GABA DA GABANTA 💫 Page1 Cool ce! Free book ne, Comment kawai nake buƙata please, if not zanyi abunda bakwa so 🌝 Typing ba kullum ba, sai an ganni kawai. Ƙirƙirarraren labari ne, ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba. Wannan rubutun mallakina ne, ban yadda a juya shi ta kowacce siga ba sai da izinina, kuma ban yarda a sɗora mini shi a kowane website ba sai da izinina. BISMILLAHIRAHMANNIRAHIM Dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekaru hamsin, zaune akan benci hannunsa riƙe da 'yar ƙaramar radio, yana saurara. Wata Haɗaɗɗiyar mota ce ƙirar Annoconda, aka kwararo dogon layin da Ita, wanda gudun da motar take ta haddasa tashin wata 'yar ƙaramar guguwa. A ƙofar wani makeken gate motar tayi birki, aka fara wani irin horn, sai kace yaƙi. A gigice ya yasar da radiyon da ke hannunsa, ya miƙe a zabure ya nufi gate ɗin, yana gaganiyar buɗe shi. Yana buɗe gate ɗin, aka turo hancin motar, zuwa wani sashi na gidan. Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga Motar, gata nan dai kamar bata cin abinci, ban da yanayin jikin ta da kuma kayan da suke sanye jikinta, ba ka ce mace bace, saboda tsabar rama, sai dai fatar jikinta za ka kalla ka gane 'yar hutu ce, da ga ita sai doguwar rigar material, da hula a kanta tana sanye da wani uban takalmi me shegen tsini. Ta nufo gurin da dattijon nan yake kokawar maida gate ɗin ya rufe tsigil- tsigil, tana zuwa ta ƙare masa kallo sannan tace "wai kai dan Allah wani irin mutum ne? Kai ta abu kamar mara jini a jiki ko wanda baya cin Abinci? Duk Abincin da kake ci kamar gara amma ba ka da wani Amfani iye?, wallahi daga yau na kuma dawowa, ka barni a waje ina horn sai na tatala maka rashin mutunci, aikin banza ni ban ga amfanin ajiye ka a gate ɗin gidan nan ba, Daddy ya nace lallai sai kai za kai gadi" Shiru dattijon ya yi, ya sunkuyar da kai, yana jin yadda Yarinyar ke surfa masa fitsara, 'yar da ba ta fi 'yar cikin sa ba. Ta buɗe jakarta ta ɗakko dubu uku ta zubar da ita a ƙasa, ta ce "gashi nan ka ɗauka ka siyo mini Irish, za'a dafa mini, na store ya ƙare" Cikin girmamawa ya duƙa ya ɗau kuɗin yace "ranki ya daɗe sai dai ban gane me ki ka ce in siyo ba" Ta kalleshi a wulaƙance sannan ta ce "Kai abun naka ma ya yi maka yawa, to dankali nake nufi, kai Allah ya rabamu da rayuwar ƙauye rayuwar jahilci" Bace mata uffan ba, ya juya ya fara tafiya, ita ma ta nufi hanyar shiga cikin gidan. Wani ɗaki ta shiga cikin muryarta ta iyayi take faɗin "Mummy, Mummy" "Na'am har kin dawo?" "Eh na dawo, ina wannan yaran suke?" "Suwa kenan?" "Maids ɗin nan mana" "Suna sashin su" "To na bawa wannan tsohon kuɗi ya siyo mini Irish, dan na gidan nan ya ƙare, ni kuma shi nake son ayi min fatensa da dafaffen ƙwai in yi lunch da shi" Mummy ta ce "shikenan, Allah sa kar ya yi miki shirme" "Wallahi kuwa, ni wallahi da za'a bi ta tawa kawai a sallami mutumin nan, shekara da shekaru ya ci abun da ya ci ai, Amma Daddy ya dage lallai sai shi ze din ga gadin nan, dan Allah Mummy ki ba shi shawara a canza tsohon nan" Zare ido Mummy tai tace "ke Fadila rufa mini Asiri ina zaman zamana, ba ruwana" Ɗan tura baki ta yi, sannan ta ce "Any way, bari in je in kwanta dan na gaji sosai, idan ya kawo sa karɓa, ayi mini fatensa a saka yaji sosai, sai a dafa mini ƙwai guda uku a ɗora a kai ". Mummy ta ce "Ina fatan kin gaya musu da kan ki?". Fadila tace "Ai ni ƙarasawa kitchen ɗin ma wahala zai bani, ni dai kya gaya musu". Ta ƙarasa Maganar tare da juyawa, ta bar ɗakin. Tana zuwa nata ɗakin, ta jefar da takalmanta a tsakar ɗakin, ga gurin ajiye jakunkuna, amma ta yi jifa da ita wani gurin, ta cire hular kanta ta yar a ƙasa, ta haye kan ɗan matsakaicin gadonta tana hamma, tare da yin miƙa". ******* Zaune take a gaban murhu, tana tura busassun kararen tafasa, sai uban hayaƙi ne yake tashi, sai fifita wutar take da wani ɗan ƙaramin murfin bokiti, tana jan majina, ga idanunta sun yi jawur saboda yajin hayaƙi. Can da ƙyar wutar ta kama, a hankali ta furta "Alhamdilillah" ta sake gyara zaman tukunyar da ke kan murhun. Sai da ta tabbatar wutar ta kama sosai, sannan ta miƙe ta tattare duk tarkacen da ta tara a gurin, ta gyara gurin, ta bar iya murhu da kararen da ke cikinsa. Ta koma ta ɗakko garin masara a cikin buhu, da ƙwarya da rariya, ta samu guri ta zauna akan tabarmar kabar da ke shimfiɗe a ɗan ƙaramin tsakar gidan, ta fara tankaɗe. Wata farar mata ce ta fito daga wani ɗaki, hannunta riƙe da carbi, take faɗin "Masha Allah, yarinyar kirki wutar ta kama kenan?". Shiru tayi ba ta amsa ba. "Ke Amina magana fa nake miki". Firgigit ta dawo daga tunanin da take, ta fara kokawar kwance buhun garin masarar nan. Matar tace "Amina, wai tunanin me kike yi haka ne?". Wadda aka kira da Amina, ta yi ajiyar zuciya tace "Inno, Wallahi tunanin jarrabawar placement ɗin mu nake yi". Inno ta taɓe baki tace "Ai sai ki yi tayi, wannan bokon ko ita ce karatun shiga aljanna yaci ace kin haƙura haka". "Inno, dan Allah ki fahimce ni, ina matuƙar son karatun nan ne, dan Allah ko rance ne, ki aro kuɗin nan, in biya jarabawar nan, kafin Baba ya turo kuɗi". Inno ta ce "ba abunda zan aro Wallahi, shegiyar boko da bata da wani amfani, kin yi abun da ki ka yi, sai ki haƙura haka, ki dawo ki yi Aure, amma ana ta ƙananun maganganu akan ki a garin nan, saboda baban ki ya ɗaure miki gindin wani wai sai kin yi boko, har yanzu banda tarkacen takardu, ba uban da ki ka ajiye a bokon, shekara da shekaru kina galmashura a titi yawon boko, kullum sa dai ki kawo takaddun banza ki ajiye. Ni na kusa ɗakko buhun takardun ma, in yi makamashi da shegu kowa ma ya huta". Ba tare da gazawa ba, Amina ta kuma cewa "to dan Allah Inno, ni ki bari in rubuta wasiƙa a kaiwa Baba, ya taimaka mini, ya aikon da kuɗin in biya jarrabawar, tun da ba zaki biya mini ba". Inno tace "Ke Yanzu ya turo da kuɗi ai muna da tarin buƙatun da suka fi na wannan bokon banzar ta ki amfani, ba wani kuɗi da zan bari ki kai wata makarantar boko". Amina ta ɗan tura baki tace "Inno dan Allah ki dena cewa bokon banza, Wallahi ilimi yana da matuƙar mahimmanci ga rayuwar 'ya mace". "Dalla rufe mini baki, mahimmancin me? Mu da ba muyi bokon ba mutuwa mu kayi? Ko kuwa wani abu ya same mu? Ni yi sauri ki yi ki gama mini aikina, kije wancan tijararren ƙanin uban naki, yace kije ki kaiwa matarsa Niƙa". Take Amina ta tsuke fuska tace "ba in da zani, 'ya'ya nawa ne a gidansa, amma ni aka mayar kamar jaka, in yi aikin gidanmu, na gidansa sai naje na yi musu, Wallahi ba zani ba, idan na gama girki ruwa zan ɗebo mana". Inno ta ce "Ni dai ba ruwana, kin san halinsa, kar ya zo yana mana ihu a cikin gida". "Yayi da wata ba dai da ni ba" Amina tai maganar tana hura hanci. *********** "Ke! Meye sunan naki ma? Ina Abincina da nace ku girka mini?". Wadda aka yiwa kiran wulaƙancin, ta ɗan risuna tace "Anty ai ba'a kawo dankalin ba" "What? Kamar yaya?" "Eh, Hajiya tace Baba Hassan zai kawo dankali, mu karɓa mu girka miki, amma be kawo ba". "Yanzu duk wannan yunwar da nake ji, ba'a kawo dankalin bama, balle in saka ran a dafa a bani, wato yunwa ta kasheni ba shi da asara ko? Lallai wannan an yi tsohon kawai". "Kaiii, Fadila ya ne? Tun daga ɗakina ina jiyo muryarki kina faɗa, ke da waye ne haka?" Tai maganar tana ƙarasowa cikin falon. Fadila kamar za ta yi kuka tace "Mummy, kinga tsohon nan ko? Tun da na dawo fa na aike shi, saboda yunwar da nake ji, amma wai haryanzu be dawo ba" tai maganar ƙwalla na taruwa a idonta, saboda ɓacin rai. "Sorry sweetheart,yi haƙuri a kawo miki ko custard ne ki sha, kar ki zauna da yunwa, ni kaina lamarin tsohon nan na ƙular da ni, amma kiyi haƙuri". Haka ta dinga rarrashin Fadila, kamar wata jaririya. Kaɗan ta sha Custard ɗin, ta nemi guri ta kwanta a kan kujera tana chatting, Matar gidan kuma ta maida hankalinta kan kallo. Sallama ya din ga kwaɗawa a ƙofar falon, amma daga Fadila har mahaifiyarta, babu wanda ya iya amsawa. Hakan ya sa shi shigowa, da uban buhu a kansa, a zatonsa ba kowa a falon. Yana shiga yai kiciɓis da Fadila, da babarta a falon, wanda hakan ya haddasa masa faɗuwar gaba. Ya dake tare da faɗin "Hajiya sannunku da gida, nace dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri, Wallahi na sha wahala sosai kan in samo saƙon naki, dankali yayi wuya, kiyi haƙuri dan Allah". Takaici ya hana Fadila Magana, sai wani uban tsaki da ta ja, ta gyara kwanciyarta. Ganin ba ta da niyyar Magana, ya sa ya miƙe ya kuma sunkutar buhun, zai yi ciki da shi, har ya kai ƙofar da zata sada shi da kitchen, A sukwane Fadila tace "Kai zo nan, zo da sauri". Ba shiri ya juyo cikin hanzari, ya dawo falon. "Wane irin dankali ka siyo ne?" Tai maganar tana kallonsa cike da masifa. Yace "ranki ya daɗe dankali ne dai da kika ce". "Oya kwance buhun nan, in ga wane iri ne?". Ba musu ya sunkuya, ya kwance buhun, ya zura hannu ya ɗakko wane irin murgujejen dankalin Hausa, jikinsa duk ƙasa, kamar a jefi mutum da shi yana nunawa Fadila. "Innalillahi, meye wannan? Nice zanci Wannan abun? Mummy kalli abunda ya siyo, ni na taɓa cin wannan abun ne?". A dirirce yace "hajiya ai shine dankalin". "Shut up please, ba Irish nace ka siyo mini ba? Banda jahilci i even repeat myself, irish potatoes, kawai sai ka kawo mini wannan abun? Is not late for you, yakamata ko yaƙi da jahilci ka je kayi, ko ka dinga gane abubuwa, kar ka yadda tsufa ya ƙarasa riskarka cikin jahilci. And Carry that rubbish and leave my view, before I open my eyes, ka ɗauka kaje ka ci, wannan abincin yunwa ba zan iya ci ba, ka tashi ka bani guri" Kalmar Jahilci, ta fi komai ɓatawa Baba Hassan rai, tare da tsaye masa a wuyansa, wani irin zafi da raɗaɗi ya dinga ji a zuciyarsa, duk da kasancewar sa mutum mai haƙuri, amma yau ya ƙulu, tabbas ba dan yana duba wasu abubuwa ba, da tuni ya bar aikin nan, amma maigidan mutum ne mai alkhairi da karamci a gareshi, kuma idan ya bar wannan aikin be san wanne ze yi ba. Haka nan ya tashi, ya ɗau buhun dankalin nan, ya baro falon zuciyarsa a cunkushe, yana jin kamar yayi kuka, amma ya danne, saboda be san me hawayen na sa ka iya haifarwa Fadila a rayuwarta ba. Fadila kuwa saboda tsabar ɓacin rai, sai da tayi kukan baƙin ciki, saboda yadda tsohon ya ɓata mata lokaci, ga kuma yunwa tana ji, amma ba yadda ta iya. ******* Tana zaune a ajinsu, wanda galibi 'yan ajin nasu, 'yan wasu ƙauyukan ne, amma daga ƙauyensu su biyu ne suke zuwa Makarantar haryanzu, sauram duk an musu Aure, wasu tun a primary ma. Abun duniya ya ishi Amina, ta rasa yadda za ta yi ta samu wannan kuɗaɗen, ta biya kuɗin jarrabawar nan. Ga lokaci yana ta ƙurewa, idan aka riga aka yi jarrabawar nan babu ita, shikenan karatunta ya koma baya. Duk yadda za tayi ta samu kuɗin nan ta yi, amma ba ta samu ba, gaba ɗaya dabararta ta gama ƙarewa. "Amina Hassan, ki zo inje Malam Lawan" cewar wata ɗaliba da ta zo ta tsaya a kan Amina. Amina tace "to ina zuwa". Sannu a hankali ta tashi, ta bar ajin, jikinta duk a sanyaye, damuwa ta hanata sukuni gaba ɗaya. Sallama ta yi a Staff room, ta tarar da Malam Lawan a zaune shika ɗai. Ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa Sannan yace "Amina, yaya haryanzu shiru ba ki kawo kuɗin jarrabawar ki ba, ga lokaci yana ta ƙurewa, yaya ne?". Jiki a sanyaye tace "Malam zan kawo insha Allah". "To ai lokaci ne yake ƙurewa, bana son a rufe baki biya ba". Amina tace "Insha Allah, zan kawo malam". "To shikenan, Allah ya dafa". Ta amsa da Ameen, ta fita ta koma aji, tana cigaba da tunani. Duk da tsananin zafin ranar da akeyi, ba ta ji, sannu a hankali take tafiya, ita zafin ranaf sam ba ya damunta Kamar yadda biyan kuɗin jarrabawar ta ya dameta. "Aminatuu" aka kira sunanta. Tsayawa ta yi ta waiwaya, wani dogon matashi ne baƙi a gefen wata bishiya. Murmushi tayi tace "Laa Saminu, ina wuni". "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya Makaranta?" "Lafiya ƙalau, ashe ka shigo garin namu?" Saminu yace "eh na shigo jiya, babanki har ya bani saƙo na kaiwa Inno ɗazu da safe". Amina tace "kashh, ina ta neman yadda zan magana da shi, kafin yayo mana aike, har an biya albashi ne?". Saminu yace "A'a, ai wata ko rabawa be yi ba, naje gaisheshi ne nace ko yana da saƙo, shine ya bani dankalin Hausa kaya guda yace a kawo muku, da dubu ɗaya". A ranta tace 'dana san za'a kawo dankalin nan, da siyar da shi a kayi, aka bani kuɗin in biya jarrabawa, dan yanzu ko me zanyi, Inno ba za ta bari a saida dankalin nan ba'. Ta kalli Saminu tace "dan Allah Saminu, ka aramini Salularka, in kira Babanmu, ina son yin magana da shi". Saminu yace "ba damuwa" ya ɗakko wayarsa, ya kira lambar baban Amina ya bata wayar. Baba Hassan kuwa yana zaune, yau tsawon kwanaki huɗu kenan, da cin zarafinsa da Fadila ta yi, amma ya kasa mantawa, ya dinga tuna lokacin da ake binsu za'a kama su a kaisu Makaranta amma iyayensu suka hana, Yanzu ga ranar ilimi. Wayarsa da ya ji tana ruri, ya ɗauka ya kara a kunnensa, tare da yin sallama. Cikin farinciki Amina tace "Babana". "Na'am Aminatu na, ya kike?". "Lafiya ƙalau Baba, munga saƙo mungode Allah ya saka da alkhairi". "Ameen Aminatu na, kuyi haƙuri ba ayi albashi bane, ya Innar ta ki?". "Lafiya ƙalau Baba, sai dai.... "Sai dai me?". "Baba ance mu kai kuɗin jarrabawa, kuma bani da kuɗi, Inno kuma tace ba zata biya mini ba" Amina ta ƙarasa Maganar Kamar za ta yi kuka. Jiki a sanyaye Baba yace "nawa ne kuɗin?". "Baba dubu huɗu ne" Baba Hassan yai shiru yace "Uwata kinga ba'a daɗe da yin wancan albashin ba, ki kai rashin lafiya na turo muku da duk kuɗin, kuma yanzu wata ko rabawa be yi ba, amma in Allah ya yadda, zan laluba, sai in bayar a kawo miki". Amina tace "to Babana, nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya bani ikon yin karatu, in zama wata ka bar aikin gadin nan". "Ameen uwata, Allah ya yi miki albarka, ki gaida mini da babar ta ki". "To Baba sai anjima" ta katse wayar, ta koma gurin Saminu, ta miƙa masa wayar tana murmushi tace "Saminu ga salular, nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi". Saminu yace "Ameen, ki gaida gida". Daga haka,ta kuma saɓar hanyar da zata sadata da gidansu. Ko da taje gidan, ta tarar da Inno ta dafa dankalin da Baba ya aiko da shi daga birni. Amina tayi murna sosai, ko bakomai yau za su huta da cin tuwo, su ci sakakken Abinci. Tai shiru da bakinta, ba ta gayawa Inno ta yi waya da mahaifinta, akan zai aiko mata da kuɗin Makaranta ba, dan muddin ta sani, ƙwacewa za ta yi, dan bokon nan da Amina take zuwa, a wuyan Inno take. Amina na ta dangwalawa da ƙuli tana ci, tana korawa da ruwan randa mai sanyi. "Salamu Alaikum" "Wa'alaikum salam" Amina ta amsa. "Wai inji Babarmu tace ki zo, ki samo musu ruwa zasu ɗora girki". Cewar yaron da yai sallama. Amina ta kalli yaron tace "ka tambayesu nawa suka sa kuɗi suka siyoni a kasuwar bayi? Idan har ba zaku ɗebo musu ruwan ba, to ku mutu da yunwa". Inno na ɗaki tana salla, amma sai wata uwar gyaran murya take yi,kamar ba salla take ba "Eheeem, Mmm, Eheeem" kamar ta kira sunan Amina a sallar nan. Amina kuwa sai da ta dire ayar zancen da take yi, yaro ya juya ya fice. Amina tace "Inno, ba fa a irin wannan gyaran muryar a salla, a bokonmu mun karanta a littafin addini, ba'a son wani sauti ya fita idan kana salla, amma kamar za kiyi magana". "Kyaci ubanki ke da bokon, wato ki kai musu wannan aiken, salon su zo su tayar mana da bala'i a gidan nana da tsakar ranar nan ko? Wai ke meyasa ba kya gudun magana ne?". Amina tai shiru ba ta tankawa Inno ba,ta cigaba da cin Abincinta. "Salamu Alaikum, kina ina ja'ira mara kunya, har a aiko kije aike, amma kice ba zaki je ba, har da baƙar magana, 'yar banzar Yarinya da ido kamar bururin gawayi" wani mutum ne ya shigo yana surfa bala'i, yana saɓa babbar riga kamar zai fuka fuki ya tashi saboda masifa. Amina ta sunkuyar da kai ƙasa, tai shiru, ya dinga zazzaga mata masifa,a ƙarshe yace "Na fuskanci wannan bokon wofin da kike zuwa, ita ce take sawa kina yiwa Mutane rashin mutunci, naga uban da ze sake bari kije bokon, Aure zan miki kan Hassan ɗin ya dawo, tun da dama shine yake goya miki bayan yiwa mutane fitsara, Wallahi ko sadakar ki ne bayarwa zanyi, uban kowama ya huta, algunhuma me suffar munafukai". Sai da yayi ya gama ya fice, daga Inno jar Amina babu wanda ya tanka masa, sai da Ya fita sannan Inno tace "kinga abunda nake jiye miki ko? Ai gara ai miki Auren, kowama ya huta, ƙila kyayi hankali, ga abunda bakinki ya janyo miki nan" Amina tace "na fuskanci bokon nan ce tasa duk aka tsaneni, ni kuwa tunda faɗar Annabi ce Sallallahu alaihi Wasallam, yace mu nemi ilimi, ko daga nan zuwa birnin Sin ne, to Wallahi a shirye nake in ɓata da kowa. Dan kawai ina zuwa boko da na motsa sai zagi, dan me zasu maida ni baiwarsu? Kawai dan banyi Aure ba ina zuwa Makaranta kowane aikin wahala sai ya dawo kaina?, To idan ba'ai mini Aure kan Baba ya dawo ba, ni zan gudu kan ai mini Auren dole, dan Wallahi na zaɓi karatuna akan wannan mutanen". Inno ta zaro ido tace "ke Amina, ba ki da hankali, ƙannen uban naki?". "Su ɗin fa, me suka taɓa tsinana mini a rayuwa? Kullum burinsu su ganni a wahala ni da mahaifina, Wallahi aka takurani, zan tattara kayana in koma birni, in ta bulayi har in gano in da Baba yake, muyi aikin gadin tare!. Domin gyara sharhi, ko shawara 07063065680 GABA DA GABANTA Page 2 By Aisha Adam (Ayshercool/Jakadiyar Arewa) (Shin kin karanta littafin DARE DA DUHU?, Wanda yake daga gamayyar alƙaluma uku, daga haziƙan marubuta uku, Zee kumurya, Nimcyluv da kuma Ayshercool, kar ku bari a baku labari, ku mallaki na mu akan Kuɗi Naira 300 kacal. *DARE DA DUHU* _Allahamdulillah Babu Abinda bright pens za su ce sai godiya a gareku. Kun amshi littafin fiye da kima. Duk cewa Fiction story amma da yawan Labarin abune na da muke fuskanta reality🌚😢_ *DARE DA DUHU* ₦300 NE Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal. Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750) Amina na zuwa nan a maganarta kawai sai ta fashe da kuka. Sai kuma jikin Inno ya yi sanyi, ta kalli Amina ta ce "Amina, ta wani fannin ƙannen mahaifinki suna da gaskiya, ba abin da ya dace da 'ya mace, mai shekaru kamar ki sai zaman aure, wannan gararambar da ki ke yi a titi, da sunan karatun boko gaba ɗaya bai dace da ke ba, yanzu da za kiyi aurenki babu me binki gidanki ya ce sai kin zo kin masa wani aiki, amma ki duba maganata". Amina ba ta ce komai ba, ta cigaba da share hawayen fuskarta, daga bisani ta tashi ta saka hijjabinta, kasancewar babban gidane ɓangare-ɓangare ne a gidan, ta zagaya ɓangaren Baffa Lawan, ƙanin mahaifinta dan kai musu niƙan. Baba Hassan kuwa ya shiga tsananin damuwa da tunanin yadda zai samo Wannan kuɗin da Amina ta tambayeshi, tabbas ya na son Amina ta yi karatu me zurfi, ko bakomai ba za a yi mata gorin Jahilci ba, kamar yadda a kayi masa, har abun ya ke masa ciwo ba. Amma a ina zai samo kuɗin? Shi ne babbar damuwar sa. **************** Kallo ɗaya za ka yi mata kasan a gajiye ta ke, hannunta riƙe da wani ƙaramin bokiti, bayanta kuma wani yaro ne da kaya a kansa ya ke binta a baya. Ƙofar wani ɗan ƙaramin gida ta tsaya, shi ma yaron ya tsaya, ta sauke masa kayan kan sa, ta buɗe jakarta ta ɗakko masa Naira ɗari ta bashi, sannan ta shiga da kayan cikin gidan. Sallama ta yi ta shiga cikin tilon ɗakin da ke tsakar gidan. Matar da ke zaune akan sallaya daga cikin ɗakin ta amsa tare da ce cewa "Sannu da zuwa". Cikin siririyar muryarta ta ce "Yawwa mama, ya jikin naki?" "Jiki da sauƙi Hafsa, ya cinikin?" Ɗan ɓata fuska Hafsan ta yi ta ce "To, Alhamdilillah amma dai yau babu daɗi, dankali be ƙare ba, na dawo da sauran fal". Matar ta ce "Bakomai, ki kwantar da hankalinki, sai mu ci da ranar nan, sauran sai ayi sadaka da shi". "To Mama, bari in je in yi wanka in zo in yi salla, in ƙarasa ayyukan gidan". Mama ta ce "Ai na gama komai ma, kiyi wanka ki ci Abincin". Hafsa ta ce "Mama, ba ki da lafiya ki kayi aikin, da kin bari na dawo ai". "A'a babu komai ai, na ji daɗin jikina Alhamdilillah". "To Allah ya ƙara afuwa, bari in yi wankan". "To shikenan" Mama ta amsa tana ƙoƙarin miƙewa daga kan sallayar. **************** Kimanin kwanaki huɗu kenan da Amina ta yiwa Baba waya akan kuɗin jarrabawarta, amma shiru bai yi mata aike ba, hakan ya ƙara tabattar mata da ba shi da kuɗin ne, ga wannan 'yan uwan na sa, suna da shi ba basu da shi ba, amma ta san ko giya ta ke sha, ba ta isa ta tunkaresu da wani batu akan makarantar boko ba. Dan sun ɗau karatun bokon 'ya mace kamar wani karatun saɓon Allah, mussaman ita da suka sanyawa ido, suna ganin mahaifinta ya bata goyon baya ta cigaba da yawon boko, ya ƙi yi mata Aure, duk sa'aninta duk sun yi Aure, dan galibi tun a sha uku wasu ake aurar da su. Ita kuwa har yanzu babu ma batun Auren a gabanta, ta ƙi bawa kowa dama balle a nemi Aurenta. Misalin ƙarfe biyar na yammaci, Amina tana kan hanyarta ta dawowa gida da ga makarantar allo, ita kanta makarantar Allon duk babu sa'anninta, sai ƙannenta amma hakan bai dameta ba sam, haka ta ke shiryawa ta tafi makarantar allo idan ta dawo daga ta boko, ita ma a makarantar bokon ma ana yi musu ƙarin litattafan addini sosai, hakan ya sa a ilimin addini ma daidai gwargwado ta samu. "Kula mana karki faɗi". Da sauri ta dawo da ga duniyar tunanin da ta tafi, ta kalli mutumin da suka kusa yin karo da juna. "Yi haƙuri" shine abunda ta furta ta na ƙoƙarin wuce Mutumin. Mutumin ya yi murmushi ya ce "Aminatu, ba gaisuwa ne?" "Ina wuni" ta faɗa a daƙile, dan ba ta son doguwar magana, kowani abu da zai haɗata da shi sam. "Lafiya ƙalau,ya Baban ki ko har yanzu bai shigo gari ba?". "Eh bai shigo ba". "Yawwa Amina, ni na gode Allah ma da yasa muka haɗu Yanzu, Amina ya Maganar mu ta kwanaki da na taɓa yi miki ne? Kinga yanzu lokacin kaka ne, da 'yan kuɗaɗena a hannuna, anyi mini girbi amfanin gona yayi kyau sosai, ki bani dama inje in ga babanki ayi Maganar Aurenmu". Ta kalle shi, fuskarta babu walwala ta ce "Idan ka Aureni kakar kuma ta wuce fa? Da me zaka riƙeni?" Ta yi maganar tana watsa masa wani mugun kallo. Mutumin ya gyara tsayuwarsa ya ce "Amina, kamar ba ki san waye ni a garin nan ba, ina da tarin gonaki da dabbobi, wanda ke kanki kin san ni ba talaka ba ne, yanzu haka wani daga cikin amfanin gona da na siyar, baki ga kuɗin da na sake tarawa ba, noman bana ba abin da zamu ce da Allah sai godiya". Amina ta yamutse fuska ta ce. "To ina ruwana da kuɗinka? Kuɗin da ba cib ake yi ba, kamar yadda na gaya maka a baya, yanzu ma zan maimaita maka ne, ni ba zan iya Auren ka ba, ka mini tsufa, duk garin nan ba wanda bai san ka akan auri saki ba, duk shekara lokacin kaka, sai ka yi Aure ka saki wasu, 'ya'ya a gidanka kamar babu me su dan yawa, sunata gararanba a gari, ba kulawa, nima haka ka ke so ka Aureni ka sakeni da 'ya'ya? Dan Allah ka yi haƙuri, ka ga a cikin 'ya'yanka ma akawai ƙawata ai ana barin halak da kunya ma. Ka dinga duba makomar wadda zaka aura, da tarin 'ya'yanka, sannan ni karatuna shine ya dameni ba aure ba a yanzu, dan haka dan Allah ka ƙyaleni". Galala ya bi Amina da kallo, be taɓa zaton tana da baki haka ba, duba da ƙarancin shekarunta. "Ke Yanzu kin gwammace ki tsufa a gari, ba kiyi aure ba? Kuma aike zan kashe miki kuɗi sosai, sai gidan da kike so zan sai miki, ba a cikin iyalina zan haɗaki ba". "In dai Auren irin ka ne, da shi gara babu Wallahi, ni ka ga tafiyata ma" ba ta kuma saurarsa ba, ta tafi ta bar shi a gurin a tsaye cike da takaici. ************** Mummy ce ta fito Falo, cikin wata dakakkiyar shadda ruwan toka, ta sha stone work, wuyanta zuwa hannunta duk gold ne, hannunta riƙe da mayafinta da jakarta. A falo ta tarar da wata mata da yara guda biyu, kai da ganin matar ka san a wahala take, saboda yadda suke sanye da kaya tamkar tsumma, saboda koɗewa. A wulaƙance Hajiya Zainab, wato Mummy ta bisu da kallo, ya yin da suka risina suna gaisheta. Ba ta amsa ba, ta ce "Lafiya daga ina?" Matar ta risuna ta ce "Hajiya baki gane ni ba? Azumi ce maƙociyarku ta nan bayan layi". Mummy ta sake ɓata fuska ta ce "Ohhh, sai yanzu na gane ki, ke ɗin ce kullum ƙara lalacewa ki ke kina ƙara muni, lafiya kuwa?" "Hajiya taimakon nan dai da ki ka saba, shine na sake zuwa yau ma a taimaka, Wallahi marayuna ne yau kwana uku ba abin da na iya ba su suka ci, su masu sickler ga ciwo ya tashi, ga babu Abinci, na buga na buga na rasa yadda zan yi, shine na ce bari in zo don Allah ko ƙanzo ne ki taimaka ki bani in ba su" ta ƙarasa maganar ta na fashewa da kuka. "Ya isa ni dan Allah yi mini shiru, ku zo ku takurawa mutane, kuna wani kuka kamar ragon mayya ku a dole sai anji tausayinku, ku haifi yara kaɗan ba zaku iya ba, ku daɗi miji su yi ta kwanciya da ku kuna haihuwa, ƙarshe ko su gudu ko su mutu su barku da 'ya 'ya". Fadila ce ta fito ita kuma cikin wani tsadadden material me kyau, tana faɗin "Mummy am ready" tana ganin su Azumi a falo, ta yi turus tare da toshe hanci ta ce "Mummy Warin meye haka?, su kuma wannan mai suke yi mana haka a falo?". A wulaƙance Hajiya Zainab ta ce "Wai yau ma dawowa ta kuma yi, ta na neman taimako". "Kuma shi ne za su shigo mana falo, sai warin datti suke yi, mai yasa ba su zauna a waje ba in kin fito kya same su?" "To ya zan yi? Wannan sakaran mai gadin ya buɗe musu sun shigo". Cike da ƙyama Fadila ta ce "dan Allah ku ɗan jirata a haraba mana, wannan gaba ɗaya kun canza tempreture ɗakin kamar zan yi amai. Ke wa kuke da suna Asabe ki ke kowa? Wata a cikin ku ta zo ta sake mopping ɗin ɗakin nan, a kunna turaren wuta". Azumi ta ji haushin abun da Fadila ta yi mata, ita da babarta amma babu yadda ta iya, haka ta koma waje ta jira. Duk wannan wulaƙanci da cin zarafin, dubu biyu kacal Hajiya Zainab ta iya bawa Azumi, wanda sai da Azumin ta durƙusa tana mata godiya. Suna tafe a mota, Mummy na cigaba da mita, da nuna tsantsar ƙyamarta ga talaka, tare da nuna kamar iyawarta ce ta sa Allah yayi ta a cikin daula. ******** Abun duniya ya saka Amina a gaba, yau saura kwanaki uku ya rage, a rufe karɓar kuɗin jarrabawar su, gaba ɗaya ta sare, ta san Baba ba shi da kuɗin nan ne, dan da akwai su da tuni ya aiko mata da su. Gefe guda baba Rabi'u ya uzzurawa rayuwarta da takura, akan Lallai sai ta amince da shi, ta yadda ya aureta. Fafur ita kuma ta ce ko maza sun ƙare, ba zata auri tsohon da bai san darajar mace ba, balle 'ya'yan da yake haifa. Ga matsin lamba na gidansu, daga ɓangaren 'yan uwan mahaifinta, na takura da aike saka ta aiki kamar baiwarsu, ga gore-gore, har da sharrin yawon banza ta ke yi a gantalin makarantar bokon da ke yi. Hakan ya haifarwa Amina shiga cikin matsananciyar damuwa, da tunani daban-daban a cikin ranta. Baba Hassan kuwa, ya yanke shawarar kiran maigidan a waya, wato baban Fadila kasancewar ba ya gari, ya roƙi Alfarmar ko a cikin albashinsa ne, a taimaka a bashi rancen kuɗin da zai biyawa 'yarsa kuɗin Makaranta. Haka kuwa aka yi, ya kira maigidan ya sanar masa da halin da yake ciki, da buƙatar da yake da ita, ba tare da wani ɓata lokaci ba ya ce masa 'Zai kira Hajiya a waya ya sanar mata, ya je ya karɓa kawai a biya mata'. Baba Hassan ya yi farinciki matuƙa, yayi ta godiya da karamcin Alhaji Ahmad, sai dai yadda zai tunkari Hajiya Zainab da maganar kuɗin kawai yake tunani, saboda rijiya ta sha bada ruwa guga ya hana a gidan nan. Ƙiri-ƙiri mai gidan zai yi alheri ta hana, ko ya ce ayi taƙi yi, kusan duk me son wani abu agurinsa sai ya biyo ta hannun hajiya Zainab, idan kuwa ka na son abun a gurinta, sai ka ƙasƙantar da kanka tamkar bawa, ta gama wulaƙantaka kafin ka samu. AMINU KANO, INTERNATIONAL AIRPORT. Tafiya yake sannu a hankali, yana jan wata 'yar madaidaiciyar Akwati, hannusa ɗaya ɗauke da wayarsa ya kara ta a kunnensa yana tsumayin a ɗaga wayar da yake kira. A ɗan hasale ya fara Magana "Wai dan Allah kana ina ne? Na sauka fa ina sauri inje gida, ni da nasan haka zaka yi mini, da babu abun da zai sa in ce kazo ka ɗaukeni" Yana gama maganar, ya sauke wayar zuwa cikin aljihunsa, yana jan guntun tsaki. Sannu a hankali ya cigaba da tafiya, ba tsammani ya ji an ce "To shugaban masu haƙuri, ina daf da kai fa, amma ka kirani kana ta wannan masifar haka" Ya kalli Matashin da yake maganar ya ce "Dalla ware malam, kana sane ma ka shanyani kenan? Dana sani gida na yi waya azo a ɗaukeni". Matashin yayi murmushi ya ce "Kai dai can da yawarka, masifaffe kawai, bani in tayaka ɗaukar jakar". Ba tare da ya ce masa komai ba, ya sakar masa akwatin, yayi gaba abunsa. Suna tafe a mota, ba wanda yake magana a cikinsu, can ɗayan ya kalli abokin tafiyar tasa ya ce "Haba Khalil, ka ɗan yi murmushi mana, ko har yanzu fushin ne?" "Ban sani ba, ni dalla ka ƙara speed ɗin motar nan, mu yi muje gida". "Ba zan ƙara ba, in ban sauke ka a titi ka hau Napep ba ba sunana Abdul ba" Khalil ya ce "Saboda na hau motarka ka ke mini rashin mutunci?". "Eh, uban waye ya sa ka kirani? na zo na taimaka maka amma kana mini wulaƙanci". Jinjina kai Khalil Yayi ya ce "Good". A bakin gate ɗin gidansu Khalil Abdul yayi parking, ya kalli Khalil Ya ce "Mun zo sai ka sauka". "Wai a nan zaka ajiyeni?". Abdul Ya ce "Au ban maka ba? Wai kai mai yasa ba a iya maka ne? Ware Malam" "Wallahi zaka gane ba ka da wayo, zan zo har gida in maka rashin mutunci" Abdul ya ce "Rashin mutunci yau ka fara yi mini? dalla fita". Ƙwafa kawai Khalil yayi, ya fice da ga motar. Asabe ce ta shiga ɗakin Fadila, za ta gyara mata, tana gyaran tana mita ƙasa-ƙasa saboda yadda Fadila ta ke watsar da komai a ɗakin yadda ta ga dama. Hatta kwano sai ta ci Abinci ba zata ɗauke ba sai an ɗauke mata. "Dan Allah kalli ɗakin nan kamar sheƙar mahaukaciya, yarinya ta na mace amma ba ta san gyara ba, saboda tsabar sangarta da iskanci, ɗan kanfai ma, sai da ta saka ta tara sai mun wanke mata, Aikin banza kawai" haka Asabe ta cigaba da tattare shirgin da Fadila ta tara a ɗakin na ta, ta gyara ta wanke mata banɗaki, tare da wanke mata ƙananan kayanta da ta tara a cikin bokiti a banɗaki". Asabe na kammalawa ta fito falo, ta tarar da Fadila ta na kallo, a wulaƙance Fadila ta kalli Asabe ta ce "ki cewa wannan wadda ku ke aikin tare, meye sunanta Hajara kowa? Za ta bar uwarta da yunwa ne, kamar yadda ta yi mini? Ta bar ni ina jiran ta kawo mini Abinci amma shiru". Asabe ta risuna ta ce "zan gayamata insha Allah". "Kar ki kuskura ki sake zuwa gabana da wannan ƙazamin hijjabin, ba kya jin yadda yake wari ne?" Wani irin haushi ya kama Asabe, amma haka ta dake ta ce "To insha Allah" Asabe na zuwa ɗakin girki, ta tarar da Hajara na ta ƙoƙarin haɗowa Fadila Abinci, ta kalli Hajara ta ce "Ance idan uwarki ce za ki bar ta da yunwa?" Hajara ta kalli Asabe ta ce "Kamar yaya?" "Kamar yadda aka ce in gaya miki" Jiki a sanyaye Hajara ta ce "Allah ya bamu abun yi mu bar aiki a ƙarƙashin mutane marasa mutunci irin wannan, tun da na shigo gurin nan fa aikin Abincin nake" "Hmm, ke dai bari, ni kaina na gaji, da ina da wata hanyar samun kuɗin, da tuni na bar gidan nan". Haka suka cigaba da tattauna matsalolin gidan aikin nasu. Bayan saukarsa daga motar Abdul, gate ɗin gidan ya nufa, ya na zuwa ya tura ƙofar gate ɗin ya ga ta buɗe. Baba Hassan ya taso yana faɗin "Waye a nan?" "Baba ni ne" Khalil ya furta a hankali. Murmushin fuskar Baba Hassan ya faɗaɗa da yaga Khalil ya ce "Kai ne da zuwa haka ba sanarwa? Maimakon ka kira a zo a ɗauke ka". "Bakomai Baba, Abdul ne ya ɗakko ni na same ku ƙalau?". "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya aikin?" "Aiki Alhamdilillah". Baba Hassan ya ce "bari in kai maka jakar" Khalil ya ce "A'a ka bar shi Baba, na gode, kayi zamanka" Khalil ya nufi cikin gidan. "Oh my God Mummy brother" Fadila ta faɗa da ƙarfi, tana maƙalƙale Khalil. Tureta Khalil yayi ya ce "Ni cikani kar ki kada ni". Mummy ce ta fito tana faɗin "Au, ashe da gaske kike, wane irin zuwa ne wannan ba sanarwa a safiyar nan, kamar korarre?" Khalil yayi murmushi ya ce "Mummy kullum idan zan shigo kuma sai na faɗa?". "Ahh ai sanarwar yana da kyau, amma dai ba wannan babur ɗin ɗan sahun ka hawo ka dawo gida ba ko? Kar kasa maƙota su mana dariya" "Mummy kenan, Abdul ne ya ɗakkoni daga filin jirgi". Fadila ta tura baki ta ce "Sai murna na ke ka dawo, amma ko kallo ban isheka ba". "To zan ɗauke ki ne ina ihu nima?" Mummy ta ce "Amma yadda ta damu da kai ɗin nan, ai yakamata kaima ka nuna mata ka damu da ita". Khalil ya ce "waye zai damu da wannan fitsararriyar? Bari in tafi ɗakina in ɗan watsa ruwa in huta". Mummy ta ce "Bari a saka masu aikin nan su gyara maka, na san yayi ƙura, tun da saukar safe kayi, akwai sauran kayan karin kumallo, sai ka karya" Ya ce "Ok shikenan". Ya tashi ya tafi dining, ya zuba abinci yana ci, Fadila sai surutu ta ke masa". Zuwa ƙarfe huɗu na yammaci, Khalil ya shirya cikin ƙananan kaya ya fice, da ƙudurin tafiya gidan su Abdul ya je ya ƙare masa rashin mutunci. Yau kwana guda, da Baba ya roƙi Alhaji Ahamad kuɗin da zai biyawa 'yarsa kuɗin jarrabawa, kuma ya bashi damar ya karɓa a gurin matar gidan, amma sanin halinta ya sanya shi a fargabar yadda zai tunkare ta da wannan maganar. Amma a rashin tayi akan bar arha, dan haka ya yanke shawarar zuwa ya nemi Alfarmar, ko Allah yasa ya dace. Jiki ba ƙwari, ƙasan zuciyarsa yana Addu'a, ya tunkari babban falon gidan. Da sallama ya shiga falon, sai dai duk da girman nan nasa da shekarunsa, baya hana shi shiga fargaba, idan har yayi tozali da Fadila, saboda gudun tozarci da wulaƙanci, kamar yadda ta kasance yanzu, ya tarar da ita hakimce a falon tana aikin na ta, na danna waya wanda a shi tafi ƙwarewa, danna waya kallon talabijin kai lomar Abinci sai kuma bacci da tarin rashin mutunci. "Barka da yamma ranki ya daɗe" Baba yayi Maganar yana risunawa. Ba ta ɗago ta kalleshi ba ta amsa sa da 'Yawwa'. Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Dan Allah hajiya fa". "Tana sashinta". 'Dama Alhaji ne ya aiko ni gurinta". "Sai ka zauna ka jirata, sai ta fito". Bai ce komai ba, ya rakuɓe a falon, yana rarraba ido. Fadila ta kara waya a kunneta tare da faɗin "Uwar bacci, tun ɗazu na ke kiranki a waya, amma shiru ba kya ɗagawa, dama ce miki zan Brother ya shigo gari fa, gara ki shirya ki bayyana". "Girl are you serious?". "Amma kin san bana miki wasa a irin wannan lamarin ko". "Wow, Alhamdilillah aikuwa zaki ganni yanzun nan" suka yi shewa a tare, sannan suka yi sallama. Baba Hassan tun yana zaman da marmari, sai da ƙafafunsa suka yi sanyi, ya gaji sosai, dan a ƙalla ya kai awa guda a zaune. Ba tsammani sai ga Hajiya Zainab ta fito, ita ma ɗauke da waya a kunnenta. Ta zauna ta cigaba da wayarta, ba tare da ta saurari in da Baba Hassan yake zaune ba, hirar kasuwancinta kawai take yi, tare da ambaton Manyan kuɗaɗe a cikin wayar. Sai da ta ƙare wayarta sannan ta kalleshi ta ce "Malam lafiya ka shigo mini falo ka ƙwafe haka kamar ana zaman fada?". Baba Hassan ya gyara zamansa ya ce "Amm, dama gurinki na zo Hajiya, Alhaji ne ya aiko ni". "Ya aiko ka, ya ce me?" "Dama na kira shi a waya ne, yarinyata zata zana jarrabawa, bani da kuɗi, shine ya ce in zo in karɓa a gurinki". "Kai kuwa malam Hassan, yakamata ka dinga jin tsoron Allah, yaushe aka baka albashi har da zaka dawo ka ce ga zance ga magana?" Cikin rauni Baba Hassan ya ce "Dan Allah Hajiya ki taimaka, ni ko rance ne, bana son karatun 'ya ta ya samu naƙasu, idan ya so sai a cire a albashi na". "Allah wadaran halin talaka, sam ba ku da godiyar Allah, mutum ko naman jikinsa ya ke yanka yana baku ba zaku gode ba. To ni bani da cash a hannuna, sai ka haƙura sai zuwa lokacin da aka ɗakko mini kuɗi a banki". Ya sake duƙawa ya ce "Hajiya ki taimaka, za su rufe karɓar kuɗin ne". Fadila a ƙufule ta ce "wai baka ganewa ne? Babu kuɗi a hannunta Yanzu, amma sai magiya ka ke". Baba Hassan ya ce "to shikenan Hajiya, Na gode" ya tashi jiki a sanyaye ya bar Falon. ******** Zuwa yanzu Amina ta gama fidda rai da samun kuɗin da zata biya na jarrabawa, dan yanzu haka tana zuwa makaranta ne kawai, kafin wanɗanda suka biya kuɗin jarrabawar su fara. Kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, haka take tafiyar, tana ƙoƙarin shiga gida ta hangi Kawu Bala, a ƙofar gida yana alwala, kai da ganin alwalar ta sa kasan jahilci ya samu gindin zama a tare da shi, saboda yadda watsa ruwan alwalar nan ko ta ina. Tana ƙoƙarin durƙusawa ta gaishe shi cikin masifa ya ce "Ke Amina zo nan". Ba musu ta zo ta durƙusa ta ce "Gani kawu". "Da ga gidan ubanwa ki ke?". "Daga makaranta" "Yawon barbaɗa da ta zubar ba?" Kallon Kawu Bala tayi, tare da jin haushin mummunar kalmar ta zubar da ya jinginata da ita. Ya kalleta ya ce "Ina son sanin dalilin da yasa, Malam Rabi'u ya nuna yana sonki, amma dan iskanci ki ka yi masa rashin mutunci". Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Kawu, ta yaya zan iya Aurensa, mata nawa ya aura ya saka a garin nan? Kalli yadda yaransa suke babu cikakkiyar kulawa, idan na Aureshi yayi yaya dani? Kuma ban fa gama Makaranta ba har yanzu". "Kinga idan na kuma magana kika yi mini zancen bokon nan, saina karairaya ki, shashasha mara kan gado, na fuskanci akan bokon nan kike wannan iskancin, na fuskanci a can suke hure miki kunne, to ba zai yuwu ba, ubanki ya tsallake ya tafi nasa guri ya bar mu da ke, ke kuma ki ɗakko mana abun kunya ba, saboda wata boko ba, dan haka daga yau na kuma ganin kin je makarantar boko, Wallahi sai na saɓa miki kin ji na gaya miki. Kuma kiji da kunnenki, zamu karɓi kuɗin Auren Malam Rabi'u, ba zaki cigaba da gandamewa a gida ba, sa'oinki na gidan Aure suna neman aljanna, ke kuma kina tamɓele a titi da uwar jaka da sunan boko, shegiyar bokon da ke ba kuɗi a ke baki ba sai wahala, da wannan wahalar banzar gara in ba zaki yi Auren ba, ki shiga cikin maza a dinga zuwa da ke gona kina noma". Tuni hawaye ya wankewa Amina fuska ta ce "Dan Allah kawu kayi haƙuri, ku bari in ƙarasa makaranta, ko ina gamawa ne sai in yi Auren, in ya so ku aura mini wanda ku ke so, amma banda Malam Rabi'u dan Allah". "Au ke zaki faɗi abunda ki ke so ayi?, ai kuwa ba ki isa ba, ko Hassan ubanki bai isa ya ja da maganata ba balle ke, tashi ki bani guri, Allah ya ƙara nuna mini kin fita daga cikin gidan nan da sunan wata makaranta, wuce ki bani guri, da ido kamar gujjiyar mayu". Cikin kuka Amina ta shiga cikin gida, kai tsaye ɓangarensu ta wuce, ta tarar da Inno tana surfe. Sakin taɓaryar Inno ta yi, ta nufo in da Amina ta shigo tana kuka, tare da faɗin "Ke Amina lafiya? Waye ya rasu kike wannan kukan?". Cikin kuka Amina ta ce "Kawu Bala ne wai ya ce kar in sake zuwa makarantar boko, wai Aure za suyi mini". Tsaki Inno tayi ta ce "Shine za ki shigo kina mini wannan uban ihun, bokon banza da na wofi, matsa daga kusa da ni kar in makeki". "Haba Inno, kema haka zaki ce? Yanzu kin yarda su aura mini Malam Rabi'u baban su Furera?" Zaro ido Inno tayi ta ce "Malam Rabi'u kuma? Wannan mara mutuncin?" "Shi fa, kawu Bala ya ce wai za su karɓi kuɗinsa na Aurena". Jiki a sanyaye Inno ta ce "To Amina kiyi haƙuri, kin san duk gidan nan babu wanda yake musu da Kawu Bala, ciki kuwa har da mahaifinki, shi yasa na so kafin su farga su yanke makamancin wannan hukuncin, ki fitar da mijin Aure, amma yanzu lokaci ya ƙure Amina, kin san tun da ya waiwaye ki ba wanda ya isa ya sanya shi canza Magana". Amina ta ɗora hannu a ka, ta zunduma ihu ta durƙusa a gurin ta na faɗin "Wallahi idan aka aura mini mutumin nan an gama da rayuwata, sunana bazawara, dan Allah ku ƙyaleni in yi karatuna". Inno ta ce ki rufa mana Asiri, kar ki sa su ɗauka wani abun ne, ki sa su shigo su yi mana tijara". Miƙewa Amina tayi ta shige ɗakinsu, tana cigaba da kuka har cikin ranta. ******** Tamkar wasu taɓaɓɓu haka suke ta shewa a falon. Wata siriyar yarinya ce Kamar Fadila, cikin skirt high west, da wata body hook, sai hula a kanta, ta yi simple make up. Hatta yanayin rawar kanta da iyayinta irin na Fadila ne. Dama hausawa suka ce, sai hali yazo ɗaya ake abota. Fadila ta kalli ƙawar tata ta ce "Yusra kin ga yadda ki kayi kyau kuwa? Ni kaina na yaba, ina ga shi wanda aka yiwa kwalliyar?". Yusra ta ce "Girl brother nan naki sai a hankali, Allah ya sa in ishe shi kallo". Fadila ta ce "dalla kar ki damu, zai yaba haba sai kace ba namiji ba, dole ya ƙyasa, yanzun nan zai shigo, muje ɗakina in ƙara gyara miki kwalliyar nan, a ƙara powder da turare". Haka kuwa aka yi, suka shiga ɗakin Fadila, da yake Fadila gwanace gurin kwalliya da gyaran jikinta, tsaftar muhalli ce komai sai dai ayi mata. Yusra ta kuma fitowa ta yi ras da Ita, suka dawo falo suka cigaba da hira. Suna tsaka da hirar ne, suka ji shigowar mota gidan, Fadila ta leƙa ta window, da sauri ta dawo tana faɗin "Girl, gashi nan, shine ya dawo". Cikin hanzari Yusra ta sake feffesa turare, da sake gyara zama. Khalil ne ya shigo falon, hannunsa riƙe da wayarsa da makullin mota. Yana shigowa gaba ɗaya Yusra ta rasa nutsuwarta, saboda tsananin kwarjinin da Khalil yake da shi. "Ina wuni Brother" Yusra ta faɗa cikin fargaba. "Yawwa sannunki" ya amsa yana ƙoƙarin shigewa. Fadila ta ce "Brother, baka gane ta bane? Yusra ce fa". Khalil yayi murmushi ya ce "Na ganeta mana, ai nace mata Hi ko?". Yayi Maganar yana hararar Fadila. Ba Yusra ba, Fadila kanta ta ji haushin yadda Khalil y nunawa ƙawarta halin ko in kula, duk da wannan tarin hoda da turare da ta saka saboda shi. Gyara sharhi ko shawara 08081012143 Ayi following account ɗina a Arewabooks@ Ayshercool7724 Da kuma Watpad Ayshercool 7724 Share Please 🙏 GABA DA GABANTA Page3 By Aisha Adam (Ayshercool) (Shin kin karanta littafin DARE DA DUHU?, Wanda yake daga gamayyar alƙaluma uku, daga haziƙan marubuta uku, Zee kumurya, Nimcyluv da kuma Ayshercool, kar ku bari a baku labari, ku mallaki na mu akan Kuɗi Naira 300 kacal. *DARE DA DUHU* _Allahamdulillah Babu Abinda bright pens za su ce sai godiya a gareku. Kun amshi littafin fiye da kima. Duk cewa Fiction story amma da yawan Labarin abune na da muke fuskanta reality🌚😢_ *DARE DA DUHU* ₦300 NE Via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal. Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750) DADICATED TO BRIGHT PENS Saroro suka yi gaba ɗaya suka bi bayan Khalil da kallo. Yana shiga sashin Mummy ya dawo falo, ya kalli Fadila ya ce "Ke ina Mummy ne?" Fadila ta tsuke fuska ta ce "Ba ta nan". Ya ce "ok" Yusra ba ta gajiya ba ta ce "Yaya a dawo lafiya". "Ameen thanks" daga haka ya fice. Fadila ta ja wani uban tsaki, ya yin da Yusra ta yi shiru tana tunani. Fadila ta ce "Girl, ki yi haƙuri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawari insha Allah sai Brother ya so ki". Yusra ta ce "Till when dear? Wallahi ba zaki gane yadda nake son Yayan nan naki ba, amma kwata-kwata ya ƙi damuwa dani". "Kin san me? Kar ki damu, You know he is very classic, shi komai nasa baya son raini, shi yasa amma zamu shawo kansa very soon". Yusra ta ce "Shikenan, Allah yasa, bari in wuce gida". Fadila ta ce "Muje in raka ki" suka fito harabar gidan, suna cigaba da tattauna yadda za su ɓullowa lamarin Khalil. **************** Ta gama shirinta tsaf, cikin dogon hijjabinta, sai dai ta janyo kujerar tsugono ta zauna, ta zubawa kayan gabanta ido. "Hafsa, ya har yanzu baki tafi ba, ko almajirin da zai taya ki ɗaukar kayan ne bai zo ba?". Hafsa ta ce "Mama, jarin mu ne yayi ƙasa, ana samun ciniki Alhamdilillah, amma kin ga a ciki muke komai, har magungunanki a ciki muke siya, kuma jarin ba ƙaruwa yayi ba, itace ma bashi na karɓa, mai ma kuɗin rabi na bayar aka bani, na cika sauran daga baya idan nayi cinikin yau". Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Na sani Hafsa, ni babban abun da ya dameni, shi ne mu zamana bamu da taro ko sisin da muke juyawa, amma insha Allah komai zai wuce, watarana sai labari, Allah ya kawo dalilin da zai rabaki da wannan siye da siyarwar bakin hanyar, bana so raina ba ya mini daɗi". "Bakomai Mama, Allah ya kawo mana mafita ya baki Lafiya, dangin mahaifina abun da suka yi mana, Allah ya ninka musu" ta ƙarasa Maganar hawaye na zubowa daga idanunta, alamun tana cikin damuwa. Mama ta girgiza kai ta ce "A'a Hafsa, Allah ya shirye su kawai, ki daina kukan nan" Mama tayi Maganar tana share mata hawaye. Hafsa ta share hawayenta ta ce "Naji tsayuwar Napep a waje, bari in tafi kar in yamma, me zan taho miki da shi?". "A'a bana buƙatar komai, Allah ya tsare, ki kula da kan ki, kar ki wasa da mutuncinki". "To Mama insha Allah" ta kwashi kayan sana'arta, ta fita da su. ********** Fadila na falo tana kallo, duk tayi kaca_kaca da falon, in da suka ci Abinci ita da Yusra sun bar komai a falon, ga tarkace duk ta tara shirgi, Asabe na ta kaiwa tana komowa tana gyarawa, ita kuwa ta hakimce akan kujera tana ciye-ciye. Mummy na zaune a gefe, tana danna wayarta, tana chatting da abokan kasuwancinta. "Hmm, wai kin san me Yaya Khalil yayi mini kuwa Mummy?". "A'a sai kin faɗa". "Gaba ɗaya ya gama yarfani yau ɗin nan, mussaman na yiwa Yusra waya akan ya zo gari, ta bar abun da take ta zo gidan nan, amma kin ga da ta gaishe shi da yadda ya amsa?". Mummy ta ce "Ai ni na rasa gane kan yayan nan naki, sam ba shi da alƙibla, yarinyar tana da kirki da hankali, gata 'yar masu kuɗi, sam banga aibunta ba". "Kema dai kya faɗa Mummy" suna tsaka da hirar sai ga Khalil yayi sallama". Mummy ta amsa ban da Fadila, da ta kuma haɗe rai. Khalil ya ce "Mummy na dawo ɗazu ki bani National id card ɗina, zan cike wasu takaddu, amma ba kya nan". "Eh naje duba shagona ne na zoo road, sun yi mini waya wai wasu kayan sun ƙare". Khalil ya sauke idanunsa a kan Fadila ya ce "Yawwa, ke kuma na dawo gareki, daga yau idan yarinyar nan ƙawarki ta kuma zuwa, ki ka sa tana mini shishshigi sai na makeki a gabanta". Mummy ta ce "wai kai shikenan ba'a masa abun Arziƙi kenan? Meye laifin Yusran nan ne?". "Ba na son raini, kawai sai in fara Soyayya da ƙawar ƙanwata, dan abun Kunya? Wata bushshiya da ita ba fasali". "Kai dai ba'a yi maka abun arziƙi, ban da wulaƙanci meye laifin yarinyar nan? dan ma ka samu ance ana sonka da wannan masifar taka da zafin rai". Khalil ya ce "Dama bance ace ana sona ba, a bar ni in samo Yarinya daidai da ni, wadda ta yi karatu me zurfi mai hankali da tunani". Mummy ta taɓe baki ta ce "Ka ji da shi dai, a garin zaɓen zaka zaɓo mummuna, ni dai fatana a samo mini 'yar babban gida, kar a kwaso mini 'yar talakawa, wanda ba su san mutunci ba". Khalil ya ce "Mummy kin ga yadda ginina na Abuja yayi nisa kuwa? Tunanin yarinyar da ta dace da gidan nan nake". "A samo wadda za'a iya kai maka kayan Arziƙi dai shine fatana" Khalil ya kalli Fadila da ta haɗe rai ya ce "Ke yaushe zaku fara lectures ne?". "Saura sati biyu" ta faɗa tana cunkusa baki. "To ki maida hankali dai, dan Jami'a ba gurin zuwa ayi sakarci bane". Hararsa ta yi a fakaice, dan ya gama ƙular da ita yau ɗin nan. "Ki yiwa yaran nan magana su kawo mini Abinci na kan dining, and Abdul ya ce yana gaisheki". Fadila ta ce "Waye wani Abdul kuma?". "Ban sani ba" Khalil ya bata amsa. "Nifa ya dena wani rawar kai a kaina, me zan yi da shi?, yana lecturer mai na sama ya ci balle ya bawa na ƙasa?". "Fadila me kike cewa?" Khalil yayi Maganar a fusace. "Ai nima naga cewa kayi ba ka son ƙawata, ita da tafi wani Abdul komai, nima dan me zan so shi, kuma shima ya san ni ba kalarsa ba ce, Nasan albashinsa ko mayukana da turaruka na ba zai siya ba". Khalil zai yi Magana Mummy ta dakatar da shi ta ce "Kar ka takura ta ƙyaleta, nima ban goyi baya ba". "Amma Mummy me yasa? Naga Abdul ɗin nan abokina ne, tare muka yi School, kun san halayensa gaba ɗaya". "Kai babanka ne ya biya maka kaje karatu, shi kuma gwamnati ce ta bashi tallafi, aikin da yake ma ba babanka ne ya samo masa ba? Idan yana da kunya ai ya san Fadila ba sa'ar sa ba ce". Shiru Khalil yayi jin Mummy ta goyi bayan Fadila, amma har ga Allah bai ga aibun abokin nasa ba, kuma ya san da Fadila za ta Aure shi, za ta ji daɗi saboda yana da kirki, kuma yana matuƙar sonta, amma ya kasa gaya mata saboda yadda Izzarta take masa kwarjini. ************ Amina ce zaune a ɗaki, ta sanya langar koko a gaba, tana ta uban kuka tamkar wadda aka cewa babanta ya mutu. Inno ce ta ɗaga labulen ɗakin ta ce "Wai ba zaki daina kukan nan ki tashi ki karya kumallo ba?". Shiru Amina ta yi, ta cigaba da raira kukan ta". "Ji min 'yar abar da malam ya hana ni faɗa, ba magana nake miki ba, ai ni Kawu Balan ya gama yi mini komai da ya hanaki zuwa bokon nan". Sake fashewa da kuka Amina ta yi ta ce "Haba Inno, haka zaki ce?". "Eh haka nace, me ake da wata boko? Ki tashi ki karya ki zo ki ɗebi kayan wankin nan, ki je ki wanko mana su". Haka Amina ta tashi, ta ɗauki kokon nan ta kafa kai, babu siga sam a cikin sa ga gasarar ta yi tsami sosai, amma haka ta kafa kai tana zuƙarsa kaɗan-kaɗan. ************** Baba Hassan ya zabga uban tagumi, ya san ko ba'a gaya masa ba, Amina na can a cikin damuwa akan kuɗin da ta tambaye shi, amma babu yadda ya iya dan yayi iya yin sa, amma bai samu ba, kuma ya san da gayya Hajiya Zainab ta hana shi kuɗin nan, ba wai dan babu kuɗin ba. Yana ganin shige da ficen Khalil a gidan, amma ba zai iya tambayarsa ba, duk da ya san idan ya tambaye shi zai bashi, amma yana jin nauyin yaron sosai. Gashi ya san idan ya kira mai gidan ya ce ba'a bashi kuɗin ba, nan ma wata matsalar ce, yana gudun haɗa fitina a tsakanin ma'auratan, kuma dama shi kansa mai gidan akwai taƙama, ba ya son takura sam. Haka Baba Hassan ya din ga tunani, amma ya kasa gano mafita gaba ɗaya. ************** "Mummy wai Ina Fadila ne? Tun da na shigo ban ganta ba". Mummy ta ce "zai wuce ace tana bacci ne?". "Bacci a yanzu Mummy? Ƙarfe sha biyu da rabi fa" "To ta fito ta yi breakfast, ta koma ɗaki ta kuma kwanciya". "Amma Mummy kika ƙyaleta, da haka za'a Jami'ar?" "To yanzu dai tun da ba Jami'ar ta shiga ba, ai ka bar ta ta huta ko? Gwanin na iya, sarkin hantara da zare idanu". Girgiza kai ya yi ya ce "Idan ta shiga makaranta, wani sakarcin idan ance tayi ba za tayi ba". "Ai ni shiyasa na so babanku ya kaita ƙasar waje, kamar yadda ake kai kowacce 'yar gata, amma ya ƙi wai rawar kanta ta yi yawa, da shikenan ba ruwanta da tashin hankalin Jami'oin Nigeria" "Aikuwa tun da haka ba ta samu ba, dole ta koyo sabawa da tashin hankalin Jami'oin Nigeria, kuma ko ina aka kaita ba'a samun ilimi ta sauƙi". Mummy da ta gaji da tsarin Khalil ta ce "Jeka na ji Babana". Be kuma cewa Uffan ba ya fice. Daga gida kuwa kai tsaye gidansu Abdul ya wuce, wanda ɗakinsa ya ke jikin gidansu da banɗakinsa da komai, dan haka Khalil ba sai ya shiga cikin gidansu Abdul ba. Abdul yana zaune yana marking tes ɗin ɗalibai, Khalil ya yi sallama. Abdul ya amsa masa tare da cewa "Daga ina haka?". Khalil ya zauna ya ce "Wallahi da ga gida, ni duk garin ma ji nake ya isheni". "To sai ka tattara ka koma in da ka fito, dama ni mamaki ma na ke, kawai ka baro aikin ka ka dawo gida ka zauna". Khalil yayi murmushi ya ce "Har wani aiki ake? Ni Wallahi ginina ne ya dameni, ka san wannan Plan ɗin da muka fitar shi nake yi fa". Abdul ya ce "Kai, amma fa zai ci kuɗi da yawa". "Aikuwa yana ci sosai, amma ka san kuɗi ba matsala ta bane". "Na sani, kana ta gini ba matar Aure, kuma maimakon kayi ginin a nan, amma ka tafi Abuja" "To ba'a can nake aiki ba, Kano ina da gida, Yaushe za'a ƙarasa naka ginin ne malam Abdul?" Abdul ya yi murmushi ya ce "Abubuwa ne sai a hankali, ka san siblings ɗina, ni ke hidimar karatunsu, rayuwar sai Alhamdilillah, ga yaran Yaya Hameed da ya rasu ya bari, nine kamar babansu Yanzu, ni ke kula da su, ka ga ba zan bari su wulaƙanta ba dan ba ransa". Khalil ya yi murmushi ya ce "Allah sarki, duk faɗan da muke yi da kunna ni da ka ke wasu lokutan, Halayenka abun koyi ne Abdul, Allah ya ƙara maka Arziƙi, Insha Allah da an samu wani space ɗin aiki zamu haɗe a Abuja". Abdul ya ce "Kai Khalil, wannan aikin ma da na samu ta silarka na ke yi na ji daɗi, bani da bakin godiya, amma ka bar ni kawai, na nemi kasuwanci in haɗa". "Wallahi ba ka isa ba, dole mu tafi tare, kuma filin jikin in da nake gini a Abuja, ka kawo half ɗin kuɗin, in cika maka kawai ya zama naka". Abdul yayi dariya ya ce "Ba zaka ƙare a kai na ba, amma Allah yasa ginin da na ke a Kano ya burge Fadila, wai ni kana ma miƙa mata saƙon gaisuwata kuwa?" Jikin Khalil ne yayi sanyi amma ya dake ya ce "Malam kawai ka rabu da wannan yarinyar". "Saboda me? Ko dai ba zaka bani ita bane, saboda ni talaka ne?" "Kai haba dai, wace irin magana ce wannan, ni ba ruwana ka nemi soyayyarta kawai, zan wuce maka gaba gurin Daddy, yanzu dai ka tashi muje yawo". "Yawo kuma? Kai zaka mini aikin marking ɗin?". "Kai dalla ka dena takurawa kan ka malam, zo muje Chilling kawai". "Gaskiya ka hanzarta ka zo ka koma in da ka fito, duk ka addabeni tun lokacin da ka dawo". "Wallahi sai ka taso" Abdul ya ce "To Jarababbe ai ka bari in tashi in kintsa ko a haka zan fita?". "To kintsa mu fita". Khalil yana jin daɗin abotarsa da Abdul, iyayen Abdul talakawa ne, ƙoƙarin sa da kuma rahamar ubangiji ya sanya ya samu Scholarship, na karatu a Malesia, wanda a nan suka haɗu da Khalil, Mahaifiyar Khalil ba ta son mu'amalarsu Saboda shi ba ɗan masu kuɗi bane, amma Khalil ya nacewa Abdul. Abdul ya fuskanci Mahaifiyar Khalil ba ta son sa, dan haka ba ya son zuwa gidan sam, Khalil yana da izza irin ta yaran masu kuɗi, saboda ko ba komai ɗabi'a naso take, amma bai san yana yi ba, kuma sam baya nunawa Abdul Izzar. Babban abun da yasa yake son Abdul shine, mutum ne mai wadatar zuci, ga girmama mutane, dan idan mahaifin Khalil yana gari, wataran ya kan sai abun da yake da shi, yaje ya gaisheshi, hakan yasa shi kansa mahaifin Khalil yake son Abdul. Ganin ba yadda Hajiya Zainab ta iya ne, ya sa ta ƙyalesu suke abota, hatta motar da Abdul yake hawa, Khalil ne ya bashi. Mahaifin Khalil shine ya samarwa da Abdul aikin lecturing, ya yin da nasa ɗan ke can Hukumar Land a Abuja. Abdul ya daɗe yana son Fadila, amma ya kasa gaya mata, saboda yanayin yadda ta ke gudanar da al'amuranta. Hakan ya sanya ya gayawa Khalil yana son ƙanwarsa, Khalil ya ji daɗi, amma ya san ba abune mai yiwuwa ba, saboda yadda ahalin su ke ƙyamar talaka!. ************** Yau ta kasance ita ce ranar Fadila ta farko a Makarantar Jami'a, sai da aka sha yaƙi da ita, sannan ta tashi ta shirya da safe, tamkar wata ƙanƙanuwar yarinya. Mummy sai mita take tana in dai haka Fadila zata cigaba, Wannan karatun ba mai yiwuwa bane ba sam. Da kanta tayi driving motarta zuwa School, sai dai ta dinga bin 'yan ajin nasu da wani irin kallo mai kama da na ƙasƙanci. Guri ɗaya ta ware, can gefe guda ta yi zamanta, ba tare da ta shiga sabgar kowa ba, sai hura hanci kawai da take yi. Malamar farko da ta shigo fara yi musu lectures, ta yi musu nasiha sosai a kan mahimmanci mai da hankali a kan karatu, da irin yanayin yadda rayuwar Jami'a ta bambanta da ta sakandare. Ba laifi malamar ta sha gayu tsaf da ita. Ajin ya haɗa da waɗanda suna kammala Sakandire suka samu gurbin karatu, da waɗanda suka shafe lokaci a gida ba a samu gurbin karatu ba, a taƙaice dai ajin ya haɗa yara, matasa da kuma dattawa. Ƙarfe sha biyu, Fadila ta ɗau jakarta ta koma gida, ba dan an gama lectures ɗin ba, sai dan yadda gaba ɗaya zaman makarantar ya ishe ta, ga warin hammata da wasu daga cikin samarin ajin suke yi, duk da wadattaciyar iska da fankoki da suke ajin, amma bai hana wasu idan suka gifta taji ba, wanda hakan ya sa ta fara jin tashin zuciya ta ce ba zata iya zama ba. *********** Kamar kullum bayan sallar magariba sannan kayan sana'ar Hafsa suka ƙare, ta tattara kayanta ta nufo gida, sai dai tun daga yadda ta ji Mama ta amsa mata sallama ta san jikin Maman babu daɗi. Cikin azama Hafsa ta shiga ɗakin tana faɗin "Mama ya naji muryarki haka? Jikin ne?". Mama dake kwance ta tashi zaune da ƙyar ta ce "A'a lafiyata ƙalau Hafsa har kin dawo" ta yi maganar tana haki. "Mama gashi kina haki, amma kice mini lafiyarki ƙalau? Bari in ɗauko miki maganinki" Hafsa ta tashi da sauri ta nufi in da take ajiyewa Mama magungunanta, Mama kuwa bin Hafsa tayi da ido, cike da tausayawa. Hafasa na duba gurin magungunan babu sai fankon ledar maganin, ta kalli Mama jiki a sanyaye ta ce "Mama dama maganin ya ƙare baki gaya mini ba?" "Bana son tayar miki da hankali ne, kuma dama kin ce jari yayi ƙasa, bashi yayi yawa, kinga dole a lallaɓa kar mu cinye jarin gaba ɗaya". "Haba Mama, ai lafiya gaba take da komai, kuɗi kona waye ai gara in taɓa in sai miki magani, bari im je gurin Magaji, idan yana nan ya zo ya duba jinin naki, sai in taho miki da maganin". "To Hafsa, kar ki daɗe amma, kiyi maza ki dawo ga wani Abinci can na ajiye miki" Hafsa ta ce "To mama, daga nan ta fice". Kai tsaye chemist ɗin Magaji ta tafi, ta tarar ba kowa a shagon sai shi da wani abokinsa, wanda duk unguwarsu ɗaya. Tayi musu sallama suka amsa mata, ta kalli Magaji ta ce 'Magaji dan Allah so nake a duba mini awon jinin Mama, idan ya hau ne sai a bata maganinta, na dawo na tarar tana haki". Magaji ya ce "Gaskiya ina da abun yi yanzu". "Don Allah ka taimaka, bata da lafiya sosai" tayi maganar cikin damuwa. Magaji ya ce "Ashe alfarma tana da daɗi Hafsa? Ai da har gida nake zuwa ina yiwa mahaifiyarki gwajin, amma na nuna ina sonki, ba kunya kika nuna ba kya sona, kuma saboda kina da kunya shine kika kuma dawowa neman alfarma a gurina". "Ita Alfarma ana nemanta ne a in da ya dace, ana alfarma akan komai amma banda So, ban taɓa keta bulle na na nemi Alfarmar wani ba, saboda gudun ƙasƙanci sai a gurinka, kuma ka nuna mini iyakata, daga yau ka rubuta ka ajiye, idan ni Hafsa na kuma neman Alfarma a gurinka, kai mini duk cin mutuncin da ka ga dama" tana gama faɗin haka ta juya ta bar Chemist ɗin. Tana tafiya Magaji ya ce "Aikin banza, yarinya ba 'yar uban kowa ba, sai izza da girman kai, tana 'yar talaka futuk, tana suyar awara akan kwalbati, amma zan nuna ina sonta ta wulaƙantani". Abokin Magaji mai suna Nura ya ce "Nikam burgeni take, ba ruwanta da shirme da rawar kan 'yan matan unguwar nan, a nutse take". "Kai dalla ware, ba wata nutsuwa, duk buge ce, ni ban ma san tsautsayin da ya kaini cewa ina sonta ba, bayan ma 'yar mace ce, har wata nutsuwa ko tarbiyya ce da 'yar mace?". Nura ya ce "A'a Magaji, da ta yarda da soyayyarka, ba zaka kirata 'yar mace ba". Haka Magaji ya cigaba da sukan Hafsa, Nura yana karewa. Hafsa kuwa ganin kuɗin hannunta ba su da yawa, ta san ba zasu isa ta kai Mama Asibiti ba, haka ta haƙura taje wani Chemist ɗin ta sai mata irin maganinta, duk da akwai buƙatar a sake gwada jinin amma babu yadda ta iya. Khalil ne ya shigo ya tarar da Fadila tana gayawa Mummy yadda 'yan ajinsu suke, da yadda wasu suke addabar su da warin hammata. Khalil ya ce "Zaki ga warin hammata, kije ki yi musu hauka suyi miki dukan tsiya, dan ba kowa zai ɗau rashin kunya ba". "Aikuwa da na saka an kulle mini yaro kowaye ubansa a garin nan" Mummy tayi Maganar tana zazzare ido. Khalil ya girgiza kai ya ce 'To ni dai jibi in Allah ya kai mu zan koma gurin aiki". Mummy ta ce "Allah ya kiyaye hanya, dama ka takurawa 'ya ta, gashi kuma next week babanku zai shigo gari". Khalil ya ce "Allah bai yi zamu haɗu ba, ma yi waya da shi". ************** Gaba ɗaya yau Amina ta wuni jikinta babu daɗi, wanda tsabar damuwa da kuka ya haifar mata da ciwon kai, yau 'yan ajinsu suke zana paper ƙarshe babu ita, haka ta sha kukanta ta godewa Allah. Inno ta tursasa mata cin abincin dare, dan wuni tayi ba ta ci komai ba, sai kwanciya. Tana tsaka da cin tuwon ne, ɗan gidan Baffa Lawan yayi sallama ya ce "Amina kije Malam Rabi'u yana sallama da ke a waje". Amina ta ce "Ka je kace masa bana nan". Yaron ya juya ya fice. Inno ta ce "Wato ke dai Amina ba kya gudun magana ko?". "Inno to ni ya ake so in yi? Ni Wallahi ba zan iya Auren wannan mutumin ba". Suna cikin Magana Baffa Lawan ya shigo yana hayagaga yana ɗaga murya. "Wato wuyanki ya yi kaurin da za'a ce ana sallama da ke ki ce aje ace ba kya nan? Zaki tashi ki je ko sai na kakkarya ki, sakarya yarinya mara Albarka". Amina na kuka ta tashi ta Sanya hijjabinta, Baffa Lawan ya cigaba da sababi yana cewa Inno ce ke goya mata baya take rashin mutunci. "Kuma ki san da saninki, na saka gonar babanki a kasuwa, an samu mai saye gobe za muje mu karɓo kuɗin, ai miki kayan ɗaki ds su, Hassan ko yana nan ko ba ya nan, zamu aurar da ke" Ƙara fashewa da kuka Amina ta yi, ta nufi hanyar fita tana goge hawaye. Malam Rabi'u yana tsaye a ƙofar gida, yana ganin Amina ta fito ya fara murmushi, duk da babu wadataccen haske a gurin, amma hakan be hanashi ƙare mata kallo ba. "Amaryata barka da wannan lokaci, ya Mutanen gidan?". "Yanzu tsakani da Allah ka yi mini adalci kenan? Dan me zaka takura sai ka Aureni? Nace maka ba zan iya aurenka ba, ana dole ne?". Malam Rabi'u ya ce "Ai ko ba kya so na ni ina sonki, kuma wan mahaifinki ya ce ya bani ke, kuɗin Aure kawai zan kawo wani satin, kuma ba za'a sanya lokaci mai tsawo ba". Wani haushi ne ya sake kama Amina, ba ta kuma ce masa uffan ba, ta juya ta koma cikin gida tana wani tunani a ranta. *************** Ku san sati biyu da fara lectures, amma kullum sabbin ɗalibai zuwa suke yi, sai dai haryanzu Fadila ta kasa sakewa da 'yan ajin, sai wasu 'yan mata su biyu, suma dan ta ga irinta ne 'yan ƙarya yaran masu kuɗi, suma ba wani sakewa take da su sosai ba. Ana tsaka da lectures, sai ga wani matashin saurayi ya shigo, dogo ne sosai wankan tarwaɗa, yana sanye da wani yadi ash, amma yadin nan yayi haske saboda tsufa, amma ya sha guga, kansa ya sanya hula tashi ka fiye naci, sai ɗan ƙaramin asuwakinsa a bayansa, hannunsa ya naɗa shi da wani ɗan ƙaramin carbi. Sallama ya yi, wanda ya sanya gaba ɗaya hankalin 'yan ajin dawowa kansa, saboda yadda yayi Maganar Kamar cikin iyayi. Aka amsa masa, lecturer ya ce "Kai Ustaz da ga ina?". "Daga gida Malam" ya faɗa cikin girmamawa. "Gida dama yanzu ne lokacin da yakamata ka zo aji?". "A'a malam ayi mini afuwa dan Allah, Insha Allah ba zan sake ba" Lecturer ya bashi iznin ya je ya zauna. Ƙafarsa Fadila ta kalla, ya sanya takalmi soso irin na maza, takalmin duk ya cinye, ga ƙafarsa tayi futu-futu tamkar an haƙo shi daga rami. Aikuwa Fadila ta tuntsire da dariya, gaba ɗaya aka juyo ana kallonta, shima waigowa yayi ya kalleta, ya ga ƙafarsa take kallo tana cigaba da dariya, ganin abun da take wa dariya, ya Sanya wasu daga cikin ɗaliban suma yin dariya ƙasa-ƙasa, gaba ɗaya sai wata kunya ta kama shi, sai ya ji babu daɗi sam akan abi nda Fadila ta yi masa. Lecturer da ya juyo ya ga Fadila ce tayi wannan dariya, bai tsaya jin me take yiwa dariya ba ya ce ta fita ta bar ajin. Domin gyara sharhi ko shawara 08081012143 Kar a manta ayi following account ɗina na Arewabooks https://arewabooks.com/u/ayshercool7724 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) P4 Arewabooks https://arewabooks.com/u/ayshercool7724 Watpad Ayshercool 7724 Ko a jikinta, Fadila ta ɗauki jakarta, ta fice daga ajin. Shi kam wannan bafulatanin ustazu, ya nemi guri ya zauna, yana ɓoye ƙafarsa, dan ba ƙaramin kunya ce ta kama shi ba, a saboda dizgin da Fadila tayi masa. Fadila kuwa gida tayi tafiyarta abin ta, hankali kwance dan tama manta da abin da ta aikata, kuma ba ta damu da korarta da malami ya yi daga aji ba, dan ita gani tayi ma ya taimaketa. ************ A 'yan kwankin nan da dangin mahaifi, suka sako Amina a gaba, duk ta rame ta yi zuru zuru, ga rashin samun damar zana jarrabawa, gashi Kawu Bala ya hanata zuwa ko ina shi da Kawu Lawan idan ba aike ba, ciki har da makarantar allo, kuma dan wani tsabar wulaƙancin, daga can cikin gidan ma, gurin iyalansu, sai a aiko taje a aiketa, ko a sata wani aiki mai wahala, duk dan a cuzguna mata a ɓata mata rai, abin duniya ya haɗu yayi mata yawa, gashi ba ta da waya balle ta kira Baba ta sanar da shi halin da take ciki, gashi su kawu sun matsa a kan lallai ko yana nan ko ba ya nan, sai sun siyar da gonarsa sun mata Aure. Abin da yake ƙara mata damuwa shi ne, bayan aikin gadin nan, da ɗan gurin da suke zaune a cikin gidan nan, to da Allah suka dogara da Wannan gona kuma guda ɗaya tal, siyar da ita na nufin tozarta Mahaifin Amina ne. "Amina, wai ke sai kin ɗorawa kan ki wata rashin lafiyar saboda wannan tunanin da kike, sannan hankalinki zai kwanta?" Cikin damuwa Amina ta ce "Ba haka bane Inno? Tunanin ne yake zuwa ko ban shirya ba". "Yo dama wani tunani ne zai tsaya jiran sai kin shirya? Na san ba zai wuce tunanin boko ba". Amina ta girgiza kai ta ce "Inno ni na haƙura da karatun boko ma, ni yanzu auren nan nake tunani bana son Auren nan sam, sai kuma gonar Baba da zasu sayar, dan Allah Inno ki saka baki, su ƙyale mana gonarmu" Buɗe baki Inno ta yi ta ce "Ni kaza! Rufamini asiri, kin san ko mahaifinki ba ya jayayya da maganar kawu Bala, balle ni 'yar karo da aka auro". "To ko ni inje in same shi, in masa maganar?, bamu fa da Komai sai gonar nan, kuma ni wallahi ba zan yadda ayi mini wannan auren ba". "Ke ki rufawa kanki asiri, kin ga Amina kiyi haƙuri ki runugumi Auren nan, tun kafin su yi miki wani sharrin, kin san kawu Bala da kaidi kamar mace" "Aikuwa a aurawa wata ba dai ni ba, dan Wallahi da raina da lafiyata ba zan auri Wannan mutumin ba, mara imani wanda bai san darajar Aure ba, mata nawa ya mayar zaurawa, ya auri mace ya saketa ita da 'ya'yanta banda 'ya'yan da ke gidansa, duk kaka sai ya saki mata ya auri wasu haka kurum a kashe mini rayuwa". "Rigimar ki tayi yawa Amina, ke ba a gaya miki gaskiya ki bi, amma ki rubutawa babanki wasiƙa a kai tasha, gara ya zo garin nan a san abun yi, ya san halin da ake ciki". Amina ta yi murmushi ta ce "Ashe dai bokona na da muhimmanci Inno, amma ai baba bai iya karatu ba, wa zai karanta masa, ni nafi son muyi magana da shi a waya" "To a ina zaki samo tarhon?" Amina ta ɗan yi jimm sannan ta ce "Ashirun gidan Jimmale kamar yana da waya". "A'a ni kin san bana san alaƙa da wannan matar, yanzu sai kiji ƙananun maganganu". Amina ta ce "to idan na tuna wata mafitar na gaya miki". Inno ta ce "To shikenan". ************ Sai haki take ta rasa wace kwanciyar za ta yi, domin ta ji daɗi, komai ba ya mata daɗi, Hafsa na zaune a gefenta, tana ta jera mata sannu, tana yi mata fifita. Cikin Muryar marasa lafiya Mama ta ce "Hafsa, ki tashi ki dafa ƙullin awarar can, kar yayi tsami". Cikin damuwa Hafsa ta ce "Mama ba zan iya zuwa gurin suyar awarar nan ba, alhalin kina cikin yanayi na ciwo, ni yanzu hankalina ya koma kan yadda zan samo kuɗi mu tafi Asibiti". "Haba Hafsa, jikina fa da sauƙi kece kike sanyawa kan ki damuwa, amma da sauƙi Alhamdilillah". Cikin halayarta ta miskilanci Hafsa ta ce "Wannan nishin ma da kike duk cikin sauƙin ne? Kin ji yadda ki ke numfarfashi kuwa? Na san fa kina jin jiki sosai, ni dama ciwon ya dawo kaina in ga kina walwalar ki da lafiyarki". "Auzubillah, haba Hafsa, sai kace wata mara imani, ni aka ce miki zan iya jurara ganinki cikin ciwo ne? Ki mini Addu'a kawai, Allah ya bani lafiya, kije gurin sana'arki, ko ba yawa ki samo wani abun, mu sai sabulun wanki". Da ƙyar Mama ta takura Hafsa, ta tashi ta fara kiciniyar haɗa kayan sana'ar, ba dan ranta yana so ba. ***** Duk yadda ya so zuwa Makaranta da wuri, Allah bai yi ba, dan be samu ba sai da ya makara, yana zuwa tuni hall ya cika an fara gabatar da darasi. Baya son zama a can baya, saboda baya ƙaunar zafi ko kaɗan. Wani space ya hango, dan haka cikin hanzari ya nufi gurin yana ƙoƙarin ɗosanawa ya zauna, tare da ciro wata 'yar jotter da ga aljihunsa. "Kai meye haka a kusa dani zaka zauna dan ba ka da hankali?". Cikin magiya ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ba kusa da ke zam zauna ba, gani na yi da sauran guri, dan Allah ki bari in zauna". "Wallahi ba ka isa ba, kut haka kurum Wallahi ba za a kashe ni da warin hammata ba, ka nemi wani wurin". Ganin ta fara ɗaga murya har an fara kallonsu, ya sanya shi cire takalminsa a ƙasa ya zauna a kai. "Kai ba gurin zama ne ka zauna a ƙasa?"Cewar malamin da ke darasi a lokacin. "Malam bana son zaman baya ne, kuma na makara" "Ba ka gudun ka ɓata kayan ka?". "Ba komai, na karkaɗe". Malamin yayi murmushi ya ce "kun ga irin wannan ustazan, da basu ɗau duniya da zafi ba, su ne ƙwarin aji they make it in life". Fadila ta kalli uwar hular kan gayen nan, tashi ka fiye naci ce a kansa, saboda tsabar tsufa har zaren hular ya fara tashi, babu datti a jikinta, sai azabar tsufa, ya takure ƙafafunsa da suka yi busu-busu da ƙura, ya zauna akan takalmansa. Kamar kullum wata dariya Fadila ta kuma yi, tana cigaba da ƙare masa kallo ta ce "wai su ƙwarin aji manya" yana jinta, sai dai ko ɗagowa bai yi ba ya kalleta ba, ya cigaba da 'yan rubuce rubucen sa, duk da ba ya jin daɗin abin da yarinyar take masa. Malamin ya cigaba da gudanar da darasinsa, sai da ya kusa kammalawa sannan ya bada damar tambaya, aikuwa ɗan ustazun nan ya ɗaga hannu, malamin ya bashi dama ya miƙe, ya fara tambayarsa sai dai da harshen turanci yake yi, kuma da alama turancin bai zauna a bakinsa ba, dan sai fama yake ya tattara yayi bayani yadda malamin zai fahimta. Fadila ta ce "Wai turanci ya ga ta kansa, kai kuwa kayi da hausa mana tunda turancin baka iya ba" iya na kusa da su wanda suka ji mai ta ce, suka kwashe da dariya, wanda hakan ya sanya jikinsa yayi sanyi. Malamin ya ce ya cigaba da tambayar, dan tambaya ce mai matuƙar mahimmanci, wadda za'a ƙaru da ita sosai, ya girgiza kai ya ce wa malamin ya gama tambayar. Aikuwa malamin ya dinga fashin baƙin tambayar nan, dan iliminne mai zaman kansa a cikin tambayar. A ka kammala lectures, kowa ya fita sabgar gabansa, masu neman Abinci su siya da sauransu. Fadila na tsaye a jikin motar ta ustaz ya zo wucewa, tana ganinsa ta tuna yadda ya dinga kokawa da turanci ɗazu a aji, aikuwa ta sake bushewa da dariya, yana jinta amma ya sake sunkuyar da kansa ƙasa ya wuce ba tare da ya ko ɗaga kai ya kalli in da take ba. ********** Amina ta dawo daga siyan itace, ta shigo sashinsu taji kawu Bala yana yiwa Inno bayani, wai ranar juma'a Malam Rabi'u zai turo magabatansa, su kuma sun sanya gonar Baba a kasuwa, malam Rabi'u yace zai siyi gonar. Jiki a sanyaye Amina ta ƙarasa ta ajiye itacen, ya mai da dubansa kan Amina ya ce "Au to faɗuwa ta zo daidai da zama, iyayen mijinki zasu kawo kuɗi ranar juma'a in Allah ya kaimu, kuma zai sai gonar mahaifinki ya siya ya bamu kuɗin mu yi miki kayan ɗaki". "Amma baffa idan ka siyar da gonar baba, mai zamu dinga nomawa?". "Rufen baki, mara kunya, ko shi Hassan ɗin ubanki bai isa in magana ya ce zai yi jayayya ba, ke kin je 'yan kwangilar yahudawa sun hure miki kunne har zan faɗa ki mayar ko? To na yanke hukunci na gama" Shiru Amina tayi, zuciyarta na wani irin raɗaɗi, har ga Allah bata son a salwantar da 'yar gonar nan ta su, ga uwa uba wannan Auren da bata ƙaunarsa sam. Bayan tafiyar Kawu Bala, Inno ta ce "Amina yanzu meye abin yi, ta yaya zamu samu mahaifinki balle a sanar masa da halin da a ke ciki?". Amina ta ce "'Nima ban sani ba" Inno ta ce "Ni dai bana son a sayar da gonar nan, kuma da idan sun sayar wata uwar arzikin zasu saya miki na kayan ɗakin da sauƙi, amma na san abin da Allah ya nufe su zasu saya miki, sauran su riƙe abun su". Ita dai Amina ba tace komai ba, saboda takaici ya hanata Magana sam. ********** Abun duniya ya isheta, duk yadda Ummanta ke nuna jikinta da sauƙi, amma ita hankalinta dai yafi kwanciya da ace sunje Asibiti an duba umman nata sosai, sai dai idan har suka ce za suyi jigilar zuwa Asibiti a dubata, to zasu shiga cikin jarinsu sosai, duk da haka ba yadda Hafsa ba tayi ba, a kan Umman ta amince su tafi Asibiti Allah ya kawo wata hanyar, amma Umman taƙi haka Hafsa ta ƙyaleta. Hafa na zaune a bakin rariya, tana wankin waken awara, Umma ta kalleta ta ce "Yanzu Hafsa har yanzu shiru ko ba kowa?" Sarai Hafsa ta gane abin da Umma ke nufi, amma tayi shiru taƙi amsawa. "Nifa wannan miskilancin naki ne yake ƙular da ni, da ke fa nake Magana". "Umma to me zance, kema fa kin san ba kowa ɗin". "Ko a gurin sana'ar taki baki haɗu da kowa ba?" "Umma kefa kike cewa in tsare mutuncina, ni da na fita sana'a ina ni ina kule kulen maza?". "Ba haka nake nufi ba Hafsa, daidai gwargwado kina samun masu sonki, amma kin ƙi ki tsaida hankalinki, kuma ko wannan rashin fara'ar taki da haɗe rai, ya isa ya hana samarin kulaki". Hafsa ta ce "Aikuwa su sha zamansu, dan ni ba su ne a gabana ba". "Au haka ma zaki ce? Ai shikenan idan dangin ubanki suka kuma waiwayoki kya shiga hankalinki ai". "Ai ba su da wani iko da ni, dan haka ba su da damar da zasu ɗaga mana hankali, har yanzu ban manta da wahalar da muka sha a hannunsu ba". "Ki manta ɗin dai shine yafi alkhairi, dan akwai gaɓar da dole a neme su a rayuwarki, mussaman a gurin Aure, dan kin san dai ni ba zan aurar da ke ba ko?". Shiru Hafsa tayi, dan ko zancen Mutanen nan ba ta ƙaunar ayi sam. *********** "Daddy" ta faɗa da ƙarfi tana rungume shi, kamar wata 'yar yarinya. "Fadila ke dai ba kya girma ko? Don't you know, that you are now a big girl?" Mutumin yayi Maganar yana murmushi. Tura baki Fadila tayi ta ce "Daddy wannan karon ka daɗe da yawa, kuma mu kayi waya da kai jiya baka gaya mini zaka dawo ba". "Eh dama nace bari in yi surprising ɗin ku ne kawai" "Kamar yadda Yaya Khalil yayi mana kenan, sai ganinsa kawai muka yi a gida". "Eh munyi waya, ya gaya mini yazo, na so in biya in ganshi ma, amma Allah bai nufa ba, ya school ɗin, dama Mum ɗinku tace mini kin fara zuwa". "School gata nan so boring and frustrated". "Da haka duk muka yi karatun, kawai ki maida hankali kiyi abin da ya kai ki, abin da duk baki gane ba, idan da wanda ya fiki ganewa ki zauna ya koya miki". "Taɓ, salon a rainani ace mini daƙiƙiya, i better Google what ever i dont understand". "But is not as accurate as what someone will guide and teach you, anyway i wil find someone to be assisting you at home after school" Cewar Alhaji Ahmad. "A nice idea Daddy, thank you ina Mummy?" "Nima ita nake jira, tana sashinta go and have some rest" Fadila ta miƙe tare da yasar da jakarta a nan falo ta wuce. Hajara ce ta shigo tana kwashe kayan da Fadila ta zubar a falon, ta risuna ta gaida Alhaji Ahmad, hannu ya ɗaga mata tare da faɗin sannu kawai. Hajiya Zainab ta fito cikin gayu, ta zauna kusa da maigidan nata tana ta kwarkwasa, kamar Amarya. Fadila ce ta kuma fitowa ranta a ɓace, ta tarar da Hajara na gyaraa falo, cikin faɗa ta fara yiwa Hajara magana "Wace ta gyara mini ɗakina a cikinku?" Hajara ta ce "Asabe ce" "Wai wasu irin banzaye ne ku? Kira mini ita, yarinya sai daƙiƙancin tsiya, kira min ita". Alhaji Ahmad ya ce "Yaya, mai ya faru ne?". "Daddy na gaji da halin maids ɗin nan, sai ka yi ta maimaita musu abu ɗaya amma basa ganewa". Mummy ta ce "Wallahi ni kaina ina mamakin rashin tunanin na yaran nan, kai ta maimaita magana basa ganewa". Asabe ce ta ƙaraso ta ce "Gani". "Eh gaki na ganki, wai jahilar ina ce ke? In ta maimaita magana ba kya ganewa, na gaya miki kar ki sake maimaita mini bedsheet, da na tashi a cire shi a wanke, na bar underwear a toilet, kin wanke banɗaki kawai amma baki wanke mini ba, ni kike jira inje School in dawo in wanke? Idan naki ne zaki bar su baki wanke ba? Ko da yake ku dama ƙazanta a jininku take". Asabe ta duƙa ta ce "dan Allah ki yi haƙuri, Hajiya ce ta samu aiki, ayyukan sun yi yawa yau saboda dawowar Alhaji". "Shut up I don't care malama, aikina na sani dana saki kiyi mini, idan ba zaki yi ba you can park your load and go back to your useless village, 'yar ƙauye mara ganewa kawai" Tun ɗazu Hajiya Zainab suna falon, suna jin yadda 'yar su ke wannan zazzaga amma ba su tofa ba, sai yanzu Alhaji Ahmad ya ce "Easy Daughter, ai ta baki uzurinta, ke ki je kiyi mata aikin, and ke kuma 1ki daina yiwa mutane shouting haka ba daɗi". "Daddy ni kaina ba jin daɗin shouting ɗin nan nake ba, suke sani Wallahi". Haka Asabe ta wuce sashin Fadila ranta a matuƙar ɓace, da jin zafin cin zarafin da Fadila tayi mata. Da sassafe, bayan kammala ayyukan gidan, iyalan na kan dining suna cin abinci. Hajara ta tarar da Asabe tana ta haɗa kaya. "Asabe wannan kayan da kike haɗawa fa?". Asabe ta ce "Ƙauyenmu zan koma". "Saboda me?" "Ba zan iya jure zama ana cigaba da ci mini mutunci ba, na haƙura da aikin na nemi wani gurin". "Haba Asabe, yanzu kan ki samu wani gidan aikin fa?". "Allah ba zai hana ni ba, na gaji da cin mutuncin nan". Hajara ta ce "Na shiga uku ni Hajara, Asabe idan kika tafi aiki da jarabar mutan gidan nan kashe ni zai a gidan nan". "Allah ya baki yadda zaki, amma ni ba zan iya ba na gaji, zan iya wankawa yarinyar nan mari". Asabe ta fito falo da kayanta, ta kuma gaishe da su, Alhaji Ahmad ne ma ya ɗan saki jiki ya amsa. Asabe ta ce "Dama ina so zanje gida ne, ance mahaifiyata babu lafiya, zan je jinyarta bani da tabaccin zan dawo". Mummy ta ce "To ki gaida gida" Fadila ta ce "Allah raka taki gona" Asabe jiki a sanyaye ta miƙe, Alhaji Ahmad ya kirata, ya sa hannu a aljijunsa, ya ɗauko kuɗi masu yawa zai miƙawa Asabe. Mummy ta yi caraf ta ce "Na meye kuma zaka bata wannan uban kuɗi haka? Naga an biyata kuɗin aikinta, wannan kuma na menene?". Daddy ya ce "Ai wannan watan ya kai a biyasu, tun da jibi in Allah ya kaimu zai mutu, kuma ai tayi aikin watan, gara a biyata kuɗin aikinta, kuma a bata na siyan magani, ai ko bakomai an moreta a gidan nan" ba dan Mummy ta so ba, ya bawa Asabe kuɗi kusan dubu sittin ya sallameta. Hajara kuwa zullumi ta shiga da taradaddi, ta san duk wata wahala da ɗawainiyar gidan nan kanta zata dawo ita kaɗai, ga mutanen gidan da shegen sa aiki su kuma ga son jiki, in an bar 'yar aiki ta huta to fa dare ne yayi, suna su biyun ma da ya suka ƙare, balle yanzu sai ita kaɗai. ********* "Yawwa Hanne, yau da Yamma Malam Rabi'u zai kawo kuɗin Auren Amina, duk da ina samun labarin yadda kike zigata take masa rashin mutunci, bata saurarsa to ki sani duk wani ƙulle ƙullenki da makircinki ba zai hana Auren nan ba". Inno ta ce "Ni wani ƙulle ƙulle zan akan auren nan, ni da nake 'yar karere?" Tayi maganar cikin ladabi kuma a sanyaye. Kawu Bala ya ce "Oho miki dai, kuma anwa gonar Hassan kuɗi, dubu ɗari uku, zai kawo kuɗin gonar da na Auren, sati biyu kawai za'a saka ba wata bidi'a za a tsaya yi ba". Amina dake ta ƙoƙarin tuƙa tuwo ta zabura ta ce "Gonar baban ce dubu ɗari uku? Wallahi kawu cutarku zai yi gonar nan tafi haka". "Zaki rufe mini baki ko sai na zo na danna kanki a murhun nan? Fitsararriya mara kunya ina Magana kin tsoma baki, naga uban da ya isa ya hana a siyar da gonar nan ayi auren nan" Amina ta sunkuyar da kai, ranta na mata ƙuna, Shikenan duk wata kadara da Baba ya mallaka an kaɗar da ita. Albarkacin Asabe, ya sanya Alhaji Ahmad ya biya sauran ma'aikatan da ke gidansa kuɗaɗen albashinsu, duk da watan bai mutu ba. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa ma'aikatan ba, dan idan baya nan sai sabon wata ya kwan bakwai, matar gidan ba ta biyasu haƙƙoƙinsu ba. Baba Hassan ji yake ina ma tun kan a rufe jarrabawar su Amina, aka biya albashin nan, da ko duka kuɗin ya kama zai bada albashin nasa ta biya jarrabawar. Da yamma Baba Hassan ya nemi izini, ya tafi tasha in da su Saminu ke lodin can garin su Baba Hassan, Saminu ɗan garinsu ne, shi yake bawa duk wani saƙo da yake kai wa su Amina. Kamar yadda ya saba yi, ya ɗan yi siyayyar kayan Abinci, da sabulun wanka da wanki da su man shafawa, ya ɗora kuɗin kashewa ya kaiwa Saminu tasha ya ce ya kai wa su Amina, ace musu yana nan tafe yazo ya gansu da ya samu lokaci. Amina ta yi murna da ganin Saminu, dan har satar hanya tayi, da ƙafafuwanta ta tafi babbar tasha ta garinsu, tana neman Saminu amma baya nan. Sai gashi katsam ya kawo musu aike daga wurin Baba Hassan. Bayan gama gaisawa da Inno da Amina, Amina ta gyara zama ta ce "Dan Allah ka kira mana Baba a waya, ina son Magana da shi". Saminu ya ce "Sai dai wayar tawa babu kuɗi sosai, amma bari in jarraba kiransa a waya". Saminu ya kira wayar Baba Hassan, amma shiru ba ta shiga. Saminu ya ce "Amina wayar ba ta shiga, idan da wani saƙo ne ki bani in kai masa". Shiru Amina ta yi, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin zafi. Inno ce ta ce "Hmm, ka sanar masa 'yan uwansa za su aurar da Amina ga Malam Rabi'u Jarmai, kuma zasu sayar da gonarsa su yi mata kayan ɗaki". Saminu ya kalli Amina ya ce "Wace irin magana ce haka? Ina laifin su jira ya dawo? Kuma kamar ba su san halin Rabi'u Jarmai ba, karatun nata fa" Inno ta ce "Kaga kar ka tunzurata, Aure ba laifi bane gallafirin da take a titi da sunan boko sam bai yi ba, amma wanda zasu haɗata da shi ɗin ne ba mutumin kirki ba ne" Saminu ya jinjina kai ya kalli Amina da hawaye suka wanke mata fuska ya girgiza kai ya ce "Kiyi haƙuri Amina, insha Allah zan sanar wa da Baba Hassan ɗin, ki daina kuka". Amina ta jinjina kai, tana ji a jikinta idan har Baba ya samu labari, wataƙila ya iya taimaka mata ta samu sassauci. Su kayi sallama da Saminu ya tashi ya tafi. Tun da Saminu ya tafi, jikin Amina yayi sanyi, tana tunanin ya Baba zai ji idan yaji ana shirin katse cikar burinsa a kanta, da kuma salwantar da 'yar gonar da ta rage ya mallaka. Bayan tafiyar Saminu, Inno ta shirya ta fita, saura Amina kaɗai a gidan. "Assalamu alaikum, wai ana sallama da Amina" cewar wani yaro da ya afko ba sallama. Amina ta ce "Kai kar ka sake shigo mana gida ba sallama, kuma ka koma kace masa ba zan zo ba, ya san in da dare yayi masa" Amina ta shige ɗaki abin ta, tamkar ba da ita ake sallama ba, sai da yayi kusan aike huɗu amma mirsisi ta ƙi fita. Allah ya taimaketa Inno ba ta nan, balle ta tursasata sai ta fita. Amina na nan zaune, tana sake duba litattafanta na makarantar boko tana hawaye, ta ƙallafa ranta a kan karatu, ta ɗakko littafin da ake shigar mata da makinta na haddar Alqur'ani a makarantar boko. Ta haɗa kai da gwiwa ta din ga kuka, tana tunanin meye mafita, dan ko a ƙafa a ka ɗaura mata Malam Rabi'u Jarmai, sai ta gutsure ƙafar ta huta, amma ta yaya zata iya daƙile wannan Auren? Tana cikin kukan wani tunani ya faɗo mata, cikin hanzari ta miƙe tsaye. Sai dai murayar da ta jiyo ana kwaɗa sallama ce ta sanya gabanta ya faɗi, ta dafe ƙiji tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"! Domin gyara sharhi ko shawara 08081012143 GABA DA GABANTA Page 5 AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Litatafaina na AƘIDATA DA RUƊIN ƘURUCIYA duk na kuɗi ne Please. Ta taga Amina ta leƙa, sarai ta ɗau Muryar su waye, kasa amsa sallamar ta yi dan bata san da wani idon zata kallesu ba. Yadda suke kwaɗa sallamar ba ƙaƙƙautawa ne ya sanyata amsawa, tare da fitowa daga cikinu ɗakin. Kallo ɗaya ta yi musu gabanta ya faɗi, dan bata san da wacce suka zo ba, 'ya'yan Malam Rabi'u jarmai ne, wanda ƙawayen ta ne, sai dai su duk sun yi Aure, har da mai yara biyu, Iklima da Shema'u. Amina ta ɓoye damuwarta ta ce "Shema'au sannunku da zuwa, ku shigo". Iklima ta ce "Ji munafuka, mu shigo ina, algunguma ki rasa wanda zaki aura a garin nan dan rashin ta ido sai mahaifinmu, Wallahi kin ji kunya Amina". Shema'u ta karɓa da "Ai zuwa mu ka yi mu ja miki kunne, Wallahi baki isa kiyi kishi da iyayenmu ba, gidanmu kamar kabari ne, Wallahi kika shiga azaba da wahala sai sun koreki da ƙafafuwan ki, gara tun wuri ki san abin yi". Jiki a sanyaye Amina ta ce "Shema'u ku yi haƙuri, ni kai na ba son Auren nan nake ba Wallahi, kuma har yanzu ban ji a jikina zan iya Auren mahaifinku ba.... "Ba wani nan rufe mana baki, kwaɗayi ne ya sanya zaki auri baban mu ba wani abu ba". Amina ta ce "Wallahi ba haka bane, ku tambaya ku ji Wallahi ni ba son mahaifinku nake ba". "Yi mana shiru munafuka, har akwai yarinyar da ta isa ta ce ba ta son babanmu, zaki aure shi dan kwaɗayi, an yi kwantai a gari an ƙare a hanyar boko, ba abin da bokon ta amfana miki, kin gama gantalinki za a liƙawa babanmu, Wallahi ki ka aure shi ƙannenmu sai sun illata ki". Amina ta ce "Naga ina ta lallaɓa ku kun kasa ganewa, to bari in fito muku a yadda kuke so, ni bana son mahaifinku shine ya nace mini sai ya aure ni, sai wani ihun kwaɗayi kuke yi, meye a gidan naku kuɗin baban naku da ba ci ake ba, tuwo safe rana dare, miyar gidanku kamar ruwan tsarki, kullum a wahala kuke, ya auri wannan ya saki waccan, insha Allah babu abin da zai sa in Auri babanku iyayenku ma fama suke, ta kan su suke yi". Shema'u ta ce "Kutt, baban namu kike gayawa haka?". "An gaya masa ɗin, yayi zuciya ya daina mayar da 'ya'yan mutane dan yana da kuɗi". "Gara namu uban an san aure yake yi yana saki, wayasan me naki uban yake aikatawa a birni". "Bakomai tun da ba'a san me yake ba, naku uban kuwa kowa ya san me yake yi, me ake da mutumin da bai san martaba da darajar Aure ba" ganin Amina ta fisu baki ya sanya suka fita suna ƙananun maganganu. Amina ta koma ɗaki tayi shiruu, tana tunanin mafita, tabbas ta san idan ta auri Malam Rabi'u kashinta ya bushe, dan a gidan nan babu kalar yaran da babu dan wasu daga manyan 'ya'yansa yayyen su Shema'u 'yan daba ne, ga uwar gidansa ita ce babbar masifaffiya, gidansa tuwo kwano uku zuwa biyar ake tuƙawa, idan ranar girkin ki ce ke zaki tuƙa wannan tuwo, sai a kwan uku ana cinsa. "Kai ba zai yiwu ba, Wallahi ba zan yadda in auri wannan mutumin ba". "Ke Amina, au zama ki ka yi kina koke-koke, har da surutai ba zaki dangana ba?" Ta jiyo muryar Inno. Cikin kuka Amina ta ce "Wallahi Inno ba zan auri Malam Rabi'u ba, yanzun nan su Shema'u suka bar gidan nan, ba ki ga cin mutuncin da suka yi mini ba, wai kar in auri babansu ni ce musu nayi ina son babansu, Inno wallahi bana son Mutumin nan ki gaya musu". "Amina ta yaya zan ce musu ba kya son sa ni a wa? Yanzu haka da na dawo ya tsareni a ƙofar gida, wai sun karɓi kuɗin Aurenki, da kuma kuɗin gonar mahaifinki, wai za'a kawai Jamila dillaliya dubu hamsin a samo miki gado ɗan hannu, a kaiwa Liti kafinta shima wai idan da kujeru na hannu a sai miki, an saka sati uku bikin". Fashewa Amina ta kuma yi da kuka ta ce "Wallahi ba zan auri wannan mutumin ba, tun yanzu 'yan'yan sa sun fara zuwa suna ci mini mutunci, kuma dan tsabar mugunta an siyar masa gonar babana da arha ya siya, kuma a siya mini kayan ɗaki 'yan hannu, dan an mayar da ni mara galihu". Bakinta Inno ta gwaɓe ta ce "Dan ubanki 'yan uwan mahaifin naki kike gayawa haka, salon su zo su ji suce ni nake ziga ki? Ke a rayiwarki ba ki san tawakalli ba da duk abin da Allah ya tsarawa bawa ba shi da ikon kuskurewa ba, kamar iyaye suke a gurinki fa". "Ni Wallahi ba iyaye na ba ne, tin da suke son kassara rayuwata, da tozarta mahaifina an cutar da shi an raba shi da gonarsa ba da saninsa ba". Inno ta bi Amina da kallo, Amina kenan akwai haƙuri wasu lokutan, wasu lokutan kuwa akwai gardama da taurin kai, dan Inno ta fara fagabar yadda Amina ke cigaba da adawa ƙarara da Auren da ake son a yi mata. ***************** Kamar kullum sun kammala lectures, lecturer ya ce zai yi musu wata test, amma ya bawa kowa damar ya yi amfani da wayarsa wurin samo amsar tambayoyin da zai yi. Suka dinga murna ɗaliban, malamin ya rubuta tambayoyi uku, a kan allo ya ce su amsa a mintuna goma kacal! Nan da nan suka duƙufa suka ɗauko wayoyinsu, suka fara binciken aikin da aka ba su. Rarraba idanu ya shiga yi, dan ba shi da wayar da zai amfani da ita wurin gudanar da aikin, ya juya hagu da damansa kowa ya duƙufa yana yi, amma ban da shi. Takarda ya samu ya sunkuya ya fara rubutun sa cikin nutsuwa. Fadila ta ɗago ta kalleshi, yana ta rubutu amma ba daga waya yake kwafa ba. Ta taɓe baki ta taɓo ƙawarta Ta nuna mata shi ta ce "Kalli ko mai yake rubutawa oho, mutumin da ba turanci ya iya ba, kuma ba waya ce da shi ba amma yana ta rubutu shi dole ga ƙwaro" kamar yadda suka saba suka kwashe masa da dariya. Bai ko ɗagoba ya cigaba da rubutun, sai dai duka bun nam da ake, ɗaliban suka gaza samo amsoshin tambayoyin a Google, ƙarshe abin da ya sawwaƙa suka rubuta lokaci ya cika suka bayar. Fitar malamin ke da wuya, ɗaliban suka fara ƙoƙarin fita daga ajin, tafiya yake sannu a hankali, babu gaggawa gashi ita kuma sauri take, so take ta bar ajin ya tsare mata hanya kuma ya ƙi sauri. "Dalla malam ka bani hanya, sai tafiya ka ke kamar mace, ko nan ɗakin ka ne?" Tsayawa ya yi, ya waiwayo ya kalli Fadila ido cikin ido, ya rasa mai ya tsarewa yarinyar nan haka, bata hanya ya yi yace "Bisimillah, wuce" ratse shi ta yi ta wuce tana cigaba da mitar yadda yake tafiya kamar mara lafiya. Shi dai bece mata uffan ba, ta wuce. Department ɗin su Yusra ta tafi, kasancewar duk a makaranta ɗaya suke, ta yi sa'a ajinsu Yusra ba kowa dan haka ta shiga kan ta tsaye. Yusra ta duƙufa ta na ta chatting a waya, Fadila ta zare wayar hannun Yusra, hakan ya tilasta mata ɗagowa, tana ganin Fadila ta yi murmushi ta ce "Beb daga ina haka?". Fadila ta zauna tare da faɗin 'Daga class, nace bari in zo in ganki". "Kai amma naji daɗi, ya lectures ɗin?". "Alhamdilillah, muna nan muna fama, ya naku?". "Alhamdilillah, muma hakan ne". "That's good, da wa ake chatting ne haka?". Yusra ta yi murmushi ta ce "Wallahi ba kowa, ina duba wani ankon da za muyi ne, na bikin Sister ɗina, so ina duba IG ne ko zan samu style". Fadila ta ce "Ok na zata sabon kamu aka yi mana". Yusra ta girgiza kai ta ce "Ba wani sabon kamu, samari akwai su, amma ni hankalina duk baya kan su". "Don't mind girl, in dai brother na ne, insha Allah ina nan ina miki fighting ina ta kafa ki a wurin Mummy, mu bi komai a sannu zai amince ne". "To beb, Allah ya amince. Ni wai ke ya ake ciki ne? Ko haryanzu ba ki da gwani" "Hmm ni fa ba ta wannan shirmen nake ba, ni ban baki labari bama, wannan abokin Yaya Khalil ɗin Abdul yake kowa? Wai shine ya ke nuna yana sona" "Ohh wannan abokin yayan naki da muka taɓa haɗuwa, wani mai abin dariya?". "Shi fa" "To meye aibunsa beb? Yana da kirki sosai". "Taɓ, lecturer ne fa mai ya samu ya ci balle ya bani? Aikin ma fa Daddy ne ya samo masa". "Ai ba wani abu Fadila, idan har kina son sa wannan duk ba abin damuwa bane". 