, a'ah. Tasa wani almajirin Malam ya share mashi daki, na shigar masa da jakunkunansa, da daddare kenan. Ina shirin fitowa ya tare min hanya "wai ni har yanzu ban ji inda kika sa gaba ba" na ce "nasa gaba kamar yaya?” Ya fizgoni jikinsa yace "that’s the kind of welcome I like". Ganin muna neman shiga wani limit, daya wuce tunanina, na kuma san ba dai-dai bane duk da wata irin duniyar dana tsinci kaina, na kwaci kaina da kyar na ce "a’uzubillah da kai Sa'idu. Kana mantawa nan ba Ingila bane, mu musulmi ne diyan musulmi, idan ka manta in tunasar da kai. Ban zanci a duk inda ka samu kanka, duk runtsi zaka yada tarbiyyar Malam ba. I really felt disappointed…" hawaye suka zubo min, na juya na fito na barshi kamar mara lafiya ko magana baya iya yi. Dana dawo daki na kwanta ina tunani, sai na rinka tambayar kaina anya Sa'idu yana kaunata? He didn’t seem a real lover, but an expert deciever, watau kwararren mayaudari ne kawai. Ban san mecece soyayya ta hakika ba, amma na sha jin kawayena na cewa, duk namijin dake taBa yariya a waje, ba aurenta zai yi ba, kuma ko ya auretan ba zatayi wata daraja a wurinsa sa ba. Na yi kuka na yi kuka amma na kasa yakice Sa'idu a raina, duk yadda na so yin hakan kuwa. Da safe suna gaisawa da Rabi ni ina shan koko, ko kallo bai isheni ba. Babu ko kunya ya badawa idonsa toka wai "Ya Rabi, me na yiwa yarinyar nan ne take ta hararata?” Ta dubeni na sadda kai ina mamakinsa, da tsinewa bature daya murje wa dan bahaushe kunya. Ta ce "haushi take ji kaki kunce jaka har yanzu ka miko mata tsarabarta”, haushin Ya Rabi ya kamani amma ban tofa masu ba, yayi murmushin daya kara masa kyau yace “ayya Nuratu - hasken al'umma, me kike ci na baka na tsiyaya? Ai ke tsarabarki ‘exraordinary’ ce, ba sai an bude jaka ba, jakarki daban ce, sukutum za’a miko miki ki bude abinki da kanki". Sa'idu yana da wata tafkekiyar gona, tana can a bayan gidan mu. Yana kiwon fararen dabbobi da shuke-shuken kayan marmari. Duk zuwan da yayi a can yake karar da yawancin lokutansa, haka duk dan abinda ya tara a gyaranta da kara ingantata yake tafiya. To balle yanzun da yaje ya karo ilimi kiwo irin na turawa ai san abin ya kara haBaka. Kullum zai fita tun safe yana can tare da ma'aikatan suna ta gyara gidan gonar, don haka in ya fita sai yamma lis zai dawo gidan. Don haka Rabi ta dauki nauyin aika masa abincin ranarsa can gidan gonar, kuma wani kuskure da tayi, a wuyana. Ta haka Sa'idu ya samu ya lallasheni da dadadan kalamai na yaudara, tareda yin amfani da masifaffen son da nake mishi ya wanke kansa daga wancan zargin da nayi masa a baya. Ya ce shi bai yi da wata manufa ba, is just to show me how much he is eager to see me. An ce so hana ganin laifi, tuni na yafe masa muka shimfida soyayyah mai korran ganyayyaki. Haka dana yi la'akari daga kasar da yake rayuwa sai nayi masa uzuri, nasan kuma soyayya ta kansa komai, kuma shi yana kokari ma sosai musaman ta fannin Ibada ina jinjina masa, dole kowanne Dan adam yana da ajizanci, kuma daga ranar koda wasa bai sake kwatawaba. Mukan wuni sur cikin gonar cikin fararen dabbobin nan, shi yana watsawa tantabaru gero, ni ina tusawa dokin sa abinci a baki, haka muke ta hidima da dabbobi da tsintsayen har sai rana tayi anyi sannan mu koma gida, da yake nima ina cikin hutu ne. Ya gaya min watanni uku zai yi ya koma amma kafinnan saida wata kwakkwarar magana a tsakanin mu, sai yaje yayi mun shirye-shiryen da suka dace kafin in zana jarrabawar WAEC ya dawo a daura mana aure ya tafi dani. Hakan kuwa aka yi, ya sanar da Malam Ali maganar mu, amma nauyi da jin kunya ya hanashi sanar da Ya Rabi wadda a lokacin ta soma zargin soyayya a tsakanin mu, ko yaro kankani ya dubi kwayar idanun Nuratu da Sa'idu, zaiyi shaidar zuzzurfar soyayya. Tunda Sa'idu ya tafi, sai na koma wata irin sukuku, gani nan mai lafiya, ba mai lafiya ba. Na koma yin komai ‘slowly’ na zamo ‘calm’, kamar mai ciwon sikila. Hoton Sa'idu cikin ‘snow’ da na sace cikin dakinsa ba tare da sanin sa ba, shine na mayar abokin barci na, kullum yana karkashin pillow, motsi kadan in jawo in kalli abina. Haka a daddafe na zana WAEC na kammala sakandire, sai zaman jiran dawowar abin kauna. A kullum ranar Allah sai mu share awa gauda muna hira a waya, ko tausayin aljihun sa baya yi shida yake dalibi, saidai ni inji tausayinsa in katse layin yadda ko ya kira ba zai shigo ba. Watanni suka shude suka zama shekara, na soma kidaya ranar zuwan Sa'idu, domin yace wannan karon bagatatan zai yi min ko ya kamani da saurayi na muna zance. Don haka ne tunda aka shiga watan 'December' na kasa tsaye na kasa zaune, a kullum sai na share dakin Sa’idu sau uku, lalle kuwa da yake yana son ganina da shi, kullum cikin tisawa nake. A kuma ranar wata laraba ne malam ya yiwa Yaya Rabi maganata da Sa'idu da yace da shi yana dawowa sai a daura auren, domin hatta gidan da zan zauna ya kama mani a can London, da visa ya samar min. Da daddare inata faman tisa lalle a kumbata, Rabi na zaune a gefena tana kame min kalbar data yi min da robar kyauro don kada ta warware, ta dubi lallena tayi dariya ta ce "su Nuratu manyan duniya, duk wannan lallen na tarbar zuwan maigidan ne?” Na cusa kaina a cikin rigarta, saboda matsananciyar kunyarta da naji, tace "a’ah ni cikani, kada ki karya ni banga auren naki ba. Amma Nuratu duk kwalisar nan taki, da yangar da kikewa samari, ki rasa inda zaki kare sai a mai mata?” Na wani irin zaro kaina daga jikinta cikin ‘slow motion’ nace "MATA? Wane ne mai matar?” Ta yi tsaki tace "kina nufin baki san Sa'idu yana auren Sa'a 'yar kanwar Dubu ba? Tana can Ingilan da yaronsu Imran kamar Faruq, a cikin gidannan aka yanka ragon sunan sa………" Na dora dukkan hannuwana aka na kwarara ihu, nace "Wayyo Allah! Wayyo Babana….." A take na fadi a wurin na suma. Wuni nayi bana cikin hayyacina, koda na farfado surutai kawai nake barkatai ina cewa "Sa'idu ka cuce ni…. ka yaudareni sai Allah ya saka mani……" Sai bude ido nayi na ganshi tsaye a kaina, rike da hannayena da suka yi sanyi kalau. Yana murmushi kamar a mafarki naji shi yana cewa "ban cuceki ba Nuratu, ban yaudareki ba. Yaya za'ayi in yaudari abinda nafi so fiye da rayuwata? Shine me, don inada mata, sai aka ce Allah ya haramta mani yin aure uku a gaba?” [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Na fiddo ido cikin kaduwa, ta yi murmushi ta girigiza kai cikin tabbatarwa, “Zaki iya tuna ranar da kika hawo Acaba daga makaranta? Motar da nake ciki tana biye dake, har kofar gidan. Imran da abokinsa suna tsaye jikin mota, da alama daga ke har shi ranku a Bace yake, don duk kuna ta hararar juna, kika shige cikin gida baki kula su ba. Sannan naje makarantar ku watarana inada daga cikin mota mai duhun gilassai, ina ganin ki da wata malama, Kabila, a zaune bisa benci a bayan ajin ku, kun dade kuna magana da bansan me kuke cewa ba kina ta kuka. Sai na ji hankalina ya tashi, don abinda na kawoma raina kawai Sa'a ce take takura miki. Na yi wa Faruq magana yace kwata-kwata ba haka bane, shima ya lura a kwanakin kina cikin damuwa, watakila sabida tafiyarshi Singapore ne. (Ni na samo mishi makarantar ba tare da sanin ku ba, ba don komi ba sai don jin Sa’idu ya samarwa dan shi aiki mai tsoka shi bai samu ba, to ashe gajen hakuri nayi, don ba’a fi sati uku a tsakani ba ya sanar dani shima nashi aikin ya fito a Bankin Nijeriya (central bank) a lokacin komi na tafiyar ya rigaya ya kammala, sai ya zabi tafiya karo karatun akan aikin) yace amma Hajiya Sa'a babu ruwanta da ke, sannan ne hankalina ya kwanta. Faruq kafin ya tafi Singapore ne ya zo Damagaram ta jirgi, na yi masa kyakkyawar tarba a gidana (Govt. House Damagaran), ya kawo min wadannan zobban naki na (Sepphire) da kika bashi ajiya, tsayin shekaru goma, yace “halin rai, komi na iya faruwa”, sai na ce “balle ma insha-Allahu zaka je ka dawo lafiya, sannan komai na Zaynab ai naka ne”. Na dade ina bashi takardun kadarorina da shares gami da takardun wani gida dana dade da saye a Paris, duk da sunanki. To duk ranar sai ya tattaro ya dawo min dasu, jikinsa a masifar sanyaye yake. Na ce "Faruq zaka tayar min da hankali. In hakane ka fasa tafiyar mana, ka kama aikinka?” Yace “nima dole ce zata sani tafiyarnan Yaya Nuratu, akwai dalilina na zaben karatun akan aikin. Al'amarin yana neman kwaBewa; ZAYNAB IS DEEPLY IN LOVE WITH IMRAN, and I cannot tolerate it". Nace saboda me?” Ya sunkuyar da kai cikin matsananciyar kunya da fidda rai, yace "don nima ina sonta". Nayi murmushi na ce “kawai kace Zaynabu ta kusan nemana da kafafunta, ta kusan biyoni mu zauna tare. Shine me don