[10/23, 8:59 PM] CUTIE~RIAM: [10/23, 8:52 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *BY:RIAMCOOL* *Mikiya writter's Association* *Bismillahirrahamanirahim dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangiji da ya bani damar kammala littafin Bayan wuya hakikanin gsky Ina godiya ga masoyana da suka nuna mani zallar love a litattafaina ,ga shi na sake dawo maku a KULU lbr Mai rikici da sarkakkiya fatan za ku bani hadin kai My Habibties* *P.1&2* A lulume garin yake da bak'in hadari wan da ya saka bishiyun cikin jejin kad'awa da k'arfi yayin da ba ka jin sautin komai sai sautin kad'awarsu da Kuma walk'iya da tsawar da ake yi A hankali nake k'ara ware manyan narkakkun idanuwana na zubasu a sararin samaniya ina kallo yadda baƙin hadarin ke gudun tseral a sararin samaniya, hankalina a tashe na fara ɗaga ƙafafuwana da niyyar barin jejin domin gudun kar ruwan saman ya dakeni, sai dai bakin Alƙalami ya bushe, nan take wasu ruwa masu ƙarfin gaske suka tsage, sosai nake gudu ina jefa ƙafafuwana duk inda suka faɗa, yayin da ƙayayyuka suka sossokar min ƙafa amma ba ta ita nake ba, nafi jin ruwan ya dakeni, domin ni kaɗai nasan wahalar da zan sha idan ciwona ya tashi,burina bai wuce na ganin na isa cikin gari ba,tamkar wacce za ta tashi sama haka nake ɗaga ƙafafuwana ina jefasu duk inda suka faɗa yayin da suke man raɗaɗi amma a haka na dage ina fyalla gudu har na isa cikin gari, yayin da numfashina ke gargada yana sama da ƙasa da taimakon Ubangiji na samu na shiga ragargajajjen gidan ina mayar da numfashi, ban iya ɗaga fatar bakina nayi sallama ba saboda nauyin da tayi man, ɗaga labulen ɗakin zanyi na tsinkayi Muryar Mamah Khubrah "Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un, wallahi ta kashe ta KULU ta kashe man yarinya" duk yadda nake jin jikina bai hanani faɗuwa ƙasa ba ina mayar da wani wahalallen numfashi wan da nake jin ya sarƙafe man duk wata kafa ta fitar numfashina, da ƙyar na iya samun ɗaga bakina na kurma ihu wanda nake ji ko zan samu sassaucin abinda nake ji, tamkar an jefosu haka na gansu sun fito sunyi carko_carko a kaina,idanuwansu sharkaf da hawaye kamar yanda nima nawan yake yana malalar da hawaye, "KULU kin kashe man yarinya hankalinki ya kwanta,amma wallahi ki sani kema sai kin tafi inda kika tura man yarinya" Mamah Khubrah ta faɗa tana tunkaroni da wuƙar dake hannunta,da sauri na rintse idanuwana ina jiran tsammani,sai dai shirun da naji ne na ƴan second ya sakani ware idanuwana sai dai abin da na gani ne ya sakani ware idanuwana, ganin yadda Mama Khubrah ke zubar da jini ta baki,hakan ya sakani kai dubana ga wacce ke gabanta wan da iya ni kaɗai ce ke ganinta,hannu ta miƙo man tare da kama nawa hannun ta fita dani Kamar yanda ta saba fita dani ta zaunar dani a kogo yauma hakan ce ta faru, zaune nake ina sauke ajiyar zuciya hawaye na sintiri a kumatuna "KULU" naji ta ambaci sunana wan da ya sakani ɗago da fuskana ina dubanta tare da furta "Diyana wane laifi na aikata maki da kike kashe mutanen dake tare dani" "Kulu ba wani laifin da kika aikata man,ina yin hakan ne ga duk wan da ke yunƙurin cutar dake,sannan Zainab ba kashe ta nayi ba, na ɗauki ruhinta ne a jikinta" Share hawayen dake fuskana nayi ina furta "Diyana na roƙeki da Allah ki mayar mata da Ruhinta kar ki ƙara yunƙurun kisan kai a kaina, ki bari ayi man dukkan abinda za ayi man Ni kaina na gaji da baƙar ƙaddararriyar rayuwar da nake ciki,na san tun lokacin da Mahaifiyata ta yar dani ƙaddara ke bibiyata, ita kanta Mahaifiyata na san tsanata tayi har ta yasar dani dokar jeji,to zafin mi zanji da waɗanda suka ɗaukenj suka renini duk da azabar da suke bani tun ina ƴar ƙanƙanuwa wacce ko kaɗan bani ganinta ina matuƙar ji dasu duk da ba suyi dani ina kallonsu a wani matsayi wan da bai kamata ace ta silata an cutar da su ba ko dan Baba" na ƙarashe zance da kuka kafaɗa ta Diyana ta kama tana bubbugawa tace "naji zan mayar mata da ruhinta Kulu,ni ɗin Uwa ce a gareki ba zan so zubar hawayenki ba, tun lokacin da Mahaifiyar ki ta ajiye ki a rukata na ajiye ki a matsayin ƴata, duk ni ɗin ba Ƴar Adam vace amma na zaɓi rayuwa dake kulu tabbas ke ɗin asalinki wani jini ne mai ƙarfi wan da nake da tabbacin ke ɗin ba Mutum bace kamar kowa,ke ɗin kin kasance sirki biyu" "Diyana ban gane ni ɗin sirki biyu bace shin ni ɗin ba Ƴar Adam bace hala ina da sirki da jinin Aljanu? ? Shi ya saka Mutane da yawa tsanata" na faɗa da hawaye murmushi ta saki tana girgiza kai tace "zuwa gaba za ki san dukkan wani tarihinki wan da ni kaina shi nake da burin sani wan da duk ƙarfina na gagara sanin asalinki da kuma tarihinki, tabbas ke ɗin babban jini ce mai cike da ƙarfin Izza da kuma ƙaƙƙarfan iko" ta faɗa tana share man hawayen dake sintiri a fuskana,tare da yi man maganganun da tasan ina so sannan kuma suke kwantar man da hankali Abinci ta Bani naci sannan ta mayar dani har gidammu wan da nake ɗarɗar ɗin shiga cikinsa domin ban san mi zan tarar ba, DA fargaba na kurɗa kaina a ɗakin Mama Khubrah sai dai yanayin da na iske su ne ya sakani sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ganin Zainabu ta tashi alamun Diyana ta mayar mata da ruhinta dubana na kai gun Mama Khubrah wacce itama ke ta faman hararana tamkar idanuwanta za su faɗo "Toh tsinanniyar Tsintacciyar Mayya Allah ya nufi Zainabu kwananta basu ƙare ba, ba kiyi nasara ba, da ace wallahi kin kashe man yarinya kema sai na kashe ki, wato dan karna ɗau mataki ya sakaki fara sha man jini a ɗazu kika zubar min dashi to wallahi sai nai maki dukan da jinina ya zuba hakanan Malam ya tsinto mana bala'i" ta ƙarashe zancen da miƙewa tana nufo wurina gadan_gadan za ta dakeni "KHUBRAH wallahi kika daketa sai ranki yai mummunan ɓaci za kiyi tsantsar nadama,sannan nai maki abin ban taɓa maki ba a duk tsawon shekarun da muka kwashe dake,shin ita Kulu da take Ƴar tsintuwa ba Mutum bace?" BABA ya faɗa da tsantsar ɓacin ran da ya bayyana a fuskarsa Duk da Mama Khubrah najin shakkar Mijin nata bai hanata faɗar "wallahi Malam ba zan ƙyale Kulu ba sai na ɗauki mataki a kanta naga ƙarshen maita ko ita Sarkin Mayu sai na kawo mata ƙarshen maitarta ,sannan ta san a ɗakin da za ta kwana ba dai a wannan ɗakin nawa ba sai dai ta kwana a waje" tana gama faɗin hakan ta fincikoni tana fito dani waje tai wulli dani wan da ya sakani faɗuwa ina fasa ƙara sakamakon ƙashin hannuna da ya bugu da wani dutse dake girke a ƙofar ɗakin da gudu Baba ya fito yana miƙar dani ya rarrasheni, tsaye muke daga mu har shi ga hadari ya ƙara harhaɗuwa da alamu dai wasu ruwan za a sake yi,kallona yayi yana faɗin "KULU ko za ki kwana a ɗakina ni sai na fita waje na kwana a shagon Ilah" ban musa ba na shiga ɗakin Baba shi kuma ya fita rufe ɗakin nayi ina kwanciya hawaye na biyo kuncina, a hankali na fara jin jikina na sauya man yayin da na dinga gani abu mai sheƙi da kuma walwali a duhun yana tunkaroni miƙewa zaune nayi ina ja da Baya kafin wani haske mai tsanani ya bayyana, wan ba komai bane ya saka wannan haske sai wata narƙeƙiyar macijiya wacce tai man ƙur da idanuwa,yayin da Kanta ke ɗauke da Kambun sarauta, kallona take tana ɗaga kai ,ban ida shiga ta shin hankali ba sai da naji tana magana "me ya saka da kimarki da darajar ki kike rayuwar ƙunci da ƙasƙanci,ke ɗin fa Babban jini ce wanda ya kamata ace a halin yanzu kina daula hadimai na bauta maki" ta ƙarashe zance da ɗaga wutsiyarta na baya za ta shafo ni,sai dai tun daga lokacin kuma ban kuma sanin inda kaina yake ba sai dai na tsinkayi dukan ƙofar da ake yi tamkar za a cire ƙofar, A hankali na ware idanuwana na tashi na buɗe ƙofar ɗakin wan da naci karo da Halime Babbar ƴar Khubrah,kallona take irin na tuhumar nan ganin ana sanyin damina amma jikina ni sharkaf yake da zufa ina mayar da numfashi " dama ke ce a ɗakin ba Baba, waye a ɗakin naki ? naga kina mayar da zufa kar dai ace naman wani ne kike dahuwa da jikinki za kici" girgiza mata kai nayi ina faɗin "a a wallahi bacci na tashi yanzu " fizgoni tayi tana faɗin "dallah fito kiyi mana girki da gyara gida" da toh na amsa har a lokacin hankalina sam ba ya tare dani ya karkata can ya zuwa wata duniyar tunanin, wan da nake tambayar kaina "wacece ni,Miye alaƙana da har nake iya ganin wani baren jinsi ba nawa na ƴan adam, na fara gazgata zancen Diyana tabbas na cewar ni ruwa biyu ce,to amma miye alaƙata da Macijiyar ji" bani da mai bani amsar waɗanan tarin tambayoyin ******************************* *Masarautar JOHAAN* A hankali wani sautin busa mai cike da firgitar da Bayi na cikin gidan Sarautar ke karaɗe ko ina wan da ke masu nuni da cewar akwai wani gagarumin Abin da zai faru a cikin gidan wan da a iya bayin gidan ne suka shiga ruɗani, yayin da kafin su ankara duk wani bawa da aka gani ake korasu da matsanancin bugu har izuwa ƙofar Fada wan da ta cika da mutane mabanbanta, tun da ake dukan fatar jikin nasa ta ɗayaye amma shi sam ko ɗar iya abin da ya sani kawai yana cikin farin ciki marar misaltawa musamman da yaga cikar burinsa ya gabato.............. *Riamcool ce* [7/17, 8:06 PM] RIAMCOOL: *kULU* *By; RIAMCOO* *Mikiya writter's Association* *Bismillahirrahamanirahim* *P.3&4* Dukkansu zubewa su kai a bakin Fadar yayin da suke mayar da numfarfashi,daka musu tsawa wani dogari yai wan da ya sakasu ɗagowa, kallonsu nan take aka fara cinikayyar su ya zuwa wasu masarautun,tun lokacin da akai cinikayyarsa ya zuwa Masarautar da yake burin komawarsa ya tsinci kansa a matsanancin farin ciki miƙewa yai tsaye yayin da fadawan masarautar suka nufosa, tamkar za su rissina masa sai dai kallon da yai masu a faƙaice da kuma ƙyalla musu ido ɗaya ya saka su juya akalarsu ya zuwa daka masa matsananciyar tsawa, wanda ya sakasa shima duburburcewar ,yana nufar inda aka tanadi wasu Amalanke da ake zuba bayin a ciki, shiga ciki yai Yana bin masarautar Benin da kallo wacce akewa laƙani da JOHAAN wacce har ya zuwa datsewar numfashinsa ya san da cewar ƙabilarsa ta Ogboni ba zasu mance illatarwa da ƙabilar Ozo su kayi musu ba, hakan ne ya saka sa shigowa a cikin masarautar JOHAAN domin ɗaukar sirrinsu ta yadda su ƴan ƙabilar Ogboni za su fuskancesu Wani ajiyar zuciya ya saki yana fito da wata sirriyar sarƙa mai ɗauke zanen wani kan halitta mai ƙaho,ɗagawa sama yayi yayin da ya fara magana kamar haka "Olorun jowo ran awon ara ilu Ogboni lowo, bawo ni mo se kuro nijoba yi nigba ti mo yan lati pada, mo gbe ori awon eeyan si inu mo si se ileri lati mu eje won. (Ya abin bauta ka taimaki ƴan ƙabilar Ogboni ka bamu nasara a kansu, ka sa yadda na bar masarautar nan a lokacin dawowata na ɗauki kawunansu ni kuma nayi Alƙawarin zan shayar da kai jinanansu)" yana gama faɗin hakan ya mayar da sarƙar nashi tafiya suka fara yi yayin da suka yiwa masarautar JOHAAN nisa hakan ne ya saka su dakata wa da Amalanke, fitowa yayi daga cikin bayin yayin da suma Dogarawan suka fito a motocin su sai dai dukkansu suka faɗi ƙasa suna masu rissina masa tare da furta magana da Yaren yarbanci " ọmọ ọba (Yarima) Abiodun Adewale femi takawarka lafiya Ya Abiodun Adewale femi takawarka lafiya sha kundum shamaki,takawarka lafiya ubangabasawa Yariman masarautar OYO Mai shayar da abin bauta jinane takawarka lafiya Bijimin duniya waye zai shiga masarautar JOHAAN da Ƙulli ya fito da rai in ba kai ba,mun rantse da Abin bautar mu Dodo soluwole kai ɗin Yariman sa ne baya ga Yariman HANDAASH takawarka lafiya Yariman yaƙin matsafa........" Shiru su kayi sakamakon ɗaga musu hannu da yayi, yana mai basu umarni da su miƙe da hannunsa,miƙewa su kayi yayin da suka nufo wurinsa suna mai saka hannayensu a fuskarsa su ɗebe masa jemammiyar fuskar da ya liƙa a fuskar sa wacce za ka rantse da cewar ba ta roba bace, nan take haɗaɗɗiyar fuskarsa ta asalin kyawawan Yoruba ta bayyana mai cike da tsantsar kyau wan da ya kasance Black beuty sai dara daran idanuwansa na asalin ƙabilar Ogboni da madai_daicin lips nasa da kuma zara_zaran gashin giraren ido da gewayayyen sajensa wanda yai yawa tsabar daɗewar da yai ba a askesa ba,sai dai fuskar nan a haɗe take tamau babu alamun wani haske a tattare da ita ko annuri, kallo ɗaya za kayi masa ka tabbatar da shi ɗin ƙaƙarfane ta ko ina kama daga siffar jikinsa, shiga yai cikin ɗaya daga cikin motocin yayin da suma Dogarawan suka shiga sun jima suna tafiya before su isa a cikin garin Oyo wan da tun a matsayar shiga suka fara tarar da manya manyan motoci na Alfarma ƙirar lamborghini a jejjere buɗe masa a kayi ya fito da cikakkiyar Izza da ƙasaita wan da ya saka Mutane ihu da kirari wan da yake ƙara jin wata cikakkiyar Izza na zauna masa,Zama yai a Back seat Yana mai lumshe idanuwansa, yana ƙara jin wata nutsuwa na ziyartarsa, *MASARAUTAR HANDAASH* cike take da tarin manyan makaɗa da kuma bushe_bushe yayin da Mutanen cikinta ke cike da tarin farin ciki da murnar dawowar Yarima Abiodun Adewale femi,sai dai a wani ɓangaren ba za a rasa tarin masu baƙin ciki da dawowarsa ba kamar yanda ya kasance a gun Boluwatife matar Babansa tsaye take a gaban wani baƙin gunki yayin da idanuwanta sun kaɗa sunyi ja magana ta fara tana faɗin "Ọlọ́run, ẹ̀ṣẹ̀ wo ni mo ṣẹ̀ tí ogun ìbọ̀rìṣà mi sì jẹ́ ìtẹ́wọ́gbà"(Ya abin bauta wane laifi na aikata da tsafina yaƙi karɓuwa?" dogon numfashi taja yayin da taci gaba da faɗin "na kwana ina shayar da kai jinane da ruwan jikin mutane amma tsafina bai tafi dai_dai ba akan Abiodun, mi ya sa na gaza yin nasara akan Abiodun har yanzu,me ya saka masarautar JOHAAN ka sa gano Abiodun??? na so ace Abiodun bai dawo ba" ta faɗa wani sabon kukan takaici na kamata Motsin da taji gunkin nayi da kuma sheƙewar wata dariya da ta tabbatar mata data Boka Olusegun ne, "Boluwatife!!!" Ya ambaci sunanta da ƙarfi wan da ya sakata kallonsa "Boluwatife kin gaza nasara akan Abiodun ko? na faɗa maki daman ba za kiyi nasara akan tonuwar asirin Abiodun a masarautar JOHAAN ba, ballantana a samu damar kashe sa, sai dai kina da dama ɗaya wacce zan faɗa miki duk da ba lallai ki yarda ba" ya faɗa yana tunkarota "faɗa man ita Olusegun" ta faɗa da son samun mafita dariya ya kuma kecewa da ita yana faɗin "mafitarki ɗaya ce a yanzu ya zama dole ki koma bautawa Abin bautar Abiodun ta hakan ne za ki iya nasara akansa" "Olusegun!!!" ta faɗi sunanshi da ƙarfi yayin da matsanancin ɓacin rai ya bayyana a fuskarta *************** KULU tun lokacin data ga macijiyan nan ta kasa sukuni ga shi duk yinin ranar ba taga Diyana ba,ga Mama Khubrah ta kasa ta tsare akan ba zata fita ba hakan ya saka jikinta yin sanyi Tuwon dake gabanta ta tasa yayin da ta gaza ci "idan ba za kici ba akwai masu ci,ji tsabar iskanci a baki abincin ki ƙici, wallahi dan ma yana na nemowar Malam da ba za kici shegiya ƴar tsintuwa haka za ki ƙare mayyar banza" Mama Khubrah ta faɗa tana kai mata ranƙwashi a kai hawaye ne suka zubo mata ta saka hannu za ta share taga Diyana a gabanta tana sakar mata murmushi tare da miƙo mata hannu wan da ya sakata miƙa mata itama da murmushi ɗauke a fuskarta miƙewa tayi ta fito ba tare da kowa ya ga fitar ta ba Kai tsaye cikin jeji suka nufa cikin kogon suka zauna wan da Diyana ta bata Abinci mai rai da lafiya,"Diyana" Kulu ta kira sunanta kallonta tayi tana faɗin "Kulu mi ya faru ne" "Diyana dan Allah ni wane ne asalin jinsina naku ko bil'adama ko kuwa Jinsin dabbobi nake??" na faɗa idanuwa cike tab da ƙwalla "Kulu ke ba jinsimmu bace iya abinda na sani kawai ke ɗin sirki biyu ce" "asalin wane sirki kenan" na faɗa ina kallonta Itama kallon nawa tayi tana faɗin "har yanzun wannan ne na gaza ganowa ke wace asalin sirkin jinsi ne dake" Diyana ta faɗa ajiyar zuciya na saki ina furta "Diyana jiya fa naga wata maciya ta ziyarceni" da mamaki take kallona tana faɗin "kamar ya KULU?" dukkan abinda ya faru a daren jiya na faɗa mata wan da naga nan take yanayinta ya sauya........... [7/19, 5:10 PM] RIAMCOOL: *KULU* *By: Riamcool* *Mikiya writter's Association* *Bismillahirrahamanirahim* *P.4&5* "Kulu tabbas ke ɗin rayuwarki lulluɓe take da wani mayafin sirri wan da ba lalle ni na gane alaƙarki da macijiyan nan ba,sai dai tabbas wannan Aljanar macijiya ce kika gani kuma mai ƙarfin iko,ita ɗin ta shafi wani ɓangare na rayuwarki haka zalika ita ɗin sarauniyar Aljana ce" Diyana ta faɗa tana kallona Kallonta nai ina faɗin "Diyana ni kaina na gaza gane wace rayuwa nake gudanarwa wacce tamkar ba Ƴar Adam ba saboda tsanar da akai man, shin ta ya zan koma rayuwa cikin jinsin jinnu na fita daga jinsin ƴan Adam" "Kulu hakan ba zai yiyu ba dole ne kiyi rayuwa cikin Bil'adam saboda ke ɗin tushen ki nan yake duk da an haɗa jininki da wani sirki" Ajiyar zuciya mai ƙarfi na sauke wasu hawaye Masu zafi na zubo man,"KULU ba dai za ki daina kuka haka ba ko? ita fa ko wace rayuwa da kika gani da yadda Ubangiji ya tsara maka ita ya kamata ace idan da sabo kin saba,ki koyi juriya da dauriya Kulu" ta faɗa tana rungumoni jikinta murmushi na saki ina share hawayen nace "To na daina Diyana" "Yawwa ko kefa" Diyana ta faɗa ganin Azahar ta gabato ya sakani miƙewa,Diyana da kanta ta rakani gida kamar yadda ta saba,jikina sam ba ƙwari na shiga ina jin zuciyata ta cunkushe man da wani matsanancin baƙinciki da kuma ƙunci,ina jin wani kaɗaici na mamayeni Bakina ɗauke da siririyar sallama na shiga wan da ya janyo hankalin Mama Khubrah dake faman sauke tukunyar Abinci, da wani matsiyacin kallo ta bini tana gyara ɗaurin gaban da tayi tace "daga gidan ubanwa kike?" "Jeji"na furta ina rakuɓewa a bango "Aw kin san da sarai fa tallah za ki fitar min amma kika kama hanya kika nufi jeji,shin wai ni a jejin nan uwar me kikeyi ne? wanda tun kina ƙanƙanuwa kike zuwansa" "Yi haƙuri" na furta da tsoro domin nasan idan na bata haƙuri nayi laifi idan kuma ban bayar ba shima laifin nayi,hannu ta saka tana jawoni tare da sakar man ranƙwashin da ya saka kaina sarawa hankaɗa ni tayi tana faɗin "ki tashi ki ida haɗa kayayyakin tallar ki fita da ita" ban musa ba na miƙe na harhaɗa sannan na samu nai Arwallah na gudanar da Sallah, Roban taliyar na aza a kaina sannan Saminu Yaronta ya ɗauki Roban waken da Manja, kai tsaye inda nake ajiye tallan kusa da Baba wanda ke siyar da rake Nan na zauna, ina zama aka fara rurrufe ni masu siyan taliya wan da daman dana fita kamar jira ake haka ake rufeni wajen siyen taliyar, ina yi Baba na tayani siyarwa, harna siyar dukanta tas, nan take kuma naji zazzaɓi ya fara rufeni kallona Baba yayi yana faɗin "Kulu ya akayi ne naga kaman duk kin sauya" "ba komai kawai kaina ke man ciwo ne" "Ayya tashi ki tafi gida, ga wannan ki siyo magani kisha" ya faɗa yana fito da Naira Hamsin sanin ban da kuɗi ya sakani karɓa na bawa yaro ya siyo min nasha anan,ganin ba zan tafi gida ni kaɗai ba ya saka Baban tattara raken yana mayarwa shago, kallonsa nayi ina faɗin "Baba sai ka tafi gida baya ba ka siyar da raken bafa" Murmushi yai Yana faɗin "Kulu kin saba komawa gida tare dani daga tallah,ba zan barki ki tafi ke kaɗai ba ina da kuɗin cefanen yau,muje" ya faɗa yana kama hannuna Murmushi na saki ina ƙara jin qaunar Baba wan da yake