'Bama na son sa dan ba class ɗina ba ne, wani baƙi da shi mara aji, sai surutun tsiya Mummy ma ba zata amince ba". Yusra ta yi murmushi ta ce "To Ubangiji Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi gaba ɗaya". "Ameen dear, tashi muje mu samu abin da zamu ci". Suka rankaya gaba ɗaya suka fita daga ajin. ******** Saminu kuwa bayan tafiyarsa daga gidan su Amina, ya koma tasha, sarkin tasha ya sanar da shi an samu wasu 'yan biki da zasu je kai amarya can Lagos, a jira su kwana biyu a dawo da su, idan ya amince zai kai su zasu biya shi, biya mai kyau sun ce ba sa son Manyan motoci saboda tsaye tsaye. Jin zai samu kuɗi masu yawa, ya sanya Saminu ya amince, ba tare da ya tuna saƙon Amina zuwa ga mahaifinta ba, washegari da Asubar fari ya ɗebi 'yan kai amarya yayi Lagos. Amina kuwa ta din ga zuba ido taga ta ina Baba zai dawo gari, sai dai babu Baba babu alamar sa, kullum garin Allah ya waye cikin zuba ido take ta ga Baba ya dawo, amma shiru. Gashi ta ƙara tsangwamar kanta, duk ta yi baƙi saboda damuwar da ta sanyawa zuciyarta, gashi 'ya'yan Rabi'u Jarmai kusan kullum cikin zuwa gidansu suke suna ja mata kunne a kan Auren mahaifinsu. Ga su Kawu Lawan suma kullum da kalar ta su tijarar da suke zuwa su yi mata, hakan ya sa ta ƙara tsangwamar kanta, ko Abincin kirki ba ta iya ci sai kuka. Gashi tuni su Kawu Bala suka karɓi kuɗin Aurenta, Naira dubu hamsin komai da komai har sadaki, kuma suka amshe kuɗin gonar mahaifinta. Tana kwance a ɗaki da yamma, wani irin zazzaɓi ya rufeta, dama duk dare da shi take kwana, yanzu kuwa tun yamma ya rufeta, tana ƙudundune a bargo tana ta rawar sanyi, Inno na tsakar gida tana dafa mata rai ɗore ta bata ko zazzaɓin ya sauka, sai ga hayaniyar mutane. Uwargidan kawu Bala da ta Kawu Lawan ce suka shigo, suka kalli Inno suka ce "Ke Hanne kayan Amina muka kawo, ki gyara wurin da za a ajiye". Inno ta ce "Ga filin tsakar gida nan, a zo a ajiye su". Nan fa samarin 'ya'yan su suka fara kokowa da shigo da kayan, wasu irin ruɓaɓun kayan gado ne, aka yi musu fentin ha'inci, dan garin shigo da su ƙasan sip ya ɓare, zanin kujerun nan kuwa daƙal daƙal, ga ƙamshin fenti ga warin rima kayan suna yi, kai da gani ka san na ha'inci ne. Inno ta yi shiru tana bin kayan nan da kallo, duk sun ɓare garin kokowar shigowa. Uwargidan kawu Bala ta ce "To Inno, su Malam sun fita sun yi iya yin su ga kayan gadon Amina nan, saura kema naki ɓangaren aga irin bajintar da zaki yi a ɗakin amarya". Inno ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Haka ne, Allah ya nuna mana ya sa ayi da mu". Suka amsa da Ameen, suka ringa guɗa, suka gama hayaniyar su suka fice. Amina ta ɗaga labule ta fito daga ɗakin su, ta kalli kayan nan, ta kalli bayan sif ɗin nan, yadda wani wurin ya kusa burmawa, da in da ya ɓare wurin shigo da kayan, shi kansa allon gadon, sari ya cinye wani wurin aka liƙe shi da fenti. Ta fashe da kuka ta ce "Yanzu a kan wannan matsiyatan kayan aka siyar da gonar Baba? Wallahi sai Allah ya saka mana". Inno ta ce "Dan Allah ki rufa mana Asiri, kar su dawo su ji abin da ki ke faɗa" "To su ji ɗin ina ruwana, Wallahi su da Allah, duk cikin yaransu da aka aurar, ba wadda aka yiwa wannan wulaƙanci sai ni, kalli wasu irin kaya kamar wata mara galihu, Allah ka saka mini" tayi maganar kamar zata shiɗe, saboda yadda haƙoranta ke haɗuwa saboda zafin zazzaɓi. Inno ta ce "Ni dai haƙurin nan dai shi zan baki, ki barwa Allah Komai dan Allah karki wani abu da zai sanya su zo su ɗaga mana hankali". Ta share hawayenta ta ce "Inno, anya Saminu ya gayawa Baba halin da ake ciki?" "To gashi dai har yanzu shiru ba muji ɗuriyarsa ba" "Inno ko bokonmu zanje, wurin malamanmu in ari waya in kira Baban?". "A'a ni bana son abin da zai janyo magana, ko kin manta da sun hanaki zuwa bokon nan, ki kiyayeni. Zan shiga banɗaki ki ɗau kofi ki tsiyayi rai ɗoren can ki sha, ki ɗau Abinci ki daure ki ci". Amina ta jinjina kai. Tana ganin Inno ta shiga banɗaki, ta ɗau hijjabinta ta fice daga gidan. Duk da yadda take jin jiri, kanta yana juyawa, amma zuciyarta ta bushe, sai zuba sauri kawai take yi. Uwar tafiya ta kwasa ba ta wasa ba, ta isa ƙaramar tashar garinsu, cikin rukunin direbobin nan taje ta gaishe su. Suka amsa wani mai suna Lado kan kara ya ce "Ya aka yi ne? Amarya da yawo ke da aka kusa ɗaura miki Aure?". Banza ta yi masa ta ce "Dan Allah Saminu nake nema". Wani ya ce "Saminu ya je Ikko, amma ya kamo hanyar dawowa gida". "Dan Allah ko zaku taimaka ku kira mini shi a waya, na bashi saƙo zuwa wurin Baba amma na ji shiru". "Ba matsala, bari a kira shi" cewar Lado. Amina ba tayi niyyar tankawa Lado kan kara ba, amm ganin zai taimaka mata ya sanya ta ɗan saki fuskarta. Ya kira Saminu ya miƙa mata wayar, cikin azama ta karɓa ta koma gefe. "Salamu Alaikum, Saminu Amina ce 'yar wajen Baba Hassan". Saminu ya rafka salati ya ce "Amina, dan girman Allah kiyi haƙuri, Wallahi na manta shaf da saƙonki na tafi ikko, amma kin ganni a hanyar dawowa, na miki alƙawarin yanzun nan, zan kira Baban in sanar masa". Amina cikin kuka ta ce "Dan Allah ka taimake ni Saminu, kar a wulaƙanta rayuwata" "Kar ki damu Amina, zan sanar masa Insha Allah" suka yi sallama ta bawa Lado wayarsa, ta yi musu godiya ta kama hanyar gida. Tun a hanya duhun magariba ya fara rufawa, ba ta damu da yadda sanyin dogayen zangarniyar bishiyoyin hatsi ke kaɗawa suna ratsata ba, wanda hakan ya ƙara asassa tsananin zafin da jikinta ke ɗauka, ga gefen cikinta da ya ƙulle, saboda yunwa amma ba ta damu ba, sai sauri take yi, in da ba mutane ta kwasa da gudu dan ta isa gida da wuri. Allah ya taimaketa ba wanda ya ganta suruf ta shige gida. Ta tarar Inno bata nan, ta shiga banɗaki tayi alwala ta koma ɗaki ta tayar da sallar magariba. Inno ce ta shigo gidan tana 'yan maganganu, tana ɗaga labule ta hango Amina na salla, aikuwa ta rafka salati ta ce "Ke daga ina haka? Kika ɗaga mini hankali nake ta yawon nemanki?". Amina ta idar da salla ta yi Adduointa, sannan ta kalli Inno ta ce "Inno tasha naje ko Saminu yana nan, wai ashe bai gayawa Baba saƙon nan ba, yana Ikko ma, aka kira mini shi a waya, shine ya ce mini zai gaya masa". "Kuma shine sai ki tafi baki gaya mini ba, kin ɗaga mini hankali, nan suka aiko suna neman ki, amma ba kya nan na rasa ƙaryar da zan musu, wato ke dai Amina ba kya gudun magana ko? Ke duk abin da zai sa su zo su ci mana mutunci kin san shi kuma zaki aikata ko?" Shiru Amina ta yi taƙi magana, Inno ta yi ta banbaminta ta gama, Amina ba tace komai ba. Baba Hassan kuwa kusan suman zaune yayi, bayan Saminu ya kira shi a waya ya wassafa masa irin katoɓarar da 'yan uwansa suke shirin aikatawa, na cefanar da gonarsa da kuma aurar masa da tilon 'yar sa ga mutumin banza da suke shirin yi. Baba Hassan bai iya cewa Komai ba sai kashe wayar da ya yi, ya san nan duniya ko me zai yi bai isa ya hana wannan auren ba, sayar da gonarsa bai ɓata masa rai ba kamar yadda ake shirin salwantar da rayuwar 'yar sa, dan abin da ya shirya shine, shekara mai zuwa ya biya mata kuɗin jarrabawar, kuma ya dinga tattala 'yan kuɗaɗe saboda harkar makarantar ta, sai dai kash ga abin da 'yan uwansa ke shirin aikatawa. Amina har zuwa sallar isha'i zazzaɓin jikinta bai sauka ba, ga wani irin koren amai mai ɗaci da take tayi, Inno sai jiƙe-jiƙe take tana ɗura mata, Amina mirsisi ta ƙi sha, saboda wannan jiƙe-jiƙen da take sha su suke ƙara sanyata amai. Yarone yayi sallama, wai Amina ta je in ji Malam Rabi'u Jarmai. Inno ta ce "Ka je ka ce masa ba ta da lafiya". Yaron ya fita ba jimawa, ya dawo ya ce "Wai Kawu Lawan ya ce idan ba ta je ba ya zo sai ya zane ta". Inno ta kalli Amina ta ce "Amina, lallaɓa kije, bana son fitina da tashin hankali". Amina ta buɗe baki za tayi Magana, Inno ta girgiza mata kai ta ce "Yi haƙuri, daure kije" haka ta ɗau hijjabinta tana kuka, ga zazzaɓi a jikinta ta fita. Jarmai na ganinta ya washe baki yana faɗin "Amaryata ba faɗa mai ya kawo gaba fisabilillahi?". "Kaga saurara mini, Azzalimi kawai aka sayar maka da gonar Baba ka saya, alhalin ka san kuɗin gonarsa ba haka yake ba, to Wallahi ba zan auri Azzalimin mutum irinka ba, ga yaranka marasa tarbiyya da suke mana zarya a gida suna zagina, ba zan iya ba". "Aikuwa zaki iya, da kin shiga gidana kin sha jar miya zaki watstsake muyi zaman mu". "Jar miya a Ina? Da jar miyar a gidan naka ka ke kai yaranka bara wasu suna talla? Ina alamar jar miya a jikinka ko jikin 'ya'yanka, saboda tsabar cuta da zalunci ina kai ina ni, da ƙanan shekaru na ka haɗani a wannan gidanka na gayya, to bari kaji in gaya maka, ko da sarƙa a ka ɗaura Aurena da kai sai na warware shi, kuma ba dai in je gidanka ba sai dai a kai maka gawata". "Ni kike gayawa wannan miyagun maganganun?" Yayi Maganar yana matsawa kusa da ita, wani azabar warin baki gami da na sigari ya daki hancinta, ga ƙarin rana yana yi, kayan jikinsa ne kawai wankakku, suma sai ƙarnin koren sabulu suke. Ja da baya ta yi ta ce "Kar ka sake matsowa kusa da ni, na gaya maka ɗin, idan kana da zuciya ka biya ka karɓe kuɗin Aurenka ka fasa Aurena, idan kuwa ba haka ba idan ba a kai maka gawata gidanka ba, sai gidanka ya zama sansanin tashin hankali da bala'i na gaya maka". "Yaro man kaza, mu zuba mu gani ni da ke shege ka fasa, gidana ne Wallahi sai kin shige shi sai na Aureki". "Za kuwa mu gani, na bika ta lallalami kaƙi fahimta, zan fahimtar da kai ta hanyar nuna maka ni 'yar zamani ce, tsohon kawai". Saroro ya bi Amina da kallo, bai taɓa zaton za ta iya gasa masa miyagun maganganu haka ba, dan kowa kallon saliha yake mata, ga haƙuri da biyayya, a zatonsa duk irin halin mahaifinta ne da ita zai samu tuɓus, ashe abin ba haka yake ba. Ita kuwa Amina gida ta shige abinta, Inno na tambayarta yaya aka yi, amma tayi shiru saboda yadda zuciyarta ke tafasa, ko ƙaunar jin sunan Rabi'u Jarmai ba ta yi, balle a kai ga batun Auren su. Ta haɗa kai da gwiwa ta dinga rusa kuka, Inno kam ta gaji da rarrashin Amina dan haka ta zuba ido. Baba Hassan kuwa bakinsa ɗauke da Addu'a, ya shiga falon gidan da sallama, a zatonsa ya je daidai lokacin da zai samu Alhaji Ahmad, sai dai kash bai fito ba, sai Hajiya Zainab ya tarar a falo, tana ta bawa Hajara umarni cikin tsawa da wulaƙanci. Kasancewar abu ne na gaggawa, ya yanke shawarar sanar da Hajiya Zainab, Alfarmar da ya zo nema, ya risuna ya gaida ita cikin girmamawa, ta amsa ba yabo ba fallasa. "Hajiya dan Allah wata alfarma na zo nema a wurinki". "Haka dai, Alfarma ba yau ba gobe ina jinka". Ya gyara zamansa ya ce "Wallahi wani al'amari ne ya taso mini a garinmu cikin gaggawa game da iyalina, nake son dan Allah a bani dama, ko kwana biyu in je in yi in dawo". Ta ɗago ta kalleshi ta yatsina fuska ta ce "Idan zamu fita ko mun dawo, mu zamu dinga kokowa da ƙofa wurin buɗewa da rufewa kenan?". "A'a hajiya, ga Hadi nan sai ya riƙa mini kan in dawo". "Ban lamunta ba, aikin Hadi daban a gidan nan, naka daban dan haka ba in da zaka a yanzu, idan kuwa ka tafi, to ka tafi kenan" Baba Hassan yayi shiru ya rasa abin da yake masa daɗi, ya tashi gwiwa a sanyaye ya bar falon. Idan ya kuskura ya bar aikin gadin nan, tofa rayuwarsa da ta iyalansa za ta shiga wani hali, dan ba shi da wata sana'a da ya iya. Amina kuwa tun Asuba take amai, ciwo ya ƙi sauƙi kullum sai gaba yake yi, ƙarfe shida da rabi sai ga Kawu Bala da Lawan tare da matansu, da wasu daga cikin yaransu kamar wanda za su je ritsa kwarto, sun shigo suna zazzaga bala'i tun daga hanyar shigowa. Suna zuwa suka tarar da Amina a zaune dirshen tana amai. Ladiyo Uwar gidan Kawu Bala ta ce "Wallahi malam zancen ya tabbata, abin da ake ta gudu, wannan aman ai irin na masu ciki ne". Inno ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wane irin masu ciki kuma bata da lafiya ne fa". "Ƙarya kike munafuka, dama ance mini an ganta a tasha wai taje wurin Saminu, dama zuwan da Saminun yake gidan nan kenan, Kuna lalacewa, kafira mai siffar munafukai, har an samu wanda zai rufa miki asiri ya Aureki, amma zaki tozarta mu, ashe dagaske ne kullum sai kin je tasha kin bada jikinki a baki kuɗi, wannan cikin ba zaki haife shi a gidan nan, jibi in Allah ya kaimu idan an sakko daga sallar juma'a za'a ɗaura aurenki da Rabi'u, kuma ba wata bidi'a da za a yi, ɗaurin Aure kawai za ai a kai ki dama da ke da bazawara ba maraba, kin gama tsufa a titi da rabawa maza jikinki". Wani malolon baƙin ciki ya tokarewa Amina ƙirji, ba ta san lokacin da zafin maganganun wan mahaifin nata suka sanyata jan tsaki a fili ba. Ai kuwa hakan ya tunzura shi, ya nufi dangar kara, ya ciro kara suka rufar mata da duka. Inno ta dinga kururuwa tana faɗin "Kuyi haƙuri, ba ta da lafiya". Ladiyo ta ce "Wallahi ku casa ta, ko Allah ya sa cikin jikinta ya zube". Tun Amina na iya motsi tana kuka, har ta sare sai wata irin ajiyar zuciya take, jikinta duk ya farfashe saboda duka. Bayan tafiyarsu Inno ta ɗumama ruwa, ta gargasawa Amina jikinta tana faɗin "Kin ga Abin da nake gaya miki ko, shiyasa na gaya miki taurin kai ba shi da rana Amina" Kwanaki biyun nan, jikin Amina ya ƙara zafi, wai sunan amarya ba kitso ba ƙunshi tana kwace ba lafiya, iyalan su Kawu Bala suka kwashi raftar kayan da suka yiwa Amina aka kai mata gidan Malam Rabi'u. Ranar Juma'a kiran Sallar farko, Amina ta ɗebi kuɗi, daga kuɗin da ake bawa Inno gudunmuwar Aurenta, dama tun dare ta haɗa kayanta Inno na bacci, kiran sallar farko, ta kwashi kayanta ta fice daga gidan. Tana tafe a hanya tana kuka ta ce "Babana maganin kukana, na san wataƙila har yanzu saƙona bai riske ka ba, shi yasa baka kawo mini ɗauki ba, duk da ban san wurin da zan sameka a birni ba, amma gara in tafi da tambaya har Allah ya sanya in dace in gano in da kake, dan da in auren nan gara in mutu a hanya". Arewabooks https://arewabooks.com/u/ayshercool7724 GYARA SHARHI KO SHAWARA 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) P6 Follow my Arewabooks account Ayshercool7724 https://arewabooks.com/u/ayshercool7724 Tafiya take tana ratsa tsakanin gonaki, ga duhu ga babu haske, amma hakan bai dameta ba, babban burinta shine ta ga ta baro cikin ƙauyen nan cikin salama, ba tare da wani ya ganta ba. Baba Hassan kuwa bacci ma ɓarawo ne ya ɗauke shi, tunanin mafita kawai yake yi, zuciyarsa ta dinga raya masa kawai ya haƙura ya tafi ƙauye, komai zai faru ya faru, idan ya so ya haƙura da aikin, amma gefe guda yana tunanin idan ya bar aikin gadin me zai yi? Wace sana'a zai yi? Wata shawara yake ta jujjuyawa a ransa wadda ba shi da tabaccin zata karɓu. A haka har garin Allah ya waye, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake gudanar da komai, yana nan zaune a bakin gate yana ta jujjuya yadda zai ɓullowa lamarin, wajen ƙarfe goma Fadila ta fito ta fita, wajen ƙarfe sha ɗaya kuma Alhaji Ahmad ya fito, cikin wani ash ɗin yadi, an fito masa da motar sa da zai fita da ita. Alhaji Ahmad yana ƙoƙarin shiga mota, Baba Hassan ya cin masa, cikin girmamawa ya gaisheshi, Alhaji Ahmad ya amsa cikin mutuntawa. Baba Hassan ya duƙa ya ce "Yallaɓai dan Allah alfarma nake nema". Alhaji Ahmad ya gyara tsayuwa ya ce "Ina jinka". Baba Hassan ya ce "Dama Yallaɓai game da 'yar wajena ce, jarrabawar nan ba a samu damar yin ta ba" "Subhanallah, garin yaya?" "Kuɗin aka kai a ƙurarraren lokaci, to yarinyar tawa tana son ta yi karatu sosai da sosai, to ka san mutanenmu na karkara, 'yan uwana ba son karatun nata suke ba, to rashin samun damar rubuta jarrabawar ya sanya suna ƙoƙarin su Aurar mini da ita. Shi ne nace dan Allah tun da dama Asabe ta tafi, a taimaka mini a ɗauki yarinyar tawa ta maye gurbin Asabe, idan ya so kuɗin aikin nata sai a sakata a makarantar boko, a dinga biya mata kuɗin makarantar". Alhaji Ahmad ya ce "Malam Hassan wannan ai ba wani abun damuwa bane, bakomai ka kawota ai ilimi ga 'ya mace abin so ne, idan na dawo an jima ka tuna mini zan yiwa mutan gidan magana, ka kawota". Wata ƙwallar farinciki ta cikawa Baba Hassan ido, ya zube ƙasa yana faɗin "Na gode, Na gode Allah ya jiƙan magabata ya yauƙaƙa Arziki, Allah ya biya maka buƙatunka na Alkhairi duniya da lahira, yadda ka Sanya farinciki a cikin zuciyata da ceto 'yata ubangiji Allah ya faranta maka, yayi maka tukuici na Alkhairi". Alhaji Ahmad ya ce "Haba Malam Hassan, kar ka damu dan Allah wannan ai ba wani abin damuwa bane, Allah yayi wa yaranmu albarka baki ɗaya". "Ameen Yallaɓai godiya nake". Baba Hassan ji yake kamar an yaye masa damuwar da yake ciki, dan yana zuwa ɗakinsa yayi sujudu shukur, ya lalubo wayarsa ya kira Saminu. Sai da ta kusa tsinkewa Sannan Saminu ya ɗaga, suka gaisa Baba Hassan ya ce "Saminu, dan Allah idan ka tashi tahowa, duk yadda zaka yi ka taho mini da Amina garin nan, ko a tasha ka ajiyeta sai ka kirani in zo in tafi da ita". Saminu ya ce "To shikenan, amma ba zan taho yau ba gaskiya, sai dai gobe in Allah ya kaimu" "Bakomai, amma dan Allah kar ka bari su farga su san da ita zaka taho, idan kuka taho daga baya nazo in musu bayani, idan suka san zaka kawo mini ita ba zasu bari ba". Saminu ya ce "ba komai, kar ka damu Baba insha Allah zan kawo maka ita lafiya". "To shikenan Saminu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" ************ Yau Juma'a dan haka wankan hijjabi ta yi, pink tun daga sama har ƙasa, ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, ta shigo tana rataye da jakarta pink, hannunta riƙe da robar ruwa da mukullin motarta, bai san yadda aka yi ya shagala da kallonta ba, tayi kyau ƙarshe, ga wani irin sassanyan ƙamshi da take yi. Sai dai ta yi missing ɗin lectures ɗin farko da aka yi, dan suna takun saƙa da malamin, dan haka yau ba ta yi attending darasin sa ba, kuma darasin da yayi da lissafi a ciki, kuma ko da kai aka yi lissafin a ajin, abu ne mawuyaci mutum ya fahimta saboda yayi tsauri da yawa. "Kai lafiya kar ka cinye ni dalla" tayi masa maganar cikin tsawa. Sunkuyar da kansa ya yi daga kallonta, ya koma kallon wani wurin daban. Class rep ne yayi dariya ya ce "Kai Fadila wannan tsawar haka?" "To ya sani a gaba da kallo, sai na faɗi tukuna aikin banza". Dariya ƙawayenta suka din ga yi, wata wadda ake cewa Amra ta ce "Kyau ki ka yi masa ko ustaz?" Tsaki Fadila ta ja ta ce kwaji da shi. Babu jimawa wani lecturer ya shigo, wanda ya basu class work ya ce su yi da waya, nan ya dinga yi musu mita ya ce "Ace gaba ɗaya ajin nan babu wanda ya fahimci tambayar da na yi sai mutum ɗaya, ina sane nace ku duba waya, dan na san idan har baku fahimci tambayar ba, babu yadda za ayi ku samo amsar. Waye Yazeed Hashim Shareef?". "Sir" ya faɗa tare da ɗaga hannunsa sama. Gaba ɗaya idanun mutan ajin suka dawo kansa. "Wow, dama na gaya muku ustazan nan sune ƙwarin ajin, Malam Yazeed fito ka mana bayanin yadda ka fuskanci tambayar da na yi, har ka samu damar amsawa" Yazeed ya fita gaban aji, ya ce "Sir zan iya yi da Hausa?". "Yi da duk yaren da kafi iyawa" Yazeed na haɗa ido da Fadeela ta ƙunshe baki tana sinne dariya, ta ɗan ɗaga murya ta ce "Sir gara yayi mana da hausar dai, da turancin nan bama ganewa" Malamin bai kawo komai a ransa ba, ya yin da 'yan ajin suka gane me Fadila take nufi da faɗar hakan, su kai ta yi masa dariya. Tun a nan ya rasa karsashin da zai yi bayanin, duk ya ji jikinsa yayi sanyi, amma ya daure ya aro jarumta, ya daidaita nutsuwarsa, cikin kamalarsa ta zance da iya sarrafa harshe, yayi bayanin yadda ya fuskanci tambayar da yadda ya bi amsa tambayar. Malamin da kansa ya tafawa Yazeed ya ce "Weldone Ustaz, you are genius man, ka burgeni ƙwarai mutane masu sharp brain irinka ba su da yawa, Allah ya ƙara basira" Yazeed ya ce "Thank you sir". Malamin ya ce "Gaskiya duk ajin nan babu wanda ya amsa daidai sai Malam Yazeed, dan haka kowa yaje ya sake faɗaɗa bincike a kan bayanin da yayi, zan yi test a kansa, idan kuma kuna buƙata ku tuntuɓe shi yayi muku bayani sosai". "Gaskiya mu dai Sir kai mana bayanin da kan ka" cewar Fadila. "Meye baki gane ba a bayanin da yayi?". "Ni ban gane komai ba" ta faɗa cike da rainin hankali. "Well, zaki iya zuwa ki same shi ya yi miki bayani". "A'a Sir gaskiya gara ka yi mana da kanka". "Ba zan ba" ya bata amsa. Tura baki tayi cike tsiwa da harare-harare. "Leave my class" malamin ya faɗa yana nuna mata hanyar fita. Kamar kullum, ta saɓi jakarta ta fice, tana fita ya kalli 'yan ajin ya ce "A ciro takarda, kowa ya rubuta attendence, attendance 30 marks, test 10 marks. Takardar attendence ta fara zagawa, har ta zo kan Yazeed, ya kalli takardar attendance ya kalli wurin zaman Fadila, ya rubuta sunansa sannan ya rubuta Fadila Ahmad Musa. Bayan kammala lectures, malamin ya ƙirga ɗaliban ajin, ya ga mutum ɗaya ya hau kai, aikuwa ransa ya ɓaci, ya ce "Waye ya rubutawa wani attendance? Kowaye ya faɗa kafin in binciko shi da kaina". Yazeed ya miƙe tsaye cikin jin kunya ya ce "Ni ne Sir". "Wa ka rubutawa?" Yayi shiru. Malamin ya kalli Attendance ɗin ya ɗago ya kalli Yazeed ya ce "Yazeed Hashim Sharif, Faidla Ahmad Musa, da kai da ita kun rasa wannan 30mrks ɗin". Tana ƙarasawa ƙaramar tashar garinsu, ta tarar an fara lodi, kasancewar fuskarta sanye da niƙabi ne, babu wanda ya gane wacece, ta samu wuri ta shimfiɗa ɗankwalinta ta yi sallar asuba, daga nan ta shiga motar da za ta kai ta babbar tashar ƙaramar hukumar su. Gari da sauran duhu, haka suka ɗauko hanyar barin ƙauyensu, babu abin da Amina take a zuciyarta sai Addu'a, da fatan Allah ya kaita lafiya ba tare da kowa ya ganta ba. Ƙarfe bakwai suka isa babbar tasha, ta shiga tambayar direbobin nan Saminu, tare da yi musu kwatancen sa, wasu suka ce ba su gane shi ba, wasu kuma suka ce sun gane shi, amma ya kwan biyu bai shigo tashar ba, ganin gari na cigaba da haske, ya sanya ta fara tsoron kar a biyo sawunta, dan haka ta shiga motar da ake lodin Kano!. Haka tayi ta rarraba ido, kamar agola a rabon gado, tana kallon hanya, tare da mamakin manyan gine gine da tituna da ababan more rayuwa da suke shimfiɗe a maraya, yayin da ƙauyuka ko oho, banda yau da Allah ya sa ta fito maraya ta gani da idanunta, da sai ta ce ƙaryane a garin Kano babu irin wannan manyan ababan more rayuwar, duba da yadda rayuwar karkara take da wahala, saboda rashin isar da ayyuka yadda yakamata har karkarkara. Sai da suka yi kusan tafiyar awanni biyu cir a mota, sannan suka iso babbar tashar mota ta kabuga da ke cikin ƙwaryar birnin Kano. Ware idanunta tayi a kan manyan motocin da ke shiga suna fita a cikin tashar, wadda ta sha banban da tashar su ta ƙauye, sai a yanzu ta gane tayi wauta, ta ina zata fara neman Inda Baba yake? Ga Saminu ya ce mata yana Ikko, amma yau zai ƙaraso, to idan ya ƙaraso ina za shi? Nan Kano ko can gida? Gaba ɗaya ta rasa abin yi, ga jikinta babu daɗi, cikinta sai hautsunawa yake, saboda yunwa da kuma doguwar tafiyar da suka yi ta mota wadda ba ta saba ba. Ta samu can wani wuri a ƙarƙashin wata bishiya, ta rungume kayanta tayi zamanta tana kalle kalle. Saminu kuwa cikin dare suka sauka, dan haka washegari da safe baccinsa ya kwanta ya sha hankali kwance saboda gajiyar tafiya. Sai wajen sha biyu saura ya tashi yayi wanka kasancewar juma'a ce, ya shirya dan ya fara biyawa ta gidansu Amina, ya sanar mata da saƙon Baba sannan ya ce ta shirya su haɗu a tasha washegari da safe, ba tare da sanin a ranar za a ɗaurawa Aminan Aure ba. Ko da yaje gidansu Amina, sahsensu ya nufa ya tsaya a bakin ƙofa yayi salama, aka amsa masa tare da bashi izinin shiga. Sai dai yana shiga yayi tozali da Inno a zaune, idanunta sun yi jawur sun kumbura, sai ajiyar zuciya take yi, ga mata duk a zazzaune a kusa da ita. Saminu ya ce "Subhanallah, babar Amina lafiya kuwa? Aminan ce ta rasu ko kuwa mai ya faru?". Aikuwa Inno ta sake fashewa da kuka,maƙwabciyar su Inno ce ta iya cewa "Ka san yau za'a ɗaurawa Amina aure, har kafi anje an yi an gama komai yau ɗaurin Aure, an wayi gari an nemeta an rasa". "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, an nemeta an rasa kamar yaya? Ba sai wani satin ɗaurin Auren ba?". "A'a an dawo da shi yau, sai wayar gari aka yi babu Amina babu dalilinta a garin nan". Saminu ya girgiza kai ya ce "Ta ina zan fara gayawa mahaifinta wannan mummunan labarin haka? Kunga illar Auren dole kenan". "Wallahi Hanne ba ki isa ba, duk in da yarinyar nan ta shiga garin nan kin sani, Wallahi sai kin nemota dan ba zaki mayar da mu ƙananan mutane ba, yau ɗaurin Aurenta ace an nemeta an rasa, duk mun zagaye garin nan kowa yace bai ganta ba" Kawu Bala kenan, har wani irin yawu ne yake tsartuwa daga bakinsa, saboda azabar masifa da jaraba. Inno kuwa ta sake fashewa da kuka, ita ba batun Auren ne ya dameta ba sanin in da Amina ta tafi ne ga bata da lafiya shi ne babban damuwata. "Wallahi yau duk in da yarinyar nan take sai an nemota, ko gawarta aka tsinto a gidan Jarmai za a mata sutura, Wallahi Hanne ko ki fito da Amina, ko in je har birni in ɗauko miki 'yan doka su kama ki. Kuma bari kiji in gaya miki ko kuna so ko ba kwa so, ko tana nan ko bata nan sai an ɗaura mata Aure dan ubanta Hassan". Saminu ya ce "Haba Baba Bala, a fara mayar da hankali wurin gano in da Amina ta shiga mana, wannan faɗan ai duk ba shi ne abun yi ba". Aikuwa ya dawo da idonsa kan Saminu "Au munafuki Algungumi, ashe kana nan, bana raba ɗaya biyu da haɗin bakinka yarinyar nan ta gudu, dan na lura da take takenka, ance har tasha take zuwa wurinka". "Me za ta je tasha ta yi mini, iyakacina da iyalan Malam Hassan saƙo ne su bani in kai masa ko ya bani in kawo musu, kaga tafiyata ba zaka ɓata mini suna ba, Babar Amina Allah ya bayyana ta" dag haka Saminu ya fice, yana jinjina lamarin mugunta na 'yan uwan mahaifin Amina, su b ta ɓatan yarinyar suke ba, ta yadda za a ɗaura kar sunan su ya ɓaci suke yi. Malam Rabi'u Jarmai ne ya zo har gidansu Amina yana bala'i a kan idan har ba a ga Amina ba, a dawo masa da kuɗinsa, idan an ganta a san abun yi. Kawu Bala ya dinga ba shi haƙuri ya ce "Haba Jarmai, ka kwantar da hankalinka za a ganta duk in da ta shiga, idan ma ba a ganta ba, za a ɗaura muku aure a haka, duk in da ta shiga da Aurenka a kanta idan ya so ds ta dawo sai a daƙumota a kaita gidanka". Jaramai ya ce "Amma ka raina mini hankali, tana nan baku kula ba ta gudu saboda kun mayar da ni mahaukaci, sai a aura mini gaibu, ni ba zan yadda da wannan sagegeduwar ba, na baku daga nan zuwa ranar Lahadi, idan an ganta to idan ba a ganta ba, ku san yadda za kuyi ku sallame ni". "Ke Fadila, jarida zazzafa" cewar Amra da ta samu Fadila a Cafeteria. Fadila ta ce "Jaridar me fa?". "Bayan fitar ki daga class, Mutumin nan ya ce ayi Attendance, 30mrks duk wanda baya nan babu shi a 30mrks ɗin nan, ba kawai sai gayen nan yayi miki ba" "Wane gayen?". "Wannan Zaidu yake ko Yazeed, wanda aka ce shi ya ci class work, aikuwa ya gano shi ya ce da ke da shi ba ku da 30mrks ɗin nan". Fadila ta ja tsaki ta ce "To uban waye ya sashi yayi mini? Allah ya ƙara" "Kai mutuniyar baki da dama, Allah ya ƙara ma zaki ce?". "Idan ba Allah ya ƙara ba me zance? Ni muje class ɗin ma in ƙare masa ta tas kar ya sake mini shishshigi a lamurana". Aikuwa Amra ta dinga zigata, suka nufi aji, suka tarar da shi yana wurin zamansa, yana motsa bakinsa a hankali da alama karatu yake yi. "Kai wurinka na zo" Fadila ta yi maganar tana tsare shi da manyan idanunta. Ya ɗago kai ya kalleta, ba tare da ya ce komai ba. "Uban waye ya saka ka yi mini Attendance? Na ce maka ina buƙata ne? Ai ni malamin nan ya gama mini komai da kaima ya soke naka Attendance ɗin, uban shishshigi kawai" lumshe idanunsa yayi a hankali, ba tare da ya ɗago ba, balle ta sa ran zai tanka mata. "Da kai nake magana fa" "Wai ni?" Yayi Maganar yana kallonta. "Au duk maganar da nake, baka ma san da kai nake ba saboda ka raina mini hankali?". "Yi haƙuri" ya faɗa a taƙaice. "Aikin banza kawai" ɗan murmushin gefen baki yayi, tare da kau da kansa gefe, dan tuni idanun sauran 'yan ajin ya dawo kansu. Class rep ya ce "Haba babbar yarinya, duk ajin nan babu wanda ya tuna da ke ya yi miki Attendance sai shi, amma sai taimako ya zama faɗa?". "Kaga saurara mini babu ruwanka da ni, ai ba da kai nake ba, na gaya masa ina buƙatar taimakonsa ne? Ya ji da tsummar rayuwarsa kan yayi tunanin shiga rayuwata ya taimaka mini". "Dalla class rep ka daina shiga sabgar yarinyar nan, gaba ɗaya ba ta da kunya Wallahi" cewar wani matashi shima mai ji da kansa, wanda suke kira da Babson. "Lokacin da aka raba kunyar ni ba a haifeni ba, idan an raba kana nan zaka iya ɗebar mini a taka". Babson ya ce "Ni kike gayawa haka?". "Na gaya maka ɗin waye kai? Banza useless" Ganin Babson ya miƙe ya hayayyaƙowa Fadila, kuma bakin Fadila ya ƙi mutuwa, sai cigaba da tunzura Babson take. Yazeed ya miƙe ya riƙe Babson ya ce "Ɗan uwana dan Allah kayi haƙuri ka ƙyaleta. Fadila ba mutuncinki bane ki dinga rigima da mutane mussaman maza, muryarki al'aura ce, sai ɗagata ki ke yi... "Dalla yi mini shiru, ji yadda kake ambatar Sunana kamar kai ka raɗa mini, idan ba ka kiyayi shiga sabgata ba saina kwarfeka na bi ta kanka a gaban mutane" Dariya jama'ar wurin suka fara, tana fama da kayan rama, kamar a busheta ta faɗi, amma ta kalli zabgegen namiji kamar Yazeed ta ce zata kwarfe shi. Babson ya ce "Dan Allah ku ƙyaleni in tattaka wuyan yarinyar nan, in kawo ƙarshen fitsararta". "Sai dai kayi ka kaɗai, ƙazami mai warin hammata kawai" ba dan Yazeed yana riƙe da Babson ba, da ba abin da zai hana ya yiwa Fadila mahangurɓa. Baba sai kiran wayar Saminu yake, a kan batun tahowar su tare da Amina, Saminu ya tabattar masa da cewar Amina ta ɓata an nemeta an rasa. "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abin da Baba Hassan ya dinga maimaitawa, tare da dana sanin rashin zuwansa ƙauye akan lokaci, take ya fara dana sanin zaɓar aikin nan a kan zuwa ƙauye wurin tilon 'yar sa. Gaba ɗaya Baba ya rasa abin yi, jikinsa banda rawa babu abin da yake, banɗaki ya fara zagawa yayi gudawar fargaba, sannan ya ɗauro alwala ya zo ya tada salla ya kaiwa Allah kukansa, sannan yayi tunanin mafita. Baba Hassan mutum ne mai matuƙar tawakalli, dan haka ba lallai ka karanto damuwar da yake ciki a halin yanzu. "Baiwar Allah, ke tun safe na ga mota ta sauke ki, amma kin zo nan kin duƙunƙune a nan, lafiya kuwa?". Amina da ke jin jiki ta kalli mutumin ta ce "Dan Allah a tashar nan kake?" "Eh a nan nake". "Dan Allah ka san wani Saminu, ɗan garin Shanono, direba ne shima" Yayi shiru sannan yayi ajiyar zuciya ya ce "Gaskiya ban san shi ba, amma ke ina zaki je?" "Wurin Babana na zo, kuma Saminun ne kawai ya san in da Baban yake". "Idan ba zaki damu ba muje in baki masauki mana" "Nace maka ina buƙatar masauki ne? Ka bari na gode kawai". Amina na nan zaune ta ji ana cewa wani Sarkin tasha, miƙewa ta yi tabi bayan Sarkin tashar, zuwa wani Office da ya shiga, ba tare da ya san tana bin sa ba. Yana ƙoƙarin zama ya ga Amina a tsaye a bakin ƙofar ofishin, ta zuba masa ido. "Lafiya kuwa?". "Dan Allah yayana tambaya nake" "To Allah ya sa lafiya, ya sa kuma na sani" "Dan Allah ka san Saminu direba, yana zuwa daga Shanono?". "Ahh na san Saminu wani dogo baƙi, yana jan mota KIA?" "Eh shi, dan Allah idan kana da lambar wayarsa ka kira mini shi" "Eh ina da ita, amma ta sayarwa ce" "To nawa ce?" Amina ta faɗa da mamaki. "Eh, amma ba da kuɗi ba, ƙofar ofishin nan kawai zamu rufe, mintuna kaɗan sai in baki wayar ma kyauta". Amina ta kalleshi tsaf tayi ajiyar zuciya, kawai ta juya ta bar wurin, tana tunanin wannan wane irin abu ne haka? Babu wanda zai iya yi maka alfarma a birni, sai ya nemi mutuncinka?. "Da in koma gida a mini wannan Auren, gara in cigaba da yawo a nan" ta faɗa a fili. Ta koma in da ta bar kayanta ta yi alwala tayi sallar Azahar Tana nan zaune, sai ga wanda ya fara yi mata magana da farko ya dawo wurinta, ya ce "Ke, na gane Saminun da kike nufi, ke 'yar uwassa ce?". Amina ta jinjina masa kai, alamar eh. "Ok bari in kira miki shi a waya" ya kira wayar Saminu ya bawa Amina. "Saminu gani a tashar Kano, dan Allah ka gaya mini ina zan bi inje wurin Baba?". "Amina, dama nan kika tafi, kin sa ana ta nemanki a gida?". "Dan Allah ni dai ka taimaka mini, kuma kar ka gaya musu in da nake dan Allah". "Shikenan, kwantar da hankalinki, kin ganni a hanya na kusa shigowa 1 21Kano, idan na shigo zan kai ki in da yake". "Yawwa na gode sosai, Allah ya kawo ka lafiya" Ta miƙawa mutumin wayarsa, tare da yi masa godiya, ta zauna tana jiran zuwan Saminu. Mutumin nan ya zauna ya dinga yiwa Amina surutu, amma ko uhmm ba ta ce masa. Sai bayan la'asar Sannan Saminu ya iso, wata irin ajiyar zuciya Amina ta dinga saukewa tana murmushi. "Yi haƙuri Amina na barki kina jira, Amina wannan ramar da kika yi fa?" Maimakon ta bashi amsa sai ta hau kuka, Saminu ya ce "Yi haƙuri, share hawayenki, nayi miki laifi nima dan ban gayawa Mahaifinki da wuri ba, kuma da na gaya masa dama cewa yayi in kai masa ke. Muje maza in kai ki" Mutumin da ya kirawa Amina Saminu ya ce "To Amina ba sallama?" Shiru ta yi masa tana cigaba da share hawaye. Saminu ya ɗaukar mata kayanta, ya sa a motarsa ta shiga, ya je ya sayo mata gurasa da nama da lemo ya bata, ta riƙe a hannunta amma ta kasa ci. Suna tafe yana bata labarin yadda gidansu ya hargitse, ita duk tausayin Inno ne yafi damunta. Ko da suka shiga cikin unguwar tudun Yola, rukunin gidajen da Baba Hassan yake gadi, Amina ta saki baki, tana ganin gidaje tamkar a ɗauka a ci. Da Saminu yayi parking ya ce mata sun zo, nan mamaki ya ƙara baibayeta, gate ɗin gidan ma kawai abin kallo ne. Saminu ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa ƙofar gate ɗin, amma ya ji shiru, ya tura ƙofar suka shiga, lokacin Baba Hassan na fitowa daga ɗakinsa na gadi, a guje Amina ta ruga da gudu ta nufi in da Baba yake ta riƙe hannunsa ta fashe da kuka. Baba kasa Magana yayi, sai kallon Amina yake yana murmushi, shi dai a duniya ba abin da ya rage masa da yake ƙauna kamar Amina. Saminu ya ƙaraso yayi masa bayanin komai, Baba Hassan ya dinga yi masa godiya, sannan ya ce dan Allah idan ya koma garinsu, ya haɗa shi da Inno a waya yayi mata bayani, amma bayan ita kar ya gayawa kowa abin da ya faru. Saminu ya tabbatar masa da zai yi hakan, daga nan suka yi sallama ya tafi. Baba ya zauna Amina ta gaya masa duk abin da ya faru a ƙauye, ya jinjina kai shi kuma ya gaya mata yadda suka yi da Alhaji Ahmad. Amina ta dinga murna jin batun cigaba da makaranta. Amma Baba ya ja mata kunne a kan yanayin mutanen gidan da halayarsu, A ƙuruciya ta Amina gani tayi ai dan wannan ai mai sauƙi ne. Baba ya dinga jadadda mata "Sai kin yi haƙuri, rayuwar birni da ta karkara ba ɗaya bace, su mutane ne masu ƙyamar talaka ki iya kan ki, kiyi musu aikinsu su biya miki kuɗin Makaranta". Amina sai murna take, ashe da rabon burinta zai cika a rayuwa. Baba ya ce "Muje in gabatar da ke a wurin su". Amina ta bi bayan Baba da kayanta a bagco, tana ta kalle-kalle, kamar zata faɗi. Ya yin da Baba ke ta Addu'a Allah ya sa Amina ta shigo a sa'a, ta samu ta kammla makarantar Sakandire ɗin ta. Ayshercool 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) P7 Tuni Amina ta manta da zazzaɓin da take fama da shi, dama na fargaba da damuwa ne, ita wancan Auren da ta baro ya fi komai yi mata daɗi, ga kuma wannan abin farinciki da ta zo ta riska, ba ta taɓa zaton abubuwa za su zo da sauƙi haka ba. Har sun kai bakin ƙofar da zasu shiga cikin falon gidan, Baba ya tsaya ya kalli Amina ya ce "Uwata ina sake jadadda miki, sai kin yi haƙuri kin kauda kan ki, ki kwantar da hankalinki duk abin da suka ce ki yi, babu musu haka wanda suka ce ki bari, banda shishshigi ki zauna kiyi haƙuri mu samu ki kammala makarantar ki lafiya ƙalau". Amina ta yi murmushi ta ce "Insha Allah Baba ba zan baka kunya ba, zan yi duk abin da kace" ya jinjina kai sanan ya tura ƙofar ya shiga da sallama. Alhaji Ahmad ne kawai ya amsa, Hajiya Zainab kuwa na zaune, Fadila na kwance a kan cinyarta, tana kallon T.V. Baba na gaba Amina na biye da shi, suka ƙarasa cikin falon, Amina ta zube har ƙasa ta gaida Alhaji Ahmad, ya amsa mata cikin mutuntawa. Ta kalli Hajiya Zainab ita ma ta gaisheta, sai da ta yi mata kallon sama da ƙasa sannan ta ɗauke kanta ta amsa da ƙyar. Alhaji Ahmad ya ce "wannan ce yarinyar taka?". Baba ya ce "Eh ranka ya daɗe" Alhaji Ahmad ya kalli Mummy ya ce "Madam, ga yarinyar da na yi miki magana ɗazu, 'yar wurin Malam Hassan, dan haka sai ku haɗata da masu aikinku ku nuna mata aikin da zata ringa yi. Sannan yanzu ana hutun makaranta ne, amma da zarar an koma Makaranta za'a kai ta makaranta insha Allah". Baba ya ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi". Amina ma ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi". "Ba komai, ki nutsu ki mayar da hankali kiyi karatu da kyau kin ji ko?". "Tom insha Allah na gode sosai". Duk wannan abun Mummy da Fadila basu tofa ba, Baba Hassan ya gama godiyar sa ya tashi ya koma bakin gate in da yake aikinsa. Amina na zaune tana jiran a bata masauki, amma babu wanda ya kuma kulata, sai ma cigaba da hirarsu da suka yi. Kusan mintuna arba'in tana zaune, ga yunwa tana ji, gurasarta na cikin kayanta, tana so ta keɓe ta samu ta ci, amma ba wanda ya kuma saurararta. Ba tsammani ta ji muryar Fadila tana kiran "Hajara" Amina a ranta ta ce "Ji wata murya kamar aljana". Hajara ta ƙaraso falon hannunta riƙe da duster, ta ce "Gani". "Dan Allah kai yarinyar nan can wurinku, ta zo ta sanya mutane a gaba da kallo". Sai yanzu Mama ta ce "Ki kaita ɗakin da Asabe ta bari, da safe zan mata orientation" Hajara ta ce "to" ta kalli in da Amina take, yarinya ɗanya sharaf, tubarkallah baƙa ce mai kyau da ita, sai dai kayan jikinta zai tabattar maka da akwai rangwamen gata. Hajara ta yi matamurmushi ta ce "Ta so muje ciki". Amina ta ce "To bari in ɗakko takalmana a bakin ƙofa, kar wani ya samin". Wani irin kallo Fadila ta yiwa Amina, jin abinda tace, Daddy kuwa murmushi kawai yayi. Amina ta ɗakko takalmanta silifas ɗan madina mai zanen yatsu. Hajara ta ɗaukar mata jakarta suka shiga ciki, Hajara ta buɗe wata ƙofa suka shiga wani falon. Amina ta ce "Kai, sanyi sosai, naga lokacin bazara ne, amma sanyi sosai nan" Hajara ta ce "Na'ura ce take sanyaya ɗakin ai" Amina ta ce "Ok ita ce A.C air condition?" Hajara ta kalli Amina jin ta yi turanci ta ce "Eh ita ce". Ta kai Amina ɗakin da Asabe ta bari, ɗan madaidaici ne da ƙatuwar katifa, akwai mudubi da banɗaki a cikin ɗakin. Hajara ta ce "Ga ɗakin ki nan" Amina ta zaro ido ta ce "Wannan duk ni kaɗai? Amma tare zamu dinga kwana a ɗakin ko?" "A'a kowa da ɗakinsa, ga banɗaki nan bari in kawo miki sallaya ko zaki salla, bari in je kitchen in samo miki Abinci" "To Na gode" bayan fitar Hajara, Amina ta dinga kallon ɗakin, ta leƙa banɗakin tas da shi. 'Allah sarki Inno, da na san haka zan samu komai a wadace da mun taho tare, wannan aljannar duniya haka?" Ta shiga banɗakin, ta dinga taɓe- taɓe, Dan Amina akwai rawar kai wasu lokutan, hakan ne ya sanya take iya wasu abubuwan. Ta yi alwala, ta yi sallar magariba, ta janyo kayanta tana ƙoƙarin ɗauko gurasarta ta ci, sai ga Hajara ta shigo da kwanuka, ta ajiye a gaban Amina, sannan ta zauna kusa da Amina ta ce "Ya sunan ki ne?". "Sunana Amina". "Masha Allah, ni kuma Hajara" Nan Hajara ta dinga bawa Amina labarin yanayin mutan gidan, tare da sukar Hajiya Zainab da Fadila, ita kuwa Amina hankalinta sam baya kan Hajari, yana kan daddaɗar doya da miyar ƙwan da Hajara ta kawo mata, lokaci guda kuma tana tunanin Inno. Daren ranar Amina kasa bacci ta yi, saboda tsoro da rashin sabo, haka ta kwana da fitila a kunne. ************* Alhamdilillah kwanakin nan Hafsa tana yin ciniki sosai, dan har da dankali take haɗawa yanzu bayan awara. Dan har da miya take haɗawa idan mutum yana so ya siya da miya. Wata mota ce tayi parking a ɗan gaban in da Hafsa take suyar awarar ta, mutumin ya sauke glass ya leƙo da kansa, ya kalli Hafsa yayi mata alama da taje. Kallo ɗaya ta yi masa gabanta ya faɗi, ta ɗauke kanta ta cigaba da abin da take yi irin ba ta ganshi ɗin nan bama. Wani almajiri ne yaje kanta ya tsaya ya ce "Wai ki zo inji mai motar can". "Kace masa ba zan zo ba" Almajiri ya koma ya sanarwa mutumin saƙon Hafsa. Mutumin ya ce "Ka nuno mata ni kace ni nake kiranta". Ko da yaron ya zo ya kuma sanar mata saƙon mutumin, ta kalli yaron a fusace ta ce "Zaka matsa daga kai na ko sai na kwaɗeka?" Ba shiri yaron ya matasa ya bar wurin, da Hafsa ta iya tsare gida bata son wargi. Mutumin ne ya fito daga motar ya ƙaraso kan Hafsa ya tsaya, ya dubeta a wulaƙance ya ce "Ke ni nake miki magana ki ka share ni?" Ko nuna ta san ƙurar da ta kwaso shi ba ta yi ba, ta cigaba da fifita wutar gabanta. "Aikin banza wulaƙatancciya, a haka zaki ƙare rayuwarki a wahala, daga ke har mahaifiyar ki haka zaku ƙare, kaɗan ma kuka gani, muddin ina raye sai kun fito titi kuna bara" Wani murmushi ta yi mai ciwo, ta cigaba da sabgar gabanta. Ya dinga jifanta da miyagun maganganu, a gaban mutane. Mai shayin da ke gefen in da Hafsa ke sana'arta ne ya ce "Haba bawan Allah, ta yi shiru ba ta tanka maka ba, sai ci mata mutunci kake a gaban mutane ya haka ne?" "Kaga saurara mini, ba da kai nake ba, ba ka san meye tsakanin mu ba" "Koma meye tsakaninku wani abu ne da ya shafe ku, nan kuma titi ne bai kamata ba abin da kake yi". Banza yayi masa ya cigaba da surfa rashin mutunci son ransa, amma duk yadda ya so Hafsa ta tanka masa taƙi, ya gama bala'in sa ya hau motarsa ya tafi. Bayansa ta bi da kallo har ya ɓacewa ganinta, sai da ya bar wurin wasu hawaye masu zafi suka shiga zubowa daga idanunta 'Allah ka nuna mini ƙarshen mutumin nan da ire irensa kan ƙasa ta rufe idona'. Ganin tana kuka, Mansur mai shayi ya ce "Kiyi haƙuri Hafsat, mutane irin wannan sai haƙuri ba su da mutunci ba su da kirki" Hafsa ba ta ce masa uffan ba ta cigaba da share hawaye, haka ta kammala cinikin nan babu daɗi ta haɗa kayanta ta koma gida. Tun da Hafsa ta koma gida Mama ta fuskanci akwai damuwa a tattare da Hafsa, duk da Hafsa ba mai yawan magana ba ce, kuma ba Yarinya ce mai fara'a ba, amma shirunta da ƙaruwar haɗe fuskarta ya sanya Mama ta gane hakan. "Hafsa lafiya kuwa?" "Lafiya ƙalau" ta amsa a ciki. "A'a ba lafiya ba, mai yake faruwa ne?" "Mama bakomai fa". "To koma meye Allah ya ye miki, Idan ba ki gaya mini damuwarki ba, ban sani ba ko akwai wani wanda ki ke da shi a waje da zaki gaya masa" Hafsa ba ta kuma cewa Mama komai ba, ta cigaba da abinda take yi. Wasu lokutan Mama tana jin haushin miskilancin Hafsa, amma kuma gado ta yi haka mahaifinta ma yake, amma har gara shi a kanta, babban abin da Mama take ji shi ne, ba kowane namiji ne zai iya jure halin Hafsa ba. Mama ta zuba mata ido, saboda kar Mama ta cigaba da takura mata da tambaya, ya sanya ta dinga ƙaƙalo aiki tana yi, ta kwaso kayan wanki ta wanke a daren, ta tsiri wanke wanken kayan kitchen gaba ɗaya, ta je ta sayo waken awarar gobe, duk wannan aikace-aikace da take yi, ba ta kula Mama ba, ta zauna zata fara gyaran wake, Mama ta yi gyaran murya ta ce "Ajiye waken nan, ki zo ki zauna ki huta, ba zan sake tambayar ki meke damunki ba, tunda dan gujewa tambayar tawa ya sa ki ke ta wannan aikace aikace". Aikuwa sum sum kamar munafuka Hafsa ta koma ɗaki, ta nemi wuri ta kwanta ba tare da ta ko ci Abincin dare ba, Mama kuma ba ta kulata ba ta ƙyaleta. Amina ta wayi gari a birni, ta gabatar da sallar Asubahi, ta zauna ta na karanto azkar ɗin ta kamar yadda ta saba, tana nan zaune ta ji motsi dan haka ta tashi ta fita, aikuwa taga Hajara ce ke kaiwa tana komowa. Amina ta gaida Hajara cikin girmamawa, dan dama Hajara ta girmeta, Hajara ta amsa tare da cewa "Har kin tashi?". "Eh na tashi, nuna mini hanyar fita waje, in je in gaida Baba". Hajara ta nuna mata, Amina ta fita ta tafi. A ƙofar ɗakin Baba ta tsaya ta ƙwanƙwasa, ya ce "Waye a nan?" "Baba ni ce" Baba Hassan ya buɗe ƙofar, ta durƙusa ƙasa ta gaishe shi, ya amsa sannan ya ce "Ya a kai kika fito da duku-duku haka?" "Baba gaisheka na zo na yi, sannan in ganka" Yayi murmushi ya ce "To bismillah" suka shiga ɗakin da Baba yake, abin ka da 'ya da uba, an daɗe ba a haɗu ba, suka dinga hira ta bashi labarin abubuwan da suka faru a ƙauye, har ƙazafin cikin da suka yi mata, da sayar da gonarsa da irin kayan da suka saya mata ta gaya masa. Baba ya yi ajiyar zuciya ya ce "Bakomai, watarana sai labari, ni dai fatana da burina ki mayar da hankali kiyi karatun nan kin ji uwata" "To Baba zan yi insha Allah" "Yawwa uwata, Allah yayi miki Albarka". "Ameen Baba, amm ai zakaje ƙuye su biyaka gonarka ko?" "A'a Amina, ai gona ta riga ta salwanta, zan dai je garin in musu bayanin kina wurina". "Baba ba wani mataki da zaka ɗauka? Dubu ɗari uku fa suka sayar da gonar". "Ba komai, Allah ya mayar mini da alkhairi". "To Wallahi Baba ka yi musu Allah ya isa". Baba Hassan ya buɗe baki ya ce "Uwaki nace, yayyen nawa zan yiwa Allah ya isa?" Sai Amina ta fara hawaye "Haba Baba, tun da na buɗe ido suke cutarka, kai baka cewa komai, su yi ta zaluntar ka dan sun ga babu mai tare maka, Wallahi Allah zai saka maka" Baba Hassan ya ƙurawa Amina ido, yana jin soyayyar 'yar ta sa a ransa, ita dai a duniya kar a taɓa mata shi, ko a cutar mata da shi. Ya sa hannu ya share mata hawayen fuskarta ya ce "Tashi maza ki koma ciki, kar su neme ki, zamu cigaba da hirar" da ƙyar Baba ya sa Amina ta tashi ta koma cikin gidan. A falo ta tarar da Hajara, na ƙoƙarin fara moping, a nan ta tsaya Hajara ta dinga nuna mata yadda ake ayyukan gidan, da wuraren da suke ajiye kayan amfani. Daga nan suka shiga kitchen, suka fara ƙoƙarin haɗa Abincin karin kumallo. Ƙarfe takwas da rabi suka kammala komai, Hajara ta lura Amina ba ta da ƙyuwa sam, ga kaifin basira. Sun gama shirya Abincin a kan dining, Hajiya Zainab ta fito daga sashin Fadila, tana gaba Fadila na binta a baya. Hajara ta risuna kamar baiwa tana gaida Mummy da Fadila, Amina kuwa da murmushi a fuskarta ta gaida su, sai dai yadda suka amsa gaisuwar a wulaƙance ne ya bawa Amina mamaki, dan ita Fadila ma ko amsa gaisuwar ba tayi ba. Hajiya Zainab ta kalli Amina sannan ta mayar da kallonta ga Hajara ta ce "Ina fatan kin fara nuna mata yadda aikin gidan nan yake?". "Eh Hajiya na fara nuna mata" "Yawwa, ki buɗe kunnenki da kyau ki ji abin da zan gaya miki, da dokokina na gidan nan, idan kika karya mini doka korarki zan ki koma in da kika fito. Na farko bana son ƙazanta, bana son munafunci da sa ido, duk abin da zaki ga an yi a gidan ba ruwanki, tun da ba gidanku bane ba. Sannan bana son munafunci da gulma, sannan duk wanda ya saki a gidan nan kome kike dole ki ajiye kiyi abin da aka saki. Ina da yara biyu ɗayan namiji ne baya nan amma yana zuwa hutu gida, ba na son shishshigi a kan abinda ya shafi rayuwata da ta yarana. Abu na ƙarshe idan kin san ki na da wani mugun hali na sata ko makamancin haka ki tabattar kin baro su can a ƙauyenku, dan ba zan ɗauki duk wani rashin daraja da rashin ɗa'a ba" Amina ta ji haushin kalaman da Mummy ta yi amfani da su wurin yi mata bayanin aikin nata, amma ba ta nuna hakan ba sai ma cewa ta yi "Insha Allah zan kiyaye" Mummy ta ce "Fadila do you have anything to say?" "Nothing much, you have said it all. Kawai ni dai a bi abinda nake so a gidan nan a zauna lafiya, idan kuma akasin haka ya faru, za a ga abin da zai biyo baya" Mummy ta ce "To, kar ki sa ran zuwan ki gidan nan, kamar buƙata ta biya ne, zan jarrabaki na 'yan kwanaki in ga kamun ludayin aikin naki, idan yayi mini shi kenan, idan bai mini ba kuma ki koma in da ki ka fito, idan yayi mini ɗin, sai in ga sashin da zaki din ga kula da shi a gidan nan". Amina dai ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta. Hajara ta ce "Amina ta so muje mu cigaba da aikin" Amina ta tashi ta bi Hajara, tana mamakin yadda Hajiya Zainab da 'yar ta ke gatsa magana ba girmama ɗan Adam sam. Hajara ta ce "Amina sai fa kin yi haƙuri, idan har kina son zamanki a gidan nan dole ki ji ki ƙi ji, dan ba ki ga komai ba in dai wannan matar ce" Amina tayi ajiyar zuciya tare da jinjinawa Hajara kai. Ɗakin Fadila suka nufa, Suna shiga ɗakin Amina ta yi turus, ɗakin kaca kaca, har da kwanukan Abinci a ɗakin. Ga takardu da litattafai ko ina, har da kofi a kan gado, ta cire kaya duk ta watsar a ɗakin, banda takaddun biscuit da na chocolate duk a ɗakin a watse. Ga ɗaki har ɗaki mai kyau, amma kamar makwancin mahaukaciya. Amina ta ce "Wannan ɗakin waye?" "Ɗakin 'yar masu gidan ce, kin ganshi nan dai kamar ɗakin jaka, gashi ba ta son ƙazanta, amma fa Komai sai dai a yi mata. Idan ta tashi daga kan gado, cire bedsheet ake a bayar a wanke, ana wanke mata banɗaki sau uku a rana. Haka ma gyaran ɗaki, kuma idan zaki gyara mata ɗaki sau goma idan ta shigo komai a in da ta ga dama zata watsar da shi. Idan ta dawo daga unguwa ko Makaranta, tun daga falo take fara zubar da kayanta, sai dai ki bi Falon ki kwaso mata kayan, tana da kyauta ba kamar uwatta ba, amma duk alkhairinki a gareta, rana ɗaya idan ki ka yi mata abin da bata so, sai ta ƙare miki cin mutuncin da sai kin rasa ina zaki saka kanki, idan ba ki sa'a ba kuwa har uwatta zasu haɗu su ci miki mutunci, dan haka sai ki shirya! Sai kin mayar da kan ki baiwa a wurinsu zaku zauna lafiya". Nan take jikin Amina yayi sanyi, tana iya jure komai aiki wahala da makamantansu amma ba ta son wulaƙanci, ta fara wasi wasin anya zata iya kuwa? Zata iya jure a ci mata mutunci a kan abinda bai kai ya kawo ba?. Haka suka gyarawa Fadila ɗakinta, suka koma sashin Hajiya Zainab suka gyara ko ina, amma babban abin da ke sake bawa Amina mamaki bai wuce yadda Hajiya Zainab ke ta faman yi musu tsawa ba, ko Magana za a yi musu, sai cikin tsawa da harara. Kwanaki biyu kenan ɓatan Amina ya karaɗe ƙauyen nan gaba ɗaya, ga Jarmai ya ɗagawa su Baffa Bala hankali, dan ya riga ya gama saka rai da samun Amina. Inno kuwa tsawon kwanakin nan, ba ta iya cin Abinci, duk ta zube saboda kuka, da tashin hankali ko bacci bata iya yi, kullum tana kan sallaya tana riƙe da carbi. Har malaman makaranta su Amina sai da suka zo, suka yiwa Inno jajen ɓatan Amina. Kamar ko yaushe, Inno na zaune ta duƙufa tana jan carbi, ta jiyo muryar Saminu yana sallama. Ta amsa masa tare da bashi damar shigowa, ya shiga ya zauna suka gaisa, sannan ya ce "Baba Hassan ne ya aiko ni wurinki". Inno ta ce "Ka sanar masa da batun ɓatan Amina ne?". "Ai Amina ba ɓata tayi ba". Inno ta kalleshi da mamaki, amma ta sunkuyar da kai ta ce "Na sani, Amina guduwa ta yi saboda wannan auren da za ayi mata, ba yadda ba ta yi dani ba a kan in sa baki, amma nasan ko na yi magana ba su ji ba, ni babbar damuwata babu wanda ya san in da take, ta ɓatawa kanta suna a garin nan" ta ƙarasa Maganar tana share hawaye. "Maman Amina ki kwantar da hankalinki, Amina na tare da babanta a birni" Dafe ƙirji Inno ta yi ta ce "Kamar yaya?". Nan ya kwashe komai ya gaya mata, sannan ya ɗora da cewar "Baba Hassan ya ce, kar ki gayawa kowa, ya ce zai zo da kansa garin nan idan komai ya lafa, wayata ta ci speaker ne jiya, da na kira miki shi a waya". Inno ta kuma ƙasa da muryarta ta ce "Dan Allah Saminu da gaske ka ke, tana lafiya ƙalau a wurin babanta?". "Wallahi Babar Amina ba zan miki ƙarya ba, tana wurin Baba Hassan". "To Alhamdilillah, Allah kai ne abin godiya, Allah na gode maka, Saminu Allah ya yi maka albarka, insha Allah zan shiru da bakina, babu wanda zan faɗawa sai ya zo da kansa" Inno ji tayi tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha dan tsananin farin ciki. Kwanakin Amina huɗu a gidan, Alhaji Ahmad ya shirya komawa wurin aikinsa, ya tabattar wa da Baba Hassan cewa, Khalil zai shigo gari, idan an koma Makaranta shi zai kai Amina Makaranta. MEYE HASASHEN KU GAME DA LITTAFIN NAN? INA JIRAN RA'AYOYIN KU. DAN ALLAH BANA SON THANKS ƊIN NAN, KO STICKER. Domin samun update a kan lokaci Follow my Arewabooks Account @ Ayshercool7724 My Watpad account@ Ayshercool 7724 Ayshercool 08081012143 GABA DA GABANTA P8 AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Amina ta yi murna sosai a kan batun kai ta makaranta, tsananin ɗoki da shauƙi ya sanya ta manta da duk wani batun rashin mutuncin da Hajiya Zainab da 'yar ta ke musu. Kafin Alhaji Ahmad ya tafi, Baba ya tambaye shi yana son a bashi dama sati mai zuwa ya je ganin gida. Alhaji Ahmad ya amince masa da ya je. Bayan an idar da sallar Asubahi, Rabi'u Jarmai ya ritsa kawu Bala yana masifa "Gaskiya Bala na gaji, yau kwanaki goma kenan ba yarinyar nan babu labarinta, dan haka na haƙura, kuje ku kwashe ruɓaɓun kayan da ku kai gidana, sannan ku dawo mini da kuɗaɗe na". Kawu Bala ya ce "Haba Jarmai, ya zaka yi mana haka? Dan Allah ka yi haƙuri, na gaya maka ana ganin yarinyar nan, za a ɗaura muku aure a kai maka ita gidanka" Jarmai ya ce "Allah ya sawwaƙe, yarinyar da ta iya guduwa daga gidan iyayenta tsawon kwanakin nan, ai kowa ya san bariki ta tafi, dama can waya sani ko a ɓoye yawon bokon nan abin da take yi kenan, kawai ku biyani kuɗina ko in kai ku wurin 'yan sanda a birni". "A'a ba za ayi haka ba, insha Allah zamu dawo maka da kuɗaɗenka, ba zata kaimu ga haka ba" "Ato a san abin yi tun da wuri, kan ta kacame mana". Kawu Bala ya tafi gida yana jujjuya lamarin a zuciyarsa, ya san jarmai ba shi da mutunci a kan kuɗi ba abin da ba zai iya aikatawa ba. Kawu Bala na zuwa gida, ya sa aka taso masa Lawan suka keɓe. "Lawan, Jarmai fa na neman ya tona mana asiri a garin nan, yanzun nan ya tare ni a masallaci ya ce mu dawo masa da kuɗinsa ko ya kai mu wurin 'yan sandan birni" "Kai Jarmai ba shi da mutunci Wallahi" "Ai ba laifin Jarmai ba ne, duk laifin wannan shegiyar yarinyar ce, da ta na nan ai da duk haka ba ta faru ba, Allah wadaran yarinyar nan" Kawu Lawan ya ce "matsiyaciya ba, na san tana can ta bazama bariki, dan da tana garin nan da tuni an ganota, ko ubanta ya san ta gudu oho" "To waya san musu" "Ni anya makuwa ba da haɗin bakin Hanne yarinyar nan ta gudu ba?" "Nima na fara zargin haka, dan ban yadda da matar nan ba, amma yanzu yaya za muyi da Jarmai" "To yanzu dai ya za ayi a mayarwa da wannan masifaffen kuɗinsa?" Kawu Bala ya ce "Yanzu dai idan gari ya yi haske, aje gidansa a kwaso kayan nan, a mayarwa da Larai dillaliya, kai kuma ka lalubo abin da za a samu a wurinka". "Me kuwa za a samu a kuɗin, kar ka manta a kuɗin aka saiwa Gali babur, ka cika kuɗi ka sai babbar gona, ai ni ban wani mori kuɗin nan ba". Kawu Bala ya ce "Haka ne, amma duk da haka dole kayi wani abu, ko 'yar wurinka Abu zamu ba shi a madadin Amina?" Kawu Lawan ya zaro idanu ya ce "Ni in ɗauki 'ya ta in bawa Jarmai, Allah ya kiyaye ya sutura, Wallahi gara ta mutu ba aure, sai ka ce baka san waye Jarmai ba? Ka aura masa Sa'a mana ai ita ma ta isa Aure". "Kai baka Aura masa Abu ba, sai ni zan aura masa sa'a? Wannan mutumin banzan Allah ya kiyaye, dama dai Aminan ce. Yanzu dai idan gari ya yi haske, za a kwaso kayan a mayarwa dillaliya, mu san yadda za mu yi a haɗa masa kuɗinsa". "To shikenan, Sai an jima, amma dai Wallahi ka je ka ritsa Hanne, dan wataƙila ta san komai, matar munafuka ce". Bala ya ce "Bar ni da ita, zata gane kurenta" Yauma wankan doguwar rigar da ta yi, ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba, sai da tun da ta shigo kallo ɗaya yayi mata suka haɗa ido, ya sauke idanunsa cike da fargabar kar ta yi masa wata tijarar a cikin mutane, dan ya fuskanci tamkar wani jin daɗi take yi idan ta ci mutuncin sa. Kasancewar babu malami a ajin, ya sanya Captain ya ce wa Yazeed, ya fito ya ɗan yi musu tutorial, a kan wasu courses ɗin. Yazeed bai musa ba, ya fito ya karɓi abin rubutu, sai da ya fara da addu'a, sannan ya kalli 'yan ajin ya fara yi musu bayani da yadda ya fahimci tambayar da malamin nan yayi a ranar da ya ce suyi amfani da waya, sannan ya shiga gaya musu dabarun da ya bi wurin gane amsar tambayar. Fadila ji tayi ba zata iya zama jin shirmen da Yazeed yake yi ba, duk ajin a rasa wanda zai yi tutorial sai shi, ita gaba daya ta gama raina shi, ta ɗau jakarta tana mita, a fili take cewa "Instead of a nemo malamin da ze mana covering Wannan period ɗin, kawai an samu a gaba wani yana shirme, mutumin da ko turanci bai iya ba me zai koyawa wasu?". "Babbar yarinya wai dan Allah mai yasa ki ke haka ne? Wannan fa ba girmanki ba ne, bawan Allah nan mutum ne, ba zai ji daɗi ba abin da ki ke yi masa". "To kar Allah ya sa ji daɗin mana, ya daina shishshigi da son nuna ya fi kowa iyawa" Babson ya ja wani uban tsaki ya ce "Dalla ku share wannan mahaukaciyar ku cigaba da yi mana abin da yakamata". "Ba zan kula ka ba, barber ka ke ko me? Talauci ne yake ɗawainiya da kai ka ke wannan shirmen" ta yi tsaki ta fice. Har ta yi ta gama Yazeed bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, ya karɓi wayar Captain, ya cigaba da yi musu bayani. Captain ya ce "Yazeed, dan Allah ka yi haƙuri, na sani abin da yarinyar nan take yi maka babu daɗi, amma dan Allah ka yi haƙuri" Cikin dakiya da basarwa Yazeed ya ce "Kar ka damu Captain, ni ban damu ba" ya cigaba da abin da yake yi. "Kina Ina? Munafukar banza fito nan" Sai da cikin Inno ya kaɗa, dan tun da taji muryar su Kawu Lawan, ta san ba alkhairi. Fitowa ta yi daga ɗaki tana faɗin "Lafiya kuwa?" "Kya tambayi lafiya mana, munafuka ha'ina, ki zo ki fito mana da in da yarinyar nan Amina ta ke, dan babu yadda za a yi ta gudu ba tare da haɗin bakin ki ba". "Haba Yaya Bala, ni meye nawa a ciki? Ya za ayi in goyi bayan Amina ta bijire muku, ko ta gudu? Nima fa Amina 'ya ce a wurina, ba zan goyi bayan ta aikata abin kunya ba, ni ban san in da take ba". Bala ya ce "Ai kuwa ƙarya ki ke yi, kuma yadda ki ka haɗa baki da ita kika sa ta gudu, sai ki koma ki haɗo abin da ya samu a mayarwa da Jarmai kayan aurensa, tun da ta gudu". "Meye haɗina da kayan auren Jarmai? Bayan kuɗinsa da komai ku ya dabƙawa kuma babu abin da kuka bamu a ciki?". "Rufewa mutane baki, amma dai kin san abin da aka yi kuɗin ko? Kayan katako aka sayawa Amina da su" "Amma yaya Bala, ina a kuɗin gonar mahaifinta aka saya mata kayan? Ni dan me za a ce in bada wani kuɗi" "Au tuhumar mu zaki yi, to Wallahi sai kin kawo wani abu, dan sunan mu ba zai ɓaci a banza ba a dalilin ku ba, mutanen banza kawai" Galala haka Inno ta bi su Lawan da kallon mamaki da kuma ƙarfin hali. Amina aiki suke sha a gidan nan kamar ba gobe, kasancewar Amina nai kaifin ƙwaƙwalwa ya sanya nan da nan ta iya abubuwa, ita aikin fa suke ba ya damunta, dan in dai aiki ne ta riga ta saba da shi tun a ƙauye, dan sam ba ya mata wahala, ita wulaƙanci da kallon ƙasƙantattun da ake musu ne yake damunta, shima da tuna ga burinta da yake ranta wanda take sa ran cikawa sai ta yi ƙoƙari ta manta komai. Dan kusan kullum idan ta je wurin Baba nasihar sa kenan a gareta, ta yi haƙuri. Amina na ta saka ran ganin wanda zai kaita Makaranta ya dawo, amma shiru ba ta ga ya dawo ba, kuma ba ta ji ana batun dawowar ta sa ba, ta dai yi shiru ta danne abun a ranta, dan abin ya fara damunta, idan aka aiketa ita da Hajara, tana ganin 'yan Makaranta hakan ya tabattar mata da an koma Makaranta. Yau sun gama aikin su kaf, sun gyara ko ina, wanda ƙarfin aikin ma Amina ce ta yi shi, ta zauna a falo tana kallon TV, sai ga Fadila ta dawo daga makaranta, ta shigo falon ba ko sallama, ta dire jakarta a falon, da mayafinta ta kalli Amina ta ce "Ki kawo mini su ɗaki". Amina tabi bayan Fadila da kallo ta taɓe baki, a ranta ta ce "Kin shigo ba ki mini sallama ba balle sannu da gida, kuma kin yi dakon jaka da mayafi tun daga makarantar, ƙarasawa da su ɗakin ki shi ne aiki a wurinki, ai kuwa ba zan kai ba' daga haka ta tashi ta bar falon, tayi tafiyarta wurin Baba. "Uwata, in ce ko dai kin gama duk ayyukan da aka saka ki kan zo nan?" "Eh Baba, na gama komai". "Yawwa Uwata ta kaina, banda ganda ko gardama dan Allah, yi nayi bari na bari". "Insha Allahu Baba, nace yaushe zaka je ƙauye ne? Da na ji kace a wannan satin" "Eh a wannan satin na so zuwa, amma nafi son in ga yaron nan da zai kai ki Makaranta ya dawo, an kai ki kin fara zuwa sai inje". "Wallahi Baba kamar ka san abin da ke raina, na yi shiru ne kawai dan kar in takura maka, amma naga an koma Makaranta". "Mu ƙara haƙuri dai, tun da ya ce za a kai ki, na san za a kai ki insha Allah" "To shikenan Baba, amma nace mai zai hana idan zaka ƙauyen muje tare ina kewar Inno da yawa". "So kike muje su sake riƙe ki ko?" Da sauri ta girgizawa Baba kai. "To idan ba haka ba, ki cire rai da zuwa ƙauye, har sai Allah ya sa kin kammala sakandirenki" "To Baba Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi". "Ameen Uwata ta kaina" Ta shantake abinta, ta cigaba da hira Baba, har sai da aka yi kiran sallar magariba, sannan ta koma ciki. Kamar yadda Fadila ta bar jakarta da mayafi suna nan a wurin, Amina kuma bata bi ta kan su ba, ta wuce ɗakin da take. Fadila ba ta tashi sanin Amina ba ta kai mata jakarta ɗaki ba, sai da ta tashi tafiya makaranta da safe, ta nemi jaka ta rasa, ta duba ɗakinta kaf ba ta jaka ba, dan haka ta fito falo tana neman Asabe, dan ta ji in da ta ajiye mata jaka bayan ta gyara mata ɗakinta, sai dai tana fitowa ta ga jakarta da mayafinta a in da ta ajiye su, buɗe baki ta yi da mamaki, bayan ta tuna taga 'yar mai gadi jiya a falo. Cikin fushi ta fara ƙwalawa Hajara kira, Hajara da ke kitchen ta jiyo kiran Fadila ta taho da gudu, ta durƙusa. "Ina wannan yarinyar da ku ke aiki da ita?". Hajara ta ce "Wai Amina?". "Ko ma wacece, ki kira mini ita yanzun nan". "To bari in kirata, naga yau tun da aka yi sallar asuba bata fito ba, kuma ba ta saba hakan ba" "Ke dalla ɓace mini daga gabana ki je ki kira mini ita, kin tsaya kina mini wasu surutan banza" Cikin hanzari Hajara ta bar wurin, ta nufi ɗakin Amina, ta tsaya a ƙofa tana ƙwanƙwasawa. Amina ta na zaune, tana rubutun Alƙur'ani a cikin littafin da ta taho da shi daga ƙauye. Saboda yau ji ta yi tana kewar makarantar Allo, da tana ƙauye da tuni tana nan ta wanke allonta, ta yi rubutu, dan haka yau ta zauna bayan sallar Asubahi ta fara rubutunta. Tana jin Hajara na buga ƙofa tana faɗin "Amina ki buɗe ƙofa, Fadila tana nemanki". Yamutsa fuska Amina ta yi, tare da tura baki, ta cigaba da abin da take yi. "Amine ki buɗe mana" "Dan Allah Hajara ki ƙyaleni, kullum da wuri nake fitowa, yau wani aiki nake yi, kiyi abin da zaki iya, sauran ayyukan ki bar mini idan na fito zan yi" "Ke bafa saboda aiki ba, Fadila ce take neman ki". Tsaki Amina ta yi ta ce "Kwa ci kan ku, ba wanda ya isa ya ɗagani daga zaman nan idan ba Allah ba, ko Baba ne ya kirani ba". Fadila ganin zata makara Hajara ba ta dawo ba, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice ranta a ɓace, ta ƙudurce a ranta idan ta dawo sai ta koyawa su duka biyun hankali. Amina ba ta fito ba sai ƙarfe tara na safe, dan rubutunta ta zauna tai ta yi. A kitchen ta tarar da Hajara, "Anty Hajaru sannu da aiki". "Zaki ga Hajaru ganin idonki, yau kin caza mana bala'i, ba yadda ban ba ki fito amma ki ka yi mirsisi ki ka ƙi, ƙarshe sai tafiya ta yi, yau kashin mu ya bushe daga ni har ke idan ta dawo". Amina ta ɗage kafaɗa ta ce "Oho, duk masifar 'ya dai na san ba zata ɗauki raina ba, sai dai tayi ta ci kanta ita kaɗai". Buɗe baki Hajara ta yi tare da riƙe haɓa ta ce "Ke Amina dama haka ki ke?". Amina ta share Hajara, ta nufi ƙofar fita tana cigaba da ƙunƙuni. Tana fita harabar gidan ta hango Baba, ya shirya cikin wani milk ɗin yadi. Ta ƙarasa ta gaishe shi ta ce "Baba ya naga kamar fita zaka yi?". "Eh mana, dama ke nake jira in ga fitowarki in yi miki sallama, ƙauye zani". "Baba da gaske?". "Ahh ji ja'ira zan miki ƙarya ne?". "Wayyo Allah, Baba ka gaishe mini da Inno, na so zuwa in ganta, sannan dan Allah ka bata haƙuri, na san na sata a tashin hankali tahowar nan da na yi, bari inje cikin gida in ɗauko maka Abincin karina ka kai mata". Baba ya ce "A'a ba za ayi haka ba, zan musu tsaraba a hanya". "Baba dan Allah ka tsaya, yanzu zan dawo". Amina ta ruga cikin gida. "Hajara, dan Allah bani leda in zubawa Baba Abincin karina ya kaiwa Innota". "Au yau zai je garin naku?". Amina ta ce "Eh yau zai je". Hajara ta ce "Wane irin in baki leda, viva zaki samu, har kayan marmarin nan na cikin firinji da suka kusa lalacewa, duk ki bashi ya kai mata". "Ahh Hajara sata fa kenan, ba a bani ba". Hajara ta ce "Dalla bari kiga, idan ki ka tsaya sai sun baki, ba zasu taɓa baki ba, sai dai su ruɓe ki kwashe ki zubar, kuma ai ba ayi mana iyaka a kan Abincin gidan nan ba" Hajara ta ƙulle soyayyen dankali kaya guda da miyar ƙwai, da manyan magwaro da lemo, ga uwar kankana har da su biscuit. Ita dai Amina taji a ranta duk babu daɗi, tamkar sata suka yi. Hajara ta rakata suka kai wa Baba, Baba ya duba kayan nan ya ce "Amina wannan kayan fa, kin tambaya ki ka ɗakko?" Hajara ta ce "Baba Hassan, ai ba ayi mana iyaka da Abincin gidan nan ba, kuma idan aka barsu ma a banza za su lalace, su ba su ci ba kuma ba su bayar ba, sai dai mu kwashe mu zubar". Baba ya karɓa ya kama hanyar tafiya. Fadila a gaggauce ta shiga ajinsu, kasancewar yau ta makara sosai, sai dai tana shiga ta tarar da lecturer ya na arranging ɗalibai, zai yi musu test. Lecturer da farko ji yayi tamkar ya koreta, saboda ba ta da kunya, amma ya ƙyaleta ya sakata a bencin gaban Yazeed. Sai wani haɗe rai take, tana hura hanci ita a lallai bata so aka ajiyeta a wurin da yake ba. Nan malamin ya rubuta musu test ɗin, tare da sake tuna musu, test ɗin maki Ashirin ce, Attendance ɗin da yayi kuma maki talatin, zai yi jarrabawar sa maki hamsin. Sannan ya kawo wani lecture yayi invigilating ɗin su, shi zai je wani ajin yayi lectures. A tambayar da ya yi musu ciki har da abinda Yazeed ya koya musu a aji, hakan ba ƙaramin farantawa ɗaliban rai ya yi ba. Kowa ya duƙufa ya fara rubutu, amma Fadila ta shiga rarraba ido, kamar an kwashewa karya 'ya'ya. Yazeed yana ta rubutunsa, yayin da malamin ke ta zagawa yana dudduba su. Yazeed ne ya lura babu abin da Fadila ta rubuta, banda sunanta lambar Admission ɗinta da question. Ya girgiza kai, a gurguje ya ƙarasa nasa, sannan ya waiga ya ga lecturer ba ya kusa da su, ya sanya bironsa ya taɓo Fadila. "Dalla meye haka?" "Ya naga ba ki rubuta komai ba?". "To ina ruwanka da ban rubuta komai ba? Aikin banza ɗan sa ido kawai". "Sorry ba sa miki ido na yi ba, bari in karanto miki". "Bana so". "A'a, kar ki manta fa bamu da Attendance ni da ke, kuma ya ce exams ɗin ma 50mrks ce, kar a kafe exams a ga kin faɗi, za a raina ki. Buɗe papern, in dinga karanto miki kina rubutawa". Ba kunya ta ware paper, ta gyara zamanta, yana karanto mata tana kwashewa a ta ta paper. Cikin rashin sa'a, invigilator ya hango su, aikuwa yana zuwa ya rubuta wa Yazeed -10 marks a paper ɗin sa, ba tare da ya hukunta Fadila ba. Babu wanda ya san mai ya faru, sai Fadilan da Yazeed, dan lecturer bai yi magana ba, kawai zuwa ya yi kan Yazeed ya tsaya, yayi masa minusing, yana yi masa minusing ɗin kuma, Yazeed yai submitting paper ya tashi ya fita. Fadila kuwa ko a jikinta, ita dai tun da Allah ya sa ta samu abin da ta rubuta shikenan, Yazeed yayi asarar maki arba'in a test. Inno kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, ganin Malam Hassan a gida, ta dinga murna, nan ta tashi ta fara ƙoƙarin ɗora girki, ya ce "Ba sai kin dafa komai ba, dafa ruwan zafi ga kayan shayi na taho da shi, 'yar ki kuma ta bada kayan kari a kawo miki". Inno ta ce "Aikuwa Malam ina ta baza ido in ganku tare, ni nan Saminu ya ce mini tana wurinka, ko dai ƙarya yayi mini?". "A'a bai miki ƙarya ba, ke dai gama ki zo mu yi Magana". Bayan Inno ta dafo ruwan zafi, Baba Hassan ya ajiye mata tulin soyayen dankali da miyar ƙwai, Inno ci take tana santi, tana anya na taɓa cin abinci mai daɗin wannan a duniya? Baba Hassan ya yi murmushi, ya ce "bani labari, yaya aka yi da ba na nan game da Amina?". Nan Inno ta kwashe komai ta gaya masa, har zuwa ɓatan Amina. Shima nan ya warware mata cewar, Amina wurinsa ta je, kuma ga hukuncin da ya yanke a kanta. Inno ta ce "Amma malam kaja ganin hakan daidai ne? Yarinyar nan ba ta ɓatawa kanta suna ba kuwa? Kun ɗau bokon nan kun sa a ranku kai da ita kamar ibada". "Hannatu, boko ba ibada ba ce, amma ba zaki gane rashin boko na cutar mu ba, sai kinji birni kin ga amfanin boko, insha Allah zamu yi alfahari da ilimin da Amina za ta samu". "To ubangiji Allah ya sa". "Salamu Alaikum! Salamu Alaikum!" Aka shiga kwaɗa sallama. Murayar kawu Lawan ce yake kwaɗa sallama shi da Bala. Baba Hassan ya fita cike da fara'arsa yana musu sannu da zuwa, ya shimfiɗa musu tabarma a tsakar gida, suka zazzauna Baba Hassan ya gaida su cikin mutuntawa a matsayin su na yayyensa. Maimakon su amsa sai kallon Banza da Bala ya yi masa ya ce "Ina fatan labri ya iske ka na abin kunyar da 'yar ka ta yi? Mun zaɓa mata miji za muyi mata aure, amma ta tsallake ta gudu ta shiga yawon duniya". Baba ya ce "Ashsha, ba yawon duniya ba dai Yaya Bala". "To yawon me ta tafi? Waye ya san in da take, ta bi ta ɓata mana suna da zuriyar mu a gari". Baba ya ce "Yaya ba ina goyon bayan abin da Uwata ta aikata bane, amma sanin kan ku ne duk garin nan ba wanda bai san Jarmai ba mutumin kirki ba ne, maiyasa za a bashi Aurenta?" Lawan ya ce "Idan ba a bashi ba haka za a barta ta cigaba da yawo a gari soƙai-soƙai sa'ar iayyenta ba aure, saboda wata matsiyaciyar bokon banza, to ka sani idan ta dawo daga yawon banzan nata ba dai a gidan nan ba, ta je idan dai bariki ce, na baya ma ba su ci riba ba". Baba ya ce "Subhanallah, Amina dai ba wani ta tafi ba, tana tare da ni a in da nake aiki a can birni, kuma gidan da nake sun ɗauketa aiki, da albashinta zasu dinga biya mata kuɗin Makaranta". Tafa hannu suka shiga yi suna salati. "Hassan, yanzu abin da ka aikata ka yiwa kan ka adalci kenan? Yanzu wannan zabgegiyar budurwa ka kai birni ta yi boko? A ƙauyen ma ya muka ƙare da ita, har muna faɗa ta faɗa saboda ta yi boko, shi ne ka kaita birni ta yi boko?" Cewar Lawan yana zazzaro idanuwa. Bala ya ce "Ka kyauta da kuka haɗa kai da 'yar ka kuka ɓata mana suna, mun gama shirin biki da gayawa jama'a ɗaurin Aure, amma ta gudu, ga Jarmai ya ɗaga mana hankali mu biya shi kuɗinsa. Amma in Allah ya yadda, tun da aniyar alkhairi muka yi niyyar ɗaurawa, amma kasa ƙafa ka rusa kai da ita, ku ka nuna bamu isa ba, insha Allah naku burin ba zai cika ba, in Allah ya yadda sai ta yi cikin shege a birnin nan, sai ta dawo da mummunan abin kunyar da sai ka kasa haɗa ido da mutane, sai bokon nan ta zame muku bala'i da masifa kai da ita!!!" Dafe ƙirji Baba ya yi ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Inno da take ɗaki tana jiyo su ɗora hannu ta yi a ka, jin jafa'in da ake janyowa Amina. Lawan ya ɗora da cewa "Ai yadda ya ja mana abin kunya a garin nan, sai 'yar ta sa ta janyo masa abin faɗa da nunawa, ka ɗau balagaggiyar yarinya ka kaita cikin wani ahalin da ba muharammanta ba, wai dan ta yi boko, muna nan za aje a dawo da abin nunawa, zaku gani daga kai har ita, hakkinmu ba zai bar ku ba da kai da ita, muna nan mun zuba ido, zaka gani. Yaya Bala tashi mu tafi". Gaba ɗaya jikin Baba yayi sanyi ƙalau da mugun bakin da yayyaensa suka yiwa Aminan, anya ba za a haƙura da bokon nan ba Amina ta dawo ayi Auren nan ba?! Domin samun update a kan lokaci, Follow me at Arewabooks Ayshercool7724 Watpad Ayshercool7724 Ayshercool 08081012143 GABA DA GABANTA P9 AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Haka su kawu Bala suka ƙaraci faɗansu, kamar zasu tashi sama, suka kaɗe rigunansu suka fice. Baba ya yi shiru ya rasa abin da yake masa daɗi. Inno ce ta fito jiki a sanyaye tana kallon Baba. "Malam, an ya ba za'a haƙura da wannan karatun ba, ka dawo da Amina gida ba, irin wannan mugun alkaba'i da suke janyowa yarinyar nan, nifa gaba ɗaya jikina ya yi sanyi Wallahi". Baba ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Insha Allah, babu abin da zai faru sai alkhairi, ina sa ran a sanadiyyar Amina mutanen garin nan su ga amfanin ilimi mussaman ga 'ya mace". "Amma Malam, ni fa na karaya wallahi". "Ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai samu Amina sai alkhairi Insha Allah". Hajara na dininga tana kwashe kwanukan da aka karya a kai, Amina kuwa duk ta sauke kayan kallon falon, tana musu duster saboda ƙurar da suka yi. Hajiya Zainab ta fito daga sashenta, tana ƙarewa falon kallo, dan ta samu wani laifi da zata sauke musu masifa amma ba ta samu ba, zuwa yanzu ta fara jin daɗin aikin Amina, dan sam bata da ƙyuya, kafin ace ta yi ma tayi, kuma ba ta son ƙazanta sam. Hajiya Zainab ta ce "Yawwa Hajara, in an jima Khalil zai dawo, ki ɗauki mukullin sashinsa a shiga a gyara masa, sannan ku sanarwa da Isyaku ya wanke masa motarsa, dan na san da ya dawo zai buƙaci ya fita da ita, sai kuma a yi girkin rana da shi, ni zan fita wataƙila har ya dawo ban dawo ba". Hajara ta risuna cikin ladabi ta ce "To Hajiya, insha Allah za ayi yadda ki ka ce, sai kin dawo". Har Hajiya Zainab ta kai bakin ƙofar falon, ta waigo ta kalli Amina da take ta aikinta ko kulasu ba ta yi ba ta ce "Ke, wato kin fi ƙarfin ki gaishe ni ko?" Amina ta ɗago ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Hajiya na gaishe ki ɗazu da ki ka fito karyawa". "To kin fi ƙarfin ki sake gaishe ni ko kice mini sai na dawo ne?" Amina ta ce "A'a ki yi haƙuri, A dawo lafiya Allah ya tsare". Ba ta amsa ba ta ce "Ki shiga ɗakina ki tattara kayana suna nan ki ninke ki shirya mini su, amma sai kin musu kabbasa tukuna". "To zan yi insha Allah" Hajiya Zainab ta juya ta fice. Amina a ranta ta ce "Dan jaraba, dole sai an ƙaƙalo abin da za a ƙasƙantar da kai' Ta ɗago ta ce "Yaya Hajaru, wanda zai dawo ɗin nan, shi ne wanda zai kai ni makarantar?". Hajara ta ce "Eh shi ne". "Allahu Akbar, to shi ya yake? Yana da kirki ko shima dai duk haka suke?". Hajara ta ce "Eh to, ba na ce ba, shi dai gashi nan miskili ne dai sosai, kuma bai fiye shiga abin da ba ruwansa ba, kuma ba ya wani shiga sabgar 'yan aiki, shi yasa idan nace miki ba shi da kirki na yi ƙarya, dan bai taɓa yi mini ba" Amina ta washe baki ta ce "Allah ya sa dai kar yayi mini nima, koma ba shi da kirkin lallaɓa shi zan yi, in bishi a sannu in ta masa biyayya dan ya kai ni Makaranta, ni ɗauko mukullin sashin nasa, muje a gyara". Hajara ta riƙe haɓa ta ce "Ohh ni Hajara, yadda ki ke ƙaunar karatu Amina, Allah ya cika miki burinki ya sa al'umma su amfana" "Ameen Yayata". Ko da su Amina suka shiga sashin Khalil, mamaki Amina ta dinga yi, ɗakinsa har ya fi na Fadila tsaruwa, komai akwai sashinsa har da kitchen da kwanukansa da komai, hatta fridge da cooking gas duk akwai. Amina ta zage suka ƙara tsaftace ko ina, sannan suka baro sashin. Amina na ta fatan Allah ya sa yana dawowa babu ɓata lokaci ya kai ta Makaranta. Alhamdilillah, Hafsa ciniki ya nata haɓɓaka, sai ai babban abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya bai wuce yadda maza ke zuwa su taru a wurin ba wanda sam hakan ba ya yi mata daɗi, gashi wasu 'yan iska wasu na kirki, da yake gata ga wurin mai shayi, wasu ma haka zasu zo su zauna suna shan sigari a wurin. A haka wasu suke nuna suna sonta, da zarar ta musu halin nata na miskilanci, sai zagi da cin mutunci, ita dai bata taɓa ɗaga kai ta kula kowa ba balle ta bar abin faɗa. Abin na damunta, amma ba ta gaya wa Mama ba, dan da zarar ta ji abin da yake faruwa, zata iya dakatar da cigaba da sayar da awarar, kuma idan ta dakatar sana'ar me za suyi?. Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru, take ta Addu'a Allah ya kawo musu mafita. Tun bayan fitowar su daga test, Fadeela sai murna take yi, ko bakomai ta samu abin da ta rubuta, amma sam ba ta ji ta damu da abin da ya faru da Yazeed ba, dan a ganinta ai ba ita tace ya taimaka mata ba. Tana tsaye tana waige-waige, ta hango Yusra tana ƙarasowa in da take, ta kalli Fadila ta ce "Girl ya na ganki duk wani iri ne?" "Bari kawai unexpected test aka yi mana". Yusra ta yi murmushi ta ce "Baki shirya ba kenan?". Fadila ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Ina na wani shirya, ni gaba ɗaya ma bana gane course ɗin, gashi dama muna takun saƙa da lecturer, kinga wata applied question da ya yi mana, abin ba a magana". "Amma dai kin rubuta wani abu ko?". "Me kuwa na rubuta? Wani ne ya gaya mini na rubuta, shi kuma aka yi masa minusing marks". Yusra ta ce "Subhanallah garin yaya?". Nan Fadila ta bata labarin Yazeed. "Girl gaskiya ba kya kyautawa, ban ji daɗin abin da kike masa ba". "Ni na sashi ya dinga mini shishshigi? Kinga ni muje in samu wani abun in ci yunwa nake ji". Yusra ta kalli agogon hannunta ta ce "No, kinga yau Friday, zo muje masallacin cikin school mu saurari huɗuba, idan aka yi sallar juma'a, sai mu je muci Abincin daga nan mu tafi gida". Fadila ta ce "Masallacin Juma'a sai ka ce wasu maza?". "Kin ji ki, ai mata ma na zuwa sallar juma'a, ma samu muji huɗuba" Haka Yusra ta takurawa Fadila, suka tafi masallaci, a hanya Fadila take sanar wa da Yusra da batun dawowar Khalil. Suka dinga planing ɗin yadda zasu shawo kan Khalil a kan ya so Yusra. Suka ƙarasa masallacin mata, suka shiga suka zauna. Sai dai shiru liman bai zo ba, balle a fara huɗuba, can aka fara gyaran murya aka fara da buɗewa da addu'a, can kuma ya fara gabatar da huɗuba cikin harshen larabci. Subhanallah, kai ba ka ce mai yin huɗubar ya taɓa jin yaren hausa ba, duk da Fadila ba ta jin larabci, amma ta nutsu tana sauraren yadda huɗubar ke ratsata, bugu da ƙari yaren larabci na matuƙar burgeta, aka jima ya fara huɗubar da Hausa, wanda yayi huɗubar akan tsoron Allah da riƙon gaskiya yayi, ya yi amfani da hikima sosai a wurin gabatar da huɗubar. Bayan ya kammala kuma, aka tada salla. Subhanallah sai da ya fara karatun Alkur'ani, a lokacin wata nutsuwa ta sake saukarwa Fadila, muryarsa mai daɗin amo da saurare, ga wurin yayi tsit kamar ruwa ya cinye su. Fadila ji ta yi tamkar kar a idar da sallar nan, saboda tsananin daɗin karatun, tabbas makarancin gwani ne wurin iya sarrafa harsashe, dan hatta a cikin huɗubarsa akwai salo na narka zuciyar mai sauraro, karatunsa akwai amo mai sanyawa zukata nutsuwa. Haka aka idar da sallar nan suka nufi wurin cin abinci, amma still Fadila na cigaba da jiyo karatun nan a cikin kunnuwanta, tamkar ta magantu sai kuma ta yi shiru, suka tafi cin Abinci. Bayan sun kammala cin abincin, Yusra ta tafi don ta kammala lectures ɗinta na ranar, Fadila kuwa suna da lectures 2-5. Ko da ta shiga ajinsu, ta tarar da duk matasan samarin nan na ajin su, sun kewaye Yazeed, shi kuma ya ɗan ɓata fuska duk da da wuya ka ga fushi a fuskarsa, dan mutum ne mai yawan murmushi, da alama dai sun takura masa, sai sunkuyar da kansa yake yi. Captain ya cire hular kan Yazeed, ya duƙa a gaban Yazeed yana cewa ya Sheikh, a shafa mana karama. Wani siririn kyau ne ya bayyana a fuskar Yazeed, bayan Captain ya cire masa hula, yana da wani kwantaccen baƙin gashi, da ya haɗe da sajensa ya kwanta a fuskarsa, zuwa ɗan madaidaicin gemunsa. Ya miƙa hannu ya karɓi hularsa tare da mayarwa kansa. Yamutsa fuska Fadila ta yi ta ce "Dan Allah ku tashi ku bani wuri, kawai kun kafa daba kun cikawa mutane kunne da hayaniya". Captain y kalli Fadila ya ce "Ke kul, mun kafa dabar kwasar tabarraki ne, ashe muna zaune da babban malami amma babu labari, ai tun da nake zuwa sallar juma'a ban taɓa jin huɗubar da ta ratsani kamar wadda Sheikh, Malam Yazeed ya yi ba" Saroro Fadil ta kalli Captain ta ce "Kamar yaya?". "Ai duk wanda ya je sallar juma'a yau a masallacin school ɗin nan, ya ji yadda ya dinga zuba larabci, sai ma da ya fara karatun Alqur'ani, kamar mutum ya suma dan daɗi" She can't believe that Yazeed ne ya yi wannan karatu, guntun tsaki ta ja, ƙila ma ƙaryar Captain ce kawai. Zama ta yi a wurin zamanta ta yi shiru, tana tunanin muryar da aka yi huɗuba, tabbas muryar Yazeed ce, ko da be fiye surutu ba, amma muryarsa a nutse take cike da nutsuwa da kuma iyayi, kamar yadda take faɗa. Shi kuwa Yazeed tuni ya bar ajin, dan baya son abin da suke masa sam. Nan taji ana hirar, limamin masallacin ne ba lafiya, ya shirya zai taho, ya yanke jiki ya faɗi, kuma ba a samu information da wuri ba, an tsaya mujadalar wanda zai ja Sallar, shi ya karɓa ya yi. Har aka shigo lectures, Fadila na satar kallon Yazeed, da son tabattar yanzu daga bakin wannan ɗan tahalikin wannan karatun ya dinga fitowa ɗazu? Sam babu kama. Karaf Yazeed ya ɗago ido, suka haɗa ido da Fadila, wata uwar harar ta watsa masa, kamar ba ita take kallonsa ba. Ɗauke idonsa yayi, yana fatan Allah ya sa ba wata tsiyar Fadila take shirya yi masa ba. Amina wuni tayi tana sintiri tsakanin falo da harabar gidan, dan ganin me kaita makaran ya dawo, amma babu shi babu alamar sa. Gaba ɗaya har ranta ya fara ɓaci ta fara tunanin ko dai ba yau ɗin zai dawo ba. Shi kuwa Khalil tuni ya dawo, dan tun bayan azahar ya dawo, ya shiga sashinsa, ya yi wanka ya yi kwanciyarsa dan a gajiye yake sosai. Ya makara sallar la'asar, dan haka a ɗakinsa ya yi ta, sannan ya shirya ya fita. Amina kuwa tana zaune a falo, ta zubawa TV ido, tana kallo, tana fuskantar wani abu daga larabcin da ake fassara yaren jaruman. Ba tsammani ta ga mutum ya faɗo falon, dogo da shi kawai ya sa kai ya nufi sashin Hajiya Zainab, ba tare da ko sallama ya yi ba. "Kai bawan Allah daga ina? Zaka faɗowa mutane haka ba sallama kawai ka miƙa wuya kamar raƙumin jeji zaka wuce". Cak ya tsaya, ya waiwayo ya kalli bakin mai wannan maganar, gabanta ne ya faɗi da suka yi ido huɗu da shi, sai yanzu ta tuna da uwar ba'ar da tayi masa, ga kammaninsa sak da Alhaji Ahmad sun bayyana, ba in da ya bar mahaifinsa a kamanni, sai dai yafi Alhaji Ahmad ƙuruciya ko ba a gaya mata ba ta san wannan shi ne wanda aka ce zai dawi. Amina ta hau kame-kame "Yi haƙuri dan Allah, na manta Hajiya ta ce zaka dawo, kuma kaga kaine ma da ka shigo ba ka yi ko sallama ba, amma dai Hajiyar bata nan ta fita, ina wuni". Ƙare mata kallo ya yi a ransa ya ce "Ko wacece wannan, a ina aka samota kuma oho?" Bai kula ta ba ya cigaba da tafiyarsa. Yana wucewa Amina ta ce "Subhanallaahi, na yi shirme wannan shegen bakin nawa, Allah ya sa kar ya gayawa babarsa na masa rashin kunya. Amma ai ba rashin kunya ba ce gaskiya ce ka shigo zalau-zalau babu sallama". Amina na nan zaune ta taradaddin abin da ta aikata, Hajara ta fito falon, sai dai Amina ba ta gaya mata me tayi ba. "Amina ya na ganki wani iri ne haka?" Amina ta girgiza kai ta ce "Ba komai". "To shikenan, mai yakamata a dafa ne yau da daddare?" Amina ta ce "Nima ban sani ba, a dafa abin da ya sawwaƙa" "Wai naga gaba ɗaya yanayinki ya canza". "Ba komai fa, kawai ina tunanin Baba ne". "Ke Amina, baban da ɗazu ya tafi kuma zai dawo". "Ai ba yau zai dawo ba, wataƙila sai gobe ko in Allah ya kaimu jibi" suna tsaka da hirar sai ga Khalil ya fito, nan da nan Amina ta yi shiru. Hajara ta risuna ta ce "Ina wuni Yallaɓai, ashe ka dawo?". "Eh na dawo, Fadila ba ta dawo daga school bane?". "Eh har yanzu ba ta dawo ba". Khalil ya ce "Well Shikenan". Hajara ta sake risunawa ta ce "A kawo maka Abinci ne?" "Eh ajiye mini a kan dining, zan shigo in ci". Amina dai ba tace komai ba, sai zazzare ido da take yi. Bayan fitarsa Hajara ta ce "Shi ne fa wanda zai kai ki makaranta, da ki ke ta jira ya dawo, ya dawo amma ba ki iya gaishe shi ba". "Na gaishe shi mana, ai ina zaune a nan falon ya zo ya wuce". Hajara ta ce "Au to, ai na zaci baki kula shi bane, shi gaskiya ba shi da matsala sosai, be fiye wulaƙanci kamar ƙanwarsa ba". Ita dai Amina fatan ta, Allah ya sa kar abin da tayi masa ya sanya ya ce ba ze kaita makaranta ba. Fitarsa babu daɗewa ya dawo, ya zaune a kan dininga ya zuba Abinci ya fara ci. Amina sai satar kallonsa take, ko zai yi magana amma bece komai ba. Tana cikin wannan zullumin Fadila ta faɗo falon babu ko sallama, ranta a haɗe da alama ta gaji matuƙa. Sai dai tana ƙarasa shigowa falon, tayi tozali da Khalil ta saki murmushi. Ya kalli Fadila shima ya yi mata murmushin ya ce "'yan Jami'a" dire jakarta ta yi ta nufi dining ɗin tana cigaba da murmusawa cike da gajiya, ta janyo kujerar kusa da Khalil ta zauna tare da furta "Welcome home dear". "Ai ke zan yiwa welcome, ya school ɗin?". Ta taɓe baki ta ce "School gamu, muna ta shan wahala". Ya tsiyayo lemo mai sanyi ya kai bakinta, ta buɗe bakin tana sha tana lumshe ido, Amina zuba musu ido ta yi a ganinta wannan ai fitsara ce, su a ƙauye ai ko kusa da yayyanka namiji baka zama, balle a kai ga bada abu a baki. Khalil kuwa hirarsu suka cigaba da yi cike da kewar juna. Allah ya rufawa Amina Asiri ganin Khalil ya sanya Fadila ta laifin da Amina tayi mata da safe. Fadilan ta shiga bawa Khalil labarin abin mamakin da taji game da Yazeed cewa take "Brother bai fa iya turanci ba, ka ji kwaɓar da yake yi idan zai turanci, amma baka ji larabci ba, ni fa har yanzu mamaki nake, anya kuwa shi yake yi?". "Dama waye ya gaya miki sai ka iya turanci shi ne ka ke da ilimi?". "Ai ni na gama raina gayen ne gaba ɗaya, kai ka ganshi, kaga dressing ɗin da yake idan zai zo school? Wannan aka bashi taimako karɓa zai yi" Khalil ya ce "Ke kika ga haka, irin wannan basu da duniya ba balle abin da yake cikinta". Ta ɗan taɓe baki, tare da janyo plate ɗin gaban Khalil, ta sanya cokali ta fara ci. Labarin batun Amina tana wurin Baba a birni, za ta yi karatun boko kuwa ya cika gari, wasu suka dinga Allah wadai da tirr da abin da Baban ya aikata shi da Amina a ganinsu wannan tsantsar rashin hankali ne, da rashin sanin ya kamata. Ko da labari ya iske Jarmai, a ƙulu iya ƙuluwa, yayin da iyalansa suka dinga Allah ya ƙara. Gidansu Amina ya tafi, zuciyarsa cunkushe da takaici, na yadda ya ga samu sannan ya ga rashi. Ya sa aka yi masa sallama da Baba Hassan. Babu wani jinkiri kuma Baba Hassan ya fita, ya ƙarasa in da Jarmai ke tsaye tare da yi masa sallama ya miƙa masa hannu su gaisa, Amma Jarmai ya ce "ka ga ni ba wannan ne ya kawo ni wurinka ba, illa in zo in tabattar maka da na samu labarin abin a ya faru, ka haɗa kai da 'yar ka ta gudu, bayan nan an karɓe ni kuɗin Aurena, to tun wuri kaje ka samu 'yan uwanka, ku haɗu ku dawo mini da kuɗina, kafin in ɗauki matakin da ya dace a kan ku". Baba ya girgiza kai ya ce "To ai kaga ni ba ni na karɓi kuɗin Auren nan ba, bani da masaniya akan komai sai yanzu, dan haka bani zaka tambaya ba". "Oho dai, ni dai a biyani kuɗina kawai, aikin kawai mutanen banza" Baba dai bin Rabe kawai ya yi da ido, yana mamakin ƙarfin hali da rashin ta ido irin na Jarmai. Da Hajiya Zainab ta dawo, kusan raba dare suka yi da 'ya'yanta a falo suna hira, kowa yana kawo hirar abin da ya dame shi, suka ci Abincin dare tare, suka yi ta hira sai bayan sha biyun dare, sannan suka watse. Har washegari shiru, Amina ba ta ji Khalil ya yi Magana ba, hakan ya sa ta fara sarewa, wata zuciyar ta ce 'kije ki masa magana' wata kuma ta ce "Ki ƙara ba shi lokaci, kar ki yi garaje' gaba ɗaya ta bi ta ƙosa, gashi idan suka haɗu ko gaishe shi ta yi, sai dai ya kalleta ya ɗauke kansa, amma ba zai amsa ba. Ko aiki ne sai dai ya kira Hajara ya sata, amma ba zai kula Amina ba. Amina ba ta da zaɓin da ya wuce ta cigaba da Addu'a, dan haka ta duƙufa da sallar dare tana fatan Allah kar ya kawo abin da zai mata katanga da samun ilimin ta. Idan taga Fadila ta shirya zuwa Makaranta, abin ba ƙaramin burge Amina yake ba, tana da burin zuwa Jami'a amma ba ta da tabbacin Baba zai iya ɗaukar nauyinta zuwa Jami'a, shiyasa take taƙaita burinta a iya Sakandire kawai. Yadin jikinsa kawai ta hango ta san shi ne, saboda zuwa yanzu zata iya ƙirga adadin kayan da yake sawa idan zai zo, dama takalmansa guda biyu ne kacal yake zuwa da su. Sai da taje daidai in da yake, sannan ta tada wata irin ƙura, ta bule shi da ƙura ta yi gaba abinta. Duk wanda suka ga abin da ya faru ba su ji daɗi ba, su kai ta bashi haƙuri, ya nuna musu bakomai ya cigaba da tafiya zuwa ajinsu. Yau a bencin bayan Fadila ya zauna, yayin da ita kuma take jikin window. A nata gudanar da lectures kamar kullum. Tari ne ya sarƙe Yazeed, ya saka hankici ya toshe bakinsa, ya kifa kansa yana ta fama, yana tarin ƙasa ƙasa, ya ɗago idanunsa sun yi jawur. A lokacin lecturer ya fita amsa waya, dan haka Yazeed ya fara kira sunan Fadila a hankali, ta waiwayo tana yamutsa fuska ta ce "Meye?". "Dan Allah ki taimaka mini, jikin window nake so ki bani, ki dawo wurina dan Allah ba dan ni ba, bana son zafi, bana iya numfashi sosai". Wata uwar harara ta yi masa ta ce "Au Allah, Sannu ajebo ai ni banga alamar hakan a tare da kai ba, ai da sai ka dinga dakon A.C ko fanka daga gida kana dasawa a wurin zamanka, ba in da zan tashi in je" ta juya ta cigaba da rubuce rubucen ta, shi kuma lecturer ya ɗora da bayani. "Dan Allah Fadila" ya faɗa yana jan numfashi. "Excuse me sir, kaga Wannan mutumin ya takura mini, sai kiran sunana yake ya hanani jin abin da ake yi". Lecturer ya ce "Malam meye haka? Kalleka da gemu a haka kamar na Allah, tashi daga wurin nan ka koma baya, seat ɗin ƙarshe na last row" Jimm Yazeed ya yi, sannan ya tashi tsaye a hankali ya nufi in da malamin ya yi masa umarni. Babson da ke kusa da Captain ya ce 'Shima gayen nan kamar wani maye, duk in da yarinyar nan take yana nan, tai ta sawa ana dizga shi, ni gani nake kamar sonta yake yi". Captain ya ce "Wallahi ƙila ƙarya take masa, ka san yarinyar 'yar wulaƙanci ce, ta gama raina shi, ni dama ƙanwata yake so, matar da ta auri wannan ta huta, mutum sai haƙuri kamar me". "Aikuwa in dai wannan shegiyar ce ba zata taɓa son sa ba, idan ta auri irinsa cutarsa zata yi, wai ita 'yar mai kuɗi wata banza da ita". Captain ya yi dariya Ya ce "Kai dai kawai ba kwa shiri ne". Tun yana iya ƙunshe tarin da yake, har ya kasa ya miƙe da sauri, saboda ya ɗau excuse ya hanzarta barin ajin, amma kan ya kai ga haka, ya silale ya faɗi a wurin. Nan 'yan ajin suka waiwaya dan ganin meke faruwa, sai dai Yazeed ko motsi ba ya yi, lecturer ya sa a ɗauke shi a fita da shi, ya samu wadattaciyar iska, dan da alama He is asmatic. Ita kuwa Fadila ko waiwayawa ba ta yi ba, balle ta san waye ya faɗin. Mintuna sha biyar, malamin ya ƙarƙare lectures ɗinsa, Fadila ta zari jakarta ta yi waje, dan gidansu Yusra zata je, saboda yau Yusra ba zata shiga school ba. Har ta gota in da ta ga 'yan ajinsu suka yi cincirindo, kawai sai ta ji tana son sanin waye ya samu asmatic attack ɗin. Ta koma da baya ta leƙa Yazeed ta gani a kwance, babu alamar yana numfashi, idanunsa a rufe! AYI TA HAƘURI DA NI RASHIN POSTING A KAN LOKACI, KU SANYA NI A ADDUOINKU, ALLAH YA BANI INGANTACCIYAR LAFIYA. TO GET THE LATEST UPDATE OF THE BOOK, FOLLOW ME ON WATPAD AYSHERCOOL7724 AREWABOOKS AYSHERCOOL7724 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) P10 Zaro idanu Fadila ta yi, ganin Yazeed tamkar ya mutu, a mimmiƙe a wurin, jikinta ne ya yi wani irin sanyi, ta tuna yadda ta ji muryarsa yana roƙonta, ta bashi wurin zamanta saboda ba ya son zafi. Cikin rawar baki Fadila ta ce "Class rep ba za a kai shi Clinic a duba shi ba?". "Eh, A motar Hamisu muke so a kai shi, kuma motar tayi faci, sun je a gyara a zo tafi da shi". Cikin rawar murya ta ce "Kaga ku ɗauko shi da sauri, muje a kai shi a tawa motar". Babu wanda ya taɓa zaton Fadila zata iya abin Arziƙi haka, ganin yadda ta uzzurawa Rayuwar Yazeed. Cikin hanzari ta yi gaba, ta je ta buɗe motar, aka ɗauko Yazeed aka sa shi a motar Fadila, amma ta haɗe rai ta ce Mutum biyu ne kawai za su shiga, dan ba zata kwashi ƙartin banza a motar ta ba su hautsina mata ciki da warin hammata ba. Aikuwa Fadila ta sha zagi a wurin samarin ajin nan, ba ta bi ta kan su ba, ta take motar da ƙarfi ta bula musu ƙura, ta bar harabar wurin da gudun tsiya. Suna tafe lokaci lokaci, numfashin Yazeed yana dawowa, sai dai baya wuce ƙirjinsa, ga wani irin sound da fitar numfasin nasa ke fitarwa kamar numfashin zai rabu da gangar jikinsa. Gaba ɗaya hankalin Fadila a tashe yake, tana ji a ranta idan Yazeed ya rasa ransa, to tana da kamasho a cikin faruwar hakan. "Fadila ya naga kin fita daga cikin School, ba Clinic ɗin School za a kai shi ba?" Cewar Captain da ke rungume da kan Yazeed. "Gara a kai shi wani Asibitin, i don't want too much wahala, akwai asibitin da muke da retainership file, a nan muke ganin likita, bari muje can kawai". Shi Captain ma abin na Fadila mamaki yake bashi, ganin yadda duk ta ruɗe. Suna zuwa aka karɓi Yazeed, cikin kulawa aka shiga da shi Emergency room, Nurse ta kawo family file ɗin su Fadila. Doctor Aliyu ya kalli Fadila ya ce "Fadila wannan kuma a ina kika samo shi?". "Doctor he is my class mate, ya samu asmatic attack ne, shine nace mu kawo shi nan". Doctor Aliyu ya gyara zaman glashinsa ya ce "Dama can yana da Asma ne?". Fadila ta ce "I don't know fa, i have no idea kawai a duba shi ni dai kar ya mutu, amma ga abokansa nan a tambaye su". Captain ya ce "Ni dai ban sani ba, kin san ba shiga mutane yake ba, balle ayi hira ya faɗi yana da wani ciwo, ko kai Aminu ka taɓa jin ya faɗa?" Ya yi maganar yana kallon wanda suka kawo Yazeed tare. Aminu ya ce "kai baka sani ba balle ni, ni da banda gaisawa babu abin da yake haɗamu". Doctor Aliyu ya ce "Baku taɓa ganin yana shan wani magani ba?". Captain ya ce "Doctor, bawan Allah nan fa ba magana yake ba, ba ya kula kowa ba ya son hayaniya, kaga ƙawarsa nan Fadila ita yake kulawa ita kuma ba ta saurararsa, wataƙila da tana saurararsa, da ita ya gaya mata". Fadila ta haɗe rai ta harari Captain ta ce "Zan maka rashin mutunci ka kuma haɗani da shi, a ina na zama ƙawarsa? Yanzun ma akwai dalilin da ya sa na tsaya a kan a kawo shi Asibiti". Doctor Aliyu yayi murmushi tare da girgiza kai, kasancewar sa family doctor ɗin su, kuma nan Asibitin suke zuwa idan ba su da lafiya ya sanya ya san Fadila da halayenta. Gaba ya yi suka bishi a baya. Suna shiga Emergency, suka tarar da Yazeed kwance an sa masa Nebulizer, yana mimmiƙe a kan gado. Gaban Fadila ya kuma faɗuwa ganin halin da Yazeed ke ciki, ta tuna yadda ta baɗe shi da ƙura da hayaƙin mota, wataƙila ma hakan ne ya sa ciwon ya tashi. Doctor Aliyu ya cewa Aminu, ya zo ya taya shi a caje Yazeed, ko akwai magani a jikinsa, dan galibi masu irin wannan matsalar suna yawo da magani a jikinsu. Suka caje jikin Yazeed, jotter shi ce kawai a jikinsa da biro, sai carbi da Naira hamsin, suka ajiye a drower kusa da shi. Doctor Aliyu ya ce "Na so inga irin maganin da yake sha, amma bakomai bari mu gani zuwa anjima ko zai farfaɗo, na rubuta allurai a yi masa". Fadila ta ce "Amma Aliyu, kana ganin zai warke gani nake kamar mutuwa zai yi fa" tayi maganar ƙwalla na ciko idanunta. Aliyu ya ce "Ikon Allah, dama akwai abin da zai raunata miki zuciya haka Madam? Zai warke insha Allah, your besty will recover insha Allah, amma ki dinga kula da shi sosai, kin san ciwon nasu baya son wannan weather, banda yawo ba mask, ko zuwa wurin hayaƙi ko ƙura". "Dan Allah ka daina haɗani da shi, wai wani besty" Yayi murmushi ya ce "To na daina" Aminu ya yi musu sallama ya tafi gida, Captain ma yace zai je school ya dawo, suka bar Yazeed da Fadila kawai a Asibitin. Fadila sai kaiwa take tana komowa a reception ta kasa zama wuri ɗaya, tana yi tana leƙawa ɗakin da Yazeed yake, kasa jurewa ta yi, ta shiga ɗakin da Ya ke kwance. Ta taka a hankali, ta ƙarasa gaban gadon da yake kwance, ta kalli abubuwan da aka ciro a aljihunsa, ta ɗauki jottersa da carbinsa ta saka a jakarta, saboda kar idan ya tashi, zasu tafi a manta da su. Gani ta yi yana motsawa a hankali, ta ƙura masa idanu, tubarkallah idan ta ce Yazeed yana da muni tayi ƙarya. Gani ta yi yana rirriƙe katifar gadon da yake, yana ɗaga ƙirjinsa sama, sai kuma ya saki katifar, yana miƙe mata hannu, amma idanunsa a rufe. Ƙara matsawa ta yi jikin gadon, tana masa sannu, sai dai bai san me take yi ba, hasali ma bai san meye yake yi ba. Sai miƙa hannu yake yana riƙo duk abinda ya ji a kusa da shi, cikin sa'a ya riƙo hannun Fadila, hannunsa kamar ba na namiji ba, saboda taushi, sai ta zama kamar wata sokuwa ta rasa abin yi, a hankali yake murza yatsunta, yana jujjuya kansa, hawaye na zuba a gefen idanunsa, ga wani irin gumi da yake tsatstsafowa a goshinsa. Fadila zama ta yi tamkar wata gunki, wani irin abu ne ya fara kai kawo a jikinta, tun daga kanta zuwa ƙafafuwanta, wani baƙon yanahu ya ziyarce ta, tsigar jikinta na tashi, wani irin yanayi na ratsata, saboda a rayuwarta idan ba Khalil ko Daddy ba, babu wani namiji da taɓa samun wannan kusancin da shi haka, har hannunta a cikin nasa, sai doctor Aliyu, idan ba ta da lafiya zai mata allura ko sa ruwa, shi ma faɗa suke yi da shi, ta ce "Ba zai taɓa ta ba". Ƙoƙarin zame hannunta take daga na Yazeed, cikin jin zafin ciwo ya matse mata yatsu da ƙarfi, wanda har sai da ƙasusuwan yatsunta suka yi ƙara. "Washhh Allah, kai dalla ka sakar mini hannuna sai ka karya ni tukuna?" Ta faɗa a shagwaɓe. Ƙoƙarin miƙewa zaune Yazeed ya fara yi, ya kai hannu zai cire abin Nebulizer, ta riƙe hannunsa ta ce "Ka bari magani fa aka samaka" ta faɗa raunane. Bai saurareta ba ya cigaba da ƙoƙarin cirewa, da sauri ta fita ta kirawo doctor Aliyu, har Yazeed ya cire Nebulizer ya kifa ya kusa faɗowa daga kan gadon. Da hanzari Aliyu, ya gyara masa kwanciyar ya mayar masa da Nebulizer, ya je ya ɗauko wata allura ya yiwa Yazeed. A hankali bacci ya kwashe shi. Aliyu ya ce "Gaskiya ciwon nan nasa ya zama chronic, ki kirawo masa wani daga gidansu mana, a san halin da yake ciki". "Ni ina na san wani nasa, ɗan ajinmu ne fa kawai". "I see, amma kin damu da shi da yawa". "Ni ban damu da shi ba, kawai dai na san koma menene ya sameshi nice sila, idan ya mutu zan iya cewa ina da hannu a ciki shiyasa na damu". "Shikenan, ki zauna tare da shi, duk abin da kika gani ki mini magana". Fadila ta ce "to" Ta koma ta samu kujera, ta zauna a kusa da gadon nasa, ta ɗauko wayarta ta hau chatting da Yusra, a nan take bawa Yusra haƙuri, saboda rashin zuwanta gidansu, kuma ta bata labarin abin da ya faru. Amina na ɗakinta, sun kammala aiki tayi wanka, ta shirya tana ƙara gyara nata ɗakin, Hajara ta yi sallama. Amina ta amsa tare da kallon Hajara. "Ki je in ji Khalil". Amina ta ce "Waye kuma Khalil?". "Wanda zai kai ki makaranta" Ta buɗe baki ta ce "Haba da gaske?". Hajara ta ce "Zan miki ƙarya ne?" Kan Hajara ta gama rufe baki, Amina ta yi waje, ta nufi falo. Ta tarar da Khalil ya kammala breakfast, Hajiya Zainab na zaune a kusa da shi tana masa hira. Amina ta ƙarasa ta durƙusa a gabansa ta ce "Gani". Bai kalleta ba ya ce "In the next 30minutes, ki shirya zamu je a kai ki makaranta" Washe haƙora Amina ta yi cikin murna ta ce "Tom, Na gode Allah ya saka da alkhairi, ai ni na shirya ma, bari in je in jiraka". Hajiya Zainab ta kalli Khalil ta ce "Ban gane ba, kai ne zaka kaita makaranta?, ka bari babanta ya dawo ya kai ta mana". Khalil ya ce "No, kin san bakomai zai iya yi mata ba, Daddy ne ya bada umarnin hakan". Tsaki ta yi ta ce "Ni bana son irin haka, a ɗorawa mutum wahalar da ba ta sa ba, ba damar ka janyo mutum ɗaya, sun dinga ɗora maka ɗawainiya da wahalarsu kenan". Amina da ba ta kai ga barin falon ba, tana jin hajiya Zainab, amma tayi shiru ta wuce ɗakinta, ba tare da ta yi magana ba. Tana zuwa ɗaki, ta canza hijjabi, ta ɗauko littafi ɗaya a litattafanta da ta taho da su daga ƙauye, da bironta ta samo leda ta zuba su a ciki, ta ɗaure murmushin kan fuskarta ya kasa gushewa. Hajara sai kallon Amina ta ke "Amina sai kace wadda aka yiwa bushara da zuwa makka, wannan fara'a haka". Murmushi Amina ta yi ta ce "ni dai na tafi, sai na dawo" tayi waje a guje cike da farinciki. Wuri ta samu a nan harabar gidan ta zauna, tana jiran Khalil, ba ta wani daɗe ba saiga shi ya fito da waya a kunnensa yana waya, bai kula Amina ba ya nufi hanyar gate zai fita, ba ta da zaɓi illa ta tashi ta bi bayansa. Abdul ne zaune a cikin motarsa, ya ƙurawa gate ɗin ido. Khalil ya ƙarasa ya buɗe gaban motar, ya shiga. Amina kuwa tsaye ta yi, tana zazzare ido, Abdul ya miƙa hannu, ya buɗe mata motar, ta shiga ta zauna sannan ta risunar da kanta ta ce wa Abdul "Ina kwana?". "Lafiya ƙalau, ya kike ya gida?". "Ina lafiya ƙalau Alhamdilillah". "To Masha Allah, sannunki" ya mayar da dubansa kan Khalil da ke danna wayarsa ya ce "Malam ba gaisuwa ne?" Hararsa Khalil ya yi ya ce "Dan Allah ja mu tafi, anƙi a gaishe kan". Abdul ya ce "Haka ka iya, sarkin faɗa" A hankali Abdul ya ja motar suka fara tafiya, cikin motar ga sanyin AC, ga ƙamshin turaren jikinsu, ga ƙamshin droomer, duk ya cika motar, yanayin ya yiwa Amina daɗi sosai, sai kallon gari take ta jikin baƙin glass ɗin motar. Gaba ɗaya tsarin zubin ginin makarantar ya sha banban da irin zubin makarantunsu na ƙauye, ginin kawai ba ƙarmin burge Amina ya yi ba. A wurin parking Abdul ya tsayar da motar, Amina na ƙoƙarin buɗe motar, Abdul ya ce "Ki zauna muje mu fito tukuna, ni ya sunanki ne ma?". "Amina Hassan" Ya ce "Masha Allah, nice name, ki zauna muje mu dawo". Amina ta amsa da to. Abdul da Khalil, suka nufi dogon ginin da ke cikin harabar makarantar. Tana nan zaune a mota, kusan mintuna sha biyar, sai ga Abdul ya dawo, ya buɗe wa Amina motar ya ce "Bismillah zo muje" Amina ta fito daga motar, cike da farinciki tana sake ƙarewa makarantar kallo. Cikin ofishin shugaban makarantar suka shiga, suka tarar da shi a zaune tare da wasu malamai biyu, sai kuma Khalil. Har ƙasa Amina ta zube tana gaishe su. Director yayi murmushi ya amsa mata, tare da yi mata umarnin ta zauna. Ta samu wuri ta zauna, tana cigaba da ƙarewa ofishin kallo, a ranta ta ce "Allah sarki principal ɗinmu, insha Allah sai na gina masa Office irin wannan, mai irin wannan kujerun, shima a dinga sa masa turaruka masu ƙamshi". Muryar director, ta ji yana tambayarta sunanta da harshen turanci, ta ɗago tare da amsa masa, ya tambayeta sunan makarantarsu, ajinta nawa? Shekarunta nawa? Gaba ɗaya cikin harshen turanci, kuma ita ma cikin harshen turanci take mayar masa. Gaba ɗaya Khalil bai zaci ko Makaranta ta taɓa zuwa ba, dan a haka ya yiwa director bayani. Nan malaman nan suka fara yiwa Amina interview, sai dai duk ta basu mamaki, saboda kaifin basirarta, gashi duk abin nan cikin harshen turanci suke yi, kuma ko tangarɗa babu a bayanan nata da turanci. Aka yi mata tambayoyi a fannin lissafi, gaba ɗaya tayi soliving ba tare da amfani da calculator da aka bata ba. Director ya ce "Kai Khalil kace gifted ku ka kawo mana? Alhamdilillah na yi farinciki sosai da sosai, yanzu zamu bata aji, ƙarfe biyu muke tashi daga makaranta, na ji daɗi sosai na yaba da ƙwazanta, insha Allah zamu yi ƙoƙarin bata ilimi yadda ya dace, yanzu za'a kaita aji insha Allah". Amina ta ce "Ai bani da litattafai, littafi ɗaya na ɗauko". Director ya ce "Kar ki damu, duk kayan rubutu mu zamu baki, har da jakar Makaranta ma" Amina ta sake faɗaɗa fara'arta ta risuna ta ce "Na gode, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata". Suka amsa da Ameen, babban abin da ya ƙara burge su da Amina, shi ne yadda take da tarbiyya da ladabi sosai. Suka fito daga Office ɗin tare da director, da su Khalil. Abdul ya kalli Amina ya ce "Idan an tashi daga Makaranta, kar ki je ko ina, ki tsaya a wurin da muka ajiye mota yanzu, zamu dawo mu ɗauke ki, saboda kinga baki san hanya ba". "To yaya Na gode, Allah ya biya muku buƙatunku na Alkhairi, ya sa ku gama da duniya lafiya, Allah ya shiga lamarin ku, ya saku farinciki kamar yadda ku ka sani" ta ƙarasa maganar har da hawaye a idonta, dan ba zata iya misalta farincikin da take ciki ba. Abdul ya yi murmushi ya amsa da "Ameen, ki dage kiyi karatu da kyau Allah ya bada sa'a, ga wannan in an fito break ki sayi wani abun" yayi Maganar yana bata ɗari biyar. Girgiza masa kai ta yi ta ce "A'a na gode zan iya zama har a tashi ban ci komai ba, a ƙoshe nake" tayi gaba tana ɗaga musu hannu. Wani irin murmushi ne ya suɓucewa Abdul, yarinyar ta burge shi, duk da ɗan karen surutunta, amma acting ɗinta zai tabattar maka da ga gidan tarbiyya take. Tsakin Khalil ne ya dawo da shi daga tunanin da yake, ya bi bayansa zuwa mota, suna tafe Abdul na yiwa Khalil hirar Amina da yadda ta burge shi. Banza Khalil ya yi masa, dan tun haɗuwar sa farko yarinyar ta yi masa tsiwa yake jin haushinta, ga ta da shegen surutu da iyayi kamar jefaffiya. An samu numfashin Yazeed ya daidaita, sai bacci da yake yi, saboda allurar da aka yi masa, har azahar Fadila ta je ta yi salla ta dawo bai farka ba, tana nan zaune taga ya fara motsawa a hankali, ta zuba masa dukkanin idanunta, dan babban fatanta dama shi ne taga ya tashi ya warware. Captain ya kira Fadila a waya cewar 'yan ajinsu zasu zo duba Yazeed, amma tace ya ware an sallame shi, saboda bata son ƙananan maganganu. A hankali ya buɗe idanunsa, yana ƙarewa ɗakin kallo, ya kalli hannunsa dake ɗauke da canular anyi hanging ɗin drip. A hankali ya juya ɗaya ɓangaren, ya yi tozali da fuskar Fadila, sai da gabansa ya faɗi, ƙoƙari yake ya gane, zahiri ne ko mafarki. "Sannu" ta furta kamar an mata dole. Ya jinjina mata kai alamar yauwa. "Ina ne nan?" Ya yi maganar yana kallonta. "Da ina ya yi maka kama?" "Yi haƙuri gani na yi ban san environment ɗin ba, dan Allah zan sha ruwa" ya ƙarasa maganar da sigar magiya, tare da tashi zaune ya jingina. Kamar ya yi mata dole, ta tashi ta buɗe ɗan ƙaramin fridge ɗin ɗakin, ta ɗauko ruwan roba mai sanyi ta miƙa masa. Ruwan sanyi ƙarara dan haka ya karɓa ya ajiye a gefe. "Ba zaka sha ba ka sa na ɗauko?