tana son Imran, ba dan uwanta ba ne?” Ya zazzaro ido yace “baki gane irin soyayyar da nake nufi ba, soyayyah, ta soyewa fa Zaynab kewa, Imran?” Na tuntsire da dariyar data kara kular da shi, nace “so what, wanene mahaukaci tsakanin Sa'idu da Malam? Ka kwantar da hankalinka, inshaAllahu Zaynab bata da miji sai Umar Faruq". Sai yayi murmushi. Na kuma cewa “ka yarda dani, am her mother, kwanannan zata biyo ni cikin tsana da kiyayya, and am ready to welcome her (a shirye nake da in karBeta) da duk wacce ta zo". Ya ce “ni nasan Zaynab bazata yi miki da dadi ba. Kuma tafi son Babanta a kanki, idan ta gane shine Babanta, bazata gujeshi ba, amma ke baki da uzurin da zata karBa, she is quite strict (me ra'ayin rikau ce) ba zata taBa karBarki a matsayin Uwa agareta ba…..” Na lumshe ido cikin jin zafin kalaman shi, na budesu a kanshi na ce "sai dai idan BANI NA HAIFE TA BA". Da wannan Faruq ya tafi". Ta yi shiru tana murmushi, nima murmushin nake kamar gonar auduga, cike nake da kunyarta kuma. Ta dago haBata tace "to Zaynabu 'yar Babanta, kin ji kowace ce Nuratun da kike zagi…. da gaske ne ba zaki taBa karBata a matsayin UWA a gareki ba….????” Nayi azama, na rungumeta, ita ma ta rungumeni, sai hawaye sharr! sharr!! Daga idanun kowannen mu. Na ce “ki bar fadin ina zaginki, waye zai zagi mahaifiyarsa? Sai mai nemawa kansa masifa. Na koyi wani abu ne daga Ya Im, na rashin Boye abinda ke cikin zuciyata, koda zai Batawa mutum, zan ji dadi idan na amayar da shi. Allah tun daga jin sunanki a bakin Innata, nake kaunar ki, nake begen in ganki…kawai ina yakar zuciyata ne da yin hakan, sabida haushin ki da nake ji akan Innata…" Na zame daga gefen gadon, na kwantar da kaina a cinyoyinta, gwiwoyina bisa kafafunta nace "ki yafe mini". Ta kai hannunta cikin lallausar sumar gashin kaina, tana shafawa a hankali ta ce "ya wuce Kyautar Inna, nima ki yafe mini, Allah ya yafe mana bakidaya”. BAYAN WATA DAYA Yadudu, Hajiya Azzo, Hibbani da Moiram matar Baffa Aliyu, suna zaune falon Nuratu suna tattaunawa akan tafiya sayayyar kayan auren Haiti da za'a tafi Singapore. Na fito daga daki rike da shaddodi guda biyu 'yan Mali, yellow da brown dinkakku dukka dinkin Mali na manyan riguna. Nace "Nuuratu wanne zan saka?” Ta dago ta dubeni tace “sanya wanda duk yayi miki, ai na Nuratunki ne". Hibbani tayi salati tace "wannan ba kayanki bane?" Yadudu ta muskuta ta ce "umh, Zaynabu me kika ce? Sunan Uwar taki kike fadi gatsar-gatsar?” Na juya daki da gudu ina dariya, in ajiyo Aunty Hibbani tana cewa "yanzu saboda Allah Nuratu kaya daya kuke sawa? Ai sai ku sa a samu a jarida, wannan ai tsiya ce" ta yi dariya tace "nayi-nayi ta bari taki dainawa". Na fito shar da ni cikin yellown shadda babban riga da zane da dan gyale. Wuyana da kunne na cikin ‘emirald’ rike da karamar jaka, na coge a bakin kofar dakin barci ban shigo cikin falon ba na yi kan-kan da ido, ina murmushi nace "Nuratu.., au Mamie…, yaushe zamu je ki sayo mini kayan?” Ba tare data juyo ta dubeni ba, tana fuskantar Hibbani, tace “sai ranar da nayi arziki, har yanzu bani da arzikin da zan saya maki kaya…." Na karaso da gudu na rungumeta nace “haba-haba Mamie, ni da ke bata Baci.. " Hibbani kallon mu take, muna burgeta, ta yi murmushi tace "kyaleta ki shirya tare dake zamu tafi Singapore, siyayyar kayan auren ‘yar uwarki, daga nan sai ki sawo duk duk abinda kike so" nayi tsalle na makalkaleta. Qassim ya shigo cikin shiri har da trolley dinsa, kamar hadin baki mun yi ankon yellown kaya, sai dai shi shet ce yellow da bakin wandon Jeans, idanunsa akaina ya dubi Mami yace "Aunty ni nayi harama, zan koma bakin aiki” tace "to Qassim, Allah hokku sa'a”. Ya dubeni yace "inye, su bera anyi kilin, to a zo a yi mun rakiya ‘airport’ mana? Irin wannan kwalliya bai kamata ki dankare a gida ba” nayi murmushi (tun ranar da muka fahimci ‘yar mace, da dan namiji muke, muke bugawa), ba don komi ba nake bude baki ina ramawa ba sai ma don kada zancen Haiti ya tabbata, wato ya furta min soyayyar da ya dade yana Boyewa. Gashi a yanzun ta gaza Boyuwa ta fito karara cikin fararen kwayar idanunsa. Na ce “ba dole in yi kilin ba, ko na dinga razana matar ka, tana nan-nan- da ni ba?” Haka muka fita muna tayi, suka bimu da kallo cikin jin dadi. Muna fita Yadudu ta soma furzar da abinda ke ranta, wanda ya taso da ita takanas tun daga Damagaram, wato burinta na a hada mu aure da Qassim, babban abinda ya faranta mata kuma shine fahimta da tayi yanzunnan muna son juna. Shiru tayi bata yi magana ba, amma su Hibbani suna ta sawa abin albarka. Muna bayan motar Nuratu Roll-Royce wadda (personally) ta hawanta ce ita kadai, ni da Qassim, sanyin raBa na ratsamu. Direban Mami na jan mu. Ya lumshe ido ya kwantar da kansa a bayan kujera cikin damuwa. Hasken hantsi yana haska bakin gashin kansa, wanda ke kwance lub, a wuyansa sai sheki yake kai ka ce ‘shampoo’ yake yi, amma wannan halitta ce. Qassim jajur yake fiye da ni, kamar ka taBa jini yayi tsartuwa, ga kuma yanayi irin na arzikin da hutu sai suka taru suka mai dashi kamar wani balaraben Kuwait. Ganin damuwar da yake ciki duk sai nima na ji na damu. Nace "yaya ne my Qassim?” Sai ya bude idanunsa da suka kankance, cikin mamaki yace “don Allah sake fadi, 'yar kanwalle?” Na harareshi nace "wannan ne kuma baka isa ba…" maganar ta makale a makoshina, ganin irin kallon da yake yi min cikin kwayar idanun shi, da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, jikina yayi sanyi, ya mace murus. Na sadda kai ina wasa da yatsun hannu na dana kawata da jan lalle, tun sanda na fahimci yana daga cikin abinda Mami ke ado da shi, yake kuma kara maida ta cikakkar mace, nima na dimance shi. Yayi murmushi yace "wannan (pretending) din naki, bashi zai hanani furta maki abinda bakya so in furata ba, Zaynab ina sonki, ina kaunar zamowarki abokiyar rayuwata a tun ranar da na fara haduwa dake, tun kuma kafin in ganki. I love you in your veil (na sonki cikin niqabinki) kuma na so ki yau a zahirin ki. Mene ne amsar ki? You are no more a child now (ke ba yarinya ba ce a yanzu) nasan tuntuni kin fuskanci inda nasa gaba, sai dai ban san dalilin da yasa kike basar da ni da gangan ba”. Na yi shiru banyi magana ba, a dai-dai lokacin da direban ya karya kan motar muka shiga cikin airport, ya tsare ni da ido cikin jiran amsa. Na bude murfin motar zan fita, ba tare da nasan amsar da zan bas hi ba, cikin wata rarraunar murya ya ce "May be am not good enough to be your husband)……” Na juyo cikin mamaki nace "me ya sa kace haka?” Jinin mu daya, tushen mu daya. Sannan kana da wani matsayi mai GIRMA a gareni, domin kayi mun abinda har in koma ga mahalicci na, bazan taba mantawa ba. Kai ne ka hada ni da mahaifiyata, kaine silar cikar farin cikin rayuwata, wanda ban taba tunanin zan tsinci kaina ba a tun barowata gida…." “akwai wani matsayi da zaki bani Zaynab, daya wuce na zama mijin ki?” Ya katseni. Na girigza kai “baka gane bana Yaya Qasim, ba zan taba yin auren soyayya ba…...” Idanuwansa sunyi nauyi sosai, da kyar yake iya bude su yace "….well-well, sai wane iri? Kodayake na gane; you are a multi-millonnaire, waiting for a billonnaire like you…. (ke miloniya ce, kina jiran biloniya dan uwanki), haka ne ko ba haka ne ba?” Ya tsatstsreni da idanunwasa da suka kada suka yi jawur. Na soma tababar ko Qassim ya sha kayan maye ne? Kai, babu kama, tunda nake a gidan su ko taba, sigari, ban taBa ganinshi da ita ba. Kenan soyayyar dake idanunshi ta bugar da shi babu mamaki. Na fita daga motar na barshi nan, na jingina da sassalkar motar cike da tunanin al'amuran rayuwa. Na mika tunanina ga kalamin Qassim, eh, nima na yarda a yanzun kam (billonnaire) ce. Ko daga motocin da aka mallakamin makullansu, ba'a maganar abin banza sarkokin (Gold). Duwarwatsun ado na Diamond (farin yakutu), emerald (jan yakutu), sapphire (shudin yakutu) da ni kaina bansan adadin su ba. Inada gidaje guda biyu nawa na kaina cikin birnin Paris da Singapore, (inda harkokon Nuratu suka fi yawa) da makeken shagon sayar da turarurruka ‘designers’ nawa na kaina shima a Paris, ba’a maganar (estate) guda cikin Damagaram da makeken gida a unguwar plateux (Niamey), banda kananun abubuwa watau hannun jari na bankuna. To amma Qassim ya manta cewa duk wannan dukiyar shi ya fini GIRMA? Ya fini gata, ya fini daukaka ya fini komai. Ko babu komi tsarkakakken asali shine komai, amma duk wannan agareni aikin banza ne. Ko na daga ido na dube su nayi farin-ciki, tunani daya zanyi ya sani dakacen…. inama ba'a haifeni ba. Wannan ciwo ne da har abada ba zai gushe daga zuciya ba, sai karfafa