nuna man soyayya wan da ko ƴaƴan cikinsa bai nuna mawa,haka zalika yake nuna mani zallar tausayinsa a kaina, harga Allah shi ya nake jinsa wani na musamman a rayuwata nake jin nafi son shi fiye dani kaina, "na san ba kici Abinci ba,bari na siya miki ko Awara ne kici sbd nasan kina sonta" tsinkayi muryarshi "A a Baba ka barta da kuɗin Awaran da za ka siya man a siyi wani abu" na faɗa da tausayinsa Bai bi ta kaina ba haka ya siya min Awaran mai zafi ya bani, da murna na karɓa ina godiya, ko da muka shiga gidan babu wan da yabi kaina, kuɗin tallan na miƙa wa Mama Khubrah ta karɓa tana irgawa sai da ta irga taga banyi ɓatan ko biyar ba sannan ta barni na wuce ɗaki, ina shiga na taras da ba kowa ajiyar zuciya na saki ina fito da Awaran na buɗe na fara ci ina lumshe idanu saboda daɗin da tayi man, ina cikin ci ne na ji an bankaɗo labulen ɗakin "iyeeee wato ke ba za kici abinda aka girka ba sai dai kici Awara sannu ƴar ƙwai nasan Baba ya siya miki to wllhy ba za kici ba sai kin kawo ta nan tun da ba Ubanki bane tsintacciya" Zainabu ta faɗa tana fizgar ledan Awaran dake gabana Shiru nayi ban ce mata ƙala ba haka zalika ban ɗago idanuwana na kalleta ba,har ta ƙarashe man zagin cin mutunci sannan ta fita,jingina nayi da bangon ɗakin ina mayar da numfashi hawaye na zarya a kuncina, a daren ranar ma da ƙyar nai bacci zuciyata fal da tunanin abin da zan kuma gani sai dai har nai baccin ban kuma ganin komai ba. A haka rayuwata taci gaba da tafiya babu wani sauyi ƙalubalen gidammu na ƙara gaba yayin da wajen Baba kaɗai nake samu na raɓa naji sanyi, sannan yake takawa su Mama Khubrah birki ga wani abin da suke Mani A hankali nake jin hayaniya na tashi a tsakar gidan da kuma Kukan su Mama Khubrah dake tashi cikin gidan, da sauri ta fito "Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un mota ta take Malam ya mutu ya barni ashe Ajali ne ke kiransa harya fita na shiga ukku ni Khubrah" na tsinkayi Muryan Mama Khubrah wacce ban fahimta ba sai da naji ana faɗin "ku shigo da gawar sa" wani Mutum ya faɗa Ban ida gazgatawa ba sai da naga an shigo da gawar Baba wan da jikinsa ke sharkaf da jini, ban san sadda na fasa wata uwar ƙara da kururuwa ba ina faɗuwa nan ƙasa sumammiya ban ida sani inda kaina yake ba sai da na tashi naga ana min firfita da kuma koke koken dake tashi a gidan , da gudu na miƙe ina nufar inda naga an saka gawar a mankara "Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un Baba bai Mutu ba wllhy ku dawo man dashi, shi kaɗai gareni duk duniya mai sona idan ya tafi wurin waye zan raɓa naji sanyi,fitar da yai a ɗazun ashe fita ce ta har abada babu rabon ya dawo ,yanzu Baba ka tafi tafiya ta har abada wacce babu dawowa, ban san ya zanyi da rayuwata ba ni Kulu ku taimakeni" na faɗa tamkar wata zautacciya yayin da na fashe da wani matsanancin kuka, Dukammu gaza Magana mu kayi sai kuka tsakanin ni da su Mama Khubrah yayin da su sun sami dangin su masu rarrashinsu ni kuwa babu wan da yabi ta kaina balle har naji sauƙin abinda nake ji a zuciyata,rirriƙe gawar mu kayi yayin da za a ɗaukesa wan da da ƙyar aka ɓanɓaremu nida Zainabu,ina ji ina gani aka fita da gawar Baba Bayan kwanaki sha biyar Mutuwar Baba ba ƙaramin tashin hankali ta jefani ba wan da azabar gidan namu ta ƙara ninkuwa *Masarautar HANDAASH* Da rinannun idanuwanta Boluwatife ke kallon Boka Olusegun tana faɗin "Olusegun ba zan taɓa bin Addinin Abiodun ba, dan na yarda da kaine shi ne dalilin da ya saka na baka yarda na a kanka, Ina son ka samo wata mafitar ban da wannan dariya Olusegun ya fashe da ita yana faɗin "Boluwatife !!!! Mafita ɗaya ce wanda Dodon Bauta ya bani amma zan ƙara roƙon Alfarma a wajensa na tabbatar ba zai kunyatar dani ba, amma kafin nan ina da buƙatar da ki bayar da jinjirin cikin jikinki wan da Abin bauta na tabbatar ba zai ƙasa a guiwa ba wajen cikar muradinki Duk da tashin hankalin da take ciki bai hanta sake shiga cikin wani ba wan da ya sakata wata zabura tana kallon Boka Olusegun............. Ayi manage banda charge 🥺nex page zan yi mai yawa in Sha Allah Love yhu All my Habibties😘 [7/23, 12:27 PM] RIAMCOOL: *KULU* *BY: RIAMCOOL* *MIKIYA WRITTER'S ASSOCIATION* *Bismillahirrahamanirahim* *P.7&8* *Jiya nayi mistake ɗin Number page,page 5&6 zan saka na saka 4&5* Sosai Boluwatife ke kallon Boka Olusegun yayin da mamakinta ya gaza ɓoyuwa da yarensu na Yarbawa take faɗin "Olusegun kana nufin cikin da na daɗe ina so sai da ƙyar abin bauta ya ƙaddara mani samuwarsa,gsky ba zan iya bayar da cikin jikina ba zan san nayi" ta faɗa zuciyarta da alamu karyewa dariya ya saki yana faɗin "kije kiyi tunani Boluwatife" Ba tare da ta sake kallon Olusegun ba ta fice a ɗakin, ta ɗan yi tafiya mai nisa before ta isa inda bararonta suke, sai yanzu na ƙare mata kallo dakekiyar macece Choculate color mai manyan idanuwa fuskarta a haɗe,yayin da jikinta ke sanye da dakakken leshi da murjani a wuyanta, tamkar hadarin gabas haka fuskarta ke ɗaure tamau yayin da take tafiyar Barorinta na take mata baya, a haka harta isa inda Motocin Abiodun suke yayinda ake ta miƙo mata gaisuwa da kirari amma sam hankalinta ba anan yake ba ya karkata ne ya zuwa ta ga Abiodun ɗin yadda ya koma, A hankali takai dubanta gun Mahaifiyar Abiodun wacce itama fuskarta ke ɗauke da maɗaukakin farinciki yayin da shi kanshi Sarkin fuskarsa ke fitar da Annuri wan da jikinsa ke sanye da wani dakakken Farin leshi ƴar ciki da babbar riga sai wuyansa dake sanye da murjanan shima yayin da hannayensa ke riƙe da sandar azurfa, Ajiyar zuciya ta saki tana kai dubanta ga Motocin yayin da ta zuba idanuwa taga fitowar Abiodun,a dai_dai lokacin ne aka buɗe murfin Motar bai fito ba illa ƙafarsa ɗaya daya fara fitowa da ita ya ɗan ɗauki kusan Five minutes before ya ida fito da ɗayar ƙafar ihun da yaji Mutane nayi na farincikin ganinsa shi ya bashi damar ida fitowa Yayin da sai da Boluwatife ta dafe ƙirji ganin cikakken Namiji Abiodun Mahaifansa da ƴan uwansa kuwa bakunansu sun gaza rufuwa sbd farincin ganinsa cikin ƙoshin lafiya, Yana isowa inda Mahaifin nasa yake ya faɗi ƙasa yana kai masa gaisuwa,ɗagosa Mahaifin nasa yayi yana rungumesa, tare da faɗin "Kaabo ọmọ-alade mi, Abinabawa tẹsiwaju lati daabobo ori rẹ" nan take busa da kaɗe_kaɗe suka fara tashi,gun Mahaifiyarsa yake yana rungumeta wacce itama ta rungumesa tana faɗin"Kaabo, Alade, O ṣeun, Ọlọrun, ti o dabobo ọ lati awọn ibi ti ijọba yii."(Barka da dawowa Yarima Nagode Abin bauta da har ya cigaba da kare ka daga sharrin Matsafan Masarautar nan) ta faɗa tana jefawa Boluwatife kallo dukkansu ɗunguma sukai ya zuwa Babban Falon gidan,wanka Abiodun ya shiga yayi, fitowa yai daga Toilet ɗin jikinsa ɗaure da Towel ƙirar nan ta jikinsa tamkar ta doki koda ya fito hadimansa Mata na tsaye na jiran fitowarsa, kansa suka fara taje masa suka ɗaure masa baƙin dogon gashin kansa, sannan suka fara shafa masa haɗaɗdun lotion masu daɗin ƙamshi da tsada, sosai suka shirya sa cikin kayan su na Yoruba masu tsada da jinin sarauta,haka zalika ɓoyayyen kyawun Abiodun ya fito koda ya fito dukkansu suka ɗunguma ya zuwa Baban wajen da Da aka ɗiba a cikin masarautar yayin da yasha Kaya na Alatu da more rayuwa a ciki,sosai aka haɗa babbar liyafa yayin da wurin ke ɗauke da Abinci kala da kala *KULU* Zaune nake a tsakar gidammu yayin da hankalina ya karkata ya zuwa aikin da nake wato tsince shinkafa, sallamar da naji ita ce ta sakani ɗagowa ina kallon Talatuwa wacce ta dubeni tana faɗin " Khubrah na ciki kuwa" gaisar da ita nayi ina furta "eh tana ciki" wucewa tayi tana shiga cikin ɗakin ni kuwa na mayar da hankalina akan aikin da nake Tunda Talatuwa ta shiga suka gaisa da Khubrah ta dubeta tana faɗin "Khubrah nazo miki da wata magana ne dama idan har za ki amince" kallonta Mama Khubrah tayi tana faɗin "faɗi ko wace magana ce in Sha Allah zan amince" gyara zamanta Talatuwa tayi tana faɗin "nake ga Khubrah tunda ba kece kika haifi Kulu ba sana hasali ma ba ku san asalinta ba mi zai hana ki Kaita masarautar Kudu wacce ake cinikayyar Bayi wanda nima zan kai BINTU a can, wallahi KHUBRAH maƙuddan kuɗaɗe ake samu ni kaina an bani maƙuddan kuɗaɗen BINTU kin gansu anan" ta faɗa tana zaro maƙuddan kuɗaɗen dake cikin kwagirinta zaro ido Khubrah tayi tana kallon kuɗin tare da faɗin "Haba Talatuwa ai babu abinda zai hanani kai KULU kuwa can ban san da wane baki zan gode miki ba,na kawo man wannan maganar daman gashi kuwa ina cikin halin na rashi,yanzu wa zan bawa KULU ya bani kuɗaɗen" na tsinkayi maganarta wan da dai_dai nazo shiga a ɗakin, baya naja ina furta Innalillahi'wa'inna ilaihirraji'un, mi Mama Khubrah ke nufi, shin siyar dani za tayi dan Baba bashi da rai ko dan na kasance ƴar tsintuwa marar galibi??? Nai wa kaina waɗannan tambayoyin hawaye na zuba a idanuwana da son ƙara jin zancen nasu na kai kunnena aɗakin ina sauraronsu yayin da Talatuwa ke faɗin "kin ga ki bar komai a hannuna goben nan zan yiwa Shu'aibu magana komai za ayi yi, jibi ki shiryata a Kaita inda za ki karɓo kuɗin" Sosai Mamah Khubrah ke godiya,jin motsin tahowarsu ya sakani barin bakin ƙofar ɗakin Bayan ban ɗaki na gewaya ina wanke fuskana don kar a gano wani abun duk yanda naso ɓoye damuwana ya gagara dole sai da fuskana ya nuna har sai da Mamah Khubrah ta gane man, tsoron ta kar ace na san abinda suka ƙulla ita da Khubrah ya saka ta tambayeni amma sai na ce mata kaina ne ke ciwo, Kwance nake na ƙurawa kwanon ɗakin idanu inata juye juye yayin da damuwa ce fal cike a raina Wacece KULU kulu dai tun tana Ƴar jinjira Malam Hadi ya tsinceta a gona wan da ya ɗauke ta ya kawo ta fadar mai gari tare da neman Alfarma ya riƙe ta duk da ya san mawuyacin abu ne Matarsa Khubrah ta riƙe ta saboda rashin Mutuncinta Da ƙyar da rarrashi ta amsheta wan da ba wata kulawa da take bata, sai dai rainon Ubangiji da taimakon Aljana Diyana da take tare da ita wacce ita ke ciyar da ita tun tana jinjira, tun tana ƙarama ta buɗi ido ta ganta da Diyana, Lokacin data fara girma Malam ya sakata makaranta Boko da islamiyya wanda take da ƙoƙari sosai sai da abinda ke damunta bai wuci gorin da take fuskanta gun yaran Khubrah da ita kanta Mama Khubrah na cewar ita ƴar tsintuwa ce, ga ƙarin damuwar ta bai wuci yadda Mutane ke nuna mata kyara da hantara ba,ko cikin yara bata da ikon yin wasa saboda hantara,tun tana kuka harta daina shiga cikin yaran hakan ya sakata tasowa cikin kaɗaici sai dai Diyana ce mai ɗebe mata kewa wacce takewa kallon Mahaifiya Tun tana shekara goma asalin kyawunta ya fara fitowa wacce ta kasance ita ba fara ba sannan ba baƙa ba wato irin fatar nan ce mai tsada Choculate color sai manyan idanuwanta masu jefa me kallonsu a wani yanayi,bakinta ɗan madai_daici, sai dogon gashin kanta da kuma wanda ya kwanta mata luf luf a gaban goshi, sannan ya fitar mata da kwantaccen sajenta, tun tana karamar ta kasance sam bata da hayaniya, ka ƙoƙari don tana aji biyar ta iya karatun Hausa da turanci wan da yake da nasaba da koyawar da Diyana ke mata sannan hada ƙarin wasu yaririka tana jinsu har larabci tana ji,hakan ya saka Baba ke matuƙar ji da ita sosai yake nuna mata so fiye da yaransa wannan ya sa su Zainabu da Mahaifiyarsu ke nuna mata ƙiyayya A.lokacin da take shekara sha biyar lokacin ne kuma ta fara gane ganen abubuwa masu ban mamaki wan da take shiga cikin damuwa, sannan a duk lokacin da wani ya ɓata mata rai sai yaji a jikinsa ko kuma yayi ta rayuwarsa lura da hakan dasu Mama Khubrah su kayi suke mata kirari da Mayya har cikin gari shi yasa ko kaɗan bata da wani namiji mai cewa yana sonta duk da kyawunta kuwa,hakan be dameta ba duk da babu ranar da zata zo ta koma ga Ubangiji ba tare da ta zubar da hawaye ba, har ya zuwa yanzu.. More comments more Typing *Riamcool ce* [7/28, 7:05 PM] RIAMCOOL: *KULU* *By: RIAMCOOL* *Mikiya writter's Association* *Bismillahirrahamanirahim* *P.9&10* Kwanciyata na gyara ina ƙara jan dogon numfashi wan da nake jin ya sarƙafe, a daren ranar bacci sai dai ɓarawo ne yai nasarar ɗaukana Washe gari ko da na tashi dukkan wata damuwata nai yunƙurin ɓoyewa, kasancewar shawarar da Diyana ta bani, sannan tai Mani Alqawarin zata kasance dani a duk inda nake wannan ya saka hankalina kwanciya duk da banda yaƙinin inda za a kaini zan rayu, na tabbatarwa kaina da cewar inda zan tafi a can mutuwa zata riskeni, nakan ɓoye nayi kuka koda zan samu zuciyata ta lafa da raɗaɗin azabar da take man Bayan kwanaki biyu Talatuwa ta dawo da Shu'aibu yai maganar a shirya KULU washe gari da safe za a wuce da ita, sannan anan take ya baiwa Mamma Khubrah kuɗaɗe a ƙalla sunkai 300k wan da sai da ta ruɗe, tsabar daɗi,a washe garin ranar tun kafin Asuba ta tayar dani,na shirya Abincin mai rai da lafiya ta bani, zaune nake na tanƙwashe ƙafafuwana, hawaye cike taf a idanuwana wan da nake jin zuciyata na ƙara azalzala da wutar takaici "Mamah Khubrah" na kira sunanta a hankali hawaye na malala a kwarmin idanuwana da na'am ta amsa tana jifana da wani matsiyacin kallo wanda ya sakani haɗiye abinda ya tokare man maƙoshi Da ƙyar na iya buɗe bakina ina furta "Mama Khubrah shin wane laifi na aikata maki da kika zaɓi ki siyar dani ina ƴar Adam mai daraja da ƴanci kika zaɓi ki tozarta ni ta hanyar siyar dani,na tabbatar da don na kasance Ƴar tsintuwa ƙasƙantacciya marar daraja da ƴan........" ban idasa ba sakamakon wani gigitaccen mari da ta sakar man wan dai yai sanadiyar dakatar da duk wata kafa ta jikina na wucin gadi "KULU ke har kina da bakin magana ki sani ko mi naga damar yi da rayuwarki ba kida ƴancin bude baki kiyi magana, ke ɗin kin kasance tamkar baiwa ce a wurin to naji bani ra'ayinki Don haka na zaɓi siyar dake a can kije masarauta kiyi bautar mai digi, anyi rayuwarki ne dan kiyi bauta da wahala" na tsinkayi kalmominta wadan da nake jinsu tamkar ɗigar darma a zuciyata, tabbas na san a maganganun ta akwai ƙamshin gaskiya, na tabbatar da Baba na nan ba zai taɓa barin haka ta faru ba, sai dai mutuwa mai yankan ƙauna Hawayen da ke ambaliya a kuncina na share ina kawar da kaina daga kallon da take man, ko da gari ya waye shirye nake da bakon kayana, ƙarfe tara nasafe kamar yadda Shu'aibu ya faɗa yazo, za a wuce dani ,duk muzgunawar da gidan suke mani sai naji zuciyata ta karye wasu hawaye Masu raɗaɗi sun zubo man na rabuwa da su ko ba komai na san nan ya fiye man inda zan tafi, haka suma su Zainab ɗin ba su san in da zan tafi ba sai da Mamah Khubrah ta sanar dasu nan take yanayinsu ya sauya ko ba komai suma sun ji ba daɗi dan dai babu yanda za suyi da Mahaifiyarsu ne, da kanta Mamah Khubrah ta yafo mayafi ta rakoni wajen Shu'aibun da ke tsaye shi da BINTU wacce take ta sharɓar hawaye, duk yanda nake jin tausayin kaina sai naji nafi jin na BINTU iya Allah ya kiyaye hanya kaɗai Mamah Khubrah tai mana ba tare da ta kalleni ba ta koma a ciki kamar wasu Munafukai haka Shu'aibu yabi damu ta bayan gari wan da dukkamu babu wani wanda ke cewa wani kanzil tsakanina da BINTU [10/23, 8:52 PM] CUTIE~RIAM: https://chat.whatsapp.com/GcmnE97DYD2CazxjAdld2n *KULU* *By: RIAMCOOL* *Mikiya writter's Association* *Bismillahirrahamanirahim* *P.9&10* Kwanciyata na gyara ina ƙara jan dogon numfashi wan da nake jin ya sarƙafe, a daren ranar bacci sai dai ɓarawo ne yai nasarar ɗaukana Washe gari ko da na tashi dukkan wata damuwata nai yunƙurin ɓoyewa, kasancewar shawarar da Diyana ta bani, sannan tai Mani Alqawarin zata kasance dani a duk inda nake wannan ya saka hankalina kwanciya duk da banda yaƙinin inda za a kaini zan rayu, na tabbatarwa kaina da cewar inda zan tafi a can mutuwa zata riskeni, nakan ɓoye nayi kuka koda zan samu zuciyata ta lafa da raɗaɗin azabar da take man Bayan kwanaki biyu Talatuwa ta dawo da Shu'aibu yai maganar a shirya KULU washe gari da safe za a wuce da ita, sannan anan take ya baiwa Mamma Khubrah kuɗaɗe a ƙalla sunkai 300k wan da sai da ta ruɗe, tsabar daɗi,a washe garin ranar tun kafin Asuba ta tayar dani,na shirya Abincin mai rai da lafiya ta bani, zaune nake na tanƙwashe ƙafafuwana, hawaye cike taf a idanuwana wan da nake jin zuciyata na ƙara azalzala da wutar takaici "Mamah Khubrah" na kira sunanta a hankali hawaye na malala a kwarmin idanuwana da na'am ta amsa tana jifana da wani matsiyacin kallo wanda ya sakani haɗiye abinda ya tokare man maƙoshi Da ƙyar na iya buɗe bakina ina furta "Mama Khubrah shin wane laifi na aikata maki da kika zaɓi ki siyar dani ina ƴar Adam mai daraja da ƴanci kika zaɓi ki tozarta ni ta hanyar siyar dani,na tabbatar da don na kasance Ƴar tsintuwa ƙasƙantacciya marar daraja da ƴan........" ban idasa ba sakamakon wani gigitaccen mari da ta sakar man wan dai yai sanadiyar dakatar da duk wata kafa ta jikina na wucin gadi "KULU ke har kina da bakin magana ki sani ko mi naga damar yi da rayuwarki ba kida ƴancin bude baki kiyi magana, ke ɗin kin kasance tamkar baiwa ce a wurin to naji bani ra'ayinki Don haka na zaɓi siyar dake a can kije masarauta kiyi bautar mai digi, anyi rayuwarki ne dan kiyi bauta da wahala" na tsinkayi kalmominta wadan da nake jinsu tamkar ɗigar darma a zuciyata, tabbas na san a maganganun ta akwai ƙamshin gaskiya, na tabbatar da Baba na nan ba zai taɓa barin haka ta faru ba, sai dai mutuwa mai yankan ƙauna Hawayen da ke ambaliya a kuncina na share ina kawar da kaina daga kallon da take man, ko da gari ya waye shirye nake da bakon kayana, ƙarfe tara nasafe kamar yadda Shu'aibu ya faɗa yazo, za a wuce dani ,duk muzgunawar da gidan suke mani sai naji zuciyata ta karye wasu hawaye Masu raɗaɗi sun zubo man na rabuwa da su ko ba komai na san nan ya fiye man inda zan tafi, haka suma su Zainab ɗin ba su san in da zan tafi ba sai da Mamah Khubrah ta sanar dasu nan take yanayinsu ya sauya ko ba komai suma sun ji ba daɗi dan dai babu yanda za suyi da Mahaifiyarsu ne, da kanta Mamah Khubrah ta yafo mayafi ta rakoni wajen Shu'aibun da ke tsaye shi da BINTU wacce take ta sharɓar hawaye, duk yanda nake jin tausayin kaina sai naji nafi jin na BINTU iya Allah ya kiyaye hanya kaɗai Mamah Khubrah tai mana ba tare da ta kalleni ba ta koma a ciki kamar wasu Munafukai haka Shu'aibu yabi damu ta bayan gari wan da dukkamu babu wani wanda ke cewa wani kanzil tsakanina da BINTU, sosai muka ci uwar tafiya kafin mu fita daga cikin garimmu a lokacin mun jigata sosai da tafiya ga ƙishi ga yunwa, a haka har muka isa inda aka jejjera amalanke, kayammu muka zuba a ɗaya daga ciki sannan muka shiga, kallona BINTU tayi tuni hawaye suka wanke mata fuska tana ɗora hannayenta bisa kai ta kurma ihu tana faɗin "na higesu ni BINTU mutuwa ba ki man rana ba kin rabani da uwata da ubana yau gahi an hiyar dani" ni kaina hawayen naji suna neman zubar min amma sai dai dole nai ƙoƙarin shanyesu ina taune leɓena na ƙasa, tare da furta sunayen Allah Muna ji muna gani haka muka dinga tafiya har Allah ya iso damu cikin birni a lokacin ne Shu'aibu ya siya mana Abinci wanda da ƙyar muke tura shi ,daga nan mota muka hau wacce za ta kaimu har garin OYO tafiya bata wasa muka yi ba, dan Sallah ce kaɗai ke tsayar