MACE A YAU Written by Shatuuu The story of Sulaim and Khulthum, the two besties and bussoms. Completed Shatuuu095@wattpad KAINUWA WRITERS ASSOCIATION [6/16, 10:31 PM] Anty Fauzar: 💄💅💖 👜👠💖 *MACE A YAU!* 💄💅💖 👜👠💖 01 ✍️Shatuuu ♥️ Shatuuu095@wattpad 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION This page completely, wholly goes to Anty Sumayya...... I hail you "Abu daya zan fada miki shi ne yanzu kin girma kin mallaki hankalin kanki, Kinsan daidai da wanda ba daidai ba, Kinsan idan akace *budurci* ko virginity Kinsan me hakan yake nufi, nasan Kinsan shi ne Abinda ya zaunar damu gidan mazajenmu har yanzu, idan kika Bari ya kubce miki I'm so sorry to say bana tunanin zakiyi darajar da wadda ta kaishi gidanta zatayi, inason Kiyi tattalin shi don kuwa shi zai fadi tarbiyya da kika samu. Kada wani ya baki abu ki karba Kici, Kada wani ya kaiki alley ko wani isolated area, Kawaye kisan wacece kawarki da kuma wa kike mu'ammula dasu .... Abu na karshe ki kula da addininki sannna kiyi hakuri shi ne rayuwa! " Se lokacin Mami tayi shiru yayinda Baki daya Sulaim tayi shirun tana sauraren mahaifiyar ta, dago kanta tayi muryar ta Cikeda rauni tace Inshaaa Allah Mami, bazan Baki kunya ba, zan zame miki abin alfahari! Kai Mami ta gyada tace "Allah yayi miki albarka, idan kikayi haka kin gama mana komai" "Amin" Sulaim ta furta kafin Mami tace Kije ki shirya da munyi La'asar Zamu fita, make sure kin saka dan kunne da sarka. Murmushi Sulaim tayi wanda ya fito da dimple dinta hakan yasa tayi kyau sosae dukda maganganun Mami taba ta suke ga kuma kewar gida da ta Fara ji Tun kafin lokacin tafiyar. Mikewa tayi jiki a sanyaye 1 Don komawa dakinta, dakin yana facing wanda ta fito Daga ciki, tura kofar tayi nan take komai na ciki ya bayyana, oil paint ne jikin bangon dakin purple colour wanda yasa dakin yayi dan duhu kadan, gadonta Irin silver poster bed dark purple, se wata resting chair a gefe, Daga Dayan barin akwai study table da kujerar shi sannan walk in closet da kuma toilet, akwai stickers a mammane jikin bangon dakin hakan yasa dakin ya zama very girly. Tana ta jan kafa ta fada gadon tayi rub da ciki, hakan ya kasance aladar ta duk lokacin da take son tayi tunani ko kuma ta zama emotional haka nan. Ta jima a Wannan yanayin kafin kiran sallar laasar ya tashe ta, mikewa tayi ta shiga toilet wanda komai na ciki yake light blue ta daura Alwala, wani lungu ta isa a dakin ta shimfida sallaya ta Bada farali, Tana idarwa taji ana knocking hakan yasa tace Yes... Come in please Yarinya ce wadda shekarunta bazasu wuce sha uku ba ta shigo tace Anty Mami tace ki shirya. Kai kawai ta gyada hakan yasa yarinyar ficewa ita kuma ta isa gaban dressing mirror dinta ta Fara assessing kanta, atamfa ce jikinta turquoise green se circle pattern pink, dinkin skirt da Riga ne, kasancewar batada kiba yasa kayan sukai mata cas a jikinta, powder ta shafa ta gyara daurin dankwali ta feshe jikinta da turare sannan ta yafa pink veil ta dauki jaka tayi hanyar fita, kafin ta kai ga bude kofar ta dawo da sauri ta janyo drawer ta dakko dankunne da bracelet sanin matsawar ta fita haka se Mami ta dawo da ita, saboda Mami mutum ce da ta dauki abubuwan mata da muhimmanci. Tare suka fito Daga dakunan su, seda Mami ta gama assessing Sulaim kafin ta gyada Kai Tace "ko ke fa gashi kinyi kyau abinki kin fito a mace" Murmushi kawai tayi saboda ita din ba Mai yawan magana bace, batada surutu ko kadan wanda hakan yake fito da gentility dinta. Jakar Mami ta karba ta rufo dakunan kafin suka sakko downstairs, gidan ya hadu karshe duk yadda zuciya zata kai ga hasashe to abin ya wuce haka. Suna isowa tsakiyar falon sega wani matashin saurayi ya turo main kofar parlour Sanye da kananan kaya wanda sukai masa kyau suka fito da tsantsar yarintar shi, da murmushi saman fuskarsa ya karaso har inda suka ja tunga, Mami ina zaku je da yammar nan? Ya tambaya Yana maida dubansa kan Sulaim wadda Ke kallonshi fuska dauke da murmushi, Inda Jawad ubana ya aikeni. Baki daya suka saki dariya Don karan Mami da Jawad babu wasa, fuska ya bata yace Haba mana Mami daga tambaya, Kallon Sulaim tayi tace Leka kice dasu Iya Abu mun tafi. To Mami" ta amsa mata kafin ta rabe Jawad ta nufi wata kofa, Baifi 5 minutes ta dawo suka fita duka su ukun banda tsokana babu Abinda Jawad kewa Mami ka rantse da Allah Kace Mami din kakar shi ce, a haka suka isa bakin wata bakar Prado se kyalli take, suna isa wani daga cikin sojojin dake bakin gate ya iso tareda saluting Mami, kanta ta gyada alamun ta karba tace Babu damuwa, da jawad zamu fita. Kanshi ya gyada yace OK Ma'am Jawad ya amsa key din ya shiga Mami ta kame a baya yayinda Sulaim ke gefen Jawad, suna tafe suna hirarraki gwanin shaawa. A gaban wani katon mall yayi parking suka fito, cikin nitsuwa suka taka ciki inda babu bata Lokaci suka Fara shopping yawanci cosmetics ne, toiletries se suka fada boutique din inda Mami ta dinga dibar kaya yawancinsu Abayas ne se kuma suit suit na mata. Sun kusa 2hours a ciki kafin akai musu packaging aka kai har mota Jawad se cin magani yake Don babu Abinda Mami ta siya mishi, daya isheta da mita se cewa tayi Jawad kudinka ne ko nawa? Itakam Sulaim murmushi kawai take a haka har suka je gida. Bayan kwanaki biyar aka gama dukkan shirin tafiyar Sulaim BUK inda anan ta samu admission into Law, kullum zancen Mami daya ne Sulaim ta kula da wayanda take mu'ammula dasu da kuma addininta, sanin son da Sulaim ke yiwa Law batada matsala hakan yasa Bata taba ce mata tayi karatu ba don tasan zatayi. Mami is very caring kuma Bata wasa da yayanta especially akan Sulaim wadda gani take amana ce Allah ya bata kuma duk idanun duniya na kansu, da zarar wata baraka ta auku zasui dariya tareda Allah ya kara..... This is the world we live in! Da kanta ta hada mata kaya duk Abinda tasan zata bukata seda ta saka mata tareda sake jadadda mata kula da kanta da addininta. Kasancewar early February ne garin na Kano yayi lum shi babu Rana kuma haka babu zafi se guntun sanyi da bai gama wucewa ba. Cikin bakar Benz Ja'afar ke driving Wanda shi ne male version na Mami saboda yadda kamannin Mami suke prominent akan Fuskarshi, babu yabo babu fallasa haka yake murza steeree Cikeda kwarewa yayinda a gefenshi Sulaim Ke Zaune tana cikin abaya wadda stones suka kawata ta, fuskarta tayi fayau se idanunta da ta boye su cikin dark shade hakan ya bayyanar da pointed nose dinta. Itama fuskarta tayi kyau sede she looks pale. A baya kuma Mami ce Tana rikeda newspaper itama tayi kwalliyarta da yake ita mutum ce me kwalliya. Gefenta Dan gidanta ne Jawad Hannunsa rike da waya Yana ta danne danne ga uban headphone ya saka hakan yasa gaba daya hankalinsa baya cikin motar. Wayarta dake hannun Sulaim ce ta Fara ringing, ba tareda ta duba ba ta mika mata se ji sukai tana fadin Soja marmari daga nesa, I salute you Baki daya dariya suka saki Don sunsan Jabir ne his father's inherent the thug of war..... A tsanake yace Mami barka da warhaka Barka dae, ya aiki dasu Imratu? Gaba daya suna lapiya? Kun tafi Kano din. Kai Mami ta gyada kamar yana gabanta tace Gamu a BUK road, mun kusa gidan. Dan tsaki yayi yace Mami place me on speaker Haka kuwa akai Sega muryarshi ta cika motar Baki daya, duka suka gaisheahi yana fadin Sulaim Duk Abinda Subay'a tayi miki just call me kinji? Murmushin nan dai shi tayi tace Angama Yaya JB Se kuma ya koma kan Ja'afar yace Mutumin make sure you strictly warn Subay'a cewar autar Mami ce Sulaim Kada tayi wani Gigi.... Kafin ya bashi amsa Mami tace Bakuda kirki matar yayan naku kuke yiwa haka, kanada digit dinsa call him but not through my phone. Daga haka kit ta kashe wayar aikuwa suka saki dariya kafin suka koma yadda suke. A unguwar rijiyar zaki dake gefe daga tsakiyar birnin na Kano anan gidan babban yaya Junaid yake inda a tsarin Baba da Mami nan ne gidan da Sulaim zata zauna Zuwa lokacin da Allah yayi. Horn yayi take aka wangale gate din inda farfajiyar gidan ta bayyana, Cikeda kwarewa ya danna motar ciki ya samu gefe yayi parking motar wanda hakan ya janyo hankulan mutane dake cikin gidan. Yara biyu ne suka fito a guje baki daya bazasu wuce shekaru shida da uku ba, gurin Mami suka Fara isa suka dane ta saboda lokacin kowa ya fito, itama hannunsu ta rike baki daya suka nufi kofar parlour, seda sukai sallama aka amsa kafin suka shiga baki dayansu, babu kowa se Nanny din yaran da take tattare toys din da Ahmad yayi wasa dasu, suna zama Sega wata farar mata ta fito wadda shekarunta bazasu wuce 25 ba, kyakyawa ce Irin shouting beauty hakanan take irinsu masu manyan kyau kuma as kana Zaune dasu time zaka gane cewar ba wani mashahurin kyau bane ba haka Subay'a take mace daya tak wajen Junaid uwa ga Muhammad da Ahmad. Kujera daya ta samu ta xauna fuskar ta babu annuri ko daya tace Mami sannu da zuwa Inda sabo kowa ya saba da halin subay'a, babu Wanda taki jinin gani sama da 'yan uwan Junaid hakan yake tsoratar Dani Irin zaman da xa'ayi tsakaninta da innocent Sulaim. Lapiya lau Subay'a ya yaran. Lapiya. Daga haka babu Wanda ta kara yiwa magana se Sulaim da Jawad suka gaisheta suma tana ta cika da batsewa ta amsa, dama Ja'afar tasan karya take tayi tunanin zaiyi mata magana Don ya fita zafin kai. Ko ruwa bata basu ba suma babu Wanda ya nema cikinsu se su Muhammad ne Ke ta faman basu labarai yawanci na school da islamiyya. Har wajen Mintina sha biyar suka shude Bata ce musu Kala ba haka suma, se Mami tace Subay'a Junaid baya nan ne? Dago idonta tayi daga Kan wayarta data Ke dannawa tace Ahmad go call your Papa. Baki daya tsananin mamaki ya mamaye su kada ma Sulaim taji labari don tasan yadda Matar Yaya Jabir take musu yadda kukasan ta hadiye su Don Imratu is one among millions, unlike Subay'a wadda ita dole yaki ke tsakaninta da dangin miji. Ja'afar ne ya bude Baki yace Amma ke anyi....... Sabr! Sabr!! Ja'afar Mami ta katse shi kanta ta sake girgizawa tace Don't do that, allow her. Shiru parlour ya ratsa, Sulaim na kara girmama hakurin Mami cikin ranta, is not like tunda tazo duniya take tareda Mami amma shekaru hudu da tayi tareda su Bata tunanin akwai rana daya da taga wata baraka daga gurin Mamin ko alamun rashin hakuri ko fada she's the best woman she have ever seen a rayuwarta, Shiyasa Mami is her role model. A hankali Cikeda nutsuwa da tsantsenin inda kyakyawar kafarshi zata taka ya fito Daga wata karamar kofa, dogo ne Yana da tsayi, jikinshi a murmure yake babu alamar rama ko daya, shi ba fari bane haka zalika baya cikin layin bakake, yana Sanye da jallabiya brown me short sleeve, kanshi babu komai banda suma wadda batada yawa kasancewar shi ma'abocin aski, ko cikin mata aka samu mutum me tsaftar Junaid lallai se ayi barka. Bakinshi dauke da sallama ya iso parlon sede ganin Mami da ahalimta yasa yaja ya tsaya kafin ya maida dubansa kan Subay'a wadda gaba daya hankalinta yana kan wayarta, Mami kada kice min tun dazu kukazo? Subay'a me yasa baki kirani ba se yanzu? Sulaim ya banga an kawo muku komai ba? Duka cikin seconds yayi maganar ko nace tambayar, baki daya kallonshi suke da tausayi Don Yana son yan uwanshi musamman Mami da Sulaim. Murmushi Mami tayi tace Relax Junaid, yanxun nan muka zo, zauna a gaisa ko. Kasa ya tsugunna yana sauke ajiyar zuciya ya gaida Mami sannan ya samu cushion ya zauna, nan sauran suka gaishesu se kuma hira ta balle, can Sega Subay'a da abinci da drinks itada masu aikinta. Babu Wanda ya kalli abincin bare suci se Jawad ne dake food monger ne baya wasa da abinci. Subay'a. Mami ta kira sunanta lokacinda suka Mike don tafiya, dagowa tayi batareda ta amsa ba itama Mamin she wasn't expecting such don haka ta cigaba da fadin Ga Sulaim na kawo gidanku zata zauna, ban taba rokarki abu ba amma yau na roke ki da Allah ki kulamin da amanata kamar yadda kike kula da Ahmad da Muhammad. Kinsan wacece ita idan kika cuce ta Keda Allah! Tana gama fadar haka ta nufi kofar fita, duka suka mara mata baya Harda Sulaim wadda ta Fara sharar kwalla. Shatuuu ♥️ [6/17, 7:38 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU!* 02 ✍️Shatuuu ♥️ Shatuuu095@wattpad 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION Fitowarta kenan daga daki, fuskarta dau tayi wani Irin haske kamar fitila Sede babu digon kwalliya a fuskar hakan yasa fuskar ta kumbura saboda rashin kwalliyar Don ba sabon Khulthum bane zama babu make up, Duk bala'i Duk masifa Bata taba fita se tayi kwalliya hakan yasa matsawar ta fita batai kwaliyya ba to se ta koma tamkar Marar lapiya. Gidan karami ne Wanda dakuna kwatakwata biyu ne a ciki kanana wanda Bana tunanin zai cinye gado da wardrobe amma hakan bai hana mazauna gidan alfahari dashi ba. Se Bandaki a gefe da ko kofa babu se buhu, Daga gefe akwai langa langa (zinc) da aka gewaye Dan karamin guri da ya bada kitchen wanda duk ranar da ruwa ya taso bansan a ina matar gidan zatayi girki ba. Tunda ta fito baki daya babu annuri ko digo saman fuskarta, tana sanye da bakar riga wadda tayi dabbare dabbare, tabarma ta shimfida sannan ta dubi yan matan dake tsaye kikam tace Bismillah. Babu musu suka zauna ita kuma ta koma ciki, dakin wata yan kwananniyar katifa ce a shimfide a mata shimfidawa bedsheet, Daga gefe na hangi akwatuna wajen biyar a jibge ga kuma katuwar Ghana must go a Cike taf da kaya, daga gefe kwanuka ne cikin kwando, daidai Bayan kofa ta tsaya inda buhun Lalle yake a jingine ta diba sannan ta tsugunna ta kwaba da sinadaranta, seda ta gama tsaf sannan ta fito inda yan mata biyun ke jiranta, seda suka gaisa kafin ta Fara da wadda nake tunanin Itace babba, Tunda suka Fara bata ce dasu uffan ba se waya da take abinta. A hankali yara suka Fara dawowa daga islamiyya, biyu Maza se uku mata, ko sallama basui ba suka shigo hakan yasa Khulthum tace Dan ubanku ku fita a gidannan kuyi sallama. Babu Wanda ya kalleta cikinsu sema dakin dake gefen nata da suka shige, tsaki tayi ta cigaba da kunshin sega Amira ta fito ta zo inda ake kunshin ta tsaya Don babu Abinda take so irin yadda Khulthum ke designing kafafun mutane Amma Khulthum taki barinta ta koya. Uban me kike Yiwa mutane Akansu? Dallah bar gurinnan. Sumsum ta wuce, ta samu dan nesa da gurin ta zauna don Tana hangowa, amma ganin haka yasa Khulthum daukar mafici ta wulla mata tareda fadin Ke mayyar Inace ne, dallah tashi kafin na karya ki. Mamaki sosae ya kama yan matan har daya a ciki tace 'Yar President dan Allah ki Bari ta gani mana. Dake duk wanda yasan Khulthum da 'Yar President ya Santa saboda idan kuka hadu a waje karya kake Kace daga wannan gidan take, sede kayi tunanin Irin yar wani shegen ce baka taba tunanin Wannan kufan ne gidansu ba. Rabu da ita, wanke wanke zatayi tasan aikinta ai. Turo Baki Amirar tayi tace Ki bayar a siyo OMO Kinsan babu. Batace komai ba ta cigaba da kunshin har ta gama Sega sallamar wata dattijuwar mace ta shigo da kuma alamun Matar gidan ce saboda yadda suke kiranta da Mama. Bakin kofa ta zauna, yanmatan suka gaisheta Khulthum tayi mata sannu da zuwa sannan ta koma gefe tana waya. Amira maghariba ta kawo Kai ace har yanxu ba ayi wankewanke ba. Mama to babu OMO a gidan ya kare. Tsaki Mama ta danyi ta dubi inda Khulthum ke Zaune tace Ummu bayar a siyo OMO Kada dare yayi. Kafin Khulthum ta bada ansa A'isha ta fito tace A hada da kudin ashana da gishiri saboda suma sun Kare. Wai gidan ubanwa ake kai kayan gidannan ne? saboda ba ubanku ke bada kudin ba yasa kuke almubazarranci. Ni na gaji Wallahi. Gaba daya babu Wanda ya tanka hatta Maman se ta kunce bakin zaninta ta ciro hamsin tace Gata nan canjin da na dawo dashi Maza kiyi sauri ki sayo a tsallake. Karbar kudin tayi ta fice, yayinda Khulthum ta Fara kiran Amir, amsawa yayi tace Je ka karbo min kayan guga kasan gobe zan fita. To Ya fada ya cigaba da tsayuwa, tasan Abinda yake so amma se ta share shi ta cigaba da Abinda take, ganin da gaske bazai je ba ta ciro 200 ta mika masa, murmushi yayi yace Yanzu kika Yi magana hajiyata. Daga haka ya fice. Ana Idar da sallar isha'i yayi daidai da gama shirin Khulthum, tayi wani Irin fittinnan kyau, babu kuma abinda Ke tashi Daga jikinta banda wani kamshi me dadi. Gyara zaman mayafinta tayi ta fito Daga daki, tabarma ce a shimfide inda duka yaran Ke Zaune se A'isha da take bakin murhu tana karasa abincin dare, babu Wanda tace wa Kala tayi hanyar zaure se Mama ce tace Kulthum ina zakije. Tsayawa tayi batare da ta juyo ba tace Ashir ne a waje Yana jirana. Daga haka tayi waje ta bar su da kamshinta, a kofar gidan Ashir na tsaye gefen Lifan dinshi ya durkufar da kanshi yayinda wani magidanci ke tsaye wanda ya tabbatar min cewar shi ne mahaifinki Khulthum saboda fuzgar kama da suke da Amir, matsowa tayi tace Baba sannu da zuwa Juyowa yayi yace Sannu dai khaltume, kin barshi Yana ta faman jiranki. Kanta ta sunkuyar ba tareda tace komai ba amma tana takaaicin sunan da Baba ke kiranta dashi Se Kace lokacin jahilliya zai dinga kiranta da khaltume, wucewa Baban yayi nan suka gaisa itada Ashir wanda bakinshi ya kasa rufuwa tamkar gonar auduga shidai Allah ya Dora masa zazzafan son Khulthum yarinyar tayi masa, kallonta yayi yaga Baki daya hankalinta yana kan machine kafin ya kai ga magana tace Wai se Yaushe ne zaka siya mota? Ni na fara gajiya da ganin ka da Lifan dinnan. Dan dariya yayi yace Rai dai Khulthum kuma ma banda abinki nida ba aiki nake ba ina zan samu kudin mota. Tsaki tayi tace Maganar kenan kullum, sa'oinka nawa ne suke da mota? Kanshi ya dafe yace Khulthum Haba mana, stop comparing me to others, ni daban sauran daban kowa yadda Allah ya tsara mishi daban. Kara bata rai tayi zatayi magana yayi saurin beating dinta yace Don't suffocate the environment please, kinga yadda kikayi kyau...... Bana tunanin duk duniya akwai Wanda yayi Saar Irin tawa. For the first time Tunda ta fito ta saki murmushi wanda yake na gaske daga karkashin zuciyarta tace Kaima kayi kyau. Kanshi ya gyada yace Not as beautiful as you, so gobe zaki fara lecture ko? Idan ta tuna wannan jinta take burinta yana daf da cika, idan ta tuna makaranta kuma university itadinma BUK tana jin kamar da saa aka haifeta Abu daya zan rokeki, ki maida hankali Kiyi karatu, kada kina comparing kanki da wasu kowa rayuwarshi daban Allah ya tsara mishi abu na karshe ki kula min da kanki ki rike min alkawari. Bata ce dashi komai ba Don alkawarin yayi tsauri Bata tunanin zata iya wannan amma karatu confirm zatayi to dole ne ma ai duk kudin da ta kashe wajen registration da komai tayi wasa ai kanta tayiwa. Ranar ta kasance Monday...... Monday tushen aiki Formula uwar lissafi. Tun asuba Sulaim ta farka, gaba daya kewar Mami take dukda Kwana biu da tayi amma ji take tamkar sunyi shekara basu tare, sallah ta Fara yi sannan tayo wanka ta Fara shiryawa tana yi tana azhkar har ta Kamalla ta Fara kiran Mami sede kafin ta kai ga shiga Mamin ta kirata through her other phone, sun kusa 10 minutes suna waya Tana sake mata nasiha da jin ko akwai wani abu amma tace komai lafiya, a haka sukai sallama kafin ta fito parlour, lokacin shida daidai ta buga, parlon babu kowa amma tana jiyo motsi Daga kitchen hakan yasa ta nufi can, yanmata ne guda biyu suna ta aikin hada breakfast, da sallama ta shiga suma duka suka amsa suka gaisheta fuska a sake, ta ja kujera ta zauna Tana bin movement dinsu da yadda suke aiki Cikeda kwarewa da alamu dai sun samu training a wannan harkar, hira suke Yi suna sako ta a ciki Jefijefi tana basu amsa a haka suka kammalla komai daidai shigowar matar gidan, Tana Sanye da bakin skirt irin boutique dinnan daya Kama Nata jiki se top Fara da matching waist coat a jikinta, kanta bakar hula ce, Tana shigowa gaba daya sukai shiru tamkar ruwa ya cinyesu se gaisheta da suke, kamar kullum babu digon wasa ta amsa se sannan Sulaim tace Ina Kwana Juyowa tayi ta dube inda Sulaim ke Zaune, ita bata Lura da ita ba ma kwatakwata, Memakon amsa gaisuwar Tace Me kike Yi anan? Aren't you going for lecture? Kanta ta gyada tace Na shirya kawai shigowa nayi. Kafada ta daga Irin damuwarki ce ta dauki abinda zata dauka ta fice itama Sulaim sallama tayiwa su Atika ta nufi dakinta ta shirya cikin simple gown ta lace, ta hada komai cikin karamar backpack dinta ta fito parlour, wannan karan kusan tare suka fito gaba dayansu har yaran. Yaya ina Kwana? Ta gaida Junaid wanda ya fito Yana nannade hannun rigarshi, with concern yace Auta kin tashi Lapiya Brightest smile ta saki tace Lapiya lau Alhmdllh. Basu Kara fadin komai ba suka nufi dining table inda Atika take tsaye Tana jiransu, suna zama Muhammad ya tashi ya dawo cinyar Sulaim, kallonshi Subay'a tayi tace Koma seat dinka. Baki ya turo tareda kankame Sulaim, murmushin nan tayi ta shafa kanshi tareda rada masa abu a kunne, take ya fara dariya hakan yasa Ahmad shima tasowa ya dawo gefenta, cikin iyayen basu Kara fadin komai ba haka aka ci abinci wanda kusan Rabi wasa ne tsakanin Sulaim dasu Ahmad. Subay'a ce ta Fara tashi tare da wiping bakinta da saviette ta matso inda Junaid yake ta bashi peck a kumatu tace Ni na wuce Murmushi kawai yayi yace All the best! Thanks! Ahmad bye.... Muhammad be a good boy. Daga haka ta zari key din motarta da handbag tayi waje abinta. Junaid ya kalli Sulaim wadda tayi shiru deep in her own thoughts yace Sakawa Muhammad uniform kuzo mu tafi. Tohm Yaya . Basufi 10 minutes ba suka fito shirinsu tsaf waya a kunnenta tana waya, tunda ta fito Junaid Ke binta da ido har Seda ta gama wayar ta kalli gefenshi kafin yayi saurin dauke idonshi, bata damu ba tace Yaya we're set, ina Ahmad zai zauna. Se yaji dadi ganin she's concern akan yaranshi yace Nanny dinsa tana hanya ki barshi gurin cooks din can. Cikeda gamsuwa ta wuce ta kaishi se kuka yake akan shi binta zaiyi, haka ta taho tana jin wani iri cikin ranta. Seda yayo baya ya sauke Muhammad a Al'azhar kafin ita dashi suka nufi new site, kasancewar sune most reserve a yaran Mami yasa tafiyar haka akai yita shiru kamar babu mutane. Cikin sa'a wayarta ta Fara ringing, hannunta ta zura ta ciro ta Daga purse tana dubawa taga LUFF, se taji bazata iya picking ba haka wayar ta katse Ja'afar ya sake kira anan ne Junaid ba tareda ya kalleta ba yace Pick up your call. Swiping tayi ta Kara kunnenta take Wannan muryar tashi me dadin sauraro ta Fara zagaye mata ko ina na jikinta wanda take ya saka mata wani Irin shauki, ta tabbatar Ja'afar is beyond words ya iya tafiyar da Wannan harkar. Uhmmm ina Kwana? Murmushi tayi ta kalla gefen Junaid wanda Baki daya hankalinshi a zahiri yana kan titi ne amma a badini yana gurin Sulaim. Eh muna hanya........ To zan kiraka Anjima a gaida Mami da Yaya Jawad. Wannan furucin Nata ya tabbatar masa Ja'afar ne, maida wayar tayi handbag dinta a haka suka isa Faculty of Law, wani Irin dadi taji a zuciyarta this is the beginning of the journey...... Tare suka fito ita dashi, a nutse suke tafiya a haka ya rakata har class Seda ta zauna kafin ya fita dama tun a mota yace Duk Abinda take so ta kirashi saboda shima a Faculty yake. Ranar Bata wani Saba da kowa ba, taji dadin classes din musamman na English for legal writing, amma logic dinnan ne se a hankali. A haka ranar ta Kare Junaid ya dawo daukarta batareda ta Saba da kowa ba don Tana ganin is too early ta samu kawa. *I've seen every of your prayers, your comments and wishes. I'll forever remain grateful...... But dont be xpecting post everyday because I've so many things to attend to but will try my every best to see that I didn't keep you waiting......Thanks for understanding* Shatuuu ♥️ [6/20, 11:56 AM] +234 701 517 3116: *MACE A YAU!* 3 ✍️Shatuuu ♥️ Shatuuu095@wattpad 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION Tunda me napep ya direta a layin da zata shiga gidansu kasancewar machine ne kadai yake iya shiga shida keke cikin kwanciyar hankali amma sauran kam sede addu'a saboda yadda kwata take cike ga kuma tsuku da gurin yayi kowa yasan idan akace Rimin kebe a kano Irin merciless ghetto area dinnan to nan gidansu Khulthum yake, tunda ta sakko mazan dake zaune yan kashe wando suke buga ihun Talaka me girman kai....... Se wasu suce .......Allah zai kona shi. Sarai tasan da ita suke da Wannan sabon su ne har ta Saba, haka ta ratse ta wuce, gaba daya yau bata wani fahimci karatu ba saboda yadda take kalle kalle tun kafin ta shiga class taga yadda yara kanana suke zuwa cikin manyan dankara dankaran motoci, shiga iri iri ta Kece raini se taji tamkar kowa ita yake kallo a gurin, ga hottest phones da ta dinga gani a hannun mutane ita kuwa tata Nokia torch light ce. A haka ta isa gida amma Tun Daga nesa ta hangi Ashir a tsaye da dukkan alamu ita yake jira , se taji for the first time ta rainashi taji bata tunanin tana ganin Irin wannan mazan a waje zata iya Auran Ashir ta cigaba da zama ghetto gaskiya ina, yadda ta tashi cikin talauci gaskiya ba zata dawamma a cikinshi ba no! And never! Tana zuwa inda yake ta tsaya tana dubanshi shima kallonta yake yana mata murmushi, Duk gajiyar ce haka ko gaisuwa ban samu ba, bare Ayimin murmushi Murmushin ta danyi tace Na gaji Wallahi, ruwa kawai nake son naji a jikina. Kanshi ya gyada yace Bari na barki ki shiga gida dama zuwa nayi na ji yadda ramar ki ta kasance, amma anyways gobe ki shirya da wuri zanzo na kaiki.... Ina? Tayi saurin tambaya, dariya yayi yace School mana Tunda munada machine inaga zai rage kudin xirga xirgar Da sauri ta girgixa kanta tace A'a dan Allah nagode, Dan Allah Kada ka gwada hakan, I'll be OK hakan nan. Bata jira abinda zai kara fada ba ta shige zaure a ranta tana fadin lallai Ashir Bakada hankali wasu na Zuwa a mota kawai se a ganni kwam kan Lifan Haba dai! Allah ya kiyaye. Shikam baki bude ya tsaya Yana mamakin sanyin Khulthum, hakan nan dai jiki babu kwari ya burga Lifan dinsa ya wuce. Zaune ta samu Mama da Aisha se Amir suna hira, gidan kalkal yasha Shara gwanin shaawa saboda daga Mama har yaran babu Wanda zakaga element na kazanta a tattare dasu, shikanshi simintin dake malale tsakar gidan an wanke shi tas se kyalli yake, dama bawai tana sallama bane Tunda ba koya maka akai ba kuma baji take a Nayi ba balle tayi picking, haka ta shigo kadaran kadahan kana kallonta kasan rana ta daketa ga gajiya da tayi mata rubdugu, gefen dakin da suke Kwana ta zauna wanda kusan nata ne ma kawai Kwana kawai yaran keyi amma baki daya kayansu da komai yana dakin Mama saboda Khulthum ta kafa ta tsare. Da kulawa Mama tace Khulthum an dawo Daga makarantar. Fuska ta yatsina tace Mama akwai wahala. Murmushi Mama tayi tace Se hakuri, Aisha tashi zubowa Yayarki abinci. Turo Baki A'ishan tayi tace Mama ita taje ta zuba da kanta mana, Kinsan ko an zuba mata zatace ba zata ci bane. Mama tanada wani abu matsawar ta saka Abu ka Kiyi to tabbas zata tashi tayi da kanta, Sede abinda ka koyawa yaro shi zai tashi dashi don kuwa ance Tun ranar gini Tun ranar zane, idan baka aje ba Kada Kace zaka dauka. A wannan zamanin kayiwa yaranka tarbiyya ma ya aka Kare balle Bakai ba, tashi tayi da kanta taje kitchen ta zubo mata abinci ita kuwa tana zaune ta harde kafarta se cika take tana batsewa, saboda yadda Khulthum bata fara'a ko tayi kwatakwata Bata mata kyau, mutum ce da bata fara'a a cewarta gwara ka tsare gida saboda gudun raini, gata da girman kai kuma haduwar ku ta farko kallon kaskanci Xata fara Yi maka not knowing dukkan kaskanci a kanta ya kare, haka babu wata muamala me kyau tsakaninta da yan uwanta, idan tayi musu magana to tabbas aike ne ko rashin mutunci. Mama na kawo abincin Khulthum ta yamutsa fuska tace Mama wannan ne abincin?.....Innalillahi! Ta dafe kanta, kallonta duka sukeyi babu wani mamaki a ciki don wannan shi ne least abinda Khulthum zata iya yi Balle yau Baba bai bada kudin cefane ba haka ya fice Don yace shi ko sisi bai Kwana da ita a jikinshi dama gurinta yake karba idan Irin haka ta faru to Tun safe ta tafi makaranta hakan yasa ya fice abinshi itakuwa Mama ta sirfa gero ta hada da wake ta dafa matsayin kundin kaza. Kafin Mama ta fadi wani abu tuni Khulthum ta shige daki, se gata da kwano ta fito hakan ya tabbatar musu abinci zata siyo, Wallahi Mama duk laifin kine abinda Khulthum takeyi, kawai saboda Bakuda kudi mu talakawa ne shi ne take Wannan rashin mutuncin, kina kallo ta fita Siyan abinci amma kin kasa magana, Haba Mama! Amir ya fada bayan fitar Khulthum, Aisha ce tace Wallahi kua talauci ba hauka bane kawai don Bakuda kudi se ya zamana shi kenan se ta dinga juya Ku? Kun kasa yin komai kun zuba mata ido. Nanma har Aisha da Amir suka gama 'yan mitocinsu Mama batace uffan ba. Babu dadewa Khulthum ta dawo da abincinta me rai da lafiya. Safiya ce ta asabar, gabaki daya gidan yayi shiru kasancewar kowa hutawa yake, a hankali aka turo kofar dakin na Sulaim inda take kwance saman gado tayi daidai, a hankali Atika ta Dan taba ta, dake baccin bayan asuba ne ba wani Nisa yayi ba hakan yasa ta bude idonta, se kuma ta rufe idon saboda yadda hasken yayi mata yawa, a hankali ta sake budewa lokacinku ta gama adjusting to rays din. Ina Kwana Anty Sulaim. Bata fuska tayi tace Atika lapiya dai ko? Kanta ta gyada tana kuma murmushi tace Lapiya lau, an gama breakfast. Hannunta ta daura a kai tace Amma Atika se a barki, ina bacci...... Se kuma tayi shiru kawai kafin tace Ina fitowa. Daga haka Atika ta fice Sulaim ta sauka tayi brush sannan ta wanke fuskarta ta zura hijabi ta fito, Ahmad da Muhammad na parlour sunyi wanka an saka musu kaya me kyau Wanda zai baka clue din fita zasui, suna jin sallamar ta suka nufe ta inda ta tsaya tana jin maganganun su Tana dariya, a haka Junaid da Subay'a suka fito, hannunsu ta rike baki bude tace Yaya good morning, Ina Kwana Anty. Seda ya kare mata kallo wanda idan bawai kana kallonsa bane ba zaka fahimta ba kafin yace Morning Sulaim Subay'a ya kalla wadda Baki daya hankalinta yana kan Ahmad yace Suby answer her. Dago kanta tayi ta kalli Sulaim wadda itama kallanta take, ciki ciki tace Lapiya. Tana rufe bakinta Atika ta iso ta fada musu an gama komai, tare suka jera zuwa dining, Atika ta bubbbude warmers da plates din, babu inda Subay'a ta sauke idonta se akan danwaken dake gefe, What nonsense is this Atika? Ta fada Tana daga murya hakan yasa gaba daya kowa hankalinshi ya koma kansu, Dan wake? Wayace kiyi. Sulaim ce ta dubi Subay'a tace Ni na saka Ayimin Inaso zanci. Wani kallo ta watsa mata yayinda Atika jikinta ke rawa don halin Subay'a bbu wasa, Dama seda ta fadawa Sulaim strictly ake bin timetable din ba'a canjawa se da izinina Subay'a amma tace itadai ayi mata Wayace miki ana canja mana tsarin timetable dinmu? Wa ya Baki izinin ki bawa cook dita order? This is....... Meye haka Subay'a? Bana son irin haka, Bana so kowa Yana da right ya zabi abinda zaici, ba dole Se wanda kika gindaya ba. Junaid ya katse ta, iya kulewa takai , take ta aje spoon din hannunta ta koma daki, bai kara fadin komai ba, itama Sulaim din se taji komai ya fita mata a kanta hakan yasa ta Mike da nufin komawa dakinta Amma tana aje wannnn spoon din taji wannan sharp eyes din da duk duniya bata tunanin akwai Wanda kallonsa yake affecting dinta kamar Junaid ba, kallonshi is skin piercing se ya tsaga dukkan fatar mutum ya shiga jiyoyinsa, kallon yasa ta duburburce ta Fara fadin Yaya bari nayi wanka...... Kici abinci tukun Ya fada a nitse amma muryar kawai zatace maka order aka bayar, haka nan babu yadda zatayi ta zauna taci abinci, dake wasu abubuwan Sulaim exactly Irin na Junaid take hakan yasa seda Subay'a ta fito basu gama breakfast ba, gefenshi ta tsaya tace Zamu wuce. Ba tareda ya kalleta ba yace Allah ya kiyaye. Itama been the Subay'a yasa Bata bi takanshi ba taja yaranta wanda tuni suka gama shiryawa don al'ada ce duk wata Saturday din duniya zata tafi gidansu wanda ke Magajin Rumfa a cikin kano. Amma daga aurenta zata iya irga sau nawa taje Kaduna gidansu Junaid, bai taba mata maganar hakan ba Sede ya kwashi yaran Yaje dasu. Shi ya fara gamawa yace By 2pm zan fita idan zaki bini to? Agogon dake jikin bango ta kalla, karfe Tara da yan Mintina hakan yasa tace Allah ya kaimu. Daga haka suka koma dakunansu, wanka ta Fara yi ta Nemo kayanta ta aje, gado ta fada ta janyo system ta Fara kallon Indian film na We're Family tana kalla tana cin popcorn, a haka har tazo karshen film din, yadda Kajol take bankwana da yaran yadda duk yadda take son yaran, take protecting yaran, take basu dukkan wata kulawa da soyayya ya tsinka zuciyar Sulaim gashi ta mutu ta barsu, haka kowacce uwa Ke son danta? ai kawai se ta tuna Mummy da Daddy dinta, kawai se ta kifa kanta ta Fara kuka tamkar yau aka dakko ta Daga makaranta akace sun rasu haka abin ya dawo mata sabo dal, ta dinga kuka Tana Shesheka I missed you Daddy and I missed you Mummy.... Allah ya haskaka kabarinku. Tafi Mintina talatin tana Abu daya kafin ta tashi ta nufi bayi ta wanke fuskarta sannan tayi sallah ta daga hannunta sama cikin kaskantar da Kai tace Allah ni baiwar kace me tarin kurakurai, Allah ka gafarta min ka haskaka kabarin Mummy da Daddy........ Se kuka ya kara kubce mata, ita kanta tasan ba karamin kokari tayi a rayuwarta ba at this tender age ace ba tada Uwa bare Uba. A hankali ta kifa kanta kan gadon Tana sauke ajiyar zuciya a hankali bacci ya dauketa, cikin baccin taji ringing din wayarta hakan yasa a firgice ta tashi se taga sunan Junaid hakan yasa ta Mike zuwa gaban dressing mirror tana kallon fuskarta ko yaro ya kalleta yasan Tasha kuka Balle Junaid, khol ta murza a idon ta dauki shade ta saka ta fito. Tunda ta fito ya maida dukkan hankalinshi kanta, Abun da yafi burgeshi da Sulaim shi ne tafiyar ta yadda take tafiya a hankali Cikeda nutsuwa babu hargowa a ciki shi yake burgeshi. _Your gaze Junaid it's Haram!_ Inner self dinshi ya fada mishi hakan yasa yayi kasa da kanshi, itama shade din da ta saka shi ya bata damar kare mishi kallo, as usual kananan kaya ne jikinshi short sleeve top se denim jeans da wrist watch me kyau da ya dace da fatar Hannunsa yayi masa kyau, Tana zuwa gabanshi ya Mike ta biyo bayanshi har mota babu Wanda yace uffan, seda ya hau titi sannan yace Remove those shade zasu hanaki ganin hanya. Babu musu ta ciresu cikin sa'a ya sauke idanunsa a kanta, take gabanshi ya fadi ganin yadda idanunta sukai swollen, gangarawa yayi gefen titi yace Meye samu fuskarki? Me ya sakaki kuka. Ai kukan da ya ambata se ta kuma sakin wani she's missing them shekaru biyar kenan amma kullum tana jin mutuwar sabuwa a ranta. Gaba daya hankalin Junaid ya tashi yayi juyin duniya taki magana, yayi lallashin har ya gaji amma taki tayi shiru hakan yasa yayi dialing number Mami, Tana dagawa ya fada mata Abinda yake faruwa aikuwa tace ya hadata da Sulaim din, jin muryar Mami ya kara tada mata hankali hakan yasa abinda ta Fara cewa Mami I'm missing you! Murmushi Mami tayi tace Shiyasa kike kuka? Idan nayi miki aure kuma fa? Shima kuka zaki dinga yi idan kina son ganina? Kiyi hakuri next week zanzo gaisuwa kanon nida Babanki, is that OK? Kanta ta gyada taji dadi kuma hawayen suka dauke Allah ya mata replacing Mummy da Mami , Daddy kuma da Baba. Seda ta tabbatar ta daina kukan kafin tayi magana da Junaid, haka suka cigaba da tafiya jefi jefi yana mata tambayoyi dukda yawanci akan makaranta ne. Acan kuwa Mami tana tunanin dalilin kukan Sulaim don tasan tana missing dinsu amma bazaiyiwu ace shi ne yasa take Wannan kukan ba kuma daga muryarta kasan ta jima tana yi. A haka dai ta hakura akan koma Menene idan tazo zata gani. Ranar Junaid da Sulaim sun Sha yawo se maghariba ya maida ta gida Har lokancin subay'a bata dawo ba. Shatuuu ♥️ [6/21, 8:05 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU!* ✍️Shatuuu ♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Birnin kudu local government ce a jigawa state kuma tana karkashin Dutse emirate, yawancin mazauna garin Fulani ne se kuma hausawa, garin suna da duwatsu da kuma Nono. Malam Muhammadu shi ne sakataren local government a wannan lokacin don haka yanada rufin asiri sosae, matarshi kwaya daya Maryamu se yaransu biyar Lukman, Fatima, Aminu, Sauda da Hafsa. Baki dayansu babu Wanda baiyi karatu ba hatta matan saboda shi yayi karatu yasan dadin karatun hakan yasa duk yadda ake tsegumin shi seda yasa sukai karatun. Lukman shi ne soja a cikinsu kuma yana rike da matakin General , Umma Fatima classroom teacher ce Tana aure da yaranta a Ningi, Mama Sauda kuma Nurse ce Tana FMC birnin kudu tana aiki sannan Tana auren wani Barrister shima dan garin ne, se Anty Hafsa Itace take aure a Niamey kasar Niger. General Lukman soja ne mijin Hajiya Nafi wadda asalinta yar kebbi ce sun hadu da ita a saudiyya sunje aikin hajji anan Bayan sun dawo aka Yi dukkan wasu formalities sannan sukai aure. A maiduguri suka Fara zama sannan suka koma Abekuta anan ta haifi Junaid me tsananin Kama da Uncle Aminu tamkar shi ya haifeshi. Baiyi shekaru uku ba aka maida Baba aiki Minna hakan yasa Mami wadda Barrister ce kawai tabar aiki da Gwamnati Sede private Tace idan sukai settling ta samu tayi joining wani abun sannan ta dakko kanwarta Zahra ta rike wadda ta auri uncle Aminu daga baya. Seda Junaid yayi kusan shekaru biyar kafin Mami ta haifi Jabir, Bayan shekara uku ta haifi Ja'afar, har ta fitar da rai da haihuwa wajen shekaru Tara sannan ta haifi Auta Jawad. Junaid shi ya gado Mami shi yayi Law a university of Nsukka yayi serving a Niger sannan ya dawo gida lokacin sun koma baki daya kaduna anan cikin Jaji, a high court yayi practicing na shekara biyu sannan ya koma ABU yayi masters sanann yayi academician anan ya hadu da Subay'a ita kuma tana banking and finance, asalin Subay'a yan Kano ne mahaifinta dan Rano ne mahaifiyarta yar Bichi suna da kudi sosae kuma yan Boko ne gashi basuda namiji ko daya baki dayansu mata ne hakan yasa sukeda zumunci Don haka idan Kaje gidajensu zakaga haka suke tafiyar da rayuwar su iri daya a cewarsu uwarsu batada da namiji so babu Wanda zaiyi disrespecting dinta Shiyasa ya kasance basu girmama dangin miji. Danshi na farko Ahmad Wanda Keda shekaru shida se na biyu me shekaru uku Muhammad. Yanzu haka he's a lecturer a faculty of Law cikin BUK. Jabir shi ne na biyu his father's son, sosae yake kama da baba kuma shi ne soja me rank din Conel Yana Delta shida matarshi Imratu yar jigawa ce a garin Babura ta social media suka hadu, tana level 3 akai Auren a UDUS haka dai aka samu ta kammalla karatun suka tattara Zuwa delta. Tana da kirki tasan mutuncin mutane sede basu taba haihuwa ba hakan yasa suka daga hankalinsu Amma Baba da kanshi yayi musu nasiha akan komai na rayuwa MUQQADARI NE, kada su manta hakan wannan yasa suka Kwantar da hankalunsu, tsakanin subay'a da Imratu babu wani kyakyawan muamala saboda Imratu bata son raini itakuma kullum kallon kaskanci take mata hakan yasa Basa shiri ko kadan haka nan Jabir basu shiri da subay'a wanda ya kuma shafar ita Imratun. Ja'afar shi ne na uku pharmacist ne Yana aiki a cikin kaduna bashida aure, shima kusan halinsu daya da Jabir sede shi mutum ne me kulekulen yan mata shi kanshi bazai iya irga yan matanshi ba saboda yawansu, gaba daya ya fisu kyau hakan yasa yake ganin jin yakai, ko Baibi yan mata ba definitely Za'a bishi. Amma Duk Wannan yan matan yana son Sulaim Yana ganin Ita kadai ce taste dinsa Don currently tare suke, yana ganin ita reserve dinshi ce Sede besan hakan kuskure ba ne Don duk Abinda yake Sulaim na sane dashi . Jawad shekara daya kawae ya bawa Sulaim shi ne abokinta wanda ko abu ya sameta shi take Fara fadawa yana ABU yana engineering. Uncle Aminu neurosurgeon ne matarshi Anty Zahra, daga Zuwa wani course Germany shi kenan suka retaining dinshi yake musu serving acan. Duk wata Niima da Allah yake bawa mutum sun samu haihuwa ce kawai Allah bai kawo ba, sunje asibitin Amma shiru har suka hakura Se kuma kwatsam Sega Anty Zahra da ciki, murna kam ba'a magana haka suka ta murna suda danginsu. Wata Yana kaiwa lokacin shi ta haifi yarta mace me Kama da ita sosae sede Bayan ta haihu ta Fara wani Irin bleeding na fitar hankali, Duk yadda akaaso tsayar dashi abu ya faskara hakan yasa Uncle Aminu signing aka cire mahaifar baki daya, hakan yasa Bata kuma haihuwa ba Daga kan Sulaim. Baki daya suka dawo Nigeria a gidan Mami suka zauna akai suna Yarinya aka saka mata Ummu_Sulaim Daga nan suka tafi birnin kudu inda tayi watanni uku kafin suka koma Germany. Kowa nasan Sulaim musamman yaran Mami Tunda basuda mace a gidan Tun lokacin Baba yaso karbarta amma ganin kamar itakadai ce abinda suka mallaka yasa ya hakura. A Kwana a tashi Bbu wuya gurin ubangiji haka Sulaim tayi ta girma har ta shiga secondary school dinta, sun sota ta sosu sun bata dukkan abinda Allah ya wajabta iyaye su bayar to babu abinda Sulaim ta rasa, sun mata gata kuma sunyi mata tarbiyya. On the fateful day, Tana tashi Daga school taki bin school bus don tayi da Mummy da Daddy dinta akan da kansu zasu zo daukarta sede kafin nan ma Sega mota daga office din Daddy anzo tafiya da ita, duk tunaninta basu samu dama zuwa bane Shiyasa, sede tana Zuwa compound dinsu taga an taru ga reporters, police, Nigerian Ambassador da sauran mutanen embassy, se gawarwaki guda biyu an rufesu da farin likafani, Tunda ta zo gurin kawai taja ta tsaya bata yi gaba Balle tayi baya Tanan dai a tsaye ta kusan Mintina goma kafin aka fahimci zuwanta, Alhaji Salisu shi ne Ambassador din, riko hannunta yayi ya isa da ita inda gawarwakin suke ya bude fuskokinsu, Mummy's ce da Daddy tamkar suna raye babu digon ciwo jikinsu, itadai kawai shiru tayi tana ta kallonsu amma ta kasa furta komai, addu'ar da aka saka ta tayi ma take kasa tana nan har aka zo tafiya dasu don musu sallah saboda Baba general ya wakilta Ambassador yayi duka necessary saboda bazasu samu tasowa ba se Washegari. Haka Sulaim na kallo aka tafi dasu amma hawaye ko dis bai digo mata ba, akai musu sallah aka binne su sannan aka tafi da Ita Nigerian embassy dake kasar, Tunda taje Matar Alhaji Salisu take ce mata Sulaim Mummy ta rasu Daddy ma haka, bazaki kara ganinsu ba kiyi kuka kinji Amma ko dis ta kasa gashi ko uhm bata furta ba itadai ta zama gata nan gata nan dai ita kamar statue haka ta zama. Har su Mami suka iso Sulaim Batayi ba duk yadda taga ana kuka Tana son Yi Amma ta kasa, seda aka gama komai aka taho da ita Nigeria anan ta Fara wani Irin kuka me Cikeda tashin hankali, shi kenan se ta dawo musu da mutuwar sabuwa aka Fara wani mourning din. Tasha kuka Sulaim kamar bazata taba dariya ba, don seda aka Fara hadata da therapist kafin aka samo kanta. Hakan yasa ta bata shekara daya bata fara school ba. Jawad shi ne abokinta na farko Bayan Mami kullum suna tare se Ja'afar Wanda ya nuna mata soyayya me tsayawa a zuciya, shikam Junaid ba a gari yake ba amma yanada matsayi cikin zuciyarta saboda duk lokacinda ta ganshi se Daddy ya fado mata kuma dake farkon tafiyar Daddy Germany da Junaid yayi hakan yasa sukeda abubuwa da yawa ita dashi in common. A haka ta dangana ta Fara school inda ta karasa secondary dinta shi ne ta Fara law..... Sulaim kenan. Khulthum Itace yar Mama (Hadiza) ta farko , mahaifin Khulthum malamin wata islamiyya ne a wani kauye a malumfashi, shi ne mijin Mama na farko wanda uwar miji da danginshi suka hanata sakat Seda ya saketa da cikin Khulthum haka ta koma gida a Kano babu dadewa ta haifi Ummu_Khulthum shi kuma Malam Sule Allah yayi masa rasuwa. Bayan ta yaye Khulthum tayi wani auren shi ne ta haifi Amir, A'isha, Maryam, Amira da auta Osama. Mahaifinsu aikinshi shi ne hada guga da dinkewa Dan haka se ranar da Allah ya kawo ciniki akeyi da Wannan Za'a kukuta ayi cefane, to yanzun anzo era da kwatakwata kusan a birni guga bashida amfani shi kuma sanaar da ya iya kenan. Hakan yasa suke cikin bakin talauci. Dadi daya se Khulthum ta iya kunshi takeyi, Idan akace sallah tazo to gidannan ba'a rufeshi saboda mutane, se ya zamana Yarinya Tana da abin batarwa to most lokuta ita ke bada kudin cefane hakan yasa ta raina su, raini na fitar hankali kuwa, dakuna biyu ne a gidan amma kayanta ne kawai a ciki yaran nasu na gurin iyayensu idan ka shiga gidan tunani zakayi cewar Khulthum ce yar gidan sauran su ne agola. A haka aka Fara daukarta tana zuwa gidajen masu kudi tayi lalle wannan shi ya fara bude mata ido taji tabbas bazata iya cigaba da zama a wannan halin ba. Ashir shi ne saurayin ta na karfen kusan kowa tare ya sansu dukda itadin tana kula wasu amma a zuciyarta Ashir shi ne reserve dinta, to kuma se ta shiga makaranta ta Fara ganin kankarrrun masu kudi, yan karya hakan yasa akalar Rayuwarta ta Fara juyawa. Wannan kenan. To people of Allah kunji asalin kowa! Ya kuke ganin xa'ayi? Yanzu zamu shiga cikin labarin sosae. Shatuuu ♥️ [6/23, 10:17 AM] Heedaya Bunu: *MACE A YAU* 5 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Sulaim! Sulaim!! Sulaim!!! Mtsssss Sulaim ta buga tsaki jin yadda ake kwala mata Kira, ita a karan kanta bazata iya tuna Yaushe taji ana kiranta irin haka ba, gyara zamanta tayi babu alamun ko niyyar zataje kiran da Subay'a ke yi mata, haka ta cigaba da revising books dinta don Bata fiye son barin karatu ya tarar mata ba. Tana nan Zaune se ga Atika ta shigo ko bata fada ba tasan aiko ta akai hakan yasa tace Kije ki ce mata gani nan. Ba tareda Atika tayi magana ba ta fice sannan Sulaim ta Mike ta fito fuskarta babu walwala, Subay'a na zaune kan daya daga cikin cushion din da suka kawata parlour, Tana cikin abaya baka kasancewar Friday ce basu saka suit, dawowarta kenan daga office don ko kaya bata canza ba. Kafarta daya kan daya tana ta girgixa ta ga fuskar nan a murtuke. Ance Kina kirana? Sulaim ta tambaya lokacinda ta tsaya akan Subay'a bawai Sulaim tana da rashin kunya bane no, idan kaja girmanka tafi kowa girmamaka amma idan ka nuna mata Kai Bakada mutunci zata saka wannan rigar don ku daidaita differences dinku. Bakiji tun dazu Inata kwala miki kira ba. Subay'a ta fada a kufule, zama Sulaim tayi tace Na jiki mana kawai naga kiran yayi yawa ne..... Yimin shiru fitsararriya..... Tashi kije na fasa fada. Batace da ita komai ba ta Mike kuwa ta koma dakinta ta cigaba da bitar ta sede tayi murmushi idan ta tuna karonsu da Subay'a. Ta dan jima a zaune taji zaman ya isheta hakan yasa ta Mike ta fito hannunta rikeda wayar ta, babu kowa a parlor hakan yasa ta samu dogon cushion ta kwanta kafin ta Fara neman layin Ja'afar, a iya lissafinta Kwana biu kenan basui waya ba kullum ya kira tayi bacci ita kuma Bata samu damar returning masa call din ba. Hello Sweetm Shi ne Abinda ya fara fada Yana amsa call din, murmushinta me kyau tayi wanda wushiryar dake bakinta ta bayyana se ta Fara rikidewa zuwa fuskar Junaid, Don ita da babanta take kama kuma Junaid photocopy Uncle Aminu ne. Hi Luff Ajiyar zuciya duka suka sauke, shima daidaita kwanciyarshi yayi tareda rike wayar da kyau yace Kinsan yadda Nayi missing dinki kuwa, gaskiya kano zanzo na ganki. Dariya ta saki a hankali daidai bude kofar parlour amma saboda yadda ta shagala Bama tasan an shigo ba. Kai da Yaushe nazo har zaka dinga ihun kayi missing dina, though I missed you too Se yayi dariya yace Kaji ta Ashe Kema Kinaji, to ya komai hope babu Wanda yake hunting life dinki? Haba dai waye ya isa bayan ka kankane ko ina, Sulaim is for Ja'afar babu wani. Tarin da taji yasa ta dago a hankali ta dubi gurin, Junaid ne a tsaye da dukkan alamu ya jima da shigowa, idanunsa da suke farare sun Dan canja kadan, gaba daya ya zuba su akanta, yadda yake kallonta yasa ta duburburce ta Yi saurin kashe wayar tareda mikewa Sede kafin ta tako inda yake har yayi gaba ya nufi inda kofar parlour shi take. Komawa tayi ta zauna tayi shiru a ranta tana fadin me yasa yake min irin kallon nan kamar Nayi masa laifi? Ko dai wani abunne? Gaba daya se ta kasa sakewa hakan yasa ta koma daki Tana ta jujjuya abin, a saka Ja'afar ya kara kira amma se taji bata bukatar sake magana dashi haka tayi ta ringing Batayi picking ba Daga karshe Tayi picking Daga muryarta ya fahimci bata mood din hakan yasa yayi mata sallama donshi ma aikinsa yake. Junaid kam a parlonshi ya cire takalman kafarshi tare da Adana su cikin rack dake gefe, cikin bedroom dinshi ya shiga wanka yayi, haka Yake neat tamkar na mace, Junaid Nada tsafta kuma yanada kula baya tarayya da kazanta hakan yasa ko baa gyara mishi ba zaiyi sparing Lokaci ya gyara da kanshi. Komai da ya cire seda ya maida shi inda ya dace, towel ya daura ya shiga bayi ba tareda ya Bari abinda ya faru tsakaninshi da Sulaim ya dawo masa ba. Haka yayi wanka yayi Alwala sannan ya fito a tunaninshi Subay'a ta shigo amma har lokancin babu Wanda ya shigo kuma sunsan ya dawo. Jallabiya yasa Fara tas hade da hularta, ya jika jikinshi da turarenahi wanda ko kudi ya baka indai daga jikinshi ya fito to Seka ji wannan kamshin saboda yadda ya kama jikinshi. A parlor yayi tunanin zaiga Sulaim nan ma Bata nan haka ya wuce massallaci akai maghrib sukai meeting na magidantan unguwa sannan akai isha'i kafin ya dawo gida. Ko dining bai kalla ba ya wuce parlonshi yayi kusan Mintina ashirin Subay'a bata zo ba, hakan ya kara dagula masa lissafi ta barshi da abinda yake ji mana, inda tasan yadda zuciyarshi take ciwo a halin yanxu baya tunanin zata barshi shi daya, kuma wannan halinta ne ba wai yau ta Fara ba yayi maganar har ya gaji amma bata fasa ba but yau Yana ganin xa'ayi sabon zama. Yana nan Zaunen Sega ta shigo, tayi kyau babu karya, lace ne jikinta skirt da riga wanda yayi mata kyau tayi kwalliya a fuskar ta, dankwalin ta daura shi yadda ya dace gashi se kamshi take hakan se ya saukar masa da nutsuwa yaji duk ya zubar da makaman yakin nashi, amma a ranshi Yana Raya idan suka cigaba da haka lallai zai zama kullum shi ke cutuwa amma yau Tasha. Kamar tasan me yake tunani tana isa gun da yake zaune ta riko Fuskarshi ta Fara bashi wani hot kiss wanda ko minti bai cika ba ta kashe masa dukkan jikinsa tasa ya manta da wanzuwar wata mace Bayan ita. Subay'a kenan. A dining kowa ya hallara banda uwar gayya Sulaim har lokancin tana iya hango tsagoran bacin rai idanun Junaid ta kasa manta hararar da ya zabga mata dazu hakan yasa taga gwara tayi zamanta idan suka gama cin abincin ta fito taci nata, amma hakan bata samu ba Don kuwa aiko Ahmad yayi akan tazo abinci is ready. Turo Baki tayi kamar Junaid dinne yazo da kanshi tace Kace na koshi Shikuwa ya juya Yaje ya isar da saqon shi, share maganar yayi ya fara cin abincinshi, Subay'a na mishi hira, Sede ya kasa jurewa don ya Saba da ganinta gefensu tana tauna abinci da wannan mitsitsin bakin nata, wayarshi ya janyo ya tura mata _Come on fito Kici abinci _ Tana jin shigowar message din tasa hannunta ta janyo wayar Don tunaninta Ja'afar ne ashe me gayya me aiki ne, baki ta Kara turowa tareda buga kafa Cikeda shagwaba kamar yana gabanta tace Mhm Mhm Bazanci ba. Shikam bawan Allah gaba daya hankalinsa Yana kofar dakinta ita kadai yake da muradin gani amma taki fitowa ita kuma Subay'a bata Lura ba, a haka ya kara tura Mata wani text din _Don't let me come and meet you a dakinnan, ranki zaiyi mugun baci wallahi_ Yadda text din ya nuna mata seriousness dinsa yasa ta fito Tana ta cin magani, da idanun shi ta Fara arba yayinda ya lumshe idanun shi Yana jin yadda sanyi ke zagaye jikinshi, haka Kuma ya sauke ajiyar zuciya wadda har Seda Subay'a ta dubeshi. Zama tayi ta janyo plate ta bude abincin, baki daya daga shinkafa, macaroni se salad. Abincin kenan kullum su ake sarrafawa ita kuma ta gaji, ga abinda ya faru daxu ga tursasawar Junaid akan taxo taci abinci ga yanzu idanunshi da suka hanata sakat, kawai se ta kifa kanta ta Fara kuka.... A'a abin mamaki duka suka bita da ido, wani mugun tsaki Subay'a taja tareda mikewa tace Jimana bataciyyar Yarinya, zaki samu a gaba da kuka. Daki ta wuce abinta yaranta suka bita dukda son su lallashi Antynsu amma Subay'a ta buga ta tsare. Shikam Junaid Daga kukan yasan tsantsar shagwaba ce amma dukda haka se kukanta ke sukar mishi Vena cava. Fork din hannunshi ya aje yace Sulaim Kanta ta dago Baki daya fuskarta ta baci da hawaye, kallonta yayi yace Ya akai, don nace Kici abinci? Pouting face dinta tayi tace Ni bashi nake so ba. Murmushi yayi wanda yasa yayi kyau sannan ya zaro ido a ranshi yace Anzo gurin Me kike so. Seda ta gama share fuskarta sannan tace Tuwo! Kuma yadda ta fada irin seriously dinnan, wani kallo yake binta dashi with full of mamaki sannan ya dubi wall clock din karfe Tara ta gota, kallon fuskarta yayi yaga yadda take kallonshi kuma da alama jira take yace a'a ta sake Daga mishi hankali. Atika! Ya Kira a nutse, within seconds Atika ta iso Cikeda mamaki Don shi baya saka aiki, yana kallon fuskar Sulaim yace Tuwo nake so yanzu Kallon time tayi tace To Yallabai! Daga haka ta wuce kitchen dake sunada miya cikin fridge. Daga haka bai kara magana ba ya bar mata dining din ya koma kan cushion tareda maida channel din zuwa aljazira yana kallon news. Itama share shi tayi ta cigaba da zamanta Tana jiran abinci, to 10 Atika ta kawo tuwon da miyar ogun wadda a ido ma kawai cewa take "eat me" ajewa tayi ta juya yayinda ya dawo da dukkan hankalinshi kanta hakan yasa ta ji duk ya takurata se ta turo Baki, kanshi ya dauke Yana shafawa a ranshi yace "Sulaim case" ita dama haka take rasuwar su Daddy yasa ta rage shagwabar amma Bayan ta gama secondary se abun ya fara dawowa kuma indai tanayi dole Se ta dauki hankalinka wasu lokutan ko magana take se Junaid yaji kamar don tasan tana rikitashi Shiyasa take amma ina haka take normalcy dinta kenan. Seda ta koshi ta tattare Kwanukan kafin yace Babu Abinda kike so kuma? Kanta ta gyada tana murmushi, shima martani ya mayar mata kafin yace To your bed. Haka ta wuceshi zuwa dakinta, haka kawae se ta tsinci kanta Cikeda farin ciki, ta dinga hango murmushin Junaid se kuma ta saki murmushi ta kankame pillow, ko Ja'afar bata tuna ba bacci ya dauketa. Shima a nashi bangaren se goma da Rabi ya kashe komai ya nufi dakin Subay'a, tuni ta dade da bacci, a hankali yake ta kallonta yana mamakin yadda take ita babu ruwanta batada damuwa, bata wani daga hankalinta akanshi, duk lokacinda ya kwanta kanshi sede idan tana bukatarshi idan yayi magana tace ita a gajiye take dawowa kuma shi babba ne so yake Abinda zata yiwa Ahmad da Muhammad tayi mishi. Kanshi ya girgixa yace "Subay'a " se kuma ya wuce dakinshi inda yayi Alwala sannan ya kashe wutar dakin amma duk yadda yaso bacci yace no tunanin Sulaim zaayi, hakan ce ta faru ya dinga tunanin ta yana tariyo abinda tayi mishi dazu a dining a haka barawo ya lallabo ya sace mana babban yaya Junaid! To fa people of Allah! Have seen your comments so far nasha dariya amma naji dadi, Kada Ku damu yadda kukeso haka zaayi. Gaisuwar girma zuwaga yan SHATUUU KINGDOM...... 🤝🏻🤝🏻🤝🏻 Shatuuu ♥️ [6/23, 5:20 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 6 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad LLB1 yayi shiru saboda wata zazzafar test da akeyi ta philosophy, gaba daya kowa hankalinshi yana kan paper dayake rubuta test dinshi, inda Sulaim take naje abin mamaki Tana zaune gefen Khulthum wadda itama dukkan hankalinta ya ta'alaka wajen test din. Baifi minti goma ba daya daga cikin malamin yace Pens up. Aje pen din Sulaim tayi tareda sakin ajiyar zuciya, yayinda ta gefenta ma hakance ta kasance, a hankali suka dinga bi suna tattara papers din kafin suka fice. Khulthum ce ta Fara kallon inda Sulaim take wadda hankalinta yana kan wayarta tana karanta text din Junaid akan idan ta tashi ta sameshi a office dinshi, se ta tsinkayi muryar Khulthum tace Ya test din? Murmushi tayi Wanda ya fito da gapped teeth dinta ta dago tace Alhamdulillah, tayi sauki not as expected. Yadda tayi magana shi ya fara jan hankalin Sulaim, itama martanin murmushin ta mayar mata tace Gaskiya kam amma...... Kafin ta karasa class rep dinsu ya bayyana gaban class inda ya bada announcement din Logic class baxaiyi taking place ba don haka kowa is free now. Kowa murna yayi mussaman yan nesa da suke son barin kano ranar don an tafi mid semester break, tare suka mike suka jero har wajen class, Sulaim tace Bari na tafi ana jirana se Bayan break. Murmushi Khulthum tayi tace Allah ya kiyaye nima na tafi ayi Hutu lapiya. Kanta ta gyada mata kafin kuma tace Bansan sunanki ba fa. Nima haka, Sunana Ummu_Khulthum Ido Sulaim ta dan zaro kafin tace Ummu_Sulaim Tare da mika mata hannu sukai musabaha, basu bar gurin ba seda sukai exchanging phone digits, Khulthum na fito da wayarta wata Infinix note ce hannunta ta zama babbar yarinya don a cewarta dole a dama dasu, shi kanshi kayan dake jikinta ba karamin amsar ta sukai ba, hardly ka hasaso cewar ga daga gidan data fito, yadda take tafiya a hankali kamar bazata taka kasa ba shi ya fara janyo hankalin Huzaifa dake tsaye gaban motarsu da dukkan alamu wani abun yake jira, ita bata Lura da shi ba hankalinta Baki daya ya tafi tunanin Sulaim, yarinyar ta burge ta she's simple yet classy, kuma kana kallon yanayinta kasan Daga gidan data fito don wani zobe na gold data lura dashi hannun Sulaim din, fatarta ma is flawless. Tana ta wannan tunanin taji alamar anyi parking gefenta, amma da yake Khulthum is Khulthum ko daga idonta Batayi ba balle ta kalli gefenta inda motar take haka ta cigaba da tafiyarta, Huzaifa dake ciki yayi murmushi sannan ya bude motar ya iso inda ta tsaya ita a dole napep take nema nan kuwa addu'a take a ranta Kada ya tafi. Abinda ya fara futawa shi ne Kin burge ni.... Kizo Nayi dropping dinki dan kyakyawa kamarki bai dace rana ta doke ta ba. A hankali ta juyo da fuskarta ta sauke Kan tashi, bashida tsayi don idan ya fita da kadan zai fita, kana kallonshi kasan dan Hutu ne kuma dan gayu, naira tana kuka hannunsu. Nagode Ta bashi amsa kafin ta kara matsawa gefe don tarar napep, shima juyawa yayi ya Daga kafada alamar Kinyi missing yaja motarshi ya barta a gurin Cikeda mamaki Don bata taba tunanin hakan zai faru ba, tabbas ta bar opportunity dinnan ya wuce ta, a haka a kufule ta samu napep shima ya dinga raina mata hankali dayake ya sameta a Bagas se bata kulashi ba, haka ta isa gida abin Yana ta damunta. Sulaim na zuwa kofar office din Junaid tasa hannunta tayi knocking, cikin deep voice din nan tashi yace Come in. Hannu tasa ta bude kofar, bakinta dauke da sallama ta shiga, yana zaune kan kujerar, yayinda wani wanda ta saba ganinsu tare kuma take tunanin shima lecturer ne Yana zaune opposite him. Yaya barka da Rana Ta furta lokacinda ta iso tsakiyar office din, kafin ya amsa ta dubi bakon nashi shima ta gaisheshi maimakon amsawa se yace Sulaim right? Kanta ta gyada, shi kuma Junaid ya zabga mishi harara wanda yasa ya kwashe da dariya cikin kankan da murya yadda Sulaim ba zataji ba yace Se na fada mata Wallahi. Itadai tana tsaye ta dauke kanta daga kallonsuu taji Junaid yace Auta koma kan cushion ki zauna kafin na gama. Babu musu tayiwa kanta masauki tareda tunanin Yaushe rabon da yace mata auta ita kanta ta manta last time din. Wayarta ta ciro ta Fara abubuwa da bansan me takeyi ba, wajen Mintina talatin ta dago idonta cikin sa'a shima kallonta yake se suka hade cikin na juna, dauke kanta tayi shi kuma ya bata rai Wanda kadan ne Ridwan dake gefe baiyi dariya ba haka suka karayi wajen sau uku sannan Junaid ya gyara murya yace Ya akai ne? Bakinta ta turo tace Tafiyan fa? Idonshi ya kura mata yace Zuwa ina kenan? Kaduna mana, yau fa an tafi mid semester break. Kanshi ya dauke don kwatakwata bayada niyyar ta tafi wani gurin better ta zauna don shi se yanzu yake ganin Tun tuni me ye dalilin da Tunda su Daddy suka rasu bai dakko ta ba ya bari su Mami suka dauketa. Ganin yayi shiru yasa tace Yaya flight din fa 6pm zai tashi Da sauri ya dago Cikeda mamaki yace Waye yayi miki booking, you didn't even let me know. Tun last week Ja'afar yayi mata booking ko Mami bata sani ba, to yanxu tasan inhar yasan Ja'afar ne tafiyar sede a fasa, Mami tayi booking fa, Junaid baice komai ba ya mike shida Ridwan suka fita, suna fita ta Mike kafafuwanta. Acan Ridwan yace Ka kyaleta ta tafi, kada kana takura mata idan ba haka ba Abinda muke nema bazamu samu ba. dafa kanshi Junaid yayi ya sake jinginar da jikinshi a jikin mota yace I don't want her to go, nafi son kullum ina ganinta by my side. Kallonshi Ridwan yayi yace Kada ka zama me son kanka, to me yasa bazaka fada mata ba. Da sauri Junaid ya dubeshi Yana zaro ido kafin kuma ya fara girgiza kanshi yace Is not yet time and kasan yanzun haka tare suke da Ja'afar, ni ina tunanin shi yayi booking flight dinnan Don there's no way Mami zatayi batareda sani na ba. Tabdi! Ja'afar Yana son ta? Ridwan ya fada Yana kara jinjina abin kafin yace Abokina ka hakura mana. Murmushin takaici yayi yace Da zan iya da tuni na hakura, bazan iya bane na kasa dangana. To idan bazaka iya hakura ba is better you let her know, yarinyar da alama bazatayi wahalar shawo Kai ba. Dariya Junaid yayi yace Ba haka bane, shi ne kawai Abinda mutane Ke gani a tattare da ita amma ni nasan taurin kan Sulaim se addu'a. Sun dade suna tsaye har Sulaim ta gaji da jiranshi zata kirashi ya turo kofar ya shigo, tashi tayi ta zauna Tana kallonshi, shima kallonta yake har ya zauna inda Ridwan ya tashi yace Kinyi sallah? Kanta ta gyada yace Mu tafi kenan? Take wani murmushi ya subuce mata, bai kulata ba suka fito Zuwa mota, lokacin awa daya ta rage flight dinsu, kallonshi tayi yadda yake tuki kamar bayaso tace Yaya zanyi missing flight din fa Baice da ita komai ba ya cigaba da takunshi itama tayi iskar kare dashi tareda daukar wayarta tana ta danne danne taji muryar shi yace Zaki dauki abu a gida ne? Dago kanta tayi tace A'a na saka a booth Tun safe Seriously? Kin gaji da ganina ne har haka? Kawai abinda yaji bakinsa ya furta kenan, lumshe idonsa yayi a ransa Yana fadin you messed up Junaid. Itakam kallonshi tayi tace A'a Yaya, ina son kawai zuwa ne. Kanshi ya gyada bai kuma fadar komai ba saboda gudun kwafsawa haka ya kaita airport seda aka gama komai kafin suka rabu, tana ta murna wadda ta kasa boyuwa shi abin har mamaki yake bashi ma. A airport tana sauka ta fito a departure hall ta hangoshi a tsaye ya harde hannayensa Kan kirjinsa, Yana cikin Kaftan coffee da hula a kanshi yayi kyau har ya gaji da kyau, Kada Ku manta Duk yaran Mami Ja'afar Yafi kowa kyau, idanunshi Yana cikin eyeglasses fari tas, sede yana tsaye da wata azabbabiyar kyakyawar Yarinya Irin lousy kyau dinnan wanda abinda zaka fara hangowa kenan, suna tsaye Sunata dariya Irin abinda ake fada yayi dadi, gaba daya se Sulaim taji tamkar karta karasa gurin amma se ta dake ta isa inda suke fuskarta babu walwala ta zagaya Dayan kofar ta bude ba tareda tace komai ba ta shiga ta zauna amma ko bata fada ba kunsan how it feels kaga Abinda kake fadi tashi a kanshi, kake fatan ya zama naka na har abada yake tsaye da wata, abinda taji yace shi ya sake dugunzuma ta Bari na wuce Kada baby sis tayi ta jira. Seda ta zagayo inda Sulaim ke Zaune tace Baby Sis ki kulamin da baby na naga Yana ji dake. Kamar an buga mata guduma haka taji "Baby sis" like serious, shiru tayi ta sunkuyar da kanta Tana ta battling da hawayen dake son zubo mata se taji ta wulakanta.... Yes wulakanci ne. Shima jiki a sanyaye ya shigo but being the Ja'afar se cewa yayi Sweetm se ki bani tsoro yadda kika Bata rai dinnan. Ko kallonshi Batayi ba ta bata rai Haka ya aje wayar shi saman cinyarta ya fara driving sede yadda yake driving kawai will tell you cewar baiji dadi ba. Haka suka tafi shiru kamar anyi rasuwa Duk Surutun Ja'afar kasa magana yayi se can yace Susu ba fushi zakiyi ba at least let me explain. Ban tambayeka ba. Come on Susu why you behaving like this. Mtsssssssw Taja tsaki wanda ba Ja'afar ba hatta ni Seda nayi mamaki, yadda take kada kafarta da kuma fuskarta ya nuna bacin rai sosae. A haka bai sake magana ba har aka bude gate din gidan, wani sharp breath tayi inhaling at least she's home. Yana gama parking ta aje masa wayoyinsa ta fice, tana bude parlon Mami ta fito daga kitchen hannunta rike da katon tray, a guje ta nufe ta itama aje tray din tayi ta rungume abarta, wani Irin farin ciki ya dinga shigarsu a hankali Mami tace Haka unexpected Autar Mami? Murmushinta tayi daidai shigowar Ja'afar, bai kulasu ba ya wuce inda zai kai shi dakinsu iatakam Mami tabi Zuwa sama rikeda tray din, ganin yanayin ta yasa Mami tace Auta kamar ranki a bace yake? Boye fuskata tayi cikin hannunta tace Babu komai na gaji ne Mami, Ina Baba ? Yaje massallaci jekiyi wanka kafin ya dawo. Babu musu tayi dakinta, se lokacin da ta shiga bayi Abinda ya faru daxu ya fara dawo mata, wannan shi ne Karo na uku da suna Irin haka itada Yaya Ja'afar se take ganin kamar ta sake mishi da yawa ne, a haka tayi wanka tana ta tufka da warwara. Seda ta shirya sannan ta dauki wayarta Don duk expecting dinta Junaid ya kirata amma ko message babu hakan yasa ta kirashi, yana zaune kan sofa a parlonshi Ahmad yana ta damunshi akan se sunje siyo chocolate yayinda Subay'a ke dakinta kannenta sunzo, kiran Sulaim ya shigo, kawai murmushi ne ya kwace masa tareda jin sanyi cikin zuciyarshi. Shi kanshi mamakin yadda son Sulaim yayi masa Illa har haka yake, gashi ita bata wani damu dashi ba a yadda take abubuwan ta, a haka dai kiran ya katse. Kamar tana gabanshi tayi pouting lips dinta Wanda har ya zama jikinta tace He'll not pick shima. Tana shirin fita taji yayi returning call din, wani murmushi ta saki ta dauki wayar ta kara a kunnenta Sede kafin tayi magana ta Fara tuhumar kanta dalilin da yasa ta kirashi, meye take jinta special saboda yayi returning call dinta....... Sulaim are you there? Idan tayi Rantsuwa cewar babu mahalukin da duk duniya ya iya kiran sunanta Irin yadda Junaid ya ke kira Batayi karya ba, Harda gunna, kalkala sufra, madda da komai yake kira, kowanne harafi se ya bashi hakkinsa..... Mhm Mhm Shima ya furta Yana rike wayar sosae, itakam jikinta duk yayi wani yum hakan yasa ta kwanta Talk to me, ya kika je? A hankali in a whisper tace Lapiya lau, Mami na gaisheka Dan murmushi yayi me sauti har tajiyo shi Ina amsawa, kije Kici abinci. Pouting bakinta tayi tace To Yaushe Xaka zo. Da sauri ya zaro idanunshi amma yaji dif ta kashe wayar saboda cajinta ya dauke Shit! Ya furta Shatuuu ♥️ [6/25, 4:12 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 7 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Tana tsaye gefen titi hannunta yana dauke da Leda baka da tambarin Sahad stores, Tana Sanye da skirt da riga na atamfa purple da pattern na mint green, yayi mata kyau, kanta ta yane shi da mint green mini veil, hakan ya bawa surar jikinta fita dukkan wani shape seda ya bayyana. Tana nan tsaye wata flashy car ta wuce, se kuma a hankali akayo reverse ya dawo daidai saitin inda Khulthum ke tsaye yayi wining glass dinshi kasa....Huzaifa ne the rich brat shidin yaron wani senator ne a Zamfara Yana level 4 a engineering cikin BUK , kana kallonshi kaga kwallo wanda duniya take damawa dasu. Murmushi yake tayi yace Abokaina suna kirana lucky Hu saboda I'm always lucky, luck is always by my side. Gashi mun kara haduwa. Kallonshi tayi batareda ta canja yanayin fuskarta ba tace Amma kanada naci Dariya yayi yace Wanda ya nace shi zai dace ko ba haka hausawa sukace ba ? Dauke kanta tayi, shi kuma se ta bashi dariya ita a dole Se ta ja aji , Ki shigo bai dace rana tana dukan kyakykyawa kamar ki ba. Bude gaban motar tayi ta shiga yayinda murmushi ya kwace masa, suna tafe Yana mata hira a haka har ta dan fara warewa, bai tambayeta inda zataje ba itama sanyin AC da daddan freshener yasa ta manta, se ganinsu tayi a kofar More and More, dubanshi tayi tace Banan zan zo ba. Irin dariyar shakiyanci yayi yace Ooops nayi tunanin na dakko ki ne we're on a date, amma dukda haka muje ko abu me sanyi ne kisha. Ledar ta aje cikin motar sannan suka jero, mutuniyata ta saki fuskarta dama Irin rayuwar da take so kenan, rayuwar jin dadi da yawace yawace kamar yadda take ji take kuma gani idan aka dauke ta gidan yan gayu kunshi. Tunda suka shiga suka samu guri take ta juye juye hakan ya so bawa Hu dariya amma instead se ya musu placing order. Yana zama wayarta ta Fara ringing alamun kira na shigowa, se taji kunyar fito da purse dinta saboda yadda ta kode, dauke kanshi yayi hakan ya bata damar daukowa Sede take yanayinta ya canza saboda Ashir ne me kiran, silent ta maida wayar a haka aka kawo musu Burger da chilled Smoov, itadai tasan tana kallon abubuwan a kofar bakeries haka amma bata taba tasting ba, amma haka ta danne ta dinga ci da kadan kadan har suka gama sannan ya bada bill dinsu suka fita, a motar yake ce mata A level nawa kike ne? Dagowa tayi tace Level 1 nake. Kallonta yayi kafin ya maida titi yace Shiyasa Naga Baki gama sakin jiki da mutane ba. Dan dariya tayi a haka har suka iso wani ice cream joint na cold stone yayi musu ordering suka zauna cikin motar suna sha yake mata bayanin kanshi tunda taji yace babanshi senator ne kuma d only heir of them tasan tayi babban kamu. Gaba daya Khulthum ta manta cewar wai ta fito Kai dinki ne seda Hu yace Baby da me kika fito yi ne. Bakinta ta rufe tace Kasan saboda yadda ka shagalta Danni I totally forgot dinki zan kai. Dariyar shima yayi yace Lucky Hu! Bai tambayeta inda take Kai dinki ba se kawai taga sun tafi wani tailoring centre a nan wajen new hospital road, yawancin duk budurwar da yayi nan yake kaita a mata dinki, irin designers dinnan Don haka Khulthum tayi shiru Tana tunanin yadda zata iya kai dinki gurin, Amma ta waske suka shiga gurin, yadda suke da mutanen gurin ya tabbatar mata akwai sabo sosae tsakaninsu within 30 minutes an gama komai Harda billing kuma take ya biya through POS hakan ya kara mishi daraja da martaba idanunta. Suna fitowa ana kirayen sallah maghrib hakan yasa yace Bari muje na kaiki gida, yau munsha yawo. Murmushi tayi tace Gaskiya kam. Suna tafe Yana mata tambayoyi saboda yadda taga yanada kudi kuma tasan ba wani abu bane yasa ta fada mishi Daga inda take, baiyi mamaki ba saboda ya Lura dukkan guraren da sukaje are new to her, ko da wannan ma zai shawo kanta Tunda akwai son abin duniya tun a yau yayi marking. Seda yayi mata takeaway me kyau kafin ya nufi inda ya Dakkota lokacin sallar maghrib ta wuce ana shirin sallar ishai. Nuna min Kwanar da zamu shiga. Kanta ta girgixa ba dadi ranta tace Mota bata shiga Se taga bai wani damu ba hasalima wayar ta ya karba Bayan ya gama jujjuya ta sannan ya saka numbers dinshi yayi saving mata kafin ya kirayi kanshi shima yayi saving a tashi. Daga haka sukai sallama ta fito Tana jin tamkar kada ta fito, kamar yadda kullum take tafiya haka ta cigaba da tafiyarta sede tana zuwa tsakiyar layinsu taji an sha gabanta, idanunta ta dago don ganin wanda yake muradin zagi, se kawai taga Ashir tsaye, yana tayi mata wani Irin kallo me Cikeda tuhuma da zargi. Itama kallonshi take tana karantar mood ensa, Baki daya ranshi a bace yake. Ganin haka yasa ta saki murmushi tace D kayi ta jirana ko? Wallahi....... Hannu ya daga mata hakan yasa tayi tsit yace Waye ya fita dake ya kuma dawo dake a mota? Meye Sanye jikinki haka Ya fada Yana nuna bingilin mayafin da ta yafa a kanta Wanda iya wuya kadai ya tsaya, wareshi tayi tace Ni? Akace an fita dani? Wa na sani? Yan unguwa nan munafukai ne. Se kawai yayi murmushi ganin yadda Lokaci daya take raina masa hankali, bai kuma cewa komai ba ya bata hanya Don ta tafi sede ko an inch ta kasa takawa hakan da ya gani yasa yace Kije gida Seda safe. Yana fadar haka ya buga Lifan dinsa within an eye blink ya bar gurin, itama cigaba tayi da tafiyarta har ta isa gidan tundaga zaure taji Mama tana cewa A'isha Kin Dakkowa Khulthum Kwanukan ta ko? Se ta dawo baki wanke ba tazo Tana mana diban albarka. A'isha dake zaune kofar daki Tana yankan farce da fitila tace Tai ta zuwa mana ina ruwan wani. Kafin Mama tayi magana se suka tsinkayi sallamar Khulthum, inda Mama kawai take ta kalla tace Na dawo Mama. A... A.... Sannu da zuwa. Imagine! Wanann ne Karo na farko da Khulthum ta fita takai isha'i a waje, ba tareda sunsan tun asali ina taje ba kuma yanzun babu Wanda zaice Daga ina take.... Akwai sakaci sosae na rasa dalilin da yasa iyaye irinsu Ke sakaci da whereabouts din yaransu, talauci ba hauka bane is a trial and test that are never meant to be easy. Saboda Kai talaka ne Seka bar yaranka sakaka kamar tumakai kada ka manta cewar yara Allah ne ya baku amana and you must account for every deeds da kukai a nan duniya. As expected zata yi magana kan Kwanukan ta amma ta share ta shige daki ta cire kayanta sannan ta fito tayi wanka, tana fitowa mama tace Khulthum yaronnan Ashiru yazo nemanki Tun rana. Juyowa tayi tace Mun hadu dashi, anyi abinci ne? Ta tambaya Tana duban inda kitchen din yake, Eh anyi, a zubo miki ne? Kanta ta girgixa tace A'a Daga haka komawa daki tayi inda ta tarar da A'isha tana kife kwanuka, kamar bazata tanka ma taba se kuma ta kasa kasancewar hakan ba halinta bane tace A'isha waye ya dauki Kwanukan nan? Banza Aisha tayi mata hakan kuwa ya harzuqa ta Tace Ke dan ubanki ba dake nake ba Inkana son zagi nemi yaran ghetto na fada ina kallonsu, juyowa Aisha tayi tace Kada ki kuma zagin ubana Ubanki Ta bata amsa almost immediately, Na zageshi akwai abinda zaki iya yi ne? Dariya Aisha tayi tace Mutumin da bai bar babarshi ba ai ba abin mamaki bane Don kin zagi ubansu, Sede ki sani wanda kike zagi shidinne Gatanki ba gantallalun danginku ba. Hey! Khulthum case, dama ance Baki yasan me zai fada amma baisan Meye martani ba. Taji Ciwon abin hakan yasa ta durfafe ta suka fara kokawa, Dama Tun suna yara Khulthum ce Marar karfi, yanzu haka ma Bata canza zani ba, kafin Mama tazo Aisha ta jibgi Khulthum gashi Daga ita se zanin wanka wanda tuni ya nemi nashi gurin. Da sauri ta yar da wayar tare da fitowa parlour a sukanne, yadda ta bude kofar kadai will tell you Abu take so, gaba daya idanu Baba da Mami suka zuba mata hakan yasa se spirit dinta ya ragu, ta tako a sannu ta zauna daidai kafar Baba Tana gaisuwa, shima da dukkan faraa ya amsa mata yana tambayarta karatu da kuma su Junaid and family, Duk suna lapiya sunce a gaisheku. Murmushi yayi ya cigaba da kallonshi se Sulaim tace Mami ina Wayarki? Dakina Daga haka ta koma dakin Mamin ta dakko wayar ta zauna gefen gado ta kuma kiran Junaid, Duk tunaninsa Mami ce amma yana jin muryar Sulaim ya gyara zamanshi tare da sake rike wayar a ranshi yace This girl will be the death of me! Are you there? Ta furta mishi, Am there Sulaimi, ya kikaje? Alhamdulillah! Ta bashi amsa se kuma sukai shiru baki daya hakan yasa sukaji tamkar gaba daya globe ya daina rotating round the universe, tamkar Lokaci ya tsaya ne cak! Seda Junaid yace Have you eaten? He always ask that, bata son Meye hadinshi da abinci ba, kanta ta gyada tace I've eaten, abincin Mami kayi missing. Dariya ya danyi yace Nima Wifey ta bani me dadi Dif taji Abu ya tsirga mata Wifey ta maimaita kafin tace I've to go zanyi bacci. Kafin yayi magana ta kashe wayar se taji duk yayi spoiling mood dinta wai Wifey! Ta dade da wayar hannunta tana tuhumar kanta dalilin da zatayi fushi Dan ya ambaci matarshi, to idan bai ambaci Subay'a ba Sulaim zaice. Haka tayi ta reminiscing abin cikin ranta a haka Mami ta iske ta, ta dade a tsaye Tana kallon ta ba tareda Sulaim din tasan da shigowarta ba. Taba ta tayi hakan yasa tayi firgigit tace Mami....... Kallon da Mamin tayi mata yasa ta kasa karasa Abinda zata fada se sunkuyar da kanta da tayi. Amsar wayar daga hannun ta tayi tace Kije kiyi shirin bacci I know you must be tired ko? A sanyaye ta Mike batace komai ba ta fita a dakin yayinda Mami ta shiga call log dinta Eldest ta gani wanda ya tabbatar mata Junaid Sulaim ta kira. Call duration ta duba wajen 7 minutes hakan yasa taji abu ya darsu a zuciyarta amma koma dai Menene she will keep eyes on both of them. Shatuuu ♥️ [6/27, 3:29 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 8 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Daidai bugawar agogon dake Makale jikin bangon dakin daidai fitowar Subay'a daga parlonta, tana sanye da Abaya beige color tayi rolling da milk din mayafin da sukaxo tareda abayar. Junaid na zaune kan two seater gabanshi system dinshi ce akan center table se kafafunsa da ya daura akai. Aiki yake sosae Don Tun Azahar yake Abu daya sallah ce kawai ke tashinshi. Tun kafin ya san da zuwanta turaren da take using me dadin kamshi ya bayyana kanshi, lumshe idonsa yayi a hankali kafin ya bude su ya zube a kanta, ko bata fada ba yasan fita zatai saboda kayan dake jikinta, Papa aikin ne har yanxu? Ta tambaya Bayan tayiwa kanta masauki a gefenshi, kanshi ya gyada tareda dagowa ya furzar da iska me huci yace Wallahi kua Mimi dake haka yaran Ke ce mata. Shagwabe fuska tayi wadda tasan baya taba resisting ta saka hannunta a kan sumar shi wadda babu gashin ma saboda yadda ake saisaye ta akai akai. Tace Sulma ta haihu an hour ago. Dagowa yayi Sulma sister Subay'a ce tare akayi musu aure shekara takwas kenan amma bata taba haihuwa ba se yau shi baisan tana da ciki ba ma. Murmushi ya saki yace Mashaa Allah Alhamdulillah! Me ta samu? Baby girl! Addu'a yayi sannan ya cigiba da aikinsa duk da yasan abinda ta ke nufi amma se ya share ta. Ta kusan 5 minutes ganin idan ta zauna haka Itace a cuce hakan yasa tace Papa ina son Zuwa ne. Bai kalleta ba yace Se da safe is already late yanxun. Baki ta turo tace Haba mana Honim har na fadawa Yaya Suhaila tazo mu wuce tare. Pen din hannunshi ya aje tare da rufe system din ya dago ya zube idonshi cikin nata, kasa jurar kallon tayi hakan yasa tayi kasa da kanta, babu alamar wasa yace Subay'a kullum kin fison ki nuna min abinda kike so shi zaayi? Abinda zuciyarki ta Raya miki se kin yishi. Banda kin raina ni ma se da kika shirya kika hada connections dinki sannan zaki zo ki fada min? Nace ba zaki je ba idan kuma ban isa ba ga hanya nan. Yana Kai aya ya Mike ya fara tattara kayanshi ranshi a bace saboda ganinshi raini ne kawai dan ta samu yana tolerating dinta shi ne zata dinga duk Abinda ta ga Dama, shi ba irin sauran mazajen yan uwanta bane da zasu dinga biye wa matansu. Tashi tayi ganin ya nufi daki ta bishi, ranta a bace amma Tunda ita take neman abu dole ta yi kasa da kanta. A bedroom ta sameshi Yana jona system dinshi, a hankali ta bude Baki zatayi magana yayi saurin daga mata hannu yace I've said enough kiyi yadda kike so, idan Kinje ya rage naki.. Bata jira komae ba ta fice daidai shigowar Suhaila parlon, dama ita daya ce shi mijin na waje dan haka tana shigowa ta Fara fadin Subay'a fito mu tafi ko ma dawo da wuri. Yadda taga Subayan yasa tace Kada kice ya hanaki Zuwa? Kanta ta langwabar Cikeda bacin rai tace Wai se gobe. Baki Suhaila ta tabe tace Ke kuma se goben kenan? Kowa ya tafi se ke daya zaki zauna se Kace tsoronshi kike ji, ni Wallahi na rasa me ke damun Junaid dinnan. Ba Abinda yake damuna, magana ce na gama amma idan Ke kike auranta you can go with her. Haka suka tsinkayi muryarshi Yana fada Ashe Tun shigowar Suhailan ya fito dan daukar Flash dinshi. Itama Suhaila Bata da mutunci tace Oh haka kace to Wallahi se taje, Sede kayi duk abinda zakai. Kunsan hali ya banbanta hakan yasa bai ko daga kai ya kalleta ba ya wuce bedroom dinsa, Suhaila ta dubi Subay'a wadda jikinta yayi sanyi tace Zo mu tafi? Ina? Na fasa kinga ranshi ya baci kawai nazo da safen Ta fada Tana me jin takaicin Junaid, su takwas suke gurin hajiyar su amma baki daya Junaid shi ne me matsala bai taba yadda an juyashi ba kamar yadda ake juya sauran sirikan kuma lokacinda ta aureshi tunani suke sun auri wawa Ashe ba anan abun yake ba. Cikeda bacin rai Suhaila tace Karki cemin threat din Wannan hopeless element din zai sa ki fasa zumunci? Idan akwai me Zuwa gurin Sulma ai a bayanki ne. Itama tana jin hakan amma Tunda take da Junaid Bata taba ganin ya Daga murya haka ba, it's unlike him Wannan yasa taji tsoron fitar take. Nidai kawai kije Yaya Suhaila kinga kar na bullowa kaina wani aikin. Wata harara ta watsa mata Tace Kinsan Allah kafata kafarki wawuya kawai. Haka Suhaila taja Subay'a suka tafi, Junaid dake jin komai ya saki murmushi ya fito lokacin har sun bar gidan. A cikin mota kasa sakewa tayi, suna gaisawa da Ishaq ta bame bakinta, tana jin yadda suke hira amma ita kam babu Wannan damar a haka suka iso Standard hospital dake tarauni lokacin goma Harda yan Mintina amma dakin da take kamar rana, Tun a parking space suka hadu da mijin Safina, Surayya da ita Sulma din. A waje ya tsaya suka shiga ciki a cikin su takwas Samina ce kawai bata nan itama sun je Mexico ne itada yaranta, Tun dazu da taji labari take jin tamkar tayi tsuntsuwa ta taho amman babu Hali. Suna shiga suka samu hajiya tana zaune kan wata kujera dake dakin su kuma sauran suna kasa an shimfida carpet se hira suke yayinda Sulmar idanunta ke a runtse tun dazu take son ta runtsa Tunda an sha artabu amma by mere kallo abin bazai samu ba. Suna zama aka Fara sabuwar gaisuwa se hira ta kuma ballewa, Sulma ma haka ta shiga anayi da ita. Mukhtar mijin Suhaila ya shigo Yaga baby sannan yayi musu barka ya koma waje hakan yasa hajiya tace Subay'a ke ina naki dan ka gadama ko bai gadamar ba. Kafin ta bada ansa Suhaila tayi caraf tace Kinsan hajiya me yayi mana...... Nan ta kwashe komai ta fada musu, wani mugun zagi Salima ta saki tace Shiyasa kika shigo jiki a sanyaye, Ke wacce Irin Shashasha Allah ya hada mu da ita? Ke me miji ko to Samina ma da bata kasar jibi zata iso. Ba haka bane..... Rufe min baki Hajiya ta fada Sau nawa ina ja miki kunne akan mijinki, yaro daya kusan shekara takwas kin zauna Yana juya ki Kece koma baya cikin yan uwanki, to ki sani har ayi suna babu Wanda na daukewa zuwa yaga Sulma don gobe gidana zan tafi da ita. Da sauri Sulma tace Gidanki hajiya? A'a munyi dashi gida zan zauna. Suhaila ce ta maka mata harara se Safina cewa tayi Ikon Allah, wannan fa rule ne is not yadda kukai dashi haka ne policy yake kuma haka zakiyi biyayya. Kanta ta kada tace A'a gaskiya.... Dallah rufewa mutane baki Surayya ta fada waaddda kusan shi ne lokacinda tayi magana, hajiya kuwa kawai kallonsu take a ranta tana tunanin yadda zata daidaita su. Basu suka fito ba se 11pm har da Rabi, dukkansu suka fito Sunata hira da dariya, masu drivers suka shiga masu miji suka bisu shikam mukhtar ranshi a tsananin bace yake Amma babu damar magana a haka suka isa gidan Junaid, mukhtar ya fita ya buga amma shiru Wasawasa sunfi Mintina goma suna bugawa babu Wanda ya bude musu gashi akwai echo kasancewar dare yayi sosae, gaba daya suka fito Subay'a ta rasa inda zata saka ranta taji sanyi, gaba daya ta rasa a duniya abinda Ke mata dadi kuma ta kira wayarshi a kashe haka tasu Atika da gateman hakan yasa tana kuka tace Kinga abinda nake fada miki ko Yaya Suhaila dama nasan Wallahi Junaid se ya bata min rai. Tsaki Suhaila tayi hakika Bata taba katari da dan iska Irin Junaid ba, ita tunanin hakan bai zo mata ba shikam mukhtar dadi yakeji a ranshi Yana inama yanada courage din Junaid. Haka Suhaila ta kira hajiya ita kuma Tace subay'a tabi su ta Kwana a can. To fa people kunji wannan! Tunda ta fita Junaid ya sanar dasu su rufe gida sannan kowa ya kashe wayarsa yana ganin is high time ya kamata ya fito ma Subay'a a yanayin da take so dama bahaushe yace idan kida ya canja to salon rawar ma canjawa yake. Haka Subay'a Tana gani suka nufi gidan Suhaila dake gaba dasu, Tun tana kuka Suhaila Na bata Baki har ta share ta. Haka wannan Daren ta rabashi tana tuntuni da da nasani Marar amfani. It's too late to cry when the head is cut off. Shikam Junaid baccinsa yayi dukda yana missing Sulaim komanta maganarta, shagwabar ta, murmushinta da ita kanta don tun ranar da sukai waya taje kaduna basu sake magana ba dukda dimbin urge din dayake jin akan son jin muryarta amma a haka ya hakura shi lallai Lokaci baiyi ba. Da Asuba ya hada musu kaya shida yaran ya sallami duka cooks din sannan ya zubawa Matar gidan kayanta yawanci na office ne sannan ya rubuta wani abu cikin takarda ya bawa driver dinsa da key din motarta akan yakai mata gidan Suhaila, shikuma ya tasar mawa Kaduna shida yaran. Turkashi! Seda ya gama parking sannan ta bude kofar ta fito, idanunta suna cikin wani glasses square shape fari me fadi Wanda ya rufe kusan har kusa da cheeks dinta yayi mata kyau kuma ya bawa hancinta dayake dogo damar fito da aihnahin pointedness din nasa, fuskarta babu ko fara'a akasin yadda asalin Sulaimi take, cikin nitsuwa take takowa har tazo daidai kofar parlour taga an bude Ja'afar ne, Fuskarshi shima babu walwala amma yana ganinta tamkar dama ita yake jira ko kuma nemanta yake oho musu, hannunta ya jawo wanda yasa tayi saurin kallonshi tareda kicinayar kwacewa amma ya damke da kyau seda ya kaita har bakin motar shi kafin ya sake mata hannun aikuwa kamar jira take ta sakar mishi duka a kirjinshi tareda fadin Don't ever touch me kaji na gaya maka. Murmushi yayi yace Ba wannan ne damuwata ba, the fact that kawai dan kin ganni da wata se kiyi ta fushi? Kwananki uku Amma you shun my calls ina miki magana kina basarwa Duk saboda wannan to shikenan Sulaim am sorry she's just a friend and nothing more I'm really sorry bazaki kara kamani da irin laifin ba. I'm sorry please Luff. Tunda ta Fara magana take kallonshi wani side na zuciyarta na fada mata karya yake wani kuma want to believe him Sede na farkon Yafi rinjaye amma se ta bashi another chance Tace Yaya Ja'afar I will never take shit from you ever again, never! Da nayi amma yanxu the world is vast I can't, Nasan halinka kuma duk wanda kake tare dasu na sani amma I never taught it can go to the point where kacewa budurwarka I'm your baby Sis. I won't take that. Idan yan matanka kake so Dan Allah kaje ni bazaka Bata min Lokaci ba. Wani madaukakin mamaki ya addabe shi da gaske Sulaim ce ke blabbing words dinnan? Eh gaskiya university ba karya bace, wannan ba karo bane na farko da ta ganshi da wata ba amma she never fuss on it se yau tabbas akwai aiki gaban Maza. Naji it's OK zan kiyaye yanzu smile mana. Harara ta maka masa ta juya Don komawa ciki sede kamar ance daga kanki taga Junaid a tsaye jikin railers da suka kawata balcony saman, ya zuba hannayensa cikin pockets din wandonsa yana kallonta, wani Irin kallo yake mata me Cikeda dimbin tambayoyi, tuhuma da kamar you failed me haka ta gani cikin idanun shi, sauke kanta tayi ta kasa motasawa Daga gurin Ja'afar dake tsaye bai lura ba Yana mata dariya yace Sweetm idan ba zaki shiga ciki ba zo muje kisha ice cream. Kawai zuciyarta ta Raya mata kibi Ja'afar haka kuwa tasa kafarta a nutse a kuma sanyaye ta fada motarshi, Junaid da yaji kamar ya Kurma ihu haka yaja dogon huci tareda lumshe idonsa. To fa one word for the page, for Junaid, for Ja'afar, for Sulaim and for Subay'a da danginta. Shatuuu ♥️ [6/28, 7:40 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 9 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Yana bude idanunsa wanda suka kusan Mintina biyar a lumshe, se ganin shigowarta yayi hakan ya bashi mamaki Don a iya saninshi tabi Bayan Ja'afar ne su fita. Itama Sulaim din bata kuma dubar inda Junaid yake ba ta shige cikin parlour, Mami ce kadai a zaune se Muhammad da Ahmad, suna jin muryar ta suka taho a guje suka rungume ta, itama rungumarsu tayi tana ta murmushi, kwanaki biyar kawai da zuwana kaduna take jin tayi missing dinsu sosae. Hannunsu taja suka samu guri kan carpet suka zube suna tayi mata surutu wanda Seka rasa inda suka gadoshi kasancewar iyayensu kaf babu me surutun sede ko idan Jawad da Ja'afar sukai wa Kara. Auta kin dawo? Dagowa tayi ta dubi Mamin tace Na dawo Mami, Tace Tana gaisheki sannan da zarar kayan sun iso zakiji sakonta. Kai Mami ta gyada tace Yayi kyau, Allah ya miki albarka, Junaid Yana tambayarki kun hadu? Take yanayinta ya canza dama dalilin da yasa Mami yin maganar kenan tana zargin akwae Abinda Ke aukuwa between the two. Bamu hadu ba, tare yazo dasu Ahmad? Eh Kawai Mami tace ta cigaba da Abinda take itakuma tana wasa da yaran. Wani ihu Subay'a ta saka lokacinda mukhtar ya mika mata key din motarta hade da farar takarda cikin farar envelope, Yaya Suhaila na shiga uku ya sake ni, Abban Fannah kaje ka bashi hakuri , na shiga uku! Baki daya babu wanda ya samu courage din tunkarar ta, hatta shi mukhtar wanda Tunda Sabi'u driver ya bashi takaddar yake murna cikin ransa Don Yana son su koyi hankali baki dayansu. Amma yadda Subay'a ke yin abu se yaji baki daya tausayinta ya kamashi, itakam Suhaila ba karamin rudani ta shiga ba saboda tasan duk inda aka je tanada kamasho cikin wannan abin. Subay'a kam bazata ma iya fadar yadda take ji ba se kawai ta rabe su ta shiga dakin da ta Kwana ita bata bude takardar ba saboda tsoron content din ciki haka kuma Bata daina kukan da takeyi ba har Seda ya tashi Fannah yarinyar Suhaila, ganin halin da uwarsu Ke ciki yasa ta Mike ta fito parlour Don jin Karin bayani, a parlor babanta kawai ta tarar da Suhaila ta koma dakinta saka kaya gwara su tafi Asibiti ko gidan hajiya. Abayar da tasaka jiya ta sake mayarwa ko brush ba tayi ba ta fito hawaye Yana mata zarya, ita bata taba tunanin Junaid zai iya makamancin haka ba, ko sau daya bata taba kawowa dan abinda ya faru jiya can lead to such commotion. Tare suka fito da Suhaila wadda lokacin tace Abban Fannah Bari muje gidan hajiya, Fannah do the right thing. Bata jira amsar daya daga cikinsu ba tayi hanyar waje, ita ta karbi motar tana driving bayan Sulma ta tabbatar musu kowa na asibitin, don haka can suka nufa. Kiyi hakuri Subay'a ban kawo abin zai zama haka ba, amma kema tunda Kinsan halin mijinki ai you shouldn't have followed me. Kunji fa bayan seda tace bazata je ba ta tursasa mata amma yanzu take dora mata blame din itadai jinta