Imani kadai. Ban taba tunanin yin tutiya da dukiyar Nuratu ba. A tunanina da ni da shi duk daya ne a gareta, tunda tare na gansu. Shi kansa ya lura zancensa ya taBa zuciyata, don haka ya fito ba tare da ya kara magana ba. Muka jera tare cikin (reception) kai kace wasu zarah ne cikin taurari, muna matukar kama, mun kuma yi bala'in dacewa da juna, sai dai zuciyar kowanne babu dadi. Sai da naga dagawarsu na juya muka komo gida. Ina dakin da ya zamo nawa ina rage nauyin kayan dake jikina. Ta shigo niki-niki da butar shayi da 'yan kananun kofuna irin nasu, nayi hanzarin karBarta na ja kankanin teburin gilashi na aza, ta zauna akan ‘stool’ ta zuba tana firfitawa, ta kurBa a bakinta taji zafin yayi dai-dai yadda take so, sannan ta miko min. Raina a jagule yake, duk da haka na daure na amsa na kai baki na. Dacin shayin yayi min dadi, zafinsa ya ratsa har cikin hanjina, na samu relief daga bacin ran da na samu kaina aciki babu gaira babu dalili. Idanunta masu kaifi a kaina tace "me ya dadar dake haka? Kun biya wani wajen ne kamin ku je (airport) din?” Na yi murmushi, tuni na gano tsabar tsoron, dake cikin kyawawan idanunta. Amma sai na yi kamar ban gane ba, ina kurbar shayin ina kallonta ina murmushi nace “ina kuwa zamu je bayan can din?” Ta dan saki fuskarta ta ce "ko nan gaba, kada ya kuma cewa ki zo ki raka shi wani waje ki kwashi jiki ki bishi, duk wata rakiya ayi ta iyaka bakin gate….,” nace “to Nurtu….” Karaf, a kunnen Yadudu dake shigowa, ta dauki kofin shayi daya ta muka min a tsakiyar kaina ta ce "ba zaki daina kiran Nuratun nan ba?” Na dafe kaina ina dariya, ita kuwa ta mike tana hada kan kofunan shayinta ko a jikinta, tace da Yadudu “rannan ma cewa ta yi wai Nuratu Mainasara, yaushe zamu je wajen Haiti?” Yadudu sai muka koma bata dariya. Don ta lura itama Mamin, ta fi son Nuratun da nake kiranta da shi. *** *** *** Mun sauka a Singapore, da sanyin asubahin safiyar litinin. Nade nake cikin jar liffayar Mouritania mai ratsin fari. Takalmina mai tsayi ne sosai sanan na yi amfani da abin kare hancin da na fito da shi daga jirgi, na toshe hancina, daga sanyin dake barazanar jawo min mura. Nuratu na cikin shudiyar liffaya itama, takalminta ‘flat’ ne, don haka da muka jera yau sai na fita tsaho. Aunty Hibbani da Moiram suma suna tare suna hirar su, sai 'yan sandan ciki mata guda biyu cikin fararen kaya, dake bin Mamie inda duk ta aje kafarta. Ta fiddo waya cikin ‘reception’ ta bude ta sanya layinta na kasar ta maida ta rufe ta shiga lallatsawa, na kwantar da kaina a gefen kafadunta na dama, domin ba karamin gajiya na yi ba. Sai muka yi wani irin kyau kamar kawa da kawa. Tana magana cikin harshenda ta san ko (alif) bana ji a ciki, (french). Tun daga fuskarta har cikin zuciyarta cikin nishadi take. Ta dubeni tana cigaba da maganar ta, sannan ta rufe wayar. Ta kai hannunta na dama ta rufe min ido, ta ce " I 've a green, great, giant surprise for you… what would I 've in return? (Menene tukuici na?)" Na ce “karki damu Mamie, fara bani albishir din tukunna, zan baki kyautar turare, bayan shi kuwa zan kai ki makkahh….” Maganar ta kakare a makoshina. Sakamakon wata 'yar ubansu mulmulalliyar motar da ban taBa ganin irinta ba, ta yi parking nesa damu kai kace kwai ne. A kullum malam bature na kara kero motoci, da kusan ba wacce ban gani a (Kangiwa Estate) ba, amma ban taBa ganin irin wannan ba. Domin kankantarta ta isa, har nayi tunanin yadda mutum uku zasu iya zama a cikinta. Glassanta masu duhu ne, amma ba (tinc) ba, domin zaka iya ganin adadin kawunan mutanen dake cikin motar, saidai banda kamanninsu. Na kuma fahimci mutum biyu ne a ciki. Gabadaya hankalina ya tafi ga maotar, da son ganin wadanne irin mutane ne zasu fito daga cikinta? Don haka Nuratu ta zame ta bar ni nan ina kauyancin mota, ta nufi inda su Moiram ke zaune suna cin gugguru. Matasa ne guda biyu masu jini a jika, suka bude murafen motar suka fito a tare, dayan ya saya idanunshi cikin bakaken (dark glasses), ya zaga baryar da dayan yake, suka tsaya suna Magana, ba tare da ya juyo ba. Dukkanninsu suna sanye cikin farar shadda dinkin Dakar, da hula zanna-bukar. Ban san abin da ya dauki hankalina haka kan wadannan matasa ba, tunda ba'a yau na fara ganin kyawawan maza ba. Karewama ga jar fata nan sunata sha'anin su a harabar ‘airport’ din, amma wadannan masu duhun, su suka dauki dukkan (attension) dina. Kamar yadda suke cikin shiga daya, to ba haka halittar su take daya ba. Daya dogo ne, siriri mara kauri, sannan yana da hasken fata, wanda ya hadu da jin dadin rayuwa ya maidashi kamar wani ‘half-caste’, watau ruwa biyu. Daya mai matsakaicin tsawo, baki kuma kakkaura, yana sanye da farin (medicated glass) wanda ya zamo (everyday-glasses) a gareshi. Kirjina na ji ya fara bugawa da sauri-da-sauri, numfahsina ya soma samun tangarda, kafafuna suka soma kokarin kayas da ni. Gabadaya suka juyo fuskarsu dauke da murmushi. Suka nufoni cikin sassarfa da takun GIRMA kai kace wasu 'ya'yan saraki ne. Idan har ba karya zuciyata ke gaya min ba, ba kuma gizo idanuwana ke min ba, to IMARAN ne bakin mai hasken kuma UMAR FARUQ din Nuratu da Inna Rabi. To gun wa zani? Yayan ko Faruq din da har yau ban san matsayin da zan kirashi ba? Ko dai inyi amfani da Kalmar nan ta bature da yace (blood is thicker than water?) In tafi ga dan uwana da nake nema ruwa a jallo? Kwana da kwanaki wata da watanni? To amma anya Faruqun ya cancanci hakan? Wani zubin ruwan ya kan fi jinin karfi, koda shi jinin ya fishi kauri. Don haka maimakon haka. Sai na juya da gudu na kankame Mamie. Nuratu zata kashe ni da ban mamakinta. Na kasa gasgata abinda idanuna suka gane min. Watakila dai irin mafarke-mafarken nan ne da bana rabo da su, masu nuna min wai wata rana….,, zamu hadu da Ya Em a inda ban zata ba. Dariya suka yi suka karaso gaban Mamie, suka zube a kasa suna gaisheta ita kuma sai kokarin kwakwaleni take a jikinta cike da jin kunya ta ce "wallahi ko ki cikani ko ince su koma inda suka fito”. Da gudu na saketa na karasa da gudu na rungume Ya Em, sannan ne wasu irin hawayen farin ciki, suka zubo mini. Yana sharemin da hankicin sa yace "is o.k Zaynab, ina nan tare dake, muddin rai, ba zan kuma zuwa ko'ina ba" ya cirani yayi min nuni da Faruq din daya juya mana baya yana masa waya. Dai-dai lokacin shi kuma ya juyo yana cewa "eh, muna nan Singapore har shi Imran din, ita Hajiya zasu yi wata sabga ne sai sati mai zuwa.." ya kashe wayar yana karasowa inda muke. Imran yace "shi Faruq ba za’a gaishe shi ba?” Na kai hannuna na rufe fuskata ina murmushi, yau wata matsananciyar kunyar Faruq nake sosai, irin yadda ban taba jin kunyar wani da namiji ba. Yayi kwafa yace “kada ta gaishenin, kyale yarinyarnan Imran yadda ka ganta, muguwa ce”. Ko kallona bai yi ba yayi gaba wajen su Mamie. Abin yayi min ciwo kwarai. To amma ganin Ya Em a yau yasa na soma tunanin babu abinda zai kuma sani bakin-ciki a rayuwata. Mota ce ta musamman tazo ta debi su Mami, ni kam nace kafata-kafar dan uwana. Faruq ya harareni, harara sosai ya ce "wannan mota tawa ce, bata dan uwanki ba, babu ko kwabon shi wajen siya min ita, kuma bana daukar mugaye a cikinta. Wadanda basu damu da halin da wasu zasu fada a dalilin su ba, kansu kadai suka sani da nasu farin cikin. So ki nemi mai daukarki a mota, tun wuri, tun dare bai miki ba, ko ki jira in maida dan uwan naki gida, ya aro mota ya dawo ya daukeki, don shima tsintarsa nayi, a titi, bashi da komai sai muguwar zuciya irin taki, data kware wajen jefa iyayenku a halin kaka-ni-kayi….” sakin baki nayi galala! Ina sauraron cin mutunci, amma shi Imran da yake bashi da zuciya ko a jikinsa, sai dariya yake yana gyada kai kamar kadangaren bakin tulu. Ai ni ko mayyace wallahi na hakura da motar nan. Ban ankara ba ya ja kayarshi a guje suka yi gaba. Na tabbata da da kura a wurin, da sun bade ni, mugun badewa kuwa. Sai Allah ya taimakeni duka wajen ‘ceramic’ ne. Motar su Mamie ce tayi ribas ta dauke ni. Raina ya baci sosai da wannan wulakancin da Faruq ya yi mani, ban san sanda hawaye suka zubo min ba. Na ce babu komi, indai nice maganin 'yan maza ce. Wanda ya fika wulakanci ma na ganshi ya dawo, ya zube gwiwoyinsa a kasa da hawayensa yana rokona gafara. Kai haye kayi ba gada kayi ba. Moiram da karin abin haushi tace “ya basu daukeki ba?” Hibbani ta ce “sabida batayi wanka ba, ta kwana a jirgi, tana tsami”. Mamie abin ya bata dariya, don haka ta yi murmushi. Wani gida ne hawa daya, korran (grass carpet) sun yanyame shi tun daga kofar shiga har rufin gidan. Karamin gida ne (Flat) babu gate sai kofar shiga