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido. "Yayi mini sanyi da yawa" Doctor Aliyu ne ya shigo ɗakin, ya tarar da Yazeed a zaune "Masha Allah, Alhamdilillah ka farfaɗo kenan?" Ganin farar riga a jikin Aliyu ya sanya Yazeed gane cewa likita ne. "Eh doctor". "To yaya kake jin jikin yanzu?" "Alhamdilillah, bana jin ciwon komai, sai rashin ƙwarin jiki". "Ok, shima insha Allah zai ware, for how long kake da Asma?" Yazeed ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Gaskiya an jima, da farko pnuemonina ne, sai ya koma asma, to daga baya ya zama chronic, a hankali kuma da na ƙara girma, sai na rage samun attack ɗin, dan har ina aiki a cikin hayaƙi, ƙura idan ba tayi yawa ba ba ta damuna, rabona da ciwon ya tashi nafi shekara huɗu, sai yau na sheƙi hayaƙi da ƙura, na fara tari kuma daga nan ban san abinda ya sake faruwa ba" Haka kurum Yazeed ya bawa Fadila tausayi, ya sha wahala sosai daga ɗazu zuwa yanzu. Nan Aliyu yayi ta bawa Yazeed shawarwari tare da rubuta masa wasu magungunan, ya ce a sayo masa wani abun ya ci. Fadila ta fita ta bawa security Asibitin kuɗi, dan ya siyo wa Yazeed Abinci. Mamaki ne fal da tambayoyi a cikin ran Yazeed, amma ya san idan ya tambaya ba zai samu gamshashiyar amsa ba, sai ma dai baƙar Magana. Sallamar Yusra ce ta katse masa tunaninsa, Fadila na ganin Yusra ta miƙe tana faɗin "Beb sai da ki ka zo?" "Na kasa jurewa ne, na ce gara in zo in ga mai jikin, kuma naga Alhamdilillah shi ne a zaune ko?" Fadila ta ɗan taɓe baki ta ce "Sannu bawan Allah" Yazeed ya ce "Yauwa sannu da zuwa" "Allah ya sa kaffara ne" Ya amsa da Ameen. Security ne ya shigo da ledar wani restuarant, ya miƙawa Fadila ta sa hannu ta karɓa ta ciro dubu ɗaya ta bashi, ta fito da takeaway ɗin, ta buɗe dankali da miyar jajjage sai uban yankan naman kaji a kai, ta ajiye wa Yazeed ta ce "Gashi nan kaci, Aliyu ya rubuta maka sallama, in ka gama sai in ajiyeka a gida in wuce gida". Yazeed ya ƙurawa Abincin ido, amma yaƙi ko motsawa balle ta sa ran zai ci. "Magana fa nake maka kai mini banza" "Alhamdilillah na ƙoshi" ya furta yana kaucewa haɗa ido da ita. "Ban gane ka ƙoshi ba, amma a gabanka ya ce a samo maka Abinci ko?" Yusra ta ce "Kai kuwa ka daure ka ci mana, ko baka cin irin wannan?". Yazeed ya ce "Wannan ba cimata bace ta ɗan talaka, ba zan iya cin Abincin nan ba, Na gode sosai da kulawarki a gareni Fadila, ba zan manta ba har abada, amma wannan cimar ku ce ba irin tawa ba, zan ƙarasa gida na samu abin da zan ci a can" Tsaki Fadila ta yi ta miƙe tsaye, ta kalli Yazeed cike da masifa "Ni zaka rainawa hankali ka gayawa baƙar magana, in wuni a Asibitin nan saboda kai, na san silata ciwonka ya tashi amma ka raina mini hankali, tun safe nake Asibitin nan saboda kai, ko ruwa ban kai cikina saboda zullumi, amma daga tashin ka ka fara ɓata mini rai" ta cillo masa ledar magungunan da aka kawo daga Pharmacy ta ce "Gashi nan, idan ka ga dama ka ɗauka shima idan ba ka ga dama ba ka barshi a wurin aikin banza kawai" Yusra ta riƙota tana faɗin 'Haba Fadila ba a haka, ai sai ki zobe ladan ki, baki ga ba shi da lafiya ba, ki dinga haƙuri dan Allah" "Dalla sakar mini hannuna, ba za ai haƙurin ba" ta figi jakarta tayi waje fuuu. Yazeed kam murmushin gefen baki yayi, ya sauko daga kan gadon a hankali, Yusra tayi ta bashi haƙuri ya ce "Bakomai kar ki damu" sun kai ruwa rana da Yusra kafin ya yarda ya karɓi maganin, shima mutuncin yarinyar ya gani ya karɓa. Ya shafa aljihunsa ya ji babu komai, dan haka ya sadaƙar jotter sa, da hamsin ɗin jikinsa sun zube, a halin da yake ciki ya fara daɓawa da ƙafafuwan sa dan tafiya gida, ya samu masallaci ya rama sallolin da bai yi ba, daga nan ya wuce gida. Ƙarfe biyu Abdul ya addabawa Khalil a kan su koma su ɗauko Amina, ko da suka koma tana in da Abdul ya ce ta tsaya, goye da ƙatuwar jakarta ta makaranta. Tana ganin motarsu ta faɗaɗa fara'arta, ta ƙarasa ta buɗe motar ta shiga, wannan karon Khalil ne yake tuƙi dan a motarsa suka zo, ta gaishe su Abdul ya amsa, amma Khalil ya yi mata banza. "Amina 'yan makaranta, ya makarantar ya baƙunta?". "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, bari in nuna maka litattafaina an cika mini jakata da litatafai, gobe in Allah ya kaimu za a bani Uniform, Baba ya sai mini takalmi da safa" Ta zuge jakar tana nuna masa, yace "Masha Allah, Allah ya sa a amfana, bari da yamma zanje da kaina in sayo miki takalmin". Amina ta girgiza kai ta ce "A'a Baba fa zai saya mini, kar ka damu, sai daɗi nake ji na koma Makaranta". Abdul ya ce "Sai kice Alhamdilillah, wai ni kuwa ya aka yi kika iya turanci haka?". "Malaman mu ne suke koya mini, a makarantar mu ana zuwa da ni debate ko quiz, su suke koya mini, kaga kuma muna da ƙaton Library, amma babu ɗalibai sosai 'yan garinmu ba su damu da karatun ba, akwai litattafai sosai a ciki, kuma ina da dictionary da nake duba Words, mu uku ni da wasu ƙawayena ake mana extra lessons a ƙauyenmu" Abdul ya jinjina kai ya ce "Lallai ashe gifted ce?" "A'a ni ba gifted ba ce, dagiya nake yi in gaya maka" "To ya aka yi ki ke son cigaba da karatu a nan? Ko can babu senior secondary School". Yamutsa fuska ta yi, ta tura baki sannan ta ce "Ƙannen Baba ne za su yu mini Aure, wai ba sa son ina zuwa boko, ni kuma na gudo wurin Baba" "Da an yi asarar talent, wannan ƙwaƙwalwar ta ki atleast yakamata ko secondary ki kammala ai" Amina ta sake ta dinga bawa Abdul labarin yadda tai karatu a ƙauyensu faɗi ba a tambayeka iri iri. "Ke shut up dalla!" Khalil ya buga mata wata uwar tsawa, da sai da cikinta ya kaɗa. Abdul ya ɓata fuska ya ce "Khalil ya haka?, Ya muna hira da yarinya zaka yi mata tsawa?". "Duk ta bi ta cikawa mutane kunne, ko haɗiyar yawu ba ta yi, i hate nonsense, ta kuma magana Wallahi sai ta sauka". "Khalil waye ya gaya maka irin wannan yaran ana katse musu hanzari? A irin wannan surutun nasu ba sa na banza, kuma ba a kan karatu take Magana ba?" Khalil yai wa Abdul banza ya cigaba da tuƙi. Tun da Amina ta firgita da tsawar da Khalil ya yi nata kasa magana ta yi, sai jikinta da ke ta tsuma. A ƙofar gida suka sauketa, ta yiwa Abdul godiya ta shiga gidan. Khalil ya wuce kai Abdul gida, suna tafe suna faɗa. Abdul ya ce "Kana hantarar 'yar mutane ba abin da tayi maka, ƙila ma ita zaka saka a wannan gidan da kake ta ƙerawa" Khalil ya ce "Kai fa mahaukaci ne wasu lokutan, da Mummy kaɗai ta isheni, kai idan aka ce zan auri wannan yarinyar sai ka yadda?" "Eh mana ba mace ba ce? Meye aibunta 'yar duma duma black beauty" "Yawwa an zo wurin, sai kace mini sonta ka ke yi" Abdul ya ce "Ai ni ka san wadda nake so, kuma alamu sun nuna ba za ka bani ba" Kalil Yayi guntun tsaki ya ce "Kai ka fiye shirme Wallahi" daga haka ya basar da zancen ya kai Abdul gida ya sauke shi yayi gaba. Wata hanya ya biyo, domin ya yi yanke, ya samu sauƙin go slow. A ƙofar wani kanti yayi parking, dan ya sai ruwan roba, na motarsa ya ƙare, ya miƙawa wani yaro kuɗin ya ce ya karɓo masa. Ya gyara zamansa, ya kashingiɗa da seat ɗin motar, ya ɗan waige ya hango wata matashiyar budurwa tana juya awara a cikin mai, tana sanye cikin gogaggen hijjabi ash, sai dai fuskar nan tata a ɗaure tamau, wani matashi na gefenta a kan babur, da alama tsarata yake yi, amma ko sau ɗaya ba ta ɗaga kai ba, balle ta kalle shi!. Follow my Arewabooks Account Ayshercool7724 Watpad Ayshercool7724 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Domin samun update a kan lokaci, ko samun book ɗin daga farko Follow me on Watpad Ayshercool7724 Arewabooks Ayshercool 77724 What's app 08081012143 P11 Zuba mata idanu ya yi, yana kallon yadda take gabatar da sana'ar ta ta cikin nutsuwa, ba hayaniya ko ƙazanta komai nata a nutse, amma mamaki ne ya biyo bayan tunanin da yake yi, me wannan budurwa take haka a titi? Yafi dacewa ace tana gidan Aure, ko kuma tana makaranta, amma kalleta a titi tana suya. Yaron da ya aika ne ya kawo masa ruwan, ya barwa yaron sauran canjin, ya cigaba da kallon in da Hafsa take, sai dai yadda take gudanar da lamarin nata ne, da gani ka san za ta yi izza, saboda sai shan ƙamshi take, tare da haɗe rai dan kar ma wani ya kawo wargi. A hankali Khalil ya yi you tune, ya koma hannun da Hafsat ke zaune tana gudanar da sana'ar ta. Parking ya yi a gefenta, ya fito daga motar, ya ƙaraso in da take suyar awarar ya kalleta ya ce "Sannu dai" ba tare da ta ɗago ba ta amsa masa ƙasa ƙasa da 'Yawwa". Ya miƙo mata dubu biyu ya ce "Zuba mini abin nan na 2k" wani irin kallo Hafsa ta yiwa Khalil, irin kallon ka raina mini hankali ma, ba ta ce masa uffan ba, ta cigaba da sallamar yaran da ke gabanta. Khalil gani ya yi ba ta da niyyar sake ko ɗaga kai ta kalleshi, ya kuma matsawa ya ce "Magana fa nake yi, ki sa mini na 2k" "Ka bari idan ka san sunan abin da nake sayarwa, sai ka dawo in sayar maka" ta bashi amsa. Khalil ya ce "To, ikon Allah am serious ki karɓa ki bani". "Malam nace ka bari ka san sunan abin da nake sayarwar sai ka siya". Yaron da ke tsaye zai sayi awara ya ce wa Khalil, "Sunan abinda take sayarwa Awara". Khalil ya ce "Ok na gode sosai, ki bani awara ta dubu biyu". Ba tare da kalleshi ba ta ce "Ni awarata ba ta kai ta dubu biyu ba, ta ɗari biyar kawai za ka iya samu". "To bani ta ɗari biyar ɗin, sai ki riƙe canjin" Hafsat ta ɗago idanunta ta harari Khalil ta ce "Malam ba fa bara nake ba, sana'a nake yi". "Ai nima bance bara kike ba, kyauta ce kawai na baki, ta ɗari biyar ɗin ki rabawa yara sadaka, sai ki riƙe canjin". Ba ta kuma tankawa Khalil ba, ta cigaba da iza wutarta, ya tsaya ya zuba mata ido, ta gama soya awarar dake cikin mai, ta zuba masa a leda ta miƙa masa . Khalil ya ce "Ai ba ni zaki bawa ba, sadaka zaki bayar". Hafsa ta ce "Ai kai ma kana da hannu, zai fi kyau ace kai ka raba musu da kanka" Nan Khalil ya shiga jinjina halin yarinyar, ana mata abin Arziƙi amma ba ta gani, sai jin kai da tsabar taƙama. Ya sa hannu ya karɓi ledar awarar, ya miƙa mata dubu biyun, ta kalli hannunsa da yake riƙe da dubu biyun, ta ɗauke kanta ta cigaba da sabgar gabanta. "Ikon Allah, yau Allah ya haɗani da gamona, to ga dubu ɗaya tun da ba zaki karɓi dubu biyu ba". Nan ma ɗauke kai ta yi, ta ƙi kallon in da Khalil ya ke. "Idan ba zaki karɓa ba zan tafi da awarar ba tare da na biya ba". "Ka daɗe baka tafi ba" ta furta a hankali. Khalil ya durƙusa ya sa mata dubu ɗayan, a gefenta sannan ya juya ya fara tafiya. Ko ɗago kanta ba tayi ba, balle ta dubeshi, fifita wutar ta kawai take yi. Yayi gaba ya bawa wasu almajirai awarar, ya kuma waiwayawa yana kallon Hafsa, cike da mamakin wannan tsatstsauran ra'ayi nata. Amina kuwa tana shiga gida, ta tarar da Baba ya dawo daga ƙauye, wurinsa ta nufa cikin fara'a, shima ya tareta da murmushi yana faɗin "Alhamdilillah". "Baba an kai ni Makaranta, na zama 'yar Makaranta". "Alhamdilillah, Allah yayi miki Albarka ya cika miki burinki 'ya ta". Amina ta ce "Ameen, ka san wani abu Baba?". "A'a sai kin faɗa uwata". "Baba sufa wannan makarantar a aji biyar ake gamawa, babu aji shida, zuwa baɗi ta gaba insha Allah zan gama sakandare". Baba ya ce "To Alhamdilillah, Allah ya baki miji na gari a birni kiyi Aure, wanda zai kula da cigaban karatunki" Jikin Amina yayi sanyi ta ɗan yi shiru tana nazari. Baba ya ce "Ya kika yi shiru, ko kin fi son ki koma ƙauye ki auri Jarmai?" Da sauri ta ɗago ta kalli Baba ta ce "A'a Baba, nifa ko sunan Mutumin nan bana ƙaunar ji, ni ban tambayeka ya hanya bama, ya ka baro Inno?". "Duk suna lafiya sunce a gaishe ki, Jarmai kuma ya sa su Yaya Bala a gaba a kan lallai su biya shi kayan Auren da ya kai, yazo ya sameni wai nima saina biya shi, ni kuwa nace masa sisinsa ban gani ba balle in ci, dan haka yaje can wurinsu ya karɓa, amma da ina da kuɗi da na rage masa wani abun". Amina ta kalli Baba ta ce "Ka jika Baba, Mutanen da ba tare da kai suka ci kuɗin ba, akan ne za ka biya abinda ba kai ka ci ba, banda asarar da suka yi maka ma. Baba kalli litattafaina fa, wai duk wannan litattfan nawa ne" tayi maganar tana nuna masa cikin jakarta. Baba ya buɗe baki, text books kawai sun kai goma sha shida, banda na rubutu, ga math set, da calculator komai akwai, shi kansa Baba ya san wannan kayan sun fi ƙarfin kuɗin aikin da Amina take yi musu. Baba ya ce "Uwata mutanen nan sun mana karamci, duk na san kina da ƙwazo, amma ki ƙara sannan ki ƙara yi musu godiya, idan mai gidan ya dawo, ki kuma yi masa godiya". "Insha Allahu Baba zan masa, idan na yi salla fa har Addu'a nake masa, Allah ya ƙara masa Arziƙi da lafiya, ba zan manta alkhairinsa ba" "Yauwa uwata, har 'ya'yansa ma da matarsa da ahalinsa duk ki dinga saka su a Addu'a". Amina ta ɗan tura baki ta ce "wannan 'ya'yan nasa da basu da kirki". "A'a fa uwata, yanzu ba Makaranta ɗansa ya kai ki ba? Idan mutum ya miki ba daidai ba, ki bishi da alkhairi albarkacin addu'a da kike musu, sai Allah ya miki abin da ba ki zata ba" "To Baba zan dinga yi musu insha Allah, bari in je in wanka nayi salla, ka ci Abinci kuwa?" "Eh naci, Hajara ta kawo mini, maza kije ki yi salla" Ta amsa da to Baba, ta miƙe ta shiga cikin gidan, cike da fara'a da jin daɗi. Kallo ɗaya Mummy ta yi mata tare da kwaɓe baki, ganin yadda ta goyo uwar jakar Makaranta tana washe baki. Amina tayi mata sannu da gida, amma da ƙyar ta iya amsa mata. Hajara ma tsokanar Amina ta dinga yi, tare da tayata murnar samun cigaba da zuwa makaranta. Fadila ba ta dawo gida daga Asibiti ba, sai bayan biyar na yamma, ta dawo a gajiye matuƙa, kuma rai a ɓace saboda abin da Yazeed ya yi mata, kai tsaye sashenta ta wuce, ba tare da ta nemi ko in da Mummy take ba, dan ba abin da take son yi, banda ta yi wanka tai salla ta ci Abinci. Duk da ranta a ɓace yake, amma abin da ta tarar a part ɗinta, yayi mata daɗi sosai. Tayi wanka tayi salla, ta fito ta nufi kitchen da kanta, a kitchen ta tarar da Hajar da Amina na ƙoƙarin ɗora girkin dare, sai bawa Hajara labarin makarantarsu Amina take yi. "Wacece ta gyara mini ɗaki a cikin ku yau?". Amina ta ce "Nice". "Biyoni" ta yi maganar cikin bada umarni. Bayan Fadila Amina ta bi, tana fargabar kar abin Arziƙi ya zama na tsiya. Da suka ƙarasa ɗakin Fadila, Fadila ta ƙare wa ɗakin kallo sannan ta ce "Naga aikin da ki ka yiwa ɗakin nan, kin canzan labulaye kin wanke waɗancan, kin ɗaga gado da wardrobe kin gyara kin canza musu fasali, na ji daɗin hakan, keep it up Ina son sauye sauyen Abubuwa lokaci zuwa lokaci". Amina ta ce "To insha Allah" Fadila ta ce "ɗan tsaya" ta ƙarasa ta ɗakko wata babbar ledar siyayya ta store, ta sakawa Amina turamen atamfa uku, da dogayen riguna, sai hoda da turare ta ce "Gashi nan kije kya saka" Amina ta karɓa cikin fara'a ta ce "Na gode Ubangiji Allah ya ƙara Arziƙi" ta amsa da Ameen. Sai da Amina ta fara zuwa ta nunawa Baba kayan, sannan ta je tana nunawa Hajara, sai dai ran Hajara ya sosu, dan tun da take ba'a taɓa bata makancin wannan kyautar ba a gidan. Amina ta ce "Yaya Hajaru, ki ɗau doguwar riga ɗaya, zan ɗinka atamfa biyu in ajiyewa Inno ɗaya". A fuska Hajara ta ce "An gode madalla" amma a zuciyarta kuwa sam ba ta ji daɗin hakan ba. Tun da Khalil ya baro wurin Hafsa yake tunanin mai ya fito da ita zaman titi da irin wannan sana'ar haka? Gashi ita ba gwanar fara'a ba, balle ya samu ya tambaye ta, to matar da ko fara'a ba ta yiwa kwastomominta, ga taƙamar tsiya ina zata saki jiki har kayi mata wasu tambayoyi? Duk yadda ya so ya manta da batun Hafsa, ya cigaba da sabgarsa, amma ya kasa, duk in da ya motsa tunaninta kawai yake yi, har haskowa yake irin kyan da zata yi, idan har tayi dariya ko murmushi. Bala'in Jarmai ya sanya su Bala a uku, dan duk in da ya tsuguna zaginsu yake a garin nan, kuma duk inda ya gansu ya dinga yi musu tijara kenan a kan kuɗin aurensa. Haka suka ƙuƙuta, suka mayarwa da dillaliya kayan gadon da suka saiwa Amina, amma tayi musu sayen wulaƙanci, suka tattara dubu talatin da ƙyar suka kai masa, a wulaƙance Jarmai ya karɓa sannan ya kalli Kawu Bala ya ce "Amma dai ka san na baku kuɗi sun kai dubu tamanin ko?" Bala ya ce "Haka ne" "To banci nanin ba, nanin ba zata ci ni ba, ba ƙira ba abin da zai ci gawayi, ina ganin mutuncinku ne shi yasa ban kai ku ƙara birni ba, kuma wannan dubu talatin na karɓeta ne dan kar nayi biyu babu, amma daga nan zan fara wucewa wurin mai gari, in fara kai masa ƙarar". Kawu Lawan ya ce "Haba Jarmai, dan Allah kar mu yi haka da kai mana, insha Allah zamu ciko maka sauran kuɗinka, kayi haƙuri". Jarmai ya gyara wata daƙalƙalalliyar babbar rigarsa ya ce "Ai haƙuri shi ne kawai in ga uwar kuɗina a hannuna". Kawu Bala ya ce "Insha Allah, zamu cigaba da lalubawa zamu baka sauran kuɗinka" da ƙyar suka lallaɓa Jarmai, ya haƙura bai kai su ƙara ba. Washegari da Fadila ta koma Makaranta, Captain ya tambayeta ya mai jiki, ta sanar da shi tun a jiyan aka sallame shi ya tafi gida, 'yan aji suna son suyi tsurku su ji yadda abubuwa suka wakana, amma sanin halin Fadila ya sanya ba wanda ya tanka mata. Ta dinga zuba ido, ta ga ta ina Yazeed zai shigo aji, amma babu Yazeed babu alamar sa, har aka yi lectures ɗin ranar aka gama. Nan cikin Fadila ya sake ɗurar ruwa, ta san ba zai wuce ace jikin ne ya hana shi zuwa Makaranta ba, nan zuciyarta ta dinga saƙa mata abubuwa daban daban, ciki har da tunanin ko jikin ne ya tayar masa ya mutu? Nan da nan ta yi saurin kawar da wannan tunanin daga ranta. Da aka tashi daga Makaranta ta samu Captain ta ce "Musa, kun yi waya da gayen nan ne?" Captain ya ce "Wa kenan?". "Wanda muka kai Asibiti jiya" Murmushi ya yi ya ce "Hajiya Fadila ta mu, sunan nasa ne ma ba za a iya faɗa ba. Wallahi tun jiya nake kiran wayarsa, amma ba ta shiga, kuma ina kyautata zaton jikin ne ya hana shi zuwa yau" Fadila ta ce "Ok shikenan" Daga haka ta wuce ta nufi motarta, tana cigaba da tunani. A kwanakin nan kowa da abin da ya dame shi a jama'ar gidan, Khalil ya kasa sukuni saboda tunanin Hafsat, gashi ya kuma komawa amma bata nan bai sameta ba. Fadila kuwa gaba ɗaya tunanin halin da Yazeed yake ciki ne ya dame ta, dan a rayuwarta bata taɓa aikata abin da ya dameta ba kamar abin da ta yiwa Yazeed ba, saboda ta tsorata da irin yanayin ciwonsa. Bata taɓa ganin mutum a mawuyacin yanayi na ciwo kamar Yazeed ba. Tana zaune a aji, tana ƙoƙarin ɗauko littafi tayi rubutu, ta ga jotter Yazeed, ta ɗauko jotter ta fara bubbuɗewa, rubutunsa a tsare yake kamar musamman yake shirya rubutun, sai dai fahimtar abinda ya rubuta ɗin sai ƙwaro ko kuma shi kansa da ya rubuta abin sa. Rubutu ne na turanci, jotting ɗin lectures ɗin da ake yi ne, sai yayi sentence ɗaya biyu ya gauraya su da rubutun larabci, ga wasu irin manyan Words na turanci, da bata taɓa jinsu ba. To ya akai ya iya turanci a rubuce, amma bai iya a baki ba? 'Maybe yana da matsalar public speaking ne' ta bawa kanta amsa. Bakomai ta iya ganewa a jotting ɗin nasa ba, saboda yadda yake rubutun larabci kamar rubutun yarensa na haihuwa. Ɗan taɓe baki tayi, ta ajiye jotter, tana fatan Allah ya sa dai ba jikinsa ne ya hana shi zuwa Makaranta ba. Khalil musamman sai ya shirya ya tafi unguwar su Abdul, yayi shawagi domin kawai ya ga Hafsat, cikin ikon Allah yau yayi sa'a ya tarar da ita a bakin kaskonta bayan magariba, tana ta harhaɗa kayanta ta tashi. Parking ɗin motarsa ya yi, ya fito da sauri ya ƙarasa in da take. "Sannu dai" Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce "Yawwa". "Ba dai har kin tashi ba?" "Me kaga ina yi?" "Oh sorry haka ne, na gani haɗa kaya ki ke yi, yanzu ba zan samu ba?". "Eh ta ƙare". "Kwana biyu na zo ba na ganinki, meyasa ba kya fitowa?" Hafsa ta ce "Eh da yake ai ba aikin gwamnati nake ba, kuma ba wani ne ya ɗauke ni aiki ba balle a tuhume ni" Murmushi Khalil ya yi, yana jinjina hali irin na Mai awara, ya ɗan sosa kai ya ce "Haka ne, am sorry" "Yawwa dama ina nemanka" tai maganar tana saka hannu a jakarta. Khalil ya ce "Kina nemana kuma? Allah ya sa ba laifi na miki ba" Ɗari biyar ta miƙo masa tana faɗin "Karɓi canjinka da ka tafi ka bar mini ranar" "Ai ba bashi bane, kyauta na baki". "Ai bance maka ina buƙata ba, ka karɓi canjinka". Khalil ya ce "Ai kyauta na baki, kuma ba kyau mayar da kyauta". "Meye tsakanina da kai, da haka kurum zaka bani kyautar kuɗi" "Alkhairi ne tsakanina da ke. Naga kamar gida zaki tafi, ko zamuje in sauke ki?" "Malam ka karɓi kuɗinka, zan tafi dare nayi" "Da ban dawo ba ya zaki?". Ƙoƙarin saƙala masa kuɗinsa take a hannunsa da harɗe a ƙirjinsa. Ja da baya yayi yana kallonta tare da sakin murmushi ya ce "ke dai kin fiye gaddama, dama zuwa na yi in ganki, kuma na sai awara, tun da ban samu awara ba na samu ganinki, shikenan, ki gaida gida" galala ta tsaya tana kallon Ikon Allah, Khalil kuma yayi gaba abin sa yana jin wani nishaɗi da ya rasa na menene. Yana tafe a mota yana tuna yadda tai kicin-kincin da rai tana bashi kuɗinsa, sam bai gaji da ganinta ba, amma ya lura ba ta son takura, magana kuma na bata wahala, shiyasa ya tafi ya ƙyaleta. Shiru yayi yana tunanin menene haka yake ji game da yarinyar nan? Wani irin baƙon al'amari yaji yana ratsa zuciyarsa, duk Hafsa daga gaban kaskon wuta ta tashi, ƙamshin turarenta ya haɗe da ƙaurin mai da na hayaƙi, amma a hancin Khalil ƙamshi ya bashi mai daɗin gaske. Amina kuwa zuwa makaranta ya kankama, dan ta gane hanya, Baba ne yake bata kuɗin mota, ta hau abin hawa ta tafi, idan an tashi ma ta taho gida. Kullum da kiran sallar farko, Amina idan ta tashi bata komawa, duk wani aiki da zata yi, sai ta tabattar ta yi shi, har karin kumallo sai ta dafa, ta gyara ko ina sannan take shiryawa ta tafi makaranta. Sati ya shuɗe kusan kwanaki takwas, Yazeed bai dawo Makaranta ba, gaba ɗaya hankalin Fadila a tashe yake, dan ba wanda ya san gidan su Yazeed balle a samo information akan halin da yake ciki, gashi wayarsa ba ta shiga sam. Fadila Addu'a take, da fatan Allah ya sa ba mutuwa yayi ba, dan da ƙyar in ta tambayi malamai ba a ce tayi azumi sittin ba, saboda abin da ta aikatawa Yazeed, dan da gayya ta balbale shi da hayaƙi da kuma ƙura, duk dan ta muzguna masa. Yau Saturday, kuma suna gaf da fara exams, dan haka akwai lecturer da ya ce, lallai su shiga Saturday, dan bai yi covering course ɗinsa ba. Jiki a sanyaye take tafiya dama gashi ta makara, dan ƙarfe goma ya ce aje, yanzu kuma sha ɗaya saura mintuna goma sha biyar, haka ta tunkari ajinsu tana fatan Allah ya sa malamin ya bari ta zauna, tuni har malamin ya fara lectures, Allah ya taimaketa bai koreta ba. Tun da ta shiga ajin ya ƙura mata ido, ɗaga idon da za tai suka yi ido huɗu da Yazeed. Gabanta ne ya faɗi ganin yadda yayi wata muguwar rama, sauke facemask ɗin sa yayi, tare da yi mata murmushi, gaba ɗaya ya rame sosai, sai dogon hancinsa da ya sake fitowa. Tsuke fuska tayi, ta basar kamar ba ta ganshi ba, ta nemi wani wurin ta zauna, tare da ɗauke kanta da sashen da Yazeed yake. Sai dai lokaci lokaci ta kan kalleshi, tare da sake tabattarwa da kanta yayi rashin lafiya sosai. Haka aka gudanar da lectures ɗin aka gama, aka yi Attendance. Da yawa ɗaliban zasu zauna ne a school, suyi karatu, saboda gabatowar exams, wanda ita ma Fadilan ta yanke shawarar ta zauna ta yi karatu, dan idan taje gida bacci zata yi, sai dai kafin nan akwai buƙatar ta ɗan samo abun motsa baki, da zai ɗebe mata kewa yayin karatu. Bayan tafiyar malamin daga aji, akai ta yiwa Yazeed ya jiki. Fadila tana ta hanzari ta tunkari motarta, ta saka key tana ƙoƙarin buɗewa ta ji an kira sunanta "Fadila" waiwayawa tayi, taga Yazeed a bayanta. Cikin murmushinsa da ya zame masa ɗabi' ya ce "Kina lafiya?" Ta ɗan yamutsa fuska ta ce "Lafiya ƙalau". "Dama na ce bari in zo in sake yin godiya ne, game da taimakon da ki ka yi mini, na gode sosai Allah ya bar zumunci" Wata uwar harara ta watsa masa, ta buɗe ƙofar motar. "Au ashe fa ni mai laifi ne, na manta a ranar na ɓata miki rai, kiyi haƙuri dan Allah, naga baki ji daɗin abin da nayi ba". "Ashe kana sane kai min abin da kayi mini ko?" Tayi maganar tana hararasa. "Ai nace kiyi haƙuri ban kyauta ba" "Kaji da shi" tayi maganar tana ƙoƙarin shiga mota. Cikin harshen larabci Yazeed ya ce "هل يمكنني الحصول على jotter الخاص بي" (*Can i have my jotter*) Kallonsa ta yi saroro, ba tare da ta gane me yake faɗa ba. Ya kuma maimaita mata abin da ya faɗa. Tsaki tayi ta ce "Malam speak what I can understand". Wani irin ƙasaitaccen murmushi Yazeed ya yi ya ce "Ni kuma gashi ban iya turanci ba, amma dai ina roƙon ki bani jotter ta ne, zan ɗan kwafi lectures da na yi missing, ance mini suna wurinki" Tura baki tayi, tana wani basarwa, ta fara duba jakarta, ta zaro jottersa da bironsa ta miƙa masa. Sansana jotter ya yi ya ce رائحته جميلة ( *It smells nicely*) Ƙaramin tsaki ta ja tana kuma ƙoƙarin shiga mota. Riƙe ƙofar motar yayi ya ce "Malama kayana da saura" kamar ba shi yayi Maganar ba, ya wani basar, dan ba zaka taɓa cewa yana magana haka ba. "Ban gane ba" ta faɗa tana kallonsa. "Ina kuɗina?" Ya faɗa ransa a haɗe. "Hamsin ɗin?" Ta faɗa a wulaƙance. Yazeed ya ce "Eh ai tawa ce ko?" Tsaki tayi ta saka hannu a jakarta ta ɗauko ɗari biyar ta ce "Ungo". "Ni tawa nake so, amma dai shikenan na bar miki, ki zo muje muyi karatu tare, ki koya mini abin da aka yi bana nan, sannan baki mini ya jiki bama, kin kusa halaka ɗan marayan Allah, ni yakamata ma ki gaya mini laifin da na yi miki kika tsane ni haka". "Dan Allah ka bani wuri in tafi, ka tsayar da ni kana ta mini surutan banza". "Subhanallah, yi haƙuri na takura miki, shikenan ki gaida gida" ya matsa ya bata wuri, ta shige motar ta, ta sauke glashin ta ce "Ka matsa kar in tada ƙura ka kama sumewa mutane". "Idan na suma ma in dai kina nan ai ba damuwa" hararsa tayi, ta bawa motarta wuta ta wuce ta bar wurin. Shi kansa Yazeed bai san yadda aka yi ya tsinci kansa, da ƙoƙarin tsawaita hira da Fadila ba, dan a rayuwarsa kusan shi mutum ne mai tsoron duk wani abu da zai haɗa shi da mata. Sake shanshana jotter yayi, sai ƙamashin turaren Fadila take, ya fara bubbuɗewa, kawai ya ci karo da rubutun da ba nasa ba, kusan duk lectures ɗin da aka yi baya nan, ta rubuta masa a ciki. Zubawa Jotter ido yayi, a hankali ya ce "Allah ya sa ki fara jin abin da nake ji a kanki" can kuma ya ce "Subhanallah, ba ajina bace" shikaɗai yake wannan surutan, daga baya kuma ya ja jiki ya nufi masallaci. Amina ta gama aikinta tsaf, ta zauna a falo tana karatu, Hajiya Zainab bata nan, Hajara kuma ta tafi yin sayayya. Turo ƙofar falon aka yi, Amina ta waiwaya, taga baƙuwar fuskar da bata saba ganinta ba. Yusra ta ce "Ina mutan gidan kuwa, naji kamar ba kowa?" "Sun je Islamiyya a koya musu sallama, da yiwa wanda suka tarar sannu" Amina ta bata amsa. "Ke, wacece ke kika gaya mini wannan maganar?" "Ahh musulma mana Hajiya, ai a koyarwar addinin musulunci idan ka zo wuri da sallama kake farawa, kuma ka yiwa na zaune sallama, amma kawai kya shigo kanki tsaye ki hau Magana. Bisimillah shigo amma dai nan gaba ba a haka" saroro Yusra ta bi Amina da kallo, dan ba su taɓa haɗuwa ba sai yau. Ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon Yusra take, amma Amina ta miƙe ta ce "Hajiya ba fa banɗaki zaki shiga ba, ya zaki shigo mana da takalmi falo, ciresu a nan wurin ki ƙaraso" Yusra cire takalman tayi tana kallon Ikon Allah wurin Amina, dan ba ta san matsayinta a gidan ba. Yusra ta zauna, Amina kuma ta wuce kitchen, ta haɗowa Yusra ruwa da lemo, ta kawo gabanta ta ajiye mata ta ce "Ga ruwa ki sha, 'yan gidan basa nan, idan kuma zaki ci Abinci ne ki faɗi wanne zan dafa miki? Dan an cinye na rana, na ɗan gidan nan ne kawai ya yi ragowa" Sai yanzu Yusra ta gane matsayin Amina, a ranta ta ce 'Ina Mummy ta samo wannan tantiryar mara mutuncin 'yar aiki? Ka rashin kunya ga karrama mutane'. "Ba Abinci na zo ci ba, ai ban miki kama da mai jin yunwa ba" Dariya Amina ta yi ta ce "Haba Yayata,. Idan a jiki ake gane yunwa ko rashinta, ai cewa za ai baki taɓa cin abinci ba ma" ai gaba ɗaya Amina ta kashewa Yusra bakin Magana. Ƙamshin turaren da ya karaɗe falon ne, ya sanar musu da zuwan Khalil, sai dai tun kan ya shigo, Yusra ta rasa nutsuwarta. Kansa tsaye ya shigo, da sallama iya wuyansa wadda shika ɗai yaji kayarsa, jiki na rawa Yusra ta risuna tana gaishe shi. Amma ya amsa ba yabo ba fallasa, haka ya shigo falon da takalmansa, sai da yaje dining ya ajiye takalman a kan step ɗin dining ɗin. Amina kuwa ta ƙulu, saboda yadda ya biyo har ta kan carfet da takalmansa, a fusace ta miƙe taje ta kwaso takalman Khalil ta je ta watsa su waje tana mita cike da tsiwa "Ai ni ba baiwarku ba ce da zan dinga aiki kuna takawa, sai na sake!" SHARE PLEASE GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 P12 Sai da ta watsa takalman waje ta dawo falo, ta lura da yadda duk suka bita da kallo, mussaman Khalil da ya ke mata Wani irin mugun kallo, sai a lokacin ta sha jinin jikinta ta gano ta yi wauta. Ɗan marairaicewa ta yi ta ce "Dan Allah kayi haƙuri ba dan halina ba, na gaji ne sosai yau na sha aiki, bayana har ciwo yake, na canza wancan carfet ɗin na bayar wanki, na saka sabo wankakke kuma ka taka mini da takalimi ai kaga ba zan ji daɗi ba, aikin da wahala, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba". Rai a haɗe ya ce "Ke na fuskanci ba ki da kunya ko? Tun ranar farko da na fara ganinki a gidan nan na fuskanci haka". Amina kamar zata fashe da kuka ta ce "To ai na ce kayi haƙuri, ba zan sake ba insha Allah, kuma rashin kunya ba halina ba ne, ba zan sake ba kayi haƙuri" "Rufe mini baki malama, ki ɓace mini daga nan wurin 'yar ƙauye mara kunya kawai" Amina ta juya baya ta murguɗa masa baki, tana yatsina baki a ranta ta ce "Ko ba komai, na faɗi abin da ke raina, ba zaku mayar da ni baiwarku ba" Yusra ta jinjina hali irin na Amina, yarinyar akwai iya nuƙufurci, yanzu za ta maka laifi, kuma ta nemo abin da zata goge laifin nata. Ta ɗan ƙurawa Khalil ido da yake zaune yana cin Abinci, cikin son lallai sai ya kulata ta ce "Yaya Khalil ita ma wannan maid ɗin Mummy ce?" Ba tare da ya kalli in da Yusra take ba ya ce "Me ya hana ki tambayeta tun tana nan?" Yusra ta ji haushin amsar da ya bata, amma ta haɗiye ta tsuke bakinta, tana cigaba da satar kallonsa. Yusra gajiya tayi da zaman Jiran Fadila, ta kirata a waya amma taƙi shiga, gashi Khalil ko kallon in da take ya ƙiyi, gasjiya tayi ta tashi ta kalli in da Khalil yake ta ce "Na tafi sai anjima, na kira lambar Fadila ba ta shiga". "Ok ki gaida gida" Yusra ta fito gwiwa a saɓule, a harabar gidan ta ci karo da Abdul, a jikin motarsa, yana ƙoƙarin kiran waya. Murmushi Abdul ya yi ya ce "Wata sabon gani, Yusra dama kina nan?". "Ina nan Yaya Abdul, ya kake ya gida?". "Lafiya ƙalau Yusra, yaushe rabon da na ganki, ya school?". Yusra ta ce "School Alhamdilillah". Abdul ya ce "Masha Allah, kin zo wurin ƙawar taki ne?" "Eh, na tarar ma ba ta nan, ta je school wai za suyi lectures yau". "Allah sarki, to shikenan, ki gaida gida" "Yauwa gida ya ji, na gode". Abdul ya kira wayar Khalil, "Gani a cikin gida, naga baka part ɗinka" "Shigo falo, ina cikin gida" Abdul ya ɗan yi jimm, ya ce "To bari in shigo". Ya nufi cikin gidan, yana fargabar karɓar da zai samu a wurin matar gidan. Da sallama ya shiga falon, ya hangi Khalil a kan dining, yana cin Abinci. "Ashe kana nan kana kintsa cikinka". Khalil ya ce "Ai sai da kintsa cikin, ƙaraso mu ci". "Ni bana jin yunwa, na ji gidan shiru ko ba kowa ne?" Abdul ya yi maganar yana zama a kan ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin. "Eh basa nan, Fadila tana Makaranta, Mummy kuma ba ta nan". "Allah sarki, na so inga Fadila ko ba zata kulani ba, ai yau na ga ƙawar nan ta ta Yusra, rabona da ita ina ga tun kan mu tafi karatu". Khalil ya ce "Hmm ka san wani abin takaici kuwa?" "A'a sai ka faɗa" "Wai wannan yarinyar Yusra ce, suka haɗa kai da Fadila wai sona take". Dariya Abdul ya yi ya ce "Amma ta taimaki ƙaton tuzuru, to kai ya ake ciki? Yarinyar ai ba laifi". Khalil ya yi tsaki ya ce "Ƙawar ƙanwar tawa, dan rainin hankali ni sa'anta ne?" Abdul ya ce "Ji wani zancen banza, dan sa'ar ƙanwarka ce shi ne ba zaka aureta ba, ai masoyi abin a kula da shi ne, meye dan ta ce tana sonka?". "Dalla, bana son raini, kuma ni bana son ramammiyar mace, na fi son in ga mace a cike" Abdul ya ce "Banda cin fuska dai malam" "Kaji da shi, ni idan an yi sallar magariba, zamu je ka rakani wani wuri, in nuna maka wani abu" Khalil ya ce "Me zan gani?" "Kai dai ka bari, idan muka je ka gani" "Ni ina Amina 'yar Makaranta ne?". Wani dogon tsaki Khalil yayi ya ce "Sai ka tashi ka tafi nemanta ai". "Wai kai kowacce magana akai maka sai ka kushe" banza Khalil ya yiwa Abdul, ya kammala cin abincin sa, ya dawo ya zauna a falo, suka kunna tv suka cigaba da hira da Abdul. Fadila kuwa keɓe kanta tayi a makaranta, ta sha karatu sosai da sosai, duk wasu abubuwan sun mata tsaurin da ba ta gama gane su ba, tana buƙatar wanda zai ƙara yi mata bayani. Tana kallon yadda aka haɗa group group, Yazeed yana sake yiwa ɗaliban bayanin abin da ba su gane ba, amma taƙi zuwa gani take idan ta je ta faɗo. Sai bayan la'asar Sannan ta bari school ta tafi gida, a Falo ta tarar da Khalil da Abdul suna kallon ball suna hira. Tana ganin Abdul ta wani haɗe rai, Abdul kuwa faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce "Sannu da Zuwa". Cikin ko in kula ta amsa, dan ya fidda ran zata amsa ma. Khalil bai kulata ba ta wuce ɗakinta, sai da ta bar falon sannan ya ce "Dan Allah Abdul ka daina shiga sabgar yarinyar nan tana yarfaka". "Kawai dai kace in haƙura ba zaka bani ita ba?". "A'a ni bance ba, amma yarfin da take maka yayi yawa" "Ba komai a hankali zamu daidaita". "Ai sai kai tayi" Sai da aka yi sallar magariba sannan suka bar falon, suka tafi masallaci domin yin salla. Bayan sun fito daga sallar ne Khalil ya cewa Abdul "Muje ka rakani in nuna maka abin da nake gaya maka, amma mu fara biyawa in gaida Mama" Abdul ya ce "To muje, Allah ya sa abin kirki zaka nuna mini, ba shiririta ba". "Ni ne ma nake maka shirirtar?" "To ai kai ɗin ne wasu lokutan sai a hankali, muje dai in gani" Haka suka tafi, suna tafe suna faɗa suka isa unguwar su Abdul, suka shiga Khalil ya gaisar da Maman Abdul, kamar yadda yake ɗabi'arta ta karɓi Khalil hannu bibbiyu, tana ta kwarara musu Addu'a da sa musu albarka, saɓanin mahaifiyar Khalil idan ta ga Abdul, ta dinga masa kallon banza kenan tana hura hanci. Bayan fitowarsu daga gidan su Abdul, Khalil ya ja mota zuwa unguwar su Hafsa, wanda take a gaban ta su Abdul, bai yi parking a ko ina ba sai a wurin suyar awarar Hafsat. "Wai mai za muyi a nan ne?" Abdul ya tambayi Kahlil yana kallonsa. "Zo muje zaka gani" Suka fito daga motar suka tunkari wurin mai awara. Abdul ya kasa haƙuri ya sake cewa "Wai wurin wa zaka ne?". Khalil bai bashi amsa ba, sai janyo hannunsa da yayi suka ƙarasa. Hafsa na ganin Khalil ta tsuke fuska, tana ɗauke kai. Sallama Khalil ya yi, Hafsa ta amsa tamkar an mata dole, suka zauna a bencin da ke wurin, Abdul kuwa sai bin Khalil yake da kallo ransa cike da tambayoyi. "Barka da warhaka 'yan mata" Khalil ya faɗa yana murmushi. Wani irin kallo Hafsa ta yi masa, wanda bai gane ko na meye ba, sai dai kawai yaji tsigar jikinsa ta tashi da kallon da tayi masa. "Ke baki gaishe ni ba, kuma na gaishe ki kin ƙi amsawa". Hafsa ta ce "Ni gaskiya malam takura mini kake yi, wai me kake nema a wurina ne?". Khalil ya ce 'Ban taɓa ganin wanda ba ya maraba da coustomer ba sai ke Hafsa" ɗagowa tayi da sauri ba tare da ta yi niyyar magana ba ta ce "Waye ya gaya maka sunana?" "Ban sani ba" ya bata amsa. Ɗan ɗage kafaɗa tayi ta cigaba da fifitar wutarta, Abdul dai sai bin su yake da kallo. "Zuba mana ta dubu ɗaya" yayi Maganar yana kallon zobunan hannunta. "Ba zan sayar ba, sai dai in baka ta iya canjinka ɗari biyar da ka bar mini" Khalil ya ce "Ƙadiran ala man yasha'u, wai ke wace irin Yarinya ce haka, Wallahi ba zan karɓi ɗari biyar ɗin nan ba, ki zuba mana ta yadda na ce mu tafi". Murguɗa baki tayi ta ƙi magana, ta cigaba da sallamar mutane. "Sauri fa muke, ki sallame mu mu tafi" ya faɗa yana nazartar ta. "Amma kamar ba ɗaure muku ƙafafuwa na yi ba ko?" Khalil ya kwantar da murya ya ce "Zuciyata ki ka ɗaure, ba ƙafafuwana ba" Abdul yayi gyaran murya ya ce "A taimaka a sallame mu ƙanwata, ya damu yana son cin awarar ne, shiyasa na rako shi". Hafsa ta ce "Ba fa ci yake ba, yana zuwa wurin nan ne kawai dan takurawa rayuwata, bana son yi masa wulƙanci, amma gaskiya yana takura mini, sana'a nake bana son yadda maza suke taruwa a wurin nan, ba yadda zan yi ne, shi kuma sai ya zo ya sani a gaba da surutai". Abdul ya ce "Kina da gaskiya, amma kiyi haƙuri dan Allah, Yanzu zuba mana sai mu tafi". Hafsa ta ce "Ba zata kai ta yadda ya ce ba". "To zuba mana wadda ta samu, sai mu tashi" Hafsa ta zuba ta ɗari shida, ta kalli Abdul ta ce "Ta ɗari shida ce, akwai ɗari biyar ɗin sa a wurina, ɗarin kuma na bar maka" Abdul ya ce "A'a ba za ayi haka ba, ai mun cinye ribar, bari dai in biya" Hafsa ta ce "A'a ka bar shi Wallahi, ka bashi ta ɗari biyar ɗin sa, wadda na baka kuma, ka ci ko ka bayar, ka yiwa mamana Addu'a Allah ya bata lafiya". Abdul cikin tausayawa ya ce "Allah sarki, ubangiji Allah ya bawa Mama lafiya, ya sa kaffara ne" "Ameen na gode" Sai Khalil ya zama hoto, yana mamakin yadda Hafsa, ta ɗan saki jiki ta yiwa Abdul magana, amma shi take nuna yana takura mata. Suka miƙe zasu tafi, Khalil ya sa hannu a aljijunsa, ya ciro dubu uku, ya ajiye wa Hafsa. Miƙewa tayi da sauri ta ce "Malam karɓi kuɗinka, ya zan yi da su?" Khalil ya ce "Yi makama shi da su" Yayi gaba abinsa, ta kalli Abdul ta ce masa "Dan Allah ungo ka bashi kuɗinsa, ni bana son irin wannan abun, meye haɗina da shi zai dinga yi mini haka?". Abdul ya ce "Nima fa yanzu kika mini kyauta na karɓa, dan haka ba a mayar da kyauta, ki saiwa Mama lemo da shi ba yawa, sai mun sake dawowa" yayi gaba ya barta baki a sake da kuɗi a hannu. Har suka fara tafiya, Khalil bai ce komai ba, can Abdul ya numfasa ya ce "Khalil, me kake nufi ne? Khalil ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shi ne abin da haryanzu ban tabattar ba, a kallon Farko da na yi mata, na shiga wata duniya da na kasa tantance, tausayi ne ko menene" "Khalil soyayya kenan fa" "Ba zan musa maka ba Abdallah, abin da nake ji game da ita, yayi yawa ina jin zan iya komai dan in dinga ganinta a kusa da ni, haka kurum nake jin kishin sana'ar nan ta ta, tana zaune kiwa na kallonta". Abdul ya ce "Tirƙashi, kai Izza ita miskilanci da rashin son raini". "Ai Abdul baka ga komai ba, yarinyar nan tana da jin kanta, ga ta da ba kowa ba, sai jan aji, kamar zata wahalar da ni, amma na yi mamakin yadda tai maka Magana, ni sai dai ta harareni ta gaya mini baƙar magana" Abdul ya ɗan murmusa ya ce "To ai kaine mutumina, kai ma izzar ce da kai da faɗan tsiya, mata kuma ba a musu haka, mussaman idan ana son farautar zuciyarsu. Idan har kana son Yarinyar nan ka ajiye taka Izzar, ka bita a yadda ta ke" "Abdallah wai wace irin izza, bani da wata izza Wallahi". "Haka dai kake gani, yanzun nan kana mini describing ɗin ta, amma kana cewa gata dai ba kowa ba, meye wannan idan ba izza ba, koma dai menene ai sonta ka ke" "Au dan na faɗi haka izza ne?" Abdul ya ce "Khalil kenan, Amma tsakaninka da Allah, son Aure kake mata, ko dai wani abu daban?". "Haba Abdullahi, ka taɓa ganina da harkar banza ne?" "Ba haka nake nufi ba, akwai so wanda kake wa mace dan ka aureta, wata kuma burgeka take kana son ka mu'amalance ta kamar ƙanwarka, wata kuma tausayinta ka ke ji kawai" "Nifa da gaske nake, Aurenta zan yi tayi mini". Abdul ya ce "Ina muku fatan Alkhairi, Allah ya tabbatar da alkhairi" a ransa kuwa yana jinjina yadda iyayen Khalil zasu amince ya auri mai 'yar talakawa mai suyar awara a bakin hanya. Fadila shirye shiryen fara exams ya yi nisa, tana ta fama da karatunta, sai dai girman kai ya hana ta koyi abin da ba ta iya ba, a ganinta hakan tamkar ƙasƙanci ne a gareta. Tana zaune ita kaɗai a seat ɗin baya, ta ƙurawa littafi ido, Yazeed gabansa na faɗuwa ya tunkari in da take a zaune, sallama ya yi mata, ta amsa a ciki ba tare da ta kalleshi ba. "هل يمكنني الجلوس" (Can i seat) Kallonsa ta yi, ta ɗauke kanta, Yazeed ya zauna a kusa da ita, ya kalli littafin hannunta ya ce "Sannu da ƙoƙari". "Dan Allah malam kar ka zo ka isheni karatu zan yi". Yazeed ya ce "Nima karatun zan yi ai" ya ciro jottersa ya ce "Ban miki godiya ba, naga kin rubuta mini duk abubuwan da aka yi bana nan, Na gode sosai ubangiji Allah ya ƙara basira. Amma dan Allah ina son ki ɗan yi mini bayani, akwai abin da ban gane ba". "Baka iya karatu bane da sai na maka bayani ko yaya?". "Karanta rubutu a rubuce ba shi ne ba, ka gane me ake nufi ko da ba ka iya karantawa ba shi ne mafi mahimmanci". "Dan Allah ka tashi ka bani wuri". "Ok, zan tashi amma bari in nuna miki wani abu" Ya ɗauki littafin gabanta ya kalla sannan ya ce "Ba wannan topic ɗin yakamata ki duba ba, idan har ki ka gane bayanin wannan topic ɗin shikenan, malamin ba zai tsawwala tambayoyi a nan ba". Ya buɗo wani topic ɗin ya ce a "A wannan yakamata ki fi mayar da hankali" Yamutsa fuska tayi, tare da tura baki kamar zata yi kuka. Yazeed ya ce "Ya dai?". "Ni fa na gaji da karatun nan, kaina kamar zai fashe bana gane komai ma" "Kece kika wahalar da kan ki, ki ke karanta abin da ba shikenan ba, idan Malami yana bayani, ki dinga rubuta abin da kike fahimta a game da darasin, idan kika koma gida sai ki faɗaɗa bincike, sai ki haɗa ki tsinci abin da zaki tsinta ki haɗa, amma idan ki ka ce handout zaki haddace baki fuskanci darasin ba, zaki iya samun idea escape ma a wurin exams. Dan haka idan ana lectures a daina yiwa malamai tsiwa ana korar mutum daga aji, wani abin idan har aka yi baka nan ya riga ya wuceka kenan" Murguɗa masa baki tayi, jin statement ɗin sa na ƙarshe, tare da cewa "Ina ruwanka da an koreni, bana son sa ido, ban littafina". "Zan baki littafinki, amma kan in baki duba wannan, sai in ƙara yi miki bayani, zaki ga yafi sauƙi a kan wanda kike yi" kallon rubutun nasa tayi, har da wani larabci a ciki. "Kaga nifa bana gane larabci" tai maganar tana wani basarwa. Aikuwa Yazeed kamar an kunna fanfo, ya dinga zuba yana mata bayani tana saurarensa, babban abinda ya sanya shi farinciki, bai wuce saurarensa da take yi ba. Sai da ya gama, tayi ajiyar zuciya, dan idan ta ce ba ta gane me yayi mata bayani ba tayi ƙarya, dan duk abin nan da ake, haddacewa kawai take ba ganewa ta yi ba. "Na fahimta, Na gode sosai". "Never mind ranki ya daɗe, bari inje masallaci" Ta jinjina masa kai, bayan tafiyarsa, ta ɗau jakarta ita ma tayi waje ta nufi gida. Khalil an fara yi masa way da ga wurin aiki, a kan lallai ana buƙatar sa, ji yake kamar ya ce Ya fasa komawa, saboda yadda yake jin Hafsa a zuciyarsa, ji yake kamar ba zai iya tafiya ya daɗe bai ganta ba. Ana gobe zai koma, ya je gidansu Abdul ya yi masa sallama, suka sake tattaunawa a kan yadda Khalil zai ɓullowa Hafsa, suka yi sallama Khalil ya tafi wurinta. Wannan karon ba Mutane sosai a wurin nata, dan da alama ta kusa tashi ne ma. Yana yin sallama a wurin, ta haɗe rai tare da amsawa ta ɗauke kai. "Ina wuni tun da ke baki iya gaisuwa ba". "To ai nima bance ka gaishe ni ba". Khalil ya numfasa ya ce "shikenan, ba faɗa na zo muyi ba, sallama na zo muyi zan koma wurin aiki insha Allah". Hafsa ta ce "To ni ina ruwana da zaka tafi?". "Amma dai at least ai kya yi mini A dawo lafiya ko?". Hafsa ta ce "To Allah ya kiyaye hanya" "Ameen Hafsat, ya jikin Mamana?" "Wace maman taka?". "Mamanmu mana, mamanki ai mamana ce ko abin ba kara ne?". "Jikin Mama da sauƙi". Khalil ya ce "Masha Allah, Alhamdilillah, amma sauƙi na bahaushe ko kuma ta warke?" "Da sauƙi sosai" Hafsa ta bashi amsa a lokacin da hankalinta ya koma kan wata coustomer. Khalil ya sa hannu ya ɗau wayarta mai madannai, wadda ta sha jiki da yawa, lambarsa ya sa a wayar, ya kira lambarta ta fito a tasa, ya ajiye mata wayar. Ya yi gyaran murya, wanda ya sanya ta waiwayo. Ya ce "Ko zamu je in duba Maman ne?" Ta ɗan waro idanunta ta ce "Saboda me? Ince ga wa ya zo dubata?". "Coustomer ɗinki, mai takura miki, kuma wanda yake fatan ya Aureki. Duk da ban gaya miki dalilin da ya sanya na nace ina ta bibiyarki ba, Hafsa ina sonki ne, kuma Wallahi da gaske nake, ni Aurenki zan yi, ina kishin ganinki a wurin nan kina wannan aikin" Ai tuni ɗan annurin yau da ya gani a fuskarta, saboda zancen Mama da ya yi, ya gushe daga fuskarta, ta haɗe rai sosai da sosai tayi shiru taƙi magana. "Hafsa maganata ce ta ɓata miki rai?" "Dan Allah ka rabu dani, kar ka sake zuwa in da nake, ni ban fito sana'ata dan wani ya tausaya mini ba, ba ruwanka da sana'ata, kuma kar ka sake zuwa wurin nan, idan ba haka ba zan iya dena zuwa ni, in bar maka wurin". A ɗan rikice Khalil ya ce "Amma Hafsa... "Malam bana son jin wata magana, ka ƙyaleni" tayi maganar a hasale. Haka Khalil ya tashi ya baro wurinta, jiki a sanyaye, yana mamakin halayen Hafsa, wace irin Yarinya ce haka, dan ance ana sonki ki birkice ki kama masifa?. A sanyaye haka ya koma gida, yana tunanin mafita, amma dole ya san abin yi, da zuciyarsa ba zata iya haƙuri da Yarinyar nan ba. Da ya koma gida, a Falo ya tarar da Mummy, da Fadila suna kallo, suna hira, Amina nata gyara dining, in da suka ci Abinci suka bar wurin. Fadila na ta bawa Mummy labarin Yazeed, yadda ya iya larabci amma bai iya turanci ba hadda cewa "Mummy kin gan shi kuwa, kayan da yake sakawa? Amma sai ƙwaƙwalwa kuma baya iya turanci a baki". Mummy ta taɓe baki ta ce "Wasu lokutan dama haka ne, yaran nan marasa galihu da suke tashi a wahala, suna da ƙoƙari, sai dai na banza ne, dan ko sun gama karatun ba aiki suke samu ba, sai da su zama masinja a manyan ofisoshi". Amina da ke aiki a ranta ta ce "Ji mata da mugun baki, wato ɗan talaka ba zai huta ba, iyayenmu su yi muku bauta, muma muyi muku da 'ya'yanku, insha Allah ta Allah ba taku ba' "Khalil lafiyarka kuwa, ka zo ka zaun kayi shiru haka?". "Mummy bakomai". "Ya fa bakomai? Ga yanayinka duk ya canza". "Mummy wata Yarinya ce" sai kuma yayi shiru. "Mai Yarinyar ta yi?" Mummy ta tambaya cike da zaƙuwar son jin ƙarshen zancen. "Mummy Bakomai" ya faɗa cikin damuwa. "A'a ka fara magana kace bakomai, ko dai ka fara Soyayya ne?". "Eh to, Yarinyar ce dai haryanzu ban samu shawo kanta ba". Mummy tayi murmushi ta ce "Ikon Allah, dama akwai lokacin da zaka samu macen da tayi maka, sarkin kushe kushe? A ina take kuma 'yar waye? Ina fatan ba gidan tsiya zaka je ka ɗauko mana sirika ba?" Gaban Khalil ne ya faɗi, be bawa Mummy amsa ba ya miƙe, ya ce "Idan komai ya daidaita za muyi maganar". Fadila kuwa wani takaici ne ya mamayeta, da tausayin Yusra da take ji, gaba ɗaya haushin Khalil ya kamata, ta tashi ta bar falon ita ma. Haka Khalil ya kwana yana tunanin dalilin da ya sanya, Hafsa ta canza fuska dan kawai ya ce yana sonta, shi dai ya san ba muni ne da shi ba, dan ƙarewa ma mata ne suke rushing a kansa, bai taɓa tunanin Soyayya zata iya kai shi wurin mai awara ba, dan da shi a yadda yake tsara rayuwarsa, macen da ta kammala degree ma yake so, very matured lady, haka yayi bacci rabi da rabi. Washegari tun sassafe, Fadila da Mummy zasu je unguwa, dan haka suka raka Khalil airport, su kuma suka wuce in da zasu. Hajara ma shiri tayi, ta tafi kasuwa saboda akwai kayan da babu, mai zuwa kasuwar sayowar kuma Hajiya Zainab ta koreshi. Amina taje wurin Baba suka sha hira, daga nan ta koma cikin gidan, tana ɗan ƙara dudduba abin da za tayi. Ta dawo babu daɗewa aka fara bubbuga ƙofar falo. Amina ta je ta buɗe ƙofar falon, wasu mata ta gani su huɗu, sai yara su ku san biyar. Amina ta ce "Sannunku da zuwa" Suka amsa mata da yauwa, ta basu wuri suka shiga falo, suka zazzauna. Ɗaya daga cikin matan ta ce "Ahmad ɗin yana nan ne?" Amina ta ɗan yi jimm, tana tunanin wanene Ahmad. Matar ta ce "Me gidan" Amina ta ce "Au, ai ba ya gari bai dawo ba, sai da ki kai magana naga kuna kama, 'yan uwansa ne ku?". Matar ta yi murmushi ta ce "Eh ƙannensa ne da iyayensa". Amina ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Allah sarki, sannunku da zuwa gashi duk ba sa nan, sannunku" nan da nan Amina ta tafi kitchen, ta dinga jido ruwa da lemuka a fridge, tana kawo musu, ta koma ta haɗo musu fruit a ƙaton faranti, ta zo ta zube musu, cikin hanzari ta koma kitchen, ta ɗora girki, ta sake dawowa falo tana musu sannu da zuwa. Ɗayar ta kalli Amina ta ce "Amma dai ke baƙuwa ce a gidan nan ko?". Amina ta ce "Eh baƙuwa ce, aiki nake yi ban cika wata biyu bama". "Allah sarki yarinyar kirki, Allah ya yi miki Albarka. Mun zo duba wani ɗan uwa ne da aka kwantar a Asibiti, muka ce bari dai mu biyo mu duba Ahmadu, tun da shi ya watsar da mu mu bari muzo". Amina ta ce "Allah sarki, ai kuwa kun kyauta zumunci ai Akwai daɗi". Nan da nan kamar sun san juna tun tuni, Suka saba da Amina, abinka da wanda ya ce maka ungo. Ta shirya musu lafiyayyen girki, yaji uban nama, ta kawo ta ajiye musu, aikuwa suka zage, suka ci Abincin nan, suka yi sallar azahar, Amina ta ware musu A.C ta kunna musu kallo. Hajara ce tayi sallama, daga kasuwa ta dawo wujiga wujiga. Sai dai tana ganin matan da ke Falon tai turus, ta gaishe su, suka amsa mata, Amina ta tashi ta tayata ɗaukar kayan da tazo da su zuwa kitchen. Suna zuwa kitchen Hajara ta kalli Amina ta ce "Amina, waye ya saki bawa baƙin nan hidima haka, har da girki?" Amina ta ce "Ban gane ba" "To ki shirya hukuncinki a wurin matar gidan nan, Allah ya sa ƙarshen zamanki a gidan nan bai zo ba, dan wannan mutanen arziƙin ruwan pure water suke samu idan sun zo, shi yasa suka daina zuwa". Amina ta ce "Amma Hajara 'yan uwan mai gidan ne fa". Amina ta faɗa cikin damuwa. "Ke ki ka san 'yan uwan mai gidan ne, amma ki shirya karɓar mummunan hukuncin da zaki fuskanta a wurin!!!. IDAN BA A COMMENT ZAN DAI NA TYPING TABBAS, KO YA KOMA PAID, IN ƁATA LOKACI INA TYPING, KU BINI DA THANKS😏😏😏 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 P13 Gaba ɗaya jikin Amina ya yi sanyi, jin abin da Hajara ta gaya mata, mussaman batun korar nan da ta ambata, jiki a sanyaye ta ce "Amma Hajara ai baƙon ka annabinka, ka yi baƙi 'yan uwan mai gida ka wulaƙanta su?". "Na gaya miki kefa ki ka san wannan, ita ba ruwanta, kawai ki saurari kwandon bala'in da zata zo ta sauke miki a ka, kiyi fatan ya tsaya a iya tijarar da zata miki" Jikin Amina yayi sanyi, amma babu yadda zata yi, tun da har ta riga ta musu kyakywar tarba, kuma ita ba taga aibun abin da ta aikata ba. Jiki ba ƙwari ta fito falon, ta tarar sun fara haramar tafiya. Amina ta ɓoye damuwarta ta ce "Ya naga kun fara shirin tafiya? Ba zaku jira su dawo bane?". "A'a kar yamma ta yi mana, gara muje mu tari motar garinmu". "Au dama ba a garin nan ku ke ba?" Ƙaramar cikinsu ta ce "A'a, mu daga jigawa muka zo" suna tsaka da maganar, Hajiya Zainab ta turo ƙofar falon, Fadila na bayanta. Tana shigowa ta yi turus ganin mutane a falon, ta bi su ɗaya bayan ɗaya da kallo, ta sauke idanunta a kan farantan da ke falon, alamar an ci an sha, dan har da taunannun ƙasusuwa, da ragowar kabeji a cikin farantan, ta sauke idanunta a kan Amina, da tayi tsuru-tsuru kamar ta yiwa sarki ƙarya. Cikin takunta na isa da taƙama ta ƙarasa shigowa falon, tana cigaba da yi musu kallon ƙasƙanci. Ɗaya daga cikinsu ta ce mata "Sannu da zuwa" Sai da ta sha ƙamshi sannan ta ce "Yauwa" tayi gaba ta nufi sashinta, Fadila ta bita ba tare da ko gaida su ba. "Hmm mai hali baya fasa halinsa, ayi dai mu gani idan tusa zata hura wuta, Ahmad dai ɗan uwanmu ne, ko anƙi ba za a taɓa canzawa tuwo suna ba" Amina ta ce "Dan Allah ku yi haƙuri". "Babu komai, ke dai mun gode sosai da karamcin da kika mana, dan rabon da mu zo gidan nan a kalle mu da mutunci har mun manta, mu mun tafi sai an jima". To muje in rakaku. Amina ta bisu Suka fita tare, na ta sake basu haƙuri, ta rakasu har haraba, sannan ta dawo ta kwashe kwanukan da suka ɓata, ta gyara falon tsaf, ta shirya wa su Hajiya Zainab na su Abincin a kan dining, ta koma kitchen ta yi wanke-wanke, tana ta tsumayin jin kiran Hajiya Zainab amma shiru, ba tace mata komai ba. La'asar liƙis, Bayan an idar da sallar La'asar, Khalil ya kasa jurewa, ya ɗau wayarsa ya fara lalubar lambar Hafsa. Hafsa kuwa ta kammala haɗa kayanta na fita wurin sana'a, ta tsaya yin sallar la'asar. Wayarta ce ta fara ringing, har ta katse ba a ɗaga ba, aka sake kiran wayar, Mama ta gaza haƙuri ta ɗaga ta ce "Salla take" ta katse wayar. Da Hafsat ta idar sa salla, ba ta bi ta kan waye ya kirata ba, ta cigaba da shirin fitarta, tana daf da fita aka kuma kiran wayar a karo na uku. Ba tunanin komai ta ɗaga tare da yin sallama "Assalamu alaikum warahmtullah". Khalil ya yi wata ajiyar zuciya sannan ya amsa ya ce "Babyna ya kike?". Sarai ta ɗau muryarsa, amma ta haɗe rai ta ce "Wake magana?". "Khalil ne". "Wane Khalil ɗin" ta faɗa tana yatsuna fuska. "Khalil coustomern ki, kuma masoyin ki" ɗif ta kashe wayar, tare da wani guntun tsaki, ta ja kayanta ta bar gidan. Hajiya Zainab ce ta fito cikin taƙama, fuskarta babu annuri ta kalli Hajara, da ke ta kiwa tana komowa a falon ta ce "Ke kina gidan nan ki ka bari aka saukar mini wannan mutanen a gida? Uban waye ya bada izinin aikata hakan" Jiki na rawa Hajara ta ce "Wallahi Hajiya bani bace ba, ba laifi na bane, ni bama na gida na je kasuwa sayayya, Amina ce" Hajiya Zainab ta wani hura hanci, tana huci ta ce "Tana ina?" "Tana wurin Babanta" "Wuce ki kira mini ita, daga ita har shi ɗin" Hajara ta ce "To" ta bar falon jiki na rawa ta nufi harabar gidan. Amina na zaune tana karatu, suna hira da Baba jefi jefi. Hajara ta ƙaraso ta ce "Wai kuje in ji matar gidan" cikin Amina ne yayi wata tsuwwa, saboda tashin hankali. Baba ya kalli Amina ya ce "Uwata, lafiya kuwa? Ina fatan ba wani laifin kika aikata ba?" Amina ta girgiza kai ta ce "Ban yi laifin komai ba Baba" Baba ya ce "To Allah ya sa, tashi muje muji". Amina ta tashi suka bi bayan Hajara, ko da suka shiga falon, kallo ɗaya Amina ta yiwa Hajiya Zainab, ta san babu mutunci, babu afuwa a tare da fuskarta. Baba ne ya gurfana a gaban Hajiya Zainab, hakan ya sa Amina ma ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta gurfana ɗin. "Waye ya baki iznin ki ɗau Abincina ki girka ki bawa wannan wahalallun mutanen?" Tai maganar cikin isa tana tsare Amina da idanu. Amina ta ce "Ba kowa". "Abincin naki ne, ko kuma da izinin wa ki ka yi hakan?" Amina ta ce "Wallahi ni ban san ba a bawa baƙo Abinci a gidan nan ba, naga idan wasu suka zo ana basu, kuma ce mini suka yi daga nesa suke, 'yan uwan maigidan ne, shi yasa na basu Abinci". "Kin taɓa ganin ire-iren wannan mutanen a gidan nan da zaki basu abinci na?, har ki kwashe mini kaya a fridge ki ba su? Talakan ubanki ne ya saya ya ajiye, da zaki ɗebar mini kaya kiyi gwaninta da su?" Damm! Ƙirjin Amina ya buga da ƙarfi, talakan ubanki ta maimaita abin a zuciyarta. Baba ya ce "Dan Allah, dan Annabi kiyi haƙuri, laifina ne da ban gaya mata dokar ki ba, amma dan Allah kiyi haƙuri ba zata sake ba". "In yi haƙuri ko kar in yi bai shafeni ba, zaka biya kuɗin abin da ta salwantar a albashinka, kuma wannan shi ne na farko kuma na ƙarshe, idan ta sake makamancin laifin nan, sai ta bar mini gida, ta koma ƙauyen da fito, ta je can ta cigaba da hauka da jahilicin da ta zo da su" Wata irin ƙunar rai ce ta kama Amina, jikinta har rawa yake saboda baƙi ciki, da ɓacin rai, da gari banza ne wani ya hɗata da Baba ya ci mutuncin ta, da sai in da ƙarfinta ya ƙare, amma yanzu babu damar magana. Baba ya ce "Ba damuwa Hajiya, insha Allah ba zata sake ba" ya kalli Amina ya ce "Uwata ki bata haƙuri" Amina kamar zata fashe, haka ta risuna ta ce "Allah ya baki haƙuri, ba Baba ne ya sai Abinci ba, insha Allah ba zan sake aikata haka ba". Hajiya Zainab ta ce "Kima sake, kiga ƙarshen rashin mutunci" Baba dai ya kwantar da kai, ya cigab da bawa Hajiya Zainab haƙuri. Sai da ta sallame su sannan suka tashi, Baba ya ja Amina waje, ya kalleta ya ce "Uwata, yanzu har kin manta da nasihar da na miki a kan zamanki a gidan nan? So kike sai kin yi dalilin rasa damarki ko?". Amina ta ce "A'a Baba, ban san dokar gidan ba ce ba saukar baƙi, amma insha Allah ba zan sake ba". Baba ya ce "To ki kiyaye, ki daina shiga abin da babu ruwanki, ko kuma aikata abin da ba a saka ki ba, kin ji ko?". "To Baba insha Allah ba zan sake ba" "Yauwa uwata, Allah yayi miki Albarka, maza koma ciki abinki" Amina ta juya ta koma, ranar na mata ƙuna, yadda aka ƙasƙanta mahaifinta a gabanta, a kan laifin da ita ta aikata ba shi ba. Haka ta koma ɗakinta sukuku, ta zauna baƙin ciki ya isheta, ta tuna yadda Baba ya gurfana a gaban matar da ya girmeta nesa ba kusa ba, ba ta kalli furfurar kansa ba, ta dinga zazzaga masifa, da Amina tana da burin idan ta samu ta cigaba da makaranta, amma taga kamar abin ba mai yiwuwa bane, saboda gaba ɗaya zaman gidan ya fara sire mata. Sai wajen ƙarfe tara na dare, sannan Hafsa ta dawo daga wurin sana'arta, ta tarar Mama ta dafa mata ruwan wanka, ga kuma girkin dare ta yi, ta zauna ta ci Abinci, tayi sallar isha'i sannan ta shiga ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai, kasancewar dul zafi duk sanyi Hafsa ba ta wanka da ruwan sanyi, saboda tana jin daɗin zuba ruwan ɗumi ko mai ɗan zafi a jikinta. Ko da Hafsa ta fito daga wanka, mai ta nema ta shafa, tana yi suna hira da Mama, wayarta ta fara ringing, ta kai hannu ta duba, taga lambar Khalil, wanda sai a yanzu taga missed calls huɗu ya yi mata tana wanka, katse kiran ta yi, tare da kashe wayar gaba ɗaya. Mama tana kallonta ba tace mata komai ba, sai da ta bari Hafsa ta gama shirinta tsaf tana ƙoƙarin jan bargo. "Hafsa" Mama ta kira sunanta. "Na'am Mama". "Waye ya ke kiranki a waya?". "Mama ba kowa" "Ba na miki magana ne dan muyi jayayya ko ki mini musu ba, amsa kawai nake buƙata daga gareki" Mama tayi maganar babu alamar wasa a tare da ita. Hafsa ta ce "Mama kawai fa.. "Kar ki mini ƙarya Hafsa, namiji ne yake kiranki waye?". "Mama, ba komai fa tsakanina da shi, kawai zuwa yake ya sai awara a wurina". "Ina jinki sai kuma aka yi yaya?". "Cewa ya yi yana sona" Hafsa ta ƙarasa maganar kamar wadda tai saɓo. "Shi ne kuma ki ke wulaƙanta shi, har ya kira ki katse wayar? Anya Hafsa rayuwa zata cigaba a haka? Bai kamata kowa ya nuna yana sonki ki koreshi ba, ki bashi dama mana, na ɗaga wayar kina banɗaki, ya gaisheni, naji alamun nutsuwa a tare da yaron. Amina ina buƙatar in ga aurenki kan bar duniya, kina gani yau ina da lafiya gobe babu, ina son in ganki a hannu na gari kan in mutu Hafsa". Cikin matsananciyar damuwa Hafsa ta ce "Mama dan Allah ki daina irin wannan maganar, kin san fa komai Mama, mai zai sa in yi wani ganganci,gara kawai mu cigaba da rayuwarmu ni da ke a haka". "Hafsa, duk abin da ya wuce, to ka bar shi a baya kawai, karki waiwaya kan abin da ta wuce idan har ba na Alkhairi bane, ki sa ka magogi ki goge abin da ya shuɗe ki fuskanci rayuwarki, zama haka ba zai yiwu ba, ke macece zamanki a bakin hanya kina wannan sana'ar dan babu yadda zan yi ne, zamanki a ɗakin ki shi ne rufin asirinmu gaba ɗaya". Hafsa ta kwaɓe fuska za ta yi kuka ta ce "Ni dai dan Mama... Mama ba ta bari ta ƙarasa ba, ta ɗaga mata hannu ta ce "Ya isa, tun da ke dai ba a baki shawara, ki je kiyi abin da kike ganin daidai da ke ne" "Mama dan Allah kiyi haƙuri, ba nayi ne dan in ɓata miki rai ba". "Rabu dani ni" Mama ta faɗa a ƙufule. Haka Hafsa ta kwanta cike da damuwa, ta shiga tuno irin hali da yanayin ƙaddarori, da suka haɗu da su na rayuwa ita da Mama. Saura kwanaki uku a fara exams, akwai teses ɗin da Yazeed ya yi missing, lokacin da bai zo ba ba shi da lafiya, wasu malaman sun karɓi uzurinsa sun yi masa, wasu kuwa sai wahalar da shi suke yi. Ɗaya daga cikin malaman da ke wahalar da Yazeed, saboda ya rasa Attendance ɗinsa, kuma ya ce wanda bai yi Attendance ɗinsa na ƙarshe ba, ya sa a ransa ya faɗi jarrabawarsa. Sannan ya fito da wani littafi ya ce lallai kowa sai ya saya, littafin naira dubu biyu ne, kusan sati biyu kenan ana sayar da littafin. Kwatsam, saura kwanaki uku jarrabawa, ɗalibai na ta fama da karatu, ya shigo ajin, ya ce zai yi musu lecturer, kuma da wannan littafin zai yi amfani, duk wanda ba shi da littafin ya tashi ya fita, ko kayi Attendance idan baka da littafin nan, to baka da exams ɗin sa, ko da kuwa ka cinye duka. Idan kuwa baka da Attendance, amma ko baka da Attendance, muddin kana da wannan littafin to ka haye exams ɗin sa. Idonta ne ya sauka a kan Yazeed, da ya yi shiru, ko motsawa bai yi ba, balle a sa ran ya fito da nasa littafin, A kunyace tsirarun waɗanda ba su da littafin, suke tashi suna fita daga ajin, malamin yana ta musu bala'i cikin tozarci. Fadila ce ta miƙe tsaye, ta nufi hanyar fita, ta ajiyewa Yazeed littafinta ita kuma ta wuce zata fice. "Hey Madam zo nan" sautin muryar malamain ta daki dodon kunnuwanta, cak ta tsaya sannan ta waiwayo fuskarta babu alamar wasa, cike da izzarta ta kalli malamin, tana sauraren mai ze ce. "Ina littafinki?" Ya tambayeta yana tsareta da ido. "Bani da shi sir, ban samu na saya ba" ta faɗa ba tare da wata shakka ko damuwa ba. "Shi kuma wancan littafin da ki ka ajiye masa fa" ta yi mamakin yadda aka yi ya ga ta ajiyewa Yazeed littafi. "Ba nawa ba ne, na sa ne ya ara mini". "Ƙarya ki ke yi, Malam fito nan" Yazeed ya fito jiki a sanyaye, yana jinjina irin ƙasƙancin da za a masa a gaban mutane. Ga ajin yayi shiru an maida ido kan su. Lecturer ya kalli Yazeed ya ce "Littafinka ne ko nata?" Yazeed zai yi magana, Fadila ta ce "Sir ba fa ƙarya nake maka ba, littafinsa ne ba nawa ba" Yazeed baya son ya faɗi wani abin da zai janyowa Fadila matsala, ko cin mutunci, hakan ya sanya ya kasa magana. Lecturer ya karɓi littafin daga hannun Yazeed, sai dai yana buɗewa ya ga sunan Yazeed da Admission number ɗinsa. Shi kansa Yazeed bai san ya aka yi ta rubuta ba, Ya miƙawa Yazeed littafin sannan ya kalli Fadila ya ce "Kina nufin baki sai littafin ba?" "Eh na saya, amma nayi karatu na manta shi a aji, na dawo ban ganshi ba". Malamin ya ce "Ok, ku koma ku zauna, amma ki sake sayan wani". Yatsina baki ta yi, suka koma wurin zamansu. Har malamin ya yi ya kammala karatun, Yazeed yana kallon Fadila lokaci lokaci, yana jinjina abin da ta yi masa, ba dan tayi hakan ba da ya fuskanci tozarci da ƙasƙanci a gaban 'yan aji. Bayan fitar malamin, Yazeed yana son yiwa Fadila magana, amma 'yan aji sun saka ido, suna son ganin Action ɗin da su Fadila za suyi, amma Fadila ta haɗe fuska tamau, wani na kawo raini zata balbale shi da masifa da tsiwa. Yazeed ma basarwa yayi, amma ƙasan zuciyarsa so yake ya yi mata magana. Class rep ne ya shigo da takaddu a hannunsa, na wata test da suka yi. Ya fara rarrabawa kowa test ɗin, sai dai abin da ya ƙara bawa Yazeed mamaki, bai wuce yadda aka miƙo masa takadda ba, ya karɓa yana dubawa, wannan dai ba rubutunsa ba ne, dan lokacin da aka yi test ɗin ma ba ya nan, gashi nan ya ci 7/10. Shiru yayi yana sake nazartar rubutun, tabbas na Fadila ne, dan bai manta wanda ta rubuta masa a littafin sa ba. Yana waigowa ya hangeta ta tashi zata bar ajin, cikin sauri ya tashi ya bi ta ƙofar baya, ya bi bayan Fadila, tana ta sauri ta nufi in da motar ta ke ajiye. Sauri yake sosai, yana kiran sunanta, tazararsa da ita ba yawa sosai, tana jinsa ta share shi, ta cigaba da sauri. Sai da taje in da motar take sannan ya cinmata. Ajiyar zuciya ya yi ya ce "Ina ta magana kin mini shiru". "Malam lafiya ta yi maganar kamar bata taɓa ganinsa ba" "Dama... "Kaga sauri nake tafiya zan yi" "Ga littafinki" ya yi maganar yana miƙa mata littafin. Sai a lokacin ta waiwayo ta kalleshi da fararen idanunta da ke matuƙar narka zuciyar Yazeed. "Ka riƙe kawai" ta faɗa tana ƙoƙarin ɗauke kanta daga fuskar Yazeed. "A'a ba za ayi haka ba, Halaccin da ki ka yi mini yanzu ma, Na gode sosai ubangiji Allah ya saka da alkhairi, kuma ga test ma kin yi mini, duk da hatsarin da ke cikin hakan, Na gode sosai ƙanwata". Ɗagowa tai ta kalli Yazeed "Wacece ƙanwar taka?". "Fadila mana" ya bata amsa, ta yamutsa fuska ta ce "Ka kiyayeni, ni na maka kama da ƙanwarka, ƙila ma na girmeka tsaurin ido kawai, na ce ka bar littafin, ka bani hanya zan kunna mota in tafi". Wani irin murmushi Yazeed yake, wanda sai da haƙoransa suka bayyana, wanda ya ƙara masa kyau, daga murmushi ya fara dariya, har da rufa baki, dan ba ƙaramin dariya Fadila ta bashi ba. "Saboda kina ganin tsayin mu ɗaya, shi ne ki ke cewa kin girmeni, ai ko da ki ke doguwa tubarkallah na fiki tsayi, balle ki kalli wannan tsofaffin idanuwan nawa, ki ce mini wai kin girme ni" "To sannu tsoho" ta faɗa tana kallonsa. "Yau ba zaki tsaya karatun ba?". "Eh" "To shikenan, Allah ya sauke ki lafiya?" "Kamar yaya Allah ya sauke ni lafiya, masu ciki fa ake gayawa haka" Yazeed ya ce "Subhanallah, ba haka nake nufi ba, ina nufin Allah ya kai ki gida lafiya". "Inyee me ake tattaunawa ne haka besty da besty, yau munga ƙarshen ƙauna, kowa na ƙoƙarin kare ɗan uwansa a kowacce gaɓa da ɗayan yake fuskantar barzana" Cewar Captain da ya ƙaraso yana dafa Yazeed. Fadila ta haɗe rai ta ce "Nifa bana son sa ido, kar ka kuma ce mini wani bestynsa na gaya maka". Yazeed ya ce "A'a Nothing like besty in Islam, she's my sister in Islam, ƙanwata ce ta Addinin Musulunci ko Fadila?" "Kai ka sani" tai maganar tana hararasa. "Kwa dai ji da shi, muna nan mun kasa mun tsare mun zuba ido, muga yadda ƙarshen wasan zai kaya, kwana biyun nan, kullum sai naga ka lallaɓo jikin motar nan kun keɓe kuna ƙusƙus, idan tai wari zata bazu mu ji ai" daga haka ya juya ya tafi yana murmushi. "Kaga ustaz ka ke ko Sheikh, ka Matsa zan kunna mota, ni bana son damuwa yanzu ka zo kana suma, ace ni ce". "Sunan nawa ma baki sani ba, amma kin iya rubutawa a cikin littafi ko? Da kuma test ɗin da kika rubuta mini, ni ina ga zanje in gayawa malamkn nan gaskiya, ni ban yi test ɗinsa ba, ƙanwata ce ta yi mini". "Sai ka dawo" da haka ta rufe motar, ta kunnata ta ja ta a hankali ta bar wurin. A hankali Yazeed ya dinga shafa sajensa yana murmushi, shi dai in dai Fadila ta kula shi, yana kasancewa cikin farin ciki mara misaltuwa tsawon wannan wuni. Khalil ya riƙe wuta, wurin yawan kiran Hafsa a waya, kuma sai ya daidaici tana gida yake kiran, gudun kar Mama ta ɓata rai, sai ta ɗau wayar ta amsa masa ciki ciki. Idan ha ji haka sai ya ce ta bawa Mama ya gaisheta. Duk wulaƙancin da take masa, baya gajiya da safe da yamma sai ya kirata, bayan saƙonnin Soyayya da yake tura mata, amma ko ɗaya bata kulawa, balle ya sa ran zata amsa saƙonnin nasa. Sai dai kasa jure ganinta yayi, dan haka ya ƙudurce a ransa zai zo ko a ranar ne ya ganta ya juya ya koma, ba tare da yaje gida ba Tana zaune tana fama da masu sayan awara, ta samu ta sallami da yawa daga cikin masu sayen, katsam ta ɗaga kai, taga fitowar wanda ta fi tsana a rayuwarta. Gabanta ya faɗi dan ba ta san da wacce ya zo ba, dan a kullum idan zasu haɗu ba shi da burin da ya wuce yaci mutuncinta, haka kwanaki ya zo ya sameta har wurin sana'arta a gaban mutane ya ci mutuncinta ba tare da kunya ko shakka ba. Kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kanta, ta cigaba da abin da take yi. "Au haryanzu kina aikin wahalar nan? Ko da yake ba abin mamaki bane ba, tun da ke da uwarki ba ku gaji arziƙi ba, titi dai a nan zaku ƙare" Hafsa ta sunkuyar da kanta, tana jin wata irin ƙuna a cikin zuciyarta, wanda suka haddasa mata zubar hawaye. Mai shayin kusa da Hafsa ne ya taso ya ce "Haba Malam, kai wani irin mutum ne mara tunani, kullum sai ka zo cikin mutane kana cin zarafinta, haba malam kamar ba musulmi ba". A fusace mutumin ya ce "Ba ruwanka da ni malam, ka fita harkata a wannan sabgar, waye ya sa da kai, wannan Yarinyar har wadda za a tausayawa ce, uwatta ta goya mata baya tan zama a kan titi tana tallan kanta, ta ɓige da suyar awara tana karuwanci, ko da yake ai barewa bata gudu ɗanta yai rarrafe, abin da taga uwarta na yi ne" Yadda miyagun matashin suka daki zuciyarta, ba tare da ta shirya ba, ko wani tunanin ba, ta daki kaskon man da ke kan wuta, ya ƙonawa mutumin ƙafa. Wani irin uban ihu ya saki, nan da nan ƙafa ta yi ja, ya yin da babu alamar nadama a tare da Hafsa. Salati da salallami mutane suka fara yi da ganin abinda ya faru. Har Hafsa ta yi wannan aika aika ta gama, kuka take yi, mutane suka dinga bashi rashin gaskiya. "Ba dai ni ki ka yiwa haka ba, to Wallahi zaki gani, zaki ga abin da zan miki, sai kin gwammace kiɗa da karatu da ni ki ke zancen". Mai shayi ya ce "Ai ni kin mini daidai Hafsa, ɗan iskan banza kawai, bari in aika yaro ya sayo miki man ki, ki ƙarasa ki tashi. Amina ta girgiza kai ta ce "A'a, gida zan tafi" ta yi maganar tana share hawaye. Mai shayi ya sai mata mai, ya bata, da ƙyar ta karɓa, ta tattara kayanta ta tafi gida, dan ba zata iya cigaba da zama ba. Da ta je gida ma ba ta bari Mama ta gane ba halin da take ciki ba, Maman ma ba ta bi ta kanta ba, dan ta fuskanci Hafsa yau tambotsan nata take ji. Washegari da sassafe, Hafsa na shirin zuwa ta kai markaɗen wake, aka ƙwanƙwasa ƙofar gida. Hafsa na shirin zuwa ta buɗe, Mama ta ce "Ƙarasa bari in leƙa in ga waye" Mama ta sanya mayafi, ta ƙarasa ƙofar gidan, tana buɗewa sai ga 'yan sanda biyu a tsaye da motarsu a farkon layi. Gabanta ne ya faɗi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yallaɓai lafiya kuwa?". "'yar ki muka zo nema" "Me 'ya ta tayi muku?" "Yanzu ba lokacin yaɗa rahotanni bane, idan muka je can kya ji abin da tayi". Jin Mama shiru ne ya sanya Hafsa ta tashi ta bi bayanta, sai dai tana zuwa soro ta yi turus, ganin 'yan Sanda. "Mama lafiya kuwa?". "Kece Hafsa?" "Eh nice" "An bamu iznin mu kama ki, dan haka ki zo mu wuce station". Ayshercool 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 Page14 "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" shi ne abin da Mama take ta maimaitawa, ya yin da Hafsa tayi tsumu tsumu tana tunanin wani lafin ta yi, da har 'yan sanda za su zo gida kamata?. Mama ta kalleta cikin tashin hankali da firgici da yaya mamaye fuskarta ta ce "Hafsa me kika aikata haka, da za a zo har gida ana ƙoƙarin kamaki?". Hafsa ga girgiza kai ta ce "Ni Mama ban yi komai ba, ban taɓa kayan kowa ba ba abin da ya haɗani da wani". "Ke malama, ba lokacin tattauna wannan maganar ba ne, wuce mu tafi" Suka ingiza ƙeyar Hafsa, tana kuka tana kiran Mama, a gaban maƙota, wani maƙocinsu Hafsa ya yi ƙoƙarin dakatar da su, ya ji ba'asi amma suka ƙi saurarsa, Mama ta ce su bari ta ɗauko mayafi su tafi tare, nan ma suka ƙi suka ce ta biyo su a baya. A kiɗime Mama ta shiga gida, ta yafo mayafi, ta rufe gidan hankali tashe ta nufi titi. Tuni Maman ta fara jin haki, saitin zuciyarta ya mata nauyi, alamun hawan jininta zai tashi, kai tsaye station ɗin unguwarsu ta nufa, amma da taje aka ce mata ai ba wannan police station ɗin aka kai Hafsa ba. Rushewa Mama tayi da kuka, tana tunanin ina aka kai Hafsa, 'ya mace a hannun 'yan sanda, ta kuma bazama ta tari wani abin hawan ta tafi wani division ɗin. Khalil ji yake tamkar ana hura masa wuta a ƙirjinsa, babban burinsa kawai shi ne ya ganshi a garin Kano, a gaban kaskon wutar suyar awarar Hafsa, ya yi tozali da fuskarta da take sa shi nishaɗi da nustuwa. Da fari ya jira ya yi booking ɗin jirgi, ya taho bayan kwana biyu, amma ya ji ya kasa jurewa, kawai ya ɗauki motarsa da yake amfani da ita a nan Abuja, ya nufo gida, yana tafe yana murmushi, zuciyarsa cike da muradin tozali da fuskar Hafsat. Kusan wuni Mama ta yi tana bulayi, amma ta rasa station ɗin da aka kai Hafsa. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, kuka kam babu irin wanda ba tayi ba, 'ya mace a hannun 'yan sanda abin da tayar da hankali sosai. Tana komawa gida maƙota suka fara tambayarta yaya ina Hafsan, cikin kuka ta ce ta rasa station ɗin da aka kai Hafsa, yanzu ma kuma bazama za tayi neman in da aka kaita. Maƙocinsu mai suna Malam Sani ya ce "A'a Maman Hafsa ba za ai hak ba, bari in ɗauki babur ɗina in je in zazzaga nima, amma ki nemi wuri ki zauna ki huta, tunda dama ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba". Da ƙyar suka rarrashi Mama, ta haƙura ta zauna, Malam Sani shima ya tafi zagawa stations ɗin da suke nan shiyarsu. Ko mintuna Arba'in ba ayi ba, Mama ta kasa jurewa, ta sake ɗaukar mayafi, ta cigaba da yawon neman Hafsa. Khalil kuwa, a Hotel ya sauka, yayi wanka ya ci Abinci, dan kwana ɗaya zai yi ya koma, baya son Mummy ta tuhume shi dalilin dawowarsa a yanzu, bayan bai daɗe da tafiya ba. Wajen ƙarfe biyar na yamma, yayi kwalliya ya ɗau motarsa zuwa wurin sana'ar Hafsa, amma ya tarar bata nan. Ya ɗakko wayarsa ya kirata, wayar ta shiga amma ba a ɗauka ba. Fitowa yayi daga motar, ya ƙarasa wurin mai shayin dake kusa da wurin da Hafsa ke sana'a, suka gaisa sannan Khalil ya ce "Dan Allah Hafsa fa?". Mai shayi ya ce "Gaskiya yau ba ta fito ba, kuma ban jin zata zo, da zata zo da tuni ta almajiri ya fara kawo mata kaya". "Dan Allah ina ne gidansu?" "Taɓ, yo wannan ina zata saki jiki da wani har a san gidansu, ni dai na so naji ance gidansu a nan wajen makarantar brilliant yake, daga nan sai ka tambaya". Khalil ya ce "Masha Allah, na gode sosai, Allah ya sa dai tana lafiya". Har Khalil ya juya zai tafi, wani a cikin rumfar mai shayin ya ce "Ai nifa ina ga rashin fitowar tata yana da nasaba da abin da ta yiwa mutumin shekaranjiya, dama ya ce zata gani, maybe ko tsoro ta ji kar ya mata wani abu". Cak Khalil ya tsaya, ya waiwayo, ya kalli mutumin da ke maganar, ya ce 'Malam wani abin ne ya haɗata da wani?". Mai shayi ya ce "Wallahi wani mutumi ne yake yawan zuwa wurin nan, ya yi mata zagin rashin mutunci a gaban Mutane ya tafi, babu wanda ya san abin da ya haɗata da shi, aikuwa shekaranjiya ta watsa masa mai a ƙafa ya ce zata gani, wataƙila shi ya sa yau bata fito ba" Cikin hanzari Khalil ya ce ya gode, jikinsa na rawa ya koma mota, gidansu Abdul ya fara zuwa, dan ya fishi sanin kan unguwannin. Yana tsaye a ƙofar shagon Abdul, ya kira shi a waya, Abdul ya ɗaga tare da "Assalamu alaikum". "Wa'alaikum salam, kana ina ne? Na zo shago baka nan?". Abdul ya ce "Wane shagon?" "Shagonka mana, ina Kano fa, dan Allah kana ina akwai matsala ne". "Subhanallah, Allah yayi mana maganin matsala, fito titi mu haɗu" Khalil ya ajiye wayar, ya ja mota ya koma titi. A titi ya samu Abdul ya ɗauke shi suka tafi. Abdul ya ce "Wai ina zamu ne? Tukuna ma me ka dawo yi?, kwata kwata yaushe ka tafi da har ka dawo?". Khalil ya kwashe komai ya gaya masa, Abdul ya jinjina kai ya ce "Ikon Allah, to Allah ya sa lafiya muje mu nemi gidan" Suka ƙarasa makarantar da aka kwatanta musu, da tambaya da ƙyar suka gano gidan, sai dai suna zuwa suka tarar gidan a rufe. Khalil yayi mamakin ganin gidansu Hafsa, ɗan ƙuƙuta kamar ɗakin tattabaru. Hakan yayi daidai da dawowar Malam Sani daga taya Mama neman Hafsa. Ganin yana ƙoƙarin shiga gidan kusa da na su Hafsa, ya sanya Abdul ya ƙarasa, ya yi masa sallama, Malam Sani ya amasa masa, suka gaisa. Khalil ma ya ƙaraso, suka gaisa da Malam Sani, Abdul ya ce "Dan Allah munga kaine maƙwabcin wannan gidan, munzo wurin su Hafsa ne, kuma basa nan ga layin ba kowa balle mu tambayi wani". Malam ya ce "Kunga dawowar nan tawa? Daga neman in da yarinyar take nake Hafsa, tun safe 'yan sanda suka tafi da ita, ba wanda ya san ina suka kaita, mahaifiyarta sai bulayi take tana neman ta, duk station ɗin da taje sai ace bata nan, shine nima na ɗau babur na zaga nima ban dace ba, gashi mu bamu san wani nasu ba, kowani tsayayyen namiji, balle muje tare a cigaba da nemansu, su kaɗai suke zaune a nan" Khalil ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, me Hafsa ta yi haka har da za a kamata? Yarinyar da babu ruwanta da kowa ya za ai ace tayi laifin da za a kamata?" Nan da nan fuskar Khalil ta sauya, ya harzuƙa matuƙa. Abdul ya ce "Ka kwantar da hankalinka mana, yanzu ba kumfar baki ce abin yi ba, mota zaka ɗauka muje division ɗin unguwar nan, muje mu ji me zasu ce" Da ƙyar Khalil ya kwantar da hankalinsa, Abdul ya karɓi tuƙin, suna tafe Khalil sai zufa yake duk da sanyin AC dake motar, ace an kama Hafsa tun safe, amma babu wanda ya san ina ma aka kai ta. Kallon tausayawa Abdul yake wa Khalil, dan da alama ya faɗa soyayyar yarinyar nan da yawa, babban abinda yake fargaba shi ne yadda mahaifiyar Khalil zata karɓi batun auren Khalil da Hafsat ba. Abdul na parking, Khalil ya buɗe motar da sauri, kamar zai faɗi ya shiga cikin station ɗin. Abdul ya ƙarasa kashe motar da hanzari, ya fito ya bi bayan Khalil, dan kar yaje yayi kataɓora. Khalil ya yi sa'a D.P.O yana nan, aka yi musu iso suka shiga cikin ofishin DPO. Bayan sun gaisa Khalil ya yi masa bayanin meke tafe da su. DPO ya ce "Gaskiya ba station ɗin nan aka kawota ba". Khalil ya ce "Ai a shiyyarka take, dan haka ka bincika mana in da aka kai ta" Abdul ya ce "Haba Khalil, ka bi a hankali mana, ya kake magana a haka?" "Bar shi yayi mini rashin kunya, yanzu in sa saka mini shi a cell". Khalil ya ce "Ni zaka dubi kamata kace a sakani a cell, ai ko kisan kai nayi nafi ƙarfin sarƙa Wallahi" "Shut up Khalil, meye haka wai?" Cewar Abdul da yake zarewa Khalil ido. "Malam ka daina zare mini ido, kana ji zai raina mini hankali dan yana kan wannan kujerar" da ƙyar Abdul ya sa Khalil ya yi shiru, ya lallami DPO da ƙyar, sannan ya bincika musu in da aka kai Hafsa. Tuni su Fadila sun fara jarrabawa, kuma ba ƙaramin ganin amfanin abin da Yazeed yake koya mata tayi ba, a sauƙaƙe take karatunta, kuma take rubuta jarrabawar ta cikin nasara. A gobe ne zasu rubuta jarrabawar course ɗin da ta tsana, saboda bata ganewa, tana matuƙar buƙatar taimakon Yazeed, amma ba zata iya cewa ya koya mata ba, dan a ganinta idan tayi hakan ta faɗo. A haka ta tunkari ajinsu, ranar ba su da jarrabawa, wasu daga cikin ɗalibai ne suka shigo karatu. Sassanyan ƙamshin turarenta ne ya shiga hancin Yazeed, wand ya saukar masa da wata irin nutsuwa ta mussaman. Yana zaune cikin ɗalibai, yana musu tutorial, galibinsu mata ne, duk sun kewaye shi, ciki har da wata yarinya Azima, sai nanuƙar Yazeed take, shi kuma yana takure jikinsa, yana matsawa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san a takure yake musu koyarwar nan. A hankali ya ɗaga idanunsa ya sauke su a cikin Fadila, da take tsaye tana kallonsa. "ماذا حدث ىااختي" Ya faɗa yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi. A hankali ta janye idanunta, tare da lumshesu, ta nufi wurin da take zama, hakan ya so tafiya da hankalin Yazeed, dan ta ƙasan idonsa ya cigaba da binta da kallo, har taje ta zauna, saboda ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, ta ɗanyi kwalliya yau, sai dai abin da bai masa daɗi ba shi ne yadda ta yi parking ɗin gashinta, ta fito da shi. Captain ne ya kalli Fadila ya ce 'Babbar yarinya, irin wannan wanka haka kamar zaki gasar sarauniyar kyawawan Nigeria?" Harar captain ta yi ta basar, wani irin kishi ne ya kama Yazeed, amma ya danne ya cigaba da ƙoƙarin cigaba da abin da yake. "Malam Yazeed wai ya ne, sai gaba muke kana dawowa baya?" Azima ta yi maganar tana ƙoƙarin taɓa shi. Cikin sauri ya janye jikinsa ya cigaba da koya musu, sai dai lokaci lokaci ya kan ɗaga kai ya kalli Fadila, da sun haɗa ido, sai ta harareshi ba gaira ba dalili. Gaba ɗaya suka kasa gane kan Yazeed, hankalinsa yana kan Fadila. Haka ya ƙarasa musu ya tashi. Azima ta ce "Aikin banza, wannan gayen ba shi da zuciya, da yaga yarinyar nan yayi ta rawar kai, tana wulaƙanta shi". Amra da a baya ƙawar Fadila ce, amma yanzu ƙawancen na su ba sosai ba ta ce "Ke ina ruwanki to, tunda bake yake shigewa ba". Fadila ta bar ajin, amma motarta na wurin da ta saba ajiyeta, haka Yazeed yai ta dubawa, har ya gano ta, tana zaune a wani wuri ita kaɗai, tana waya. Ba tsammani taga Yazeed ya zauna kusa da ita, wani irin shocking ta ji a jikinta, gaba ɗaya ta nemi nutsuwarta ta rasa. Bakinta ne ya hau rawa ta kasa cigaba da wayar da take yi, ta waiwayo ta kalli Yazeed, taga ita yake kallo gaba ɗaya jikinta ya ƙara yin sanyi, haka kurum ta ji wasu hawaye da bata san na menene ba suka taru a idonta, ga wani irin mugun kwarjini da yayi mata, wanda da bata taɓa sanin yana da shi, musamman kasancewar kusan kullum da facemask a fuskarsa, yau kuma ya cire, ga sajensa ya ƙara yawa, gashi ya ɗan tsare ta ido. Yazeed ya yi murmushi ya ce "Gani naga kamar kina son ganina". Kallonsa tayi ta sake haɗe rai. Kamar ba za tai magana ba ta ce "Ka matsa daga kusa da ni". "Zan matsa, amma meyasa hannunki yake rawa, ko baki da lafiya ne?" Ɓoye hannun tayi tana jin yadda jikinta ke cigaba da rawa, ba tare da tasan dalilin hakan ba. "Fadila" ya kira sunanta. "Kallonsa ta kuma yi, amma ta ji idanunsa sun yiwa nata nauyi a nata idon" "Naga kina nema ne ne, shiyasa na biyoki nan". "Ni ba nemanka nake ba" ta faɗa tana kauda kanta gefe daga kallonsa. Yazeed ya ce "Ba nemana ki ke ba, amma kika tsaya kina kallona? Shikenan na ji, ɗauko littafin in koya miki, kina son in koya miki abu, amma kin kasa gaya mini, ba ke kika ce in koya miki ba, ni nace zan koya miki, ɗauko mu yi" Kallonsa tayi da mamaki, tana tunanin yadda akai ya san abin da ke ranta. "Ba mamaki zaki tsaya yi ba, ɗauko muyi abin da yakamata". "Malam ka Matsa daga kusa da ni" ta faɗa tana haɗe rai. Yazeed yayi murmushin sa mai ƙayatarwa ya ce "Ko na matsa ba zaki daina jin abinda kike ji ba, kuma hannunki ba zai daina rawa ba, amma gashi na matsa, kawo littafin in ga me kika karanta a kan course ɗin". Miƙewa tsaye tayi ta ce "Dan Allah malam ni ka ƙyaleni, sai kace dole, ka fita daga harkata kar ka sake zuwa in da nake, bana buƙatar taimakon naka, ni ai bance maka ina son ka koya mini abu ba". Shima ya miƙe tsaye ya ce "Am sorry, Allah ya baki haƙuri, na yi miki shishshigi, ba zan sake ba insha Allah" Jakarta ta ɗauka tai gaba, tana cigaba da yadda jikinta ke tsuma kamar wadda tai artabu da aljan. Cikin ikon Allah su Khalil suka gano in da aka kai Hafsa, tun safen nan ba ta ci komai ba, sai kuka da take yi, kuma taƙi magana, fuskarta duk tayi jawur saboda kuka, an rufeta a ceil. Su Khalil basu tarar da DPO division ɗin ba, sai yaransa, bayan sun gaisa Aminu ya sanar da su cewar sune wanda suka zo wurin Hafsa. Ɗansandan ha kallesu ya ce "To mintuna uku kacal zaku yi, dan kotu zamu kaita". "Wai a kan ta aikata wane laifin?" Khalil ya yi maganar a hargitse. Abdul yayi saurin dakatar da Khalil ya ce "To Yallaɓai, a bari mu gantan". Aka fito da Hafsa, idanunta jawur, tana rarraba ido taga Mama, kawai taga Khalil da Abdul, aikuwa tayi sak tana kallonsu, ta ƙaraso gaban teburin ta tsaya tana sunkuyar da kai. "Hafsat, me kika yi aka kawo ki nan?" Khalil ya yi maganar yana kallonta cikin kulawa. Fashewa da kuka Hafsat tayi, ta kasa magana. "Ai na zata faɗa ba, tayi attempting illata mutum, kina mace amma kina abin 'yan daba, ta ƙonawa mutum ƙafa da mai, kuma ta rarumo makami tana nema ta sokawa mutum" cewar wani ɗan sanda mai jajayen idanuwa. Tsaki Khalil yayi, ya ce "Wanan dalilin ne ya sanya aka kawota nan, wace irin magana ce wannan? Ta yaya zata ɗau makami tace zata illata wani, Yarinyar da ko kuzarin kirki ba ta da shi?" "Kaga shi mugu fa ba a ido ake ganinsa ba, wanda ya kawo ƙararta ya ce bai yadda da sulhu ba, a kai su kotu a bi masa hakkinsa" Khalil ya ce "Shi dabban ina ne da zai kai mace kotu ya tsaya a kotu ya ce wai ta ɗau makami zata masa illa? Wace doka ce ma ta bada damar a riƙe mutum tsawon wannan lokaci family ɗinsa ma ba su sani ba, a bani belin ta". DPO ne ya shigo yana zazzare ido "Yaya, Yaya, meke faruwa nake jin hayaniya haka?" "Welcome sir, wannan ne ya zo zai mana tsageranci, wai sai an bashi belin wannan 'yar dabar". "Wallahi ka kuma ce mata 'yar daba, saina ɓata maka rai". "Kai nutsu, nan station ne, kar kai mana fitsara" Cewar DPO yana zarewa Khalil ido. Abdul ya ce "Dan Allah Khalil abi komai a sannu". Khalil ya ce "Wallahi ba zan bi a sannu ba, ya za'a kama yarinya ba bisa ƙa'ida ba, kuma aci zarafinta, sun ajiyeta daga ita sai su a wuri ko danginta basu san in da take ba?" DPO ya ce "Au rashin kunya zaka mini, kai ku mayar da ita ceil, ba za a bada belin nata ba, sai ta ɗau nauyin maganin wanda ta illata". Khalil ya ce "Bari in ɓullo muku in da ya dace" kawai ya fita daga cikin station ɗin, kuka Hafsa ta saka, da taga Khalil ya juya ya fita. Abdul ya bi bayansa da sauri. Mintuna bakwai, DPO ya fito a gigice yana faɗin "Suna ina? Wannan wane irin ɗan tijara ne, maimakon ya tsaya a sasanta sai ya kunno mini wuta daga saman ƙololuwa? Ku kira mini shi mana". Khalil ne ya shigo ya ce "To zaku bani ita ko kuwa?". "Za a baka, ai ban sai kai waye ba, ashe ɗan gidan controller Ahmad Dutse ne". Khalil Ya ce "Wannan matsalarku ce, a bani ita kawai". DPO ya ce "Ai irin haka bayani ake yi, ba bankaɗo mini wita daga sama ba, wadda zata ƙone 'yar kukeear tawa ba, a fito da ita". Aka fito da Hafsa, DPO ya ce "Amma zaku dawo gobe in Allah ya kaimu, za'a kashe case ɗin da wanda ya shigar da ƙarar". Aka bawa Khalil wata takarda ya yi rubuce-rubuce, Sannan aka bawa Hafsa damar bin Khalil. Suna fitowa harabar wurin Khalil ya ce "Babyna ba suyi miki komai ba dai ko?". Ta jinjinawa Khalil kai. "Ki gaya mini ko sun miki wani abun?" Ta kuma girgiza masa kai. "To Allah, maza muje mota, Mama na can gida bata san in da ki ke ba". Ba musu ta bi Khalil, ya buɗe mata bayan motar ta shiga, Khalil ya shiga ɗaya gefen ya zauna, Abdul kuma ya ja motar suka tafi. A ƙofar gida suka tarar da Mama, tana ta kuka, maƙota sun kewayeta suna ta bata haƙuri suna rarrashinta, amma sai gursheƙen kuka take yi. Da gudu Hafsa ta fito daga motar ta rungume Mama tana kuka, Khalil da Abdul suka ƙaraso, suka gaida Mama sannan Abdul ya ce bari suje suyi sallar magariba, sai su dawo dan an fara kiran salla. Maƙota suka dinga shiga yiwa Mutane su Mama jaje, wasu dama zuwa ganin ƙwaƙwaf suke yi. Bayan sun dawo daga salla, suka koma gidan su Hafsa, Mama tayi mus iso zuwa cikin gidan, ta shimfiɗa musu sallaya suka zauna, yayin da ita da Hafsa suke zaune a kan tabarma, Hafsa tana kusa sa Mama kamar za a ƙwace mata ita. Khalil kuwa sai mamakin ƙanƙantar gidansu Hafsa, kai da gani ba sai an gaya maka ba suna fama da rayuwa, wani irin tausayin Hafsan ya ƙara kama shi. Suka kuma gaisawa, Mama ta ce "Sai dai ban gane ku ba, ko jami'ansa tsaro ne na farin kaya?". Abdul ya ce "A'a Mama, ni sunana Abdul, wannan kuma Khalil" nan ya kwashe yadda suka gano Hafsa har suka dawo da ita gida. Mama ta ce "Allah sarki, yau gani ga Khalil muna gaisawa a waya, ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi, Allah ya jiƙan magabata, idan suna raye Allah ya ja da ransu, yadda kuka faranta mini ubangiji Allah ya faranta muku" Abdul ya ce "Ameen Mama, bakomai ai yiwa kai ne" Mama ta mayar da dubanta ga Hafsa ta ce "Hafsa, meya haɗaki faɗa da namiji a wurin sana'arki har ki ɗau makami?". "Mama wai kin yadda zan ɗau makami in illata wani?" Tayi maganar a raunane. "To Hafsa meya haɗaki faɗa da wani, har a kai ki wurin hukuma?". "Mama ni ban nunawa kowa makami ba, Ƙona shi nayi da mai a ƙafa". Mama ta buɗe baki ta ce "Hafsa wa kika ƙona da Mai?" Cikin kuka ta ce "Mama Najib ne fa, yana zuwa wurin sana'ata ya ci mini mutunci, na kasa jurewa na ɗau wannan matakin" "Amma Hafsa kin taɓa gaya mini? Sai ki yanke wannan hukuncin haka?" Khalil ya ce "Mama ayi haƙuri, kinga kamar haryanzu a tsorace take" Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, na gode muku sosai Allah ya jiɓanci lamuranku" Abdul ya ce "Ameen Mama, gobe in Allah ya kaimu zamu zo muje station ɗin, a rufe case ɗin gaba ɗaya". "To Allah Ubangiji ya kai mu na gode sosai". Har ƙofar gida Mama ta rako su Abdul, tana ta cigaba da sa musu albarka. Khalil ya buɗe motar ya ɗauko wata ƙatuwar leda ya ce "Ga Abincinta da muka sai mata a hanya ba ta samu taci ba" da haka suka yi sallama su Abdul suka tafi gida. Suna tafe Khalil na sake jinjina yanayin rayuwa da su Hafsa ke fama da shi. Hall ɗin exam ya cika ya batse, ɗalibai sun duƙufa suna ta rubuta abin da suka sani. Fadila kuwa abin da ta sani bai kai ya kawo ba, ta ɗaga kai taga yadda Yazeed idaan ya samu dama yake taimakawa na kusa da shi, ga lokaci ya ja, tuni wasu ɗaliban sun fara bayar da tasu jarrabawar suna fita, amma ita tana zaune bata rubuta abin kirki ba, kanta ya ɗau zafi sai gumi take ta goshi. Cikin sa'a ɗalibai suka ragu daga hall ɗin, invigilator ya mayar da Fadila kusa da Yazeed, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Fadila ba, tana sa ran Yazeed ya taimaka mata. Sai dai taga Yazeed ya yi mursisi ko kallon in da take yaƙi yi. Wankin hula na neman kai Fadila dare, lokaci na ta tafiya, a kowane lokaci za a iya karɓewa, saboda lokaci ya kusa cika. Bata ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da taga Yazeed yana tattara takardunsa, zai tashi yayi submitting. TOFA, ZATA BAR YAZEED YYO SUBMITTING, KO KUMA ZATA SAUKE IZZA TA NEMI TAIMAKO? Domin gyara, sharhi ko shawara 08081012143 READ THE CHAPTER 15 AT AREWABOOKS https://arewabooks.com/chapter?id=6386388f094c9b1220e3fdb9. GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 P 15 Ganin da gaske Yazeed yana shirin tashi ya tafi ba tare da ta kammala ba, ya sanya a hankali fadila ta ce "Ban gama ba fa" Wani miskilin murmushi ya yi, ba tare da ya bari Fadila ta gani ba, ya ɗan tsuke fuska ya kalleta ya ce "Magana kike?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Ban ji me kika ce ba?" "Ban gama ba?" Ta furta a hankali. "Kina buƙatar taimakona ne?" Ta jinjina kai alamar eh. Yazeed ya gyara zamansa ya ce "Me kike buƙata?" Nan ta gaya masa wanda ba tayi ba a tambayoyin. Ya ajiye mata takardarsa ya ce "Gashi nan kwafi". "Ka karanto mini, bana iya ganowa sosai". Murmushi Yazeed ya yi, yana karanta mata a hankali. Invigilator ne ya fita, hakan ya bawa sauran ɗaliban ajin, damar cigaba da taimakawa junansu, tuni Fadila ta manta ta matsa kusa da Yazeed tana wanke takardarsa, jin jikinta ya fara rawa ne ya sanya ta lura tana kusa da shi, dan haka da sauri ta ja da baya, tana sauke numfashi. Kallonta yayi yai murmushi ya ce "Kin gama ne kika matsa?" "Ban gama ba" ta faɗa a raunane. "To ƙarasa mana, zan tashi in kai fa". "To ka karanto mini mana" "Ki kwafa mana ni na gaji" ya faɗa yana jin daɗin yanayin. A hankali ta kuma matsawa kaɗan ta cigaba da kwafa, amma tuni gumi ya fara yankomata, tana rubutu hannunta na rawa. "Ki nutsu mana, lokaci ya kusa ƙurewa kuma sai rawar jiki ki ke, kin kasa rubutun" da ƙyar Fadila ta ƙarasa saboda gaba ɗaya bata iya tantance yanayin da take shiga idan tana kusa da shi, idan yana nesa da ita ne take iya tatala masa rashin mutunci son ranta, amma da sun samu kusanci sai ta rasa nutsuwarta, sai da ta gama sannan Yazeed yaje yayi submitting. Ajiyar zuciya ta dinga saukewa a jere, saboda yadda ta sha da ƙyar, bayan ta fito ta hango Yazeed a wurin motarta yana waya, da 'yar ƙaramar wayarsa, ya jingina da jikin motar dan haka ba halin ta buɗe motar. Tsayawa tayi ya kammala wayar, tana ta tunani a zuciyarta, godiya zata yi masa ko kawai ta share shi? Ya juya harshe sai zuba larabci yake a waya tamkar bai taɓa jin hausa ba, abin ya ƙara bata mamaki, abubuwa da yawa suna bata Mamaki game da Yazeed. Ya kammala wayar sannan ya waiwayo ya ce "Am sorry na tsayar da ke". "Never mind" ta faɗa a sanyaye. "Za muyi karatu ne ko yau ma tafiya za ayi?" Yayi Maganar yana tsareta da idanunsa. "Ni yunwa nake ji, kuma na gaji sosai". انت جميل ياحببتي Ya faɗa yana lumshe idanunsa. Kallonsa ta yi dan bata gane me yake nufi ba. "Yunwa ki ke ji, kuma ke kin gaji, kar ki nuna kin san Yazeed gobe in Allah y kaimu a exam hall". "Eh ai nima ba daƙiƙiya ba ce, yau ɗin ma dai kawai na kakare ne" tai maganar cikin tsiwa tana masa kallon up and down. "Ni a ina nace miki daƙiƙiya ukhti? kalen faɗa ne dai kike yi, kuma ba zaki yi dani ba, aje gida a ci Abinci lafiya". Ɗan taɓe baki tayi, ta hau motarta ta kunna ta ja ta bar wurin. Ƙarfe goma na safe, Su Khalil suka je suka ɗauko su Mama, Khalil sai kallon Hafsa yake yi, amma tun da ta gaishe shi bata sake ce masa uffan ba, sai hira da suke da Mama jefi jefi. Goma da rabi suna station ɗin da aka karɓo Hafsa, suka isa wurin, DPO sai haba haba yake da su, har da yiwa Hafsa wasa, wai "Hajiya Hafsa babu gaisuwa ne?" Wata uwar harara ta watsa masa ta kauda kanta. Suna nan zaune sai ga Najeeb ya ƙaraso da shi da wasu matasa guda biyu. Mama na ganinsa ta haɗe rai, taƙi ko kallon in da yake, ya shigo yana ɗingisa ƙafa. Shima wani banzan kallo ya yiwa su Hafsan sannan ya ƙarasa ciki ya zauna, suka gaisa da DPO ya maida idonsa kan Khalil da Abdul dake wurin, yana mamakin su kuma wannan daga ina?. DPO ya ce "Yauwa Najeeb, ga wanda suka zo suka yi belin Hafsat a jiya, dama na gayyace ku ne gaba ɗaya a zo a zauna a teburin sulhu, tun da dai shi sulhu alkhairi ne". "Kamar yaya aka bada ita beli, haba DPO haka muka yi da kai? Yarinyar da ta nemi ta halakani". "Dama kai ne kasa aka kamata? Har kake iƙrarin dan me aka bada belinta?, kai ko kunya baka ji, wannan ce zata halaka ka garjejen ƙato da kai?" Khalil yayi Maganar yana zaro ido. Najib ya ce "Kai kuma awa? Me ya kawo ka cikin wannan case ɗin, abu ne na family issues 'yar uwata ce ina ruwanka?". "Wallahi ni ba ɗan uwan bane, babu wata alaƙa tsakani da shi, dan Allah Yallaɓai ka mini tsakani da shi kar ya sake zuwa in da nake, ba ruwanshi dani, dan Allah" Hafsa tayi maganar tana kuka. DPO ya ce "Wai dama ka santa ne?" Ya tambayi Najib. "Yallaɓai 'yar uwata ce, wani misunderstanding ne kawai ya gifta ake samun wannan akasin" Duk da sanyin hali irin na Mama, amma nan da nan fuskarta ta sauya, ta ce "Kar ka ƙara danganta kanka da 'yata, baku da wata alaƙa da mu". Najib ya ce "Ai dama ba dake na ce ba, bani da wata alaƙa da ke, amma ina da ita da Hafsa". "Shut up malam" Khalil yayi masa tsawa. "Wallahi kai mana rashin hankali a nan, sai na saka an samaka sarƙa, mahaukaci kawai". DPO ya ce "Dan Allah ya isa haka, wannan hayaniyar duk ba mafita bace. Ke Hafsa meye haɗinki da shi, da har kika ƙona shi?". Hafsa ta share hawaye ta ce "Karo kusan uku kenan, yana zuwa wurin sana'ata yana ci mini mutunci yana zagina a gaban mutane, ni kuma na gaji na rasa yadda zan yi kawai na zuba masa mai a ƙafa, kuma ina da shedu a gaban mutane yake zuwa kaina yana ci mini mutunci". "Amma me yasa baki yi wannan bayanin jiya ba, da muka tambayeki?". Khalil ya ce "Amma duk ba kuyi wannan binciken ba, kuke iƙrarin zaku kaisu kotu, anya makuwa ka san aikinka?" DPO ya ce "Wannan abu dai duk kuskure ne an riga anyi shi, saboda shi abin da ya zo ya gaya mana daban, ita kuma taƙi Magana, amma insha Allah yanzu za a rufe case komai ya wuce". "Eh, a rufe case amma ba komai zai wuce ba, idan aka rufe wannan case ɗin ni kuma zan shigar da ƙararsa a kan cin mutuncin da yayi mata, kuma Wallahi CID zan kai shi, ba dai abun wa ka sani wa ya sanka bane? Zan masa abinda ya yi". Abokan Najib da suka rako shi wanda ba suyi magana ba tunda suka zo, ɗaya daga cikin su ya ce "Dan Allah dai kayi haƙuri komai ya wuce, kuskure ne an yi, ayi haƙuri". "Dalla rufe mini baki, waye ya sa da kaiz' ba dai kuna ƙaryar rashin mutunci ba, kawai ya sa aka kama yarinya aka rufe, bayan laifinsa ne, ba zaku bar nan wurin ba zan waya azo a tafi da shi, koma a haɗa da ku duka" yayi Maganar yana zaro wayarsa daga aljihu, aka dinga bawa Khalil haƙuri,ƙarshe sai da Mama ta saka baki ta ce "Bakomai Khalil, wannan taimakon da ka yi mana ma mun gode, bana son wani abu ya sake shiga tsakaninsa da 'ya ta, kawai ka sa a musu iyaka, kar ya kuma zuwa wurin da take". Da ƙyar Khalil ya haƙura aka rufe case ɗin nan, dan sai da Abdallah shima ya saka baki, sannan aka rufe case ɗin, suka ɗau su Hafsa a mota suka tafi mayar da su gida. Najib kuwa mamaki ya dinga yi, waye Khalil a ina su Hafsa suka samo wanda ya tsaya musu haka? A iya saninsa basu da kowa basu da Komai, amma ya akai Khalil ya shigo rayuwarsu, ya so ya kuma amfani da damrsa ya wulaƙanta Hafsa son ransa, daga ita har Mama, amma ya lura wannan Khalil ɗin yafi shi zafin kai da masu gidan rana, idan ya matsa shi ne zai kwana a ciki. Khalil ya so yaji alaƙar dake tsakanin su Mama da Najib, amma ganin kamar basa son zancen ya sanya shi yin shiru. Yau ma har gida suka kai su Hafsa, Mama nata musu godiya da sa albarka, Mama ta nufi gida, Hafsa ma ta biyo ta. Mama ta kalli Hafsa ta ce "Ke wace irin Yarinya ce mara lissafi? Har a miki wannan abin Arziƙi amma ba zaki tsaya ki sake masa godiya ba? Maza koma kije ki kuma yi masa godiya". Cikin sanyin jiki ta koma inda su Khalil ke ƙoƙarin tafiya, taje ta tsaya ba tare da ta ce uffan ba. Khalil ya sauke glashin motar, ya kalleta ya ce "In zo ne?" Ta jinjina masa kai alamar eh. Ya buɗe motar ya fito, ya tsaya a gabanta ya ce "Gani ranki ya daɗe". Ta ɗan yi turus, Sannan ta ce "Dama, ce maka za yi Na gode sosai da taimakon da kayi mini, Allah ya saka da alkhairi". Khalil ya yi murmushi ya ce "Meye abin godiya, dan mutum ya yiwa matarsa abin daya dace?" Da sauri ta ɗago ta waro masa manyan idanunta. "Kin san wani abu Hafsat?" Ta girgiza kai. "Ina kishinki da yawa, bana son zaman da kike a titin nan, dan Allah ni dai ki daina". "Idan ban zauna a titi na yi sana'a ba, da me zamu rayu?". "Ba zai gagara ba Hafsa, ni dai dan Allah ki daina, kuma very soon nake son ayi zancen aurenmu". "Na gode sosai da taimakon da ka mini, amma ni ba zan aureka ba, ka ƙyaleni a yadda ka ganni kawai" "Amma Hafsa saboda me?" Ƙwalla ta taru a idanunta ta ce "Dan Allah kar kayi amfani da damar ka taimakeni ka turasasa mini yin abin da bani da ra'ayi a kansa, dan Allah ka ƙyaleni". "Hafsa ba kya tausayina ko? Kin san so kuwa? Saboda ke fa na baro aikina na taho, kawai dan na ganki, meyasa ba zaki dubeni ba. Ko ina da wani aibu ne ban sani ba?". "A'a, baka da wani aibu ni dai kawai ka rabu da ni". "Shikenan tunda haka kike so, jibi in Allah ya kaimu zan koma, zan zo muyi sallama, ina sonki sosai Hafsat. Kalmar ina sonki, ta daki Hafsa sosai, dan har cikin kwayarta taji tasirin kalmar, amma ba ta jin zata iya yadda da soyayya balle tayi aure, gara su cigaba da lallaɓa rayuwa ita da Mama. Khalil bai taɓa zaton akwai ranar da zata zo, ya dinga 'yar talakawa kamar Hafsa yana neman soyayyarta tana gara shi ba. Aminatun Baba Hassan kuwa, ta ƙara kilewa sosai da sosai, tayi sababbin ƙawaye, gashi nan da nan ta zama sananniya a makarantar saboda ƙoƙarinta da kuma surutunta, suna ta shirye shiryen fara jarrabawar zango na farko. Amina ta mayar da hankali wurin tattalin haddar Alqur'aninta bata zube ba, dan tana yawan tilawa kuma ta cigaba da rubutun alƙur'ani tana sake gyara kura kuranta,ta ɗora haddarta tana samun masu duba mata a makarantar. Hajara ce a sashen Mummy, tana ta aikace aikace, Hajiya Zainab ta fito ta tarar da ita a falonta, ta kalli Hajara ta ce "kira mini 'yar mai gadin nan" Hajara ta ce to, ta tafi kitchen ta kirawo Amina. Suka dawo tare. Hajiya Zainab ta kalli Amina ta ce "Muje sashen maigidan na nake so a gyara a yiwa kwalema, gobe in Allah ya kaimu zai dawo". Amina ta ce "To, amma na ɗora girkin rana". "Bar shi ita ta ƙarsa, muje in buɗe miki wurin" Amina tabi bayan Hajiya Zainab, zuwa sashen da take kyautata zaton shi ne na Alhaji Ahmad. Masha Allah, yafi ko ina kyau da tsaruwa a gidan, duk ya yi ƙura amma hakan bai hana sashin yin kyau ba, duba da kayan alatun da aka ƙawata wurin da shi. "Gashi nan, ki gyara duk abin da yakamata, karki mink rawar kai ko kiyi abin da ban saki ba, ki gama aikin da na saki ki fito". Amina ta ce "To insha Allah". Bedroom kawai guda biyu ne a sashen, kowanne ya sha furnitures na alfarma. Falon kawai gari ne guda, dan set ɗin kujeru biyu ne a falon. Amina mamaki ta dinga yi, duk wannan aljannar duniya, amma ace mutum sai ya bar gida har wurin watanni uku ba nan, yana wata uwa duniya ta daban. Amina haka ta dinga tular uban aiki, da tana ganin kamar aikin babu yawa, amma da ta fara taga aikin nayi ne, haka ta zage, wanke wannan goge wancan, karkaɗe can haka ta kusa wuni tana fama, sai dai idan za tayi salla ta ajiye aikin taje tayi. Sai da ko ina ya zama tsaf ta gyara, sannan ta koma da baya, tana ƙarewa ko ina kallo, ta tabbatar komai ya gyaru tsaf, hankalinta ya sauka a kan katafariyar plsma tv wadda ta kusa cin rabin bango, tunani ta fara yi a ranta, ko a cikin wannan tv mutane sunfi girma a kan sauran ƙanan tv. Take zuciyarta ta raya mata ta kunna taga ya zata ga mutanen cikin. Aikuwa Amina ta ƙarasa, ta kunna Tv da fari sai da ta rage yadda ta ware idanunta, saboda hasake da kuma yadda taga mutane sun bayyana a tv, kamar ta zura hannu ta ɗauko su. A hankali ta buɗe idon, ta cigaba da kallon mutanen tv, shaf ta manta da a ina take, ta samu wuri ta zauna a kan kujera, tana cigaba da kallon Tv. Sai ga Amina ta bararraje ta shantake, ta cigaba da kallo abinta hankali kwance. "Ke ubawa ya baki izinin zama a kan kujerar nan? Lallai ne gidan ubanki ne nan ɗin?" A tsorace Amina ta waiwaya ta kalli in da Hajiya Zainab ke tsaye tana nunata da yatsa. Da sauri Amina ta tashi tsaye, tana rarraba ido. "Waye ya ce ki zauna a falon mijina, har ki harɗe ƙafa kina kallo, nawa ne a ciki kuɗin babanki da aka haɗa aka gina ɗakin aka zuba furnitures ɗin?" Babu babban abin da ke ƙular da Amina irin da tayi laifi, sai a fara ambaton Baba ana ci masa zarafi. Amina tayi shiru tare da sunkunyar da kai, tana jin yadda sautin maganganun Hajiya Zainab ke amsa kuwwa a cikin kunnuwanta, suna sukar zuciyarta. Maganganun Baba ta tuna, da yake nanata mata ba yau ba gobe a kan tayi haƙuri, dan ta samu ta kammala karatun ta lafiya, hakan ya saka nutsuwa da haƙuri ya shigeta, a sanyaye ta ce "Dan Allah kiyi haƙuri, insha Allah ba zan sake ba". "Ki ma sake, munafuka sai kin yi rashin mutunci ki koma kina wani kwantar da kai, ni zan fita Yanzu, ki zo ki wuce ki bar sashen nan, idan na fita daga ke sai halinki a gidan, idan kin ga dama, ki kuma aikata wani rashin mutuncin, sai kin koma in da ki ka fito" Amina dai ba tace uffan ba, sumi-sumi ta bar falon, ƙasan zuciyarta kamar ta ƙundumawa Hajiya Zainab ashariya, dan ɓacin rai. Ɗakinta ta koma kawai ta fashe da kuka, dan ta samu sassauci daga zafin da maganganun Hajiya Zainab ke mata a zuciyarta, gaba ɗaya zaman gidan ya sire mata, sai da tayi ta gaji, sannan ta wanke fuskarta ta fito, tana fitowa babban falon gidan ta ci karo da wasu manyan mata, kai da ka gansu kaga gogaggun 'yan duniya, sun sha ado sai baza ƙamshi suke. Ɗaya ta kalli Amina ta ce "Ashe da mutane a gidan, muke ta kwaɗa sallama amma shiru". Amina ta ce "Eh da mutane, amma masu gidan basa nan". "Tayi nisa ne?" Suka tambayeta. Amina ta ce "Ai da yake ni ɗin ba 'yar ta bace, balle in san in da ta tafi, bata gaya mini ba sai dai ku kirata a waya" "Ikon Allah, ke baki iya magana bane?" Amina tai shiru ba tace komai ba, suka sami wuri a kan kujera suka zauna, Amina ta kalli ƙafar ɗaya daga cikin su, fuskarta fara tas ta sha mai, amma ƙafarta kamar ta ƙone ga ƙafar ta ta kamar ta maza, ga taƙi ɗaukar bleaching ɗin. A zuciyarta ta ce "Ikon Allah, wata ƙatuwar ƙafa kamar ta Jarmai". "Ke ɗan bamu ruwa, ƙishirwa ta dameni". Amina ta koma ciki ta ɗoro pure water biyu a plate ta kawo ta ajiye musu. "Hajiya Sarah, yau nake ganin ikon Allah, wace irin 'yar aiki Zainab ta samo haka bagidajiya, ke mun miki kama da wanda zasu sha wannan ruwan? Babu na roba?". "Ai gidan nan baƙi ba su da hurumin shan ruwan roba, na leda kawai aka ce in bayar guda ɗaya" tayi maganar tana ɗan hura hanci, alama matan sun fara takurata. Nan suka cigaba da hirarsu da 'yan zage-zagensu, Amina kuwa ta bar musu falon. Kusan Mintuna talatin Amina ta kuma fitowa da niyyar idan sun tafi, ta gyara falon amma ta tarar da su basu da niyyar tafiya, sai ma ƙure tv da suka yi suna kallo. Ba tunanin komai ta wuce ta kashe socket ɗin tv gaba ɗaya. "Ke lafiya, meye haka?" Cewar Hajiya Turai. "Ai ba wuta solar ce, kuma ta fara ƙara a kowane lokaci zata iya ɗaukewa, mai siyo fetur kuma baya nan, dan haka idan ta ɗauke ni za a saka zuwa sayen fetur ni ba namiji ba, kinga ai gara in kashe ai reserving solar". "Ke wai ke meye matsayinki a gidan nan ne?". " 'yar aiki" ta faɗa kanta tsaye. "Kin san mu suwaye da kike mana wannan iskancin?". "A'a Anty, ba laifina bane dokar matar gidance a haka". Hajiya Sarah ta ce "To bari Zainab ɗin ta dawo muji daga bakinta" Komawa kitchen Amina tayi, a ranta tana ƙunƙuni. Sai daf da magariba sannan Hajiya Zainab ta dawo gidan, ko da ta shigo falo ta tarar da su Hajiya Turai, suka sanya wata uwar shewa. "Hajiya Turai yaushe ki ka shigo ƙasar nan?" Hajiya Zainab tayi maganar tana ƙoƙarin zama, cike da mamakin da ya mamaye fuskarta. Turai ta ce "Sati na ɗaya, nace bari nayi miki zuwan bazata". "Amma Sarah meyasa baku gaya mini zaku zo ba? Ai da ban fita ba. Hajiya Turai mutanen Saudiyya" Nan suka ɓarke da hirar yaushe gamo. "Kun ci abinci kuwa?". "Wane Abinci, ke dai a garin yayime yayimenki sai kin yayi mo mai zane ki, wata tsigalalliyar yarinya muka tarar marar mutunci, ko ruwa hanamu tayi sai pure water ta bamu". Hajiya Zainab ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan Yarinyar ta zame mini jaraba, tun da tazo gidan nan nake fama da ita". "To ki sallameta mana" Hajiya Sarah ta faɗa tana yatsuna fuska. "Yarinyar ce tunda nake masu aiki, ban taɓa samun 'yar aiki mara son jiki kamarta ba, ba ta jin jikinta wurin aiki, ba ta da ƙyuya ba munafunci, sai iya shege da rashin mutunci a cikinta. Sai naji kamar in koreta amma sai in tuna irin aikin da take mini in ƙyaleta". "Ai irin haka warning zaki kasa mata, koma ki bata suspension, Yarinyar bata da kunya sam". Rai a ɓace Hajiya Zainab ta dinga ƙwalawa Amina kira, ita sam Amina ma bata san ta dawo ba, ƙasa-ƙasa take jiyo kiran, ta fito falon tana sussunkuyar da kai kamar mara gaskiya. "Ke shine nayi baƙi kika wulaƙanta su, ki ka basu ruwan leda dan baki da mutunci?" "Hajiya kefa kika ce kar in sake bawa duk wani baƙo ruwan roba balle Abinci sai pure water, shiyasa na basu". "Kuma dan baki da hankali wannan sun miki kam da waɗancan ne? Ƙawayena ne wannan tun na ƙuruciya saboda baki da mutunci sai ki wulaƙanta su? Ke nifa na gaji da wannan iskancin naki, bari shi me gidan ya dawo, ki koma ƙauye ki cigaba da shan baƙar kuka. Kin zo birni kin sha miya zaki miƙe ƙafa kina mini iskanci" ta sunkuyar da kai tayi shiru ba ta ce uffan ba, suka haɗu su uku suka mata wankin babban bargo. Tun abin na damun Amina, ta fara daina jin komai, ta fuskanci kamar ɗabi'a ce ta masu kuɗi, wulaƙanta wanda suke ƙarƙashin su, suka ƙare mata zagi da cin mutunci tsaf, sannan suka sallameta. Harabar gidan ta koma, tayi zamanta ya yin da Baba yake bakin gate yana aikinsa. Abdul da Khalil ne zaune a ɗakin Abdul, Khalil ya zuba uban tagumi. Abdul ya ce "Wai kai Khalil meye haka ne? Sai ka sanya damuwa a ranka ka kasa sukuni?". "Abdul ba zaka gane bane, ni kaina ban taɓa zaton abubuwa zasu cakuɗe mini haka ba. Baka san yadda nake jin yarinyar nan a raina ba, amma naga tana da taurin kai, babu alamar zan sameta na karaya Abdul". "Haba Khalil, kar ka karaya, ka san meye matsalarka? Garaje da gaggawa idan kabi komai a sannu zai zo maka a sauƙaƙe, yanzu kana jin abin da nake ji game da ƙanwarka ko? Hmm haka al'amarin so yake, na san babban yaro kamarka da mata ke rushing a kansa, abin mamaki ne ace ya maƙalewa 'yar talakawa kamar wannan, amma haka sha'anin so yake. A yanayin Hafsa kamar akwai wani ɓoyayyen abu da yake damunta a zuciyarta, dan haka domin shawo kanta, sai ka rage shishige mata, da cigaba da nuna mata soyayya, ka danne son kawai ka nemi ku saba da ita. Ka dinga kyautata mata da kulawa ka fara gano meye matsalarta kan ka cigaba da nuna mata soyayya". Khalil ya ɗan yi shiru sannn ya ce "Kana ganin hakan mafita ne?. "Ita ce babbar mafita, tunda soyayyar ce ba ta so, to ka bar shi a friendship ka gama fuskantar ta tukuna". "Shikenan, zan jarraba hakan, insha Allah gobe in Allah ya kaimu zan koma wurin aiki, zan jarraba shawarar taka". "Wai da gaske ba zaka gida ba?" "Abdul idan naje Mummy tuhumata za tayi a kan dalilin dawowata, ba sai naje ba, sai nan da kamar 3weeks zan kuma dawowa insha Allah" "To shikenan, Allah ya kaimu sannan ya daidaita ku". Yau sai shida na yamma suka kammala jarrabawar yau, kanta har wani juyawa yake yi saboda ta gaji yau sosai da sosai, da ƙyar take iya ɗaga ƙafafuwanta, saboda zaman ajin. Jarrabawowin yau Alhamdilillah tayi abin Arziƙi da kanta, dan tayi karatu sosai da sosai. "Hmmm Madam, glucose yayi ƙasa ne naga kina tafiya da ƙyar?" Cak ta tsaya tana ɗan sauke numfashi, ta waiwayo ta sauke masa gajiyayyun idanuwanta da suka ɗan yi ja saboda gajiya. "Yau ko nemana ba ayi, tun shekaranjiya ko kallon in da nake ba balle a harareni. Amma ina fatan kin gama komai dai ko?". "Ban gama ba, jira nake kazo ka ƙarasa mini" Sauke facemask ɗinsa ya yi ya ce "Me kika ce?". "Ban sani ba" ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba. "Kalleni ki faɗa mana idan ba tsoro ba" ɗagowa tayi ta kalli Yazeed, sai dai tayi saurin janye idonta daga nasa. "Dan Allah ka rabu dani". "Muje in rakaki wurin motar". "Ina da ƙafa ai" ta faɗa tana cigaba da tafiya sannu a hankali. "Ai ƙafar taki ce kamar ta gaji, da ƙyar kike tafiya, ko in ɗauke ki in kai ki motar ne?" Ɗagowa tayi ta kalleshi ta mayar da hankali a kan tafiyarta. Yusra ce ta tunkaro in da suke tana murmushi, ta kalli Yazeed ta ce "Patient ɗinmu, kai ne ka warware haka?" Yazeed ya yi murmushi ya ce "Alhamdilillah, jiki ya ware". "Haka ake fata dama, madam zuwa nayi mu tafi gida tare, yau ba mota a hannuna". Fadila ta ce "Gaskiya a gajiye nake gida zan tafi sai dai in ajiye ki a hanya". "Aikuwa baki isa ba, nima a gajiyen nake, ka sa baki ta kaini gida mana" Yusra tayi maganar tana kallon Yazeed. Yazeed ya ce "Wane ni, ku gaida gida". "A'a ka tsaya, saita ɗaukemu wallahi, muje ko rage maka hanya muyi". "A'a ba zan hau ba, Allah ya kai ku lafiya". Yusra ta ce "Dan Allah ka zo muje, ko a hanya mu ajiye ka". "A'a ni ba zan hau ba, wa zai hau motarta, ko tuƙinma bata iya ba, ta watsar da mu a hanya, ku sauka lafiya" kallon Yazeed tayi, tama rasa me za ta ce masa. Fadila na ƙoƙarin kunna mota ne, Yusra ta ce "Wallahi Fadila kun dace da gayen nan, anya ba sonki yake ba?" "Amma baki da hankali ko? Ke na miki kalar sa, karki ɓata mini rai". "Wallahi Fadila ni tausayi yake bani gaba ɗayansa, Wallahi kamar sonki yake" Fadila ta haɗe rai ta ce "Yusra bana so, karki sake haɗani da shi" "Ai shikenan, bari mu zuba ido mu sha kallo". Wani irin horn Fadila take yi a ƙofar gidan tamkar zata daki gini idan ba a buɗe ba, Baba kuma ya shiga banɗaki a lokacin, ba tare da ya kammala abin da yake ba, ya fito bagatatan ya buɗe mata gate ɗin, ai ko kashe motar ba tayi ba, ta fito ta hau Baba da bala'i ta in da ta shiga bata nan take fita ba, ya risuna ya dinga bata haƙuri. Haka ta nufi cikin gida fuuu kamar guguwa, ba ta tsaya ta saurari Mummy tana da baƙi ba ta hau bala'i a falon "Gaskiya Mummy ku sallami wannan tsohon, haba ai ko aikin gwamnati ne ha kai yayi retire mutum sai bai san aikinsa ba, ya bar mutane a waje ina ta faman horn sai kace wani kurma, gaskiya na gaji a sallame shi. Ga securites nan na kamfani Daddy ya ɗauko amma ya dage a kan wannan baƙauyen, mara kuzari, saura kaɗan in zage shi yau". Jikin Amina ne ya ɗau rawa, ta kalli Fadila ta ce "Baban nawa zaki zaga?". DOMIN GYARA SHARHI KO SHAWARA 08081012143 READ THE CHAPTER 16 OF GABA DA GABANTA AT AREWABOOKS https://arewabooks.com/chapter?id=638b441e942c7e82ce7bfb71 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 P16 "Eh, shi zan zaga ko akwai abin da zaki iya yi a kai?" Fadila tayi maganar cikin isa da iko. Maganganun Baba ne suka dawowa Amina a cikin kunnuwanta, tabbas idan ta ɗau mataki, ta san dole ta koma ƙauye, kuma babu abin da zai hana aurenta da Jarmai, jikinta na rawa hawaye na zuba daga idanunta, ta juya ta koma jikinta a sanyaye, Allah kar nuna mini ranar da za'a zagi Baba a gabana, ba zan iya jurewa ba. Fadila ba ta kalli baƙin Mummy ba, ta wuce ɗakinta tana cigaba da huci kamar wata mesa. Hajiya Turai ta ce "Wai dama 'yar mai gadinku ce?" Mummy ta ce "Eh, 'yar sa ce". "Lallai ne, ai gara da Fadila tayi mata hakan, yaran nan idan ana saurara musu miƙe ƙafa suke yi su yi ta iskanci kamar a gidan ubansu" Hajiya Zainab ta ce "Wallahi kuwa, ai Fadilan ce dai-dai da su". Fadila kuwa a gajiye ta ƙarasa ɗakinta, ta jefar da mayafinta, ta tuɓe doguwar rigar jikinta, ta shiga cikin banɗaki, ta haɗa ruwa mai ɗumi tayi wanka, ta yo alwala ta fito, sallar magariba ta gabatar ta idar, sannan ta shirya kanta cikin riga da skirt, na English wears ta fito. Sai a wannan karon sannan ta gaida baƙin Mummy, ta wuce kitchen. Amina ta gani a tsaye idanunta sun yi jawur, kamar ta kwana ta wuni tana kuka. "What do you cook for dinner?" Fadila ta tambaya cikin ko in kula. Zuciyar Amina na tafasa, tamkar ta ce mata ubanki na dafa, amma ta dann ta ce "Tuwon semovita". "Ban ci Abincin rana ba, dan haka ba zan ci tuwo ba, ki dafa mini cous cous vagetable cou cous da irish, ki hanzarta kuma" tana gama maganar ta jiya ta fice. Muciya Amina ta rarumo, ta ɗaga sama kamar ta bi bayan Fadila, ta sauke mata wannan dogayen kafaɗun nata, masu kama da dirakun firamaren garinsu. Amina tana kuka tana yiwa Hajiya Zainab Allah ya isa, ta yiwa Fadila girkin nan ta kai mata, ta koma ɗakinta. "Hafsa ni dai ina tsoron sake komawarki wurin sana'ar nan, bana son wannan yaron ya zo ya kuma ɗaga mana hankali". "Mama idan ba wannan sana'ar ba wacce za muyi? Idan a gida nace zan cigaba da saida awarar nan, ya zama mu uku muke awara a layin nan fa, kusan duk wata sana'a da zamu yi, a na yinta a cikin unguwar nan, zama haka ba zai yiwu ba Mama". "Haka ne, amma dama can sana'ar nan ba sonta nake ba, bana ƙaunar zaman titin nan da kike yi, ni ban san ma yadda aka yi yaron nan ya san inda kike sana'a ba". "Mama ba zai ƙara zuwa ba insha Allah, kuma kinga ai Khalil ya sa an mana tsakani da shi". Mama ta ce "Ni kuwa naga kwana biyu ko kiranki ba ya yi a waya, ko wani abun ki ka yi masa ne?" Hafsa ta ɗan yi jimm, sannan ta ce "A'a babu abin da nayi masa". "Ai maganrki ba abar yadda ba ce wasu lokutan, bana raba ɗaya biyu wani abun ki ka yi masa, ai shikenan kan ki kika yiwa, sai muyi ta jerawa a gida, 'yan unguwa suna mana ƙazafi, Da kin amince wa yaron nan, na tabattar zai riƙe mini ke amana, yaro mai rufin asiri kamar wannan, ya liƙe miki alhalin ke ba kowa ba, ai kuwa Wannan son shine na gaskiya". Gaba ɗaya jikin Hafsa ya yi sanyi, ta tuna maganganun da ta gayawa Khalil, kan ya tafi duk da abin arziƙin da yayi mata, wanda ba dan shi ba, da bata san iya wulaƙancin da Najib zai yi mata ba. Ko ya dai na sona ne, tunda ya daɗe haka bai kirani ba? Ta tambayi kanta. 'gara ma ya haƙura ya daina sona, dan ba zai iya aurena ba' ta sake bawa kanta amsa. Khalil kuwa daurewa kawai yake yi, amma zuciyarsa na raya masa ya kira Hafsa yaji lafiyarta, kar yaje wani abun ya sake samunta, amma idan ya tuna da shawarwarin Abdul, sai ya haƙura da kiran nata. Har washegari Amina bata sake ba, tana jin ɗacin abin da aka yi mata a zuciyarta, sai da taje makaranta ne ma, ta ɗan haɗu da ƙawayenta shine ta ɗan sake, amma cikin zuciyarta babu daɗi sam. SHANONO. Can garin su Amina kuwa, facalolinta matan su Bala, suka sakota gaba, da zagi da kums habaice habaice, tare da yiwa Innon fatan masifu daban daban, a kanta da kuma Amina da Baba Hassan. In anjima suma su Lawan ɗin da kansu suke zuwa su isketa suyi mata bala'i, suka tattara wani tsohon keken Baba na hawa suka sayar, suka harhaɗa dan biyan Jarmai kuɗinsa, saboda yadda ya sako su a gaba, da fitina da cin mutunci, abu har gaban mai gari ana musu sulhu. Ƙauye dama tuni ya ɗauka, batun guduwar Amina birni, dan tayi karatun boko, mutan ƙauyen nan suka dinga Allah wadai da abin da Amina da babanta suka aikata. Yau su Fadila suka kammala jarrabawar wannan zangon karatun, ji take kamar gama makarantar tayi, saboda yadda duk jarrabawar ta takurata. Sir Abdulmaleek Kankia, wanda suke kira da Sir Kankia, ya zo wucewa ya kalli Fadila da ke tsaye, tana ƙoƙarin kiran waya cikin nishaɗi. "Fadila Ahmad Dutse" ya kira sunanta. Ta ɗaga kai ta kalleshi, shi ne lecturer da ya so ya kori Yazeed a kan littafi ranar, zuba masa ido tayi ba tare da ta ce komai ba. "Ko ba sunanki bane?". "Suna na ne mana" "In ba zaki damu ba, ina son ganinki a office ɗina". "For what?" Tayi maganar tana kallonsa. "For something very important to discuss" "Ka faɗa mini a nan mana, meye sai na bika Office?" "Abu ne da ya shafi jarrabawar ki". "Jarrabawata kuma?" Ta faɗa da mamaki. Ba tsammani ta ɗaga kai, ta hango Yazeed ya zuba mata idanunsa, ta rasa wani irin kallo ne, na tuhuma ne, ko kuma na menene ta kasa ganewa. Bayan sir Kankiya tabi da kallo, a hankali kuma ta ja jiki ta nufi wurin da Yazeed yake tsaye ya ƙureta da ido. "Fadila meya ke ce miki ya tsare ki haka? Fadila ta tsuke fuska ta ce "Meye na tuhumata kuma ina ruwanka?". "Da ruwana Fadila, ki gaya mini dan Allah". Ta ce "Cewa yayi wai in je, a kan wani abu ne da ya shafi jarrabawata". "Meya faru da jarrabawarki?". "Nima ban sani ba, ko dan mun yi iri ɗaya ne da kai" tayi maganar cikin sanyin jiki. "Ai ba jarrabawarsa ce muka yi iri ɗaya ba, amma kije kiji mai zai ce". "Am scared gaskiya" ta faɗa da rauni. "Meye abin tsoro kuma babbar yarinya, ai babu damuwa ina jiranki, kije ki dawo" Fadila duk tunaninta a kan jarrabawar su ne, haka ta nufi hanyar da zata tafi office ɗin Sir Kankiya. Ƙwanƙwasa ƙofar Office ɗin yayi, "Yes come in" A hankali ta tura ƙofar Office ɗin, ta shiga. Tun da ta shiga ya zuba mata ido, har ta ƙarasa cikin Office ɗin. Haushi ne ya kama Fadila, saboda ta tsani kallo a rayuwarta. Zuwa tayi ta tsaya tana kallonsa ta ce "Gani" Kankiya ya yi murmushi ya ce "Zauna mana". Ta ɗan hura hanci, ta ja kujera ta zauna, tare da basar da Kankiya. "Fadila Ahmad Dutse" ya kira sunanta. Ta ɗago fararen idanunta ta kalli Sir Kankiya. "Ke 'yar garin Dutse ce?" Ya tambayeta yana kallonta. "Babana ne ɗan garin" ta bashi amsa a daƙile. "Garin babanku ai garinku ne". "Sir dan Allah meyasa ka kirani? Meya faru da jarrabawata?". Sir Kankiya ya ce "Eh to, ba wani abu bane na damuwa da tashin hankali, akwai yiwuwar komai zai daidaita, amma ki rubuta mini lambar wayarki". "Me yasa zan bada lambar wayata?" "Saboda idan da buƙatar sake neman ki sai in neme ki kai tsaye" "To ai ni har yanzu ban san meya faru da jarrabawar tawa ba". "Zaki sani nan gaba kaɗan, ki rubuta mini lambar wayarki" ba tunanin komai, Fadila ta rubuta masa lambarta, sannan ta tashi ta fice daga Office ɗin. A harabar rukunin ofisoshin malaman ta tarar da Yazeed, ta kalleshi da mamaki, ta ɗauka tuni ya tafi. "Yaya aka yi? Meyafaru da jarrabawar?" Ya tamabayeta cikin ƙosawa. "Nima ban sani ba, bai gaya mini ba, sai dai karɓar lambar wayata yayi, ya ce idan akwai buƙatar a neme ni, za a kirani". Yazeed ya kalleta da mamaki ya ce "Ya karɓi lambar wayarki?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Hmm Mutumin nan sonki yake yi, ba wata jarrabawar ki da ta samu matsala". "What, ka san me kake cewa kuwa?" "Eh mana, think, idan wani abu ne ya faru da jarrabawarki shi ke da alhakin kiranki, You have all his attendance, kina da Attendance ɗinsa, teses ɗinsa kina da 25mrks, ga exams ɗinsa kin rubuta, meye matsalar kuma?" Ita babban abin da ya bata mamaki, ya a kayi Yazeed ya san makinta na test da kuma Attendance, ita wasu lamuran nasa ma tsoro yake bata. Gashi ya wani haƙiƙance sai masifa ya ke yi. "Idan ma sona yake ina ruwanka?" Ta faɗa cikin tsiwa. Cikin dakewa da maziya, Yazeed ya ce "Babu ruwana, Allah ya sanya Alkhairi, ya kaimu lokacin aure Mrs Kankiya". Wani mugun kallo Fadila ta yiwa Yazeed, tare da jan guntun tsaki tayi gaba. Da sauri ya sha gabanta, ya ce "Am sorry Please, yau fa zamu tafi hutu, Yakamata mu rabu lafiya ko ƙanwata?". "Ni ka ƙyaleni" tayi maganar a ɗan hasale. Zuba mata idanunsa tayi, wanda hakan ya sa taji wani abu na yawo a jikinta, da bata san menene ba. "Fadila me yasa kika tsane ni, me nayi miki, kina gani bana iya sakewa da kowa a makarantar nan, duk da ba kya ƙaunar ganina, amma ni ina jinki tamkar ƙanwata ciki ɗaya, dan Allah ki sassauta tsanar da kike mini, ko nayi miki wani laifin ne?" Shiru Fadila tayi, tana bin Yazeed da kallo, a hankali ta lumshe idanunta. "Fadila" ya kira sunanta. Ta ɗago ta kalleshi. "Me nayi miki kika tsane ni ne? Ko dan ni bagidaje ne, ban iya wanka ba, kuma ban iya turanci ba?" Ya ƙarasa Maganar yana kallonta. Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta kasa ko motsawa. "Let's be friends" Yazeed ya faɗa cikin sigar rarrashi. Ɗan tura baki tayi tana fici fici da ido, wata irin kasala na cigaba da tsirga mata, tun daga kanta har ƙafafuwanta. "Talk Fadila" ya faɗa yana marairaicewa "To wai ni me zance?" Ta faɗa tana tura baki gaba. "Be my sister" ya furta saɓanin abin da yake zuciyarsa. "Kaga, dan Allah ka bani hanya in wuce, gida zan tafi" tayi maganar a shagwaɓe. Babu tsammani, suka ga Kankiya ya ɓullo daga wajen da ofisoshin nasu suke, ya ɗan yi turus yana kallon su. Tunani Fadila ta shiga yi, da gaske mutumin nan sonta yake ya karɓi lambarta, amma da ya rainawa kansa hankali, wannan suka jero ai cewa za'a yi mai aikinta ne, wani sirirn tsaki ta ja ba tare da ta san ya fito ba. Wucesu ya yi ba tare da ya ce musu uffan ba, duk suka bishi da kallo, har ya bar wurin. Fadila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kaga ni na tafi" "Ok muje, nima tafiyar zan yi" ba wanda ya kuma cewa wani uffan, kowa yana saƙawa da warwarewa a ransa. Ta buɗe motarta ta shiga, Yazeed ya kalleta ya ce "To ayi hutu lafiya, kar a ajiye litattafai a daina karantawa, i will miss you ukty" Kallon Yazeed tayi, ta ɗan yi murmushin gefen baki. Har motar Fadila ta ɓacewa ganin Yazeed, yana tsaye yana kallonta, yana jin yadda zai yi kewarta. Da yamma Amina na harabar gidan, wurin Baba, tana ta zuba masa surutu, gabanta ga littafi da biro, tana karatun jarrabawa. Horn ɗaya aka yi ƙwaƙƙwara, Baba ya miƙe jiki na rawa, yaje ya buɗe gate ɗin, Zakiru direban Alhaji Ahmad, ya silalo da hancin motar, cikin harabar gidan. Ɗan dakatawa Zakiru yayi da motar, Baba ya ƙarasa Alhaji Ahmad ya sauke glashin motar suka tsaya magana da Baba. Amina haushinsa take ji yanzu, tun da Allah ya sa 'yar sa taci wa babanta mutunci, kwasar litattafanta tayi, ta bar wurin dan karma ta gaishe shi, ta shige cikin gida, a falo Hajiya Zainab ta dakatar da ita "Ke daga ina haka nake ta nemanki?". "Ina wurin Baba ne". "Ke nifa bana son sakarci, idan baban naki kika zo yiwa aiki, sai ki koma can bakin gate wurinsa, idan ya so ya dinga biya miki kuɗin Makarantar". Fadila da ke kwance a kan doguwar kujera, ta ɗan taɓe baki tana kallon yadda Amina ta haɗe rai. Alhaji Ahmad ne ya yi sallama a falon, zumbur Fadila ta miƙe jin Muryar mahaifinta, da sauri ta ƙarasa in da yake ta rungume shi "Oyoyo Daddy". "Welcome sweetheart" yayi Maganar cike da kulawa yana sake rungume Fadila. Hajiya Zainab ta ce "Ashe ka sauka?". "Wallahi kuwa, kin ganni nan sai yanzu" Amina tabi Fadila da kallo, Yadda ta ƙanƙame mahaifinta cikin kulawa da ƙauna. Ji tayi ina ma zata iya zagin Alhaji Ahmad, Fadila taji abin da ta ji, lokacin da taci mutuncin nata mahaifin, sai dai kash hakan ba tarbiyyar Amina bace, ko da wasan wasa ba zata iya aikata hakan ba, haka ta wuce ta bar musu falon suna cigaba da farincikin dawowarsa. Hafsa fa ta ɗan shiga damuwa, saboda rashin kiran wayarta da Khalil ya daina yi gaba ɗaya, gashi kuma ita ba zata iya kiransa a ta ta wayar ba, saboda a ganinta hakan bai dace ba. Amina ma sun fara jarrabawa a makaranta, ayyuka sun ɗan yi mata sauƙi, kasancewar yanzu Fadila bata zuwa Makaranta, ta rage tashin sassafe. Tun da Alhaji Ahmad ya dawo basu haɗu ba, har ta tafi makaranta bai fito ba, wasu lokutan baya dawowa sai dare sun kwanta. Duk kashedin da ake mata a kan zuwa wurin Baba tayi zamanta, ba ta ji ba, dan yau ma tana wurinsa suna hira, kasancewar yau Asabar, Baba yana gyara flowers ɗin harabar gidan, tana taya shi. Ƙamshin turaren Alhaji Ahmad ya cika wurin, Baba ne ya miƙe da sauri fuskarsa ɗauke da murmushi, yana yiwa Alhaji Ahmad barka da fitowa. "Ina wuni" Amina ta faɗa kamar an mata dole, dan ta san Baba zai iya yi mata faɗa idan bata gaishe shi ba. Ya waiwaya ya kalli in da Amina take "Lafiya ƙalau, ya school ɗin?". "Lafiya ƙalau". "Good" ya mayar da dubansa kan Baba ya ce "Malam Hassan ya aikin? Babu dai wata matsala ko?" Baba ya ce "Babu matsalar komai ranka ya daɗe". "To Alhamdilillah, Allah ya yi jagora". Baba ya amsa da "Ameen". Amina a ranta ta ce "Shi dai gashi nan, shima yana da wannan taƙamar, sai dai baya wulaƙanci kamar yaransa da matarsa' ta ɗan taɓe baki ta cigaba da sabgar gabanta. Fadila ce zaune a kan gadonta, tana zazzage jakarta ta Makaranta, ita kanta bata san me take nema ba, wata takarda ce mai ƙyalƙyali ta faɗo daga tsakanin litattafanta. A hankali ta miƙa hannunta ta ɗau takardar ta buɗe, rubutun larabci ne a jiki, an cika paper da rubutun larabci. Ba rubutun kowa bane face na Yazeed, tamkar inji ne ya tsara rubutun ba hannun mutum ba, ta dinga jujjuya takardar amma ba ta fahimci komai ba, sai sunansa da ya rubuta da Larabci da signing, haka nan taji tana son sanin me takardar ta ƙunsa, ƙarshe ma sai ta fara tunanin ya aka yi takardar ta shiga jakarta?. Bacci take ji sosai, dan haka ta watsa litatafan ƙasa tai kwanciyarta a kan takadar, wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita. "Ukty, yau kin yi kyau fiye da koyaushe, idanunki kamar ƙara musu kyau ake masha Allah" ya faɗa yana murmushi. Haɗe rai tayi tana kauda fuskarta gefe guda, matsawa yayi jikinta Sosai yana mata magana. Jikinta ne ya hau rawa, taji tamkar ta fashe da kuka, ga wannan baƙon yanayi da yake kaiwa yana komowa a jikinta. Fuskarta duk hawaye ta kalli Yazeed "Wai ni meyasa nake jin haka idan ka masto kusa dani?". Ya ɗora kansa a kan kafaɗarta ya ce "Me kike ji?" "Nima ban sani ba" ta faɗa muryarta na rawa. Bakinsa yake ƙoƙarin sakawa a nata, amma ta fara ƙoƙarin kauda kanta, sai dai riƙon da yayi mata bana wasa bane. "Yazeed dan Allah" ta faɗa fuskarta duk hawaye, jikinta kuma na cigaba da rawa. Sai da Yazeed ya yi galaba a kanta, wurin saka bakinsa a nata. Ba zata iya misalta ko rarrabe wane yanayi haka suka wanzu a ciki ba ita da Yazeed. "Yazeed" ta faɗa da ƙarfin gaske, ta tashi daga baccin a razane, fuskarta duk hawaye, tana haki. Amina dake durƙushe tana tattare litattafan da Fadila ta zubar a ƙasa ta kwashe ta gyara ɗakin, sai da ta razana, ta saki litattafan. Ita ma ta maimaita "Yazeed kuma" Fadila sai haki take tana rarraba ido, ta kai hannu fuskarta taji hawaye. Ta kalli in da Amina ke tsaye tana binta da kallo. Ji tayi tamkar yawun Yazeed ne a bakinta, saboda bata taɓa zaton mafarki ne ba gaske ba. Da sauri ta duro daga kan gadon, ta tafi banɗaki tana zubar da yawun bakinta. Amina tabi bayanta da kallo, tana tunanin dama ana mummunan mafarki da rana tsaka haka? Kodayake in mutum baya Addu'a ba abin da ba zai sameshi ba. Haka Fadila ta dinga zubar miyau, tamkar a gaske mafarkin ya faru, har irin ƙamshin turaren da ke jikinsa, take ji a hancinta. Bata haƙura ba sai da ta sa brush ta wanke bakinta, sannan ta fito daga banɗakin. La'asar liƙis, Khalil ya shigo garin Kano, salla kawai ya tsaya yayi, kai tsaye gidansu Hafsa ya nufa. A ƙofar gida ya tsaya yana sallama, Mama ce ta leƙo da kanta, tana ganin Khalil ta fara murmushi, ya duƙa har ƙasa ya gaida ita, ta amsa masa cike da kulawa tana faɗin "Khalil kwana biyu" "Mama ayyuka ne suka yi mini yawa, kuma da yake ba a nan Kano nake aikin ba, shiyasa". "Allah sarki to Allah ya dafa, kuma gashi bata nan, tana wurin bikin wata ƙawarta" Khalil ya ce "Dama Hafsa na ƙawaye?". Mama ta ce "Kaima ka fuskanci halinta kenan, tana da su irin wanda suka yi Makaranta a baya". "To Mama ina ne wurin bikin?" Mama ta gaya masa yayi mata godiya ya tafi. Ba tsammani taga lambar Khalil yana kiranta, duk da bata yi Saving lambar ba, amma ta haddacce ta tsaf. Cikin hanzari ta ɗaga wayar, sai dai bata iya jin komai saboda hayaniya. Tashi tayi ta fita harabar wurin bikin, jikin wata mota ta tsaya, ta saka wayar a kunnenta tare da yin sallama. "Wa'alaikum salam, Baby ya kike?" Taji maganarsa a bayanta. Da sauri ta waiwaya taga Khalil a tsaye a bayanta. "Ya aka yi ka san ina nan ka zo?" Ta faɗa cikin mamaki. "Miracle" ya faɗa yana dariya. Ƙare mata kallo ya shiga yi, tana sanye da riga da skirt na atamfa, ta kashe ɗauri, hannunta ya sha lalle. "Ina wuni" ta faɗa a taƙaice. Maimakon ya amsa mata sai ya shiga ɗaukarta hoto a wayarsa. Haɗe rai ta yi ta ce "Ka bari bana so". "Tom na bari, kin yi mamakin ganina ko kya ce na fiye naci, ba laifina bane, laifin zuciyata ne". Hafsa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta. "Kin yi shiru, ashe biki kuke babu labari. Nayi mamaki da mama tace mini bikin ƙawarki ne, ashe kina da ƙawaye?". Abinda ba ta taɓa yi masa ba tayi, murmushi wanda sai da dimples ɗinta da bai taɓa sanin tana da su ba suka lotsa. A hankali ya furta masha Allah beautiful. "Ina da ƙawaye mana, kana mini kallon bani da kirkin da zan yi ƙawaye ko? Babbar ƙawata ce tun muna yara muka tashi tare shiyasa na zo bikinta". "Ashe ma bikin namu ne, duk da ba a gayyaceni ba muje, a bani wurin zama da Abinci daga Abuja nake ko gida banje ba Wallahi" ɗan zaro ido tayi dama ga idanun nata tubarkallah. "Me yasa baka je ka huta ba?". "Ganinki nake son yi" ta jinjina kai, ta shiga gaba ya bita a baya, wurin taron yayi kyau da tsari, ta sama masa wurin zama, tasa aka kawo masa Abinci da abubuwan sha. "Shikenan ko kana buƙatar wani abun?". "Eh ke nake buƙata a kusa da ni, ki zauna idan kika tafi ban san kowa ba, kar ace na zo gayyar soɗi. Ta ɗan murmusa kaɗan ta samu wuri ta zauna. Ba kunya Khalil ya fara cin Abincin nan, duk da hakan ba ɗabi'arsa bace, cin kowane irin Abinci, kuma a gaban mutane, amma so yake Hafsa ta sake da shi, dan haka ya zage yana ziri. "Allah ya nuna mana ranar bikinmu, muna kan high table kamar wannan couples ɗin, wane irin kaya zamu saka?" Shiru tayi masa tare da ɗan taɓe baki. "Hafsa meyasa ba kaya sona ne?" Yayi Maganar da dukkan nutsuwarsa. Ta ɗauke kai tamkar ba ta ji abin da yace ba. Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Tashi muje in mayar da ke gida, tara saura yanzu". "Dama jira nake ka gama, yanzu zan tafi nima". "Na gama muje" ba tare da ko sallama ta tsaya ta yiwa Amaryar ba suka fito ita da Khalil. Suna zuwa inda motarsa take ta ce "To ka gaida gida". "Me kike nufi?" "Zan hau Napep in tafi gida" Khalil ya ce "Ke kin isa ma? Dan Allah kar muyi haka da ke" da ƙyar Khalil ya lallaɓata, ta amince ta shiga motarsa. Suna cikin tafiya ta ce "Ina Yaya Abdul?" "Yana nan, ko wurinsa ban je ba, sai Allah ya kaimu gobe, ya batun case ɗin nan kuwa, ina fatan dai bai kuma dawowa ba?" "Eh bai sake ba" "Ai ba dan Mama ba, da sai na sa an rufe mini shi Wallahi, in ga ƙaryar iskanci, amma naji ya ce "Shi ɗan uwanki ne ko?" Shiru tayi ba tayi magana ba, Khalil ya kalleta ya ce "Ya naji kin yi shiru?". Kawai sai ta fashe da kuka, irin kukan nan me taɓa zuciya da bayyanar da tsantsar damuwa da ma'abocin yinsa ke ciki. Da sauri ya yi parking ɗin motar, ya ce "Dan Allah kiyi haƙuri, ban san maganata zata ɓata miki rai ba, kiyi mini afuwa" Sake rushewa tayi da kuka, tamkar zata shiɗe, wanda hakan ya sake ɗaga wa Khalil hankali, bai san lokacin da ya kai hannu ya ɗago fuskarta cikin damuwa ba "Dan Allah kiyi haƙuri" yayi Maganar a hankali yana share mata hawayen dake ta zubowa ba ƙaƙƙautawa daga cikin idonta. Duk rarrashin da ya yi mata, bata yi shiru ba, sai da tayi mai isarta, sannan ta kalli Khalil ta ce "Mu tafi dare yana yi". "Ai ba zan iya tuƙin ba, kin sani a zullumi, ina son sanin dalilin wannan kukan naki, da kuma dalilin da yasa ba kya sona, Hafsat ban miki bane ko ina da wani aibu". Ta kashingiɗa da jikin seat, a hankali ta ce "Baka da wani aibu, hasali ma a karamcinka duk da halin ko in kula da nake yi maka, bai hana ka taimake ni ba, Amma meye amfanin fara son ka bayan a gaba na san zan iya samun tangarɗa a aikata hakan?" "Wace irin tangarɗa? Ina sonki Hafsa" Ɗago kai tayi ta kalli Khalil cikin rauni "Ina ganin hakan a idonka, amma... Sai kuma tayi shiru hawaye na zubowa daga idanunta. "Akwai ƙaddarar da zata iya zame mana shamaki, bana son in fara sonka, wani abu yazo ya kawo mana tangarɗa, ka san wacece ni ka guje ni". Khalil ya haɗa hannayensa ya ce "Dan Allah Hafsa, ni ba ruwana da wata ƙaddara in dai bata haramta mana aure ba a shari'a, Ina sonki, amma wace ƙaddara ce haka da kike tunanin zata zame mana shamaki da cikar burinmu, tunda ai kina sona ko?" MASU BUƘATA DAGA FARKO, AKWAI A AREWABOOKS KO MANHAJAR WATPAD. AYSHERCOOL 08081012143 https://arewabooks.com/chapter?id=638e2c023cc3212f4202c4d8 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 P17 Shiru Hafsa tayi, ba tayi magana ba. Khalil ya ce "Yau Allah ya haɗani da gamona ni Ibrahim, Baby magana nake Please answer me" yayi Maganar yana kuma marairaicewa. Kwaɓe fuska tayi kamar za tayi kuka "Ni ka ƙyaleni ko in yi kuka Subhanallah, ba ƙaramin narka zuciyar Khalil Hafsa tayi ba, saboda a rayuwarsa yana son shagwaɓaɓɓiyar mace. "Kar ki yi kuka Please" yayi Maganar yana kwaiwayonta. "Ni ba haka nake magana ba" "To ya kike yi?" Yayi Maganar yana kallon in da take. "Kaga muyi sauri, kar Mama taga na daɗe ta hanani zuwa na gobe in Allah ya kaimu". "Allah ya sa ta hanaki zuwa" ya faɗa yana kunna motar. "Allah ya sa ta hanani zuwa ko?" Ta maimaita tana leƙa fuskarsa. "Eh mana, gaba ɗaya ma ni kishi ne ya ke damuna, duk an gama ganinki, ga mayafinma ba wani babba ba" Kallon kanta tayi da mayafin, ta sake jan mayafin tana rufe jikinta. "Me zaki rufe bayan an gama ganin komai?" "Me aka gani?". "Kyakywar surarki mana, shiyasa duk naji haushi ai" haɗe rai tayi, tana sake gyara zamanta. Haka Khalil ya yi ta janta da hira, ga mamakin Khalil ashe Hafsa na magana sosai, duk a hirar tasu ma, idan ba ta ga dama ba, shiru take taƙi tanka masa, amma yau ta ɗan sake da shi. Har ƙofar gida ya kaita, sannan ya kalleta ya ce "Babyna, yau zan kwana cikin farinciki, duk da ban samu amsar tambayar da nayi miki ba, amma naji daɗin kulani da kika yi, Ina sonki Hafsa" Hafsa ta ɗaga ido ta kalli Khalil, haka nan taji tana tausayinsa, tabbas ya nuna mata so, ko ga wannan sintirin da yake yi a kanta. "Sai da safe, ka samu kaje gida ka huta, Allah ya kiyaye hanya". "Ameen my love" ya furta a hankali, ta buɗe motar ta fita ta nufi gida, har ta shige gida, yana tsaye yana kallonta, sannan ya ja mota ya bar wurin. Sai ƙarfe goma Sa'annan Khalil ya isa gida, Mummy ce ta rage ba ta kwanta ba, taji ana knocking ƙofar Falon taje ta buɗe, mamaki ne ya cikata da ta ga Khalil. "Kai, saukar yaushe?". "Yanzu Mummy". "A wannan daren? Baka samu Flight ɗin yamma ba ne?". Ya shiga cikin falon yana faɗin, a mota fa na dawo. "What, mota kuma? Amma baka da hankali, da wani abu ya faru fa, yadda gari babu tsaro?". "Ai ba abinda ya faru Mummy, baki bacci ba ashe?". "Eh ban kwanta ba tukuna, bari in taso masu aikin can, su girka maka wani abun ka samu ka ci". "No bana jin yunwa, a ƙoshe nake, na shigo ne ma kawai dan kusan na dawo, naga motar Daddy a waje yana gari ne?". "Eh yana nan kusan sati guda kenan yana gari". "Masha Allah, shikenan sai da safe" "To Allah ya kaimu lafiya" ya fice daga falon ya nufi sashinsa. Mama ta lura da yadda Hafsa ke murmushi lokaci lokaci, amma ba taji ta ce mata komai ba. "Nace Khalil ya biki wurin bikin ne?". Hafsa taji tambayar a bazata. "Eh yaje mun gaisa" "Yazo nan nemanki ai, nace masa kina wurin biki" Hafsa tayi shiru tana cigaba da tuna yadda suka kasance yau, haka nan take jin nishaɗi itama a ranta, Khalil ya damu da ita sosai. Bayan ta kwanta, ta shiga cikin abin rufarta, ta ɗau wayarta ta turawa Khalil saƙo kamar haka _*Ya kaje gida? Na gode sosai. Hafsat*_ Khalil yana ƙoƙarin saka wayarsa a silent ya kwanta, saƙon Hafsa ya shigo wayarsa, jujjuya saƙonya dinga yi yana murmushi. 'insha Allah sai kin zama tawa Hafsa'. Ya yi mata reply da *"Na koma lafiya, amma ai kamata yayi ki kirani kiji, mura fa ta kamani saboda sanyi na daɗe a waje"*_ Ta yi masa reply da "Subhanallah, Allah ya baka lafiya, Asuba ta gari". Kissing ɗin screen ɗin wayar ya yi, ya kwanta, tare da ƙanƙame wayar a ƙirjinsa. Ya ƙudurce a ransa washegari zai jewa Abdul da labari me daɗi a kan Hafsa na daf da fara soyayya da shi. Fadila har fargabar kwanciya bacci take, saboda babu wani abu da yake zuwa mafarkinta, Kamar yadda Sheikh Yazeed yake zuwa, abun har mamaki yake bata, gashi ta rasa wanda zata gayawa, kawai ta yanke shawarar washegari za taje gidansu Yusra ta bata labari, ko da wata shawara da zata iya bata. Ba ƙaramin farinciki Alhaji Ahmad ya yi ba, da ganin Khalil, dan a wata shida sau ɗaya suka haɗu, tun bayan fara aikin Khalil, Alhaji Ahmad mutum ne mai son iyalinsa da kyautata musu, duk abin da suke so shi yake musu, baya son duk wani abu da zai taɓa masa su. Yau gaba ɗaya sun haɗu a kan dining, suna karyawa, sai hira suke cikin nishaɗi da jin daɗi, tamkar basu da wata damuwa a rayuwarsu. Amina ta kallesu sai taji sun burgeta, ita kuwa gidansu duk sun rarrabu, dan nemwa kansu mafita, sun baro Inno ita kaɗai a ƙauye cikin jarabar su Kawu Lawan, nan Baba yana gadi ita kuma tana aikatau, duk dan samun abin da zasu rufawa juna asiri. "Ya Ubangiji Allah ka wadatamu, ka wadatamu da halal ka nesanta mu da haram, Allah ka sake haɗa kanmu a wuri guda cikin farinciki, Allah yasa sanadin karatu nan nawa, ya kawo canji a rayuwarmu" tayi Addu'ar a zuciyarta. Haka ta jira suka kammala, ta kwashe kayan da suka ci Abincin, ta gyara wurin kamar ba ayi Komai a wurin ba. Suka kuma komawa falo suka baje, suna ta hira da iyayen nasu. Daga bisani Alhaji Ahmad yayi musu sallama ya koma ɗakinsa, dan gabatar da wasu ayyuka. Khalil ya yi shiru yana kallon hotunan da ya yiwa Hafsa jiya, duk da bata so ya yi mata hotunan, amma tayi kyau matuƙa, Kamar a saceta a gudu. Mummy ce ta fizge wayar ta ce "Bani nan in ga abin da kake kallo haka ko ƙwsƙwaran motsi baka yi" Mummy ta zubawa hoton Hafsa ido, ta kalli Khalil ta ce "Ita kuma wannan fa?" Khalil ya yi shiru bai ce komai ba. "Ko ita ce wadda kake so ɗin?". Jin abin da Mummy ta ce, ya sanya Fadila tashi da sauri, ta karɓi wayar. Ta kalli hoton Hafsa kwaɓe baki ta ce "Taɓ dan Allah kalleta ga kumatunta da ido kamar wata Philippines, ko ɗan murmushi babu a fuskarta gaskiya ka faɗo". "Bani wayata dan ubanki, ta fi ki kyan gani dai". "Wallahi na fita kyau, Dan Allah Bro dame wannan tafi Yusrana, amma ka watsa mini ƙasa a ido". Haɗe rai Khalil yayi ya ce "zan tattakaki Wallahi". Mummy ta ce "Kar kuyi mini faɗa ni, ita wannan ɗin a ina take? Kuma 'yar wanene?". Gaban Khalil ne yayi mummunar faɗuwa, shi kansa sai yanzu ya sake ankarewa akwai damuwa a soyayyar su. Miƙewa yayi ya kalli Mummy ya ce "We will talk later" yana gama maganar ya fice. Fadila ta ce "Mummy, ke sai ki bari ya auri wannan mummunar?". "Ke Fadila, kina taya Yusra kishi dai, amma ai ba ta da muni, ba laifi". "Wallahi Mummy ba ta da wani kyau, kalleta fa wata 'yar lukuta da ita, ko fara'a babu a fuskarta Wallahi Mummy kar ki bari ya kwaso mana 'yar wahala". "Barni da shi tukuna na ga iya gudun ruwansa". Fadila ta miƙe ta ce "Mummy, a round 11 zan je wurin Yusra". "Ok sai kin dawo" Khalil kuwa bayan ya fita daga falon, ɗakinsa ya wuce, ya shirya don zuwa wurin Abdul su tattauna, a kan yadda suka yi da Hafsat a daren jiya. Yana tafe a mota yana saƙe-saƙen yadda zai ɓullowa lamarin, amma shi babbar damuwarsa a yanzu shi ne ya tabattar da soyayyarsa a wurin Hafsat. Fadila na gaban mudubi, tana shiri dan zuwa gidansu Yusra, wayarta ta fara ringing, ta janyo wayar da ke kan mudubi, ta ɗaga ta sakata a speaker, ta ajiye ta cigaba da abin da take yi. "Assalamu alaikum warahmtullah" aka yi sallama daga cikin wayar. "Wa'alaikum salam" ta amsa tare da yin shiru dan jin wanda ya kirata. "Fadila Dutse ya kike?". "Wake magana?". "Ai kya amsa gaisuwar tawa da fari ko" "Idan baka da abun yi ni ina da shi koma waye". "Kankiya ne" ita gaba ɗaya ta manta da waye ma wani Kankiya, banda yanzu da ya kirata, maganganun Yazeed ne suka dawo mata, da ya gaya cewar sonta kankiya yake yi. Tsuke fuska tayi ta ce "Ina jinka" "Ya kike ya hutun, hope kina jin daɗin hutun?" "Sir ya aka yi ne, kace jarrabawata akwai matsala zaka kirani, kuma ka kirani kana tambayata wasu abubuwa daban" "Eh, saboda ba saboda jarrabawa na kiraki a wannan karon ba, saboda inji lafiyarki ne" "But you have no Business with that" "Who told you so, nafi kowa buƙatar son sanin lafiyarki". "Sir sai anjima, am busy now" ta katse kiran ta ajiye tana huci, tare da harar wayar. Nan da nan ta kammala shirinta, ta ɗau mota ta nufi gidan su Yusra. A ƙofar gidan su Abdul, Khalil yayi parking ɗin motar, kan ya fito sai da ya fara kiran Hafsa a waya, dan yaji ya take, a wannan karon yadda take amsa masa wayar ba ƙaramin daɗi yake masa ba. "Ina kwana" bayan ta amsa salamarsa ta gaishe shi. "Yau wace rana an gaishe ni" yayi maganar yana murmushi. "Mhmm shi ne abin da ta iya cewa kawai". "Kin tashi lafiya ya mamana?". "Mama lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya mutan gidan? Ya jikin naka?" "Kowa lafiya ƙalau, amma meya same ni?". "Kace mini kana mura mana" "Lallai kin fara damuwa dani, mura na warware Alhamdilillah, ina fatan kina lafiya ba wata matsala?" "Ƙalau nake Alhamdilillah". "To Masha Allah, zan shigo anjima insha Allah, da ƙarfe nawa zan zo?" Khalil yayi Maganar yana shafa sumar kansa. "Idan an yi sallar isha'i, lokacin ne na dawo gida" "To shikenan dear, me zan taho miki da shi?". "Bakomai" ta bashi amsa. "A'a nifa bana son haka, dan Allah ki gaya mini" yayi Maganar cikin shagwaɓa. Dariya ya bawa Hafsa, "Wai shagwaɓa kake yi, gaskiya Mama na fama". Dariyar shima yayi ya ce "Ai kuma kece yanzu zaki dinga faman, duk shagwaɓata ai ban kai ki ba, haka fa kike cewa malam ka rabu dani kar ka sake zuwa in da nake" ya yi yana kwaiwayonta in zata yi masa tsiwa. Rufe fuska tayi kamar yana gabanta "Am sorry, kayi haƙuri na san na gaggaya maka maganganu marasa daɗi, ba halina bane bana son kowa ya matsi ratuwata ne" ta ƙarasa maganar a sanyaye. "Na fahimta, kar ki damu sai na zo ki gaishe mini da Mama" "Zata ji insha Allah" ya katse kiran, sannan ya fito daga motar. " 'yar yarinya da wa kike wayane haka kike ta wannan fara'a?" Mama tayi maganar bayan ta shigo cikin ɗaki, Hafsa na kan katifa tana ta murmushi, shiru tayi tana ɗan mazewa ba ta zaci Mama na jiyo ta ba. "Ya kika yi shiru, ko Khalil ne?" Hafsa ta gyaɗa mata kai. Mama ta zauna a gefen katifar tana faɗin "Yauwa ko ke fa? Ki dinga sakar masa fuska, shi har abada wanda yace yana sonka ya gama yi maka komai" A raunane Hafsa ta kalli Mama ta ce "Amma Mama... "Shhh na san mai zaki ce Hafsa, ki kwantar da hankalinki, in dai da gaske Khalil yake sonki, na san ba zai gujeki dan ƙaddararki ba, nayi farinciki da shigowar wanda yake saki walwala rayuwarki, duk da halinki na miskilanci da taurin kai". "Mama taurin kai kuma?". "Eh taurin kai mana, ke baki san yadda kike da taurin kai ba, ai sai dai Allah ya shirya mink mini ke". Hafsa kam shiru tayi tana tunani, tabbas ta fara jin Khalil a zuciyarta, dan ma tuntuni basar da shi take, amma Khalil ya haɗu ta kowane ɓangare amma tana tsoron tayi zurfi a sonsa ya san ko ita wacece, ya zo ya rabu da ita, kamar yadda ya faru da ita a baya. "Girl, kince mini akwai Magana, kuma tun da kika zo kin yi shiru, yakamata muyi magana" Fadila ta ɗan yi shiru tana kallon Yusra, sannan ta ce "Ai ke rainin hankali ne ya miki yawa, ina tsoron in gaya miki ki raina mini hankali" Dariya Yusra tayi ta ce "Idan ma na raina miki hankali, ai mun saba kema kina mini, ina jinki". "Zan gaya miki damuwata, idan kika gayan ba daɗi zan zage ki ne tsaf in tashi in tafi gida". "Nima ina da bakin ramawa ai". Fadila ta labartawa Yusra abin da ake ciki, game da mafarkin da take yawan yi a game da Yazeed, da kuma abin da Yazeed ya gaya mata a game da Kankiya. Yusra ta ce "To sai me dan kina yawan mafarkinsa, kin sa shi a ranki ne, kuma kuna yawan haɗuwa a school shikenan". Fadila ta ɗanyi tsaki ta ce "Ke ba kya gane abubuwa, ba fa Normal mafarki nake kawai in ganshi ba" Kan Fadila ta gama maganar, Yusra ta tuntsire da dariya. "Ke nifa bana son iskanci, gayen nan ya taimakeni lokacin exams, duk da yadda na raina masa hankali, Wallahi idan ya zo kusa dani bana iya cewa komai, sai dai jikina yayita rawa, jikina yayi wani iri, inji kamar zan yi kuka, wasu hawaye su cika mini ido". Me Yusra za tayi banda dariya, harda hawaye, dan sai da Fadila ta fara ƙuluwa, can Yusra ta ce "Ba faɗa da malam ba daren, yarinya ƙila zuwa yayi yai tsayuwar dare a kanki, saboda iskancin da kike masa, sai ki shiga hankalinki ai" "Ban gane me kike nufi ba ai" "Wataƙila Addu'a yayi miki yarinya, waye ya gaya miki ana ja da malamai?". "Ke ni ki bani shawara kawai" "To ni wace shawara zan baki? Tun da dai bani nake haɗaku a mafarkin ba, you need each other maybe shima yana mafarkin da ke, kin sashi a ranki ne kawai". "Wai ya za ayi in sa shi a raina, a kan me zan a shi a raina? Ni shishsigin da yake mini ma haushi yake bani, dan dai kawai yana taimaka mini sosai ne". Yusra ta ce "To ni yanzu me zance miki, idan ba damuwa ki kayi da shi ba, yawan mafarkinsa da kike alamane da yake nuna ruhinku na tare da juna, kuma jikinki na gaya miki yana buƙatar Aure, kuma ɗan ustazu yake so" tayi maganar tana dariya. Haɗe rai Fadila tayi ta ce "Laifina ne da na zo wurinki" "To idan ba haka ba, duk mazan duniya da wanda kike gani yau da kullum ba wanda kike gani sai shi, na fassara miki abin da kike buƙata kina jin haushi na. Meke saka miki rawar jiki dan kuna tare? Idan baki wasa ba, wataran sai dai kiga kin rungumeshi. Zahiri ki zata mafarki ne, shi zuciyarki da gangar jikinki ke buƙata" Tsaki Fadila tayi, ta tashi ta ɗau jakarta ta ce "Sai kiyi da wata dan ubanki". "Ubana ya gode matar Ustaz". "Allah ya isa shegiya, kije dan kanki, Allah ya tsareni haɗa jiki da wannan yarom". "Zaki ga yaro, Amma dai kin san ba ƙazami bane" Banza Fadila tayi mata ta nufi hanyar fita. Yusra ta ce "Amaryar Ustaz ko Kankiya, ranar Saturday ki aiko a karɓar miki chocolate cake zan yi" Ko waiwayowa Fadila ba tayi ba, ta yiwa maman su Yusra sallama ta fice. Khalil ma cike da farinciki ya je wurin Abdul, sun sha hira sosai, yayin da Abdul ya ƙara bashi shawarwari tare da bashi ƙarfin gwiwa a kan yadda zai cigaba da neman Soyayar Hafsat. Bayan sallar isha'i, Khalil ya sha kwalliya cikin cofee ɗin yadi mai laushi, ya sanya hula tare da feshe jikinsa da turare. Ya ɗau hanya ya nufi gidansu Hafsa. A kan dandamalin ƙofar gidansu tayi musu shimfiɗa, ta kalleshi tana murmushi ta ce "Kayi kyau sosai" "Ko baki faɗa ba ai ni mai kyau ne" "To ai sai ka bari a faɗa, na ma janye ba kai kyau ba" Khalil yayi dariya ya ce "Daga baya kenan, ina Mama" "Mama na ciki tana gaisheka" Hafsa ta kawo masa ruwa a Jug, suna hira yana sha, rabon da Khalil ya sha ruwan borehole har ya manta, sai dai ya sha na roba, amma ya sai gashi zaune yana ɗaɗɗakar ruwan borehole. Sosai ya dinga jan Hafsa da hira, yau kam ta biye masa sosai, ita kanta ta san ta samu farincikin da ta daɗe ba tayi ba. "Hafsa kina sona?" Ya jefo mata tambayar. Gaba daya annurin fuskarta ya ɗauke, tayi shiru ba ta ce komai ba. "Hafsa meyasa kike gudun amsa mini tambayar nan ne?". "Saboda ƙaddarata" "Mecece ƙaddarar taki gaya mini, zan fahimceki". Ta share hawayen da suka fara zubo mata ta ce "Zan gaya maka idan ka sake dawowa, amsarka bayan jin mecece ƙaddarata ita zata amsa maka tambayar da kake mini na idan ina sonka" "Ki gaya mini yanzu ko zan samu nutsuwa mana". "A'a dare ya fara yi kuma ga sanyi, zan gaya maka insha Allah" "Shikenan, jeki ki gayawa Mama zan shigo in gaisheta" Hafsa ta tashi ta tafi, shi kuna ya buɗe jug ɗin ruwan, ya zubar da sauran, ya ƙulle kuɗi a leda ya saka mata, dan ya san idan ya ce zai bata ba zata karɓa ba. Ya shiga suka gaisa da Mama, Bayan ya fito Hafsa ta biyo shi da wata leda babba, ta bashi. Ya sa hannu ya karɓa ya ce "Ni kome kika bani karɓa zan yi, ni ba irinki bane" "To ni ɗin ya nake?" "Kin fini sani ai, ranar ai a kan 500 kika kusa yi mini tijara" Murmushi Hafsa tayi ta ce "Baka da mantuwa ko?" "Ina zan manta, sai da safe" yayi mata sallama sannan ya tafi gida, aikuwa a hanya Hafsa ta dinga kiransa a waya, ya san a kan kuɗin nan ne, dan haka yaƙi ɗagawa. Gaba ɗaya zuciyarsa ta tafi a kan son sanin ƙaddarar da ke cikin rayuwar Hafsa. Da yaje gida a falo ya shigo da ledar, jin ledar da zafi tun lokacin da Hafsa ta bashi, ya san cewa abin ci ne a ciki. Ya sa Amina ta kawo masa plate da cokali, Mummy sai binsa take da kallo, tana tambayarsa daga ina yake. "Wurin Abdul" ya bata amsa. Ya zazzage ledar, Awara ce fal, da miyar jajjage ga kabeji da cucumber fal a gefe. Murmushi yayi ya juye a kan plate ɗin, ya sa cokali ya fara ci" "Me kake ci haka ne?" Mummy tayi maganar tana leƙa plate ɗin. "Mummy awara ce fa" ya faɗa yana cigaba da ci. Yamutsa fuska ta yi ta ce "Awara Khalil? Kaima ka fara irin wannan cimar yunwar? Meye haɗinka da wata awara?" Khalil ya ce "Mummy amma naga Abinci ce itama, ta burgeni ne shi ne na saya". "Duk Abincin da yake gidan nan ka rasa me zai burgeka sai awara? Me akayi a ka wata awara, wannan ƙazantar da ake sayarwa a bakin hanya, wato shi dai Abdul ɗin nan dole sai ya maida kai irinsa, shike koya maka duk wani halin ƙauyanci da shirme, yanzu idan cikin ka yayi ciwo fa?" "Mummy ba Abdul ne ya sani saya ba, ni na saya da kuɗina fa". "Tun da kake a gidan nan ka taɓa ganin an sa kuɗi an sai wanna abar? Saboda kalan yunwa da nemawa kai masifa shine kaje ka saya kana sawa a cikinka, baka san da yadda aka yi ta ba, ke zoki ɗauke wannan a bar kuje ku cinye ta" tayi maganar cikin tsawa tana kallon Amina. Mamaki ne ya kama Amina, duk a kan awarar ake wannan tashin hankalin, wato idan ma abun mutuwa ne su suci su mutu kar ɗanta ya ci. Khalil yana ji yana gani, Amina ta ɗauke awarar kitchen ta kai awarar ta ce "Aikuwa ba zamu ci ba, shi ɗin ne zai cinye a barsa, wannan matar lamarin nata ya wuce tunani" Khalil yayi fushi ya bar Falon, dan ba ƙaramin daɗi awarar tayi masa ba, dan da gani ta musamman ce Hafsa tayi masa. Ta ƙofar corridor Amina tabi, taje ta ƙwanƙwasawa Khalil ƙofa. Kamar ya share sai kuma ya buɗe. Amina ta miƙa masa plate ta ce "Ga awararka nan na kawo maka, Naga kana so" ya ɗan ƙura mata ido sannan ya karɓa ya ce "Na gode sosai". "Never mind" ta faɗa a taƙaice ta juya ta koma. Fadila tai ta jujjuya maganganun Yusar a kan Yazeed, ƙarshe kawai tayi tsaki ta bar zancen Yusran a shiririta. Sai dai ba abinda ya sauya, daga yawan mafarkin Yazeed da take yi. "Baba ga karin kumallo na kawo maka" Amina tayi maganar hannunta riƙe da wani ɗan madaidaicin faranti, tana kallon Baba. "Yauwa uwata, Allah ya yi miki Albarka". "Ameen, amma ya aka yi naga idonka yayi ja?" "Mura ce ta sakani a gaba, ta saka mini ciwon kai da zazzaɓin dare". Cikin kulawa Amina ta ce "Baba to ka karya sai in raka ka Asibiti mana". "A'a uwata, zan warware insha Allah, zan dafa rai ɗore in sha, na kuma karɓo magani a Chemist" "Baba gara dai muje Asibitin" "Ki bari idan ban warke ba zuwa gobe in Allah ya kaimu sai inje" ya ƙarasa maganar tari na taso masa" "Sannu Baba, ka karya sai ka kwanta, hannunka ma ya ɗau zafi sosai". Baba yana tsaka da karyawa, Fadila ta fito tana ta wani hura hanci, ta yiwa Baba alama da yazo. Baba na shirin tashi, Amina ta ce "Baba zauna, bari ni naje" ta tashi ta nufi in da Fadila take. Fadila ta kalleta a wulaƙance ta ce "Ba ke nake kira ba, Babanki nake kira". Amina ta ce "Bashi da lafiya ne shiyasa na zo". "And so? Baki ji me mace bane babanki nake kira bake ba" ganin kamar suna jayayya ya sanya Baba tasowa, ya ƙarasa in da suke tsaye ya ce "Gani". Fadila ta kalleshi ta miƙa masa kuɗi ta ce "Gashi nan, kaje ka tari Napep kaje gidan su Yusra zata baka saƙo ka kawo mini" Amina ta ce "Ni ki kwatanta mini gidan sai inje, Baba bashi da lafiya fa". Cikin tsawa Fadila ta ce "Nace Babanki na aika bake ba, karki sake saka mini baki a maganata" "Kiyi haƙuri dan Allah ni ki aike ni, jikinsa da zazzaɓi" "Baban naki ma ya aka cika idan an aike shi, shi da ya daɗe a birni balle ke bagidajiya 'yar ƙauye kije gidan mutae kiyi musu hauka da jahilicin naki da kika saba ki zubarwa da mutane mutunci" Baba yayi gyaran murya ya kalli Amina ya ce "Uwata, ai jikina da sauƙi sosai Alhamdilillah, bari inje maza jeki ɗau Abincina ki rufe mini yanzu zan dawo" Baba ya juya ya nufi gate, yana takawa a hankali saboda jikinsa ba daɗi. Fadila kuma ta koma ciki abunta, Amina kuwa tamkar an dasata, sai ma wasu hawaye masu zafi da suka fara biyo kuncinta. Tana nan tsaye Alhaji Ahmad ya fito, cikin suffarsa ta kwarjini da kamala, tun da ya fito Amina ta zuba masa idanuwa, har sai da ya tsargu, amma har ya gifta ta ko gaishe shi bata iya yi ba. Ya wuce ya hau motarsa, wannan karon ba direba da kansa yake tuƙi, Zakiru ya buɗe masa gate ya fice. "Tabbas kan in bar gidan nan, sai nayi maka abin da har 'yarka ta koma ga Allah ba zata manta ba, sai taji abin da nake ji idan taci zarafin mahaifina". Ayshercool 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 *Littafina Aƙidata da kuma Ruɗin ƙuriciya, na kuɗi ne, sauran duk free me* 18-19 Amina ta ja jikinta a hankali, ta koma wurin zaman Baba ta zauna, tana jin yadda sanyi ke ratsata, wani irin tausayin Baba ya mamaye zuciyarta, Allah kaɗai ya san irin ƙalubale da wulaƙancin da ya dinga fuskanta a gidan nan, amma yake dakewa yana shanyewa. A ƙalla Amina ta shafe awa guda a zaune, amma Baba bai dawo ba, haka ta tashi ta koma cikin gidan, zuciyarta na mata ƙuna game da abin da Fadila ta yi wa Babanta. Ta tagar corridor Amina ta hango Baba ya nufo hanyar shigowa cikin gidan. Da sauri ta fito falo, idon Baba duk yayi ja, saboda yadda ya sha ƙura a hanya. Fadila kuwa na zaune sai kaɗa ƙafa take, tana latsa remote hankali kwance. Baba ya ƙaraso ya ɗan risuna yana miƙa mata ledar hannunsa. "Wai kai dan Allah duk lokacin da aka aikeka, sai kaje kai zamanka?" "Yi haƙuri ba haka bane, titunan ne akwai cunkoson ababen hawa, mussaman yau da aka tashi da hazo". "Ajiye a wurin ka je, Na gode" ya ajiye mata ya miƙe, Amina ta fito ta biyo bayansa, amma Fadila ta kalleta ta ce "Ke zo nan" Amina ta tsaya cak ta waiwayo tana kallon Fadila. "Akwai undeas ɗina a toilet, ki je ki wanke mini, sannan ki sauke jakunkuna na daga hanger duk ki goge mini su" Wani abu mai ɗaci ya tsirgawa zuciyar Amina, Baba ya kalleta yayi murmushi, yana gyaɗa mata kai cikin bata ƙwarin gwiwa da kwantar mata da hankali. Amina ta juya ƙafafuwanta suna rawa, ta nufi sashin Fadila. Sai da Hafsa ta yiwa Khalil mita a kan kuɗi da ya bata haka da yawa, ta dinga mita tare da cewa ya zo ya karɓi kuɗinsa, a karo na farko da ya nuna mata ɓacin ransa tun bayan haɗuwarsu, sai kuma taji babu daɗi dan ƙarshe ma kashe wayarsa yayi. Sai da ya wuni be kirata ba, idan ta kira shi kuma yaƙi ɗagawa, gaba ɗaya ta shiga damuwa. 'Kenan da gaske na fara son Khalil? Idan kuma ya san wacece ni ya ƙi aurena fa ya zan yi?' ta tambayi kanta, take kuma taji kanta yayi mata wani irin dumm babu daɗi, ta shiga taradaddin halin da zata shiga idan Khalil ɗin ya kasa ɗaukar ƙaddarar da ta faɗa mata. Kasancewar an tashi da hazo sosai, ya sanya Hafsat take ta kula da Mama, dan kar ta fito tsakar gida ko tace za tayi wani aiki, saboda yanayin jikinta, ba ta da cikakkiyar lafiya, amma hakan bai hana tari ya sarƙe Mama ba, duk wani taimako da Hafsa zata iya bata ta bata, amma abu yaci tura, dan har numfashinta ya fara sama sama. Cikin hanzari ta tashi ta samo abin hawa, suka tafi Asibiti. Suna zuwa aka basu gado, likitoci suka fara ƙoƙarin suga numfashin Maman ya daidaita. Hafsa ta ƙurawa Mama ido, an saka mata Nebulizer, ga drip a rataye. Hafsa ta sa kujera ta zauna, ta cigaba da kallon Mama, ta riƙo hannun Mama tana tuno abubuwan da suka gabata a rayuwarsu, da kuma yadda aka yi Mama ta haɗu da wannan larurorin da suka mamayeta. A hankali wasu irin hawaye suka shiga zubowa daga idanunta, ba dan kuɗin da Khalil da ya bata ba da bata san ya zata yi da ciwon Mama ba. Kwanansu biyu a Asibiti, amma Khalil baya ɗaga wayarta, gaba ɗaya ta shiga cikin damuwa, sai da hakan ta faru sannan ta gane a 'yan kwanakin nan ba ƙaramin sabawa tayi da Khalil ba. Shi kansa Khalil daurewa yake yi, baya jin daɗin rashin wayar da ba ya yi da Hafsa, amma dole ya dinga nuna mata fushinsa idan ba ta kyauta ba, yana matuƙar son ta, kuma yana son ya taimakesu, mussaman duba da yanayin halin da suke ciki, amma taurin kan Hafsa yafi ƙarfinta. A kwana na uku ne, Hafsa na saka ran a sallami Mama, dan a kwanakin nan kuɗin wurin Khalil da ke hannunta sun ƙare, harta fara shiga na sana'arta, dan kullum cikin kawo kawo ake a Asibitin kamar ba na gwamnati ba. Ba tsammani taga kiran Khalil, amma ta share, sai da Mama ta kalleta ta ce "Ba kiran wayarki ake ba?" "Eh wayata ce". "To ki ɗaga mana" "To zan ɗaga" ta amsawa Mama amma taƙi ɗagawa. Ganin Mama ta ƙura mata ido ne, ya sanya ta ɗaga wayar, tana tura baki ta amsa masa sallamar da yayi da ƙyar. "Na je gida ba kowa, kuna ina ne?" Ta kalli idon Mama sannan ta ce "Muna Asibiti Mama aka kwantar" "What? Amma baki gaya mini ba, wane Asibitin ne?". "Ai sallamar mu za ayi yanzu, likitan dare muke jira ya sake dubata mu tafi". "Ba wannan na tambayeki ba, wane Asibitin ne?" Har ga Allah Hafsa bata son yawan ɗawainiyar da Khalil yake yi da su. "Hafsa magana nake miki fa" "Mhm nifa nace maka gida zamu taho" "Wai ya kike mini jayayya ne?" Ya faɗa a hasale. Haka ta haƙura ta gaya masa tana tura baki, dan taji haushin ɗaga mata murya da yayi. Da hanzari ya shiga falo yana dube-dube. "Ya aka yi ne?" Mummy ta tambayeshi. "A nan na bar car keys ɗina?" "Me zaka yi da makullin mota yanzu da daddare ba ka dawo gida ba kenan?". "Eh zani wani wuri ne". "Ina ne wani wuri?" Tayi maganar tana tsare shi da ido. "Mummy sai kace wani mace, wani wuri zani fa, yanzu zan dawo" yayi Maganar yana ɗaukar key ɗin da yake kan dining yayi waje. Fadila ta ce "Wurin wata zashi, ina ga wannan Yarinyar ce, ko ita aka kwantar Asibiti, ko wani nata, kan ki fito ya shigo yana waya". Mummy ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Wai ni 'yar waye Yarinyar nan, yakamata in sani tunda wuri". "Waya san masa, shi zaki tambaya". Bai fi mintuna Arba'in ba, Khalil ya sake kiran Hafsa, ya ce ta zo ta shiga da shi, amma taƙi fita, ta gaya masa lambar ward ɗin da suke. Sai da ya daure sannan ya iya shiga ɗakin, marasa lafiya sun kai mutum Ashirin a ciki, sai ƙarni da warin Asibiti da ke surnanowa daga cikin ward ɗin, haka ya daure ya shiga, tun da ya shigo ta hango shi, amma ta basar yaita lalube ya gano su. Sai da ya ƙaraso sannan Mama ta gane shi, ya nuna kamar bai ga Hafsa ba, ya durƙusa ya gaida Mama, ta amsa masa cikin kulawa. Nan ya zauna yana yiwa Mama sannu, Mama ta kalli Hafsa ta ce "Ke baki iya gaisuwa ba?". Fuskarta ba fara'a ta ce "Ina wuni" ba tare da ta kalli Khalil ba. "Mama ƙyaleta, bana neman gaisuwata, Fushi nake da ita, Mama kwana uku kina Asibiti amma yarinyar nan ta kasa kirana a waya ta gaya mini, sai ma wani cika da take tana batsewa". "Da na kiraka kana ɗagawa ne?" tai maganar tana kuma ɓata rai. Mama sai da ta ƙulu da abin da Hafsa tayi, amma tayi shiru ta rabu da ita, kasancewar likitan da zai sallami Mama bai shigo da wuri ba, ya sanya ya ce Mama ta bari sai da safe. Ya tashi zai tafi, ya sanya hannu aljihunsa, ya ciro kuɗi ya ajiye a kan side bed, Mama za tayi magana Hafsa ta rigata "A'a ka barsu gaski... Ba ta ƙarasa ba Khalil ya watsa mata wani irin kallo, da ya sanya ta haɗiye maganar da take son ƙarasawa. Ya kalli Mama ya ce "Mama in dai ni ɗanki ne, bai kamata ki ƙi karɓar abin hannuna ba, Allah ya baki lafiya, gobe Insha Allah in an sallameki, zan zo gida in sake dubaki" yayi sallama da Mama ba tare da ya ko kalli Hafsa ba, yayi gaba abin sa, tabi bayansa da kallo tana jin haushin yadda ya shareta. Bayan fitar sa sai da Mama ta yiwa Hafsa ta tas, a kan abin da take yiwa Khalil. Amina tana ta ƙoƙarin kula da Baba, amma Hajiya Zainab da Fadila suka tsiro da wani wulaƙanci, da sun fuskanci tana son wurin Baba, sai a tsiro da aikin da za'a sakata su hanata zuwa, haka kurum 'yan kwanakin nan suke tsangwamarta, ta rasa me ta tare musu. Yau ɗaya daga cikin 'yan ajinsu Amina take sauka Alqur'ani, kuma an gayyaceta, tana son zuwa ko dan ta ƙare sanin kan cikin birnin Kano. Ta nunawa Baba katin gayyatar, ya amince taje, tare da yi mata nasiha sannan ya ce ta tambayi Hajiya Zainab, kar fitar tata ta zamana laifi. Ba dan Amina ta so ba, ta tambayi Hajiya Zainab, ba ta sa ran ma zata barta ba, amma cikin ikon Allah kawai taji ta amince. Amina ta dinga murna, dama sun yi da ƙawarta Azima, zata biya gidansu su tafi tare, dan bata san gidan saukar ba. Duk da gidansu Azima bai kai na su Fadila girma da kyau ba, amma suma da gani suna da kuɗi sosai, sai dai halayyar 'yan gidansu Azima ya sha banban da na su Fadila, Maman Azima na ganin Amina, ta karɓeta da fara'a tana faɗin "Yau ga Aminan Azima a gidana, kullum sai an bani labarin Amina H shanono, yau dai gani gata" Amina ta ƙunshe fuska tana murmushi. Maman Azima ta ce "Tana can tana wanka, ita da idan ta shiga banɗaki, tamkar tana ɗakinta, bari a kawo miki Abinci". "A'a Ammi na ƙoshi" ta ɗan tsuke fuska ta ce "Hala ita Aziman bata gaya miki idan an zo gidan nan ba na bada abu aƙi karɓa ba? Dole ki ci Abinci Amina, ga ɗakin Aziman can, ki shiga sai a kai miki Abincin can" Amina ta shiga ɗakin Azima, ɗakin ya haɗu sosai da sosai. Azima na fitowa daga wanka, taga Amina, ta daka tsalle ta rungume Amina. "Ke cikani kar ki tsirara malama" Azima ta ce "Ashe zaki zo ɗin 'yar rainin hankali kawai, amma dai ba da wannan shigar zamu je wurin saukar ba?". Amina ta kalli kanta ta ce "Me shigata tayi?" "Ke ba zamuje a raina mu ba, kin san halin 'yan ajinmu, bari in shiga shagon Ammi, in ɗauko miki sabuwar riga" Amina ta zaro ido tana shirin magana, mai aiki ta shigo ɗakin, ta dinga ajiyewa Amina kayan ciye-ciye. Azima ta fita ta dawo da wata rantsatiyar doguwar riga purple da takalmi da jaka duk kalar rigar. Azima ta ce "Gashi nan Ammi ta ce a baki ki saka" da yake Ammi na da shagon botiques a cikin gidan. Jiki a sanyaye Amina ta ce "Azima, kin san ni wacece, dan Allah ki bar kayan nan, in je da na jikina" "To sai ki je ki gayawa Ammin ai" Amina fafur taƙi yadda ta saka kaya, sai da Ammi ta zo da kanta, Amina ta ce "Ammi ba ƙin karɓa nayi ba, Baba zai tambayeni ina na samo kayan nan, kuma gidan aikina zasu tambayeni". "Kar ki damu, direba ne zai kai ku, ya mayar da ke gida, sai a yiwa Baban naki bayani" Da ƙyar Amina ta yadda, ta cire hijjabin jikinta, da yayi haske saboda ya gaji, tun irin wanda ta zo da su daga ƙauye ne. Ta canza kaya zuwa doguwar rigar nan, ga uban gashinta da yake natural, ta tattare shi da tsohon ribbon. Azima ta sakata a gaba, ta saka comb tana taje mata gashin nan, ta shafa mata mai, ta kawo kayan make up, tayi mata simple make up. Azima ta ce "Ke yarinyar nan Allah yayi miki kyau, amma ko hoda ba kya shafawa haka kike yawonki" "Ke ni ƙyaleni da wata hoda" yadda Amina tayi kyau, ba zaka ce daga ƙauye take ba, Azima ta buɗe wani irin turare mai ƙamshin gaske, ta shafawa Amina ita ma ta shafa. Suna fita falo Ammi ta rungume Amina, "Kai Masha Allah da wannan kyakykyawar yarinya, bani wayata in mata hoto" Amina har mamakin karamcin Maman Azima take yi, ita babu ruwanta kamar ba mai kuɗi ba, 'to kenan masu kuɗin ba kowane me irin halin su Hajiya Zainab ba?' Da zasu tafi har harabar gidan Ammi ta rakosu, ta cewa direba "Ga su nan ka kula mini da su, ka kai su wurin walimar saukar, kar a bari magariba tayi, duk in da suka yi awa ɗaya da rabi, kai mayar da Amina gida, ga kaya nan na bata, ga wasu a ledar nan, ka yiwa Abbanta bayanin ni na bata, sai ku taho kai da Azima". Amina tai ta yiwa Ammi godiya, tayi mamakin tsananin karamcinta, sam ba ruwanta da wata ɗagawa. Haka kuwa aka yi, suka fara zuwa wurin sauka, aka yi walimar sauka a cikin ƙawayensu, Amina taji daɗin wannan fitar sosai da sosai. Kamar yadda Ammi tayi umarni, har gida aka mayar da Amina, direba ya yiwa Baba bayani kamar yadda Ammi ta umarce shi. Bayan tafiyar su Azima, sai da Baba yaita yiwa Amina nasiha tare da gargaɗinta a kan ta iya talaucinta. Khalil da ke zaune a mota yana shirin fita, ya zubawa Amina ido, bai taɓa ganinta ba hijjabi ba sai yau, rigar kamar da jikinta aka auna aka yi ta, saboda yadda ta zauna cif a jikinta, yana cikin motar ta zo ta wuce cikin gidan, hannunta riƙe da wata babbar leda. Ajiyar zuciya ya yi, ya kunna motar ya bar gidan. Amina a falo ta zauna, ta buɗe robar gugguru ta fara ci, ƙamshin turaren Alhaji Ahmad ne ya fara cika wurin kan ya bayyana, ya turo ƙofar falon da sallama, Amina ta amsa ƙasa ƙasa. Duba falon yake yana son gane daga ina yake jin tashin ƙamshin wani turare na musamman. Har ya zo zai gifta kunnuwansa suka jiyo masa muryarta "Daddy sannu da zuwa" kallon in da Amina take yayi, sai dai ba shi tabbacin ko Aminan ce, saboda yadda ta ke haɗe cikin riga mai kyau, kuma shi da hasali ma yarinyar sai ta ga dama take gaishe shi, dan haka kawai ya wuce bai amsa ba. Amina ta gama ciye-ciyenta, sannan ta tashi da nufin ta je wurin Hajiya Zainab, ko da aikin da zata yi mata, saboda tana son ta shiga ɗakinta tayi rubutunta na Alqur'ani, wanda idan tana yi, bata buƙatar takura. Kanta a ƙasa tana sauri, suka yi karo da Alhaji Ahmad dake ƙoƙarin fitowa daga sashin Mummy. Amina ta firgita sosai ɗan ƙaramin mayafin kanta ya sauka, tarin gshinta ya bayyana. Ganin ya zuba mata ido ya sanya ita ma ta ɗan tsare shi da nata idanuwan, tana ƙoƙarin gyara mayafinta. "Ba kya gani ne?" Ya furta yana kuma tsareta da ido. "Yi haƙuri ban san ka taho bane" guntun tsaki ya ja, ya raɓa gefenta ya wuce. Amina ta taɓe baki ta ƙarasa ciki. Bayan sallar isha'i, Khalil ya koma gidan su Hafsa, 'yan kwanakin nan ya sarƙi zuwa gidan, Jikin Mama yayi sauƙi sosai, Khalil ya ji daɗin yadda ya ganta, suka taɓa hira tare da sake yi mata sannu. Yau ma bai kula Hafsa ba bata kula shi ba, sai da zai tafi Mama ta ce Hafsa ta raka shi. Ba ta son yiwa Mama gardama, ta rako shi har gaban mota, ba tare da ta ce masa uffan ba, suna zuwa bakin motarsa ta juya zata koma gida abinta, cikin zafin nama Khalil ya riƙo hannunta, ya buɗe motar sa ya sakata a ciki, ya rufe ƙofar, ya zaga ɗaya site ɗin ya shiga. "Meye haka? Dan Allah ka buɗe mini in fita, sai kasa mutanen unguwa sun mini wani sharrin?" "Idan sun miki sai me? Ke da mijinki ne ai ko? Hafsa meyasa kike mini haka ne, kin fi son in ta wahala ko baki damu da ni ba?". Ta tura baki ta ce "Eh ai nima baka damu da ni ba, da na dinga kiranka ka ƙi ɗauka" "Ba dole in ƙi ɗauka ba, Hafsa komai na baki ba zaki karɓa ba, sai kin yi mita da ƙorafi bana son abin da kike mini bana jin daɗi" ya ƙarasa maganar cikin marairaicewa. Cikin shagwaɓa ta ce "To Shine sai ka daina kirana, kuma daina ɗaga nawa, dan ka sani damuwa" "Dagaske kin damu kema da bama waya?