kawai take amma gaba daya hankalinta ya tafi Irin rayuwar da zatayi idan Junaid ya saketa, kenan ta kaishi bango? Kenan ta kure hakurinshi? Dama idan bakaji bari ba kaji Hoho. A asibiti kamar jiya haka suke zaune kowacce tayi shiga ta alfarma, kayan wannan yana cewa na wannan bani waje Don a su takwas babu wadda Ke Auren talaka dukkansu masu kudi ne tamkar policy haka abin yake. Tundaga sallamar Suhaila Salina tace Lapiyarku? Hajiya da sauran suna binsu da kallo har Subayaa ta fada jikinta tare da fadin Hajiya Junaid ya sake ni na shiga uku. Gaba daya salati suka saka saboda yadda abin yaxo musu a bazata. Me ya faru? Hajiya ta tambayeta Tana dagota Daga jikinta. Ba karya ta zayyane mata komai tareda mika mata envelope din. Karba tayi itama jikinta yayi balain sanyi ta buda sede content differs from Abinda kowa Ke tunani.... It says Ki zauna a gida ki Bari har se ranar da babyn yayi Kwana arbain se ki dawo. Wani sigh of relief ta saki tareda bawa Surayya wadda ta karanto a fili nan take jikin kowa yayi dadi se kuma suka Fara zaginshi shi uban waye da zai musu gatse Wallahi ba zata koma ba se ranar da ya yanka mata kuma se Sun gwada mishi tana da gata. Itakam Subay'a batace uffan ba se godewa Allah da take, anan tayi wanka dake seminar bank dinsu ya turata Hakan yasa Bata fita Tunda online ne seminar kuma se wajen laasar ake Farawa. Baki daya suka tafi suna kara lallashinta akwai solidarity sosae a tsakaninsu. Daga ita se Sulma suka rage a dakin Bayan kowa ya fita tace Sister dama Papa bai yarda ba jiya kika fito? Dago kanta tayi fuskarta Cikeda alhini tace Seda naki zuwa tunda yaki bari amma tace Wallahi se naje. Haba Sister kina me ita Yaya Suhaila ita take aurenki ko Papa ke aurenki. Kin ganni da ne nayi sokanci nake bin duk Abinda suka gindaya min amma ki sani tun ranar da na fahimci cewar ina dauke da cikin nan naji tabbas bazan iya sake yiwa Umman D iskanci ba haka darajar D ta sake karuwa a idona. Yanzu akan D babu Abinda bazan iya ba kuma na yadda na Bata da kowa Don duk ranar da aurena ya mutu babu Wanda zai jajanta min cikinsu kin tuna yadda Yaya Safina tayi. Tunda na haihu nasan darajar da kuma naji idan ace Dana yayi aure matarshi take neman rabani dashi Se inda karfina ya kare, Umma tayi hakuri don haka I'll make it up Kema ki yadda komai ki fuskanci aurenki Sister. Share hawayenta tayi tace Ki bani shawara ya zanyi Ki jira ayi suna Seki koma kafinnan kiyi mishi text ki bashi hakuri sannan kiyi addu'a ki kuma gyara kurakuranki is never late. Haka Sulma ta dinga bata shawarwari kafin kuma suka fada wasu hirar abinsu na yan uwantaka hakan yasa ta ware abinta. Mami yau dinner amaryar Ridwan inason Sulaim ta rakani. Junaid ya fada suna zaune lokacin shida Mami, Sulaim dake gefe tayi saurin dagowaa Sede suna hada ido da Mami tayi saurin dauke kanta. Murmushi Mami tayi tace Babban Yaya ni na amince ita zaka fadawa. Wani fari tas yaji ranshi yayi mishi hakan yasa ya dubeta yace Auta ki shirya 8pm Zamu je. Se taji bazata iya missing opportunity din ba hakan yasa tace Tom. Tunda ta Idar da sallar isha'i ta bude wardrobe dinta tana assessing kayanta, tunani take tayi me zata saka a jikinta, haka kurum take son fitar dashi kunya, so take tayi kyau. Tana tsaye taji ringing din wayarta da sauri ta isa gurin amma maikmakon ganin kiran Junaid as expected se kiran Ja'afar, karamin tsaki tayi ta aje wayar can ta hango wani lace har ta kai hannu zata ciro se ga Mami ta shigo, da murmushi saman fuskarta tace Troubled? Kanta ta gyada hakan yasa Mami tazo ta tsaya tana scrutinizing kayan har takai kan wani kyakyawan code net wanda ta dinka mata a wani biki kuma aka fasa Baki daya, gold ne material din me dinkin skirt da Riga se ta dakko wani black scarf ta daura mata bayan tayi touching mata fuska da light make up, take sulaim ta fito tayi kyau kamar ka saceta. Seda ta gama komai sannan suka fito tare har kasa, Junaid ta Fara hangowa cikin milk tuxedo suit se tie Baki da leather covered baki da matching wrist watch. Yayi kyau sosae shima tamkar ka sace su. Baba yana zaune ganin sun fito yace Is like an wareni fa, se ina haka? Dariya duka sukayi Mami tace Ridwan ke kara aure shi ne zasuje dinner. Kallonsu yayi sosae bai kara cewa komai ba Mami tace Allah ya kiyaye, Junaid Kada kui dare. Inshaaa Allah Mami, Baba se min dawo. Kamshi ya gyada musu yayinda Sulaim tayi waving dinsu suka fita, zama Mami tayi ta fuskanci Baba Don taga akwai magana bakinshi, aikuwa tana zama yace Kin kusa hada wani auren ne? Me ka gani? Ta bashi amsa da tambaya , Yaranki is like they're in love amma ko nayi mistake ne? Kanta ta girgixa tace I'm not sure, so Kaga bazan ce maka komai ba amma from yadda suke exhibiting wasu signs ina tunanin kamar ....... Is not kamar they're deeply in love with each other, kawai dai ina tunanin basu fahimta bane. Kai Mami ta rike tace Amma Ja'afar fa? Dariya Baba yayi yace Keda yaranki ni nawa ido kawai. Shiru Mami tana nazarin maganganun Baba. A cikin mota babu me magana baki dayansu sunyi shiru se karar ababben Hawa dake yawo kan titin. Junior ne ya fara breaking silence din yace Yaushe zaki koma Kano? Saturday Ta bashi amsa, ita ta rasa dalilin da idan suna tare se tana jin bugun zuciyata yana karuwa sosae, ga wani uneasiness da take ji ko kuma da yayi mata magana se taji dukkan ilahirin jikinta ya amsa, ko kuma ta zama short of words gwara ma idan waya suke. Basu kuma magana ba har suka isa event center din, cike gurin yake da motoci Nawa Kece raini, guri ya samu yayi parking sannan ya dubeta yace Shall we? Murmushin nan nata me kyau tayi masa sannan ta bude kofar suka fito a tare, seda ya rufe kofar da kyau sannan suka shiga shoulder to shoulder. Dake gurin yan Boko ne masu kudi kuma komai a tsare hakan yasa kowa Yana zaune dake Baifi Mintina biyar da Fara event din, suna shigowa idanun MC ya sauka kansu kawai se ya fara fadin Kaga wasu couples wanda Bayan Amarya da ango Bana tunanin akwai wasu perfect match kamarsu, kallesu fa Gaba daya wani nishadi ya mamaye Junaid ya dago idanunshi lucky enough ya hade cikin na Sulaim take wani covolent bonding yayi taking place dukkansu seda zuciyoyinsu ta tsaya cak kafin kuma sauke idanunsu hakan yasa hanaklin kowa ya koma kansu Sega Amarya da Ango sun sakko daga inda suke Zaune dan karrama su, hakan yasa duk inda suka gifta kallonsu ake a haka suka zauna, se taga yawancin abokansu in one way or the other tasansu a Faculty yawanci lecturers dinsu ne. Suna ta zuwa suna gaisawa har wani da bakinshi baya shiru yace Ashe mun kusa zuwa wani bikin, da farko nayi tunanin uwargida ce ai. Dan murmushi Junaid yayi yace Bakaga muna kama ba autarmu ce banaso zuwa ni daya. Autarmu ta maimaita cikin ranta, shikenan matsayinta no any other special matsayi only a sister. Baki daya se taji ta gundura da zaman garin duk yadda ake abubuwa na ban dariya saboda MC akwai barkwanci Amma se taji gaba daya haushin gurin takeji. Duk Abinda take yana Lura da ita amma bazaice ga takaimaiman abinda ya bata ranta ba ganin haka yasa yace Kin gaji mu tafi ne? Da sauri ta gyada kanta, se ya Mike itama tabi bayanshi sukayiwa Ridwan sallama wanda se tsokanarshi yake ba tareda ya Bari Sulaim din taji ba. Shatuuu ♥️ [6/30, 7:28 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 10 ✍️Shatuuu♥️ 🌈Kainuwa writers Association #⃣shatuuu095@wattpad Let's call it a day! We meet in our next class and hopefully there will be test then. Malamin ya fada bayan ya kammalla darasin shi na wannan ranar, haka ya shiga tattare kayansa cikin briefcase yayinda sauran students din dake cikin ajin kowa Ke hade nashi dukda bawai sun gama classes din ranar bane Amma akwai interval na zuwa aje ayi sallar axahar, Wanda zasu ci abinci suje suci. Seda yazo fita kafin yace class rep dinsu ya bishi. Sulaim na zaune inda kusan kullum nan take zaune har tana neman maida gurin permanent seat dinta, hada book din datayi taking note a ciki Ta zura cikin wata off white back pack, dake ranar talata ce hakan yasa kowa Yana sanye da black and white, haka tsarin Law school yake a BUK every Tuesdays and Thursdays black and white ne sede wasu ranakun ko Za'a fita ko kuma zaayi mood trial to dole ne a saka wannan uniform din, hakan yakan sa su zama elegant and attractive. Yan mata uku suka taho inda take Zaune tana niyyar mikewa, Khulthum ce ta Fara cewa Sulaim tashi mu tafi. Mikewa tayi ta sabi back pack din a shoulder dinta daya wrist watch din hannunta wanda yake Baki kuma yayi kyau kan shiny caramel skin dinta ta duba. Tare suka fito su hudun Ummu_Sulaim, Ummu_Khulthum, Ummu_Aimana da Ummul_khairi.....the 4 Ummu's. Khairi tace Kuzo mu fara yin sallah kafin muje neman abinci. Khulthum ta bata rai tace Gaskiya ni yunwa nakeji, mu fara cin abincin kawai. Ke kullum yunwa kikeji baki cin abinci daga gidan ku ne? Harara ta watsa mata Wanda yasa Khairi yin dariya itakuma Aimana tace To meye abin hararar tawa, ba gaskiya na fada ba, malama sallah zamu Fara yi. Itakam Sulaim jinsu kawai take don bawai tayi wani sabo bane ita dasu last week suka dawo Daga mid semester break, ranar da ta dawo ta nemi Khulthum saboda zaman ita daya baya mata dadi to ita kuma Khulthum already tanada su Aimana hakan yasa sukai jamming baki dayansu. Amma har yanxu bata fiya sakewa ba sosae. Massalacin suka Fara zuwa suka bada farali Khulthum tana ta bacin rai wai ba'a girmama opinion dinta ba. Sulaim kam murmushi kawai take musu. Wani joint sukaje nanma kafin aje seda aka bata Lokaci kan ayi deciding gurin da Za'a ci abinci Se sulaim taji tarayyar batada amfani don lokacin tana ita kadai yanxun ta kammalla komai ta koma class amma ya zatayi Tunda ta Riga ta biyosu. A joint din sukai order fried rice da salad se Beef akai da drink. Dama se an gama ake biya kuma kana shiga gurin kasan na manyan yara ne ya'yan masu kudi don hardly kaje baka hadu da wani lecturer ba a gurin, sunsan takan iya girki. Suna fara cin abincin wayar Khulthum ta Fara ringing gaba daya suka kalleta itakam tana kokarin picking tana sakin wani lallausan murmushi Kina ina ne? Shi ne tambayar da Hu ya Fara mata, cikin daidaita muryarta ta fada masa joint din da suke. Tana aje wayar Aimana tace Wa zaki rakito mana? Khairi wadda wasu abubuwan nata na shige Dana Khulthum tace Batta yazo dama yau purse dita babu nauyi, Dan kun nace Keda Sulaim ne amman yau banyi niyyar Zuwa gurinnan ba. Dariya Sulaim tayi ta cigaba da cin abincinta saboda itama yau yunwar takeji Don Junaid Nada class din safe yau hakan yasa ya figo ta bata wani Yi breakfast din kirki ba. Suna tsaka da cin abinci Hu ya shigo shida abokansa kusan zan ce muku babu Wanda a gurin bai san lucky Hu ba, har wani kirari ake mishi Kaga yaro me kudi kana gudu luck na binka, yaro me tashe. Kusan bawai a faculty dinsu yayi suna ba entire new site ansan Lucky Hu saboda yadda yake da yanmata idan baiyi dating dinki ba to yayi flirting kawarki haka abin yake Shiyasa ko award night ake shi ke daukan most popular a cikin faculty. Abokansa uku suna bayanshi, Tunda ya shigo Khulthum baki daya ta rasa nutsuwarta, ta gyara nan ta matsa can har Aimana tace Dallah ki nutsu se kace tsutsa kin kasa zama guri daya Bari naga waye wannan saurayin. Me zasuyi banda dariya Don Aimana ita ke maganin rawar kan Khairi da Khulthum. Gefenta ya tsaya tareda dubansu Sulaim yace musu Sannunku! Suma sannu sukai mishi daidai lokacin gama cin abincinsu Aimana wadda tana kallon Hu ta ganeshi kasancewar faculty dinsu daya da yayanta kuma yana yawan bata labarinsa, mamaki sosae tayi haka yake kamar me charm indai yace yana so to dole ne mutum ya amince dukuwa da sanin halinshi da sukai, mikewa sukai Don biyan bill ya dakatar dasu yace Paid! Kuna kawayen Her Majesty ta yaya zaku biya kudin abinci. A'a Khulthum se aka Fara blushing Irin taji kunyar nan, itakam Sulaim shiru tayi tana jiran jin Abinda sauran zasu fada. Aimana ce tace No Dan Allah Karka Kara biya mana , zamu biya namu ita se ka dinga biya mata. For today thank you! Tana fadin haka taja hannun Sulaim suka fito ita kuma Khairi ta zauna godiya, yayinda Huzaifa ya bisu da kallo saboda bai taba katari da irinsu ba, kawayen yan matanshi shishige masa suke amma wannan har akan Fuskarshi take fada masa bata bukatar payment dinsa. A class Khulthum ta shigo lokacin already Ridwan was in class, dayake period dinsa ce yana taking dinsu wani course shima banashi bane mutumin bazai samu Zuwa bane Shiyasa ya turoshi, so ranar ne ranar farko da ya Fara shiga class dinsu. Tana ta yauki ta shigo class din itada Khairi, bai ce musu komai ba seda t Suka zo tsakiyar aji yace Hey! Get out of my class, irresponsible ones. Simsim kamar an dakesu haka suka fito Khulthum tana ta Balai yaci musu mutunci, se bayan La'asar ya fita kowa ya tashi ya fito, tunanin Aimana da Sulaim Khulthum tuni ta tafi dake Khairi a hostel take su uku suna day. Tana hangosu ta nufo su, Sulaim ce ta Fara fadin Me yasa kuka zo late gashi yayi yabbing dinku. Tsaki Khairi tayi tace Rabu da shege, ya dauki tsayi kamar Daren bakin ciki. Dukda maganar batayiwa Sulaim dadi ba ganin laifinsu ne for coming late, banging into the class without permission seda tayi dariya wai tsayi kamar Daren bakin ciki. Khulthum ce ta Fara magana ranta a bace tace Aimana ni banji dadin Abinda kikayiwa Huzaifa ba, har zakice wai ya rike kudinshi, don kin samu ya kalleki ma. Baki sake Aimana take kallon Khulthum kafin tace Ya kalleni? Na rokeshi ne? Ke nifa Bana son wani kato ya biya min abu har idan zan wuce yana tunanin favor yayimin, kuma Inace cewa nayi ya biya muku nida Sulaim Bama bukata.... Ke bana son nonsense stuffs kinji. Ganin ta dauki zafi yasa Sulaim tace Kai friends basa fada, Dan Allah kui hakuri meye a ciki. Khulthum dai batace komai ba se juyawa tayi ta nufi inda yake jiranta kullum ta bi bayanshi ta fada mota suka tafi, Khairi ma sallama tayi musu ta tafi hostel itada wani gaye dan class dinsu. Se ya rage Aimana da Sulaim wadda har lokancin mitar abin take, suna tsaye Sega kiran Oga Junaid ya shigo gabanta ya fadi don ta rasa me ya hanata kiranshi tace ta gama kamar yadda suka Saba bare yau tasan har ta gama lectures bai tashi ba Balle tace ko Yana gida. A hankali kamar me tsoro ta Kara a kunne tace Yaya na gama. Ki samu napep ya kawoki na wuce Tun dazu, zamuje shopping da Subay'a Zaro idanta tayi don bai taba barinta ba ko ya tafi se ya dawo ya dauketa hakan ya kular da ita ba tareda ta amsa ba ta kashe wayar, kallon Aimana tayi tace Bari na tafi me daukan nawa baya kusa. Kai ta girgixa mata tace Yanzu Yaya Nu'uman zai zo se mu Baki lift. Itama kanta ta girgixa tace A'a gaskiya ki...... Bata karasa ba Se gashi yayi parking a gefen su hakan yasa taja hannunta suka isa bakin motar, baya ta budewa Sulaim ta shiga ita kuma tayiwa kanta masauki a gaba, waya yake Don haka ko gaisuwarsu bai amsa ba in fact baisan Sulaim na ciki ba a haka suka fito Daga BUK, kafin su karaso AA Marmaro inda nan ne kwanan gidan Junaid Aimana tace Sulaim kiyi mishi kwatance. Aje wayar yayi yace Keda waye. Kafin ta bashi amsa ya hango Sulaim ta jikin mirror, bai kalla fuskarta da kyau ba se side view dinta dake gefen window take kalla, gabanshi yaji ya fadi take zuciya ta kwadaitu, muryata yaji a hankali tace Kwana ta gaba zan sauka. Kasa furta komai yayi saboda yadda ilahirin jikinshi ya amsa Daga Wannan furucin da tayi, seda Aimana tace Yaya Nu'uman magana ake maka Naji Ya fada suna zuwa Kwanar Tace zata sauka se ta karasa tunda babu Nisa, godiya tayi musu a lokacin ya samu damar kare mata kallo, itama kuma haka, fari ne sosae kamar yadda Aimana take babu laifi yanada kyau. Suna amsa mata godiyar ta nufi layinsu, tafiya kadan ta isa gidan, tura karamar kofar tayi ta shiga ta gaida maigadin sannan ta nufi parlourn, kafin ta kai ga budewa aka bude, Junaid ne shida Subay'a wadda ta dawo tun Kwana hudu da haihuwar Sulma ta bashi hakuri sosae tareda nuna nadamar ta, shi bashida matsala hakan yasa ya manta da abin suka cigaba da rayuwarsu. Bayansu Ahmad da Muhammad ne da dukkan alamu fita zasuyi, seda ta Fara gaida Subay'a sannan ta tsaya Seda suka fito sannna Junaid ya dubeta yace Ya akai se yanzu kika dawo. Kanta ta dan dauke Daga kanshi tana jin yadda yake ke beating wanda ta rasa dalilinshi kuma abin is only idan tana tareda Junaid ne tace Babu komai. Tana fadin haka ta Kara da fadin Allah ya kiyaye Tayi ciki abinta, shiru yayi a gurin ya bita da kallo se yaji kamar bataji dadi ba, se zuciyarshi take tuhumar shi akan ya bata mata rai ne? Kallon Subay'a yayi wadda tuni ta isa gefen motarshi ya Dan Daga murya yace Nayi mantuwa Bari yanxu zan fito Kanta ta gyada mishi, shikuma ya koma cikin parlour, straight dakinta ya nufa ya kwankwasa kofar. Itakam Tunda ta shiga kujera ta fada ta zauna tayi shiru haka kurum taji ranta a tsananin bace kuma babu abinda take bukata tayi irin kuka, kafin ta gama tunanin aka Fara knocking tasan su Atika ne a ranta tana mitar Daga dawowar mutum Za'a isheshi, kofar ta bude se taga Junaid a tsaye Yana kallonta, kanta ta dauke tareda pouting face dinta, se yaga tayi mishi wani kyau yaji if to say it's okay he'll hug definitely hug her dan fuskarta ta nuna ranta a bace yake amma babu dama hakan yasa yace Shopping zamuje kiyi min text din abinda kike so kinji? Unconsciously ta buga mishi Harara wadda tayi cikin sa'a ya gani hakan yasa ya zaro ido da mamaki amma se ta dauke kanta tamkar ba ita tayi ba tace Tohm. Tana fadar haka ta tura kofar ta shige, kanshi ya shafa saboda ba haka zuciyarshi ta aiko shi yayi ba, ta aiko shi yaji damuwar abinda take so sannan ya fada mata abu me dadi, who knows he will mess up but he couldn't! Bazai iya ba he lacks wannan courage din. Fita yayi suka tafi Yana ta mamakin shi Sulaim ta harara, yayinda take kwance har aka kusa kiran maghrib sannan tayi wanka ta bada farali, Tana idarwa wayarta ta Fara ringing, Bro ta gani hakan ya tabbatar mata Junaid ne se ta samu kanta da kin picking, sau biyu yana kira Tana kin dauka shima se ya hakura. Can Sega kiran Ja'afar ya shigo, Kwana biu nan se taji yau tana daukin jin muryarshi, cikin silvery voice dinsa yace Ina gate gidanku fito mu gaisa. Da gaske! Ta tambaya Tana jin wani nishadi from no where Come and see for your eyes. Kit! Ya yanke call din, Cikeda zumudi ta Mike ta zaro wani plain lace peach zani da riga, se kuma ta mayar ,ta janyo Abaya ash da silver stones se off white lace da aka saka a edge din hannun da kasan Riga... Rolling tayi da veil din kayan ta fesa turare sannna ta dauki wayarta ta fito anan sukaci Karo da Atika Uwardakina Kinyi kyau, ina zuwa haka? Sa ido yanxu zan dawo Har ta tafi ta isa bakin parlour Se ta tsaya da gaske Ja'afar take wa wannan zumudin ko kuwa? What if idan Junaid ya dawo suka hadu Don ta dan Lura baisan tarrayar su? Tayi kusan 7 minutes kafin zuciyarta tace mata go shi matarsa Ya dauka suka fita, se ke xa'ayi caging a hanaki. Da Wannan ta samu karfin gwiwa ta fita, megadi na zaune Tace dashi Baba Bari na karba sako Bata jira me zaice mata ba ta fice, Itakanta bata taba ganin motar ba tana tunanin ya sake mota ne, Tana isa inda yake ya bude mata ta fada Ciki ,tana rufewa ya ja motar with full speed ya bar layin. Da mamaki tace Yaya Ja'afar what are you doing? Dariya yayi mata yace Kin manta a kd kika ki bina kisha ice cream shi zan kaiki kisha yanzu. Dan Allah don't do this kaga yaya bai sani ba Kada ya dawo bananan. Bai kara kulata ba itakuma Bata fasa Yi masa magiya ba amma yayi iskar kare da ita, hakan ya tayar mata da hankali. A gida Junaid da Subay'a sun dawo, yana gama parking megadi ya sanar mishi Sulaim anzo an dauke ta a mota kuma baisan waye ba. Bakasan waye ba? Ni Kake cewa baka san waye ba? Ya fada Yana nuna kanshi tareda nuna kanshi wanda hakan seda yasa megadin firgita, hatta Subay'a mamaki tayi yadda ya Daga murya ashe basuga komai ba. Gidan ubanwa ka barta ta fita? Wayace ka barta ta fita? Subay'a ta matso zata rike hannunshi ya juya kanta Don't you dare touch me. Se taja baya saboda yadda ta tsorata da yanayinshi, Ya dinga masifa wadda tasa baki daya veins din kanshi suka tashi, yayi yayi se kuma yayi shiru ya dinga safa da marwa yana karkada kanshi, baki daya kwakwalwar kanshi ta cushe waye ya fita da ita? Ina kuma taje? Ganin yanayinsa yasa na aje wayar haka kada nima yar rahoto ya make ni! Lol...... Waye zai bawa Junaid ansa NE? Ya haduwar Sulaim da Junaid zata kasance? Me Ja'afar ke planning yi kadafa yayi! Shatuuu♥️ [6/23, 5:20 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 6 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad LLB1 yayi shiru saboda wata zazzafar test da akeyi ta philosophy, gaba daya kowa hankalinshi yana kan paper dayake rubuta test dinshi, inda Sulaim take naje abin mamaki Tana zaune gefen Khulthum wadda itama dukkan hankalinta ya ta'alaka wajen test din. Baifi minti goma ba daya daga cikin malamin yace Pens up. Aje pen din Sulaim tayi tareda sakin ajiyar zuciya, yayinda ta gefenta ma hakance ta kasance, a hankali suka dinga bi suna tattara papers din kafin suka fice. Khulthum ce ta Fara kallon inda Sulaim take wadda hankalinta yana kan wayarta tana karanta text din Junaid akan idan ta tashi ta sameshi a office dinshi, se ta tsinkayi muryar Khulthum tace Ya test din? Murmushi tayi Wanda ya fito da gapped teeth dinta ta dago tace Alhamdulillah, tayi sauki not as expected. Yadda tayi magana shi ya fara jan hankalin Sulaim, itama martanin murmushin ta mayar mata tace Gaskiya kam amma...... Kafin ta karasa class rep dinsu ya bayyana gaban class inda ya bada announcement din Logic class baxaiyi taking place ba don haka kowa is free now. Kowa murna yayi mussaman yan nesa da suke son barin kano ranar don an tafi mid semester break, tare suka mike suka jero har wajen class, Sulaim tace Bari na tafi ana jirana se Bayan break. Murmushi Khulthum tayi tace Allah ya kiyaye nima na tafi ayi Hutu lapiya. Kanta ta gyada mata kafin kuma tace Bansan sunanki ba fa. Nima haka, Sunana Ummu_Khulthum Ido Sulaim ta dan zaro kafin tace Ummu_Sulaim Tare da mika mata hannu sukai musabaha, basu bar gurin ba seda sukai exchanging phone digits, Khulthum na fito da wayarta wata Infinix note ce hannunta ta zama babbar yarinya don a cewarta dole a dama dasu, shi kanshi kayan dake jikinta ba karamin amsar ta sukai ba, hardly ka hasaso cewar ga daga gidan data fito, yadda take tafiya a hankali kamar bazata taka kasa ba shi ya fara janyo hankalin Huzaifa dake tsaye gaban motarsu da dukkan alamu wani abun yake jira, ita bata Lura da shi ba hankalinta Baki daya ya tafi tunanin Sulaim, yarinyar ta burge ta she's simple yet classy, kuma kana kallon yanayinta kasan Daga gidan data fito don wani zobe na gold data lura dashi hannun Sulaim din, fatarta ma is flawless. Tana ta wannan tunanin taji alamar anyi parking gefenta, amma da yake Khulthum is Khulthum ko daga idonta Batayi ba balle ta kalli gefenta inda motar take haka ta cigaba da tafiyarta, Huzaifa dake ciki yayi murmushi sannan ya bude motar ya iso inda ta tsaya ita a dole napep take nema nan kuwa addu'a take a ranta Kada ya tafi. Abinda ya fara futawa shi ne Kin burge ni.... Kizo Nayi dropping dinki dan kyakyawa kamarki bai dace rana ta doke ta ba. A hankali ta juyo da fuskarta ta sauke Kan tashi, bashida tsayi don idan ya fita da kadan zai fita, kana kallonshi kasan dan Hutu ne kuma dan gayu, naira tana kuka hannunsu. Nagode Ta bashi amsa kafin ta kara matsawa gefe don tarar napep, shima juyawa yayi ya Daga kafada alamar Kinyi missing yaja motarshi ya barta a gurin Cikeda mamaki Don bata taba tunanin hakan zai faru ba, tabbas ta bar opportunity dinnan ya wuce ta, a haka a kufule ta samu napep shima ya dinga raina mata hankali dayake ya sameta a Bagas se bata kulashi ba, haka ta isa gida abin Yana ta damunta. Sulaim na zuwa kofar office din Junaid tasa hannunta tayi knocking, cikin deep voice din nan tashi yace Come in. Hannu tasa ta bude kofar, bakinta dauke da sallama ta shiga, yana zaune kan kujerar, yayinda wani wanda ta saba ganinsu tare kuma take tunanin shima lecturer ne Yana zaune opposite him. Yaya barka da Rana Ta furta lokacinda ta iso tsakiyar office din, kafin ya amsa ta dubi bakon nashi shima ta gaisheshi maimakon amsawa se yace Sulaim right? Kanta ta gyada, shi kuma Junaid ya zabga mishi harara wanda yasa ya kwashe da dariya cikin kankan da murya yadda Sulaim ba zataji ba yace Se na fada mata Wallahi. Itadai tana tsaye ta dauke kanta daga kallonsuu taji Junaid yace Auta koma kan cushion ki zauna kafin na gama. Babu musu tayiwa kanta masauki tareda tunanin Yaushe rabon da yace mata auta ita kanta ta manta last time din. Wayarta ta ciro ta Fara abubuwa da bansan me takeyi ba, wajen Mintina talatin ta dago idonta cikin sa'a shima kallonta yake se suka hade cikin na juna, dauke kanta tayi shi kuma ya bata rai Wanda kadan ne Ridwan dake gefe baiyi dariya ba haka suka karayi wajen sau uku sannan Junaid ya gyara murya yace Ya akai ne? Bakinta ta turo tace Tafiyan fa? Idonshi ya kura mata yace Zuwa ina kenan? Kaduna mana, yau fa an tafi mid semester break. Kanshi ya dauke don kwatakwata bayada niyyar ta tafi wani gurin better ta zauna don shi se yanzu yake ganin Tun tuni me ye dalilin da Tunda su Daddy suka rasu bai dakko ta ba ya bari su Mami suka dauketa. Ganin yayi shiru yasa tace Yaya flight din fa 6pm zai tashi Da sauri ya dago Cikeda mamaki yace Waye yayi miki booking, you didn't even let me know. Tun last week Ja'afar yayi mata booking ko Mami bata sani ba, to yanxu tasan inhar yasan Ja'afar ne tafiyar sede a fasa, Mami tayi booking fa, Junaid baice komai ba ya mike shida Ridwan suka fita, suna fita ta Mike kafafuwanta. Acan Ridwan yace Ka kyaleta ta tafi, kada kana takura mata idan ba haka ba Abinda muke nema bazamu samu ba. dafa kanshi Junaid yayi ya sake jinginar da jikinshi a jikin mota yace I don't want her to go, nafi son kullum ina ganinta by my side. Kallonshi Ridwan yayi yace Kada ka zama me son kanka, to me yasa bazaka fada mata ba. Da sauri Junaid ya dubeshi Yana zaro ido kafin kuma ya fara girgiza kanshi yace Is not yet time and kasan yanzun haka tare suke da Ja'afar, ni ina tunanin shi yayi booking flight dinnan Don there's no way Mami zatayi batareda sani na ba. Tabdi! Ja'afar Yana son ta? Ridwan ya fada Yana kara jinjina abin kafin yace Abokina ka hakura mana. Murmushin takaici yayi yace Da zan iya da tuni na hakura, bazan iya bane na kasa dangana. To idan bazaka iya hakura ba is better you let her know, yarinyar da alama bazatayi wahalar shawo Kai ba. Dariya Junaid yayi yace Ba haka bane, shi ne kawai Abinda mutane Ke gani a tattare da ita amma ni nasan taurin kan Sulaim se addu'a. Sun dade suna tsaye har Sulaim ta gaji da jiranshi zata kirashi ya turo kofar ya shigo, tashi tayi ta zauna Tana kallonshi, shima kallonta yake har ya zauna inda Ridwan ya tashi yace Kinyi sallah? Kanta ta gyada yace Mu tafi kenan? Take wani murmushi ya subuce mata, bai kulata ba suka fito Zuwa mota, lokacin awa daya ta rage flight dinsu, kallonshi tayi yadda yake tuki kamar bayaso tace Yaya zanyi missing flight din fa Baice da ita komai ba ya cigaba da takunshi itama tayi iskar kare dashi tareda daukar wayarta tana ta danne danne taji muryar shi yace Zaki dauki abu a gida ne? Dago kanta tayi tace A'a na saka a booth Tun safe Seriously? Kin gaji da ganina ne har haka? Kawai abinda yaji bakinsa ya furta kenan, lumshe idonsa yayi a ransa Yana fadin you messed up Junaid. Itakam kallonshi tayi tace A'a Yaya, ina son kawai zuwa ne. Kanshi ya gyada bai kuma fadar komai ba saboda gudun kwafsawa haka ya kaita airport seda aka gama komai kafin suka rabu, tana ta murna wadda ta kasa boyuwa shi abin har mamaki yake bashi ma. A airport tana sauka ta fito a departure hall ta hangoshi a tsaye ya harde hannayensa Kan kirjinsa, Yana cikin Kaftan coffee da hula a kanshi yayi kyau har ya gaji da kyau, Kada Ku manta Duk yaran Mami Ja'afar Yafi kowa kyau, idanunshi Yana cikin eyeglasses fari tas, sede yana tsaye da wata azabbabiyar kyakyawar Yarinya Irin lousy kyau dinnan wanda abinda zaka fara hangowa kenan, suna tsaye Sunata dariya Irin abinda ake fada yayi dadi, gaba daya se Sulaim taji tamkar karta karasa gurin amma se ta dake ta isa inda suke fuskarta babu walwala ta zagaya Dayan kofar ta bude ba tareda tace komai ba ta shiga ta zauna amma ko bata fada ba kunsan how it feels kaga Abinda kake fadi tashi a kanshi, kake fatan ya zama naka na har abada yake tsaye da wata, abinda taji yace shi ya sake dugunzuma ta Bari na wuce Kada baby sis tayi ta jira. Seda ta zagayo inda Sulaim ke Zaune tace Baby Sis ki kulamin da baby na naga Yana ji dake. Kamar an buga mata guduma haka taji "Baby sis" like serious, shiru tayi ta sunkuyar da kanta Tana ta battling da hawayen dake son zubo mata se taji ta wulakanta.... Yes wulakanci ne. Shima jiki a sanyaye ya shigo but being the Ja'afar se cewa yayi Sweetm se ki bani tsoro yadda kika Bata rai dinnan. Ko kallonshi Batayi ba ta bata rai Haka ya aje wayar shi saman cinyarta ya fara driving sede yadda yake driving kawai will tell you cewar baiji dadi ba. Haka suka tafi shiru kamar anyi rasuwa Duk Surutun Ja'afar kasa magana yayi se can yace Susu ba fushi zakiyi ba at least let me explain. Ban tambayeka ba. Come on Susu why you behaving like this. Mtsssssssw Taja tsaki wanda ba Ja'afar ba hatta ni Seda nayi mamaki, yadda take kada kafarta da kuma fuskarta ya nuna bacin rai sosae. A haka bai sake magana ba har aka bude gate din gidan, wani sharp breath tayi inhaling at least she's home. Yana gama parking ta aje masa wayoyinsa ta fice, tana bude parlon Mami ta fito daga kitchen hannunta rike da katon tray, a guje ta nufe ta itama aje tray din tayi ta rungume abarta, wani Irin farin ciki ya dinga shigarsu a hankali Mami tace Haka unexpected Autar Mami? Murmushinta tayi daidai shigowar Ja'afar, bai kulasu ba ya wuce inda zai kai shi dakinsu iatakam Mami tabi Zuwa sama rikeda tray din, ganin yanayin ta yasa Mami tace Auta kamar ranki a bace yake? Boye fuskata tayi cikin hannunta tace Babu komai na gaji ne Mami, Ina Baba ? Yaje massallaci jekiyi wanka kafin ya dawo. Babu musu tayi dakinta, se lokacin da ta shiga bayi Abinda ya faru daxu ya fara dawo mata, wannan shi ne Karo na uku da suna Irin haka itada Yaya Ja'afar se take ganin kamar ta sake mishi da yawa ne, a haka tayi wanka tana ta tufka da warwara. Seda ta shirya sannan ta dauki wayarta Don duk expecting dinta Junaid ya kirata amma ko message babu hakan yasa ta kirashi, yana zaune kan sofa a parlonshi Ahmad yana ta damunshi akan se sunje siyo chocolate yayinda Subay'a ke dakinta kannenta sunzo, kiran Sulaim ya shigo, kawai murmushi ne ya kwace masa tareda jin sanyi cikin zuciyarshi. Shi kanshi mamakin yadda son Sulaim yayi masa Illa har haka yake, gashi ita bata wani damu dashi ba a yadda take abubuwan ta, a haka dai kiran ya katse. Kamar tana gabanshi tayi pouting lips dinta Wanda har ya zama jikinta tace He'll not pick shima. Tana shirin fita taji yayi returning call din, wani murmushi ta saki ta dauki wayar ta kara a kunnenta Sede kafin tayi magana ta Fara tuhumar kanta dalilin da yasa ta kirashi, meye take jinta special saboda yayi returning call dinta....... Sulaim are you there? Idan tayi Rantsuwa cewar babu mahalukin da duk duniya ya iya kiran sunanta Irin yadda Junaid ya ke kira Batayi karya ba, Harda gunna, kalkala sufra, madda da komai yake kira, kowanne harafi se ya bashi hakkinsa..... Mhm Mhm Shima ya furta Yana rike wayar sosae, itakam jikinta duk yayi wani yum hakan yasa ta kwanta Talk to me, ya kika je? A hankali in a whisper tace Lapiya lau, Mami na gaisheka Dan murmushi yayi me sauti har tajiyo shi Ina amsawa, kije Kici abinci. Pouting bakinta tayi tace To Yaushe Xaka zo. Da sauri ya zaro idanunshi amma yaji dif ta kashe wayar saboda cajinta ya dauke Shit! Ya furta Shatuuu ♥️ [6/25, 4:12 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 7 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Tana tsaye gefen titi hannunta yana dauke da Leda baka da tambarin Sahad stores, Tana Sanye da skirt da riga na atamfa purple da pattern na mint green, yayi mata kyau, kanta ta yane shi da mint green mini veil, hakan ya bawa surar jikinta fita dukkan wani shape seda ya bayyana. Tana nan tsaye wata flashy car ta wuce, se kuma a hankali akayo reverse ya dawo daidai saitin inda Khulthum ke tsaye yayi wining glass dinshi kasa....Huzaifa ne the rich brat shidin yaron wani senator ne a Zamfara Yana level 4 a engineering cikin BUK , kana kallonshi kaga kwallo wanda duniya take damawa dasu. Murmushi yake tayi yace Abokaina suna kirana lucky Hu saboda I'm always lucky, luck is always by my side. Gashi mun kara haduwa. Kallonshi tayi batareda ta canja yanayin fuskarta ba tace Amma kanada naci Dariya yayi yace Wanda ya nace shi zai dace ko ba haka hausawa sukace ba ? Dauke kanta tayi, shi kuma se ta bashi dariya ita a dole Se ta ja aji , Ki shigo bai dace rana tana dukan kyakykyawa kamar ki ba. Bude gaban motar tayi ta shiga yayinda murmushi ya kwace masa, suna tafe Yana mata hira a haka har ta dan fara warewa, bai tambayeta inda zataje ba itama sanyin AC da daddan freshener yasa ta manta, se ganinsu tayi a kofar More and More, dubanshi tayi tace Banan zan zo ba. Irin dariyar shakiyanci yayi yace Ooops nayi tunanin na dakko ki ne we're on a date, amma dukda haka muje ko abu me sanyi ne kisha. Ledar ta aje cikin motar sannan suka jero, mutuniyata ta saki fuskarta dama Irin rayuwar da take so kenan, rayuwar jin dadi da yawace yawace kamar yadda take ji take kuma gani idan aka dauke ta gidan yan gayu kunshi. Tunda suka shiga suka samu guri take ta juye juye hakan ya so bawa Hu dariya amma instead se ya musu placing order. Yana zama wayarta ta Fara ringing alamun kira na shigowa, se taji kunyar fito da purse dinta saboda yadda ta kode, dauke kanshi yayi hakan ya bata damar daukowa Sede take yanayinta ya canza saboda Ashir ne me kiran, silent ta maida wayar a haka aka kawo musu Burger da chilled Smoov, itadai tasan tana kallon abubuwan a kofar bakeries haka amma bata taba tasting ba, amma haka ta danne ta dinga ci da kadan kadan har suka gama sannan ya bada bill dinsu suka fita, a motar yake ce mata A level nawa kike ne? Dagowa tayi tace Level 1 nake. Kallonta yayi kafin ya maida titi yace Shiyasa Naga Baki gama sakin jiki da mutane ba. Dan dariya tayi a haka har suka iso wani ice cream joint na cold stone yayi musu ordering suka zauna cikin motar suna sha yake mata bayanin kanshi tunda taji yace babanshi senator ne kuma d only heir of them tasan tayi babban kamu. Gaba daya Khulthum ta manta cewar wai ta fito Kai dinki ne seda Hu yace Baby da me kika fito yi ne. Bakinta ta rufe tace Kasan saboda yadda ka shagalta Danni I totally forgot dinki zan kai. Dariyar shima yayi yace Lucky Hu! Bai tambayeta inda take Kai dinki ba se kawai taga sun tafi wani tailoring centre a nan wajen new hospital road, yawancin duk budurwar da yayi nan yake kaita a mata dinki, irin designers dinnan Don haka Khulthum tayi shiru Tana tunanin yadda zata iya kai dinki gurin, Amma ta waske suka shiga gurin, yadda suke da mutanen gurin ya tabbatar mata akwai sabo sosae tsakaninsu within 30 minutes an gama komai Harda billing kuma take ya biya through POS hakan ya kara mishi daraja da martaba idanunta. Suna fitowa ana kirayen sallah maghrib hakan yasa yace Bari muje na kaiki gida, yau munsha yawo. Murmushi tayi tace Gaskiya kam. Suna tafe Yana mata tambayoyi saboda yadda taga yanada kudi kuma tasan ba wani abu bane yasa ta fada mishi Daga inda take, baiyi mamaki ba saboda ya Lura dukkan guraren da sukaje are new to her, ko da wannan ma zai shawo kanta Tunda akwai son abin duniya tun a yau yayi marking. Seda yayi mata takeaway me kyau kafin ya nufi inda ya Dakkota lokacin sallar maghrib ta wuce ana shirin sallar ishai. Nuna min Kwanar da zamu shiga. Kanta ta girgixa ba dadi ranta tace Mota bata shiga Se taga bai wani damu ba hasalima wayar ta ya karba Bayan ya gama jujjuya ta sannan ya saka numbers dinshi yayi saving mata kafin ya kirayi kanshi shima yayi saving a tashi. Daga haka sukai sallama ta fito Tana jin tamkar kada ta fito, kamar yadda kullum take tafiya haka ta cigaba da tafiyarta sede tana zuwa tsakiyar layinsu taji an sha gabanta, idanunta ta dago don ganin wanda yake muradin zagi, se kawai taga Ashir tsaye, yana tayi mata wani Irin kallo me Cikeda tuhuma da zargi. Itama kallonshi take tana karantar mood ensa, Baki daya ranshi a bace yake. Ganin haka yasa ta saki murmushi tace D kayi ta jirana ko? Wallahi....... Hannu ya daga mata hakan yasa tayi tsit yace Waye ya fita dake ya kuma dawo dake a mota? Meye Sanye jikinki haka Ya fada Yana nuna bingilin mayafin da ta yafa a kanta Wanda iya wuya kadai ya tsaya, wareshi tayi tace Ni? Akace an fita dani? Wa na sani? Yan unguwa nan munafukai ne. Se kawai yayi murmushi ganin yadda Lokaci daya take raina masa hankali, bai kuma cewa komai ba ya bata hanya Don ta tafi sede ko an inch ta kasa takawa hakan da ya gani yasa yace Kije gida Seda safe. Yana fadar haka ya buga Lifan dinsa within an eye blink ya bar gurin, itama cigaba tayi da tafiyarta har ta isa gidan tundaga zaure taji Mama tana cewa A'isha Kin Dakkowa Khulthum Kwanukan ta ko? Se ta dawo baki wanke ba tazo Tana mana diban albarka. A'isha dake zaune kofar daki Tana yankan farce da fitila tace Tai ta zuwa mana ina ruwan wani. Kafin Mama tayi magana se suka tsinkayi sallamar Khulthum, inda Mama kawai take ta kalla tace Na dawo Mama. A... A.... Sannu da zuwa. Imagine! Wanann ne Karo na farko da Khulthum ta fita takai isha'i a waje, ba tareda sunsan tun asali ina taje ba kuma yanzun babu Wanda zaice Daga ina take.... Akwai sakaci sosae na rasa dalilin da yasa iyaye irinsu Ke sakaci da whereabouts din yaransu, talauci ba hauka bane is a trial and test that are never meant to be easy. Saboda Kai talaka ne Seka bar yaranka sakaka kamar tumakai kada ka manta cewar yara Allah ne ya baku amana and you must account for every deeds da kukai a nan duniya. As expected zata yi magana kan Kwanukan ta amma ta share ta shige daki ta cire kayanta sannan ta fito tayi wanka, tana fitowa mama tace Khulthum yaronnan Ashiru yazo nemanki Tun rana. Juyowa tayi tace Mun hadu dashi, anyi abinci ne? Ta tambaya Tana duban inda kitchen din yake, Eh anyi, a zubo miki ne? Kanta ta girgixa tace A'a Daga haka komawa daki tayi inda ta tarar da A'isha tana kife kwanuka, kamar bazata tanka ma taba se kuma ta kasa kasancewar hakan ba halinta bane tace A'isha waye ya dauki Kwanukan nan? Banza Aisha tayi mata hakan kuwa ya harzuqa ta Tace Ke dan ubanki ba dake nake ba Inkana son zagi nemi yaran ghetto na fada ina kallonsu, juyowa Aisha tayi tace Kada ki kuma zagin ubana Ubanki Ta bata amsa almost immediately, Na zageshi akwai abinda zaki iya yi ne? Dariya Aisha tayi tace Mutumin da bai bar babarshi ba ai ba abin mamaki bane Don kin zagi ubansu, Sede ki sani wanda kike zagi shidinne Gatanki ba gantallalun danginku ba. Hey! Khulthum case, dama ance Baki yasan me zai fada amma baisan Meye martani ba. Taji Ciwon abin hakan yasa ta durfafe ta suka fara kokawa, Dama Tun suna yara Khulthum ce Marar karfi, yanzu haka ma Bata canza zani ba, kafin Mama tazo Aisha ta jibgi Khulthum gashi Daga ita se zanin wanka wanda tuni ya nemi nashi gurin. Da sauri ta yar da wayar tare da fitowa parlour a sukanne, yadda ta bude kofar kadai will tell you Abu take so, gaba daya idanu Baba da Mami suka zuba mata hakan yasa se spirit dinta ya ragu, ta tako a sannu ta zauna daidai kafar Baba Tana gaisuwa, shima da dukkan faraa ya amsa mata yana tambayarta karatu da kuma su Junaid and family, Duk suna lapiya sunce a gaisheku. Murmushi yayi ya cigaba da kallonshi se Sulaim tace Mami ina Wayarki? Dakina Daga haka ta koma dakin Mamin ta dakko wayar ta zauna gefen gado ta kuma kiran Junaid, Duk tunaninsa Mami ce amma yana jin muryar Sulaim ya gyara zamanshi tare da sake rike wayar a ranshi yace This girl will be the death of me! Are you there? Ta furta mishi, Am there Sulaimi, ya kikaje? Alhamdulillah! Ta bashi amsa se kuma sukai shiru baki daya hakan yasa sukaji tamkar gaba daya globe ya daina rotating round the universe, tamkar Lokaci ya tsaya ne cak! Seda Junaid yace Have you eaten? He always ask that, bata son Meye hadinshi da abinci ba, kanta ta gyada tace I've eaten, abincin Mami kayi missing. Dariya ya danyi yace Nima Wifey ta bani me dadi Dif taji Abu ya tsirga mata Wifey ta maimaita kafin tace I've to go zanyi bacci. Kafin yayi magana ta kashe wayar se taji duk yayi spoiling mood dinta wai Wifey! Ta dade da wayar hannunta tana tuhumar kanta dalilin da zatayi fushi Dan ya ambaci matarshi, to idan bai ambaci Subay'a ba Sulaim zaice. Haka tayi ta reminiscing abin cikin ranta a haka Mami ta iske ta, ta dade a tsaye Tana kallon ta ba tareda Sulaim din tasan da shigowarta ba. Taba ta tayi hakan yasa tayi firgigit tace Mami....... Kallon da Mamin tayi mata yasa ta kasa karasa Abinda zata fada se sunkuyar da kanta da tayi. Amsar wayar daga hannun ta tayi tace Kije kiyi shirin bacci I know you must be tired ko? A sanyaye ta Mike batace komai ba ta fita a dakin yayinda Mami ta shiga call log dinta Eldest ta gani wanda ya tabbatar mata Junaid Sulaim ta kira. Call duration ta duba wajen 7 minutes hakan yasa taji abu ya darsu a zuciyarta amma koma dai Menene she will keep eyes on both of them. Shatuuu ♥️ [6/27, 3:29 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 8 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Daidai bugawar agogon dake Makale jikin bangon dakin daidai fitowar Subay'a daga parlonta, tana sanye da Abaya beige color tayi rolling da milk din mayafin da sukaxo tareda abayar. Junaid na zaune kan two seater gabanshi system dinshi ce akan center table se kafafunsa da ya daura akai. Aiki yake sosae Don Tun Azahar yake Abu daya sallah ce kawai ke tashinshi. Tun kafin ya san da zuwanta turaren da take using me dadin kamshi ya bayyana kanshi, lumshe idonsa yayi a hankali kafin ya bude su ya zube a kanta, ko bata fada ba yasan fita zatai saboda kayan dake jikinta, Papa aikin ne har yanxu? Ta tambaya Bayan tayiwa kanta masauki a gefenshi, kanshi ya gyada tareda dagowa ya furzar da iska me huci yace Wallahi kua Mimi dake haka yaran Ke ce mata. Shagwabe fuska tayi wadda tasan baya taba resisting ta saka hannunta a kan sumar shi wadda babu gashin ma saboda yadda ake saisaye ta akai akai. Tace Sulma ta haihu an hour ago. Dagowa yayi Sulma sister Subay'a ce tare akayi musu aure shekara takwas kenan amma bata taba haihuwa ba se yau shi baisan tana da ciki ba ma. Murmushi ya saki yace Mashaa Allah Alhamdulillah! Me ta samu? Baby girl! Addu'a yayi sannan ya cigiba da aikinsa duk da yasan abinda ta ke nufi amma se ya share ta. Ta kusan 5 minutes ganin idan ta zauna haka Itace a cuce hakan yasa tace Papa ina son Zuwa ne. Bai kalleta ba yace Se da safe is already late yanxun. Baki ta turo tace Haba mana Honim har na fadawa Yaya Suhaila tazo mu wuce tare. Pen din hannunshi ya aje tare da rufe system din ya dago ya zube idonshi cikin nata, kasa jurar kallon tayi hakan yasa tayi kasa da kanta, babu alamar wasa yace Subay'a kullum kin fison ki nuna min abinda kike so shi zaayi? Abinda zuciyarki ta Raya miki se kin yishi. Banda kin raina ni ma se da kika shirya kika hada connections dinki sannan zaki zo ki fada min? Nace ba zaki je ba idan kuma ban isa ba ga hanya nan. Yana Kai aya ya Mike ya fara tattara kayanshi ranshi a bace saboda ganinshi raini ne kawai dan ta samu yana tolerating dinta shi ne zata dinga duk Abinda ta ga Dama, shi ba irin sauran mazajen yan uwanta bane da zasu dinga biye wa matansu. Tashi tayi ganin ya nufi daki ta bishi, ranta a bace amma Tunda ita take neman abu dole ta yi kasa da kanta. A bedroom ta sameshi Yana jona system dinshi, a hankali ta bude Baki zatayi magana yayi saurin daga mata hannu yace I've said enough kiyi yadda kike so, idan Kinje ya rage naki.. Bata jira komae ba ta fice daidai shigowar Suhaila parlon, dama ita daya ce shi mijin na waje dan haka tana shigowa ta Fara fadin Subay'a fito mu tafi ko ma dawo da wuri. Yadda taga Subayan yasa tace Kada kice ya hanaki Zuwa? Kanta ta langwabar Cikeda bacin rai tace Wai se gobe. Baki Suhaila ta tabe tace Ke kuma se goben kenan? Kowa ya tafi se ke daya zaki zauna se Kace tsoronshi kike ji, ni Wallahi na rasa me ke damun Junaid dinnan. Ba Abinda yake damuna, magana ce na gama amma idan Ke kike auranta you can go with her. Haka suka tsinkayi muryarshi Yana fada Ashe Tun shigowar Suhailan ya fito dan daukar Flash dinshi. Itama Suhaila Bata da mutunci tace Oh haka kace to Wallahi se taje, Sede kayi duk abinda zakai. Kunsan hali ya banbanta hakan yasa bai ko daga kai ya kalleta ba ya wuce bedroom dinsa, Suhaila ta dubi Subay'a wadda jikinta yayi sanyi tace Zo mu tafi? Ina? Na fasa kinga ranshi ya baci kawai nazo da safen Ta fada Tana me jin takaicin Junaid, su takwas suke gurin hajiyar su amma baki daya Junaid shi ne me matsala bai taba yadda an juyashi ba kamar yadda ake juya sauran sirikan kuma lokacinda ta aureshi tunani suke sun auri wawa Ashe ba anan abun yake ba. Cikeda bacin rai Suhaila tace Karki cemin threat din Wannan hopeless element din zai sa ki fasa zumunci? Idan akwai me Zuwa gurin Sulma ai a bayanki ne. Itama tana jin hakan amma Tunda take da Junaid Bata taba ganin ya Daga murya haka ba, it's unlike him Wannan yasa taji tsoron fitar take. Nidai kawai kije Yaya Suhaila kinga kar na bullowa kaina wani aikin. Wata harara ta watsa mata Tace Kinsan Allah kafata kafarki wawuya kawai. Haka Suhaila taja Subay'a suka tafi, Junaid dake jin komai ya saki murmushi ya fito lokacin har sun bar gidan. A cikin mota kasa sakewa tayi, suna gaisawa da Ishaq ta bame bakinta, tana jin yadda suke hira amma ita kam babu Wannan damar a haka suka iso Standard hospital dake tarauni lokacin goma Harda yan Mintina amma dakin da take kamar rana, Tun a parking space suka hadu da mijin Safina, Surayya da ita Sulma din. A waje ya tsaya suka shiga ciki a cikin su takwas Samina ce kawai bata nan itama sun je Mexico ne itada yaranta, Tun dazu da taji labari take jin tamkar tayi tsuntsuwa ta taho amman babu Hali. Suna shiga suka samu hajiya tana zaune kan wata kujera dake dakin su kuma sauran suna kasa an shimfida carpet se hira suke yayinda Sulmar idanunta ke a runtse tun dazu take son ta runtsa Tunda an sha artabu amma by mere kallo abin bazai samu ba. Suna zama aka Fara sabuwar gaisuwa se hira ta kuma ballewa, Sulma ma haka ta shiga anayi da ita. Mukhtar mijin Suhaila ya shigo Yaga baby sannan yayi musu barka ya koma waje hakan yasa hajiya tace Subay'a ke ina naki dan ka gadama ko bai gadamar ba. Kafin ta bada ansa Suhaila tayi caraf tace Kinsan hajiya me yayi mana...... Nan ta kwashe komai ta fada musu, wani mugun zagi Salima ta saki tace Shiyasa kika shigo jiki a sanyaye, Ke wacce Irin Shashasha Allah ya hada mu da ita? Ke me miji ko to Samina ma da bata kasar jibi zata iso. Ba haka bane..... Rufe min baki Hajiya ta fada Sau nawa ina ja miki kunne akan mijinki, yaro daya kusan shekara takwas kin zauna Yana juya ki Kece koma baya cikin yan uwanki, to ki sani har ayi suna babu Wanda na daukewa zuwa yaga Sulma don gobe gidana zan tafi da ita. Da sauri Sulma tace Gidanki hajiya? A'a munyi dashi gida zan zauna. Suhaila ce ta maka mata harara se Safina cewa tayi Ikon Allah, wannan fa rule ne is not yadda kukai dashi haka ne policy yake kuma haka zakiyi biyayya. Kanta ta kada tace A'a gaskiya.... Dallah rufewa mutane baki Surayya ta fada waaddda kusan shi ne lokacinda tayi magana, hajiya kuwa kawai kallonsu take a ranta tana tunanin yadda zata daidaita su. Basu suka fito ba se 11pm har da Rabi, dukkansu suka fito Sunata hira da dariya, masu drivers suka shiga masu miji suka bisu shikam mukhtar ranshi a tsananin bace yake Amma babu damar magana a haka suka isa gidan Junaid, mukhtar ya fita ya buga amma shiru Wasawasa sunfi Mintina goma suna bugawa babu Wanda ya bude musu gashi akwai echo kasancewar dare yayi sosae, gaba daya suka fito Subay'a ta rasa inda zata saka ranta taji sanyi, gaba daya ta rasa a duniya abinda Ke mata dadi kuma ta kira wayarshi a kashe haka tasu Atika da gateman hakan yasa tana kuka tace Kinga abinda nake fada miki ko Yaya Suhaila dama nasan Wallahi Junaid se ya bata min rai. Tsaki Suhaila tayi hakika Bata taba katari da dan iska Irin Junaid ba, ita tunanin hakan bai zo mata ba shikam mukhtar dadi yakeji a ranshi Yana inama yanada courage din Junaid. Haka Suhaila ta kira hajiya ita kuma Tace subay'a tabi su ta Kwana a can. To fa people kunji wannan! Tunda ta fita Junaid ya sanar dasu su rufe gida sannan kowa ya kashe wayarsa yana ganin is high time ya kamata ya fito ma Subay'a a yanayin da take so dama bahaushe yace idan kida ya canja to salon rawar ma canjawa yake. Haka Subay'a Tana gani suka nufi gidan Suhaila dake gaba dasu, Tun tana kuka Suhaila Na bata Baki har ta share ta. Haka wannan Daren ta rabashi tana tuntuni da da nasani Marar amfani. It's too late to cry when the head is cut off. Shikam Junaid baccinsa yayi dukda yana missing Sulaim komanta maganarta, shagwabar ta, murmushinta da ita kanta don tun ranar da sukai waya taje kaduna basu sake magana ba dukda dimbin urge din dayake jin akan son jin muryarta amma a haka ya hakura shi lallai Lokaci baiyi ba. Da Asuba ya hada musu kaya shida yaran ya sallami duka cooks din sannan ya zubawa Matar gidan kayanta yawanci na office ne sannan ya rubuta wani abu cikin takarda ya bawa driver dinsa da key din motarta akan yakai mata gidan Suhaila, shikuma ya tasar mawa Kaduna shida yaran. Turkashi! Seda ya gama parking sannan ta bude kofar ta fito, idanunta suna cikin wani glasses square shape fari me fadi Wanda ya rufe kusan har kusa da cheeks dinta yayi mata kyau kuma ya bawa hancinta dayake dogo damar fito da aihnahin pointedness din nasa, fuskarta babu ko fara'a akasin yadda asalin Sulaimi take, cikin nitsuwa take takowa har tazo daidai kofar parlour taga an bude Ja'afar ne, Fuskarshi shima babu walwala amma yana ganinta tamkar dama ita yake jira ko kuma nemanta yake oho musu, hannunta ya jawo wanda yasa tayi saurin kallonshi tareda kicinayar kwacewa amma ya damke da kyau seda ya kaita har bakin motar shi kafin ya sake mata hannun aikuwa kamar jira take ta sakar mishi duka a kirjinshi tareda fadin Don't ever touch me kaji na gaya maka. Murmushi yayi yace Ba wannan ne damuwata ba, the fact that kawai dan kin ganni da wata se kiyi ta fushi? Kwananki uku Amma you shun my calls ina miki magana kina basarwa Duk saboda wannan to shikenan Sulaim am sorry she's just a friend and nothing more I'm really sorry bazaki kara kamani da irin laifin ba. I'm sorry please Luff. Tunda ta Fara magana take kallonshi wani side na zuciyarta na fada mata karya yake wani kuma want to believe him Sede na farkon Yafi rinjaye amma se ta bashi another chance Tace Yaya Ja'afar I will never take shit from you ever again, never! Da nayi amma yanxu the world is vast I can't, Nasan halinka kuma duk wanda kake tare dasu na sani amma I never taught it can go to the point where kacewa budurwarka I'm your baby Sis. I won't take that. Idan yan matanka kake so Dan Allah kaje ni bazaka Bata min Lokaci ba. Wani madaukakin mamaki ya addabe shi da gaske Sulaim ce ke blabbing words dinnan? Eh gaskiya university ba karya bace, wannan ba karo bane na farko da ta ganshi da wata ba amma she never fuss on it se yau tabbas akwai aiki gaban Maza. Naji it's OK zan kiyaye yanzu smile mana. Harara ta maka masa ta juya Don komawa ciki sede kamar ance daga kanki taga Junaid a tsaye jikin railers da suka kawata balcony saman, ya zuba hannayensa cikin pockets din wandonsa yana kallonta, wani Irin kallo yake mata me Cikeda dimbin tambayoyi, tuhuma da kamar you failed me haka ta gani cikin idanun shi, sauke kanta tayi ta kasa motasawa Daga gurin Ja'afar dake tsaye bai lura ba Yana mata dariya yace Sweetm idan ba zaki shiga ciki ba zo muje kisha ice cream. Kawai zuciyarta ta Raya mata kibi Ja'afar haka kuwa tasa kafarta a nutse a kuma sanyaye ta fada motarshi, Junaid da yaji kamar ya Kurma ihu haka yaja dogon huci tareda lumshe idonsa. To fa one word for the page, for Junaid, for Ja'afar, for Sulaim and for Subay'a da danginta. Shatuuu ♥️ [6/28, 7:40 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 9 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Yana bude idanunsa wanda suka kusan Mintina biyar a lumshe, se ganin shigowarta yayi hakan ya bashi mamaki Don a iya saninshi tabi Bayan Ja'afar ne su fita. Itama Sulaim din bata kuma dubar inda Junaid yake ba ta shige cikin parlour, Mami ce kadai a zaune se Muhammad da Ahmad, suna jin muryar ta suka taho a guje suka rungume ta, itama rungumarsu tayi tana ta murmushi, kwanaki biyar kawai da zuwana kaduna take jin tayi missing dinsu sosae. Hannunsu taja suka samu guri kan carpet suka zube suna tayi mata surutu wanda Seka rasa inda suka gadoshi kasancewar iyayensu kaf babu me surutun sede ko idan Jawad da Ja'afar sukai wa Kara. Auta kin dawo? Dagowa tayi ta dubi Mamin tace Na dawo Mami, Tace Tana gaisheki sannan da zarar kayan sun iso zakiji sakonta. Kai Mami ta gyada tace Yayi kyau, Allah ya miki albarka, Junaid Yana tambayarki kun hadu? Take yanayinta ya canza dama dalilin da yasa Mami yin maganar kenan tana zargin akwae Abinda Ke aukuwa between the two. Bamu hadu ba, tare yazo dasu Ahmad? Eh Kawai Mami tace ta cigaba da Abinda take itakuma tana wasa da yaran. Wani ihu Subay'a ta saka lokacinda mukhtar ya mika mata key din motarta hade da farar takarda cikin farar envelope, Yaya Suhaila na shiga uku ya sake ni, Abban Fannah kaje ka bashi hakuri , na shiga uku! Baki daya babu wanda ya samu courage din tunkarar ta, hatta shi mukhtar wanda Tunda Sabi'u driver ya bashi takaddar yake murna cikin ransa Don Yana son su koyi hankali baki dayansu. Amma yadda Subay'a ke yin abu se yaji baki daya tausayinta ya kamashi, itakam Suhaila ba karamin rudani ta shiga ba saboda tasan duk inda aka je tanada kamasho cikin wannan abin. Subay'a kam bazata ma iya fadar yadda take ji ba se kawai ta rabe su ta shiga dakin da ta Kwana ita bata bude takardar ba saboda tsoron content din ciki haka kuma Bata daina kukan da takeyi ba har Seda ya tashi Fannah yarinyar Suhaila, ganin halin da uwarsu Ke ciki yasa ta Mike ta fito parlour Don jin Karin bayani, a parlor babanta kawai ta tarar da Suhaila ta koma dakinta saka kaya gwara su tafi Asibiti ko gidan hajiya. Abayar da tasaka jiya ta sake mayarwa ko brush ba tayi ba ta fito hawaye Yana mata zarya, ita bata taba tunanin Junaid zai iya makamancin haka ba, ko sau daya bata taba kawowa dan abinda ya faru jiya can lead to such commotion. Tare suka fito da Suhaila wadda lokacin tace Abban Fannah Bari muje gidan hajiya, Fannah do the right thing. Bata jira amsar daya daga cikinsu ba tayi hanyar waje, ita ta karbi motar tana driving bayan Sulma ta tabbatar musu kowa na asibitin, don haka can suka nufa. Kiyi hakuri Subay'a ban kawo abin zai zama haka ba, amma kema tunda Kinsan halin mijinki ai you shouldn't have followed me. Kunji fa bayan seda tace bazata je ba ta tursasa mata amma yanzu take dora mata blame din itadai jinta kawai take amma gaba daya hankalinta ya tafi Irin rayuwar da zatayi idan Junaid ya saketa, kenan ta kaishi bango? Kenan ta kure hakurinshi? Dama idan bakaji bari ba kaji Hoho. A asibiti kamar jiya haka suke zaune kowacce tayi shiga ta alfarma, kayan wannan yana cewa na wannan bani waje Don a su takwas babu wadda Ke Auren talaka dukkansu masu kudi ne tamkar policy haka abin yake. Tundaga sallamar Suhaila Salina tace Lapiyarku? Hajiya da sauran suna binsu da kallo har Subayaa ta fada jikinta tare da fadin Hajiya Junaid ya sake ni na shiga uku. Gaba daya salati suka saka saboda yadda abin yaxo musu a bazata. Me ya faru? Hajiya ta tambayeta Tana dagota Daga jikinta. Ba karya ta zayyane mata komai tareda mika mata envelope din. Karba tayi itama jikinta yayi balain sanyi ta buda sede content differs from Abinda kowa Ke tunani.... It says Ki zauna a gida ki Bari har se ranar da babyn yayi Kwana arbain se ki dawo. Wani sigh of relief ta saki tareda bawa Surayya wadda ta karanto a fili nan take jikin kowa yayi dadi se kuma suka Fara zaginshi shi uban waye da zai musu gatse Wallahi ba zata koma ba se ranar da ya yanka mata kuma se Sun gwada mishi tana da gata. Itakam Subay'a batace uffan ba se godewa Allah da take, anan tayi wanka dake seminar bank dinsu ya turata Hakan yasa Bata fita Tunda online ne seminar kuma se wajen laasar ake Farawa. Baki daya suka tafi suna kara lallashinta akwai solidarity sosae a tsakaninsu. Daga ita se Sulma suka rage a dakin Bayan kowa ya fita tace Sister dama Papa bai yarda ba jiya kika fito? Dago kanta tayi fuskarta Cikeda alhini tace Seda naki zuwa tunda yaki bari amma tace Wallahi se naje. Haba Sister kina me ita Yaya Suhaila ita take aurenki ko Papa ke aurenki. Kin ganni da ne nayi sokanci nake bin duk Abinda suka gindaya min amma ki sani tun ranar da na fahimci cewar ina dauke da cikin nan naji tabbas bazan iya sake yiwa Umman D iskanci ba haka darajar D ta sake karuwa a idona. Yanzu akan D babu Abinda bazan iya ba kuma na yadda na Bata da kowa Don duk ranar da aurena ya mutu babu Wanda zai jajanta min cikinsu kin tuna yadda Yaya Safina tayi. Tunda na haihu nasan darajar da kuma naji idan ace Dana yayi aure matarshi take neman rabani dashi Se inda karfina ya kare, Umma tayi hakuri don haka I'll make it up Kema ki yadda komai ki fuskanci aurenki Sister. Share hawayenta tayi tace Ki bani shawara ya zanyi Ki jira ayi suna Seki koma kafinnan kiyi mishi text ki bashi hakuri sannan kiyi addu'a ki kuma gyara kurakuranki is never late. Haka Sulma ta dinga bata shawarwari kafin kuma suka fada wasu hirar abinsu na yan uwantaka hakan yasa ta ware abinta. Mami yau dinner amaryar Ridwan inason Sulaim ta rakani. Junaid ya fada suna zaune lokacin shida Mami, Sulaim dake gefe tayi saurin dagowaa Sede suna hada ido da Mami tayi saurin dauke kanta. Murmushi Mami tayi tace Babban Yaya ni na amince ita zaka fadawa. Wani fari tas yaji ranshi yayi mishi hakan yasa ya dubeta yace Auta ki shirya 8pm Zamu je. Se taji bazata iya missing opportunity din ba hakan yasa tace Tom. Tunda ta Idar da sallar isha'i ta bude wardrobe dinta tana assessing kayanta, tunani take tayi me zata saka a jikinta, haka kurum take son fitar dashi kunya, so take tayi kyau. Tana tsaye taji ringing din wayarta da sauri ta isa gurin amma maikmakon ganin kiran Junaid as expected se kiran Ja'afar, karamin tsaki tayi ta aje wayar can ta hango wani lace har ta kai hannu zata ciro se ga Mami ta shigo, da murmushi saman fuskarta tace Troubled? Kanta ta gyada hakan yasa Mami tazo ta tsaya tana scrutinizing kayan har takai kan wani kyakyawan code net wanda ta dinka mata a wani biki kuma aka fasa Baki daya, gold ne material din me dinkin skirt da Riga se ta dakko wani black scarf ta daura mata bayan tayi touching mata fuska da light make up, take sulaim ta fito tayi kyau kamar ka saceta. Seda ta gama komai sannan suka fito tare har kasa, Junaid ta Fara hangowa cikin milk tuxedo suit se tie Baki da leather covered baki da matching wrist watch. Yayi kyau sosae shima tamkar ka sace su. Baba yana zaune ganin sun fito yace Is like an wareni fa, se ina haka? Dariya duka sukayi Mami tace Ridwan ke kara aure shi ne zasuje dinner. Kallonsu yayi sosae bai kara cewa komai ba Mami tace Allah ya kiyaye, Junaid Kada kui dare. Inshaaa Allah Mami, Baba se min dawo. Kamshi ya gyada musu yayinda Sulaim tayi waving dinsu suka fita, zama Mami tayi ta fuskanci Baba Don taga akwai magana bakinshi, aikuwa tana zama yace Kin kusa hada wani auren ne? Me ka gani? Ta bashi amsa da tambaya , Yaranki is like they're in love amma ko nayi mistake ne? Kanta ta girgixa tace I'm not sure, so Kaga bazan ce maka komai ba amma from yadda suke exhibiting wasu signs ina tunanin kamar ....... Is not kamar they're deeply in love with each other, kawai dai ina tunanin basu fahimta bane. Kai Mami ta rike tace Amma Ja'afar fa? Dariya Baba yayi yace Keda yaranki ni nawa ido kawai. Shiru Mami tana nazarin maganganun Baba. A cikin mota babu me magana baki dayansu sunyi shiru se karar ababben Hawa dake yawo kan titin. Junior ne ya fara breaking silence din yace Yaushe zaki koma Kano? Saturday Ta bashi amsa, ita ta rasa dalilin da idan suna tare se tana jin bugun zuciyata yana karuwa sosae, ga wani uneasiness da take ji ko kuma da yayi mata magana se taji dukkan ilahirin jikinta ya amsa, ko kuma ta zama short of words gwara ma idan waya suke. Basu kuma magana ba har suka isa event center din, cike gurin yake da motoci Nawa Kece raini, guri ya samu yayi parking sannan ya dubeta yace Shall we? Murmushin nan nata me kyau tayi masa sannan ta bude kofar suka fito a tare, seda ya rufe kofar da kyau sannan suka shiga shoulder to shoulder. Dake gurin yan Boko ne masu kudi kuma komai a tsare hakan yasa kowa Yana zaune dake Baifi Mintina biyar da Fara event din, suna shigowa idanun MC ya sauka kansu kawai se ya fara fadin Kaga wasu couples wanda Bayan Amarya da ango Bana tunanin akwai wasu perfect match kamarsu, kallesu fa Gaba daya wani nishadi ya mamaye Junaid ya dago idanunshi lucky enough ya hade cikin na Sulaim take wani covolent bonding yayi taking place dukkansu seda zuciyoyinsu ta tsaya cak kafin kuma sauke idanunsu hakan yasa hanaklin kowa ya koma kansu Sega Amarya da Ango sun sakko daga inda suke Zaune dan karrama su, hakan yasa duk inda suka gifta kallonsu ake a haka suka zauna, se taga yawancin abokansu in one way or the other tasansu a Faculty yawanci lecturers dinsu ne. Suna ta zuwa suna gaisawa har wani da bakinshi baya shiru yace Ashe mun kusa zuwa wani bikin, da farko nayi tunanin uwargida ce ai. Dan murmushi Junaid yayi yace Bakaga muna kama ba autarmu ce banaso zuwa ni daya. Autarmu ta maimaita cikin ranta, shikenan matsayinta no any other special matsayi only a sister. Baki daya se taji ta gundura da zaman garin duk yadda ake abubuwa na ban dariya saboda MC akwai barkwanci Amma se taji gaba daya haushin gurin takeji. Duk Abinda take yana Lura da ita amma bazaice ga takaimaiman abinda ya bata ranta ba ganin haka yasa yace Kin gaji mu tafi ne? Da sauri ta gyada kanta, se ya Mike itama tabi bayanshi sukayiwa Ridwan sallama wanda se tsokanarshi yake ba tareda ya Bari Sulaim din taji ba. Shatuuu ♥️ [6/30, 7:28 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 10 ✍️Shatuuu♥️ 🌈Kainuwa writers Association #⃣shatuuu095@wattpad Let's call it a day! We meet in our next class and hopefully there will be test then. Malamin ya fada bayan ya kammalla darasin shi na wannan ranar, haka ya shiga tattare kayansa cikin briefcase yayinda sauran students din dake cikin ajin kowa Ke hade nashi dukda bawai sun gama classes din ranar bane Amma akwai interval na zuwa aje ayi sallar axahar, Wanda zasu ci abinci suje suci. Seda yazo fita kafin yace class rep dinsu ya bishi. Sulaim na zaune inda kusan kullum nan take zaune har tana neman maida gurin permanent seat dinta, hada book din datayi taking note a ciki Ta zura cikin wata off white back pack, dake ranar talata ce hakan yasa kowa Yana sanye da black and white, haka tsarin Law school yake a BUK every Tuesdays and Thursdays black and white ne sede wasu ranakun ko Za'a fita ko kuma zaayi mood trial to dole ne a saka wannan uniform din, hakan yakan sa su zama elegant and attractive. Yan mata uku suka taho inda take Zaune tana niyyar mikewa, Khulthum ce ta Fara cewa Sulaim tashi mu tafi. Mikewa tayi ta sabi back pack din a shoulder dinta daya wrist watch din hannunta wanda yake Baki kuma yayi kyau kan shiny caramel skin dinta ta duba. Tare suka fito su hudun Ummu_Sulaim, Ummu_Khulthum, Ummu_Aimana da Ummul_khairi.....the 4 Ummu's. Khairi tace Kuzo mu fara yin sallah kafin muje neman abinci. Khulthum ta bata rai tace Gaskiya ni yunwa nakeji, mu fara cin abincin kawai. Ke kullum yunwa kikeji baki cin abinci daga gidan ku ne? Harara ta watsa mata Wanda yasa Khairi yin dariya itakuma Aimana tace To meye abin hararar tawa, ba gaskiya na fada ba, malama sallah zamu Fara yi. Itakam Sulaim jinsu kawai take don bawai tayi wani sabo bane ita dasu last week suka dawo Daga mid semester break, ranar da ta dawo ta nemi Khulthum saboda zaman ita daya baya mata dadi to ita kuma Khulthum already tanada su Aimana hakan yasa sukai jamming baki dayansu. Amma har yanxu bata fiya sakewa ba sosae. Massalacin suka Fara zuwa suka bada farali Khulthum tana ta bacin rai wai ba'a girmama opinion dinta ba. Sulaim kam murmushi kawai take musu. Wani joint sukaje nanma kafin aje seda aka bata Lokaci kan ayi deciding gurin da Za'a ci abinci Se sulaim taji tarayyar batada amfani don lokacin tana ita kadai yanxun ta kammalla komai ta koma class amma ya zatayi Tunda ta Riga ta biyosu. A joint din sukai order fried rice da salad se Beef akai da drink. Dama se an gama ake biya kuma kana shiga gurin kasan na manyan yara ne ya'yan masu kudi don hardly kaje baka hadu da wani lecturer ba a gurin, sunsan takan iya girki. Suna fara cin abincin wayar Khulthum ta Fara ringing gaba daya suka kalleta itakam tana kokarin picking tana sakin wani lallausan murmushi Kina ina ne? Shi ne tambayar da Hu ya Fara mata, cikin daidaita muryarta ta fada masa joint din da suke. Tana aje wayar Aimana tace Wa zaki rakito mana? Khairi wadda wasu abubuwan nata na shige Dana Khulthum tace Batta yazo dama yau purse dita babu nauyi, Dan kun nace Keda Sulaim ne amman yau banyi niyyar Zuwa gurinnan ba. Dariya Sulaim tayi ta cigaba da cin abincinta saboda itama yau yunwar takeji Don Junaid Nada class din safe yau hakan yasa ya figo ta bata wani Yi breakfast din kirki ba. Suna tsaka da cin abinci Hu ya shigo shida abokansa kusan zan ce muku babu Wanda a gurin bai san lucky Hu ba, har wani kirari ake mishi Kaga yaro me kudi kana gudu luck na binka, yaro me tashe. Kusan bawai a faculty dinsu yayi suna ba entire new site ansan Lucky Hu saboda yadda yake da yanmata idan baiyi dating dinki ba to yayi flirting kawarki haka abin yake Shiyasa ko award night ake shi ke daukan most popular a cikin faculty. Abokansa uku suna bayanshi, Tunda ya shigo Khulthum baki daya ta rasa nutsuwarta, ta gyara nan ta matsa can har Aimana tace Dallah ki nutsu se kace tsutsa kin kasa zama guri daya Bari naga waye wannan saurayin. Me zasuyi banda dariya Don Aimana ita ke maganin rawar kan Khairi da Khulthum. Gefenta ya tsaya tareda dubansu Sulaim yace musu Sannunku! Suma sannu sukai mishi daidai lokacin gama cin abincinsu Aimana wadda tana kallon Hu ta ganeshi kasancewar faculty dinsu daya da yayanta kuma yana yawan bata labarinsa, mamaki sosae tayi haka yake kamar me charm indai yace yana so to dole ne mutum ya amince dukuwa da sanin halinshi da sukai, mikewa sukai Don biyan bill ya dakatar dasu yace Paid! Kuna kawayen Her Majesty ta yaya zaku biya kudin abinci. A'a Khulthum se aka Fara blushing Irin taji kunyar nan, itakam Sulaim shiru tayi tana jiran jin Abinda sauran zasu fada. Aimana ce tace No Dan Allah Karka Kara biya mana , zamu biya namu ita se ka dinga biya mata. For today thank you! Tana fadin haka taja hannun Sulaim suka fito ita kuma Khairi ta zauna godiya, yayinda Huzaifa ya bisu da kallo saboda bai taba katari da irinsu ba, kawayen yan matanshi shishige masa suke amma wannan har akan Fuskarshi take fada masa bata bukatar payment dinsa. A class Khulthum ta shigo lokacin already Ridwan was in class, dayake period dinsa ce yana taking dinsu wani course shima banashi bane mutumin bazai samu Zuwa bane Shiyasa ya turoshi, so ranar ne ranar farko da ya Fara shiga class dinsu. Tana ta yauki ta shigo class din itada Khairi, bai ce musu komai ba seda t Suka zo tsakiyar aji yace Hey! Get out of my class, irresponsible ones. Simsim kamar an dakesu haka suka fito Khulthum tana ta Balai yaci musu mutunci, se bayan La'asar ya fita kowa ya tashi ya fito, tunanin Aimana da Sulaim Khulthum tuni ta tafi dake Khairi a hostel take su uku suna day. Tana hangosu ta nufo su, Sulaim ce ta Fara fadin Me yasa kuka zo late gashi yayi yabbing dinku. Tsaki Khairi tayi tace Rabu da shege, ya dauki tsayi kamar Daren bakin ciki. Dukda maganar batayiwa Sulaim dadi ba ganin laifinsu ne for coming late, banging into the class without permission seda tayi dariya wai tsayi kamar Daren bakin ciki. Khulthum ce ta Fara magana ranta a bace tace Aimana ni banji dadin Abinda kikayiwa Huzaifa ba, har zakice wai ya rike kudinshi, don kin samu ya kalleki ma. Baki sake Aimana take kallon Khulthum kafin tace Ya kalleni? Na rokeshi ne? Ke nifa Bana son wani kato ya biya min abu har idan zan wuce yana tunanin favor yayimin, kuma Inace cewa nayi ya biya muku nida Sulaim Bama bukata.... Ke bana son nonsense stuffs kinji. Ganin ta dauki zafi yasa Sulaim tace Kai friends basa fada, Dan Allah kui hakuri meye a ciki. Khulthum dai batace komai ba se juyawa tayi ta nufi inda yake jiranta kullum ta bi bayanshi ta fada mota suka tafi, Khairi ma sallama tayi musu ta tafi hostel itada wani gaye dan class dinsu. Se ya rage Aimana da Sulaim wadda har lokancin mitar abin take, suna tsaye Sega kiran Oga Junaid ya shigo gabanta ya fadi don ta rasa me ya hanata kiranshi tace ta gama kamar yadda suka Saba bare yau tasan har ta gama lectures bai tashi ba Balle tace ko Yana gida. A hankali kamar me tsoro ta Kara a kunne tace Yaya na gama. Ki samu napep ya kawoki na wuce Tun dazu, zamuje shopping da Subay'a Zaro idanta tayi don bai taba barinta ba ko ya tafi se ya dawo ya dauketa hakan ya kular da ita ba tareda ta amsa ba ta kashe wayar, kallon Aimana tayi tace Bari na tafi me daukan nawa baya kusa. Kai ta girgixa mata tace Yanzu Yaya Nu'uman zai zo se mu Baki lift. Itama kanta ta girgixa tace A'a gaskiya ki...... Bata karasa ba Se gashi yayi parking a gefen su hakan yasa taja hannunta suka isa bakin motar, baya ta budewa Sulaim ta shiga ita kuma tayiwa kanta masauki a gaba, waya yake Don haka ko gaisuwarsu bai amsa ba in fact baisan Sulaim na ciki ba a haka suka fito Daga BUK, kafin su karaso AA Marmaro inda nan ne kwanan gidan Junaid Aimana tace Sulaim kiyi mishi kwatance. Aje wayar yayi yace Keda waye. Kafin ta bashi amsa ya hango Sulaim ta jikin mirror, bai kalla fuskarta da kyau ba se side view dinta dake gefen window take kalla, gabanshi yaji ya fadi take zuciya ta kwadaitu, muryata yaji a hankali tace Kwana ta gaba zan sauka. Kasa furta komai yayi saboda yadda ilahirin jikinshi ya amsa Daga Wannan furucin da tayi, seda Aimana tace Yaya Nu'uman magana ake maka Naji Ya fada suna zuwa Kwanar Tace zata sauka se ta karasa tunda babu Nisa, godiya tayi musu a lokacin ya samu damar kare mata kallo, itama kuma haka, fari ne sosae kamar yadda Aimana take babu laifi yanada kyau. Suna amsa mata godiyar ta nufi layinsu, tafiya kadan ta isa gidan, tura karamar kofar tayi ta shiga ta gaida maigadin sannan ta nufi parlourn, kafin ta kai ga budewa aka bude, Junaid ne shida Subay'a wadda ta dawo tun Kwana hudu da haihuwar Sulma ta bashi hakuri sosae tareda nuna nadamar ta, shi bashida matsala hakan yasa ya manta da abin suka cigaba da rayuwarsu. Bayansu Ahmad da Muhammad ne da dukkan alamu fita zasuyi, seda ta Fara gaida Subay'a sannan ta tsaya Seda suka fito sannna Junaid ya dubeta yace Ya akai se yanzu kika dawo. Kanta ta dan dauke Daga kanshi tana jin yadda yake ke beating wanda ta rasa dalilinshi kuma abin is only idan tana tareda Junaid ne tace Babu komai. Tana fadin haka ta Kara da fadin Allah ya kiyaye Tayi ciki abinta, shiru yayi a gurin ya bita da kallo se yaji kamar bataji dadi ba, se zuciyarshi take tuhumar shi akan ya bata mata rai ne? Kallon Subay'a yayi wadda tuni ta isa gefen motarshi ya Dan Daga murya yace Nayi mantuwa Bari yanxu zan fito Kanta ta gyada mishi, shikuma ya koma cikin parlour, straight dakinta ya nufa ya kwankwasa kofar. Itakam Tunda ta shiga kujera ta fada ta zauna tayi shiru haka kurum taji ranta a tsananin bace kuma babu abinda take bukata tayi irin kuka, kafin ta gama tunanin aka Fara knocking tasan su Atika ne a ranta tana mitar Daga dawowar mutum Za'a isheshi, kofar ta bude se taga Junaid a tsaye Yana kallonta, kanta ta dauke tareda pouting face dinta, se yaga tayi mishi wani kyau yaji if to say it's okay he'll hug definitely hug her dan fuskarta ta nuna ranta a bace yake amma babu dama hakan yasa yace Shopping zamuje kiyi min text din abinda kike so kinji? Unconsciously ta buga mishi Harara wadda tayi cikin sa'a ya gani hakan yasa ya zaro ido da mamaki amma se ta dauke kanta tamkar ba ita tayi ba tace Tohm. Tana fadar haka ta tura kofar ta shige, kanshi ya shafa saboda ba haka zuciyarshi ta aiko shi yayi ba, ta aiko shi yaji damuwar abinda take so sannan ya fada mata abu me dadi, who knows he will mess up but he couldn't! Bazai iya ba he lacks wannan courage din. Fita yayi suka tafi Yana ta mamakin shi Sulaim ta harara, yayinda take kwance har aka kusa kiran maghrib sannan tayi wanka ta bada farali, Tana idarwa wayarta ta Fara ringing, Bro ta gani hakan ya tabbatar mata Junaid ne se ta samu kanta da kin picking, sau biyu yana kira Tana kin dauka shima se ya hakura. Can Sega kiran Ja'afar ya shigo, Kwana biu nan se taji yau tana daukin jin muryarshi, cikin silvery voice dinsa yace Ina gate gidanku fito mu gaisa. Da gaske! Ta tambaya Tana jin wani nishadi from no where Come and see for your eyes. Kit! Ya yanke call din, Cikeda zumudi ta Mike ta zaro wani plain lace peach zani da riga, se kuma ta mayar ,ta janyo Abaya ash da silver stones se off white lace da aka saka a edge din hannun da kasan Riga... Rolling tayi da veil din kayan ta fesa turare sannna ta dauki wayarta ta fito anan sukaci Karo da Atika Uwardakina Kinyi kyau, ina zuwa haka? Sa ido yanxu zan dawo Har ta tafi ta isa bakin parlour Se ta tsaya da gaske Ja'afar take wa wannan zumudin ko kuwa? What if idan Junaid ya dawo suka hadu Don ta dan Lura baisan tarrayar su? Tayi kusan 7 minutes kafin zuciyarta tace mata go shi matarsa Ya dauka suka fita, se ke xa'ayi caging a hanaki. Da Wannan ta samu karfin gwiwa ta fita, megadi na zaune Tace dashi Baba Bari na karba sako Bata jira me zaice mata ba ta fice, Itakanta bata taba ganin motar ba tana tunanin ya sake mota ne, Tana isa inda yake ya bude mata ta fada Ciki ,tana rufewa ya ja motar with full speed ya bar layin. Da mamaki tace Yaya Ja'afar what are you doing? Dariya yayi mata yace Kin manta a kd kika ki bina kisha ice cream shi zan kaiki kisha yanzu. Dan Allah don't do this kaga yaya bai sani ba Kada ya dawo bananan. Bai kara kulata ba itakuma Bata fasa Yi masa magiya ba amma yayi iskar kare da ita, hakan ya tayar mata da hankali. A gida Junaid da Subay'a sun dawo, yana gama parking megadi ya sanar mishi Sulaim anzo an dauke ta a mota kuma baisan waye ba. Bakasan waye ba? Ni Kake cewa baka san waye ba? Ya fada Yana nuna kanshi tareda nuna kanshi wanda hakan seda yasa megadin firgita, hatta Subay'a mamaki tayi yadda ya Daga murya ashe basuga komai ba. Gidan ubanwa ka barta ta fita? Wayace ka barta ta fita? Subay'a ta matso zata rike hannunshi ya juya kanta Don't you dare touch me. Se taja baya saboda yadda ta tsorata da yanayinshi, Ya dinga masifa wadda tasa baki daya veins din kanshi suka tashi, yayi yayi se kuma yayi shiru ya dinga safa da marwa yana karkada kanshi, baki daya kwakwalwar kanshi ta cushe waye ya fita da ita? Ina kuma taje? Ganin yanayinsa yasa na aje wayar haka kada nima yar rahoto ya make ni! Lol...... Waye zai bawa Junaid ansa NE? Ya haduwar Sulaim da Junaid zata kasance? Me Ja'afar ke planning yi kadafa yayi! Shatuuu♥️ [7/1, 8:57 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 11 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Yaya Ja'afar shi ne soyayyar? Shine son da kake ikirarin kana yimin? Where are you taking me to? Ta fada mishi muryarta na shaking abu kadan take jira tayi breaking , bai kalleta ba se tukinshi da yake saboda shi ba wani abu yayi niyyar yi mata ba amma abinda ya bata mishi rai yadda take nuna bata yadda dashi ba kwatakwata, Tana nuna zaici wani abu ne daga gareta. Kafin wani Lokaci temper ta Fara building within him hakan yasa yayi wani wawan reverse ji Kake kiiiiiiiii! Ana taka burki Allah ya kiyaye babu wani da yake gaf dashi don da tuni labari yasha banban. Ihu Sulaim ta saki ganin Abinda Ja'afar yayi kafin wani Lokaci baki daya jikinta ya fara rawa kamar wanda aka saka mata mazari. Mummy! Daddy! Baba! Mami! Yaya Junaid! Shikenan sunan da take ambata, wani Irin gudu yake fallawa idan ka gani zakayi tunanin kodai yasha ta kada masa karya, kodai titin danshi kadai akayi ko kuma bashi da hankali. Tunda Sulaim take bata taba tsintar kanta cikin madaukakin tashin hankali kamar wannan ba. Jin ya taka burki yasa ta bude idonta Wanda hawaye ya bata su, hannunta tasa da sauri Zata bude ba tareda ta duba ina bane ita kawai tsira take nema. Lock ya danna wanda yasa ta dubeshi da sauri tareda kwalalo masa idanunta da sukayi ja waje. Is not like zan cinye ki ne, saboda banga abinda zai tayar min da hankali akanki ba, idan I wanted an affair with you ba ta haka zan biyo ba.... Rubbish! Ya gama fada Yana jan tsaki, cire lock din yayi da sauri ta bude kamar an hankado ta ta fito a guje se taga Baifi 70 meters bane away da gidansu hakan yasa ta nufi gidan da sassarfa sede Tana kama handle din gate din da niyyar rufewa taji gabanta ya fadi saboda idanunta sun sauka akan motar Junaid. Megadi ne ya taso da hanzari yace Ina kikaje Alhaji Yana ta nemanki? Gabanta taji ya kuma faduwa jin ya ambaci Alhaji, shi kenan itada Junaid se Allah yau, Bata bashi amsa ba ta wuce ciki kanta a kasa gabanta nata faduwa, a parlon babu kowa ba yadda tayi tunani ba, don haka da sauri ta nufi dakinta Sede ta na daura hannunta Kan handle din taji wannan deep voice din tashi yace Daga ina kike. Yadda ta Juyo a kidime seda wayarta ta fadi kasa, dagowa tayi ta dubeshi Yana tsaye Fuskarshi babu annuri ko digo, se ya zame mata tamkar ta zaki hakan yasa ta kasa furta komai se wasa da take da yatsunta Se na maimaita kenan? Nida yaya Ja'afar muka fita. Da izinin wa? Se tayi shiru Tana son ce masa tayi mishi text Amma babu Wannan halin saboda lokacin da taga da gaske bazai saurareta ba ta turawa Junaid short message, Tana tunanin yadda zatayi taji ya dauke ta da wani gigitaccen mari! Dagowa tayi a rikice ta fito da idanunta waje Cikeda mamaki kafin kuma ta rike gurin saboda zafin da taji, shima se ya tsaya Yana kallonta Cikeda mamakin Abinda yayi, he slapped her? Sulaim? Seriously? Itakam lokacin hawaye sun Fara mata zarya saman kuncinta saboda tsabar zafin da zuciyarta keyi, yana ta jujjuya Hannunsa Wanda yayi Marin dashi, ta shige dakin ta durkushe ta saki wani Irin kuka me taba zuciya! Dafe kanshi yayi saboda yadda yake Sara mishi ya nufi dakinsa ya zube saman gado ya lalubo wayarshi ya fara neman layin Ridwan kamar jira yake a kira ya dauka yana fadin Angon Sulaimi Baban Ahmad da Muhammad! Cikin wata Irin murya me Cikeda rauni yace I slapped her! Marinna nayi ya zanyi? Cikeda mamaki yace Wa ka mara? Subay'a Kanshi ya girgixa Don wannan lokacin yana jin inama ace Subay'a yan mara yana ganin da bai shiga halin da yake ciki yanzu ba. Cikeda nutsuwa ya kwashe komai ya fada masa, ya kara da fadin For the first time zuciya ta dauke ni na daki abinda take martabawa take ganin mutunci take kuma so sannan take tattali, ya zanyi Ridwan? I'm in a mess Wallahi. Ajiyar zuciya me nauyin gaske Ridwan ya sauke yace Aikin gama ya gama ka zartar da hukunci cikin fushi, ba halinka bane Amma kishi ne. Ina ganin ka bata space zuwa safe muga yadda zata tashi. No! I'm going to Appolgise yanzunnan. A'a Kada ka sake kamar ba namiji ba, zancen gaskiya Sulaim tayi laifi fa, hukunci kayi mata a matsayinka na brother not suitor, so ka barta. Da kyar ya shawo kanshi ya amince da hakan saboda yana ganin kamar wannan zai saka ta tsaneshi. Yana aje wayar yaga alamar sako a notification plate dinshi, yana shiga yaga Daga Sulaim ne ta turo masa 3 hours ago Yaya... Ya Ja'afar yazo zan Yi mishi rakiya Bazan jima ba That's all the content of it, gaba daya se yaji hankalinsa ya kuma tashi, me yasa zaiyi fushi ya Mari Sulaim? Kansa ya dafe wanda yayi masa nauyi ya kwanta kan gadon, Yana kwancen Subay'a ta shigo cikin kayan baccinta silk very sexy and attractive, Tunda ta shigo take kallonsa Amma baisan ta shigo ba saboda yadda yake deep in his thoughts, kallonshi take tayi zuciyarta tana hana mata abinda take zargi, Kwana biu ta Fara zargin Anya Junaid ba son Sulaim yake ba, ko Abinda yayi dazu abune da bata taba gani ba, amma yadda Lokaci daya ya birkice kamar zautacce shi ne yake daga mata hankali, kada ya kasance tana zaune ayi mata manakisa. Haka ta rungumeshi tare da fara bashi wani sensual and seductive kiss, cikin sanin bukatinshi ta Fara sarrafa shi, kafin wani Lokaci ya bada Kai tareda mantawa da existence din wata mace na iya wannan lokacin . Baiwar Allah Sulaim ta sha kuka ta godewa Allah se taji gaba daya alhakin komai akan Junaid ta saukeshi, tamkar he caused everything dinnan haka take ji. Tana nan kwance bacci ya dauketa haka tai tayi Marar dadi tana ta ajiyar zuciya. Kafin asuba har ta tashi tayi dukkan abinda zatayi ta shirya tana ta tunanin yadda zata bullowa Junaid, ita bata kawo Ja'afar a ranta don batada lokacinsa se ta gama da wanda zuciyarta ta fi karkata a kai kafin ta dawo kanshi. Idan ta tuna Yaya ya mareta se hawaye ya fara jika mata fuskar hakan yasa kanta Fara mata ciwo sannan idanunta suka dan tashi wanda zai nuna ma kowa kuka tayi. Bakwai daidai dan aike Ahmad ya shigo a guje Tana zaune kan gado ta hada uban tagumi Lokaci daya tayi rama se swollen and sunken eyes kadai kake hanga a fuskarta. Anty Papa yace kizo Aci abinci! Tohm.. Ta fada hakan yasa ya kyaleta ya tafi amma har Junaid suka gama cin abinci bata fito ba hakan ya kara tayar masa da hankali ya sake daura dukkan alhakin komai a kanshi, Subay'a ce ta Fara fita itada Ahmad se Junaid ya dauki wayarshi ya kirata amma har ta katse Sulaim batai picking ba, Yana kokarin sake kira ta fito fuskarta babu walwala ko digo, da idanunshi da suka fada ta Fara arba, ya tsareta da ido da wannan sharp gaze din nashi, se taji ya kuma takurata amma haka ta iso gareshi Cikeda dasasshiyar murya Tace Na fito Kamar yace ta zauna taci abinci Se ya share ta don yaga kamar a takure take kuma bata sakko ba har lokancin. Ko a motar ko uffan ba tace mishi ba shima bai ce mata ba se lokaci Zua Lokaci yakan kalleta itama satar kallonshi da takeyi da yau ko kallo bai isheta ba. Haka sukai tafiyar so boring ga zukata na wahaluwa. Lucky enough Mami ta kira Junaid da suka gaisa ya bawa sulaim se lokacin ta dan ware sukai magana Harda murmushi. I'm sorry kui manage yau din se a slow nasan yayi kadan amma better hakan than ace babu baki daya. No one is missing Khulthum NE? Haba kukuwa at least ask about her ko taji dadi. Shatuuu ♥️ [7/4, 7:08 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 12 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Duk yadda ka dauki rayuwa to a haka rayuwa take zuwa maka, idan ka dauke ta simple to kullum zaka ganta a saukake amma idan ka matsa ka kuma zafafa to tabbas haka zaka gani. Haka rayuwar take ga Khulthum taki tsayawa inda ya dace ta rungumi yadda rayuwar ta take sede yadda take ganin anayi, yadda wasu Ke yin tasu lifestyle din hakan nan itama take son tayi. Gashi yadda take ganin Sulaim, Aimana da Khairi babu Saar ta a ciki kana kallonsu kasan Daga wanne gida suka fito, komai nasu acan acan to itama tana son meeting up to their level kuma da taemakon Huzaifa dreams dinta basu zama shattered ba. Ya maida ita babbar yarinya yar gayu yar kwalisa, Dama ya lafiyar kura bare tayi zawo, girman kai se ya karu cigaba yaci uban na da. Ranar ta kasance Thursday, da sassafe ta kammalla komai tayi wanka ta zauna ta tsantsara kwaliyya wadda idan ka kalleta zaka rantse zata je gurin biki ne saboda yadda makeup din ya hau babu karya. Tayi kyau kamar ka saceta. Trolley dinta ta bude ta janyo skirt pencil din wanda ya kamata ga tsaga a kasa har wajen kaurin ta Baki ta saka sannan ta dauki farar top ta daura me long sleeve kafin ta janyo bakar suit coat ta daura akai baka, wig dinta ta dakko ta taje shi sannan ta fixing akanta, se data gama daidaita zamanshi kafin ta kalla large mirror din data kafe a dakin, murmushin jin dadi tayi sannan ta samu farin veil tayi wrapping kanta dashi sannan ta saka wani pointed high heel peep toe shoe fari ta zura a kafarta ta daure da igiyoyin jikinshi. Tayi kyau ko mahassadi ya san haka sede shigar is more of zuwa wani biki ko wani taro not professional Abu. Back pack me kyau Fara da adon black a jiki qaddararsa taga ana yayi ta zura books dinta sannan ta saba a baya ta fito hannunta rikeda wani karamin veil wanda zata yafa saboda yan layi amma tana shiga school se de wani kuma. Aisha na durkushe gefen murhu tana ta hura wuta da bakinta saboda yadda maficin ya yagalgale Bana tunanin zaifi bakin nata hurawa, idanunta sunyi ja saboda hayaki. Mama kuma na gefe tana ta fada akan bata tashi da wuri ba gashi har Khulthum ta fito abinci bai Gamu ba. Iya wuya Aisha ta Kai saboda idan akwai Abinda ta tsana bai wuce Irin yadda Mama take ba. Zata iya Rantsuwa tun dawowar Khulthum gidannan Bata taba moruwa ba amma komai Mama sede Tace ayi mata komai saboda Khulthum saboda jin dadinta Amma babu Wanda ta raina take wulakantawa kamarsu. Tundaga nan Aisha ta Fara jiyo Sautin takalmin Khulthum, Bowed down Khulthum ta fito bakinta tana taunar chewing gum tace Mama zan tafi se anjima. Kallonta Mama tayi ta ciro five hundred daga habar zaninta ta mika mata tace Baki ci komai ba zaki fita? Sannan yau ki daure kada kikai maghariba a waje yarannan kullum Se yazo, kudin motarki yace a baki Wannan routine ne Tunda ta Fara zuwa BUK Baifi sau hudu bane kawai Ashir ya tsallake Bata transportation fee ba, amma she never appreciate that effort of his sede kullum cikin ganin gazawarshi take tana ganin me 500 zatayi mata? Kunji fa! Seda ta dubi inda Aisha take tana kallon ta ya mutsa fuska tareda zabga mata harara saboda Tunda sukai wannan damben har yau basu shirya ba harara kawai ke hadasu nothing less and nothing more. Zanci a waje. Kanta ta gyada kawai tana son ce mata ta canza skirt amma babu fuska, hakan yasa tace Zancen Ashiru fa? Dan murmushi tayi ta cigaba da tafiyarta Tace Zamui magana dashi. Daga haka ta fice Seda tazo daidai inda Aisha take tace A cigaba da girki, jakar gida. AI kuwa A'isha ta harzuqe tace Kece jaka Wallahi wayasani ma Maza kike bi ba makaranta ba. Khulthum ba ta jita ba amma Mama ta jita ranar kuwa seda ta raina kanta. Motoci na wucewa da hanzari kowa Yana son reaching destination dinsa, Khulthum na tsaye gefen titi Tana ta bin motocin da suke wucewa da kallo a ranta tana tunanin inama ta wawaso zuciyar wani, tunanin hakan yasa ta gyara tsayuwarta tana dan karkada jiki yadda zata jawo hankali, aikuwa babu jimawa wani azababben guy cikin azabbabiyar bakar mota ya parka gefenta tareda wining glass kasa yace Kyakyawa kamarki Bata cancanci dukan rana ba. Murmushi me kyau tayi Wanda duk wanda akayiwa se zuciyar shi ta kwaidaitu da burin kasancewa tareda me shi. Lumshe idonsa yayi yace Idan da kinji yadda tsayuwarki gurinnan take taba ni ina tunanin da ko second Baki kara a waje ba. Kalamanshi sunyi mata dadi, motarshi me kyau kamar yadda yake me kyau bata wani ja ba tayi wa kanta masauki gefenshi, Tana rufewa yaja suka tafi, shima suit ce jikinsa. Suna tafe Yana bata labari yayinda take amsa mishi da Mhm, a'a ko Eh saboda dole taja class dinta. Seda ta sanar dashi inda zai kaita kuma baiyi kasa a gwiwa ba ya kaita har kofar Faculty ya amshi numbers dinta yayi storing cikin wayarsa sannan ya wuce, Baki daya ta kasa rufe bakinta tana ganin tafi kowacce mace sa'a a Wannan ranar, irin mazan da take so kenan sune taste dinta Amma me zaayi da Ashir wanda kyauta baya iya yin ta dubu Daga 500 shikenan. Tana nan tsaye Sega Khairi da Aimana sun fito Daga class, inda suke ta nufa tana binsu da kallo, kowacce cikinsu tana cikin abaya yar gaske me Tsada ,khairi tata fara ce tayi rolling Baki itakam Aimana baka tasaka all through se jikin veil dinne akwai Polk dots na fari, fuskarsu babu kwaliyya Daga powder se lip balm akai amma sunyi kyau, a ranta tace kudi kenan da Hutu Shiyasa Baku kwaliyya don kunsan no matter how you look zaku samu miji mu kuwa seda ita.......... Wannan shi ne perceptions din wasu mata not all but many na ganin se kayi kwalliya zaka samu miji, ba haka bane hasalima wani bayason kwaliyya, is not that ki fito kamar jaka a'a but powder, khol da balm a lips is OK, amma too much foundation, powder, concealer da sauransu Yana altering skin integrity saboda dukkansu chemicals ne. Baza'ayi class bane Ta Tambayesu lokacinda suka iso inda take, Aimana ta kalleta babu Abinda ta tsana kamar kwaliyyar da Khulthum take, har yau ta kasa banbance meye matsalar Khulthum ne idan ka ganta kamar ta waye amma ko oho. Khairi mutuniyarta tana washe Baki tace Kinyi kyau matar handsome in a flashy car. Dariya Khulthum tayi tace Allah ya karba bakinki