[7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: GIRMA YA FADI 2 Cikin su ya duri ruwa, idanunsu ya raina fata suka yi jigum-jigum. Ba sai ga Imran da kan wayoyi har uku ba? Har cikin dakin barcinmu ya shigo yake tambayar ina Zaynab? Da fari sun tsorata sun dauka zancen jiya ne ya kawo shi, don haka a tsorace suka ce tana toilet tana brush. Ya ce, “To madallah, ga tsarabar ku, saura in ji ana kiran ‘ya’yan banza”. Ni dai sai ihun su Azizah na jiyo don wayoyi ne ya kawo mana ‘yan uban su duk iri daya (Nokia), sai dai duka ba layi nawa ne kadai ya sanya layin ‘glo’. Ni dai tunda na karba na jefa kasan filona ban kara tunawa da ita ba, don ba ita ce a gabana ba jarabawar da nake yi ne. Yau da muka fito paper din ‘geography’ Mr. Segun ya biyo mu, tun farkon zuwan su yake min nacin na tsaya na saurare shi na ki, an turo shi invigilating ne daga Minna jami’in NECO ne, ga tsagun nan na Nufawa rankacau cike da fuskar shi, amma shi tsakanin shi da Allah sona yake yi da aure kuwa ba da wasa ba. Su Iftihal dariya yake basu, idan kuma ya rubuto masu amsa su karbe su kwafe babu ko tsoron Allah, su koma bayan idon shi suna dariyar shi. Ga mamakin su yau tsayawa na yi da Mr. Segun ina jin wadda ya zo da ita, wato yana so in kwatanta mishi gidanmu ya zo, yana so in mun kare jarabawa zai aure ni, kar in damu da matarshi da ‘ya’yansa ba zai hada mu gida daya ba. Na ce masa, “To”. Ya ce, “Wane gari nake son zama? Minna ko Sokoto?” Na ce, “Duk inda ya fi maka sauki”. Dadi ya kama shi sai washe baki yake. Daga can gefe kuma GG ne zaune a benci yana kallon mu fuskarsa a hade. Mr. Segun ya tambayi nambar wayata na ce da shi ban rike ba tukunna yau aka bani wayar, amma gobe zan kawo mishi. Ya rasa inda zai sa kanshi don dadi, muka yi sallama kamar ya goye ni ya gudu dani. Ina yin taku biyar don cimma su Azizah sai ganin GG na yi a gabana kamar an jefo shi, tsulum! Ya ce, “Wato don wulakanci Zaynab don kin ga na damu dake kike yi min duk abin da kike yi min?” Na ce, “Ba wulakanci bane GG na ga irinmu fitina ne a bayan kasa, shine nake jiye maka haduwa da fitinar mai narka-narkan mazauna”. Ya fashe da dariya, daga nan inda nake ina iya jiyo mugun doyin da bakin shi ke yi. Ya ce, “Don Allah don Annabi Zaynab ki yafe min ki bar TUNA BAYA….., wallahi tun a lokacin son ki ne ya yi min yawa nake kuma neman hanyar da za ki kula ni na rasa……” Na dan juya don gano su Azizah, na hango su duk a nutse cikin motar Ya Im suna ta jirana, shi kuma yana jingine jikin kofar motar wadda take a bude, ya dage kafarsa ta hagu ya jingineta jikin motar ya harde hannuwanshi a kirji, manyan idanun shi fes a kanmu. Ban bari ya fahimci na san da tsayuwar shi ba, da na kakaro wani lallausar murmushi na kwarawa GG bai san sanda ya sanya hannu a aljihunsa ya rarako duk abin da ke ciki ya miko min ba, ni ko sai na ce, “Mai da abinka muje ku gaisa da Yayana ga shi can, dama ya ce yana son yin abota da kai tun sanda ka sani wankin toilet, shine waliyi na a wajen shi za ka karbi aure”. Da GG ya hanga ya dubi Ya Im, kayan jikinshi da irin motar da yake tsaye a jiki, duk da ba a gano kwayar idanunshi ya saya ta da bakin gilashi (blackmail) sai ya rikice, ya ce, “A’a, ayi haka Zaynab? In ce ko ba gatsen da na yi miki a kan a koreni daga aiki kika dauka da gaske ba? Ki yi hakuri don Allah ki yi mun arziki, wannan aikin da shi nake ci, nake sha ni da iyalina da gyatumata. Kuma wallahi karya nake bani da wata gonar gado wani busasshen kango ne kawai a kauyen mu”. Na yi mai murmushin kwantar da hankali na ce, “Kai dai tunda na ce ka zo muje, to ka zo muje, baka san alheri irin na Yayana ba, cewa fa ya yi zai sa a mai da kai principal dinmu”. Ai jin haka GG ya gyara hula tare da gyara zaman kwalar rigar shi, ina tafe yana biye dani kamar wani mai take min baya. Shi kuma Ya Im ganin mun nufo shi sai ya shiga mazaunin shi ya zauna, garam ya rufe kofa ya danna wani abu a jikin hannun motar tintics suka rufe mana ido rufe bakake sidik, kan in ce me! Ya ja motarshi aguje ya bude mu da kura muka yi futuk ni da GG, amma GG bai damu da kansa ba sai sannu yake min, na tabbata da da hali ma da ya karkade min kurar da ta bata fararen uniform dina. Wata matsiyaciyar kunya ce ta kama ni, domin bayan GG akwai sauran malamai da dalibai da dama da suka ga faruwar al’amarin da basu ga dalilin shi ba. Ban ko bi ta kan GG ba na yi gate ina share hawayen wannan wulakancin da Imran ya yi mani a bainar jama’a, wata zuciyar kuwa sai ta ce dani baya da laifi, ai ba ubanki ne ya saya masa motar ba. Achaba na tara ya dawo dani gida har cikin gate, lokacin Imran na tsaye tare da wani abokin shi Jabir suna magana. Gaba daya suka juyo suka zubo min ido ina lalubo kudi a jakata don bai wa mai babur, ya kara kuluwa iyaka da ya ganni na dare a bayan mai mashin, ya kuta ya kada kai ya mai da hankalin shi ga Jabir yana ta yi masa magana amma shi hankalinshi da attention din shi duk yana kaina. Sai da na wuce cikin gida sannan Jabir ya ce (yana nuna hanyar da na bi na kule) da dan alinsa, “Wannan (fresh baben) fa Imran? Yanzu dama kuna da irin wadannan a gida ka barni ina bin kadangarun bariki karmasassu?” Imran ya wani irin juyo ya lafta mishi harara, kamar ya yi aman zuciyarshi don takaici, ya ce, “Idan za ka yi iskancinka ka san a inda za ka yi shi, me kake nufi? Kannen nawa ma basu tsira ba? To ahir dinka, kuma in gaya maka ba a nan gidan ba, kuma wallahi ka yi kadan ka lalata min kanne J.B, su basu san irin wannan rayuwar ba yara ne, kada ka sake ko da wasa ka kula su, ka ga hanya sai mun hadu…..” Yadda ya fitittike yana ta fada ko idanunshi baya iya budewa, duk sai ya ba Jabir dariya, ya kara kular da shi da cewa, “Kanwar ka? Ta ina kuma? Wannan Balarabiyar haka? Na san Iftihal da Azizah amma wannan kam ba ‘yar gidan nan ba ce, don haka ina kamu babban Yaya, kuma ka yi hakuri ni ba da manufar da ka fassarani ba nake son ta, ina nufin…. da aure!” Wayyo Allah! Karshen ta dai Imran sai shigewa ya yi gida ya barshi a nan don ya san muddin ya ci gaba da sauraron shi, za ayi batacciya, amintar shekara da shekaru ta zama tarihi. Su Azizah me za su yi da gani na ba dariya ba. Nima dariyar ce kuma ta kama ni na taya su muka yi ta yi sai da muka yi mai isar mu. Na ce, “Ni yau na ga abin da ya fi karfina, kunyar duniya yau kam na gama jin ta, kin ganni kuwa goye a bayan acaba? Sai ka ce wata karuwa, kai Allah ka yafe mini”. Mama ta shigo tun daga falo take cewa, “Meye dalilin tahowa a bar Zaynab ta hawo acaba? Kuna tunanin in Abba ya ji daga ku har Yayan ku za ku iya kwanan dadi a gidan nan?” Suka yi tsit, na yi saurin cewa, “A’a, Mama wallahi ba laifin su bane, na bi wata kawata ne cikin kwatas din malamai zan amso (past question pepers) sai basu ganni ba suka taho”. Ta ce, “Rufe min baki, ai dama kullum ke a wurin ki basa laifi, in ban da iskanci a jira ki man ko a nemo ki, sai a taho a rabu dake? Ni kam ba da ni ba, Allah wannan Abba zai yi hukuncin sa, don Zaynab ‘yar aman ce a hannu na. in kuma da wani mugun abu ne ya same ki fa a cikin makarantar shima haka za a taho a rabu dake?” Ganin ranta ya baci ba da wasa ba, gaba daya muka shiga ba ta hakuri kar ta gayawa Abba har da hawayena, ta ce, “To gaya min gaskiyar dalilin tahowar a barta, in ba haka ba, ba makawa wallahi sai na gayawa Abba”. Na ce, “Wallahi laifi na yi masa”. Ta ce, “Shi waye?” a sanyaye na ce, “Ya Im”. Ta zaro mana ido ta ce, “Laifin me?” Hantar cikina ta kada, wani fitsari ya kulle min mara ban san takamaiman abin da zan ce ba. “……. Ai laifin da Zaynab ta yi mun Mama kema in kika ji sai kin hukuntata”. Gaba daya muka juya muka dube shi, yana bakin kofar bai shigo ba, hannunsa na dama dafe da kofar fuskarshi babu alamun wasa. Ya ce, “Mama Zaynab ce mai rubuta jarrabawa su Iftihal su kwafa, da na yi magana suka mai dani shashasha, har wata gadara suke wai ai malaman duka samarin ta ne ba abin da za su yi masu. Yanzu kamar ‘ya’yan V.C a ce suna aikata examination malpractice, wai kuma har suna gaya mun har bencinsu malaman suke rubuto musu su kawo musu. Shine yau na ce bari dai in je in genewa ido na me ake a makarantar nan? Wallahi Mama a kan ido na Zaynab zance da maza har layi ake a kanta, in wannan malami ya wuce sai wannan malamin ya zo. Wani kuma har da kwaso kudi a aljihu wai zai ba ta. Sun fi rabin awa a tsaye duk ina tsaye ina kallon ikon Allah, can kuma ba sai na ga an nufo ni ba, ko me za a ce min oho, na ga wannan rainin hankali da ake min ya yi yawa, ko ba ta sanni ba ai gaba nake da ita, ya dace ta nuna ta san girmana amma wallahi yarinyar nan kamar wani direban ta ne ya zo, kamar ba ta san da tsayuwata a wurin ba, kawai sai na ja mota na barta a nan, don wallahi da na biyewa zuciyata a lokacin dukan ta zan yi”. Mama ta samu kujera ta zauna tana kallon mu tana gyada kai cikin mamaki, duk muka yi tsuru-tsuru, ba ya ni da cikina ke ta kartawa, na soma kukan da nasani da haushin Imran. Mama ta ce, “Da gaske ne Zaynab abin da nake ji? Ke da nake yabon ki sallah za ki biye ma wadannan shashahun ki kasa alwala”. Ni dai ba abin da na ce sai “Ki yi hakuri don Allah Mama”. Ta ce, “Ai ba zancen in yi hakuri bane, zance ne na hukuma. Baban ku malamin makaranta ne, wadanda suka sa dokar duk wanda aka kama da (malpractice) a kulle shi shekara biyar da tara mai tsanani. Su kuwa malaman naku ko in ce samarin naku kora ne daga gwamnati. Ku sani Bindawa Proffessor ne da bai wasa a kan harkar ilimi da ci gaban sa, ku bar ganin ku ‘ya’yan cikinsa, wallahi daure ku zai yi har sai igiya tai rara…” Idon kowacce ya raina fata, ya yi narai-narai kiris ya rage hawaye su zubo. Cikin tashin hankali na soma yi mata rantsuwar wallahi, ban taba kwafar abin da suke bamu ba, su Ifty ne. su kuma suka ce wallahi ba su ake kawowa ba ni ce, karba suke don su miko min amma ba don su kwafa ba. Imran ya juya mana baya yana ta dariya, ta ce, “Sai magana ta biyu, tunda duk aure kuke so, to ku yin hakuri ku karasa jarabawar, yaya sunan shi mai son Zaynab din da suke rabin awa suna magana?” Ta juya ga Ya Im, ya ce, “Na ji suna cewa GG”. Ta ce, “In ma G&G ne babu laifi, zamu tura masa ya fito da zarar kun ka re karatun sai mu sha biki. Ke kuma Iftihal dama ba tun yau ba Shehu yake son ki tun kina karama….., auren naku shi zai fiye min kwanciyar hankali….” Ni da Iftihal muka soma share hawaye kamar mu mutu don bakin ciki. Ta dawo ga Azizah ta ce, “Saura ke, ‘yar kwalisa, Lawal wannan yaron na gidan Malam dan dakin Inna Rakiya, na yaba da hankalinsa, gashi da hakuri, na tabbata zai iya hakuri da iyayin ki, don haka zan yiwa Abba magana da daddare in ya shigo ya sanar da Malam din duka a hada ku a aurar, in ce ko shi kenan?” Ta mike tana shirin fita, Ya Im na take mata baya yana kara zugata wai hakan da ta yi shine dai-dai, gaba daya muka bita muka rungume muna kukan da bamu shirya ba. Na ce, “Wayyo Allah Mama ki yi min rai, wallahi yau ne kawai na taba sauraron GG a rayuwata, wallahi ki je makarantar ma ki tambaya”. Da kyar da sidin goshi Mama ta fasa niyyar ta na fadawa Abba, amma ta gargademu ta ja kunnen mu, suka rantse mata ba za su sake kwafar amsa ba, ni kuma na rantse ba zan kara kula GG ba sannan ta kyale mu. Amma kam a ranar mun dandana kudar mu, mun ga tashin hankalin da bamu taba gani ba. Barin ni da na tsani a zo a ce da Abba BABA SA’IDU ga laifina. Cikin dare duk su Azizah sun yi barci, amma ni kwance nake bisa filo ina ta bitar littafina. Ba sai na ji filona na wata irin girgiza ba (vibrating), sam ni na manta da wani abu wai shi waya da na tusa a cikin folona, na wancakalar da littafin na yi zaune dirshen a tsakiyar gado na ina ta raba ido don fahimtar ta inda karar ke fitowa, kamin in nutsu in fahimci daga cikin folona ne. A sannan ne na tuna da wayar da Ya Im ya raba mana da safe. Na mika hannu cikin sanyin jiki na zaro ta, an boye nambar mai kiran bayan ma ni ban shigar da sunan kowa ba. Cikin gajiyayyar murya na ce, “Yello!” Sassanyar ajiyar zuciya ya yi ta cikin wayar kawai amma bai yi magana ba, na sake cewa, “Yello!” Wannan karon a dan zafafe, nan ma shiru kama babu kowa a kan layin, wani haushi ya taso min, ina niyyar kashewa na ji ya ce, “Zaynab kema baki yi barci ba?” Magana yake kamar baya so, ko ko an tilasta mishi yinta. Na ce a raina, “Yau na ji ikon Allah, ka kira ni ina zaman-zamana sannan ka yi mun iko?” A fusace na ce, “Wai waye ne?” Murmushi ya yi, duk da ban ganshi ba na jiyo sautin murmushin nasa har cikin zuciyata, muryarsa kamar na mai fama da mura ya ce, “Plzzzzzzzz, ki yi hakuri da abin da ya faru dazu, komi da na yi na yi ne sbaoda KISHIN KI, in san kuma baka kishi sai a kan abin da KAKE SO…” Tsaki na yi da ya katse shi gabanin idasa tatsuniyar shi, amma hakika na yi mamaki. Ji na yi kamar ma ba dai-dai kunnuwa na suka jiyo min ba anya Imran ne? “Ni fa har yanzu ban san wa yake magana ba, saboda a sanina ban bawa kowa nambata ba, sannan me aka yi min ake bani hakuri? Da kyar idan ba wrong number ka kira ba”. Cikin zafi ya ce, “Sanin cewa baki baiwa kowa no din bane zai sa ki san da wa kike magana. Na yi mamaki da yawa a kanki Zaynab tun dawowa ta, na kuma ci gaba da yi a yanzu. Na ga sauyin abubuwa da yawa cikin kwayar idanun ki, wadanda a da ba sune ba. Na ga sauyuka da dama wadanda a da ba sune a tare da ke ba. Ban san yaushe kika koyi wasu bakin halaye masu kama da wulakanci ba wadana a gaskiya ni ba zan iya jurar su ba. Idan kuma kin ce haka za ki ci gaba, to wallahi zan fito fili in fadawa kowa a gidan nan abin da muke ciki….” Na yi murmushi mara sauti na ce, “Malam kuke ciki kai da wa? Ni na ji sunana radam a bakin ka amma ni har yanzu ban san da wa nake magana ba, kuma Hausar ka bana fahimtar ta, don Allah ka je ka koyo Hausa”. Daga haka na kashe wayar na yi tsaki, amma a zuciyata ina jinjina namijin kokari na. Da safe da na bude wayar (txt msg) na fara cin karo da shi daga gare shi. “Rashin sauraro na da ki kai a daren jiya, shi ya nuna kin fara sanin kanki”. Na yi tsaki na ce a raina, “Lallai ma Ya Im din nan ya ga wallena da yawa, har yanzu bai san wace ce Zaynabu-Abu ba, bai san wace ce Abun Faruq-Abun Baba Sa’idu ba. Bai san wace ce Kyautar Allah, Kyautar Inna Rabi ba”. Ko da wasa washegari bai yi gigin binmu makaranta ba, na fassara hakan da rashin son haduwa da su GG. Yammacin ranar mun dawo kamar kullum a gajiye, na ga wata bakuwar mota mai tsananin kyau a kofar gidan. Nice na fara shigewa cikin gida saboda sun tsaya amsar sakon Mama a hannun maigadi. Ashe da rabon zan yi mugun ganin da ban taba yi ba a rayuwata. Nasa kai a corridor din da ke tsakanin cikin gida da baskwata, wani lafiyayyen kamshi ke ta dukan hancina tun daga soron farko, ina iya jiyo shesshekar kukan mace, ashe Mami ce. Ta juya masa baya tana kuka shi kuma ya daura hannunshi bisa kafadun ta zai juyota ta fuskance shi, fuskar shi cike da yanayin damuwa yana yi mata magana kasa-kasa. Kallo daya na yi musu na ji zuciyata ne neman faso allon kirjina, saboda wani mugun kishin matar nan da Allah ya dora mini, wani makoko ya zo ya tokare ni, da gudu-gudu na karasa cikin gida na shige dakin mu na fada toilet na yi ta kuka har Allah ya gajisshe ni. Ina jin wayar da ke cikin filona na ta burari har ta tsinke don kanta. Bani na fito ba sai da alwalar sallar magariba, na dasa sallah babu sassautawa, domin tursasawa zuciyata fidda Imran a cikin ta. Na tabbata na fada a matsananciyar soyayyar Imran da harshen da ba zan iya bayyanawa ba. Kishinsa nake kamar in sa bindiga in harbe Mami, duk da ya fadi ba sonta yake ba. Sai dai ni kaina na san ba karamin yaudarar kaina nake ba, haka shi din, ba karamin raina mun hankali ya yi ba, da yake gaya mun wasu maganganu na yaudara, masu nuna min mai mata kamar su Mami Abdulhadi zai taba dubar karamar alhaki kamana dake tutiya da bazar Uban su da sunan so a duniya. Waya kam ya yi ta har ya gaji, kamin ya turo sako misalin karfe goma na dare. “Ki dauki waya ki ji abin da zan ce miki, rashin daukar wayar ki ba shi zai sa ba….” Sannan ya sake kira, wannan karon bayan kashe wayar da na yi, har bude ta na yi na zare (sim) din na