damu, sosai na jigata naji cikina ya juye na fara zazzaga Amai tamkar zan amayar da hanjin cikina, da tausayi Bintu ta dinga yi man sannu ɗaga kaina kawai na iya yi, wani dogon tsaki Shu'aibu ya ja yana furta "dan uwar ki lashe aman da kikayi kin wani ɓatawa mutane mota, ki lashe ko na yi miki lilis a motar nan" hawaye tuni suka ƙara jiƙa man fuska ina furta "kayi haƙuri idan an fita zan gyara motan amma bazan iya lashewa ba" ƙwafa kawai yaja yana juyawa, ba da jimawa ba muka sauka in da Bintu ce ta gyara inda nayi Wa amai, lkcn dare har yayi, hakan yasa Shu'aibu cewar mu biyo shi,zuciyata cike da ɗar ɗar muka bisa tare da hawan adai daita ya kaimu wani guri, ɗan ƙaramin gida ne Shu'aibu ya kaimu wan da cikinsa ɗaki ɗaya ne kacal, gashi ana tsuga ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, shiga mu kayi ɗakin muna muzurai dan tsoro, wani kalar kallo Shu'aibu ya bimu dashi yana murmushin gefen baki, a hankali ya ƙara so gabanmu yana saka hannunsa yana shashafa mu tare da lumshe idanuwa, "Innalillahi miye haka ka daina dan Allah babu kyau" na faɗa ina girgiza masa kai hawaye na zuba "Zan ci uwar ki kika sake magana, wllhy dole ne na taste ɗinku kafin na kaiku gidan arnaye waɗanda basa dungura goshinsu a gabas na tabbatar duk sai sun dinga kashe dare daku, to nima yau zan kashe arna daku" ya faɗa yana washe baki, ganin yana taɓa dukiyar Fulani su, kuka Kulu da Bintu suka saka yayin da sukai ƙoƙarin ƙwatar kansu amma sam sun gaza, wani kalar ihu suka ji Shu'aibu ya fasa yana ja da baya, nan take idanuwansa suka fara kakkafewa ya faɗi, wani kalar ajiyar zuciya na saki ina murmushi tare da furta "Diyana" banji an amsa ba hakan ya sakani sulalewa ƙasa ina kwanciya bacci na ɗibata, sai da gari ya ɗan fara haske sannan na buɗe idanuwana bakina ɗauke addu'a Bintu na tayar muka fita sai dai babu ruwa hakan ya saka muka ɗauki ruwan roba mu kayi arwallah, har muka ƙarashe sallah Shu'aibu bai tashi ba, nan take gabana ya faɗi na fara tunanin karfa ace Diyana tayi halin nata ina cikin tunani haka muka ji yana tari tare da miƙewa, yana hamma, ruwan ya ɗauka yana fita ya wanke fuska da baki, kallomu yai yandaa faɗin "idan za mu fita ya zama wajibinku ku cire hijabbanku, sannan inda zan kaiku ku kiyaye wani ya gano cewar ku musulmai ne, idan aka gano tabbas kun kaɗe," shiru mu kayi yana faɗin mu tashi mu fita, Hijjabin muka cire wasu hawaye Masu zafi na biyo kuncina "ya Allah" na furta a hankali tare da tunanin wane shafin kundin ƙaddarar zan buɗe a yanzu, baya ga cikakken littafin ƙaddarar dana ƙarasar a baya, tamkar wacce aka zarewa lakka haka na bi bayansa muna fita wata motar muka sake hawa wacce kwana mu ɗaya da yini sannan muka sauka, muna sauka, muka hau a dai daita ya kaimu wani waje, inda ga mutane nan da dama ko wane a dudduƙe wan da mafi akasari su duk ƴam mata ne, layi Shu'aibu yabi tare da umartar mu durƙusa mu duƙar da kawunnanmu, layi ne yazo kan Shu'aibu nan take aka gama cinikummu ya tafi, dukkamu durƙushe muke ga wata uwar rana da ake yi wanda tuni muka fara gumi zufa na tsiyayya mun sha baƙar wahala kafin azo da wata ƙatuwar mota ta Alfarma wacce tun da nake ban taɓa ganin kalarta ba, cikin ta aka zuzzuba mu muka fara ɗaukar hanya, manmanyan gidaje muka dinga ketawa wan da a iya rayuwata ban taɓa tunani da akwai kalar su a duniya, nan na shafa'a wajen kallo, wani danƙareran get muka ga an shiga ciki wan da nan take zufa ta fara yanko man gabana ya tsananta faɗuwa ,..................... *RIAMCOOL ce* Writer of *RUSHEWAR RAYUWA* *BAYAN WUYA* *ANYA UBA NE* And now *KULU* [10/23, 9:00 PM] CUTIE~RIAM: https://chat.whatsapp.com/GcmnE97DYD2CazxjAdld2n *KULU* *By: RIAMCOOL* *Mikiya writter's Association* *Bismillahirrahamanirahim* *P.9&10* Kwanciyata na gyara ina ƙara jan dogon numfashi wan da nake jin ya sarƙafe, a daren ranar bacci sai dai ɓarawo ne yai nasarar ɗaukana Washe gari ko da na tashi dukkan wata damuwata nai yunƙurin ɓoyewa, kasancewar shawarar da Diyana ta bani, sannan tai Mani Alqawarin zata kasance dani a duk inda nake wannan ya saka hankalina kwanciya duk da banda yaƙinin inda za a kaini zan rayu, na tabbatarwa kaina da cewar inda zan tafi a can mutuwa zata riskeni, nakan ɓoye nayi kuka koda zan samu zuciyata ta lafa da raɗaɗin azabar da take man Bayan kwanaki biyu Talatuwa ta dawo da Shu'aibu yai maganar a shirya KULU washe gari da safe za a wuce da ita, sannan anan take ya baiwa Mamma Khubrah kuɗaɗe a ƙalla sunkai 300k wan da sai da ta ruɗe, tsabar daɗi,a washe garin ranar tun kafin Asuba ta tayar dani,na shirya Abincin mai rai da lafiya ta bani, zaune nake na tanƙwashe ƙafafuwana, hawaye cike taf a idanuwana wan da nake jin zuciyata na ƙara azalzala da wutar takaici "Mamah Khubrah" na kira sunanta a hankali hawaye na malala a kwarmin idanuwana da na'am ta amsa tana jifana da wani matsiyacin kallo wanda ya sakani haɗiye abinda ya tokare man maƙoshi Da ƙyar na iya buɗe bakina ina furta "Mama Khubrah shin wane laifi na aikata maki da kika zaɓi ki siyar dani ina ƴar Adam mai daraja da ƴanci kika zaɓi ki tozarta ni ta hanyar siyar dani,na tabbatar da don na kasance Ƴar tsintuwa ƙasƙantacciya marar daraja da ƴan........" ban idasa ba sakamakon wani gigitaccen mari da ta sakar man wan dai yai sanadiyar dakatar da duk wata kafa ta jikina na wucin gadi "KULU ke har kina da bakin magana ki sani ko mi naga damar yi da rayuwarki ba kida ƴancin bude baki kiyi magana, ke ɗin kin kasance tamkar baiwa ce a wurin to naji bani ra'ayinki Don haka na zaɓi siyar dake a can kije masarauta kiyi bautar mai digi, anyi rayuwarki ne dan kiyi bauta da wahala" na tsinkayi kalmominta wadan da nake jinsu tamkar ɗigar darma a zuciyata, tabbas na san a maganganun ta akwai ƙamshin gaskiya, na tabbatar da Baba na nan ba zai taɓa barin haka ta faru ba, sai dai mutuwa mai yankan ƙauna Hawayen da ke ambaliya a kuncina na share ina kawar da kaina daga kallon da take man, ko da gari ya waye shirye nake da bakon kayana, ƙarfe tara nasafe kamar yadda Shu'aibu ya faɗa yazo, za a wuce dani ,duk muzgunawar da gidan suke mani sai naji zuciyata ta karye wasu hawaye Masu raɗaɗi sun zubo man na rabuwa da su ko ba komai na san nan ya fiye man inda zan tafi, haka suma su Zainab ɗin ba su san in da zan tafi ba sai da Mamah Khubrah ta sanar dasu nan take yanayinsu ya sauya ko ba komai suma sun ji ba daɗi dan dai babu yanda za suyi da Mahaifiyarsu ne, da kanta Mamah Khubrah ta yafo mayafi ta rakoni wajen Shu'aibun da ke tsaye shi da BINTU wacce take ta sharɓar hawaye, duk yanda nake jin tausayin kaina sai naji nafi jin na BINTU iya Allah ya kiyaye hanya kaɗai Mamah Khubrah tai mana ba tare da ta kalleni ba ta koma a ciki kamar wasu Munafukai haka Shu'aibu yabi damu ta bayan gari wan da dukkamu babu wani wanda ke cewa wani kanzil tsakanina da BINTU, sosai muka ci uwar tafiya kafin mu fita daga cikin garimmu a lokacin mun jigata sosai da tafiya ga ƙishi ga yunwa, a haka har muka isa inda aka jejjera amalanke, kayammu muka zuba a ɗaya daga ciki sannan muka shiga, kallona BINTU tayi tuni hawaye suka wanke mata fuska tana ɗora hannayenta bisa kai ta kurma ihu tana faɗin "na higesu ni BINTU mutuwa ba ki man rana ba kin rabani da uwata da ubana yau gahi an hiyar dani" ni kaina hawayen naji suna neman zubar min amma sai dai dole nai ƙoƙarin shanyesu ina taune leɓena na ƙasa, tare da furta sunayen Allah Muna ji muna gani haka muka dinga tafiya har Allah ya iso damu cikin birni a lokacin ne Shu'aibu ya siya mana Abinci wanda da ƙyar muke tura shi ,daga nan mota muka hau wacce za ta kaimu har garin OYO tafiya bata wasa muka yi ba, dan Sallah ce kaɗai ke tsayar damu, sosai na jigata naji cikina ya juye na fara zazzaga Amai tamkar zan amayar da hanjin cikina, da tausayi Bintu ta dinga yi man sannu ɗaga kaina kawai na iya yi, wani dogon tsaki Shu'aibu ya ja yana furta "dan uwar ki lashe aman da kikayi kin wani ɓatawa mutane mota, ki lashe ko na yi miki lilis a motar nan" hawaye tuni suka ƙara jiƙa man fuska ina furta "kayi haƙuri idan an fita zan gyara motan amma bazan iya lashewa ba" ƙwafa kawai yaja yana juyawa, ba da jimawa ba muka sauka in da Bintu ce ta gyara inda nayi Wa amai, lkcn dare har yayi, hakan yasa Shu'aibu cewar mu biyo shi,zuciyata cike da ɗar ɗar muka bisa tare da hawan adai daita ya kaimu wani guri, ɗan ƙaramin gida ne Shu'aibu ya kaimu wan da cikinsa ɗaki ɗaya ne kacal, gashi ana tsuga ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, shiga mu kayi ɗakin muna muzurai dan tsoro, wani kalar kallo Shu'aibu ya bimu dashi yana murmushin gefen baki, a hankali ya ƙara so gabanmu yana saka hannunsa yana shashafa mu tare da lumshe idanuwa, "Innalillahi miye haka ka daina dan Allah babu kyau" na faɗa ina girgiza masa kai hawaye na zuba "Zan ci uwar ki kika sake magana, wllhy dole ne na taste ɗinku kafin na kaiku gidan arnaye waɗanda basa dungura goshinsu a gabas na tabbatar duk sai sun dinga kashe dare daku, to nima yau zan kashe arna daku" ya faɗa yana washe baki, ganin yana taɓa dukiyar Fulani su, kuka Kulu da Bintu suka saka yayin da sukai ƙoƙarin ƙwatar kansu amma sam sun gaza, wani kalar ihu suka ji Shu'aibu ya fasa yana ja da baya, nan take idanuwansa suka fara kakkafewa ya faɗi, wani kalar ajiyar zuciya na saki ina murmushi tare da furta "Diyana" banji an amsa ba hakan ya sakani sulalewa ƙasa ina kwanciya bacci na ɗibata, sai da gari ya ɗan fara haske sannan na buɗe idanuwana bakina ɗauke addu'a Bintu na tayar muka fita sai dai babu ruwa hakan ya saka muka ɗauki ruwan roba mu kayi arwallah, har muka ƙarashe sallah Shu'aibu bai tashi ba, nan take gabana ya faɗi na fara tunanin karfa ace Diyana tayi halin nata ina cikin tunani haka muka ji yana tari tare da miƙewa, yana hamma, ruwan ya ɗauka yana fita ya wanke fuska da baki, kallomu yai yandaa faɗin "idan za mu fita ya zama wajibinku ku cire hijabbanku, sannan inda zan kaiku ku kiyaye wani ya gano cewar ku musulmai ne, idan aka gano tabbas kun kaɗe," shiru mu kayi yana faɗin mu tashi mu fita, Hijjabin muka cire wasu hawaye Masu zafi na biyo kuncina "ya Allah" na furta a hankali tare da tunanin wane shafin kundin ƙaddarar zan buɗe a yanzu, baya ga cikakken littafin ƙaddarar dana ƙarasar a baya, tamkar wacce aka zarewa lakka haka na bi bayansa muna fita wata motar muka sake hawa wacce kwana mu ɗaya da yini sannan muka sauka, muna sauka, muka hau a dai daita ya kaimu wani waje, inda ga mutane nan da dama ko wane a dudduƙe wan da mafi akasari su duk ƴam mata ne, layi Shu'aibu yabi tare da umartar mu durƙusa mu duƙar da kawunnanmu, layi ne yazo kan Shu'aibu nan take aka gama cinikummu ya tafi, dukkamu durƙushe muke ga wata uwar rana da ake yi wanda tuni muka fara gumi zufa na tsiyayya mun sha baƙar wahala kafin azo da wata ƙatuwar mota ta Alfarma wacce tun da nake ban taɓa ganin kalarta ba, cikin ta aka zuzzuba mu muka fara ɗaukar hanya, manmanyan gidaje muka dinga ketawa wan da a iya rayuwata ban taɓa tunani da akwai kalar su a duniya, nan na shafa'a wajen kallo, wani danƙareran get muka ga an shiga ciki wan da nan take zufa ta fara yanko man gabana ya tsananta faɗuwa ,..................... *RIAMCOOL ce* Writer of *RUSHEWAR RAYUWA* *BAYAN WUYA* *ANYA UBA NE* And now *KULU* [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso...* *Bismillahirrahamanirrahim* *P.11&12* Sunayen Allah na fara jerowa da nufin zuciyata ta samu salama daga bugun data fara man, ban ida razana ba sai da naga wani baban get ɗin masarautar mai tambarin wani baƙar halitta da ƙaho nan take gabana ya ƙara yankewa yana faɗuwa, sosai nake jin tamkar na taɓa rayuwa a masarautar nan, nake ga wasu munanan abubuwan na dawo mani, wan da tun a wancan ƙarnin ya faru, Wata muguwar tsanar masarautar ce tai man dirar mikiya , nayi nisa a cikin tunani naji ana faɗin "Iwọ jẹ obinrin dudu" (ke baƙar baiwa fito) naji an faɗa da wata ƙatuwar murya wacce ta saka jikina kyarma sbd tsoro, jikina a mace na fito nabi layi muna tafiya, tamkar wasu dabbobi maras galihu haka aka mayar damu, sbd duka Kafin mu ƙarasa ya zuwa get ɗin ƙarshe, sosai na jigata sbd bulalar da aka shaɗa man, wajen ya fashe ga zafin rana, numfarfashi kawai nake mayarwa ina jera sunayen Ubangiji Muna kaiwa ƙarshen get ɗin aka umarce mu da mu zube a ƙasa, zubewa mu kayi ko wane kansa a ƙasa, mun fi ƙarfi 2 hours before a fara kirawo mu ko wane ana kaisa ya zuwa inda zai zauna, waje guda aka haɗamu nida Bintu, daga nan ma haka muka ci uwar tafiya kafin mu isa sashen bayi, wajen uwar bayi aka kaimu, wacce ta kasance itama yare ɗin ce, kasancewar ina jin yarensu da kuma turanci shi yasa abin bai man wahalar gane zancen ta ba, kan cewar za ta ƙara ni a cikin hadiman uwargidan sarki, wanka muka fara yi sannan muka ci Abinci, ganin marece yayi sosai ya tabbatar man da cewar la'asar ta wuce sosai hakan ya bani damar ɗauro Arwallah, ɗakin da muke ciki muka kulle sannan muka samu muka fara ramuwar sallar dake kanmu, a daren ma haka mu ka kulle muka yi sallar, kasancewar mun kwaso uwar gajiya ya saka mu kwanciya da wuri, baccin wahala na ɗaukar mu Washe gari tunda sassafe muka ji bugun ƙofa tamkar za a ɓallata, tashi nai na buɗe ina kallon Uwar bayi dake faɗin "wash your face and follow me" da ok mah na amsa ina shiga Toilet ɗin na ɗauro Arwallah sai dai ganin Uwar bayi a wajen ya saka jikina yin sanyi ganin ba zan samu damar yin sallar ba Kaya ta bani, Riga ja zane baƙi tace na saka daga yanzu su zamto cewar sune kayan Sakawata Juyawa nayi zan shige Toilet na saka naji tana faɗin "where are you going with the things in your hand" "I'll wear it". na faɗa, zaro ido waje tai tana faɗin "It's a change of clothes and you have to go Toilet"shiru nayi ina zare ido kar ta gano ni bahaushiya ce, dan Shu'aibu sai da ya gargaɗemu akan mu nuna musu mu ba hausawa ba ne "Which tribe are you, the ozo or ogboni tribe" na tsinkayi muryarta wacce gabana ya faɗin, yawun tsoro na haɗiye ina furta Ogboni girgiza kai tayi tana taɓe baki, a kunyace na sauya kayan a gabanta, fita tayi na bita a baya wanda naga muna ƙara tinkarar get Wanda nabi da kallo tsabar kyansa tamkar wata sokuwa, "da gani da zallar gold aka ƙera shi" na faɗa a zuciyata jigajigan securities, ne ke gadinshi kasancewar sun san uwar bayi shi yasa bamu samu wahalar shiga, ba , daskarewa waje guda nayi ganin wani hamshaƙin waje daya bayyana, har tuntuɓe na kusa yi, tsabar kallo, ban ida tsurewa ba sai da muka shiga wani hamshaƙin wuri daya saka brain ɗina dakatawa da aiki, ganin zallar gwala-gwalai ne ke walwali a wajen, taɓani uwar bayi tayi hakan ya saka tunanina dawowa, tamkar raƙumi da akala haka na dinga bin uwar bayi harya zuwa wani babban Falo wanda ya fi na can da haɗuwa kamar wata sokuwa haka na zama wajen kallo kafaɗata da uwar bayi ta buga ne ya saka hayyacina dawowa ya zuwa gangar jikina, wani yawu na haɗiye ganin yadda uwar bayin ta zube a ƙasa tana mai taɓa wata matashiyar budurwa wacce a ƙalla ba zata wuci 23 yrs ba, tsawar da naji uwar bayi ta doka man akan ban zube a ƙasa ba ya sakani zubewa kamar yanda tayi jikina na karkarwa, ba tare da matashiyar budurwar nan tayi mgn ba ta ɗora ƙafafuwan ta ya zuwa gadon bayammu tana karkaɗasu, tamkar na fasa ihu tsabar takaici, hawayen da naji na ƙoƙarin zubo man na danne, sbd na tabbatar a haka zan ƙarashe rayuwata cikin ƙunci da takaicin duniya, tafi ƙarfin 15 minute sannan ta sauke tana kallommu a yatsine, Tashi mu kayi sannan tai mani nuni da hannu alamar na taso, miƙewa na matsa kusa da ita hannayena ta ɗora ya zuwa kafaɗunta alamar nai mata tausa, banbaranƙwai naji abu na fara mata a hankali tana lumshe idanu, duk yanda nai ƙoƙarin danne hawayen dake ƙoƙarin zubo man sai da na kasa, ba tare da na bari wani ya gani ba na sharesu na ci gaba da aikina, kallona uwar bayi tayi tana faɗin "Alamu sun nuna ki zauna a baiwar gimbiya Sontum ,daga yau duk wani hidima kece za kina yi mata, sannan ki faɗa mana sunanki" cikin ɗan razani na faɗa musu Josina amma ana kirana da KULU,ba tare da wani yace ƙala ba Uwar bayi ta wuce, ni kuwa bayan na gama mata tausa ne ta haɗani da wata baiwa wacce tai man bayanin abubuwan da zan dinga mata, hankalina bai tashi sai da naji wai har kaya nice zan saka mata, a lkcn ihu ne kaɗai ban fasa ba, haka naja na tsaya a bayanta duk idan ta buƙaci wani abun nice ke yi mata,a yinin ranar sosai nasha baƙar azaba wacce ko maƙiyina bana yiwa fata [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: https://chat.whatsapp.com/GcmnE97DYD2CazxjAdld2n *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso* *Bsmllhrhmrhm* *P.13&14* Tamkar na fasa ihu tsabar zullumi haka nake ji Addu'a ta bata wuci Allah ya sa tace na tsaya daga bakin ƙofar shiga, sai dai Addu'a tawa bata karɓu ba, haka na shiga wan da babu abinda ke tashi a Baban Falon idan banda ƙamshi ga wani lallausan Cafet da nake jin ƙafafuwana luntsume ciki, ina son ɗago da idanuwana, na basu abinci amma babu dama tsabar kar nayi laifi, jiki a ɗaɗɗare na faɗi nayi gaisuwa wan da babu wanda ya kulani "What are you doing here?if you don't come and work as a slave" naji furucin wata dakakkiyar murya ta mace wacce ta sakani haɗiye wani yawu ina kallonta da Alamu dai itama Baiwar ce sai dai amma tana da iko a kan Bayi dubana nakai gun Sontum sai dai naga sam bata a wajen wannan ya nuna cewar ta shige ya zuwa ciki ajiyar zuciya na saki ganin ban shiga ba, dama sam ban sa haɗuwa da mutanen ciki musamman mai zuciyar fir'auna ABIODUN da naji suna faɗi don nidai harga Allah tun kafin na saka sa a idona tsoronsa ya cika man zuciya da fargabar haɗuwa dashi duk gyaran da Babban Falon yasha sai da ta sakani sake masa wani gyaran, Fruit ta sakani yankawa Ina gamawa na kai mata "go inside and reach the King's Lady " naji furucinta wan da ya sakani zaro idanuwa ina ɗaukar Fruit ɗin ya zuwa ciki a hankali na kutsa kaina ina duƙar da kaina ƙasa wan da tun daga bakin ƙofar shiga ya kasance duk barrori ne, masu hidima yanayin da naji bugun zuciyata na hauhawa da kuma ficewar tsoron da yai man ƙawanya azuci ya sakani ɗago da manyan idanuwana na saukesu ya zuwa wata babbar mace wacce taci ado na ban mamaki haɗaɗɗiyar bayeraba mai madarar Izza cike da mulki , kallo guda za kai mata ka tabbatar ita ce matar sarki Sontum ce liƙe a jikinta wan da zaka tabbatar ita ce Mahaifiyarta a hankali na faɗi nayi gaisuwa na ajiye mata Fruit ɗin a gabanta, *Ɓangare guda kuwa* Tun lokacin da ABIODUN ya dawo ya zuwa Masauratarsa dukkan wani sirri na masarautar JOHAAN ya kawo wa Masauratarsa da kuma shirya Babban tuggu na gani sun rushe masarautar JOHAAN da dawo da mulkin ya zuwa gare su, Babbar Fada ce ta Alfarma wacce ta gaji da haɗuwa tsabar kyau sai dai duba ɗaya za kayi wa Mutanen cikinta ka tabbatar da akwai damuwa data shimfiɗu akan fuskokinsu musamman ma Sarki Adewale femi , zufar data tsatstsafo mishi ya share yana faɗin “Ìyọnu àjálù wo ni yóò ṣẹlẹ̀ ní ìjọba Handash,(wace musiba ce ke tunkaro Handaash) na tabbatar jinin