gidan. Fasalinsa kamar kwale-kwale, sannan gefensa (stream) ne mugadanar ruwa yana bulbular da ruwa, garai garai. Mamie tasa mukulli ta bude muka shiga falon, kowanne ya zube a kujera a gajiye. Gidan a gyare yake fes, kai kace da mutane a ciki, tuni Moiram ta hau barci. Mamie 'shower’ ta je tayi ta kwanta a dakin barci bata kara saukowa ba, ni kuwa zugum nayi cikin tagumi. Ina son in tambayi ina su Ya Im bana son taga gajen hakuri na. Na shiga tunanin inda Faruq ya samo Imran, to ko dama wajensa ya gudo? Dana ga wannan ba zata kai ni ba, na yi dakin da Mamie ta shiga, tayi nisa cikin barcinta sosai sabida kwanan zaune da mukai cikin jirgi, na bude jakarta na fiddo wayarta na dawo ‘corridor’ din gidan na jingina da karfen (balcony) ina fuskantar mugudanar ruwan dake gudana garai-garai da shi (Spring), na soma laluben sunayen mutanen dake cikin wayar a nutse, har na iso wada ta yi ‘saving’ da wani suna Dan dukusuru, hakanan akwai “Imin Sa’idu”. Na sha mamaki kwarai, ashe tuntuni Nuratu tasan inda Imran yake? Ko da yake bai kamata inyi ta bata lokacina wajen mamaki ba, tunda ‘kudi’ sune kare magana. Na kira IMIN SA'IDU (kamar yadda ta kirashi) tayi ta ‘ringing’ har ta kusan katsewa kamin ya amsa, cikin tsananin ladabi yace "Yello Mamie, kun huta ne, mu zo?” Nayi ajiyar zuciya nace “kuna ina ne Ya Im?” Yace “ba zaki kwanta ki huta ba?” Na ce "ni dai don Allah ka gaya min inda kuke” Yace “muna gidan Faruq, cikin ma’aikatar su (Informatics)” nace “to ka yi min kwantance in zo” yayi dariya yace “iye, ‘yar gari, zaki bata, kuma ke don baki da zuciya duk wulakancin da yayi miki yanzunnan sai ki zo gidansa?” Na girigiza kai nace “babu ramuwar gayya tsakanina da shi” yace “wonderful! Sai da ni Imran ko?” Na lumshe ido ina dariyar TUNA BAYA…. “kai haba Ya Im, shi Faruq din ne ni kaina nasan ban kyauta masa ba". Yace "zancen gaskiya Allah-wallahi kika zo korar kare zai yi miki, ranshi a bace yake dake fiye da tsammaninki" na ce “babu komi, kome zai min zai jure, karewa ma hakuri zan bashi" ya ce “to ki bari zamu zo anjima, idan Mamie ta tashi bakyanan bazata ji dadi ba, kafin nan zan dage wajen lallasar miki shi, kin san mai hakuri da tausasawa bai iya fushi ba” na ce “to nagode, my precious." Sai azuhur Mamie ta tashi, ta sake wanka ta zuba alkyabba tazo ta zauna ta harde kafafu a falo tana amsar sakonni, wasu cikin (pocket-computer) dinta wasu cikin waya, wasu kuma daga ‘post’ aka kawo mata yanzunnan. Ta ce Hibbani ta dafa mata abinci, bata son na Otal. Hibbani tace “tun kan ki sauko na duba firjin kichin din babu komi ciki”. Ta dubeni ta ce “jeki ki kirawo min direban nan a waje”. Na mike tsam na fita muka dawo tare dashi, tana zana masa aike kala kala, sannan ta shiga buga waya kantuna da masana’antu tana fadin abinda take bukata. Cikin minti ashirin sai ga motoci a kofar gidan suna sauke katon-katon na lemuka da kayan abinci, danyen kifi da danyen nama kilo-kilo. Da kansu suka jera kowanne a mahallinsa cikin kitchen. Na taya Aunty Hibbani muka shirya abinci sannan na shiga shirya wani na musamman tace "wannan kuma fa?” Na yi murmushi kawai, ta ce “au to, na maigida Faruqu ne kenan? To shin yanzu Yaya zaki da Qassim, da alama bahaushen ya fimu samun shiga” na dinga dariya don ban san amsar da zan bata ba. Na fito daga wanka kenan ina shafa na jiyo sallamar su Ya Im, hakannan na nasamu kaina da rashin jin dadin fushin Ya Faruq dani, na yi gaggawar shiryawa na fito cikin fararen riga da siket yan kanti (Nina-Ricci) na feshe jikina da turaren (final touch) na cakuda da (Mont blanc), na nade gashin kaina cikin bakin ribbon na taddasu duka a falo suna cin abinci bias ‘dining’. Kallo daya Ya Faruq ya min ya dauke kansa ya maida hankalinsa ga maganar da suke yi da Mamie, Imran ne kurum yayi min murmushi. Mamie da Faruq suka mike, Hibbani ma ta fito cikin shiri sakale da Jakarta, Moiram kuwa tana mike akan doguwar kujera (tana fama ne da laulayin karamin ciki, don haka ta faya kwanciya). Ya dubi Imran a gicciye ya ce "yaa! Kai ba zaka bimu ba ne?” Ya girigiza kai, ya kada kafada "ina bukatar privacy da ‘yar uwata” wani dadi ya ratsani, ina satar kallon Faruq sabida kyan da yayi min cikin kananan kaya, wadanda ba al’adarshi bace sanyasu. Ya kyabe baki yace “kai madallah, ai dama mugu shi ya san makwantar mugu, kuma mugu baya sirri sai da mugu dan uwansa…” amma a hankali, yadda su Mami da sukayi gaba bazasu jiyo ba. Na lalubi kujerar da Mamie ta tashi, na zauna da kyar zuciyata na tafasa, na dukar da kaina ina zukar numfashi da kyar ina fesarwa da kyar. Imran ya maido hankalin shi akaina yayi ajiyar zuciya yace “kiyi hakuri da Faruq, nima bansan sanda ya koma haka ba". Na ce “kyaleshi kawai, amma kome me nayi masa, ai sai ya sameni ya gaya min in bashi hakuri, sai yayi ta ce min muguwa, muguntar me nayi masa?” Yayi murmushi “kin yi masa mugunta mana, kin daga masa hankali. Duk nasihohin da yayi miki kika shure kika tafi, inda bai san inda kike ba. Alhalin yana shirin angwancewa. Don ko a kansa bai taba kawowa wai kinsan sunan Damagaram ba, ya ce min lokacin ya shiga tashin hankali sosai har ya kusan zaucewa. Musamman wasikar da kika bar mishi wai zaki je yin ramuwar gayya akan mahaifyarki, alhalin kina mace. Ya ce inda kin san kina son zuwa wajen Mamie, ki tambayeshi mana? Ki gani idan bai kawo ki ba, sai kawai ki yi wasa da rayuwarki, ki kama hanyar Nijar ke kadai wannan kasada ce babba. Haka Malam da Halima har yau basu da cikakkiyar lafiya, sabida zullumin inda kika fada da halin da kike ciki. Halima duk ta dauki laifi ta azawa kanta, domin kuwa amana malam ya bata ke. Banda BABAN KI, da akace nisan kwana ne kadai ya kawoshi yau inda muke”. Na yi ajiyar zuciya nace cikin wata irin murya abin tausayi. “Ya Em ina BABA SA'IDU?” Ni kaina ban zaci har abada zan kuma furta wannan kalmar ba. To amma BABA SA'IDU, wani bangare ne na zuciyata, da matsayinsa ya zarta na kowa har da Mamie da Innata. Ya sadda kansa kasa yana duban kyawawan yatsun kafafunsa yace "nima har yau ban kara sa shi a idanuna ba. Amma ina samun labarinsa wajen Faruq. Ya ce ya ji sauki har ya koma aiki. Hajiyarmu ce dai ta gamu da ‘stroke’ (shanyewar barin jiki) tun wata faduwa da tayi data samu labarin komai, sai dazu ne kawai Faruq ya gaaya mishi cewa duk muna tare anan Singapore, har Mamie, yace zasu zo Yamai su same mu. Faruq ya ce ya bari sai sati mai zuwa sabida ita Mamin wata hidimace ta kawota. Amma ni lallai kamin sati mai zuwa zan je gida, don an ce jikin Hajiya yayi tsanani sosai kuma kullum ni take kira”. Na lumshe idon cikin tausayawa rayuwar mu bakidaya nace "Allah ya bata lafiya" yace “amin” daga haka sai duk mukayi shiru, cikin rashin sanin abin cewa. Na dago bayan wasu 'yan dakikai na dubi ya Im, cikin jin nauyi nace "Ya Im, aure fa, sai yaushe?” Yayi murmushi, bayan ya turo hularshi gaban goshinsa ya ce "sai nayi naki da Faruq” nayi murmushi nima nace "ai ni a yanzu haka Ya Im, babu soyayya cikin al'amarina, sai kauna, kana tunanin zan iya auren mutumin da bani da birbishin soyayyarsa, ko digo daya, sai kauna ta ‘yan uwantaka?” Ya ce “wannan shine aure, na hakikah, Zaynab, mai karko, albarka da dorewa. Amma fa ga masu hankali. Soyayya ba komai bace, domin abu ce mai gushewa, musamman idan an kawar da sha'awar dake tsakanin masoyan. Amma ita kauna ta fisabilillahi, itace wadda ake aure da ita, daga baya ta sayo soyayya mai ‘lasting’ har tsufa, har mutuwa. A kuma tashi ranar gobe kiyama, cike da kaunar juna. Kin ganni nan nima ba zan taBa yin auren soyayya ba, zan yi aure ne saboda Allah, da kare kai daga dattin zina da rudin shaidan. Idan muna da rabon soyayyar, sai ki ga mun sameta a gaba. Ma’ana a gidan auren. Koda bayan hayayyafa ne. A wurina soyayya ba komai ba ce face wani abu dake sanya zuciyoyin ‘yan adam cikin halaka, bakin ciki, nadama, tashin hankali, kiyayya, da kaka-ni-ka-yi. Duk da haka tana da dadi; so sweat, yet so painful. Don haka ki auri Faruq da zuciya daya, ina mai tabbatar miki duk duniya bayan iyayenki da ni, sai Faruq a masu kaunarki. Ya soki tun kina jaririya, cike da sanin (who you are). Ya cigaba da son ki a girman ki, cike da tabbacin (ba zai taba aurenki ba). Ya tsayawa rayuwar ki tamkar Uwa da Uban ki. Kuma har abada wannan itace kauna, wadda ba’a ko’ina ake samunta ba, sai mai sa'ar gaske. Ina kara tabbatar miki ba zaki taba yin dana-sanin auren Faruq ba…..!” Na kai hannu na yarfe hawayen da suke ta zuba, nace “nima nasan da hakan, kawai ina ganin shi kamar wani Baba na ne….” yayi murmushi yace "as time goes on, zai wuce kamar ba'a