sanya a dirowa. Muna kalaci da safe duk mun yi shirin tafiya, zuwan Shehu kawai muke jira. Ya turo kofar dakinmu ya shigo ko kayan barcin (pyjamas) dake jikinshi bai cire ba, babu alamun wasa ko kankani a tare da shi, idanun shi sun dan tasa alamun rashin wadataccen barci a daren baki dayansa. Suka duka suka fara gayas da shi, ya amsa ba tare da ya dube su ba idanunshi a kaina, ya ce, “Ya yi kyau, kuma abin da ki kai kin cancanci a a baki lambar yabo. Sai dai kar ki manta kina wahalar da kanki ne kawai a banza Zaynab wannan ba za ta fisshe ki ba. Gara ma ki fito fili ki nuna musu abin da kike boyewa, amma ni babu gudu babu ja da baya Zaynab, I said it infront of all those you are kidding (na fada a gaban wadanda kike rainawa hankali cewa) I LUV U very-very much!” [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Naki tashi, na kara matsawa jikin Malam sosai nace “Inna ya zaki ce in ta shi? Baki fara tambayar dalilin suman Malam ba, baki nemi dalilin tashin ciwon Baba Sa'idu ba?" Ta karfi tasa hannu ta finciko ni, ina tirjewa tana kara jana da karfin da na kasa amincewa na Inna na ne, ta jefe ni a daki tasa kuba ta datse mu. Imran ya bita da kallo, a ransa yana cewa ashe dai da gaske ne, da Iftihal ke cewa Innar Zaynab, mahaukaciya ce? Malam Ali yayi ajiyar zuciya, ya karanto karshen ayoyin suratul Hashri, yayi salati ga Annabi, ya yi istigfari, yayi hamdala ga Allah yayi tasbihi ya tsarkake shi, yace "hakika Ubangiji ba karamin hakuri yake da mu ba. Idan da zamanin sauran Annabawa ne, da tuni an kifar da mu. Idan da Ubangiji bai yiwa Annabinmu alkawarin ko me zamuyi, bazai kifar da mu ba, har zuwa tashin kiyama, da mai yiwa hukuncin mu sai ya fi na al'ummar Annabi Nuhu, yafi na al'ummar Annabi Ludu, yafi na Yunus yafi na Yusufa, ya kuma fi na al'ummar Fir'auna. Amma yana hakuri da mu, har zuwa sanda zai kamamu a hannu, ya tambaye mu yadda muka gudanar da rayuwar mu, abisa tsarin da yai mana ne ko a’ah? Ba karamin cuta Yahudu da Nasara sukai mana ba, ba kuma don komai sukai hakan ba sai don sani da suka yi cewa su dama taBaBBune, wuta ta tabbata a gare su. Don haka suka jamu a jikinsu suka dulmiyar damu da akidunsu da sunan cigaban, ilimi, wayewa, da 'yancin kai (independence). Su ZINA ce ta haifesu, a cikinta suka tashi, kuma a cikinta suke rayuwa. Don haka suke bakinciki da mu da muke da tsarkakakken asali, suka nuna mana ita din ba komai ba ce (Zinar), alhalin bakin-cikin da take haifarwa, ya fi jin dadin dake cikinta yawa. Banda tsayawa gaban Sarki Allah, ranar gobe kiyama”. Ya yi shiru yana share hawaye, Imran jikinsa yai sanyi, don ya fara shan jinin jikinsa, cewa Malam da Baba Sa'idu sun dauka ‘zina’ suke aikatawa shida Zaynab, shine dalilin shigarsa cikin halin da suka same su. Ya ci gaba da cewa “tsakaninmu da nasara sai Allah ya isa, don cuta kam ya gama yi mana, ya lalata tarbiyyar da iyaye, kakanninmu, sarakunan mu na gargajiya da malamanmu na addini suka wanzar da rayuwarsu a dora mu akai, kadan ne, kuma masu rabo, zasu gane hakan. Da in haifi 'ya'yan da zasu rinka aikata zina, gara da ban haifa ba, gara da nake haifarsu suna mutuwa wallahi….". Gabadaya falon sukace "Wa’iyazu billahi Malam, dukka 'ya'yan Musulmi 'ya'yan kowa ne, kada bacin rai ya kaika ga son kai, sai dai ace Allah ya shirya 'ya'yan musulmi bakidaya, ya ganar da su illar aikata zina, ya kuma basu iko da karfin imanin nisantar ta". Ya share hawayen da suka kara yanko masa, ya dubi Baba Sa'idu, wanda har yanzu numfashinsa bai koma da-dai ba, amma duk abinda Malam din ke cewa yana shiga kunnuwansa, yana gasgata kowacce kalma dake fita bakinsa. Kana ya maida dubansa ga IMRAN, ya dade yana kallon shi, da idanunsa da suka kada suka yi jajur kamar gauta, yace "Imrana!” Cikin kakkausar murya. Bai amsa ba, illa ya dago lumsassun idanunsa ya dubeshi, yana sauraron abinda zai ce da shi, tuni zuciyarsa ta gama sanin me Malam din zai ce? Kasancewarsa mai karantar mutum tamkar yadda yake karanta inji, ya kuma gane inda yasa gaba tun kamin bakinsa ya furta. Ya manta cewa ko zaka iya karantar mutum, bazaka iya karantar abinda ke karkashin zuciyarsa ba, domin ita zuciya wata abin sirri ce da Allah (S.W.T) ya bamu, domin Boye abubuwan da baki, ido da kwakwlwa ba zasu iya karantarsa ba. Eh, tabbas ya sunsani abinda Malam din zai ce, amma bai zaci zai yi GIRMA da bunkasar haka ba, bai zaci zai yi muhimmancin wannan ba, bai zaci kwakwalwarsa, tunaninshi, zuciyarsa da gangar jikinsa zasu kasa daukar nauyin abinda ke fita daga karshe daga bakin Malam din ba. Ya fi sakan uku bayan kiran sunan nasa da yayi, kafin ya ce masa komai, haka shima ko ta-tafas bai ce masa ba, balle ya nuna zakuwarsa ga son jin abinda Malam din zai ce da shi, wanda yake da yakinin ba mai dadin ji ba ne, ba kuma na tausasawa ba ne kamar yadda ya saba yi masa. "Meke tsakaninka da Zaynabu, ina nufin, me muka gani kuna aikatawa dazunnan kai da ita? Dubi mahaifinka, ko kana da masaniyar irin abinda kuke yi kai da Zaynabu, shine sanadiyyar shigarsa cikin wannan wahalar, tun shekaru goma sha takwas da suka wuce? Ya taBa gaya maka "ciwon zuciya” yake ba ciwon hawan jini ba? Ya taBa gayama da koda daya yake rayuwa?" Baiyi magana ba, amma fuskarsa ta nuna tsantsar tashin hankali da firgicin da kalaman Malam din suka jefe shi a ciki, yayi hamzarin duban Baban daya runtse idon sa a hankali, cike da nadamar wannan rana, cike da tunanin kodai kada ya bari Malam Ali ya fasa kwan ne? Shin idan Imran ya ji meke akwai tsakaninsa da Zaynab, da matsayin ta gareshi, zai ci gaba da yi masa wannan rungumar mai cike da kauna jin kai na iyaye da yayi masa? Babu shakka GIRMA ZAI FADI!, To amma kafin ya hana Malam Ali furtawar kamar yadda ya umarceshi, akwai bukatar sanin hakikanin meke tsakanin Imran din da Zaynab? Zargi kawai suke basu tabbatar ba, kuma abin da ya gani bai yi kama da babban abin ba, yafi kama da matsananciyar soyayya (romance), sai wata aba wai ita maganar aure, in haka ne fadin gaskiya ya zama tilas, in ba haka ba, wace hujja garesu ta hanasu yin auren? Lallai wanda ya rigaka kwana, dole ya riga ka tashi, kuma wanda yaki daukar shawarar na gaba da shi, yana tare da aikin dana sani. Da yabi maganar Rabi tun farko, na barin Zaynab a Gwarzo ta yi karatunta cikin mutunci tare da su Hafsisi, da duk haka bata faru ba. Da ina zata ga Imran din har su kulla soyayya? Da yayi mata aurenta a kauye, cikin rufin asiri ba tare da faduwar girma ba, tunda har yau in ka dauke Inna Dubu, Faruq da Inna Rakiya, babu wanda yasan Zaynabu-Abu wacece a gareshi? Gaskiyar Rabi ne zaman Abu tare da ita, shi ne babbar martaba da mutuncin yarinyar. Kuma kan-kan din da take da ita, tayi da-dai, bashi Sa'idu bane bata so ya raBeta, tattalin mutuncinta take. Baya tausayin kansa da Imran, kamar yadda yake tausayin, Zaynab, Allah Sarki! Shin ya zata ji a zuciyarta, idan ta ji cewa ba Inna Rabi ce mahaifiyarta ba? Ya zata ji a zuciyarta, Idan aka ce shine mahaifinta na hakika? Ya zata ji a zuciyarta, idan ya bayyana gareta cewa ya sanar da itane ta dattin zina? Duk kaunar nan da take masa, tabbas kiyayya zata koma mai tsanani, ninkin-ba-ninkin wadda Inna Rani ke masa. Wasu siraren hawaye suka fito daga idanuwansa zuwa cikin kunnuwan sa, musamman da yake a kife yake kwance flat, bisa cinyoyin Imran, yayin da Imran din ke shafa kirjinsa a hankali saboda bugun da zuciyar Abban ke yi, ji yake tamkar ya fiddo zuciyar Abban ya maida jikinsa, shi yayi fama da mai ciwon. Abba Baba Sa'idu, Uba ne na kwarai, abin alfaharin 'ya'ya da daliban UDUS bakidaya, dama al'ummar Nijeriya gabadaya. Kamuwar irinsu da ciwon zuciya ba karamin lahani bane ga rayuwarsu, ba karamin nakasu bane ga gudummawar da suke baiwa al'umma, musamman ta fuskar cigaban ilimi. A daular Usmaniyya gabadaya, a wani nazari da aka yi cikin shekaru ashirin da suka gabata, Jami'ar Sokoto na daga cikin koma bayan jami'o’in Nijeriya, amma tun daga zuwan jagorancinta hannun Sa'idu, cikin shekaru kalilan, za’a iya sanyata cikin sahu na hudu na jami'o’in Arewa dake kan gaba wajen bada shaidar karatu mai inganci da cusa kyawawan dabi'u ga dalibanta duk da cewa dama (Islamic University) ce. Saboda nisa da yayi a tunani, bai ji tambayar da Malam din yayi masa ba, ya sake kiran sunansa a karo na biyu tare da maimaita masa tambayar da yayi masa, yayi firgigit ya dube shi cikin nutsuwa yace "Ka kwantar da hankalinka Malam, wallahi-wallahi kaji rantsuwa na dan musulmi kenan, babu wani abu makamancin wanda kuke tunani da ya faru tsakanina da Zaynab, ni musulmi ne kuma nima ina tsoron Allah, ina kuma tuna ranar gamuwata da shi, ko bayan wannan Zaynab tafi karfin haka a gareni, tafi karfin in nemeta da haramun, sai dai in nemeta da AURE. In maisheta uwargida na uwar 'ya'yana saboda addini da tarbiyar ta, da kowanne namiji zai kwadaitu da zamantowar ta matar aure agareshi. Abinda kuka gani ba shi kenan ba, illa kun kawo wa ranku hakan kawai, saboda hakan da kuka riga kuka sa a ranku. Rungumarta kawai nayi ina rarrashinta ta amince in gabatar da zancen neman aurenta gareka, tana ki, don a cewarta matsayin mu ba daya ba, wanda ni ban taBa kawowa raina hakan ba. Amma a yanzu mun sulhunta a junanmu, albarkarku da amincewaku kawai muke nema, domin muna matukar kaunar junanmu". Ya dukar da kai yana wasa da kan wayar sa, saboda wata kunyar Malam din da tazo ta lulluBeshi irin wadda bai taBa ji ba. Baba Sa'idu cikinsa ne ya murda, sai far-far kawai tabbacin gudawa na haduwa, ya mike ya zauna sosai ya soma tari kuful-kuful, Imran yai hanzarin mika masa ruwan da ya bashi magani a kwano yana ta faman "sannu Abba”, Malam Ali zamewa yayi ya dau buta ya zaga bayan gida, fiye da minti goma sha biyar kamin ya fito yana takawa da kyar, domin ba duka ya samu yayi ba wata ta makale taki fitowa saboda tashin hankali. Yana shigowa shima Baban ya tashi yana dafa bango, ya dauki butar da Malam din ya aje shima ya zaga. Shiru-shiru bai fito ba, ba kuma wanda yayi magana a falon, daga baya Malam ya sake tashi ya koma bakin kofar ‘toilet’ din yana jiran fitowar Sa'idun, domin zuwa lokacin wadda ta makale masa ta dai-daita, itama ta yi shirin fitowa har ta soma mintsininsa ta fara zuba kadan-kadan, don haka Sa'idun na fitowa ya afka ya dinga shararata. Imran dai zaune yake tamkar an kafe shi, yana kallon su cikin nutsuwa daya bayan daya, a ransa yana cewa "ku gama gudawar, fargaba da tsoron na lalata muku 'ya, kuzo ku aura min ita in lalatata sosai da hujja, sai kace a kanku aka fara haihuwar 'ya mace, in bata ta din zanyi, me ya hana tun a can gidan mu inyi hakan, inda babu mai sa mana ido, sai anan? Kuma a dakin soro kusa da dakinka, wannan na shiga wannan na fita kuma kofa a bude? Don ni bani da wayo ko don kun maisheni mai karancin tunani? Yarinyar nan shekaru shidda muna tare da ita, duka a shekarun banyi hakan ba sai yau a gidan Ubanta? A gaban Uwarta a dakin Yayanta Haba! Ai keta haddin sai yai yawa. Inda sun san ita tuntuni ta shiryawa lalatar, har ta nemi ta lalatashi, kafin ta yi hankali tafi karfin zuciyarta, ashe da ranar dukkansu sai Darussalamu “kun san ba kwa son mu aikata zinar, maiyasa tun muna kanana ba kuyi mana aure ba, kamar yadda (S.A.W) ya umarce ku? Ni yanzu talatin nake neman rufawa, nayi karatu na dade ina aiki, cikinku wa ya taBa tarata ya ce Imran ya dace ka yi aure? Ita kuwa Zaynab shekarunta goma sha takwas, amma kuna cewa ba zatayi aure ba sai ta yi shekaru ashirin da biyu, ta san WACE CE ITA? Shin wane sani ne ga diya mace da ya wuce na tayi al'adarta ta farko a gidan mijinta? Allah ya halicceta da son kusantar da namiji, addini ya ce kuyi mata aure, tun bata kawo hakan ba (Shekara tara), amma baku yi ba, wai ku tayi ta karatu meye amfanin karatun diya mace, musamman na boko? In ma yana da amfani to yafi kyautatuwa tayi shi a dakin mijinta, amma ba’a gaban iyayenta ba. Sannan yanzu ku zo ku ishe mu Allah yace Annabi ya ce, bayan ku kun baro fadarsu tun ran gini, sai ranar zane zaku fada mana???? (To iyaye, maza da mata kuna ji fa). Bai san sanda yayi tsaki ba amma kasa-kasa, dai-dai sanda Malam da Baba Sa'idu, suka nabba’a a mazauninsu, amma wannan karon da bango ya jingina, bada jikin Imran ba. Imran din yayi saurin jawo tuntu dake gefensa, ya sanya masa har zuwa lokacin Abban bai kara yarda sun hada ido da shi ba. Malam Ali ya dube shi cikin karfin hali da karayar zuciya, yace "wato ita rungumar, a wajenka ba komai ba ce Imran, har kana kiranta ‘kawai’, ko kasan daka kama hannun matar da ba taka ba, gara ka kama sandar wutar jahannama?” Ya kara dukar da kai cikin girgigizawa "Na tuba Malam, kayi hakuri, ba zan sake ba, kuskure ne. Na tuba nabi Allah na bika, kada ka yi amfani da wannan a matsayin abinda zai hanaka aura min Zaynab, ban san yadda rayuwata zata kasance ba……". Duk dariyar da Malam din ke yi, bai san sanda hawaye suka zubo masa ba, shikansa Abban hawaye ya soma, Malam ya sa haBar taguwarsa ya share zufa da fuska duka, yace (yana mai kawas da fuska daga gareshi). "Aurenka da Zaynabu-Abu bazai taBa yiyuwa ba Imran, ka zamo musulmi na kwarai, mai yarda da karbar kaddarar yadda duk Ubangiji ya shirya masa rayuwa, hakan ne zai sa ka ci riba, kaga mai kyau a rayuwarka". Ya dago ya dube shi, ba tare da alamun damuwa ba ko mamaki ko kankani a tare da shi, ya ce "Hujja? Komi yana da dalili, to meye dalilinku na hana mani auren Zaynab, alhalin duk muna son juna? Inada wani mugun hali ne ka gayamin nayi maka alkawarin dainawa. Idan kuma kaima kana la'akari da hujjar Zaynab ne, na amince in dawo nan, in baro iyayena da 'yan uwana, in baro aikina da gidanmu dake saku tunanin ni wani ne, in dawo nan in zauna tare da ku, in ya so sai in dinga kula da gonar Abba dake nan…". Inna Dubu ta tashi zata fita, tana kuka kashirBan da hawayenta, bata iya jure ganin wannan abin bakin-cikin da ban takaici, ta wani bangaren abin tausayi. Har ta kai bakin kofa Malam yace da ita "dawo ki zauna, don kema wat shaida ce da zan gabatarwa Imran da Zaynab su yarda da hujjata". Ya maida hankalinsa ga Imran, da a yanzu ya koma bashi tausayi, duk kawaici, kunya da ladabi irinnasa, a yau idanuwansa a bude yake masa magana tabbacin suna neman kure ladabinsa, don shi baiga dalilinsu na son yi mai yawo da hankali ba, don kawai yana son auren diyar su, yana sonta yana kaunarta itama hakan, sai dai in abin akwai zalinci da son zuciya a ciki. Malam yace "ko daya bana la'akari da uzurin Abu, domin (inna Akaramakum indallahi ataqakum), watau mafi girmanku a wurin Ubangiji shine wanda ya fi jin tsoron sa, hakannan ban taBa daukar Ubanka a matsayin mai kudi ba, da shi da abinda ya mallaka da mukaminsa a gwamnati, ban san su ba, bana kuma son in san su, balle in ga girmansu. Har yau almajiri na nake kallonsa, wanda ya duka nan a gabana ina koya masa (Alhamdu), har kuma na saukar da shi Alqur'ani mai girma da sauran littafan addini. Don haka inda a ce Zaynabu 'YA TA CE, ba yadda za’a yi in hana maka aurenta, koda kuwa kai din dan shugaban kasa ne ba dan Sa'idu ba. To amma Imran ita Zaynab 'YAR SA CE, da ya haifa da jikinsa. Ina la'akari ne da ayar nan ta Ubangiji (S.W.A) dake cewa "hurrimat alaikum ummuhatikum wa banatikum wa khalatikum wa akhwatikum wa ummahati nisa'akum……. har zuwa karshen ayar. To ita ZAYNAB-ABU, 'yar sa ce, ina nufin kanwarka ce, ta jinni, tunda itama Sa'idu ne ya haifeta, kenan ta zama (muharramarka). Don haka maganar aure ta kau. Sai zumunci, wanda shi dama dole ne kuma ana yin sa. Yanayin rayuwa gami da take da fadar Allah da akai, shine yayi sanadiyyar hakan, ya kuma rubuto cewa Zaynabu bazata tashi a gaban iyayenta biyu ba, amma ta zauna na lokaci mai tsawo tareda mahaifinta wanda ita kanta bata san hakan ba. Imran, a matsayinka na DA NAMIJI mai cikakken hankali, ina fatan zaka fahimce ni, ka yarda da kaddarar da Allah ya daura maku, kada ka butulcewa mahaifinka domin ya yi tsarkakken tuba, tubanda Ubangiji (S.W.T) ya yi alkawarin karBar shi, wato tuban da akayi shi da tabbacin ba za’a sake komawa izuwa zunubin ba. (Kamar yadda Malam mai akhdhari (ahalari) ya fada). Wannan kuma tsakaninsa