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Kina sona kenan?" Yayi Maganar da dukkan nutsuwarsa. Shiru ta ɗan yi, sannan ta kalleshi ta ce "Kana sona da gaske?" "Ina sonki mana" "Bari in fara gaya maka waceceni, da ƙaddarar da ta sameni, ban sani ba ko zaka iya cigaba da sona a haka". Hafsat Usman Dikko, shi ne cikakken sunan Hafsa, mahaifinta haifaffen garin Kano ne, mahaifiyarta ma haka. Mahaifin Hafsa shikaɗai mahaifiyarsa ta haifa a gidansu ta rasu wurin haihuwa, ya taso a tsakiyar 'yan uba, cikin tsangwama da kyara. A haka a wahale yayi karatun Addini da na zamani, kasancewar Usman mutumin kirki, mai ladabi ga kowa da kowa ya sanya 'yan unguwarsu kowa yana son sa. Ya haɗu da mahaifiyar Hafsa, mai suna Safiyya, a nan wani filin ƙwallo da yake zuwa, a nan cikin unguwar gwale. Sai dai itama basu da ƙarfi, dan marainiya ce, yayanta ne yake ɗawainiya da su. A lokacin da Usman ya auri Safiyya, ba shi da wata tsayayyiyar sana'a, sai dai mutum ne mai zuciyar nema, sai dai yana da kwalin degree har biyu amma babu aikin yi, gidan da suka tare ma a ciki, gadonsa ne na mahifiyarsa a nan cikin unguwar ɗorayi, wani ɗan ƙaramin gida, haka suke rayuwa. Kwatsam, Chairman ɗin unguwarsu tsohon abokin mahaifin su Usman ne kan ya rasu, ya bawa Usman offer, a hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa. Yayi murna ba kaɗan ba, a lokacin 'yan uba suka sake sako shi a gaba, da sharri da jafa'i kala kala dan su cikinsu babu wanda ya yi karatun boko sai shk. Lokaci ɗaya Allah ya ɗaukaka shi a kan harkar aiki, ya mallaki gida da abin hawa, ya mallaki shaguna a nan cikin umgu su, wasu ya bada haya wasu ya zuba kasuwanci ya janyo 'ya'yan 'yan uwansa, amma suka dinga cutarsa. Amma duk da haka Allah bai sa yayi baya ba, kullum gaba yake yi, cikin ikon Allah a nasarorin da ya samu, har da karramawa daga fadar shugaban ƙasa, saboda gaskiyarsa da gudun rashawa. Gidansa kullum cikin jama'a yake, masu neman taimako, hannunsa a sake yake hakan ya ƙara masa farinjini. Kusan shekara biyar Safiyya na ɓari, bata haihu ba, sai da aka dage da addu'a da neman magani sannan Allah yasa ta samu cikin jikinta ya zauna, watanni tara Allah ya sa ta haihu, ta haifo ɗa namiji kyakywa mai kama da Usman sak, aka sha shagalin suna aka sanya masa suna Abubakar Sadik, sunan mahaifin Safiyya. Sadik ya taso cikin gata da kulawa, shekararsa uku a duniya, dangin Usman suka dinga mita a kan Cewar ba a kai musu Sadik, a dinga kaishi saboda ya saba da 'yan uwansa. Ba dan Safiyya ta so ba, aka haɗa kayan Sadik, aka kaishi gidan wan Usman, mai suna Aminu, sai dai kwanan Sadik biyu aka dawo da shi wai bashi da lafiya, duk ya fita hayyacinsa, aka kaishi Asibiti aka yi gwaje-gwaje aka tabattar da wani abu yaci, kwana ɗaya ya rasu, daga Safiyya har Usman sun shiga tashin hankali na gaske, wanda a sanadiyar damuwa da rashin lafiya da Safiyya tai tayi, aka gano tana laulayin wani cikin, a haka ta haifo Hafsa. Lokacin da aka haifi Hafsa, Usman Arziƙi ya ninka na baya, Hafsa ta tashi cikin gata da kulawa. A can wurin aiki, abokan aiki suka sako Usman a gaba saboda cigaba da yake samu, mussaman ta fuskar tsayawa a kan gaskiya, a dangi kuma 'yan uba na ta son ganin bayansa, banda 'yan unguwa da tasu hassadar duk da tarin kyautatawarsa a gare su. Bayan haihuwar Hafsa, Safiyya tayi ɓari yafi bakwai, wanda sai da likitoci suka bata shawarar, a ɗaure bakin mahaifarta ta haƙura da yinƙurin ɗaukar ciki saboda lafiyarta. Kasancewar Hafsa ce 'ya ɗaya tilo a wurinsu ya sanya suka ɗora mata duk wata so da ƙauna, Safiyya take ta kulawa da ita, taƙi yarda ta saki jiki ta bawa su Aminu da iyalansu 'yarta. Shekarar Hafsa goma sha ɗaya, aka yiwa Usman wani ƙarin girma, yaje Abuja aka yi walima, tun da ya dawo ya fara rashin lafiya, aka dinga yawon Asibiti amma babu wani cigaba ba a gano abinda ke damunsa ba, kullum ciwo gaba yake yi, wanda hakan ya yiwa 'yan uwansa daɗi, dan sam basu damu da halin da yake ciki ba, daga matarsa sai mahaifiyarta da wanta ne suke ta ɗawainiya da shi. Shekara guda yana jinya, Allah ya karɓi abin sa, Safiya ta shiga cikin tsananin tashin hankali da damuwa, tayi kuka kamar babu gobe, mutane aka cika gidan makoki dan an san za a ci a sha, tun kan a share sadakar uku, Aminu da 'yan uwansa Hadi da Ashiru suka fara maganar rabon gado, wani ɗan uwan mahaifinsu ya ce ai sa bari a rufa Arba'in. Kwanaki Arba'in da ɗaya da rasuwar Usman, suka zo da wani mutum wai shine Alƙali zai yi rabon gado, gaba ɗaya sun sa ran dukiya ta su ce, saboda ba shi da ɗa namiji, Safiyya ta fito da wani rubutu da yayi kan ya rasu, yayi rubutu fiye da rabin dukiyarsa ya sakata a harkar cigaban Addini, manyan kadarorinsa kuwa duk ya saye su da sunan Hafsa, ya mallaka mata su, ɗan abin da ya bari babu yawa sam. Nan fa suka ce basu yadda ba, ƙarya take ita ta rubuta, ganin suna neman su gwada mata fin ƙarfi, ya sanya ta garzaya kotu, Allah ya taimaketa Alƙali ya tabattar da wasiyyar da Usman ya bari. Bayan Safiyya ta gama idda, ta dinga samun manema, amma ta ce ita ta gama aure a kan Usman, saboda ta san ba zata samu madadinsa ba. Mahaifiyarta da ɗan uwanta suka dsge a kan dole tayi wani auren, wani mutum mai suna Musa, shi Safiyya ta tsayar, saboda yana da matuƙar kirki da halaye masu kyau kwatankwacin Usman. Sai dai su Aminu yayyen Usman na jin batun za tayi aure, suka tada husuma, wai ba za tayi aure ta kai dukiyar marainiya wani wurin a cinye ba, ƙarshe ma suka ce sai dai ta basu Hafsa, ba zata yi agolanci a wani gidan ba, ko kuma ta auri Aminu. Da suka tada masifa da tashin hankali, mahaifiyar Safiyya ta ce tayi haƙuri ta auri Aminu, ko ba komai Hafsa ba zata tashi gidan wasu ba, ba dan Safiyya na so ba ta yiwa mamanta biyayya. Bayan auren Safiyya da Aminu, yayanta shima ya rasu, ɓarayi suka tare shi a hanya, suka kashe shi, abubuwa suka sake yiwa Safiyya zafi, na rashin da tayi gaba da baya. Bayan aurenta da Aminu, ya dinga basu kulawa da tattali, duk da a gefe guda iyalansa suna nuna musu tsantsar ƙiyayya da kyara. A haka ya lallaɓa Safiyya, tayi musu gyaran gida, aka sai motoci biyu a gidan dan amfanin mazauna gidan. Ya dinga lallaɓata da kyautatawa da asiri, ya dinga karɓe dukiyar nan ɗaya bayan ɗaya, dan ba ta iya masa musu a kan komai, da ya ce ta bashi take bashi. Sai da ya tabattar ya ƙwace komai, ya shiga bushasha shi da 'yan uwansa da iyalinsa, ya fara azabtar da Safiyya da 'yar ta, Hafsa da take 'yar gata gaba da baya, ba ta san wahala ba, amma a tilas aka mayar da ita tamkar baiwa saboda wahala da ita da mahaifiyarta. Duk wata azabar aikin gidan nan suke yinta, ga hantara da wulaƙanci, Abinci sau ɗaya tal a rana ake basu, kuma Safiyya ba ta isa ta fita daga gidan ba ko wani ya zo in da take ba. A haka duk wasu alamun girma suka bayyana a tare da Hafsa, kasancewar tana da jiki, duk da wahalar da suke ciki, bai hana surarta fitowa ba. Nan samarin gidan suka fara kai mata hari, suna nema su keta mata haddi. Ta kasa gayawa Mama, sai dai tai ta kula da kanta, tana koke koke. Duk san Hafsa da makaranta ƙarshe sai da suka rabata da Makaranta. Saboda yawan kuka da Safiyya take ba ji ba gani, ya Sanya ta haɗu da wani matsanancin ciwon ƙirji, da ya haifar mata da larurar numfashi. Cikin samarin gidan nan ba wanda yafi uzzura mata, kamar Najib, Najib bashi da mutunci ko ɗa'a, ya samu dukiyar marainiya a wurin mahaifinsa kullum cikin yawo da abokai da shaye-shaye yake, bashi da burin da ya ga Hafsa yayi ƙoƙarin haɗata da jikinsa, ganin taƙi amincewa da hilatarta da yake yi, ya sanya ya fito ya ce Aurenta zai yi, yana sonta. Babansa ya ce ya bashi, sadaki kawai za'a bayar a ɗaura Aure, ai 'yar uwassa ce. Hafsa idan abu na damunta ba ta fiye faɗa ba, ita hasali ma bata magana sai ta ga dama, dan haka sai dai tayi ta faman kuka. Aka aiko wa Mama cewar mahaifiyarta babu lafiya, da ƙyar Aminu ya barta ta je, amma ya ce ba zata tafi da Hafsa ba. Haka ta rarrashi Hafsa ta shirya ta tafi, sai dai ko da taje gida, ta tarar jikin mahaifiyarta yayi tsananin, da ba zata iya komawa gida ba, ta barta a halin da take ciki ba. Har dare Mama bata dawo ba, hakan ya jefa Hafsa cikin damuwa, tun tana jiran dawowar Mama, har ta haƙura ta kwanta bacci. Cikin dare taji mutum a kanta, tana ƙoƙarin tashi, aka danne ta ana ƙoƙarin rabatabda suturar jikinta, shaƙa mata wani abu aka yi, ba ta shaƙi abin sosai ba, jikinta yayi sanyi ƙalau ta kasa motsawa, sai gani take dishi-dishi, wani abu mai nauyi yana rinjayar kanta. Tabbas ko ba a gaya mata ta gane shi, Najib ne ba wani ba. Ba ta sake farkawa ba, sai da garin Allah ya waye, gari yayi haske, ta ji saukar ruwa a fuskarta, ta buɗe idanunta a hankali, tana kallon Mama da ke kanta a rikice tana kuka tana tambayar Hafsa meyasameta?. "Mama Najib ne" shi ne kawai abin da ta iya furtawa. Mama tayi kuka tamkar ranta zai fita ita da Hafsa, ta taimakawa Hafsa ta gyara jikinta, ta kama hannun Hafsa zuwa wurin Aminu, mahaifin Najib, ta gaya masa abin da ɗansa ya aikata. Amma ya hau bala'i, sai da ya janyo hankalin mutanen gidan, uwar Najib ta ce sun yiwa ɗanta sharri. Mama ta ce "Tun da haka ne, wurin 'yan sanda zata kai ƙara" Aminu ya hanata fita, ya cigaba da azabtar da su, kullum Hafsa cikin kuka take ita da Mama, Mama tun bata magana, har Mama ta buɗe baki ta yiwa Aminu Allah ya isa a gaban iyalansa. Babu tausayi ko imani, ya ware ƙwanji ya dinga dukanta, Hafsa taje cetonta, ya haɗa da ita da Hafsa ya dinga jibgarsu, duka na wulaƙanci kamar dabbobi sannan ya haɗawa Mama da saki uku ba tausayi ba tsoron Allah. Haka suka koma gidan da mahaifiyar Mama ke jinya, ba Abinci babu mai basu kulawa, ita ma ta zo ta rasu, hakan ya jefa Mama cikin tsananin damuwa ta haɗu da larurar hawan jini, da ya haɗu da Asma suke addabar rayuwarta tamkar zata rasa ranta. Duk da haka Najiba bai fasa bibiyar Hafsa ba, saboda rashin Kunya, Mama ta kaisu wurin 'yan sanda shi da mahaifinsa, amma yayi amfani da dukiyarsu ya toshe bakin 'yan sanda, saboda Najib, Mama ta sayar da gidan da suke ciki na mahaifiyarta, suka tashi suka koma ɗorayi, gidansu na farko da ta rayu ita da Usman farkon Auren su. Da kuɗin gidan, ta mayar da Hafsa Makaranta, sai dai Hafsa ta ƙara rasa kuzari da shiga damuwa, tun bayan Najib ya keta mata haddi. Zamansu a gidansu Najib da tashinta cikin tsnagwama da takura, ya ƙara nesanta da farinciki ko cikakkiyar walawala ba ta yi, balle fara'a. Ƙarshe suka cinye ragowar kuɗin, babu mai basu Abinci, duk da tarin alkhairan mahaifinta ga al'umma, babu wanda ya dube su bayan rasuwar su, da ƙyar Hafsa ta kammala karatun sakandare, daga baya Hafsa ta fara wannan sana'ar ta sayar da awara. Hafsa ta rushe da wani irin kuka, jikinta har karkarwa yake yi, Khalil ya yi shiru, ya kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi. Ayshercool 08081012143 RUƊIN ƘURUCIYA https://arewabooks.com/chapter?id=6220844388e1ec3a041032a8 _*ƘURUCIYA: Ita ce mataki mafi hatsari da kowane ɗan Adam yake tsallakewa kan ya zama babban mutum me cikakken hankali. Sai dai wannan mataki da ɗan Adam ke tsallakewa shekaru ne masu hatsarin gaske, idan ya wuce su lafiya ana saka masa ran samun kyakywar rayuwa zuwa tsufa, idan kuwa aka samu tangarɗa rayuwa ta samu tawaya zuwa tsufa. SHIN KE UWA CE? SHIN KINA CIKIN WANNAN MATAKI NA ƘIRUCIYA HAR YANZU, KO KUWA KAI NAMIJI NE KANA DA 'YAN UWA MATA? Ya dace ki karanta wannan littafi. Rayuwar matasanmu a makarantun sakandare, hatsarin wasu al'adun bahaushe ga 'ya'yayensu mussaman mata, illar sangarta, Cutar depression, shaye-shayen matasan yara mussaman mata, dama abubuwa da baku yi zato ba, suna nan a cikin wannan littafi, ku garzaya manhajar Arewabooks don mallakar naku, ko ku kira wannan lambar don sayen naku a kan kuɗi ƙalilan 08081012143*_ Ayshercool. GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) To get the latest update of the story Follow me on Watpad Ayshercool 7724 Arewabooks Ayshercool 7724 What's app 08081012143 *Littafina Aƙidata da kuma Ruɗin ƙuriciya, na kuɗi ne, sauran duk free me* 20-21 Wani irin abu mai bala'in ɗaci ne, ya shiga tsirgawa Khalil tun daga maƙogwaronsa zuwa cikinsa, duk da sanyin AC dake cikin motar, bai hana shi tsatstafar da wani irin gumi ba, idanunsa suka yi jawur. Yayi shiru ya rasa abin da zai ce, sai kukan Hafsa da ya cika motar ya ke masa amsa kuwwa a cikin kunnunwamsa. Tamkar mai koyon magana ya fara shirya jimlar da zai rarrashi Hafsa da ita, sai dai suka maƙale a iya wuyansa, ya kasa furata su a kan harshensa. Da ƙyar ya iya cewa "Is ok, kukan ya isa haka, kije gida, ki samu wuri ki kwanta ki huta" Hafsa ta kalli Khalil tana son karantar wani abu a fuskarsa, amma ta kasa kasancewar, ya kauda kansa gefe. Cikin ɗan ragowar kuzarin da ya rage mata, wanda take jin tamkar ba zai iya ɗaukarta ba, ta buɗe murfin motar, ta ja ƙafafuwanta da suka gama yi mata sanyi kamar ba a jikinta ba, zuwa cikin soron gidansu, wanda duhu ya mamaye, ta durƙusa ta haɗa kanta da gwiwa ta cigaba da rera kukanta. Sai da Khalil ya tabbatar ta shiga gida, sannan sannu a hankali ya kunna motar ya bar wurin, cikin tsananin tunani da damuwa Khalil ya nufi hanyar gida. Ikon Allah ne kawai ya kai Khalil gida, saboda tuƙi yake sam hankalinsa baya jikinsa, dan lokaci lokaci ya kan daki sitiyarin motar tasa da ƙarfi yana huci. Amina ta zazzage kayan da Ammin Azima ta bata, har da kayan kwalliya, da wasu dogayen riguna da atamfa, ga kayan ciye-ciye. "Ohh ni Amina, Allah sarki ashe akwai masu kuɗi masu mutunci, matar nan har da rungumeni kamar 'yar da ta haifa, a gidan nan kuwa bayan hantara da kyara ba abin da suka saka gaba, muma Allah kai mana arziƙi na halal muyi ta jawo 'yan uwa talakawa muna ci tare. Hafsa kuwa sai da tayi kuka mai isarta, sannan ta share hawayenta ta shiga gida. Mama ta ce 'Khalil ɗin ya tafi ne?" Jinjinawa Mama kai kawai tayi, ta shiga ƙoƙarin gyara shimfiɗarta ta kwanta. "Ko dai halin naki na wulaƙanci kika yi masa ne? Naga kin dawo ba walwala jiki duk a sake" Murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo Hafsa tayi ta ce "Haba Mama, ba abin da nayi masa, lafiya ƙalau muka rabu, bacci nake ji ne". "To shikenan, ba zaki ci Abinci ba zaki kwanta". "Eh, na ɗumama da safe, cikina ya ɓaci ɗazu" "To shikenan, Allah ya sawwaƙe" Hafsa ta nemi wuri ta kwanta, ta shige cikin bargo, ta ɗauko 'yar wayarta ta zuba mata ido, tana tunanin ko Khalil zai kirata a wayar, har ku san sha ɗaya na dare, ta kasa bacci tana dakon saƙon Khalil kamar yadda ya saba, amma shiru nan da nan wata karaya ta zo mata, ta sawa zuciyarta cewa Khalil babu lallai ya cigaba da sonta ko ya aureta, Gashi ta kamu da soyayyarsa ba da wasa ba. A hankali ta sanya hannu ta toshe bakinta, ta lumshe idanunta hawaye suka dinga zuba daga idanunta. "Hafsa ya naji kamar kina nishi? Ko mura kike?" "Eh Mama" "Sannu, daga yanzu idan ya zo ki dinga yi muku shimfiɗa a soro, kinga garin da sanyi sosai, har da wannan iskar ta saki mura" Hafsa ji tayi tamkar ta ce "Mama ba zai dawo ba' Amma ta ce "To" ta ja bakinta ta tsuke. Khalil juyi kawai yake a kan gadonsa, ya rasa in da zai sa kansa yaji daɗi, idan aka jima sai ya tashi zaune yayi tagumi ya rirriƙe kansa, idan ya gaji sai ya koma ya kwanta. Tunani daban daban a zuciyarsa, me yasa dangin Mahifin Hafsa suka kasance a haka? Tuna nasu dangin mahaifin yayi, yadda suke nuna musu ƙauna da soyayya, amma sam Mummy ba ta son alaƙar su da su, tabbas da sune suka tsinci kansu a halin da su Hafsa suka tsinta, ya san babu yadda za ayi, dangin mahaifinsu su wulaƙanta su haka. Gaba daya bacci ya gagari idanun Khalil, saboda damuwa. Washegari da safe ma haka ya tashi duk babu daɗi, dan haka ya kashe wayoyinsa, dan karma wani ya takura masa. Har ƙarfe sha biyu na rana ba Khalil babu dalilinsa bai fito ba, balle ya karya kumallo. Mummy ta kasa jurewa ta tafi sashin Khalil, abin mamaki ta ganshi a ƙudundune a kan gado. Da sauri ta ƙarasa tana kiran sunansa, tare da janye bargon. A hankali ya ware idanunsa a kan Mummy, sai da ta tsorata da yadda taga idanunsa sun yi jawur, jijiyoyin kansa duk sun kumbura. "Khalil lafiyarka ƙalau kuwa?" A hankali ya gyara kwanciyarsa, ya tashi zaune yana sauke ajiyar zuciya. "Magana nake maka fa, baka da lafiya ne?". "Da ciwon kai na kwana ne" "Amma shi ne baka gaya mini ba? Kalli yadda duk ka koma wani iri, kwanciyar ce zata yi maka magani? Tashi kayi wanka ka karya, muje in kai ka Asibiti". Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Mummy ki bari ba sai naje Asibiti ba, zan warke". "A'a ban yadda ba, tashi kayi wankan, sai in kira Aliyun ya zo gida ya dubaka" haka Khalil ya tashi ya nufi banɗaki, yana jan ƙafa kamar wanda yake maye. Ko da Mummy ta koma ta tura Amina, taje ta gyarawa Khalil ɗaki ta kai masa Abinci. Wasa-wasa kan Doctor Aliyu ya zo, wani irin zazzaɓi ya rufe Khalil, ga jiri da yake ɗibansa yana daga kwance. Nan da nan kowa hankalinsa ya tashi a gidan, suka shiga damuwa Daddy da baya nan ma ya dawo gida, duk suka kewaye Khalil da Mama ta lallaɓo shi, ta dawo da shi falo ta bashi Abinci, shi ma da ƙyar ya ci ya ce ya ƙoshi. A tambayoyin da Aliyu ya yi masa, ya fuskanci kamar wani abu ne a ransa yake damunsa, amma ganin Khalil na kakkaucewa ya Sanya ya ƙyaleshi, ya rubuta allurai da ruwa ya bayar aka sayo. Ita Amina har mamaki abin yake bata, murƙusheshen ƙato kamar Khalil, amma dan yana zazzaɓi an kewaye shi, sai sannu suke masa, wanan na shafa kansa wannan na wannan, fuskokinsu duk damuwa. Suna nan zaune aka ƙwanƙwasa ƙofar falon, Amina ce ta tashi ta je ta buɗe, Abdul ta gani a tsaye. Murmushi tayi masa tare da gaishe shi, ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Khalil na ciki ne? Na kira wayarsa a kashe, kuma na zo ɗakinsa tun ɗazu baya nan". Amina ta ce "Shigo gashi nan bashi da lafiya" "Subhanallah" shi ne abin da ya furta, ya shiga falon da sauri. Mummy na tozali da Abdul ta haɗe rai, haka ma Fadila, suka wani tsuke fuska tamkar sun ga kashi. Abdul ya sha jinin jikinsa, amma ya basar, ya ƙaraso ya gaida Daddy, Daddy ya amsa masa cikin sakin fuska, Mummy kuwa da ƙyar ta amsa masa, ya miƙawa doctor Aliyu hannu suka gaisa. Abdul ya ce "Daddy meya sameshi haka? Shekaranjiya mun haɗu lafiyarsa ƙalau". Daddy ya ce "Ka san shi Allah ba yadda ba ya juya lamuransa, yau dai ya tashi jiki babu daɗi, ni ban sani bama, na fita muna shirya wata seminar da za ayi da a Kano. Khalil ya buɗe idonsa ya kalli inda Abdul yake. Abdul ya ce "Khalil, sannu ya jikin" Khalil baya son yin magana, dan haka ya yiwa Abdul alama da ya matso kusa da shi. Abdul ya matsa kusa da Khalil yana masa sannu. Ya kamo hannun Abdul, ya ɗora a goshinsa, a hankali ya furta "Abdul kaina kamar zai fashe". "Sannu zai daina, ya a kai ka kwana babu lafiya baka gayawa kowa ba?" "Ka bari kawai, ka zauna a nan kusa dani" "To ina nan kusa da kai" Haushi ya kama Mummy, Fadila kuwa kallon da Abdul ke mata ne, ya sa ta ja tsaki, tana harare harare. Doctor Aliyu ya kalli Fadila ya ce "Autar Mummynta, ina abokin nan naki kuwa ya jikin nasa?" "Ya warke" ta bashi amsa. "Masha Allah, yana nan dai ƙalau ko? Ko shi ne sirikin Mummy ne?" Haushi ne ya kama Fadila ta ce "Ban sani ba" ta miƙe ta bar falon, Mummy ta bita da kallo. Ta kalli Aliyu ta ce "Wai a kan wa kake magana ne?" "Wani abokin karatun ta ta kawo mana Asibiti, bashi da lafiya yana fama da asma, shi ne nake tsokanarta". Mummy ta ɗan gimtse baki, tana hura hanci. Abdul yana nan zaune, har ruwan da aka sakawa Khalil ya ƙare, lokacin la'asar tayi, Khalil ya ce masallaci zai tafi. Mummy ta ce "Ka haƙura kayi salla a gida, saboda jirin". "A'a Mummy, zan bi Abdul" ba dan Mummy ta so ba, ta ƙyale shi. Khalil ji yayi kamar ya gayawa Abdul, halin da ake ciki, amma yaji wannan sirrin Hafsa ne, idan ya bayyana bai yi mata adalci ba. Suka je suka yi salla, Abdul ya ɗau Khalil zuwa wurin da suke zuwa shan fura, dan yaji daɗi, ya bawa Abdul labarin abin da dangin Mahaifin Hafsa suka yi musu, amma ya ɓoye masa batun fyaɗen nan. Ya ɗora da cewa "Abdul, nayi mamakin jin yadda dangin mahaifinta suka yi musu haka, dangin Daddy nake tunawa, irin karamcinsu da soyayyarsu a garemu, danma Mummy ba ta son alaƙarmu da su". Abdul ya ce "Khalil, lokaci yayi da yakamta ka cigaba da zumunci da dangin mahaifinka, ko da Mummy ba ta sani ba". "Ka san wani abu, ina ganin zan shigar da ƙarar yayyane mahaifin Hafsa a ƙwato musu hakkinsu". Abdul ya ce "A'a Khalil, bakomai ne ake amfani da dukiya ko ƙarfi wurin ƙwatarsa ba, ka mayar da hankali wurin mallakar yarinyar, da kyautata musu, su bar su da Allah kawai, ba abin da dukiyar zata amfana musu, dan ba guminsu bane a banza zasu kaɗar da ita". "Abdul, ji nake tamkar in nemo yaron nan da ya kai Hafsa wurin 'yan sanda in kashe shi" a razane Abdul ya kalleshi ya ce "Kayi hauka ne kake zancen zaka kashe wani, me yayi maka?" Taune lips ɗinsa na ƙasa yayi, yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin lugude, kansa na sarawa, yayi shiru bai kuma cewa komai ba. Ba dan Hafsa na gudun kar Mama ta gane wani abu na faruwa ba, da ba zata fita wurin sana'ara ba ma, haka ta fita wurin sana'ar nan sama sama haka take, loka lokaci tana duba wayarta, ko zata ga kiran wayar Khalil ko saƙonsa, amma shiru ba ta gani ba. Hakan ya ƙara jefata cikin damuwa da karaya, ta saddaƙar Khalil ya rabu da ita kenan, ba zai iya ɗaukar ƙaddarar da Allah ya jarabceta ba. Gashi wani irin son Khalil take ji a ranta. Khalil ya ɗan samu sauƙi, amma sam ya kasa kunna wayarsa, saboda gaba ɗaya kaɗaici yake so baya son damuwa sam, saboda ciwon kai da yake damunsa haryanzu, duk da tunanin Hafsa da tausayinta sune suka haifar masa da halin da ya tsinci kansa a ciki, yana son ya kirata a waya yaji ya take, amma ganin idan ya kirata bai san me zaice mata ba ya sanya ya fasa kiran nata. Amina ta lura ƙarfe bakwai saura, Daddy ya ke shiryawa ya fita, ko karyawa ba ya yi. Ƙarfe shida saura tana kitchen tana aiki, taji motsi a falo, dan haka ta fito falon, Daddy ta gani yayi shirin fita, sai zuba ƙamshi yake. "Daddy ina kwana" ya ɗaga idonsa ya kalli Amina, dake tsaye tana kallonsa. "Lafiya ƙalau" ya amsa mata. "A kawo breakfast ne? Naga zaka fita baka karya ba". "No, ina daf da makara, ba saina karya ba". "Ok, bari in kawo maka mota, sai ka tafi da shi". "Ok, shikenan" Amina ta koma kitchen, ta haɗo Abinci a cikin kwanuka ta saka a kwando, ta kaiwa Daddy mota. Mama tana banɗaki tana wanka, Hafsa ta saka wayarta a gaba, tana ta gursheƙen kuka, sam ba ta san Mama ta fito daga wanka ba, sai ganin Mama tayi a tsaye a kanta. Da sauri ta wayance ta fara ƙoƙarin goge hawayen. Mama ta ce "A'a, ai ba sai kin wayance ba, kin san adadin lokacin da na ɗauka atsaye a kanki? Ni dama a kwana biyun nan tun da muka dawo daga Asibiti naga kamar kina cikin damuwa, sai dai bana son takura miki ne, saboda ke idan baki ga dama ba mutum in zai mutu, ba zaki faɗa masa damuwarki ba. Yanzu gaya mini meye dalilin wannan kukan?". "Mama bakomai". "Bakomai Hafsa, ba zaki gaya mini ba kenan, me kike kallo ko kike jira a wayar da kika sata a gaba kina kallo?". Bata san lokacin da ta sake rushewa da kuka ba, tare da faɗin "Mama Khalil". Mama ta zauna kusa da ita ta ce "Meyafaru da Khalil ɗin?". "Mama na gaya masa, be sake kirana ba, ina ga ba zai iya aurena a haka ba, Mama ba zan taɓa yafewa dangin mahaifina ba, sun mini mugun tabo, ba kowa zai yadda da ni ba" Jikin Mama yayi sanyi ƙalau, ta rungomo Hafsa a jikinta, ta runtse idanunta hawayen tausayin Hafsa na tsiyaya daga idanunta. "Taki ƙaddarar kenan Hafsa, a haka Allah zai baki wanda zai so ki a haka, ki daina kukan nan" ƙanƙame Mama Hafsa tayi, ta cigaba da rusa kuka tamkar wadda uwarta ta mutu. Sai bayan la'asar Sannan Alhaji Ahmad ya dawo gida, da Amina ya fara tozali, tana kunna wa falo turaren wuta, tana sanye da doguwar rigar atamfa, ta ɗaura ɗankwalin atamfar. "Sannu da zuwa" ta faɗa cikin girmamawa. Ya amsa mata da cewa "Yauwa sannu, ga kwanukan ki can a mota, kije ki ɗauko na gode sosai". "To Daddy, bari in gama kunna turaren zan ɗauko" ta cigaba da zaga falon, dan ko ina ya samu ƙamshin turaren, ya nufi sashinsa kai tsaye. Sai da Khalil ya kwana uku, sannan ya samu ya rabu da wannan matsanancin ciwon kan, ya ɗan ji ƙwarin jikinsa, yaji ba abin da yake buri banda ya ga Hafsa. Da magariba ya shirya cikin ƙanan kaya, ya sha turare bai ko tsaya yiwa Mummy sallama ba, saboda baya son ta tutsiye shi da tambayar ina za shi?. Fadila na ɗakinta, tana game a waya, Mummy ta shigo tana ɗan tsareta da ido. "Mummy ya dai?" "Wace maganar na ji doctor Aliyu yana yi ɗazu?" "Wace magana kenan Mummy?" "Wa kika kai Asibiti?" Fadila ta ce "Ba wani bane, wannan Yazeed ɗin ne da nake baki labari" "To meye haɗinki da shi da zaki kai shi Asibiti? Nifa bana son jaye-jaye me haɗin kanwa da kuka?" "Mummy, bani da wata alaƙa da shi, bani da wani zaɓin da ya wuce in kai shi Asibiti Mummy, na taimaka masa ne saboda.. "Saboda me? Wanene ɗinki shi?" "Mummy matsalata da ke saurin ɗaukar zafi, ki tsaya ki saurareni Mummy, da ban yi hakan ba da tuni ina nan ina rama azumi sittin". Mummy ta ce "Kamar yaya?" Nan ta warwarewa Mummy abin da ya faru, ta ɗora da cewa "Shi ne saboda son gulma yake wani tambayata a gabanki, ni babu wata alaƙa tsakani na da Yazid". "To ai shikenan, duk da haka a dai kiyaye, dan ba zan amince a kawaso mini gayyar tsiya cikin zuriya ba". Fadila tayi murmushi ta ce "Mummy kenan, ki sha kuruminki, ai nima na san ni ba kalar talaka ba ce" "Ƙwarai kuwa, ai mun tattauna da Hajiya Turai, akwai ƙaninta da ya taɓa ganin hotonki ya ce mata yana sonki, a U.K yake aiki, ina jiran ya dawo ne tukua kan in sanar da ke, sai kuma Allah ya kawo hira na ke gaya miki" Yamutsa fuska Fadila ta yi, taƙi magana. "Ya kika yi shiru?" "To Mummy me zance? Ni dai in bai mini ba, ba ruwana da wata U.K" "Ke dalla can, zai ma yi miki" Fadila ta ɗan taɓe baki, sai dai kawai taga fuskar Yazeed na mata gizo. Har Mummy ta ƙarasa surutanta ta fita daga ɗakin, ba wani gane me take faɗa take ba. Wayarta ta miƙa hannu ta ɗauko, ta ci karo da saƙon Kankiya, da yake addabarta da su. Wani uban tsaki ta ja, ta kashe wayar, maganar Yazeed na ƙoƙarin zamowa gaskiya, Sir Kankiya sonta yake yi. Ɓangaren Hafsa kuwa, wunin da tayi koke koke ita ma ya sanya, ciwon kai ya kamata, dan ko wurin sana'ar ba ta fita ba, ta kasa cin abinci sai aikin rarrashi da Mama take yi. Wayarta ce ta ɗan yi vibrating, ta miƙa hannu ta duba. Message ne. "Ina waje" Da sauri ta tashi zaune ta ce "Mama, Khalil ne wai yana waje" Mama ta ce "Alhamdilillah" da sauri Hafsa ta tashi zata zari hijjabi. "Haba ke kuwa, kije ki wanke wannan kumburarriyar fuskar ta ki, ki canza wasu kayan mana" Cikin azama Hafsa ta je ta wanke fuskarta, jiki na rawa ta fara neman kayan da zata sauya. Tausayin Hafsa ya kamata, tabbas Hafsa ta kamu da son Khalil sosai. Ta ɗau dadduma ta nufi hanyar fita har da tuntuɓe. Yana tsaye a jikin motarsa tana ganinsa ta tsaya cak, tana kallonsa. "Shi ne kika shanya ni, da juyawa zan yi in koma ai" Kawai ta fashe da kuka. Khalil ya ce "Subhanallah, Kuka kuma? Me nayi?" Kuka take sosai, ta kasa cewa komai. Ya karɓi sallayar hannunta, ya shimfiɗa a kan dakalin gidan, sannan ya zaunar da ita, ya fuskanceta "Am sorry, na tafi ban kuma kiranki ba, bani da lafiya ne, baki ga na rame ba?" "Na zata ba zaka dawo ba" ta faɗa cikin kuka. "Baby me zai hana ni dawowa?" Magana take son yi, amma ta kasa. Khalil ya gyara zamansa ya ƙara matsawa kusa da ita ya ce "Ya isa haka dan Allah, so kike ki kuma sani a damuwa? Ki daina Please" da ƙyar ya samu ta sassauta kukan da take ta ce "Na zata ka daina sona ba zaka dawo ba, saboda abin da na gaya maka, ko kana ganin ƙarya nake yi". "Haba Hafsa, Wallahi ba haka bane, labarinki ya tsma zuciyata to the extent tun da na bar wurinki bani da lafiya, sai yau na samu sauƙi. Ina da ƙanwa mace, mai rawar kan tsiya da tsiwa, sai dai idan makamanciyar ƙaddara irin taki ta sameta wani ya muzanta ta yaƙi aurenta, ko ya ce ƙarya ne abin da ya sameta bai mini adalci ba, Saboda na fi kowa sanin halinta, duk rashin jinta, tana da kamae mutuncinta, kwatankwacin yadda kike. Meyasa zan ƙi dawowa gareki, dan wani abu da kika rasa a sanadin ƙaddara wanda ko ni ɗin ne na karɓe shi, iya na lokaci ɗaya ne, kyawawan ɗabi'unki da halayarki da su zan rayu tsawon rayuwata?. Matasa da yawa bama yiwa kanmu adalci, wurin zubar da mutunci da ƙimarmu kan mallakar abin da Allah ya halarta mana na aure. Sai dai akwai tsautsayi da ƙaddara, abin da kika gaya mini na yarda ɗari bisa ɗari, kuma ni banji cewar zan iya rabuwa da ke saboda haka ba, ina son ki Hafsa, kuma ni aurenki zan yi, dan Allah ki daina wannan kukan" "Dan Allah haryanzu kana sona?" Tayi maganar tana kallonsa. Yayi mata murmushi ya ce "Ina sonki mana, kema kina sona?" Murmushi take haɗe da hawaye ta ce "Na zata ba zaka dawo ba ka daina sona, shiyasa nayi ta kuka" "Allah sarki Sweetheart ɗina, ni damuwa ce ta sani rashin lafiya, na kashe wayoyina, amma kina zuciyata am sorry for not hearing from me" Hannayenta biyu ta haɗa a fuskarta ta cigaba da kuka. "Babu ya isa haka mana, ki daina kukan nan mana" "Kukan farinciki nake ka ƙyaleni" Murmushi yayi ya ce "Dole ki kuka, Allah ya azurta ki da ɗan shawalwalin saurayi kamata, ɗan beauty da ni" Murmushi tayi, duk da akwai hawaye kwance a fuskarta. "Yanzu gaya mini, kina sona?" "Sai nayi shawara" ta faɗa tana dariya, wadda ke ƙara mata kyau. "Kin ma isa? Sai kin faɗa ai". "Ina sonka Ibrahimul mu'azzam" ta faɗa tana kauda kanta gefe guda. "Alhamdilillah, Masha Allah, bana jin ko Daddy da ya raɗa sunan nan, ya taɓa daɗi a bakinsa kamar yadda ya yi a naki bakin, Ibrahimul mu'azzam. Kai amma na sha gwagwarmaya kan in shawo kan wannan Japanese baeb ɗin" "Nice Japaneese ɗin kuma?" "Eh mana, My Japanese doll" murmushi suka yi gaba ɗaya, Khalil ya dinga kwantar mata da hankali, da sake bata tabbacin iya wuya, zai aureta yana tare da soyayarta. Suka kasance cikin nishaɗin da sai da ya wanke musu zukatansu daga dukkanin damuwowin da suke ciki. Khalil ya nisa ya ce "Ina ga idan na sake dawowa, zan shigar da ƙarar dangin mahaifinki, in ɗaukar muku lawyer, a ƙwato muku hakkinku. Hafsa ta girgiza kai ta ce "A'a, ni bana son duk wani abu da zai sake haɗamu da su, mun barwa Allah, wanda ya tara dukiyar ma yau yana ina? Allah ya karɓi abunsa, ni fatana Allah ya bamu mafita kawai" "Allah sarki babyna, insha Allah very soon zan aureki, mu wuce wurin nan, sonake ai komai da komai a abinda bai wuce 6months ba" Hafsa ta ce "Kai, yayi wuri da yawa ai". "Ba wani wuri, amfanin soyayya aure, sai munyi aure za muyi soyayya ta gaske" "Ni ban isa aure ba" ta faɗa a shagwaɓe. "To ni na isa, ki bari idan muka yi auren, sai mu gani in dagaske baki isa auren ba" Jin Khalil zai ɓaro magana ya sanya ta ja bakinta ta tsuke. Kayan ciye-ciye ya bata, tare da bata saƙon gaisuwar sa zuwa ga Mama, ya yi mata sallama ya tafi. Ba kowa a falo, sai Daddy yana ta aiki a computer, Amina ta hango hasken lantarki a falo, ta fito falon da nufin ta kashe wutar, ta tarar da Alhaji Ahmad yana ta aiki a kan system. Komawa tayi kitchen, ta yayyanka fruit ƙanana, ta ha ɗa cofee, ta ɗoro a plate ta fito falon. "Daddy sannu da aiki" Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Yauwa sannunki" Ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a gabansa ta ce "Ga wannan naga kana ta aiki" "Masha Allah, na gode sosai kuwa" "Ba komai" ta juya zata koma ya ce "Yauwa, an kirani daga makarantarku ɗazu, sun ce kije ranar Saturday" "Ok Allah ya kaimu, zan je insha Allah" "Good". "Gobe in Allah ya kaimu ma da wuri zaka fita?" Daddy ya ce "Eh da wuri zan fita muna seminar ne" "Ok, to shikenan sai da safe" Ta juya ta nufi in da ɗakinta yake, ta ci karo da Hajara a tsaye tana binta da kallo. Shareta Amina tayi ba tare da ta kula Hajara ba, ta wuce ɗakinta tare da faɗin "Kema Allah zai mini maganinki" RUƊIN ƘURUCIYA https://arewabooks.com/chapter?id=6220844388e1ec3a041032a8 _*ƘURUCIYA: Ita ce mataki mafi hatsari da kowane ɗan Adam yake tsallakewa kan ya zama babban mutum me cikakken hankali. Sai dai wannan mataki da ɗan Adam ke tsallakewa shekaru ne masu hatsarin gaske, idan ya wuce su lafiya ana saka masa ran samun kyakywar rayuwa zuwa tsufa, idan kuwa aka samu tangarɗa rayuwa ta samu tawaya zuwa tsufa. SHIN KE UWA CE? SHIN KINA CIKIN WANNAN MATAKI NA ƘIRUCIYA HAR YANZU, KO KUWA KAI NAMIJI NE KANA DA 'YAN UWA MATA? Ya dace ki karanta wannan littafi. Rayuwar matasanmu a makarantun sakandare, hatsarin wasu al'adun bahaushe ga 'ya'yayensu mussaman mata, illar sangarta, Cutar depression, shaye-shayen matasan yara mussaman mata, dama abubuwa da baku yi zato ba, suna nan a cikin wannan littafi, ku garzaya manhajar Arewabooks don mallakar naku, ko ku kira wannan lambar don sayen naku a kan kuɗi ƙalilan 08081012143*_ Ayshercool. 08081012143 Ayshercool GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) P22-23 Arewabooks Ayshercool7724 Amina ta shige ɗakinta, ta cigaba da saƙa da warwara a cikin ranta, daga bisani ta tashi ta hau gyaran kayanta, dan ba ta jin bacci sam, ita wannan hutun duk ya isheta so take ayi a koma makaranta. Kamar yadda Daddy ya gaya mata, ranar asabar ta shirya ta tafi makaranta, taje ta tarar Quiz ne aka yi musu, domin fitar da gwanayen da za'a tafi da su Abuja, wurin yin babban Quiz na ƙasa. Suka gabatar da quiz, da kuma mini exam da aka yi musu, wanda iyayensu suka je, suka karɓar musu results ɗinsu, Amina na ji tana gani, haka ta dawo gida ba a bata result ɗin ta ba, haka ta dawo gida duk ranta babu daɗi. Khalil jinsa yake tamkar an masa bushara da wani abu na musamman, wata irin Soyayya da shaƙuwa ce suka shiga yi a tsakaninsa da Hafsa, a haka hutunsa ya ƙare, ya koma wurin aiki, cike da kewar Hafsa. Ya labartawa Abdul yadda yayi nasara, Hafsa ta karɓi soyayyarsa, Abdul ya taya shi murna sosai, sai dai a ransa yana tausayawa Khalil gwagwarmayar da zai sha da mahaifiyarsa kan ta amince. Hutunsu Fadila ya ƙare, ji take tamkar ta ɗora hannu a ka tayi kuka, dan sam bata son stress da takurar makaranta. Wannan semester da sabuwar mota dal ta koma school. Bayan ta ƙara kusan kwanaki uku a kan hutun nasu. Kwanaki ukun da ba ta zo ba, har an yi wasu lectures ɗin bata nan. Haka kawai ta fara waige-waige a ajin, ko zata hango Yazid, amma sam ba ta ganshi ba, tana cikin tunanin ko shi ma bai dawo hutun bane, Kankiya ya shigo ajin. Yana shigowa ta haɗe rai, dan ko san ganinsa ba ta yi, tun da ta fara ganin zancen Yazid na daf da zama gaskiya, saboda yadda yake uzzura mata da saƙonni, da kuma kiran waya ba gaira babu dalili. Har kankiya yayi lectures ya gama yana satar kallon Fadila, da ba kowa ne ya san yana mata ba, sai ita ɗin da ya addabawa da ido. Amina na zaune a gaban TV stand, tana gogews, aka turo ƙofar falo haɗi da sallama. Ta ɗaga kai tana amsa sallamar. Hajiya Turai ta gani a tsaye, ta gama ƙarewa Amina kallo daga sama har ƙasa, tana sanye da doguwar riga ta ɗaura ɗankwalin atamfar, kai ba ka ce 'yar aiki ba ce. Ta ɗan taɓe baki ta ce "Hajiya Zainab na nan ne?" Amina ta ɗan kalleta ta ce "Eh tana nan, ki zauna yanzu zata fito". Hajiya Turai za tayi magana, sai ga Hajiya Zainab ta fito cikin shiri, da alama fita za tayi. "Hajiya Turai, har kin ƙaraso?". "Eh, yanzu na shigo ashe ma kin shirya" "Wallahi kuwa, ai na san ba kya son jira, bari muyi mu tafi" ta mayar da hankalinta kan Amina ta ce "Ki kula mini da gida da kyau, ki kammala girki da wuri, bana son Fadila ta dawo ba a gama girki ba". "To insha Allah" Amina ta faɗa cikin girmamawa. "Wai ni kuwa Zainab, haka kika bar Yarinyar nan tana miki yawo a gida, ga mijinki ga ɗanki, ba zata dinga saka hijjabi ba, naga wancan zuwan da muka yi da hijjabi a jikinta, tafa fara girma kalli ƙirjinta a cike fam, kalli ƙugunta" Amina a ranta ta ce "Ji 'yar bala'i har ta ga ƙirjina, ta rasa in da zata kalla sai nan, wannan ai iskanci ne, tubarkallah". Mummy tayi wata dariyar ƙeta ta ce "lallai Turai kin manta wacece Zainab ne, Ai Alhaji Ahmad na riga na zame masa teku, na sha kansa ba yadda ya iya da ni, gidan nan daga ni sai 'ya'yana, da can bai ƙara aure ba sai yanzu da girma ya kama shi, Khalil kuwa shima ya san bai isa ya kawo mini jinin babu cikin zuriyata ba" Sukayi dariya tare da yin shewa suka fice. Kwaɓe baki Amina tayi, ta cigaba da aikinta a ranta ta ce "Ko ni me zanci da dattijo ma oho, in banda tsautsayi wa zai auri jinin wannan matar ko ya auri mijinta, bala'inta ya ishi mutum?' ƙarshe dai Amina ta manta da batun Hajiya Zainab, ta fara tilawarta tana yi tana aikinta. Ta kammala goge gogenta, ta miƙe zata bar wurin, tayi ido huɗu da Alhaji Ahmad, da ke tsaye yana kallonta. Shan jinin jikinta tayi kamar mara gaskiya, ta ɗan diririce, dan sam ba ta zata yana gidan ba. "Ina kwana" ta furta tana kauda kanta gefe. Bai amsa mata ba ya ce "Kawon breakfast" "Ai ban san kana gida ba, an cinye komai sai dai in wani abun zan dafa maka" "No, haɗo mini coffee kawai, ina da biscuit sai in haɗa" yana gama maganar ya juya ya bar wurin. Mamaki ne ya kamata, babban mutum kamar wannan ya ce zai karya da biscuit. Kitchen ta nufa, cikin azama ta fara feraye dankali. Hajara ta shigo kitchen ɗin ta sameta tana gyara dankali. "Amina me kuma zaki da dankali?" "Babansu Fadila ashe yana gida, hajiya ba ta yi mana bayani ba, ba a yi breakfast da shi ba, shi ne nake haɗa masa" "Yayi" shi ne abin da Hajara ta ce ta bar kitchen ɗin. Nan da nan Amina, ta dafa tea da dankali, ta haɗa a tray ta tafi kai masa, sai dai ta shiga tunanin ina zata kai masa?. Ta yanke shawarar kai masa kan dining, taje ta ajiye ta cigaba da sabgoginta, sai kuma ta tuna ba yadda za ayi ya san ta kai masa, idan ba gaya masa tayi ba. Cike da faɗuwar gaba, ta nufi part ɗinsa, ta shiga da sallama, yana zaune a falonsa yana kallon labarai. Bai waiwayo ba ya amsa mata. Cikin ladabi ta ce "Ga Abincin can a kan dining". "Kawo min nan" ya faɗa a taƙaice. Amina ta ɗan yamutsa fuska ta koma falo, tana mitar Alhaji Ahmad ya fiye mulki, sai dai shi baya wulaƙanci kamar matarsa da 'ya'yansa, sai dai miskili ne na gaske. Da sallama ta koma falon, taje gabansa da tray a hannu ta tsaya, ta kalli kan Centre table ya miƙe ƙafafuwansa a kai, ta wuce Kan dining ɗin dake falon, ta ajiye masa. Har ta juya zata fita a hankali ya ce "Nan zaki kawo mini" Amina ba ta san lokacin da tura baki ba, ta sake ɗauko trayn ta dawo gabansa, ta kalli ƙafafuwansa dake kan Centre table, in da yakamata ace ta ajiye kayan Abincin. "To a ina zan ajiye?" Tayi maganar tana satar kallonsa, dan ba ƙaramin kwarjini yake da shi ba. Shareta yayi, ya cigaba da latsa remote ɗinsa. Ta ajiye a saman carfet, ta juya zata fita "Zo nan" ya faɗa ba tare da ya kalli in da take ba. Ta dawo ta tsaya. Ya sauke ƙafafuwansa daga kan Centre table ɗin, yayi mata nuni da ido, a kan a nan zata ajiye masa Abincin. Kamar Amina ta fasa ihu, dan ta ƙulu sosai, haka ta ɗau tray ɗin ta ajiye a kan table. "Come back in the next 30minutes" ya faɗa yana gyara zamansa. Amina ta bar falon tana "yau naga tsiya da wasali, da iko da mulkin mulaka'u na masu kuɗi, a haka kamar na Allah ashe shima ya iya tsiya, aikuwa ba zan koma ba" ta leƙa ɗakin Hajara ta ce "Mai gidan nan ya ce kije nan da mintuna talatin" Hajara ta zare ido, ita a zamanta a gidan nan banda gaisuwa ba abin da yake haɗata da Alhaji Ahmad, ko aiki baya sata, me zai sa ya ce ta je? "Amina nayi laifi ne?" "Nima ban sani ba, ya ce dai kije" A rikice Hajara ta ce "Na shiga uku Allah ya sa ba korata zai yi ba ni Hajara" Amina ta koma ɗaki abin ta, yayin da Hajara ta tasa agogo tana lissafin mintuna talatin cikin zullumin rashin sanin dalilin kiran da mai gidan yake mata. Sai da Hajara tayi Addu'oi sosai sannan ta tunkari sashin Alhaji Ahmad. Tayi sallama ya amsa mata, ta ƙarasa ta shiga falon, ta zube a ƙasa ta ce "Alhaji gani, Amina ta ce kana kirana". Da mamaki ya kalli Hajara ya ce "Ni kuma?" "Eh haka ta ce mini, tun ɗazu ta ce bayan mintuna talatin kana kirana" ya ɗan yi shiru tare da jinjina kai ya kalli Hajara ya ce "Kirawo mini ita" Hajara ta koma ta kirawo Amina, sai dai bata ɗakinta, sai da tai ta dubawa ta ganota a ɗakin Fadila tana gyara mata. Nan Hajara ta isar mata da saƙon Alhaji Ahmad na kiranta da ya yi. Sai kuma a lokacin ita ma cikinta ya ɗuri ruwa, sumi-sumi tabi bayan Hajara suka koma falon Alhaji Ahmad. Ya kalli Hajara ya ce "zaki iya tafiya" Sai a lokacin Amina ta ga tayi wauta, ya mayar da hankali ya cigaba da kallon TV, tamkar bai san da wanzuwar Amina a wurin ba. Amina tun tana sanya ran zai kulata, har ta sare gashi ta gaji da tsayuwa, ya ɗago ya kalleta, yayi mata alama da ta je gabansa. Ba musu ta je in da yayi mata nuni. "In zauna?" Ta faɗa a raunane. Ya ɗaga manyan idanunsa masu matuƙar haske da kwarjina, ya tsareta da idanunsa ya ce "Na ce ki dawo in the next 30minutes, amma kin turo mini wata, kin kyauta kenan? Ko kuma kin san dalilin kiran?" Amina ta ɗaga kai ta kalleshi, amma tayi saurin janye idanuwanta ta ce "Dan Allah kayi haƙuri, nima sai da ga baya na ga nayi laifi, kayi haƙuri" "Kwashe kwanukan nan, kije ki dawo, ko bana falon ki jirani" ta amsa masa da to, ta kwashe kwanukan ta fita sai dai tana zuwa kitchen ta tarar Hajara na tsaye na jiran dawowar ta. "Amina me ya ce miki? Naga kin daɗe" haɗe rai Amina tayi tana tura baki taƙi kula Hajara, ta lura kwanakin Hajara ta koyi munafunci da sanya ido. Ko da ta koma Alhaji Ahmad baya falon, dan haka ta zauna a kan carfet tana jiransa, dan bata manta kashedin Hajiya Zainab ba a game da zaman kan kujera ba. Ta daɗe a zaune, sai ga Alhaji Ahmad ya fito, sanye cikin wani baƙin yadi, ya haska yadin kasancewarsa fari, sai zuba ƙamshi yake yi. Yaje ya buɗe wata drower ya tako in da Amina take, wadda tuni ta miƙe tsaye, ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ranar Sunday in Allah ya kaimu, zani wani ɗaurin Aure haɗeja, ƙarfe shida da rabi zan fita, a ɗan sama mini abin da zan ci kan in tafi" Kamar mara gaskiya Amina ta sunkuyar da kai ta ce "To, insha Allah" "Karɓi nan" Ya miƙa mata envelope ɗin hannunsa. Ta ɗago ta kalleshi sannan ta kalli envelope ɗin, amma ta kasa karɓa. "Karɓi mana" yayi Maganar yana sake miƙa mata. Jiki a sanyaye ta sa hannu ta karɓa, ganin tambarin makarantarsu a jiki ne, ya sanya hankalinta ya ɗan kwanta. "Buɗe da sauri, zan fita" jiki na rawa Amina ta fara kokowa da envelope ɗin, tana ganin takarda ta san result ne, aikuwa gabanta ya faɗi, hannunta ya hau rawa. "Ko ba kiyi abin Arziƙi bane, kika tsorata haka?" Bata san lokacin da ta ɗaga masa kai ba alamar eh. "To ciro mu gani" ya faɗa yana cigaba da tsareta da ido. Ta zaro paper, ta shiga dubawa duk grades ɗinta A ne, First position ta gani a jiki. Wani irin farinciki mara misaltuwa ya ziyarci zuciyarta, ta ɗago ta kalli Alhaji Ahmad fuskarta ɗauke da murmushi, ga hawaye a lokaci guda na farinciki da suka zubo mata a kan fuskarta, a kan gwiwarta ta zube ƙasa tana kallonsa. "Yadda ka faranta mini, ta hanyar maida ni makaranta, Ubangiji Allah ya faranta maka, ya sa ranar alkiyama ka karɓi littafinka a hannun dama" har cikin kansa addu'a da tayi masa ta tsirga masa. "Ameen ya Allah, Na gode tashi tsaye" A hankali ta miƙe tana cigaba da share hawayen fuskarta. "Makarantarku sun kirani, naje na karɓo result ɗin ki, nayi farinciki sosai da yabon da suke miki, na ƙoƙari da jajircewa, sai dai an ce ba kya jin magana haka ne?" Amina ta sunkuyar da kai alamar a'a. "Ya zaki ce a'a bayan nima kinyi na gani" "Dan Allah kayi haƙuri na daina, kar ka gayawa Baba" "Anyway, an sanar da ni cewar kin ci wannan jarrabawar da suka yi muku, 15th December in Allah ya kaimu, zaku je Abuja, wurin baban Quiz na ƙasa da sauran festival da ake yi na makarantu, zasu fara yi muku lessons na mussaman" Amina ta ɗan yi jimm, da ta san abu ne mawuyaci Baba ya barta taje Abuja, amma ta dake tayi murmushi ta ce "Allah ya kaimu, na gode sosai Allah ya ƙara buɗi yasa ka fi haka, inje in nunawa Baba result ɗin?" Ya jinjina mata kai. Ta juya da sauri ta bar falon. A harabar gidan ta tarar da Baba da Zakiru direban Alhaji Ahmad, suna hira, da fara'arta ta tunkaresu, ta miƙawa Baba takardar hannunta. Ya karɓa tare da kallonta ya ce "Uwata menene wannan?" "Baba sakamakon jarrabawata ne, ka duba ka gani". "To ai kin san sai dai ki karanto mini". "Baba ta ɗaya na zo, duk ajinmu na fi kowa maki" Baba ya faɗaɗa murmushinsa yana faɗin "Alhamdilillah, dama na san uwata ba zata bani kunya ba" Zakiru ya karɓi result ɗin yan dubawa, ya murmusa ya ce "Baba Hassan lallai wannan 'yar taka ƙwaruwa ce, Allah ya dafa 'yar gidan Babanta" Amina tayi murmushi ta ce "Amin Malam Zakiru na gode sosai, ka mini alƙawarin cigaba da koya mini karatun addini, amma haryanzu ka ƙi saka lokaci" Zakiru ya ce "Ba ƙi nayi ba Amina, kinga yanayin aikin namu, wasu lokutan nike kai Alhaji duk in da za shi, idan ba haka ba kuwa gyaran harabar gidan nan kaɗai da aike ta isa ɓata lokaci. Kuma da zarar sun ga muna karatun nan za'a iya tsiro wani abu daban, amma insha Allah zan saka mana lokaci" "To shikenan, na gode sosai" Alhaji Ahmad ne ya fito harabar gidan, Zakiru ya nufi in da motarsa take, dan shi zai fita da shi. Baba kuwa ya nufi Alhaji Ahmad, ya cigaba da yi masa Addu'a da godiya. Alhaji Ahmad ya ce "Ba komai, ai ɗa na kowa ne, naji daɗi sosai kaga zan cigaba da samun ƙwarin gwiwar biyan kuɗin makarantar, tun da tana abin da ake so" Baba ya ce "Haka ne, Allah Ya ƙara arziƙi" Ya amsa da Ameen ya nufi mota. Yau da azahar Fadila ta dawo gida, duk da Sir Kankiya yayi ƙoƙarin ganawa da Fadila a Office ɗinsa, dan har ya tura mata saƙo yana son ganinta a Office ɗin sa, amma ta share tayi tafiyarta, dan zuciyarta raya mata take taje ta tatala masa rashin mutunci, dan ta fara gajiya da takurar da yake mata. Haka nan take mamakin meye ya hana Yazid dawowa Makaranta. Amina tayi farinciki sosai da sakamakon ta na makaranta, ta fara ƙoƙarin cigaba da hora kanta a kan darrussan kimiyya, tun kan a neme su a makaranta, a fara yi musu lesson. Amina ta rage jin haushin Alhaji Ahmad a kan abin da iyalansa suke mata da kuma shima abin da yayi mata. Ranar lahadi tun da ta idar da sallar Asubahi bata koma ba, ranar lahadi da su da masu gidan basu fiye tashi da wuri ba, saboda ba wanda yake fita a ranar. Amina ita kaɗai ce idonta biyu, ta ɗora girki saboda Alhaji Ahmad zai fita. Kan ƙarfe shida da rabi, Amina ta kammala girkin, har ta tsaftace falo ta kukkuna turaren wuta. Tana ta sake goge kan dining, sai hamma take, saboda baccin da take ji. "Sannu da aiki" ta jiyo muryarsa. da sauri ta waiwaya, ta kalli in da yake tsaye "Ina kwana" ta faɗa tana ɗan lumshe ido. Maimakon ya amsa sai ya kuma maimaita mata "Sannu da aiki". Ta fuskanci baya son yayi magana a share, dan haka ta ce "Yauwa na gode, ga breakfast ɗin". Alhaji Ahmad ya ƙarasa ya zauna, ya kalleta ya ce "Afuwan na katse miki bacci" ta ɗan girgiza kai ta ce "Bakomai" Ya bubbuɗe flask ɗin, yayi mamakin ganin ƙosai da soyayyen dankalin Hausa, da kuma koko. Kawai sai ta ga murmushi ya mamaye fuskarsa. "Ke kika yi girkin nan?" Haka nan Amina ta tsinci kanta da tura baki, to wa yayi idan ba ita ba, saboda kawai ya raina mata hankali yake tambayarta. "Hajiya am talking to you" "Eh nina girka" Ya jinjina kai, ya zuzzuba ya fara ci, yaji daɗin girkin nan sosai, yana son Abincin gargajiya sosai da sosai, amma sam Hajiya Zainab bata so, gashi na wuraren sayarwa baya masa daɗi sam ko a Lagos haka nan yake maleji ba daɗinsa yake ji ba. Ya tsare Amina ya hanata tafiya, sai da ya gama, ta kwashe komai, sannan ya tashi zai tafi, Amina ta bi bayansa, har ya shiga mota ya hangota, ya tsaya yana jiran ƙarasowarta, ta miƙa masa wata jaka, be tambayi ta meye ba, ya karɓa ya duba, akwai manyan robar ruwa guda biyu a ciki, sai babban kwalin lemo, sai wata jarka guda ɗaya, ya ɗauko jarkar yana dubawa, fura da Nono a ciki. Ya kalleta ya ce "Ina kika samu fura?" "Mamana ce ta aiko mini da ita daga garinmu, na baka ne saboda hanya amma idan ba ka sha shikenan bani". Yayi murmushin gefen baki ya ce "Bayan wauta ashe kina da hankali, ga ruwa ga lemo ga fura duk an bani kar inji yunwa a hanya, Na gode sosai" "Bakomai Allah ya sanya Alkhairi" "Ameen ya Allah" ya zura hannu a aljijunsa ya ɗauko kuɗi ya miƙa mata ya ce "Ungo wannan, kya sayi wani abun na gode sosai" ga mamakinsa sai ta girgiza masa kai alamar ba zata karɓa ba. "Meyasa ba zaki karɓa ba?" "Baba zai mini faɗa, kuma yana bani kuɗi shima" "Ke kuma sai ki gayawa Baban na baki kuɗi?" Cike da wauta ta ce "Ai ni duk abin da aka yi sai na gaya masa, saboda idan nayi ƙarya yana ganewa" "Ai yanzu ba zai sani ba, idan ma kika gaya masan, kice ni na baki" "Ni dai a'a gaskiya, ban taɓa riƙe kuɗi me yawa ba, ba ruwana, kuma dama ai aiki nake kuna biyana meyasa zaka bani kuɗi?" "Ai nima babanki ne, ki karɓa" Girgiza kai tayi ta ce "Babansu Fadila ne, ni Baba ne Babana" shi mamaki ma ta bashi, yaran yanzu da son abin duniya, amma ta dage ba zata karɓa ba, baya son cigaba da takura mata, dan haka ya ce "Shikenan, na gayawa Baban idan na baki abu ba kya karɓa" ba ta ce komai ba ta juya sumi-sumi ta koma ciki. Tana zuwa ɗakinta, ta nemi wuri ta kwanta, dan ta samu ta rintsa, cikin barci, taji hayagagar Hajiya Zainab a ƙofar ɗakinta. "Uban waye ya ce a girka mini wannan abin a gida, gidan nan yayi miki kalar in da za a sha wannan kayan fitsarin da saka gudawar, taso ki fito ki girka mana wani abin da zamu ci" iya ƙuluwa Amina ta ƙulu ƙarshe, bata ga meye aibun koko da ƙosai ba, kuma banda wulaƙanci ga Hajara nan amma ba za a sata aikin ba sai ita. A gajiye take matuƙa tana son hutawa, amma an tasheta da tijara, duk aikin da tayi a gidan kan su tashi ba su gani ba, haka ta fito rai a ɓace ta kuma shiga kitchen. Ranar Litinin lectures da komai ya cigaba da gudana, amma ba Yazid babu dalilinsa. "Bismillah" taji sautin murayarsa ya shiga cikin kunnuwanta, a rikice ta kalleshi, sai ka ce Aljani sam ba ta ga shigowarsa ba sai zamansa a kusa da ita. Ɗaga kai ta yi ta kalleshi, tana son yin magana amma ta kasa. "Ukty, ko nemana ba kya yi, ban dawo school ba babu ko cigiya" "Ni nake biya maka school fees da zan damu da rashin zuwanka?" "Kar mu fara haka dake daga dawowata mana, ya kike ya hutun?" Ɗan kallonsa tayi amma taƙi magana, Sir Kankiya ne ya shigo ajin, hakan ya sa kowa shiga hankalinsa saboda ba shi da wasa sam ga kwarjini da yake da shi. Yana ganin Yazid a zaune kusa da Fadila, ya haɗe rai "Kai malam babu wani wurin zaman ne, sai nan kusa da mace?" Yazid ya kalli ajin kowa in da ya ga dama yake zama, kuma ba wai matsarta yai ba, amma Kankiya na neman ya dizaga shi a cikin mutane. Fadila ta ce "Tare muke zama da shi" "Yaushe kika fara ƙarya? Ai ba dake nake ba, next time ka nemi wani wurin daban ka zauna" Yazid ya jinjina kai tare da sunkuyar da kai. Fadila ba ƙaramin ƙular da ita Kankiya yayi ba, amma ta basar, aka cigaba da lectures. Mistakenly biron Yazid ya faɗi ƙasa, ya durƙusa ya ɗauko amma ya kuma jiyo muryar Kankiya yana faɗin "Kai wane irin mutumin banza ne, kalleka a haka kamar mutumin kirki, zo ka fita ka bar mini aji" Saroro Yazid yayi yana son gane laifin da yayi, gaba ɗaya idon 'yan ajin ya dawo kan Yazid. "Zo ka bar mini aji nace" Yazid ya miƙe ya bar ajin, ba tare da yayi ƙoƙarin kare kansa ba. Fadila taji haushin abin da Kankiya yayi, ya kammala lectures ɗinsa ya fice, ta ɗauki biron Yazid da littafinsa, ta nufi ofishin Sir Kankiya. "Me Yazid yayi maka kake ta ƙoƙarin tozarta shi?" Tayi maganar cikin ɓacin rai. "Yana bibiyar abin da nake so, idan yana son zaman lafiya ya kammala karatunsa hankali kwance a makarantar nan, to ya nesanta kansa da ke". "Wai kai wane irin mutum ne? Ni nace maka ina sonka ne? Nayi maka kala da ajinka, nayi maka kalar auren mutum kamar kai? Babu wata alaƙa a tsakanina da Yazid, abokin karatuna ne kawai, dan haka kar ka ɓata masa career" "Wannan ke ta shafa, da ke da shi, muddin ya cigaba da shiga sabgarki, zan iya kawo ƙarshen karatunsa a makarantar nan, idan kuma kin musa mu zuba mu gani, ba zan cutar da ke a harkar karatunki ba, Saboda ina sonki, amma gwargwadon wulaƙancin da kike mini, gwargwadon yadda zan cigaba da taka Yazid a cikin Jami'ar nan!!! Ayshercool 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM AYSHERCOOL P 24_25 Iya wuya Fadila ta zo, saboda tsabar takaici da ɓacin rai, ta kalli Sir Kankiya ta ce "To mu zuba ni da kai, idan baka ɓata Career Yazid ba, ni zan ɓata taka rayuwar, na ga alamar baka san wacece ni ba, ba zan saka a hukunta min kai haka ba, kaci bulus, saina fara nuna maka ka ba kowa bane ba, face me sanye da rigar tsiya da zai ƙare a cikinta". "Fadila ni kike gayawa haka dan ina son ki?" "Na gaya maka ɗin, da na gaya maka ne? Me Yazid yayi maka? Koma menene tsakanina da kai ne, meye nasa, Wallahi ko na rasa mijin Aure ba zan auri mutum irinka ba" tayi maganar cikin huci, ta ja jakarta ta fice fuuuu kamar iska, ta bar office ɗin, cike da ɓacin rai. A haraba ajinsu ta hango shi, yana tsaye shi da wasu 'yan ajinsu, fuskarsa babu wata damuwa, kamar abin da ya faru bai ɓata masa rai ba. Ganinta a tsaye tana kallonsa ne, ya sanya shi takowa zuwa in da take tsaye "Ukty daga ina?" So take tayi masa magana amma ta kasa, ta miƙo masa littafinsa da bironsa. Yayi murmushi ya karɓa ya ce "Na gode, ni nama manta da na ajiye su, da sa anzo wata lectures ɗin in tuna" Kallonsa take tare da tunanin wai shi a rayuwarsa baya fushi ne, babu wani abu da yake ɓata masa rai, taje ta gama baloƙoƙo a kansa, amma shi abin da ya farun ko a jikinsa. Juyawa tayi ta nufi department ɗin su Yusra, dan tattaunawa a kan wannan matsalar. Ta kira Yusra a waya, Yusra ta gaya mata a in da zasu haɗu. Tun da Yusra ta hango Fadila, da yadda ta ɗaure fuska ta san akwai damuwa, Fadila ta ƙarasa ta zauna tana huci. "Baby me, waye ya taɓa mini ke ya sanya ki fushi haka?" "Yusra zuciyata na raya mini wani abu, amma ina gudun aikatawa daga baya ace nayi laifi, shiyasa na zo wurinki". "Subhanallaahi, me zaki aikata?" "Wani lecture ɗinmu zan saka a kama mini" Yusra ta zaro ido ta ce "Kina da hankali kuwa?" "Na taɓa ciwon hauka ne? Malama Wannan Kankiyan zan saka a kama mini" Nan ta labartawa Yusra komai cike da ɓacin rai. Yusra ta jira Fadila ta gama baloƙoƙonta, sannan ta nisa ta ce "Yanzu duk a kan Yazeed ɗin kike wannan tada jijiyar wuyan haka? Karo na farko da naga tsantsar tausayi a fuskarki kodai kodai?x 'Yusra ya kike nema ki mayar da maganata shirme, ko wani abu daban? Ke da kinga Yazeed kin san ba masu hali bane, karatunma Allah kaɗai ya san da yadda yake yinsa, idan aka ɓata masa career saboda ni, an masa adalci kenan? Bafa mahaukaciya bace ni, zanje in aikata abin da ya dace tun da ba zaki bani shawara ba" Yusra ta ce "Tuba nake, Allah ya baki haƙuri. Shawarata a gareki shi ne kamar yadda Kankiya ya buƙata kawai ki nesanta kanki da Yazid, ke har ki gama makarantar nan, kin da gatan da babu wanda ya isa ya taka ki, Yazeed kuwa fa, ko kuma kije ki kai ƙarar Kankiyan, a miki tsakani da shi" ɗan shiru Fadila tayi, daga bisani ta ɗauki jakarta ta kalli Yusra ta ce "Ni banji wannan shawarwarin naki, sun ratsani ba, zan san abin yi" Yusra ta riƙo hannun Fadila ta ce "Fadila kar ki je aikata abin da zai janyo muku Matsala" Fadila ta zame hannunta daga na Yusra ta fice. Khalil ne zaune a Offi, sai jujjuyawa yake a kan kujera, hannunsa riƙe da waya ya saka a kunnensa, yana jiran Hafsa ta ɗaga. "Assalamu alaikum" ta faɗa muryarta ƙasa-ƙasa. "Sweetheart, ko bacci kike na tashe ki?" "Bakomai, na ɗan koma bacci ne ina kwana?" "Eyya am sorry, ban san bacci kike ba, na fito Office ne na kiraki in ji lafiyarki" "Ina lafiya ƙalau, ya aikin?" "Aiki Alhamdilillah, bari in barki ki huta, anjima mayi waya, koma ki cigaba da baccinki" "No ai na riga na tashi, gara in tashi in fara shirin kayan sana'ata" "Hafsa" ya kira sunanta. "Na'am" ta amsa. "Bana son fitar da kike titi" "To idan ban fita ba me zamu ci?" "Haba Hafsat, ni haryanzu ban gane ba, kin ƙi ki bani dama yadda Yakamata, Wallahi Hafsa dan abin da zaku ci, zuwa abin buƙatar ku ba zai gagara ba" Hafsa cikin sanyin muryarta ta ce "Ba hakkinka bane, ka bari zuwa lokacin da Allah ya sa ka aureni, ko me kai mini a wannan lokacin ba laifi, amma yanzu.. "Shhhh Hafsat, kina kokwanton ba zan aureki bane? Wallahi ina matuƙar kishinki fiye da yadda kike tunani, zuciyata bata mini daɗi sam ganinki a titi Wallahi". "Ka raina matsayin da Allah ya ajiyeni ne?" "A'a subhanallah, ba haka nake nufi ba Sweetheart, da haka ne ai ba zan tunkareki da batun soyayya ba, dan Allah ki bani haɗin kai, ɗaukar ɗawainiyarku ba komai bane, muna da kuɗi sosai, mijinki ya tara muku kuɗi, ki kwantar da hankalinki mu ci guminmu" Murmushi Hafsa tayi ta ce "Rana ta fara yi, bari in tashi in ɗora girki, ka kula mini da kanka sosai" "Wayo zaki mini ko?" "Ba wayo bane" Khalil yayi murmushi ya ce "A girka dani, in an gama a zo a ciyar da ni a baki, ina kallon kyakywar fuskarki" "Kayi aikinka My, see you later" ta katse kiran. Khalil ya sumbaci wayar, tare da ƙanƙameta a ƙirjinsa. Amina tuni ta fara zuwa extra lessons da suke a cikin hutu, ta mayar da hankalinta sosai a kan zuwa makaranta. Duk da yau juma'a bata iso gida ba sai ƙarfe biyar na yamma, ta dawo a gajiye, a falo ta tarar da doctor Aliyu yana gwada BP Alhaji Ahmad. Saroro ta tsaya tana kallon Alhaji Ahmad, da doctor Aliyu, gefe ga Hajiya Zainab a zaune, tana so tayi magana, amma taga hakan tamkar shishshigi ne, dan tsaf Hajiya Zainab zata iya dizgata, dan haka ta yi musu sallama ta wuce ɗakinta. Ta isa ɗakinta, ta canza kaya tayi salla, amma ta kasa cin abinci, haka nan taji tana son sanin meyafaru ake masa gwaji. Ta sake fitowa falon, a wannan karon Hajiya Zainab hankalinta na kan TV, Alhaji Ahmad kuma yana kwance a kan kujera, ya lumshe idanunsa, lokaci lokaci yana ɗan yamutsa fuska. Amina a ranta ta ce "Wata ƙila bashi da lafiya" Amina ta je ta nemi Abinci ta ci, ta fito ta tafi wurin Baba, suna nan zaune suna hira ita da Baba, tana son tayi masa maganar Alhaji Ahmad, amma ta fasa ta cigaba da hirarta. Wani razananne horn da ake yi tamkar yaƙi, ya sanya a gigice suka miƙe ita da Baba, Baba ya nufi gate ɗin, yana kiciniyar buɗewa, amma aka cigaba da horn ɗin. Baba ya buɗe gate ɗin, Fadila ta kwararo motarta tamkar zata bar doron ƙasa ta tashi sama. A hasale ta fito, dan kallo ɗaya zaka yi mata ka san a fusace take, ƙiris take jira dama, ta nufo Baba cikin masifa, Amina ta miƙe cike da shirin ko ta kwana, ta shirya mayarwa da Fadila duk wani rashin mutunci da take shirin aiwatarwa. "Ka kurmance ne bamu sani ba?" Baki a ɗan sake ya girgiza kai ya ce "A'a" "To wulaƙanci da rainin hankali ne ya sanya zan zo in tsaya ina horn ka ƙyaleni?" "Amma naga ai ba wani daɗewa ki kayi kina horn ɗin ba, kuma baki ga jikin girma ba, kan ya buɗe gate ɗinma ai sai a hankali". Cikin tsawa Fadila ta ce "Na saka da ke ne? Jikin tsufa waye ya masa dole ya zauna, ku koma in da kuka fito mana, idan ya san ba zai iya ba sa ya bari amma sai ka ce.. "Fadila kar ki kuskura ki faɗi maganar banza a kan mahaifina, uba talaka da mai kuɗi duk ubane, dan haka kar ki sake ki zagar mini uba a gabana, na gaji" "Idan na zageshi me zaki yi, baki da abin da zaki ja da ni, ki ka sake kika yi mini wani rawar kai, a yau ba sai gobe ba sai kun bar gidan nan daga ke har shi, shashasha, wawuya 'yar ƙauye kawai" Jikin Amina har wani rawa yake yi, Bana ya riƙo Amina, yana girgiza mata kai, tare da hanata Magana, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga sintiri a kan kuncinta. Fadila ɓacin ran da Kankiya ya cusa mata ta zo ta sauke a kan Baba Hassan. Fadila na gama saukalen rashin mutuncinta, ta shige cikin gida. Amina takaicin Baba ya hanata magana, ya sanya ita ma ta nufi hanyar shiga cikin gidan, A falo ta tarar da Fadila zaune a kusa da Daddy tana masa sannu. Amina ce ta shigo fuuu, idanunta jawurr tana kuka. Haka nan hankalin Daddy ya koma kan Amina, da ta wuce idanuwanta jawur, yana tunanin meyafaru da ita take wannan kukan haka?. "Ke zo nan" ta jiyo muryar Hajiya Zainab. Ran Amina a matuƙar ɓace ta tsaya cak, saboda ji take tamkar ta jiyo, ta zazzagi Hajiya Zainab ita da Fadila. "Ko ba zaki zo ba ne kina jin ina kiranki" Amina ta dawo falon ta tsaya, ta sunkuyar da kanta ƙasa. Hajiya Zainab ba ta damu da kukan da ta ga Amina tana yi ba ta ce "Je ki kira mini Babanki" Amina ta ɗago idanunta da suka yi jawur, ta sauke a kan Amina. "Ko ba zaki bane ina miki magana saboda salon iskanci kina jina kin yi shiru" Amina ta jiya jiki a sanyaye, ta koma harabar gidan ta samu Baba yana jin radiyo. "Uwata lafiya kuwa kukan dai kike? Ko wani abun suka sake yi miki?" "A'a cewa aka yi ka zo" "Ba dai wani abun kika yi ba ko?" "Eh, kawai cewa aka yi ka zo" Baba ya miƙe yana faɗin "Muje to Allah ya sa lafiya" Suka koma falon tare, ta ƙasan ido yake kallon Amina. Amina ta tsaya tana jiran taji me za'ace wa Baba kuma. Alhaji Ahmad tashi yayi ya wuce ɗakinsa, dan baya son hayaniya. "Gidan Hajiya Turai zaka je, ka karɓo mini saƙo, kaje ka dawo da wuri kar ka barni ina jira" Cewar Hajiya Zainab da take kallonsa a wulaƙance. Cikin girmamawa Baba ya fice, dan aiwatar da aiken da Hajiya Zainab tayi mata. Amina tun da ta ƙule ɗaki bata sake fitowa ba, ko Abincin dare ba ta samu ta iya ci ba, saboda yadda ranta yake a ɓace, Amina ta rasa dalilin da yasa Fadila ba ta da abin da yake mata daɗi irin cin mutuncin Baba a kan buɗe ƙofa, Babu wani laifi da Baba yake yi ta ci mutuncin sa sai a kan buɗe gate. Bayan sallar isha'i, Amina tayi kwanciyarta, ba tare da ta nemawa cikinta abin da zata ci ba, amma ta ɓige da juye-juye bacci ya gagara, har dare ya raba, ga ɓacin rai ga yunwa da ta uzzurawa cikinta. Ba shiri ta tashi ta nufi falo, dan neman abin da zata zuba a cikinta, ta fara alwala tare da gabatar da salla raka'a biyu, sannan ta kwaso litattafanta ta fito falo, ta yanke shawarar zuwa barandar waje, tayi karatun a can, ta san idan tayi hakan zata iya mantawa da damuwarta ta fuskanci gobenta a kan karatun da ta saka gaba, daga ranar da ta kammala karatun sakandare zata bar gidan nan, dan ji take tamkar kan tabar gidan nan sai ta yiwa Fadila dukan da sai an kaita Asibiti. Amina tayi nisa a tunani, jefa ƙafarta kawai take a cikin falon, tana son ta lalubi ƙofar falon ta buɗe, ba tsammani tayi karo da wani abu, ware baki tayi za tai ihu, amma taji an rufe mata baki. Mutsu mutsu ta fara yi, zata ƙwace jiki ba ƙwari ya ce "Shhh Ahmad ne" yayi Maganar yana sakar mata baki. "Waye Ahmad kuma?" Ta faɗa bakinta na rawa, duk da ta gane ƙamshin turarensa. "Daddy" ya faɗa a hankali. Amina ta dafe ƙirjinta ta ce "Wayyo Allah, na zata aljani ne Wallahi" "Idan Aljanin ne shikenan, ba zaki addu'a ba sai ihu?" "Ai wannan tunanin ana yinsa ne idan mutum yana cikin hayyacinsa" tayi maganar tare da ɗan ja da baya, saboda kusancin da ke tsakanin su. Cikin duhun ya ce "Me kike yanzu baki bacci ba?" "Baranda zani karatu" "Ok, yayi kyau" ya furta ya raɓa ya bi gefen in da yake jin alamun tana tsaye. Amina ta ƙarasa ta buɗe ƙofar, ta fita baranda, hasken lantarki ko ina, ta zauna ta bubbuɗe litatafanta, ta fara duddubawa. Gani tayi an kunna wutar falon, haske ya gauraye falon. Tashi Amina tayi ta leƙa falon, taga Alhaji Ahmad ne ke ta zagaya falon. Ji yayi kamar ana kallonsa, dan haka ya waiwayo, sai ya ga Amina a tsaye tana kallonsa. Amina ta ce "Jikin ne dai?" Ya jinjina mata kai yana cigaba da zaga falon. "Wai me ya sameka, naga kana ta zagayawa?" Tayi tambayar kanta tsaye. "Suga na ne ya hau, da kuma jinina shima ya hau, ƙafafuwana ne suke zafi da cikina" ya samu kansa da bata amsa, ba tare da shi kansa ya san dalili ba. Cikin tausayawa Amina ta ce "Allah sarki sannu, dama kana da suga amma komai ma kake ci, ba'a tsara maka Abincin da yakamata ka ci? Naga bakomai masu ciwom suke ci ba fa" Daddy ya cigaba da aikin zagayensa ba tare da ya kuma cewa komai ba. "Allah ya baka lafiya" ta faɗa tare da juyawa ta koma wurin karatunta. Kusan mintuna talatin ta tashi ta kuma leƙawa, ta ganshi a zaune ya mimmiƙe ƙafafuwansa sai lanƙwasa yatsun ƙafarsa yake yi. "Sannu Daddy, Allah ya baka lafiya" ya jiyo siriryar muryata a kunnensa. Murmushi kawai ya yi bai amsa ba. "Haryanzu ƙafar na maka zafi ne?" Ya jinjina mata kai alamar eh, tare da lumshe idanunsa, da ganin yadda yake gumi zaka san yana jin ciwon sosai. Komawa tayi, mintuna kaɗan ta dawo ta ce "Daddy zo ga ruwa na zuba maka a bokiti, kazo ka sanya ƙafafuwan ko zasu daina" "To zan zo" ya bata amsa ba tare da ya buɗe idonsa ba. Ta koma ta cigaba da karatunta, harta fidda ran zai fito, sai gashi ya fito, ta ajiye masa kujerar zama, da bokiti ta zuba ruwa. Ya zauna a kan kujerar, ba tare da ya ce mata komai ba, ya janye jallabiyarsa, ya zura ƙafafuwan a cikin ruwan, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sanyin ruwa ke ratsa shi, yana samar masa da releif, tun daga ƙafafun nasa zuwa ga ilahirin gangar jikinsa. Amina ta cigaba da rubuce-rubucenta, a hankali yake samun releif daga zugin da ƙafarsa ke masa, ya buɗe idanunsa ya na kallon Amina, da take ta aikin karatunta. Shi dai Allahn da yayi shi ba mutum ne mai shiga sabgar mata ba, shi ko wasa da yara bai fiye yi ba, dan magana ma bata dame shi ba, amma har cikin ransa yake jin daɗin yadda take nuna damuwarta da shi. "Naga kin kasa wannan, kawo mu gani" yayi Maganar yana kallon littafin gabanta Ba musu ta miƙa masa littafin dake hannuta, tare da biron. "Me aka yi miki kike kuka ɗazu?" Yayi tambayar yana kallon littafai da ke hannunsa. "Wai ni?" Amina ta tambaye shi. "A'a" ya bata amsa. Shiru tayi ba ta bashi amsa ba, ta fara wasa da littafin gabanta. A hankali yake rubutun cikin nutsuwa, mintuna kaɗan ya miƙa mata littafin. Buɗe baki tayi tana kallonsa, "ya aka yi kayi mini, tun ɗazu nake fama na kasa" Be ce mata komai ba, ya cigaba da kallonta, ita kuma ta cigaba da bin littafin da kallo tana murmushi. "Wane course zaki karanta, idan kika kammala sakandare?" "Ni sakandare kawai nake son nayi, Baba bashi da halin da zai biya mini jami'a". "Wane course zaki karanta a jami'a idan kin kammala sakandare" ya maimaita mata. "Bani da zaɓi" "Meyasa?" Ya faɗa a taƙaice. "To idan na sakawa raina ga abin da nake so, ai babu me biya mini, shiyasa ni bana tunanin wata jami'a". "Zaki iya medicine?" Yayi Maganar yana kallonta. Ƙwalalo ido Amina tayi ta ce "Taɓ, korata za a ayi, bani da ƙoƙari" "Kina wahal dani, bana son doguwar magana, ke in an tambayeki sai kin yi amfani da different formulas kafin ki amsa". "To yi haƙuri" Ya sunkuyo da fuskarsa kunnenta, wanda hakan ya haddasa mata faɗuwar gaba "Gaya mini, me zaki karanta?". "Kome Allah ya sa na samu, ina so". Ta amsa tana janye jikinta gefe. "Idan kin yanke shawara ki gaya mini, zan ga abinda zan iya yi a kai" "You mean zaka barni in cigaba da karatu a gidan nan, naji ance ɗawainiyar jami'a ba kamar na sakandare bane" "In dai karatun bai fi ƙarfin talaka kamar ni ba, zan yi wani abu a kai Insha Allah, kina da ƙwaƙwalwa bai kamata a barta haka ba ki tsaya iya Sakandire ba" Daddy ji yake tamkar suka ɗai ne a duniyar, dare ya tsala, ko tunanin wani ya zo wurin baya yi. Hawaye ne ya wanke fuskar Amina, tana kallon Alhaji Ahmad, amma ta kasa Magana. "Komai aka yi miki sai kuka?" "Na gode sosai Daddy, kana da kirki sosai ba kamar.." Sai kuma tayi shiru. "Ba kamar wa ba? Hmm ko kusa karki bari ta ji kin faɗi wani mummunan abu a kanta, kin san abin da zata iya yi miki, let's keep this as our secret, kar ki gayawa kowa sirrinmu ne, ciki har da Baba, idan kuwa kika bari zancen ya fito, to abinda ya biyo baya ba ruwana, dan ba lallai Zainab ta bari" Amina ta ɗan kalleshi, yana da zuciyar taimako, amma yana shakkar matarsa. "Insha Allah ba zan gayawa kowa ba, na rufe bakina, Allah ya baka abin da kake so duniya da lahira" "Ameen" ya amsa tare da jingina a kujera. Bacci ne ya ɗauke shi, ƙafafuwansa na cikin bokitin ruwa, Amina ma bacci ne ya kwasheta, ta kife kanta a gefen kujerar ta hau bacci. (ALLAH YA SA HAJIYA ZAINAB TA ZO TA KAMA KU🥴) Ayshercool 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM AYSHERCOOL 26-27 Tsananin sanyin da yaji yana ratsa shi ne ya sanya ya buɗe idanunsa, gari ya ƙara yin duhu baƙi ƙirin, ba kajin motsin komai sai haushin karnuka a waje, ya kalli in da Amina ta dunƙule a wuri ɗaya, ta jingina da kujerar da yake kai tana bacci, da alama tana jin sanyi sosai, amma bacci ne a kanta. A hankali ya zare ƙafafuwansa daga cikin bokitin ruwan nan, ya tattara litattafanta da ta baza a wurin, bironta ya ɗauka yana shafa mata a fuska, yamutsa fuska ta yi, ta kai hannu ta kori abin da yake bin fuskar tata, amma ya kuma shafa mata. "Ki tashi kije ki kwanta" Amina ji take tamkar a kan katifarta take, dan haka tayi wani irin juyi tana ƙoƙarin faɗawa jikinsa ta cigaba da baccinta. Cike da rashin sabo, da yi mata kallon 'yar cikinsa, ya sanya hannayensa ya ɗagata ya tsayar da ita a kan ƙafafuwanta, ya ɗan girgizata ya ce "Open your eyes" a hankali take buɗe su tana lumshewa, tamkar zata faɗi. Ya danƙamata litattafanta, ya buɗe musu ƙofar falon, ya kunna fitilar wayarsa, ya rakata har bakin part ɗinsu, sannan ya wuce sashen Hajiya Zainab. Ya tarar da ita ta rashe, sai baccinta take hankali kwance. Ya lallaɓa ya hau kan gadon, cikin ikon Allah, ya rage jin zafin da tafin ƙafarsa ke yi masa sosai. Ya janyo bargo, ya rufa musu shi da Mummy, ya kwantar da kansa a wuyanta, yana shaƙar ƙamshin turaren da take fitarwa mai daɗin gaske a hancinsa. Tuna halinta ne ya sanya shi sassauta rungumar da yayi mata, dan yanzu sai ta farka ta hau shi da masifa. Amina bata farka ba sai asuba, dan sai da ta kusa makara, sai da ta farka ta ganta a tsakar ɗaki a kan litattafanta tana bacci, sannan ta tuno abubuwan da suka faru jiya da daddare, gaba ɗaya ta ɗauka mafarki take yi, a hankali ta tashi ta shiga toilet, tayi alwala ta dawo tayi sallar auba. Bayan ta idar, ko karatun Alqur'ani da azkar ba ta samu yi ba, saboda kanta har wani nauyi yake yi mata, ta haye kan katifarta ta hau aikin bacci. Hajara tamkar ta tashi Amina, ganin har ƙarfe takwas bata fito ba, sai kuma ta fasa, saboda itama ko ƙarfe nawa zata kai ba ta fito ba, Amina ba ta damuwa balle ta taso ta, aikinta kawai take yi, dan haka taga idan ta ce sai Amina ta taso, to tabbas bata kyauta ba. Wasa² har goma saura, Amina baccinta take yi, A lokacin Alhaji Ahmad ya fito karyawa, tare da Hajiya Zainab. Ya tarar da Hajara na ta shirya Abinci a dining ɗin, haka nan yaji yana son ganin Amina, dan galibi ita yake gani tana shirya Abinci, amma har Hajiya Zainab ta zuba masa Abinci, yana son ganin ta ina zai ga Amina, kamar ba raba dare suka yi tare ba jiya. Ɗanɗanon Abincin kawai ya ci, yaji ya banbanta da nata, ya kalli in da Hajara ke mopping ya ce "Ina wannan Yarinyar take?" Hajara ta kalleshi ta ce. "Wace yarinyar ranka ya daɗe?" " Wadda kuke aiki tare?" "Bata tashi ba" Hajara ta faɗa tana sunkuyar da kai. "Yau ba taje makaranta ba ne?" "Ai sun yi hutu" ta bashi amsa, bai ce komai ba ya cigaba da cin Abincin da a bakinsa na Amina yafi daɗi. Hajiya Zainab ta kalleshi ta ce "Kai meye damuwarka da taje Makaranta ko ba taje ba?". "Saboda kuɗina nake biya, dan haka yakamata in bibiya" "Shiyasa tun farko ni ban so ka kaita makarantar kuɗi ba, sai a kaita ta irinsu, amma ka kaita cikin yaran da ba sa'aninta ba a fannin rayuwa da arziki" Alhaji Ahmad yayi mata shiru ya cigaba da cin Abincinsa. Ƙarfe goma saura, gaba ɗaya ɗalibai sun tattara hankalinsu a kan malamin da yake tsaye yana kaiwa yana komowa kamar mazari, a ajin yana gabatar da darasi, sai ga Yazid a wahale, kamar an koro shi, cike da fargaba ya fara yinƙurin shiga ajin. "Hey stop their, ko ɗakin babarka idan zaka shiga sai ka nemi izini, balle aji" cewar malamin da yake yiwa Yazid kallon banza. "Am sorry sir" ya faɗa cikin ladabi. Gaba ɗaya ajin suka yi shiru, suka mayar da hankalinsu kan Yazid. "Yanzu ne lokacin da yakamata ka zo aji? Ni in baro gidana tun bakwai takwas tayi mini a nan, amma ka zo yanzu kuma kai tsaye ka ce zaka shigo mini aji?" "Ayi mini afuwa malam, insha Allah ba zan sake ba" "Sorry for yourself malam, ɓace mini daga nan" Yazid ya yunƙura zai kuma magana, amma malamin ya buga masa tsawa ya kore shi. Duk iya wulaƙanta mutum da Fadila ta ƙware a kai, taji babu daɗi yadda malamin ya kyari Yazid ya koreshi, ga shi 'yan aji gaba ɗaya sun zuba masa ido, duk da Yazid mai sa'a ne a wasu lokutan, kuma mutum mai haƙuri da ladabi, amma wasu lokutan yana yawan shiga komar malamai su wulaƙanta shi. Duk da Yazid ya bar ajin, hakan bai hana malamin cigaba da ƙananan maganganu, a kan Yazid ba. Bayan fitar malamin daga ajin, Yazid ya shigo ya samu wuri ya zauna, ba tare da ya kalli kowa ko ya kula wani ba. "Kowa ya tabattar ya mallaki littafin da Sir Bello ya ce a saya, dan da alama wani abun yake shirya mana a kan littafin nan, zai iya kada mutum idan ba shi da shi a jarrabawa, dubu uku ne, ga takadda nan ta na zagawa, duk mai so ya rubuta sunansa, na bada aron kuɗina naje kasuwa na sayo mana, duk mai so sai ya bada kuɗinsa in bashi" Cewar Captain dake tsaye a gaban ajin, yana bayani daki-daki kamar me koyar da karatu. Tana hangen Yazid daga in da take zaune, kamar mara lafiya, sai ya kifa kansa a kan benci, sai kuma ya tashi yana ɗan lumshe idanunsa yana buɗewa, idanun duk sun yi ja, sai tayi tunanin ko duk dan saboda abin da lecturer yayi masa ne. Aka miƙawa Yazid takarda, ya rubuta sunansa in zai sai littafi, amma ya girgiza kansa, ya mayar da kansa ya kifa kamar yadda yake da farko. Da takardar ta zo kan Fadila, sai ta sayi kwafi biyu a take, ɗaya nata ɗaya na Yazid, amma tana jinjina yadda zata bashi littafin, dan bata son yawan shiga sabgarsa. Tana nan zaune taga ya tashi ya fita, ita ma ta tashi ta bi bayansa, tana biye da shi, ba tare da ya sani ba, taga ya shiga wani aji da babu kowa, 'yan ajin suna wurin excursion, mutanen da ke ajin 'yan tsirari ne, wasu na cin abinci wasu na abin da ya damesu. Wuri ya samu can ƙarshen ajin, ya je ya samu wuri ya zauna ya kifa kansa. Ta tsaya daga bakin ƙofa tana saƙawa da warwarewa, daga bisani ta yanke shawarar shiga. Har taje inda yake bai ɗago ba, ta saka hannu ta ɗan daddaki ka bencin da yake kai. A hankali ya ɗago ya kalleta, idanunsa sun yi jawur, ta kalli ƙafarsa tayi futu futu, kamar wanda yayi tafiya a sahara. Sauke mask ɗin fuskarsa yayi, tare da sakar mata murmushin ƙarfin hali "Ya aka yi kika san ina nan?" Ɗan taɓe baki tayi, ta saka hannu a jakarta, ta ɗauko littafin da ta saya masa da handout ta ajiye masa "Gashi nan, kuma ya rarraba group a aji, ya bada assignment za'a yi presentation next week in Allah ya kaimu, na saka sunanka, sai kaje ka dudduba handout ɗin" Zuba mata idanunsa yayi gaba ɗaya amma ya kasa magana, sai kallonta kawai da yake yi. "Magana fa nake maka, amma ka zuba mini ido". A hankali ya ce "Yi haƙuri zan yi magana, numfashina ne yayi mini nauyi" A ɗan tsorace ta kalleshi "Jikin ne?" Lumshe idanunsa yayi, ina ma yana da damar gayamata abin da yake damunsa, rabonsa da Abinci tun kunun jiya da safe, Ulcer ta riƙe masa ciki da ƙirji har bayansa, haka ya lallaɓa ya taso ya taho Makaranta da wuri, saboda saurin da yake yi, yaji numfashinsa yana isa huhunsa da ƙyar, a wahale ya ƙaraso makarantar. "Yazid" ta kira sunansa, karo na farko da yaji sunansa a harshen Fadila, wanda kiran sunan nasa ba ƙaramin tasiri yayi a zuciyarsa ba, ya haifar masa da wata nustuwa ta mussaman ba. "Kaje Asibiti ne?" "Eh na sha magani" ya bata amsa da ƙyar, dan baya son yin ƙarya ko kaɗan. Ya jingina da teburin, ya lumshe idanunsa, ita kuma ta tsaya a tsaye, ita bata zauna ba ita bata tafi ba tana kallonsa. Kamar wadda aka yiwa dole, ita a lallai bata damu da shi ba ta ce "Ko zaka tafi gida ne?" Ya girgiza mata kai ya ce "Zan ji sauƙi yanzu insha Allah, ganinki ɗin nan ma kawai ya sanya mini nutsuwa da jin na warke" tsuke fuska tayi ta harare shi, tare da ɗan hura hanci. "Allah ya sawwaƙe, ni na tafi" ta juya ta nufi hanyar ficewa, ta bar masa handout ɗin da littafin ya zubawa bayanta ido, har ta bar ajin. Ɓangaren Amina kuwa, bayan tayi wanka ta nemi abin da za ta ci taci, bayan ta tabattar da an kaiwa Baba nasa Abincin, ta koma ɗakinta ta ɗora da rubutun Alqur'ani da take yi. Sai wajen azahar sannan Amina ta fito, ta haɗa wanke wanke tayi, tare da gyara duk in da aka ɓata, duk da Hajara taji haushin yadda yau Amina taƙi kataɓus ta sha baccinta, haka ta jure ta danne fushinta, saboda ita ma Aminan ba ta mata ƙorafi. Yau Alhaji Ahmad a gida ya wuni, sai ƙarfe huɗu sannan ya shirya zai fita, yau ba da Zakiru direba zai fita ba, shikaɗai zai fita, ya shiga motar, yana ƙoƙarin kunnawa, ya hango Amina a wurin Baba, riƙe da littafi, tana ta aikin nata na surutu, tana yi tana kallon littafin hannunta, Baba kuma yana ta ɓare gyaɗa yana miƙa mata, tana karɓa tana ci. Ya ɗan jima a zaune a cikin motar yana kallonsu, gwanin sha'awa, ita 'ya mace duk in da Allah ya baka ita, ya baka Sarauniya ko da kuwa kai ba sarkin bane, Alhaji Ahmad yana son yaga ana tattala mace,baya son ya gansu a wulaƙance, shiyasa yake matuƙar ji da Fadila, shi namji duk in da yake zai iya kula da kansa, amma mace tana buƙatar kafaɗar da zata jingina. Sai karɓe gyaɗa take daga hannun Baba tana ci, tana nunawa Baba littafinta, duk da Baba mutumin karkara ne, kuma ba wanda yayi ilimin zamani ba, amma wasu lokutan yadda yake gudanar da rayuwarsa a waye, ba girman kai ba hayaniya. A hankali ya fara jan motar, zuwa wurin gate, daidai in da suke ya tsaya da motar, Baba ya taso da sauri, ya tsaya jikin motar ya risuna yana gaida Alhaji Ahmad, Ya amsawa Baba cikin sakin fuska, Amina ta wani basar, kamar bata san da wanzuwarsa a wurin ba. "Aminatu ina wuni" Alhaji Ahmad ya faɗa lokacin da ta ɗago suka haɗa ido, tana ƙoƙarin mazewa ta kau da kanta. Baba ya ce "Ja'ira ke wace irin Yarinya ce Uwata, baki iya gaisuwa ba?" "Yi haƙuri, ina wuni?" Ta faɗa a kunyace. "Ƙyaleta malam Hassan, tun da bata gaisheni ba, ai gara ni in gaisheta, tawa gaisuwar zaki amsa" Amina tayi shiru cike da kunya, dan ta san bata kyauta ba sam. "Zo" yayi Maganar yana kallonta. Ta tashi daga kan bencin, ta matsa jikin motar. "Meyasa baki je lesson ba yau?" "A makarantar aka ce mu huta yau" ta bashi amsa tana kallon ƙasa. "Kina gane karatun dai ko?" Ta ɗaga kai alamar eh. Alhaji Ahmad ya kalli Baba ya ce "Buɗe mini gate ɗin" Baba ya amsa da to, ya tafi buɗe gate. Ya sake mayar da dubansa gareta ya ce "Me zaku dafa yau da daddare?" "Hajiya ta ce, a dafa kuskus da miyar ganye" ta bashi amsa tana kallon ƙasa Alhaji Ahmad ya ce "Likita ya sanya mini ƙa'idoji, saboda sugar na da ya hau, ki dafa mini faten dankalin turawa, da alayyahu, zan yi dinner da shi, yau zaki karatun dare ne?" "Eh insha Allah" "Idan na dawo, zan miki magana ki kawo mini" Ta jinjina masa kai, shi kuma ya ja motar ya fice. Har aka yi lectures aka gama, Fadila na ankare da Yazid, a hankali yake komai, bashi da lafiya, faɗa ne ba zai yi ba, gefe guda kuma ta danganta abun da wulaƙanci da malamin ɗazu yayi masa, sai kuma ta tuna Cewar abu ne mawuyaci, kaga wani abu mai kama da fushi a tare da Yazid kome za a yi masa, wannan murmushi dai sai ka ganshi a fuskarsa. Amina ta koma cikin gidan, tayi sallar la'asar, ta shiga kitchen, dan ta san babu lallai Hajar ta kuma yin wani abun, tunda kusan ita tayi aikin yau. Tun azahar Fadila ta dawo gida, dan har tayi wanka ta kintsa ta dawo falo ta zauna, suna hira da Mummy. Da sallama aka buɗe ƙofar falon, daga Mummy har Fadila suka mayar da hankalinsu kan ƙofar, wata farar mata ce ta shigo, ita da wata matashiyar budurwa, suturar da ke jikin matar kawai ya isa ya nuna maka Arziƙi ya zauna. Suka yi sallama, Hajiya Zainab ta amsa tana bin su da kallon rashin sani. Suka ƙarasa cikin falon suka zauna, suka gaisa da Hajiya Zainab, ta amsa ba yabo ba fallasa, dan suma taga ba kalar talakawa bane. Matar ta faɗaɗa murmushinta ta ce "Na san ba zaki shaida ni ba, wannan 'ya ya ce Azima, suna Makaranta ɗaya da yarinyarki Amina, na shigo nan unguwar wurin wata ƙawata, Azima ta nuna mini gidan, nace bari in tsaya mu gaisa" Mummy ta haɗe rai ta ce " 'yar aiki dai ko?" Maman Azima ta ce "Eh to hakan, ai ɗa na kowa ne, dan in saya ya sanya na ce 'yar ki" "A 'a ba wata sayawa, meye haɗina da ita da zaki jingina mini ita wai 'ya ta? Aiki kawai take mini" Mamaki ya kama maman Azima, yadda Hajiya Zainab ke zaƙalƙalewa, tamkar wadda aka dangantawa ɗan shege. "To shikenan na fahimta, 'yar aikin ki, mu gaisa sai in wuce" A wulaƙance Mummy ta ce "Sai ku jira ta fito, dan dai bani zan tashi in tafi yawon kira muku ita ba, ko kume tashi kibi wannan ƙofar, kitchen na nan, ki kirawota" tayi maganar tana kallon Azima. Azima ta kalli Amminta, Ammi ta jinjina mata kai. Azima ta tashi, ta ta shiga ƙofar, cikin ikon Allah, ta tarar da Amina na ta aikinta. "H Shanono" Azima ta faɗa da ɗan ƙarfi, Amina na waigowa taga Azima tayi tsalle ta rungumeta tana murna. "Azima, ya akai kika zo baki gaya mini ba?" "Ke sauri muke, Ammi na falo muje ku gaisa zamu tafi" Cikin mamaki Amina ta ce "Dan Allah dagaske har da Ammi kuka zo, muje in ganta" Tare suka fito falon da Azima, Amina ta ƙarasa gaban Ammi ta durƙusa tana gaisheta. Cikin fara'a Ammin ta amsa "Lafiya ƙalau Amina, ya karatu Azima ta ce mini makarantarku ta zaɓe ki, a Quiz ɗin su na ƙasa" "Eh Ammi" "To a dage ai ta karatu, Allah ya bada sa'a, Azima ce ta nuna mini layn naku, na ce bari in Shigo mu gaisa" "Amma kuwa naji daɗi Ammi, bari in kawo muku ruwa ku sha" "Babanki ya saya ya ajiye ne?" Cewar Mummy, cike da son ta wulaƙanta Amina a gaban mutane. Jikin Amina yayi sanyi ta sunkuyar da kai, Azima tayi mamakin abin da Hajiya Zainab ta faɗa, dan bata taɓa sanin irin zaman da Amina take kenan ba, saboda duk surutun Amina bata wannan zancen. Ammi ta ce "Bakomai Amina, a ƙoshe muke ina da ruwa a mota" Ta ƙarasa maganar suna miƙewa tsaye, jiki a sanyaye Amina ta ce "Bari in rakaku mota". "Ke, da kika samu na barki ku ka gaisa, zaki wuce ki cigaba da yi mini aikina ko saina taso kanki?" Har cikinta haka Amina taji ɗacin dizgin da Hajiya Zainab ke mata a gaban baƙi, sai dai ta kasa daurewa sai da hawaye suka zubo mata, cikin ƙoƙarin mayar da hawayen, ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Ammi ku gaida gida, Azima sai mun haɗu a school, next week za'a koma insha Allah, Ammi na gode sosai". Kasancewar Ammi mai matuƙar son 'ya'ya, ya sanya ita ɗa ko ba nata bane yanzu zai shiga ranta, ba ta son biyewa Hajiya Zainab, zasu iya yin babu daɗi, dan ita ta zo gidan, kuma bata san me hakan zai haifarwa da Amina ba, haka suka bar gidan rai a matuƙar ɓace. Ko da Amina ta koma kitchen, tana aiki tana kuka, kamar wadda babarta ta mutu. Fadila ta gyara kwanciyarta ta kalli Mummy ta ce "Mum, meyasa ki ka yi haka? A Arziƙin da yake gidan nan, meye dan an bada ruwa?" "To uwata, ai naji matar tana naniƙa mini yarinyar ne, gara in nuna mata matsayin yarinyar a gidan nan" daga haka Fadila ba ta kuma cewa komai ba. Wata irin shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Hafsa da Khalil, duk da baya gari, amma kusan kullum suna tare a waya, gashi a wannan karon ya kasa samun excuse of duty ya koma gida, ko dan ya ga Hafsa, saboda yadda ya dinga komawa gida a kai a kai a baya. Yanzu yana zaune a ɗakinsa yana video call da Abdul, yana sake labarta masa irin so da shaƙuwar da ke tsakanin sa da Hafsa. Har yake ce masa "Ka san wani abu, ina kuma dawowa gida, zan yi magana a gida a san abin yi, dan ginina na nan Abuja ya kusa kammaluwa. Abdul ya ce "Mhmm haka ne, to yanzu tsakanin Mummy da Daddy, wa zaka fara sanarwa?" Ɗan Jimm Khalil ya yi, saboda Abdul ya tuna masa wani abu da yake yawan mantawa, ya san ko Daddy ya amince ida Mummy bata amince ba a isa an yi auren nan ba. Nan da nan ya yiwa Abdul sallama, ya ajiye wayar ya dulmiya kogon tunani. Ɓangaren Hafsa ma tun da Allah ya sa Khalil ya sanar da ita very soon zai turo iyayensa, take tunani wurin wa zai tura iyayen nasa? Dangin mahaifinta da basu ɗauke su a bakin komai ba ko kuma wa? Idan kuma dangin mahaifin nata suka mata sharri a wurin iyayen Khalil fa, mussaman idan suka ga suna da rufin asiri fa? Ire-iren wannan tunanin ya hanata sukuni, kuma ta kasa tattauna shi da kowa ciki har da Mama. Amina tun tana jiran Daddy ya dawo, har ta fara gajiya, dama a falo take zaman jiran nasa, ta kasa karatun sam saboda damuwa da ɓacin rai, ta zubawa TV ido tana kallon wani Film a MBC2 Captain Philips, gaba ɗaya tausayin jarumin ya cika mata zuciya, ji take tamkar ta shiga ta kai masa ɗauki, bayan damuwar da take ciki, ta ƙara da ta film ɗin da take kallo. Film ɗin ne ta samu ya ɗauke mata hankali, dan har ta fara tunanin ta ajiye masa Abincin a falo tayi tafiyarta, dan kowa ya kwanta sai ita kaɗai. Sai wajen goma saura ya shigo Alhaji Ahmad ya shigo falon, ya shigo da sallama, Amina ta ɗan kalleshi ta amsa a hankali ta mayar da hankalinta kan tv. Be kulata ba ya nufi sashinsa, da sauri ta ce "In kawo Abincin?" "Dama kin ganni?" Ya faɗa ba tare da ya waiwayo ba. "Eh" ta faɗa a sanyaye. "Zan fito in karɓa, ki jirani" ya wuce abinsa. Kawai Amina ta fashe da kuka, yadda aka mayar da ita kamar wata baiwa, kowa abin da ya ga dama yake mata, banda wulaƙanci wannan wane irin abu ne, bayan wancan jiran da tayi, sai tayi wani again? Ta cigaba da share hawaye, tare da dana sanin zuwanta birni. Sai goma da rabi, Alhaji Ahmad ya leƙo falon ya ce "Yauwa kawo mini falona, ki haɗo mini da apple guda uku, sannan ki taho da littafinki da biro" Amina ba ta amsa ba, ta tashi tana cigaba da share hawaye. Alhaji Ahmad ya bita da kallo, da tunanin meye ya sakata kuka. Ta ɗauko kayan Abincin, ta nufi sashin Daddy, tana ta Addu'a, tare da ƙudurce tana kai masa zata ajiye masa ta fito. Sai dai da ta shiga taga baya falon, ta tsaya saroro tana bin falon da kallo. Ta wani corridor ya leƙo, ya yi mata alama da hannu ta zo, gabanta ne ya shiga faɗuwa, tabi bayansa tana waige-waige, dan bata taɓa sanin da wurin ma a cikin gidan ba. Wani ɗaki ya buɗe ya shiga, Amina ta tsaya daga ƙofar tana leƙa ɗakin, ya haɗu ɗakin, an malaleshi da wani irin lallausan carfet, ga wani irin sanyin Ac da ƙamshin turare da ke tashi, sai kuma computer ta kai goma sha biyu a cikin ɗakin. "Ƙaraso mana" yayi Maganar yana ƙoƙarin kunna wani socket,kamar sokuwa haka ta ƙarasa shiga, tana waige-waige, ya nuna mata in da zata ajiye masa Abincin. Ta zo ta ajiye, zata juya ta fita, ya ce "Zo ki zauna a nan" ya nuna mata kujerar dake gaban wata Computer. Da ƙyar Amina ta ɗan ɗosana ta zauna, fuskarta duk sauran hawaye. "Kukan me kike?" Ai kamar ya kuma taɓo mata in da yake mata ƙaiƙayi, ta fashe da kuka. Be kuma ce mata komai ba, ya zuba Abincin, tare da gyara zaman gilashinsa, ya fara ci, sai da tayi ta gama, yana danna system ya ce "Ina jinki, kukan me kike?" Ji tayi kamar ta gaya masa abin da Mummy tayi mata, amma ta fasa ta ce "Bacci nake ji, kuma kaƙi ka zo ka karɓi Abincin, duk na gaji" Murmushin gefen baki yayi ya ce "Ko dai ke da matar gidan ne, kike ƙoƙarin hucewa a kaina?" Wasa ta shiga yi da hijjabinta, ba tayi magana ba. Ya miƙa hannu, ya kunna system ɗin gabanta, ya shiga wani video, yadda ake koyar da tips na cin quiz a sauƙaƙe. A nan ta mayar da hankalinta ta nutsu tana kallo, har tana jotting wasu abubuwan a littafinta, shi kuma ya cigaba da cin abinci. A haka video ya ƙare, ta ɗago tana kallonsa, sai dai hankalinsa na kan system ɗin gabanshi yana dannawa. "Kin gama gani?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "To yi mini bayanin me kika fuskanta?" Nan ta yi masa bayanin abubuwan da ta fuskanta. "Masha Allah, kina fahimta sosai". "To zaka tambayar mini Baba zuwa Abujan, kar in ta wahalar banza ina karatu?" "Zaki je insha Allah" "Zaka tambayar mini Baban?" Tayi maganar tana sake tattara hankalinta a kansa. "Insha Allah, akwai abokina a Abuja, idan ma baya son in da za ajiyeki ne, sai ki zauna a can wurin abokina, zuwa a kammala ku dawo" "To kai a ina kake aiki?" "Lagos" ya bata amsa "Amma aka ce a Abuja kake, kuma meyasa baka koma ba?" "Eh na koma Lagos da aiki, na zo hutun ƙarshen shekara" "To wannan computocin me kake da su?" Amina tayi maganar tana kallon ɗakin. "Bayanai na, dana aikina ne a ciki" Amina tayi murmushi ta ce "Aikuwa ina son in iya danna computer Wallahi, ka koya mini aikin da kake nima in dinga danna computer" Alhaji Ahmad ya lumshe idanunsa ya a buɗe su a kan Amina, duk da baya son yawan surutu, amma abin da yafi buƙata a yanzu da shekarunsa suka fara ja, irin abubuwan ɗebe kewa, da zama ayi hira da shi, Hajiya Zainab kuwa hankalinta a kan kasuwancinta da kuma 'ya'yanta suke, bata fiye biyewa zama da shi ba, balle tayi masa hiraraki, shiyasa ya kan tsinci kansa da jin daɗin yawan tambayoyin Amina, da kuma surutan ta marasa ma'ana wasu lokutan. "Ba ka ce komai ba" "Me ma kika ce?" "Aikin da kake a computer zaka koya mini, nima in dinga taɓawa" "Sayar da kuɗi nake" ya bata amsa yana murmushi. "Sayar da kuɗi kuma, ta yaya za a sayar da kuɗi kuma?" "Ana yi mana, ni ina sayarwa" yayi Maganar yana murmushi. Amina ta ɗan yi shiru ta ce "Ban taɓa ji ba". "Yau ai gashi kin ji" ganin tana hamma ne ya sanya ya ce "tashi kije ki kwanta". Amina ta tashi ta nufi hanyar fita. "In biyoki da kwanukan ne?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi dan ta ji". Ta waiwayo ta dawo ta kwashi kwanukan tayi waje. Kashe komai yayi, ya tashi shima ya bar ɗakin, sai dai ya bar shi a buɗe bai rufe ba ya tafi ɗakinsa. Da safe Alhaji Ahmad ya shirya da wuri, dan yana da wani uzuri na gaggawa. Hajiya Zainab tayi masa rakiya, yana shirin fitowa ya tuna ƙaramar wayarsa a ɗakin Computers ɗinsa ya barta, ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Duba mini wayata a ɗakin aikina please" Ba tare da ta ce komai ba, ta tafi ɗauko masa wayar. Sai dai data tashi dawowa, yayi tozali da littafin Amina da ta bar shi a ɗakin a hannunta, ta nufo shi tana masa wani irin kallo da ya kasa tantancewa. AYSHERCOOL 0808102143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA) PAGE 28-29 Sai da hantar cikin Alhaji Ahmad ta kaɗa, saboda tsananin tsoron da ya shiga, har wata ƙishirwar wucin gadi ce ta kama shi, amma cikin dakiya da maziya ya maze ya bari ta ƙaraso. "Meye wannan nake gani haka?" Tayi maganar tana nuna masa littafin. Cikin rashin fahimta ya kalleta ya ce "Ban fahimta ba" "Littafin 'yar aiki na gani a ɗakin aikin ka". Alhaji Ahmad ya miƙe tsaye ya ce "Eh, na shiga zan yi amfani da ɗakin, amma duk yayi ƙura, duk da ba na shiga sai ina buƙatar yin aiki, ai Yakamata ki dinga sakawa ana gyarawa, ko gogewa ne ayi, ganin ba ayi hakan bane ya sa na bawa yarinyar umarnin gyarawa, ina ga mantawa tayi da shi a ciki". Har zuciyarta ta ji ta gamsu da bayanin da yayi mata. 