yi ba. Zaynab ke mai sa'a ce; iyayen dake matukar son ki, mijin dake mutuwar kaunarki, dan uwan dake shirye da sadaukar da rayuwarshi kan duk wani mai shirin illata mutuncin ki, saboda haka ki gode Allah, ki manta komi. Babu dan adam din da yake cikakke 100%, dukkanin mu muna da gibi a wani fannin daban. Idan Allah ya baka wannan, sai ya hana maka wancan, domin ya jarrabi imanin ka. Ina cigaba da yi miki addu'ar samun dawwamammen farin-ciki a gabadayan tsayin rayuwarki……". Na zamo daga kujerar da nike zaune, nayi zaman rakuma agabansa. Cikin muryar girmamawa, matsananciyar kauna da tsananin ladabi nace "Ya Im, kai kuma fa? Me kake shiryawa taka rayuwar? In gaya maka gaskiya, farin-cikina da kake ambato, ba zai taba cika ba ina ganinka haka incomplete, shattered….!" Ya kamo hannuna cikin nasa yace "kada ki damu da ni, namiji ne, zan iya karbar rayuwar a duk yadda ta zo!!" Sai na fashe da kuka sosai, na ce "ni dai don Allah kayi aure, ka koma gida, ka koma aikinka ko ka nemi wani. Ka nemi gafarar Baba Sa'idu, me yayi maka haka da zafi? Ni aka yiwa kuma tuni na yafe mishi, tun ma kafin in san laifin da yayi min na gayawa Innana NA YAFE MISHI, kaima ka yafe mishi in har da gaske kana son farin cikin nawa…". Ya fiddo hankici yana share min hawaye yace "is o.k Zaynab, na yi miki alkawarin yin duk abubuwan da kika lissafa. Amma bayan kema kin daure kin nemi gafarar laifin da kika yiwa Faruq, kun koma dai-dai" na ce “nayi maka alkawari Ya Im”. A dai-dai lokacin da Faruq ya shigo, niki-niki da kwalaye, Mamie ta biyo baya sannan Hibbani. Ya dire kwalayen bisa kujera, ya dubemu yayi dariya yace “Allahu Akbar! Mamie kin ga yadda ake hirar 'yan uwantaka, har da hawaye da majina sabida kauna" ta yi murmushi ta yi daki ta rabu da shi, shi Faruq sam baya jin kunyarta kamar ba mai shirin zama sarakuwarshi ba. *** A cikin kwanaki hudu, duk sayayyar da za’a yi wa Haiti an gama ta, sai dai Mamie komi biyu-biyu take dauka. Mun samu hutu da nutsuwa sosai, amma duk yadda na so da in ba Faruq hakuri, ya ki hakan, ya ki saurarena. Ana I jibi zamu baro Singapore ne suna tare da Mamie a falo, suna wasu tsare-tsaren sabon gidan da zata saya a nan don tace wannan da muke ciki nawa ne, da sunana ta saye shi tun da dadewa. Na karaso na kwantar da kaina akan cinyarta nace "Nuratu na kawo miki karar Dan dukusurunki". Ba ita ba hatta Faruq basu san sanda suka fashe da dariya ba. Ya kuma koma yayi dif, ya dinke, kamar bashi yayi ba, ya ce "ke, wanene Dan dukusurun? Ina wasa dake ne?” Na dube shi cikin kwayar idanunsa, tuni ya koma Ya Faruq dinsa, ya shiga sosa keya da ‘yan mukullayenshi domin bayewa Mamie halin da ya samu zuciyarshi da gangan jikinshi a ciki, yace " Mamie yariyar nan zan soma zane ta, ta fara kawo min wargi” tace "me Dan dukusurun nawa yayi miki, a gaya mun inyi hukunci” na ce "haka kawai yake shareni, ko ya kirani muguwa, sannan bashi da lokaci na". Ta maida dubanta gareshi, tana murmushi ta ce "to kai Dan dukusuru na kaji laifuffukanka, ko kana da ja?” Yace “eh, ita ce duk ta jawo Mamie” “da ta yi me?” Ta tambaye shi. “Ta taho kan gaban kanta, bada izinina ba, ta tayarwa da Malam da Halima hankali. Inna Dubu har yau bata daina kukan tafiyar Abun ta ba. Har da bar min wata banzar wasika wai wani "DA FATAN WATA RANA ALLAH YA HADA MU CIKIN ALHERINSA". (Sunan littafin Takori mai zuwa). Mami ta yi murmushi cikin jin dadI, ta jinjina kai tana yiwa Allah godiya, a bisa rahamomin da yake yi mata. Ta ce "to ai gashi a yanzun ya hadaku cikin alherin nasa, sai ku yafi juna. Ita kanta rayuwar da komai dake cikinta dan afuwa ne. Da Allah baya afuwa a garemu, da dukkan mu bamu kawo yau ba. Wanda kuma duk yayi afuwa ga dan uwansa musulmi, shima Allah zai masa afuwa. Ba mamaki a lokain tana cikin ‘tension’ ne da har ba zata tsaya yin tunanin abinda ya kamata ba, ka yi hakuri ka yafe mata!". Kallon da yayi min da wani irin murmushin da bai taba yi ba, kuma bata ganinsa da shi ba. Shi yasa ta tashi ba shiri ta bar mana falon. Ya taso ya dawo gabana tamkar ya shige cikin jikina, yace "Eye. na'am, maimaita sunan a bakinki Zaynab?” Nayi kasa da murya sosai. Na ce “YA FARUQ" yace “ashe kin gane, to ko kef a? Wancan sunan na Nuratuna ne ita kadai. To yaya? Bani labarin hijirarki dalla-dalla, har na 'yan fashin da suka kusa yi min shigar sauri….” na mike na zaura daki da gudu, babu ko waiwaye, yana kirana amma ban juyo ba. *** *** *** Daga Singapore Paris muka wuce, birnin Suisra. Nuratu ta saya min sittiru kamar har abada bazan sake sayen wasu ba, takalma da jaka da kayan kawa na mata, kai ka ce katafaren shago za’a bude. Kayan shafa da turare, wannan ba’a maganarsu. Su kansu su Faruq sun girgiza da dukiyar da take kashewa a kaina. Amma ita din ko a jikinta. Imran tun daga Singapore ya hau jirgin gida Nijeriya ya koma Sokoto. Muna shirin tahowa ne wani babban al'amari da ya dimautamu ya faru, an yiwa Aunty Hibbani waya daga Chadi, ana gaya mata rasuwar Ahmad Fiance din Haiti a sanadiyyar hatsarin jirgin sama. Jikkunanmu suka yi sanyi kalau. Na daga kai na dubu tsibin kayan auren Haiti, da ake shirin yin lodinsu, amma wai duk sun tashi a banza. Tausayin 'yar uwata ya kamani. Ni din shaida ce akan matsanancin son da take masa. A take Mamie ta nemi da a canza mana ‘booking’ zuwa Malaysia domin mu taho da Haiti, wadda a karshen satin dama zata dawo. Aka sanar da ita babu jirgin sai sati mai zuwa, tunda ba passenger. Tayi alkawarin saye sauran kujerun gabadaya, muka daga zuwa Malaysia, inda muka kara hawa wani jirgin muka karasa makarantar su Haiti (University of Malaya) dake a Kuala Lampur. Allah sarki Haiti! Da gudunta ta taryemu, ta rungume wannan ta koma ta rungume waccan. Daga karshe ta kama ni tamakalkale tana kyalkyatar dariyar farin ciki. Tare da ita muka taho a washegari, babu wanda ya gaya mata sai da muka dawo gida Yamai. Kwatanta halin da ta samu kanta a dan tsukin ba zai fadu ba, tayi kuka ta yi ciwo daga baya ta dangana. Shi Faruq ya wuce gida Gwarzo domin sanar da Malam halin da ake ciki. A karshen satin muna cin abinci nida Haiti, misalin karfe hudu na yamma. Muka ji dirin motoci da wani irin cin taya mai nuna anyi doguwar tafiya mai dogon zango. Mami ta sakko daga bene cikin shiga ta alfarma, rike da falmaran din Alhaji Badeggi zata kai masa dakinsa domin yana shirin fita ne, a cewarsa suna da manyan baki da zasu tara a (Guest House) din su. Kamin in idasa goge bakina da ‘tissue’ in mike don fita ganin su waye? Iftihal da Azizah, sun fado a tsakiyar falon mu, suna kira da babbar murya "Ina Aunty Abu? Gamu nan mun biyo ki tunda mu, kin guje mu". Sai kuma ga Inna Dubu, Hajiya Azumi da Inna Rakiya. Na mike jiri na kwasata, kafin in kai ga su Ifitihal, na fadi, na sume. Lallai wani fairin cikin yafi gaban kuka, ko dariya. Na bude ido a hankali, Imran da Iftihal ne suke min firfita. Na mayar na rufe, a hankali na kamo hannun Ya Em, sannan na Iftihal, Azizah ta dora hannunta akan goshi na tace “haba don Allah Aunty Abu, ki tashi, me yayi zafi har da suma? In baki son ganin mu ai sai ki gaya mana mu koma, ba ki fadi ki suma ki tayar da hankalin masu kaunarki ba. Ke dai ban san yaushe zaki daina yawar nan taki ba!”. Nayi murmushi, kana na mike na rungume su. Wasu hawayen suka shatato mini, wani na bin wani. A hankali nace “Azeezah, you are always the way you are (kullum kina nan a yadda kike)” ta ce “naji, ki tashi ni don Allah muje, BABA yana kiran ki”. Dam! Dam!! Dam!!! Zuciyata ta buga, kirjina ya harba, kwakwalwata ta hautsina kamar ince da ita wane Baban? To amma wannan tambayar ma ai rainin hankali ce a gareta. Baban guda nawa ne? Banda Babana ABBA BABA SA'IDU? A hankali dai, cikin matsananciyar fargaba, na yunkura na mike muka jero mu uku a tare. Su Mama Hajiya Azumi, suka bimu da kallo cikin kauna da sha'awar da muka basu. Nuratu ta dubi Hajiya Azumi, ta ce “Allah shine mai GIRMA, amma ba kowa ba!” Inna Dubu ta ce “wannan haka yake, Allah shine mai GIRMA! Mu duka shirme muke amma shi kadai yasan abinda ya boye a rayuwar bayinsa". Suka girgiza kai cikin karuwar Imani a zuciyoyinsu [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Allah sarki Yaya Rabi, koda hakan ta faru dani bata yi fushi da ni ba. Daga baya ta hakura ta fawwalawa Allah al'amarin. Ta kuma ta dauki dukkan laifin da fushinta mai tsanani ta dora akan Sa'idu. A cewarta ba hali na bane, koma menene shi ya koya mini. In ni yarinya ce ai shi mai hankali ne, da har yake da aure har da Da, anjima kuma sai ta yarfa hannuwa ta ce "wannna rashin tsoron Allah da mai yai kama? Wannan duniya ina zata da mu? Wanda ka amincewa shi yake cutar ka. Wanda ka yiwa alkairi shi yake maka sharri. Idan na cuci Sa'idu a tsayin zamana da shi, da yayi min wannan sakayyar, Allah ka fitar mishi. Nima ka fitar min hakkina akan wannan cuta da cin amana da yayi mini”. Daga baya har mukan zauna mu koka al'amarin a tsakanin mu. Ina kuka in ce “ni bana tausayin kaina, sai na abinda zan haifa. Me zan gaya masa ya yafe min samar da shi dana yi ta dattin zina? Wallahi ni kaina Ya Rabi, ban san ya akai hakan ta faru da ni ba, ji nake kamar cikin mafarki, sai daga baya na Ankara, na gane ashe ba mafarki nake ba, zahiri ne". Sai ta share hawayenta ta ce "ni kuma ke nake tausayi. 