da Ubangijinsa ne, idan har ya yafe masa, mu nan bamu da abinyi banda daukar darasi daga gareshi, kada kace hakan zai sa ka daina girmamashi ko ka daina ganin GIRMANSA Allah ba zai barka ba, tunda ba kai yayiwa laifi ba, wannan tsakanin bawa da Ubangijinsa ne. Ka yi aiki da hankalinka na da namiji, wanda yafi na 'ya'ya mata. Ka ji tausayin mahaifinka, ka janye niyyarka na auren Zaynab ina kake so ya sanya kansa? Idan ka dage cewa sai ka aureta, abin dake Boye shekaru goma sha takwas a tsakaninmu dinnan dake zaune a dakinnan, sai Rabi da dan uwanka, zai fito duniya ta sani, wanda hakan zai zubar da GIRMAN mahaifinka, ya sanya rayuwar Zaynab cikin kuncin da bazata taba rabuwa da shi har abada ba, ya lalata mata rayuwa, ya sanya ta tsani kowa harda kanta kuwa. Kayi juriya ka karfafa imanin ka, ka yarda hakan Allah ya ga dama daku gabadaya". Sai ya soma janye jikinsa sannu a hankali daga kusa da Abban, tamkar yaga wani abin tsoro da kyama. Rokon Allah yake cikin zuciyarsa, idan mafarki yake ya farkar da shi. Ya koma kallon su a tsorace, kafin ya mike tsaye idanunsa a rufe, yaki budesu ya kalle su, don gani yake idan ya bude ya kalle su, to GIRMANsu da kimar su da ke cikin idanunsa ZAI FAdi. Ya soma magana yana ja da baya a hankali. “Baba Malam ina ganin GIRMANKA, ina darjanta furfurarka da farin gemunka, ina ganin kimarka da mutuncinka, kada kayi sanadin da zasu FADI a idanuna. Idan ba zaku bani auren Zaynab bane, na hakura, ba sai kun SHEGANTATA ba, ba sai kun lalata mata suna ba. Zan juri rashin aurenta amma ba zan juri ganin tagayyararta, a rayuwa ba. Ba zan bari wani cikin ku yayi mata wannan tozarcin ba, koda zan rasa raina ne Zaynab bazata rasa ‘identity’ dinta na Zaynab Aliyu Gwarzo ba. Zanyi shari'a da ku har kotun koli akan hakan, koda duk abinda na mallaka zai kare sai na karewa Abu martaba, da mutuncinta. ……. Me wannan baiwar Allah tayi muku da zafi, data cancanci irin wannan tozarci? Abba daure kace nine shegen, ba Zaynab ba. Wa zai aure ta? Wa zai ije mata bukatun gangar jikinta na shekara da shekaru ta hanyar aure, alhalin kun ce ita shegiya ce? In gaya maku gaskiya idan ma ba’a aure tsakanin Wa da kanwa, to daga kan mu za’a fara. Tunda kace ‘yar ka ce, to ina sonta, ina neman aurenta a hannunka V.C Sa'idu, don ni yanzu ka tashi daga nawa Baban na hakura na barwa Zaynab, ni na zama shegen na ji na yarda, na amince, ko zaku baiwa SHGE auren diyarku?" Ya bude idanuwan da ya rufe gabadaya, yana sauraro amsar su, bil haqqi, shi da zuciya daya yake Magana. Kallo daya zakai masa ka tabbatar ba’a hayyacinsa yake duk maganganun da yake yi ba, suna dai fita ne kawai daga fatar bakinsa. Ganin duk sunyi shiru sun dukar da kan su kasa, basu da niyyar amsa masa, ya sake jefosu da wata tambayar da ta addabi kwakwalwarsa; "Tukunnama in tambayeka Abba, ko kuwa Malaminka zan tambaya? Ta yaya akai ka zamo Uban nata? Kai ka fara auren Inna Rabin, ka saki, Malam din naka ya aura, koko yana aurenta, don ya baka daki a soron gidansa, kana kwana, ka nemeta har kuka yi cikin da kuka haifi Zaynab, saboda ka ganta ‘yar fara kyakkyawa……..?” Inna Dubu ta dauki warin takalmin shi dake dai-dai inda take zaune, ta saita bakinsa ta maka masa iya karfinta, jini ta hanci ta baki, ya soma bilbila, amma bai fasa magana ba "Kaima kenan da zamaninku baku san menene so ba, ka kasa kauda idonka akan Innar sai ni da na zo a wannan karnin, nasan menene abinda zuciyata ke so? Na san su waye mata irin Zaynab diyar Inna Rabi, shine kuke yi min bakin cikin, kar in dandani irin abinda ka dandana a jikin Innar, shine za’a ce wai Allah yace kar na aure ta, Allah bai ce kar ayi zina ba, sai ni mai neman aure ta tsaftatacciyar hanya. To ai Allah shi ya ce ayi aure, ba ayi zina ba, don haka zan auri Zaynab no matter what don ina sonta…, ba ruwana da wata rayuwarka ta can baya….., ba ruwana da wani 'yar ka ce tunda babu wanda ya shaidi aurenka da mahaifiyarta……” cikin kuka Inna Rakiya ta ce "Kai dannan, mahaifinnaka kake gayawa haka?" Ya maida kallonsa a kanta, idanunsa kuru-kuru kamar ya cinyeta "Inna shi bai yi tunanin watarana, zai janyo mana irin wannan mutuwar zuciyar ba, a sanda yake shan shagalinsa da Innar Abu? Bakya tunanin mu yanzu gabadayan zuri'armu ya lalata mana suna? A bar ta baiwar Allah Zaynab, da bata ji ba, bata gani ba, idan ta samu wannan almara ina zata tsoma zuciyar ta? Soyayya mai sauki ce, kuma ba dole bace, amma zuciyarta zata mutu. Duk wani buri da take da shi a rayuwarta zai zama TARIHI! kaunar da nake yiwa Zaynab, tafi gaban ta soyayya kadai, kaunarta nake kamar yadda nake kaunarsu Iftihal, ban taBa kawowa raina sha'awarta ba. Kawai inada burin ta zamo uwar 'ya'yana ne, saboda hakuri, tarbiyyah da juriyarta. Mace ce mai matukar juriya da fin karfin zuciya. Amma duk juriyar ta wannan al'amarin ba zata jure shi ba………”. Sai anan ne ya samu hawaye suka fito, amma tun sanda ya fara maganar idanunsa a bushe suke. Idan ka kalli Maigirma V.C Professor Sa'idu Salisu Bindawa, a wannan lokacin sai ya matukar baka tausayi. Lokaci guda shekarunsa guda hamsin da biyar, sun fito baro-baro akan kyakkyawar fuskarsa, wadanda ada jin dadi ke boye su, suna sake mayar da shi matashi dan shekaru arba'in a duniya. Babu shakka yayi nadama irin wadda bai taBa yinta ba a rayuwarsa. Ya dade yana tunanin zuwan wannan rana, wadda ko ba-dade-ko-ba-jima ya tabbatar babu makawa sai ta zo, amma bai taBa zaton zata zo mai irin haka ba, bai taBa tsammanin soyayya tsakanin dan lalenshi da 'yar lelenshi ce zata zamo sanadiyyar zuwanta ba. Allah ka yafe mana! A hankali Imran yabi bango ya durkushe akan kafafunsa, ya dunkule hannuwansa a kirjinsa hawaye masu zafi suka soma bi ta kasan idanunsa yana rokon Allah ya dauki ranshi kamin wannan abu da yake ji yazam tabbatacce, yasa mummunan mafarki ne yake yi ya farka. Baya tausayin kansa sai Zaynab, bai san sanda ya ce da karfi "Allah ya isa tsakanin mu daku… Abba!" Malam Ali ya mike ya dauki allon da yake yin rubutu kamin shigowar Abban ya kantara masa a tsakiyar ka, amma ba kakkarfan duka da zai mai lahani ba cikin kwakwalwaba, da karfi ya ce "Ina jiye maka fushin Mahaliccinka Imran! Na dauke ka yaro mai hankali, tunani, da rangwame cikin al'amarinka, shine zaka nuna min halin yahudawa na rashin girmama iyayen su? Wallahi idan kayi wasa sai Sa'idu ya rigaka shiga Aljanna, fushinsa ya kaika Sa'ira. Domin dai shi lafiya ya rabu da iyayensa suna masu sanya mai Albarka. Ni dake tare da shi shekaru arba'in da doriya, bai taBa batamin ba, kullum albarka nake sa masa na kuma tabbata albarkarce ke bibiyarsa har yau. Kai din nan baka isa ka shiga tsakanin bawa da mahaliccinsa ba. Idan Ubangijinsa ya yafe masa, kai keda kaicon fushin iyaye a rayuwa……” Abban ne ya yi tari yayi gyaran murya, muryar sa bata fita sosai, in banda tsit din da dakin yayi, da maiyuwa ba za'a ji abinda yake cewa ba. "Kyaleshi ya zageni son ransa Malam, ina girman yake? Ai ya riga ….YA FAdI! Saidai ka gaya masa ba rarrashin sa muke ba gaskiya ce kawai muke gaya mishi domin hakkin hakan da Allah ya dora mana, amma ba tsoronshi nake ji ba, illa son tserar da shi damu kanmu daga fushin Ubangiji mai tsanani da zai same mu in muka bari ya auri shakikiyarsa. Na fada na kara Zaynabu 'YA TA CE, ke nan KANWARKA ce, don haka BA ZAKA AURE TA BA! Ba kotun koli ba, ai an gaya maka in banda mu da muke zaune a dakinnan da Faruq da Innar Zaynabu, babu wanda yasan al'amarin nan. Don haka dauko filo ka turmushe kowannenmu, har sai ya daina numfashi, ita ma Innar ka je kayi mata hakan sai ka dauki Zaynab ka tafi da ita in da ake sonta, inda ba za'a tazortata ba, tunda mu ka ce BAMA SONTA! Sharri ne zamu yi mata don mu hanaku aure. Sai ku tafi can inda ake sonku, inda ba’a sanku ba ayi muku auren don kuwa mu nan musulmi ne 'ya'yan musulmi rainon musulunci, babu mai aura maka Zaynab a matsayinta na kanwarka ko a lahira bamu da hakkinka tunda mun gaya maka abinda baka sani ba. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Abban kuwa da suka kai wa karar korarsu ya yi, ya ce Imran ya kyauta mishi, ya yi mishi dai-dai har mota zai sake masa don gode mishi a kan hakan, yanzu haka samarin banza muka fara kulawa. Suka shiga yi mai rantsuwar Allah ba abin da muke yi. Ya jawo wayar cajinshi ya soma tsula musu suka kwasa da gudu wurin Mama suna neman mafaka. Ni kadai na san dalilin Ya Em na yin hakan, sai ko Allah da ya halicce shi. Idan na zauna ina tunanin al’amarin sai in gicciye in yi ta kuka, in ji na tsani kaina amma shi Imran din nayi-nayi in tane shi na kasa, sai kaina da a kullum nake kara tsana. Duk kuma wannan barazanar tashi ta daure fuska, sababi gami da zare ido basa kara min komi sai abin nan dake kara kamari game da shi a tare dani. Idan abin ya ciwo ni sai in sanya takalmi in dauki hanyar dakin su. Faram-faram sai na kusa kaiwa sai in yi tunanin Ya Faruq suna tare ko yaushe, kuma dai kwata-kwata babu wata ‘ya mace a gidan da na taba gani ta shiga baskwata. Shi kuma kamar ya sani ko kuwa mai karantar abin da ke cikin zuciya, sai ya rage shigowa gidan in ba lokacin cin abinci ba, shima din fuska a daure. Yana ci yana hade girar sama da ta kasa, yana harare-harare da sexy-eyes dinsa masu kara dimauta ni, inda mu kuma duk zamu bi mu kasa sukuni ko kwakkwaran motsi har sai ya tashi ya bar wajen, in da zai barbade ni da kamshin daddadan turaren sa ‘eternity moment.’ Idan ya bar wurin, ji nake kamar zuciyata zata fashe, domin ganin shi ma kadai, sauki ne ga ciwo na. Muna zaune a falo da daddare ana hira da Mama, ya shigo yana goge gilashinsa da hankici, ya dubi Mama ya yi murmushi ya ce, “Maman ‘yammata mu fa gobe zamu daga kodago, zamu fara shiga ofis in Allah ya yarda”. Ta ce, “To Imran Allah ya ba da sa’a ya kade sharrin makiya da na abin hawa, yasa a fara a sa’a, ya fidda haram daga cikin halal…” Ya ce (cikin jin dadin addu’ar ta) “Amin-amin Mama, na gode da addu’ar ki”. Ya cira kai ya dube mu a gicciye. Ni dai zuciyata kadai ke fat-fat kamar in daura hannu aka in saka ihu, jin cewa Imran zai tafi Abuja bakin akinsa da babu ranar zuwa, aikin da an fi watanni uku da samuwarshi suna ta yi mai jeka-ka-dawo, sai yanzu Allah yaiwa takardun daukar fitowa kamar yanda Iftihal ta gaya mani. Ban yi aune ba sai ga hawaye sun shararo mani, na yi saurin sar da kai, na yi azamar dauke su da yatsuna biyu ban kuma yarda na dago ba balle wani ya ga halin da na shiga. Yana murmushi kamar ba shi ba ya ce, “To ‘yammatan gaya, ‘yan gatan Mama, shalalen Abba me zan samu ne?” Gaba dayanmu mun yi mamakin yadda yau ya kula mu har yana janmu da wasa, to ko don ya ga tafiya zai yi ne? Sai muka ji banbarakwai aka rasa mai amsawa. Mama ta ce, “Ba abin da za ka samu daga wadannan ‘yammatan nawa, tunda ka hana masu zukar iska da rawar gaban hantsi, ni na san yau ransu kal kamar takarda”. Ya yi dariya ya ce, “Wai haka Zaynab?” Ko dagowa ban yi ba, sai ya mai da akalar tambayar shi kan Azizah kada Mama ta gane akwai wata ‘yar tsama a tsakaninmu. Cikin lallashi yake cewa, “Yanzu don Allah don Yaya na son ‘yan kannen shi su zama zarra a karatu sai su ji haushin shi? Su ce ya takura masu? A zatona wanda kake kauna shi kake so da ALHERI (sunan littafin Takori mai zuwa), amma ba za ku san gata nake muku ba, sai a nan gaba idan kun fito da A3, B3, C3 a NECO da WAEC”. Duk suka yi murmushi, nan ma ban dani. Karewa ma sai na mike kamar mai son shiga toilet, ya bini da kallo kamar zai ce wani abu, ya ga babu alamun wargi don haka ya sa kai ya fita yana cewa “Mu kwana lafiya Mama”. Mun yi shirin kwanciya Iftihal ke cewa, “Tabdijam! Kwanan nan mugun mutumin nan zai soma kama millions, wulakanci kuma zai karu”. Azizah ta ce, “Gaskiya kam, aiki a AGIS din Abuja (Abuja Geographical Information System) ai sai mai sa’a, ni dama Faruq ne ya samu ba shi ba, ‘yammatansa ma na san yanzu duk watsar dasu zai yi a samo (new catch) na Abuja”. Iftihal ta ce, “Duk abin shi ai bai isa ya watsar da Adda Mami ba….” Na yi lamo cikin bargona ina sauraron hirarsu mai ban haushi tana kona zuciyata, wani makoko ya zo ya tokare ni a kahon zuci. Na shiga zubar da hawayen da ban san dalilinsu ba, na tafiyar Imran ne? Na jin zancen ita wannan Mami ne? Ko-ko na wulakancin shi ne wallahi ban sani ba. A ranar na rantse yadda na ga rana haka na ga dare, saboda KISHIN ita wannan Mami da suka ambata dake kokarin hanani numfashi. Tun bayan tafiyar Ya Im duk sai na zamo wata sukuku babu kuzari, ramata ta soma fitowa fili, haka su Azizah suka fara damuwa da rashin walwalata, da rashin cin abinci na. Bayan suna ganin yanzu ne ya dace in saki jiki, mu ci duniyarmu da tsinke tunda dodon namu baya nan. Basu sani ba, sau dubu gara sanda yake nan din, ko ban ganshi ba zan iya leken shi ta window, zan jiyo muryarshi in yana dariya da mutane, zai mana fada, zai hantare mu in ji muryar sa wanda duk wannan sauki ne a gare ni. Amma yanzu ko turaren shi babu a gidan, ya bishi can inda yake, sai ni da aka bari da radadin zuci. ‘Performance’ dina a school kullum yana karki babu bana iya barci sai murkususu a kan gado, sai na shiga karewa a tsaye kamar kudin guzuri, kasusuwa suka yi min sarka a wuya, idanuna suka burma loko kai ka ce farfadowa na yi daga doguwar jinya. Hajiya Azumi ramata ta fara damun ta, rashin walwalata ya soma addabar ta, ta yi tambayar duniyar nan na ce mata babu komi sai ciwon kai da nake fama da shi da daddare, ta rubuta magani ta ba Shehu ya sayo min kullum ina ta sha, amma sauki sai wajen Allah. Rannan ta ce, ko dai tunanin Rabi da Malam ne? Na bita da eh. Ta ce, in kwantar da hankalina, ba sati biyu ya rage mu samu hutu ba sai in tafi. Shima Faruq bayan sati biyu da tafiyar Imran gurbin da ya nema na karatun kwamfuta a (Informatics-Singapore) ya fito ya fara shirye-shiryen tafiya. Hankalina ya kara tashi, domin Faruq ne kadai nake iya gayamawa damuwana, amma shima wannan ba zan iya fada mishi ba, ban san yadda shima zai dauke ni ba, tunda wanda Allah ya doran lalurar a kansa, a lalatacciya kawai ya dauke ni. Ya fadi ya kara fadi, duk da bai fito fili ya ware ni ba na san dani yake. Wani lokacin in na zauna ina tunanin maganganun shi na baya, kamin in fada mishi ciwon marata, sai in ga kamar abin da yake nuna mini a zahiri ba haka yake a zuciyarshi ba. Akwai dalilin shi na yin hakan. Amma in na tuna kalaman shi “jarababbiya, duk wanda ya aure ki ya shiga uku!” Sai in tabbatarwa kaina Imran wulakanta ni kawai yake. Washegarin tafiyar Ya Faruq a cikin ajinmu kuka kawai nake su Iftahal na rarrashi na, sun dauka kukan tafiyar Ya Faruq nake basu san abin ya fi gaban nan ba. Gaba daya rayuwar Sokoto ya fice min a rai, ina ganin nisan kwanakin da suka rage tafiyana gida gaban Innana mai sona. Na yi dakacen zuwana gidan baba Sa’idu, don na san da a ce ina gida gaban Innana da duk haka ba ta faru dani ba, da ban dora idanuna a kan Imranan nan da ke wahalar da rayuwata a yau ba. Lokacin fita cin abinci ya yi, Anti Rose malamar da ke koyar damu (compuer-studies) ta ce kowa ya taho (computer-room) za ayi (practical) bayan cin abinci. Kowa ya tafi sai ni kadai aka bari a ajin, na kifa kai cikin benci ina ta rafzar kuka. Kasancewar na fi kowa iya (computer) a ajinmu yasa Anti Rose ta sanni, ta ke kuma nan-nan dani. Sai dai ko ita ta yi kuka dani a jiya kan makina na test dinta da ta ce ba ta ji dadinsa ba. Ba yadda Azizah ba ta yi ba in tashi mu tafi na ce ban zuwa, dole suka kyale ni suka bi sauran ‘yan ajin suka tafi suna ta kakabin sai ka ce a kaina aka fara tafiyar dan’uwa. Can sai ga Anti Rose da kanta ta zo ta zauna a kan tebirina. Anti Rose tana da aure da ‘ya’ya biyu, za ta yi shekaru talatin a duniya, ‘yar kabilar Igala ce. ta daura hannunta a kaina tana lallashi na ta ce in biyo ta muje bayan ajinmu. Muka zauna a kan kujeru masu fuskantar juna, cikin dabaru irin na manya take tambaya ta abin da ke damuna nake neman gurgunta karatu na a shekarar da ya dace in kara azama, wato (semi-final). Da fari kuka nasa mata, ta kwantar dani a kafadunta na yi kukana mai isata, ba ta katse ni ba har sai da na yi shiru don kaina. Zuciya ta nutsu da Anti Rose, don sai na jita kamar Mamana saboda yadda ta nuna matukar damuwa da halin da nake ciki, yadda ko iyayen rikona basu damu da su tirkeni haka don jin abin da ke damuna na hakika ba. Na warware mata tun zuwana gidan Abba, da farkon haduwata da Imran shekaru uku a baya, amma al’amarin bai zafafa a gareni ba sai a wannan shekarar. Na warware mata irin abin da nake ji cikin jikina da zuciyata baki daya game da Imran, wanda na kasa boyewa har ya gane, da kuma abin da ya ce dani, da sabuwar halayyar da ya tsiri yi mana daga baya, wanda na san don ni kadai yake yi tunda su Ifty ina ruwan su? Sai kuma tafiyar da ya yi ba zato na ba tsammani, wadda ta janyo min azabar zucin da nake ciki yanzu. Anti Rose ta dade tana dubana kamin ta jefo mun tambayar da ban tsammana ba, “Zaynab kina karatun soyayya, ko kuwa kina kallon fina-finai irin na batsa?” Na zaro ido cikin tsoro, firgici da tashin hankali, na shiga rantse mata bana yin ko daya, ni ban ma san su ba, ban san a inda ake samun su ba. Ta sake kallo na sosai ta ce, “Shekarun ki nawa?” Na gaya mata goma sha biyar. Ta ce, “To kin san abin da ke damun ki a kan Imran?’ Na girgiza mata kai da karfi, idanuna kuru-kuru cike da tsoron amsar da za ta bani, kirjina na harbawa kamar ana luguden sakwara, haka gaba dayan kafafuna sun sage, makoshina a bushe rayas! Ta ce, “Lust! Ko kin san wannan kalmar? Kin fada a soyayyar sa, wadda matsananciyar sha’awa ce jigon soyayyar taki. Kin shi sha’awar shi fiye da kaunar shi (lascivious passion), wanda hakan ba karamin hatsari ne ga rayuwarki ba, kasancewarki yarinya karama cikin shekarun (adolcense) wannan bai dace da ke ba. Ki godewa Imran domin shi mai hankali ne, mai kaunar ki ne, ba don ya kasance mai kaunar ki ba, tunani da hangen nesa, da tuni ya biye miki kun aikata ba dai-dai ba. Abin da na fahimta a labarinki shine, da fari Imran yana son ki, ko-ko in ce ya fara kaunarki. Amma da ya fahimci irin taki soyayyar, ke jigonki sha’awa ce ba kauna ba. Shi yasa yake hora ki, yana so ki kiyo kaunar sa ba sha’awarsa ba, ta hanyar nuna miki kuskuren ki a fili. Amma don son zuciya irin naki kin sa kafa kin take ke dai kawai ya yi miki abin da kike so. Ina kara gaya miki Imran mai kaunar ki ne domin da baya kaunar ki da tuni ya yi amfani da damar da ya fahimta daga gare ki ya gurbata miki rayuwa, yadda rayuwar ki za ta gurgunce, abin nufi, bayan kawar miki da wannan sha’awar ya barki, a lokacin da ke kuma ba za ki iya rabuwa da shi ba, hakan zai zamo nakasu ga rayuwarki kuma har abada ba zai kaunace ki ba, ba zai aure ki ba in ba wani babban rabo ba, tunda ya riga ya keta miki mutunci a banza. Na yi mamakin inda kika samo wannan halayen, gaki dai a fuska yarinya saliha (innocent) mai addini, wadda kuma ga dukkan alamu kin fito gidan tarbiyya za ki tsinci kanki cikin sha’awar aikata ZINA tun baki gama sanin kanki ba……” Tunda ta fara magana hawaye nake yi, amma da ta zo nan sai na dago ido cikin matsananciyar razana na dube ta. Wannan dama shine ZINA, da Innana ke tsorona da aikatawa, da Innana ta gaza samun kwanciyar hankali a gaba dayan rayuwarta don tsoron kar in aikata, da Ya Faruq ya wanzar da muhimmin lokacinshi wajen gaya mun illar ta, da abin da take haifarwa. Amma rana daya na so in rushe tarbiyyar shekara da shekaru, in rushe ginin shekara da shekaru, in rugurguza zuciyar Innana dake cike taf da bakin cikin rayuwar da har abada ba za ta daina ba, wanda na tabbata ZINA ne tushen bakin cikinta ko ba a fada min ba, idan na yi la’akari da irin kalamun da ke fita bakinta. Anti Rose ta lura da irin razanar da na yi, ta girgiza kai domin kara tabbatar min da gaskiyar kalamanta, ba kuma tare da ta bukaci jin komi daga gareni ba ta ci gaba da cewa. “Na yi mamaki na biyu kasancewar kin ce bakya karance-karancen banza ko kallace-kallace, don haka duk yadda akai wannan abun a cikin jininki ne, ina nufin a halittarki ne, wanda ba sai da Imran ba, da kowa ma da zuciyarki ta kyasa, in har zai amince miki za ki iya aikatawa Zaynab….” Na rushe da kuka, na ce, “Don Allah Anti Rose ki daina gaya mun haka, ki daina yi mun mugun fata, Allah ya tsareni. Kalamanki kamar digar dalma suke a zuciyata, Allah ya hana, Innana da Ya Faruq sun dade suna min gargadi a kan hakan, Allah ya dauki raina kamin ranar da hakan za ta sameni…… Innana ta ce da in aikata zina gara mata mutuwana da rayuwata, nima mutuwar na fi so da in aikatata….” Ta ce, “Ki yi shiru Zaynab in gama maganata sannan mu samo solution ga problem dinki, kuka da maganganun fatar bakinki ba shine ba, ba za su amfane ki da komai ba saboda ba ke ce kike sarrafa zuciyarki ba….” Na tsagaita da kukan, amma ban bar hadiyar zuciya ba, kallon ta kawai nake da sauraron sabuwar bakar maganar da za ta yabo mani, domin cikin kalamunta kakaf babu na tausayawa, sai masu bakanta zuciya, wanda in na nutsu na yi amfani da hankalina zan fahimci gaskiya kawai take gaya mini. “Zaynab idan kina son Imran, kina kaunar da ya zamo abokin rayuwar ki, zuciyar ki ba za ta fi ba da karfi ga son ku aikata abin da kike so din nan ba, illa kokari za ki kiga kin mallake shi gaba daya, wato ya zamo (life-partner) dinki na har abada ta halastacciyar hanya! Amma ina tabbatar miki Imran ba zai taba yarda ya aure ki a haka ba, tunda ya san ciwon kansa. Ko ya aure ki hankalinsa ba zai kwanta da ke ba, zai dinga tunanin ranar da baya nan, ko ranar da ya baki wannan abin da kike son shi kenan za ki daina son sa ko komawa wani, tunda hakan kawai kika sawa zuciyarki. Soyayya ta kwarai kuma ta gaskiya ba ta nufin physical relationship kadai, wato (gamayyar jiki). A’a, matual intimacy, understanding one another (kusanci da fahimtar juna) sune tubali na kwarai wajen gina soyayya. A duk inda soyayya ta rasa wadannan to jigonta sha’awa ne, kuma sunanta rusasshiya. To ke Zaynab a sayayyarki babu wannan, kuma ina kara gaya miki Imran yana kaunarki! Amma ba zai nuna miki ba sai kin koyi kaunar shi, domin ke sha’awarshi kike yi ba son shi kike ba. Kinga ke musulma ce, a addininku zina ba ta kamace ki ba, ko mu da muke addinin kirista a wurinmu zina haramun ce. Sai dai da sani muke takewa. Ki yi kokari ki fi karfin zuciyarki ki koya mata son Imran da kaunar sa, ki daina sha’awar sa kwata-kwata, ki dauki komi nashi a ba komi ba, a matsayin wani wanda bai isheki kallo ba, wani wanda ba shi da abin da zai burgeki da shi. Ki daina kawata komi nashi a ranki, ki dauke shi da da babu duk daya. Ki zama mai kame kanki da bakinki da idanunki a gaban sa. Ba shi kadai ba, duk wasu maza ma domin da ba don kin yi katari da mai tsoron Allah ba da tuni farin cikin rayuwarki ya zama tarihi! Ki samu wani abu wanda zai dauke miki hankali daga tunanin Imran, ki daina zama ke kadai. Ki mai da hankali a kan karatun ki za ki sha mamakin Imran. Sai ya tsugunna da gwiwoyinsa yana rokonki ki aure shi Zaynab, ni na gaya miki. To a sannan ne kika ci ribar soyayyar ki sai ayi muku aure. A sannan kina da ‘yancin baiwa gangar jikinki abin da take so, za kuma ki mallaki Imran din da kike mafarkin samu tare da komi nashi, daga kanshi har yatsun kafa cikin kwanciyar hankali, amma ba yanzu ba da ko sakandire baki gama ba”. Hankalina ya kwanta da shawarwarin Anti Rose, a raina ina godewa Allah da ya matsi bakina na gaya mata matsalata, da tuni na san na kai kaina na baro, don tuni na fara tunanin in fara kula samarin da ke zarya a kaina, wanda na san dukkansu abin da yake kawo su kenan ba na Allah da Annabi bane. A wani bangaren godiya nake kwararawa Ya Im, Imranan da bai biyewa son zuciyata ba, gaskiyarsa ne da ya ce kuruciya ke dawainiya dani. Na kara jin GIRMAN sa da kimarsa gami da mutuncinsa sun karu a idanuna. Sannan wani nutsattsen abu mai dadin da baya misaltuwa ya tsarga a zuciyata (so na hakika), wanda babu sha’awa ko son zuciya a cikinsa. Na dago sannu a hankali ina murmushi na dubi Anti Rose na ce, “Ko na gama sakandire Anti Rose ba za a barni in yi aure ba, amma zan iya rike kaina. Babana da Abban Imran sun sha cewa sai na yi shekaru ashirin da biyu, wato a lokacin na san kaina, na san ko ni WACE CE”. Anti Rose ta ce, “A kan me? Sam, idan kin kare makaranta Imran ma ya nuna a shirye yake da ya aure ki, ki fito gar da gar ki nuna amincewar ki. In ta kai ta kawo ko uwar dakinki ne ki samu ki rufe ido ki gaya mata matsalar ki, na san za ta fahimce ki ta kuma fahimtar dasu. Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, ba ke kadai ce hakan yake faruwa dake ba, sannan you are not the last! Akwai da yawa, halitta ce”. Na ce cikin tsananin girmamawa, “Anti Rose na gode”. Ta ce, “Kada ki damu Zaynab, ai ke ‘yata ce. duk wasu yara da aka kawo mana nan amana ce aka kawo mana, yadda ba zan so ‘yar cikina Nkiru ta shiga halin da kika shiga ban ganar da ita illa da kuskuren dake ciki ba, haka ba zan kyale ki ba. Ki daure ki bi shawarwarina Zaynab, am sure you’ll laugh some day! Na tabbata miki za ki ga yakini a ciki. Duk wani ci gaba da aka samu, ki neme ni ki sanar dani in san a matakin da muke, da kuma (next-step) da ya dace mu dauka”. Muka mike dukkanmu ni na nufi aji, ita kuma ta nufi hanyar (staff-room), ina tafiya kamar a kan kwai, ina godewa Allah a zuciyata da kuma Anti Rose. A wani bangare kuma jin kunyar kaina nake da kunyar Ya Im. Wai kirista ma kenan ta san illar zina (abin da iyayenmu mata da yawa basa ba da hankali a kai su fadakar da ‘ya’yansu mata a wannan zamanin). Wallahi sai na ji ni sakayau, kamar an dauke mun wani nannauyan dutse a ka. Na alkawartawa raina jajircewa da jurewa bin shawarar Anti Rose, insha Allahu! Sai Ya Im ya yi mamakina, ya kuma yi nadamar jefa ni a halin da ya jefa ni ya tsallake ya barni, maimakon ya zauna ya ganar dani a matsayinshi na mai hankali fiye dani. Tun daga ranar na soma azumin tadauwa’i wanda in na yi yau gobe ba zan yi ba (wannan Mazon Allah (S.A.W) ya yi ikirarin sa maganin gusar da sha’awa ne) kuma alhamdulillahi na ga nasibi a ciki, domin jina na yi kamar ba ni ba na koma ZAYNABU-ABU na kamar yadda nake a gaban Malam da Innana, ban san wani wai shi Imran ba. Ga nafilifilin dare ina yi, haka nan bana rabo da karatun Alqur’ani dare da rana, ko ina zamu akwai dan karamin Alqur’ani na bugun Misra cikin jiki, ko cikin aji in ba abin da nake zan fiddo ina karantawa madadin hira ko zama shiru. Su Iftihal da Mama sun ji dadi kwarai da sauyin rayuwata ta kunci da kuntatawa kai, da suke tunanin saukin ciwon kan da nake fama da shi cikin dare na samu. Muka zana jarrabawar mu cikin kwanciyar hankali muka samu hutun karshen shekara, inda in mun dawo zamu shiga aji shida. Murna wurinmu kamar me zamu zamo seniors wanda hakan shine babban burin Azizah a ce ta gama makaranta ta shiga jami’a. A kullum ta kan ce tana son zama Adda Mami ne budurwar Ya Im, sbaoda haduwar ta. Azizah tun muna kanana muguwar ‘yar iyayi ce, komi nata sai designer, don haka duk ta fimu daukar ido. Ni da Ifty rayuwarmu ba yabo ba fallasa, domin bamu da karya kuma bamu da karanta, in ka dube mu za ka san ba abin da muka nema muka rasa. An shirya tafiya Bindawa dubu dangin Abba, daga nan kuma za a dubo Malam Ali a kuma barni in yi hutun kirsimeti na a can. Su Azizah sun ce Porthearcourt za su gidan Antin su in sun dawo, don haka tun ana sauran sati daya muka soma shirye-shirye. Ni dai farin ciki har guda biyu ya tarar mani, ga murnar ganin iyayena don rabona da Gwarzo watanni shida kenan cif, don a wancan hutun ban je ba mun tafi yawon bude ido na yankin Senigal gaba daya gidan. Murna ta biyui kuwa zan kara samun nutsuwa da hutun zuciya ta hanyar yin nisa da duk wani abu da zai tuna min Imran. Na san yanzu su Hafsisi ma duk sun zo hutun zamu TUNA BAYA…. su debe min kewar su da na kan samu kaina da yi a yawancin lokuta, domin dai kowa ya bar gida….. Hausawa suka ce wai gida….. ya barshi. Abba ya raba mana kudi kamar ko yaushe zamu Gwarzo ko Bindawa don yin tsaraba, bayan nashi da baya fasawa. Duk da Inna Rabi ba ta taba yin amfani da tsarabar da nake kai mata ba, a kan idona take rabarwa kishiyoyinta ko almajiran Malam, hakan bai sa dai-dai da rana daya da zan je na fasa ba. Wannan kuma nasihar Abba ne, ya kan ce, “Ba ta yi amfani da shi ne abin nema ba Zainabu, albarkar ta muke nema”. Don haka muka shiga kanti muka soma ragargazar sayayya. Na kan saya mata dirkeken vasiline ne (Bebe and Maman) da manya-manyan gwangwanin NIDO da MILO da sauran kayan shayi, sai sinkin sabulun wanka, omo, da na wani da turamen atamfofi biyar manya da kanana. Mun dauko hanyar Katsina cikin babbar (peageout 506) din Abba mai cin mutane goma, hudu a layin farko, hudu a kujerar baya, biyu a gidan gaba. To Abba ne shi kadai a gaba, mu da su Hajiya Mama da sauran yara muna baya. Abba yana ta yiwa Shehu direba fadan ya ja mota danja ba ta ba shi hannu ba shi dai baya daddara da shiga kurkuku. Azizah tana ta dariya domin ta tsani Shehu. Ta ce, “Anti Abu za ki iya tuna ranar da su Ya Im suka dauko mu daga makaranta ranar da aka saki wankin kashi? Ya Im yana ta balbalemu wai ashe Shehu ne ya ba shi haushi, ya taho daukarmu ya wuce danja ba ta sallame shi ba, ashe akwai ‘yan sanda a kusa suka cafkeshi shi da motar, aka aikowa Abba shi kuma ya tura Ya Im ya fiddo shi. To ashe haushin Shehu ne mu ma ya shafe mu, ya kusan cinye mu, amma kin ganshi bai daddara ba, da Abba ma a mota bai fasa ba”. Mama ta buge bakinta ta ce, “Sa’anki ne? Bana son rashin kunya”. Hajiya ta ce, “Ai ita in ba ta yi labarin an sa Zaynab wankin kashi ba bata jin dadi”. Abba ya juyo kadan da waya a kunnensa cikin mamaki ya ce, “Wankin kashi? To ke me kika yi suka saki wankin kashin?” Na dukar da kai ina murmushi ina tuno fuskar GG a ranar da maganganunshi, ban san sanda na yi dariya ba. Su Azizah dama kiris suke jira suka shiga taya ni muka yi ta yi, har cikinmu nya kulle amma na kyafta musu ido kar su fadawa Abba don fada zai balbale mu da shi fiye da fadan Imran, ya ce dama ba karatun muke ba sai shashanci. A Bindawa ni ‘yar gida ce, kowa na sona saboda nutsuwata da ta sha bamba da ta su Azizah. Bani da rawar kai ko kadan ba wai yabon kai ba. Haka nan a ko yaushe kokari nake in ga ban zake ba a al’amarin iyalin Baba Sa’idu (I always limit myself in to hierarchy of numbers). Ko abu aka bamu mu ukun nan bana fara dauka, sai Iftihal sun bar wanda basa so. Hakan da nake yana da dada musu, yana kuma kara musu kauna ta. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: GIRMA YA FADI ! 