[12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EuFGI1TIgdlAhVJXP2XqPJ *ƳAN ADAIDATA SAHU* (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH *ASSALAMU ALAIKUM* Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. Ga no ta ku tura mn screen shrt domin samun shiga paid grp da zarar free pages sun kare 09013181851 Page 1️⃣➡️2️⃣ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Kwance take a saman gadonta ta takarkare sai sakin munshari take hankali kwance, daga can gefe jikanta ne Jabiru ɗan kimanin shekara sha takwas yana kwance a tsakar ɗakin a kan katifarsa. Idanunsa biyu dama yana jiran Iya Ansai ta yi nisa a cikin baccinta dan ya fara mafarkin ƙarya babu ɓata lokaci ya buɗe baki ya ce. "Ina za a kai ku ne Hajiya? Kuɗinki naira ɗari bakwai ne" Haka yake ta faman maimaitawa, tun Iya tana jin abin cikin bacci har dai ta tashi ta wartsake. Jin alamun tashinta sai Jabiru ya ƙara kaimi wajen faɗin abin da yake faɗa wannan karon har yana ƙarawa da faɗin. "Ku hau zan ɗan sha mai a wancan gidan man sai mu tafi" "Allahu akbar kabiran, ni dai Ansai ina neman kai kaina wuta wallahi, ina zan kai girman zunubin cin amanar yaro maraya, na kasa cika masa burinsa na siyan arincaɓa (Adaidata sahu). Ni yanzu bani da komai da zan siyar na siyawa yaron nan arincaɓa ga shi son abin yana shiga ransa har cikin baccinsa mafarkin abin nan yake" Ta faɗa a fili tana share hawaye. Duka abin da take Jabiru yana jin ta kuma yana ganinta ta hasken farin watan da ya shigo ɗakin. Fitila ta kunna ta sakko daga kan gadon har lokacin tana kuka tare da jan hanci, ta nufi wajen akwatin ƙarfenta ta buɗe ta zauna zaman dirshan a gaban akwatin ta shiga ɗaga atamfofinta da suke a linke, a can ƙasan ta ɗakko wata leda sai da ta dakata ta waiwaya alamar kar ko wani yana kallonta, ganin dai babu alamar mutum kuma Jabiru har lokacin yana ta maganganu shi a dole mai mafarki. Ledar ta kunce sai ga wata ledar a ciki haka ta shiga kukkuncewa har dai ta kai ledar ƙarshe a ƙalla sai da ta since lodoji takwas sannan ta fito da abin. Irin danƙwala-danƙwalan sarƙar tsakiyar nan ce irin ta mutanen da, sarƙa da ɗankunne da kuma abin hannu masu duwatsu rafka-rafka. Ɗaɗɗagawa ta shiga yi a fili ta ce "Ko a ina zan samu masu siyan waɗannan? Yanzu lalacewar zamani ta zo har an daina saka murjani, lokacin zamanin da, da a wancan lokacin ne na siyar da sarƙar nan ya isa in siyawa yaron nan arincaɓa in fita haƙƙin maraicinsa dan bana son abin da za a ce Jaburu (Jabiru) Ya yi maraicin uwa ni ce nan uwarsa ni ce ubansa, dan ubansa da shi da babu duk uwar ubansu ɗaya ba kula yake yi da shi ba ni kuwa sai Allah ya saka mini so da ƙaunarsa fiye da ƴaƴan nawa ma, amma dai kyakkyawan zato ina ga ma sarƙar nan tafi zinare daraja" Ta faɗa tana mayar da kayan. sarƙar tata ta mayar cikin ledojin nan haka ta saka su a leda cikin leda, ta rufe akwatin ƙarfen ta tashi ta koma ta zauna a bakin gadon hannunta riƙe da ledar da fitilar tocilan ɗin nata. "Da safe sai Umaru ya nemo inda zai siyar da sarƙar nan, ya kawo kuɗin nan a siyawa yaron nan arincaɓa wallahi ba zan zauna in mutu Allah ya ƙona ni ba, ya kama ni da cin haƙƙin maraicin ɗan nan, ni kaina na san darajar sarƙar nan ta fi ta daham(Gold) Yo sarƙar da tun ta armena(Aure) Amma har yanzu gata nan kamar sabuwa dal, dan haka ina ga idan aka siyar har sai an samu sauran kuɗi wataƙila ma sauran kuɗin ya isa a siya masa fege(Fili) A masa gini a sama masa mata ya yi aure tun da shi ma na ga shegiyar jaraba ce da shi" Ta faɗa tana ɗaga filo ta saka ledar sannan ta sauka daga kan gadon ta je wajen katifar Jabiru ta shiga ɗan bubbuga shi a hankali. Miƙa ya yi tare da matso hawaye ya tashi zaune. "Sannu ka ji Jaburu, wannan aboki naka da ya baka labarin arincaɓar nan da ake tuƙawa a binni ana samun kuɗi, sannan ya nuna maka hoton ta wallahi ya ɗau alhakin ka ya shiga haƙƙina, haka kawai ya hana mana zaman lafiya da yin bacci cikin kwanciyar hankali" Ta faɗa tana rushewa da kuka irin na tsoffi. "Ki yi haƙuri Iya Ansai tun da na yi ido biyu da Adaidata sahun n... "Jaburu ina faɗa maka wallahi ka guji yin saɓo, tun ba yau ba nake raba ka da kiwon kyallu amma kana cewa kyallu ta haihu, in banda kuna son kuke yin saɓo ina ka taɓa gani an ce "sahu" Idan ba sahun sallah ba haka kawai ka guji fushin Allah a kan ka tam ni dai babu ruwana bana ciki" "Haba Iya Ansai wai sai yaushe za ki fahimta ne" "Sai ranar da ubanka ya fahimta" Ta faɗa cike da faɗa. Kafin ta ɗora da maganar ya saki kuka irin na sangarta. "Ash-sha ai ka ji irinta kai kuma baka san wasa ba haba Jaburu ya za a yi na ɓata maka rai dan Allah da manzonsa ka gafarce ni, kar ka saka wutar Allah ta ci ni a kan ɓatawa marayan Allah rai" Ta faɗa tana roƙonsa har da ajiye fitilar hannunta ta haɗe hannayenta kamar wanda aka ce ta masa wani gagarumin laifi. "Zan yafe miki amma gaskiya ni sai kin san yadda za a yi a saya mini, kin ga ni ba sana'a nake ba, amma in kina ganin ba za a saya mini ba sai in haƙura dama ai in kana maraya sai dai ka ga masu uwa suna samun ab... ",Haba dan Allah Jaburu ai kai ba maraya bane uwa ce kawai ka rasa amma ni ai ni ce uwarka ni ce ubanka, kuma tun da har ka ce za ka yi sana'ar arincaɓan nan ai dama babu maraya sai rago, na maka alƙawarin a gobe ba sai jibi ba za a siyo maka shi sabo fifil a ledarsa dan na ɗakko kadarata wacce take ajiye shekara da shekaru wacce darajarta ta fi ta daham(Gold) Ita za a ɗaga a siyar a siya maka dan ni a kan son da nake maka hatta kaina zan iya yankewa in baka bare abin duniya ai na haƙura da murjanin nan nawa" Ta ta fsana dafa kansa, wani shu'umin murmushi ya saki a ransa yana jin daɗin tarkonsa ya kama tsuntsu dan dama ya san arina wai an saci zanin mahaukaciya, ya san dama dole duk runtsi sai Iya Ansai ta saka an siya masa Adaidata sahun. "Allah ya saka ki a aljanna Iya Ansai ki sha jar miya da naman kaza" "Amin, amin ɗan nan, ai addu'ar nan da kake minj kaɗai ma ta isheni tun da na kyauttawa maraya, ai mJaburu da ranka ya ɓaci gwara ko tafiya tsirara ne in yi dan cikar burinka" Ta faɗa tana ɗan darawa ta ɗauki fitilarta ta koma ta hau gadonta shi ma ya kwanta. "Ai sai ka juya ka sha baccinka mu jira wayewar gari" "Yanzu kuwa Iya Ansai tawa ta kaina gaki ga ni a aljanna" "Kai amin Jaburu da na ji daɗi wallahi" Ta faɗa tana ɗan matse ƙwalla ta koma ta kwanta bacci ya yi awon gaba da su. *DA ASUBA* Da faɗuwar gaba Iya Ansai ta falka, saboda tinowa da ta yi ta fito da ajiyarta ta kadararta ta ajiye a ƙasan filo tsoronta ɗaya kar ko an shigo tana bacci an yi awon gaba da sarƙar, da yake lokacin da ta buɗe idanunta ta kai hannu ta kunna fitilarta sai ta ganta a can gefe ɗaya filon da ta saka sarƙar a ƙasansa ta ƙaƙume shi, shi ma yana can da ban. Hakan ya sanya ta yi tunanin ko ɓarawo ya shigo. "La'ilaha ilallahu muhammadur rasulullahi S.A.W" Ta shiga rafka salati a zuciyarta gabanta yana tsanata faɗuwa tana ɗaga filon. "Na shiga talatin da tara ni Ansai ɗiyar mai siyar da allo jikar mai siyar da tawada, idan aka ɗauke sarƙar nan ta murjani nan mai tsawon tarihi an taƙaita ni an sace dukiya mai ɗinbin yawa, ya zan yi da alƙawarin da na yi wa marayan nan jiya cikin sulusin dare?" Ta faɗa a ranta hawaye suna ambaliya ta wurgar da filon a can gefe tana lalumawa ashe zanin gadon ne ya rufe ledar shi ya sa bata ganta ba. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ƙwarara guda uku. "Allah ya taimake ni, da ina zan kai nauyin alƙawarin da na yi wa marayan nan, ai da na ɗau alhakinsa, ai kuwa da wanda ya ɗau sarƙar nan sai na saka an gewaya laya dan ɗinbin dukiyar nan ba za ta tafi a banza ba" Ta faɗa tana sako ƙafafunta ƙasa ta sakko sai da ta waiwaya ta tabbatar babu kowa kuma Jabiru yana ta munshari sannan ta ɗaga zaninta ta saka a cikin aljihun ɗan tofinta(Siket na tsofaffi da suke sakawa a cikin zani). "Ina yin sallah zan kirawo yaran nan mu zauna ai gwara ni in siyar da kadarata in siya masa ina raye ba zan bari ya yi maraici ba" Ta faɗa tana nannaga zip ɗin ɗan tofin sai da ta tabbatar ya zigu sannan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita. Alwala ta ɗauro lokacin duk an shiga masallaci, da yake bayin nata a ɓangarenta yake dan haka babu ruwanta da zuwa can tsakar gidan bayan ta gama alwalar ta dawo ɗakin tana kiran sunan Jabiru. "Kai Jaburu ni ina dalilin wannan bacci naka kai kullum baka zuwa sallar asubahi sai dai idan rana ta fito katakau ka zo kana sallah da ƙadangaru, yo sallah da ƙadangaru mana kana kai sujada ƙadangare ma yana gyaɗa kai ai shi ma lokacin ne yake sallah" Ta faɗa tana nufar shimfiɗar tasa ta shiga bubbuga shi amma ko gezau bai yi ba baki ta taɓe ta yi gaba ",Wallahi ba zan biye maka ba, haka kawai kai baka yi sallar ba ni ma in je ban yi ba lokaci ya ƙure a yi ba wan ba ƙanin wato babun baɗinuhu" Ta faɗa tana shimfiɗa sallayar ta kabbara sallar. Har ta idar da sallar amma Jabiru yana ta munshari. Bayan ta shafa addu'ar ta jiyo ƙaran ƙofar gida alamun dawowar ƴaƴan nata daga masallaci, tashi tsaye ta yi ta fito daga ɗakin nata ta taho tsakar gidan lokacin su duka kowa ya shige ɗakin matarsa. "Mamman( Muhammad ne ake kiransa da Mamman) Umaru!" Ta shiga ƙwalla musu wani kira mai kamar babu lafiya. Shiru kake ji tsakar gidan babu kowa sai muryarta da take ta faman rafka musu kira. Baba Mamman ne ya fara fitowa daga ɗakin matarsa, sai Baba Umaru ma ya fito da sauri yana gyara zaman hularsa. "Oh Allah na tuba waɗannan yara da jarabar son mata kuke wallahi, a ce ku bakwa rabuwa da ɗakin mata yo ina dalilin an kwana ana abu ɗaya da safe ma a ɗora sai ka ce jaraba, maimakon ku tafi turakar ku amma sai ku ƙare a bibiyar ɗakin mata dan jaraba kowanne ya kama mace ɗaya kamar rai kun kasa ƙara aure su ba haihuwa suke yi ba sai cikawa mutane masai da kashi(Toilet) Ai dama wajenku Jabiru ya yi gadon jarabar nan dole ma idan an siya masa arincaɓar nan sauran kuɗin a gina masa gida a masa aure kar ma a zo yake lalume ƴaƴan mutane a lungu ake A'i ina indo" Ta faɗa a ranta tana bin ƴaƴan nata da kallo da suka zo cike da girmamawa. "Gamu Iya" Kowanne ya faɗa yana ɗan sunkuyar da kai saboda kunyar da ta lulluɓe su dan sun san halin Iya yanzu sai ta ce sun je sun maƙalewa matansu. "Yo kwa zo ku tsaya mini getse-getse, kamar bishiyar dalbejiya, kuna sunkuyar da kai kamar mararsa gaskiya, ku wuce muje ɗakina maganar sirri nake so mu yi tun da yanzu gari ya fara haske kafin kowa ya fito tsakar gida, a mana laɓe a ji abin da za mu tattauna, yo kar a samu wani ya ji wannan babban batu a je a bini har gadon baccina a maƙure ni da filo saboda son dukiya" Ta faɗa bayan ta rage murya kamar mai raɗa sai wani dogon wuya take tana kallon ɗakunan matan ƴaƴan mata gudun kar wani yaji mai take cewa. Duk da sun san halin mahaifiyar tasu amma sai da mamaki ya mamaye musu zuciya, sai dai babu wanda ya isa ya tambayi dalili, dan haka umarni kawai suka bi Baba Mamman ne ya fara yin gaba cikin ɗan sauri-sauri dan ya je ya tashi Jabiru ya yi sallah saboda basu da wani kataɓus Iya ta hana a tashe shi zuwa masallaci wai har yanzu yaro ne, kuma kar a shiga haƙƙin marayan Allah a tashe shi daga bacci a ɗauki alhakinsa har sun yi sun gaji sun ƙyale. Yana shiga ya ɗaɗa masa duka da sauri ya tashi yana muzurai da murza baya. "Wuce ka je ka yi sallah sakaran banza da wofi kuma saura in ji ka ce wa Iya ni na tasheka" Ya faɗa yana aika masa wata uwar harara. Tashi ya yi yana gyaɗa kai kamar ƙadangare yana shirin fita daga ɗakin sai ga Iya ta kawo kai Baba Umaru yana biye da bayanta. "To Jaburu har ka falka da sassafen nan garin ko gama wartsakewa bai yi ba?" Ta faɗa tana tsare shi da idanu. "Eh ai dama tun fitarki na motsa" Ya faɗa yana ratsewa ya fice ita kuma ta taɓe baki ta shiga ɗakin. "Kai Mamman kar dai a ce kai ka katsewa marayan nan baccinsa, wallahi Mamman ka kiyayi fushin ubangiji a kan ka idan kana shiga haƙƙin maraicin yaron nan" "Haba Iya ni ma da na shigo zaune na same shi a kan katifarsa" "Ayyo ko da na ji" Ta faɗa tana samun wuri ta zauna daga can gefe shi ma Baba Mamman ɗin dama a zaune yake. "Umaru, Umaru, wai ina kake ne kai kamar ba ɗakin uwarka ba sai ka raɓe a jikin bango kamar wani ƙadangare" Ta faɗa cikin ɗaga murya ganin Baba Umaru bai shigo ɗakin ba. Baba Umaru kuwa ya tsaya ne a wajen yana yi wa Jabiru faɗan ƙin zuwa masallaci yana faɗa masa duk ranar da ya mutu Iya ba za ta je kabari ta cece shi a kan azabar da za a masa ta wasa da sallah ba. Yana cikin faɗan ya ji ta kira shi da sauri ya shiga bakinsa ɗauke da sallama ya samu wuri ya zauna. "Uhm Bismillahi bari in tashi in saka mana labule rufin asirin ɗaki" Ta faɗa tana tashi tinƙis-tinƙis ta nufi ƙofar su dai da ido suka bi mahaifiyar ta su suna mamakin tarasun da ta yi da farar safiyar nan. Bayan ma ta saka labulen sai da ta garƙame ƙofar ta saka sakata, da kallo suka bi junansu kowanne yana raya cewa abin babba ne tun da har da su rufe ƙofa tamkar za a yi wani munfurci, bayan da safen nan babu kowa ma bare ta ce wani zai shigo. "Ai shi batun dukiya abu ne na sirru(Sirri) Komai yana son a yi cikin hikima asiri a rufe" Ta faɗa lokacin da ta dawo ta zauna. Babu wanda ya tanka illa iyaka kowanne mamaki ya kashe masa baki jin ta ambaci dukiya. "Umaru maza fita ka ɗakko tocilan ɗin nan taka mai cin batira shida, na ga jiya ka mata sabon zubin sabbin batira" "Iya mai kuma za a yi da fitila bayan gari ya waye tangararai?" "Au Allah Umaru idanu ka fini da har kake cewa gari ya waye yo ai na san da garin ya waye amma na ce ka ɗakko ai tun da ka ji haka akwai magana kuma akwai amfanin da za a yi da ita a wannan zama namu, sannan idan ka ɗakko fitilar ka kalli gabas da kudu yamma da arewa ka tabbatar babu wani wanda ya ganka" Ta faɗa cikin halin ko in kula. Baba Umaru kallon Baba Mamman ya yi sai Baba Mamman ɗin ya gyaɗa mas kai alamar ya bi umarnint, tashi ya yi yana cewa "To Iya" "Au Allah, to wallahi Umaru ka fita idona in rufe, kana neman shigar mini hanci da ƙudundune yanzu har ni in yi magana saboda ka raina ni sai ka kalli Mamman ya gyaɗa maka kai, kamar ƙadangaruwa" "Allah ya huci zuciyarki Iya ba haka bane" Ya faɗa yana tashi ya buɗe ƙofar ya fita jin kaɗan sai ga shi ya dawo riƙe da fitilar. "Mayar da ƙofar nan ka rufe ruɓuk bana son tonom silili" Bai ce komai ba ya rufe ƙofar ya saka sakatar dan dai a zauna lafiya sai dai su duka suna mamakin abin da za a yi da fitila bayan gari ya waye kuma ma abin wai har da rufe ƙofa da saka sakata. "Ka tabbatar babu wanda ya ganka ko Umaru?" Ta tambaye shi daidai lokacin da ya zauna. "Babu wanda ya ganni" "Yawwa ko da na ji, ai na san ku kaɗai ne ƴaƴana kuma ku kaɗai ya kamata mu rufe mu binne kowanne sirri" Ta faɗa tana tsare su da idanu. "Haka ne Iya" Suka haɗa baki waje faɗa dan sun ƙosa su ji abin da ya sa ta tara su wanda take ta nannago bayan ta ambaci dukiya, bayan kuma a iya sanin su ko kuɗin siyan ƙosai sai sun bata amma kuma yau ɗaya tana maganar dukiya sai dai suna ta maganar ko dai shiriftun tsufa ta fara duk d sun san ragas take sai dai in yau shiriftun ya same ta. "Ko dai mafarki ta yi ta tsinci kuɗi a leda" Baba Mamman ya faɗa a ransa dan ya rasa mazaunin da zai ajiye maganar tata. "Iya dai ko cewa za ta yi bara za ta fara tun da mun kasa cikawa Jabiru alaƙawari, take maganar dukiya bayan tana ta neman kuɗin da za ta siyawa Jabiru adaidaita kuma yau tana maganar dukiya" Baba Umaru ma yake maganar a zuciyarsa. "Bismillahir rahmanir rahim" Bismillar da Iya ta yi ta katsewa kowa zancen zucin da yake. Da kallo suka bita ganin ta tashi tsaye ta basu baya ta ɗaga zani tana ta lalumen siket ɗin ɗan tofinta. Kowa ya zubawa sarautar Allah ido. Sai da ta gama ta dawo ta zauna tana jan hailala da salatin annabi S.A.W. Da kallo suka bi ledar hannunta. "Iya ba dai tsuntuwar kuɗi kika yi ba, kuma irin wannan ai da tun da zamu masallaci kika bayar aka kai cigiya" Baba Mamman ya faɗa yana bin ledar da kallo. "Wallahi kuwa dan ma kar a zo a fara yekuwa ana cewa za a gewaya laya" Baba Umaru ma ya faɗa yana kafe ta da idanu. Baki sake galala take kallon su kafin ra yi ƙarfin halin cewa "Oh Allah na tuba ni Ansai an zo zamanin da yara suke yi wa iyaye hawan ƙawara, yanzu bakwa bari in mutu ku binne ni ba, ina abu kuna tarar numfashina, to masu gewaya layar sun daɗe basu gewaya ba" "A'ah Iya ba a yi haka ba, mu ai ba ma so mu rasa ki ba" Baba Umaru ya sake faɗa. "Mtsss aikin banza shafa lalle a ɗuwawu" Ta faɗa tana fara since ledar. Babu wanda ya ƙara magana illa iyaka sun zubawa sarautar Allah ido, ɗakin ya yi tsit baka jin komai sai ƙaran ledar da Iyar take sincewa. "Haba Umaru hasken fitilar taka fa yana barin saitin ledar lai da za kake haska saitin inda nake buɗewa" Ta faɗa tana ɗago kai ta aika masa wata harara da ta sa ya gyara riƙon fitilar. "Kai ma Mamman baka saita sosai ba, yo ni ina dalili ina ɗan mafari kowa hankalinsa yana wani wuri, wato kowanne yana tunanin ƙeƙasassiyar matarsa matan fa ba haihuwa suke ba duk da kun tara mana taron yuyuyu, sai cika mana masai suke da kashi sun kasa haihuwa sai shegen cin abincin tsiya kamar gara" Ta faɗa tana aikawa kowanne su harara. Basu tanka ba dan idan da sabo sun saba da halin mahaifiyar tasu. Baki a sake suke bin abin da ta fito da shi daga ledar ganin sarƙar tsirkiya irin ta ƴan da, wato irin manyan tsakiyar nan da ake yin sarƙa da su murjani. "Iya mene ne wannan?" Suka haɗa baki wajen tambaya da mamaki fal a maganar su. "Ƙundun ubanku ne, na ce ƙundun ubanku ne, in banda yaran zamani har kun sa na yi suɓutar baki ina zagin marigayin ubanku, in fito da kayan kuɗi tsababa amma kuna mini tambayar rainin wayo da rainin hankali" "Kayan kuɗi?" Suka ƙara haɗa baki a karo na biyu. "Aikin ɓur in ji tusa, ai ni a nawa ganin duk mai zuwa sama ya taka leda haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya, to abin da ya gagare ku ne ni na taƙarƙare zan yi, dan ku gane irin so fa ƙaunar da nake yi wa Jaburu(Jabiru) Tun da kun kasa siya masa arincaɓa (Adaidata sahu) Shi ni na ce bari na ceto zuciyar maraya daga damuwa ko na samu rabauta ranar ƙiyama, wannan kayan sarƙoƙin a yanzu na san ya ƙara daraja fiye da tunanin duk wani mai tunani yanzu na san ya fi zinari(Gold) Daraja girman nan nasa na san ba ƙaramin kuɗi zai yi ba. Dan haka na ɗakko a siyar a kawo kuɗin a siya masa arincaɓa, a siya masa fege(Fili) A siyi kayan gini da kuɗin masu gini a gina masa gida ka ga ko aure za a masa an huta, sauran kuɗin in je makka da madina ɗakin manzo ku ma kwa sami kasonku na ladan ganin ido ku ja jari" Tun da ta fara magana bakin su yake buɗe wanwar kowa sakin baki ya yi kamar layar mai tafiya yake bin Iya da kallo na tsagwaron mamaki ganin tsakininta da Allah take magana. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 *ƳAN ADAIDATA SAHU* (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH *ASSALAMU ALAIKUM* Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page2️⃣ "Iya Yanzu da kuɗin murjanin ne za a siya masa adaidatan, har da fili a yi gini sannan ki je makkah duk a ciki?" Baba Mamman ya yi ƙarfin halin jefa mata tambayar. "Au Allah, ni abin da na kasa ganewa ma shi ne tambaya kake yi ko neman sani? Magana aka baka ita a buɗe amma kana mini wata magana mai kama da rainin wayo" Ta faɗa tana aika masa harara. "Ba haka bane Iya abin ne dole a sanya ayar tambaya yanzu waye zai siya wannan murjanin?" Baba Umaru ya faɗa cike da tsoron maganar da za ta faɗa. "Yo ni da zan nemo masu siya ma ina zan tara ku ai da sai dai ku ga arincaɓar a ƙofar gida, amma ni wannan duk ba damuwata bane, idan kuna ganin a garin nan masu siya da daraja zasu yi wuya sai a ranci kuɗin mota a je birni a siyar idan an kawo kuɗin sai a biya wanda aka ranci kuɗin motar ba shikenan ba dai tun da yake kuɗin motar kuke yi wa ido" Ta faɗa tana karkata kai gefe. "Iya ba maganar babu masu siya da daraja bane... "Yawwa ko da na ji" Ta katsewa Baba Mamman hanzari. "Iya wallahi fa babu wanda zai siya wannan tsakiyar, ban sani ba ko wajen ƴan gwangwan wato baban bola, irin wannan masu yawo da baro suna siyan tsoffin kaya da ƙarafe, idan ya siya da daraja wallahi bai fi ya baki ɗari biyu ba ita ma sai an kai ruwa rana tun... Baba Umaru da ya taƙarƙare yana rattabo bayani ganin Iya ta tsaya tana kallonsa sai ya yi tunanin fahimta take ashe haushi ne ya turnuƙe ta, ya fara ƙoƙarin ƙara ƙaimi wajen mata bayani bai ankara ba ya ji ta wanke fuskarsa da mari. "Bolo, na ce bolo, dan gwafar ubanka saɓo kake so ka yi? Murjanin nawa ne tun na aurena da ubanka za a bawa baban bola ya siya? Abin da nake saka ran samun miliyoyi a jikinsa,dan na san iwar haka darajarsa ta fi ta zinare (Gold) Amma dan baƙin ciki ka ce wai jaka ɗaya(200) Za a bani sai ka ce wata wacce uwata ta ce in je na gani, sarkar da ko masu ajiye kaya a gidan tarihi suka samu siya za su yi, a ajiye ta a gidan tarihi' Ta faɗa tana rushewa da wani marayan kukan takaici dan gani take Umaru ya gama rainata har zai ce ta kai sarƙar da ta kwashe shekara da shekaru tana ajiya amma a ce wai baban bola za a kai wa ya siya. "Allah huci zuciyarki Iya" Baba Umaru ya faɗa yana dafe da kunci. "Iya ki yi haƙuri amma gaskiya ya faɗa miki, dan ko baban bolan ko masu kayan gwangwan ɗin da ya ambata to wallahi ba lallai su siya bama ko da naira ashirin ne, ni ina ganin ki ajiye kike saka kayanki, dan ko ta kwanan baya da aka tsiro yayinta za ki ga ana yin su masu ƙananan tsakiya ne, kuma basu fi ɗari biyar ake siyar da setin su ba yanzu ba a yayinsu sosai bare kuma wannan murjanin da yanzu sai kaɗan daga cikin yarbawa ne suke sakawa yarbawan ma maza s... Tun kan Baba Mamman ya kai aya shi ma ya samu nasa kason marin Iya sai muzurai take cike da ɓacin rai ta buɗe baki cikin muryar kuka ta ce "Amma ƙur'anin Allah kun gama cin tuwo a kaina,dan cin fuska murjanin ne yarbawa suke sakawa yarbawan ma maza" Ta faɗa tana ɗaga sharɓeɓiyar sarƙar da idan ta saka sai ta zo har kan cikinta saboda tsawo kallon sarƙa da tuna irin burikan da ta daɗe tana ci a kanta ya sanyata fashewa da kuka tamkar a gidan mutuwar da ba a ɗauke gawa ba Baba Umaru ne ya buɗe baki zai yi magana amma ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu. "Ya isa! Ku tashi ku fice mini daga ɗaki bana cikin masu wauta kamar ku banzaye masu tunanin banza da baku da aiki sai bin ɗakin matayenku, ku tashi ku ɓace mini a gani tun kan ran kowa ya ɓaci dan idan aka jima kuna cigaba da aibata murjanin nan ina iya ɗaga muku nono d... Tun kan ta kai aya suka tashi sumi-sumi ɗaya yana bin bayan ɗaya Baba Umaru da fitilarsa ko kashewa bai yi ba suka buɗe ƙofar suka fice. "Mutanen banza kowa da kai tun na haihuwa, ana harkar arziƙi suna yin batun tsiya, to wallahi a bakin ku, da kuɗin murjanin nan zan cika gaba ɗaya burikan da na lissafa muku, mu zuba mu gani, murjanin nan tun yana sabo na daina sakawa, bai fi a ƙirga ba sakawar da na masa n ajiye saboda na san idan da rai akwai ranar da zai yi dajara ake nemansa ido rufe" Ta faɗa tana ɗaga sarƙar ta mayar da su cikin ledojin ta ƙulle ranta duk a matuƙar ɓace dan babu abin da ya ɓata mata rai ya kuma dagula mata lissafi sama da yadda suka ce wai baban bola ne ko ƴan gwangwan za su siya, kuma abin haushin ma wai a bata ɗari biyu. "Na yi alƙawarin babu wanda zan ƙara kirawo wa a cikin ku a kan batun siyar da sarƙar nan, da kaina zan tafi na siyar a yau ba sai gobe ba, a ɗuro mini kuɗin a ledar viva dan na san sun yi kaɗan a ƙaramar baƙar leda, kai sai na siyo buhhunan barkono guda takwas ma dan daga na dawo idan suka ga ana shigo da buhhunan barkono su san kasuwa ta yi kyau dan sai sun ƙaryata kansu da kansu na cewa sai baban bola ne zai siya, dan yau har kasuwa sai na je dan sai tayin da ya mini dan ba zan siyar da araha ba in zo daga baya in ji wani zai siya da gwaɓi in ke cizon yatsa" Ta faɗa a zuciyarta tana zuwa ta buɗe akwarin ƙarfen nata ta saka ledar a ƙasan kayanta. Tana shirin rufe akwatin sai gani ta yi an bankaɗo labule baki ɗauke da sallama Aliya matar Baba Umaru ta shigo ɗauke da samirar turon Iya da baban kofi mai koko a ciki. Da hanzari Iya ta rufe akwatin ta yi saurin matsawa daga wajen tana haɗe rai ta ce. "Na ga ikon Allah faɗa da mai gari ranar salla, ke dai Aliya mai hali ba ya fasa hakinsa wallahi yanzu a ce ba za ki yi sallama ba ki fara nemen izini sannan ki shigo ij an baki dama in ba a baki ba ki koma, amma sai dai ki bankaɗo labule gidif ki shigo sai kin zo tsakiyar ɗaki ki yi sallama" Ta faɗa tana aika wa Aliya harara. Aliya kuwa turus ta yi jin maganar Iya dama ta saba da ɗora hau a gado irin na Iya shi ya sa ma ko damuwa basa yi dan abu kaɗan sai ta ringa sababi. "A yi haƙuri Iya sallamar nan dai sai da na yi uku ƙwarara a waje na ji shiru ba a amsa ba, to sai na yi tunanin ko kina bayi shi ya sa ma na shigo" Ta faɗa tana durƙusawa za ta ajiye kwanon tuwon da jug ɗin koko. "Ke dakata! Kar ki ajiye mini tuwon nan naku ci kat ka mutu, abu ɗanye lagaf baya wani dahuwa ku a duniyar nan a ce baku iya tuwo ba ya nuna, ake ci ana santi a ji turo ya tuƙu ya dahu dumurmur da shi kullum abu lagafgaf kamar ɗanmalele" Ta faɗa a fili tana yatsina fuska, a zuciyarta kuma ta ce "Taɓɗi! Allah tsari gatari da saran shuka, ni Ansai Allah raba ni da aikin da na sani haka kawai ni da zan damƙi sulalla yau, zan zauna cin tuwo da koko haka kawai su ruɗe mini ciki in kafa yin kashi ina sawu bayi, ai ni yau sai dai in ci tsire da balangu da lemon kwalba in siyo kayana idan zan dawo, mu yi burunshi (Brush) Ni da Jaburu"Ta faɗa a zuciyarta tana kallon kwanon tana yatsina fuska kamar ta ga kashi. "A yi haƙuri Iya za mu gyara" "Ko ku gyara ko ku cigaba da yin ɗanyen naku ya rage" Ita dai Aliya bata ce komai ta tashi ta fita daga ɗaki "Idan ma kasuwa ta yi yadda nake so, kayan abincina zan siya in ke girkina in huta da wannan ci kar ka mutun" Ta faɗa tana taɓe baki. Bayan ta watsa ruwa ta ɗauki galleliyar atamfarta ta saka, tana cikin naɗa gwaggwaron su na tsofaffi Jabiru ya shigo yana tafiya yana kumbura baki lo sallama babu ya shigo ya zauna. "Jaburu shalelen Iya ɗan gaban goshina waye ya taɓa mini kai" "Yo ba yunwa nake ji ba ina can masallaci da na yi sallah na kwanta nake bacci sai yanzu na falka cikina sai ƙugi yake yana ƙwallawa ciroma kira" "Kai amma ban ji daɗin maganar nan ba, amma ungo jaka guda (200) Ita kaɗai ta rage mini amma da yake yau akwai bushasha na san za mu riƙi miliyoyinta, ka je ka siya waina yau babu kai ba cin tuwo" Ta faɗa tana miƙa masa kuɗin bakinsa da nata washe kamar gonar auduga. "Allah tsunduma ki aljanna Iya, ga shi kin ce yau za a cika mini burina" " Amin ɗan nan da yardar Allah kuwa yanzu zan tafi na ci kasuwar sarƙar murjanina, kuɗin ma a ledar viva zan sako shi na siyo mana tsire da balangu da lemon kwalba sai mun ci mun ture yau, dag ana dawo za a siyo maka arincaɓa kai har gida zan sa a siya maka a maka aure ni kuma in je makka in siyo maka kayayyaki" Ta faɗa tana dafa kafaɗarsa. Wani tsalle ya doka yana ta murna. "Amma gwara mu je in raka ki" "Babu in da za ka je ni kaɗai mintina kaɗan zan dawo iyayenka na ce su je su siyar suka watsa mini ƙasa mai tsakuwa a ido, yanzu da kaina zan je in siyar yanzu kuma zan dawo ka san masu kai kayan irin su barkono da kalwa su ne suke jimawa a kasuwa suna talla da neman mai siya ni kuwa da zan kai kayan maƙudan kuɗi ina zuwa za a cake a bani"Ta faɗa tana tuna irin daɗin da za ta ji idan ta damƙi kuɗin. "Ai kuwa yau ina ɗakin nan daga na siyo waina zan dawo in yi zaman jiranki" Ya faɗa yana fita domin zuwa siyan waina ransa kuwa fari ƙal. "Yawwa gwara ka zauna ka jira ni" Ta faɗa tana linke ledar vivan ta buɗe akwatin ta ɗakko ledar sarƙar ta saka a ɗan tofinta ta yafa mayafi ta ɗauki ledar vivan aka sako takalmi ɗan madina aka fito ana wata tafiya irin ta masu jiran zuwan kuɗi. "A dawo lafiya" Aliya da Maimuna da suke tsakar gidan suka haɗa baki wajen faɗa. "Allah sa, kuma kar wanda ya sake ya kai mini dambu ɗaki dan idan na gani ma zuciyata tashi za ta yi wanda kuka kai na safe ma suna nan ajiye yadda aka kai mini ni yau wankin ciki zan yi" Ta faɗa ba tare da ta jira amsar sh ba ta saka kai ta fice. Tun da ta fito bakinta yake a washe tafiya kaɗan ta saka hannu ta taɓo ledar sarƙar cikin aljihun nata, sai ka ce wanda ledar za ta ɓace. "Bari na fara zuwa gidan Dillaliya dan kar in tafi in siyar a kasuwa ta ga ban biyo ta hannunta ba ta samu alkairi" Ta faɗa lokacin da ta karya kwanar gidan Dillaliyar. "Allah dai ya sa tana nan ita ɗin uwar ƴan yawo" ,Ta faɗa idanunta kafe a ƙofar gidan dan tana zaton ko ƙofar a rufe. Cikin sa a kuwa a buɗe tana zuwa ta tura ƙofar ta shiga da sallama, amsa mata ta yi. "Lale marhabin da iya Ansai" Cewar Dillaliya da take sanye da doguwar atamfa an cokara ɗaurin ɗankwali. "Yawwa ana gida kenan" "Wallahi kuwa ban kai ga fita ba, amma ina shiri dan yanzu zan fita karɓar basussuka" "To madallah" "Daga toi ko daga matoya?" Cewar Dillaliya tana dariya. "Uhmm daga gida nake kuma tafe nake da abin arziƙi na ce bari na biyo ta hannunki kin san ƴan magana sun ce dillalin jariri shi ya san kuɗin wada" "Wannan haka yake, amma kuma sai na ganki hannu na dukan cinya Iya" "Eh kin san ba kowace ganima ake gani ba a hannu ba, wannan a aljihu na taho da ita ledar da za a saka kuɗin ce ma na rage buri na ɗakko viva, dan ba dan na kai zuciya nesa ba buhu zan ɗakko" "Ikon Allah na zaune ya faɗi, yanzu iya sai ka ce wacce ta riƙo damid(Diamond) ko lu,u-lu,u ko kuwa babban zinare" Dillaliya ta faɗa tana kama haɓa cike da mamaki a zuciyarta kuma tana fatan wata banza ce ta faɗi ita ma ta kwashi rabonta dan ta san dai dole ta wanki gara dan tsohuwar ba lissafin kuɗaɗe masu yawa za ta sani ba, dan a nata tunanin Iyar ko tsuntuwa ta yi. "Kina kan hanya Dillaliya ai babu maraba to idan ma akwai to sai dai abin da na ruƙo ya doke waɗanda kika lissafa a kuɗi" "Na shiga aljanna na maƙale ni Dillaliya, bani in sha Iya Ansai saboda na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba" Dillaliya ta faɗa cike da ƙosawa dan a son kuɗi irin nata har ta fara tunanin idan har sarƙar gwal ce ta zo da ita to babu makawa ta dannawa Iyar filo har sai ta daina numfashi, idan ya so idan dare ya tsala ta fitar da gawar ta jefar dan ba za ta bari a yi babu ita ba dan sai ta ci karenta babu babbaka. Murmushi Iyar ta shiga yi irin na ni kaɗai na san abin da na riƙo. "Iya sai ja mini rai kike" "Bari dai na fiddo ba dan kin nuna kin matsu bama kuma ni ma ina son a je a yi mini hanyar masu siya kema ki samu rabonki da sai kin bani goron albishir" "Kar ki damu daga baya ma zan biya bashin goron albishir ɗin" Ta faɗa cike da jin haushin tsohuwar. Hannu iya ta saka a aljihun ɗan tofin nata bayan ta wangale zanin jikin nata, ledar ta fito da ita tana ƙoƙarin sincewa Dillaliya ta karɓe ledar hannunta har karkarwa yake tana sincewa. "Taɓ akwai gwarama kenan tsuntsu daga sama gashashshe ina zaune har gida rabo na minallahi, dole ma ki garzaya barzahu a yanzu ba sai anjima da dan na ji sarƙar da nauyinta Allah kaɗai ya san gram in da za ta yi i aka auna" Dillaliya ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta kai ledar ƙarshe. Tana buɗewa suka yi ido huɗu da sarƙar murjani irin mai rafka-rafkan nan mai kama da ta yarbawa, sakin ledar Dillaliya ta yi cike da takaici Iya ta bi ledar da kallo rai a ɓace ganin Dillaliya ta jefar mata da kayan kuɗin da take saka ran karɓarsa ba kaɗan ba. "Haba Dillaliya wannan irin jefarwa ai sai ki rage musu farashi haba ke da zan ga kina murna kina tsalle kina sanya mini albarka na kawo miki kayan arziƙi har gida"Takaici ya hana Dillaliya magana sai da ta haɗiya wani malolon baƙinciki sannn ta buɗe baki ta ce "Ina kayan kuɗin? Wannan ne abin arziƙin ko dai na tsiya ni amma tsinta kika yi a bola ko?" "A kakar bola na tsinta bana son iya shege Dillaliya ni za ki wa tonon silili, da cin fuska, ki kalli sarƙar miliyoyi ki ce a bola na tsinta to wannan tun ta aurena ce " "Ai ni ba zan biye miki ba sai dai in ce ki kwashe tarkacenki ki fice mini a gida dan duk wanda na kai wa ya siya sarkar nan cewa zai yi bani da hankali dan wannan ko ƴan gwangwan da baban bola ba za su siya ba, su ne dai masu siyan tarkace, saboda son banza har da wani ɗakko ledar viva za ki sanya kuɗi to ai ko naira biyar babu mai siya" "Ke kuwa Dillaliya Allah wadaran naka a lalace in ji jakin gida da ya ga jakin daji, ke ma ta su Umarun za ki mini da suka ce sai dai a kai wa baban bola, dan wulaƙanci sarƙar tawa ta mutan da wacce na daɗe ina tanadi" Haushi ya sanya Dillaliya tashi tsaye tana nuna wa Iya hanyar waje. "Ko baki faɗa ba tafiya zan yi kuma wallahi kin yi wa arziƙi dundu, aikin banza jiran jirgi a tashar mota" Iya ta faɗa tana tashi daga zaunen da take ta saka ledar sarƙarta a ajjihunta ta fito daga gidan tana sababi. "Wai ko dai akwai ƙamshin gaskiya lamarin nan, ya za a yi a ce bakin su ya zo ɗaya da su Umaru? Wani ɓangare na zuciyar Iya ta jefa mata tambayar. "Babu wani nan kawai tsabar baƙinciki ne da hana ruwa gudu" Wani ɓangaren na yaudararriyar zuciyarta ya bata amsa. Hankali kwance ta kama hanyar kasuwa tana addu'ar Allah sa ta samu masu siya da daraja. Tun da ta shiga kasuwar take yawo abinka da kasuwar ƙauye duk sai Iya take ganin kuɗin da take hari za a bata gaba ɗaya zai iya saye kayan kasuwar gaba ɗaya. "Malam nawa-nawa" Cewar wata budurwa da ta ɗaga abin hannu na tsakiya mai ƙanana. Hankalin Iya gaba ɗaya kan su ya koma ganin mutumin sana,arsa siyar da kayan tsakiya na wuya da kunne da na hannu duk ya rarrataye wasu kuma suna zube a kan tabarmar gabansa. "Naira hamsin -hamsin" Ya faɗa yana kallon yarinyar Iya kuwa gabanta ne ya shiga faɗuwa ya saki baki tana kallonsu. "Yo ke ai taki ta mutane da ce kuma mai manya -manya" Wani ɓangare na zuciyarta ya bata amsa, wata ajiyar zuciya ta sauke dan har ta ji hankalinta ya ɗan kwanta. "Uku ɗari idan ka siyar" "kawo" Ya faɗa ko musu babu. "Yanzu abin hannun ne guda uku ɗari, saboda ma rashin darajar su ko musu bai yi ba?" Iya ta faɗa a zuciyarta tana ɗaga ƙafafunta da suka yi sanyi ƙalau ta nufi wajen mai kayan. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://chat.whatsapp.com/Duq93sLLgjCKV0uuildAH1 ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH GARAƁASA💃GARAƁASA💃💃💃 Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page3️⃣ Sai da ta tsaya ya sallami yarinyar sannan ta matsa kusa da shi kamar za ta masa raɗa. "Ala gafarta malam ina son magana da kai" "Sarƙar za a baki ko abin hannu" "Abin da na zo maka ya fi gaban wannan" Ta faɗa tana waiwaya wa hagu da dama kamar wata munafuka, ganin kowa yana sabgar gabansa sai ta ji hankalinta ya kwanta. "Kamar yaya?" "Babu komai sai alkairi dan haka ka kwantar da hankalinka ni ba da sharri na zo ba, taimakon juna za mu yi, wato ina ɗauke da kayan kuɗi ne a jikin nan nawa, to shi ne nake so mu yi sirri tsakanina da kai Allah ya zame mana shaida" Ta faɗa har lokacin tana masa maganar kamar raɗa amma kuma ana iya jin duk abin da take cewa, daga gefe guda wasu samari ne guda uku a zaune a wani benci ɗaya daga cikinsu yana zuƙar sigari kana ganinsu ka ga ƴan jagaliya, dan duk kamar ma sun shayu idanunsu jawur. Duk abin da Iya take yi suna kallonta a fakaice kuma suna jin abin da take faɗawa nutumin sai dai babu wanda zai ce ma suna sauraron su, domin dama duk wanda ya iya allonsa sai ya wanke. "Wane irin abu ne na dukiya a jikin ki amma ni ban ga alama ba" Ya faɗa yana wani washe baki har da saka harshe ya lashi leɓɓansa saboda ya ji maganar kuɗi shi kuma dama mayen kuɗi ne duk da ya san ƙuda wajen kwaɗayi akan mutu, amma dai yanayin yadda Iya take magana ya fahimci gaskiya ce babu sirkin ƙarya dan haka sai ya ji ya amince da ita. "Ba zan iya ambata maka ba saboda cikin kasuwa bashi da sirri, wuri ne na jama'a kuma wuri ne na ka zo na zo, sai dai ina maka albishir da cewa idan har ka nuna mini inda aka siyar da kayan nan to na tabbatar za ka samu abin da za ka gina kan ka da shi, dan ba lallai ma ka ƙara kasa sana'ar tsakiya ba, saboda ni kaina ina tunanin za a siyi hajar da mafi darajar kuɗin da ba lallai su lissafu ba" Mutumin mai kimanin shekara sittin ya zaro idanu dan gaba ɗaya mamakin Iya ya kashe shi hakan ya sanya ko dogon tunani bai bari ya wahalar da kansa ba take yanke ya amince. Gaba Iya ta shiga ya take mata baya ko takan kayan sana'arsa bai bi ba dan yana ganin banza ta faɗi. Da yake daga inda ya kasa kayan nasa akwai wajen da wata ƙofa take fita sai kawai suka bi ƙofar da ta fito da su daga kasuwar sauri Iya take yana binta iska sai kaɗa babbar rigarsa take wacce ya saka babu ko ƴar ciki. "Mu tsaya mana a nan" "A'a baka ganin daga ni har kai girma ya fara mana sallama kar a je wani ya warce kafin mu nemi ɗauki ya gudu gwara dai hanyar lafiya a bita da shekara" Sai da suka zo ƙofar wani gida suka tsaya Iya tana son fito da sarƙar tana tsoro saboda idanun jama'a duk da babu wanda ya kawo su a ka amma ita ganin ta riƙo kayan kuɗi sai take jin bata yarda da wajen ba. "Malam mu shiga daga zauren gidan nan in nuna maka mu yi komai cikin sirri in ya so idan ka gani ka faɗi wajen da za mu je a siyar sai mu je ka san shi kuɗi da kuma kayan kuɗi suna son sirri, ba a son fitar da tsiraicin su saboda duniya yanzu ba gaskiya... "Wannan haka yake ai kawai mu shiga muka baro cikin kasuwa ma har shiga zaure ya mana wahala" Ya faɗa yana bin bayanta dan shi saboda son kuɗi da kuma ganin banza ta faɗi sai kawai bai kawo cewa ko za ta cutar da shi ba. Sai da suka shiga zauren gidan Iya ta ɗan hango cikin gidan sai ta ji shiru kamar ma babu kowa dan haka sai ta ɗan tura ƙofar, hakan sai ya saka mutumin wani tsoro ya rufe shi dan sai ya fara tunanin ko aljana ce a take gumi ya wanke masa fuska jikinsa ya shiga karkarwa. "Haba bawan Allah wallahi da mutum kake tare ba aljana bace" Cewar Iya dan yanayinsa ya nuna mata hakan. "Kalli ka ga ƙafafuna babu kofato farce ne" Ta faɗa tana ɗaga zaninta yatsun ƙafar suka bayyana sannan ne ya ji hankalinsa ya ɗan kwanta. Baki ya washe cikin ƙarfin hali ya ce. "Wallahi har na ruɗe" "A haba wallahi mutum nake da a ce aljana ce ai da ba sai na nemi ka biyo ni ba da kaina zan kawo ka ta saman iska" Kai kawai ya gyaɗa mata kamar wani ƙadangare. "A shegen son kuɗin nan nawa ai in kukar bulukiya ce ma za ta iya tafiya dani, ni wallahi bansan ma ya aka yi ban yi tunanin ko aljana bace sai yanzu" Ya faɗa a zuciyarsa idanunsa kafe a kan Iya yana son ya ga ta fito da kayan kuɗin nan da take ta famar ambata. Tana ta ƙoƙarin fito da ledar shi kuma ya shiga waiwayen cikin gidan daga inda yake tana son ya tabbatar cewa babu mai ganinsu dan ya ga alama gidan kamar babu kowa a ciki. "Idan na dannawa ƙofar nan sakata na maƙure tsohuwar nan sai na ƙwace koma mene ne na gudu da shi dan da arziƙi a garin wasu gwara a garinku" Ya faɗa a zuciyarsa yana fakon Iya da take ƙara zurmuƙa hannu cikin ɗan tofin nata ya ma kasa gane mai ya sa take ta nuƙu-nuƙu ga shi a gefe ɗaya gabansa yana dukan uku-uku dan kar ya je garin ƙwacewar ta rafka ihu asirinsa ya tono a je a masa duka a kasuwar nan, dan ya lura daga ganin matar za ta yi wuyar sha'ani dan ba lallai abin da ta ruƙo ɗin ya karɓu ta daɗin rai ba mai raba ta da abin sai ya yi da gaske. Basu gama tantancewa ba sai gani suka yi an banko ƙofar gidan da ƙarfi, samarin nan ƴan jagaliya guda uku ne wanda suke zaune kusa da mai siyar da tsakiyar nan ashe duk abin da su Iyar suka tattauna a kan kunnuwansu, sannan dama suna biye da su dan ganin yadda za ta kaya sai kuma aka yi sa'a su Iyar suka shiga zauren gidan samarin. Suna shigowa ɗaya ya danƙarawa ƙofar sakata idanun nan nasu jaawur, Iya da ta haɗe rai cikin hanzari ta mayar da ledar sarƙarta aljihu ta shiga aika musu harara. "Yawwa gwara da kika mayar aljihu kar a rabamu da dukiyar mu, dan ni yanzu har na sakata a cikin tsarin rayuwata duk dama waɗannan ƴan shaye-shaye sai mu doddoke su ba wani ƙarfi za su yi tun... Maganar zucin da mutumin yake ta tsaya ne ganin su duka ukun sun ɗaga riga sun fito da wuƙaƙe soke a jikin wandunan su, sun fito da su daga gidan wuƙar, idanu su Iya suka shiga zarewa musamman Iya da ta ji ta tsure lokaci guda hankalinta ya tashi dan take yanke zuciyarta ta faɗa mata ƴan fashi ne su, dan ta gan su lokacin da take faɗawa mutumin zancen sai dai bata taɓa zaton sun ji mai take cewa ba, ashe dai shuka ta yi a idon makwarwa. "Na shiga uku ni Ansai fashi da rana tsaka ni ina zan sa kaina idan suka ƙwace sarƙar nan bayan burikan da muka ci a kanta ni da Jaburu" Ta faɗa a zuciyarta jikinta yana karkarwa ganin babban cikinsu wani ƙato da shi ya ɗaga kakkaifar wuƙar ya kai saitin wuyanta yana mata wani muzurai da idanunsa jajaye. "Ku wuce mu shiga ciki" Suka faɗa cikin tsawa daga Iya har mutumin nan basu da tsumi basu da dabara haka suka shige cikin gidan kowa an saka masa wuƙa a wuya. "Lahaula wala ƙuwwata illa billahi aliyal azim,tabarakal lazi bi yadihil mulku wa huwa ala kulli shai'in ƙadir" Shi ne abin da Iya ta tsira da shi wajen ambata a zuciyarta ƙirjinta sai dakan lugude yake, tana jin wani taahin hankali marar misali dan tana ganin idan suka rabata da sarƙar nan tata wacce ta kwashe sama da shekaru tana ɓoyonta a ƙasan akwatin ƙarfe saboda irin wannan rana, to tana jin mutuwa ce kaɗai ba za ta yi ba dan baƙinciki. "Allah ka cece ni in koma wurin sana'ar tsakiyata, kar mahaukatan ƴan shaye-shayen nan su burma mini wuƙa in shiga uku, a shegen son banza na na baro kayan da suke mallakina na zo wurin da za a jinyata ni ko akasheni ma gaba ɗaya" Cewar mutumin nan a zuciyarsa yana wani zare ido kamar wanda ya yi wa sarki ƙarya. "Kai gaba ɗaya ku zubewa mutane a nan kuma ku fito da kayan kuɗin nan" Babban cikin nasu ya faɗa bayan sun shigar da su cikin ɗaki da yake ciki da falo ne sai suka ajiye su a falon. "Ni dama ban santa ba kuma ban ga kayan kuɗin ba suna jikinta" Mutumin ya faɗa cikin karkarwar murya dan wannan karon wuƙar har taɓa wuyansa aka yi da ita. "Innama amruhu iza arada shai'an an yaƙula lahu kun fa yakun" Iya ta faɗa a zuciyarta lokacin har hawaye sun yi wa fuskarta sallama, saboda irin yadda ta ji a zuciyarta da a ka ce ta fito da kayan kuɗi. "Ba, ba, babu wani kayan kuɗi a jikina dama murtala biyu (40) Zan bashi ya siyowa yara goruba zan kai musu tsaraba" Iya ta faɗa bakinta yana karkarwa tana addu'a a ranta Allah sa su yarda da batun ta. "Ah kin manta bishiyar ɗorawa za a siyowa yaran ba goruba ba" Ɗaya ya faɗa yana aika mata harara. "Gaskiya nake faɗa muku babu... "Idan ba za ta bayar ba ku farka cikinta sai ku ɗakko mana kayan kuɗi... Tun kan ya ƙarasa aka ɗaga rigar Iya, Iya tan zare idanu jin an ce a farke mata ciki kuma ta ga babu alamun imani a tare da su. "Ku yi wa iyayenku kar a farka ni kamar wata ledar tsakar ɗaki, dan Allah ku mini rai zan fito da kayan kuɗin, dama sarƙa ce da ɗankunne da abin hannu... Tun kan ta ƙarasa maganar suka fara yi wa junansu murmushi irin na mun yi babban kamun nan, babban nasu har wani gya kai ya yi, dan sun san ba zai wuce a ce sarƙar gwal bace tun da an ce kayan kuɗi kuma an ce sarƙar da ɗan kunne. "Kai amma matar nan kin gama da ni ƙur'anin Allah kuwa ashe sarƙar gwal ce a jikin ki kika yi jinkirin faɗa ga shi wasu a banza a wofi za su je su mori kuɗin ni da kika sakawa a rai ina kallo" Mutumin nan ya faɗa a zuciyarsa har da hawayen takaici suna sarto masa. "Fito da ita" "To bawan Allah amma dan Allah ka cire mini wuƙar nan daga wuyana, haba mu ba ragunan layya ba amma an ɗora mana wuƙaƙe a wuya" Cewar Iya tana saka hannu a aljihun take ƙoƙarin fito da ledar sarƙar, tana fito da ita ta kasa miƙa masa dan ji take har ranta za a raba ta da abin da ta fi so, hannu ya kai ya warce a lokaci guda yana sakin wuƙar hannun nasa dan yana ganin kakar su ta yanke saƙa sun samu abin da za su daɗe suna mora, dan dama ƙwace da yankan aljihu ne ya kai su kasuwar shi ne sana'ar su. Kurrrr kowa idanunsa kafe a kan ledar da yake kuncewa banda Iya da ta sunkuyar da kai ƙasa hawaye na kwaranya baƙinciki ya cika mata zuciya. "Allah kar ka kamani da ƙin cikawa Jaburu alƙawari, wayyo ni zan saka marayan Allah ya shiga damuwa" Iya ta faɗa a ranta tana jin ɓacin rai. "Ni da na ce a yau za a siyo masa arincaɓa(Adaidaita sahu) Amma ga shi zan koma babu kuɗi... Babu wanda ya lura da Iya kowa idanunsa suna kan ledar musamman da suka ga an saka mata uban ledoji wata cikin wata mutumin nan ji yake da a ce yana da yadda zai yi da gaba ɗaya zai musu rubdugu ya bubbuge su har Iyar ya gudu da sarƙar amma babu hali. Sai da ya fitar da ledojin saura ɗaya wacce a ciki ne sarƙar take, hannunsa har karkarwa yake wajen fito da sarƙar yana zarowa mai za su gani, sai ga sarƙar murjani danƙwala-danƙwala, kowa sakin baki ya yi ganin abin da suka ɓata lokaci a kansa, guda ɗaya daga cikinsu ya fashe da dariya dan wallahi abin ya bashi dariya sosai ma yadda suka raja'a amma a ce a kan wani abin banza da wofi ne. Hatta mutumin nan sai da dariya ta so ƙwace masa amma sai ya damƙe bakinsa yake yin dariyar a zuciyarsa dan ba ƙaramin dariya abin ya bashi ba, a gefe ɗaya kuma ya yi farinciki da ba sarƙar gwal ɗin bace saboda yadda bai mora va su ma kar su mora. "Buhun ubancan kayya! Ke tsohuwa mu za ki rainawa hankali ki yi wasa da tunaninmu a kan wannn abin?" Ya jefawa Iya tambayar yana jefa mata harara da jajayen ƙwala-ƙwalan idanunsa, sannan ya dakatar da ɗayan nan da yake dariyar dan shi mai maganar shi ne ogansu, a take kuwa ya haɗeye dariyar a inda mutumin wannan ma ya sake danne tashi dariyar saboda ya ga an tauna tsakuwa dan aya ta ji tsoro. "Wallahi ba haka bane, dan Allah ku mini rai kayan maraya ne za a siya idan an siyar da sarƙar dan haka dan Allah na yarda kuma za ku samu kaso mai tsoka dan Allah kar ku raba ni da ita" "Kai karɓi ƙazamin abin nan je ka saka shi a shadda (Toilet) Ka zuba ruwa ya wuce" Ogan ya faɗa yana cillawa ɗaya daga cikinsu, wani kukan kura Iya ta yi za ta ƙwato amma ya ɗaga mata wuƙa a take ta koma ta zauna tana sakin kuka mai cin rai. "Ni da na hana nake cewa an raina mini hankali a baiwa ƴan gwangwan sai ga shi za a saka a masai (Toilet) " Ta faɗa a zuciyarta tana sakin kukan takaici. Suna nan ya dawo ya ce ya jefa har ya zuba ruwa sarƙar ta tafi. "Gaskiya matar nan kin ci dubu sai ceto a kan wannan abin da yanzu babu mai siya ko da kobo ne kika rabo ni da wajen kayan sana'ata da nake yi cikin rufin asiri kika kawo ni cikin wannan masifa da ban san mai za a mini ba... "Ku tattale mutumin nan ku masa shayi da sabuwar addar nan" Maganar babban cikin nasu ta katsewa mutumin nan zancen zucin da yake. "Shayi fa ka ce ɗannan wallahi ɗan wanzan ya mini shayi tun ina ƙarami" Ya faɗa hankali tashe jin za a masa aika -aika. "Kai ba shayi za a masa ba ku getse masa mafitsarar tun daga farkonta a cire ta duka ku saka mini a leda zan b karena" "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ka yi mini rai dan Allah kar ku yi kisan kai" Ya faɗa yana rushewa da kuka, Iya duk da tana cikin alhinin jefar da sarƙarta amma kuma sai da murmushi ya suɓuce mata ganin yadda mutumin ya saka hannu biyu ya danne gaban wandonsa yana ciccira idanu. "Zan dawo kan ki, ki daina gaigaye dan za ki ci tumo, mu duka nan sai mun yi watanda da tsufanki dan bana ce ƴanmatancinki ba dan yanzu kin tsufa" Idanu Iya ta zaro jin ɗanyen aikin da ya ce za su mata. "Na shiga uku da tsufana za a mini fyaɗe yaran ƙanana dan jaraba Allah ka cece ni kar su keta mini haddi" Iya ta faɗa a ranta tana karanto lahaula. Idanu ta runtse ganin an banƙare ƙafafun mutumin nan za a cire masa wando. "Allah ka fishshe ni aikin da na sani, kar ka sa idanuna su yi mugun gani" Ta faɗa a ranta, mutumin kuwa ganin sun zamo masa wando ya shiga ƙoƙarin ƙwatar kansa, ɗayan ya mayar da hankalinsa wajen Iya biyun sun maida hankali wajen cire masa wandon ya dage ƙarfinsa ya datsa musu haƙora kowa a hannu suka sake shi suna sakin ihun azaba kafin su tantance ya zuba a guje ko da suka biyo bayansa har ya buɗe sakatar ya gudu haka suka dawo jijjiga hannu saboda azaba. "Ku dai an yi sakarkaru wallahi ko biyu shi kaɗai kuna sabon jini shi kuwa da ya sha miya amma ya gudu" "Taɓ dan ba kai ya datsawa haƙoran bane wallahi yadda ka san kacar keke haka muka ji zafin cizon" Suka faɗa suna kallonsa wani dogon tsaki ya ja. "Wayyo ni Ansai yanzu sai ni kaɗai babu mai ceto na Allah ka kawo mini ɗauki" Ta faɗa a ranta. "Ku kinkime ta ku kai mana ita cikin ƙuryar ɗaki (Bed room) Yau sai ta faɗawa aya zaƙinta sai mun mata fata-fata za ta san mu ta rainawa hankali" Iya tana ji tana gani mutum biyun suka mata cali-cali kamar wata igiya, aka shige da ita ɗakin da babu komai sai kayan wankin su, ban da wari babu abin da kayan suke, a haka suka ɗora ta a kan tulin kayan wankin. Suna ajiye ta suka fito falon, hannu Iya ta saka a lajihun ɗan tofinta ta ɗakko abu ta damƙe a hannunta. "Ni zan fara shiga idan na fito ku ma sai ɗaya ya shiga ya fito ya ba ɗayan" Yana faɗa ya shige ba tare da ya jira cewar su ba ya shige "Haba ɗan nan ka ji tsoron Allah mana kai kuwa tsohuwar Allah ta'ala amma ku haike mini da tsufana da komai" Iya ta faɗa cikin karkarta kai ko Allah zai sa su ƙyaleta. "Ke tsohuwa ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba" Ya faɗa yana zare wando, fakar idanunsa Iya ta yi ta ɗago allurar da take jikin sirinji. "Allah sarki Jaburu wawtarka ta mini rana yau, kai da na aika ka siyo mini allura wacce ake sakawa a zarw ka siyo mini allura da sirinji na saka a ɗan tofina yau ga shi za ta mini amfani ta mini rana" Ta faɗa a ranta tana ɗagowa ta shammace sa ta riƙe ƙasan sirinjin ta daɓa masa a cinya,a take ya zaro idanu cikin azabar da ya kasa yin ihu zubewa ya yi a wajen a ƙasa yana faman zare idanu. Hannu Iya ta saka ta zare sirinjin da yake haɗe da aluurar dan har allurar ta nitse a jikin cinyar ta bar shi yana murƙususun azaba, a hankali ta lallaɓo ta leƙo falon hango su ta fi suna cire nasu wandunan sun bata baya sai dai kowanne yana gefe guda. Da sanɗa ta fito ta ɗaga sirinjin nan mai allura ta daɓawa ɗayan a gefen mazaunai guda ɗaya ta zare ta ƙara sukuna masa da ƙarfi a ɗaya ɓarin mazaunan a take ya dare ido sai ga shi ya zube a ƙasa hannu biyu dafe da mazaunan. Ɗaya ya yi nisa wajen gyara belt ɗin wandon nasa da yake wandon ya zo masa cinya sai dai bai gama cirewa ba sai belt ɗin ta sarƙafe, shi ma bai ankara ba ya ji cakuwar wani abu mai kama da mashi, yana shirin yin ihu ya ƙara jin a soka masa a ɗaya ɓarin. "Ihu an kawo mana farmaki maƙiya sun kawo hari a yi hanzarin yin shirin yaƙi sun fara sakin mashi ko ta ina duk sun soke mini mazaunai" Ya faɗa da ƙarfi yana sakin ihu ya zube a ƙasa Iya kuwa ko zare masa bata yi ba ta fice da gudu takalmin ma ƙafa ɗaya ta ɗauka. Ficewa ta yi a gigice da yake ƙofar gidan an ɗan yi wurin alamar shigowa da machine ba tare da ta lura ba ta taka aikuwa suuuu ta tafi ta je a zaune da haka ta rarrrafa ta bar ƙofar gidan amma dan ƙarfin hali har lokacin ledar vivar tana hannunta. Gaba ɗaya ƙugunta ya bugu ƙafafunta kamar ba a jikinta ba suke dan ba ƙaramar faɗuwa ta yi ba dan haka sai ta zauna a wajen wata bishiya tana jiran ƙugun nata ya lafa ta tafi. Wani mutumi ya zo wucewa da rogo dafaffe a leda fara da ya ganta zaune da leda a hannu sai ya ɗauka almajira ce dan haka ya karɓi ledar ya saka mata rogon a matsayin sadaka Iya bata iya ce masa komai ba. Tana nan zaune da yake la'asar lis lokacin dan haka hango wani mai baro yana cewa. "Dako, ina wanda za a masa dakon kaya muna ɗaukan kaya zuwa tashar mota ko zuwa gida" "Kai bawan Allah zo ga dako" Da sauri ya nufo ta yana zuwa ya saki baki ganin bai fa ko da ƙullin kaya bane a wajen nata. "Tsohuwa ya ban ga kayan dakon ba" "Ɗan nan ni za ka ɗauka a baron taka, ni za ka yi dakon" "Haba Baba ɗan musulmi da rangwame aka san shi yo ina zan yi dakon ki to ma wa zai saka ki a baron kin zauna daɓas a waje guda. "Ka saka ni a baron zan biya har kuɗin ɗaukan nawa wallahi hantsilowa na yi to kwankwason nawa ne kamar ba a jikina ba" Jin haka sai ya kinkimi Iya ya saka a baro tana ta ƙorafin ya saka ta da ƙarfi kamar ya jefa buhun goruba, shi dai bai amsa mata ba ya tambaye ta inda zai kai ta ta faɗa ya tura baron suka fara tafiya, ita ba a kwance ba ita ba a kishingiɗe ba ƙafagun nan nata sun yi sama su kake hangowa. . Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://www.youtube.com/@MAMANAFRAHNOVEL ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keke napep) NA MAMAN AFRAH GARAƁASA💃💃💃💃💃 Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Ga link nan na chanel ɗin duk wanda ya yi SUBSCRIBE ɗin ya tura mn screen shrt PC. Page 4️⃣ Jabiru haka ya wuni babu abin da ya ci yana jiran dawowar Iya ta kawo tsire da balangu da lemon kwalba su yi wankin ciki, ga shi ya kasa zaune ya kasa tsaye tun da ta ce a yau za a siya masa Adaidaita sahu. Bayan kaf ƙauyen nasu ma babu adaidaita sahun amma saboda ɗora rai da kuma sangarcin da Iya ta masa shi ne za a siya masa, tun yana saka ran dawowarta har ya fara fusata ga shi kuma yunwa tana ƙwaƙularsa amma ya ƙi cin komai. Waje ya fito yana kallon hanya, daga can gefe su Baba ne zaune a tabarma dan su da suka ga Iyar ma bata nan duk tunaninsu gidan ƙawarta Jummai ta tafi. Jabiru kamar daga sama ya hango wata kamar Iya a cikin baro ƙafafun nan suna reto ɗaya da takalmi ɗaya babu bai gama dawowa daga mamaki ba sai da suka kusa ƙarasowa ya ji muryarta tana faɗin "Can ne gidan ga jikana Jaburu can a tsaye" Tana faɗa tana nunawa da hannu. Da sauri Jabiru ya matso kusan baron yana rarraba idanu ta inda zai ga ledar kuɗin dan shi ba ma ta halin da Iyar take ciki yake yi ba, ba ya ma tunanin ya aka yi aka kawo ta a baro, ledar ya warta daga hannunta ya ɗaga ya zazzage a ƙasa kullin rogon nan ne ya faɗo ashe har da ƙarago a ciki wurgar da ledar ya yi yana cewa "Iya ina maƙudan kuɗin kar dai ɓarayi ne suka tare ki" Ya faɗa daidai ƙarasowar Baba Mamman da Baba Umaru da wani maƙocinsu da suke zaune tare, salati suke suna bin Iya da kallo. "Kai lafiya mene ne hakan, mai ya same ta?" "Haba Baba kwa tambayi agwagwa hanyar rafi ai kawai ku tambayi kaza ku sha labari, ni aikin kuɗi nake dako na ɗakko" Ya faɗa yana wani ɗaga kai sama irin na marar kunya. " Haba ɗan nan yanzu ni ce ma kazar a gaban ƴaƴana kake ce mini kaza kuma kake cewa dakona ka ɗakko sai kace wata buhun barkono" Cewar Iya tana sakin kukan takaici amma ba takaicin maganarsa take yi ba takaicin sarƙarta take yi.Jin ta kasa tashi sai ta koma ta kwanta tana cewa "Umaru ku ɗago ni ku shiga da ni cikin gida tun kafin jama'a su fara taruwa ana cewa an ɗakko uwarku a baro, baku ji haƙarƙarin nan nawa ba yaron nan mai baro ina ga jefa ni cikin baron ya yi" Ta faɗa har lokacin tana kukan. Jabiru kuwa so yake ya ji batun kuɗin sarƙar amma yana tsoron iyayen nasa su ce bai damu da halin da Iyar take ciki va. "Ko ma dai a yaya na saka ki ai na taimake ki kuma ni a kan sana'ata nake kuma aikin kuɗi nake" "Kai nawa ne kuɗin naka"Cewar maƙocin su Baba ganin da Baba Mamman da Baba Umaru sun fito da Iya daga baron za su shiga da ita gidan. "Dubu ɗaya ne, ɗari biyar kuɗin ɗaukanta na saka ta a baro ɗari biyar na tuƙo ta da na yi" "Wallahi ƙarya yake duka daga ɗaukan nawa har turani a baron jaka ɗaya(200) Za a bashi ni da ba nauyi gare ni ba" Iya ta faɗa tana daga hannun su Baba ana daidai shiga zauren gidan da ita, babu wanda ya bi ta kanta aka bashi dubu ɗayarsa ya tafi yana wani fito. Ɗaki aka shiga da Iya tana ta raki tana faɗin "Waɗannan yara ƴaƴan Allah bani, wanda suka kwashe kayansu daga gaban ma'aiki, yadda kuka saka mini tsabar dukiya a masai Allah ya bi mini haƙƙina" Ta faɗa tana rushewa da wani marayan kuka. Su Baba da suka buɗe baki za su yi magana ma dakatar da su ta yi ta ce "Ku fice mini daga ɗaki mutanen banza da kun je kun siyar mini mai zai fitar da ni" Sumsum suka fice babu wanda ya tanka dan su basu ma fahimci mai take magana a kai ba. "Wai Iya Ansai ina dukiyar ne kin ce leda za ki ciko da kuɗaɗe amma na ga ledar sai rogo da ƙuli kamar wasu mayunwata" "Kai Jaburu wa ma yake ta kuɗi ina rogon da ƙulin ɗakko mini in ci cikin nan nawa tun safe babu abin da ya shiga cikinsa, ina can ina gallafiri cikina kamar an yi sata rogon ma sadaka aka bani... "Haba Iya ya za ki ce wa yake ta kuɗi bayan kin saka mini a rai kuma ai ni ma tun wainar da na ci da safe ban ci komai ba ina jiran ki kawo nama da lemo" "Wai kai ka san rijiya da bayan da na tsallake kuwa? To aradu ƙattai uku majiya ƙarfi suka so haike mini Allah ya sa akwai alurar nan na ƙwaci kaina da ita ai ni na san halin da na shiga yau" "Iya ina kuɗin da za a siya mini ni fa na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba, ga shi har an doshi magariba babu adaidatan" "Wai kai baka da tausayi ne duk bayanin da nake maka baka ji ba, tun safe ban ci ba ban sha ba, ba sallah ba salati, ga rijiya da bayan da na tsallake na ce ka bani rogon nan na afa a bakin salati na je na yi sallah wa yake zancen kuɗi bayan ba a siyar da kayan kuɗin ba to ɓarayi ne ƴan fasa ƙwabri masu hana ruwa gudu suka ƙwace sarƙar suka saka a masai (Toilet) Ta faɗa tana muskutawa daga inda aka zaunar da ita ta ɗan rarrafa inda kwanon tuwo da kokon da aka kawo mata na safe ta ce "Ina kwanon abincin rana?" Cikin kuka Jabiru ya fara magana. "Ba ke kika ce kar wanda ya kawo dambu ba ai ko rabawa basu yi da mu ba,wayyo Allah maraici Allah jiƙanki Babata na yi maraici" Ya faɗa yana ƙara fashewa da kuka. Iya bata masa magana ba sai da ta buɗe kwanon tuwon nan ta ci sosai sannan ta ɗaga kokon ta kafa kai bata ajiye ba sai da ta sha fiye da rabi. Ajiyewa ta yi tare da sakin wata gyatsa, sai sannan hankalinta ta ji ya ɗan dawo jikinta ta gyara zama ta yi tagumi da hannun hagun ɗinta ta fashe da kukan ita ma gaba ɗaya ɗakin ya ruɗe da kukan su ita da Jabiru. "Kai duniya Allah jiƙan tsohuwarka Jaburu Allah sa kwanciya ta zame mata hutu, wallahi ba da son raina haka ta faru ba ka san abin da baka san shi ba wuyar sha'ani gare shi ashe dai wannan abu babu wanda zai siya ni nake rashin hankalina"Ta faɗa cikin kuka tana zayyane masa abin da ya faru. Nan ta shiga lallashin sa tana cewa. "Ka yi haƙuri Jaburu gobe an ce masu rabon dabobi za su dawo garin nan, to an yi sanarwa cewa wannan karon da dabobin za su zo ba irin wancan zuwan ba da suka zo su bayar da takarda sai daga baya su dawo su kawo dabobi, duk da an ce zafin nema ba ya kawo samu amma na san wanda ya riga wani kwana dole ya riga shi da tashi gobe asubanci zan yi in tafi yadda zan samo sa da saniya ka san matar bukari wancan zuwan shanu takwas ta samu wasu akuyoyi biyar wasu ma rago ne, to kowa dai rabonsa yake samu ni in sha Allahu shanu zan samu narka-narka wanda za su ishe mu buƙatun mu in an siyar" Ta faɗa tana kallon fuskar Jabiru da ta washe kamar gonar auduga dan shi ma ya ji labari a gari cewa gobe zaa yi wa mata rabon dabbobi wanda wani hamshaƙin mai kuɗi yake rabawa talakawa sai dai a takarda ake rubuta sunayen dabobin da yawan dabbar da za a baya mutum sai a watsa kowa ya ɗauki ɗaya idan aka duba sai a ba mutum dabbar da ya zaɓo sunnanta a takarda. Da wannan Iya ta shawo kan Jabiru ya kwantar da hankalinsa har ta je ta yi alwala ta yi sallolinta tana ja wa ɓarayin nan tsinuwa da Allah ya isa. Da daddare ta kira su Baba ta sanar da su cewa kada wanda ya bar matarsa ta je wajen rabon dabobi saboda ita za ta je dan haka bata so ake nun ta ana cewa ita da sirikanta sun je tare, wai sai dai su bari idan an ƙara dawowa sa je. Haka suka yi ta nuna mata cewa ta yi haƙuri amma ta kafe sai haƙuri suka ba matan nasu dan a zauna lafiya amma ba dan ran su ya so ba su ma matan sun yi biyayya ne kawai ba dan komai ba domin kowa ya ci burin zuwa wajen ko dan mutum ya samu abin kiwo wancan karon wanda suka samu sun samu alkairi sosai. *DA ASUBA* Tun kan a kira assalatu Iya ta tashi daga bacci, dan ma kar ta je baccin gajiyar jiya ya sanya ta makara fita da wuri wajen rabon dabobi dan ta ci alwashin a can za ta yi sallar asuba dan ta hau layi ta samu manyan shanu, bata san cewa ko layi ake hawa kowa rabonsa yake samu. Ana kiran assalatu ta yi alwala ta ɗauki sallayarta sai da ta ji fitar su Baba masallaci sannan ta tashi Jabiru ta sanar da shi idan ya tashi da sassafe ya share jigon da za a ɗaure shanayen kuma ya samu murɗiga-murɗigan ita ce ya musu jigo yadda ana kawo su ɗaure su za a yi. Amsa mata ya yi yana murna dan yau ko nauyin bacci bai yi ba da yake zancen abin duniya ne. Lokacin da ta fito titin shiru babu mutane dan lokacin duk an shiga masallacin asuba sai mutane da take hanga tsilli-tsilli wanda suka makara suna kan hanyar masallacin. "Kai yau akwai shagali idan na samu shanaye taɓ lallai za a ga ɗaga kai ni ko raini bana so Allah sa ma in samo shanaye biyar wayyo daɗi garke guda zan yi na shanaye" Take faɗa a zuciyarta tana tafiya duk daɗi ya cika ta gani take ta samu shanaye ta gama. "Kai ranar nan da ana bani labari na sha dariya wai wata ce ta samu kaza da zakara yo ita kuwa garin yaya" Iya ta faɗa a fili tana tuntsurewa da dariyar mugunta a haka ta ƙarasa wajen da yake filin makaranta ne kuma asabar ce ranar sai ya zamana babu makaranta. Ko tsoro bata yi wajen duhu dilim ta shimfiɗa sallaya ta ajiye fitilar ta ta kabbara sallah ta idar.Tun tana sa ran zuwan mutane wajen har dai ta fara jera hammar yunwa amma bata damu ba burinta kawai ta samu rabonta. Sai ƙarfe takwas manyan motoci suka fara zuwa, motar shanaye, raguna, akuyoyi, da wacce take cike da akurkin kaji irin abin nan da masu tallar kaji suke zuba kaji, sai kuma wanda suke ɗauke da ƴaƴan kaji wato ƴan tsaki, jaririn kaji. Tun da motocin nan suka tsaya idanun Iya a kan motar shanaye tana ƙiyasta wanda za ta samu dan sai ta hangi ƙoshashshe a zuciyarta ta ce "Wannan ma yana cikin nawa" Mata sun cika wurin fal dan haka masu rabon suka tsara yadda suka hau layi aka watsa takardu sai kowacce ɗaya bayan ɗaya ta je ta zaɓi takarda ɗaya. Sai da adadin da suke so su ɗauka suka gama ɗauka sannan suka dakatar dan dama takardun da aka watsa ɗin sun ƙare. "A taho ɗaya bayan ɗaya ana kawo takarda" Haka aka sanar da su, kowacce tana kai wa ana karanta abin da ta zaɓo ana bata, wasu saniya wata akuya wata ɗan akuya kowa dai da abin da yake samu. Wata mata da aka haɗa ta da samarin da ,a su kai mata shanu biyu ƙosassh gida sai faman godiya take har da hawayen farinciki. Wata kuma da wata mtsatstsiyar akuya ƙarama, tun da ta kama igiyar ta fara tafiya Iya take mata dariyar ƙeta a zuciyarta har da ce mata "A gaida gida" Ana zuwa kan Iya wato layinta ya zo har wani rausaya-rausaya take, ta je tahj miƙa takardar. "Ƴan tsaki guda uku (Wato ƴaƴan kaji jarirai guda uku su ne Iya ta canko. Wani irin amsa kuwwa maganar ta yi wa Iya a kunne a take annurin fuskarta ya ɗauke. mm "Ƴan tsaki uku Malam sai mka ce wata mayya, ko dai shanaye uku kake nufi?" "Ya shanayen nan? Ƴan ztsaki dai, ba ga shi a rubuce ba" "Babu wani ko dai baka iya karatun bokon bane, kai na kusa da shi karɓi ka karanta dan Allah kar ya mini maguɗi" Ta faɗa lokacin har idanunta sun fara cikowa da ƙwalla. "Baiwar Allah ƴan tsaki kika canko guda uku dan haka su me rabonki" Ɗayan ya faɗa yana kallon Iya da har ta fara share hawaye tare da fyace majina. "Kai jama'a wannan abun naku dai ya zama zaɓe wato sai wanda kuka zaɓa kuka dama kuke ba wa abin arziƙi yanzu saboda Allah ina abin kirki a ƴan tsaki Mai mutum zai ce ya samu kawai dai harkar ƙasar nan ce ta mulkin Tilibu(Tinubu) Amma in ba haka ba ai ba a kyauta mini hatta ku ma'aikatan na riga ku zuwa wajen nan, tun da assalatu na fito, ko sallar asuba a nn na sallata amma sai ga shi wanda suka zo daga bisani sun fini samun abin kirki, har ina yi wa wata dariyar ƙetar samun motsotsuwar akuya ashe dai ni ko kaza ba zan samu ba sai ƴan tsaki... "Haba Baba wa kika gani ya yu musu a wurin nan kowa fa aka bashi albarka yake sawa ya tafi" Ɗaya daga cikinsu ya faɗa. "Yo ya na yi ai faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi, gado dai ba na uwata ba aka bani ƙyallan zani ai na samu" Ta faɗa tana matsawa kusa da mai bada ƴan tsakin ya ɗakko wani ƙaramin kwali ya saka mata ƴan tsaki guda uku ya miƙa mata ta karɓa tare da juyawa cikin ɗacin rai ta bar wajen tana tunanin yadda za su ƙarƙe da Jabiru. A hanya tana ta ganin wanda suka samo shanaye da raguna suna tafiya samarin da suka riƙo musu abin da suka samo suna biye da su, duk wanda Iya ta yi wa kallo ɗaya ba ta maimaitawa saboda takaicin ganin ita tana riƙe da kwali da sallayarta sai fitila. Jabiru da yake tsaye wajen jigon da ya yi wa shanayen da Iya za ta samo ya kasa zaune ya kasa tsaye jiran zuwanta kawai yake, jikinta sanyi ƙalaw ta shigo gidan bakinta ɗauke da sallama. Wani uban tsalle Jabiru ya doka ya taho wajenta har yana neman faɗuwa. "Ga Iya, ga Iya" Ya faɗa cike da murna. "Iya na gama jigon su waye suka taho miki fa shanayen namu bari in taro su" Ya faɗa yana ƙoƙarin yin hanyar wajen ba tare da ya lura da yanayinta ba. Hannu ta kai ta riƙo rigar Jabiru idanunta yana cikowa da ƙwallah ta ce "Jaburu ban samu shanaye ba" "A'uzubillahi haba Iya mai za mu yi da raguna ai buƙatunmu sun wuce raguna" "Kayya! Jaburu abin ya wuce raguna sai dai mu ce lahaula wala ƙuwwata" Tun kafin ta gama faɗa masa sauran ƴan tsaki ta samu kukan ƴan tsaki ya karaɗe masa kunnuwa. "Ciyat-ciyat" Suke ta kuka. Ƙaran da ya ji ne ya sanya ya warci kwalin hannun Iya ya ajiye a ƙasa cikin sanyin jiki ya buɗe. "Ciyat-ciyat" Ya yi idanu huɗu da kajin suna ambaton ciyat sai wata ƴar leda wacce aka ƙulla dusar da za a basu. "Ƴan tsaki fa kika samo Iya" Ya faɗa yana fashewa da kukan takaici, Aliya da Maimuna da suke ɗaki suna jin komai suka tuntsure da dariya dan suna ganin hakan ma alhakinsu ne da ta hana a bar su su je wajen rabon. "Wallahi Jaburu ka dai gan su suna ciyat-ciyat dan baƙinciki tun da duku-duku nake wajen rabon sallar asuba ma a can na yi wai amma dan wulaƙanci in rasa abin da zan canko sai ƴan tsaki" Ta faɗa tana tsallake kwalin ƴan tsakin ta tafi ɓagarenta cike da takaici, su Baba dama basa nan sai matan nasu da suke mata dariya a ɓoye daga cikin ɗaki. Jabiru a gaban kwalin nan ya zauna yana ta risgar kukan takaici su kuwa ƴan tsakin suna ta yawon a wurin suna cin abinci a ƙasa, Iya ma a ɗaki ta zauna tana mammatsewa hawayen, tana nan zaune a bakin gado Jabiru ya shigo d hawaye shaɓe-shaɓe ya yi zaman dishan yana kuka wiwi "Haba Jaburu ka yi haƙuri mana bana son zubar hawayen maraya kar ka saka a rubuta mini alhaki a kan na yi sanadin zubar da hawayenka, Allah ya sani ya kuma gani na yi iya bakin ƙoƙarina amma ban samu damar faranta maka ba" Iya ta faɗa tana rushewa da wani marayan kukan. "Haka ne Iya Ansai amma ki bar ni in yi kukan maraici na san da mahaifiyata tana raye da yanzu ta yi duk yadda za ta yi ta siya mini adaidaita sahun amma ga shi... "Haba Jaburu kar ka zama ɗan adama mai manta alheri mana, kar kuma ka zama ciki mai manta kyautar jiya, kana gani dai yadda na sha fama amma hakan bai samu ba ya kake so in yi ko sata zan yi" Ta katse masa maganar ita ma tana kukan shaɓe -shaɓe da hawaye. "Iya kina da abin da za ki siyar fa ki siya mini" "Yanzu Jaburu in ba ƴan atamfofin da nake sakawa ba zan siyar in yi yawa tsirara ba, mai nake da shi dama sarƙar nan ce kuma ga shi yadda hali ya kasance" Yo Iya bakya faɗawa su Baba su baki kashin gonarki ki siyar ki siya mini indai da gaske kina son hana hawayen maraya malala... Kukan Iya da take yi ne ya tsaya cak dan lokaci guda ta haɗiye sai ga ta ta tashi daga zaune ta tsaya a kan ƙafafunta baki a buɗe "Anya Jaburu kana cikin hayyacinka kuwa gonar da ake nomawa muke ci a cikinta za ka ce in ce a bani rabona?" "Shikenan Iya babu damuwa a cigaba da noma gonar" Komawa ta yi ta zauna daɓas tana share hawaye a take wani gumi yana keto mata ba dan son Jabiru da ya mata katutu ba da babu yadda za a yi ta yi ko da maganar nan ne, tana sane da cewa ko sati ba a yi ba Alhaji Audu mai kuɗin garin nasu ya zo yana son ya sayi gonar ta masa tatas ita da su Baba Mamman a kan cewa ba za su taɓa siyar da gonar gadon da mijinta kuma baban su Baba Umarun ya mutu ya bari a matsayin gado. Amma dai ynzu haka za ta daure ta tinkari su Baban da maganar. "Kar ka damu Jaburu zan musu magana a siyar da kasona a bani in saya maka"Ta faɗa dan ta faranta masa, fa gudu ya ƙarasa yana ƙanƙame ta yana ta murna da sanya mata albarka ita dai sai amin take cewa dan babu yadda za ta yi bata son ɓatawa maraya rai ne kawai amma da kaf duniya babu mai sakata ta siyar da kason gonarta da take ji da shi wanda mijinta ya bar mata. *MAGRIBA* Su Baba ta tara domin sanar da su munimmiyar maganar sayar da gonar dan ba za ta juri ganin Jabiru cikin ɓacin rai ba gwara ko ma mai za su ce su faɗa. "Mamman" Iya ta kira shi da wata murya mai kamar lallashi "Umaru" Shi ma ta kira shi "Na'am Iya" Suka haɗa baki wajen amsawa. "Dama wata magana ce nake so na faɗa muku amma a matsayin umarni take ba shawara ba, ina so ku samu Alhaji Audu ya saya yankin gasona na gonar mahaifinku" "Gona kuma Iya?" "Haka kuka ji na ce" "Iya mai za ki yi da kuɗin gona kuma? Bayan kin san gonar nan ita ce rufin asirinmu gaba da baya kuma ko ranar nan da Alhaji Audu ya zo da maganar sai da kika faɗa da bakinki amma kuma ynzu ki zo da wata maganar da ban" Baba Umaru ya faɗa yana bin ta da kallo mai cike da ayar tambaya. "Sake shawara na yi, so nake a yanka mini ɓangarena tun da mallakina ne ba na wani ba kuma da kake maganar mai zan yi da kuɗi ni har wata buƙata nake da ita wacce ta wuce siyan arincaɓar Jaburu" Kallon kallo aka shiga tsakanin Baba Mamman da Baba Umaru. "Iya wai kin taɓa ganin adaidaitar a gari nan?" "Yo ni tun da uwata ma ta haife ni ina na taɓa ganinta" "To yanzu idan ya kawo nan qaye zai hau? Kuma kina ganin ƙauyan nan kaf sai mutum ya zagaye shi bai gaji ba wuye zai hau adaidatar a kai mutum ina ko gona za a kai mutum, garin nan duk rairayi ne ta yaya wata adaidaita za ta tuƙu, sannan zamanin tsadar man nan ya zai ke da siyan mai, uwa uba ma bai iya tuƙawa ba amma har kina cewa a siyar da gona a siya masa kin manta gonar nan ce kaɗai muke da ita, mu ma ba wani aiki muke ba da ita muka dogara a cikinta muke noma amfanin gonar da za mu ci idan aka yamke ta aka siyar shin sauran zai iya muke noma amfanin da zai ke kai mu shekara?.. "Kai umaru ba a koti kake ba da za kake jero tambayoyi kamar ka kama ɓarawo ko marar gaskiya, in bai iya ba ba sai a koya masa ba kuma sana'a ai sai an gwada a kan san na ƙwarai kuma in ma gonakin zai ke kai mutane ai babu laifi tun da ba gidan giya zai kai su ba, kuma da kake maganar noma amfani duka nawa muke matayen naku da ba haihuwa suke ba ko ni ɗan cikin nan nawa da a wani abincin kirki nake ci ba shi ne sai ana nomawa da ɓangarena ni dai ga abin da na ce" Ta katse Baba Umaru cikin kaushin murya. "Shikenan Iya za mu je wajen Alhajin mu masa maganar yadda muka yi za ki ji" Cewar Baba Mamman cikin lallashi. "Yawwa ko da na ji ko ku fa ai hakan ya fi amma kuke musu da ni ai duk ɗan da yake musawa uwarsa ba zai wanye ƙalaw ba, ku je to Allah muku albarka" Da amin suka amsa suka fito daga ɗakin nata waje suka nufa suka kira Jabiru sula sanya shi a gaba da faɗa da kuma kashedin kar ya sake ya ce su suka masa magana dan haka ya nuna ya ji zai faɗa wa Iyar cewa ya fasa siyan adaidaitar kamar yadda suka buƙata amma kuma a zuciyarsa yana tunanin yadda zai shirya wata gadar zaren da zai bi ya hau a sannu ba tare da kowa ya gane ba. "Sha kuruminka Jaburuna za a siyar da gonata a siya maka arincaɓar da kake so" Ta faɗa tana washe baki kamar gonar auduga. "Iya ni fa na fasa siyan adaidatar nan kawai kar ki siyar da gonarki ki bari idan Allah ya hore kya siya mini" Ya faɗa muryarsa tana rawa alamar maganar ba daga zuciyarsa take ba turasasa shi aka yi. "Jaburu anya ba aljannu suka shige ka ba, kai da bakin ka kake cewa kar a siya maka arincaɓa? Ko dai makuwa ka yi ne, anya ba matan babannin nan naka bane suka shiga suka fita suka cire maka son arincaɓar saboda suna baƙin cikin za ka samu sana'ar yi" Ta faɗa cikin ɓaɓatun faɗa irin na tsofaffi tana sakin kukan tausayinsa dan tana ganin asiri aka masa. "Ras nake Iya kawai dai na bari ne an ce adaidaitar yanzu yana tsada idan ya sakko sai a siya" "Allah sarki Jaburu ashe dai kana da hankali da dogon tunani, wallahi har na ji sanyi a raina da na fahimci ba asiri aka maka ba yin kan ka ne" "Allah sarki Iya Ansai ta" Ya faɗa yana murmusawa. "Allah sarki Jaburuna" Ita ma ta faɗa tana ƴar dariya. Fita ya yi ita kuma ta ce da daddare ta samu su Baba da maganar ba sai an siyar da gonar ba a bari tukunna. Jabiru yana ta tunanin yadda abubuwa za su kasance yadda zai yi abu cikin ruwan sanyi ba tare da kowa ya gane ba. Lokacin da Iya ta shiga bayi domin yin tsarki za ta yi sallar isha'i a sannan Jabiru ya fakaici ido ya shige ɗakin nata, kayan da ya shigo da su a leda ya buɗe ya saka bankaɗeɗiyar babbar rigar farin boyel da ya aro bayan ya saka ya ɗauki farin hirami ya naɗa a kan masa, ya ɗauke ledar ya saka a aljihu ya koma bayan ƙofa ya rakuɓe. Sai da ta gama alwala ta shigo ɗakin tana ɗan zancen ta ita kaɗai hijabi ta saka ta shimfiɗa sallaya, sai da ta yi kabbara ya lallaɓo ya fito daga bayan ƙofar takalminsa yana cikin aljihunsa, a hankali ya lallaɓa ya je bayan Iya ya tsaya, sai da ta yi raka'a biyu ta zauna ta yi zaman tahiya ta sake tashi ta yi raka'a ɗaya lokacin da ta kai sujada a lokacjn cikin sanɗa ya yi saurin komawa gabanta ya zauna, ya naɗe ƙafafunsa yana fuskantar ta. "Allahu akbar!" Ta faɗa lokacin da ta ɗago daga sujadar, ganin mutum zaune a gabanta sanye da farin kaya har da rawani ga shi ɗakin dama babu haske sai na fitilar da ba wani fitowa hasken ya yi ba dan ba za ka gane fuskar mutum ba. Gabanta ne ya yanke ya faɗi lokaci guda ta shiga tunanin aljani ne ko kuwa mala'ikan mutuwa ne ya zo ɗaukan ranta. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://www.youtube.com/@MAMANAFRAHNOVEL *ƳAN ADAIDAITA SAHU* (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH BABBAR GARAƁASA💃💃💃💃💃💃💃💃 Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page5️⃣ Idanu ta runtse tana jin yadda bugun zuciyarta yake bugawa da sauri-sauri dakyar tsamu ƙarfin gwiwar tashi tsayen ta kawo ɗaya raka'ar, idanunta har lokacin a rufe, gabanta yana faɗuwa. "Allahu akbar" Ta faɗa lokacin da ta kai sujada ta biyu tun da ta yi sujadar take ta faman cewa "Allah ka yafe mini kura kuraina, Allah ka jinkirta mini mutuwata ba yanzu ba sai na aurar da marayan nan Jaburu Allah ka sa mala'ikan nan ya tafi ba tare da ya ɗau raina ba" Ta faɗa tana son ɗagowa amma tana tsoro ta buɗe idanu ta gan shi, har sai da ta zo yin sallama sannan ta buɗe idanun ta kalli hagu da dama ta yi sallamar a hankali kamar mai raɗa. Yana nan zaune kansa a sunkuye bai ɗago ba. Karkarwa jikinta yake tun ƙarfi ta kasa jin ƙarfin da za ta iya barin wajen da take ma. "Ansatu" Ta ji ya kira sunanta da wata murya kamar ta larabawa dan ya yi muryar uztazai sai hakan ya ƙara bata tabbacin mala'ikan mutuwa ne, musamma da ya kira sunanta na gskiya bai ce Ansai ba kamar yadda ake kiranta da shi ba. So take ta amsa amma kuwwar da cikinta yake yi ga shi bakin nata ya ƙi ko da ba laɓɓanta ne damar su buɗu bare har ta kai ga yin magana. "Ansatu a yau ne wa'adinki ya cika, yau za ki koma ga ubangijinki, dama kwanakin ki suna ƙaruwa ne saboda yawan zumunci kin san idan ɗan adam yana yawan zumunci Allah yana ƙara masa kwanaki, to kuma kina taimakon maraya amma yanzu kin kasa masa abin da yake so" Ya faɗa cikin muryar nan ta ustazanci yana wani maƙale muryar. "Wallahi ban daina zumunci ba wajen kawu Ribaɗo ma ina yawan zuwa kafin Allah ya masa rasuwa, wallahi maganar Jaburu kuma ɗazun nan ya ce a bar siyen arincaɓar sai ta sakko saboda ta yi tsada" Ta faɗa cikin rawar murya tana fatan Allah sa kar ya ɗauki ran nata. "Ai yanzu ma bata ɓaci ba za ki iya zuwa ki siyar da gonar gaba ɗaya ma ba sai kin bi ta kan ƴaƴanki ba, ko garin ne ku bari ke da marayan da kuɗaɗen sai ki siyar cikin sirri ku tafi birni a saya masa farin cikin maraya ba ƙaramin abu bane" "Wallahi zan siyar a yau ba sai gobe ba zan je wajen Alhaji Audu gobe za mu daka sakko mu tafi" Ta faɗa cikin tsoro da karkarwar baki dan tsoron tana magana da mala'ikan mutuwa har da sakin fitsari a zaunen. Sai da ya tsorata ta sosai ya tabbatar ta tsorata sannan ya ce "Ki rufe idanunki ki yi sujada saboda kar guguwar ɓacewata ta tafi da ke... Tun kan ya ƙarasa faɗa Iya ta durƙushe ta yi sujadar idanunta ɓam a rufe, laɓɓanta kaɗai sun fahimci halin da take ciki saboda karkarwar da suje suna haluwa da haƙoranta, ta saman bayanta ya lallaɓa ya tsallaka ya silale ya fice daga gidan baki ɗaya. Kayan ya je ya mayar wa mai su. Tun da ta yi sujadar take ta faman istigfari har Jabiru ya dawo har zuwa lokacin bata ta shi daga sujadar ba. Da sallama ya shigo yana ƙwala mata kira, yana cewa ga batir ɗin da ta bashi kuɗi ya siyo. A kiɗime ta ɗago ta sauke numfashi batir ɗin ya saka ya kunna fitilar haske ya gauyaraye ɗakin. Ta haɗa gumi jargaf tamkar an sheƙa mata ruwa har jikin hijabin nata. "Iya lafiya dai kika ɗago baki salance ba ke da kike sallah?" "Jaburu baka ga kowa ba?" "A ina Iya" "A'a shikenan a bar kaza a cikin gashinta, maza ina so za mu fita da kai fita cikin sirri" "To Iya ai dama da ke muke sirri babu wanda zai ji "Jaburu za mu tafi gidan Alhaji Audu" "Mai za mu yi a can Iya" "Bakin ka alekum Jaburu" Da to ya amsa mata, dan ba ya son jan maganar tun da ya san mai za su je yi. Babu wanda ya lura Iya da Jabiru suka bar gidan sai gidan Alhaji Audu bayan ta sanar da su Baba kar su je ta fasa siyar da gonar. Sun tarar da Alhajin a falonsa bayan matarsa ta musu iso aka fita aka bar Iya da Alhaji sai kuma Jabiru da yake zaune a gefe, bayan an gaisa Iya ta ce "Alhaji na zo da wata magana ne dama, amma ina fatan ka amince mini ka taimaka ina cikin matsuwa" "An zo wajen da nake son a zo" Cewar Alhajin a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce. "Babu komai Ansai ai indai ina da hali zan miki" Ya faɗa cikin kwantar da murya dan ya gama gano lagwanta. Jabiru kuwa sai dariya yake a zuciyarsa ganin cikin ruwan sanyi burinsa zai cika. "Dama magana nake so na maka a kan gonar gadon nan da ka je da maganarta ranar nan... "Haba ai babu komai tun da noma ta kuke ki bari wata rana idan kuka tashi siyarwa sai a siyar... "Ban tari numfashinka ba amma na zo ka karɓi jinginar ɓangarena a cikin gonar, ka bani kuɗin sai kake noma ɓangaren nawa, amma kuma idan na mayar maka da kuɗin sai ka mayar mini da gonar ina cikin buƙatuwa kuma kar wanda ya ji maganar nan a sirri nake so a yi kar wanda ya sani. Dan gobe asubanci zan yi mu bar garin nan ni da Jaburu ba tare da kowa ya sani ba" "Gaskiya hakan ba zai iyu ba" "Na shiga uku ni Ansai shikenan mala'ikan mutuwa zai zo ya ɗauki raina in har ban cikawa marayan nan buri ba wayyo Allah ka kawo mini ɗauki" Ta faɗa a zuciyarta tana jin faɗuwar gaba dan bata son ta mutu yanzu. "Lahaula wala ƙuwwata illah billah, haƙata ba za ta cim ma ruwa ba kenan duk abin da na yi ya tashi a banza kenan?" Jabiru ya faɗa a zuciyarsa kamar ya yi kuka. Tun da Iya ta dage tana ta bashi haƙuri dan ganin bai hana ba dan bata son ko kaɗan ta mutu, shi kuwa Jabiru ya san dalilin da Iyar ta nace a kan cewa sai an karɓi jinginar gonar. "Sai dai na karɓi jinginar duka gona amma ba wani ɓangare na gona ba, idan har kin dawo da kuɗi a mayar muku gona idan baku kawo ba gona ta zama mallakina" Shiru Iyar ta yi tana nazari ganin in ta bada gonar duka da mai za suke noma suna cin abinci amma tsoron kar mala'ikan mutuwa ya zo ya tafi sa ranta sai ta amince babu musu dan tana ganin idan har suka bar garin da kuɗin hayar adaidaitar za su tara su kawo a biya kuɗin gonar. Naira miliyan uku, basu dan dama ya gama sanin wurin dan ranar nan har cewa su Baba mamman ya yi zai ƙara a kan naira miliyan ukun ɗin amma suka ƙi. Hannun Iya har karkarwa yake ta saka ta riƙo jakar miliyoyin kuɗin dan dama shi ɗan kasuwa ne kuma bai fiya ajiye kuɗi a banki ba. Babu wanda ya san sun dawo gidan haka suka lallaɓa suka koma gida babu wanda ya san wainar da suka toya da za su tafi ne ma ya kirawo matarsa dan ta zama sheda sai takarda da ya ba Iya ta saka hannu alamar ta karɓi kuɗi. Da dare Iya a kan jakar ta yi rufda ciki a kai daga ita har Jabiru babu wanda ya yi baccin kirki dan Iya ko bacci ɓarawo ya ɗauketa a tsorace take farkawa hannunta damƙe da jakar, amma a ranta ko da na sani bata yi ba na bayar da jinginar gonar, sai dai tana da yaƙinin Jabiru zai tara fiye da kuɗin a sana'ar adaidaitan wanda za su dawo da shi su mayarwa sa Alhaji Audu ya mayar musu da gonar tun kafin ma damuna ta yi hakan ya sanya ta ce za su yi asubanci domin zuwa birnin Kano a can za a siya adaidaitan a nemi kuɗi a can ta san muddin ta zauna dole ƴaƴan za su samu labarin abin da ta yi amma idan ta bi Jabirun suka tafi tun da bai san ko ina ba kamar yadda ita ko Kanon ma bata taɓa zuwa ba tana dai jin labarinta kuma haka mala'ikan ya bata umarni a kan su tafi birni tare. Jabiru kuwa ransa fari tas yana jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwarsa da ta sama masa mafita a kan cikar burinsa cikin sauƙi. *DA ASUBA* Iya a kiɗime ta sakko daga saman gadon nata, tana ƙanƙame da jakar kuɗin dan ko kaɗan bata cikin kwanciyar hankali, gani ma take kamar dai ɓarayi za su zo su burma mata wuƙa su ƙwace kuɗi a haka ta kwana cikin taraddadi. A hankali ta shiga tashin Jabiru tana masa magana raɗa-raɗa. "Kai Jaburu tashi mu san inda dare ya mana, kar gari ya waye asiri ya tono a samu matsala" Ta faɗa masa lokacin da ya tashi zaune. "Dan aradu ban shirya mutuwa ba yanzu duk da daman mutuwar ba wai ana mata shiri bane, amma gwara dai in zauna in yi istigfari sauran laifukana su wanku" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da tunanin mala'ikan mutuwar da ya ziyarce ta jiya ya faɗo mata bata san cewa Jabiru ne ya mata iya shege irin na yaran zamani ba. Jakar kuɗin ta zazzage ta yi wani ɗauri da wani ƙaton ɗankwali a ƙugunta ta kwashi kuɗin ta ɗura a ciki da yake kuɗaɗen suna ɗaɗɗaure da kyaure sai ya zamana saitin mararta ya yi tozo kamar mai ciki saboda kuɗin da kuma tudun ɗankwalin da ta loda. "Iya ya kika cire su daga jakar?" "Kai tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, yo har a nunawa na rigingine farin wata ai ka san an ce mugu shi ya san makwancin mugu, yanzu idan muka tafi da su a jaka ɓarayi za su iya tare motar mu amma idan na saka a cikina na yi dibarar mu ta manya Allah za su yi tunanin ko juna biyu ne" "Haba Iya tsofe-tsofe da ke za a ga wani juna biyu" "Kai Jaburu bar ni in mutu maza su kai ni ba mata ba, wannan dibarar da ita za mu tafi dan haka mu lallaɓa mu bar gidan nan Allah zai kai mu lafiya ka san bahaushe ya ce dogaro ga Allah jari ne" Ta faɗa tana kallon ɗakin nata ta cikin hasken farin wata. "Allah sarki ɗakina saduwar alkairi sai na dawo na san lokacin da za mu dawo da kuɗi dumu-dumu a jikinmu wataƙila ma sai dai a gina mini ɗakin siminta amma kai ba zan sa a rusheka ba zan barka ko dan tarihi" Ta faɗa a ranta tana leƙo waje dan tabbatar da ba kowa, haka suka lallaɓa suka bar gidan Jabiru yana riƙe da wata babbar leda mai ɗauke da kayansu kala bibbiyu. Tun da suka fito suka nufi bakin kasuwar ƙauyen sai dai babu wata mota da za ta tashi tun da lokacin da duku-duku ne ko sallar asuba ba a shiga ba. Jabiru ne ya je ya tado wani abokinsa mai hayar machine dan dama ko da sun hau motar ma a tashar garin nasu babu wacce za ta kai su Kano kawai dai za ta kai su garin da za su samu motar ne. Su duka biyun suka hau machine ɗin da yake abokin Jabirun ya ji kuɗi da za a bashi mai tsoka da yake Iya ta ɗauka musu kuɗi a cikin kuɗin gonar, lokacin da suka je garin Ɗirani an fito daga sallar asuba dan haka a tashar ya sauke su, Iya ta bashi kuɗinsa yana murna ta kuma bashi saƙon wajen su Baba Umaru a kan ya sanar musu tana cikin ƙoshin lafiya kuma duk abin da Alhaji Audu zai faɗa musu dangane da gona gaskiya ne sai dai ta nannage shi a kan cewa ba zai faɗi saƙon ba sai da yamma, ita ta yi hakan ne dan jar su daɗe basu dawo ba su kuma su Baba su ƙaryata Alhajin duk da tana da yaƙinin dawowar su da wuri saboda bahaushe ya ce fata na gari lamiri. A tashar suka yi sallar asuba gari na wayewa aka fara lodi su Iya ne farkon shiga motar amma tun kan su shiga ta sanar da direba cewa ba za a ta biya wa Jabiru kuɗin mota ba mai mota kuwa ya ce ba zai ɗauke shi a kyauta ba. Ko da Jabirun ma ya ce ta biya sai ta ce "Kai Jabiru baka da hankali ka san dai kuɗin arincaɓa ne idan muka taɓa kuɗin nan da yawa aka zo bai isa ba fa? Daga ni har kai babu wanda ya san kuɗin arincaɓar" Ta faɗa masa cikin raɗa dan haka shi ma sai ya yarda. Da mota ta cika Iya ta garƙama Jabiru a kan cinya ko da mutane suke ce mata ya yi girma ta riƙe shi a cinyarta sai ta ce "Ni Ansai na ga ɓatan nono a ƙirjin budurwa, ku dai ƴan adam bakwa mutuwar ɗakin ku sai ta wani, ai dama na san a rina wai an saci zanin mahaukaciya to Jaburu dai jikana ne kuma da kuke batun na ɗora shi a cinya nawa ma Jabirun yake yaron da ba a daɗe da yaye shi ba" Ta faɗa tana sababi babu wanda ya ƙara cewa komai a haka mota ta tashi ta kama hanyar Kano ta dabo tumbin giwa. Tun da tafiya ta yi nisa sai idanun Iya suka raina fata saboda ƙagewa da ƙafafunta suka yi domin Jabiru ya yi bacci duk jikinsa ya saki, amma a haka ta daure duk da iskar da ake yi ta haɗa guɓi sharkaf ga yunwa babu abin da suka ci. *KANO* Tun da motar su ta shigo garin Kano bakin Iya yake a sake kamar layar mai tafiya, ganin garin cike da motoci da machina ga adaidaita sahu sai kuma jama'a kamar me. "Na shiga aljanna na maƙale ni Ansai, haƙiƙa bahaushe ya yi gaskiya da yake cewa zo mu ci tuwo ya fi tuwon daɗi, dan Allah haka dama Kanon take wallahi yadda ake bada labarinta ta wuce nan, kai jama'a ji yadda motoci suke tari-tari babu adadi" Ta faɗa a fili tana riƙe da haɓa mamaki ya cika ta duk abin nan da ake Jabiru bacci yake bai san wainar da ake toyawa ba ƴan cikin motar kuwa sai dariya suke jin kalaman Iya. "Jaburu, kai Jaburu kai tashi da Allah can kai sai bacci kamar kasa" Ta faɗa tana ɗaka masa duka dan ya tashi kar take kallo ita kaɗai. Ƙaran horn na motoci da machine da hayaniyar jama'a su ne suka sanya Jabiru wartsakewa ya saki baki da jajayen idanunsa na masu bacci yana bin garin da kallon mamaki. "Laaaaaaaaa Iya kin ga adaidaita sahu wallahi sak yadda aka bani labarinta kuma iri ɗaya da ta hoton littafin nan" Ya faɗa da ƙarfi yana nunawa ta window bakin nan a washe kamar gonar auduga. "Dan Allah Jaburu ka ce har ka hangi arincaɓar a ina take?" Iya ta faɗa tana ɗaga suya dan ta ha ga tun da ita duk wannan faɗi tashin da take bata san ma ya adadidaita sahun yake ba dan bata ma taɓa gani ba ko da hoto kuwa. "Haba Iya duk gasu nan sun cika garin ko ina, su ne fa waɗannan ruwan ɗorawar (Yellow) Masu kamar mota" Ya faɗa daidai lokacin da direba ya faka motar a bakin tasha dan ba cikin tasha zai shiga da su ba, wajen kuma iya ganinka masu adaidata sahu ne sun lallaya adaidaitan. Tun da aka buɗe motar kowa ya shiga fitowa amma Iya gaba ɗaya sai jikinta ya yi sanya ga sanyin da ƙafafunta suka yi saboda zaan da Jabiru ya yi a kanta ga shi har lokacin mamaki ya ya mamaye mata zuciya na ganin adaidaitan a haka ta fito. "Baba adaidaita sahun ne?" Wani matashi mai neman fasinja ya tambayi Iya. "Hajiya ina za a kai ki?" Wani ma daga gefe ɗayan ya zo yana tambayar Iya, ita kuma ta saka hannu biyu ta dafe cikinta dan ita ganin jama'ar garin ma duk sai hankalinta ya tashi a nata ganin mutane sun yi yawa garin ma ya yi girma. "Jaburu yanzu dama a kan wannan abun ne ka sanya na ɗaga hankalina, na rinƙa tada zaune tsaye duk dan ganin ka mallake shi, Jaburu a kan wannan abun ka sanya na siyar da gonar gadon da muka gada wajen Malam ni da su Umaru... "Wai mai ya kawo wannan maganar ne Iya? Kin manta ni da kaina na ce ki bari sai ta sakko ke da kan ki kika ce mini mu je jiya wajen Alhaji? Kuma dama ai haka adaidaitan take" "Yo mene ne ma bai kawo ba yanzu a ce saboda wannan abun mai ƙafafu uku ne na siyar da gonar gado, ka san yadda gonar gado take kuwa, wannan abu riɗimɗim a kife kamar wani kunkuru sai wani shegen labule da ake sakawa kamar ana munafurci a ciki, kana ganin masu hayar arincaɓar ma yadda ka san san almajirai sai suna bi jama'a suna fadanci kafin su samo fasinja, ni ba na ɗauka wani abin kirki ne, abin arziƙi duk tunanina zai yi shige da jirgin sama ni wannan abun ko birge ni bai yi ba shi ya sa ma ko farkon shigowarmu garin nan idanuna suna maƙale a kan motoci da machina, sai kuma mutane da nake kallo dan ni wannan abin ma da na gansu wallahi a tunanina motar lodar agwagi da talo-talo ce" Ta faɗa tana rushewa da kukan takaicin an rabo ta da gida ga takaicin ganin adaidaita sahu ba yadda ta tsammata ba. "Haba Hajiya ya za ki zo nan ki cika mana kunne da kuka kamar dai ana zaman makoki?" Wani matsashi ya faɗa yana kallon Iya da take tsaye da Jabiru yana bata baki. "Kai ina ruwan biri da kada?" Iya ta jefa masa tambayar tana harararsa. "Dama babu amma kuma ki sani nan wajen ba wajen kuka bane gwara ku je gida ki samu wuri ki zauna, kowa dai ya san wajen nan ba ya rasa ƴan daba da ɓarayi masu ƙwace... Dididimdim gaban Iya ya bada wani sauti dan ta tsorata sosai da ya ce ƴan daba ne da masu ƙwace dan bata manta da karon su da wanda suka raba ta da sarƙar murjaninta ba bare kuma yanzu da take ɗauke da maƙudan kuɗi in aka ƙwace mata an taƙaice ta. "Dan Allah yaro ka yi haƙuri da kalamina dama mu baƙi ne a garin nan babu inda muka sani babu kuma wanda muka sani ka taimaka mana edan Allah" "Iyeee taɓ sai dai ku biya mu je gidan da nake kwana amma fa gaba ɗaya maza ne a gidan sai mata maza " "Zan biya yaro kuma batun maza ma ka ajiye a gefe na san duk basu fi jikokina ba, mata maza kuma ai su ma halittar Allah ne zan biya na sati guda kafin in samu in fara wanke wanke da shara sai in ke biya duk wata... "Haba Iya wane wanke wanke kuma?" Jabiru da bai san manufar Iya ba da ta faɗi hakan ya tambaya. "To ina ruwanka ita ma ai sana'a ce kuma ma ke samun abin zubawa a bakin salati" Iya ta faɗa jin Jabiru zai mata ɓaran ɓarama dan ta san zai iya nuna wa akwai kuɗi a jikinta aje a murƙusheta a ƙwace cikin dare. "To kya samu kike kwanan dai amma batun wajen aiki sai dai ki fita ki nemo da kan ki" "Wannan ba abin damuwa bane" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma sai ta ce "Mun kawo kan mu ni Ansai yanzu muna zaune a cikin mutunci da sutura amma mun zo wajen kwana ma zai ke gagararmu, ni ban san mai ya ɗauki hankalina ba ma ban yi tunanin mazauni ba" Ta faɗa a zuciyarta tana ɗan jin da na sanin tahowar amma kaɗan dan har yanzu bata saduda ba dan ta ci alwashin cikawa Jabiru burinsa duk da dai ta ga adaidaita sahun ba kamar yadda ta tsammata ba. Yana gaba suna biye da shi, Iya kuwa sai aikawa Jabiru harara take tana masa kashedi da idon wanda shi ko kaɗan bai gane manufar hakan ba ita kuma tana masa hakan ne dan ar ya yi suɓul da baka wajan bayyana dalilin zuwansu Kanon da kuma abin da suka riƙo dan ta san ba ƙaramin aikinsa bane. Ɗan sahu ya kira ya faɗa masa inda zai kai su suka shiga amma Iya dakyar ta shiga. Sun zauna shi abokin tafiyar tasu a aljihu ya zauna wato can kusa da direban a bayan kuma Iya da Jabiru. "Oh inda ranka ka sha kallo, taɓ dama in ka ji makaho yana cewa a yi wasan jifa to ya taka dutse ne" Cewar Iya cikin al'ajabin idanunta ƙurrr a saman adaidaitan daga ciki bayan ta kama ƙarafan jiki da hannu biyu ta rirriƙe tamkar mai tsoron faɗuwa. "Ke tsohuwa kar fa ki zage mu muna zaune ah to na ji sai yada magana kike" Abokin tafiyar ya faɗa cikin muryar gagararre. "Allah ka rufi bakina ka.ɓoyi muryata ni shegiya in ji kaza haba ɗan nan ni ina na ga ƙarfin halin zaginku wallahi karin magana ne dai na yi, ka san ban taa shiga arincaɓar nan ba hasali ma ban taɓa ganinsa ba sai yau wallahi ko a falsafar hoto ban taɓa gani ba shi ne fa nake ta al'ajabi lallai Allah buwayi ne gagara misali" Iya ta faɗa cikin sanyaya murya dan ita tsoron Kanon ma duka ya kama ta bare kuma shi wannan mai zubin ƴan sara sukan "Ah ko da na ji ai na ɗakko da ni kike ne" "Ah wallahi" Jabiru kuwa sai dariya yake dannewa ganin Iya tana kaffa-kaffa da saurayin tamkar wani ubanta. Sai da mai adaidaitan ya tsaya a daidai gidan da saurayin ya nuna masa, baki sake Iya take ganin wani wawakeken gidan ƙasa wanda kamar saukar damina yake jira ya ruguje saboda yadda ya tsufa duk ya rufta. "Ba dai a wannan ruɓaɓɓan gidan za mu sauka ba kamar wasu masu gudun hijira ai da wannan gida gwara gadar da ake cewa ana kwana a ƙasanta a garin legas duk tsiya dai ita babu alamar rugujewa a tare da ita amma wannan gida daga ganinsa kabari salama alaikum ne ko kuma a kira shi shiga da likkafaninka" Iya ta faɗa a ranta lokacin da take ƙoƙarin fitowa. "Nawa ne kuɗinka?" Saurayin nan ya tambayi mai napep ɗin dan saboda ƙarfin hali ma ko ciniki bai yi da mai napep ɗin ba kan cewa a nawa zai kawo su. "Dubu ɗaya ne" Iya kuwa tun lokacin da ta ji yana tambayar kuɗin sai ranta ya cika da murna ganin banza ta faɗi sun zo a ɓagas za a biya musu kuɗi kyauta tana shirin buɗe baki ta fara jero masa godiya ta ji ya ce "Iya sai gare ki na tambaya miki kuɗin sai ki biya shi" Baki sake Iya take kallonsa jin abin da ya yi kallon Jabiru ta yu da ya yi saurin ɗauke kai yana danne dariyarsa dan tuni ya hango jirginta ya san ta ɗauka banza ce ta faɗi sai kuma ta ji wani batun da ban. "Na ji abu bambarakwai wai namiji da suna hajara, wannan ai shi ae kira hajaran majaran, ashe dai da ya yi gwargwaɗan a gaban araincaɓar ba shi zai biya kuɗin ba" Ta faɗa a zuciyarta tana ɗakko kuɗin ko ragi bata da damar nema ta miƙa. Har ya tada napep ɗin zai tafi Iya ta ce "Dan Allah tsaya ɗana zan maka tambaya" Dakatawa ya yi yana kallonta sai da ta ƙarasa wajen kamar mai raɗa ta ce "Ka yi haƙuri da tambayata, ni baƙuwa ce a garin nan, dan Allah duk waɗannan arincaɓar da na gani a can bakin tasha bila adadin kamar jamfa a jos dukansu akwai masu su?" "Mene ne arincaɓa?" "Irin wannan kunkurun da kake tuƙawa" "Taɓ lallai tsohuwa an gaishe ki wallahi kin ci gaisuwar ban girma" "Dama girman ne ya kama ni ɗan nan amma ka san an ce matambayi ba ya ɓata" "To nan da kika gani kowa da nashi kuma kowa ya san wannne ne nasa a wajen nan wani abu ne aka yi?" "Ikon Allah na zaune ya faɗi, babu abin da aka yi kawai dai cewa na yi Allah ƙara muku kaifin basira da kowa daga cikin ku yake iya gane wanne ne nasa duk kuwa da yawansu kuma kaloli ɗaya ne" "To mun gode" Ya faɗa yana jan napep ɗin a guje ya bar wajen. Tsayawa ta yi tana bin sa da kallo tana ta mamaki wai a kan wannan kunkurun abun suka baro gida ita bata taɓa kawowa cewa haka adaidaita sahun ma yake. "Amma kuma ana samu wallahi, ji fa yadda sawu ɗaya ya yi aka bashi naira dubu guda ko canji babu kuma ko ragi ban ji an nema ba duk da unguwar tasu akwai nisa kuma lungu ce, yanzu mu idan muka fita tun safe ai ina ga kafin dare mun yi cinikin da ba lallai mu iya lissafa su ba" Ta faɗa a ranta. "Iya ki zo mu shiga mana" Jabiru da ya ga abin nata ba na ƙare bane ya faɗa yana kallonta sai lokacin ta dawo daga tunanin, tana ɗagowa ta ga saurayin nan ya zubawa cikinta da ya yi tudun kuɗin nan idanu. Ganin ta gan shi sai ya wayance yana kauda kai gefe, gaban Iya ne ya faɗi a take ta shiga tunanin ko dai maye ne shi wanda suke gani har hanji. "Duk wanda zai ga hanjin da yake cikin ka kuwa ganin kuɗi ba zai masa wahala ba tun da an ce suna ganin kayan cikin mutum kamar suna ganin abin da aka rufe da rariyae rankaɗe" Wani sashe na zuciyarta ya bata amsa. Gaba ɗaya sai ta diririce. "Iya gaki kin tsufa amma kuma juna biyu gare ki tsoho kika baro gida?" Saurayin ya tambaya yana ɗan basarwa. "Ayya yaro ba juna biyu bane ƙaba ne ya fito mini, to ko an yanke haka yake ƙara fitowa amma ba ciki bane ni yanzu idan ina da juna biyu ai har a mini waƙar soriye a garinmu" Ta faɗa gabanta yana faɗuwa tana fatan ya yarda da maganar ta. Kai kawai ya kaɗa alamar gamsuwa ya yi gaba suka bishi a baya. Tin da suka fara tunkarar cikin gidan suke jin hayaniya, amma abin mamaki sai Iya take jiyo muryar mata bayan ya ce mata duka gidan maza ne. Suna shiga idanun su suka sauka a kan ƙartan maza suna sanye da riga da zani har da gwaggwaro suka yi da ɗankwali. "Ƴan daudu" Shi ne abin da Iya ta faɗa a zuciyarta, ita da ba abin da ta tsana irin ƴan daudu. "Ni Ansatu yau kuma arangama muka yi fa shigowa gidan waɗanda Allah ya tsinewa, yo ai Allah ya tsinewa mai kamanceciniya da jinsin da ba nasa ba wato maza masu shigar mata ko mata masu shigar maza to ko dama su ne wanda yaron nan ya ce mata maza?" Ta sake faɗa a zuciyarta cike da mamaki kafin ta gama tantancewa wani garsameman ƙato wanda ya saka riga da da zani ya sha ɗaurin ɗankwali yana rataye da wata shegiyar jaka mai kamar zabira fuskarsa da jagira har da janbaki ya taho wajen Iya yana tafiya yana yanga hannun nan nasa a maƙale yana wani mere baki ya zo ya ce "Oyoyo ni dai ga ƙawata na samu, tare da muke haƙawa muna binnewa ba tare da kowa ya sani ba ko ya ji kan mu ai dama daidai ruwa daidai tsaki" Ya faɗa yana ɗaga hannunsa bai sauke a ko ina ba sai a kan kafaɗar Iya. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:51] Mom mashkur & Afrah: https://www.youtube.com/@MAMANAFRAHNOVEL ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH GARAƁASA💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 . Page6️⃣ "A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim, haba wannan ai sai ka sa a kife mu garsameme da kai ka taɓa mini kafaɗa, haka kawai ka ɗora mini jakar tsaba kaji su bini" Iya ta faɗa tana doke hannunsa tare da matsawa gefe ta riƙe haɓa da hannu ɗaya ɗayan kuma yana dafe da cikinta inda kuɗin nan suke. "Haba ƙawas ya kike batun garsamemen ƙato, kina ganina ƴar suwulwular yarinya shafalfal son kowa ƙin wanda bai samu ba ko ƙawancen ne bakya so ki yi dani, ai ƙawance ba sai da sa'anka ba in kina ganin kin mini tsufa" Ɗan daudun ya faɗa cikin karya muryar mata irin ta ƴan daudu. Ko amsa Iya bata bashi ba ta tsaya kallon gidan da ɗakuna ne birjik gasu nan a laye daga gani kasan gidan haya ne hayar ma da ya amsa sunan haya dan gidan ya tara mutane kala da ban da ban. "Hajiya ga gida an kawo ki sai kuma mu je wajen mai gayya mai aiki ki yi signing" Saurayin nan ya faɗa yana kallon Iya. Iya jin ya ce ta yi signing kuma ita bata ma san mai yake nufi ba sai ta ji abin wani banbarakwai wai namiji da suna hajara dan haka kallonsa ta yi cike da neman ƙarin bayani ta ce. "Haba ɗan nan ni fa hayar ɗaki na nema na sati guda amma kana maganar in yi sijin(Gidan kaso) Mai ya yi zafi shi ba wuta ba mai na muku da za a danƙara ni a sijin fisabilillahi wa rasulihi?" Ta faɗa cike da jimanta abin da yake ƙoƙarin samunta fuskar nan ta nuna alamar damuwa ƙarara. Gaba ɗaya sai wurin ya kaure da dariya, saurayin ne ma ya tsayar da tasa dariyar dakyar ya ce "A haba madam ba fa sijin ake nufi ba wai ki saka hannu ma'ana ki bayar da matsabban shaidar zamanki a cikin gidan " "Ayyooo ɗan nan yanzu na ji batu ai mu da yake ba jin yaren nasarar nan nake ba, ka san ni ɗiyar mai allo jikar mai siyar da tawada ina zan san wannan abu ni Ansai in dai kuɗi ne ba a rasa wanda za a bayar ba duk da ina tsoron rasa abin sakawa a bakin salati dan wannan kuɗin shi kaɗai ya rage mini shi nake kira sama da ƙasa yake amsawa ga shi haka muka baro garin mu (Ɗan moɗi) Babu abin da muka saka a hanjin mu da yake asubanci muka yi tun da duku-duku muka fito saboda kar mu yi saɓani da mota ta tafi ta bar mu" Ta faɗa tana kallon kaskon da wani ɗan daudu ya zage yana soya awara ga kuma doya a gefe. Bai tanka mata ba illa taɓe baki da ya yi, gaba ya shiga suka bi bayansa wani ɗaki ya shiga na biyun ƙarshe. Wani dangajejen namiji ne a zaune a tabarma ya sha ɗauri ɗankwali ture ka ga tsiya. Baki sake Iya take kallonsa. "Oh jama'ar annabi na ga annabi in na yi hali na gari ni Ansai, su gidan nan gaba ki ɗayansu ƴan daudu sun fi yawa ya zaman namu zai kasance?" Iya ta faɗa a zuciyarta a fili kuma sai ta ce "Gafaran mu dai" "Ah, ah marhabin lale da manyan mata maganin ƙanana ƙanana ai ni dama na fi son ake samun jinsin mu idan za a samo ƴan haya, yo ina dalili a kan mai za a ke kawo mana jinsin maza wallahi ba na jin daɗin zaman nan gida ɗaya da maza duk sai mutum yake kasa sakewa, dan dai babu yadda za ka yi yo gidan haya ai ba sai yadda kake so za ka samu ba gida ne na kazo na zo" Ya faɗa yana wani karkarya murya yana fari da idanu. "Dama mana ai haka abin yake sai haƙuri" Iya ta faɗa ba dan ranta ya so ba ita bata son ko da haɗa hanya da ƴan daudu ne saboda suna kamanceceniya da maza kuma ta san hakan babu kyau amma tun da zama ya haɗa babu yadd za ta yi, sun zauna ɗan daudun ya kalle su ya ce "Daga gani kun sha hanya amma sai dai haƙuri yau babu komai na afawa a bakin salati a ɗakin nan saboda azumi nake na ramuwa yau, kin san idan al'ada(Priod) Ta same ka cikin watan azumi babu yadda ka iya sai dai ka ajiye azumi yo dama ai jinin al'adar ma ibada ne" Ya faɗa yana wani sinne kai alamar jin kunya. "Kai jama'a mu kuma da haka muka fara wai kuturu ya ga mai ƙyasbi" Iya ta faɗa a ranta . "Yo ka sunkuyar da kai mana ƙato da kai ka zage ka sha azumi cikin azumi da nufin jinin al'ada saboda rashin tsoron Allah" Ta sake faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce "Ai dama mu mata azumin mu ya gaji haka yanzu za ka ga mace tana azumi in an jima sai ya karye dole dama sai dai ramakon mu da yake ma girma ta kama mu yanzu al'adarma sai dai mu ga ana yi" Iya ta faɗa dan ganin an zauna lafiya dan ta lura ƴan daudun su ne ƙarfin gidan kar su je a kore su suke neman inda za su fake. "Zaman dindindin za ki yi a gidan?" Ɗan daudun ya jefawa Iya tambayar. "Taɓ yo ai da rashin sani karen gwauro ya kori bazawara, wa ya aike ni bare ya ga na daɗe ku zama da ku a gidan nan ai ba zan lamunta ba ma samu mafaka dai kafin mu samu mu kufce" Ta ce a zuciyarta a fili kuma ta ce "Sati guda zamu yi" "Dubu goma" "Kai malam ka ji tsoron Allah ka ji tsoron ranar mutuwarka yanzu sati gudan ne zan biya jaka hamsin(10000)? Kamar wacce za ta kwana a ɗaki goma" "Haba ki saka minjaye a maganar ki mana, da ƴar uwarki mace fa kike magana ba da namiji ba, ki ce dai haba malama ko kuma haba mai gayya mai aiki" Ya faɗa cikin karairaya. "Ashsha mantawa na yi ashe dai duk mu ne ai kuɗin hayar sati gudan ne na ji babu sauƙi wai ciwon arne" "Za ki iya yin gaba ki nema dan ni ma ba gidana bane hayar nake mai gidan ne ya bani dillanci" "A mini sauƙi dan Allah, idan muka bar nan ina muka kama muka riƙe ai da hanau gwara mannau" "Haka za ki ce amma ba wai ki tsaya gardama ba kamar dai kin kawo turɓaya(Ƙasa) Lokacin da za a gina gidan" "Yo ba dole na ce a mini sauƙi ba ai na ji ana jaka ɗari ai kuwa a lamarin babu sauƙi sai na Allah, kuma faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar dashi, dan dai ma tunani baiwa ne in ma ba dan wauta da take sa biri ganin ayaba kamar takobi ni da ba gidana ba" "Babu wani dogon batu ki bayar da dubu bakwai" Haka ya ta bayar da kuɗin ba dan ranta ya so ba amma ta san kawai an cuceta, haka suka fito tana hangar lokacin da aka ba saurayin nan kuɗi da alama cin hancin ya kawo customer ne, ta san kuwa kawai sun ci tuwo ne a kan Iyar. Wani tangamemen ɗaki aka nuna musu wanda ko tabarma babu. "Wannan mutane sama da hamsin ne suke kwana a ciki k... "Hamsin fa ka ce ɗan nan kuma a ciki mu ma za mu kwatsu? " Iya ta katse saurayin nan. "Eh mana a dubu bakwai ɗin kike so a baki ɗaki guda ku biyu" "A'a amma dai duka mata ne a ciki ko?" "Ke wannan ba garƙameman ƙato bane kika taho da shi, kuma ki ce ke a ware miki wasu jinsi, to gidan haya kamar motar haya yake ko ina ka samu ka zauna babu banbancin jinsi tun da kowa kuɗi ya biya" Saurayin ya faɗa yana juyawa ya fice daga gidan yana wani boƙara. "Ah idan ka haɗu da ƴan duniya sai haƙuri, in ban da abin ka ka haɗa su da ƙaramin yaro Jaburu da babu abin da ya sani " Ta faɗa a