JOHAAN na a cikin masarautar nan tun ranar da Bugun zuciyana ya sauya numfashina ke cikin gargada na tsoron faruwar abinda Soluwole ya faɗa, Mo n sa fun isẹlẹ naa, ABIODUN gbọdọ kuro ni Ijọba yii (ina gudun faruwar abun ya zama dole ne ABIODUN ya bar masarautar nan") dukkan mutanen cikinta sosai suka girgiza da Kalaman sarkin Adewale femi Eyin Oba wa Adewale, e jeki a so pato nipa ipo ti e ba n kuro ni ABIODUN lo si ijoba yii, e ranti ABIODUN ni ohun ija wa pataki, ti olori ilu Handaash si dabi Abin Buta Soluwole. (Ya Sarkimmu Adewale Femi ka ƙara jiɓantar lamarin kana ganin barin ABIODUN a masarautar nan mafita ce, ka tuna cewar ABIODUN shine makamin masarautar JOHAAN ,kuma jigo a gare ta shi ɗin tamkar Abin Bauta Soluwole muke ganinsa" wazirinsa ya faɗa tare da duƙar da kansa ƙasa Shiru yai yana nazartar maganar waxirin nasa tabbas gaskiya ya faɗa Tun faɗowar ABIODUN ya zuwa doron duniya ya tabbata dashi ɗin jigo ne ga masarautar sa, ko kaɗan bai son ƙaddarar ABIODUN ta juye ya zuwa yadda aka faɗa masa kuma tabbas ya san da zata faru ɗin amma koda rayuwarsa zai rasa ba zai taɓa bari hakan ya faru akan ABIODUN ba, tabbas bokansa ya faɗa masa cewar Jinin Handaash na a cikin masarautar nan, sosai idanuwansa sukai ja sannan shatin jijiyoyin kansu su kayi ruɗu ruɗu tsabar tashin hankalin da yake ciki Jin kansa na neman tarwatsewa ya saka sa sallamar mutanen fadar, tun lokacin da ya shiga sosai abubuwa ke dawo masa, wanda yake jin babbar muguwar tsanar masarautar JOHAAN na masa ƙawanya a zuci shigowar Boluwatife ya saka shi mayar da hankalinsa ya zuwa kanta wacce ta gaji da kyau tsabar haɗuwa, a hankali ta zauna kusa dashi tana masa murmushin da tasan na kashe masa zuciya sannan ya bayyanar mata da sirrin dake ransa, bayan wasu ƴan Mintuna ta ɗago da manyan idanuwanta tana kallonsa wanda take son gano wani abun cikin yarensu take faɗin "Ya shugaba majiɓancin lammuran Masarautar JOHAAN Baba ga yarima ABIODUN majiɓancin lamurran Handaash tabbas da akwai damuwa a ranka, sannan zan so ka bayyanar man da ita, inji idan da akwai mafita" ta faɗa cikin sigar ladabi da daddaɗar murya mai kwantar da ran Sarki Adewale Femi tamkar wanda ke son dama a tayar da zancen haka ya miƙe yana saka idanuwan nasa a cikin na matar tasa, "Boluwatife tabbas ina cikin damuwa sannan dake kaɗai zan iya shawara a cikin lumana ki samar man da mafita, da akwai babbar musiba a Masarautana ko kin san da cewar da Akwai Jinin Handaash a masarautar nan,a da na yanke Shawarar ABIODUN ya bar masarautar nan na tsawon wasu shekaru masu tarin yawa gudun faruwar abinda aka faɗa a wancan ƙarnin" ya faɗa da tsantsar damuwar dake cin ransa Wani shaiɗanin murmushi ta saki wanda bai fito a bayyane ba sai ma tarin damuwar data shimfiɗa a kan fuskar nata tana faɗin " tabbas ka kawo Shawara sai dai da akwai......" bata idasa ba sakamakon maganar daya fara yi " na sani Boluwatife ABIODUN ɗina shine jigon masarautar nan bai cancanci ya barta ba ABIODUN ɗina shine cikar kamalar Masarautar Handaash sannan makami Babban Jigo, dole mu canza shawara" murmushi ta saki dukda ba hakan taso ba, ta ɗan jima before ta miƙe ta fita barorinta na take mata baya har izuwa Sashen ta, tun da ta shiga ta faɗa a babban gadon nata tana lumshe idanuwanta tare da shafa cikin jikinta daya bayyana Me ya za har yanzu ta gaza cimma ƙudirinta a wannan karin ba za tayi ƙasa a guiwa ba ya zama dole tai ƙoƙarin ƙara cusawa Oba Adewale Femi son fitar da ABIODUN a masarautar nan wannan ce damar ta , *LONDON* *ABIODUN* Kwance yake a bakin Swimming pool Ya lumshe Manyan idanuwansa ya kai a ƙalla ten minutes before ya waresu a hankali yana mai ɗan yatsina fuska ganin kallon da wata Baturiya ke wa haɗaɗɗiyar Baƙar fatarsa wanda tsabar kyau har wani sheƙi take tana walwali from his navel or wherever a murmuɗe ganin tana ƙara bin His broad chest and eyes are wide open ya saka sa jan Dogon tsaki yana faɗin "Witch" Tamkar hadarin gabas haka ya saƙe ɗaure fuskarsa yana miƙewa nan take cikakkiyar ƙirarsa ta bayyana, dogon kitson daya sha ya zubo a dokin wuyansa, Headphone nasa ya ɗauka yana liƙawa a kunne ya fara tafiya cikin gadara da cikakkiyar Izza interesting what to look at, tamkar haɗin Baki Ƴam matan turawan suka haɗa baki wajen furta "wow, handsome man" Ba tare da ya juyo ya kalli ɗaya daga cikinsu bcox shi sam ma bai san da su sbd Headphone ne a kunnesa yana jin waqar Naira Marley................. *RIAMCOOL ce* Love U all my Habibties💖😻 [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *By RIAMCOOL* Mikiya writer's Asso....... P.15&16 Haɗaɗɗen masaukinsa ya nufa yana zama bisa ɗaya daga cikin kukerun Falon tare da lumshe Manyan idanuwansa yana ɗan kaɗa ƙafa before ya cire Headphones ɗin yana ware idanuwansa akan phone din dake ringing, hannu yakai yana ɗauka a hankali yai picking duba ɗaya za kayi masa ka san tabbas kiran mai muhimmanci ne duba da yadda ya tattara nutsuwarsa da kuma yalwataccen murmushin dake ɗauke a kyakkyawar fuskarsa har yai sanadiyyar lotsawar kumatunsa wan da ba ƙaramin sihirtaccen kyau yai ba "Hello" ya faɗa to drown wani ajiyan zuciya mai martaba Adewale Femi ya saki daga ɗayan ɓangaren yana mai lumshe idanuwansa jin muryan Yaron nasa "ABIODUN how are you? hope you are in good health," ya faɗa da murmushin karfin hali dake ɗauke a fuskarsa "Yes, Daddy, I hope you are safe, but I heard your voice in worry, I hope there is nothing wrong with you" ABIODUN ya faɗa da ɗan damuwa,murmushi mai sauti ya saki yana faɗin "Yes, ABIODUN, I just want you to leave LONDON and come, there is something important, like this help" Oba Adewale Femi ya faɗa da ɗan damuwa da kuma rashin son maganar ABIODUN yace "Daddy I will come but tell him your worries (Daddy zanzo amma ka faɗa man damuwarka") "nothing ABIODUN" Oba Adewale Femi ya faɗa da ƙarfin hali tare da katse kiran yana sauke ajiyar zuciya wasu hawaye Masu raɗaɗi na zubo masa, na tunawa da shawarar da ya yanke na fitar da ABIODUN a cikin Masarautar sa A ɓangaren ABIODUN ma haka ya shiga cikin damuwar yana tunanin ko wani abu ya faru da masarautar nasu da har Mahaifin nasa ya gaza furta masa, nan take yaji zuciyarsa ta gaza nutsuwa , kamar ya kira Mahaifiyarsa sai kuma ya fasa ganin ko ya kira ba Lallai ace ta san sirrin Oba Adewale Femi ba,kyawawan lips nasa na ƙasa ya jiza yana shafa manyan kitson kansa tare da lumshe Manyan idanuwansa he went into thinking abubuwa da dama, da ƙyar ya samu ya rintsa a daren washe gari tun da safe ya sa aka shirya masa private jet,ya zuwa Nigeria garin OYO, A hankali yake bin matattakalar jirgin yana saukowa cikin nutsuwa da jarumta, da kuma cikakkiyar Izza mai yawo a jininsa,wan da idanuwan Mutane suka fara yawo kansa Musamman ganin prince ABIODUN, ganin yanda idanuwan mutanen ke yawo a kansa ya saka shi jan ƙaramin tsaki yana kawar da kansa gefe guda, kai tsaye wajen jiga_jigan motoci na Alfarmar da aka shirya masa ya nufa tare da shiga ɗaya daga cikin cars ɗin hakimcewa yai a Back sit yana duba watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa tare da ɗan ciza lips nasa wanda ya zame masa Al'ada kai tsaye Masauratar Handaash su ka yiwa tsinke wan da a duk daƙiƙa ɗaya zuciyar ke masa wani irin bugu wan da bai san dalilinsa ba, *KULU* ni kuwa tun lokacin da na shiga wajen uwargidan sarki nake Allah yasa na fito lafiya ba tare da nayi laifi ba sai dai Addu'a ta bata ci ba domin kafin na fito sai da nasha tafikan uwargidan sarkin har biyu akan ta kamani wai ina kallonta, sannan ta bani aiki mai tsanani akan na dawo ɓangaren ta nice zan dinga gyara ko ina da duk wani abinci tare wai da kular mata da Babban ɗan ta wato Prince ABIODUN lokacin da tace hakan hantar cikina ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba, dan harga Allah ban son abinda zai haɗa ni da mugun ɗan ta kamar yanda naji ana faɗa, bata barni haka ba sai da ta sakani nai aikin da na jigata ba kaɗan tunda na shigo ɗakin nake ta huttai da nishi tsabar gajiya ga sallolin dake kaina, ga babban tashin hankalina mutane na a ɗakin domin a ɗakin Bayin gidan aka Maido mu mu kusa 8 ne a ciki wanda kowa a takure yake bacci, a boye na yi Arwallah na fita daga Bayan ɗakin inda na tabbatar da ba za' a kamani ba na yi Sallolin before na dawo ɗakin , ina rarraba idanuwana don naga Bintu ganinta a kwance ya sakani tunkarar inda take ina ɗaka mata duka a baya tare da ƴar dariya Are you tired? hararana ƙasa _ƙasa tai tana cewa "ke Hegiya Alqur'ani kin san ba jin harhen nasaran nan nake ba ki man harhena kawai ni ban iya harhen kahurai ba a to" ta faɗa tamkar mai raɗa ƴar dariya nai ina kwanciya tare da furta " Bintu kin gaji ne" hawayen dake maƙale a idanuwanta ta samu tana matsowa tare da furta "wallahi KULU masarautar nan akwai zalunci da yawa ko kin san......." sai kuma tai shiru kuka yaci ƙarfin ta ƙasa ƙasa, gani idanun mutanen ɗakin ya fara dawowa ɗakin ya sakani kama hannunta ina miƙar da ita zuciyana a cunkushe da damuwa ganin hawayen Bintu wanda nake ji har a cikin raina, fita mu kayi na zaunar da ita ina kafeta da idanuna ni kaina ji nake da zan iya kukan babu abin da zai hanani fashewa dashi ," haba Bintu ki yi shiru da huƙurin cinye jarabawar mu, haka Allah ke son ganimmu ba Wai don bai sommu ba, don ita ƙaddara zanen zabo ce duk wayonka baka isa ka tsallake ta ba, Bintu kiyi duba dani wace rayuwar ce ban gani ba?ni ɗin nan ko ɗumin Mahaifiyata ban ji ba, ban san asalin wace ni ba shin ni ƴar waye ban sani ba , shin Ƴar shege ko Ƴar sunan? ban sani ba Bintu, naga kyara da tsanana cikin Al:umma naga ƙuncin rayuwa wacce ban san iya adadin ta ba, Allah ya jarabceni ta hanyoyi da dama" na faɗa wasu ƙwallar takaicin rayuwa na zubar min shiru Bintu tayi tana share hawayenta tace "Kulu tabbas kinga rayuwa,na haƙura na karɓi ƙaddarar da Ubangiji ya ɗora man" Murmushin karfin hali na sakar mata ina faɗin "faɗa min abinda ke damunki da har kika kasa faɗa man" "KULU ina cikin matsananciyar damuwa ana so a keta man Haddi a masarautar nan daga mazan har matan wallahi da idona jiya naga wani abu ita waccan ochuchuwa take kowa? suna iskanci da wani mugun bafaden nan Ayomide kin sannin ban iya rufi tsinannan katsalanda na ya jawo min, hine na jira suka gama, nai masu maganar Ƙurame akan cewar na ga suna iskanci kuma sai na faɗa, to hine suka kama man dariya, Ayomide harda taɓa ƙirjina ya tsotsi bakina ta ƙarfi, sannan Ochuchuwa ta dinga taɓa man ƙirji har na gaza ƙwatar kai na, suka gama tattaɓeni,nayi kuka ban faɗa miki ba, to hine yau Ochuchuwa ta gayyato qawayenta suka riƙeni suna tattaɓa ni, dan har kayana suka cire man haihuwar uwata suka ganni za suyi man fyaɗe Allah ya bani sa'a na kuɓuce musu" ta ƙarashe zancen cikin kuka da ƙunar rai ɗan jim nayi ina rintse idanuwana,gabana na faɗuwa jin furucin Bintu, haƙuri na bata tare da rarrashinta sannan ta ƙara jajircewa wajen riƙe mutuncinta , wan da sosai na girgiza da lamarin gidan Sarautar, sannan na tsunduma Tunanin DIYANA wacce na rabu da ganinta ban san dalilin ƙin ziyartana ba, hawaye naji sun ƙara cika mun ido na tabbatar da Diyana ma na rasata "ba nida kowa yanzu?" na tambayi kaina wan da ban san maganar ta fito ba sai da naji Bintu na faɗin "KULU kina dani mana, kamar yanda ban da kowa sai ke haka kema bakida kowa sai ni, mu haɗu mu rungumi ƙaddarar mu" ta faɗa da ɗan murmushin karfin hali murmushi nai mata ina miƙewa muka shiga ɗakin, tun da muka shigo na lura da kalar kallon da Ochuchuwa ke bina dashi don idan ba gizo idanuwana su kai man ba har lashe leɓe take, hakan ya sa nace Bintu ta kwanta tai baccinta cikin salama babu abinda zan bari ya faru da ita, baccin dai a ɗaɗɗare ta yisa ina jin yanda take faman sauke ajiyar zuciya, nima kwanciyar nayi amma sam na gaza yin Bacci wanda na tabbatar kowa yai bacci, ajiyar zuciya na sauke wanda nima baccin ya ɗan fara ɗaukana Washe gari tun da safe ko wane ya nufi ɓangaren aikinsa, ni kam raina cike fal da damuwa da zullumi na nufi sashe Uwargidan sarki Tunda na shiga Babban Falon zuciyana ke ƙara hauhawa da bugawa ina jero sunayen Ubangiji, gefe naja na tsaya ganin sai bayi ke hada hada a Falon da gyare gyare, wata ce ta dafa ni tana furta ""you are KULU" yeah na furta ina dubanta "ok Follow me" kamar yanda tace haka na bita muna shiga wani coridor da ya kaimu stairs mai mugun tsayi da yasha floor Cafet ,a hankali muka nufi babbar ƙofar ɗakin wan da a kaf ɓangaren gidan nan ban taɓa cin karo da kalarta ba bcox yanayin girmanta da kyawunta, security door , handle ɗin ƙofar ma Automatic digital biometric lock ne irin na zamani wanda ba kowa ne ke shiga cikinta ba Da kanta matar ta buɗe man tana furta na shiga na gyara ɗakin kaf, da to na amsa ina kutsa kaina a cikin ban san lokacin dana ƙara murtsike idanuwana ba ina jijjiga kai, tare da ƙara mamakin daman a gidan duniya da akwai kalar waɗannan kayan Alatu da more rayuwa, wllhy ko a mafarki ban taɓa cin karo da kalar wannan haɗaɗɗen wajen ba, a hankali na kara ware idanuwana da nufin ƙara basu abinci sai dai karaf idanuwana suka sauka ya zuwa wani tangameman photon Wanda na kafe da ido ina kallon fuskar kyakkyawan mutumin dake cikinta , ya sha Suit baƙaƙe ga manyan kitson kansa da ya zubo har dokin wuya , babu abinda yafi jan hankalina sama da murmushin da ya saki har gefen kumatunsa ya lotsa, ga manyan dara daran idanuwansa da ya qara warowa wanda ya bada wani fatsion na daban, ko tantama ban yi wannan shine mamallakin ɗakin kuma Prince ABIODUN ɗin da ake nufi jarumin gwarzon masarautar [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso.....* Bismillahirrahamanirrahim P.17&18 A hankali nake bin Stairs ɗin ina sauka hannuwana riƙe da kwankwasona wanda tsabar gajiya ce ta sakani riƙewa wanda a hakan ma wai ban idar da aiki ba, "wash" na furta a hankali time ɗin dana sauka daga shegiyar Stairs ɗin mai tsayi,kallona Baiwar tayi tana faɗin"You're going to cook now" cike da gajiya na amsa da ok tare da furta "a ina ne kichen ɗin?" na faɗa da harshen turanci ba tare da tace man komai ta nuna man hanyar da zan bi ya zuwa kichen ɗin, Tun kafin na ida isa ƙamshin girki ya fara ziyartana wanda har wani lumshe ido nake ina ƙara baza hancina , a hankali na kurɗa kaina a haɗaɗɗen kichen ɗin ina mai bin kuku's ɗin da kallo wanda dukkansu maza ne ni kaɗai ce mace kasancewar basu Sanni ba ya sakani gabatar da kaina, sanin cewar ban iya kalar girkinsu ba ya saka duk wani abun yankawa na yanka masu, haɗaɗɗen Yamnita and vegetables stew suka girka da fish fillets and liver Wanda a cewarsu sune favorite food ɗin ABIODUN shi ya saka aka girka masa ,kasancewar yana hanyar isowa masarautar, cikin haɗaɗɗun warmer masu masifar kyau aka zuba masa, wani Kuku Mosis ne ya umarceni dana shirya Abincin tsab a Dining, sannan kafin na shiga na tabbatar na tsabtacce jikina har turare na saka sbd ABIODUN nada tsauri da kuma ƙyama idan har ya ganni a haka zai iya amai, wani yawun takaici na haɗiye ina ɗaga kaina na fice ba wani ɓata lokaci nai wanka tare da sauya wasu kayan suma dai irin na bayin ne sanin cewa ban da turare ya sakani ficewa kaina tsaye ina faɗa wa Mosis ɗin cewar ban da turare, turarensa ya bani na shafa, sannan na ɗauki Abinci naje na fara jerawa wanda na iske Abinciccika da dama da juice duk an shirya wanda nake mamaki na tabbatar ko mutum Talatin ba lallai su cinye abincin dake shaƙe akan dining ɗin ba , *ABIODUN* Ko da suka iso Masarautar kai tsaye sashen Mahaifiyarsa ya wuce, Hakimce take a bisa ɗaya daga cikin kujerun Falon Hadimai na hidimta mata, wanda ta ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana shan ƙamshi,Ahankali ya saka ƙafafuwansa ya zuwa Falon ba tare da yayi magana ba, sai dai ɗan gyaran murya wanda ya ankarar da Maman nashi, murmushi ta saki tana miƙewa ya zuwa gunsa tai hugging nasa tana shafa fuskarsa tare da faɗin "Welcome to my son how are you?" ɗan murmushin da ba lallai ka gane yana yinsa ba yai mata tare da sumbatar goshinta yana faɗin "fine awujo" (umma) da yake haka yake kiranta murmushi ta saki tana sakinsa tare da furta kọkọ lọ lati wẹ ( ka fara zuwa kai wanka) "Ok Awujo" ya furta yana wucewa ya zuwa part nasa,A hankali ya shiga ɗakin yana mai lumshe idanuwansa jin wani daddaɗan ƙamshi ya ziyarcesa bai san lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ba, yana buɗe idanuwansa ya sauke akan Babban Falon nasa wanda aka canzawa tsari yasha gyara da ado na musamman, shafa kitson nasa yai yana ɗan taune lips nasa, Bedroom nasa ya shiga inda ya samu mata Bayi a ciki ko wace kanta a ƙasa yayin da suke jiransa ya shigo ,ƙara haɗe kyakkyawar fuskarsa yai yana shiga Toilet har ruwan wanka da turarukan jiki duk sun haɗa masa, kai tsaye wanka yayi sosai sannan yai na ruwan turare, Towel kawai ya ɗora ya fito Nufosa su kayi da nufin yi masa shafa sai dai cikin tsantsar ɓacin rai ya furta "even if that one of you goes out, don't let the one that ends up with me Before I count three, leave because I don't want to see your ugly face" ya furta a masifance Tuni jikinsu ya hau kyarma ko wace nason rigan ƴar uwarta fita sbd suka tsaya tsab zai iya kashe su tsabar masifarsa , ƙaramin tsaki yaja yana ganin duk laifin Awujonsa ce da take mayar dashi ƙaramin yaro idan banda abinta miye na wani bashi Hadimai mata masu masa shafa dukda kasancewarsu Dattijai ne, da baiyi tsaye ba ya tabbatar har wanka za su iya masa ma "Just abastard" (Ƴan iska kawai) ya faɗa a ƙufule cikin ƙanƙanin lokaci ya gama shirinsa tsaf jikinsa sanye da dakakkiyar shaddar wacce taji haɗaɗɗen ɗinkin Yoruba wuyansa saƙale da murjanai masu masifar kyau da tsada, haka zalika kansa sanye da hularsu mai tsada ta yoruba wacce ta ɓoye kitson da yai,sosai yake baza uban ƙamshi kai kace Company turare ne a jikin nasa, ƙafafunsa sanye da loafters cover shoe cikin taƙama da isa ya fito daga ɗakin yana sauka down stairs wacce za ta kaisa wajen Awujonsa, babu kowa a Falon nata duk ta sallami Hadiman nata, tana ganinsa ta kama hannunsa tana furta "let's go eat food" *KULU* Ni kuwa tun lokacin dana ajiye Abincin nake tsaye kasancewar duk in ka ajiye Abinci ba zaka bar wajen ba har sai anzo an kammala ci sannan, sosai na gaji da tsayuwar,Ƙamshin turaren da naji na dumfaro inda nake ya sakani ɗago da idanuwana sai dai karaf suka sauka akan Mutumen da naga photonsa wanda nake da tabbacin shine ABIODUN sosai na shagala da kallonsa sai nake ga duk kyawunsa da na gani a photo ashe ba kyau bane ganinsa a zahiri yafi, zungurar man ƙafa da wata baiwa tayi ya saka hankalina dawowa ya zuwa gangar jikina,sai naji kunya na kuma gode Allah da yada Uuwargidan sarkin can bata gani ba wacce nake da tabbacin ita ce Maman ABIODUN sbd ga kamanni nan sun bayyana a tsakaninsu Zama yai yana ɗan ƙara haɗe rai, kallommu da ɗai ɗai Maman ABIODUN ɗin tayi tana sallamar bayin da muke tare ya rage ni kaɗai ce hakan ya saka ni tsurewa waje guda ina zare idanun tsoro da wani tsinannan kallo ta bini tana daka man tsa tare faɗi Ubanki ne zai yi serving nasa kika zura mana idanu" ta faɗa a harshen turanci jikina na ɓari na tunkaro inda warmers ɗin suke na fara serving nasa dukkan wani abu da aka shirya masa sai da na zuba masa, ina ja baya na tsaya tare da duƙar da kaina ina shanye hawayen dake son zubo man,ita kuwa ta fice tana faɗin yaci Abincin sosai da kafin ta dawo ba tare da ABIODUN ya kalleni ba ya fara cin Abincinsa musamman ma Yamnita Nd Vegetable stew ɗin yana gamawa ya miƙe da nufin barin wajen sai dai cikin rashin sa'ar kauce masa muka haɗa jiki dashi wanda ya saka shi ɗago da Manyan idanuwansa ya zuba su a kanta da nufin yi mata masifa, da cin mutunci, tuni jikina ta fara kyarma na rintse idanuwa bakina na karkarwa idanuwana na ambaliyar ruwan hawaye wanda na tabbatar Mari ne zai sauka a kuncina, kallonta yake a karon farko kenan da har ya tsaya yana ƙarewa mace kallo yana kallon ɗan mitsilin bakinta dake son furta wani abun, ganin yanda jikinta ke karkarwa ya saka shi murmusawa yana ɗan ƙara zuba mata narkakkun idanuwansa "Open your eyes" na tsinkayi muryarsa wan da ni nai tunanin saukar lafiyayyen mari a fuskana A hankali nake ware manyan idanuwan nawa wa ƴanda suke cike tab da ruwan hawaye, sosai gabansa ya faɗi yan zubawa idanuwan nata kallo yana karantar wani abun cikinsu, bai san lokacin da ya janye ba yana ɗan kuma haɗe ransa tare da furta "you can go" cikin tsoro na furta "ok sir" ina haɗa hanya na wuce bayanta yabi da kallo tare da murmusawa yana faɗi "A cowardly girl"................ RIAMCOOL ce......... [10/23, 9:01 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *BY RIAMCOOL* *MIKIYA WRITER'S ASSO.....* *Bismillahirrahamanirrahim* *P.19&20* Yana gama faɗin haka ya fice ya zuwa sashen BOLUWATIFE,wanda tun lkcn da ya fito ya zuwa Babbar Farfajiyar Masarautar ya zuba ma waje guda idanuwa yana ɗan lumshe Manyan idanuwansa, jin kirarin da fadawa suke yayinda suke a zube ƙasa, ɗan haɗe ransa yayi yana ɗaga musu hannu Alamar su bari kai tsaye sashen BOLUWATIFE ya nufa *Boluwatife* Tun daren da taji Oba Adewale Femi ya faɗi ABIODUN zai dawo ta shirya Babban tuggun da take gani haƙarta za ta cimma ruwa, tun a daren ranar da zai dawo ta nufi gun Boka Olesegun Kamar yanda ta saba a koda yaushe yauma ɗin tsaye take tana faman karanta wasu ɗalasimai waɗanda ba ganesu kake ba dan na yau sunfi na koda yaushe muni, baiwarta Febo dake tsaye sosai ta tsure waje guda tana jin tsoro duk da ba yau ne ganinta na farko ba, kafin suyi wani ƙwaƙƙwararan motsi duka suka fara jin brain nasu na juyawa tsikar jikinsu na tashi,kunnuwansu na musu wani kalar sauti Dummmmmmmmm, sauyin iskan da suka ji ne ya saka su buɗe idanuwansu, akan Boka Olesegun dake murmushi mai bayyanar da zaƙwaƙwurin muninsa da razani "Boluwatife me ke tafe dake ne?" ya faɗa da razananniyar muryarsa, bakinta ta buɗe ta fara magana cikin ƙunar rai "haba Boka Olesegun na gaji fa da ganin ABIODUN a masarautar to ga dama ta zo min tabbas jinin JOHAAN ya bayyana a Masauratar nan tunda Oba Adewale Femi (Sarki Adewale Femi) ya furta da bakinsa, ya bayyana cewar yana son ABIODUN ya bar masarautar nan a farkon zancensa, amma daga bisani kuma ya fara kokwanton hakan, ka taimakeni ya zartar da hukunci daya yanke a farko nice nake son cikin dake jikina ya zamto yariman Masarautar Handaash" ta idasa da zubar wasu hawayen takaici da tsanar ABIODUN dake ranta Dariya ya fara yi wacce kai kace ba zai taɓa dakatawa da ita ba, daga bisani kuma ya haɗe rai tamkar baƙin hadarin da zai zubar da ruwan halakarwa, "Boluwatife na faɗa miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, mafitarki biyu ce ko kibi Addini ABIODUN sbd Dodonsa bautarsa yafi naki ƙarfi idan kina haka ba zaki galaba akansa ba, na biyu ko dai kiyi sadaukarwa da cikin dake jikinki shine za ki iya nasara akansa" da rinannun idanuwanta take kallon Bokan nata tana furta "Babu wata mafitar ban da wannan domin ɗaya daga cikinsu banji ina iya bi ba" "Boluwatife ba kya da zaɓi ban da wannan, amma zan fara baki wani maganin da za kiyi ammfani dashi ki ciyar dashi zai fara galaba akansa" Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki tana mai mashi godiya bayan ya bata maganin da yanda za tayi amfani dashi Washe gari jin da kanta tai masa girki da magungunan da Boka Olesegun ya bata, bayan ta gama shirya komai ta Hakimce a kujeran Falon tana jiran shigowarsa Ƙamshin turarensa ya sanar mata da shigowar ABIODUN cikin wani kalar farinciki da ya fito tsantsa a fuskarta ta miƙe tana faɗi"Welcome my beloved son" Murmushin ganinta yayi yana mai ware hannayensa ya rungume ta tare da faɗin "thanks" ya faɗa tamkar wanda bai son magana A fuska kawai wannan murmushin da annurin fuskarta ke fita amma a ƙarƙashin zuciyarta ƙuna take, kukan zuci ne fal a cikinta ƙiyayyarsa tai mata ninkaya ta dabaibaye dukkan wani loko nata, rugumarsa da tai ji take ƙara acce garwashin wuta ne ta taɓa da da hali tabbas babu abinda zai hanata ɗaukar rayuwar Abiodun ta yadda gawarsa ma ba zatai kyan gani ba Cire jikinta daga nashi tai tana ƙara ƙaƙalo masa murmushin da dauriyar yinsa kawai take, tsabar iya makircinta, ya saka ba zaka taɓa cewa ba a zuciyarta yake ba hannayensa ta kama ta zaunar dashi tana ta masa maraba, a zuciyar ABIODUN kuwa sosai yake jinjina girman ƙaunar da Boluwatife ke masa yana mamakin yanda Awujonsa ke son rabashi da ita Maganar ta ce ta katsesa tana furta masa da yaci abinci girgiza mata kai yayi alamar ba zai ci ba cikin dmw tace " My son, what do you mean you don't eat food I prepared this food with my own hands" ta faɗa da dmw Murmushi yayi yana faɗin "I ate food in Awujo, that's why my stomach was full and I couldn't put any food in it" Ba don taso ba ta kyalesa amma a zuciyarta ta ayyana dolensa yaci Abincinan "tohm shikenan amma ka tabbatar girkin dare a wurina za kaci tun da kaci na wajen Awujenka" ɗaga mata kai yayi alamar to, yana tattaro dukkan nutsuwarsa ya mayar da ita a gunta tare da faɗin "Mama Bolu,wani abun ne ke faruwa da masarautar nan ne da har Daddy ya gaza faɗa Mani, sannan naga tsantsar tashin hankali a wajensa wan da ban samu damar tattaunawa dashi ba, amma nasan dukkan wata damuwa na Daddy ke kin sani ki faɗa mani babban dalilinsa na cewar na baro London nasan ba lafiya ba" ya faɗa cikin harshen turanci murmushi tayi tana mayar da hankalinta gunshi tare da shimfiɗa damuwa a fuskarta tana faɗin "Son tabbas dan dmw da akwai ta a masarautar nan abin da Mahaifinka ke gudu a tsayin shekaru yau gashi yana shirin faruwa a masarautar nan sbd jinin JOHAAN na a cikin masarautar nan" Sosai maganar ta dake shi amma yai ta maza ba tare da ya iya mgn ba, miƙewa yayi ya fita zuciyarsa sam babu daɗi Kai tsaye sashensa ya nufa yana kwanciya yi tare da lumshe idanuwansa Oba Adewale Femi kawai yake jira ya dawo daga fada domin ya ƙara jin ba'asin zancen Da ƙyar ya samu baccin gajiya na ɗaukar sa, wan da ya daɗe yana before ya farka wanka ya sake yi yana son nufar Mahaifinsa wanda ya tabbatar a yanzu ya dawo daga fada Zaune yake yana sauke numfashi jin mahaifinsa ya gama kora masa jawabi tamkar yanda Boluwatife ta faɗa masa, "wane shiri yanzu ake ciki" ABIODUN ya faɗa shiru Oba Adewale Femi yai yana kallon itama Mahaifiyar ABIODUN ɗin wacce take sauraronsu, "ABIODUN a iyakar bincikena tun kafin abun ya faru an sanar damu ba wata mafita mafita ɗaya ce mai tsauri ita ce barinka a Masarautar HANDAASH" Daga shi har Maman nashi kallon Oba Adewale Femi suke cikin tsantsar mamaki da zallar razani bakinsa na rawa ABIODUN ke furta Dad, you know what you're talking about" ABIODUN ya faɗa cikin kodai mahaifin nasa ba a hayyacinsa yake ba sai dai maganar da yaji ya furta ne ya saka shi gazgata lallai yana hayyacinsa "ABIODUN, I am aware of what I am saying that you should leave this kingdom" ya faɗa da hawayen dake biyo kuncinsa wanda tun da suke basu taɓa ganin koda ɗigon hawaye a idanuwansa ba sai yau da ya furta ABIODUN yabar masarautar sa da bakinsa akan wani dalilin da ba lallai ya faru ba hasashe ne kawai cikin masifa da tujara Maman ABIODUN ta fara faɗin "ABIODUN has nowhere to go, he will never leave this kingdom, on what is an illusion, there is no war about it." hannu ya Adewale Femi ya ɗaga mata yana mai mata kallon takaici da rashin hankali ƙofa ya nuna mata ta fita, wan da cikin fushi ta fita tana mai zazzaga masifar ɗanta ba zai bar masaurar nan ba ABIODUN kuwa ya gaza furta komai wanda numfarfashi kawai yake fitarwa , *KINGDOM OF JOHAAN* Wani kalar zafi da huci ke fitowa daga jikinta sosai take mayar da numfarfashin azabar da take ji a duk lokacin da zata haihu sai dai na wannan karin daban yake , Azababben zafi ne ke ratsata tun daga kanta har izuwa tafin ƙafarta dalilin haka ya haifar mata da karkarwa tamkar wacce taji kiɗan gangi wanda haka ne ya haifar mata da gumin dake tsatstsafowa daga ko wane loko na jikinta A hankali ta ƙara lumshe Manyan dara daran idanuwanta tana ambata Jesus a hankali wan da a fatar bakinta ne kaɗai za ka gane, Gimbiya Josmie dake tsaye kanta tuni idanuwanta suka cicciko da ruwan hawaye tana faɗin "Ki daure za ki iya da amincewar Jesus" ta faɗa da harshen turanci cikin dakiya da jajircewa Matar dake naƙudar ta buɗe idanuwanta tana kallon Josmie tare da buɗe busasshen leɓenta tana girgiza kai hawaye na biyo kuncinta ............... *RIAMCOOL ce* Writer of RUSHEWAR RAYUWA BAYAN WUYA ANYA UBA NE AND NOW *KULU* [10/23, 9:03 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso.....* *Bismillahirrahamanirrahim* P.21&22 "Josmie ba zan iya ba na tabbatar a wannan karon ma Abinda zan haifa ba lallai ya tsira ba, shima halakar man dashi za ayi, na roƙi Yesu Jesus da in har za a halakar man da wannan yaron na cikina to na fi son mutuwa taxo ta ɗaukeni ba zan tashi ba kawai" wanda duk wannan maganar da take ta nayi ne cikin ƙarfin hali ba fita take sosai ba, iya fatar bakinta dake motsi kawai za ka gane abinda take cewa girgiza kai Josmie tayi ruwan hawaye na ƙara ambaliya a kwarmin idanuwanta, "Za ki tashi da yardar Jesus sannan ki reni yaronki da hannunki a wannan karin babu abinda zai faru da yaron cikinki" dukda azabar da take ji hakan bai hanata mayarwa Josmie amsa ba, "da gaske wannan karin ba za a halakar man ya yaro ba, kamar yanda aka halakar man da ƴaƴana ba ɗaga mata kai Josmie tayi tana mai murmushi wan da yake haɗe da kukan tausayi, yayinda da lkc guda kuma tai wani nishi mai ƙarfi daya haddasa fitowar jariri wan da ya canyara kuka a lkc ɗaya, lamo tayi tana mai lumshe idanuwanta tana jin wani bacci bacci na niyyar fixgarta sai dai tai ƙoƙarin hana kanta sbd wannan baccin dake fixgarta shine sanadin duk halakar ƴaƴanta, a wannan karin ba zata bari hakan ya faru ba, don haka tayi ƙoƙarin ware manyan idanuwanta masu matuƙar kyau akan yaron dake hannun Josmie yana canyara Kuka Murmushi mai haɗe da sautin kuka ta saki "Josmie yau nice na ware idanuwana akan abinda na haifa wan da hakan bai taɓa faruwa ba" iya ɗaga mata kai kawai Josmie tayi tana murmushin farinciki, cikin lkc ƙanƙani Masarautar JOHAAN ta san da cewar Gimbiya ARUSH ta haihu sannan ɗa Namiji Tun lokaci da. Mai martaba ya shigo ya zuwa ɗakin da ARUSH ɗin take ya kafeta da idanuwa yayinda shima hawayen farinciki ke fita "na haihu a wannan karon ba tare da banga fuskar abinda na haifa ba, nayi farinciki da godiya ga Yesu domin shi ne ya bani damar ganin wannan yaron ina son ku tabbatar man da cewar tabbas zan rayu da yarona, ku bashi kariya daga halakakkun gidan sarautar nan, ku tsare shi daga makircin maƙiya" ta faɗa da ƙwalla cike taf a idanuwanta wanda murmushi da annurin ke akan bisa kyakkyawar fuskarta shima murmushin ya saki yana kama hannayenta duka tare da saka idanuwansa akan nata "ARUSH I can assure you that this time our child will not perish" murmushi mai haɗe da dariya ta saki tana rungume sa, wanda duk abinda suke Gimbiya Josmie na kallo tana sakin murmushin farinciki yayin da ta kaiwa mai martaba Yaron sosai ya riƙesa yana kallonsa wan da murna ce fal a ransa ganin ya samu Magajin masarautar Handaash, a daren ranar sosai akai shagali yayin da farinciki ya ninkaya a masarautar Handaash yayinda a gefe ɗaya na munafukai da kuma maƙiya ba haka suka so ba, baƙi ciki ne fal cike da zuciyoyinsu, sosai take haki da furzar da iska mai zafi tana mai sake jan wani numfashin tana fitar dashi yayinda idanuwanta sun kada sun yi ja kai kace gauta, "ina ina da hakan ya faru me ya saka a wannan karin Yaron ARUSH ya tsira?? tun bisanin shekara Ashirin nice ke galaba akanta mi yasa a wannan karin banyi galaba ba akanta, ga shi abinda nafi tsana ne shine samuwar wani ɗa Namiji a gidan sarautar nan kayi duk yanda za ayi kaga ka halakar da yaron nan" ta faɗa da dakakkiyar murya ta tsofi wacce har kyarma take Mutumin da tsawon shekaru yake tare da ita but har a wannan lkcn bai taɓa ganin fuskarta ba idan banda yamishashsun idanuwanta wan da tsabar tsufa ya saka su yamushewa, itama a nata ɓangaren bata nuna masa cewar ta ganesa ba, duk da kalar ɓadda kamar da yake hakan ba zai hanata ganewa bcox makira mace ce mai haɗarin gaske Jijjiga kansa yai yana shaƙe murya"in dan wannan karki damu ki saka a ranki tamkar anyi an gama ne duk da na dan ba mu kaɗai bane masu harar yaron nan ba" dariya mai nuna zallar jin daɗi tayi tana furta "nayi Alqawarin ARUSH ba ke babu jin daɗin haihuwa haka zan ci gaba da ɓatar miki da yara" sosai suka tattauna yan da ɓatar da yaron zai kasance a ɓangaren ARUSH kuwa duk da kalar tsaron da aka bata amma sam taƙi ta kwantar da hankalinta tai bacci gani take idan har tayi bacci a wannan karon ma zata rasa yaronta tamkar yanda take rasawa, har yanzun tana jin ɗaci da kuma raɗaɗin abinda ke faruwa da ita *KINGDOM OF HANDAASH (Masarautan Handaash)* Tun lkcn da KULU dana bar wajen ABIODUN zuciyarna ke mani dukan Uku uku ban nutsu ba har sai da naga n abar sashen na koma ya zuwa namu, ni kaɗai ce a cikin ɗakin namu yayin da kowa ya kama gabansa, a hankali na fara ganin wulgawar haske wanda ya sakani rufe idanuwana ana fatan Allah ya sa Abinda zuciyans ke raya mani gsky ne Ina buɗe idanuwana hasashena ya faɗa mani gsky domin kuwa Diyana ce a gabana fuskarta ɗauke da murmushi, faɗin kalar yanayin farincikin da na shiga ba zai musultu ba,jikinta na faɗa ina mai fashewa da kukan farinciki tare da faɗin "Diyana a ina kika shiga? kika barni ba kya son ziyartana" Kaina ta shafa yayin da take kafeni da idanuwanta wanda tsabar kaifinsu sam bana iya saka nawa a cikinsu, "KULU masarautar nan shigowarta da aiki ni kaina ban shigo ba sai da na shirya, akwai haɗarurruka da dama a cikinta,da dalilin shigowana a ciki" "Diyana ban gane ba ki fahimtar dani yanda zan gane" na faɗa da tsoron dake raina fal Murmushi ta saki tana furta "a halin yanzu ba zaki gane ba amma nan gaba kaɗan za ki fahimci abinda nake son sanar dake,a halin yanzu na fara sani wacece ke a sanadin masarautar nan da kika shigo na san Ahalinki a halin yanzu" da mamaki shimfiɗe a fuskana nake dubanta "Diyana kin san wace ni? shin su waye iyayena , kina nufin duk kin san wannan???" na jero mata tambayoyi gefe ɗaya ta kalla tana furta "eh duk na sani" "na tabbatar kina da hanyar sadani dasu kuma ke mai taimako ce a koda yaushe ina mai roƙonki ki taimaka ki fitar dani a masarautar nan wllhy ina ji a jikina na zauna a cikinta da akwai abinda zai faru dani" "KULU hakan ba zai taɓa faruwa ba a halin yanzun sbd babu bawan da ya isa ya shallake qaddararsa dole ne ki fuskanceta ƙadaddararki na ata ko ina ba lallai ko kin koma a mahaifarki su karɓe ki ba, ki fahimta da akwai qaddara mai ƙarfi da zata haɗaki dasu" tana gama faɗin hakan ta ɓacewa ganina yayin da ta barni cikin tunani mai zurfi da kuma zubar hawaye waɗanda na rasa na miye yayinda maganganuta ke ƙara kai kawo a brain nawa "me ce qaddarar da zata faru dani a masarautar nan har ta haɗani dasu?" Naiwa kaina wanna tambayar wacce bani da mai bani amsa Kuka sosai naci harna gode Allah a ranar sbd tsabar kukan dana sha kaina sai da yai ciwo abinci kanshi dan Bintu ta takura min da naci na ɗan tsakura *ABIODUN* Tun lkcn daya gama sauraren ɗanyen hukuncin da Mahaifin nasa ya furta ya rasa kalmomin da zai yi amfani wajen mgn jikinsa a sanyaye ya miƙe yana mai ganin jirin da har ya kusa yar dashi a ƙasa ba don mai martaba Adewale Femi ya riƙesa ba da tuni yasha ƙasa da rinannun idanuwansa da suka jiƙu da ruwan hawaye Adewale Femi ke kallon Yaron nasa "ABIODUN did not say anything" "There is nothing I can say to leave me in this emirate, it is the end of my life." ABIODUN ya faɗa with tears in his eyes Riƙo hannayensa Mai martaba yai yana kallon idanuwan ABIODUN "kar kace haka mana ba zaka rasa rayuwarka ba akan ka bar masarautar nan ni kaina tamkar numfashina zai fita haka nake ji, sai dai idan za kayi man Arqawali ni kuma zan Barka a masarautar nan" ɗan jimmm ABIODUN yai yana ɗaga kansa alamar ya amince "ABIODUN na san da cewar a halin yanzu mace bata gabanka balle kuma soyayya, ina son Kai man Arqawali ba zaka so wata ƴa mace a masarautar nan, dukda kai ɗin mai na tabbatar mai aji ne sai dai ance ka guji makiri duk inda yake na tabbatar ko wace ita tana nan tana bibiyarka domin ka faɗa komarta ban son haɗa jini da maƙiyammu" ɗaga kansa ya sake yi a karo na biyu yayin da ya rungume mahaifin nasa yana mai tabbatar masa ya ɗaukar masa Arqawali lkcn da ya bar sashen Mahaifinsa ya shiga ya zuwa nasa ɗakin wan yanda ya barsa haka yake alamun ba a sake gyara masa ba, a ƙufule ya fita inda yaci karo da securities nasa maza ɗaya daga ciki ya kira ya gyara masa komai da komai Kuku's suka shirya masa abinci, kaɗan ya ɗan tsakura ya kwanta don ya samu relief ni kuwa washe gari tun da Asuba na tashi mukai sallar mu a ɓoye tamkar yanda muka saba , sai da gari ya ɗan fara haske before na nufin sashen Uwargidan sarki domin gyarawa Yaronta sashensa da kuma yi masa girki, a lkcn bani kaɗai bace dan haka na shiga sahun kingin Bayin muka gyara ko ina tsab, lkcn ƙarfe takwas na safe na shiga kichen inda muka fara yiwa Uwargidan sarki abinci ta da kingin yaranta, sannan mukai wa Prince ABIODUN nashi daban shima inda muka girka masa Rice stew and vegetables stew + pawpaw Yayin da duk aikin da muke Kuku Mosis na mini fira wani nayi murmushi wani nayi dariya Wani kalar Cinyan Dabba naga ya ɗauko mai tsoka da mai wan da sam ban taɓa ganin da akwai mai kal ar naman ba a Akuya rago da sauran naman mu na musulmai "what meat" zaro idanu yai yana furta "You mean you don't know Pork meat" ɗan sosa kaina nayi ina yatsina fuska cikin wayancewa nace "Awww I know" ok ya furta yana murmushi A zuciyana kuwa cike yake da ƙyamar da ƙyar na shiga taya shi wanke naman muka gyarasa sosai farfesunsa mu kayi yayinda sai ƙamshi yake zubawa tsab muka kammala, muka jera a Dinning cikin gajiya da aiki na nufin ɗakin ABIODUN zuciyana fal da tsoro A buɗe ɗakin na sameshi hakan ya bani damar turawa ina tura kaina a ciki tare da gyaran murya shiru naji hakan ya sa na fara gyara parlourn tsab ko ina sai ƙamshi ke tashi cike da gajiya na shiga fara leƙa bedroom nasa sai dai sam babu kowa a ciki ajiyar zuciya na sauke ina shiga tsab shima n gyara na wanke Toilet Da ɗan sarsarfa yake hawan step ɗin benen jikinsa sanye Da Kayan game, cikin kuzari ya tura ɗakin nashi yana mai lumshe idanuwansa jin ƙamshi ya dokar masa hanci buɗe idanuwansa yai yaga ko ina tsaf alamun an gyara motsi yaji a bedroom nashi hakan ya saka shi tunkarar ciki,motsin mutum naji a bayana wanda ya sani juyowa a hanzarce gabana na dukan ukku ukku ganin wanda nake tsaye gabanshi............... *Ma sha Allah my Habibties 💖 😻 Ina matuƙar gdy da addu'o'inku gareni much love Habibties 💖* *RIAMCOOL ce* *Writer of* RUSHEWAR RAYUWA BAYAN WUYA ANYA UBA NE AND NOW *KULU* [10/23, 9:03 PM] CUTIE~RIAM: https://whatsapp.com/channel/0029VaeDIuFAO7RJJlNmLi0u *A lover from the beginning You can follow my channel* *KULU* *BY RIAMCOOL* *Mikiya writer's Asso....