3 Na zauna dum, naki ko motsi, har ya gama fiddo jakunkunan da yazo da su a but din motarsa, ya zagayo ya bude min kofa ya ce "you are welcome to gwauro's house…" na hadiyi miyau da kyar nace “zai fi kyautuw ka fara shiga, ka yiwa mutanen gidan bayani na, ba wai kawai su ganni a kansu ba, idan sun yarda da bakuntana falillahil hamdu, idan basu yarda bama babu damuwa, sai muje ka kama mun (Guest House) wannan ma ba karamin taimaka ne kayi mun ba and I really appreciate”. Ya sarke 'yan yatsun shi cikin na juna,yayi baya dasu suka bada kara, kas. Yana murmushi yace "you seem lacking confidence in everyone' kina da gaskiya, Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro ne. Allah ya kiyayeki da kwana a (Guest House), domin da jin muryarki an ji 'yar mutunci, wanda ta san ciwon kanta. Ki yarda da ni, bani da niyyar cutarki, hanyace ta hadamu kuma Allah ya kulla zumuncin mu. Yadda kowanne dan uwa na jinni, ba zai ci amanar 'yar uwarsa da suka fito ciki daya ba, haka ba zanci amanar ki ba. Feel free with me, am not that type of person, don haka fito ki biyo ni, nayi miki alkawarin ba zaki yi nadamar bina ba”. Sai kawai nayi kundumbala na bude motar na fito, muka jera zuwa ciki, yayin da maigadi ya biyo mu da kayan sa. Tun daga falo ya daga murya yana cewa (Manma na dawo), daga can kuryar daki ta amsa “mon fils tu ed rtour (sannu da zuwa dana)” kafin ta dogaro sandarta ta fito tana laluben bango. Idanuwanta a bude farare tar-tar amma na fahimci bata gani. Da sauri ya karasa ta lalubi kanshi ta rungume suna magana cikin harshen su. Na yi tsaye tamkar an kafeni, ina kallon dattijuwar da nan take wani abu ya tsirga min a cikin kirji, a dalilin kamanninta da Innata. Ya ce “bani kadai bane Manma, ina tare da bakuwa ne, har da ita 'yan fashin suka tare mu, gashi bakuwa ce a Nijar shi yasa na taho da ita, ta sauka a wajen mu kada ta fada mugun hannu" tace “ina fata kasa an kamesu duka? Tunda ka tafi nake maka addu'ar Allah ya kara daukakaka akan aikinka” da alama bai ji dadin hakan da tace a kunnena ba, ya basar ta hanyar kamo hannunta zuwa kujerar da nake. Tasa hannu tana lalubani sai kyalle take ji. Na zare niqabin ta shafa fuskata sosai, sai kuma tayi murmushi tace “budurwa ce ko? Da alama zatayi kyau, tunda ga dogon hanci ina ji, gashi kace ba daga alkaryarmu take ba". Na daga ido na dubeshi yana kallona, da baki a bude, amma ya kasa magana. Ta ce "kawo mata ruwa mana? Ko sai na buge maka kai da sandata?” Ya hadiye mayataccen kallon mamaki da tsoron da yake mani, ya nufi kofar da jikina ya bani kitchen ne, ya dawo da gorar ruwan (Ragolis) da lemon (Don Simon) masu sanyi, sai raba suke, yake ya ja tebur ya aje mani har yanzu idonsa akaina, ya ce “Laliya bata zo ta dafa miki abinci bane Manma?” Ta lalubi kujera ta koma ta zauna ta ce "bar Laliya da son kudI, yanzu haka wai ta tafi karBo zakkane gidan KANGIWA, bayan albashinda ka bari na bata jiya-jiyannan". Ya hade rai sosai yana cewa "ni kam zan sallameta, ya zan dauko yarinya ina biyanta, domin ta kula da cikin uwata amma ta fita ta bar min uwa da yunwa, Allah bata isa ba tayi kadan, ko ita 'yar Uban wane ne” daga ni har gyatumar dariya muka yi, ya soma tattare hannun rigarsa da alama kitchen din zai shiga da kansa, ta ce "dadi na dakai kenan Mon Amour (masoyina), babu hakuri. Mutumin dake yi maka hidima kullum ranar Allah, rana daya da bai samu yayi ba sai ka yi masa uzuri". Ya ce “nayi uzurin Manma, me kike so na dafa miki cikin mintuna goma sha biyar?” Ta ce “dafa mun kabeji, bakuwarka kuma ka tambayeta abinda take so" ya juyo gareni "bakuwata ke kuma mai kike so?” Tsohuwar tace "au ko sunanta baka sani ba?” Kunya ta kamani, domin ban kyauta ba, na ce “sunana Zaynab, shine bai fada min sunan sa ba Mama, shi yasa nima ban fada masa ba". Yayi murmushi, amma bai dago daga abinda yake yi ba, wato zuba lemu a tambulan ya kai bakinsa, ta soma laluben sa wai zata dake shi, ta ci karo da bango kamin ta kai kas yayi maza ya cafo ta, ya kwantar da ita akan doguwar kujera, ya ce "dukkan ku kuyi hakuri, sunana mai tsada ne. Ina fadarsa ne kawai ga matar da nake matukar so, don haka Manma ki tambayamin bakuwata, shin ta shirya amsa na a matsayin mijin aurenta, in gaya mata sunana?” Kafin gyatumar ta amsa na yi hanzarin tarar numfashinta da cewa "ban shirya ba, ba kuma zan amsa ba, don haka ka rike sunanka mai tsada, bana son ji”. Ya russuna ya kwantara da kansa a cinyar gyatumarsa, cikin matsananciyar nadama yace "ina fatan ba fushi kikayi da tsokanata ba?” Nace “ta yaya zanyi fushi da mutumin da ya karBi bakuncina, alhalin bai san ko ni wace ce ba, bai ji tsoron kada in cutar da gyatumarsa dake da lalaru ba? Bai sani ba mutum ce ni koko ina daga jinsin jinnu? Bana daga cikin mutanen dake yin fushi da wanda yayi musu alheri, komai kankantarsa. Daga baya kuma ya bata musu, sai iny masa uzuri. Jeka dafowa Mamarmu abincinta, mon amour, ko ba haka ne sunan da na ji Mama na kiranka ba?” Ya mike yana dariya yace "inda kinsan menene ma'anar Mon-amour, da baki kirani da shi ba". Daga kwance tace “rabu dashi diyata, ko kin rasa masoyi me zakiyi da wannan tsololon?” Daga can (kitchin) ya amsa “lala Manma, amman kin yanke ni. Na rantse, duk fadin garinnan, kafin a samu saurayi mai kiba ta aiki ne ja" ta ce "a inda babu masu kibar ba". Haka sukayi tayi tana tana yankansa yana kare kansa, kamar wasu kaka da jika. Akwai alamun shakuwa da matsananciyar kaunar juna a tsakaninsu. Yana ji da ita, tana ji da shi, sun fahimci juna, don haka ne bata wani tsaurara magana a kaina ba, don tasan ba zai kawo mai cutar ta ba. Cikin mintuna goma sha biyar din da ya ambata, sai wani irin kamshi ya game gidan gabadaya. Ya iso rike da kwanon silver mai fadi, dafadukan kabeji ne da aka dafa ruwa-ruwa, an kuma yanka kabejin manya-manya. Ban taBa ganin irin wannan abincin ba, kamar in tambaya amma ina tsoron gwasalen da ya yi min dana nuna ina son jin sunan sa. Don haka naja bakina na yi tsit. Ya koma ya shiryo min farin kuskus da aka dafa da koren wake da karas sunyi shar a ciki da miyar hanta, da aka yanka hantar kanana-kanana, a gefe kuma soyayyen nama ne irin wanda ake soyawa a ajiye, domin bukatar gaggawa da lemun (7-alive) ya ce “to Zaynabu, aci da hakuri kinsan girkin gwauro ne" Maman ta ce "gwauro, ko tuzuru?” Ya koma gabanta yana bata kabejin a baki da cokali, yace "duk wanda kuka ga ya dace da ni, dai-dai ne." Maman ta ture lomar da zai sanya mata a baki, ta ce "nidai don Allah ka daure kayi aure Babana, na gaji da wannan wahalar da kake da ni bata dace da kai ba, da wane zaka ji? Da wannan aikin mai hatsari koda kula da gyatumarka, alhalin kai baka da mai kula da kai?” Ya sunkuyar da kai kasa bai ce mata komi ba. Da lama bai so tayi maganar a gabana ba. Na sauko daga kujera na dawo gabanta na karbi silvern a hannunsa, nace “ni idan na baki zaki ci? Ki yi masa hakuri Mama aure ai lokaci ne" na cigaba da bata tana karba tana ci bata ce komai ba. Ban juya na kalle shi ba amma jikina ya bani kallona kawai yake yi. Sai data koshi na bata ruwa tasha, sannan na karasa cin nawa, na lura har zuwa lokacin zaune yake a inda yake, bai tashi ba. Na daga ido na dubeshi, don ganin abinda ya hana shi Magana, fararen idanunsa har yanzun akaina suke, cikin kollon da ba yau na fara ganinsa a idanun maza ba. Na ce cikin basarwa “kai baka ci abincin ba" ya lumshe ido a hankali, maimakon ya masa min abinda na tambaye shi, sai ya mike yana cewa “idan kin gama kiyi amfani da wannan dakin, (ya nuna dakin da dan-alinsa) duk abinda zaki bukata akwai a ciki, domin kanwata ke yin hutu a dakin idan tazo daga makaranta, duk abinda babu kiyiwa Mamana Magana, zata fada miki inda yake". Ya fita daga falon ba tare da ya waiwayo ba tace "yarinya jeki kiyi sallar azuhur, ki kwanta ki huta zuwa la’asur, ai kinga duniya nidai wannan aiki bana sonshi, to ya kafe ne, amma wannan sai da rai dame yai kama?” Na so in tambayeta kowa ne irin aiki yake wanda bata so? Naga wannan ba damuwa na ba ne. Damuwa na shine in samu masauki, in gabatar da abinda ya kawo ni, sannan in nemi dangin Innata. Kenan abinda ya kawoni daban, suma rayuwarsu daban. Saidai babu shakka tsarin rayuwar su shi da mahaifiyarshi ya burgeni. Cikin 'yan awannin da nayi tare dashi, na fahimci abubuwa da dama game da shi. Duk matar da tayi sa'ar aurensa ta yi babbar sa'a, domin zata zauna lafiya. Kasancewarsa mutum mai saukin kai da duk wasu qualities da ake nema daga da namiji, uwa-uba irin mazannan ne da albarkar Uwa ke bibiyarsu, saboda tsananin biyayyar da suke mata da nuna jin kai a gareta, tamkar zasu kwanta mata. Karfe tara na dare muna falo tare dashi muna kallon labarun Jiha, duk da cewa ba abinda suke fada nake ji ba, kasancewar faransanci ake yi amma ai ina ganin hotuna, aka nuno 'yan fashinmu da aka kama daren jiya, ina kallonsa yana ta murmushi ko me ya tuna? Oho can kuma ya dubeni ya ce "wai don Allah menene a katuwar jakar nan ne da kika riketa kamar rai?” Na harareshi, Maman tace "yau naji ikon Allah, wannan shine kaka uwarka ta haifeka, wai naci abinci acikin cikina ace in amayar da shi aga kalarsa. Akan me zata gaya maka abinda ke cikin jakarta? Kana binta bashi ne?” Ya yi dariya yace "Allah Manma, in da kinga irin rikon da ta yiwa jakar, duk karfin dan fashinnan kasa kwatarta yayi a hannunta, sai babbansu yace "ku miko min ita in rage dare da ita, tunda ta hanamu jaka, ta bamu abinda yafi jaka" ta wawuri filon kujera ta saita inda yake azaune ta maka masa, bata san cewa ni ta makawa ba. Ya dinga yi mata dariya ya tashi ya fita ba tare da ya lura da (wallet) dinsa data fado daga aljihun gaban rigarsa ba. Na kai hannu na dauka na bude, don tsabar neman magana irinnawa, kudi ne irin nasu (Saifa) a jere gwanin ban sha’awa. ina zaro ID card kamin in duba sai gashi kamar an jeho shi yayi wuf ya karBe yace "Eye, bin kwaf, na tambayi menene a cikin jakarki, ance nayi miki tambar kaka Mamanki ta haifeki, shine ni zaki yi mun tsirara?” Na fiddo ido nace "ka fassara wane irin tsirara kake nufi, kada Mama ta dauka ‘nakedness' wannan kazafi ne," ta wawuro kofin dana cika mata da ruwa ta kwara masa ta ce “fita ka bawa mutane wuri, kasa yarinya agaba da magana kamar Aku? Ni ban san ma yaushe ne bakinka ya bude ba". Yana kokarin hada kwayan idonsa da nawa, yayi murmushi “nima ban san sanda ya bude ba, Manma, ba mamaki sabida zuwan Zaynab ne". 'Yar tsohuwar taji kunya, tayi gum, da bakinta, ta kurawa allon talabijin ido kai kace tana ganinsu, ta koma sauraron abinda ake cewa, can kuma tace "kaga bana cikin shirmen ku, karo min sautin, naji kamar ana ambaton diyata”. Kyakkyawar fuskarta ta cika akwatin talbijin din, kamar ta fito tayi magana. Kasancewar (t.v)n katuwar gaske ma’abociyar kyakkyawan hoto (flat-screen). Tana gabatar da jawabi cikin faransanci da accent din Paris mai burgewa, a wani taron bude makarantar yaki da jahilci a babban birni Niamey, Nuratu Mainasara ce. Ni kadai naji ina gwama numfashi, domin yakar burgenin data yi da matsananciyar kiyayya. To amma ko (hasidin iza hasada), dole Nuratu ta burgeshi. Hutu da jin dadi sun Boye zahirin shekarunta, sun maidata kamar wata matshiya 'yar shekara ashirin da biyar, ko ni da nake budurwa in my tenth ba zan nuna mata komai ba, sai a zaBe ta da gudu a barni. In kuwa aka koma ta fannin gyaran jiki sai ka dauka tana ‘modeling’ ne. Duk wannan kallon kurullar da nake mata, da hanci da nake hurawa, ashe yana hankalce da ni. Ya fice bai kuma dawowa ba. Gaba dayan hankalin Maman yana kan akwatun talbijin, na matsa jikinta sosai nace "Mama a ina gidan talbijin din garin nan ya ke ne?” Tana fadamin ina daukewa da biro cikin ‘jotter’ na, nace “baku da gidan Radio ne?” Ta dauko fankon idonta ta daura mini, ta ce cikin zargi “me ya hadaki da gidan radiyo da talbijin?” Nayi murmushi mai wanke zargi nace “lah! Ba wani abu, cigiya nake so in bayar a kan dan uwana da ya Bata, shine kuma dalilin barowata gida, ance ana kyautata zaton an ganshi a cikin garin nan." Jikinta yayi sanyi tace "amma da kin gayawa Mon amour, wannan karamin aiki ne a gareshi, cikin kwana daya in har yana cikin garin nan zai nemo miki shi." Na yi shiru ina tunani, wannan na nufin shi dan sandan ciki, ko kuwa Security na jiha (SS). Gaskiya kam biri ya yi kama da mutum. Kenan shine yayi cunen da aka kama 'yan fashin mu? Dole in yi taka-tsan-tsan dashi kenan kada ya zamo silar rugujewar cikar burina. Gaskiya mana bai tsaurara tambaya akaina ba, me nazo yi, wa nake nema da sauransu; a tafin hannunsa kawai yake kallona. Jin nayi shiru tsohuwar tasha jinin jikinta, tayi nadamar sakin bakinta da katoBarar da tayi, sai ta yi hanzarin gyara zancenta da cewa “Ina nufin zai iya sawa a nemo miki shi, tunda shi dan gari ne kuma namiji. Amma mace kamarki tace zata yi neman wani cikin babban gari irin Damagaran, ai ta hada kanta da aiki ". Na yi murmushi nace "wai ai cigiya kawai zan bayar" ta fada mini kwatancen nan ma na dauke da birona ba tareda ta san ina yi ba. Washegari mai aikinta Liliya ta dawo, sai muka hadu ni da ita muka shirya abin karin kumallo, cikin dan lokaci na saba da ita domin 'yar kauye ce ta sosai mai shegen surutun tsiya. Cikin dabara muna hira da ita na sako zancen Mainasara, nace “na ji ace jiya kinje karBar zakka, ke nan Mainasara tana garin nan?” Ta kama baki ta ce "tabdI, bafa ita ce take rabon zakkar ba, aikowa take yi, ita tafi zama Niamey sabida acan mijinta da 'yan uwanta suke. A gidan kakanta ne ake rabon zakkar cikin (Kangiwa Estate). Gabadaya tushen su arziki ne domin marigayi Kangiwa Mainasara, kakanta kenan, yayi shugaban kasar nan shekaru ishirin a baya. Babanta Alhaji Sani Kangiwa, yayi ministan kudi anan Damagaram. Bayan ya sauka ya nemi kujerar Gwamnatin mu, gab da zai lashe zaBen ya je Nijeriya kai diyarshi neman magani sukayi hatsari shi da ita suka mutu, Nuratu kadai ta tsira. Saida ta yi shekaru masu yawa a Nigeria, rana daya sai gata ta dawo, shinefa tun daga lokacin ta rungumi siyasar mahaifinta, ta kuma sami nasara a kowanne fanni na rayuwarta, duk a dalilin kyakkywar zuciyarta da taimakon talakawa. Ba don neman kudi take siyasa ba, sai don daukaka tushenta a tsakanin sauran jihohi tsararrakin ta. Idan nace zan gaya miki abinda wannan baiwar Allah ta mallaka a kasar nan, cewa zakiyi karya ne domin babu wata mace cikin kasarnan gabadaya data mallaki rabin-rabin abinda ta mallaka, to amma ita kanta gada ta yi. Tana da rijiyar man fetur nata na kanta, don haka gidan mai wannan tanada akalla guda goma na kashin kanta” ta sunkuya ta tube takalmanta, irinnasu ne tafka-tafka na fata “hatta wadannan takalman da muke sawa, da jakunkuna da muke ratayawa da sauran kayan amfanin cikin gida da ake sarrafawa da fata kamar su tuntu, filallika da sauran su da akafi amu gidan manya duka daga fatar Mainasara ne. kasurgumar 'yar kasuwar fata ce da take baiwa kasashen Italiya, Farisa da Tailan (Thailand) suna sarrafawa zuwa takalman kwalisa, da ake shigo mana da su. Nuratu nada bankuna na kashin kanta, wadanda mafi yawa dukiyarta ce kadai a ciki, wadanda duka ta gaje su ne daga Kangiwa, kada ki dauka mahaifinta ne kadai dan sa, a’ah, yana da wasu 'ya'yan duk suna Niamey, suma suna da gadon arzikin su dai-dai da nata. Abinda yasa ta zarce su kuma ya kara mata arziki fiye dasu shine kasuwancin fata data fi maida hankali akai. Kiyi fatan Allah ya hadaku watarana a cikin gidannan, zakiyi bankwana da talauci…..". A razane na daga ido na dubeta “a cikin gidannan?” Na fada cikin raina, amma a zahiri murmushi nayi. Cikin raina nace ko a mafarki kada Allah ya hada ni da ita balle a zahiri. A fili kuwa sai na ce "nan gidan kuma?” [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Dana tabbatar Yaya Halima ta yi nisa a barcinta, sai na dora mata a gefen filonta dai-dai inda tana bude ido zatayi tozali da ita. Na mike na dauro cikakkiyar alwana na shimfida darduma a tsakar gida, na dasa Sallah, yi nake kamar bazan daina ba, ina rokon Allah ya yi min jagora, ya kareni daga sharrin abin hawa dana mutum da aljan, a cikin wannan tafiyar da zanyi. Har aka yi kiran assalatu. Na samau jam'in sallar asubahi ina idarwa na koma dakin na canza kayan jikina, na fara da sanya ‘vest’ Kaman yadda yake a al’adata kana na daura atamfa (Super Holland) shudiya mai ratsin ruwan hoda da kore, na fiddo sarkarnan na daura a wuyana, kunne da hannayena gudun kada wani ya kwace jakar, na kawo bakar abaya (after dress) mai kauri na dora, na kawo niqab na rufe fuskata ruf, sai kwayar idanuna kawai, na rataya jakar hannuna wadda take mai girma sosai da takalminta marassa tudun dunduniya, (suna cikin kyayyakin da iyalin V.C suka hada min a dawowata), hatta abayar da ke jikina sabuwa ce dal a ledarta, Hajiyar Imran ce ta bani, a matsayin sallamrta, ban dauki kaya ko kala daya ba sai na jikina, komi ina yinsa ne cikin takatsantsan, yadda na tabbatar motsina ba zai tada ta daga nauyayyan barcinta ba. Har na fito na sake komawa ina kallon Yaya Halima, dake barci cikin nutsuwa, amma ga busassan hawaye nan like a idonta. Tausayinta ya kamani, na tabbata nayi sallama da mai kaunata. Ji nake kamar ina yi mta kallon karshe ne. Na juya da baya da baya na fito daga dakin sakamako wata zuciyar dake neman raunana min gwiwa, da tunanin anya abinda kike shirin yiwa Faruq da Halima kin kyauta? Da gudu-gudu na karasa soro na zare sakatar, a lokacin da na jiyo motsin fitowar malam Harisu mijin Yaya yana fitowa daga bandaki, da yake yau ba'a dakin Yayar yake ba, yana dakin amaryarta Hadiza ne. Na soma taku a hankali a gefen titi, garin babu haske sosai domin ga dukkan alamu alfijir bai gama ketowa ba, misalin karfe biyar da rabi na asubahin safiyar litinin. Idan ka ganni a lokacin sai na baka tsoro, saboda shigar bakaken kaya da niqab