zuciyarta. *DARE* Bayan su Iya sun ɗan miƙawa cikinsu ɗan abin da ba a rasa ba, duk da ba wani ƙoshi suka yi ba sun dai ragewa yunwa ƙarfi ne, dama abincin siyarwa ba wani albarka gare shi ba. Bayan ɗakin ya cika maƙil da maza da mata maza wato ƴan daudu kowa yana sabgarsa saɓanin Iya da take jin ta a damuwa saboda tana ganin daga kwana ɗaya ba za ta iya cigaba da kwana a gidan ba. Shi kuwa Jabiru kwanciya ya yi lokaci ƙanƙani ya fara sakin munshari haka ma Iya ta totsu daga can ƙarshen bango ya zamana Jabiru ne a kusa d ita dan gaba ɗaya jeruwa aka yi aka hau layi sai ya zamana idan wannan ya sanya kansa a nan sai wancam ya saka ƙafarsa a wurin wato suka yi kai da ƙafafuwa. "Kai jama'a gamu ga Allah ɓarawo a hannun mata, ni dama na san a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya za a yi a kwamutsa mutane a ɗaki sama da mutum hamsin kamar akuyoyi a karar siyar da dabbobi, haba ni Ansai in ba dalili mai sa a leƙa gaban sirika ba ina zan zo in kwanta cikin gardawa haka ga shi nan sai sakin tusa ake ko ta ina tamkar ana sakin bom a filin yaƙi na rasa ma ta wane ɓangare tusar take fitowa abinka da manyan ƙartai sai ji kake ƙara yana fita booottttt" Cewar Iya a zuciyarta lokacin da dare ya tsala warin tusa ya hana ta sakat har wani ɗaci-ɗaci take mata a maƙoshi ga munshari da ya cika ɗakin tamkar an dannewa raƙumi wuya da igiya. Jin matsin ya yi yawa saboda an takure ta a jikin bango, gashi duk sanyin da ake ɗan yi amma saboda numfashi ya yi yawa a ɗakin. "Haba garda'u fisabilillahi dan kun gan ni tsohuwa babu ƙarfin kirkin da zan turo ku shi ya sa kuke turarreniya, wato ga Ansai karkatacciyar kuka mai daɗin hawa ba dan ba dan ba, amma ba komai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki" Ta faɗa tana nishi dakyar jin an matse Jabiru ya matse ta tamkar wanda gini ya ruguzowa haka ta ji matsin. "Tabbas tun ba a je ko in ba tusa ta fara ƙarewa bodari, kuma ruwa ya ƙarewa ɗa kada, tun ba a kwana ba ga shi yunwa tana neman mini lahani babu abincin kirki ga shi har ina neman kasa banbnce alif da ambaki bare in ware lam, Allah sarki Maimuna da Aliya matan arziƙi bayin Allah koyaushe su kawo mini abinci amma ina musu ikon irin namu na sirikai ga shin yanzu ɗanyen tuwon nasu ma nake nema amma ban smu bare ma na san ba ɗanyen bane, amma ba komai ai sana'a muka fito domin sana'a tafi ka je maula" Ta faɗa a zuciyarta amma har lokacin bata karaya ba. A haka bacci ɓarawo ya ɗan so sace ta ga gajiya, amma hannunta rufe a hancinta dan har lokacin tana jin ƙaran fitar tusar nan tamkar wanda suka wuni suna cin alala daga ta ji darrrr daga can ɓarin sai ta ji buttttbottt daga wancan gefen. Ji ta yi an dafa ta kamar a cikin bacci da yake dama rufda ciki ta yi saboda kuɗin da yake ƙunshe a cikinta, sai ya zamana hannun ɗaya yana hanci ɗaya a cikinta. Ji take kamar a mafarki aka ƙara dafa bayanta, kafin ta gama tantancewa dan da farko ma ta ɗauka Jabiru ne. "Jaburu ko fitsari zan raka ka? Ai da kake iya baccin ma ka yi ƙoƙari a cikin wannan ɗakin da ya gama ɗumama da tusar garada dan ma kai yaro ne taka tusar ko ka yi ma ba a ji ƙaran fitowarta sosai ba bare warinta " Ta faɗa tana murtsuke fuska da hannun da ta toshe hanci. Cidak ta ji an ɗaga ta kafin ta samu zarafin ƙwatar kanta ko yin magana an saka hannu an danne mata baki, Sai haura ƙafafu take tana zare idanu lokaci guda hankalinta ya tashi dan ba komai bane ya faɗo mata irin kuɗin da yake jikinta za a mata fashi a ƙwace, amma daga jin yanayin ruƙon da aka mata ya tabbatar mata da cewa wanda ya riƙe ta ba ƙaramin ƙato bane kuma majiyi ƙarfi. Hannu biyu ta saka ta danne cikinta. Gidan sai tashin munshari babu alamar mai ido biyu ma a gidan hankalin Iya ya yi matuƙar tashi ganin an nufi wata ƴar hanya da ita baj zame da ita ba sai wani ɗaki yana shiga ya rufe ƙofar ya maƙala sakata. "Allah sarki Jaburu ga Iyar ka a nan za a raba ta da kuɗin arincaɓar da kuka ci buri tare, shikenan mafarkin ka ba zai zama gaskiya ba na siyan arincaɓa, ni kuma mala'ila zai dawo ya ɗauki raina, su kuma iyayenka gonar ta salwanta tun da babu inda za au samu kuɗi su biya Alhaji Audu kuɗin da muka bada jinginar goma shikenan ni Ansai zan tafin in bar ƴaƴana da yunwa basu da gonar nomawa, ga Jaburu na bar shi a garin Kano a gidan ƴan daudu ba lallai ya iya komawa gida ba, ni kar ma in je su rinjaye shi ya faɗa daudun, dan na san suna ƙwace kuɗin nan ba lallai na fito daga ɗakin ba mala'ikan mutuwa zai ɗauki raina"Ta faɗa a zuciyarta. "Ni Ansai wai ni aka yi wa ɗaukan baibai(Baby) Da girmana a mini ɗaukan jarirai... Jin an ɗora ta a kan wata shimfiɗa daga nan akalar tunanin nata ya sauya sai yanzu ta gane ashe ba neman kuɗi ya zo ba. "Allah ƙadiran wa maridan yo ai ta kwana gidan sauƙi ashe ma ka ce ma'adanar ɗan tofi (HQ) kake nema ai bana hana ka ba da tun a can ma ka mini raɗa a kunne da ba sai ka ba kan ka wahalar kinkimoni ba, da ƙafafuna zan biyo ka ka san dama an daɗe ba a haɗu ba tun da mijina Malam da ya fara tsufa aka bar wannan harka ta gabatar da sunna" Iya ta faɗa masa cikin raɗa-raɗa a zuciyarta kuma sai ta ce "Ba kai ɗan duniya hayaƙin taba ba, ai ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka, ban da tijara ta ƴaƴan zamani na yi jika da kai ka zo neman lalata da ni bari na yi ta maka bariki sai in ga ƙaryarka na san dai ai ƙarshen alewa ƙasa" . Cak ya dakata daga jan zanin Iyan da yake mamaki fal ransa ganin ma ita take neman ɗage zanin da kan ta, saurin saka hannu ya yi ya dafe zanin nata baki sake yake binta da kallo ta cikin hasken farin watan da ya ratsa ɗakin, wani farrrr ya ga ta yi da idanunta har sai da baƙin idanun ya ɗauke sai farin tsabar farfarin da take yi. "Wannan tsohuwar da ganinta ƴar duniya ce tun tana budurwa ta yi dumiyanci, wataƙila ma tana ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki, in ba tsohuwar ƴar duniya ba wacce ta taɓa duniyanci a baya a ce tsofe-tsofe da ita amma ko a jikinta wato bata ma tsoron komai wallahi ko da kuɗi ba zan tara da ke ba dama asirin yin arziƙi aka mini malamin ya ce idan na tara da tsohuwa burina zai cika amma tun da haka kike ba zan kwasawa kaina jangwam ba in zo in samu dukiyar ta ƙi ciyuwa da daɗin rai yo ina ɗauke da ƙanjamau kabari salama alaikum ai tunanin mutuwa ma ba zai bari na ci kuɗin cikin kwanciyar hankali ba" Ya faɗa a zuciyarsa yana ja mata zanin ya rufe mata a fili ya ce. "Tashi ki koma makwancinki" "Haba baibai(Baby) Wannan kalmar Iya tana jin ta ne a bakin samari a garinsu da suke cewa ƴan matansu baby shi ne ta kama ta riƙe. Ai ma yi abin da ya sa ka kawo ni ko da zan tafi... "Ki tashi ki bar ɗakin nan" Ya faɗa cikin tsawa dan shi zuwa yanzu ma tsoron Iyar ya shige shi, shi da aka ce ya tara da tsohuwa ma tunnin diramar da za a yi da ita yake ya ɗauka sai ta ƙarfi sai ga shi ma ko a jikinta. "Ai kaɗan ma ka gani wallahi ba kai ɗan duniya ba" Ta faɗa a zuciyarta ganin ya tsorata da lamarin. "Ba zan Iya tafiya ba baibai(Baby) Ka ɗauke ni dai ka kai ni irin ɗaukan da ka mini na indiyawa" Takaici ne ya sa ya kama gefen rigar Iyar ya fara ja ƙiiiii sai ga ta a tsaye yana janta kamar wata akuyar da aka sakawa igiya ita kuwa ta kama saitin cikinta ta damƙe da hannu biyu dan dama ita ta yi tunanin Ko sauraronta bai yi ba ya buɗe ƙofar ya turo ta waje ya mayar ya rufe yana jin wani tashin hankali da faɗuwar gaba. "Shegen sama wai kura ta hangi biri, wato wa ya faɗa maka barno gabas take ai dama ta yaro kyau take ba ta ƙarko" Cewar Iya a zuciyarta lokacin da ta baro ɗakin tana zuwa ɗakin ta nemi wuri ta zauna dan ɗosanawa ma kawai ta yi dan wurin ma bai ishe ta kwanciya ba, a haka akankira assalatu tana zaune jingine da bango tana gyangyaɗi. *DA YAMMA* Suka yi wa mai gayya mai aiki sallama a kan cewa za su je Iya ta samo gidan aikin wanke-wanke da shara, haka suka ɗauki kayansu fakaice suka bar gidan dan Iya ta ce su da zaman gidan ƴan daudu haihata -haihata duk da basu san ina za su je ba. "Wai Iya sai yaushe za ki siya mini adaidaitan ne? Kin kama kuɗi kin ƙunshe sai yawo kike da shi a cikin riga sai wani ya bibbige ki ya ƙwace... "A bakin ka Jaburu wallahi bakinka ya sari kashi ehe wannan kuɗi babu wanda ya isa ya karɓa, kuma da kake batun arincaɓa ai za a siya daga ni har kai babu wanda ya san inda ake siyarwa kuma wannan gidan da muka kwana kana gani dai babu wani na kirki kai gaba ɗaya duniya ma yanzu na kirki wuya suke kar aje mu damƙa maƙudan kuɗin nan da suke tattalin arziƙina da na iyayenka a gudu a barmu da gwale idanu" Ta faɗa idanunta kafe a kan wani mata shi da yake tsaye a layin, shi kaɗai da yake layin tamkar an yi shara. Sanye yake da riga da wando pencil sai gashin kansa da ya tara an masa aski mai layin kitso. "Jaburu ina ganin wancan saurayin mu tambaye shi inda ake siyar da arincaɓar ka san an ce matambayi ba ya ɓata" Shi dai Jabiru da to ya amsa. "Ɗan nan dan Allah tambaya muke" "Tsoho da ya yanka rago ba ɗan nan ya saka mini ba Haƙilu ya saka mini ana kirana ƊAN HARƘALLA" Shiru Iya ta yi jin ya ce wai Ɗan harƙalla. "Anya akwai abin arziƙi a nan kuwa ɗan harzaƙalla sai ka ce wani mai ƙwacen wayoyi" Ta faɗa a ranta tare da sakin murmushin ƙarfin hali ta ce "Allah sarki Haƙilu rashin sani ne da ya fi dare duhu" "Tambayi abin da kike son sani" Ya faɗa yana wani ɗaga kai sama yana fito, alamar gagara. "Dama gidan haya muke tambaya inda za mu samu da kuma inda ake siyar da arincaɓa... Tun kan ta kai ƙarshen maganar sai kawai ta ga ɗan harƙalla ya sauke kansa daga kallon saman da yake kuma ya dakata da fiton, a take ya saka hannu a aljihu ya fito da wani carbi ya fara ja cikin girmamawa ya ce "Baba ina wuni ya wajen manyan fatan kowa lafiya, amma Baba gonaki kika siyar ne?" Ya faɗa yana ƙarewa Iya kallo tamkar dai yana son gano inda kuɗin yake a jikinta. "Wayyo tsuntsu daga sama gashashshe, lallai yau na yi baban kamu a ɓagas" Ya faɗa a zuciyarsa yana jii tamkar ya taka rawa. Mamaki ne ya cika Iya jin ya ce ta siyar da gonaki a take ta fara tunanin ko dai aljani ne in ba haka ba ya aka yi ya san gona ta siyar. "Ya aka yi ka san gona na siyar?" "Allah sarki Iya kinsan yawanci iyayenmu na karkara gona ita ce kadara, amma mene ne ɗayan abin da kika ce arincaɓa" "Allah sarki haka ne, ina nufin kunkurun da ake hayarsa wanda za kake ganinsa ko ina a cikin garin nan naku kamar an yi asakon barbela" "Adaidaira sahu" Jabiru ya faɗa yana washe baki dan yadda ya ji ana batun siyan adaidaitar sai ya ji wani daɗi ya mamaye masa zuciya. "Allahu akbar kabiran, ai gidan kuka zo, ai ni nan dillalin siyar da gida ne m ba wai haya ba, kuma a kuɗi ƙalilan, sannan adaidaita sahu ma ina siyar da shi" Ya faɗa a fili yana washe bakin jin kuɗaɗen da suke neman shigowa hannunsa, a take wani tunani ya faɗo masa ɗazu yana tahowa a ƙasan wata bishiya ya wuce wani mai napep shi da wani yana cewa mai napep ɗin " Kai ai da kai da kasa duk ɗaya ne, mutum a ce bashi da aiki sai bacci kai da ka fito nema amma ka nemi bishiya ta kafa bacci sai magriba ta ƙarato ka kwashi jiki ka koma gida bayan ka san matarka dan ku rufawa juna asiri ta saya adaidatan, amma saboda nauyin baccinka sai a haɗa da kai da adaidaita sahun a ɗauke baka sani ba kana bacci" Wannan maganar ce take yi wa Ɗan harƙalla amsa kuwwa a kunne a take ya gano abin da zai yi. "Mu fa ba siyan gida za mu yi ba haya muke nema" "Ai da haya da siyan duk kusan kuɗinsu ɗaya, akwai wani wanda nake da shi har hawan bene akwai a kuɗi mai sauƙi zan siyar muku da shi" Ya faɗa yana tuno gidan Babban Yayansu Aminu wanda soja ne babba ma kuwa a Legos yake aiki shi ne ya gina gidansa mai mugun kyau an kusa bikinsa to gidan babu kowa a ciki shi ne Ɗan harƙalla ya hango yadda zai siyarwa su Iya gidan ya amshe kuɗin ya arce in ya so komai ta fanjama fanjam. "Gidan bene fa ɗan nan? Yanzu har muna da kuɗin da za a siyar mana da gidan bene? Ko dai haya kke nufi, amma a siyar mana adaidaita a siyar mana gidan bene duka kuɗin fa bai ƙarasa miliyan huɗu ba dan mun taɓa kuɗin" Cewar Iya cike da mamaki hannunta a kan cikinta tana tattaɓa kuɗaɗan dan gani take ashe ita muguwar mai dukiya ce tun da tana da kuɗin siyan gida da napep. "Kai jama'a faɗuwa ta zo daidai da zama, mu wallahi gaba ta kai mu gobarar titi, ashe dai gwara da muka mayar da faɗan da ya fi ƙarfinmu wasa wato muka bar gidan ƴan daudun nan ashe dai rabo ne auren budurwa da ciki, ga shi yanzu zan mallaki gida mai hawan bene a birni, wannan ai dole ma idan muka samu dama mu tafi mu taho da su Umaru mu ƙauro garin nan " Ta faɗa a zuciyarta tana jin tamkar ta taka rawa. "Taɓ miliyan huɗu lallai lallai gaba ta kai ni gobarar Jos" Ya faɗa a zuciyarsa yana raya cewa garin zai bari ko dai ya yi nisan kiwon da sai an kai ruwa rana kafin ma a ji labarin inda yake dama wata rana sai ya yi wata guda ma ba ya zuwa gida saboda ya gagari kowa. "Ai a miliyan huɗun har canji zan baku saboda cefane kin san mu a islamiya an koya mana yadda ake taimako" "Allahu akbar ɗan nan Allah baka lada" "Yanzu ku jirani a nan yanzu zan dawo, amma kar fa ku tafi yanzu zan dawo" Ya faɗa yana tuno yadda zai yi ya sato mukullin gidan Yayan nasa a ɗakin Hajiya. "A haba mu kam ai ba gudu ba ja da baya, ko nan da can ba za mu matsa ba, muna nan ai mun ga wurin zama yo Allah na tuba gidan bene wasa ne, yo ko cewa ka yi mu shekara guda a tsaye a wajen nan ai mu babu tafiya sai dai mu zubawa sarautar Allah ido mu ga har ka dawo" Iya ta faɗa tana kallonsa. "To babu komai, ai akwai mukullin wani gida wanda nake ganin ya fi daceqa da ku to na bauar ajiya ne shi ne zan karɓo" "A dawo lafiya" Iya da Jabiru suka haɗa baki wajen faɗa da sauri ya juya ya bar waje da sauri. Ya sha wuya kafin ya samu sato mukullin gidan Yayan nasu, da take babu wani nisa duka unguwa ɗaya ne da gidan nasu sai dai akwai nisa tsakanin da gidan Yayan nasu, yana ɗakkowa ya wuce layin da ya biyo ɗazu cikin sa'a kuwa babu kowa a layin sannan adaidaitan yana nan kamar yadda ya gani ɗazu sai dai yanzu abokin mai napep ɗin ba ya nan. Tin kan ya ƙaraso wajen napep ɗin yake jiyo ƙaran munsharin mutumin wani murmushi ya saki, sai da ya ƙare masa kallo abin mamaki kan nan ya karkace har da su yawun bacci saboda nauyin bacci sai da ya tabbatar babu mai kallonsa sannan ya ɗakko wani filo ƙarami irin na kujera a can boot ɗin napep ɗin ya ajiye a ƙasan bishiyar, cikin sauri ya saka ƙarfinsa ya kinkimo mai napep ɗin da ya langaɓar kai kamar matacce dakyar ya kai shi ya kwantar tare da ɗora masa kai a kan filon haba wa mutumin ka mai napep ya gyara kwanciya tare da cigaba da sakin munshari. "Taɓ wannan ai kai ne sauna kira mana shashasha in ka ga sakarai ku taho tare, in ban da sakarci jiran jirgi a tashar mota ta yaya za kake bacci kamar an zare maka rai" Ya faɗa a ransa tare da kunna napep ɗin ya zuba aguje. Amma mai napep ɗin ko motsi bai yi ba. Su Iya suna nan zaune sai ganin Ɗan harƙalla suka yi ya zo a adaidata sahu gaba ɗaya daga Iya har Jabiru tsaye suka miƙe daga tsugunnun zaman jiran gawon shanun da suke baki sake suna al'ajabi. "Kai, kai, kai kai, kyankyatsi wannan ne arincaɓar Jaburun?" Iya ta faɗa cike da mamaki. "Cancaɗi lallai kuwa zan sha zabga gudu aradu" Cewar Jabiru baki kamar gonar auduga. "Yo ba dole ba ka yi gudu Jaburu ai sai mun lale kuɗinmu sab... "Ku shigo mu tafi saboda ana jirana a kasuwar adaidaita sahuna mutane sama da hamsin za su siya wannan ma dakyar na karɓo muku shi dan ana ta rububun shi saboda kyan tayoyinsa" Ya faɗa tana ta waige waige irin na marar gaskiya amma da yake su Iya a ruɗe suke da ganin napep ɗin babu wanda ya lura a cikin su. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/14, 13:01] Mom mashkur & Afrah: https://youtu.be/nRgkQ4KXcGM?si=YXzOdqPbrjwtLizS ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH GARAƁASA💃💃💃 akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page 7️⃣ Iya sai washe baki take shi kuma Jabiru yana tattaɓa jikin napep ɗin yana ji cewa wannan nasa ne. Shi kuma Ɗan harƙalla gaba ɗaya ma ba ya cikin nutsuwa saboda kayan satar da ya ɗakko dan haka ma zagaye ya yi ko ta layin gidan nasu bai bi ba ga shi yana ta zulumin cewa shi bai ma ga kuɗin da tsohuwar take ta faman cewa tana da shi ba kar ya je ya jefa kansa a rijiyar kasada, sai dai ya kissima a ransa cewa matsawar suka je gidan ya samu babu miliyoyin kuɗin nan a wajen su sai sun gwammace kiɗa da karatu domin kuwa sai ya sa sun banbance tsakanin aya da tsakuwa. Da hanzari ya fito daga napep ɗin, ya tsaya waige-waige dan ya tabbatar babu mai ganinsa duk da unguwar babu mutane kamar sabuwar unguwa ce tun da sai an shiga ciki sosai daga gidan su ɗan harƙallar unguwa ce da kowa yana gidansa a rufe. Su Iya da suka fito suna ta kewaya napep ɗin suna tattaɓawa basu lura da cewar Ɗan harƙalla ba a nutse yake ba domin kuwa shi marar gaskiya ko a cikin ruwa sai ya yi gumi. Su Iya hankalinsu bai kai ga cewa a ƙofar gidan da za a siyar musu suke ba sai da suka ga Ɗan harƙalla yana ƙoƙarin buɗewa baki sake suke kallonsa ganin yana buɗe wani haɗaɗɗan gida mai ƙaton get. "Kai yaro kana cikin hankalinka kuwa ko dai ka yi makuwa ne? Ka lura da gidan da kake buɗewa kuwa?" Iya da ta ƙarasa wajensa ta faɗa cike da mamaki. "Nan ne gidan mana" "Kai jama'a daɗi kashe ni wahala ta huta tabbas na yarda idan ajali ya kira ko ba ciwo sai an je, yau ni Ansai ce zan mallaki wannan danƙareran gida a cikin binne?" Ta faɗa cike da mamaki tana saka hannu daga cikin rigarta ta fara wajen ɗaurin nan da ta yi ta saka kuɗi, dan har ranta yanzu tana ganin ko da a ce ba a basu komai ba daga cikin kuɗin ai sun samu kadarar da har sai jikokin jikoki sun mora. Jabiru tsalle yake yi kawai saboda farinciki dan shi yana ganin zuwa birni ya musu rana. Dan haka Ɗan harƙalla yana wangame get har rige-rige ake na shiga tsakanin Iya da Jabiru, Ɗan harƙalla kuwa da sauri ya shiga napep ɗin ya tada ya shigo da shi cikin gidan ya mayar da get ɗin ya rufe, a nan inda ya faka napep ɗin a gefe da yake filin wajen yana da girma sosai dan ba ƙaramin gida bane, su Iya kuwa suna nan suna ta kalle-kalle dan tuni sun doshi can cikin gidan ma. Sai dai yana zuwa da ya buɗe babban falon da yake part ɗin Yayan nasu sai Iya da Jabiru suka dakata da shiga. "Kai Haƙilu ya za a yi ka ce mu taka ruwan mudubi mu yi tafiya ni tun da uwata ta haife ni ma ina na taɓa jin an yi daddaɓe tsakar ɗaki da mudubi wannan da gani salon mugunta ne wallahi, duk da na san kyauta ba ta hana arziƙi amma garin son banzana ba zan yarda in yi abin da zan zo ina daman ban yi ba Allah fishshe ni aikin dana sani yadda na tsufa da ƙafafuna haka zan mutu da su ba zan mutu da gundulallun ƙafafu ba wallahi" Ta faɗa tana ƙara ja da baya tamkar ta ga zakin da yake neman abinci. "Wallahi Iya kar ki taka haka kawai mu zame a banza" Jabiru da ya koma can gefe kamar ya ga wuta ya faɗa yana wani kumbura baki. "Na shiga aljanna na maƙale ƙauyawan nan sai sun saka asirina ya tono, ina so in yi in fece amma suna neman zuwa da matsala haka kawai bayan ko ina na gidan tayis ɗin ne" Ɗan harƙalla ya faɗa a zuciyarsa yana danne ɓacin ransa dan ya san idan ransa ya ɓaci abin ba zai yi kyau ba. "Allah sarki wannan ai tayis ake kiransa ko wane gidan ƴan gayu shi ake sakawa a ɗaki baya karya mutane hasali ma daɗin takawa gare shi sai mutum ya ji siiiii idan ya taka" Ya faɗa cikin sanyin murya yana fara takawa suka ga ya shige ya yi zagaye amma ko alamar faɗuwa, a haka suka fara takawa kamar masu koyon tafiya har suka ƙware ya nuna musu ko ina na gidan suna ta san barka. "Taɓa wannan sai mun gama haɗa kuɗin gonar nan za mu je mu kaiwa Alhaji Audu mu taho da su Umaru amma sai kowanne ya saki juyar matarsa dan yanzu gidan nan sai dai su auri matan birni amma ba su Aliya ba dan wannan gidan aka kawo su dauɗa zai yi" Iya ta faɗa tana zaunawa a wata luntsumemiyar kujera. "Kai jama'a garin daɗi ba kusa ba in ji kyankyaso da ys leƙa masa, luntsumi irin wannan kujera mai laushi kamar ba a duniya ba" Cewar Iya tana gyara zama. "Ga mukullin adaidaita sahun ni zan tafi a sallame ni" Ɗan harƙalla ya faɗa yana kallon kuɗin da Iya ta fito da su dan ya matsu ya tafi kar asiri ya tonu" "Yaro ka tafi ina? Ai baka ƙarasa laifinka ba dan wannan da kake gani hotiho ne babu abin da ya sani a jikin arincaɓa sai ka koya masa" Ta faɗa tana nuna Jabiru. Da sauri Ɗan harƙalla ya kalli Jabirun yana jin wani haushinsa. "Kai kuwa mene ne abin wahala a tuƙa adaidaita sahu, mukulli kawai za ka kunna fa kake tuƙawa kamar dai yadda ake tuƙa machine" "Kai raba kan ka da Jaburu marayan Allah ne ko amalanken shanu ba ya hawa bare machine, wannan ma dan shi ya ambata cewa yana so ni kuma kaf duniya Jaburu ne ƙaddarar soyayata shi ya sa ma na cika masa burinsa" Ta faɗa tana kafe Ɗan harƙalla da ido wanda tashin hankali da damuwa suka bayyana ƙarara a tare da shi dan shi niyyarsa dama yana karɓar kuɗin ya gudu amma kuma suna neman ɓallo masa ruwa. "To babu damuwa zan koya masa amma dai a cikin gidan nan dan bana so mu fita waje mutane za su ce abin kunyane duk girmansa bai iya tuƙa adaidaita sahu ba sai an koya masa" "Kai Haƙilu ba shi kaɗai za ka koya wa ba har da ni, ka san tare za muke fita sana'ar hayar to ko da wata ran ma idan shi ba zai fita ba sai ni na fita, kuma batun fita ma a bar shi duk da abin kunya gaba muka bashi ba baya ba, wannan gidan ai ko jirgin sama ya isa a koyawa mutum ba arincaɓa ba" Ta faɗa tana tashi ta miƙa masa kuɗin, ya saka cikin wata jaka da ya zo da ita, shi dai bai ce komai ba jin wai har ita za a koyawa. Ɗan harƙalla a mazaunin direba, sai ya ce Jabiru ya zauna a hannun adaidaitar kusa da shi, Iya tana baya ta tashi tsaye duk da a duƙe take dan ba zai iyu ta miƙe tsaye ba, ta daddafe ƙarfen nan ta yi dogon wuya tana kallon abubuwan da ake nuna wa Jabiru dan bata so a barta a baya. Haka ya wuni yana koya wa Jabiru adaidaita sahun amma dai bai wani ƙware ba sai dai ya ɗan fara iya ja, dan da aka bashi ya gwada tuƙawa Iya har da rawa da juyi ganin Jabiru yana tuƙa adaidaita sai jinjina masa take tana masa kirari shi kuma yana jin kansa ya masa gingiringim. Dan yanzu sai ta ji tana mugun ƙaunar adaidaitan sahun. Bayan ya gama da su ya musu sallama ya basu dubu goma a cikin kuɗin, Iya godiya kamar ta ari baki dan tana ganin ya musu komai haka ya musu sallama dan shi har lokacin ba a nutse yake ba duk da ya san da wuya wani zo gidan amma dai an ce marar gaskiya ko cikin ruwa sai ya yi gumi. Haka ya fito ya dan har da gari da sugar Iya ta bashi ya siyo musu a wani shago, yana basu ya kama gabansa dan lokacin ma la'asar lis. Iya da Jabiru kuwa sai kewaya gida suke suna wadaƙar su ga nepa ga ruwa a famfo sun rasa inda za su saka kan su dan murna. WASHE GARI Sai da suka sha garin nan da Iya ta haɗa dan sai wajen ƙarfe goma ma suka shirya domin tafiya hayar adaidaitan. "Kai Jaburu nawa ce da kai komai baka yi da karazana ka dai ga yadda garin nan yake da arincaɓa kaca-kaca gasu nan maimakon mu fita tun da sanyin safiya mu samu rabon mu amma har rana ta ƙwalle muna gida" "Haba Iya ai rabonka ba ya wuce ka kuma ko su masu hawan za su so su hau adaidaita wanda ake wuta ba wanda ba ya gudu ba ni kwa nan idan na ringa falfala wuta sai kowa ya san na ƙware" Ya faɗa yana fashewa da dariya dan gaba ɗaya daɗi ya mamaye masa zuciya sai ɗaga mukullin adaidaitar yake. "Ya yi rinfa sha shirgi Jaburi, dodon ƴan arincaɓa, na Umaru ɗan gidan Mamman jikan Ansatu bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi" Iya ta faɗa tana wani ɗaga hannu sama tana jinjina masa shi kuma sai wani kaɗa kai yake kamar ƙadangare jin irin kirarin da Iyar take masa ji yake kamar ya zama tsuntsu kan gudu saboda yana son ake zuga shi. *ƘAUYEN ƊANMOƊI* Tun da su Iya suka tafi babu wanda ya lura, sai da gari ya waye Baba Umaru ya je gaisheta amma sai ya tarar wayam, bayan da suka gano cewar Iya da Jabiru basa nan sai suka shiga gari yawon cigiya da sanarwa. Labarin da mai machine ɗin nan da ya kai su Iya wajen hawa mota da ya zo musu da shi na saƙon da Iyar ta bayar sun shiga tashin hankali dan sun san mahaifiyarsu babu inda ta sani a binni bare kuma Jabiru da kansa dusa ce kawai babbar damuwar ma samun labarin kuɗin jinginar gonar gadon da suka karɓa. Haka suka dangana tare da bin su Iya da addu'a domin babu wanda ya san inda za a same su ma, ga damuwar bada jinginar gonar gadon da Iyar ta yi gonar da suka dogara ita. *KANO* Jabiru Iya ce ta taimaka masa suka buɗe get ɗin gidan, sai da suka wangame shi tas tamkar dai ba adaidaita sahu za a fito da ita daga ciki ba sai ka ce wanda za a fito da tirela. Bayan sun fito da adaidaitan Iya tana turo shi dakyar. "Kai Jaburu anya kuwa za a yi abin arziƙi yo ni ai duk ƙarfina da kuma garin da na sha ya ƙare a turo maka arincaɓan, anya wannan ba sai ina siyan maganin ciwo tara ba na ciwon jiki" Iya ta faɗa lokacin da ta kama tsantsa tana kallonsa yadda ya shiga ya yi wani zama na gagararru ya wani wawwangale ƙafafu tamkar mai karyayyun cinyoyi. "Rufe gida Iya nafi so mu fantama cikin gari yin abin da ya kawo mu" Ya faɗa yana gyara zama tamkar wani wanda zai tuƙa jirgin sama. Bata tanka masa ba ta saka mukullin ta kulle get ɗin ta taho ta kama ƙarfen ƙofar gaban napep ɗin ta ɗare, ta zauna a gaban wajen aljihu. "Iya ke da za ki shiga baya kya zauna a nan kar fa ki faɗo" "Kai Jaburu na sha tabara na sha lahaula ni nan da kake gani nan gani nan bari ce farar tumfafiya, yo mu da zamu zuba fasinja a baya ya za a yi in zauna a yi asarar wajen mutun guda ai a nan zan zauna ni ce nan kalbus sayyara (Karen mota) " Ta faɗa tana tuntsurewa da dariya, kallonta Jabiru ya yi ya girgiza kai tare da tada adaidaita sahun. Burrrr ya bada wani ƙara kafin Iya ta tambaya dalilin ƙaran Jabiru ya fusgi adaidaitar sun fita da gudu, sosai Iya ta kama ƙarafan ta riƙe saboda shirin ko ta kwana dan ta lura da lamarin tuƙin Jabirun sai da shiri. Gajab-gajab yake shiga ta ƙananan ramukan kwatocin layi dan haka sai napep ɗin ya kasance yana sama yana ƙasa yana yin gefe da gefe. "Jaburu anya kuwa ka nuna koyar tuƙin nan sai in ke ganin kamar dai hannun naka bai gama faɗawa ba, ga shi ban san inda za a samu ɗan harƙal... Kafin ta kai ƙarshen maganar sun canɓala wata kwata wacce bata da wani zurfi irin hanya ce aka yi wa wata makwararan wani gida, Iya a gigice ta yi sauri fitowa daga gaban ta koma baya kasancewar da suka yi gajab sai adaidaita sahun ya mutu ya tsaya cak. "Iya ya kika bar mazauninki?" "Kai Jaburu duk ƙaunata da arincaɓa (Adaidaita sahu) Da kuma ƙaunarka gare ni ba zan bari in mutu a banza ba" Ta faɗa tana gyara zamanta dakaka. Shi dai bai ce komai ba ya cije leɓe ya ƙara tada napep ɗin ya saki wata wuta, Jabiru da yake tuƙi sai jin hannayen Iya ya yi duka biyu ta ƙanƙamo wuyansa tamkar wanda ta shaƙe biri da igiya. Da hannu ɗaya ya riƙe adaidaitan ya saka ɗaya ya ƙwaci kansa dakyar wanda sanadin hakan adaidiitan ya ƙwace kaɗan ya rage su bugu da bishiya dakyar ya karkatar da shi ya kashe. "Wallahi ko dai ki sauka ki dawo gaba ko kuma ki koma gida ki jira in dawo... "In ka isa in nutse a wurin nan Jaburu a sayi arincaɓar da kuɗin gonar gadona da na ƴaƴa ka zo mini da maganar banza wallahi ƙafata ƙafarka" Ta katse masa maganar "To dawo wajen zamanki wannan kina shaƙo mini wuya ai sai ki kashe mana kasuwa babu wanda zai shiga" "Ko da na ji amma ni babu gidan da zan koma aradu Jaburu nan gani nan bari farar tumfafiya" Ta faɗa tana dawowa gaban ya ja suka cigaba da tafiya. Haka suka rinƙa yawo a cikin gari, babu inda suka sani sai mai da suke ƙonewa a banza, a haka har suka zo ƙofar ɗin asibitin Aminu Kano. Wani tsoho da furfura ta gama baibaye masa fuska ƙafarsa babu takalmi sai wani ƙullin kayansa a cikin rigar filo, da net (Gidan sauro) Riƙe a ɗaya hannun yana ɗan gudu-gudu yana waiwaye da gani ma ba lafiya ce ta ishe shi ba, tun kafin ya ƙaraso yake ɗagawa Jabiru hannu alamun Jabirun ya je da napep ɗin. "Iya kin ga mun samu fasinja" Jabiru ya faɗa cike da zumuɗi dan dama babu wanda ya tare su dan ko suna tafiya idan suka ga mutum har ɗan tsayawa suke amma babu wanda ya shiga sai su ga an tsayar da wanda yake gabansu ko bayansu sun kasa gane ko dai mutane sun lura da Jabirun ɗanyen direba ne Allah ne masani. "Alhamdulillahi! Ai fa dama mahaƙurci mawadaci, duk mai haƙuri ya kan dafa dutsenhar ya sha romonsa yanzu ba gashi ba an tsayar da mu, ni wallahi dama tafiyar nan dan babu shiri muka taho binnin Kanon nan da sai na karɓa maka maganin kasuwa yadda ida muka fito hutun kirki ba za mu yi ba mun rinƙa jidar mutane kamar dabobi ko kamar kyauta muke ɗaukansu" Iya ta faɗa tana jijjiga kai alamar Allah ne ya san halin jaki da bai bashi ƙoho ba. Tsohon nan yana haki haɗe da ɗan tari ya faɗo cikin adaidaita sahun cikin ƴar muryarsa da bata fita ya buɗe baki ya ce "Mu je yaro, mu je kar su biyo sawuna suna kama ni kwanana ya ƙare ban gaji da duniya ba" Baki sake Iya ta bi bakin tsohon da kallo ganin haƙorin kirki ma babu a ciki duk sun zube sabo da tsufa sai jefi-jefi. "Jaburu wannan fa da alama mun yi babbn kamu ina tunanin kakarmu ta yanke saƙa, miliyoyin da muka kashe jiya ne za mu mayar da gurbinsu" Iya da ta kai bakinta kusa da kunne Jabiru ta faɗa cikin raɗa. "Kamar ya Iya? A ina ne kakar tamu za ta yanke saƙa to ai ina ganin ko zare kakar mu ba za ta samu ba bare ta yanke saƙa indai a jikin wannan ne" "Baka da hankali Jaburu ta yaro kyau take ba ta ƙarko, wannan da kake gani daga gani ba ƙaramin kuɗi gare shi ba kasan akwai masu kuɗin da suke saka maƙudan kuɗi a leda su libga tsumma to shi ma wannan daga gani kuɗi ne shaƙe a cikin rigar filon nan dan haka kawai mu yi wuff da shi" Ta faɗa tana cikin raɗa kannewa Jabiru ido. Gyaɗa kai Jabiru ya yi alamar gamsuwa da maganarta. "Mu tafi yaro, mu tafi unguwa uku za ka kai ni" "In ce dai ka tanadi kuɗi yo zuwa unguwanni uku a garin nan ai ba ƙaramin abu bane, ana tafiya ana samun goluso(Goslow) Haka na ji ana faɗa ɗazu" Iya da bata san sunan unguwa bane unguwa ukun ta faɗa tun da su ba sanin sunayen unguwannin suka yi ba. "Kai yaro ja mu tafi wannan tsuhuwar bata san ma unguwa ce unguwa ukun ba kai da yake aikin ka ne mu je dan Allah zan ke nuna maka hanya" Ya faɗa hankali tashe yana waiwaiye. Haka Jabiru ya tada nape ɗin suka tafi ruuuu. Iya da Jabiru dai sai daɗi suke ji domin suna ganin rigar filon nan ƙwace goruba a hannun kuturu ba zai yi wuya ba duk da tun da ya zauna a napep ɗin ya ƙanƙame net (Gidan sauro) Da rigar filon nan. "Yaro adaidaitan naka dai ko yana buƙatar juyen baƙin mai ne yo abu sai ruguguu yake kamar tashi cidar ruwan sama" Cewar tsohon nan da yake yi wa Jabiru kwatance dakyar sanadin yadda yake jin adaidatan sahun tamkar jujjuya shi ake yi saboda gaba ɗaya ya kasa fahimtar mene ne matsalar, bai san cewa ɗanyen direba ya hayo ba ɗanyen ma ɗanye sharaf. "Ba arincaɓar bane yake buƙatar juye, mai arincaɓar ne yake buƙatar ya yi juye, juyen ma na rigar filon hannunka amma da sannu za ka gane shayi ruwa ne" Iya ta faɗa a zuciyarta rana wani murmushi. "Baba yana da ɗan matsala ne amma ba babbar matsala ba" "Kai jama'a " Tshohon ya faɗa a fili yana ƙara ƙanƙame filon da net ɗin. Tun fa suka fara tafiya tsohon ne yake kwatanta inda za a bi har dai aka kusa layin da gudan nasa take, dai faman ajiyar zuciya yake tamkar yaron da ya sha kuka ya ƙoshi. 'Yaro kan kwanar can da taya take nan ne gidan nawa yake" Ya faɗa cike da ɗan zumunɗin ganin an kusa zuwa a sauke shi ya huta daga tunanin rayuwa ko mutuwa da yake ta faman yi da fargaba tun da ya shiga adaidaitan ganu yake kamar dai ma direban bai san hannunsa ba ma. Tsoho ganin dai kamar ma Jabiru bai ji abin da yake nufi ba sai dai ya ji Iya ta ce 'Kai dai wannan tsoho da kwanzantu kake aradu, to ka buɗe kunnuwanka rass ka san ma wannan arincaɓar da ka shigo direbanta ɗanye ne sharaf kamar alayyahun fa aka tsunko yanzu dan haka faɗar a yi kwanar gidanka ma mara ɓata baki ne kawai ka yi fatan saukarmu lafiya dan yanzu a halin da ake ciki yanzu arincaɓar nan ki kwana ba zai sha ba" Iya ta faɗa hankali kwance dan ta ga duk babu jama'a hakan ya nuna za su ci duniyar su da tsinken tsire. "Ɗanye!!!" mutumin tsantar tashin hankali ya a bayyana a tare da shi ya fara ƙoƙarin fita daga napep ɗin da Jabiru ya ƙara sakar masa wuta sai kangal-kangaltu suke saboda ba wai ya ƙware bane sai napep ɗin ya yi can sai ya yi nan dan tuni an wuce kwanar da tsohon ya ce a nan layin gidansa yake. "Gaba dai gaba dai Jaburu mai tuƙin ƙwararru, kai ko wanda suka ƙera arincaɓar ma baya suke take maka kai ne ɗaya tamkar da miliyab a kaf masu tuƙa arincaɓar Kano, tuƙinka azimun ne dan mutum ko da kuɗinsa sai da rabonsa, Jaburu masallacin kura mai yawan ƙasusuwa yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai ya yi dare" Iya ta taƙarƙare sai zabgo masa kirari take tamkar ta ari baki, shi kuwa Jabiru ai tuni ma Iya ta ɗora shi a keken ɓera dan ji ya yi kansa ya masa wani gingiringim musamman da ta ce shi ne shugaban ƴan adaidaitan Kano baki ɗaya. A take ya manna wuta yana wani daddagewa tamkar dai da ƙarfinsa ne yake tuƙin, tsohon nan kuwa sai ya fara zabgo salati ganin an wuce inda za a kai shi a take zuciyarsa ta raya masa cewar ƴan yankan kai ne ko dai suna da haɗin baki da ƴan yankan kan shi ya sa aka turo su, da yake shi ne mai tsautsayin sai aka rufta da shi. "Hadiri malafar duniya, baƙin hadari fito ta gabas kowa ka kashe kare ka ka kashe in ni ka kashe mutun ka kashe" Iya ta sake zuga Jabiru wanda hakan yake ƙara ruɗa tsohon nan yana ji dama bai hau adaidaitar tasu ba tun da yana ganin ga shi ya yi gudun gara ya tarar da zago. " Ban da lalacewa a kashe mutum a ce kare aka kashe jama'ar annabj, na ga annabi in na yi hali na gari wato kowa ya kashe kare ya kashe in ke ya kashe mutum ya kashe ko? To wallahi in ya kashe ki ma alade ya kashe" Cewar dattijon a zuciyarsa a fili kuma sai ya ce "Dan Allah ku taimaka mini kar ku kai ni a yanke mini kai, wallahi kan nan nawa tsufa ya sa ya yi lagafgaf har loɓawa yake ko an yanke babu kuɗin da zai yi" Ya faɗa yana kuka shaɓe-shaɓe. "Jaburu ka ji mutuminka ya ɗauka kansa za a yanke mu bai san kuɗin hannunsa kawai muke buƙata ba ko yankan kai muke ai sai dai mu nemi samari ɗanyu sharaf masu rusheshen kai yadda za mu zama muloniya" Iya ta faɗa cikib raɗa. Kai kawai Jabiru ya gyaɗa mata. "Jama'a taimako, za a tafi da Malam Tukur a gille masa kai" Malam da yake ɗaga hannu hagu da dama yana neman ɗauki ya faɗa duk da babu mutane sai jefi -jefi kuma babu wanda ya hango shi bare ya san abin da yake cewa sai dai suna mamakin gudun adaidaitar ne kawai. Shi kuma Dattijon nan su Iya ne suke kiɗan su suke rawar su tun da basu san cewar inda ya fito asibiti bane bare su san mai ya fito da shi, su dai sun ɗauka gudun famfalaƙin dukiyarsa yake, basu san cewa mai jinya bane ya gudu daga asibitin ba. "Ni Tukur na ga ta kaina, wannan mutane ba za su sauke ni ba, dan na ga babu niyya ango ya kwana da wando, tabbas na yi gudun gara na tarae da zago da a tunanina wanda za shi sama idan ya taka leda ya ci ƙarfin tafiya amma dai yau na tabbatar ba haka bane" Ya faɗa a ransa yana ta share hawaye. Jabiru sai da suka shige can ciki ƙarshe-ƙarshe inda ake sabbin gine-gine ba a gama ba. "Jaburu ga kango can, ka ga nan babu kowa mu je can mu ci karenmu ba babbaka, tun da mu da haka muka fara kuturu ya ga mai ƙyasbi" Inna ta faɗa a fili tana murmushin jin daɗi ganin za su samu maƙudan kuɗi a ɓagas su mayar da gurbin kuɗin gonar da sukabayar jingina. Jikin dattijon ne ya jau ƙyarma dan zuwa yanzu ya saddaƙar da cewa kwanansa ya ƙare. "Tabbas ba a gujewa mutuwa duk inda mutum yake ajalinsa yana biye da shi sai dai in lokacinsa ne bai yi ba" Ya faɗa a ransa yana jin dana sanin baro asibitin da ya mutu a can ɗin mutuwa cikin salama ba irin wannan mutuwar ba da za a raba shi da kansa ɗungurugum yana ji yana kallo. Jabiru ne ya fara fitowa ya tsaya a ƙofar da baya inda dattijon yake, Iya kuma ya fito tana hangar ko ina sai da suka tabbatar babu kowa. "Jaburu mu kai shi cikin kangon kar mu warci abin nan a nan ya je ya mana ihu mu gudu a bi mu a far mana, amma a cikin nan sai mu yi maganinsa babu wanda ya gani" Ta raɗawa Jabiru a kunne kai ya gyaɗa mata. Artabu aka fara da dattijo ya kafe a kan cewa ba zai sakko ba ya ƙanƙame rigar filonsa da net ɗin sa yana zubar hawaye. "Wato taurin kai da tirkiya za ka nuna mana, to ai idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi" Cewar Iya tana damƙe baki. Haka suka masa cali-cali da yake dama ɗan falaulayi da shi babu ƙiba ga uwa uba jinya sai ya zamana bashi da nauyi cidak suka ɗago shi, Iya ta riƙe ƙafafu Jabiru ya riƙe uban jikin ga an cusa masa gefen net ɗin nasa a baki dan kar ya yi ihu ga kuma har lokacin rigar filon a ƙanƙame a ƙirjinsa ya danne da hannuwansa, rigar filon da su Iya suke son kai wa wawaso. Ɗakunan ma wani cikin wani haka yanayin kangon yake ga tsawo gare shi gidan amma haka suka shige can ciki suka kai shi ɗakin ƙarshe baka ganin komai sai ruwan hawaye sharaf-sharaf kamar an kunna lalataccen famfo. Jaɓar aka ajiye Malam Tukur tamkar ana jefar fa kayan wanki. "Ku mini rai kar a yanke mini kaina" Ya faɗa duk da akwai net a bakin amma kana iya jiyo diri maganar. Babu wanda ya kula shi suka saka net ɗin suka ƙulle masa ƙafafu. "Kuɗi ko rai" Iya ta faɗa tana kallonsa. "Gwara ma ka bayar salin alin dan idan na kira oganmu da bindigu za su taho kuma suna zuwa babu sauƙi ciwon arne za su ɗakko maka kai... Tun kan Jabiru ya kai ƙarshen maganar Malam Tukur ya saki wani marayan kuka marar sauti, domin ya san ƴan magana sun ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah, yana jin abarin yadda ake cewa ƴan kidinafin suna ɗauke kan mutane da bindiga yau kuma abin ya zo kansa. "Kar ku mini ta ƴan kidimashin(Kidnaping) Kar ku mini ta ƴan boko haram ku mini ta ƴan mahammadiyya wato haƙuri halin annabawa, wallahi ni ko sisi bani da" Ya faɗa dan lokacin an cire masa net ɗin daga bakin. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/15, 16:07] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH 😂😂😂😂😂 Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page 8️⃣ "Jaburu zazzage mini rigar filon nan nashi mu kwashe rabonmu tun da ya ƙi ya bayar sai a ƙwaƙwata ta ƙarfi mu arce mu bar shi a nan" Cewar Iya tana aikawa Malam Tukur wata uwar harara. Da sauri Jabiru ya ɗauke rigar filon hannunsa har rawa yake wajen zazzagewa, amma me wani dogon wandon shadda ne da ya gaji da koɗewa, sai wani katalallan silifas wanda saboda sakawa tsakiyar har ta cinye, sai lemon fata guda uku biyu ɗayan ma a yanke yake. Baki sake Iya da Jabiru suka bi shi da kallon jin haushin saka ran samum maƙudan kuɗin da suka yi a jikinsa. "Dama na faɗa muku ni bani da ko ƙwandala, dama ko kuɗin adaidaitar da kuka ɗakko ni sai naje zan ranta in baku, saboda nan inda kuka ga na fito asibitin Malam Aminu ne, hawan jini nake bansan lkcn da aka kwashe ni muraran rai a hannun Allah aka kaini asibitin ba, bayan an san bana ƙaunar zuwa asibiti, to shi ne na farfaɗo na faɗawa ɗana mu bar asibitin nan saboda na fi son na ganni a gida amma suka ƙi, ni kuma ganin Malam Audi na kusa da ni ya margaya(Ya mutu) Rai ya yi halinsa shi ya sa na yi wa kaina ƙiyamul laili na haɗo kayana na yayumo gidan saurona (Net) Da yake duk ƴan zaman jinyar suna waje na lallaɓa na bi ta ɗayar ƙofar zan gudu shi ne fa wasu ma'aikatan jiya suka ganni suke kirana da yake su ne masu kula da mu kuma sun san ba a sallame ni ba. Suka biyo ni shi ne na gudo dan kar su mayar da ni dan ni ban shirya mutuwa ba duk da sai kwana sun ƙare" Ya kai ƙarshen maganar yana saka bayan hannunsa ya share hawayen da suke zuba shaɓe-shaɓe. "Kuturun kare amma kai wannan da ɗanyan aiki a gabanka jajawur ma kuwa, yanzu dama ka san babu kuɗi a cikin ƙunshin rigar filon nan sai tarkacen banza da wofi amma ka sanya muka ba kanmu wahala? Ai kuwa sai mun jibgeka ladan wahala da ka bamu" Cewar Iya tana dunƙule hannu. "Wallahi Iya ga man da muka ƙona ina fa ya yi mu yi sati guda cur muna amfani da shi" Jabiru ya faɗa cike da ɓacin rai. "Yo ba dole dama a ƙona mai ba baka ji ya ce unguwa uku ba, to unguwar tasu ce aka haɗa uku a wuri ɗaya nisan unguwa guda uku a guda ɗaya ga wannan dogon zangon da muka ɗakko zuwa wurin nan ka ga in aka haɗa unguwa huɗu kenan" "Yo ai dole ma mu jibge shi ta bakin naki" Ya faɗa yana dunƙule nasa hannun. Iya da take saitin jikin katangar ne bata lura da wani miciji da ya sako kansa ba, babu wanda ya lura Malam Tukur yana ta bada haƙurin kar su duke shi saboda bashi da cikakkiyar lafiya amma babu wanda ya saurare shi, Iya ta daddage ƙarfinta ta sakarwa Malam Tukur ƙulli ta ɗago dan sai da ta sunkuya ta kai masa ƙullin, ɗagowar da ta yi ya yi daidai da sakowar micijin wuyanta ya laulaye mata wuya, Iya jin motsin abu ya kanannale mata wuya ta kai idanunta wajen aikuwa ta yi mugun gani idanu ta zaro tana rarraba idanun cike da fargaba ta sauke idanun nata a kan Jabiru da ya sauke wa Malam Tukur ƙulli har biyu. "Allah ka yafe mini zan yi hakan ne ba dan in cutar da maraya ba sai dan in ceci kaina, domin na san matsawar Jaburu ya ga micijin nan to ko ni ce ubansa da ya diro da shi duniya ba zai tamaka mini ba saboda tsoron da yake da shi kamar farar kura guduwa zai yi ya bar ni micijin ya kashe ni in zama mushe" Ta faɗa a zuciyarta tana nufar hannun Jabiru ta riƙo tare da riƙo kafaɗarsa ta kai wuyanta kusa da na shi wuyan kamar micijin ya gane mai take nufi ai kuwa ya haɗo da wuyan Jabiru ya kanannaɗe su a tare. "Iya ya haka kika maƙalƙale ni? Ya na ji kin maƙala mini abu a wuya ko tsumma ne" "Duba da kyau Jaburu abin ya fi ƙarfin tsumma abinda yake wuyanka ya fi ƙarfin mai rai" Ta faɗa cikin tsoro idanun nata har sun cika da hawaye, na tausayin kanta da kuma tausayin maraya da ta masa haka. Bai wani kawo komai ba ya miƙa hannu gefen wuyan nasa bai yi wa hannnun masauki a ko ina ba sai a wajen jelar micijin ya damƙo dan ya ga mene ne yana damƙa ya ji wani santsi bai kawo komai ba ya kalli hannun nasa ai kuwa ya yi arangama da jelar miciji damƙe a hannunsa, da sauri ya maida kallonsa kan Iya ya ga kan micijin a nata wuyan ya nannaɗe. Idanu ya shiga zarewa tamkar za su faɗo dan shi hatta ƙadangare tsoro yake bare kuma mai gayya mai aiki miciji, micijin ma a naɗe a wuyansa ai kuwa babu lafiya a take ya ji fitsari ya cika masa mara. Salatin da ya ji Iya ta yi ƙarfin halin karantowa shi ya kama ya cafe yana fatan Allah sa su ƙwaci kansu kar abu ya gagare su. "Haba Jaburu kaima ai sai ka nemi naka salatin ko wata addu'a ka kama amma ma kama abu ɗaya gwara dai kowa ya kama nasa ko Allah ya sa a dace" Ta faɗa lokacin ruwan hawaye sun yi wa fuskarta sallama fuskar da ta jiƙe da gumi sharƙaf sai ta haɗu da ruwan hawaye. "Alhadisil auwal,hadisi na ɗaya... 'Haba kai kuwa Jaburu ai sai ka samo na hamsin ko ɗari ka karanto ka san an ce in mutum zai roƙa to ya roka da babban masaki, amma ka fara daga na ɗaya fisabilillahi Allah na tuba ka mini aikin gafara" Cewar Iya dan ita ta ɗauka idan ya karanto hadisi na hamsin ɗin sai sun fi saurin samun mafita. Jabiru bai ma san abin da Iya take faɗa ba dan tun da ta zo duniya shi bai taɓa cin karo da tashin hankali mai lasisi kamar na yau ba, dan haka ma da Iya bata ba kanta wahala ba wajen masa bayani dan da ta yi haƙuri daga wurin alhadisil auwal ɗin a nan ya tsaya babu inda zai iya ɗarawa dan ƙasurgumin jahili ne. "Murtala a haɗa da murtala, murtala biyu kenan (Ashirin a haɗa da ashirin arba'in kenan), Zobiya a haɗa da zobiya, zobiya biyu kenan (Hamsin a haɗa da hamsin ɗari kenan)" Haka Iya ta shiga karantowa tana maimaitawa dan har a'uziyya take yi idan za ta faɗa saboda tsurewa da ta yi da gigicewa duk ta dibirbirce. Malam Tukur yana nan zaune a gefe kamar yajin ƙosai yana ganin abin al'ajabi da mamaki. Suna cikin wannan fargabar ne kawai sai suka ga micijin ya rabe a biyu ɓangare ɗaya inda da kan a wuyan Iya ɗaya ɓangaren inda da jela a wuyan Jabiru. Sai tashin hankalin ya fi na farko. Iya kuwa ganin abin ba na ƙare bane kuma gudun kar ta je ta rasa ranta da rana tsaka a hayar ADAIDAITA SAHU sai ta fara lallaɓawa ta tsugunna dan ta ji an ce idan miciji yana wuri ko ƙwaƙƙwaran motsi ba a yi bare kuma ita da yake kanannaɗe a wuyanta. A gaban Malam Tukur ta yi masauki dan tana ganin yanzu basu da wata mafita da ta wuce shi, tsugunnawarta ke d wuya Jabiru ma ya ɗaga nasa sanyayyun ƙafafun. Sai da ta je ta miƙa hannu biyu ta damƙo ƙafar Malam ta dama, Jabiru ya tsugunna kenan sai jelar micijin ta dawo gaban fuskarsa ta shafa wajen saitin idanunsa hakan ne ya sanya gabansa ya cigaba da bugawa gifgifgifgif dan tunaninsa ko makanta ce za ta same shi, shi ya sa jelar ta taɓa idanunsa tsabar tsoro bai san lokacin da ƙarshen wata waƙa da suke yinta suna yara ya kufce masa ya fito ba Iya sai ji ta yi ya ce "Malamai ku ji tsoron Allah za a kai akuya makaranta" Ya faɗa cikin ficewar hayyaci. " Ai ba akuya ba za a kai makaranta in saniya za a saka a cikin aji (Class) Sai ka yi da gaske yau za ka kuɓuta" Iya ta faɗa a zuciyarta tana da na sanin ɗakko tsohon nan da suka yi ga shi silar haka sun haɗu da jafa'in da basu san ranar fita daga ciki ba. Jabiru bai ankara ba sai jin jelar ta yi ta sauka a kan laɓɓan bakinsa lamarin da ya ƙara dagula masa lissafi. Cikin lallaɓawa ya samu shi ma ya zauna daga saitin gefen kakar tasa ya riƙo ɗaya ƙafar tsohon ta hagu da hannu biyu kamar yadda ya ga Iyar ta yi. "Dama ƴan magana sun ce duk wanda ya samu rana sai ya yi shanya, wato shi ma wannan tsohon mai mazaunai kamar na tsatstsewala dan ya ga muna neman taimakonsa amma ya yi biris tare da yin kunnen uwar shegu" Iya ta faɗa a zuciyarta. "Iya tun da ke kin kwana biyu ana murmurawa a duniyar ki saka hannu ki ɗaukewa marayan Allah miciji daga wuyansa, kin ga ni ɗan yaro ne" "Au Allah, to ba murmurawa ba ko gurgurawa aka yi ba zan kashe kaina a kan ka ba da kake maganar yaro ai ko mahaifa ƙarewa" Ta faɗa cikin muryar kuka. "Malam Tukur ka yi wa iyayenka ka cecemu daga wannan halin" Duka haɗa baki wajen faɗa. Kafin su rufe bakin su sai suka nemi micijin sama da ƙasa suka rasa kallon kallo aka shiga tsakanin jika da kakarsa. Amma kuma mai a take muryar da ta ziyar ce su damuwa ɗimuwa da tashin hankali ya maye gurbinta domin kuwa Malam Tukur ne ya koma tattabara, daga Iya har Jabiru sai ga su riƙe da ƙafar tattabara a maimakon ƙafar Malam Tukur da suka riƙe da hannu. "Mun shiga uku ni Ansai kenan dama ba da bil adama ba muke tare ba, lallai yau mun ɗakko ruwan dafa kanmu" Cewar Iya a zuciyarta tana son ta yi ƙarfin ɗauke hannuwanra dafa riƙon ƙafar tattabarar amma ta kasa samun ƙardun gwiwar hakan daga ilahirin jikinta domin kuwa jikinta karkarwa yake kamar mazari. "Wal fauru da gaggautawa fararun farilla ne, fasalun fiɗ ɗaharati fasali a kan tsarki" Iya ta faɗa a zuciyarta wajen ƙoƙarin ganin ta samu kamo addu'a domin tsira daga sharrin jinni tun da dai ga shi sun gani gamo suka yi. "Innalillahi mun yi angamo ni Jabiru ashe aljani ne" Ya faɗa a zuciyarsa lokaci guda gumi yana baibaye shi saboda yanzu wani sabon tashin hankali ya tsinci kansa wanda ya fi na lokacin da ya ga miciji a wuyansa saboda miciji har gwara shi idan ya sare ka to wani lokacin in aka maka magani kana samun salama amma su mutanen ɓoye su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba, idan ka shiga gonarsu sai su yi ta bibiya tare da addabar rayuwarka. Kuka gaba ɗayansu suke yi daga Iyar har Jabirun babu mai lallashin wani dan sai yanzu ne ma da suka yi ƙoƙarin janye hannayensu sai suka ji hannayen tamkar an haɗa sufagilu an damƙare ko alamar fita baya yi tamkar tif da taya. Kuka suke da magiya da neman ɗauki dan ita tattabarar ko motsi bata yi ba illa idanu da take ƙiftawa tana ɗan waige-waige da kanta. "Wayyo ni Ansai wallahi na yi da na sanin zuwa binni ba dan kuɗin Alhaji Audi da na ciyo bashin jinginar gona ba da a yau ba sai gobe ba za mu koma ƙauyenmu tun da abin ya fara da angamo da aljannu" Cewar Iya a zuciyarta tana yi wa tattabarar ƙuri da ido dan idan har ba gizo idanunta suke mata ba sai ta ga ma tattabarar kamar murmushi take yi tana haɗawa da harara har da fari da idanu. "Iya kuka fa tattabarar nan take kalli yadda hawaye suke zuba a idanunta kuma wallahi ni har ƙaran sheshshekar kukan nake ji" Jabiru ya faɗa cike da tashin hankali. "Kai Jabiru ittaƙillaha ka ji tsoron Allah, ina ganin abin da idona tana murmushi da harara har sa fari da ido amma ka ce kuka take" "Wallahi Iya kenan abin da kike gani da ban wanda nake gani da ban mun shiga uku mu kam" Iya dai bata ƙara samun bakin magana ba illa iyaka ta cigaba da rattabo duk addu'ar da ta zo bakinta. "What is your name" Suka tsinkayi magana daga bakin tattabarar" Iya ce ta juya ta kalli Jabiru, shi ma Jabiru juyawar ya yi ya kalleta, a take fitsarin da ya cika marar Jabiru tun lokacin da maciji yake wuyansa ya samu nasarar zubowa tsuuuu, Iya kuma tun lokacin da Malam Tukur ya rikiɗa ya zama tattabara wata iska ta taru ta cika mata ciki sai dai tana dannewa ne dan bata son ta saki tusar ya zamana ta yi laifi sai dai maganar da tattabarar ta yi ya sanya ta saki iskar tusar kaɗan ba da yawa ba ƙwiiiii tusar ta bada ƴar ƙara kaɗan tamkar an hura matse ƙaramar balo an sace ta kaɗan. "I say what is your name?" Tattabarar ta maimaita bakinta yana buɗewa alamar maganar kamar mutum. "Wallahi tallahi, billahil lazi huwar rahmanu babu abin da na sani a yaren nasara, ko bihim ban sani ba, kuma shi ma Jaburu bigibagiro ne babu abin da ya sani duk girman kan nan nashi da kike gani kan kwakwa ne babu karatu ko na allo bare na firimari(Primary) A mahammadiyar babu abin da ya sani a bokoko a wutar ma kan fanko ne haka nan yake sinkin fakitin" Iya ta faɗa hawaye yana ta zuba dan ta san tabbas rashin iya amsar da ake musu magana zai iya zama wata gagarumar matsala. "Maa is'muki? (Ya sunanki) Ta faɗa da larabci ba tare da ta fassara ba" "Iyi? Na'am, wallahi babu almuski a wajena kin ga ko madarar turare ƴar ɗure ban shafa ba da yake ma tafiyar babu shiri muka taho jiya" Iya da take ganin ta bada amsa ta faɗa tana haɗiyar yawu dakyar. "Min aina anta?( Daga ina kake? )" Ta faɗa lokacin da ta juya kai saitin Jabiru da ya fara ciccira idanu dan gaba ɗaya ma ya tsure bai san ya aka yi ita Iyar ta bada amsa ba ga shi babu damar ya ce ta fassara masa bai san cewa ita ma dukan iska bace cafar amsar ta yi ba wai ta amsa daidai bane. "Ka bada amsa dan ubanka kana ji ana tambayarka an maka shayi(Kaciya)" Iya da bata san ya aka yi maganar ta fito daga bakinta ba sai dai ta san cewar tsabar son Jabiru ne ya sanya ta faɗin hakan dan bata so a cutar da shi kuma dai ta san bai san amsar ba. "An mini shayi wallahi Mammadu wanzam ne ma ya mini da askarsa mai kaifi" Ya faɗa yana zare idanu da sauke wata ajiyar zuciya irin na sha dakyar ɗin nan. Kamar almara ko kuma a mafarki haka Iya da Jabiru suka ji hannayensu sun ɓanɓaru daga jikin tattabara. Iya Ansai ajiyar zuciya ta sauke mai lasisi dan ta ɗauka amsar da suka bayar ce ta cecesu hakan ya sanya ta ji kanta ya yi ɗingirigim. "Kai jama'a na ga annabi in na yi hali na gari, ashe dai ina jin yare da yawa ba tare da na sani ba, wallahi duk a tunanina ban da Hausa ta malam bahaushe kan nawa ba ya ja a kan komai ashe dai ni ma har ina jin da ban? Da farko na ɗauka bami nake amsawa ba sai da na amsawa Jaburu, ai yau Jaburu ya ƙara sanin amfanina tun da ga shi har wasu yaruka na yi wa mutanen ɓoye" Ta faɗa a ranta lokacin tana ƙiftawa Jabiru idanu alamar su ari na kare wato su gudu. Gira ya ɗaga mata alamar gamsuwa dan haka ganin tattabarar ta juya kai daga kallon su sai suka fara sanɗa domin ficewa daga kangon da suka kawo Malam Tukur su masa ƙwacen kuɗi sai kuma ga shi ido ya juye da mujiya. Jabiru ne ya fara tashi tsaye ita ma Iya ta lallaɓa ta miƙe za su gudu da yake Jabiru ne a hanyar da za ta fita da su to kuma shi ne a gaba. Sun juya kenan tattabarar ta juyo ganin abin da suke ta ɗaga ƙafa ɗaya ta sauke a bayan Iya, Iya da ke shirin aron na kare sai ta ji saukar wani abu a bayanta kamar ƙaya da wutsiyar ido ta kalla sai kuwa ta yi ara da tattabarar ta yi reran ta ɗaga ƙafa ɗaya daga hakan Iya ta fahimci ƙafar tattabarar ce a bayanta. "Na shigesu ni Ansai Jaburu yau kam za ka ga duniya rawar ƴan mata na gaba ya koma baya, dan yanzu zan maido da kai baya ni in koma gaba sai a yi a zubda yaran gona gutsi-gutsi su yi kuka, dan na ga kai akwai ya babu ne kakar wajen uba kana namiji amma sai dai ni tsohuwa in taimaka maka" Cewar Iya a zuciyarta. Jabiru ma kamar an ce ya waiga ya ga abin da tattabara ta yi wa Iya dan haka a raya a ransa cewar ba ,a a yi biyu babu ba gwara shi ya gudu dan da muguwar rawa gwara ƙin takawa, dan ma kar a yi ba wan ba ƙanin karatun ɗan koli. "Dama ni na san da wuya tsohon nan ya barmu mu tafi salin alin domin in maye ya manta uwar ɗa a zai yu ta manta ba. "Jaburu yau dai mun yj bonono rufe ƙofa da ɓarawo" Iya ta raya a ranta tana jin tashin hankali su da ba kowa gare su ba a garin amma sun jawowa kan su jangwam. "Tabbas akwai sauran rina a kaba, Iya sai haƙuri" Ya faɗa yana ɗaga ƙafa zai gudu dan ba zai tsaya shi ma a ɗora masa ƙafar ba. Iya ma nata ƙafafun ta ɗaga a nata tunanin su gudu tare amma ina tana motsawa tattabarar ta sauke ƙafar daga bayanta ta taɗe mata ƙafafu rigif Iya ta zube a ƙasa tamkar tsohon ginin da damuna ta tarar. Idanu ta zaro tana daga rufda cikin. "Wallahi Jaburu sai dai mu yi mutuwar kasko dan ba zan bari ka gudu ka barni ba" Ta faɗa tana saka hannu ta taɗo ƙafar Jabiru jif kake ji shi ma ya zube da azama ta miƙa hannuwa ta damƙo ƙafarsa ta riƙe gagam. "Wayyo Allah mu kuma da haka muka fara kuturu ya ga mai ƙyasbi" Jabiru ya faɗa a zuciyarsa da duk tunaninsa tattabarar ce ta yi nasarar kama shi bai san cewa Iya Ansai bace ta rafke shi. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay LITATTAFAN MARUBUCIYAR TAKU RAYUWAR MARYAMU GIDAN MIJINA ƳAN UBANCI ƳAR KANWATA SANADIN KISHIYA NE ALAKAR YARINTA BEELAL YAR ZAMAN WANKA MAI FARAR KAFA KARA'IN INNA DELU JALLI JOGA UNGOZOMA ƳAN ADAIDAITA SAHU TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/16, 14:00] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH *Shin kin tura naki screen short ɗin na SUBSCRIBE domin yin tafiyar da ke? Free pages yana dab da karewa idan kuma 5OO za ki bada acc no yana jiki* 🥰 Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page9️⃣ Kafin ƙiftawa da bismillah sai ga Jabiru da Iya wanda duka basu san ya aka yi ba sun dai gan su zaune dakaka a gaban tattabarar tana miƙo musu baki, sun kasa gane inda abin ya dosa dan gaba ɗaya sun sare. Taku ɗaya biyu tattabarar ta yi ta juya musu baya Jabiru da har yanzu bai cire ƙudurinsa na tafiya ba dan ya ci alwashin sai ya gudu in dai ya samu hali, dan ya ga babu alamar za a musu lamuni su bar wurin dan babu niyya ango ya kwana da wando. Ganin tattabarar ta basu baya ya fara jan mazaunai a wurin a hankali dan sai da ya ɗan faki idanun Iya da take ɗan mammatse hawaye dan lokacin da suka gan su zaune gaban tattabara da su ma kan su basu san yadda aka yi suka zo wurin a zaune ba dan su duka suna a rufda ciki ne, ya ga hannun Iya riƙe da ƙafarsa ɗaya hakan ne ya bashi tabbacin cewa da ya yi yinƙurin guduwa ba tattabara bace ta damƙo ƙafarsa ba kakarsa ce dan bata son ya tsere ya barta shi kuma yanzu ya ɗaura aniyar barin wurin ko ta halin ƙaƙa tun da yana ganin shi har yanzu yaro ne sabon jini yana da sauran shekaru a gaba idan Allah ya sa da kwanansa saɓanin Iya da ta sha duniyarta yana ganin ita ko yanzu ta koma ga Allah daidai ne. Da sauri da sauri yake jan mazaunan duk ya kukkuje a ƙurunƙusan tsakuwar da take wajen zafi da raɗaɗi yana ziyartarsa amma babu halin tashi tsaye saboda tsaro kai har da tsoro ma. Har ya je ƙofar ɗakin da suke ciki sai lokacin ne Iya ta farga da abin da yake faruwa, wata shala ya yi ya kifa ya ƙara kifawa sai kuwa ƙafa mai na ci ban baki ba a haka ya arce sai waje duk da da sai da suka shige can ciki amma da yake hankalinsa a tashe yake ba ganin inda yake saka ƙafarsa yake ba haka ya bazamo ya fito da mugun gudu yana haki har ya fito daga gidan tare da jan iska a hancinsa da ƙarfi. "Wash na shaƙi iskar ƴanci" Ya faɗa a ransa yana nufar adaidaita sahun nasa babu jira ya miƙa mazaunai zai zauna amma mai? A lokacin da Iya ta hango shi bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen sanar da tattabara dan bata ƙaunar Jabiru ya tafi ya barta dan haka ita ma sai ta ji tun da bai kalli tsufanta da ƙaunarta gare shi ba da ta siyar da ranta ta zauna to tabbas ita ma ba za ta ji nauyin faɗawa tattabarar ba. "Jabiru zai gudu, Jabiru ya gudu" Ta faɗa cike da tsoro. "Muna kallonsa kar ki ga na juya baya to ina da idanu a ƙeya" Tattabarar ta faɗa ko waiwayowa bata yiba. A can ƙofa kuwa Jabiru da ya shiga adaidaita sai kawai ya ji tamkar an fisgo shi daga cikin kamar a saman iska haka ya ji ana ta janshi da baya da baya. Iya tana zaune ta zubawa sarautar Allah, ido ta dai ga tattabarar bata fita ba, amma kuma ta kasa gane ya aka yi ta ce tana ganinsa ta bar shi ya tafi sai ta kasa natsuwa hankalinta a tashe dan tana ganin shikenan wataƙila a yi tsirenta. Tana zaman jiran tsammani a zuciyarta tana mamaki da al'ajabin halin da suka tsinci kansu. Kamar daga sama Iya ta fara hango Jabiru da ake janyo shi da baya da baya tun kafin ya shigo wurin an buga shi a bango ya fi a ƙirga dan hatta bayansa sai da ya ji allon bayansa tamkar zai rabe biyu sai da aka kawo shi gaban Iya jaɓar aka warɓar da shi sai ga shi a reran yana mayar da numfashi, Iya kuwa dakyar ta yi nasarar danne dariyar da take cin ta saboda dai ta ga Jabirun ya gudu ya barta da tafiyarsa ta san wataƙila har ya shiga adaidaitan amma ga shi salin alin an maido da shi aikin mutanen ɓoye ai sai su. Dama an ce in za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere da a ce ya tsaya ya taimaka mata sun gudu tare wataƙila su tsira tare amma yanzu ga shi babu wani ɓata lokaci sun zama ɗaya. Cikin taɓaɓɓan baki Jabiru ya kalli Iya tamkar ya saki ihu dan takaici ganin an maido da shi wannan kango da ya yi wa laƙabi da baƙin kango. "Da abu ya haɗo ka da mutanen ɓoye sau ɗaya gwara ya haɗo ka da bil adama sau dubu saboda shi bil adama in dambatuwa ma za ku sai ku dambatu ku kwashi ƴan kallo in bai fi ba ƙarfinka amma mutanen ɓoye sha'aninsu wuya ne da shi, yanzu ga shi dai tattabarar tana cikin kangon amma ni da na fita an maido da ni a saman iska a saman iskar ma da baya da baya ba tare da ina ganin gabana ba ya Allah ka fishshe mu aikin da na sani" Jabiru ya faɗa a ransa. A hankali tattabarar ta shiga juyowa sai dai me tana gama juyowa mai makon su ga tattabarar sai suka ga ta zama agwawa. A 360 Jabiru ya tashi zaune daga reran ɗin da yake dan dama tun da aka jefo shi bayansa ya bugu da wurin ko motsawa ya gagara yi amma yanzu ganin abin ba na ƙare bane ya miƙe babu shiri, suka liƙe a waje ɗaya tamkar kantuzar da aka cura ta haɗe. "Za ku shiga cikin rigar filon nan kafin ƙiftawa da bismillah matsawar ɗaya daga cikin ku ya bari ɗaya ya riga shi shigewa cikin rigar filon nan to fa zai samu an mayar masa da ƙafafunsa sun dawo wajen kansa ƙansa kuma ya koma ƙasa a haka zai cigaba da rayuwa har ranar barinsa duniya!" Suka tsinkayi muryar Malam Tukur ta cika cikin kangon har tana yin amsa kuwwa. Iya sau biyu tana yunƙurin tashi tana komawa daɓas saboda tsabagen fargaba da tsurewa ta san dai idan ba aljannun bane za su mayar da su kiyashi tayaya da girmansu goɗai-goɗai a ce su shige cikin rigar filon zanin gado, ai ta san dai ko kura ta rame ta fi ƙarfin a yagalgala namanta. Har rige-rige ake wajen ɗaukan rigar filon amma cikin rashin sa'a Jabiru ya riga yi Iya ɗaukan rigar ita ma cikin azama ta miƙa hannu ta karɓo suka riƙe su biyu kowa yana ja yana son ya riƙe gefen da zai bi ta wurin da zai shiga cikin rigar filon. Iya kallon rigar filon ta yi tana jin kamar ta saki kuka amma babu hali. "Minti ɗaya aka baku ... Tun kan a ƙarasa maganar kowanne ya miƙa kansa kawunansu suka gwaru da juna amma basu damu da raɗaɗin da ya ziyarce su na gwaren da suka yi ba dan kowanne au burinsa kawai ya shige cikin rigar filon. "Iya ki yi wa Allah da mazonsa ki bar ni in shige ni ne fa Jabirunki marayan Allah" Jabiru ya faɗa cikin raɗa-raɗa dan ya san matsawar su biyu za suke miƙa kansu cikin rigar filon to tabbas za a yi biyu babu domin kuwa babu kan wanda zai shiga bare a yi zancen shigewar mutum ciki har ƙafafunsa. Wata uwar harara Iy ta gallawa Jabiru jin furucinsa. "Baka da hankali Jaburu wato ga Iya kuka mai daɗin hawa, ni in haƙura wato kai ka shige a mayar mini da ƙafafuna saman kaina, kaina kuma a ƙasa wanda hakan zai sa kowa ma ya guje nu in ma ba a samu masu kai ni bakin ruwa sun ce ƴar ruwa ce ni ba, in ce nan nake roƙon ka ɗazu har ƙafarka na riƙe dan ka tallafa mini mini mu gudu tare mu tsira tare amma ka yi kunnenki uwar shegu ka tsere ka barni wai kai gaja sabon jini ko? Da yake Allah almusawwiru ne ba ya bacci gyangyaɗi ba ya kama shi sai ga shi cikin ruwan sanyi ƙarara an dawo da kai gani ga ka tif da taya to dan haka a nan ka ajiye maganar jika da kaka kowa ya yi ta kansa wato nafsi-nafsi" Ita ma ta faɗa cikin raɗar tana masa hararar ƙasan ido. Wani takaici ne ya turnuƙe Jabiru dan shi a nashi tunanin tun da shi yanzu yake cikin ganiyar shekarunsa ai sai ta tausaya masa ita kuma ta ci nata zamanin dan haka yana ganin ko cikinta aka ce za a mayar mata bayanta a maido ata da bayanta cikinta ba za ta damu ba dan yanzu ai a nashi ganin mutuwa ce kawai ta rage mata. Leɓansa ya danne da haƙori yana raya cewar sai ya shige ya barta in ya so idan ta ga ya shige ta haƙura dan ba zai bari su yi mutuwar kasko ba ko kuma a yi ba wan ba ƙanin karatun ɗan koli. A kusan tare suka ƙara kai kawunansu cikin rigar filon tsabar yadda kaka da jika suka kai kansu cikin rigar filon kuma rigar filon ta musu kaɗan sai kawai rigar filon ta fara yagewa daga kan. Ɗinke amma cikin su babu wanda ya saurara kowa ƙoƙarinsa ya ture kan ɗan uwansa ya samu nasa kan ya shige dan gudun kar hukuncin ya hau kansa. "Minti ɗaya aka baku amma kun gagara shigewa, duka jikinku har ƙafafunku za ku shige ni kuma zan rufe rigar filon sai in tafi daku bangon duniy... Tun kafin ya kai ƙarshen maganarsa daga Iya har Jabiru suka shiga rige-rigen fito daga kan nasu daga ciki dan jin maganar da ta girmi tunaninsu dan da a nasu tunanin kan nasu kawai za su saka a ciki amma yanzu sun ji wani sabon salo kiran sallah da usur, wato har ƙafafun su kuma bayan har ƙafafun ma ashe bangon duniya za a tafi da su a cikin rigar filo. "Turƙashi! Ana dara ga dare ya yi yanzu kenan burinmu na tuƙa arincaɓa a Kano ba zai cika ba haka za mu tafi bangon duniya ƙasar aljannu mu bar su Mamman da bashin jinginar gonar da muka karɓa basu ji ba basu gani ba, mun ga ta kanmu wai an rufe kwarto a cikin ɗakin mai gida" Cewar Iya a zuciyarta. "Wayyo Allahn mu shikenan mu kuma tamu ta ƙare, wato dai bngon duniya za a tafi da mu dan na san ko a garin gaɓa-gaɓa wannan runɗuma-runɗuman kan namu mai kama da bishiyar giginya ba zai shige ciki ba bare kuma har ƙafafunmu kamar wasu jarirai" Jabiru ya faɗa a zuciyarsa idanunsu suna cika da ƙwalla. "Bari ku ga aiki da cikawa" Agwawar nan ta faɗa tana nufo su, da sauri suka mayar da kan nasu garin cusa kai sai rigar filon ta rabe biyu saboda dama ta tsufa ga shi kuma an bata ƙarfi. Ganin ta zo gabansu ga shi sun yaga rigar filon ma babu inda za su shiga. "Allah na gode maka" Iya ta faɗa da ta ga rigar filon ta yage sai dai tumo da cewar idan mutum bai shiga rigar dilon ba hukunci da za a masa mai zafi ne sai gabanta ya shiga dakan lugude. A take wata iska ta taso ta ɗaga su Iya sama amma ba sosai ba sun dai bar ƙasa amma saman da aka yi da su ko tsawon mutum ba zai yi ba aka fara jujjuya su Iya bata yi ƙasa a gwiwa ba ta datsi tsakiyar suratul fatiha take karantawa da ƙarfi har sai da ta kai ƙarshen surar ta sake sakowa daga farkon sura tana faɗa Jabiru yana maimaitawa sun karanta fatihar kusan sau goma sannan ne fa didimm aka sake su daga saman suka faɗo ƙasa. Babu zato ba tsammani suka nemi agwagwa suka rasa , shirin guduwa suka fara yi sai dai sai da suka ɗauki hanya sai kawai suka ga agwagwar ta ƙara fitowa. Jabiru ko tsayawa bai yi ba ya falfala da mugun gudu Iya ta take masa baya a haka aka fara wasan tseran daga cikin kangon kafin ka ce kwabo Iya ta sha gaban Jabiru ta wuce shi dan ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba ya tsere ya barta ta shiga uku ga zaninta sai cincewa yake tana ɗaurawa daga cikin kangon zuwa wajen ta sake ɗaurin zane ya fi a ƙirga goshin nan nata kuwa duk ta gware a banza saboda gudun ceton rai. Tsabar ruɗewa da suka zo gaban napep ɗin a tare maimakon Iya ta shiga bayan napep ɗin ko kuma ta zauna a aljihun sai kawai ta kama napep ɗin tana ta ƙoƙarin hawa saman sa ƙafafunta suna zamewa sbodnsantsi ganin babu haza ta saka ta zauna a mazaunin direba kiɗime, shi ma Jabiru da yake a ruɗen yake ai kawai ya shiga baya ya zauna ƙwam yana hangen ƙofar kangon dan gudun kar ta kwana domin yana tsoron abin da ya faru da shi ɗazu ya faru da shi yanzu na mayar da shi cikin kangon da aka yi a saman iska. Iya duk zaman da ta yi da yake a ruɗe take jira take ta ji Jabiru ya ja napep ɗin sun tafi amma kuma sai ta ji ɗiff. "Jaburu ka ja mu san na yi mana kar a samu mashkila" Sai lokacin ma Jabirun ya lura da ashe a baya yake a zaune, a hanzarce ya taso daga bayan sai da ta ga ya zo zai shiga sannan ta gane katoɓarar da ta yi na zama a mazaunin direba ko uffan bata ce ba ta tashi ta koma bayan har tana tuntuɓe. Girrrrr Iya ta fara jin wani irin ƙara da napep ɗin yake da aka fara tafiya tamkar zai girgiɗe mata mazaunai sai da ta duba ta gane ashe ta cikin wasu tsakuwoyi da wani gini ya zube aka barbaza a wajen ya bi da napep ɗin kuma daɗin daɗawar ma ba ta hanyar da suka biyo suka bi ba kawai ya hausa wata hanyar ne. da yake ƙarshen unguwa ne wajen ma kamar jeji haka yake. "Jaburu, kai Jaburu" Jabiru ya tsinkayi muryar Iya tana rangaɗa masa kira, gabansa ne ya faɗi tashin hankalin da yake ciki ya linku dan duk tunaninsa cewa za ta yi ga aljanin nan ya fito a cikin napep ɗin da haka sai ya sha jinin jikinsa tare da jan wani uban birki dan ya gwammace ya fita daga napep ɗin ya gudu a ƙafa dan ba ya jin zai samu wani sauran ƙarfi da nutsuwar da har zai iya tuƙa napep. Iya kuma ganin ya ja birki wanda sanadin hakan ta yi gaba da ƙarfi dan kaɗan ya rage ta hantsila waje, sai da ta yi jarumtar damƙe ƙarfen napep ɗin wanda bakinta ya kusa arba da buguwa a jikin ƙarfen, dan da a ce bakinta ya yi masauki a jikin ƙarfen ba lallai a samu ragowar haƙora a ciki ba. So yake ya fita a guje sai dai yana tunanin mai zai je ya zo, kar ya tafi da gudu ya ƙarar da ƙarfinsa a gudun sai ya yi nisa ya tsinci aljanin a gabansa an yi ba a yi ba kenan wai rufin ƙofa da ɓarawo. "Jaburu yawwa dama rai ɗore na gani(Majamfari, wani ganye ne da ake tafasawa mai zazzaɓi ya turara jikinsa da shi) Ka ciro mini in mun je gida kar zazzaɓi ya rufe ni ake A'i ina Indo, ka san an ce riga kafi ya fi magani d... Tun kan ya gama jin abin da xa ta ce wani haushi ya turnuƙe shi a take ya game babu wani aljani da ya shigo napep ɗin dan haka ya warci napep ɗin da mugun gudun da ita ma Iyar ta yi zaton ko aljanin ya hango ya taho jin irin fisgar da ya yi wa napep ɗin. Dan haka bata yi wata-wata ba ta yi dibara ta ɗare can bayan napep ɗin(Boot) Ta shige ji kake jijif ƙaran faɗawarta, ƙafafunta ta ƙudundu ne ta totsu tare da kifa kanta ita a dole ta ɓuyowa aljani. Allah da ya taimake shi yana bin wata siririyar hanya sai ya ga sun dawo hanyar da suka bi wajen da Malam Tukur ya ce kwanar gidansa, ko kallo kwanar Jabiru bai yi ba gudun ma kar ya kalla ya yi arba da rundunar aljannu dan haka sai ya bi inda suka biyo. Iya da take baya jin napep ɗin ya tsaya cak an daina tafiya sai cikinta ya bada ƙukuluuuu domin bata san mai zai wakana ba, tana can ƙarshen bayan da ta shige ta cusa kanta. "Iya Ansai sai ki fito ki buɗe mana gidan" Ta ji muryar Jabiru. Shiru ta yi tana kissima abubuwa da yawa dan kar ra je ta fito ta ga cewar wata arangamar suka sake yi, dan yanzu Jabiru ya sar mata tun da har ya iya gudu ya bar ta a cikin kango yanzu sai take ji a ranta sai tana kaffa-kaffa da shi dan gudun ɓacin rana. "Ni miƙo mini mukullin in sha'awar zama adaidaitar kike" Kanta ta ɗago a hankali tana yin dogon wuya tamkar wata munafuka dan tabbatar da gaskiyar abin da yake faɗa, hango get ɗin gidan nasu da suka mallaka a jiya sai ta ji wani sanyi ya baibaye mata zuciya, haka ta fito tana cewa "Kai jama'a shiga matsatsi ina ya ga daɗi, Allah ka raba mu da matsin kabari" Ta faɗa lokacin da fito tana kallon Jabiru da ya yi wujiga -wujiga duk ya haɗa gumi sharkaf, wata dariya ce ta so kufce mata amma sai ta maje ta ce "Yanzu Jaburu sai ka dawo da mu gida, ko cinikin naira biyar bamu yi ba, haka kawai mun ƙone mai a banza da wofi ai da ka bari mun samu fasinja ko jaka biyu mun yi(400) Ma rage asara" Ta faɗa tana saka hannu a ɗan tofinta ta fito da mukullin gidan. Wani kallon kin samu matsala ya jefa mata, dan yana ganin ko ƙoƙarinsa bata gani ba da ya iya dawo da su gida bai yi ɓatan kai ba, sannan da irin jarumtar da ya yi wajen iya tuƙa napep ɗin duk da halin da yake ciki na tsoro da fargaba. " Allah ka bamu ikon haɗa kuɗin da muka bada jinginar gonar nan, Allah ka kawo mana kasuwa mai albarka albarkacin ma'aiki S.A.W kar damuna ta zagayo Alhaji Audu ya hana gonar nan" Iya da ta ji Jabiru ya ƙyaleta ta jero addu'ar tana mai ɗaga tafukan hannayenta sama. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: https://youtu.be/qEcb6XGVcBg?si=_yNQhtP6MlL7zcUy ƳAN ADAIDATA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRA *Shin kin tura naki screen short ɗin ki na SUBSCRIBE? Free pages yana dab da karewa idan kuma 5OO za ki bada akwai acc no a jiki* Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page1️⃣0️⃣ Bai ce mata uffan ba har zuwa lokacin, gidan ta buɗe musu ya shigar da napep ɗin ciki ya mayar da get ɗin ya rufe. "Ah ni Ansai kai ma wannan arincaɓa (Adaidaita sahu) Ka ga ta kanka yau ba dan kai ba da mun faɗawa ƴan garinmu, ko dai mu faɗawa aya zaƙinta" Cewar Iya tana shashshfa jikin adaidaitar. "Iya na ga fa duk tsaruwar gidan wannan amma babu abinci da za a ci da safe ma sai garin kwaki muka ci muka fita, ni dai yanzu ba zan ci gari ba" Ya faɗa yana wani kumbura baki. Salati Iyar ta kwasa tamkar wanda aka yi wani gagarumin abu har tana tafa hannuwa ta ce " Au Allah Jaburu ni Ansai yau na ga samun wuri tusar asuba, yanzu garin kwakin ne kake cewa ba za ka ci sau biyu ba, da a can gida ne ma kana can kana fama da ɗanyen tuwon Aliya da Maimuna amma yanzu shi ne har kake cewa baka ci garin da safe ba yanzu ka ƙara to ai sai ka bari sai ka fara cinikin arincaɓar tukunna mutumin da tun almuru muka fita amma muka ringa bilayi bamu samu fasinja ba daga ƙarshe muka ɗauki aljani ya bamu wuju-wuju sai yanzu muka dawo gida ba azahar ba la'asar ga magriba ta kawo kai amma maimakon ka ɗaura alwala ka kalli gabas ka gabatar da salloli sai ta abinci kake wato kai sarki ci kamar gara ko?" Ta gama rattabo maganar tana kallonsa da mamaki. Shi ma kallon nata yake dan ya ga sai ka ce wanda ya yi saɓo. "Yo Iya a can gida kika ce amma nan ai ba gida bane birni ne a birni wa yake cin abinci ƙasƙantacce da ban ce miki ba ma shinkafa da miyar dage-dage(Jar miya) Shi ne har kike ganin wautata. "Wannan kuma sai dai in kaina za ka kai a yanke sai ka auni shinkafar da miyar dage-dagen ka ci" Ta faɗa tana shigewa ta bar shi da baki a sake. Bayan sallar magriba suna zaune zugum babu mai cewa komai, Iya ta ce "Oh Allah ka tashi ƴar mai allo jikar mai siyar da tawada" Ta faɗa tana tashi ta fice daga falon Jabiru ya bi ta da kallo, ta jima sai gata ta dawo da kwano ta zauna ta ce "Bismillah ga marar imani na annabi ya ce ya ƙoshi" Ta faɗa tana kallon Jabiru da ya turɓune fuska tamkar ya saki kuka. "Wai ba da kai nake ba Jaburu baka zo mu ci garin nan ba sai ka je ulsa(Olsa) Ta kama ka in shiga uku, yo idan kana fama da cutar yunwa ni ina na kama na riƙe wa zai nemo kuɗin da za mu sauke wancan uban bashin jinginar gonar da muka libgawa kanmu" Ta faɗa lokacin da ta cika luday da garin ta shanye. "Ni fa ba shan garin nan zan yi ba, daga can wajen baki shigowa layin nan na ga wani mai siyar da gurasa ki bani in siyo kawai" Banza ta masa ta cigaba da shan garin sai da ta ji ta ƙoshi ta saki wata gyatsa tare da hamdala sannan ta zaro ɗari biyu ta miƙa masa. "Ai sai ka je ka siya ɗan baiwa haihuwar sa'a wallahi Jaburu ba dan son da nake maka ba kuma ina tsoron ɓatawa marayan Allah rai da wani abun bana yarda in maka shi ba" Shi bai tanka mata ba ya fita ya siyo ya zauna ya cinye dan cewa ta yi ba za ta ci ba. "Kai Jaburu kalli gidan na wutar tar-tar kamar da rana ga kayan kallo girke a falo amma muna zaune zugum kamar masu ciwon baki ko kuma masu zaman makokin mutuwa, bayan yanzu ko gidan makoki kowa sha'aninsa yake, ka tashi ka jona mana kallon mu ga su Ali Nuhu da Adamu Zango mana" "Wa ai in kin ganni a lahira kaini aka yi sai dai ke ki jona amma ni ba zan je garin kunnawa ba wuta ta jani in mutu a banza" "Au Allah wato ga Ansan mahaukata sai in yarda in taɓa wutar nepa in jona kallo bayan kaima mai jini a jika baka yarda ba sai ni da duk jinina ya zama tsohon jini kuma sauran-saura zan taɓa in je ta tsotse ɗan sauran da ya rage mini in baƙunci lahira ban shirya ba, to su sha zaman su kayan kallon" *WASHE GARI* Iya bakam ta yi babu wani baccin kirki da ya ga idanunta tana ta tunanin wayewar gari su fita nema, dan yanzu ji take duk duniya babu abin da take so da ƙauna fiye da adaidaita sahun nan saboda in ta tuna ɗinbin dukiyar da ta kashe kuma ma kuɗin jinginar gonar gado sai ta ji ko ƙuda yanzu ba ta ƙaunar ya taɓa. Sallah ta tashi ta yi da asuba ta zauna tana lazimi dan ta san k me za a yi ba zai tashi ba dan haka sai da gari ya yi shaaaa sanan Jabiru ya yi sallah abin da ya bashi mamaki shi ne yadda ya ga Iya da sanyin safiyar nan tana riƙe da tsumma mai lema tana ta faman goge adaidaitar. "Iya yau dai ko mafarki kika yi mai daɗi har kike mini aikin goge adaidaita... Wani kallo ta masa da ga sa ya kasa ƙarasa maganar da ya yi niyya ya tsaya yana jiran abin da za ta ce. "Jaburu kake gyara maganarka wallahi, arincaɓarmu dai ni yanzu baka ji yadda arincaɓar nan ya shiga raina ba bana ƙaunar ko ƙuda ya taɓa shi ka san kayan kuɗi, dan haka ma nake roƙon ka kake masa tuƙi na tsanaki ban da tuƙin ganganci dan bana so ko ƙwarzane ya same shi," "To shikenn tun da haka kika ce ko abin tsoro muka haɗu da shi a hankali zan ke tafiya" "Ka jika kai kuma da wani abu yo ai ina ana dara fidda uwa ake, ina maganar idan ba a ga komai ba kuma ma babu abin da zai ƙara hala mu da abin tsoro" Bai tanka mata ba ta ci gaba da gogewa tas suka shirya suka fito. "Yau kam mun yi sakko Iya" "Jaburu da sanyin safiya ake kama fara, na ga alama a garin nan idan muna tsayawa kallon ruwa kwaɗo ƙafa zai mana" Sun zo daidai wata bishiya sun tsaya za su sayi pure water sai suka ji wasu samari masu adaidaita sahu suna hirar cewa yanzu sun gaji da abubuwan da hukumar ƴan karota take fitowa da shi duk sun bi sun addabi ƴan adaidaita sahu. Wannan magana da suka ji shi Jabiru bai kawo komai ba sai bayan sun fara tafiya Iya ta ce "Wai ni Jaburu su waye ƴan farautar da na ji suna faɗar sun damu mutane ƴan arincaɓa? Kar fa mu je a yi watanda da kan mu dan ni sai na ji duk zaman garin ma ya fara gundurata ka san dama duk wani abu daga birni yake farawa kar a je a yi wuff da kanmu" "Iya ba wasu bane fa illa masu bada hannu a kan hanya, kuma ba ƴan farauta aka ce ba ƴan karota" "Yo ni ina na sani, kuma Allah na tuba amma su har a kan wani an basu aikin tare hanya sai su takura jama'a ai ni da zarar mun haɗa hanya da su indai ba bindiga gare su ba sai na musu tsiya" Ta faɗa tana gatsinan gefen hanci. Dariya Jabiru ya yi. "Iya Ansai nan fa ba gida bane" "Daji ne? Na ce daji ne" "A'ah wai kar ki taro abin da bashi bane ba hukuma wa zai ja da su" Baki ta taɓe bata ce komai ba a haka har suka hayo kan kwalta. "Iya kin ga fa wanda ake magana a kan su, baki ji ranar da muka zo garin nn ba mai adaidaita sahun yana cewa ƴan karota sun ƙaro wulaƙanci to ni ma a nan na gane su" "Ikon Allah wai dama waɗancan ne" "Eh" "Yo ce mini za ka yi masu ƙoƙarin haɗa mutane haɗari" "Kamar yaya Iya masu ƙoƙarin hanawa dai" "Yo tsakani da Allah, sai ka ga sun tara motoci da arincaɓa dodo-dodo har sai lokacin da suka ga dama za su ce a tafi ka ga kuwa yadda ake tafiya riiii ɗin wannan ai sai a samu haɗari" Banza ya mata, da yake an dakatar da su ne amma daga haka suna hango wani tsoho mai adaidaita da basu san mai ya yi ba an dakatar da shi a gefe wani ɗan karota sai masifa yake masa shi kuma yana ta hala hannu da alama haƙuri yake bayarwa. "Ka ga abin da nake faɗa maka mutanen nan basu da imani" "Na gani aradu Iya amma sai mun ramawa mutumin nan bari ki ga" Ya faɗa yana cije baki. Da yake su ne a ƙarshe a kan layin dan haka ana bada hannu sai ababen hawa suka tafi riiiii amma Jabiru sai ya tafi a hankali sai da suka wuce kawai wannan ɗayan da yake wa tsohon nan masifa Ya tsaye ya kafa wani ƙwamemen gulashi baƙi dama shi ma baƙin ne. "Allahu akbar kabiran kamar kumbo kamar kayanta, ji shi baƙi ya saka baƙin tabarau (Gilashi) Sai faman hura hanci yake da waninwuya kamar mariƙin lema, ga wani gemu ziyat kamar jelar tsatso" Cewar Iya a zuciyarta Jabiru ganin tamkar an sanar da jama'a abin da zai yi dan sai ya ga titin kamar an yi shara da yake ababen hawan duk sun yi gaba, yana zuwa a guje ya yi ciki da mutumin nan, Ɗan karota bai lura ba shi ala dole yana bakin aiki zai ita taka kowa son ransa kuma dama shi yana cikin waɗanda basani ba sabo, yana wannan tsayen ƙiƙam sai jin wani abu ya yi ya kwashe shi kafin ya ankara sai ya ji tamkar an yi sama da shi sai da ya yi da gaske ya zo da rubda ciki a saman gaban adaidaita sahun, da hannu biyu a dafe yana ciccira idanu amma shi bai san cewa adaidaita bane duk a tunaninsa ma tirela ce ta haɗu da tirela shi ne tsautsayi ya haɗa da shi babu wanda ya ankara da abin da ya faru daga cikin abokanan aikinsa hankalinsu yana wani waje sai dai mutane da suke can gefe suke hangowa daga cikin abokan aikin kuwa mutum ɗaya ne ya gani shi kuma abokin faɗansa ne basa jituwa dan haka da ya hangi abin da yake faruwa sai ya shiga dariya har da riƙe ciki a zuciyarsa yana fatan Allah ƙara. "Ya yi Jaburu rumfa sha shirgi, Jaburu dodon ƴan arincaɓa na Umaru bada kan ka a sare ka je gida ka ce ya faɗi, ɗan gidan Mamman jikan Ansatu ƙwararran mai tuƙi ku wanda suka riga ka koyar tuƙin tsoronka suke" Iya da abin da Jabiru ya yi ya birgeta ta shiga rattabo masa kiraru tamkar ta ari baki har wani sako ƙafa waje take irin na samari idan suna aljihun adaidaita da suke yi. Jabiru a take ya sake jin kansa ya masa wani gingiringim domin kirarin da Iyar ta masa ba ƙaramin zuga shi ta yi ba dan haka sai ya ƙara wutar gudun. "Jaburu bi da mu ta gidan sama dama bamu taɓa hawa ba" Cewar Iya tana nuna masa gada, Jabiru kallon gadar ya yi shi tsoro ma yake dan yana ganinta ta yi wani tudu da gangare kamar wani sirnane amma kuma dan kar ya bada kansa a wajen kakar tasa musamman da ya ji tana masa kirari. Gadar ya nufa gadan-gadan ya hau, ɗan karota kuwa yana kan gaban adaidatar santsin gilas ɗin jiki na gaban sai zamo da shi yake yana ƙara ƙanƙamewa ya damƙe bakin nan sai faman jan salati yake ga ruwan hawaye suna ta sintiri a kumatunsa tamkar babu gobe. Shi duk a tunaninsa tirela ce ta yi sama da shi ya faɗa samanta dan haka ma idanunsa a rufe suke ruff dan ya san muddin tirelar ta jefo da shi kwankwatsewa zai yi ba lallai ya shura da rai ba ma wataƙila sai an harhaɗa ƙasusuwansa waje ɗaya a binne ba tare da an masa wankan gawa ba sai dai a yayyafa ruwa dan a take ma tunanin wani abokinsu ko arba'in ba a masa ba da mutuwarsa kuma irin haka ce ta faru da shi wannan tunanin ya sanya hankalinsa ya ƙara kai wa ƙololuwa wajen tashi ya sare matuƙa yana jin bankwana da duniya baki ɗaya yana hailala da salatin annabi istigfari yana neman gafarar Allah yana jin ina ma a bashi dama ya koma gida kafin ya mutu ya nemi gafarar matarsa dan ko yau kafin ya fito sai da ya mata shegen duka ba tare da ta masa laifin komai ba ya san zaluntarta yake. "Ki yafe mini Falmata na san da alhakin ki ma ni kuma ga irin mutuwar da zan yi ta faɗowa daga saman tirela Allah sa ma a yayin faɗowata kar ta take ni ta murtsuke" Ya faɗa cikin tausayin kansa tare da tunanin makomarsa kasancewarsa namiji mai cin zalin iyalinsa, haka ya mayar da kansa ya kwantar yana ji ina ma ina ma. Jabiru kuwa gudu ya ƙurewa adaidaitar musamman da ya gan su ɗare-ɗare a saman gada sai ya ƙara jin kansa ya masa girma domin ya tabbatar yanzu ya ƙware a tuƙi tun da har yana tuƙi a kan gada wacce bai taɓa hawa ba. Iya wani daɗi ne ya lulluɓe ta musamman idan ta hango ababen hawan d suke can ƙasa suna warici sai ta ji tamkar a jirgin saman da yake yawo a sararin samaniya take. Haba Jaburu tamkar ka manta yadda ƴan ɗakko amarya suke kwabo a mashina a garinmu ai kama ta ya yi kake kwabo da mutumin nan mai ɗamara(Ɗan karota) Amma in bai jijjigu ba ba zai san darajar mutame ba ka ga an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo" Iya tana gama faɗin haka sai Jabiru ya fara kwana -kwana da adaidaitar, ɗa karota a take ya ji tamkar ana tirelar ce ta fara tashi dama a lokacin ne ya ci gaba da bankwana da duniya. Har lokacin idanunsa a rufe ruf sai da aka zo wajen round da yake Jabiru ba wani ƙwarewa ya yi ba sai kawai napep ɗin ya yi gajaf a take ɗan karota ya ji tamkar an fisgo shi an warɓar gefe a nanya faɗi da reran jama'a aka shiga kayya -kayya kafin a zo Jabiru ya ɗauki hanya a guje ya kwatse da sauran napep ɗin amma sai ya banbanta da su saboda kana ganinsa ka san tuƙin gamganci yake, motar ƴan karota da ya hango cike fal da ahalin karota shi ne abin da ya ɗaga masa hankali da shi da Iya, hanya suka ɗauka ɗoɗar yana gudu ya kutsa wata hanyar da ta sada shi da wata unguwar masu ƙaramin ƙarfi sai dai har lokacin yana hango motar karotan tana biye da su duk da akwai tazara sosai a tsakanin su. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: https://youtu.be/SmW933P9SlI?si=v8wQ0i6QtglW1gAG ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH *SHIN KIN TURA NAKI SCREEN SHORT ƊIN NAKI NA SUBSCRIBE? GARAƁASA CE FA DA SUBSCRIBE KAWAI ZA KI MORE DA KARATU A ƁAGAS, NA KUSA GAMA FREE PAGES 5OO NE IN BA ZA KI YI SUBSCRIBE NA YOUTUBE CHANEL BA* 😂😂😂😂😂 Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page1️⃣1️⃣ "Mun shiga uku Jaburu wannan rundunar da aka ciko mota da su tamkar mun yi kisan kan mutane ɗari, shikenan na san kuma tamu ta ƙare wallahi in suka kama mu kashin mu ya bushe sai dai rayuwar gidan kaso(Gidan yari) Daga can kuma a bindige mu har ƙiyama" Cewar Iya tana sakin kuka irin nasu na tsofaffi gaba ɗaya ido ya raina fata tsoro ya bayyana ƙarara daga ita har dodon ƴan arincaɓar. "Aradu yau mun ɗakko ruwan dafa kanmu, ni kuwa suna kama mu zan ce kece kika saka ni in kaɗe shi da na kaɗe shi kika ga adaidaitan ya warce shi sai kika ce in hau gidan sama kike mini kirari" Ya faɗa lokacin shi ma hawaye sun cika idanun sai yana runtsa idanun yake ganin gabansa. *ƳAN KAROTA* Tun da suka fahimci abin da yake faruwa a take aka sanar da shugabansu sai ya basu umarnin a bi bayan adaidaitan dan su a nasu tunanin ma mahaukaci ne dan in ba mahaukaci ba waye zai kaɗe mutum kuma ya tafi da mutum ɗin a saman abin hawa ko tsayawa babu kuma ma sun lura tuƙin ganganci yake kamar a bai iya tuƙa adaidaitar ba. Lokacin da suke bin su akwai tazara tsakanin su, dan haka ma ko da suka zo inda suka ga abokin aikin nasu ya faɗi a take suka tsaya suka ɗauke shi a sume tamkar matacce, shi ne kuma suka bi bayansu dan suna ganin idan suka tarki tafiya kai shi asibiti adaidaitan zai ɓace musu. *IYA DA JABIRU* Kuka suke wiwi a tare tamkar wanda aka musu mutuwa babu mai lallashin wani, layin da suka bi kwalta ce dan haka sun zo daidai wata bishiyar dalbejiya(Maina) Mai ya ƙare adaidaita ya tsaya cak! Kallon Jabiru Iya ta yi ta ce "To Jaburu mu yafi juna ko ta Allah za ta kasance" Ta faɗa tana masa kallon ƙarshe dan ta fara tunanin wataƙila su harbe su nan take. Da farko bai ce mata komai ba sai kuma ya ce "Ni dai fita zan yi in gudu a ƙafa... Tun kan ya kai ƙarshen maganar ta kalle shi wannan karon kuka mai sauti take yi hawaye nan kamar an kunna lalataccen famfo ta ce "Haba Jaburu arincaɓar fa(Adaidaita sahun)?"Wani kallo ya mata irin na ana ta kai wa yake ta kaya ya ce "Sai ki ɗauka ki ɗora a kan ki ki tafi da shi, in sun zo sai su haɗa da ke da adaidaita sahun su harbe" Ya faɗa yana saka ƙafa zai fice ta riƙo rigarsa ta ce "Yanzu Jaburu... Tun kan ta faɗa ya katse ta da cewa "Iya ki fito mu yi ta kan mu mutanen birnin nan babu tausayi ko imani a lamarinsu" "Amma Jabiru mu ɓoye arincaɓar mana kar mu tsira su tafi da ita" Fitowa ya yi da sauri ganin duk babu mutane ya ce ta fito suka shiga tura adaidaitar suka ganganra da ita daga kan kwalta wata kwana suka shiga da ita cikin sa a suka samu wani ƙaton bahu irin wanda ake ɗinka buhun simintin nan danyawa suka rufawa adaidaitar sai suka fito daga layin a guje suka nufi ɗaya layin na hannun damar su, ƙaran motar da suka jiyo ya basu tabbacin ƴan karotar ne, hanya biyu ce a layin dan haka cikin rikita Iya ta yi hagu Jabiru ya yi dama. *IYA* Miƙewa ta yi zimbet tana gudu amma dan kar a gane ta ita kaɗai a zargi wani abu ganin layin da jama'a maza da mata kowa yana sabgar gabansa sai ta ce. "Jama'a kowa ya yi ta kansa ƴan garkuwa da mutane ne a wancan layin suna tafiya d wanda tsautsayi ya rufta... Mutane jin haka sai kowa ya bazama dan dama ko sati ba a yi ba da ɗauke ƴar me unguwar har gida suka zo suka tafi da ita kuma har yau basu maido da ita ba. Gaba ɗaya sai layin ya hargitse aka shiga rafka gudun famfalaƙin ceton rai. Wani mai shago a guje ya fito daga shagonsa shagon da yake wa mutane tijara ga babu alfarmar bashi ko na naira biyar yana ta ƙafafa da shagon amma tau sai ga shi ko shagon bai rufe ba ya bazamo a guje, mai awarar da take soyawa a gaban shagon ta sauke ta juye man amma kaskon bai gama hucewa ba jin abin da Iya ta faɗa sai ta kinkimi mazubin kuɗinta man kuwa bata san ta tuntsurar da shi ba ta bi ta kan kwanon ta wuce a guje ko waiwaye babu. Mai shago na zuwa shi bai san ma ya aka yi ya sunkuya ya suri kaskin suyar awarar ba shi dai kawai ya ga ya kifa kaskon a suɗaɗaɗan kansa da ya sha askin ƙwal kwabo, duk da zafin da ya ziyarce shi amma a haka yake gudu ɗauke da kasko a kife a kansa. Wani mai baro da ya zo ɗaukan buhhunan gawayi da suke ajiye a jikin bishiyar maina (Dalbejiya) Sai wata tsohuwa makauniya tana gefe a zaune da kwanon silba a gabanta tana bara kwanon da ƴan canjinta a ciki, jin abin da Iya ta ce sai mai ɗaukan gawayin ya rikice dan ya san idan ƴan garkuwar suka ɗauke shi sun ɗauki banza dan daga shi har iyayensa basu da kulin da za a iyo famsarsa, hannu da ya miƙa a maimakon ya sauke a kan buhun gawayi sai ya sauke a kan makauniyar wannan ta zaune a kusa da bahhunan, wacce ta rikice da jin abin da aka ce ta suri kwanon bararta ya maƙala a hamata tana lalumen sandarta sai ji ta yi an sure ta an yi sama da ita har za ta yi ihun firgita da tsurewa sai ta ji an ajiye ta a cikin baro an shiga tura baron da ƙarfi. Ɗif ta yi da bakinta. "Allah na gode maka, da ka bani wanda zai tuƙani dan dama ni da nake makauniyar nan kafin in kai gida ma an ɗauke ni" Ta faɗa a zuciyarta tana jin daɗi tare da ƙanƙame kwanon bararta dan ta san dai cikin rashin sani Isa mai dako ya ɗora ta a baro ya tura a tunaninsa buhun gawayi ne bai damu da nauyin da ya ji ba ya wuce misali burinsa kawai ya je inda zai samu mafaka ba tare da ya yi arangama da masu garkuwa da mutane ba. Mai siyar da manja manjansa a cikin bokitin fanti babba a kan, yana rumfarsa sai kwalabe masu manjan wani yaro ya bashi ɗari biyu zai zuba masa a leda amma ji an ce masu garkuwa d mutane sun iyowa unguwar tsinke sai ya shiga cika kofin awon manjan yana sauyewa yaron a kansa, sai da ya zuba masa kofin wajen kofi goma sannan a rikice ya suri bokitin manjan maimakon ya ɗora ƙasan bokitin a kansa sai kawai ya kifa bokitin gaba ɗaya ya juye manjan a kansa da jikinsa a haka ya sheƙa gidansa a guje jiki jaɓa-jaɓa da manja. Yaron nan ma ganin an masa wanka da manja kuma mai manjan ya gudu sai ya juya ya tafi gida yana kuka. Iya kuwa da ita ake gudun mata sai tseren shiga gidaje suke da yaran su, wani tsoho yana zaune a kan tabarma zabgegen carbinsa yana maƙale a hannunsa sai sandarsa a gefe guda, da kwanon silbar da aka kawo masa ruwa sai hularsa danya cire ya ajiye . Yana ta mismis da baki. Babu abin da tsohon nan ya tsana sama da ƴan boko haram da duk wani abu da ya danganci bindiga da yake ƴan asalin garin maiduguri ne can Borno state tun da aka tsiri saka bama -bamai Allah ya kuɓuto da su suka yi hijira suka dawo Kano, hankalinsa yana tashi in ya ji ana batun masu garkuwa da mutane musamman da ya san shi talaka ne fitik babu cin yau babu na gobe, ya san muddin aka tafi da shi sai dai a kashe shi domin ba za a samu mai fanso sa ba. "Jama'ar musulmi, al'ummar annabi kowa ya yi ta kansa masu garkuwa da mutane sun wa wannan unguwa kutse suna wartar wanda tsautsayi ya rufta da shi" Tsohon yana zaune ya jiyo muryar Iya ta wawake baki tana faɗa, a kiɗime ya tashi ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi cike da tsoro ya wawuri silbar da ya shanye ruwa a tunaninsa hularsa ce haka ya kifa kwanon silbar a kansa ya miƙe yana ambaton Allah a ransa, carbin da ya ajiye ne ya yi wa ƙafarsa dabaibaiyi domin harɗe shi ya yi, da sauri ya tsugunna yana ambaton Lahaula wala ƙuwwata a zuciyarsa dan gaba ɗaya ta ɗafa hankalinsa ga shi ba gani yake ba, yana gama ware carbin daga ƙafarsa ya yi wurgi da shi gefe gabansa yana dukan tara-tara Iya ganin tsohon nan duk ya diririce dakyar ta danne dariyarta ta nufi wajensa tana faɗin "Malam ka taimaka mini da wajen fakewa hanya ce ta kawo wannan abu yake neman rutsawa da ni ga shi gidana da nisa kar a je su kwashe ni in shiga uku" Duk jawabin da take ko saurarenta bai yi ba burinsa shi ma ya shige gidan dan ba ya ma gane mau take faɗa. Ƙofar shiga gidan ya yi wa kutse kansa kife da ƙatuwar silbar da ya kifa a matsayin hula, har ya kusa shigewa ya tuna da tabarmar da yake zaune wacce ta amaryarsa ce ga ta masifaffiya dakyar dama ta ba shi ya san kuwa ko da a ce bom ne ya tashi ba zuwan pan garkuwa da mutane ba to tabbas idan ya shiga gidan nan babu tabarmar sai ya dawo ya ɗauka dan ya san halinta ba kanwar lasa bace ga shi ba ta da uzuri a kan komai. "Na rasa dalilin da ya saka ni auren Gajegala masifar matarnan da tada turnuƙinta ko lokacin muna gabas(Mai duguri) Bata saurara mini bare kuma yanzu na rasa ranar da za ta saduda" Ya faɗa a fili yana dawowa da ɗan gudu-gudu ya warci tabarmar bujukura wacce ko naɗewa bai yi ba saboda rashin nutsuwa ga shi yana jin tashin ƙaran takalman jama'a da suke gudu domin tsira daga tarkon ƴan bindiga masu garkuwa da mutane. "Yanzu a kan tabarmar nan babu tausayi babu tsoron Allah, sai ta dawo da ni " Ya faɗa lokacin da ya yayumo tsohuwar tabarmar da ta fara zazzarewa saboda tsufa amma a hakan gani take tamkar sabon kafet ta bashi. Iya da take tsaye daga gefe haushinsa ya ƙular da ita na banza da ya baiwa ajiyarta a kan neman taimakon mafaka da ta yi a wajensa saboda ta tsira kar Ƴan karota su ganta duk da ta san ba lallai ne ma sun ganta ba lokacin da take cikin adaidaita sahun bare har su shaidata sai dai shi marar gaskiya ko a cikin ruwa gumi yake, kuma dai tana ganin binciken su zai iya sawa su gano ta dan haka ta fi gane ta shige gidan mutane ta ɓuya idan ƙurar da ta ɗakko su ta lafa sai ta fito ta san na yi duk da tana ta tunanin Jabirunta amma ta san shi ma zai yi ƙoƙarin tserewa tun da dai maƙasudin abin da zai saka a gano su sun masa maɓoya babbar maɓoya ma kuwa wato adaidaita sahun su. Sai da ya kusa shigewa zaure gidan ta riga shi shigewa, yana zuwa zai wuce ta saka ƙafa ta danne tabarmar da ya yayumo ya ja ya ƙara ja amma ya ji an danne tabarmar ga shi da yake tsohuwa ce yana tsoron ya figeta ta yage a banza ya shiga uku ta ce sai ya biya ta tabarmar ga shi a wannan zamanin da ake ciki na Tinubu bashi da kuɗin tabarmar ba shi da dalilinsu dan haka sai ya fara ja a hankali tare da dawowa da baya ya ɗan sunkuya zai taɓa da hannunsa domin gano a inda matsalar da ta riƙe, sunkuyawar da ya yi Iya ta yi amfani da hannunta ƙwanƙwasa kwanon silbar kansa tamkar mai ƙwanƙwasa ƙofa, a kiɗime Malam ya tashi bai ma san lokacin da ya saki tabarmar ba dan shi a iya saninsa babu komai a kansa sai hula amma jin ƙaran silbar sai ya gigita shi dan a nasa tunanin masu garkuwa da mutanen ne suka ƙaraso za su tafi da shi. Har ya fara alamun bazama zai cikawa rigarsa iska tabarmar da ya saki ta faɗo masa da sauri cikin damuwa ya sake durƙusawa yana cewa "Dan Allah ko za ku tafi da ni ku mini lamuni in kai wa Gajegala tabarmarta dan na san in kun tafi da ni babu mai biyan kuɗin fansa idan kun gaji da ajiyata kun kashe ni Gajegala ba za ta yafe mini tabarmar nan ba dan a al'amuranta babu imani" Ya faɗa lokacin da ya tsugunna ya saki wani marayan kuka marar sauti jin an sake dukan wani abu a kansa ƙwal wanda a nasa tunanin ma ko bakin bindiga ne. "Ai babu lamuni tsakaninmu da kai tun da ka zo hannu har tabarmar ma za mu haɗa mu tafi... Cewar Iya cikin yin muryar gardi amma kuma ganin wulgawar motar Ƴan karota shi ne abin da ya dakatar da ita daga maganar da ta fara, shi kuma Malam tuni ya rikice jin abin da ta fara faɗa. "Malam mutanen ɓoyena ne suke son su ɗaga mana hankali, ni ma neman mafaka na zo zauren gidan naka amma ga tabarmar ka shige gida kar tsautsayi ya rufta da mu, dan na ji gaba ɗaya unguwar ta rukice sai kayya-kayya ake" Ta faɗa cikin daidaita asalin muryartar tare da yayumar tsahuwar tabarmar ta miƙa masa hannu yana karkarwa ya karɓa ko halin godiya bai samu yi mata ba, ya shige. "Ba dan na hangi wucewar motar da take farautar mu ba wallahi da sai ka gwammace kiɗa da karatu dan sai na baka wuju-wuju" Ta faɗa a ranta tana ɗan yin dogon kai ta hangi layin babu kowa sai motar da yake ta faman bilayi da alama ma basu fahimci abin da yake faruwa ba. *JABIRU* Tun da ya durfafi layin da ya bi babu abin da yake sai zabgar gudu dan hatta takalmansa ya watsar da su saboda haƙarsa ta cimma ruwa. Mutane ana ta masa kallon mahaukaci. "Da sannu za mu dawo kamar mahaukatan daga ni har ku" Ya faɗa a ransa lokacin da ya zo gifta wasu ƴan mata guda uku da suke tsayawa a saitin wata haɗaɗɗiyar mota wani mai camera yana ɗaukansu hoto sun raja'a an sha mayafi sai juyi ake. Takalmin su Jabiru ta kalla lokacin da ya tsagaita gudu, ganin tsinin takalmin ya yi yawa kowacce ɗogo-ɗogo kamar za ta kere katanga a tsayi su a dole an sha wankan an yi gayu sai wani ɗaga waya ake da ganin su ka san ƴan ƙarya ne kawai. "Kai wai lafiya za ka shigowa mutane unguwa kana gudu ko dai mahaukaci ne kai kowa ya yi ta kansa" Wani matashi da ya tara wata uwar suma suna zaune su huɗu a kan benci kowa yana danna waya kamar an musu wahayi da danna wayar ya faɗa yana aikawa Jabiru harara yana masa kallon ɗan ƙauye kidahumi, ganin sai da ya zo saitin su ya sunkuya yana haku tare da mayar da numfashi. Hannu Jabiru ya ɗaga yana nuna bayansa hanyar da ya biyo yana huci. "Wai uban meye ne kake nuna wa ko angamo ka yi?" Ɗayan ya faɗa yana tashi tsaye yana wani gyara wandonsa tiri kwata. "Yanzu ne na zo wucewa ta ɗaya kayin can wasu da suka mini kama da ƴan bindiga kasancewar suna kan machina kuma da bindigu rataye a jikin su fuskokin su a rufe na ji ɗaya yana waya yana cewa. "Oga bom uku aka saka a mabanbantan wurare, saura ƙiris su tashi fa zarar sun tashi za su iya tada unguwar nan gaba ɗaya har ma da wanda suke maƙotaka da su yana gama faɗar hakan suka gudu a machina ni kuna na fito daga maɓoya... Tun kan ya kai ƙarshen maganar samarin nan huɗu sun zabga a guje har ɗaya yana tuntuɓe, guda biyu suka yi karo da duka gabzu da junansu wajen yin gudun famfalaƙi, ɗaya kuwa kambas ɗin da yake ƙafarsa ya cire ɗaya, ɗayan kuma ya ga dai ba zai iya tsayawa cirewa ba dan jar ya ɓata lokacin dan ya san ba ƙaramin gudu bane a gabansa kafin ya bar unguwar dan gudu da tsira da ransa kar bom ya tashi. Mai tiri kwatan nan ashe dai dama wandon nr babu belt shi ya sa yake gyarawa ai yana fara gudun wandon ya silliɓe har sai da Jabiru ya hango baƙaƙen mazaunansa amma shi bai damu da mazaunansa da suke tangararai a bainar titi ba ya fi damuwa da ya gudu kar ya mutu a tashin bom. Da yake Jabirun ba a hankali ya yi maganar ba, ƴan matan nan ƴan ƙarya a kan kunnuwan su aka faɗa, mai ɗaukan hoto wurgi ya yi da camerar ɗaukan hoton ya cire takalama falfalfal sai ga shi ya zo ya gifta Jabiru ko neman ba a si da ƙarin bayani babu wanda ya yi kowa burinsa ya tsira da ransa da yake ƙasar ta zama sai addu'a koyaushe komai yana iya faruwa sai dai fatan Allah ya karemu da kariyarsa amin. Kallon sa Jabiru ya yi dan a yadda ya falfalo a guje ya fi kama da mahaukaci sabon kamu wanda ana kama wa sai dai a masa masauki a Dawanau. Ƴan matan nan kuwa su uku suna jin abin da Jabiru ya faɗa wa samarin nan sai su ma suka fara neman hanyar tsira dan dama su duka ƴaƴan gidan mutunci ne ƴaƴan malamai waɗanda ko mayafi iyayen su basa barinsu su yafa amma kuma sai su fito da hijabi daga gida idan sub fito sai su yafa mayafi ba tare da iyayen sun san wainar da suke toyawa ba, wacce take riƙe da ledar hijaban nasu bata ma san ta yi wurgi da ledar ba dan da a ce bom ya tashi da su a banza gwara su je gida da mayafi iyayen in tsire su za su yi ma su tsire dan wannan rana ita ake kira da yauma tubulas sara'ir wato ranar tonon asiri da yake ba a unguwar ma suke ba gidan ƙawar su ne suka zo. Haka suka zo riii suna gudun amma kamar masu tsallan kwaɗo saboda ɗamammen siket da kowacce take sanye da su wanda aka zige zip ɗin su dakyar saboda yadda ya ɗame musu jiki ga wannan takalmi kamar masu gudu yara ƴan koyon gudun tantanta wanda basu ƙware da gudu a tafiyar ba wanda tafiyar bata gama nuna ba amma dan karambani suke yin gudu. Wanda ba za su yi SUBSCRIBE ba idan suna bukatar littafi za su biya 5OO ta acc Faiza abubakar 9030283375 Opay TALLAH! TALLAH!!! TALLAH!!!💃💃💃 Hajiya shin kin gaji da siyan zannuwan gado suna koɗewa suna yin gashi? To ki garzayo wajen MAMAN AFRAH domin siyan masu inganci, babu kalar zannuwan gadon da babu a wajenmu. Idan kuma kin gaji da zama babu sana,a ne ki zo in baki sarin zannuwan gadon a farashi mai rahusa ki ɗora ribarki domin sana,ar ana samun alkairi sai kin gwada. Ina wacce ta gaji da siyan turarukan wuta masu ƙauri a garwashi, Ina da turaren wuta mai ƙamshi da daɗewa a ɗaki, idan kuma sana,ar turaren wutar kike ina bada farashin sari ina aikawa duk inda kike. Akwai humra mai musulmin ƙamshi da zaunawa a jiki, wacce nake wa laƙabi da sumar da mai gida don ƙamshi. Muna da Toilet cleaner in har toilet ɗinki ya dafe baya fita to ki gwada namu idan kika siya babu ruwan ki klin wajen wanki kumfa yake ya wanke bayi fesss ga ƙamshi da yake yi ɗaya za ki siya ko sari duk muna bayrwa. Akwai freshner mai ƙamshi, turaren wanka luquid soap, izal hypo, duk ina bayarwa sari a farashi mai rahusa. Ina wacce ta gaji da siyan shampoo da man kitso wanda bata ganin cigaba a gashin kanta da na ƴaƴanta? Gashin kamar gashin doki babu laushi sai tauri kina tajewa yana miki zafi, ki samawa gashinki da na yaranki mafita. Muna bayar da sari🥰 Akwai cotton material da lesuka da atamfofi, abaya, takalma, kayan yara siyan ɗaya ko sari. Tuntuɓe ni a wannn lambar 09013181851 [12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken nape) NA MAMAN AFRAH Page1️⃣2️⃣ Abin da suka kasa lura da shi, shi dai mai bada rahoton tashin bom wato Jabiru, tun fa da ya bada labarin mai yake wakana bai matsa daga inda yake ba yana nan sunkuye inda yake yana kallon duk abubuwan da suke wakana dariyar da takw cin sa ta kasa barinsa sai danneta yake abin da yake saka shi dariya kuwa yadda jama'a suke masa kallon mahaukaci lokacin da yake nasa gudun amma yanzu da suka ji dalilin gudun nasa sai su nasu gudun ma ya fi nasa, lallai mutane basa son mutuwa ita kuwa mutuwa a kullum kusanto mutum take! Sai dai in lokaci bai yi ba shi ya sa wanda ya tafi bai yi bai yi sauri ba wanda bai tafi ba kuma bai yi jinkiri ba tana nan tafi saboda duk mai rai mamaci ne. Ɗaya daga cikin su ce ta yi ƙarofin halin cire takalmin ta rungume a ƙirjinta tamkar wani zai ƙwace mata shi, saboda ta san sai da ta yi adashe da kuɗaɗen samarin da take yaudara ta siya takalmin dan kawai ta kece raini a cikin ƙawaye saboda ta ga shi suke yayi, abin da yake ba Jabiru dariya yadda siket ɗin nasu ya sauka har ƙasa duk dan gayu haka aka buɗe shi daga ƙasa, wannan dalilin ya sanya idan suna gudun sai iska take ɗaga siket ɗin tamkar filfilwar wasan yara da suke yi da takarda da kara da tsinke wacce idan suna gudu iska take kaɗawa haka siket ɗin ƴan matan suke ɗagawa filfilfil. "Na cikin gidaje ku fito dan tsira da rayukan ku an saka bom a unguwar nan ya kusa tashi ma, bom har uku ƴan bindiga suka saka" Ƴan matan nan suka ware murya suna faɗa dan su yi ceton sauran jama'a da suke cikin gida basu san abin da yake faruwa ba. Kafin kance kwabo sai ga mata suna tuttuɗowa daga cikin gidajen su tamkar tururuwa kowacce tana fitowa sai ta hangi ƴan matan nan sun miƙe layin suna zabgar gudu ga wasu maza can a gabansu wanda su ma gudun suke tamkar ana hankaɗa su wannan dalilin ne ya sanya daga sun fito sai su gane cewa inda mata da mazan ne suka yi shi ne wajen tsira shi ya sa kowacce ta fito sai ta ranƙaya habyar da ta ga sun yi. Wani mutumi da ya siyar da shanunsa guda biyu jiya ya zo gida da kuɗin yana cewa sai gobe zai kai banki dan haka sai ya ɗauki wata jaka ya saka kuɗaɗen a ciki yana tsaye a tsakar ɗaki matarsa tana kan gado tana zaune tana masa Allah da annabi a kan ya bata kuɗin cefane a cikin kuɗin yana ta masifa cewar ko naira biyar ba zai bayar ba ko dai ta siyi abincin ko kuma ta zauna da yunwa, dan shi babu mai saka shi ya taɓa kuɗinsa dan kuɗinsa na kayan lefen amaryarsa ne da zai aura, ya ajiye jakar a kan gado yana ta kalle kallen inda zai mata maɓoya a cikin ɗakin da yake jakar irin wacce ake goyawar nan ce mai kamar ta ƴan makaranta bai ankara ba sai ya ji ana faɗin an sanya bom a unguwa ya kusa tashi hakan ya sanya ya ruɗe wani tashin hankali ya ziyarce shi, matar ma hankalinta ne ya tashi dama bata da ɗa ko ɗaya tun da suka yi aure bata samu rabo ba wannan dalilin ne ma ya sanya yake mata wulaƙanci shi ne zai yi aure, tana shirin tashi tsaye domin guduwa ta tsira sai ji ta yi an kinkime ta an saɓa ta a baya, mamaki al'ajabi ne ya baibaye ta dan ta san dai mijinta ko karen hauka ne ya cije shi ba zai taimaka mata va sai dai ta yi ta kanta amma kuma ga shi har da ɗaukanta ya saɓa ta a baya hakan ya sanya ta fara godewa Allah a kan ko canji ne ya samu na lokaci guda yake son su tsira a tare don a nata zaton ta ɗauka guduwa zai yi ita ma ta yi ta kanta amma sai ta ji ya warce ta ya saɓa a baya ko nauyinta bai ji ba shi da ko a irin soyayyar nan ta ma'aurata bai taɓa ɗaukanta ba amma yau ga shi dalili mai sa a leƙa jikin sirika ya ɗaga ta cancaras ya goye a barsa. A ɓangaren miji kuwa bai san cewa matarsa ce ya goya ba da yake a kusa a ita ya ajiye jakar kuɗin a kan gado jin an ambaci tashin bom a lokaci ƙanƙani a ruɗe da kuɗinsa da kuma gudun kar ya mutu wani ya auri amaryar da ya ci burin aure wacce ya tafi ƙauyensu saboda ita ya siyar da kadararsa ta shanu dan su yi aure. Duk a tunaninsa jakar ce ya goya ba matarsa ba dan yadda matar ta maƙalƙale sai ya ɗaukan hannuwan jakar ne ya maƙala, ita kuma matar ganin ya goye ta sai tausayi irin na mata ya sanya wani son sa da ƙaunarsa ya ratsa ta ta miƙa