* *Bismillahirrahamanirrahim* *Assalamu alaikum ina gdy ga waƴanda ke mun addu'a , sannan masu biyoni pc suna min complain ɗin bana musu Update da wuri waye da miye, na faɗa muku fa ban da lafiya, ne tun da nake Novel ban taɓa tsaitsayawa ba ba tare da dalili ba, akwai wacce tamin mgnr da banji daɗinta ba, gsky mutane ku san kalar mgnr da za ku faɗa dan Allah, Allah ya kyauta* P.23&24 Shi kuwa ba tare da ya kalli inda take ba ya raɓa ta gefenta yana wucewa tare da ɗan ƙara haɗa rai yana wucewa ta gefena, nannauyar ajiyar zuciya na saki ina hamdala ganin dukkan aikin daya kamata nai masa, Abinci kaɗai nake jira yaci, ida fitowa nayi daga bedroom ɗin na tsaya a falo ina jiran fitowarsa Shi kuwa tun lkcn da ya shige kai tsaye Toilet ya nufa da nufin yin wanka ko ina fes but ruwan wanka ne bata haɗa masa ba, da kanshi ya haɗa abinda sam bai taɓa yi ba, kuma bai damu da sai ya kira ta haɗa masa ba, ko da ya gama wanka shiryawarshi tsaf yai cikin kayan pajames yana zuba uban ƙamshi, jin cikisa na kukan yunwa ya saka shi tunkarar Falon, tsaye ƙiƙam ya ganta haka zalika idanuwanta na a ƙasa, jikinta na ɗan kyarma kawar da kanshi yai daga kallonta yana nufar dining ɗin, A hankali na fara ɗaga ƙafafuwana da suka min nauyi, haka zalika jikina naji ya fara kyarma tamkar wacce aka kaɗa wa kiɗan gangi, da ambaton Allah a bakina na nufi dining ɗin wanda da ƙyar nai serving nashi ina ja da baya tare da mayar da wani wahalallen numfashi, haka zuciyana na ƙara bugawa, hannu na saka ina dafeta bakina na jeranta sunayen Ubangiji, dukkan wani motsinta yana gani da yanayin yacce take abu, shi sai yake ganin tamkar marar gsky, bai san lkcn da ya ja ɗan siririn tsaki ba, Abinci kaɗan ya ɗan tsakura ya umarceni na kwashe kayayyakin daya gama cin Abinci, saida na sake gyara ko ina, "Come back here, I sent you to go out" ya faɗa a kausashe lkcn da nazo fita Girgiza kaina nayi ina faɗin srry a hankali cikin shakka da tsoro,siririn tsaki yaja yana ci gaba da danna wayarsa daga bisani kuma ya ajiye wayar yana ƙara kallonta tun daga ƙasa har sama, "Is it true that your body is always in pain?" Ya faɗa da ɗan yatsina fuska, girgiza masa kai kawai na iya ina mayar da kaina ƙasa Sake kallonta yake da rinannun idanuwansa wanda sam a wannan karin ya gaza sarrafa kanshi, so yake ya dinga kallonta a haka, tun ranar da idanuwansa su kayi masa tozali da KULU brain ɗinsa ta rasa samun nutsuwa, haka zalika zuciyarsa bata daina buga masa ba ,"Lift your face" ya faɗa da son jefa idanuwansa a cikin nata ɗago da idanuwana nayi waɗanda suka tara ruwan hawaye ina kallonsa a karo na farko kenan da na jefa idanuwana a cikin nashi, sosai yake ƙare mata kallo,idanuwan nata suka fara fizgarsa da yanayin yanda suke cike tab da hawaye, shi sam ba ma'abocin mgn bane ko tambaya amma a kan Baiwar da bai san asalin ta ba sai ya tsinci kansa da son jeranta mata tarin tambayoyi "your eyes never tire of tears" ya sake tambayarta share hawayen nai Ina girgiza kaina tare da kallonsa nace "I have an eye problem" ƙara taɓe baki yai yana faɗin "you can go" Ok na furta ina russunawa ƙasa na fice, wani wahalallen ajiyar zuciya ya saki yana taune lips nashi na ƙasa, sam ya gaza fahimtar al'amarin da akwai tarin ƙaddarori da dama dake tunkarosa shi ya san da haka, bai san lkcn da wasu tarin hawaye Masu raɗadi suka zubo masa ba wan da shi kaɗai ne yasan dalilin zubarsu Tun lkcn dana fita nake sauri sauri ina sauka daga Stairs ɗin,kaina na Sara min tamkar zai tsage gida biyu, ga wani zazzaɓi da nake jin yana son rufeni, na tabbatar bai rasa nasaba da yunwar dake ƙwaƙular hanjin cikina, Kai tsaye inda muke karɓan Abincimmu na nufa ina bin layi har yazo kaina, Flat na miƙa aka zuba min Teba da miyar kuɓewa wacce sam ba sonta nake ba amma tsabar yunwar dake addabana zai sakani naci Wuri ɗaya na samu ina zama tare da zubawa Flat ɗin Abincin ido ruwan hawaye na ambaliya a kwarmin idanuwa wllhy ko a mafarki ban taɓa tunanin zanyi rayuwa kalar wannan ba, na tabbatar da qaddara zanen zabo ce, haka zalika ina ji a jikina yanzu ne Alƙalamin ƙaddarata ya soma rubuta ƙaddararriyar rayuwana, yau she ne zan cinye jarabtar da Ubangiji ya ɗora min? wannan ne ban sani ba, Allah da ya jarabceni da hakan shi zai yaye man damuwata, na tabbatar da Ubangiji ba wai baya sona bane da har yayi ni haka ya mayar dani ƙasƙantacciya, wacce na zamto baiwa mai bautawa wasu tun ban san wace ni ba ban mallaki hankalina ba, "yanzu haka zan ƙare wane zai auri baiwa?? na samu nima rayuwar ƴanci na tabbatar a haka rayuwata zata qare cikin azaba da bautatawa ba tare dana raya sunnar ma'aiki ba," na ƙarshe mgn a hankali tare da sake zubar wasu siraran hawaye waɗanda ban san ranar daina zubarsu ba ba don raina yaso ba haka naɗan tsatstsakura naci ba tare da ina jin daɗin Abincin ba, Kwanaki na tafiya makwanni na shuɗewa sam babu wani canji haka koda yaushe nake azabtuwa da ayyuka waɗanda suka lillinku,sosai na fara ƴar rama tsabar damuwa dana fara sakawa kaina, wani lkcn nakan sha kuka ba adadi, ban da mai rarrashina sai Bintu wani lkcn kuma sai dai na rarrashi kaina, A hankali nake bin bishiyoyin cikin masarautar da kallo ina mai lumshe idanuwana wannan shi ne karo na farko da nai tafiya mai tsayi a masarautar nan harya kawoni ya zuwa wajen daya wadatu da korayen bishiyu, ga wani sassanyan ni'ima da iska dake ratsa jikina ban san lokacin dana saki murmushi ba ina nufar babbar ceɗiyar da ta wadatu da ganyayyaki harta saki wadatacciyar inuwa mai sanyi,zamewa wajen nayi ina mai sauke nannauyar ajiyar zuciya, tare da duban gefena wan da nake jin sautin tafiya, saurin janye idanuwana nayi ganin wan da ke tunkaroni fuskarsa ɗauke da wadataccen murmushi wan da yake fallasa man abubuwa da dama, "Prince ABIODUN " na ambata a hankali zuciyana na sake man dukan ukku ukku duk tako ɗaya da zai yi A hankali ya fara yawo da idanuwansa ya zuwa fuskarta yana mai sake sakin murmushin daya ƙara fallasa sirrin kyawunsa, "JOSINA" ya ambata a hankali wan da wannan sunan da shine yake kirana,sakamakon ce masa da nai sunana ne a haka ba tare da na ɗago da fuskana ba na amsa da "Yes Sir" ina mai sake makure jikina waje ɗaya, ɗan ɓata fuska yai yana furta "Stop calling me Sir" ya faɗa a shagwaɓe shiru nai ba tare da na bashi amsa ba ina mai wasa da yatsun hannayena "you can be a friend from today" naji saukar muryarsa wacce tai man ámsa kuwa sanna na daina jin wani gamsasshen iska na ratsa jikina, lkc guda na tsinci kaina da zuba masa idanuwa waɗanda lkc guda suka tara ruwan hawaye, "wllhy sam ban dace da kamar ka Mutum mai daraja da ƙima a idon duniya za kayi Abota da ƙasƙantacciyar baiwa kamarni ba, na tabbatar na amince ban yiwa maka adalci ba,kayi haƙuri na zauna a iya matsayin da nake" na ƙarshe zance da sauke idanuwana a ƙasa Shi kanshi ya san da cewar tabbas gsky ta faɗa amma sai dai sam zuciyarsa taƙi bashi damar gazgata hakan,sannan bai taɓa jin cewar zai iya cika Alqawarin Mahaifinsa KULU ita ce sanadin dukkan juyawar rayuwarsa da buɗe masa shafin kundin ƙaddararsa A hankali ya sauke idanuwansa a kanta yana mai furta "ke sam ba baiwa bace kar kiyi tunanin ko ban san asalin ki ba, ki sani tun kafin shigowarki a masarautar nan na san da cewar ƙaddarata zata gibta a tsakanina dake,tun ganin farko da nai maki Alƙalamin ƙaddarata ya sauya, nasan asalinki nasan jininki, a wannan karin KINGDOM OF JOHAAN sunyi nasara, sai yanxu na idar da gazgata zancen mahaifina cewar ba hasashena bane" wan da duk wannan zancen da yake yana yi ne da harshen turanci wanda idanuwansa sun kaɗa sunyi, ja lkc ɗaya jijiyoyin kansa sukai ruɗu ruɗu, yana miƙewa ya bar wajen Kallo na bisa dashi wan da sam na kasa gane zancen da yake man "ko dai ya zare" na furta a hankali "na san jininki a wannan karon KINGDOM OF JOHAAN" na maimaita mgnr ƙarshensa a hankali wacce ita ce tafi tsaya man,sosai na shiga tunanuka da dama da kuma ruɗu, da damuwa *ABIODUN* Tun lkcn da ya bar wajen KULU ya samu wata bishiya yana zamewa a hankali wasu siraran hawaye Masu zafi suka fara wanke masa fuska ya gaza sarrafa kansa a ta wannan ɓangaren wace ƙaddara ce ke gabatoshi da son haɗa jini da maƙiyansa, tun tasowarsa babu wani abin da yafi tsana sama da KINGDOM OF JOHAAN, sai dai jarabta da ƙaddarar ce zata kasance a haka KINGDOM OF JOHAAN sunyi nasara a wannan karon ba zai iya tsallake tarkonsu Ya faɗa komar son KULU son da ba zai iya ciresa ba son da yake ji koda yankan naman jikinsa take ba zai iya rabuwa da idata ba, a da bai gazgata cewar ita ɗin jinin JOHAAN bace sai da bincikensa ya tabbatar masa haka zalika idanuwanta sun tabbatar masa da ita ɗin wacece ................ *RIAMCOOL ce* *Writer of* RUSHEWAR RAYUWA BAYAN WUYA ANYA UBA NE AND NOW *KULU* [10/23, 9:04 PM] CUTIE~RIAM: https://whatsapp.com/channel/0029VaeDIuFAO7RJJlNmLi0u *Masu so daga farko kuyi fllwng wannan channel ɗin* *KULU* *BY RIAMCOOL* *MIKIYA WRITER'S ASSO......* *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHIM* P.25&26 A hankali siririn hawaye suka soma zarya a kumatunsa, wan da bai san da zubarsu ba sai dai yaji ɗuminsa, kenan hasashen tsayin shekaru da bincike zai tabbata, sosai ya daɗe a bakin bishiyar yana mai jin zuciyarsa da tamkar ba a ƙirjinsa take ba Ganin kansa ya fara sara masa ya saka shi miƙewa yana fitowa in da ya bar fadawansa nan ya samesu ba tare da yai magana ba ya fara tafiya tamkar wan da aka zarewa lakka, kai tsaye sashensa ya nufa domin bai san wata hayaniya, yana so ne ya keɓe shi kaɗai ya samu nutsuwa da damar yanke mafita Ruwa ya samu ya ɗan ƙara watsawa yana kwanciya zaɓi ɗaya gareshi ko dai yabi mafitar da Mahaifinsa ya yanke na barin masarautar ko kuma ya faɗa wa Mahaifinsa wacece KULU 'sai dai a ɓangare ɗaya na zuciyarsa bai jin shawara ta biyun za ta yiyu muddin Mahaifinsa ya gano wace ita a Masarautar nan to tabbas kuwa mummunan hukunci ne zai yanke a kanta wan da bai fatan tabbatuwar hakan, sosai yai nisa a dogon tunani wan da sai dai yaji hannu na yawo a fuskarshi, buɗe idanuwan nasa yai yana saukesa akan Awujonsa wacce itama ta kafesa da idanuwa tana mai karantar yanayinsa "Think about what you are" ta tambayesa cikin kulawa da ƴar damuwa, yatsina fuska yai yana furta "nothing I have a headache" da damuwa fal a ranta ta furta " let me call you Family Doctor" "No I will drink medicine, tea I need to drink" ya furta a ɗan shagwaɓe murmushi tai tana shafa kanshi tare da miƙewa sawa tai aka haɗa masa wanda da kanta ta bashi yasha sannan ta bashi maganin sai da taga yai bacci sannan ta bar ɗakin *KULU* ni kuwa sosai na daɗe a wajen ba tare dana gano kalma ɗaya da yake nufi ba, ganin ba zan gano ba ya sakani miƙewa ina nufar sashen Bayi ban sami kowa ba sai Bintu wacce ke kwance itama a lokacin zazzaɓi ne ya rufeta, zama nai ina mai taɓa jikin nata naji da sauƙi domin babu zafi, "kin sha magani?" na tambaye ta a hankali girgiza kai tayi hawaye na fita a idanuwanta "a a ban sha ba, ban san inda ake karɓowa bane" shiru nayi ina share mata hawayen daga bisani nima na haɗe kaina da guiwa ina mai sake jin matsatsin rayuwa, Washe gari tun da na tashi na gabatar da aikina tsaf komai na haɗa masa sai sannan na tafi dan sam ba nison haɗuwata dashi, nufina idan ya gama nazo na kwashe wuraren da yaci abinci Bayan an ɗan jima na koma sai dai yanda na kawo Abincin haka na iske shi da alamar ma ko taɓawa ba ayi ba, Bedroom ɗin na shiga sai dai ƙarar ruwan da naji ya tabbatar min da cewar yana Toilet , Wani wahalallen numfashi na sauke "kenan haƙata bata cimma ruwa ba?" na tambayi kaina Ina tsaye a wajen ya fito ba tare da na kalles ba na furta "Morning Sir" hannayensa zube a Aljihun wando fuskarsa da wadataccen murmushi ya furta "Morning too" kujeran Dining ɗin na ja masa ya zauna tare da serving ɗin shi , "sit down and eat" ya furta ba tare da ya kalleni ba, zaro idanuwa nai ina girgiza masa kai alamar ba zanci ba, ɓata fuska yai yana furta "I will stop eating too if you don't eat." Kallonsa nai ina sakin murmushi da mamakin yadda yake tamkar wani ƙaramin yaro, ba tare da naso ba haka na zauna naci Abincin duk yanda naso tafiya hanani yai yana zuba min fira wan da nima samun wuri ya sa na manta matsayin da nake na biye masa, Bayan watanni kaɗan wanda a lokacin mun cika shekara ɗaya a masarautar sosai abubuwan suka juye man yanda banyi zato da tsammani ba, ta tsakanina da Prince ABIODUN,sosai muka shaƙu shaƙuwar da na gaza tantancewa, wacce a hankali ta fara rikiɗa ya zuwa soyayya me zafi wacce ni kaina a lkcn nasan da cewar tabbas ba'a kamu da son ABIODUN duk da nasan yaudarar kaina nake ko kaɗan ba zan taɓa zamowa mallakinsa ba duba da matsayin da nake hawaye ne suka fara wanke mun fuska lkcn da na tuna ba fa zan taɓa mallakarsa ba, hannayen da naji a kuncina shi ne ya bani damar ɗago da idanuwana na saukesu a kansa wan da shima kallon nawa yake "why are you crying" ya tambaya a hankali da ƴar damuwa "Remembering that there was a time when we parted and all the pain we did with you,na faɗa a hankali da ƙara shigar da manyan idanuwana a nashi waɗanda suka tara ƙwalla girgiza kai yayi yana furta "Don't even think about that, I'm not ready for a life of separation, we'll have each other for a long time even though I know who you are." ya faɗa yana mai furzar da iska hannayensa na a fuskana wan da a hankali ya fara yawo dashi ya zuwa wani sashe na jikina wan da yake san cimma wani ɓangare saurin riƙe hannayensa nai ina girgiza masa kai Ina mai furta "Ka daina taɓa jikin da bai zama mallakinka ba, duk da nasan kai a Addininka bai zama laifi ba amma a nawa Addini ina saɓawa Ubangiji ko kaɗan ni ɗin nasan ba zan taɓa mallakarka ba ko da ace kowa naka ya yarda za mu zama mallakin juna Addinina bai bani damar mallakarka ba sbd Addinina da naka ba ɗaya ba" na furta ina mai sauke idanuwana a ƙasa hannun nashi ya fizge yana mai mani kallon me nake nufi, "Josmie ban gane abin da kike nufi ba" ya furta "Eh ba za ka gane ba sbd ko kaɗan baka fahimceni sannan tun da nake da kai ba ka taɓa sanin wacece ni ba ya nai rayuwa miye Asalina wannan duk baka sani ba" na furta ina mai sake nisantar jikina da nashi A ɗan zafafe ya fara magana "Josina Don't think that I don't know what I'm doing, don't play with my mind, you know that I know who you are, you are the bloodline of the kingdom of Johaan and the daughter of the king Valentino" Sosai brain ɗina ya cunkushe da maganganunsa na gaza gane me yake nufi me yasa yake kirana da jinin wata masarauta baya ga ni ɗin ba wata bace face baiwa wacce bata san mulki ko sarauta ba baya ga bauta, sannan ƙasƙantacciya har yake wani kirana da ni ɗin jinin wani mulki ce sannan ƴar wani sarki wai Valentino "ka yarda da abinda na ce maka wallahi ni sam ban san wata masarauta wai ita JOHAAN ba za kayi mamaki idan nace maka ni ɗin tsintacciyar marar ƴanci ce ban san wani mulki ko sarauta ba, a zamana da kai na wani san daɗin zama da mutum kafin wanzuwar ka Ni kaɗai ce a duniyata hasali ma ba nida iyaye tun asali ban sansu ba, ni ɗin tsintacciya ce marar ƴanci rashin ƴancina ne har ya saka ni zamowa baiwa a masarautarku zatona ko tunani bai taɓa kawo man da cewar zan yi wata rayuwa a masarauta ba, ni ɗin sam ba ƴar asalin yanki bace, za ka ƙara mamakin jin cewar ni ɗin daga AREWA nazo masarautarku ka yarda dani ban san wata Masarauta ita JOHAAN ba" na faɗa da son ya gazgata zancena Mamadin naga yarda a idanuwansa sai naga yana bina da wani tsinannan kallo wan da tun zamana da shi bai taɓa man wato kallon kin raina man hankali da kuma ƙarya nai masa................ *Posting zai dawo a iya kwanaki biyar ma'ana zan cire Asabar da Lahadi * RIAMCOOL ce *Writer of* RUSHEWAR RAYUWA BAYAN WUYA ANYA UBA NE AND NOW *KULU* [10/23, 9:05 PM] CUTIE~RIAM: https://whatsapp.com/channel/0029VaeDIuFAO7RJJlNmLi0u *Duk wacce ke so daga farko za ki iya fllwin Channel ɗina* *KULU* *BY RIAMCOOL* *MIKIYA WRITER'S ASSO.....