'Ya mace kike, komi Sa'idu ya yi nasa ado ne, kece keda kaico! Duk wanda ya aureki nan gaba sai ya goranta miki. Haka dan cikinki da kyar idan zai yafe miki. Ki daina cewa kina jin tausayin sa, muddin ina raye, ba zai taBa sanin cewa bani na haife shi ba". Na fiddo ido na ce "me kike nufi?” Tace “ina nufin ni zan zamo uwarshi. Malam Ali ya zamo Ubanshi. Idan har su Dubu sun rike wannan amanar. Shi kuwa Sa'idu bar ni da shi, yace ya taba sanina ma balle abinda kika haifa, sai ya gwammace uwarsa bata haife shi ba, sai ya gwammace bai taBa sani na ba. Zan nuna masa bakar Rabi, don farar Rabi ya sani". Anan kuma sai ta koma irin sambatunta na tsinuwa da la'anta Sa'idu, wani zubin kuma sai ta sa kuka. A lokacin Faruq ya fara hankali, domin ya gama aji uku na sakandire. Ya damu da rashin walwalata da rashin fitowata muje yawo yadda muka saba. Sai yazo dakin mu ya sani gaba yayi tagumi yace "Nuratu na baki da lafiya ne?” Inyi ta muku-mukun Boye cikina, cikin katon hijabin da nake zurmawa, hawaye ya zubo mani. Yau nice na zama daddawa, daga daki sai daki, ko baki akayi a uwar daki Rabi ke kulleni, idan an tambaya ina Nuratu, tace bata nan. Ba’a gaya masa ba, amma shi da kansa ya fuskanci halin da nake ciki. Jikinsa ya yi sanyi lakwas, ya zama wani zalau, kamar bulala, sai dai ya bude baki yayi magana ya kasa, sai dai ya yi ta bina da ido. Cikin wannan halin ne a watan July, a wata laraba nakuda ta kamani. Cikin daren nayi ta murkususu ni kadai, kamin asuba na haifeki. Ko irin kukan da jarirai keyi a yayin da suka iso duniya, ke baki yi ba, wanda ya sani tunanin watakila kema kina bakin cikin zuwanki duniyar, kuma har zuwa wannan lokacin babu Sa'idu, babu labarinsa. Sa'a ta janye kayanta tsaf, don ko 'yar wayar da yake yi min fiye da watanni uku ya daina. Yaya Rabi ta daukeki ta yanke maki cibi, idanunta cike da kwalla da bakin cikin da harshe ba zai iya bayyanawa ba. To amma wata kudura ta Ubangiji, daga ni har ita mun kasa dauke idon mu a kanki. Wata irin kauna irinta da da mahaifi ke ratsa zuciyar kowannen mu, kamar mu dake, har ta Baci, kwata-kwata baki yo komi na Sa'idu ba. Gashi yala-yala har ya rufe idonki, sai da ta dauki sabuwar reza ta rage shi, sannan kika samu kika bude idanunki, farare kal, kika kuwa tsayar da su a kaina. Hankalina ya tashi, tsoron ranar da zaki sake tsareni da wadannan idanun, ki tambayeni dalilin gurbata maki asali da nayi, shine ya gigita ni, wanda ni kaina ban san amsar da zan baki ba. Hakannan bana jin zan iya kara hada ido da mutanen dake cikin gidannan, musamman Inna Dubu, Malam Ali da kanina, Faruq. Wace irin tambaya zai min idan ya ganni rungume da jariri, alhalin ya san bani da aure? Me zan yi in wanke bakin cikina da zai sameki, idan kika fara hankali? Tambayoyin suna da yawa, wadanda suka gigitani, har na fara tunanin guduwa, in da ni kaina ban sani ba, ba don komai ba sai don tserar da mutuncina da naki, wanda na tabbata furucin da Yaya Rabi tayi, na maisheki diyar cikin ta, ba zai yiwu bw in har ina nan. Domin kauna ta da da mahaifi ta wuce misali, ta kuma wuce duk wani bad-da kama da za'a yi a Boyeta, na kuma tabbata Rabi zata kula da ke, fiye da yadda ni zan iya sakin jikina in yi hakan. Uwa-uba ina neman yadda zan yi inyi nisa da Sa'idu, nisan da har abada ba zai taBa sanin in da nake ba. Ban san dalili ba, amma na tsani Sa'idu, ko sunansa ba na son ji. Ko mai irin kamanninsa bana fatan sake gani a rayuwata, balle wata mu'amala ta hada mu. Ban taba sanin soyayya na komawa kiyayya ba, sai a kaina da Sa'idu. Allah kuma shine masanin wannan sirrin. Cikin duku-duku asubahin dai Yaya Rabi taje ta taso Dubu, ta zo ta daukeki tana share min hawaye tana istigfari. Ta je ta taso Malam shima ya zo jikinsa babu inda baya rawa, abinda ya fara yi bayan lakanta maki kalmar shahadah, shine ne tofa miki addu'ar kariya daga zina a al'uararki. Ya kuma ce Allah yasa ke cikon addinin musulunci ce. Ya kuma dauke ki a matsayin wata kyauta gareshi daga Allah (S.W.T), saboda duk 'ya'yan da ya haifa mutuwa suke, Faruq kadai ya tsaya. A lokacin ne yayi maki huduba da Nana Zaynab. Ya kuma kiraki ‘Kyauta’. Dubu ta je ta dora ruwan zafi a murhu don yi min wanka. Malam ya tafi masallaci don bin jam'in sallar asubahi, a daki kuma Rabi ta shiga ban daki domin gabatar da alwalar sallar asubahi. Na daukeki na rungume a jikina tsan-tsan, hawayen dake ambaliya a kuncina na jika taki fuskar, na kuma kura maki ido, kurr! Sai dai a raina nasan ba kallon karshe nake miki ba, ko ba dade ko ba jima nasan zaki bi ni, duk inda nake, in har ni na haife ki, in kuma muna raye. Maganar kulawa kuma bani da kaico akanki, inada yakinin zaki samu kulawa ta uwa da uba da dan uwa, irin wanda in ina nan, ba zaki sameta ba. Don haka nayi gaggawar ajiyeki, ina da kudi masu yawa ire-iren wadanda Sa'idu ke bani in zai koma, ba kuma abinda nake yi da su, don haka na kwaso su na zuba a jaka. Duk ciwon dake jikina, rashin karfi da jirin dake kwasana, amma a haka na dafa bango na yafa mayafi na fito. Dubu na daga can madafi, ta durkusa tana ta hura wuta a murhu idanunta sai tsiyaya suke abin tausayi, da gani irin azababben utacennan ne Allah ya hadata da shi, nayi sanda na wuce zaure, malam bai rufe kofar ba bayan fitarsa masallaci, don haka ban wani Bata lokaci ba wajen ficewa. Almajiran Malam duk suna cikin shagon su, wasu kuma suna kwankwance suna barci a harabar gidan, yayin da masu hankalin sun bi malam masallaci. Sai bayan da na danyi tafiya ne na fuskanci jini yana zuba a jikina. Don haka nasha kwana a wani lungu da babu kowa, na sunto dankwalina nayi kunzugu dashi sannan na cigaba da tafiya ko gani bana yi sosai. Ban dauki hanyar tasha ba don nasan can ne waje na farko da Malam zai sa a fara bi na. Na rika bin gefen titin fita garin Gwarzo bana ko waiwaye. Na yi tafiya a kalla (kilo mita uku da rabi) kafin in ji wata mota ta makeni akan kwalta. Saboda jinin da ke kwasata, ban san cewa a tsakiyar titi nake tafiya ba. *** *** *** Na bude ido ne na ganni kwance a gadon asibiti, ana yi min karin jini. Domin na zubar da jini da yawa. Hannuna na dama daure cikin bandeji, gwiwoyina da wasu bangarori na jikina duk sun kukkuje. Daga baya ne likita ya shigo yake gaya min na samu karaya ne har biyu a hannuna na dama, sai 'yan kujewa da ba'a rasa ba, sannan ya fadi abinda yayi matukar bani mamaki, wai mijina daya kawoni ya tafi gida, yana dawowa zuwa karfe shida na yamma. A lokacin kuma hudu ta yi har da mintuna ashirin. Ya sake kallona sosai, ya ce ina "Baby din naki? Ai zaki iya zama tare da shi anan gadon asibiti, ko don kada nonon ki yayi ciwo. Idan yazo kice yana iya dauko miki shi" na bishi da “to" kawai. Na lumshe ido a hankali, in saka wannan in kwance wannan. Ni Nuratu kuma kaddarorin da Allah ya dora min ke nan? Na tabbatarwa kaina ba zan zauna har sai na warke a sibitin nan ba, koma yaya ne, ina bukatar yin nisa da Kano. Nan kuwa nasan ba zai wuce Kano din ba, don kuwa itace mafi kusa da Gwarzo. Na kai dubana ga mamana da suka cika tam. Suna shirin fara zuba, wani gululu yazo ya tokareni kamin in balle da kuka. Kuka sosai wanda ba zai wanke radadin dake raina ba, ba zai wanke tausayinki da tausayin halin dana baroki ciki ba, ba zai wanke takaicin rabuwata da 'yar uwata ba, da muka taso tare tun zuwana duniya, ba zai wanke tunanin masifar dana jawo mata, na gudu na barta da shi ba, ba zai wanke radadi da kulafucin uwa ga danta, dake narkar da zuciyata ba. Misalin karfe shidda na yamma, aka turo kofar aka shigo. Wankan tarwada ne makimanci ga shekaru arba'in. Yana da tsagin barebari biyu-biyu a kuncinsa, mutum ne mai cikar kwarjini da kamala. Akwai alamun tsoron Allah a tare da shi, rashin son wasa ta ko’ina, yanayin sutturarsa, agogon dake daure a hannunsa, da irin takalminsa mai walkiya da sheik, ya nuna ba karamin mutum bane. Wasu mutun biyu ne a bayansa, ga alama