'haka ne, hankalina ne bai kai a gyara ɗin ba, kuma nafi son idan za a gyara ɗin, a gyara ina wurin kar ayi maka ɓarna. A dawo lafiya" "Yauwa na gode" ya amsa cikin mazewa ya juya ya bar Falon, yana yiwa Allah godiya da ya rufa masa asiri. Amina kuwa da shirirtarta, tunani ta dinga yi a kan ta yaya ake sayar da kuɗi, kamar yadda Daddy ya gaya mata, amma bata iya gano ta yadda za'a sayar da kuɗi ba. Lesson ɗin da take zuwa Makaranta ta fara gajiya, dan babu hutu sam, ga aikin gidan nan ba afuwa, kullum da abin da za'a ƙaƙalo a saka ka. Yau Fadila a makare ta zo ita ma, motarta ta so ta bata matsala a hanya, sai dai tana zuwa ta tarar da kankiya ne a cikin ajin, bata ko bi ta kansa ba ta shiga ajin, sai dai ta hango Yazeed a wurin zamanta, a jikin window. Tuno ranar da tayi masa wulaƙanci tayi, har ciwonsa ya tashi, dan haka ba tace masa komai ba ta zauna a kusa da shi. Wani irin warning glance sir Kankiya yayi mata, amma ta share shi, ta ciro littafinta daga jaka. Gaba ɗaya annurin fuskar Kankiya ya ɗauke, ya ɗaure fuska gashi baya son ya aikata wani abu, da zai sa wani ya fuskanci son Fadila yake, kuma yana adawa da Yazid. Haka ya gama lectures ɗin yana harar Fadila, ita kuwa ta nuna sam bata san ma me yake yi ba. Bayan fitarsa ta ɗan saci kallon Yazid, ta basar, shikuwa ƙamshin turarenta ya hanashi sukuni. Littafinta ya janyo, ya juya bayan yayi rubutu "Ina kwana ukuty?" Kallonsa tayi, gata gashi maimakon yayi mata magana, amma saboda wani salon rainin hankali shine ya rubuta mata. Banza tayi masa taƙi kulashi. Ya sake rubuta mata 'Ya kika yi shiru, ko in tasar miki daga wurinki, naga kin haɗe rai?" Babban abin da ya bata mamaki,bai wuce yadda yake rubutun da irin handwriting ɗinta ba. Kallonsa tayi cikin mamaki tana sake kallon rubutun, ba wanda zai ce ba nata bane. Ganin tana kallonsa tare da kallon rubutun ne ya sanya shi ɗage mata gira ɗaya. "Talk" ya sake rubuta mata. "Bani littafina, tun da kurmancewa kayi yau" Murmushi yayi ya ce "Ban kurmance ba, azumin magana nake". Ta zura littafin a jaka, ya miƙo mata wasu takardu, tasa hannu ta karɓa tana dubawa. Presentation ɗin da za suyi ne, na 'yan group ɗin su gaba ɗaya yayi musu, kuma a rubuce ya kai fullscap bakwai,tabi tsararren rubutun nasa da kallo, sannan ta kalleshi cikin mamaki 'Wai duk daga jiya zuwa yau kayi wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh. "Amma ai ka wahalar da kanka da yawa, wannan uban rubutun haka? Shikenan Sai mu kai Cafe a buga?" Duk da yau baya son yin Magana, amma yaji daɗin yadda ta yaba ƙoƙarin sa. Dan haka ya ce "Eh, da ina da babbar waya ko system, da a ciki zan mana sai ayi printing, kowa a bashi wanda zai yi presenting" Fadila ta ce "System ɗina na mota, bari in ɗauko sai in fara typing ɗin, kar aikin yayi maka yawa" ƙarara yake ganin tausayawa a idonta. "Muje in rakaki" Suka tashi suka jera zuwa in da motarta take, ta buɗe ta ɗauko system ɗin sannan suka dawo aji. Ya nemi wuri ya zauna, ta buɗe system ɗin ta kunna, hotonta ya bayyana a kan lock screen, ta saka password sai ga wani ya bayyana a wallpaper ɗin ta, ba ƙaramin tafiya da Yazeed hotunan suka yi ba. Amra ƙawar Fadila a baya, banda yanzu da ta daina shiga sabgar ta, saboda Amran na da wasu halaye da ba su yi mata ba, ta ƙaraso in da su Yazid suke zaune, suka gaisa sama-sama da Fadila. Sannan ta kalli Yazeed ta ce "Yaya Yazid dan Allah wurinka na zo, 'yan group ɗin mu zaka ɗan taimaka mana a kan presentation ɗin da zamuyi" "A yanzu dai aikin namu yake yi, kuna iya jira zuwa ya gama" Fadila ta bata amsa. "Bafa da ke nake ba" Amra ta mayar mata da martani. Yazeed ya ce "Afuwan Amra, bari in kammala namu, sai in zo" Guntun tsaki Fadila tayi, ta cigaba da operating system ɗin. Janyo System ɗin gabansa yayi, dan a ganinsa bata sauri a typing ɗin, tunda ya zuba yatsunsa a kan keyboard ɗin nan yake sarrafasu cikin gwanancewa kamar wani inji. Fadila ta ƙureshi da ido, shi kusan komai ya iya, ana batun Mutane gifted bata taɓa gazagata hakan ba, sai a kan Yazeed. Ji tayi kamar ta tambayeshi a ina ya koyi computer, amma ta basar. Lokacin sallar azahar yayi, Yazeed ya ce "Zai je yayi sallah, idan ya dawo zai cigaba. Ta tashi ta bashi wuri, ya tafi salla, ita ma tashi tayi ta bar System ɗin a wurin saboda careless, ta tafi yin salla da cin abinci. Bayan ya dawo ya tarar da komai yadda ta barshi, ya zauna ya tattara mata litattafanta, minimising yayi, ya zubawa kyakywar fuskarta da ke kan screen ɗin system ɗin ido, yana jin yadda wani abu ke sake fuzgarsa game da ita. "Ina sonki Fadila" ya furta yana cigaba da ƙarewa screen ɗin kallo. "Malam Yazeed wai haryanzu baka gama ba?" Ya ji murayar Amra a kunnensa. Yazeed ya kalli Amra ya ce "Ku mini haƙuri, na kusa gama namu, idan na gama zan zo in sha Allah" "To shikenan" ta amsa masa tana ƙoƙarin barin wurin, Fadila ta shigo hannunta da leda, ta ƙaraso ta zauna, tana kallon screen ɗin system ɗin. "Ka kusa gamawa ne?" "Eh, saura kaɗan, so nake in yi in gama, wancan group ɗin suna jirana". Fadila ta yamuatsa fuska ta ce "Kaga kayi mana abinmu a nutse Please, ba suna da waya ba suje suyi mana, ko su tafi Library" Yazida ya ce "A'a ba'ayi haka ba, zasu ga ban kyauta musu ba, kuma wulaƙanci babu daɗi" Taɓe baki tayi ta miƙa masa leda ɗaya gabansa. Ya kalli ledar ya ce "Meye wannan?" "Abinci" ta bashi amsa. "Alhamdilillah na gode, amma na ƙoshi" Cikin tsiwa ta ce "Saboda na zuba wani abu a ciki?" Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Idan ma kin zuba wani abu a ciki da ina jin yunwa ba ruwana cimyewa zan yi" "Wannan shi ne karo na biyu na baka Abinci ka ƙi ci, meye dalili?". Yazeed ya ce "Nifa yau azumi nake" "Dama ana azumi ranar talata?" "Eh mana, azumin Annabi dawud, yau kayi gobe ka sha ruwa" Tsuke fuska tayi ta ce "Sannu waliyyi, kamar fa raina mini hankali kawai kake yi, ba wanda zai iya irin wannan azumin" "Inji wa? Gwauraye na yin irin wannan azumin, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ne ya bawa samari shawarar yawan yin azumi idan... Sai kuma yayi shiru. Gaba ɗaya Fadila bata gane in da zancen Yazeed ya dosa ba. "Kaga ni ban taɓa ji ba, ka dubo wata ƙaryara dai kayi" Ɗan tsuke fuska yayi, ya saka idanunsa a nata, "Ni ne nake ƙaryar?" Tsiwa ta so yi, amma sai ta kasa jikinta yayi sanyi, idanun Yazid suka yi tasiri a kanta, wanda sai da idanunta suka yi nauyi, ta janye idanunta tana ɗan tura baki. Ɗauke idonsa yayi shima, yana jin daɗin yadda yake yi mata kwarjini wasu lokutan, har ta kasa magana. Kusan mintuna goma, yana typing, ya ƙi taɓa ledar Abincin. Can ta kuma kallonsa ta ce"Wai ba zaka ɗau Abincin nan ko ruwan ka sha ba?" "Wai ina ruwanki dani ne, nace miki azumi nake" "Wane irin azumi ne da za'ace wani azumin samari, ba azumin tsofaffi kawai ake ba?" Sosai Yazid yake dariya, wata amsa ya so ya bata, amma yaga amsar tayi nauyi da yawa, dan haka ya ƙyaleta ya cigaba da dariya. Ganin yadda yake dariya sosai, haƙoransa suka bayyana ya sanya ta ce "Wallahi ba azumi kake yi ba" ta faɗa cike da tsiwa. "Subhanallah, ya aka yi kika san ba azumi nake ba? Shikenan ba azumi nake ba ba zan ci ba" Haushi ne Yakamata, ta miƙe tsaye ta fara jan system ɗinta. Ya kalleta ya ce "Ya dai?" "Bani System ɗina tafiya zan yi" riƙewa yayi yana murmushi ya ce "Sorry yi haƙuri, zan ci" yayi maganar wani irin farinciki yana ratsa shi, kamar a mafarki yake ganin faruwar al'amarin, wai Fadila ce take jin haushi dan be karɓi abin hannunta ba. "Kar ma kaci, bani tafiya zan yi" "Yi haƙuri in ƙarasa, sai muje Cafe a cire, nima sonake na gama da wuri, idan lecturer nan bai zo ba, zanje wurin sir Kankiya, mun haɗu a masallaci ya ce idan na gama lectures in je Office ɗinsa" Ɗan saroro tayi, ta kalleshi ta ce "Me kayi masa?" "Nima ban sani ba, kawai dai ya ce inje" "Yi sauri ka ƙarasa muje" "Muje ina?" "Wurinsa" ta bashi amsa. "Ai bece muje tare ba" Fadila ta ce "Ni dai yi sauri ka gama" Ita kanta har mamakin kanta take yi, yadda yau ta saki jiki da Yazeed, ita gaba ɗaya a rayuwarta bayan 'yan gidansu sai Yusra, sukaɗai ne mutanen da suke bata nishaɗi, dan ita ba shiga harkar mutane take ba, amma Yazid mutum ne mai matuƙar barkwanci, duk haushinsa da kake ji, sai ta fuskanci in ka zauna tare da shi zai baka dariya, sai dai shima ba kowa yake shiga harkarsa ba, balle ka gane tsananin sauƙin kansa, gashi baya fushi abinsa, ga rashin girman kai. Gaba ɗaya ya manta da su Amra da ke jiransa, ya kammala typing ya kalleta ya ce "to muje Cafe a cire, sai a rabawa 'yan group" "Sai fa kaci Abincin nan" Ya ɗan waro ido "In karya azumin nawa?" "Ai ba azumi kake yi ba" tayi maganar tana sake tsareshi da ido. Ta saka shi a gaba, ya ciro pack ɗin Abincin, soyayyar doya ce da miya sai uban nama fal a cikin miyar, sai ruwa da lemo. Ruwan yai bisimillah ya fara sha. Fadila ta ce "Kana malami kana ƙarya, yanzu azumin kenan?" "Niba malami bane, ɗalibi ne, kuma aike kika karya mini Azumin" "Wata ƙaryar again" tayi maganar tana hararasa. Bece mata komai ba, ya fara cin doyar da ƙamshin miyar kawai ya sanya yawun bakinsa tsinkewa, Fadila ta juya masa baya tana danna waya, yayin da shi kuma gaba ɗaya ya kasa sakewa, Yazeed yana da matuƙar gudun zuciya da abin da zai sa a masa gori wata rana, ya ci Abincin nan ne kawai dan yana son ganin yayi abin da zai sa Fadila taji daɗi, ba wai dan yunwar da ta addabi cikinsa ba. Ya kammala ya dinga yi mata Addu'a, har sai da ta haɗe rai, saboda godiyar tayi yawa. Sai da suka fara zuwa Cafe, suka ciro aikin, sannan Fadila ta ce suje wurin Sir Kankiya. Sai dai da suka je, suka tarar baya nan, suka zauna zaman jiran Kankiya, Yazid ya cewa Fadila ta tafi kawai zai jira shi, amma taƙi, saboda ba ta san me zai cewa Yazid ba. Ƙarshe Fadila ta gaji da zaman, tayi masa sallama ta tafi, a kan Cewar duk yadda suka yi da shi ya gaya mata. Yazid ji yake kamar yayi tsalle dan murna, saboda kulawar da Fadila ta nuna masa yau, zuciyarsa bata taɓa kamuwa da tsananin son abin da yake kasancewa da shi ba kamar Fadila. Alhaji Ahmad ya dawo gida, kusan ƙarfe biyar na yamma, sai dai daga yadda suka gaisa da Baba, ya lura kamar akwai damuwa a tare da shi. Alhaji Ahmad yayi parking, tare da kallon sa ya ce "Malam Hassan, lafiya naga kamar kana cikin damuwa?" Baba ya risuna ya ce "Amina ce haryanzu bata dawo daga Makaranta ba, gashi ban san makarantar tasu ba balle in bi bayanta, nayi wauta yakamata ace tun tuni na san makarantar ta su" Daddy ya ce "Subhanallah, kwantar da hankalika, bari in je makarantar da kaina" Baba ya ce "A'a ranka ya daɗe, da ka kwatanta mini ni sai inje in duba" "Haba Malam Hassan, Amina ai 'ya ta ce, idan Fadila ce zan wakilta wani ya nemota ne? Bari inje" yayi reverse ya ja motar ya ya nufi makarantar su Amina. Alhaji Ahmad kai tsaye cikin makarantar ya shiga, ofishin director ya shiga, suka gaisa, Daddy yake tambayarsa yaji shiru haryanzu Amina bata koma gida ba. Director yayi murmushi ya ce "Mun tsaresu ne, lesson ake tayi musu, lallai muna son wannan karon branch ɗin Kano, muci comptetions ɗin wannan shekarar, kuma Alhamdilillah Amina akwai basira, duk da ɗazu na zagaya ajin nasu, taƙi mayar da hankali wai ita ta gaji gida zata tafi" Daddy yayi murmushi ya ce "Dole ta gaji, tun safe fa, kuma gashi in Allah ya kaimu next week, za kuyi resuming makaranta, kaga ita gaba ɗaya bata huta ba kenan" "Haka ne, amma da anyi an gama shikenan, kuma idan Allah yasa tayi nasara, zaku yi alfahari da hakan, tana da ƙwazo sosai" "Gaskiya ne, yanzu dai a ƙyaleta, tun da tace ta gaji ba ganewa zata yi ba, a turota mu tafi gida" Director yayi murmushi ya ce "Dama yanzu za a tashe su su tafi, kuma dan wannan ranka ya daɗe ai da ko waya kayi, da kaina ma sai in dawo da ita gida ba sai ka zo ba" "Ba komai, a turo ta mu tafi" Suka fito daga Office ɗin tare da Alhaji Ahmad. Tunda aka sanarwa da Amina Babanta ya zo ɗaukarta, ita zatonta Baba ne, ta san a rina, yadda tayi yammar nan, dole hankalinsa ya tashi ya biyo bayanta. Sai jefa ƙafa kawai take, idanunta sunyi fuci-fuci sun yi jawur, jakar ma yadda ta saƙalata da gani ta mata nauyi. Mamaki ne yakamata ganin Daddy a harabar makarantar. Murmushi yayi mata ya ce "Sannu, sai kace wadda ake bawa training ɗin sojoji, duk kin yi wujiga-wujiga". Aikuwa kamar ƙiris take jira. Kamar za tayi kuka ta ce "Ni ba zan ƙara zuwa lesson ɗin nan ba, duk anfi wahalar da ni, gashi na gaji ga yunwa nake ji, bayana sai ciwo yake da cikina" tayi maganar a wahale, ƙwallar haushi na taruwa a idonta. Alhaji Ahmad yayi murmushi ya ce "Eh gaskiya kam basu kyauta miki ba, ace mutum yana jin yunwa, kuma ga mutum rago Sarkin kuka, ace an hana shi tafiya gida dole a sa mutum ya gaji ai, har ya fara kuka" ya ƙarasa maganar yana murmushi. Amina ta gane tsokanarta ya ke yi, sai kawai ita ma tayi murmushin, sannan ta ce "Ya aka yi ka san makarantar mu?" "Tunani nayi, zuciyata ta bani nan ce makarantar" ɗan shiru tayi tana tunanin ya za ayi haka ya yiwu. Buɗe mata gaban motar yayi ya ce ta shiga. "Wai gaban motar zan shiga?" "A'a tayar motar zaki hau". Ya faɗa tare da zagayawa mazaunin direba. Ƙarewa motar kallo take, irinta kusan uku ne a gidan, Alhaji Ahmad ne kawai yake hawansu, baya hawa ƙananun motoci sai manya manya, ko nauyi basa masa wurin tuƙawa. Tayi maganar a zuciyarta. Sai da tayi bismillah sannan ta hau motar, wani irin sanyi tare da ƙamshi suka ratsa hancinta, abinka da wanda yake a gajiye, ta sake kashingiɗewa a jikin seat ɗin motar. Ya sawa motar lock tare da rufe glasses ɗin, ya ƙaro sanyin A.C ya fara jan motar. "Tun da nake ban taɓa hawa mota me daɗin wannan ba, ko ta Khalil ba ta kai wannan daɗi ba". "Allah ko?" Ya faɗa yana murmushi. "Wallahi kuwa, kamar in bacci, to wai motar bata da nauyi ne, naga tayi girma da yawa kuma kana tuƙata a haka" "Ko in sauka in baki wuri ki gwada kiji" "A' a rufamini Asiri, ina zan iya" Sai kuma tana ɗan yamutsa fuska ta riƙe cikinta. Ya kalleta cikin kulawa ya ce "Ya dai?" "Cikina ne yake ciwo" "Yunwa kike ji, daga yau idan zaki zo lesson, ki dinga zuwa da Abinci, zan bawa babanki kuɗi, ya dinga baki kina sayen Abinci" A ɗan tsorace ta ce "Taɓ salon ya ce roƙonka nayi, ni bana roƙo, kuma daga yau ba zan sake zuwa wannan lesson ɗin ba, na gaji ai nasara ta Allah ce, ba wannan izayar ce zata sa in ci ba" tayi maganar ranta a ɓace. Alhaji Ahmad ya ce "Baki san abin da yake tattare da yin nasararki ba, kiyi haƙuri nasara sai an wahala take samuwa, sannan idan mun je gida, za kiyi wa Maman Fadila bayanin abin da ya kai littafinki ɗakin aikin mijinta" Zaro Amina tayi ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, a can na bar shi kenan? Na shiga uku me zance mata?" "I don't know" ya faɗa yana ɗage kafaɗa. "Na shiga uku ni Amina, Daddy kai ka jawo mini, baka gayamata kai kace in kai maka Abinci ba, shikenan wataƙila ta koreni karatuna shikenan, idan kuma tayi mini Afuwa kuma ta zageni ni da Baba" kan ta kai ƙarshen maganar, kuka ya ƙwace mata. "Ke kuka baya baki wahala ne? Da wasa nake miki na karɓi littafin, na gaya mata ni na saki aiki a ɗakin, littafin yana wurina, meyasa kika ruɗe haka?" Ajiyar zuciya Amina tayi, tana godewa Allah da ya ƙwaceta, da yau ta san tijarar da zata sha ba ta da iyaka. Tausayin ta ne ya kama shi, da alama ita ma zata sha gwagwarmayar rayuwa kan ta cinma nasara, ya ɗan lumshe idanunsa ya ce "Allah ya rangwanta miki" ya furta a hankali ba tare da Amina ta ji ba. A ƙofar gida yayi parking ya kalli Amina ya ce "Sauka ki shiga, idan kuma in shiga dake ne, idan ta ganki ki mata bayanin abin da ya kai ki motar mijinta kuma shikenan". "A'a yi haƙuri bari in sauka, Na gode Allah ya saka da alkhairi". Bai amsa mata ba, sai binta da yake da kallo. Baba na ganin Amina ya tareta, yana tambayar ba'asin meye ya faru ta daɗe haka? Amina tayi masa bayani, tare da gaya masa Alhaji Ahmad ne ya ɗaukota. "To ki dai kula Amina, hanklina ya tashi sosai" "To Baba ka cigaba da yi mini Addu'a" "Aminatu Addu'a kullum cikinta muke ai" A falo ta tarar da Hajiya Zainab da Khalil, ta durƙusa ta gaishe su, Khalil ya amsa Hajiya Zainab kuwa ko kallonta ba tayi ba, Amina da ta juya baya a hankali ta ce "kanki ki ka yiwa da baki amsa ba' Khalil ji yake kamar ya janyo dare, dan yaje ya ga Hafsa, sai wata fara'a yake ta mussaman. Alhaji Ahmad yayi sallama a falon, suka amsa masa gaba ɗaya, ya kalli Khalil ya ce "Kai saukar yaushe?" Khalil ya amsa da "Ɗazun nan Daddy" "Masha Allah, ya aikin?" "Aiki Alhamdilillah Daddy" "Masha Allah, Ina Fadila ne?" Mummy ta ce "Ta dawo tana ɗaki tana baccin gajiya" Ya jinjina kai ya wuce part ɗinsa. Fadila kuwa bayan littafinta ta juya, tana kallon rubutun da Yazid yayi, sai mamaki take yadda aka yi ya iya kwaikwayon rubutunta, Yazid yana da abubuwan ban al'ajabi. Tunowa tayi da maganarsa wai Azumin samari yake yi, kawai tayi murmushi ta rufe littafin. Khalil miƙewa ya yi, ya bar Falon saboda an fara kiran sallar magariba, yaje masallaci ya dawo, ya shirya cikin wasu haɗaɗɗun ƙananan kaya, ya feshe jikinsa da turare, ya ɗauki kayan siyayyar da ya yiwa Hafsa, ya ɗau motarsa ya fice. Ta wurin da take zaman suya ya fara bi, yaje ya tarar da ita tana ta fama da hayaƙi, ga masu siya sun zagayeta. "Ke ungo nan bani ta naira ɗari ki riƙe canjin" yayi magana yana bata dubu ɗaya, sam bata san Khalil ya zo wurin ba sai muryarsa da ta ji. Murmushi tayi tana kallonsa sanann ta ce "Gaskiya ni wannan zuwan be mini ba, kai kayi kwalliya ni kalleni cikin hayaƙi, kuma baka gaya mini zaka zo ba ba zan kula ka ba gaskiya" Dariya yayi ya tsuguna a kusa da ita "Ni ko a yaya na ganki ƙara kyau kike yi, kawo abun fifitar in fifita miki, sallami waɗan nan" "A'a ka bari kawai, kar kayi ƙaurin hayaƙi" Karɓe abun fifitar yayi, yana ffifita mata wuta, ita kuma tana sallamar masu saya. Suna yi suna hira cike da nishaɗi da jin daɗi. Khalil ya saka ta raba sauran sadaka, ya ce ya saya, ba dan ta so ba Khalil ya tayata suka kwashe kayan, ya rufe motarsa suka hau ɗan sahu tare suka tafi gidansu Hafsa, tare da ledar da yayi mata. Ya zauna a ƙofar gida, ya jirata ta shiga gida tayi kwalliya sama-sama ta fito. Sosai suke hira da Khalil, yana bata labarin wurin aiki. Can ya nisa ya ce "Babyna yaushe zan turo su Daddy ne? Na gaji da zaman Abuja ba mata" "To ni me zance?" "Ban gane me zaki ce ba? Zan sanarwa da Daddy insha Allah zuwa next months zan turo, ginina saura kaɗan, shiyasa zan bari sai na kammala sai in turo" ɗan shiru tayi, sannan tayi ajiyar zuciya. "Ya kika yi shiru, ko ba kya sona?". Murmushi tayi ta ce "Ina sonka Sosai, in ba kai ba sai maliya" tayi maganar cikin dariya. "Wayyo daɗi, dagaske Hafsa?" "Da gaske nake mana" "Kar ki saka in tattaro mutane a ɗaura mana aure yanzu" Hafsa ta ce "Sai kace auren sadaka" "Ai sai yafi albaraka, yakamata mu fara shirin biki ma" "Ka san wani abu, yanzu kaje gida ka huta, kaga yau ka dawo" "A taƙaice dai korata kike yi?" "Ya za ayi in koreka, ni kaina ban gaji da ganinka ba, kaga motarka tana can, ga sanyi ko so kake kayi mura? Kaje gida ka huta kaji nawan" "Yau ɗin nan jina nake wani na musamman, tattali da kulawa ta zahiri daga abar ƙaunata" "Ni kaina mamakin kaina nake yi, ka kawo sauyi da farinciki a rayuwata, na gode Allah da ya sa baka yi zuciya ka rabu dani ba" "Baby Hafsat, duk wanda yaji halin da kika shiga, dole zai tausaya miki, Hafsa ina sonki, zan ɓoye sirrinki zan miki adalci in sha Allah in kula da ke, dan Allah ki aureni kar ki canza ra'ayinki a kaina" "Zuciyata na gazgata duk kan kalaman da kayi mini, kuma ina sa ran ba zaka bani kunya ba, ina sonka Mu'azzam" "Kar ki sa in suma dan daɗi mana" tashi tsaye tayi tana dariya, "muje in raka ka titi" "A'a gari da sanyi, koma gida ki huta, idan naje gida zamu yi waya" "Allah ya kai mini kai gida lafiya" "Naga idan ban yi da gaske ba, yau a a soron Mama zan kwana" ya bata ledar siyayarta ya tafi. Jinsa yake kamar wani sabon ango, cike da nishaɗi da jin daɗi ya nufi gida. Kai tsaye cikin gida ya nufa, domin ya ci Abincin dare. Sai dai yana shiga falon ya tarar da Mummy a tsaye tana huci, tamkar wuta. "Mummy lafiya kuwa?" Ya faɗa yana binta da kallo. "Ban sani ba, daga gidan uban wa kake?" Khalil ya ce "Mummy ban gane.... "Nace daga gidan uban wa kake?" "Wurin Abdul" "Sai naci........... Kai da Abdul ɗin, ni zaka tozarta Khalil? Saboda tsiya da abin kunya? Uban me kake a gaban kaskon mai awara?" Ƙuuuuuuu cikinsa ya bada wani irin sauti gumi ya shiga tsatstsafowa daga goshinsa. Cikin dakiya ya ce "Mai awara kuma?" A hasale ta ce "A'a Ubanka" Ayshercool 08081012143. GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA) Page 30-31 *Zuwa ga masau sanya mini litattafaina a shafukansu ba da izini na ba, na barku da Allah, Allah ya saka mini, ina wahala kuna ci da gumina* *Albishirinku masoya, littafin Dare da duhu, da ya samu kyakkyawan rubutu daga gamayyar marubuta uku, AYSHERCOOL, ZEE KUMURYA DA KUMA NIMCYLUV Ya kammala a document, ga mai buƙata ya tuntuɓi wannan lambar dan mallakar naku a kan kuɗi ₦500 kacal* Cike da matsanancin tashin hankali, Khalil ya ce "Dan Allah Mumy waye ya gaya miki?" "Au tuhumata ma kake yi? To ubanka ne ya gaya mini" "Mummy walla.. "Zan taka ka ka mini rantsuwa, mutumin banza da na wofi sakarai, dama ina ankare da take taken ka, na zuba maka idanu in ga in da ka saka gaba, Hajiya Salma da Turai sun je duba shago, suka ganoka a gaban kaskon awara, suna kallonka kuka hau napep, saboda kalen tsiya kuka tafi, har wurin suka je suka tambayar mini, aka ce kana zuwa wurinta wai sonta kake, wallahi Khalil ka bani kunya, kamar bani na haifeka, ko ka manta matsayin ubanka a ƙasar nan? Babu 'yar wanda zaka kalla a manyan attajiran ƙasar nan a hanaka, amma saboda lalacewa da rashin sanin darajar kai, saboda tsiya, bama 'yar masu abinci a restaurant ba, mai soya awara a titi, ashe ita ce gayyara tsiyar da kazo da ita nan kana ci ran nan ko, an maka barbaɗe a ciki ka ci, idan takensu sammako ni a tafe na kwana, ni Zainab ban durƙusa na haifi ɗan da zai kawo mini jinin matsiyat ba, daga kai har ita zan yi maganinku, zan tsananta bincike a kan yarinyar". Kamar Khalil zai ɗora hannu a ka cikin mariraicewa ya ce "Mummy, dan girman Allah kar ki yiwa Hafsa komai, ba ta da laifi ni na kai kana nace ina so" "Zaka rufen baki ko saina falla maka mari, sakarai sususu, dalla ɓace daga gabana ka bar mini falo, zan ga uban da ya tsaya mata har ta liƙe maka" "Dan Allah Mummy ni ki hukunta ni, marainiya ce fa" "Khalil ni nake faɗa kana faɗa? Zan kwarara maka ashar fita ka bar mini falo" ta ƙarasa maganar a fusace tana nuna masa hanyar fita. A sanyaye Khalil ya fice, yana jin yadda wani abu ya tokare masa ƙirji saboda tsananin damuwa da ɓacin rai. Amina ta sha jinin jikinta, ta tsorata da irin ƙyamar da take yiwa talaka, ta rasa me talaka yayi mata tayi masa wannan tsanar haka, ɗanta na cikinta ta saka a gaba, ta ƙare masa cin mutunci saboda ya nuna yana son 'yar talaka, ƙiyyyar ta wuce misali. Fadila kuwa tana tare da Mummy aka kirata a waya aka sanar mata da anga Khalil, tare da mai awara, dan haka bata ji tausayin abin da Mummy ta yiwa Khalil ba musamman idan ta tuna yadda ya watsa mata ƙasa a ido, a kan soyayyar da Yusra take nuna masa. Khalil kuwa wani irin gumi ne ya dinga tsatsatfo masa, saboda azanar tashin hankali, dama ya san a rina, amma yaso ace shi da kansa ya lallaɓata ya sanar da ita, amma wannan algunguman matan suka ɓata masa komai. A gaskiya yana son Hafsa, sai dai ya san babu yadda za ayi ya samu goyon bayan Daddy, muddin ba Mummy ce ta amince ba. Ya tashi zaune yayi shiru, yana cigaba da tunani, wannan shi ake kira da ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa, ya gama gwagwarmayar samo soyayyar Hafsa da ƙyar, a lokacin da ya ke ƙoƙarin ya miƙa hannu ya kamota kuma, Mummy na ƙoƙarin shiga tsakani. Hafsa kuwa cike da murna ta dinga bubbuɗa kayan da Khalil ya saya mata, turaruka da kayan kwalliya, sai kuma kwalin sabuwar waya mai tsadar gaske. Ta dinga murna tana jujjuya wayar nan, tana yiwa Allah godiya ashe ita ma zata yi ta'amalli da kayan zamanin nan. Vibrating ɗin wayarsa ce ya dawo shi daga tunanin da yake yi, ya kai idanunsa kan screen ɗin wayar yaga beauty. Ji yayi kamar kar ya ɗaga, amma ya miƙa hannu ya ɗauka cikin dakiya ya ce "Baby" "Sweetheart, na gode sosai da sosai, Allah ya saka maka da alkhairi, waya na gani sabuwa dal har da layuka guda biyu, Allah ya ƙara maka lafiyar neman halal, Allah yaja kwanan mahaifanka, ya biya musu buƙatunsu na alkhairi ya kare su a duka in da suke, yadda kake faranta mini, Allah yasa ka shiga aljanna kafaɗa da kafaɗa da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam kamar yadda ya alƙwaratawa masu kula da maraya" Gaba ɗaya jikin Khalil yayi sanyi, idan Allah ya karɓi Addu'ar Hafsa, yasan ya gama dacewa a duniya da lahira, macen da tun kan ya aureta komai ƙanƙantar kyauta ta dinga kwarara masa addu'a kenan, ina ga idan ya aureta, Hafsa bata taɓa roƙarsa komai ba, kai hasali ma ita kanta tana ƙoƙarin ganin ta bashi kyautuka, duk da arzikin da yake da shi, lokaci lokaci, sai ta saka masa katin ɗari biyar wai ga rabonsa nan, yau tayi ciniki sosai. Wani irin ƙaunarta ya ƙara dabaibaye zuciyarsa, a hankali ya ce "Tare da ke Babyna" "Ya naji muryarka kamar baka walwala, lafiya kuwa?" "Lafiya ƙalau, bacci kawai nake ji" "Ok, to bari in barka sai da safe, ka kwanta" Yayi saurin cewa'No, ki yi mini hira mana, raina ne babu daɗi" Cikin damuwa ta ce "Subhanallah, ko na ɓata maka rai ne kan ka tafi?" "Haba, ni da kika faranta mini mana, ba abin da kika yi mini" "To Alhamdilillah, Allah ya yaye maka damuwarka, ka san shi ɗan Adam dama ba a ƙyaleshi haka, sai dai ka kasance mai yawan godiya ga Allah, da kuma ambatonsa a halin daɗi ko akasin haka" Khalil ya lumshe idanunsa yana sauraron bayananta sannan ya furta "Ina sonki Hafsa, dan Allah duk ƙalubalen da zamu fuskanta kar ki rabu dani, na saba da jin daɗin kasancewata da ke, musamman yadda kike kwantar mini da hankali. Kina da haƙuri sosai da hankali, ni dai ina sonki" "Nima ina sonka, dan kama fini haƙuri, ka kwanta kayi bacci" "Allah ya tashemu lafiya" Ta amsa masa da Amin. Ya ajiye wayar, ya rintse idanunsa yana hango irin halin da zai shiga, idan aka raba shi da Hafsa, ita kanta yana tausaya mata, saboda tana matuƙar son sa, kuma ta saka ran samun afuwar rayuwa ita da mahaifiyarta saboda shigowar sa rayuwarsu. Hajiya Zainab kuwa har ta kwanata tana mita da banbami, a kan abin kunyar da a ganinta Khalil yake shirin janyo musu, musamman a cikin ƙawayenta, haka ta cigaba da communicating da su Hajiya Turai, suna cigaba da zigata, a kan duk yadda za tayi ta yi ta raba Khalil da yarinyar nan, dan kar ya ja nata abin kunya, kuma kar ayi masa asiri a mallake mata shi. Amina kuwa ta gama tsinkewa da lamarin Hajiya Zainab, dan bata taɓa zaton al'amarin zai yi zafi haka ba. Washegari Amina tayi shirinta cikin doguwar rigar da Maman Azima ta bata, ta tafi makaranta, kasancewar lesson ne kawai ba da uniform suke zuwa ba, bada ban Alhaji Ahmad ya rarrasheta a kan ta yi haƙuri, ta cigaba da Zuwa lesson ba, da babu abin da zai sanya ta kuma zuwa, dan gaba ɗaya ta gaji da yawon lesson ɗin nan. Ta bayan layin gidan tabi, sai dai duk da kasancewar unguwar ta masu hannu da shuni ce, akwai wanda suke masu ƙaramin ƙarfi ne a unguwar, wasu tsirarin mutane ta gano a ƙofar wani gida, ana ta fito da kayan cikin gidan waje, wata mata da tsohon ciki da yara kusan biyar suna gefe sunata kuka, yayin da wani mutum da alama shine mijinta, yake ta rirriƙe wani mutum yana bashi haƙuri tamkar zaiwa mutumin sujjada. Amina sai ta tsaya tana kallon ikon Allah, wasu tsirarin mutane kasancewar safiya ce, suka tsaya suna taya mutumin bada haƙuri, shi kuma wanda ake bawa haƙurin sai kumfar baki yake yi "Wannan wane irin wulaƙanci ne? Tun yaushe kuɗin nasu ya ƙare, amma ƙaryar yau daban ta gobe daban yaƙi biya, gaskiya ba wani ɗaga ƙafa, akwai mutane a ƙasa suna neman gidan nan, kuma ma sayar da gidan zan yi" "Dan girman Allah ka taimaka mini, maiɗakina tana watanta na haihuwa, idan Allah ya sauketa lafiya, kan nan na samu kuɗin biyaka, ka san asara na tafka kwanan nan a kasuwa, na gobara da ta ƙona mini kaya" "Kaga ni fa sayar da gidana zan yi, idan ka samu kuɗinka kawai ka kama wani gidan" Kasa jurewa Amina tayi, kawai ta wuce su ta tafi makaranta, tana tafe tana kuka, tare da tausaya wa mutumin nan da iyalansa, tabbas talauci babu daɗi, da ana taimako yadda Yakamata, masu kuɗin dake unguwar nan zasu iya sai wa kowane talaka gida, saboda sun ninka talakawan dake unguwar yawa, amma kowa kansa ya sani, sai ranar juma'a zaka ga can gidan ana rabon gurasa can gidan ana rabon alala. Amina ta dinga jin inama ita wata ce, yadda ta san raɗaɗin talauci, idan Allah ya yi mata arziki ba zata taɓa barin na kusa da ita a wahala ba. A haka ta ƙarasa makarantar, da tunane tunane daban daban a zuciyarta, tare da fatan Allah ya bata nasara a rayuwa ta zama wata. Yazid ya nemi afuwar su Amra, na rashin samun damar tsayawa jiya ya koya musu assignment ɗin su, sai yau ya tsaya yana koya musu, Fadila na hango shi, amma ba ta nuna tama ganshi ba, balle ta kula shi, sai da ya gama da su sannan ya taho wurinta. "Dan Allah yau ɗaya ki gaishe ni mana, ke kullum sana gaishe ki?" Ta ce "Ni na saka ka gaishe ni?" "A'a ni naga yakamata in gaisheki, in ji ya lafiyarki" Maimakon ta bashi amsa ta ce "Yauwa nace ya ku kayi da Kankiya jiya?" Yazid ya ce "Jiya har ƙarfe biyar ina school ɗin nan, amma bai dawo ba, yanzu haka ma da wuri na shigo yau, na je ofishin sa, amma sakatarensa ya ce mini baya nan, na zauna na jira shi amma bai zo ba" "Kaga ka share shi kawai" "Meyasa zan share shi? Ko wani laifin nayi masa ne dan Allah ki gaya mini?" Fadila ta kalleshi ta ce "Ni ya za ayi in sani idan ma laifi kayi masa?" "Saurayinki ne fa, zai iya gaya miki" Haɗe rai tayi ta ce "Ni nayi maka kama da sa'arsa? Ai zaren ba kalar yadin ne, nafi ƙarfinsa dan haka kar ka sake haɗani da shi". Wani irin sanyi jikin Yazid yayi, lecturer ma fa kenan, ina ga shi karan kaɗa miya, bai ajiye ba, bai bawa wani ajiya ba. "Meye naga ka wani yi shiru?" "Bakomai, kawai ina tunanin dalilin da yasa yake kirana ne, ko dai zai ja mini kunne ne akan ki?" Da sauri ta kalleshi ta ce "Me kake nufi?" "Ina nufin ya ce kar ya ƙara ganin mu tare" A ranta ta ce 'kai wannan sai kace aljani, ya fiye saurin gane abubuwa' "Ya kika yi shiru?" "Ai ni da zai ya kiraka yayi maka warning ɗin, da ya taimaka mini, ka liƙe mini da yawa, na rasa irin wannan abun, kai gashi kome mutum zai maka ba fushi kake ba". Murmushi yayi, ya sake matsawa kusa da ita, wanda hakan ya fara haddasa mata mutuwar jiki. "Idan yayi mini haka bai mini adalci ba, kina daga cikin mutanen da zuciyata ta aminta da su shiga rayuwata, daga ranar da kika fara yiwa takalmin ƙafata dariya, zuwa rashin iya turanci na, ban ji ba daɗi a kan yadda kike mini dariya ba, sai wadda sauran 'yan aji suka yi mini, rayuwata da ke maybe temporary ne, da mun gama school shikenan, amma wataƙila in Allah ya ƙaddara ke matarsa ce tare zaku rayu har abada" Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Dan Allah Fadila, ki bashi haƙuri kar yayi Wani yunƙuri da zai raba abotarmu, let's be friends" Ta ce "Kai ka gaya masa mana, kuma ina ka taɓa ganin ana abota tsakanin namiji da mace?" "Ba ayi, amma ina son mu mu fara" yayi maganar muryarsa can ƙasa. Share shi tayi ta cigaba da danna wayarta. Gaba ɗaya ya tattara hankalinsa a kanta yana kallonta, ko ƙiftawa baya yi. "Dan Allah ka daina kallona haka, ni gaskiya ka takurawa rayuwata wallahi" ta faɗa a tsiwace tana jujjuya ido. Ya ce "Kamar bani da zuciya ko?" "Dama ina ka ganta" murmushi yayi bai ce komai ba, ya tashi tsaye ya bar mata seat ɗin. "In kana da zuciya kar ka sake zuwa wurin da nake, kuma kar ka sake kulani" bai waiwayo ba, yayi gaba yana murmushin da shikaɗai ya san ma'anarsa. Amina ta na aji ana lesson, ƙarfe sha ɗaya na safe, malaminsu ya shigo ajin, ya kalli Amina a ya ce "Amina ɗauko jakarki ki zo" cikin mamaki ta bi malamin da kallo, ta ga dai lokacin tashi bai yi ba, to ina zata? Haka ta ɗauko jakarta, ta biyo bayansa cikin mamaki. Ga mamakinta Daddy ta gani a tsaye a ƙarshen barandar ajinsu. Ƙarasawa ta yi ce "Daddy lafiya kuwa?" Maimakon ya amsa sai ya ce mata "Ina kwana" Ɗan sosa kai tayi sannan ta ce "Yi haƙuri, ina kwana?" "Ai ni na fara gaishe ki, yau bamu haɗu ba sai yanzu, kuma na riga gaishe ki" Amina ta ce "Yi haƙuri" "Ai ba laifi ki ka yi mini ba, amsawa kawai zaki yi" "Ai kunya nake ji, ba zan iya amsawa ba" tayi maganar tana sunkuyar da kai. Dariya yayi ya ce "Zo mu tafi" Ba musu tabi bayansa, zuwa mota, ya buɗe ya ce ta shiga. Mamaki ya mamaye mata, tana son ta tambayeshi, amma tana tunanin kar tayi wani laifin. Sai dai kasa jurewa tayi ta ce "Daddy ina zamu je ne?" "Sayar da ke zan yi" ya bata amsa. "To ai idan ka sayar da ni ba zan yi tsada ba" Ya ɗan buɗe baki ya ce "Inji wa? Tsada za kiyi sosai, har an biyani kuɗin ma" dariya Amina tayi tana cigaba da kallon titi, sai dai ga mamakinta, sai taga ba hanyar gida suka nufa ba. Ta sake kallonsa ta ce "Amma Daddy.. "Shhh" ya katseta. Haka ta zubawa sarautar Allah ido, sun ɗan yi tafiya mai nisa, suka shiga wata unguwa, titunan unguwar kanta sai lokaci lokaci ababen hawa ke wucewa. Gaban wani ƙaton gate Yayi parking, wani ɗan sanda ya leƙo, sannan ya koma ya buɗe gate ɗin. 'yan sandan sun kai huɗu a cikin gidan, suka dinga ɗaga masa hannu suna gaishe shi, amma bai kula su ba. "Daddy suna gaisheka fa" Amina tayi maganar tana waiwayawa. "Eh na gani" "To ya baka amsa ba?" "Kai ke kam tambayoyinki sun yi yawa" bata kuma magana ba tayi shiru. Yayi parking a ƙatuwar harabar gidan, ya kashe motar ya fice. Amina zamanta tayi a cikin motar, tana waige waige. Ya buɗe motar ya kalleta ya ce "sauko mana" A ɗan tsorace ta ce "Daddy dan Allah ina ne nan?" "Wurin wanda ya saye ki na kawo ki" Gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, ta bi idonsa da kallo. "Sauko mana" ya kuma maimaitawa. Jiki a sanyaye, ta sauko daga motar, tana bin gidan da kallo. Yayi gaba tabi bayansa, gidan yafi wanda suke ciki girma sosai da sosai, kuma ya tsaru, ya ciro mukulli ya buɗe ƙofar shiga cikin gidan. Wani irin ƙaton falo ne, da sai ka taka steps Sanan zaka isa ga kujerun. Fuskantar da Amina tayi babu mutane a gidan ne, ya sanya jikinta yayi sanyi, ta ɗan tsorata. "Shigo mana" yayi maganar yana kallonta. Ƙarara yaga tsoro kwance a fuskarta, hakan ba ƙaramin burge shi yayi ba. Babu tsammani taji ya riƙo hannunta cikin nasa, aikuwa ta tsorata, tamkar zata zura da gudu. Murmushi yayi ya ja hannunta, zuwa wani tangamemen kitchen, sannan ya saki hannunta ya kalleta ya ce "Amina, ke 'ya ta ce, kar ki saka a ranki zan wani abu da zan cutar da ke, amma duk da haka naji daɗin reaction ɗinki akan hakan, kiyi haƙuri na ɗauko ki ba tare da na gaya miki dalilin hakan ba, nan gidana ne galibi ina saukar baƙina a ciki, Abokaina zasu zo garin nan, shi yasa na ɗauko ki ki musu girki dan Allah, bana son yin order na restaurant saboda na yadda da girkin ki, amma idan kinga da takura bakomai, ki bar shi". Jiki a sanyaye ta ce "Zan yi" "In kin san na takura miki ki bar shi kawai" Ta girgiza kai ta ce "A'a, baka takura mini ba, amma me zan girka" tayi maganar tana jin yadda kaɗaicewarsu ta takurata. "Ko me kika girka yayi, zuwa azahar zasu zo insha Allah, na ajiye komai, idan kina buƙatar wani abu sai ki mini magana" ta jinjina masa kai alamar to. Ya juya ya bar kitchen ɗin, sai da Amina ta tsaya ta gama ƙarewa kitchen ɗin kallo, tana tunanin to ita Hajiya Zainab zaman me take, da mijinta zai yi baƙi amma ba zai kaisu gidanta ba ayi musu girkin a can, sai a nan ba? Ganin bata da amsa, ya sanya ta fara tunanin abin girkawa. Khalil kuwa jinsa yake tamkar mara lafiya, gaba ɗaya ya rasa abin da yake masa daɗi, sai da yunwa ta ishe shi, sannan ya shiga cikin gidan neman abin da zai ci, sai dai jin Abincin yayi tamkar magani, ya ajiye Abincin ya tashi, shi babbar damuwarsa, kar Mummy ta ce zata yiwa Hafsa wani abu, gashi har ɗakinta ya je ya sameta ya sake bata haƙuri, yayi mata bayani, amma taƙi saurararsa, ta ƙare masa zagi ta koreshi. Ba zato babu tsammani, Sir Kankiya ya shigo ajin su Fadila, yana muzurai ya fara yi musu bayanin cewa yayi musayan lokacin gabatar da darasi, da malamin da yakamata ya shigo ajin, ya wuce ya ajiye litattafan hannunsa ya fara ƙoƙarin ciro maker daga aljihunsa, yana ɗaga ido, suka yi ido huɗu da Yazid. "Kai jiya bance maka kaje office ɗina ina son ganinka ba?" Yayi Maganar yana tsare Yazid da ido. "Naje sir ban sameka a office ba, har kusan biyar ina jiranka" "You Are very stupid, ni zaka yiwa ƙarya?" "Ba ƙarya nake ba sir" "Shut up, tashi ka bar mini aji, kar ka sake attending lectures ɗina, mara ɗa'a kawai, and mark you no 75% attendance no exams" Gaba ɗaya Fadila sai ta rasa me ma zata yi ko tace, abubuwan na Kankiya sun wuce misali sun zama hauka. Ga mamakinta Yazid ko yunƙurin bawa Kankiya haƙuri baiyi ba, ya tashi ya bar ajin. Kan azahar tayi, Amina ta gama girkin da Daddy ya sakata, duk ta gaji, ta wanke dukkan abin da ta ɓata. Ta bi hanyar da suka shigo ita da Daddy, ta koma ƙaton falon nan, sai dai baya nan, kitchen ta koma tayi alwala ta dawo carfet ɗin falon tayi salla. Bayan ta idar Alhaji Ahmad ya shigo, ya kalleta ya ce "Sannu da aiki" "Yauwa, na gama, sai in tafi gida ko?" Tayi maganar a ƙagauce. Yayi murmushi ya ce "Zaki tafi gida, yanzu dai ga ɗakin da zaki kai abincin can, zaki jirani, idan sun kammala sun tafi, sai mu koma gida tare. Amina ji tayi kamar ta fasa ihu, ita gaba ɗaya bata son wannan ƙeɓewar ta su. Da kansa ya tayata suka shirya komai a ɗakin, ya bubbuɗe kulolin Abincin sai ƙamshi yake yi. Ya kai Amina wani ɗakin, bayan ya sa ta ɗebi Abincin, ya rufeta a ɗakin. Ya koma taro baƙinsa. Amina dai gaba ɗaya a tsorace take, wannan gidan sai ayi garkuwa da mutum ma ba wanda ya sani, Amina ta ci Abinci, ta gama amma zaman ya isheta, dan haka ta kwanta a nan ƙasan carfet, wani nannauyan bacci ya kwasheta. Ya ɗan jima a tsaye a kanta yana kallonta, sannan ya durƙusa daf da ita "Amina ki tashi kiyi sallar la'asar mu tafi" A hankali ta buɗe idonta, firgigit ta tashi zaune, saboda ganin Alhaji Ahmad a tsaye a kanta. Miƙewa tsaye tayi, tana murza idonta. "Ni mu tafi kawai" "Ba zaki sallar ba?" Ta ɗaga kai alamar eh. Ta durƙusa zata ɗau kwanon da taci Abinci ya kalleta ya ce "Bar shi a nan, za a gyara komai insha Allah, muje sai kin yi salla zamu tafi, biyar da rabi fa" Hankalinta bai kwanta ba sai bayan tayi sallar, taga sun fita daga gidan sun hau titi sosai, sun fito daga gidan nan. Suna tafe a hanya Daddy ya ce "Naji daɗi sosai, kin fitar da ni kunya, suna ta godiya, Allah yayi miki albarka, Ahmad ya gode sosai" Ta ɗan kalle shi "Waye Ahmad?" Ta tambaya, dan ta manta sunansa ne. "Baban Fadila da Aminatu" murmushi tayi ta ce "Au na manta sunanka ne" Ta kashingiɗa a jikin seat, tana lumshe ido. "Kin gaji ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. "Eyya, sannu to, and please wannan ma sirrinmu ne, kin taimakawa Daddynki, ya fita kunyar abokansa is our secret" "Tom, ba zan faɗawa kowa ba insha Allah" tayi maganar tana murmushi. Ya zura hannu a aljihunsa, ya zaro kuɗi a envelope ya miƙawa Amina. Ta kalleshi ta ce "Na menene wannan?" "Kuɗi ne na baki, tukuicin abin da kika mini ne, na katse miki karatun ki kin mini aiki" "Ai dama dai sai ka nuna banbanci duk da kace ni 'yar ka ce" tayi maganar tana tura baki. "Banbancin me fa?" "Idan kasa Fadila aiki biyanta kake?" Mamakin Amina yake, sam yanzu bata shakkarsa, ko shakkar faɗa masa magana. "Eh to, na kan mata tukuici da wani abu, dan na faranta mata rai" "Ai ni kayi mini abubuwa da dama, kana ciyar dani, ga wurin kwana, ga kuma karatuna, me zai sa sai ka kuma bani wani abu?" "Wannan ai duk daban" Ɗan shiru Amina tayi sai kuma ta ce "Daddy" "Na'am 'yar Daddy" "In roƙeka wani abu?" "Kan ki tsaye makuwa, me kike buƙata?" Nan ta labarta masa, gidan da ta wuce ɗazu da safe, ana fito musu da kaya. "Yanzu me kike so ayi?" "Dan Allah ka biya musu, tunda kana da kuɗi" "Waye ya ce miki ina da kuɗi?" "Kai ka gaya mini sayar da kuɗi kake, kuma kalli motarka da gidanka, ai dai kana da kuɗi sosai" Murmushi yayi, ya shafi dogon gemunsa, da yake baƙi da fari kaɗan kaɗan a cikinsa. "Daddy baka ce komai ba" "Sai na tambayi mata ta, idan ta amince sai a biya musu" Haɗe rai Amina tayi ta ce "Ashe ba za a biya musu ba kuwa" "Me kike nufi?" "Ai wannan matar 'yar hana ruwa gudu ce, ba zata taɓa barin ayi abin arziki ba" Daddy ya haɗe rai ya ce "Matar tawa ce 'yar hana ruwa gudu?" Amina shiru tayi tana ɗan kallon gefe dan da zata samu dama, sai ta ɗuɗɗurawa Hajiya Zainab Ashar dan ta huce. "Kayi haƙuri, amma wallahi bata da.... "Ke!" Ya daka mata tsawa da sai da ta razana ta kalleshi. "A gaban nawa zaki zagi uwar 'ya'yana" ji tayi kamar ta ce "Nima a gabana take zagin babana' amma ya koma mata Alhaji Ahmad ɗinsa, dole ta haɗiye maganarta. Parking ya yi ya kalleta ya ce "Fitar mini daga mota" "Gida da nisa fa daga nan" ta faɗa kamar tayi kuka. "I don't care, get out" ya faɗa in a serious tone. Buɗe motar tayi a fusace, ta fice ranta a ɓace. Ɗan guntun murmushi yayi, ya ja motarsa yayi gaba. Da ƙafa Amina ta nufi hanyar gida, tana tunanin yadda zata ƙarasa gida a ƙafa. Ran Amina ba ƙaramin ɓaci yayi da abin da Alhaji Ahmad ya mata ba, yana ta mata kirki, amma dan ta faɗi magana a kan waccan azababbiyar matar ya mata wulaƙanci, duk wahalar da tayi masa, amma bai gani ba, meye ya hana ita 'yar lelen matar tasa tayi masa?. Haka Amina tayi ta zancen zuci tana mita a ranta. Horn ɗin motar da ta ji yayi mata yawa a kunnuwanta ne, ya sanyata waiwaya. Murmushi me motar ya sakar mata, gani tayi kamar ta sanshi, ta hau tunanin a in da ta san shi. "Gida zaki ne?" "Eh" ta bashi amsa. "Kamar baki gane ni ba, Bilal ne na nan layinku, muna gaisawa fa idan zaki tafi makaranta" sai yanzu ta tuna shi, yana yawan yi mata adawo lafiya, idan zata tafi makaranta. "Sannunka ya kake?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, taho mu ƙarasa". Ɗan shiru Amina tayi, yamma tayi liƙis, ta san yanzu haka Baba ya fara tunanin ina ta tsaya, kuma idan ta ce da ƙafa zata ƙarasa kuma, magariba zata rufa mata. Dan haka bata da zaɓi illa tabi Bilal. Suna tafe a hanya yana mata hira, ita gaba ɗaya hankalinta baya kansa, fatanta kawai su ƙarasa gida. Suna zuwa ƙofar gidan, Amina ta fara ƙoƙarin buɗe motar tana masa godiya. Bilal ya ce "Bakomai, muje nima in gaida Baban" Amina dai ba ta ce masa komai ba, baya son gwaleshi, bayan ya taimaketa. Tare suka shiga cikin gidan, sai dai Baba baya nan, Dan an fara kiraye kirayen sallar magariba. Amina ta kalleshi ta ce "Ina ga ya tafi masallaci, na gode sosai". Bilal ya ce "To ko zaki bani lambar wayarki?" "A'a ai bani da waya" suna cikin maganar, sai ga Alhaji Ahmad ya fito zai tafi masallaci, tun daga nesa ya fara yi musu wani irin kallo, musamman Amina, Amma Amina ta basar ta mayar da hankalinta kan Bilal. TOFA ME KUKE TUNANI. MASU SAN POSTING KULLUM, SU BIYANI IN BUƊE MUSU VIP, ZAN DINGA POSTING KULLUM INSHA ALLAH AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM (AYSHERCOOL) PAGE 32-33 Duk da Amina ta sha jinin jikinta da irin kallon da Alhaji Ahmad ya yi musu, amma ta maze ta ƙi ko ɗaga kanta, balle ta nuna ta san ita yake yiwa wannan kallon. Bilal ya gaida Alhaji Ahmad, amma ya amsa masa sama-sama ya fice, Amina na ganin fitar Alhaji Ahmad, ta yiwa Bilal sallama ta shige cikin gida. Fadila kuwa tun da Kankiya ya Kori Yazid daga ajin, hankalinta yake a tashe, ta rasa meya kamata ta yi, tamkar a kan ƙaya take haka ta dinga jiran Kankiya ya fita ita ma ta fita, ganin ba shi da niyyar fita ne, ya sanya ta tashi ta nemi excuse zata fita, amma Fafur Kankiya ya hanata, ji tayi tamkar ta je ta shaƙe shi ta gwara kansa, wata irin tsanarsa ta ninku zuciyarta. Sai da yayi kusan awa biyu da wani abu sannan ya bar ajin, yana fita Fadila ta fita, ta dinga duddubawa ko zata ga Yazid, amma babu Yazid babu dalilinsa, duk in da ta san zata ganshi ta duba amma bata ganshi ba, hakan ya sa tayi tunanin gida yayi tafiyarsa, alamar yayi zuciya. Tunani ta dinga yi, wani irin hukunci yakamata ta yiwa Kankiya, wani mataki yakamata ta ɗauka a kansa, amma sai ta yi tunanin kar tayi wani abu a kai, ya kuma cutar da Yazid, haka nan ba tare da ta yanke shawarar komai ba, ta shiga motarta ta tafi gida cike da damuwa. A gidanma kasa sukuni tayi, gashi ita ba lambar Yazid ba, balle ta kira shi a waya taji meyafaru bayan fitarsa daga aji ba. Tana tsaka da wannan tunanin, sai ga kiran Kankiya, ji tayi kamar tayi jifa da wayar, amma tayi yaƙi da zuciyarta ta ɗaga. "Amincin Allah ya tabatta a gareki amaryata" ji tayi kamar ya watsa mata wuta a zuciyarta, ko muryarsa ba ta ƙaunar ji sam. "Me ka kirani kayi mini, wai ban maka kashedi a kan kirana ba?" "Kina fushi da ni dan na kori saurayinki daga aji ko? Ai abinda na gaya miki ne Fadila, muddin ba zai rabu da ke ba, zan ta wahalae da shi ne" "Wai kai waye ya gaya maka Yazid saurayina ne? Babu wani abu mai Kama da soyayya tsakani na sa Yazid, kuma bari in gaya maka wani abu, wallahi muddin baka kiyaye ni a kan batun soyayyar nan ba, sai na maka abin da har ka mutu ba zaka manta ba* Yayi dariya ya ce "Ni ma kuma zan yiwa Yazid ba, dan naga a duniya idan ana son ɓacin ranki, to a taɓa Yazid" Sai kuma yayi ƙasa da murya ya ce "Haba Fadila, duk ke kika saka al'amura suka zama so complicated like this, ni ina da kishi sosai da sosai, shiya sa ba zan iya jure ganinki da wani ba, wallahi idan Yazid ya fita daga harkarki babu ruwana da shi. Yanzu gaya mini yaushe zan zo gidanku?" "Abudrrasheed Kankiya, banda ina ganin darajar alli da duster, da sai na nuna maka wacece Fadila, na lura rashin sanin wacece ni ya sanya kake mini karan tsaye yadda ka ga dama" "Hmmm, koma dai menen ai nasan ke mutum ce, kuma duk matsayinki dole zaki aure wataran ƙarƙashin inuwar wani, Fadila mu daina samun wannan saɓanin, in daina wahalar da ɗan mutane, ki fita harkarsa ki bani dama in gwada miki soyayya" "Shikenan, ni da kai mu zuba mu gani,ka koma ka ƙarewa kanka kallo, sannan ka ƙare mini kallo kasan wacece ni, kan kace kana sona ka san matsayina tukuna, wallahi ka cigaba da takura masa zan nuna maka abin da zan iya yi a kai" Kankiya ya yi ajiyar zuciya ya ce "Saboda shi Yazid ɗin duk kike gaya mini wannan maganganun?" "An gaya maka ɗin, kayi abin da zaka iya" daha haka ta kashe wayar , tana jin tamkar ta sa a ɗaure Kankiya, ita tausayin Yazid take ji, idan aka ɓata masa career an cuce shi, amma Kankiya na son amfani da wannan damar ya tilasta mata ta so shi, bata taɓa tausayin wani ɗan Adam a rayuwarta ba, kamar yadda take tausayin Yazid. Ita kawai kyawawan halayensa take kallo, sai taga kamar idan aka cutar da shi ba a yi masa adalci ba, yana da halaye masu kyau, ba ya cutar da kowa to shi mai zai saka a dinga cutar da shi. Ta tuna irin kasadarsa mussaman a ɗakin jarrabawa, dan kar wani ya faɗi, da tsananin biyyarsa ga malamai, amma hakan bai hana a dinga dizga shi a gaban aji, ba tare da duba halayensa masu kyau ba. Dafe goshinta tayi, ji tayi kamar kanta ya fashe Saboda rasa mafita. Ɓangaren Khalil ma yana cikin ɗumbin damuwa, Hafsa ta buɗe what's app a wayar da ya bata, har tayi masa magana ta what's ɗin, sai wani ƙara lallaɓa shi take, tana bashi kulawa ta mussaman, da Adduoi, nasiha gami da kalaman soyayya, wanda hakan ke ƙara masa sonta a ransa. Gaba ɗaya Mummy ta ɗauke masa wuta, ta daina shiga harkarsa, duk dan saboda yana son Hafsa. Gaba ɗaya fushin da Mummy take yi da shi, bai yi masa daɗi ba, hakan ya sanya, ya kuma ƙoƙarin zuwa ya rarrasheta, sannan yayi mata bayanin halin da su Hafsa ke ciki, ko Allah ya sa ta fahimce shi. Da sallama ya shiga bedroom ɗin Mummyn, ya tarar da ita a kan gadonta, tana danna Computer, gefenta kuma ga calculator, da alama kuɗi take ƙirgawa. Tun da ta ɗaga kai ta kalleshi sau ɗaya, ta mayar da kai ta cigaba da abin da take yi. "Mummy sannu da aiki" "Yauwa" ta amsa a daƙile ba tare da ta kalleshi ba. "Mummy wurinki na zo" "Ai na ganka, ina kuma jinka" Khalil ya ɗan gyara zama tare da sosa kai ya ce "Mummy, dama game da Hafsa ne, yarinyar nan da aka ce miki an ganni a wurinta, Mummy yarinyar marainiya ce ne, Da mahaifinta mai abin hannunsa ne, kan ya rasu ya saya mata kadarori, sai dai bayan rasuwarsa dangin mahaifin suka ƙwace komai, shiyasa kika gansu a haka, amma tana da kirki da kuma hali mai kyau, ba ta da wata matsala yarinyar" Ai tamkar dutse yayi wa wannan dogon jawabin, dan danna calculator kawai take tana shigarwa cikin Computer. "Mummy ba ki ce komai ba" "Me kake so in ce maka, ai kai an shanyeka, ni kuwa ba a shanye ni ba a hayyacina nake, nayi mamakin wurin wani malami suka je haka, da har ka iya zuwa ka tunkare ni ni Hajiya Zainab, kake mini wannan maganar banzan, ban sani ba ko orphanage Home ka buɗe, zaka fara rainon marayu da marasa galihu, da har zaka yayi mo min wannan shirgin tsiyar, Khalil banda rashin hankali irin naka, ina kai ina mai suyar Awara a titi, ba bu ilimi mai zurfi, ta gama zaman titi maza sun gama kalleta, in anjima ta ci kwalar namiji, kuma ka ce mini ita ce sirikata,ai kai ma ka san kayi ƙarya" "Mummy wallahi ba haka Hafsa take ba, tana.... "Dalla rufe mini baki, ina magana kana wani kwantar da murya ce, cece, ni zaka lallaɓa in anince da auren 'yar matsiyata, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, daga yau babu kai babu yarinyar nan, na yanke duk wata alaƙa da take tsakaninka da ita, wallahi na bibiya na tarar ba ka rabu da ita ba, hukuncin da zan yanke maka ba zai maka daɗi ba" "Mummy dan Allah, ki duba lamarin nan" "Ni kake cewa in duba lamarin nan, wato sihirin har ya kai ka fifita ta a kaina" Cikin rauni ya ce "Ba haka bane Mummy, wallahi ba suyi mini asiri ba, suna buƙatar tainako ne Mummy, kuma muna son juna sosai" Mummy ta jinjina kai ta ce "Da kyau Khalil, suna buƙatar taimako ko, sannu gwamnati kowa naka, tashi ka fita ka bar mini ɗaki" ta nuna masa hanyar fita. Zai kuma magana, ta sake haɗe rai ta nuna masa hanyar ficewa, haka ya haƙura ya bar mata ɗakin zuciyarsa babu daɗi. Amina kuwa ba ƙaramin haushin abinda Daddy yayi mata taji ba, haka ta shiga ɗakinta, tayi alwala tayi sallar magariba, ta shiga kitchen ta hau aikin Abincin dare, kasancewar Hajara ce tayi na rana tunda ita tana makaranta. Gaba ɗaya Amina a gajiye take, tunda kusan wuni tayi aikin da Daddy ya sakata, aikin da a ƙarshe ya sakamata da direta a titi yayi tafiyarsa saboda tayi maganar matarsa. Ta gama girkin, ta kai dining, ta ɗau na Baba ta tafi ta kai masa, ta tarar da Baban a cikin ɗakinsa na gadi, yana jin radiyo. Har zata fita, Baba ya kirawota, ta dawo ta zauna tana kallonsa. Ya ɗauko wata 'yar jaka ya miƙa mata, ta sa hannu ta karɓa, ta buɗe jakar wani babban kwalin waya ta gani a ciki, ta saka hannu ta ciro wayar tana kallon Baba. "Baba wannan wayar fa?" Baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Alhaji Ahmad ne ya bani, ya ce in baki, wai saboda ki samu sauƙin karatu, sai dai har ga Allah ni bana son ki mallaki wayar hannu yanzu, amma bana son yi masa jayayya kuma naji ya ce saboda karatunki, ina fatan dai ba roƙonsa ki ka yi ba?" "Haba Baba, ka san bana roƙo, wallahi ni ban roƙe shi ba" "To sai kiyi masa godiya, duk da nima nayi masa" "To, insha Allah zan masa" Ta tashi tana jujjuya wayar ta bar ɗakin Baba. Har ga Allah tana matuƙar son waya, mussaman duba da yadda ƙawayenta ke da wayar, amma ita ba ta da ita, sai dai da ta tuna da abin da Daddyn ya yi mata, sai haushi ya kamata har ta ce "Mayar masa zan yi, ban so" ta jiye wayar a gefen katifarta tana harar wayar tamkar Alhaji Ahmad ɗin ne a gabanta. Washegari da Safe Amina bata da niyyar zuwa lesson, ta tashi ta hau aikace-aikacenta, ta shiga kitchen ta ɗora sanwa, ta yi girkin safe ta kammala, ta zo ta shiryawa masu gidan nasu Abincin, sannan ta kaiwa Baba nasa ta dawo, ta fara mopping ɗin falo. Hajiya Zainab ce ta fara fitowa, Amina ta gaisheta ta amsa mata da ƙyar kamar an yi mata dole, sai kuma Fadila ta fito, Alhaji Ahmad ne ƙarshen fitowa, ba tare da Amina ta kalli in da yake ba, ta gaishe shi, yana jinta ya shareta, kamar ba da shi take ba. "Good morning Daddy" Fadila ta faɗa tana ƙoƙarin haɗa tea. "Morning sweetheart, how are you" "Am fine Daddy" Ya ɗan ƙara kallon Fadila ya ce "Meke damunki ne, you look dull today" Fadila ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Nothing much, stress ne na school kawai" "To Allah ya bada sa'a, yau weekends ki samu ki huta sosai" "Ok Dad" Ya mayar da hankalina kan Mummy ya ce "My Z ina Khalil ne?" Mummy da ta kai loma bakinta, ta ƙarasa taunawa sannan ta ce "ƙyale shi kawai" 'in ƙyaleshi kamar yaya, ban gan shi a wurin cin Abinci ba" "Ka san halinsa wasu lokutan, maybe bacci yake yi" "Is ok" Daddy ya faɗa yana cigaba da cin Abincinsa. Yana yi yana satar kallon in da Amina ke mopping, tayi kicin kicin da rai, ko kallon in da suke bata yi, aikinta kawai take. Ɗan guntun murmushi yayi, ya cigaba da cin Abincinsa. Bayan sun kammala ci, Mummy ta miƙe tsaye, ta kalli Fadila ta ce "Fadila je ki shirya muje ki rakani gidan Hajiya Turai" Fadila ta ɗan tsuke fuska ta ce "Mummy ki je ki kaɗai, ni bana son fita" "Aikuwa sai kin je, tashi maza muje" Fadila tana tura baki, haka ta tashi, ya wuce ɗaki, dan ta fara shirin yiwa Mummy rakiya, idan ba haka ba ta san halin Mummy, idan ta dinga mata mita sai taji babu daɗi. Suka wate suka bar Daddy a falo, Amina kuma na zaune na goge TV. "Ke da waye jiya na gani a tsaye a gidan nan?" Amina ta ɗaga kai ta duba falon, amma bata ga kowa ba, dan haka ta san da ita yake, maida kai tayi ta cigaba da aikinta. "Ko in zo in maimaita miki ne?" Ta ce "Ba kowa" "Kina nufin ƙarya nake kenan?" Ta girgiza kai alamar a'a. "Ke da waye?" "Bilal ne, a nan layin yake, bayan ka ajiye ni a hanya, ya ɗauko ni" Alhaji Ahmad ya ce "Ban tambayeki wannan ba, abu ɗaya nake son gaya miki, kar ki sake kawo mini wani gida, kin zo gidan nan ne dan kin yi aiki da karatu, idan saɓanin haka ne a ranki, to zan sanar da Malam Hassan tun wuri ya san matakin da zai ɗauka, karki ƙara kawo mini wani gida kinji na gaya miki, idan kuma aure kike so sai kiyi bayani, amma gidana ba wurin tara maza bane" kamar kibbau haka ta dinga jin maganganun Alhaji Ahmad, ba ƙaramin ƙona mata rai suka yi ba, ba tace masa uffan ba, sai wasu hawayen ɓacin rai da suka cika mata ido, bata son ya ga lagonta, dan haka ta tashi ta kwashe kayan aikin nata, ta bar masa falon. Alhaji Ahmad ya shirya ya fita, sai dai ya ci karo da Wayar da ya sayawa Amina a cikin motarsa, ya ɗau wayar ya jujjuyata, ya ɗan yi shiru sannan ya jinjina kai tare da faɗin lallai ma yarinyar nan. Ya ajiye wayar ya cigaba da tuƙinsa. Hajiya Zainab ce tare da Hajiya Turai a falonta suna hira, yayin da Fadila ke gefe a zaune tana latsa wayarta. Hajiya Turai ta ce "Wallahi kar ki saurarawa yaron nan, kiyi dagaske ki miƙe a kan abinki, idan ba haka ba wallahi kina kallo za a shanye miki shi, sai yadda aka yi da shi" Mummy ta ce "Wallahi Turai Khalil ya bani mamaki, ban taɓa zaton yaron nan zai kai kansa wurin maƙasƙanciya kamar mak awara ba, me aka yi a kai mai awara? Banda kalen tsiya da rashin sanin darajar kai, ya janyo mini abin faɗa a cikin ƙawaye" "Bari Hajiya Zainab, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halinsu ba, banda abin Kalil waye yake janyo talaka jikinsa, ai kowa arziƙi yake nemawa kansa, ai baki ga abin haushi ba yadda yarinyar ke washe baki, kamar gonar gyaɗa, Allah ya kashe ya bata" Mummy ta ce "To wallahi yayi kaɗan, muddin bai rabu da yarinyar ba, zaiga abin da zan masa daga shi har ita" Turai ta ce "Ai zuwa zaki har gida, mu kasawa yarinya warning ita da uwarta" Fadila dai ba ta tofa ba, dan a ganinta Khalil shi ne ya janyowa kansa, ga Yusra nan, ba abin da Allah ya rageta da shi, amma ya watsar da ita ya ce baya so. Turai ta kalli Fadila ta ce "Daughter, ke kuma wa zaki kawo mana, ina fatan dai ba wahalalle kema zaki kwaso mana ba" Fadila ta ɗan kwaɓe fuska da murmushin gefen baki. Turai ta ce "Ai ba murmushin ba, ni dai ɗana ya gani ya ce yana so, insha Allah da ya dawo zan haɗaku, dan har Babanaa ya zan zancen" Mummy ta ce "Ai na fara mata zancen kwanaki, kin san yaran naki ne, miskilaine kamar ubansu, na fara mata maganar ba ta ce mini komai ba dai tukuna, amma dai na san zasu daidaita" Fadila ta sake gyara kwanciyarta a kan kujera, dan wannan hirarrakin nasu ya isheta, so take su tafi gida kawai. Sai da Khalil ya tabattar da Mummy ta fita, sannan ya shiga falon, ya saka Hajara ta kawo masa kayan breakfast ya karya, ya ci ne dan kawai yana jin yunwa, ba dan yana son cin Abincin ba. Bayan ya gama ya fito daga ɗakin, ya haɗu da Amina a kan baranda, ya kalleta fuskarsa ba walwala ya ce "Daga yanzu idan kun gama girki a dinga zuba nawa ana kai mini ɗakina" Amina ta ce "To insha Allah" Fadila har suka taho gida, Mummy tana yi mata bayanin yadda ɗan Hajiya Turai yake, ita dai Fadila lissafin, yadda zata yi da Kankiya da kuma batun Yazid ne ya dame ta. Khalil kuwa gidansu Abdul ya wuce, dan ba shi da aminin da yake gayawa damuwarsa wanda ya wuce Abdul ɗin. Tun a kallon fako, da Abdul ɗin ya yiwa Abokin nasa, ya san tabbas akwai damuwa, dan a yadda Khalil ya saba, da yazo yake fara zolayarsa, amma yau yana shigowa, ya wuce kan gadon Abdul ya kwanta, yayi shiru ba tare da ya ce musu komai ba. Abdul bai kula shi ba, sai da ya kammala abin da yake yi, sannan ya dawo ya zauna a kusa da Khalil, ya kalli Khalil ya ce "Kalil, meke faruwa ne, tashi kayi mini bayani" Kamar Khalil na jiran ƙiris, ya tashi zaune, yana share gumin da ya tsatsafo masa, ya kalli Abdul ya ce "Abdul, na ga samu, ina shirin ganin rashi" "Kamar yaya kenan?" "Abdul, Mummy, Mummy" Abdul ya sake gyara zamansa ya ce "Me ya faru? Me Mummyn tayi" Kamar Khalil zai yi kuka ya ce "Bayan wahalar da na sha wurin farautar soyayyar Hafsa, na yi nasara na samu, tana sona mun shaƙu, sai dai ina shirin zuwar wa da Mummy maganar Hafsa, ƙawaywen Mummy sun gano ni a wurin Hafsat, sun sanarwa da Mummy, baka ga cin mutuncin da ta mini ba, yanzu haka ma ta ce lallai in rabu da Hafsa, dan Allah Abdul yanzu ta yaya zan koma in janye maganata da Hafsa, bayan ta gama bank dukkanin yarda, da saka ran samun salama a wurina tayaya Abdul" Abdul ya jinjina kai ya ce "Akwai damuwa, ka san iyaye gaba suke da dukkanin wani abu na san rai da son zuciyarmu, amma kuma yakamata ita ma Hafsa a duba a yi mata adalci, kaima kana da ƙanwa mace, alhakin Hafsa zai iya kama Fadila da bata ji ba bata gani ba" "Kai Abdul, ba zan iya haƙura da Hafsa ba, duk da ban san wane irin mataki Mummy zata iya ɗauka a kaina ba, bana jun zan iya rayuwa babu ita!!! DOMIN SHIGA VIP GROUP, POSTING KULLUM KU TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA) P34 Abdul ya gyara zamansa ya sake fuskantar Khalil ya ce "Ibrahim, kai ka wuce aboki a wurina yanzu, kai ɗan uwana ne, ba zan so ka aikata abin da zaka zo kana dana sani ba, kar ka biyewa soyayya ka zo ka rasa yarda da soyayyar mahaifiyarka, Ka bi komai a hankali, har Allah yasa Mummy ta fahimta, shawara ta farko mai zai hana kaje ka samu Daddy, shi ka yi masa bayanin, na san zai fuskance ka kuma zai yiwa Mummyn bayani" Khalil yayi wani guntun murmushi sannan ya ce "Abdul ya kake abu kamar ba ka san wacece Mummy ba ne? Kai ka san babu yadda za a yi na samu goyon bayan Daddy, muddin Mummy ba ta son abu, ba zata taɓa yarda ba, kuma wallahi ina matuƙar jin tausayin Hafsa, idan na rabu da ita ban san wane hali zata shiga ba, bari ayi sallar magariba, muje tare ka shaida yadda yarinyar nan ta shaƙu da ni, ta yarda dani ta saki jiki zan Aureta, amma Mummy tana barazanar rabani da ita, dan Allah Abdul ko Hafsa na da wani aibu da so ya rufe mini ido ban gani bane?" Abdul a ransa ya ce 'Talauci, shine aibun da mahaifiyarka bata so' amma a fili ya ce "Ai Hafsa yarinyar kirki ce, ba ta da wani aibu, ba wanda ba zai so haɗa zuriya da ita ba, kuma tana cikin yanayin da take buƙatar taimako, zaman soya awarar nan bai dace da ita ba sam" "Yauwa Abdul, ashe ka gane, wallahi yana daga cikin dalilan da ya sanya nake son taimakonta, Hafsa da gidan Aure ko makaranta ta dace, ba da zaman titi ba, Abdul na tsara irin rayuwar da zan yi da ita, yadda ta sha wahala a baya duk da farkon rayuwarta 'yar gata ce, amma ina son in ɗauke mata komai, yadda ba zata taɓa kukan wani abu ta rasa ba, sai abin da bani da damar sama mata, Abdul ba zaka gane ba, that girl deserve a shoulder to rest, akwai matsala idan Hafsa ta auri mutumin da bai San mecece ƙaddara ba, kuma bai san kimar mace ba, ya zan yi Mummy ta gane ne?" Abdul ya jinjina kai, So kenan, mai sa mutum ya duƙa, ya susuce duk izzarsa da kuma taƙamarsa' A yadda Khalil yake ɗan gayu matashi mai ji da kuɗi, idan aka ce maka zai ɗauko mace kamar Hafsa ya ce yana so zaka ƙaryata, amma ya zauna sai sambatu yake yi. Abdul ya ce "Khalil, naji duk bayananka, kuma na fuskance ka, zan tayaka da Addua, sannan zan cigaba da tunanin menene mafita ga al'amarin nan" da ƙyar Abdul ya ɗan rarrashi Khalil, ya rage damuwar da yake ciki. Amina bayan barinta falo, da ta koma kitchen kuwa saida tayi kuka sosai, ita gaba ɗaya gorin nan da ake yi mata da kuma takura ya isheta, shikenan dan tana karatu wani ba zai kulata ba, kuma ita Bilal ba cewa yayi yana sonta ba, 'yan ajinsu suyi ta bada labarin samarinsu, amma ita sai samarinta na ƙauye, gashi Alhaji Ahmad yayi mata gori kuma ya hanata tsayawa da saurayi, ta zauna a kitchen tana ta kukanta. Hajara ta shiga kitchen ɗin ta tarar da ita, a zaune tana share hawaye. "Amina kukan me kike kuma?" "Ba komai" Amina ta faɗa a daƙile. "Kawai jin daɗi ne ya sanya kika zauna kina kuka?" "Nace miki bakomai, ki ƙyaleni" Amina ta faɗa a ƙufule, dan sa idon Hajara yayi yawa, komai ta gani so take sai taji ƙwaƙwaf, yadda aka fara da yadda za a ƙare. Ta miƙe ta cigaba da aikin tana yi tana kuka, kamar ƙaramar yarinya. Tun daga wannan ranar, Amina ba ta yadda ko hanya ta haɗata da Alhaji Ahmad, ganin idan ta gaishe shi ya daina amsawa, sai dai ya tsaya ta ƙureta da ido, dan haka gaisuwarma ta daina gaisheshi. Idan suka haɗu sai ta basar ta wuce abinta. Da magariba Khalil ya takurawa Abdul, ya shirya suka tafi gidansu Hafsa, kasancewar ta san da zuwansu, ya kirata ya sanar mata, ya sanya ta shirya har da yi musu girki, ta saka ɗaya daga cikin kayan da ya kawo mata, a ɗinke, wani less mai matuƙar kyau da ya kawo mata shi a ɗinke. Tun da ta fito hannunta riƙe da babbar darduma, Khalil yake kallonta, tayi masa kyau fiye da kullum, ga wani irin tausayinta da ya ƙara mamaye masa zuciya. Tana Zuwa tayi murmushi ta ce "Yaya Abdul, kwana biyu ka ɓuya da yawa" Abdul yayi murmushi ya ce "Ai tunda Allah yasa ku ka daidaita, bai kuma nemana in masa rakiya ba, shiyasa ba kya gani na" "Yaushe zan nemeka, ka zo ka samana ido" Khalil ya faɗa yana sake mayar da hankalinsa a kan Hafsa. Ta shimfiɗa musu sallaya, suka zauna ita kuma ta zauna daga gefe. "Babyna kina lafiya, ya kasuwa?" "Alhamdilillah, ya gida ya su Mummy?" "Suna lafiya ƙalau, kin yi mini kyau fiye da kullum, kamar in sace ki in gudu, Abdul ko zagawa zamuyi mu tataro mutane a ɗaura mana auren nan ne kawai mu huta?" Abdul a ransa ya ce "Da ka ci ubanka la'ada waje a wurin babarku' Amma a zahiri ya ce "Eh to idan ƙanwar tawa ta yadda, sai muje neman mutane a haɗu a ɗaura ai" Hafsa sai sunkuyar da kai take tana jin kunya, Khalil ya leƙa fuskarta ya ce "Babyna, ki gaya masa kin amince, mun Matsu mu mallaki junanmu, ko yanzu a shirye muke a ɗaura" Ƙunshe fuska Hafsa tayi, tana jin wata irin kunya tana ratsata, gaba ɗaya shi Khalil baya jin kunya. "Ya kika yi shiru, in dai Abdul ne ki daina jin kunyarsa, a ɗaura mana aure next year by now insha Allah idan baki haihu ba to muna nan muna rainon Babynmu a cikinki" Miƙewa Abdul yayi ya ce "Khalil wannan fitsarar ta ka, ba ita ba ni kaina kunyar kake bani, bari in koma mota In jiraka" Dariya Khalil yayi, Abdul ya nufi ƙarshen layi in da suka bar motarsu. Khalil ya matsa ya sake mayar da hankalinsa kan Hafsa ya ce "Amaryata, ɗago mana in ƙare miki kallo, baki ga yadda kika mini kyau ba" A ɗan shagwaɓe ta ce "Wai sai ka ta bani kunya a gaban mutane" "Suwaye mutanen, Abdul ɗin? Ni banga wani abin Kunya ba" "Ni na gani ai, amma kayi mini kyau sosai" "Da gaske?" Ta jinjina masa kai, yayi murmushi ya ce "Kyau sai ma ranar bikinmu yarinya" Tayi shiru ba tace komai ba. "Babyna" ya faɗa murya ƙasa-ƙasa. Ta ɗan ɗago ta kalleshi. "Kiyi magana mana" "Yau ba 'yan maganar, na rasa me zance" "You must say something, bari muyi Auren zobe, wata azurfa na saya mana tun last month, sai wannan watan Allah ya sa suka iso" Ya ciro wata 'yar ƙaramar box blue black, ya buɗe sai ga wasu zobuna masu matuƙar kyau a ciki. Ya ɗauko na matan, ya kamo hannun Hafsa, ya kama yatsanta ya saka mata zoben. Da ɗan sauri ta janye hannun nata, tana jujjuya zoben tana murmushi. Ya miƙa mata masa hannun, ya ce "Nima sa mini" Ya miƙo mata yatsansa, cikin rashin sabo, ta zira masa zoben. Hannunta ya kamo cikin nasa, ya ciro wayarsa, ya ɗauki hoton hannunsa da nata sanye da zobunan. Daga nan ya zarce yana ɗaukarta hoto, hannunta da ke cikin nasa ba ƙaramin takurata, yayi ba amma ta kasa cire hannunta daga nasa, yayi ta musu hoto. Ba tare da ya cire hannunsa a nata ba ya ce "Hafsa zaki aureni?" "Meyasa kake yawan maimaita tambayar nan? I will marry you in sha Allah My" tayi maganar tana masa murmushi. "Murmushin nan naki yana killing ɗina, ki ce kina sona?" "Ina sonka sosai, duk ka koya mini rashin kunya" "Kina da kunya sosai, amma naji daɗi da kika rageta sosai a kaina, ina son matata ta zama mai kula dani sosai, ina sonki Babyna, ki cigaba da yi mana addua, Allah ya tabattar da Aurenmu, ya bamu ikon cin duk wata jarrabwa da ka iya taso mana" "Ina yi mana" "Yauwa Habibty, zuba mini Abincin in ci, kuma a bakina zaki bani" Ta noƙe kafaɗarta ta ce "A'a zan dai zuba maka, sai bayan nikah zan dinga baka a baki" Haka ta zuba masa Abincin nan, yana ci yana zuba santi yana koɗata. Ya kammala ci, ya ce "dama wancan ba ci zai yi ba, ya ce lemo kawai zai sha, na gode sosai matata in sha Allah, bari in tafi" Hafsa ta marairaice ta ce. "Ni kar ka tafi yanzu, ban gaji da ganinka ba" "Allah sarki sweetheart, ni kai na bana son tafiya, ban gaji da ganinki ba" "Shikenan ma yi video call, kar kayi dare muje in raka ka mota" Khalil ya ce "A'a, bana son ki wahala, ki ce ina gaida Mamana" "Ni baka taɓa haɗani da Mummy na gaisheta ba" Ɗan dam yayi, sai kuma ya ce "Karki damu zan haɗaku" Yana nan tsaye, sai da ta shiga gida, sannan ya nufi in da motarsu take. Jiki a sanyaye ya shiga motar ya zauna. Abdul ya kalleshi ya ce "Baban soyayya, ka shanyani kana can kana soyewa, Allah yasa baka ƙone ba" Khalil ya Shafi gemunsa ya ce "Kamar kar in taho, ina son yarinyar nan" "Nima na ga alama, zan taya ku da Addua in sha Allah". Da haka Khalil ya ja motar, ya tafi kai Abdul gida. Washegari Monday, su Amina zasu koma makaranta, ta yi gugar uniform ɗinta, ta wanke jaka da takalminta, ta shirya litattafanta, tana ta kallon jakarta tana jin shauƙi da farincikin komawa makaranta, ta dinga tuna rayuwar da tayi a ƙauye, yadda ta dinga makaranta a wahale, wataran sai dai ta saci hanya ta je makaranta, idan ta dawo ta ci duka, amma nan duk da tarin ƙalubalen da take fuskanta, akwai Abinci, akwai wurin kwana mai kyau, gashi duk wani aiki da ake sakata, ba a sakata lokacin makarantarta. "Kai Allah ya saka maka da alkhairi" ta faɗa a fili, sai kuma ta tuna da abin da Alhaji Ahmad yayi mata, sai ta tura baki tana ƙunƙuni kamar tana gabansa, ta tashi ta tafi wurin Baba. Ganin fara'a a fuskar Amina ya sanya Baba yin murmushi ya ce "Uwata, murmushin me kike haka ne?" "Baba ka san gobe in Allah ya kaimu zamu koma makaranta, shine nake ta jin daɗi, na wanke uniform ɗina na goge, shi ne nake jin daɗi" Baba ya ɗan yi ajiyar zuciya, ya ce ina zuwa. Ya tashi ya shiga ɗakinsa ya fito da ƙatuwar leda, ya miƙawa Amina ya ce "Gashi in ji Alhaji Ahmad, jaka ce da takalmi ya ce a baki, kuma wai idan kinje makaranta ki je ki karɓa sabon kayan makaranta, Uwata ban taɓa zaton Alhaji Ahmad zai kyautata miki haka ba, bani da bakin yi masa godiya, sai fatan ya gama da duniya lafiya, Uwata ki same shi ki durƙusa har ƙasa ki yi masa godiya Amina" Maimakon Amina tayi murna, sai ta ɗan tura baki, dan ji tayi ma kamar ta ce bata so. "Uwata ya naga kin haɗe rai" "Ba komai Baba murna nake yi, Allah ya saka masa da alkhairi, na gode sosai, amma ai ni takalmi na da jakata da Uniform ɗina suna da kyau" "Ba sai ki adana abinki ba, kuma ya mini ƙorafin idan ya baki abu ba kya karɓa, wannan kuma kin yi daidai, ki cigaba da kula da mutuncinki" "To, In sha Allah Baba Na gode sosai" Ta miƙe da ledar a hannunta ta koma ciki, Hajara na ganin Amina da leda, ta fara washe baki, "Amina sayayya aka yo mana haka?" Ko kallonta Amina ba tayi ba, ta wuce ɗakinta. Zuwa tayi ta zauna ta bubbuɗe ledar, jaka ce mai tsadar gaske, da takalmi da safa, kai da ganinka san kaya ne masu matuƙar tsada. Fadila sai dubawa take taga Yazid a ajin, amma babu Yazid babu dalilinsa, har aka yi lectures ta farko aka gama, ba taga Yazid ya zo ba. Suka yi ta 10_12 ma, still Yazid bai zo ba, gashi tana lectures ɗin 2-4 za suyi presentation ɗin nan, amma Yazid bai zo ba, gashi presentation ɗin nan shi ne zai ɗau maki mafi yawa. Taje ta yo salla ta je Cafeteria ta ci Abinci, ta nufo aji. A wuri ɗaya ta hango shi a zaune, ya sunkuyar da kansa, da alama wani abu ne mai muhimmanci ya ɗauke masa hankali, ba ta san ya aka yi murmushi ya suɓuce mata ba, ta nufi in da yake zaune "Kai dama zaka zo school ɗin nan, amma kayi missing ɗin har lectures biyu?" Tayi maganar ba tare da ta zauna ba, Yazid ya ɗago a hankali ya kalli Fadila, ya mayar da kansa ya cigaba da kallon wayarsa dake hannunsa. "Am talking to you" tayi maganar tana kallonsa. Ya ce "Ina jinki ai" "Kana jina Kai mini banza?" Cigaba da kallon wayarsa ya yi. Haushi ya kama Fadila, ta sa hannu ta zare wayar daga hannunsa, ko ɗaga kai bai ba balle ya kalleta. Duk da ƙaramar waya ce amma Alqura'ani ne a kai yake karantawa. Zama tayi a kusa da shi "Wai yau ma azumin maganar ka ke yi?". Kashingiɗa yayi da jikin bencin, ya ware mata idanunsa a kanta, still bai ce komai ba. Da sauri ta janye nata idanun, jin tsigar jikinta na tashi, ga wani gumi da bata san na menene ba yana tsatsafo mata a goshi, ta kasa tashi ta kasa komai, shi kuma ya cigaba da kallonta, kamar ya samu majigi. Samun kanta tayi da miƙewa tsaye, tana ƙoƙarin barin wurin, amma cikin shammata ya janyo hannunta wanda hakan ya tilasta mata zama jikinsu na daf da haɗewa har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskarta, Allah yasa ajin babu mutane, kowa sabgar gabansa yake yi. Sosai jikinta yake rawa, kamar wadda ake yiwa gangi, ga idanun Yazid da suka dasa mata wani shocking da yake tsirga mata tun daga kanta har yatsun ƙafarta, yawun bakinta har wani bushewa ya yi. Bakinta ya dinga bi da kallo, ɗan madaidaici a kyakykyawar fuskarta, da ya ƙware a wurin iya tsiwa da masifa. "Bani wayata" ya furta yana sake ƙoƙarin sanya idonsa a nata, amma ta hana hakan, ta hanyar sunkuyar da kanta. "Bani mana" ya sake maimaitawa, amma ta kasa motsi, sai jujjuya idanunta da take yi. Hnnunsa ya sa ya zare wayarsa daga hannunta. Mafarkan da take da shine suka dinga dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, maganar Yusra ce ta dawo mata 'Wataran sai kin rungumeshi a zahiri' Firgigit ta dawo hayyacinta, daga duniyar da ta lula, har ta kasa gane mafarkan da ta saba yi ne, ko kuma zahiri ne, dan wani irin yanayi ta shiga wanda da ta kasa fassarawa kanta wane irin yanayi ne haka. Miƙewa tsaye tayi, ta bar wurin da sauri, tana ta sauke numfashi a jejjere. Yazid kuwa binta yayi da kallo, yana kallon yadda ta birkice a lokaci ɗaya, duk taurin kan Fadila, ba wuya ya sa ta shiga taitayinta. Fadila ta cigaba da rarraba idanu, tana jin yadda halin da ta shiga ya kasa barinta haryanzu. A hankali ɗalibai suka cigaba da dawowa ajin, saboda shiga lectures ɗin su ta ƙarshe, wadda daga ita kowa zai tafi gida, kuma wadda a ita ne, zasu gabatar da presentation ɗinsu. Lokaci na cika malamin ya shigo ajin, kasancewar mutum nai kiyaye lokaci, kowa ya nutsu ya shiga taitayinsa, kasancewar malamin ba shi da wasa Sam. Kowane 'yan group sun nutsu, sun haɗu wuri guda, suna tattauna yadda za su gudanar da presentation ɗin su, banda 'yan group ɗin su Fadila, ita tana nata wuri, Yazida ma haka, sauran 'yan group ɗin ma haka. Aka dinga kiran groups ɗaya bayan ɗaya, suna gabatar da presentation ɗinsu, duk karsashin group idan lecturer da 'yan bani na iyan aji suka fara suburbuɗo tambaya, duk karsashin 'yan group ɗin, sai sun karaya. Da haka aka zo kan group ɗin su Fadila, aka kira su, suka fito ɗaya bayan ɗaya, suka jeru a gaban aji, sai dai Yazid bai fito ba, sai da suka gama fita gaba ɗaya sannan Yazid ya fito, yana zuwa ya tsaya a kusa da Fadila, suna fuskantar 'yan aji. Ji tayi tana neman diriricewa, a hankali ya furta mata "Ki nutsu mana, you are facing the class" Suka fara gabatar da presentation, aka zo kan Wanda Fadila za tayi, gaba ɗaya ba ta da confidence, saboda a halin da Yazid ya sakata, sai dai yadda take zuba turancin ne zaka san ya zauna sosai a bakinta. Suka gama gudanar da presentation, aka zo fannin amsa tambayoyi, lecturer ya fara yi musu tambaya, Yazid ke da karsashin amsa tambayoyin, tun da shi ya yi Assignment ɗin, sai dai ba ya iya public speaking da harshen turancin yadda yakamata, a rubuce ne dai ba laifi, amma banda a baki. Yana ƙoƙarin bada amsar, sai larabci ya suɓuce masa, ya dinga haɗawa da hausa yana bayani. "Kai Malam, bafa ajin larabci bane, ba nahawu muke yi ba, da turanci zaka mana bayani" cewar wani ɗalibi. Yazid ƙoƙari yake ya kuma gudanar da bayanin, amma turancin yaƙi fita yadda yakamata. Ana haka, Amra ta kuma yankowa Yazid wata tambayar. Ƙoƙarin amsawa yake, gashi ya san amsar, amma bisa kuskure sai ya dinga haɗawa da larabci, babban abin da ya ƙonawa Fadila rai, bai wuce yadda wasu daga 'yan ajin ke masa dariya ba, ba ita ake yiwa dariyar ba amma abin ya ƙular da ita sosai. Shi dariyar da suke masa, bata dameshi ba, ganin turancin ya ƙi yiwuwa kawai ya juya harshe zuwa larabci, ya dinga zuba bayani, wanda ya tilastawa 'yan ajin yin shiru suna kallonsa, ba zaka taɓa cewa ya jii hausa ba. Fadila ce ta fara yi masa tafi, 'yan group ɗin ma suka ɗau tafi, lecturer kam zuba musu ido yayi yana kallon ikon Allah, ya miƙe tsaye ya ce "Kai Sheikh haka za muyi da kai, wa zai fassara mana me kace mu da bama jin larabci?" Yazid ya ce "Sir, ban iya turanci ba, kuma na ji sun ce ba sa so da Hausa". Lecturer ya dafa kafaɗar Yazid ya ce "Ka burgeni sosai, Allah ya ƙara hazaƙa, ina ɗan jin larabci kaɗan, na kuma fahimta, and you zaki zo mini da abin da kika fahimta a bayanin da yayi a next lectures" lecturer yayi maganar yana kallon Amra. Lecturer yayi nasiha sosai, da nuna musu kuskuren abin da suka yi, na son ƙure Yazid dan bai iya turanci ba. Fitar lecturer babu daɗewa, class rep ya fita gaban allo, ya dinga faɗa a kan abin da Amra da wasu 'yan ajin suka yiwa Yazid, duk da irin taimakon da yake musu, a kan koya musu wasu abubuwan da ya shige musu duhu. Amrah ta ce "Nifa bana son raini, ai naga Fadila ce ta fara yi masa dariya a ajin nan a kan bai iya turanci ba, amma ba wanda ya ce mata komai dan ana tsoron ta sai ni" "Kar ki ƙara saka sunana a shirmenki, ni ba sa'ar yinki bace wallahi" Fadila ta faɗa daga wurin da take tsaye, tana ƙoƙarin haɗa jakarta ta fice. Hayaniya ce ta nemi ɓallewa a ajin, Yazid kuwa tuni ya sulale yayi tafiyarsa. Saura ƙiris Fadila ta tsinke Amra da mari, da ƙyar aka lallaɓata aka sallameta ta tafi, dan Fadila ba ta fiye shiga harkar mutane ba, amma idan ama taɓata ta ƙware a masifa, bata ragawa kowa. Kusan ƙarefe goma saura na dare, Mummy ta shiga in da su Amina suke, ta ƙwanƙwasawa Hajara ƙofa, Hajara ta buɗe ta fito tana mutstsuka ido, alamun ta fara bacci. Hajiya Zainab ta kalli Hajara a yatsune ta ce "Ki dafawa baban su Fadila tea, ki ajiye masa a dining, zai fito ya sha" Hajara ta risuna ta amsa da to. Haka ta shiga kitchen, kamar tayi kuka, dan taji daɗin baccin da ta fara yi. Ta kammala dafa shayin, ta fita falo, ta tarar da Alhaji Ahmad a zaune a falon. Ta risuna ta ajiye masa shayin, ya miƙe tsaye, ba tare da ya kalli Hajara ba ya ce "Ajiye a nan, ki turo Amina ta kai mini falona" daga haka ya wuce ya barta saroro tana binsa da kallo. Hurry up and subsribe the VIP GROUP at affordable price. 08081012143 07063065680 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL) 35 "Too wai meke faruwa a gidan nan ne?" Hajara ta faɗa a fili, sai da ta gama surutanta da mamaki, sannan ta tashi ta tafi kiran Amina" Amina na zaune a tsakiyar katifarta, ta baje litattafanta, tana ta aikin nata na karatu. Hajara ta ɗaga labulen ɗakin Amina, ta kalleta, ita lamarin Amina ya fara bata tsoro, kullum tana nace da littafi kamar masifa, har aiki idan tana yi, tana kallon littafi, saboda tsananin saka boko a ranta. Amina da bata son Hajara ta shigo ɗakin ba sai yanzu da ta ɗago kai, ta ganta a tsaye tana kallonta. "Lafiya kuwa?" Hajara ta ɗan geɓare baki ta ce "Maigidan nan ya ce ki kai masa shayi falonsa, yana son ganinki" "Ni kuma? Ba ke na jiyo Hajiya tana cewa ki dafa masa shayin ki kai masa ba?" "Na dafa masa, amma ya ce ki kai masa" Hajara ta faɗa a hasale. Haɗe rai Amina tayi tana ɗan tura baki, ganin Hajara ta zuba mata ido, tana nazartar action ɗinta ya sanya Amina ta ce "Ina shayin ya ke?" "Mhmm yana falo" "To zan kai masa, ina ga zai mini maganar tafiyar mu Abuja ne, wurin competition, ina ga makarantarmu sun masa magana" tayi maganar cike da son kawar da mugun tunani da mummunan zargi a zuciyar Hajara. Amina ta ɗan buɗe baki ta ce "Au Wai dagaske Habujar zaki?" Amina ta ce "Ai ban sani ba, sun ce zasu kira shi a waya ne su sanar masa, ina ga shi yasa ya ce in kai masa shayin, bari in je" Amina ta miƙe ta zura dogon hijjabi, a kan kayan da ke jikinta na bacci. Hajara tabi bayanta da kallo ta ce "Lallai yarinya, ni zaki rainawa hankali, zan zuba ido dai in ta bibiya" Amina ta ɗau kayan tea ɗin, ta tafi falon Daddy, tana fatan Allah yasa idon Hajiya Zainab biyu, kuma ya sanya tana ɗakin, yadda tana ajiye masa tea ɗin zata dawo ta cigaba da sabgarta, dan bata son wani abu ya sake haɗata da Daddy. Da sallama ta shiga falon, yana sanye da jallabiyya fara ƙal, hannunsa riƙe da remote. Ya amsa mata ba tare da ya waiwayo ya kalleta ba. Ta zo gabansa ta ajiye tea ɗin a kan center table. Ta juya zata tafi ta tsinkayi muryarsa yana faɗin "Sai yanzu kika ga damar zuwa?" Tsayawa tayi cak tana kallonsa, tayi masa shiru tana kallon gefe guda. "Zo nan" ya faɗa cikin command. Ta juyo ta dawo ta tsaya a gabansa tana kallon ƙasa. "Zaki saka kaina yayi ciwo, kin tsaya mini a ka kamar sa'anki" Ta nemi wuri a ƙasa ta zauna, tana cukuikuye hannunta a hijjabinta, kamar mara gaskiya. Ya ɗan kalleta ya kallia shayin ya ce "Haɗa mini tea" Ba musu ta matsa gaban teburin, ta fara haɗa tea, tana tunanin ina Hajiya Zainab take, a irin wannan lokacin da har Daddy ke samun damar keɓewa da ita? Zancen zucin da take, ya bata damar antaya sugar da yawa a cikin shayin. Sai da ta gama haɗa tea ɗin nan, sannan ya kalleta ya ce "Amma bani kika haɗawa ba ko?" Yayi Maganar yana tsareta da ido. Ta ɗago da sauri ta kalleshi. Ya ce "Eh mana, wannan kan ki kika haɗawa, wannan sukarin da kika zuba, idan na sha ai sai in rasa raina, kodayake dama haka kike so ko? Oya Sake haɗa mini wani ki shanye wannan da kika cika sugan" A raunane ta ce "Ni na ƙoshi" "Ai kuwa sai kin sha, haɗa mini wani" Haka ta sake haɗa masa wani, ba tare da ta zuba sugar sosai ba, ta ajiye masa. Ta tsaya jiran ya bata umarnin tafiya. "Ki ɗauki shayin nan ki shanye na ce" "Wallahi na ƙoshi" tayi maganar kamar za tayi kuka. "Sai fa kin sha" Amina tayi shiru tana mamakin wannan takura haka. Ya cigaba da shan shayinsa, kamar ya manta da ita a wurin, can har ta fidda ran zai magana ya ce "Meyasa na bada abu a baki, dan kin raina ni kika dawo mini da shi ko? Kuma kika daina gaisheni, gani ga ki idan muka haɗu, sai kiyi fuska ki ƙi gaisheni, meye dalili?" Tuni ƙwalla ta taru a idon Amina, ta ce "Bakomai" "Akwai ko mai, sai kin gayamini dalili, ko mu kwana a nan tare" Ɗan waro idanunta tayi, amma ba ta iya cewa komai ba. "Wallahi idan na rufe ƙofar falon nan da mukulli, sai kin kwana a falon nan, kuma kin San halin Zainab ni ba ƙwatar ki zan yi ba a wurinta" Cikin marairaicwa Amina ta ce "Dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban rainaka ba Daddy" "To menene idan ba raini ba" ya faɗa yana zuƙar tea hankalinsa kwance. "Ba kai ne ba" sai kuma tayi shiru, saboda kukan da ya ƙwace mata. Daddy ya ce "Ikon Allah, to gama kukan sai ki mini bayani, kafin ki gama ma na gama shan shayin nawa" Aikuwa Amina ta gyara zama, ta dinga kuka, sai da tayi mai isarta ba tare da Daddy ya ce tayi shiru ba, tana yi ta goge hawaye da hijjabinta. Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Kinga ga tissue nan, ki dinga goge hawayen da majinar da ke ƙoƙarin zubowa, kar ki mini ƙazanta ina cin Abinci" aikuwa sai ta ƙaro sautin kukan nata, jin ya jefeta da kalmar ƙazanta. Ya ce "Cigaba da ɗaga murya, Allah yasa ta jiyo ki, ta zo ta tarar da ke kin saka mijinta a gaba kina kallonsa" Ba shiri Amina ta fara ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Shi kuma ya dinga murmushin gefe ɗaya, yadda ba zata gani ba. Sai da ta gama kukan, sannan ya ce "Masha Allah, in kin gama ina jinki" "Ba kaine Kai mini gori ba, shi yasa na dawo maka da wayar ka" Dariya yayi ya ce "Subhanallah, Ohh ni Ahmad, to mai yasa kika daina gaishe ni" "Daina amsawa kayi, idan na gaisheka sai ka harareni" Sosai Alhaji Ahmad yayi dariya da jin abin da Aminar ta faɗa cike da wauta da ƙuruciya. "Ni Ahmad naga ta kaina, na yi miki gori nace me?" "Cewa kayi gidanka ba wurin tara maza bane, kuma ni Bakomai tsakanina da shi, ranar da ka ajiyeni a hanya ne, ya kawoni gida sai gaisawa da muke da shi shikenan" "Saboda na ce Kar ki sake kawo wani gidan nan shine kike jin haushina? Amina na fiki shekaru, hankali da kuma gwagwarmayar rayuwa, muddin kika haɗa karatunki da shirmen samarin zamanin nan, to ba zaki mayar da hankali ba, idan ki ka biyewa samarin zamani da soyayya karatunma sai ya gagareki, soyayya ba abin da ba ta sakawa. kuma ni idan kin gaisheni ba hararki nake ba, bana amsawa ne saboda ki fahimci kin mini laifi, ki bani haƙuri amma ki kayi mirsisi ashe ke nan fushi kike dani ne ko? Wace irin 'ya ce haka mai fushi da babanta har ta daina kula shi, ya bata abu ta mayar masa anya kuwa kina Baban da ni?" Amina tayi shiru ta sunkuyar da kai. "Shikenan, ni bari in sauko in baki haƙuri" Da sauri ta ce "A'a kayi haƙuri dan Allah kar ka bani haƙuri" "To tunda fushi kike, har da cewa na miki gori gara in bada haƙuri ai" "Kayi haƙuri dan Allah, bana fushi da kai" "To sai kuma me nayi miki?" "Kace mini ƙazama" ta faɗa har cikin ranta. "Yaushe kuma na ce miki ƙazama?" "Yanzu" ta faɗa tana tura baki. "Eh ai ƙazamar ce, kalli yadda kika ɓata hijjabinki da hawaye, kuma haka kike mana girki, kina mana ƙazanta, shi yasa Abincin yake daɗi ashe". "Mhmm ka daina ce mini ƙazama" "To ki daina goge hawaye da hijjabinki" Ya ɗan tsura mata ido, sannan ya ce "Jeki janyo drower can, wayarki na ciki, ki ɗauko ki haɗo mini da abin gwajin suga na" tamkar wata kurma haka ta tashi, taje ta ɗauko abin da ya sakata, ta dawo ta zauna, ya sauko daga kan kujerar ya zauna a kusa da ita, hakan ya sa ta sake takurewa. Ya fito da kayan gwajin, ya yi gwajin sugan nasa, ya kalleta ya ce "Kin gani sakamakon daina kula dani, suga na ya hau duk abin da kika ga dama, dafawa kike ki bani, suga na ya hau ya kai sha biyu da ɗigo uku" Ita dai ba tace masa komai ba, sai sunkuyar da kai, kamar mara gaskiya. A ranta ta ce 'Hakkin azababbiyar matarka ne ai bani ba, abin da aka ce in dafa ai shi zan dafa' Ya miƙa mata wayar ya ce "gata nan, lokaci lokaci, zan dinga karɓa ina dubawa" Ta Sanya hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode Allah ya saka da alkhairi, naga takalmi da jaka ma, Baba ya bani Allah ya ƙara buɗi" "Amin rigimammiya, mutanen nan ma da kika mini Maganana akan su an biya musu kuɗin shekara biyu, na bawa Maigidan fili ya gina kamar yadda kika nema" A gigice Amina ta kalleshi ta rasa me zata ce masa sai ta sake fashe masa da kuka. "Ke wai komai ma kuka kike masa, tashi ki tafi Allah ya bamu alheri" "Allah ya biyaka da Aljanna Daddy" Yayi murmushi ya ce 'Ameen, tare da ke da kika ankarar da ni nayi aikin alkhairi. To Yanzu mu shirya ko?" Yayi Maganar ƙasa-ƙasa. Ta ɗaga masa kai alamar eh. "Bana son ɗaga kai, amsa mini zaki" "Eh mun shirya" ta faɗa cikin jin kunyar abin da tayi. "To shikenan, tashi muje in rakaki bakin ƙofa" ta miƙe tsaye hannunta riƙe da kwalin wayarta. "Kun koma makaranta yau ko?" Tace "Eh Daddy. kayi magana da Baban kuwa a kan tafiyar?" "Kar ki damu, zamu yi maganar in sha Allah, ke dai ki cigaba da karatu" "Ina nan ina yi, ka dinga yi mini addu'a" "Sai kin biya tukuna, kawo abin sadaka, ai miki Adduar" dariya Amina tayi ta ce "Zan kawo, idan kai mini addu'ar na ci" "To shikenan, kije ki duba wayar, abin da baki gane a ciki ba, sai ki mini magana" "To Daddy na gode" ta juya ta fice, Daddy ya tsaya yana binta da kallo, harta ɓacewa ganinsa, sannan ya koma ciki, yana shafa gemunsa. Hajar kuwa tun da Amina ta tafi wurin Daddy take yi tana leƙa falo zuwa kitchen, dan taga dawowar Amina, amma shiru babu Amina babu dalilinta, ji take tamkar ta zama tururuwa ta rarrafa taje ɗakin Alhaji Ahmad, ta gano meke faruwa Amina ta zauna haka? Tun tana zuba ido taga dawowar Amina har ta gaji, ta tafi ɗakinta ta zauna tayi shiru tana tunani, tashi ta kuma yi ta leƙa ɗakin Amina, ta tarar da ita a tsakiyar katfarta tana kunna sabuwar waya. "Amina ashe kin dawo, naga kin daɗe daga kai shayi, ki kayi wannan zaman?" "Kai Hajara, ban gane me kike nufi ba, da na kai masa shayin fa suna tare da Hajiya, na ajiye musu na tafi baranda na cigaba da karatuna, me zai zaunar da ni kuma?" Sai kuma cikin borin kunya Hajara ta ce "Au, na zata wani laifin ki kayi ai, duk hankalina ya tashi, wannan sabuwar wayar fa" Amina ji tayi kamar ta zagi Hajara, amma idan ba ta bi Hajara a sannu ba, zata sanya kwaɓarta tayi ruwa, dan haka ta ce "A makaranta ne aka bamu, saboda mu dinga amfani da ita wurin karatu" "Allah sarki, lallai wannan makaranta taku ana ji daku, lallai da safe na shigo a bani in gani" Amina tayi murmushin yaƙe, ta cigaba da kunna wayarta, bayan Hajara ta fita Amina ta raka bayanta da harara, cike da jin haushin saka idon da take mata. Hafsa na cikin bargo ta ƙule, ta saka wayarta a silent, tare da rage mata haske, suna chatting da Khalil, sai su daɗe suna chatting basu san dare ya yi ba, ita kanta tana mamakin kanta yadda ta yi wani irin sabo da Khalil, wanda har ya kai idan Khalil baya son abu, har rawar jiki take ta daina, duk abin da ta san zata yi yayi farin ciki tana masa. Haka shima ɓangaren sa tattalata yake tamkar ɗanyen ƙwai a kan dutse, shima yana kaucewa duk wani abu da zai sanya ta ɓacin rai ko damuwa, yana matuƙar tausayinta, hakan ya sanya yake tattalinta yake gudun abin da zai ɓata mata rai ko tayi fushi. A Hanyar Yazid ta tahowa makaranta, suka haɗu da class Captain ɗinsu, ya ɗauko Yazid a babur ɗinsa, suna tafe yana bashi labarin faɗan da Amra da Fadila suka kusa yi jiya, a kan abin da Amran tayi masa. Yazid dai bece komai ba, sai ɗan murmushi da yayi, Captain ya cigaba da bashi haƙuri, a kan irin abubuwan da wasu daga cikin 'yan ajin suke masa. Zuwansu yayi dai-dai da tsayuwar motar Fadila. "Ahh Yazid ga Bestynka nan ta ƙaraso" "Wace kuma Besty na?" Yazid yayi maganar cikin ko in kula. "Fadila mana" Ta rufe motar ta ɗan tsaya tana jiran ƙarasowarsu. "Captain" ta faɗa tana ɗan murmushi. Captain ya ce "Na'am tsigai, sarkin tsiwa" "Kaga ka kiyayeni bana so" Yazid yaƙi ko kallon in da Fadila take. Ya yin da ita kuma take satar kallonsa, Captain ya ce "Bari in yi gaba ku gama ganawa, dama zan karɓo mana Assignment, sai kun taho" yayi gaba ya bar su a tsaye. Captain na barin wurin, Yazid shima ya yi tafiyarsa ya barta a wurin, gaba ɗaya sai taji babu daɗi shareta da ya yi, ko dai Kankiya ya kira shi ya yi masa warning ne a kanta, shi ya sanya ya daina kulata?. Ɗan taɓe baki tayi, ita ma ta nufi aji tana cigaba da zancen zuci. Sai yau Azima ta dawo daga hutu, suka rungume juna ita da Amina suna ta murna. "Azima shi ne kika ƙi dawowa sai yau?" "Ke bari, munje hutu da Mummy ne, sai jiya muka dawo" Amina ta ce "Masha Allah, ya Mummyn?" "Mummy na nan lafiya, ya Baba da mutanen gidanku marasa mutunci" Amina ta ɗan ɓata fuska ta ce "Meye haka?" "Ba dole in faɗa ba, mutuncin ne da su? Wallahi matar nan ta bani mamaki Amina, a gaskiya kina haƙuri sosai, Allah ya ƙara miki haƙuri" "To Azima idan ban yi haƙuri ba yaya zan yi? Tun da karatu nake son nayi" "Ke zan yiwa Mummy magana, wallahi da zaki yadda ki dawo gidanmu, ki daina wannan aikin, Mummy zata dinga biya miki kuɗin makaranta, meye dubu sittin Allah na tuba, Mummy zata biya miki" Waro ido Amina tayi ta ce "Azima dubu sittin kuma? Dubu sittin ne kuɗin makarantar?" "Au ke da baki sani ba? Dubu sittin ne fa kawai duk term, sai sauran abin da ba a rasa ba, Mummy tana da kuɗi sosai, ga shi Daddynmu ya mutu ya bar mana kuɗi, ni da Yaya Sagir da nake gaya miki, wallahi da zaki yadda Mummy cewa tayi zata ɗauke ki ki dawo gidanmu, ita tana sonki" Shiru Amina tayi tana tunani, Yanzu duk term naira dubu sittin Alhaji Ahmad yake biya mata na makaranta, kuma gashi ance na shekara ya biya mata, ga kuɗin litattafai da sauransu. "Ya naji kin yi shiru? Zaki yadda ki dawo gidanmu?" Firgigit Amina ta dawo daga tunanin da ta tafi, ta ce "Azima Baba ba zai yarda in nisa da shi ba, nima ba zan so hakan ba, amma naji daɗi da ƙauna da karamcin da Mummy take nuna mini, shi wannan aikin da nake na lokaci ne, watarana sai labari. Kuma in Allah ya kaimu next year fa zamu gama, da an gama wannan competition ɗin fa za'a fara yi mana lesson ɗin Jamb da na Waec da Neco, Kinga lokaci kaɗan ya rage mana". "Haka ne Amina, Allah yasa mu gama lafiya" "Ameen" Amina ta amsa. Har aka tashi Yazid bai yi gigin zuwa in da Fadila take ba, gaba ɗaya sai taji babu daɗi, dan a 'yan kwanakin ta saba da shi da nacinsa, ba tare da ta shirya hakan ba. Hajiya Zainab ta sha mamakin yadda Khalil ya iya daina shigowa cikin gidan, ko gaisheta yayi balle ya ci Abinci, duk dan saboda ta raba shi da wata 'yar matsiyata. Dan haka a fusace yau ta tafi ɗakin nasa, ta tarar yana zaune yana dannan system, walpaper system ɗn, hoton hannunsa da na Hafsa ne sanye da zobunan da ya saya musu. "Sannu mara mutunci salamamme" A razane ya ɗago ya kalli Mummy. "Yanzu Khalil wuyanka har ya yi kaurin da dan nayi maka faɗa na hanaka kula wata matsiyaciyar yarinya zaka daina shiga harkata, ka daina shigowa cin abinci?". "Mummy ba haka bane kaw .... "Yi mini shiru, gaba kake da ni ko Khalil, ka kyauta ka cigaba kar ka fasa, wannan yarinyar ce dai ko, to na rabaka da ita har Abada. Idan kuma ka ƙi ji, ba zaka ƙi gania ba. Ta juya ta fice tana huci, ba ta jin zata iya yiwa Khalil sassauci a kan al'amarin nan sam. Khalil ya dafe kansa da yayi masa wani irin nauyi, da har yake barazanar yi masa ciwo, ya rasa Wannan wace irin ƙiyayya ce haka Mummy take yiwa talaka, meye aibun Hafsa banda talauci, kuma ai komai na Allah ne. Washegari ma a school, Yazid ya ƙi kula Fadil, ya cigaba da sabgoginsa, sun yi lectures na farko, sun samu break, Fadila ta kasa jurewa, ta tsinci kanta da tafiya wurin da yake a zaune, a can ƙarshen ajin. "Ustaz wurinka na zo" Ya ɗago ya kalleta "Waye kuma Ustaz?" "Kai mana" "Baki san suna na bane?" "Eh sunan naka ne bana riƙewa" Yazid ya gane ba zata iya kiranshi da sunansa bane a gabansa, amma dan rainin hankali ba zata faɗa ba. "Magana fa nake maka" "Ba fa kurma ne ni ba, ina jinki" "To ba zaka amsa ba" "Ki faɗi sunana mana idan so kike in kulaki" yayi maganar ba tare da ya kalli in da take ba. Share maganar tayi ta ce "Abu nake son ka koya mini dan Allah" "Ba zan koya ba" ya bata amsa direct. Ji tayi kamar ba taji daidai ba, dan haka ta ce "Me kace?" Ya waiwayo ya kalleta ya tsuke fuska ya ce "Ba zan koya ba nace, idan kin koyi faɗan sunana sai in koya miki" Nan da nan ya ga ɓacin rai ya bayyana a fuskarta, kawai ta juya ta bar wurin, ranat yana mata suya, 'laifina ne da nuna na damu da kai, shi yasa har ka yi mini wulaƙanci' ta faɗa a zuciyarta. Tana bada baya Yazid ya fara dariya ya furta "Yarinya ba wayo" yana ankare da ita har suka kammala lectures na biyu, sai cika take tana batsewa, taji zafin abin da ya yi mata sosai. Sai da ya daidaici lokacin da yafi sakata a kwana, ya hautsina mata lissafi, ya dawo daga salla, lokacin da ɗalibai suka ragu daga ajin, wasu suka tafi salla wasu cin abinci, ya lura ko sallar babu alamar ta je, ta Kwantar da kanta a kan benci. "Bestyna, what are you thinking about? Tashi muyi karatun ɗauko littafin muyi karatun" Sarai ta gane muryarsa, amma tayi masa banza, taƙi ɗagowa. "Common, ɗago mana" yayi maganar yana zama a kusa da ita. Da sauri ta tashi zaune, ta kuma matsawa ciki, tana haɗe rai. "Ɗauko littafin muyi karatun" "Kaga malam ka ƙyaleni bana so" ta faɗa tana jin kamar a lokacin ya ce ba zai koya mata ba. "Haba Ukty, kefa kika fara wasan nan, kika ce idan ina da zuciya kar in sake kula ki, kuma ina da zuciya a ƙirjina, tana aiki kuma, kawo hannunki ki taɓa kiji" yayi maganar kamar zai riƙo hannunta. "Wai meye haka ne, kar ka sake ka taɓa ni" "Ashe kina tsoro, kawo muyi lesson ɗin kin ji Bestyna" "Bana so, na gaya maka ka ƙyaleni zan maka rashin mutunci wallahi" "To ni rashin mutunci wanne ne baki yi mini ba, duk haddace in kin mini ba haushi nake ji ba, ni ɗanawa nayi yau, amma ki yi haƙuri muyi da wasa nake miki" Ɗauke kanta tayi, tana kallon gefe guda, irin yayi idan ya gaji ya tashi. "Baƙin gashi, fararen idanuwa, dogon hanci, bakin tsiwa, matsakaicin tsayi, fa tubarakallahu ahsanul khaliƙin, You Are beautiful" murguɗa baki tayi tana kuma ɗauke kai. "Shikenan, idan kin sakko kya kulani, ni na tafi gida, saurayinki ne zai shigo lectures yanzu, gara in fita in tafi, tun kan ya shigo ya dizgani a gaban mutane saboda ke". "Kar ka sake cewa saurayina, na gaya maka" "Saurayinki ne mana, idan ba saboda ke ba me nayi masa ya tsaneni, bai san ba wata alaƙace ta kirki tsakanina da ke ba, ki mini tsiwa lokacin da kike so, ki lallaɓani idan kina buƙatar wani abu a wurina, ko ba haka ba ne?" "Kai ka sani" "Dama ni na sani mana, ki kalli idona ki maimaita abin da kika faɗa in ba tsoro ba" Sake kifa kanta tayi, tai masa shiru, tana jinsa ya ɗau biro, yana mata rubutu a jikin hannunta, taƙi ko motsi, sai da taji alamar ya tashi ya tafi, sannan ta ɗaga hannun ta duba, da larabci ya yi mata rubutu, sai dai ba ta gane meya rubuta ɗin ba. Ɗaga kai tayi taga har ya kai ƙofa, a ranta ta ce 'A haka kamar baya magana, amma ya iya wulaƙancj kala-kala'. Khalil ya rasa yadda zai yi da ransa, gashi ya cinye satinsa biyu, amma babu wani daidaito a tsakaninsa da Mummy, balle ya sanya ran zata fahimce shi. Kusan ƙarfe goma na dare, yana kwance a kan gado, ya rungume pillow, yana ta zuba soyayya a waya shi da Hafsa. "Baby, ina ga haryanzu Abincin da kika mini, bai gama narkewa a cikina ba, har yanzu bana jin yunwa" "Ni dai ban yadda ba, idan ulcer ta kama mini kai, sai mun yi faɗa" "Allah Hafsa bana son cin abinci, ga kewar ki ta isheni zan koma wurin aiki" Ta Kwantar da muryarta ta ce "Eyya, ai ba komai, ka kwantar da hankalinka, zamu dinga waya". "Ai ni nafi sonki a kusa da ni Babyna, ginin gidanki ya kusa kammala insha Allah, idan na je zan ɗauko miki video ki gani, idan da abin da bai miki ba sai a sauya" Hafsa ta ce "Wace ni in ce ga abin da bai mini ba, komai kai daidai ne, Allah ya yassare maka halal, ya tabattar mana da alkhairi" "Ameen my sweet, yadda gari yake da sanyin nan, ace kina kusa da ni, kin dafa mana tea, ina sha ina kallonki cike da so da ƙauna" Tayi dariya ta ce "Abin da ka hango kenan?" "Eh mana, da mun yi aure ba ruwaa da bargo, kin isheni" Ta ɗan tura baki ta ce "Zaka fara ko? To sai da safe" ya buɗe baki zai yi dariya, yayi tozali da Mummy a tsaye a kansa, wadda ganin bai shigo cin abincin dare ba, duk da faɗan da tayi masa ya sanya ta biyo shi ɗakinsa, ta zo ta tarar da shi yana waya da Hafsa. Mugun kallon da ke masa ne ya sanya shi, rikicewa ya katse wayar yana kallonta" AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM AYSHERCOOL PAGE36 Cikin rikicewa da inda-inda Khalil ya ce "Mu..mmm...Mummy dan Allah ki tsaya ki ji" "Me zan tsaya in ji banda wanda na ji Khalil, ai naji komai ka saurari matakin da ni kuma zan ɗauka". "Innalillahi, Mummy dan Allah kar ki yiwa Hafsa komai, marainiya ce" "Eh marainiya ce, kai ne baitul mali ai, kai ne mai arziƙin ɗaukar nauyinta a ɗora maka wahala, kana nan kana gina mata gida ko? Sai ta shiga in gani, kaje ta dafa abu tayi barbaɗe barbaɗe ta baka kaci, zaka gamu dani" ta fice fuuu ta bar ɗakin. A sukwane Khalil ya bita, yana kiran sunanta. Ya cinmata a falo. "Mummy dan Allah kar a yiwa Hafsa wani abu, ni ki hukuntani, ba zata iya ɗaukar hukuncin da zaki mata ba" "Rufen baki Khalil, ni zaka mayar ƙaramar yarinya, wato har Asirin da suka yi maka ya fara tasiri a kanka ko? Matsa ka bani wuri kan in make ka" Ya haɗa hannayensa biyu cikin magiya ya ce "Dan Allah Mummy ko sau ɗaya ki saurareni, wallahi mun shaƙu Hafsa bata da wani aibu, dan Allah ko sau ɗaya ki saurareni" Shareshi tayi ta wuce ɗakinta, Khalil ya zauna a kan kujera ya dafe kansa, wani irin gumi ya tsatsafo masa a goshi, duk da a yanayi ake na sanyi. Amina da ke gefe tana kallon Tv tayi shiru, jikinta yayi sanyi tamkar ita ake yiwa faɗan, gaba ɗaya taji babu daɗi, Saboda Hajiya Zainab ta iya tijara. Ita Amina abin har mamaki ya bata, ɗanta ma ba ta ƙyaleshi ba, duk dan ya ce yana son 'yar talaka ake wannan dambarwar bala'in. Jiki a saɓule Khalil ya miƙe, ya bar falon yana tunanin meye mafita, bai taɓa yiwa Mummy turjiya a kan wani abu ba, amma a wannan karon zuciyarsa na raya masa ya tirje, tun da Aurensa da Hafsa bai saɓawa Addini da kuma Al'ada ba, gani yake idan ya fasa aurenta bai mata adalci ba, kuma bai san wani irin hali zata shiga ba kuma bai san hannun wa zata faɗa ba, babban abin daya ƙara tsaya masa shi ne, bai wataƙila idan ya rabu da ita halin da zata shiga na damuwa ya fi na baya, tun da dama shigarsa rayuwarta ne ya bata ƙwarin gwiwa sakewa da rage mata damuwar da take ciki. Washegari Daddy ya fito falo, ya tarar da Amina a zaune, tana jiran lokaci ya cika ta tafi makaranta "Ina kwana" Amina ta gaishe shi. "Lafiya ƙalau, yau ban hararekin ba ko?" Murmushi tayi tana sake janyo jakarta jikinta. "Har kin shirya tafiya makarantar?" "Eh jira nake lokaci ya cika" "Ok, school ɗin ku sunyi mini waya, a first term za a yi muku registration ɗin Jamb da SSCE ko?" Amina ta ce "Eh haka suka ce mana" "To ki ƙara dagewa, idan result ɗinki yayi kyau, hope baki manta da sirrinmu ba ko?" Cikin murmushi Amina ta ce "Eh, ban manta ba, zan yi karatu sosai in sha Allah" Daddy ya ce "Good girl" hakan yayi daidai da fitowar Fadila, cikin shirin tafiya makaranta. Ba ta kawo komai a ranta ba, ta zauna, ta zuba Abinci ta fara ci. "Ina Mummynku ne?" Daddy ya tambayi Fadila. "Bacci take, ta ce kar wanda ya dameta" "Ok, nima fita zan yi yanzu". "To Daddy a dawo lafiya" Fadila ta faɗa tana shan tea. Da ido ya yiwa Amina alamar, ta biyo bayansa. Amina ta miƙe ta saɓa jakarta, tabi bayan Daddy. Sai da suka fito daga falon, sannan ya tsaya Amina ta ƙarasa in da yake, ya dubeta ya ce "Muje in ajiye ki a School ɗin, sai in wuce in da zani" Amina ta ce "Amma Ba wani wurin zaka ba? Kar ka makara fa, zan hau Napep" Yadda ya tsareta da ido ne, ya ɗan tsuke fuska ya sanya ta yin shiru, yayi gaba ta cigaba da bin bayansa. "To bari in je in gaida Baba" "Ki sauri" ya faɗa tare da nufar in da motocinsa suke. Amina ta isa wurin Baba, ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi. "Lafiya ƙalau Uwata, kin tashi lafiya?" "Lafiya ƙalau Baba, ya aikin" "Alhamdilillah, zaki tafin ne?" Amina ta ce "Eh, amma wai ya ce zai ajiyeni a makarantar" Cikin rashin fahimta Baba ya ce "Shi wa?" "Baban su Fadila" Baba ya ɗan yi shiru, saboda ya lura a 'yan kwanakin nan akwai wani ɓoyayyen abu tsakanin Alhaji Ahmad da Amina, yanzu bata tsoronsa kwata-kwata, ga wata shaƙuwa a tsakanin su. Ga yawan kyautata mata da yake yi, ya yita sayen abubuwa yana bawa Baban ya bata, tuna miyagun fatan da su Bala suka dinga yi a lokacin da ya sanar da su Amina zata taho birni karatu. Kan Baba ya ce komai, Alhaji Ahmad ya ƙaraso in da Baba yake da mota, ya sauke glashin motar, Baba ya taso da sauri, suka gaisa da Alhaji Ahmad. Ya ce "Zan sauke Amina a makaranta sannan in wuce" Baba yana matuƙar jin nauyin Alhaji Ahmad, mussaman duba da irin alfarmar da Ya yi masa a kan Amina, haka ya danne ya ce "To shikenan babu laifi, Allah ya saka maka da alkhairi" "Ahh kar ka damu babu komai". Amina ta zaga ta shiga mota, Daddy ya ja motar suka bar gidan. "Daddy a kashe Ac nan sanyi fa" Amina ta faɗa tana duunƙule jikinta saboda sanyi. Kwaikwayon muryarta ya yi ya ce "Ba za a kashe ba zafi nake ji" A ɗan shagwaɓe ta ce "Allah sanyi nake ji, mura zan yi idan baka kashe ba" "Mayar da ita ɗumi, ai kina kusa da wurin" yayi maganar yana mayar da hankali a kan tuƙinsa. Ta ce "Ai ban iya ba" "Ohh Ashe fa 'yar ƙauye ce" Ta ɗan zumɓura baki, tana kallonsa ta gefen ido. Miƙa hannunsa ya yi, ya canza zuwa ɗumi, tamkar zai taɓata, hakan yasa ta takure jikinta har da ɗan rintse ido. Yayi murmushi kawai sannan ya ce "Kin gane kan wayar taki kuwa?" "Eh na gane, wayar tana da kyau sosai, ga Camera mai kyau, duk nasa lambar ƙawayena da ta Baba a ciki, har what's app aka buɗe mini" "Waye ya buɗe miki?" ' "Ƙawata Azima" "Kar ki sake zuwa da wayar makaranta, kuma ban yadda ki saka lambar wani namiji a ciki ba" Ta ce "Dama sau ɗaya naje da ita makarantar, ba zan sake ba, amma har lambar mazan ajinmu ma ba zan saka ba? Kuma an sani a wani group fa na makarantarmu gaba ɗaya". Daddy ya ce "To daga haka kar a ƙara, idan ba haka ba what's app ɗin ma zan hana" "Tom na gode sosai, zan kiyaye in sha Allah" "Kin sa lambar ƙawaye Amma kika kasa ko yi mini flashing a wayar taki, ko kuma da safe ki gaisheni a wayar, bayan har kuɗi na saka a layin, kuma da lambata a ciki" Amina ta zaro ido ta ce "Haka kurum, in kiraka ta ɗaga in ce mata me?" "Ita wa?" "Au, ba kowa" "Saifa kin faɗa, ita wa?" "A'a, haka kurum in faɗa in je ka ajiye ni, a titi" Kawai yayi dariya ya cigaba da tuƙi. A ƙofar makarantar ya ajiye ta, ya ce "In an tashi zan turo a ɗauko mini ke, ko in zo da kaina" Amina ta kalleshi ta ce "A ɗauko ni a kaini ina? Ina da kuɗin mota fa" Ya haɗe rai ya ce "Haka nace" "To Allah ya baka haƙuri, Allah ya kaimu a tashin" ta ƙarasa maganar tare da buɗe motar ta fice. Ƙarfe goma da rabi ma safe, sannan Mummy ta tashi daga bacci, tayi wanka ta karya, ta cigaba da tunanin ta ina zata ɓullowa lamarin Khalil, yadda zata rabashi da yarinyar nan. What's app ɗinta ta buɗe, ta duba group ɗin su, da suke ita da Hajiya Salma da Turai, tayi sallama. Cikin ikon Allah duk suna online, suka amsa mata, suka gagaisa tare da tambayar junansu yara da kasuwanci, Mummy ta tura musu saƙon Voice message. "Jama'a ku bani shawara yadda zan ɓullowa lamarin yaron nan, haryanzu fa yaƙi rabuwa da ita, jiya har naje ɗakinsa na tsaya a kansa yana waya da ita, bai san na zo ba, har gaya mata yake, wai zai yi mata video na gidanta na Abuja". Nan da Nan Hajiya Salma ta haɗa group Video call, "Lallai ma Zainab, to wani matakin kika ɗauka?" "Zage shi nayi tsaf, amma banga alamar zai saduda ba, bina yake kuma yi, wai zai yi mini bayani, na rasa mema yakamata in yi" Turai ta ce "Ke, ta bayan gida zaki ɓullowa lamarin, Khalil dai ɗanmu ne, ba zaki cigaba da zuba masa ido ba a mallake miki shi a banza ba" Mummy ta tari numfashinta ta hanyar cewa "Kamar kin san har da maganar tayi masa girki ya ci naji, gaba ɗaya jiya da ƙyar nayi bacci wallahi" Hajiya Salma ta ce "Kut kinga Zainab bamu ga ta zama ba, ba mun san in da yarinyar take ba, ai mu muka ganota a hanyar zuwa plaza, zuwa za muyi mu kasa mata warning, ko nemi gidansu muje har gidan nasu mu samu uwarta, mu musu wankin babban bargo, idan suna da zuciya zasu rabu da shi, kinga ko ya ƙi Allah ya haƙura" Mummy ta ce "Amma kamar ƙasƙanci ne, mu wanke ƙafa mu tafi gidan talakawa yawon yi musu warning, gaskiya Khalil ya gama da ni, wai 'yar masu awara a kan kwalta, wannan yaro duk matan garin nan" Hajiya Salma ta ce "Meye wani ƙasƙanci, biyan buƙata ai yafi dogon buri, da su mallake shi fa, da munyi nasarar raba su, ki nemo masa mata ya aura" Mummy ta ce "Haka za ayi, bari ƙarfe huɗu bayan sallar la'asar, mu haɗu ku rakani muje" Turai ya ce "Allah ya kaimu yammar" suka amsa da Amin. Ganin yau ƙarfe goma babu malamin da ya shigo, ya sanya Fadila tafiya Library, dan Captain ya sanar da cewa malamin ba zai samu shigowa ba, kuma ga exams na gabatowa. Ta nutsu sosai ta mayar da hankalinta kan littafin da ke gabanta, ba zato ba tsammani taji an ja kujerar da take ta baya, kamar zata faɗi, a razane ta ƙwala wani marayan ihu, saboda ta tsorata sosai da sosai. Sai da hankalin wasu daga cikin tsirarun ɗaliban da ke cikin libraryn ya dawo kansu, bai saki kujerar ba, ya leƙo fuskarta ta sama yana kallonta yana murmushi. Ta marairaice kamar zata yi kuka ta ce "Dan Allah ka sauke kujerar nan kar in faɗi" "Ba zan bari ki faɗo ba ai". "Dan Allah ka ajiye kujerar, bana so" "Haka kike shagwaɓaɓiya, faɗi sunana sai in saki kujerar" "Dan Allah ka bari, zan faɗo fa" Sake matso da fuskarsa yayi saitin tata ya ce "Sai kin ce Yazid tukuna" "To ajiyeni sai in faɗa" "Ni zaki yiwa wayo yarinya, faɗi ko in kai ki ƙasa a kan kujerar" yayi maganar yana sake jan kujerar baya. "Wayyo Allah Daddy, Yazid na faɗa ka ajiyeni dan Allah" "Wow, sake maimaitawa in ji" "Dan Allah ka bari" tayi maganar tana rirriƙe hannunsa, jin yadda yake kuma baya da kujerar. "Kar ki saka mutane su juyo suna kallonmu, ke zasu gane ni na da mask a fuskata, sake faɗa" A hankali ta ce "Ai na faɗa" "Ki ka ce me?" "Yazid" "To daga yau, kar ki sake zuwa ki tsaya a kaina, cikin tsiwa kina wani cewa Ustaz" "To naji, ajiye ni" Zuba mata ido yayi, yana kallon bakinta, yadda take motsashi a hankali cikin tsoro. A hankali ya mayar da kujerar yadda take. Dafe ƙirji tayi tana sauke ajiyar zuciya, saboda yadda ta tsorata. Kujerar gabanta ya ja ya zauna, yana kashe mata ido. Wata uwar harara ta watsa masa. "Da kika samu na saukeki shine ki ke hararata ko" wata harar ta kuma watsa masa tana ta sauke ajiyar zuciya. Jan littafin gabata yayi ya ce "Kawo mu gani, me kike karantawa" Janye littafin tayi ta ce "Ina ruwanka da abin da nake karantawa". "Hmm babu ruwana, me kika ce zan koya miki jiya?" Cikin tsiwa ta ce "Ai na ce maka na fasa, bana son koyarwar taka" "Aikuwa karki nuna kin sanni a exam hall" Hararsa tayi ta saka takalmanta zata tashi. Ya ce "Haba Besty, zauna muyi karatun mana, tun da kika shigo school ɗin nan nake biye da ke, kika je wurin Yusra, ki ka koma Aji, sannan ki taho nan" "Wallahi ka takura mini" Yazid yayi murmushi ya ce "To ya zan yi tun da bani da abokai, ana abota da ni ne saboda abin a za a mora wurina na karatu, ni kuma nafi son ayi abota da ni saboda Allah" "To ni ina ruwana da wannan bayanan naka?" Ɗan tsura mata idanu yayi yana nazartar yanayinta, a hankali ya furta "Happy birthday in advance" Waro idanunta tayi tana kallonsa, "Waye ya gaya maka birthday na?" Murmushi ya yi ya ce "Password ɗinki na System da kika saka na gane date of birth ɗinki, gobe in Allah ya kaimu shekarunki Ashirin da biyu, Happy birthday 'yar yarinya". Fadila ta ce "Allah ya hore maka saka ido, da bin ƙwaƙwƙwafi, kai dama ɗan sanda ka zama" Yayi murmushi ya ciro leda a aljihunsa, cikin fargaba ya miƙa mata. "Meye wannan?" A ɗan sanyaye ya ce "Karɓi ki gani, sai dai ban sani ba, ko kina karɓar abin da ya fito daga hannun talaka kamar ni ba, first gift as a brother, and at the same time friend" Ɗan taɓe baki tayi, ta karɓi ledar ta buɗe, ta fara ciro abin da yake ciki, turaren lailatul sahara da Bushra, da kuma wani abun hannu da zobensa, da gani dai ba mai tsada bane, amma taji kyautar ta kama zuciyarta. Ɗan murmushi ta yi ta ce "Kai ka mini kyauta ta farko wannan birthday, na gode sosai" "Da gaske Kin karɓi kyautar da nayi miki?x yayi Maganar da mamaki, dan bai taɓa zaton zata karɓa ba. Tayi murmushi ta ce "Gashi kuwa kana gani" ta ɓalle abin hannun ta saka, ta zura zoben. Ta ce "Na karɓi abin hannun Ustazu" tayi maganar tana dariya, tana kallon hannunta. Yazid yayi mata ƙuri da ido, yana kallon yadda take murmushi, da yake matuƙar burge shi, sai dai ya san cewa abu ne mawuyaci idan ya bayyana mata haƙiƙanin abin da yake zuciyarsa ta yarda da shi ba. Yanzun ma ya aka cika, shirin nasu baya ɗaukan lokaci, suke ɓatawa. "Ya ka zuba mini ido ne?" Ta miƙa masa greeting card ɗin da yake cikin ledar, wanda rubutun larabci ne a jiki ta ce "Fassara mini wannan" Ya kalleta ya ce 'Ki karanta mana" "Amma dai ka san ban iya ba" "Birthday wishes ne kawai" ta ce ok Ta jujjuya katin tana kallon adon da ke jikins, ta ɗago ido, taga yadda ya ƙureta da ido. "Wai kallon me kake mini ne? "Ba komai, lokacin salla yayi, muje muyi salla" ta jinjina kai ta miƙe, ta ɗau jakarta, da ledar da ya bata suka fita daga libraryn. Da yamma Fadila ta dawo gida, tana dawowa ta shiga falo ta watsar da jakarta a falo kamar yadda ta saba, ta shilla ɗakinta da gudu, saboda fitsarin da ya matseta. Daidai lokacin Mummy ta fito cikin shiri, zata je ta ɗauki su Hajiya Turai. Jakar Fadila da ta gani yashe a tsakar ɗakin ne ya sanya ta gane Fadilan ta dawo gida. Miƙa hannu tayi zata ɗaukewa Fadilan jakarta, taga leda a ƙasa. Ta ɗau ledar ta buɗe, sai taga turare guda biyu da kati a ciki. Sansana turaren tayi tana yamutsa fuska, tamkar wadda ta shaƙi warin bola. Fadila ta fito daga ɗakinta, dan zuwa ɗakin Mummy, amma taga Mummyn tsaye hannunta riƙe da ledar da Yazid ya bata. "Mummy fita zaki ne?" "Eh fita zan yi, me kike da wannan a jakarki?" Ta nunawa Fadila turarukan tana yatsune hanci. "Bani aka yi" Fadila ta bata amsa. "Waye ya baki wannan tarkacen, turare kamar na 'yan bori" Fadila ta miƙa hannu ta karɓa tare da faɗin "Wallahi turarukan da ƙamshi, wani ne ya bani" "Waye wani?" "Wani ɗan ajinmu ne?" "Meye haɗinki da shi da zai baki wannan tarkacen ki karɓa?" "Bani da wani haɗi da shi, muna mutunci ne kawai, and i can't reject it, ba zai ji daɗi ba, kuma bani kaɗai ya bawa ba" "Shikenan, kar dai ki sake ki shafa wannan turarukan ki shiga jama'a, kowa yaji wannan turaren ya san mai arha ne, wani wari suke kamar na ciyawa, ni zan ɗan fita zan je wata unguwa" "Ok Mummy, safe journey" "Thank you" ta amsata ta fice. Alhaji Ahmad bai tura ɗan aike ba, shi da kansa ya je makarantar ya ɗauko Amina, suna tafe suna hira, ya ajiyeta a ƙofar gida ya shiga da motar ciki, dan ko Baba bai san tare suka dawo ba. Gaba ɗaya hankalin Hafsa yana kan mutanen da take sallama, tana yi tana iza wutar awararta. Wata danƙareriyar mota ce ƙirar Highlander tayi parking a gefen inda Hafsa take. Sam hankalinta baya kan abin da yake wakana wajen abin da yake gabanta. "Ke!" Taji an yi shouting a kanta. Cikin ɗabi'arta ta ta miskilanci, ko ɗaga kanta ba ta yi ba, ta cigaba da sallamar mutane, dan ba ta kawo ma da ita ake ba, saboda yanayin yadda aka yi maganar cikin isa da gadara. "Ke da ke nake magana, nayi magana kika mini banaza" Jin an dunguri kanta ne ya sanya ta ɗaga kai, ta kalli Hajiya Turai dak zazzaro mata ido, amma ba ta ce uffan ba. "Wai ba da ke nake ba? Ko bayan talauci kuma naksashiya ce ba kya ji ne?" Cewar Hajiya Salma. Kamar ba za tayi Magana ba kuma sai ta ce "Me nayi miki ne?" Tayi maganar cikin rauni. "Uwarki ki ka yi mini? Ina magana kina jina dan iskanci kika shareni?" "Uwata ta gode" Hafsa ta sunkuyar da kai, tana fifita wuta. Saboda rashin girma, da iya duniyanci, Hajiya Turai ta saka ƙafa tayi fatali da awarar da Hafsa ta riga ta tsame, ta kuma yi ball da wadda take cikin bokiti tana soyawa. A gigice Hafsa ta miƙe tsaye ta kallesu "Baiwar lafiya,me nayi miki zaki zo wurin san'ata kina watsar mini da kaya? Ni ban sanku ba ban taɓa ganinku ba balle in ce ko wani laifin nayi muku" Hajiya Turai ta ce "Ashe ƙaramar fitsararriya ce, yanzu da na zubar da wannan tsiyar, ai gashi kin bani dukkan hankalinki, dana ɓarar da tsiyar da kuka dogara da ita, ba kece Hafsa ba? Kin samu yaro kin asirce shi, yana muku bauta, 'yar matsiyata ce, ni na zata ma wata haɗaɗiyar yarinya zan gani, kalleki kalli kayan kayan jikinki, Khalil ya miki kama da sa'an Aurenki?" Sai yanzu Hafsa ta gane ina suka dosa, kuma a kan me suke mata wannan tijarar, da tuni mutane suka fara taruwa suna kallon abin da ke faruwa. Hajiya Salma ta kalli Hafsa a wulaƙance ta ce "Ɗanmu ba tsarar aurenki bane, ki duba cikin kwararon matalauciyar unguwarku, ba zaki rasa Irinki ki aura ba, ko kuma 'ya'yan kwalta lalatattu irinki, da babu yarinyar kirkin da zata zo bakin titi tana kasa kaya, tana cakuɗeɗeniya da maza, ka ce ta kirki ce, ki nemi irinki daidai ke ki aura, Khalil ba sa'an yinki bane" Turai ta kalli wasu almajirai ta ce "Kai zo ku ƙarasa zubar mini da wannan kayan ƙazantar, zan biyaku, idan na karya jarin in ga uban da zai ɗorasu, matsiyata gayyar yunwa an samu mai kuɗi ana rawar jikin bin malamai a asirce shi aci dukiya" Hafsa zuba musu id tayi tana kallon ikon Allah, tana kallon yadda ake cigaba da yi mata watsi da kaya, bayan ta kwashi zagi da cin mutumci a bainar nasi, Hafsa a yau tayi dana sanin sanin Khalil da tayi, dan haka ta yunƙura tayi wani abu wanda daga shi, zata yanke alaƙar ta da Khalil. Ta ɗauko wayarta ta fara dannawa, zuciyarta na mata wani irin zafi, amma ta dake taƙi yin hawayen, ta shiga neman lambar Khalil. Hajiya Turai ta yiwa Hajiya Zainab alama da ta fito. Hajiya Zainab ta buɗe motar, ta fito ta nufo in da suke a tsaye da cincirindon mutane. Gaban Hafsa ya faɗi, dan ko ba a gaya mata ba, kammanin matar da ta gani da Khalil ta san mahaifiyarsa ce. Tuni ta turawa Khalil saƙo kamar haka "Please man, idan ban takuramaka ba, ka taimaka mini da dubu goma" Da saƙon ya isa wayar Khalil, yayi mamaki, dan ko da abu mai kamar wasa, bata taɓa roƙonsa abin ficika ba, amma yau tana neman dubu goma Bai yi tunanin komai ba, ya tura nata dubu talatin. Mummy ta ƙarewa Hafsa kallo, dan ta gano wani aibun nata, saboda ta ji daɗin cin mutuncinta, amma ba taga alamar wani aibu ba, bayan na talauci. "Ni ce uwar Khalil, na zo ne nan ne da mutanena, dan in sake ja miki kunne, muddin baki rabu da shi ba, yadda na saka aka watsar da wannan tsiyar da kuke kasawa ku dogar da shi, haka zan saka a rushe mini in da kuke zaune, saina tabattar da kun dauwama cikin tsiya. Wannan gayyar iskar da kike kasawa, da dudu kuɗinsa bai wuce kuɗin ruwan robar da Khalil yake sha a sati ba, da na sa aka watsar, kaɗan nayi miki, kin san waye Khalil kuwa? Kin san waye ubansa a ƙasar nan, kin masa asiri zaki mallake mini shi? To ahir ɗinki wallahi, kuma daga yau na saka almakashi na datse duk wata alaƙa dale tsakaninki da Khalil, saboda ba sa'an Aurenki bane, naji ya ce ke marainiya ce, sai ki jira idan ya buɗe orphanage Home, sai ki requesting ko zaki samu gurbi" Hajiya Salma ta ce "Talaka kenan, akwai ladabin dole, ga yadda ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, irin wannan cinikin ne idan dare yayi suke tara maza su lamube su su basu kuɗi, banda haka ina wata awara zata riƙe mutu" "Khalil ya biyani kuɗin asarar da akayi mini, kuma daga haka insha Allah in dai ni 'yar halak ce, bani ba Khalil har abada, in sha Allah na rabu da shi" Hajiya Turai ta ce "Kar ma ki rabu da shi, kici ubanki ko ba dan Allah ba, ai karo da karo sai rago" DOMIN SHIGA VIP GROUP KU TUNTUƁENI TA WANNAN LAMBAR. AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL) Page37 Hafsa tabi bayan su Hajiya Turai da kallo, da mamakin irin tsanar da ta gani ƙarara a idon Mummy. Jikinta a sanyaye tabi wurin da aka watsar mata da kaya da kallo, ga sauran mutane da suke tsaye a wurin, Mussaman majalisar mai shayin nan, da wanda suke jin haushinta bata kula su, da wanda take burgesu saboda kamewarta, wasu suka jajanta mata, abin takaicin shi ne yadda har su Hajiya Turai suka yi mata tijara suka gama baby wanda yayi yinƙurin dakatar da su ko basu haƙuri sai son jin ƙwaƙwaf. Daga irin zage-zagen da suka yi ne, wasu suka gane cewa mahaifiyar Khalil ce da jama'arta. A gaggauce Hafsa ta durƙusa, ta dinga tsince kayanta da aka baje su a wurin kamar abun banza, zuciyarta na wani irin raɗaɗi da zafi, ta dinga ƙoƙari ta danne hawayenta, mai shayi ya tayata tsince kayan, ya so saka baki, amma ganin su Hajiya Salma sun yi kama da manyan 'yan duniya ya sanya bai iya saka baki ba. Ya tsare mata abin hawa ta shiga, mai shayi ya ce "Ayi ta haƙuri Hafsa, haka rayuwa take" Ita dai ba ta ce masa komai ba, sai da taga mai Napep ɗin nan ya ja baburin, ya bar wurin, sannan ta fashe da wani irin kuka, mai ban tausayi da ratsa zuciya. "Yaushe zan samu sauƙin rayuwa ni Hafsa, daga wannan sai wannan, Astagfriullah" ta faɗa a hankali tana ƙanƙame jikinta, tana cigaba da raira kukanta, tana jin yadda zuciyarta tayi mata nauyi, shikenan Khalil ɗin da ta saka rai, ta fara samun afuwa a tare da shi, shima zai kauce, zata koma waccan duniyar da yayi ta ƙoƙarin fito da ita daga ciki, mai tarin damuwa da rashin gata. Kan su kai gida, tuni idanunta sun yi mitsi mitsi, sun yi jawur kamar wadda aka sawa teargas, ta sauko ta sallami mai Napep, ta kwashi kayan da wasu suka yi buɗu- buɗu da ƙasa, ta shigo da su ta ajiye a tsakar gida. Mama ta kalli kayan ta kalli Hafsa ta ce "Ke lafiya kuwa? Meye ya sameki wanan kayan ya aka yi suka yi kaca-kaca da ƙasa haka?" Hafsa na ƙoƙarin dannewa, amma ta kasa kawai ta nufi ɗaki da sauri, tana zuwa ta faɗa kan katifar Mama, ta fashe da wani irin kuka, jikinta har rawa yake yi. Mama ta biyo ta cikin tashin hankali, tana faɗin "Hafsa ki gaya mini, meyafaru wannan wane irin kuka ne kike yi, Ki gaya mini menene" Mama tayia maganar cikin matsananciyar damuwa tana ƙoƙarin ɗago Hafsa. Hafsa kasa magana tayi, kuma ta kasa yin shiru, nan da nan hankalin Mama ha ninka tashi, cikin rauni ta ce "Dan Allah ki gaya mini maiya faru, ko dai Najib ɗin ne dai?" Hafsa ta girgiza kai alamar a'a. "To Hafsa ki gaya mini menene, har bugun zuciyata ya sauya wallahi, dan Allah ki mini bayani" tayi maganar hawaye na cika idanunta. A birkice Hafsa ta tashi zaune, tana girgizawa Mama kai ta ce "Mama dan Allah kar kiyi kuka" "To Hafsa ya zan yi, kin shigo kina wannan uban kukan, ga kayan sana'arki duk ƙasa, dole hankalina ya tashi" Hafsa ta sunkuyar da kanta, wasu hawayen ma zubowa, ta saka hannunta ta share hawawnta, ta ɗan ɗago ta ce "Mama ina ga bani da sa'a a rayuwata" "Subhanallah, kamar yaya, Meyasa kike faɗan haka?" "Mama Khalil" ta faɗa tana sake fashewa da kuka. Cike da zaƙuwa sa son jin ƙarshen zancen, Mama ta ce "Me Khalil ɗin yayi miki?" Cikin kuka mai ƙuna zuciya, da dashewar murya, Hafsa ta ce "Mamansa ta zo ita da wasu mata inda nake sana'a, ta ce bani babu ɗanta, wai ni ba sa'ar aurensa ba ce ba, saboda ni talakace, suka ci mini mutunci a gaban mutane, suka zubar mini da kayan sana'ata. Ai kema Mama kin san ai ba dan kuɗinsa nake son sa ba ko?" Mama tayi shiru, ranta ya ɓaci, idan Hafsa na cikin damuwa, tana iya haɗiyeta taƙi faɗa, amma tabbas tun da ta kasa ɓoyewa Mama, ta faɗa mata kai tsaye, abin ya girmama. "Yanzu dan kawai kina 'yar talaka shi ne suka je suka yi miki Wannan cin mutuncin?" Hafsa ta ɗaga mata kai tana kuka. "Shikenan, share hawayenki, Allah ya kawo miki mafi alkhairi, ita kuma Allah ya ganar da ita, in dai Khalil ne ba shine autan maza ba ai" Hafsa ta faɗa jikin mama tana kuka, Mama ta rungumeta sosai tana rarrashinta, ganin Hafsa bata ganinta ya sanya ta lunshe idanunta ita ma, hawaye suka shiga kwararo mata, ita ta matsa Hafsa a kan ta yarda da Khalil, sai da ta yadda da shi tayi nisa a son sa wannan matsalar ta kunno kai, Mama ta share hawayenta ba tare da Hafsa ta gani ba ta ce "Ga ruwan wanka can na dafa miki, na kammla girkin dare, idan an yi sallar magariba, sai kiyi wanka ki zo ki ci Abincin dare. Hafsa jin Mama kawai take, amma Abincin nan ba ciyuwa zai yi ba a wurinta. Khalil kuwa ya dinga jerawa Hafsa waya, amma ko ɗaya bata ɗauka ba, ta share wayar, ƙarshe ma ta saka wayar a silent, ta jefata bayan katifarta. Daddy na zaune a kan kujera 3seater, Fadila na kusa dashi, tana ta 'yan ciye-ciyenta tana masa hira irin ta uba da ɗa. Amina kuma na ƙasa a zaune tana kallon tashar da suke kallo. Fadila ta ce "Ke ɗan jeki ɗakina, ki ɗauko mini wata leda a kan madubina" Amina ta tsani ke ɗin da Fadila kan kirata da shi, ko ita ko Mummy, amma ba yadda ta iya, haka ta tashi, ta nufi ɗakin Fadilan. Ta je ta ɗauko ledar ta kawo, ta miƙawa Fadila, Daddy ya ɗan ƙure Amina da ido, yana mata murmushi. Amina dai bata nuna ma ta san ita yake yiwa murmushin ba. Fadila ta ɗauko turarukan da Yazid ya bata ta ce "Daddy, sansana wannan turaren kaji, da ƙamshi?" Daddy ya ce "Wow, lailatul sahara, na so turaren nan sosai, ina kika samo shi?" "Wani ɗan ajinmu ne Yazid ya bani, as a birthday gift, but you, you even forget about it, you don't even wish me" tayi maganar cikin shagwaɓa. "Ohh my dear, ai naga birthday ɗin naki sai gobe in Allah ya kaimu zai cika, kuma ni banga kina mana organising komai ba". Fadila ta ce "Yusra zata yi mini cake, then just chill with you tonight, mu ci Abinci tare snap pictures together that's all, ba zan haɗa hayaniya ba" Ya ce "Hmm, alright Allah ya kaimu" "Ameen Daddy, amma me zaka bani as my birthday gift?" Ya ce "Mmmm, what do you want?" "Kome ka bani yayi" "To shikenan, Dubai or Umrah" Fadila ta ɗan zaro ido ta ce "Daddy Umrah, ina son komawa Saudiyya" "Fine, amma ke da Mummyn ki zaku je, idan kun yi hutun makaranta" "Alhamdilillah, Daddy na gode sosai, Much Love my Hero" tayi maganar tana rungume Daddy tana murmushi. Amina da ke gefe, ta kwaɓe baki, ganin yadda Fadila ke ta nan nan da babanta, tana zuba taɓara, amma ta iya zagewa ta wulaƙanta wani, ba tare da tunanin yadda take jin son babanta a ranta haka kowama yake ji ba. "Daddy, ka san Mummy cewa tayi wai turaren nan wari suke yi kar in shafa" Daddy ya ce "Aikuwa turaruka ne masu kyau" Fadila ta nuna masa hannunta ta ce"Kalli, har abin hannu ya bani, da turaren nan, Daddy baka ga ƙoƙarinsa ba sai dai Yaizd bai iya turanci ba, kaga yadda yake larabci kamar balarabe" "Dama ai haka lamarin ilimi yake, kuma turanci yare ne kawai" Hajara ce ta leƙo falon, ta ga Daddy zaune shi da Fadila suna hira suna kallo, Amina kuma ta kame a ƙasa ita ma kallon take yi. A ranta zuciyarta ta ce Lallai ma yarinyar nan, ina can ina aiki, kin zo kin zauna a cikin masu gida kina kallo A fili ta ce "Amina, ko zaki zo ki yanka mini alayahhu muyi mu kammala girkin dare kan Hajiya ta dawo?" Daddy ya ce "Kallo, take yi, kiyi aikin a hankali ba sai kin yi gaggawa ba, tun da ba yanzu za aci Abincin ba" Da ɗan mamaki Fadila ta ce "But Daddy, she's also a maid, ai ba kallo ta zo yi ba" "Yes i know, she's facing her SSCE, yakamata tayi passing, kuma abin da take kalla is educative, bana son yin asarar kuɗin makarantar da nake biya" Jiki a saɓule, gwiwa a sace Hajara ta koma kitchen, tana masifa tare da mamakin yadda Amina ke abin da taga dama, da wasu abubuwa da ke faruwa, wanda ta kasa gane kan in da suka dosa. Fadila ta tashi tsaye ta ce "Daddy, zanje in ɗan yi karatu, exams is around the corner" "Ok Best of luck" "Thank you" ta nufi ɗakinta. Sai da ya tabattar Fadila ta bar falon, sannan ya ce "'yar Daddy" shiru Amina tayi ta cigaba da kallonta. "Amina am talking to you fa" a hankali ta waiwayo ta kalleshi. "Ya naga kin haɗe rai, any problem?" "Nothing" ta faɗa a taƙaice. "Oya kawo mini Apple, da ruwa" ta miƙe ta nufi kitchen, ta tarar Hajara ta cika tayi famm, tana aiki ita kaɗai. Tana ganin Amina ta ce "Yauwa, ga alayahun nan, kk ɗauka ki yanka" "Wai baki ji me Daddy ya ce ba? Kallo nake yi, kuma wallahi da nice ba zan takuraki sai kin yi aikin nan ba, duk ni zan abina, amma ke ba damar in ɗan huta sai ki sa mini ido, ke fa wuni kike a gida ni kuma ga makaranta ina zuwa haba. "Amina rashin kunya zaki mini?". "Ni ban miki rashin kunya ba, kece ba kya jan girmanki" Daga haka Amina ta ƙarasa gaban fridge, ta buɗe ta ɗauko Apple, ta ɗora a kan plate da wuƙa ta bar kitchen ɗin, ta bar Hajara da mamakin da tambayoyin da babu mai bata amsarsu. Ta kawo wa Daddy ta ajiye masa. "Yanka mini mana 'yar Daddy" Amina ta zauna ta yanka masa ta miƙa masa, yasa hannu ya karɓa yana ci. Can Amina ta ce "Daddy, ya sugan naka ya sauka kuwa?". "Ban duba ba, naji daɗin jikina Yanzu sosai Alhamdilillah" "To Allah ya raƙa lafiya" "Ameen 'yar Daddy, anjima ki hau online muyi hira" Ta ɗan kalleshi ta ce "Karatun fa?" "Wai ke ba kya hutawa karatun nan ne? Ki dinga hutawa ranki" "Ai ba iya karatun boko nake ba, bana son haddata ta zube dole sai ina tilawa" Cike da girmamawa ya kalli Amina ya ce "Masha Allah, 'yar Daddy, kina nufin kina haddar Alqura'ani?" Ta jinjina masa kai alamar eh. "Kai, dole in san abin yi, ban goyi bayan haddar nan ta zube ba, kin haddace duka ne?" "A'a, ban haddace duka ba" Daddy ya ce "Matso nan kusa da ni muyi magana" Amina ta matsa kusa da ƙafafuwan Daddy, ya ajiye ɗan ƙaramin plate ɗin da ta zuba masa Apple a kai, a kusa da ita, sannan ya ce "Na daɗe banga mutum mai ƙwazo kamarki ba, zanga abin da ya dace, yakamata in samo wanda zai cigaba da koya miki a gida ina biyansa" Amina ta washe baki ta ce "Ai ba sai ka kirawo wani ba, direbanka Zakiru malami ne, ka ce ya dinga koya mini, sai ka dinga biyansa shi" Daddy yayi murmushi ya ce "To shikenan, zan yi Magana da shi in sha Allah" "Na gode Daddynmu" Yayi murmushi ya ce "idan kin yi tilawa, ki dinga yiwa Daddynki Addu'a". "Me zan roƙa maka?". "Abubuwa da yawa, amma ba zan gaya miki ba, kan ki yayi ƙarami ba zai ɗauka ba" Hajara kuwa tana laɓe ta hanyar shigowa falon, tana hango Amina da Alhaji Ahmad, amma ba ta jin me suke cewa, bata iya hango Alhaji Ahmad, amma tana ganin Amina tana murmushi, Amina ta miƙe, ta ɗau ragowar plate ɗin da Alhaji Ahmad ya gama da shi, ta ɗan tsaya a kan Daddy tana sauraren abin da yake faɗa mata. Idan ba gizo idanun Hajara suke mata ba, kamar shagwaɓa Amina ke yiwa Daddy, shikuma ya kashingiɗa yana kallonta. "Na shiga uku ni Hajara, me ake aikatawa a gidan nan ne? Ita ma matar gidan uwar gantali, tana can yawo ana munafurtarta, kai amma wannan an yi tsohon banza, wannan 'yar tamilon 'yar zai tsaya tana masa barikanci yana kallo, yo ko ya aka yi ma ta samu wannan damar oho?" Amina ta nufi hanyar ƙofar kitchen, sai ga Hajiya Zainab ta turo ƙofar falon, sai da Amina ta ɗan razana, ta tsaya ta zubawa Hajiya Zainab ɗin ido. "Ke uban me kike kallo, sai kace mayya kin tsaya kin zubo mini ido, ko kin aike ni ne?" Amina ta girgiza kai, ta nufi barin falon. "Ki kawo mini ruwa, da exotic ƙishirwa ta isheni" tayi maganar tana ƙarasawa in da Daddy yake. Hajara na ganin Amina ta ce "Mmm su Amina manya, kina sha'aninki" ko kallon Hajara Amina ba ta yi ba, ta cigaba da sabgarta. Alhaji Ahmad ya ɗan ɗaga murya ya ce "Sweetheart kin dawo?" Mummy ta ce "Na dawo, kana gida kenan?" "Na dawo tun ɗazu, ban sameki ba masu aikinki sun ce mini ba kya nan" "Eh, fita ce ta sameni da gaggawa" Ya ce "Ok, sannu da zuwa". "Yauwa, Fadila ta dawo ne?" Ta faɗa tana zama a kusa da Daddy. Daddy ya ce "Ta dawo, yanzu ta gama yi mini mita, wai gobe in Allah ya kaimu birthday ɗinta, ban wishing ɗinta ba" Mummy ta ce "Ƙyaleta rigimammiya" Daddy ya ce "Nan ta nuna mini turare, wai an bata gift, amma ni ban bata komai ba" Mummy ta ce "Naji ta ce za'a yi mata girki, ayi hotuna tana ta lissafinta dai". Daddy ya ce "Na yi mata alƙawarin umara, zaku je ke da ita, maybe idan sun yi hutu" Mummy ta ce "Inyee 'yar gidan Daddy, to Allah ya kaimu, dama nima ina son zuwa, to Allah ya kaimu" "Wai ni Khalil ya koma ne?" Daddy yayi maganar da ɗan damuwa. A daidai nan Amina ta kawowa Hajiya Zainab ruwa da lemo. Hajiya Zainab ta ce "Mata da wannan yaron, wani halin rashin mutunci ya ɗaukar wa kansa, amma zan yi maganinsa" Daddy ya ce "No, wani abun yana damunsa ne, idan har yana gidan nan, ba zai ɗauke ƙafa daga shigowa gidan nan ba" Mummy ta ce "Ka rabu da shi kawai" ta mayar da idonta kan Amina ta ce, "Ki buɗe ki zubamini, kin zo kin tsaya a kanmu kina rarraba ido". Amina ta tsuke fuska, ta fara ƙoƙarin zuba wa Hajiya Zainab ruwa a kofin, ta zuba zata miƙa mata ruwan, Daddy ya kalli Amina ya kashe mata ido ɗaya. Aikuwa sai hannunta ya kama rawa, har ta zubawa Hajiya Zainab ruwa a jiki. "Ke mahaukaciya, ba kya gani ne? Ke wace irin dabba ce, kalli yadda kika zuba mini ruwa a jiki, ba kya gani ne?" Cikin rawar murya Amina ta ce "Kiyi haƙuri, ba da sani na bane" Dama Hajiya Zainab har yanzu a ƙule take, duk da sunje sun yiwa Hafsa rashin mutunci, amma bata huce ba, dan haka take ƙoƙarin ƙara hucewa a kan Amina, a hasale ta ce "Dalla ɓace ki bar gabana, dabba kawai" Hawaye ne suka cika idon Amina, amma Daddy ya shiga girgiza mata kai alamar kar tayi kuka. Duk yadda Mama tayi da Hafsa, a kan ta daure ta ci Abinci, ƙi tayi, tana sallar isha'i, ta kwanta, ta zubawa wayarta ido, tana kallon yadda kiran wayar Khalil da saƙonninsa ke shigowa babu ƙaƙƙautawa, amma bata ɗaga ko guda ba. Ƙarshe ta saka wayar a flight mode, ta shiga gallery, tana kallon hotunan Khalil da ke wayarta, da Videos ɗin da yake haɗa musu, na hotunansu shi da ita. Wata irin soyayyarsa ce take sake fizgarta, tana jinta wani iri iya awannin data kwashe daga fitarta zuwa wurin sana'a zuwa yanzu da ba suyi waya ba, ta san yana can cikin damuwar rashin ɗaga wayarsa da ba ta yi ba. Ta ƙanƙame wayar a ƙirjinta, ta toshe bakinta, ta cigaba da kuka, dan tun a yanzu ta fara jin kewarsa, tana matuƙar ƙaunar Khalil har cikin ranta. Fadila ce tsaye a gaban mudubi, sanye cikin doguwar rigar abaya, ta ɗan gyar fuskarta, ta ɗauki turaren wurin Yazid ta shafa, ta ɗaura abin hannun, sannan ta ɗauki wasu turarukan ta shafa, ta ɗauki jakarta ta jefa mukullin motarta a jaka, ta tafi ɗakin Mummy. Bata tarar da ita a falon ba, dan haka ta wuce ɗakin Daddy. A can ta tarar da su a falon Daddy, a tare ta gaishe su suka amsa. Daddy ya ce "Har kin shirya?" "Eh Daddy, and karku manta, tonight in Allah ya kaimu, za muyi party" Daddy ya ce "To Allah ya kaimu" Ta ce "Amin" ta ɗau jakarta ta fito falo, a falo ta haɗu da Amina, ta kalli Amina ta ce "Yauwa, idan kin dawo daga school, zan ɗan yi mini party na birthday na, dan haka a gyara ko ina, zamu zo ni da Yusra, za ayi decorations a falon nan" Amina ta ce "To, Allah ya kaimu" Fadila ta fice, ba tare da ta amsawa Amina ba. A ƙofar ajinsu taga Yazid, kamar me jiran wani abu. Tun daga nesa yake mata murmushi, har ta ƙaraso. Tana ƙarasowa ta tsaya tana kallonsa ta ce "Wa kake jira ne? Naga kana ta fara'a kamar an maka kyautar wani abu" "Ke kawai nake jira, in ga kwalliyar ranar birthday, kin yi kyau sosai". Ta ce "Ikon Allah, ba zaka daina sa ido ba ko?" "Ai ke kaɗai nake sawa ido, bayan ke bana sawa kowa" ba ta kuma cewa komai ba ta shiga aji. Yazid kuwa murmushi ya yi, ganin abin hannunta da ya bata, da kuma tashin ƙamshin turaren lailatul sahara a jikinta. Lectures ɗaya tayi attending, ta tafi gidansu Yusra, ita Yusra basu da lectures. Ta tarar Yusra ta gama haɗa mata cake ɗin ta da duk wani snacks da za tayi amfani da shi, suka rankaya tare zuwa gidansu Fadila. Kusan wuni suka yi, suna decorating ɗin falon, Amina na taimaka musu da wasu abubuwan, yayin da ta zuba ido tana ganin yadda suke gudanar da komai. Khalil ya kasa jurewa, ya shiga damuwa da tashin hankalin rashin sanin dalilin da ya sanya Hafsa bata ɗaukar wayarsa, dan haka da yamma ya shirya ya tafi wurin sana'arta, dan ya san a daidai wannan lokacin ba zai sameta a gida ba, ta fito sayar da awara. Sai dai tun daga nesa ya ga wurin nata ba kowa. Ya ƙarasa ya yi parking ɗin motar, ya sauko ya nufi wurin, ya shiga wurin mai shayi, suka gaisa da Khalil. Khalil ya ce "Hafsa ba ta shigo bane?" "Eh, ba ta zo ba yau, ai wasu mata ne suka zo wurin nan jiya, suka watsar mata da komai na kayan sana'arta, suka yi mata zagin tsamar nama suka tafi" A firgice Khalil ya ce "Tsaya, ban gane ba me tayi musu?" "Oho ina na sani, biyu ɗima-ɗima, ɗaya sirirya a wata ƙatuwar mota, haka suka zo suka yi rashin albarka suka tafi, dama da ganinsu kaga 'yan duniya, na rasa a in da Hafsa ke zuwa tana kwaso rigima, rannan sun yi da wannan ɗan iskan, jiya kuma da waɗa nan mata" Khalil dana fahimtar me mai shayi yake faɗa masa yai, ya juya da hanzari a koma wurin da motarsa take, ya shiga ya rufe, ya bar wurin. A bakin layin su Hafsa ya yi parking, ya sauka ya taka da ƙafafuwansa, zuwa ƙofar gidansu, ya samu wani yaro a ƙofar gidan, ya aika shi ya kira masa ita. A ƙalla ya shafe mintuna Ashirin a tsaye a ƙofar gidan bata fito ba, ba wai taƙi fitowa bane, dan ta muzguna masa, sai dai tunanin halin da su biyun ka iya shiga, ta daɗe tana kuka, da ƙyar Mama ta rarrasheta ta fito. Ko da ta fito, bata ƙarasa in da Khalil ya ke ba, a bakin soron gidansu ta tsaya. Kallo ɗaya ya yi mata yaga yadda ta rame, idanunta sun yi jawur alamun tayi kuka har ta gaji. Da sauri ya nufi bakin soron, ya tsaya cikin damuwa ya kalleta ya ce "Hafsa baki da lafiya ne? Ina ta kiran waya ba kya amsawa, kalli yadda duk kika fita hayyacinki, meke faruwa ne?" Duk yadda ta so dakewa, sai da hawaye suka zubo mata, ta miƙa masa wata babbar jaka, ta ajiye a gabansa, sannan ta kalleshi ta ce "Khalil, jiya na maka text, ka turo mini kuɗi, ka bani ninkin abin da na nema, na nemi kuɗin nan ne dan mayar da asarar da aka yi mini, na kayan sana'ata, Khalil daga rana mai kamar irin ta yau, ka sa a zuciyarka baka taɓa saɓnin wata mai kama da ni bama, balle tuna mun yi soyayya. Jiya mahaifiyarka ta zo ita da wasu, sun yi mini kashedin babu ni babu kai. Tabbas sun yi gaskiya, zaren ba kalar yadin bane, ni da kai bamu dace ba, kyautatawarka a garrni ta ruɗeni na fara sonka, ba tare da na kalli banbancin matsayinmu ba. Ga shi nan duk wani abu daka bani, na tataro na dawo maka da su, zoben nan ne kawai ba zan iya dawo maka da shi ba, saboda kana cikin mutane masu muhimmanci da suka shigo rayuwata, na san ba zan taɓa iya mantawa da kai ba, Na gode Khalil Allah ya haɗa kowa da rabonsa" ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye, ta juya ta shiga cikin soron. Cikin zafin nama Khalil ya bita, ya riƙota ya juyo da ita tana fuskantar sa. Kamar zai fashe da kuka ya ce "Haba Hafsa, ina duk alƙawarin da kika yi mini na kasancewa da ni, duk ƙalibalen da ka iya tasowa kuwa, dan Allah karki ce zaki rabu da ni ba, dan Allah kar ki mini haka, in dai Mummy ce zan yi mata bayani, zata fuskance ni kuma, dan Allah Hafsa, muna son junanmu karki yanke wannan hukuncin" "Bakin Alƙalami ya riga ya bushe Khalil, idan na ce bana sonka nayi maka ƙarya, amma duk wani abu da za ayi iyaye ba sa so ba zai taɓa yin albarka ba, banga alamar Mummy zata fahimceka har ta bari muyi aure ba, dan Allah Khalil kar ka sake shigowa rayuwata, Allah ya haɗa kowa da rabonsa" Ta zame hannunta daga cikin nasa da ya riƙe, ta shige cikin gidan tana kuka. Contact me for the VIP group AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM AYSHERCOOL PAGE 38 Wani abu me mai nauyi ya tokarewa Khalil ƙirji, bai taɓa tunanin Mummy zata aikata abin da ta aikata ba, na zuwa ta ci mutuncin Hafsa a gaban mutane. Tamkar wanda aka zare wa lakar jiki, haka ya ja jikinsa ya buɗe motar, ya shiga ya zauna, ya kifa kansa a kan sitiyarin motar, ya rasa abin da yake masa daɗi, ya rasa ta ina zai ɓullowa wannan lamarin, gab ɗaya komai ya cakuɗe masa, ya shafe a ƙalla mintuna Ashirin a cikin motar ya kasa ko da kunna motar, balle ya ja. Ganin bashi da wata mafita a cikin wannan tsayuwar da yake yi, ya sanya ya kunna motar, ya fara tuƙi, sai dai jin jikinsa yake tamkar an zare masa dukkan wata laka dake jikinsa, da wani dishi dishi yake gani, da ƙyar yake iya jan motar, ya nufi gidansu Abdul. Shagon Abdul a rufe yake, alama Abdul ɗin baya nan, Khalil ba shi da kuzarin da zai kira Abdul, dan haka ya cigaba da zama a cikin motar ta sa yana kuma tuno maganganun da Hafsa tayi masa. Bai san iya adadin lokacin da ya kwashe a zaune a cikin motar nan ba, knocking ɗin glass ɗin motar da aka yi ne ya sanya shi dawowa play, har ya sauke glashin motar, Abdul ne a tsaye yana kallon Khalil "Ya aka yi baka kirani a waya ba, ka zauna a mota kana bacci?" Khalil baice komai ba, ya buɗe motar ya fito, Abdul ya wuce ya buɗe ƙofar shagon, Khalil ya shiga ya nemi wuri ya kwanta, ba tare da ya ce wa Abdul komai ba. Abdul ma bai takura shi sai yaji meke damunsa ba, ya ƙyaleshi. Fadila kuwa sai yamma suka gama shirin komai, suka zauna yin kwalliya, har su Hajiya Turai sun zo, Daddy maa da wuri ya dawo gida, sai dai Fadila ba taji daɗin rashin Khalil a wurin ba, ta yank Cake suka yi hotuna, zuwa magariba kowa ya watse. Hafsa kuwa bayan shigarta gida wani sabon kukan ta zauna tana cigaba da yi, Sai da Mama ta ga kukan ya yi yawa sannan ta sameta a ɗaki ta ce "Hafsa, wannan kukan da kike fa babu in da zai kai ki, kiyi haƙuri, kiyi Addu'a Allah ya zaɓa miki mafi alkhairi, ko kin auri Khalil tunda mahaifiyarsa ba ta ƙaunarki, ba zakiji daɗin zama da shi ba, kiyi haƙuri Allah ya musanya miki da mafi alkhairi" Hafsa ba ta cewa Mama komai ba, dan ita kaɗai ta san me take ji a ranta, a kan rabuwarta da Khalil, ta sani rabuwarsu ba yana nufin rayuwarta ta zo ƙarshe bane, amma samun wanda zai maye mata gurbin Khalil abunne mai wahala, ita ta riga ta gama yadda ba ta da sa'a a rayuwata, duk wani abin alkhairi da zai tunkarota, sai ya lalace. Can Mama ta nisa ta ce "Yanzu wace sana'ar kike ganin zamu koma yi? Bana son ki cigaba da fitar nan tunda na fauskanci babu alkhairi a hakan, kowa ya tashi sai ya sameki a can ya yi miki wulaƙanci a cikin mutane, yanzu dai bari zuwa jibi in Allah ya kaimu idan kin yi tunanin wani abun da zamu yi sai ki mini magana,tun da muna da Abinci. Jinjina kai kawai Hafsa tayi, ba tare da ta iya cewa komai ba. Har Khalil ya gama zamansa a ɗakin Abdul, bai cewa Abdul ɗin komai ba, sai bayan sallar magariba, sannan ya yi wa Abdul Sallama ya tafi gida. Ko da ya fito zai tafi gida, zuciyarsa ji yake kamar ya sake komawa gidansu Hafsaz ko zata sakko ta saurareshi, amma yadda yaga hawayen nan a idonta cikin damuwa ya ƙara tabattar masa da gaske take, ta bar shi. Haka ya shiga motarsa ya tafi gida. Ita kanta Fadila rashin walwalar Khalil ya fara damunta, kwata kwata ya daina shigowa cikin gidan, ko ba komai ko su haɗu suyi faɗa yana ɗebe mata kewa. Ta kalli Mummy da ke zaune tana cin cake, su Hajara kuma na gyara falon,. "Mummy, wai dan Allah haka za'a zubawa Yaya Khalil ido? Kinga fa ya daina shigowa cikin gidan nan sam, ko ma bashi da lafiya ne?" Mummy ta ce "Lafiyarsa ƙalau, duk a kan na raba shi da waccan yarinyar ne, yake fushi da wannan iskancin, na ɗau matakin ƙarshe da nake ganin ya dace, in shi ba zai rabu da ita ba, su dolensu su rabu da shi, idan har suna da zuciya" "Amma Mummy wane matakin kika ɗauka" Mummy ta yi murmushi ta ce "Ke ina ruwanki, ba dai nace miki na ɗau mataki ba" Fadila na shirin yi magana sai ga Khalil ya shigo falon, gaba ɗaya ya rame duk yayi wani iri. Fadila ta ce "Yauwa brother, na je ɗakinka babu adadi ina nemanka, yau birthday na duk an yi hotuna babu kai". Be kula Fadila ba ya ƙarasa in da Mummy ta ke, ya kalleta ya ce "Mummy, ban taɓa zaton zaki mini abin da kika yi ba, dan kawai na ce ina son 'yar talaka ba, yanzu Mummy meye laifin yarinyar da za'a wulaƙanta ta haka? Me tayi ita?" "Au Yanz zuwa kayi ka titsiyeni ko ka tuhumeni a kan wannan shegiyar yarinyar? To ka kyauta daidia nake da kai, zan ga ni da kai waye ya haifi wani" Kamar Khalil zai fashe da kuka ya ce "Mummy ba haka bane, Mummy da girmanki da mutuncinki yarinya ce fa ƙarama Hafsa, 'yar cikinki kuma sirikarki" Miƙewa Mummy ta yi ta ce "Zan tsinke ka da mari, ni zaka zo ka tsayaa kaina kana gaya mini maganar banza, ka kiyayeni Khalil, wallahi ka cigaba da bibiyar yarinyar nan, zan maka abin da tunaninka bai taɓa kawo wa zan maka ba, kuma idan ta cigaba da bibiyarka, wallahi saina ƙasƙanta ta na tozartata fiye da abin da nayi mata yanzu, idan yaso ka nemi wata uwar ka canza ni" Khalil ya girgiza kai ya ce "A'a Mummy, ke uwata ce, ba yadda za ayi in iya canzaki, ko in fifita wata a kanki, Mummy ina nuna miki illar abin da kika aikata ne, ita ma 'ya ce, uwa ce ta haifeta ya tata uwar zata ji da wannan abin da kika yi mata? Haba Mummy" "Lallai Khalil, wuyanka ya riƙa ya isa yanka, ka nuna mini ka kawo ƙarfi, gara da na farga na miƙe tsaye, kan kwaso mini wadda zata dinga juyaka, idan kaga na bari kayi aure, to matar da na zaɓa maka ce, tun da naga baka da hankali" Idonsa fal hawaye ya ce " Shikenan Mummy, kin yi nasara kin rabani da Hafsa, shikenan Mummy" "Kar ma ta rabu da kai, da ta cigaba da bibiyarka dai, da taga ƙaryar talauci, sakarai kawai" Ta wuce fuuuuuu ya bar falon. Khalil ya zauna ya dafe kansa, yana girgiza kan yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa. Fadila ta zauna a kusa da Khalil ta ce "Brother, wai me Mummyn tayi maka ne?" Ya ɗago idanuna da suka yi jawurr, jijiyoyin kansa duk suka mimmiƙe suka kumbura, ya kalli Fadila ya ce "Yanzu fisabilillahi Fadila ya dace ace Mummy taje da ƙawayenta, sun ci mutuncin yarinyar mutane a gaban al'umma, suka watsar mata da kaya a cikin ƙasa, ita meye laifinta?" Fadila ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Haka ne, gaskiya Mummy bata kyauta ba, amma kaima Yaya Khalil meye kaika, duk matan duniya ka nacewa wata mai awara, ai koma menene kaine ka janyo mata, tunda Mummy ta nuna bata so ai saika haƙura" Kalaman Fadila ƙara masa ɓacin rai suke, dan haka ya tashi, ya bar falon zuciyarsa babu daɗi. Sosai Amina taji tausayin Khalil ya kamata, mussaman ita wadda ake ce anje an ci mutuncin ta a gaban mutane. tana mamakin baƙar zuciya irin ta Hajiya Zainab, babu tausayi ko Allah a ranta, gani take kamar ita ta yiwa kanta arziki ba Allah ne ya bata ba. Fadila ɗan taɓe baki tayi, ta tashi ta bar falon, duk da Khalil ɗin ya bata tausayi, amma a ganinta matakin da Mummy ta ɗauka yayi daidai, dan Khalil yana da taurin kai wasu lokutan. Amina wasu lokutan mantawa ma take da wayar da Daddy ya bata, saboda bata son ta ɗauke mata hankali da ga kan karatunta sam. Da Asubar fari Khalil ya shirya kayansa, ya ɗauki motarsa ba tare da ya yiwa kowa sallama ba, ya fice daga gidan. Abdul yana zaune yana azkar, bayan idara da sallar asba, yana jiran gari yayi haske yayi wanka, ya ga wayar Khalil. Yasa hannu ya ɗaga wayar yana faɗin "Lafiya kake mini wannan kiran haka da sassafe?" "Ina ƙofar gidan ku, airport nake son ka kaini, jirgin Bakwai da rabi zanbi in koma Abuja" Mamakine ya kama Abdul, dan ba suyi wannan zancen da Khalil ba jiya, ya miƙe, ya saka hula ya ɗau wayarsa ya fita, aikuwa yaga motar Khalil. Ya rufe shagon nasa, sannan ya nufi wurin da motar Khalil ɗin take. Ya buɗe motar ya shiga, ya kalli Yadda fuskar Khalil duk ta kumbura, ga idanunsa mu duk sun kumbura sun yi ja, kamar wanda bai yi bacci ba. "Wai Khalil meke damunka ne? Meyasa zaka koma yau bayan kace mini sai next week zaka koma?" "Abdul, Hafsa ta rabu dani, ba zata aureni ba" ya faɗa tamkar zai fashe da kuka. Abdul ya ce "Subhanallah, saboda me?" Cikin damuwa Khalil ya ce "Abdul, could you imagine Mummy da kanta iya da ƙawayenta wai suka je suka yiwa Hafsa warning a kaina, suka watsar da kayan sana'arta a gaban mutane? Abdul waye ni ɗin ne? Me aka yi aka yi ni? Yanzu ya dace abin da Mummy tayi, girmanta ne yin hakan?" Abdul ya ce "A'a Khalil, yi haƙuri, Mummy uwa ce kar ɓacin rai ya sanya ka faɗi wata maganar a kanta" "Haba Abdul, ka duba lamarin nan dan Allah, yanzu dama da yaya na samu kan yarinyar nan, maimakon idan ma rabuwar ce, a bari mu rabu ta daɗin rai, in mata bayani mu rabu cikin mutunci, amma anje an ci mutuncinta, meye laifinta? Har Abada ba zata taɓa ganin mutuncin Mummy ba, na rasa dalilin da yasa Mummy ke biyewa wannan ƙawayen nata suna zigata tana abubuwan da basu dace ba, idan nayi yinƙurin gayamata Gaskiya, ta ƙare mini zagi ta nuna mini haryanzu bani da hankali, amma ka duba wannan lamari meye na Hafsa a ciki?" "Haka ne Khalil, bai kamata Mummy ta aikata hakan ba, amma hakan ba shi yake nufin ka faɗi abin da kake so a kanta ba, kayi haƙuri ka cigaba da yi mata addu'ar Allah ya ganar ita. Ita kuma Hafsa idan rabonka ce, Allah ya daidaita lamarin, ya tabbatar muku da alkhairi, idan kuma ba alkhairi bace, Allah ya haɗa kowa da rabonsa. Khalil ya sauke wata ajiyar zuciya ya ce "Baka san wani abu ba, cewa fa tayi wai bani ba zaɓar macen da nake so na aura, ita zata zaɓa mini, kuma wallahi na san duk wannan matan ne suka kitsa mata ta hau ta zauna, Mummy tana valueing maganar ƙawayenta fiye da kima" Abdul ya ce "Kayi haƙuri abokina, ka cigaba da yi mata Addu'a" Khalil ya ce "Shikenan, muje airport, kai sai ka dawo da motar, idan ka samu lokaci ka mayar musu da motar can gida" "To shikenan, Allah ya tsare" Khalil ya ja motar suka tafi. Kamar kullum, yau ma Amina ta kammala shirinta na makaranta, cikin gogaggun uniform ɗinta, ta saɓa jakarta a bayanta, ta fita wurin Baba, ta tsaya suka gaisa da Baba, Baba ya ce "Uwata, kuɗin makarantar da nake baki ba sa isarki ne?" Cikin rashin fahimta Amina ta ce "A'a Baba me ka gani?" "Alhaji Ahmad ne ya bani kuɗi, kusan dubu goma, wai idan zaki tafi makaranta, in dinga baki isasshen kuɗi, saboda ba kya tafiya da Abinci, yunwa na damunki a makaranta" Amina ta mariraice Fuska ta ce "Wallahi Baba ban ce masa wani abu aba, ranar da na wuni a makaranta ne a wurin lesson, yazo ya ɗaukeni na ce ba zan sake zuwa lesson ba, mun wuni a makaranta ina jin yunwa, amma wallahi Baba ni bance masa komai ba" Baba yayi ajiyar zuciya ya ce "To Uwata, ba zan fasa yi miki nasiha ba, ki iya kankina duk in da kika tsinci rayuwa, kar ki sakankance da mutumin nan ki jamana wata matsala a gidan nan" Amina ta ce "To Baba in sha Allah" "To ni yanzu wannan kuɗin zan baki dubu uku, idan sun ƙare sai ki kuma yi mini magana in baki wasu, amma bance kiyi ta kashe-kashen banza ba" "A'a Baba, dubu biyu ta isheni duka watan nan, ka sayawa Inno kayan shayi a aika mata, ita ma ta dinga cin mai daɗi kamar yadda muke ci a nan" Baba yayi murmushi ya ce "Uwata kenan, ke dai ki karɓa, ni na san abin da zan yi" Amina ta miƙe daga tsugunon da tayi, ta ce "Baba, bari in tafi, bani yadda ka saba bani, idan na dawo sai muyi maganar kar na makara" Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya cirowa Amina naira ɗari uku ya bata, ta saka hannu biyu ta karɓa, tayi masa sallama ta fita. Tana ta sauri ta ƙarasa titi, ana ta wucewa da yaran masu kuɗi a cikin motoci zuwa makaranta, ba tsammani taji an kira sunanta. Ɗan tsawa tayi ta waiwaya, Bilal ta gani cikin suit baƙaƙe. Ya ƙaraso in da take yana faɗin "Amina, makaranta zaki tafi ne?" Amina ta ce "Eh, ina kwana?" "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ɗan jirani in shiga gida in ɗauko mota, in kai ki mana" Amina ta ce "A'a sauri nake, ka bari na gode" "Haba Amina, dan Allah ki tsaya in kai ki" "A'a ka bari wallahi na gode" Bilal ya ce "Gaskiya ban ji daɗi ba, to muje in rakaki titi" "A'a karka damu dan Allah, zan ƙarasa" Bilal bai saurreta ba, ya cigaba da binta, suna tafiya tare, gaba ɗaya hankalin Amina baya kan Bilal, sai surutu yake mata, ba tare da tana amsa masa ba. Sun ƙarasa titi tana jiran mota, ba tsammani sai ga motar Daddy ta zo wucewa, lokacin da ta fito daga gida ko tashi baiyi ba, amma har ya shirya ya fito, sai da ya zo daidai in da suke, sanan ya ɗan ja motar a hankali, yayi musu horn, dan Amina ta san ya ganta, sannan ya ja motar da sauri ya bar wurin. Sai da cikin Amina yayi ƙara, ba ta san hukuncin da Daddy zai yi mata ba, saboda yayi mata gargadi a kan Bilal. Sai da Bilal ya tabattar da ta hau mota, ya biya kuɗin, sannan ya juya ya koma. Yau Fadila ita da kanta taje wurin zaman Yazid, sai kallonta yake yana murmushi, ta miƙa masa wata 'yar ƙaramar jaka ta ce "Gashi nan, kayan birthday ne, na kawo maka" "Ohh ni Yazid, har da ni a cikin kayan, to Allah ya sanya abin da kika bani ɗin na iya ci" "Idan ma baka iya ba saika koya" Ya ce "To shikenan, zauna muyi wata Magana" Fadila ta nemi wuri ta zauna, ya ɗan dubeta ya ce "Da kika ƙara shekara a duniya, kuma kika kama hanyar komawa ga ubangijinki, wace Addu'ar ki ka yi?" Fadila ta ɗan taɓe baki ta ce "Wace Addu'ar kuma?" "Au ke baki Addu'a ba, sai iyayi" "Ba wani iyayi, family and friends sun yi wishing ɗina, that's all" Yazid ya ce "No, yakamata ki roƙi Allah gafara, ki yiwa kanki kyakkyawan fata a cikin abin da ya rage miki a rayuwarki, kiyi Addu'a a kan karatunki, da kuma fatan Allah ya kawo miki abokin rayuwa na gari, wanda yake sonki" Ta ɗan kalleshi ta ce "Waye abokin rayuwar?" "Miji mana, na gari mai sonki saboda Allah, ko da kuwa Kankiya ne" Haɗe rai ta yi, ta ce "Wai sau nawa zan gaya maka, kar ka sake haɗani da mutumin nan, bana son irin haka na gaya maka" Yazid ya ce "Ikon Allah, to ke haka ake yi? Ba Addu'a nayi miki ba, ai idan kana neman azaɓin Allah, barwa Allah komak ka ke, baka zaɓe-zaɓe" "Over my death body in auri wanan mutumin mara tunani" Da sauri Yazid ya ce "Subhanallah, Ukty malaminki ne fa" Ai tamkar da kankiyan take magana, ta ce "And so what? Ko na rasa mijin Aure ni ba ajinsa ba ce, yana rayuwa kamar wani bagidaje da bai san meya ke yi ba, a haka zan so shin?" Jikin Yazid yayi sanyi, Kankiya ma kenan, da ya na ɗaukar wanka, ina ga shi, da kayan sawarsa ma ba su fi a ƙirgasu ba. Har tayi shiru ta cigaba da mita, "Allah na tuba, ko a ƙafata a ka ɗaura mini shi ba sai na kwance shi na yar ba, kai mini wata Addu'ar banda Wannan, ni waima waye ya ce maka zan yi Aure ne? Da in yi Aure da kar in yi duk normal ne" Yazid yayi murmushi ya ce "A hakan da kike?" Ta ɗan kalleshi da mamaki ta ce "Kamar yaya a hakan da nake?" Ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa ya yi ya ce "Bar zancen, amma kina buƙatar abokin rayuwa na gari, ai kin kai girman da kin zama mutum 'yar yarinya" "Haka nace maka?" "Ko baki faɗa ba yanayinki ya nuna Besty, anyway mu bar wannan maganar, Allah ya baki miji nagari, ko da Yazid ne" Da wani irin sauri ta kalli Yazid, tare da yamutsa fuska kamar wadda ya gayawa saƙon mutuwa ta ce "What? Wane Yazid ɗin?" Tayi maganar babu alamar wasa a tare da ita. "Kai bari kaji in gaya maka, tun wuri ka mayar da hankalinka, am still the Fadila you know, kawai naga rashin dacewar wulaƙancin da nake maka ne, ya sanya nake kulaka, kan ka yiwa kanka fatan zama mijina, Yakamata ka san waceceni, ba sa'arka ba ce ni, we are just friends, tun da abin da kake tunani kenan, friendship ɗin ma is over now, Fadila ba matar ire-iren mutane kamar baka ce". Yazid yayi shiru, bai taɓa zaton Fadila zata yi masa haka, ta bishi da wanan kausasan kalaman ba, tun ma bai kai ga furta cewar yana sonta ba, matuƙa kalamanta sun tsaya masa a zuciyarsa. Ita kuwa tana gama yanka masa wannan maganganun, ta tashi ta bar wurin da yake. Ya bita da idanuwa, yana jin zafi a ransa. Ko da yake maganganun Fadila suna bisa turba, ita ba sa'ar aurensa ba ce, matsayinsa da nata ba ɗaya bane ba, amma idan aka duba matakan addini, yana da duk wani qualities da za a aureshi domin su. Shiru yayi yana jin yadda duniyar ta yi masa zafi, yana ji a ransa dama bai yi mata wannan maganar ba, da wataƙila sun cigaba da gaisawa. Gaba ɗaya Ajin ta bari, ta tafi department ɗin su Yusra, tana zuwa ta tarar da malami a ajinsu Yusra, dan haka ta jira sai da suka kammala lectures, malamin ya fita, sannan ita kuma ta shiga ajin. Yusra ta kalli Fadila da ɗan mamaki a fuskarta ta ce "Girl ya dai? Na ganki rai a ɓace". Fadila ta zauna tana ɗan hura hanci. "Ke wai meye ne?" Yusra ta faɗa tana sake tattara hankalinta a kan Fadila. "Kin san wani abin takaici da raini?" "A'a sai kin faɗa" "Yazid fa sona yake" ta faɗa cike da takaici. "Au da da nake gaya miki baki yadda ba? Me yayi miki ne?" "Wai Allah ya bani miji nagari ko shine" Yusra ta kwashe da dariya ta ce "Gaskiya Fadila baki da wayo, ke ce baki da tunani wasu lokutan, idan ba sonki yake ba mai zai saka yayi ta bibiyarki har ya dinga taimaka miki, yayi ta miki abubuwan da zai burgeki" Fadila ta ɗan yi shiru ta ce "Lalli bani da hankali, kawai na ɗauki alaƙarmu ne a friendship, ni mai yasa mazan nan suka rainani, amma Yazid tsaurin idonsa ya kai in da ya kai, ina shi ina mace kamar ni?" "Kar ki cika baki malama, tun da ya fara bijirowa a mafarkanki da kika gaya mini, akwai alamar cigaba da tarayyarku ka iya sanyawa ki fara son shi, saboda gayen yana da kirki sosai" "Ashe kuwa da Mummy ta kwaɗani ta cinye, kin san a tashin hankalin da Yaya Khalil yake dan ya ce yana son mai awara, hmm naga wautar Yaya Khalil" Yusra ta ce "Ikon Allah, shi kuwa Yaya Khalil meya yi masa zafi?" "Oho masa, duk yadda suke da Mummy,tayi masa fata fata, ko cikin gida ba ya iya shigowa, ba kiga ko jiya bai shigo wurin birthday na ba. Ina gama alhakinki ne" "A'a kar ki ce haka Fadila, Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi" "Amin dai, da nazo na gaya miki maganar nan har naji sanyi, ni wallahi tausayi yake bani ma, Kankiya ya sako shi a gaba da yawa a kaina, ni kuma bana son a lalata masa karatunsa saboda ni, amma shi ma Kankiya tara sh nake, idan ya kaini bango sai ya rasa aikinsa wallahi" "A'a Fadila ki bi a hankali dai" "Ai a hankalin nake bi, ke kin san da ba a hankalin nake bi ba, Kankiyan shi da koyarwa a jami'ar nan har Abada, banda ke babu wanda ya san abin da ke tsakanina da shi, sai Yazid, shi kuma wannan ko ban gaya masa abu ba, ganowa yake kamar aljani" Yusra ta ce "Do you know one Funny thing? Kin iya faɗar sunansa wallahi, har wata madda kike Yaziiiid" Tsaki Fadila tayi ta ce "Ke bana son wulaƙanci, bana son duk wani abu zai sake haɗani da shi, kowa yayi rayuwarsa kawai". Yusra ta ce "Shikenan, tunda kin huce yanzu a kan yadda kika zo mini" "Bari kawai ya ƙular da ni ne, da wani shegen takalminsa irin na danƙon nan, sai uban saka jallabiya kamar limamin harami" Yusra ta kwashe da dariya ta ce A'a kar ki zafafa dai" Fadila ta kai kusan twenty minutes tare da Yusra, sannan ta koma department ɗin su. Da idanun Yazid ta fara cin karo, kallo ɗaya zaka yi masa, ka gane jikinsa yayu sanyi, guntun tsaki tayi ta wuce wurin zamanta. Ƙarfe biyu daidai, aka tashi daga makaranta, Amina tayi sallama da 'yan ajinsu, ta fito gate. Wata uwar mota ta gani a bakin gate ɗin makarantar ta su a tsaye, da wasu 'yan sanda biyu a jikin motar. Bata kawo tunanin komai a ranta ba, ta cigaba da tafiya. Ji tayi kamar ana binta a baya, ta waiwaya taga 'yan Sandan sun biyota. Gabanta ne ya faɗi , tana sake dubwa taga wa suke bi. Ɗaya ɗan sandan ya ce "Amina ko?" Idanuwa waje Amina take binsu da kallo, tana tunanin meye haɗinta da 'yan sanda suka biyota makaranta. "You Are under Arrest!!!" AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM AYSHERCOOL PAGE 39 Ƙara waro manyan idanuwanta ta yi ta ce "Arrest for what ni Amina?" Tayi maganar bakinta na rawa. "Arrest by Alhaji Ahmad Dutse order" ɗaya ɗan sandan ya faɗa yana murmushi. Sai kuma tayi saroro tana binsu da kallo, dan ta kasa fahimtar kan lamarin gaba ɗaya. "Kinga Kwantar da hankalinki, baki gane ni ba ne?" Yayi maganar yana nuna kansa "Ni ban taɓa ganinka ba balle in gane ka" ta faɗa hawaye na taruwa a idonta. "Ranar da kuka zo gidan Alhaji Ahmad ke da shi, muna aiki a gate ɗin gidan, ai ni na ganeki shi ne ya ce mu zo mu ɗaukoki, ya aikemu ne ya ce mu biyo mu ɗauke ki" "Taɓ aikuwa ba zan biku ba, ku 'yan sanda abin yarda ne? Haka kawai ku sani a motar 'yan sanda kamar wata ɓarauniya, naga ai da kansa yake zuwa ya ɗaukeni wataran" Ɗan sandan ya kalli motar da suka zo da ita, helux ce me baƙin glass, ya sake dubanta ya ce "Lambar motar ta aiki ce, ba tamu ce ta 'yan sanda ba, ta Alhaji Ahmad ce, kuma ba sace ki za muyi ba" Amina dai cike da tsoro ta ce "Kunga, ku gaya masa mu haɗu a gida, amma ni ba zan hau motar 'yan sanda ba, kalli jikinku da kaki, kawai idan na shiga ku wuce dani prison" Ɗaya ɗan sandan dai mamakin ƙarfin hali, da kuma taurin kan Amina yake, ɗayan kuma sai lallaɓata yake. "Kinga bari in kira miki shi a waya" "Aiko shi zaka kira nan wurin ba zan hau mota da 'yan sanda ba" ta faɗa tana duba hanyar da zata bi ta gudu. Wayarsa ya ɗan danna, Sannan ya saka a kunnensa. "Yauwa barka dai yallaɓai, gamu a ƙofar makarantar, mun zo ɗaukanta, amma ta ce ba zata hau mota ɗaya da mu ba, infact ma bata yadda kai ka turo mu ba" Daddy ya ce "Na san a rina, bata wayar" Ɗan sandan ya kalleta ya ce "To kinga, ya ce a baki wayar kuyi magana" A ɗan tsorace ta kalleshi ta ce "To idan na karɓa nayi maganar, zaku barni na tafi?" "Eh, sai abin da ya ce dai" Kamar wadda ake miƙawa kashi, haka ta karɓi wayar, tana Addu'ar Allah ya sa ba tana Magana wani abin zai sameta ba, ko matsafa ne. "He..h....hello Daddy" "Mmwummm" shi ne abin da ya faɗa daga cikin wayar. Kamar mai tsoron magana ta ce "Daddy kana jina?" "Mmm" "Daddy dan Allah kayi magana, wasu ne wai zasu tafi da ni in jika" "Baki iya sallama ba sai Hello?" Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa a kan kujerar 3seater. "Yi haƙuri a tsorace nake ne, 'yan sanda ne fa suka zo zasu tafi da ni" "Eh laifi kika yi, na turo su su kamo mini ke" Zaro ido tayi kamar tana gabansa ta ce "Laifi ni ɗin, me nayi da zaka haɗani da police?" "Sai sun kawoki zaki ji laifin da ki kayi, idan kuma kika cigaba da yi musu gardama, za su saka miki handcuff su sako mini ke a motar su kawoki". "Na shigesu ni Amina, 'yan fashi fa ake sawa wannan sarƙar, dan Allah kayi haƙuri" tayi maganar cikin shagwaɓa tana marairaicewa. "Oya, ban da gardama ki biyosu ni na turo su" Jiki a sanyaye ta ce "To" ta miƙawa ɗan sandan waya, ta bisu, suka buɗe mata mota, ta shiga suka ja suka tafi. Gaba ɗaya zatonta gidan da suke zasu tafi, amma taga sun sauya hanya. "Bayin Allah ya haka?" Ta faɗa tana waige waige. "Meyafaru?" Cewar ɗan sandan da ya haɗata da Daddy a waya. "Naga mun tafi wani wurin daban, ba Tudun yola zamu ba?" "Ba nan zamu ba, gidan da kuka je tare ya ce a kaiki" "Na shiga uku ni Amina" ta faɗa a hankali, tare da sallama cewar wani aikin zai kuma sakata yauma, gashi ta gaji matuƙa yau ɗin nan. Tana ta zancen zuci, har suka isa gidan, parking suka yi a cikin gidan, wurin ajiye motoci, Amina yau har da motocin da bata gani ba wacan karon ta gani yau, har mamakin yadda Daddy yake yi da motoci take. Suka buɗe mata ta fito, ta ɗaga kai ta kalli gidan sannan ta ce "To yana ina Daddyn?". "Ki shiga, yana ciki" "Ciki ina kenan?" Ɗan sandan ya fara ƙufula da surutunta da tambayoyi, amma ya daure ya ce "Hanyar da kuka shiga wancan karon, ita zaki bi. Cike da fargaba da salati, Amina ta nufi hanyar da suka bi tare suka shiga gidan a wancan karon. Babu kowa a makeken falon, sai dai ko ina fes da shi. Ko yana ina oho? Ta tambayi kanta da bawa kanta amsa. Wata siriryar hanya ta bi, zuwa falon da ya saka ta jera Abinci ranar da yayi baƙi. Ta tura ƙofar ta shiga, ya ɗago idonsa ya kalleta a cikin uniform ɗinta, riga da skirt sun mata kyau sosai, sai uwar jakarta ta goyo. Shi kuma yana sanye da yadi mai taro taro maroon, kansa babu hula, yana shan ruwa a kofi. Girmansa da kwarjininsa suka cika mata ido, ta ƙarasa cikin falon, ta durƙusa ta ce "Ina wuni?" "Ban ganshi ba" ya bata amsa. Ɗagowa tayi tana mamakin irin amsar da ya bata. Ya ɗan ɗage mata gira ya ce "Yes, ban ga yini ba, ko in ce yana gidan biki ko?" Amina ta sunkuyar da kai, saboda haka kawai take jin ta takura, wannan keɓewar tasu bata dace ba. "Na saka an kamo mini ke, saboda laifin da kika yi mini". "Laifi kuma?" Tayi maganar a ɗan raunane. "Eh laifi mana, ai ke ba kya daina laifi, na fuskanci kina da taurin kai" Amina tayi shiru tare da sunkuyar da kanta ƙasa, dan ita dai bata san laifin da tayi ɗin ba. "Me nace miki game da tsaya da wani, dan tsabar rashin ji kuma a titi, zaki tafi makaranta" Sai yanzu ta tuna, da safe ya gansu tare da Bilal, ta ɗago ta ce "Daddy tsaya ka ji nayi maka bayani" "A zaune nake ai, ba wani bayani da zaki yi mini, ba kya jin Magana ne kawai, kuma zan gayawa Malam Hassan ɗin abin da kike" Ta marairaice ta ce "Ka tsaya ka ji dan Allah, wallahi shi ne ya biyoni wai sai ya rakani, ai kaga ba zan kore shi ba, wulaƙanci babu kyau" Alhaji Ahmad ya gyara zamansa ya ce "Ni meye ya hana ki nemi in rakaki?" "Ni a wa? Ni dai dan Allah kayi haƙuri, ka sa a mayar da ni gida" "Aminatu ba kya ji sam, sai na ɗau mataki a kan abin da kika yi" "Wallahi Daddy ina ji, kayi haƙuri, ni ban san ya zan masa ba, amma zan gaya masa ka ce kar ya sake shiga harkata" Kan Alhaji Ahmad yayi magana, aka kira shi a waya, ya sa hannu ya ɗaga wayar, ya kai kunnensa. Ba ta jin me ake cewa daga cikin wayar, ta dai ji yana cewa "Jiki Alhamdilillah, ya yi sauƙi jinin ma ya sauka, shi ma sugarn nawa ya sauka sosai" Amina dai ta sake gyara zamanta, tana ɗan satar kallon Alhaji Ahmad. "Eh, da ina tunanin zan ɗan je wata ƙasar in ɗan huta, amma a yanzu na samu wata Cartoon me Sani nishaɗi" Dariya yake sosai a wayar, sannan yayi sallama da wanda suke wayar, ya ajiye, ya kalli Amina a ya ce "Oya, a ɗan sama mini abin da zan ci, kan ki tafi" Ɓata fuska Amina ta yi, ta ce "Dan Allah Daddy..." Sai kuma tayi shiru. "Ina jinki" ya faɗa yana danna wayarsa. "Kaga Baba bai san ina nan ba, kuma ni Hajara tabi ta saka mini ido, gani take wani abu ne a tsakanina da kai" "Wani abu kamar me?" "Ranar fa da ka ce in kai maka shayi na daɗe, bina ta dinga yi tana tambayata wai ya aka yi na daɗe, da ranar da ka ce ba zan tayata aiki ba, duk ta bi ta saka mini ido, ita ma ka dinga sakata aiki kar ta zata da wani abu a tsakanin mu" Dariya ta ga yana yi, ya ce "Akwai wani abu a tsakaninmu mana, tsoron me kike ji?" "Ni meye a tsakaninmu?" Ya ɗan yi murmushi ya ce "Kinga, yanzu dai tashi ki je kitchen, ki sama mini wani abun in ci" Ɗan tsuke fuska tayi, tana jin Daddy ya takurata. Daddy ya ɗan zuba mata ido ya ce "Ko in haƙura?" "A'a zan yi" ta faɗa a sanyaye. "Yauwa Cartoon ɗin Daddy, a taimakawa Daddy" "Cartoon kuma?" Ta faɗa tana ɗan tura baki. "Eh mana, tashi da sauri, dan ki kammala da wuri mu tafi gida" Amina ta ajiye jakarta, ta nufi kitchen, sai da ta ɗan tsaya tana tunanin mai zata girka, wanda zai iya ci saboda ciwonsa. Ta cire ƙaramin hijjabinta ta rataye ɓalle rigar saman ta rataye, ya zama daga ita sai rigar uniform ta ciki, da skirt ɗinta, sai kuma hular hijjabin, kana ganin gashinta da ta ɗaure da ribbon. A nutse ta fara gudanar da aikinta, tamkar tana kitchen ɗin gidanta. Gaba ɗaya Yazid bai fahimci lectures ɗin yau ba, saboda yana cikin damuwa, yayi mamakin abin da Fadila ta gaya masa, bai taɓa tunanin jin wannan maganganun daga bakinta ba. 'banda abinka kai ma Yazid me ya aikeka, ina kai ina ina wannan yarinyar, suturar da take sawa kawai, ta isa ta nuna maka ruwa ba sa'an kwando bane' wata zuciyar ta tunasar da shi. Haka nan jiki babu ƙwari, ya ja jiki yaje yayi sallar azahar, daga nan ya wuce gida. Khalil kuwa tun da Allah ya sanya ya sauka a garin Abuja ƙarfe tara na safe, ya wuce gidan da yake zaune a can garin Abujan, ba im da ya kuma fita ya je, sala ce kawai take fito da shi daga gidan, ko Abinci ya kasa yin order ya ci, loka lokaci ya kan buɗe saƙonnin Hafsa da take turo masa a baya, da hotunanta ya zuba musu ido. Maganganunta ha dinga tunawa, da take jadadda masa na ya riƙeta da amana. Har ga Allah ya ci burin auren Hafsa ya zauna da iga saboda Allah, ya sama mata farinciki, amma Mummy ta ɓata komai, babu Wanda za aayi masa abin da Mummy ta yiwa su Hafsa ya iya haƙuri, sai dai idan ba shi da zuciya. Duk yadda Khalil ya so ya yi tunanin mafita kasawa ya yi, ƙarshe ma kansa ne ya fara ciwo, amma ya kasa yadda zai iya cigaba da rayuwa ba tare da yana cigaba da magana da Hafsa ba, ya ɗauki wayoyinsa duka ya kashe su, ya ajiye. Amina ta gama girki, sai aikin yanka salak da take yi, tana ta decoration ɗinsa a tray. Ji tayi kamar motsi a bayanta, ta juyo gaba ɗaya dan ganin meke motsi a bayanta, sai taga Daddy ne ke shigowa. Tsananin kunya ce ta kama Amina, saboda jikinta babu hijjabi, sai rigarta ta uniform 'yar ciki, kuma rigar ta kama jikinta sosai. Da sauri ta kai hannu tana kare ƙirjinta, ta juya da sauri, sai kuma ta tuna shi kansa skirt ɗin a matse yake, kuma tayi stock in ɗin rigar. Murmushi Daddy ya yi, ya nufi fridge ɗin kitchen ɗin, still Amina ta kasa sakewa, sai ɓoye ɓoye take. Muryar Daddy ta jiyo yana cewa "Me kike ɓoyewa ne? Ai ni ba ke nake kallo ba, na gaji da jirane na zo na ɗauki fruit ne, ina jin yunwa sosai". Kunya ce ta sake kama Amina, har ta kasa cigaba da abin da take yi, dan bata taɓa zaton jin hakan daga bakin Daddy ba. Ai bata gama tunanin ba ta ji shi a tsaye a bayanta, ji tayi tamkar ƙasa ta tsage ga shige dan jinta take a wani yanayi da ta kasa tantance wane irin yanayi ne haka. Gaba ɗaya ƙamshin turarensa ya cika mata hanci, idan tayi ƙwaƙwƙwaran motsi babu abin da zai hana jikinta ya haɗu da nashi. Miƙa hanunsa yayi, ya ɗauko wuƙa ɗaya a cikin jerin set ɗin wuƙaƙen, dake gefen Amina. "Calm down, ba taɓa ki zan yi ba, wuƙa zan ɗauka" ya faɗa a kunnenta a hankali. Ƙiri-ƙiri Amina ta kasa cigaba da aikin, saboda yadda Daddy ya hanata motsi. Ringing ɗin wayarsa ce ta cika kitchen ɗin, a tunanin Amina zai matsa ne, amma ga mamakinta sai taga bai matsa ba, ya ɗaga wayar ya sanya a kunnensa. "Hello Madam" ya faɗa yana kallon gashin Amina. "Kayi nisa ne" kasancewar Yana kusa da Amina, tana iya jin abin da ake cewa a wayar, jin muryar Hajiya Zainab a wayar ne ya sanya hantar cikin Amina kaɗawa. Daddy ya ce "Ya aka yi?" "Eh zan fita ne, idan ka dawo akwai Abinci a dining" Ya ɗan shafi gemunsa ya ce "Ba za'a jira in dawo ba?" "A'a sauri nake, ban san lokacin da zaka dawo ba" Atishawa ce ta ƙwacewa Amina, kan Daddy ya katse wayar, tana ƙarewa kuma ta ce "Alhamdilillah" sai kuma ta ɗan zaro ido, tuna waya Alhaji Ahmad ya ke. "Kai da waye ne naji kamar muryar mace" Daddy ya koma gefen Amina, ya ɗan kalli Amina sannan ya ce "Na je wurin Alhaji Sambo ne, ma'aikatansa ne" Hajiya Zainab ta ce "But it seems that you are so close to the lady that sneeze" "And who told you she is Lady? Sakatariyarsa ce ta shigo Office ɗin" "Take care" ta faɗa cikin isa ta katse wayar. Ya zubawa Amina ido, ta ɗan ɗago ta kalleshi, ta mayar da kanta ƙasa. "Kin sani ƙarya, Shi ne kika ƙaƙalo atishawa ki ka yi, dan ta san muna tare ko?" Amina ta ce "Ni ba ƙaƙalowa nayi ba, zuwa tayi" "Yanzu idan nace miki ƙazama ki ji haushi, a kan Abinci na kika yi atishawa ko?" "A'a, ai na kawar da kaina, kuma kai ne ka ke wurin shiyasa ban matsa ba" "Yarinya idan asirinki ya tonu a wurinta, kina bibiyar mijinta sorrynki Amintako" Amina ta ɗan tura baki ta ce "Ni mai zan yi da mijinta? Kuma ai bani na kawo kaina ba, kai kace a ɗauko ni" "A'a yarinya faɗi gaskiya dai, kina bibiyar dattijon mijinta, ba ruwana ni" "Taɓ, ni mai zan yi da tsoho? Ni yaro zan aura" "Haba?" Daddy ya faɗa yana kai ayaba bakinsa. Ta jinjina masa Kai. "Lallai kin samu kanki, da Allah bai sa kin auri Jarmai ba, dole ki faɗi haka" Waro idanunta Amina tayi ta ce "Daddy ina ka san Jarmai?" "Ina ruwanki matar yara, ƙarasa mini aikina, yunwa nake ji sosai fa" Ya juya ya bar kitchen ɗin. Mamaki ne ya cika Amina, ya aka yi Daddy ya san Jarmai. Ta tsaya ta saka rigarta ta uniform, da hijjabinta, ta dinga kai kayan Abinci tana kaiwa gaban Daddy tana ajiyewa. "Ƙarasa ladanki mana, ki zuba mini" Amina a ɗarare dai ta zuba masa shinkafa kaɗan, ta zuba masa ganye cikin plate. "Wow, kina kula da dattijon nan sosai, God bless you dear" Ita dai Amina ta takure, tana jiran ya gama, ya bata umarnin tafiya, dan ta gaji da zaman nan. "Matso muci tare" Amina ta girgiza masa Kai "Na ƙoshi" "Aikuwa ba zaki tafi gida ba, muna nan zuwa bayan sallar isha'i" Amina ta marairaice ta ce "Dan Allah Daddy kayi haƙuri, ban san me zan gaya wa Baba ba". "To matso mu ci Abinci" "Wallahi Daddy ban taɓa cin Abinci da wani a kwano ɗaya ba, ba zan iya ba" ta faɗa a rikice. "Aminatu kenan, wasa nake miki, wannan rikicewar taki ce ke sani dariya. Amaryar Jarmai" "Dan Allah Daddy a ina ka san Jarmai" "Ina ruwanki? Juya ki daina kallona kar in ƙware" ta juya masa baya, ta daina kallonsa kamar yadda ya buƙata. Tana juya baya ya dinga mata dariya ƙasa-ƙasa, gaba ɗaya ya rikita ta lokaci guda. " 'yar Daddy" ya kirata. Ta waiwayo ta ce "Na'am" "Abinci yayi daɗi, Daddy ya gode sosai, zo ki ci naki" "Daddy na ƙoshi, gida nake so na tafi" "Sai kin ci Abinci zamu tafi, tafiyarku Abuja saura 2weeks, dan haka kan nu tafi zaki je garinku" "Me zan yi a ƙauyen? Tsoro nake ji kar ina zuwa su Baffa Lawan su riƙeni suce saina Auri Jarmai" "Idan har ina raye, ba wanda ya isa aura miki wanda ba kya so, zaki je ne dan ki musu sallama, kinga zaki tafiya mai nisa ne, zan saka Zakiru ya kai ki ki musu kwana biyu a dawo mini da ke" "To kun yi maganar da Baba ne ya yadda da tafiyar?" "Ba ruwanki da wannan, nace ki bar wannan maganar a hannuna ai" Amina tayi murmushi ta ce "To Daddy, na gode Allah ya saka maka da alkhairi" "Ameen Meenalin Daddy, nima na gode sosai kina kula dani da lafiyata, duk da ƙalubalen da kike fuskanta a gidana, ki cigaba da haƙuri watarana sai labari kin ji" "To Daddy" "Yau, ci Abinci sai mu tafi gida, zanje in yi sallar la'asar, kwanukan kuma da komai ki bari za a gyara" Ta jinjina masa kai, shi kuma ya miƙe ya bar ɗakin. Ta zuba Abinci ta ci, ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, dama tana fashin salla, dan haka ta zauna zaman jiran dawowar Daddy. Alhaji Ahmad na shigowa, Amina ta tashi tsaye, tana ƙoƙarin ɗaukar jakarta. Daddy ya kalli fuskarta, ya ce "ya na ganki a tsayem" "Ba tafiya zamu yi ba?" "Ban gama abin da nake ba" ya faɗa yana kallon agogon hannunsa. Amina ta kwaɓe fuska ta ce "Haba Daddy, lokaci ya ƙure fa, huɗu fa" kallon yadda take maganar tsakani da Allah yake, wanda gaba ɗaya shagwaɓa take yi. "Let me see your bag" yayi maganar yana miƙa hannunsa. Fuskarta babu daɗi, ta miƙa masa jakarta. Ya karɓi jakar ya nufi wani ɗakin. Kwaɓe fuska Amina tayi, ta samu wuri ta zauna, gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci, so take ta tafi gida duk ta gaji, kawai ta ji wata irin ƙwalla ta taru a idonta. Bai wani jima ba ya fito hannunsa ɗauke da jakar, ya nufo im in da take a zaune ta takure tana zumɓura baki. " 'yar Daddy, kin gaji ko?" Ta ɗaga masa kai. "To tashi mu tafi, am sorry" ya faɗa cikin sigar rarrashi. Ta tashi tsaye, ta ce "To Bani jakar" "A'a bari in riƙe miki muje" Amina ta ɗan kalleshi ta ce "A'a Daddy ai bai kamata ba" Daddy ya yi gaba yana faɗin "To me is normal" Amina ba ta da zaɓi sai na bin bayan Daddy. Bayan fitowarsu ma'aikatan gidan suka nufo su suna masa barka da fitowa. Gaba ɗaya sai ya sauya ya koma Alhaji Ahmad ɗinsa, kamar ba shi ne wanda ya gama zolayarta a ciki ba da suna su biyu. Ya kalli wani daga cikin ma'aikatan ya ce "A shiga a gyara kitchen da sauran abin da aka yi amfani da shi" "Ok sir" Alhaji Ahmad ya buɗe motar, ya saka jakar Amina a ciki, Sannan ya kalleta ya ce "Bismillah" Amina ta shiga ya rufe ƙofar, sannan ya zaga ya shiga motar shima. Amina ta jingina da jikin kujera ta ce "Washhh Allah" "Sorry kin gaji ko?" Jinjina masa kai kawai tayi, tana sake lumshe ido. "Daddy" ta kira sunansa. "Meenalin Daddy" ya amsa yana tuƙinsa cikin nutsuwa. "Meyasa ka bawa Baba kuɗi ya dinga bani, yana zargin ni na roƙeka fa" "Ai na gaya masa baki roƙeni ba, ni nayi niyya kawai na bayar nace ya dinga ƙara miki in zaki makaranta, bana son na baki ni da ke, na san ba zaki karɓa ba, kuma bana son wani zargi ya shiga, shi ya sanya na bashi, kuma ai ba kuɗi me mai yawa ba" "Amma meyasa ba ka bawa Hajara sai ni?" Tayi masa tambayar a bazata. Kallon Amina ya yi ya kawar da kai bai yi magana ba. "Daddy ka amsa mana" "Bana son yawan tambaya fa, matsayin Amina daban a wurina, ita ma matsayinta daban" Amina ta ce "To meye banbancin matsayin namu ne? Naga duk masu aiki ne a gidanka" "Ki ƙyaleni" ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. "Dan Allah Daddy" "Kin raina ni ko? Ni kike titsiyewa hakam" Da sauri ta ce "A'a" "Baki san da wa kike tare ba ko? To idan nace bana son abu, bana so" "To Allah ya baka haƙuri Daddy, ba zan sake ba in sha Allah" "Good girl" Ga mamakin Amina, Yau Daddy bai ajiye ta a ƙofa ba, sai da yaje bakin gate ya fara horn. "Daddy bari in sauka mana" ta faɗa tana ɗaukar jakarta da taji ta ƙara nauyi" "A'a sai mun shiga nayi parking" yayi maganar yana horn. A ɗan rikice ta ce "Daddy kar Baba ya ganni, ko Hajiya fa". "Ki tanadi abin gaya musu" maganar ta sa tayi daidai da buɗe gate da Zakiru yayi maimakon Baba ya buɗe. Gaba ɗaya Amina ta rikice, sai dai ba taga Baba a harabar gidan ba, Alla Alla take yayi parking, ta fito kan wani a gidan ya ganta. Bayan Daddy yayi parking, cikin hanzari Amina ta fara ƙoƙarin buɗe motar, amma taji a rufe. Tana waiwayowa ta kalli Daddy, taga ya kashe motar yana dariya. "Daddy dan Allah ka buɗe, kar Hajiya ta ganmu" "Kamar kin san idan ta ganki kece a ciki, ni ba ruwana" "To ka buɗe mini dan Allah" "To ka buɗe mini dan Allah" ya kwaikwayi muryarta da tuni ta samu rauni, kamar tayi kuka. Murmushi ya cigaba da yi yana kallonta, sai da yaga idanunta sun ciko da hawaye, sannan ya cire motar daga lock. Da sauri ta fita daga motar, tana ɗan leƙa wurin zaman Baba, ko zata hango shi a wurin. Daddy ya rufe motar ya ce "Ki nutsu, Baba baya nan wadda kike tsoron ma haka, ko kin manta muna tare ta mini waya?". Ajiyar zuciya tayi ta ce "Na manta ne, ina tsoron ta mayar da ni ƙauye in rasa karatuna, dan da na yi laifi sai a fara cewa za'a mayar da ni ƙauye". "Allah ya sa ta jiki, zaki yi mata bayani dalla-dalla" "Allah yasa na sauka daga motarka, balle in faɗi wani abu ka saukeni a hanya, da wani abu zan faɗa" "Aminatu kin raina Daddy fa" "A'a ban raina Daddy ba, Daddy yana da kirki ne sosai, ba kamar..." Sai kuma tayi shiru. "Ba kamar wa ba? So kike muyi faɗa ko?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. Hajara ce tayi turus a falo ganin Amina da Alhaji Ahmad tare, da alama tare suka shigo. "Idan ba kya son muyi faɗa, to ki kiyaye abin da zan yi fushi" "To na daina" Ya jinjina kai ya ce "Go and have rest, see you later" Baban abin da ya bawa Hajara mamaki shi ne, yadda ganinta bai sa sun farga sun daina hirar da suke ba, cike da wani yanayi da ta kasa fassarawa. Daddy ya nufi hanyar sashinsa, Hajara ta risuna tana "Barka da zuwa" ɗaga mata hannu kawai ya yi, fuskarsa a haɗe, kamar ba shi ne ya gama ƙarewa Amina kallo yana murmushi ba. Waiwayowa tayi ta kalli inda Amina take, Amina ta kalleta sama da ƙasa, ta nufi na su sashin, sai kuma ta tsaya ta kalli Hajara ta ce "Kiji ki ƙi ji, ki gani kuma ƙi gani, idan ki ka matsa kuma hmmm" sai tayi murmushi kawai ta wuce Hajara, ta barta a tsaye sororo tana kallon Amina. AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM AYSHERCOOL AREWABOOKS AYSHERCOOL7724 WATPAD AYSHERCOOL 7724 40 Saroro baki buɗe, Hajara tabi Amina da kallon mamaki, gaba ɗaya gani take kamar ba Aminan da ta sani ba ce, wani ɓoyayyen abu take gani a kan fuskar Amina mai kama da ƙudurin da zata iya jurewa kowace irin barazana. Banda haka, ta yaya zata shigo falon matar gida tare da maigidan cikin wani yanayi da haryanzu ta rasa muhallin da zata saka shi. Soyayya ce kenan? Ta tambayi kanta. 