hannu ta ɗaukar masa jakar ta a haka ya bazamo daga cikin gida niƙi-niƙe goye da matar da yake ma tana da jiki sosai hakan ya sanya yake gudun tinƙis-tinƙis ko takalmi babu ga shi daga shi sai singileti yana fitowa ya ga inda jama'a suke dirfafa sai gudu ake mata wasu ɗauke da yara sai kuka ɗiya suke ganin abin da basu taɓa gani ba shi ma a haka ya bi ayari tamkar ƴan gudun hijira sai tada ƙura ake a layin sai ka ce masu gudu a sahara. Wani gida da yake kallon gidan da mijin nan ya fito goye da matarsa, ita kuma matar gidan tana wanke -wanke ta ji ana cewa bom zai tashi kowa ya yi ta kansa, tsabar rikicewa kwandon wanke-wanken ta ɗauka ta kifa a kanta a tunaninta hijabinta ne a haka ta taho tana gudu kai a kife da ƙaton kwandon zuba kwanukan wanke-wanke tana fitowa ta bi bayan mijin nan da yake goye da matarsa, ta cikin tular kwandon take kallon yadda yake zandama gudu ko ƙaƙƙautawa babu shi ne abin da yake bata darita duk kuwa da halin da ake ciki na tashin hankali. Dan kowa a unguwar ya san mijin matar bashi da mutuncin ba ya ganin kan uwar kowa da gashi amma dai ita kanta ta san wuya ce in ji tsula ta sanya shi goyon matarsa kallon su take tana gudu kwandon yana kangal-kangal amma da yake bata ma san abin da ta kifo a kan nata ba da sai ta yi wa kanta dariya. Kowa ya bazamo har da masu himilin kayan wanki a ƙulle a zannuwa dan gudun kar su yi asarar kaya sai su kinkima su ɗora a kai suke zabga gudu, wata mata ta fito ɗauke da randar ƙasa wacce ake zuba ruwa yake sanyi ita kaɗai tana gudu tana faɗin "Gwara na rasa komai a akan na rasa randar nan saboda sanyinta ƙafata ƙafar randata" Ta ficr fuuuu. Jabiru ya take wa wasu miji da mata makafi baya da suka fito daga wani gida kowa riƙe da sandarsa amma a hakan mijin yana dafe da kafaɗar matar a haka suka fito, Jabiru da shegantaka ganin suna sauri basa gudu duj da kaancewar su makafi amma bai tausaya musu ba ya buɗe baki ya ce "Ya fara ƙara bom jama'a ya kusa tashi kowa ya ƙara ƙaimi wajen gudu kuna dai ganin an ce a film ɗin turawa wasu sai sun kusa tsira idan bom ya tashi sai ka ga ya tashi da su bayan taku kaɗan ne za su ƙara yi su tsira" Wannan jawabi nasa ya sanya makahon nan ɗauke hannunsa daga kafaɗar matarsa ya daina dogara sandar ita kanta sandar sai ya mata hawan doki yadda yara suke yi ya shiga zabgar gudu. Matar tasa ma gudun take tana kiran "Malam kana ta ina?" Amma Malam ba ya ma jin ta dan ya daɗe da bada tazara a tsakaninsa da ita yana can gaba yana biye da wata mata mai siyar da taliya da manja ta gama tace taliyar kenan sanarwar ta sauka a kunnuwanta haka ta ɗoro robar taliyar haɗe da kaskon manjan tana zabgar gudu abinta. Jabiru shi ne a ƙarshe sai kwasar dariya yake yana ta mamakin gudun mutuwar da jama'a suke ya tabbatar da a ce za su san ƙarya yake sai sun sumar da shi in ma sanadin dukan da za su taru su masa basu kashe sa ba, bare kuma in suka san ta'asar da ya aikata wa Ƴan karota suka biyo su shi da kakarsa ya tabbatar sai sun kai shi hannun ƴan karotan sun damƙa shi i ma mai za a masa na hukunci a masa. "Dan wulaƙanci Barira maimakon ta kinkimo tukunyar tuwon nan shi ne ta kamo hannun ƴaƴan suka gudu ita ce kaza uwar ƴaƴa, ta bar tukunyar a gida sai an je wurin yada zango yara suke kukan yunwa hallaw ga Badamasi uban nemo abinci sai in ƙara tafiya neman abin da za su ci bayan ana cikin halin tsoro ai kamata ya yi duk inda mutum zai je ya tafi da guzuri gudun ko ta kwana" Jabiru ya ji wata muryar mutum a bayansa yana gudu yana faɗa tamkar zai ari baki wai a kan matarsa Barira bata ɗakko tukunyar tuwo ba. Waiwaya wa ya yi ya ga mutumin wani ɗan lukuti ɗauke da wata tukunya lamba uku jikinta duk miyar kuka da ludan ɗaukan tuwon ma a cikin tukunyar da alama ɗumame ne a ciki tukunyar duk baƙin tukunya a jiki duk ya goga a jikin farin yadinsa amma bai damu ba shi kawai ta tuwon yake dan kar ya tafi nemo wani. "Haka kawai a zamanin Tinubun nan yadda masara da hatsi suke tsada kai hatta maggin miya tsadar da ya yi bai taɓa yin irinsa ba amma dan rashin tausayi tana ganin ba ita ta nemo ba ta gudo ta bar ɗumamen a gida bom ya tashi a unguwar tukunyar ta yi ƙurmus a can inda muka je kuma a saka ni salati da salallami na nemo wani abin da yara zasu ci" Ya faɗa yana yi yana ɗan gudu. "Hmmm! Kai ba tsuntsu mai wayo ba to ai tsuntsu mai wayon ma ta dabara ake kama shi, in dai tukunya ce da kan ka za ka jefar da ita yanzu nemowar da ka ƙi dai sai ka sake nemowa tun da kai Allah ya ɗorawa nemowar ba matarka ba da ta kwashi ƴaƴan ma ai ta yi ƙoƙari dan wauta irin taka da kuma ƙiwiya sai a bar ɗan mutun a ɗakko tukunyar tuwo?" Jabiru ya faɗa a ransa yana ɗan rage gudun da yake sai da mutumin nan ya wuce shi ya bashi ƴar tazara ya wangame baki ya ce "Jama'a a ƙara wuta dai a ƙara mai wajen gudu ga wani ƙara can daga nesa hayaƙi yana tasowa da alama ɗaya daga cikin bom ɗin ya tashi" Kowa da yake ta kansa yake babu wanda ya samu damar waiwayowa bare ya ga da gaske hayaƙin ne yake tashi ko kuma su lura cewar basu ji wani ƙaran tashin bom ba duk sai suka danganta hakan da rashin nutsuwar da suke ciki. Mutumin nan mijin Barira wanda yake ɗauke da tukunyar tuwon ɗumame jin gudu sosai yana neman gagararsa sai ya yi wurgi da tukunyar tuwon ya fara sheƙa gudun a ransa yana cewa. "Haba sai yanzu na ji ina gudu sosai ashe dai tukunyar nan ce take hana ni rawar gaban hantsi" Jabiru kan dariya sai da ya kasa gudun ma ya dakata sai da dariyar ta tsagaita sannan ya daure ya ci gaba yana zuwa inda mutumin ya yi wurgi da tukunyar sai ya ga tukunyar da ban, murfin da ban ludan ma ya yi nasa wuri sai tuwon da yake ta masifa a kansa ashe ba wani tuwon kirki bane duka guda huɗu ne wato yankan ɗumamen huɗu wanda bai fi ma yaran su cinye lokaci guda basu ƙoshi ba tun da yankan ma ƙanana ne. Sai da ya tabbatar jama'ar unguwar nan su yi nisa ya dawo wani shago da mai shi ya bazama ya bari a buɗe ya ɗauki cincin da lemo a frige mai sanyi ya ci ya yi hani'an ya kwashi wani cincin ɗin ya zuba a aljihu da lemo roba ɗaya ya ce "Oh ni ko ina Iya Ansai ta buya ita kuma na san dai yanzu yadda kawo ya bazama babu wani mai bada labari idan an tambaya wato idan ƴan karota sun zo sun ce basu ga wasu masu napep sun shigo unguwar ba, kin ga babu mai cewa ya ga wani saurayi ko wata tsohuwa ta zo da alamar rashin gaskiya a tare da ita ko ma ƴa unguwar su ce basu yarda da su ba bare har a shiga bincin a unguwar a gano inda muka ɓoye adaidaitar mu yanzu dai cincin da lemo ba sata na yi ba wale-wale aka yi fa su ba adana ba" Ya faɗa a ransa yana kallon shagon tare da fashewa da dariya a fili ya ce "Kaico ni Jabiru jikan Iya Ansai yanzu da gari banza na zo na ce ko alewar naira biyar a bani a shagon nan sadaka sai an kai rana za a bani in ma ba a mini korar kare ba, amma sai ga shi an bar shagon a buɗe na shiga ciki ina wadaƙa har da shan lemo da cincin kai Allah dai ya biya" Ya faɗa yana fitowa daga shagon ya samu wani kango ya buya cike da tsoron abin da ya faru jiya a kango da su da mutanen ɓoye amma haka ya daure ya zauna a ciki sai da magriba ya fito domin zuwa ya samu kakarsa su san na yi. "Amma kuwa wannan an yi ɗan iskan saurayi to mene ne rubarsa da ya yi hakan? A she dai ƙarya yake babu wani bom haka kawai ya bazama mutane da yara kowa yake gudun famfalaƙi, hatta jama'an tsaro da aka sanar da su suka kasa zuwa unguwar kowa yana tsoron ya zo abu ya ritsa da shi" Cewar wasu samari da suke tsaye a layin da Jabiru ya baza su ya zo wucewa yaji ana ta batun abin da ya faru. "Wannan an yi ja'irin yaro haka kawai ya tafa ha kulan jama'a ina barci na ji matata tana tashina a kiɗime cikin gagan barcin nan na suri sandata muka fito ko gama warewa ban yi ba, kai da abu ya yi abu sai gani na hau saman sandar tamkar wani ƙaramin yaro wato ina dokin kara irin na yara da sandar bara ta" Cewar makahon nan da suke magana da wani mutum. "Yo Malam Abashe ba har gwara kai ba ni fa nan na saɓi matata a bayan nan nawa wallahi duk tunanina jakar kuɗina ce ta goya wai ashe ita ce kuma sabo da rashin tausayi da imani irin nata sai ta yi lifet a bayana nake zabga gudu da su tumemiyar mace a bayana ga tana ɗauke da jaka duk ni kaɗai, wallahi bayan nan nawa kamar na ɗauki buhun dusa biyar haka nake jin yana ciwo ko ina amsawa yake, kawai dan takaici sai da muka je inda aka yada zangon nan zan sakko jakata sai na ji tana min sannu goɗai-goɗai ta sakko ni mamaki da al'ajabi ya hana ni maganaa nan na tabbatar cewa tsoro da firgita babu abin da ba ya sakawa kalli bayana fa, Allah sa kar ya yi kanta" Ya faɗa yana juya masa bayansa. "Yo da wane idon zan gani, haba dai sai ka ce wanda ya goyi raƙuma ko goɗiya? Tabarakallah yo ai ka samu lada ga ladan tseratar da iyalinka ga ladan goyo" Malam makaho ya faɗa yana ƴar dariya. Takaici ne ya hana shi magana wai ya samu lada, haka Jabiru ya zo sumi-sumi ya fice ta gabansu babu wanda ya lura da shi dan ko ina ma sai hayaniya suke tun da a ransu basu taɓa saka cewa wanda ya yi abin zai iya dawowa unguwar ba ma, tun fa sun gano ƙarya ya shirga musu tun da dai ko hayaƙin toyin ƙone shara babu bare wani hayaƙin tashin bom. Iya ma ganin duhun magriba ta saɗaɗo ta buɗe ƙofar gidan ta fito dan tun da Malam ya shige gidan nan ko ƙwaƙƙwaran motsi bata ji ba bare ta sanya rai za su fito ta tabbatar yau ko sallah sai dai su harhaɗa. Wajen napep ɗin ta nufa tana ta addu'ar Allah sa Jabiru bai yi wauta sun kama shi ba ko su tafi da napep ɗin nasu baki ɗaya. Dan haka tana dosar wajen sai ta ga napep ɗin yana nan yadda suka bar shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ta lallaɓa ta shige bayan adaidaitar ta zauna sai da ya zauna a fili ta ce "Ni ƴar nan ina zan gano Jabiru?" "Gani" Cewar Jabiru da yake zaune a mazaunin direba sai dai ya sunkuya shi ya sa Iya bata lura da shi ba da ta shigo, da farko sai da ta tsorata i dai jin muryarsa sai ta ji wani sanyi da daɗi, haka suka yace buhun suka ka bar wajen tare da bin kwaltar suka koma ta inda suka biyo dan in suka luluƙa Jabiru ba zai gane hanyar gida ba, dan haka suka saddaƙar suna addu'ar Allah ya sanya saɓani da su da ƴan karota a haka suka samu Allah ya taimake su suka koma gida. Nan Jabiru ya bata cincin da lemo tana sha suna hira suna dariya kowa yana bada labarin abubuwan da suka faru Iya kan dariya har da runtsirawa. "Gaskiya Jaburu ka cika jikana aradu" Ta faɗa tana ƙara yin dariyar sai da ta cinye cincin da lemon suka yi sallah kowa ya watsa ruwa. "Oh ni Ansai yau ma haka muka ƙare gallafirin mu babu cinikin ko kwabo sai mai da muka sheƙe sai dai tun da mun kuɓuta daga hannun mutanen can ai shikenan" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta kwanta bacci. *ƳAN KAROTA* Tun da suka bi bayan su Iya haka suka sha walgigi amma basu ga ko mai kama da su ba dama Allah bai sa ko lambar jikin napep ɗin sun gani ba bare har su samu wata hujja wajen neman su ga shi kuma basu gan su da idanunsu ba shi kansa wanda suka kaɗe ɗin da ya farfaɗo bai gane komai ba dan sai ya zama kamar wani zautacce ce ma dakyar dai ya dawo daidai. 09013181851 [12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 Page1️⃣3️⃣ Washe gari ko da Iya ta shirya Jabiru sai cewa ya yi jikinsa duk ciwo yake na gudun da ya sha yi jiya dan haka yau sai dai su huta. "Qur'ani baka isa ba Jaburu wanda ya fito nema ina shi ina hutu abin ma ya zama rashin hankali wallahi, haka kawai ka san bashi na ciwo muka taho birnin nan dan ganin na cika maka burinka amma maimakon ka zage dantse ka nema sai ka ce wai jikinka yana ciwo ni ma ai in gudun ne na yi ko dan ni jikin ƙarfe gare ni ba na tsoka ba" Cewar Iya tana tsaye riƙe da tsantsa shi kuma yana kwance ya yi ɗai-ɗai a kan gado. "Ni dai ban ce ba amma dai ai kya bari mu huta ko yau da gobe ne jibi sai mu fita m... "Wallahi ka yi tsalala kamar shayi ana zaune ƙalaw har za mu kwana biyu bamu fita nema ba kamar wasu wanda aka yi wa baki wato kai gaka ɗan daɗi gida ka samu kuntsumemiyar katifa a gado in aka barka sai ka wuni kana baccin asara, to ka tashi fita babu fashi" Ta faɗa tana ɗaka masa duka a ƙwabri da sauri ya tashi yana kumbura baki ya fito haka ya yi alwala ya yi sallarsa. "Wai nan sallah ce aka yi gari ya waye rangararai ai wannan sallar ƙadangari ce ai su ne suke ɗaga kai da hantsi" Ta faɗa tana taɓe baki. "Wai ya za a yi da abinci ne Iya?" "Ban sani ba wato kai ka fi so muke ƙwamushe ɗan kuɗin hannun namu da Allah ya sanya yaron nan Ɗan harƙalla ya bamu sai mun kashe mu zo mu tsugunna bayan kasuwar arincaɓar har yau bamu san ta ina take ci ba, ko ficika bamu yi ba wataƙila ma yau sai an saka mata mai" "Haba Iya ci ai ya zama dole kin san dai ciki manta kyautar jiya gare shi, ki siya mana ko waina ce in mun fita " To na ji, amma garin masara zan auno yau ake tuƙa tuwo ina dalili ina ɗan mafari zan ke cacar kuɗi ni ba gwabnati ba" Ta faɗa tana shigewa bayi ta yi wanka ta fito. Tun da ta shirya take fama fa Jabiru a kan ya yi wanka amma ya ƙi, haka ya ɗauki mai ya lallafka sai sheƙi yake tamkar an zuwar da man gyaɗa kwalba guda a kansa. Haka suka fita ta kulle gidan tana ta mitar zai ke kashe musu kasuwa in ba ya wanka saboda za a ke ji yana warin dauɗa. Bayan sun ci waina da ƙosai a wajen wata mata da take soyawa suka tafi suka ringa bilayi Gidan mai suka je suka sha mai na dubu ɗaya, Iya tana ta faman mita a kan kuɗin da ta bayar amma Jabiru ya yi kunnen uwar shegu da ita haka ta gaji da mitar ta yi shiru. Ranar ma haka suka wuni amma babu fasinjan da suka samu ga suna ɗan tsoro duk inda za su kutsa saboda kar a je ƴan karota su gano su, ganin dai babu ciniki gudun shanyewar mai a banza sai Iya ta ce su samu inuwa su zauna ai rabon mutum ba ya wuce shi indai suna da rabo to fasinja zai zo har inda suke. Har la'asar babu wanda ya ɗaga musu hannu ga shi tun wainar safe basu ci komai ba sallah ma a wajen Iya ta yi Jabiru ne ya je masallacin unguwar ya yi sallah ya ɗakko mata ruwan ita ma ta yi. Suna zaune a cikin napep ɗin bacci ya yi awongaba da Iya ta jingina sai sakin munshari take. Jabiru da yake zaune kansa sunkuye kamar an ce ta ɗago kai ya hango wata budurwa tsaleliya ƴar duma duma, tana tafiya hannun nan a maƙale tamkar lauje sai wani hura hanci take. Tun da ya kafe ta da ido daga nesa har ta zo gifta adaidaitan bai ɗauke idanunsa ba ƙurrr yake kallonta ko ƙiftawa ba ya yi, ita kuwa tana ankare da shi amma sai ta yi kamar ma ba a yi ruwansa a wajen ba. "Malam tafiya za ka yi ne?" Ta masa tambayar a yangance tana farfara idanu Jabiru da shegen son mata ya ga matar birni a take ya fara kaɗa kai kamar ƙadangare dan da ta yi magana sai ya ji tamkar an watsa masa ruwa mai ƙanƙara, domin abu ne ya haɗe masa goma da ashirin ga daɗin sautin ta ga kuma abinka da ba a saban ba yau sun samu fasinja. "Ko ba tafiya za ka yi bane?" Ta jefa masa tambayar lokacin da ta ɗan dawo da baya har tana ɗan wani karkata kai gefe. Wannan karon har wata in ina ya ji ta same shi. "Eh, eh, eh tafiya zan yi" "Ohk " Ta ce tana ƙoƙarin shiga bayan, Jabiru kan kallonta sai da ƙeyarsa ta amsa saboda ƙoƙarin waiwaye ba komai yake birge shi ba sai yadda bakinta ya sha jambaki da lips stick sai sheƙi yake. Tana shiga babu wani dogon tunanin tambayarta inda zai kai ta sai kawai ya saka mukulli ta tashi adaidaitar ga shi babu wata nutsuwa a tare da shi duk ya susuce dan shi a take sai ya ji ya kamu da son budurwar i dai yadda ya ga yanayinta ya san ko a ƙafa aka ɗaura mata shi sai ta kunce ta jefar. Riiii ya warce adaidaitar ya yi wata uwar kwanar da ta sanya Iya da take bacci ƙafarta ɗaya a waje ɗaya a ciki jin za ta wuntsulo cikin bacci ta ji hakan sai ta ɗauka ma ko faɗa ne ya tashi tsakanin fulani da hausawa a ƙauyen su wani ya hankaɗa ta dan ita a cikin bacci take kuma ta ma manta cewar a Kano suke, yanzu ba a ƙauye ba bare har ta tuno zaune take a cikin adaidaita sahu. Jabiru da yake ta Allah, Allah ya nuna ƙwarewarsa wajen tuƙi kar budurwar ta ce ta fasa hawa ta sauka ga shi yana jin shauƙin ganinta duk ƙamshin turarenta ya buɗaɗe napep ɗin, kwata-kwata ya ma manta da wata Iya tana bacci bare har ya tashe ta ta gyara zamanta duk kuwa da tana sakin munshari, ita kuma budurwar ko da ta shiga tana ɗan danna waya bata ma lura da Iya ba bare har ta yi la'akari da munsharinta, Iya da buɗe idanunta kanta ya sauka a saman napep ɗin kawai sai ta gane bacci take dan ta tuna a inda take, da sauri ta maido ƙafarta tana rafka salati ta rirriƙe napep ɗin da hannu biyu. "Lahaula wala ƙuwwata illah billah, Jaburu amma yau na ƙara tabbatar da cewa albasa bata yi halin ruwa ba, idan ubanka Umaru ne ya mini wannan ƙanƙanci dama ai na san a rina an saci zanen mahaukaciya, wato kai ga mai arincaɓa ko abin nema ya samu, ni Ansai gamu ga Allah ɓarawo a hannun mata" Cewar Iya da ta takarkare tana faɗa cike da faɗa ganin kamar tana magana da bango. "Wai dan matar ubanka wacce bai aura ba Jaburu ba magana nake maka ba, ji yadda ka sha wata uwar kwana sai ka ce za ka karya kan arincaɓar? Kana ganin ƙafata a waje amma ko ka ce in tashi in mayar da ƙafar ciki son ka guntule mini ƙafa in dawo yawo da sanda to ahir ɗinka wallahi ko so kake ka kashe ni ka ci gadon arincaɓar da kuɗinta ma bamu biya ba kai da ba wani ƙwa... Bata ƙarasa ba Jabiru da sai yanzu ma ya lura da masifar da take faman masa ya ji tana neman masa ɓaran-ɓaramar cewar bai ƙware a tuƙin ba ta sanya ƴar fasinjar da suka samu su rasa kuma shi ba rasa ta ɗin ne damuwarsa ba shi bai gaji da ganinta ba. Signa yake mata a kan ta yi shiru kar ta jiƙa musu aiki, ita kuma budurwar tun da ta lura da Iya sai ta ji duk ta cika mata kunne da ɓaɓatu, ta mudubi Jabiru ya lura da yatsina fuskar da budurwar take tana yi wa Iya kallon tara saura kwata Iya kuwa da bata san wainar da ake toyawa ba tana birinkaɗuwarta sai ta ce "Uban kuturu ma ya yi kaɗan bare na makaho ɗan banza, ni za ka watsawa ƙasa a ido har ka isa ina magana kake nuna in yi shiru wato ga Ansan mahaukata ni da bakina a dake ni a hana ni kuka... Kansa ya mayar gefe yake mata nuni da baya. Wata harara ta aika masa tare da juyawa ta kalli bayan dan tunaninta cewa yake ta koma baya ta zauna. Wani irin washe baki ta yi tamkar ba ita take ta faman faɗa ba yanzu ta ce "Ayyo Jaburu ai sai ka ce Iya muna da baƙuwa, yo ni ai na ɗakko shashancinka ne jiran jirgi a tashar mota ka ja arincaɓar baka tashe ni bawan Allah ashe dai fasinja muka samu a'ah wallahi sago abin sai sambarka" Ta faɗa tana gyara zama bakin nan ya ƙi rufuwa saboda murna. Jabiru ma daddagewa ya yi ya washe haƙoransa da basa samun wanki ya ci gaba da tuƙi ba tare fa ya tambayi budurwar inda za a kai ta ba ita ma kuma bata ce ga inda za a kai ta ba. "Ɗiyata ina wuni, ya gida?" Iya ta faɗa dan ji take tamkar an saka ta a a janna dan daɗi sosai take jin farin cikin samun fasinjan da suka yi, dan har ta fara ganin sun kusa haɗa kuɗin bashin da suka ciyo tun da Allah ya tarfawa garin su nono sun fara samun fasinja. "Lafiya" Kawai ta ce ta mayar da kanta tana cigaba da danna waya. "Jaburu ina za ka kai ta ne, na ga ta kama bakinta ta ƙame ƙam kamar mai ciwon haƙori bata maka kwatancen. Shi Jabiru sai yanzu ma ya tuna bai faɗa mata take kwatanta inda za a kaita ba sam ya manta duk ta dagula masa lissafi da za ta zauna wuni guda yake kallonta yana ganin bakin nan nata mai jambaki da yake ƙyalli da ba zai gaji ba sai ya biya ta kuɗin kallonta ma da zai ke yi. "Tirƙashi! Wato fasinja ne ma zai ke kwatanta inda za a ke kai shi" Budurwar ta faɗa a zuciyarta cike da mamaki ita dama dan ba takamaimana wurin zuwa gare ta ba shi ya sa ma bata ce ga unguwar da zai kaita ba nufinta idan yana tafiya in ta ga inda ya mata sai ta sauka saboda akwai abin da ta fito yi. "Ina, ina za a kai ki?" Ya faɗa yana in ina da inda-inda Cike da mamaki Iya take kallon Jabiru dan sai yanzu ta lura da rashin nutsuwarsa sai dai diriricewarsa ta wuce a ce saboda samun fasinja ne. "Jaburu yaushe ka fara in ina ban sani ba?" "Lah ba in'ina bace Iya" Ya faɗa yana yin murmushin yaƙe. "Kake tafiya kawai duk inda na ga ya mini to zan ce ka tsaya na sauka" Ta faɗa da shaƙeƙƙiyar muryarta da take gwalli. Wani daɗi ne ya lulluɓe Jabiru jin furucinta dan dama shi bai gaji da ganinta ba dan sai satar kallonta yake ta mudubi. Iya kuwa mamaki ne ya cika ta jin wai a yi ta tafiya da ita sai inda ya mata za ta sauka. "Taɓɗi! Wannan ina ma tun safe muka haɗu da ke yo ai da mun gama cinikin yau a kan ki" Iya ta faɗa a zuciyarta tana ganin sun kasa sun siyar tana ta faɗin sai kuɗin da suka yanka mata za ta bayar tun da bata san ma ina za ta je ba bare har a yi cinikin da alama kulin sun mata yawa. "Bari zan siya kati a can" Ta faɗa cike da yanga. Wani uban birki Jabiru ya ja maimakon su je saitin wurin siyar da kati sai dai tun kan a ƙarasa ya tsaya haka ta fita tana taɓe baki da yatsina fuska hannun nan a lanƙwashe. "Jaburu yau mun yi babban kamu sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci, tun da dai ita kanta bata san ina za ta je ba" "Wallahi Iya ni son ta ma nake dama ta aure ni" "Amma dai Jaburu baka da hankali, ka duba zuƙeƙiyar mace ya wannan irin su ne matan da ake cewa wanke hannu ka taɓa, kuma wannan ko da kuɗinka sai da rabonka kana ganin tana mana kallon ƙasƙanci kamar ta ga kashi, kai da baka ajiye ba baka ba wani ajiya ba da a ce kana da kuɗi to ko kuturu ne kai ba za ka rasa matar da za ta so ka ba amma ka ga yadda baka da ƙwandalar nan baka da naira biyar to aradu kai da shanddar kashi ɗaya kuke a wajen mata" "Iya to ba sai mu je gida ba tun da dai... "Jaburu rufani ka saya ni ba da ni ba wannan ɗanyen aiki ai shi ya sa na ce dama da sarƙar nan tawa ta siyu da har kuɗin aurenka a ciki za a ɗauka saboda jaraba irin taka yaro bai tafasa ba zai ƙone haka kawai in yarda ka haikewa yarinyar mutane son ka sa a kore mu daga garin nan" Hawaye ne suka fara sintiri a kumatunsa ya kumburo baki. "Rufa mini asiri Jaburu kar ka watsa mini tsaba(Hatsi, gero) Kaji su bini a kan mai ido zai ci wuta haka kawai kana maraya ka sa a ƙona ni a kan ban cika maka burinka ba, ka yi haƙuri bari ta dawo mu san yadda za a yi mu je gidan tana shigowa ka ɗauki hanyar gida d... Shigowarta napep ɗin ne ya dakatar da Iya daga maganar da take son ƙarasawa shi kuma da sauri ya goge hawayen murna fal cikinsa ya ja suka cigaba da tafiya. Hanyar unguwar su ya ɗauka ita dai ta ƙwame a baya bata ce komai ba. "Baiwar Allah zan ɗakko saƙo a cikin gida tun da Allah ya sa mun biyo ta hanyar" Cewar Iya cikin sanyin murya. "Ikon Allah wannan gidan ne gidan matar nan? Ko dai ɗanta ne ya mutu ya bar musu gado wannan haɗaɗɗan gida" Budurwar ta faɗa a zuciyarta "Ba damuwa" Ta faɗa idanunta kafe a kan gidan. Iya kuwa fita ta yi ta fito da mukullin daga ɗan tofi ta buɗe get ɗin ta shige dama ta ƙiftawa Jabiru ido, jim kaɗan sai ga ta ta fito. "Baiwar Allah dan Allah ki shigo ki taimaka mini in kamo kaya" Cewar Iya da ta zo har gaban napep ɗin. Shiru Budurwar ta yi tana mamakin mai ya sa bata ce shi ya je ya kamo mata kayan ba, ko dai basu yarda da ita bane, saurin kawar da zancen zucin ta yi ta ajiye jakarta ta fito tana ƙarewwa unguwar kallo, sai da suka shige cikin gidan Iya tana gaba budurwar tana bin ta a baya har cikin ɗaki kawai sai Iya ta shammace ta ta fita ta banke ƙofar ta saka mukulli da sauri budurwar ta fara buga ƙofar tana faɗin a buɗe amma Iya lokacin har ta kusa bakin get tun daga bakin get take ƙwallawa Jabiru kira, shi kuma ya fito da sauri yana washe baki ko mukullin napep ɗin bai cire ba ya shigo. "Maza tana ɗaki ka san ni indai a kan abin da zan faranta maka rai ne Jaburu to babu abin da ba zan yi ba haka kawai yo tsuntsu daga sama gasasshe" Ta faɗa tana garƙamawa get ɗin mukulli ta bi bayan Jabirun dan ta je ta masa gadin ƙofar ɗakin. 09013181851 [12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH Page 1️⃣4️⃣ "Na san Allah zai yafe mini, Allah mai yafiya ne ko shi ma Jaburun ai Allah sai ya gafarta masa, ni kaina na san ba abin kirki bane in taimaka masa ya ƙwamushe ƴar mutane, kuma ma va a son ka aikata saɓo batan ka san saɓi ne ka ce ka tuba daga baya to amma dai ya na iya bana son ɓacin ran Jaburu marayan Allah, in ban da ma dai saka rai a abu ina shi ina wannan sangamemiyar mata, a toh tun magriba ta gabato sai mu haɗa ta mu kore ta mu kulle gidan mu shiga gari ai ba lallai ta shaida gidan bama" Cewar Iya da take tsaye, ganin tsayuwar ba za ta yi ba sai ta juya ta kalli get ɗin ta jijjiga kai irin ko an jiyo ihu babu wanda zai shigo kawowa budurwar ɗauki ta juya domin zuwa can ta yi wa Jabiru gadin ƙofar. "Jaburu mazan fama kenan na Iya mai gaza mai rikicin gangan" Ta faɗa tana murmudawa tare da samun kujera ta zauna tare da harɗe ƙafa ɗaya a kan ɗaya. *JABIRU* A can cikin ɗaki kuwa tun lokacin da Jabiru ya je ya buɗe ƙofar da kasancewar Iya a jiki ta bar mukullin, dan haka yana buɗewa ya shige ya kulle ya cire mukullin ya kefa saman drower ɗakin. Budurwar ya tunkara da take ta raɓewa a jikin bango domin yanzu ta gane ta kuma fahimci abin da ake so a aiwatar a kanta. "Ka yi haƙuri dan Allah kar ka aiwatar da ƙudurinka a kaina" "Babu zancen haƙuri ƴar yarinya kawai ki bada kai bori ya hau, bar ganin kina da jiki to ƙarfin namiji da mace ba ɗaya bane bare ni nan Jabiru" "Dan Allah ka yi haƙuri" Ta faɗa hawaye suna sintiri a fuskarta. "Ai da kin adana hawayenki da haƙurinki wataƙila anjima su miki amfani amma yanzu babu tasirin da za su yi, kin san wanda ya yi nisa ba ya jin kira" Ya faɗa yana tunkararta ganin ya cire riga ya wurgar sai suka fara ƴar tsere a ɗakin har ya yi nasarar kamota aka shiga kokawa, haka Jabiru ya jefa a gadon ya shiga cire mata riga tana ja yana ja sai dai bai lura da komai ba sai da ya farɗi rigar mamanta sai ga famfas (Pampers) Ta yara duƙunƙune guda biyu suna tseren faɗowa da mamaki sosai Jabiru ya bi famfas ɗin da kallo yana tashi zimbet daga kan gadon hankalinsa a tashe domin kuwa ya gane ba mace bace namiji ne ya yi shigar mata, dan ba komai ne ya ƙara ɗaga masa hankali ba sai yadda dantsen namijin yake a murɗe ashe rigar mata ce da ta rufe shi ya sa ba a lura ba sai yanzu ya gani muraran da idanunsa. Gefe can ya rakuɓe jikinsa yana karkarwa idanunsa kafe a kan famfas ɗin nan guda biyu wanda suka zubo wanda yake yi wa kallon mama(Breast) Ashe dai ciko ne aka yi aka mayar da shi banzar bazara. Matashin nan kuwa dan ba a kira shi budurwa ba yanzu dan ya tashi daga wannan jinsin dama a rashin sani karen bebe ya ɓata. Tsaye ya tashi fuska a murtuke ya nufi gaban mudubi ya ɗauki toilet paper ya goge kwalliyar fuskarsa da jambakin gaba ɗaya, hannu ya sanya ya cire ɗaurin ɗankwalin da Jabiru bai cire ba dan shi Jabiru zip ɗon rigar ya cire shi ya sa abin bai kai ga cire ɗankwali ba. Yana cirewa sai ya ciro hular gashin da take ɗauke da kitso yaraf-yaraf sai ga gashin kansa mai cibiri-cibiri irin na matasan zamani, siket ɗin atamfar jikinsa ya zame sai ga tiri kwata na jeans a ciki wurgi ya yi da su tare da nufar inda Jabiru yake yana muzurai kana kallon fuskarsa ka san taƙadari ne babu wani alamar imani ko tausayi a tare da shi. Kallon fuskarsa kawai Jabiru yake tun bai san mai zai faru ba har gumi ya gama jiƙa shi ga wani fitsari da yake neman kufce masa dan ya san dai yau babu zama an ɗaurawa karya zani dan yau sai ta Allah, an kama kwarto a turakar mai gida. Sosai Jabiru yake jin tsoro musamman da ya san ƙofar ya kulle ta da mukulli dan ƙarfin hali ɓarawo da sallama ma sai ya jefa mukullin saman drower ga shi yanzu baya ta haihu. "Wayyo Allah ni Jabiru faɗan da ya fi ƙarfunka maida shi wasa, ni kaza garin tone-tone na na tono wuƙar yankana" Ya faɗa a ransa yana ƙoƙarin haɗa laɓɓansa a fili ko Allah zai bashi ikon haɗa kalmomin da zai famshi kansa da su a wajen mutumin da ya ɗauka mace ce ashe dai ƙaron gardi ya kawo ɗaki ya garƙame. "Wallahi ba halina bane ka mini rai in sha Allahu an yi na farko an yi na ƙarshe nan gaba mace ko ta kare ce (Karya macen kare) Na gani a hanya babu ni babu ita bare macen mutum" Ya faɗa hawaye suna zubowa ratata yana ƙare mannewa da jikin bango tamkar dai bangon ya tsage ya shige ciki. "Ka dana kalamanka da sannu za su maka amfani amma ba yanzu b a dan wanda ya yi nisa ba ya jin kira" Matashin ya faɗa da wata kakkausar murya ta ƙaton namiji, muryar da ta ƙara razana Jabiru tare da saka shi a kogin da na sani tsumu-tsumu, a take ya ji duka jarabar da yake ji a kan budurwar da har ya kasa haƙuri ta yi gabas ya yi yamma. "Na rantse da Allah na tuba, ni daga yau ma na zama mata maza bana sha'awar mata ma baki ɗaya ni ko aure ma ba zan yi ba bare na ƙara tarkar haikewa wata mace ka rufa mini kwandon asiri" Cewar Jabiru murya tana rawa domin ganin matashin nan ya dunƙule hannu ya nufo fuskarsa gadan-gadan. Tun kafin ƙwaƙwalwarsa ta gama tantance masa abin da za a masa ya ji saukar wani naushi mai ha'ula'i wanda a take ji da ganin Jabiru suka yi ƙaura daga gare shi na wasu daƙiƙai kafin ya saki wani ƙara mai gunna sai ga shi yaraf ya zube saman silin ɗin ɗakin yan juya masa tamkar yadda famka take juyawa. Iya tana zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ta jiyo ihun Jabiru wata dariya ce mai sauti ta kufce mata, da sauri ta saka hannu ta danne bakinta tana ɗan kallon ƙofar da za ta sada ta da tsakar gidan irin kamar kar wani ya ganta a zuciyarta ta ce "Oh ni Ansai zan je garin wutar tawa in yi suɓutar baki, ah lallai Jaburu an samu abin da ake so ki jo yadda ya saki ihu tamkar wani zaki a tsakiyar daji" Ta faɗa tana ƙara tuntsurewa da dariya marar sauti, dan ita a nata tunanin Jabiru yana can yana haikewa ƴar mutane ne bata san cewa ido ya daɗe da juyewa da mujiya ba. "Wannan ce ƙaddararki yarinya sai ki ɗau halin annabawa (Haƙuri) Dan aikin gama ya gama sai dai a bi wani sarkin ba wannan ba lallai Jaburu jarumi ne " "Wayyo Allah!" Jabiru ya ƙara fasa ƙara jin an kifa masa wani naushin a gadon baya, dan ɗago shi saurayin ya yi tsaye daga kwanciyar reran ɗin da ya yi a tsakiyar ɗakin. Iya kuwa jin ihun Jabiru a karo na biyu har da kiran wayyo Allah, sai ta ƙara cika da farin ciki a take ma sai ta tashi tsaye ta gyara ɗaurin zani ta shiga rausaya kai kamar ƙadangaruwa tana waƙar "Fati fatima mai zogale" Tana yi tana juyi abin ta tamkar sallah. Tana ta rawa shi kuwa Jabiru ana haɗa masa jini da majina a ɗaki a nata tunanin ihun daɗi yake bata san baƙar azaba ake gana masa ba. Sai da ta yi rawar ta gaji dan kanta ta zauna har lokacin tana jin ihun Jabiru dan daga ƙarshe sai ma ta daina jin ihun sai kuka. "Yi kukan ka Jaburu ai dama a rayuwa ana kukan wahala ko damuwa sannan ana kukan daɗi to kai dai yau kukan daɗi kake, ita yarinyar ba a ma jin kukan ta sai nashi ake jiyowa ko kunya ba ya ji ya zage yana ihu da kuka, wannan in muka koma ƙauye in za a masa aure ai sai dai a masa gidansa da ban dan ba za a kawo shi cikin gida irin na wanda ake kawo su gidan iyaye su zauna a musu kewayen su a nan amma shi wannan tun da haka yake ɓaran ɓarama yo wannan ai sai ya cika gida da iface-iface amma in aka ware masa gidansa sai ya je can in hamimiyar doki zai ke yi ma gidansa ne" Ta faɗa a ranta lokacin da rake jin kukan nasa ya fara yawa. "Uhm in ji ami ciwon haƙori bari dai in tashi in ke kar yaron nan ya yi wa ƴar mutane ɓarna, yo ai abin ya wuce hankali kai da za ka yi abu saisa-saisa ka kashe ƙishirwarka amma sai ka nannage a ɗaki kamar wata matarka ta sunna" Ta faɗa lokacin da ta je jikin ƙofar ta kara kunnuwanta ko za ta ji kukan macen amma shiru wai malam ya ci shirwa. "Kai wannan ɗiya ko dai ba budurwa bace? Ko kuma dama ƴar hannu ce , amma in ba haka ba ana haike miki ko ɗan kukan ƙwatar kan nan naki ba za ki yi ba kai zamani sai a bar shi" Ta faɗa a ranta tana taɓe baki. "Jaburu, Jaburu, Jaburu haba kai da baka iya cin ƙwan makauniya ba yanzu fisabilillahi dan dai baka mutuwar tsakar ɗakinka sai ta wani ya za a yi ka daɗe kana abu ɗaya har na gaji da maka gadin ƙofa haka kawai ka cika gida da iface-iface da kuka da kururuwa, so kake sai an yi abin kunya wai uwa ta cinye sirika ranar aure, kai da na maka gwaninta za ka watsa mini ƙasa a ido ko dan abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake yi, ai yarinyar ma ta maida faɗan da ya fi ƙardinka wasa kake mayar da shi amma ai ka wuce gona da iri" Ta faɗa cikin ɗaga murya yadda zai ji dan ta ga abin na sa ba buɗe ƙofar zai yi ya fito a tun da babu niyya wai ango ya kwana da wando. Duk wannan maganar da takw inu take bayan hari domin kuwa lokacin Jabiru ya ci dukan da ko hannunsa ba ya iya ɗagawa saboda jigata bakin nan an fasa masa shi ya kumbura ya yi tsawo ya yi zototo. "Au ƙyale ni ma ka yi to ai gobe ma rana ce ta jibi har tafi yawa, ai wauta take sanya biri ya ga ayaba kamar takobi, wato ga Ansai ƙaramar danga mai... Tun kan ta ƙarasa maganar sai ta ji alamar saka mukulli a jikin ƙofar da ta jingina ta kara kunnenta, matsawa ta yi daga jikin ƙofar domin ta basu wuri su fito. "Hab ko kai fa a ce baka san annabi ya faku a tun daɗewa sai abu ɗaya kake ga shi mun bar arincaɓa a waje duk hankalina ba a kwance yake ba" Ta faɗa tana juyawa za ta koma tsakiyar falon. Bata san cewa ba Jabiru ne yake buɗe ƙofar ba matashin ne ya ɗakko mukullin tun da a gabansa ya ɗora a saman drower. Yana buɗe ƙofar ya koma ya kama ƙafar Jawo ƙafafun Jabiru. "Ai gwara dai ka fito kar ka mayar musu da ƙafar ƴa kamar ta agwagwa, in kuma abin ya wuce aiki ya zama aika-aika ne sai mu nemo ruwan zafi ta gasa jikinta ta kama gabant... Juyowar da ta yi ta sauke idanunta a kan wani namiji mai wando tiri kwata ko riga babu sai gabanta ya bada wani rassss, kafin ta mayar da idanunta kan Jabiru da ake janyowa wanda yake kwance magashiyyan tamkar wanda ba ya lumfashi, kallon rashin fahimta take gaba ɗaya sai kanta ya juye ta ma kasa samun ƙwaƙƙwaran tunanin da za ta yi, saboda ita dai bata san ta inda aka samu ƙaton namiji wanda ya tuɓe yake musu yawo zagadam-zagadam a gida ba, abin tambayar ma shi ne ina yarinyar budurwa? Matashin da fuskarsa take a haɗe tamkar baƙin hadarin gabas. Yana jan Jabiru a ƙasa sai da ya kawo shi tsakiyar falon ya warɓar da shi tamkar wani tabarmar leda, Jabiru da babu abin da yake iya faɗa ko ya aikata sai kallo da idanu sai kuma zubar da hawayen azaba da idanunsa suke yi sai ya ji ya yi da na sanin fita hayar adaidaita sahun ma yau gaba ɗaya bare har ya haɗu da wata ya ɗakko ta. "Jaburuuuu" Iya ta yi ƙarfin halin faɗa jikinta yana karkarwa ta kasa gane mafarki take ko idanunta biyu tana wasi-wasin cewar ko dai sun sake wani gamon ne. "Ai kuwa in dai wani gamon muka yi a gobe ba sai jibi ba za mu bar wannan Kanon ina dalili sai baƙar azaba muke sha har yau ko cinikin ƙwandala bamu yi ba sai ɓarnar kuɗin siyan abinci " Ta faɗa a zuciyarta tana kallon ƙafafin matashin sai dai ganin farce kamar nata ba kofaton aljannu ba sai abin ya ƙara ɗaure mata kai. Jabiru sai ƙoƙarin magana yake yana son ambatar sunan Iya amma yadda bakinsa ya yi tsawo kamar shantu ko bututu sai ya ji ko I ɗin farkon sunan Iyar va zai iya faɗa ba bare har ya ƙarasa da faɗin YA. Yana jaɓar da Jabiru sai ya nufi wajen da Iya take tsaye tun kafin ya ƙarasa sai jikin Iya ya kama rawa kamar mazari tana jin dama ta iya layar zana da tuni ta ɓace a kan wannan tsoron da take ciki da bata san takamaimai dalinlin damuwar ƙato a ɗakin a bare kuma har ya nakaɗawa Jabiru duka ita kuma da ya nufo ta sai ma ta rasa mai zai mata tabbas ta tabbatar idan ya mata duka irin dukan da ya yi wa Jabiru to kuwa sai gawarta!. Yana zuwa bai yi wata-wata ba ya sanya hannu ya finciki hannun Iya ya juya zai koma ɗakin da ya fito da Jabiru daga ciki. "Na yi imani da Allah da ranar lahira kuma aradu na yi alwala da kabbarar harama" Cewar Iya cikin tsoro tana turjewa dan ta san yana shiga da ita ɗakin sai gawarta tun da jikinta ba zai ɗauki jigilar da jikin Jabiru ya ɗauka ba. Ganin ko saurarenta bai yi sai ta ƙara kaimi wajen faɗin "Ka yi wa iyayenka ka rabu da ni, tsohuwa ce ni idan kuma gidan kuke so mu bari to har garin nan za mu tafi mu bar muku" Ta faɗa da sauya akalar maganar ko mutanen ɓoye ne. "Idan gemun ɗan uwanka ya kama da wuta sai ka shafawa naka ruwa" Ta faɗa a zuciyarta hankalinta ya kai ƙololuwar tashi ganin gadan-gadan ya nufi ɗakin da ita, ga shi babu wani mai ceton ta hatta Jabirun da take ganin zai kawo mata ɗauki gashi nan tana gani magashiyyan a kwance ko uhum ba ya iya cewa bare ta sa ran zai taimake ta, shi kansa yana halin da yake buƙatar taimakon. "Tabbas faɗan da ya fi ƙarfinka kai bawa wasa kake mayar da shi ina kaza ina faɗa da giwa ana zaune ƙalaw gwara dai na lallaɓa na rabu lafiya da wannan mutumi, amma ni abin tambayar ban san lokacin da ya shiga ɗakin ba sai dai in lokacin da na shiga ni da wannan yarinya yana ɗakin ya yi likimo kai ina jin ma shi ya farwa yarinyar ba Jaburu ba dan yadda Jaburu yake babu wata alama ta aikata sunna a tare da shi, tabbas da sauran rina a kaba ashe dai ni wani na yi wa tanadi har cikin gida har ɗaki ba Jaburu ba kuma dan rashin ta ido bayan ya kalailaye ƴar mutane babu sadaki shi ne ya nakaɗawa jikan nawa duka ni ma yanzu yake son a jaɓi banza sai ka ce ya samu bayi, ni ina nan zaune ina wa Jaburu gadin ƙofa ashe dai bonono na yi rufin ƙofa da ɓarawo haba shi ya sa nake jin ihun Jaburu ya yi yawa duk tunanina sunnar da yake aikatawa yake yi wa ihun ashe dai ashe dai" Ta faɗa a zuciyarta. "Wato ke tsohuwar banza shi ne kika mini shigo -shigo ba zurfi kika kai wa jikan ki ni har ɗaki duk a tunaninki mace ce to ba mace bace ni ne nan kika kai masa ɗakin kin ga sakamakon da ya karɓa a hannuna" Ya faɗa rai a ɓace yana aika mata harara. Wani irin dimmm di dimmm gaban Iya ya bayar jin wai ashe ba mace bace ta kai wa Jabiru ashe ƙato ne ta saka ya shiga ya garƙame ƙofa ashe rabon ya ci na jaki ne. Idanunta ta ɗaga wanda suka kaɗa suka yi jawur saboda tsoro ta sauke a kan cibiri-cibirin gashin kansa tana mamakin ina kitson da taga ya zubo a kafaɗarsa tana al'ajabin ya aka yi aka haihu a ragaya ta ji ya ɗora da faɗin "Ni maraya ne dan haka ma a shagon wasu abokaina nake kwana, na zaɓi hanyar wannan ta yaudarar maza a matsayin mace ne dan in ke samun kuɗi ina kashe uzurin gabana, ina saka wa a mini kwalliyar nan na yi mama(Breast) Da famfas na bazama yawo dan bani da takamaiman wajen zuwa ina yawo a ƙafa wata ran na shiga napep idan na ga wani mai abin hannun sai na sauka na san yadda zan ribace shi ya ce yana sona idan ya tashi kaini gida sai na faɗi unguwar ƙarya na nuna wani gida ya sauke ni a ƙofar ya sallame ni da kuɗi ya tafi in zamu yi waya na yi muryar mace, in zai zo na je wajen gidan da na ce gidanmu ne to a haka nake samun abin da nake so dan na san ina garsamemen namiji babu mai ɗaukan kuɗi ya bani shi yasa na zaɓi hakan, shi ya sa ma da jikan ki ya ce ina zai kai ni na ce idan na samu wurin sauka zan sauka saboda bani da takamaiman wajen zuwa, dan haka sai kin karɓi sakamako kamar yadda ya karɓa, amma ke ba dukan ki zan yi ba kin san hadisi ya ce kama tidinu tidaan (Duk abin da ka yi sai ana maka) To ke ma yanzu zan haike miki kamar yadda kika so ɗanki ya haike mini kika goyi bayansa, kuma ɗauke nake da cutar ƙamjamau kin ga za ki samu guzurin zuwa kabari" Ya faɗa yana fisgar hannunta tana turjewa ya shige ɗakin ya banko ya saka mukulli Jabiru sai idanu ya runtse hawaye masu zafi suna kwaranyowa saboda ko yatsansa ba zai iya ɗagawa ba dan ba ƙaramar kila ya sha ba tabbas ya ji maza. "Lahaula wala ƙuwwata illah billah Jaburu kana ganin abin da nake gani kuwa ni Ansai da tsufana mai ƙanjamau zai haike mini, wayyo Allah duk abin da ya samu shamuwa dama watan bakwai ne ya yawo mata" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta ga ya rufe ƙofar ruf sai lokacin ta ji tashin hankalinta ya ninku. "Yau ya zan yi ina mafita ya zan yi in tsira, na jawa kaina ni dai zuwa birni bai mini rana ba amma tabbas duk abin da ya samu rago inuwa ce ta jawo masa" Ta faɗa a zuciyarta hawaye suna kawaranya tana kallon yadda aka yi wurgi da ita a kan gado a gidan da babu kowa sai kowar wake wato Jabiru da babu abin da zai iya tsinanawa ga gida a garƙame ɗaki ma a garƙame da mukulli. akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 [12/23, 15:52] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH Page1️⃣5️⃣ Babu abin da bakin Iya yake ambato sai magiya a kan ya haƙura ya ƙyale ta amma ya yi kunnen uwar shegu da magiyar da take masa, saboda shi ma bata ji tausayinsa ba take gadin a masa fyaɗe a matsayinsa na mace bata san cewa shi namiji bane. "Haba amaryata ke da za mu angwance mene ne na damuwa ke da kika yi gam da katar na samun yaro ɗanye sharaf, ai kin dace da tsuntsu daga sama gasasshe" Ya faɗa cike da sheƙiyanci yana saka hannu ya warto leɓen zaninta, da sauri ta saki rigarta da ta riƙe ta mayar zuwa ƙugunta waɗan nan ƙafafu kuwa ta haɗe su waje ɗaya ta matse ita ala dole mai ƙarfi. "Haba ɗan nan mai za ka yi da tsohuwa mai shekaru aru-aru wacce ta ga jiya ta ga yau, duk na yamalmale na yi yaba babu mamora a jikina... "Kar ki ce haka baby ai ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba... Fashewa Iya ta yi da kuka jin ya kira ta da suna baby kuma ma wai ita ce ruwan kashe gobara yau, ruwan kashe gobarar ma a wajen ɗan da ta yi jika da shi. "Haba baby duk kukan ɓaci ne wannan ɗin?" Ya tambaya yana ƙara jan leɓan zanin Iya wanda ta daddage iya ƙarfinta tamkar a filin yaƙi ta danne. "Ka yi wa darajar iyayenka ka ƙyale ni ɗan nan, wallahi na faɗa maka babu wani wurin moro ka je ka samu ƴan mata masu jini a jika" Ta faɗa cikin muryar kuka hawayen nan shaɓe-shaɓe, jin bai tanka mata ba sai ta ɗaga ido ta kalle shi ganin ya tamke fuska tamkar magribar ɗinya sai ta sha jinin jikinta, jikinta ya shiga karkarwa dan yanayin da ta ga fuskrsa a ciki yanzu ya mata kama da rashin sassauci kuma komai zai iya faruwa. Rigar ya farɗa ita ma ta ɗago hannunta ɗaya daga ƙanƙame zaninta da ta yi ta kai jikin rigar saitin ƙirjinta ta danne ɗaya hannun kuma yana riƙe da zaninta. Rigar ya ƙara fisga tamkar zai yaga. "Haba kai kuwa mai za ka ɗauka a nan wurin da kake faman ja?" "Abin da ake ɗauka mana" Ya faɗa yana ƙara tamke fuska. "Wallahi billahillazi huwar rahmanu na faɗa maka babu wata mamora, shi kansa maman(Breast) Ya gama ganin wahalhalun duniya, ya yamutse ya jeme tare da yagalgalewa, babu abin da ya fi dacewa da a kira sunansa ma sai jelani" Ta faɗa lokacin da ta sauke idanunta a ƙirjinta ta ga ko alamarsa babu . Ganin ya ja rigar da ƙarfi kuma da yake rigar atamfar dama ta gama cin duniyarta duk ta tsofe jin an nuna mata ƙarfi sai keeet ta yage daga gaba tun daga ƙasa har sama hannuwanta ne da suke cikin rigar kaɗai ya hana rigar fita sai rigar ta zaman kamar falmaran, a firgice Iya ta wuntsila gefe guda a kan gadon sai ta yi wata uwar shala sai gata a tsakiyar gadon ta tashi tsaye cankarkar tana muzurai da haki, ganin ya ƙara tahowa sai ta tsugunna ta saka kanta a kan gadon ta yi wata adungure sau biyu sai ga ta a bakin gadon ta zara ƙafa ta dira idanu ta sauke a kan ganan rigarta da yake a buɗe wayam sai kuwa ta yi ido huɗu da mamanta da suke reto, ganin ya taho wajenta sai ta shiga ɗan gudu a cikin ɗakin da take ɗakin yana da yalwa sai kuwa su ma maman nata suka fara ɓalai-ɓalai suna gwaruwa da juna. Dariya ce ta so suɓucewa matashin ganin abin da take yi ita ala dole ƙwatar kanta za ta yi bayan da ya ga dama a cikin minti ɗaya zai gama da ita. Tana ta faman riƙe gaban riga har ta manta ta saki zanin nata kuma zanin bai ɗauru sosai ba saboda jansa da marashin ya yi ta yi ita ma tana ja, dan haka zanin ya warware daga tsantsa bata sani ba har leɓen ɗaya ya fara jan ƙasa, matashin da yake bin ta suna zagaye ɗakin sai ya saka ƙafa ya take leɓen zanin nata sai kuwa ga zanin a ƙasa ta bar shi bata lura ba ya sunkuya ya ɗauka ya rataya zanin nata a kafaɗarsa. "Na gode Allah da kika cire zanin da kan ki kin hutar da ni" Ya faɗa yana kallon Iya da take riƙe da gaban rigarta da hannu biyu ta yi wajen madubi. Da sauri ta waiwaya ta kalle shi ai kuwa ta yi mugun gani domin kuwa zaninta ta gani a wuyansa a rataye da sauri ta sauke idanunta ta ganta daga ita sai ɗan tofi(Siket ɗin da tsofaffi suke sakawa a ciki wanda ake ɗinka musu mai aljihu) A take ta shiga rafka salati da ƙarfi tamkar za ta ari baki. "Na shiga uku ni Ansai wannan yaro an yi ja'irin yaro, yau na gayyato taƙadiri har cikin gidana wai ni ɗin nan tsofai-tsofai da ni bai lura da tsufana ba zai haike mini dan jaraba irin ta yaran zamani, yo ni ba gwara ba ya lakaɗa mini dukan irin yadda ya yi wa Jaburu a kan wannan baƙi kuma ɗanyen aiki da sheɗan yake kwaɗaita masa, na shiga tara ba ma uku ba yanzu yadda ya ɓarka mini riga kuma ya yi nasarar cire zani ai sai abin da Allah ya yi ɓarawo a hannun mata" Ta faɗa a zuciyarta tana jin ina ma ta samu ta kuɓuta da idan ta zangaya da mugun gudu Allah kaɗai ya san a inda za ta tsaya. "Yo Ansai ko buɗe miki ƙofa aka yi ina za ki je a haka, ke dai wanda babu kaya a jikinsa ai baku da banbanci" Cewar wani ɓangare na zuciyarta. Idanunta ta sauke a kan ɗan tofin nata sai ta ga gaba laya a tsangale da yake ba wani tsawo ne da shi ba. "Kin yi kyau baby kamar turawan nan masu saka tsangalelan siket d... Salati Iya ta kwasa jin yana haɗa ta da matan turawa wanda aka ce shigar su tamkar tsirara take, kuma ko ranar nan ta ga wata baturiya a garin Kano duk cinyoyi a waje har take cewa Jabiru wannan ai daman ma sangalarta ta fito(Tsirara ba kaya) Ya ce mata ai baturiya ce su ba ruwansu amma shi ne dan wulaƙanci zai haɗa ta da arna. Da ta ga yana kallonta ma daga inda yake sai ta saɓa da gudu ta yi wajen drower tana gudun ne sai ga kuɗinta sun faɗo daga aljihun ɗan tofin nata. Taku ɗaya biyu saurayin ya yi sai ga shi ya isa wajen kuɗin ya sunkuya ya ɗauka Iya da ta je take neman maɓoya ko da kuwa saman drower ɗin ne ta haye dan ta tsira da tsufanta da mutuncinta kamar an ce ta juyo sai kuwa idanunta suka yi arangama da mummunan gani, domin kuwa hango gaba ɗaya tattalin arziƙin su a hannun saurayin sai da hankalinta ya tashi domin kuwa sai da ta kai hannu ta lalumo ɗan tofin ta ji wayam ta tabbatar da cewa kuɗinta ne. Ita kanta bata san ya aka yi ba kawai sai ganinta ta yi a sukwane ta ƙarasa gabansa. Idanunta ƙurrr a kan hannunsa da yake ɗauke da kuɗin. "Yawwa baby kin taho... Tun bai kai ƙarshen maganar ba Iya ta gane katoɓarar da ta yi, da sauri ta juya a sukwane ta koma inda ta fito wato wajen drower. Dariya sosai matashin yake dannewa yadda har idanunsa suka kawo ƙwalla saboda yadda dariyar ta ci ƙarfinsa amma yake dannewa, shi dariyar da take bashi wai ita ala dole tana gudunsa shi kuwa in ba bakin uwa ne ya kama shi ba mai zai sa shi tarawa da matar da ba halaliyarsa ba kuma tsohuwa. Nufar wurin da ta je ta rakuɓe a jikin drower ta ƙanƙame jikinta, yana zuwa ya saka hannu ya ja ƙafarta wani uban ihu ta saki tana faɗin "Wayyo Allah na wayyo Jaburu wayyo matantakata(HQ) Wayyo mashayar yara(Breast)" Ta faɗa lokacin da ta daddage ƙarfinta tana faɗa. Ƙafar ya sakar mata tare da juyawa yana dariya marar sauti ya koma ya fara tattara kayansa da ya cire ya fara mayarwa jikinsa lokacin Iya ta ɗago tana kallonsa ya mayar da komai sai ga shi tamkar mace, mamaki ya cika Iya ta ce a zuciyarta. "Da na san daga waje mace kake, daga ciki kuma namiji da babu wani abu da zai sa in yarda da ƙudurin Jaburu bare har ta kaimu ga wannan mummunam halin" Babu inda ya fi bata mamaki irin lokacin da ya saka bra ya ɗauki famfas ya sassaka ya ɗora riga tsaf ya fito babu mai cewa ba mace ba ce, ga hular gashin da ya saka ya ɗaura ɗankwali. Mukulli ya sa ya buɗe ƙofar ya juyo cikin muryarsa ta mata da yake canjawa ya ce "Bye-bye baby nah sai na sake dawowa" Ya faɗa yana juyawa zai fice. "Na gode ɗan nan da ka barni da mutuncina Allah maka albarka ya baka sana'ar yi ka daina shigar mata dan wallahi babu kyau" "Amin, amma fa ku daina gode mini ba za ki gane komai ba sai na fita na arce da adaidaita sahun ƙofar gida...Bai gama faɗa ba ya juya ya fice daga ɗakin, a tamanin da tara Iya ta taso ta ma manta da yanayin da take ciki dan ba komai ya ɗaga mata hankali ba illa jin wai zai arce da adaidaita sahun da suka ci bashi suka siya, ta tabbatar idan har ya ɗauke adaidaitar to tabbas ya tabbata gonar da suka bayar da jingina ta zama mallakin Alhaji Audu. A sukwane ta fito daga ɗakin har tana ƙume goshi a jikin ƙofar ɗakin amma ba shi bane damuwarta burinta kawai ya rufa musu asiri kar ya ɗauke adaidaitar. Matashin kuwa yana zuwa falo ya ga Jabiru a yadda ya bar shi ko juyi ba ya yi. *JABIRU* Tun da ya ji an shige da Iya ɗakin an kulle yake ta faman yin kukan zuci domin bashi da yadda zai yi, ko ƙarfin kwabo babu a jikinsa ga fuskarsa da bakinsa sai raɗaɗi suke masa musamman bakinsa ji yake tamkar an saka gishiri a ciwo saboda tsabar raɗaɗin da yake ji ga jikinsa sai ciwo yake masa ko motsawa ya kasa ji yake tamkar wanda cutar shanyewar duka jiki ta same shi, ba ma cutar ɓarin jiki ba. Salati da Iya take yi da magiya kuwa ji yake tamkar ya zama tsuntsu ya je ya ƙwace ta baƙinciki da takaicin ya kasa ko da motsawa ne sai ya zamana kawai hawaye ne suke ƴar tsere a dandamalin fuskarsa. Lokacin da ya ji Iya ta ce Wayyo Allah! Wayyo Jabiru sai ya runtse idanunsa saboda ya ji tana ambaton wayyo matantakarta da mashayar yara hakan ya tabbatar masa da cewa tuni aikin gama ya daɗe da gamawa. Yana cikin wannan halin ne ya ji an buɗe ƙofar amma ya kasa ko da ɗago kai ne ya ga wanda ya fito sai idanu yake rarrabawa tamkar kwarton da aka kama a ɗakin sabuwar amarya. Matashin nan yana zuwa ya saka ƙafa ya buga ƙafar Jabiru da ƙarfi. "Kar ka ƙarasa ni dan Allah" Cewar Jabiru a ransa dan ya tabbatar idan ya ƙara nakaɗa masa wani dukan sai dai a ɗauki gawarsa dan ba zai amfanu ba. Sai da ya ƙara buga masa ƙafa a kwankwanso. "Ash..." Ya faɗa a zuciyarsa yana jin har gwara ranar da suka yi gamo da aljanin nan a kan wannan baƙar rana. Hangar mukullin get ɗin ya hanga a inda Iya ta tashi sai ya ƙarasa ya ɗauka, ɗaukansa ke da wuya sai ga Iya ta fito a hautsine dan gaba ɗaya ta sha'afa da shigar da take jikinta burinta kawai ta dakatar da matashin daga ƙudurinsa na ɗaukan napep ko Allah zai sa ya amince ya tausaya musu. Jabiru da yake kwance a reran sai ganin ƙafafun Iya ya yi watsal ta tsallake saman kansa, har tana bige masa haɓarsa, ganinta da ɗan tofi gaban rigar a yage ya rabe a biyu sai ɓalai-ɓalai rigar take iska tana ɗaga ta sai ya ji wani tausayinta ya kama shi yana ganin sanadinsa kuma a son zuciya irin nashi ga shi da tsufanta an mata fyaɗe, dan shi duk a tunaninsa matashin ya haikewa Iyar. "Dan Allah, dan darajar ma'aikin Allah S.A.W ka yi wa iyayenka kar ka ɗauki arincaɓar nan, wallahi wata badaƙalar ce a kan arincaɓar da kuɗin bashi aka siya kuɗin bashin ma gonar gado aka bayar jingina... "Kar ki sake kirana da namiji baki ga shigata bane za ki sauya mini suna da siffa?" Ya faɗa yana karkarya muryarsa. "Allah baki haƙuri, dan Allah kar ki tafi da arincaɓar nan" "Sunana Ma'ishsha, dan haka ki kirani da sunana in ya so ko ma menene sai ki faɗa. "Daga baya kenan wai an yi sadaka da karuwa" Cewar Iya a zuciyarta a fili kuma sai ta ce "Ma'isha... "Ma'ishsha aka ce" "Dan Allah ka barni in yi wanda na iya saboda bakin ne bakin tsufa sai abin da ya fito ne ake ganewa. Ko saurarenta bai tsaya yi ba ya tafi yana yangarsa kamar yadda yake lokacin da suka haɗu, takalminsa ya saka a ƙofar ɗakin Iya da take masa magiya ta je za ta bi bayansa ta yi tuntuɓe da ƙafar Jabiru da yake kwance yaɓar a wajen. Girif ta niƙu da ƙasa amma saboda hankalinta ya yi gaba tana faɗuwa ta tashi zaune ta saka hannu ta ɗaɗawa Jabiru duka a ƙafar ji kake ɗal, da sauri ya runtse idanu. "Allah wadaran naka ya lalace in ji jaki dawa da ya ga an ɗorawa jakin gida kaya" Cewar Iya a zuciyarta ta tashi ta yi waje. Tun daga ƙofar ɗaki take masa magiya shi kuma har ta taddo shi yana tafiya da hannu a maƙale ko kallonta bai yi ba ya buɗe get ɗin, yana fita sai Iya ma za ta rufa masa baya amma me? Sai lokacin ta tuna da halin da take ciki na shigar da take jikinta duk da cewar magriba ta yi amma ba za ta iya fita waje a haka ba. Kuka take wiwi tana roƙonsa amma sai da ya je wurin adaidaitar ya shiga mazaunin direba ga mukulli a jiki Allah da ya sa ma babu wanda ya je wurin, hannu biyu Iya ta ɗora a ka tana girka kuka. Murmushi ya yi ya fito ya ɗakko jakarsa da take bayan adaidaitar tare da ɗagawa Iya hannu ya juya ya tafi abinsa ko waiwaye babu. "Allah miki albarka Ma'isha, da kin ɗauki arincaɓar nan da kin mana ƙanƙanci" Cewar Ita a fili tana sauke ajiyar zuciya Gida ta koma da sauri ta sako kaya ta fito ta buɗe get ɗin ta zo take tura napep ɗin da iya ƙarfinta, dakyar ta samu yake gangarawa, da haka ta samu ta shigo da shi gidan ta ƙulle sai ta rungume adaidaitar ta kwantar da kanta a jikin adaidaitar ta sauke wata ajiyar zuciya. "Oh ni Ansai tsautsayi dai ba ya wuce baƙo ko ɗan gari" Ta faɗa a fili tana juyawa ta koma cikin falon inda Jabiru yake kallonsa ta yi sheƙeƙe ta saki wani tsaki mai sauti ta ce "Ai yau dai na ga asara yawun bacci da safe, kai yanzu dama she sangamemen ƙato ne shi ne ka zauna ya naɗa maka duka ka ringa kuka kamar matar marigayi, duk ka cika gidan nan ni na ɗauka ma sunnar kake aikatawa, ashe dai kai ake jaɓa tamkar an samu jaki, to ai shikenan gobe ma rana ce ka ƙwallafa rai a matar da ba taka ba yanzu ai ga shi nan an mayar maka da baki kamar na jaɓa" Ta faɗa tana harararsa tun da tana ganin duk shi ne ummul aba'isin faruwar komai. 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *ZAN CIKAWA KOWANNE MUTUM ƊAYA 1Ok* *PROMO PROMO PROMO Ina *neman mutum 20 wayanda suke da 25k za mu yi team work na 52U,*zan cika wa kowanne mutum ɗaya 1Ok*zanna basu 1Ok in account ya bude, na tsawon wata 6, in sha Allah in dai kun bada hadin kai kowa za'a ba shi kudin sa, ke dai* *kawai kudin ki ki ka sani In sha Allah, wacce ta yarda dani kuma tana da kudin tayi magana in sakata a list* 1_ 2_ 3_ 4_ 5_ 6_ 7_ 8_ 9_ 10_ 11_ 12_ 13_ 14_ 15_ 16_ 17_ 18_ 19_ 20_ *Wacce take da kudin in ba ki da pls kar ki shiga*🧏🏻‍♀️ *Za ki iya yin hannu da yawa, amma lissafin zai fara ne in mutum 20 din sun hadu Ga Karin bayani* *Zamu yi Team Work na 52u ga wanda suke da 25k a hannu zan cikawa kowanne mutum ɗaya 1OK ta yanda a cikin wata daya kacal zaka fara morar kudin 52u da yardar Allah. Duk wanda ya shirya zai iya yimin magana _ 👇* 09013181851 *MAMAN AFRAH TEAM* Duk Wanda zai yi sai ya min magana insa shi a list ya tura kudin activation dinshi 25k, a maimakon 36k duk wata zan dinga bashi 15k har wata 3 in account dinshi ya bude an sallame shi sai ya koma yaci gaba girbe abinda account ke ba shi👌 Allah ya bamu sa'a ya 🤲ha damu da mutanen kwarai ya bar Mana 52u🤲 💃💃💃💃💃💃 SAURA PAGE 1 MU GAMA FREE PAGES WANDA ZAI KARE, WANDA BAI YI SUBSCRIBE BA YA YI WANDA ZAI BIYA 5OO to. Akwai youtube chanel ɗin da za a mana SUBSCRIBE duk wanda ya yi zai nuna min shaidar ta hanyar screen shrt idan na tabbatar zan saka shi a paid grp. ɗaya zaɓin kuma mutum zai iya biyan 5OO domin samun cigaban labarin har karshe, bana yabon kaina kuma ban ce na iya ba amma kun san ALKALAMIN MAMAN AFRAH BA YA RUBUTA SHIRME😍🥳 kar ki bari a yi tafiyar nan babu ke da subscribe kaɗai za ki gwangwaje da karatu. a nawa ganin ko babu littafi na ce a taimaka mini da subacribe ina ganin kamar na fi karfinsa a wajenku😍😊🙌🤗 ku masu mana ne har ma ku samo wasu su yi mana, ynz ma idan za ki iya saka wasu su yi ni dai screen shrt kawai nake bukata shaidar an yi SUBSCRIBE🥳🥳 Labari mai cike da barkwanci kun san yadda kuka dara a ƳAR ZAMAN WANKA, JALLI JOGA, KARA,IN INNA DELU, UNGOZOMA. 09013181851 [12/23, 17:22] Mom mashkur & Afrah: ƳAN ADAIDAITA SAHU (Masu keken napep) NA MAMAN AFRAH Page1️⃣6️⃣ Sai da ta yi ta masa masifa sannan ta samo wani man zafi a kan mudubin ɗakin ta lallafta masa a zototon bakin haka ya sha zunduma ihun zafin man a ciwon har jikinsa sai da ta shashshafa masa, haka dai suka kwanta ranar da takaicin kuɗin da matashin nan ya gudu da shi, babu abin da suka ci,da safe ne ma Iya ta samu ragowar garin nan sigan ma ya ƙare amma a haka ta jiƙa ta sha. Da yake zuwa safe jikin Jabiru ma ya warware bakin ma ya sace sai kumburi kaɗan haka suka shirya wajen goma na safe domin zuwa nema saboda ko biyar basu da ita ga babu abinci. Sun shirya suka fito Iya ta rufe gidan suka hau suka tafi, Jabiru sai tuƙi akei a sannu ga rashin karyawa da bai yi ba ga kuma bai gama dawowa daidai ba. "Jaburu ka ga wata tsaleliya can daga gani mace ce sak ba mata maza ba, ina nufin mace ce ba irin na jiya ba mai suna Ma'isha yake ko wa" Ta faɗa cike da zolaya ganin ko sun ga mace a hanya sai yake kauda kai ko kallon su ba ya son yi. Bai tankawa Iya ba har ta gaji ta ƙyale shi. "Iya Allah sa dai yau mu samu fasinja amma wallahi in ba haka ba za mu banu bamu da abinci gaskiya mu dage da neman fasinja" "Wallahi Jaburu abin ne sai du'ai" Wata mata ce haka bata fi shekaru sittin ba tana tafiya a wani layi da suka shawo kwana, da yake layin babu kowa tana tafiya kai da ganinta ka san hutu ya zauna ma'ana kana ganinta ka san akwai masu gidan rana. Riƙe take da wata jaka irin jakar da ma'aikata suke zuwa office kana kallon jakar a cike take da wani abu. "Iya ji yadda matar can ta riƙo jaka kamar ma dakyar take tafiya saboda nauyin jakar da alama ma kuɗi ne masu yawa a ciki" "Na gani Jaburu dama wannan zamani wasu ne suka san babu amma wasu basu san ma mene ne babun ba, ina ma mu ne da kuɗin nan da mun warke kakar mu ta yanke saƙa" "Wallahi kuwa ai kuɗi sun yi, to Iya ko dai tun da ba kowa jakar za mu warce mu gudu?" "Wallahi kamar ka shiga raina Jaburu amma ina tsoro" "Babu wani tsoro ai a guje za mu bar layin tun da dai ba kowa" "To bari na fita na warto mana sai mu gudu ai yanzu sai dai Allah gafarta mana ƙasar ce sai a hankali kuma mu ma dai jiya ka ga ai saurayin nan ne ya yi ciki da faɗi da kuɗinmu ina ga ma Allah ne ya maido mana da mafi alkairinsu" Ta faɗa lokacin da Jabiru ya rage tafiya ganin sun zo dab da matar. Matar ta sakankance tana tafiya sai ji ta yi an warce jaka tana waiwayowa sai ganin ta yi wacce ta warta ta shige napep kafin ta yi ihun a kawo mata ɗauki har sun bar wajen a guje ga ba kowa a layin. Su Iya kuwa afujajan suka ƙarasa gida suna zuwa Iya ta buɗe get suka shige suka kulle da yake unguwar dama kamar ta munafukai babu kowa a layin nasu kowa yana gidansa bai damu da wani ba, dan tun zuwansu har yau basu taɓa ganin yara ma a unguwar ba bare manyan. "Kai kakanninmu sun yanke saƙa ba ma kakar mu ba" Jabiru ya faɗa lokacin da ya ji nauyin jakar. "Ai sai mun sati bama fita sai dai mu je mu siyo nama da nonon roba, sai mun murmure sannan"Iya ta faɗa tana ƴar dariyarsu ta manya ta saka mukulli ta kulle ƙofar falon. "Ya kike rufewa?" "Saboda tsaro ba dan tsoro ba, gwara mu irga kuɗin a tsanake ka san su kuma al'aura ne suna son a suturte su" Ta faɗa tana zama a tsakiyae falon ta barbaje Jabiru ma ya zauna suka saka jakar a tsakiya. Jabiru ne mai buɗe gaba ɗayan su sai da suka miƙe tsaye saboda tsananin kaɗuwa da suka yi ganin kuɗi na mamaki wanda ya shallake tunanin su. Da sauri suka koma suka zaune a tare idanunsu ƙurrr a kan kuɗin da gaba ɗaya ƴan dubu-dubu ne rafa-rafa har rige-rigen kai hannu ake tsakanin Iya da Jabiru kowa sai ɗauka yake yana ajiyewa a gabansa sai da suka fito da gaba ɗaya rafofin daga cikin jakar har lokacin suna mamakin yawan kuɗin "Ita kuwa matar nan ina za ta je da himin kuɗi haka? Kuɗi dami-dami, wannan kuɗin ai ya wuce misali" Jabiru ya faɗa yana kallon Iya hannunsa hagu da dama riƙe da rafa ɗai-ɗai "Kai dai bari Jaburu wannan ai shashanci ne faɗa da sirika ranar biki, in ba sakarci jiran jirgi a tashar mota ba wane tsautsayi ni zai sa ta fito da kuɗi haka?" "Rabon mu ne ya rantse" "Tabbas dama an ce rabo rawani, yanzu dai mu wari wanda za mu je mu siyo kayan abinci kai har da gawayi in ke mana girkin mu sauran kuɗin kuma mu adana muna cin kaji da kayan daɗi kafin mu saka rana mu je mu kaiwa Alhaji Audu kuɗinsa dan na san kuɗi har ƙara siyan wata gonar ya isa a yi" "Gaskiya Iya kuɗi sun yi a rayuwa ni ko gajiya bana yi da kallon su" Ya faɗa yana washe haƙora. "Yo ba dole ba ai ni da ake cewa kallon korayen ganye yana saka ƙwarin ido to ban yarda ba, ni dai kallon kuɗi ne yake ƙaramin ƙwarin ido" Ta faɗa tana dariya Suna cikin jin daɗin ganin tsagwaron kuɗin sai kawai kuɗi ya fara sawaya yana komawa hatsi(Gero) A tsorace suka tashi tsaye dan gaba ɗaya sai suka tsorata. Rige rigen gudu cikin bedroom domin su tsira amma sai ƙofar beroom ɗin ta ƙi buɗuwa suna rarraba idanu sai kawai suka ga wannan matar mai jaka ta fito zaune a wajen jakar sai dai wannan karon har da farin gemu a duka kuncinan ta a maimakon a haɓarta. Jikin su Iya ne ya shiga tsuma kowanne yake karkarwa kamar mazari, Iya ta fara waiwayen neman mafaka sai kawai ta ji goyo a bayanta ko da ta ɗan juya sai ta hango jarirai har uku ta cikin mudubin falon, goye a bayanta amma babu zani haka kawai suke maƙale da ita a'uziyya ta shiga ambato a zuciyarta amma kafin ta kai ƙarshen a'uziyyar sai ta ga wasu jariran guda biyu a hannunta kallon Jabiru ta yi irin kallon ka ga wata masifar da muka jefa kanmu Jabiru ya rasa bakin magana kafin ƙiftawar idanu sai ga cikin wata tara a ɓullo a jikin Jabiru. "Labbaika lahumma labbaik, labbaika la sharikala labbaik" Cewar Iya a zuciyarta wannan karon hatta laɓɓan bakinta karkarwa suke yi. "Iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in" Cewar Jabiru a zuciyarsa jin hatta bayansa ma an banƙara masa shi ga wannan rututun ciki tamkar naƙuda za ta tashi a lokacin. Iya idan ta kalli jariran hannunta sai ta hango na bayanta a madubi, sai ta kalli cikin jikin Jabiru basu gama dawowa daga duniyar shan mamaki ba, sai kawai suka ga matar nan da jakar sun ɓace. Suna ɓacewa jariran Iya gaba ɗaya suka saki kuka kowanne yi yake inya-inya. "Jarirai biyar Allahumma ajirni fi musibati" Cewar Iya a zuciyata tana lallaɓawa ta yi zaman ƴan bori a wajen tare da sakin kukan ita ma. "Haka jiya aka lakaɗa mini na jaki yanzu kuma ga shi na tashi ta cikin haihuwa ina matsayin namiji" "Yo wane irin kana namiji ni yanzu da nake mace ma ina zan kai jarirai har rai biyar, ko da kukan su aka barni ai an gama saka ni a tsantsar masifa da tashin hankali aradu ni Ansai mun haɗu da jarabawoyi dai a lamarin mu na tahowa birni hayar arincaɓar nan, abin takaicin ma da har yau bamu mori kuɗin arincaɓar ba ko naira biyar sai baƙaƙen azabobi da muke karɓa daga wannan sai wancan... Jan wuyan rigarta da aka fara yi daga baya shi ne ya dakatar da ita daga maganar da take yi hango mudubi ta yi daga nan inda take zaune da yake mudubin dogo ne daga sama har ƙasa kana gani idan mutum kwa yana tsaye daga kansa har ƙagarsa yana hangowa a ciki, baki sake take ganin jariran kowanne ya jan rigarta kuma bayan jarirai duka daga gani sabuwar haihuwa ne in ba kwanan su ɗay ba to basu fi kwana biyu ba a duniya amma har suka iya jan riga suna jan suna kuka. Bata gama dawowa daga shan ruwan mamakin da suka shayar da ita ba sai ta ga na hannunta ma sun miƙa hannu kowanne yana fisgar rigarta, hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa mama suke nema. "Ba zan iya ganin wannan ɗanyan aiki ba abu kamar almara a ce ɗan jariri ya san yake jan riga? Dan dai dama ba jariran mutane bane komai ma suka yi babu mamaki" Iya ta faɗa a zuciyarta tana ɗagowa ta kalli Jabiru domin ta ga shin shi ma yana kallon abin mamakin da take kallo ko kuwa, amma tana ɗagowa sai ta ga ya kifa kai a bango yana rera kuka tamkar wanda aka ce an masa mutuwa. Kafin ta maido idanunta kan jariran sai jin hannun ɗaya ta yi ya sako ta ƙasan rigarta yana lalumar mashayarta. Da sauri ta ɗaga na hannun nata za ta yi wurgi da su amma sai ta ji su tamkar an saka mayen ƙarfe an haɗa ta da jikin su ko ɓanɓaruwa ba za su yi ba. "Na ga annabi in na yi hali na gari ni Ansai yau kuma wace kitumurmura aka shirya mana" Ta faɗa a zuciyarta ita ma tana sakin kukan takaici. "Ansai ki basu mama su sha, wato ki shayar da su su duka, kuma ina so in sanar da ke cewa basa ƙoshi wannan sai su wuni suna tsotsa basu san ƙoshi ba" Ta ji murya an ata magana amma bta ga mai maganar ba. "Kam bala'i na shiga talatin ba ɗaya ni Ansai, wato har sunana ma ake kira to ni da ba shayarwa nake ba ina ni ina shayar da jarirai kuma ma yaushe rabon duniya da aiyaraye ina ruwan ma yake a mamar to ko akwai ruwan ma ai ba zan shayar da ƴaƴan aljannu ba" Ta faɗa a zuciyarta lokacin da ta ji an kira sunanta kuma sai kukan nata ya tsaya cak hatta Jabiru da yake kukan sai ya dakata cike da tsoro dan ya san dai tun da aka ba Iya umarnin shayar da jariran to ana dab da bashi umarnin ya shayar ɗin shi ma tun da aka saka masa tsohon cikin haihuwa. "Ba, ba, babu ruwa ko ɗigo a ciki alqur'an aradu rabona da shayarwa tun shekaru aru-aru yanzu maman nawa ko na basu maɗas yake babu komai" Ta faɗa cike da tsoro tana wurwurga idanu a falon. "Ki basu su mamula ruwan zai zo" Ta ji an faɗa. "Duka fa maman guda biyu ne ya zan yi da sauran yaran" Ta faɗa hawaye yana zubowa tamkar wanda ta shekara bata yi kukan ba, saboda yawan hawayen da yake kwaranyowa kana kallonta ka san tana cikon tashin hankali. "Wayyo bayana wayyo cikina" Ta ji Jabiru ya faɗa yana riƙe ciki da baya. Idanunta masu cike da hawaye ta zaro su cikin sanyin murya da ƙarfin hali ta ce "Ba dai haihuwa za ka yi ba Jaburiu ni Ansai na ga ta kaina namiji da ciki da kuma naƙuda" Ta faɗa tana kallonsa. "Iya kamar cikina zai fashe" "Jaburu ba cikinka bane mararka ce dama haka mata suke jin ciwon mara idan suna naƙuda" Ta faɗa tana kallon jariran cinyarta da ta ji kowa ya kamo mamanta guda ɗaya ta ƙasan rigarta, sai kuwa ta gan shi jalele suna ƙoƙarin kaiwa baki, ga shi babu damar ta ƙwace saboda suna hannunta kuma ba za su ajiyu ba bare ta ajiye su, bakinta ta kai tana son ta ƙwace amma sai ta ga bakinta ba zai iya ba. A haka ta ɗago kanta ta sauke idanunta a kan Jabiru mai naƙuda. "Iya ki kawo agaji dan Allah" "Ka daure Jaburu ni ma ka ga waɗannan ba ajiyuwa za su yi ga shi sai fama nake da su a kan sai sun sha mini mama, ni wannan abu ban san wane irin abu bane kai da kake matsayin namiji amma ga cikin haihuwa a jikin ka tsoho kuma ga naƙuda ta tashi mun ga ta kanmu ni Ansai babban tashin hankalin ma ban san ta ina ɗan zai fito maka ba" "Iya!!!"Ya faɗa da ƙarfi cikin zafin ciwo. "Ka daure dai Jaburu haka naƙuda take wallahi lokacin da na haifi ubanka ma zafin ya fi wannan haka na sha gwagwarmaya ai haihuwa ba kanwar lasa ba ce, duk macen da ka ganta fa ɗanta ka kalle ta kawai s... Maganar ta maƙale ne jin an daɓa mata haƙori a maman ta, idanu ta zaro ta mayar da kallonta kan jariran ashe dai da hankalinta ya koma kan Jabiru mai naƙuda ashe sun samu nasarar kafa mata baki. "Na shiga aljanna in na yi hali na gari ni Ansai haƙori kuma a bakin jarirai? Ban lura da haƙoran ba da suna kuka" Ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta. Bata gama mamakin ba ta ji Jabiru ya saki ƙara tana maida idanunta kansa sai ta ga ya durƙushe a wajen ganin babu yadda za ta yi da jariran nn masu mamanta a bakinsu tsna jin suna datsa mata haƙora tamkar masu cizon ta da gayya, sai kawai ta yi dabara ta miƙe tsaye ga na bayanta ma basu bar kukan ba kuma suna jan rigarta duk sun cika gidan da kuka, dama jariri ɗaya ma in yana kuka cikawa mutane kunne yake bare jarirai biyar dan dai na hannun nata da suka saka maman a bakin su sai suka yi shiru a haka ta ƙarasa kusa Jabiru. "Marata Iya bayana" "Jaburu kamar fa haihuwar ta zo gadan-gadan, ni Ansai yau na ga abin da ya fi ƙarfina Allah ka kawo mana ɗauki a wannan gida da muka garƙame kan mu babu ma wanda ya san muna ciki bare a zo a taimake mu" Ta faɗa tana sakin wani marayan kuka. "Wayyo ni ban taɓa jin ciwo haka ba, ina ga mutuwa zan yi" "Bar ambaton mutuwa Jaburu ciwon naƙuda kawai ai haka mata suke fama, kama ƙafata ka riƙe amma kar kake nishi sai ka ji nishin ya zo da kansa" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma sai ta ce "Yau na ga baƙar masifa da rana tsaka, to ni wannan yaro ta ina ɗan nan zai fito masa in dai ba ta wajen kashi ba ko kuma cikin nasa ya buɗe ɗan ya fito na san dai a halittar namiji babu mafitar ɗa kai wannan abu da wuyar sha'ani yake ni Ansai" Ƙafarta Jabiru ya kama sai kuwa ta ji ya fara nishin fitowar ɗa, a gefe ɗaya kuma ga jariran bayanta sun ɗago rigarta kowa ya samu jikin fatar bayanta yana gwagwiya tamkar sun samu goruba, dan kowanne tana jin yadda tsinin haƙoransa suke cakar mata fata. Daurewa kawai take amma shi take tamkar ta yi ƙaramar hauka a take ta ji ta yi dana sanin zuwansu birnin ma gaba ɗaya. *Last free pages domin shiga grp ki karanta har karshe ki tura 5OO ta acc faiza abubakar 9030283375 Opay ki tura shaidar biya ta 09013181851* . . Kar ki bari mu yi tafiyar nan babu ke akwai cakwakiya a gaba ba zan ce komai ba🥰 KU MATSO DOMIN JIN DADDAƊAN LABARI . ZAN CIKAWA KOWANE MUTUM ƊAYA DUBU GOMA 1OK Shin kin taɓa jin labarin 52U? Yadda mutane suke register da cin moriyarsa, da dala 21 ake yi $21 kimanin 35k. Duk wacce za ta yi register a team ɗina zan cika mata dubu goma 1OK ta kawo 25k sannan duk wata zan ke bata 15k tsawon wata 3 idan acc ɗinta ya cika wata shida zai buɗe sai ta cigaba da kwashe kuɗaɗenta. Mutum 2O nake nema kar ku bari damar nan ta wuce ku ki mini magana a PC 09013181851