dake fuskata, hatta takalman kafata bakake ne kirin. Ina tunanin yaushe zan kai tasha da wannan tafiya da nake yi mai kama da ta mai ciwon cinya, sai na kara sauri. Gab da zan shiga tashar garin Gwarzo wata bakar mulmulalliyar mota mai walkiya (pg 406) dana tabbatar ta Ya Faruq ne da muka dawo cikin ta jiya, ta zo ta gilma ta gabana, na yi saurin boyewa a bayan wata Daf da tayi lodin shanu zuwa Lagos, cike da mamakin me ya fito da Ya Faruq cikin wannan duhun asubahin, kuma ina zai je? Domin in banyi kuskure ba, zance hanyar fita gari ya dauka, ko dai Kana ko kuma Sokoto. Na yi ajiyar zuciya cike da wani matsanancin tausayinshi daya tsirga mini, shin ko yaushe Allah zai kuma yin saduwar fuskokinmu? Shin ko yaya zai ji a ransa, idan ya sami wasika ta? Abubuwa ne da idan na tsaya tunanin amsar su, zai sani fasa kuduri na in zauna tare da su, wanda zaman ba wani amfani ke gareshi ba, illa in shirya nadar bakin cikin rayuwar shegantaka cikin garin Gwarzo da dangin Faruq . Kada Allah ya nuna min wannan auren. Na karasa cikin tashar wani dan kamasho yana ta tambayata "Hajiya Kano, Kaduna, Lagos ko Abuja?” Hawayen ne dai suka kara ciko idona, ban san sanda bakina ya furta ba a hankali "Nijar”. Yyace babu motar kasar Nijar a nan, sai dai ki hau ta Katsina ki sauka a Jibia, daganan sai ki hau ta Nijar din” bani da zabi banda na ce masa “to", ya yi min jagora zuwa wata (Peugeot Station Wagon) mai zuwa garin Jibia, na biya kudin da suka cajeni na nufi can ‘seat’ din baya na zauna a jikin taga, ina ta kalle-kalle na tunda nasan babu mai gane ni, balle a kaiwa Malam labari. Sai da muka Bata a kalla rabin awa har na fara tunanin sauya mota, kada Yaya Halima ta tashi tasa mijinta ya biyo bayana, ni ko na rantse ko zan dinga kwana a kango, ba zan kara kwana a cikin garin Gwarzo. Sai Allah ya kawo pasinja hudu ris a lokaci daya motar ta cika, muka daga zuwa garin Jibia. Sha biyu da rabi na rana muna cikin tashar garin Jibia. Ba da wani Bata lokaci ba direbanmu ya sanya ni a motar Niger ita ma peogeut ce, wani yaro ya zuro min tallar gorar Yoghurt din (Mai dabino) mai sanyin gaske, sai a lokacin na tuna rabona da abinci tun kokon da muka sha kwanaki biyu da suka wuce da marigayiya INNA TA. Na karBa na biya tare da ledar ruwan (pure water) guda biyu, kafin minti daya duk na zuke su. Na fiddo (Al'ma'asurat) cikin jikata na soma karantawa har motar ta cika, muka tasamma Jamhuriyar Niger. Da aka zo (boarder) wato iyakar Nijeriya da kasar Nijer ne muka samu mukai sallahn azuhur da la'asar (kasaru), bayan gama bincike-binciken su suka daga mana kafa muka wuce. Tafiya ake babu cin zango akalla awanni biyu, sannan ne na soma hango Dogayen RAKUMA da rairayin SAHARA. Wata nutsuwa da ni'ima sauka a zuciyata, muka shiga cikin Maradi. Sai na daga niqab dina ina kallon mutane irin INNATA; farare sol, masu fararen idanu, dogaye masu lange-langen jiki da yalolon bakin gashin kai. Na maida nikab dina na rufe a sanda muka shiga cikin tashar da za'a sauke mu. Na fito daga mota nayi mika sosai, kasusuwana suka ce kakas, na matsa ga direban daya kawo mu nayi masa sallama, ya amsa nace "don Allah Yayana Damagaran zani" ya ce "Wai, ashe kuwa kina da sauran tafiya, bus zaki hau koko fijo in hadaki da wasu direbobin?” Na ce “gara bus din, saboda bana son irin wannan gudun saida rai da kuke, yayi yawa” yayi dariya yace "da bama gudun, da yanzu baki shigo Jamhuriyar Niger ba. Amma in gaya miki gaskiya zakiyi dare, ki kuma yi saukar dare, domin tafiyace ta awanni uku a gabanki kafin ki kai Damagaram tunda kince a bus zaki. Ga kuma motar can ina hangowa fasinja biyu ne kacal a cikinta, don haka babu lokacin tashinta koda za’a kwana ne kuwa sai sun cika zasu tashi. Don haka ina baki shawarar ki nemi wajen saukar bakI, ki kwana, gobe in Allah ya kaimu kiyi sammako domin hanyar bata da kyau" na yi tsuru-tsuru a raina nace na shiga uku ni Zaynab! Ina zani in kwana ina 'Ya mace? Kai gara duk abinda zai faru ya faru amma ba zan yarda da kowa ba, mutum abin tsoro ne, kuma mugun mutum bashi da kama a fuska. Na nisa nace indai akwai motar to ka taimaka ka sani, saboda ban san kowa a garinnan ba, kuma kasancewata mace, kana ganin ya kyautu inje Hotel in kwana ni kadai?” Ya girgiza kai “a’ah bai kyautu ba kam, kinyi tunani yarinya, shige muje, waccan (J5) din Damagaram zata je, Allah ya tsare ya kaiku lafiya". Nice a kujerar karshe cikin mota J5 mai zuwa garin Dagamaran daga MaradI, gajiyar mota gami da duhun mangariba daya fara shigowa suka saukar min da kasalar data sanyani gyangyadi a hankali, daga nan kuma sai barci na sosai, na kwanaki biyu cif da ban samu nayi ba. Bani na farkaba sai da naji rurin motar ta soma tafiya wato pasinja sun cika, na duba agogon hannuna misalign karfe shabiyu na dare. Naji zuciyata ta buga, nayi dakacen karbar shawarar direbannan. Tafiya ta mika duhun dare ya shigo sosai muna ta wuce bukkokin buzaye wani lokacin kurar sahara ta turnike sabida rashin kyawun birjin ta yadda direban ke kasa ganin abinda yake gabansa duk da fitilar motar mai hasken gaskece. Na maida kai na kwanta jikin kujerar gabana. Barci na yayi nisa cike da mafarkai barkatai, masu dadi da marasa dadi duk a game da abinda zan tarar a tafiyar da nake yi. Wanda ya fi daukar hankalina shine na Innata, cikin korayen kaya ciki wani wawakeken koren lambu, zaune bisa wata kujerar azurfa sai murmushi take, fuskarta cike da annuri. Dana karaso kusa da ita sai ta ce dani "na gode Kyauta, da cika min burina na shekara da shekaru da zakiyi, wato neman Nuratu. Sai dai bana farin ciki da kudurinki akan mahaifiyarki, domin iyaye duk yadda suke, duk lalacewar su, sunfi karfin ayi ramuwar gayya a kansu…” Daga haka ta shige cikin koren lambun nan, ba ko waiwaye, ta barni anan ina cizon yatsa, ina son ta tsaya in yi mata bayanin dalilina na daukar fansa akan 'yar uwarta? Sai bata bani wannan damar ba. Ta juyo tana mai daura hannu bisa bakaken laBBanta ta ce "Shhhhh! Nuratu mai kirki ce". Daga haka ta shige abinta, ko waiwaye bata sake yi min ba…… kuuuuuuuuu! karar wani irin cin taya da neman hantsilawa da motar ta yi, tare da ficewa da tayar baya tayi ta nufi jeji, motar ta tsaya cikin kudurar Ubangiji a tsakiyar titi tamkar wani kututture ya tokareta, shi ya farkara dani daga dogon barcina cikin matsanancin firigici da tashin hankali. Mutanen motar nata kwarara salati cikin saddakarwa da mutuwa, direba ya fita tare da wasu fasinja daga cikin motar suna dubawa inda suka fahimci wani karfe ne mai tsini aka ajiye a tsakiyar titin da gangan, wanda in bai Bula taya ba, to ya jawo hatsarin da zai yi sanadiyar rasa rayukan al'ummar da ke cikin motar duk da tazo wucewa. Ganin wannan karfen yasa cikin gabadaya matafiyan ya duri ruwa, don alama ce dake nuna akwai 'yan fashi a kan titin, wadanda suka sassauka suka dawo cikin motar da gudu sai direban motar da karen motar ne kadai suka yi ta maza suna kici-kicin zaro safayar taya su daura. Sai gasu suna fitowa cikin bakar shiga, daya- bayan daya, fuskar kowanne sunke cikin bakin kyalle, jibga jibgan da su ko a lahira bana fatan kara tuna wadannan fuskokin, da suka yi sanadiyar zubowar fitsarin daya kulle min mara, 'ya'yan hanjina suka hautsina bansan ya akayi nayi hankalin cizgo sarkar wuyana na cusa cikin (brazier) ba, karkarwar jiki ya sani kasa taBuka komai bayan hakan sai Innalillahi wa Inna ilahi raji'un nake ta ambato, ba aya ba wakafi. Suka yi magana cikin wata irin murya mai kama da karar saukar aradu cewa kowa da ke cikin motar ya fito ya kwanta a kasa, ko kamin su rufe baki duk mun aikata yadda suka ce. Amma fa ni ina makale da jakata, ban barota a motar ba kamar yadda sauran jama'ar sukayi. Tsayin minti goma sai kwashe kayan motar suke suna shigewa dasu maBoyar su cikin wani irin zafin nama cikin mintuna uku kacal sun kwashe komi kamin babbansu ya umarci a caje mu duka, a kwaso abinda ke jikin mu. Suka dinga bin mu daya bayan daya suna lalubewa har aka zo kaina, suka daka min tsawa na ciro masu zobunan hannuna da 'yan kunnayena, duka haka na zube musu jikina babu inda baya karkarwa, idanuna a rufe gam don ganin munanan fuskokinsu shine babban tashin hankali ga dan adam ba wai abinda zasu kwace masa ba. Daya daga cikinsu ne ya haska da tocilan ya kyalla ido akan bakar jakar dake makale a kafaduna wadda da fari ta saje da kayan jikina, ya fizgota naki saki, ya-ja na-ja don ina ganin babban tashin hankalina to shine rabuwana da wannan jaka, a kasar da ban san kowa ba, ban kuma san in da zani ba. Daga can gefe babbansu ya hango mu muna kici-kici da jaka, karfin halina ya bashi mamaki, ya daga murya yace "kai Fetso, sakar mata jakar ka daukota aka ka kawo min ita nan in rage dare da ita, Allah yasa ba tsohuwa bace" ya kuwa kinkimeni aka ya direwa Ogansa, yasa hannu yana kokarin cizge niqabin nawa yana cewa "idan bazaki bamu jaka ba, kya bamu abinda yafi jaka" ya cizge nikabin ya cillar, yasa hannu ya salube abayar jikina cikin wani irin gwaninta ya cillarta gefe, ya keta rigar atamfar dake jikina tat sage gida biyu tun daga sama har kasa, na kwala ihu na kamo yagaggiyar rigar na kankame da dukkan karfina, yace "wow! What a sweet voice!” Tare da dallare fuskata da tocilan dinsa yana cewa "…may be the face may be as sweet as the sweet voice…….." Ragowar maganar kakarewa tayi a makoshinsa, shima ya kwala wani irin ihun tare da cillar da tocilan din yace "Her Execellency, Mainasara….” Gabadaya yaran suka hau gudu cikn daji, shima cikamin rigar yayi yana ja da baya tamkar bai yarda da kansa ba. Wata zuciyar kuma na ce masa in ita dince sai me? Ka tsaya ka kwashi rabonka… Allah ne ya kawo ma tsuntsu daga sama gashashshe……. Wata kuma tana cewa a’ah, kama ce kawai, me zai kawo Mainasara motar kasuwa? Ya za’ai ta fita haka sakaka batare da shamaki ba? Ai ita mai jiki ce, kuma zatafi wanan shekaru…….. to bai dai samu hakikanin matsaya ga tunaninsa ba, karar motocin 'yan sanda da harbin bindiga gami da watsuwar su cikin jejin ya sashi rantayawa ana kare domin tserar da rayuwarsa. Ina ji wani matashi a bayana, wanda tun tahowar mu a kusa dani yake zaune sai dai ban juyo na kalli fuskarsa ba ko sau daya, ya yi tsaki yace "Wadannan kananan ‘yan fashi ne, sun ci mu da buguzum, ko bindiga basu da ita" ni dai saboda tashin hankali, tuni na shide, numfashina ya yi sama, na durkushe akan kafafuna kankame da jikina. Wannan matashin ya daukomin abaya, jakata da niqabina dake yashe a kasa, ya matso ya mikomin yanayi min magana a hankali "ki kwantar da hankalinki, Allah ya tserar da mu, ungo kallabinki daura, ga jakar ki ma basu dauka ba". Hausarshi bata fita sosai, na mika hannu na karBa amma naki dagowa, shi kuma durkushe yake a gabana cike da zakuwar son ganin fuskar da aka kira da ta (Mainasara) kamar ya sanya hannu ya dago kan nawa. Ya sake cewa "nan da dan lokaci za'a gyara tayoyin motar mu, mu karasa cikin Damagaram" nan ma ban ce komai ba, kamar da dutse yake magana, rokon Allah nake ya kyaleni in samu in daure igiyar abayata sosai, duk da cewa akwai doguwar shimi (vest) a cikin jikina. Shi da kansa ya gane tsugunonsa ya takura ni, ya ja tsumman rayuwarsa ya kara gaba. Na yi ajiyar zuciya na daura igiyar sosai na rataya jakata na doshi sauran abokan tafiyar mu, ashe duk abin nan da nike yana biye dani a baya kamar tsohon maye. Mutanen motar tare da 'yan sandar dake tare damu suna yi musu tambayoyi suka shiga yi min barka da arziki, wata dattijuwa ce ta bani dariya da tace "bude rigar in gani, ince ko basu cire miki rigar mama ba?” Na daga mata kai cikin matsananciyar kunya, ta ce "ita ce kadai ce mai gwal a cikin mu, kuma sun kwace” sukace "Allah ya biyaki da alheri nace "amin". Wani daga bayan mu yace “a’ah ‘yan sandannan zasu dubo su baki abinki in har sunyi nasarar damko su”. Har karfe hudu na asuba ana abu daya, domin gabadaya tayoyin motar sun yi faci, ‘yan sandan kuma wasu na tare damu wasu sunyi ciki sun watsu a dajin har Allah ya basu nasarar kamo wasu daga cikin ‘yan fashin da jibgin kayan al’umma, suka dannasu a mota suka yi gaba, ragowar guda biyar kuma sun tsaya suna ware mana kayan mu kowa yana fadar nashi amma ni ‘yankunne na ba’a maganar su, sabida kankantarsu babu wanda ya gansu sai sunga tashin mu tukunna. Daga can gefe cikin hasken farin wata na hangi saurayinnan tare da 'yan sanda suna ta magana ta tsayin awa guda, ban san me suke cewa ba kasancewar da harshen faransanci suke magana. Daga baya ne da motar ta gyaru muka mika yana zaune a Barin dama na kujerar da nake, ni kuma ina Baryar hagu, sai wasu mutum biyu a tsakanin mu. Ba muyi tafiyar awa daya ba muka tsaya wani masallacin kauye muka yi sallar asubahi daga nan muka mika. Karfe shidda na safe muka soma shiga yankin Damagaram. Dam-dam-dam! Na ji bugun zuciyata ya karu, wani irin dummm! Na ji a cikin kaina, haka idanuna sunyi min nauyi saboda wani irin kwarjini da Allah yai mata. Na daga kai ga kototon (advertisement board) wato irin allonnan da ake amfani da shi wurin yin kamfen ko talla a manyan tituna da manyan hanyoyi, wanda shine ya janwo min faduwar gaba. Na kura mata ido, bata da maraba da Innata, sai dai ta fita haske da kyakkyawan jiki. Ko’ina postarta ce a ciki da wajen garin Damagaram, masu nuna goyon baya a gareta ne zarcewa da gwamnatinta wanda aka rubuta da harshen faransanci. Nayi tir, na yi Allah wadai a zuciyata, nace a raina, shin idan sun san cewa ta aje shigiyar diya a kuruciyarta, ta gudo ta barta, ta sanya 'yar uwarta cikin bakin cikin da yayi sanadiyyar danganarta da kushewarta, zasu yarda su kara zaBarta a matsayin gwamniyar su a karo na biyu? Idan har mutum mai tabo a rayuwarshi baya shugabanci, na rantse, NURATU MAINASARA, ba zata kuma hawa kujerar Gwamniya ba! Sai na lalata siyasarta, sai na lalata sunanta, sai na dauki fansar bakin cikin rayuwar da ta jefa Innata na taraddadin inda take, da halin data ke ciki tsayin shekaru goma sha takwas har ta mutu da shi a zuciyarta. Sai na daukarwa kaina fansar rabani da duk wani farin cikin rayuwa da ta yi, sai na dauki fansar dan uwana Imran a kanta….. Ban san sanda na soma sheshshekar kuka ba, tun inayi a hankali har ya fito cikin motar mutanen motar suka ji shi, su a tsammanin su har yanzu tunanin abinda 'yan fashinnan suka yi min nake, shine har ya sani kuka. Wannan dattijuwar tace "yarinya ai kin auka arziki, ki godewa Allah ba kuka zaki yi ba. Keta haddin da akewa al'ummar mu a wannan hanyar a shekarun baya, ai ba zaki so ki ji shi ba, banda yanzu da muke cikin gwamnatin “mace tamkar da maza Hajiya Nuratu Mainasara”, ai da wannan tallafin da kika samu baki same shi ba. A gaba dayan gwamnatocin da mukayi a baya, bamu samu gwamnatin da tayi tsaye akan harkar tsaro da yaki da miyagun dabi'u kamar ta Mainasara ba. Ruwa ya wadace mu, wuta kuwa bamu da matsalarta, idan kuwa aka koma ta fannin lafiya a garuruwan kasar Nijer baki daya ba zaki samu nagartattun asibitocin gwamnati kamar namu ba, duk a cikin shekaru ukun da Mainasara tayi tana aikinta. Ta fannin ilimi kuwa, fensir wannan bamu san nawa ake sayawa 'ya'yan mu ba, duk ita ce take basu har littafin rubutu. In kuma aka koma ta fannin albashin ma'aikata da malam makaranta, duka Nuratu ta ninkashi. Farin rashin abincin da akayi kuwa akasar nan shekarar baya, mu mutanen Dagamaram bamu san da shi ba. Ta yi mana ayyukan da maza da dama, suka kasa, ta cika dukkan alkawurran data daukar mana, ta cikawa jihar mu burinta na shekara da shekaru. Don haka kuri'armu duk na wannan karon ma mun tabbatar mata nata ne, mu al’ummar Damagaram! Tunda ai munyi Gwamnatin mazan shekara da shekaru bamu ga me suka kulla mana ba, sai zalinci, sata, cin hanci, da rashawa, amma a gwamnatin MAINASARA babu wannan". Daga can gidan gaba wani magidanci ya karBe, “kin manta da inganta tituna da hanyoyin sadarwa, kafin Nuratu, ina muka samu wannan gatan?” Wani ma ya cafke, "kwarai kuwa, ga dakakkiyar zuciya da rashin tsoro, don duk barazanar abokan adawa baya sata fasa kudurinta na alheri. Duk girman buzu da rawaninsa baya bata tsoro, balle ya sata cin amanar talakawan Jihar ta. Ni kam da ana