daya ‘escourt’ ne dayan kuma direba, rike direban yake da kaya niki-niki cikin kwali, da ledoji abincin (city sweats), ya daura bisa lokar dake jikin gadona, yayin da mai tsaron lafiyar tasa ya ja masa kujerar dake fuskantar gadon da nike kwance, suka juya suka fita. Yafi mintuna uku bai ce min komai ba, da alamunsa ni yake son in fara yi masa magana. A raina nace amma zaka kwana anan, ka kade ni da mota sannan ka yi min iko? Ko tunani ya yi bai kyauta ba, sai ya ce "Sannu da jiki ko?” Na amsa da ka, ya sake cewa "Garin yaya kike tafiya a tsakiyar titi, kuma da sanyin asubahi ke kadai, alhalin kina mace, wadda bata yi mun kama da mai taBin kwakwalwa ba?” Nace "Eh, lafiya ta dalau, yanayin rayuwa ne yasa hakan”. Yayi murmushi, cikin sanyin murya kuma ya ce "kiyi hakuri, Im not here to interfere (bana zo don na inyi miki shishshigi bane), kawai dai nayi mamaki ne. Ko zaki daure ki gaya min wurin aikin mijinki, in je in zo da shi domin anan na yi musu karyar nine mijinki, kuma ni na kadeki a bias rashin sani a kofar gidan mu, don kurum su karBeki ba tare da sun Bata mana lokaci ba. Ba yadda direbana bai yi ba don ya kauce miki, kina kara shan gabansa, karshe dole motar ta shafeki, sun gaya miki kin samu karaya a hannu ko?” Na gyada masa kai, ya ce "to a ina za'a samu mijin naki, ko can kauyen zan koma in bincika?” Ban san sanda na muskuta ba, hannuna ya amsa, azabar har cikin kwakwalwata, har kuma yatsar kafata amma na cije leBBana nace "bani da aure". Ya zuba min ido curiously (cike da son sanin abubuwa da yawa da suka shafe ni) ya ce “sunana Kabir BADEGGI. Iam politician (watau dan siyasa ne). Ni mutumin Nijar ne, amma na girma a Maiduguri, hannun gyatuma ta, saidai a yanzu haka da girma ya hauni, na koma mahaifata ina tafiyar da harkar siyasata a can. Kina yi min kama da wasu mutane acan na kwarai dana sani, nake kuma tare da su. Ki daure ki dubi girman Allah, ki gaya min gaskiyar inda kika fito, in sadaki da iyayenki. In ma wata matsala ta fito dake, ni na yi alkawarin zan tsaya maki. Ba zan barki ki fada a lalataccen hannu ba, hannu da hannu zan danka ki ga iyayenki, ki yarda dani". Na runtse ido cikin tababar in yarda dashi din ne ko a’ah? Bai yi min kama da mutumin banza ba, bai yi min kama da makaryaci ba, haka bai yi min kama da mayaudara irin SA'IDU ba. Magana yake daga fatar bakinsa, har zuciyarsa, haka idanunwasa na tabbatar da abinda ke fita bakinsa. Har da mulmulen sallah a goshinsa, abin nan da ake kira "sujjadah". Shi ba wani kyakkyawa bane, kawai kamili ne, da babu alamun wasa da yaudara cikin al'amarinsa”. Ta yi murmushi, nima murmushin nayi. Don sanin ko wa take nufi. Amma can a karkashin zuciyata ina KISHI, da nake kalubalantar zuciyata mai cewa BABANA SA'IDU nake tayawa. "Kabir Badeggi kenan. Wanda zuciyata ta aminta da shi a lokacin daya. Naji ya kwanta min tun bai furta wata kalma mai nufin soyayya a gareni ba. SaBanin Sa'idu da yayi amfani da wayewar shi, wayonshi da kyawun halittarshi ya saye soyayyata. Hakannan na jishi da wani GIRMA a idanuna, ta yadda nake jin har ba zan iya bude su gaba daya in dubeshi ba. Ban san sanda furucin ya suButo daga bakina ba, na samu kaina da cewa cikin rada, sannan idanuna a rufe "Nima ai asali na 'yar Nijar ce". Yayi murmushi yace "what a coincedence! Nijer, a wace Jiha?” Na ce "Damagaram" ya yi dan dumm! Yana kallona da dukkan fararen idanunsa, yace "Damagaran, ikon Allah, ina yawan zuwa wajen aminina Shettima, yaya sunan ki?" Na sake runtse ido sosai, saboda yadda sanyin muryarsa ke kassara gabban jikina, na ce cikin rashin kuzari. "Nuratu Mainasara". Jawo kujerarshi yayi gabana, yana kallona sosai kamar ya cinye ni, ya kai hannu ya zare hular zanna dake kansa yace "kina nufin ke, jinin KANGIWA ce, kuma kanwa ga Shettima Mainasara?” Na bude hakorana duka ina dariya, jin wani ya ambato min wani suna daga cikin sunayen da nike matukar girmamawa, dana dade ban ji ba, shekaru masu yawa nace "a’ah Baba Shettima Baba ne a gareni. Shine dan autan su mahaifin mu". Yace "Nuratu ke kamar kanwace a gareni. Akwai mutunci da harkar neman abinci sosai tsakanina da Babanninki. Don haka ba sai kin warke ba zan sayo mana tikitin Yamai, in danka ki ga Iyayenki duk da ban san abinda ya fito da ke ba, sannna in komo in tafi inda da nayi niyyar zuwa kika hanani. Amma don Allah kiyi alfarma gareni, ki gaya min me ya kawo ki dajin dana ganki? Me ya kawoki Nijeriya?" Gaba daya fuskata sai ta sauya, da wani irin lulluBaBBen Bacin ran da shi kanshi sai da ya fuskanci hakan. Ya yi saurin gyara zancen sa da cewa "kodayake ‘this may be your personal issue, am sorry, very sorry" na yi murmushi kadan, ganin yadda ya damu sosai da damuwata. Ban san bayanin da ya yiwa likitocin ba. Washegari ya dawo ya kira Nurse ta taimakamin na shirya, bayan ya bata wani bakar leda shake da kaya. Na sha mamaki da naga har da su (always pad) kodayake hatta gadona Bace yake da jinni, duk da kunzugun dankwalin dake jikina. Ta hada min ruwan zafi mai matukar zafi ta yi mun wanka, bayan ta zaunar dani sosai a cikin ruwa zafin don ta lura haihuwa nayi, tana yi min tambayoyi game da Babyna nace bakwaini ne, an sanya shi cikin (incubator). Ta hada min shayi mai kauri sosai, ta kuma hadani da gashashshiyar kazar (Capetano) daya kawo cikin plate ta badeshi da yajin daddawa tace in ci sosai, don mijina ya gaya mata doguwar tafiya zamuyi zuwa Jamhuriyyar Nijer. Cikin kayan daya kawo ta fidda min sabuwar doguwar riga dal daga cikin ledarta, irin wadanda ake kawowa daga Dubai da mayafin su, kalar su toka-toka (ash) har da sabbin (panties) duk sai naji ina jin kunyar hada ido da shi kuma. Ita kuwa ko a jikinta, aikinta kawai take sai cewa take maza sanya mana, yana jiranki a mota. Da ganin irin kulawar da take min na jinjinawa asibitin. Don hakane dana fito na daga kai na ga ‘sign board’ mai dauke da sunan asibitin, an rubuta PREMIER CLINIC. Sai na ce a raina ashe ba'a banza take yi ba. Haka ta kama hannuna har gaban motar. Direbansa da ‘escourt’ dinsa suna gaba, ni da shi muna baya. A sannan ne wata nutsuwa tazo min, sanyin A/C dana dade ban ji ba ya ratsani. Na lumshe ido na rausayar da kai gefe muna hira jefi- jefi akan su Baba Aliyu, har muka zo Airport din Aminu Kano, inda kai tsaye muka hau jirgin da zai kaimu Niamey. Zuciyata cunkushe da tunanin fuskar da zan fuskanci dangina da ita, sai da zuciyar ta yi amanna da in fadawa Yadudu gaskiyar abinda ya rabo ni da gidan Ya Rabi. Da kuma dalilinmu na kin neman su alhalin mun san inda suke, wannan kam ni kaina bani da masaniya akai, nasan dai Malam Ali yana addu'a sosai a kanmu, wadda tasa ko sunan dangin mu bama tunawa. Gara ma ni wani lokacin nakan tuno Yadudu, amma Ya Rabi ko zancen kasar Nijer bata son ta ji anyi a gabanta. Tun a filin jirgi yayi wa Baffa Aliyu waya yace gashi nan tare da diyarsu Nuratu. Baffa ya ce "wace Nuratun? Ba dai 'yar Yaya Sani mai rasuwa ba?” Ya ce ita dai, shima Allah ne ya hadasu, yayi-yayi kuma na ga fada masa daga inda na fito na ki. Don haka kafin minti goma sha biyar filin jirgin saman (Mano-Dayak) ya cika taf, da motocin, iyalin Mainasara. Na hangesu kwansu da kwarkwatarsu KANGIWA FAMILY, maza da mata, tsofaffi da 'yan mata. A tsakiyar su na hango tsohuwa Yadudu, ta kara tsufa kwarai da gaske fiye da yadda na barta. Amma kayan alfarma ne a jikinta. Na karasa da gudu muka rungume juna muna ta kuka. Ta ce "Nuratu ashe Allah yayi zan kara ganinki ina raye? Ina 'yar uwarki, me yasa bata taho tare dake ba?” Nace “labarin mai tsawo ne Yadudu, muje gida tukunna". A babban falon Baffa Aliyu cikin unguwar nan muka hadu, aka sallami yara-yaran irin su Qassim, lokacin Hibbani tana budurwa kamar ni. Ina kuka na fede musu biri har bindi, tun auren Ya Rabi da mahaifinmu ya bayarwa malam Ali, na ce malam Ali mutumin kirki ne, ba'a rasa ci ba ba’a rasa sha ba cikin gidansa, kuma yana sonta, ku kwantar da hankalinku. Ku barta ta yi zaman aurenta, haka Allah ya tsara mata. In ya so sai a dinga kai mata ziyara akai-akai, abinda har yau Allah bai basu ikon yi ba, kuma da wannan nadamar suke kwana suke tashi a halin yanzu. Sannan na gangaro ga labarina da Sa'idu, na fada musu komai ban rage ko kalma daya ba, saboda nasan su iyayena ne da bani da kamarsu, hakannan mutane ne masu ilimi, tawakkali da barwa Allah komi. Wannan shine ginshikin rayuwar iyalin Mainasara, wadda ke kara bunkasa su har gobe. Mutanene da suke muhimmanta yarda da kaddara da hukuncin Allah, mai kyau ko mara kyau a gare su. Na kare da cewa duk hukuncin da kuka yanke a gareni dai-dai ne. Ni