* *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHIM* *P.27&28* "Josina don't think I don't know what I'm doing You think that I will believe all the words you say to me" ya faɗa da zummar miƙewa, hannayenshi na riƙo ina mai sake narkar da idanuwana hawaye cike tab ciki, girgiza masa kai na fara yi ina furta "Abin da na faɗa maka gsky ne wllhy ni sam ban san wata Masarauta JOHAAN ba ka yarda dani, ina mai maka rantsuwa da Ubangijin daya halicceni ni sam ba ma ƴar Asalin yankin nan bace ka yarda dani" Jikinsa a matuƙar sanyaye ya ranƙwafo yana saka hannayensa ya share man hawayen dake ambaliya tare da sake tsurawa ƙwayar idona kallo tamkar mai son gano wani abun, a hankali ya furzar da iskan bakinsa yana furta "kince ba kisan JOHAAN ba amma ni tabbas naga jinin JOHAAN a ƙwayar idanuwanki" "Prince ABIODUN kar kayi saurin yanke hukunci furucin da kake na cewar kasan wace ni, ka janye shi, ni kaina ban san wace ni ba, ban san Asalina ba, waye ya haifeni duk ban sani, ba" Wani zazzafan iska ya sake furzarwa yana mai lumshe idanuwansa wan da ya kusan kai 5 minute ba tare da yai magana ba sbd yanda yake ji, "kenan ita ɗin ba tasan wace ita ba, ba tare da manufa aka turo ta masarautarsu ba, duk da ta kasance jinin masarautar JOHAAN ce wato ƙaddara ita ce sanadin turota, taya zai fuskanci wannan al'amari???" Yaiwa kansa wannan tarin tambayoyin wan da ba shi da mai bashi amsa A hankali ya buɗe idanuwan nasa yana zuba su a fuskarta cikin gazgatar da zancenta ya furta "na yarda dake da abin da kika faɗa man, ina son daga yanzu ki cire ran cewar ba za ki mallakeni ba, ki sa a ranki na zama naki,duk da ni kaina nasan ko zan haɗiyi zuciya na mutu ba lallai iyayena da masu mara musu baya su amince ba" "Ni kaina na san da hakan sannan ko da ace sun Amince bai zama lallai ni na mallakeka ba, Addinina bai yarje min ba" na furta Murmushin takaici ya saki yana furta "har iyanzu na rasa gane wane Addinin ne kike magana da har bai yarje miki da aurena ba, Josmie na gaza gane kanki ko dai ba sona kike ba iƙirari ne kawai a baki, ko dai kin shigo masarautar nan dan ki uzzurawa rayuwata da soyayyarki, Why kike son cutar da rayuwata ta hanyar sanyaya man jiki da kalamanki, kin san kalmar da nafi tsana naji ta fito a bakinki na cewar ba za mu mallaki juna ba tsakanina dake" ya faɗa da idanuwansa waɗan da suka fara canza launi hannayensa na saki ina mai miƙewa ba tare da nai masa magana ba har sai da na ɗaga ƙafafuwana da zummar tafiya "kayi haƙuri da abinda nake faɗa maka na san da cewar kai ma ka san da gsky nake faɗa sai dai hangen ka na son cimma ƙudirinka ya hanaka gane abinda kake son cimmawa," Ina gama faɗin hakan na wuce zuciyata na mai sake buga mun na tabbatar da nayi gangancin faɗawa soyayyar ABIODUN wan da ban lura da illar hakan ba sai a yanzun Manyan idanuwansa ya rufe yana mai gazgata zancenta but why he will do it is not their fault, it is his heart's fault da har ya gaza yarda da gaskiyar da yake gani, "Soluwole ka taimakeni" ya furta a hankali *Adewale Femi* Duk yan da yaso hankalinsa ya kwanta akan ABIODUN sam ya gaza hakan har a ƙarƙashin zuciyarsa ya gaza yarda da in har ABIODUN bai bar Masarautar sa ba ba zai tsallake tarkon JOHAAN ba, Zazzzafan iskan dake bakinsa ya furzar yana mai lumshe idanuwansa zuciyarsa na sake buga masa a duk tsawon daƙiƙa ya tabbatar da ba zata daina buga masa ba har sai Jinin JOHAAN ya bar masarautar nan, da kanshi yake son gano wace ce ita da har ta sake a masarautar sa ba tare da wani yaga alama ba zai yi shiri sosai,dan tabbatuwar ganota Wani wahalallen numfashi ya sauke yana kallon Wazirin nasa wanda ya kasance jininsa ɗan uwansa Chubandoo " na san da ba ka san dalilin da yasa nake nemanka akan maganar da za muyi da kai mai muhimmanci ba , na san da cewar ka san da tun a wancan ƙarnin da ya shuɗe dubar masarautar nan ta tabbatar da cewar Jinin JOHAAN zai shigo a masarautar nan ya gusar da farinbcikin cikinta da nasarori sannan duba ya tabbatar da ba ko wane bane zai shigo face mace, wacce ita ce za ta auri Yariman Masarautar nan, a kwanakin baya da suka wuce tabbas jinin JOHAAN ya shigo a cikin masarautarmu wan da tun ranar data tsallako ƙafarta a masarautar nan zuciyana ya fara bugu sannan duban Boka OChucco ya tabbatar da lallai ta shigo wan da bana fatan wannan mummunar baƙar ƙaddarar ta faru" ya ƙarshe zancen da sauke nannauyar numfashi Sosai Waziri ke bin Mai martaba da kallo bakinsa ya gaza furta komai idan ban numfarfashin da yake saukewa tamkar wan da yai gudun tseral zuciyarsa na wani irin masa zillo da bugawa sai da yakai kusan Ten Minutes a haka sannan ya furta "Your Highness, surely there are many problems that will happen in this emirate where there is blood in the emirate of Johaan,dan tabbatas da manufa su kayi haka sannan da shiri da ƙulli nake ga me zai hana mu tasarwa Yarima tsaye sannan mu turawa KINGDOM OF JOHAAN da saƙon cewar mun ɗaro tarkonsu tabbas ƴarsu da suka turo za mu kashe, idan har ba su fito sun bayyanawa duniya manufarsu ba" Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗaya kansa alamun ya gamsu da shawarar da Chubandoo ya bayar "amma sai dai kuma sbd ƙara kiyayewa ina son *MATEO* ya dawo daga ƙasar US sbd sakawa ABIODUN Ido dan a halin yanzun sam shi ma na gaza yarda dashi" mai martaba ya faɗa jinjina kai waziri yai alamar ya amince duk da ya tabbatar da yaron nasa MATEO ba lallai yaso zuwa masarautar ba sai dai komai da dalili *Masarautar JOHAAN* Bayan haihuwar ARUSH sosai aka sha hidima ta ban mamaki da kuma bajinta, haka zalika hatta da Manyan Ƴaƴan Sarki wato Ƴaƴan Gimbiya Josmie dake ƙasashen waje suna aure sai da suka hallara taya murnar samuwar Yarima a masarautar su wan da sun riga da sun fitar da rai da kuma tsammani, A ɓangaren ARUSH ma sosai take kula da Yaronta wan da abubuwan dake faruwa da ita ya sakata ƙara dagewa da kulawa dashi,babban abin da ke tayar mata da hankali shi ne bai wuci cewar shima an ce mata tabbas tamkar yanda ake ɗaukar mata kingin ƴaƴa to a wannan karim ma shima ba lallai yasha ba Tamkar yanda ta saba ko wane dare idan za su kwanta yaron na a jikinta yau ma haka ta kasance wan da a hankali ta fara jin wani nannuyan bacci na son fixgarta ƙoƙarin hana kanta tayi amma hakan bai yiyu ba, jikinta dake maƙalƙale da jaririn aka kama da ƙarfi yayin da ake son rabata da yaron sai dai amma sam ta ƙi bada damar hakan bcox riƙo ba na wasa tai wa yaron ba, cikin huci da zafin rai Matar dake tsaye a gabanta ta daka mata wani ƙaƙarfan ƙarfe a hannu wan da yai sanadiyyar sakin yaron tana ƙwalla ƙara mai firgici "me yasa kuke son cutar da rayuwata ku ƙyaleni da azabtarwar da kuke man na roƙeƙu a wannan karin kar ku rabani da gudan jinina tamkar yanda kuke rabani da kingin ƴaƴana Azabtarwar taku ta isa haka har yanzun ban mance da sauran Yarana ba na san ko wacece ke za ki san ciwo da zafin da Mahaifiya za taji yayin data rasa Yaronta ,zan iya baku komai dana mallaka muddin za ku ƙyale mun Yaro, ku sani shi fa bai san komai ba idan laifi nai muku nice da hukuntawa ba shi ba, ko wace ke kin san da cewar ke ce mai nasara da galaba a kaina tun lokacin da ƙaddara ta shigo dani Masarautar nan nake haɗuwa da manyan abubuwan da har yanzu tabonsu bai bar zuciyana kunyi nasara ku ƙyaleni haka nan" ta faɗa tana mai sake fashewa da wani kuka mai ciwo wan da ke fitowa har a ƙarƙashin zuciyarta shedaniyar dariyar da taji an fashe da ita before a tsagaita ana furta "ARUSH har yanzun ba muyi nasara a kanki ba kin tsere min kin min fintinkau taya kike tunanin zan iya barin rayuwarki ki huta ke ce silar shigowa rayuwata ke ce rusa dukkan wani farincikina taya kike tunanin zan ƙyaleki kaɗan kika gani" Ana gama faɗin hakan aka fashe da dariya yayin da matar ta zuro hannu da zummar ɗaukar sa sai dai caraf Arush ɗin ta riƙe "a gabana da ba za ki ɗaukar mun Yaro ba sai dai idan rayuwana kika fitar ki san........" Bata idasa ba sakamako wani abu da matar ta watsa mata a fuska wan da ya sakata sakin wani wawan ihu mai cike da hargitsi da azaba wan da har lokacin yaron na a hannunta riƙe ƙam haka za lika idanuwanta na a rufe Jin shiru na wasu ƴan daƙiƙu ya sakata ware idanuwanta jikinta sharkaf da zufa yaron na maƙale a jikinta wata wawauyar ajiyar zuciyar ta saki tana mai bin ɗakin da kallo ganin Josmie da kuma Mai Martaba wan da yake kallonta da damuwa fal a ranshi a hankali yazo wajen ta yana rungumeta luf tai a jikinsa tana sauke numfashi da ajiyar zuciya tare da fashewa da kuka mai tsanani Bubbuga bayanta ya fara yi yana furta "ARUSH what's going on you're yelling ?" ɗago da fuskarta tayi tana girgiza kai tare da faɗin "whatever happened to me da ake son ɗaukar mun Yaro baya ga waɗan da aka ɗauka ba zan iya ci gaba da zama Masarautar na ba muddin kuwa aka ci gaba da yunƙurin ɗaukar mun Yaro" hannayenta Josmie ta kama tana furta "ARUSH me kike faɗi ne haka? kin san harda sawa ranki da kikayi har ya saka kike mafarki yanzu haka fa ihunki da kururuwarki ya saka Hadimai sanar damu, ki cire komai a ranki babu abinda zai faru dake da Yaronki,ki mance abubuwan da suka faru dake a baya.......... *Hmmmm na gaji da rashin comments naku ɗaiɗaiku ne masu so nima zan daina takura kaina akan dole sai nayi,masu yi man ina godiya sosai* *Musamman ƴan Amanar,Rahina Aminu, Ummi Suraj, Aunty Hauwa Safinabala,Mariyanbaba ngd ssoaii Allah ya bar zumunci* *RIAMCOOL ce* Writer of RUSHEWAR RAYUWA *BAYAN WUYA* *ANYA UBA NE* And now *KULU* [10/23, 9:05 PM] CUTIE~RIAM: *KULU* *BY RIAMCOOL* *MIKIYA WRITER'S ASSO.....* P.29&30 Wani zazzafan iska ARUSH ta furzar yayin da har lokacin hawaye ba su daina tsiyaya a idanuwanta ba, A hankali mai martaba ya saka hannayensa yana ɗauke mata su wan da har lkcn bai yi mgn ba tsabar damuwa da lamarin matar tashi,an ɗau kusan 10 minutes ba tare da wani yayi mgn ba sai bubbuga bayanta da yake wan da ya saka ta yin shirun tana mayar da ajiyar zuciya "ARUSH why are you still refusing to calm down"King Velentino ya faɗa yana mai janyeta a jikinsa tare da ɗago da fuskarta girgiza masa kai tayi tana furta "sam bana tunanin da akwai ranar da zan iya kwantar da hankalina muddin abubuwan da suka faru basu gushe a zuciyata ba sannan ba a daina bibiyar rayuwata ba, bcox of what da ake zaluntana tsawon shekaru kana kallo da idanuwanka ko su waye ina tare da su sannan sun fito fili a zahirance sun bayyana ko tantama ba nayi a cikin su sune masu ɗaukar........" bata idasa ba sakamakon wata gigitacciyar tsawar da ya buga mata yana jifanta da manyan idanuwansa waɗan da suka janza launi tsabar ɓacin rai na lokaci guda "ARUSH babban kuskuren da za kiyi shi ne saka ƴan uwana da dangina a cikin lamarin ki haka zalika babban da nasanin da za kiyi shi ne kuskuren ƙara ambatar cewar Sune silar sace miki yara, ki sani sam ba za ki taɓa haɗani da ƴan uwana ba haka zalika ƙullinki bai isa ya sakani rabuwa da su ba ko kuma aminta da zantattukanki ,ki gyara kalamanki" ya faɗa cikin tsantsar ɓacin rai tare da hankaɗa Arush ɗin gefe guda tana faɗuwa da ita da yaron hannunta a hanzarce Josmie tazo tana ɗagata wanda idan ban da kuka babu abinda take haka zalika zuciyarta na azalzala da zafi da kuma raɗaɗi "Sai yaushe ne za ka dawo hanya ka fara gane abinda nake furta maka,gsky ne na tabbatar ɓatar maka da hankali akai....." bata idasa ba sakamakon rufe mata baki da Gimbiya Josmie tayi tana girgiza mata kai Alamar tai shiru, shirun tayi tana ci gaba da kuka wanda har muryanta ya dishe,wan da bata damu da hakan ba dan idan da sabo yaci ace ta saba tun ɗaura ƙafarta a gidan ya zame mata kurkuku, shine mafarin buɗe mata ƙofofin ƙaddararta, wan da ba tasan ranar rufesu ba Share mata hawayen Josmie tayi tana karɓar yaron hannunta tare da furta "ARUSH ki yi shiru ki mance komai a halin yanzu ki kwanta ki bacci ni zan riƙe maki yaron na tabbatar ba wani baccin kirki kike samu ba," ba ta iya furta komai ba illa ɗaga mata kai da tayi tana kwanciya kanta na wani irin sara mata ita kuma Josmie ta fita tare da rufe mata ƙofar ɗakin misalin ƙarfe 3 na dare yayin da ba ka jin sautin komai idan ban da bugun zuciyoyin mutane da kuma fitar numfarfashinsu, Babban Hall ne dake shaƙe da mutane, wan da ko wane ya rufe fuskanshi da baƙin kyalle haka zalika jikunnansu sanye da baƙaƙen kaya ɗaya daga cikinsu ne yai gyaran murya da alamar shine shugaban wannan kungiyar nasu da wata kalar shaƙaƙƙiyar murya wacce duk nacinka baka isa ka gane ko waye ba "na tabbatar kowa da kowa ya san dalilin da yasa muka taraku anan, shin ko kunsan muddin ba mu fara aiwatar da aiki ba rayukammu na cikin babban haɗari, yanzun babban abin da nake so a fara aiwatarwa shine kawar da Arush wan da shine zai ida bamu damar tunkarar Mai martaba, ba na son ko kaɗan wannan masarautar ta wanzu a ci gaba tamkar yanda aka bamu umarnin wargaza ta da ɓatar da tarihinta dole ne mu fara shirin yaƙi, ba nason wani ya saka yaƙini da duba cewar Masarautarsa ko wane ya manta da babinta da babin cewar ya taɓa rayuwa a cikinta sannan Mahaifarsa ce abin tunƙaho,mu mance da wannan dukkammu mu fara shiri" shiru su kai na lokaci kaɗan before su sauke numfashi ɗaya daga cikinsu na furta "dukkammu mun Amince sannan mun saka yaƙinin cewar za muyi wannan aikin tamkar yanda ƙungiya ta bukata,a halin yanzu wane mataki za mu fara bi?" wata dariya shugaban ya saki daga bisani ya tsagaita yana furta "matakin da za mu bi Akan ARUSH ne da Yaronta sune za mu fara kawar da su" na'am su kai da maganar ta shi yayin da lokaci guda ta shiga matsanancin ɓacin rai da damuwar ganin akwai masu son rusa mata daɗaɗɗen mafarkinta, da burinta ta cikin ƙyallen data rufe fuska take ƙare musu kallo yayin da take ƙara jijjiga kanta,zuciyarta na buga mata Bayan ta fito daga Hall ɗin taron a hankali take bin wajen da kallo,kai tsaye wani babban farfajiya ta samu ta tsaya wan da ke cike da itatuwa, sosai kanta ya kulle ta rasa me za tayi, Idanuwanta ta rufe tana furta wasu maganganu, ta ɗauki tsawon lokacin ta nayi before ta tsagaita, tana buɗe idanuwanta, dai dai ƙafarta ta ɗaga tana duba wajen yayin da ta saka hannaye tana ƙaƙular wajen harta tone wajen , Babbar laya ce duƙunƙune a cikin hannu ta saka tana ɗauka tare da warware ta ta fito da takardar dake ciki, a hankali ta fara magana da kirari "Babban Sheɗani DUNA magaucin jinin mai taken DUNA sha jini kaci hanta babban shaiɗani mai ƙahonni Babban makirin Aljani mai saka munaƙisa kaine Daba idan baku harka ta ɓaci kaine Ubana maganin kukana mai ilimin sanar dani tuggu a yanzu nazo ka warware mun abinda ke tunkaroni ka sani tsayin shekaru ina da burin hawa karagar Mulki muradina na Mulki masarautar JOHAAN na kafa tarihin da ba a taba kafawa a Africa ba" tana gama faɗin hakan tai shiru yayin da ita kaɗai ke jin maganar da ake mata, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana furta "na san da wannan sai na kawar da yaron Arush ɗin da ita wannan ba zai min wahala ba" Dariya taji an fashe da ita wacce har cikin dodon kunnenta, ake yi "Makirar mace ke har kina tunanin idan kika kawar da yaron Arush da ita kin gama da babunsu ina, da akwai wata jinin tata wan da wannan kuskurenki ne wan da kika aikata tsayin shekaru" aka ƙarashe maganar da wata shaiɗaniyar murya mai amo da zallar nuna taƙadaranci Wata masifaffiyar zufa ce ta yanko mata ta lokaci kaɗan haka jikinta ya ɗauki kyarma da zafi kanta ya fara zafi da sara mata "Duna me kake nufi? Ka yi man bayani yan da zan gane" "Abin da kikaji na furta na cewar Jinjirar da kika ɓatar tsawon shekaru Ashirin a yanzu hakan tana a raye, wan da in dai kina son cimma burinki da ƙudirinki to tabbas ya zama dole ki ganota ki fara kawar da ita sannan ki koma ya zuwa mahaifainta da ƙanenta, kiyi harmar ganota" ana gama faɗin hakan ta daina jin komai yayin da numfashinta ke fita da sauri_sauri zufa ta sake wanke mata jiki tana jin wani mugun zafi na ratsata duk iskan da Ubangiji ya wadata a wannan daren ita sam ta gaza jinshi tsabar bala'in da take ji sulalewa tai a bishiya tana zama tana ƙara harhade numfashinta, tun da take bata taɓa jin bala'i kalar wannan ba kenan shirin da tayi na tsayin shekaru bai faru ba,gujewa masifar tsayin shekaru da tayi bai yi,ba wannan wace kalar yarinya ce wacce ta tsallake tarkon ta???, ta kai ta ne inda babu wani mahaluƙin da ya isa yaje wajen ba tare da ya mutu ba ta kaita ne inda ƙara ace mutuwa taxo maka lokaci guda bisa ga inda ta ajiyeta,wane ya ceceta harya reneta yaushe hakan ya faru bata sani ba??? tai wa kanta waɗannan tarin tambayoyin *King Velentino* tun lokacin da ya baro Arush ya ke zaune sosai abubuwa suka jagule masa, yan zun ne ya tabbatar da mulki bala'i ne masifu da dama sun afkar masa tarkuna da dama ake ɗala masa daga masarautu da dama sosai zuciyarsa ta jagule masa zuciyarsa na ci gaba da bugawa yayin da yazo buɗe saƙon da Masarautar Handaash ta aiko masa rufe idanuwansa yai ya fara karanto Addu'ar su ta Christian sannan ya buɗe ya fara karantawa "Saƙo daga Masarautar Handaash tabbas ka cika kai cikakken mai wayo ne ka ɗana mana tarkon da ba lalle ya kamamu ba, ka sani har a gobe mune da riba, domin sirrukan da ka daɗe kana ɓoyewa mu na lokaci kaɗan mun ganosa ko kasan da Yariman Masarautar Handaash ya shigo masarautarku yayi rayuwa ya naɗar mana sirrukanku wan da ba tare da anga wata sheda ba ya fito ya dawo ya zuwa Masarautarsa, na tabbatar da cewar da munaƙisa ka turo jininka a cikin Masarautarmu to yau ga shi mun bincikota in har kana son ta rayu ya zamar maka wajibi da dolenka na lallai ka dawo a ƙasammu mu mulki masarautar ku," wata ajiyar zuciya ya saki brain ɗin shi ta cunkushe ya rasa gane me suke nufi "ƴa fa suke magana to shi yana da wata ƴa ne bai sani ba? baya ga ƴaƴansa ukku mata kuma biyu sunyi aure ɗayar na waje tana karatu wacce ko a yau sunyi waya, me suke nufi wane babban tuggun suke ƙullawa masarautarsa?" Ya tambayi kansa yana mai jin wani sabon ta shin hankali na lulluɓesa na jin cewar PRINCE ABIODUN ya shigo masarautarsa ya naɗar masu sirrukan Masarauta Ubangiji ne kaɗai ya san abin da zai wakana da kalar ta'adin da za suyi masa ya zamar masa wajibi ne shi ma ya fara shiri cikin ƴan kwanaki sosai rukuni ukku ke shiri yayin da Rukunin ƙungiya ke na su na son kawar da Arush haka zalika Itama matar take bincikenta na gano Yarinyar da aka ce mata rana raye, sosai ta hau bincike, Bishiyun jejin take kallo wan ta kafe Babbar ceɗiyar da idanuwa mai ƙullin jan ƙyalle wannan ya tabbatar mata da cewar Duna na wajen "na tabbatar da kana jina kana ganina a yau kace na dawo domin ganin fuskar yarinya na dawo da ƙwarin guiwata ka gwada man fuskarta" ta furta da sauke numfashi Faran takarda ce ta faɗo a tafin hannunta ɗagawa tai tana dubawa tamkar T v haka take ganin yarinyar tun daga kanta take kallonta har izuwa ƙwayar idanuwanta wan da sak ta Mahaifinta haka zalika fuskanta ta Mahaifiyarta tamkar anyi copy na Arush haka yarinyar take babu abinda ya bambanta su illa ƙwayar idanuwansa da ba kala ɗaya bace da ARUSH wannan ko tantama ba tayi tabbatas ƴar Arush ce da ta ɓatar tsayin shekaru , sai dai Babban burinta bai wuci ta gano asalin ina take zaune a halin yanzun "Duna na riga da naga fuskanta saura sanin in da take ko dan tunkarar in da take naga bayanta" ta furta da murmushin ganin nasara ta gabatota Cikin dakakkiyar murya aka furta "tabbas na riga da na gano a inda take zaune za kiyi matuƙar Mamaki idan kika ji cewar tana zaune MasarautarHandaash,shiga masarautar ba zai miki wahala ba muddin kika shirya tuggu" wani murmushi ta saƙi mai nuna tsantsagwaron makirci tana furta tabbas zan yi hakan a halin yanzun zan dakatar da masu son kashe Arush matakin farko da ya kamata nabi shi ne fara ɓatar da hankalin ARUSH sannan na bi shirin dana ƙulla *ARUSH* Cikin bacci ta fara jin kamar sheaheƙar Kuka wacce ta fara hautsina mata lissafi, da brain a hankali ta buɗe idanuwanta tana saukewa a kan narƙeƙiyar macijiyar da ta kafeta da idanuwa tana zalzalo da harshe haka idanuwanta suna wani kalar shuɗewa A hankali Arush ta sauko daga kan gadon tana zuwa akan mucijiyan da nufin dafata sai dai ɓat ta ɓace, a dai dai lokacin ne kuma taji dirar wani abu a gabanta yayin data ɗago idanuwanta tana ƙarewa Mutum ɗin dake tsaye gabanta yayin da aka lulluɓe fuska da jiki kafin tai wani ƙwaƙƙwaran motsi aka murƙusheta tare da shaƙa mata wani abu nan take brain nata ya juye hannayenta take son kaiwa ya zuwa Yaronta amma sam ta gaza hakan bakinta ya fara rawa da son magana amma ba hali nan take idanuwanta suka fara jujjuyewa *MASARAUTAR HANDAASH* *KULU* Kwance take yayinda taji cikin baccin ana fara shasshafata da wani abu mai sulɓi a ɗan firgice ta buɗe idanuwanta tana saukewa a kan narƙeƙiyar macijiyar data kafeta da idanu wacce ko tantama ba tayi mucijiyan data gani a waccan kari ne, baki take so ta buɗe ta fasa ihu ko za taji sassauci amma sam ta gaza haka jikinta ya fara karkarwa idanuwanta suka fara kakkafewa tana son somewa wata tsawa taji an daka mata wacce ya sa ta yin laƙwas ta buɗe idanuwan nata tana haɗiyar wani mugun yawu jin muciyar na magana "ban zo wajenki da niyyar cuta miki sai ma taimakonki da nake so nayi tabbas rayuwarki na a haɗari babba, yanxu ne taskar mabuɗin ƙaddararki za ta fara buɗe wa tamkar yacce ta Mahaifiyarki ta buɗe tun a matakin shekarun da kike, ina son dukkan abin da kika gani ya haye miki karki fitar da rai da matakin nasara a baya, rayuwarki lulluɓe take da cutuwa , wacce muddin baki cire tsoron dake ranki ba ba zaki taɓa ci gaba ba, ba lallai idan kin ganni yanzu ba ki sake ganina a karo na gaba ki amfani da kalmomin da na faɗa miki cikin hikima da basira, ki cire tsoro ki fuskanci ƙalubalen rayuwarki ƙaddararki yanzun ne za ta soma a baya ba komai bace" tana gama faɗin hakan ta kafeni da idanuwanta waɗan da idan nawa idanuwan ba gizau su kayi ba kamar har hawaye naga suna zubarwa, a hankali ta saka wutsiyar ta tana shafa mun kai tana furta "ki gazgata zancen da kika ji ana faɗi na cewar ke jinin Masarautar JOHAAN ce ba ƙarya aka furta miki ba" tana gama faɗin hakan ta ɓace yayin da ni kuwa zufa ke ƙara tsatstsafo min ina mayar da mugun numfarfashin na gaza tantance tsakani ruɗu da tsoro wane ne yafi yawa haka maganganunta na fara aunasu a ma'aunin lissafi, Waje guda na makure ina ƙara jan dogon numfashi tare da bin mutane dake kwance ɗakin da kallo, Na daɗe a zaune har gari yai haske Bintu ce ta buɗe idanuwa ta ganni zaune ina ƙarewa Mutanen ɗakin da kallo kallona tayi tana furta "kulu mai ya hanaki shiryawa ki fita?" "Ba komai" na furta a taƙaice sbd yanda nake jin kaina ,Azalzala mata da ake ta taho shi ke bai bani damar ci gaba da magana ba, haka ta fice Ganin sun fita ya sakani miƙewa nima jikina sam ba ƙwari na shirya ganin har rana ta fara fitowa Kamar yanda na saba sashen sa na nufa in da na tarar bai nan alamar ya fita game samu nai na gyara ko ina na ajiye masa break fast nashi ganin bai dawo ba ta sakani yin Arwallah a gurguje ina na kabbara sallah wan da nake roƙon Ubangiji yafiya kan jin hutarkirin da nayi Motsin da naji a bayana ne ya bani damar juyowa gabana na wani irin bugawa zuciyana na wani irin harbawa da sauri _sauri da wani kalar mugun kallo da kuma tsananin tashin hankali yake kallona bakinsa na rawa ya furta "You Are a Muslim?" Hawaye sosai suka cika man idanuwa ina ɗaga masa kai hankalina a matuƙar tashe ,bai iya furta magana ba illa fatan Allah ya sa shine kaɗai ya ganta wani bai ganta ba cikin zubar da hawaye na furta "na tabbatar ban cancanci yafiya ba ƙaddara ce ke bibiyar rayuwana kai mun rai kar ka faɗawa kowa" a mamakina murmushi naga ya sakar mun yana furta "Josmie ko kaɗan ba wan da zai sani fatana dai ace ni kaɗai ne ya ganki kina salla,dan duk wanda aka kama Musulmi a masarautar na kashesa ake, abin da bana fata kenan," Ajiyar zuciya na saki ina ƙara godewa Ubangiji, "Thanks" na furta a hankali, hannayena ya kama yana kallon idanuwana da murmushi cikin wani salo ya fara murzawa da son kawo fuskarsa a tawa saurin kaucewa nai ina kwace hannuna "pls ka daina ni sam Addinina bai bada damar wan da ba muharramina taɓani ba" mamadin naga damuwa ko ɓacin rai sai naga akasin hakan yana murmushi "idan na aureki fa?" "Shi ma auren ba zai yiyu ba" na furta a hankali Annurin dake fuskarsa ya ɓace yana mai jifana da kallon son karin bayani "Josmie ban gane me kike nufi ba " "Ina nufin Addinina bai yarje mun auren wan da ba Musulmi ba, ba zan taɓa aurenka ba har sai ka kasance kai ɗin musulmi ne wan da na tabbatar ba mai yiyuwa bane, na sha gaya maka cewar ni dakai ba zamu taɓa mallakar juna ba, sbd nasan ba aure a tsakanina dakai har sai ka karɓi musulunci wan da abu ne mai wahala" na furta "Ko kaɗan Josmie akan na rayu dake zan iya aikata komai kin tabbatar mun da sai na musulunta zan iya mallakarki to tabbas zan musulunta sannan na mallakeki a yau zan tabbatar maki da abinda kike ganin ba zai faru ba tabbas zai faru a yau ɗinna" ya ƙarashe zancen cikin sanyin murya Ni kuwa sosai nake kallonsa da mamaki wasu hawayen farinciki na sake wanke mun fuska ina ƙara jinjina girman ƙaunar da yake mun, kafin nayi mashi wani magana ya fizgi hannuna, wata ƙofa naga ya nufa wacce ban san da zamanta a dakin ba, ta ita muka fito wata farfajiya wacce ba kowa a wajen sai manyan motoci cikin sauri ya jani muna shiga ɗaya daga cikin motocin umartana yai dana kwanta a back seat don kar a ganni, kwanciyar nai ina mai jin zuciyata na harbawa da sauri, tayar da motar yai inda muka dumfari get ɗin ba tare da sanin shi bane aka buɗe masa wanda sosai yai tafiya before mu fita get ɗin masarautar Hankalina a masifar tashe nake kallonsa ina furta "what are you planning to do?" "I will marry you I tried for you, I'm not ready to live a little breakup I will assure you of the war that you think will not happen "naji saukan furucinsa Wanda yai dai dai da bugawar zuciyana "Aurena fa kace za kayi baka tunanin matsalar da zata biyo baya kayi haƙuri ka mayar dani zan zauna a matsayin da nake" na furta Ba tare da ya ƙara mun mgn ba ya ci gaba da tafiya, munyi tafiya mai tsayin gaske before yai parking mota a wata unguwa wacce kai da ka gani ka san ta maras ƙarfi ce p cap ya saka da face masks yanda ba za a iya ganeshi ba umartana da na zauna a mota yai, ya fita a hankali yake bin unguwar da kallo zuciyarsa na buga masa haka zalika yana mai jinjina girman kasadar da zai yi,sai dai zai iya komai a kan ya mallaki kulu bakin wani gida yaje yana mai tsayawa yana tunanin yanda zai fara gabatar da maganarsa, gyaran Muryar da yaji anyi ita ce ta mai do sa daga tunanin daya tafi ɗago da idanuwansa yai yana saukesu akan Dattijon dake tsaye gabansa wan da da alamu shine mai gidan hannun Ya miƙa masa sukai musabaha, before ABIODUN ya ɗan nisa yana furta "na san da cewar ba ka Sanni ba sai dai ganina kawai da kayi da wata babbar buƙata nazo maka domin na sha jin cewar kai ne babban Malamin Musulunci a garin nan, na zo maka da maganar cewar ni ma a yau ina son ka musuluntar dani tabbas zan shiga a jerin sahun Musulmai" "Allahu Akbar haƙiƙa na tayaka murna da har ka gane addinin gaskiya za kabi sahummu"dattijon ya faɗa Ɗakin soron gidan ya ja ABIODUN suka zauna nan take ya karɓi musulunci , sosai mutumin ke murna in da duk wani abu ya fara koya masa ganin bai da lkcn koyon ya saka shi samun biro da littafin ya rubuta dukkan Abinda Ya dace Musulmi yayi kama daga wanka da banbance su Arwallah sallah,haka zalika yace ya zaɓi sunan da yake so, cikin sunayen da aka bashi zaɓi sosai yaji sunan ALIYU ya kwanta masa dan haka ya zaɓeshi "Sai dai har yanzun ina da wani Abun da zaka min shine aura mun wacce muke tare da ita" ABIODUN ya faɗa "Ba damuwa ina ita yarinyar" Dattijon ya faɗa ba tare da ya bashi amsa ba ya je ya taho da kulu wan da idan banda zuciyana dake bugawa babu abinda yake haka zalika ɓangare guda na tsinci kaina da faruncikin musuluntar da ABIODUN yayi "Tabbas kina da Babban rabo a duniya da lahira, tun da ki zamto musuluntar sa, kika kawo shi ya zuwa addini gsky a halin yanzu ya zo min da maganar aurenku," Dattijon ya furta yana mai kafeni da idanuwa Ba tare dana bashi amsa ba ya ci gaba da cewar "sai dai ina da tambayar ke ina mahaifanki suke duk da nasan ba lallai shi iyayensa sun sani ba" "Ban da kowa nima sanin iyayensa ba za su amince ba ya samu zuwa nan" Jijjiga kansa yai yana furta, "ma sha Allah na ɗauki nauyin biyawa Aliyu sadaki" Jinjina da godiya mu kayi masa wan da ba tare da ɓata lokaci ba ya tara shedu aka ɗaura mana aure akan sadaki 30k, Sosai yai mana nasiha ya ƙara tunatar dani kan koyawa ABIODUN abubuwan Addini Sallama mu kai masa da godiya muka bar wajen,koda muka dawo mota sosai yake zuba murmushi da farinciki hannayena duka ya kama yana ma ƙara narkar da idanuwansa a cikin nawa "na tabbatar ba sunanki Josmie ba ko za ki iya gaya min sunanki na zahiri yanzu" Murmushi na saki ina furta "HAUWA'U amma wan da aka fi kirana da shi shine KULU" murmushi ya saki yana mai furta "Hauwwa" Murmushi nai, a hankali ya saka hannayensa yana mai rungumeni tsam a jikinsa tare da sauke ajiyar zuciya tallafo da fuskana ya yi yana haɗe bakimmu waje guda yana tsotsa, cikin wani kalar salo da ya haifar mun da shiga cikin wani yanayi na daban, sosai na muka ɗan sha soyayya before mu tsagaita mu dumfari Masarauta wanda ƙirjinanmmu ke ci gaba da bugawa Lkcn da muka shiga ciki sosai gabana ya tsananta faɗuwa ina mai jin jikina ya sauya mun yadda muka fita ba tare da an gammu ba haka muka dawo ba tare da wani ya gammu ba, ɗakinsa na koma ina mai zama tare da mayar da numfarfashi zuciyana fal cike da tsoro, da ƙarfi aka buɗe ƙofar Falon wan da dukkammu sai da gabanmu ya faɗi sakamakon ganin Uwar gidan sarki wacce ke bina da tsinannan kallo tana bin ABIODUN tare da furta "Where did you enter? It's been a while since you've been home. and you let someone know that you are not going out" ɗan yatsina fuska yai yana furta "Awujo I am a small child and when I go out I have to announce" Ba tare da ta mashi magana ba ta juyo wajena tana kallona wan da muka haɗa idanu, a masifance taxo kaina tana ɗaga hannayenta tana sakar min marin da sai dana fasa ihu tsabar zafi ga wajen da ya ɗan fara fashewa, "I am your generation and you will make eye contact with me and get out of here and you will be punished badly" Sosai ABIODUN yaji marin wan da har sai da ya rintse idanuwansa yana mai jin zuciyarsa na mashi zafi, "Son" yaji saukar muryan Mahaifiyarsa wacce ke shafa masa kai, zuciyarsa a cunkushe ya amsa da "Yes" Cikin ɗan damuwa ta dubesa tana furta "ko kasan goben nan Mateo zai dawo sbd umarnin da Mahaifinka ya bayar kan ya dawo ya saka maka ido akan bai yarda da kai ba sbd gujewar mu'amalantar jinin JOHAAN " Shiru yai na lokaci kaɗan yana mai jin wani yanayi a tattare dashi haka za lika idanuwansa sosai suka tara ruwan hawaye na tuna cewar ya karyawa Mahaifinsa Arqawalin daya ɗaukar masa, Da mamaki Maman nashi ke kallonsa tana furta "Abio kukan me kake hakan?" "Ba komai idona ne dake ɗan ciwo , Awujo ina da buƙatar keɓewa ni kaɗai" ya furta a hankali wanda ranshi da zuciyarsa sam ba daɗi Ɗan ɓata rai tayi tana kallonsa "Abio ba gsky ka faɗa mun ba dole da akwai dmw a ranka ka faɗa Mani me ke damunka" shiru yai yana furta "Awujo ba komi ki bani maganin ciwon kai nasha" Ba tare da ta sake magana ba itama ta ɗauko masa Box ɗin maganin sanin ba zai ƙara mata magana ba sbd shi kaifi daya ne ba shi tai yasha tana fita ranta cike fal da damuwa, ABIODUN kuwa sosai ya ke son sake keɓewa da kulu Babban ta shin hankalinsa shi ne bai wuci jin cewar gobe Mateo zai dawo wan da sam bai ji daɗin hakan ba, ya tabbatar da ba zai dinga samun damar keɓewa da kulu ba, Wankan shiga musulunci yayi tamkar yanda aka koya masa,abubuwan daya rubuta ya fara koyo wan da cikin hukuncin Allah dandanan ya iya wasu abubuwan Har yai Sallar La'asar har zuwa ishsha'i wan da har lokacin bai sake ganin Kulu ba wan da sosai ya ɗan shiga damuwa *KULU* Tun lokacin dana fita na wuce ya zuwa sashemmu hawaye na zuba, ɗakin na dumfara wan da wajen yake a kulle Sama_sama na fara jin ihu da nishi na tashi wan da ya sakani ɗan tura ɗakin a tunanina ko wani ne ba lafiya Sai dai abinda na gani ne ya sakani ja da baya ina ambatar sunan Allah wan da idanuwana suka kafe kan Ochuchuwa da Febo da suka danne Bintu suna shirin cimma manufarsu, hankalina a matuƙar tashe na nufi wajensu, mamadin naga shakku ko nadama sai naga sun sheqe da dariya, suna nufoni rufe idanuwana nayi sakamakon ganin jikinsu haihuwar uwarsu,. Hannu Febo ta saka tana fizgoni wan ɗa ko kaɗan ban yi motsi ba illah raina da ya fara ɓaci zuciyata ta fara sosuwa, zanenta Bintu ta rufa tana zuwa bayana ta ɓoye, wan da idan ban da kuka babu abin da take, ihun da naji Ochuchuwa ta saki ne ya sakani kallonta muna zaro idanuwa ganin yanda jinin ke zuba a gabansu ga kumfan daya fara fitowa a bakunansu hankalina a tashe naja hannun Bintu muka fita don na tabbar da cewar Diyana ce kuma tabbas sai ta kashesu yanda ta fitar musu da kumfa a baki ta sakar musu dafi Waje na samu ina zama, a matuƙar tsorace Bintu ke kallona tana furta "Kulu me ye hakan waye ya fitar musu da jini" "Manta da babinsu Bintu naji da abinda ke damuna," na furta da hawaye "Wace damuwa?" Ta tambayeni da son jin qarin bayani Sosai na zauna na bata labari wan da take kallona da al'ajabi da kuma jinjina wa lamarin Ubangiji,sosai ta bani baki da rarashi kan na kwantar da hankalina, Mun dade sannan muka fara jin ihun mutane da koke koke tunkarar wajen mu kayi wanda muka tarar da gawar su Ochuchuwa,hankalina sam bai tashi ba bcox na saba da kalar wannan abun, bayi da kansu su kai musu al'adar su suka samu wajen aka birne gawarsu *Washe gari* Tun da sassafe kake jin sautin bisa wacce ke nuni ana buƙatar ko wane ya hallara ya zuwa Fadar sarki kama daga iyalan sarki har Bayi,mutanen gari Ban san mi ya sa ba na tsinci kaina da bugawar zuciya haka zalika na tsinci kaina a damuwa Misalin ƙarfe 8:00am dukkammu muka hallara wajen wan da Babbar Fadar ta kacame da mutane da dama sai dai ko wane da ɓangarensa bayi daban mutanen gari daban, mu dake bayi muka jera layi , sosai nake kallon wajen da Sarkin yake da nufin ko zan ga ABIODUN,sosai idanuwana suka sarƙafe da nashi murmushin da ba lallai a gane yana yin sa ba ya sakar mun, wan da nai saurin kawar da kaina gefe sosai wajen yai tsit yayin da ba ka jin sautin komai sai maganar mai martaba Adewale Femi, wanda yake furta "na san mutane da dama za suyi mamakin yanda akai na buƙacesu, ba komai bane face ina son a yau na gano munafikin ɗan aiken da JOHAAN su ka aiko a yau ɗin nan zan fitar da jinin JOHAAN wan da muddin na kama shi sai na azabtar da ko waye kafin na yanke masa hukuncin kisa,tabbas ko wacece za ta riski mummunan hukunci, ki fito da kanki ko wacece" Lokaci guda zuciyar Kulu data ABIODUN ta buga sosai ya shiga ruɗu da ta shin hankali "yaushe Mai martaba ya yanke wannan hukuncin ba tare ɗaya sanar dashi ba, ya Allah wace ƙaddara ce ke gabatoshi haka?" ya furta a zuciyarsa Ni kuwa sosai gabana ya tsananta faɗuwa "ba ƙarya aka faɗa miki ba tabbas ke jinin JOHAAN ce" na furta a hankali ina tariyo maganganun ABIODUN Diyana Mucijiyar data sanar dani harna fara gazgazgatawa , kenan nice wannan jinin da masarautar ke nema, wannan ce ƙaddarar da ake furta Mani za ta auku gareni me zai faru dani ban sani ba a hankali wasu siraran hawaye Masu zafi suka fara saukar mun a kunci ba tare dana bari wani ya gani ba na share ina mai addu'ar neman sassauci shiru wajen yai kowa kansa na ƙasa ganin hakan ya saka mai martaba umartar da akawo wani zobe wan da ake buƙatar kowa ya saka in har dutsin wannan zoben ya kawo jaaa to kai jinin JOHAAN ne Ruɗu bana wasa ABIODUN ya shiga ba,bai ida shiga ta shin hankali ba sai da yaga zoben wanda da kanshi ya dauko wannan zoben a JOHAAN ,bakinsa ya gagara furta komai idan ban da jikinsa ɗaya ɗan fara kyarma kanshi ya ɗauki zafi zoben nan aka fara sakawa Bayi wan da kowa aka saka mawa bai kawo jaa, duk layin wani idan yazo sai zuciyata ta sake bugawa, ga ko ina da tsaro babu damar guduwa, layi ne yazo kan Bintu wacce daga ita sai ni, hawayen dake maƙale a idanuwanta na shanye lokacin da layi yazo kaina hannayena na miƙa ina mai rintse idanuwana, da fatan Allah ya sa ba nice Jinin JOHAAN ba, shirun da naji na ƴan daƙiƙu ya bani damar buɗe idanuwana, wani kalar zaro idanuwa nai ina girgiza kai ganin Zoben ya nuna ja a dutsen, bakina ya fara rawa hawaye suka fara fitowa a ciki kowa na wajen sosai yake kallona musamman Sarkin dake man da wani kalar tsinannan kallo mai nuna zallar tsana, ban ida dawowa daga ruɗun dana tafi fa naji an wani harɗeni da sarƙa mai masifar zafi wacce tai sanadiyyar faɗuwata ƙasa kaina na buguwa da girkakken dutsen dake ajiye, nan take na ƙwalla ƙarar azaba jini na tsartuwa Tun lokacin da jan ya kawo a zoben ABIODUN ya rintse idanuwansa bai ida dawowa hayyacinsa ba sai da yaji ƙararta buɗe idanuwansa yai yaci karo da jinin dake tsartuwa a goshinta da bai kasance mai dauriya da wayancewa ba tsab za ka iya karantar yanayinsa na shiga tashin hankali Bintu kuwa wacce bata da dauriya tuni ta fashe da kuka tana furta "na higa ukku ni Bintu za su kashe Kulu" da mugun gudu ta nufi wajen mai martaba tana faɗuwa " mai martaba kai man rai karka kahe mun ƴar uwa" ƙafarsa Mai martaba ya saka yana shure Bintu tare da bada umarni a haɗata da Kulu a ɗaure wacce turjejen da take da burburwa ya harduƙa wani Dogari ya bugaa mata babban ƙarfen dake hannunsa a kai wanda ta tafi Luuu ta faɗa a hannun *MATEO* wan da shigowarsa kenan a masarautar da wani kalar kallo yabi ta yana ida yada ita ƙasa tare da yatsina fuska Ihuuu mai ƙarfi na fasa ganin numfashinta ya tsaya cakk, ga jinin dake zuba tamkar an buɗe famfo,cikin rashin imani wani bafaden ya fara jana da sarƙar a ƙasa wanda duk inda ya ja sai wurin ya kwalje yana tsirtuwar jini Har akan ƙafar mai martaba aka jawoni wan da a lokacin na fara ganin dishi_dishi bakina ya gaza buɗe wa,cikin rashin imani da tsana Adewale Femi ya saka ƙafafuwansa yana take man wuya tare bubbuga mun sandar hannunsa, hannu ya miƙa aka bashi babban karfen daya tanada a cikin wuta hannayena ya kama yana aza mun ƙarfen yayin daya sake buga mun kai da wani dutsen nan take jinin ya biyo hancina da baki, yayin da naji dukkan wani numfashi da motsi ya tsaya mun Wata gigitacciyar ƙara ABIODUN ya saki yayin da hankalin mutane ya dawo kanshi a ciki harda mai martaba, dake kallonsa a mamaki ganin yanda jikinsa ke rawa haka zalika hawaye na biyo kuncinsa "Abinda kake gudu tabbas ya faru me yasa za ka min haka ba ita ya kamata ka hukunta ba ni yadace ka fara hukuntawa kafin ita domin ita ba tada laifi nine da laifi da har na aureta,a halin yanzun ta zama mallakin ita ɗin matata ce ita ce wacce na zaɓa akan rayuwar masarautar .........." Alhm anan na kawo qarshen littafin kulu Book 1 mu haɗe a Book Two *To fa yanzun wasan ya fara,yanzun ne lvr kulu da buɗe shafin ƙaddararta zai soma,shin me ke faruwa da masarauta JOHAAN , su waye ke ƙulla tuggu da makircin kashe ARUSH da Yaronta,wace ƙaddara ce ta bibiyi Arush a tsawon shekaru ,wace mai sace Mata yara wacce ita ce sanadin sace Kulu a halin yanzu kuma take neman kawar da ita, shin za tayi galaba wajen haukatar da Arush kuma ta kashe Kulu kamar yanda tai iƙirari shin wai wace gaba ce tsakanin masarautu biyu da har HANDAASH ta tsani jinin JOHAAN shin ya Kulu da Bintu za su kasance kashesu za a yi kokuwa, me zai biyo baya baya ga jin furucin ABIODUN, ku biyoni a Book Two wan da zai baku amsoshinku ya warware muku cakwakiya da sarƙaƙkiyar dake ciki, ku sani fa KULU ba a fara komai a cikinsa ba yanzune lvrn zai fara cike da tarin abubuwa, idan kina son mallakar na biyu za ki biya ɗari Ukku kacal ta wannan Account ɗin 9074759493 Maryam zubairu sani opay bnk idan kuma kati ne za ki turo na ₦400 za ku turu shaidar biyanku ta wannan number 09074759493* *Mai son tuntubata ga number 09074759493 or 08109554986 *