'a'a ba zai taɓa yiwuwa ba, mutumin da yake aiki a wani gari daban gari mai cike da goggagun mata masu ji da kansu, mai ɗumbin dukiya mai tarin yawa, ta yaya zai ɓige da son 'yar cikinsa, 'yar cikin nasa kuma mai aiki 'yar ƙauye?. Sukuku haka Hajara ta bi hanyar da Amina tabi, tana tunanin yadda zata samo zaren labarin, ta gane a wani ma'auni zata ajiye alaƙar Amina da Alhaji Ahmad. Cike da tsananin gulma da take cin Hajara, ta bi Amina ɗakinta, ta tarar da Amina ta cire uniform ta ɗaura towel zata shiga wanka. Hajara ta kalli Amina tana ƙaƙalo murmushi ta ce "Wai nikam Amina, ban gane me kike ce mini ɗazu ba, naji kamar wata karin magana ki ka yi" Amina tayi murmushi ta ce "Idan baki gane ba, ki barshi a haka kawai" "Ba zaki mini bayani ba kenan, yau naga kin daɗe a makarantar" "Eh, ai kin san muna zama yin lesson, shi ya sanya" Hajara ta ce "Haka ne, tare kuka dawo da shi Alhajin kenan?" "Eh Hajara, tare muka dawo, yaje ya ɗauko ni daga makaranta ne, shikenan? Ina son zan shiga wanka" "To bari in baki wuri, Lallai Amina kin shigo gidan nan da ƙafar dama" Amina bata kuma saurarrta ba, ta shige banɗaki ta bar Hajara. Hajara ta riƙe haɓa tana sake jinjina kai, ga labari amma babu bakin bayarwa, dan ta san ko giyar karnuka ta sha, ba ta isa ta tunkari Hajiya Zainab da wata magana makamanciyar Wannan ba, dan ta san kome zai faru tare da ita zata kwaɓewa, to ta isa ma tayi wani yinƙuri na furta wani mummunan abu a kan maigida meye hujjarta?' A fili ta ce "Allah ma ya ƙara, ni tsorona Allah ya sa ba lalubeta yake yi ba, ita matar gida tana can gantali kamar 'yar akuya kullum tana tafe kamar iska" Ɓangaren Hafsa kuwa, ta rame tayi duhu, gaba ɗaya ta daina walwala, waccan rayuwar tata ta baya ta sake dawo mata sabuwa fil, cike da sabon salo mai ɗauke da ciwo irin na soyayya. Tun daga koke koken nan da tayi, take fama da ciwon kai, tayi ta ƙoƙarin kawar da tunani da damuwa da Khalil, amma abu ya gagara tun tana ɓoyewa kar Mama ta gane, har abu ya zo ya zarce mata da zaɓi mai zafin gaske. A hakan Mama ta gane, saboda ganin yawan kwanciyar da Hafsa take yi, ga rashin cin Abinci. Cikin dare Mama ta tashi, domin yin sallar dare, ama ta dinga jin sheshsheƙar kukan Hafsa, ta miƙa hannu zata yaye abin rufar Hafsa, amma taji jikinta zafi rau. "Hafsa meye haka? Meke damunki ne?" "Mama bakomai" "Kamar yaya babu komai, ji yadda jikinki yayi zafi, Hafsa kin ɗora kanki damuwa kina nema ki hallaka kanki, Hafsa ƙaddara ba zata samu bawa yayi tawakkali ba?" Hafsa ta ja jikinta da ƙyar ta zauna, ta ce "Mama ba laifina bane ba, kawai rashin lafiya nake yi" "Haba Hafsa, nifa na haifeki ba ke kika haifeni ba, na sani kin shaƙu da Khalil haryanzu kina son sa, amma ki cigaba da Addua, Allah ya kawo miki mafita, bana jin daɗin ganinki a wannan yanayin ko Abincin kirki ba kya ci, kuma ni baki gaya mini baki da lafiya ba" Hafsa dai tayi shiru, ba tace komai ba. "Tashi ki lallaɓa kiyo alwala, ki zo ko raka'a biyu kiyi, kiyi Addua Allah ya bamu mafita gaba ɗaya, ina da guntuwar gasara sai in dama miki kunu ki sha, sai in baki paracetamol" Cikin yanayi na jin jiki Hafsa ta ce "A'a Mama, dare yayi sosai, bari in sallar kawai" "A'a ba komai, bari in dama miki, yunƙura ki tashi" Hafsa ta yunƙura za ta tashi, ama jiri ya kwasheta ta koma luuuuu zata faɗi. Duk da Mama bata da cikakkiyar lafiya, haka ta yunƙura ta rungumo Hafsa, suka kusa faɗuwa. Cike da damuwa Mama ta ce "Hafsa har jikin naki ya kai haka?" "A'a Mama, jiri ne kawai ya ɗan ɗebe ni" Mama ta kama Hafsa ta zauna, sannan ta ce "Kinga zauna, bari in je in dama miki kunun, in baki maganin, zuwa in Allah ya kaimu sai mu tafi Asibiti". Hafsa ba ta ce komai ba, sai lumshe idanunta da ta yi, tana sake jin jikinta babu daɗi. Bayan sallar isha'i Amina tana ƙoƙarin buɗe jakarta ta ciro litattafanta, ta ci karo da tarin kayan ciye-ciye na biscuit da chocolate, da wani turare da kwalinsa kawai abin kallo ne, jan kwali ne kwalbar turaren ma ja ce, mai matuƙar ɗaukar hankali. Ta fesa turaren a hannunta ta sansana, wani irin sassanyan ƙamshi ne da turaren mai kwantar da hankali. Ko ba a gaya mata ba ta san turare ne mai tsada sosai. Murmushi Amina ta yi, tana sake jujjuya turaren da kallon tarkacen kayan ciye-ciyen. Wani murmushi Amina tayi, wanda ita kaɗai ta barwa kanta sanin ma'anar murmushin. Fadila kuwa a ɗakinta ta ci Abinci ita kaɗai, tayi wanka tana saka kayan bacci tana shafa mai, ta kalli turarukan wurin Yazid, ta zuba musu ido tana kallonsu tamkar Yazid ɗin take gani a wurin, tunani ta shiga yi a kan barkwancinsa, da yadda yake ta nuna mata kulawa daga fara shirin su zuwa yanzu, mutum ne mai haƙurin gaske da kawaici, ta tuno yanayin da ya shiga a lokacin da ta gaya masa tafi ƙarfin sa, har aka tashi jikinsa babu wani kuzari. Guntun tsaki tayi a fili tana tunanin sai me dan tayi masa warning a kan ya fita daga harkarta, ai ya san ruwa ba sa'an kwando bane, kuma kamar yadda Yusra ta gaya mata, sanyin halin Yazid da kyautatawarsa zata iya sawa ta fara son shi ba tare da shirya hakan ba, gara ma tun wuri ta raba gari da shi. Wayarta ce ta kawo haske, ta kalli in da wayar take taga message ne ya shigo, ta ɗaga wayar ta duba sai taga missed calls biyar, duk na Kankiya saboda wayar na silent bata san ya kira ba. Ta duba saƙon ta ga roƙonta yake wai yana son ta bashi dama ya zo gidansu. Dire wayar tai tana harar wayar tamkar ita ta turo mata saƙon, "Zan ɗau mataki a kanka, idan ya so ka yiwa Yazid ɗin abin da ka ga dama ku ta shafa" tayi maganar tana ƙoƙarin kauda wani abu mai kama da tausayi a ranta game da Yazid. Mummy ce ta faɗo ɗakin Fadila babu ko sallama fuskarta cike da damuwa. Fadila ta kalleta ta ce "Mummy ya dai?" "Kin yi waya da Khalil ne?" "Mummy wane Khalil kuma, wayar me zan yi da shi bayan yana gidan nan" Mummy ta ce "Khalil baya gidan nan, sai yanzu na farga, tun safe banga gilmawarasa ba, na duba babu motarsa, naje in tambayi wancan shashashan tsohon when last Khalil ya fita, amma na tarar baya nan, sai direban babanku ne ke buɗe gate ɗina, wai ya nemi iznin babnku ya tafi ƙauye, shi kuma bai san lokacin da Khalil ɗin ya bar gidan nan ba" Fadila cikin mamaki ta ce "Ikon Allah, to Mummy ki kira wayarsa mana" "Na kira taƙi shiga sam, gaba ɗaya hankalina ya ɗaga" "Ko ya koma wurin aiki ne?" Fadila ta sake tambaya. "To wa ya sani ne? Kuma sai ya koma wurin aiki bai mini sallama ba, yaya hakan zai yiwu, kar inje a sace mini ɗa a banza, sai sa na gaya wa babanku, ya samar muku da security, yawonmu haka a gari is not safe, duba sa matsayin da ya riƙe a ƙasar nan, amma ya ce mini no need, ai ga irnta nan" Fadila ta ɗanyi shiru sannan ta ce "Mummy, bana tunanin sace Yaya Khalil aka yi, wataƙila ya tafi wani wurin ne dan huce haushin abinda kika yi wa yarinyar da yake so" Cikin mamaki Hajiya Zainab ta ce "Kuma haka ne ko? Yanzu sai Khalil ya bar gidan nan ya tafi wani wurin ba tare da na sani ba saboda haka? Aikuwa idan haka ne da ya ci ubansa, sai na nuna masa nice uwarsa kuma dole ya bini" "Mummy kibi a hankali, kar garin neman gira a rasa ido" "Rabu dani da wata ido da gira, zan cigaba da bincikawa muddin na tabbatar haka ne idan bai yi wasa ba saina ci mutuncinsa". "Amma me Daddy ya ce?" "Rabu dani da Daddyn nan na ku, nayi masa Magana amma bai mayar da abin serious ba, wai Khalil ba yaro ne ƙarami ba, duk in da yaje zai dawo kar in damu kaina" "Mummy, gaskiya Daddy ya faɗa, ki kwantar da hankalinki zuwa Allah ya kaimu da safe mu ga yadda hali zai yi" Jinjina kai Mummy ta yi ta bar ɗakin Fadila, gaba ɗaya ta rasa nutsuwarta saboda rashin sanin halin da Khalil yake ciki, da kuma a ina yake, ta ɗora alhakin duk wannan abun a kan Hafsa, wadda take can tana fama da kanta. Da safe wajen ƙarfe tara na safe, Mama ta shirya ta dafawa Hafsa ruwan wanka, da ƙyar Hafsa ta rarrafa tayi wanka, kasa cin Abincin ma ta yi, Mama ta taimaka mata, ta shirya suka tafi Asibiti. Tashin farko teses kawai sun yi na dubu biyu aka rubutawa Hafsa, aka yi mata likita ya tabbatar da jininta ya hau, ga malaria mai zafi da ulcer. Mama ba tayi mamaki ba jin Hafsa tana da hawan jini, likitan ya ɗan nazarci fuskar Hafsa sannan ya ce "Ƙanwata meke damunki a 'yan shekarunki kika kamu da hawan jini, jininki ya hau fiye da yadda za a iya cewa ko zafin zazzaɓin ne ya sanya jinin ya hau" Hafsa ta sunkuyar da kanta, tana muza yatsunta na hannu. "Magana fa nake" ya sake maganar yana ɗan dukan teburin gabansa. Hawaye ne ya taru a idon Hafsa, Mama ta ce "Likita rabu da ita kawai, duk saboda ta rabu da wani saurayinta, shi ne ta saka kanta a uku, nayi nasihar nayi rarrashin amma ta saka abin a ranta" Likitan ya ce "Mahaifiyarta ce ke ko yayarta?" Mama ta ce " 'ya ta ce" Likitan ya ce "Ba abune mai sauƙi ba Hajiya, musamman ga mu mutanen wannan zamani, muna bawa soyayya muhimmanci sosai da sosai, dole zata shiga damuwa, saboda abun ba sauƙi amma kiyi haƙuri ki cigaba da Addu'a ko kina son Mama ta rasaki at your young age, ko ki kamu da ciwon zuciya?" Hafsa ta ce "A'a" "Tukuna ma, gaya mini sunansa, sannan maiyasa ya yaudareki?" "Ba yaudarata yayi ba" "Ok na gane, kin san kowane bawa, akwai rubutacciyar ƙaddararsa, kiyi haƙuri, ga magunguna nan da ruwa, zan riƙe ki a Asibitin nan tsawon kwanaki biyu, sai naga jikinki yayi kyau, jininki kuma ya sauka" Mama ta yiwa likitan godiya, da jin daɗin yadda ya nuna damuwarsa ga Hafsa, ta riƙe Hafsa suka fita ma'aikatan jinya suka basu gado, Mama taje ta biya kuɗin, da kuma sayo magunguna. "Baban Fadila nifa ban gane manufarka ba, yaya zan gaya maka ban san in da yaro yake ba, amma ko a jikinka" "To yaya zan miki ni? Khalil dai ba yaro bane ba ƙarami, da hankalinsa kuma ke da bakinki kika gaya mini abin da kika yi masa, dan haka yayi wani wurin ne, dan yaje ya ji da tension ɗin da kika saka masa" Cikin ɓacin rai ta ce "Kana nufin saboda na rabashi da 'yar matsiyata shi ya sanya zai bar gida ban san in da ya tafi ba? To wallahi ko zai mutu ba zai kawo mini jinin tsiya a matsayin sirika ba, zai ga yadda zan yi da shi, bai isa ba wallahi" Daddy ya ce "Dan haka sai ki daina tayar mini da hankali a kansa, matsla ce da kika kunnota ke zaki maganinta" "Au haka ma zaka ce?" "To me zance ni?" "Zaka ga me zaka cex" ta bar falon Daddy Fuuu ranta a ɓace. Amina har ta tafi makaranta Baba bai dawo ba, bata san ya aka yi ya tafi ƙauye ba sanarwa ba, bai gaya mata zai tafi ba suka haɗu da Safe tayi masa sallama zata makaranta, amma bai gaya mata cewar za shi ƙauye ba, sai da ta dawo daga makaranta. Tayi ta ƙoƙarin kiran wayarsa, amma wayar bata shiga, sai ta shiga damuwa tana fatan Allah ya sanya komai lafiya. Haka ta dawo daga makaranta tana sa ran ganin Baba, amma ta dawo ta tarar bai dawo ba. Sai wajen la'asar sannan Baba ya dawo, Amina ma bata san ya dawo ba, kawai ta fito da niyyar ta duba ko ya dawo ta tarar da shi yana salla. Murna ta dinga yi tana godewa Allah, da ya sanaya yana lafiya. Ta jira ya idar da sallar, yayi Adduoinsa sannan ya kalleta ya ce "Uwata ya makaranta?" "Lafiya lau Baba, amma baka gaya mini zaka tafi ƙauye ba, sai da na dawo nake ji jiya" Baba ya ce "Eh, tafiyar ce ba ta shiri ba, nayi ta ƙoƙarin ma in kira wayarki in haɗaki da babarki, amma wayar taƙi shigowa" Amina ta ɗan ɓata fuska ta ce "Kash, nima nayi ta ƙoƙarin kiranka amma ba ta shiga, Baba dan Allah ka saiwa Inno waya, in dinga jin muryarta" Baba yayi murmushi ya ce "ai na bayar a saya mata, har layi na bawa Saminu nace ya sai mata mai ɗan kyau wadda zata iya gane kanta" Amina tayi murmushi ta ce "Yauwa Baba, yaya ka baro su, ya kowa da kowa" Baba ya ce "Duk suna lafiya suna gaisheki, Sa'a an saka bikinta. Mun yi magana da Alhaji Ahmad, yayi mini maganar zuwanki birnin tarayya a kan harkar karatunki, da fari dai na ɗan yi jayayya amma daga baya ya mini bayani na amince, ina fatan zaki kula da kanki Amina, ki riƙe mutuncinki, ki tuna ke ba 'yar kowa bace, ki kula da tarbiyyar da muka baki" Washe baki Amina ta yi ta ce "Baba, ka amince inje ɗin?" "Eh uwata, na amince ina miki fatan alkhairi, sannan ya ce mini zaki gida kiga gida kuma kiyi musu sallama, saboda doguwar tafiya zaki yi" Hawayen farinciki suka cika idanun Amina, ta kalli Baba ta ce "In Allah ya yarda ba zan baka kunya ba Baba, zan kula da kaina, ka mini Addu'ar samun nasara" "Addu'a ai kullum cikinta nake, Allah ya yi miki albarka, ga kayayyaki can babarki ta haɗo wai in kawo miki" Cikin murna Amina ta nufi wurin kayan da Baba ya nuna mata, ta ɗau ledar Vivan, tana jin yadda take jin kewar Inno a ranta. Har zata fita daga ɗakin Baba ya ce "Yauwa na haɗu da wannan malamin naku na makarantar boko, na manta sunansa, ya cc in gaisheki" "Laa Malam Sunusi?" "Eh shi" "Allah sarki, ina amsawa, yauwa Baba a kawo Abinci ne, ko in dafa maka wani abun?" "A'a ba sai an kawo ba, nan da kika ganni a ƙoshe nake" Amina tayi murmushi ta juya ta bar ɗakin Baba. A falon gidan ta tarar da Hajiya Zainab tana kaiwa tana komowa a falon, da waya a hannuta kamar ka taɓata ta fashe sai cika take tana batsewa. Tana ganin Amina da leda ta ce "Ke!" Amina ta tsaya tare da kallon in da Hajiya Zainab take. Cikin kaushin murya ta ce "Daga ina kike?" "Naje wurin Baba ne ya dawo" Amina ta bata amsa. "Maza kije ki kira mini shi, dama shi nake jira" tayi maganar tana hura hanci. Sai da Amina ta ɗan tsaya tana kallon Hajiya Zainab, tana son gano dalilin da ya sanya take son ta kira mata Baba. "Ba zaki je bane kika tsaya kina kallona haka?" Amina ta ajiye ledar hannunta, ta juya ta fita, tun daga nesa Baba ya hangota ta nufo shi, fuskarta a haɗe, tsayaqa6 yayi yana jiran ƙarasowarta. "Uwata lafiya naga kin dawo?" "Matar gidan ce ta ce na kiraka" Baba ya ce "To, Allah ya sa ba wani laifin ki ka yi ba, ko ni nayi ba" "Nima ban san meye ya sa take nemanka ba" "To muje, koma meye sai na ji" Suka rankaya suka nufi falon. Suka shiga Baba yayi sallama, amma Hajiya Zainab tayi biris tana ta wani kumbura wuya kamar kasa. Ta ƙarewa Baba kallo a wulaƙance, irin kallon yake ƙonawa Amina rai. "Jiya da yaushe ka bar bakin gate ɗin nan?" Ta jefowa Baba tambayar. Cikin girmamawa ya ce "Sai goma na safe ranki ya daɗe?" "Kenan kana nan Khalil ya fita?" "Eh, nina buɗe masa ƙofa, bayan sallar Asuba ya ɗau mota, na buɗe masa ƙofa ya fita". "Wane irin mutum ne kai da zaka buɗe masa ƙofa ya fita bayan sallar Asuba, ina ya ce maka zai tafi?" "A'a Hajiya, bai gaya mini ba, ko gaisawa ba muyi ba ya fita" Wani uban tsaki ta ja, sannan ta ce "Kai dai banga amfaninka a zaman gadin nan ba, tayaya yaro zai fita bayan sallar Asuba, amma ka kasa tambayar ina zai tafi" Ikon Allah Amina ta tsaya tana kallo, aikin Baba buɗewa da rufewa to meye huruminsa na sanin in da wani zai je a gidan? "Yaya dai meke faruwa ne?" Suka jiyo muryar Alhaji Ahmad, da ya fito yana ta zuba ƙamshi cikin wani vowel baƙi. Ya kalli Baba Hassan da ke tsaye fuskarsa cikin damuwa, ya risunar da kai kamar mai neman gafara. "Malam Hassan, ka dawo ashe?" Baba ya ce "Eh na dawo ranka ya daɗe" Baba ya Kalli Mummy ya ce "Meke faruwa ne?" "Ka jiye mini wannan rainin hankalin mana, wai Khalil ya fita daga gidan bayan sallar Asuba amma ya kasa tambayarsa ina za shi ko ya sanar mana, ni na gaji da sokoncin wannan mutumin" "Sokonci kuma?" Amina ta tambaya rai a ɓace. Nunata Hajiya Zainab tayi ta ce "Idan ina magana kina saka mini baki, sai na ɗauke ki da mari, da ubanki nake magana, na faɗa sokwanci, sam bai san aikinsa ba, nace maka ka sallame shi ka samo mana masu gadi na hukuma, wannan ko wani abun ne zai faru ba sai dai ya same mu ba, ba uwar da zai iya tsinana mana ba" Ga mamakin Amina ta sai ta ji Alhaji Ahmad ya ce "My dear kiyi haƙuri, ki bi komai a hankali, sanin in da Khalil za shi ba alhakinsa bane ba, kuma yana iya ƙoƙarinsa, bai kamata ace kina tada jijiyoyin wuya haka ba" "Ba dole in tada jijiyoyin wuya ba, ka bar wannan mutumin a shiritarsa ɗana ya bar gida, gaskiya Allah amfana aikin da yayi haka, ya koma in da ya fito, na gaji". Baba ya risuna ya ce "Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri, in Allah ya yadda hakan ba zata sake faruwa ba" Amina ta zata Alhaji Ahmad zai ɗau wani mataki, amma ya ɓige da lallaɓa Hajiya Zainab a kan tayi haƙuri. Wani mugun kallo Amina ta yiwa Alhaji Ahmad, idanunta suka cika da hawaye ta ɗau ledarta ta wurin Baba kawai ta bar falon, saboda yadda zuciyarta ke mata zafi zata iya zagin Hajiya Zainab. Alhaji Ahmad ya lura da yadda Amina ta ɗau zafi, amma ba damar yayi wani yinƙuri a lokacin, haka ya dinga rarrashin Hajiya Zainab, ya ce Baba ya koma bakin aikinsa. Baba kansa ba ya jin daɗin yadda Hajiya Zainab ke masa a wasu lokutan, amma ba yadda ya iya idan ya bar aiki makomar karatun Amina da kuma iyalinsa baki ɗaya yake tunani. Kan ya ƙarasa wurin gate ɗin, aka fara horn. Ya ƙarasa da sauri jikinsa na tsuma, ko Fadila ce ta dawo, kar ya yi wani laifin ya kuma jawa kansa wani cin mutuncin. Yana buɗewa yaga motar Khalil, ɗan tsayawa Baba yayi, yana kallon motar. Abdul yaje yayi parking ɗin motar ya fito ya nufo Baba, Baban ma nufarsa yayi ya ce "Malam Abdul, ya na ganka kai kaɗai ina Khalil ɗin?" Abdul ya ce "Ai Khalil ya koma wurin aiki ne, ya aikin Baba Hassan?" Baba ya ce "Alhamdilillah" "Mutanen gidan kuwa suna nan?" Baba ya ce "Eh ka shiga suna ciki" Abdul ya nufi cikin gidan. A falon ya tarar da Hajiya Zainab, tare da Daddy, yana ta aikin rarashinta a kan rashin sanin in da Khalil yake. Abdul ya shiga da sallama, Daddy ne kawai ya iya amsa masa. Ita Mummy ma sai yanzu ta tuna da Abdul, ƙila ya san in da Khalil ya tafi, amma ko ya sani ma ita bata da lambarsa balle ta kirashi ta tambaye shi, ko da yake ta san wataƙila Khalil ɗin ɗin yazo nema shima dan da ya san in da yake, ba zai biyo shi gida ba. Har ƙasa Abdul ya durƙusa ya gaishe su. Daddy ya amsa masa cikin sakin fusak Daddy ya amsa, ita kuwa Hajiya Mummy ba ta bi ta kan gaisuwarta sa ba. Abdul ya ce "Dama motar Khalil ce na dawo da ita gida" "Motar Khalil kuma? Ina shi Khalil ɗin ya kex Mummy ta faɗa tana zazzaro wa Abdul ido. Mamakine ya kama Abdul, ganin da alama ba su san ina Khalil ɗin ya tafi ba. "Mummy, wajen ƙarfe shida ya sameni a gida, ya ce in kai shi airport zai koma Abuja, sai in dawo da motarsa gida, naje wurin aiki ne shi ya sa ban dawo da ita ba". "Amma kai baka da mutunci, har ya haɗa baki da kai ya tattara kayansa ya koma aiki, ban san in da yake baka gaya mana ba sai yanzu, kasa hankalinmu duk ya tashi bamu san ina yake ba". "Wallahi Mummy ni ban san bai gaya muku ba, kawai... "Dalla rufe mini baki, ai duk wata ƙulla-ƙullar rashin gaskiya kaine kake bashi shawara, na san wataƙila kaine kake hure masa kunne, yaje ya gano wata 'yar talakawa ya maƙale wai ita yake so" Abdul ya sunkuyar da kai yayi shiru ya gaza cewa komai. Daddy ya kalli Abdul ya ce "My son, tashi ka tafi Allah yayi maka albarka, ka gaida maman naka" Abdul ya ce "To Daddy sai anjima" Sai da Abdul ya fita, sanan Daddy ya ce "Zainab wai meke damunki ne? Dan kawai ɗanki ya miki laifi sai ki dinga bin wanda ba su ji ba ba su gani ba da miyagun maganganu da cin mutunci?" "Au haka kace? Suwaye ma mutanen wa na yiwa ƙarya wancan sakaran tsohon da bai san aiinsa ba ko wannan yaron mai kama da maye ya liƙewa ɗana ya ƙi rabuwa da shi duk wata harkar ƙasƙanci shi ne yake nuna masa" Ran Daddy ya ɓaci, ya miƙe ya ce "Sai kiyi abin da kika ga dama ki ki cigaba kar ki fasa, idan kika kaini bango kin fi kowa sanin halina" Bayansa tabi da harara, ta tashi tai nata wuri. Fadila kuwa tun da taje makaranta, ba ta ga Yazid ba sai lokacin lectures kawai, da an yi yake ficewa daga ajin sai lokacin wata lectures ɗin, kuma ko da wasa bai yadda ya kalli in da zai ga Fadila ba, balle a samu kuskure ko ido su haɗa. Ita ma tayi nata ƙoƙari, wurin ganin ba ta ko nuna ta san da zamansa a ajin ba, ta cigaba da harkokint. Sai dai yin hakan taji ta takura kanta sosai da sosai, ko ba komai Yazid mutumin kirki ne, kuma ya taimaketa sosai a first semester, wanda garin taimakon nata ne har ya rasa wasu marks ɗin, amma hakan bai hana shi zama overaller ba! Bayan Daddy ya dawo daga sallar isha'i, ya tarar da Amina tana shirya Abincin dare, fuskarta babu walwala sam, idanunta duk sun ƙanƙance da alama tayi kuka. Dining ɗin ya ƙarasa yana murmushi "Meenali me aka dafa ne yau?" Banza ta yi masa ta cigaba da abin da take yi. "Ba kya jina ne?" "To ni me zance" ta faɗa bata ko kallon inda yake. "Amma magana fa nake miki" Idanunta da suka cika da hawaye ta ɗago tana kallonsa. "Ka zama mai kulawa da mutuntawa a gareni, ka ɗauki lamurana da muhimmanci amma a gabanka matarka take ciwa mahaifina mutunci, idan nayi magana ka ji haushina, ka san yadda nake ji a duk lokacin da iyalinka suka ci zarafin mahaifina a gabana? Kawai dan muna talakawa? Mu muka yiwa kanmu? Duk lalacewar uba uba ne, balle babu lalacewa a iyaye, ni kar ka sake nuna mini wata kulawa, babban abin da za a mini a rayuwata shi ne a girmama mahaifina ya fi mini duk wani tattali da kulawa" ikon Allah Alhaji Ahmad ya tsaya yana kallo, tuni idanunta suka yi jawur hawaye ya wanke mata fuska, ta bar falon ta bar shi a tsaye. AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM AYSHERCOOL PAGE 41 Alhaji Ahmad ya shafi gemunsa, bai zaci Amina zata iya tsayawa ta yi masa tsiwa haka ba, amma ta wani fannin da gaskiyarta, ba bu wanda zai jure a dinga cin mutuncin iyayensa haka kurum, dan kawai talaka ne, amma ai ba shi yayi mata laifin ba. Amina kuwa ɗaki ta koma, ta zubar da hawaye sosai tayi kuak, ba zata iya ƙirga adadin yadda aka sakata kuka ba a gidan nan, iya cin mutuncin da ake mata baya damunta a kan wanda ake yiwa Baba. Komawa aiki ya gagari Khalil, daga masallaci sai gida, sai yaji yunwa zata kassara shi, sannan yake order Abinci ya ɗan ci kaɗan. Haka nan yaji yana son ya kunna wayar, yayi trying layin Hafsa. Da saƙonnin Mummy ya fara cin karo rututu, a kan ina ya tafi, bai sanar da ita ba? Message ɗaya ya iya yi mata reply ya ce 'ina wurin aiki' Ya lalubo lambar Hafsa, ya fara kira, cikin ikon Allah ya ji wayar ta shiga, tashi yayi zaune ya gyara zamansa, yana jiran ya jibta ɗaga wayar, amma har wayar ta kaste bata ɗaga ba. Ya kira ya kai sau biyar, amma bata ɗaga ba. Message ya tura mata kamar haka "Dan Allah Hafsa, ba dan ni ba ko sau ɗaya ki ɗaga wayata mana, magana nake so muyi" yana tura nata ya ajiye wayar ya dafe kansa. Mintuna kaɗan ya ji kira ya shigo wayarsa, da sauri ya miƙa hannu ya ɗauko wayar, a zatonsa Hafsa ce amma ya ga sunan Mummy, ya ɗaga wayar ya kai kunnensa tare da yin sallama. "Sannu Khalil, wato saboda mace ka zama ɗan kanka ko? Ka shirya ka koma aiki ban sani ba, saboda bani da amfani a wurinka, sai kawai ka aiko mini da motarka ko?" "Ba haka bane Mummy, bana jin daɗi ne, kuma na riga nayi booking ɗin jirgi shiyasa na san at that time babu lallai kin tashi" "Ai dole kaji babu daɗi, tunda na rabaka da waccan yarinyar mana, laila majnun baban soyayya, da ni kake zancen Khalil" ta katse wayarta. A saɓule ya ajiye wayar ya cigaba da riƙe kansa. Fadila kuwa zaune take a kan gadonta tayi tsuruu, gaba ɗaya mood ɗin da taga Yazid bai yi mata daɗi ba, haka nan ta ji ta damu, cikin ƙoƙarin kauda tunanin Yazid daga ranta, ya sanya ta ɗau wayarta ta fara game, ita a dole bata damu da Yazid ba. Alhamdilillah, Hafsa ta ɗan farfaɗo ba kamar lokacin da aka kaita Asibiti ba, an samu jinin ya ɗan sauka. Likita yayi ta mata nasiha, da rarrashinta a kan ata kwantar da hankalinta, ta miƙa lamuranta ga Allah, sannan ya sallamesu. Kusan duk kuɗin hannunsu ya ƙare, saboda zaman Asibiti, ga babu kayan Abinci. Hafsa ta ɗan ji daɗin jikinta, sai dai ta kasa mantawa da batun Khalil, babu abin da ya canza daga soyayyar da take yiwa Khalil ɗin. Kayan da Khalil ya bata ta tattara ta bashi bai karɓa ba, a soron gidansu ya bar mata, dama tunu ta cire layin wayarta daga wayar da ya bata zuwa tsohuwar tata. Da suka dawo gida ta duba wayar, sai ta ga missed calls ɗin Khalil rututu a ciki, da tarin messages, ba dan ta so ba haka ta saka lambar Khalil a blacklist, tana jin kamar da zuciyarta ta haɗa ta saka a black list ɗin. Bayan Amina ta gama koke kokenta, kuma sai ta fara tunanin akan abin da ta yiwa Daddy, sai taga kamar bata kyauta ba, saboda ya kyautata mata har ƙarawa Baba albashi yayi ba tare da ko matar gidan ta sani ba, ita ma Baba da ya gaya mata ya gargaɗeta a kan kar wanda ta gayawa, dan Alhaji Ahmad ya ce masa ko Aminan kar ya gayawa, banda kyautatawa da yake mata a kai a kai da ƙoƙarin bata kariya a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin cin mutuncinta, gaba ɗaya kuma sai jikinta yayi sanyi. Da magariba Hafsa na zaune, ta saka tuwon da Mama ta zuba mata, amma ta kasa ci, Mama sai hira take yi mata dan ta ɗebe mata kewa. Wayar Hafsa ce ta kawo haske alamar kira ya shigo, kasancewar wayar a silent take, Mama ta ɗauko wayar ta miƙawa Hafsa. Hafsa ta girgiza kai ta ce "Mama ƙyale wayar nan kawai" "A'a ai ba a yi haka ba" Mama ta ɗaga wayar tare da yin sallama. "Wa'alaikum salam, Mama ina wuni?" Mama ta kalli Hafsa jin muryar Khalil. "Lafiya lau Khalil, ya aiki?" Waro ido Hafsa ta yi jin Mama ta ambaci Khalil. "Aiki lafiya lau Mama, ina ta kiran Hafsa a waya bata ɗagawa, daga baya ma wayar bata shiga" Mama ta ce "Ai da yake ta ɗan yi rashin lafiya ne, ɗazu muka dawo daga Asibiti" Cikin damuwa Khalil ya ce "Subhanallah, ya jikin nata?" "Taji sauƙi Alhamdilillah, bari in bata wayar" Mama ta miƙawa Hafsa wayar, ta tashi ta bar ɗakin. Hafsa ta kalli sabuwar lambar, sannan ta saka wayar a kunnenta. "Assalamu alaikum, Hafsat" "Na'am" ta amsa a sanyaye. "Hafsa why? Meyasa laifin Mummy zai shafeni, ko mun rabu ai bai kamata ki yanke duk wata alaƙa da ni ba" Hafsa tayi shiri ba ta ce masa komai ba, sai ma jin kewarsa na damunta. "Hafsa kiyi magana mana" "To me zance?" "Shikenan, Yanzu ya jikin naki?" "Naji sauƙi" "Allah ya baki lafiya, gaba ɗaya ina cikin damuwa ko aiki na kasa yi, na kira ba kya ɗagawa daga baya ta daina shiga, sai sabon layi na saya na saka na kira sannan kika ɗaga, dan Allah Hafsa kiyi haƙuri abin da Mummy ta yi miki ya wuce, ina ta ƙoƙarin saita komai, in Allah ya yarda za mu yi Aure" Hafsa ta lumshe idanunta sannan ta buɗesu ta ce "Khalil" "Na'am Hafsa" "Duk abin da iyaye ba sa so aka aikata shi baya albarka, baya zuwa ko ina, dan Allah Khalil kayi haƙuri ka ƙyaleni, dole mu haƙura da juna" Khalil ya maraice ya ce "Dan Allah Hafsa... "Shhhhhh" ta katse shi. "Ko Mama ce ta ce na rabu da kai, idan har bata son alƙarmu zan rabu da kai har abada, Yakamata mu yiwa Mummy biyayya, dan Allah Khalil kar ka sake kirana, kayi haƙuri" "To ki tsaya kiji" ba ta jira mai zaice ba, ta kashea wayar, ta cire layin gaba ɗaya daga kan wayar. Ta haɗe kai da gwiwa tana ta ƙoƙarin mayar da hawaywnta amma ta kasa. Mama tayi sallama ta shigo ɗakin, ta zauna ta ce "Yaya kiran me yake miki?" "Haƙuri yake bani, wai mu koma kamar da" Mama ta girgiza kai ta ce "Ai hakan ba zai yiwu ba, tun da mahaifiyarsa bata so, Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alkhairi" "Ameen" Hafsa ta amsa jiki a sanyaye. Khalil kuwa sakin wayar yayi a ƙasa, sai a Yanzu yaji wasu irin lafiyayyun hawaye suna zubo masa, bai taɓa zaton zai iya kuka a kan mace ba, babban abin da yasa yake jin zai iya taking kowane risk saboda Hafsa shi ne ya sani ba kowane namiji ne zai iya karɓar Hafsa da ƙaddararta ba, gashi so yake mata na fisabilillahi, ji yake a duniya banda uwar da ta haifeta babu wanda ya kai shi ya sonta da ƙaunarta. Daddare Amina zata kwanta bacci, ta dinga kallon wayarta, da sukan yi chatting da Daddy da daddare kafin tayi bacci, tayi ta masa shirme da shirirta yana biyeta. Sai dai yau ko saƙo ɗaya bai turo mata ba, ta duba what's app taga yana online. Sallama tayi masa, sai dai ya buɗe ya gani amma ya share, ga zauna shiru shiru amma bai mata reply ba. Ajiye wayar tayi cike da damuwa, tana sake ganin rashin kyautuwar abin da ta aikata wa Daddyn. Kwanaki biyu kenan, babu wanda ya nemi wani tsakanin Fadila da Yazid, a kwana na uku kuwa bai zo makarantar ba gaba ɗaya, gashi ana ta shirye shirye na fara exams, ana fa teses baya nan, abu kamar wasa har aka tafi kwana na uku baya zuwa makaranta, gashi shi ba wani aboki ne da shi ba, balle ta tambaya. "To ma ina ruwana da rashin zuwansa' ta tambayi kanta, ta cigaba da ƙoƙarin mantar da kanta batun Yazid. Amina kuwa nadamar abinda ta aikata ya addabeta ya hanata sukuni, ta kai ta kawo, idan taga Daddy ta gaishe shi, sai dai ya amsa sama-sama, alamar fushi yake da ita. Gashi ta rasa hanyar da zata bi wurin bashi haƙuri. Ranar asabar da safe, tana gyarawa Hajiya Zainab falo, ya shigo falon, Amina ta risuna ta gaishe shi. "Lafiya lau" ya amsa. Ya wuceta ya nufi bedroom ɗin Hajiya Zainab. A tsaye ya tarar da Hajiya Zainab, ta sanya skirt ɗin lace, tana kwalliya a gaban mudubi, ba ta saka rigar ba tukuna. Ya ɗan ƙare mata kallo sannan ya nufi in da take yana faɗin "Bainu ba kya tsufa" Ta ce "Hmm, ka fito kenan, ya ka kwana da jikin?" "Ba zan amsa ba, tun da baki kwana da ni ba, duk da kin san jikina babu daɗi". Hajiya Zainab ta waiwayo ta kalleshi ta ce "Sai kace wani ƙaramin yaro, da ban kwana da kai ɗinba, ba ga ka nan ras da kai ba, jikin yayi sauƙi". Ya ƙarasa bayanta ya tsaya, ya rungumeta ta baya, ya zagaya hannayensa a cikinta, tare da kwantar da kansa a kan kafaɗarta ya ce "Ko ba komai kasancewarki a kusa dani, zai sa naji daɗi" Ɗan ƙoƙarin ture hannunsa take ta ce "Kaima dai, ba magungunaka suna nan ba, ka sha ka kwanta kayi bacci, ko kaje Asibiti mana" "Duk ba wannan nake buƙata ba, ke ɗin dai, attention ɗinki, kulawarki da hirarki domin ɗebe mini kewa, musamman na ɗauki hutun shekara saboda in kasance da ku, duba da yanayin aikin ina daɗewa bama tare amma duk kinfi mayar da hankali a kan 'ya'yanki, business ɗinki da sauransu, ni ba kya kulawa da ni sosai, ina buƙatar kulawa nima" yayi maganar yana cigaba da ƙanƙameta yana shaƙar ƙamshin man da ta shafa. Ɗan tsuke fuska ta yi ta ce "Ahmad meye haka ne? Dan Allah Yakamata ka san yanzu ba da bace bafa, mun girma fa yanzu,da auren wuri muke yiwa yaranmu da yanzu muna da jikoki, yanzu jikinmu hutu yake buƙata ba wannan abin ba, abin da aka yi a baya Allah ya amfana". Alhaji Ahmad ya sake ƙasa da muryarsa ya ce "Am not old for that, ban san me kike nufi da ni ba, ban yi girman da na wuce samun kulawa da tatali daga iyalina ba, Please kar muyi haka da ke" "Kaga dan Allah ka rabu da ni, unguwa zan fita ni" "Unguwa ƙarfe goma na safe, ke kenan kullum cikin fita da wadda na amince, da wadda ban amince ba? Dan Allah ki zauna a gida mu wuni tare yau" "A'a wallahi, fita ta tana da muhimmanci sosai, zan zaga shaguna na, daga nan zanje biki, classmate ɗinmu na auran 'ya" ta zame daga jikinsa tana ƙoƙarin ɗaukar rigar kayanta ta saka. "Haba Zee, shikenan let's have some fun before you go" yayi maganar yana kuma ƙoƙarin rungumota. Cikin tsawa ta ce "Wai meye haka ne, na ce maka bana so, dan Allah wai sai yaushe zaka girma, you don pass this level, haba dan Allah" Lumshe idanunsa yayi, ransa a ɓace, ya kalleta da idanunsa suka fara sauya launi, "Zainab, ki bini a hankali tura ta kai bango" "Da tura ta kai bango, saika rushe bangon ai, shikenan shekara da shekaru ana abu ɗaya, shekaru sun ja ma amma mutum bai san ya girma ba" Daddy bai kuma ce mata uffan ba, ya juya ya fice. Amina tana mopping a babban falo ya fito, kallo ɗaya tayi masa ta fuskanci akwai damuwa, amma bata da ikon magana, haka ya koma nasa sashin. Babu daɗewa Hajiya Zainab ma ta fito, ta sha uban ado sai ƙamshi take, hannunta riƙe da mukullin mota, sai yatsuna fuska take ta dubi Amina da take ƙarasa mopping ta ce "Idan an tashi girkin rana, ba sai an yi da ni ba, dinner ayi abinci mara nauyi" Amina ta ɗan basar ta ce "Shikenan" dan a duniya idan da mutumin da ta tsana bai wuce Hajiya Zainab ba, saboda rashin mutunci da wulaƙancinta. Fadila ta zuba wa wayarta ido, tun da garin Allah ya wayez tayi salla tayi wanka a ɗakinta ta karya, ta koma kan gadonta ta naɗe take chatting tana game, gaba ɗaya ba ta jin daɗin komai, ta rasa meye yake mata daɗi, Khalil baya nan, ta saba ko baya nan sukan yi chatting amma yanzu taga last seen ɗinsa ya kai 3days,taga alamar kamar ita ma haushinta yake ji. Ta gaji da latsa wayar, ta ɗauko litattafanta ta fara karantawa, ta tsinci kanta da duba ire iren rubutun da Yazid kan yi mata a cikin littafi. Tayi ajiyar zuciya ta cigaba da karatun ta. Hajara yau naɗewa tayi taƙi yin aikin komai, wai mura ce take nuƙurƙusarta, dan haka ba zata iya aikin komai ba, ta barwa Amina aikin gida gaba ɗaya, sam hakan bai dami Amina ba, yadda zata ga Daddy ta bashi haƙuri ne ya dameta. Bayan girkin rana da tayi na duka gidan, ta koma ta ɗora faten wake da dankalin turawa saboda Alhaji Ahmad. Ta tsara masa abinci, sai dai ta shiga zullumin karta kai masa ya yi mata wulaƙanci, tun da fushi yake da ita. Ta fara zuba na Baba ta kai masa, sanan ta kaiwa Fadila nata ɗakinta, ta tarar da Fadilan na toilet tana alwala, ta kalli yadda ta baza liatattafai a kan gado, kamar wata 'yar Nursery. Ta kalli wani rubutun larabci, da ke rubuce a wani littafi da yake a buɗe. Amina ta karanta larabcin, kasancewar Amina tana jin larabci kaɗan-kaɗan ya sanya ta fahimci rubutun na soyayya ne, daga ƙarshe ya rubuta sunansa Yazid. Ɗan shiru Amina tayi tana tunanin a ina ta san wannan sunan na Yazid, jin alamun buɗe ƙofar banɗakin ya sanya Amina saurin ficewa daga ɗakin. Amina, Tana fitowa taga fitar Alhaji Ahmad, ɗan dafe kanta tayi tana tunanin ina za shi haka bai ci Abinci ba, amma jin ana sallar azahar, ya sanya ta ce ko masallaci za shi. Ta koma ɗakinta tayi wanka, tayi sallar azahar ita ma, ta canza kaya ta gyara jikinta. Cikin sa'a da ta kuma fitowa, taga ya dawo, sai dai fuskar nan tasa babu annuri sam, ya wuce sashinsa. Da sauri ta koma Kitchen, ta haɗo kayan Abinci a tray, har da favorite fruits ɗin sa, ta nufi falonsa tana Addu'a. Sallama ta yi, amma ta ji shiru ba a amsa ba, tayi addu'a ta shiga, tana fatan Allah ya sa yana falon. Aikuwa ta hangoshi kwance a kan 3seater, idanunsa a rufe. Ta ƙarasa gabansa ta ajiye trayn a ƙasa. Ta miƙe ta kalli in da yake kwamce ta ce "Daddy" ya buɗe idonsa ya kalleta. "Ga Abincin rana na kawo maka" ya jinjina mata kai ya mayar da idonsa ya rufe. Amina ta zauna a kan gwiwowinta a hankali ta fara magana "Daddy ka tashi ka ci Abincin" Ba tare da ya buɗe idonsa ba ya ce "Ki bar shi a wurin zan ci" A ɗan marairaice ta ce "Dan Allah ka tashi zaune" sake buɗe idomsa yayi, ya tsareta da ido wanda sai da ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa. A hankali ya tashi zaune, ya kalli agogon hannunsa, ya fara shirin tashi tsaye, da sauri Amina ta ce "Daddy Abincin fa?" "Ki bar shi a nan, ranar Alhamis in Allah ya kaimu, ki shirya da wuri, Zakiru zai kai ki ƙauye" Kan ya tashi tsaye, Amina ta ƙarasa gabansa a kan gwiwowinta ta ce "Dan Allah Daddy, kayi haƙuri, na san ban kyauta ba kana fushi da ni, dan Allah kayi haƙuri" Kallonta yayi ya ce "Laifin me ki ka yi mini kike bani haƙuri?" "Daddy na maka laifi mana, baka cancanci in maka magana a yadda nayi maka ba, raina ne ya ɓaci sosai, amma ban kyauta ba, dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba" Ya ɗan girgiza kai ya ce "Hmmm" "Dan Allah kayi magana, duk na damu da laifin da nayi maka, kayi haƙuri" "Shikenan ya wuce" "Ka haƙura?" "Eh ya wuce" Ta ɗan marairaice fuska ta ce "kamar ba ka haƙura ba fa" Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Meyasa kika ce haka?" "Haryanzu ranka a haɗe yake fa" "To ai bani da lafiya ne, amma nace miki ya wuce ai" Cikin damuwa ta kalleshi ta ce "Jikin ne haryanzu? Sannu Allah ya baka lafiya" Ya amsa da Amin. "To in zuba maka Abincin?" Ya jinjina mata kai. Ta zuba masa Abincin a plate ta saka cokali ta miƙa masa. Ya karɓa ya kalleta ya ce "Zauna a nan yayi maganar tare da nuna mata kusa da shi a kan kujera. Ɗan turus tayi tana ganin rashin dacewar hakan. Amma kasancewar shiri take nema, haka ta tashi ta zauna a kusa da shi. "Amina?". "Na'am Daddy" "Banji daɗin abin da ki ka yi mini ba, kema kina cikin masu mini kallon anfi ƙarfina a gidana ko? Duk abin da nake yi, ina da dalili ina ƙoƙarin baki kariya, bana son ki bar gidan nan karatunki ya samu matsala, amma saboda yadda nake da ke kika kalli tsabar idona ki gaya mini magana haka ko Amin? Da wani ne ya mini abin da kika mini saina hukunta shi, ko da kuwa matar gidan nan ce, amma shikenan. Idan kin dawo daga ƙauye upper week zaku tafi Abuja, before na so inje Abujan nima, in ga competitions ɗin naku, dan sun bani invitation as a special guest, amma I don't think zan samu zuwa" Hawaye ne ya cika idon Amina ta ce "Dan Allah Daddy kayi haƙuri, gaba ɗaya na san ban kyauta ba, amma ba Baba ba, ko kai na gani wani ya maka haka sai inda ƙarfina ya ƙare, Matarka da 'yarka sun tsani Baba, ban san me yayi musu ba, wallahi ko dukana za suyi ba zan damu ba a kan su ci mutuncin Baba, ina jin zafi a raina, amma dan Allah Daddy kayi haƙuri, ba zan sake ba" Ya kai lomar abinci bakinsa ya haɗiye, sannan ya ce "Ba komai ya wuce" "To amma naga haryanzu ka haɗe rai" "Abubuwa da yawa suna damuna, ga kuma yanayin jikina dan haka am not in mood, ai nace ya wuce" Cikin damuwa ta ce "Sannu Allah ya baka lafiya, Daddy kaje Asibiti" Ya ce "Zaki rakani?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. Ya cigaba da cin abinci, can kuma ya ce "Yauwa, idan zaki tafi ƙauyen me kike ganin za a saya ki kai musu?" "A'a ba sai an sai musu komai ba" Amina ta faɗa tana ƙoƙarin zuba wa Daddy ruwa. "Idan zaki tafi ƙauye, me kike ganin ya dace a sai musu?" Ya kuma maimaitawa, hakan ya tabbatar mata he is serious. Ta ce "Lemo da ayaba" Ɗagowa yayi ya kalleta ya ce "Dubiya zaki je ko kai ziyara?" "Ziyara" "Kuma sai ki kai musu lemo da ayaba?" Amina ta tura baki ta ce "To ni me zance?" "Idan ina magana kina cewa ke me zaki ce, zamu ɓata" "A'a na daina, bana son mu kuma ɓatawa, in muka ɓata ba na jin daɗi" Murmushi ya yi ya ce "Are You serious?" Ta ɗaga masa kai alamar eh. "To shikenan, ki daina mini abin da zamu yi faɗa" "In Allah ya yarda na daina Daddy, amma zaka zo wurin taron namu na Abujan?" Daddy ya ce "Babu tabbas" "Dan Allah Daddy ka zo, ko ba ka haƙura ba haryanzu?" "Ai nace miki ya wuce" "To shikenan, na gode sosai, Baba da kansa yayi mini maganar zuwa Abujan, Allah ya biyaka da Aljanna Daddy, in Allah ya yadda ba zan baku kunya ba, zan yi abin da ya dace" Yayi murmushi ya ce "Allah ya sa, bayan sallar la'asar ki shirya, zaki rakani ganin likita" Ta miƙe tsaye ta ce "To, amma me zance wa Baba?" Ya miƙe ƙafafuwansa ya ce "Baba baya nan a lokacin" "Ina za shi?" Daddy ya yamutsa fuska ya ce "Tambayoyinki sun yi yawa" "To yi haƙuri, na tafi". Ya jinjina mata kai, tare da lumshe idanunsa" Ta juya da tray ɗin Abincin ta fita. A falo tayi kiciɓus da Hajara, Hajara ta dubeta ta ce "Amina daga ina haka?" "Kaiwa maigidan nan Abinci" Hajara ta waro ido waje ta ce "Ikon Allah, da kika kai masa kuma shi ne kika zauna kika jira ya gama kika fito da kwanukan, ni fa na zata ma ba kya nan, tun ɗazu nake falon nan ban ga gilmawarki ba" "Hajara, na kai masa na rana, sai ki kai masa na dare kema" tayi tsaki ta wuce, dan ta fara ƙuluwa da shegen sa idon da Hajara take yi mata. Amina na tsaye a gaban mudubi, ba wata kwalliya tayi ba, amma tayi kyau sosai, wata doguwar rigar abaya ta saka, wadda Babar Azima ta kuma aiko mata da ita, ta ɗan gyara fuskarta tayi tsaf da ita, ta riƙo wayarta a hannu ta fito falo. Ko da ta fito ta tarar da Daddy a tsaye yana jiran fitowarta. Kashe mata ido ɗaya yayi ya ce "You look beautiful in this outfit" Murmushi Amina tayi ta ce "Thank you Daddy" Hajara da ta daskare a wuri ɗaya, har ƙara leƙa fuskar Daddy take, dan ta sale tabattarwa kanta abin da take gani ba mafarki bane ba, babban abin da yake sake ɗaure mata kai, wanzuwarta a wurin ba ta sanyawa su bar abin da suke yi, bata ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da taga alamar fita zasu yi tare. Corridor dake cikin sashin Hajiya Zainab Hajara tabi, ta leƙa dan akwai taga da take kallon wurin parking space, aikuwa idanunta suka dake gane mata Alhaji Ahmad ya buɗewa Amina gaban motarsa ta shige, shima ya zagaya ya shiga ya kunna motar. Fita tayi da sauri ta nufi falo, taji tamkar taje ta kira Fadila ta ce ta zo taga cin amanar da akewa babarta, amma ta tuna Fadila ta tuna halinta na rashin mutunci, dan a 'yan kwanakin nan ta hanata zuwar mata ɗaki ma gaba ɗaya, Amina ce kawai ke kai mata Abinci idan na zata ci a dining ba, ko kuma gyara mata ɗaki. Fadila na kwance a kan gadonta kamar mai ciwo, tana chatting a Instagram tana taya wata riga, notification na what's app ya shigo wayarta. Komawa tayi what's app ɗin dan duba meke faruwa, saboda taga an yi maganganu da yawa a what's app group ɗin su na makaranta. Da saƙon Captain ta fara cin karo "Yau na haɗu da wani abokina wanda ya san Yazid, ya ce Yazid na Asibiti babu lafiya sosai, ku sa shi a adduoinku Please" "Innalillahi wa innalillahi raji'un" AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM AYSHERCOOL AREWABOOKS AYSHERCOOL7724 WATPAD AYSHERCOOL7724 43 Gaba ɗaya suka waiwaya dan ganin waye haka? Gaba ɗaya hankalin Amina ya riga ya gama tashi, Hajara ce a tsaye a wurin makunnin ƙwan, ganin duk suna zuba mata ido kuma sai ta hau kame-kame tana faɗin "Amm.... Ban san.." Ɗauke kai Daddy yayi daga kallon in da Hajara take, ya mayar kan Amina ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Karki manta anjima zan aiko a kai ki banki, a buɗe miki account" Noƙe faɗa tayi ta ɗan tura baki ta ce "Ni ba zani ba" "Me kika ce?" "Bakomai" ta faɗa taka sake tura baki. Murmushi ya yi ya wuce sashinsa, Amina ta cigaba da mopping ɗin ta suka mayar da Hajar daidai da kujerun da suke falon. Gaba ɗaya Hajara rasa abin yi tayi, a baya tunane tunanenta sun fi karkata ga zargi, amma a yau ta sake tabattar da abin da ke tsakanin Alhaji Ahmad da Amina wata alaƙa ce mai ƙarfi da girman gaske, wadda da alama alaƙar tayi ƙarfi sosai da sosai. Kamar yadda Daddy ya ce, da kansa yaje makarantar su Amina, bayan an tashi sukaje banki, aka yi mata duk abinda yakamata, ya saka kuɗi a ciki naira dubu ɗari biyu. Mamaki ne ya cika Amina ta ce "Daddy wannan maƙudan kuɗin me zan yi da su, idan Baba ya gane fa?" Daddy ya ce "Ta yaya Baba zai gane, sai dai idan kece zaki gaya masa, kuma ai ba wasu kuɗi ne masu yawa ba, Zakiru zai kai ki ki sayi duk abin da kike so, ban fiye son shiga wurare bane saboda identity ɗina, ba dan ke ba wurare da yawa ba zan iya zuwansu ni kaɗai ba, kuma ni bana son a takura rayuta duk in da zaka sai da masu baka kariya" "Amma meyasa baka so a ganka? Kar a ganmu tare aje a gayawa Maman su Khalil ko?" Ya ce "Eh, kin san bana son ɓacin ranta da damuwarta" "Eh amma ni kana son ganin nawa" tayi maganar da iya gaskiyarta. "Mhmm, me yasa kike haɗa kanki da ita? Ita matata ce ke kuma" Sai yayi shiru. A ƙule Amina ta ce "Eh ita matarka ce, ni kuma 'yar aiki ba talaka mara galihu" "Yauwa Ashe kin sani, amma ni bance miki talaka mara galihu ba" yayi maganar da salon ya sake kunna Amina. Aikuwa ta kai ƙololuwa dan taji haushi ba kaɗan ba. "Banda rigima irin taki, ina na taɓa ganin wannan ƙarfin hali in ba a wurinki ba, nace kina son mijinta kince me zaki da tsoho". Cikin tsiwa ta ce "Allah ya kiyaye in yi kishi da wannan matar, ta kasheni da bala'i wadda ba ta san darajar ɗan Adam ba" "Zaki fara ko? Ban gaya miki bana so ki dinga duk wata magana da zata shafi matata ba". Amina ta ce "Amma ai kai ka fara bani ba, wallahi Daddy seriously yakamata ka kula sosai, Allah ya baka dukiyar da zaka amfanar da al'umma, amma an gindayeta wuri ɗaya daga ita sai iyalanta, duk wanda ya raɓoka zai mora an dinga yi masa gori kenan da kallon banza, wallahi idan baka gina lahirarka ba daga ranar da ka mutu, wanan dukiyar aka raba musu, su sadaka ma Allah ya kai ladan kabarinka sai wanda ya dubi Allah. Na san naganganuna sun yi tsauri da yawa, amma dan Allah kayi haƙuri Daddy, wallahi gaskiya nake gaya maka. Dan Allah yanzu dan Allah ya baku arziki ya dace aje aci mutuncin 'yar mutane dan Khalil ya ce yana sonta, ba a gabana aka yi ba, amma yadda ya zo yana faɗar zancen naji zafi sosai saboda nima tsatson talaka ce, da na motsa a gidan nan sai kyara da gori, wallahi Daddy kaf mutanen da ke aiki a cikin gidanka suna yi ne dan basu da wata sana'ar da zasu samu su rufawa kansu asiri, ban da haka mai zai sa ka zauna a gabanka ana kiran mahaifinka nusari, soko da sauran miyagun maganganu?" Ta ƙarasa maganar hawaye mai ƙarfi suka ƙwace mata. Ba ƙaramin tasiri maganganun Amina suka yi a zuciyarsa ba, duk da ba wata babba bace ba, amna wasu lokutan tana da matukar hangen nesa da son faɗar gaskiya. Yana jinta tana kukan Amma bai rarrasheta ba kuma bai ce mata komaia ba, har tayi ta gama tayi shiru. Wasa² rashin sanin halin da Yazid yake ciki ya addabi Fadila, tun tana dannewa har ta kasa ya kai ga ta kira Yusra a waya. Ta zayyanewa Yusra duk abin da ke faruwa. Yusra ta ce "To ni yanzu da kika kirani me kike so in yi miki? Da kina da lambarsa ne ma sai a kirashi, ko kuma ki tanbaya a 'yan ajinku ko akwai mai lambarsa" Cikin damuwa ta ce "An bani lambar na kira baya shiga" "Wai to meye duk kika bi kika ɗaga hankalinki?" Fadila ta ce "Haba Yusra, kamar ba a gabanki kinga halin da yake shiga idan ba shi da lafiya ba, ko da yake ke lokacin da kika zo ya farfaɗo, ni da muka kaishi Asibiti ban zaci zai rayu ba, yau fa ina miki maganar yafi sati baya zuwa school, aikuwa duk abin da zai san ya yaƙi zuwa makaranta ba ƙaramin abu bane ba" "Na gane, yanzu dai ki kwantar da hankalinki, ki cigaba da Addu'a Allah ya sa yana lafiya, da an san ko unguwarsu ne ma da anje an tambayi in da gidansu yake" Fadila ta ce "Ni banji wanda yace ya san unguwarsu ba, shikenan dai sai anjima" ta ajiye wayar tare da dafe goshinta, gaba ɗaya tana cikin zullumi. Khalil dauriya kawai yake yi, ko yaje zuwa wurin aiki sai dai baya iya wani abin kirki, lamarin Hafsa ha tsaya masa a rai nesa ba kusa ba, yana matuƙar sonta da tausayinta, baya son ta faɗa hannun wanda bai san ƙaddara ba, tsananin yardar da tayi da shi ne ya sanya ta gaya masa wani babban sirri na rayuwarta, da baga gayawa kowa ba sai shi, yanzu gashi Mummy ta shiga ta fita, yanzu da wani ta gayawa wannan sirrin ba shi ba, ha zamana kuma bai aureta ba, shikenan haka zai ta kallonta da abin koma yayi ta yaɗawa a gari. Duk shirin da Amina take yi na zuwa ƙauye, da hidmar da take tayi da kuɗi babu wanda ya tambaye ta ina ta samu kuɗi, hatta wayar hannunta da aka wayi gari aka ganta da ita, Hajiya Zainab bata tuhumeta a ina ta samo ba, sai tsananin saka idanu da take fuskanta daga wurin Hajara. Ita kuwa Fadila abin da ya dameta daban dan baka ba ta Amina take yi ba, dan idan ta ga dama sai ta wuni a ɗaki bata fito ba balle su haɗu. Musamman da aka tashi daga makaranta, Amina ta tafi gidansu Azima, mamansu ta sa aka kaita wurin masu gyaran kai, aka wanke kan aka yi mata kitso ƙanana masu kyau, aka yi mata lalle ja da baƙi, sai bayan la'asar ta dawo daga gidansu Azima. 'yan kwanakin nan Daddy ya auri zaman falo, saboda kawai ha dinga ganin Amina, yana zaune shi da Hajiya Zainab Amina ta shigo gaba ɗaya ya mayar da hankalinsa kan Aminar, ba tare da Hajiya Zainab ta lura ba. Amina na zuwa ɗakinta ta ajiye jakar makaranta, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kyan da kitson kanta yayi. Wayarta dake kan mudubi ce tayi vibrating. Ta janyo wayar ta duba, sai taga saƙon Daddy ne "Lalle yayi kyau sosai, ki shirya mana dinner a dining yau, ina son zan sake gani" Murmushi Amina tayi tana sake kallon lallen, tare da mamakin ya aka yi harya ga lallen nan. Emojin murmushi ta tura masa tare da saƙo kamar haka "Ya aka yi har kaga lallen nan?" "I watch everything about you, dan haka ba abin mamaki bane, zan jira a dining ki kawo Abincin dare in kuma gani" Tana daga tsaye sai murmushi take tana bashi amsa, ta tura masa "A gajiye nake, Hajara ce zata shirya dining" "Kin mai da ni kamar wani kakanki ko? Idan baki zo ba ba ke ba zuwa ƙauye, and i mean it" Ɗan kwaɓe fuska tayi ta masa reply da "Tuba nake ranka ya daɗe, ba zan iya ɗaukar wannan hukuncin ba, zan zo in sha Allah" Murmushi ne ya suɓuce masa da ganin abin da Amina ta rubuta masa. "Ba zan haƙura ba, a haɗa mini fruit salad" Tayi masa reply da "An gama as you wish" "Wai dariyar me kake tayi ne kai kaɗai, ka tattara hankalinka a kan waya gaba ɗaya?" Daddy ya ɗago ido ya kalli Hajiya Zainab ya ce "Ke ma ba taki wayar ce a hannunki ba, hira nake da mutane na" Ta haɗe rai ta ce "Mutanenka suwa kenan?" "Nika ɗai nake rayuwa a duniyar ne, babu abokai da 'yan uwa da zan hira da su in murmushi?" Yayi maganar ransa a haɗe, tuna tana lallaɓa shi dan ta karɓi kuɗi a hannunsa ne ya sanya ta bar zancen ta sauya akalar zancen zuwa wani. "Baban Fadila anya Khalil yana da hankali kuwa?" Cikin rashin fahimta Daddy ya ce "Kamar yaya kenan?" Ta ɗanyi ƙwafa sannan ta ce "Ko kiran wayata fa ba yayi, fushi yake da ni kenan?" "I don't know, bana ce ba, ya kan gaisheni ni dai ta chat" "Lallai Khalil, aikuwa zan nuna masa nice uwarsa, a kan yarinyar talakawa zai ɗau fushi da ni?" Daddy ya ce "Idan yana sonta ki ƙyaleshi mana, Khalil fa ba yaro bane ya mallaki hankalinsa, he knows what is right for him, ki ƙyale yara su zaɓi abin da ya dace da rayuwarsu" A fusace ta ce "Over my dead body, yarinyar fa a bakin titi take sayar da kayan shirme, ai ba kimar gidan nan bace kaje nemawa ɗanka aure gidan matsiyata, Allah ya suttura, haryanzu Khalil bai san me ya dace da shi ba, dan haka ni zan zaɓa masa mace 'yar gidan daraja ya aura" Daddy ya ɗan gyaɗa kai sanan ya ce "Ba kya ganin hakan zan haifar masa da matsala? Karki aura masa 'yar mutane ya wahalar da ita, tun da ba shi ya ce yana so ba" "Shi ya isa ya tsallake umarni na? Yaje ya yi ta fushin kar ya fasa, zan maganinsa ne" Daddy dai be kuma cewa komai ba, ya cigaba da taɓa wayarsa. Kamar yadda Daddy ya gaya wa Amina, yana dawowa daga sallar isha'i ya nufi dining yayi zamansa, yana jiran Amina. Sai dai ko da Amina ta kammala girkin, ta shiga tayi sallar isha'i, Hajara ta je ta fara shirya kayan Abinci. Ba tare da ya kalli Hajara ba ya ce "Turo mini Amina ta ƙarasa kawo Abincin" "To" ta amsa gwiwa a saɓule. Ta tarar da Amina a Kitchen, ta zuba ruwa tana sha, "Alhaji ya ce ki ƙarasa kai sauran Abincin" "Ban da abu irin naki dama Hajara, ni da ki ka barwa girki nayi ai sai ki bari in ƙarasa ladana, amma na zo na tarar kin fara kaiwa" ta wuce ta ɗauki plates, da jug ɗin da ta yi fruit salad ta fice. Hajara tayi ƙwafa ta ce "Ayi dai mu gani, Allah ya tona muku asiri muga ƙaryar iskanci" Cikin sa'a Amina ta tarar Hajiya Zainab da Fadila ba su fito cin abincin ba, sai shi ka ɗai a dining. "Kana ta kallona idan na faɗi fa?" Amina tayi maganar tana jere plates ɗin hannunta. "Nace ki kawo Abinci in kuma ganin lalle, amma kika turo wata ko?" Amina ta girgiza kai ta ce "Bani na turota ba" Ya ce "Well, mu ga lallen" Ta ɗago masa dogayen yatsunta, da suka lalle baƙi da ja. "Wow Masha Allah, a yiwa lallen nan kuɗi zan saya" Ta ce "Ai an riga an biya mai lallen, Babar ƙawata ce ta biya" "Na san an biyata, wani biyan zan yi ai na musamman" "Ni dai a'a ka daina bani kuɗi haka" Muryar Hajiya Zainab suka jiyo tana waya, nan da nan Amina ta nutsu ta fara ƙoƙarin barin wurin, Da kallo Daddy ya raka Amina, yana jin ba daɗi zuwan Hajiya Zainab ta katse musu hira. "Nifa gaba ɗaya na kasa gane kan yaran nan, kowanne da salon tsirfar da ya tsira, shi wancan yayi zuciya ya bar gida ya daina kula kowa, ita wannan ta tsiri zaman ɗaki, da rashin walwala na tambayeta wai pressure ne na karatu wannan wane irin abu ne?" Daddy ya ce "Wani abu na damunta ne?" "Yo ni ina na san mata, 'yar ganin dama, koma wani abu na damunta sai ta ga dama ai zan sani" Alhaji Ahmad ya miƙe ya ce "Ba zai yiwu wani abu na damunta, kuma a zura mata ido ba. Ɗakin Fadila ya nufa, yayi knocking sannan ya shiga, tana zaune a kan Carfet ɗin ɗakinta, hannunta riƙe da littafi tana kallo. Alhaji Ahmad ya ƙarasa yana faɗin "Autana, karatun kike yi haka?" "Eh Daddy" ta faɗa a sanyaye. Shi kansa ya karanto damuwa a tatare da Fadilan, duk da gwnaace wurin iya tsiwa da surutu idan ta ga dam, but her silent part dominate the other side of her. "Amma ya ban ganki a dining wurin Dinner ba?" Tayi murmushi ta ce "Bakomai Daddy, kawai ina son yin karatuna a cikin nutsuwa ne, da kuma cin abincin nikaɗai kar wani abu ya ɗauke mini hankali" Daddy ya ce "No, i want see you by my side, ta so muje in tabattar kin ci Abinci, sai ki zo ki cigaba da karatunki kinji sweetheart" Tamkar ƙaramar yarinya, haka Daddy ya lallaɓota suka fito, ya riƙo hannunta zuwa dining yana yi mata hira. Mummy ta kallesu ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Eh, da yake babanki ne ai gashi nan kin fito, ni da kika raina ce mini ki kayi in ƙyaleki ai" Daddy ya ce "Please Madam, karki damar mini baby" yayi maganar yana zaunar da Fadila a kan kujera. "Ka mayar da ita cikinka, ƙarewar Baby ma" "Eh ba ruwanki da mu" Alhaji Ahmad yana matuƙar ɗaukar al'amuran Fadila da muhimmanci, dan wasu lokutan bai fiye damuwa da Khalil kamar yadda ya damu da ita ba, yake gudun abin da zai ɓata mata rai ba. Sosai ya dinga ƙaƙalo hirarraki yana yi mata, a haka har ta ɗan saki jiki ta ci Abinci sosai, har zuciyarta ta fara raya mata ko ta gaya wa Daddy, abin da ke faruwa amma kawai ta share, ta kamala cin abincin ta tafi ɗakinta. Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, yau ne Amina zata je garinsu, tun bayan watanni tara da ta shafe bata garin nasu duk da ba rabuwar daɗi aka yi ba, kuma bata san wane irin karɓa za suyi mata ba, hakan bai hanata yin murna da farin ciki ba, na zuwa ganin gida da zata yi, musamman ganin Inno, da shi ne babbar damuwarta. Da Asubar fari, ta ɗau akwatinta ta kai jikin motar da za su yi tafiyar a ciki, ta tsaya suna gaisawa da Zakiru, Zakirun hana tsokanarta "Ke fa yau kamar salla take a wurinki, zaki je gida" "Zakiru waya ƙi gida, kowa ya bar gida ai ba bisa son ransa bane ba, gida akwai daɗi sosai" Zakiru ya ce "Haka ne, Alhaji yayi mini maganar zan cigaba da koya miki karatu yana biyana, yaushe zamu fara ne?" "Ehh, nima mun yi maganar da shi, ka bari in dawo daga ƙauye, sai mu sanya lokaci, yadda ba zai shafi aikin da muke ba, kar ya zama abin magana". Zakiru kamar Amina ta taɓo masa in da yake masa ƙaiƙayi ya ce "Ke dai bari, wannan gida Allah ya nuna mana iyakar wannan mata, ke dai kije ki shirya da wuri, yanzun nan mu kama hanya" Gyaran murya suka ji a bayansu, Zakiru ya ɗa rikice yan risunawa ya gayar da Alhaji Ahmad. "Bamu wuri" Daddy ya faɗa ransa a haɗe, Zakiru ya bar wurin, Amina ta tsaya tana kallonsa. "Can't you greet me?" Yayi maganar yana tsareta da ido. Ta ce "To ai gani nayi ka haɗe rai" "Ba dole in haɗe rai ba, kawai kin zo nan kina ta zuba da wani" "Daddy Akwatina fa kawai na kawo ya saka a mota" "Eh daga nan kuma kika tsaya surutu ba, kin gama shiryawar ne?" Ta ɗan gyaɗa kai ta ce "Eh, na shirya kaya kawai zan saka" Ya ɗan tsareta da ido sannan ya ce "Ki kula sosai, zan dinga kiranki a waya in ji idan kun sauka" "To in sha Allah" tayi maganar tana kallon ƙasa. "Yauwa, banda yawo idan kin je ki zamanki a gida idan ba in da ya zama dole ba, bana son yawo ki zamanki a gida kin ji" Ta ɗaga masa kai alamar eh. "Talk" "To Daddy" ta faɗa a shagwaɓe. "Idan ma kika tafi yawo, za a gaya mini kuma zan haɗu da ke, maza kije ki ƙarasa shiryawa kiyi breakfast, kuzo ku tafi" Amina ta jinjina kai, ta wuce ciki. Cikin lokaci ƙalilan, ta kammala kintsawa, ta karya tana ta murna, Hajara ta rakota, har suka fito Hajiya Zainab bata tashi ba, dama lokacin tashinta bai yi ba. A kan baranda suka tarar da Daddy, yana tsaye yana danna waya, Baba kuma yana gefensa a tsaye. Murmushi Amina ta yiwa Baba ta ce "Baba tare zamu tafi?" Baba ya girgiza kai ya ce "Ai ni naje na kuma komawa, ke kaɗai zaki tafi" Tare da Daddy suka rakata har mota, cikin ƙasa da murya Daddy ya ce "Saura kije ki saki baki, kiyi ta hira da shi a mota" ba ta ce komai ba tayi shiru. Ya ce "Safe journey" Ta amsa masa da "Thank you" Amina ta shiga mota, tana ɗaga musu hannu, suka tafi. Gaba ɗaya Fadila damuwa ta fara shafar karatunta, saboda rashin sanin a wani hali Yazid yake, saboda tana matuƙar tausayin halin da yake shiga idan ba shi da lafiya. Da ko ba komai da yana nan yana takura mata, ajiyar zuciya ta ɗan sauke tana kallon agogon hannunta, ranar Litinin zasu fara jarrabawa, amma babu Yazid babu dalilinsa. Saura mintuna goma lokaci ya cika malamin da suke da shi ya shigo, babu zato babu tsammani ta ji aji ya kaure da hayaniya. Babson ne da Captain, tare da Yazid a tsakiyarsu, Captain ya riƙo side ɗin Yazid na hagu, Yazid yana takawa a hankali yana murmushi. Ba ƙaramin faɗuwa gaban Fadila yayi ba, Yazid ya rame fiye da tunani, ga wani irin haske gauuu da yayi, sai sajensa da ya ƙara yawa. Kana ganinsa ka san yaji jiki, koma yana kan sha, amma kasancewar ya zame masa jiki murmushi ne kwance a fuskarsa. Mutanan ajin ne suka fara yi masa sannu, suna masa ya jiki, sai gaisawa da mutane yake, yana musabaha da mazan. Fadila ta zuba masa ido, sai dai ta kasa ko motsawa daga in da take, sai dai ƙasan zuciyarta da take murna kasancewar babu wani babban abu da ya same shi. Kankiya ne dama zai shigo ajin, ya shigo ajin fuskarsa a haɗe ransa babu annuri sam, hakan baya rasa nasaba da canza lamba da yayi ya kira Fadila, tayi masa wankin babban bargo ta ci mutuncinsa. Ya shigo yana ta muzurai, da hura hanci, da fari bai lura da Yazid da ke zaune a ajin ba, sai daga baya bayan ya yi rubutu a kan board ya juyo. Ya sauke idonsa a kan Yazid, sake haɗe rai yayi ya kalli ce "Me kake yi a class ɗina?" Yazid yayi shiru bai ce komai ba. "Zo ka fita ka bar mini aji, dan baka da mutunci shi ne zaka zo ka zauna mini a aji, zo ka bar mini aji, kuma ka sa a ranka ba zaka zana jarrabawata ba, come and leave my class usless" Kalmar usless ɗin nan ba ƙaramin ƙonawa Fadila rai tayi ba, ji tayi kamar ta zagi Kankiya. Captain ya ce "Sir kayi haƙuri ba shi da lafiya ne, yau ya dawo" "Shut up! Nace ka sa mini baki ne? Ai ya riga ya san na hana shi zama a ajina, tashi ka bar mini ajina" Yazid ya ja jikinsa a hankali, ya tashi tsaye, sai da ya tashi Fadila ta lura da Cannula a hannunsa, a hankali yake jan ƙafarsa, tare da dafe gefen cikinsa ya fice daga ajin. Kankiya yayi tsaki ya ce "Nonsense" Miƙewa Fadila ma tayi, ta ɗau jakarta ta nufi hanyar fita, tana jin Kankiya na kiranta amma tayi masa banza ta bar ajin da sauri. Hajiya Zainab ce ta shigo ɗakin Daddy tana masifa "Wai ni ina wannan sakaran direban naka ya tafi? Tun ɗazu nake nemansa, yazo ya karɓo mini saƙo a wurin Hajiya Salma. Cikin ko in kula Daddy ya ce "Na aike shi ne" "Zuwa ina? Jiransa nake yi ni akwai in da zani" "To ke ki ɗauki mota kije ki karɓo da kanki mana, ko ta yi miki aike" "Haba Baban Khalil, ina gaya maka uzurina kana gaya mini wani abu daban, dan Allah ka kirashi ya zo ya je mini aiken nan" Alhaji Ahmad ya tashi zaune ya ce "Na aiki Zakiru Shanono, zai kai Amina gidansu" "I don't get you, and what does that mean? Meyasa zaka aike shi ya kaita ƙauye, a matsayinta na wa?" "Mahaifinta ya nemi hakan, dan ba zai yiwu ya bar yarinya ita kaɗai ta tafi ba" Rai a ɓace ya ce "I don't care, me yasa zaka yanke wannan hukuncin ba tare da na sani ba, 'yar aiki tafi aikin gidana muhimmanci kenan? Ubanta ya kaita mana, yanzu waye zai je mini aiken nawa?" Miƙewa tsaye Daddy yayi ya ce "Zainab, ba Khalil bane da Ahmad kike Magana, duk wanda yake aiki a ƙarƙashina yana da damar ya nemi alfarma a wurina nayi masa" ya fice ya bar mata ɗakin. AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA AISHA ADAM AYSHERCOOL 44 Ganin Alhaji Ahmad ma ya ɗau zafi sosai, ya sanyata saurin saukowa daga nata fushin, dan da wuya yayi fushi amma idan yayi fushi wahalar sha'ani ne da shi fiye da tunani. Dan haka ta ce "Naji shikenan ya wuce, na haƙura da saƙon na san yadda zan yi" Bedroom ɗinsa ya wuce ya barta, tabi bayansa tana cigaba da lallaɓa shi, amma ya shareta ya ƙi saurarta. Ba ƙaramin yarfa Kankiya Fadila tayi ba, ganin yadda yake muzurai ake tsoronsa amma Fadila ta yarfa shi a gaban ɗalibai, hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, kuma hakan ya jefa zargi a zukatan ɗaliban, mai zai sa Fadila ta tsinka malamin haka duk da yadda ake tsoronsa. "Yazid, Yazid" tsayawa yayi ya waiwaya da jin muryarta a cikin dodon kunnuwansa. Ta ƙarasa in da yake da sauri, bai ƙosa ba ya jira har ta cin masa. Cikin damuwa ta ce "Sannu, ya jikin naka? Ashe baka da lafiya?" "Eh, amma da sauƙi sosai Alhamdilillah" "Wai meya sameka ne?" "Rashin lafiya ne" ya bata amsa. "Wane irin rashin lafiya?" Ta kuma tambayarsa cikin kulawa. "An mini aikin appendix ne, sai kuma asma da ta dameni shikenan amma da sauƙi sosai" "To yanzu ina zaka daga nan?" "Gida zan tafi" "Ok, to muje in sauke ka" Da sauri ya girgiza mata kai ya ce "A'a ki bari na gode zan tafi" "Ba ka ganin a yadda kake tafiya, kazo muje in sauke ka" "Na gode, amma ba zan hau motarki ba, ban kai in hau mota irin wannan ba, ba ta dace da hawan talaka kamata ba" daga haka ya juya yana tafiya a hankali. Tsayawa tayi tana cigaba da kallon yadda yake tafiya a hankali, har ya ɓacewa ganinta. Tafe suke suna hira jefi jefi ita da Zakiru, yana bata labarin yanayin zamantakewar gidan kafin zuwanta. "Ai nake gaya miki, ko 'yan uwan maigidan nan duk zumuncinsu sun haƙura sun daina zuwa, sun zuba masa ido, shi kansa sai lokaci lokaci yake zuwa, dama bata yadda yaranta suje ba, kuma fa 'yan gari ɗaya ne, saboda azabar baƙin halinta, duk son sa da yayi taimako sai dai yayi bata sani ba. Ai matar nan bana zaton tana son taga Annabi" Amina ta ce "A'a karka ce haka, amma ina mamakin ita ko nata 'yan uwan basa zuwa sai ƙawaye" "To ina taga wasu 'yan uwa ma, sukan zo wasu lokutan suna ba wani kallon arziki take musu ba, amma a hakan tana jidar kaya ta bani in kaiwa wasu daga 'yan uwanta, ai ita idan kika ga tana rawar kai tana nan nan da kai, to mai kuɗi ne kai, duk ta kanainaye maigidan baya jin maganar kowa sai tata, ai har gara yanzu a kan da, sanyinsa yayi yawa, sai ya fito cikin mutane ya fito yana taƙama baki Ga yadda ake girmama shi a waje ba, amma a gidansa ba shi da kataɓus ga shegen son 'ya'ya kamar masifa, waccan tsigalaliyar 'yar ta sa idan ta zauna tana taɓara abin takaici, gata halinta ɗaya da uwarta na rashin mutunci, ba kunya idan nayi kuskure take ƙare mini zagi, ai Alhaji Ahmad yayi ta kowane fanni amma a gidansa dai damisar kwali ne" "Zakiru ya isheka haka, wasa yayi wasa banda tsikarin uwar miji da taɓarya" tayi maganar ranta a haɗe. Zakiru ya ce "Kamar yaya kenan?" "Ina ruwanka da abin da ke faruwa a gidansa kake ce masa damisar kwali, kai waya san yadda taka matar ke juyaka, ya isheka bana son wannan hirar" Zakiru ya yi murmushi ya ce "Allah ya baki haƙuri, tuba nake" Amina ta basar da shi ta haɗe rai. Message ɗin Daddy ne ya shigo wayarta. "Yaya hanya, kun isa kuwa?" Tayi masa reply "A'a muna hanya" "Ina fatan ba kya jin yunwa, idan kina jin yunwa ya tsaya ki ci Abinci" "Ka manta na karya kafin mu tafi, mun shiga Shanono, mun kusa gida in sha Allah" "Ok, to Alhamdilillah, ki gaishe su" "Thank you, za su ji" ta ɗan yi murmushi ta ajiye wayar. Hajiya Zainab ce zaune a ɗakinta tana waya da Hajiya Salma "Dan Allah Salma ki ƙara haƙuri, kwanan nan duk na kasa gane kan babansu Khalil, ya ce zai bani kuɗin amma sai wasa yake mini da hankali, da abu ya ɗan haɗamu sai ya hau fushi, a yadda yake ɗin nan idan na matsa, zai iya hana kuɗin nan, kuma ni kinga na tattare kuɗin hannuna na yi order kaya, kuma ba zai yiwu in kwashe sauran kuɗin hannuna in baki ba, saboda suma juyasu nake". Hajiya Salma ta ce "Ni yanzu ya zan yi? Turai ta bani aron million biyu, dama na wajenki nake jira da million bakwai coustom suka ce zan bayar a sakar mini kayana, da ƙyar suka bari a 5million, kuma kinga Alhaji kwanan nan ya ƙara mini jari ya ce ba zan samu ba" "Kiyi haƙuri, zan cigaba da lallaɓa shi saina karɓa zan baki in Allah ya yarda, kuma ina ga zan je Abuja a satin nan in Allah ya yarda" "Too, Zainab me zaki yi a Abuja kuma?" Hajiya Zainab ta ce "Wurin yaron nan Khalil mana, gaba ɗaya ya ɗauki gaba da ni, ubansa kawai yake tuntuɓa, ba ruwansa dani" "Kaii yaran zamanin nan, anya ba asiri suka yi masa ba, duk yadda Khalil yake miki biyayya, amma yanzu a kan wannan yarinyar ya daina shiga harkarki" "Bari kawai Hajiya Salma, bana son babansa ya gano actual abin da nayi masa, kin san halinsa a kan 'ya'yansa, gaba ɗaya ina cikin damuwa dole in je Abuja" "Ke Zainab, ai ba a yiwa yaran zamanin nan haka, ba ke yakamata kije ba, ki kai yarinyar wurin malamai, idan ma wani abun suka masa a karya shi, sannan ki nemo masa wata matar, akwai 'yar ƙanwata Hajiya Badi'a ai kin santa Kursum ki haɗa shi da ita kawai" "Kin kawo shawara haka za ayi, zai ga tsiya" "Ai kawai ba sai kinje ba, sai bayan an kai kuɗi da komai, ki ce masa ya zo ga mata shine zaki hukunta shi ki nuna masa ke uwace" Hajiya Zainab ta ce "Hakan ma yayi, na gode sosai Salma, zan zo gidanma da kaina mu ƙarasa tattaunawa" "To shikenan, sai Allah ya kawoki" suka yi Sallama Hajiya Zainab na jin ta gamsu da shawarar da Hajiya Salma ta bata. Amina tayi ta kwatantawa Zakiru hanya har ƙofar gidansu, suna parking ta buɗe motar ta tafi da gudu cikin gida, wasu daga yaran su Kawu Bala suna ƙofar gida suka bi motar da aka kawo Amina da kallo, dan ɗaya ce daga irin jibga jibgan motocin da Alhaji Ahmad yake hawa ne aka kawota. "Inno! Inno!" Amina ta dinga ƙwalawa Innon kira. Inno ta saki ƙwaryar hannunta, ta buɗe hannayenta Amina ta zo ta rungumeta, Inno ta ƙanƙame Amina kamar zata mayar da ita ciki, Amina kuwa kuka ta fara yi tana jin tsananin kewar Inno. "Amina, Amina na rasa mema zance" "Inno, yaushe rabon da in ganki?" Inno ta ce "Yau ai gashi kin ganni" Tuni wasu daga cikin yara har da 'yan matasa na maƙotansu, suka cika tsakar gidan suna kallon Amina. Suka shiga ɗakin Inno, Amina sai sake ƙanƙame Inno take yi. "Amina ya gida ya karatun bokon?" "Karatu lafiya lau Inno" Inno ta riƙe haɓa ta ce "Ohh, Amina buri ya cika ana can ana boko" "Inno kenan, ai zaki ga ribar boko in Allah ya yarda, bari in yiwa Zakiru magana ya shigo ku gaisa" Inno ta ce "Waye shi kuma?" "Direban gidan da nake aiki ne" "Au ai na zata siriki ne" Dariya Amina tayi ta ce "Ba wani siriki" Amina taje ta kira Zakiru, ya shigo gidansu Amina, suka gaisa da Inno, daga nan suka ɓige da hira kasancewar Inno ta san garinsu Zakiru yayarta tana aure a can. Mutane sai shigowa suke suna sun zo yiwa Amina sannu da zuwa, nan kuwa gulma suke zuwa yi, suna ta maganganun Amina ta zama ƙatuwa, gashi ta yi fresh ta zama 'yar gayu, ga uwar waya a hannunta. Zakiru ya kalli Amina ya ce "Amina ko zaki haɗani da wanda zasu tayani kwaso kayan da ke motar" Amina ta miƙe tana faɗin "Ai ko nima sai in ɗauka" Ya kalleta ya ce "Ki ɗauki me? Zo muje ki gani fa" Amina tabi bayan zakiru zuwa mota. Ya saka hannu ya buɗe mata boot, waro ido tayi ta buɗe baki da tayi tozali da abin da ke cikin Boot ɗin. Kayan Abinci ne kamar za a buɗe kanti, ta kalli Zakiru ta ce "Zakiru, wannan fa?" "Aike Amina kin ciri tuta a gidan nan, shekaranjiya ya saka na ɗau motar nan muke je da shi muka sayo, jiya da daddare ya ce mini a wannan motar zamu tafi, kar in bari ki san da kayan" "Na shigesu ni Amina, Zakiru kalli uban kayan fa" "Ke ki gode Allah, Allah ne ya baki, da waccan matar ta sani ba zata bari a baki ba" Amina ta ce "Zakiru kaima ka ɗiba" "A'a nima ya sallameni, bari in kira wasu su tayani" Haka aka dinga kwasar kaya ana shiga da su gidan su Amina, nan da nan sai ga matan su Baffa Lawan da yaransu sun cika gidan suma. Sai da Zakiru ya tabattar da an gama kwashe kayan an shiga da su, yayi musu sallama ya ajiye musu bandir kuɗi ya ce in ji Alhaji Ahmad. Gaba ɗaya Mamaki ya gama kashe Amina, amma ta basar kamar bata wani damu ba. "Ohh Amina, kalli yadda kika koma, lallai yanzu kin wuce ajin Jarmai, birni ya karɓeki" Cewar Amaryar Kawu Bala. Suka yi ta yaba Amina, suna son jin ƙwaƙwaf, ance musu gidan da Baba yake aiki a nan Amina ma take yi, amma shi tun da yake bai taɓa zuwa da wanan kayan ba, kuma ba a taɓa kawoshi a irin wannan mota ba sai Amina. Suna ta son su tanbaya suyi tsegumi, amma Amina ta haɗe rai ta haye Gadon Inno tana latsa wayarta, dan ba zata manta wulaƙanci da rashin mutuncin da suka dinga mata ba a baya. Gaba ɗaya Fadila ji daɗin reaction ɗin da Yazid yayi ba, ji tayi gaba ɗaya bata son zaman makarantar, dan haka ta ɗauki motarta ta wuce gida. Zuwa azahar sai ga su Baffa Lawan, an je har Gona an sanar da su, ga Amina can an kawota a wata ƙatuwar mota daga birni. Basu ƙara tsinkewa da lamarin ba, sai da suka ɓangaren su Amina, suka tarar da uban kayan Abinci fal tsakar gida, cikin ɗaki kuma kayan sawa ne da kayan ciye-ciyen da Daddy ya saiwa Amina. "Ke ina Aminar take, wanann kayan kuma na menene?" Cewar Baffa lawan yana shafa buhun shinkafa. Inno ta ce "Bismillah Baffa ku shigo" "Ba zamu shigo ɗin ba, ina Hassan ɗin ma tukuna?" Inno ta fito tare da faɗin "Ai ita kaɗai ta dawo ban da shi, shi ya zazzo a 'yan kwanakin nan" Bala ya ce "Ina Aminar ne?" "Tana ɗaki" "Eh lallai, rashin tarbiyyar ta ta har ta kai ta kasa fitowa ta gaishe mu?" Inno ta ce "A'a ba haka bane ba, ke Amina fito mana" banda Inno ta saka baki babu abin da zai sanya Amina ta fito. Gaba ɗaya suka bi ƙofar ɗakin Inno da kallo, Amina ta yi ƙiba, fatarta ta ƙara haske. "Ina wuninku" Kawu Bala ya riƙe baki ya ce "Ba shakka, yanzu dama irin wannan rayuwar Hassan ya zaɓi kiyi, shi ya sanya ya tattaraki ya kai ki birni? Ko in ce kuka haɗa baki kika gudu, yawon ta zubar ai shikenan gaki ga duniyar nan, kin ƙi sunnar ma'aiki kin shiga duniya bin yaran yahudawa" "Kawu Bala, Tazubar kuma?" "Eh yawon ta zubar mana, idan ba haka ba wani irin aiki ne kike yi haka da kika samo wannan kayan, tun da uban naki yake aikin a birni ya taɓa zuwa da makamancin haka ne?" Ran Amina yayi bala'in ɓaci, kawai ta tashi ta bar musu tsakar gidan, dan idan ta cigaba da zama zata iya rama cin zarafin da suke mata. "Ka gani ko Yaya Bala, wai mu muke mata magana ta tashi ta tafi, idan ba bariki ba mai zai kawo haka?" Ita dai Inno tayi mus shiru, suka gama cin mutuncinsu suka tafi. Inno ta koma ta samu Amina a ɗaki ta ce "Amina kiyi haƙuri, wallahi tun da kika tafi suke surutai da ƙanann maganganu" Amina ta ce "Aikuwa sai sai suyi, dan bani da lokacinsu, na gaba ya riga yayi gaba, kuma Inno a ɗibar musu wani daga kayan Abincin nan a basu, aniyarsu ta bisu" Da yamma Amina ta shirya, ta tafi sada zumunci wurin sauran 'yan uwa, kowa sai son ya ganta yake yi, masu ƙananan maganganu kuma suka cigaba da yi. Su Bala kuwa da aka ɗebi kayan Abinci aka basu, lumi suka karɓe duk da suna iƙrarin kayan haram ne. Da daddare Amina da Inno suna tare, Amina tayi musu girkin dare, suna ta hira Inno na bata labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, haka ita ma Amina ta dinga bawa Inno labarin birni makaranta da yanayin rayuwar mutanen birni. "Gaskiya Inno an mana nisa, cigaba yana birni, in Allah ya yarda a dalilin karatun nan nawa sai garin nan ya samu cigaba na gaske" "To Allah ya sa, amma da fari nima naso kiyi aurenki duk da ba Jarmai na ke so ki aura ba, amma yadda na ganki ɗin nan naji daɗi sosai, kin san bayan tafiyarki Jarmai mata biyu ya aura ya saka" Amina ta ce "Allah ya rufa mini asiri, da tuni nima ina ciki" Wayar Amina ce ta fara vibrating tana kawo haske, ganin sunan Daddy ya sanya ta kalli Inno ta ce "Ina zuwa" Ta miƙe ta bar ɗakin ta koma wani, ta zauna sannan ta amsa wayar tare da yin sallama. Sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya amsa ya ɗora da cewa "Da ba zaki ɗaga bane?" "Wace ni in ƙi ɗaga wayarka, ina tare da Inno ne ina cin abinci" "Ok, nayi zaton kin yi bacci ai" "Ai dare bai yi ba sosai" Daddy ya gyara kwanciyarsa Sannan ya ɗora da cewar "Ina fatan kin ci kin ƙoshi" "Na ƙoshi sosai ma, gani ga Inno muka ci fa, nayi kewarta sosai" Yayi murmushi ya ce "That's good, ni kuma na kasa cin Abincin" Ɗan waro idonta tayi ta ce "Me yasa?" "Ba a bani wanda nake so ba, fruit kawai naci na kwanta" Cikin damuwa da tausayawa Amina ta ce "Meyasa baka sa an dafa maka wanda kake so ba? Kar ka kwana da yunwa fa" Ya shafi cikinsa ya ce "Abincin ne bana jin daɗinsa idan bana ki ba, na san da kina nan zaki dafa mini abin da nake so" "Kar ka kwana da yunwa kaji Daddy, dan Allah ka ci wani abu" "To me zanci, kar ki damu zan kwana haka ba wata damuwa" Noƙe kafaɗa tayi ta ce "Ni ban yarda ba" Dariya yayi ya ce "Rigima ko?" "Allah da ina gida da komai dare saina dafa maka Abinci, me zai sa a bar mai nemowa ya kwana da yunwa, rashin kyautawar yayi yawa" Har cikin ransa yaji daɗin abin da ta faɗa, na nuna damuwa da shi sosai. "Ai nace karki damu, na ƙoshi na sha fruit sosai da cock" "Cock kuma?" Ta faɗa da ɗan ƙarfi. "Eh Cock" ya bata amsa. "Daddy ba a hanaka sha ba?" "To ya zan yi idan ban sha ba?" "Daddy baka kiyaye lafiyarka sai wani abu ya sameka, daga tafiyata ka cigaba da ciye-ciye ko" Sosai ta bashi dariya ya ce "Da wasa nake yi, ban sha ba" "Har naji daɗi na zata ka sha" "Mhmm ban sha ba Meenali" Amina ta ɗan numfasa ta ce "Daddy" "Mmm" Ta ɗan tura baki ta ce "Ka amsa mana" "Na amsa ai" yayi maganar yana murmushi. Ta ce "Kace Na'am Meenali" Dariya yayi ya ce "Kina son sunan kenan?" "Eh mana, idan ka faɗa sai in jini kamar wata irin babbar 'yar gayun nan, nan kuwa 'yar ƙauye ce" Ba ƙaramin dariya ta bawa Daddyn ba, "Allah ya shirya mini ke" Ta sake nutsuwa ta ce "Daddy, kayan daka saya muka taho da....." "Shhhhhh" ya katseta. "Daddy ka tsaya ka ji me zance" "Keep quiet" yayi maganar cikin bada umarni. "Daddy dan Allah ka bari nayi magana" "I say keep quiet" Ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah Daddy" "Amina i said you should keep quiet, tun da ba kya ji saida safe" Da sauri ta ce "Yi haƙuri dan Allah nayi shiru" "Idan nace bana son abu just leave it immediately" "To in sha Allah" "Yauwa ko ke fa, i hope dai baki fita ko ina ba?" Amina ta ɗan sosa kai ta ce "In gaya maka gaskiya?". "Kin fita kenan?" "A'a ai ban yi nisa ba, gidan 'yan uwanmu naje, kaga ba zan daɗe ba zan dawo" "Meyasa baki gayamini ba" "To kayi haƙuri" Cikin kwaikwayonta ya ce "To kayi haƙuri, mara ji kawai, kije ki kwanta sai Allah ya kaimu da safe kuma" "To Daddy, ko in hau Online" "A'a hutawa zaki yi, kun sha tafiya, ki gaida Mutanen gidan" Amina ji tayi bata son ta katse wayar, amma ta maze ta ce "To, Allah ya tashemu lafiya, don't forget to recite Suratul mulk before you sleep, zan kawo maka Abinci a mafarki" tayi maganar tana dariya. "Meenalin Daddy, my joy giver zan karanta in sha Allah bye bye" ya kashe wayar, dan shima idan ya biye mata ba zai katse kiran ba. Ya lumshe idanunsa tare da ɗora wayar a kan ƙirjinsa yana murmushi. Ɗaki Amina ta koma, ta tarar Inno na shirin kwanciya. "Inno har kin gama cin abincin?" Inno ta ce "To yaya zan yi idan ban ci na tashi ba, kin je kin shantake kin shanyani, wai ma da wa kike wayar ne?" Amina ta ɗan sosa kai ta ce "'yan ajinmu ne fa" Inno ta gyaɗa kai ta ce lallai kam. Fadila na zaune a babban falo, tana shan tea tana kallon wani Indiyan series, Mummy ta fito falon ita ma. "Au baki bacci ba dama?" Fadila ta ce "Eh Mummy, na kasa baccin ne" Mummy ta zauna a kusa da Fadila ta ce "Ke, wata shwara Hajiya Salma ta bani a kan Khalil, kuma ina ga hakan zan yi, dan in nuna masa kuskurensa" "Shawarar me kenan?" "Ai da Abujan zanje in ga halin da yake ciki, ya ɗau gaba dani ko gaisheni baya yi sai ya ga dama, shi ne Salma ta ce in rabu da shi, kawai in nema masa aure sai dai in ce ya dawo ga mata" Fadila ta kalli Mummy ta ce "Kuma kina ganin hakan mai yiwuwa ne?" "Me zai hana shi yiwuwa? Hakan ne kawai zai sanya in yi maganinsa, kuma in raba shi da waccan yarinyar da ya ɗora ransa a kanta". "Gaskiya bai kyauta ba sam, nima ko magana nayi masa sai ya ga dama yake kulawa, amma kar ki aura masa wadda baya so ya wahalar da 'yar mutane a banza, kin san halinsa". "Shi ya isa, zan nemo masa yarinyar wadda ta dace da shi, ba wannan shiriritar gayyar tsiyar da ya kwaso ba" Fadila ta ce "Shikenan, Allah ya sa a dace". Hajiya Zainab ta amsa da "Ameen" Ɓangaren Hafsa kuwa, sayar da ƙosai suka koma yi a cikin gida, da kayan su maggi da kayan kaɗin miya, Hafsa tayi iya ƙorainta ta cire Khalil daga ranta, amma abun ya gagara, a zahiri ta cigaba da sabgoginta, tare da nuna komai ya wuce, sai dai walwalarta ta ragu sosai tana ta dannewa dan kar Mama ta gane tana cikin damuwa, sai dai ita kanta Maman ta damu sosai da rabuwar ta su. Har zuwa wannan lokacin, Hafsa ba ta daina ɓuya tayi kuka ba, saboda ba ƙaramin so take yiwa Khalil ba. Dan har a yanzu wasu lokutan ji take yi tamkar ta mayar da layinta ta kirashi, amma sai ta fasa ta cigaba da danne abin a zuciyarta, tare da miƙa lamuranta ga Allah. Washegari jama'a basu fasa cigaba da zuwa ganin Amina ba tare da yi mata sannu da zuwa ba, wajen ƙarfe goma na safe tayi wanka ta kintsa, ta cewa Inno zata je makarantar bokonsu, ta gayar da malamanta na makaranta. Inno ta amince, Amina ta shirya ta tafi makarantar. Malamanta sun ji daɗin ganinta, Malam Sunusi ya ce "Amina, sai wayar gari muka yi muka samu labarin wai kin gudu, kwatsam na haɗu da mahaifinki a kasuwa ya ce ai kina can wurinsa a birni" Amina ta ce "Wallahi Sir a lokacin nan bani da wani zaɓi da ya wuce in gudu wurin mahaifina, Auren dole 'yan uwan babana za suyi mini a lalata mini karatuna, ni kaina ba a son raina na tafi ba, amma ina can wurin Babana" "To Masha Allah, ya karatun naki, yace mini kin cigaba da karatunki" "Eh sir na cigaba, ni shekara mai kamawa in Allah ya yarda zan gama Sakandire" Nan malaman suka yi ta saka mata albarka tare da yi mata fatan sa'a da nasara. 'yan ajinsu duk babu, wasu sun yi Aure wanda Allah ya taimake su kuma sun cigaba da karatun. Sai wajen azahar Amina ta baro makarantar, ta nufi gida, sannu a hankali take tafiyarta sam bat jin zafin ranar nan, duk da akwai nisa a tsakaninsu da makarantar, amma bata damu ta hau abin hawa ba, a ƙafa ta tafi tana tafe tana tunanin abubuwan da suka faru a baya. Sautin ƙarar wani akwalan babur ne ya cika mata kunne, tana ƙoƙarin kaucewa babur ɗin amma burki ya ƙwacewa mai baburin ji kake gauuuu!! AYSHERCOOL 08081012143 GABA DA GABANTA BY AISHA ADAM AYSHERCOOL 45 Gafe Amina tayi da sauri, shi kuma ya daki bishiya, ya kusa hantsilawa, Allah ya taimake shi bai faɗi ba, ya saki baki ya bi Amina galala da kallo "Amina" ya faɗa cikin mamaki. Haɗe rai Amina tayi ta ce "Wannan wane irin abu ne, da ka bugeni fa shikenan ka cuce ni?" "Haba Amina, ai kya bari mu gaisa, dama da gaske kin dawo garin nan, Allah mai iko" "Kaga Jarmai, babu ruwanka dani dan Allah, ka fita daga harkata" "Haba Amina, ki tsaya muyi magana mana" Wata uwar harara Amina ta watsa masa ta ce "Muyi magana kace mini me? Da ka nemi jefa rayuwata cikin masifa" "Amina ai shi masoyai ba zai taɓa zama maƙiyi ba" "Can da yawarka, ai ni ban taɓa sonka ba, kuma ba zan ba ka fita daga harkata na gaya maka". Ta juya ta cigaba da tafiya, hawa baburinsa yayi ya cigaba da binta, amma tayi masa banza kamar da dutse yake ba da ita ba, a haka har suka iso cikin gari, sai da ya bita har gida, amma ko ɗaga kai bata kuma yi ba, balle ya sanya ran zata saurareshi. A tsakar gida ta tarar da Inno tayi alwalar sallar azahar. "Amina ina kika tsaya haka kin daɗe?" "Ina makaranta, na tsaya wurin su Malam Sunusi na taho hanya wannan Jarman ya kusa bugeni da babur har ƙofar gidan nan ya biyoni yana mini magana, wai in saurareshi" Inno ta jinjina kai ta ce "Lallai Jarmai ba shi da kunya, kinga yadda ya dinga yiwa su Baffa Bala zarya, yana neman ya kai su ƙara, suka ce ya bari idan aka ganki zasu ba shi ke, ya ce ko kyauta suka bashi ke ba zai karɓa ba, wai kin tafi yawon duniya" Amina t girgiza kai ta ce "Allah ya rabani yawon duniya, yaje aniyarsa ta bishi" "Kije kiyi salla, ki zo ki ɗibi Abinci, nayi waya da babanki a kan kayan nan da aka kawo, ya kira wayarki amma kin barta a gida, ya ce a ɗebarwa maƙota ma" Amina ta ce "Na manta da wayar ne, a ɗebar musun, bari in yi salla" "Aikuwa ana ta kiranki a wayar, ni dai ban iya ɗagawa ba haka na barta" Amina ta ce "Idan nayi sallar na duba waɗanda suka kirani, na san ba zai wuce Daddy ba". Tun ranar da Kankiya ya kori Yazid daga aji, bai kuma zuwa ba, Fadila dai ta gaji ta sake kiran wayarsa, cikin sa'a taji ta shiga, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga kiran. "Assalamu alaikum" Ta amsa da "Wa'alaikum salam warahmatullah, Yazid" "Na'am" ya amsa yayi shiru. "Kana jina?" "Eh ina ji" "Fadila ce" "Na gane, ina jinki" taji haushin amsar da ya bata, amma ta basar ta ce "Ya jiki?" Ya ce "Jiki Alhamdilillah, da sauƙi sosai" "Naga baka kuma zuwa school ba tun ranar, shine na yi zaton ko jikin ne haryanzu". "Hmm in zo saurayinki ya kuma korata, jikin ne ban gama warkewa ba, wurin da aka mini aikin yana ciwo, likita ya ce in zauna a gida, ina ga sai lokacin exams zan shigo" "To Allah ya baka lafiya, tun lokacin da ka daina zuwa na sanarwa HOD in sha Allah duk zaka yi exams ɗinka ba wata matsala" Yazid ya ce "Masha Allah, na gode sosai" "Amma ka bani direction ɗin gidanku, ko Asibitin da kake, zan zo in dubaka" "No, unguwarmu ta talakawa ce sosai, idan kika ce zaki zo, motarki zata iya ɓaci, kuma ba zan so in wahalar da ke ba, na gode sosai" Jiki a sanyaye ta ce "Ba damuwa ka gaya mini in zo" Ya girgiza kai ya ce "Kar ki damu, hakan ma na gode sosai, sai anjima" ya katse kiran. Ta sauke wayar daga hannunta tana bin wayar da kallo. Haryanzu Khalil yana fama da ciwon kai mai zafi, duk da yana ta ƙoƙarin danne damuwar da yake ciki, amma kallon hotunan Hafsa da duba previous chats ɗinsu ya zame masa kamar ibada, idan bai yi ba baya jin daɗi, gaba ɗaya ya rame sosai. Gidansa da yake ta ɗoki yana ginawa, yana ƙaƙale gaba ɗaya ya dakatar da ginin, dan ji yake idan ba Hafsa ba babua wadda zai iya sanyawa a cikin wannan gidan. Bayan sallar la'asar yaga missed video call ɗin Fadila. Kiranta yayi dan yaji dalilin kiran nasa da take yi. Ya ci sa'a tana Online, ta ɗaga wayar. Ɗan zuba masa ido tayi, cikin damuwa ta ce "Yaya Khalil baka da lafiya ne?" "Lafiyata ƙalau menene?" Ta ɗan rausayar da kai ta ce "Yaya Khalil me nayi maka ne?" "Kamar yaya?" "Naga idan nayi maka magana sai ka ga dama kake amsawa, ko a waya baka kirana" Ya ɗan ɓata fuska ya ce "Ayyuka ne suka yi mini yawa sosai" "Na sani, ba wani aiki da yayi maka yawa, ka rame fiye da yadda kake tunani, duk wanda ya ganka ya san kana cikin damuwa ne. Dama na kira in gaya maka ne, Mummy tana nan tana fushi da kai, wai kana gaba da ita, Hajiya Salma ta bata shawarar ta aura maka wata yarinyar, tun da haka ka zaɓa gara ka san abin yi" Zaro ido yayi ya ce "Ban gane ba, kamar yaya a aura mini wata yarinyar, idan bana sonta fa?x" "Nima ban sani ba, haka kawai Mummy ta gaya mini, gara ka dinga kiran Mummy kana gaisheta" "Fadila ya ake so in yi da rayuwata? Yaya za ayi in gaba da Mummy, duk lokacin da na kirata sai ta mini faɗa ta ƙare mini zagi a kan Hafsa, ita kanta yarinyar mutuncina ya zube a idonta, ace uwata taje ta sameta ta ci mutuncinta wai ta rabu da ni, wanene ni ɗin? Kuma yanzu haka bama tare, yarinyar ce ta ƙarfafa mink gwiwa a kan mu rabu da juna, tun da Mummy bata so, amma gaskiya idan Mummy ta aura mini wata daban wadda bana so bata kyauta mini ba" Fadila ta ce "To ni dai ban gaya maka dan ka tashi hankalinka ba, na gaya maka ne kawai dan ka san abin da kake ciki" Ya jinjina kai tare da fesar iska daga bakinsa ya ce "Shikenan, na gode sosai" yayi disconnecting ɗin kiran, ya cillar da wayar gefe, ya dinga murza goshinsa, yana mamakin yadda Mummy ke biye shawarar ƙawayenta fiye da komai. Sai da Amina ta idar da sallar azahar, sannan ta turawa Daddy saƙo "Can i call you?" Kusan mintuna goma da tura masa saƙon, Daddy ya kirata. Wani nishaɗi ne ya ratsa Amina, ganin kiran Daddy ta ɗaga wayar tare da faɗin "Ina wuni?" "Kin dawo kenan?" "Eh, amma makarantarmu naje na gaida malamaina, ba wani wurin naje ba" "Kin dai fitan, baki gaya mini ba" ya faɗa yana kwance agogon hannunsa. "Kayi haƙuri, zan dinga tambayarka" "Well, ya gidan ya kowa da kowa?" "Kowa lafiya lau, ka san wani abu?" "A'a, sai kin faɗa" "Jarmai fa na haɗu da shi a hanya ya biyoni" ɗan tsuke fuska Daddy yayi, amma ya ce "Wow, kin haɗu da tsohon zuma kenan?" "Allah ya kiyaye, ka san yadda na tsani mutumin nan, Allah dai ya taimakeni, bayan tafiyata mata biyu ya aura ya saka" Daddy ya girgiza kai ya ce "Kashh bai kyauta ba gaskiya, to ke yanzu idan ba kya son Jarmai wa zaki aura?" "Kai fa kace ba zan yi soyayya Yanzu ba" Kawai Daddy ya fara dariya, ita ma ta biye masa suna dariyar tare. "Meenalin Daddy, am missing you gaskiya, da wurin zan tura a dawo mini da ke, ina son ganinki sosai" "Wallahi Daddy nima ina son in ganka, kuma ka kusa komawa aiki ko?" "Eh Meenal, hutuna ya kusa ƙarewa" Ta ɗan langaɓar da kai ta ce "Shikenan idan ka tafi na daina ganinka sai a waya?" "Will you miss me?" Yayi maganar yana ƙasa da muryarsa. "Zan yi mana sosai" "Ai zamu dinga waya, kin san kina dawowa zaku yi tafiyar nan, ki cigaba da karatunki kin ji" "To Daddy amma daia zaka zo Abujan?". "Babu tabbas, zan tura Khalil dai lokacin zai yi clashing da time ɗin aikina" Ai sai Amina ta fara kuka tana diddira ƙafa "Daddy ba fa haka muka yi da kai ba, ni dai dan Allah ka zo, ko in fasa zuwan" Daddy ya ɗan buɗe baki ya ce "Ki fasa zuwan, da kuwa munyi faɗa da ke" "To dan Allah ka zo" shiru yayi yana sauraren yadda take masa shagwaɓa, ya lumshe idanunsa yana shafa ƙirjinsa, ya ɗan jaa numfashi ya ce "Meenal" "Na'am" "Bana son rigima, ki cigaba da karatunki, zan turo a ɗaukeki jibi in sha Allah" "Daddy" "Shhhhhh, maza kiyi abin da nace" Ta rausayar da kai ta ce "To shikenan" Ya ce "Yauwa Meenalina" "To daddare zaka kirani?" "Dare lokacin matata ne, sai da safe kuma in Allah ya kaimu" shiru tayi ba tayi magana ba. "Hello, kina jina?" "Eh, ina jinka" tayi maganar tana jin haushin amsar da ya bata ɗazu. "Za muyi Video call da safe in sha Allah, ina son in ganki" "Da safe aiki zan yiwa Inno" Sai da dariya ta kusa ƙwacewa Daddy, ya ce "Idan kin gama aikin zan kiraki, ki ce ina gaisheta" daga haka ya katse kiran. Ajiye wayar Amina tayi, tana hararar wayar. Amina ta sada zumunci sosai a ƙauye, wasu ta burgesu matuƙa da suka ganta, wasu kuma ƙanan maganganu suka cigaba da yi a kanta. Babu kunya babu tsoron Allah, Jarmai ya cigaba da sintiri a wurin Amina, bayan ba irin cin mutuncin da ƙagen da bai yiwa Aminan ba, bayan barinta ƙauyen. Kwanan Amina huɗu ta fara haɗa kayanta, ji take kamar karta tafi, tun ana ya gobe zata tafi, Daddy yake kiranta a waya, yana jadadda mata ta shirya da wuri, zai aiko a tafi da ita. Ƙarfe sha ɗaya na safe, Amina ta gama shirinta, yaran Baffa Lawan suka shigo gidan wai ga 'yan sanda nan, Amina ta zo. Inno ta dafe ƙirji ta ce "'yan sanda kuma, meye haɗinmu da 'yan sanda?" Amina ta ce "Bari in leƙa in gani" Amina ta saka takalmanta, ta leƙa waje, motoci uku ta gani, da kuma 'yan sanda suna kaiwa suna komowa a ƙofar gidan, yara da matasa suka tsatstsaya suna kallo. Baƙin glashin wata mota aka sauke, saiga Alhaji Ahmad a ciki a zaun, yana sanye da baƙin glass, da dark blue ɗin shadda ba ƙaramin kyau yayi ba. Buɗe baki Amina tayi da mamaki ta ce "Daddy" Alama yayi mata da hannu, tazo. Ƙarasasa Amina tayi gaban motar tana masa murmushi. "Daddy dama kai zaka zo ka ɗaukeni?" "Eh mana ba gani ba, i hope kin gama shiryawa?" "Na shirya, amma zaka zo ku gaisa da Inno ko?" Daddy ya ce "Eh mana, je ki mini iso" "Amma baka gaya mini zaka zo ba, da na maka girki" "Kar ki damu, jeki mini iso mu gaisa" Da sauri Amina ta nufi cikin gidan tana kiran Inno. "Ke lafiya, meya kawo 'yan sanda?" Cikin washe baki Amina ta ce "Inno Alhaji Ahmad ne fa, zai zo ku gaisa" Amina bata tsaya ƙarasa yiwa Inno bayani ba, ta ɗauko uwar tabarma, ta shimfiɗa a tsakar gidan, ta ce "Inno ki sako mayafinki bari in ce ya shigo". Tare da Amina suka jero suka shigo, ya samu wuri ya zauna a kan tabarma, Inno ta fito suka gaisa, ta shiga jero masa godiya, amma ya ce ba komai karta damu, ya zo tafiya da Amina ne, saboda makaranta. Inno ta zubo man shanu fal da fura ta bawa Alhaji Ahmad, ya karɓa tare da yi mata godiya. Amina ta kai Akwatinta mota, Inno ta rakota har ƙofar gida, a nan suka iske su Bala. Amina ta ce "Daddy, ga 'yan uwan mahaifina nan, ga Baffa Lawan da Baffa Bala" Ta kalli su Bala ta ce "Baffa, ga Alhaji Ahmad, wanda muke zaune a gidansa ni da Baba. Saboda tsananin kwarjini Alhaji Ahmad, haka suka zube jiki na rasa suka gaishe shi, ya amsa musu yayi musu alheri, sai dai sai da Amina tayi kuka da taga zata tafi ta bar Inno. A motar da Alhaji Ahmad ya ke Amina ta shiga, yara suka taru suna ɗaga musu hannu suka bar ƙauyen. "Daddy, wai yana ganka da 'yan sanda kamar zaka kama mai laifi?" "Saboda tsaro, ai a ƙa'ida ina yawo da su saboda tsaron lafiyata, yanzunma dan doguwar tafiya zan yi ne, amma Allah ne ke karewa ai" Ta ɗan kalli Daddy ta ce "Mmn kayan nan sun maka kyau, kamar wani ango sai ƙamshin turare kake" Daddy ya gyara hular kansa ya kalleta ya ce "Kamar wani ango ko? Zaki maimaita a gabanta" Amina ta tsuke fuska ta ce "Ita wa?" "Lovely Zeena" Ta ɗan taɓe baki ta ce "Lovely manya" "Ke, kin fiye tsaurin ido fa, wai me matata tayi miki ne kike kishi da ita?, gaya mini gaskiya what is in your mind about her husband?" Yayi maganar muryarsa can ƙasa. Amina ta kalleshi ta ce "Like?" "Nothing" daga nan yaja bakinsa yayi shiru. Ko da suka isa cikin garin Kano, maimakon su wuce gida, guest house ɗinsa suka wuce. Amina ta kasa yin shiru ta ce "Daddy ya na ganmu a nan kuma, ba gida zamu wuce ba?" "Eh ba gida zamu wuce ba" yayi maganar ransa a haɗe dan kar ta sake yi masa wata tambayar. Gaba ɗaya ba haka ta so ba, da aka yi parking ma bai ce ta sauko ba, dan kanta ta sauko tabi bayansa. Sai da suka je tsakiyar falon gidan, sannan ya kalleta ya ce "Ki shiga wancan ɗakin, kiyi sallolinki, za a kawo miki Abinci ki huta da la'asar Zakiru zai zo ya kai ki gida" Jiki a sanyaye ta ce to, dan ita duk ba haka ta so ba. Ta ware mayafinta ta yafa sosai, tayi sallar azahar, tayi adduointa, ta kira Inno ta sanar mata sun sauka, yanzu zasu ƙarasa gida, sun ɗan jima suna waya sannan Amina ta kashe wayar. Ajiye mayafinta tayi a kan gadon dake ɗakin, ta tafi gaban mudubi tana duba fuskarta, ta kwance ɗan kwalin kanta tana sake gyara shi, kawai aka turo ƙofa, tsayawa yayi a bakin ƙofar yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya sai ta ɗan rikice, gashi tayi nesa da mayafinta da ke kan gado. Lumshe idanunsa yayi ya buɗe, kamar wanda aka yiwa dole ya ce "Zo ki karɓa" yayi maganar yana miƙo mata leda. Kasa motsi tayi daga in da take tsaye, saboda kunya da ta gama mamayeta. "Meenal, am talking fa" Sunkuyar da kanta tayi ƙasa, ta fara tafiya a hankali, tana jin yadda idanunsa ke yawo a jikinta, ta ƙarasa in da yake tsaye ba tare da kalleshi ba. "Menene? Ya naga kina sunkuyar da kai meyafaru" Yayi maganar tamkar bai san meya sanyata cikin ɗari-ɗari ba. "Babu komai" ta faɗa ba tare da ta kalleshi ba. "Ga Abinci nan, da kin yi sallar la'asar kije haraba Zakiru na jiranki, ni zan tafi yanzu, zanje wani wuri" Ta karɓi ledar hannunsa ta ce "Na gode" Kamar yadda ya gaya mata, bayan sallar la'asar ta tarar da Zakiru a harabar gidan yazo ɗaukarta, ita har mamaki ma take yi, Daddy baya tsoron ko Zakirun ya gayawa Hajiya Zainab cewar suna yawo tare, har gidansa ya kai ta. Zakiru bai nuna mata komai ba, sai tambayarta ya ta baro mutan gida, a haka har suka isa gida. Baba na ganinsu ya taso da murnarsa zuwa wurin motar, Amina ta fito tana masa murmushi tare da gaishe shi. Ya amsa mata cikin sakin fuska ya ce "Ya hanya, ya babar taki?" Amina ta ce "Lafiya lau Baba, kamar kar in dawo gida da daɗi" Baba yayi murmushi ya ce "To ko zaki koma ne?" "Ai Baba ba dan wannan tafiyar ta makarantar mu ba, da ba zan dawo yanzu ba" "To shikenan, maza shiga ciki ki samu ki huta" Amina ta juya ta ɗau Akwatinta da Zakiru ya fito mata da ita, Baba sai sannu yake masa, Amina ta ja Akwatinta zuwa cikin gidan. A falo ta tarar da Hajiya Zainab da ƙawayenta su Turai, sun ci Abinci duk sun bar kwanukan. Amina ta ce "Ina wuninku?" A yamutse suka amsa mata, dan Hajiya Zainab bata amsa ba, sai ma kallonta da tayi ta ce "Zo ki kwashe kwanukan nan" Mamakine ya kama Amina, Hajiya Zainab dai ba makauniya ba ce ba, taga Akwati a hannunta yanzu ta dawo, amma saboda tsabar son ta wulaƙantata wai ta zo ta kwashe kwanuka. "Ko ba zaki zo bane, kika cake a wurin kina kallona?" Amina ta jingine Akwatin, ta zo tsakiyar falon, ta kwashe kwanukan ta kai Kitchen, ta zo kuma kwashe sauran, Mummy ta kuma kallonta ta ce "Idan kin gama, na fito da labulaye na barsu a kan gado, zaca cire na part ɗina gaba ɗaya a sanya wannan, Carfet ɗin bedroom ɗina ma, zaa a canza wani, wannan fita da shi za ai, Zakiru ya kai shi Car wash. Amina kawai ta jinjina kai ta tashi, ta kai kwanukan ta dawo ta ja Akwatinta. Hajara ce ta fito daga ɗakinta, sanye da hijjabi alama salla tayi, ta washe baki tana faɗin "Amina ashe kin dawo ya hanya?" "Lafiya lau Hajara, ya aikin?" Hajara ta kwaɓe fuska ta ce "Aiki gashi nan, kin tafi kin barni, matar gidan nan da alama akwai abin da yake damunta, kullum cikin sauke mini kwandon bala'i take, da na motsa sai hantara, haka ita ma 'yar ta ta, kai wanan masifa ni Hajara wanan mutane kamar gadonta suka yi" Amina ta ɗan taɓa baki ta ce "To Allah ya kyauta". Hajiya Turai ce ta kalli Hajiya Zainab ta ce "Ita kuma wannan 'yar aikin taki daga ina na ganta da uwar akwati?" "Wai nan ƙauye ta je" Turai ta ce "Ni fa gani nayi tana wani ƙara kyau" "Ke ni bar ni da zancen banza, Hajiya Salma, ya batun yarinyar nan da kika ce in haɗata da Khalil, da wuri zan duk abin da ya dace, kan ya lallaɓa ya koma wurin waccan shahshashar ban sani ba" Hajiya Salma ta ce "Karki damu duk ranar da kika shirya, ki zo muje kiga yarinyar" "Allah ya kaimu jibi, zan zo muje" Amina ta shiga aikin canza labulaye, kamar yadda Hajiya Zainab ta umarce ta, Amina ba ta gama aikin nan ba sai bayan sallar isha'i, gaba ɗaya ta gaji. Kasancewar tafiyarsu ta ƙarato, ya sanya Amina ta duƙufa cigaba da bitar karatun da tayi, ana sallar isha'i, ta shige ɗakinta, hatta Abinci a ɗakinta ta ci. Wajen sha ɗayan dare ta ga kiran Daddy, ta ɗaga ta saka wayar a handsfree taƙi magana. A hankali ya ce "Meenalin Daddy" "Na'am" "Au na zaki kulani ba, ki ka ɗaga wayata ki ka yi shiru?" "Ai kaima watarn haka kake mini" "To naji, zan samu tea?" Amina ta ɗan tura baki ta ce "Ni gaskiya a gajiye nake, daga dawowata aka sani canza labulaye da Carfet, da nayi niyyar ko girki na yi maka, amma ko akwatina ban ajiye ba aka sani aiki" "Waye ya saki aikin?" "Ai kai ma ka sani" "To shikenan naji, da safe idan Allah ya kaimu, ki mini girki kin ji Meenalina, am missing your delicious food, kuma kinga kin fi kowa sanin Abincin da ya dace da ni" Ta yi wani murmushi kamar tana gabansa ta ce "I Will in sha Allah" "Ranar Wednesday zaku tafi, so ki cigaba da shiri, idan da wani abu da kike buƙata ki sanar da ni" "Eh, abu ɗaya nake so" Cikin zaƙuwa ya ce "What it is?" "Your presence their" tayi maganar a shagwaɓe. "Rigimar ce ko, sai da safe" ya kashe wayar. Ajiye wayar tayi tana cigaba da mita, ta mayar da hankali ga karatunta. Cikin rashin samun mafita, da rashin karsashi Khalil ya kira Mummy a waya, sai da ta kusa katsewa sannan ya samu ga ɗaga. "Yau ka ga dama ka neme ni kenan?" Yaji muryarta maimakon ko gaisawa ta bari suyi. A saɓule ya ce "A'a ba haka bane, bani da lafiya ne" "Eh, ko ba baka da lafiya ba? Kana fama da ciwon so ko, gubar Asirin da suka zuba suka baka a Abinci bata sake ka ba, to ka sani in kai sun shanye ka ni basu shanye ni ba". "Mummy dan Allah duk a bar wannan maganar, ni kiranki nayi na gaisheki" "Ka riƙe gaisuwarka bana so, jibi in Allah ya kaimu zanje naga iyayen yarinyar da na zaɓa maka, next za a kai kuɗin Aurenka da ita" "Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah Mummy kar ki mini haka" "Ai tuni ma an riga an yi, idan ka ga dama kayi mini biyayya, idan ba ka ga dama ba kabi 'yar matsiyata mai awara a hanya!! AYSHERCOOL 08081012143