dai kwanciyar hankalina kadai shine kada yarinyar ta gane ba Ya Rabi ce ta haifeta ba, amma ba don bana son ta. A da, tunanina shine in dauko ta in taho tare da ita, sai nayi tunanin yaya zan dauko 'ya in kawo masu alhalin ban yi aure ba? Mu kuwa 'yan siyasa ne, jinin mu da Bargonmu, masu tarin makiya, amma ba wai don ni in yi siyasa ba kamar yadda tunaninki ya baki. Don a lokacin kwata-kwata ban taBa kawowa raina in cika burin mahaifina ba, wato in zamo makwafinsa. Kawai ina jin su Baba Aliyu ne, da tasu siyasar. Na tabbatarwa kaina zamanki tare da Ya Rabi, shine babban kwanciyar hankalinki, mutuncinki, nasaba da martabarki amma ba wai nawa ba. Wallahi-wallahi tilas ce ta sani baroki da Ya Rabi, domin abin zai yi mata yawa. Naga yadda kaunarki ta shigeta tun sanda take yanke miki cibi, ko ido bata iya daukewa akanki. Na san in na bar mata ke, kamar na zauna tare da ita ne, ko babu komai zaki debe mata kewar abubuwana da yawa, domin duk wata halittata irin taki ce, hatta sumar kanki, kuma babu maraba da ita, sai ki rantse itace ta haifeki. Yadudu kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita. Su Baba Aliyu kuwa sun kasa magana. Sun kuma rasa me zasuyi dani su huce. Shettima yafi kowa zuciya cikin danginmu, shine ya fara tamaula da ni a falon, ya rika duka kamar ba zai barni ba. Ganin irin jinni da majinar da ya haDa min ne Yadudu ta mike jikinta na kyarma ta rufu a kaina. Ta ce “ka kashemu mu biyu, mu tadda mahaifinta. Daga nan sai in yi masa bayanin irin rikon da kuka yiwa zuri'arsa a bayan ransa. Shida ya kari rayuwarsa gabadaya cikin hidimar ilmin ku, cikin kyautata muku. Tunda ya rasu cikinku wa ya kara waiwayar 'ya'yan da ya tafi ya bari, alhalin kuna da tabbacin suna raye cikin kasar Nijeriya? Sai yau da ta biyoku da kanta, ta fada maku abinda ba matse bakinta kukayi ta fada maku ba? Da Nuratu lalatacciya ce, tana kuma son lalacewar, da bata dawo cikin ku ba. Da ta karasa cikin duniya ta cigaba da lalatar ta. Amma dawowa ta yi ta fada maku amanar kanta, wanda daga ita sai Allah sai 'yar uwarta suka sani, sabida tana da yaqinin ku iyayenta ne bazaku taba yanketa ku yar ba, babu abinda zai faru ga dan adam, face ya kasance rubutacce a lauhul mahfuz, don haka ita Nuratu haka Allah ya rubuta mata. Amma dubi kwayar idanunta, ba tayi kama da shaidanun 'ya'ya ba. Don haka Nuratu ko a yau ki koma kizo da diyarki, ni zan rike maki, kina da dukiyar da zaki rike 'yarki, ba tare da taimakon kowa ba. Babu wanda yake sama da aikata kuskure, sai dai wani yafi na wani, kuma idan kika roki Allah da cika sharuddan tuba, hakika zai yafe maki. Ya yafe wanda yafi wannan. Ban taBa ganin yarinya mai tsoron Allah irinki ba. Nawa ne suka yi cikin, suka je suka zubar, ko su haife su kashe, ko su yar a bola? Ba tare da iyayen su sun sani ba? Amma ita tazo ta gaya muku abinda baku sani ba, don tana da tabbacin kune iyayenta, a cikin kowanne hali, ba zaku kita ba. Yau da mahaifinta yana raye ….. Shettima zakayi mata irin wannan dukan fitar ran daka yi mata a gabansa?” Ta kama hannuna ta tayar dani, jinni na bulbula ta hanci ta baka mika ni har gabansu, tace "gata nan ku yankata, sai dai ku sani, in gemun dan uwanka ya kama da wuta, to ka shafawa naka ruwa…..". Kamilu yace “Yadudu ai baki bari kinji me muka ce akanta ba, shi kuwa Shettima kin san zuciya irin tasa. Me yayi zafi? Me ya kawo wannan maganar? Allah ya huci zuciyar ki. Nuratu tamu ce, haka ko me tayi ba zamu yada ita ba, amma dole mu ladabtar da ita, don ta kiyayi gaba, da yiwa 'yan bayanta hannunka mai sanda, kuma ko Yaya Sani yana raye, bazai kalubalanci hukuncin da Shettima yayi mata ba. "Ke Nuratu!” Ya kira ni da kakkausar murya. Na dago kumburarrun idanuna na dubeshi, amma ban ce komi ba. “Da gaske ne abinda kika gaya mana?” Na daga kai ina hadiyar zuciya "to waye Uban 'yar?” Nace almajirin mijin Ya Rabi ne, sunansa Sa'idu, a yanzu haka yana karatu a Ingila, nasan kuma bada jimawaba zai dawo ya tadda ita. Wallahi-wallahi Baffa Aliyu, nima ban san ya akai hakan ta faru da ni ba, kawai na bude ido ne na ganni da cikin a jikina, ko shima Sa'idu bai san da zancen cikin ba" yace “to kun shirya yin aure ne idan ya dawo?” Na share wasu ambaliyar hawaye daga kundukukina, nace “har abada babu zancen aure a tsakaninmu. Ina nufin ba zan iya auren sa ba". Ya ce “zancen banza, to waye zaki aura wanda ya fishi?” Nasa kuka sosai na ce "wane irin aure, GIRMAN JUNA YA FADI? Nidai kuyi hakuri makaranta zan koma". Dukkan su sai suka yi shiru, aka rasa mai bakin magana. Daga karshe suka hadu suna yi min nasihohi, kowa da irin tashi, masu ratsa zuciya, at last, suka ce “Allah ya zaBa min abinda yafi alkairi ga ryuwata,” akayi addu'a taron ya tashi. Bada jimawa ba na bawa Baffa Aliyu takarduna na sakandire ya samo min gurbi a jami'ar Niamey, na soma nazarin kimiyyar siyasa (Polictical Science), sai dai muna yi da harshen faransanci ne. Ina shekara ta biyun karshe Badeggi ya fito gaba-gadi da son aurena, duk da gaskiyar labarina da Shettima ya gaya masa, yace ya ji ya gani. Ya taBa aure matarshi ta haifa mishi 'ya'ya har biyu, ta rasu a wajen haihuwar na ukun. Biyu maza ne, duk sun girma, AbdulHakim da Abdulsamad, a yanzu haka manyan ma'aikata ne sa'annin Qassim, macen kuma itace Niyaz, wannan 'yar budurwar da nasa ta yi miki magana ranar da Qassim ya kawo ki. Kai tsaye na nemi alfarmar Kawunnina da suyi min uzuri in kammala karatu na, zanfi samun nutsuwa. Duk da matsananciyar kaunar dake tsakaninmu, maza tsoro suke bani. Na kudurce a raina na daina baiwa soyayya muhimmanci akan ingancin rayuwar diya mace. Na fito da (First Class Degreee) a shekara ta (1990). Na kuma yi (winning scholarship abroad) daga jami'armu zuwa babbar jami’ar Paris. Daga Baffa Ali, Adam, Shettima Kamilu da Kabiru, babu wanda yayi yunkurin hanani tafiya karatun digiri na biyu na tsayin shekaru biyu kacal, a cewar Baffa Aliyu a kyaleni in je, tunda yanzun ni ba karamar yarinya bace zan iya kula da kaina. Don haka na tafi tsawon shekara daya da rabi kacal na dawo da kwalin digirina na biyu, muka yi aure mai suna aure, wanda yayi tambari cikin kasar Nijar ciki da bai dinta, cike da matsanancin so da kaunar da har yau ba'a taBa samun ma'auratan da suka dade tare da juna, ba tare da wani saBani ya gitta a tsakanin su ba, kamar ni da Badeggi, a gaba dayan Kangiwa family. A lokacin Kabir ya samu damar darewa shugaban jam'iyyar mu, wadda tafi kowacce jam'iyya karBuwa a kasar Nijar. Haka kawai kamar da wasa rannan na soma tunanin me zai hana in cikawa mahaifinmu burinsa, da ya tafi da shi a zuciyarsa? Wato tsayawa gwamnatin Damagaram, domin kara fiddo ta da banbantata da sauran jihohin mu. Na samu Baffannina muka tattauna, mijina ma ya bani goyon baya dari bisa dari. Ba jimawa na tsaya takara, Kangiwa suka tsaya mini, talakawan garin Damagaram suka yi min alkawarin kuri’unsu, domin Babana. Ana yin zaBe kuwa na lashe, wannan wani abun tarihi ne da ba’a taba samunshi cikin kasar Nijar ba, wato Gwamantin diya mace. An samu sabanin ra’ayi da yawa, musamman daga Malaman addini da abokan hamayyar zuri’ar mu, inda gari ya rincabe, domin talakawa sun maya sun rantse idan ba ni da suka zaba ba, sai dai a kone garin kowa ya huta, sabida basu ga me mazan suka yi masu ba banda wawashe dan arzikin su, wanda bai kai ya kawo ba, da kyar aka samu aka sulhunta da babbar kotun kasa, wadda ta tabbatar da tsarin mulkin kasar Nijar bai haramtawa mace yin gwamnati ba. Don haka aka rantsar da ni. Muka tattara muka koma (Govt. House) nida mijina da 'yan uwana masu yawa. Na karBo Haiti da Qassim, da 'ya'yan Baba Shettima uku, da dyar baba Adam wadda kwananan na aurar da ita, da kuma Niyaz diyar Bedeggi, duk na hada na rungume suna karatu a wajena. Haihuwa mun nemeta sama ko kasa Allah bai bayar ba. Likitoci sun tabbaar matsalar daga gareni ce, amma Kabiru yace ko zamu dawwama a haka, ba zai auri kowa ba, na ishe shi rayuwar duniya da lahira. Ya dade yana yi min zancen mu daukoki a lokacin, ina kin amsawa. Abinda bai sani ba shine na tada dan aike musamman da lambar wayata ya kaiwa Faruq, a lokacin ya fara karatu a Sokoto, yana sanar dani komai kuke ciki. Akwai kakkarfan aminci tasakanina da Faruq dina, daga baya ma na shirya masa tikiti na aika mai don yazo ya same ni, yace mun a’ah suna tare da Imran koyaushe, bazai iya yin tafiya batare da sanin sa ba, sai na aika Qassim ya gano min gidan Sa'idu, ba tare da yasan dalili ba, ba kuma tare da shi kansa Faruq ya sani ba. Na yi Badda kama nazo Sokoto fiye da sau biyar, har kofar gidan Babanki…..”