tazarce sau goma, da na cigaba da jefawa Nuratu kuri'ata har a nade birnin Damgaran. Babu abinda zamu ce akan Mainasara sai Allah ya karya makiyanta, ya tabbatar da kujerarta ta gaba, ya zama jagoranta a rayuwa, kada ya bawa makiya da mai nufinta da sharri iko a kanta…." na yi murmushi, a raina nace "irin mu ke nan, amma yabin da ake miki ba zai sa ni yin kasa a gwiwa ga fiddo musu ainahin your real colour ba, sheep in a wolf clothing. A dai-dai lokacin da motar ta tsaya cikin babbar tashar Damagaram, kowa ya fito ya kama gabansa, anan ne idanuna suka raina fata, don ban san inda zani ba. Na tsaya ina ta raba ido har a cikin tashar hotunan ta ne a ko ina. Garin cike yake da hayaniyar siyasa data kacame a lokacin da bana fahimta, domin yarurruka ne sukeyi daban-daban, ko kuwa nawa kunnen ne, oho! Duk da cewa mafi yawa hausa suke yi amma wata irin gurbatacciya ce da wadda na taso a cikinta. Na matsa ga wani mutum mai sai da shayi a irin dogayen butocinnan nasu masu garwashi a kasa, nayi msa sallama, kallona kawai yake bai ce min komai ba, bai kuma amsa sallamata ba. Na dangata hakan da rashin yarda dani sabida yanayin shigata data ban-banta data sauran matan dake wucewa, ga nikab dana maka kamar matar limamin masallacin Makkah. Na tambayeshi ko ina ne gidan saukar baki mafi kusa? Yayi magana cikin harshe faransanci mai nuna baya jin yare na, na canza na koma turanci, nan ma ya gyada kai, bai gane ba, to fa! Na matsa ga na kusa da shi wani mai saida taba shima duka yarukan nawa ba jin su yake ba, dukkan su buzayene na sosai nade cikin bakin rawani, sai idanun su da dogon karan hancin su kawai kake gani. Sai na koma kwatanta musu gidan saukar baki (Guest House) nake nufi, sai ya yi gaba abinsa ya rabu dani, a ransa nasan cewa yake in gaskiya ne abun naki, ki bude fuskarki mana. Ni kuwa tun daga kan dan fashinnan, dana fahimci fuskar nan ta zaga ko'ina a Niger, ba zan kara yin saken da zan budeta ba. Don bansan me hakan zai kuma jawomin ba. Sai na tafi bakin hanya na tsaya ina kallon giftawar motoci akan titi jefi-jefi, don bansan wace iri ce tasi ba. Cikina in banda kiran ciroma babu abinda yake, nayi wujiga-wujiga da yunwa, gajiya rashin kwanciyar hankali da rashin barci. Daga baya na naji wani zazzakan horn din mota irin na YA IM, watau mara gigita mutum, mara karar dake gundurar mai jinta. Naki juyawa na cigaba da tafiya cikin nutsuwa, domin bana daya daga cikin mutanen da ‘horn’ din mota ke sa su waiwaya. Ya wuce ni yayi parking tsaleliyar farar motarsa mai kofa daya (hemi) can gaba da ni kadan, kamin ya fito ya kulle ya doso inda nake tsaye. Saurayi ne ba'abzinen usli jajur da shi, mai lallusa kuma suma nannadaddiyar suma baka wuluk kaman ya hada jinsi da larabawa. Ganin da nai mishi cikin hasken farin wata da duhun dare, shi ya hanani gane hakan a daren jiya. Sanye yake cikin (dark green) shadda ‘yar Mali dinkin tazarce sai daukar ido take, abinka da farin mutum, kada ki so kiga yadda kalar shaddar ta fito da shi, kansa ba hula, wadda na lura ba al'adar mazan garin ba ce. Matashinnan ne da muka shigo mota tare dashi daga MaradI, ban san daga ina kuma yaje ya dauko mota cikin mintuna ashirin ba, ban san dalilin sa na son yi min shishshigi, cikin rayuwa ba, bayan a zahiri ko fuskana bai gani ba. Sai murmushi yake mun tun daga nesa kamar gonar auduga, daya ga ina shirin wuceshi batare da niyyar tsayawa ba, sai ya fiddo hannunsa wanda ke cikin aljihun damansa, yana mun kwalele da sarka ta. Nayi hanzarin kai hannu zuwa inda na ajiyeta, watau cikin ‘bra’ dina, babu ita babu dalilinta, watau ban san sanda ta fadi ba, ba mamaki sanda dan fashinnan ya wancakalar da ni ne. Na bude baki ina murmushin jinjinawa kokarinsa, wane ne a wannan zamanin zai tsinci zinare (White-Gold) yayi tunanin maidawa mai shi? Sai dai-daiku, masu tsananin tsoron Allah. Na ja burki a gaban sa, na mika hannu da nufin ya bani, sai ya maidata cikin aljihunsa ya ce "idan kece kika tsinci abun mutum, kamin ki mika masa, ai ya kamata ki tabbatar cewa nasa ne, ko ba nasa bane?” Na yi murmushi "idan baka yarda cewa tawa ba ce, meye dalilinka na tsayar dani ka nuna min?” Yace "from your voice, I guessed you are a girl in tender age, me ya kaiki yin tafiya irin wannan cikin dare, ba tare da mijinki ko dan uwanki ba?” Na tsuke fuska, don a fahimtar dana yi, yana son kai tsayuwar tamu da tsawo, nace "baka yi mun kama da mutanen dake shiga abinda babu ruwansu ba, this is my personal world, don haka in zaka bani sarkata, ka bani, in ba zaka bani ba, in kara gaba" yace a tausashe "me yayi zafi, gyara kayanka, ba sauke mu raba bane, ina zaka? Ba zo mu tafi tare bane, don haka maida wukar, ga sarkar ki” nayi murmushi na karBa nayi gaba ina cewa "ban taBa jin irin wannan hausar ba. Tsaya a inda kafi wayau, kada ka shiga gonar da ba taka ba, in hausawa suka ji sai suyi maka dariya, don kuwa ba bahaushe bane, Badamagare ne". Ya sha gabana yace "a kasar nan, ni cikakken baushe ne kuwa, kamin ki samu wanda zai miki kyakkyawar hausa haka, zaki dade. Don haka inma ki tsaya ki nemi taimakon da kike nema daga gareni, ko kuwa kiyi gaba ki sha wuya, mutum nawa kika samu da irin tawa hausar da kike rainawa?" A raina nace "kwarai babu” amma a zahiri sai nace "turanci na zai fidda ni a ko‘ina cikin duniyar nan". Dariya yayi, data fiddo jerarrnn fararen hakoransa reras kamar shi ya shiryawa kansa, yace "Mu ba rainon Ingila ba ne, rainon Farisa ne, don haka dauki turancinki ki jefa a wannan katuwar jakar taki data kusan janyo miki salalon tsiya, ki koma dashi inda kika fito, ki dauko faransanci, sannan ne zaki shiga ko'ina a cikin mu. We need no your Engilish…" ban san sanda na murmusa ba, hakannan naji ina kaunarshi, ban san dalili ba, ban jin zan gaza da sauraron tattausar hausarshi koda zamu kwana ne a hakan kuwa. Koma wane ne, farat daya naji jini na ya hadu da nashi. Daga fatar jikinshi, sutturarshi zuwa motar da yake ciki kadai ya isar maka kimanta daga inda ya fito, bi ma'ana, da gani babu tambaya cewa shi wani ne, ko kuma dan wani ne a Damagaram. Don haka nayi gaba, domin baya daga cikin ire-iren mutanen da nake jin zan amincewa cikin garin, nafi son in nemi gidan talakawa 'yan uwana in fara sauka, in ga kamun ludayin mazauna garin, kafin in nemi dangin Innata. Bai hakura ba dai ya sake shan gabana, ya mairairairce kaman wani kan karamin yaro yace “in kin amince ‘I would like to be your host’ (zan so zama mai masaukin ki) don na fahimci ke bakuwa ce, baki kuma san kowa ba". Na yi hamzarin dubansa saboda mamakin yadda yasan hakan, ya dagan kyakkyawar girarshi yace "yes, kuma ba kowa ke karBar bakon da bai sani ba a garinnan” . Nace “shine kai zaka yi kasadar karBar bakuncin nawa, bayan ko fuskana baka sani ba? Idan kuma dodanniya ce fa ko aljanace?” Ya ce yana mai murmushi "na yarda na amince ta cinye ni har hanji na". Tunda muka soma tafiya a motar babu wanda a kara ce da dan uwansa uffan, sanyin A/C ne ya kara sani samun nutsuwa da warwarer gajiya, nake jin shirun namu ne bai yi masa dadi ba, don haka ya mika hannu ya sanya kaset na faifan mawakan 'soulsquad music' sautin na tashi a hankali har muka iso wata keBantacciyar anguwa da tafi mun kama da iri-iren gidajennan namu na GRA, domin dukacin ginin gidajen iri daya ne, kansu daya haka tsarin su ma daya. Ya karya motar a kofar shiga flat na ashirin da biyu, yayi (horn) mai gadi ya bude muka shiga. Korran (Grass Carpet) ne malale a gabadayan harabar gidan banda sauran shuke-shuke kala-kala da suka kawata gidan saosai. ka ramin gida ne hawa daya, da aka yi gininshi da jan dutse kaman a kasar China. Daga kofar shigowa gidan bazaka taba tsammanin haka cikin gidan yake ba. Babban abinda yafi burge ni da tsarin wannan gida shine kacokam ginin gidan a tsakiyar gidan yake, sannan hanyar da zaka bi zuwa cikin gidan duka (grass carpet) ne mai taushi. Na zauna cikin motar na kasa fitowa cike da tunanin a wane matsayi zanje wajen matarsa? In kuma babu matar aure a gidan haka zan zauna da gardin namiji, a irin wannan gidan ihunka banza? Kai da sake, wai an baiwa mai kaza kai. Mu kammala a littafi na 3. [7/11, 3:58 PM] +234 706 160 2791: Duk wasu kalami na kwantar da hankali Ya Faruq ya gaya min su a wannan rana, tamkar yawun bakinsa ya kafe, tamkar ya fido zuciyarsa ya nuna min, tamkar harshensa ya tsinke don tabbatar min da abinda yake fadI, jinsa kawai nake, amma hawayena basu bar kwarara ba, wanda na tabbata har abada ba zasu daina ba, haka zuciyata ko daya bata russuna ba ga kudirinta akan NURATU da BABA SA'IDU. In Allah ya yarda sai sun zubar da hawaye, fiye da wanda na zubar. Fiye da wanda Inna ta kwashe shekaru goma sha takwas tana zubarwa akan su. Tare dashi muka kamo hanyar Gwarzo, cikin masiffafar motar da ya iso da ita daga asibitin AKTH dake Kano, yana ta kara kwantar min, da hankali, da kalami masu taushi da kara imani. Akwai inda yace “Zaynab in nine ke, babu abinda zai sa inta zubar da hawaye na har haka, tunda da Allah yayo fitowana a hakan bai barni haka ba. Sai ya sanya matsananciyar kaunata zuciyar iyayen nawa, yayi mun gata irin wanda baiyiwa sauran 'ya'ya irina ba. Kina ina iyayen da suka haifi 'ya'ya kamar ki, suka kai su bola suka zubar, don gudun abin kunya? Kina ina ake tsinto 'ya'ya irin ki ana kaisu gidan marayu, ana kyamar su ana zuwa kallon su? Ke kuwa Babanki sonki ya ke fiye da sauran 'ya'yan da ya haifa ta hanyar auren. Son ki yake fiye da komai na rayuwar duniya, son ki yake ta yadda da da hali, daya mallaka miki duk abinda ya mallaka a duniya. So yake ki zo kusa da shi, saBanin 'ya’ya irin ki da ake neman maraba da su. Kina ina uwar da ta haifi 'ya ta irin hanyar data haifeki, ta kasheta da hannunta, ta tura ta a masai tayi ‘flushing?’ Ke kuwa na tabbata duk inda mahaifiyarki take, cike take da kaunarki da tausayinki, domin soyayyar gaskiya ce tsakaninta da mahaifinki, illa makiya da sharrin Shaidan, gami da kaddara da suka tarammusu. Ki godewa Allah, domin yace “in baku godewa Rahmata ba, hakika zaku godewa azabata”. Ki yafewa iyayenki, ki taya su rokon Allah ya yafe musu, domin babu wanda yake sama da aikata ‘kuskure’ cikin rayuwarsa. Dukkan mu masu saBo ne in one way or the other, amma Ubangijin mu hakuri yake da mu, yana yi mana afuwa har zuwa ranar da kowanen mu zai karBi sakamakon sa, sai ki dage wajen kyautata lahirar ki, ki gani idan zaki taBe. Wannnan shi ne gata na karshe da zakiyiwa rayuwarki, amma ba kuka ba. Kuka babu abinda zai sa babu abinda zai hana, saidai ya kara dagula zuciya, ya raunana imaninta. Muminai na hakika basa kuka akan komai, sai akan tsoron Allah, wannan shine lokaci na karshe da zaki nunawa Innarki kaunar da kike ikirarin kina yi mata, ta hanyar yi mata addu'a da nema mata gafara. Ina yi mana ta'aziyya Zaynab domin bake kadai aka yiwa mutuwa ba, mu biyu ne Zaynab, nima nayi rashin uwa abokiyar shawara kuma mai kaunata…….." Yasa hankici ya share hawayen idanunsa, ya miko mini da hannunsa na dama, ayayin da yayi amfani dana hagun wurin tukin motar "maza share su Zaynab, Inna bata cancanci mu dinga yi mata kuka ba." Na mika hannu na karBa, amma ban san sanda kukan ya kara subuce min ba jin kalaman sa. Na kifa kaina a cinyoyina nayi ta yi ba kakkautawa, don ni har yanzu na kasa amincewa raina wai Innana, ta rasu! To ni in haka ne wa nake da shi a yanzun? Zaman wa zanyi? Ina zani? Tunda mutumin da na rika a matsayin mahaifina, an ce ba shi ya haife ni ba. Mutumin da nake kauna fiye da kowa a duniya, nake ganin GIRMANSA da kimarsa fiye data kowa, a yau bani da wanda na tsana a duniya tamkar shi. A yau kam na daina ganin beken Innata, dana kwashe shekaru goma sha takwas ina gani. Baba Sa'idu ya cuce mu, ya ci amanarta. Ya barmu da tabo da bakin cikin da har abada ba zai gogu daga jikin mu da zuciyar mu ba. Wai ni Zaynab ce 'yar zina? Gaskiya mana! Biri ya yi kama da mutum!! Yadda na tsinci kaina da tsananin son aikata zina, tun 'yar ficiciyata ashe ban yar a kas ba, tsotsa nayi a nono, ba don kariyar Ubangiji da kokarin dan uwana Imran ba. Da ashe bakin cikin yafi haka.. Da tuni nima na aje shagen…… wayyo Allah! Inama ba'a halicce ni ba…….!!” Magana nake cikin zuciyata, ban sani ba tsabar bakin-ciki ashe a fili nake yi. Ya Faruq ya kaashe motar a gefen titi, shima ya kifa kai akan sitiyarin ban san a halin da yake ciki ba. Na sani da da hali, da ya jawo ni jikinsa yayi min lallashin da ba'a taBa yi min ba, yayi min lallashin da wani da namiji bai taBa yiwa diya mace ba, domin nuna mata matsayin da take dashi a zuciyarsa, da yadda damuwarta ta zamo tashi. Ya kasa ce min komai illa tsinkayar numfashinsa da nake, wanda ke fita da sauri-da-sauri kamar na mai ciwon asma. He really lack a word to express his feelings, his sympathy and how much he cares. Gane hakan dana yi ne ya sani yin karfin zuciyar dagowa in share hawayena, na kuma rasa hanyar da zanbi in ganar da shi na daina kukan domin idanunsa a rufe suke ruf. Sai na kai hannu ga ‘horn’ din motar na danna a hankali. Ya bude idanunsa da suka kada suka yi jawur ya dubeni very pale. Sai na samu kaina cikin wani sabon al'amari, wato abubuwa da dama dana gano cikin kwayar idon Ya Faruq, su suka tuna mani da Imran. Bai ce komai ba, ya ja motar muka ci gaba da tafiya, gab da sallar magariba muka iso gida, sai a can bakin hanya ya kashe motar domin gabadayan unguwar babu masaka tsinke, ana yiwa Malam Ali ta'aziyyar mai dakinsa. Zuciyata ta kara tsinkewa, hawayen suka kara malalowa. Na tabbatar Inna ta a yau ta wuni a makwancinta. Ni kadai zan kwana a wannan gadon karfen namu, ni kadai zan rufe da katon bargon mu, ni kadai zan cigaba da rayuwar hakannan ni kadai zan cigaba da dandanar bakin-cikin Nuratu da Baba Sa'idu, ita kam Allahu Arrahmanu ya hutar da ita, wata shari’ar, sai a lahira! Tafiya nake tamkar akan kaya, ina keta daruruwan jama'ar da suka zubo min ido, ina cewa a raina suna ta kallon SHEGIYA, wadda bata da Uba, wadda aka haifa ta hanyar zina. Na yi murmushi, sabida kuna da suyar da zuciyata take yafi gaban kuka. Lallai wata mutuwar Rahmace, inama nice Inna! Koda yake burin Innata ya cika. Ko ba komai na tayata farin cikin cikar burinta, tunda kuwa sai bayan ranta…… na dandani bakin cikin ‘illegitimacy’. Sai bayan ranta wani ya tabbatar min da cwa ni shegiya ce, haka sai bayan ranta na samu amsoshin tambayoyin da suka addabi kwakwalwata, suke banbantani da sauran 'ya’ya, suka tabbatar min da cewa ni 'yar gaba da fatiha ce. Na daga kaina sama a hankali, ina karanto rayuwata ta baya, dana tabbatar na yi sallama da ita. Yanzu ne zan shiga rayuwata ta hakika (ta marassa galihu, marassa ‘identity’). Inna ce galihu na, Malam ne ‘identity’ dina, duka a yau na rabu dasu (ita ta tafi, shikuma zan rabu da shi). Ba zan iya rayuwa cikin kasar ba tare da Innata ba. Na sanya kafata cikin gidan, cinkoson mata ya kara tayar min da hankali, tamkar in ce da kasar ta tsage in shige. Tsoro nake kada wata cikinsu ta kirani da 'shegiya' babu mai kare a min a yau, tunda babu Innata cikin gidan. Ala dole na ja baya zan juya da gudu. Yaya Halima ta ratso cikin mutane itama da gudunta ta kamo ni, ta kankame ni tana kuka haka daga bayana naji nayi karo da mutum ashe Malam ne ya sawo kai, Ya Faruq na biye da shi, sai kallon su nake a tsorace, don gani nake kamar korata zasu yi daga gidan su. Sai makyarkyata nake yi kamar mazari. Malam ya shiga tofa min addu'o’i iri-iri a tsakar kaina. Ya Faruq ya kama hannuwana duka biyu hawaye cike da idonsa, yace "Baba Malam, don Allah Halima ta tafi da Abu gidanta bazata iya nutsuwa cikin taron matan nan ba, ina gudun kada ta samu matsala a kwakwlwarta, ka yi hakuri don Allah tabi Halima tunda kace baka yarda in kaita gidan Baba Sa'idu ba…." na gwalo ido da karfi jin abinda yace, na ce "nima bazani ba Malam dukana zasu yi, kora ta zasuyi, ba zasu barni in zauna musu a gida ba. Ni da gidan Baba Sa'idu har abada…. har shi Baban….. Babu ni, babu shi har abada……." Na fashe da kuka shima Faruq sai ya shiga share hawaye da hankicinsa duk irin dauriyar da yake yi kuwa. Ban taBa ganin Ya Faruq yana kuka ba, tunda