yanzu na hadu da wani azababben guy har nan ya kawoni. Dariya khairi tayi cikin jin dadi tace Haba! Shiyasa Naga Bakin ya kasa rufuwa. Kinga lecturer wai se karfe biyu zaiyi holding class din shima ba Zuwa zaiyi ba idanshi zaizo wani Dr waye? Oho! Ta fada Tana son taunawa, itadai Aimana na tsaye batace uffan ba seda suka gama tace Muje Nan cikin quarters akwai gidan yayata mu zauna kafin time din. Seda sukai nisa sannan Khulthum tace Banga Sulaim ba ko bata zo ba? Aimana ta girgixa Kai tace Tazo Tana class Class? Kuka baro ta? Ita kadai? Tsaki Aimana tayi tace Meye zai kamata, kamar tana da damuwa ne munyi munyi taki biyo mu Shiyasa muka barta. Kai Khulthum ta kada amma se taji babu dadi cikin ranta har zuciyarta take son Sulaim, there's something unique about her. Aimana dake tsakiyarsu ta kalla Khulthum in a polite manner yadda tasan words dinta bazasu Bata ran Khulthum ba tace Nikam Khulthum me yasa kike wearing makeup zuwa school ne? Kwatakwata bai dace ba se kace ba professional course kike taking ba. Kafin Khulthum ta bada ansa, khairi tayi caraf tace Ke Aimana ina ruwanki? Bakya gani kiyi shiru ne? Hararar ta sakar mata Tace Nasa bakinki, I taught ba da ke nake ba, Khulthum as I was saying ki rage kwalliyar nan batada amfani a matsayinki na student. Kinada kyau basai kin hada da artificial fixations dinnan ba shi ne banbancin ki da gidan biki. Khulthum batace komai ba don ta rasa abin fada se can tace Kwaliyya ai Itace mace, in the first place Meye ruwanki da kwaliyyata so bakyayi shikenan ni bazan yi ba? Rayuwarki daban tawa daban. Very calm ta fadi hakan kamar ba Khulthum ba, Aimana taja bakinta ta tsuke tana nadamar dalilin da yasa tayi magana. Kwanaki hudu kenan da faruwar incidents din Sulaim, Ja'afar da Junaid... Love triangle kenan.... Ta rame tayi xuruxuru saboda yadda ta kwarzabi Rayuwarta she's going through a hard phase, ita kanta idan kace Meye damuwar ba lalle ta sani ba Sede mu hadashi da Marin Junaid don har lokancin ba sui communicating da Ja'afar ba ita tayi parking dinsa a side. Junaid kam ba'a magana ta hukunta shi ko kuma nace tana hukunta shi kamar yadda take hukunta kanta ba tareda sanin ta ba. Shiyasa gabaki daya ta zama moody ta rasa me yake mata dadi gaba daya kanon ma ta fita a kanta sede babu damar tafiya Don kuwa 2 weeks ya rage a fara exams. Tana nan Zaune a class itada daidaikun mutane yawanci karatu haka itama ta daure ta samu tayi karatun hakan yasa ta danji dadi a ranta. Mikewa tayi saboda yadda cikinta yake gugi, jin hakan yasa ta tuna yau Batayi breakfast ba kuma jiya ba taci dinner ba kuma ga mamakinta Junaid ko takanta bai bi ba hakan shi yake sakawa take kara zama very mad at him, yaya zaiyi laifi kuma ya fita fushi wannan ai son kai ne, da hanzari ta Mike ta dauka handbag dinta ta fita a class din don taci abinci wayarta dake rike a hannunta ta Fara ringing alamun kira na shigowa, a mamakance ta sake duba wayar Dan tabbatar da cewar Junaid ne me kiran, shi dinne kuwa haka kurum se taji tamkar ana cire mata damuwar dake dankare a cikin ranta da ziciyarta. Ni dai nace magulmata...... Halo wattpaddians double, triple, quad appreciation goes to you for the comments and votes. Thank you very much..... I'm proud of you and as such d page is completely yours. Shatuuu♥️ [7/5, 11:46 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 13 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Hello pipu of whatsapp...... Here's your page habibties I'm very grateful..... Have the page* Se kawai ta samu kanta da kin picking call din a ranta tana fadin ko iya haka aka tsaya babu damuwa tasan Rabin damuwarta ta tafi, ita kanta tana mamakin halin da ta jefa kanta a ciki, yadda ta dauki Junaid ta bashi wani mugun mukami a zuciyarta..... Wayarta ta sake ringing a Karo na biyu hakan yasa batada wani zabi face tayi picking, kafin tayi magana cikin muryarshi me Amon dadi yace Ina jiranki a office yanzu. Ta bude Baki dan protesting taji ya kashe wayar babu yadda zatayi haka ta juya ta nufi offices din dake cikin faculty. Kafin ta isa kiran Yaya Jb ya shigo, soja kenan marmari Daga nesa. Dan tsayawa tayi ta amsa call din suka gaisa yana tambayarsa ko akwai matsala ta nuna mishi babu komai sannan yace mata Ayi mana addu'a zamuje Riyadh ganin wani gynae ni da yayarki. Kanta ta gyada kamar yana kallonta, Tana jin tausayin Yaya Imratu da Ya Jb komai is abundant cikin rayuwarsu haihuwa ce kawai Allah bai kawo ba, to dama mutum Tara yake ba goma ba amma tasan ba kowanne so bane yake zama samu. Allah ya kiyaye Yaya yasa a dace mu samu baby. Da sauri yace Amin Lil, wannan adduar taki ina fata ubangiji ya amsa ta. Yayarki na toilet me zance mata? Kace ina gaisheta, safest trip and Allah's khair. Murmushi yayi sannan sukai sallama kafin ta ja kafarta Zuwa office din Junaid, haka kurum se zuciyarta ta Fara increasing bugun da takeyi wanda kullum idan hakan ta kasance se ta rasa gane ko dai she's psychologically sick ne ko kuma me? Itakanta tayi iyakar tunani akan me yasa take jin ireiren stuffs dinnan idan ta doshi inda Junaid yake, Sede ta rasa amsar ta kuma rasa me Bata. Seda tayi knocking yayi mata izinin shiga kafin ta murda kofar ta shiga, yana zaune kan kujerar shi, table din yana cike da takaddu daban daban, ya cire coat din saman se white long sleeve shirt a jikinshi, tie dinma yayi loosing dinshi kadan, idanunsa cikin farin medical glasses wanda yasa yayi kyau sosae dukda Fuskarshi na nuna gajiya amma hakan bai hana kyanshi, cikar haiba da kuma zati fita ba. Tunda ta rufe kofar ta tsaya a gurin ba tareda tace dashi komai ba, se lumshe idonta da tayi saboda yadda Acn office din ke aiki babu hutawa, se taji inama tayi bacci. An kusa Mintina biyar kafin ya aje pen din hannunshi tareda mikewa yayi baya da kujerar ya iso tsakiyar office din tareda zura hannayenshi cikin aljuhun wandonshi yace Zo ki zauna. Babu musu ta taho kamar wata chameleon ta zauna kan soft sofas din da suke aje daga extreme din office din. Seda ta zauna kafin ya iso shima ya zauna Yana dubanta Irin kallon da bai taba yi mata Irinshi ba, kallo ne Wanda ta ko ina ta kasa fassara shi se ya zamana idanun nashi sun takura mata ainun, taji tamkar ta Mike ta fice, ga zuciyarta is adding more issues to her yadda take bugawa tamkar zata balla chest wall dinta ta fito. Bakinta ta turo mishi hakan yasa yayi murmushi sannan yace Sulaim Tamkar magnet haka muryar ta fito wadda ta tilasta mata dole seda ta dago ta zube idanunta cikin nashi. Yadda taga idanun nashi yana wani maiko tamkar an disa mai ciki ga wasu molecules dake fita daga nashi idanun suna piercing Sclera and cornea dinta yasa babu Abinda ta iya yi face ta maida kanta kasa. Murmushi me taushi ya kuma saki yace Me yasa kika daina min magana? Me yasa kika daina cin abinci? Bata dago kanta ba bare ya saka ran zata bashi amsa se ma yatsunta ta dinga wasa dasu. Ganin haka yasa ya sauke ajiyar zuciya me nauyin gaske tareda sake tattara hankalinsa kanta yace Saboda na mareki ko? I'm sorry.... I'm very sorry I shouldn't have been mad na yanke hukunci cikin fushi I'm sorry kinji. Maimakon magana kawai se ta Fara kuka kamar wadda aka tuna mata wani abu, tayi cupping fuskarta a tafukan hannayenta tana kuka Wanda ita kanta bata san dalilinshi ba, Oh God! Sulaim please ki daina kukan nan bakisan yadda kukanki ke damuna ba.... I said I'm sorry ko na juya fuskata ki rama. Dago idonta tayi ta kalleshi tareda tunzura bakinta tana share hawayen fuskarta, to meye abin kukan ta tambayi kanta, dadi kuma ta dinga ji tareda jin komai ya wuce tunda har yasan yayi laifi kuma ya bada hakuri Zaki rama din na juyo? Ya fada cikin wani Irin sauti Wanda seda yasa taji ilahirin Tsikar jikinta ta zuba tareda lumshe idonta se kuma ta turo Baki tace Ni bance ba Nima ban ce ba Sede idan baki hakura ba feel free ki rama indai zaki daina fushi Dani kinga we're even. Tissue box din dake aje Kan glass center table din ta dauka ta goge fuskarta kafin kuma ta kalleshi ta sakar murmushi, shima murmushin yayi mata yana jin wata nutsuwa ta baibaiye shi sede wata zuciyar na ganin me yasa zai zauna Yana apologizing ma karamar Yarinya wannan ai ya siyarwa kanshi raini ne, Baibi takanta ba don idan ya biyewa thoughts dinnan haka zasuyi ta zama da Sulaim bai gyara barakar da ta wanzu tsakanin su ba har Ja'afar yayi nasarar dauketa. I mikewa yayi ya koma mazauninsa tareda daukar wayarshi yayi kira dake hankalinta kwatakwata baya kanshi tana nan tana lissafi farin cikin da Lokaci daya ya zama ta bata ji abinda yace ba se gani tayi an shigo an hada lunch a inda take Zaune Kan table. Dagowa tayi ta dubi abincin sannan ta dubi Junaid wanda ke sallamar dan aiken kafin ya dawo da hankalinshi kanta, suna hada ido ta dauke kanta tareda yin wani side murmushi shikam kanshi ya girgixa yace Fara ci gani nan sakkowa . Babu musu saboda bata kasance me yin musun ba ta bubbbude wrapped plates din dake gabanta, jollof rice ce da hadadden salad se pepper soup na kayan ciki. Nata ta zuba cikin separate plate ta Fara ci, saboda yunwar da take ji gani take Bata taba cin abinci Irin wannan ba, Seda ta kusa gamawa kafin ya sakko yayi joining dinta. Massalaci ya fita ya barta tayi a office din, yana Dawowa daya da Rabi tayi gashi ta dan kintsa mishi kan table din nashi da shelf dinsa. Yaji dadi har yace Tukwicin abinci na aka min gyara. Dariya tayi siririya kafin ta Mike tace Yaya na tafi class, munada class by 2pm. Kanshi ya gyada yace Better go, we meet after. Ficewa tayi shikuma ya tsaya Yana kallon ficewar tata seda ta rufe mishi kofar kafin ya saki murmushi tareda shafa kanshi a ranshi yace Junaid what's all this? Shima baisan amsan ba haka ya Fara shirin abinda zai aiwatar. Sulaim na fita taji tamkar irin born again dinnan zuciyarta tayi wasai kamar anyi mata albishir. Tana zama a sit dinta mutanen ta suka shigo baki daya inda take suka zo. Kinci abinci? Aimana ta tambayeta, murmushi tayi tace Naci, kun dawo? Khulthum ta gyada Kai kafin suka Fara hira ko nace yawanci suna brainstorming ideas ne akan karatun da sukai babu laifi Baki dayansu kwari ne kansu na ja. 2pm daidai ajin yayi tsit saboda shigowar lecturers guda uku na gaba kana kallonshi kasan ya manyanta na bayanshi is a well known personnel amma a gurin Sulaim kadai hannunsu na rike da Apple System dinshi wannan gajiyar dake tattare dashi lokacinda ta sameshi a office yanzun babu se kamar farin ciki da yake tattare dashi though babu wani fara'a a tattaredashi amma kuma Sulaim ta fahimci hakan. A bayanshi level coordinator dinsu ne . Gaba daya ajin yayi tsit level coordinator yazo ya gabatar da Prof shu'aibu as Deen din faculty, cikin nitsuwa ya basu welcoming address wanda bai samu yayi ba Don lokacin matriculation Dinsu baya gari so bai samu yaje ba. Ya basu fatherly advice sannan ya dan tabo musu Irin gwagwarmayar da yasha wajen karatu, don haka yake basu shawarar they should never give up no matter what. Yana gamawa ya fice saboda meeting da zasui da VC a haka ya fice sannan level coordinator ya bawa Dr Junaid damar yin magana. Yana tsaye gaban podium din, ya gyara zaman glasses dinsa, ya kunna system dinshi kafin ya dago idanunshi masu haske ya dubi students din dake Zazzaune. Khulthum Tunda ya dago ta bude Baki tare da fadin Khairi kinga wata halitta? Da sauri Sulaim ta kalleta, se taji Khairi tace Oooooo dama akwai Irin wannan charming guys din a Faculty nan, gaskiya ya hadu. Sulaim Baki daya se taji haushi baki daya ya rufeta, ga tana ta kallon yadda Mata ke kallonshi da admiration fal idanunsu wani Irin nauyi taji kirjinta yayi mata kawai se ta janyo wayarta ta kunna data ta shiga instagram, lokaci Zua Lokaci tana jiyo muryar da take ratsa mata ilahirin jikinta sede ta kasa dago idonta ta kalleshi saboda batasan kallon da mutane Ke yi mishi Amma baki daya hankalinta yana kanshi. Duk yawancin Maganganunshi suna kan exams din da zasui da rules da suke guiding exams. Yana gamawa ya bada room for question kawai wata budurwa very courageous tace Sir we need to know your name Dama kanshi Yana kan wayarshi hakan yasa seda ta maimaita kafin ya tuna cewar bai yi introducing kanshi ba, a nutse yace I'm Dr. Junaid Lukman Birnin kudu, I'm a lecturer here amma Bana daukar class dinku se kunzo level 3, I'm the exam officer of the Faculty. Daga haka aka ta mashi tambayoyi yana bada amsa amma ko sau daya Sulaim bata bari sun hada idanu ba Duk yadda yake son hakan saboda tun zuwanshi class din ya marking inda take. Seda ya gama komai kafin ya basu best wishes sannan ya fice. Daga haka class coordinator ya sallamesu, suna fitowa taga message din Junaid akan ta jirashi yanzu zasu wuce gida. Tare suka fito duka su hudun kuma Monday Za'a Fara exams don haka sukaiyi akan zasui karatu su hadu Washegari. Sulaim tace Gaskiya I'm not sure idan zanzo amma dai zan fada ma yaya idan ya yadda. Aimana tayi dariya tace Kanwar Yaya, kullum yaya zanso naga wannan Yayan. Dayake Sulaim Abinda tafi ambata kenan Yaya, tayi dariya a ranta tace ai yau kowa yaga Yaya. Sunanan tsaye Sega Motar Hu ta iso kafin ta Daga kafarta kamar Da hadin baki Sega Ashir akan Lifan dinshi sannan da azababben guy cikin azabbabiyar mota shima ya iso, idanu a waje ta dubi Sulaim wadda ita tasan Ashir saboda sun taba fita tare suka hadu dashi anan yasan Sulaim itama ta sanshi, Hu kuwa Duk sun sanshi se Yusuf Wanda dazu ta hadu dashi. Kallon Aimana tayi tace Ya zanyi dan Allah? Aimana ta dauke kanta don batasan me zatace da ita ba Balle Sulaim wadda Baki daya mamakin abin take amma ga mamakinsu se kawai ta nufi inda Hu yake da murmushi da komai tace Yau duka bamu hadu ba Inata missing dinka. Murmushi yayi yace I missed you more, Munje ko? Kanta ta girgixa tace Ga uncle dina can yazo daukata muje ku gaisa. Tana fadar haka ta nufi inda Yusuf ke tsaye ko kallon inda Ashir yake Batayi ba se kallon ta yake mamaki kamar ya kasheshi, Tana zuwa suka gaisa kafin Hu ya iso tace Ga brother na ku gaisa yazo daukata. Yana zuwa suka gaisa tabi Yusuf suka tafi Hu yaja motarshi yayinda Ashir ya iso inda su sulaim suke seda suka gaisa, Sulaim tayi introducing dinsa ma su Aimana shima haka, Su waye wanda Khulthum taje gurinsu suka fita a mota? Yayi directing tambayar ga Sulaim, kallon Aimana tayi tace Answer him please. Hakan yasa ya kalla Aimana yace Aimana Ku Fada min Kada Ku damu ba zance mata ku kuka fada ba, sannan na dade da sanin tunda Khulthum ta samu admission halayenta sun canza, gaba daya ta dauki wata rayuwa da bata taba kuma bata dace da ita ba. Kafin Sulaim tayi magana kiran Junaid ya shigo ta musu sallama akan ko meye Ashir yayiwa Aimana bayani. Shatuuu ♥️ [7/6, 7:09 PM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 14 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Disposable cup din dake Cikeda da sassanyan ruwa ta kafa bakinta akai Seda ta shanye tas kafin ta wulla cikin bin dake gefen table dinta. already ta kamalla tattara kayanta lokaci kawai take jira yayi ta samu ta koma gida don Baki daya yau a gajiye take tubus kamar wadda Tasha wani aikin. wayarta da tuntuni take cikin hand bag taji vibration dinta hakan yasa ta ciro ta ganin sunan Beloved Hajiya yasa tayi murmushi yau Baki daya bata kirata ba, seda ta Bari ta katse kafin ta kirata Hajiya barka da yamma Barka ka dai Subay'a Hajiya ta fada Daga Dayan bangaren, Ya aiki ko har kun tashi? Kai subay'a ta girgixa tace Muna kokarin tashin dai. Allah ubangiji ya taimaka ya muku albarka Baki daya. Cikeda jin dadi Subay'a tace Amin Amin Hajiyata. Itama Hajiyar taji dadi Don tanason yadda Subay'a ke yi mata. Dama nace idan kin samu dama zuwa anjima ko zaki shigo akwai muhimmin abu da Zamu tattauna. Dan zaro ido Subay'a tayi tace Ba dai wani abunne ya faru ba ko hajiya? Murmushi hajiya tayi don haka sauran ma sukai Babu komai, kawai dai bazan iya jira bane har Zuwa Sunday. To shikenan Bari yanxu zanzo. Tana kashe wayar ta Mike da kayanta tayiwa colleagues dinta sallama Don suma shirin tafiya suke , seda ta shiga mota sannna ta nemi number Junaid ita Baki daya ta manta warning din da yayi mata akan se ta zartar da abu kafin ta sanar mishi. Lokacin Sulaim da Junaid sun manta sun fita saboda dadewar da sukai da komawa gida, yana parlonshi Yana reviewing questions da aka mishi sending a matsayinshi na exam officer call din Subay'a ya shigo, agogon dake kafe a jikin bangon ya kalla karfe shida har ta gota, picking call din yayi Dear ka koma gida? Na koma tun 3pm. Dama zanje gidan Hajiya ne Murmushi ya danyi don yasan kiran kenan dole wani gurin Zata biya, Allah ya kiyaye! Bai jira amsarta ba ya kashe wayar tare da mikewa Don shirin sallar maghrib. Jallabiya yasa blue black sannan ya dauki farar hula ya saka ya aje wayoyinshi ya fito, Yana Zuwa parlourn Sulaim na fitowa daga dakinta, da dukkan alamu aiki take a kitchen, Tana ganinsa ta tsaya tace Yaya massallaci? Kanshi ya gyada mata yace Eh! Ko zamu tafi tare kiyi acan? Dan dariya tayi tare da rufe fuskarta tace Ni? Shima dariyar yayi Cikeda jin dadi yace Inasu Muhammad kirasu muje tare. Komawa daki tayi ta fito dasu dama sunyi Alwala tace Allah ya kiyaye. Har ya kai kofa ya juyo yaga tana tsaye inda ya barta tana ta murmushi har wushiryar ta siririya ta bayyana, shima murmushin yayi mata tareda saka hannun shi ya mata alaman Taxo, babu musu ta isa inda yake tsaye tareda barin space kuma har lokancin murmushin take, Addu'ar me zanyi miki idan nayi sallah. Dan rolling idonta tayi tace Naci exams. Se ya bata fuska yace Shikenan? Ni kuma fa Cikin rashin fahimtar inda zancenshi ya dosa tace Bansan me kake so ba ai. Kanshi ya gyada yace Shikenan Daga haka ya fice abinshi, dariya tayi ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kitchen bayan ta cire Hijabin jikinta dama ba sallah zatayi ba , hakan yasa ta shiga suka karasa girkin itada su Atika dukda yawancin girkin su keyi ita supervising kawai takeyi se murmushi wanda yaki daukewa Daga fuskarta har Atika Tace Saurayinki kike tunawa ne haka? Hararar ta Sulaim tayi ta cigaba da aikinta seda suka gama sannan ta koma daki ta janyo wayarta da books dinta se kawai taga message din Ja'afar _If at all I can turn the clock, I'll never have done what I did, I'm very sorry Susu for that day. Allah shi ne shaida ta I never intended to harm you..... Please sweetm I'm sorry and I love you! Another chance dear_ Iska me zafi ta furzar, tareda kife wayar tayi shiru Tana tunani yadda zatayi, to ya zatayi da Ja'afar hakura zatayi? Ko kuma me? Gashi yadda words din suka fita are so sincere Amma Kwana biyunnan ita kanta hankalinta ya kwanta amma matsawar Ja'afar ya dawo yanzun zai sake dagula mata lissafi. Se taji inama Za'a canza mata Ja'afar da Junaid, Junaid to her yanada komai da take burin samu inama inama.... Kawai se ta kwanta saman tiles din Tana ta juye juye abinta ta rasa yadda zata hada abin. Yau kam Khulthum ba takai dare Ba, karfe hudu ta isa gida, Tana shiga ta samu se Mama kawai sauran duka basu nan. Seda ta gaida ta kafin ta shige daki tayi wanka ta shirya cikin wata atamfa tazo ta zauna kan daddumar data shimfida. Kallon Mama tayi tace Mama jarabawa zamu Fara ranar litinin me Zuwa. With lot of concern Mama tace Allah ubangiji ya bada sa'a, yasa a dace Amin Mama, Amira sun tafi makaranta ne? Eh yanzu nasan suna hanya. Kanta ta gyada ta Fara revising books dinta, Kwana biu cikin kudi take jin kanta don Huzaifa Yana sakar mata kudi daidai yadda ya dace ga Yusuf da ta hadu dashi yau, Architect ne a wani construction company gashi yana taking private contract wannan yasa yake da kudi shi ne abinda ya fada mata. Kallon Mama tayi tace Anyi abinci ne? Kai Mama ta girgixa tace A'a yace Se ya dawo zai bada kudin cefane. Allah ya kaimu Ta fada Tana cigaba da karatunta. Tafi awa tana karatu sannan su A'isha suka dawo, Amira da kananan suka gaisheta, Ta kalli Amira tace Duba cikin jakar da na fita da ita ki kawo min purse dita. Tashi tayi ta dakko ta kawo mata, Amir! Meye ke kuma zaki ishi mutane? Harara ta maka masa tace Siyo mana macaroni uku da nama da kayan miya. Ta fada Tana mika masa 1500. Kowa Seda ya kalleta Cikeda mamaki itama kuma tasan haka zata faru amma tasan hakanne kadai zaisa abinda take shirin aikatawa. Mama kam farin ciki sosae ta dinga sawa Khulthum albarka, Aisha ana kawowa ta Fara aikin girki yaran se murna suke yau zasu ci nama wanda aka dade ba a hadu ba. Ana Idar da sallar maghrib Amir ya shigo Khulthum tashi kije Ashir yana nemanki fa. Tsaki tayi ta Mike don Tana son bin komai a sannu don Kada ta kwafsa. Bata wani canja kaya ba kamar yadda take duk lokacinda Yazo ta nufi waje, yana tsaye gefen Lifan dinshi wanda a yanzu take ganin shida gurgu basuda maraba. Ko gaisuwa bai samu ba ta tsaya tana jiran taji abinda zai fara fada, shima kallonta yake yana mamakin Khulthum wai wannan Khulthum dinsa ce yarinyar nan Itace idanunta suka bude har haka lallai yarinyar nan shi mamaki take bashi, Ashe mamaki yana gaba Idan Bakada abin fada zan koma ciki. Ta fada Tana nufar zaurensu, seda ta shige ciki sannan Amir ya fito ya tarar da Ashir wanda mamaki yake neman kasheshi a tsaye yace Har kun gama? Kanshi ya girgixa yace Kayi min magana da Mama Dan Allah Lapiya dai? Kayi mata magana Haka kawai yace dashi, haka ya wuce ciki ya tarar mama na tsaye kan Khulthum tana tambayarta dalilin da yasa ta dawo ......dama kwana biyu Naga take takenki baki daya tunda kika shiga makaranta halayenki ya canza kin koma wata iri........ Mama wai Ashir yana son magana dake . Wani harara ta dallawa Khulthum sannan tace Amira dakko min mayafi na. Ana miko mata ta nufi gurin shi Khulthum tamkar zatayi bindiga a ranta tace Lallai Ashir kana ganin wannan ce hanyar bullewa kada ka damu Dani kake magana. Mama gefe guda ta zauna cikin mutunci da mutunta juna suka gaisa itada Ashir, nan ya fara fadin Mama kiyi hakuri kila kina wani abun na katse miki aikinki Babu komai dannan, inajinka Dama akan Khulthum ne Mama, Dan Allah Inaso ki tambayeta ko akwai abinda nayi mata kwatakwata Kwana biu nan taki dadi kuma ni naga Tunda manya sun shigo ya kamata na sanar dake halinda ake ciki. Se yayi shiru, itakuma tayi zugum seda ta tabbatar yakai aya tace Da farko zan baka hakuri, yaran yanzu ka haifesu baka haifi halunsu ba, Inshaaa Allah zan zauna naji matsalarta idan yaso se asan abinyi. Kadai yi hakuri. Babu komai Mama kada dai kiyi fushi. Dan murmushi tayi amma Lokaci guda ya dauke saboda jiyo takun Khulthum da tayi, kamar Aljannah saboda yadda tayi dolling fuskarta, Tana cikin wani royal blue paper lace da farin mayafi iya kafada tayi kyau har ta gaji abinta. Ke gidan ubanwa zakije? Mama ta tambaya a fusace, Nikam ina tunanin Wannan ne Karo na farko da Mama ta Fara fito na fito itada Khulthum, shima Ashir kallonta yake Baki daya idanunsa sun Kada sunyi jawur dayake ya haska gurin da wayarshi kirar Tecno hakan ya haska gurin Kake ganin komai daidai. Harara ta watsa mishi idanunta Cikeda tsana Tace Mama bako Nayi fa Ubanki Keda bakon kinji ubanki nace Marar mutunci yarinyar nan. Baki ta turo tareda bubbuga kafarta a kasa, sannan ta ficewarta Mama na kwalla mata kira amma ko Waiwaye! Turkashi! Seda Subay'a tayi sallar isha'i sannan ta nufo gida dama kiran Ba wani abu bane wai kawai son ganinsu take. Seda taci abinci cikin yan uwanta kafin ta tuko motar ta hankalinta a kwance don tasan babu Abinda Junaid zaiyi mata Tunda da tace zataje bai musa ba. Tana parking a gefen motarshi ta nufo cikin gidan kafadarta rataye da jaka, se jakar system dinta a hannunta, Tana yin sallama taji Sulaim ta amsa mata karo na farko taji jin muryar Junaid ya fadar mata gaba, sosae gabanta ya tsananta bugawa tamkar wadda tayi bugun marathon haka taji, se kawai ta tsaya a gurin, Sulaim din na Sanye da wani shiny silk material dark purple da pattern na light purple a jiki, dinkin simple gown se mini veil da tayi rolling dashi dan Bata taba zama babu mayafi jikinta saboda wannan tarbiyyar mummy ce hade da Mami, ta rigada ta san akwai aure tsakaninta da Junaid so bata taba zama babu lullubi jikinta that's the rule. Tana dining tana jera plates da spoons yadda kasan Itace matar gidan, shikuma me gayya me aiki yana zaune kan carpet da books din Khulthum din Yana sake highlighting mata abubuwan da suka shige mata duhu, Sede Tunda ta tashi gaba daya yaji ya daina fahimtar Abinda yake karantawa, sukam su Ahmad suna ta wasa abinsu suna jin muryar Mamansu sukai kanta. Shigowa tayi idanunta sun canza kala baki daya taji Anya ba akwai Abinda yake Zaune ba a muhallinsa ba? Anya ba akwai Abinda yayi breaking along the line ba amma ta rasa Meye, taga kwata kwata Junaid baya damuwa da alamuranta kamar da, ko bata nan bai taba damuwa sannan Hana fitar da yake duka ya barta tana tambaya zaice Allah ya kiyaye to abin ya fara damunta, ta Fara zargin kanta da yin sake data bar Sulaim zama mata a gida. The game is about to start..... Kowa Yana rike da hurdle let's see wanda zai cimma burinsa. [7/17, 5:39 PM] Asma'u Madugu: *MACE A YAU* 15 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Mama kasa fadin komai tayi ga matsanancin bacin rai da yake taso mata, Tamkar an dasa Mama haka ta tsaya ta kasa gaba Kuma ita Bata koma ciki ba, gashi Baki daya kunyar Ashir dinma takeji, mikewa yayi ba tareda ya sake furta komai ba ya wuce abinshi, to me zaice? Duk yadda yayi tunanin saiyawar khulthum ashe tunaninsa ya wuce hakan. Yana fitowa ya same ta tsaye gefen Yusuf se murmushi take tamkar bakinta zai yage, shima hakan ce gareshi Yusuf din, Bai Kara kallon inda suke ba dan surely zuciyarshi zata iya fashewa. Kice dazun da muka hadu banga komai ba kenan? Yusuf ya fada Yana sake Kare mata kallo, murmushi tayi tace A hakan? Ta fada tana masa wink, dan dariya yayi yace Kice kada nayi underestimating dinki? Bata kuma fadar komai ba hakan yasa ya canza topic da fadin So kina ganin ban takura miki ba idan na turo iyayena, saboda gaskiya ni da gaske nake Kuma aure nake son yi I'm not getting any younger kullum girma Kara kamamu yake. Gabanta taji ya Fadi,wani irin aure daga zuwanshi, gaskiya itadai she's not ready bata gama fahimtar halayenshi ba kawai se a fara zancen aure ita duk ba wannan ba bata shirya aure ba a wannan lokacin, Bata gama kashe kurar Ashir ba ita Bata San abinda zata tarar a gida ba don tasan dole Mama ranta zai baci. Kinyi shiru ko Baki shirya ba? Ya fada yana assessing fuskarta , Dan murmushi ta Kuma saki tace Haba dai, kasan first semester nake level one so bazai yiwu ace daga fara karatu se aure ba, if you can be a little more patient na shiga level two Ina ganin Babu matsala. Shima murmushi yayi bayan ya gama saurarnta se yace Abinda Kika fada is in place, sede Ina ganin aure baya hana karatu kowanne Yana da matsayinshi what matters Shi ne Zan barki ki karasa idan munyi aure. Wata dariya ta saki, a ranta tace Lallai Kai har kana tunanin zaka barni ko aa ai ni ba irin wannan matan bace Amma a fili se tace A'a bana jinka zaka barni nayi Amma sede hakan Shi ne burina Dana iyayena. Ganin ta dage yasa yace ya amince amma bawai yakai zuciya ba don ya fahimci auren ne baya gabanta Baki daya Kuma idanunta a bude suke. Sun Dan Kara taba Hira ya ciro katuwar ppaer bag daga back seat dinsa ya Mika mata, se farar leda, karba tayi ta mishi godiya daga haka ta mishi sallama se gida. Ko dar bataji ba don tasan Babu abinda zaayi mata. A nutse ta shiga cikin gidan Mama na zaune Kan sallaya ta idar da sallar ishai baki daya abin duniya ya iaheta ta rasa yadda zatayi. Kada khulthum ta watsa musu kasa fa a ido? Saboda taga take takenta abinda take niyyar yi kenan. Tana shigowa daki ta nufa tana jin Mama Tana kiranta bata amsa se cewa tayi Mama kada ki damu indai maganar Ashir ce kada ki saka baki. Ni kaina nayi tunanin Mama zatace wani abu amma se cewa tayi Khulthum idan zaka rabu da mutum ba ta haka ake ba, a hankali ake bin komai. Aisha ce tace Mama haka kawai Zaki fada? Mama bakwa kyautawa abinda kuke, Ashir Bai canci haka ba wallahi. Khulthum dake daki ta leko tace To uwata munafuka ke idan kina sonshi kije Zaki zauna kina gutsiri tsoma. Aisha batace Mata komai ba ta mike don harhada kwanukan da akai amfani dashi. Mama shiru tayi Don tasan tabbas abinda Aisha ta fada gaskiya ne, is not in place bai dace ta fada haka ba Amma Babu yadda zatayi sede idon kawai. *** Agogon dake daure kan tsintsiyar hannunshi ta Rolex ya kai duba, Tara na dare ta gota gashi goma daidai ya kamata ya tafi gurin da ya kamata Amma Babu yadda zaiyi wane Shi Gwoggo nasan ganinshi yaki zuwa, hakanan ya ja motar ya nufi asalin gidansu dake cikin unguwar kuntau a Kano. Makeken gida ne na alfarma tun daga gate din zai tabbatar maka da kudi ya zaunawa masu gidan. Bude mishi gate akayi ya shiga ciki yayi parking sannan ya fito Yana amsa gaisuwar masu gadin gidan. Tamkar rana haka yake saboda yadda ko Ina yake a haskake, parlon ya nufa tana zauna kan kujera gabanta an aje mata mug cikeda tea Akan saucer, matar ta manyanta sosae sede yadda take cikin Jin dadi bazai nuna manyanta tata ba. Gefenta daga kasa ya zauna cikeda girmamawa yace Gwoggo barka da dare Seda ta gama kallonshi a tsanake ta kurba tea din sannan tace Barka ka dai Musbahu. Kanshi ya sunkuyar gabanshi Yana faduwa don baisan abinda yasa take nemanashi ba, itama ta Lura da hakan shiyasa tace Dama na kiraka naji yadda muka tsaya Akan zancen auren ka, Musbahu wannan karo na nawa ne Ina yi maka magana? Kanshi a kasa dama jikanshi ya bashi maganar kenan hakan yasa yayi shiru seda tace Bakaji tambayar tawa ba ko? Girgiza kanshi yayi yace Bazan iya irgawa ba. Good Ta fada kafin ta sake kurbar tea tace Mata nawa na kawo maka ka nuna min you're not interested in them, daga kace wannan se kace wancan don haka kayi marking date din yau a matsayin Rana ta karshe da zan Kara daga maka kafa, watanni biyar kawai na baka ka kawo min Mata Shima don na fitarda hakkin ka ne Amma banda haka wallahi da da kaina Zan baka mace. Kanshi a kasa har lokancin a ranshi Yana fadin to ai akwai Lokaci kenan, shifa bawai aure ne bayaso ba kawai dai bai taba ganin akwai abin burgewa a jikin 'ya mace ba balle har yayi Sha'awar su shi a iya rayuwarsu zai iya counting matan da yayiwa magana dasu a girman shi yanzun hakan zai iya kirga matan da yayi mu'amula dasu shima don dole ne don ita kanta Gwoggo Tasha sawa ayi mishi addu'a don tunaninta ko aljana ce ta aureshi amma shiru babu sauyi. Inshaaa Allah Gwoggo kafin lokacin zan kawo miki. Kanta ta gyada tace Zaka iya tafiya. Take ya Mike kuwa yayi mata sallama don Dama a takure yake sosae, shikam haka ya tashi cikin tsananin tsoron mahaifiyarshi kuma har yanzun daya girma Bata canza zani ba saboda baya mantawa kafin rasuwar mahaifinshi yana yawan mata fada akan ta daina irin takura mishi. Musbahu yana fitowa ya sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda sake kallon agogon hannunsa, it's almost time hakan yasa ya figi motar ya fice baki daya daga harabar gidan, a motar ya Kira babban amininshi na hannun dama Kabir Seda suka gaisa sannan ya sanar mishi yadda sukai da Gwoggo, Ina ganin ya kamata kayi hakuri kawai kayi aure Tunda Naga Gwoggo da full force Taxo Kabir ya fada, sake dafe steering yayi yace I thought of that nima, amma ta yaya zan fara neman mace idan naje ya zanyi? Dariya sosae kabir yayi har ya kusa batawa Musbahu rai, sannan yace We'll talk about it later, kadai kayi amfani da damar ka ta Daren yau. Dariya sukai sannan sukai sallama. *** Cikin tsantsan Subay'a ta karaso parlon yaran sun rike both hands dinta, Tunda ta shigo idanunta Ke kan Sulaim wadda ta cigaba da Abinda take tamkar bata ga shigowar Subayan ba, gefen Junaid ta zauna tareda fadin Papa na dawo. Ta fada Tana shafa Fuskarshi, Allah ya taimaka shugabar kishin duk duniya wato Sulaim bata lura ba Don hankalinta yayi nisa kan shirya dining Sede itama a ranta taji babu dadi tana ganin kamar Subay'a din wata barrier ce tsakaninta da Junaid. Shikam Junaid hannunta ya rike tareda nuna mata su Ahmad yace Barka da dawowa. Se ya Mike ya nufi dining din, yana zama Subay'a ta taso ta zauna gefenshi tareda janyo plate ta Fara serving dinsa, Sulaim na ganin haka ta zuba nata ta bar gurin Zuwa dakinta, saboda gani tayi Subay'a ta Fara bashi abincin cikin baki tasan matsawar ta zauna a gurin zuciyarta fashewa zatayi, da taje dakinma saka abincin tayi a gaba tana ta kallo Baki daya farin cikin da take ciki ta nemeshi ta rasa, a hankali ta aje spoon din hannunta ta daidaita zamanta don tuhumar kanta dalilin da yasa take haka, in the first place Meye tsakaninta da Junaid da take jin zuciyarta nayi mata nauyi Duk lokacin da ta ganshi da matarshi, ko dai sonshi take? Se kuma ta Fara fadin No! No it's not possible, it's never gonna happen, to amma Koda tayi denying it obvious abinda takeji game da Junaid so ne, runtse idonta tayi tana girgiza kanta Tana fadin No! Never!! It will never ever and will never happen. Kifar da kanta tayi tana ta tunani wanda ta rasa na Menene Sede babu me bata amsa. Shatuuu ♥️ [7/17, 5:42 PM] Asma'u Madugu: *MACE A YAU* 16 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad A firgice ta Mike Daga gadon saboda jin har an shiga sallah, da sauri ta shiga toilet tayi Alwala tazo tayi sallah, qurani ta janyo tayi karatu na thirty minutes kafin tayi azhkar se wanka. Tana fitowa ta shirya cikin skirt da riga na atamfa sannan ta zauna gefen gado ta Fara revising book dinta. Nanma she took almost an hour tana abu daya kafin ta aje littafin saboda kiran Mami daya shigo Mamina Ta fada lokacinda ta Kara wayar a kunnenta , da murmushi Mami tace Auta kin tashi lapiya? Lapiya lau Mami ya gida, Ina Baba? Ga Babanki Ta mika mishi, Baba Ummu_Sulaim ya shirin exams? Alhamdulillah Baba. Allah ya bada sa'a, focus ok Inshaaa Allah I'll. Yawwa Allah yayi muku albarka. Amin Amin ga Mamin. Mami ma addu'a tayi mata sannan sukai sallama. Tana aje wayar taga message din Ja'afar Exams are near Subject are not clear Question appear And answers disappear Oh! My dear Don't be fear Bcoz im here 2 wish u, All clear! Have a great exam fest all the best! Itakam Ja'afar ta rasa yadda zatayi dashi, kullum text uku ne morning, afternoon and night. Da karfinahi ya dawo to ita bata san yadda zasui ba. Tsaki tayi ta Mike tayi ta saka hijab sannan ta dauki Jakarta ta fito, kusan duka tare suka fito, Anty ina Kwana? Babu yabo babu fallasa tace Lapiya Daga haka ta wuce kitchen dan su Atika basu kai ga fito da breakfast ba, Ahmad ne ya nufo inda take Sanye cikin uniform na school tas dashi, dukda bawai Subay'a ke mishi wanki ba amma tanada tsafta dan bazaka taba ganin wani abun kazanta a tattare da ita ba ko yaranta na kullum they appear neat. Cinyar Sulaim ya zauna Yana fadin Anty morning Murmushi tayi tana shafa kanshi tareda sake gyara mishi collar Riga tace How was your night? Fine Ya fada Yana grinning ear to ear, kafin ta kuma wata maganar se ga me gayya me aiki Junaid ya fito waya a kunnenshi ya rike da kafadarshi, Dayan kafadar Yana rataye da briefcase dinshi se daya hannunshi Yana saka link jikin Orange long sleeve Shirt dinsa ta kamfanin marks and Spencer, se black trouser na kamfanin tummy Hilfiger, yayi kyau sosae kamar kada ka barshi ya fita. Yana Zuwa tsakiyar parlon, ya aje wayar kafin Sulaim ta gaisheshi Subay'a ta fito bayanta Atika na binta da Jeren warmers, inda yake ta iso tace Har ka fito? Kanshi ya gyada yace Yana sake duban wrist watch dinsa baki kirar Penurai, takwas saura kadan shi kanshi yayi mamakin yadda suka makara, ba akai Ahmad school ba, ita bata fita aiki ba sannan exams din Sulaim nine ne Wucewa Zamuyi mun makara. Kallonshi tayi tace Kaine ka makara yau bazanje ba saboda open day dinsu Ahmad ne se nine Za'a Fara. Kanshi ya dan daka yace It skipped my mind baki daya, Allah ya kiyaye mu zamu tafi , banga Muhammad ba Ya fada Yana juyawa alamun nema kafin ya maida dubansa ka Sulaim wadda tayi shiru deep in her own thoughts. Still on bed, Abincin fa? Kanshi ya girgixa yace Zubawa Sulaim taci kafin ta shiga hall. Kanta ta kawar tace Tazo ta diba da kanta mana. Kallon Sulaim yayi wadda take ta kallon Subay'a yace Tashi ki zuba abinci kyaci a hanya. Kanta ta girgixa Tana zumbura Baki tace Na koshi Kallonta yayi ya tamke fuska yace Bazaki tashi ki dauka ba se ranki ya baci? Subay'a tayi murmushi Irin haka take son yana ma wannan yarinyar me shegen tsaurin ido, Kallonshi Sulaim tayi yadda taga Fuskarshi yasa ta Mike Don babu wargi Balle tayi musu, kitchen ta shiga ta dakko silver tea flask karami ta tsiyaya plain tea, Dan karamin flask ta zuba Fried yam da egg sauce sannan ta zuba cikin karamin basket tabi bayanshi. Seda yayi warming motar kafin ta shiga suka bar gidan Nayi lefi ne Ya fada Yana kallon titi. Ina Kwana Don tasan shi ne dalilin tambayar , tabe bakinshi yayi yace Bazan amsa ba, ni kwata kwata baki damu Dani ba, Mintina nawa Nayi saman kanki amma ko second glance baki bani ba. Maganar tazo wa Sulaim a bazata hakan yasa ta dago idonta tana kallonshi wani Irin abu taji Yana fuzgar ta like a magnetic attraction, sauke idonta tayi ta kasa fassara abinda yake nufi _bata damu dashi ba ita kuwa ita ta damu dashi_ a hankali taji zuciyrta tana budewa wani Irin unimaginable feeling taji ya baibayeta har ta kasa boye murmushin din da takeyi. Kanshi ya girgixa ya kara fadin Allah sarki kuma gata na, bazaa bani amsa ba kenan? Bakinta ta turo kadan tace Nima bakace ya shirin exams ba. Dariya yayi yace OK ramawa kikayi kenan? To we're even yanzun. Have you read well? Ko yanzun akawo paper? Kanta ta gyada tace Ready for the battle. Kallonta yayi a ranshi Yana tunanin har wanne Lokaci ya dauka kafin ya sanar da Sulaimi halin da yake ciki? Karfa wani Daga gefe yazo ya dauke abinda yake ta tattalawa kanshi. A kofar Faculty yayi parking, kallonshi tayi shima kallonta yake cikin ido yana murmushi itama se ta samu kanta da sakar mishi tattausan murmushi kafin ta bude kofar se yace Sulaim Juyowa tayi har lokancin bakinta a bude yake ga wushiryar ta a bayyane haka dimples dinta dake both sides sun lotsa, tamkar ana fuzgarshi haka ya daga hannunshi se yayi saurin saukewa don yasan hakan ba girmanshi bane. Kallonshi take ta langwabar da Kai tace Yaya Tamkar ruwan sanyi haka kiran da tayi mishi ya isa gareshi, dagowa yayi yace All the best, idan kin fito Kada ki tafi se five Zamu je gida, kizo office ki huta sannan ki karanta na gobe OK? Kanta ta gyada daga haka ta rufe mishi kofar cikin nitsuwa ta taka kofar venue din tana jinta tamkar tana shawagi ne cikin gajimare, wani Irin farin ciki taji da nishadi wanda ta dade bata ji makamancin irinsa ba. Shima hakan ce a bangarenashi Don seda yaga ta zauna kafin ya shafa kanshi ya wuce murmushi fal Fuskarshi. Tana nan Zaune Khulthum ta iso ta zauna gefenta amma saboda yadda Sulaim hankalinta ya tafi akan maganganun Junaid yasa ko daya Bata fahimci zuwan Khulthum ba harseda ta dafa ta kafin ta kalleta, itama Khulthum din kallonta tayi tace Ke tunanin me kike Ita kanta bata san ta saki wani Irin murmushi ba seda ta kalla facial expression din Khulthum kafin ta saki murmushi tace Sannunki, ina Mama? Tabe bakinta tayi tace Mama na gida, Ina Yaya? Wani smile ta saki wanda yake straight deep down from the ventricle tace Office. Sosae Khulthum ta ke kallonta kafin tace Anya Yaya ne kuwa? Me fa? Kanta ta girgixa tace Back to real business muyi revising. Haka sukai ta brainstorming har invigilators suka shigo aka Fara, tunda aka ce start Sulaim ta dukufa abinta tana ta rubutu se time to time Tana sakin murmushi, can tana last question taji sassanyan kamshin Fierce cologne by Abercrombie and Fitch ko bata dago ba tasan duk duniya mutum daya take jin wannan kamshin a jikinshi kuma shi ne _Junaid_ a hankali tamkar me tsoro ta dago idonta shi ne kuwa yana tsaye kyem a kanta sede Fuskarshi babu walwala he's not the Junaid she left a mota wannan examination officer ne kuma senior lecturer dinta. A hankali ya motsa bakinsa ya furta Stop staring, kiyi rubutu. Bakinta ta turo mishi ta maida kanta kasa amma ta kasa cigaba da rubutun saboda yadda taji ya cika gurin gashi bugun zuciyarta is increasing its pace. Ganin haka yasa ya bar gurin kafin daga bisani ya fice a hall din baki daya. Ana cewa pens up ta aje nata akai tattara suka fito baki dayansu, su hudu suka tsaya gefen hall din kowa na fadar albarkacin bakinsa, exams dai babu laifi ta yi dadi sede addu'a. Khairi da Khulthum suka tafi hostel don Khulthum zata shiga toilet yayinda Aimana da Sulaim suka nufi office din Junaid, baya nan se messenger dinsa ne ya bude mata, Kan sofas din suka zauna Aimana tana tabin office din da kallo tace Office din waye? Gira ta daga tace Easy mana, office din Yaya ne Yaya dai Yaya dai every time, dama nan yake aiki? Dariya Sulaim tayi wai Yaya dai all the time itafa bata jin wani fadar Junaid da take amma se suce wai common saying dinta kenan. Eh he's a lecturer here Kai ta gyada tana admiring gurin kafin kuma ta gyara zama tace Sulaim Kallonta Sulaim tayi ta tsaya da danna wayarta tace Yaya? Ina wannan brother nawa da ya taba Zuwa daukarmu Yaya Nu'uman? Ta fada Tana nuna mata hoton Nu'uman a wayarta, karba tayi ta kalleshi, yes she remembers him, wannan shiru shirun shi ne kadai abinda zata fada a kanshi. Na tuna shi. Ya min maganar Yana sonki..... So?! Sulaim ta fada Tana zaro ido waje, dariya Aimana tayi tace Keep calm and chill, nace mishi Kinada Yaya. Da confusion tace Yaya kuma? Kafadar ta ta rike tace Sulaim kenan, wannan Yayan da kike fada is not just an ordinary Yaya akwai wani abu karkashin zuciyarki, tell me kina sonshi ne. Shiru Sulaim tayi ta kurawa Aimana idanu tamkar amsar tamabayar tana Kan fuskarta ne, baki daya se ta shiga cikin dilemma she's confuse ba kadan ba, ta yaya zaace tana son Yaya Junaid, Yaya fa mijin Subay'a no way he's just an important person cikin Rayuwarta. Yaya, is an important mutum a rayuwata, Mummy da Daddy suka rikeshi har ya fara aiki, Kinsan ni am an orphan banda uwa banda uba, gidansu ake riko na. Yanzun Yaya shi ne komi nawa kinga dole Nayi maganarshi. Kinyi misunderstanding abin. With a pity face tace Ayya sorry for the loss, Allah ya jikansu Amma zancen Yaya ki tuhumu kanki. Kafin ta bata amsa Sega Yaya ya shigo shida Ridwan. Mikewa tayi ta nufi inda yake yayinda Aimana take mamakin dama Dr Junaid shi ne Yaya? Haba no wonder Sulaim ta falling. Gaisheshi Aimana tayi fuska a sake ya amsa Yana tambayarta exams, itama ta bashi amsa kafin ya maida dukkan hankalinshi kan sarauniyar tashi dake gaisawa da Ridwan Amarya na tambayarki Bakixo kin ganmu ba. Dan murmushi tayi tace Yaya bai kawo ni ba. Da sauri Junaid ya daga hannunshi sama in surrender yace Count me out of maganar nan, Ke Yaushe kika ce zakije tsakaninki da Allah? Turo bakinta tayi tare da jujjuyawa hakan yasa Junaid dafe kanshi tace Ka manta ranar. Baki bude Junaid yace Yaushe kika koyi sharri ke kuwa. Dariya sosae sukai Harda Aimana dake gefe, Ridwan ya dauki abinda ya shigo dashi ya fice yana ta dariya shi kawai yana ganin Sulaim ma tana son Junaid din, shi kanshi ya rasa dalilin Junaid na kin fadawa yarinyar yana sonta amma zai kara tuntubar shi akan inda aka Kwana. Kan sofar ya zauna Yana facing dinsu yana ma Aimana tambayoyi kafin ya maida dubansa kan Sulaim wadda ta bata rai kamar ba ita take dariya ba, a hankali ya dubeta yace Me nayi kuma? Bakace ya exams ba A'a sau nawa zan fada ne? Ya exams din to Cikin nitsuwa tace Alhamdulillah! Tashi yayi yace Kin Faye damuwa Walhi, Bari nayi aikin gabana, Bari kuci abinci ko? Kanta ta gyada mishi ya koma seat dinshi ya fara aiki Bayan ya bada order. Aimana ta kalli Sulaimi tayi kasa da murya Tace What a perfect match! Me? Keda Yaya mana, Kuna son junanku Amma is like kamar baku fahimta ba. Dan Allah Kiyi shiru Kada yaji, nace miki he's very important cikin rayuwata! Waye ya yadda da sulaim? Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 17 nd 18 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad A Kwana a tashi babu wuya gurin ubangiji, ranaku gudu suke suna shudewa tare da kara kusanta mu da kabarinmu, fata daya Allah ya sa mu cika da imani. Exams ana tayi har yaxo saura daya su gama , ranar Friday sun fito Daga Logic and philosophy paper, paper rana ce hakan yasa suna fitowa Junaid Yana jiranta a mota. Ciki ta shiga fuskarta babu annuri ko digo dama kuma yaji a bakin invigilators suna fadin exams din tayi wuya. Tana zama ya fara driving kafin ya kalleta don har lokancin ba tayi mishi magana ba yace Ya exams din? Dama abinda take jira kenan ta Fara kuka se yayi shiru Yana Dana sanin yin magana, ta kusan minti biyar tanayi bai hanata ba Sede bawai yana jin dadin sauraran kukan nata bane, seda ta share hawayenta kafin yace Kiyi hakuri kinji, you will make it. Kanta ta gyada se taji tsoron ta kusan kashi hamsin ya wuce taji ta samu hope da courage. Yaya Na'am Ya fada ba tareda ya kalleta ba. Gobe Inshaaa Allah wajen nine zamuje karatu ni da friends dina. Juyowa yayi ya dubeta idonta har yayi Dan ja saboda kukan da tayi, A'a Kai Yaya Kice musu su zo nan gida kuyi tare hankalina zaifi kwanciya. Kanta ta gyada tace Tohm. Daga haka sukai shiru ya cigaba da tukin shi Yana tunanin sakon Mami da safe akan ranar laraba yayiwa Sulaim booking flight ta tafi Kebbi gurin dangin Mami da Anty zahra. Shi a so samunshi ne tayi zamanta Tunda hutun Baifi 2 weeks ba amma Tunda Mami tace haka zaayi bai isa canjawa ba. A wani Pizza joint yayi parking ya shiga ciki ya batta a mota, da Wannan ta kirasu Khulthum ta fada musu yadda Yaya yace Dama Aimana ce suke tunanin ba Za'a barta ba to itama ba'a samu matsala ba. Tana aje wayar daga kiran Khairi call din Ja'afar ya shigo.... Dam! Taji gabanta ya fadi Yaushe rabon taga wannan sunan ya kirata har ta manta, kamar bazata dauka ba se kawai taga bari taji me zaice mata. Tana picking wannan muryar tashi me dadi yace Susu! Se ta lumshe idonta saboda yadda sunan ya ratsa ilahirin jikinta, its been a while da aka kirata da hakan, so she missed been addressed as Susu. Nasan kina jina, nasan kinga messages dina Baki daya, this time around I'm ready Sulaim, bazan Kara miki wasa da zuciyarki ba, I promise you only one more chance _Baby give me one more chance to be the one to hold your hands, may be we could learn to love again...._ Shiru tayi words suna sinking cikin jikinta tareda sake auna su cikin kwakwalwar kanta, for how many times Ja'afar zaina mata fake promises, kullum maganarshi one more chance. Anya ba wasa take da rayuwar ta ba? Anya Ja'afar is the right person? Sulaim please Taji ya katse mata tunaninta, hakan yasa ta bude idonta har lokancin Junaid bai dawo ba tace Na gaji Yaya Ja'afar bakasan darajar Abinda kake so ba Sweetm ni ne fa, your Luff ko kin manta? Dan murmushin takaici tayi wai ta manta, sede ta bude Baki da niyyar magana Junaid ya bude kofar ya shigo hakan yasa ta kasa magana shi kuma Junaid Yana zama yace Yi hakuri na barki ke daya, I met an old friend. Kanta ta gyada tace Uhm. Dake hijab ne jikinta daya kalleta baiga wayar ba don haka ya cigaba da fadin Tare mukai NSUKKA dashi Yana da kirki, se yau Allah yayi muka hadu. Dama hakane kam Ta fada Tana zare wayar daga kunnenta saboda ba zata iya cigaba da wayar a gabanshi ba. Aikuwa Ja'afar ya dinga kira tana katsewa se taji Junaid yace Waye ke kiranki? Kallonshi tayi taga hankalinshi Yana kan titi tace Yaya Ja'afar! A bazata maganar tazo mishi hakan yasa yayi wani juyi ya kalleta kanta a kasa taki dago idonta ta kalleshi, se yaji duka ilahirin jikinshi yayi sanyi saboda ya tabbatar Ja'afar baya tareda Sulaim Yaushe suka hade Yana gefe Yaya! Sulaim ta kwalla kara saboda motar dake gabansu amma dukda haka Seda ya buga mishi kuma bugun ba sosae bane ba inda Allah ya taimaka, Gaba daya ilahirin jikinta rawa yake tsabar yadda ta tsorata, se ta Fara kuka, bai bi ta kanta ba yayi parking gefen titi ya fito, shima wanda aka bugawar ya fito mutane har Sun taru, ana maida yadda akai. Fuskarta a rufe da tafukan hannayenta taji an kwankwasa mata kofar side din da take, dago idonta tayi wanda har ya canza kala saboda firgici, da idanun ta bishi da kallo kana kallonshi basai anyi maka bayani ba ya hada jini da larabawa, fari ne sosae tamkar ka taba shi jini ya fito, yana da tsayi sede bayada kiba ya hadu karshe babu karya. Cikin turanci me tsafta babu blonders yace Ke kyakyawa ce, can I please have your digits. Yadda ya tsare ta da ido se taji ba zata iya hanashi ba, hakan yasa ta mika mishi hannunta shi kuma ya bata wayarshi ta saka mishi numbers din ta mika mishi tace Sulaim Lumshe idonsa yayi yace What a nice name baby. I'm Salim Daidai bude motar da shigowar Junaid idanunshi bai sauka akan kowa ba se akan Salim, wani Irin mummunar faduwar gaba ce ta ziyarce shi Lokaci guda, bai gama dawowa daga wancan shock din ba gashi yazo ya tarar da wani, shikam wanne irin abu ne yake faruwa dashi daga wannan se wannan kada yarinyar nan ta fasa mishi zuciyarshi. Sulaim Bata Lura da halin da Junaid yake ciki ba amma gaban ta se faduwa yake, Salim ya juya ta side din da Junaid yake ya bashi hannu tareda fadin Barka da Rana. Batareda ya kalleshi ba yace Barka ka dai. Daga haka ya sakar mishi hannu ya bawa motar key, tamkar a bye pass haka ya dinga sharara gudu Fuskarshi tamau tamkar bai taba dariya ba, itakuma taki dagowa bare taga yanayinshi. A haka suka isa gida yana parking yace Get out! Da sauri ta kalleshi idanunta a waje Tana son tabbatar da Junaid ne ya fadi hakan? Shi dinne yana kallonta da idanunshi yayi jawur wanda ya Kara tsoratar da ita Are you deaf? Get out of my car stupid kawai. Maimakon tayi yadda yace se hawaye ya fara zubar mata Daga idanu, ita me tayi mishi, ita tace kada ya kalli gabanshi while driving zai zo ya huce a kanta, shima se ya tsaya Yana kallon ta, gaba daya se yaji duka hankalinshi ya tashi why will he shout at her? Bakin hijab dinta tasa ta goge fuskarta sannan ta bude murfin motar ta fito, stupid kwakwalwar ta ta maimaita mata, se hawaye suka kara sakko mata a kunci. Dama Batayi expecting kowa ba a parlon haka kuwa babu kowa Don haka straight dakinta ta nufa tana shiga ta maida kofar ta rufe sannan ta kifa kanta ta Fara rera sabon kuka, ita ba tsawar da yayi mata bace damuwarta a'a fushin da taga yayi shi ne matsalar ta. Cikin mota Junaid na zaune yayi clutching fist dinsa kamar wanda yake naushin wani, why zai dinga tufka and wasu suna warware masa? Se yaji zuciyarshi na fadin you're selfish Junaid, Kace kana sonta ne? Tanada magic ne da zata karanta abinda Ke zuciyarka? Wani dogon ajiyar zuciya yaja sannnan ya bude motar ya fito ba tareda ya koma takan Pizza dake Bayan seat ba. Misalin karfe takwas da rabi na Daren wannan ranar Sulaim ta fito don tasan tabbas an gama abinci kuma tunda tayi masa laifi is better ta fita basai ya tura kiranta ba saboda gaba daya ta dauki alhakin komai ta daura akanta dukda batasan takamaimai Abinda tayi mishi ba amma yadda yayi dazu tasan tabbas ita taja komai. Gefen Ahmad ta zauna Bata kalli inda suke ba dukda yana ta taba ta amma bata biye mishi ba saboda Junaid baya kan table din kuma yaranshi da matarshi har sun Fara cin abinci hakan ya bata clue din he's not eating. Plate ta janyo ta dauki slice din Pizza daya ta saka sannan ta tsiyaya tea ta Fara sha amma hankalinta sam baya kan abincin don taste din ma Bata jin dadinshi, hankalinta Baki daya yana kofar parlour Junaid. Har kowa ya tashi tana nan Zaune kuma bata cinye slice daya ba. Har Tara da rabi tana nan Zaune Bata san jiran me takeyi ba tadai San ta kasa tashi ta tafi, Baki daya tana jinta a takure Tana jin akwai Abinda is not in place, it doesn't supposed to be. Yana kwance yayi nisa da aikin da yake cikin system Subay'a ta shigo ta zauna gefen shi tareda kai hannunta saman kanshi tana shafawa a hankali sannan tace Dinner is set. Dago kanshi yayi ya kalleta tayi kyau sosae saboda Dama ita ma'abociyar kwalliya ce, hannunta ya rike yace Inada aiki sosae se Zuwa anjima kawai kije kuci, zan ci nawa Shikuma ya fadi hakan saboda yana avoiding haduwarsu shi da Sulaim ne amma yunwa yake ji, kanta ta gyada batareda ta ce komai ba ta Mike Don ficewa yace Dear, kice Sulaim ta fita taci abinci kada ta kwanta haka. Da sauri Subay'a ta jiyo jin Abinda ya fada, tsira mishi idanu tayi ta koma inda ta tashi ta xauna tace Junaid meye tsakaninka da yarinyar nan. Kallonta shima yayi baiji komai ba kuma Abu daya ne zai hanashi ba ta amsa for Sulaim's well-being idan ba haka ba da se ya bata amsa daidai tambayarta. Me kike cewa? Ya fada Yana kallonta straight cikin idanu Kaji abinda na fada ai, Meye tsakaninku kake mata wannan extraordinary kulawar, Junaid sonta kake? Tsaki kawai yayi ya cigaba da aikinshi dukda tambayar tata tazo mishi a bazata saboda bai taba expecting zata dago shi ba amma akwai Abinda Junaid bai sani ba ko minti daya sukai tareda Sulaim a gurin mutane definitely se an dago su to balle Subay'a wadda Ke tare dasu kullum dukda batada fahimtar abu sosae sannan ba ta cikin mata masu saka ido akan mazajensu. A fusace ta fice shi kuma ya dafe kanshi Yana sauke ajiyar zuciya a gaggauce kamar wanda yayi kuka, ya dade kafin zuciyarshi ta nutsa sannan ya cigaba da aikin da yake daidai da Lokaci daya Sulaim Bata bar zuciyar shi ba, fuskarta kawai yake hangowa tana kallonshi lokacin da yayi mata tsawa, sannan kunnuwanshi nayi mishi amsa kuwwar kukanta kamar an tsikare shi ya Mike bai ma duba time ba ya fito Zuwa parlourn ga mamakinshi tana zaune kan dining din tana ta juya tea din dake cikin mug kana kallonta kasan itadai tana gurin amma tunaninta da hankalinta duka suna wani wajen, har ya zauna batasan yazo gurin ba seda kamshin turaren shi yayi awaking dinta. Seda ta kwantar da yaranta kafin ta kwanta gefensu ita ba kullum take Kwana dakin miji ba ranar da abin nata ya motsa zataje shima se ya zuba mata ido, wayarta ta janyo ta Fara neman layin Sulma cikin sa'a ta shiga kuwa amma har ta katse Batayi picking ba hakan yasa ta kara kiranta wannan karan tayi picking Sister Kin duba agogo kuwa goma tayi fa, ina fata lapiya? Sulma ta tambaya Inafa lapiya sister? Me ya faru ni uwar Amna Dan tsaki Subay'a tayi tace Ina yarinyar da nake gaya miki tana karatu a gidanmu? Shiru Sulma tayi tana son tunawa kafin can tace Yarinyar nan wadda iyayenta suka rike Papa? Da sauri Subay'a Tace Ita fa, sister Junaid sonta yake! So!? Haba dai Sister wanne irin so kuma? Wallahi ba wasa nake miki ba, walahil azim sonta yake. A'a dai Sister sede idan baki lura ba ta yaya Papa zaiso wannan yarinyar? Kede kawai insecurities ke damunki amma da Papa zaiyi aure ai da tuni yayi, Dan Allah ki fitar da hakan daga zuciyarki babu wani abu. Amma ke how sure are you? Hawayenta ta goge tana jin haka ne kuma tabbas insecurities Ke damunta Tunda tasan Junaid ba tsoronta yake ba idan har yana son yarinyar da da ta tambayeshi se ya fada mata koda zatai Meye ne. Yana bata kulawa wadda ta wuce gaban misali Shikenan? Karki manta yarinyar marainiya ce kuma batada kowa se su idan basu kula da ita ba yakike so suyi. Kiyi hakuri sister ki kwantar da hankalinki Zamuyi magana da safe Abban Amna Yana jirana. Babu yadda Subay'a zatai haka sukai sallama ta koma ta kwanta zuciyarta kamar zata fito ga wani kululun abu da ya tokare mata makoshi amma ta kasa Miqewa ta sameshi. Yana zama ta Mike Don komawa daki Amma cikin gaggawa yace Koma ki zauna Babu yadda zatayi haka ta zauna Tana jujjuya fork din data dauka, bai kara ce mata komai ba ya dauki tea ya kai bakinshi Yana Sha yana dubanta se lokacin ya fahimci kuka take. Tsaki yayi Wanda yasa ta dago idonta tana kallonshi tareda fadin Yaya kayi hakuri Shuru yayi ya aje mug din hannunshi tareda runtse idonshi, Sulaim is not helping matters kara tabarbara komai take idan ba haka inhar tasan yadda kukanta yake dukanshi baya tunanin zata yi Koda fushi balle takai ga yin kuka. Is ok, tashi kije ki kwanta. Kanta ta girgixa Tana share hawayenta Tace Kuma fushi kakeyi fa, ni bansan Meye nayi maka ba Kinsan bana son musu ki tafi daki. Haka ta Mike ina mamakin kukan me takeyi, seda ta shiga daki kafin ya dafe kanshi, inhar ya cigaba da haka tabbas zuciyarshi ta gaji da boyewa, he's tired ya kamata yayi uncaging zuciyarshi ya sanar mata amma yana ganin kamar Lokaci baiyi ba, Yana ganin is too early hakan ya kasance. Washegari karfe bakwai Sulaim ta fito da books dinta tayi bak yard din gidan inda nan ne window din Junaid yake ta zauna kan kujera dake aje a gurin ta Fara karatu Tunda jiya Bata samu tayi ba batasan se su Khulthum sunzo ana karatu tayi kirikiri. Tayi zurfi sosae cikin karatun taji muryar Junaid Daga dakinshi Yana fadin Ya zanyi Ridwan na rasa tattaro karfina Naje, ina ganin kamar Lokaci baiyi ba. Tsaki tayi ta cigaba da Abinda take, se can wayarta ta Fara ringing tana dagowa taga Junaid dinne, Seda gabanta ya fadi kafin ta tattara courage din ta dauka kafin ta gaisheshi yace Ina kika je Kallon gurin tayi tace Ina backyard karatu nake A hankali ya sauke ajiyar zuciya yace Ki dawo ciki. Bai jira amsarta ba ya kashe wayar sannan ta tattare books dinta ta nufi cikin gidan, suna zaune a parlour suna kallo, ta zauna a gefe tace Yaya ina Kwana, Anty an tashi lapiya? Lokaci daya suka amsa mata, Subay'a Tana ta binta da ido tamkar tana son gano wani abu a tattare da ita, haka ta wuce daki tayi wanka ta shirya cikin gown ta material sannan ta zauna gefen gado ta dauki wani picture dake jikin wani kyakyawan frame ta kalla tana shafawa idanunta sun cicciko da kwalla, hoton Daddy da mummy ne suna murmushi sosae, da na kalli hoton tabbas Junaid da Baban Sukam yake kama tamkar yayi kaki haka suke. A hankali ta furta Allah ya jikanku ya rahmushe ku. Kafin ta aje ta dauki wayarta ta turawa su Khulthum address din. Tana nan Zaune ta dauki wayarta ta kunna data ta shiga Wattpad don debewa kanta kewa, dake bata iya karatun Hausa ba yasa yawancin novels din library dinta are English. Wani a ciki ta Fara karantawa kafin wani Lokacin har hankalinta ya kau Daga tunane tunanen da take. Atika ce tayi sallama ta shigo tace Anty Sulaim Kinyi baki a parlour. Da sauri Sulaim ta Mike ta fito fuskarta kamar gonar auduga Don murna she can't believe cewar su Khulthum ne, ai kuwa su dinne suna Zazzaune Khulthum tana ta kalle kalle, kujera ta samu ta xauna Tana fadin Sannunku da zuwa har nayi fushi. Khairi ta maka mata harara tace Ke kika sani dai Dariya sukai sannan suka gaisa tace Muje ku gaisa da Anty Subay'a. Tashi sukai suka bi bayanta har parlon Subay'a Tana zaune itada su Ahmad tana koya mishi two letter words, dago idonta tayi tana kallonsu fuskarta kamar kullum har suka zauna suka gaisheta ta amsa musu sannan suka Mike suka koma dakin Sulaim inda Atika ta cika musu gaba da abinci da drinks seda suka ci suka sha ana hira sannan suka Fara karatu. Se Azahar sukai sallah sannan Khulthum ta bude Jakarta ta ciro hadadden lallai da cone na kunshi tace kowa ya zauna ta mishi kunshi, gaba daya suka tsaya kallanta Irin kada kiyi mana jagwalgwalo fa, dariya sosae Khulthum tayi for the first time ever ta Fara basu labarinta tanayi tana musu kunshin da suke gani a Temple of Hennah. A karshe tace Don haka gaba daya rayuwata na tsara ta a Auren me kudi don yadda na tashi a talauci bazan dawwama a talauci ba. Khairi for the first time ta fadi abin hankali tace Bake zakiyi deciding haka ba Allah shi zai tsara miki yadda zakiyi, kuma akwai masu kudin da kwatakwata hankalinsu ba a kwance yake ba. Sulaim tace Hakane Wallahi, Kede Kiyi addu'a kuma kinga Ashir dinnan Allah ki daina wulakanta shi. Dariya Khulthum tayi tace Ku bazaku gane ba, ki kalla dakin da kike ciki fa Bana aurenki ba na gidanku, kingani da banbanci sosae. Kai Sulaim ta girgixa tace Ke kuwa ki godewa Allah wasu basu da gida gaba daya fa, kuma kina zancen me kudi kince Marar aure, to at that tender age ina kike tunanin zai samu kudin da kike mafarkin Kiyi? Akwai su Bakiga Huzaifa ba, ba kiga Yusuf ba? Se lokacin Aimana tayi magana tace Ki daina wannan zancen Huzaifa ba kudinshi bane na iyayenshi ne kuma ko yau suka fadi suka mutu dole a raba gado, yusuf is too young ace yanada kudin da yake dashi Kinsan sana'ar da yake? Kimsamshi waye? Baki sani ba kun hadu a titi kawai ya gaya miki kin zauna akai, Bari in fada miki bawai zagi ne ba amma yanzu rayuwar da ake Bani gishiri na baka Manda, Dan wane se dan wancan kin taba jin dan Dangote ya auri yar Malam Ayubah? Baki taba ba Sede dan Mangal da dan Ndimi, dangote da 'yar yaradua! Ina ma zaki gansu ke balle suce sun kyasa is better ki zauna daidai inda Allah ya ajeki ina ganin burin ki zaifi saurin cika amma idan kika matsa zakiyi da na sani nan gaba. Tabbas abinda Aimana ta fada is in place, daidai ne daidai kudinka iya shagalinka ki tsaya inda kike kada rudin social media ya fitsare miki kanki, *MACE A YAU* ta dauki buri ta daurawa kanta se tayi abinda waccen tayi is not right ki zauna inda kike rabon kwado baya Hawa sama ko yaje se ya sakko haka bahaushe yace kuma haka yake. Most charming guys masu kudi at a young age are arm robbers, thieves, gays ko wani abun ina ganin guntun gatarinka yafi sari ka bani. Is high time we change that fact na cewar mijin da zan aura se ready made not sugar daddy, single ta yiwu babanki at that age baya da komai to meyasa zakice se Kinyi, *KALUBALEN MU* wannan Itace *RAYUWARMU A YAU* sannan komai *MUQQADARI NE* daga Allah shi zai tsara maka komai Amma rashin yadda da hakan yana daya daga cikin *MATSALARMU A YAU* kuma ita mace Allura ce cikin ruwa *ME RABO KA DAUKA* Shiyasa *GIDAJENMU* bazasu taba rabo da matsala ba saboda hakan ya kamata mu gyara rayuwarmu. Shatuuu ♥️ [7/15, 10:32 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 19 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Duk wanda aka yiwa maganar da Aimana ta fadawa Khulthum idan har zai dauka yaci ace ko da na wannan lokacin ne ya dauka amma khulthum gani take to idan ta tsaya a wannan gurin me ta samu? Wacce ribar zatace ta samu? Babu! Tunda har yanzu cikin samarinta babu Irin Wanda idan ta tsaya sukai hoto dashi tayi posting zataji ana comments da irin "oh Allah ina kika hadu dashi? Awwnnn Dama kinsanshi ne? I'm envying you? Wannan crush dina ne" words of such haka take so to wanne ne a ciki? babu shi. Tana gama yiwa Khairi ta aje cone din tayi mika sannnan ta koma gefen gado ta zauna Tana ta kallonsu kamar yadda suma suke kallonta, se tayi murmushi tace Dangin babana basu nema na, sun Kori Mamata da ni basu kuma nemeni ba, so inason na auri me kudi wanda aurena se ya girgixa ilahirin Nigeria, se sunyi Dana sanin abinda sukai. Tana yin shiru Khairi da Aimana suka kwashe da dariya, Harda rike ciki saboda maganarta ta basu dariya, a yanxun ka kyautata rayuwarka ma kaga ba daidai ba Balle ka rike wani shirme, yadda sukeyi babu kakautawa itakam Sulaim tambayar kanta take shi aure ba bautar ubangiji bane ko kuma shi source din yanke talauci ne? Kinsan ni ban taba mafarkin auren me kudi ba, ni akaran kaina nake son Nayi kudin. I want to be my own boss naci gashin kaina ba under umbrella wani ba. Khairi ta bata amsa Bayan ta gama dariyar. Kinga wannan ra'ayinki ne, so nima hakane ra'ayina Duk inda me kudi yake ko saurayin waye inhar yayi min I'll definitely make him mine. Baki bude Sulaim tace Muyi kaffa kaffa kenan.? Gaskiya kam yadda nake ji da baby tsaf zan miki duka akanshi Khairi ta fada suna kara kwashewa da dariya Don su duk tunaninsu wasa take, abinka da wayayyu take aka bar maganar aka cigaba da zancen wani Korean movie da Sulaim ta samo musu lokacinda taje kaduna daga gurin Jawad Kings woman. Sunata hira Aimana tace Nifa babu jaki a film dinnan irin Min Feng yana sonta amma shi dole gadinta yake a karshe ya tashi a tutar babu se Kisa da akai mishi Dariya Sulaim tayi tace The useless brat ba kuma bata taba recognizing halin da yake ciki ba. Khairi tace Hakane fa, gwara mashi fa yana ganinta amma kinga Jin Ke dinnan Allah kadai yasan yadda na tsaneshi naji dadin kasheshi da akai Wallahi. Khulthum tace Ni kuma baki daya Yin Zheng din na tsana Ido a waje Khairi tace King baki daya? Gaskiya kin zake. Kafin a Bata amsa sukaji ana kwankwasa kofa, Khulthum ce ta Mike ta nufi kofar ta bude gaban Sulaim ya dinga faduwa tamkar wadda Abu ya biyo ta, a ranta addu'a take ubangiji yasa ba Junaid bane Don maganar Khulthum ta tsaya mata a rai so se taji batason su hadu. Fortunately sega Atika ta shigo hannunta rike da fararen envelope guda uku, Tana shigowa ta Kara gaishe dasu Aimana kafin ta mikawa Sulaim tace Alhaji yace a Baki, wai ina Wayarki? Se lokacin ta tuna wayar ma baki daya a silent take hakan yasa tace Oh tana silent, ya fita ne? Eh Ta bata amsa sannan ta fice, Khulthum da babu kunshi jikinta yasa ta miko mata wayar Sega missed call na Yaya, ya Ja'afar, Salim da wata unknown number. Ita basuyi waya da Salim din ba jiya ya Kira tayi bacci gashi yanzun ta Kara missing call din nashi. Junaid ta Fara kira bai dade yana ringing ba yayi picking Wayan a silent yake ne Ko kuma kina ta surutu ba Ya fada Yana kallon Ahmad dake gefenshi. Murmushi tayi tace A'a ne fa. Shima murmushin yayi yace Anyways, ga sako nan ki basu ki gaishesu ni na fita Kallon envelope din tayi tace Mungode Allah ya saka da alkhairi Zasuji, a dawo lapiya. Kai ya gyada yace Akwai Abinda kike so na taho miki dashi? Kai ta girgixa tace A'a, se kun dawo. Daga haka sukai sallama ta dauki envelopes din batareda ta buda ba ta mimika musu tace Yaya yace a baku Duka sukai godiya suka zura cikin handbags dinsu nan hirar ta koma kan Junaid wanda Aimana ce kawai tasan shi amma su basu taba ganin shi ba To Sulaim ki aureshi mana kiga yadda yake kula dake Yana kaffa kaffa da ke. Khulthum ta fada , Sulaim Baki bude tace A gidanshi muke fa matarshi tana nan, wayace muku wai soyayya muke. Tsaki Khairi tayi tace Ki cigaba da denying abin ai a bayyane yake, ko tone din muryarki ansan akwai magana. Haka sukai ta yi mata se ta sharesu kawai, ana La'asar aka cire kunshi yayi kyau sosae suka dinga mamakin dama haka Khulthum take dama tanada wannan talent din amma take neman tsayawa dogara da namiji. Wajen 5pm aka zo daukarsu Khairi zata bi Khulthum Hu zai sauke ta a BUK, yayinda Nu'uman yazo daukar Aimana. Suna fitowa tace Muje kui sallama da Anty. Parlonta suka nufa Sede Tun kafin su bude kofar muryoyi Ke tashi Wanda ya tabbatar musu tayi baki, da sallama suka shiga yan uwanta ne dukda wannan ne Karon farko da Sulaim ta gansu dukkansu Amma tana ganinsu jefi jefi suna Zuwa, mutane ne yan rainin hankali da suke ganin kowa bai iya ba su kadai suka iya to haka suke, ga kallon wulakanci. To tunda suka shigo suke binsu da ido suma su Khulthum haka, tare suka gaishesu Subay'a dake zaune tace Ya akai? Sulaim ta kalleta saboda taji haushin tambayar, se ta kyaleta tace Zasu tafi ne. To Kawai tace takaici kamar me haka Sulaim taji suna fitowa Surayya tace Subay'a wannan yarinyar ce kanwar Junaid din? Subay'a ta dago tareda fadin Ita ce fa Kan babban bala'i! Kika barta take Zaune a gidanki Sulma tayi saurin fadin Me yasa kuke haka itada gidan dan uwanta. Samina tace Yaya Sulma dan Allah Kiyi shiru, Amma Yaya Subay'a this is carelessness, how sure are yarinyar ba spy bace. Tsaki Suhaila tayi tace Ke ta spy kike, taje tayi ta leken asirinta who cares? What matters kada ta juyawa Junaid kwakwalwar kanshi, kinga kyau kamar Aljana. Didim!!! Gaban Subay'a ya fadi kada fa hakan ta kasance, kada fa turo ta akai don a aura mishi ita! A'a Kada kui haka, Sister kada ki manta maganar da mukai dake, babu wani alaka tsakaninsu amma idan kinji shawarata kenan kada ki tada hankalin ki a banza kuma yazo baida niyya yaga Abinda ake gani a tare da ita. Samiha tace Gaskiya kika fada Sulma sede ina ganin kiyi watching yarinyar, saboda kallon da take miki kadai Irin na baki gabana haka take miki. Dakyar Subay'a ta hadiyi mugun yawu tace Kallon da takeyi min kenan Tun zuwanta gidannan, akwai wasu abubuwa tattare da yarinyar na rasa Meye kawai idan na ganta gabana faduwa yake, Wallahi tsoro take bani. Wata ashar Samina tayi tace Haba Yaya Subay'a Kada ki badamu dan Allah wannan yarinyar? Da Ummin Yaya Safina I'm sure ta gurmeta zata na fadar miki gaba, idan ta kawo miki raini Kici ubanta shi ne kawai. Haka sukai ta zugata ita kuma baki daya ta duburburce taki fada musu ainahin signs din data gani saboda gaskiya hankalinta ya kasa kwanciya da Junaid. A waje kuwa Hu ya fara isowa suka gaisa sannan ya dauki gimbiya da khairi se BUK, suna nan tsaye Aimana tana Bata labari Nu'uman ya iso, yana parking ya fito ya zo inda suke tsaye suka gaisheshi ya amsa kafin yace Sulaim nace ina sonki kawar ki ta Hana ta kankane ko ina. Dariya sukai saboda yadda yayi maganar tamkar irin kana son Abu an hanaka, Sulaim tace Kayi hakuri I'm already taken! Aimana ta kalleta da sauri amma se ta kawar da kanta saboda tasan karya tayi amma a yanxun tana ganin har Yaushe zata cigaba da Tara samari kuma batajin son su a ranta, don ita tana ganin zuciyarta..... Se kuma tayi shiru yayinda Nu'uman yayi murmushi me ciwo yace Ban fidda rai ba, ban hakura ba amma inason na zama admirer from the side, in karba number ki? Kanta ta gyada kawai she can't say no, yayan Aimana ne dole tace Babu damuwa, Aimana ki bashi. Murmushi sukayi sannan sukai sallama suka barta a gurin har kewarsu ta Fara damunta. Tadan jima a tsaye kafin ta shiga ciki bata bi takan kowa ba ta wuce dakinta ta gyara sannan ta yi tilawa. Karfe Sha daya da Rabi na dare daidai lokacin Sulaim ta dade da yin bacci wayarta ta Fara ringing, da kyar ta janyo wayar ta kara a kunnenta Sede muryar Salim tasa ta bude idonta da kyau Princess Nayi laifi ne? A hankali cikin bacci tace Bacci nake fa! Seda muryar ta ratsashi hakan yasa yace Ooops sorry Yi baccinki. Bata jira ba kuwan ta koma ta kwanta se bacci abinta. Washegari akai last paper kuma babu laifi tayi dadi, suna fitowa Khairi ta wuce Jalingo itama Aimana ta wuce gida ya rage se Sulaim da Khulthum the bussoms kenan. Yawwa Khulthum akan maganar Ashir ne ya kuke ciki. Tsaki Khulthum tayi tace Rabu da wawa, wai yaki hakura Kince ya hakura ne? Eh mana, baya cikin type dina Sulaim so kike na yaudareshi? Na fada mishi gaskiya ni bazan aureshi ba. Haba Khulthum yace yakai kudin me kuke cewa abin? Sulaim ta fada Tana son taunawa Na gani ina so, Twenty thousand ce fa! Yazo ya karba abarahi . Khulthum ni kawar ki ce, ke kinfi karfin kawa gurina you the sister I never had, ki nutsu ki Daidaita kanki rayuwar duniya batada tabbas a wannan zamanin har kika samu kamar Ashir kike wulakantawa mutum me bright future ahead? A'a fa ki guji dana sani. Bazan taba yi ba, Dan Allah Sulaim ki kyaleni da zancen Ashir hakanan kodai asiri yayi miki ne? Dariya sosae Sulaim tayi tace Ina ganin kamar ya cancanci ya zama mijinki ne Shiyasa na dameki, to ki fitar da Yusuf kui aure mana Tsaki Khulthum tayi tace Baida arzikin mijin da nake burin aura, wayeshi? Wa ya sani? Waye ya sanshi? Kin gane kuma ni yanzun babu aure a tsarina. Kai Sulaim ta girgixa tace Wanne irin miji kike so Murmushi me kyau tayi tace Me kudi, shekarunshi kamar talatin bai taba aure ba haka bayada yan mata, bayason mata ma baki daya, kyakyawa wanda yan uwanshi basa zaman kasar Balle su saka mana ido, me hadadden gida da mota. In takaice miki Handsome in a flashy car and a top rich Man..... Shi ne burina. Shatuuu ♥️ [7/17, 10:44 AM] Shatuuu😍: *MACE A YAU* 20 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Where are all the fantastic, fabulous, awesome and gorgeous Damsels of SHATUUU's KINGDOM and Damsels of Maman Mama novels..... Take This page as a token of appreciation.... Thank you very much ladies for always having my back, for always being there for me..... You're such a darlings* Idanunshi a kulle tamkar wanda yake bacci amma kwatakwata ba baccin bane cikin idanunshi hasalima baya tunanin a Wannan Daren akwai possibility shi din yayi bacci saboda yana cikin mawuyacin hali, Yana cikin tsananin tsukun rayuwa wanda soyayya ta jefashi a ciki, soyayya me zafi wadda take neman tayyar mishi da hankalinshi take neman wargatsa mishi Duk wani karfi da a da yake tunanin yana dashi to Amma soyayyar Sulaim ta nuna mishi shidin ba kowa bane ba kuma komai bane. Idan zai iya tunawa jibi ne Sulaim zata cika eighteen years da haihuwa he remember vividly lokacinda aka haifeta lokacin baifi lokacin shekarunsa wajen sha shida don ya Kare secondary school dinshi, through out rayuwarshi yayi tane akan bata kulawa ta kanwa bai ko taba tunanin zai rikeda ya zama wannan zazzafan son ba, gashi wadda yake dan ita bata masan halinda yake ciki ba sha'aninta kawai take abinta babu wata damuwa a tattare da ita amma shi gashi nan walwala da sukuninshi gaba daya soyayyar Sulaim tayi tafiyar ruwa dasu. Kwanciya ya gyara ya kalli agogon dake jikin bango karfe takwas da rabi ba wani Dare bane yayi hakan yasa ya janyo wayarshi ya fara kiran Mami, lokacin Mami tana zaune itada Imratu wanda suka dawo jiya daga Saudia, likitoci sun tabbatar musu lokacin haihuwa ne baiyi ba amma babu wani abu dake damunsu dukda haka se suka basu guidelines da zai boosting fertility din nasu, to Sede ayi fatan Allah ya sa a dace. Mami barka da dare Barka dae Uban Sulaim Dama Duk lokacinda ta yanke abu akan Sulaim din shikuma ya nuna rashin amincewar shi haka take ce masa, kowa yasan Mami tace ayiwa Sulaim booking jirgi ta tafi Kebbi to yau ya kamata a gama komai se aiki ya rike Junaid bai samu yaje ba ya kirata akan ta tafi wani satin Tace dashi ya Bari ta turo Ja'afar ya kaita a mota, aikuwa Junaid yayi tsalle ya dire yace babu Wannan maganar zai bar Duk Abinda yake ya kaita da kanshi, to kafin su gama magana tayi Baki tayi mishi sallama akan zasui magana da daddare. Murmushi yayi kayatacce yace Kai Mami wai Baban Sulaim Baban Sulaim mana, yanzun ni na rigada na turo Ja'afar Don Tun shida na yamma ya iso kano, gobe da safe zasu wuce. Kanshi ya dafe yana tunanin me zaiyi kuma shifa tafiyar ce baki daya baya so Sulaim tayi ita da Ja'afar amma Mami ta kasa fahimta bai sani ba Mamin tun dadewa ta harbo jirginsu ta rigada tasan cewar akwai kakkarfar soyayya tsakanin Junaid da Sulaim dukda a farko Junaid ne kadai amma daga baya se ta fahimci Sulaim ta afka, tayi farin ciki sosae tunda tasan waye Junaid ita ta haifeshi Duk cikin 'ya'yanta babu mutum me tsananin hakuri, kauda kai da juriya Irin Junaid tasan idan har ace Jabir Ke auren Subay'a da tuni gayyar ta watse amma daidai da rana daya bai taba mata complain akan zamansu da ita ba dukda tasan cewar a takure yake sede tayi alkawari kwaya daya duk ranar da ya kawo wata zai aura zata Goya mishi baya Sede a yanzun tana tantamar idan zata yarda da wannan abin kasancewar su biyu Junaid da Ja'afar sunyi tarayya akan son Sulaim To Mami Allah ya kaimu goben. Sanyin halin Junaid na Kara masa matsayi cikin zuciyar ta Mamin, tasan baya so amma bazai mata musu ba. Ina sulaim din take. Dan dariya yayi yace Mami tana dakinta ina nawa sede ko idan za'akai mata wayar ne? Itama murmushin tayi tace Zan kirata kawai a gaida Subay'a da yara. Daga haka sukai sallama ya kifar da wayar shima ya kifar da kanshi, Baki daya yau ranar Bata masa dadi ba ya yini cikin aiki a office ga wannan ya kunno kai, ya zaiyi kenan? Zuwa zaiyi ya tunkare ta da zancen? What if it happens tanason Ja'afar? Se ya zama me son kanshi bayan yasan idan Ja'afar ne zai iya dedicating mishi ba Sulaim ba ko Abinda yafi Sulaim dinne? To shi Yana babba me yasa yake son kanshi da Yawa? Tambayoyi barkatai wanda babu amsarsu kuma suke neman tarwatsa kwakwalwar kanshi saboda kanshi ya fara Sara mishi, Sede wata zuciyar tace babu yadda xa'ayi ta sadaukarwa da Ja'afar abar kaunarta idan kuma hakan ta kasance bazata taba hutawa ba kuma bazata yafewa Junaid din ba kuma se Allah yayi musu hisabi on the resurrection day! Cikin hakane Subay'a ta shigo tayi kwaliyya bawai iya ta fuska ba har a jikinta, tayi kyau har ta gaji da yinshi, babu Abinda Ke tashi jikinta banda kamshi me mutsar da kwantar da zuciya Sede a yau babu Abinda Ke bakanta ma Junaid rai Irin ganin Subay'a saboda yana ganin rashin kulawar ta gareshi yasa shi cikin wani hali, saboda lokacin ai son baiyi karfi ba Tunda har idan yana tareda Subay'a yakan manta da Sulaim amma saboda rashin bashi muhimmanci se Wannan implantation na kaunar Sulaim wanda aka dasa shi can kan Septum na zuciyarshi seda yayi yado ya taba Ventricles, Atrium, bundle of hiss, inferior and superior Vena cava, Aorta da dukkan wasu jijiyoyin dake zuciyarshi har yakan ga Subay'a ta rikide mishi ta koma Sulaim. Gefenshi ta zauna ta Daura hannunta Kan hannunshi ta zuba idanunta cikin nashi tana karanto halinda idanun ke ciki, taga So me karfi wanda ba mallakin ta ba, taga fear na kar na rasa Wannan abin, taga haushi na wannan ta watsar dani, idanunshi masu haske sunyi ja alamar yana cikin wani hali. Better half! Ta kira cikin wani salo wanda duk karfin zuciyarka se ka jishi har kwakwalwar ka, Balle Junaid that's helpless wanda bashida makoma soyayyar Yarinya mitsitiya tana neman maida shi rago. Ya kalli Subay'a wadda idanunta suka Fara maiko alamun taruwar kwalla Better half Meye ke damunka? Meye matsalar ka? Yaushe rabon naga kayimim murmushi? Baka nemana, ka daena cin abinci. Dan Allah ka fadamin ni matarka ce Bakada kamata. Sosae yake kallonta saboda yaso abinda take fada gaskiya ne, amma karya take, ina ya zama better half dinta ta ina? Da ta bashi muhimmanci da bazai shiga Wannan halin ba. Baice ko uffan ya Mike ya fada bayi kamar five minutes ya fito Fuskarshi da kanshi na digar da ruwa, seda ya goge kafin yace Abinci kikazo ki kirani mu ci ko? Let's go Haka ya fice ya barta a gurin, hawayen suka samu damar sakkowa daga idanunta. Waye ya maida mata miji haka? Wayake so har haka? Ko dai waccan yarinyar yake so? Da Wallahi ko ta tsiya ko ta arziki se ta bar gidan. Hawayen ta goge tabi Bayan Junaid wanda har ya zauna yayi serving yaran dashi kanshi, Sulaim Bata gurin bai kirata ba bai kuma damu ba a cewarshi kenan amma baki daya hankalinshi Yana kan me takeyi?! Tana kwance ta tasa system a gabanta tana kallo, ita bata kallon Korean dramas Amma Tunda ta dawo Nigeria Jawad ya kwadaita mata su gashi yanzu batada abin kalla se su, yanzun ma wani Empresski take kalla ko nace maimaici Don ta jima da kallonshi amma yadda yayi kyau yasa take maimatawa, ta Gama shirinta tsaf gobe kawai take jira ga dokin ganin dangin uwa ga dadin sun shirya da Ja'afar zaayi tafiya tare Sede acan kasan zuciyarta akwai wani abu da take ji Marar dadi, Ta rasa ko meye abin amma Lokaci guda har yana son yayi overcoming baki daya farincikin da take ciki, lokuta da dama takanji inama ace itada Babban yaya zasu tafi, wannan murmushin nashi, wannan muryar very deep amma me dadin saurare, me kuma mutsar da Mai laifi, wannan idanun masu haske tamkar an disa musu abu a ciki, wannnan sharp and piercing looks din nashi masu maidata jin she's helpless! Kai everything about Junaid is just perfect.... Ta jima tana mafarkin inama ace shi ne Ja'afar, Ja'afar ne shi, Tasha ayyana idan ace Itace Subay'a she will never ever mess up kamar yadda Subay'a ke barin damarta. Tamkar karfe da magnet haka Sulaim taji mummunan force of attraction haka cilak ta Mike ta doshi kofa sede Allah ya taimaka tayi assessing kanta Ashe half gown ce jikinta da sauri ta dawo ta cire rigar ta dauki abaya ash ta saka ta yafa mayafin ta fito batareda sanin meye dalilin fitowar ba ashe she wants to see him, she wants to see all Abinda ta lissafa akanshi. Almighty Allah so kind, da idanun ta Fara tozali Bata jira ba ta sakar mishi tattausan murmushi wanda for life ba zai taba manta wannan murmushin ba, shima bai bata lokaci ba ya mayar mata da wanda ya fiahi Lokaci daya suka runtse idanunsu gam! Wani Irin chemical reactions, chemical bondings ya fara taking place, within seconds magnesium ya hadu da sulphate, hydrogen da oxygen, sodium da chlorine and many more. Ina Subay'a? Ta tafi daki amsa call din hajiya!...... Sorry kawata Kinyi missing.... Lokaci daya suka bude idanunsu wanda suka sauke akan junansu Sede lokaci daya kunya ta lullube Sulaim meye haka takeyi? Meye ke damunta? Juyawa tayi zata koma daki tamkar an fisgo Junaid yace Sulaimi! Cak ta tsaya tana kokawa da numfashinta sboda yadda Sautin muryarshi ya illata mata oxygen supply dinta Baki daya, a hankali ta juyo ta dubi inda yake bai tashi ba Sede dukkan hankalinshi na kanta, da ido ya mata alaman taje gareshi haka ta tafi cikin nitsuwa ta zauna inda ta Saba zama, idanunta a kasa idanunshi masu huda mata jiki da tarwatsa dukkan kuzarinta suna kanta hakan yasa ta takura matuka shi kuma kallonta yake yana mamakin kanshi, shifa ko Subay'a ya rantse da Rabbul Ka'aba lokacinda yake sonta baiji Rabin Abinda yake ji akan Sulaim ba, yarinyar ta shammace shi da yawa, ta shiga rayuwar shi tayi masa karan tsaye, tayi ma zuciyarshi shigar ba zata....... Abincin da ya Fara ci ya tura Mata yace cikin sassanyar murya Kici! Wannan muryar ba wadda xaayiwa musu bace hakan yasa ta dauka ta Fara ci shi kuma ya maida kanshi kan call din Ja'afar da ya shigo masa daidai wannan lokacin. Farin cikin da ta tsinci kanta a wannan Daren ba shida na biyu, Rana ta farko ta Fara tuhumar kanta me take ji game da Junaid? Kada ya kasance zancen su Aimana su Khulthum su khairi ya tabbata, tabbas da zuciyarta ta zalunce ta Tunda babu possibility shidin zai so ta...... Amma fa wannan tunanin Sulaimi ne...... To bangaren Junaid Wannan Daren matarshi ta kasance Tate dashi an Raya Daren, sayayyarta da ta kwanta ta dan kankaro wani potion daga ciki, Tana bacci ya Mike yayo Alwala ya fara kai kukanshi ga Rabbul Izzati! Baice Allah bani Sulaim ba a'a yayi addu'ar Allah ya bashi alkhairi idan ita ce, idan kuma babu alkhairi Allah yasa zuciyarshi ta dangana! Washegari karfe bakwai Ja'afar ya iso, Junaid ya takura masa seda sukai breakfast tare, Karo na farko cikin mutunci suka gaisa shi da Subay'a daga nan Sulaim ta fito sede jikinta dukka yayi sanyi se satar kallon Uban Ahmad take, shima hankalinshi na kanta Yana kallon duk Abinda take amma bai nuna ba. Takwas daidai suka rakosu har bakin mota an zuba kaya da komai, Junaid ya miko mata envelope wadda bandir din sababbin 200 naira notes ne sannan yace Wannan naki ne, ki Turon account details dinki zan turo miki kudin da zaki bawa mutane, Kai kuma Ya juya kan Ja'afar Be careful as you drive, Bana son Wannan gudun please. Murmushi Ja'afar yayi yace An gama babban yaya. Itakam zuciyarta kunci take so take ko digon hawaye ya zuba mata taji sauki dukda ta rasa me yasa take jin hakan, Ahmad da Muhammad suka zo sallama aikuwa Ahmad se kuka zai bita, dama kukan take nema se kuwa ta Fara, Ja'afar yayi tsaki yace Kin fiye shirme meye abin kukan. Shikam Junaid kanshi ya girgixa mata yace Ya isa haka Allah ya tsare . Bata amsa ba amma tana ta kokarin shanye kukan a haka tana gani ta tafi ta bar Junaid kewarshi ta mamaye ta har ta kasa sakin jiki sui hira sosae itada Ja'afar seda Junaid yayi mata text din _Those tears mean alot, is not every time ya kamata suna zuba. Allah ya kiyaye hanya_ Wata Irin ajiyar zuciya ta sauke tanajin sabon abu Wanda bata san Meye ba Yana huda mata jiki yana shiga zuciyarta, Lokaci daya kasala ta mata rubdugu Daga wannan se bacci me Cikeda farin ciki! Gbam! Gbam!! Gbam!!! Muuna kallon kowa a 3D screen.... Ehen rate this page on a scale of 10..... Shatuuu ♥️[7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 21 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Seda suka zo Funtua kafin Sulaim ta farka Daga baccin da take shima sanyin AC Ke damunta dukda akwai hijab a jikinta amma bai hana taji sanyin na ratsa ta ba, daidaita zamanta tayi ta dubi inda Ja'afar yake tirelessly driving, a kirjinshi yaji ta farka hakan yasa ya dubeta yace Sweetm kin tashi? Kanta ta gyada tareda janyo bottle water dake gefenta ta Fara sha, seda Tasha Rabi kafin tace Munzo Gusau? Kanshi ya girgixa yace Yarinya wasa farin girki muna Funtua. Bakinta ta turo ta janyo wayarta ta Fara danne danne, ita kanta bawai tasan me takeyi bane, Sweetm se Yaushe zanyi making move ne, ya kamata by now ace kowa yasan halinda muke ciki? Da sauri ta dago kanta ta dubeshi se murmushi yake, kanta ta girgixa tace Kai a'a gaskiya! Kallonta yayi yace A'a me? Sulaim bafa aure nace muyi ba at least mu sanar dasu Mami yadda Lokaci nayi dama ansan da maganar. Kanta ta girgixa tace Nidai a'a gaskiya To saboda me? Yaya yace Se naje level 3 kafin nan Idanunshi a waje yace Kice babanki bai amince ba, shikenan yadda kike so haka xa'ayi. Cikeda jin dadi ta sauke nannauyan ajiyar zuciya har Seda Ja'afar ya dubeta sede ya cigaba da tukinshi, itama ganin ya bar Wannan zancen yasa ta ware suka Fara hira dukda karfin hirar shi ne, hira me dadi me tsayawa a rai. Lokacinda suka isa garin jega sun gaji likis, nanne garinsu Mami asalin mahaifarsu itada Mummyn Sulaim anan family house dinsu yake cikin Shiyyar Ni'ima, katon gida ne ginin zamani me part biyar a cikin compound din, Tunda aka bude musu gate din wani Irin yanayi ya lullube Sulaim ta tuno lokutan da suke zuwa tareda Mummyn ta, Allah sarki mummy Allah dai ya kara haskaka kabarinsu ,bazata taba daina kewar su ba, komai zata samu bazata taba daina cewar ina ma Daddy da mummy suna raye. Cikin parlour kayattace wanda idan ka shiga zakayi tunanin gidan wata Amarya ce amma ko daya mahaifiyar Mami ce a gurin Hajiya Juwairiyya itada megidanta Alhaji Alkasim se jikokinsu guda uku da suke Zaune dasu, Hanan yarinyar Kawu Ali wanda ke bin Mami iyayenta suna birnin kebbi, Amaturrahman diyar Kawu Mamman shi kuma Mummyn Sulaim ke binshi sa'ar Sulaim dince yan watanni ne tsakaninsu, se Najib shi kuma Yayan Hanan ne. Sauran part din gidan na sauran yaransu ne su Mami idan sunxo se su bude su Zauna. Tunda tayi sallama Yaya Hanan dake zaune ita daya cikin parlour ta taso ta rungume Sulaim tana fadin Oyoyo Autar Mami. Oyoyo Yaya Hanan Ihunsu ya janyo hankulan mutanen gidan, Amaturrahman ce ta Fara fitowa itama tana buga nata ihun kafin Hajiya ta fito Cikeda farin ciki. Cikin parlour suka zauna anata gaishe gaishe kafin Hajiya tace Ummu tashi kuje ki dan watsa ruwa kar maghariba tayi, Jafaru kaima wuce dakin Najib ka watsa ruwa. Duka suka Mike Don Dama abinda suke jira kenan, Amatu ce ta kaita dakin hajiya don sun San indai tazo nan take sauka, wanka ta Fara yi Allah ya taimaka tana period hakan yasa bata dauki bashin sallah ba. Gefen kujera ta zauna ta janyo wayarta, missed calls kalakala haka ta tarar, a hankali ta Fara da Baba ta sanar mishi sunje lapiya sannan ta kira Mami kafin daga karshe ta kira Junaid. Yaya ina yini? Lapiya lau Auta kunje lapiya? Lapiya lau kowa Yana tambayarku. Kanshi ya gyada yace To ayi Hutu lapiya, Duk inda ya kamata ki tabbatar Kinje. Kanta ta gyada kafin sukai sallama ta Mike Don ficewa se kiran Salim ya dakatar da ita Haba princess Kinsan yadda kike wahalar da zuciyar Salim kuwa. Dan murmushi tayi tace Ni din? Ke mana inda Kinsan yadda kika hana Salim sakat I don't think zaki cigaba da gasa ni fa. Dariya tayi daidai shigowar Yaya Hanan, ta bita da kallo sannan ta shige ciki, itama sulaim din se tace Kaga a gajiye nake ka Bari mayi magana anjima Ina kika je? Ya tambaya Naje jega ne Dama ke yar jega ce ? Kasan jegan ne? Farin sani kuwa amma Kada ki damu ki huta zan baki mamaki. Kashe wayarta tayi a ranta bata ji komai game dashi ba, ita haka kurum ma take jin Bata wani aminta dashi ba. A parlor kowa na zaune har Alhaji Kasim Baffa shida Yaya Najib da Yaya Ja'afar suna zaune se zuba hira ake, gefen Baffa taje ta tsugunna ta gaishe dashi, Cikeda farin ciki ya amsa Yana saka mata albarka tareda yiwa Anty Zahra addu'a wanda hakan yaso bata atmosphere gurin. Tana gama musu kunshin ta mike tsaye Tana buga Hamma tareda kashe torch din wayarta, seda tayi mika kafin ta shiga daki Don shirin wanka, tana shiga ta Fara daukar wayarta tayi dialing number Sulaim, bugu daya ta dauka Hajiyan Kebbi kunje lapiya? Khulthum ta tambaya Cikeda kulawa, itama sulaim Daga dayan barin tace Bakiga text dina bane? Ina isowa na miki. Kanta ta girgixa tamkar tana gaban Sulaim din tace Ban gani ba Wallahi, kunshi nake yiwa wata Amarya. Cikeda jin dadi Sulaim tace Ranki ya dade, kina wuta fa Dariya Khulthum tayi tace Kinganni shiryawa zanyi Yusuf zan raka dinner abokinshi. Dinner Kuma? Ke Khulthum Rabu dani naje naga gari Kede ki zauna kiyi ta ninkaya a son Yaya! Tsaki Sulaim tayi tace Your skull is thick Wallahi, se anjima. Dariya Khulthum tayi ta kashe wayar ranta fal ko ba komai yau zataje gurin da bata taba Zuwa ba. Fitowa tayi daure da towel taje ta sheka wanka kafin ta dawo daki tayi shafe shafenta kafin wani Lokaci ta fito tayi dau kamar a saceta, fuskarnan dolled up. Kunsan fa Sulaim kyakyawa ce babu karya, fatarta tana da haske amma bawai can ba, zama a iya saka ta layin matsakaita, asalin skin color dinta me kyau ne Amma saboda yadda take bleaching skin din yasa tayi haske kamar rana. Fuskarta round face ce me manyan idanu hancinta Yana da tsayi, bakinta matsaikaici ne sede batada cikar gashin gira hakanan eyelashes dinta ba can dogaye bane Amma bazaka saka Khulthum a matsayin marar kyau ba, kallo daya kayi mata se ka Kara Balle uwa uba jikinta, shape dinta me kyau bata cikin gajeru haka bata cikin masu tsayi average height gareta. Tanada hips wanda ya kawata ta yake saka ta jin ita din tayi Saar halitta, tana ji dashi tamkar kwai. Wani cord net peach dinkin fitted gown ta saka wadda ta kamata sosae daga kasa ta bude, high heel ta dakko Baki ta saka, haka dankunnenta bakake sannan ta daura wani bakin scarf yayi kyau, ya amshe ta haka ta fito Tana fitarda fitinannen kamshin da sai wanda ya kai zuciya nesa ne zai iya jurewa. Tana fitowa sukai kicibis da Mama wadda dawowarta kenan daga suna itada A'isha, matar badai yawo ba. Kallonta tayi tace Khulthum ina zaki da daddare haka. Agogon dake manne a hannunta ta kala takwas da rabi sannan ta dubi wanda tayiwa kunshin tace Zan fita ku bawa Amira kudin ta aje min Ta fada Tana nuna Amira don duk gidan sunfi shiri da Amira hakanan tafi yadda da ita, se kuma ta dubi Mama wadda tayi jagalo tana kallon Khulthum din tace Dinner zanje, anjima zan dawo? Ta fada Tana juyawa Don ficewa, Mama ta dubeta tace To yanzun saboda Allah wani Irin biki ne se dare, kalleki ko lullubi babu, a haka zaki fita? Kafarta ta buga tace A haka ake zuwa, kuma ba dadewa zanyi ba fa. Badon Mama taso ba tace Allah ya kiyaye ki kula da kanki. Bata jira cewar su ba ta fice, nan A'isha ta zauna dabas tana mamakin Khulthum Yaushe idanunta suka bude har haka, to idan an Fara biki 8pm Yaushe zaa saka ran tashi kenan? Yar president tana wuta fa! Kalla batafi two hours ba yadda tayi dolling fuskarta. Daya daga cikin yan kunshin ta fada, amaryar ta girgixa Kai tace Ni kuma na raina mata Wallahi yadda ake zuzuta ta banyi tunanin nan ne gidansu ba. Mhmmm ga shegen girman kai! Ke ni abinda yake dauren Kai yadda bata girmama iyayenta, Zuwa na kusan biyar kenan amma Karki so kiga disrespect. Fitowar A'isha ya saka sukai tsit. Ita kuwa Khulthum tana fita sukai karo da natacce kamar yadda ta rasa mishi yanzun wato Ashir, dauke kanta tayi tamkar bata san Allah ya halicce kamar shi ba, shima se ya bita da kallo tamkar idanunshi zasu fado kasa har ta bude motar Yusuf tayi wa kanta masauki. Haka yana nan Zaune Yusuf yayi reverse ya fice abinshi. Ashir ya runtse idonshi tareda kaiwa iska naushi, Allah kadai ne bai saka zuciyar Ashir fashewa ba, shi kanshi baisan lokacin da ya dauka yana zaune kan Lifan dinshi ba. Yanzun ya daina mamakin Khulthum abu daya ya yanke gobe zai sameta ayi Wacce xa'ayi don ya gaji, yanzun ya fahimci kwatakwata Khulthum ba shi ne a gabanta ba, ya tuna wata magana da ta taba fada mishi cewar matsawar ta samu me kudi to zata iya barinshi tayi aure me kudi, don haka better yayi kudi. Dukkan tunaninshi ya tafi a wasa take amma yanzun ya tabbatar da gaske take. A FABS event center dake Magajin Rumfa nan ake kayataccen bikin, Tunda suka shigo taji ta kaskanta, taga mata iri iri Maza daban daban Kala Kala. Sede babu halin jamming dasu don Yusuf ya kafa ya tsare, basufi 20 minutes ba yace mata ta tashi zata rakashi wani guri, kamar kada ta tafi haka taji don Bata gama feeding idanunta ba. A cikin harabar Royal Tropicana Hotel yayi parking lokacin agogo ya buga Tara daidai. Kallonshi tayi yayinda yake kakkashe sauran abin motar yace bai ko kalleta ba Muje ko? Ina ne nan? Ta tambaya gabanta na faduwa Bakiga Hotel aka rubuta ba ko bakya ganewa ne? Wani mugun yawu ta hadiya tace Kaje ni zan jiraka daga nan! Kallonta yayi yace Me yasa kike abu kamar baki waye ba? Muje Karkiyi dare Tsoro sosae cikin idanunta tace............ Shatuuu ♥️ [7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 22 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad I'm so sorry people of shatuuu kingdom.... Labarin haka ya tafi dole haka zaayi. Nasan Kuna son Khulthum amma kui hakuri don't throw me out of the kingdom pleaseeeeeeeeeeeeeee Idanunta a runtse amma ba bacci take ba Sede hawaye da suke zuba daga idanunta, me take ji yau nadama ce? Wadda batada amfani ko kuwa? Mikewa tayi ta dubi wayarta dake gefen pillow dinta, unlocking tayi don duba karfe nawa, it's 1am na dare amma idanunta babu alamar akwai wani abu waishi bacci, yau tana tunanin ta karyata maganar da bahaushe yace Bacci barawo ne! Yau duk satar shi bai isa satarshi ba, baccin ma dama ce kuma samun guri ne amma yau tasan babu Wannan damar babu Wannan gurin. Mikewa tayi ta dubi Amira da A'isha dake bacci sadidan amma ita ya kauracewa idanunta. Gefe daya ta koma ta hada kanta da gwiwarta ta saki kuka a hankali me cin rai amma kasancewar dukka bacci suke me nauyi yasa babu Wanda ya farka. *Some hours ago* Idanunta Cikeda tsoro tace Bangane Abinda kake nufi ba Yusuf, Dan..... Bai bata damar karasa maganar ba ya samu damar hade bakinsu guri guda, cikin nitsuwa yake Bata sensual kiss me tafiyar da hankali da kuma sanya nutsuwa ga wanda ake yiwa. Sede komai is based on nutsuwa da kwanciyar hankali, Khulthum ta rasa duka kokarinta kawai ta kwace kanta sede waye yace mata shi Yusuf din rukon wasa yayi mata. Kuka sosae take tasa hannayenta Baki daya tana dukanshi amma ko gezau baiyi ba, Seda ya nutsu kafin ya sake ta, Yana mata wani Irin duba irin na goggagun yan duniya wanda suka kware a bariki, se lokacin ta lura Baki daya he's not that gentle yusuf she knew wannan Ya koma mata wani iri Wanda batasan ta yadda ma zata muku describing dinshi ba. Meye kike kuka? Is just a kiss Hannushi dake saman kafadarta ta doke, cikin idanu take kallonshi hawaye na bin kuncinta tace Dama ba so na kake ba? Dama yaudara ta kazo yi, jikina kake so? Kallonta yayi ya langwabar da Kai kalar tausayi yace Come-on Baby, zuciyarki da jikinki duk mallakin Khulthum ne kinga don naso abu daya daga cikin ai ke naso. Ki share hawayenki I didn't mean to kinji, mistake ne Babe. Muje na kaiki gida. Rufe fuskarta tayi da palms dinta ta shiga kuka Tana tayi amma Marar sauti, bata san ya takeji a zuciyarta ba amma kunci ne fal a ciki tana ganin tamkar rayuwarta ta tarwatse kenan. Shikam Yusuf pretending kawai yake amma haushinta yakeji fal zuciyarsa, Tana tunanin taci banza ne, karya take ai bani gishiri in baka Manda dan haka definitely se yayi Abinda yayi niyya. Shi da take tambayarshi Dama Baya sonta ne mamaki ta bashi, Bayan bai taba ganin kwayar so cikin idanunta ba se zallar zalama da son abin duniya, Tunda ita son abin duniya take to tabbas zai bi hakan ya karbi abinda yake so. Har kofar gida ya rako ta lokacin goma saura, Seda ya saka ta gyara fuskarta don kar a fahimci wani abu sannan ya kara assuring dinta shi he never mean any harm, kawai sonta ne yake saka yake jin wani mugun feelings akanta wanda tasan idan da so definitely akwai Sha'awa. *Present* Asabar fari tayi sallah sannan ta samu bacci ya dauketa, kasancewar babu inda zataje yasa se karfe goma na safe ta tashi lokacin Mama ce kawai a gidan. Da shirin wanka ta fito ta fara lekawa dakin Mama tace Ina Kwana Mama. Lapiya lau Khulthum, me ya samu idanunki suka kumbura. Kanta tayi saurin juyar wa tana ganin kamar Maman tasan Abinda yayi transpiring tsakaninta da Yusuf. Mmm.... Kin.... Ga... Bacci ne Kanta ta gyada kafin ta bar gurin da hanzari to avoid further questions. Seda ta shirya kafin ta dauki wayarta tana ganin ya kamata ta fadawa Sulaim abinda ya faru, ko ta bata shawara. Sede tana Fara ringing tayi saurin katse kiran saboda tana tunanin me zata fada mata, Bayan sau nawa tana mata fada akan kule kule yanzun ai dariya zatayi mata batasan wannan ba Sulaim bace, ba kowacce kawa ce Sulaim ba she's one among millions, kuma ba zata taba barinta cikin wannan halin ba...... Tunaninta ya katse lokacinda Sulaim tayi returning call din, babu yadda zatayi haka tayi picking Din sede kafin ta kai ga fadin Abu Sulaim din tace Kin kyauta Khulthum ko dan birthday wishes dinnan babu kowa yayi min banda ke. Kai Khulthum ta girgixa Wayyo bestie's birthday ta manta amma taji rashin dadi, cikin lallabawa tace Ayya! I'm sorry Wallahi kaina ke ciwo yanzun tashi na kenan. Ayya Allah ya baki lapiya. Amin..... Happiest birthday dear Murmushi Sulaim tayi tace Thank you.... Kinsan wannan Salim da na baki labarinshi? Kanta ta gyada tace That Arab? Yawwa Kinsan Mamanshi ce Egyptian, babanshi kuma full blood shuwa ne. Shekaranjiya that's ranar da naje Jega yake cemin yasan jega he'll surprise me, dazu wajen 8 na safe naga blinking din location dina kamar ana tracking dina...... Me ya faru? Khulthum ta katse ta idanunta a warwaje, Sulaim ta buga tsaki tace Labari fa nake Baki Kiyi shiru, se nayi saurin kashewa Kinsan ko Mintina ashirin ba'ayi ba Yaya Najib yazo yace nazo nayi bako, I was like waye? Tunda banda AP da kowa kinga jiya birnin kebbi muka wuni, Amma Hajiya tace na wuce Kada na wulakanta mutum. Unbelievable Salim ne Zaune Kan motarshi Yana ta fitarda murmushi. Ya dinga tsokanata wai naji tsoro kar ayi tracking dina. Ya kawomin birthday gifts dinshi. Seda tayi shiru kafin Khulthum tace Amma yayi surprising dinki gaskiya. Amma Sulaim kina sonshi ne? Wani disgusting look ta bawa wayar tamkar tana gaban Khulthum tace Nope he's very charming tsoro yake bani gashi ni inada Ja'afar dina amma kinga Salim dinnan idanunshi ya bude da yawa, Kinsan he tried hugging me seda na dakatar dashi kafin wai missing dina yasa yaji he can't resist. Ikon Allah Shi ne kawai Abinda Khulthum ta iya fada don da zata iya da ta fada mata amma she can't saboda tana jin nauyin maganar. Kinsan halin mazan kenan fa yanzun, kowa slight space yake nema kiga ya kawo miki zancen banza, Na fattake shi shida birthday gift din saboda kada yayi tunanin dan ya bani wani stupid birthday gifts dinsa yana nufin ya siyi jikina kenan. Shiyasa nake ce miki duk wannan su Yusuf din kiyi hankali dasu don idanunshi kawai is telling you he's not a good person kada Kina amsar abin hannunsu Dan naga yanxu ba'a kyauta dan Allah se dan compensation da wani abin. Kede Allah ya kyauta haka. Daga haka suka kara hira sannan sukai sallama, nan Khulthum ta zauna gefen katifar tana tunano zantukan Sulaim, ko dai Abinda take fada gaskiya ne? Ko dai Abinda ya fada karya ne? Amma taga nadama karara cikin idanunshi sannan idan......se kuma ta kasa karasa wancan sentence din don tasan she's deceiving herself. Mama ce ta leko don jin shirun yayi yawa, Tana daga labulen suka hada idanu se Kuwa Khulthum ta Mike da sauri tamkar Marar gaskiya ko dan dama batada gaskiyar ai. Kizo wani na nemanki. Gabanta taji ya fadi Amma haka ta Mike ta dauka hijab wanda ta manta rabon da ta saka shi ta nufi zaure, yaro ne in his mid teens ya mika mata envelope babu bayani ya juya. Itama cikin daki ta koma Don tasan me aikenan Yusuf ne Don kuwa ga kamshin turaren shi na Oud wanda kamar signature dinshi ne a komai nashi ya kama. Tana zazzage envelope din seda gabanta ya fadi sababbin 1000 naira notes ne a Mike basukai bandir ba amma sunfi rabi, da sauri ta kwashe kar wani ya shigo, se karamar takadda yayi rubutu na ban hakuri da sake jadadda mata son da yake mata tareda rokonta ta manta da abinda ya faru jiya............. Shatuuu ♥️ [7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 23 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Where are all the talented and intelligent Writers online? Ina son fadar a little thing about writing, the moment kika dauki pen, phone, Tab ko system with the intention of writing online, To tabbas you've sign your life into seeing love, kindness, gratitudes , Bullshit, Criticism, negativism especially idan Kinyi suna. This is life but one thing you need to tell yourself is how ready I'm to face this challenges? How strong is my threshold to withstand all this? By now it's supposed to be we are All used to abubuwan readers. Sede I'm pleading on behalf of the grateful ones, the righteous ones kada muna hukunta su da laifin wasu, is not right gaskiya. What matters is hakuri and appreciation, always look at the positive side of things not the negative side. _Sor for this I dedicate this page to every writer whether in touch or apart, pick up your pens, phones, tabs and systems and continue writing, perhaps through this we can change even if it's a single life....._ Thank you* Hannunshi rikeda wayarshi kirar Samsung, Yana zaune kan kujera a main parlon gidan yana scrolling through Daily trust application dinshi da yake karanta news, yayi nisa sosae a karatun yaji alamar email ya shigo mishi hakan yasa ya katse don duba Menene. Gyara zamanshi yayi ganin Abinda bai taba tunani ba a Kwana kusa. Shekara daya kenan da ta wuce Mami tasa shi yayi applying wani conference da ake na Barristers annually a Estonia dake Europe. Abin is very educational and Yana bada opportunities sosae amma kafin mutum ya samu se yayi shekaru yana applying amma shiru, to yanzun ga approval email Daga gurinsu na yayi registeraton. Farin ciki sosae ya Mamaye shi da hanzari yayi forwarding email din wa Mami sannan ya kirata yace ta duba. Yana zaune yayi registeraton online kafin ya Mike zuwa dakinshi ya canja Daga jallabiyar jikinshi Zuwa wani brown trouser da shirt baka, agogon da baya taba fita babu ya dakko brown ya daura kan Farar fatar Hannunsa, bude bedside drawer yayi ya ciro passports dinshi Dana Subay'a saboda yaga tafiyar is in 10 days time ne so dole yayi making komai in a snappy kada a samu matsala. Bata nan taje office shi kuwa yau Baki daya babu inda yaje Yana gida shi daya se missing Sulaim da yake, a lissafinshi gobe zata dawo Amma Tunda ta tafi sau biyu kawai sukai waya ranar da ta isa jega, se bayan yayi mata depositing kudi cikin account dinta tace mishi ai taga alert din that's all! Hakan da takeyi Sagar mishi da gwiwa take, Tana nuna bata ma lura da halinda yake ciki ba kenan? Tana nuna ko kadan bata damu ba. A tsarinshi tana dawowa he'll let the bomb out of the shell amma wannan tafiyar ta zame mishi tsaiko amma da zarar ya dawo it's over sede rashin fadar ya zama tarihi Don zai fada ne ko zuciyarshi ta nutsu. Yana ta driving Yana kiyasto idan yace Sulaim I love you! Yadda zatayi yasan zata bude wannan idanun nata masu sake daga mishi hankali, kila ta turo wannan 1cm bakin nata kamar yadda ya saba, she can even cry a sanin da yayiwa Sulaim na shagwaba amma shi so yake tayi smiling wannan brightest smile din Nata da zai bayyanar da wushiryar ta yasa two sided dimples dinta su lotsa.... Se yayi murmushi tamkar abin ya faru ya fara jin tamkar yana yawo cikin cloud ne, ya fara jin wani nishadi Yana ziyartar shi.... That's love! Wayarshi dake kan dash board ce ta Fara ringing, Da sauri ya dakko ta don ya manta a gurin ya aje ga rana. Cikeda girmamawa yace Baba barka da rana Barka ka dai Dan Aminu (shi ne sunan da Baba ke kiranshi kasancewar shi din ya rike shi har rasuwar shi, Baban Sulaim kenan) Baban ya fada Daga Dayan bangaren, kafin ya cigaba da fadin Yanzun na dawo Maminku ke bani daddan labari, mashaa Allah long awaited day has come, Allah yasa ayi a sa'a Seka hanzarta kayi registration ko? Da murmushi Junaid yayi yace Nayi tuntuni yanzun flight nake son booking da Nigerian Airways nida Subay'a. Cikeda gamsuwa yace Hakan yayi kyau, Allah ya jikan Aminu da Fatima. Shi kanshi Junaid yakan tuna inda Daddy Aminu na raye Irin farin cikin da zaiyi saboda kullum zancenshi "Son make me proud inada high expectations a kanka" here he's sede ya bishi da addu'ar kam sannan ya rike amanar Sulaim din, Shiyasa yake ganin auren Sulaim din shi ne Abinda yafi komai muhimmanci. Ya zakuyi da yaran to? Muryar Baba ta katse mishi tunanin da yake, a hankali yace Gobe Sulaim zata dawo jibi ta tafi birnin kudu, idan mukaje daurin Auren se ta dawo ta zauna dasu Ahmad itama lokacin ta koma school kafin mu dawo. Amman Baba ya ka gani? Murmushi Baba yayi yace Hakan yayi, is better ta Fara sabo dasu Tun yanzun. Junaid bai fahimci inda maganar Baba ta dosa ba amma Mami dake gefenshi ta fahimta hakan yasa bayan ya aje wayar sunyi sallama da Junaid tace Baba me last sentence dinka yake nufi? Kallonta yayi yace Zan aurawa Dan Aminu 'yar Aminu! Kanta ta girgixa da tsananin mamakin Baban tace Tace Tana sonshi ne? Ko yace yana sonta ne? Kafada ya dage yace We wait for the time. Ja'afar fa? Ta tambaya Tana karewa Baba kallo Who's more submissive to her love? ********** Tashin shi kenan daga bacci ya sakko kafafunshi Daga gadon shi na alfarma, ya kusan minti biyar a zaune kafin ya Mike tareda Fara rage short din dake jikinshi ya daura towel a kugunshi hakan ya fito da aihnahin structure dinshi, by mere looking kakkarfa ne kuma yana gyming saboda yadda biceps and triceps dinsa suka murde, ga packs dinshi sun fito sosae very prominent, namiji har namiji wanda ko a fuska ka kalleshi Seka kara dubanshi saboda tamkar mace yake don kyau. *Musbahu* kenan dan gwoggo. Yafi awa a toilet kafin ya fito Sanye da blue din bathrobe ya shiga dressing room dinsa inda wani tafkeken wardrobe yake a jibga kaya wanda mutum zai iya shekara ba tareda ya maimaita ba. Wando Baki ya saka da bakar top sannan ya feshe jikinsa da daddan turare kafin ya fito inda ya samu komai in place. Wayarshi ya dauka ya fito parlonshi inda nanma aljannar duniya ce, haka ya zauna kan cushion yana jiran aka kawo mishi breakfast, Yana nan Zaune yayi shiru deep in thought bai kuma san tunanin me yake yiba yaji an turo kofar, cook dinshi ne Hannunsa wayam babu komai. Kasa ya tsugunna ya gaisheshi kafin yace Gwoggo Tace Kaje part dinta, kaida ita zaku yi breakfast. Wata Irin faduwar gaba ta ziyarce shi, Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Me kuma ya kunno kai shidai yasan wa'adin da aka daukar mishi na fito da mata akwai kwakwaran watanni hudu da suka rage. Cikin hanzari Fuskarshi na nuna tashin hankalin da yake ciki ya Mike ya zura wani Gucci slippers ya fita Baki daya Daga sashen. Baison Zuwa part din gwoggo ya dade saboda yawancin cousins dinsa Daga wannan ta tafi wannan tazo suna binshi da admiration look wanda baya so. Ga tsoron gwoggo da yake tun yarinta. Har yanzun tsoronta yake most of the times Yana contemplating ko ita ta haifeshi amma yasan ita ce haka zuciyarta take, a cikin idanun akwai soyayyar amma bazata nuna mishi ba. Mintina biyar suka kaishi part din Nata, dayake he's strict yasa masu musu hidima da hannu yake amsa gaisuwar su. Tana zaune kan sofa wadda take tata ita daya by mistake bazaka taba ganin wani ya zauna a gurin ba se ita daya, gabanta fresh milk ce me dumi cikin mug se yan mata biyu akan kujera suna hira. Gefen kafarta yaje ya zauna Cikeda girmamawa yace Gwoggo barka da safe. Kallonshi tayi sonshi na tsarga mata tace Barka dae, muje muci abinci. Anan yan matan da suka hadu karshe amma ko second glance bai basu ba hasalima a ciki ciki ya amsa musu gaisuwar shima don alfarmar idanun gwoggo ne. Varieties ne kan table din haka cook din gwoggo tazo tayi musu serving kafin suka Fara cin abinci. Shiru har suka gama sannan gwoggo tace Amra zata je booking flight zata koma Indonesia next week ka fita da ita. Tamkar ya daura hannunshi yayi ihu haka yaji amma babu hali, calmly yace Tayi sauri inada board meeting da shareholders dinmu na *TitαΦ Oils* Da sauri Amra ta Mike yarinyar very calm and gentle gata kyakyawa Duk cikin cousins dinsa tana da babban matsayi a gurin shi, na farko 'yar favorite uncle dinshi ce kuma sunan gwoggonshi gare ta, yasan tana sonshi amma bai taba kamata da wani kallonshi ko nuna mishi ba, hasalima Bata Zuwa gidansu se on special occasions ko gwoggo ta matsa. Da zai iya da ya aureta amma idan ya aureta wannan secret din zai bude kowa ya sani is better ya hakura. Ina fata TitαΦ Flours babu matsala don board directors sun kawo min korafi. Kanshi ya gyada yace Akwai gwoggo amma Nayi sorting abin shi yasa ban miki zancen ba. Kanta ta gyada ta kurbi madarar dake gabanta daidai fitowar Amra cikin kyakyawar shiga very decent tayiwa gwoggo sallama sannan tabi bayansa wanda tuni ya fice bayan yayiwa gwoggo sallama. A mota ta tarar dashi gefenshi ta zauna ya tada motar ba tareda ya kalli inda Take ba Balle ta saka ran zai mata magana. Duk yadda zuciyata Ke azalzalata akan tayi mishi magana haka ta danne har suka isa sannan ya ciro kudi daga pocket din motar ya mika mata a dakile kamar bayaso yace When you done Kimin text. Karba tayi don tasan ba'a musu dashi tace Jazakalllahu khairan. Allah ya kyautata rayuwar gwoggo. Baisan ya juyo ya wanke ta da murmushi ba saboda har cikin zuciyarshi tsananin farin ciki yaji ya mamaye shi. Itama yau kam ta tashi da dama murmushin is OK for her haka ta fice daga motar ta barshi Yana mamakin kanshi! **** Takwas daidai na safe jirginsu Sulaim ya sauka kan runway dake cikin international airport of Aminu kano dake cikin birnin Kano ta dabo ci gari! Cikin nitsuwa ta sakko idanunta suna ta zagaye don hango abinda ya addabe ta, ya hanata sakat kwanaki bakwai kadai ba karamar axabtuwa zuciya tayi da rashin ganinshi ba, yanzun ta yadda bawai Yaya ne Junaid ba ta gama concluding cewar sonshi take kuma so me wahalarwa a jiya ta tabbatar da hakan amma taki yadda da hakan tana ganin wani laifin tayi zuciyarta zata hukunta ta da mafi tsaurin laifi shi ne son Junaid tana ganin zuciyarta ta zalunce ta, ta kaita inda zata wulakanta amma tasan Rayuwarta inhar da gaske sonshi take will definitely be shattered. Yana tsaye gefen motarshi, yayi pocketing Hannunsa wani Irin farin ciki yake ji Marar misaltuwa, ji yake tamkar yayi ta dariya kowa yazo yasan halinda yake ciki, it's been long bai sata cikin idanunshi ba. Seda ta gama komai sannan ta fito inda ta hango shi tsaye cikin daruruwan mutane amma ta ganeshi, ga mamakinta wani Irin farin ciki from no where wanda tun kafin barinta kano rabon da ta tsinci kanta a haka, zuciyarta ta bude wani sanyi ya dinga ratsa ta, wata nutsuwa Tana shigarta. Shikenan ta faru ta Kare, zuciyarta is cruel ta cuceta. Inda yake tsaye ya bada baya ta tsaya kamar me koyon magana tace Ya.. Ya. Da sauri ya juyo saboda muryar da yaji ta ratsa shi da yawa, idanunshi ya sauke Kan fuskar ta dake sunkuye yace Auta sannu da zuwa Wai Auta? Karo na farko taji haushin sunan at least he should address her with Sulaim amma auta is so casual Haba. Ranta a bace tace Yawwa. Daga haka ta zagaya gefenshi ta shiga yafi five minutes Yana kallonta tareda mamakin me ya bata mata rai suddenly haka? Ko ganinshi ne ya bata mata ranta. Kanshi ya gyada rai a jagule ya tada motar. Suka bar premises din gurin shirun da yayi yawa yasa yayi turning radio station suna shirin Barka da Hantsi a Freedom radio. Se time to time yakan tambayeta yadda ta Baro kowa shima answers dinta a takaice suke hakan yasa ya kyaleta ko missing can din take. Suna isa gida yana parking ta fito tare da dubanshi tace Thank you. Kallonta kawai yayi a ranshi Yana mamakin wannan halittar. Tunda ta shiga daki bata kara fitowa ba ko abinci bata bi ta kanshi ba shikam ya fice yana ta kokarin kammalla shirin tafiya Estonia. _Anytime you lonely can I be the one you calling? I hope you understand? Please take my hands and go with me my love_ ** Kwanaki takwas cif Tunda aka samu matsala tsakanin Khulthum da Yusuf, guess what? Idan akace Kai kwadayye ne an gama, the worst thing a duniya shi ne ka Bari makiyinka yasan weaknesses dinka Khulthum ta bari Yusuf ya sani don haka kwanakin ya karar dasu wajen kashe mata kudi, wajen nuna mata ita din masoyiyarshi ce kuma ya nuna mata jikinta ba shi ne a gabanshi ba kafin wani Lokaci sun dinke Duk Wannan nadamar tayi evaporating into the clouds. Ta koma sabuwar Khulthum wadda take jin da ba rayuwa take ba yanzun takeyi. La'asar sakaliya, yamma har ta Fara yi suka iso cikin motar Yusuf ta mishi rakiya wani guri, tayi kyau cikin pencil skirt da long sleeve top matching da takalminta. Tayi kyau taji ta tayi fitting da mutanen da ta samu a gurin saboda yawancinsu Irin shigar ce a jikinsu se wanda tasu tafi nata watsewa, kanta scarf ne me Dan girma ta daura wrap me kyau akanta, Yana parking ta wareshi tayi rolling amma dukda haka nayi tunanin ya akai Mama ta barta ta fito a haka? Hannunta ya Kama yayi kissing wanda yasa taji electrons suna passing jikinta. Dagowa tayi bata hanashi ba se murmushi da ta sakar mishi. Hannunta ya saki yace Se gobe kenan? Kanta ta gyada tace I'll miss you Ko? Ya fada Yana kashe mata ido, murmushin tayi na assurance ta fito rikeda nylon da karamar handbag dinta, yadda take tafiya kamar chameleon tana Kada jiki kamar wadda take fadawa mazan gurin look at me. Tana ji suna ihun da suka saba amma ko kallonsuu Batayi ba. Sede me tana zuwa ta tarar Ashir yana tsaye tamkar jiranta yake. Gabanta seda ya fadi Amma ta dake taci mazu zata wuce ta gaban shi kawai taga yayi blocking hanyar, dago idonta tayi ta watsa mishi kallo me Cikeda kaskanci Tace Bani hanya! Bai taba mata kaskantaccen kallo ba me Cikeda tsantsani ba se ranar yace Nayi da na sanin furta kalmar so gareki, naji kunyar tunanin Baki matsayin uwar 'ya'yana, Nayi asarar Bata Lokaci na gurinki...... Dakata Ashiru ko whatever your name is! Kayi kadan ka cimin mutunci saboda wata useless 20,000 dinka da kake tunanin ta siya maka ni! Allah ya kiyaye. Nima na fika bakin cikin tarayya da kai abun kunya na tsaya da bai not knowing dubannin mazan dake waje suna jirana.... Hopeless element kawai!! Tana gama fadar haka ta balle Jakarta............ Shatuuu ♥️ [7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 24 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad .....Ta Balle Jakarta wadda a ciki kudi ne da ya tasarwa 50k, cikin fushi ta irgo 20k ta zura mishi cikin aljihun gaban shaddar dake jikinshi sannan tace Ga tsiyar ka nan, ga kudinka da Kake tunanin ka siye ni dashi, aje can me tsautsayi ta dauka amma banda ni Ummu_Khulthum na wuce ajinka Wallahi. Tana gama fadar haka ta buga mishi kallon wulakanci sannan ta wuce ciki abinta, kallonta yake tayi bakinshi a bude tamkar statue haka ya zama a tsayen yana tunanin da gaske Khulthum ce? Da gaske? Shi ne abinda ya samu bayan shekarun da ya dauka zaman jiranta, Yana dakon sayayyarta. Tabbas kowa ka kalleshi ka barshi kawae. Zan iya ce muku Wannan shi ne mafarin lalacewar rayuwar Khulthum, that's what makes Khulthum what she was a halin yanzu amma ko yaya kuma kome Khulthum ta zama ita ce sanadi. Cikin gida ta shiga tana jin tamkar ta taka Arfa tana jin ta yakice kwallon mangwaro, Tana jin Duk duniya she's free. Kowa harkarshi yake hakan yasa ta shige daki ta Adana kudaden sannan ta cire kayanta ta zauna itada zani se vest Tana kallon film cikin system.... Ni dai nasan Khulthum batada system amma bansan inda ta samu ba. Tana nan kwance ta jiyo muryar Baba yana kwallawa Mama kira. Tsaki tayi a ranta tana fadin na tsani gidannan kayi aurenka babu ruwanka da hayaniyar nan. Bata Kara jin duriyar Baba ba se bayan 10 minutes sannan taji salatin Mama tana fadin Amma yarinyar nan anyi 'yar banza. Khulthum! Khulthum!! Khulthum!!! A hankali ta Mike Tana mitar kiran da ake mata kamar wadda tayi sata kuma Bama haka ba ita batai tunanin cewar abinda ya faru tsakaninta da Ashir zai iya shigowa gidan da wuri har hakaba. Fitowa tayi ta yafa dan karamin mayafin abaya Tunda taji muryar Baba, suna tsaye tamkar zakaru itama taje ta tsaya tana binsu da kallo Dan ubanki me kika yiwa yaron can Ashiru? Kallon Mama tayi ta kalli Baba Wanda fuskar ta kasa boye damuwar da yake ciki tace Shi ne ake ta kwalla min kira kamar nayi wani laifin. Mama wadda zuciyarta na wuya tasa hannunta ta bige bakin Khulthum tace Mu sa'anunki ne kike mayar mana da magana? Uban me kika yiwa bawan Allah nan. Tsaki tayi a ranta tace ni kuma bawan shedan kenan? Dauke kanta tayi hakan yasa Mama tayo kanta zata buge ta Baba yace Karki taba ta, khaltume zauna. Babu musu ta zauna kamar yadda yasa Mama ta zauna shima hakan yayi kafin ya gyara muryarshi yace Ina saurareki Baba bana son shi, nace mishi ya rabu dani yaki saboda kamar zargina yake kuma yayi tayimin gori...... Shi ne kika maida masa Dubu ashirin dinshi? Mama ta katse ta, Baba ne yace Maman Aisha Kada ki Kara magana se na baki izinin yin hakan, ke khaltume kikace bakya son shi? Kanta ta gyada batareda ta furta komai ba, kai Baba ya jinjina yace Lokacinda kika kawo Ashiru a matsayin me nemanki, ke Kika karbi kudinshi ko ni? Kai ne Yayi kyau, me yasa yanzun kika bashi Bayan Baki sanar dani ba, karamin mutum kike son maidani? Bakinta ta turo a ranta tace wai karamin mutum? Shi babba ne Dama? Talaka futuk se shegen policy na banza da na wofi! Ganin haka yasa Baba ya gyada Kai tareda ciro sababbin 1000 naira notes guda ashirin ya mikawa Khulthum yace Ga kudinki nan na mayar mishi da nashi, Amma ki sani kin nuna min ni ba ubanki bane kuma duk Abinda zai faru dake hannuna bazan kuma sawa a ciki ba. Ke kuma Maman Aisha Ya juya kan Mama Ya cigaba da fadin 'yar ki ce na tsame hannuna daga kanta, Duk wani abinta kukai wa dangin mahaifinta. Haba Malam! Haba Kanshi ya girgixa yace Ki bar maganar kawai. Aisha! Dama tana kusa se gata ta fito ta tsugunna gefen Khulthum wadda Tana ta Harare Harare a ranta tana ayyana taji dadi da me yake mata zai zo Yana kumfar baki kamar ubanta, ita Wallahi tun tuni take son komawa dangin ubanta me take tsinta anan? Banda wahalarsu da aka daura mata. Zancen da Baba yake Yi ne ya saka ta dawo hayyacinta .......Daga yau inhar kin daukeni mahaifi inason duk lokacinda Ashiru ya shirya ki aureshi, don na Karba kudin 'yar uwarki na maida kanki. Mama ce tayi saurin fadin Haba Malam, ya zaayi haka? Idan Khulthum a bacin rai ne fa tana son abinta fa? Mamaki kwance saman fuskar Baba yace Dama na dade da sanin haka, khaltume a gurinki ita kadai ce 'Ya , na miki uzuri saboda haka dan fari yake amma son kan naki yayi yawa. Ki sani na Bata dama don haka A'isha ki sawa ranki bakida miji se Ashir sede idan wani cikinku ne ya mutu ko kaddarar rayuwa! Mikewa yayi Don ficewa Khulthum tayi saurin mikewa tace Basai an nuna min cewar banida uba ba, basai an nuna ni agola bace Aisha ita ce yar masu gida, idan da kara kwarton uwa ai uba ne, naki abu sannan abawa Aisha shi ba? Da idan kunsan yar ku kuke son ya aura meye abin labe...... Ke amma 'yar iska ce, Baban kike fadawa haka saboda bakida mutunci? Amir ya fada wanda Shigowarshi kenan yaji diban albarkan da Khulthum take musu. Juyowa tayi ta kalleshi tace Nayi din kuyi abinda zakui, Dan rashin mutunci..... Bata karasa ba saboda yadda Amir yayo kanta tamkar zaki sede bai Kai ga yin abinda yayi niyya ba Baba ya dakatar dashi tareda fadin Kyaleta, batada laifi. Uwarku ce me laifi don haka ko na fita kada wanda ya kulata. Allah yayi muku albarka. Yana fadar haka ya sa kanshi ya fito, Mama daki ta wuce tunda ba Abinda zatace kuma a ganinta Baba yaso kanshi ne da yawa. Cikin makeken office dinshi na Managing Director of TitαΦ Flours Yana zaune kan kujerar yana rocking kanshi, Kwana biu nan bashida nutsuwa sosae ya rasa inda zai saka ranshi yaji dadi. Knocking yaji yasan bazai wuce secretary dinshi ba hakan yasa ya bada izinin shigowa, Sir, Kabir is here Let him in Ya fada batareda ya dago ba, ba'a fi 3 minutes ba Sega Kabir ya turo kofar ya shigo, Yana ganinshi ya Mike suka dawo kan cushion din office Bayan sun gaisa aka kawo musu coffee, Seda suka shanye tas kafin Kabir yace Akwai wani move ne? Naga Kwana biu kamar kana da damuwa. Tsaki Musbahu yayi yace Ba kamar bane ina da ita, kana ji ko Amra zan aura ne? Cikin rashin fahimta Kabir yace Amra? Kada Kace min 'yar Baba Balarabe Ita dai! Cikeda mamaki da kuma takaicin maganar Musbahu Kabir yace Amma me TitαΦ ka samu matsala, ina tunanin ka yaje har zakai tunanin Auren Amra? Then Jeka fadawa gwoggo me kakeyi mana. To ya zanyi Kabir? Gwoggo is insisting! Ya fada Yana dafe kanshi, shi ya rasa Wannan masifar na se yayi aure? Shi yace baya so to me ye ne matsalar mutane. Maslaha mu nemi Yarinya Marar gata wadda ko tayi kuka babu me damuwa ka aura, amma Amra Tana da gata bazata taba jurar zama da kai ba. To fa! Kunji wata sabuwar. Wanene Musbahu? Meye yake boyewa? Me yasa bayason aure? Lokaci daya Junaid da Subay'a suka dawo gida, kowannensu basai yayi maka bayanin gajiyar da yayi ba a kwance take a saman fuskarsu. Suna shigowa kowa ya shige part dinshi se takwas sannan suka hadu duka parlor, Junaid na koyawa Ahmad homework ita kuma Subay'a Tana surfing internet a system dinta. Sulaim dama bata fito ba Tunda ta dawo Tana dakinta dukda taji hayaniyar sun amma tana ganin Lokaci yayi da zata nisanta kanta daga Junaid Tunda har zuciyarta tayi gangancin sonshi. Ganganci ne mana Tunda tana son abinda bazata samu ba, Abinda is beyond level dinta. Da hanzari Junaid ya Mike jin sallamar Jabir da Imratu, Jabir a gaba Imratu na bayanshi suka shigo har cikin parlon sede fuskar Junaid kamar zata yage saboda murmushi Yana son a kawo mishi ziyara sosae yake jin dadi amma yasan halin Subay'a ke sawa yan uwanshi Suki Zuwa. Kan 2 seater suka zauna Ahmad tuni ya bar homework din yayiwa kansa mazauni cinyar Daddy (kamar yadda suke cema Jabir) shi kuma Muhammad ya sauka Daga cinyar Subay'a ya koma kan Imratu wadda se caressing dinshi take a ranta tana addu'ar samun nata na kanta. Imratu ce ta Fara fadin Yaya ina yini. Da murmushi ya amsa sannan suka gaisa da Subay'a suna tambayar juna aiki kafin kuma Jabir suka Fara hira dukansu, Subay'a ta kwalla kiran Atika Bata karasa fada ba ta fito dauke da plate da bowls, seda ta aje Kan dining sannan ta iso ta gaisheda su Jabir kafin tace Gani Bakiji anyi baki ba, kiyi setting table mana. Dan Dukar da kanta tayi Cikeda ladabi tace Ina shirin fito da abincin kuma naji shigowarsu shi ne muke kara wani dish din amma yanzu zan kawo. Tsaki tayi ta cigaba da Abinda take itakuma Atika ta koma kitchen ranta a bace kwatakwata Subay'a batada dadin zama sudai adduar su daya Abinda suke tunani tsakanin Sulaim Da Junaid ya kasance. Imratu ta dubi Subay'a Tace Maman Ahmad ina Sulaim ko bata dawo ba. Dagowa tayi tace Bansani ba ko ta dawo, ban dai ganta ba. Kanshi ya girgixa Jabir sannan Junaid yace Ahmad kirawo Anty a daki. A guje ya nufi dakinta lokacin ta gama sallar ishai amma bata tashi akan carpet din ba Ahmad ya shigo yace Papa yace.... Kafin ya karasa tace Kace ina zuwa. Seda ta bata Mintina kafin ta Mike ta nade Sallayar ta cire Hijabin da abayar sallar sannan ta yafo mayafi Kan baggy skirt din jikinta da faffadar top, kanta cikin hula ta saka kalar skirt din ta fito bakinta dauke da sallama wadda take a ciki ciki. Kamshin turaren ta na Zahrat Banafsat ya fara mishi sallama, aikuwan shi ya fara juyawa ya bita da ido har ta shigo parlour fuskarta babu annuri ko digo, sede idanunta sun kasa jurar rashin kallonshi, zuciya Tana tuhumarta why zata yi shakalatun Bangaro ma abinda zuciyar ke so _I love you... Please say you love me too... This three words they could change our lives forever and I promise you that we'll always be together. Till the end of time!_ Dagowa tayi ta dubi inda ya kafe ta da idanu ya manta da kowa a gurin, kawai se taji kamar ana zare mata damuwar dake cikin zuciyarta, har batasan ta sakar mishi murmushi ba seda ya mayar mata martani, se Jabir yayi gyaran murya wanda ya dawo dasu hayyacinsu. Jabir ya kwashe da dariya tareda kallon Subay'a wadda take deep a abinda take. Shatuuu ♥️ [7/29, 6:16 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 25 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Dariyar da Jabir yayi yasa Junaid ya kalleshi da sauri, Subay'a ta dago, Imratu ta dubi mijinta tana mishi kallon kaima ka gani? don kuwa Tunda Sulaim ta fito take Lura dasu har wannan flashy smile din da sukayiwa juna. Sulaim kam tuni ta isa jikin Imratu ta rungume ta tana fadin Fushi nakeyi daku har Yayan ma. Dagota Imratu tayi tace Kya yi mu bamuyi fushi ba se ke? Bakinta ta turo Irin nayi fushi ta dubi Junaid Yaya kace su bani hakuri. Baki sake Subay'a take kallon shagwabar da yarinyar ke yiwa mijinta. Gyara zamanshi yayi yace Ku bata hakuri yanzunnan. Me Jabir zaiyi idan ba dariya ba, tabbas ana abu cikin gidannan. Subay'a mikewa tayi kamar zata tashi sama ta wuce kitchen nan da nan suka hada baki wajen fadin Afuwan! Are you OK? Ya fada Yana mata kallo me Cikeda kulawa, kanta ta gyada Imratu ta bugi bayanta mamaki fal fuskarta. A table kowa maida hankali yayi kan cin abinci dukda ana exchanging glance Lokaci Lokaci tsakanin Junaid da Sulaim. Tabbas kafin ka samu careless wife irin Subay'a zaka dade Duk Wannan Abinda ake hankalinta baya kansu tana can tana tunanin maganar da hajiya tayi mata dazun dasuka hadu da safe. Ta rasa ta ina zata bullowa ala'lamarin gashi bata san dago maganar Tunda har yayi mata maganar zuwa Estonia tana ganin zata Bari su dawo se ta tunkareshi taji! Parlon Junaid Jabir dashi suka kebe don zantawa kasancewar sun jima basu hadu ba, yayinda Subay'a ta koma dakinta, Imratu da Sulaim suka wuce dakin Sulaim din. Hira sosae suke tsakanin su kasancewar ba karamin sabo bane tsakanin biyun. Suna hira Sulaim na harhada kayan da zatayi amfani dashi a Birnin kudu Don Junaid ya sanar mata tareda su Yaya Jabir zata wuce suma can din zasuje , wata katon gift ta dakko anyi wrapping da farin sheet se kyalli yake, Imratu tace Wannan fa? Jujjuya shi tayi tace Sakon Yaya Ja'afar ne, Yaya Hanan ta bayar a bashi. Kai ta gyada ta bi Sulaim din da kallo a ranta tana tunanin Sulaim batasan tsakanin Hanan da Ja'afar ba kenan? Kasancewar ita ba mai shiga abinda babu ruwanta bane yasa ta kauda tunanin da take dole wata Rana komai Zai bayyana amma bata taba yiwa Sulaim shaawar auren Ja'afar ba, kwatakwata he's not a Man, idanunshi baya zama Kan mace daya. Idan banda zalama da kuma iskancin Ja'afar Tunda har hankalinta yana kanshi Bata tunanin ta cancanci hakan. Sede bata sani ba yau Abinda idanunta suka hango yana faruwa tsakanin Junaid da Sulaim ko idanunta ne ko kuma gaske ne? Abu daya ta sani time will tell! Da murmushi saman fuskar Jabir ya dubi Junaid wanda hankalinshi na kan Jabir din yace Bros Kana son Sulaim ne? Baiyi mamaki ba saboda yanzun son Sulaim nema yake ya maida shi rago, nema yake yasashi ya zama desperate and Babban abin Yana ganin idan ya cigaba da kauran baki to zai iya furtawa gaban Subay'a ba kuma zai taba son hakan ya faru ba at least Subay'a matarshi ce, first love dinshi bazai taba wulakanta ta ba Sede idan ita ta wulakanta kanta kamar yadda suke yanzun. Kana son sani ne ko confirming Kake son Yi? Junaid ya tambaya Fuskarshi dauke da murmushi, shima murmushi yayi yace Confirmation ne. Then is true, I love her! Babu mamaki a Fuskarshi se wani farin ciki da at once ya lullubeshi yace Amma naji dadi, Baban Sulaim zai auri Sulaim itama Naga kamar tana ciki, a ina kuke? Kanshi ya shafa Lokaci daya murmushin ya dauke dif se kamar fear da wani abu da shi Jabir din ya kasa karatowa Junaid yace Ba ta sani ba, ban fada mata ba. Why? Waiting for what? I dunno Jabir, banda courage din. Haba Bro, Sulaim ce fa, your Sulaim ita ce Kake tsoro? Ni zan fada mata da kaina Da sauri ya girgixa kanshi yace No please! I promise ina dawowa daga Estonia I'll let the word out Inshaaa Allah. Yasan Junaid baya magana biyu su kuma bazasu taba barin such a golden opportunity ya wucesu ba, dama bai kamata ace bare ya auri Sulaimi ba Tunda basu san wani hannun zasu mika ta ba. Hira cikin nishadi sukai dukda Jabir se zolayar Junaid yake akaan Sulaim. Abin gwanin shaawa don bazakai tunanin cewar brothers bane sunfi Kama da abokai. Wajen goma Jabir ya dubi Junaid yace Bari mu wuce ko room bamui booking ba. Cikin rashin fahimta Junaid yace Kana nufin hotel zakuje, already an gyara wancan dakunan, idan baiyi maka ba se ku zauna anan. Babu yadda Jabir ya iya haka suka koma part din dake gefe don dama don haka aka tanadi gurin. Wallahi yau ba se gobe ba Seka fada min Abinda Ke tsakaninka da waccen yarinyar. Subay'a ta fada idanunta taf da hawaye, Haba ta gaji bazata iya ba, kowa daukarta yake shashasha a gidanta mijinta na son wata. Kallonta yayi yaga yadda take tada jijiyoyin wuya amma tausayinta yakeji kuma for Sulaims safety yasa bai kulata ba ya cigaba da Abinda yake cikin system. Gefenshi ta matso tareda kawar da system din daga gabanshi ta Maye gurbin tace Wallahi se ka fada min Junaid kaji na rantse. Idanunta na digar da hawaye da Lokaci daya sukai nasarar wanke mata fuska, abin ya fara kaishi Anty bango amma baisan bacin rai yasa yayi Abinda zai yi Dana sani daga baya yasa ya Mike don zuwa cikin bedroom dinshi, Sede kamar wata zakanya ta rigashi isa gurin tareda blocking hanyar tace Ai kaji abinda nace, babu inda xakaje se ka fadamin. Dagowa yayi ya dubeta, se kuka take kamar wadda akaiwa mutuwa Amma yadda take abin ransa ya baci hakan yasa yace You want to know right? OK! Son ta nake kamar yadda kike zargi kuma aurenta zanyi. Is that all? Lokaci daya numfashinta ya fara fita cikin sauri sauri tamkar wadda tayi gudun marathon. A gigice Subay'a ta farka daga wannan mummunan mafarkin, hannunta ta kai ta kunna bedside lamp din Lokaci daya haske ya gauraye dakin, idanunta suka sauka kan Junaid dake zaune kan carpet ya kura mata idanu, itama kallonshi take hawaye wani na bin wani dukkan jikinta na rawa wanda hakan ya tabbatar masa mummunan mafarki tayi! Hannunshi ya mika mata babu musu ta zura nata tareda sakkowa ta lafe jikinshi kukanta na Kara karuwa jinta jikinshi, Baki daya tashin hankali da tsoro suka addabe ta, Tana son tambayarshi ko Abinda ya fada mata cikin mafarki gaske ne sede tana gujewa kunnenta mugun ji. Cikin sassanyar murya yace Yana shafa gashinta wanda ya bayyana sakamaakon hular da tayi nata gurin har Zuwa bayanta You had a nightmare? Kanta ta gyada tana sake bawa hawayen idanunta damar zuba freely. Gogesu yayi da tafukan hannayenshi yace Ya isa haka, Bakiji you're safe ba kina arms dina just pray ko zaki fadamin? Da sauri ta girgixa mishi kanta hakan yasa ya rabu da ita, daga karshe da kukan ya lafa ya jata suka koma gado batareda ya karasa tsayuwarshi ba. Da kyar bacci ya dauki Subay'a saboda ta kasa manta mafarkin. Washegari Tunda suka tashi ta Fara bashi wata care wadda ko lokacin farkon aurenshi ban tunanin an bashi, haka shima saboda Kwana tayi da zazzabi Shiyasa tausayinta kawai yakeji. Tare sukai wanka ta shirya shi sannan ta shirya kanta kafin ta fito don ganin yaranta. Tana fitowa sukai kicibis da Sulaim wadda take kokarin komawa dakinta. Kallo ta bita dashi gabanta na faduwa kamar zai balla kirjinta Don fargaba, tsana Sulaim ta mata dirar mikiya Sede ita Sulaim din bata ma lura da halinda Subay'a ke ciki ba hasalima tana gaisheta ta wuce dakinta zuciyarta a cunkushe tana ganin kamar ita din tsaiko ce tsakaninta da Junaid din. Tare sukai breakfast gaba dayansu, kasancewar Junaid na ganin har lokancin Subay'a bata ware daga firgicin mafarkin jiya ba yasa yake nan nan da ita, motsi tayi kwakwara zaice Are you OK Dear? Hohohoho? Hakan da yayi ba karamin Sosa ran Sulaim yayi ba, itakuma Subay'a kamar ta zuba ruwa kasa Tasha. Can ana tsaka da cin abinci mistakenly Subay'a ta kware cikin hanzarta Junaid ya balle murfin bottle water dake gefenshi Don ka'idar shi ce shan ruwa after breakfast, da kanshi ya kafa mata a baki Wanda idanun Sulaim sukai kir Akansu, zuciyarta ta buga da sauri kuma ta janye idanunta tareda daukar spoon sede tana dibar abincin hannunta ya kifar dashi saboda rawar da yake, Jabir ne ya gyara murya yace Sulaim are you OK? Se lokacin Junaid ya dubeta idanunta sun cika taf da hawaye kadan suke jira sui splitting mata a fuska. Meye ke damunki? Junaid shima ya tambaya amma se ta dauke kanta daga kallonshi Tace da Jabir Na koshi. Then jeki karasa shiri muna gamawa zamu wuce. Da sauri ta Mike har tana tuntube ta nufi dakinta, baki daya suka bita da ido Subay'a na mata rakiya da harara, she hate the girl that is just the fact! Tara na safe suka fito baki dayansu a gefen mota, ita Subay'a tuntuni ta fice itama yaran dake Muhammad ma an kaishi kingdergaten, Tunda ta fito ya lura fushi take wanda ya rasa dalilin da yasa Sulaim Keda saurin fushi haka to shi bai masan ko me akai mata ba amma dukda haka kallonta yayi tana kokarin bude bayan motar yace Sulaim. Ko tana so ko bata so dole ne ta juya Don kuwa zuciyar ta bazata yafe mata ba matsawar taki yin hakan. Cikin ido suke kallon juna kowa nutsuwarsa na dawo mishi, tayi saurin dauke kanta ta sunkuyar tana mitar abinda yasa take kallonshi, envelope ya mika mata yace Se Saturday. Amsa tayi ta mishi godiya sannan ta shiga ciki Jabir Yana kallonsu yana murmushi sannan sukai sallama sannan suka dau hanyar. Awanni biyu cif ya kaisu gurin Birnin kudu, gaba daya Sulaim a gajiye take sosae kamar dukanta akaI sauki daya ta sha bacci wanda da wannan damar Imratu ta samu itada Jabir ya tsegunta mata abinda Ke faruwa. Itama farin ciki sosae tayi amma tana ganin yadda zaayi da Subay'a. Kwananta uku a Birnin kudu Mami, Baba, Jawad da oga Ja'afar suka iso, wannan kwanaki uku babu Daren da Batayi kuka ba saboda yadda zuciyarta Ke axabtuwa da rashin Junaid a Rayuwarta, baki daya tayi mamaki yadda Lokaci daya soyayyar Junaid take neman farautar farin cikin ta. Duk yadda take cikin dangi anata shirin biki Amma ita abin baya burgeta ko daya hasalima kullum tana dakin Neneh kamar yadda ake kiran kakarsu, Mama Sauda da kullum Se taxo gidan tayi fadan har ta gaji, Sulaim ce kadai tasan Abinda Ke damunta ita kadai tasan kuncin da zuciyar ta ke ciki. Ranar Sulaim murna gata ga Mami duk inda Mami zataje Sulaim Tana bayanta Mama Sauda ta dinga mata tsiya wai makon uwa ne da ita itakam sede dariya. Da daddare babu kowa parlor kowa na dakinshi Sulaim ta fito da gifts din, wayarta a kunnenta tana kiranshi Ja'afar don ya karba, Luff ina parlon kasa kazo. On my way Sweetm. Baifi 5 minutes ba ya fito cikin 3 quarter jeans da top armless, Baki daya ta bayyanar da damtsen shi dake a murde saboda gyming. Zama tayi akan carpet shima ya zauna gefen ta Yana kallonta yace What do we have. Me zance tsautsayi? Ko kuma karar Kwana? Sulaim Bata bashi amsa ba ta farke wrapping sheet din tace Yaya Hanan tace na kawo maka. Cikin sauri ya kai hannunshi don kwatar komai Amma it was late don ta riga tayi tozali da rose flowers biyu, turare amma Abinda yafi daukar hankalinta shi ne wani kyakyawan frame me rubutu kamar haka _When you are in love, the heart works faster than the brain, without the brain the body survives but when the heart fails the body dies! You're my heart and I love you!- Dago idonta tayi tana kallonshi kamar yadda shima kallonta yake ba tareda yasan abin yi ba......... Shatuuu ♥️*MACE A YAU* 26 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Halo people of *SHATUUU's KINGDOM and MAMAN MAMA NOVELS* Double hey! Triple godiya for the love and everything I'm very happy having u guys as my Buddies 😘 *A broken heart can be pieced back together, it might be a heart again but it's still a BROKEN HEART* Shima cikin idanu yake kallonta kamar yadda take kallonshi mamaki karara saman fuskarta. Sulaim lemme explain. Wani kallo ta watsa mishi wanda a take yasa shi rufe bakinshi Wanda DA ya bude da niyyar sake wani protest din amma kallon da tayi mishi yasa ya hadiye maganar tashi, mikewa tayi daga zaunen da take har lokacin hannunta na rike da frame din, kallonshi kawai take da idanunta da suke cike taf da hawaye Wanda by mistake tayi magana to tabbas zasu zubo, wata Irin bugawa zuciyarta take, wani Irin ciwo take ji kirjinta nayi mata, frame din ta doka da kasa akan tanganyar tiles babu jira glass din gaban ya tawarwatse, perf din ta dauka shima ta buga da bangon parlon sannan ta toshe bakinta da hannunta dan kuka ne ya taho mata tun karfi, then komai ya kare kenan her only hope ja'afar bai daina kule kule ba bayan ample of chances da ta bashi, zuciyata data mika mashi that's the pay back daya bata. Ga zuciyarta mayaudariya, macucia, azzaluma data zalunce ta take son Junaid wanda baisan abinda take ciki ba, take hawaye ya balle mata babu waiwaye ta nufi staircase a million don tana bukatar break, me tayi haka da tayi deserving such treatment? Me tayi. _Call the man who deals in love beyond repair, he can heal the world of heart in need of care... Shine the light ahead when the next step is unclear....._ Jaafar na tsaye tamkar an dasa shi akan kafafuwanshi haka ya tsaya yana kallonta, ya kasa furta komai na kare kai saboda yadda idanun sulaim suke ko shi waye bazata saurareahi ba, to shima bashida abin fada sede idan karyar da ya saba zai mata. Jagwab ya zauna kan kujera tareda buga tagumi ya rasa abinda yake ji Yafi Mintina goma kafin Zuciyarshi tace mata nawa ke binka kana dodging? Mata nawa kuke soyayya dasu?don kwaya daya tace batayi shi ne abin damuwa? Abin daga hankali?kanshi ya girgiza ya mike yana daga kafadarshi irin ko a kwalar rigarshi but deep down him yasan he missed an angel Don ko ya yarda ko yayi denying Sulaim is still Sulaim. Sede yana ganin tayi kadan ta juya shi kuma yasan son da take mishi ba zata jure been away from him! Se muce tunanin Ja'afar kenan ba namu ba! Ko ba haka ba Shatuuu's kingdom and Maman mama people? Mami Zaune Kan kujera a parlonta se Jabir da Imratu dake gefe, Jawad na kan carpet yana cin abinci Se Subay'a da Junaid wanda zuwansu kenan kasancewar very late ya tashi a office Shiyasa basu zo da wuri ba kuma Mami tace lallai ya bar Duk Abinda suke shi har da Subay'a din su taho, yaran babu yadda Junaid bai yi ba akan su taho tare se cewa tayi wai sauro jigawa yaran bazasu iya coping ba zata kaisu gurin Sulma. Maganar ta bugeshi saboda yana tsananin son jigawa, Yana son mahaifarshi bai son wani ya karce su amma baya son magana hakan yasa baice da ita komai ba ita kuma gani take tamkar she won the medal and lottery! Mami ta dubi Mama Saude dake gefenta tace Nikam Maman Nusaiba ya akai har Sulaim tayi kwanaki hudu amma bataje gidan Engineer da Zunnuraini ba. Dazu wajen daurn aure sukewa general complain. Tabe Baki tayi tace Tunda Taxo se jiya Naga ta ware, bansan abinda yake damunta ba amma akwai damuwa a tattare da ita hakan yasa na kyalle ta. Kai Mami ta dafe don ta lura da hakan kuma ko yau da safe Seda ta tambayeta da ta sameta tana kuka a daki Amma se tace babu komai dama tana jiran Junaid yazo ne taji abinda Ke samun 'yar gidan nashi. Kallonshi tayi tace Junaid kaji da kunnenka ni na rasa yadda zan bulo mata bansan me take so ba. Subay'a ta tsirawa Mami idanu don yadda ta ji zancen Mamin banbarakwai, ita bazata lallaahe ta ba se mijinta? Lallai wannan rainin hankali ne ma. Junaid ya dago idanunshi ya rasa me zaice shima yana bukatar kulawar sede Lokaci daya hankalinshi ya koma kan Sulaim din so yake Yaji damuwarta. Imratu kira min Sulaim. Tohm Mami Ta fada Tana mikewa yayinda suka cigaba da tattaunawa Sede baki daya hankalin Junaid din ya koma kan Sulaim, me ke damunta? Meye matsalar ta? Bakinta kadai amsar take hakan yasa hankalinshi rabuwa kashi kashi gashi Imratun is staying longer than expected kusan Mintina goma sun wuce Bata dawo ba. Mami kizo Yaji muryar Imratun ta katse mishi tunanin da yake, ya manta Subay'a na gurin ma yace Me ya faru? Mami mikewa tayi tabi Bayan Imratun, Junaid da Mama da Jabir Harda Jawad suka bi bayansu ya rage Subay'a kawai wadda ta kasa digesting abinda kwakwalwar kanta ke karanta mata. Tana kwance tayi rub da ciki, ta nutsa kanta cikin pillow tana ta kuka bawai Marar sauti ba ba kuma me kara Ba amma kana shigowa xakaji sheahekar shi, Mami ce ta Fara isa gefenta ta dago ta tareda fadin Sulaim Menene? Me zatace mata for all this while your son who happens to be a monster ya yaudareni ko kuma ina cikin muguwar azababben son babban danki..... Kai life is unfair a ganinta, Wanda kake so baisan Kanayi ba, Wanda Kake da hope akanshi ya debo kasa ya bula maka cikin ido, to ya zatayi? Babu wani dalili da zaisa taji rayuwar ta da dadi .....that's emphatic NO! Kankame Mami tayi ta Kara sakin kuka Wanda fitarshi ba sauki bane se radadi da takeji cikin zuciyar ta, inama inama ana cire so a yar tabbas da tuni ta cire na Junaid ta yar dashi Amma hakan is impossible. Washegari an gama biki baki daya ita Sulaim da Ciwon Kai ta tashi wanda da kyar take iya budesu saboda yadda suka kumbura suka mata nauyi na gaske... Wa yace mata kuka karamin Abu ne. Tana kwance kan gado tayi shiru idanunta a runtse kamar me bacci Sede kallo daya ya isheka amsar she's awake. Mami da ta shigo ta karaso jiki a matukar sanyaye ta zauna gefenta, gaba daya guilty tension ke damunta tana jin tamkar bata rike marainiyar da kyau ba, jiya haka ta kwana da tunanin Sulaim a ranta to ya zatayi bata san Meye matsalar ta ba. Sulaim idanunki biyu tashi ki zauna. Babu musu a hankali ta tashi ta xauna idanunta ta bude a hankali kafin tayi saurin rufesu saboda yadda rana da tayi haske take barazanar kashe mata su. A hankali ta kuma budewa wannan karan da dan sauki kafin kuma a hankali tayi balancing da rays din. Mami ina Kwana Ta fada da dusashiyar muryarta Lapiya lau, ina jinki fadamin me ya saki kuka jiya? Dagowa tayi ta kalli Mamin tana tunanin abinda zatace wanda zaisa Mamin ta yarda da ita don kuwa tana ganin last thing da zai taba faruwa da ita shi ne tona asirin zuciyarta she can't ko Khulthum bazata iya fadawa ba Balle mahaifiyar gwarzonta Junaid! Mummy da Daddy na tuna Ta fada lokaci daya tareda kankame Mamin ta Kara sakin wani sabon kukan, I missed you more than words can say, I missed you ta fada karkashin numfashinta. Tuni Mami ta Fara lallashi har ta samu sulaim tayi shiru tayi wanka sukai breakfast tare kafin ta Sata tayi bacci. Dama anci bashi tana kwanciya ya dauketa. Mami haka ta zauna zuciyarta fal tausauyin sulaim. Turo kofar dakin Junaid yayi muryarshi dauke da sallama, Yana Sanye cikin Kaftan coffee wanda sukai mishi kyau suka kawata shi rare shiga kenan don yawancin shigarshi ba manyan kaya bane amma yau se girmanshi, kwarjini da cikar haiba ta fito sosae, yayi kyau babu macen da zata kalleshi bata Kara kalla ba amma banda ni Woooooo... Lol... Fuskarshi tayi fayau idanunshi sunyi sunken ciki saboda rashin bacci, tarin gajiya, soyayya da uwa uba rigimar Subay'a don jiya Allah ne yasa bai bude zuciyarshi ba saboda ta kaishi bango tana tuhumar shi akan nuna kulawa ga Sulaim wadda ita kadai ya kamata ta samu hakan. Tun yana shiru har ya biyeta ganin ta fishi danyen Kai yasa ya juya mata baya tayi ta gama ta kwanta, a lokacin hankalinshi ya nutsu ya fara tunanin Meye ke damun Sulaim har ya sata take Irin wannan kukan haka. Mami barka da safiya Barka dae, ya Subay'a take Kanshi ya shafa don yasan Bata shigo gaida Mamin ba don a bargo ya barota. Lapiya lau zazzabi take yi ne Shiyasa, ya Sulaim din ta fada miki wani abu? Kai ta gyada ta shafo Fuskar Sulaim din tace She's missing her parent. Tausayinta sosae ya kara kamashi, rashin iyaye babu dadi bai san zafin ba amma zai iya fada. Ya kamata , Allah ya jikansu. Amin, Allah ya bawa Subay'a lapiya ko zakuje Asibiti? Kanshi ya girgixa yace No Tasha magani, Anjima zamu wuce jibi ne tafiyar Estonia. Murmushi tayi tace Yayi kyau Allah ya kaiku lapiya amma kana ganin Sulaim zata iya zama dasu Ahmad. Kanshi ya gyada yace Banida haufi kanta, idan ba ita ba duk kano bazan barsu hannun kowa ba Sede su dawo kaduna. A haka suka gama hirar Bayan La'asar su Sulaim se Kano, Tun a motar batace komai ba Tunda Subay'a na nan gashi kanta har lokancin ciwo yake mata. A haka suka isa gida inda komai yake daidai a muhallinsa. Da daddare ya fadawa Sulaim tafiyarshi tare da sabon responsibility da ya hau kanta. Ko kadan bata damu ba tana ganin Nisan zuciyoyinsu zaisa sonshi ya yaye Daga zuciyarta. Ranar Sunday karfe hudu na yamma Sulaim, Ahmad da Muhammad suka raka Junaid da Subay'a airport Bayan komai da yasan zaa bukata a tafiyar ya bar mata, ita kuma da farko tace yaran gidan hajiya zata kaisu Amma Junaid yace karta fasa haka ta hakura ta fito musu da komai da tasan zasu bukata tare da cewa Sulaim Idan kika zaluncesu Allah bazai barki ba. Ko ta kanta Sulaim Bata bi ba don da tasan yadda takeji da Bata Fara fada mata zancen banza ba. Akan idanunsu jirgin ya fara tafiya kan runway kafin ya cilla sama, idanu Junaid ya runtse wani sabon abu yana piercing zuciyarshi kamar kullum son Sulaim daban yake da na kowa incomparable!!! *Have you ever been hurt? The place tries to heal a bit and you just peel the scar off hurting yourself over and over?* Shatuuu ♥️[7/27, 5:21 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 27 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Sati daya kenan da tafiyar su Subay'a komai na gidan a hannun Sulaim yake wani sabon responsibility ya hau kanta tamkar Marar gidan haka take ji. Alarm din dake gefen bedside drawer ne ya fara ringing alamar lokacinda akai setting dinshi yayi. A hankali ta bude idonta Wanda yake Cikeda bacci tasa hannu ta kashe tareda gyara kwanciyarta don baccin bai isheta ba, sede ta kasa komawa saboda yadda ake ta kiraye kirayen sallar subhi, haka ta mike Tana mutsitsika idanta tayi zauna bayan tayi addu'a ta shiga toilet, wanka ta Fara yi sannan ta daura Alwala ta fito. Bayan ta Idar da sallah ta wuce kitchen inda ta tarar har su Atika sun Fara aiki, gaiswaw sukai sannan ta dubi Atika tace Atika jeki ki tashe su kiyi musu wanka Bari na karasa girkin. Tohm Ta amsa mata sannan ta wanke hannunta ta fice don aiwatar da umarnin Sulaim, kallon kayan da Atika ta fito dasu tayi, wasu ta mayar ta dakko wasu kayan ta Fara aiki, tanayi tana Azkhar baki daya zuciyarta na rage damuwar da take jibge a ciki. Daki ta koma lokacin Atika ta gama shirya mata su Muhammad suna zaune kowanne rikeda madara cikin glass cup, Tana shigowa ta kallesu Ahmad yace Anty morning Kanshi ta shafa tace Morning Boy. Ahmad ta dauka Wanda idanunshi suka cicciko da kwalla it's normal kullum se yayi kukan Papa da Mimi har ta Saba. Jijjiga shi tayi a ranta tana fadin Inama ace inada wanda zan kwanta a jikinshi nima nayi kukan rashin Papan naku da nayi baku kadai kuke missing dinshi ba. Seda yayi shiru kafin ta ajeshi ta nemi Abaya fuschia pink ta saka sannan ta daukesu suka fito dining, serving dinsu tayi sannan ta Fara cin Nata tana duba time don Kada suyi latti. Suna gamawa ta dakko lunch boxes dinsu, school bags dinsu da Nata suka fito parlour anan wayarta ta Fara ringing, Duk tunaninta ma Salim ne don rashin Ja'afar, rashin Junaid yasa ta saki jikinta sosae da Salim sukai wani Irin sabo sosae me wuyar faduwa Dan hausawa sunce a rashin uwa akanyi uwar daki. A rashin wannan gwarzon mazajen guda biyu da zuciya ta kasa kankare su tayi Abota da Salim. Yaya ina Kwana Ta fada Bayan tayi picking, muryarshi deep da dadin saurare yace Yakuke gaba daya. Lapiya lau Ta bashi amsa Tana zura key cikin handbag dinta, Megadi yace min baki fita da motar napep kuke Hawa me yasa? Kanta ta girgixa tace Babu komai. Kyautar Batayi miki ba? Da sauri tace A'a Yaya dama I was planning yau mu fita da ita. Sounds better, se munyi waya Anjima ki gaida yaran. Kafin ta bashi amsa ya kashe, ajiyar zuciya me nauyin gaske ta saki gaba daya wani yanayi ya mamaye mata jikinta. A hankali ta taka zuwa wani couch dake parlon ta ciro key din motarshi da Tun ranarda zai tafi Estonia ya bata akan suna zuwa ko ina Tunda yasan ta iya driving don dawowarta Nigeria lokacin rasuwarsu daddynta Tana cikin mental breakdown Baba yasa Jawad ya ke koya mata don hakan ya dauke mata hankali da kewa amma ko kadan a lokacin umarni kawai take bi Don ba yadda xatayi amma Lokaci gani take meye sauran farin ciki Bayan rashin iyayenta babu wani abu da ya rage Amma dake Allah Allah ne se gashi ba'a shekara ba ta koma normal self dinta. Tare suka fito ta shiga mazaunin driver Muhammad da Ahmad suna baya Sunata wasa a haka ta ajesu a makaranta kafin ta wuce BUK, Tana parking idanunta suka sauka akan Khulthum wadda wata flashy car ta ajiyeta, cikin wani Hadadden lace take kallonshi will give you insight akan tsadarshi color din ash da baki kasancewar ta Fara yasa ya mata kyau sosae sede dinkin da akai ma kayan an kacaccala shi, sun mata gyam a jikinta tamkar idan tayi nishi kamar zai tsage. Ita ta Fara nufo inda Sulaim din take wadda take kokarin rufe motar, kallonta Khulthum take da mamaki tace Sulaimi wannan motar fa? Harara ta maka mata tace Almost a month bamu tare amma Abinda kika fara tambaya shi ne mota, gaskiya kina da matsala. Dariya Khulthum tayi tace Don't mind me kawata mamaki nayi ne, kodan babu mamaki kuna da saa a rayuwarku komai naku me kyau na 'yan gayu masu kudi. Bata ce mata komai ba suka nufi lecture room a haka aka kammalla ta farko babu khairi babu Aimana hakan yasa koda ya fito sukai zamansu cikin class din nasu aka Fara hira can Sulaim tace Meyasa through out last week baki zo school ba? Kai Khulthum ta girgixa tace Ni fa Kinsan yanzun karatun ya fara isata. Isarki fa? Sulaim ta tambaya da mamaki, kanta ta gyada tace Ki Bari kawae na samu abinda Yafi karatu, Kede ki Bari kawae, ke bazaki gane ba. Dariya Sulaim tayi karo na farko tun tafiyar Junaid don ko hira tsakaninta da Salim karkari tayi murmushi, idanunta kawai zaka kalla kasan tana cikin damuwa me tarin yawa sede ko an tambayeta amsar daya ce banajin dadi. Yanzu muke level 2 har kika gaji ko dan kince bazan gane ba ai, by the way Ashir ya kirani yana min wasu maganganun da na kasa fahimta Meke faruwa ne? Wayarta ta janyo tana fadin Ki rabu da wawa kawai! A'a Khulthum kiji tsoron Allah gaba daya kin canja ba kamar farkon Sanina dake ba, Kinsan Maza da kika saka a gaba Bbu inda zasu kaiki se halaka. Ya isheki malama, wai nawa Ashir ya biya ki gurin Yi masa campaign ne. Na fada maki uncountable times Wallahi bazan auri talaka ba, me yaci me ya bani. Kafin ta bata amsa khairi ta shigo itada Aimana nan aka bar Wannan maganar suka dauki sabo har malamin ya shigo kafin suka tattara hankalinsu kanta. Dadinta daya ranar lecture Zuwa 12pm ne hakan yasa ana tashi ta yi musu sallama dan tafiya gida sede suna fitowa dukkansu ta hango Salim tsaye jikin motarshi, ya sakale hannunshi Yana jiranta. Kallonsu tayi tace Finally yau kowa zai hadu da Salim. Khulthum da sauri tace Shi ne Salim din? Kanta ta gyada suka nufi inda yake tsaye Yana sakin murmushi me kayatarwa, Tana zuwa ta saki masa murmushi tace Kazo kenan? Kinyi tunanin bazan zo ba ko? Wane ni nazo banga princess ba. Murmushi tayi Don Salim ya iya zance, kallon su Aimana tayi tace Ga friends dina ku gaisa. Kallonsu yayi suka gaisa sannan yace Mu wuce? Girgiza Kai tayi tace Nazo da mota se wani lokacin. Khairi tayi musu sallama yayinda Khulthum tace Sulaimi Bari na bishi ya ajeni Tunda zaku wuce da Aimana. Hannunta ta karkada tare da kallon Salim wanda yake danne danne a waya tace In bazaka damu ba ka aje ta please. Hannunshi ya zura cikin pocket dinshi yace Babu damuwa, se munyi waya. Sallama sukai da Khulthum wadda Allah kadai yasan me ye cikin zuciyarta. Aimana ta shiga suka tafi tunda kusan hanya daya ce. Acan Khulthum tana ta tunanin yadda zata Dana tarkonta Don wannan guy din Irinshi take burin samu, sun kusa Mintina goma suna tafiya cikin wani salo Khulthum tace Baka tambayi inda Zamu je ba. Kallonta yayi saboda yadda muryarta ta ratsa shi har kwakwalwar kanshi Na manta fa. Murmushi tayi ta Fara bashi address daga nan sukai shiru har ya kaita inda take sauka ta dubeshi tana wani murmushi wanda a iya rayuwar Salim baa taba masa makamancin Irinshi ba hakan yasa ya sake baki da hanci yana kallonta. Dariya ta danyi wanda yasa hakoranta farare tas suka bayyana tace Nagode. Ta kama handle zata bude a ranta tana addu'ar Allah ya sa ya tsaidata, addu'a ta karbu dan ji tayi ya riko hannunta idanunshi cikin nata shima yana sakar mata murmushi me tsayawa cikin zuciyar wanda ya gani. Can I have your number!? Ya furta a hankali, murmushi tayi tace Ni kawar Sulaim ce fa! Kallonta yayi ya Sosa kanshi yace Then? Come on Baby Wallahi kin birgeni ban taba tunanin a Nigeria akwai wayayyun mata irinki ba, Sulaim din me? She's just a friend and nothing more!! Gbam! Gbam!! Gbam!!! Who saw this coming ne? Seda ta dakko su Ahmad kafin ta sauke Aimana bayan ta shiga sun gaisa da Maman Aimana kafin ta nufi gida. Wanka suka Fara yi sannan sukaci abinci ta shiryasu Zuwa islamiyya da yake tare ake kaisu da yaran makotansu yasa Bata kuma fita ba se kallo da ta zauna yi Lokaci Lokaci tana tsamannin kiran Salim zai shigo amma har su Ahmad suka shigo sukai dinner bai kira ba itama bata wani bata Lokacinta ba tayi shirin bacci. ESTONIA Kwanaki sun shude har sati yayi da barowarshi Nigeria. Tunda suka zo bai fiya samun wasu time na kanshi ba saboda conference din da gaske akeyi, abin Yana mishi dadi sosae amma yana kewar wani Bangare na jikinshi, lokuta da dama yakan ayyana me sulaimi take Yi yanzun? Ko taci abinci? Ko tana missing dinshi? Shi bai fiye damuwa dasu Ahmad ba Don yasan they are safe amma ita abar tunani ce. Idan yana tareda ita babu nutsuwa yanzun sunyi nisa da juna zuciya taki hutawa yana ganin mallakar sulaim Shi ne kadai abinda zai sa yaji nutsuwa da kuma kwanciyar hankali to ta yaya? Hannunsa yasa ya kashe shower dake zuba a jikinshi gajiyar tana ta wartsakewa a hankali sannan ya dauki towel ya goge jikinshi tas sannan ya dauki farar bathrobe me flowers purple a jiki, fitowa yayi anan ya samu Subay'a tuntuni tayi bacci, shikam Yana mamakin Yawon Subay'a Tunda suka shigo kasar nan baki daya Bata zauna ta hutawa ranta ba kullum tana cikin yawo ga Kawaye da ta yiwa kanta dasu kullum suna waje se yanzu yake ganin rashin amfanin zuwa da ita Tunda babu Abinda take mishi se gaisuwa, kafin ya fita tana bacci ya dawo bata dakin se bayan maghrib itakuma ta gaji likis bazata moru ba hakan yasa ya kyaleta ya zuba mata ido. Farin wando ya saka 3 quarter se Riga fara itama ya dauki wayarshi ya fita zuwa balcony Don kiran Sulaim, karfe Sha daya da Rabi anan gurinsu yasan Nigeria karfe Tara ne da rabi. Dab da zata katse Sulaim ta dauka bakinta dauke da sallama Cikeda nutsuwa ta gaisheshi Inasu Ahmad? Kallon inda suke kwance tayi tace Sunyi bacci tun dazu, ya conference din? Kanshi ya shafa yana jin sanyi na ratsa ilahirin jikinshi yace Alhamdulillah! Gashi mun shigo second week. Kanta ta gyada se kuma sukai shiru har na kusan minti biyar kafin tace Seda safe? More like a question, rausayar da kai yayi yace OK, goodnight! A hankali ta sauke numfashi Don ba haka ta so ba, taso Sui ta kira amma ya ta iya? Haka sukai sallama kowa cikinsu zuciya na axabtuwa da rashin dan uwanta! Shatuuu ♥️ [7/28, 2:52 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 28 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Daga labulen dakin da Khulthum ke Zaune Mama tayi ta bita da kallo sosae amma da yake hankalin Khulthum din yayi kan film din da take kallo cikin system dinta. Shigowa Mama tayi da kyau tareda zama Kan katifar da A'isha take kwance, yau ta tashi da zazzabi hakan yasa ko kofar daki bata iya Zuwa ba Tana nan a kwance ta rame sosae saboda ko babu zazzabi A'isha na cikin damuwar hadin da Baba yayi mata da Ashir saboda kullum tana kallon Ashir a matsayin brother dinta Wanda zai auri yayarta and nothing more abin ya buge ta da yawa donma ita bata kula samari saboda past experience da ta samu, don kuwa kowa yazo gunta idan har Khulthum ta fito to se ya koma kanta bata taba mantawa akwai wani da take so sosae Khulthum ta fahimci yadda take son gayen se idan yazo se Khulthum ta fito a haka har hankalin gayen ya fara karkata kanshi what she saw at last was sun dinke da Khulthum hakan yasa ta daina kula kowa Tunda tana ganin inhar Khulthum na nan she's nothing fa ce background wadda take shining in the absence of Khulthum. Amma abinda ya Bata mamaki Kwana biyu da akai abin, Kwana biu da maida kudin Khulthum kanta Sega Maman Ashir da kanta tazo ganinta, Allah ya taimaka Khulthum bata nan. Matar me kirki wadda tasan darajar mutane wayayyiya ta dinga jadaddawa Aisha cewar haka Allah ya tsara ta karbi kaddarar ta da hannu bibibyu Allah shi kadai yasan sauyin me yake nufi. Da daddare sega Ashir yazo shida abokinshi da farko kamar bazata fita ba amma Amir ya dinga balbala mata masifa akan ta fita Mama kuwa ko kallonsu Batayi ba a cewarta Aisha ta bata mamaki da ta karbi abinda yake na Khulthum ta manta lokuta Nawa Khulthum tana snatching samarin Aishar. Tun tana Dari Dari dashi taga shi ya saki jikinshi da ita tamkar bai da damuwa but deep down inside him he's having an internal battle na karbar wannan canjin saboda zuciya ta ginu ne akan soyayyar Khulthum, Lokaci daya yayi receiving shockest blow daga gurin ta. Da farko kin amincewa yayi da canjin Seda Babanshi ya nuna mishi maida hannun kyauta baya shedan ne kawai ke yin hakan. Ya jera kwanaki yana zuwa gurinta har ta Fara sakin jiki dashi Amma basu taba haduwa da Khulthum ba se kwatsam ranar bai tafi da wuri ba Daga gurinta har Khulthum ta dawo Daga yawonta. Ranar wani Alhaji me naira a kasan layinsu wanda Khulthum taje yiwa matarshi kunshi suka hadu mutumin Yana da kudi, irin arziki na fada fa sede Irin azzaluman nan ne wanda kudinsu yake iya waje amma banda gidanshi bai wadata dasu ba arzikinshi bashi da amfani garesu, ya jima da sanin Khulthum Sede wancan sanin da yayi mata a nutse take iyakarta tara samari, idanunshi Yana kanta yana watching moves dinta ta hanyar ya ranshi se kuma ya samu labarin ta zama yar hannu saboda yadda Maza dabandaban suke direta cikin saa suka hadu a gidanshi shi kenan aka kulla kullaliya. Tunda ta hango ta tabbatar Ashir ne da A'isha tace da Alhaji Yiwa wayancan na tsayen full light. Murmushi yayi yace An gama gimbiya Da haka ya dalle fuskokinsu , wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci Khulthum saboda yadda taga suna dariya baki dayansu, wani abu taji ya dirar mata a kirji saboda haukan karya take Ashir zuciya zaiyi wahala ta samu madadinshi. Jikinta na rawa ta bude motar tareda daukar handbag dinta ta fito ko kiran da Alhaji keyi mata bata saurara ba shima se yayi reverse kawai ya fice. Tamkar lioness ko tigeress haka ta nufesu idanunta sun kankance saboda kishi wanda bata san tanayi ba, Tana zuwa ta dauke Aisha da mari tare da fadin Macuciya har dariya kike kin kwaci abinda ya..... Tas taji akan nata kuncin wanda yasa maganar katsewa ta juyo Ashir ne! Ashir ne!! Ashir ne!!! Shi ne ya mare ta Yana huci yace Kada ki sake ko da wasa hannunki ya Kai kanta shashasha kawai. Ashir ni ka mara? Ni Ummu_Khulthum? Ni? Ta fada mamaki da tsoro da kuma bakin ciki suna sake shigarta An mareki din do your worst. Hannunta ta shiga Tafawa tana kallon A'isha wadda idanunta sunyi ja saboda bacin rai, Lallai na yadda duk inda namiji yake munafiki ne, se kace min Khulthum tuntuni bake nake so ba Aisha nake so basai kayi putting drama ba. Matsiyaci kuma ka sani nafi karfinka ke kuma Se tayi dariya kawai wadda gwara ace kuka take kafin ta shige cikin gida, straight daki ta wuce ta fada gado ta saki kuka me ciwo na haushin Har yanzun bata daina son Ashir ba. Daga Wannan ranar gaba me tsanani ta shiga tsananin Khulthum da sauran yaran Mama hatta Amira ta daina kulata itama dama bawai shiga sabgarsu take ba hakan yasa ta manta dasu ko abinci akai ta daina ci a cewarta takamarsu tana cin abincin da ubansu ya kawo Shiyasa suke iskanci Mama ita nata kallo ta rasa abinda zata fada hatta Baba kallonshi take don yabi bayan ya'yanshi Tunda yaga Mama akwai saura. Aisha ya jikin? Bude idonta tayi a hankali ta kalli Mama tace Da sauki Mama kina ta aiki ko? Se hawaye ya fara mata zarya, she hate been sick saboda aiki a jinin jikinta yake idan ba tayi ba bata jin dadi Balle tana son Mama sosae Bata son ganinta tana aiki ko kadan. To meye abin kukan Allah ya baki lapiya. Amin ta furta Tana maida idanunta ta rufe. Se lokacin Khulthum ta ankare Mama ta shigo hakan yasa ta tashi ta xauna tana kallon Mama tace Yaushe kika shigo? Yanzun nan Kanta ta gyada zata maida earpiece din kunnenta Mama ta dakatar da ita ta hanyar fadin Zauna magana Zamuyi. Dan tsaki tayi tace Dan Allah ki Bari se anjima Wallahi kallo nake. Cikeda rashin jin dadi Mama tace Ki tsaya mana me yasa kike haka ne? System din ta tura gefe sannan ta zauna ranta a bace tace Ina jinki. Kallonta Mama tayi, Tana son Khulthum gaba da kowa da komai a Rayuwarta amma halayen Khulthum ta rasa inda ta kwaso su baki daya tarbiyya tayi mata karanci. Ina kike Zuwa ne Kwana biu bakya dawowa da wuri. Cikin ko in kula tace Ina nake zuwa banda makaranta, kiji Mama da wata magana. Kai Mama ta girgixa tace Me yasa baki san Irin maganar da zaki na fada ba, ni mahaifiyarki ce fa. Allah Kece Mama da wata tambaya wai ina nake zuwa? Zargina Kema kikeyi Da sauri Mama ta girgixa Kai tace Haba dai ya ma zakiyi wannan tunanin naga dai yaron hasiya karfe hudu ya dawo gida amma ke se bayan isha'i. Kai ta girgixa don ta gane wa take nufi wani Rabiu makocinsu yana level 4 same faculty. Mama Nifa Bayero nake zuwa shi kuma Kinsan legal me kallon kofar gadon kaya wannan yake Zuwa fa. Aisha na jinsu a ranta tace jahilci baiyi ba gashi dai ta ninke mama a baibai. Tana fitowa daga wanka ta hango wayarta na haske da sauri ta karasa kan couch din, Tana zuwa taga hajiya ce me kiran Dammm! Taji faduwar gaba ga Junaid Yana zaune kan gado yana aiki a system dinshi kasancewar weekends ne baije ko ina ba kuma itama ya hanata fita. Aje wayar tayi ta Fara shiryawa cikin sassaukan kaya. Seda ta gama tazo ta zauna har lokancin bai daina aikin da yake ba. Inason magana dasu Ahmad. Dagowa yayi ya dubeta kafin ya maida kallonshi ga system din yace Kira Sulaim mana suna tare ai. Banida number dinta. Kallonta ya kuma Yi sannan ya janyo wayarshi ya fara dialing sulaim bugu biyu ta dauka lokacin tana kitchen tana aiki Sulaim how are you? I'm fine Alhmdllh. Ta bashi amsa Tana tattara dukkan nutsuwarta ta mayar kanshi. Inasu Ahmad Mamansu zatayi magana dasu. Seda gabanta ya fadi jin ya ambaci Subay'a, ajiyar zuciya ta sauke tace Jiya kakarsu tazo ta gansu ta tafi dasu. Idonshi ya zaro yace You let them? Me yasa baki kirani ba. Kawai tayi murmushi tana tuno yadda sukai da hajiyar itadin ta raina su Subayan Baki daya batayi tunanin basu waye har haka ba, su shida sukazo jiya zasu tayar mata da hankali ita kuwa tace Allah ya raka taki gona. Ba dake nake ba? Ya tambaya jin tayi shiru. Yaya me zance musu, kayi hakuri to. Gaba daya se yayi shiru Ta kashe mishi Baki Tunda ta karbi laifinta dukda Yafi kowa sanin su waye su Subay'a da ikonsu akan abinda basu isa dashi ba Balle wannan. Kashe wayar yayi ya dubi Subay'a da ta tsura mishi ido yace Ki kira gidanku kiji. Daga haka ya cigaba da aikinshi ta zauna Tana ta kallonshi haka kawai take jin Bata yadda da Junaid ba ko kadan. Dagowa yayi yace I've said all, yau ko an canja miki ni ne Naga kallon yayi yawa. Ya fada Yana mata wink, kallonshi tayi tace You love her right? Dagowa yayi Yana kallonta kamar yadda take kallonshi wata zuciyar tana ingiza shi akan ya fada mata amma wata na nuna mishi Sulaims' well-being shi ne abin ji. Bakya son zaman lapiya kwatakwata Subay'a, what if I love her Zaki hanani aurenta ne? Ko zaki hana zuciyata son Abinda tayi niyya? If I where you Subay'a da da wannan tambayar da kike da kanki kikayiwa fada. Sannan kice a maida su Ahmad gidansu. Unbelievable! So take ta yadda da Abinda Junaid ke fada mata what if I love her zaki hanani aurenta? Kenan kana sonta? Ta Kara tambayarshi idanunta jawur, Baice da ita kanzil ba ya cigaba da Abinda yake a ranshi Yana Allah Allah Sati ya cika su koma Nigeria ya bawa kanshi 'yanci. Yana fita sallar maghrib ta wuce balcony tayi dialing number Hajiya seda ta katse ta Kara bugawa kafin ta dauka tana korafin me ye yasa Tun dazu bata kira ba. Hajiya ki bar maganar kawai. Se kuma ta Fara kuka sosae tana jin zuciyarta tamkar zata fito Daga kirjinta. Tsaki Hajiya tayi Subay'a tace Hajiya kinsan Junaid...... Ya isheni Malama, bakida aikin da ya wuce complain Karki tashi ki kwatarwa kanki 'yanci kiyi ta zama Tunda ke shashasha ce. Kuma maganar tafiyarku Keda su Samiha tana nan, visas dinku gaba daya are ready se kisan yadda zakiyi. Hajiya ni bazanje ba gaskia.... Ke Subay'a ki shiga hankalinki ranki zai baci, ubanwa nake yiwa gata idan baku ba? Hajiya dan..... Se Anjima ta kashe wayar, shiru Subay'a tayi tana ta tunani yadda zata bullowa Junaid, tasan future impossible shi ne yardar Junaid Amma ya zatayi hajiya fa? Her only happiness! Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 28 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Daga labulen dakin da Khulthum ke Zaune Mama tayi ta bita da kallo sosae amma da yake hankalin Khulthum din yayi kan film din da take kallo cikin system dinta. Shigowa Mama tayi da kyau tareda zama Kan katifar da A'isha take kwance, yau ta tashi da zazzabi hakan yasa ko kofar daki bata iya Zuwa ba Tana nan a kwance ta rame sosae saboda ko babu zazzabi A'isha na cikin damuwar hadin da Baba yayi mata da Ashir saboda kullum tana kallon Ashir a matsayin brother dinta Wanda zai auri yayarta and nothing more abin ya buge ta da yawa donma ita bata kula samari saboda past experience da ta samu, don kuwa kowa yazo gunta idan har Khulthum ta fito to se ya koma kanta bata taba mantawa akwai wani da take so sosae Khulthum ta fahimci yadda take son gayen se idan yazo se Khulthum ta fito a haka har hankalin gayen ya fara karkata kanshi what she saw at last was sun dinke da Khulthum hakan yasa ta daina kula kowa Tunda tana ganin inhar Khulthum na nan she's nothing fa ce background wadda take shining in the absence of Khulthum. Amma abinda ya Bata mamaki Kwana biyu da akai abin, Kwana biu da maida kudin Khulthum kanta Sega Maman Ashir da kanta tazo ganinta, Allah ya taimaka Khulthum bata nan. Matar me kirki wadda tasan darajar mutane wayayyiya ta dinga jadaddawa Aisha cewar haka Allah ya tsara ta karbi kaddarar ta da hannu bibibyu Allah shi kadai yasan sauyin me yake nufi. Da daddare sega Ashir yazo shida abokinshi da farko kamar bazata fita ba amma Amir ya dinga balbala mata masifa akan ta fita Mama kuwa ko kallonsu Batayi ba a cewarta Aisha ta bata mamaki da ta karbi abinda yake na Khulthum ta manta lokuta Nawa Khulthum tana snatching samarin Aishar. Tun tana Dari Dari dashi taga shi ya saki jikinshi da ita tamkar bai da damuwa but deep down inside him he's having an internal battle na karbar wannan canjin saboda zuciya ta ginu ne akan soyayyar Khulthum, Lokaci daya yayi receiving shockest blow daga gurin ta. Da farko kin amincewa yayi da canjin Seda Babanshi ya nuna mishi maida hannun kyauta baya shedan ne kawai ke yin hakan. Ya jera kwanaki yana zuwa gurinta har ta Fara sakin jiki dashi Amma basu taba haduwa da Khulthum ba se kwatsam ranar bai tafi da wuri ba Daga gurinta har Khulthum ta dawo Daga yawonta. Ranar wani Alhaji me naira a kasan layinsu wanda Khulthum taje yiwa matarshi kunshi suka hadu mutumin Yana da kudi, irin arziki na fada fa sede Irin azzaluman nan ne wanda kudinsu yake iya waje amma banda gidanshi bai wadata dasu ba arzikinshi bashi da amfani garesu, ya jima da sanin Khulthum Sede wancan sanin da yayi mata a nutse take iyakarta tara samari, idanunshi Yana kanta yana watching moves dinta ta hanyar ya ranshi se kuma ya samu labarin ta zama yar hannu saboda yadda Maza dabandaban suke direta cikin saa suka hadu a gidanshi shi kenan aka kulla kullaliya. Tunda ta hango ta tabbatar Ashir ne da A'isha tace da Alhaji Yiwa wayancan na tsayen full light. Murmushi yayi yace An gama gimbiya Da haka ya dalle fuskokinsu , wata mummunar faduwar gaba ce ta ziyarci Khulthum saboda yadda taga suna dariya baki dayansu, wani abu taji ya dirar mata a kirji saboda haukan karya take Ashir zuciya zaiyi wahala ta samu madadinshi. Jikinta na rawa ta bude motar tareda daukar handbag dinta ta fito ko kiran da Alhaji keyi mata bata saurara ba shima se yayi reverse kawai ya fice. Tamkar lioness ko tigeress haka ta nufesu idanunta sun kankance saboda kishi wanda bata san tanayi ba, Tana zuwa ta dauke Aisha da mari tare da fadin Macuciya har dariya kike kin kwaci abinda ya..... Tas taji akan nata kuncin wanda yasa maganar katsewa ta juyo Ashir ne! Ashir ne!! Ashir ne!!! Shi ne ya mare ta Yana huci yace Kada ki sake ko da wasa hannunki ya Kai kanta shashasha kawai. Ashir ni ka mara? Ni Ummu_Khulthum? Ni? Ta fada mamaki da tsoro da kuma bakin ciki suna sake shigarta An mareki din do your worst. Hannunta ta shiga Tafawa tana kallon A'isha wadda idanunta sunyi ja saboda bacin rai, Lallai na yadda duk inda namiji yake munafiki ne, se kace min Khulthum tuntuni bake nake so ba Aisha nake so basai kayi putting drama ba. Matsiyaci kuma ka sani nafi karfinka ke kuma Se tayi dariya kawai wadda gwara ace kuka take kafin ta shige cikin gida, straight daki ta wuce ta fada gado ta saki kuka me ciwo na haushin Har yanzun bata daina son Ashir ba. Daga Wannan ranar gaba me tsanani ta shiga tsananin Khulthum da sauran yaran Mama hatta Amira ta daina kulata itama dama bawai shiga sabgarsu take ba hakan yasa ta manta dasu ko abinci akai ta daina ci a cewarta takamarsu tana cin abincin da ubansu ya kawo Shiyasa suke iskanci Mama ita nata kallo ta rasa abinda zata fada hatta Baba kallonshi take don yabi bayan ya'yanshi Tunda yaga Mama akwai saura. Aisha ya jikin? Bude idonta tayi a hankali ta kalli Mama tace Da sauki Mama kina ta aiki ko? Se hawaye ya fara mata zarya, she hate been sick saboda aiki a jinin jikinta yake idan ba tayi ba bata jin dadi Balle tana son Mama sosae Bata son ganinta tana aiki ko kadan. To meye abin kukan Allah ya baki lapiya. Amin ta furta Tana maida idanunta ta rufe. Se lokacin Khulthum ta ankare Mama ta shigo hakan yasa ta tashi ta xauna tana kallon Mama tace Yaushe kika shigo? Yanzun nan Kanta ta gyada zata maida earpiece din kunnenta Mama ta dakatar da ita ta hanyar fadin Zauna magana Zamuyi. Dan tsaki tayi tace Dan Allah ki Bari se anjima Wallahi kallo nake. Cikeda rashin jin dadi Mama tace Ki tsaya mana me yasa kike haka ne? System din ta tura gefe sannan ta zauna ranta a bace tace Ina jinki. Kallonta Mama tayi, Tana son Khulthum gaba da kowa da komai a Rayuwarta amma halayen Khulthum ta rasa inda ta kwaso su baki daya tarbiyya tayi mata karanci. Ina kike Zuwa ne Kwana biu bakya dawowa da wuri. Cikin ko in kula tace Ina nake zuwa banda makaranta, kiji Mama da wata magana. Kai Mama ta girgixa tace Me yasa baki san Irin maganar da zaki na fada ba, ni mahaifiyarki ce fa. Allah Kece Mama da wata tambaya wai ina nake zuwa? Zargina Kema kikeyi Da sauri Mama ta girgixa Kai tace Haba dai ya ma zakiyi wannan tunanin naga dai yaron hasiya karfe hudu ya dawo gida amma ke se bayan isha'i. Kai ta girgixa don ta gane wa take nufi wani Rabiu makocinsu yana level 4 same faculty. Mama Nifa Bayero nake zuwa shi kuma Kinsan legal me kallon kofar gadon kaya wannan yake Zuwa fa. Aisha na jinsu a ranta tace jahilci baiyi ba gashi dai ta ninke mama a baibai. Tana fitowa daga wanka ta hango wayarta na haske da sauri ta karasa kan couch din, Tana zuwa taga hajiya ce me kiran Dammm! Taji faduwar gaba ga Junaid Yana zaune kan gado yana aiki a system dinshi kasancewar weekends ne baije ko ina ba kuma itama ya hanata fita. Aje wayar tayi ta Fara shiryawa cikin sassaukan kaya. Seda ta gama tazo ta zauna har lokancin bai daina aikin da yake ba. Inason magana dasu Ahmad. Dagowa yayi ya dubeta kafin ya maida kallonshi ga system din yace Kira Sulaim mana suna tare ai. Banida number dinta. Kallonta ya kuma Yi sannan ya janyo wayarshi ya fara dialing sulaim bugu biyu ta dauka lokacin tana kitchen tana aiki Sulaim how are you? I'm fine Alhmdllh. Ta bashi amsa Tana tattara dukkan nutsuwarta ta mayar kanshi. Inasu Ahmad Mamansu zatayi magana dasu. Seda gabanta ya fadi jin ya ambaci Subay'a, ajiyar zuciya ta sauke tace Jiya kakarsu tazo ta gansu ta tafi dasu. Idonshi ya zaro yace You let them? Me yasa baki kirani ba. Kawai tayi murmushi tana tuno yadda sukai da hajiyar itadin ta raina su Subayan Baki daya batayi tunanin basu waye har haka ba, su shida sukazo jiya zasu tayar mata da hankali ita kuwa tace Allah ya raka taki gona. Ba dake nake ba? Ya tambaya jin tayi shiru. Yaya me zance musu, kayi hakuri to. Gaba daya se yayi shiru Ta kashe mishi Baki Tunda ta karbi laifinta dukda Yafi kowa sanin su waye su Subay'a da ikonsu akan abinda basu isa dashi ba Balle wannan. Kashe wayar yayi ya dubi Subay'a da ta tsura mishi ido yace Ki kira gidanku kiji. Daga haka ya cigaba da aikinshi ta zauna Tana ta kallonshi haka kawai take jin Bata yadda da Junaid ba ko kadan. Dagowa yayi yace I've said all, yau ko an canja miki ni ne Naga kallon yayi yawa. Ya fada Yana mata wink, kallonshi tayi tace You love her right? Dagowa yayi Yana kallonta kamar yadda take kallonshi wata zuciyar tana ingiza shi akan ya fada mata amma wata na nuna mishi Sulaims' well-being shi ne abin ji. Bakya son zaman lapiya kwatakwata Subay'a, what if I love her Zaki hanani aurenta ne? Ko zaki hana zuciyata son Abinda tayi niyya? If I where you Subay'a da da wannan tambayar da kike da kanki kikayiwa fada. Sannan kice a maida su Ahmad gidansu. Unbelievable! So take ta yadda da Abinda Junaid ke fada mata what if I love her zaki hanani aurenta? Kenan kana sonta? Ta Kara tambayarshi idanunta jawur, Baice da ita kanzil ba ya cigaba da Abinda yake a ranshi Yana Allah Allah Sati ya cika su koma Nigeria ya bawa kanshi 'yanci. Yana fita sallar maghrib ta wuce balcony tayi dialing number Hajiya seda ta katse ta Kara bugawa kafin ta dauka tana korafin me ye yasa Tun dazu bata kira ba. Hajiya ki bar maganar kawai. Se kuma ta Fara kuka sosae tana jin zuciyarta tamkar zata fito Daga kirjinta. Tsaki Hajiya tayi Subay'a tace Hajiya kinsan Junaid...... Ya isheni Malama, bakida aikin da ya wuce complain Karki tashi ki kwatarwa kanki 'yanci kiyi ta zama Tunda ke shashasha ce. Kuma maganar tafiyarku Keda su Samiha tana nan, visas dinku gaba daya are ready se kisan yadda zakiyi. Hajiya ni bazanje ba gaskia.... Ke Subay'a ki shiga hankalinki ranki zai baci, ubanwa nake yiwa gata idan baku ba? Hajiya dan..... Se Anjima ta kashe wayar, shiru Subay'a tayi tana ta tunani yadda zata bullowa Junaid, tasan future impossible shi ne yardar Junaid Amma ya zatayi hajiya fa? Her only happiness! Shatuuu ♥️ [7/29, 4:30 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 29 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Two weeks Later! Hannunta ta dauraye a sink din toilet sannan ta goge da towel tareda kallon kanta jikin mirror tayi murmushi sannan ta fito ta dauki handbag dinta da key din mota ta fito, Ahmad da Muhammad na Zaune suna kallon cartoon se Atika dake gyaran parlon saboda gama lunch dinsu kenan. Anty zanje Muhammad ya fada Yana daga mata hannu, kanta ta dafe tace Yanxun zan dawo kunji, me zan siyo muku? Kuka Muhammad ya fara hakan yasa dole ta koma dakinta ta dakko musu kaya ta Fara canja musu. Tana gamawa suka fito tare Tace da Atika Duk abinda ya kamata dan Allah ayi bazan dade ba. Kanta ta gyada tace Allah ya kiyaye hanya uwar dakina. Murmushi Sulaim tayi ta fita zuwa mota. Yau Baki daya bata fita ba ta dan kwana biyu Bata fitan ba kasancewar Ahmad bashida lapiya yayi reacting ma man shanu, Seda sukaje asibiti anan aka fada mata yana da allergy da man shanun. Don Haka har daukin fitar take uwa uba gobe gwarzonta Junaid zai dawo Tana jin kamar yau din Bata sauri Shiyasa Tun safe suke aikin gyara da share sharen gida, yanzun ma shopping zataje don so take ta fara aiki yau dinnan. Shoprite suka Fara zuwa tayi siyayya yadda ya dace sannan suka fito ta dubi Ahmad tace Waye zaisha ice-cream? Ni! Duka suka fada, dariya tayi tace Bari muje See Sweet muci burger. Daga haka ta cigaba da driving ta saka wakar Celine Dion ta That's the way it's! Tana son wakar saboda tana kara mata courage akan son Junaid da take. To bansan yadda zan kira zuwan Sulaim See Sweet ba, Zamu iya kiran abun tsautsayi ko karar kwana. A parking space dinsu tayi parking ta fito suma su Ahmad suka dafo mata baya Sede kafin ta shiga hankalinta ya kai kan wata karamar kyakyawar farar mota anyi parking nesa da tata, ta kusan minti uku tana son tuna me motar, cap ta tuna ita ce motar da Salim yaje gurinta dashi a Jega. Kenan he might be in. Murmushi ta saki at least sun Kwana biu basu hadu ba dukda ya rage kiranta a waya da Kuma yawan zaryar da yake mata a school, if she can remember rabon da su hadu Tun ranar da ya bawa Khulthum Lift bai kara Zuwa gurinta ba. Kanta ta girgixa ta rasa me soyayya take nufi da ita, shikenan da an faro ringidi ringidi se gayyar ta watse, ranta a jagule tuna son Wanda bai ma San tanayi ba da take ya kara bata ranta. Da suka shiga da kanta tayi order suka zauna suna ci. Suna gamawa ta Mike Don ficewa wayarta ta Fara ringing hakan yasa ta koma ta zauna tareda karawa a kunne tace Yaya Hanan Daga Dayan bangaren Hanan tace Sulaim yakike Lapiya lau Alhmdllh, Yasu Alhaji Tsoho? Duk suna lapiya Ta bata amsa sannan tace Baki bawa Ya J sakona ba? Waye Ya J? Sulaim ta tambaya with confusion don da gaske bata gane ba Come-on Ja'afar nake nufi Gaban Sulaim ya fadi jin ta ambaci Ja'afar Lokaci daya taji ranta ya baci tuno artabunsu shima bai kara nemanta ba Abinda bai taba yi ba a tsawon soyayyarsu no matter who's at fault Ja'afar zai sakko ya Bata hakuri Amma wannan Karon bai kuma duba inda take ba. Tun tana saka idon ko zai kira har ta hakura Sede she's lonely, her heart is lonely she needs someone. Ki tambayeshi mana, ni zan rike miki abu ne. Tana fada ta kashe wayar tare da kokarin mikewa amma hakan ya gagara sakamaakon mugun ganin da idanunta sukai. Idanu ta zaro Don tabbatar da Abinda Ke gabanta Amma the image seems Kai is real kawai, Khulthum ce cikin fitted gown kanta babu dankwali se fixed hair da ta zubo har bayanta, fuskarta completely dolled up Tana ta dariya hannunta rike da na Salim wanda yake cikin Denim jeans da top yayi kyau sosae kunsan yadda mutumin yake se Sulaim take ganin tamkar an dada mishi kyau ne. Shima dariyar yake yasa Dayan hannunshi ya rungumo Khulthum zuwa jikinshi suna sakkowa daga upstairs Din, haka suka wuce ta don da duka zaa Tambayesu bana tunanin sunsan da wanzuwar halitta a gurin. Kanta a take ya fara sarawa idanunta sukai ja, zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri kamar zata fito Daga thoracic cage dinta. Tafi 15 minutes kanta a kasa kafin abinda take ji ya sassauta saboda kiran sunan Allah da takeyi. Hannun yaran ta Kama suka fito se surutu suke mata amma ina bata hayyacinta. Daga haka ta saka kurani tana saurare har sukaje gida. Booth ta bude me gadi ya fito da kayan sannan ta kulle motar ta nufi ciki hankalinta har lokancin bai gama dawowa jikinta ba. Atika shigo da kayan ciki, zan dan kwanta Zuwa anjima mu fara aiki. Kanta ta gyada ta fita ita kuma ta kunna musu cartoon channel sannan ta shige dakinta ta fada gado tayi rub da ciki! Tana kan sallaya tana addu'a Allah yasa dukkan abubuwan da suke faruwa cikin rayuwarta ya zama mabudin bude kofofin alkhairi. Knocking akai hakan yasa ta karkare adduar ta fito, Atika ce rike da Muhammad wanda yayi bacci, sulaim tace Ya akai yayi bacci ai kuwa my baby you're going to wake up yanzunnan. Hannu tasa ta karbeshi ta nufi parlour dashi dake ta gefen dining area dinsu akwai sink nan taje ta wanke mishi fuska, Yana bude ido ya bare baki don yin kuka tace Yi hakuri babyn Anty muje na baka sweet kaji but don't sleep. A kafadarta ta dora shi Ahmad na rike da hannunta har lokancin ita daya tasan Abinda takeji a zuciyarta amma haka dole ta yakice abin ta nufi kitchen dan fara aiki. Kan working space ta daurasu duka ta ciro candy ta basu suka Fara aiki itada Atika ita kuma Laraba tana gyara abubuwa da yanke yanke. Seda komai ya zama ready Washegari akan ta harhada abubuwa. Da wurwuri ta kwanta Don yaran ma tuni sunyi bacci itama tana son kadaici tana son yin tunani Bata taba tunanin Khulthum zata iya abinda tayi mata ba amma wata zuciyar tuna mata take matsayin Khulthum din a gareta. Ta dade kafin bacci me nauyi ya dauketa. Asubar fari ta tashi da dama dama saboda murnar dawowar Junaid, wayarta ta dauka ta Kara duba arrival time dinsu daya turo mata 9am. DA sauri ta karasa kitchen ta Fara aikinta har takwas da Mintina kafin ta kammalla ta wuce daki dama tuntuni an shirya mata su Ahmad hakan yasa tana fitowa ta dakko Wannan sabon farin lace da cone pattern baki a jiki, dinkin skirt da Riga ne, har ta ware se ta jingina da jikin bango tana tuhumar kanta dalilin da yasa zatayi kwalliya har haka? Mijinta ne? Ko saurayinta ne? None of the above so meye abin zakewa kawai se ta mayar ta dakko gown na atamfa milk da red. Tana gama shiryawa wayar Aimana ta shigo, da sauri ta dauka gabanta na faduwa don batasan Abinda zai fitar da ita Aimana how far? Test din Family Law Nanda 30mins kiyi sauri. Oh no! Ta furta ranta a bace amma ya zatayi haka ta dauki key da veil da Jakarta ta fito gaskiya an karya mata budget da yawa. Atika test gareni na fita, nasan su Yaya sun kusa Dan Allah komai ya zama in place. Kanta ta gyada tace Se kin dawo. Waving tayiwa yaran ta fice cikin hanzari, ranta duka a jagule kamar zatayi kuka. Tana yin parking ta fito sega wasu yan mata su biyu suna tsaye ko abu suke jira oho. Tana fitowa dayar tace mata Dan Allah ke sister Dr Junaid ce? Kallonta Sulaim tayi, irin Ajebos dinnan ne yar gayu kana kallonta kasan naira ta Jikata yadda take magana kadai abin kallo ne. Me ya faru? Ta tambaya Tana kare musu kallo har yar rakiyar. Dama ina crushing dinsa ne so please ko zakiyi hooking dinmu up? Batace komai ba saboda abinda zai fita a bakinta ba Mai dadi bane hakan yasa ta gewaye su zata wuce, dayar tace Please mana help a soul, Munga Kuna Kama sannan ga motarshi Kina zuwa da ita. Ta fada Tana nuna motar da hannunta, juyawa tayi tace Mijina ne ba yaya na ba! Gaba daya suka zaro ido tare da kokarin kare kansu ta wuce ta Barsu a gurin gwiwa a sake, ranta a matukar bace ta shiga cikin class din, ina irin yanayin da Kake jin tamkar kowa da komai is against you, irin you're helpless haka ta dinga ji idanunta sukai ja tamkar me shirin kuka. Idanunta akan Khulthum dake gefen Khairi ya fara sauka, Tana zaune Tana duba wayarta, yi tayi kamar zata wucesu se ta fasa ta dawo ta zauna kusa da Aimana, kafin suyi magana Dr. Halliru me family law din ya iso, babu bata Lokaci aka Fara test, test din tayi wuya duk yadda kayi karatu hakan ya karawa Sulaim tension. A haka aka kammalla ya karba sannan ya fice, mikewa tayi Don tafiya taji Aimana na fadin Ki zauna akwai mood trial Anjima. Kanta ta dafe tace Tafiya zanyi kice banida lapiya. Hannunta Aimana ta rike tace Zauna Sulaim me yene yake damunki? Shi ne furucin da bata so idan tana cikinhi damuwa aikuwa se hawaye da sauri ta tsugunna don Bata son wani yaga halin da take ciki, Aimana ta damke hannunta batareda tace komai ba su kuwa su Khulthum suna ta faman instagramming so basu lura da halinda ake ciki ba. Seda ta sha kukanta kafin ta Mike fuskarta a rufe ta fita don wanke fuskar at least taji dan sanyi cikin Zuciyata she have let out some emotions. Ruwan hannunta tasa ta wanke fuskarta sannan ta dawo ciki kafin ta karasa ta hangosu sun nufota itama bayansu tabi anan Khulthum ta kalleta ta tabe Baki tace Ke kuma yau me ya sameki kike bata rai. Aimana tayi saurin fadin Batada lapiya ne. Allah ya sawwaqe. Ta fada itakuma khairi ta juyo tace Ayya kanwar Yaya sannu. Kanta ta gyada musu har suka isa joint din da suka saba cin abinci. Khairi ce tayi placing order yayinda Sulaim ke mamakin sauyawar Khulthum akanta, tabbas tayi mamaki ba kadan ba ta yadda Khulthum tayi watsi da ita Abinda bata taba ba kenan, kowa yasan yadda Khulthum da Sulaim suke different Womb sisters. Seda sukaci abincin sannan Khairi ta Fara magana tace Tohm, kowa ya bani hankalinshi nan saboda muhimmiyar magana zanyi. Babu Wanda baiyi complying ba saboda Khairi is always not serious amma duk lokacinda tayi magana a nutse to tabbas she's serious. Seriously, banji dadin Abinda ya faru ba, cikin class kowa se ya nuna mu saboda friendship dinmu Tun level 1 amma se kawai abu ya shigo ciki na cin amana da yaudara. Tayi shiru Tana binsu da ido, Khulthum tace Malama ki fadi Abinda zaki fada mana. Kallonta tayi tace Komai a kanki ne Khulthum, ta yaya kina kawar Sulaim ki kwace mata saurayi? Da sauri Sulaim tace No please Khairi..... Da sauri Aimana tace What the hell? Khairi da gaske? Khulthum dake binsu da kallo tace Eh da gaske ne! Se meye a ciki? Khairi tayi mata kallon wulakanci tace Se jin kunya, Wallahi kinji kunya ki rasa ...... Ke rufewa mutane Baki kija gefe, ina ruwanki Naga zan iya ne. Sulaim ganin attention din mutane zai dawo kansu ga Khulthum ta Fara daga murya yasa tace Dan Allah magana ya wuce indan Salim ne let her have him Sede abu daya na sani, Salim is a bad person Tunda zai iya ketare dangantakar mu yayi soyayya dake. Have him sannan ki sani Salim bashi ya hada mu ba Allah ya hadamu. Khulthum cikin ranta taji babu dadi sosae saboda bata taba tunanin haka Sulaim zatayi reacting ba, amma bata nuna ba se ta Mike tace Ai na fada muku Duk wadda tayi sake da nata sede wani bashi ba, Sulaim Allah ya bada karfin zuciya Tana fada ta fice, khairi ta Mike zata bita Aimana ta hanata, Duk sukai shiru ranar haka aka tashi babu dadi kuma taki basu fuskar yin magana ma. Ana gama mood trial kowacce ta fito sukai sallama ta shiga mota ta nufi gida, farin cikin da take ciki ilahirin shi ta nemeshi ta rasa kuka kawai take son tayi ko taji sanyi Amma ya kamata ta isa gida kilan idan taga farin cikin rayuwarta ta ji sanyi. Honk tayi Baba ya bude mata ta daga mishi hannun ta shigo inda ta samu motoci kusan hudu tasan 'yan sannu da zuwa ne. Parking tayi ta fito Tana sauke ajiyar zuciya, nan aka bude kofa Subay'a ta fito tayi kyau se kyalli take ga haske da ta kara tayi kubul jikinta, take wani kishi ya dirar musu lokaci daya, bayanta yan uwanta ne su hudu Baki daya suka saki Baki suna kallonta lokacinda take rufe motar Junaid din. Dauke kanta tayi ta nufo inda suka ja tunga tamkar masu jiranta. Dama ranta a bace yake hakan yasa ko inda suke bata kalla ba ta gebare su tayi ciki. Salima wadda karo na farko da ta Fara ganin Sulaim tace Wacece Wannan yarinyar Subay'a? Cikin Bacin rai tace Sulaimi ce kanwar Junaid Bata ganmu bane? Idan idona daidai ya nuna min kamar motar Junaid na gani a hannunta. Surayya tayi dariya tace Subay'a da gaske ne? Ko kuwa hallucination nake motar mijinki a hannun wata? Samina tace Ku muje Dan Allah, ko bakuga kallon da take mana ba ..... Na yan iska ko? Suhaila ta fada muryarta Cikeda tsanar. Mu fara kashe kurar dake gabanmu kafin mu dawo kanta. Ku muje. Haka suka wuce suka bar Subay'a tsaye tamkar mutum mutumi, Tunda suke da Junaid bai taba ko da wasa bata motarshi ba amma gata hannun Sulaim Wallahi yau ko ita ko sulaim. A ciki kuwa......... Who wants to know wani Irin kallo zaayi tsakanin Junaid da Sulaim? Don't miss it out! Ga Junaid ya dawo will he let the word out? Meye Subay'a zatayi kuke ganin? Shatuuu ♥️ [7/30, 10:36 PM] Ayshatuuuu: *MACE A YAU* 30 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Hey pipu.....I'm sorry for the late update, wallah yau kam I was so busy ne.... Amma gashi na baku sleeping mate, I hope everybody will enjoy it! Na taba fada muku yadda Sulaim take? OK let's go Sulaim is an Epitome of beauty kyakyawa ce ta gasken gaske. Fara ce fari me sanyi me kuma haske bamai dau ba, saffa saffa. Fuskarta oval shape ce wadda ta samu brows me cikakken gashi baki wuluk tamkar anyi shaping haka girar take wadda saboda yadda gashinta na kai yake har goshi yasa yake neman haduwa da girar fuskarta. Idanunta suna da haske me rikitarwa, idonta nada girma amma saboda yadda suka Saba da kuka yasa ba a ganin girman saboda bata ware su da kyau se on special basis. Hancinta Mashaaaa Allah very pointed me kyau Wanda yayi fitting fuskarta, bakinta ba me girma bane daidai yake, lebenta sirara masu taushi, Tana da wushirya me Dan girma sannan da both side dimples. Sulaim ba gajeriya bace doguwa ce saboda ta gaji tsayi daga gurin Daddy da Mummy Baki daya, jikinta me kyau ne well shaped Sede tsayinta ke boye kirar ta ta. Sulaim mutum ce very gentle, Tana da nutsuwa sosae, Tana da addini sauran kunfi kowa sanin su! A hankali ta cigaba da takawa zuwa parlon, fuskarta babu walwala ga gajiya da tarin kunci da suka mata kakanakayi, sede gabanta babu Abinda yake banda faduwa sosae, zuciyarta ta tsananta bugawa ga dauki. Tana yin sallama sassanyan kamshin Fierce cologne by Abercrombie and Fitch yayi mata sallama wanda ya tabbatar mata mamallakin turaren na gurin, cikin nitsuwa ta dago idonta ta dubi kujerun parlour, Yana zaune idanunshi a kanta Wanda ko kyafta idon ya kasa samu yayi, tamkar an canza ta haka yake kallonta ko kuma bai taba ganinta ba se ranar. Tayi mishi haske dukda rama da tayi amma idanunta kadai shows farin cikin da Bata taba tunanin zata tsinci kanta a ciki ba Wanda ganinshi ya Kore tarin kuncin da take ciki na abubuwan da suka mata yawa. Idanunta ta kyafta se hawaye Sharrrrrrr! Ya fara mata zarya kuma ta kasa daina kallonshi, hawayen yaki daina zuba mata. A hankali ya mike ya nufi inda take tsaye hannunshi cikin pocket dinshi, sede murmushin dake fuskar shi ya dauke se tarin damuwar ganin hawayen da take yi. Menene kuma? Are you not happy? Ya fada a hankali wanda I'm sure ba kowa bane zaiji se itan da dukkan hankalinta ke kanshi taji, da sauri ta girgixa kanta tace A'a. Then why kike kuka? Hannunta tasa ta goge fuskarta tace Banida lapiya. Da sauri ya kalleta yace Je canza kaya kizo muje asibiti, me yasa baki fada min ba? Why will you stay with sickness haka. Kanta ta girgixa ganin yadda ya rikice tace Kaina ne kawai yake ciwo kuma ina tunanin stress ne. Wata ajiyar zuciya me nauyi ya saki wanda Sulaim ta Lura sakamaakon kirjinshi da ya bude sannan yayi relaxing. Duk da haka jekiyi changing I'm waiting for you. Ya fada Yana kallon wrist watch dinsa, babu musu ta wuce dakinta kamar tana taka iska haka take ji saboda wani abu me sanyi da yabi ya mamaye jini, tsoka da jiki. Tana shiga ta wuce bayi ta cire kayanta ta saki ruwa, ta kasa tantance me takeji farin ciki takeji wanda babu kamar shi, Yaya ya dawo me take nema kuma? Baki daya ta manta da Khulthum, Hanan, Ja'afar da Salim. Junaid ne kawai a duniyarta a Wannan lokacin. Tana fitowa fuskarta tayi fayau ga wani lallausan murmushi akai wanda yaki tafiya se ajiyar zuciya datake saukewa akai akai, sau uku tana dakko kaya Tana mayarwa a karshe ta samu wani Lace off white an mishi ratsin pink dinkin gown me kyau ta saka. Ita yanzun ta Riga ta sawa ranta Duk yadda za'ai Duk me zai faru da izinin Allah se ta karkato hankalin Junaid kanta Koda kuwa duniya zata zageta amma a ganinta Lokaci yayi da zata kwatar wa kanta 'yanci, ta gaji da yadda kullum zuciyarta take wahalar tuwa akan maza a karshe ta tashi da heartbreak, wannan karan tabbas kida zai canza. Kusan Lokaci guda suka fito, shi yayi changing Zuwa mark and Spencer trousers Baki se tummy Hilfiger top ash, hannunsa ya daura bakin agogo wanda ya zauna daidai akan hannun nashi. Yayi kyau na fitina har Khulthum taji inama shi din nata ne da sun fasa fitar nan don tasan dole Za'a kalleshi, ita kuma Abinda bazata iya withstanding ba kenan. Are you set? Ya fada Yana kare mata kallo, a ranshi Yana tasbihi ga Allah saboda kyakykyawar halittar da yayiwa abu mafi soyuwa cikin zuciyar shi, son sulaim ya mishi shigar ba zata, ya kainanye shi bashida katabis se yadda tayi dashi. murmushi tayi tace Eh. Martani ya mayar mata wanda seda ta lumshe idonta saboda yadda murmushin ya wanke mata zuciya. Je ki tayar da motar gani nan. Kanta ta gyada ta fice yayinda ya nufi parlour Subay'a don yaji shigowarta yana dakinshi. Tana zaune ta zabga tagumi deep in thought, kana kallon ta kasan akwai abinda take so amma ta kasa furtawa. Sallamarshi yasa tayi firgigit tare da dubanshi ta ganshi da alamun fita zaiyi saboda shigar jikinshi. Zan kai Sulaim Asibiti. Bata da lapiya? Ta tambaya Tana tsatsare shi da ido tana ganin hakan zai girgiza shi, murmushi yayi yace Eh. Banga alama ba Ta bashi amsa Tana duban idanunshi, shima kallonta yayi yace Ke baki gani ba, ni na gani. Daga haka ya juya ya fice ya barta a gurin Tana bacin rai, ita yanzun Sulaim Bata gabanta abinda yake gabanta gobe shi ne damuwarta a hankali zata dawo kanta. Tana hangoshi ta matsa mishi drivers side ya shiga sannan suka fita, zuciyoyinsu cike da farin ciki da nishadi, suna jin tamkar su biyu kadai suka rage cikin duniyar. Dukda bawai magana suke ba amma yanayin kawai ya isa ya nutsar da zuciya, balle su da suka kusan shafe wata basu tare ai wannan ranar is memorable. Duk tunaninta asibiti zasuje Amma se taga sunyi hanyar grand square, dagowa tayi ta dubeshi, kallonta yake yace Ba kan ya daina ciwo ba? Dama ba kukan an ganni bane? Dagowa tayi ta turo Baki Cikeda shagwaba ta Harare shi. Daidai lokacin yayi parking kawai se ya tsaya Yana murmushi yace Sulaim like serious harara ta kikayi? Da sauri ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana murmushi. Kallonta ya kuma Yi yana ganin inama kada ta Kara kuka saboda yadda sanyi ke ratsa shi ganin dariyar da takeyi. Muje. Ya furta cikin wata husky voice wadda ta ratsa ta har cikin kanta, ta bude side dinta ta fito Tana sake gyara zaman Veil dinta. Tamkar couples haka suka jera ciki fuskokinsu kawai ka kalla will tell you how happy they are been by each others company. *We could build up a universe, right here all the world could disappear would it notice* Ice-cream kawai yayi mata order, triple treat chocolate, vanilla da strawberry kowanne scoop dinshi cikin cup, Mika mata yayi sannan ya zauna opposite dinta tareda tsare ta da ido wanda suke Kara ninka soyayyar shi cikin zuciyar ta. Hannunshi ya mata alaman ta sha. Babu musu tasa spoon din Cikeda nutsuwa ta fara kaiwa bakinta, Duk wani move dinta akan idanunshi amma a zahiri wayarshi yake dubawa kafin kuma ya shiga amsa call. Yana dawowa ta mika mishi cup din da sauran ice-cream a ciki tace Gashi Kasha. Kanshi ya girgixa yace A'a wannan maganin Ciwon Kai ne, kinga ni kuma lapiyata kalau ko? Ya fada Yana kashe mata ido wanda yasa zuciyar ta harbawa da sauri, a ranta tana tunanin me Junaid ke nufi da ita ne? So yake ya fasa mata zuciya?. Seda ta gama sannan ya kaita wani Pizza joint dake kan new hospital road ya kaita yayi mata order pizza slice biyu, Dakyar ta cinye Daga nan yace mata Ina kike son Zuwa kuma? Shiru tayi tana tunani kafin tace Cinema! Kanshi ya shafa yace Shi ne inda kike son Zuwa? Kanta ta gyada tana murmushi, agogon hannunsa ya kalla lokacin hudu tayi hakan yasa ya tsaya yayi sallah batace zatayi ba shima bai ce mata ba don Abinda yayi believing ba yadda za'ai ka cewa mace tayi sallah kilan tana off. A cinema shoprite sukaje ya tambayeta na wanne kasa tace India. Can sukaje bayan ya karba mata popcorn se tace Kai kuma fa? A'a na Ciwon Kai ne wannan ai, Ke kadai zaki ci abinki. Murmushi tayi ta cigaba da bin bayanshi har suka karba ticket ana shooting Goliyinka Ram Leela Ras Leela. Bata taba kallon film din ba amma tasan famous wakar film din, suna ta kallo ko ita kadai takeyi don shi hankalinshi Yana kan wayarshi seda aka kusa yaji alamar sheahekar kuka, da sauri yace Oh God! Meye kuma na kukan? Hannunta tasa ta goge fuskarta tace Sun kashe kansu fa? Su waye? Ram da Leela na film din. Tsaki yayi yace Tashi mu tafi. Mikewa tayi ta bi bayanshi ba tareda ta ce komai ba, gaba daya se yaji ranshi ya baci if at all yasan cewar ranta zai baci Wallahi bazata kalla film din ba. Duk kokarin ganin ya faranta mata rai haka kurum wani fiction yazo ya bata mishi komai. Basu suka koma gida ba se bayan sallar ishai seda ya tabbatar ta samu farin cikin da yake son ganinta a ciki, babu ko digon damuwa cikin kwayar idanunta kafin suka nufi gida amma abin mamaki duk wannan abin ya kasa Furta "L" word din. A parlor Subay'a na zaune da Ahmad se Muhammad da ya sata a gaba yana kukan shi Anty zaije, Tun tana lallashinshi har ranta ya baci ta daddake shi, nan Kuwa ya kara Sautin kukanshi, abin ya dameta ga Junaid bai dawo ba, ga tsanar sulaim dake kara nunkuwa cikin zuciyar ta, ga tsoron yadda zata tunkareshi da maganar nan. A haka suka shigo gidan, rigerigen taro Sulaim Ahmad da Muhammad sukai, ta tsugunna ta rungumesu jikinta tareda daga Muhammad sama ya fara dariya sannan ta riko hannun Ahmad zuwa cikin parlour. Zama tayi ta dubi Subay'a dake kallonta tace Kun dawo lapiya? Lapiya. Ta bata amsa Tana bin bayan Junaid, tabe Baki tayi ta dauki yaran zuwa dakinta, seda ta shirya su tsaf kafin ta shirya itama don bacci amma taji an turo kofar, fitila ta kunna da mamakim ganin Subay'a tsaye Tana kallonta, itama kallanta tayi batace mata uffan ba, se dan kanta tace Yarana fa. Gasu Sulaim ta bata amsa, aikuwa ta karaso da nufin daukar Muhammad Yana bude ido ya fara ihun shi gurin Anty zai Kwana haka Ahmad dole ta hakura ta koma gurin Junaid wanda tuni yana gado yana aiki da system gefenshi ruwa ne kan table Yana Sha time to time tareda murmushin tuno Outing dinsu, se yakejin tamkar they went for a date. Gefenshi ta zauna tareda mika mishi envelope tace Papa gashi. Ture system din yayi ya bude envelope din, visa dinta ce ta zuwa Cyprus se wasu takaddu na makarantar da zataje masters din. Glasses dinshi ya cire yace...... Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 31 nd 32 Double page ✍Shatuuu♥ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Zare glasses din idonsa yayi ya aje papers din kan table din sannan ya dago ya aje maida hankalinshi kanta, ya kusan minti biyar Yana kallonta tareda nazarin yanayin da take ciki wanda hakan Ke Kara mata uneasiness a tattare da ita, kafin yace Explain yourself Dago idonta tayi rashin gaskiya da tsoro karara a idonta, tamkar ba Subay'a ba haka ta koma. Hajiya ta aiko min jiya akan gobe da safe zamu wuce Abuja mu tashi zuwa Cyprus. Two years ne program din, zan na dawowa every six months. Kuma ni, Sulma, ya Suhaila da Yaya Salima Zamu tafi. Ta fada Tana kawar da kanta , kanshi ya girgixa yana Kara mamakin Subay'a, da gaske ita hankalinta ya bata ta tafi ta barsu kenan. Ya dade bakinshi a rufe yana harhado kalamun da suka fi sauki ya mata magana dasu domin already cikin ranshi ya fara baci, baisan me Subay'a ke nufi dashi ba, baisan me ta dauki aure ba gaba daya. Idan kika tafi, a hannun wa kika barwa ni da su Ahmad? Ko marayu kike son mu zama? Ya fada Yana kara kallonta, inda baisan wacece Subay'a ba da zaice tana da gaskiya Amma Subay'a crook ce, kasa bashi amsa tayi ita dama Abinda bata so kenan a Junaid tambaya, idan ya tsareka da ido ko kana da gaskiya se ka duburburce hakan yasa indai zasui irin wannan maganar tafi son se ta shirya kafin ta sameshi. To Amma yau abin is different and seems difficult, kuma tun safe take harhada abubuwa da zata fada mishi. Bakida amsa right? Kinsan dalilin da yasa nake daga miki kafa akan abubuwan da kikeyi? Bai jira amsarta ba ya cigaba da fadin Saboda wasu lokutan tursasa ki ake akan Kiyi abu, ke kuma babu yadda zakiyi tunda haka kika tashi kika tarar anayi a gidanku. Wannan karan nasan kin raina ni Baki dauke ni a bakin komai ba don ina tantamar idan kinsan me kalmar aure take nufi, me kuma ta kunsa....... Da sauri ta katse shi da fadin Nace maka fa yau suka kawo min, bansan da maganar ba kwatakwata. Dago kanshi yayi yana dubanta Cikeda mamaki yace Se Yaushe xaki daina karya a rayuwarki? Duk Abinda kike babu Wanda bansani ba, maganar masters dinku ke kika Fara bawa Hajiya shawara akan kuje Cyprus ko ba haka akai ba? itama ta biyeku tayi. Saboda kin raina ni for more than four months da maganar se ana gobe zaku tashi sannan zaki fada min? Kece mijin ko ni? Shiru yayi ya dafe kanshi saboda zuwa lokacin ranshi ya gama baci, mijin Sulma ya kirashi ya sanar dashi abinda ya faru, tun lokacin yake jiran ta fada mishi don yayi niyyar barinta inda ta fada mishi a lokacin amma serves her right, don yana son nuna mata wannan karan tayi karya shike aurenta ba ita ba. Papa Dan Allah na amshi laifi na, amma kar ka hanani tafiya asarar kudi zaayi kuma hajiya..... Shi yasa bazaku taba zama gidan miji ba, ni Nake aurenki ba hajiya ba, a yanzun I've every right over hajiya a kanki, zancen asara I promise to refund abinda ta kashe buri na kawai ki zauna a gidanki. Kanta ta girgixa tace Papa please Murmushin takaici yayi ya zame Daga Zaunen da yake ya kwanta tare da juya mata baya yace Idan kin tashi fita Kunna min AC, ki sani in har nine mijin, ni na aureki, ni Allah yace na shygabance ki ban amince ba amma zaki iya tafiya sede..... Bai karasa ba ya saki murmushi. Itama Ta sani Tunda ya fadi haka to bazai sake magana ba, to zaman me zatayi? Ita tana cikin tsaka me wuya Don kuwa Hajiya tayi rantsuwa akan kowa se Yaje yanzun ita kadai ce matsala haka ta mike jikinta a sanyaye ta fita zuwa dakinta. Ta dade a tsaye Tana kallon kayan da tayi parking cikin trolleys, kayansu Ahmad da ta hada musu. Zama tayi gefen kujera tana tunano zancen su itada Junaid tasan gaskiya ya fada bata taba zama matar kirki ba ko uwar arziki, ita a duniya aikinta shi ne priority dinta not her family amma tasan tafiyar ta Zuwa Cyprus dole ce, tasan halinshi da ta tafi zuciyarshi zata huce babu Abinda zai iya mata Don sabonta ne ya hanata Abu ta tsallake amma wani bari na zuciyar ta gargadi yake mata da babbar murya akan Kada ta tafi. Junaid Na kwance idanunshi rub a rufe amma ba bacci yake ba, haushin kanshi yake ji yana jin duk Abinda Subay'a takeyi kamar dukka laifinshi ne, ya tuna yadda Tun yana nemanta Mami ta nuna kin amincewa saboda ance uwarta tana juya ubanta Amma lokacin ba karamin so yake ma Subay'a ba haka Daddy Aminu yayi fadi tashin ganin kowa ya amince sunyi aure saboda yana yawan fadawa Junaid "Tarbiyyar da nayi maka, inason ka zama tsayayyen namiji wanda son mace bazai Kada shi ba, ya zamana kai ke ruling gidanka ba matarka ba" amma gashi yayi failing to the extreme kuwa. Yasan Matar da ya aura, mutane ne dukkansu masu son duniya hakan yasa duk tafiyar da zaiyi zai tafi da ita don ta kashe kishirwar da takeji amma bai tsira ba, shi kuma in har ta tafi se yayi mata hukuncin da yasan har ta mutu bazata taba mantawa ba. Washegari, babu Wanda ya fito a cikin su biyun, Sulaim ce kadai take ta kokarin shirya su Ahmad da kanta zuwa makaranta. Tana gama shiryasu tace Kuje ku gaida Mimi da Papa. Suka fice ita kuma ta karasa gyara dakin ta fitar da kayan wanki sannan ta hada abinci Se Gasu sun fito dukkansu har Junaid da Subay'a, gaisheku tayi sannan suka Fara cin abincin. Suna gamawa Junaid ya koma daki don ya dakko key da briefcase su tafi, itakam Subay'a zama tayi ta janyo yaran ta rungume wannan tayi kissing wancan idanunta taf da kwalla. Sulaim ce ta Fara fitowa suka hada ido da Subay'a kowacce seda gabanta ya fadi, sulaim ta Fara dauke kanta yayinda Subay'a ta kura mata ido zuciyarta na fada mata tafiya zatayi ta bar mijinta da yarinyar nan? Bayan Abinda take zargi tsakaninsu. Se tayi murmushi kawai saboda ta tuna waye Junaid, meye matsayinta a zuciyarshi. Yana fitowa ya mikawa Sulaim briefcase dinshi da key din motar yace Ku jirani gani nan Zuwa. Amsa tayi ta ja yaran waje yayinda ya dubi Subay'a yace mata Zan wuce office, na bar miki kudi akan decoder na cefane, bazaki je office ba? Kanta ta girgixa ta taso ta rungumeshi tare da furta I'm so sorry and I love you. Shima rungumeta yayi Yana murmushi yace Is ok ya wuce, I've to go. Sakinshi tayi Bayan ta bashi peck a kumatu ya fice saboda kukanta na karyar mishi da zuciya. Yana Zuwa suka wuce, kamar ko da Yaushe seda suka kai su Ahmad school kafin suka wuce, Sulaim Ya fada cikin muryar daukar hankali, Dago kanta tayi ta dubeshi tace Na'am. Kallonta yayi Yana tantamar Abinda zai fada mata amma yana ganin is high time ya kamata ya fada mata. Jin yayi shiru yasa ta maida kanta gefe Sede abinda kunnuwanta suka jiyo mata yasa cikin hanzari ta dubeshi daidai lokacin da yayi parking don tabbatar da furucin daga bakinshi ne ko kuwa, kallonshi take kamar yadda yake kallonta, Sede kowa da Irin wanda ke cikin idanunshi. idanunta sunyi haske gashi ta bude su wanda hakan yasa yaji ilahirin jikinshi ya mutu, a hankali ya bude Baki yace Ba se kin amsa ni yanzun ba, I want to you to think over it. Amma ki dauke kasancewa ta cousin dinki ki dauka ni Baki sanni ba kawai na ganki ne nace *INA SONKI, ZAKI AURENI?* Da sauri ta kalleshi mamaki fal fuskarta, a take wani murmushi ya kwace mata, idanunta cikin nashi tana jin wani nishadi na daukarta se kuma ta sauke idonta a hankali kafin ta lalubi murfin motar ta bude ta fice dukkan jikinta a sanyaye. Yaya Yana sonta? Tambayarta yake zata aureshi? Yana son ta completing puzzle din da ya kasa? farin ciki se take jin tsoro Yana shigar ta, Me yasa bata amsa mishi ba. Tafiya take a hankali Cikeda nutsuwa ta isa class zuciyarta cunkushe haka kanta yayi mata nauyi Tana son tayi tunanin dalilin da zaice yana sonta. Can bayan class ta zauna ita daya saboda yau bata da raayin jin lecture din gaba daya, Tana nan Zaune taga shigowar Aimana hakan yasa tayi saurin Dukar da kanta dan kar ta ganta, Seda ta zauna sannan ta dago kanta Sega Khairi sun shigo itada roommate dinta wata Amina, bata ga shigowar Khulthum ba kawai ta hango ta acan gefe itada wata Maimuna suna hira. Hakan ya tabbatar mata Khulthum tayi nisa Tunda ta Fara ma'amula da yarinyar saboda tayi kaurin suna cikin faculty akan iskanci kuma yarinyar ta samu kyakyawan backing na lecturers din da take bi, to dama idan Khairi na basu labarin yadda yarinyar take abu a hostel se Khulthum tana kareta OK gashi yanzun tayi joining dinsu. Sagay ne dasu kuma very strict mutumin yake Tunda ya shigo class din yayi tsit, itama shiru tayi hankalinta Baki daya baya cikin class din tayi nisa sosae gurin tunani tabbas Tasan tana son Junaid so kwaya daya tak nashi ne amma bata taba tunanin he feels the same way ba, bata taba wannan tunanin ba. Ji tayi an buga table din dake gabanta hakan yasa ta dago da sauri, Sagay ne a gabanta ita bata san yazo ba ma kwatakwata ba she was deep in thought. Cikin karaji yace Stand up and get out of my class ! Babu musu ta mike bata ma ce mishi ko yayi hakuri ba saboda tasan shi office din Junaid, suna yawan haduwa. Jakarta ta dauka ta fice baki daya daga class din sede tana fitowa sukai kicibis da Junaid wanda yake kokarin wucewa. Tsayawa tayi kanta a kasa gabanta nata faduwa, shima kallonta yayi yace Ina zakije? Kanta ta girgixa tace Koro ni yayi? Me kika Yi? To anan tayi shiru don batasan me zatace mishi ba, bata concentrating ko kuwa? Ajin ya nufa hakan yasa tabi bayanshi suna zuwa yayi knocking dan ya Riga ya kulle kofar. Budewa Junaid yayi ya tako har gaban Me Sagay, da sauri ya sakko ya mikawa Junaid hannu suka gaisa Cikeda girmamawa don he seniors him. Kallon kofar yayi ya yiwa Sulaim alamar ta shigo, aikuwa ta shigo tayi kicinkicin da fuska, kallonta Junaid yayi yace I'm sorry na shigar maka abin class dinka. Kanshi ya girgixa yace Ba damuwa sir, she wasn't concentrating that's why na Kore ta amma taje ta zauna. Kallon Sulaim yayi yace Go and sit down. Kanta ta gyada tace Thank you sir Batareda ta kalli Junaid ba ta wuce gefen Aimana ta zauna amma da ta Fara kokarin concentrating se ta koma tunanin Junaid haka period din ta kare bata tsinci komai ba. Ita a karan kanta tayi tunanin idan Junaid yace yana sonta wanne irin farin ciki zata shiga amma se gashi tsoro ya hanata sakat, ta kuma rasa tsoron da take amma tana jin kada shima ayi irin ta sauran mazan. Babu yadda Aimana batayi ba akan taji abinda Ke damun Sulaim din amma fir taki, suna nan Zaune junairu ya kirata, seda taji gabanta ya fadi kamar bazata dauka ba se ta dauka ta kasa magana se shi ne yace Kizo office Ina jiranki. Sauke wayar tayi tace da Kuzo muje office din Yaya. Mikewa sukai dama tuntuni Khairi ke mitar dama Dr Junaid ne Yayan amma ita ba'a fada mata ba. Dariya kawai Sulaim tayi tace Gashi yanzun kin sani. Suna tafe Aimana tace Wai ni Khairi ya akai kika san tsakanin Khulthum da Salim ne? Tabe Baki Khairi tayi tace Rabu da yan iska, kinga ta bi Sahun su Maimuna ko? Sulaim tayi dariya tace Ke Khairi ina ruwanki? Meye naki haka ta zabarwa kanta, nima fa na gansu a see sweet am sure ranar da ya bata lift suka hade. Kai Aimana ta girgixa Cikeda mamakin Khulthum tace Ban taba kawowa zata iya abinda tayi ba, Allah ya shirya kawai. Daga haka suka rufe shafinta suka fada hirar idanun Sulaim lokacinda Sagay ya koreta, Kinsan yadda na tsorata kuwa? Har cikin kaina Seda naji ihunshi. Aimana tace Tambaya ya dinga jero miki Ke kuma se murmushi kike kamar wani yayi proposing. Dariya suka sakeyi hakan yasa Sulaim jin dadi dadi a ranta, suna isa suka shiga dukkansu suka gaisheshi ta nuna musu kujerun suka zauna, Inda yake ta nufa ta zauna kujerar dake facing dinsa tace cikin sanyin murya Tace Yaya ina yini. Aje pen din hannunshi yayi yace Zauna mana. Zama tayi cikin nutsuwa wanda yake burgeshi yace Se 4 zaku tashi? Kanta ta gyada tace Eh. Key din motar ya mika mata yace Gida zan tafi, ki taho kawai. Kafada ta girgixa tace Kaje da ita ni zan biyo Aimana. Sure? Ya tambaya murmushi kwance a Fuskarshi yau Yana jin shi daban da kowa Yana jin tamkar babu Wanda ya tashi da saa kamar shi a wannan ranar. Itama ganin yadda yake ta murmushi yasa ta sake jikinta, ranta fal farin ciki duk wannan fear da take ciki dazu yanzun babu kuma in dai zata cigaba da ganin tarin farin ciki a Fuskarshi tana ganin babu abinda zai hana ta kasance tare dashi har abada. Junaid Suna fita ya shafa kanshi tareda mikewa ya dauki abinda zai dauka ya cewa messenger dinshi duk wanda yazo yace dashi ya wuce gida. Yana shiga motarshi ya fice Seda ya biya ya dakko yaran kafin ya nufi gida haka kurum yake jin something is not in place Amma ya kasa figuring me Nene. Haka suka isa gida sunata tsalle shikuma Yana dariya, yaran kansu are happy Amma a haka Subay'a ke son tafiya ta Barsu. Bai tarar da ita a parlor ba, se kawai ya wuce daki, Dama suna shigowa Laraba ta karbesu Don Yi musu wanka, seda yayi wanka yayi sallah kafin ya nufi dakin subay'a amma Tun Daga parlor gabanshi ya fadi, ta canza curtain Zuwa wanda idan zata yi tafiya take sawa, sofas dinta ta rufe da ledojinsu, da sauri ya shiga bedroom dinta not wanting to believe abinda zuciyarshi ke fada mishi, babu bedsheet kan gadon, wardrobe ya bude important kayanta duka basu gurin, Dayan bedroom din ya tafi nanma same case. Da sauri ya fito ya nufi kitchen for the first time, Atika na hada salad taji kamshin turare hakan yasa ta juo da sauri se ganin Junaid tayi, gaba daya ta duburburce don Bata taba ganinshi a kitchen ba, Me zaa baka? Ta tambaya gabanta na faduwa, kallonta yayi yace Ina Subay'a taje? Kanta ta girgixa tace Nima bansani ba amma sun fita da kaya itada yayarta amma gashi. Ta ciro paper daga Apron din jikinta ta mika mishi, cikin hanzari ya karba sannan ya fice Zuwa parlor, Baki daya yasan raini kam subay'a ta gama ko bai karanta abinda Ke cikin paper ba yasan ta tafi Tunda yaga dakinta a haka. _Dear, I'm sorry da Abinda zaka tarar amma babu yadda zanyi tafiyar ta zama dole. Ka yafe min zan kula maka da kaina sannan zan dawo gareka. I missed you. Subay'a_ Daga haka ya dafe kanshi wanda ke barazanar tsagewa saboda yadda kwakwalwar shi ta cunkushe, hannunsa ya saka ya rufe fuskarsa wadda tayi jawur saboda tsananin bacin rai. Yana nan Zaune Muhammad yazo yana kukan Mimi. Wannan ya kara daga mishi hankali ga har lokancin uku batayi ba Balle yasa ran dawowar Sulaim. Atika ce Taxo ta daukeshi Cikeda mamakin halin da ta samu Junaid. Shima dakinshi ya koma ya kwanta bayan ya samu Muhammad yayi shiru Ahmad kuma yayi bacci, ya dade yana tunanin abinda zaiyi Amma ya kasa tuno Abinda ya dace yayi saboda baya son yanke hukunci cikin fushi amma Wallahi yasan har Subay'a ta koma ga Allah bazata manta wannan abin da zai mata ba. Wasa wasa haka Junaid ya zauna a daki shi daya zuciyarshi na tafarfasa a haka akai sallar laasar ya fita zuwa massallaci kafin ya dawo Sulaim ta dawo, Tana shigowa Tajiyo kukan Muhammad, da sauri ta nufi kitchen dan can ta jiyo kukan, Tana zuwa ta karbe shi daga hannun laraba tana girgiza shi tace Waye ya taba min babyna? Mimi Ya fada Yana kara Sautin kukan shi, kallon Atika tayi tace Ina Mamansu ne? Atika tace Tun safe akazo aka dauketa. Juyawa tayi ta fita tana mamakin Subay'a she's never a good mother neither a good wife. Komawa tayi parlor tare da Lallashin shi Sega Junaid da Ahmad sun shigo, kallonshi tayi taga wani tashin hankali kwance a Fuskarshi wai a hakan ma ya ragu kusan 70cent Bayan yayi sallah tareda kai kukanshi ga Allah, se taji gaba daya ranta ya baci har Seda ta saki tsaki. Zama tayi shima ya shigo ya zauna ya kalli Muhammad dake jikinta yace Kin dawo kenan? Kanta ta gyada tana patting bayan Muhammad se yaji inama ya zama Muhammad ko ya samu wannan care din shima. Na dawo Yaya, ya gidan? Dan murmushi yayi mata yace Alhamdulillah, gobe zanje kaduna akwai sako? Kanta ta dago da sauri tace Zanje nima Murmushi yayi a ranshi Yana ganin wannan yarinyar will kill him tamkar bashi bane dazu ya rasa inda zai tsoma ranshi amma daga ganinta har ya fara dawowa hayyacinsa. A'a kiyi hakuri next week zan kaiku kinji? Turo mishi Baki tayi tana bubbuga kafa hakan yasa ya tsira mata ido kamar bazai dauke idonsa ba, ganin haka yasa tayi saurin daidaita kanta ta Mike zuwa dakinta tana jin tamkar tafi kowa saa a rayuwarta. Washegari Seda ya kaisu makaranta kafin yayi mata sallama yace Gobe Inshaaa Allah zan dawo, kinji? Kanta ta gyada tace Tohm Allah kaemu, safest journey a gaida su Mami. Zasuji dear, kuma haka zan tafi babu ko kallon da zan na tunawa dashi, babu something sweet? Hannunta tasa ta rufe fuskar ta tana dariya, a hankali kamar me rada tace I will miss you. Matso da kunnenshi yayi saitin bakinta yace Kikace me? I'll miss you..... Wata kayatarciyar dariya ya saki yace I'll miss you more *my Dove* Jin yace dove yasa ta kalleshi se yayi dariya yace Se munyi waya. Fitowa tayi tana jin farin ciki na ratsa zuciyata tamkar ta tashi sama, Yaya Junaid! Karfe goma na safe ya isa kaduna seda ya gama dukkan abinda zaiyi sannan ya nufi gida, luckily Mami da Baba suna gida. Mami ta kasa boye murnar da take ciki tare sukai breakfast sannan suka zauna hira dukkansu. Junaid ya rasa ta ina zai fara se can cikin damuwa ya sanar dasu halin da ake ciki, Baba couldn't say a word se Mami ce ta Fara salati tace Wani hukuncin ka yanke? Sakk [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 33 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Da sauri Ja'afar ya juya don komawa dakinshi saboda maganar da yaji Junaid ya furta tamkar kibiya haka ta sokar mishi zuciya, bai taba kawowa zaiji Irin wannan mummunar maganar ba kenan yayi wasa da damarshi, kenan Abinda Sulaim ta dade tana fada mishi akan Watarana yana gani zata zabi wani over him. Hannunsa ya cusa kanshi wanda yake Cikeda gashi da ake bashi kulawa tamkar na mace. Me yayiwa rayuwar shi kenan? Me ya amfana a rayuwarshi. Ya sani yana da 'yanmata amma son gaskiya na Sulaim ne itakadai take da features da yake bukata Daga gurin matar da zai aura se gashi ya luza akan fushinshi na banza wanda ya sani laifinshi ne amma yaki waiwayar ta Yana takamar tana mishi son da bazata jure rashin shi ba. Kujerar dake kusa dashi ya fada kamar me shirin kuka saboda yadda zuciya take tafarfasa, yasan ko Yana hauka bai isa karawa da Junaid ba a fagen neman mace, Abu daya zai nunawa Junaid shi ne yarinta Amma Bayan haka bai da komai ba kuma da Abinda zai tunkara Sulaim dashi. Ya tuno lokutan da take yawan ce mishi *If you love someone, make sure you hold that person tight but if you didn't, others will surely do!* ga maganarta ta tabbata, ta samu Wanda ya fishi shi kuma ya tashi a tutar babu, he has completely messed up! Se muce Ja'afar ayi hakuri! Baba ya bude Baki da niyyar magana farin ciki fal zuciyarshi har ya gagara boyewa seda ya bayyana kan Fuskarshi, Mami tayi saurin fadin Aure kace Junaid? Seda gabanshi ya fadi Don Mami hardly ta kirashi da Junaid, idan ta furta to tabbas abu yayi tsamari. Kanshi a kasa yace Eh Mami aurenta nake son Yi. Saboda 'yar gaban goshi bata nan, saboda kana son amfani da ita ka hukunta matarka, ai Junaid har yanzun Kai ba namiji bane, bakayi wayon rike mata biyu ba Tunda har ka kasa controlling mace daya, se biyu. Kanta ta girgixa ta cigaba da fadin 'Yata Sulaim ba wadda zaayi auren huce haushi da ita bane, don haka ka manta da maganar auren ka jira matarka ta dawo. Ita kanta Mami ta tsorata da yadda idanun Junaid suka koma amma ta dake, ta dauke idanunta kar ma tausayinshi ya rinjaye ta, bawai tana kin abin bane tafi kowa farin ciki amma dole ta nunawa Junaid laifinshi saboda ya sakar ma Subay'a da yawa, idan Jabir ne bazai taba haka ba. Idanunshi jajur tamkar jini haka cikin wani tashin hankali wanda ya baibaye zuciyarshi Lokaci daya saboda jin furucin Mami, amma ya sani shi yake nema dole ya Dukar da Kai, cikin nitsuwa da kwantar da murya yace Mami Wallahi bazaki taba kamani da wofantar da 'yarki ba, kinsani mutumin da Daddy Aminu da Anty Zahra suka nuna suna so ma bazan bari a cutar dasu ba Balle gudan jininsu Sulaim kiyi hakuri. Kanta ta kawar gefe tana jin yadda zuciyarta Ke tausayawa Junaid, Ka bar maganar kawai. Juyawa yayi ya dubi Baba with pleading eyes akan ya saka baki amma ya Kaudar da kanshi don suna yara idan Mami ta hana abu gurin Baba suke zuwa haka shima idan ya hana amma yau abin Yana neman juyewa. Ko cikin tunaninshi bai taba tunanin cewar zai kawo proposal din auren Sulaim ayi declining amma gashi yayi. Mikewa yayi saboda Baba yace mishi yaje ya huta. Babu musu ya Mike ya nufi masaukinshi dake cikin gidan, Tun zuwanshi aka gyara hakan yasa ya wuce bayi Don yin wanka. Gaba daya zuciyarshi tamkar ana gobara haka yakeji , kenan rayuwarshi ta koma idan yana neman abu bazai samu ba a wannan lokacin. Ana gama lectures suka fito kamar Koda Yaushe dukda yanzun sun zama su uku don tuni Khulthum ta cire kanta daga garesu, to ba kullum take Zuwa ba ma yanzun a sha ruwan tsuntsaye take wa Zuwa makarantar. Aimana tace da Sulaim Bayan sun Yi sallama da Khairi ta wuce hostel. Kwana biu duk kin zama wata iri, Meye ne Ke damunki dan Allah? Kallonta Sulaim tayi tace Babu komai Aimana, kawai Kwana biyu Bana jin dadi ne. Dama tasan bawai zata fada mata bane amma dole Tunda tare suke. Kodai Salim dinne har yanzun? Wata muguwar harara ta maka mata tace Lallai ke dinnan, Salim kuma ni Sulaim ce ba Khulthum ba. Dariya tayi tace Haka ne kam, kinga muyi sauri saboda Yaya Nu'uman bazai zo ba. Hakane kinga Yaya Yaje kaduna gashi bai ma kira yace min yaje ba. Sulaim ta fada fuskarta dauke da damuwa. Kallonta Aimana tayi amma batace komai ba har suka samu napep suka shiga zuwa gida. Koda Sulaim taje gida duk tunaninta zata tarar Subay'a ta dawo amma ga mamakinta kofar parlonta a kulle, yaran suna zaune suna kallo suna jiyo sallamar ta suka taho tarar ta. Rungumarsu tayi tana shafa kansu tareda tambayar kowa school kafin suka raka ta daki Don yin wanka. Tana fitowa taga kiran Imratu ita Duk tunaninta Junaid ne Tunda call dinsa take ta expecting amma shiru, dauka tayi ta placing wayar a speaker saboda tana shiryawa. Da wasa da dariya kamar yadda suka Saba suka gaisa sannan Imratu tace Ke ashe Hajiyar gidanku Cyprus ta tafi karatu? Cikin rashin fahimta Sulaim tace Wace hajiyar gidanmu kuma? Dallah, Subay'a nake nufi. Idanu a waje Sulaim Cikeda mamaki tace Cy what? Dan Allah da gaske. Wallahi, yanzun ya kira Soja yake fada mishi wai ya hanata Bayan ya tafi office ta tafi. Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Yaya Imratu Nikam a rayuwata I've never seen a bad mother and wife kamar Subay'a ba. Ayya Shiyasa Yaya jiya Tunda na dawo gidan daga school naga akwai damuwa tattare dashi. Ba dole ba Sulaim, bari kiji abinda yasa na kiraki, kinga a yanzun babu Abinda Papan Ahmad ke bukata Irin support, inason as much as u can kiyi supporting dinshi ki bashi kulawar da ya rasa, ina son ki zame mishi sanyin idanuya Kina jina? Baki Sulaim ta turo tace Kai! Ni kuma a wa? Se kace matarshi. Tsaki Imratu tayi tace Matsala ta dake kenan taurin Kai, ai ya fadawa soja cewar yayi miki proposing kuma bana son ki yaudare kanki kina son Papan Ahmad.... Ni kuma? Shi ya fada miki? Lallai ma Wallahi ba wani. Seda Imratu tayi dariya yadda take so sannan tace Hakan da kikayi ya tabbatar min zargin mu, Papan Ahmad bai san Kina son shi ba amma shi Yana miki so me suna so, me tsanani wanda ya gaza boyuwa. Inason Kiyi amfani da damar da Allah ya baki, ki bashi Abinda ya rasa cikin rayuwarsa..... Kenan zan aureshi ba don so ba sedan Maye gurbin wata? Dama shi yasa yace Yana sona jiya saboda matarshi ba Tanan? Kai Imratu ta dafe saboda batai tsamannin abin zaizo haka ba. Shekarunki Nawa sulaim? Last month nake nineteen. Ke Yarinya ce har yanzun, kiyi tunani sosae akan maganar mu, kuma inason Kisa a ranki ko da Subay'a ko babu ita Junaid na sonki, he proposed jiya without knowing ta tafi, ki sani ke kadai ce hope dinshi a wannan lokacin idan kika barshi then Bana tunanin Kinyi mishi da kanki adalci. Kafin Sulaim ta bata amsa ta katse call din, kasa tashi tayi daga gurin ta xurfafa tunanin maganganun Imratu, tabbas ko haka bata faru ba Tana jin tausayin Junaid tausayi me tsanani na gasken gaske wanda hakan shi ne Abinda ya fara saka sonshi cikin zuciyar ta, to yanzun bazata iya ba kenan? Abubuwa nawa Junaid yayi mata, wani Irin sacrifice ne bai mata ba, wannan kadai ya isa ya tabbatar mata Son gaske yake mata. Tun rasuwar Daddy dinta komai nata shi ke daukar nauyinsa, cin ta, sha, sutura da karatun ta. Ita kuma se ta kasa bashi farin ciki, ta kasa amsar soyayyarshi. Da sauri ta girgixa kanta, ta Mike jiki a matukar sanyaye ta nemi shirt da dogon wando ta saka sannan ta rufe kanta da hula. Wayarta ta dauka ta kira Imratu tana picking murya a sanyaye tace Yaya Ya zanyi to ? Murmushi Imratu tayi tace Kada kice mishi kin amince a baki, ki kyaleshi amma ki bashi kulawa yadda ya kamata. Kin gane? Kanta ta gyada tace Inshaaa Allah. Daga haka sukai sallama ta koma ta zauna ta Fara neman layin Junaid, cikin sa'a ta shiga Sede yana kallon "Dove" kamar yadda ya saka mata tana kira amma ya kasa picking saboda har lokancin Samasama yake jin kanshi kuma muryarshi da yayi magana zata nuna halin da yake ciki. Ganin baiyi picking ba yasa ta hakura kawai Amma hankalinta yana gunshi. A haka har dare yayi baiyi returning call din ba. Seda su Ahmad sukai bacci sannan ta tuna da safe Jawad yace mata yana kaduna Don haka ta Fara kiranshi. Friend Yaya Junaid Yana nan? Ta tambaya yana picking, Kya Bari mu gaisa ai, Yana dakinshi na kai mishi ne? Da sauri tace Yes please! Kashewa yayi ya nufi dakin da Junaid yake, Yana zaune kan carpet ya kurawa screen din system dinshi ido ga abinci Kan tray an jera Amma bashida appetite din ci. Dago idonshi yayi Wanda ya fara washewa Daga jan da yayi ya dubi Jawad da ya zauna gefenshi yace Sulaim tace na kawo maka waya zatai maka magana. Kanshi ya gyada cikin sanyin murya yace I'll call her. Seda safe. Sallama yayi mishi ya tafi shi kuma ya kashe system din ya koma gado don kiranta, har ta gaji da jira ta Fara chatting kiranshi ya shigo, wani sanyi taji ya mamaye dukkan jikinta babu shiri ta saki murmushi sannan tayi picking. My Dove, I'm sorry Dukda bata san dalilin da yasa yake kiranta da Dove ba, amma she have already fallen for the name! Bakinta ta turo tace Bakaga call dina ba tun dazu? Baka kira kace kaje lapiya ba, Muhammad suna ta tambayarka. Murmushi yayi me sauti Wanda seda Tajiyo hakan yasa ta sake fadin Murmushi kakeyi ma ko? Hannunsa ya rufe bakinsa dashi yace Come-on Dove nace I'm sorry ko, nazo na samu abubuwan da suka cushe min Shiyasa. Duk yaran sunyi bacci? Kanta ta gyada tace sunyi bacci, ina Mami Mami tayi bacci, smile mana A'a Ta fada Tana bata fuska, hakan yasa yayi dariya a hankali wadda ta ratsa sulaim har Seda ta sauke ajiyar zuciya. Haka sukai taba hira kafin yace Kiyi bacci, nayi magana Za'a zo daukarku gobe Inshaaa Allah. Nima very early zan dawo. Good night? Kanta ta gyada kamar yana kallonta tace OK, night. Daga haka sukai hanging kowanne zuciyarshi fes, musamman Junaid da yaji hankalinshi ya Dan kwanta Don Yana ganin bazai samu matsala da ita ba, Mami ce damuwarshi. Washegari bakwai ya fito cikin shirin tafiya, a parlor Baba ya samesu suna kallon news din safe a Aljazira, seda suka gaisa yace Zan koma Kano. Baba ne yace Da wurwuri haka? Abinci fa? Kanshi ya girgixa yace Se naje zanci. Kai Mami ta girgixa tace Zauna yanzun Za'a kawo breakfast. Bai musa mata ba haka ya tankwashe kafafunsa Yana kallon news dukda hankalinshi Yana kan maganar da sukai jiya amma su kuwa hirarsu suke tamkar basu san dashi a gurin ba. Ba a jima ba aka kawo breakfast babu musu yaci sannan ya Mike yace Zan wuce se next week zan kawo su duka. Baba yace Allah ya tsare Mami tace Ayi tuki a hankali, ka kula da kanka. Murmushin jin dadi yayi sannan ya aje musu envelope ya kara musu sallama a ranshi Yana fadin Mami is using son da nake yiwa Sulaim ta hukunta ni akan tafiyar Subay'a. Unexpected right? Mami ta bamu mamaki har ni kaina? Na aza zata amince Amma taki ga Baba yaki magana. So Wacce shawara zaku bawa Junaid? Yana jira.......see you later Team #Junaid and Sulaim# Shatuuu ♥️ [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 34 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad CYPRUS Kwanaki bakwai kenan da saukarsu Subay'a birnin na Cyprus, tuntuni aka kama musu Dan apartment me dakuna uku dake Sulma itada mijinta sukaje shima zaiyi wani course a can. Se apartment din da take yana facing nasu, kuma bashida Nisa zuwa makarantar da suke. Tunda suka sauka a garin gaba daya hankalin Subay'a ba'a kwance yake ba, Dama da safe jirginsu ya sauka Don haka suna zuwa suka Yi 'yan gyare gyare suka kwanta dan huce gajiya amma Subay'a se juyi kawai take ta kasa baccin, hankalinta ya tafi akan Junaid, ko me zai yi bayan ya tarar ta tafi, ko ina yaranta suke. Haka dai tayi tayi har bacci ya samu ya dauketa. Se dare suka fita dan ganin gari, to a Wannan ne ma zamu ce ta saki jikinta Don garin ya burgeta Sosae da sosae, se eleven suka dawo nan suka baje a parlor suka ci abincin kowacce ta kira mijinta ganin haka yasa Subay'a sulalaewa zuwa dakinta Don nufin kiran Junaid sede tsoro ya hanata yin hakan. Washegari suka shirya kowacce ta nufi department dinta don Fara daukar lectures amma Subay'a babu Abinda take ganewa bata fahimtar komai dukkan hankalinta yana Nigeria, ga wani ciwon mara da takeyi me tsananin gaske wanda iya shi kadai ya isa hana mata nutsuwarta. Kafin suyi Kwana uku a garin ta rame tayi fari, tayi xuruxuru se idanuwa a warwaje. Abinda ya daga mata hankali Tunda Yaya Suhaila ta tambayeta Abinda Ke damunta Tace babu basu Kara komawa ta kanta ba, suka cigaba da sha'anin gabansu. Hakan yasa ta kulle kanta a daki ranar ta dinga kuka saboda ta riga ta gano kuskurenta, tasan da Junaid ne bazai taba barinta a Wannan halin ba amma gashi yan uwanta da suke bata da kamarsu sun manta da rayuwar ta, basu damu da ita ba a cewarsu ta dagawa kanta hankali saboda namiji kilan yana can ya manta da ita gaba daya gwara ta saki jikinta kawai. Duk ganin hakan da take Kara daga mata hankali yake yasa tayi wanka a daddafe ta shirya cikin abaya baka tayi rolling ta fito inda ta tarar Suhaila na waya da Fannah, Tana fitowa taji Suhaila tace Ga Mimin nan ma. Mika mata wayar tayi, Subay'a ta karba suka gaisa da Fannah tana ta bata Sautin abubuwan da take so, Subay'a ta mata alkawari sannan ta kashe wayar tace da Suhaila. Zanje gurin Sulma. Me yake damunki ne, kinga yadda kika rame kuwa? Salima wadda fitowar ta kenan daga daki ta iskesu tsaye. Baki Samiha ta tabe tace Tace Sulma zata fadawa damuwarta, Kinsan ita kadai ce me hankali cikin mu. Salima ta ja hannunta suka koma kujera tace Fada min Menene. Hawaye a hankali ya fara gangaro mata Daga idanu, se kuka me Cikeda nadama me tsanani, me yasa tabi son zuciyarta ta taho gashi ta kasa samun farin ciki Koda na awanni ne. Sosae ta dinga kuka hakan yasa Suhaila jikinta yayi sanyi ta dawo ta zauna Itama suna lallashinta. Amma ta kasa daina kuka ana haka sukaji sallamar Sulma hannunta na rikeda na Amna yar Kimanin shekara da wani abun. Tunda suka amsa tasan babu lapiya, hakan yasa ta shigo da sauri sede ganin 'yar uwar da tafi soyuwa cikin zuciyar ta na kuka yasa Gaba daya taji hankalinta ya tashi, gefenta ta zauna ta kasa furta komai se patting bayanta da take a haka har tayi shiru, Salima tace Kuje daki ta fada miki abinda yake faruwa. Tare suka shiga daki su kuma suka koma dakunansu zuciyoyinsu babu dadi, haushin kansu sosae sukeji na barinta da sukai cikin damuwa for almost 3 days kenan, Anya su din sisters dinne kamar yadda take daukarsu. A daki Subay'a ta gyara zama ta kwashe duk yadda sukai da Junaid ta fadawa Sulma tana kuka Marar dadin saurare, gaba daya wuta ta daukewa Sulma don Bata taba tunanin wautar Subay'a ta Kai wannan extent din ba, Amma yanzun ba lokacin putting blames bane mafita shi ne Abinda zasu nema. Cikin nitsuwa Sulma tace Sister bakya neman shawara, Tunda yace ki hakura me yasa zaki taho? Kinsan fushin Allah kuwa akan kin bin miji, he said all this to you and you left without his consent? Ya salam! Sosae Subay'a ke kuka tace Na gane kuskure na sister, Nayi dana sanin abinda nayi don haka Nigeria zan...... Bata karasa ba saboda wani sharp pain da ya turnuke mata mara, hakan yasa ta rike cikin tana fitarda wata Irin Kara da ta jawo hankalin su Salima dake dakunansu, a guje har suna Karo da juna suka nufi dakin Subay'a wadda Ke durkushe jini yace a bashi guri ya nuna nashi basirar, suna bude kofar sukai karo da Sulma wadda Ke kokarin fita kiran su, ba wanda yayi magana saboda firgici, Sulma ta Fara kiran Daddyn Amna, Salima ta kira ambulance, Suhaila kuwa tana kokarin hada kaya. Kuka Sulma take sosae saboda yadda Subay'a ke axabtuwa. Within wani Lokaci Daddyn Amna ya iso kusan tareda ambulance din akai Asibiti da ita. Anfi two hours kafin aka basu izinin shiga gurinta, Tana kwance idanunta na digar da hawaye, jini da aka karbo daga Lab Yana jikinta haka suka sameta suna mata sannu don nurse din ta tabbatar musu idanunta biyu. Fita Daddyn Amna da Sulma sukai Don zuwa enquiring akan maganar subay'a. Seda suka zauna doctor yayi musu bayanin ciki ne da ita na wata daya da kwanaki ya samu zubewa, sunyi mata wankin ciki sannan yayi directing dinsu inda zasu biya bill din. Suna fitowa Sulma ta sauke ajiyar zuciya saboda dadin da taji cikin ya fita kada yazo ya shiga gararin rayuwa kamar yadda uwarshi zata jefa shi a ciki, itama uwar batasan halin da take ciki ba Balle dan da bai zo duniya ba ma. Honey ka kira Yaya Junaid ka fada mishi halinda ake ciki. Wayarshi ya fito da ita ya fara neman layin Junaid lokacin yana zaune a office yana magana da Ridwan akan case din auren dan duk yadda Junaid yake tsamannin maganar ta wuce haka, Duk yadda yaso Mami ta fahimci inda ya dosa Amma taki hakan yasa duk hankalinsa baya jikinsa, ya rasa abinda Ke mishi dadi, the only moment dayake samun nutsuwa shi ne idan yana tare da Sulaim din to yakan manta da cewar rabasu ake son Yi, kullum tamkar son ta ake Kara mishi cikin zuciyarshi, abubuwan da a da suka fi karfin shi yanzun a saukake yake samun shi, hakan yasa sonta ya mishi mugun kamu, in har ya dawo gida to damuwa ya gama samunta Sede idan kebewa yayi a daki Amma Sulaim da gaske take ta kwace shi, Ta shiga rayuwar shi ta bashi yadda yake so, Mami ce kawai matsalar a Wannan lokacin itama ya rasa ta inda zai shawo kanta kuma baisan saka wani cikin maganar yafi son sui ita dashi. Jabir ne ma ya shiga amma ta ce ya fita ba huruminshi bane hakan yasa ya hakura. Seda Daddyn Amna ya kira sau biyu sannan Junaid yayi picking, jin muryarshi yasa ya saki jikinshi sukai magana anan yake sanar dashi halinda Subay'a take ciki, Yanzun ya zaayi kenan? Ya tambaya bai masan abinda yake ji akan abinda yaji ba Tana kwance amma jikin da sauki yanzun. Kanshi ya gyada yace Ka Turomin account details dinka, zan tura maka bill din asibitin se sako da zaka bata. Inshaaa Allah zan turo maka. Bari akai mata wayar. Bai amsa shi ba ya kashe wayar, me zaice mata ko ita me zatace mata. Bai tashi a gurin ba seda ya tura komai, Tunda ciyarwar ta akanshi take dole ko ina taje Tunda da aurenta akanshi dole ya bata abinci. Kwanaki uku tayi a Asibiti sukai discharging dinta ta warke garau se tarin damuwar da take ciki don ta samu sakon Junaid a hannun Daddyn Amna, Tana dawowa Tace da Sulma Nigeria zata koma amma hajiya tace Allah ya bata saa, daga Wannan kuwa se ta hakura abinta ta dangana ta Fara fafutukar kiran Junaid amma Tunda yayi picking sau daya yaji muryarta, yayi blocking contact dinta don har yanzun fushi yakeyi da ita kuma bai zo gabar yanke mata hukunci ba. Sorry for d little page.... We meet later Inshaaa Allah! Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 35 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Gabaki daya yau dinnan jinta take tamkar tafi kowacce mace sa'a a Wannan ranar, jinta take tamkar something great awaits her, hakan yasa ta Mike ta daura towel don yin wanka ta Ajiye wayar ta, ta nufi bayi. Ta jima tana wanka tayi sitbath don yau dinnan jinta take samasama gwara ta kalkale ko ina. Tana fitowa ta Fara gyara jinkinta da sababbin mayukan da ta Fara amfani dasu, tayi kyau se sheki take tana daukar ido, ta daina bleaching ta zama babbar yarinya wadda zamani ke yayi, Dama tana bleaching saboda rashin kudi yanzun kam kudi Sede ka kalla amman ba dai ta kalla naka ba haka abin yake. Saffa saffa tayi kwalliyar tata saboda yanzun ta Fara blending da 'yan gayu ta yarda da abinda Aimana tace mata yan gayu basu kwaliyya ta hauka ta gani duk lokacin da zasu fita se on special occasions. Trolley ta bude ta Nemo wani dandatsatsen lace na idon duniya dinkin fitted gown me kyau, ta saka a jikinta. takalmi da jaka ta saka bayan ta kalli katon mirror data kafe a dakin. Tana fitowa call din Haris ya shigo, wani abokin Ashir ne wanda ta biya shi Yana fada mata move din Ashir don kome zatayi tafi son tayi Abinda yafi nashi, tafi son taji wanne step yake takawa hakan yasa ta bashi wannan aikin Haris ya ake ciki? Ta tambaya kanta tsaye Bayan tayi picking, Seda ya gama mata kirarin da ya saba sannan yace mata Wani satin zai wuce Texas, wani abokin babanshi yayi sponsoring dinsa yaje yayi Chemical Engineering. Idanu ta bude tace How genuine labarin nan yake? Murmushi yayi yace 100%. Kanta ta gyada zuciyarta Cikeda hassada tace Karka damu, nagode. Daga haka bata jira cewar shi ba tayi cutting layin, tareda kaiwa iska naushi cikin takaici don Abinda take tsananin son gani shi ne Ashir ya kaskanta ita kuma tayi gaba amma babu komai jikinta na Bata akwai babban abu dake jiranta. Hakan yasa ta daidaita kanta ta fito Zuwa tsakar gida, Mama na Zaune tana yiwa Amira tsifa, Aisha na girki se Amir dake gefe yana duba books dinshi dake ya fara zuwa school shima. Kuma Tunda abin ya faru Baba Ke iya bakin kokari wajen ganin ya kawo abinda zasu saka cikin bakinsu, yasan barin Khulthum da yayi tana ciyar dasu shi ne Abinda ya kashe shi, ya zubar mishi da kima da darajar shi, ya Jawa yaron kunne akan ko me zata kawo Kada wani ya ci, su barta da tsiyar ta akwai ranar nadama. Sede akwai abu daya dake hunting dinsa yana ganin ko yaya ne akwai gazawar shi wajen lalacewar rayuwar Khulthum Tunda shi yayi alkawarin kula da ita Tunda ita din marainiya ce amma here she's ya tabbatar abinda yake zargi akan yarinyar kusan gaske ne amma ya kasa samunta da maganar. A pounded yam joint dake lodge road anan ne inda Khulthum ta hada AP dinta da Salim don tuntuni tafi karfin kwanyar Huzaifa ta wuce class din Yusuf wanda Zamu iya cewar shi ne ya fara bude mata idanu to such life amman yanzun Khulthum tafi karfinshi, ta girmi tunaninshi ta Riga ta zama abinda bai taba tunani ba. Juice kawai tayi order saboda tana jiran Salim yazo se suyi lunch tare, a hankali take sipping cikin yanga da class na mussaman da take Kara, wayarta take daddanawa tana duba latest fashion trends saboda tana son tana tafiya daidai da zamani. Tun tana enjoying abin har ta Fara gajiya da zaman baki daya ta Fara neman layin Salim Amma network ya hana communication din haka tana gani ta hakura ta cigaba da surfing cikin wayarta. Kamar daga sama ta Fara jiyo kamshi me sanyi me kuma sanyaya zuciya Yana shiga kofofin hancinta, karku manta Khulthum din da data yanxun akwai banbancin, dukda urge da take ji na sanin me turaren haka ta danne ta cigaba da Abinda take har Seda sukai wajen Mintina goma kafin Kabir yayi clearing throat dinsa yace Kinada class! A hankali ta dago fararen idanunta wanda suke rikita Maza ta aje Kan fuskar Kabir wanda ya bude hanci, baki, kunne yana kallonta ya shagala sosae. Mutane da yawa sun fadi hakan. Ta fada Tana maida kanta Kan wayarta, cikin Mintina uku Kabir ya gama assessing dinta, balle da ta kalli idanunshi ya gama hango tsantsar zulama a ciki. Murmushi ya saki yace Bari Naje Naga kamar I'm not welcomed here kamar Kina jiran wani ne. Kanta ta dago tareda kallon shi tace Ina jiran wani amma ya gaza cika alkawari bai zo ba, Kaga kenan I'm waiting for no one. A hankali yaji Tana dada fitting gurin da yake son sakata hakan yasa yace Then, ni kike jira dama, bari muyi order ko. Murmushi tayi tace Hakan ma yayi. Cikin nitsuwa suka ci abinci suka gama babu Wanda ke magana dukkansu har suka kammalla, kafin ya dubeta yace Muje ko? Kanta ta gyada tareda mikewa tabi bayanshi yayi settling musu bill sannan suka nufi wata golden Benz dake Parke a gefe, seda ta shiga kafin ya bude shima ya shigo ya fara driving Yana ta harhada kalaman da zai fada mata, Amma se yaga tamkar abin yayi wuri ya kamata ya fara tuntubar me gayya me aiki kafin. Seda ya rakata har gida, Tun daga unguwar, layin har Zuwa gidansu ya tabbatar khulthum ce kadai zata iya wannan aikin ita kadai tayi soothing abinsu, Tana da kyau na shiga taro, zamansu ya fahimci akwai turanci a bakinta, kuma babu damuwa ta waye dukda ya Lura ba wayayyiya bace tayi forcing kanta tayi blending da rayuwar da take ciki! Bayan sun rabu yayi mata alkawarin kiranta yayi mata bayanin dalilinshi, da haka suka rabu tana ta anticipation na Abinda zai kasance kuma. Yana barin gurin Khulthum ya wuce gaida don secretary Musbahu ya tabbatar mishi Musbahu na gida. Haka akai mishi iso ya shiga suka gaisa da Musbahu dake zaune yayi zurfi akan aikin shi, Seda ya kammalla kafin ya dawo kujerar dake facing Kabir yace Akwai wani move ne? Dauke da murmushi Kabir yace Babba ma kuwa, yau ka gama damuwar gwoggo sede wani abin. Wa ka samu? A ina? Cikin nitsuwa ya fayyace mishi komai ya kara da fadin Idanunta na fada maka cewar kwadayyayi ce, kuma she's no one don ta Fara Law an anguwarsu ance ta bari ta fada tarkon shedan , kaga tayi daidai da taste dinmu. Murmushi me kyau Musbahu yayi yace Abokina....... Se kuma yayi shiru hakan ya tabbatar mawa Kabir ya rasa wanne word zai mishi godiya. Sun tsara duk steps din da zasu dauka akan maganar sannan suka rabu. Ranar ta kasance Monday, karfe shida na safe Junaid, Sulaim, Ahmad da Muhammad suka dauki hanyar Kaduna, ko Sulaim Bata fada ba murna farin ciki ne fal cikin zuciyata har ta gaza boyeahi ya fito karara kowa na gani. Junaid farin cikin da ya gani yasa shima yaji duk duniya kuncinshi ya yaye, farin cikin rayuwarshi, sanyin idaniyarshi na farin ciki shi waye da zai yi bakin ciki amma dukda haka deep down inside him Yana jin tsoron approaching Mami, yana jin yau yakai karshe in har Bata amince ba to tabbas komai zai iya faruwa. Sunyi nisa sosae motar shiru babu me magana yaran duk sunyi bacci, Sulaim tayi breaking silence din da fadin Yaya Juyowa yayi ya dubeta sannan ya kara dafe steering tare dage girarshi daya yace Yaya..... Yaya.. Yaya! Shi ne kadai abinda bakinki ya iya fada, come on nothing sweet ko? Dan murmushi tayi Cikeda kunya ta rasa abinda zata ce mishi, shi kuma dariya yake kasa kasa don yasan ya kashe mata baki ba zata kara magana ba. Daga nan yace Dove. Har cikin zuciyar ta taji Wannan sunan, she loves the name without even knowing me yake nufi, tasan whatever ya fito Daga bakin Junaid daban yake kuma me ma'ana ne, a kalla tayi soyayya da mutane kusan uku amma akwai unique abubuwa a tare dashi, abubuwa da ko bai nanata son da yake mata ba tasan a yanxun Itace a birnin zuciyarshi kuma ita take Jan ragamar shi Sede bawai ta manta Subay'a bane a'a tana nan daram cikin ranta, musamman in yayi kwance kwance ya kasheta da daddan kalamai se taji kada fa Subay'a ta dawo abu ya canxa, Tana kishin Subay'a sosae me zafi ma kuwa. Kina ganin soyayyar Dana nuna miki ta sati biyu is sufficient for you ki zauna Dani? Kallonshi tayi yana driving cikin kwarewa, ta yaya zatace son da yake gwada mata bai isheta ba, ko kuma yace Bata yadda Yana sonta ba, kanta ta girgixa Tana ganin lokaci yayi da zata bude mishi zuciyarta amma tana ganin kamar Lokaci baiyi ba amma abinda take kallo kadai cikin idanunshi sonta ne me tsananin gasken gaske aciki, ga kuma tsoro wanda duk yadda taso fahimtar tsoron menene ta kasa hakan yasa ta zame mishi shoulders da zai kwanta akai lokacin bukata. *If you in d rain I'll cover u, lost I'll found u my love don't lie, E no dey lie, don't worry I'll be here and I'll catch you if u fall, I no lie, I no dey lie, give me ur hands and I'll show u which way to go, lemme be ur guide, hold on don't be afraid trust me and have some faith u be alright u be fine* Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 36 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Lokacinda suka isa gidan, shiru tamkar masu gidan basu tashi ba, se ma'aikata dake ta aikin gyara gidan. Yana gama parking ya juyo ya dubi Sulaim da take kokarin tashin Ahmad yace Ku shiga ciki, zan wuce wajen seminar din. A gaida su Mami. Murmushi tayi ta gyada Kai tareda fadin Mami zataji, take care please. I'll definitely do that Dove. Murmushinta me kyau tayi daga nan ta tashi su Ahmad suka shiga ciki shi kuma ya wuce. Da murna dukkansu suka shigo gidan, sojojin dake bakin gate suka kawo musu kayansu ciki. Tun a tsakiyar parlour Ahmad yake kwalla kiran Mami wadda ke kitchen tana kokarin hadawa Baba breakfast Don batayi tunanin zasu zo da sassafe haka ba. Fitowa tayi ta tsaya bakin kitchen tana binsu da kallo fuskarta Cikeda murmushi da murnar ganinsu. Mami! Sulaim ta fada lokacin da ta isa inda take tsaye. Ummu_Sulaim sannunku da zuwa marhaba.. Murmushi tayi tace Mami kun tashi lapiya? Lapiya lau Sulaimi, Me ya samu Muhammad yake cin kunu. Kai fita a gidannan dan kaniya kawai! Turo Baki yayi ya nufi Sulaim wadda Ke ta dariya, rungumeta yayi Mami ta kame hannun Ahmad dake sunfi shiri saboda copy din Baba ne, Muhammad kuma gidansu Subay'a yayo. Yi hakuri rabu da Mami ko? Kanshi ya gyada, Mami ta girgixa kanta Tana jin tsantsar soyayyar Sulaim na kara ratsa ta, dubi yaran uwarsu ta tsallake su ta tafi wata duniyar ita kuwa gata tana bauta musu. Ina shi Yayan naki. Oh! Ya tafi seminar se anjima zai dawo, yace na fada miki. Kanta ta gyada tausayin Junaid na shigarta, kallon Sulaim tayi wadda ta maida hankalinta Kan Ahmad dake nuna mata wata kurjewa da yayi, ganin yadda ta bashi dukkan hankalinta tare da rarrashin shi dukda Ciwon ya dade ya kara tabbatar wa da Mami babu macen da ta cancanci zama da Junaid se Sulaim amma ita bata son takura mata Don tana ganin kamar bata son Junaid Ja'afar take so Tunda tasan suna soyayya da Ja'afar, bata son shiga hakkin yarinyar ne. Kuje daki ku huta, idan na gama zan turo se muci abinci. Banda musu. Daga haka ta janye su Ahmad zuwa dakinta, suna zuwa ta Kara gyara dakin sannan ta dan kwanta tareda janyo wayarta ta kunna data, babu jimawa taga sakon Junaid ta whatsapp, Seda tayi murmushi kafin ta bude, hotonshi ne tana tunanin yanzun ya dauka don kayan da suka taho dashi a jikinshi ne Yana zaune kan kujera, gabanshi ya bude system da papers a gaba yana murmushi. A kasan yasa @seminar Murmushi tayi ta kurawa hoton idanu ita kanta tana mamakin Irin son da take yiwa Junaid, tasan bazata iya misalta shi ba. Sulaim: You looking better than ever dear Junaid: Mhm, Haba dai? Sulaim: Eh mana. Junaid: Har kwalliyar jiya ma? Ina kallonki kina ta kallo na idan na juyo Seki dauke kanki. Sulaim: Ni? 🙄 Junaid: I love you, se mun hadu anjima zakiyi bayani. Dariya tayi tana Tunanin lokacinda ta kalleshi don ita she can't remember that, aje wayar tayi ta kwanta babu jimawa bacci ya dauketa a haka Mami ta leko ta samu duk sunyi bacci kawai se ta kyalesu kawai ta koma gurin Baba dake shirin tafiya Abuja. Basu suka tashi ba Se Sha biyu na rana, shima kukan Muhammad ya tashe ta akan Tea zai sha, mikewa tayi ta tashi Ahmad tayi musu wanka ta canja musu kaya sannan tayi itama ta shirya cikin atamfa skirt da riga buttered yellow da patteren na green. Dankwali ta daura ta dubi kanta jikin mirror, tayi kyau sosae kayan sunyi mata cif kasancewar ta danyi kiba hakan yasa ta dauki karamin veil ta yafa sannan ta kamo yaran suka fito. Parlon Mami ta Fara lekawa babu kowa cikin parlon hakan ya tabbatar mata tana kasa. Tana sakkowa shi kuma Ja'afar Yana shigowa, dukkansu seda gabansu ya fadi, Ja'afar ya tsura mata idanu Yana kallon wani kyakyawan transformation a tare da ita, dauke kanta tayi ta cigaba da sakkowa yayinda yayi tsaye shi bai koma ba shi bai shigo ciki ba. Kallonta kawai yake yana mamakin canzawar da tayi, kyaun da tayi, ya dauka idan suka hadu zai ganta tamkar irin bedridden patients dinnan se gashi ta nuna mishi Ramar da takeyi da dalilinshi ne. Seda ta zauna kan cushion kafin ta dago idonta ta dubi inda yake tsaye, oh Allah me ya samu jafaru har haka? Gaba daya yayi duhu ya rame. Murmushi ta saki tace Yaya Ja'afar ina yini? Kallonta yayi Yana jin kamar ta raina mashi hankali shi yasa take fadin haka, hakan yasa ya dauke kanshi daidai lokacin Mami ta fito don duk Abinda suke Tana hangosu ta window din kitchen, kenan sun rabu kome take tunani, idanunta kan Sulaim ya fara sauka tace Kinje kunata bacci ko breakfast bakui ba, Maza tashi ki dakko muku. Kanta ta gyada tana murmushi ta nufi dining da yaran, nan Mami ta dubi Ja'afar Wanda ya karasa shigowa tace Kai kuma fa? Tsaki yayi yace Zan tafi Asibiti, afternoon zanyi. Kanta ta gyada tace Allah ya kiyaye, ayi a sa'a. Daga haka bai kara ko kallon su Ahmad dake faman kiranshi ba ya fice ita kwa Sulaim Bata masan yanayi na. Da daddare Junaid ya dawo, dakinshi ya fara wucewa yayi wanka da sallah kafin ya nufo cikin gidan, Yana shigowa ya fara karo da Sulaim ta sakko zata kai abu kitchen, ita bata ma lura dashi ba dukda turarenshi ya sanar mata da isowarshi gurin amma tayi tunanin gizo ne kawai har Seda yace Dove. Fuskarta me kyau ta jiyo da sassanyan murmushi tace Ya...... Kafin ta karasa taga ya bata rai hakan yasa ta dan dage girarta Irin what Dinnan? I hate when you call me Yaya, why not Junaid. Idanunta ta dan zaro tare da rufe bakinta ta girgixa kanta tace I can't gaskiya Then? Ya fada Yana folding Hannunsa a kirjinshi ya kafeta da wannan sharp and piercing eyes din nasa. Rausayar da kai tayi gefe tace Bakaje gurin Mami ba fa. Dariya yayi kasakasa dan ya fahimci she wants to dodge dayar maganar, hannunshi ya watsar cikin iska ya matso kusa da kunnenta yace You know I love you right? Murmushi tayi ta gyada mishi Kai, shima ya mayar mata ya kama staircase handle yace Banci abinci ba. Daga haka ya wuce ita kuma ta tsaya anan kamar wata sokuwa se murmushi take tana cin Dan yatsanta da ta zura cikin bakinta, jinta take a saman bakwai tana jinta tamkar babu wani farin ciki da zata samu matsawar Bata tare da Junaid, tayi nisa sosae a tunanin kawai taji an damke hannunta cikin zafin nama ana janta, da sauri ta bude idanunta zata saki ihu taga Ja'afar ne hakan yasa ta Fara kicinayar kwacewa amma rikon yayi tsauri da yawa bata isa ta kwace ba. Seda ya kaita gefen parlon inda babu me ganinsu sannan ya hada ta da bango yace Sulaim me kikeyi? Me ye hadinki da baban Ahmad? Wata harara ta watsa mishi tace Me idanunka suka gane maka? Sonshi nake. Wata dariya ya saki yace Amma you're insane ko, that's completely impossible Yarinya. Tureshi tayi har Seda tayi mamakin inda ya samu karfin don yadda yayi taga taga tamkar zai kai kasa amma ya daure ya tsaya, a hankali tace Shi kanshi impossible fada yake I'mpossible ka gane. Ke mayaudariya ce, deceiver, heart breaker..... Dariya tayi tace They all fit you Yaya, Daga haka ta wuce tana dariya amma ya sake janyo hannunta hakan yasa ta doke hannun ta juyo a fusace ta ce Kada ka sake, don't ever..... Bata karasa ba ta bar gurin tamkar zata kifa saboda bacin rai. Kitchen ta wuce ranta dukka a jagule tana mamakin har kura ce zatace da kare Maye? Lallai Ja'afar! Seda ta Daidaita nutsuwarta kafin ta dauki tray din ta hau dashi, parlon is tensed saboda yanayin fuskokinsu, jikinta a sanyaye ta aje mishi abincin sannan tace Yanzun zaka ci? Kanshi ya girgixa yana kakaro murmushi wanda tasan baikai yadda ake so ba yace Se Anjima, Kanta ta gyada ta nufi ciki don kwanciya Bayan ta tambayi Mami ko Tana bukatar wani abun. Tunda ta kwanta take juyi tana jin better half dinta baya cikin nitsuwarshi, inama zata iya ta tunkareshi taji meye yake damun shi, meye taji Yana fadin Mami kina ja min rai da Yawa! Ko me yake so Mami ta hanashi? Kanta ta kwantar kan pillow ta runtse idonta tareda janyo Muhammad jikinta ta rungume a haka bacci ya dauketa me nauyin gaske wanda har Junaid ya kirata yana son fada mata ta gayawa Mami tana sonshi amma batai picking ba. Shikam hankalinshi baki daya ya tashi don ya rasa me Mami take so kuma? Me zaiyi yayi proving da gaske son yarta yake? Taki yarda taki fahimta. Idanunshi ya runtse se yaji vib da sauri ya bude idanunshi amma yaga Subay'a ce wadda duk tunaninshi Sulaim ce, tsaki yayi ya maida idanunshi ya rufe can aka kuma kira ya bude idon ya janyo wayar yayi blocking duk wani call Daga Cyprus don bai shirya jin rubbish Daga bakinta ba. Washegari Bayan sunyi breakfast Mami ta wuce daki ta bar Junaid da Ja'afar da Sulaim, parlon yayi shiru se Lokaci zuwa Lokaci biyun Kan dago su dubu junansu saboda chatting suke ta whatsapp. Junaid: Mami tace bata yadda na aureki ba saboda wai bana sonki. Juanid: kije ki fahimtar da ita ina sonki Kema haka. Kanta ta girgixa ta dago ta kalleshi se taji jikinta yayi sanyi tayi replying Sulaim: I can't, kunyarta nake ji. Dagowa yayi ya dubeta da pleading look sannan yayi typing Jumaid: Kema haka kike gani Bana sonki ko? Sulaim: no I'm sure of the love, amma bazan iya tunkarar ta da maganar ba. Kanshi ya dafe tareda mikewa ya nufi dakin Mamin, Tana ganin hakan ta bar parlon Zuwa dakinta. Yana shiga ya sameta Zaune Kan cushion idanunta cikin fararen medical glasses hannunta rike da wani littafi na judges tana dubawa. Tunda yayi sallama ta amsa, ta aje littafin ta bishi da kallo har ya zauna gefen gadon ta yace Mami sannu da hutawa. Hutu yana gurinku Baban Ahmad. Dan murmushi yayi sannan yace Mami dan Allah badan na isa ba Mami ki taimaka min ki yadda da proposal dina. Junaid! Ka bar Wannan maganar kawai dan Allah. Kanshi ya dafe saboda yadda yake kokarin tsagewa gida buyu saboda azabar Sara mishi da yakeyi yace Kiyi hakuri Mami amma idan kika fada min dalilinki ni kuma na miki alkawarin zan hakura. Kanta ta girgixa don tasan bazai taba hakura ba tace Kasan Ja'afar na sonta? Jiya bayan Kaje ka kwanta yazo yana min kuka akan na aura mishi Sulaim, bana son tarwatsa gidana da hannuna, idan na aura maka ita zaice na soka, idan na aura ma Ja'afar banyi maka adalci ba! Hatta itama Sulaim din Mami, maganar akan wa ake ba Sulaim bace? Ki kirata ki tambayeta wa take so cikinmu inhar ta Ja'afar shikenan magana ta wuce Mami. Amma inason kisan cewar Ja'afar bashi bane right choice ga sulaim ba. Inda ace Jabir ko Jawad ke sonta, bazaki taba jin nace ina sonta ba amma Ja'afar no Mami! Kuma ki tuna ranar da Daddy ya cika Kwana bakwai da rasuwa kika cemin idan lokacin auren Sulaim yayi ni zan zaba mata miji..... Wannan ya Junaid, kayi hakuri ka manta da sulaim nafi son ta kawo bare na aura mishi ita. Mikewa yayi a hankali idanunshi sunyi ja, veins en kansa sun tashi, ya kalli Mami sannan ya tsugunna gwaiwowinshi a kasa ya kama hannunta yace Nagode Mami amma NA HAKURA DA SULAIM Abinda Mami bata taba kawowa ba kenan, maganar tayi mugun bugunta amma ta kasa tabuka komai. Hakan baikai yadda maganar ta sauka kunnuwan Sulaim ba wadda ta zo niyyar kawowa Mami wayarta da Baba ke kira taji NA HAKURA DA SULAIM. Bata Gama shiga tashin hankali ba seda Junaid ya fito ko kallonta baiyi ba, uwa uba yanayin da yake ciki. Wani kuka ne ya taho mata hakan yasa ta koma daki Tana jin kamar zatayi hauka, Tana jin bakin ciki, radadi da zafi Marar misaltuwa cikin zuciyar ta! Window taje ta tsaya daidai lokacin ya bude motarshi ya shiga! *When you feel alone I'll be your shoulders, with the tender touch you know so well. Somebody once said is the soul that matters, Baby who can really tell when two hearts belong so well, may be the walls will tumble and sun may refuse to shine.... When I say I love you...* Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 36 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Lokacinda suka isa gidan, shiru tamkar masu gidan basu tashi ba, se ma'aikata dake ta aikin gyara gidan. Yana gama parking ya juyo ya dubi Sulaim da take kokarin tashin Ahmad yace Ku shiga ciki, zan wuce wajen seminar din. A gaida su Mami. Murmushi tayi ta gyada Kai tareda fadin Mami zataji, take care please. I'll definitely do that Dove. Murmushinta me kyau tayi daga nan ta tashi su Ahmad suka shiga ciki shi kuma ya wuce. Da murna dukkansu suka shigo gidan, sojojin dake bakin gate suka kawo musu kayansu ciki. Tun a tsakiyar parlour Ahmad yake kwalla kiran Mami wadda ke kitchen tana kokarin hadawa Baba breakfast Don batayi tunanin zasu zo da sassafe haka ba. Fitowa tayi ta tsaya bakin kitchen tana binsu da kallo fuskarta Cikeda murmushi da murnar ganinsu. Mami! Sulaim ta fada lokacin da ta isa inda take tsaye. Ummu_Sulaim sannunku da zuwa marhaba.. Murmushi tayi tace Mami kun tashi lapiya? Lapiya lau Sulaimi, Me ya samu Muhammad yake cin kunu. Kai fita a gidannan dan kaniya kawai! Turo Baki yayi ya nufi Sulaim wadda Ke ta dariya, rungumeta yayi Mami ta kame hannun Ahmad dake sunfi shiri saboda copy din Baba ne, Muhammad kuma gidansu Subay'a yayo. Yi hakuri rabu da Mami ko? Kanshi ya gyada, Mami ta girgixa kanta Tana jin tsantsar soyayyar Sulaim na kara ratsa ta, dubi yaran uwarsu ta tsallake su ta tafi wata duniyar ita kuwa gata tana bauta musu. Ina shi Yayan naki. Oh! Ya tafi seminar se anjima zai dawo, yace na fada miki. Kanta ta gyada tausayin Junaid na shigarta, kallon Sulaim tayi wadda ta maida hankalinta Kan Ahmad dake nuna mata wata kurjewa da yayi, ganin yadda ta bashi dukkan hankalinta tare da rarrashin shi dukda Ciwon ya dade ya kara tabbatar wa da Mami babu macen da ta cancanci zama da Junaid se Sulaim amma ita bata son takura mata Don tana ganin kamar bata son Junaid Ja'afar take so Tunda tasan suna soyayya da Ja'afar, bata son shiga hakkin yarinyar ne. Kuje daki ku huta, idan na gama zan turo se muci abinci. Banda musu. Daga haka ta janye su Ahmad zuwa dakinta, suna zuwa ta Kara gyara dakin sannan ta dan kwanta tareda janyo wayarta ta kunna data, babu jimawa taga sakon Junaid ta whatsapp, Seda tayi murmushi kafin ta bude, hotonshi ne tana tunanin yanzun ya dauka don kayan da suka taho dashi a jikinshi ne Yana zaune kan kujera, gabanshi ya bude system da papers a gaba yana murmushi. A kasan yasa @seminar Murmushi tayi ta kurawa hoton idanu ita kanta tana mamakin Irin son da take yiwa Junaid, tasan bazata iya misalta shi ba. Sulaim: You looking better than ever dear Junaid: Mhm, Haba dai? Sulaim: Eh mana. Junaid: Har kwalliyar jiya ma? Ina kallonki kina ta kallo na idan na juyo Seki dauke kanki. Sulaim: Ni? 🙄 Junaid: I love you, se mun hadu anjima zakiyi bayani. Dariya tayi tana Tunanin lokacinda ta kalleshi don ita she can't remember that, aje wayar tayi ta kwanta babu jimawa bacci ya dauketa a haka Mami ta leko ta samu duk sunyi bacci kawai se ta kyalesu kawai ta koma gurin Baba dake shirin tafiya Abuja. Basu suka tashi ba Se Sha biyu na rana, shima kukan Muhammad ya tashe ta akan Tea zai sha, mikewa tayi ta tashi Ahmad tayi musu wanka ta canja musu kaya sannan tayi itama ta shirya cikin atamfa skirt da riga buttered yellow da patteren na green. Dankwali ta daura ta dubi kanta jikin mirror, tayi kyau sosae kayan sunyi mata cif kasancewar ta danyi kiba hakan yasa ta dauki karamin veil ta yafa sannan ta kamo yaran suka fito. Parlon Mami ta Fara lekawa babu kowa cikin parlon hakan ya tabbatar mata tana kasa. Tana sakkowa shi kuma Ja'afar Yana shigowa, dukkansu seda gabansu ya fadi, Ja'afar ya tsura mata idanu Yana kallon wani kyakyawan transformation a tare da ita, dauke kanta tayi ta cigaba da sakkowa yayinda yayi tsaye shi bai koma ba shi bai shigo ciki ba. Kallonta kawai yake yana mamakin canzawar da tayi, kyaun da tayi, ya dauka idan suka hadu zai ganta tamkar irin bedridden patients dinnan se gashi ta nuna mishi Ramar da takeyi da dalilinshi ne. Seda ta zauna kan cushion kafin ta dago idonta ta dubi inda yake tsaye, oh Allah me ya samu jafaru har haka? Gaba daya yayi duhu ya rame. Murmushi ta saki tace Yaya Ja'afar ina yini? Kallonta yayi Yana jin kamar ta raina mashi hankali shi yasa take fadin haka, hakan yasa ya dauke kanshi daidai lokacin Mami ta fito don duk Abinda suke Tana hangosu ta window din kitchen, kenan sun rabu kome take tunani, idanunta kan Sulaim ya fara sauka tace Kinje kunata bacci ko breakfast bakui ba, Maza tashi ki dakko muku. Kanta ta gyada tana murmushi ta nufi dining da yaran, nan Mami ta dubi Ja'afar Wanda ya karasa shigowa tace Kai kuma fa? Tsaki yayi yace Zan tafi Asibiti, afternoon zanyi. Kanta ta gyada tace Allah ya kiyaye, ayi a sa'a. Daga haka bai kara ko kallon su Ahmad dake faman kiranshi ba ya fice ita kwa Sulaim Bata masan yanayi na. Da daddare Junaid ya dawo, dakinshi ya fara wucewa yayi wanka da sallah kafin ya nufo cikin gidan, Yana shigowa ya fara karo da Sulaim ta sakko zata kai abu kitchen, ita bata ma lura dashi ba dukda turarenshi ya sanar mata da isowarshi gurin amma tayi tunanin gizo ne kawai har Seda yace Dove. Fuskarta me kyau ta jiyo da sassanyan murmushi tace Ya...... Kafin ta karasa taga ya bata rai hakan yasa ta dan dage girarta Irin what Dinnan? I hate when you call me Yaya, why not Junaid. Idanunta ta dan zaro tare da rufe bakinta ta girgixa kanta tace I can't gaskiya Then? Ya fada Yana folding Hannunsa a kirjinshi ya kafeta da wannan sharp and piercing eyes din nasa. Rausayar da kai tayi gefe tace Bakaje gurin Mami ba fa. Dariya yayi kasakasa dan ya fahimci she wants to dodge dayar maganar, hannunshi ya watsar cikin iska ya matso kusa da kunnenta yace You know I love you right? Murmushi tayi ta gyada mishi Kai, shima ya mayar mata ya kama staircase handle yace Banci abinci ba. Daga haka ya wuce ita kuma ta tsaya anan kamar wata sokuwa se murmushi take tana cin Dan yatsanta da ta zura cikin bakinta, jinta take a saman bakwai tana jinta tamkar babu wani farin ciki da zata samu matsawar Bata tare da Junaid, tayi nisa sosae a tunanin kawai taji an damke hannunta cikin zafin nama ana janta, da sauri ta bude idanunta zata saki ihu taga Ja'afar ne hakan yasa ta Fara kicinayar kwacewa amma rikon yayi tsauri da yawa bata isa ta kwace ba. Seda ya kaita gefen parlon inda babu me ganinsu sannan ya hada ta da bango yace Sulaim me kikeyi? Me ye hadinki da baban Ahmad? Wata harara ta watsa mishi tace Me idanunka suka gane maka? Sonshi nake. Wata dariya ya saki yace Amma you're insane ko, that's completely impossible Yarinya. Tureshi tayi har Seda tayi mamakin inda ya samu karfin don yadda yayi taga taga tamkar zai kai kasa amma ya daure ya tsaya, a hankali tace Shi kanshi impossible fada yake I'mpossible ka gane. Ke mayaudariya ce, deceiver, heart breaker..... Dariya tayi tace They all fit you Yaya, Daga haka ta wuce tana dariya amma ya sake janyo hannunta hakan yasa ta doke hannun ta juyo a fusace ta ce Kada ka sake, don't ever..... Bata karasa ba ta bar gurin tamkar zata kifa saboda bacin rai. Kitchen ta wuce ranta dukka a jagule tana mamakin har kura ce zatace da kare Maye? Lallai Ja'afar! Seda ta Daidaita nutsuwarta kafin ta dauki tray din ta hau dashi, parlon is tensed saboda yanayin fuskokinsu, jikinta a sanyaye ta aje mishi abincin sannan tace Yanzun zaka ci? Kanshi ya girgixa yana kakaro murmushi wanda tasan baikai yadda ake so ba yace Se Anjima, Kanta ta gyada ta nufi ciki don kwanciya Bayan ta tambayi Mami ko Tana bukatar wani abun. Tunda ta kwanta take juyi tana jin better half dinta baya cikin nitsuwarshi, inama zata iya ta tunkareshi taji meye yake damun shi, meye taji Yana fadin Mami kina ja min rai da Yawa! Ko me yake so Mami ta hanashi? Kanta ta kwantar kan pillow ta runtse idonta tareda janyo Muhammad jikinta ta rungume a haka bacci ya dauketa me nauyin gaske wanda har Junaid ya kirata yana son fada mata ta gayawa Mami tana sonshi amma batai picking ba. Shikam hankalinshi baki daya ya tashi don ya rasa me Mami take so kuma? Me zaiyi yayi proving da gaske son yarta yake? Taki yarda taki fahimta. Idanunshi ya runtse se yaji vib da sauri ya bude idanunshi amma yaga Subay'a ce wadda duk tunaninshi Sulaim ce, tsaki yayi ya maida idanunshi ya rufe can aka kuma kira ya bude idon ya janyo wayar yayi blocking duk wani call Daga Cyprus don bai shirya jin rubbish Daga bakinta ba. Washegari Bayan sunyi breakfast Mami ta wuce daki ta bar Junaid da Ja'afar da Sulaim, parlon yayi shiru se Lokaci zuwa Lokaci biyun Kan dago su dubu junansu saboda chatting suke ta whatsapp. Junaid: Mami tace bata yadda na aureki ba saboda wai bana sonki. Juanid: kije ki fahimtar da ita ina sonki Kema haka. Kanta ta girgixa ta dago ta kalleshi se taji jikinta yayi sanyi tayi replying Sulaim: I can't, kunyarta nake ji. Dagowa yayi ya dubeta da pleading look sannan yayi typing Jumaid: Kema haka kike gani Bana sonki ko? Sulaim: no I'm sure of the love, amma bazan iya tunkarar ta da maganar ba. Kanshi ya dafe tareda mikewa ya nufi dakin Mamin, Tana ganin hakan ta bar parlon Zuwa dakinta. Yana shiga ya sameta Zaune Kan cushion idanunta cikin fararen medical glasses hannunta rike da wani littafi na judges tana dubawa. Tunda yayi sallama ta amsa, ta aje littafin ta bishi da kallo har ya zauna gefen gadon ta yace Mami sannu da hutawa. Hutu yana gurinku Baban Ahmad. Dan murmushi yayi sannan yace Mami dan Allah badan na isa ba Mami ki taimaka min ki yadda da proposal dina. Junaid! Ka bar Wannan maganar kawai dan Allah. Kanshi ya dafe saboda yadda yake kokarin tsagewa gida buyu saboda azabar Sara mishi da yakeyi yace Kiyi hakuri Mami amma idan kika fada min dalilinki ni kuma na miki alkawarin zan hakura. Kanta ta girgixa don tasan bazai taba hakura ba tace Kasan Ja'afar na sonta? Jiya bayan Kaje ka kwanta yazo yana min kuka akan na aura mishi Sulaim, bana son tarwatsa gidana da hannuna, idan na aura maka ita zaice na soka, idan na aura ma Ja'afar banyi maka adalci ba! Hatta itama Sulaim din Mami, maganar akan wa ake ba Sulaim bace? Ki kirata ki tambayeta wa take so cikinmu inhar ta Ja'afar shikenan magana ta wuce Mami. Amma inason kisan cewar Ja'afar bashi bane right choice ga sulaim ba. Inda ace Jabir ko Jawad ke sonta, bazaki taba jin nace ina sonta ba amma Ja'afar no Mami! Kuma ki tuna ranar da Daddy ya cika Kwana bakwai da rasuwa kika cemin idan lokacin auren Sulaim yayi ni zan zaba mata miji..... Wannan ya Junaid, kayi hakuri ka manta da sulaim nafi son ta kawo bare na aura mishi ita. Mikewa yayi a hankali idanunshi sunyi ja, veins en kansa sun tashi, ya kalli Mami sannan ya tsugunna gwaiwowinshi a kasa ya kama hannunta yace Nagode Mami amma NA HAKURA DA SULAIM Abinda Mami bata taba kawowa ba kenan, maganar tayi mugun bugunta amma ta kasa tabuka komai. Hakan baikai yadda maganar ta sauka kunnuwan Sulaim ba wadda ta zo niyyar kawowa Mami wayarta da Baba ke kira taji NA HAKURA DA SULAIM. Bata Gama shiga tashin hankali ba seda Junaid ya fito ko kallonta baiyi ba, uwa uba yanayin da yake ciki. Wani kuka ne ya taho mata hakan yasa ta koma daki Tana jin kamar zatayi hauka, Tana jin bakin ciki, radadi da zafi Marar misaltuwa cikin zuciyar ta! Window taje ta tsaya daidai lokacin ya bude motarshi ya shiga! *When you feel alone I'll be your shoulders, with the tender touch you know so well. Somebody once said is the soul that matters, Baby who can really tell when two hearts belong so well, may be the walls will tumble and sun may refuse to shine.... When I say I love you...* Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 37 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Tun tana zuba idon ganin kiran Kabir a wayarta har ta hakura amma ranta tana tunanin Irin rashin mutuncin da zatayi mishi shi da Salim. Ta tsani rashin cika alkawari no matter what indai tayi alkawari ko alkhairi ko sharri se tayi kokarin ganin ta cika shi. Misalin karfe Sha biyu na dare har bacci ya fara awan gaba da ita taji ringing din wayarta, hakan yasa ta bude idonta a hankali ta janyo wayar, new number ce hakan yasa tayi tunanin Kabir ne. Tashi tayi ta zauna sannan tayi picking call din, muryar kabir din taji Yana fadin Ran gimbiya ya dade ! Gyara zamanta tayi tace Tare da naka. Muryarshi ya gyara yace Naso tun dazun na kiraki amma hakan bai samu ba saboda wata yar hidima da ta tsayar dani. Ina fata baki damu ba. Ko daya Don na manta mun hadu da Kai! Dariya kabir yayi yana mamakin halin Khulthum, shi bai mata bayanin kanshi ba amma gashi har ta gane shi kuma tana gaya mishi hakan. Ayya! Lemme get straight to the point, wato Khulthum tun da na ganki naga kin dace da wani friend dina Musbahu, saboda yadda yake fadar features din matarshi da yake so, se naga kina dashi. Abokin ka kuma? Ta fada da mamaki, Bama kanshi yake yiwa kamu ba abokinshi yake yiwa to fa? Kuma ma aure ta! Jin tayi shiru yasa Kabir yace Ko dai wani ya Riga mu ne? Mu nemi wata. Kanta ta girgixa kamar yana kallonta tace Ni yanzun babu aure cikin tsarina kwatakwata, ban shirya committing suicide ba. Suicide!? Ya tambaya idanu a warwaje Of course haka nake daukar aure suicide, tunanin yin aure kawai is suicidal attempt, saboda tamkar ka dinga cin jollof rice ne kullum na shekaru babu adadi, babu free life komai an take ka anyi caging dinka. Kanshi ya girgixa yana Kara tabbatar da Khulthum tayi fitting position din matar me titαΦ. Kada ki damu gobe da karfe Tara na safe zanzo na kaiki inda yake, idan har mukaje kika ji Baki son aurenshi kada ki damu bazan Kara takura miki ba. Seda safe. Daga haka ta kashe wayar ta kwanta ta rufe idonta zuciyar ta fal tunanin wanene Musbahu? Meye aikinshi? Dan wanene? Washegari da wuri ta tashi ta gyara dakin tayi wanka, ta Nemo kayan da take son sakawa, yau shadda ta dakko wadda Tasha embroidery design me kyau, shaddar coffee ce akai aikin milk a jiki don haka tayi amfani da milk accessories, dinkin skirt da Riga da yayi fitting dinta. Karfe Tara daidai ta kammalla komai da takeyi ta fito Tana fitar da kanshi me kashe jiki. Mama dake zaune tsakar gida Tana zuzzuba abinci taga fitowar Khulthum, itafa yarinyar nan ta Fara tsorata ta, ta Fara bata tsoro ina yarinyar take zuwa da Wannan uwar kwalliyar kamar me zuwa dakin miji? Ina zakije da Safiyar nan? Wai ina tukunna kike Zuwa kike kaiwa dare Baki dawo ba. Anya Khulthum hanyar da kika dauka zata bulle miki? Murmushi tayi tace Mama gidansu Sulaim zanje wadda nake Baki ku gaisa a waya. Take bakin Mama ya washe Tace Yarinyar arziki Sulaim ki gaida min ita sosae, bari na baki kuka da Daddawa ki kaiwa babarta. Bata fuska tayi tace Haba Mama Duk Wannan kwalliyar na kare da daukar kuka? Zan dai ce Kina gaisheta . Daga haka ta fice Don tuni taji kiran kabir tasan yazo, Tunda ta nufoshi yake Raya Irin kyau da Allah ya bawa Khulthum inda ace Musbahu is Musbahu da yayi Saar mace, komai daya dace mace tana dashi Bata rasa ba. A kofar tangamemen company TitαΦ Flours anan yayi parking tare da kallon Khulthum wadda take bin ko ina da kallo, idanunta kawai zaka kalla kasan abubuwa ne fal ciki, mamaki, tsoro. Tare suka jera anata gaishe dashi har suka isa inda lift yake suka shiga ya danna 3rd floor inda anan office din Musbahu yake. Duk yadda taso daurewa kar kauyancinta ya fito seda ya fito tun ba a wajen lift ba, ji take kamar ta kankame Kabir, shi kuwa hankalinshi Yana kan wayar da yake bai lura da yanayinta. Tana tsayawa suka fito Yana gaba tana bayanshi cikin nitsuwa tana satar kallon gurin se taga first floor ba kawai bane compared to Wannan don hadasu ma bai taso ba. Seda secretary dinsa ya sanar dashi shigowar su Kabir ya bada izini kafin suka shiga ciki. Lokacinda ta hango cikin office din seda numfashinta ya kusa daukewa, wata nannauyar ajiyar zuciya ta aje har Seda kabir ya juyo tareda kallonta yace Bismillah. Cikin takun jan hankali ta shigo ta zauna kan kujerar da Kabir ya nuna mata, Seda ta zauna sannan yace Se kin fito. Kafin ta bude Baki tayi magana har ya fice, yayinda Musbahu ya juyo da Fuskarshi Baki daya yana facing Khulthum wadda tayi mutuwar zaune, wannan kyakyawan me kudin shi ke sonta? Gira ya daga mata yana binta da kallo sosae sannan ya tako a hankali yazo ya zauna cushion din dake opposite din inda take. Ya jima yana kallonta haka kurum taji ba zata iya kallonshi cikin idanu ba, idanun sun mata kwarjini da yawa, taji tsoro Yana shigarta sannan tana ayyana Anya kuwa kamar wannan yace yana sonta, Anya line dinnan intact yake ko wani abu yayi breaking? Khulthum right? Ya fada Yana kawar da kanshi cikin siriryar murya wadda zaka rantse mace ce. Kanta ta gyada a hankali ta kasa dago idonta balle ta kalleshi, murmushi ya danyi yace Nasan Kabir ya miki bayani a kaina, Abinda bai fada ba zaki fahimta with time, zan aureki Inshaaa Allah nan da sati biyu zan turo gidanku sede akwai wasu dokoki da nake dasu kuma duk Wacce ta aureni se tasan da Wannan. Na farko in kika aureni na miki murna Keda kishiya har abada, bazan Kara kallon wata mace ba da sunan ta birgeni ba, na biyu namiji ya haifeni, cikin maza na tashi, Maza ne Abokaina idan kin ganni dasu bana son tambaya. Na karshe ni kaina bansan iya dukiyar da na makalla ba, babu Abinda zaki nema ki rasa don haka inason ki tsaya a matsayinki. Idan kikayi haka we're good. Dago idonta tayi wanda ta lumshe saboda yadda words dinsa ke sinking cikin kwakwalwar ta sede bawai auna su take ba, a'a greed ya dibe ta saboda furucin karshe, me take so kudi, me kudin gaske, me kyau gashi yazo! Ina Aimana da Tace masu kudin Nigeria duniyarsu daban take? Gashi ta cin musu cikin kano batareda ta wahala ba. Kanta ta dago tace Na amince! Kanshi ya gyada yace Jibi juma'a zanzo na gaida babanki. Daga haka ya koma inda ya tashi, Sega Kabir ya shigo suka danyi maganganu wanda ba jinsu take ba hankalinta yana wata duniyar. Suna gamawa ya Mika mata sabuwar iPhone X! da envelope sannan ya maida kanshi kan Abinda yake yana jin hankalinshi Yana kwanciya saboda zai cikawa gwoggo daddan barinta shima ya samu hankalinshi ya kwanta. Gado ta zauna ta saki kuka me ciwo, me radadi, shi kenan ya daina sonta, ya hakura bazai aure ta ba kenan? Mikewa tayi ta dakko wayarta ta Fara kiran Imratu wadda take kitchen, Tana ganin kiran ta dauka amma jin kukan Sulaim yasa jikinta yayi sanyi, hankalinta ya tashi tace Sulaimi Menene Yaya yace ma Mami ya fasa aurena, ya zanyi? Shi ne kike wannan kukan Sulaim? Yaya fa Anty! Yaya!! Idanunta ta runtse hakan ya kara bawa hawaye damar gangarowa, sunanshi kawai da take fada ji take dukkan jikinta na amsawa, zuciyarta na harbawa da sauri da sauri! Oh Allah what will life be without Junaid?! Shi ne kawai Abinda ayyanawa. Sulaim ki nutsu kina jina, Mami tana da dalilin Hana papan Ahmad aurenki, duk inda akaje aka dawo Kece a Wahale. Mami bata san Junaid na sonki ba seda matarshi ta tafi sannan ya gabatar da bukatar shi, Ta yaya kike tunanin baza tayi tunanin amfani yake son yi dake wajen hukunta subay'a ba? Wannan abinda take threat ne tafi kowa farin ciki kuma shima Yayan bazai taba hakura dake ba, fada kawai yake don haka kiyi shiru ki nutsu Kada kiyi abinda zaki koma jin kunyar Mami har abada. Kin gane? A hankali taji zuciyrta tana sanyi, taji ta gamsu da maganganun Imratu hakan yasa ta share hawayenta Tace Nagode Anty. Kanta ta gyada tace Allah ya zaba muku mafi alkhairi. Amin ta furta da dusashiyar muryarta. Suna sallama ta kwanta gefen gadon hawaye na Mata zarya, ita dai soyayya bata karbeta ba, da zarar ta saki jikinta da mutum se wani abu yazo ya datsa tsakiyarsu, yanzun dukkan hope dinta yana kan Junaid gashi yanzun abubuwan da suke kunno kai. Ta dade a gurin bata daina kukan ba seda bacci yayi gaba da ita bayan Azahar ta Mike kanta nayi mata azababben ciwo kamar zai fado amma a haka tayo wanka da Alwala tazo tayi sallah sannan ta Fara neman layin Junaid sede har ta gama ringing ba'ayi picking ba, hawayenta ta share ta aje wayar akan gado ta fito parlour Don neman su Ahmad ko taji saukin abin dake damunta. Tana fitowa taji mummunan labarin da har duniya ta nade bazata taba mantawa dashi ba, ba zata taba daina kuka akan wannan abin ba haka........ Muryar Mami ce cikin kuka take fadin Junaid ya rasu......?! Shi ne kadai abinda Sulaim ta jiyo taji tamkar an saka Rodi an caka a kahon zuciyarta, hakan yasa ta rike kirjinta wanda yayi mata nauyi, se baki da ya gifta daga idanunta ta zube sumammiya a gurin. _Innalillahi wa Inna ilahil rajiun! Kui hakuri haka labarin yake, dole haka xa'ayi!!!_ *If only you could see the tears in the world you left behind, if only you could heal my heart just one more time, even when I close my eyes there's an image of your face and once again I come to realize you are a loss I can't replace......* Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 38 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *I've seen your comments all Wanda nake in touch dasu, kuyi hakuri Amma akwai abu da nake son ku fahimta ko a rayuwa ta dan Adam akan samu irin wannan abubuwan suna faruwa, ina son kusan cewar ba kowanne so ne yake zama samu ba... Haka rayuwar take ko kuma Kaga dole Se ka bi rough hanya kafin ka wuce ta smooth one. To haka rayuwar take is not everything that's at our disposal, akwai abubuwan da dole Se Kasha wahala kafin ka samu.... Nagode sosae Allah ya bar zumunci naga comments dinku nima ina baku hakuri, nasan Wanda suka fadi wasu abubuwan is out of anger banyi fushi ba ina fatan wanda sukai fushi su sakko.* Wata razanannen ihu Ja'afar yayi wanda ta janyo hankalin Mami da Baba dake parlon, da gudu ya isa Kan sulaim din ya fara jijjiga ta Yana kiran sunanta amma ko motsi ba tayi balle asaka ran zata farfado, Ahmad da Muhammad da suke wasa suka taho kanta suna kukan AMMIEY don Junaid yace musu sunanta kenan baya son anything like Anty. Sosae Mami take kuka kamar ranta zai fita hakan ya janyo hankulan ma'aikata dake gidan suka hayo saman. Mama talatu me aikin Mami ta dakko ruwa ta zubawa Sulaim wanda Daga Baban har su Ja'afar saboda tashin hankali Babu Wanda yayi tunanin hakan, wata ajiyar zuciya me nauyin gaske ta saki kafin ta Fara bude idonta a hankali har tayi adjusting da hasken gurin, murmushi ta saki don ta tabbatar mafarki tayi, mummunan mafarki ma kuwa, wai yayanta mahadin rayuwarta ya rasu, yabi Daddy da Mummy Kai ai kuwa da ta cika marainiya Don tana ganin farin ciki sede a lahira kuma! A hankali ta gyara kwanciyarta amma se taji muryar Ja'afar yana fadin Mami ta farka! A hankali Baba ya durkusa ya riko hannunta, idanunshi sunyi ja yace Ummu_Sulaim me ya faru dake. Wani numfashi taja me karfi, ta kalli Mami wadda take kuka cikin karyewar zuciya, Ahmad da Muhammad, ga Ja'afar sannan Baba, ga ma'aikatan gidan kowa hankalinshi a matsanancin tashe, kuka ta saki ta damke hannun Baba tace Baba Yaya ya rasu da gaske? Ya tafi ya Barni? Bayan ya min alkawarin bazan Kara kuka ba shine ya tafi....... Me yasa? Me yasa? Ko ya ka kai da danne zuciyarka se kayi kuka, saboda yadda take kuka from the bottom of her heart, how's that feeling Irin abu kike jira all your life se kuma yazo lokacin kike gaf da samu abin ya barki..... That's shattered dreams!!! Juyawa Baba yayi ya dubi Ja'afar yace Nayi booking tickets Tun kafin na shigo gidan, ka wuce airport yanzun Zamu karaso. Wani kuka Sulaim ta Kara saki cikin matsanacin tashin hankali tace Shi kenan I'm shattered, na zama marainiya Baba, banida gata kuma a duniya. A takaice Seda Sulaim tasa Baba ya zubarda hawaye Balle Mami wadda da kyar ta debo kayanta da na Baba, haka suka fito with a heavy heart Zuwa Airport. Sulaim Tunda suka shiga jirgi ta rungume Ahmad da Muhammad a jikinta tana zubar da hawaye wanda ta rasa a yananyin da take ciki, yaran sunyi shiru se kallon kowa suke. Tunda Sulaim take bata taba ganin most dreadful journey Irin wannan ba, tamkar da kafa take tafiya haka take ji, a haka ya kare bazai kare ba suka sauka a cikin Aminu Kano international airport. Ana Fara fitowa, Ja'afar ya dakko Muhammad a kafada, yana jan hannun Ahmad, Baba hannun Sulaim ya kama wadda take ta kallonshi yasan bayani take bukata amma yasan bazata taba fahimta ba Yafi son taga komi da idanunta. Basu jira wani yazo daukarsu suka samu cab ta daukesu zuwa National orthopedic hospital dake Dala a birnin Kano. Tun a gate suka so hanasu shiga amma kallon Sulaim kadai bazai barka kayi Abinda kayi niyyar ba. Ta lalace Lokaci guda ta rame, idanu sunyi jawur tamkar garwashi ko jikinta ka kalla kasan akwai damuwa. Jeans ne jikinta se top Fara iya gwiwa da karamin veil wanda babu inda ya rufe mata, haka kuma babu Wanda ya lura da shigar dake jikinta Don babu me wannan nutsuwar. Dr. Halliru suka Fara hangowa me Family law da Ridwan suna tsaye suna jiran isowar su, Tunda ta hada idanu da Ridwan ta saki hannun Baba ta nufeshi kamar zata kifa tareda ruko hannun shi tace Ka fadamin Yayana ya tafi ya barni? Na zama marainiya ko? Bai cika alkawari ba, he said he'll be my home, my shelter, the shoulders I'll cry on....... Ja'afar ne ya ruko ta dan baki daya Ridwan da Halliru sun kame a gurin tamkar gunki, me Zasu ce mata? Ya mutu? Ko kuma he's battling with his breathing. Kuka sosae take har suka isa building din SOPD inda Tanan suka hau sama zuwa new Aminity. Hannunta ta fixge Daga hannun Ja'afar tana kokawa da numfashinta, so yake ya fita amma hanashi take ta fison ko zai fita ya fita bayan ta ga Rabin rayuwarta, taga better half dinta. Tayi nasara cigaba da tafiya sede kawai kafar take wullawa batasan inda take zuwa ba. Suna isa kofar room din, doctors wajen ashirin suka fito Daga ciki, Blue Team, Pink Team, White team da Green Team kowanne yana son ganin Team din da zaa aje Junaid din ciki. Dukansu Suka tsaya suna kallon Sulaim wadda ta taryi babban consultant din Pink Team dake gaba, ta rike hannunshi me rikeda waya da stethoscope da bai samu ya makala a wuyanshi ba tace Doctor tell me is he truly dead? How is he? Tell me he's waiting for me inside. Gaba daya gurin yayi tsit ana jiran amsar bakinshi. Your husband is OK, yana jiranki kije gareshi. Babu jira ta kutsa ciki lokacin nurses biyu na kanshi, daya yana sa mishi blood daya kuma yana daidai ta dakin. Baki daya tsayawa sukai suna kallonta babu Wanda yayi mata magana har ta dira gwiwarta a kasa ta ruko hannunshi hakan yasa ya saki karamar kara, da sauri ta sake shi hawaye na bin idanunta, ta kalli Fuskarshi babu ciwo a jikinta amma tana iya hango jini Yana fitowa daga kunnenshi da hancinshi. Kifar da kanta tayi tana wani Irin kuka me zafi wadda yake Marar dadi ga kunnuwan me saurare. A station na nurses doctor ya zauna shi da Baba don yi mishi bayanin halin da Junaid din yake ciki. Sir! Bayan accident din da yayi bamu samu ganin karaya ko daya ba sede ya bugu wanda ya taba kanshi shi ne muke kira "Head injury" shima mild ne saboda gashi yana bleeding ba ta ciki yake ba. Se dislocation a hannunsa da karan hancinsa. To matsalar he's unconscious amma Inshaaa Allah Zamu ga Duk yadda zamui da izinin Allah ya dawo hayyacinsa. Kai Baba ya gyada yace Nagode kwarai, Allah ya Baku saa. Daga haka suka tattauna da nurses din akan bills da zai yi depositing a account office dinsu. Daga haka ya wuce dakin da Junaid lokacin kowa ya shiga ya ganshi kuma koke koken ya ragu sosae don hatta Sulaim tayi shiru sede bata magana haka Mami wadda ta kasa daina blaming kanta as cause of everything. Tunda Ridwan yace Accident yayi Bayan ya shigo Kano dayake shi ne last call dinshi yasa bayan abin ya faru shi aka Fara kira shi kuma ya kira Baba Wanda bai iso gida ba Yana hanyarshi ta dawowa daga Abuja. Yadda ya shigo gidan hankali a tashe yasa Mami tayi tunanin mutuwa Junaid din yayi!!! Basufi awa a gurin ba Imratu da Jabir Harda Jawad suka iso hankalinsu a matukar tashe Amma ganin yana raye yasa suka nutsu aka Fara jajantawa. Kafin isha'i labarin accident din ya kai Birnin kudu, Jega, Kebbi da Birnin Kebbi se kira suke a waya don jin jikin na Junaid amma magana daya ce he's still unconscious. Karfe goma Baba ya tattara Mami, Ahmad, Muhammad, Imratu, Jawad da Sulaim don su tafi, aka bar Ja'afar da Jabir a gurin shi, Sulaim kuka akan ita bazata tafi ba a gurinshi zata Kwana, seda lallashi kafin ta yadda ta bisu shima ta dinga kuka tamkar ranta zai fita saboda gani take idan bata kusa dashi mutuwa zaiyi. A gidan Junaid driver din Baba ya ajesu Sulaim, Baba yana tayiwa Imratu kashedin ta kula da Sulaim, su kuma suka wuce zuwa hotel don su Kwana. Daren ranar ba sai na fada ba babu Wanda yayi baccin arziki Balle Sulaim me gayya me aiki! Washegari tun da sassafe ta shirya amma Baba da yazo yace mata ai basu Bari aje gurin patient se karfe uku na yamma.... Hey pipu tamkar sokuwa haka ta dinga kuka tamkar don shi Allah ya halicce ta, babu Wanda ya lalashe ta don bazatayi shiru ba, Baki daya tausayi Take bawa Baba, ji yake idan yana da halin tashin Junaid da se ya tashe shi kodan Sulaim kodan hankalinta ya kwanta amma bashida wannan halin. Wajen karfe biyu Mami ta karaso ita dasu Mama Sauda, Umma Fatima, Neneh ta birnin kudu da Hajiya ta Jega, suka saka Sulaim a gaba Sunata mata nasiha amma ina a ranta fada take bazaku gane ba, dukkanku da aurenku, iyayenku na da rai Nikam banida kowa ban kama komi ba. Haka suka dunguma Zuwa Dala sede Alhamdulillah yau ya fara responding ba dai kamar jiya ba. Hakan ya kwantar musu da hankali suka kara samun hope. Da daddare Bayan Mami sun kwanta itada Baba ta matso jikinshi ta daura hannunta a Fuskarshi tace General! Dagowa yayi yace Nafisatou! Haka yake fada idan soyayyar ta motsa. Nasan ban kyauta ba Abinda nayiwa Junaid amma Allah ya sani inada dalili na.... Hannunta ya riqo gam yace I know and I understand you Shiyasa kikaga ban saka baki ba kwata kwata nasan duk Abinda kikayi kina da dalili. Rest well please. Hawayenta ta goge tace Inada abu daya da zan rokeka kuma Dan Allah gobe juma'a ka daura auren Sulaim da Junaid! Da sauri ya kalleta yace No! Nafisatou mu Bari ya tashi tukunna. Kanta ta girgixa Tana kuka a hankali tace Dan Allah Baba just do this for me please ! Ta fada hawaye na Kara wanke mata fuska, hannunta ya Kama yace Is ok gobe kike so right? Kanta ta gyada yace Inshaaa Allah . Daga haka ya sauka a gadon ya dauki wayarshi ya koma can gefe yana waya, ya jima yanayi ba da mutum daya ba sannan ya dawo ya kwanta. Shatuuu ♥️[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 39 ✍️Shatuuu ♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Ranar ta kasance juma'a, jumaatu babbar rana, Tunda Junaid ya fara rashin lapiya wannan shi ne Karo na farko da Sulaim ta samu tayi bacci shima bawai niyya tayi ba a'a taci bashi da yawa dole ta biya, hakan yasa bayan ta Idar da sallar Asuba tana zaune kan praying mat wadda tun ranar da ta iso gidan ta shimfida ta, wanka da Alwala kawai ke tada ita se idan zasu tafi Asibiti amma dama abinci ta dade da daina ci, yoghurt kadai take iya sha shima se wani na tsaye a kanta. Ta rame ta lalace tayi baki tamkar ba Sulaim ba, babu komai ya rage fuskarta banda kwalakwalan idanu da suke a warwaje kamar na owl. Suna zaune Bayan sunyi sallar Imratu ta dube ta tace Sulaim bazaki sawa zuciyarki salama ba ki rungumi kaddarar da Allah ya aiko miki ba. Duk wannan damuwar da kike ciki bazata Hana Kun Fayakun aiki ba. Ki kwantar da hankalinki kiyi mishi addu'a gwargwado iko. Hannunta tasa ta share hawayenta tace Anty Imratu, kina ganin Yaya zai tashi? Kina ganin zai samu sauki bazai mutu ba? Wallahi ya mutu mutuwa zanyi. Ta fada Tana fashewa da matsanancin kuka me cin rai, me taba zuciya. Rungumota Imratu tayi tana bubbuga bayanta alamun rarrashi Don gaba daya tausayin Sulaim din take sosae, yarinyar tana cikin mawuyacin hali tana bukatar dauki. To daga nan ne bacci me nauyi ya dauketa wanda Bata farka ba se karfe goma da rabi shima hayaniyar da ta cika gidan ita ta farkar da ita. Gabanta na wani Irin bugawa, tsoro Yana kara shigarta ta mike jikinta a matukar sanyaye tamkar an watsa mata ruwa haka ta fito amma se ranta yayi matukar baci saboda at first tayi tunanin Junaid ne ya rasu Amma tana fitowa se tayi kicibis da su Mami anata hada Hada tamkar wanda suke shirin yin biki. Fasa fitowar tayi ta koma daki ta kwanta tareda kifa kanta ta saki kuka me ban tausayi, bakin ciki sosae takeji cikin zuciyar ta, wato yaya Yana can a kwance unconscious su kuma saboda basu damu ba yasa suka zo Harda hada Hadar biki lallai ma! Yaya Maryam wadda ta kasance first born din Umma Fatima ta shigo don duba ko Sulaim ta tashi ta ganta a wannan halin. Gefenta taje ta dago ta, tare da fadim Haba Sulaim kin dinga kuka kenan? Se Yaushe zaki hutawa zuciyarki, Allah zai yayewa Junaid ko. Kanta ta girgixa tace Amma kuna kallo Yaya Yana Asibiti unconscious, shi ne zakuzo kui ta hayaniya. Murmushi Maryam tayi tace Kiyi shiru mun daina, taso muje Umma na kiranki. Babu musu ta Mike tabi bayanta, parlon daya kasance na Junaid anan Mami da 'yan uwanta suke da kuma 'yan uwan Baba, Tana shiga ta tsugunna ta gaeshesu Sede farin cikin da take hangowa akan fuskarsu yasa ta Fara tunanin kodai Junaid ya farka ne amma ai da Za'a Fada mata. Zama tayi inda Amma ta nuna mata. Wata budurwa me Kimanin shekaru ashirin ta dubi Amma tace A fara? Kanta Amma ta gyada tare da duban Sulaim tace Duk Abinda yazo cikin rayuwarki, ki karbeshi hannu bibibyu kinji? Hawaye na zuba daga idanunta ta gyada Kai, zuciyarta na son sanin dalilin da yasa ake mata wannan Mulken mulken Amma ba Wannan ne a gabanta ba, karfe uku kawai take jira tayi ta tsallake koma Menene taje ga yayanta. Tamkar an dade da sanar da mutane wannan daurin Auren haka massalacin na Alfurqan dake cikin Alu avenue ya cika da dumbin mutanen dake zaune don shaida auren na Junaid da Sulaim. Ja'afar shi ne Wanda ya wakilci Junaid, yasha manyan kaya tamkar aurenshi, Fuskarshi babu yabo babu fallasa cikin zuciyar shi Yana gwada Irin asarar da yayi amma ko babu komai dan uwanshi ya samu, yasan it was all his fault ba laifin kowa. Karfe daya da Rabi, Bayan an kammalla sallar juma'a babban Limamin massalacin Wanda Baba ya bashi wallicin Junaid don abokinshi ne Tun school days, Baba Abdul Aziz wanda abokin Daddyn Sulaim ne shi Baba ya bawa wallicin Sulaim. Babu bata Lokaci dubban jama'ar dake ciki da harabar massalacin suka shaida daurin Auren Muhammad Junaid Lukman Birnin kudu da Ummu_Sulaim Aminu Birnin kudu akan sadaki Dubu Dari Biyu. A take aka shafa fatiha kafin aka ja doguwar addu'ar rokawa Junaid lapiya. A gidan Junaid kam Sulaim Tasha gyara na gani na fada, within hours ta canza Baki daya tamkar ba ita ba, tayi kyau sosae tamkar an Bare ta sabuwa. Ga wani kamshi da takeyi kamar an mata barin turare. Seda suka gama pampering jikinta kafin suka Fara zana mata lalle ja. Lokacin daga ita se Najaatu wadda Ke kunshin, sauran biyun Aliyah wadda gyaran Kai tayi mata se Mamaaa wadda Itace head din ita tayi gyaran jiki. Cikin sanyin murya Sulaim tace Me yasa ake min wannan abin, Yayana yana Asibiti amma har nake da lokacin kunshi. Murmushi tayi tace Kede ki Bari na karasa miki kinji. Kanta ta gyada kawai, ta cigaba da ambaton sunan Allah tareda lumshe idonta Wanda ya fara washewa Daga jan da yayi. A hankali taji tamkar ana zubawa zuciyarta ruwan sanyi, Lokaci daya taji wata nutsuwa Tana shigarta, taji wani bakon yanayi me dadi wanda ta manta rabon da ta shiga Irinshi, ajiyar zuciya ta dinga saukewa har lokancin idanunta a lumshe suke. Seda Najaatu ta kammalla kafin ta bude idonta tace Dan Allah idan kin fita ki tambaya Wace Imratu ki Turon ita. Inshaaa Allah ta fada haka kurum take jin tausayin Sulaim din a zuciyara saboda kana kallonta zakaga tana cikin damuwa. . Kafin Imratu ta shigo taji gidan ya kuma kacamewa da guda da ihun murna a'a nanma kanta ya kara shiga duhu tana tunanin abinda yake faruwa? Tun tana zuba idon ganin Imratu har ta hakura ta cigaba da zama, can Sega Najaatu Taxo ta cire kunshin, subhannalllah! Kwaai zaka iya fada saboda masifar kyau da yayi. Wasu abubuwa ta shafa mata sannan ta hada bakin lalle ta Fara mata shima me kyau. Shi bai dade ba aka cire kuma har lokancin babu Wanda ya shigo gurinta hakan yasa taji Duk ta damu tana son sanin abinda yake faruwa da ita, don tasan ko Meye dole it has to do with her, amma ko a ranta bata kawo ta auri Junaid bane. Har dakinta Mamaaa ta kaita lokacin babu mutane da yawa a gidan ya dan sarara, kowa ta kalla Fuskarshi annuri ne kawai ke fita amma da idan ta nufesu se taga babu fuakar ta Tambayesu. Ita ta hada mata ruwan wanka me hade haden kamshi da stuffs dinsu wanda Bata San meye ba, tayi wanka da kyau dama tana son Ruwa hakan yasa duk dadewar da tayi a ciki bai dameta ba. Amma hankalinta gaba daya yana kan Junaid don har hudu tayi tasan yanzun Duk anje an ganshi ita daya ce kawai. Tana fitowa aka barta tayi sallah Sega Mami ta shigo hakan yasa duka suka fita, Mami ta zauna Tana ta kallon Sulaim din wadda tayi kasa da kanta, gabanta na tsanan ta faduwa don batasan me Mami zatace da ita ba. Sun kusa Mintina talatin in awkward silence kafin Mami tayi breaking silence din da fadin Ummu_Sulaim! A hankali Cikeda nutsuwa ta dago idanunta da sukai haske kamar an diga zaiba a ciki ta kalli Mami kafin ta dauke kanta don haka kurum taji kunyarta take ji. Yau Friday, juma'a kenan babbar rana ga Dukkanmu. Wani barin na zuciyarta yana fada min Nayi shishigi amma wani barin na fadamin daidai kenan. Bayan mun rabu jiya mun yanke shawarar aura miki junai...... Da sauri Sulaim ta dago Tana kallon Mami wadda kallon yasa ta kasa karasawa, wasu Irin mixed emotions ne cikin idanunta da kan fuskarta, lokaci daya madaukakin farin ciki ya mamaye mata zuciya da dukkan jikinta! Amaryar Junaid! Oh Allah ta ayyana cikin ranta kafin kuma ta saki kuka a hankali wanda yasa Mami tace Bakya murna ne? Da sauri ta girgixa kanta Tana share hawayenta kuma ta kasa furta komai banda hailala da kirari da take yiwa Allah daya cika mata barinta ko tace burinsu, Allah ya tayar mata kafadun Junaid ta gaya mishi ta zama mallakinshi, inama yana nan tasan murmushin nan zaiyi wanda ko fushi take yayi se taji ya tarwatsa fushin, ta tuno idanunshi masu kaifi da Hana mutum sakat! Kuka ta dinga Yi tana Shesheka wanda Mami ta tabbatar na tunanin halinda Junaid yake ciki don tasan Sulaim ko abinda tayi a wannan jinyar tashi ya isa ya tabbatar wa da kowa son da take mishi. Bayan sallar isha'i Mami da Umma da Amma suka shirya Sulaim cikin zani na soft cotton material Baki da long sleeve top Fara kal, kanta da Aliyah tayi mata parking gashinta in an assemble bun ya tashi yayi kyau aka saka mata bakar hula me kyau, sannan amma ta ciro wata lafaya me tsananin kyau Fara tas da sequence bakake a jiki se edge dinta wani black lacy ne aka mishi ado. Haka suka shirya ta tayi kyau Tana fitarda kamshi na musamman me kwantar da zuciya. Flat Takalmi bakake Mami ta sata tasa sannan suka kama hannunta se mota inda Jawad ke mazaunin driver, suna shiga ya cillar mota zuwa orthopedic dake Dala! Gabanta babu Abinda yake banda faduwa lokacin da Amma ta tura dakin suka shiga kanta na kasa ta kasa dagowa don batasan ganin Junaid a halinda ta barshi. Gefen gadon Amma ta aje ta sannan ta Ajiye mata wata jaka batareda tace da ita komai ba tasa kai ta fice, ta jima tana zaune yadda ta barta gashi ta kasa dago idanunta Balle ta kalli dakin dukda tasan gurin Junaid aka kawo ta, kenan ta zama matarshi da gaske an daura auren kenan! Allah kenan yana amsa addu'a ya bawa Bawa Abu lokacin da ya debe tsammani. A hankali taji alamar an bude kofa an fito, tasan ba shigowa akai ba Daga toilet aka fito, to ko dai wani na ciki ne? Amma se kawai taji muryar da ko a ina take ko me takeyi ta jita tasan ta wacece, wannan karan a hargitse ta dago idonta ta dubi inda ta jiyo muryar shi, shi dinne her beloved, her everything, her world, her life yana tsaye jikinshi da jallabiya yayi haske amma akwai rama sosae tamkar bashi bane wanda ta bari jiya baisan waye a kanshi ba. Hannunsa ya bude mata Fuskarshi tamkar gonar auduga Don fara'a, babu musu ta Mike Tana sassarfa ta isa gareshi Tare da fadawa cikin kirjinshi ta saki kuka, a hankali ya zagaye hannuwansa a bayanta, ya rungumeta Tsam Yana jin wata nutsuwa wadda zai iya rantsewa bai taba jin makamancin hakan ba! Shatuuu ♥️ [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 40 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Daga office din Musbahu Bata Kara zuwa ko ina ba ta biyo Kabir don ya kawota gida, Tunda yanzun ta samu abinda take so Tana ganin kamar yawace yawace ya Kare ya Kuma kamata ta zauna ta nutsu ta tsara yadda zatayi rayuwa tare da Musbahu. Suna zuwa gida tayi sallama da Kabir akan se sun zo Washegari sannan ta shigo gida fuskarta dauke da wani madaukakin murmushi, murmushi ne daga kasan zuciya wanda yake nuni da burina ya cika. Babu kowa tsakar gida hakan yasa ta shige daki ta cire kayanta, tare da kurawa kanta ido jikin mudubi, bazata taba gajiya da yiwa Allah godiyar kyau da diri da yayi mata ba don tasan shi ne Abinda yake jawo hankulan Maza kanta, juyawa tayi ta shiga karewa kanta kallo tasan tana Hulda da Maza, tayi Hulda sosae dasu amma ko da wasa batayi Kuskuren bada kanta ba, zaayi romancing, smooching, fingering da duk wani abu amma bata yarda da penetration ba saboda tana ganin shi din shi ne pride dinta, shi ne darajarta ta 'Ya mace! Katifa ta koma ta kwanta, ta janyo wayarta wadda tuni ta kashe da taje office din Musbahu, kunawa tayi babu tunanin komai ta Fara kiran Aimana, Bata dade tana ringing ba Aimana wadda mamakin kiran yasa tayi picking tace Khul...... Katseta Khulthum tayi da fadin Ba wannan na kiraki kiji ba, na kiraki na fada miki aure zanyi. Aimana da bata fahimci inda maganar Khulthum ta dosa ba tayi ihun murna tace Ke amma naji dadi Wallahi, Yusuf ne. Wata harara Khulthum tayiwa wayar tamkar Aimana na gurin tace Kina abu tamkar har zuciyarki bayan bakin ciki ne fal, Bari kiji na samu miji Wanda har ki mutu bazaki taba haduwa da Irinshi ba! Kince masu kudi ba'a haduwa dasu ina son kisan cewar na samu kuma zan aura.... Kije ki samu rijiyar da tafi kowacce zurfi cikin kano state ki fada don bakin ciki!! Bakin cikin Aimana guda daya ne Bata samu ta rama ba, bata fadi Abinda take son fada ba, ba kuma ta samu ta mayar mata da martani ba ta kashe. Haka ta Bata kusan Mintina ashirin tana kiran Khulthum amma taki shiga kawai se ta kira Sulaim ita kuma wayarta a kashe. Tsaki tayi tana addu'ar Allah ya hada su itada Khulthum Koda cikin mafarki ne Wallahi se ta sha mamaki, ita har ta isa ayi mata bakin ciki, bakin cikin me talauci ko kuma rashin tarbiyya? Da daddare wajen karfe Tara tana kwance tana kokarin hada wayarta da power bank, Amira ta leko tace Yaya Khulthum kizo Baba yana kiranki. Kanta ta gyada tace Kice gani nan. Amira ta fice ita kuma ta cigaba da Abinda take babu niyyar ma fitar, jin shiru yasa Baba ya kalli Mama yace Kije ki Kira min ita Tunda ke Uwarta ce, ni kuwa kinga ba haifar ta Nayi ba. Kai Mama ta girgixa ranta a bace saboda yadda Khulthum ke jawo mata magana. Tana zuwa ta sameta a kwance, kunnenta da earpiece ta lumshe idonta saboda yadda wakar ke ratsata, wani duka Mama ta kaiwa cinyar ta wadda ta bayyana saboda kwanciyar da tayi zaninta ya tattare, wani tsalle ta buga wadda yasa wayarta faduwa kan simintin dakin, idanunta ta bude idonta Cikeda masifa se taga Mama ce amma dukda haka tace Mama ya haka? Ubanki nace, tun dazun Baban A'isha ya turo kizo amma kika ki zuwa saboda kin shahara ko? Tsaki ta saki tareda daukar wayarta wadda tuni ta fashe, gashi babu screen guard, ihu ta kwalla tace Haba Mama Wallahi nidai Baki kyauta min ba. Wani dukan Mama ta kai mata tace Tashi muje. Mikewa tayi tana kunkuni ta nufi inda Baba yake Zaune, ranshi a hade wai kar ma taga fuskar da zata kawo mishi wargi, itama bata ran tayi tamkar me shirin wata tsiyar. Yadda ta tsaya tsegege ta kama kugu yasa Mama Dalla mata harara, amma se ta dauke kanta tana Kara hade fuska tamau. Ba karamin bata ran Baba abin yayi ba yace Ke! Kin jiyowa tayi seda Mama tace Khulthum bakyaji? Ba dake yake ba? Juyowa tayi tace Mama Ke yace fa! Bakiji ba? Zauna Ya furta Yana danne bakin cikin dake addabar zuciyarshi, yasan komai Khulthum ta zama har dashi , Tunda ya bata yarinyar bai hanata yin komai saboda tana bashi kudin cefane gashi yanzun babu Wanda ta kyale cikinsu. Kanshi ya girgixa Cikeda takaici kafin ya dubi Mama yace Duk inda na wuce se anyimin magana akan Khulthum tana Tara maza don haka na gaji ko dai ta fitar da miji tayi aure ko kuma ta koma malumfashi. Yana aje numfashi tace Gobe zaa zo gaisheka. Tana gama fadar haka ta mike zuwa Dakinsu ta kwanta, Mama ta biyota tana ta fada amma Khulthum ko kallonta Batayi ba, hakan yasa Mama ta dinga kuka Tana fadin Wannan shi ne ladan haihuwa Khulthum, Kinyi daidai Yarinya wannan Itace sakayyar goyon da nayi miki! Khulthum bata motsa ba har su A'isha suka dinga rarrashin Mama kafin ta tafi ta kwanta zuciyarta tana gobara! Washegari ta kasance juma'a, kamar yadda Musbahu a ranar Bayan anyi sallar juma'a yazo shida Kabir ya gaishe da Baba Alkasim wanda ya gayyato abokinsa guda daya. Cikin mutunta juna suka gaisa, nan Musbahu ya sanar musu yana son Turon iyayenshi wani satin ayi finalizing komai. Anan Baba ya sanar mishi asalin Khulthum iyayenta na malumfashi Don haka zaiyi magana da babarta aji. Da haka aka tashi maganar bai nemi ganin Khulthum ba duk yadda Kabir Ke rokonsa Amma yace bai da wannan lokacin ya bada kudi a Bata ai kuwa tayi murna don Musbahu bata ga wani lokacin batawa tayi soyayya ba kudin dai. Da daddare ya gabatar da kudirinshi ga Gwoggo.... Kuzo kuga murna gurin baiwar Allah, nan ta dauki waya ta Fara kiran uncles dinshi akan wani satin zaaje nema masa aure, yadda take murna yasa zuciyar Musbahu karyewa ya bar gurin yana jin ya tsani Abinda yake aikatawa.! Sede wani kuskure daya da aka tafka Gwoggo bata saka an bincika wacece Khulthum ba Tunda tana ganin a nutsuwar Musbahu bazai kawo abin kunya ba, su kuma dangin Khulthum Dana ubanta Musbahu yayi musu girman da zasu bincike shi! Tirkashi _Just a smile and the rain is gone, can hardly believe it... Yeah! There's an angel standing next to me reaching for my heart!_ Sun jima sosae a tsaye a gurin yana rungume da ita, yana bubbuga bayanta ita kuma tana ta hawaye a jikinshi. Kasa yayi da kanshi saitin kunnenta ya hura mata iska wadda tasa babu shiri ta saki ajiyar zuciya tareda kankame shi. A hankali ya kamo hannunta zuwa kan gadon da ta baro, seda ya zaunar da ita tukun ya janyo farar kujerar dake gefen gadon ya zauna Yana dubanta da idanunshi wanda Lokaci daya tayi Kasa da nata saboda bazata taba iya jurar abubuwan dake fita daga nashi idanun suna shiga cikin nata. Dove! Kinsan how your tears are piercing my heart, inda Kinsan yadda nake jin kukanki tunanin zaki iya yin fushi balle kuka. Hannunta tasa Wanda yasha lallai ta goge fuskarta tare da sakar mishi tattausan murmushi, lokacin ya lura da zanen henna hakan yasa ya riko hannyenta ya kura musu ido kafin ya fara shafa su cikin wani Irin salo da Hannunsa Wanda yasa su jin tamkar electrical current ake passing jikinsu, a hankali ta janye hannunta saboda abin affecting dinta yake sosae, langwabar da Kai yayi shima ya turo bakinshi yace Rowa ba kyau! Murmushi tayi ta rufe fuska da hannayenta, Tana jin mahaukacin farin ciki da bata taba mafarkin shiga Irinshi ba, hannun ta Mika mishi a hankali tace How does it happened? Tashi yayi ya dawo gefenta ya zauna, baki dayansu suna jin numfashin junansu, lafayar ya fara warewa har ya cire ta gaba daya sannan ya ajeta a gefe ya dago fuskarta ya kalleta yace Dove! Kinsan me yasa nake kiranki Dove? Kanta ta girgixa, ajiyar zuciya ya sauke yace Doves are beautiful and very gentle, gentility dinki da kyau da Allah ya baki shi yasa kikai suiting da Wannan sunan..... I love you my Dove so much, na miki alkawarin kasancewa a tare dake Duk runtsi duk wuya, ba lallai ki samu farin cikin da kike tunani ba ko kuma kike mafarkin samunshi ba amma Inshaaa Allah xanyi iya bakin kokari na! Hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin kauda su, Tana jin dukkan damuwarta ta yaye dukkan wani kuncin ta Yana yayewa kamar evaporation na steam. Lokacinda muka gama magana da Mami nace mata na hakura, I was shattered, I threatened her inason Tace min nazo ta bani ke amma haka raina a mugun bace na taho Kano, I was lucky duk yadda hanyar batada kyau amma haka Allah yasa na iso kano, se a cikin gari sannan bansan yadda akai ba kawai nasan munyi Karo shikenan. Se jiya Mami tace kin fita da yan Mintina na farka, I was lucky kaina ne kawai ya bugu amma brain din is OK, bacin rai da nake ciki yasa na zama unconscious. Gashi at least Bayan accident I was able to have you! I love you baby. Hawayen dake mata zarya a kumatu ta goge ta bude Baki don yin magana ya hanata maganar ta hanyar hade bakinsu waje daya. Washegari Misalin karfe takwas da rabi, akazo handing over, Junaid na zaune kan carpet yayinda Sulaim ke kwance kan gadon ta kudundune tamkar ita ce marar lapiyar a cikin duvet. Hirar da nurses din keyi da Junaid yasa ta farka ta yaye bargon Zuwa wuyanta tana binsu da kallo. Daya daga cikin nurses din tace Amarya Anya jinya kike kuwa? Kin wullo mana patient kasa kin hau gado. Dariya sukai Junaid yace A'a sister Karki takura mata fa. Dariya suka kuma Yi sister tace Dariya take kamar ba ranar take ta kuka ba kamar ranta zai fita. Haka dai aka gama sukai mishi Allah ya sanya alkhairi da fatan Karin lapiya. Suna fita ya rufe dakin da key sanann ya dubeta yace Sakko Kije kiyi wanka. Mika tayi bbau musu ta sakko ta nade blanket din ta gyara gadon sannan ta nufi bayi, ta jima tana wankan sannan ta fito da hijabi jikinta lokacin baya dakin, hakan yasa tayi saurin ciro kaya a jakar da Amma ta kawo mata, wata simple gown ce baka se inner wears dinta, Seda ta saka sannan ta shirya tayi shafe shafenta kafin ta gyara gurin, tayi kyau kamar ba ita ba, kofar ta nufa daidai lokacin Junaid ya sako kai ya bigeta tayi baya zata fadi yayi saurin tarota jikinshi. Ajiyar zuciya ta sauke ta biyo bayanshi suka Fara breakfast. Seda suka gama tsaf yace Dove are you happy ko tursasa ki nayi kika aureni? Da sauri ta girgixa kanta tace I'm so happy that I can't express exactly how I feel, Amma nasan zaka fahimci how exactly I feel, felt and feeling and I love you so much! Hannunsa ya bude mata babu musu tayiwa kanta masauki jikinshi!!! *I lay my love on you, it's all I wanna do, every time I breathe I feel brand new, you open up my heart show me all your love and walk right through......* Shatuuu ♥️ [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* ✍️SHATUUU♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Assalamu alaikum Sweerie pies..... how's Sallah fatan kowa yayi sallah lapiya? Amin.... Allah ya maimaita mana Dearies. Inshaaa Allah zaku iya jina anytime from now, Allah ya karba ibadunmu. I've seen your comments and votes, Wallahi I can't ask for more... You guys are the best, I love you so very much.... Allah ya bar mu tare. Aci nama lapiya! Shatuuu ♥️ [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 41 ✍️shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Monday Morning Mikewa yayi daga kan carpet din da yake Zaune akai Tun bayan Idar da sallar asuba yake Zaune a gurin yana tilawa, gaba daya a takure yake jin kanshi tamkar anyi chaining dinshi haka yakeji, ya gaji zaman asibitin nan Tunda shidai yanzun yasan lapiyarshi kalau babu Abinda Ke damunshi, amman baya son ya nemi discharge din Tunda su suka kwantar dashi suka San Meye matsalarshi. Inda Dove dinsa take ya isa, ta kudundune cikin Duvet cover abinta se sharar baccinta take, Tunda sukai sallar asuba ta koma ta kwanta, gefenta ya zauna ya yaye cover din hakan yasa tayi juyi ta turo mishi karamin bakinta, murmushi yayi yace Dove makaranta fa, is already six. Bata fuska tayi ba tareda ta dago ba tace Ni ba zanje ba gaskiya. Idanunshi ya dan zaro Yana murmushi yace Why? Ni ba patient relative ba ce. Wannan karan seda yayi dariya yace Kinji ki da me kikeyi min? Come on tashi Kada ki makara. Zumbura Baki tayi ta Mike Daga gadon Tana ta Bata rai tana fadin Dama ba sona ake ba, if not me yasa zaace se naje school. Dariya yayi kasakasa Yana shafa kanshi, shikam Allah ba karamin so yake mishi ba da ya bashi Sulaim, Tunda Mami da Baba suka mishi albishir bai kara daina murmushi ba, she gave him every reason to smile, she never cease to amuse him. Yarinyar tana tafiyar da soyayyar ta kamar yadda ta fada mishi xai gani gashi kuma yana gani. Seda ya linke Duvet din sannan ya fita don yasan bazata iya shiryawa ba idan yana nan. Masifar kunya ce da ita don common peck ya bata se tafi 10 minutes idonta a kasa. Balle kwanciya dama se ya bari tayi bacci sannan yake hawowa gadon ya kwanta idan ba haka ba ta dinga mutsu mutsu kenan. Zama yayi Yana ta kallon yadda ake hadahada cikin asibitin, ita kuwa seda ta leko taga baya nan sannan ta fito ta shafa manta na Jergens ta fesa turarruka a jikinta sannan ta dakko wani lace zata saka ta tuna Monday ce yau black and white, hakan yasa ta maida ta dakko Bakar abaya Fara tas da Polk dots na baki a jikinta, powder ta shafa hade da balm ta kalla kanta tayi murmushi ganin yadda ta fito tayi kyau. Kanta ta taje ta gyara zaman ribbon din sannan tasa hula baka ta Fara gyaran dakin lokacin bakwai ta buga. Kafin ta leka kiranshi taji ya bude kofar ya shigo a nutse bakinsa dauke da sallama haka idanunshi kur a kanta yana jin wani sonta na fuzgar shi hade da nutsuwa cikin zuciyar shi. Kan carpet ya zauna lokacin tana tsiyayo ruwan zafi Daga flask zata hada tea, tayi kicinkicin da fuska ita a dole fushi take. Tana gama hadawa ta zauna gefen gado ta Fara sha tana ciccin magani tare da kawar da kanta Duk kuwa da tasan kallonta yake, shima share ta yayi Yana murmushi ya maida hankalinshi kan newspaper da aka kawo mishi. Seda ta gama ta dauki madaidaicin veil Baki me Polk dots farare mahadin Abayar jikinta tai rolling sannan ne ta dubeshi tace Yaya zan tafi. Kanshi ya dago tareda zare glasses din idonsa yace Zo kiji. Babu musu ta nufi inda yake ta sunkuyo, hannunta ya kamo ya zaunar da ita yace Yayan akewa fushi? Da fushi zaki tafi school? Kanta ta girgixa, kallonta yayi yace To Kiyi min murmushi na gani mana tawan! Murmushin ta sakar mishi hakan yasa ya janyota jikinshi tareda rada mata abu cikin kunne, kwace jikinta tayi tana dariya shuma yanayi yace Kin yadda? Kanta ta girgixa tace No! Zaki sani Ya bata amsa kafin ya Mike ya dakko wata Leda me kyau yace Amma tazo jiya Kina bacci tace na baki. Karba tayi ba tareda ta bude ba ta Mika mishi tace Ka aje min idan na dawo zan duba. Kanshi ya girgixa yace A'a kije kya duba a school. Babu musu ta karba suka fito tare Yana ta tsokanar ta wai amaryar Asibiti, itama tana ce mishi angon Asibiti, a haka suka zo station din nurses ya dan tsaya yace zai rakata gate zata tafi makaranta. Sallama sukai suma suna ta tsokanar ta, har gate ya rakata inda Jawad ke jiranta cikin mota, Seda yaga ta shiga kafin ya juya yana jin kawarta cikin jikinshi da zuciyarshi, hakika Sulaim tanada kaso mafi girma cikin zuciyar shi. Tana zuwa school sukai sallama da Jawad ta nufi class, inda suka saba zama taje ta zauna babu jimawa Aimana da Khairi suka iso kamar wanda suke Daga guri daya. Cikeda farin ciki suka zauna suka sata a tsakiya. Khairi ta dubeta tace Sulaim wannan kyau haka, ga kamshin amare da kike fitarwa. Aimana tayi saurin fadin Wallahi, kinga sati biyu kawai ta zama very matured se kyalli take. Gyara zamanta tayi tana jin ta inda zata Fara su fahimce ta, cikin nitsuwa tace Kuyi hakuri nasan kuna ta nemana a waya baku sameni ba, Wallahi Yaya yayi accident I some how fainted..... Idanu suka zaro.... To muka taho Kano na bar wayata a Kaduna. Tohm kuma yau Kwana biu aka daura mana aure ni dashi. Maimakon ganin bacin rai saboda bata fada musu ba, se gani tayi suna ihun murna har hankulan mutanen class ya fara dawowa kansu, Salma kwalam, Hidaya da Halimatou suka zo jin kwakwafi Aimana ta Mika musu invitation da Sulaim ta karbo hannun Junaid ashe shi ne sakon Amma din, su Mami sun yanke zaayi biki in a week time don ta tare basu son a ja abin, event din Kamu ne se dinner da friends din Junaid suka hada mishi anan Kano. Aimana ce ta dinga raba invitation card Khairi tana harhada yadda abin zai kasance da yadda zasu fitarda anko a samu a sati daya. Ranar gaba daya haka ta kare sun manta da wata Khulthum Seda Sulaim tace da Aimana Bani Aron Wayarki na kira Khulthum na fada mata. Nan Khairi ta Fara dariya tana bawa Sulaim yadda Aimana sukai da Khulthum, Aimana Cikeda bacin rai tace Ki bar shegiya kawai, Allah naji haushi Allah ya hadani da ita. Sulaim tace A'a ai ya wuce ki rabu da ita kawai, bani number idan naje na Kira da wayar Friend (Jawad). Rubuta mata akai jikin paper sannan kowa ta kama hanyarta, ta dan jima tana jiran Friend amma bai zo ba gashi bata da waya kuma, batayi azancin dakko kudi ba. Mikewa tayi ta nufi office din Ridwan daidai sun fito shida Sagay, da Mai Sogha da Dr Halliru, gaishesu tayi Ridwan Yana musu bayanin ita ce amaryar Junaid, gaba daya sukai mata Allah sanya alkhairi suka basu guri, anan ta samu ta fada mishi Abinda Ke faruwa, Muje na kaiki dama can zanje. Godiya tayi mishi tabi bayanshi suka tafi a motarshi, maimakon Asibiti se suka nufi gida, kamar zatayi magana se ta kyaleshi har suka iso yayi parking yace Ki fadawa Junaid ina waje ina jiranshi. Kanta ta gyada ta sake godiya sannan ta shiga ciki, Tunda ta bar gidan ranar jumaa da daddare bata kuma dawawa ba se yau, cikin nitsuwa ta Koda Yaushe ta shiga gidan daidai Jawad zai fito Yana ganinta ya fara fadin Dan Allah Friend Kiyi hakuri Wallahi Mami ta aikeni. Hararashi tayi tace Ba ruwana da Kai. Dariya yayi yace Se Amaryar babban yaya! Dariyar ta Kara saki tayi ciki tana jin farin ciki sosae a ranta. Koda ta shiga da Muhammad ta Fara cin Karo yana kuka yana kiran sunanta, take taji gabanta ya fadi tuna cewar Ashe akwai uwarsu fa, ita Wallahi ta manta ma gaba daya ta manta da rayuwar wata Subay'a don idan Suna tare manta wa take da wata Subay'a. Tsugunnawa tayi ta daukeshi tana lallashi suka shigo ciki, Mami ce a Zaune Kan kujera se Junaid a gefenta yana nuna mata abu cikin wayarta, sallamar ta yasa baki daya suka dago idonsu suna kallonta, zama tayi akan carpet tace Mami ina yini? Lapiya lau Sulaimi ya makaranta? Alhamdulillah. Ta fada sannan ta dubi Junaid wanda ke kallonta tace Yaya ina yini? Hararar ta yayi, sannan ya amsa, kanta ta dauke don ta fahimci Abinda yake nufi tace Yaya Ridwan Yana waje Yana jiranka. Da sauri ya mike yayiwa Mami sallama ya fice, kallon Mami tayi tace Mami zanyi wanka. Jeki se kin fito. Kwanaki haka suka cigaba da ja sosae ana ta shirye shiryen gagarumin bikin Ya'yan gata, ranar alhamis suka wuce kaduna gaba dayansu, sun tarar gidan ya cika da mutane, Tunda sukaje Mami ta dakko su Aliyah suka shiga Kara kimtsa Amarya, ranar jumaa Aimana, Khairi, Khulthum wadda ta shammace su Taxo don basu taba tunanin zata zo ba, don da Sulaim ta fada mata cewa tayi itama shirin nata bikin take. Ranar Friday akai Kamu na idon duniya wanda ya amshi sunanshi kamu, Amarya tayi kyau kamar babu gobe, yan class dinsu Hidaya sani Lawan, Halima Ahmad Ya'u da Salma Hassan Kwalam suka halarta, Yan SHATUUU's KINGDOM kamar kasa sunyi kyau kuma sun kayata gurin haka mutanen Maman mama novels da Kainuwa Fans group duka sun bayyana cikin ankonsu me kyau. Dab da zaa gama komai Junaid yazo da tashi tawagar, akai pictures sannan aka kamasu tare. Washegari ya tashi Saturday ranar Mami tayi yini, gidan ya cika sosae anci an sha anyi biki. Ranar Sunday da safe Mami da Baba, Junaid da Sulaim suna zaune Baba yayi musu nasiha sosae akan aure da kuma hakkokin junansu, Mami tayi nata sannan aka rufe taro da addu'a, da yamma suka isa Kano inda ta tare dakin Junaid akan zai karasa ginin shi, ita Sulaim batayi kuka ba saboda bataga dalilin kuka ba tunda jinta take tamkar taje yawo kaduna ne ta dawo kano. Karfe Tara aka fara kayattaciyar dinner wadda ta samu dubban mutane suka halarta, sunyi kyau Sulaim da Junaid kafin wani Lokaci hotunansu ya baza media. Shatuu ♥️ [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 42 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad _Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu gorgeous damsels! Barka da sallah! Allah ya maimaita mana many years to come. Ga barka da sallah na hope you guys will like it?_ Hannunshi cikin nata suka iso kofar parlon, takan tuna lokacin da suke dawowa daga school, kaduna a matsayin cousins to yau gashi ta dawo a matsayin mata, matar aure kuma matarshi. Wani sanyi taji Yana ratsa mata jiki har ya kai hannu ya bude parlon, shi dinne dai, yasha gyara an canza kujeru da carpets din. Saman kujera suka zauna a gajiye saboda yadda suka gaji. Idanunta ta daga ta dubi agogon parlon, karfe goma Harda rabi kallonshi tayi taga ya zuba mata dukkan idanunshi, sunkuyar da kanta tayi taji wani nauyin shi ya kamata. Hannunta da har lokancin ke cikin nashi ya matsa yace Bacci? Kanta ta gyada, Mikar da ita tsaye yayi, suka nufi parlonshi, wani niimantaccen kamshi ne gauraye da sanyi suka dokesu, komai na ciki an canza zuwa sababbi, parlon yayi kyau sosae bedroom dinshi ya nufa da ita har lokancin bai sake mata hannun nata ba. Shima komai an canza yayi kyau, Daga can lungu ta hango jerin trollies Kala wajen hudu da yake Wannan ne Karo na biyu da ta taba shigowa bedroom dinsa. Kallonta yayi yace Jeki wanka kinji? Kanta ta gyada ta Mike ta nufi toilet ya dakatar da ita ta hanyar fadin Da kayan zaki shiga? Bazaki cire ba? Bakinta ta turo tace Mhmmm. Kanshi ya shafa saboda yadda yake samun mugun effect a jikinshi duk lokacinda ta turo wannan karamin bakin nata, ji yake tamkar an jona mishi electric current cikin jininshi. Juyawa yayi ya fita don ya manta ya Bar abinci cikin mota. Tunda ta shiga take bin ko ina da kallo, toilet din very neat and tidy, komai in place. Kayan ta cire cikin dabara don karsu jike, ajesu tayi a tsanake ta Fara wanka, seda ta kammalla sannan ta dauro Alwala ta fito Tana jin tamkar tafi kowacce mace sa'a. Bathrobe ne jikinta se towel ta rufo saman kanta, yana shigowa tana fitowa, kallonta yayi yaga ta Bata rai yasan kada yayi mata magana ne hakan yasa ya shareta ya fara cire kayan jikinshi, seda ya kammalla sannan ya shige toilet, zama tayi ta Fara tunanin abinda zata saka a jikinta, nan ba dakinta bane tasan bata aje komai ba. Mikewa tayi ta bude kofa ta fice Zuwa Tsohon dakinta, Tana tura dakin taji ya bude Sede babu komai nata, gadaje ne biyu blue da coffee se wardrobes biyu, shelf da study tables babu tantama na Ahmad ne da Muhammad, don gasu a kwance abinsu suna shan bacci, Atika a kwance kan karamar katifa. Ciki ta shiga ta tsugunna kan Muhammad tayi kissing dinsu sanann ta juya bayan ta kashe wutar dakin a ranta tana tunanin ina ya kai mata kayanta? A parlor ta tarar dashi ya shimfida praying carpet daya a gaba daya a baya da hijab saman ta. Tana shigowa ya bita da kallo har ta zauna baice mata komai ba seda tace Kayana? Tashi yayi ya shige bedroom din ita kuma tabi bayanshi har gaban trollies din yace Ga lefenki I hope you will like them, Ya bude wardrobe dake can karshe jikin bango se ga kayanta sun bayyana, ya cigaba da fadin Is that all. Murmushi kan fuskarta ta gyada Kai. Seda ta saka sleeping dress sukai sallah kafin brain din Sulaim ta dawo aiki, Aure fa tayi kuma idan zata tuna ba ana having affairs ba, gabanta taji yayi mummunan faduwa har ta furzo yoghurt din da ta Riga ta kai baki sakamaakon fara cin kaza da suka Fara, da sauri Junaid ya matso kusa da ita tare da kokarin kama hannunta Amma ta matsa baya idanunta taf da hawaye tace A'a! Kallonta yayi cikin rashin fahimtar Abinda take fada yace Menene Kanta ta hada cikin cinyoyinta ta Fara kuka ilahirin jikinta na rawa saboda fargaba da tsoron yadda zata kasance, ta tuna Auren Afra cousin dinsu, Washegari sukaje tamkar ruwa haka suka sameta a kwance, to ita ta yaya zata amince ayi mata haka. Tasowa yayi ya nufo inda take ya rungume ta batareda ta farga ba, kuka ta kara saki tana son kwace jikinta amma ina bai bata wannan damar ba se ma Kara kusantata da jikinshi da yayi, seda ya tabbatar ta nutsu kafin ya sake ta yace Muje ki kwanta. Binshi tayi a baya har suka iso daki yace Ki kwantar da hankalinki kiyi baccinki, Abinda kike tsoro bazan yi miki shi ba.... Matsoraciya rigimammiya kawai. Turo bakinta tayi ta haura gadon ta kwanta yayinda Junaid ya fice a ranshi Yana fadin "perks of marrying a baby" dama tuntuni ya shirya ma hakan don yasan za'ai hakan. Shima shirin kwanciya yayi ya nufi dakin inda tuntuni bacci yayi awon gaba da ita. Gyara mata kwanciya yayi cikin jikinshi amma bata farka ba, dariyar yarintar Sulaim yayi ganin Tunda aka daura aure tare suke Kwana banda zuwanta kaduna amma se yanzun hankalinta ya dawo jikinta. Sake rungume ta yayi Yana karewa fuskarta kallo yadda take bacci peacefully and innocently. Murmushi yayi Yana jin abu me karfi Yana sake bin jikinshi game da Sulaim. Inda yayi niyyar yi mata wani abun da yi zaiyi yadda take wannan baccin. Gyara kwanciyarshi yayi lokaci daya Subay'a ta fado mishi, Allah babu yadda baya tsara abinshi, Subay'a ta tafi ta bashi space ya auri love of his life Sulaim. Runtse idonshi yayi yana tunanin yadda sukai da Mami jiya da take tambayarshi ko Subay'a tasan zancen auren yace Bata sani ba, Mami ta dinga fada sannan tace ya tabbatar ya sanar da ita idan ba haka ba ranshi zai baci! Shi dariya Mami ta bashi wai ya fada mata? Lallai! Kamar yadda tayi surprising dinshi da tafiya Cyprus haka zai surprising dinta da Sulaim. Bayan ta Idar da sallar asuba ta gyara dakin sannan ta fito dakin su Ahmad, har lokancin basu tashi ba amma Atika Bata nan wanda ya tabbatar mata tana kitchen, da sauri ta juya kitchen din saboda gargadi sosae Mami tayi mata akan barwa me aiki girkin miji. Tana shiga Atika har ta Fara kokarin Fara soya Irish wanda ta Riga ta Fere itada Laraba. Kallonsu tayi suma suna kallonta dauke da murmushi wanda ya tabbatar mata suna farin cikin kasancewar ta uwar dakinsu. Cikeda ladabi suka gaisheta tana ta dariya ta kullum sannan tace Atika jeki shirya su Ahmad, Bari na karasa girkin. To Atika ta fada Tana ficewa sannan Sulaim ta dubi Laraba Tace ita taje ta Fara gyara gida. Seda suka fice ta dukufa sosae tana girki Cikeda nutsuwa da kwarewa. Kamshin turarenshi ya fara sanar mata ya shigo. Gas din ta kashe sannan ta juyo fuskarta Cikeda murmushi tana kallonshi kamar yadda yake kallonta, ita ta Fara fadin Ina Kwana? Ciki ya karaso ya bude mata hannayenshi alamar ta rungumeshi ai kuwa babu musu ta shige jikin shi, Lokaci daya suka sauke ajiyar sannan ya karkato kanshi saitin kunnenta yace Wannan ce gaisuwar! How's your night ina fatan ba Za'a Kara kukan jiya ba? Ya karasa fada Yana dariya, tureshi tayi ta nufi kofa ya bi bayanta yana dariya, dakinsu Ahmad ta nufa hakan yasa ya wuce nashi Cikeda jin dadin yadda take kula dasu Ahmad din. Karfe bakwai duka suka iso dining, suka zazzauna ta Fara serving din yaran kafin ta hade nata da na Junaid, he was impressed Don Abinda yake shirin fada mata kenan se gashi tayi. Suna kammalawa yace Mu wuce Kada kuyi latti. Kallonshi tayi tana Kara gyara zama tace Se next week zanyi resuming. Idanunshi ya zaro yace Kidding right? Maida fuskar ta tayi very serious tace Nifa gaskiya na gaji da karatun. Kanshi ya girgixa yace That will never happen kinji? Tashi school zaki tafi so kike Baba yace na Hana yar shi karatu ko? Turo bakinta tayi tana fadin Dama ba sona ake ba zaace se naje school! Yana dariya yace Naji indai akan school ne na yadda. Daki ta nufa Don gyara kanta, har zuciyarta bata son Zuwa saboda bacci take ji Tunda Kwana biu duk a Wahale take. Skirt da riga tasa white and black sannan ta daura suit a sama ta yafa veil ta dakko books dinta ta fito sukai kicibis zai shigo, seda ya kare mata kallo kafin ya ja hannunta suka koma ciki ba tareda ya furta komai ba. Daya daga cikin trollies din ya bude take Abaya different designs cike fal amma Daga Fara, baka se mixed white and black. Kallonta yayi yace Ga sunan, sukadai nayi approving Kisa. Ita din ba Mai musu bace hakan yasa ta ciro daya daga ciki Fara heavily adorned with sparkling stones and sequence bakake, tayi mata kyau. Kallonta yayi yace It fits you Dove. Kinyi kyau. Lagwanbar da kanta tayi tana murmushi a haka suka fice don kiris ya rage su Ahmad su makara, iyayensu sun zauna soyayya. Yau kam har cikin class ya rakata kusan a cike class din yake saboda 8 har ta dan gota donma wanda suke dashi bai samu zuwa da wuri ba. Tunda suka shigo ajin yayi shiru idon kowa na kansu musamman ma Junaid kowa na mamakin shi ne mijin dama? Seda ta zauna sannan ya Mika mata handbag dinta bayan ya amsa gaisuwar su Khairi. Yana fita Aimana ta Fara dariya tana fadin Kaga love birds, bazai iya barin ki shigo ke daya ba se an rako ki. Ta Yayan ba! Itakam grinning take ear to ear kamar bakinta zai yage, kafin ta bada amsa lecturern Y shigo majestically hakan yasa sukai focussing akan lectures din, seda ya kammalla ya fice sannan suka Fara zolayarta ita dai murmushi kawai take saboda babu baki Tun asali ita bamai magana bace dalilin da yasa bata fiye sakewa cikin cousins dinta ba saboda ireiren wasan, Mami Tasha nuna mata tana mayarwa amma Sede murmushi kamar sokuwa. Sunanan zaune suna revising books dinsu Junaid ya aiko messenger shi akan tazo. Aimana ta dubeta ganin bata da niyyar tashi tace Ke bazaki tashi kije kiran miji ba? Hararar ta tayi tace Ke ina ruwanki? Sa ido kawai. Khairi tayi tsaki tace Wannan munafukar wai kunyar wa takeji? Allah yasa bamu ba, Allah kadai yasan abinda ku ka gama a gida shi ne xakixo kina susunke kai. Duka ta kai mata ta Mike Don Zuwa gareshi. Lokacinda ta isa office dinshi shi daya ta tarar har yayi Alwala zaije masjid don yin sallar axahar, kallonta yayi yace Se yanzun ko? Langwabar da kanta tayi a shagwabe ta hade hannayenta alamun ban hakuri , ruwan hannunshi ya fatsa mata ya fice yana fadin Naje sallah. Kanta ta girgixa a ranta farin ciki ne fal tana jin ya isheta rayuwa idan kuma ya wuce haka kila kwakwalwar kanta ta zauce. Aje handbag dinta tayi, tayi Alwala tayi sallah sannan ta zauna jiranshi. Shi daya ya dawo bayanshi dasu Ahmad da yasa aka dakko su, suna ganinta suka yo kanta suna fadin Ammiey! Kansu ta shiga shafawa tana tambayarsu school da komai, yana tsaye Yana kallonta taji kaifin kallon hakan yasa ta dago fuska dauke da murmushi, gefenta ya dawo ya zauna tareda sauke ajiyar zuciya me nauyi yace Your only concern is Ahmad and Muhammad. Papansu fa? Kin manta Mami tace ki kula Dani. Bata fuska tayi tana shafa kan Muhammad dake cinyarta tace Bakajin tausayinsu, Mamansu bata nan, kai kuma kanada Mami sannan kana Dani ko? Janyota jikinshi yayi gaba daya tausayin yaran na Kara ratsa shi, basu ma tambayar Mamansu ko sun manta da ita ne oho! Wasawasa haka rayuwa ta mika, soyayya me tsayawa a zuciya, kwanciyar hankali Marar misaltuwa haka Sulaim da Junaid suka samu, matsalarsu daya duk dare se Sulaim ta birkice mishi ta dinga fushi ko kuma yana kusantar inda take ta bare baki tana kuka, se kawai ya biye mata yadda take so hakan yasa take ganin ta fishi wayo. A haka sukai Kwana hudu, a ranar ya kai gejin da hakurinshi ya Kare, he wants her Amma yasan Za'ai rigima ba karama ba amman ya shirya wa koma me zatayi. Tunda ya fita sallar maghrib bai dawo ba dama yace mata se anyi isha'i zai shigo, dakinsu ta wuce tayi wanka tazo ta shirya bayan ta barar da turarruka jikinta, trollies dinnan ta nufa Don dakko kaya, English wears take so don ta gaji da saka native. Budewa tayi da wani bakin trouser ta Fara cin Karo hakan yasa ta dakko shi sannan ta hado da silk shoulder off half gown kalar milk, sakawa tayi ta kalla jikin mirror yadda kayan suka amshe ta sukai mata kyau tamkar bakuwar foreigner, tayi masifar kyau. Gashinta tayi combing ta daura scarf baki sannan ta maida trolley ta rufe tana mitar rashin inda zata jeresu don yace mata zamanta gidan is temporary wannan gidan Subay'a ne, ai fadar Subay'a da yayi Harda kukanta hakan ya tabbatar mishi tsananin kishin da take dashi. Ammiey! Ta jiyo jin Ahmad na kiranta, da sauri ta zura flat milk vine ta fito don jin dalilin kiran da yake mata. Cikeda nutsuwa ta bude kofar parlon ta fito bakinta na fadin Yaron Ammiey...... She couldn't finish the sentence saboda mutanen da ta gani a tsaye suma fuskokinsu tsoro, mamaki da tsana, Hajiya ce yes Hajiyan Subay'a! Surayya da Samina Sun sakata tsakiya. Wata muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta amma haka ta hadiye mugun yawu ta nufo inda suke, Bata kai ga karasowa ba taji knocking a kofa, ba tareda ta zauna kamar yadda tayi niyya ba ta wuce don bude kofar, Junaid ne tsaye hannunsa rike da ledoji, kallonta ya tsaya yi saboda masifar kyau da tayi mishi don wannan ne Karo na farko da ya ganta cikin ireiren kayan, kayan ya aje ya rungume ta tsam tareda Daga ta sama yana juyi da ita, ita kanta yadda taga sonta me tsanani cikin idanunshi sam ta manta da ruwansu Hajiya cikin gidan. Se dan kanshi ya ajeta sannan ya jawo ta ciki, shima da fuskokinsu yayi arba wanda kana kalla zakaga tashin hankali da tsoro ya karu akan tsanar, mamakin da da suke ciki. Hannunta ta zare Tare da jansu Ahmad don kaisu daki Samina tayi saurin shan gabanta tace Ina zaki kaisu? Karuwa ka...... Don't! Don't!! Don't you ever call my WIFE with that name, Matata ce aurenta Nayi kamar yadda na auri 'yar uwarku. Kutmar uba kenan! Fadin Samina wadda kirjinta har ya fara sama da kasa saboda yadda masifa ke Cinta dama copy din Suhaila ce idan bata nan to Samina ce substitute dinta. Juyawa Junaid yayi ya dubi Sulaim wadda idanunta kamar su fado saboda firgici se ta bashi dariya saboda he has never in his life cikin wannan tsoron. Kuje daki Dove Keda yaran. Kanta ta gyada ta ja yaran suka wuce shi kuma ya zauna tareda Fara gaida Hajiya amma bata ansa ba tace Junaid abinda idanuna da kunnuwana suka jiye min gaske ne ko kuwa? Aure kayi? Kanshi ya gyada yace Eh gaskiya ne Hajiya. Wata ashar Surayya ta saki tace Amma Junaid Bakada hankali! Wa kake tunanin a cikinmu zai zauna da kishiya? Subay'a Wallahi baka isa ba se ka saki waccen matsiyaciyar! Har cikin ranshi yaji zagin da Surayya tayiwa Sulaim hakan yasa ya dago idonsa da suka Fara canza kala yace da Hajiya Ki ja musu kunne kada wadda ta kara zagin Matata, yadda sukejin Subay'a 'yar uwarsu ce nima haka nake jin SULAIM To fa people kunji wannan? Tun kafin Subay'a uwar Boko taji labari kenan! Inhar Samina zata iya haka on behalf of Subay'a then wanne mataki Subay'a zata dauka a karan kanta? Let's go people..... shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 43 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Hajiya ta riga ta sanya wa zuciyarta duk yadda takai da takatsantsan akan abu to se ya faru musamman kan Subay'a wadda duk cikin 'ya'yanta ita ce me bata matsala saboda son da takewa Junaid. Numfashi ta fizga tare da duban Junaid tace Amma ka taba ganin anyi aure ba'a sanar da Matar gida ba, me yasa gaba daya maza Bakuda adalci? Bakuda alkawari? To Wallahi 'yata bazata zauna da kishiya ba, ban zauna da ita ba haka babu Wacce a cikinsu zata zauna da ita! Kallonta yayi a ranshi Yana bakin cikin kasancewar yaranshi sun fito daga tsatsonta, bai taba ganin sallamamiyyar uwa ba Irin hajiya ba, kallonta ya karayi har bazai bata amsa ba se kuma yace Wanda bai yiwa wani adalci ba, Hajiya ta ina yake tsammatar ayi mishi adalci. Aure na riga nayi shi, idan zata zauna kanta idan ba zata zauna ba aure mutum biyu ke yinshi zata iya tafiya babu damuwa! Zancen baki zauna da kishiya ba wannan tsarin Alhaji ne ni kuma nawa tsarin shi ne aje mata biyu a gidana. Idanu waje Hajiya take kallon Junaid kamar taji yace Subay'a can go, itakam Tunda ta Fara haduwa da Junaid matsayin siriki abubuwata ke lalacewa. Mu zuba mu gani! Murmushi yayi yace Allah ya kiyaye hanya, gashi ko ruwa baku sha ba. Yana sane yayi furucin don ya kara tunzurasu, aikuwa Surayya ta juyo Tana fadin Bazaa sha ba, Kaga mun zo maka a tsiyace, Allah ya kiyaye Wallahi. Dakyar ya iya controlling dariyar da tazo mishi, hajiya haka jikinta a sanyaye ta fito suka mara mata baya, suna shiga mota Samina ta dakko waya don sanar da Subay'a halin da ake ciki, hajiya ta kwace wayar ranta a mugun bace tace Kada wanda ya sanar mata halinda ake ciki, taje ta dawo ta samu abinda ta bari, ba ita mai biyayya Ba? Tafi kowa bin miji se ta dawo ta tarar da sakamaakon abinda ta bari. Surayya hankali tashe tace Haba Hajiya ta yaya? Babu Abinda zamui mata kenan? Me zaki mata? Mijinki ne? Duk yarinyar da na aurar se nayi mata kokarin da babu macen da zata kara burgeshi amma bansan inda subay'a take Kai Nata ba. Wani abu da Hajiya bata sani ba, itafa Subay'a su kadai take nunawa tana bin miji sau da kafa hatta Abinda suke bata na kayan gyaran mata ba sha take ba wasu lokutan idan suka taru flushing dinsu take, kuma se ranar da ta ga dama sannan take Zuwa turaka wasu lokutan se tafi sati bata je ba. Ina ganin lokaci yayi da zanbi shawarar Hansa'u. Wacece Hansa'u? Surayya ta tambayi Samina wadda a lokacin mafita kawai take nema. She's a neighbor, wajen wani malami da take Zuwa nan zamuje a raba auren, don indai ina numfashi cikinmu babu Mai zama da kishiya. Kada na sake Naji, ko by mistake wata taje gurin boka to ban yafe mata ba, boka idan yana maganin matsala shi yayiwa kanshi mana. Turo Baki Samina tayi jin furucin Hajiya, tace Bafa boka bane hajiya Malam ne. Ubanki nace kinji! Akan duniya zaki salwantar da lahirar ki, ni dai Allah ya sani ban taba kai kukana wajen wani ba kuma ban yadda wata takai ba, idan har kissa da kisisina ba zata zaunar daku ba, to duk Ku kashe Auren kuzo mu hada kafada. Kuma na maimaita Kada wanda ya fada mata halinda ake ciki! Tunda ta furta hakan kowa yayi shiru har suka isa gida. Acan gidan Junaid ya jima Zaune a parlour yana mamakin zuri'ar su Subay'a, gabaki daya babu hankali a cikin su, dukkansu taron tsintsiya ne babu Shara. Sulaim na zaune kan kujera ta kammalla koyawa Ahmad homework dukda hankalinta baya jikinta, ko kallonta kayi kasan a tsorace take, a haka Junaid yayi sallama ya shigo, idanunta ta dago Tana kallon shi kamar yadda yake kallonta, Yana Zuwa inda take Zaune yasa hannunshi ya rankwashi kanta, da sauri ta Mike hannunta akai Tana turo Baki tare da kwabe fuskarta saboda zafin rankwashin har brain dinta. Bata fuska yayi yace Wuce muje ki bamu abinci Tunda ke matsoraciya ce, kin tsaya Kina zazzare ido saboda su samu gut din Yi muki abu ko? Banza tayi mishi ta kamo hannun yaran Don fita ya fuzgo ta, ta fado jikinshi, rungumeta yayi ta Fara kokarin kwacewa har tayi nasara don kuwa bai saka karfi ba, kallonshi tayi tace Ahmad fa suna nan. Bakinshi ya tabe Irin who cares dinnan ya wuce ya barta a wajen tana zumbure zumbure. Tunda ta dawo daga kwantar da yaran take fushi kamar yadda ya zame mata alaada, ko kallonta baiyi ba don abu biyu ne zai hanashi having dinta that's if she's on period se kuma wani kadari daga Allah amma yau night dinnan is all about him and her. Agogo ya kalla yaga Tara tayi hakan yasa ya dubeta yace Dove bacci zanyi. Kallon time tayi sannan tace Ni kuma kallo zanyi. Harara ya maka mata yace Get up muje, wayace miki ana barin miji ya kwanta shi kadai? Ko dan yi zamanki Kiyi kallonki zanyi waya da Matata. Wani Dam taji a kirjinta saboda ambatar matarshi da tayi, da sauri ta Mike ta kashe komai sannan tayi gaba, shi kuwa me zaiyi banda dariya, lallai Sulaim at 19years har ta iya kishi. Yana Zuwa ya tarar har ta canja kaya Zuwa na bacci, wata silk Riga ce me hannun vest iya cinya se tight da ta saka a ciki Zuwa gwiwarta ranta a bace ta haye gado, shi ya rasa hadin Sulaim da bacin rai. Seda ya kammalla komai da ya saba kafin ya hayo gadon lokacin tana waya da Mami, yana zuwa ya jayota jikinshi tareda Fara zuba mata kiss wanda yasa ta saki wayar babu shiri saboda wani moan da keson escaping Daga bakinta saboda kiss din ba na wasa bane, bakinta ta bude da niyyar protesting kawai taji ya hada bakinsu ya fara bata wani kiss wanda Lokaci daya ya rikita jikinta da kwakwalwar kanta, Ta manta ita wacece, me take so da Maye bata so, what exist lokacin a duniyarta is only Junaid and nothing else. Seda ya tabbatar ta gama fadawa trap dinshi kafin akai me gaba daya. Wayyo wayaga bakin kuka.... Lol.... Tasha kuka kamar ranta zai fita, Seda ya nutsu don kuwan ita babu nutsuwa a tattare da ita kafin ya fara lallashinta amma ina se kara birkice mishi take tana kara rikita mishi lissafi. Kawai jikinshi ya sakata ya rungume Yana patting bayanta don duk yadda yaso bude bakinshi he couldn't bazai iya ba, Abu daya ya sani he will never let go of her, she'll forever remain in his embrace till death do them apart! Washegari fuskarta tayi jajawur ga wani wahallen zazzabi da ya rufe mata jikinta, ga bacci da take ji tamkar idanunta zasu rufe, ga jikinta ciwo yake mata amma haka ta mike a daddafe Bayan taji fitar Junaid massallaci saboda bai tashe ta ba dan ta huta. Bandaki ta shiga ta tara ruwa kamar yadda Yaya Imratu ta sanar mata lokacin har wani dariya takeyi saboda tana ganin babu amfanin hakan. Sitbath tayi sosae taji dan karfi ya dawo mata kafin tayi wanka tayo Alwala ta fito ta tada sallah. Tana idarwa wani bacci ya fara fizgarta amma haka ta daure ta Mike ta Nemo wata Abaya coffee me karamin hannu tasa hula sannan ta fito jinta take tamkar wata sabuwa, wani nauyi ya hau kanta, zuciyarta wasai babu wani kunci idan ka dauke bacci da Ciwon jikin dake damunta. Tana isa kofar Dakinsu Ahmad Junaid na shigowa Fuskarshi kadai zaka kalla kasan yana cikin madaukakin farin ciki wanda yaki boyuwa saboda yadda Junaid din ke ta murmushi. Tana jin sallamar shi tayi saurin tura dakin ta shige saboda azababben kunyar shi da take ji, binta ciki yayi ya tadda ta Tana tsaye Tana lallashin Muhammad dake kukan da ya saba na duk safiya. Gadon Ahmad ya zauna akai yana kashe Sulaim da wani kyakyawan kallo wanda Seda taji butterflies suna yawo cikin cikinta, dauke kanta tayi don Bata son tuna Abinda ya faru jiyannan. Yana nan Zaune har ta gama Abinda zatayi batace dashi komai ba haka shima Sede duk inda tayi to zai bita da idanunshi, kuma yana iya hango yanayin da take ciki. Tana barin dakin ya mara mata baya, se yaga ta nufi kitchen hannunta ya riqo hakan yasa ta dago a wahalce tace Yaya girkin su Ahmad fa! Your only concern is Ahmad and Muhammad, what about yourself? You need a break Bana son musu. Babu yadda zatayi haka ta bishi ya kwantar da ita bayan ya bata tea Tasha, aikuwa bacci me nauyi ya dauketa, bata farka ba se 12pm sannan ta Mike Tana jinta wasai, fayau tamkar iska zata dauke ta. Babu kowa dakin hatta gidan yayi shiru, wanka taje tayi a ranta tana jin son Junaid Yana bin dukkan jikinta, Tana jin tamkar task ne daya kamata tayi completing yanzun ta Gama, dukda Tasha wahala jiyan nan Amma bataji komai na takaaicin Junaid ba se ma sonshi da yake kara huhhuda jikinta yana zagaye cikin blood dinta. Wannan ranar ta dauki alkawari me nauyi akan duk runtsi duk wuya da izinin Allah se ta kawo mishi farin ciki wanda bai taba mafarkin samu ba, tayi alkawarin biyayya matsawar ranta sannan kuma zata soshi no matter the hardship, the situation and the circumstances! Lace ta dakko purple da peach me circle pattern dikin gown me kyau, dankwalin ta daura tayi kwalliyar ta daidai misali sannan ta zauna ta kira Mami suka gaisa kafin ta fito parlour, yana zaune kan kujera yana aiki cikin computer dinshi, gabanshi ya aje takaddu da ruwa an tsiyaya cikin tumbler. Dagowa yayi don ko batai magana ba yasan ta iso gurin, jikinshi ya fada mishi sannan kamshin turaren ta na Zahrat Banafsa ya isar da saqon. Shutting system din yayi tareda ture table din daga gabanshi ya miko mata hannunshi, babu musu ta Kama har lokancin idanunta a kasa. Rungume ta yayi sosae tamkar zaa kwace ta, bakinshi yakai kunnenta yana fada mata kalmomi masu tsananin tsada, ya fada mata yadda Daren jiya ya kasance. Ranar haka ta Kare suna tattalin juna, wata sabuwar chapter aka bude cikin gidan! Bari mu leka muji yadda amaryar TitαΦ ke ciki, Hajiya Khulthum ikon Allah! Cikin dankareriyar Prado baka wuluk Hajiya Nana da Hajiya Rafi'a wanda suka kasance kannen Gwoggon Musbahu ne. Su biyu kadai ta wakilta don suje kawo lefen Khulthum don Tunda ta samu labarin yarinyar yar talakawa ce yasa bata son hada mutane saboda zance da surutai, to suma a gurin nasu bata tsira ba. Nana ta Fara fadin Nikam Yaya Rafi'a Bakiji abin so strange ace Musbahu ya rasa duk fadin duniya inda zai aure se cikin ghetto? Tabe Baki Rafi'a tayi tace Bari dai Nana, Nifa haka kurum ban yadda da Musbahu ba totally. Kinsan yanzun he's 36 Amma ko sau daya bai nuna alamun mace na burgeshi ba, kullum idanunshi cike suke fal da tsanar mata kuma yasha furta hakan coincidence inaji baisan ina gurin ba. Hmmm Kede Bari Yaya, Wallahi the same thing da nake gani amma uwarshi tace aljana ta aureshi. Dariya suka kwashe da ita tareda tafawa sannan Nana tace Ai Allah ya hallici soyayya da feeling tsakanin mace da namiji so Duk yadda ka kai da kamewa ko kuma me zance dole ne saboda wannan is in blood! Balle shi Mai kudi ba! Haka sukai ta hira har suka iso gidan inda suka tarar mota da kyar take shiga layin. Haka driver ya kutsa ta Baya sannan suka samu ta wuce. Immediately suka Fada gidan don Nana fadi take Allah ka rabamu da ghetto! Rafi'a tace Allah ya rabamu tuntuni se wanda suka debowa kansu. Gidan cike yake dam da mutane da wanda aka gayyata da wanda sukazo ganin kwakwaf ai kuwa sun gani ba kadan ba, don kuwa anyi lefe har na rashin hankali, kudi sunyi kuka da idanunsu. Daxasu tafi suka ki karbar komai haka suka wuce, se ga uwar gayya tazo tayi wani Irin kyau tamkar ba ita ba saboda tuni ta Fara gyaran jiki don tasan inda zata shiga she doesn't mind Abinda ta kashe tasan zata fanshe. Ihu, habaici ranar tayi shi dakayar tayi bacci saboda kallon kaya bata taba tunanin zata samu haka ba. An saka ranar biki Nanda sati biyu masu Zuwa..... Se muce Allah yasa munada rai!! Cyprus. A hankali suke takowa saman titin da ya malale ko ina cikin makarantar. Subay'a tayi fari, tayi kyau kana kallonta kasan Hutu ya samu gurin zama. Somehow dai hankalinta a tashe yake dukda yawan kwantar mata da hankali da Sulma keyi saboda rashin daga call dinta da Junaid yake. Inajin karshen month dinnan zan tafi nigeria gaba daya sati biyu nan inajin tamkar akwai Abinda akeyi acan, yanzun gaba daya Junaid nake son gani sister. Sulma dake saurarenta tace Haba dai, amma lokacin ai kun kusa exams a department dinku. Tsaki tayi tace Na gaji da karatun Wallahi, tunda naxo banida kwanciyar hankali karatun duk simplicity dinsa amma Wallahi bana ganewa, Meye amfanin shi? Is better na koma na daidaita gidana na daidaita rayuwar aurena Sister, I've messed so much, nasan nayi wasa da damata, Junaid yayi kokari yanzun haka zan koma na gyara Abinda na bata. Ta fada with sincere repentance cikin muryar ta. Sulma dake saurarenta tace Hakane kam amma Tunda har Munzo yanzun inaga kiyi hakuri Zuwa yadda aka tsara se mu koma duka ko? Kanta ta girgixa tace Bazaki gane ba Sister, alhakin Junaid, Ahmad da Muhammad Wallahi bazai barni ba, is better I go back and amend whatever I torn. Is never late sister. Haka suka ta hira duk yawanci Subay'a ke tsare tsarenta har suka isa gida. Seda Subay'a tayi sallar ishai kafin ta kwanta yau batajin fita ko ina Tana son shiga social media taji me ake fada ne, meye latest. Data ta kunna ta kifar da wayar Don komai ya gama shigowa, seda ta kammalla kafin ta Daga wayar ta Fara da whatsapp inda tayi replying messages dinta kafin ta koma IG. Tana shiga da stories din Junaid ta Fara cin Karo, seda gabanta ya fadi don ita ta bude mishi IG kuma baya ma wani amfani dashi Amma what's so important daya daura. Daidaita kwanciyar ta tayi, ta rike wayar a hannunta tana jiran su bude Se idanunta suka sauka akan caption din dake rubuce #My Dove# the love of my life.... The best thing that ever happens to me.... I so much love you habibty♥️ Tana karasa karantawa take hotunan suka bayyana, tamkar tashin bomb haka hotunan suka Dakar mata zuciya, hotunan biki ne na kowanne event se wanda sukai ayau sunje shan ice cream Yana Sanye da black trouser da white top itakuma tana cikin black plain Voil na gown anyi mata ado da farin lace a wuya da hannu, kana kallonsu kaga Wanda hankalunsu yake a kwance wanda soyayya ke gara musu, gabansu bowl ne an saka scoop din ice cream guda uku, hannunsu rikeda spatula karama sun kai bakinsu suna murmushi me tsayawa a rai. A hankali taji wayar ta sulale Daga hannunta se kan tiles, kanta a take ya fara juyawa tamkar zata fado a gadon, zuciyarta tamkar zata balle kirjinta ta fito hakan yasa ta bude Baki ta saki ihu me karfi da ya janyo hankulan Samiha da Salima dake cin abinci a parlor! Hohohoho! Rate the page on a scale of 10 One word for the love birds #JUNSU# One word for the couples to be #MUSKHU# One word for the defeated #Subay'a# To me for the love birds #Allah ya bar kauna# for couples to be #mute# for defeated Subay'a #sorry# Does Subay'a still have a chance? Let's talk people, next chappy depenads on your comments. Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 44 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad _Hip Hip Hip hooray!!! My hearty congratulations goes to all the Writers of kainuwa, for marking our 2 years anniversary.... I pray Allah Azzawajal continue to guide us, lighten our path and may he forgive all of our shortcomings. Anty Fauzar mu 'yar amanah and others take this page as we celebrate together_ Babu Wanda yayi sallama cikinsu suka turo kofar suka shigo, a kwance suka sameta gwanin tausayi tana kuka Riris Tun karfinta, wanne irin masifa ce ta shigo rayuwarta? Baki daya suka tsaya turus tamkar gumaka saboda ganin halin da take ciki, Salima ce tayi karfin halin karasawa gefen gadon ta zauna Tana fadin Haba Subay'a! Me yake damunki? Shikenan ke kullum cikin Daga mana hankali kike, idan da Kinsan mijinki haka yake me yasa zaki ketare umarnin shi! Fada mata dai Yaya Salima, batada aikin da ya wuce tayar mana da hankali kamar ke daya ce me miji. Itakam ko fahimtar Abinda suke fadi batayi, ina ruwanta ma dasu, babu me fahimtar halin da take ciki idan ba ita kanta ba. Kishiya! Junaid aure! Shi ne kadai abinda take maimatawa cikin zuciyar ta, kuka kawai take don gani take shi ne abu mafi muhimmanci a wannan lokacin, shi kadai zaiyi wiping mata dukkan kuncin da take ciki. Ganin bata kulasu ba yasa Samiha tace Tunda bazata Yi magana ba, let her be. Suka fice ransu a bace suna mitar halayen subay'a, ita kuwa tashi tayi ta zauna tareda hada kanta da gwiwarta tana sakin kuka me Cikeda tashin hankali, da tafasar zuciya. idanunta sunyi jawur a lokacin Abu daya take bukata shi ne someone to talk to and that someone is none but Sulma. Mikewa tayi ta dauka abayar da ta cire ta mayar jikinta, mayafin abayar ta yafa sannan ta tsugunna ta dakko wayar da ta fadi, ko lapiyarta Bata tsaya dubawa ba ta fito, ilahirin jikinta a sanyaye yake tana jin tamkar an sassare mata gabban jikinta, ga hawaye dake mata zarya cikin idanunta zuciyarta nayi mata zafi tamkar garwashi haka takeji. Suna Zazzaune ta fito babu Wanda ta kula haka suma se rakiyar tsaki da ta samu daga gurin Samiha. Sulma na zaune tana kallon wani TV show a Arabian channel, gefenta Amna ce rike da feeding bottle Tana shan tea a ciki, Daddynta baya gari sunje field trip cikin wani gari hakan yasa ita kadai ta rage a gidan. Tunda ta jiyo sallamar Subay'a ta Mike don kuwa tasan babu lapiya ko daga amon Sautin muryarta, kanta ta dafe tana tunanin Anya ta Taba ganin mutum me masifar matsala Irin 'yar uwarta. Tun suna yara haka take, mutum ce da bata daukar shawara in zatayi Abu se ya kwabe mata sannan zata zo ta daga muku hankali haka take kuma har suka Girma babu Abinda ya canza zani. Gefenta ta zauna ta hade fuskarta da tafukan hannayenta tana kuka me cin rai, Wanda yake tabbatar maka wanda yake ba karamar tashin hankali da walagigin rayuwa yake ciki ba, kuka ne wanda Subay'a keyi na rashin sanin makomarta, na tashun hankali Cikeda nadamar da bata da amfani a wannan lokacin. Sulma Bata ce mata uffan ba dukda she's disturbed da kukan amma ya ta iya? Me zatayi? Kyaleta tayi taci kukanta me isarta wanda tasan ko babu komai she'll shed away some of her pains. Kowa yasan kuka is a powerful pain reliever, just try it. Seda tayi ta koshi tayi to her satisfaction kafin kuma ta goge fuskarta tare da kallon Sulma wadda fuskarta kawai zaka kalla ka hango tsantsar damuwar da take ciki, hannunta Subay'a ta kama Tana sakin murmushi wanda babu komai cikinshi banda zallar pain wanda dashi gwara tayi wani sabon kukan amma ya zatayi, Kiyi hakuri sister, inajin inama ina da wanda zan kawo wa kukana bayanki at least na daina tayar miki da hankali, I'm not good to myself balle to be good to others. Bana neman shawara ina yin duk Abinda zuciya ta taji ya kwanta mata don Nayi satisfying ego dina. Inama ace ni ce ke, inama ace Nayi kwaikwayon kyawawan halayenki da wasu abubuwan sun zo min da sauki. Hannunta Sulma ta rike bakinta ya kasa furta komai saboda abubuwan da take hangowa cikin idanun Subay'a wanda Bata taba gani ba. Wayarta ta dauka ta bude mata pictures din idanunta na zubar da hawaye ta Mika mata. Jiki a sanyaye ta karba sede biyu kadai ta iya kalla jikinta ya fara rawa, ta aje wayar tareda runtse idonta. Wasu hawaye masu zafi a Karo na barkatai suka shiga zubowa Subay'a, kuka sosae ta kuma fashewa dashi tana fadin Kinga ni ko? Junaid yayi aure, ya auri yarinyar da tafi kowa sanin flaws dina! Yarinyar da duk duniya bana fatan na bude ido Naga tana numfashi! Nayi kuskure babba na gasken gaske kuwa! Na tafi na baro mijina under the care of abinda nake ganin sonshi cikin idanunshi. I deserve it...... Toshe mata Baki tayi tareda janyota jikinta tana lallashinta, har Seda tayi shiru kafin Sulma tace He punished you da aurenta. Kanta ta girgixa tace A'a Sister kin tuna Abinda nake zargi? Na zargi yana sonta zamana ya zama kamar barrier tsakaninsu, I never in my life taught barin gurin zai basu space din cika burinsu, se gashi ya cika burinshi. Ya zanyi I destroyed myself with my hands.... My very own hands Sister. Shiru tayi ta Mike Kara dawowa ta zauna idanunta basu daina barin hawayen da suke ba, bata taba mafarkin akwai ranar da zata wayi gari taji makamancin wannan kuncin ba, kai ko ce mata akai a duniya irin wannan feelings din does exist to tabbas zata karyata mutum, yau gashi Itace ta tsinduma kanta a ciki. A yanzun ta fahimci maanar zaman lapiya shine kabi Abinda Allah da manzonsa suka ce, ta tuna wata levtures da ta taba attending akan biyayyar aure, manzon Allah SWA yace Idan da zansa ayiwa wani sujjadda Bayan Allah to miji ne! This is to show how manzon Allah SWA yake son nuna girma da kuma daraja ta miji amma a yanxun ta take Nata tayi yadda take so. Zan tafi Nayi booking next flight to Nigeria. Ta fada Bayan ta koma ta zauna, Sulma Cikeda damuwa tace Hakan yayi amma zaki dawo ko? Kanta ta girgixa tace Not necessary, zan koma na gyara Abinda na bata, Kede Kiyi min addu'a na dace. Dafa kafadarta tayi tareda fadin Duk Abinda zaki tarar ina fata zaki rufe idanunki, kiyi hakuri kada ki tada hankalin ki me faruwa ta faru. Dariya Subay'a tayi tace Life has taught me so much, ba se kin dora ni a hanya ba sister. Yanzun bana bukatar kowa yace min ga yadda zanyi. Kanta ta gyada mata kafin suka Mike ta rako ta har bakin kofa, daga nan sukai sallama ta koma ciki jikinta a matukar sanyaye, Tana fatan hakan ya zama babbar shiriya gareta. Bangaren Subay'a kam tunda ta shiga dakinta ta kwanta tare da fara booking flight sede next flight to Nigeria is in a week time. Tasha kuka kuwa saboda tana ganin hakan yana Kara nisanta ta da kudinrinta. Tundaga wannan ranar ta daina fita, Ta kashe wayar ta. Hakan yasa ta zama very lonely and bored. Ranar da sati ya cika ranar ta kammalla shirinta tsaf, an hour to the time ta fito da kayanta tsaf ta nufi airport don ko Sulma Bata fadawa ba Balle su Suhaila wanda basa gidan Baki daya sun tafi lecture. Tana zuwa babu bata Lokaci akai screening da komai sukai boarding jirgin da ya Lula zuwa Nigeria. KADUNA. Mami na Zaune itada Baba Wanda ya dawo shekaranjiya daga umra, suna kallo jefi jefi suna hira akan matsalolin da suke addabar Nigeria. Nikam matar Junaid har yanzun bata dawo ba? Baba ya tambaya idanunshi kan Mami, gyara zamanta tayi tareda fadin Inafa bata dawo ba, don bance tasan da zancen Auren ba. Kai Baba ya kada yace Junaid baiyi Saar uwar 'ya'ya ba, kwatakwata yarinyar tafi kama da yaran da basuda uba Amma bansan abinda mahaifinta yake ba har uwarsu Ke wannan hidimar. Tsakin takaici Mami ta saki tace Ka manta Ance shima haka yake fama, kawai kaddarar Junaid ce hakan, Shiyasa bazan saka baki ba akan hukuncin da zai yanke mata ba, kawai bazan Bari ya saketa ba amma lokaci yayi da zai daidaita gidanshi. Hakane Nafisa, Amma ya kike ganin zaman Ummu_Sulaim da Junaid zai kasance? Dariya Mami tayi don ta fahimci me Baba yake nufi, Kada yarshi tayi bora. Wannan is sort already, yanxun yace Malta zasuje early next month, kafin su dawo ginin da yake ya kammalla, Kaga kowacce da gidanta. Sallamar Ja'afar yasa Baba bai bada amsa ba, sema wani muhimmin zance da ya fado mishi ganin Ja'afar din, shima ya kara kyau dukda yayi rama a fuska amma kana kallonshi zaka San Hutu yana aiki a gurin. Zama yayi kan carpet ya gaishesu, suka amsa sannan Baba yace Ja'afar Babanka Ibrahim dazun ya kirani akan maganar ku kaida Haulat! Haulat? Haulat kuma Ja'afar ya fada a birkice, Wacce Irin magana kuma Eh Haulat dai, babanta yace ta fito da miji zai mata aure tace Kai kuke tare. Da sauri yace Wallahi karya take Baba, Mami...... Karka sake ka kira Sunana, Haulat kake denying, sau nawa ina ganin pictures din ta cikin wayarka, Mamanta Tace min har Abuja Kake Zuwa zance. Baba yana kallon Ja'afar yadda yayi kicin kicin da fuska Cikeda tashin hankalin jin inda yake neman afkawa. Haulat ita daya Allah ya bawa Alhaji Ibrahim Kasim kanin Mami da Anty Batuul wanda suke Zaune a Abuja, Haulat babu laifi tana da kyau kuma tanada tarbiyya Sede yarinya ce shakwaf da batafi 16 years ba amma tanada girman jiki, kuma tana daya daga cikin yan matan Junaid sede Itace me least wadda yake ganin zai iya aura se gashi an rikeshi rum a hannu! Kai Ja'afar yimin bayani, ya zancen Maminku yake? Da gaske ne Baba, amma ni ba sonta nake ba..... Yaudarar ta kake, kasan duk Abinda kake ina sane dashi, kasan haka kayiwa sulaim ko? Sulaim kuma Mami? Ni nace miki Bakace ba, I read it a diary dinta, Hanan fa? Kanshi ya dafe wanda yake Sara mishi kamar zai fadi, waye ya mishi wannan ta'asa, Baba kasa magana yayi saboda mamaki, ranshi a bace yace Wallahi ko baka sonta Ja'afar Seka aureta, kuma wannan shi ne magana ta karshe. Ki zama cikin shiri next week zamu tura a bamu Haulat a Karo na biyu Bayan Sulaim! Subay'a na hanya, who will volunteer to sweep her room for her, ya haduwar zatayi da Junaid da Sulaim matafiyan Malta? Ina labarin mutanen Texas da A'isha? Ga Ja'afar ya ballo aiki, Ina TitαΦ da Amaryarshi. Tell me your opinion about this page and what might happen next. Shatuuu ♥️[8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 45 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Ina masoya Anty Sumayya Abdulkadir Takori? Ga dama ta samu cikin sauki da kudi kalilan zaki karanta littafinta na _A BARI YA HUCE...._* Jirgin daya taso Daga Murtala Muhammad INT'L Airport dake Lagos ya sauka a Aminu Kano INT'L Airport dake birnin Kano. A hankali passengers ke fitowa kowanne da yanayin da Fuskarshi ke ciki, wasu gajiya, wasu yunwa, wasu excitement, wasu tsoro ne karara kwance akan fuskar tasu kamar Hajiya Subay'a wadda tamkar kace mata kett ta zura a guje saboda tsabar yadda take a firgice batasan abinda zata tarar ba a wajen Junaid don ita a halinda take ciki bata Sulaim take ba so take ta fara kashe kurar kafin ta koma kan Sulaim din. Bata expecting kowa ya zo daukarta ba Tunda babu Wanda yasan tazo din haka ta tari napep wanda if she can remember vividly bata tunanin ta taba hawa commercial ride Tunda take a rayuwarta. Kwatance tayi mishi yana ta basarwa tareda ciccin magani ya amsa zaije, seda ya kalleta tsaf yaga yadda kudi ya samu gurin zama yace 600 zai karba, bata ja ba haka ta hau suka nufi gida, gabanta Yana ta faduwa lokaci lokaci tana share hawayen da yake bin kuncinta. A kofar gate din ya ajeta tareda nade hannunshi Yana jiran ta fito amma ina tayi nisa sosae cikin duniyar tunanin da take akan abinda zata tarar idan ta shiga, ko wanne irin tarba zata samu, tasan bazai taba sakinta ba amma zai iya hukuntata da mafi munun hukunci shi ne Silent treatment halin Junaid ne ya kyaleka akan laifinka Sede ya barka da guilty tension haka yake. Juyowa me napep din yayi ganin yana ta mata magana Bata bashi amsa ba, ya juyo yace Hajiya ki sauka ki bani kudina ina ta miki magana kinyi min banza. Dagowa Subay'a tayi ta share hawayenta tace Yi hakuri Malam. Tsaki yayi ya ciro cigar daga pocket dinshi yayi lightning tareda Fara zuka, Jakarta ta bude ta ciro purse Amma babu Nigerian currency se na can inda ta baro, jikinta har rawa yake tace Bari na shiga na dakko maka kudin dan Allah anan babu. Wata ashar ya saki tareda bule ta da hayakin bakinshi wanda yasa ta fara tari babu kakautawa don idan akwai Abinda Subay'a ta tsana shi ne warin cigar Amma Kinci uwar rainin hankali, da Kinsan bakida kudi xakixo ki shigar min napep na kawo ki! Subay'a ta kullu take Hali ya motsa ganin yadda kankanin yaro yake mata rashin kunya, Amma a hankali ta dinga petting kanta tana fadawa kanta yanxun is not the right time tayi haka, kawai ta lallabashi ta samu ta bashi kudin taje taga yadda gidan yake ciki. Kayi hakuri mana shiga kawai zanyi na kawo maka. Tsaki yayi hakan ya kara bata mata rai amma ya zatayi, yau tana jin tamkar ba Subay'a bace, kamar ba ita ba wadda fuskar wargi mutum bai samu Balle Ya kawo mata hauka amma imagine Yau Itace wannan kanin bayan nata yake mawa haka. Trolley dinta taja ta Fara knocking wabda shima ta kusan shafe Mintina goma kafin me gadin yazo, ranta a matukar bace tace Bakasan aikin ka ba kenan wawa kawai! Shi baima bi ta kanta ba yayi ciki abinshi hakan ba karamin mamaki ya bata ba, to Meke faruwa? Her remaining dignity is lost also? Ta tuna yadda jiki na rawa ma'aikatan gidan ke mata biyayya amma yau Itace ko matsayin gaisuwa Bata samu ba. Kanta ta girgixa Tana jin wani daci cikin ranta wanda har bakinta take iya jin dacin. Ciki ta shiga gabanta Yana dukan uku uku, lokacinda ta tura kofar parlour ta shiga Seda ta runtse idonta saboda wani yanayi da ya ratsa ta, gidan da ta bari ba tareda izinin Junaid ba, Ta tsallake yaranta wanda take jin duk duniya ba abin da takeso tamkarsu Amma a haka ta tsallakesu ta tafi biyawa zuciyarta bukatarta. Da sallama dauke a bakinta ta karasa cikin tsakiyar parlour, ko ina tsit se kamshi wanda ya zama bakonta da take iya shaka, komai ya canja an canza komai in just 3 months kawai, se taji ta tamkar bakuwa, tamkar is the first time of her being a gidan. Jin shiru yasa ta nufi kofar dakinta don shiga Sede Tana rike kofar taji Atika na fadin Wacece? Idanunta ta dan runtse tare da aro jarumta ta juyo Tana facing Atika wadda ta fito Daga dakin Sulaim, Tana kallon Atika Bata wani canja yanayin fuskarta ba da ta ganta, hakan ya ruguza mata lissafi tareda sakar mata da gwiwa. Amma haka ta dake tace da Atika wadda take Mata wani kallo wanda Subay'a ta kasa fassara manufar kallon Amma yafi kama da you lose! Ina mutanen gidan? Daidaita kanta tayi ta tsugunna kamar yadda ta Saba Don kuwa Subay'a na nan matsayinta Koda sakinta Junaid yayi Balle da aurenshi har yanzun a kanta. Tun shekaranjiya suka tafi kaduna. An fadi Yaushe Zasu dawo? Kanta ta girgixa tace A'a Ammiey bata fada ba. Cikin rashin fahimta Tace Wacece Ammiey? Anty Sulaim! Ta Bata amsa take taji Wani abu ya tokare mata makoshi Jin Sulaim ce Ammiey! Juyowar da kanta tayi tana murda kofar amma a rufe hakan ya tabbatar mata Junaid ya tafi da key din, purse dinta ta bude don neman spare key Amma fit babu shi don kuwa ta barshi anan tana sauri bata dauka ba. Kallon Atika tayi da take rurrufe kujerun parlour da ledarsu hakan yasa tasan mutanen gidan ba yanzun Zasu dawo ba kuma alamu sun nuna sun bawa ma'aikatan Hutu. Batare Tace komai ba ta dauki Jakarta da trolley ta koma don tasan anan gidan a yanxun she's not welcomed. Tana fita ta tarar me napep din ya gama shaka tana tsayawa yace Amma Hajiya wannan rashin mutunci ne ko ki bar mutum a tsaye Yana jira. Hakuri ta shiga bashi sannan ta lallaba shi ya kaita gidan hajiya, nanma Bata samu hajiyar ba amma ta aika mishi kudindhi kafin tyi wanka ta kwanta ta Fara kuka saboda bata taba wulakanta Irin na Wannan ranar ba, dole ranar ta shiga history dinta! Meye kuke ganin makomar Subay'a a gidan Junaid? Wayarta dake gefe tana faman ringing ta kai hannu Wanda yasha lallai Baki me azabar kyau, tafukan hannayenta Baki daya jan lallai ne tamkar a India. Ita kanta Khulthum kara kallon kanta take not believing Itace wannan, buri Yana daf da cika, Tana daf da zama mata, Amarya kuma uwargida uwar yaran Musbahu me TitαΦ! Tun ranar da aka kawo lefe bata kara fita ba idan ba ya zama dole ba, shiri kawai take don bata bukatar ace batai fitting ba a matarshi ba kamar yadda mutane suke fada, wasu na ganin kawai don wata manufa zai aureta yayinda wasu Ke ganin asirce shi tayi. Koma dai me nene Khulthum dai Kwana biu kacal ya rage ta shiga daga ciki. Gidansu ya cika har makota don komai da zaaci Musbahu ya kawo kuma Tun ranar da ta iske shi office dinshi basu Kara haduwa ko jin muryar juna ba, wabda hakan ko a jikinta Don ko taso damuwa idan ya hankado mata uban kudin se taji ta manta dashi. Hakan yasa babu Abinda sukai na kananan mutane komai ya tafi yadda Khulthum Take so yadda kuma ta tsara. Su A'isha sun zama yan kallo don seda ta samu Mama take Mata korafi akan kudin Musbahu amma Mama tace bata son gulma aikuwa ta rufe bakinta ta cigaba da harkarta itada Ashir wanda ta riga ta damke shi a hannunta. Yana Texas inda ya fara karatu cikin nasara don yayi mata alkawarin komai na lafawa zai dawo ya aureta su samu yadda zasui. Hello Sulaim Sulaim dake zaune gefen Mami tana cin abinci tace Khulthum longest time. Idanunta ta dan lumshe tareda fadin Ina nan. Dama zan fada miki gobe Za'a Fara bikin. Wanne biki? Sulaim ta tambaya don ita rabonta da Khulthum ma tun data kirata tayi mata godiya da bangajiya basu Kara communicating ba dukda Sulaim ta kikirata akan school, test da exams bata picking, tayi mata text se tayi replying da ta bar school tuntuni hakan yasa Sulaim Bata Kara komawa ta kanta ba, don Tana ganin tafi karfin wulakanci a gurin Khulthum din. Bikina mana Ta fada sounding serious. Idanu Sulaim ta zaro tace Aurenki Khulthum amma se ana gobe kike fadamin? Anya Khulthum are we still friends. Dariya Khulthum tayi tace Ki manta kawai abubuwa suka hade min Kede se kinzo. Kai Sulaim ta girgixa tamkar Khulthum na ganinta tace Bazan samu damar Zua ba saboda anjima jirginmu zai tashi zuwa Malta Allah ya sanya alkhairi. Daga haka bata jira amsarta ba ta kashe tareda kallon Mami wadda da dukkan alamu bayani take jira. Briefly tayi mata bayani tare da fadin Ko ina gari Mami ba Zuwa zanyi ba Balle kuma bana ma garin Mami batace komai ba se dariya da tayi sannan kuma tace Kin gama hada komai na tafiyar? 7pm sharp jirginku zai tashi. Turo Baki tayi tace Ni Mami bana son tafiya na barki. Ja'ira rufe min baki. Dariya Sulaim tayi tana fadin Kai Mami yanzun kin daina so na. Ta fada Tana sake turo bakinta Cikeda shagwaba. Hararta Mami tayi ta maida fuskar ta serious I tace Sulaim! Inason ki maida hankalinki ki rike mijinki, kiyi mishi biyayya sau da kafa kinji? Karki manta bake daya bace kuma komai Daren dadewa Subay'a zata dawo gida. Nasan Junaid Yana sonki nasan bazai wulakanta ki ba inason ki rike darajarki saboda duk yadda mace take ita Gem ce a priceless one ma kuwa. Yanzun Auren Duk ya koma wani iri amma dukda haka ba duka aka taru aka zama daya ba, inason kisan cewar idan maza suna da laifi a aure to mata ma akwai tasu problem din. Inason ki dage Kiyi ibada Koda hakan ne kawai zai sadaki da Aljannah...... Mami ta jima tana mata nasiha da bata dabarun zama wanda jikinta yayi sanyi tamkar an watsa mata ruwa. Suna gamawa ta wuce daki don biyar na yamma tayi tasan duk inda Junaid yake to yana hanya. Wanka ta Fara yi sannan ta shirya cikin Abaya fuschia pink da bakin heart pattern a jiki. A hankali ya bude kofar ya shigo jikinshi Sanye da trouser na kamfanin marks and Spencer se milk din top ta Zara se silver wrist watch a hannunshi na hagu me kyau na kamfanin Frank Miller. Yayi kyau sosae amma Sulaim bataji Shigowarshi ba saboda nisa da tayi wajen daura bakin wedge sandals a kafarta kuma ta kasa, se kawai taji hannunshi ya zura mata igiyar. Dagowa tayi ta dubi inda yake tsugunne ya maida dukkan hankalinshi kan Abinda yake, murmushi me kyau ta saki daidai lokacin da ya dago idonsa ya zube cikin nata wanda Lokaci daya ya shagaltar dasu Seda wayarshi dake cikin Aljihu ta Fara vibration kafin ya mika mata hannu ta Kama suka fito babu Wanda yayi magana. Baba ke driving da kanshi se Junaid a gefenshi, Bayan seat kuma Mami ce da Sulaim wadda ta kwantar da kanta akan kafadar Mamin tana jin wata kewar Mamin na ziyartar ta kamar kada ta tafi amma Junaid is everything for her, he's her entire world that revolves around the globe, he mean everything, idan tace everything she mean komai da komai na duniyar nan a bayan Junaid yake a gurinta. Seda sukai sallama dasu Mami Sulaim Harda kukanta, Junaid Yana ta dariya sannan suka wuce aka gama screening komai ya kammalla kafin sukai boarding jirgin wanda ya tashi zuwa birnin Valletta dake kasar Republic of Malta! Shatuuu ♥️ [8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 46 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Halooooooooooo.... Pipul of wattpad here's a page for all the votes, comments and recommendations. thank you very much Jazakumullahu khairan! Tun daga parlor yarinyar da keyiwa hajiya hidima a gidan ta sanar mata Subay'a ta dawo tun dazun, da hanzarin ta ta nufi dakin dan Zuwa ganin lafiya saboda tun shekaranjiya su Suhaila suka kirata suka sanar da ita sun dawo basu same ta ba, baki daya hankalinsu a tashe yake haka itama hajiyar hankalinta a matukar dunguzume yake. Koda aka tambayi Sulma itama cewa tayi bata fada mata ba don ta manta sunyi maganar haka wannan kwanaki biyun ya kasance cikin matsaltsalu kashi kashi. A dakinta ta samu Subay'a kwance kan gado ta kudundune cikin bargon dake ninke gefen gadon , da sauri hajiya ta iso ciki har tana tuntube, bargon ta yaye wani dumi ya bugeta ta Hangi Subay'a kwance tana ta karkarwar sanyi, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zauna gefen Subay'a tareda yaye ilahirin bargon wanda yasa Subay'a bude idanunta wanda sukai ja ba idonta harta fuskarta tayi jawur tamkar tumatir saboda azabar kukan da tayi, Tana jin Duk duniyar ta ishe ta, ji take ta tsani komai don se yanzun wani azababben kishi ya dirar mata anyi mata kishiya? Mijin ya tafi da kishiyar tata? Hawaye masu dumi suka sake gangaro mata wanda ya tilasta mata lumshe idonta saboda barazanar tsagewa da kanta keyi, ita kanta tasan tunda tazo duniya bata taba kukan da tayi Yau ba, Kai ita totally ma bata taba tunanin zata tsinci kanta cikin wannan rayuwar ba, Bata taba kawowa a hankali ta cewar Junaid zai iya kallon wata mace da admiration Balle har zuciyarshi ta kwadaita aurenta, ta tuna dimbin son da ya nuna mata lokacin yana neman aurenta, ta tuna yadda ya dinga fadi tashin samo mata farin ciki amma ita ko sau daya she never reciprocate, Abinda take son gani shi ne Tana juyashi kamar muciyar tuwo to every direction she desires, Wanda hakan ya fara jefa rayuwarsu cikin matsaltsalu don sam Junaid yaki daukar wanann abin. She remembers maganganu na lallashi, fada, nasiha, threats da yayi mata Daren da taje mishi akan zata wuce Cyprus, har ce mata yayi he'll refund hajiya abu daya yake so ta zauna dukda babu tsiyar da take mishi Shida 'ya'yanshi don aikinta da family dinta is her number one priority amma haka ta tsallake komai ta wuce! Idan ba rashin adalci Irin nata ba, taya take expecting Junaid ya zauna tsawon watanni shida shi daya ba tareda mace cikin rayuwar shi ba? Duk kuwa da cewar mutum ne shi me kokarin masking ainahin Abinda zuciyar shi take ciki amma ina bata yi musu adalci ba so dole rayuwarta ba zata taba tafiya daidai ba! "Oh ni! Uwar Mata Subay'a me zan gani haka? Meye ne yake damunki?" Idanun Subay'a ta kara lumshewa a ranta tana fadin duk ke kika sani a halinda nake ciki don dai ke uwa ce! "Subay'a tashi ki fada min Abinda Ke damunki" Bude idonta tayi a hankali ta kalli Hajiya wadda hankalinta yake a tashe saboda yadda fuskarta ke a dugunzume, a hankali ta bude bakinta tace "Hajiya ki bar ni kaina ciwo yake min kamar zai fashe" "Assha, kwanta ki huta" Kafin Subay'a ta kuma furta wani abu ladidi ta shigo bakinta dauke da sallama ta tsugunna tare da sanarwa Hajiya Alhaji Yana jiranta a parlor, mikewa tayi jikinta a sanyaye ta fito inda Alhaji ke tsaye Yana waya, tana fitowa ya maida wayar aljihun gaban shaddar jikin shi, ya jiyo yana fuskantar ta ran shi a bace fuskar shi a murtuke, abune da Hajiya a iya zamansu sama da shekaru talatin baza ta iya tuna ranar da taga Fuskarshi a haka ba, ga wani wulakantaccen kallo da yake binta dashi Irin Shekeke dinnan. Se kwarjini da taga ya kara, baki daya taji ya cika gurin har taji tsoronshi ya darsu cikin ranta. Kut ta hadiye wani abu daya tokare mata tare da kirkiro murmushi zatayi magana amma yayi beating dinta yace Bani keys din part dincan na gefe yanzu. Idanunta ta sauke Kan shi, kawai se ta tsinci kanta da juyawa ba tareda tayi mishi musu ba ta wuce dakinta kamar sokuwa ta tattaro keys din Baki daya ta kawo mishi. Yana karba ya wuce abinshi babu wani bayani ko wata magana hakan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba. What's Alhaji up to? Rana bata karya sede uwar diya taji kunya wannan shine popular Hausa proverb da muka sani, tabbas ya tabbata Ummu_Khulthum Suleiman Malumfashi ta zama mallakin Musbahu Suleiman Jimeta akan sadaki zunzurutun kudi naira dubu Dari bakwai. Mutane sun halarci wannan daurin Auren duniya ta shaida saboda yadda Musbahu ya daukaka a duniyar business da Entrepreneurship, the young billionaire kenan, Musbahu me TitαΦ Dan Gwoggo na Khulthum! Anyi biki na Kece raini ba Daga bangaren Amarya Ba ba Daga bangaren Gwoggo ba, anyi harkar girma don kuwa Khulthum ta sakar ma Mama kudi Don ta fitarda da ita kunya aikuwa babu karya ta fitar da itan. Parties iri iri seda tayi kala biyar babu Wanda Ango ya halarta se wata English dinner da business partners dinshi suka hada mishi anan garin Abuja, haka yasa aka mishi booking flight ita dashi suka tafi karfe shida na yamma, anan aka shirya ta tayi kyau tamkar ba ita ba sannan driver yaxo ya dauketa ya kaita inda Musbahu yake, yayi kyau shima cikin grey tuxedo suit hannunsa daure da bakin agogo na kamfanin Boss, yayi kyau sosae kana kallonshi kaga fulanin usul, lokacinda ta isa gareshi waya yake, ya juya bayanshi a hankali ta kare mishi kallo Tana Kara godewa Allah mijin da ya bata wanda ko daya bata taba tunanin zata samu kamarshi ba. Amma here she's with mijin da duk duniya tasan ta auri mijin nunawa saa. Juyowa yayi Don Tun shigowarta yaji a jikinshi saboda turarenta da ya ziyarci kofofin hancinsa, kallonta yayi he has to admit the fact that Khulthum kyakyawa ce wadda bazai yi shayin shiga da ita kowanne guri ba, Sede yasan babu digon son shi cikin zuciyar ta, kudin shi take yiwa zai cika mata burinta kamar yadda zata zama protector ga rayuwarshi. Kanshi ya dauke ganin sun hada idanu kar tayi tunanin ta burgeshi ne, itama kanta ta dauke a ranta tana fadin duk wannan girman kan naka se na sauke maka shi! Tare suka fito Zuwa wata lambhorgini baka wuluk da take tsaye Tana jiransu. Kunsan abin wayayyu, Manya wanda kudi ya zauna musu, dinner was great karfe Tara aka tashi Khulthum ta tafi da kyaututtuka iri iri. A Daren suka dawo kano, Washegari ranar ta kasance lahadi tun safe yan uwa, munafukai, abokan arziki, Kawaye sukaje ganin daki kowa idan ya dawo banda zancen gidan babu Abinda suke, gida ne da suke ganin tamkar drawing ko kuma a film saboda yadda ya hadu. Da daddare Misalin Tara Gwoggo da kanta tazo ta tafi da Khulthum, babu wata nasiha da akai mata don kowa tsoron magana yake ganin gidan da Khulthum din ke ciki waye zaiyi gigin barar da kujerarshi, hatta Mama bata wani Yi mata fada ba kawai tace mata tayi abinda ya dace. Har daki Gwoggo ta kaita tazo itada Musbahu wanda gaba daya jikinshi a matsanancin sanyaye yake gefen ta ta sanya su ta shiga tsakiyarsu tare da kamo hannunsu cikin nata fuskarta kadai zaka kalla kasan tana cikin farin ciki Marar misaltuwa, furucinta kadai seda ya kara jefa zuciyar Musbahu cikin Anya kuwa? "Allah ubangiji yau ya cika min burina da ya dade cikin zuciya ta, Allah yasa yau naga matar ka Musbahu, ina fata zaku zauna da junanku lapiya, zaku sauke dukkan hakkokin da ubangiji ya daura muku. Ina fatan kunsan cewar shi aure is for two parties babu yadda za'ai ace na mutum daya ne, kowannenku Yana da nashi role din dayake playing. Dukkanku babu yaro ina fatan zaku zauna lapiya!..... " Ta dade tana tuna musu hakkonkinsu kafin ta hada hannayen su guri daya ta fice baki daya daga gidan, ta koma nata. Sun dade a haka kowannen su da Irin tunanin da yake har wasu mintuna suka shude kafin Musbahu ya cire lallausan Hannunsa Daga nata, ba tare da ya furta komai ba ya fice daga dakin. Mikewa tayi itama, ta Fara kallon dakin da yake mallakinta, duriyar da aka dankara a ciki don ko cokali ba Taxo dashi ba anan ta samu. Touring part din Nata tayi, kana shigowa zakaga karamin parlor me dauke da cushions guda biyu se center table da carpet, ta gefe jikin bango akwai wani hadadden console a manne. Daga nan se siririn corridor wanda yasha ado da manyan frames da akai painting a jiki na flowers masu kyau, a karshen corridor akwai tafkeken parlor wanda ya kunshe kujeru set uku kowanne da kalarshi da kuma design dinshi. Parlon kadai abin kallo ne, anan wawakeken kitchen wanda ya kunshi kayan alatu na idon duniya electronics iri iri kusan duka ma batasan yadda zatayi amfani dasu ba. Bedrooms biyar ne, uku nata biyu na Baki. Gidan yayi kyau. Dakinta ta koma ta shiga wanka zuciyarta Fara kal kamar shinkafar tuwo, shiryawa tayi cikin wata sexy sleeping wear iya gwiwa baka tayi kyau kamar ba ita ba Balle yadda Tasha gyara don ta durzu a wajen masu gyaran jiki Shiyasa ta Kara kyau sosae kamar ka tabata jini ya fito, kwanciya tayi idanunta a lumshe tana planning yadda abubuwa zasu tafar mata. Tun tana zuba idon ganin ta inda Musbahu zai bullo har wani nannauyan baccin gajiya yayi tafiyar ruwa da ita. Washegari Bata tashi ba Se sha daya na safe, seda ta tsala wanka kafin ta fito tayi kyau cikin wani dankareren bakin lace wanda aka mishi ado da manyan flowers fuschia pink, parlor ta fito inda ta tarar komai in place, dining an shake shi da different dishes na gida dana waje. Can ta wuce tana bubbudewa amma ko abinci kwaya daya Bata san sunanshi ba. Tana kokarin zama Sega wata matashiyar budurwa Sanye da uniform tazo ta gaisheta cikin Pigin English, ta gabatar da kanta matsayin Linda Itace me kula da abinci. Zama Khulthum tayi Cikeda isa Tana karkada kafa ta dubi Linda tace "you're welcome here, inason duk lokacinda aka gama abinci kafin ayi serving dina se an fada min sunanshi da asalin dish din wanne kasa ne " Da sauri Linda ta gyada Kai tareda fadin "Noted Ma'am" A hankali ta Fara bubbudewa tana mata bayanin komai, Khulthum tana saurare saboda ta rike don babu girma ace Bata san wannan abubuwan ba. Bata jima da kammalla cin abincin ba Maimuna da Safiyya wanda suka zama sababbin kawayenta suka zo gidan, Bedroom dinta suka baje ana tashan shafta Bayan ta saka an cika musu gaba da abubuwan tabawa. Maimuna tace "Hajiya gidannan yayi kyau babu karya se Munji kin Fara laulayi " Dariya tayi tana jin yadda sanyi ke zagaye ilahirin jikinta, tana jin burinta ya kammalla cika bata da sauran matsala kuma. Seda sukai La'asar sannan suka tafi, dake an ware mata driver da me kaita da kuma na bakinta, haka tasa ya kaisu har gida, suna ta fasa mata kai ita kuma tana Kara girman kai. Dama Tun kafin a kawo ta Tace da Mama kada wadda tazo mata gida Washegari Tunda duk sunga gidan to hakan ma yayi, Shiyasa yau Batayi Baki ba se zagayen gidan da ta karayi. Har aka Idar da sallar isha'i bata ji shigowar Musbahu ba, mikewa tayi ta dauki wayarta da niyyar kiranshi ta tuna bata da contact din shi, abinma se ya bata dariya don ko a labari bata taba jin hakan ba. Duba kanta tayi tana cikin wata Indonesian Abaya beige color, Abayar tayi mata kyau sosae abinka da farar mace, kanta na cikin wani milk scarf wanda ya zauna daidai da tsarin jikinta. Flat milk vine ta zura ta fito bayan ta feshe jikinta da sassanyan Arabian turaren ta. Tana fitowa Linda na kokarin setting table, kallonta tayi tace "Ina ne part din Musbahu? " "Ma'am ta gefen naki yake" Kanta ta gyada ta nufi kofa zuwa nashi haka kurum gabanta ya dinga faduwa, amma ta cigaba da nufar part din, babu kowa a parlorn se sanyi da kamshi dake tashi, parlon ya hadu ba iyaka don haduwar shi will put her own into shame! Rarraba idanu ta tsaya yi se taji bude kofar bedroom din dake fuskantar ta, hankalinta ta mayar kofar take wani charming guy wanda shekarunsa bazasu dara 23 ba ya fito bayansa Musbahu ne Fuskarshi a wani yalwataccen murmushi ne wanda ake gani kamar sau daya a shekara!... Lol.... Ko kallon inda take baiyi ba sema guy dinne ya gaisheta ta amsa Tana nemarwa kanta masauki cikin daya daga cikin Royal Cushions din dake cikin parlour. Tafi Mintina talatin zaune kafin Musbahu ya shigo Yana binta da kallo Marar ma'ana, kasa tayi da kanta har ya sami guri ya zauna sannan yace "Me ya faru? " Da sauri ta dago idonta tana kallonshi don ba haka ta Zata zaice ba, ta yaya ma zai mata wannan maganar Bayan yasan ba hakan ya kamata yayi ba. "Naga baka shigo bane, nazo naga lapiya" Tana rufe bakinta yace "Lafiyata kalau, bana san sake ganinki a part dina, duk Abinda kike so zaki iya kirana, idan kuma ina bukatar abu zaki ganni. Ina fata zaki kiyaye saboda gudun mummunan gani" Cikin rashin fahimtar furucinshi na karshe ta dago Amma har ya nufi dakinshi, kanta ta dafe a ranta tana fadin Khulthum me kika siyawa kanki? Tana nan Zaune tana jiran ya fito ta fada mishi batada contact dinsa amma shiru, har ta Mike zata fita Sega wani matashi wanda shekarun shi bazai wuce 19 ba ya shigo kuma straight dakin da Musbahu ya shiga nan shima ya fada ko kallonta baiyi ba. Kwadayi mabudin.......... Shatuuu ♥️ [8/26, 5:03 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 47 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Where are you my best friend, beloved and my other half, the first person I know _Salma Hassan Kwalam_ take this page please! My everything.... The person that always brags I'm not missing you but keeps on calling asking se Yaushe zaki dawo? That's my sister for me* _VALLETTA_ Sulaim na tsaye gaban water dispenser hannunta rike da Tea mug, ruwan zafi ta tsiyayo sannan ta dawo cikin parlon dake suite din nasu, tea bag ta jefa ciki tareda cube din sugar. Seda ta juyo kafin na samu damar kare mata kallo, tayi kyau kamar ba gobe dukda babu Abinda ta shafa a fuskar Amma kana kallonta kasan Hutu, Jin dadi da kwanciyar hankali sun samu guri. Ta kara haske fatarta se glowing Take tare da murmurewa. Tana Sanye da mini skirt fari me ditson gold, rigarta wadda ko cibiyarta bata rufe ba gold da fari farin lacy design a jiki, kanta babu dankwali se parking da tayi in a ponytail design. Transparent golden jacket ta daura saman kayan wadda akaiwa ado da gashi me laushi a jiki. Single bedroom din dake cikin suite din ta nufa, Junaid na tsaye jikinshi Sanye da bathrobe wanda ya tabbatar mata da fitowarshi kenan daga wanka, tea din ta Ajiye Kan dan table din dake gefen gadon wanda Junaid ya maida gurin wajen aikinshi system dinshi a gurin take dindin da papers yana aiki, gurin no go area ne ga Sulaim don ya hana ta saboda yace aikin school yake bai son ta gani Tunda she's still thier student. Inda yake ta isa fuskarta dauke da madaukakiyar fara'a wanda ya bayyanar da hakoranta, wushiryar ta da kuma dimples dinta da suka lotsa baki daya, shima wani kwantaccen murmushin ya dinga binta dashi wanda yake sa takan manta har kanta, murmushin nan ba karamin kwantar mata da hankali yake ba, tana jin duk duniya in har zata cigaba da ganin Wannan murmushin Fuskarshi to she need nothing again in her life, he's everything he needs, har ta isa inda yake bai daina murmushin ba, zagaye hannunta a jikinshi tayi tareda kwantar da kanta kan kafadarshi ta na mishi kallo cikin idanu. Hannunsa yasa ya shafa kanta yace Kinyi kyau Dove. Thank you.... Se tayi shiru bata karasa ba saboda yadda ya tsareta da idanunshi Yana jiran tace Yaya, sakinshi tayi ta isa kan gadon ta zauna tareda fadin Hearthrob! Gurarshi guda ya daga tareda karasowa inda take ya zauna Yana rike hannunta tareda fadin I'm I as sweet as that? Dariya ta saki tana rufe fuskarta, janye hannunta yayi tareda matso da ita jikinshi yace Comeon Dove tell me mana! Ya fada kamar yaro a shagwabe, turo bakinta tayi tace Kafi haka ma. He was stunned saboda yadda tayi maganar Daga karkashin zuciyarta yake, wani farin ciki Marar misaltuwa ya kara mamaye ilahirin jikinshi, tashi yayi Daga gefenta bata tsammata ba ya daga ta sama yana rocking dinta tamkar baby, se dariya takeyi tana jin kamar duk duniyar nan su biyu kadai suka rage kuma babu Wanda ya kaisu farin ciki "Hearthrob Kaga I'm feeling dizzy" Jin hakan yasa ya sauketa tareda danneta suna maida numfashi kafin kuma Sulaim ta Fara ihu "Ka daga ni " Kafada ya maqe alamun No, hannunta tasa ta Fara tutture shi har ta samu ya zame zuwa gefenta ya kwanta Yana sakin ajiyar zuciya, wannan shi ne babbar dacewa auren abinda kake so yake sonka don shi yasan yasha Kwana! Tare suka shirya Don yace mata zasuje restaurant din dake cikin hotel din suyi breakfast, jeans ta saka wanda ta cikashi tayi dam revealing dukkan wasu curves dake jikinta, Top ta zura wadda ta sha rubutu masu yawan gaske with different colors, wata lallausan kimono baka ta daura tareda rolling karamin veil daya sakko ya rufe mata kirjinta, tare suka nufi kofa se Lokacin ta tuna da ashe tea zata sha, dariya tayi Wanda yasa shi dubanta amma baiyi magana ba, haka abin yake lokuta da dama takan manta abubuwa da yawa, Junaid ya zama babban jigo cikin rayuwarta. Simple abinci na breakfast aka musu serving, Cikeda nutsuwa suka ci sannan suka fita don yin walk, garin badai dadi ba ga weather dinsu itama is favourable, a yanzun Satinsu biyu kenan da isowa kasar, Seda sukai kwanaki hudu ko kofar suite dinsu basu leka ba suna ciki suna honeymoon dinsu me kyau, hakan yasa suka shaku sosae har Sulaim ta zama 'yar gari a fannin, wannan zaman ta kara fahimtar abubuwan da Junaid yake so da wanda baya so, shima kuma da Wannan damar ya daura mata mugun sabo dashi wanda an inch suka kasance basu kusa se jikinsu ya fada musu, haka Kuma yayi nasarar kawar da 60% na kunyarshi a kanta. A Kwana na biyar suka samu cab ta dinga kaisu gurare cikin Valletta basu suka dawo suite dinsu ba se yamma likis Wanda gajiya take neman ruguza su. Kwana biu suka huta sannan suka dora da gurare cikin kasar ta Malta. Daf da Za'a Fara shiga sallar Azahar ta zauna kan wani bench dake gefen titi shi kuma ya shiga massallaci don yin sallah, wayarta ta dakko ta Fara chatting nan taga message din Jabir da na Anty Imratu, cikin hanzari ta bude na Imratun it says "Matar Yaya, Nanda eight months kui expecting baby from me Inshaaa Allah" Gaba daya se taji tamkar wani awaited burunta ne aka cika mata shi, Anty Imratu nada ciki, dukda ta kasance a yanayin rashin sallah hakan bai hanata yin sujudus shukr ba don nuna godiyar ta ga Allah. Tana dagowa ta Fara kiran Jabir Allah ya taimaka wayar ta shiga aikuwa yana dauka ta Fara fadin "Alhamdulillah Yaya! I'm so happy for you guys " Ko ba'a fada ba tasan yana cikin farin ciki Marar iyaka "Nagode sosae mutanen Valletta, Ina Yaya " "Yana sallah" Ta bashi amsa, kanshi ya gyada yana Kara mata godiya bai jira sunyi sallama ba ya kashe saboda wani call dake shigowa, Jin dadi sosae yasa bakinta kamar zai yage ta Kira Mami da Imratu Amma amsa daya ce wayarsu is not reachable at the moment. Haka ta hakura badan taso ba, wani Irin dauki take ji take kamar ta shiga massalacin ta fada mishi sakon Amma babu Hali, haka Tanan Zaune se murmushi take tana jin tamkar tayi tsuntsuwa Zuwa Nigeria don taya su Yaya Jabir murna, dama rayuwar hakuri ce kawai gashi su At longest last gashi sun haihu, Dama haka abin....... Bata karasa tunanin ba taji tattausan hannaye sun rufe mata idanu, ko baa fada ba tasan Junaid ne don kuwa turarenshi ya tona asirin shi, dariya ta saki tareda fadin Heartthrob! Sakar mata ido yayi, tare da jiyowa ya tsaya a kanta yasa hannunshi ya rankwashi kanta, kanta ta yi saurin mikewa tare da Dora hannunta daidai inda ya rankwashe tan, ta zumburo bakinta idanunta sun cika taf da hawaye don taji zafin rankwashin ba karya! Wuceshi tayi har lokancin Bata daena sosa kan ba, ganin haka yasa yayi saurin bin bayanta tareda shan gabanta Yana mata Abinda yasan shi ne weakness dinta wato wannan kayataccen murmushin, Hararshi tayi tana bawa hawayen damar zuba kan kuncinta, da sauri ya zaunar da ita don rabon da yaga hawaye a fuskarta tun ranar da zasu zo Malta, yasan wancan ma shagwaba ce amma wannan fa? He's the cause Bayan alkawarin da Yayi mata da kanshi akan he'll do whatever it takes to see batai kuka ba. Poor him gashi baaje ko ina ba ya sata kuka. Itama ganin yadda Fuskarshi Lokaci daya yasa ta share siraran hawayen zafin rankwashin tace I'm OK, kawai heartthrob mugunta kamin" Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungumota jikinshi ya rada mata abu a kunne, dariya sosae ta dinga yi hakan ya mantar da ita rankwashin da yayi mata. Seda suka koma suit dinsu ta Fara fada mishi cikin Imratu, sosae yayi murna sannan ya kira Jabir sun jima suna magana har bacci ya fara fizgarta akan carpet din kafin taji ya matso da ita jikinshi Yana fadin "Raguwa kawai, 3 months har yanzun kin kasa conceiving se bar mana babies kike suna ficewa" Ya fada Yana murmushi, hannunta tasa ta toshe kunnenta tana jijjiga Kai irin bata ji ba, dariya yayi yace "Take your time dear" A hankali yayi slipping bakinshi cikin nashi, itama cikin bukata ta bashi hanya suka Fara kissing junansu......... 🎤Zuciya ta da taka abokan juna, da basu rabuwa ko a gun Kwana! Ina a farke ko a cikin barci na kai nake tunani cikin kwakwalwa ta.... 🎶 The page is very small I know.... Just manage OK..... I love you guys! Irin one love dinnan! Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 48 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Ranar ta kasance Lahadi wanda yayi marking Kwanaki ashirin da uku da Subay'a ta baro garin na Cyprus ta dawo gida zaman jiran gawon shanu, zaman da bata san Meye makomar ta ba, zaman da wanda take dominshi bai san tanayi ba. Gabaki daya tayi rama ta kare tamkar kudin guzuri, Duk wannan abubuwan da ta dauka ta aza a kanta sun sauka da kansu ba ita ta sauke su ba. Hajiya kam bata wani koma ta kanta ba don itama tata ce ta same ta, kwata kwata ta rasa direction din Alhaji ya saka gaba, ta kasa fahimtar ina ya nufa, ita karan kanta Tana iya Kwana biu bata saka shi idanunta ba, da sassafe yake fita as early as six am sanann bazai shigo gida ba se ta twelve am, hakan seda ya tayarwa da Hajiya hawan jininta wanda ta dade da mantawa cewar Tana dashi saboda yadda take bin doka tareda kaffa kaffa. Hankalinta a tashe ta nufi dakinshi bayan taci kwalliya kai kace sabuwar Amarya ce amma har dare ya raba gida biu babu alamar Alhaji, Karo na farko da Hajiya ta samu kanta da zubar da hawaye don tasan komai ya lalace kenan! Ita babu Abinda bata yadda ta aikata ba Irin neman taimako hannun wanin Allah, a ganinta Allah kamar yadda yayi alkawari bazai yafe shirka ba, Tasan bin malaman tsibbu manyan shirka ne hakan yasa as much as she can take kokarin ganin ta kaucewa hakan. Amma haduwa da hatsabiban Kawaye seda suka gama mata dukkan hudubiobin tsiya suka jefata hanyar malamai hakan yasa ta dage a tsaye wajen ganin 'ya'yanta imanunsu ya tsaru kuma tayi wannan nasarar don kuwa kowanne abu ya lalace ita kanje gurin malaminta ya gyara abubuwan Sede bai taba nasara akan Junaid ba hasalima baya kwatanta aiki akanshi don se ya rushe saboda tsananin adduar da rike Allah da yayi. Wayarta ta janyo a hankali tana jin Lokaci yayi da zata bi Abinda zuciyarta Ke raya mata, ya kamata ta Fara gyara mistakes din da tayi kusan shekaru bakwai tana yi. Lokacinda Subay'a ta Fara dialing number Mami gabaki daya wata iriyar kunya ta mamaye ta hade da tsoro me firgitarwa saboda bata san wanne irin karba Mami zatayi mata, zuciyarta taji tana bugawa da karfi saboda jin call din ya fara ringing, ga mamakinta se jin muryar Mami tayi tana fadin Subay'a! Baki daya se ta duburburce ta Fara kame kame words din bakinta dukka suka dauke har Mamin ta Kara fadin Subay'a Kina jina? Ma...Ma.... Mi ina yini iiii Ta fada Tana stammering, murmushi Mami tayi tace Lapiya lau Subay'a kin dawo lapiya? Yasu Hajiya Se kawai hawaye ya Balle mata, dama haka rayuwar take kayiwa mutum sharri ya saka maka da alkhairi, gashi ta gani taga wanda suka gaji arziki suke Daga gidan girma Wanda jira kawai suke mutum yayi nadama sui embracing dinshi. Three weeks kenan Mami. Bude Baki tayi Cikeda Al'ajabi tace Amma babu labari, kina ina yanzun? Ina gidanmu Shiru Mami tayi don ta rasa me zatace, what if idan Subay'a bata san yayi aure ba taji a bakinta? Hakan babu dadi amma se tace Ai Junaid din yayi tafiya zuwa Malta amma cikin week dinnan muke expecting dinshi, yaran kuma suna Delta wajen Imratu. Wata ajiyar zuciya ta sauke jin inda yaranta suke in a safe hand, tasan wacece Imratu bazata cutar da yaran ba amma ita abu daya kawai take jira Mami tayi testifying auren Sulaim da Junaid don gani take karya ne Duk dare gani take kamar idan ta tashi zata ganta gefen mijinta amma ina ta riga tayi sake da damarta, Dama Anty Takori tace A BARI YA HUCE shi ke kawo rabon wani.... Mami ce ta katse mata tunaninta da fadin Ki gaishe min da Hajiyar da 'yan uwanki. Kanta ta gyada tace Inshaaa Allah Mami nagode! Daga haka sukai sallama ta kwanta tare da sakin kuka don tayi hakan saboda Mami ta shiga lamarin amma poor her Mami bata bata Koda number Junaid din ba. Ta dade a kwance se ta jiyo muryar da ta Sata saurin mikewa don if she's not mistaken Suhaila Tajiyo, da sauri ta fito Zuwa parlourn amma mamakinta ya girmama saiamakon ganin sauran yan uwanta su bakwai gata ta takwas, kowaccensu ka kalla jikinta babu wani kwari haka suka samu guri cikin kujerun suka zauna, itama gefen sister ta zauna Tana fadin Meye haka kamar wanda akai mutuwa zakuzo dukkanku jiki a sanyaye. Babu Wanda ya bata amsa don babu me bakin amsar, hakan ya kara daga mata hankali se ta Mike Tsam ta nufi bedroom din Hajiya ta sameta hankalinta a matukar tashe tana amsa waya, gefe ta zauna Tana jiran hajiyar ta kammalla wayar wadda ta fahimci da Anty Kubra take wayar hakan ya kara bata mata ranta don ta tsani Anty Kubrar saboda ta hannun daman Hajiya ce, babbar aminiyarta ce wadda dukkan wani abun hajiya babu Wanda bata sani ba akan hajiyar dasu su Subay'a duk Abinda Hajiya keyi wannan matar ke daura ta akan hanya, hakan yasa Subay'a ta tsane ta itama Matar ta sani Shiyasa basa shiri kuma Subay'a ta zama koma baya a tallafin da Anty Kubra ke kawowa sauran. Ya akai Subay'a? Hajiya ta tambayeta bayan ta aje wayar don hankalinta yadan dawo jikinta saboda Antyn tayi mata alkawarin yau dinnan Za'a sabunta aiki, Nawa Alhajin yake da har zai zauna Yana daga mata hankali ita kuma ta wani tsaya har kwanakin nan tana kunsar bakin cikinshi. Hajiya bazaki rabu da Anty Kubra ba? Hajiya kina kallon Abinda ya fara kunnowa cikin rayuwar mu, Duk yadda kike tsaye kanmu amma haka Junaid yayi aurenshi! Inace hakan ya zame mana izina gaba daya...... Da sauri Hajiya ta katse ta da fadin Ke gidan ubanwa kika ji Junaid yayi aure? Waye ya fada miki? Itafa Hajiya bata san dalilin dawowar Subay'a ba don Bata bi ta kanta ba kasancewar itama tana cikin matsalar Ashe.... Ba wanda ya fada min Hajiya, a social media na gani Shiyasa na dawo na daidaita rayuwar aurena kafin wankin hula ya kaini dare. Hajiya ta bude Baki ta bata amsa Subay'a ta tari numfashinta da fadin. Kizo parlour Kinyi baki! Tana fadar haka ta fito jikinta a matukar sanyaye, tabbas basui Saar uwa ba don kaso mafi girma ita ce ta watsa musu rayuwar gidan mazajensu, ita ta dora musu halin cewar mace ita ce shugaba gidan aure ba miji ba hakanan ta sakasu suka dinga zuba iskancin su wanda duk a cikinsu Sulma ce kadai ta fita zakka. Tana isa parlon ta koma inda ta tashi babu Abinda ya canza, gurin is so tensed and not favorable kwatakwata hakan yasa taji ta gundura har Seda Hajiya ta iso idanunta a warwaje ganin Suhaila, Sulma da Kuma Salima mutanen Cyprus, ga kuma Surayya, Samina, Samiha da Sakina. Gabanta Yana bugawa da sauri sauri tamkar zai fito tazo ta zauna Tana fadin Meye ne kuka dawo kuma? Meye kukazo kuka zazzauna kamar marasa...... A makogaro maganar ta makale ganin Abinda idanunta Ke hangowa, Alhaji ne Sanye da trouser na kamfanin Zara se top wadda ta amshe shi, kanshi anyi masa saisaye hatta Fuskarshi an rage kasumbar da ta cikata, yayi kyau tamkar lokacin yana ganiyar 20s dinsa, Baki daya tsufan ya wuce se yarinta karara da ta bayyana a tare dashi. Duk wannan bashi bane damuwar Hajiya ba a'a kyakyawar Yarinyar da shekarunta bazasu wuce sha Tara ba tana Sanye da pencil trouser Baki da top ja kanta babu dankwali ta zubar da gashin kanta Wanda ya sauka har ya dan wuce dokin wuyanta Baki sidik Yana sheki, ita kanta yarinyar tamkar anyi barin perf jikinta saboda tsabar yadda take fitar da fitinannen kamshi, kyakyawa ce ta gasken gaske don kallo daya zakai mata ka gaskata hakan. Fuskarta ta nuna tsantsar yarinta ga kuma kyabe fuska da tayi kamar me shirin yin kuka, se kara shigewa jikinshi take. Surayya ce ta Fara mikewa idanunta tamkar xasu fado kasa ta bude bakinta Dan magana Alhaji yace Duk Wacce tayi magana se nayi mugun saba mata. Jagwab ta koma ta zauna, Sulma hawaye ta Fara itada Subay'a Bayan sun kankame hannayen junansu, Samina kuwa kana kallonta itada Suhaila kasan a cike suke taf da masifa don fuskarsu har tayi jawur saboda tsabar Abinda yake cinsu basu fitar dashi ba. Salima tafin hannayenta tasa ta rufe fuskarta, yayinda Samiha da Salima suka kurawa Alhaji da yarinyar idanu tamkar basu taba ganin Alhajin ba ko kuma ya zama wani bako, Surayya ta Mike tareda kamo Hajiya wadda ta rigada ta daskare a wajen saboda tsabar yadda ta fita a hayyacinta ta zama tamkar statue wadda aka dasa ta a gurin! Tsoron Surayya kada hajiyar ta fadi ta samu stroke su shiga ukunsu! Na Tara ku anan saboda na gabatar muku da Matata, amaryata, sabuwar uwarku Asiya! Ina....... Alhaji.... Hajiya ta katse shi mid sentence shima ya katse ta da fadin Mistakenly kika Kara saka min baki Se na sauke igiyar aurenki. Jin wannan furucin ba karamin dukansu yayi baki daya ba, itakam Asiya ba su bane a gabanta don ko kallon arziki babu wadda ta yiwa hasalima tana jin an takurata Zuwa gurin nan hakan yasa ta dubeshi a shagwabe tace Honey mu tafi mana. Mikewa yayi ya kama hannunta baice dasu komai ba ya nufi wajen part din zuwa na gefen inda anan ne zata zauna. Kamar hadin baki gabaki daya Suka fashe da matsanancin kuka saboda a ganinsu an tozarta su, sun manta tozarcin da saukai yiwa wasu, sun manta rashin arzikin da sukai a nasu gidajen. Hajiya kam tamkar fool haka ta koma Ta rasa me zatace se binsu take da ido tana jin inama ita ke kukan da suke at least ta samu sassauci. Basu gama wannan tunanin ba Alhaji ya dawo shi daya, ya hadasu ya wanke su tas har uwarsu, yace yayi cancelling Cyprus kowacce ta koma dakinta, kada su sake Zuwa mishi gida weekly kamar yadda suke sede Bayan wata dai dai, sanann ya basu awa daya suci abinci kada ya samu mutum daya a gidan! Who saw this coming? Ina Subay'a zataje? How will everything be? Let's continue d journey to its end!!! Shatuuu ♥️[9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 49 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad *Of course, today is a special day, my beautiful, elegant favorite sister has clicked 12 years today. Maman moon, Oum Abdallah are all a year older... I pray Allah continue to shower his endless blessings, mercies and support upon them. Be blessed dearies!* Kowanne ka kalla cikin su takwas din kasan ba karamin duka maganar Alhaji tayi musu ba, tamkar saukar aradu haka Maganganunshi suka isa kunnuwansu, Baki daya ba kansu suke tausayawa ba Illa Hajiyarsu da zata kwashi bakin ciki cikin gidan, gaba daya Asiyar Nawa take ba zata wuce shekaru goma Sha Tara ba, to Samina ita ce autarsu wadda ta dade da bawa shekaru ashirin baya, yanzun haka shekarar ta ashirin da uku. Amma Alhaji ya rasa wadda zai aura matsayin matarshi se wannan mitsitsiyar yarinyar da Fannah 'yar Suhaila kadan ne Bata girme mata ba. Yanzun duk wannan cika bakin da suke na su basu zama da kishiya, nasu su kadai ne mata gidajensu se gashi Anyiwa uwarsu da jikarta. Kuka sosae suke wannan karan har ita kanta Hajiyar, gaba ki daya jinta take tamkar ba ita ba, Tunda take bata taba jin Irin wannan wulakncin ba ko a labari se gashi ya faru a karan kanta. Samina ce ta Fara mikewa tayi hanyar fita ko dankwali babu a kanta, cikin sauri Surayya ta Mike tareda fadin "Ke samina ina zaki je? " Juyowa Samina tayi idanunta sunyi jawur, ga hawaye da yayi mata kacakaca a fuskarta tace "Zanje gurin waccan yarinyar da Alhaji ke kiranta Uwarmu, Wallahi se na targada mata kashin ta" "Idan baki targada ta ba, ni na karairaya ki shashashar wofi! " Haka ta tsinkayi muryar Alhaji Yana fada a bayanta da yake ya dawo Dan ganin ko sun tafi, da sauri jiki na rawa Samina ta shigo tayi Bayan Hajiya jikinta na rawa saboda tsabar tsoro, ita dama haihuwarta an gama asirce Alhajin don haka a laushinshi tubus ta sameshi amma dukda haka basa kawo mishi wargi, bar su dai da basu bin takanshi idan zasui abu idan hajiya ta amince shi kenan. Su Surayya su suka san waye Alhaji Alkasim, su suka san true definition dinsa, Shiyasa suka hango wautar Samina da take tunanin ketare umarnin shi. "Uban me kuke har yanzun Baku tafi ba? Kun manta Abinda na fada kenan? " A rikice duka suka Mike kowacce ta Fara maida mayafinta da tazo dashi, Hajiya ganin hakan yasa tayi ta maza tareda kallon Alhajin tace "Babu inda zasu je Kasimu, babu inda zasuje nace, ku koma ku zauna nace gidan ubanku ne babu Wanda ya isa ya koreku Daga ciki. Idan banda asara da lalacewa Irin taka tsofe tsofe da Kai Kaje ka auro yarinya Saar jikarka, ai Wallahi kaji kunya ka bani mamaki, kuma tsakani na da kai Allah ya isa! 'ya'ya babu inda zasuje na fada" Maimakon yayi fada se yayi murmushi tareda fadin "Kika ce babu inda zasuje?" Kanta ta gyada ta kallesu dukkansu sunyi tsaye kamar zakaru tace "Babu inda zakuje, gidan ubanku ne" Bai ce mata komai ba ya ficewarshi , dariya tayi tana tunanin aiki ya fara dawowa, dukkansu suka zauna amma a tsorace banda Sulma da tace "Hajiya ki Bari mu tafi kawai, wannan fadi in fada da kuke ke da Alhaji, bashi da amfani, aure ya riga yayi, hakuri ne kawai namu. Dama ai munsan ranar nan dole Se tazo ranar da komai zai kwabe mana" "To Muslim Sister, Assheikh, Malama. Naji nace naji idan ke bazaki zauna ki tayani kukan abinda ubanku yayi min ba, kije Allah ya kiyaye dadin abin ba ke daya bace 'yata da tuni takaicin ki ya kasheni" Sumsum Sulma ta samu guri ta zauna tunda ta rasa Wanda zai Goya mata baya, dukkansu sunyi shiru masu sharar hawaye Nayi, Masu kulle kulle cikin zuciya sunai dukda sunji maganganun Sulma kuma gaskiya ta fada amma furucin Hajiya bazaisa su Goya mata baya ba, don idan aka bi salsala duk saboda su waye ta shiga wannan halin? Saboda su dinne, don su samu soyayyar uba ba tareda an raba ta zuwa ga wasu yaran ba amma a karshe abinda ake gudun shi ya faru! Dawowa alhajin yayi, mamaki kwance a Fuskarshi ganin yaran suna zaune, a ranshi ya Raya dole ne ma yayi abinda yayi niyyar, Seda ya tsaya gaban Hajiya kafin ya ciro farar takarda Daga aljihunshi ya Mika mata tareda fadin "kije na sake ki! " Dif parlon yayi saboda wani abu da ya ratsa dukkansu, Subay'a ta lumshe idonta a hankali tana jin ita ce next person da hakan zata faru a kanta, Hajiya was dazed and confused ta kasa Koda kwakwaran numfashi me tsawo, tunaninta Baki daya ya dauke se harbawa da zuciyarta Ke yi tsabar firgici. Juyawa Alhaji yayi Bayan yace "Duk tsawon rayuwar ku Baku taba kallona a matsayin uba mahaifi ba, se shashasha da kuke daukata. Mahaifiyar ku ita ce mutum a idonku Don haka nake son ku tattara har ita ku tafi duk inda zakuje amma ku manta na haifeku" Yana gama fada ya juya don ficewa amma ya gagara hakan sakamaakon Sulma da ta tsugunna ta rike mishi kafafunsa kamar zata balla su, kuka take wanda me saurarenta ma dole zuciyarshi ta karye, kallonta yayi a ranshi Yana jin tausayin ta da ta kasance Yarinyar Hajiya, Yarinya me hankali da hangen nesa wadda ita daya take binshi bata manta cewar shi din uba ne a gareta ba, yana sonta a kaf cikin yaranshi babu Wanda ya ke da gurbin da take dashi, Amma bazai bari ta karya masa Abinda yayi niyya ba, hakan yasa ya janye kafafunshi ya fice baki daya. Ta jima tana kuka kafin ta Mike ta koma ciki inda ta samesu suna hadawa Hajiya kayan ta wadda ko uhm ta kasa furtawa se hawaye da take tana binsu da idanun ta. Wasu cikinsu kuka suke, wasu kuma sun shiga taitayin su kamar Subay'a, Salima da Sakina. Suna gamawa Surayya ta dafo Hajiya suka fito tareda kulle sashen gaba daya Bayan Subay'a ta fito da nata kayan zuciyar ta Cikeda zulumin inda zata nufa. Dukkansu da motarsu suka zo hakan yasa kowacce ta shiga tata se Subay'a ta shiga ta Sulma. Surayya ce a gaba hakan yasa suka mara mata baya zuwa Darmanawa inda anan gidan aurenta yake. Ita kadai ta shiga da motarta dukkansu a waje sukai parking sannan suka shiga kayataccen parlon gidan Wanda ya sha gyara ga dukiya da aka narkar a ciki. Yaran ta basu nan sunje gidan su mijinta suna Family meeting hakan yasa gidan masu aikinta kadai suka rage. Dakin dayake spare cikin gidan ta bude ta kai wa Hajiya kayanta se a sannan Hajiyar ta dinga kuka Tana karawa, a ganinta bata cancanci hakan Daga gurin Alhajin ba. Yaran dukka suka saka ta a gaba suna kuka wasu na lallashinta. "Kaico ni! Haka Alhaji ya zaba yayi min, hakan ya ga yayi mishi daidai? Seda na gama mishi aiki na bauta mishi sannan zai sakeni? " Kuka yaci karfinta, su kansu sunsan fada kawai take amma Babu abu guda daya da take yi cikin abinda ta lissafa, su a karan kansu sukan manta cewar wai suna da Uba, se suje gidan su yini amma ko sashen da yake basu kalla kasan ba. Gashi nan karshensu dukka yazo Allah se ya fara daga kan uwarsu wadda ta dorasu a hanyar! "Surayya miko min wayata na kira Kubra dole a gaggauta aikin" "Wacce Kubrar? " Suka hada baki, Suhaila tace "Hajiya Baki daddara ba, har tunanin sake komawa ga laifinka kike? Haba Hajiya ko ni nan na bar komai na tuba nabi Allah don ya nuna mana iyakarmu, ya nuna mana shi ya halicce mu" Surayya tace "Mufa tsakanin mu da Anty Kubra Allah ya isa! Saboda ita ta jefa mu cikin wannan rayuwar, Hajiya ki manta da komai ki rungumi Allah kilan hakan yasa Alhaji ya maida ki dakinki Amma ni dai yau na girgiza matuka " Samina wadda se lokacin tayi magana tace "Nufinku yarinyar can taci bulus? Shi kenan ta Kori Uwarmu Daga gidan ta, Wallahi ni nan se nasan yadda na Kwata mana 'yancin mu" Hajiya wadda jikinta yayi matukar sanyi, kalaman yaranta suka shige ta farat daya tace "Kaiyya auta, babu wata wadda ta koreni ni na Kori kaina, ina fatan hakan ya zame mana darasi gabaki daya, kowaccenku ta gyara gidan ta kafin Lokaci ya kure mata, Kawaye basuda amfani Don na gani a karan kaina. Subay'a ki tattara ki tafi Kaduna ki jira mijinki ya dawo sannan ki zauna da abokiyar zamanki lafiya don munyi sake babba. Haka nima bazan zauna anan ba akwai gidana dake tarauni can zan koma har Zuwa yadda Allah ya tsara! " Tabbas sunga saurin nadamar Hajiya amma basu san Hajiya ta Fara laushi ba tun zuwansu gidan Junaid da sukaga yayi aure, Tun lokacin jikinta ya bata karshenta yazo Amma taki aminta da hakan ta cigaba da bin son zuciyarta gashinan ga inda ya kawota!!! Amarya Kinsha kamshi Koda kin kashe dan masu gida! Haka abin yake, haka bahaushe yace Amma ga Khulthum zata iya karyata wannan popular saying din, zata iya Rantsuwa cewar ba gaske bane Don kuwa ta shaida hakan. Aure de gashi tayi shi, irin wadda take mafarkin yi kullum, ga dukiya nan ta samu kana kallonta kasan Hutu da jin dadi Ya samu guri Sede rashin kwanciyar hankalin da take ciki yasa idanunta suka Fada ciki sosae, kashinta na wuya ya bayyana. Tana zaune tayi wanka tayi kyau cikin wata Holland wax purple me kyau da tsari, dinkin plain zani da riga wanda yayi mata kyau da cifcif a jikinta, ko dankwali bata daura ba haka take Zaune tana tunanin yadda komai ya juye mata, aure kusan sati hudu amma sau biyu kadai tasa miji a idonta, ranar da aka kawo ta da ranar da taje gurin shi a part din shi. Kwanciyarta ta gyara ta janyo wayar ta dake jikin socket tana caji ta Fara kiran Sulaim saboda tana bukatar wanda zatayi magana dashi Amma ta buga tafi a irga amsa daya ce a kashe se lokacin ta tuna Ashe lokacin kanta yana rawar aure ta fada mata zataje Malta. Kawai se ta Fara kiran Maimuna wadda kamar jira take ta dauka. Seda ta gama tsokananta "Matar Manya amaryar TitαΦ uwar Magajin TitαΦoils, foods and flours!" Da idan Maimuna tayi mata wannan kirarin Jinta take tamkar a saman gajimare amma yanzun se take jin wani banbarakwai kwatakwata Bata fitting da abin ba. "Ki Bari kawae Maimuna, ina cikin matsala!" "Wacce Irin matsala kuma? Haba dai mu a cikin matsala kuma a ciki" A ranta cewa tayi nima haka na dauka amma gashi ba hakan bace ta kasance, ta dauka cewar idan ka auri me kudi ka gama dacewa cikin duniya, to gashi babu inda akaje abubuwa sun lalace! Cikin nitsuwa ta warwarewa Maimuna dukkan abinda yake damunta, dariya Maimuna tayi tace "Amma kin bani Mamaki uwar Magaji, Karki manta lokutan da kike saka Maza dripping Amma gashi mijinki kin kasa juyashi, ni har ina tunanin gobe inzo da PT strip nayi gwaji. Yanzun har wata daya babu wani abu, ina tactics dinki suke? Kije kiyi seducing dinshi idan yaki zan kawo miki tablet kiyi mishi amfani dashi. Kiyi amfani da damar ki kafin ta kubce miki sannan ki yi amfani da damar ki ta mace ki janyo hankalinshi. " Wannan magana ta shiga kunnuwan Khulthum hakan yasa ta Mike Bayan sunyi sallama ta nufi kitchen inda ta bada order plantain, porched egg da coffee, komawa tayi ta sake wanka ta shirya tsaf tayi barin turare sannan ta dora katon hijabi ta dauki tray din zuwa part dinshi. Tana zuwa tsakiyar parlon Sega wani hadadden saurayi ya fito Daga wancan bedroom din da taga sauran sun shiga wancan karan, kallonta yayi Baice mata uffan ba ya fice abinshi. Jikinta a sanyaye ta nufi bedroom din gabanta Yana mugugun faduwa tare da fara tunanin Meye Musbahu yakeyi da Maza har haka??? Ku biyoni a next page dan jin yadda zata kaya tsakanin Musbahu Dan Gwoggo da Amaryarshi Ummu_Khulthum uwar magaji. Shatuuu ♥️ [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 50 to 51 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Its a long journey I know, yeah! I'm concluding the novel Inshaaa Allah on or before 1st September. So from now on Inshaaa Allah double in one page zamu Nayi. Thank you very much for all the support, prayers, love and comment..... That's what kept me going, that's what makes me update daily, I'm so much grateful for everything* _My heart goes out to Salma Hassan Kwalam, Tee Zarewa, Anty yaya (Sadiya Lawan), Anty Fatima sadi, Yaya Baby, Anty Asma'u, A'isha, A'isha imam, Aisha kaagu, Aisha Akko, Aisha Ahmad, Aisha sheikh, Yaya Umma, Farida S maina, Abida Suleiman, Ammasheikh, Anty Hijja, Daughter Farida, Oum Annur, Maman Zarah, Amaryar yaya Mousa, my Najeeyba, Maman Hanif, leiymahs delicia, Sister Sadiya, Sister deejah, Sister Ummin D/batta , Fatima idris, Nanah ganuwa, Fatima ummi, Yaya Nana, Pyaule, heedaya Bunu, Aisha major, Jidda Hamisu, Fatyn zulayha, Hanifa, Khadeeyja DRB....including all and all the ghost readers in the SHATUUU's KINGDOM .....without you many things won't be possible thank you!_ Cikin dakiya da jarumta Uwar magaji ta Kai hannunta Kan handle din kofar, gabanta a lokacin ya kara bugun da yake amma haka ta murda kofar ta shiga, sanann ta maida kofar ta rufe tareda murda key din da yake jiki.... Kunji karfin Hali kamar dakinta. Zare key din tayi ta daura saman tray din dan yau ko Wacce aljana ce ta aure mata miji as they said, ko da bashi da lafiya yau se tayi yadda tayi. Tana juyowa idonta bai sauka a ko ina ba se makeken Italian bed din Musbahu, kafin cikar seconds jikinta ya fara bari tamkar mazari, idanunta Manya ta Kara ware su kirjinta tamkar zai balle, tamkar an ingiza hannunta tray din dake hannunta ya kubce jikake Tas! Tas! Ceramic plates, cups da bowls din dake kan tray din Baki daya sun fashe wanda a take yayi awakening Musbahu da partner dinshi Daga abinda idanun Khulthum dani na kaina suka gane min...... Khulthum kidimewa tayi ta juya da sauri ganin yadda Musbahu ya sauka Daga kan gayen dake kwance malale akan gado tamkar ruwa Don ya kasa katabus gara Musbahun ya samu courage din mikewa. Gaba daya Khulthum ta manta ta rufe kofar hakan yasa ta dinga jijjiga kofar tamkar zata balla kofar amma ko gezau kofar baiyi ba a haka Musbahu ya iske ta, hannunshi ya daura akan kafadar ta, tamkar garwashi haka taji ga wani masifar tsoro da ya kara turnuke ta, juyo da ita yayi Fuskarshi tamkar ta zaki wanda ya shekara bai ci ba gashi kuma ya hadu da abincin shi, babu ko imani digo a Fuskarshi ya fuzge Hijabin dake jikinta, take jikinta ya bayyana cikin wata riga wadda Baki daya net ne fari tas wanda in har Namijin da yake lafiyayye ne to tabbas sai hankalinshi ya tashi amma ko a jikinshi se wani mugun kallo da yake bin ta da shi na bakida Abinda zaki birgeni dashi. Tsugunnawa yayi don tun sakkowarshi daga gado yaga key din bedroom din, kofar ya bude, Khulthum dake gefe ta taho cikin wani azababben sauri zata fita ya rike hannunta tamau yadda duk wannan tirjiyar da take ta gagara kwace hannunta, juyawa yayi Yana duban wannan gayen da tuni ya Mike ya maida kayanshi jikinshi ya fito ya wuce ba tareda yace uffan ba, yana fita Musbahu ya maida kofar ya rufe tareda zare key din daga kofar ya cigaba da jan hannun Khulthum wadda ilahirin jikinta rawa yake, tasan tayi iskanci a waje amma ko sau daya a Rayuwarta bata taba tunanin haka daga Musbahu ba, Gay! Neman Maza yake! Hannunta ta kara kokarin kwacewa amma ya mata rikon tsauri, ganin tana neman wahalar da shi yasa ya hankada ta kan gadon, kafin tayi wani yunkurin kubcewa har ya hayo gadon, idanunta ta Kara budewa tareda bude bakinta tana fadin "Dan Allah...... " Muryarshi ya bude wanda Tunda take bata taba jin Irin wannan Amon ba, shikanshi ya isa firgitata "Ba hakkinki kika zo karba ba? Fine" Wajen Mintina ashirin babu Abinda yake tashi cikin part din na Musbahu banda ihu da kururuwar Khulthum tamkar wadda ake zare mata ranta, Tana kwance babu komai jikinta se rizgar kuka take tamkar an bata sakon mutuwa, a hankali kofar da nake tunanin Itace ta toilet ta bude, the Charming Musbahu ya bayyana cikin wata farar bathrobe, kanshi ruwa Yana ta diga, kamar kullum fuskarnan babu digon annuri akai, daidai inda take ya tsaya Yana Kare mata kallo tareda jin ihunta na kokarin tarwatsa mishi kwakwalwar kanshi bawai don tausayinta ba a'a se Don naturally baya son hayaniya. "Kinzo ki karbi hakkinki sanann kinzo kiga me nake aikatawa, ban so kika ga hakan ba saboda kada zuciyarki ta buga, Amma duk Abinda na fada miki kada ki cika bincike amma kika saka kafa kikai fatali da hakan. Ina fatan you're satisfied, idan kina bukatar Kari zan baki saboda ban taba kawowa Anal sex haka take da dadi ba se yau" Yana gama fadar haka ya wuce cikin walk in closet dinsa ko Mintina ashirin bai kara ba ya fito ya shirya cikin sweat pants black da Top maroon , kallon ta ya kuma Yi har lokancin Bata motsa Daga gurin ba amma kukan ya dauke sakamaakon dusashewar da muryar ta yayi saboda yadda ta bude murya da makogaro tana kwarara ihu. "Tashi ki fitar min a daki" Ya fada cikin kakkausar murya, jikinta na rawa ta Mike tare da daukar Hijabin da ta zo dashi tayi waje a million, sosae hakan ya bashi dariya, ya dauke kanshi babu ko dar na tsoro cikin zuciyarshi, ta hutar dashi da tazo ta ganewa idanunta komai, ba se yayi bayani ba. Khulthum Seda ta taka kafarta cikin part din sannan ta ji wani Irin azababben radadi ta gurin Bayan gidanta, kafafunta sunyi mummunan sagewa ga tarin gajiya da tayi mata rubdugu, da kyar tana Jan kafa ta isa dakinta ko gado kasa hawa tayi haka ta kwanta kan carpet idanunta na zubar da hawaye. A hankali ta samu damar tuno Irin mugun ganin da tayiwa Mijinta, hade da wani katon namiji ba ma mace ba, babban laifun da Allah ya hallaka mutanen Annabi Lut AS Amma ita mijinta kenan, ga wani haramci da ya tafka wato Anal sex, saduwa ta dubura wadda Allah da manzonshi sukai Hani akan hakan, Kaddara ta kenan! Auren GAY!!! Karfe daya na ranar litinin motar da ta taso Daga Kano zuwa kaduna ta sauke passengers dinta a Tashar DIT dake alheri radio. A hankali Subay'a ta sakko daga motar janye da trolley, hannunta da handbag yar karama, tana Kallon mutane yadda suke ta kai kawo, Bata kalla kowa ba duk yadda 'yan union suke tambayarta inda zataje amma bata kula kowa ba, hankalinta yana ga Irin tarbar da zata samu daga inda zataje. Napep ta tare tare dayi bashi address din gidan, ya yanko kudi daidai suturar jikinta ya fada mata ta shiga suka wuce zuwa gidan da ta manta rabon da kafafunta su taka. Kofar gidan Rtd Gen. Lukman Birnin kudu Subay'a ta tsaya tana tunanin ta inda zata Fara, ta jima a tsaye ba tareda sanin inda ta kama ba, ga kuma Anxiety.... The fear of Unknown, ta isa bakin kofar dan fara kwankwasawa taga an bude tangamemen Gate dinsu. Jawad ne ciki wanda ke kokarin fita zuwa Aiken Mami, kamar yasan tana tsaye ya juyo idanunsa gurin karaf suka hade. Fitowa yayi tare da nufo inda take tsaye kanta a kasa saboda tsabar kunya, ta tuna lokutan da Jawad ke zuwa gidan ta tayi mishi banza. "Maman Ahmad Yaushe kika zo? " Kanta ta dago tace "Yanzun. Mami na ciki? " Kanshi ya gyada yace "Tana ciki Ki shiga" Kanta ta gyada ya koma mota itakuma ta shiga, dake sojojin dake gate din sun Santa, hakan yasa suka gaida ta, Smith har kokarin karbar trolley din hannunta yayi amma ta mishi godiya ta wuce ciki. Tunda ta zura kafarta tasan akwai wani muhimmin abu da zai faru a gidan saboda yadda gidan ya hargitse bawai datti ba a'a very neat and tidy ga kamshin turaren wuta da nasu fresheners na lavender flavor da ya cika gurin, Amma duka masu aikin se kai kawo suke ko Lura da ita basui ba Seda Imratu ta sakko hannunta cikin na Muhammad wanda ya sha wanka an shirya shi cikin kaya masu kyau. Kallon kallo sukayi da Imratu kafin Imratun ta dan saki fuskarta tare da karasowa inda take tsaye, Muhammad bai lura da Subay'a ba wasanshi kawai yake har Seda suka zo gaf da juna kafin yace "Mimi" Lumshe idonta tayi don wata kwalla ce ta cika mata idonta, tsugunnawa tayi ta rungume shi Tsam cikin kirjinta tana sakin ajiyar zuciya, kanshi ta dinga shafawa tana jin abubuwa da dama suna taba mata zuciya, a hankali ta furta "I missed you son" Kwace jikinshi yayi yana fadin "Mimi kizo kiga yadda Mami ta gyara komai yau da Daddy da Ammiey zasu dawo! " Dam taji kirjinta ya buga, a hankali ta Mike tsaye Daga tsugunnon da tayi ta saki Muhammad, shi kuwa bai lura da ita ba ya ruga sama se Imratu ce ta karba trolley dinta tace "Muje ko" Hawayen dake kokarin sakko mata ta shanye tareda sniffing hancinta ta bi bayan Imratu zuwa sama, tamkar ta juya haka taji inda tasan Abinda zata tarar kenan da babu yadda zaayi ta dawo gidan. Suna zuwa parlon ta tarar Mami na Zaune gefen ta Ahmad yana danne danne a system din Mamin. Mamaki sosae Mami tayi ganin Subay'a a wannan lokacin Kuma Harda trolley, ganin yadda tayi kasa da kanta Mami tace "A'a Subay'a sannu da zuwa, Ahmad bakaga Mimi ba? " Zama Subay'a tayi yayinda Ahmad ya taso da murmushi a Fuskarshi ya rungume ta sanann ya cigaba da Abinda yake, kafin wani Lokaci an cika mata gabanta da lemuka da abinci, lemo kadai ta iya sha sannan tace da Mami "Mami zanyi sallah" Kallon Imratu Mami tayi tace "Kuje Imratu " Tare suka nufi dakin da Imratu ke zama idan tazo anan aka sauki Subay'a seda ta nuna mata inda komai yake kafin ta fice ta barta akan sallaya. Seda ta Idar da sallah sannan ta hada kanta da gwiwarta ta saki kukan bakin ciki hade wani masifaffen kishi da ya turnuke ta Lokaci daya, Da gasken kenan da kishiya zata zauna, da gaske Sulaim ta zama kishiyarta ta kwace mata mijinta, kuka sosae ta dinga yi har Bata san lokacin da ta dauka a haka ba, amma tasan tafi karfin awa daya Don har fuskarta seda tayi jawur ga babu Wanda ya kara ko nemanta a gidan. Ganin haka yasa ta Mike ta cire kayanta ta fada toilet tai wanka ta dauro Alwala nadama fal cikin Zuciyata babu Abinda take banda inama ace Nayi kaza! Inama ace banyi kaza ba!! Amma ina Lokaci ya kure tuni sede a tari wani lokacin. Bubu ta wani cotton lace ta saka ta yafa mayafin kayan sannan ta samu guri gefen gado ta zauna, tamkar jiran zamanta ake taji ihun Ahmad yana fadin "Daddy! Ammiey!! Oyoyo!!! " Idanunta ta runtse da karfi, tareda dafe kirjinta hawaye suka Balle mata duk kuwa da yadda take kokarin ganin ta Hana su zubar Amma it is natural dole hakan ya kasance. A parlor Junaid na gaba ya Saba Ahmad a kafadarshi Fuskarshi murmushi ne kwance akai me nuni da tsananin kwanciyar hankali da cikar buri, a bayanshi Dove ce hannunta rike da na Muhammad da yake rigimar se Sulaim ta daukeshi amma taki, tana ganin Mami ta nufe ta da gudu ta rungume ta wanda hakan ya kusa kada su baki daya, take parlon ya cika da murnar dawowar Love birds, a tsakiya suka saka Mami kowa na bata labari, farin cikin da take ciki yasa ta manta da wata Subay'a. Da kyar ta samu suka tafi wanka kafin su dawo itada Imratu sun gyara gurin sannan sun shimfida dining mat an Jere warmers din abinci. Junaid ne ya fara hawowa shida Jabir suna dariya, Junaid ya kara kyau se kyalli fatar jikinshi take, kana kallonshi kasan bashida wata matsala. Gefe guda suka zauna se sannan Sulaim ta fito tayi kyau cikin gown ta atamfa ABC wax, tayi kiba ba wai cancan ba amma ta murje ta murmure, yaranta sun saka ta a tsakiya suna tambayar ta tsarabarsu. Bata zauna ba Mami ta cigaba da tayawa aiki duk yadda Mamin taki amma se kyaleta yayi, Duk inda tayi idanun Junaid na binta Yana jin tamkar ranar farko da ya Fara ganinta kenan, tsabar kallon da yake mata Seda Jabir ya zungureshi yace "Haba mana" Dariya Junaid yayi yace "Bazaka gane ba " Dariyar Jabir ya sake yi tare fadin "Really?" Shareshi yayi ya cigaba da binta da kallo, Yana ganin lokacinda tayi pouting lips dinta alamar kallon ya isheta hakan. Gaba daya suka zazzauna aka Fara cin abinci Cikeda nutsuwa da nishadi hadi da soyayya, Mami ce ta aje spoon tareda kallon Imratu wadda ta tattara dukkan hankalinta Kan chicken Salad din da take ci, "Imratu kirawo ta taci abinci" Mikewa Imratu tayi a ranta tana tunanin yadda abubuwa zasu kasance, itakam Mami tausayin Sulaim take ji yadda ta saki jikinta sosae tana tunanin ta manta Junaid na da wata matar. Da kyar Imratu ta samu Subay'a ta biyo bayanta don tasan ranta ne kawai zai baci don yadda ta dinga jiyo muryoyinsu yasa jikinta ya kuma yin La'asar Don tasan suna cikin farin ciki. Sulaim ke facing dakin don haka idanunta akan Sulaim din ya fara sauka, haka itama Sulaim din ita ta Fara ganin Subay'a, idanunta ta dan zaro saboda yadda taji kirjinta ya buga kusan tare da Subay'a din, gaba daya ji tayi taste din abincin ya bace, taji gaba daya zaman ya gundure ta, a hankali ta cigaba da taunar abincin tareda sunkuyar da kanta Tana ambaton Allah saboda wani Irin abu ne ya tokare mata makoshi, Mami na kallonta amma bata ko kula ta ba ta dubi Subay'a tace "Kizo ki zauna mu ci abinci mana" A lokacin Junaid ya dago idanunshi wanda suka sauka tar cikin idanun Subay'a wadda ta dauke Nata cikin saurin gaske, se ta samu kanta da kasa yiwa Mami musu ta zauna a gefen Ahmad Wanda suna ta tsakurar abincinsu ba Lallae idan sun San tazo gurin ba, Aje spoon din hannunshi Junaid yayi ya Mike don barin gurin, Mami ta dubeshi tace "Har ka gama? " Kanshi ya gyada ya tafi abinshi ba tareda ya ko kalli kowa ba, bai taba tunanin Subay'a batada kunya ba se yau, kenan ta bullo mishi ta bayan gida inda bai isa ya ja ba, kwanciya yayi Yana jin tamkar an rugurguza mishi wani plan ne. A parlor kam tunda Subay'a ta fito gurin yayi shiru se karar spoon dake tashi, a hankali daya Bayan daya suke tashi ya rage daga ita se Mami se Sulaim wadda ta kasa tashi har Seda Mami tace "Auta kwashe kayan nan kije ki Kira min Yayanki" Da sauri ta Mike ta fara tattare kayan jikinta kamar an mata duka, babu wani kuzari haka ta nufi kitchen ta kai kayan sannan ta nufi dakin Junaid, A kwance ta same shi yayi zurfi a tunani Amma sassanyan turarenta yasa shi saurin dagowa don bai kawo ita din ba ce amma se ya ganta a tsaye kana kallon fuskarta kaga me cike da damuwa, mikewa yayi Yana jin abubuwa suna kara kunce mishi a kanshi, Yana Zuwa inda take ta fada jikinshi Lokaci daya ta saki kuka Wanda ita kanta bata san me yasa take kukan ba, tasan dai zuciyar ta bata mata dadi tana jin wani zafi a kirjinta. Janye tayi daga jikinshi ya shiga share mata hawayen a hankali cikin kunnuwanta ya ce "Everything will be OK, kinji? " Kanta ta gyada mishi don ya fahimci kishi ke damunta, ba tun yau yake ayyana zuwan wannan ranar ba gashi ta zo a lokacinda shi kanshi bai shirya ba, hannunta ya ja suka fito Yana ta fada mata kallamai wanda yasan suna saka ta farin ciki, a haka har suka isa parlon Mami da Subay'a na nan inda ta barsu. Kusan tare Mami da Subay'a suka dubi hannayen Sulaim da Junaid, gaba daya Mami kunyar Subay'a ta kama ta hakan yasa ta watsawa Junaid harara, Dan chuckling yayi ya saki hannun nata ita kuwa straight ta nufi dakin Mami gabanta na kara faduwa. Zama yayi Fuskarshi a murtuke tamkar bashi bane wanda ya gama dariya yanzun ba, kallon Mami yayi wadda ta hade rai itama don da gaske Junaid so yake ya bata kunya. "Junaid me nasha fada maka akan rayuwa? " Kanshi ya girgixa Cikeda kosawa ga kukan Subay'a na taba zuciyarshi tareda karya mishi zuciya Amma dukda haka abinda yayi niyya bazai fasa ba "Hakuri of course Mami!" A hankali Subay'a ta dago idonta Wanda yayi jawur hatta fuskarta tayi ja, kallon Mami tayi sannan ta dubi Junaid da ya kara hade rai, Mami tace "A yau ba'a matsayin mahaifiyarka nake maka magana ba, ina maka magana a matsayin wannan babbar kawar ta ka....." Da sauri ya katse ta, ta hanyar dawowa gefenta Daga kasa tareda rike hannunta yace "Mami don't please.... Mami please!" Da sauri Subay'a ta Mike har tana tripping foot dinta, tsoron abinda kunnuwanta zasu iya jiye mata suke takeyi, tasan abu na karshe saki ne su zama zawarawa itada uwarta. Ajiyar zuciya Junaid ya sauke tare da fadin "Mami ranar da zan tafi Malta, kin tambayeni me zan yiwa Subay'a idan ta dawo? Nace sakinta zanyi ko? " Kai Mami ta gyada don ta rasa bakin magana saboda yadda aka daure ta da jijiyoyin jikinta. "Kika roka mata hakuri da sassauci, nayi hakuri saboda darajarki amma Wallahi tallahi, billahil azim se Subay'a taje gida ta koyi Menene aure! Se ta gane ni Allah yace na shugabance ta! Nine leader ni nake aurenta ba ita ba! Inason ta nutsu ta gane kuskurenta. Mami kada ki hanani, hakan is an opportunity Allah ya bani na daidai ta gidana... I'm sorry" Ya karashe maganar Yana daura kanshi akan cinyar Mamin, yau an tuna da kenan. Itama Mamin tausayinshi ne ya cika mata zuciya ta shiga shafa kanshi tare da fadin "Hakan yayi, kayi hakan is ok amma ina son duk Abinda zai faru ka kalli Ahmad da Muhammad, taci darajar haihuwarsu, ko a alkiyama filin hisabi wani yana cin albarkacin wani. OK? " Kanshi ya gyada yana jin sanyi Yana ratsa shi, Mami ce ta Fara mikewa tayi dakinta don kuwa hankalinta duka yana kan Sulaim wadda ta shige daki, tana shiga ta sameta as expected ta hada kanta da gwiwarta tana ta kuka me cin rai, gefenta ta zauna ta janyo ta jikinta tana patting bayanta alamun rarrashi haka tana jin babu dadi cikin ranta, wannan shi ne Abinda ta gudar wa Sulaim din tun farko, Auren mijin wata, to ya zasui kaddarar ta ce! "Me kike ji auta?" Cikin kuka da yarinta Tace "Mami ina jin abu ya tokare min wuyana, zuciyata zafi take min, kirjina yayi min nauyi, Mami bana son Yaya!" Da sauri Mami ta toshe mata Baki tareda fadin "Kar na kuma jin kin fadi haka, kishi yake damunki kuma it's normal kaji kishi akan abinda kake so, kishi halal ne, Nana A'isha Harda Nana Khadija wadda bata taba gani ba tayi kishi da ita, Tasha barar da abinci idan an kawowa manzon Allah SWA Daga dakin Nana Safiyya kasancewar ta great cook. Kinga ba laifi kikai ba amma ina son daga yau kada ki kara kuka Dan kinga Subay'a, inason Kiyi amfani da kishinki me da ilimi ki kwaci mijinki, mace ce kamar ki, Baki fita ba bata fiki ba, me biyayya da wanda ya iya zama da miji shi zai kwace miji, shi zaiyi winning Sulaim. Inason ki maida hankalinki ki manta Yana da mata, ki Kafa kanki a gurinshi, kiarki Bari wata ta kwace shi kinji? " Kanta ta gyada har lokancin kukan bai tsaya ba amma ta rage, kuma radadin ya ragu sosae "Uwargidan mutum ita ta kafa shi, ita ce foundation dinshi, Duk yadda ta zubar da darajar ta Tanan matsayin uwargida wadda ta sanshi. Ko zaku shekara talatin tare bazaki taba sanin shi kamar yadda tayi ba, haka duk lalacewar uwargida idan miji ya rabu da ita, duniya se ta zageshi, Bana son ki daga hankalinki akan hakan ina fada miki don kisan matsayinki, zaman mijinki kike not for any other person. Ki kwantar da hankalinki sanann ban yadda ko kallon banza Ya hadaki da Subay'a ba, ku gaisa that's all nothing more kinji? " Kanta ta sake gydawa tana jin damuwar da take ciki ta Fara yayewa, Mami uwa ce ta gari cikin hikima ta dinga koyarda Sulaim yadda zata kwaci kanta, bata barta tayi bacci ba Seda ta cire mata inferiority complex dinnan ta gina mata jin ta isa, Junaid ba mijin Subay'a bane ita daya aa mijin sune dukkansu me kyan hali ita ce tauraruwa a zuciyar shi. Washegari tun safe suke aiki da Mami da Sulaim don Imratu cikin jikinta me saka morning sickness ne hakan yasa ko fitowa Batayi ba. Gaba daya Sulaim zuciyarta da gangar jikinta kewar Junaid suke Don rabonta dashi tun jiya, ko sallama bai zo yayi musu ba da zai kwanta. Sun kusa kammalla aikin kamshin turaren shi ya iso cikin kitchen din wanda yasa Sulaim saurin lumshe idonta saboda nutsuwa da ta mata dirar mikiya, shigowa yayi ciki tareda tsugunnawa ya gaida Mamin wadda ta amsa kamar ko Yaushe, fita tayi don basu guri tareda fadin "Auta ki karasa" Tana bada baya ya matso ya rungume ta tareda sakar mata wasu trails na kisses a wayanta, Kara ta dan saki tareda janye jikinta tana murmushi ta riko hannunshi tareda fadin "Good morning " Harar ta yayi yace "Ba wannna maganar, jiya kika sha bacci ko missing dina Bakiyi ba, ni kuma ina can Inata missing dinki" Kashe gas din tayi sannan ta juyo Tana facing dinshi tayi dage kasancewar ya kereta a tsayi, a hankali ta hade bakinsu guri guda tana mishi wani seductive and sensual kiss, seda ta gama sannan ta rungumeshi tare da fadin "Ka yadda I missed you? " Da sauri ya gyada kanshi don ya yadda kam. Baki daya suka hadu don cin abinci amma babu Subay'a, Imratu dake ta shan kunun gyada ta dubi Mami tace "Tace na fada miki ta tafi kano" Babu Wanda ya kuma maida maganar suka ci sannan Mami ta hada Junaid, Jabir , Imratu da Sulaim ta Kara musu nasiha. Wajen laasar Mami ta rako Sulaim da yaran zasu tafi Kano. Maimakon gidan da suka saba zama se sukai parking kofar wani flat duplex akan BUK road, kallonshi tayi kamar yadda take kallonta, kunnenta ya matso dashi yace "Wancan gidan aro ne, wannan namu ne ni dake and our babies to come" Shatuuu ♥️ [9/2, 9:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 52 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Of course, you know that this page is yours the people of Maman mama novels, ina godiya sosae da goyon bayanku.....* A'ISHA ASHIR Bari mu leka muji yadda rayuwar Wannan bayun Allah ta kasance bayan Auren Khulthum. Rayuwa ta mika musu, abubuwa sun sauya ciki Harda Fara makarantar Aisha wadda ta samu gurbin karatu cikin North west University wadda iyayen Ashir suka dauki nauyin karatun. Amir shima yayi nisa cikin karatun da yake ga kuma budi da Allah yayi mishi gurin kasuwancin da Khulthum ta dade tana mishi dariya, wato saida gwanjo. Sede gashi Allah ya albarkaci abin har ya fara gyara musu dan gidan da suke ciki, wannan abin ba karamin faranta ran Malam Suleiman yayi ba domin yasan tabbas Allah ya amshi adduar da ya dade yana Yi. Ranar wadda ta kasance asabar tun sassafe A'isha ta tashi kamar yadda ta Saba, babu Wanda ta tada haka ta fito daga daki ta Debi ruwa tayi wanka sannan ta dawo daki ta gyara kanta ta shirya cikin doguwar rigar farin material me fatsi fatsin Baki. Dukda ba mai tsada bane amma yayi mata kyau, fitowa tayi ta hura wuta sannan ta Fara Sharar tsakar gida, ta hada wanke wanke tayi a lokacin Amira ta fito Tana ta murtsuka idanu, kallon A'isha tayi tace "Kai Yaya A'isha duk ke daya kika yi wannan aikin?" Harara A'isha ta makawa Amira tare da cigaba da aikinta sannan tace "Waye zai biyewa lalacin ki, kamar ba mace ba ace se yanzun kike tashi a bacci" Baki Amira ta turo tace "Rayuwarki tayi tsauri Yaya A'isha, amma ina yiwa Yaya Ashir samun ki" Sunan kawai da Amira ta ambata Seda wani sihirtaccen murmushi me kayatarwa ya kubce daga kyakyawar fuskar A'isha, Dama ita din ma'abociyar murmushi ce amma na Ashir na daban ne. Ita kanta ko cikin mafarki ko burika Irin nata bata taba tunanin zatayi soyayya da Ashir ba, Ashir daban yake wanda samun mutum kamarshi se an sha wuya, kullum rana se A'isha ta kara godewa Khulthum akan bar mata Ashir da tayi. Halayenshi kadai sun isa ya sace zuciyar mutum dashi. Mutum ne me takatsantsan akan dokokin Allah, hardly Kaga ya ketare abinda Allah da manzonshi sukai Hani akan, mutum ne that's very caring dukda ya kasance baya kasar amma bai taba jera hour biyar ba tareda ya ji muryar A'isha din ba, hakan yasa suka mugun sabo da kuma shakuwa da junansu. Da farko kasa sakin jikinta tayi saboda tana ganin kamar ana amfani da ita ne wajen huce haushi Amma a hankali yadda yake tsumata da Wannan zumar tashi yasa ta bada Kai bori ya hau. Cikin nitsuwa suka dinga shimfida soyayya me Cikeda amana, karko da kuma fahimtar halayen juna, cikin kankanin lokaci sukai clearing differences dinsu hakan yasa basu sha wahala ba. Amira dake gefe tana kallon Yayar tata da tayi zurfi cikin tunanin Ashir wanda ko bata fada ba hakance don wani Irin soyayya me rikitarwa ce tsakaninsu. Daki ta koma jiyo ringing din wayar A'ishan, murmushi tayi ganin Ashir dinne hakan yasa tayi saurin kai wa A'ishan wayar tareda fadin "Gashi nan dan halak ya huttar dake" Maficin dake hannunta ta wullawa Amirar wanda ta zulle Zuwa daki Tana dariyar kunyar A'isha. Se kira na biyu ta samu ta dauki wayar dan tuni wancan call din ya katse "Yau Queen da rowar murya kika tashi? " Dan murmushi tayi tace "Ni na isa, tana daki wayar" Kanshi ya jinjina tareda fadin "Dan Allah Queen ki dinga hutawa da Wannan ayyukan da kike, ace kullum mutum tamkar inji yayi ta aiki babu Hutu Haba mana! Shiyasa dole a matso da date din aurenmu!" Dariya ta saki a hankali wadda take nuna Irin nishadin da take ciki, shima lumshe idonsa yayi yace "You will not answer me right? Anyways Dama zan miki zancen next week zan dawo" Da sauri ta Mike wani Irin farin ciki Marar misaltuwa ya mamaye mata jikinta da zuciyarta tace "I'm so happy blood, Awnnnn!" Haka suka Bata Lokaci me tsayi suna waya har ta kammalla ayyukanta, lokacin sukai sallama shima don ganin mutanen gidan sun Fara fitowa ne. Tunda Mama ta fito take shiwa Aisha albarka, har zuciyarta take jin dadin wannan halin na A'isha ko ta so ko taki A'isha tafi Khulthum sau dubu kuma Tun ranar da Khulthum ta bar gidan taji wata nutsuwa ta saukar mata, taji tamkar an sauke mata wani babban nauyi ne daga kanta, haka bata ji wani kewar ta ba, to ta yaya zataji Bayan nemar mata magana kawai take yi, yanzun hankalin kowa ya kwanta tunda bata nan. Bayan sun kammalla cin abincin Baba ya dubi A'isha yace "Ya kamata kuje ku ga dakin 'Yar uwarku, ko mai ya faru ina son ku manta da hakan, Ummu_Khulthum yar uwarku ce" Kai A'isha ta gyada tana jin komai ya wuce dama ita bata rike Khulthum ba don kuwa tasan ba'a canjawa tuwo suna Yana nan a tuwonshi! Tare suka shirya Mama kamar ta Goya su da taji inda suke haramar Zuwa, dukda Tunda Khulthum ta saka kafarta ta bar gidan babu Wanda ta taba Kira da sunan gaisuwa, se Mama dince kan kirata time to time. Tunda aka sauke su A'isha kofar gidan Baki daya suka saki Baki da hanci suna kallon wannan tafkeken gidan, mamaki cike a zuciyar kowannensu saboda babu Wanda yazo ganin daki don ba'ayi rabuwar arziki ba Balle har su raka ta in fact lokacin bikinta ma gaba suke me tsanani. Seda A'isha ta kira Mama ta tabbatar mata gidan ne sannan suka kwankwasawa, kasancewa securities din sun saba da kawayen Khulthum masu didif didif a gidan suka Barsu suka shiga tareda nuna musu part din Khulthum din. Daidai zasu shiga Musbahu na fitowa daga part din Sanye da jallabiya brown, Fuskarshi babu digon annuri an dinke tamkar anyi masa sakon mutuwa, a tare suka gaishe shi kawai se ya samu kanshi da amsawa saboda kana kallon Amira Kaga Khulthum saboda yadda suke kama da junansu sosae, "Ku shiga ciki mana tana nan " Ya fada Yana basu guri tareda Kare musu kallo, kana kallonsu kasan talauci yana damunsu Amma a idanunsu zaka fahimci they're contented. Gaba daya bin parlon sukai da kallo saboda tunda suke a rayuwarsu basu taba gani Balle har su shiga makamancin gurin. Zama sukai kan kujera shi kuma ya nufi dakin don kiranta, tana kwance inda ya barta ko hannu ta Kasa dagawa, kamshin turaren shi da taji yasa ta mugun firgita don babu Abinda take tsoro yanzun a rayuwarta shi ne Musbahu, azabar da yake mata Allah kadai yasan hakan amma tasan kaddarar ta ce hakan! "Kinyi baki" Bai jira amsarta ba ya fito Bayan yasa a kawo musu abinci, baki daya A'isha tsoron karbar da Khulthum zatayi musiu take, da Khulthum bata da komai take rashin mutunci Balle gata da kyakyawan miji na nunawa duniya, ga kudi da katon gida. Ai se abinda yayi gaba, suna nan Zaune zaman kurame Don babu me magana cikinsu se gata ta fito, ta kintsa kanta cikin voile Red dinkin skirt da Riga, tayi kyau amma tayi Baki, idanunta sunyi ja tareda fadawa ciki, fuskarta kadai zaka kalla ka gano tsantsar damuwa da tashin hankalin da take ciki, tana ganinsu A'isha ta nufe su da sauri tareda rungume su dukkansu, sunyi mamaki canzawar ta da kuma Wannan ramar da tayi. Tsakiyar su ta shiga tana jin kamar an jefata a Aljannah, dadi kamar me daga baya ta kwashesu Zuwa dakinta tana ta musu hira har suka saki jikinsu suka ci abinci. A'isha karshen gado ta koma ta kwanta tare da amsa kiran wayar Ashir, tunda ta Fara wayar hankalinta Baki daya ya bar dakin da mutanen dakin, Khulthum na ankare da ita Tana ta son jin da wanda A'isha ke waya hakan yasa ta tambayi Amira wadda ta bata amsa da "Yaya Ashir ne" It takes a huge of sacrifice typing this peace..... Dan Allah kui manage dashi. Shatuuu ♥️ [9/6, 6:55 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 53 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Thank you for patiently waiting, thank you for the prayers! Amarya na dakinta* Amira bata jira gama ganin reaction din Khulthum ba ta cigaba da fadin "AI an saka ranar biki, wata uku ya rage yana zuwa Hutu xa'ayi bikin su tafi tare. Wanda ya dauki nauyin karatun nashi ya hada da nata" Wani yake Khulthum tayi tace "Ikon Allah, to Allah ya kaimu " Tana fadar haka ta mike ta fita daga dakin, Rana ta farko a cikin rayuwarta da ta Fara jin tayi kuskure, Rana ta farko da ta Fara jin wani abu yana bin zuciyarta na Anya ta yiwa rayuwarta daidai? Taji anya akan turba me kyau take? Jingina tayi da kofar dakin dake gefe idanunta na cikowa da wata zazzafar kwalla, a hankali wasu abubuwan na rayuwarta suka Fara bayyana a idonta, tamkar wani flashback a film haka suka dinga bayyana mata, tabbas kwadayi mabudin wahala ne, tabbas wanda ya hau motar kwadayi zai sauka a Tashar wulakanci, gashi nan bataje ko ina ba ta fara gani, kwatakwata Watannin ta biyu kawai cikin gidan amma gashi Anyi mata mummunan tabo cikin zuciyarta da rayuwarta baki daya. A halin yanxu babu Abinda take matsanancin tsoron ji Irin muryar Musbahu Balle ta ganshi, idan kuwa hakan ta kasance ba karamar gigicewa take ba saboda irin axabtuwa da take, ta yi kukan tayi Allah ya isa wa Maimuna ta Kuma tsine mata yafi cikin carbi Don Tana ganin ita ta Fara kaita ta baro ta, Sede Khulthum ita ta Fara cutar kanta, ita ta Fara kashe kanta da hannuwanta kamar yadda tayi destroying kanta ba tareda taimakon kowa ba. Kuka sosae Khulthum ta tsaya a gurin Tana yin, kuka Marar sauti Marar dadi dake fitowa Tun Daga karkashin zuciyarta, kuka ne takeyi na rashin makama, na bakin cikin halin da ta jefa kanta ciki, kuka take sosae tamkar ana cire mata wani sassa Daga jikinta. Ta dabbaka a kukan da take taji hannu an dafa kafadarta ko bata juyo ba tasan waye Musbahu ne, take jikinta ya dauki rawa da kyarma tamkar kura ta hadu da zaki, kukan da take dif ya dauke se hawaye dake sakko mata a fuska, juyo da ita yayi tana fuskantar shi Sede maimakon ganin Fuskarshi a murtuke kamar kullum se taga sassauci a Fuskar tamkar "pity" a kwance wanda suna hada ido yayi saurin tamke fuskar tashi a ranshi Yana kokarin yakice tausayinta da ya Fara rinjayar shi daga zuciyarshi, "Bakin sun tafi ne? " Da sauri ta girgiza kanta batareda ta iya furta kalma ko daya ba saboda yadda ta kidime, Fuskarshi ya kara daurewa yace "Ku shirya muje gaba daya" Yana fadar haka ya fice, wani farin ciki taji ya sauka a ranta at least zata fita daga gidan. Dakin dayake kusa da ita ta fada ta wanko fuskarta amma dukda haka alamun kuka na nan hakan yasa ta dauki kwalli ta zizara akan idanunta tareda shafa powder sannan ta dauki ciro lace me kyau da akai dinkin gown me tsari, Seda ta shirya ta karewa kanta kallo jikin mirror, tasan in har mace ake nema to tabbas ta kai mace, babu inda zaka kushe ta wala halitta ko kyaun fuska amma tayi fatali da wannan baiwar ta Allah da ya bata kawai ta dorawa kanta matsanancin kwadayi da yayi clouding mata vision dinta har ta kasa ganin wutar data tunkaro ta, Lokaci daya ta tuno ranar da ta iske Musbahu a office farkon haduwarsu abinda ya fada mata wanda kusan gugar zana ce amma dayake burinta a rayuwa kudi ne kawai yasa bata fahimta ba, here she's today ko hakkin Ashir tasan bazai barta ba, mutumin da ya so ta yayi hakuri da halayenta amma tayi fatali da hakan ta ki aurenshi. A hankali ta tura kofar dakin dasu A'isha suke ciki, dukkansu sun shirya tamkar Dama jiranta suke Tana shigowa suka Mike, kallonsu tayi tace "A'a ku tsaya tare zamu fita" Kai A'isha ta gyada tana mamakin yadda bakin Khulthum Ya mutu, ga wata rama Marar tsari da Khulthum din tayi, gaba daya ta koma wata iri kamar ba ita ba, matching veil ta dakko ta yafa sannan ta dakko wata Leda ta shiga zuba kayan kwaliyya da atamfofi tana gamawa akai knocking softly jikin kofar, wata Irin muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta har Seda ledar hannun nata ta kubce daga hannun nata wanda yasa Aisha kallonta Cikeda mamakin Abinda ya sata rikicewa har haka. Duk yadda Khulthum taso regaining nutsuwarta amma Shigowarshi da kuma kama hannunta da yayi cikin tattausan hannunshi yasa ta kuma rikicewa haka dai suka nufi mota babu me magana yayi driving dinsu Zuwa gida, yana parking Bata jira komai ba ta bude ta shige gidan kusan a guje, wani Irin missing din gidan taji, ji tayi tamkar an cire ta daga wuta haka taji, ga wata nutsuwa da ta kwarara mata. Da Baba suka Fara cin Karo wanda yayi Alwala don yin sallar isha'i, kallonta yayi itama ta tsaya abin mamaki ta tsugunna har kasa ta gaisheshi daidai lokacin su A'isha suka shigo, suma mamaki kamar ya kashe su, amsawa Baba yayi ya fice da hanzari Don A'isha tace tare suke da Musbahun Yana waje. Ciki suka shiga inda ta tarar Mama ta Idar da sallah Tana zaune Tana cin tuwo, da gudu ta isa gareta ta rungume ta tana sakin wani matsanacin kuka Wanda takiyi ranar da zaa kaita tana ganin dan me zatayi kuka tunda ta yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda sede what she thought is not what she met, it was two different things that are parallel to each other. Gaba daya Mama hankalinta ya tashi har suma su A'isha wadda suka tabbatar Khulthum ta fada mugun hannu daga yadda take abubuwa, tambayar duniya Mama tayi mata amma shiru a haka Musbahu, Baba da Amir suka shigo inda Aisha ta shimfida mishi tabarma ta kawo mishi tuwo, babu musu ya saka hannunshi Yana ci kuma abincin yayi mishi dadi sede gabanshi faduwa yake ganin yadda Khulthum ke kuka, hakan yasa yayi saurin gamawa yace "Zamu tafi, bata da lapiya ne" Nan Baba ya sata gaba da nasiha ita kuwa kuka kadai take a haka babu yadda zatayi ta biyo bayanshi Mama na kwantar mata da hankali, suna shiga mota ya kalleta ya maida kanshi kan tukin da yake har Seda suka kusa gidan Gwoggon kafin yace "Nan ma idan Kinje Kiyi kukan" Wani dummm taji a kirjinta haka ta biyo bayanshi Zuwa ciki, Rana ta uku da Taxo gidan gwoggo kenan, Tana zaune kan kujerar ta ta kullum da kullum. Wannan Karon papers ne hannunta tana dubawa idanunta Sanye da medical glasses wanda ya Kara boye tsufan da tayi. Zama sukayi kan carpet suna gaisheta, baki daya ta maida hankalinta Kan Khulthum wadda ta lura kamar kuka take, ko gaisuwar Bata amsa ba ta dubi Musbahu dake gurfane gabanta tace "Me ka yiwa Ummu_Khulthum dinne? " Da sauri ya dubi sashen da Khulthum din ke Zaune yace "Babu komai Gwoggo, kawai tana kukan Munje gidansu ne, Bata son tahowa" With care ta kalla Khulthum din a ranta tana karyata Abinda Musbahu yace Amma ta share tace "Se ka barta ta Kwana, kasan pains of barin gida kuwa? Se ka tafi yau anan zata kwana" Wani sanyi Khulthum ta ji a ranta, yayinda Musbahu yaji bakin cikin hakan dan ya Tama wannan Daren gwoggo ta wargatsa mishi budget Amma babu damuwa yayi yadda ya saba. Haka babu yadda zaiyi ya tafi Khulthum ta saki Jikinta sosae da Gwoggon taci abinci sannan tayi bacci wanda ta manta rabonshi da Irin wannan, don tasan she's far more than safe, babu me sex da ita through anus babu me tormenting dinta. Washegari se yamma Musbahu ya shigo gidan dan daukar Khulthum, Gwoggo na Zaune Kan kujera tana waya yayinda Khulthum ta dakko glass bowl Daga kitchen wadda take cike da hadadden Kwadon rama da yasha kuli kuli na gwoggo ne, sallamarshi kawai tasa jikin Khulthum Fara bari har bowl din ta kwace Daga hannunta ta fadi kan saman tiles ta fashe, da sauri gwoggo ta Mike ta nufi inda Khulthum din ke tsaye se rawa jikinta yake saboda firgita, hannunta ta kama Tana tambayarta ko akwai wani abu? Kanta ta girgixa tayi saurin barin parlon, Gwoggo was puzzled hakan yasa ta dubi Musbahu dake tsaye yayi kirikiri kamar shege a rabon gado! Bangaren Hajiya Subay'a uwargida gidan Alhaji Junaid angon Sulaim, karfe shida na ranar litinin, Subay'a ta shigo gida Daga gurin aiki da ta Riga tayi reporting don taga zaman bazai kareta ba don tamkar wanda take zaman nashi ya manta da anyi hallitar ta a doron duniya. Ta dawo gidan da babu inda take fargaba da tsoron zuwa Irin gidan Alhajin saboda yadda Alhajin ya koma wani iri tamkar bashi ba, ranar da ta dawo Daga Kaduna Dama babu Wanda ta nema ta wuce gurin Alhaji wanda tamkar zaiyi mata Baki don fada kuma yace ta zauna ga guri nan, awanni biyu basu cika ba Sega Samina ta dawo da takardar sakinta, tashin hankali kenan Seda suka kwamata basu Yi abubuwan da sukai ba, Duk ba Wannan ba yadda karamar Yarinya Asiya ta juyar da tunanin ubansu, gata fitsararriya tayi ta shiga iri iri babu ko dar a cikin jikinta, I Samina taso zubar da hali Salima ta hana ta don itama mijin ya saketa hakan yasa sauran suka daidaita zamansu cikin gidan saboda gudun abinda ka iya Zuwa ya dawo. A haka suke zaune su uku tamkar marayu haka suke dadinta daya ma suna fita aiki hakan Ke rage musu wasu abubuwan amma Bayan hakan da tuni zukatansu sun fashe. Kullum rana Subay'a na zuba idanun ranar da Junaid zai zo ya tafi da ita amma har ta gaji da jira, tayi kuka har babu iyaka tayi nadama wadda ta kasance Marar amfani Tunda tayi lokacin da alkalami ya riga ya bushe. Baki daya taji alhakin komai yana kan hajiya don kullum suka zauna se sunyi maganar a ganinsu hajiyar ce sanadin komai, ita taja komai, ita ta jefa su halinda suke ciki. Lokacinda ta isa Asiya tana tsaye a parlor Tana taureren wuta, Subay'a ko kallonta Batayi ba don idan da abinda ta tsani gani bai wuce Asiya ba, Tana shiga ko Jakarta bata aje b taji Alhaji na kwala mata Kira, cikin hanzari ta fito Tana amsawa, yana tsaye ashe bata Lura dashi ba ta wuce ga bata gaida Asiya ba, nan ya balbale ta da fada tamkar zai kai mata hannu haka ya dinga fada wai idan ta raina Aisya to shi ta raina, duk wannan bai dameta ba Seda yace "Akan wannan yarinyar babu Abinda bazan iya ba, 'yan iska da kuka ki zaman aure, haka dukkanku zaku dawo" Kuka sosae ta dinga yi itada Samina wadda taji komai daga daki, basu taba tunanin haka zasu kare ba amma gashi Abinda Sulma ke fada ya tabbata ranar da na sani. Seda suka gama kukansu sega Salima da mummunan labarin kishiyar da zaayiwa Surayya da Suhaila. Ji sukai Anya a duniyar suke kuwa yadda masifa take afka musu dukkansu Lokaci guda! Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 53 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Thank you for patiently waiting, thank you for the prayers! Amarya na dakinta* Amira bata jira gama ganin reaction din Khulthum ba ta cigaba da fadin "AI an saka ranar biki, wata uku ya rage yana zuwa Hutu xa'ayi bikin su tafi tare. Wanda ya dauki nauyin karatun nashi ya hada da nata" Wani yake Khulthum tayi tace "Ikon Allah, to Allah ya kaimu " Tana fadar haka ta mike ta fita daga dakin, Rana ta farko a cikin rayuwarta da ta Fara jin tayi kuskure, Rana ta farko da ta Fara jin wani abu yana bin zuciyarta na Anya ta yiwa rayuwarta daidai? Taji anya akan turba me kyau take? Jingina tayi da kofar dakin dake gefe idanunta na cikowa da wata zazzafar kwalla, a hankali wasu abubuwan na rayuwarta suka Fara bayyana a idonta, tamkar wani flashback a film haka suka dinga bayyana mata, tabbas kwadayi mabudin wahala ne, tabbas wanda ya hau motar kwadayi zai sauka a Tashar wulakanci, gashi nan bataje ko ina ba ta fara gani, kwatakwata Watannin ta biyu kawai cikin gidan amma gashi Anyi mata mummunan tabo cikin zuciyarta da rayuwarta baki daya. A halin yanxu babu Abinda take matsanancin tsoron ji Irin muryar Musbahu Balle ta ganshi, idan kuwa hakan ta kasance ba karamar gigicewa take ba saboda irin axabtuwa da take, ta yi kukan tayi Allah ya isa wa Maimuna ta Kuma tsine mata yafi cikin carbi Don Tana ganin ita ta Fara kaita ta baro ta, Sede Khulthum ita ta Fara cutar kanta, ita ta Fara kashe kanta da hannuwanta kamar yadda tayi destroying kanta ba tareda taimakon kowa ba. Kuka sosae Khulthum ta tsaya a gurin Tana yin, kuka Marar sauti Marar dadi dake fitowa Tun Daga karkashin zuciyarta, kuka ne takeyi na rashin makama, na bakin cikin halin da ta jefa kanta ciki, kuka take sosae tamkar ana cire mata wani sassa Daga jikinta. Ta dabbaka a kukan da take taji hannu an dafa kafadarta ko bata juyo ba tasan waye Musbahu ne, take jikinta ya dauki rawa da kyarma tamkar kura ta hadu da zaki, kukan da take dif ya dauke se hawaye dake sakko mata a fuska, juyo da ita yayi tana fuskantar shi Sede maimakon ganin Fuskarshi a murtuke kamar kullum se taga sassauci a Fuskar tamkar "pity" a kwance wanda suna hada ido yayi saurin tamke fuskar tashi a ranshi Yana kokarin yakice tausayinta da ya Fara rinjayar shi daga zuciyarshi, "Bakin sun tafi ne? " Da sauri ta girgiza kanta batareda ta iya furta kalma ko daya ba saboda yadda ta kidime, Fuskarshi ya kara daurewa yace "Ku shirya muje gaba daya" Yana fadar haka ya fice, wani farin ciki taji ya sauka a ranta at least zata fita daga gidan. Dakin dayake kusa da ita ta fada ta wanko fuskarta amma dukda haka alamun kuka na nan hakan yasa ta dauki kwalli ta zizara akan idanunta tareda shafa powder sannan ta dauki ciro lace me kyau da akai dinkin gown me tsari, Seda ta shirya ta karewa kanta kallo jikin mirror, tasan in har mace ake nema to tabbas ta kai mace, babu inda zaka kushe ta wala halitta ko kyaun fuska amma tayi fatali da wannan baiwar ta Allah da ya bata kawai ta dorawa kanta matsanancin kwadayi da yayi clouding mata vision dinta har ta kasa ganin wutar data tunkaro ta, Lokaci daya ta tuno ranar da ta iske Musbahu a office farkon haduwarsu abinda ya fada mata wanda kusan gugar zana ce amma dayake burinta a rayuwa kudi ne kawai yasa bata fahimta ba, here she's today ko hakkin Ashir tasan bazai barta ba, mutumin da ya so ta yayi hakuri da halayenta amma tayi fatali da hakan ta ki aurenshi. A hankali ta tura kofar dakin dasu A'isha suke ciki, dukkansu sun shirya tamkar Dama jiranta suke Tana shigowa suka Mike, kallonsu tayi tace "A'a ku tsaya tare zamu fita" Kai A'isha ta gyada tana mamakin yadda bakin Khulthum Ya mutu, ga wata rama Marar tsari da Khulthum din tayi, gaba daya ta koma wata iri kamar ba ita ba, matching veil ta dakko ta yafa sannan ta dakko wata Leda ta shiga zuba kayan kwaliyya da atamfofi tana gamawa akai knocking softly jikin kofar, wata Irin muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta har Seda ledar hannun nata ta kubce daga hannun nata wanda yasa Aisha kallonta Cikeda mamakin Abinda ya sata rikicewa har haka. Duk yadda Khulthum taso regaining nutsuwarta amma Shigowarshi da kuma kama hannunta da yayi cikin tattausan hannunshi yasa ta kuma rikicewa haka dai suka nufi mota babu me magana yayi driving dinsu Zuwa gida, yana parking Bata jira komai ba ta bude ta shige gidan kusan a guje, wani Irin missing din gidan taji, ji tayi tamkar an cire ta daga wuta haka taji, ga wata nutsuwa da ta kwarara mata. Da Baba suka Fara cin Karo wanda yayi Alwala don yin sallar isha'i, kallonta yayi itama ta tsaya abin mamaki ta tsugunna har kasa ta gaisheshi daidai lokacin su A'isha suka shigo, suma mamaki kamar ya kashe su, amsawa Baba yayi ya fice da hanzari Don A'isha tace tare suke da Musbahun Yana waje. Ciki suka shiga inda ta tarar Mama ta Idar da sallah Tana zaune Tana cin tuwo, da gudu ta isa gareta ta rungume ta tana sakin wani matsanacin kuka Wanda takiyi ranar da zaa kaita tana ganin dan me zatayi kuka tunda ta yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda sede what she thought is not what she met, it was two different things that are parallel to each other. Gaba daya Mama hankalinta ya tashi har suma su A'isha wadda suka tabbatar Khulthum ta fada mugun hannu daga yadda take abubuwa, tambayar duniya Mama tayi mata amma shiru a haka Musbahu, Baba da Amir suka shigo inda Aisha ta shimfida mishi tabarma ta kawo mishi tuwo, babu musu ya saka hannunshi Yana ci kuma abincin yayi mishi dadi sede gabanshi faduwa yake ganin yadda Khulthum ke kuka, hakan yasa yayi saurin gamawa yace "Zamu tafi, bata da lapiya ne" Nan Baba ya sata gaba da nasiha ita kuwa kuka kadai take a haka babu yadda zatayi ta biyo bayanshi Mama na kwantar mata da hankali, suna shiga mota ya kalleta ya maida kanshi kan tukin da yake har Seda suka kusa gidan Gwoggon kafin yace "Nan ma idan Kinje Kiyi kukan" Wani dummm taji a kirjinta haka ta biyo bayanshi Zuwa ciki, Rana ta uku da Taxo gidan gwoggo kenan, Tana zaune kan kujerar ta ta kullum da kullum. Wannan Karon papers ne hannunta tana dubawa idanunta Sanye da medical glasses wanda ya Kara boye tsufan da tayi. Zama sukayi kan carpet suna gaisheta, baki daya ta maida hankalinta Kan Khulthum wadda ta lura kamar kuka take, ko gaisuwar Bata amsa ba ta dubi Musbahu dake gurfane gabanta tace "Me ka yiwa Ummu_Khulthum dinne? " Da sauri ya dubi sashen da Khulthum din ke Zaune yace "Babu komai Gwoggo, kawai tana kukan Munje gidansu ne, Bata son tahowa" With care ta kalla Khulthum din a ranta tana karyata Abinda Musbahu yace Amma ta share tace "Se ka barta ta Kwana, kasan pains of barin gida kuwa? Se ka tafi yau anan zata kwana" Wani sanyi Khulthum ta ji a ranta, yayinda Musbahu yaji bakin cikin hakan dan ya Tama wannan Daren gwoggo ta wargatsa mishi budget Amma babu damuwa yayi yadda ya saba. Haka babu yadda zaiyi ya tafi Khulthum ta saki Jikinta sosae da Gwoggon taci abinci sannan tayi bacci wanda ta manta rabonshi da Irin wannan, don tasan she's far more than safe, babu me sex da ita through anus babu me tormenting dinta. Washegari se yamma Musbahu ya shigo gidan dan daukar Khulthum, Gwoggo na Zaune Kan kujera tana waya yayinda Khulthum ta dakko glass bowl Daga kitchen wadda take cike da hadadden Kwadon rama da yasha kuli kuli na gwoggo ne, sallamarshi kawai tasa jikin Khulthum Fara bari har bowl din ta kwace Daga hannunta ta fadi kan saman tiles ta fashe, da sauri gwoggo ta Mike ta nufi inda Khulthum din ke tsaye se rawa jikinta yake saboda firgita, hannunta ta kama Tana tambayarta ko akwai wani abu? Kanta ta girgixa tayi saurin barin parlon, Gwoggo was puzzled hakan yasa ta dubi Musbahu dake tsaye yayi kirikiri kamar shege a rabon gado! Bangaren Hajiya Subay'a uwargida gidan Alhaji Junaid angon Sulaim, karfe shida na ranar litinin, Subay'a ta shigo gida Daga gurin aiki da ta Riga tayi reporting don taga zaman bazai kareta ba don tamkar wanda take zaman nashi ya manta da anyi hallitar ta a doron duniya. Ta dawo gidan da babu inda take fargaba da tsoron zuwa Irin gidan Alhajin saboda yadda Alhajin ya koma wani iri tamkar bashi ba, ranar da ta dawo Daga Kaduna Dama babu Wanda ta nema ta wuce gurin Alhaji wanda tamkar zaiyi mata Baki don fada kuma yace ta zauna ga guri nan, awanni biyu basu cika ba Sega Samina ta dawo da takardar sakinta, tashin hankali kenan Seda suka kwamata basu Yi abubuwan da sukai ba, Duk ba Wannan ba yadda karamar Yarinya Asiya ta juyar da tunanin ubansu, gata fitsararriya tayi ta shiga iri iri babu ko dar a cikin jikinta, I Samina taso zubar da hali Salima ta hana ta don itama mijin ya saketa hakan yasa sauran suka daidaita zamansu cikin gidan saboda gudun abinda ka iya Zuwa ya dawo. A haka suke zaune su uku tamkar marayu haka suke dadinta daya ma suna fita aiki hakan Ke rage musu wasu abubuwan amma Bayan hakan da tuni zukatansu sun fashe. Kullum rana Subay'a na zuba idanun ranar da Junaid zai zo ya tafi da ita amma har ta gaji da jira, tayi kuka har babu iyaka tayi nadama wadda ta kasance Marar amfani Tunda tayi lokacin da alkalami ya riga ya bushe. Baki daya taji alhakin komai yana kan hajiya don kullum suka zauna se sunyi maganar a ganinsu hajiyar ce sanadin komai, ita taja komai, ita ta jefa su halinda suke ciki. Lokacinda ta isa Asiya tana tsaye a parlor Tana taureren wuta, Subay'a ko kallonta Batayi ba don idan da abinda ta tsani gani bai wuce Asiya ba, Tana shiga ko Jakarta bata aje b taji Alhaji na kwala mata Kira, cikin hanzari ta fito Tana amsawa, yana tsaye ashe bata Lura dashi ba ta wuce ga bata gaida Asiya ba, nan ya balbale ta da fada tamkar zai kai mata hannu haka ya dinga fada wai idan ta raina Aisya to shi ta raina, duk wannan bai dameta ba Seda yace "Akan wannan yarinyar babu Abinda bazan iya ba, 'yan iska da kuka ki zaman aure, haka dukkanku zaku dawo" Kuka sosae ta dinga yi itada Samina wadda taji komai daga daki, basu taba tunanin haka zasu kare ba amma gashi Abinda Sulma ke fada ya tabbata ranar da na sani. Seda suka gama kukansu sega Salima da mummunan labarin kishiyar da zaayiwa Surayya da Suhaila. Ji sukai Anya a duniyar suke kuwa yadda masifa take afka musu dukkansu Lokaci guda! Shatuuu ♥️ *MACE A YAU* 54 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Umma dandago,Rashida muktar,Hafsat el-marzuq,maimuna el-marzuq, Ummu Lubna, Nobles cakes n more and all other well wishers, lovers behind the curtain.... Nagode sosae Allah ya bar zumunci da soyayya* Dauraye hannunta tayi a sink din toilet din sannan ta kashe tareda kallon fuskarta jikin mirror din dake saman sink din. gashin da ya zubo mata wajen idanunta ta dauke da hannuwanta sannan ta fito baki daya daga toilet din, babu kowa cikin hadadden bedroom din Nata wanda dukkan furniture din dake kafe a ciki yake golden da Baki, sunyi kyau sosae, kujerar dake gaban dressing mirror ta jawo ta zauna tareda goge jikinta dake smooth yana ta daukar idanu yayi shar dashi Irin glow dinnan. Cikin hanzari ganin lokaci ya fara tafiya yasa tayi saurin shiryawa cikin wata Maroon exclusive wax da fari dinkin skirt da Riga me Peplum, tayi mata kyau abinka da farar mace wadda take ganiyar kuruciyarta, ga soyayya da kulawar miji duka, turarrukan ta ta fesa sannan ta fito Zuwa wani tamfatsetsen parlor me balain kyau, kujerun ciki da carpet din yan Persia ne, kalarsu kalar furnitures din bedroom dinta ne wato gold da Baki, wani corridor ta bi wanda aka Jere kananan frames na flowers, carvings da portrait innovations se hakan ya kayatar da gurin. Kofa ce ke facing gurin, ta murda a hankali ta tura kofar yana tsaye ya juya baya da dukkan alamu links Yake daurawa a hannun long sleeve coffee top din dake Sanye jikinshi, a hankali ya juyo Yana kallonta wani nishadi na kara shigarshi, yana jin nutsuwa hade da mugu mugun sonta na bin dukkan wani channel da jini ke ratsawa. Sulaim na isa inda yake fuskarta da murmushi ta dan rankwaba tare da fadin "Ina Kwana? " Hannunta ya kamo cikin nashi yana kare mata kallo tareda fadin "Kinyi kyau Dove, da duk wannan kwaliyyar Za'a tafi school din? " Bakinta ta turo tace "Ina kwalliyan yake ne? Powder ce kawai na shafa se kwalli da balm! " Dariya yayi ganin yadda ta Bata rai, cikin kwantar da murya yace "Bance wani abu ba fa, Ehen yau class din Dr. Ammar kuke dashi ko?" Kanta ta gyada tana maida hankalinta Kan gyara mishi link din da kuma collar rigar tashi, "He's not coming, so ina ganin ba se Kinje ba" Wani karamin ihu ta saki tana fadin "At least someone can rest" Bakinshi ya tabe yana Mika mata wayarshi yace "Lazy fellow! " Kafadarta tayi shrugging Irin Kara fada dinnan, sannan suka fito Zuwa parlourn inda ya zauna suma su Ahmad da Muhammad an shiryasu cikin uniform. Seda ta gama shirya breakfast din kan dining mat dake ba kowanne Lokaci bane suke ci kan table ba, suna kamalla breakfast din suka Mike kowannensu na kokarin fita inda ya dace, kallonta yayi bayan ta rakasu bakin mota yace "Dove Anjima zaki fitan? " Kanta ta gyada tace "Eh Inshaaa Allah Zamu fita tareda su Aimana " Kanshi ya gyada yace "Na bar miki sako kan gado, Allah ya kiyaye hanya" Godiya tayi mishi yana harar ta Daga haka sukai sallama ya wuce ita kuma ta koma ciki ta Fara gyara inda ya dace da taemakon Nanny su Muhammad. Parlor ta dawo ta zauna Tana kurbar tea tareda kurawa wani frame dake kan center table din ido, hoto ne Daddynta da Mummynta, Junaid da ita, idan zata iya tunawa wannan hoton anyi shi lokacinda ta gama primary ne akai mata graduation party, tana ta dariya dukkan wushiryar ta siririya me kyau ta bayyana haka dimples dinta masu matukar daukar hankali sun lotsa, hannunta cikin na Junaid wanda yake dariya da sauran iyayensu, a hankali ta kai hannunta ta dauki hoton wasu abubuwa na tsirga mata, hakika tayi kewar wannan fuskokin da ace suna da rai ko wanne irin farin ciki zasu kasance ganin sun auri junansu. Allah kadai ya san Irin murnar da zasui, Allah dai ya jikansu ya rahmushe su yasa sun huta, Tana fatan su kasance tare a Aljannah don ko bata fada ba tana kewarsu dukda bata rasa komai ba amma iyaye daban suke. Wajen karfe Sha biyu ta kammalla abincin Rana ta sake wanka ta shirya cikin Farar Abaya me bakaken stones tayi mata kyau kamar me, a ranta tana ta mitar rashin zuwansu Khairi tare da tunanin Irin rashin mutuncin da zatayi musu. Ai bata gama wannan tunanin ba taji sallamar Aimana da Khairi, hade fuska tayi yayinda su ma suka Bata rai suka zazzauna, se kuma Aimana ta Mike ta debo musu ruwa da lemu daga fridge wanda ke aje a corridor da zai kaika kitchen, Tana zama Sulaim tace "Lallai Bakuda mutunci har wani ku bata min Lokaci sannan kuzo Ku fini fushi" Aimana ta zabga mata harara Tana sauke gwangwanin Shani din da ta daddaka saboda rana da suka kwaso tace "Babbar Marar mutunci ai Kece, har wani yau Dr Ammar ba zai zo ba mijinki ya fada miki kika barmu rana ta Kare a kanmu" "Duba wayoyinku Allah yana fadamin na muku text" Duka suka dakko aikuwa ga text dinta tun safe, borin kunya yasa aka Fara hira ta Mike don zubo musu abinci Khairi tace "Karki fara, yau gidan Amarya Khulthum Zamu ci lunch, Kede tashi kawai mu tafi" Haka kuwa akai babu jimawa suka yiwa Lodge road tsinke, da taemakon text din address din Khulthum da tayiwa Sulaim, a bakin gate Sulaim tayi parking Baki daya suka fito suna karewa gate din kallo, shi kanshi abin kallo ne, seda akai formalities kafin suka samu suka shiga inda kowacce ta jinjina alamarin Khulthum, Aimana da bata iya shiru tace "Ikon Allah! Khulthum ta auri me kudi ina taya ta murnar cikar buri " Duka suka jinjina abin lokacinda kafafunsu suka taka parlon, ya hadu karshe kamar wani palace, babu kowa se karar plasma da AC dake ta aiki babu kakautawa, Khairi ta ciro wayarta tayi dialing number Khulthum din bugu daya ta dauka tamkar wadda take bacci tacr "Inata jiranku....." Katse ta tayi da fadin "Muna parlor to uwar complaint" Ta manta wani ciwo da kasanta da bayanta yake mata tayi saurin Durowa daga gado wanda taji wani sharp pain ya soketa se kuma abu yana bin kafarta, da sauri ta daga rigar dake jikinta, wani muguwar faduwar gaba ta ziyarce ta ganin Kashi ne ya biyo kafarta, hannunta na hagu tasa ta lakato tare da kaiwa hancinta, wani wari taji wanda ya tabbatar mata Kashin ne, tayi shiru Tana tunanin abinda yake faruwa da rayuwar ta, toilet ta shige cikin sauri ta gyara jikinta tareda sake feshe jikinta da turarruka sanann ta fito jikinta kamar an zare mata laka haka ta fito, ganinsu yasa ta danji sanyi tareda tuno da, school days dinsu, lokutan fada da suke itada Aimana, kurara Maza itada Khairi, secrecy dinsu itada Sulaim, Gasu nan duk tsiyar da tayi musu sun amsa gayyatar ta sunxo gareta basui fushi ba. Idanunta suka ciciko da kwalla tana tunano yadda Aimana ta dinga hanata auren me kudi, yadda Sulaim ta dinga mata fada akan yadda take treating Ashir, Gashinan ita ke kuka Su they've moved on already, hawaye ya sakko mata duk yadda tayi kokarin hana hakan amma ta gagara, ta tuna yadda Khairi ta dinga binta akan ta dawo makaranta tayi kunnen uwar shegu dasu, gashi tun ba'a je ko ina ba komai ya lalace, Abinda take neman ta samu amma babu amfani. Gaba daya jikinsu yayi mugun sanyin ganin yadda Ummu_Khulthum ta zama, yadda ta lalace ta kare musamman ganin yadda hawaye Ke yi mata zarya a kumatunta, duk se sukai shiru kowa da Abinda yake tunani, Seda tayi kuka me isarta wanda yake me ciwo da karawa zuciyarta zugi a yanzun kam bata da wani buri na rayuwa komai ya fitar mata akanta bata jin akwai Abinda yake burgeta kuma, to meye zai burgeta, me zaayi da mata'ul hayat... Kyalekyalen rayuwa? Basuda amfani, kuma bahaushe yayi gaskiya da yace son zuciya bacinta. Sulaim ce ta Fara bude bakinta da yayi mata nauyi tace "Khulthum Kiyi hakuri ki bar kukan haka, komai da yake faruwa da dan Adam Kaddara ce.... Kiyi hakuri kilan ribar ki na gaba" Hawayenta ta share tace "Kayya Sister ina wata riba? Babu da ne naci riba yanzun gashi ina girbar abinda na shuka. Kaddara kuma da kike magana na yadda komai na rayuwa MUQQADARI NE daga Allah, amma everything in life is predestined.... Bai gama zama kaddarar ba Shiyasa Allah da manzonshi sukace kayi addu'a it can change it, ni meye banyi ba, meye baku fada min ba naki yadda nace Se na auri me kudi, gashi na samu na aura here I'm and only God knows where I'm leading my life to" Se kuka ya kara kwace mata hakan ya kara saka su cikin tashin hankali gaba daya suka shiga rarrashinta har tayi shiru ta daina kukan kuma babu Wanda ya tambayeta halin da take ciki, a haka ta wanko fuskarta suka hadu suka ci abinci aka tuna baya. Tunda Sulaim tace bata son kamshin ketchup suka saka ta a gaba wai ta harbu hakan yasa Khulthum ta ware ana ta hira inda take jin yanzun suna level 3 second semester tayi kukan zuciya yadda ta rusa rayuwarta da hannunta. Seda sukai La'asar sannan suka shirin tafiya nan ta Kara jin tamkar ta bisu Amma babu Hali Don Tana tunanin tabbas akwai abinda Musbahu yayi mata, ya cuceta amma tana ganin babban azzalumi shi ne Kabir wanda yayi hooking dinsu kuma Tunda aka kawo ta gidan Bata kuma ganinshi ba se wancan satin yazo kamar an jefo shi lokacin fitar Musbahu kenan daga dakinta ta gama azzabtuwa Don yanxun maza sun fita kan Musbahu ya rage Hulda dasu sosae se kan Khulthum kuma har lokancin Anal sex din yake, kullum da Ciwon baya da kasa take Kwana, kullum dare Tana jin tamkar ba zata kai Washegari ba, ta tsani rayuwar da Abinda Ke cikinta amma ya zatayi haka zatai managing Tunda ita ta jawa kanta. Kuka sosae ta dinga yiwa Kabir Tana fadin ya cuceta shi kanshi yayi mamakin ganin Khulthum yadda ta rame tamkar ana tsotse ta, ya dinga bata hakuri shi Wallahi baisan hakan ce zata kasance ba amma zai San yadda zaayi da haka suka rabu. Har a mota babu Wanda ya bude Baki yayi maganar halinda Khulthum ke ciki bawai don sun manta ba sedan babu abin fadar ma, kome zasu fada bayada amfani. Jiki a sanyaye Sulaim ta karasa gida, babu kowa yaran sun tafi islamiyya shi kuma oga ya fada mata se dare zai shigo. Har maghariba tana zaune yaran suna ta tambayarta me yake damunta amma ta kasa cewa komai a haka a daddafe ta yi girkin dare, ta tsalo wanka ta shirya cikin cotton lace Red da farin zare da akai designing manyan flowers a jiki, tayi kyau babu karya ta dawo parlour ta zauna tareda kurawa agogo ido, wayarta dake hannun Muhammad ta Fara ringing hakan yasa ya miko mata, wani yanayi Marar dadi ta tsinci kanta a ciki saboda ganin sunan Khulthum na yawo a kan screen din, har zuciyarta take jin tausayin ta don fuskarta kadai zai fada maka Bata da nutsuwa. "Kunje gida lapiya? Nagode Allah ya bar zumunci " Murmushi Sulaim tayi tacr "Lapiya lau babu komai ai" Se kuma sukai shiru, Khulthum tana tunanin daga inda zata Fara haka ta daure cikin sarkakkiyar murya ta fayyacewa Sulaim halin da take ciki, tamkar ruwa ya cinye ta haka Sulaim tayi Bayan Khulthum tayi shiru, ta rasa me zatace mata, Wacce shawara zata bata a karshe nasiha kawai tayi mata sannan ta tuna mata laifufukan da tayiwa Mama ya kamata ta gyara, ta nemi gafarar wanda ta batawa. sannan tayi addu'a Allah, ta nema gurin ubangiji shi ka dai kadai zai gyara Musbahu ba mutum ba! Shatuuu ♥️[9/7, 6:28 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 56 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad Washegari aka tashi da kwalleliyar rana kasancewar a watan April muke ga kuma ranar juma'a ce don haka rana ta haska wanda zakai tunanin Irin sha biyun ranar nan ne, a firgice Sulaim ta Mike Daga kan couch din data kwanta bayan tayi sallar asuba bacci yayi gaba da ita, mikewa tayi ta zauna ta daga kanta zuwa kallon agogon dake manne a bangon parlour, ajiyar zuciya ta sauke ganin shida da yan Mintina, kitchen ta wuce ta jona toaster tareda farke sardine ta hada da Attaruhu, albasa da seasonings tasa spoon ta farfasa sannan ta zuzzuba a sliced bread tayi toasting ta jera a plate, custard ta dama ta hada Tea black kawai me kayan kamshi sannan ta fito dasu ta Dora Kan dining Table din sannan ta nufi dakinshi, yana zaune kan sofa yana kallon news, gefenshi ta zauna tareda kwantar da kanta akan kafadar shi tace "Morning heartthrob" "Morning Dove, Kinada son jiki dama Cat nake ce miki" Murmushi tayi tareda kokarin dauke kanta daga kafadarshi amma ya hana hakan, "Munada lecture fa ko baza kije ba? " Fuskarta ta bata Tace "Bacci nake ji kar naje nayi ka Kore ni" Dariya yayi yace "Wannan dole ne, tashi mu shirya yau bazan koreki ba" Haka suka shiga wanka sannan suka shirya akai breakfast a daddafe saboda makara, tare suka fito dukkansu har yaran seda suka ajesu kafin suka wuce makaranta. Misalin karfe daya na Rana Subay'a ta dauki handbag dinta tareda tattare komai nata tayiwa makotanta sallama, gaba daya ilahirin jikinta a tsorace take saboda wannan kiran gaggawar da Alhajinsu yayi mata dole haka ta je gurin manager yayi excusing dinta don zazzabi take fama dashi. Tana isa kofar gidan taji wata mummunar faduwar gaba saboda ganin motar Junaid yayi parking a kofar gidan, hawaye masu zafi suka shiga sakko mata don tasan takardar sakinta ya kawo mata, ta dade cikin motar tana kuka sosae ko ta samu zafin da zuciyar ta take ya ragu, kuka tayi har fuskarta tayi ja haka idanunta, tayi tunanin kukan zai rage wasu abubuwan amma ko daya se kara tayar mata da hankali da yayi, ita a yanzun duk ta fahimci Abinda Sulma ke fada mata cewar Allah idan yace kayi abu to idan ka kiyi se ya saka dole ka yishi ko baka so Bayan ka gama shan wahala, itakam gadhi ta gani akan kanta. Babu yadda ta iya haka ta fito jikinta a sanyaye ta shigo parlon part din Hajiya anan ta ta tarar Samina na kwance tana kallo yayinda take watsa popcorn a bakinta. Gefenta ta samu ta zauna Tana fadin "Samina Alhaji Yana ina? " Dagowa tayi tace "Yana part din Amaryarshi mana" Daga haka ta Mike zuwa daki ta canza kaya kafin ta nufi part din Asiya, Tun Daga kofa take jin fadan Alhaji Yana fadin "Dan ubanta! Ai da sakinta kayi idan yaso ta Kara hankali ai" Wata ajiyar zuciya ta sauke ta yi sallama sannan ta saka kai ta shiga, idanunshi ya dago Yana kallanta, Yana kallon yadda matarshi ta koma, wani sanyi yake gani a tattare da ita, itama kallonshi tayi jikinta ya kara sanyi don wani kyau Taga yayi, ga nutswa a tattare dashi lokaci guda she felt humiliated saboda tasan her presence is same as her absence, ta tuna ranar da suka maida Suhaila gidanta yadda babansu Fannah ya rame, gidan gaba daya ya lalace saboda Suhaila Bata nan Amma kalli yadda mijinta ya koma bata tunanin ta taba ganin kwanciyar hankali a kwayar idanunshi kamar yadda ta gani a yanzun, hawaye masu dumi fresh suka zubo mata. Gefe ta zauna kanta a kasa tana jin yadda Alhaji ke sirfa mata masifa Har yana fadin duk Abinda tayi ya saketa itakam kuka kawai take kasan zuciyarta wani sanyi taji don tasan mijinta ya dawo gareta ne. Alhaji na fita kukanta ya tsananta wanda yake damun Junaid 🎶_Baby give me one more chance to be the one to hold your hands, maybe we could learn to love again.... Yeah yeah_ hakan yasa ya Mike zuwa inda take Zaune ya tsugunna akan gwiwarshi ya dago fuskarta wadda tayi kaca kaca da hawaye, da sauri ta Fada jikinshi ta rungumeshi tamkar zaa kwace mata shi, 🎤_I don't deserve it, I know I don't deserve it but stay with me a minute, I swear I'll make it worth it, I failed you, feel like a failure I know that she gave you everything! One last time I need to be the one to take you home, one more time I need to be the one to hold your hands_ Seda ta nutsu kafin ta dago Daga jikinshi kanta a kasa saboda masifaffiyar kunyarshi da take ji. Zama ya gyara tare da kallonta a tsanake kafin yace "Duk lokacinda a aure aka Fara yaji, ko kuma ace kije gidanku to Abu na gaba da zai biyo baya saki ne...... " Da sauri ta dago idonta ta kalleshi don tunaninta lallashinta zaiyi, ko gezau baiyi ba se ya cigaba da fadin ".....Saboda tuntuni darajar da dignity sun Fara zama weak, bazan tuna miki abubuwan da suka faru ba don they're already in the past, Amma ina son zanyi miki albishir cewar inada mata yanzun wadda bata taba sabamin ba, she pampered me kamar jariri, tana girmama ni ta daukeni shugaba kuma Bata taba ketare umarnin da na bata, Bata min musu tana da juriyah......and many more ke kuma hakan sune lapses dinki kinga duk Abinda nake nema na samu Amma ina daraja ki saboda abu guda biyu na farko saboda ina sonki na aureki, na biyu 'ya'yan mu da muka Haifa. Inason idan kin koma ki gyara mistakes dinki Amma idan hakan yaki komai zai iya faruwa" "Batun aurena da Sulaim ina son ki sawa zuciyarki ina sonta ina kaunarta shi yasa na aureta, ban aureta don na huce haushi ba, ina son kisan Sulaim din wata aba ce me daraja cikin rayuwarta, Karki ce na miki wulakanci ko daya Kema ina sonki Amma ina son ki daraja kanki, ki martaba kanki sannan ki nuna mata Kece uwargidan kuma ran gidan idan ba haka ba kina zaune zaki zama yar kallo. After Asr zan dawo mu tafi" Mikewa yayi ya fice yana jin wani bakon yanayi a tattareda shi, yasan Za'a ga rashin kyakyawar shi Amma hakane kadai zaisa Subay'a ta dawo hankalinta. Sulaim ta gama lectures tana ta jiran Junaid dan taje office ance ya fita ga wayarshi bata shiga, hostel ta tafi wajen Khairi wadda take gyaran Kwana, sunayi suna hira har bacci ya dauke Sulaim. Se wajen biyu ta farka tayi sallah sannan taga missed call din Junaid, cikin hanzari tayi returning call din "Kina ina ne? " "Ina hostel gurin Khairi " "On my way" Kashe wayar yayi Itama ta Mike Tana kwallawa Khairi kira, tana shigowa tace "Yaxo zan tafi" Harararta Khairi tayi tace "Custard din fa " "Hada zan sha a mota" Aikuwa ta dakko madara ta hada mata ta rufe cikin wani mug me murfi yayi kyau sannan suka fito Khairi na ta tsokanar ta. Bata kulata ba don Duk hankalinta yana kan mijinta, suna zuwa suka gaisa ta Mika mata handbag dinta da cup din sannan sukai sallama, Yana fara driving ta Fara shan custard dinta, kallonta yayi yace "Wai ni baby akwai sirri ne a shan custard kullum se Kinsha ko sanmin bakya yi, kin koyi rowa ma " "Kai Heartthrob har rowa kuma, ni din ko?" Dariya yayi yace "Wasa nake miki 'Yar albarka my honey" Spoon daya tasa mishi a baki ya amshe haka har suka cigaba da tafiya yana mata hira, suna zuwa gida ta wuce kitchen Don tasan kowa yunwa yake ji, biyo ta yayi lokacin tana kwashe macaroni and cheese din data hada, kwantar da kanshi yayi a jikinta, tureshi tayi yana binta har ta hakura, cikin nitsuwa yace "Dove anjima Mimin su Ahmad zata dawo, ina fatan zaki kasance kamar yadda kike, ina fatan zaki goya min baya, ki cigaba da supporting dina Kina min addu'a na samu Nayi adalci a gareku" Shi kanshi ya sani kuma he felt yadda jikinta ya saki yayi sanyi Amma a haka ta daure saboda wani kishin shi dake ratsa ta tace "I'll always be there for you through every hardship, through all the thick and thin times.... I love you" Kiss ya sakar mata a wayanta Wanda yasa ta saki wani moan a hankali, haka suka cigaba da aikin Yana ta mata nasiha da Kwantar mata da hankali tareda bude mata dukkan sirrin zuciyarshi. Misalin hudu da Rabi Subay'a da Junaid suka isa gidansu wanda ya kasance mafarin komai, inda suka Fara gina rayuwarsu inda komai ya lalace, sun dawo a karo na biyu don sake daura wata rayuwar. Dama Tunda ya fita ta Kira yan uwanta suka je suka gyara ko ina banda bangaren Junaid, Alhaji bai ce mata komai ba don fushi yakeyi da ita haka ta biyo mijinta suka koma. Suna shiga gidan abubuwa da dama suka dinga dawo musu, soyayyarsu, fadansu, sabani da kuma happiest moments dinsu. Ko ina an gyara yayi tas dashi se daukar idanu suke ga kamshin freshener don Bata son turaren wuta a cewarta ita bata son hayaki so Shiyasa kullum da room freshener take amfani. Tamkar wata Bakuwa haka ta zauna a dadire, jinta take tamkar ba tayi fitting gurin ba. Ganin haka yasa ya dawo kusa da ita tare da fadin "Mimi ko ruwa bazaa bani ba? Haka zan zauna da kishirwar" Mikewa tayi tamkar Dama jira take ta wuce daki zuwa fridge ta dakko ruwa da tumbler ta kawo mishi tareda fadin "Papa ruwan babu sanyi" "Ba damuwa lemme have it a hakan" Haka ta tsiyaya mishi yana sha Yana Bata labari har ta dan ware kafin ya tarkata tata Zuwa bedroom inda aka sauke soyayya! Sulaim na dakin da kayan su Ahmad suke Tana hadawa cikin katon trolley, gaba daya jikinta babu wani kuzari a tattare da ita haka wani masifaffen kishi ke addabar zuciyarta, seda ta kammalla hada kayan sannan ta janyo trolley ta fito da ita gefen kujerun parlour. A haka aka kira sallar maghrib ta wuce daki tayi a lokacin Mami ta kirata, Daga jin muryata se kuka wanda take ta rikewa tun kafin fitar Junaid, Seda ta yi shiru sannan Mami ta yi mata nasiha tareda koyarda ita yadda zata danne kashinta Daga haka tayi sallama ita kuma ta fada wanka. Tana fitowa ana kiran isha'i se kawai tayi sallah sannan ta shirya cikin atamfa gown me kyau. Parlor ta dawo inda Ahmad ya dawo gefenta ya rakube kanshi ta shafa sannan ta kawo musu noodles din data dafa sukaci. Tana tattara gurin Junaid yayi sallama ya shigo kasa kasa ta amsa zuciyarta na wani Irin zugi, Yana tsaye bai karasa shigowa ba tazo ta gefensa zata wuce ya riko hannunta tareda hada ta da jikinshi, tureshi ta Fara yi hakan yasa ya jata Zuwa kitchen din rungume da ita, kuka ta shigayi sosae jin wani kamshi na daban a jikinshi, zaunar da ita yayi yace "Suuuuuuu......is this how you will support me? Kina kuka kina karya min gwiwa dan Allah share hawayenki wayace miki ana kuka akan kishiya who told you that? Bayan kinsan ina sonki you're part of my happiness then me kike so kuma? Kiyi shiru kizo muje I need to talk to both of you!" Janye jikinta tayi ta wanke fuskarta a sink batareda ta furta komai ba ta nufi bedroom dinshi inda ta shafa powder da kwalli se ta ware a haka suka fito da yaran dukka, ganin katuwar trolley yasa ya dubeta yace "Dove maida su Ahmad zakiyi ne? " Kanta ta langwabar tace "Eh Mimin su is back me yayi saura kuma? " Kanshi ya girgixa zai magana tayi saurin fadin "Heartthrob please don't, shi ne daidai kowa ya rayu da danshi nima mine will definitely come" Ta fada tareda bashi peck a hannu, babu yadda ya iya haka suka nufi gidan Subay'a dake babu nisa tsakaninsu Koda kafa zaka iya zuwa, Amma saboda dare a mota sukaje, Tunda suka shigo Sulaim ta nemi guri ta zauna shi kuma ya shiga ciki yayinda yaran suke ta tsalle da ihu, tare suka fito itama gabanta Yana faduwa, da gudu Ahmad da Muhammad suka Dane ta, rungumesu tayi a jikinta tace "My boys" Take kowa suka Fara bata labarin Ammiey su, shigowa cikin parlour tayi ta zauna gefen Junaid wanda ke gefen sulaim suka sashi a tsakiyarsu, Sulaim ta Fara gaisheta, Subay'a batada munafurci Dan haka kasakasa ta amsa don ji take kamar ta rufe ta da duka, wani haushin ta take ji. A hankali Junaid ya kama hannun Sulaim ya matse saboda yadda yaji jikinta na rawa, cikin nitsuwa da daddan kalamai ya gabatar da kowacce a matsayin matar aurenshi da yake so, soyayya tasa ya aureta, kowacce ta kama girmanta baisan damuwa. A haka ya raba Kwana bibibyu sannan ya maida Sulaim ya koma, ranar Sulaim da kyar tayi bacci saboda damuwa da kishi amma da ta dage da addu'a se komai ya lafa mata! Shatuuu ♥️ [9/9, 9:59 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 57 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣shatuuu095@wattpad Driver na parking hamshakiya Hajiya Gwoggon Musbahu ta fito Daga bakar Prado da tayi parking, yanayin ta kadai zai tabbatar maka baa nutse take ba, idanunta sunyi jajur hatta fuskarta tayi ja hankalinta a matsanancin tashe yake, Tun ranar da Khulthum ta fasa bowl saboda jin sallamar Musbahu ta diga question mark Akansu Baki daya, don hakan bazai taba faruwa ba se idan yarinyar cutarta yakeyi, hakan yasa ta rike Khulthum din na tsawon sati daya tana ta bugar cikinta ko zata samu tayi mata leaking wata maganar amma fur yarinyar taki haka dole ta bashi matarshi ta tura aka kira mata Kabir ta tsare shi akan se ya fada mata a ina Musbahu ya Nemo Khulthum saboda duk da tunanin hakan bai zo mata ba amma ta Fara tunanin ya akai Musbahu ya tsallake ya'yan masu kudi ya auro 'yar ghetto, Kabir Baki daya ya rasa dalilin da zai fada mata sede yace "Gwoggo ni na hadasu saboda naga yaki aure kuma se ya yadda" Kanta ta girgixa tace "Kabiru ban yadda daku ba Sam, tabbas akwai manufarku ta yin hakan, bana son wani ya fada min shi yasa nake Baku chance ka fadamin" Shiru yayi don shima Gay dinnan na Musbahu ya fara isarshi don Duk tunaninshi idan yayi aure especially yara masu budewar ido zai daina Amma abinda ya Lura kamar abin ya kara tsananta ne, shi kabir ba Gay bane amma Shi womanizer ne na gaske kuwa. Amma yasan babu uwar da zataji danta Yana aikata abinda Allah ya haramta saboda muninshi yasa aka kifar da al'umma guda aka bisu da ruwan duwatsu Daga jahannama..... Waiyazubillah!.... Kame kame ya fara hakan yasa gwoggo ta sallameshi tareda Fara binciken aka ran kanta, Tunda ta Fara binciken Abu daya ake fada mata Musbahu ba'a taba ganinshi da mace ba Sede Maza, kullum ka ganshi tareda Maza yake. Haka ta hakura ganin babu wani abu a ciki sede kawai Washegari Sega Khulthum tazo yini, gabaki daya ta kara lalacewa ta fita a hayyacinta wannan ya kara tada hankalin Gwoggo, da yazo daukarta ta dinga kuka kamar ranta zai fita hakan ya tabbatar mata da wani abin is definitely wrong some where. Bayan sati biyu ta aika aka kirawo wanda yake kula da part din Musbahu tana mishi tambaya Yana amsawa amsar Itace indai yana gida to Maza suna zuwa amma shi baisan me akeyi ba, Daga nan ta Kira me Kula da Khulthum itace ta fayyacewa Gwoggo dukkan abinda ta sani, Abinda Yafi daukar hankalin Gwoggon shi ne furucin da Matar tayi Khulthum tana masifar tsoron Musbahu sannan inhar zasu shiga daki to har ya fita tana ihu wannan constant ne. Da Wannan abu Gwoggo ta yanke hukuncin Zuwa kawai ta ganewa idanunta komai don zuciyarta ta Fara zargin Anya danta ba Gay bane? Hakan yasa bayan tayi sallar ishai ta shirya aka kawo ta gidan, ta jima a tsaye Tana tunanin inda zata Fara dosa part din Khulthum ko na Musbahu a karshe ta yanke hukuncin Zuwa na Musbahu, tundaga parlonsa komai neat yake dama tasan haka danta yake, dukka sauran kofofin a rufe suke kirif se kwaya daya wadda take hango haske daga ciki, Rana ta farko da taji Tana tantamar shiga inda danta yake Amma haka ta dake ta tura kofar a hankali, ta shiga bakinta na nanata ambaton Allah, da sauri ta dafe bango tareda jingina da shi sakamaakon jiri dake kokarin zubar da ita, idanunta ta runtse saboda abinda ta gani, as usual Musbahu ne da wani kwance tamkar mata da miji, kuka sosae gwoggo ta saki ganin they're so engrossed to the extent that they didn't even noticed her presence. A hankali ta danne Abinda take ji ta juya don fita amma ta fasa ta tako zuwa gadon jikinta se rawa yake ta saka hannunta ta dada mishi duka, firgigit ya juyo wata Irin hantsulowa Musbahun yayi ganin Gwoggo tsaye a kanshi idanunta hawaye na Mata sintiri, gaba daya ya durkushe a gurin cikin wani yanayi Wanda yaji tamkar an zuke mishi ruwan dake jikinshi ko hannunshi kasa dagowa yayi, Jan kafafu Gwoggon tayi ta fice jikinta se kyarma yake idanunta sun kasa dauke mata abinda ta gani, part din Khulthum ta nufa inda ta samu babu kowa itama a parlon nata, dakinta ta nufa tana turawa taji cikinta ya hautsina saboda azababben wari da ya doki nostrils dinta, da sauri ta maida kofar ta rufe jikinta a mugun mace, kamar ance ta juya ta hango inda aka Adanawa Khulthum turarruka da kuma Humra, gurin ta isa ta dan diga a hannunta sannan ta shafa a hancinta Amma dukda haka warin ya baci akan hakan dai ta samu ta Kara bude kofar ta shiga tamkar zatayi amai saboda mugun doyin da dakin yake, haka ta shiga tana daurewa idanunta sunyi jawur ta daina kukan amma kana kallonta zaka gane tsantsar tashin hankali akan fuskarta, Bata san hawaye sun kwace mata ba Seda ta ji salty taste a bakinta, Khulthum ce kwance tamkar mataciyya Baki daya gadon yayi kacakaca da Bayan gida (Kashi) gwoggo jiki na rawa ta isa gareta ta manta da wani wari ko kyankyami tsoronta daya kada ace yar mutane ta rasu a hannunsu itakam da ta shiga uku. "Khulthum! Khulthum!! Khulthum!!!" Gwoggo ta fada muryarta na wani Irin shaking tareda bubbuga gadon hakan yasa Khulthum bude idonta a hankali wanda ya shige ciki sosae tsabar wuya da kuma jinya, a hankali hawaye ya fara mata zarya a idanunta, Gwoggo na kuka ta riko hannunta tareda fadin "Me yake damunki, Tun Yaushe kike a haka? " Kasa magana Khulthum tayi se kuka da take wanda hawaye ne kawai ke bin fuskar Amma babu energy din Kara, Gwoggo baki daya ta rasa inda zata saka kanta, ta rasa abinda yake mata dadi ga ta rasa taemakon da zaayiwa Khulthum, a hankali ta sake kallon Khulthum wadda idanunta suke a lumshe banda ciwo, nadama, Dana sani da abubuwa barkatai babu Abinda Ke damunta. Gwoggo tasowa tayi ta Fara cire ma Khulthum kayan dake jikinta, ta lullubeta sannan ta yafa mata zani da ta dakko Daga wardrobe din, a hankali cikin hikima ta janye bedsheet din sede duk yadda taso Khulthum ta Mike Don yin wanka hakan ya gagara don lokacin Khulthum din idanunta nema suke su kafe hakan ya kara tada hankalin Gwoggo matuka ta dinga kuka Tana salati a ranta tsoro ne fal da tsananin takaici da bakin ciki, toilet ta shiga ta zubo ruwa a wani karamin bucket hade da soft towel ta dawo sede tana Fara goge mata jikin taga yadda bayanta Zuwa mazaunan ta sun mele sosae, gurin yayi jawur fatar duka babu, a tsorace Gwoggo ta goge ta sannan ta dakko mata doguwar riga wata me sauki ta saka mata. Fitowa tayi inda ta samu ma'aikatan part din suka taimaka mata ta fito da Khulthum, a mota aka saka ta Gwoggo jiki babu kwari tace da driver ya kaisu Asibitin Nassarawa, haka kuwa akai can aka admitting Khulthum wadda bata san waye a kanta ba, hakan yasa ana karbar ta aka dukufa don ceto rayuwarta. Fitowa Gwoggo tayi ta zauna ta Fara lalumar number Kabir cikin saa yayi picking ko gaisawa basuyi ba tace "Ina Asibitin Nassarawa kazo ka sameni yanzun nan" Bata jira me zaice ba ta katse kiran zuciyarta a kuntace, hannunta tasa ta rufe fuskarta tare da sakin kuka me ciwo, kuka na rashin sanin abinyi, kuka me Cikeda tashin hankali da tozarta, abin zai baka mamaki idan kaga yadda Lokaci daya Gwoggo tashin hankali ya zabgar da ita, she's a very strong person wanda kafin a samu abinda Ke sata waver babba ne amma Koda wasa bata taba kawowa halinda Musbahu ke ciki ba, Koda wasa bata taba tunanin haka danta yake ba. Tana a wannan halin medical team din suka fito inda anan ta tari Doctor Tana fadin "How's my daughter? Bata mutu ba ko? " Kanshi ya girgixa yace "Ki nutsu hajiya ki daina kukan nan haka, yarki tana nan Sede a iya binciken da mukai ya nuna mana ta samu Fecal Incontinence shi ne inability na mutum yayi controlling fitowar Bayan gida, muna tunanin hakan ya faru saboda Anal sex (Saduwa ta dubura) da ake ita Shiyasa makullin gurin ya zama weak take fitar da kashi wanda yasa ta samu Decubitus ulcer, amma Inshaaa Allah Zamu tackling abin" Wucewa yayi yayinda Gwoggo ta damke kanta Wanda yake barazanar tsagewa saboda yadda kwakwalwar kanta ta toshe, Anya Musbahu mutum ne ba dabba ba? Anya Musbahun da ta sani ne danta kamili me kawaici? Anya kuwa? Hawaye ya kara gangaro mata Bata taba tunanin hakan zai kasance ba, ta rasa uwa, uba, miji amma bata taba dandana Irin bakin cikin da take ciki yau, Bata taba dandana takaici da bakin ciki irin wannan ba, haka dai aka kawo mata prescription daidai nan Kabir ya iso hankalinshi a tashe saboda yadda yaji muryar Gwoggo tana shaking. Yana Zuwa ya tsugunna har kasa yana gaisheta amma bata ansa ba tace "Inason visa ni da Khulthum zuwa India jibi, ga wannan ka karbo" Ta fada Tana mika masa prescription, jikinshi a sanyaye ya karba ya Mike yayi hanyar pharmacy dukda Yana son tambayar Marar lafiyar amma babu fuska amma a jiki yaga sunan Khulthum Wanda ya tabbatar masa Itace marar lafiyar, haka yaje ya siyo ya dawo sannan ya fara processing visa din abinka da kudi masu gidan rana, tuni aka harhada komai hade da booking flight. Kabir na kammalla Aiken Gwoggo ya fara neman layin wayar TitαΦ sede har ta gama ringing sau kusan shida Musbahu baiyi picking ba baya ma tunanin akwai wayar da zai iya dauka, Tunda Gwoggonshi ta fita yake durkushe a gurin har partner din nashi ya fice shikam kwakwalwar kanshi Gaba daya ta kulle, ina yanayin da Kake ji Irin tamkar an zuke maka ruwan jiki to haka ta kasance ga Musbahu, babu inda a jikinshi baya rawa ga wani matsanancin nauyi da kirjinshi yayi, me yasa upon all the people on universe babu Wanda zai kamashi red handed se Gwoggon shi, hajiyarshi, mahaifiyarshi. For the first time Yaji wasu siraran hawaye na diga daga idanunshi, haka ya kifa kanshi a gurin yana wani Irin kuka me ciwo, nadama wadda Lokaci ya riga ya kure, it's late to cry when the head is cut off. Da kyar a daddafe ya zura jalabiyya ya fito parlour yana jin tsanar kanshi da halayenshi, yana jin Wacce riba yanzun ya samu da wanne idanu zai kalla baiwar Allah Gwoggo wadda ta sadaukar da rayuwarta akan tarbiyarshi, Rana ta farko da yaji ya tsani Abinda yake aikatawa, yaji inama bai kawo wannan lokacin ba, ya jima yana jin ringing wayarshi amma bazai iya dauka ba don mugun sarawa da kanshi keyi. Kusan Mintina arbain yana Zaune with a heavy heart sega Kabir ya shigo ko sallama babu amma duk hazarinshi ya katse ganin TitαΦ a mawuyacin hali wanda kusan shekarsu ashirin Amma bai taba ganinshi a haka ba ko da lokacinda Alhaji Habibu ya rasu. Gwiwa a sage ya isa gareshi tareda dafa kafadar shi yace "TitαΦ meye ke faruwa? Me ya sameka " Lumshe ido Musbahu yayi wanda yayi sanadin sake zubar wasu hot tears daga idanunshi, wannan kadai ya sake gigita Kabir don a iya sanin shi yasan cewar Musbahu Gay ne Wanda mace batada gurbi cikin zuciyarshi Balle har rashin lapiyar ta ya taba shi haka, yasan ko meye y faru has to do with Gwoggo don yanayin damuwar tasu iri daya ce hakan yasa ya daidaita zamansa yana tambayarshi ainihin abinda ya faru yasa ya koma haka. Musbahu ya gwada fada mishi kusan sau hudu amma se ya kasa shi kuwa Kabir damuwa ce fal zuciyarshi Daga karshe da kyar da sudin goshi aka samu yayi maganar, ya fayyacewa Kabir halinda Gwoggon ta sameshi a ciki, a wannan lokacin Kabir yafi Musbahu shiga rudu, ya rude ya gigice ya rasa abin da yake mishi dadi, haka suka zauna tamkar kurame tsabar kaduwa da tashin hankali. Bayan Kwana biyu babu Abinda ya Lafa , Khulthum tana cikin mawuyacin hali, balle gwoggo wadda ta koma kamar ba ita ba ta zabge ta lalace saboda yadda zuciya take cikin wani hali, bata fadawa Maman Khulthum halinda Khulthum ke ciki ba ta dai sanar da ita tafiyar gaggawa ta samesu zuwa India, haka Mama ta bisu da addu'a zuciyarta Cikeda tausayin diyarta, don tunda Khulthum take kuka Tana rokar kowa yafiya Mama tasan da matsala, ga rashin kyan gani da Khulthum din tayi Wanda shi daya ma nightmare yake bata, haka dai ta danne damuwarta. A India straight asibitin da Gwoggo ke Zuwa suka wuce, Gwoggo ta kawo ta badan ta raina treatment din Nigeria ba a'a se dan Tana son bawa zuciyarta da kwakwalwarta Hutu, kuma babu laifi an shirya samu ita kanta Khulthum ta Fara responding ma kulawar da ake bata, Shikuwa Musbahu baisan a wani yanayi ko Hali yake ciki ba, gaba daya ya lalace Lokaci guda, zuciyarshi ta gaza nutsuwa balle kwakwalwar kanshi ta samu ta huta ya koma kamar wani zarare, don tunda Gwoggon shi ta ganshi bai kuma taka kafarshi waje ba, gaba daya wayoyinshi ya kulle su ya hana kowa zuwa inda yake banda Kabir wanda ke tausar shi Yana bashi baki. A hankali kwanaki suka shude yayinda Al'amuran ke kara tabarbarewa Musbahu, Zuwa lokacin yaje gurin gwoggo yafi a irga amma babu wanda ya san inda ta tafi ko Kabir kin fada mishi yayi saboda warning din da Gwoggon tayi mishi, shikam Musbahu nemanta yake ta yanke mishi duk hukuncin da tayi niyya amma ya rasa ta hakan ya kara tabashi. Sannu a hankali Khulthum ta Fara warewa, cikin ikon Allah da taemakon gadgets din da akayi amfani sphincter dinta ta dawo aiki Sede kowa yasan ba'a bari a kwashe daidai amma babu laifi lafiya ta samu!!! Shatuuu ♥️ [9/13, 9:11 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 58 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *This page is entirely, wholly dedicated to my ghost readers, those who read and go without voting or commenting, shatuuu ♥️ still appreciate and she loves Evey single one of you* _Oh yeah... It was revealed in the Qur'an that every soul must surely taste the bitterness of death..... Allah baya barin wani don wani yaji dadi, this is life nothing is permanent, everyone of us is waiting for his time..... Kui hakuri nasan kunnuwana se sun gaji da jin complains, don't mind me... I love you_ A hankali ta Mike ta nufi toilet din dake cikin dakin da suke, Babu laifi jiki yayi kwari sosae sede dukda haka ba'a sallame su ba don ana mata sphincter training hade da treating wasu infections din da suka samu matsugunni a cikin jikinta. Alwala tayi ta fito inda carpet din sallah yake a shimfide, hijab ta zura tareda kai dubanta gefen da Gwoggo take takure, gabaki daya Matar ta rame tayi xuruxuru kana kallonta kasan akwai abu me girma dake hanata sukuni a zuciya, Tunda suka zo kasar Abu biyu take banda ibada da tarairayar Khulthum babu Abinda take, hakan yasa Khulthum din hankalinta ya kwanta kafin wani Lokaci ta Fara maida jikinta tana murmurewa gashi babu inda take zuwa banda ta sakko daga gado taci abinci Se sallah ko wanka kafin wani Lokaci me tsawo AC tayi aikinta, skin din Nata ya zama flawless tayi shar se daukar idanu take. Abu daya ne cikin zuciyarta damuwar past dinta Wanda suke hunting dinta babu dare babu Rana har ta kan zauna Tasha kuka kamar ranta zai fita, ko sau daya bata ga laifin Musbahu ba, bata kuma ji haushin Abinda yake mata ba saboda whatever life be ita ce ta saka kudinta ta siya, ita ta kai kanta har gidan Musbahu ta kuma dauki kafafunta ta kai dakinshi, inda hakane meye laifin Musbahu wanda Allah ya aiko shi don tayi realising mistakes dinta through him? Ita kanta a rayuwarta tasan she deserves abinda Yafi haka, tasan ta wulakanta mutane ta ketare iyakar da Allah ya gindaya mata to ta yaya zata ga daidai? A bangaren TitαΦ kam abin ya wuce gaban magana, Tunda suka hada idanu da gwoggo ta zare nutsuwa, farin ciki da dukkan komai ta wuce dashi. Gaba daya ya koma tamkar mahaukaci ya lalace ya daina fita ko ina sede gida se kuma massallaci, hakan ya tada hankalin Kabir sosae don dama Irin su Musbahu basu iya tashin hankali ba Tunda ba magana suke ba Balle su fadi wani abun suji sanyi a zuciyarsu, Wata ranar alhamis Anty daddafe ya samu ya isa office saboda korafi da yake samu daga gurin board members dinshi akan shafe wata daya da yayi baya Zuwa office kuma bai nada kowa ba hakan yasa babu yadda ya iya ya koma, sede kallo daya zakai masa kasan Maza suna wani hali. Ya dade rikeda Biro hannunshi ga tarin papers cikin files da suke jiran signature dinsa amma ya gagara nutsuwa ya karanta content din ciki Balle har ya saka hannu. Tamkar wanda aka tsikara haka ya Mike ya dauki key din motarshi bai ko amsa maganar da secretary dinsa ke mishi ba ya biyo lift Cikeda hanzari ya wuce zuwa motarshi ya tayar tareda buga wani uban horn take securities din dake gurin suka Mike afijajan, Allah kadai ya tsare zuwan shi gida, ko gate bai shiga ba ya yi wani mugun parking sannan ya fito ya shigo cikin compound din a hargitse wanda yasa securities din dake gurin maida dukkan Hankalinsu kanshi sede ko kallon inda suke ya durfafi part din Khulthum, da kafarshi ya hankada main kofar dake ba a rufe take ba yasa ta budi Sede wani Irin yanayi na sanyin jiki ne ya mishi rubdugu Lokaci daya saboda yadda parlon yayi kura alamar babu mutane a gurin, wannan sassanyan kamshin da se yau yake jin ina zai sake jin irinshi, jiki a sanyaye ya nufi dakinta Sede wayam ya gani babu kowa a ciki, kaya ya hango a tukunkune akan gado hakan yasa ya isa gurin tareda saka hannunshi ya bude amma wani wari ne ya dake shi hakan yasa ya ja da baya yana kallon yadda kashi ya bata mishi hannunshi, runtse idonshi yayi da karfi don yasan Khulthum ta samu wannan matsalar ta dalilinshi ne, don ana ya gobe zasu hade da gwoggo ya iske ta a dakin kwance a wannan halin hakan yasa yayi ficewrshi, yanzun ma tunawa yayi bafa Gwoggo kadai ya zalinta ba hatta Khulthum ya zalinta kuma idan bata yafe ba bazai taba samun kwanciyar hankali ba. Wasawasa Musbahu haka ya koma kamar wanda ya zare kwatakwata nutsuwa babu ita a rayuwarshi hakan yasa Kabir yanke shawarar fada mishi inda Gwoggo take ko Za'a samu ya daidaita saboda ba karamar asara ake tafkawa a oil, flour da food company din saboda rashin shi. Wannan yasa Kabir kammala mishi komai ya rakashi airport yana tsaye har jirgin ya daga sede a wannan lokacin Musbahu yaji Anya Yana son ganin Gwoggo? Wani hukunci zata yanke mishi. Misalin bakwai na safe a agogon dake kasar ta India, an kammala bawa Khulthum maganinta na safe hakan yasa ta shiga tayi wanka sannan ta fito jikinta daure da towel wanda ko gwiwa bai Kai ba, Gwoggo ta fita karbo wani sako hakan yasa Ita daya kawai ta rage a dakin, a hankali taji an turo kofar an shigo amma ba'ayi sallama ba amma kamshin turaren da ko a kabari taji shi zata gane maishi, kafin wani Lokaci jikinta ya fara rawa tamkar mazari ko wadda ake kada mata wani abu haka ta jiyo amma se me shi dinne! Musbahu ne tsaye helplessly, idanunshi sunyi jawur ga wata uwar kasumbar da ya Tara ta cika Fuskarshi tamkar wani Tsoho haka ya koma, a hankali ta dinga ja da baya tana girgiza mishi kanta yayinda shima yake takowa cikin nutsuwar da ya rasa Yaushe ta dawo jikinshi, wani kuka ta saki jin ta kai karshen bango, runtse idonta tayi jin ya riko hannunta cikin nashi tamkar Marar lapiya ya bude bakinshi karo na farka ya kira sunanta wanda yasa ta bude idonta da sauri suka sauka cikin nashi kwayar idanun, Khulthum ta sha hada idanu eye ball into eyeball amma se ta tsinci kanta cikin wani yanayi me wuyar fassarawa ta manta rabon taji Irin wannan tun akan Ashir, a hankali ta lumshe idonta saboda kallon is so intense ga effect dinsa sosae yake ratsa jikinta. Shi dinma hakan ce ta kasance bai taba tsayawa da mace so close haka ba, bai taba kallon mace cikin idanu ba, Ashe haka abin yake, is this how it feels se yaji tamkar zuciyarshi na budewa ne yaji wani bakon yanayi me nauyin gaske yana shigarshi and that's *LOVE* Hannunta na cikin nashi yace "Ban canci second glance daga gareki ba, I know I was bad I was never good amma dukda haka ina Baki hakuri ki yafe min, kilan Allah ya sassauta min laifukan da nayi mishi" Kuka sosae Khulthum take lokacin ta zura wata bakar abaya wanda tun zuwanta ire iren su take sawa kawai a jikinta, hannunta tasa ta kara rufe fuskarta zuciyarta wani Irin sanyi take ji, tasan ko babu komai Allah ya yafe mata Tunda har ya kaddaro shiryuwar Musbahu to ta yaya zatace bata yafe mishi ba, Bayan itama wasu sunyi overlooking kurakuranta sun yafe mata kuma jikinta yana Bata Allah ya gafarta mata sannan Hajiya Shatuuu ta yafe mata hakan yasa ta sauke hannunta tareda kallon inda yake Zaune ya tsira mata idanu tace "Allah ya gafarta mana duka,.... " Bai barta ta kammalla statement dinta ba ya iso inda take ya rungume ta so close, so tight and so romantic. For the first time Musbahu yaji sanyi a zuciyarshi yaji wani abu ya darsu cikin zuciyar shi. A wannan halin Gwoggon shi ta shigo bakinta dauke da sallama sede bata iya karasawa ba ganin Musbahu shima a rikice ya Mike se kuma ya sunkuyar da kanshi saboda wata kunya da ta lullubeshi, Khulthum kwatakwata Bata san Abinda Ke faruwa ba, amma kallonsu da tayi tasan they need privacy hakan yasa ta dauki siririn mayafi ta yane kanta dashi ta fice tareda janyo musu kofar ta samu wani guri ta zauna Tana jin tamkar tayi completing wani mission ne. A cikin daki kuwa dukkansu shiru sukai kowanne Ya kasa magana se Musbahu ne ya isa inda Gwoggon Ke zaune ya Dukar da kanshi tareda dira gwiwarshi a kasa yace "Gwoggo ki dake ni, Kiyi min fada amma your silence is killing me... Nasan kwatakwata banyi daidai ba, nasan Allah ya hana amma nakeyi, na cutar musu yarsu banida wani uzuri gwoggo Dan Allah ki yanke min hukunci" Gwoggo ita ta haifi Musbahu amma ta manta lokacin da taga yana kuka hakan yasa ta janyo kanshi ta Dora a cinyarta Hakan ya tsananta kukan da yake itama ta Nayi a haka suka shafe lokuta kafin Gwoggo tace "Na yafe maka, kayi Istighfar ka nemi yafiyar Khulthum, ka rike sallah Tana Hana alfasha sannna kayi Tuba sahihan kada ka komawa laifinka ka gyara tsakaninka da matarka, ka dage da ibada Allah zai lamuranmu sannan ka manta na ganka ka dauka hakan bai faru ba, let's move on" Wata nannauyar ajiyar zuciya Musbahu ya sauke hawaye na Kara mishi sintiri, is the thing he never expect, dukkan tunaninshi ya tafi a wahalar da zaisha kafin Gwoggon ta saurareshi Amma Allahu Akbar gashi ta karbeshi ta yafe mishi. Kwanaki biyu suka Kara aka sallami Khulthum suka wuce saudiyya Don yin umara, Khulthum da Musbahu dukkansu masu laifi ne hakan yasa suka dage da addu'a ibada don har gwoggo na musu fada akan rashin hutawa da suke sede akwai wata shakuwa a hankali da ta Fara samun matsugunni cikin zuciyar kowannensu, a hankali suka Fara damuwa da Al'amuran juna wanda gwoggo ke Lura dasu a haka sukayiwa Nigeria tsinke. Hannunshi dake jike da ruwan da yayi Alwala yasa ya shafa fuskar subay'a wadda Ke baccinta hani'an, a hankali ta gyara kwanciyarta hakan yasa ya dan bubbuga pilon da take kwance se ta bude idonta Wanda bacci ne fal cikinsu ta kalleshi, shima kallonta yayi yace "Babe time for prayers! " Kwabe fuskarta tayi kamar zatayi kuka saboda yadda bacci yake dadi kuma tasan nacin Junaid dole Se ta tashi haka ta mike ganin ta tashi yasa ya fice abinshi, yana zuwa yayi raka'atanul fajr sannan aka shiga sallah Yana idarwa kamar yadda ya saba idan Subay'a keda girki to ana Idar da sallah zai wuce gidan Sulaim, haka idan Sulaim dince Keda girki haka zaije gidan Subay'a hakan ba karamin kwantar musu da hankali yake ba don sosae yake kwatanta adalci don idan Yana tareda Sulaim tana jin tamkar ita kadai ce a duniyarshi haka idan Subay'a ce Wannan yasa kowaccensu take Zaune lafiya. Sulaim na cikin daki ta Idar da sallah gabanta bowl ne Cikeda custard wanda Seda ta dama tukun ta tada sallah tsabar yadda yawunta Ke tsinkewa ko addu'a batayi ba ta janyo bowl din ta Fara sha babu kakautawa, turarenshi ne ya fara isar mata da sakon zuwanshi dake idan yazo key dinshi yake sawa kawai ya bude ya shigo. Kallonta ya tsaya yi baki bude ganin yadda ta zage tsakaninta da Allah, shigowa yayi ya karba spoon din hannunta yace "Wai Dove meye sirrin custard ne? Ke yanzun da asuba ma sha kike" Bakinta ta turo mishi tace "Shiyasa nake sauri Karka shigo ka sameni, Barka da Asuba Heartthrob" Zama yayi a gabanta tareda debo custard din ya kai mata bakinta sannan yace "I'm fine baby sede missing din wannan shagwabar" Rufe fuskarta tayi tana murmushi tace "Kai Yaya na" Bai bata amsa ba sakamaakon ringing din da wayarshi dake cikin Aljihun jallabiyar jikinshi ta Fara ringing ya ciro, haka kurum yaji gabanshi yayi mugun faduwa Amma haka yayi picking "Mami barka da asuba" Jin an ambaci sunan Mami yasa ta dago da sauri ta Kalli Junaid lokaci guda taga yanayinshi gaba daya ya canja damuwa kwance saman fuskarsa, ga kuma saurin mikewa da yayi Sannan ya fara ambaton "Innalillahi wa Inna ilahil rajiun!!! Ya hayyu ya kayyum" Cire wayar yayi Daga kunnenshi Cikeda tashin hankali yake kallon Sulaim wadda itama take kallonshi gabanta se faduwa yake, hannunta ya Kama Yana jin yadda harshenshi yayi nauyin abinda zai fada mata, haka kurum taji gabanta yayi mugun faduwa cikinta yayi wani Irin hautsinawa, a hankali kamar me rada tace "Yaya waye.....? " Se hawaye Sharrrrrrr ya fara zubar mata daga idanunta tsabar tsoron me zai fada, matsota yayi Zuwa jikinshi ya rungume hakan yasa ta kara fashewa da kuka, shima jiki a sanyaye yace "Kiyi hakuri Allah yayiwa Imratun Ja'afar rasuwa! " Kallonshi ta tsaya yi kamar wata doluwa saboda son comprehending abinda ya fada take, rungumeta yayi Tsam a jikinshi saboda yasan she's in shock ko ba'a fada ba, hakanan dai tayi shiru har ya kira Subay'a yace ta shirya yanzun zaizo su wuce kaduna don acan ta rasu Amma ga mamakinshi se cewa tayi "Allah ya jikanta amma kui gaba na taho inda uzurirrika" Baice mata komai ba ya kashe wayar tare da rike Sulaim ya zaunar da ita akan gado shi kuma ya nufi wardrobe dinta ya janyo trolley ya zuba musu kaya zuciyarshi a cunkushe tareda tunanin halin da Jabir yake ciki. Tunda Khulthum ta zauna Bata kuma magana ba har driver din da zai kaisu yazo, haka ya janyo hannunta suka shiga mota inda ta kwantar da kanta kan kafadarshi tareda runtse idonta, babu Abinda take iya ji se wani azababben Ciwon Mara dake damunta a Wannan lokacin idanunta ta runtse tareda matse hannun Junaid. Ita batayi kuka ba ba kuma tayi magana ba ta kuma kasa tantance Abinda take ji banda Ciwon mara. A haka suka isa Kaduna babu Wanda yake magana har suka isa gidan inda tuni Imratu ta dade a makwancinta, saboda yadda gidan yake a cike haka babu yadda Junaid zaiyi ya bar Sulaim ta shiga ita daya, idanunta sunyi ja saboda azaba da kuma tashin hnkli, a parlor kasa ta tarar da mutane dankam inda ta hango Mami wadda kallo daya zai fada maka tashin hankalin da take ciki ga idanunta sunyi luhuluhu tsabar kukan da Tasha, cikin nitsuwa ta taka har gaban Mami sede kafin tayi magana wata mata dake kusa da Mamin tace "Meye wannan yake bin jikinki? " Da sauri Mami ta dubi Sulaim din, jini ne ya bata mata zaninta hakan yasa Mami janyota jikinta amma kafin wani Lokaci jini ya Balle mata ga azababben Ciwon mara kamar zata mutu, tuni hankalin kowa ya kara tashi, Mami ta rasa yadda zatai se kuka se Maman su Yaya Hanan ce ta kira Junaid a waya aikuwa se gashi shida Ja'afar hankali a tashe akai Asibiti da ita amma cikin dake jikinta na watanni uku ya fice Wanda babu Wanda ya san da zamanshi. Gashi ta zubar da jini sosae wanda dole Se an kara mata! Shatuuu ♥️ [9/12, 10:38 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 59 ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *Halo people of Wattpad Wallahi page din naku ne, you guys are Muah.... I can't stop loving you exactly like the way I can't stop thanking you for always supporting me and gingering me Up!* Mami na Zaune gefen gadon da Sulaim ke zaune ta hada kanta da gwiwarta tana kuka kamar ranta zai fita, yau Kwananta hudu a asibitin an samu anyi mata wankin ciki sannan Tasha jini Leda uku, yanxun ta dawo hayyacinta sosae don haka ita yanzun take kukan mutuwar Imratu, kuka sosae take Tun Mami na lallashinta har ta share ta itama tana matsar kwallar saboda yadda take tuna wacece Imratu a rayuwarta, tasan bata haifi mace ba amma Sulaim da Imratu sun mantar da ita wannan rashin da tayi. Babyn dake kwance cikin peach Cot ta Fara kuka alamar ta farka, da sauri Mami ta cirota Daga Cot din ta Fara jijjigata har yarinyar tayi shiru, tsaida kukan Sulaim tayi ta miko hannunta babu musu Mami ta mika mata babyn, karbar ta tayi ta rungume a jikinta wani Irin son babyn na ratsa zuciyarta rayuwa kenan duk yadda ake dokin cikin Imratu ashe ajali ne don ita kanta batasan abinda ta Haifa ba tasan ta haihu Daga nan jikinta ya rikice duk wani taemakon da ya dace an bata amma Allah yayi lokaci yayi haka ta rasu ana kallo. Jabir kowa yasan yadda yake son Imratu babu Wanda yafi shi shiga tashin hankali haka ya rungume Mami Yana kuka kamar karamin yaro tamkar ba soja ba. Sede muce Allah yasa ta huta! Mami da ta gama hada mata Madarar da akai musu prescribing ta mikowa Sulaim wadda ta Fara bata tana jin tausayin yarinyar a zuciyarta, tasan me ake kiran maraici tasan zafinshi dukda babu Abinda ta rasa amma iyaye daban suke ko me ka samu a rayuwa kuma ko mai ka zama dole iyaye daban suke amma tasan wannan ba zata rasa gata ba, bazata taba maraici ba kamar yadda itama ba tayi ba tasan wannan family bazasu barta haka ba, ita kanta she's covered with love, tasan Abinda suke mata ko Daddy da Mummy na raye ba Lallae suyi mata hakan ba. "Sulaim ba zaki daina kuka ba, Imratu ta tafi addu'a kawai take bukata amma wannan kukan naki yayi yawa, Kema kinga yadda kike bazai helping condition dinki ba" Haka ta tsinkayi muryar Mami a kanta, hakan yasa ta goge hawayen fuskarta tareda daura babyn akan kafadar ta don tayi gyatsa sannan tace "Mami tausayin Baby nake ji, zata tashi batada uwa" Karo na farko tun bayan rasuwar Imratu da Mami tayi murmushi tareda kama hannunta tace "Kina nan zatayi rashin uwa? Nasan idan kina raye ba zata taba kukan maraici ba, inason ki rungume ta ki zame mata uwa kinji Auta ta? " Da sauri Sulaim ta gyada kanta tare da kara kankame babyn daidai shigowar Baba da dukkan yaranshi. Idanunta cikin na Junaid wanda ya dan fada Balle kuma Baban baby idanunshi sunyi jawur ya rame sosae se ido da karan hanci. Kana kallonshi dole tausayinshi ya kama ka saboda yana cikin mawuyacin hali wanda shi kadai yasan yadda yake axabtuwa da rashin Imratu. Dukkansu kan carpet din da Mami ta shimfida suka zazzauna, seda suka gaggaisa aka Kara jajantawa juna rashin Imratu da barin da Sulaim tayi kafin Baba yace "Jabir bansan pain din mutuwar mata ba, amma nasan pain din rasa 'ya Dan a gidan aure kaine sirikina Imratu ce 'yata don haka dole a bawa kowa hakuri don munyi babban rashi, Allah ya jikanta ya bamu hakurin juriya, ya kyautata namu zuwan, Allah ya Raya mana babyn" Baki daya suka amsa da Amin hawaye na bin kuncin Jabir wanda baisan har Yaushe ne zai fita daga kuncin rashin matarshi ba, yayinda Sulaim ke kuka sosae tana rikeda babyn wadda Ke baccinta hankali kwance. "Babban yaya a kullum bana son nida Maminku mu zama mun saka idanu akan rayuwar gidanka amma halayen uwargidan ka Yana bani mamaki, kasan bata zo tayi mana ta'aziyya ba balle ta duba abokiyar zamanta dake jinya, Anya kuwa muna kan hanyar daidai? " Maganar Baba tasa Junaid sunkuyar da kanshi kasa saboda azababben kunya da ta lullube shi baisan har wani Lokaci ne Subay'a zata shiryu ba don dazun da ya kirata ce mishi tayi Hajiya zata koma gidan Alhajinsu shi ne suke shirye shiryen tarewar he couldn't say a word Don takaici amma yanzun zuciyarshi ta Fara wasiwasin Anya zai iya jurewa halayen Subay'a da da yanzun akwai banbanci matuka. "Baba........" Katse shi Baba yayi da fadin "Tuni nake maka akan gyaran gidanka to me ba dole Se tazo ba dubanta sunzo, Jabir wannan baiwar Allah wani hukunci ka yanke a kanta, she needs a mother" Hawayen dake bin kuncinshi ya goge, Junaid ya dafa kafadarshi don ya samu karfin gwiwa hakan kuwa ya karfafa mishi gwiwa yace "Munyi magana da Babanta yace na barta anan gurinmu Tunda shi baisan waye zai kula da ita ba, kayi mata huduba da Nafisa Sunan Mami haka Imratu tace sannan na Mika ta gaba daya hannun Sulaim ita ce uwarta! " Idan nace kowa yaji dadin hukuncin Jabir understatement kenan, sosae Sulaim ta Kara kuka yayinda Junaid ke tayi mishi godiya, haka familyn nan suka yini Cikeda farin ciki da kuma alhini da yamma aka sallamesu suka koma gida nan Jabir ya tattaro komai na Nafisa Su'ad ya kawowa Sulaim inda ta dauki shawarwarin Nurses din don kula da yarinyar. Washegarin Ranar sadakar bakwai ranar gidan ya koma daidai kowa ya koma bakin aikinshi har shi Jabir din wanda aka mishi transfer ya koma Kano hakan yasa yaji dadi don Yana tunanin komawa Delta ya rayu babu Imratu, Junaid da Sulaim Harda Subay'a wadda tazo ranar sadakar bakwai suka juya kano, babu alamar rashin jin dadin Abinda tayi don gani take ai babu dole ace se ta zo Tun ranar da akai rasuwar, Junaid kam baice mata komai ba se kallonta da yake Yana tunanin yadda zaiyi da ita. Sulaim suka Fara saukewa wadda ta gaji sosae, Tana zuwa ta Kwantar da Su'ad yarinyar me hakuri Sede tasa yatsanta cikin baki tana tsotsa, seda tayi wanka sannan tazo tayi mata ta goya ta ta Fara gyaran gidan, tana kammalawa ta janyo kayan Su'ad ta shirya cikin abin kayanta wanda shima lokacin ta hada, wayarta ta bude nan text na gaisuwa da tambayar lafiya ba tazo makaranta ba Daga gurinsu khairi, zama tayi ta dinga bi tana replying har tazo kan Aimana anan ta kirata tana fada mata Abinda ya faru sosae Aimana mutuwar Imratu ta dake ta don sunyi sabo sosae lokacin bikin Sulaim din. Hakan yasa mutuwar ta bigeta sosae, suna kashewa ta kira Mami ta sanar mata ta iso nan ta Kara mata nasiha sosae sannan sukai sallama. Junaid na isa gida kowannensu ya wuce dakinshi don yin wanka, zuciyarshi Sam babu dadi a yanzun kam dole ya aiwatar da abinda ke ranshi, fitowa yayi ya shirya cikin kanan kaya sannan ya fito parlour, Subay'a na fitowa ta shirya cikin bakin high waist skirt ta daura farar top akan blue din skirt din, kanta ta daura blue din scarf wanda ya kayatar da ita tayi kyau sosae kamar matashiyar budurwa, ga kamshi dake tashi Daga jikinta me sanyaya zuciya da nutsuwa. Tana fitowa Atika na kokarin jera abinci a dining gaisheta tayi cike da girmamawa tareda Yi mata gaisuwa don ita kanta rasuwar ta bige ta ba kadan ba, samasama ta amsa daidai shigowar su Muhammad wanda ta kaisu gidan Suhaila, hannunta tasa a bakinta alamun suyi shiru sannan ta bisu daidai ta manna musu peck a goshi tace "Welcome home boys din Mimi? Ina Amma (Suhaila)" A tare suka Fara bata labarin Kwana Dayan da sukai gidan Suhaila gaba daya ta tattara hankalinta Zuwa kansu tana ta murmushi a wannan lokacin taji wayar ta ta Fara ringing tana dagowa taga My Everything tasan nemanta yake amma a haka tayi picking tace "Na'am " "Ina jiranki a bedroom dina yanzun" Bai jira amsarta ba yayi hanging wayar, tsaki tayi ta cigaba da sauraron 'ya'yanta, shikam Yana daki Ya zubawa kofar shigowa ido yaga ta inda zata shigo amma shiru har ya dauki waya zai sake kira se ya fasa ya janyo wayarshi ya fara surfing internet a haka har ya gama amma babu ko keyar Subay'a, me son kuka se aka jefashi da kashin awaki inaga Ya samu dalilin kukan, haka zuciyarshi ta Kara baci se huci kawai yake amma Junaid been Junaid a lokacin yayi calming kanshi se gashi ta shigo fuskarta a hade ita a dole batasan raini, zama tayi gefen kafafunshi tace "Muna tareda su Muhammad Shiyasa ban zo ba" Kallonta yayi a tsanake wanda har Seda ta zama uncomfortable sannan ya daga pillow din da yake kwance akai ya zaro wata farar takarda ya mika mata, Lokaci daya jikin Subay'a ya fara karkawa ta kasa dago hannun balle ta karba, kallonta yayi yace "Ki karba mana!" Ya fada Yana buga mata tsawa, hannunta, bakinta Kai ilahirin jikinta rawa yake tsabar yadda ta tsorata take cikin tsoro, wata tsawa ya daka mata batasan lokacinda tasa hannu ta karba paper ba Sede tuni hawaye ya wanke mata fuska ta kasa bude paper shikam yadda ranshi yake a matukar bace ce mata yayi "You can't read right? Lemme help you " Ya karba takardar ya bude tareda kafe ta da idanu kamar yadda take kallonshi cikin wani yanayi Wanda bai taba ganin Irinshi ba, he's sure da idanu na iya yin magana to tabbas nata zasuyi, all he saw was ban hakuri, roko da Dana sani amma a wannan lokacin bazasu taba tasiri cikin zuciyarshi a wannan lokacin sede next time *NI MUHAMMAD JUNAID LUKMAN na saki Matata SUBAY'A YUNUS saki biyu bisa wasu dalilai* Tamkar jini ya daina gudu a jikinta haka taji, take fuskarta tayi wani Irin Fari ,Mika mata takardar yayi tareda mikewa Don bar mata dakin saboda wani kuka da ta saki Don wannan shi ne last thing da ta taba tunanin Junaid zaiyi mata, da sauri ta sakko kasa tareda rike kafafunshi tace "Papa na tuba nabi Allah na bika, Kada kayi min haka, kada ka wulakanta soyayyar mu, nasan I was never good amma give me another chance" Baiso yin magana ba amma dole yayi saboda yaga she needs clarification akan abin "Da Nayi hakuri lokacin ke daya ce amma yanzun bazan iya ba, ke idan banda butulu irinki har Imratu zata rasu kiki Zuwa gaisuwa ai ko banda ni taci albarkacin 'ya'yanki da ta rike miki, sannan har yanzun baki san me ake nufi da aure ba har yanxu Bakiyi hanakali ba, kije me tsautsayi ya dauka! " Kuka sosae Subay'a take amma ko kallon inda take baiyi ba yayi wucewarshi Zuwa Dakinsu Ahmad inda ya tarar dasu suna cin pringles suna tsomawa cikin mayonnaise wadda aka hada da Venigar, suna ganinshi suka rungumeahi, shafa kansu yayi sannan ya zauna kan Mini cushion din dake aje a dakin yace "Waye zaije gurin Ammiey" In chorus sukace "Ni! " Kanshi ya gyada yace "Kowa zaije" Mikewa yayi ya hada musu kayan da ya zama basic yasa a katuwar trolley sannan yace suje su jirashi a mota, dakinshi ya koma har lokancin tana durkushe inda ya barta ko kallonta baiyi ba ya shige dressing room dinshi ya hado kayan da zai bukata ya fito lokacin hawaye kawai take don tasan ta makara lallai Junaid ya shammace ta don Bata taba kawowa zai iya rabuwa da ita ba se gashi ya bata unexpected blow! Tana kallo ya fice ya barta a gurin ganin haka yasa taji karfi yazo mata ta fito a daki ta nufi nata, ta tsaya tsakiyar dakin tana tunano Irin halin da ta shiga wancan komawarta gidan amma me yasa tayi repeating same mistakes gashi ta kare a babu, sosae ta shiga kuka babu kakautawa haka ta shirya kayanta ta fito bayan ta daura Abaya saman kayan sede har lokancin kuka take sannan tayi clutching takardar sakin Tana jin yadda zuciyarta Ke zafi da radadi anma Lokaci ya kure. Hajiya na Zaune Kan sofa gefenta Fannah ce wadda tazo Hutu, kanta babu dankwali Tana ta bawa Hajiya labari suka ji shigowar Subay'a, seda gaban hajiya ya fadi saboda ko ba'a fada ba tasan aure ya Kare, Fannah daki ta wuce ranta babu dadi, Hajiya ta ruko Subay'a wadda ta sake wani kukan tace "Hajiya ya sakeni, na kashe auren na cuci kaina, na shiga uku! " Wani wawan mari taji da Bayan hannu Wanda yasa ta gigice hatta Hajiya batasan Alhaji ya shigo ba se saukar Marin ne ya sanar mata da zuwanshi, "Se kizo mu zauna Tunda haka kika zaba jaka Marar hankali, kuma Wallahi Keda farin ciki har abada " Alhaji ya fada sannan ya fara kiran sauran yaranshi akan a Daren yau suje su kwashe kayanta kada su bar komai, hajiya ta dinga rokonshi akan ya bari a sasanta wani mugun kallo yayi mata yace "Kin cuci Rayuwar yaranki haka zasui ta fitowa daya bayan daya, kuma Wallahi Subay'a se kinyi dana sanin kashe aurenki se na nuna miki ni ne ubanki! " Kuka sosae take haka ya fice kuma kamar yadda ya fada haka aka kwaso kayanta kowannensu mamaki yake don sunyi tunanin a cikinsu babu Wanda zai kuma wannan saken se gashi Subay'a tayi. Sulma da tazo kasa magana tayi jin Abinda ya faru tace "Dama nasan hankalinki bazai taba kwanciya ba har se kin kashe auren, congratulations Sister kinyi kokari you've succeeded se ki jira hukuncin Alhaji" Sosae Subay'a Tun ba a je ko ina ba ta fara nadama wadda Lokaci ya riga ya wuce! Sulaim na kitchen ta kammalla hada miyar kifi se farar shinkafa da ta dafa, gefe ta hada salad sannan ta samu guri a kitchen din ta kunce su'ad Daga bayanta ta Fara bata Madarar dake cikin feeding bottle din, Seda ta koshi kafin ta sabo ta a kafada ta shiga daki inda ta gyara kanta sosae kamar tasan mijinta na hanya, pencil skirt tasa Wanda ya wuce gwiwa amma bai Kai idon sawunta ba baki me wasu glitters da suke ta haskawa, tasa top gold wanda kamata kadan sannan ta bude wani dan kit ta ciro chain na gold da dan karamin pendant ta daura a wayanta tasa dan kunnenshi tareda shafa maroon paint lip, kafin wani Lokaci tayi kyau kamar Mamie water.... Beautiful Oyinye. Bakar ribbon tasa ta hade kanta in a Bun sannan tasa hula baka da golden ribbon a gaban, turarruka masu sanyi tasa ta dakko karamin Cot din Su'ad ta kaita parlo ta kwantar sannan ta dakko system dinta ta Fara karatu wasu slides da Aimana ta turo mata na lecture din da tayi missing. Sallamarsu Muhammad yasa ta aje System din gefenta tareda nufarsu ta rungumesu tana jin yadda tayi kewarsu har cikin zuciyar ta, ganin zasu fara ihu yasa tace "Kui shiru kuzo Ku gani" Gabaki daya sukai tsit suka biyo bayanta har inda Cot din Su'ad yake tace "Ga kanwarku nan " Gaba daya suka tsira mata idanu suka Fara murna hakan yasa ta Fara motsi Sulaim ta matsar dasu don kada su tashi, tana dagowa ta hangeshi yana tsaye ya harde hannayensa Kan kirjinsa ya zuba mata ido, murmushi tayi tareda yi mishi wink, kanshi ya kawar ya bude mata hannayenshi alamar ta rungumeshi, kanta ta girgixa Tana zumbura Baki, shigowa yayi ya Daga ta sama hakan yasa ta kankameshi tana dariya Wanda ya kwantar mishi da hankali tareda saukar masa da nutsuwa, juyawa tayi taga Ashe yaran sun shige ciki, tare suka ci abinci yana ta zolayarta da tsokana tana dariya, dake bai shigo da kayan ba yasa bata kawo komai a ranta ba tayi tunanin yaran ya kawo mata Tunda sun jima basu hadu ba, amma ga mamakinta har dare bai ko Yi alamun tafiya ba, wanka tayi ta gyara su'ad tasa Nighties dinta ta kwantar da ita sannan ta fito Yana zaune Yana kallon news ta zauna gefenshi tareda fadin "Zamu kulle gida fa!" Juyowa yayi yace "Kora kuma Dove, anan zamu Kwana ga yaranki sun Fara bacci" Idanu ta tsura mishi kamar tana son karanto wani abu tace "Be serious Heartthrob bacci nake ji" Dariya ya danyi tareda gyara zamanshi yace "I'm sorry Amma ina sake neman alfarma akan ki rike su Muhammad a gurinki har Zuwa lokacinda ni bansani ba, nasan Kinyi kankanta da wannan burden din amma inason ki daure Kimin wannan taemakon" Kanta ta girgixa tace "I can't gaskiya su koma gurin Miminsu " Idonshi ya zaro Don wannan ne Karo na farko da Sulaim tayi mishi musu hakan yasa yace "Dove ni ne fa" Kanta ta gyada tace "Me yasa zaka yanke hukunci kana cikin fushi, why will you do that, nace maka kayi hakuri ka zauna da ita ko albarkacin ya'yanta amma ka nuna min banda mukamin baka shawara, then babu Wanda zan rike I'm sorry!" Shiru yayi saboda tsabar mamakin furucin Sulaim akan bazata riskesu ba, Daga karshe tashi tayi ta wuce dakinta bawai don komai ta fadi hakan ba sedan tana son su Muhammad su tashi suna daraja mahaifinsu amma inhar suka tashi babu uwa lallai zasu zargeahi akan wulakanta babarsu. Da kanshi ya kai yaran suka kwanta sannan ya biyo ta daki ya samu tana kwance gefen yarta, hannunsa yasa ya dauke Su'ad sannan ya matso da uwar wadda ta Fara kokarin kwacewa ita a dole fushi take dashi Seda ta gama ture turenta kafin ya fara zuba mata ruwan kisses kamar zai haukata ta daga karshe ya kashe ta da soyayyarshi me tsada, Seda suka nutsu sukai wanka sannan ya kwanta kan cinyarta tana wasa da gashinshi tareda kallon Baby Su'ad dake baccinta hankali kwance "Nayi tunanin a yadda kika sanni bazaki zargeni da rashin adalci ba, Sulaim ya zanyi this is the last thing da zan iya dauka Daga gurin Subay'a na bata dukkan chances da take bukata amma har cemin tayi idan na gadama na saketa, to na nuna mata sakinta is the simplest thing da zan iya nidai kawai I need your support plz Kada ki barni no matter the hardship kinji" Sunkuyowa tayi ta manna mishi peck sannan tace "Allah ya daidaita komai and I will forever remain yours till death do us apart, I'm sorry for dazun" Mikewa yayi ya hade bakinsu guri daya........... Tired I need a break...... Gobe Inshaaa Allah I'll post the final episode fadan karshe kenan! Shatuuu ♥️ [9/13, 6:29 PM] Shatuuu❤: *MACE A YAU* 60 _FINAL CHAPPY_ ✍️Shatuuu♥️ 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION #⃣Shatuuu095@wattpad *I've seen the critics akan sakin Subay'a, of course Subay'a need to go she need to learn her lesson, Kada Ku manta tayi amfani da son da Junaid ke mata take iskancinta amma ga page ne se ku gani ko hukuncin yayi muku. This mark the end of MACE A YAU I hope you guys liked it, ina fatan zaku cire lessons din ciki kui amfani dasu kubar sauran. I love each and every person who was, is and will be with me through this journey.... May Allah shower his endless blessings upon you.....nagode sosae Allah ya bar zumunci da kauna.... One Love💕* _GODIYA TA MUSSAMAN_ My wattpad follwers SHATUUU's Kingdom damsels Ladies of Maman Mama Novels Kainuwa writers association group Kainuwa fans club 1 to 12 Zauren Sadeeya novel Ummu hanash novel group Mace tauraruwa Ummu Safwan novel group Taskar Marubuta group _My gratitude also goes to Anty Sumayya Takori, Anty Nafisa Tafida, Anty Fauza 'yar amanah..... You guys are my personal persons♥️_ Bayan Watanni Uku Shigowar Musbahu cikin bedroom din Khulthum din yasa ta rufe Wardrobe din da take sake gyarawa saboda kayanta da aka kawo daga gurin guga, zama yayi gefen gadon idanunshi na kanta har ta karaso ta zauna a gefenshi tareda fadin "Yanzun nan zan taho" Hararar ta yayi yace "Shiyasa naga kina gyaran wardrobe" Dariya ta danyi tareda mikewa ta Kama hannunshi Tana fadin "Oooo gashi na tashi muje na shirya ka" Kafadarshi ya noke yace "Goyo nake so" Baki ta bude tareda sakin dariya tace "Tabdijam, Too Big fa! " Rankwashi ya kai mata akanta tayi saurin kaucewa tareda barin gurin Tana yi mishi gwalo, kanshi ya gyada yace "Ni ko?" Dariya tayi mishi ta bude kofar ta fice, hannunshi ya ware ya biyo bayanta a ranshi Yana Raya present situation dinshi, ko cikin mafarki bai taba kawowa cewar akwai rana da zai zauna da mace haka ba bai taba kawowa ba, bai ma taba tunanin cewar a mace akwai abin burgewar da har zaisa yana aiki Yana tunanin dawowar gida, har yana jin dokin dawowa gida, har yana jin tamkar yafi kowanne saa a rayuwarshi. A farkon dawowarsu daga India yasha wahala kafin yayi coping da rashin Abinda yake, ya kasa tunkarar Khulthum don gani yake Yana Zuwa tabbas zai cigaba da Anal sex dinne da ita amma haka ya kaurace mata sede kira kawai a waya yaji yadda take, ya jima a Wannan halin idan ya hadu da maza se yaji Yana son komawa ruwa ga yadda suke kawo mishi attack ta ko ina Seda ya tsaya a tsaye akan addu'a da neman gafarar Allah sannan ya samu ya dace har ya fara hango abubuwa a tareda Khulthum na burgewa hakan yasa ya fara shiga jikinta itama ta saki jikinta dashi ta Fara bashi kulawar da ya kamata shima baya taba wofantar da Al'amuran ta a haka shakuwa da sabo suka shigesu har basu san soyayya ta samu guri a zukatansu ba a haka rayuwar ta cigaba da tafiyar musu har ta mallaka mishi kanta Wanda wanann taste din yasa yaji tabbas ya cuci kanshi da ya zauna Yana biye ma zuciyarshi akan wanda suke jinsi daya, tundaga ranar suka bude shafin soyayya tayi kiba ta murmure hankalinta a kwance, Duk Saturday a gidan Gwoggo suke yini. Iskar bakinta ta hura mishi hakan yasa ya saki murmushi tareda zama ta Fara serving dinshi ya nutsu yana ci suna hira har ya kammalla ya goge bakinshi tareda mikewa Yana gyara rigar jikinshi, itama mikewa tayi tana fadin "Har ka koshi? " "Cikina kike so ya fashe? " Dariya ta danyi ta dauki briefcase dinshi tayi gaba yana bayanta har ta iso bakin motar da driver ke jiranshi, bude mishi back seat tayi seda ya shiga kafin ta rike marfin motar tana kallonshi kamar yadda yake kallonta yace "Ki fita da wuri ki dawo da wuri bansan na dawo bakya gida " Salute tayi mishi tace "Angama Yallabai" Murmushi yayi sannan yaja hancinta suka saki dariya gaba daya Cikeda farin ciki da nishadi, rufe motar tayi ta daga mishi hannu sannan ta wuce cikin gida Bayan ta ga ficewarsu Daga gate din. Tana shiga ta tarar komai an gyara hakan yasa ta wuce dakinta ta shirya cikin milk din Voile lace da red flowers tayi kyau sannan ta harhada abinda take bukata ta fito Tana jin sanyi cikin zuciyarta, gaba daya rayuwar tayi mata rangwami Allah Yana sonta da ya hukuntata kuma ya maida ta akan hanya, gashi ta fahimci kudi ba komai bane farin ciki da kwanciyar hankali shi ne jigon rayuwa wanda yanzun haka ta samu batada matsala da kowa don a yanzun renovating gidansu Mama take wanda Musbahu ya bata kudin duk wanann rowar ta daina Don ta rigada ta samu kawa ya rabeta se ya jiku. Tana fitowa driver dake kaita Duk inda zataje ya taso dama tuni ta sanar dashi inda zataje, aikuwa bai sauke ta ko ina ba se gidan Aminiyarta Sulaimi, Sulaim ta kammalla dukkan abinda zatayi na tarbar su tana kwance kan carpet se Su'ad da ta Fara wayo tana gefenta tana mata wasa yarinyar kamar an ciro fuskar Jabir an saka mata saboda yadda take masifar Kama dashi. Sallamar Khulthum yasa Sulaim tashi ta zauna fuskarta dauke da murmushi, shigowa Khulthum tayi ta zauna suka gaisa tana rikeda Su'ad "Allah sarki Sulaim wayo Su'ad take karawa kullum" Murmushi Sulaim tayi tace "Gata nan kam, Matar nan kin ganki kuwa Musbahu ya dage fa" Dariya sosae Khulthum tayi suka Fara hira yawancin Khulthum ce ma me maganar Tana Kara bata labarin yadda komai ya koma normal tsakaninsu a lokacin ma ciki gareta na watanni biyu, Sulaim murna tayi sosae a haka su Aimana suka karaso kafin wani Lokacin tuni hira ta barke ta Yaushe gamo. Karfe hudu na yamma Jabir yayi parking kofar gidan su Junaid, dake yawanci nan yake wuni idan bashida aiki hakan na kara kwantar mishi da hankali, Tundaga kofar parlon yaga takalma yasan tayi Baki amma haka ya shigo da sallama bakinshi lokacin Su'ad na hannun Aimana tana canja mata diaper da kaya, Sulaim na gefenta tana waya da Junaid wanda ya tafi Kwara attending wani conference. Sulaim ce ta Fara amsawa sannan Aimana dake Khairi da Khulthum sun fita wani guri zasu karbo sako, zama yayi kujerar dake gefen Sulaim tana facing Aimana, seda suka gaisa da Sulaim kafin Aimana ta gaisheshi haka kurum ya kura mata idanu ba tareda ya amsa gaisuwar ba har Seda Sulaim ta buga handle din kujerar sannan ya ja numfashi tareda dauke kanshi ba tareda ya amsa ba, itama mikewa tayi ta nufi bedroom din Sulaim hannunta rikeda Su'ad ga idanun Jabir da sukai mata rakiya har ta kule cikin corridor din, zamanshi ya gyara tareda kallon bangaren Sulaim ashe kallonshi take hakan yasa ya saki dariya tareda daga hannun, itama dariyar tayi tace "Zaka shiga ne? " Murmushi kawai yayi yace "Zan samu abinci? " Kanta ta gyada Bata Kara cewa komai ba ta hada mishi a dining sannan ta dawo parlour tana lissafi cikin ranta, yana gamawa ya kalli corridor da Aimana tabi sannan ya dubi Sulaim wadda ta tsareshi da idanunta masu kaifi "Yaushe kika zama yar sa ido ne wai? " Kanta ta girgixa tace "Ni na isa baka dauki Su'ad ba" Tsaki yayi don yasan Jan magana take ya fice baice mata komai ba. Wasawasa se karamar magana ta zama babba tun Jabir Yana dauke idanu amma picture Aimana da akai storing a kanshi ya kasa barin kanshi hakan yasa ranar wata Thursday da daddare kamar yadda ya saba ya shiryo ya taho gidan. Suna parlor suna kallo yayi sallama inda Ahmad ya taroshi suka shigo ciki, Seda suka gaisa kafin suka ci abinci sannan Sulaim ta kwashi yaran suka tafi Dakinsu don tayasu homework anan ta bar Su'ad hannun Junaid suna hira shida Jabir. Har ta gama yaran suka kwanta ta dawo ta tarar Jabir bai tafi ba, gefen Junaid ta zauna tareda daura kanta a kafadarshi ta kalli Junaid tace "Bacci nake ji fa! " Ya gane me take nufi hakan yasa ya saki dariya tareda kallon Jabir yace "Gwauro Zamu rufe kofa dare yayi" Fuskarshi ya yamutsa yace "Ni Abu ne ya kawoni kuma specifically gurinki Ammin Su'ad" Kanta ta dago tace "Ni kuma?" Kanshi ya gyada tareda gyara zama yana shafa kanshi yace "Wannan friend din taki, kina ganin zan iya aurenta? " Gaba daya mamaki ya daskarar dasu don babu Wanda yayi tunanin Jabir Zai nemi aure a Kwana kusa Amma se gashi ya basu mamaki, sun kansu basu sha wahala ba Aimana ta amince a hankali abubuwa suna tafiya har iyaye suka shiga cikin abin suna shiga level 4 akai Auren se ya rage Khairi ce kawai batai aure ba itama kuma wanda zai aureta dan jaligon ne yana jira ta kammalla sannan ayi abin. A hankali kwanaki suka shude kowacce dakika na zama Mintina haka mintina na zama awanni har cikin Khulthum ya tsufa Gwoggo ta takura dole Musbahu ya maida ita can shima kuma ya tare acan din, ko sati bata rufa ba ta haihu danta namiji me kama da Musbahu, ranar suna aka Sakawa yaron Muhammad anyi shagali Irin na gasken gaske kuwa, Tana arbain ta wuce gidansu inda suka samu afuwar rayuwa suka zama tamkar basu ba yadda haihuwa tayi rana ba Daga Khulthum ba, ba Daga A'isha ba haka Amir kowanne na iya bakin kokarinshi. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda Musbahu ya nema mata admission a wata university dake Michigan State inda take Law din Don ya wanke kanshi ya kafata ta kamu kafu sosae. Bangaren uwar dakin su walida Hajiya Subay'a kam ta yadda ubanta shi ne Alhaji don seda taji tamkar ta bar gidan ya muzgunawa rayuwarta yasa ta bar aikin bank din da take ya hanata fita ko ina Tana gida kullum tsamannin ganin anzo bikonta take amma shiru gashi hajiyar ma bawani dadi takeji Daga gurin ta ba haka yan uwan, Seda tayi shekara daya cif a gida ta gane batada wayo, ta gane Junaid shi ne rufin asirin ta sannan ya maida aurensu inda ta zage damtse sosae ta zage ta shiga taitayinta yaranta duka suka dawo gurinta. Watanta biyar da dawowa ta samu ciki lokacin ita kuma Sulaim ta yaye Su'ad yarinyar ta girma sosae tana yawonta amma ciki shiru babu labari tun abin bai dameta ba har ya fara damunta amma bata taba nunawa ba haka Subay'a ta haihu Sede babyn kwananshi biyu ya rasu, a wannan haihuwar anan Hulda ta Fara hada Subay'a da Sulaim kullum se taje gidan an gyara gidan ta wuce school ana gama lectures ta dawo se dare ta koma gidanta haka har akai Kwana bakwai sannan ta daina Zuwa. Bayan sati biyu Subay'a ta Fara fita tazo tayiwa Sulaim godiya shikenan zaman lafiya ya kara wanxuwa cikin rayuwarsu har Su'ad na Zuwa tayi weekend abinta. Five Years Leap A wannan lokacin tuni su Sulaim sun Gama Law har Law school inda a shekarar da suka shiga suka kammala anan ta zama cikakiyyar Barrister, buri ya cika se lokacin hankalinta ya dawo jikinta ta dawo gida ta gina sabuwar rayuwa itada mijinta da yarta Su'ad wadda a lokacin Aimana ta Haifa Namiji me sunan Baba ana kiranshi Abid, itama Subay'a ta kara haifar namiji Mahmud. Tun Sulaim na damuwa akan ciki har ta hakura saboda yadda Junaid dasu Mami ke Kwantar mata da hankali akan ai Mummynta ma Seda tayi shekara bakwai da aure kafin ta haihu hakan yasa ta hakura bawai Dan bata son haihuwar ba sedan kwantarwa mijinta hankali. Ranar ta kasance Monday Tun sassafe ta tashi ta shirya breakfast Don a ranar Haulat matar Ja'afar zata koma kaduna tazo tayi Kwana biu kuma da sassafe zata tafi ga Junaid zaije office haka Su'ad dake primary one zataje school. Seda ta kammalla komai sannan ta nufi dakin Junaid tabar Su'ad Haulat zata shirya mata ita, wanda dawawarshi kenan daga massalacin asuba inda ya biya gidan Subay'a sannan ya dawo. Zama tayi gefenshi tareda fadin "Heartthrob Ina Kwana? " Kanta ya shafa yace "Lafiya lau Dove dita, how was your night baby " Murmushi tayi tace "It was...... " Ta fada kusada kunnenshi, mikewa tayi ganin yana son rama cizon da tayi mishi a kunne ta fada toilet ya biyota suka kammalla wanka anata watsin ruwa sannan ta fito mishi da kayan da zaisa Itama ta shirya cikin plain material baki me kyau dinkin Bubu style yayi mata cif sakamaakon cikowar da jikinta yayi, turare ya dauka nashi na kullum fierce cologne by Abercrombie and Fitch, hancinta tayi saurin toshewa jin yadda zuciyarta ta tashi lokaci daya ga hautsinawar da cikinta yayi, kafin tayi yunkurin wani abu se amai hakan yasa ya nufo ta da sauri amma yana karasowa ta Kara rikicewa ta dinga amai wanda ya tayar mishi da hankali, kafin wani Lokaci ko tsayuwa kirki bata iyawa dole ya kira Jabir akan ya hada yaran duka ya kaisu school akan zaikai ta Asibiti. Kafin suje wani Asibiti dake kusa dasu private akan gwarzo road har zazzabi ya rufeta tana ta surutai, Junaid iya rikicewa kam yayi a haka suka isa aka Fara bata taemakon gaggawa har bacci ya dauke ta sannnan aka tura jininta screening, result din na fitowa ya nuna tana dauke da ciki, murna understatement ce, farin ciki kamar zasu hadiye junansu, kafin wani Lokaci Mami ta iso inda ta tarar Aimana da Subay'a suna gurinta ana ta Faman pampering dinta. Da daddare Junaid ya shigo lokacin ita daya ce tana Zaune Akan carpet ta Idar da sallah saboda jikin nata yayi sauki sosae Alhamdulillah, gefenta ya zauna tareda janyo wani farin flask wanda ya shigo dashi, yana budewa yawunta ya tsinke dama zaman da tayi so take ta Kira Mami taji abincin ba a kawo ba, plate ya janyo ya fara xuba mata pepper chicken wanda akai garnishing da Irish potatoes, sosae ta nutsu taci dukda akwai yaji amma ko a jikinta haka ta gama ci ta goge bakinta da hannunta Tasha zobo sannan ta kwantar da kanta kan kafadarshi, a hankali yasa hannunshi Yana shafa fuskarta yace "Precious babynmu na hanya, I can't wait to hold the baby in my arms" Murmushi tayi tareda sake shigewa jikinshi tace "Thank you for the love, thank you for everything and thank you for the baby and..... " Bai bata damar karasa maganar ba ya shiga bata wani sassanyan kiss me tsayawa a zuciya wanda yasa suka manta cewar a asibiti suke!!! Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Shatuuu ♥️