nake. Don haka nayi saurin tsayar da nawa, ba don na zuciyar ya kafe ba. Malam ya ce "bude mata dakinsu ta dauki abinda za tayi amfani da shi, ki kula min da Zaynabu amana Halima, kafin zuwa ranar sadakar uku in daura auren ta da Umar Faruq…” Cikin tsananin firgici, mamaki da zargi, na daga ido na dubi Malam Ali, cike da mamakin wane Uba ne na kwarai, zai aurawa dansa dan halak 'SHEGIYA?' Ba mamaki mutuwar matarsa ta samar masa motsuwa a kwakwalwa, domin ni kaina shaida ce kan matsanancin son da yake mata. Ban ce komi ba, na sunkuyar da kaina kasa, domin idanuna sun gano min abubuwa saBani ga tunanina, sun gano min Malam ragas yake, ragagasgas kuwa, sai dai in nice ban ji sosai ba. Amma kwayar idanunsa na tabbatar da abinda yake fadI, haka yake har zuciyarsa. Na maida dubana ga Faruq, don ganin wace irin karBa ya yiwa zancen mahaifinsa? Idanunsa akaina suke, cike da tarin abubuwa da dama, wanda a lokacin rashin kwanciyar hankali bai barni na tsaya ga son tantance ma'anar su ba. Ya lumshe idonsa cikin nawa, ya jefa ni da wani irin 'loving smile’ da har yasa 'ya'yan hanjina sai da suka karkada, domin babu tantama al'amuransa a yanzun, sun juye sun rikide na IMRAN ne sak. Sai naki gasganta hakan da gangan, domin ni ban yarda da abinda ake kira (love at first sight) ba, sai dai tausayi da ceton rai. A ganina ni ba abin tausayi bace, tunda ina da lafiya zan nemawa kaina madogra, in daukarwa kaina da Inna ta, fansa, wanda ba zasu yiyuwa ba, in har da aure a kaina. Ko zanyi aure ai Faruq yafi karfina; shi dan gatane, dan halal ne, mai dangi, sai dai in je duniya in nemo shege dan uwana, wanda ba zai taBa goranta min (illegitimacy) ba. Na shige dakin Inna na da zummar dauko kayana, to amma me? Duk inda na juya ita nake gani a kowacce kusurwar dakin tana 'yan hidimdimunta da basa karewa. Na zauna a gefen gadon karfenta, na dauki bargonta da muka kwana a cikin sa daren jiya na rungume a kirjina, hawaye na malalo mini. Nayi kuka na yi kuka har hawayena suka kafe, sai dai kukan zuci, wanda akace ya fi na zahiri radadi a zuci. Yaya Halima ce ta shigo ta soma hada min 'yan komatsaina, cikin ka tuwar akwatina da na zo da su daga gidan Baba Sa'idu, ta daurawa Zilkiflu ya tafi da shi gidanta, ta kamo hannuna muka fito daga dakin tasa kuba ta rufe. Idanun matan nan dai har yanzu suna kaina, suna ta kus-kus din dake kara daga min hankali. Daga can dakin Inna Dubu Hafsisi ta fito, ta dubeni shekeke, daga ni har Yaya Halima dakatawa muka yi muna kallonta, domin daga ganin irin tsayuwar da tayi, hannu a kugu, ta kuma tare min hanyar wucewa. Kasan bata arziki bace. Cikin daga murya yadda duk wanda ke gidan zai ji, ta ce "to Abu, burin ki ya cika, naji ana zaki auri Faruq ba ni ba. Dadin abun dai ni ba ‘shegiya’ bace 'yar sunna ce. Igiyoyi uku kwarara na aure suka samar dani kuma kowa ya shaida. Kenan ba sai an rufa asiri za'a aureni ba. Ashe dama duk wannan kumbiya-kumbiyar da mahaukaciyar ki Innarki ke yi dake, don kar mu san ke SHEGIYA CE? To ai gara ma da ta mutun, da bazamu sani ba, sai a cigaba da dinke mu a bai-bai. Don haka ba Faruq ba, in ma ALHAJI SA'IDU, dadironki zaki aura, ki je na bar miki, nafi karfin in hada kishi da shege wall….”. Ganin Hafsisi mu kai tayi sama ta kuma fado tik, a kasa. Ya Faruq dake shigowa yayi kwallon ‘tennis’ da ita da kafarsa ta dama, sai jini ta hanci ta baka. Ta kwala ihu iya karfinta shi kuwa ya sake bin ta yana tumurmusa da kafa a tsakar gidan, duk cikin matan an rasa mai kataBus din kwatar ta sabida irin mugun dukan fitar hankalin da yake mata da kafafaunsa, sai mahaifiyarta Goggo Lantana data dora hannu aka ta kwarara ihu, tace "Dubu kawo dauki, zai kashe min 'yar akan 'yar gaba da fatiha…… Karya ake ba shegiyar bace? Ka dauka yau aka haifemu a garinnan bamu san 'yar Nuratu ba ce karuwar Sa'idu.....?" Idanun Yaya Faruq suka rufe ruf, baya ko ganin gabansa, ya fizgo Inna Lanto ya maka da bango, ta kuma kurma ihu data fadi tim, akan kwankwasonta. Ya dunkule hannu ya nausa mata a bakin sai ga hakora biyu, wanda dama lallabasu ake sun biyo jini da yawu sun zubo akan cinyarta. Malam ne da Inna Dubu suka shigo da gudu daga can dakin soro inda suke karBar gaisuwar Hakimin Gwarzo da tawagarsa, suka kwaci Hafisisi da Innarta da kyar, bayan ya hada musu jini da majina, ya fita yana huci ya dauki motar sa a guje ya bar garin kwata-kwata. Rungume Yaya Halima na yi, ina ta kukan fitar hankali ko uffan ban ce ba, haka muka baro gidan zuwa gidanta. A ranar ne labarin da jama'ar garin Gwarzo suka dade suna kokontonsa, ya bayyana gare su. Abinka da dan karamin gari, cikin daren labari ya bazu a ciki da wajen kauyen Gwarzo, cewa ashe Abu diyar Malam Ali, ba 'yar sa ba ce, SHEGIYA CE. A daren daga ni har Halima bamu rintsa ba, ita cin kuka take saboda tausayin raywata ni ko a lokacin idanuna sun bushe, zuciyata ta kekashe. Kalamin Hafsisi sun kyafar da hawayena. Babu shakka abinda ta fadi haka yake babu kuskure a ciki, domin ta fini kusanci da Faruq, ta fini sanin ciwonsa ta fini sanin muhimmancinsa, don Innarta kanwar Inna Dubu ce uwa daya uba daya, dole ta taya dan uwanta jimamin kakaba mishi 'yar zina da za'a yi, ko ni na jajanta masa, haka duk wani mai kaunar sa dole ya jajanta masa. Maganar ta daya ce ta taBa zuciyata kuma ta sani fidda hawaye, (dadironki Alhaji Sa'idu), me wannan kalmar ke nufi? Tana nufin…. zaman da kikayi kina karatu gidan Baba Sa'idu, zama ne na karuwanci, na zina, irin wanda mahaifiyarki, NURATU, ta yi tare da shi har suka sameki…….. Ban san sanda ba na ce "Ya Allah, ka dauki raina in huta da wannan rayuwar, Ya Allah kada ka barni in kara kwana cikin duniyar nan, Ya Allah ka bi mun hakkina akan Nuratu da Baba Sa'idu…" Yaya Halima tasa dankwalinta ta toshe min baki, cikin kuka ta ce “Abu kada bakin ciki ya fidda ke a addininki, kada Bacin rai da maganar mutane ya raunana imaninki, kada bacin zuciya ya kaiki ga aikata dana sani. Naji dadin yanda kika karBi al'amarinki da farko, amma kina nemn lalata ladan da kika samu na yarda da kaddara da fawwalawa Ubangiji komai da kika yi. Wannan ba zai hanaki shiga Aljanna ba, idan har kin kyautata ayyukanki sai ki wuce cikin aljannar mu 'ya'yan halal din bamu wuce ba. Rayuwar duniya duka guda nawa take? Kada ki manta, bafa zama muka zo yi a cikinta ba, to na meye zamu damu kanmu da kaluben dake cikinta? Ki yi saurin yin Istigfari ga kalamunki, tun mala'iku basu rubuta ba………." Na share hawayen da suka yanko mini, na daga kai sama nayi duba ga al'arshin Subhana, wadda ya kawata da wata da taurari, ya maye duhun dare da hasken su. Na saukar da idanuna akan yatsaun kafata nace "Mutane suka koma bani tsoro Yaya Halima”. Itama ta share hawayenta ta ce “Ba kiyi tuban da nace kiyi ba har yanzu Zaynabu-Abu". Na daga kai sama a hankali, tsigar jikina na tashi, kana na sunkuyar. A hankali nace “Astagfirullah!” Ta kamo ni ta rungume a kirjinta, hawayena na sauka a gadon bayanta, nace "ni yanzu ina zan dosa ne Yaya Halima? Ba Uwa ba Uba balle dangi. Ga tabon da duk inda na shiga baza’a goge min shi ba, bayan ba ni na dorawa kaina ba. Ko zan rika kwana a titi, ba zan doshi hanyar gidan Baba Sa'idu ba, ba kuma zan kara kwana gidan Baba Malam ba, sai dai gaisuwar neman albarka daga gareshi da Inna Dubu, haka ko zan mutu ba aure, ba zan auri Ya Faruq ba. Idan nayi hakan na tauye shi, domin shi cikakken mutum ne mai cikakken hali da cikakken usuli, bai cancanci auren mai gurBataccen usuli kamana ba…" ta katseni cikin daga murya “ki daina fadar haka Abu, Faruq na sonki a tun ranar da aka haife ki, shekaru dai-dai yau kusan goma sha takwas….” A razane na dago ido na dubeta, tunanin maganganun Inna na ya zo mani. Wannan na nufin Faruq shine mutum na hudu, cikin masu tabon bakin-cikin BABA SA’IDU, shine ma’abocin soyayyar shekaru goma sha takwas, amma bazai bayyana ba sabida Baba Sa’idu?” Ta lura da yadda maganarta ta taba zuciyata, ta daga min kai (in affirmation), “kwarai ni na sani, Innarki Allah ya jikan rai ta sani, haka Malam da Inna Dubu. Sai dai ya rantse zai iya hakuri har illah masha Allahu, don ba zai taBa ba bari ki gane ba Baba Malam ne ya haife ki ba. Wannan zai dagula rayuwar ki ne, ya jefa ki a wani hali na tsanar duniya da abinda ke cikinta, hadi da ke kanki. Ga kalamunsa a yau sun tabbata. Haba Abu! Sai kace ba musulma ba? Me hakan zai kara ga rayuwar ki me hakan zai rage? Wannan ba shine karshen rayuwar ki ba, idan har kin kyautata zuciyar ki. Ya dawo a dai-dai lokacin da kika suma, da girgizar mutuwar Innarki, da abinda kika tsinkaya su Malam suna fadi, shine ya daukeki ya kaiki asibiti. Ki bar cewa ina zaki Abu, in har kin yarda da ni, kin yarda ni din mai kaunar ki ce, ki zauna tare da ni. Ki bar cewa bazaki ki auri Faruq ba, domin kaunar da yake maki da wadda Baba malam ke maki bata shafi abinda ke kike tunani ba. Wallahi-wallahi Abu saboda ke ne Faruq ya tafi Singapore, saboda lura da yayi cewa kin fada a kaunar dan uwanki, shima Imran din yana son ki, yace shiyasa ya tafi, don a cewarsa ba zai iya jure ganin wannan abin takaicin ba, ya san dai ko yaya ne su Baba Malam ba zasu taBa bari ku auri juna ba”. Na ja gefe na hade kaina cikin gwiwoyina, cikin kuka na ce "kema kinyi mun laifi Yaya Halima. Don me yasa tun a sanda muka zo miki nan ni da Imran, a matsayin muna son juna, baki gaya min ba? Wannan kaunata kike yi ko neman jefani a halaka? Daga ke har Faruq baku da abinda zaku gaya min a yanzu, har da ku aka hada baki aka lalata rayuwata ni da dan uwana. Ko kin san Imran ya tafi inda ba’a san inda yake ba, ba’a kuma san a halin da yake ciki ba? Na hada ku duka na tattara cikin littafin su Baba Sa'idu, har daku aka nakasta rayuwar mu…" Na mike ina kuka sosai kamar raina zai fita, na yi cikin daki, ta kamo gefen zani na, na fizge "Abu kada ki ce min haka, ta yaya kike tunanin zance dake Imran dan uwanki ne, abinda duk duniya babu wanda ya taba tarar ki ya gaya miki? Kina son Innarki tayi karata ne, ko nima ta tsaneni? Wace irin dauka kike tunanin Malam da Faruq zasu yi mini idan zancen ya fito daga bakina, munafuka ko maciya amana……?”. Na toshe kunnuwanada ‘yan yatsuna nayi ciki ina cewa "Ba wani malam da Faruq, amma ai kya dan nuna bakya ‘supporting’ al'amarin, amma har wani cewa kike zaki saya mani Banbar aurena da dan uwana…?” Wani abu yazo ya tokare a makoshina “kai Yaya Halima kema kin cuceni…" na cigaba da kuka. A lokacin ne Halima ta harzuka, ta ce “shikenan Abu, kome kike tunani kije ki yi, nagane da gangan kike kin fahimtana. Tunda kuma kince bana sonki, to na gode, amma kar ki sake cewa ba zaki auri Faruq ba, in kinyi haka kinyi butulci kuma ko Allah ba zai barki ba". Ta haura tabarmarta ta shiga daki ta hau gado ta kwanta, ban sake kulata ba jakar hannuna na dauko na dauki (jotter) nayi wa Faruq 'yar gajeriyar wasika, na kirga kudina dake cikin jakar dana dawo da su daga gidan Baba Sa'idu, kudi ne masu yawa ire-iren kudin da shi Baban yake bamu ne da wanda bakki masu zuwa da abokan su Ya Em ke bamu lokaci zuwa lokaci. Na dauki 'yan kananan abubuwan amfanina da bazasu fi karfin jakar ba na zuba, na zuge. Na jawo akwatina ina binciken sarkar da Mama (Hajiya Azumi) ta bani randa zan taho daga Sokoto, wato sarka da dan kunne gami da zobe da abin hannu guda daya (English Gold) da kyar na ganta, a kasan 'DIARY dina. Jikina na rawa na dauko shi domin na fidda rai da tsammanin inda yake, rabona da ganinsa tun ranar da mukayi maganganun dana rubuta da Inna na. A yau dana bude shafukansa, tun daga farko har karshe na irin al'amuran da nake rubutawa, sai naga na samu cikakken ma'ana na abubuwan da suka shige min duhu, na samu amsoshin tambayoyinda suka dade suna addabar kwakwalwata. Wato dai ya tabbata gareni, Inna ta tsani Baba Sa'idu ne ta kuma kasa yafe masa a dalilin ita ta dauki amanar rayuwarsa, tamkar danta na cikinta, inda shi kuma ya sakamata da yiwa kanwarta ciki na bata hanyar aure ba. Ta ce “zata yafe masa ne kadai ranar dana yafe masa" wato ranar dana gane ni 'yar shi ce, da ya samar dani ta hanyar zina. Na kuma yafe masa. Ta kasa komawa cikin danginta ne domin batasan me zata ce dasu ba a game da Nuratu, da bata san in da take ba. Amma a duk ranar da ta ganta, to a ranar ne zata dawo garesu. "GIRMAN su Hajiya Sa'a yana hannunta." Wanda ke nufin, a duk ranar data fadawa duniya Sa'idun nada shegiyar diya, GIRMAN SU ZAI FADI! "Ita Hajiya Sa'ar ce kece dani SADAKA YALLAH? Bata fadin babban? Wato (Bata fadin ni shegiya ce?)” Wannan na nufin Hajiya Sa'a, tasan tsakanin Abba Baba Sa'idu da mahaifiyata, Nuratu, ta kuma san rayuwar su ta baya. To amma abinda ban sani ba shine shin Hajiyar ta san cewa sun haifeni? Kai babu kama, sai dai ya zamanto cewa ta san soyayyar tasu, amma bata sanda suka kai ga yin cikina, har suka haife ni ba. Tabbas da bata dinga aibatani akan su Hassan ba. Da bata dinga yin fariyar "su da gidan Uban su ba". In haka ne akwai sauran kallo a gaba. Domin kuwa ko ba-dade, ko ba-jima, sai na je na tsaya a gaban Hajiya Sa'a, na gaya mata ko ni WACE CE? In tabbatar mata da cewa BARAROJI kuma SADAKA YALLAH 'yace ga V.C Professor Sa'idu Bindawa. Na kai hannu na shafe hawayena. Idanuna ya kai ga shafin karshe, wanda ya warware min rudanin da zuciyata ke ciki, na kokonto da tunanin ina zan dosa? Wa nake da shi a halin yanzu da ya wuce Baba Sa'idu? Wani farin ciki ya ziyarci zuciyata, ban san sanda fatar bakina ta suBule da murmushi ba, naji kamar an dauke min wani nauyayyan dutse ne aka. To amma ina da tabbacin in sun san ta hanyar da 'yar tasu ta haifeni, zasu yarda su karBeni a matsayin JININ SU har su bari in zauna a cikin su? Inada tabbacin in sun san cewa ita kanta 'yar tasu, gudu tayi ta barni, tun ranar data haifeni don tsira da mutuncinta, zasu yarda su karBeni? Wata zuciyar tace " na Allah basa karewa Zaynab, a ko'ina ba'a rasa na Allah, irinsu Ya Faruq da Yaya Halima, wadanda tunanin su ya sha banban dana sauran mutane, ra'ayin su ya banbanta dana sauran al'umma. Su irin wadannan mutanen kamar wasu mala'ikun Rahma ne da Allah ke saukarwa bayinsa masu matsala irin nawa. ‘They are just like angels in the midst of people' wadanda suke a shirye da sadaukar da kansu domin farin cikin wani. Wannan ne ya kara sani dubar rubutun da nayi shekara daya da wata daya da ya wuce, daga bakin Inna ta; "Kyauta mu ba baroroji bane, sune 'yan kasarmu dake daji, mu 'yan kasar Nijar ne, 'yan usulin wani gari Damagaram, amma iyayen mu da 'yan uwan mu a babban birni Yamai (Niamey) suke zaune, har yanzu suna can”. “In kika shiga Niamey, kika ce kina neman wani daya shafi iyalin MAINASARA KANGIWA, ko yaro kankani ya san wannan sunan.." Don haka na cusa littafin cikin jakata, na kishingida ina jiran garin Allah ya waye in kama hanyar kasar Nijar neman dangin Innata, in gaya masu rasuwar ta, in rokesu alfarmar su barni in zauna tare dasu, ta hanyar cewa ni ‘yar ta ce. Kamin a hankali in nemo Imran, inyi masa aure da Adda Mami, daga nan nasan ina da Uban da zai rikeni ya kuma cigaba da yi min addu'a ko bayan raina. Wato in zauna tare da shi da iyalinsa muddin rayuwata. Na dauko wasikar da na rubutawa Ya Faruq, na sake binta a nutse, ko akwai wani gyara a ciki? Na tabbatar, babu. Ga abinda na rubutawa dan uwana rabin jiki UMAR FARUQ; "Ya Faruq . Zuciyata ta kasa amincewa da wai in cigaba da zama da Yaya Halima, bayan sanin ko ni wace ce? Gangar jikina ta kasa amincewa da kai wai a matsayin miji, domin tana ganin baka cancanci hada jiki da kazamtacciya kamata ba; You are pure as a clean glass, and I'm a green, but rotten leaf. Har ila yau, zuciyar ta takasa yafewa Nuratu da V.C Sa'idu, don ni ba zan taBa kuma kiran sa ‘Baba’ ba, ba zan taBa iya kiranta ‘Inna’ ba. Don haka na tafi, inda a hankali nake tunanin zan samu labarinta. In tambayeta dalilin shegantani da tayi, ta kuma nemo min dan uwana a duk inda yake cikin duniya a dalilin bakin cikinta. ‘I know it will hurt, but you donno how deeply it hurts the victim’. Faruq ka yafe mani, ka yi mun godiya ga Innarmu, ina nufin (Inna Dubu). Ina fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa".