[2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... RAYUWA* *LABARI NE NA MUSAMMAN* *TAFIYAR TA DABAN CE, HAKA MA SALON NA DABAN NE* DAGA MARUBUCIYAR *CANJIN BA ZATA* *WA GARI YA WAYA* *HATTARA* *RANAR NAKA* MARYAM IBRAHIM LITEE No.1 SHIMFIƊA Abdurrashid ne tsaye a Office ɗinsa waya kare a kunnensa sai sakin tsaki yake. Usman abokinsa ko a ce amininsa ya shigo Office ɗin, sun dubi juna ya ƙaraso ciki. Me ya faru na ga kamar ranka a ɓace? Usman ɗin ya ce mishi daidai yana zama, tsakin ya kuma ja "Hamida nake ta kira wayarta ta ƙi shiga, fita za mu yi da major Daniel zuwa Suleja. An cire network a inda za mu kar ta ji ni shiru." Usman ya ce "Ni ma na tashi, gida zan wuce yanzu, zan leƙa in sanar mata kafin in shiga gida." Abdurrashid ya ce "Yawwa." Tare suka fita sai da Usman ya ga tafiyar su kafin ya faɗa motarsa ya bar wurin zuwa gidan Abdurrashid. ******** Hamida da ke tsaye gaban mudubi tana ƙare ma kanta kallo kwalliyar da ta ɗanɗasa tana jiran isowar ogan. Less ne mai asalin tsada kalarsa ruwan zuma dinkin doguwar riga ta kamata ta fidda komai na halittarta, ta gyara gashinta ta yi ɗauri mai kyau, ga ƙamshi mai daɗi tana yi. Jin knocking ya sa ta fitowa tana tunanin mai taya ta aiki ce saboda makaranta da take zuwa da ta fita ba daɗewa tunaninta ko mantuwa ta yi. Ta buɗe ƙofar sai ganin Usman ta yi haɗe rai ta yi tana jin da ta san shi ne da ba ta buɗe ba, za ta mayar da ƙofar ta rufe ya danno dole ta yi baya "Saƙo ne daga mijinki, za ki hana ni in shigo." Ta ƙara ɓata rai ganin shu'umin kallon da yake jifanta da shi, ta ja tsaki "Ka faɗi saƙon ka wuce." Ƙamshin da take yi da wanda falon ke yi ya shaƙa sai ya lumshe ido kafin ya buɗe su tar bisa ƙirjinta idanuwansa har sun canja kala don wata fitina da yake ji. "Ƙamshi kike, falonki ƙamshi yake, ki taimake ni in raɓi wannan ƙamshin naki, ko ba zan same ki ta aure ba don giftawar Abdurrashid ki bar ni in mayar da kwaɗayina na wutar sha'awarki da ke ruruwa a raina ki bani dama in nuna miki irin son da nake miki. Mijinki ya tafi Suleja ya nemi wayarki bai samu ba ki bani dama. Ja da baya Hamida ta soma ganin yana nuho ta ga wani uban tsoro da ya rufe ta ganin daga ita sai shi ta shige daki ta datse ta faɗa gado tana kukan wannan wace irin masifa ce, sai da ta ji tashin motarsa ta miƙe ta leƙa ta window. Kasa fitowa ta yi tana zaune a ɗakin har sai da Abdurrashid ya dawo, yamma sosai ya dawo. Ganin ƙofar a buɗe kuma ba ta fito tarar shi ba ya ba shi mamaki sai da ya shigo ciki ta fito ganin ta duk a wani firgice ya ƙara ba shi mamaki "Me ya same ki? Ya tambaye ta yana harɗe hannayensa a ƙirji ganin yadda ya tsare gida ta ƙaraso ta sanya kanta gefen kafaɗarsa don iya tsawon nata kenan "Mene ne na ce? Ya kuma maimaita tambayarta "Ji na yi kamar ana motsi a gidan." Tsaki ya ja jin me ta ce hannunta ya kama zuwa ɗakinsa bakin gado ta zauna tana bin shi da kallo sai da ya gama duk abin da zai yi suka fito zuwa dinning ya yi nisa da cin abinci ya dube ta ganin ba ta da niyyar ci ya cigaba da tsare ta da ido duk da ta gane me yake nufi ba ta cin ba har ya ƙare ya ce "Kin ci ne? Ta ɗaga mishi kai alhali ba abin da ta ci ita ba ta san yadda za ta yi da wannan masifa ba. *********** ASALIN LABARIN Lokaci ne na hunturu hazo duk ya rufe sama buji hadi da iska ke kada jama'a. A cikin garin Daura, a unguwar Tawalala gidan Mal Muntari Dattijuwa Innawuro ce tsugune a filin tsakar gidan, gabanta turmi ne sai kwarya da take kara lailaye hurar da ta cura. Riga da zane ne a jikinta na atamfa, sai dayan zanen da ta nade shi a kanta. Akwai giccin daidaikun matan gidan a wurin, wasu na girki wasu kuma suna aikin ta su hurar, walau ta sayarwa ko ta sha a gida, don gida ne da ya yi suna kasantuwarsa gidan yawa jama'a suna masa lakabi da gidan Fulani don asalin su mutanen Adamawa ne. Har gida ake shigowa sayen hurar su. Sunan Hamida dattijuwar ta shiga kira, yar yarinya da shekarunta ba za su haura sha uku ba ta fito daga wani daki da ke can yamma da gidan dauke da madaidaicin farin bokitin roba, ta karaso tana fadin "Ga ni Innawuro." Mita dattijuwar ta shiga yi "Kika shige daki sai mutum ya rasa me kike?" Murmushi yarinyar ta saki, cikin shagaba take cewa "Shiryawa fa nake Innawuro." Ba tare da ta kuma magana ba Innawuro ta mike ta nufi rumfarta inda yarinyar ta fito, tukwanen kasa ne shanye a wurin zama ta yi ta fara shafe su da farar kasa, tana hangen yarinyar tana harhada kayan da ta yi amfani da su, sai da ta maida komai a mazaunin sa sai ta dauki dan bokitin da ta fito da shi wanda ta zuba kawunan hurar da Innawuro ta cura. "Assalamu alaikum." Wata murya ta kwararo daga kofar shigowa gidan, Hamida ta ta da kanta tana duban inda ake sallamar, doguwar mace ce ingarma, wadda ke tsaye ba alamar rankwafawa, kyakkyawar bafulatana irin su maza ke wa kirari da mace me fasali ko ta yi aure ba mu dangana ba. Sanye take cikin wani tsadadden less lullubin gyale ta yi tana rataye da jaka kamshin turarenta ya cika wurin kana ganin ta ka san kanta a waye yake. Hamida ta karasa wurin ta da sauri tana mata sannu da zuwa, yara biyu ke biye da ita suna rike da kaya ta rungumo kafadar Hamida suka shiga dakin Innawuro. Abin ka da gidan yawa kafin ka ce me kowa ya ji Gwoggo ta Kano ta zo, sai shigowa ake ana gaishe ta tana ta rabon tsarabar da ta yo musu. Hamida da ta gama gaishe ta sai ta mike don tafiya aiken da za ta zuwan Gwoggon tasu ya dakatar da ita. Kafadarta ta dafa "Za ki bi ni diyata mu yi tafiyar mu birni ko? Wani iri Hamida ta ji ba ta yi magana ba sai ta yi murmushi ta fice har ta dauki bokitin ta bar gidan maganar na yawo a ranta sanin yayar mahaifin nata da ba ta taba haihuwa ba yaran yan'uwanta take dauka ta tafi da su Kano suna taya ta sana'arta ta sayar da abinci. Ni karatu zan samu Malam ya bar ni, ba za ni Kano sayar da abinci ba. Ta fadi a ranta daidai ta kawo gidan da za ta kai aiken, wanda tsakanin su gida hudu ne. Gini ne na zamani, ta shiga da sallama a kofar daki ta ga maigidan yana tsaye, ya yin da matar gidan ke zaune saman wata farar kujera, matar ta fara gaishe wa wadda tana ganin Hamida ta kunbura kamar an sa mata yeast, mijin shi fara'a ya fara "Amaryata ke ce tafe? Hamida ta wuce dakin mahaifiyarsa da sauri ta gaishe ta ta mika mata hurar, ta juyo ta baro gidan tana jinsa a bayan ta duk kuma kiran da yake mata bata waiwayo ba har ta shige gida. Ba ta yarda ta shiga wurin Innawuro ba sasan su ta mike da mahaifiyarta ta fara cin karo tana zaune a tsakar dakinta tana bai wa karamin danta magani. Kallo daya ta yi wa Hamida ta mayar da kanta ga abin da take, kusa da mahaifinta ta zauna wanda ke zaune yana cin abinci, kannenta su biyu maza su na zaune su ma su na cin abincin ta yi wa babanta sannu da zuwa ya ce ta je ta zubo kai ta girgiza ta ce ta ci abinci. Kannenta suna gamawa rige rige suke su taho wurin ta, sai dai ita tashi ta yi ta soma gyara wurin da suka bata, ta hada kwanonin za ta wanke babanta ya ce ta bar su akwai sanyi. Ta dan jima tare da su, ta mike ta koma sasan Innawuro ba ta samu Gwoggon su ba wanda ta yi murna da hakan don gudun da take kar ta kuma yi mata zancen bin ta Kano, sai dai ta tambayi Innawuro ina Gwoggo Indo? Ta ce tana dakin Malam. Malam Abdurrashidu wanda kowa ke kira da Malam Audu ya dubi kanwarsa bayan ta gama ba shi labarin makasudin zuwan ta, ta zo ne a ba ta Hamida ta tafi da ita birnin Kano. Duk da ba ya son daukar yayan yan'uwansa da Tilon kanwar tasa wadda Allah bai ba haihuwa ba take yi, don shi da daya Allah ya bar masa mai suna Aliyu, Ga ta ita kadai ce mace a cikin, su maza shida da iyayen su su ka haifa, ba zai iya duban ta ya ce mata A'a ba, sai dai yana tuna yadda za a raba Innawuro da Hamida, Hamida ta daban ce a wurin ta, amma ba shi da karfin halin furta hakan. Ya ce Mata "Yaushe ne tafiyar? Ta ce sai jibi, don akwai bikin diyar kawarta da za ta halarta. Ya ce" Allah ya kaimu. Ta mike tana godiya ta bar shi cikin mutuwar jiki yadda zai soma labarta ma Innawuro. Gwoggo Indo na komawa ta samu Hamida ta fito wanka tana murza mai, daga ita sai zane ta yi daurin kirji. Gwoggon ta shiga kare mata kallo tana sake sake a ranta. "Shekarun ki nawa yanzu Hamida? Hamida ta dago ido ta dube ta "Sha uku ne Gwoggo." Ta gyada kai Wannan nan da shekaru hudu zuwa biyar da za a yi maganar auren ta ba karamar mace za a gani ba. Gwoggo Indo ke fadi a ranta. Doguwa ce mai murjajjen jiki, ga ta fara kamar sauran yaran gidan nasu, sai dai ba ta da dogon gashi irin nasu sai dai na tan ma yana da cika har gaban goshinta ya kwanta lambam wanda ya kara kayata yar kib kib din fuskarta ga idanuwanta dara dara sun kara fidda kyanta. Yadda jikinta yake lukwi lukwi za ka za ci yar gidan wani hsmshakin ce, don ta fi kama da yayan hutu. Ajiyar zuciya ta fidda tuna abin duniyar da za ta samu wurin mazan da za su mutu kan son yarinya. Ta mike ta dubi Innawuro da ke damun hura, "Bari in je gidan bikin nan Innawuro." Ta ce "Haba dai, ba ki bari ki sha hura ga ta ina da ma miki." Ta dubi tarin kwanonin da aka tara mata daga sasan yan'uwanta ta ce "Cikina ba wuri Innawuro, kun cika shi taf, bari in je." Suka yi mata fatan dawowa lafiya ta fice. Sai da aka yi sallar Isha'i Hamida ta koma sasan iyayenta ta yi hira da babanta da kannenta, mahaifiyarta saboda kunyar yar fari ba ta shiga sabgarta. Sai da ta ga mahaifiyarta ta fara yi ma kannenta shimfida sai ta yi musu sai da safe ta baro sashen. Har kuma lokacin Malam Audu bai iya sanar ma kowa bukatar da kanwarsa ta zo masa ba, yana dakinsa yana juyayi, ya yin da Innawuro ke nata dakin tare da Alh mustafa dan kawarta wanda Hamida ta kai hura gidansa dazu. Takalmin da ta gani kofar dakin yasa ta gane ko waye, ta shiga da sallama shi ya amsa da fara'ar da bai iya hana kansa ita matukar zai ga yarinyar, sanin idan ba ta gaishe shi ba za ta sha fada wurin Innawuro ya sa ta gaishe shi, sai ta tsallake can karshen gado mai rumfa ta yi kwanciyarta bayan ta lalubo littafin hausa da ta samo aro. Tana karatunta suna hirar su har ya tashi tafiya sai da Innawuro ta gama kirga kudaden cinikin tukwanen kasarta da aka kawo mata,da kudin hurar da Mustafa ya kawo mata sai ta hau gadon da Hamida take "Me yasa idan Alh Mustafa ya gan ki ya yi miki magana ba ki yi masa? Kara lafewa ta yi kamar tana barci "Ina sane sarai ba barci kike ba." Turo baki ta yi kamar tana kallon ta "Ni to me zan ce mishi? Duk inda ya gan ni sai ya yi ta takura mini." Ba takura ba ce kauna ce, mai son ka ai ya fi wanda bai son ka." "Kauna kuma Innawuro? ", E kauna Hamida, don yau dai ya zo mini da zancen yana rukon ki, har sanda za a yi maganar auren ki, ya ce in gaya wa Malam. Kin ga ke ba za a dade ba aure zai dauke mini ke. Hawaye Hamida ta shiga yi "Ni Innawuro na fada miki ban son aure karatu nake so, ki roki Malam ya bar ni in ci gaba da karatu ga su Habiba (kawarta) har za su je js2. Innawuro ta lalubo wayarta ta kunna torch din wayar haske ya wadaci wurin har tana ganin yadda hawaye ke sauka bisa kuncin Hamida. Janyo ta ta yi ta shiga rarrashin ta kamar yadda ta saba, don ba ranar da za ta fito ta fadi ba ta yi mata kukan son ta ci gaba da karatu ba, don yarinya ce mai kulafucin karatu sai dai rashin sa'ar da ta yi kakanta Mal Muntari tun yana raye bai yarda da karatun yaya mata ba, iyakar su primary school bayan mutuwarsa kuma Mal Audu babban dansa ya dora kan wannan akida ta mahaifin na su, don da yarinya ta kare karatun primary za ta ci gaba da zuwa Islamiya har Allah ya kawo mata miji ta yi aure, to ita ma dai bara ta kammala karatun primary school ta bi sahun yan'uwanta da suka rayu a gidan ba ta zuwa ko'ina daga Islamiya sai taya Innawuro da Innarta aiki, sai karance karancen littattafan hausa saboda son karatunta duk inda ta gani sai ta aro ta zo ta karanta. Lallashi sosai ta yi mata amma yin shirun Hamida ya gagara don gani take kamar auren za a yi mata, don Mustafa tun tana karama kwarai lokacin ko aure bai ba yake mata wasa duk inda ya gan ta sai ya rika kiran ta matarsa. Da kyar ta hakura ta yi barci. Da safe da wuri ta fita ta tashi ta je sasan su ta taya Innarta aiki. Maimakon ta dawo wurin Innawuro wani sasan daban a cikin gidan ta mike, an gyara shi ya fita na zamani sabanin sauran sasan gidan ginin kasa ne. A kofar farko da ta shiga wanda shirin da aka yi masa zai fahimtar da kai kitchen ne, wata mace ta samu zaune ta ta sa gas a gaba da tukunya a kai, kallo daya ta yi wa Hamida ta maida idonta kan tukunyar. Hamida ta gaishe ta ta amsa a dakile "Ya Aliyu ya tashi? Hamida ta tambaye ta, ba ta yi magana ba sai kai da ta daga, ta wuce ta ta murda handle din kofar da ke kallon ta ta yaye labulai ta shiga da sallama, tsararren falo ne ta hango shi kan dinning yana break past ya amsa sallamarta ya yafuto ta da hannu ganin tana niyyar zama kan kujerun da suka yi wa falon kawanya. Kamar wadda kwai ya fashe mawa ta karasa inda yake, ya turo mata kujera ta zauna a sanyaye turo mata kwanonin da ke gabansa ya yi amma ta gaza taba komai, shi ma tsayawa ya yi ya dogare hannayensa a habarsa ya zura mata ido "Mene ne damuwar? Wa ya taba mini yar kanwata Innawuro ce ko Malam ko yaya Fatima? (Innarta) girgiza kai ta yi sai ga hawaye nan take ya ci serious yana tambayar abin da aka yi mata cikin kuka ta soma gaya masa damuwar ta yadda take son karatu da kuma wannan Mustafan da ya da me ta. Rarrashin ta ya yi ya ce zai je ya samu Malam ya kara rokon shi ya bar ta ta je makaranta, maganar Mustafa kuma wasa ake mata. Da haka ya samu ta yi shiru. Matarsa Uwani ta shigo dauke da wani bowl ta dire shi gaban mijinta, dan tsakalar abin da ke ciki ya yi sai ya mike umarni ya ba Hamida ta kwashe kwanonin ta je ta karya. Yana tsaye ta hada komai tare suka fita yana cewa Uwani sai ya dawo. ta raka su da harara kamar idonta zai fado don wani malolon bakin ciki da ta ji ya tokare ta, tana bala'in kishin shakuwar da ke tsakanin yarinyar da mijinta, duk da bakin da jama'arta ke ba ta na kar ta wani damu Aliyu shi kadai ya tashi dakin mahaifiyarsa shi da mahaifiyar Hamida, daga bisani bayan ta yi aure aka kawo musu yayen Hamida, da shi a ka yi renon ta har ta isa yaye aka kawo musu yayen ta, kallon kanwa yake mata duk da in ya koma ta wurin mahaifiyar ta diya ce a wurin sa. Amma zuciyarta me kishin ta ki yarda da hakan gani take kamar wata rana zancen zai sauya. Aliyu na gaba Hamida na bin shi a baya da tire niki niki. Dakin mahaifinsa ya shiga ita kuma ta shige na Innawuro, tana sauke tiren Innawuro ta bi ta da kallo don ta gano daga inda kwanonin suka fito "Ga shi Innawuro ya Aliyu ya ce in taho da su." Kai ta gyada mata "To kwashe ki je ku ci da kannen ki." Ai sun tafi makaranta Innawuro, Ke ba za ki ci ba? Ta girgiza kai tana ci gaba da muttsuka kwanan nan hurarta, ta gama ta kafa kai sai da ta shanye ta mike don soma ayyukanta, yau dai ba za ta yi hura ba, don tana da costomomi masu saye kowa kuma da ranar da take yi masa. Tashi Hamida ta yi ta dauko flacks da kayan shayi ta san Innawuro ta cika mata shi da ruwan zafi me dauke da Lipton da kayan kamshi, ya Aliyu ke sawo musu kayan shayi daga Malam har Innawuro babu mai sha. Karinta ta yi mai kyau wanda ya rage kuma ta adana ma kannenta, za ta fita ta wanke kwanonin Aliyu ya shigo, suna gaisawa da mahaifiyar sa ta wuce ta yi wanke wanken. Ta dawo daga kai ma Uwani kwanoninta Aliyu ya fito Innawuro na biye da shi tana yi masa addu'a ita ma Allah ya bada sa'a ta ce ta san ko za ta ji yadda suka yi da Malam sai ya dawo. Gado ta haye don ba aikin da za ta yi wa Innawuro Innawuro kuma ta wuce dakin Malam, ganin sa zaune cikin damuwa wadda ta lura tun jiya ya rage walwala yasa ta tambayar sa lafiya? Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa, don haka ta maza ya yi ya gaya mata. Dauriya mai yawa wannan baiwar Allah ta sanya don hana bayyanar wannan tashin hankalin da ta shiga jin wannan zance me kama da saukar kirsimati, a fuska, amma hatta jikinta rawa yake, addu'a ta yi sai dai duk yadda ta so basarwa su ci gaba da hirar su kamar yadda suka saba hakan gagara ya yi ta mike don barin dakin ya ce ta turo mishi Hamida Yana soma gaya mata ta matse kanta a cinyoyinta tana hawaye, da ya sallame ta dakin Innawuro ta koma tana mata kuka da magiya ita ba za ta kano ba ta koma saida abinci, ita karatu take so. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.. No.3 DAGA MARUBUCIYAR *CANJIN BA ZATA* *WA GARI YA WAYA* *RANAR NAKA* *HATTARA* MARYAM LITEE Ba ta ko kai ga zama ba Gwoggo Indo ta mara mata baya. Gefen katifar suka zauna, Gwoggo ta shiga bude ledojin "Ya aka yi kika dawo daga fita? Baki ta tabe "Ba fa shi ba ne, direbansa ya turo ya kawo mini tsarabar chaina, shi yana can karshen ta matarsa ta hana shi fitowa, kin san mijin ta ce ne. A haka kuma yake so ya aure ni mace na juya shi. Gwoggo Indo tana mayar da kayan da ta ciro ta ce "Ai don dai kin ƙi ne, amma wallahi da sai kin aure shi, to mu ma zama za mu yi? Tashi za mu yi mu nema yadda ta nema. Kuma shi kin ga kullum ya zo maganar aure yake." Baki ta kuma tabewa "Kyale shi Gwoggo, gara mini Alh Uba." ta ce "Na kyale shi, amma ya maganar sanya mini Easy? Na dawo na tarar da wuri yadda na bar shi." ta ce "Ki yi hakuri Gwoggo, ya ce direba ne zai kawo mai sanyawar, kuma shi ne ya je dauko ku sai dai gobe." Ta ce "Yawwa don zafin garin nan ya zo sai ya kusa tafiya da mutum." Suna ta hirar su Hamida tun tana ji har barci ya yi awon gaba da ita. Ta dai farka cikin dare ta gan ta lullube cikin lallausan bargo, Aina rike da wayarta tana charting, ta juya ta ci gaba da barcinta. Asuba na yi lokacin da Innawuro ta saba tashinta ta farka. Ta mike ta yo alwala ta zo ta yi sallah har da karatun alkura'ni da ta saba. Ba ta tashi a wurin ba zama ta ci gaba da yi tana tuna Innawuro da mu'amalarsu, da kuma iyayenta da yan'uwanta. Murda kofar da aka yi yasa ta daga kai Gwoggo Indo ce, soma gaishe ta ta yi ya yin da take kokarin zama, ta amsa cikin fara'a da tambayarta gajiyar tafiya. Ganin yadda take amsawa yasa ta ce "Ki saki jikinki kin ji Hamida? Da ni da Ibrahim abu guda ne babu banbanci, ki dauke ni kamar shi, uwar mu daya uban mu daya, ciki guda muka kwanta." Hamida ta ce "To." "Ko ba ki ga Aina harkokinta take ba ta da wata damuwa ba? Kai ta daga "To ke ma haka nake so ki rika yi." kan ta kuma dagawa sai ta ce "Wane aiki zan miki Gwoggo? Kafin ta yi magana Aina ta yaye abin rufarta ta tashi zaune tana mika, kafin ta mike wata yar riga mai hannun best take sanye da ita, kanta ba dankwali ta shiga bathroom ba tare da ta yi magana ba. Gwoggo Indo ta mike "Mu je ki gyara mini daki." Tare suka fita Hamida na biye da ita a baya. Dakin barcinta zuwa toilet ta gyara mata, ba ta ga mijinta ba Malam Buhari, da ta tambaya don ta gaishe shi Gwoggo ta ce yanzu ya fita wurin aiki. Daga inda take tana juyo hirar masu aikin Gwoggo, itan ma fita ta yi wurin su. Sai da ta gama gyara ko'ina tsaf! har falo, kitchen ne ba ta shiga ba don Aina tana aiki a ciki. Tana gyara dakin Aina Ainar ta shigo dauke da trey ta ce "Zo ki zauna mu karya." Da kanta ta hada mata tea me kauri ta turo mata chips da kwai, da ta kammala ci Aina ta fita, zuwa can ta dawo dauke da faranti da farfesun kaza ke ciki ta ajiye gaban Hamida nan ma cewa ta yi ta ci don idan suka fita ba samun zama ta ci abinci za ta yi ba. Sanya naman kazar bakinta sai da kunnenta ya motsa don dadin da ta ji, sai ta gane gaskiyar Gwoggo Indo da ta kira waya lokacin suna hanya bayan sun kare wayar sai mita take Ita fa shi ya sa ko ganin gida za ta Daura take bari sai jama'a ta dawo lahadi ( don ba sa yin girki Asabar da lahadi) don ta fi so ta hada komai da kanta. Kammalawarsu Aina ta zare cattle din da ta jona ta shiga wanka. Hamida ta kwashe kayan da suka bata ta yi kitchen, sai da ta wanke ta gyara kitchen din sai ta fito. A falo ta tarad da Gwoggo da Aina zaune kowacce ta sha kwalliya, Gwoggo Indo atamfa ta daura dinkin riga da zane, sai ta dora after dress mai matukar kyau, tana rataye da jaka mahadin takalmin kafarta. Aina ma atamfar ce, sai dai ita riga ce da skirt ne matsattsu da Hamida ta lura ita yanayin shigar ta kenan. Sai takalmi da jaka, falon ya gauraye da kamshi. Gaba daya suka dube ta! Aina ta dubi dallelen agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta sai ta ce "Ki je ki yi wanka Hamida, ke mu ke ta jira. Sai ta yi sauri ta shige ciki don ta shirya Gwoggo ta bi ta da kallo kafin ta maido idonta kan Aina "Sai kin samu zama sai ki samo mata kayanki a rarrage mata. Da kai ta amsa sai ta ce "A ina za a ajiye ta? Dan shiru Gwoggon ta yi sai ta ce "Ina son ajiye ta a shago ta koyi saida kaya, ina son kuma ajiye ta wurin abinci ta rika bayarwa." Aina ta ce "Ba da abincinta yana da matukar tasiri, a fara ajiye ta wurin sayar da abincin yanzu kafin nan gaba mu gani, ko Umar yana da amana zai kula miki da shagon provision din." gyada kai ta yi cike da gamsuwa da shawarar. Hamida ta fito cikin bakar jallabiya Gwoggo Indo ta bata ita tsaraba bara da ta je Umura. Ta dora bakin hijab, sosai ta yi kyau duk da ba wata kwalliya ta yi wa fuskarta ba. Ganin fitowarta sai suka mike Aina ta rufe ko'ina. A kasa suke takawa sun jera gwoggo da Aina kamar wasu kawaye, Hamida na biye da su a baya. Aina ta ce "Amma ya kamata ki raba ta hijab din nan Gwoggo." Murmushi ta yi "Kar sanya hijab dinta ya dame ki Aina, ba abin da sanya hijabinta zai sa, ina ji a jikina dauko Hamida wani babban jari ne, don kyakkyawar mace kadara ce. Sai suka yi dariya. Har suka isa Hamida na kara kallon wuraren. Kusa da get din fita wurin saida abincin yake shagon saida kayan masarufi na manne da shi. Masu aikin tuni suna wurin sun gyara komai, nar Hamida ta ga yarinyar jiya har suka yi hira take gayawa Hamida ita diyar daya daga cikin masu aikin Gwoggo ce sunanta Rabi. Hamida ta soma bayar da abinci bisa jagorancin Rabi, sai kuma sannan ta ga nau'in abincin da ake sayarwa akwai farar shinkafa da miyar kaji, sai waina da miyar ganye wadda sai sun zo ake suyar ta. Sai tuwon shinkafa miyar taushe ko kubewa danya. Akwai farfesun kajj irin shi ne Aina ta debowa Hamida sai na kayan ciki. Su Hamida sun ta zirga zirga daga wannan office zuwa wancan, ga shi akwai tazara mai yawa daga wurin nasu zuwa ainahin cikin company, ba nisan ya fi damun Hamida ba irin mayatar kallon mazan wurin ba ta saba ba. Da take ma Rabi korafi dariya ta yi mata ta ce su din wadansu irin mutane ne masu matukar son fararen mata. Sai karfe biyu da rabi komai ya kare maaikatan ma suka tashi daga aiki. Hamida da Rabi suka fara wucewa dakin su Rabi suka fara yada zango sai da suka idar da sallah su Gwoggo suka dawo, sai ta bar Rabi ta nufi falon inda Gwoggo Indo da Aina suke zaune suna lissafin kudaden cinikin yau. Sai mamakin tulin kudaden da ba ta taba ganin masu yawan su ba Hamida ke yi. Wayar Gwoggo Indo ta dau kara ta mika hannu ta dauko ta ta kanga a kunne "Alh Uba da kansa, ina gaisuwa ya kake ya harkokin? Ta dan tsaya ta saurara kafin ta ce "Kwarai ya ta ce, jiya na taho da ita, sai ta kuma saurarawa "Na ji to ya a ka yi? Ta kara saurarawa sai ta ce "Indai aure ne ka zo ka yi reno zan ba ka, amma ka bar wannan maganar." Sai ta kashe ta ta cilla ta saman kujera, suka hada ido da Aina sai suka saki murmushi "Aina ta ce "Da wuri haka Gwoggo? Wani kallo ta yi mata "Ba na fada miki ba, kin ga a hankali zan ja zarena zan dade ina tatsa don ko za a yi batun aurenta sai ta zama cikakkiyar budurwa, yadda duk wanda ya gan ta sai ya biyo. Dariya suka yi Aina na cewa "Gaskiyarki Gwoggo." Cikin kwanaki bakwai Hamida ta sake da kowa a gidan. Tana shiga kuma a yi komai da ita, musamman girke girken saidawar da ake, hakan ba karamin dadi yake wa Gwoggo ba. Ranar ta kama lahadi da safe misalin karfe goma zaune suke a falo. Gwoggo ta dubi Aina " Wai ni kam Laila lafiya take? Aina ta ce "Me ya faru Gwoggo? Ta ce "Tun fa dawowata da ta kira ni ta yi min sannu da zuwa har yau ban kuma jin ta ba." Ba ta jira cewar Aina ba ta dubi Hamida "Kira mini Rabi." ta mike zuwa dakin nasu, su duka kwance suke sun tattake bisa shimfida mutum biyu ke barci, ukun hirar su suke. Ta gaishe su sai ta fada wa Rabi sakon Gwoggonta. Suka jera har gaban Gwoggon sai da ta gama gaishe ta ta ce "Ku je ke da Hamida gidan Laila. Sai ta mayar da duban nata ga Hamida "Idan kun je ki ce na ce tun da na dawo ban gan ta ba, kuma ta ba ki kayan sawa." maganarta ta karshe ta sa Hamida ta ji wani gingirin! wai ta ce ta bata kayan sanyawa? Je ki canza kaya ki zo ku tafi Gwoggo ta ce mata ganin yadda ta tsaya sororo a sanyaye ta juya zuwa daki ta canza kayan ciki irin wadanda Aina ta ba ta kala goma sha biyu kuma duk masu kyau da tsada. Ta kara murza hoda ta sanya farin hijab, sai ta fito suka yi musu sallama suka fice. A hankali suke takawa cikin Estate din suna hirar su har take ji wurin Rabi kanfanin nan da suke ciki na sarrafa fata ne. Har suka kai wasu rukunin gidajen ma'aikata, gidajen duk iri daya ne kamar na su Gwoggo Indo sai dai wadannan sun fi kyau nesa ba kusa ba, don mijin Gwoggo Indo karamin maaikaci ne. Rabi ce ta yi knocking shiru ba a bude ba ta kara nan ma shiru sun ci gaba da tsayuwa ba alamar za a zo a bude har sun fara tunanin ko ba kowa suka ji takun tafiya, ganin wadda ta bude yasa Hamida washe hakora domin dai bahaushe ya ce kowa ya ga na gida ya bata ahu, sai dai kallon ba yabo ba fallasa da yar'uwarta ta ta yi mata yasa ta,gintse fara'arta ta. "Ku shigo." ta fadi kamar tana rowar a ji muryarta. Ita ma din kyakkyawa ce kamar sauran yan gidan su, matsakaicin tsawo gare ta tana da jiki jawur take kamar ka taba jini ya fito. Mahaifinta Gwoggo Indo ke bi mawa. Suka bi bayanta har cikin falonta. sun zauna wata mata ta shigo bayan ta kwankwasa Rabi ta mike ta bude mata, goye take da yaro a bayanta Hamida ta mike ta karbi yaron yar'uwarta ta mai suna Amir. Lailar ta umarci matar ta kawo musu lemo. Sun dan jima zaune ganin ba alamar za ta kara magana Hamida kuma tunda ta fadi Gwoggo ta ce ba ta gan ta ba tun da ta dawo yasa Rabi fadin sakon Gwoggo na ta bai wa Hamida kaya. Shiru ta yi kamar ba ta ji ba Hamida ta mike ta ce za su wuce. Ta ce tana zuwa, ta dan jima ta fito dauke da jaka ta mikawa hamida har da kudi, godiya ta yi mata suka fito. Washegari suna wurin saida abinci Hamida zaune ita da Rabi, daya daga cikin masu aikin ta leko ta ce Gwoggo ta ce Hamida ta kai abinci office din Alh Danlami. Gabanta ya buga ta wuce cikin mutuwar jiki. Take away aka bata mai dauke da farfesu na kayan ciki sai aka saka cikin wata leda. Tafiya take amma hankalinta ba ya jikinta don kullun aka aike ta mutumin sai ya yi mata maganar banza. Masinjansa ya fada masa isowarta ya ce ya ce ta shigo shi kuma ya aike shi, don da masinjan yake aike amma tunda ya ƙyalla idonsa kan Hamida ya daina aikensa sai dai ya yi waya ya ce a kawo masa. Hannunta na rawa ta murɗa handle din kofar ta shiga da sallama, ya amsa yana ƙure ta da kallon da ke kara sanya jikinta daukar rawa wurin da ake ajiye masa ta nufa ta ajiye sai ta juyo gani ta yi mutum yana sanya wa kofa key ta dora hannunta aka ta fashe da kuka ya tare kofar "Me kuke fitowa nema ba kudi ba? Ki bani hadin kai ba abin da ba zan yi miki ba, dubi can ya nuna mata wani tebur da tulin kudi ke ajiye. "Kwaɗayina kawai zan maida ki kwashe su duka." Sai ya soma nufo ta tana ja da baya har ta kai bango, ganin zai cimmata yasa ta daka tsalle ta yi wani wurin ya biyo ta, haka suka yi ta zagaye Office din har Allah ya gajiyar da shi sai share zufa yake da habar babbar riga. Allah ya bata sa'a ta kai ƙofa wata sa'ar bai zare keyn ba ta murza kafin ta fice ya cimmata finciko doguwar rigar jikinta ya yi dan gyalen rigar ya fadi da ma takalmanta tuni ta watsar da su fasa kukan Hamida da cafko ta da ya yi sun yi daidai da turo kofar. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... DAGA MARUBUCIYAR *CANJIN BA ZATA* *WA GARI YA WAYA* *RANAR NAKA* *HATTARA* MUTUM DA KADDARARSA SON ZUCIYA MARYAM IBRAHIM LITEE No.2 Zura mata ido ta yi cikin tunani. Da ta gaji da kukan sasan iyayenta ta yi, ta wuce Innarta tana yan ayyukanta, ba ta tayar da kai ta dube ta ba gadon Innarta ta haye tana share hawayen da suka ki daina gudu kan fuskarta. Lokaci lokaci Innarta tana shigowa ta dauki abin da ya kawo ta ta fice ba ta ce mata ki ci kanki ba. Har ta ri ga ta saba da rashin kulawar da take fuskanta daga Innar ta ta idan tana yi wa Innawuro kukan Innarta bata son ta, sai ta kwabe ta da cewa "Kul! Ba son ki ne ba ta yi ba, kara ce da kawaici irin namu na Fulani. Sai Hamida ta ce to ke ba kina wa ya Aliyu magana ba? Murmushi Innawuro ke yi ta ce "Ai Gadanga ba na fari bane, sai da na yi hudu suna mutuwa, sannan shi shi kadai Allah ya bari. Innawuro kanwa take wurin kakar Hamida wadda ta haifi mahaifiyar ta, ita kuma ta riki mahaifiyar Hamida sakamakon rasuwar yayar ta ta, da ta tashi hannun Innawuro Iro kanen Malam Audu(mahaifin Hamida) ya ce yana so suka yi musu aure ta zauna gida daya da Innawuro. Haka kannenta suka dawo Islamiya suka kewaye ta suna tambayar ta me ya same ta? Baban ta da ya shigo shi rarrashin ta ya yi ta yi da alama Malam ya fada mishi, ita dai Innar tana sauraren su. Da daddare suna zaune a daki su biyu Innawuro da Hamida. Lallashin ta take ta tashi ta sanya ma cikin ta wani abu, don rabon ta da kai wani abu bakinta tun kafin labarin tafiya da ita kano ya riski kunnuwanta. A haka Aliyu ya shigo ya same su, ya tambayi Innawuro abin da ya faru da Hamida, ta maida mishi yadda aka yi, shiru ya yi kafin ya ce "Ya ma za a yi hakan ya yuwu? Bari in je wurin Malam din. Ko da ya samu mahaifinsa da korafin ya za a yi duk tarin yaran da ke gidan nan Gwoggon tasu ta ki zaben kowa ta raba Innawuro da Hamida, kuma kowa ya san ita kenan gaban ta, aka dauke mata ita ya za ta yi? Karshe ya kare da rokon mahaifin nasa da ya roki Gwoggo Indo ta canza Hamida da wata yarinya daban, a bar Innawuro da jikarta. Shiru ya yi yana sauraron dan nasa cikin yarda da zantukan da yake fadi, sai dai ba zai iya mishi abin da yake son ba. Gyaran murya ya yi kafin ya shiga yi wa dan nasa bayanin da ya sa dole ya koma wurin Innawuro jikinsa a mace yana taya ta rarrashin Hamidar yana yi kuma yana ba Innawuro hakuri, don su biyun duka tausayi suke ba shi. Matarsa Uwani ta gaji da jin shiru don dawowar sa kenan, kaya kawai ya tube ya taho gaida iyayen sa, ta biyo shi, Zama ta yi ta gaishe da Innawuro. Ganin yadda su su biyun suka tasa Hamida sai wani rarrashin ta suke ya kona ranta, ta dai daure ta hadiye malolon bakin cikin da ya taso mata, ta tambayi abin da ya same ta. Innawuro ce ta yi mata bayani, wani farin ciki ya ziyarci zuciyarta, Allah ya kai kaya masauki ta fadi a cikin ranta, amma sai ta fuske ta ci daci ta shiga nuna alhinin ta, gajiya ta yi da zaman ganin ba shi da niyyar tashi ta fita ta koma part dinta. Innar Hamida ta shigo dauke da kwanoni, gaban Innawuro ta duka ta ajiye, yi ta yi kamar ba ta ga me suke ba, za ta juya Innawuro ta kira ta, gargadi ta yi mata idan Hamida ta shigo wurin ta ta lallashe ta. Da kai ta amsa umarnin Innawuro sai ta bar musu dakin. Da safe ma lallashi Innawuro take ta yi Hamida ta tashi ta harhada kayanta don yau za su tafi. Sallamar da ake a kofar daki ta sanya su daga kai, Gwoggo Indo ce, ta karaso ciki tana amsa sannu da zuwan da Innawuro take mata, sun gaisa ta yi mata ya taro ya tashi? Kallon Hamida ta yi wadda ke gaishe ta, yadda ta ga kwayar idonta ta koma yasa gabanta bugawa, " Kar dai ace yarinyar nan ba ta son bi na? Ta raya a ranta, kauda tunanin ta yi ta hanyar yafuto ta. "Zo nan Hamidata." Ba musu ta ajiye rigar da take ninkewa ta isa gabanta za ta tsuguna ta janyo ta jikinta "Me ya samu idon ki? Shiru Hamida ta yi "Kar dai ba ki son bi na? Nan ma shirun ta kuma yi ta ci gaba "Ki gaya mini abin da yasa ba ki son bi na, idan na ji kina da dalilin da ya fi nawa zan bar ki, kin ji yar diyata? Amma ki yi tunani da kyau duk sauran yan'uwan ki da na dauka ko wacce irin daular da take ciki, irin mazan da suke samu a can su aura." Da dabara da hila ta samu Hamida ta fada mata ba ta son tafiya ne saboda tana sa ran Malam zai hakura ya bar ta ta ci gaba da karatu. Murmushin nasara ta yi "Yaro man kaza, idan kika bi ni zan sanya ki makaranta ki yi karatun ki ba tare da Malam ma ya sani ba, ko ba ki ga su sauran duk sun yi karatun a hannuna ba? Murmushi ya subuce a fuskar Hamida "Ko ke fa yar diyata, yi maza ki shirya kar rana ta yi mana." Da hanzari ta mike duk da dadin da take ji burinta zai cika za ta yi karatu, kasan ranta cike take da alhinin rabuwa da Innawuro da iyayenta da yan'uwanta. Ta juye ruwan wankanta ta je ta yi, ta fito tana rawar sanyi kasantuwar saman bandakin budadde ne. Ta shiga daki tana shiryawa Innawuro ta shigo ta dan ji sanyi ganin ta hakura tana shiryawa, Gwoggo Indo ta yi murmushi "Kin gan ni da mutumniyar tawa ta hakura ko? Ita ma murmushin ta yi "Ai hakan ya fi." Suka maida idon su kan Hamida da ke sanya kaya riga da zane ne na atamfarta ta sallah yar rigar ta zauna mata cas! A jiki, hijab ta sanya mai ruwan kasa ta janyo takalminta shi ma na sallar ne ta goge sai ta fita don yi ma iyayenta sallama. Ta dade tsugune gaban Innarta kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta fara mata nasiha da ta kama kanta banda shashanci, duk wani namiji kar ta saki jiki da shi kai kawai Hamida ke dagawa karshe ta ce ta shiga duk dakunan mutanen gidan ta yi musu sallama a ranta tana ta ma yar ta ta addu'a Allah ya tsare mata ita ya kare mata ita daga duk wani abin ki. Shigowar babanta yasa Innar ta kauda kai kamar ba ita ke mata magana ba, zama ya yi shi ma nasihar ya yi mata kannenta sun tafi islamiyar safe kasantuwar yau lahadi, kudi ya ciro ya mika mata. Ta fita ta zaga dakunan matan gidan tana musu sallama, ba ta ga Aliyu ba ya yi sammakon fita, da wurin Malam ta yi karshe shi ma nasiha ya yi mata daidai yadda Shekarun ta zai dauka karshe ya sanya mata albarka. An rako su ilahirin mutanen gidan. Hamida tana kankame da hannun Innawuro har gaban motar da aka zo daukar Gwoggo Indo. Da kyar ta saki hannun ta shiga motar tana mayar da hawayen da suka balle mata kamar sakarai ya kunna famfo, Innawuro ma juyawa ta yi tana share kwalla. Sun dauki hanya, hawayen Hamida sun tsaya sanadin lallashin da Gwoggon take mata. Sai kallon hanya take duk kuma inda suka tsaya sai ta samu abin da ta saya wa Hamida na ci, kafin barci ya sace ta ta bingire tana kwasar barcinta. Gwoggo Indo ta dubi inda take wani lallausan murmushi ya subuce a fatar bakinta. Sun shiga Kano ta dabo karfe uku na rana. Wanda ya yi daidai da farkawar Hamida sai kallon birnin take Sharada phase 3 suka shiga, suka rika wuce rukunin gine ginen kamfanoni, wani tafkeken Get direban ya danna horn get din ya bude ya cusa hancin motar zuwa ciki sai mamaki Hamida ke yi wannan wane irin gida ne? Don dai ba za a kira shi unguwa guda ba sai dai gari guda. Sun wuce dogayen gine gine masu kyau da tsari da tun tana kirga su har lissafin ya kwace mata ta yi tagumi kawai. Wasu rukunin gidaje masu iri daya direban ya tsaida motar a gaban daya daga ciki, suka fito cike da nuna gajiya a fuskokin su, Gwoggo Indo ta kai idonta inda wata dalleliyar mota ke tsaye kusa da inda suka tsaida tasu duhun gilasan motar ba zai ba ka damar gane wadanda ke ciki ba ta bude baki za ta yi magana murfin motar bangaren mai zaman banza ya bude, yarinya budurwa wadda shekarunta ba za su haura ashirin ba ta fito cikin shigar wani yadi mai santsi take dinkin riga da skirt da suka yi dam a jikinta ga ta da ma ma sha Allah komai ya ji sai wani siririn mayafi da ta ajiye a kafadarta, wurin su tayo fuskarta kunshe da fara'a har ta karaso inda suke Hamida da ke tsaye kamar ta kada suruka don mamakin shigar yar'uwar ta ta, ita dai wannan kwalliya ta yammatan zamani da ake yi da sunan wayewa basu taba burgeta ba, ko dan ba ta kai budurwar bane? Dafa kafadarta ta yi "Sis Hamida da ke Gwoggo ta taho? Na ji dadi sosai don na yi zaton Innawuro ba za ta bamu ke ba. Dan murmushi ta yi "Sannu da gida Aunty Aina, mun same ku lafiya? Ta kama hannun Hamida zuwa cikin gidan bayan ta gabatar da Hamida ga mutumin da ya fito a mazaunin direba yana gaishe da gwoggo Indo. Ta ce "Wannan sister ta ce sunanta Hamida." Aina diyar wan baban Hamida ce, ita tun tana karama kwarai gwoggo Indo ta dauko ta. Sun shiga ciki gidan flat house ne mai kyau sai filin tsakar gida mai dan girma sai wani daki falle daya kusa da filin an daura manyan tukwane a karshen gidan mata hudu ke tsaye a wurin, nan gwoggo Indo ta tsaya don da ma tun suna hanya Hamida ta ji gwoggon tana waya ta ce a hada komai a jira ta sai ta iso. Hamida ta gaishe su suka wuce ciki wani falo suka shiga ba wani mahaukacin girma ne da shi ba amma an kayata shi da ababen more rayuwa. Kofofi uku ne falon ta ja ta zuwa daya, dakin barci ne babu gado sai katuwar katifa da aka lailaye da shimfida mai kyau, kasa carpet ne mai matukar laushi. Da hannu ta nuna mata kofa ki shiga nan ki yi wanka zan kawo miki abinci." kai ta daga mata ta shiga don yin wankan ita kuma ta fice. Da ta gama wankan sai ta dauro alwala ta fito ta kabbara sallah tana cikin sallar Aina ta dawo dauke da madaidaicin faranti ta ajiye har sai da Hamidar ta idar "Zo ki ci abinci yar kanwata." "To Aunty Aina. Da ma can sanin da ta yi ma Ainar idan sun je Daura, ita din mai kirki ce da haba haba da mutane, bata fuska ta yi "Ya kike mayar da kayan da kika cire? Dan daburcewa Hamida ta yi "Ban ga mai ba ne." yar harara ta bata "Ba ga kayan kwalliyata can ba." Hamida ta dubi inda take nuna mata wani dan tebur ne kayan kwalliya ne lodi guda shirye bisa kansa. Tv da ke makale jikin bango ta tashi ta kunna ta bar shi a tashar Arewa 24. Ta tube rigar sai ta isa gaban kayan kwalliyar mai ta murza ta juyo wurin Aina "Aunty Aina ba ki da farar hoda? "Ita kike shafawa? Sai ta daga kai "Ba na shafa ta, amma gobe idan na shiga kasuwa zan sawo miki." godiya ta yi mata za ta mayar da rigar ta tsayar da ita "Ki sake wasu kayan kawai kin san Gwoggo ba ta son kazanta." don haka wucewa ta yi inda yar jakar kayanta take ta ciro doguwar rigar atamfa ta sanya ta nufi inda abincin yake jallof din shinkafa ce wadda ta ji kifi da ganye sai juice na kwali, Aina na gefen ta tana danna wayarta, da kammalawarta hamdala ta yi ta koma kusa da Aina ta zauna ta maida hankali kan kallon maimaicin shirin gari ya waye. Da ta idar da sallar Isha'i tana zaune a inda ta yi sallar ta lalace wurin kallon Aina da ke kwalliya za ta yi bako. Wata doguwar riga ta sanya da ta kama ta tsam ta fidda duk wata sura ta ta, ta tubke dogon gashinta wanda ke ta sheki tana ma kanta wankan turare suka hada ido da Hamida murmushi ta sakar mata "Yaya dai Hamida? Ita ma ta maida mata murmushin "Kin yi kyau Aunty Aina." ta ce "Ko? Ta ce Allah kina da kyau sosai Aunty Aina. Yar dariya ta yi mai kamar shessheka "Har na kai ki kyau Hamida? bude baki ta yi "Ni kuma ai kin fi ni kyau. Ni da su Ummi (yaran gidan su) ke tsokala ta kullum, wai ni ce ba ni da dogon gashi da dogon hanci, duk sun fi ni. Ta karashe maganar tana bata fuska, don nuna yadda abin ba ya mata dadi. Wani lallausan murmushi ta kuma saki "Kyale su kin ji karya suke, ko da suka fi ki dogon gashi da hanci ba su fi ki kyau ba suna da nasu kyan ke ma kina da naki, ke naki kyan ma mai ban sha'awa kike da shi."/murmushi Hamida ta yi kafin ta kai ga magana aka turo kofar da sallama wata yar yarinya ce da ba za ta wuce sa'ar Hamida ba sai dai Hamida ta fi ta tsayi ita kuma ta fi Hamida jiki. Hamida ta duba "Ki zo in ji Aunty. Sai ta juya ta tube hijab din da ta yi sallah sai ta bi bayanta. Gwoggo Indo suka samu zaune kan daya daga cikin kujerun falon ita da maigidanta Malam Buhari, kasa Hamida ta zauna tana gaishe shi ya amsa cikin fara'a yana tambayar ta mutanen gida, Aina ta fito "Zo mu je ki raka ni Hamida. Mikewa ta yi ta isa inda Ainar ke tsaye sai ta dan rage murya "Ki yi hakuri Aunty Aina na gaji barci nake ji." Murmushi ta yi "Ba damuwa yar kanwata. " Hamida ta yi musu sai da safe za ta koma ciki Gwoggo Indo ta ce ta kwashe kwanonin da suka yi amfani da su ta mika kitchen, sai da ta kai ta wuce daki. Ta kwanta har ta soma lumshe ido Aina ta shigo da ledoji niki niki. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA DAGA MARUBUCIYAR *CANJIN BA ZATA* *WA GARI YA WAYA* *RANAR NAKA* *HATTARA* And now SHIRIN ALLAH..... RAYUWA MARYAM IBRAHIM LITEE NO.5 Akwai yar tafiya daga nan zuwa Gate din, sai da Gwoggo Indo ta faɗi sunanta aka kira uwargidan wadda wurinta suka zo ta bada izinin a bar su su shigo. Hamida sai kashe kwarkwatar ido take ganin aljannar duniyar da take gani a zahiri ba a fina- finan masu jajayen kunnuwa da ta saba gani ba. Wani falo a ka yi musu masauki a ka ce su jira Haj, zaman aƙalla minti Ashirin suka yi kafin aka zo a ka tafi da su inda Hajiyar take kishingide take tana waya, sai da ta gama suka kwashi gaisuwa. Gwaoggo Indo ta fiddo abin da ta zo mata da shi ta ɗora saman wani ɗan teburin glass da ke gaban Hajiyar, ta bi abin da aka ajiye mata da kallo "Ina fata sun yi kyan na wancan karon? Gwoggo ta karkace kai "Wane mutum in ji mutuwa, ai ba haɗi wannan na musamman ne, takanas daga nan har Chad aka kawo shi, turaren can kar ki yi wasa da shi sau daya kika yi amfani da shi kin gama da namiji." Ɗan murmushin su na masu da shi ta yi "Ai na yarda da al'amarin ki Haj Indo, nawa ne kudin? Gwoggo Indo ta karkace kai ta soma lissafi "Shi wancan maƙale mata na matsi ne, kuɗinsa dubu d.... Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu "Ki faɗi kudinki gaba ɗaya kawai." Gwoggo ta kafto ta faɗi ta ce "Zan miki transfer za ki ji alert ƙila ma kafin ki isa gida." Gwoggo Indo ta ɗan ranƙwafa "Ina godiya sosai Haj, Allah ya ƙara girma." Sannan ta yi mata bayanin yadda za ta yi amfani da su. Sun tashi tafiya ta buɗe jaka ta ciro kudi ta dubi Hamida "Karɓi yammata ki sha sweet." Dan shiru Hamida ta yi tana so ta ce ta bar shi ko Gwoggon ta fahimci abin da take son yi ne ta dan zungure ta sai ta isa inda take ta karba tare da godiya. Sun fito sun dauko hanya Gwoggo Indo ta ji shigowar sako wayarta hannunta har rawa yake ta ciro wayar ta mika wa Hamida ta duba gaya mata adadin kudaden da suka antayo cikin Acc dinta ya sa Gwoggo zaro ido "Kin gani ko Hamida? Ta ninka kudin da na fada mata, ai masu kudin nan in dubu biyar kake sayar da magani ce musu hamsin in ba haka ba sai su ce ba shi da kyau. Ita dai Hamida ba ta ce komai ba sai kakkabi take a ranta yadda aka saida wa Laila da kuma zunzurutun kudin da aka sayar ma Hajiyar. Da suka zo ƙofar gidan Laila, Gwoggo Indo wucewa ta yi ta ce Yamma ta yi, bayan Hamida ta ba ta kudin da a ka bata. Da sauri Hamida ta shiga gidan don ta kusa taushe hannu wurin ɗaura girkin. Sannu ta yi wa masu gidan da ta samu zaune a falo, Laila ta nutse a kujera tana danna wayarta Mai gidan kuma na riƙe da laptop dinsa, Amir ya bar kayan wasansa ya zo ya ƙanƙame ta. Ta sure shi suka yi daki hijab ta cire ta kama mishi hannu su fito ya ce sai dai ta goya shi, goyon ta mishi suka fito za ta wuce kitchen ta ji muryar Mai gidan na cewa "Bar girkin nan, yau ki huta anjima ma fita mu sawo." za ta koma daki ya ce "Zauna nan ki daina takura kanki da zaman ɗaki." kasa ta zauna tana yi wa Amir wasa. Washegari da zai fita ya ce wa Laila ta fada wa Hamida idan ta ƙare girki ta kawo masa Office za su shiga meeting ba zai dawo da wuri ba. Don haka da wuri ta soma aikin ta gama ta shirya sai ta dauki kwandon da ta shirya kayan abincin Laila ta yi mata kwatancen Office din. Gabanta ya faɗi ganin Office din kusa da na Alh Ɗanlami. Ta daure ta yi knocking daga ciki ya bada izinin a shigo ta shiga da sallama rubuce rubuce yake bai dago ba sai nuna mata da ya yi ta zauna da hannu, ta ɗosana ta zauna ya dauki yan mintoci kafin ya ɗago ya fuskance ta "Zuba min abincin." abin da ya fara ce mata kenan. Ta mike zuwa inda suke cin abincin ta ajiye kwandon sai ta shiga zubawa aka murɗa ƙofar sai a ka shigo "Likita bokan turai ba dai ba ka je Office ba? Ahmad ya fadi yana mikewa tsaye "Haba dai ko kuma na dawo ba? Wanda ya shigo ya bada amsa Hamida ta baro inda take don ta gama zubawa idan su ya shiga na juna da wanda ya shigo sai ta ji wani iri don wanda ya cece ta ne daga hannun Alh Danlami yau ma Allah ya kuma haɗa su, shi kuma a ransa cewa ya yi "Ita din ce dai kenan? yau ma na kuma ganinta a Office din wani, wai ina iyayenta suke take famar gantali a ma'aikatan nan? Don ya taho ya ga wata kamar ita sai ya biyo bayanta a hankali har ya ga ta shiga Office din. "Na tafi Baban Amir." ta faɗi a hankali tana barin Office din kamar ana tunkuɗa ta. Zauna mana." Ahmad ya ce yana nuna masa wurin zama ba sai na zauna ba a kan hanya nake. Ya mika masa hannu suka yi musabaha ya juya Ahmad ya bi bayansa don yi mishi rakiya. Sai da suka isa inda ya adana motarsa ya shiga ya bar wurin yana tafe kansa na chargy me ya sa duk san da zai ga yarinyar nan sai tare da namiji? Wadanne irin iyaye gare ta da basu gudun ta lalace? Ya daki sitiyari! Mahaukacin horn din da yake dannawa ya sa masu kula da gate din ɗebowa a guje suka wangale gate din, a wuce a guje abin da ya basu mamaki suka bi motar da kallo, fitowa ya yi bai ko rufe motar da kyau ba ya yi ciki. Wani ƙasaitaccen falo ya fada ba kowa ciki ya fada kan sopa ya dafe kansa yarinyar kawai ke masa yawo a ido. A ranar farko da ya soma ganinta ya gan ta ne a Office ana ƙokarin keta mutuncinta. Rana ta biyu ya ga ta bi bayan wani matashi, rana ta uku yau kenan ya gan ta Office din Ahmad da alama kuma ta saba da shi. Hannu ya sa ya daki kujerar da yake tuna yadda yarinyar ta hana mishi sakat yarinya ƙarama da iyayenta suka sake ta cikin company nan da sunan talla, alhali cike take da bunsurai maza da ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da ƙarfin aljihu sun ɓata ta. Idan ya zo nan a tunanin sai ya ce to meye nawa a ciki? Meye haɗina da ita? Tunda ya gan ta a Restaurant yake zagaya wurin ko zai ƙara ganin ta, to ko mai kama da ita bai sake gani ba, tuna ko tafiya ta yi ya sa ya daina ganin ta ya sa ya mike zumbur! Ya suri key dinsa bari ya koma Restaurant din ko zai gan ta. Sai idonsa ya shiga cikin na Auntynsa tana tsaye ta rungume hannuwa "Kansa ya shafa "Aunty. Duk da bai fi shekaru biyu ta ba shi ba yana girmamata yana mata kallon uwar da ba shi da kamarta tunda ya mallaki hankalinsa. "Tunanin me kake? Ta jeho mishi tambaya Ba komai Aunty." "To ina kuma za ka? Ko abinci ba ka ci ba? "Mantuwa na yi yanzu zan dawo." Ta bi shi da kallo har ya fice. Da shiga motarsa Restaurant din ya nufa, har masu saida abincin suka tashi ba ta ba labarinta. To ko tambayar su zai yi? Idan kuma ya tambaya ya ce me ye sunanta? Cikin wani zafi da yake ji a ransa ya ja motar ya koma gida. Ahmad bai shigo gidan ba sai Yamma lis. Tana gama abincin ta shirya musu kamar yadda ta saba sai ta koma daki. Sai dai bayan Isha'i har ta kwanta ta fara lumshe ido Laila ta shigo ta ce Baban Amir ya ce ta fito. Ta fitan sai da ta kuma gaishe shi yana cewa "Ke ba ki gajiya da zaman daki ne? Zauna a yi hira da ke." ta zauna a ɗarare, Amir ya yi barci ballantana ta samu abokin hira, tana zaune tana wasa da yan yatsunta ya ce me ya sa take zaune kawai ba ta karatu? An sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi ta ce "Gwoggo ta ce in saurare ta, za ta sanya ni." ya ce "Shekarunki nawa? Ta ce "Sha hudu ya kaɗa kai "Me zai hana ki yi zamanki nan in sanya ki boko da Islamiya? Ta dan narke fuska duk da ta gaji da zaman gidan shiru ta ce "Ka tambayi Gwoggo." "Zan tambaye ta, amma gobe zan kai ki Islamiya ta cikin Estate din nan, zuwa Monday sai in kai ki boko." Hamida ta ce "Na gode." Laila da ke sauraren su ko tari ba ta yi ba. Kamar yadda ya ce washegarin ya kai ta ya yi mata Register suka ba shi unifoam da littattafai, suka dawo gida Hamida na ta murna. Da safe kafin ya fita ya ce mata yana fita zai bayar a sawo mata jaka da za ta rika sanya littattafan makarantar. Ta ce ta gode. Sai ƙarfe uku aka kawo mata jakar tana yin sallar La'asar ta sanya unifoam sun ɗan yi mata yawa amma da yake hijab din wadatacce ne tana sanya shi shi kenan, ta yi wa Laila sallama ta fita gidan Amir na kuka sai ya bi ta. Aji hudu suka sanya ta a bisa gwajin da suka yi mata, amma yan ajin sun kusa shiga aji biyar. Ana tashi sauri ta yi ta koma gida saboda girki sai dai tana tura ƙofar falon Gwoggo ta gani zaune, jin suna gaisawa da Laila ta gane zuwanta kenan. Ta kalli Hamida baki buɗe "Ashe har makaranta suka sanya ki? Ba ku da niyyar bani ɗiyata ko Laila, to yau ƙafata ƙafarta za mu koma gida." Laila ta ba ta hakuri ta ce ta bar mata Hamida cikin satin nan za a kawo mata mai aiki. Ta ce sam ki yi aikin gidanki, zuwa sati daya dai ba mutuwa za ki yi ba. Laila ta ce "Baban Amir ba ya nan Gwoggo, idan ya dawo ba zai ji dadi ba ya samu ta tafi ba sanin sa. Ta buntsura baki "Sai fa ki yi Laila ta karuwa da ta ji mai wa'azi, ta ce ka yi kanka a ke ji, ni sinima za ni." Maza Hamida shiga ki tattaro abin da kika san naki ne ki zo mu je gida." Hamidar ta mike ta shiga ta hado ya na ta ya na ta ta fito. Gwoggo Indo ta gyara zaman mayafinta "Mu je, ke kuma Laila abin da kuka yi niyyar ba ta idan mijinki ya dawo ku kawo mata." Da haka suka bar gidan Hamida na rike da kayanta. Suna isa da Aina suka fara karo da ke tsaye da wani tana zance. Ta baro shi ta zo ta rungume Hamida suka shiga ciki, Hamida ta ce "Ko ki zo ki duba ni Aunty Aina." ta ce "Yi hakuri yar ƙanwata, zuwan ne dai ban yi ba amma kina raina kamar kudin haya." Suka yi dariya "Kin yi kumatu kin ƙara haske gidan Laila da daɗi kenan? Wata dariyar suka ƙara. Washegari ta kama Alhamis da safe bayan sun gama ayyukan da za su yi har an wuce da abincin, sai suka yi wanka jallabiya ta sa mai yankakken hannu, ta yi rolling da gyalen rigar kamar yadda Aina ta koyar da ita. Takalmi flat ta sanya. Su ukun suka tafi kamar yadda suka saba, ƙawarta Rabi an mayar da ita garin su. Karfe daya da rabi lokacin wurin cin abincin ya ɗinke da jama'a, ana ta sallamar su wani matashi ya shigo, kallo daya Hamida ta yi masa ta kawar da kanta wanda ya cece ta ne, sai ta ga ilahirin mutanen wurin suna kawo masa gaisuwa, daidai da teburin da ya nufa don ya zauna wanda ke zaune wurin tashi ya yi da sauri yana kakkaɓe masa wurin. Ta juya kawai don ci gaba da aikinta, wadda ke ba mutanen kusa da shi abinci ta matso "Yallabai me za a kawo? "Kira min waccan yarinyar." ya fadi yana nuna mata Hamida, ta je ta isar da sakon. Ko da Hamida ta zo nesa kadan da shi ta tsaya, duk da daɗin da ya ji na sake ganinta, gefe guda yana jin wani irin ba dadi da ya gan ta tana sayar da abinci, yarinya kamar wannan da ya kamata yanzu a ce tana makaranta. "Me za a kawo maka? Ta tambaye shi ganin ya bar ta tsaye bai amsa ba don wani sabon tunani da ya shige shi game da ita. Tsayuwa ta cigaba da yi har dai ta gane wannan mutumin ba shi da niyyar kula ta, ga jama'a na jira sai ta juya ta yi tafiyarta. Ya dawo daga duniyar da ya lula ya ɗago iso sai ya ga wayam waige waige ya shiga yi sai dai har ya gaji da ware ido ba ta ba alamarta, tashi ya yi ya bar wurin cikin tunani. Ranar Asabar babu aiki don haka ba sa yin abinci sai ga baƙuncin Alh Mustafa sun samu ya zo wurin Hamida. Fada Gwoggo Indo ta yi ta surfawa me Hamida za ta ci da wannan mutumin? Ban da kuma Malam da ya yi mata waya ya sanar mata zai zo ba, da ko ganin Hamida ba ta bari ya yi ba, kora shi za ta yi. Ba ta ko ce ya shigo ciki ba albarkacin tafiyar nesan da ya shawo ta ce Hamida ta fita ta same shi bayan an shanya shi na kusan awa daya. Ta sanya hijab ta fita tana tura baki, shi kuma fara'a ya ɓalle da ita yana ganin Hamida wadda bai iya hana kansa yin ta matukar zai dora idonsa kan yarinyar. A darare ta gaishe shi yana ta jan ta da labari. Abdurrashid wanda ya fito daga gidansu zai fice daga Estate din, idonsa ya gano masa Hamida yarinyar da ya tambayi daya daga cikin masu sayar da abincin ta ce mishi sunanta Hamida, wani mamaki ya kama shi ganin ta tare da wani Wai su waye iyayen yarinyar nan? Ya ƙara tambayar kansa a karo na barkatai. Ajiyar zuciya ya fidda ya tsaida motar ya jinginajikinsa a bayan kujerar yana cigaba da kallonsu, ransa na daɗa ɓaci. Mintuna sun yi arba'in suka dauka mutumin ya shiga motarsa ita kuma ta shiga gida. Wani lokacin ya dauka yana shawarar ya yi tafiyarsa ko ma mai zai faru da rayuwarta ba matsalarsa ba ce, ko kuma mai cewa ya yi sallama yau dai ya ga su waye iyayenta? Jikinsa a mace ya yi wa motar key ya karasa kofar gidan Gwoggo indo sai da ya gyara parking sai ya fito Maryam litee [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH..... RAYUWA No.4 DAGA MARUBUCIYAR *CANJIN BA ZATA* *WA GARI YA WAYA* *RANAR NAKA* *HATTARA* And now SHIRIN ALLAH... Rayuwa MARYAM IBRAHIM LITEE Jin ya sake ta yasa ta bude ido tana kallon kofar. Wani matashin saurayi ne tsaye ya harɗe hannayensa yana duban su waige -wangen inda za ta ga gyalenta ta kama yi takalmanta ta fara gani ta wawuro su kafin ta ga gyalen ta hada da shi ta nufo kofa matashin ya ba ta hanya duk abin nan kuma kuka take tana fita ya mara mata baya yana duban yadda take tafiya tana kuka sai da ta yi nisa ta tsaya ta sanya takalmi da gyalen tsirarun ma'aikatan da ke bin ta da kallo ba ta ko san suna yi ba. Maimakon shago gida ta wuce ƙwanƙwasa get din ta yi ta yi duk da ba ta da yaƙinin akwai mutum, sai kuma ta ji takun tafiya an zo an buɗe , Malam Buhari ne wanda shigowar sa kenan daga wurin aiki, ganin ta a birkice yasa ya tambaye ta abin da ya same ta ta ce ba komai, ciki ta wuce ta haye saman katifarsu tana kuka tana kullawa da kwancewa yadda za ta koma Daura. Muryar Gwoggo Indo da ta ji ba ta sanya ta ɗaga kai ba har ta dafa kafaɗarta "Me zai sanya ki yi mini haka Hamida? Me ya faru kika taho ban sani ba? Shiru ba ta ba da amsa ba tsawa ta kwatsa mata "Tashi zaune mu yi magana! Ba shiri ta tashi don ko banza ba ta taɓa yi mata tsawar ba "Na ce "Me ya same ki? Ta fada cikin zare ido cikin inda inda ta bata labarin sama sama. Wayarta da ke hannunta ta shiga latsawa "Sannu tsohon banza mai kokarin ɓata ƴaƴan jama'a." abin da ta fara cewa kenan tana huci, da alama shi ma tsiyar ya tarbe ta da ita. "E ko da nake kwaɗayayya ban zama fasiƙa ba, ka gode wa Allah da ya ce ce ka ba ka ɓata mini yarinya ba, da Kano sai ta yi maka kaɗan." A takaice dai tsiya suka kwasa ta sauke wayar tana ci gaba da masifa, bala'inta ya shigo da Malam Buhari yana tambayar abin da ya faru ba ta saurara ba da ƙyar ya lallashe ta suka bar falon. Tun daga ranar Hamida ba ta kuma yarda ta je kai abinci kowanne Office ba. Kuma ta rage walwala, abin da ya damu Gwoggo Indo kenan ta shiga tambayar ta abin da yake damun ta ta ce ba komai. Ranar da ta rutsa ta sai ta faɗi mata damuwar ta sai ta samu kanta da cewa ita makaranta take so a sanya ta. Lallaɓa ta ta yi ta ce akwai shirin da take yi, lokaci na yi za ta kaita makaranta, makarantar ma ba ta kowa da kowa ba ta yayan masu fada aji za ta kaita tana sane ba mantawa ta yi ba. Dadi ya kama Hamida hakan ya sa ta maido da walwalarta ko don ta faranta ran Gwoggonta ta da kullun take tattalin farin cikin su ita da Aina, duk da kasancewarta mace me zafi su kam ba ta yi musu. Sati uku da afkuwar abun Hamida na zaune a shagon su na provision wani matashi ya shigo ya ce ta ba shi tissue gudar dubu daya ya miko mata ta ba shi ta juya dauko masa canji, juyowarta ya fice, bin bayansa ta yi da canjin cikin sauri ta hango shi yana tafiya kamar zai kifa ita ma ta daga kafa ta bi bayansa da kyar ta kamo shi sai da ya shiga wata kwana ta ba shi sai ta juyo daidai wata mota da ta wuce a yayin tafiyarta ta gan shi tsaye gabanta ya buga tuna a inda ya fara ganin ta da abin da ya faru a ranar. Ya za a yi ta manta da mutumin da ya tseratar da ita daga shaiɗani Alh Ɗanlami? Wani irin kallo yake jefa mata da ya sanya ƴan hanjin cikinta hautsinawa, don yadda ya yi mugun ɗaure fuska da sauri ta wuce shi kamar ana hankaɗata ta shige shago. A ranar kuma da daddare sai ga Laila da mijinta wai sun zo roƙon Gwoggo ta basu Hamida mai aikinta ta koma garinsu kafin ta samu wata. Da ƙyar Gwoggo Indo ta yarda shi ma saboda tana jin nauyin mijin Lailan don yana matukar yi mata alheri. Sun taho bisa hanya yana ta nuna mamakinsa kan Hamida, wai shi bai taɓa sani tana nan ba don bai ma san ta ba. Da suka isa Laila ta nuna ma Hamida dakin da za ta zauna sama sama ta gyara dakin ta kwanta. Da asuba har ta gama abin da take ta fito ba ta ji motsin kowa ba. Sai karfe goma LailDuk a fito, Hamida ta gaishe ta sai ta tambaye ta ta karya? duk da Hamida take karamar yarinya sai da ta ji mamakin tambayar ita bakuwa ita ake tambaya ta karya. Ta dai ce a'a kitchen ta wuce ta ce Hamida ta zo ta mike ta bi bayanta, tea ta haɗa sai ta dubi Hamida "Ki duba akwai komai ki dafa abin da kike so, daga yau ma kar ki kara jirana ki shigo ki nemi abin da za ki ci in kin tashi. Hamida ta ce to ta dauki tea dinta ta fice. Ita ma tea din ta haɗa sai ta fito ta sha. Ba ta zauna ba aikin tsaftace wuri ta kama da ta gama ta riƙa jiyo kukan yaron Laila kamar ta share sai ta kasa, ta isa har bedroom dinta, ta shiga da sallama kwance take kan gado riƙe da wayarta yaron na gefenta yana kuka. Daukar shi ta yi tana tambayar me ya same shi? Ta ce "Rigima ce kawai yake ji." Hamida ta juya dauke da shi, ta kai ƙofa ta ji muryarta "Ki shiga kitchen ki duba abinci me sauki ki ba shi." Da "To. Ta amsa. Indomie ta dafa mishi ya ci sosai daga nan ya kama wasan sa. Ganin ba alamar matar gidan za ta fito don ɗora girkin rana sai ta bi ta dakin ta tambaye ta ce mata ta yi ta je ta dora da ta kara tambayar me za ta dafa ta ce komai ya yi mata ta dafa, ta fito cike da mamaki, ganin akwai komai yasa ta yi niyyar yin fride rise wanda ta koya wurin Aina da take yawan yi musu. Ta yi ta gama ta shirya musu nasu a dinning, duk kuma abin nan Amir yana tare da ita sai da ta ba shi abinci ta ga yana lumshe ido sai ta kwantar da shi. Shigowar maigidan yasa ta tattara ta koma daki. Sai La'asar ta fito ta tambaye ta abin da, za ta dafa a matsayin abincin dare kai ta girgiza ta ce ita sau daya take shiga kitchen. Hamida dai ta ce bari ta yi ta fita cike da mamaki idan ta tuna a gidan su na Daura, to ya ma za a yi iyayensu maza su dawo a ce ba a yi girki ba, ita kam bata taɓa gani ba. Kitchen din ta shiga ta yi tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya wanda ta iya su tun a Daura. Da ta gaya wa Laila tana son kuɓewa ɗanya mai mata wanki ta aika gidan Gwoggo ya karbo tana kammalawa ta shige daki Da safe ma ita ta fito ta yi musu abin karyawa. Ta koma daki ta ji tana kiranta ta fito, sai da ta gaishe su Laila ta ce ta shiga ta dauko Amir ta yi masa wanka ta ba shi abinci. Sai da ta yi mishi yadda duk aka ce mata sai ta goya shi ta gyara wa Auntynta ta daki. Ta fito goye da shi ganin babansa wanda ke kokarin fita yasa yaro soma zizzillewa sauke shi ta yi ya isa wurinsa, sai ta wuce daki, sai da ya fita laila ta kira ta ta bata Amir din. Haka rayuwar Hamida ta ci gaba da gudana a gidan laila, ita ta zama tamkar matar gidan don ita ke gudanar da komai duk da ƙarancin shekarunta. Laila irin matan nan ne da suke ɗaukar ragamar gidansu su damƙa wa masu aiki, abin da suka sani su mike kawai mai aiki za ta tsaya kan komai. Hamida dai don ta horu da aikin tun tana Daura, sannan zamanta gidan Gwoggo Indo ta kara koyon girke girke na zamani don nan din ma bata zauna ba, hakan ya bata damar iya riƙe gidan Laila wadda kodayaushe za ka samu mike tana charting. Wata ranar Asabar masu gidan suna zaune a falo, Hamida na ɗaki tare da Amir wanda ya yi matuƙar sabawa da ita. Jan rigarta yake yana faɗin Daddy ta dauke shi don miƙa shi sun zo kofa sai ta ji kamar suna fada. Yadda take jin tashin muryoyinsu sai ta tsaya Laila ta fara ji tana cewa "Ni dai ban ce ka kawo mini kowa ba, abinci ka je Restaurant ku ci." Shi ma ya karɓe da "Nan na yi niyyar kawo su, kuma tilas a girka abincin tarar su, manyan abokaina ne za su taso su ziyarce ni ina da iyalin, sai in kai su Restaurant? Zan fita za a kawo cefane." Komawa Hamida ta yi ta zauna sai da Amir ya dame ta ta fito, Laila kadai ta samu mike kan sofa tana danna wayarta. Zama Hamida ta yi tana kallon Tv da ke ta aiki. Wanda aka aiko ya kawo cefane ya yi sallama ya miko, Hamida ta karba ta kai kitchen Laila kuma ta tashi ta yi ɗakinta. Wurin awa daya da kawo cefanen Hamida ta gane Laila ba za ta yi girkin ba, sai ta tashi ta shiga kitchen iya ƙokarinta da wayonta ta yi kuma cikin ikon Allah ta yi abinci kala biyu masu dadi ta shirya komai kan tebur ta koma daki ta dauki wani littafin hausa da ta samo dakin Laila ta ci gaba da karantawa. Karfe hudu ta ji hayaniyar bakin da basu wuce su biyu ba. Yamma likis ta ji shiru alamar sun tafi ta fita ta kwashe komai ta kai kitchen ta wanke. Sai zuwa dare ta ji an turo kofarta. Kai ta ɗaga sai Ahmad ta gani ta maida kanta kasa ta soma gaishe shi ya amsa da yi mata sannu da aiki, cikin ransa kuma yana mamakin yarinya ƙarama kamar wannan ta iya fitar da shi kunya. Ya ce "Ina ɗan naki? A ɗarare ta ce "Yana wurin Aunty Laila. " ledoji guda biyu da ya shigo da su ya ajiye mata, ba tare da ta ɗago ba ta yi godiya ya juya sai ya bar ɗakin. Ƴan mintoci ta ba shi sai ta dauki ledojin zuwa dakin Laila, tana knocking ta ce ta shigo, zaune take gaban mirror tana ma kanta wankan turare, don ta sha kyau har ta gaji, wata haɗaɗɗiyar rigar barci ce mai kwalliya a kirji ga fuska ta sha make-up. "Ya a ka yi? Ta tambayi Hamida sai da ta ajiye ledojin bakin gado ta ce "Baban Amir ne ya bani." ta ce "Kwashe ki je da su kin gode, ki dauki Amir ya kwana wurin ki." kai ta ɗaga tana kai dubanta inda Amir din ke barci, ta ƙarasa ta dauke shi, sai da ta sanya mishi pamfars sai koma dauko ledojin babu Laila, ta san ta wuce dakin maigidan, ta koma sai ta koma dakin maigidan. Washegari da La'asar zafin da ta ji tana ji yasa ta watsa ruwa. Da ta fito kwalliya ta yi cikin riga da zane na atamfa tana fesa turare Laila ta shigo cikin "Ki zo Gwoggo ta zo." Da murnarta ta ajiye kwalbar turaren ta bi bayanta. Kamar yadda take cike da zumuɗin ganin Gwoggon ita ma Gwoggon haka, kasa ta zube kusa da ƙafafunta, Gwoggo ta shafa sumar kanta "Na yi kewar ki ɗiyata, kuna nan lafiya? "Lafiya lau Gwoggo ina Aunty Aina? Ta ce "Tana gida." Ta dubi Laila "Wai har yau ba ku samu mai aikin ba? Ta ce "Ba a kawo ba Gwoggo, da ma za ki bar mana ita." Saurin girgiza kai da hannu ta yi "Sam! Ku nemo mai maku aiki zan ɗauki ɗiyata, nan da wasu kwanaki ko kun samo ko baku samo ba." Ta shiga bude ledar gabanta "Yanzu Gwoggo iyakar kudin kenan ba a ragi? Gwoggo Indo ta dube ta da mamaki "Ragi kuma Laila? Wadannan fa ba irin na gama gari ba ne, wannan na manyan mata ne. Daga ke sai Haj Mariya na daukar ma ma, don ke duk tsada na san ba ki ƙyashin saye ki gyara kanki." Ta jinjina kai "Zan bayar da rabi yanzu, cikon kuma sai nan da kwana biyu." Gwoggo ta yi fara'a "Yawwa ko ke fa? Allah ya kaimu. Ta maida dubanta ga Hamida "Tashi ki yi mini rakiya mu je mu dawo? Laila ta yi saurin cewa "Ina za ku Gwoggo? "Gidan mai gayya mai aiki, oga kwata kwata." "Waye mai gayya mai aiki Gwoggo? Hamida ta tambaya murmusawa ta yi "Mai wannan Estate din, gidansa za mu maza sanya lullubinki mu je ki kashe kwarkwatar ido." hijab ta sako sai suka bar gidan. [2/9, 09:43] Original: *SHIRIN ALLAH.....* *No.6* DAGA MaRuBuCiYaR CANJIN BA ZATA WA GARI YA WAYA RANAR NAKA HATTARA* AND NOW SHIRIN ALLAH... MARYAM IBRAHIM LITEE YA tsaya yana tunanin wanda zai samu ya kira masa ita, wurin shiru yake sai zirga -zirgan ababen hawa jefi-jefi. Bakin Gate din ya zura wa ido ya dauki kimanin minti biyar kafin aka buɗe kofar da ke jikin Gate din Malam Buhari ne ya fito sai ya yi saurin ƙarasa gabansa, gaisuwa ya fara mika wa Malam Buharin amma sai ya sunkuyar da kansa har da yar rusunawa yana gaida Abdurrashid wanda ya yi wa farin sanin ɗan Mai gidan su ne, tare da kakkaɓin abin da ya kawo shi ƙofar gidansa. "Hamida nake nema." Abdurrashid ya ce kamar ya shiga zuciyarsa, ɗan jim ya yi sai ya ce "Ina zuwa, ranka ya daɗe." ya juya zuwa ciki. Gwoggo Indo ya samu tana haɗa miyar taushe, ya dube ta "Zo mana." ta tashi sai ta bi bayansa suna shiga falo ya ce "Wani abin mamaki ya faru yanzu ina fita. " "Uhm me ya faru? Ya ce "Yaron Mai gida na samu a kofar gidan nan ya ce wai yana neman Hamida. Gwoggo ta gwalo ido Hamida ko dai Aina Malam? Ya ce "To ni dai Hamida ya ce mini. Ta tafa hannu cikin matukar murna "Koma Malam ka ce tana zuwa." bata saurari cewar sa ba ta yi dakin su Aina tare ta same su da Hamida, Aina na danna wayarta Hamida na haɗa kayanta za ta wanke "Tashi ki ji Aina, abin alheri ne ya tunkaro mu, ɗan mai Estate din nan ne ya zo har kofar gidan nan neman ki." Zumbur kuwa ta tashi zaune "Ni kuma ya ce Gwoggo anya? Ta ce "Ke dan Allah ba mu da lokaci, irin wadannan ba a ja musu aji, tashi ki gani ko rana aka sanya miki tuni za a warware ta, dan gidan Engineer Shehu Bello ne fa. Aina da tuni ta kai gaban wardrobe ta soga ciro kaya Gwoggo na taya ta har suka kai ga matsaya kan wasu riga da skirt na wani yadi mai taushi tana ma fuskarta kwalliya Gwoggo Indo na mata wankan turare. Hamida da ta gama haɗa kayan wankin ta ɗiba ta yi waje. Sai da suka tabbatar Aina ta yi sannan ta fita Gwoggo na bayanta wadda ke jin kamar su tafi tare gudun kar Aina ta kwafsa musu duk da sanin gogewar Aina me wuya a samu matsala. Dakin masu mata girki ta shige windon dakin su ta waje yake sai dai ba ta hango inda ya tsaya sosai, ta dage sai ɗage take tana miƙa wuya a fatan da take ta hango su da kyau.Aina kuwa tana fita sallama ta yi masa ya dago idanuwansa da ke ƙasa cike da mamaki yake duban cikakkiyar budurwar da ke gabansa ta gaishe shi ya amsa cikin ƙosawa ta ce "Mu shiga daga ciki. Wani sanyi ya ji don zaton ko an turo ta ne ta yi masa jagora ya bi bayanta inda take tafe tana kaɗa jiki don ƙara sace zuciyarsa sun shiga tsakar gidan ba kowa sai Hamida da ke wanki daga ita sai zane da ta yi daurin ƙirji masu girkin suna can karshen gidan suna hira kallo daya ya yi ma Hamida sai ya kauda kai yana jin wani abu na yi masa yawo game da ita, har falon Gwoggo Indo ta zaunar da shi ta wuce ta kawo mishi ruwa, ganin ta koma ta zauna ya sa ya ce "Ina Hamidar ne? Wata faɗuwar gaba ta ji sai kuma ta ji duk ta daburce "E tana nan." ta ba shi amsa "Yi mini magana da ita pls. " ta mike tana jin ƙafarta kamar ba za ta ɗauke ta ba dakin Gwoggo Indo ta faɗa, kaɗan ya rage su gwabza karo don a ƙofar dakin take tana leƙe, hangowar da ta yi sun bar inda suke tsaye tunaninta ya ba ta shigo da shi za ta yi, shi ne ta yi saurin baro dakin masu aikin ta shigo nata. Ya aka yi Aina? Ta fadi tana yarfa hannu "Wai Gwoggo wurin Hamida ya zo." ta fadi cike da sanyin jiki "Hamida kuma? Gwoggo ta yi tambayar mamaki kwance kan fuskarta. "Wallahi ita ya ce." "To ko lafiya? Don ba na ce son ta yake ba, amma dai bari in je in ji." ta fara ƙoƙarin janyo mayafi ta fita ta bar Aina wadda ta fada gadon Gwoggo kwajab kamar tsohuwar jaka rub da ciki ta yi ta rufe idanuwanta. Sallama Gwoggo Indo ta yi masa ya ɗago yana amsawa, tana zama ba ta jira gaisuwarsa ba ita ta soma gaishe shi "An ce kana neman Hamida lafiya? Ya ce "E wurinta na zo? Ta ce "To bari in turo ta. " ta fita ta bar shi cikin wani takaicin da mamaki da sauri ta samu Hamida "Zo diyata." Hamida ta ajiye rigar da take wankewa ta same ta. "Baƙon nan ke yake nema, ki kula da kyau in kin je gaban shi, ɗan me Estate din nan ne." ta ƙwalawa wata yar yarinya diyar daya daga cikin masu mata aiki ta ce ta je cikin kayan Hamida ta samo mata Abaya da gyalenta ta kwatanta mata inda kayan Hamidar suke. Ta amsa ta wuce cikin sauri, dakin masu aikin ta ja Hamida, sai da yaranyar ta kawo ta sanya "To yi maza ki je." Ta ba ta umarni Hamida na fita Gwoggo Indo ta shiga zance Allah ya wadaran rashin sani in na sani ba gyara ta zan yi ba, ko da su Malam suka turo mutumin nan nake cewa auren Hamida ba yanzu ba idan yaron nan ya ce yanzun yake so a aura mishi ita ai da gudu za a yi hakan, ƙanƙanta? Mu da aka yi mana muna da sha biyu me ya same mu? Ji take kamar tana mafarki wai tilon ɗan Shehu Bello ne cikin gidanta ya biyo cikin yayanta, ita kam da wace irin sa'a ta zo duniya? Farin ciki ke ɗawainiya da ita. Hamida dai a sanyaye ta isa falon ta yi sallama a hankali wadda da ƙyar ya jiyo ta kafin ta nemi daya daga cikin kujerun ta zauna. Kanta na kasa ta ce mishi ina wuni. Zaman minti goma suka yi shiru ya mike "Ni zan tafi." ta ce Sai anjima. Ya ce "Ki bani nombarki." kai ta girgiza "Ba ni da waya." "To ki amso mini ta mamanku."Ta miƙe ta je ta samu Gwoggo Indo, jiki na ɓari a ka rubuto ta kai mishi, ya sa kai ya bar falon sai dai kafin ya idasa ficewa ya ji muryar Gwoggo na cewa "Har ka fito? Ya ce "E" ta ce "Sai kja a yi hakuri da ita karamar yarinya ce." ya ce "Ba komai. Ranar Monday daga wurin aiki wurin saida abincin su Hamida ya wuce. Ya kuma samu nasarar keɓewa da ita a cikin motarsa, bai fito ba wayar Gwoggo ya kira ta turo ta. Glass din motar tintek ne don ba ya son jama'a su fahimci shi ne. Tambayar ta ya yi me ya sa ba ta zuwa makaranta? Ta ce Gwoggonta ta ce za ta sanya ta ya ce da ma ba mamanta ba ce? Ta daga mishi kai tare da cewa yayar babanta ce ya ce ina mamanta, ba ta ko numfasa ba ta ce Tana garin su Daura. Ya ja ajiyar zuciya Babanki fa? Ta ce shi ma yana Daura nan Gwoggonta ce ta dauko ta. Ya jinjina kai "Me ya sa ba ki son karatu sai saida abinci? Saurin duban sa ta yi a karo na farko idanuwansu suka shiga na juna, ta janye nata da sauri. "Ina so." "Kina son me? "Ina son karatun." "Yanzu idan na samu Gwoggonki na ce zan sanya ki Makaranta ki bar saida abincin nan za ki yarda? Cikin sauri ta ce "E. "To zan zo gida za mu yi magana da ita." Anan ya ga cikakkar fara'ar Hamida. Ya sallame ta ta fita ya ja motar sai ya bar wurin cikin tunani. A hankali ya ƙarasa a maimakon part dinsa na Auntynsa ya wuce, zaune take ta bi shi da kallo "Yau ma ina ka tsaya? Ta tambaye shi sai da ya zauna kusa da ita ya ce "Na ɗan biya wani wuri ne." ta kada kai ba dan ta gamsu ba. Hira suka shiga yi har aka kawo masa abinci ya ci anan sai ya wuce wurinsa, sai da ya gabatar da duk abin da zai yi kafin ya haye gadonsa don ya yi barci amma tunanin rayuwar Hamida ya hana mishi sakat. Zumbur! Ya mike ya shiga sanya kaya kananan kaya ya sanya da suka yi matukar hawansa, ko da fuskarsa ba walwala bai hana shi yin kyau ba. Ya fito sai da ya biya wurin Aunty Karima kallon mamaki ta yi masa "Sai ina kuma daga shigowa? "Wani abokina zan gani anan gadon ƙaya." ta gyada kai. Ya fice motarsa ya fada ya ja zuwa gidan Gwoggo Indo da wayarsa ya kuma amfani ya shaida mata ya zo. An yi sa'a dawowarsu kenan maimakon ta tura Hamida yarinyar mai girkinta ta aika ta ce ya shigo. Ita kuma ta fada dakin su Aina, dukkan su kwance suke bisa katifa Aina charting take, Hamida na kallon silif tana tunanin Innawuro da iyayenta da kannenta har ma da yan gidan su. "Hamida ga Yallabai nan ya zo." A tare suka ɗago suka dube ta Hamida ta ce "Waye Yallabai? Aina da ta ri ga ta gane inda zancen ya dosa ba ta tsinka ba "Yallabai mana da ya zo wurin ki shekaranjiya. Ganin Hamida ba ta da niyyar tashi ya sa ta zauna bakin katifar ta dora kanta a cinyarta "Na ga kamar ba ki murna da wannan babban kamu da kika yi? Jin Hamidar ba ta tanka ba ta ƙara da cewa "Kin ga duk girman wurin nan na mahaifinsa ne, duk kuma tarin al'ummar da kika gani cikin Estate din nan karkashin mahaifinsa suke, shi din kuma shi ne da daya tilo da mahaifinsa ya haifa. Ina gidan da muka je da ke kina gidan Laila? Hamida ta ce "Na tuna shi." "To shi ne gidan mahaifinsa, ga shi kyakkyawan saurayi ga arziki Hamida, ina gani ban taba rike wadda ta yi sa'a irin wadda kika yi ba." Hamida ta ce "Ya ce zai tambaye ki ya sanya ni makaranta." Gwoggo Indo ta yi cikakkar fara'a Yawwa to kin gani? Maza ki shirya ga Aina nan ta taya ki, ni zan je in tare shi, na sanya yar gidan magajiyata shigo da shi." Ta miƙe sai ta ja musu ƙofar. Ganin Hamida ba ta motsa ba ya sa Aina ta kamo hannunta "Hamida." ta kira sunanta, ɗago fararan idanuwanta ta yi ta dube ta, "Maganganun duk da Gwoggo ta faɗa miki gaskiya ne, kin yi dace da samun miji na nunawa sa'a, kin zo Kano da hannun dama. Ki ba shi fuska kar ki dinga zuwa ki yi masa dunkum kin ji Hamidata." yarinyar ta ɗaga mata kai. Aina ta mike ta ɗauko hoda ta ba ta ta murza ta fesa mata turare, don sanye take da riga doguwa ta atamfa hijab dinta iya gwiwa ta sanya, da Aina ta nemi hana ta narke mata ta yi kamar za ta yi kuka ta ce ta je haka, sai ta fita ta bi ta da kallo tana jin wani yanayi na ina ma ita ta dace wannan ɗanɗasheshen saurayin ya ce yana so, ko da kuɗi suke abin so wannan santalelen ma ko ba shi da tarin dukiya mace za ta so a ce shi ɗin mijinta ne. Ba da wanda take kwatanta shi sai da jarumin fina-finan India hitric roshan ko da ba su kama a fuska shi din ma dogo ne mai dogon hanci, tsawo da ƙirar jikinsu ce iri daya. Gwoggo Indo tana fitowa sallama ta yi masa yau ma kuma ita ta fara gaishe shi bayan ta nemi matsuguni. Sun ɗan yi jim ya ce "Me ya sa Hamida ba ta zuwa makaranta? Ta ɗan karyar da kai "Ina son sanya ta, sai dai sha'anin rayuwar ne sai a hankali, akwai wasu kudade da nake sa rai su nake so idan suka zo sai in sanya ta." ta ƙare jawabin cikin kwantar da murya. Kai ya girgiza "Haka ne, akwai makarantar da na yi zan kai ta can, amma ba na so ta ƙara zuwa wurin sai da abincin nan." "Shi kenan, ba za ta sake ba. Ganin ya mike ya sa ta ce "Za ka tafi ba ka ga Hamidar ba? "No ƙyale ta kawai, da ma maganar makarantar na zo yi miki. Ya sa kai sai ya bar falon daidai nan kuma Hamidar ta fito Gwoggo ta dube ta "Bi shi Hamida ki yi masa rakiya." ta gyaɗa kai sai ta bi shi a baya Yana ƙoƙarin buɗe mota ya ji a jikinsa akwai mutum a bayansa sai ya waiwaya Hamida ya gani tana kakkare fuskarta da hijab din jikinta. Kallonta ya yi na wasu sakanni sai ya ce "Ki koma gida." Ya faɗa motarsa sai ya bar wurin.[ [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.. Daga marubuciyar WA GARI YA WAYA RANAR NAKA CANJIN BA ZATA HATTARA MUTUM DA KADDARARSA SON ZUCIYA MARYAM IBRAHIM LITEE No.8 Ranar Monday a makaranta da malami a ajin su amma Walida ta damu Hamida tana taɓa ta idan ta waiwayo sai ta nuna mata wani abu a wayarta, Hamida ta gaji ta ce "Ki bari mana Walida."Karaf idanuwansu suka shiga cikin na juna ita da malamin ya taso har zuwa inda suke ya tambayi Hamida surutun me take masa yana cikin aji sai ta yi shiru. Tambayoyi ya cigaba da yi mata cikin harshen turanci duk da ta soma ji amma ba ta iya mayarwa sai ta mishi shiru, hakan kuma ya harzuƙa shi sai ya ɗauke ta da mari! Wata irin wuta ta ga ta gilma ta idonta sai ta fashe da kuka. Ya koma wurin zamansa tare da nadama da ya ji ta rufe shi sanin ƴayan masu garin ne a sch ɗin ba a dukan su. Kafin a tashi fuskar Hamida ta yi fushi wurin idon ya kumbura, a haka ta koma gida hankalin Gwoggo Indo ya tashi sai fada take wurin wata Nurse maƙociyarsu ta kai ta ta ba ta magani. Ta so Hamidar ta kwanta kar ta je Islamiya amma ta ƙi ta ce za ta je za su bayar da hadda. Gwoggon ta ce "Ke kika dage kina son wata boko ga shi nan za su sabauta miki ido . Ban da Yallabai ya kai ki ai da kin gama zuwa, mutum sai ka ce ya sha maganin ƙarfe daga mari fuska ta kumbure? Hamida ta ɗago kumburarren idon "Don Allah Gwoggo ki daina ce mishi Yallabai.Ta karyar da kai "Ya zama dole ai Hamida, duk wanda kika gani a nan ƙarƙashin su yake. Ta gama sanya unifoam dinta ta dauki jakar makarantar ta ce wa Gwoggo da Aina sai ta dawo. Ko tashi ba a yi ba idonta ya ishe ta da raɗaɗi ga shi tana jin kamar zazzaɓi zai rufe ta dole ta ce wa malamin ba ta da lafiya za ta gida. Ta lallaɓo ta ta kamo hanya horn ta ji a bayan ta ba ta waiwaya ba sai ta matsa jin an ƙara danna mata shi sai ta waiwaya Abdurrashid ta gani "Shigo mu je." muryarsa ta ratsa dodon kunnenta ta zagaya ta buɗe ta shiga sai da ta zauna ya ja motar ta ce mishi "Ina wuni? Bai amsa ba tambayar ta ya yi "Me ya samu fuskarki? Shiru ta yi daga haka shi ma bai kuma magana ba, suna isa budewa ta yi ta fita shi ma ya fito da jakarta da ta baro a motar. Sallama kawai ya yi ya shiga gidan ma'aikatan Gwoggo su biyu ke zaune ƙarƙashin bishiya suka gaishe shi cikin girmamawa, a kofar shiga falon Gwoggo ya kuma wata sallamar ita ta amsa don tana tsaye kan Hamida wadda da shigowar ta ta zube kan two sitter ko hijab din ba ta cire ba. "Shigo Yallabai. In ji Gwoggo ya shigo ya ce "Wai lafiya take kuwa? Ta ce "Ina fa lafiya. Ta kwashe labarin marin da malami ya yi mata ta ba shi, kai kawai yake jinjinawa bai ce komai ba daga bisani ya ce "Ku shirya Gwoggo mu je Hospital a duba ta." ta ce "To. Bayan ita har da Aina suka fito daidai lokacin Malam Buhari ya shigo suka gaisa da Abdurrashid Gwoggo ta yi masa bayanin inda za su ya yi Allah shi kyauta tare da musu fatan dawowa lafiya. Hamida Gwoggo ta tura ta shiga gaba suka zauna baya ita da Aina. Babu mai magana a motar har suka isa barrak din Sojoji da ke Janguza ganin Sojoji ya sa Hamida ƙara duƙunƙunewa cikin hijabinta don a duniya ba abin da take tsoro sama da Soja ko da ya yi parking din ma sojojin ne suka zo suka buɗe, yana fitowa kuma suka sara mishi. Hamida ta maƙale ta ƙi fitowa Gwoggo da ta san dawan garin ta matsa ta kamo ta maƙaleta ta yi ta rufe idanuwanta da taimakon Gwoggo ta riƙa takawa, Abdurrashid da ya ri ga ya yi nisa ya waiwayo don ganin suna biye da shi ai kuwa nesa ya hango su Gwoggo na rike da ita ya tsaya suka ƙaraso Yaya Gwoggo ko jikin ne? "Ai tsoron sojoji take mutumniyar taka. Gwoggo ta fadi fara'a kwance saman fuskarta, kai ya girgiza bai yi magana ba ya wuce suka cigaba da bin sa duk kuma inda ya wuce sojojin da ke shawagi sai sun sara mishi. Da suka shiga wata Dr Maria ya tambaya a ka ce mishi ta fita ya kira ta a waya ta ce ba ta yi nisa ba ya ɗan jira ta. Wani Office ya buɗe ya ce su shigo ya yi ma su Gwoggo tayin wurin zama kafin ya fita ya ce yana zuwa. "Anya Gwoggo ba soja ba ne? Aina ta raɗa wa Gwoggo karaf kuma sai a kunnen Hamida ai kam ta buɗe ido rayau tana ware su cikin Office din, ganin yadda ta razana ya sa Gwoggo Indo ta ce "Kai da ƙyar dai don ni dai tunda nake wurin nan ban taba ji ba. Abdurrashid ya dawo tare da likitar ita ma soja ce cikin faran -faran ta duba Hamida sai da wani Soja ya je ya sawo magungunan da ta rubuta suka miƙe don tafiya nan ma Hamida na maƙale jikin Gwoggo da ta ga Abdurrashid ya tsaya kawai yana duban su ta yi yar dariya "Ai wannan ban taɓa ganin me shegen tsoron sojoji da allura irinta ba, shi ya sa na gode wa Allah da ba allura da kuka za ta zauna share share tana yi mana.Hamida sai taɓa Gwoggo take jin tonon sililin da take mata. Da ya sauke su wucewa ya yi. A falo suka yada zango Gwoggo sai yamutsa magungunan da ta ce Aina ta kawo ruwa take "Wai sai tsurar magani kawai, ba dan abin maƙulashe da za ka saya wa budurwarka ba ta da lafiya? Ni wallahi ina ce yau sayayyar da zai mana kafin mu shigo gidan nan sai ya cika boot." Aina ta fito da ruwan ta ba ta ta daga kan Hamida "Tashi ki sha to. Shan ta yi ta koma ta kwanta. Cikin hukuncin Allah zuwa safiya ta yi garau fuskar ma ta rage kumburi idon ya washe, Gwoggo Indo ta ce ta bar makarantar sai ta warware zuwan Malam Adamu sai ta ba Gwoggo hakuri ita kuma gudun kar Abdurrashid ya ji ita ta hana sai ta kyale ta. Walida sai ba ta hakuri take da aka fita break kan dukan da ta janyo mata. Hamida dai ta girgiza kai wani yaro ya same su ya ce ana neman Hamida a Office din principal, suka fita tare da Walida sai da suka kusa isa ta tsaya ta ce za ta jira ta anan. Sai ta ƙarasa mutum biyar ta samu cikin Office din principal da mataimakiyarsa sai Maths teacher ɗinsu sai Abdurrashid tsaye jikin bango hannayensa harde a kirji fuskarsa ba alamar ya taɓa dariya ganin wandon da ke jikinsa na Sojoji ya sa hantar cikin Hamida kaɗawa. Ta gaishe su sai ta tsuguna principal ya nemi ta faɗi abin da ya faru har teacher ɗinsu ya mare ta. Ta fadi amma ba ta fadi waya Walida ke nuna mata ba, sai shi principal din ne ya ce "Amma mu a binciken mu waya kika zo da ita Jikinta ya ƙara daukar rawa tana girgiza kai ta ce ita ba ta zo da waya ba. Principal ya maida duban sa ga Abdurrashid hakuri ya yi ta ba shi suna taya shi ya dubi Hamida ya ce ta je waje ta jira shi a mota. Bayan fitar tata kuma bala'i ya yi sosai kan aka kuskura aka maimaita dukan ta ba zai tafi haka ba zai ɗauki mataki. Karatu ya turo ta ba a nemi nakasa mata ido ba. Su dai hakuri suke ta bayar wa ya fita Office din, a jikin motar ya hango ta sai ya isa sai da ya shiga ya ce ta shigo ita ma fadan ya yi mata kan ta fara wasa da karatunta, ina wayar da a ka ce an gan ta da ita? Ta rantse masa ita ba ta da waya. Ya sallame ta bayan ya ba ta ledoji masu ɗauke da irin sayayyar da ya yi mata kwanaki. Lokacin da ta koma har an koma class da aka tashi Walida ta so bin ta ita dai ba ta so ba don boren da take so ta yi wa Gwoggo idan ta koma gida Allah kuma ya taimake ta Walidar ta ce ta fasa ta tuna za ta wani biki. Da ta koma gida kamar kullum ba ta samu kowa ba sai Malam Buhari da ya shigo tana shigowa. Ta ci abinci ta yi sallah sai ta koma tsakar gida a karkashin bishiya tana tsifar kanta. Ta yi nisa Gwoggo da Aina suka shigo ciki ciki ta yi musu sannu har sun shiga ciki Aina ta fito "Me ya faru na ga ranki a ɓace? Ta tambaye ta ƙara ɓata rai sai kuma ta fashe da kuka ganin haka Aina ta shiga yankawa Gwoggo Indo kira ta fito a ruɗe ɗankwalinta a hannu "Me ya faru? Ta tambaya sai Hamida ta kuma rushewa da kuka suka kamata suna tambayar abin da ya same ta "Ni wallahi Gwoggo kar ya ƙara zuwa wurina soja ne, ni ban son Sojoji gwoggo." gwoggo ta ce ta yi shiru wa ya gaya mata soja ne? ta ce yau da wandon Sojoji ya zf o makarantarmu."Sakinta kawai ta yi ta shiga ciki ta saɓo mayafinta "Ki kwantar da hankalinki yanzu za ni gidan Mariya mijinta shi ke kula da shukoki a gidan Shehu Bello, ita ma shekarun baya an ce ta taɓa musu aiki ta san komai na gidan. Ta sa kai ta bar gidan. Tsakanin su ba wani nisa sosai ta yi sa'a ta same ta ba ta daɗe da shigowa gidan ba ta je unguwa, sai da aka yi mata maraba suka gaisa Gwoggo ta ce "Wurin ki na zo Mariya wata tambaya nake son yi miki." ta gyara zama "Allah ya sa na sani." "Wani ƙarin haske nake nema game da gidan Shehu Bello wai tilon ɗansa soja ne? Ta yi dan murmushi "Ƙwarai likita ne amma na Sojoji. Ta gyara zama don uwar zance ce "Ai lokacin da mahaifiyarsa na raye shi Abdul ɗin ita na yi wa aiki, har garinsu Adamawa take zuwa da ni, ita ce uwar ɗakina mace mai matuƙar kirki da mutunci, rana ɗaya aka aura mishi su da Uwargidansa ta yanzu ita Allah ya ba ta Abdurrashid ita kuma Haj Mariya an ce ta dai taɓa yi ba rai. Bayan rasuwarta aka ba shi ƙanwarta Aunty Karima da yake ƙannenta duk mata ne su biyar mahaifiyarsu ta haifa ko shi Abdul da rasuwar mahaifiyarsa kakar ta dage sai ya koma wurinta uban kuma ya kasa ba ta sai ya ce a ba shi Karima lokacin tana budurwa in yaso sai ta riƙe Abdul ɗin don ya gane ba ta gamsu da riƙon da kishiyar uwar za ta yi mishi ba, shekarun Abdul din sha biyar lokacin mafari kenan na bar aiki gidan. Gwoggo Indo ta yi ajiyar zuciya "Allah sarki Allah ya jiƙanta, ni ma ɗazu nake ji wai soja ne, tunda nake wurin nan ban taɓa sani ba, shi ne na ce ai ko na tambayi Mariya ita ta san komai na gidan. Goggo Indo ta miƙe. Ta ce ta tsaya don Allah a zubo mata dambu da ɗanta ya shigo yana ci, ta ce ta gode ta wuce gida. Tana shiga falonta a sanyaye ta ajiye mayafi ganin duk sun zubo mata ido Aina da Hamida, ta isa kusa da Hamida ta zauna "Ki kwantar da hankalinki kin ji 'yar ɗiyata ba wani abu." "Sojan ne ko Gwoggo? Ta tambaya tana duban fuskarta don ta ga yanayin da za ta nuna. "Likita ne na Sojoji, don haka kin ga shi ba ruwan shi da Sojoji, likita ne. Nan dai ta yi ta mata dabara har ta haƙura [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH No.7 Daga MaRuBuCiYaR WA GARI YA WAYA CANJIN BA ZATA RANAR NAKA HATTARA And now SHIRIN ALLAH... MARYAM LITEE Da daddare Gwoggo Indo na zaune tana cin abinci, Hamida na gefenta idonta na kan TV. Aina da ke ɗaki ta fito "Ni fa Gwoggo halin mutumin nan ya fara isa ta, wai idan yana gida ba hali in kira shi? Ni dai ban da kin matsa da tuni na kore shi." ta zauna tana tura baki. Gwoggo ta kwantar da murya "Kar ki kore shi Aina ki yi hakuri, ina gaya miki yadda matar tasa ta nema ta samu muma neman za mu yi, wuyarta dai ki shiga gidan, duk masu zuwa shi kaɗai ya zo da maganar aure, Alh Uban da kika dage sai shi ina yake ya sulale, ya za a yi shi a kore shi? Ga Malam ya taso ni gaba da ki fitar da miji dan a satin nan aka kawo kudin gaisuwar Amina." Ido Aina ta buɗe "Amina dai za a yi wa aure? (Aminar shekara daya ta bai wa Hamida, Babanta shi ke bi wa baban Laila) "Kwarai don haka ya ce ba za a aurar da Amina kina zaune ba, har Hamida ya ce ta samu miji har ita zai haɗa." Tagumi Aina ta rafka kafin wayarta ta shiga ƙara, ta duba Gwoggo Indo ta ce "Waye? "Me yan canji ne." ta bata amsa "To yi maza ki amsa ki ji da wacce ya zo." ta yi picking yar magana kaɗan suka yi ta sauke wayar "Yana waje wai Gwoggo." "Yawwa to ki fita ki same shi ki ma shaida mishi ya fito ni ma mijin ta cen nan ya ishe ni, ki yi duk yadda za ki ƙara sace zuciyarsa don ya ƙara mutuwa kan son ki." ba ta yi magana ba Hamida ta duba ta ce ta dauko mata mayafi a daki da ta kawo a kafaɗa ta ajiye shi sai kallon ta Hamida ke yi shigarta ce ta koyaushe jikinta doguwar riga ce da dinkin ya matse ta dam sai ta fice. Kallo Hamida ta cigaba da yi har goma ta wuce wani film MBC bolly wood suka sanya mai suna krish 3 ya matuƙar tafiya da ita, har lokacin Aina ba ta shigo ba. Gwoggo Indo ba ta cika doguwar hira ba amma yau ta kasa kwanciya tana jiran Aina ta ji yadda suka yi da mai yan canji, sai gyangyadi take amma ta kasa haƙura ta je ta kwanta. Malam Buhari tunda ya yi mata magana sau ɗaya ta ce Aina take jira ya koma daki ya yi kwanciyarsa. Goma da rabi Aina ta shigo motsinta ya sa Gwoggo Indo yin zumbur tana rarumo ɗankwalinta da ya zame daga kanta "Yaya Aina, an dace zai turo? Ta jera mata tanbayoyin, ba ta yi magana ba sai da ta zauna kusa da ita "Da na yi masa maganar aure cewa ya yi a halin yanzu dai ba shi da buƙatar ƙarin aure, sai dai ko nan gaba in s..... "Shi ne kuma ya gaya miki wannan maganar banzar kika tsaya sauraronsa tsawon wannan daren? ba ki yi masa wankin babban bargo kika kamo kanki ba? Aikin banza aikin wofi yau ga tsi.. Maganarta ta ta katse ya yin da suka yi ido biyu da abin da Ainar ke miko mata, kudi ne ba ma kuma Naira ba dalar America ce. Ba ta ƙi ba miƙa nata hannun ta yi ta karɓa tana jujjuya su "Duk shi ya ba ki wadannan? Aina ta daga kai "Amma kuma don tsiya ya fito a yi aure sai ya ce ba haka ba? "Wai kuma gobe zai zo in raka shi wani taro, da ni kadai zai iya shiga wurin." Wani tsaki Gwoggo ta ja "Kyale dan iska ya je da matan nasa ba inda za ki. Su kuma wadannan kudi mun yagi rabon mu, ko a waya ya kira ki ki ce idan ba maganar aure zai yi ba ya manta ma ya taɓa sanin ki. Aure nake so ki yi Aina, Daura magana ta fara yawa har yau ba ki yi aure ba, duk yaran gidanmu ba wadda ta taɓa kai kamar shekarunki." daidai nan suka yi ido biyu da Hamida Gwoggo ta riƙe baki "Ba ki kwanta ba Hamida? Ta ɗaga mata kai sai ta mike "Wani film nake kallo Gwoggo ya ma kare yanzu." "To kashe kayan kallon." ta kashe ta wuce ciki ta bar Gwoggo da Aina suna neman mafita, don ita ma Ainar hankalinta ya koma kan ta yi aure har an fara maganar auren ƙannen bayanta, yaran gidansu ba su wuce sha bakwai an kauda su, ko Laila da Gwoggo Indo ta riƙe Sakandire kawai ta ƙare aka yi mata aure ita ce dai da alhazan birni suka yi mata caa! Tun zamowarta budurwa shi kenan ita da Gwoggo sai suka yi fatali da zancen aure, maimakon auren magana ta yi wa Ahmad mijin Laila ya samo wa Aina makaranta. NCE aka samu tun kuma da ta fara karatun idanuwanta suka ƙara budewa, duk kuma da matsin lambar da suke fuskanta daga Malam Aina ta fito da miji, Gwoggo Indo na cewa karatu take don Allah ya yi haƙuri ta ƙarasa daga ta fara. Duk da ba son karatun bokon yake ba ta sani hakanan ya hakura. Maza suna kashe mata kudi suna shan soyayyarsu ta shan minti, Gwoggo na sane amma tsabar son abin duniya ya sa ba ta tsawata mata. Da ta kammala karatun kuma duk wanda ta nemi ya fito ba ya fitowa sun fi son su yi ta soyayyar su a haka, Alh Maaruf shi ya zo da batun aure sai aka yi rashin sa'a mugun shakkar matarsa yake yi shi kuma. Ranar dai haka suka kwana Aina da Gwoggo ba daɗi. Washegari ta kama Alhamis ba Islamiya Aina ta ce wa Hamida da La'asar za su fita a gyara musu kai ta ce "To." Don haka ƙarfe hudu da rabi suka fito cikin shiri Aina riga da skirt ta sanya na Less sun kamata kamar ma da ƙyar take numfashi ta jefa gyalenta a kafaɗa. Hamida ma riga da skirt din ne sun yi cif a jikinta sai bakin gyale da bakin takalmi bayan ta murza farar hoda Aina ta sanya ta ta shafa jambaki ai kuwa ba karamin kyau ta yi ba ta daura mata dankwali tulin gashin ta ma da ya fito ta gefe da gefe bayan ta kama mata shi da ribbom ba ƙaramin kyau ya ƙara mata ba shi maSuka fito suna ƙamshi mai sanyi. Gwoggo Indo ta fita unguwa. Sun yi nisa da tafiya har sun kusa Gate don fita inda za a su samu adaidaita sahu wata mota ta tsaya ba su shaida wanda ke ciki ba har saida suka dubi mazaunin direba Abdurrashid ne baƙar shirt ce jikinsa da ta yi matukar amsarsa "Ina za ku? Ya fadi cikin rashin sakin fuska Aina ta fara gaishe shi sai ta amsa mishi tambayarsa "Za mu je wurin gyaran gashi ne." "Ku shiga mu je ya furta ba tare da ya dube su ba Aina ta bude kofar baya ta shiga Hamida ta mara mata baya sai dai kallon da Ainar ta jefa mata ya katse hanzarinta ya sa ta tsayawa, jin su shiru ya sa shi waiwayowa don ganin halin da suke ciki "Shiga mana." Aina ta ce ma Hamida sai dai ba ta motsa ba ta sake cewa "Me kike yi haka ne Hamida? Ya ce "No bar ta ta zauna nan din." har ajiyar zuciya Hamida ta fidda ta shiga ta zauna gefen Aina. Ya zuge gilasan motar wadanda suke masu duhu ne sai ya tashi motar. Aina na ta jira ya tambaye su inda za su gyaran kan sai ta ji shiru, wani ƙayataccen wuri ya kai su can kusa da Zoo road ya ce su fito. Ya mika wa Hamida Atm ya fada mata pin din ya ce su biya idan an gama masu. Suka shiga ciki ya kwantar da kujerar yana sauraron kiɗan da ya sa a motar. Aina ganin banza ce ta faɗi ya sa ta ce bari su bi ta da yakushi, bayan gyaran gashin ta ce a wanke musu ƙafa, ta kuma jidi maya mayai na kai da na jiki duk a ka cire a kudaden Abdurrashid. An gama musu yamma ta yi sosai Aina ta ce su tafi su samu shatar Adaidaita sahu sai dai suna fitowa suka yi tozali da motar Abdurrashid wurinta suka nufa Aina ta ƙwanƙwasa glass ɗin ya sauke idonsa a kansu bai yi magana ba Aina ta bude suka shiga ya ja, a hanya ya tsaya ya yi sallar magarib don haka duhu ya shigo san da suka shiga gida. Gwoggo Indo sai murna baki ya ƙi rufuwa jin Aina ta ce tare suka fita da Abdurrashid, ita ta bude ledar da Aina ta zubo mayukan tana cewa "Iya wannan ledar kawai ba ta yi kadan ba? Aina ta yi murmushi "Ita din ma ba shi ya bamu ba."Ta kwashe yadda aka yi ta labarta mataTa ɗan yi shiru kafin ta ce "Zuwa yanzu na yi tunanin ya soma jiƙa mu da Naira Aina, amma ko kwabo, gidansu kuma gida ne na kyauta indai ka shiga ba ka fitowa hannu biyu. Aina dai ta dauki ledar ta wuce ciki, da ma Hamida tun shigowar su ba ta zauna ba cikin ta wuce don yin sallar magarib, ta bar Gwoggo Indo da tunanin Allah ya sa Abdurrashid ba hannun jarirai yake da shi ba. Karshe dai ta watsar ta ce koma dai meye gidan arziki ne, kuma abin alfahari ne a ce yarta ta yi aure a gidan. Ranar Monday Abdurrashid ya turo a ka kai Hamida makaranta a ka yi mata komai har unifoam aka ba ta da littattafai. Dan aiken ya shaida wa Gwoggo Indo duk safiya zai riƙa zuwa don kai ta makaranta. Ranar kowa ya ga cikakkar fara'ar Hamida. Tun daga ranar ta fara zuwa makaranta mai suna *AHLAN Internatonal School* babbar makaranta ce ta yayan masu hannu da shuni da masu riƙe da madafun iko, idan ta dawo ta wuce Islamiya. Abdurrashid ya kan zo daga lokaci zuwa lokaci. Tana matukar ganin girmansa saboda makaranta da ya sanya ta, ba ta damu da mitar da Gwoggo ke faman yi na ba shi da alheri kullum sai dai ya zo ya kakkaɓe rigarsa ya tafi. Tana mayar da hankali sosai musamman da ya zam ba a hausa a makarantar sai dai turanci, ita kuma ba ta iya ba, ranar Alhamis da juma'a tana tsayawa lesson da Abdurrashid ya sanya ake mata har Asabar da lahadi take zuwa tana yi mata da yake tana so ba ta dau lokaci ba ta fara ganewa, ba ta shiga sabgar mutane tana matukar kama kanta duk da su mutanen suna son yin mu'amala da ita, saboda burge mutane da take yi. Yarinya guda ta fi shige mata kuma dole sai da Hamida ta saba da ita duk inda ta sanya kafa nan yarinyar mai suna Walida za ta mayar da ta ta. Walida irin yaran nan ne masu ɗan banzan rawar kai da son a ce su ɗin wasu ne, irin labaran da take ba Hamida na arziƙin iyayenta Hamida jinta kawai take don ita ba ta ga abin da ya dame ta da arzikin su ko rashin sa ba, har sai wata rana da aka kwana biyu ba ta zo ba sai Hamida duk ta ji ba ta ji dadi ba an bayar da sanarwar ba ta da lafiya, lambar wayar Walidar da ta ba Hamida ta ba Malam Adamu direban da ke kai ta makaranta ta ce don Allah za su biya ta gaishe da ƙawarta ba ta da lafiya Mamanta ce ta dauki wayar ita kuma ta yi ta musu kwatance har suka gano gidan, wani tsukakke ne a ɗan dinshe, mai dakuna uku ta gaishe ta sannan suka tafi gida. Bayan ta dawo makaranta ta ce ma Hamida gidan da suka zo gidan kakanninta ne nan kakarta ke ruƙonta wadda Hamida ta gani, ita mamanta na Hotoro, Sai da tafiya ta yi nisa tsakaninsu ta gane nan ɗin dai shi ne gidansu, matar da ta gani ita ce mahaifiyarta, yayarta ce ke aure Hotoro mijin yayar shi ya sanya su makaranta mai tsada ita da kannenta. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... DAGA MaRuBuCiYaR WA GARI YA WAYA CANJIN BA ZATA RANAR NAKA HATTARA SON ZUCIYA MUTUM DA KADDARARSA MARYAM IBRAHIM LITEE No.9 Hamida ta cigaba da karatunta suna tare da Walida wadda yanzu ta zama 'yar gida a gidan Gwoggo Indo. Kafin sati ya ƙare za ta biyo Hamida sau biyu wani satin ma sau uku. Da suka samu hutun second term Gwoggo ta je da ita Daura suka yi kwana biyu suka dawo Aina dai har yanzu tana nan, Alh Ma'aruf ya ɗauke ƙafarsa ba kuma wayarsa in ta kira shi ma ba zai dauka ba, ita da Gwoggo suna cikin tashin hankali. Wani yammaci Hamida ta shigo daga makarantar Islamiya Gwoggo ta samu zaune a falo kusa da ita ta zauna bayan ta amsa sallamarta "Yawwa Gwoggo, an ce a kawo kuɗin sauka dubu 20 sai kaji biyu sai kudin unifoam dubu b... Da sauri Gwoggo ta katse ta "Duk ni kaɗai wannan dogon lissafin? To tun wuri gara ma ki sani wancan mai son naki da ba ya ɓanɓaruwa shi zai yi komai, ki ma gaya masa, in kuma ba haka ba kina kallo yan ajin naku za su yi saukar su bar ki." Kuka Hamida ta sanya, Gwoggo ta ce "Allah na gama magana kowane irin kuka za ki yi." A haka Aina ta shigo ta same su a komai za ka same ta bayan Hamida amma yau ta ce Gwoggo na da gaskiya Hamida ta tambaye shi kawai. Kuka Hamida ta daɗa rushewa da shi. Ranar ko abincin dare ba ta ci ba Aina da ta ga ta ƙi barci sai kuka take ta janyo ta tana rarrashi "Shi ya dace ya yi miki Hamida, Gwoggo gaskiya take fada miki. Gara tun yanzu ya saba da hidimarki ba komai ya rungume hannu, share hawayenki kin ji yar ƙanwata? Ta gyaɗa kai sai ta share hawayen ta ce ta je ta wanko fuskarta sai da ta wanke ta dawo ta kwanta lamo tana tuna tsawon watanni biyu kenan tana fama da karatu don son da take ta yi na ɗaya a jarabawar saukar su. Da safe ba walwala ta tashi, haka ta shirya ta tafi makaranta. Ko a makarantar ma hakanan take sukuku sai tambayarta abin da ya same ta Walida ke yi sai ta ce ba komai. Da suka tashi maimakon Malam Adamu da ya saba zuwa daukar ta yau saɓaninsa Abdurrashid da kansa ta gani tsaye jikin motar ko da ta doshi motar tana takawa a hankali kamar wadda ƙwai ya fashe mawa. Tana isa inda yake ta ce "Ina wuni? Sai ka saurara da kyau za ka ji me ta ce, shi ma ban da ita yake kallo ganin ganin sauyin yanayinta da ba zai gane ta yi magana ba. Ya zagaya ya shiga ita ma ta buɗe ta shiga bai ko dubi inda take ba har sai da suka hau titi. 'Me ya same ki? Ta girgiza kai "Ba komai." "Ba wasa nake miki ba fa." ya faɗi a ɗan hasale. Ta buɗe baki ta yi magana sai kuka kallon ta yake ta yi sai da ya ga ba ta da niyyar shiru ya ce "Ya isa ki yi shiru, an tashi yazan amma gobe zan shigo sch din in ji abin da aka yi miki." da sauri ta ce "Ni ba abin da aka yi mini a makaranta." "To me ya faru? Shirun ta kuma yi tana cigaba da hawaye, ya tsaida motar gefen hanya ya kuma tsare ta sai ta fadi mishi abin da aka yi mata. Kan ba yadda za ta yi ta ta ce mishi sauka za su yi a Islamiya, kuma Gwoggo ta ce ba za ta biya kuɗin ba sun yi yawa. Ya tambaye ta nawa ne kudin ta fada mishi, motar kawai ya tada suka bar wurin bai kuma sake ce mata komai ba har suka isa ya sauke ta. Da yamma lis kuma sai ga shi gidan Gwoggo, ta waya kamar yadda ya saba ya shaida mata isowarsa. Ta ce ya shigo Gwoggon kawai ya samu a falo sai da suka gaisa ta shiga ƙwala kiran sunan Hamida da yake yau ɗin Alhamis ce ba Islamiya kafin fitowar Hamida ta ce "Fushin take har yanzu kenan? Sai ta yi shiru don son jin me Abdurrashid zai ce, jin bai ce komai ba sai ta cigaba "Don na ce ba zan biya kudin sauka ba ta faɗa maka shi ne take fushi."Shi dai ko dagowa bai ba sai wayarsa yake faman dannawa. Hamida ta fito cikin nutsuwa baƙar jallabiya ce jikinta sai hijab ƙarami shi ma baƙi ta zauna Gwoggo ta mike ta bar musu falon, gaishe shi ta yi suka zauna shiru kafin ya mike ya bar gidan. Gwoggo ta dawo falon tana tambayar Hamida ya yi mata zancen kudin saukar? Hamida ta girgiza kai ta zabga ƙwafa "Duk da gaya mishi da na yi da kaina? Nan ta yi ta faɗa har Aina ta dawota ji abin da kenan, hakuri ta yi ta ba Gwoggo . Ranar Asabar da Hamida ta je Islamiya malaminsu mai kula da hidimar sauka ya kira ta ya bata unifoam da sauran abubuwan da aka bai wa masu saukan. Ta koma gida tana ta murna ta gaya wa Gwoggo da Aina baki Gwoggo ta taɓe ta ce hala shi ya biya. Suna ta shirin sauka har lokacin ya gabato Ahmad mijin Laila shi ya kawo abincin da za a ci da abin sha wurin saukar Laila ta yo mata memo mai dauke da kyakkyawan hoton Hamida. Aina ce ta yi mata dinki wanda za ta sanya ranar sauka. Har ana gobe saukar Abdurrashid bai kawo komai ba, Gwoggo ta yi mita har Allah gajiyar da ita. Sai dare Hamida na wanke lallen da aka yi mata ya kira waya yana waje Gwoggo ta buntsura baki. Hamida ta shida nuƙu-nuƙu Aina ta ce jiranki fa ake Hamida. Ta ce "Ban yi wanka ba Aunty Aina Aina." Dan murmushi Ainar ta yi tana duban ta wata yar ƙaramar riga ce jikinta sai bakin dogon wando kanta sabon kitso ne da aka yarfa mata a yammacin yau. "Ai ya san hidima ake, sanya hijab din Islamiyarki daga dogo ne." ta wuce ɗakinsu don ɗauko hijabin Laila da ke zaune wurin ko tari ba ta yi ba, nan za ta kwana saboda bikin saukar. Yan daura mutum uku suka zo da ta shiga saida ta ɗebi abin da aka yi na rabo ta zuba cikin leda sai ta boye a hijab dinta ta fito, jikin mota ta same shi tsaye yana kallon ƙofar gidan har ta iso inda yake yana kallonta ta gaishe shi ya taka zuwa wurin boot ya buɗe ledoji ya yi ta cirowa sai da ya gama ya rufe boot din ya bude kofar baya ya ciro wani kwali "Zo mu gani za ki iya dauka." ta karaso gabansa sai da ta ajiye ledar hannunta sai ta karɓi kwalin "Ki kai ciki sai ki samo mai taya ki ku kwashe waɗannan. Kai ta ɗaga sai ta yi godiya ta juya ciki ta ajiye kwalin ta dawo ta dauki ta ta ledar ta buɗe front seat ta ajiye mishi ya bude ya shiga ta ce mishi sai da safe sai da ya bar wurin ta soma tattara ledojin tana kaiwa ciki. Gwoggo da Aina ke ta buɗewa, shi ma ya yo mata calendar da memo da jaka masu dauke da sunanta sai dai ba hotonta. Sai alƙur'ani hizif bi biyu sune cikin kwali. Sai kaya kala biyar masu matuƙar kyau da tsada. Gwoggo sai aka shiga murna, Hamida dai wucewa ta yi ta juye ruwan wankanta ta yo wankan ta fito ta yi sallah mai kawai ta shafa ta goga Sure sai ta kwanta tana jiyo hirar su Gwoggo har lokacin da yan Daura. Da safe da wuri Hamida ta wuce makaranta. Ita da sauran yan ajin su suna cike da farin ciki a yau, sun sanya kayan sauka an jera su a inda za su zauna, aka soma shirye-shirye. A wurin da manyan baƙi suke zaune ta hango Abdurrashid zaune kallo daya ta yi masa ta kauda idonta, ya yi kyau ƙwarai cikin wani lallausan yadi fari ga hula ya ajiye a sha tara ya yi mata kyau fiye da koyaushe Shi a ka kira ya ba maza shahadarsu, mata kuma wadda ta wakilci matar gwamna ta raba musu. Hamida ba ta samu cikar burinta ba ta yi na daya, ta dai zo ta biyu namiji ne ya yi na daya. Baki har kunne su Gwoggo da aka kira Hamida aka ba ta kyautar wadda ta zo na biyu. Daf da tashi aka shiga rabon abinci da drinks wasu jama'a masu kaya iri daya su ashirin suka shiga cikin filin suna raba take away cikin wata leda ledar na dauke da sunan Hamida sai da suka koma gida suka tabbatar da zarginsu kan Abdurrashid ne ya yi hakan don ya aika ma Hamida ta raba wa mutane. Pepper chicken ne a ciki wani kuma dambun nama irin mai kamar audugar nan sai drinks. Taro ya yi kyau jama'a kowa ya ci ya sha ya an tashi lafiya zuwa magrib yan Daura kuma sai washegari suka ɗauki hanya. Wannan hidima da Abdurrashid ya yi ta ɗan wanke shi wurin Gwoggo duk da ba haka taso ba wasu manyan kudi ta so ya miƙo ya ce a yi hidimar. Wannan kenan. Sati guda kacal da ƙare bikin saukar suka wayi gari da labarin rasuwar mahaifiyar Aina asubar fari suka bar garin Kano zuwa Daura Aina na ta sharɓar kuka Hamida na taya ta Gwoggon ma hawaye take ta zubarwa. Sun samu gida cike ba masaka tsinke ba su iske gawar ba an tafi kai ta, faɗuwa Aina ta yi tana ta rusa kuka da ta sanya jama'a da dama zubar da hawaye. A daren ranar an gama sallar magarib Gwoggo ta kira Hamida ta miƙa mata wayarta Abdurrashid ke kira ta karba sai ta bar wurin. Wani lungu can bayan ɗakuna da ba mutane ta lafe sai dai akwai hasken lantarki sai ga kiran shi ya shigo ta ɗaga da sallama bai saurari gaisuwar da take masa ba ya ce "Me ya faru na ji a ka ce an ga kun shiga mota da sassafe? Sai da ta kalli gefe da gefen da take sai ta rage murya "Maman Aunty Aina ce ta rasu. Ya yi addu'ar Allah ya ji ƙanta sai ya ce ta kai ma Gwoggo wayar zai kira ya yi mata gaisuwa. Ranar da aka yi uku aka aiki Hamida da Amina su amso waina a wani gida bayan layin su. Haka suka gifta taron mazan da suka yi dandazo a ƙofar gidan. Ƙatuwar cooler ce suka kamo shaƙe da wainar suna tafe suna hutawa dan Hamida da ke ta koken nauyi, sun shiga layinsu har sun kusa gida Hamida ta hango Abdurrashid na nufo su wata kunya da mamaki suka rufe ta ajiye hannun coller da take riƙe da shi ta yi Amina da ba ta san dalilin ajiyewarta ba ta shiga sababi "Ke dai wallahi ragguwa ce, tafiya ba tafiya ba sai ki ajiye to sai yaushe za mu kai? Hamida dai da ta sadda kai ƙasa ba ta ce mata komai ba har ya ƙaraso inda suke Amina ta jingina da motarsa tana cigaba da sababinta Hamida ta taɓa ta don ta yi shiru amma kamar tana daɗa zuga ta, har ya kama murfin motar Hamida ta matsa kusa da shi tana mishi gaisuwa, Amina sai ta yi sansarai tana tunanin ina kuma Hamida ta san wannan ɗan gayun? "Ina kika je? Ya tambayi Hamida ta ƙara ƙanƙame hannuwanta cikin farin gyalen da ta yafa ta ce "An aike mu ne." ya kaɗa kai "Ya yi kyau, ku je ku kai aiken ni zan wuce." Ta yi saurin kallonsa ganin shi ɗin ma ita yake kallo sai ta yi saurin maida idonta gefe suka yi ido huɗu da Amina da mamaki ya sandarar a tsaye, ta galla wa Aminar harara "Ba ka shiga ciki ba wurin su Gwoggo." Ta faɗa a hankali "Yadda ƙofar gidan nan ke cike na san cikin ma cike yake da mata, ki gaishe su. Ya faɗa motarsa ta matsa jikinta Amina ma ta matsa sai da ya tashe ta ta kama hannun coller "Kama mu je malama. Ta ce wa Amina "Wai ina kika san wannan ɗan gayun saurayin? Dan Allah Amina ki kama, kin san dai jiran mu ake." ba ta kama ba sai da Hamida ta yi mata alƙawarin za ta sanar da ita waye Abdurrashid. Suka tafi Hamida na mata mitar ta ga mutum ta kasa gaishe shi. Kama bakinta ta yi ba ta gaya wa kowa zancen zuwan Abdurrashid ba har sai ranar da aka yi bakwai tana ta haɗa musu kayan su gwoggo na zaune tana halin nata mita "Shi yanzu yana son ki Hamida, amma a yi mana mutuwa sai dai ta waya zai yi mana gaisuwa? Hamida ta ba ta amsa ba tare da ta juyo ba "Ya fa zo Gwoggo."Cikin mamaki Gwoggo Indo ta ce "Kamar ya ya zo? Ni ina ina da ban gan shi ba? A hankali Hamida ta kwance mata yadda aka yi taɓe baki ta yi "Shi dai ba wani, don kar ya yi alheri ya sa ya ƙi shigiwa, ko ya aka yi ma ya san nan din? Shigowar wani yaro na sasan su Laila ya sa su bin shi da kallo suna amsa sallamar da ya yi. Sai da ya gaida Gwoggo ya shaida mata Malam na kira ta mike ta bi bayansa suka fita, Hamida ta sauke ajiyar zuciya sai ta cigaba da harhaɗa kayan. Gwoggo ta jima kafin ta dawo Malam dai ya hana komawar su a yau ya ce yana son ganawa da Gwoggo idan yan gaisuwa sun gama komawa gidajensudon haka sai da suka kwana goma duk da damun da Abdurrashid ke ma Hamida ta waya sun je sun zauna ta manta da karatunta. Malam ya tara meeting gabadayansu kan Aina ta fito da miji ya sanya ranar Amina kuma tare zai musu dan haka ko Aina ta fito da miji ko shi zai nemi ko ma waye ya ba shi a Daura. Sai Hamida Alh Mustafa ya yo aike ita ɗin ma ba zai bari ta kai shekarun Aina zaune ba gara ya yi mata auren. Sun baro garin hankalin su a matukar tashe Gwoggo da Aina Gwoggo ta sha alwashin ba za ta taɓa bari a aura ma Aina kowane kwashe kwashe ba a Daura kamar yadda ba za ta taɓa bari Hamida ta auri Mustafa ba. Watan ƙaramar sallah Malam ya sanya bikin Amina ga shi saura sati biyu kwata kwata a fara azumi. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... Daga MaRuBuCiYaR WA GARI YA WAYA CANJIN BA ZATA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE No.10 Kwanan su uku da dawowa suka yi wani baƙo da daddare Malam Buhari ba ya nan ya je Daura. Har falo Gwoggo ta ce ya shigo sun gama maganarsu ya tashi ya tafi washegari kuma Aina ta yi shiri cikin matuƙar kwalliya ta ce Hamida ta zo ta raka ta kasantuwar ba Islamiya ta shirya ita ta riƙe mata madaidaiciyar jakar da ta sanya kayanta, suka yi wa Gwoggo sallama suka fito gidan. Shatar a daidaita sahu ta ɗauka wani wurin daukar hoto a Goron dutse suka je, hotuna kala-kala a ka yi wa Aina sai na karshe ta ce Hamida ta shigo. Yana ƙare Edition mai hoton ya tura mata a wayarta da ta mika wa Hamida wayar sai kallon hotunan take don hakika sun yi matukar kyau. Suka fito bayan ta biya suka dawo gida. Kwana biyu tsakani mutumin da ya zo wurin Gwoggo ya dawo suna gaisawa ta ce "Ya ya Haji Ilyasu an dace? Ya yi dariya ya yin da yake kora lemon da Aina ta ajiye mishi "Ƙwarai kuwa Hajjaju, ai 'yar taki ce ba daga baya ba. Mutum biyu suka taya, Alh Abbas banki sai Brigadier Bala Kafur, Gwoggo Indo ta zaro ido "Da gaske ko da wasa Haj Ilyasu? Ya ce "Wallahi Hajjaju, Alh Abbas banki yana so amma a huta yake so don akwai naira, ko ni tukwici na mai gwaɓi ne idan na kawo ta, ba ma ita ba ita kam ta haye don yana ba mata kudi kamar bai san zafin su ba." Gwoggo ta ce "Ina ji cigaba." Ya ce "Sai Brigadier shi da aure yake so don matarsa ta rasu ta bar mishi yara hudu duka maza, yaran ma duka suna waje suna karatu, sai dai shi ma ko bunsuru haka ya gan shi Hajjaju. Ya miƙa mata wayarsa don ta gan su a hoto. Ya ce "To ya ya Hajjaju? Ta ce "Ai kai ma ka san wanda zai yi aure zan zaɓa neman mata kuma yanzu Allah na tuba ai sai wanda Allah ya tsare. Ta kwala wa Aina kira ta fito sai ta miƙa mata wayar da yi mata bayani Ya miƙa wa Aina katin Brigadier "Na ba shi lambarki zai kira ki anjima." Aina ta gyada kai Gwoggo ta ce "Amma ka gaya mishi ba maso auren ya ja lokaci ko? Ya kama baki "Kin ga yadda ya rikice a kanta? Ai ina ganin ko cikin satin nan a ka ce zai amince." Gwoggo Indo ta gyara zama "Alhamdulillahi na ji daɗi sosai Haji Ilyasu zan maka transfer cikon kudinka." ya yi dariya "Girmanki ne Hajjaju, gobe zai iso daga Abuja don asalinsa mutumin Kano ne dan ganawa da Haj Aina a gidan gonarsa, sai dai ga shawara Hajjaju ki gargaɗe ta kar ta kuskura ta bari ya yaudare ta ta bada kanta, auren nan zai yi wuya a yi shi. Gwoggo Indo ta ce "Kar ka ji komai ba abin da zai faru Aina ta iya takunta." Sun ƙara tattaunawa ya tashi ya tafi. Ranar sun yi kwanan farin ciki Gwoggo da Aina Washegari ya zo suka gana da Aina kuɗaɗe masu nauyi ya jiƙa ta da su waɗanda ya nemi ta ba shi acc no ya yi mata transfer Gwoggo dai har rawa ta taka Aina ta samu miji kuma na kere ma sa'a. Abdurrashid ke kai da kawo a Office dinsa cikin matuƙar damuwa da tunani, yana cikin Sojojin da aka tura America yin wani course na shekaru huɗu. Ba don komai tafiyar ke ɗaga mishi hankali ba tunda ya samu labarinta sai don Hamida ya za a yi ya tafi ya bar ta da Gwoggo Indo? Wane hali zai dawo ya same ta? Ya daki tebur ba zai yuwu ya tafi ya bar Hamida wurin Gwoggonta ba, to ya zai yi? Duk iya tunaninsa kansa ya ƙulle ya rasa samun mafita. Jin da ya yi kansa na daukar zafi ya sa ya tattara ya na shi ya na shi ya bar Office din. Gida ya wuce kai tsaye bai tsaya neman Auntynsa ba ya shige wurinsa ya kwanta. Sai da ta ji shirun ya yi yawa don ta ga motar da ya fita cikinta ta leƙa shi ganin yana barci ta koma ba ta san rufe ido kawai ya yi zuwanta uku ana hudun ta same shi zaune tambayar lafiya yake ta yi ya ce E ta ce to ya fito su ci abinci ya ce ba ya jin yunwa, sai ta yi turus! ƙoƙarin jin damuwarsa ta yi amma ya dage ba komai. Kwana biyu suka dauka tana fama da shi ga mahaifinsa ba ya gari sai ta kira mahaifiyarta a waya ta gaya mata a ranar ta zo daga Yola. Abdurrashid ba shi da labarin zuwanta sai da ya dawo daga Office Zaune take a falon Auntynsa bayan carpet din da ke malale an shimfida mata darduma, ga cima kala kala nan an jera gabanta. Da sauri ya ƙaraso yana fara'ar da ba wanda zai ce ya iya ta, ya zauna gabanta ya shiga latsa ƙafarta "Daada kin sha tafiya, ga ƙafa kina fama da ita." Ita ma fara'ar ce kwance kan fuskarta na ganin jikan nata mafi soyuwa a gare ta, wanda ya fito daga babbar ɗiyarta ta mutu kuma ta bar mata shi. "Tafiya ma a jirgi Abdul, ai ba wata wuya." ta tura mishi flate "Zuba abinci ka ci Abdul." ganin bai ɗauka ba ta shiga zuba mishi ya ce "Da kin bar shi Daada zan zuba da kaina. Ba ta yarda ba cigaba ta yi ta gama ta tura mishi ta tsiyaya mishi lemo "Ka dawo wurin aiki Abdul, maza ka ci." Murmushi ya yi yadda take mayar da shi kamar Wani ƙaramin yaro "Ban yi wanka ba Daada, na canza kayan jikina.""Ka yi wankan daga baya, yanzu dai ka ci abincin." ya fara cin bai fasa murmushi ba sosai yake cikin farin ciki da ƙaunar da yan'uwan mahaifiyarsa da kakarsa ke gwada mishi. Sai da ta ga ya kusa cinyewa ta ce "Mamanka ta tado ni, wai kwana biyu kana cikin damuwa ta rasa yadda za ta yi da kai don ka ƙi gaya mata. Kai ya jinjina sai ya ture flate din "Daada kenan, ita fa Auntyn na gaya mata ba komai." hannu ta dora bisa goshinta sai ta kama kuka sambatun maganar da take yi ya daga hankalinsa "Allah ga ɗan maraya nan, kai ka san damuwarsa ka shiga lamarinsa ka yaye masa ba... "Yi hakuri Daada, ki yi shiru zan gaya miki. Sai ya miƙa mata hankacif dinsa ta goge fuska sai da ta natsa ya ce "Wata yarinya Allah ya sa min son ta Daada, ƙarama ce ƙwarai don ko shekaru sha biyar ba ta haɗa ba, kuma Course din da na ba ki labari an tura ni abin da ke ɗaga mini hankali idan na tafi na mariƙiyar yarinyar wadda take hannunta tana da son abin duniya, ina tsoron abin da zai faru. Ya ƙarashe yana kallon idonta. Ajiyar zuciya tsohuwar ta fidda "Wannan ai mai sauki ne Abdul, a ɗaura muku aure kawai Abdul kafin ka tafi a kawo ta nan wurin uwar taka har ka dawo." kai ya girgiza "Aure kuma Daada? Ina faɗa miki ko sha biyar ba ta haɗa ba." sai me don ba ta yi sha biyar ba? Mu nan da ka gan mu sha biyu aka yi mini aure kuma ba abin da ya same mu." ya kuma girgiza kai "Wannan zamanin ku ne Daada yanzu lokaci ya canza. Ni dai ina ganin zan nemi su maida ta wurin iyayen ta har in dawo." ta ce "Su iyayen ka san waɗanne iri ne? Sai ma an yi bincike kan iyayen a ina suke? Ya ce "Suna Daura amma asalin su mutanen Adamawa ne. Sai kuma ta washe baki "Ka ce tushen mu daya, ita yarinyar a ina take? Ya ce "Cikin Estate din nan suke zaune da mariƙanta, in kika gan ta Daada tana da nutsuwa da tarbiya da alama iyayenta ma mutanen kirki ne." "Za ka kai ni in ga kishiyar Abdul kafin in tafi. Daidai nan Aunty Karima ta fito kusa da mahaifiyarta ta zauna Abdurrashid ya ce "Barka da gida Aunty." ta amsa tana mishi sannu da dawowa ya juya gun tsohuwar "Zan ma kawo miki ita Daada."Aunty Karima ta tambayi abin da suke tattaunawa Daada ta yi mata bayani shi kam mikewa ya yi ya shiga ciki wanka ya yi ya shirya cikin ƙananan kaya da suka yi matukar amsarsa ya fito cikin ƙamshi. Daada da Aunty Karima suna nan zaune inda ya bar su ya ce musu zai fita Daada ta ce "Wurin Kishiyar tawa za ka? To ina gaishe ta." murmushi ya yi bai yi magana ba sai Aunty Karima da ya ce wa "Zan fita Aunty. Ta ce "Sai ka dawo Abdul." Ya fita ya fada motarsa bai burki ko'ina ba sai gidan Gwoggo da ya kira ta a waya ya ce yana waje cewa ta yi ya shigo, da ma za ta kira shi tana son magana da shi . Ya fita cikin motar ya shiga cikin gidan tana zaune falonta ta amsa sallamarsa ya shiga sai da ya zauna ya gaishe ta ta kwala ma Aina kira wadanda suka shiga ciki ita da Hamida jin zuwansa ta ce ta kawo mishi lemo da ruwa ta wuce kitchen don kawowa Gwoggo Indo ta dubi Abdurrashid "Da ma ina neman ka."(Don yanzu ta ji rokon Hamida ta bar ce mishi Yallabai) "Babban yayanmu a gida wanda shi ne yake kamar mahaifinmu ni da iyayen su Hamida ya kira ni ya yi mini magana kan aurenta. Ya yi saurin dago ido ya dube ta sai kuma ya mai da kai ya sunkuyar "Akwai yar'uwarta a gida za a yi aurenta da kuma Aina, watan sallah suka sa, da ma tun kafin dawowar Hamida nan akwai wanda yake ruƙonta to yanzu ya shigo gida yayanmu ya ce zai bayar da ita gare shi. Wata zufa Abdurrashid ya ji tana tsattsafo masa, ta cigaba "Shi ne na roƙi yayan namu kan akwai mai son Hamida a Kano ita ma tana son sa ya yi haƙuri ya bar maganar wancan da ba ma son sa take ba."Jin ta yi shiru ya ce "Zan je gida zan sanar da iyayena, yadda muka yi zan dawo in faɗa miki." ta ce "To." ya ce "Ta shirya mu je ta gaishe da kakata." nan ma to ɗin Gwoggo ta kuma cewa. Yana fita ta ƙwala kiran sunan Hamida suka fito tare da Aina ta ce "Ki yi wanka da shiri mai kyau ya ce za ku je ki gaishe da kakarsa." Da wadda Hamida za ta iya yi wa musu ce da ta ce ba za ta ba, amma kan ba yadda za ta yi ta juya zuwa ciki don yin shirin. Aina ta haɗa mata ruwan wanka ta sanya mata turaruka a ciki da ta fito kuma ta taya ta shiri simple make-up ta yi ta sanya riga da zane babban mayafi ta rufe jikinta duk da ba mai kauri ba ne ta zura takalmi sai ta fito, Gwoggo Indo ta yi murmushi "Ma sha Allah kin yi kyau yammatana, Allah ya cika min burina in ga auren ki da Abdurrashid ki shiga gidan Shehu Bello." ita dai fita ta yi tana fadin "Sai na dawo Gwoggo."Kallo daya ya yi mata duk da kyan da ta yi masa sai ya kawar da fuskarsa ta zagaya ta shiga, sai da ta rufe ƙofar ta ce "Ina wuni? A ƙasan maƙoshi ya amsa ya tashi motarsuka bar wurin. A kusa da sasan Auntynsa ya farker motar ya buɗe sai ya fita ba ta yi gigin ko taɓa ƙofar ba sai da ya ce "Ke ba za ki fito ba? Ta bude sai ta fita lokacin ya fara tafiya sai ta bi shi a baya, sannu cikin nutsuwa take takawa har ya yi nisa ya waiwayo ya gan ta can baya ya jira ta ta ƙaraso "Ke ba ki iya sauri ne? Ya ce mata cikin ɗaure fuska ba ta yi magana ba ta sunkuyar da kai. Wata ƙofa ta glass ya murɗa wadda na ciki ke ganin na waje amma na waje ba ya iya ganin na ciki, don haka su Aunty Karima da Daada da ke zaune a falon suna kallonsu ya fara shiga ta bi bayansa bakinta dauke da sallama daga Daada har Karima fara'a ce ta suɓuce a saman fuskarsu ganin zaɓin Abdurrashid. Aunty Karima ta miƙe ta taro Hamida ta kamo ta har inda take zaune Hamida ta sauka saman kujerar ta zauna ƙasa inda Daada ke zaune ta gaishe ta ta kama hannun Hamida ta sanya cikin nata "Na yaba Allah ya miki albarka yarinya." ita dai kanta na sunkuye ta ɗago kadan ta gaishe da Aunty Karima, kafin ka ce me an cika gaban Hamida da kayan taran baƙo amma ta kasa taɓa komai Aunty Karima ta ce ta ci mana nan ɗin gidan su ne. Amma Daada ta ce ta bar ta fillancin kenan. Ta zauna tsawon awa guda Abdurrashid ya shigo dan dama ko da ya kawo ta bai zauna ba fita ya yi "Oya tashi mu je." ya fadi ba tare da ya dube ta ba. Ta mike ta yi musu bankwana Aunty Karima ta shiga ciki ta fito da ƙatuwar leda ta ba Abdurrashid ta ce ya riƙe ma Hamida ya karɓa suka fita. Wannan karon ita ke gaba yana biye da ita yana biye wa tafiyarta, sun zo wurin motar wata mota ta iso har ta gifta su ta yi ribas ta dawo aka sauke glass wadda ke zaune a owners coner ta bayyana kallo ɗaya Hamida ta yi mata ta gane Hajiyar da suka zo da Gwoggo ta sayi maganin mata ce. Abdurrashid ya matsa inda take "Ba dai surukar tawa ka kawo ba ka kai min ita ba." ta fadi tana murmushi, ganin bai yi magana ba yana shafa ƙeya ya sa ta ce "To shi kenan, ku ƙarasa mu gaisa."Ya ce "To Mami. Da ɗan tazara tsakanin sasan haka suka bi bayan motar tata san da suka shiga har ta zauna cikin nutsuwa Hamida ta gaishe ta ta amsa sai ƙare mata kallo take tana son tuna inda ta taɓa ganin yarinyar ido ta rage "Kamar yarinyar Haj Indo ko da kuka taba zuwa tare ko? Hamida ta ɗaga mata kai. ya miƙe "Bari in kai ta gida Mami." ta ce "Ba laifi." ita ma ciki ta shiga rafa na dubu guda ta ba Abdurrashid ta ce ya riƙe wa Hamida ta ƙara da cewa "Ka san daddynka na hanya ko? Ya ce ""E mun yi waya ba jimawa zan yi ba. Yana ajiye ta kayan da Aunty Karima ta bata ya sanya kudin wurin Haj Mariya a cikin ledar ya mika mata ta ce ta gode ta shige ciki ya juya da motar. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... DAGA MaRuBuCiYaR RANAR NAKA WA GARI YA WAYA CANJIN BA ZATA HATTARA MARYAM LITEE No.11 A inda ya bar su Aunty Karima nan ya dawo ya tarar da su ita da Daada. Daada ta ce "Tubarkalla Abdul ka iya zaɓe yarinya mai nutsuwa da hankali, da ganin ta iyayenta mutanen arziki ne ga ta kyakkyawa." Aunty Karima ta dauka "Yarinyar fa kyakkyawa sai dai wannan yarinya sharaf Abdul ba ta yi maka ƙuruciya ba? Daada ta karɓe "Ba wani ƙuruciya za ta tashi a irin tarbiyar da yake so, duk abin da ya ɗora ta a kai za ta tashi. Aunty Karima ta kaɗa kai "Har na ji ta bani tausayi yarinya ƙarama yadda za ta iya da miskilancin Abdul. Dubi yanzu yadda ya yi mata kafin su shigo da gani ma tsoron shi take." Daada ta murmusa irin murmushin su na manya "Mace ce fa, maganin miskilancin na shi za ta yi komai ƙanƙantarta, don kar ma ki zo kina ƙorafi ɗanki kaza kaza." Aunty Karima ta yi yar dariya "Ka ji Daada wannan yar yarinya har wata dabara za ta iya? Kai Daada ta gyaɗa "Ai shi kenan Allah ya ba mu yawan rai." Abdurrashid dai na jin su bai tanka ba sai Aunty Karima da ya duba "Daddy kuwa ya shigo? Ta ɗaga mishi kai "Kana fita yana ta tambayarka ma. Miƙewa ya yi sai ya fice sasan mahaifin nasa ya isa Mami ya samu don ita ke da girki ta ce mishi ya shiga wanka zama ya yi har ya fito cikin jallabiya mai guntun hannu ta yi masa tayin hawa tebur bayan sun gaisa da dansa ya ce "Bari tukun in gaido Daada. Ya fice ta bi shi da kallo Abdurrashid ma zama ya yi yana latsa wayarsa don jiran daddyn nasa. Gaisawa suka yi da surukar tasa ya ce "Ai ina hanya Karima ke sanar mini zuwan naku." Ta ce "E mai gidan ne ya ɗago ni, ashe kishiya yake son yi mini." Alhajin edai bai gane ba ta ƙara mishi bayani inda ta ba shi labari tun daga wayar da Karima ta yi mata har zuwan Hamida yanzu. Fuskarsa ta washe da fara'a "Na ji dadi sosai don bani da buri irin in ga auren Abdul, ni da Allah bai bani yayan ba na riƙe na shi, za mu yi magana da shi inda iyayen yarinyar suke, sai a yi maganar auren kafin ya tafi, ya dawo sai a yi biki. Sun gama tattauna maganar ya koma sasansa. Mami da ta tare shi ta ga fara'ar da ya shigo da ita ta ce "Ya dai? Ya amsa mata da "Abin farin ciki ne ya same mu." ita ma ta ɓalle da fara'ar "Danki ne ya samo mata. Ta ce "Ai kuwa ɗazu ya zo da ita ta gaishe mu." Suka isa dinning ya yafito Abdurrashid ya tashi ya isa ya ja kujera sai ya zauna, uban na cin abinci yana kallonsa ya san nufin sa Abdurrashid din ya zuba ya ci ya ce "Daada ta sanya ni na ci abinci sosai. Ya ce "To shi kenan a ina ka samo mata? Mami da ke tahowa ta karɓe "Ai Abdul da dai zai canza, duk yammatan da ke garin nan yayan manya da ma Nigeriar gabadaya ya rasa wadda zai ɗauko mana sai yar masu saida abinci? Uban ya dube ta babu wani alamar firgici ko bacin rai a fuskarsa a hankali ya ce "Yar wane gidan ce? Ta ce "Cikin Estate din nan take, wani ƙaramin ma'aikaci ne Babanta. Uwarta ce mai sayar da abinci a Estate din nan. Saboda Allah ai ba girman mu ba ne." Bai ce mata komai ba sai duban Abdurrashid da ya yi "Haka ne? Abdurrashid ya gyaɗa mishi kai "Sai dai Daddy ruƙonta ake anan din iyayenta na Daura, asalinsu kuma mutanen Adamawa ne. Kai ya gyaɗa "Daada ta faɗa mini komai, zan je da kaina in ga iyayen nata. Abdurrashid ya yi yar fara'a "Na gode Daddy." ya miƙe ta falon Daddyn nasa akwai hanya da za ka bi ta kai ka har bedroom dinsa ta can ya bi. Mami ta shiga tunani mijin nata babu abin da yake musa mata idan ta faɗi, buƙatar Abdurrashid ita ce kawai sama da ta ta a wurinsa. Shi din ma Daddyn duk da ganin gaskiyarta kan abin da ta fadi hakanan yake jin wani abu na jan shi kan wadda Abdurrashid din ya kawo. Hamida na shiga falon Gwoggo ta tare ta da murna ta karɓi ledar ta zazzage less ne mai asalin tsada sai atamfa super wax sai turaruka Designers. Ta riƙa juya kudin "Kin ga halin girma, shi kenan kin samu na sallah. Mai neman Aina ya je Daura bayan dawowarsa ya tura magabatansa an tsayar da magana za a yi biki rana daya da Amina don haka Gwoggo da Aina shiri suke ta yi. Gwoggo ta je Daura ta yi ma Malam bayanin wanda ke son Hamida iyayensa za su zo bayan sallah ya ce Allah ya kaimu. Gwoggo dai ta yi sa'a wannan karon Abdurrashid ya yi mata abin da ya kamata don boot ya ciko da kayan abinci ana gobe azumi har da su irish da kwai da kayan Tea. Mami dai ba ta hakura ba yayar Engineer da ita kadai ta rage masa da suka fito ciki daya ta je ta gaya ma wadda Abdurrashid ya kawo kuma Engineer ya goya mishi baya, takanas ta taso ta samu Engineer ta nuna mishi rashin dacewar wannan aure da zai biye wa Abdurrashid a yi, hakuri kawai ya ba ta ya ce ba zai tilasta Abdurrashid ba abar shi ya auri wadda zuciyarsa ke so. Da ta tashi wurin Aunty Karima ta wuce ta ce "Da hankalinki Karima Abdurrashid zai rasa matar da zai aura sai yar tuwo -tuwo yar masu saida abinci, har Mariya ta fi ki son Abdul." Ita ma hakuri ta ba ta ta ce suna son farin cikin Abdul. Cikin fushi ta tashi ta tafi. Ana saura sati daya sallah Abdurrashid ya zo da daddare wurin Hamida sai da ta zauna motar ta gaishe shi ya amsa yana tambayar ta Exam da suke yi da ma ta san zai tambaya don haka ta fito da papers din sai ta mika masa sai da ya gama gani tare da gamsuwa da abin da ya gani sai ya fita ya ciro wata kyakkyawar jaka ya bata ya ce dinkin sallah ne in ji Aunty Karima ta yi godiya bai jima ba ya wuce. Ranar sallah dukkan musulmi yana tashi cikin farin ciki haka ta kasance a gidan Gwoggo Indo sun yi abincinsu kala biyu na sallah sun yi cincin sun soya nama. Masu aikin Gwoggo duk sun tafi gida sallah, Hamida ta je sallar idi tare da yaran maƙociyarsu Nurse Saratu. Washegarin sallah Aina za ta karɓi baƙuncin mai girma Brigadier Bala Kafur sai shiri suke ita da Gwoggo Abdurrashid dai ba wanda ya ga yar ƙafarsa ya dai kira waya ya yi wa Gwoggo barka da shan ruwa. Aina ta ce tare da Hamida za ta sun gama shiri sai ga Walida dole Aina ta tafi a motar da ya turo a ɗauke ta Hamida ta zauna wurin baƙuwarta, Laila ma ranar ta zo, wuni zungur Walida ta yi ma Hamida sai magrib ta koma gida Aina ma sannan ta dawo suka baje ana duba katinan auren da ya bata, sai nairori da ya cika mata account da su na hidimarta da kawayenta, da yake ita ba ma mai yawan kawaye ba ce, kasafinsu kawai suka kama ita da Gwoggo. Sun shirya ana saura sati guda bikin za su wuce lokacin Gwoggo ta kammala da kayan dakin Aina an kai. Aina ta dubi inda Hamida ke zaune tana duba katinan "A cikin kudin nan zan yi wa Hamida sayayyar kayan da za ta sanya da biki." Gwoggon ma Hamidar ta duba "Wace sayayya kuma za ki yi wa Hamida duk kayan da surukarta ta aiko mata? Ai sun ishe ta cin biki." Ganin kamar Ainar ba ta gamsu ba ya sa ta ce "Ba fa ƙaramin gida za ki shiga ba Aina, dole kayan daki na masu abin za a yi miki." Aina ta daga kai. Gwoggon ta ƙara kallon Hamida "Abdurrashid bai zo ba, ba zuwa ba aike." ita dai shiru ta yi Gwoggo ta yi yar mitarta ta hakura. Sai washegari da yamma Hamida na yi musu tuwo a kitchen dinsu na falo, dukkan su marmarin tuwon suke Gwoggo da Hamida don sun rabu da cin shi ya kira Gwoggo a waya lokacin tana bayan dakunan su tana tsefe kanta ta ce ya shigo ta mike ta daure kanta ta shiga ciki don shaida wa Hamida zuwan nasa shi kuma ya shigo ya yi kyau ƙwarai cikin wata farar shadda da aka yi masa karamar riga mai guntun hannu yau har da hula da ta zauna a kansa ta ƙara mishi kyau. Tana mishi maraba ta shiga falon yana bayanta sai da ya zauna ta shiga kitchen din ta shaida wa Hamida Allah ya sa ba ta daɗe da yin wanka ba don ba ta yi wanka da wuri ba shadda ce jikinta dinkin doguwar riga ta karbe ta ba kadan ba. Ta samu tana kwashe tuwon a leda ta karba ta ce ta je wurinsa sai da ta debi naman da suka soya da cincin sai ta dauki lemo ta fita a gabansa ta ajiye sai ta samu kujera can nesa da shi ta zauna tana gaishe shi, Gwoggo ta fito bayan ta kammala kwashe tuwon, nan Abdurrashid ke shaida mata babansa ya ce zai je Daura nema mishi aure ranar daurin auren Aina don ya gano abokinsa Aina za ta aura wanda ya kasance shi ne uban gidan Abdurrashid a aikin Soja. Gwoggo ta cika da farin ciki ta shiga daki ta debo katin bikin sun yi goma ta kawo mishi, suna magana sama sama Hamida ta yi amfani da damar ta koma kitchen kuɓewar da za ta kaɗa ta dauko ta dawo ta zauna tana yankawa, idon Abdurrashid na kan TV har ta gama miyar ta zubo ta kawo mishi ta dai zubo mishi amma ba ta sa ran zai ci ba ita tunaninta bai ma ba ta yana cin tuwo ba ta ji ya ce mata ina Spoon ta mike ta je ta kawo mishi ya ci sosai har ta ji mamakinsa daga inda take zaune ta ji muryar Gwoggo tana kiran sunanta ta mike tana amsawa waya ta ba ta Aliyu ne ke neman Hamida ta karba cikin jin dadi ta dawo falon tana amsa kiran cikin shagwaba tun da ta zo bai taɓa zuwa ya gan ta ba, shi kuma ya shiga rarrashin ta, sun daɗe kafin suka yi sallama Abdurrashid da ke kallon ta ta wutsiyar ido ya juyo gaba daya bai taɓa gani tana farin ciki irin na yau ba, wani kishi ya mintsini zuciyarsa sanin da namiji take wayar fuskarsa ya ɗaure dan dauriya mai yawa ya sa wurin danne zuciyarsa har ta ƙare wayar "Da wa kike waya? Ya tambaye ta cikin daka tsawa! Raurau ta yi sai ta sunkuyar da kai don ta matukar tsorata na ce "Da wa kika yi waya? Ya kuma maimaitawa gane ba za ta yi magana ba ya ja mummunan tsaki sai ya mike ya bar falon, ta ci gaba da zama shiru tana tumanin inda ta kuskuro shi. Ko da Gwoggo ta shigo ba ta gaya mata komai ba har sai da aka kwana uku Gwoggo ta ji shiru bai kira waya ba sai take tambayar Hamidar ta faɗa mata duk yadda suka yi, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta kira shi a waya tana tambayar abin da Hamida ta yi mishi ya ce tsakanin mu ne Gwoggo. Ta ce "To to a dai yi hakuri. [2/9, 09:43] Original: MAGANIN CIWON SANYI DA YAWAN 'BARIN CIKI KO RASHIN HAIHUWA : ************************* Matar dake fama da yawan zubewar ciki, ko rashin haihuwa, ko ciwon sanyi sanadiyyar shafar Aljani Jinnul Ashiq wato Namijin dare, wanda yakan zo acikin barci ya rika saduwa da mace, ta sanadiyyar haka sai ta rika fama da ciwon mara, fitar farin ruwa mai Qarni, kaikayin gaba, jin zafi yayin saduwa, daukewar sha'awa, etc. Ki samo wadannan abubuwan : 1. Tafarnuwa. 2. Garin H/rashad ko garin Hulba. (cokali 3). 3. Man Albabunaj, man gelo (castor oil). Ki fara turara gabanki da kwayoyin H/sauda, sannan ki 'bare tafarnuwar kiyi matsi da ita (adaren da mijinki bazai kusanceki ba).. Ki kwanta da matsin tare dake, sai da safe ki cire abun. Daga nan sai ki tafasa garin Hulba ko garin H/Rashad cokali 3 ki surkashi daidai yadda bazai chutar da jikinki ba, ki juye a baho ko robar wanka, sannan ki shiga ciki ki zauna tsawon minti 10 ko 15. Idan kin fito sai ki sake wanke gabanki da ruwan dumi sannan ki shafa Man Albabunaj ko Man Gelo acikin gabanki.. Zaki maimaita wannan kamar na sati biyu. Idan kikayi yau, zaki tsallake kwana daya ko biyu sannan ki sake yi. Kuma lokaci lokaci ki rika yin matsi da man Albabunaj (da rana ko da hantsi). In sha Allahu zaki rabu da ciwon sanyin, ruwan zai dena fita, kuma zaki dena jin kaikayi ko zafin. Sannan kuma shima Ashiq din zai dena zuwa yana saduwa dake. Kuma zaki dena yin 'barin, sannan koda bakya haihuwa, in sha Allahu zaki sami rabo. TUKUICI : Idan an jarraba an dace, a yiwa iyayena da Malamaina addu'ar alkhairi. Nagode. DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 08157968686 (08/06/1443 11/01/2022). [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... Daga Marubuciyar CANJIN BA ZATA WA GARI YA WAYA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE No.13 Hamida ta bi shi suka tsaya gaban motarsa ya ce "Lagos zan tafi, kwanaki uku zan yi. Mahaifina zai zo gobe har sadakinki zai bayar, ba na son mu'amalarki da wannan gayen." Wal ta yi mishi da idanuwanta jin abin da ya faɗi kan ya Aliyunta. Haɗa rai ya yi "Haka na ce ba na so." Kuɗi ya miƙo mata a karan farko da ya yi hakan, ta ɗan noƙe ya ce "Meye haka? Ta karɓa tare da godiya, ya faɗa motarsa ta mishi addu'ar sauka lafiya sai da ya ɗaga ta koma ciki Ba ta ga Walida ba Innawuro ta ce mata ba su daɗe da fita ba ita da wata ƙawar Aina, kuɗaɗen hannunta ta nuna ma Innawuro ta ce "Ni ma kin ga waɗanda ya ajiye mini, Umma ma yanzu ta fita da waɗanda ya ba ta." Hamida ta ce "Bari in kai wa Gwoggo nawa." Don tana tuna mitar Gwoggon kullum kan rashin alherin Abdurrashid. Innawuro ta ce "Ba laifi." Sai ta fita a ɗakin, Gwoggo kawai ta samu ta fito wanka "Ya tafi? Gwoggon ta soma tambayarta kai ta ɗaga sai ta miƙa mata kuɗin, ƙamshin da ta ji kuɗin suna yi ya sa ta gane daga inda suka fito "Wai su ƙanƙamo yau an ɓanɓaru kenan? Ta janyo jakarta ta saka su. Hamida ta ɗan jima wurin ta, suna maganar bikin kafin ta fito. Ranar gidan ya cika tam ba masaka tsinke baki na nesa duk sun iso. Hakanan Hamida ta daure ta kwana gidan zaman ƙunshin Amina ita da Walida. Tun wayewar garin ɗaurin aure su Malam suke ta sa yaran gidan maza share ko'ina na gidan don taran baƙi, suka ba za tabarmi a zaure da ƙofar gida. Ƙarfe goma na safiya tsadaddun motoci guda uku suka tsaya a ƙofar gidan Marigayi Malam Muntarin Adamawa. Jama'ar da suka fara taruwa sai kallon motocin suke suna tunanin mijin Aina ne ya iso da jama'arsa, sanin babban mutum ne. Saɓanin haka wasu manyan mutanen ne suka fito tare suke da Malam Buhari mijin Gwoggo Indo, shi ya isa da sauri inda Malam da yan'uwansa suke ya gaya musu isowar mahaifin mai son Hamida. Su Malam suka isa don taran su, sai dai me? Haɗa idon Malam da Engineer Shehu Bello zura ma juna ido suka yi kafin Engineer ya ce Abdurrashidu! Malam ma ya ce Shehu! Sai suka isa gaban juna suka rungume juna kafin Malam ya cire shi jikinsa "Ashe da ma kafin in mutu zan sake ganin ka Shehu? Hannun Engineer Malam din ya kama suka yi cikin gida har dakinsa, suka bar sauran jama'a cike da mamaki. Ƙannen Malam iyayen su Hamida su suka yi wa jama'ar da Engineer ya zo da su maraba suka ba su wurin zama. Suna zama dakin Malam ya shiga ƙwallawa Innawuro kira, ta iso a kiɗime ya nuna mata Engineer "Yau addu'ata ta amsu Innawuro da nake yi, idan Shehu na raye Allah ya haɗa duskokinmu kafin ya amshi raina." Innawuro ta fara gaida Engineer ba don ta tuna kamannin sa ba sai dai sunansa da ba zai taɓa ɓace mata ba. Sun gama gaisawa ta fita ta bar su suna labarin bayan rabuwa. Malam da Engineer abokai ne na ƙut da ƙut a garin su Adamawa, gidajen su maƙotan juna ne tare a ka haife su aka goya su, akwai wata irin shaƙuwa da ƙauna mai ban mamaki a tsakanin su. Gidan su Engineer ana karatun boko ya yin da Malam Muntari bai yadda da wannan aƙida ba, sun rungumi karatun Muhammadiya. Bayan ƙare karatun sakandiren Engineer ya samu Scholarship daga gwamnatin tarayya zuwa turai karatu, saboda hazaƙarsa. Zuwan shi na farko da ya dawo hutu ya samu abokinsa Abdurarrashidu mahaifinsa ya yi masa aure da Innawuro, dawowarsa ta biyu kuma labarai biyu ya samu marasa daɗi a rayuwarsa mutuwar mahaifinsa, da kuma tashin Malam Muntari da iyalansa, wanda ko labarin wanda ya san inda suka nufa bai samu ba. Haka ya koma inda ya fito cikin ɗinbin baƙin ciki. Shi ma ta fannin Abdurrashidu ya yi iya na shi ƙoƙarin wurin zuwa Adamawa ko Allah zai sa ya dace da zuwan Shehu amma bai dace ba, don mahaifiyar Shehu ta rasu tun yana ƙarami, matar mahaifinsa mutumniyar Funtua ce kuma ta koma garin su tun ƙare takabarta, Shehu shi da yayarsa su kaɗai ne wurin mahaifinsu yayar tashi tana aure a birnin Kano. Kuma shi ba su taba ziyartar ta da Shehu ba. Hakanan ya dangana don dole sai dai zuciyarsa kullum ba ta huta ba wurin tuna Shehu da addu'ar Allah ya haɗa fuskonkinsu. "Ya aka yi ka gane gidana bayan tsawon shekarun da na ɗauka ina neman ka? Engineer ya gyara zama kan tabarma "Danka na zo nema wa aure a gidanka." Malam ya dafe baki "Allah mai iko, kar dai yaro Abdurrashid wanda ya zo jiya da ganin farko da na yi masa ya kwanta a zuciyata na wajenka ne? ya ɗaga kai "Shi kadai Allah ya mallaka min na sanya mishi sunanka." Nan suka yi ta al'ajabi da ƙaddarar su ta zam iri daya, kowannen su ɗa guda Allah ya ba shi, duk da shi Malam Innawuro ta yiyyi ba rai, shi kuma Engineer sau daya Haj Mariya ta yi ba rai. Engineer ya kwance ma Malam tafiyar Abdurrashid, da gudun da yake yi kafin ya dawo Hamida ta suɓuce masa. Malam ya yi murmushi "A yau zan ɗaura auren ɗana da ɗiyar ɗan'uwana, in ya so ka tafi da ita." Engineer ya ce "Ma sha Allahu, haka da sauri? Ya ce "Don in tabbatar maka da farin cikin da nake ciki yau" Engineer ma murmushin ya yi "Ba ka kai ni farin ciki ba, don rana ba ta taɓa fitowa ta faɗi ba tare da na tuna ka ba, yau rana ce mai muhimmanci a gare ni." Malam ya leƙa ya ce a kira mishi yan'uwansa, da suka zo Baban Laila da ke bi masa shi kaɗai ya shaida Engineer. An zauna tare da ba su tarihin abin da ya shige kowa sai tu'ajjibi yake, kafin ya dubi yan'uwan nasa "Nawa ne sadakin Hamida? Ina nema wa ɗana aurenta a ɗaura duka tare da sauran yan'uwanta." Jin sun yi shiru ya dubi Baban Amina "Kai ne waliyyin Hamida nawa ne sadakinta? Ya ce "Dubu ɗari." Kowa ya ce Ma sha Allah, Allah ya tabbatar da alheri Engineer ya ce Bari ya fita ya shaida ma jama'ar da ya zo da su abin da kenan. Ko da ya shaida musu dakin Malam ya koma a ka bar su su kaɗai suna cigaba da ganawa, sai da aka kira sallar Azahar suka fito don zuwa masallaci da suka dawo aka fara haramar ɗaurin aure, Brigadier da jama'arsa sun ƙaraso don a Katsina suka kwana, haka fannin angon Amina gabadaya layin ya ɗinke da motoci da jama'a. Na Aina aka fara ɗaurawa daga ita ce babba sai Amina na Hamida ne ƙarshe sai sannan labari ya kai wa mata a cikin gida an daura har da Hamida kowa sai mamaki yake daga nan labarai mabanbanta suka yi ta zagayawa ana faɗin dalilin faruwar hakan. Sai dai cikin masu mamakin ban da Innawuro don Malam ya yi mata bayani a hannunta ma ya karɓi kuɗin da ya biya sadakin na shanunsa da ya saida da ƙaramar sallah. Ba wanda ya kai Gwoggo Indo murna yau yayanta sun yi aure kuma irin mazan da take so su samu suka aura masu hannu da shuni. Hamida ba ta da labari har sai da suka dawo gidan ta ji har da ita take ta sa kuka ta ƙi yin shiru har sai da aka kira Gwoggo Indo hannunta ta kama zuwa sasan su Hamidar don ba mutane suka haɗu ita da Innawuro suna rarrashin ta, har Innawuro na cewa ko ba ta son sa ne? Malam ya aiko kiran Innawuro ta tashi ta tafi cikin saurisai kuma ya aiko aje mishi da Hamida Tana tsugune gaban shi nasiha yake mata da ba su labarin abin da ya shude har ya ja ya ɗaura aurenta yau daga zuwa neman aure. Ya ba Innawuro sadakinta ya ce ta ba ta sannan aka shigo mishi da Aina da Amina aka kira duka iyayen su kowa ya yi musu nasiha aka ba kowacce sadakinta har aka gama kowa ya kama gabansa hamida ta koma ɗakin Innawuro kuka take. Bayan magrin ana ta tafiya kai Amina ɗakinta don Aina sai gobe Hamida kuma an ce sai an yi shawara. Innawuro ta tayar da Hamida da ke kwance rub da ciki ta mika mata furar da ta dama mata amsa ta yi don ba ta ga alamar wasa ba, ta sha ta miƙa mata ta ce ta ƙara ta ƙara ta ajiye kofin ƙasa, kuɗin sadakinta ta miƙo mata "Na cire dubu ashirin zan saya miki yar tinkiya a yi miki kiwo. Sauran kuma ki riƙe a hannunki idan akwai abin da za ki saya sai ki saya." Amsa ta yi ta koma ta kwanta. Sai da aka kira Innawuro kai amarya Hamida ta sulale zuwa sasan su, ta taki sa'a Innarta ba ta je kai amaryar ba don ƙaramin ɗanta da ya wuni da zazzaɓi. Gaban ta ta tsuguna ta saki kuka yi ta yi kamar ba za ta tanka mata ba karshe dai ta ce "Ki yi shiru ki yi haƙuri, 'ya mace haka ta gada. Ta jima tana mata nasiha game da zaman aure sai da Hamida ta ji ta yi shiru ta ciro kudin sadakinta ta ajiye ma uwar "Ki yi amfani da su Umma." Za ta yi magana suka ji motsi saurin juyawa ta yi daga ɓangaren Hamida Babanta ne zama ya yi shi ma nasihar ya yi ta yi mata ji ta yi kamar ta kwana wurin su amma sai Babanta ya ce ta tashi ta je ta kwanta. Da ta kwantan ta daɗe bacci bai ɗauke ta ba tana jin kamar mafarki wai yau ta zama matar aure. Walida ta bi jama'ar da suka zo wa Gwoggo Indo ta koma Kano don wani hali da ta shiga jin an ɗaura auren Hamida da Abdurrashid. Ƙarfe takwas na dare a ɗakin Hotel Abdurrashid ne ke zaune da laptop dinsa akan cinyarsa sai dai sam ya gaza cigaba da aikin da yake yi kafin labarin ɗaura mishi aure a yau ya riske shi. Dakin ba wadataccen haske TV da ke ta aiki hasken da ke fitowa cikinta shi ya haskaka dakin. Ya sa hannuwansa ya rafsa tagumi kafin ya mike ya cire rigar da ke jikinsa, ya matsa ya ƙara gudun fanka wayarsa da ta dauki ƙara ya sa ya kai idonsa inda take, Momi Binta ce mai bi ma mahaifiyarsa sai dai har ta yi ta yanke bai daga ba don ya san zancen ne dai da Aunty Karima ta kira ta gaya mishi ya dagula lissafinsa ita ma shi za ta jaddada masa. Gabadaya yau wayarsa a rufe ta wuni sai yanzu da ya dawo masaukinsa ya yi wanka shi ne ya kunna ta, kamar kuma ana jiran ya yi hakan Aunty Karima ta kira shi bakinta har kunne tana yi mishi albishir. Ya za a yi su yi masa haka? Yake ta rayawa a ransa, abokansa ma suka ga wannan yar jaririyar da ya ba shekaru sun kai sha biyu a ce ita ce matarsa ai dariya za su yi masa a bar shi yadda ya tsara, lokacin da zai dawo ta zama cikakkiyar budurwa. Har wayar ta tsinke sai kuma ga kiran Aunty Safiya haka suka yi ta kira bi da bi kamar jan carbi ba tare da ya amsa ko ɗaya ba sai da Daada ta kira ita kam ya san idan bai ɗaga ba hankalinta zai mugun tashi ne ta yi tunanin wani abu ne ya same shi. Ya kai hannu ya dauko ta sai ya yi picking ita ma murna take ta yi da wannan rana da Allah ya gwada mata ya zama cikakken mutum. Sauraren ta kawai yake har ta ƙare ta ce "Miskili ka fi mahaukaci ban haushi, ranar auren naka ma ba za ka yi magana ba? Ya ce kanshi ke ciwo. Sai kuma hankalinta ya tashi ta shiga jimami tare da jaddada mishi ya sha magani , jin yadda ta tashi hankalinta ya sa ya kwantar mata da hankali ya lallaɓa ta ta ƙyale shi ya kwanta tare da rasa tunanin da zai yi. *Book one na Shirin Allah free ne za a biya book 2 500 book one zai ƙare iya page 18 ne* *A sanya kuɗin karatu a 3195398684 Maryam nasir first bank* don nuna shaidar biya 07033400612 [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... RAYUWA Daga Marubuciyar CANJIN BA ZATA WA GARI YA WAYA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE No.12 An je Abuja an shirya wa Aina wuri, daga Daura mutum biyu suka zo sai nan mutanen arzikin Gwoggo su ma su biyu sai Laila cikon ta biyar. Ba su samu tafiya Daura ana saura sati daya ba sai ana saura kwana huɗu, har sai da Gwoggo Indo ta yi taron bikinta anan duk da da yawa za su bi ta har Daura, Walida ma ta ce za ta je tare da itan suka tafi da Laila da wasu aminan Gwoggo. Sun shiga Daura yamma liƙis, shigar su gidan gida ya ruɗe sai maraba ake musu, wasu na rafka guɗa na isowar Amarya, dakin da Gwoggo Indo ke sauka idan ta zo nan suka sauka. Hamida dai dakin Innawuro ta ruga don ta rasa wa tafi kewa tsakanin iyayenta da kannenta da Innawuro, kan ƙafafuwan Innawuro ta zube ita kuma ta shiga shafa bayanta murna suke sosai na ganin juna, har sai da Innawuro ta ce ta je Innarta ta gan ta. A gindin murhu ta samu uwar, duk da daɗin da ta ji na ganin Hamida ga girman da ta ga ta yi ta ƙara kyau da gogewa irin ta mutanen birni kallo daya ta yi mata sai ta ci gaba da hura wutar Hamida ta yi dan sansarai kafin ta furta cikin sanyin jiki "Umma." ta ɗago sai ta miƙe ta shiga daki, a cikin ta amsa gaisuwar Hamida har tana tambayar ta suna lafiya? Ba su jima ba ƙannenta suka dawo makaranta anan Hamida ta samu kyakkyawar tarba. Har mahaifinta ya dawo sai murnar ganin babbar ɗiyar ta su yake. Sai da ta ci tuwon dare ta koma wurin Innawuro, Innawuron ta ce Gadanga na ta neman ki, ko ya leƙa ki can? Ta girgiza kai "Bari in je in gan shi." Abinci ta samu yana ci, ya ce "Ai bari na yi in kammala sai in isko ki wurin Umman." ta yi murmushi tana daukar yaron Aliyun da bai wuce wata uku da haihuwa ba, kuma sai sannan Asabe ta yi haihuwar fari. ya nuna mata wuri ya ce ta zauna ta zauna da yaron a hannunta "Yaya ka manta da ni." Shi ma ya murmusa "Wane ni in manta da yar ƙanwata." Daidai nan Asabe ta fito daga ɗaki, ganin Hamida ya sa gabanta faɗuwa tare da ɗan tsawaya turus! sai da mijin ya ce "Ke kuma fa da kika ja kika tsaya? Saurin wayancewa ta yi ta ƙaraso, Hamida ta juyo cikin fara'a ta ce "Ina wuni Aunty? Ta amsa da lafiya a daƙile. Hamida ba ta da mu ba don ta riga da ta saba, wurin Yayanta ta juya wanda idan ta koma fannin Innarta kawunta ne don ƙane yake wurin Innarta, amma shi fannin Malam yake tsayawa bai komawa fannin Innawuro kanwa yake da ita. Hirar su suka cigaba da yi ba tare da sun lura da halin da Asaben take ciki ba, don hankalinta ya yi ƙololuwar tashi da ganin yadda Hamida ta zama budurwa, ga kyau ta ƙara na maƙerin yammata da ya fara ƙera ta. Gabadaya ta zama yar gayu, ita kam hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba idan ba gani ta yi an aurar da Hamida ba. Sallamar da ake daga ƙofa ya sa Hamida miƙewa don ta shaida muryar Gwoggo Indo, Aliyu ma ya mike ya ce "Gwoggo da kanki? Ta miƙo wa Hamida waya "Kiran Hamida ake." suka ƙara gaisawa da Aliyu sai ta juya. Kamar jira wayar ta shiga kuka, kan dole Hamida ta amsa kiran gaban Yayanta, Abdurrashid ne wanda rabon ta da shi tun zuwan da ya yi ya ta tafi da fushi. Gaishe shi ta yi ya ce "Me ya sa ta tafi ba ta kira shi ta gaya mishi ba? Shiru ta yi sanin hali ya sa ya katse kiran kawai. Ta sauke wayar ta yi ta dubi Aliyu da ke duban ta sai ta wayance da miƙewa "Yaya bari in mayar wa Gwoggo wayarta, daga nan in kwanta." ya ce "To ki huta gajiya ƙanwata." Ta dubi inda Asabe ke zaune tana danna wayarta ta cika ta yi dam! Ta ce "Sai da safe Aunty." ciki ciki ta amsa da "Allah ya ba mu alheri." ta fice sai dakin da Gwoggo Indo take da mutanenta ta mika mata wayar sai ta juya, Gwoggon ta biyo bayanta sai da suka kai harabar gidan suka tsaya "Kin ga Allah ya rufa mana asiri Abdurrashid ya kira, duk hidimar nan da nake tunanina na gare shi." Hamida dai ta ce Hmm. "Ina kuma ƙawar ta ki? Ta tambayi Hamida "Wai Walida? Ta bi yammatan amarya." Gwoggo ta tafa hannu "Wannan 'ya da saurin sabo take, yanzu har ta saba da ƙawayen Aminar? Hamida ta girgiza kai "Ba su ta bi ba, su Aunty Aina ta bi." ta ce "To shi kenan." ta ce "Bari in je in kwanta Gwoggo." ta ce "Allah ya tashe mu lafiya." Zaune ta samu Malam da shi da Innawuro ta ƙara gaishe shi sai ta wuce ciki don ta yi shirin bacci, Innawuro ta biyo bayanta wata yar madaidaiciyar cooler ta nuna mata "Nama ne aka kawo mana daga wurin ɗan'uwanki ɗauki ki ci." ta buɗe farfesu ne na naman ciki yanka biyu ta ci ta ta dubi Innawuro da ke tsaye har lokacin "Zan karya da shi da safe." Innawuro ta ce "Allah ya kaimu." ta cire kayan jikinta ta sauya da doguwar riga mara nauyi sai ta kwanta. Ta fara barci sama sama ta ji shigowar Innawuro ta gama kaye kayenta ta hau gadon ta kwanta Hamida na bayanta. Da safe ko da ta tashi ta yi sallah komawa ta yi ta kwanta sai takwas ta tashi, gyaran wuri ta taya Innawuro sai ta fita don gaida mutanen gidan. Ta sha mamakin sasan su Laila, an buge ginin ƙasa an mayar da shi bulo da bulo, ta samu Amir ya tashi bacci, Laila ta miƙo mata shi anan sasan ta samu ruwan zafi ta yi masa wanka, sai da ta gama shirya shi ta tafi da shi sasan su, ba ta yi mamakin daga wayewar gari har Innarta ta gyara wurin kamar ba mai yara ba. Ta tambayi ƙannenta ta ce sun wuce Islamiya, Babanta yana zaune yana shan koko da ƙosai, kwanon ya turo mata bayan ta gaishe shi "Maza ki sha." Shan ta yi tana ba Amir suna hirar su, har sai da babanta ya fita kasuwa sai ta bar sashen. Wanka ta koma wurin Innawuro ta yi ta so zuwa inda su Amina ke zaman sitting daga ita ce kusan sa'ar ta, to amma saboda Walida dole ta nufi inda su Aina suke. Daga can suka wuce wurin su Amina, a can suka wuni. An fara shagalin biki sosai ana gobe durin aure da safe misalin ƙarfe goma Hamida ta shiga wurin Aliyu don tun ran da ta zo ba ta ƙara shiga ba suna tare da Walida da ta saba da kowa ana ta hidima da ita. Sun shiga zai fita ya ce "To mu je." ya wuce suka bi shi a baya har waje inda Walida ke raɗa mata "Wannan hand some din fa waye? Murmushi ta yi tana duban sa tuna uban kishin Asabe a kansa, amma ba ta ga laifinta ba don ya Aliyun ne ya haɗe kyakkyawan bafulatani ne ga jiki ya ajiye na shaidar hutu da yake ciki. Za ta yi magana ya juyo sai ta yi shiru, sun isa inda ya ajiye motarsa bai shiga ba jingina ya yi jikinta yana tambayar Hamida har da ita za a Abujar? Ta ce "Ka ji ya Aliyu, in ban je gidan Aunty Aina ba wa zai je? Ya ce "Haka ne." "Aunty Asabe fa za ta? Ya girgiza kai "Ba inda za ta." Wata haɗaɗɗiyar mota da ta tsaya Hamida da Walida suka bi da kallo, ta daɗe tsaye ba wanda ya fito har suka cigaba da hirar su, Hamida ta shagala tana dariya har gyalenta da ta rufe kanta saboda ba ta sa dankwali ba yana zamewa ta kamo shi sai ta ga an buɗe motar, ganin wanda ya fito ya sa ta gintse dariyarta. Cikin mamaki suka dubi juna ita da Walida Abdurrashid ne, tana jin kunyar Aliyu ba za ta iya ce mishi wurin ta Abdurrashid ya zo ba, sai Walida da da ma ke neman shiga wurin Aliyu ta ce "Ya Aliyu ga fa saurayin Hamida ya zo." Ɗan murmushi ya yi "Kauce Hamida." ta matsa daga jikin kofar1)j motar ya bude ya faɗa ciki yana faɗin "Ki gaida surukin nawa." Hannun juna suka kama zuwa inda Abdurrashid yake da sallama suka karasa gabansa bai amsa ba illa saman lebensa da yake cijewa. Suka haɗa baki wurin gaishe shi Hamida ta ce "Ka zo mu shiga ciki." Ya girgiza kai "Waye wanda kuke tare? "Yayana ne." "Yayanki? Ya tambaya cikin ɗaure fuska "Yaya Aliyu ne, Baban shi Yayan babana ne, maman shi kuma ƙanwar kakata ce." Hamida ta yi mishi wannan bayanin don kare kanta daga fushin da ta ga Abdurrashid ya shiga. Ba ta san ambaton sunan Aliyu ƙara tunzura shi ya yi ba don ba zai manta wanda ta ambata a wayar da ta yi ba tana farin ciki, yau kuma ya gan su tare "Ok yi min iso wurin Malam." Ta juya Walida ta bi bgidan a ta ssmu Malam din na haramar fita, Innawuro ta gaya mawa ita kuma ta gaya wa Malam ɗin ya ce Walida ta koma ta yo mishi jagora. Walidar ta juya cikin mugun saƙe saƙe tunda ta zo ta ga gidan su Hamida ta ji ta ƙara raina masu kuma ɗan Shehu Bello ne ke son yar cikin gidan, wani ƙyashi ta ji tana wa Hamida tare da addu'ar watsewar abin. Ta samu Abdurrashid ta faɗa mishi saƙon ya bi ta a baya suka shiga gidan har ɗakin Malam. Sosai Malam ya yi masa kwarjini don cikar kamalar da yake da ita ya gaida Malam cikin girmamawa da nuna surukuta ya kuma gabatar da kanshi a mai son Hamida. Malam ya ji dadi sosai, ya ce Idan Allah ya kaimu gobe mahaifinsa zai zo nema masa auren ta. Sun daɗe suna hira a cikin hirar Malam yake ba shi labarin mahaifin Hamida ƙane ne a wurinsa, mahaifiyarta kuma mahaifiyarta yaya ce wurin mai ɗakinsa mai ɗakinsa ta dauko mahaifiyar Hamida tun tana ƙarama ta riƙe ta, da ta girma suka aurar da ita ga ƙanensa suka haifi Hamida da ƙannenta. Natsuwar da Abdurrashid ya samu da Malam ya sa shi ma ya ba shi labarin Course din da zai tafi, da kuma rashin son da yake ya bar Hamida a Kano, ya roƙi Malam da ya dawo da Hamida gida sai a nema mata wata makarantar anan, kafin ya dawo." Malam dai jinjinawa ya yi ya ce shekaru huɗu nan gaba Hamida ta ƙara su ba a kauda ita ba? Ya ce shi dai a taimaka mishi duk da hankalin shi ba kwance yake ba da barin ta a Daura idan ya tuna zai bar Hamida da dan'uwan nan nata. Malam saboda yadda ya ji yaron ya kwanta mishi ya ce zai duba. Abdurrashid ya yi ta godiya. Innawuro ta shigo suka gaisa, ta ajiye mishi fura da ta dama mishi, bayan ta fita kuma ta sa aka kira mata Asabe ta ce ta yi abinci mai kyau suna da baƙo sai dai zuwa sha biyu ya yi musu sallama bayan Gwoggo Indo da ta ji labarin zuwan shi wurin Walida ta zo sun gaisa, sai dai bai yarda ya tafi ba ya ce a kai shi ya gaishe da mahaifiyar Hamida, Walida Innawuro ta aika ta gaya mata mai son Hamida zai shigo ya gaishe ta. Walidar ta raka shi ya dubi sasan nasu na ƙasa ne da aka kewaye da kwano, ƙasan wurin a share yake tas, sai gefe guda randunan ruwa, da sallama suka shiga dakin kujera ƙwaya ɗaya ce rak sai tabarma da aka shimfida ɗakin sai ƙamshin turaren tsinke da aka kunna, akan tabarmar ya zauna daga uwar ɗakanta ta ɗan leƙo ta sha lulluɓi ban da aiken daga Innawuro yake da ba abin da zai sa ta yarda a turo mata mai son Hamida ya gaishe ta ta amsa ya ajiye kuɗi masu kauri a saman tabarmar suka fito haka Malam da Innawuro ma ajiye musu, a mazan gidan Baban Laila ne kadai bai fita ba, don akwai aikin da ba a ƙarasa ba a sashin nasu wanda Laila ce ta sa a ka gyara part din iyayen nata. Ya gaishe shi shi ma ya yi mishi alheri. *Book one na Shirin Allah free ne za a biya book 2 500 book one zai ƙare iya page 18 ne* *A sanya kuɗin karatu a 3195398684 Maryam nasir first bank* [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... Daga Marubuciyar WA GARI YA WAYA CANJIN BA ZATA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE No.14 Ƙarfe sha ɗaya na safe aka wuce da Aina zuwa gidan mijinta da ke Abuja. Bayan wucewar su kuma su Malam suka zauna shawara kan yadda za a yi da Hamida, Gwoggo Indo ta ce a ba ta ita na sati biyu ta tafi da ita Kano ta gyara ta, sai ta dawo da ita Daura inda yan'uwan Abdurrashid za su zo bikon ta. Malam ya ce sati biyu ya yi yawa, kwata kwata saura wata guda tafiyar mijinta. Ta ce to kwana goma ya ce ba laifi. Don haka ana tashi taron Gwoggo ta soma harhaɗa nasu ya nasu zuwa Azahar suka bar garin don shatar mota ta dauka. Suna isa ko gama hutawa ba su yi ba Gwoggo Indo ta fara haɗa abubuwan da Hamida ta ga tana ba Aina kuma ta san tana sai da su "Ai yanzu dole in miki shirin da duk san da ya san ki zai kiyaye, daga nan mu za mu fara juya shi, wannan biyayyar da kika ga ina mishi shi zai dawo yana min. Kunya ce ta lulluɓe Hamida jin zancen ta ko da take da shekaru sha biyar sarai ta fahimci inda zancen Gwoggo ya dosa don ba abin da ba ta sani ba a karance karancen da take ko da ta miƙo mata cup ƙin karba ta yi sai da Gwoggon ta yi da gaske ta sha kaɗan dole aka sa a fridge sai fada Gwoggo take ta ce ke da alama wannan shegen rashin son maganin naki ba za a yi abin arziƙi da ke ba. Tana cikin faɗan Nurse Saratu ta shigo ta tambayi abin da ya faru Gwoggo ta gaya mata abin da Hamida take na ƙin shan maganin gyara, ta ce sam ba ta kyauta ba ta dubi Hamida "Tashi mu je gidana ni in ba ki, Haj Indo ɗauko maganin." Gwoggo ta ɗauko ta ba ta Hamida har da ƙwalla. Kafin zuwan Hamida ba wata hulɗa tsakanin Gwoggo da Nurse Saratu illa ta idan an haɗu a yi ina kwana ina gajiya, amma tun zuwan Hamida take son ta bunu-bunu ta sayi abu ta aiko ta ce a ba Hamida hakan ya janyo shiri sosai tsakanin ta da Gwoggon. Tana gaba Hamida na bayanta har suka shiga gidan, an yi sa'a yaranta ba su nan suna gidan kakannin su tun sallah sai hutu ya ƙare za su dawo. Ajiye cup din ta yi ta shiga kitchen ɗinta sai ga ta ɗauke da wani cup din ta miƙa wa Hamida "Sha wannan." Hamida ta mika hannu ta karɓa don girman matar da take gani ta kai bakinta, nan da nan ta shanye saboda maganin ba ɗaci ba komai sai lemon tsami da aka saka wanda ta ji ya yi mata daɗi. "Maganin sanyi ne Hamida." Ta faɗi tana ƙoƙarin zama "Shi ya kamata mu maida hankalin ba yaranmu ya yin da muka zo aurar da su. Ba mu yi ta ɗura musu magungunan ƙara ni'ima ba, ba yanzu suke da buƙatar maganin ƙara ni'ima ba sai sun haihu tukuna, idan za mu aurar da ƴaƴanmu ba mu bar su sun je ma mazajen su da ainahin ni'imar da Allah ya yi musu ba mun ƙara musu da wani daɗi na musamman wanda idan ya sake su zai yi wahala su gamsar da mazajen su da ainahin ni'imar su. Ki yi ta zuwa Hamida ina ba ki magungunan sanyi kin ji? Hamida ta ɗaga mata kai. Tashi ta yi ta koma kitchen din ta fito da wani haɗin maganin ta ba hamida shi kam babu daɗi amma da yake ta iya dabara da madara ta haɗa tana sha ta ba ta madara ta ce sai kuma gobe. Da haka Hamida ta tashi ta tafi gida, Gwoggo ta yi ma Saratu waya ta ce ta sha ta ce tas ma kuwa, ta ce to ita za ta dinga aiko mawa tana ba ta. Ranar da suka yi kwana biyu da dawowa hankalin Gwoggo ya soma tashi tana ta magana Abdurrashid ba kira ba zuwa tunda aka ɗaura aure, wane irin abu ne haka? Hamida dai da ta fito wanka tana kwalliya tana jin ta ƙaramar riga ta sanya don uban zafin da ake zambaɗawa baƙa da dogon skirt komai ba ta sanya a kanta ba ta fito falo ta kwanta bisa dogon cushion da wani littafi da ta samo a gidan Saratu mai suna RANAR NAKA na marubuciya Maryam Ibrahim litee hakika ya yi mata daɗi. A daidai wannan lokaci da Gwoggo ke sababinta Abdurrashid bai daɗe da isowa daga birnin Ikko ba ya samu ƙannen mahaifiyarsa su uku sun iso kowacce daga inda take aure bisa jagorancin mahaifiyarsu Daada don taran ɗan nasu su yi masa murnar aure. Haj Binta da suke kira Momi Binta ita ke bi wa mahaifiyarsa a Abuja take aure wani ƙusan gwamnati take aure ita ma kuma babba ce a Jami'ar Abuja da ke gwagwalada, yaranta hudu duka mata. Sai mai bi mata Aunty Safiya ita kuma sarkin Katsina na lokacin take aure yaranta biyar mata uku maza biyu. Sai Aunty Zainab a Yola take kusa da mahaifiyarsu ita ma dai mijinta hamshaƙin ɗan kasuwa ne yaranta uku biyu mata sune manya sai karamin namiji. Aunty Karima ce autar su da Allah bai ba haihuwa ba. Wanka kawai ya yi ya fito wurin su yana ƙoƙarin gaishe su Daada ta ce "Ya na ga kana wani ɗaure ɗaure miskili ka fi mahaukaci ban haushi. Har ranar auren naka ma ba za ka yi fara'a ba? Ƙara shan mur ya yi ya zauna yana gaida iyayen nasa Daada ta ce "Ka ji yadda mahaifin naka ya yanke ko? Za a kawo maka amaryar taka bayan sati biyu da ɗaura aure, za a ajiye ta a sasanka ya ce yanzu zai fara maka ginin gidanka wannan filin na jikin gidan nan. Jin ya ƙi magana har ta yi shiru sai ta ce "Wai meye damuwar ne? Kai fa ka kawo yarinyar nan, an kuma ɗaura maka aure da ita ka kasa farin ciki." ya ce "Ko da na kawo ta ni na ce a ɗaura min aure yanzu? Just 15 years ne fa da yarinyar Aunty." Ya ƙare maganar yana duban Aunty Safiya wadda duk a cikin su ta fi tsananin kamanni da mahaifiyarsa don haka sai ya yi ta ganin ta kamar mahaifiyar tasa, ko gidajen su kafin ya je na kowa ya je na ta. "Haƙuri za ka yi ɗa na daga ka ga yadda abin ya zo." Ta ce mishi cikin sigar rarrashi . Amma Daada ɗaga kai ta yi "To sai me, ko shekarunta sha biyu ba ta isa aure ba? "To idan kun ɗauko ta ku kawo ta part ɗin Aunty Karima." ya ce ma Daada "Nakan dai za mu kawo ta sai in ga tsiya." Miƙewa ya yi ya ce musu zai je ya dawo, Momi Binta da ta kafe shi da ido cikin medicated glass dinta, ta dubi Aunty Zainab "Part din nasa za mu kai ta Zainab mu ga idan zai koro ta." Dariya sauran suka yi "Daada ta ce "Za ta yi maganinsa ne, ba dai mace take ba yake raina ta? Fitar Abdurrashid gidan Gwoggo Indo ya nufa, yau bai tsaya kiran waya ba kai tsaye ya shiga gidan da sallama. Gwoggon ce ta amsa sallamar don daga ita sai Hamida ne a gidan suna zaune a falo Hamida na kwance tana karatunta, Gwoggo na gyara ƙumbarta. Gwoggo ta yi mishi iznin shigowa ya shiga Hamida dai ko motsi ba ta yi ba har ya zauna ya gaida Gwoggo, sannan ta ce "Ina wuni? Ya share ta kamar bai ji ba, Gwoggo ta miƙe ta yi waje Hamida ta tashi, zaune amma ta gaza ɗaga idonta don kunyar shi da take ji wai shi ɗin yanzu mijinta ne. A hankali ta miƙe zuwa kitchen ta ɗauko ruwa ya bi ta da kallo wai wannan yar yarinyar ce matarsa, ta kawo ruwan ta koma ta zauna ya shiga tambayar ta game da karatunta za a koma meye da meye take buƙata? Ta faɗa mishi, kiran da Gwoggo ta ƙwala mata ya sa ta ficewa daga falon ta isa tana fadin "Ga ni Gwogg." "Ki yi mishi maganar kuɗaɗen gyaran amarya da na ƙawaye, kina dai ganin kudin da a ka ba Aina. Ta ɗaga mata kai ta ce shi kenan ta je Hamida ta koma jiki a mace sai dai ba ta san wane baki za ta buɗe ta yi masa maganar kuɗi ba. Ganin ya share ta sharewar ma har ta fi ta kullum ya sa ta janyo littafinta ta ci gaba da karatu. Jin motsin keys ɗinsa ya sa ta ɗaga kai sai ta ga ya miƙe ya fara tafiya ita ma ta miƙe ta bi bayansa har inda ya saba ajiye mota buɗewa ya yi ya ɗauko wani kwali sai ya miƙa mata ta amsa da godiya sai ta koma ciki jikin Gwoggo har rawa yake wurin karɓar kwalin ta buɗe, waya ce dalleliya samfurin Samsung. Gwoggo ta ce "Ita kenan ya ba ki ina kuɗin? Ta girgiza kai "Bai bani ba." Sababi sosai Gwoggo ta hau yi har Allah ya gajishe ta ta yi shiru. Abdurrashid zaune falon wani abokinsa ko ma a ce amininsa mai suna Usman a washegarin ranar da ya dawo Lagos fita za su yi amma Usman ɗin ya ishe shi da mitar tun aurensa wata uku kenan Abdurrashid bai zo ya ga amaryarsa ba. Shi ne yau ya zo wayarsa yake taɓawa amma yana hankalce da sakarcin da amaryar ta Usman ke ta zubawa angon nata, shi kuma yana aikin tarairayarta. Abin ya ishi Abdurrashid ya dubi agogonsa sai ya miƙe tsaye "Haba Malam ka zo mu tafi." Usman ɗin ya miƙe amaryar ta sha gabansa wai ba zai fita ya bar ta ba. Ya riƙe ta a jikinsa yana faman rarrashi Abdurrashid dai ficewa ya yi ya rabu da shi ya dan jima a motar sai horn yake danna masa ya fito ya same shi yana shiga motar Abdurrashid ya tashe ta, sai da suka yi nisa ya dube shi ta wutsiyar ido "Mace ta yi ta maka sangarta kana faman biye mata." Cikakken murmushi ya yi "To ai shi ne son." Abdurrashid ya jinjina kai "Sai ku yi ta fama ai." Usman zai yi magana ya ga Abdurrashid ya tsaida motar ya ciro wayarsa Gwoggo Indo ya kira ya ce ta turo mishi Hamida ƙofar gida. Sai duban ƙofar gidan Usman din ke yi har Hamida ta fito Material ne jikinta ɗinkin doguwar riga sai ɗan gyale da ta yane kanta. Abdurrashid bai buɗe mota ba ta tsaya saitin inda yake ta gaishe shi kafin ta gaishe da Usman, wata leda da ke kusa da inda yake zaune ya dauko ya mika mata "In ji Aunty ta ce in kawo miki." Ta furta "Na gode." Ganin ya tashi motar ta gane tafiya zai yi sai ta ja baya kafin ta juya ta shiga gida. Ƙin kallon Usman ya yi da ke mishi wani duba na mamaki har dai ya gaji ya ce "Amma dai Allah ba ita ba ce amaryar? (Don a gaban shi Auntyn ta bayar da saƙon ta ce ya kai wa surukarta.) "Ita ce, ka ga na huta da shan ɗawainiyar da kuke sha, yarinya ce ƙarama sai yadda na juya a ba ta." Usman ya yi dariya "Lallai kam! Kana raina mace mutumina, komai ƙanƙantar ta kana gane wace ce ita juya ka za ta yi kamar waina a tanda. Ka more wallahi kyakkyawar yarinya." Abdurrashid da ya balla mishi harara zai yi magana wayar Usman ta shiga ɓurari amaryarsa ce Jamila. Kare wayar su ya ce "Mutumina maida ni gida." Ya ce "Me ya faru? "Ba komai zan koma wurin amarya, kiran da ta yi min duk ta sukurkuta ni da kalamanta." Abdurrashid ya taɓe baki "Ba inda zan kaika Malam, zan sauka gida ka wuce da motar." Hakan a ka yi a Gate dinsu Abdurrashid ya sauka Usman ya juya da motar. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... RAYUWA Daga marubuciyar CANJIN BA ZATA WA GARI YA WAYA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE No.17 A farkon Gate ɗin Hamida na duban wurin saida abincin Gwoggonta sai ta ji kewarta mai yawa ta kamata. Suka wuce zuwa gida, yana parking sai da ta bari ya fita kafin ta buɗe ta fito. "Mu je wurin Aunty Karima su gan ki waɗannan 'yan rawar kan." Kai ta gyaɗa sai ta bi shi a baya. Yanzu ma kamar da safe zaune suka same su sai dai ba a falon da suka gan su da safe ba, gaishe su suka yi Aunty Karima ta kira mai aikinta ta ce a kawo musu abinci, kai ya girgiza ya ce A'a yanzu za su wuce a kai musu can. Daada ta ce "Sai dai kai a kai maka can, yarinyar nan a kawo mata anan a can daga kai sai ita ina za ta iya cin abinci a gabanka kana wannan tsare gidan? Tashi ka tafi abin ka miskili ka fi mahaukaci ban haushi." Kan ya kuma girgizawa yana ƙara shan mur "Zan jira ta ta gama." Ba Daada da ta kama tafa hannaye tana dariya ba iyayen ma dariyar suka so yi sai suka fuske. Ana kawo abincin Daada ta ce "Kai mata can ɗakin da yaran nan suke, tashi maza ki je ki ci ki samu ki isa sasanku ki yi wanka ki huta.". Ta miƙe ta bi bayan yarinyar tana jin Daada na ce wa Abdurrashid "Da yau za mu koma duka to Auntynka ta matsa sai a zauna a yi mata sati, ni dai ba za a yi wannan rashin hankalin da ni ba, na dai haƙura yau amma gobe idan Allah ya sa mun kai ba za ka dawo aiki ka same ni ba." "Me zai hana ke ma ki yi haƙurin satin Daada? Kai ta girgiza "A'a iyayenka dai da suka biye mata ganin tana kuka su zauna, zan tafi yaran ma za su tafi saboda makaranta." Bai yi magana ba sai sumar kansa da ya shafa yana sane da tausayin Aunty Karima da mahaifiyarta da yan'uwanta ke ji saboda rashin haihuwa ga shi kuma ita ɗin ita ce yar auta. Hamida na shiga ta samu kowa na harkarsa Hanan da Mimi mutanenta suka yo kanta sai da ta gaisa da kowa ta zauna ta zuba abincin, Hanan shiri suke za su fita duk da ba yunwa take ji ba saboda abin da suka ci a makaranta ta ji daɗin yadda Daada ta yi mata don ba ta san yadda za ta yi ta ci abinci gaban shi ba. Tana ci suna ɗan taɓa hira har su Hanan suka kammala shirin su suka fice sai ita da Mimi tana ta satar kallon Aunty Mami yar wajen Momi Binta ta farko tana haɗa kayanta tana kakkaɓin wai budurwa ce a haka amma aka sa Aunty Aina a gaba da ta yi girma don Hanan ta ce mata shekara biyu kacal Abdurrashid ya ba ta, ko da yake yar wajen Aunty Safiya ta farko ita ma babbar ce har ma ta fi Aunty Mamin girman jiki. Ta gama ta sha ruwa sanin Abdurrashid na jiranta ya sa ta ƙi tayin da suka yi mata na ta shiga ta yi wanka ta ce zai yi faɗa idan ta daɗe har falon Mimi ta rako ta yana zaune har lokacin ganin fitowarta sai ya miƙe ta yi musu sallama ta bi bayansa. Da suka isa wuri ya ba ta ta ciro key a jaka ta buɗe sai ta kauce ya shiga sannan ta shiga, kayan jikinsa ya soma cirewa aka yi knocking shi ya buɗe ya karɓo abinci, yana zaune yana ci Hamida ta rasa yadda za ta yi ta cire kayanta yana zaune, ganin ba ta da zaɓi ya sa ta dole ta miƙe zuwa gaban wardrobe akwatunan ta riƙa buɗewa har ta samu wanda Abayas suke ciki ba tare da ta tsaya zaɓe ba ta zaro wadda ke kusa hijab ɗin ta ɗaura a maimakon zane ta cire rigar har za ta zura Abayar sai ta tuna littattafan da take karantawa yadda rayuwar aure take, a gidan Gwoggo wanka ɗaya take yi da safe idan za ta tafi makaranta, idan ka ga ta ƙara wani to unguwa za su fita, a litattafan da take karantawa tana jin abubuwan da ake yi don kama zuciyar miji har da wanka da kwalliya. Daga ita sai hijab ɗin da ta ɗaura ya tsaya mata iya gwiwa ta wuce zuwa bathroom ɗin wanka ta yi sai ta yi alwalar sallar La'asar don ta yi Azahar a makaranta tawul ɗin ta ɗaura ta rufa da hijab ɗin sai ta fito har yanzu yana wurin cin abincin idonsa na kan wayarsa ganin haka ya sa ta ɗan saki jikinta ta zauna tana kwalliya a tunaninta hankalinsa bai kanta, ba ta san yana hankalce da duk motsinta ba turare ta fesa ƙarshe sai ta bar wurin zuwa bakin gado inda ta ajiye rigar da ta ciro ta ɗauka ta sanya ta a jikinta sai ta haye gado ta zaro wayarta a ƙarƙashin pillow tun daren jiya ta tura ta missed call biyar ta samu ta shiga dubawa Gwoggo Indo ce sai Aunty Aina sai ƙanwar Aunty Laila Sajida. Aunty Aina ta fara ƙoƙarin kira sai na ta kiran ya shigo ta yi picking da farin ciki "Aunty Aina kin manta da ni." Ita ma daga ji murmushin take ta ce "Ya za a yi in manta da yar ƙanwata? Na so zuwa Dinner ɗinku Brigadier ba ya nan ranar, shi ma bai samu zuwa ba." Hamida ta shagwaɓe fuska na yi kewarki sosai Aunty Aina." Ita ma ta amshe "Ni ma haka yar ƙanwata "Ina fata kina aiki da abin da kike karantawa a littattafan da kike ƙwaƙwahe mawa, ki kula da mijinki ba wai ki zauna ki yi dunkum ba." Ta saci kallon inda yake sai ta yi murmushi "Ba na yi Aunty Aina." "Yawwa to yanzu ne za ki yi amfani da abin da kike karantawa amma masu kyau, sai ki bar marasa kyan a inda kika karanta." Ta ce "To Aunty Aina." Ta ce "Bari in bar ki ki huta sai anjima. Murmushi ta kuma yi "To Aunty na gode. Ta kashe wayar daga can ɓangarenta tana jin mai jin tausayin Hamida ita dai tausayi yarinyar ke ba ta sai ta ga ba za ta iya da Abdurrashid ba yadda yake wayayye gogagge ba za ta iya dabarar da za ta kama abin ta ba. Hamida ta ajiye wayar tana jin wani farin ciki da hirar da suka yi da yar'uwar ta ta. Wani littafinta na makaranta ta dauko tana dubawa har lokacin La'asar ya yi tana kallon miƙewar Abdurrashid ya yo alwala da ya fito ƙananan kaya ya canza wanda Hamida ta ga kamar bai taɓa mata kyau irin na yau ba. Ya fesa turare duban inda take tsaye za ta kabbara sallah ya yi "Zan je masallaci idan na fito zan je wurin wani abokina, ko zan shigo sai na yi sallar Isha'i." Kai ta gyaɗa mishi tare da faɗin "A dawo lafiya." Ya fice ta kabbara sallah ta idar tana addu'a ta j yo kukan wayarta ta miƙe ta isa inda ta ajiye ta, sunan Mimi da ta gani ya sa ta fara murmushi tana kuma dauka ta ji muryarta tana cewa "Sai ki samu ki fito ai daga ya fita." Ido Hamida ta buɗe tana fiddo harshe ", Bai ce in fito ba ki zo mu yi hira don Allah." "Ki rufa min asiri ya yi mana kashedi." Allah ki zo ba yanzu zai dawo ba, ya ce sai ya yi Isha'i." A'a dai Aunty Hamida." "Don Allah ni dai ki zo." "To shi kenan na ji zan zo, amma ki buɗe min ƙofar kitchen iyakata nan idan na ji shigowar shi in sulale." Hamida ta yi murmushin jin zancenta "Na ji ki dai zo." "Tam gani nan." Ta kashe wayar sai ta zare hijab ɗin jikinta ta nufi ƙofa da wayar a hannunta, kitchen ɗin da suka shiga ya sada su da part ɗin Aunty Karima ta buɗe ta shiga sai ta buɗe waccan ƙofar ba jimawa Mimi ta iso tana shigowa ta mayar da ƙofar ta rufe ta murza key, wata drower da ke jikin window ta haye "Muna hira ina kallon parking space da na ga motar Hamma in fece." Hamida ta yi dariya tana zama kan wata kujera "Don Allah meye na wani jin tsoron Hamma? Mimi ta yi tambayar tana ɓata fuska Hamida ba ta yi magana ba sai murmushi da ta yi "Gaskiya ki canza taku, kwalliya za ki riƙa mishi wadda za ta ɗauke masa hankali ki daina nuna kina jin tsoron shi shagwaɓa za ki riƙa mishi in ya fara miki faɗan nan nasa sai ki shagwaggwaɓe masa." Hamida ta riƙe baki "Ikon Allah ke duk ina kika san wannan oh! Ta tafa hannaye tana kaɗa ido "Kin ji ki ba mace nake ba? Saboda Allah sai ya yi ta miki mazurai maganinsa za ki yi." Suka kwashe da dariya Girman jikin su ɗaya Hamida da Hanan sai dai sai dai Hanan ta bai wa Hamida shekara biyu don ita yanzu sha bakwai take. Hirar su suka cigaba da yi kamar sun shekara da sanin juna Hamida ta hilace ta har sai da suka shiga ɗakin da Abdurrashid ke ta kashedin kar a shigar masa ta taya ta ciro akwatunan aurenta suka duba kayan ciki ta ciccire waɗanda za ta yi amfani da su, wata uban sun atamfa da aka yi wa haɗaɗɗen ɗinki Mimi ta ciro mata "Ki sanya wannan da kin yi wanka kafin ya shigo." Suka gama duba kayan suka mayar bayan ta yi wa Mimin tayin ta ɗauki abin da ya burge ta ta ce Sam. Ƙofar ɗakin suka dawo Mimi ta yarfa ma Hamida ƙananun calabar da suka sauka kan dokin wuyanta calabar ta kai su har magrib don haka a guje Mimi ta fice. Hamida ta koma ɗaki ta yi sallah sai ta wuce gaban mirror tana duba kitsonta wanda ya ƙara ma fuskarta kyau, ta gyara fuskar ta fesa turare don zuciyarta da ke gaya mata kar ki wani ƙara wanka in kika biye wa masu kuɗin nan motsi kaɗan wanka sai mura ta kama ki a banza. Take ta yanke ma kanta kullum za ta riƙa wanka sau biyu idan ta yi da safe sai kuma dare kamar yadda take karantawa idan an yi wanka da daddare sai a yi wa Maigida kwalliya. Kayan da Mimi ta cire mata su ta sanya ai kam ba ƙaramin amsar ta suka yi ba har ta kasa barin gaban mirror tana ta duban kanta, ɗinkin ya zauna a jikinta ya kamata cas! Riga da skirt ne, tana riƙe da ɗankwalin a hannu Abdurrashid ya shigo ta nufi wurinsa tana masa sannu da zuwa da karɓar jakar da ya shigo da ita da mamaki yake kallon kwalliyar da ta sheƙa sosai ta yi mishi kyau har ya so ya shagala da kallon ta. Ko da ya cire kayan jikinsa daga shi sai singlet da boxers ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke gefe ɗaya yana kallon labaru a tashar CNN. Hamida dai bakin gado ta zauna har aka kawo masu abinci, suna zaune suna ci wanda shi kaɗai ke cin abin shi don idanuwansa da take ji suna kanta. Da suka kammala inda ya taso ya zauna ya umarci ta kawo mishi littattafanta na makaranta ta tashi ta dauko kusa da shi ya nuna mata ta zauna ta zauna a ɗarare tambayoyi yake mata tana mishi bayani yadda ta fahimta ta miƙa masa littafin ƙarshe ya haɗa har hannun nata ya riƙe hannun wanda ya sha ƙunshin amare ga shi fari tas ba ƙaramin kyau ya yi masa ba kome kuma ya tuna sai ya yi saurin sakin hannun daga haka mikewa ya yi ya koma kujerar da ya kwana jiya ya kwanta. Hamida cigaba ta yi da nazarin litattafan na ta har sai da ta soma hamma ita ta kashe kayan kallon ta kashe fitilar ɗakin, ganin kamar ya yi barci yau wasu riga da wando ta sanya da suka yi daidai da jikinta masu taushi ta kwanta, ba ta wani jima ba barci ya sace ta. Ya daɗe yana juye juye don barci da ya gaza ɗaukarsa bai taɓa tunanin yar yarinya kamar wannan za ta dagula tunaninsa ba, amma duk laifin su Daada ne ya roƙe su da kar su kawo mishi ita amma ba su ji ba, shi kuma ya yi ma kansa alƙawari shi da ita sai ya dawo lokacin ta zama mace sosai. Kamar an tsikare shi ya miƙe fitilar ɗakin ya kunna ɗakin ya gauraye da haske ya taka gaban gadon ya zura mata ido sai ga shi zaune wani abu ke mishi yawo a jiki, ƙirjinta da ya ɗago saman rigar ya tsura wa ido bai taɓa tunanin ta kai cikar haka ba, hannu ya kai zai taɓa ta sai kuma ya janye da sauri ya ɗora hannun kan fuskarsa don zuciyarsa da ke kwaɓarsa. Ya daɗe cikin wani kafin ya tashi ya koma wurin kwanciyarsa. Asubar farko Hamida ta farka zumbur! Ta duro gadon tuna ba ta wanke unioform ɗinta ba jiya. Motsinta ya farkar da shi don yau ya makara saboda rashin samun barci da wuri tambayar ta abin da ya tashe ta ya yi ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka, ta ce "Ba ta wanke uniform ba. Ya ce idan an kawo abinci ta bayar da unifoam ɗin a wanke mata, ta duba wardrobe ɗin akwai wasu. Da sauri ta miƙe ta je ta kama buɗe-buɗe sai ta ci sa'ar ganin su waɗanda ta ƙirga dozen ɗaya ne cif har na jiya, bakin gadon ta koma ta zauna don ya shiga toilet ɗin sai da ya fito ta shiga da ta fito ta samu yana sallah ita ma ta yi haramar sallar, yau ko barcin ba ta koma ba shirin makaranta ta hau yi bayan ta gyara gadon shi ma kuma ta hana shi sukuni da gilmawar da take ta gabansa, ya rasa me ya sa yau ta watsar da lulluɓin da take take mishi yawo a haka. Sun karya tare kafin suka fita yau bai biya da ita wurin Aunty Karima ba wani corridor ya bi da ya sada su da wani ƙatataccen falo da ya tsaya mata bayanin idan ta yi baƙi ta kawo su nan. Suka fita suka fita suka shiga mota suka bar gidan. Ran Hamida bai so ba da bai kai ta yi sallama da su Hanan ba wanda ba ta san dalilinsa na yin hakan ba. Sai da ta dawo ta samu ba su tafi ba suna dai ta shiri gaisawa kawai suka yi ya ce ta wuce su je. Suna cin abinci ta roƙe shi za ta je ta yi Daada sallama sabulan akwatinta ta ɗebo ta sanya a leda da za ta wuce ya ce me ta sanya a leda ta ce sabulu, ya ce me za ta yi da shi ta ce Daada za ta ba ganin bai kuma magana ba sai ta wuce. Da ta kai wa tsohuwar ba ƙaramin sanya mata albarka ta yi ba tana ta yaba hankalinta. Zamanta ta yi wurin su Hanan har sai da za su tafi, suna ta shiga motocin da za su kai su Airport shi ma ya fito sai da suka wuce ya ce su koma part ɗin Aunty Kariman hirar su suke tana sauraren su gara shi yana ɗan sanya baki idan sun tsoma shi har sai da aka yi kiran sallar La'asar ya ce zai fita daga can, ita kuma nan ta cigaba da zama har aka yi magrib sai Aunty Karima ta ce ta koma part dinsu ta yi wanka ta yi ma mijinta kwalliya. Hakan kuwa aka yi wankan ta yi ta sheƙa ado da wasu ubansun riga da wando daidai jikinta ba ta sa komai a kanta ba sai calabar ta da ta kwanto wuyanta.. Ta koma ta zauna tana taɓa wayarta duk da TV da ke aiki. Yau ma da ya shigo ganin ta a haka ba ƙaramin taɓa shi ya yi ba, ya dai maze kawai. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... RAYUWA Daga marubuciyar CANJIN BA ZATA WA GARI YA WAYA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE No.16 Wani dogon corridor suka tarar tafiya suka yi mai ɗan nisa kafin suka isa wasu ƙofofi guda biyu suna duban juna, dayar kitchen ne dayar dakin Abdurrashid. Tafkeken daki ne wanda aka ƙayata da kayan more rayuwa komai na dakin purple ne da ratsin fari. Ba su wani zauna ba bayan Aunty Zainab da ta kamo ta ta zaunar da ita bakin gado suka yi mata sallama, sai da ta tabbatar da tafiyar su ta ɗan yaye rufar tana duban dakin, haƙiƙa ɗakin ya tsaru kamar ma ta ce ba ta taɓa ganin ɗakin da ya yi mata kyau a ido buɗe ba sai dai a fina-finan kasashen ƙetare da suke kallo, duk da dai gabadaya gidan ma ko'ina ya haɗun. Karaf! Idonta ya shiga wani hoto na Abdurrashid da ya yi kyau ƙwarai da kayan soja yadda hoton ya fito raɗam kamar zai yi magana ya sa Hamida saurin kawar da idonta don sai ta ga kamar a zahiri yake kallonta. A wata kusurwar ta ga wani tafkeken hoton, su Aunty Karima ne ganin su su shida cif ya ba ta damar gane Daada ce da yayanta su duka, tana ƙoƙarin fidda mahaifiyar Abdurrashid a cikin su ta gano wani frame kan dressing mirror hoton wata kyakkyawar bafulatana ne wadda Hamida ta ga kamar Aunty Safiya sai tunaninta ya ba ta zai yi wahala ba mahaifiyarsa ba ce. Murɗa handle din kofar da aka yi ya sa ta saurin mayar da rufarta ta yi ruf, Abdurrashid ya shigo shi dariya ma ta ba shi ganin uban lulluɓin da ta sha har fuska ita nan dole amarya "Ina wuni." Ya tsinkayi muryarta. "Lafiya." Kawai ya ce ya wuce wurin wardrobe dinsa don tuɓe kayansa, yana kuma gama tuɓewar wata ƙofa ya nufa ya murɗa ya shige motsin ruwa da Hamida ta ji, ya ba ta tabbacin bathroom ne wanka yake, fitowarsa ɗaure da tawul ya sa Hamida da ta ƙyallaro idonta ta ƙasan mayafi tana yi masa kallo ɗaya sai ta kuma dunƙulewa. Sai da ya gama duk abin da zai yi ya miƙe bisa sopa "Ki tashi ki cire wannan uban lulluɓin ki yi shirin kwanciya, sun shirya miki kayanki a wardrobe." Ɗan mutsu-mutsu ta soma jin zancensa kafin ta miƙe kanta ƙasa ta isa gaban wardrobe din a hankwali ta buɗe, ganin kayan maza ta rufe ta ƙara buɗe wata ƙofar Allah ya taimake ta ta ga akwatunan aurenta, gefen su kuma an jera sleeping dress masu tarin yawa, ba tare da ta tsaya zaɓe ba ta zari ɗaya sai ta rufe, bathroom ɗin ta shiga duk abin nan da take Abdurrashid yana kallon ta ta ƙasan ido ya miƙe ya rage hasken fitilun dakin wayarsa ta ɗauki ƙara a kan kujerar da ya taso ya isa ya ɗauka sai ya yi picking abokinsa ne Usman. Ya ce "Wallahi kai kam ba ka da mutunci, yanzu saboda Allah kazar da na yi maka kara na saya maka sai ka bar ni da ita? Ni sai yanzu na gan ta. Bayan ka sulale ka ƙi kowa ya raka ka, yar kazar ma ka kai wa yarinya sai ka isa ziƙau ko haka ka ga ana yi. Ɗan murmushi ya yi "A ina zan ɗauko ku mu taho ɗakin na wa? Ku bari idan lokaci ya yi sai ku rako ni, amma yanzu raino zan yi." "Usman ya ke ce da dariya "Ka ji ɗan iska wa za ka rena? In za ka kwashi r.. Abdurrashid ya katse kiran sanin sharɓo ta zai yi. Hamida na shiga bathroom ɗin sai da ta kama ruwa sai ta canza kayan, wata jar riga ta dauko mai sulɓi hannunta na shimi ne tsawonta iya gwiwa, ba ta san yadda za ta yi ta fita gaban Abdurrashid a haka ba don haka mayafin kayan da ta cire ta mayar jikinta sai ta fito gadon ta haye, ta yi lamo ta gaza barci don wata fargaba da take ji, wai ita ce a daki daga ita sai namiji, sai dai da yake barci ɓarawo ba ta san sa'adda ya ci ƙarfinta ya yi awon gaba da ita. Daf da za a tayar da sallah ya farka hasken fitulun dakin ya ƙara, dakin ya gauraye da haske sai ya wuce bathroom ya ɗauro alwala ya fito ya hau pray mat ya kabbara sallah yana idarwa ya tashi zuwa gaban gadon yana murza hannuwansa Hamida da ke kwance abin ta da gani ta yi nisa cikin barcinta har yar rigar da ke jikinta ta yaye santala santalan cinyoyinta, daga ita sai dan pant, bai jima yana kallon ta ba ya fara kiran sunan ta, a hankali take amsawa ba tare da ta buɗe ido ba ko ta tashi "Ki tashi ki yi sallah." Ya faɗi yana fara tafiya don gudun makara. Hamida dai ba ta ma san yana yi ba don cikin cikin gajiya take, rabon ta da ta yi barci mai daɗi kuma isasshe tun kafin tafiyar su Daura ga laushin katifar da shimfidun da suka kara nutsar da ita. Har ya dawo sallar tana nan inda ya bar ta sosai ya tashe ta kafin ta miƙe idonta a rufe don ji take kamar sannan ta kwanta, a daddafe ta isa bathroom ya bi ta da kallo ko da ta fito a gado ta gan shi ya kwanta ya rufe jikinsa, ta ga hijab ya ajiye mata saman pray mat ta dauka sai yi sallar, tana gama yan addu'ointa ta kwanta saman pray mat wani barci mai dadi ya kuma daukarta "Ki tashi ki yi shirin makaranta." Ta tsinkayi muryarsa cikin barcinta, ba shiri ta buɗe ido "Wai wane irin barci kike, kin san dai yau za ku koma sch ko? Saurin duban shi ta yi, idon da suka haɗa ya sa ta sunkuyar da kai sai kuma ta miƙe, har ya yi wanka tawul ɗin da ke ɗaure jikinsa ya ba ta tabbacin hakan. Bathroom ta shiga sai kuma da ta shiga ta cire hijab din jikinta, tana wankan tana tunanin komawarta makaranta a yau, tare da mamakin hakan. Wasu tawul da ta gani guda biyu babba da ƙarami ta ɗaura babban daga ƙirji zuwa cinyoyi sai ta mai da hijab din ta fito, fitowarta ta yi daidai da knocking ɗin kofar ya tashi kan wata kujera da ya zauna riƙe da jarida yana sanye da boxer da farar singlet, tana jin shi da mai bugawar sai da ya gaishe shi sannan ya karɓo tiren hannunsa ya wuce ya ajiye a tebur ɗin cin abinci da ke dakin. Gaban mirror ta zauna ta yi farin ciki da ganin an shirya mata kayan kwalliya, mai ta murza sai ta shafa hoda karshe ta fesa turare, ta mike don neman sa wa idonta ya sauka kan sababbin unifoam ajiye a kan gado riga da wando ne sai hijab, ba ta san inda suka sanya mata undies ba don haka dole ta zura rigar da wandon ba tare da ta sanya komai a ƙasa ba, rigar ta kama ta fiye da nata na gida don haka ta yi saurin zura hilab din tana satar kallon inda Abdurrashid ke zaune yana gaɗa Tea "Idan kin kammala ki zo ki yi break past ko ba ki ga za ki makara ba? Ta nufi inda yake kanta a ƙasa, ta ja kujera ta zauna "Amma kin san za ki ɓata hijab dinki ko? Ya faɗi yana turo mata flet din da ya zuba mata soyayyar agada da ƙwai, kamar za ta yi kuka ta miƙe don cire hijab ɗin akan gado ta ajiye shi sai ta kasa komawa har sai da ya kira ta, muryarsa da ta ji cikin tsawa ya sa hantar cikinta kaɗawa, ta nufe shi cikin ɗaga ƙafa, ta fakaice yake duban ta ya yin da yake jin yanayinsa na canzawa har ta iso ta zauna tea da ya haɗa mata ya miƙo mata ta karɓa tare da furta kalmar godiya tean ta sha kawai ba tare da ta haɗa da komai ba don kunyar zaman shi a wurin, agogon hannunsa ya duba sai ya miƙe kayansa ya sa tana ganin ya gama fesa turare ta mike ta isa inda ta ajiye hijab dinta ta sanya mamaki ne ya dabaibaye ta da ta ga ya ciro jakar makarantarta ya mika mata, ta amsa suka bar dakin sai da ya rufe ya mika mata keyn ta sanya a jaka yana gaba tana bin shi a baya har falon mahaifinsa, Haj Mariya suka samu ita ta shiga ta shaida mishi zuwan su ya fito cikin malum malum kawai ba yar ciki. Sun gaishe shi suka mike har take jin tafiya Daddyn zai yi a wannan rana. Kitchien din da ke duban kofar dakinsa suka shiga akwai wata kofa ita suka shiga ta sada su da part ɗin Aunty Karima, sun samu iyayen sun tashi haka ma wasu daga cikin yaran "Me zan gani haka ni Shatu, ina za ka kai musu yarinya da farar safiya? Daada ta faɗi tana kama baki. "Makaranta." ya ba ta amsa yana zama kusa da ita iyayensa ya fara gaidawa yana sauraren sababin Daada "Bokon banza! Yarinya da ɗanyen amarci daga shigowa ɗakin miji jiya ka fito da ita ka kwashe ta wai za ka kai ta makaranta? Hanan ta ce "Ke dai Daada me ya ruwanki, mutum da matarsa? Daƙuwa Daada ta yi mata "Da ruwana ja'ira." Shi dai miƙewa ya yi yana musu sallama "Ai shi kenan, mai abu da abun shi kai naka ido." Ta ƙarashe faɗi tana taɓe baki iyayen su ka bi shi da addu'a Hamida ta bi bayansa, Mimi da ke maƙe bayan kujera don ganin Abdurrashid ta ɗago "Sai kin dawo amarya za mu shigo." Gabadaya ya waiwayo sai ya yafito ta da hannu ɗaya ya juya ya ci gaba da tafiyarsa, ta fito ta bi bayan su tana wara ido har sai da ya kai gaban motar da zai fita cikinta ya tsaya yana duban Mimi "Duk yar rawar kan da ta shigar min ɗaki sai ta sani, ku bari idan aka gina mata wurinta sai ku yi ta shiga." Ke kuma fa da kika tsaya? Ya ce da Hamida, cikin dan tsoro ta kama handle din ta buɗe ta shiga. Dunƙulewa ta yi da suka fara tafiya don ban da sanyin safiya hakan bai mishi ba sai da ya kunna A.C ƙamshi mai daɗi ke fita cikin motar, har kuma suka isa ba wanda ya ce uffan, kowa da abin da yake saƙawa a ransa. Yana tsaida motar a harabar makarantar ta soma murmushi don Walida da ta hango tsaye tana sauri ta fita, ta kama ƙofar sai dai ya rufe "Saurin me kike wa kika gani kike fara'a? Sai da ta sunkuyar da kai ta ce "Ƙawata ce." Bai tanka ba illa kuɗi da ya ciro a aljihun wandonsa ya ba ta ta yi mishi godiya ta sanya a sch bag ɗinta sai ta fita tana mishi addu'ar Allah ya tsare. Wurin da ta ga Walida ta nufa, suka tari juna da murmushi duk da ƙaiƙayin da Walida ta ji a zuciyarta na ƙyashin dami a kala da Hamida ta tsinta. Suka kama hannun juna zuwa wurin Assembly "Sai ga ki amarya, ina nan tsaye har na fara missing ɗinki kamar daga sama na ga isowarki." Murmushi Hamida ta yi ba ta yi magana ba. An kammala Assembly sun shiga Class ana ta gaggaisawa na kwana biyu ba a ga juna ba ba su lafa ba sai da malamin farko ya shigo. An fita break Hamida ba ta fita ba duk da ba ƙoshi ta yi ba da safe, aka aiko kiranta ta miƙe ta fita, wani soja ne ɗauke da ledoji biyu daga wurin Abdurrashid saƙon ya fito. Ta juya tana neman Walida don abin da za ta ci Walidar ta fita nema ta shaida wa Hamida ba ta karya ba, sun ci sun yi ƙat har suka yi wa na kusa da su tayi don duk yayan wani da wata ne kowa na ji da kansa. Ana tashi tare suka fito sai dai duk yadda Hamida ta yi da Walida ta zo su rage mata hanya kamar yadda suka saba ƙi ta yi, don ita ma tsoron Abdurrashid take. Sai da suka kusa isa inda motar take Walida ta ƙwace hannunta daga ruƙon gam gam da Hamida ta yi mata "Sai na zo ganin ɗaki amarya." Ta wuce suna ma juna murmushi Ta kama murfin motar ta buɗe ta shiga "Ya aiki? Ta ce mishi lokacin da ta daidaita zamanta a motar. Bai amsa ba sai da suka hau titi ya ce mata "Me yarinyar nan take ce miki da za ku rabu? Ɗan shiru ta yi gabanta na faɗuwa kafin ta furta "Ta ce za ta zo ne." "Ina za ta zo? "Wurina." Ta ba shi amsa "Kar wanda ya zo kika kai shi part ɗina, duk wanda ya zo ki kai shi part ɗin Aunty Karima." Kai ta ɗaga daga haka kuma har suka kai gida ba wanda ya kuma magana sai kiɗan da ya kunna yana fita a hankali. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... RAYUWA Daga Marubuciyar WA GARI YA WAYA CANJIN BA ZATA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE No.15 Washegari da Gwoggo ta haɗa wasu garuka na gyaran mata ta takura Hamida sai da ta sha, tana gama sha ta ɓalle da amai, kamar wasa amai ya miƙe ya ƙi tsayawa tun tana yi da ƙarfinta har jikinta ya fara saki. Hankalin Gwoggo ya yi masifar ɗagawa, hankali tashe ta kira Nurse Saratu da ta zo allurar amai ta haɗa za ta yi mata amma Hamida ta yi tsalle ta dire ta ƙi yarda, idan suka taro ta nan sai ta yi can tana yarfa hannu. Haka ta yi ta wahalar da su suna zagaye falon. Sallamar Abdurrashid ta sanya su kallon ƙofar suna amsawa Gwoggo da Nurse Saratu, Hamida da ke tsaye bayan kujera sai ta duƙa ta kuma maƙalewa kawai. Ya shigo ya zauna yana gaida su Gwoggo Nurse Saratu ta mike ganin zuwan Abdurrashid "Bari in je gida Haj Indo. "To yanzu ya za mu yi Maman Maama? Kin ga aman bai tsaya ba, Hamida ki fito a yi miki allurar nan." Sai sannan Abdurrashid ya dago kai "Me ya same ta? Ta ce "Tun ɗazu take amai." a hankali ya furta "Subhanallah me ta ci? Sai Gwoggo aka kama dabur -dabur "Ok ina allurar? Ya tambaya Nurse Saratu ta miƙa wa Gwoggo ita kuma ta matsa ta ba shi "Fito nan Hamida." Abdurrashid ya faɗi cikin dakewa, ƙara maƙalewa ta yi don idan dai ba mantawa ta yi ba yau shi ne karo na farko da ta ji ya ambaci sunanta ba. Ina take? Ya tambayi Gwoggo da hannunta ta nuna mishi inda take ya miƙe ya nufi wurin, Nurse Saratu kuma ta yi amfani da damar ta bar falon "Fito kawai." Ya ce mata ya yin da yake tsayawa a gabanta ta fito tsamo tsamo har da hawayenta don ta san ba makawa sai ta sha allura, tuna shi ɗin likita ne na Sojoji wandon Sojojin da ke jikinsa ya sa jikinta ƙara ɗaukar rawa. "Mu je." Ya ƙara ba ta umarni ta wuce zuwa inda Gwoggo Indo take, cikin turo baki ta ce "Ni zan sha ruwa." Gwoggo ta wuce da sauri ta kawo mata, tana gama sha ta fara yunƙurin amai da gudu ta yi dakinsu a toilet sai da ta dawo da ruwan ta fito Gwoggo na riƙe da ita suka koma falon ya ce "Zan yi mata allurar aman yanzu, sai mu je Hospital in duba ta." Hawaye Hamida ta fara ganin yana nufo ta ita kuma Gwoggo ganin ya nufo Hamidan sai ta yi waje. Yana zuwa kuma kamata ya yi zuwa kujera, ya zauna sai ya ɗora ta a cinyarsa jikinta sai rawa yake wai ita ce yau a kan cinyar Soja, ita gabadaya ma wani namiji bai taɓa mata haka ba. Hannuwansa ya zagayo kan cikinta "Me kika ci ya sa ki amai? Ya faɗa kamar mai raɗa saitin kunnenta, wani yar ta ji har cikin cikinta. "Maganin sanyi Gwoggo ta ba ni." ta samu kanta tana ba shi amsa. "Me ya sa ba ki son allura? Ya faɗa cikin wata murya da har ta fi ta farko sa ta shiga wani hali. Hannunsa da ta ji ya sa cikin jikinta yana shafa bayanta ya sa ta ƙoƙarin tashi ta gudu ya riƙe ta riƙo mai kyau, tilas ta sallama ba ta ankara ba sai dai ta ji allurar ya tsira mata. Ga mamakinta ba ta ji zafi ba, ya sa hannunsa yana liliya mata wurin ai tana jin ya sassauta riƙon da ya yi mata sai ta tashi ta gudu kujerar nesa da shi ta rufe fuska. Ya daɗe zaune yana taɓa wayarsa kafin ya miƙe ya fita ta bi bayansa a gindin bishiya suka ga Gwoggo, ta ce "Har ka fito, ba za ku Asibitin ba? Ya ce "In sha Allah ma zai tsaya, idan kuma ta ƙara sai a kira ni." Ya wuce Gwoggo na mishi a sauka lafiya. Hamida ƙin bin sa ta yi don kunyar cinyarsa da ya sa ta. ********** Wannan kenan. Abdurrashid ya ci gaba da zuwa wurin Hamida, duk kuma bayan kwana biyu yake zuwa. Family ɗinsa shirye-shirye kawai suke na bikin tarewar, ba wanda ya koma ta kan angon da ya ƙi bayar da haɗin kai, don shi kam bai shirya ma a ga yar ƙaramar yarinyar nan kamar Hamida a ce ita ya aura, sai tsiya Daada ke mishi ta ce "Ita san da aka yi mata aure shekaru sha biyu ne da ita, amma ta yi biyun hamida a girma, dan dai hamida ba ta da ƙiba ne shi ya sa yake raina girmanta. Duk kuma ƙin shi akwai Dinner da mahaifinsa ya shirya za a yi a daren da aka kawo Hamida ɗakinta, manyan mutane ne za su halarta saboda rashin sanar da su ɗaurin aure. ******"*" Ana gobe za su wuce Daura idan kuma sun je kwana daya za su yi a juyo da ita Kano, Abdurrashid ya iso da yammaci. Bai shiga ba da wayarsa ya yi amfani ya kira ta. Ba ta cikin shiri don aiki take taya masu aikin Gwoggo tuni suka koma abincin sayarwar su wanda Gwoggo Indo ta ce ba ta ga dalilin zama har sai Hamida ta tare kafin ta koma sana'arta ba, daga Abdurrashid ba ɓanɓaruwa yake ba. Cikin sauri Hamida ta shiga ta watsa ruwa wata doguwar riga ta zura ta yane kanta da gyalen rigar sai ta fita, yana cikin mota bai fito ba ta san miskilancin na kai kenan indai ya ƙi fitowa, ta zagaya ta buɗe motar ta shiga ta gaishe shi "Fita za mu yi, zan buɗe miki account saboda tafiyar da zan yi in bar ki zan dinga sanya miki abin da za ki yi amfaninki da shi." Ta ɗaga mishi kai. Daga haka motar ya tada suka bar wurin, har kuma suka isa bankin babu wanda ya yi ko tari a cikin su. Ba wani ɓata lokaci aka gama komai, muhimmin abin da ya sa ya zo da ita ma ATM da za a yi mata don an riga da an yi mata komai. Da suka fito ji ta yi kamar ta roƙe shi ya kai ta gidan su Walida duk da sanin da ta yi Walidar na nan tafe da yamma za ta kwana gidansu washegari su wuce Daura. Sai dai suna rabuwa da Abdurrashid wanda yana sauke ta ya wuce Walidar ta samu zaune ta iso, suka shiga murnar ganin juna Walida ta ce "Ya za a yi da ƙawayena da na gayyata masu son zuwa Daura? Daidai nan Gwoggo ta shigo, ta cafe "Ai ba za ta iya mishi magana ba, shi kuma ba taɓuwa yake ba." Nan Gwoggo ta yi ta surfa uban faɗa kan rashin ba Hamida komai na game da biki da Abdurrashid bai yi ba. Hamida ba ta ji daɗi ba saboda Walida na zaune amma ba yadda ta iya. ******** Abdurrashid shi ya bayar da motar da ta kai su Daura su biyar. Daga Hamida da walida sai Gwoggo da wata aminiyarta sai Laila. Taran biki suka samu a na yi, yan'uwa duk sun iso dan su iyalan gidan ma kawai Malam, suka ɗauki hanya. Sun kusa shiga Kano Aunty Zainab wadda ita ta wakilci sauran yan'uwanta zuwa Daura, ta ciro wayarta jin shigowar saƙo *Ka da ku kai yarinyar nan part ɗina, jama'a za su ɓata min wuri Aunty na roƙe ki.* Saƙon da ta gani kenan daga Abdurrashid ɗan murmushi ta yi "Ja'iri za ka shiga hannu." Ta faɗi a hankali. ****"** Wani keɓaɓɓen wuri cikin part ɗin Aunty Karima aka sauki amarya da yan'uwanta. Sai da suka ci abinci suka yi sallah a ka zo a ka tafi da Hamida don shirya ta zuwa wurin Dinner. Yayansu Momi Binta yammata su suka zagaye Hamida da ana yi mata make-up, su kuma suka zame mata ƙawaye a wurin don Abdurrashid ya hana ta faɗi ma kawayenta na makaranta bai so idan ta koma makaranta a gane ita matar aure ce, da ma ita ba faɗi za ta yi ba Walida ce mai giggiwar faɗin. Duk kuma abin nan da ake Walida na tare da ita Abdurrashid ma ba da son sa ba abokansa masu tarin yawa sun zo bisa jagorancin Usman wanda shi ya gayyace su. Manya daga ko'ina tun daga Nigeria har ma da wasu ƙasashen sun hallara. Da aka dawo Dinner ma yaran su Aunty Safiyan ba su bar Hamida ta kwana cikin danginta ba janye ta suka yi duk da su ɗin ba tsararrakinta ba ne, mutum biyu ne suke kai ɗaya. Washegari aka yi mata buɗar kai irin na su na mutanen Yola yan Daura sun ga ruwan arziƙi wanda aka tura wa Hamida da mahaifiyarta duk da su ma ɗin tushen su yolan ne hausawa suka ce kowa ya bar gida gida ya bar shi. Su yanzu al'adun Katsinawa suke yi. Idan wannan ta zo ta bayar da nata wannan idan ta fito sai ta bada sama da haka. Amarya ta yi kyau har ta gaji, ana tashi yan Daura suka wuce gidan Gwoggo Indo bayan sun sha kyaututtuka daga Engineer da kuma atamfofi da aka raba da dardumai ban da ƙananan abubuwa. Walida ma ana yin sallar magarib ta yi wa Hamida sallama ita kuma ta miƙa mata wasu kuɗi da ta amsa hannun Gwoggo Indo tare da yi mata godiya. ********"" Ta idar da sallar Isha'i a tafkeken dakin da yammatan suke Aunty Karima ta leƙo ta yafuto ta da hannu Mimi ɗiyar Aunty Zainab ta farko da ke kusa da Hamida tana danna wayarta ta ce "Pls Aunty kar ki ɗauke mana ita." Yarinyar Momi Binta ta uku da ma su biyun su ne tsararrakinta mai suna Hanan ta miƙe tana haɗa hannaye "Pls kar ki ɗauke mana ita Aunty." Aunty Karima ta kama baki "Kai ku ji mun yara, dakin mijinta za a kai ta idan kuma a gaya wa Hamman naku kun ce a bar muku ita shi kenan." A tare suka ɗaga hannaye "A'a ba mu ce ba." Dan ba ƙaramin shakkarsa suke ba, ko da ba komai yake musu ba sai dan rashin sakin fuskarsa. Ta bi bayan Aunty Karima har bedroom din Auntyn, ta wuce bathroom ta haɗa mata ruwan wanka da kanta ta fita ta bar ta wankan ta yi ta fito tana jin daddaɗan ƙamshin da take yi. Tsaye jikin madubi ta samu Aunty Karimar ta ba ta wuri ta ce ta zauna da taimakon ta ta zuba kwalliya , wasu irin kaya da Hamida ta rasa mene ne ta ba ta ta sanya, doguwar riga ce da lulluɓinta ta kama mata hannu suka bar dakin, don ta rufe har fuskarta, wani falo suka shiga wanda Daada ke zaune da ƴayanta, ta zaunar da ita gaban Daada nasiha sosai Daadar ta yi mata game da zaman aure, maganar mahaifiyar Abdurrashid da ta yi dukkan su sai da suka yi ƙwalla, a ƙarshe ta ce su kai ta wurin mahaifin Abdurrashid da Haj Mariya kafin su miƙa ta ɗakinta, Aunty Karima da Aunty Zainab su manyan suka ce su je su raka ta. Sam barka da suka fara kai ta sasan maigidan nan suka tarar da Haj Mariya har ma da yayarsa Haj Gambo, bayan ƙare gaisuwa fatan alheri kowannen su ya yi suka kuma ba da kuɗaɗen da ake ba amarya idan an kai ta wurin dangin miji. Sai suka miƙa ta sasan Abdurrashid ta ƙofar da za ta sa da ka da sasan mahaifin nasa. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH.... RAYUWA No.18 DAGA MaRuBuCiYaR WA GARI YA WAYA CANJIN BA ZATA RANAR NAKA HATTARA MARYAM LITEE Ranar juma'a da aka tashi makaranta turowa ya yi aka kai ta gida don yana da aiki. Sai da ta canza kaya ta ci abinci Aunty Karima ta kira ta a waya ta ce ta zo ta yi baƙuwa, ta isa sasan sai Gwoggonta ta gani daɗi ne ya lulluɓe ta ta zauna kusa da ita tana gaishe ta, ita ma cikin farin cikin take amsawa yadda ta ga Hamida. Hamida ta ce ta zo su je wurinta, falon da ya nuna mata ya ce za ta iya kai baƙinta ta kai ta, ta buɗe fridge ta samu akwai lemo da ruwa ta ɗauko ta ajiye gaban Gwoggon. Hira suke a hankali Gwoggo tana ba ta labarin jarin ta ya yi ƙasa saboda hidimar bikin nan, hakanan dai take rurrumawa Hamida ta miƙe ta ce tana zuwa ɗakinsu ta koma ta ɗauko hand bag ɗinta ta dawo wurin Gwoggonta. Ta tura hannunta cikin jakar ta ciro duka kuɗin da ke ciki wanda yake ba ta ba tare da ta ƙirga ba ta miƙa wa Gwoggo su duka. Sai da ta ƙirga ta ce "Waɗannan fa ba ta ko numfasa ba ta ce "Ba ni yake kullum idan ya sauke ni makaranta." Gwoggo ta taɓe baki " Mai hali dai bai fasa halinsa, duk wannan uban arziƙin ji abin da aka samu a wurin ki, shi dai na rasa abin da ya sa yake ƙanƙamo. Hamida dai ba ta ce komai ba duk da ta ji ba daɗi ranta ya sosu da yadda ta aibata shi. Wata kwalba Gwoggo ta ciro cikin jakarta sauyoyi ne a ciki sai aka zuba ruwan turare "Kin ga wannan Hamida duk dare in za ki kwanta ki ɗan tsiyaya a hannunki ki yi Bismillah ki shafa wa fuskarki, zuwa ƙirjinki har zuwa mararki, namiji duk taurin ransa ya yi amfani da ke sai ya yi ladab, sati mai zuwa zan zo in ƙarɓi kuɗinsa. Ban da ba ki son na sha an kawo kala daban daban masu kyau kina amfani da su kwana nawa za ki kama shi a hannunki, kina dai ganin yan'uwanki dubi dai Laila yadda Ahmad ya zama kamar bawanta, ba kuma boka ba Malam, kayan nan dai na mata nake kai mata duba ki ga yadda sasan su ya zama daban a gidanmu. Aina da aka kai jiya jiya da ta ce in turo Acc no dubu dari biyu ta sanyo min, amma ke Hamida duk uban wannan arziki sai tarkacen canjin makaranta. Ta ciro wani garin magani a farar leda "Ki daure Hamida ki sha wannan da madara yanzu a gabana. Fuska Hamida ta ɓata tuna maganar Nurse Saratu ta ce "Ba na sallah Gwoggo. Cikin rashin jin daɗi Gwoggo ta miƙo mata "Ki tabbatar kin sha kina gamawa." Ta gyaɗa mata kai ta je ta ɓoye ta dawo Gwoggo ta ce za ta tafi suka fito tare tana mata rakiya, hango Mami Haj Mariya tsaye da wata mata ya sa su nufar inda suke, sai da Gwoggo ta gama gaishe su Hamida ma ta bi sahu sai suka wuce har gate ta raka Gwoggon nata ta juyo za ta gifta su Mami ta yafuto ta ta isa ta tsaya "Ba ki taɓa zuwa kin gaishe ni ba, ko da yake wannan miskilin banzan ai ba zai ce ki zo ki gaishe ni ba." Ta taɓe baki Hamida dai ta tsaya shiru sai matar da suke tare ta ce "Tafi yarinya." Hamida ta juya, Haj Mariya ta kuma taɓe baki "Ai duk shegen jin kansa ya ɗauko inda za a bi da shi." Waccan matar ta ce "Me ya sa kika ce haka? Ta ce "To mariƙiyarta waccan da ta fita ba ƙaramar hatsabibiya ba ce wurin sanin maganin mata masu kyau, duk inda zan zaga in saya sai na dawo wurin ta don nata ne kawai zan yi amfani da shi in rikita Alh, ga shi ta yi kitimirmirar shigo da diyarta gidan nan, dole ina ji ina gani zan haƙura da maganinta." Waccan ta ce da ba ki yi saurin sarewa ba ki sa a yi miki bincike inda take sarowa ki fantsama can, don yanzu da ma ba za ki haɗa sirri da su ba." Ta ce "Kin kawo shawara zan gwada yin hakan." Da Hamida ta koma ɗaki Innawuro ta kira a waya, har Innarta sai da Innawuro ta tilasta ma wa ta karɓi wayar, Hamida ta gaishe ta. Tana gamawa yau wanka ta yi da wuri ta yi kwalliya da wasu riga da skirt da suka yi matuƙar karɓarta na cikin kayan aurenta, ta sanya wani siririn gyale ta rufe kanta ta zura takalma ta fita da niyyar zuwa part ɗin Aunty Karima. Fitowarta ta hango Abdurrashid da abokinsa Usman waɗanda suka ba ta baya ta wuce abin ta sai dai tana zama ta dai gaida su Aunty Zainab da ba su daɗe da shigowa gidan ba kiran Abdurrashid ya shigo wayarta tana ɗagawa faɗa ya kama mata wa ya ce ta fita yana kashe wayar ta miƙe tsam Aunty Safiya ta ce "Ina kuma za ki daga shigowa? Murmushi ta yi Momi Binta ta ce "Yi zaman ki Daugter ga kilishi nan da Zainab ta sanya aka kawo ki ci." Ta sunkuyar da kai "Shi ya ce in dawo." Ƙwafa ta yi tana cije baki "Ban da tafiya zai yi da sai na saɓa wa ja'irin yaron nan, ya bar yarinya ta shiga mutane sai ya ce kullum tana can ɗaka ƙunshe ba sai ya bar ta da Karima ba ta samu abokiyar hira ita ma." Mai aikin Aunty Karima ta kira ta ce ta ɗebo kilishi ta kawo, da ta dawo aka ba Hamida ta yi godiya ta fita. Yanzun ma tsayen ta gifta su shi da abokin nasa Usman ya yi dariya "Ka ga abokina ina tausaya ma idan yarinyar nan ta ƙara girma, don ba ƙaramin juya ka za ta yi ba." Ya harare shi "Sai ka ce wani kai Allah ya kyauta". Ya ce "Shi kenan ai muna nan, Allah ya nuna mana, bari in barka ka bar yarinya ita kaɗai." Suka yi musabaha ya faɗa motarsa Abdurrashid ya shiga ciki zaune ya same ta riƙe da wayarta bai amsa sannu da zuwan da take masa ba illa tambayar ta da ya yi ""Me kike karantawa a waya ne da ba ki gajiya da riƙe ta? Ba ta amsa ba illa ƙara sunkuyar da kai da ta yi "Ba ni wayar.". Ya ce yana kallon ta, ta tashi a hankali don idonsa da ke kanta sai ta miƙa masa a tsayen yake dubawa ganin novel ne take karantawa ya dago "Me ya sa ba ki dagewa wurin duba takardun ki na Sch sai ki dage kan wannan shiriritar? Ta ce "Ina dubawa.". Kai ya kaɗa ya wuce ya cire kayansa. Yau bai yarda sun zauna wuri guda ba don yadda shigar ta ta rikita masa lissafi ya ce su je part ɗin Aunty Karima su yi ma su Aunty Safiya hira. Suna can har sai da Aunty Zainab ta ga Hamida ta kwantar da kanta a hannun kujera ta ce "Kai yarinyar nan ta kwanta Abdurrashid." Da suka kwanta idanuwansa ya rufe da ƙarfi a fatan da yake barci ya ɗauke shi Hamida ce ta tsaya shiga Toilet bayan ta cire kayan jikinta, ta gama abin da za ta yi har za ta fito ƙafarta ta zame ta daki ƙofa sai ta faɗa kan ƙafar wani irin zafi ya ratsa ƙwaƙwalwarta ta fasa kuka lokacin da ta yi ƙoƙarin taka ƙafar ta wuce, sai hawaye wasu na korar wasu. Abdurrashid da tun fasa kukanta ya buɗe ido ya mike da azama ya yi Toilet ɗin yana turawa ya gan ta inda ta faɗi tana kuka "Me ya same ki? Ya tambaye ta "Zamewa na yi. Ta ba shi amsa ya miƙo mata hannunsa "Tashi to mu je." "Ba zan iya takawa ba ta faɗi tana cigaba da hawayen hannu ya sa ya sunkuce ta zanen da ta ɗaura ya idasa kwancewa ya faɗi ya bar ta daga ita sai fant da bra haka ya kai ta bisa gado yana soma jan ƙafar ba tare da ya lura da hannayenta da ta sanya gabadaya ta kare ƙirjinta duk da raɗaɗin da ke shigar ta tana hawaye waige waige take inda za ta samu abin da za ta rufe jikinta, sai da ya gama jan ƙafar tana mishi kuka ya shafa mata wani tube mai zafi da ta ji kamar ta saki fitsari. Ya tashi ya ɗauko mata riga mara nauyi ya ba ta ta sanya ya ba ta magani ta haɗiya sai ta kwanta lamo tana sauraron raɗaɗin da ƙafar ke yi mata gadon ta ga ya hau ya kwanta a bayanta barci ta samu ya ɗauke ta wanda ba ta farka ba sai asuba lokacin har ya fita sallar Asuba, sai dai ta taka ƙafa ta ce ba ta san wannan ba, idon ƙafar ya kumbura suntum, ta sauka ta fara rarrafe sai ga shi ya shigo cak ya ɗaga ta sai Toilet ya ajiye ta ya juya sai ya ja mata ƙofa. Ta gama abin da za ta yi tana tunanin mafita sai ta ji daga jikin ƙofa yana faɗin "Kin gama? Ta ce "I." Ya shigo ya kuma surar ta sai kan fray mat ya zaunar da ita, a zaunen ta yi sallah tana gama addu'ointa ta cusa kanta cikin gwiwoyinta barci ta ji tana ji nan ma sai ji ta yi an yi sama da ita sai kan gado ya ajiye ta ta gyara ta kwanta ya shafa mata magani sai da ya gama raɗaɗinsa ta shiga barci barci sosai ta yi sai goma ta farka Abdurrashid da ke kwance bayanta bai iya barcin ba, sai juye juye duk da yau ɗin weekend ne a ranakun yake samu ya yi barcin safe tana tashi zaune ya ce "Bari in kai ki ki yi wanka." Ta ɗaga mishi kai sai da ya ajiye ta ya ba ta wuri sai da ta gama wankan ta rasa yadda za ta taka ta ɗauko tawul sai kawai ta yanke ta mayar da rigar da ta cire, ta sanya kenan ya shigo kallo ɗaya ya yi mata ya ƙara faɗawa wani yanayi, bayan rigar kasantuwar ta ba mai kauri ba lemar jikinta ta sa ta manne mata sai ta fidda komai ya dai fito da ita ya zaunar da ita ta yi kwalliya riga ya ciro mata kalarta blue black an matse ta daga ƙirji sai aka ɗan buɗa ta daga ƙasa tsawonta iya gwiwa miƙe ƙafar ta yi ta kwantar da kanta jikin gadon har nan ya kawo mata abin kari ta karya kiran da aka yi mishi a waya ya sa ta bar kallon TV da take yi ta maida hankalinta kan abin da yake cewa a yadda ta fahimta wata daga cikin Aunty nan sa ce take tambayar abin da ya hana su fitowa har yanzu sai yake ba ta labarin faɗuwar da Hamida ta yi da raunin da ta samu a ƙafa. Ya sauke wayar ya dube ta "Su Aunty za su shigo su duba ki." Kai ta ɗaga tare da lumshe idonta da za ta iya da ta ce ya ɗauko mata wasu kayan amma su zo su same ta da wannan yar riga kanta ma a buɗe sai calabar ta da ta kwanta kan dokin wuyanta. An yi knocking daga inda yake zaune yana taɓa laptop dinsa ya amsa sai kuma ya miƙe suka shigo su dukkan su ne ya gaishe su daga inda yake suka zauna Hamida ta gaishe su suka tambaye ta ƙafa ta ce da sauƙi kaɗan suka zauna suka yi mata fatan samun sauƙi suka fita Har dare a ranar yana tare da ita ba inda ya je ko magungunan da ya ba ta waya ya kira aka kawo mishi. Zuwa daren kuma ƙafar ta ɗan saki tana taka ta ta hanyar ɗangyashi, ba ta kwanta da wuri ba don wunin da ta yi kwance har ya zo ya kwanta kan gadon tana kallon shi, chart suke da Hanan da Mimi sai kuma grp na ajin su. Har dai ta ji ta soma jin barci, wayar ta kashe bayan ta kashe datar ta gyara kwanciya ba ta da wuyar barci don haka nan da nan ya yi awon gaba da ita. Daɗin barci ya ɗauki Hamida ya ɗora kan jikin Abdurrashid wanda ya samu ya tarairayi kansa ya samu barci ya ɗauke shi, jin ƙirjinta da ya yi a jikinsa ya haifar masa da sake shiga wani hali, hannunsa ya kai ya cire ta jikinsa amma abin da yake ji ya kasa ba shi ƙwarin gwiwar yin hakan, yar rigar jikinta ya cire Hamida da kamar a mafarki ta riƙa ji ana shafa ta ta buɗe ido gane abin da ke faruwa ya sa ta saurin wartsakewa tana neman ƙwatar kanta, ƙanƙame ta ya yi yana ba ta haƙuri cikin ƙanƙanen lokaci ya mayar da komai na ta, dogon lokaci ya ɗauka yana abu ɗaya wanda Hamida ta yi kuka iya son ranta ba tare da ya tausaya mata ba. Gefe ɗaya ya koma yana mayar da numfashi Hamida ta ci gaba da kukanta har barci ya sace ta sai kuma ya mirgino ya haɗe jikinsu ƙarawar da ya yi ya sa ta ci gaba da kukan, a taƙaice dai bai bar su sun rintsa ba sai daf da shiga masallaci ya samu waya ana nemansa daga wurin aikinsa an kawo Sojoji da suka yi karon batta da yan bindiga. Gudu gudu ya tsallake ta ya faɗa bathroom ya tsarkake jikinsa ya fito ya shirya inda take kwance ya zo ya ranƙwafa "Hamida! Hamida! Sai ta buɗe idanuwanta da suka kaɗa suka yi jawur suka kumbura. "Ki yi haƙuri ki shiga ruwan zafi neman gaugawa ake min a wurin aikina, ina gama abin da ya kai ni zan dawo in taimaka miki." Kai ta ɗaga mishi ya fice cikin matuƙar sauri ta maida idanuwanta ta rufe tana jin yadda ko'ina na jikinta ke ciwo. Tana nan kwance har sai da ta ji an tayar da sallah a masallacin da ke cikin Estate din ta yi yunƙurin tashi, a daddafe ta kai kanta bathroom ruwa mai zafi ta tara da dabara da dauriyar da ta sanya ta shiga ruwan tana runtse ido, ga hawaye na gudu kan kuncinta sai da ta ji ya soma sanyi ta zubar ta sake wani, wankan tsarki ta yi sai ta yi wanka da ruwa mai zafi, sosai ta ji dama lokacin da ta fito doguwar riga har ƙasa ta samo ta sanya ta yi sallah ta lallaɓa za ta hau gado ta kwanta ta hango inda jini ya ɓata zanen gadon dole ta yaye shi ta kai shi bathroom ta sanya a laudry ta dawo kamar ta duba wani ta shimfiɗa sarawar da kanta ke yi wanda bai rasa nasaba da kukan da ta sha ga zazzaɓi da take ji zai rufe ta ya sa kawai ta kwanta, barci ya yi awon gaba da ita. *Alhamdulillahii nan na kawo karshen littafi na daya mai son karanta littafi na biyu sai ya sanya kuɗin karatu a* 3195398684 Maryam *Nasir first bank don nuna shaidar biya* 07033400612 Ma'assalam [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH RAYUWA No.22 MARYAM LITEE Kwana uku da yin haihuwar da daddare Hamida na ɗakinta tana karatun makaranta don koyaushe suka yi waya da Abdurrashid ba abin da yake jaddada mata irin ta kula da karatunta. Don haka ta ƙara dagewa ta haƙura da karatun littattafan hausa da take sai kaɗan shi ma saboda abin ya shiga jikinta, ba abin da ke ranta irin ta yi abin da za ta burge Abdurrashid wanda sai da ya tafi ta gane ba ƙaramin so take mishi ba tana cikin kewar shi har lokacin. Wayarta ta ɗauki ƙara ta ɗaga da sallama Gwoggo ce sai ta soma gaishe ta da suka ƙare gaisuwar Gwoggon ta ce "Abin da ya sa na kira ki game da gudummuwar Laila ne, Aina ta turo da na ta ke me za ki bayar? Hamida ta ɗan yi shiru kafin ta ce "Zan duba kuɗaɗen da Abba ke ba ni na makaranta abin da na samu zan faɗa miki Gwoggo." Waye Abba? Gwoggo ta tambaya Ba ta ko numfasa ba ta ce "Baban shi. Gwoggo ta ce "Shi kenan sai na ji ki." Hamida ta ce "Sai da safe." Ta katse kiran ta ɗauko jakar makarantar ta ciro kudaden ciki ta haɗe su wuri daya ta ƙirga, kamar ta kira Gwoggon ta shaida mata abin da ta samu sai ta yanke ta bari sai da safe. Da safen kuma da ta tashi tana sauri ta wuce makaranta ba ta samu kiran Gwoggon ba har sai da ta dawo tana ɗaki Aunty Karima ta shigo wata ƙatuwar leda mai ɗauke da tambarin wani store ta miƙa mata sai bundle na dubu daya, ta ce "Waɗannan zannuwan ki kai wa yar'uwarki mai jego. Kudin kuma Daddy ne ya ce a ba ki ki yi hidimar sunan." Ta karɓa tare da godiya mai yawa Daddyn ma ta je ta yi mishi godiyar. Sai da Aunty Karima ta fita ta buɗe ledar manyan Atamfofi ne guda biyu sai less asalin irin waɗanda Auntyn ke ɗaurawa ************ Ranar suna sai da suka tashi daga makaranta da ta dawo ta yi shirin zuwa gidan sunan. Baba Adamu ya kai ta ba ƙaramin farin ciki ta yi ba da ganin yan Daura. Ƙarin jin daɗinta ba har da Innawuro sai dai ba mamanta. Gwoggo Indo ta ba kayan mai jegon, da suka keɓe kuma ta ba Innawuro kuɗaɗen da Baban Abdurrashid ya ba ta ta ce su raba su hudu da babanta da Mamanta da Innawuron da Malam. Innawuro ƙin karɓa ta yi sai da ta yi ta mata magiya sai ta karbi rabi ta ce ta riƙa adana duk abin da ta samu. Sun sha hotuna sosai Walida ma ta zo mata suna Aina ma ta zo sai dai ba ta kwana ba ranar ta juya. Hamida kam sai da Innawuro ta matsa mata ta zo ta tafi gida ta ce direba zai zo ƙarfe biyar. Aunty Karima ta kira Hamida ta waya ta ce in za ta taho ta zo tare da Innawuro don sun yi waya da Malam ya ce mishi har da ita aka zo. Haka aka yi taren suka tafi murna kamar ta kashe Hamida suka kwana tare, ga shi washegarin sunan babu makaranta suka wuni da Innawuro wadda Daddy ya hana komawa gidan Gwoggo Indo, don sai washegari za su koma. Sauran yan sunan sun l) /zo da yamma sun tafi kenan kiran Abdurrashid ya shigo wayarta wanda tana gaishe shi ya soma tambayarta hoton ita da su wa ta ɗaura akan Dp ta? Ta ce "Yan'uwana ne yan Daura. Ya ce "Yaushe suka yi hoton ta ce "Jiya da suka zo suna." Cikin matuƙar mamaki ya ce "Sunan wa? Ta ce "Aunty Laila ce ta haihu." Ya ce "Kuma har kika fita kika je suna ban sani ba? Ɗan shiru ta yi kafin ta ce "Aunty ta ce "In je." Cikin yar hasala ya ce "Aunty ke aurenki ko da ba za ki gaya min ba ya yi kyau." Ƙit ya katse kiran. Rasa yadda za ta yi ta yi sai ta ajiye wayar cikin sanyin jiki ta fita falo wurin Innawuro. Washegari su Innawuro suka koma Daura da ɗinbin alhetin da Engineer ya yi musu. Hamida ba ta ƙara samun wayar Abdurrashid ba hakan ya dame ta amma ba ta da dabarar da za ta kira shi. Ranar da suka cika kwana uku rabon su da juna kwance yake a ɗakinsu shi da Usman juye juye yake ta fama don ba abin da yake so a lokacin irin ya kasance da matarsa. Usman da ke gefen shi yana waya da matarsa Jamila, kalaman da yake furtawa duk su suka ƙara tsokano shi ya miƙe yana ce mata su yi Vedio call. Abdurrashid ya bi shi da kallo ganin ya shige bathroom sai ya janyo wayarsa Data ya kunna ya shiga whatsapp cikin sa'a ya ga Hamida online Video call ya kira ta yana raya wa a ransa ina ma Hamida ta yi girma da wayewar da za ta biya mishi buƙatar shi a haka. Ganin hotonta ya bayyana ya sa shi sakin wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Sai da ya ɗaure fuskarsa ya ce "Ke in ba an kira ki ba ba ki kiran mutum ko? Sai da ta ɗan kauda idonta don kar su haɗa ido ta soma gaishe shi bai amsa ba ya ce "Ke ba ki san yadda za ki ba mijinki hakuri ba idan ya yi fushi? Ta furta ka yi haƙuri sai kallon ta yake sanye take cikin atamfa riga da zane da ɗankwalinsu. Sai wani iri yake ji don sha'awarta da ke ƙaruwar masa. Karatunta ya riƙa tambayar ta tana ba shi amsa, sun dade a haka har Usman ya fito daga bathroom ɗin yana goge kan shi da tawul sai satar kallon sa yake sanin wanka ya yi yana tuna tsiyar da yake mishi morewar auren babbar mace wayayya, yanzu ba ya kusa da ita amma ba shi da wata damuwa da sun yi Vedio call za ta biya masa bukatar shi. Ya fidda ajiyar zuciya ya dubi Hamida da ido ma ba ta yarda su haɗa ballantana ya yi tunanin ta san hanyar da za ta biya masa buƙatar ta sa. Wayar ya kashe ya miƙe don samo maganin da yake sha yake kwantar mishi da sha'awa. Fahimtar abin da yake yi ganin yana shan maganin ya sa Usman ya fara mishi dariya da shegantaka shiru ya mishi har ya gaji ya kyale shi. Hamida sun zana jarabawar First team har sun yi hutu wannan karon ta yi abin gani don na bakwai ta yi wanda tun soma karatun na ta ba ta taba kokari kamar wannan ba. Momi Binta ta ce ta ta zo gidanta ta yi mata hutu can ɗin ta tafi bayan an tambayi Engineer, sai dai ita Hamidar ba ta bari ta tafi ba sai da ta gaya wa Abdurrashid. Kwanan ta ɗaya Mimi ta dira Abujar suka haɗu su uku ga Hanan sosai Hamida ta ji daɗin zuwan ta Abuja, kasantuwarta da su Mimi ta ƙara wayewa ta naƙalci abubuwa da dama na rayuwa. Sai da hutun ta ya kusa ƙarewa ta koma Kano. Haka rayuwa ta cigaba da garawa Hamida na cigaba da karatunta idan suka samu hutu tana yinsa ne a Abuja ko Katsina gidan Aunty Safiya ko Yola wurin Daada da Aunty Zainab. Tana kuma roƙon zuwa Daura idan suka samu hutun kwata kwata kwana uku ake ba ta ta je ta dawo. An yi bikin babbar ɗiyar Aunty Binta da me bi mata haka ma yayan Aunty Safiya su biyu. Lokacin da Hamida ta kammala karatun sakandirenta lokacin kuma saura shekara guda Abdurrashid ya dawo ta yi wani irin girma ta zama cikakkiyar mace ga ɗinbin wayewa da ta yi don tana tare da wayayyun, sai dai in za su yi vedio call da Abdurrashid hijab take zabgawa wai kar ya gane ta yi girma. Kamnala sakandirenta yayin da Engineer ke son ta cigaba da karatu a Open University ita Aunty Binta shawarar a nema mata Nile University Abuja. Engineer ya ba ta haƙuri ya ce a bari ta yi Open University ɗin. Da Hamida suke labarin makarantar da za ta cigaba da Walida wadda FCE za ta cigaba, wani abu ta ji ya tsaya mata ganin kodayaushe Hamida na saman ta kafin ta ƙaƙaro murmushi ta ce "Kin caɓa." Sun fara karatu Hamida na mayar da hankali sosai har suka ƙare shekarar su ta farko Computer Science don haka dole take dagewa. Yanzu zuba idon dawowar Abdurrashid ake don za su iya dawowa a koyaushe. Wata ranar laraba Hamida ta dawo makaranta, a gajiye take don haka sauri take ta yi sallah ta kwanta, ko abinci sai ta tashi ta yi niyyar cin shi. Aunty Karima ta shigo ɗakin daidai ta idar da sallah, gaishe ta ta yi ta ce "In kin kammala ki same ni falo za mu duba gidan ku Daddy ya ce ki zaɓi kayan da za a zuba miki." Kanta ta sunkuyar jin abin da Auntyn ta ce kafin ta ce "To Aunty." Auntyn ta juya sai ta ja mata ƙofar. Ta miƙe zuwa wurin kayanta don daga ita sai zane doguwar riga mara nauyi ta ciro da gyalenta ta zura sai ta ninke zanen da hijabin. Ta fito ba ta ga Auntyn ba sai ta duba ta a ɗaki suka fito tare, Auntyn na gaba tana bayan ta ta cikin gidan akwai ƙofa da za ka shiga zuwa gidan Abdurrashid ta nan suka bi. Gini aka yi mai matuƙar tsari da kyau, shuke shuken da aka yi sun ƙara ƙayata wurin. Aunty Karima ta buɗe wurin suka shiga, ɓangaren ta daban haka na Abdurrashid. An gama komai sai dai Furnitures ne da ba a zuba ba. Sun duba ko'ina yayin da me musu wanki ya yo ma wasu mata jagora sun iso suka gaisa sai suka ci gaba da duba wurin tare ƙarshe Aunty Karima ta dubi Hamida ga wadda za ta shirya muku wuri nan, aikinta kenan sai ki faɗa mata irin abin da kike so." Hamida ta sa hannayenta ta kama kumatunta "A'a Aunty na bata zaɓi." Murmushi Auntyn ta yi ta ciro wayarta ta soma kira daga yadda take wayar Hamida ta gane da Abdurrashid take shi ma tambayar shi ta yi zaɓinsa za a shirya masa wuri ya ce ta tambayi Hamida wanda ta zaɓa mishi shi kenan. Murmushi kawai Auntyn ta yi ta sauke wayar tana faɗi ma Hamida yadda ya ce Saboda tsayuwar Aunty Karima wurin ta kasa faɗi ta ce za ta gaya mata. Sati biyu kawai aka ƙara matar ta tafi china da ta dawo kuma aka shirya wurin da ya yi matuƙar ƙayatuwa da idan ka shiga ba za ka so fita ba. Masu aiki suna shiga su gyara don kowane lokaci Abdurrashid zai iya dawowa. Wani yammaci Hamida na kwance a daki kwana uku kenan da suka samu hutu wani littafi take karantawa. Daya daga cikin masu aikin Aunty Karima ta yi knocking ta tashi ta bude ta sanar mata tana da bakuwa, kai ta daga sai ta fito Gwoggo Indo ta samu a falon ta nemi wuri ta zauna tana mata sannu da zuwa. Sai da ta gaishe ta suka soma hira,cikin hirar Gwoggo ke kara gaya mata halin da take ciki,don wurin saida abincinta yanzu ba kamar da ba ya ja baya sosai saboda sababbin masu sayarwa da aka samu a Estate din. Hamida ta yi shiru tana sauraren ta hannunta daya na cikin calabar ta tana yamutsawa sai da ta ji ta yi shiru ta ce "Zan ba ki abin da ke hannuna Gwoggo kafin in dawo." Gwoggo Indo ta yi saurin cewa "Ina za ki" "Yola za mu tafi diyar Aunty Zainab za ta yi birthday,akwai kuma bikin Mimi wani satin,zan dan kwana biyu a can kafin in dawo." "To mijin naki fa da kika ce zai dawo cikin watan nan? Hamida ta gyara zama "Ni dai abin da aka ce min kenan." Gwoggo Indo ta ce "Yaushe ne tafiyar ? "Gobe idan Allah ya kaimu." "Shi kenan,amma ni dai na fi son ki gyara kanki kafin isowar shi." Hamida ta muskuta "Ni maganin sanyi na fi so Gwoggo." "Akwai su kala kala masu mugun kyau." "To ina so,wa za ki ba ya kawo min ? "Zan ba Ladi Allah dai ya sa da gaske shan za ki yi." Murmushi Hamida ta yi "Allah zan sha Gwoggo. "Shi kenan zan ba ta idan na koma sai ta kawo miki. Ta mike ta koma daki kudi ta dauko ta kawo mata, sai dai daga ganin yadda Gwoggon ta karba ta san ta raina, sai dai ba ta yi magana ba mikewa ta yi Hamida ta bi bayanta don ta raka ta. Da ta dawo daki ta shiga ta cigaba da shirin tafiyarta. Washegari suka wuce Yola ita da Aunty Karima, bikin Mimi ne don haka Hamida ita ce babbar kawa ita da Hanan. Gidan Daada suka fara yada zango kafin suka isa gidan Aunty Zainab duka yayan Daada sun hallara saboda birthday din autar Aunty Zainab ana ta shagali a harabar gidan har Daadar suka sa aka dauko wadda aka samu ta zo da kyar wai me za ta zo yi a wannan shiriritar. Hamida wadda tun da ta tashi take jin ta wata iri tana kwance tun dawowar su daga sallon Hanan ta shigo ta yaye abin rufar da ta rufe har kanta Hamida ta dube ta "Wai da ma ba barci kike ba? Saboda Allah meye haka za ki wani shigo daki ki kwanta kowa na waje yana sha'aninsa,sai nemanki muke ni da Mimi, don Allah ki tashi ki yi wanka. Ta mike ta shiga bathroom kafin ta fito ta ce shiga to ki yi wankan na hada miki ruwa. Hamida da ke kallon ta ta mike a hankali ta shiga wankan ta yo ta fito ta samu Hanan din a inda ta bar ta tana danna wayarta. Ta wuce ta zauna gaban dressing mirror ta sheka kwalliya sai kallon kanta take yadda ta zama,ta mike neman kayan da za ta sanya ta ga wani rantsatstsen less a kan gado ta san ita Hanan ta ajiye mawa kallon ta ta yi "Less din nan ya min nauyi my Hanan." Ita ma ta dago suka dubi juna "To me za ki sa? Ta karasa inda kayanta suke wata atamfa ta ciro dinkinta karami ne da ta sanya ya zauna das a jikinta cikinta ya shafe kirjinta ya cika zanen ta yi daurin baya ta kafa dauri kamar kar ta sa mayafi da ta zura takalmi sai dai ta ciro wani karami ta ajiye shi a kafada dan kunne da sarka fashion ta yi amfani da su sai ta daura agogo . Hanan ke ta fesa mata turare har sai da ta ce "Haba mana my Hanan." Suka fita rike da hannun juna nesa da inda ake ta cashe rawa suka tsaya nan Hanan ta zo ta same su suna ta hirar su silalowar da wata dalleliyar mota ta yi zuwa parking space ya sa suka yi mata kallo daya sai suka cigaba da hirar su. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA N0.21 Ana gobe tafiyar Abdurrashid da daddare ya kwanta amma sam ya gaza barci. Wayarsa ya jawo ya kira layin Hamida wadda ke zaune tana karatun makaranta, ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama "Ki zo yanzu ki same ni." Ya faɗi cikin dakewa ga mamakinsa ji ya yi kamar za ta fashe da kuka ta ce "Kar Aunty ta gane Hamma." "Sai me don ta gane? Ina jiran ki." Ƙit ya katse kiran tagumi ta rafka da hannu biyu ta shiga tunani. Ta jima a haka kafin aka turo ƙofar ɗakin saurin kai dubanta ta yi Abdurrashid ne, ji ta yi gabanta ya soma bugawa da sauri "Tashi mu tafi." Ya faɗi ba alamar wasa a fuskarsa ta miƙe ba ta ɗau komai ba har wayarta daga ita sai wata yar yala-yalan rigar barci mai guntun hannu tsawon ta iya gwiwa sai wata yar mitsitsiyar hula a kanta. Gaba ya sanya ta yana biye da ita, ta ƙofar da za ta sada ka da kitchen ɗinsu suka bi, suna shiga bathroom ta faɗa kafin ta fito ta hau gado, shi zama ya yi riƙe da laptop dinsa har ta soma barci ta ji an rungume ta abin da yake mata ya sa dole ta wartsake. Daren dai bai bar su sun samu isasshen barci ba ta yi koke kokenta har ta gaji ta yi shiru da ƙyar ta tashi sallar Asuba da ya tashe ta, tana idarwa gadon ta koma duk da barcin da ke idonta ƙin yi ta yi tana jiran ya shigo ta shaida mishi za ta tafi. Da ya shigo ta faɗi mishi shiru ya yi sai da ya hau gadon ya janyo ta jikinsa bayani ya yi mata za a riƙa sanya mata rabin albashinsa duk wata ta riƙa yin duk buƙatunta, sai gargaɗin kar ta kula ƙawayen banza ta kuma dage da mayar da hankali a karatunta. Da ya gama gaya mata barcinsa ya shiga yi yayin da ita zullumi ya hana ta yi har dai ba ta san sa'adda ya yi awon gaba da ita ba. Zare jikinsa da ya yi cikin na ta ya sa ta buɗe ido Meye tuna abin da kenan ya sa ta fara zare ido tana ganin ya shiga bathroom ta miƙe da sauri har tana tintiɓe ta fice shigar ta ƙofar da ta haɗa sasan Aunty Karima da na shi sauri ta ƙara ta samu ta shige ɗaki sai dai haɗa idon da suka yi da Auntyn wadda ke zaune bisa dinning tana break past ya sa ta tsayawa cak cikin wata irin kunya da nauyi da ta ji sun lulluɓe ta "Ki zo ki karya." Ta ji muryar Auntyn cikin kunnanta "Zan yi wanka tukun Aunty." Ta faɗi cikin dauriya sai ta cigaba da tafiya. Wanka ta fara yi ta yi kwalliya cikin wasu riga da skirt na English wear ta rufe kanta da ƙaramin gyale. Kasa fita ta yi saboda kunyar Aunty Karima har sai da ta aiko mai aikinta kan Hamida ta zo ta yi break fast ta fita tana takawa a hankali kamar mara gaskiya kanta a ƙasa ba ta samu Auntyn a falo ba har sai da ta kusa kammalawa. Goma saura su Momi Binta suka shigo gidan har da Daada sun zo bankwana da Abdurrashid haka ya fito ya samu kakar tasa da yan'uwan mahaifiyarsa dukkan su, mahaifinsa ne dai har yau bai dawo ba. Kewaye shi suka yi suna ta mishi addu'a har lokacin da zai bar gidan ya yi barikinsu zai fara zuwa inda za su haɗu da sauran abokan tafiyar ta shi cikin su har da amininsa Usman, don haka ba damar yi masa rakiya daga shi sai direba suka bar gidan Daada tana ta addu'ar Allah ya tsare mata shi a duk inda ya samu kansa Kowa na gidan sai da ya fito har Mami Mariya da mutanen part ɗinta Suna tafiya sai aka dawo kan Daada da ke ta kuka ana ba ta haƙuri har ta sa yayan nata ƙwalla. Hamida dai tashi ta yi daga inda ta makure ta koma ɗaki sai duk take jin ba daɗi da tafiyar tasa don ta fara sabawa da shi. Tana nan kwance ta yi rub da ciki Aunty Karima ta aiko ta zo su yi sallama da su Daada yau za su koma da ta fito gaban Daada ta tsuguna Daada ta dafa kafaɗarta " Ki yi haƙuri kin ji wannan yarinya, kamar yau za ki ga ya dawo, ki yi haƙuri kin ji? Sai kuma ta fara hawaye Hamidar ma hawayen ta kama sai kuma ta bar na ta kukan tana lallashin Hamida dukkan su kowacce da abin da ta kawo ma Hamida suka ba ta ta yi musu godiya sai da suka raka su suka ga tafiyar su sai suka dawo. Suna tafiya Hamida daki ta kuma komawa ta kwanta tana jin wani irin ba daɗi game da tafiyar ta shi a haka Aunty Karima ta zo ta same ta sai da ta tashi zaune Auntyn ta ce ta je ta kwaso kayanta a can wurin nasu ta tambaye ta akwai key a hannunta Hamida ta ɗaga kai. Cikin sanyin jiki ta nufi part ɗin tana buɗe kofar sai ta ji wani iri tana kallon ɗan zaman da suka yi tare da shi a dakin, bakin gado ta zauna ta yi zugum har sai da wayarta ta ɗauki ƙara Hamma ta gani rubuce yadda ta yi saving ɗin no sa kamar yadda yayan yan'uwan mahaifiyarsa ke kiransa. Cikin rauni ta yi sallama ya amsa mata sai ya yi mata bayanin yanzu haka suna Lagos nan da awanni biyu kuma jirginsu zai tashi. Cikin makyarkyatar murya ta yi mishi addu'a nasiha ya kuma yi mata ta kula da kanta da kuma karatunta har Allah ya dawo da shi. Kai take ta ɗagawa kamar yana ganinta sun jima kafin ya ce mata ana kiran shi ya katse kiran ta rafsa tagumi da hannu biyu ta daɗe a haka kafin ta shiga ɗibar kayanta sai dai ba duka ba akwati guda ta ɗiba sai ta rufe wurin. Washegari lahadi Engineer Shehu Bello ya dira ƙasar. Aunty Karima ta tasa Hamida suka je ta gaida surukin nata. A part ɗin suka samu Mami shi Hamida ta fara gaida wa kanta na ƙasa sannan Mamin ba su jima ba Aunty Karima ta mike ta biyo ta suka fito, za ta wuce ɗaki Auntyn ta ce ta zauna falo su yi hira idan ta shiga ɗaki tunani ne zai dame ta. Hakan aka yi nan ta zauna har suka ci abincin rana sai ta shiga daki ta yi sallah ba ta kuma fitowa ba har ta yi sallar La'asar tana zaune inda ta idar da sallar ta yi shiru cikin tunani aka shiga knocking ta daga kai ta dubi ƙofar kafin ta bada izinin a shigo, cikin masu aikin Aunty Karima ne ta ce tana da baƙuwa a falo ta ce tana zuwa sai ta miƙe ta cire hijab ɗin, ta fita falon don ganin baƙuwar, Gwoggonta ta gani ta karasa da fara'a tana mata sannu da zuwa kujerar da Gwoggon take ta zauna kusa da ita tana gaishe ta Sai kuma ta miƙe ta ce bari ta gayo wa Aunty Karima zuwan Gwoggon. Tare suka fito suna gaisawa Aunty Karima ta koma ciki Gwoggo ta dubi Hamida "Mun yi waya da Malam ya ce min mijinki ya je Daura yi musu sallama. Yaushe ne tafiyar ta shi? Hamida sai ta ji ba ta ji daɗi ba da Abdurrashid bai je ya yi ma Gwoggonta sallama ta ɗago cikin jin nauyi "Ya tafi yau Gwoggo." Ta yi yar fara'a "Ashe na zo a daidai, kuɗaɗen magungunan da na kawo miki za ki kawo sai kuma cikin kuɗaɗen da ya bar miki ki bani in ƙara jarin." Waige waigen da ta ga Hamida na yi ya sa ita ma ta waiwaya ganin ba kowa ta ce "Meye kike yi kamar wata mara gaskiya? Ajiyar zuciya Hamida ta yi "Gudu nake kar wani ya ji Gwoggo." Kafin Gwoggo Indo ta kai ga magana Aunty Karima ta fito cikin shiri ta ce wa Gwoggo ta gaida gida ita za ta fita suka yi mata fatan dawowa lafiya. Sai da Hamida ta tabbatar da fitar ta ta saki wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya. Ta miƙe ta cewa Gwoggo Indo tana zuwa ɗakinta ta koma ta fito da Sch bag ɗinta a hannu inda ta tashi ta koma ta zauna ta shiga caje jakar kuɗaɗen ciki ta fitar tuni Gwoggo Indo ta taɓe baki ba dai ta yi magana ba har sai da ta miƙo mata kudin ta karɓa kamar ta karɓi kashi. "Na meye su kuma waɗannan? Hamida ta ɗan karyar da kai na break ɗina ne da yake ba ni." Na ji na break ɗinki ne, ina kuma abin da ya bar miki da zai tafi? Koko hakanan ya bar ki salin alin? Hamida ji ta yi zuciyarta ba ta yarda ta faɗa mata ya ce a riƙa ba ta rabin albashinsa ba. Don haka ba ta yi magana ba sai ƙara marairaicewa da ta yi. Gwoggo ta yi ƙwafa "Gaskiya da sake hakan ba za ta taɓa saɓuwa ba Allah ya dawo da shi lafiya, dole in saita mishi zama. Amma tafiyar shekaru huɗu ka sa kai ka tafi ba ka bar wa mace komai ba wannan wane irin maƙo ne da hannun jarirai kake da shi ? Hamida dai tuni hankalinta ya fi na ɓarawo tashi don tsananin tsoron da ya rufe ta kar cikin masu aikin Aunty Karima wata ta ji Gwoggo don yadda take buɗe murya. Ta dai gama sababinta ta miƙe Hamida ta bi ta don ta yi mata rakiya sun zo daidai part ɗin Mami Gwoggo Indo ta dubi wurin "Kin ga baiwar Allan nan ba karamin alheri nake samu da ita ba, amma saboda aurenki da Abdurrashid ta datse cinikayya tsakanin mu. Da aka kawo sababbin kaya na kira ta cewa ta yi in bar shi, kuma ni na san ba inda za ta sayi kaya masu kyau irin nawa." Hamida dai ba ta tanka ba har ta kai ta bakin get sai ta juyo. Washegari Hamida tana daki tana shirin makaranta Aunty Karima ta shigo ta yi mamakin hakan sanin ba ta fitowa da wuri bare yau ita ke da mai gidan. Cikin girmamawa Hamida ta gaishe ta ta yi murmushi "Da ma na ce ba Abdurrashid bari in duba ki kar ki yi latti." Ta ɗan sunkuyar da kanta "Na tashi Aunty." Ta ce "To ya yi." Ta ajiye mata kuɗi saman dress ing mirror "Ga shi nan in ji Daddy kuɗin break.". Ta ce "Na gode Aunty, ya fito ne in gaishe shi? Ta ce "Ki bari idan kika dawo lokacin shi ma ya dawo Office sai mu je ki gaishe shi." Hamida ta gyaɗa kai sai ta fita Hamida ta karasa shirin ta ta fita sai da ta karya kumallo ta fita inda Malam Adamu ke jiran ta. Ba su samu wayar Abdurrashid ba sai da ya yi sati da tafiya lokacin Hamida ta fara sakin jiki da Aunty Karima don yadda take saka ta a jiki duk fitar da za ta yi indai ba Hamida na makaranta ba da ita take zuwa. Walida kuma tunda Abdurrashid ya tafi sai ta sarfaci zuwa gidan Hamida duk weekend. Wani dare ta samu wayar Gwoggo Indo Laila ta haihu. Sai da gari ya waye sai ta faɗi ma Aunty Karima Auntyn ta ce sai zuwa yamma sai su shiga barkar ta tambaye ta inda gidan mai jegon yake. Ita ke driving Hamida da ta sha dogon hijab tana gefenta. Baban Amir suka fara gani zaune a kofar gida shi da Amir, cikin matukar girmamawa ya gaishe da Aunty Karima sanin ita ɗin kowace ce.. Tana wucewa ya soma tsokalar Hamida da Amarya ashe ana ganin ku? Murmushi ta yi ta kama hannun Amir suka shiga ciki. Har Gwoggo indo sun samu a ɗakin mai jegon wadda ta yi ta ina a saka da Aunty Karima. Sun ɗan zauna kafin suka tashi don komawa gida [2/9, 09:43] Original: Tana nan kwance har sai da ta ji an tayar da sallah a masallacin da ke cikin Estate din ta yi yunƙurin tashi, a daddafe ta kai kanta bathroom ruwa mai zafi ta tara da dabara da dauriyar da ta sanya ta shiga ruwan tana runtse ido, ga hawaye na gudu kan kuncinta sai da ta ji ya soma sanyi ta zubar ta sake wani, wankan tsarki ta yi sai ta yi wanka da ruwa mai zafi, sosai ta ji dama lokacin da ta fito doguwar riga har ƙasa ta samo ta sanya ta yi sallah ta lallaɓa za ta hau gado ta kwanta ta hango inda jini ya ɓata zanen gadon dole ta yaye shi ta kai shi bathroom ta sanya a laudry ta dawo kamar ta duba wani ta shimfiɗa sarawar da kanta ke yi wanda bai rasa nasaba da kukan da ta sha ga zazzaɓi da take ji zai rufe ta ya sa kawai ta kwanta, barci ya yi awon gaba da ita. Knocking ɗin da ake ya farkar da ita ta miƙe a hankali ta isa ƙofar sai ta buɗe mai kawo musu abinci ce ta karɓi tiren tana gaishe ta tare da bayanin Haj ta ce ta ji shiru ba ku fito ba, ba ku yi magana a kawo muku abinci ba. Ta ce "Shi ya fita ni kuma ina barci." Mai aikin ta juya don isar da saƙon, ita kuma ta shiga da abincin sama-sama ta ci ta rufe ta koma ta kwanta da za ta samu maganin zazzaɓi da ta sha ƙila ta ɗan ji dama, hakanan dai ta ci gaba da kwanciya har ta ƙara jin wani knocking ɗin wannan karon tana buɗewa sai su Aunty Karima ta gani yau ma kamar jiya su dukkan su, ta ba su wuri tana musu sannu da zuwa suka tambaye ta ƙafa ta ce ta yi sauƙi ita har ga Allah ta ma manta da ƙafar, don sawun giwa da ya take na raƙumi. Suna ta karantarta wayar Aunty Karima ta yi ƙara cikin masu aikinta ne take shaida mata an yi baƙuwa ta ce Hamida take nema abokiyar aikin Abdurrashid ce. Ta ce ta kawo ta. Da isowar matar ta gabatar da kanta ga su Momi Binta Abdurrashid ne ya turo ta ta duba matarsa suka ce ba matsala. Ta matsa jikin gadon tana tambayar Hamida yadda take ji ta ciro kayan aikinta tana haɗa allurai, jikin Hamida ya soma rawa ta ce tana jin fitsari ta ce ok ta sauka gadon yadda take takawa tana buɗe ƙafa ita kuma tana daɗa nazarinta. Ba ta daɗe ba ta fito ta koma bisa gadon ta ce mata ta gyara Hamida ta shiga yarfa hannu ga kunyar su Aunty Karima tana ji kuma Allah ya sani ba za ta iya tsayawa a yi mata allurar ba. Kalaman rarrashi matar ta shiga yi mata gane ba ta son allura amma Hamida ta ƙi tsayawa sai ma maƙurewa da ta ƙara yi jikin gado su Aunty Zainab da ke kallon su kowacce na ƙara ƙarfafa zarginta kan abin da ke damun Hamida. Wayarta ta ciro ta kira Abdurrashid ta ce mishi Hamida fa ta ƙi tsayawa ya ce ok ta ba ta wayar, ga mamakin Hamida maimakon magana cikin faɗa-faɗa da ta yi tunanin zai rufe ta da shi saɓanin haka cikin taushin murya yake rarrashin ta ta tsaya a yi mata ta ce ita tsoro take ji, ya ce ta ba Dr wayar ta karɓa ta ce jikinta akwai zafi ya ce ta ƙyale ta kawai idan ya dawo zai mata. Sallamar su Aunty Karima ta yi ta fita, su ma addu'ar Allah ya ƙara sauƙi suka yi mata da yi mata bankwana. Sun fito Dr na ƙoƙarin shiga motarta Aunty Zainab ta ƙarasa inda take ta ce "Kuma Dr za ki tafi ba ki duba ta ba." Ta ce "Da ma allura zan yi mata kuma da ta ƙi Dr ya ce in ƙyale ta." Kina ganin idan ta shiga ruwan zafi ba zai wadatar ba daga ba ta son allurar? Aunty Zainab ta jefa mata tambayar Ta ɗan furzar da iska "Ya danganta daga wasu matan zuwa wasu, wata ko gezau babu abin da yake samun ta daga farkon fara mu'amalarta da ɗa namiji, wata kuma za ki ga abin ya zo da tsanani sosai kamar wannan." Aunty Zainab da ta yi tagumi ta ce "Kuma kina gani Dr yarinyar nan ta isa ɗaukar ɗawainiyar ɗa namiji? Yar dariya ta yi "Ƙwarai kuwa wadda ba ta kai ta ba ma za ta iya, sai dai yanzu tana buƙatar a bar ta ta ɗan huta don da alamu ta ji jiki, na so duba ta sosai amma kin ga ta ƙi idan ya zo zai kula da kayansa. Aunty Zainab ta yi mata godiya likitar ta faɗa motarta ita kuma ta juya zuwa part din Aunty Karima labarta ma yan'uwanta yadda suka yi da Dr ta yi kowacce ta ce da ma ta zargi haka "Momi Binta ta ce "Ɗan rainin wayo to da yana a'a kar akai ta." Sauran suka fashe da dariya ita ba ta yi dariyar ba sai ƙarawa ta yi da cewa "Ni da ma ban so aka kai masa yarinyar nan ba ya je ya kashe musu 'ya, to Daada ta ce sai dai a yi haka, don haka Karima ki je ki dauko yarinyar nan ki kawo ta wurin ki maza ba haƙuri ne da su ba dubi yadda ta koma yau kawai ba kuma ɗaga mata ƙafa zai yi ba. Aunty Zainab ta ce Dr ta ce ba wata matsala na farko ne kawai, da an bar masa matarsa ga shi tafiya zai yi." Hannu ta ɗaga mata "Ban yarda ba, ki ɗauko ta Karima ki faɗa mishi in ji ni. Yanzu ki je ki ba ta abinci ki tabbatar ta ci kafin ya dawo ya duba ta." Aunty Karima ta ɗaga kai sai ta miƙe "Bari in duba sun kammala girkin in kai mata kuma ku ci kafin ku wuce. Ta wuce kitchen din ta ɗauki wasu yan mintoci ta fito mai aikinta na biye da ita da tray ba ta samu kowa ba cikin yan'uwan nata a inda ta bar su sai suka shige part ɗin Abdurrashid ita da ke gaba ta yi knocking Hamida ta buɗe tana faɗin "Sannu Aunty." Za ta karɓi tray a hannun mai aikin Aunty Karima ta hana ita ta karɓa, shigar ta ganin Abdurrashid wanda ba su san sadda ya shigo gidan ba yana gyara gado ya sa ta ji kamar ta koma sai dai ya riga ya gan ta, ta wuce ta ajiye musu tray ya gaishe ta yana ba ta labarin kiran da ya samu na gaugawa wanda shi ya hana shi shigowa, amma yanzu zai shigo ya yi sallama da su Momi ta ce "To amma don Allah ka tsaya sai ta ci abinci na zo dama in tsaya ta ci a gabana na ga kuma ka dawo." Ya ce "Za ta ci Aunty na gode." Ta juya ta fita. Sai da ya gama gyara shimfiɗar ya wuce bathroom zanen gadon da ta ɓata ya wanke sai ya fito tana ta satar kallonsa daga inda ta idar da sallah "Taso to." Ya ce yana nufar wurin cin abincin, wanda ya zuba mata ya kuma matsa mata sai da ta kusa cinye shi ya ƙyale ta da ƙyar don cewar da take ta ƙoshi. Hannunta ya kama zuwa bakin gado maimakon ya bar ta ta zauna kan cinyarsa ya ɗora ta wasa ya riƙa yi da ita yana hura mata iska a kunne wanda duk ya ta da mata tsigar jiki. Ba ta ankara ba sai dai ta ji ya soka mata allura yau ma ba ta ji zafi ba sai da ya gama liliya mata ya ja ta suka kwanta, ba ta ɗau wani lokaci ba ta yi barci ya zare jikinsa ya rufe mata rabin jikinta sai ya bar ɗakin. Ya samu suna ta shiri. Shi da Aunty Karima suka yi musu rakiya Air port. Momi kuma da kanta ta faɗa masa Hamida ta dawo part ɗin Aunty Karima. Shiru ya yi cikin tunani don ba halin tambaya sai dai ya zargi sun gane abin da ya faru da Hamida a yau. Sai da suka ga tashin su suka juyo Aunty Karima kaɗai ta koma gida shi komawa ya yi wurin patients ɗinsa. Tana ajiye mayafinta wurin Hamida ta tafi ta samu ta tashi har ta yi sallar La'asar ta tambaye ta jiki ta ce ta ji sauƙi ta shaida mata za ta koma part ɗinta don haka ta ɗauki kayan amfanin ta. Akwati guda ta cika Aunty Karima ta kira mai aikinta ta ɗauka wani ɗaki da ke jikin wanda su Hanan suka sauka Aunty Karima ta kai ta aka sanya mata akwatin a wardrobe sai ta kwanta kan lafiyayyen gadon. Auntyn ta ce "Ko za ki zo mu je falo ki ɗan huta da zaman ɗakin? Kai ta girgiza "Zan kwanta Aunty." Ok kawai ta ce ta fita sai ta ja mata ƙofa. Abdurrashid sai da aka yi sallah ya dawo, saboda aikin da ya tare shi amma duk abin da yake Hamida na maƙale a ransa ya ƙosa ya dawo don ya ga halin da take ciki. Da ya shiga ɗakin bai gan ta ba sai ya nufi part ɗin Aunty Karima ita ya tambaya inda Hamidar take ta nuna masa hanyar ɗakin da hannunta. Ya shiga da maƙallaliyar sallama ta ɗago daga kwancen da take tana amsawa zama ya yi bakin gadon yana jin sannu da zuwan da take masa kanta ya ruƙo ya ɗora saman cinyarsa yana shafa calabar da ke kanta, "Ya kike jin jikin yanzu? Ta ce "Na ji sauƙi." "Kin ci abinci? Ta ɗaga masa kai "Me ya sa ba za ki fita wurin Aunty ba kin kwanta nan ke kaɗai? Ta ce "Na fi son in kwanta." Wayarsa ya ciro ya kira Aunty Karima ya ce ta sanya a kawo masa abincinsa nan. Anan ɗin ya ci har ya sa Hamida ta ƙara, sai goma ya tafi da ya ga Hamida ta soma barci. Ya gama duk shirin kwanciya amma ya gaza barcin kewar Hamida yake ji yana jin tsaurin hukuncin Momi Binta da ta raba shi da matarsa a daidai da ya san muhimmancinta. Sumarsa ya shafa yana mai lumshe idonsa tunanin cikin nishaɗin da ya kasance a daren jiya yana gilma mishi, hannu ya sa ya shafo inda ta fi kwanciya ɗankwalinta da ke wurin ya ɗauko ya kai fuskarsa ƙamshin da take yi da ke fita cikin ɗankwalin ya natsar da shi har ya shiga barci cikin kwanciyar hankali. Da asuba yana dawowa sallar asuba ta ƙofar da ke sa da mutum da part ɗin Aunty Karima ya bi ya isa ɗakin Hamida ya samu ta idar da sallar Asuba ya ja ta zuwa gado suka kwanta, tambayar yadda ta kwana da jiki yake yi, ta ce ta samu sauƙi. Ya ce ta huta yau ba sai ta je Sch ba zai faɗa musu ba ta da lafiya. Ta ce za ta iya zuwa, ya ce a'a ta dai kwanta. Sai da gari ya yi haske ya zare ta cikin jikinsa ya fita. Ko da ya shirya bai dawo ta nan ba sanin Aunty Karima a daidai wannan lokacin barci take. Barci sosai Hamida ta yi bayan tafiyar Abdurrashid. Da ta tashi sai ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar materiyal ta fita tana ƙamshi mai sanyi. Kan ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna TV ta zura wa ido har ta ji shigowar Aunty Karima ƙara shiga nutsuwarta ta yi kafin ta soma gaishe ta, ta amsa cikin fara'a ta gayyace ta zuwa wurin cin abinci tare suka karya sai suka dawo falon suka zauna suna kallo. Kiran Gwoggo Indo da ya shigo wayar Hamida ya sa ta miƙewa ta koma ɗaki ko da suka ƙare wayar yan Daura ta kira daga nan ba ta koma falon ba a ɗakin ta zauna ta ɗauko littattafanta na makaranta tana dubawa da ta yi sallar Azahar samun kanta ta yi da son yin kwalliya don ta burge Abdurrashid ganin duk sa'adda ta yi kwalliya yadda yake yawan kallonta wanka ta sake ta yi kwalliya sosai don zama da Aina ta ƙware a naƙaltar yadda ake yin ta. Yau har da su jambaki ta gyara girarta ta feffesa turaruka less ta sanya ɗinkin riga da skirt da suka yi cif a jikinta ta yi kyau ba kaɗan ba, sai ta samu kanta da kasa fita wurin Auntyn don tana jin kunyar Auntyn ta ga ta sake kwalliya ta gane don Abdurrashid ta yi. Gado ta koma suna chart da Hanan ƙarar buɗe ƙofar ya sa ta ɗago ido ganin shi ne ta ji mamakin hakan ta duba agogo sai lokacin biyu ta yi. Sannu da zuwa ta yi masa ya miƙo hannu sai ya kamo ta ya sanya ta a jikinsa sun daɗe a hakan kafin ya ce mu je falo ki ci abinci in ji Aunty. Ta kaɗa kai ya sake ta sai suka fito falon tare da Auntyn suka ci abincin shi yana gamawa ya ce zai je ya yi barci bai fito ba sai La'asar gidan ya bari sai dare ya dawo shi da abokinsa Usman. [6/30, 10:12 PM] Maryam Ibrahim Litee: SHIRIN ALLAH... RAYUWA N0.21 Ana gobe tafiyar Abdurrashid da daddare ya kwanta amma sam ya gaza barci. Wayarsa ya jawo ya kira layin Hamida wadda ke zaune tana karatun makaranta, ta ɗauka bakinta ɗauke da sallama "Ki zo yanzu ki same ni." Ya faɗi cikin dakewa ga mamakinsa ji ya yi kamar za ta fashe da kuka ta ce "Kar Aunty ta gane Hamma." "Sai me don ta gane? Ina jiran ki." Ƙit ya katse kiran tagumi ta rafka da hannu biyu ta shiga tunani. Ta jima a haka kafin aka turo ƙofar ɗakin saurin kai dubanta ta yi Abdurrashid ne, ji ta yi gabanta ya soma bugawa da sauri "Tashi mu tafi." Ya faɗi ba alamar wasa a fuskarsa ta miƙe ba ta ɗau komai ba har wayarta daga ita sai wata yar yala-yalan rigar barci mai guntun hannu tsawon ta iya gwiwa sai wata yar mitsitsiyar hula a kanta. Gaba ya sanya ta yana biye da ita, ta ƙofar da za ta sada ka da kitchen ɗinsu suka bi, suna shiga bathroom ta faɗa kafin ta fito ta hau gado, shi zama ya yi riƙe da laptop dinsa har ta soma barci ta ji an rungume ta abin da yake mata ya sa dole ta wartsake. Daren dai bai bar su sun samu isasshen barci ba ta yi koke kokenta har ta gaji ta yi shiru da ƙyar ta tashi sallar Asuba da ya tashe ta, tana idarwa gadon ta koma duk da barcin da ke idonta ƙin yi ta yi tana jiran ya shigo ta shaida mishi za ta tafi. Da ya shigo ta faɗi mishi shiru ya yi sai da ya hau gadon ya janyo ta jikinsa bayani ya yi mata za a riƙa sanya mata rabin albashinsa duk wata ta riƙa yin duk buƙatunta, sai gargaɗin kar ta kula ƙawayen banza ta kuma dage da mayar da hankali a karatunta. Da ya gama gaya mata barcinsa ya shiga yi yayin da ita zullumi ya hana ta yi har dai ba ta san sa'adda ya yi awon gaba da ita ba. Zare jikinsa da ya yi cikin na ta ya sa ta buɗe ido Meye tuna abin da kenan ya sa ta fara zare ido tana ganin ya shiga bathroom ta miƙe da sauri har tana tintiɓe ta fice shigar ta ƙofar da ta haɗa sasan Aunty Karima da na shi sauri ta ƙara ta samu ta shige ɗaki sai dai haɗa idon da suka yi da Auntyn wadda ke zaune bisa dinning tana break past ya sa ta tsayawa cak cikin wata irin kunya da nauyi da ta ji sun lulluɓe ta "Ki zo ki karya." Ta ji muryar Auntyn cikin kunnanta "Zan yi wanka tukun Aunty." Ta faɗi cikin dauriya sai ta cigaba da tafiya. Wanka ta fara ta [6/30, 10:12 PM] Maryam Ibrahim Litee: SHIRIN ALLAH... RAYUWA No.20 Washegari da safe ko da ta yi sallah shirin makaranta ta soma. Wadda Aunty Karima ta ɗora wa alhakin gama abin karin Hamida kafin fitar ta Sch ta zo ta gaya mata ta kammala. Ta fita zuwa dinning ɗin ta haɗa tea ta zuba agada da ƙwai a flate sai ta koma ɗakin, akan mirror ta ajiye flate ta tsaya tana karyawa tana duban agogo don lokacin tafiyar su ya yi ko me ya hana Abdurrashid fitowa? Turo ƙofar da aka yi da shigowa gabaɗaya ya sa ta kai idonta wurin, a shirye yake ya yi kyau kamar kullum sauke idonta ta yi ƙasa ta yi sai ta soma gaishe shi, ya tako inda take kasa cigaba ta yi da karin sai ta juya bakin gado inda ta ajiye hijab ɗinta da Sch bag ɗinta sai ta dawo ta ɗauki kayan karin nata ya gane nufin ta ta kammala sai ya fice ta bi shi a baya. A kitchen ta ajiye sai ta bar sallahun idan Auntyn ta fito a ce mata ta wuce. Yau a makaranta Walida ba ta zo ba Hamida ta rasa yadda za ta yi ta san ko lafiya har sai da aka tashi Abdurrashid ya ɗauke ta ya hau titi ta ce "Yau ƙawata ba ta zo ba." Ta gefen ido ya dube ta kamar ba zai yi magana ba har sai da ta fitar da ran zai ce wani abu kafin ya ce "Me ya hana ta zuwa? Cikin damuwa a fuskarta ta ce "Ban sani ba, ko za ka kai ni gidan su in gano? Shiru ya yi bai amsa ba har ya sa cikinta ɗurar ruwa, don sai take ganin ta ɓata mishi ne. Sun zauna shiru har suka isa barraks ɗinsu. Suka fito ganin Sojoji ko ta ina ya kayar da gaban Hamida sai dai ganin Abdurrashid tare da ita ya ɗan kwantar da hankalinta, suka wuce Sojoji na ƙasa da shi na sara mishi. Wani kyakykyawan Office suka shiga wuri ya nuna mata ta zauna shi kuma ya hau kujerarsa Computer yake taɓawa tsawon lokaci kamar ma ya manta tana wurin har zaman ya soma gundurarta. Knocking aka yi kafin ya bada umarnin shigowa wani soja ne ya shigo sai da ya sara mishi kafin ya ajiye wata jaka da ya ɗauko me ɗauke da kayan abinci. Sai da ya juya Abdurrashid ya miƙe wurin da ya ajiye ya nufa ya zuba abincin da ke ta turiri, da hannu ya kira ta ta taso kujera ya ja mata ta zauna, shi yana tsaye "Ki ci abincin sosai ina zuwa zan duba wani patient ɗi na." Ya faɗi yana tsiyaya mata drinks sai da ya fita ya ja ƙofar ta fidda ajiyar zuciya, cokalin ta kama ta shiga cin abincin a hankali, ta ci ya yi rabin wanda ya zuba mata sai ta sha drinks ɗin ta rufe komai, nan ta cigaba da zama tana kallon TV da ke aiki a Office ɗin. Ya dawo wata ƙofa da ke a cikin Office ɗin ya buɗe sai ya shiga ya kira sunanta, a hankali ta taka ta same shi gado ne ƙwaya ɗaya rak a ɗakin yana kwance a kai, ganin ya tuɓe kayan jikinsa ya sa ta sunkuyar da kai hannuwansa ya buɗe "Zo nan." Ta ji muryarsa kan nata na sunkuye ta ƙarasa gaban gadon "Ki zo nan." Ta ji ya kuma maimaitawa ta tayar da kai ta dube shi sai ta ga inda yake nuna mata ta zo ɗin ƙirjinsa yake nunawa da hannu ba ta da zaɓi dole ta taka ta kwanta kan ƙirjinsa ya kai hannu ya cire hijab ɗin jikinta da ƙyar ya samu ya cire rigar don yadda ta kamata ta ƙanƙame jikinta a jikinsa kasantuwar ba komai jikinta sai rigar, ya shiga sha'aninsa ya yi nisa komai ya kwance masa wayarsa ta shiga kukan neman agaji bai kula ta ba har sai ta katse ta kuma ɗaukar kuka a kasalance ya kai hannu don kashe ta gabaɗaya, idonsa ya yi arba da sunan Aunty gyaran murya ya yi don saita kansa ya ɗaga wayar "Lafiya Abdurrashid har yanzu ba ku dawo ba? Ya jiyo muryarta cikin damuwa. "Lafiya lau Aunty na biya barrak ne, muna nan dawowa." Kamar za ta ƙara magana sai kuma ta yi shiru "Sai mun dawo Aunty." Ya ce cikin muryarsa da ba ta gama dawowa daidai ba yana shafa sumar Hamida da ke hawaye don azabar da take ji wadda ta kasa banbance ta da ta ranar farko. Aunty ta yi zaune saƙare da waya a hannu cikin tunani kiran Aunty Zainab ya shigo wayar ta ɗaga suna gaisawa da tambayar lafiyar iyali Aunty Karima ta kada baki "Ita Momi me cewa a ɗauko matar Abdurrashid kar ya kashe musu 'ya, to kiran da ki kai min zaune nake ina jimami, tun safe da ya fita da yarinyar nan zuwa makaranta har yanzu bai dawo da ita ba." Dariya Aunty Zainab ta yi "Kin ji ki za ki damu kanki da gangan, kina biyewa Momi sai ma ya biyo ta har ɗakinki idan ba ki mayar masa da mata ba za ki gane Allah da girma yake." Dariya suka yi Aunty Karima ta ce "Ni dai umarnin Momi nake bi." Ta ce "Ai sai ki yi ta bi ki takurawa ɗa na, bawan Allah ya kusa tafiya ku bar shi da matarsa sai ku wani ɗauke masa ita. " Aunty Karima ta yi dariya tana jinjina kai. Suka canza hirar zuwa ta wajen birhtday ɗin da yarinyar Aunty Safiya za ta yi wani satin. Bayan dogon lokaci Abdurrashid ya sarara wa Hamida bathroom ya shige yayin da ita kuma ta dunƙule wuri ɗaya wani barci na fizgarta. Ya fito yana goge kansa da tawul bai tashe ta ba, kintsa kansa ya yi sai ya fice. Ta ɗan jima kwance kafin ta yi ƙarfin halin tashi zaune sai ta miƙe a hankali ta shiga bathroom ɗin, wankan tsarki ta yi sai ta kuma yin wanka ta fito unifoam ɗinta ta mayar kasa fita Office ɗin nasa ta yi ta zauna bakin gadon don kunyar abin da ya faru tsakanin su. Ta daɗe zaune sai ga shi ya shigo "Zo mu tafi." Abin da ya ce mata kenan ya juya ta tashi ta bi shi a baya bayan ta ɗauki Sch bag ɗinta har inda ya adana motarsa. Sai da ya hau titi ya ce "Ina ne gidan su ƙawar ta ki? Ta faɗa mishi Goron Dutse ƙofar waika sai da ya shiga ƙofar waikan yake tambayar ta inda zai riƙa bi ta yi ta nuna hanya har suka kai gidan. A hankali ta buɗe ƙofar ta fita zuwa cikin gidan mahaifiyar Walidar ta samu a tsakar gida tana shara ta tari Hamida da murna tana amarya ce a gidan namu? Hamida dai sai murmushi take ta tambayi Walida da hannu ta nuna mata ƙofar ɗaki ta ƙarasa da sallama Walida na kwance saman kujera da wayarta a hannu ta ɗago tana duban Hamida "Ke kuma daga ina a haka a yammacin nan kuma da unifoam? Na zo ne in duba ko lafiya ba ki je makaranta ba, wai me ya faru? Hamida ita ma ta jera mata tambayoyin don ta samu kauda tambayar da ya yi mata "Ciwon kai na tashi da shi amma na ji sauƙi Amarya, na ga har kin fara ƙyallin goshi." Hamida ta kama baki "Ban son sharri Walida." "Allah ba sharri ba ne kin ƙara kyau a 'yan kwanakin nan. Fuska ta taɓe "To na ji." Sun ɗan zanta Hamida ta miƙe sanin Abdurrashid na jiran ta ta yi wa mahaifiyar Walida sallama suka fita tare ta gaishe da Abdurrashid ya amsa sau ɗaya sai ya kauda kansa, Hamida ta buɗe ƙofar ta shiga ya ja motar tana jiran jin ko zai mata faɗan shanya shi da ta yi sai ta ji shiru har suka isa. Ita kaɗai ta shiga part ɗin Aunty Karima shi na shi wurin ya wuce, ba ta ga Auntyn ba har ta shige ɗaki unifoam ta fara tuɓewa ta sauya da wata doguwar riga ta atamfa ba ta ɗaura ɗankwalin kayan ba wani siririn gyale ta rufe kanta. Knocking ta ji ana yi ta ba da umarnin a shigo cikin masu aikin Aunty Karima ce ta ce ta zo ne ta kwashe kayan datti ta ce suna laundry ta wuce kwasowa Hamida ta fito bayan ta tambaye ta inda Aunty Karima take ta ce tana ɗakinta. Sai da ta yi knocking ta zo ta buɗe sai ta ga Hamida hanya ta ba ta ta ce ta shigo kujerar da ke ɗakin ta nuna mata ta zauna tare da gaishe da ita, bayan gaisuwar shiru ya biyo baya sai Auntyn ta miƙe mu je falo suka fito suka zauna suna kallo har sai da aka yi kiran sallah suka miƙe don zuwa bada farali, sai da aka yi sallar Isha'i Abdurrashid ya shigo bai daɗe ba magana kawai suka yi da Aunty Karima ya bar sashen Da wuri Hamida ta kwanta don wani barci da ta ji tana ji. Da asuba ko da ta yi sallah anan inda ta idar da ta kuma ɓingirewa sai ji ta yi ana ja mata 'yan yatsu, kafin a hankali ta buɗe idonta, Abdurrashid ta gani tsugune gabanta cikin shiri yake na wani lallausan yadi da hular da ta zauna a kansa sai ƙamshi yake. Ta yunƙura ta tashi zaune tana gaishe shi ba tare da ta yarda sun haɗa ido ba "Daura zan tafi in yi godiya in kuma yi musu sallama." Saurin wartsakewa ta yi cikin mamakin jin wai Daura ya nufa da safiyar nan. Addu'ar Allah ya kai shi lafiya ta yi mishi ya ce "Ki tashi ki yi shirin makaranta kar ki makara, Malam Adamu zai zo ya kai ki." Tsaye ta miƙe kamar yadda shi ma ya miƙe ya kama hanyar barin ɗakin. Wanka ta yi ta futo ta shirya sai ta lalubo wayarta Innawuro ta kira sai dai har ta ƙari ɓurarinta ba a ɗaga ba sai ta rubuta Text massege ta tura wa Yaya Aliyu kan ya gaya wa su Innawuro Abdurrashid na bisa hanya ya taho Daura. Ta kashe wayar sai ta fito Sch bag ɗinta da hijab a hannu, ta samu an haɗa mata abin break ta karya sai ta fita inda Malam Adamu ke jiran ta. Walida ta zo makaranta suna tare har a ka tashi suka tafi tare suka rage mata hanya ganin ba Abdurrashid ba ne. Dare sosai ya dawo don haka ba su gan shi ba sai da safe Aunty Karima da wuri ta fito don tana so ta ga Abdurrashid da ba ta gani ba a daren jiya, sai da suka gaisa ya ba ta wata ƙatuwar leda da su Innawuro suka haɗo shi da ita ta karɓa ta buɗe tana godiya man shanu ne mai yawa sai ƙwan zabi ta kira cikin masu mata aiki ta ce ta kai kitchen. Ya dubi Hamida da ke tsaye ya ce su wuce. Ranar da suka dawo ɗaki Hamida ta shige ta hau gado tana tsefe calabar kanta a haka ya shigo ya same ta yana daga tsaye ya harɗe hannayensa yake ƙare mata kallo, sai duk ta takura yana tsayen har ta gama ya ce "Ki same ni ina mota." Kai ta gyaɗa sai ya fita fuskarta kawai ta gyara sai ta zura hijab a falo ta samu Aunty ta yi mata bayanin abin da kenan. Wani hamshaƙin wuri ya kai ta da sai macen da ta isa ke zuwa wurin aka gyara mata kan har ƙafa a ka wanke mata a mota ya jira ta fuskarta ta yi fayau ta ƙara kyau saboda gyaran kan na gwanaye ne. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA 24 MARYAM LITEE Hamida ta ji jiki hannun Abdurrashid sai da ya gamsar da kanshi ya koma gu daya yana mayar da numfashi, ita kuma barcin wahala ne ya dauke ta. Sai da ta farka ta ga sai ita kadai ba Abdurrashid,lallabawa ta yi ta tashi zuwa bathroom ta yi wanka ta fito ta koma ɗakinta,sallar la'asar ta yi sai ta yi kwalliya wata doguwar riga ta ɗauko cikin kayanta da Aunty Karima ta ce ta fara kawowa daga kowane lokaci Abdurrashid zai iya dawowa. Ta yi kyau sosai ta fito tana ƙamshi mai daɗi. Abdurrashid ta gani da Usman zaune a falon ta ƙarasa ta zauna tana gaida Usman saƙo da ta ji ya shigo wayarta ya sa ta dubawa Abdurrashid ne ke gaya mata ta koma ɗaki cak ta miƙe ta kama hanya Usman ya bi bayanta da kallo,don tun rabuwar su ya kasa samun sukuni da ya tuna abin da Abdurrashid zai yi da Hamida da zarar sun isa gida sai ya hankalinsa ya ƙara ɗagawa,shi ya sa ya yi ta kiran Abdurrashid a waya wai ko idan ya ɗauka ya fahimci halin da yake ciki amma sam bai ɗaga wayar ba hakan ma ya ƙara tada mishi hankali tabbatar da zarginsa. Key ɗinsa ya ɗauka don barin gidan matarsa Jamila da ke ta rawar jiki miji ya dawo ta ga zai fice da ta nemi sanin inda za shi daga dawowa ya ce ma ruwa ya yi wurin Abdurrashid yanzu zai dawo bai tsaya sauraren ta ba bare ɓacin ran da ta nuna. Yana isa ya samu Abdurrashid ya fito zuwa masallaci tare suka yi sallar sai suka shiga ciki. Hamida da ta shiga ɗaki wayarta ta janyo ta kunna ta ta shiga Whatsapp saƙon Hanan da Mimi ta yi ta gani suna mata tsiya ta bi miji ta bar su. Murmushi kawai take yi Abdurrashid ya shigo ta ɗaga ido ta dube shi "Wai ke ba ki da wasu kaya sai irin waɗannan ta dubi jikinta doguwar riga ce da ta kamata daga sama sai aka buɗe ta daga ƙasa bai saurari amsar ta ba ya shiga ciro kayanta cikin wardrobe ganin duk irin su ne ya ja tsaki ke a tafiyar da na yi gabaɗaya ma kin manta ke matar aure ce sai ya juya ya bar ɗakin. Bayan tafiyar Usman ɗaukar ta ya yi suka fita wani babban Mall ya kai ta ya zaɓar mata kaya irin waɗanda suka yi daidai da ra'ayin sa na ɗinki ya bayar da ɗinki sai suka tafi gida yana gaya mata waɗancan shi kaɗai za ta riƙa sanya nawa. Kwanakin da suka biyo baya amarci kawai suke kwasa ba shiga ba fita Hamida da Abdurrashid ban da ma Usman da ke yawan takura musu da zuwa shi kuma matarsa Jamila ta yi ma Abdurrashid waya ta kai mishi ƙarar Usman ɗin tunda ya dawo ya birkice mata,ga yawan fita baya son zama a gida. Haƙuri ya ba ta da ya yi ma Usman magana cewa ya yi share ta ƙorafi ne irin na mata. Abdurrashid ya ce A'a dai mutumina ka dai gyara. Ganin ba su da niyyar komawa Yola bikin Mimi, Hamida ta tambayi Abdurrashid ya ce ba inda za su amarci suke. Kuka ta yi ta yi bai saurare ta ba ganin hakan ba zai fisshe ta ya sa ta canza dabara. Ya fita sallar magrib ta sheƙa kwalliya ga ƙamshi na musamman tana yi wasu riga da wando ta sanya rigar kamar best take ta kama jikinta sai guntun wando da mazaunai kawai ya rufe mata ya shigo ya ga fitilun falo a kashe sai hasken TV da ke magana. Cikin matuƙar mamaki ya nufi wurin kunnawa carab! Ya ji an rungume shi ta baya wani mamakin ya kuma kama shi don bai yi zaton Hamida za ta iya masa haka ba,ya birkito ta gaban shi sai ya kunna wutar yadda ya gan ta sai ya ɗauke wuta kan kujera ya ja ta duk wasu wasanni da yake mata yau ta zage tana yi masa, gabaɗaya ta sukurkuta shi ta gigita shi don ta mayar mishi da martani ba kullum da take barin sa ya yi kiɗansa da rawarsa don kunya da rashin sabo. Maganganun da yake mata cikin fitar hayyaci ya sa ta fara kukan kissa wanda ya kiɗima shi yana tambayar ta meye ta ce bikin Hanan ya ce yaushe kike so mu tafi? Ta ce "Gobe." Sumarta ya shafa sai ya gyaɗa kai. Bayan lafawar komai ɗaki ta wuce ta gyara jikinta sai ta fito Usman ta gani zaune da matarsa a falon cikin fara'a ta ƙarasa ta zauna tana masu maraba kafin ta miƙe ta kawo musu ruwa da lemo ta wutsiyar ido ta dubi Abdurrashid da ke zaune kamar bai gama wattsakewa ba. A cikin hirar su ta ji yana gaya wa Usman gobe za su koma Yola biki don jibi ne bikin. Sun shiga ciki da Jamila ta samu ta gujewa mayataccen kallon da Usman ke mata wanda ya fara damun ta. Da ta yi wa Abdurrashid complain ɗin abokinsa ya cika yawan kallo cewa ya yi haka yake tun ba mata ba shi ya sa nake so in za ki fito ki riƙa rufe jikinki. Sun ɗan taɓa hira da Jamila kafin suka tashi tafiya ta haɗa mata kayan kwalliya ta bi ta da su zuwa mota sai da suka tafi suka juyo. Hakan aka yi washegari suka kama hanyar Yola. Sun sha shagalin biki inda aka kai Amarya Bauchi. Duk yadda Abdurrashid ya kasa ya tsare sai da ya tafi ya bar Hamida don Monday zai koma office kuma Aunty Karima ta ce sai Monday za su koma ita da Hamida. Hamida na can suka yi waya da su Innawuro inda ta ba ta labarin zuwan Abdurrashid da alherin da ya baibaye su da shi,sai ta gane daga Adamawa Daura ya wuce. Ranar da suka dawo da hantsi suka dawo Hamida ta gyara wurinta ta yi girki da kanta saboda Abdurrashid, ta yi wanka da kwalliya na jiran mijinta sai ta tafi wurin Aunty Karima don gaida Engineer Shehu Bello wanda shi ma jiya ya dawo ƙasar. Da ta dawo daga gaishe shi ta je ta gaida Mami sai ta yi ƙarshe da wurin Aunty Karima ba ta so Abdurrashid ya dawo tana nan ga Aunty Karima na mata hira hakanan dai ta daure ta ce za ta koma gida Auntyn ta ce muna hira ta yi murmushi ta ɗan ƙara zama sai kuma ta miƙe ta yi mata sallama ta fita ta zo ƙofar da ta raba gidajen nasu tana turawa suka yi kaciɓis da Abdurrashid murmushi suka yi wa juna don sun yi missing ɗin juna na kwana biyu hannunta ya kamo ya sa ta jikinsa suka nufi gidansu falon su suka yi masauki sai da ya gama yamutsa ta ya sake ta da ƙyar suka ci abinci sai suka shiga ɗaki. Ganin ya je Daura ya gaishe su washegarin dawowar ta da yamma ta same shi da zancen su je gidan Gwoggonta da ganin fuskarsa bai so ba sai dai bai yi musu ba. A ƙafa suka taka suna shan gaisuwa daga mutanen Estate ɗin idan sun hadu da su. Gwoggo tana ta ina aka saka ina aka aje da su,zaman awa ɗaya suka yi ya ce su koma gida ba ta ji daɗi ba sam da ko kwabo bai ba Gwoggonta ba tana mamakin yadda yake wa 'yan Daura alheri amma bai son ba Gwoggonta. Har sun fita ta ce mishi tana zuwa ta koma ciki ta miƙa wa Gwoggonta kuɗin da ta sanyo a jakarta "Ga shi in ji shi." Gwoggon ta amsa tana ƙoƙarin ƙirgawa tana taɓe baki "Shi duk kuɗinsa iya alherinsa kenan? Hamida ta juya tana faɗin "Sai mun yi waya Gwoggo." Abdurrashid da ya koma bakin aikinsa Hamida ma ta koma makaranta. Ranar wata Laraba ta dawo makaranta Abdurrashid ya je aiki Kaduna jiya ya tafi kwana uku zai yi. A gajiye take sam ta manta ta sa key ma ƙofar falonta ɗakinta ta wuce ta rage kayan jikinta don zafi da ake ba kama hannun yaro, doguwar riga ce a jikinta ta saman ta cire ta bar ta ƙasan mara hannu,kanta ba ɗankwali ta fito falo tana miƙa Usman da ta gani zaune cikin ɗaya daga cikin kujerun falon ya sa ta gintse hammar, ta juya ciki da sauri mayar da yar saman rigar ta yi ta ɗaura gyalen rigar sai ta kuma fitowa yana zaune inda ta bar shi yana aika mata kallon da ta tsana yake kuma takura ta ba sakin fuska ta yi mishi sannu da zuwa shi kam sai faman murmushi yake, ta wuce ta kawo mishi lemo da ruwa ba ta zauna ba kitchen ɗinta ta wuce ta zuba abincinta ta ci sai da ta gama ta zubo ta kawo mishi ta koma nesa da shi ta zauna labari yake ta mata tana amsa shi da ƙyar wata har yamma ta fara ya ƙi tafiya gabaɗaya ta takura don yana yawan yi mata haka idan Abdurrashid ba ya nan ya zo ya yi mata zaune kuma ta lura baya son ta kawo mishi laifin abokin na shi wata leda da ya ajiye ya miƙo mata yana miƙewa "Ga wannan na sawo maku ke da Jamila "Ba ta tashi ba ta ce "An gode. Sai ya yi ɗan sororo ya ajiye a wani ɗan stool da ke kusa da shi ya fita ta bi ƙeyarsa da harara. Nan ta bar ledar ba ta taɓa ba har Abdurrashid ya dawo ganin ya dawo ya same ta har an kwana tana nan inda ya bar ta ba ta ɗauke ba ya magantu "Ledar meye wannan ke ajiye tun dawowa ta ba ki ɗauke ba? ta dubi ledar kamar ba ta son magana ta ce "Usman ne ya kawo min da ya zo." Ya ɓata rai "Wai meke damunki game da Usman Hamida abokina ne fa kuma aminina ba ni da wani amini sama da shi ba na jin daɗin yadda kike mishi." Shiru ta yi ta sunkuyar da kai "Zo ki buɗe meye ya kawo miki? Shiru ta yi ta nufo ledar duk da ya fi ta kusanci da ita, ta ɗauka ta ciro ɗanɗasheshiyar sarƙa ce Dubai da ke ta sheƙin ɗauke ido bai ce komai ba ita ma haka sai juyawa ta yi zuwa ɗaki da nufin kai wa ta ajiye da gudun kar Abdurrashid ya kuma magana kan abin da ta yi. Watan su tara cif da dawowa Jamila matar Usman ta haiho ɗanta namiji Hamida ta je barka ta je suna,duk da Jamila ta girme mata nesa ba kusa ba shiri sosai suke suna ziyartar juna daga lokaci zuwa lokaci, Hamida dai ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba. Wasa wasa har ta kusa kammala digirinta wanda Exam biyu ya rage mata ta kammala haihuwa shiru. Zuwa lokacin haihuwa take so kamar ta janyo, Abdurrashid ko da ba me yawan magana ba ne ta san yana so. Addu'a dai take ta yi ko aikin hajji da umra da suka je addu'a ta farko da take fara yi Allah ya ba ta haihuwa ya ba ta ɗiya masu albarka. Tana zaune wani weekend Abdurrashid da ya leƙa barrack ɗinsu, da yamma ya dawo ya ce ta shirya su je ganin Likita ta yi ta tunanin abin da zai kai su sai da suka je ta ji complain ɗinsa kan haihuwa ne, wani abokinsa Dr Nasir suka gani an yi gwaje-gwaje da bincike-bincike sun ta sintirin zuwa Asibitin amma ƙarshe sakamakon ya nuna ba komai ba su da wata matsala lokaci ne kawai bai yi ba. Wannan ita ce rana ta farko da Hamida ta yi ta zubar da hawaye saboda rashin haihuwa,gane shi ma Abdurrashid ɗin yana so idan ya gaji daga jin lafiyarsa ƙalau zai iya yi mata kishiya. Yin wannan tunanin ya sa ta ƙara rushewa da kuka, Abdurrashid da ke ta duban ta tun dawowar su tana koke-kokenta ya ga ba ta da niyyar dainawa kamo ta ya yi ya sa bisa gado sai ya ɗora mata nauyinsa, maganganu yake gaya mata na tawakkali da dangana,sai ya shiga share mata hawaye,sai da ta haƙura suka yi soyayyar su. [2/9, 09:43] Original: SHiRIN ALLAH.... RAYUWA No.23 Maryam litee Har wadanda ke ciki suka fito suka shiga cikin gida ba su lura ba. Isowar Daddy dan wurin Aunty Safiya ya zo da gudu ya ce musu wallahi Hamma ya dawo. Hanan ta dan harare shi "Wuce nan mai karya kawai." Yaron ya dan yi narai narai kafin ya hau rantse sai ga yara sun yi hudu da gudu suna fadin Hamma ya dawo cikin suka bi su cike da mamakin ta inda Hamman ya shigo su ba su gan shi ba dan sun manta da motar da ta shigo. A babban falon gidan kowa na zaune ana ta farin ciki da murna na dawowar Abdurrashid shi din yana zaune tare da abokinsa Usman yadda su Hanan suka gaishe su sai dai ba su zauna ba suka shige ciki Hamida gado ta fada ragwab tana jin ta a wani yanayi wai yau Abdurrashid ta gani da ma zai dawo kamar yadda kullum take kwana ta tashi da tunanin hakan. Hanan da Mimi sai shegantaka suke mata Hanan na cewa Hamida za ta riga Mimi amarcewa. Sun dade a dakin kafin Aunty Zainab ta shigo "Ku da ma kuna nan ? Ke Hamida mijinki har zai tafi ba ki mishi wata gaisuwar kirki ba." Hanan da Mimi suka hada ido "Tafiya kuma Aunty? In ji Hanan"I za su je gidan Daada shi da abokinsa. Mimi ta ce "Wai yaushe ya dawo ? Aunty Zainab na juyawa ta ba ta amsa "Jiya ya dawo,fito Hamida ki je ki same shi har sun fita." Hanan ta kamo hannunta tana jan hanci wai guda take mata ganin ta ki tashi Mimi ma ta kamo dayan hannun dole ta tashi ta fara takawa suna mata sowa. Abdurrashid da ke tsaye jikin motarsa shi da Usman bayan samun wayar Aunty Zainab da ta ce kar ya tafi ya tsaya Hamida ta zo su su gaisa Usman ke ta magana yana sauraren shi "Wai yanzu duk zuka zukan yammatan nan yan'uwanka ne? Kai Abdurrashid ya daga mishi "To ina amaryar tamu don ban gan ta ba cikin su (Don ba wani sanin Hamida ya yi ba ganin sa da ita bai fi biyu ba tun kan su tafi ko a hoto bai kara ganin ta ba) "Tana nan kuma cikin su." Abdurrashid ya ba shi amsa "Na ga wata a cikin su kallo daya na yi mata ta tafi da ni kuma gaskiya zan gaya maka ina son ta." Ta wutsiyar ido Abdurrashid ya dube shi kafin ya kai ga magana Hamida ta tunkaro su ganin dan gyalen da ke jikinta bai boye komai na halitttarta ba ya bata ran Abdurrashid ganin ga Usman a wurin. Motar kawai ya bude ya fada ya ce ma Usman "Bismillah mu wuce." Ta karaso daidai Glass din da yake haramar rufewa ta tsaya ya yi bala'in daure fuska ya dube ta "A haka kike fita kina ganin daidai kike da su Mimi? Ido ta kada ba ta yi magana ba wanda ya sa ba Abdurrashid ba hatta Usman da ya kafe ta da ido sai da ya ji ya fada wani yanayi. Ganin ba ta da niyyar magana ya ce "Kauce to za mu wuce." Ta juya don komawa ciki Abdurrashid ya hadiyi wani abu don takaicin Usman ya ga bayanta. Har ya tayar da motar ya bar gidan Usman bai dawo daga kidimar da ya yi ba fahimtar Hamida da ya gani zuciyarsa ta amsa daga kallon farko da ya yi mata ita ce matar amininsa wani zafi kirjinsa ya dauka har suka shiga gidan Daada ba wanda ya yi magana kowa da abin da ke damun zuciyarsa Usman sai mamakin Abdurrashid yake kana da wannan tsaleliyar macen ka yi tafiyar shekaru ka dawo kuma ka bar ta ka kwana kai kadai. Da ya rufe idonsa hotonta ke masa gizo,wani irin yanayi yake ji da bai misalto,a wahalce ya ga wayewar gari. Har suka shirya suka yi wa Daada sallama suka koma gidan Aunty Zainab don yi musu sallama su koma Kano a yau. Sun zauna falon Daada inda iyayen ke zaune aka kawo musu abin karyawa duk da sun ce sun karya a gidan Daada suna yar hira sama sama. Hamida da ba ta san zuwan su ba ta fito don shiga kitchen ta samo ruwan zafi ta hada Tea daga ita sai rigar barci kalarta sky blue mai botura a gaba hannunta guntu ne,kanta ba komai sai kwantaccen gashinta da ta kama da ribbon sai da ta ratsa su ta ga Abdurrashid da Usman ta kara da sauri ta shige kitchen din Yayin da wani shauki ya dauki Usman wani tukukin bakin ciki ne ya turnuke Abdurrashid ganin Hamida a haka ga Usman zaune. Kasa fitowa ta yi daga kitchen din har mai aiki ta shigo ita ta aika wurin su Mimi ta ce su ba ta after dress ko hijab, after dress din aka kawo mata ta zura ta rufe gyalen sai ta fito ba ta yarda ta dubi inda suke ba ta shige daki su Hanan na zaune a dakin Mimi, Mimi na danna wayarta Hanan na yan wake wake,ta zauna tana kurbar Tea a hankali. Abdurrashid da ke zaune ya rasa yadda zai yi ya tashi zuwa dakin da Hamida take sai kallon kofar da ta shiga yake hakika ya zo ne don ya tafi da matarsa amma ya rasa yadda zai dubi idanuwan su Momy ya fada musu hakan. Da dai ya ga ba shi da zabi rufe ido ya yi ya mike ya ce ma Usman yana zuwa. Murda handle din kofar ya sa kowacce ta dago ido ganin shi ne kowacce ta shiga nutsuwarta sun fara gaishe shi kafin kowacce ta sulale suka bar dakin suka bar Hamida da ta sunkuyar da kai ganin fitar su ta soma gaishe shi,bai amsa ba sai hannayensa da ya harde a kirji ya sa mata ido "Ke haka kika ga ana tarar miji idan ya yi doguwar tafiya? Kai ta dago sai suka hada ido ta yi saurin mayar da kan ta sunkuyar "Ka yi hakuri. Kalmarki kenan a yi hakuri, me ya sa kike fita yadda kike fita ko kin manta igiyar auren da ke kanki? "Na bari ka yi hakuri. Ta kuma furtawa a hankali "To ni zan tafi sai kin dawo kenan." Saurin duban shi ta yi ganin sun hada ido ta kauda kai, ya juya don barin dakin komai ka sa cewa ta yi har ya fice ya ja kofar. Tana nan zaune ta ji wayarta ta dauki kara cikin sanyin jiki ta mika hannu ta dauko ta Abdurrashid ne ta daga ya ce "Ki same ni ina waje." Kai ta daga kamar yana kallon ta sai ta mike ta tube rigar barcin ta fada bathroom wanka ta yi cikin sauri ta shafa mai ta murza hoda ta dan sa turare,jallabiya baka da gyalenta ta sanya sai ta fita cikin sauri sanin ta bata lokaci. Wani dan lungu da idan ka fita zai kai ka parking space nan ta bi, Abdurrashid ta hango karshen lungun ya sa gudun numfashinta ya karu ta dai daure har ta isa inda yake ji ta yi ya fizgota ta ya sa ta a bango sai ya matse ta. *Wai me kike yi min haka? Kin ki fitowa ne don in gaji in tafi? Daga abin da kike min kenan, to na fasa barin ki anan da ke zan tafi." Ya fadi cikin rada da sai ita da suke hade kadai za ta iya ji. Usman da ke cikin mota yana hango Abdurrashid a lungun,ganin ya matse Hamida ya ji wani abu ya danne mishi kirji ya runtse ido cikin matukar takaici . Hannunta Abdurrashid ya kamo suka fara tafiya inda motar take a baya ya cusa ta ya koma gaba ya zauna kusa da Usman da ke driver seat ya tashi motar ya zurfafa cikin tunani ya ji Abdurrashid na taba mishi kafada kallon shi ya yi sai ya ji muryar Hamida a baya tana fadin ina kwana sanin da shi take ya amsa yana dan tonon ta. Sun isa Airport sai da suka sayi ticket din Hamida suka zauna har jirgin ya karaso. Da suka sauka airport na Kano sun samu Baba Adamu yana jiran su. Sai da suka sauke Usman a gidansa sai suka wuce sabon gidansu suka sauka,alwala Abdurrashid ya yi da shigar su ya wuce masallaci. Hamida tana ta ta alwala tana jin yana kara burge ta saboda tsaida sallarsa,kafin ta kabbara sallah sai da ta kunna wayarta don tana ganin sun baro gidan Daada ta kashe ta gudun kar a kira ta ta ce me? Baba Abu mai aikin Aunty Karima ta kira ta shaida mata sun dawo ta kawo abinci a gidansu idan sun gama. Tq cilla wayar bisa gado bayan ta kuma kashe ta ta tayar da sallar. Ta idar tana addu'a Abdurrashid ya shigo kallo daya ta yi masa ganin daga shi sai guntun wando sai ta sunkuyar da kai ya tako inda take hijab dinta ya zare sai ya dago ta ya sa ta a jikunsa ganin yana kokarin cire mata riga ta narke mishi "Yunwa nake ji." Yi ya yi kamar bai ji ta ba ya cigaba da shafa ta knocking din da aka fara ya sa ya sake ta ya zauna bakin gado ya dafe goshi da sauri ta nufi kofa don da gaske yunwa sosai take ji. Ta tari Baba Abu ta karbi babban tray da ke hannunta sun gaisa babar ta yi mata barka da dawowa sai ta juya ita kuma ta isa dinning ta ajiye za ta juya ta kira Abdurrashid ta ji shi bayanta ta bayan ya rungume ta sun jima a haka kafin ya sake ta ya ce ta ci abincin shi ta fara zuba mawa sai ta zuba ma kanta tana ci tana jin idanuwansa na yawo a kanta duk da ta ki daga ido har ta ji ta koshi ta mike ta ture kujerar ya ce "Ina za ki? Kai ta langabe "Wanka zan yi." Ya ce "Haba wane ke yarinya na dai yi hakuri kin ci abinci. Daga haka hannunta ya kamo zuwa dakinsa bai saki hannun ba sai bisa gadonsa, a ranta ta ce da ne yake dauka ta ,yanzu ko ko da yake soja sai ya yi da gaske ya iya daga ni." Nauyinsa ya daura mata yana gaya mata maganganun da suka sa ta runtse ido ya fara nisa wayarsa ta shiga neman agaji,banza ya yi da ita ta har sai da tsinke ta kuma daukar wata karar ya dauko ta da niyyar kashe ta sunan Aunty Safiya ya gani yana yawo saman screen din kasa kashewar ya yi ya daga "Hello Aunty." Daga can bangaren ta ce "Ka tafi da doughter ne ? Ya ce I Aunty." Yana jin sautin ajiyar zuciyar da ta fidda ta ce "Sai da anjima." Ta katse kiran ya cillar da wayar ya dawo kan Hamida wadda ta kashe kunne tana sauraren su. Komai ya gama kwance mishi wayar ta kuma daukar kara ,wannan karon bai bi ta kanta ba ta yi ta yi tana tsinkewa har Allah ya gajiyar da mai kiran ya hakura. [2/9, 09:43] Original: *SHIRIN ALLAH... RAYUWA* No.25 Ranar wata juma'a ba ta shiga School kwance take a ɗakinta wayarta ta yi ƙara, Jamila ce matar Usman ke shaida mata ta haihu. Ta tashi zaune fara'a kwance kan fuskarta take faɗin "Me muka samu? Ga ni nan zuwa." Ta ce "Mace ce." Ba ta daɗe da yin wanka ba ta kwanta don haka kayan jikinta kawai ta canza sai ta tura wa Abdurrashid text message za ta tafi gidan Usman Asma'u ta haihu. Don ba ya garin. Tana shirin tana tuna abin Allah, Asma'u daga dawowar su Abdurrashid yanzu haihuwa ta uku kenan ta yi maza biyu yanzu ta yi mace. Baba Adamu ya kai ta, ta iske mai jegon a bed room ɗinta ta ɗauki jaririyar suna ta hira take cewa Hamida daga wannan ta tsaya sai ta huta sai ka ce kaza duk bayan shekara biyu sai ta haihu? Wani iri Hamida ta ji ta ce "A'a dai Maman Sultan,ki gode wa Allah wani ɗaya ma yake nema bai samu ba." Sai ta ji Hamidar ta ba ta tausayi ta ce "Haka ne fa kuma, Allah ya kawo muku kuma mu sha suna. Ko da ina naƙuda sai da na yi miki addu'a,daga an ce addu'ar mai naƙuda amsassa ce." Hamida ta ce "Na gode Maman Sultan." Murmushi ta yi "Meye wani abin godiya? Abban Sultan ɗin ma ya ce sunanki ya sanya wa babyn don wai son da muke wa juna da ke." Wani iri Hamida ta ji ga sunan uwar shi bai sanya ba,ga na uwar matarsa sai ta kanne ta ƙaƙaro murmushi har da yin godiya. Suna nan zaune suna hira time ɗin da ta ce Baba Adamu ta ji shiru tana ƙoƙarin kiran shi a waya Usman ya shigo ɗakin ta gaishe shi tare da yi masa barka ya ce "In kin tashi tafiya sai in sauke ki, don na ce wa Baba Adamu ya je abin shi. Hamida ta ce"Ai yanzu ma zan tafi zan yi karatu mun kusa fara Exam." Jamila ta riƙe baki "Kar dai kin kusa kammala karatunki ? Hamida ta ɗaga mata kai "Daga wannan Exam na gama." Ta riƙe baki"Kin ga ina zaune har kin tashi wasa, kullum ina waƙar komawa karatu ɗawainiyar ciki da goyo ya hana, ai yanzu dai zan tsayar da ita Allah karatu zan koma." Hamida ta yi murmushi "Ka ji Maman Sultan." Usman da ke tsaye yana jin su ya juya ya fita ita ma sallamar ta yi mata ta bi bayansa duk da ba ta son tafiyar tasu tare ya buɗe mata gaba ta shiga. Sun fara tafiya suke zancen ranar da Abdurrashid zai dawo kafin ya ɗan dube ta sai ya maida idonsa kan hanya "Ai abokina ba ƙaramar sa'a ya taka ba, ga lafiyayyar mace ya samu yana ta more rayuwarsa shi ya sa kullum za ka gan shi yana wani ƙara annuri abin sa, to ya samu duniya ga ba ruwan shi da kataniyar yara da za su hana shi morewarsa. Ɗif! Hamida ta ɗauke wuta jin zancen Usman me zai sa ya gaya mata haka duk da a take takensa ta san zai iya hakan. Zai cigaba ta ɗaga mishi hannu "Haba mana Usman." Ta ambaci sunansa saɓanin Abban Sultan da take ce mishi "Ina matsayin matar amininka da ya ba ka yarda kana faɗa min irin waɗannan maganganun hakan sam bai dace ba." Wata 'yar dariyar da ta ba ta mamaki ya saki ya turo hula gaban goshi da gani cikin nishaɗi mai yawa yake. Ya ce "Allah gaskiya na faɗa,abokina ya caɓa ya samu luntsumemiyar mace sai dai ya yi ta buga duniyarsa ya.... Cikin tsawa ta katse shi "Ka tsaya in sauka Usman! Ba tare da nuna damuwa da tsawar da ta yi mishi ba ya ƙara faɗaɗa fara'arsa "Wallahi yau cikin nishaɗi nake mai yawa,jerawa da macen da ta amsa sunanta ma ai ba ƙaramin cinyewa ba ne." Gabaɗaya Hamida ta taso ta daddanƙara mishi magana ta ce kuma sai ta faɗi ma Abdurrashid ko a jikinsa sai shafa haɓarsa yake yana murmushi ya ce "In zan ba ki shawara ki yard kar ma ki soma gaya mishi don reshe zai iya juyewa da mujiya, ko in ce ke za ki kwana ciki don yardar da mijinki ya yi min Ta kuma cewa "Ka tsaya in sauka." Ya ƙi tsayawa ta saukan kuma bai fasa murmushn ba. Yana tsaida motar yana horn kafin mai gadi ya zo ya buɗe ta ɓalle murfin ta fice, lokacin da mai gadin ya wangale gate ɗin bai shiga da motar ba tsayawa ya yi yana duban Hamida da ke tafiya a fusace wata irin sha'awar ta na ƙara fizgar sa yana jin sai dai ya ɓata da Abdurrashid amma sai ya ba zuciyarsa abin da take so. Sai da ta sha kwana ya daina ganin ta sai ya juya kan motarsa bayan ya yi wa mai gadin da ke ta gaishe shi alheri. Ita kam tana shiga ɗakinta rub da ciki ta yi bisa gado tana tunanin wannan al'amari mai ban takaici da ɗaure kai sai lissafin yadda za ta tunkari Abdurrashid da wannan zancen ta ce amininsa ya yi mata haka da ita zai yarda ko da shi gane rashin alfanun bayyana zancen ya sa ta bar shi a ranta. Ba ta ƙara komawa gidan Usman ba waya ta yi wa Jamila ta yi mata ƙaryar ba ta da lafiya, ita kuma sai cewa take Allah ya sa ƙaruwa muka samu. Ranar suna kan ba yadda za ta yi ta je. Sai yamma liƙis da Abdurrashid ya zo wurin Usman da suka gama hirar su ya yi mata waya ta fito su tafi da ta fito yi ta yi kamar ba ta da lafiya don kar ta gaida Usman sai ta ji almurin yana cewa Abdurrashid "Madam kuwa lafiya take?" Kallon inda take tsaye za ta shiga mota Abdurrashid ya yi "To ni dai ban san wani abu na damun ta ba." Ya faɗa motar suka bar wurin sai da ya hau titi ya dube ta "Me ya same ki ake cewa ko ba ki da lafiya? Fari ta yi masa ta kaɗa ido "Ni na cewa wani ba ni da lafiya? Bai ce komai ba sai idonsa da ya mayar titi. Hamida ta kammala Exam ɗinta ta ƙarshe ta dawo gida tana murna a gidan ta iske Abdurrashid gaban Computer shi yana aiki, ta ɗora hannuwanta kan kafaɗarsa ta rungume shi ta baya tana raɗa masa yau ta kammala karatunta. Ya waiwayo sai ya janyo ta ya zaunar da ita kan cinyarsa, "Kin kammala sai a zauna gida kuma hakanan a huta Madam." Ta kaɗa hannu "Zan cigaba da karatuna sai na ga ƙarshen biro da takarda, ni ba yara ba gara in ta karatun zai ɗauke min hankali daga damuwar hakan a.... Hawayen da suka taho mata ya sa ta yi shiru sai ji ya yi hawayenta ya ɗigo masa a wuya ya sa hannuwansa ya tallafo fuskarta ya haɗa fuskokin su "Me ya sa kike son jayayya da hukuncin ubangiji? Duk waɗanda suke cikin duniyar nan ba a ba su haihuwar ba haka kika ga suna zama su yi ta koke-koke? Ki yi haƙuri daga an ce lafiyar mu ƙalau lokaci ne in sha Allah za mu haihu." Ya kamo ta suka miƙe tsaye sai ɗakin barcinsa a can aka idasa lallashin. Washegari ta samu baƙuncin Walida don sun yi waya take shaida mata ta kammala Exam ɗinta sai duban ta Hamida ke yi don sun daɗe ba su haɗu ba, ta yi wata uwar ƙiba ta zama babbar mace, ba ta cika zama ba kullum ba ta nan ba ta can da ganin ta ka san ta bauɗe ta saki layi. Tunda ta kammala NCE ba ta ci-gaba da karatu ba a can ta haɗu da ƙawayen da idonta suka ƙara buɗewa ta fara hulɗa sosai da maza masu naira. Sai karakaina Hamida ke yi tana cika ƙawarta ta da kayan maraba da baƙo. Sai da suka yi nisa cikin hirar su Hamida ta ce "Ya kamata Walida ki yi aure hakanan, dubi aurena yanzu fa shekarata tara." Ido Walida ta buɗe "Gaskiya kin daɗe da shiga ciki don dai shekaru biyar ɗin farko Ogan ba ya nan, to amma ni Hamida sai in ga meye maraba ta da ke, ko don kina cikin daula shi ya sa ba ki ga illar zaman da kike yi ba har yanzu ba haihuwa ba? Gabaɗaya Hamida ta ɗauke wuta in har Walida za ta yi mata gorin haihuwa to wa ya saura mata da ba zai mata ba? Muryar Walidar ta ji "Kodayake kin san ana gadon rashin haihuwa shi gidansu ba gidan haihuwa ba ne abin ya sa ki tsakiya." Cikin danne fushinta Hamida ta ce "Komai na Allah ne ni na dogara gare shi." Walidar ta ce "Kin ko yi farar dabara. Yawwa Hamida wata abaya da na ga kin sa a status na cikar auren ku shekara tara ita za ki ara min,akwai wata fita da za mu yi ba ta wasa ba ce,ki haɗa min da jaka da takalman da kika sa." "Haba dai ai kin wuce in ba ki aro,ina zuwa." Ta faɗi tana yunƙurawa yadda ta ce haka ta haɗo mata har da kuɗi dubu goma tunanin ta ko Walidar ba ta da kuɗi a ɗan datsin shi ya sa ta nemi aron kayan don tana ganin hotunanta da take ɗorawa a kafafen sada zumunta ba ƙaramar shiga ta alfarma take ba. Ta zo ta miƙa mata, leƙawa cikin ledar ta yi tana kallon kayan ganin kuɗin masifa ta kama a ranta "Ita wannan tana ba ni yan wannan kuɗin,tana tunanin yanzu da ce,kayan ma na tambaye ta ne don raba mugu da makami. Hamida kuma tana ta ƙara mamakin ta a ranta na yadda ba ta taɓa ba ta abu ta iya furta kalmar godiya ba. Suka ci gaba da hirar su har Walida ta yi shirin tafiya wani ne ya zo ya ɗauke ta. Da ta dawo rakiyarta ba ta zauna ba wurin Aunty Karima ta wuce suna hira har magrib nan ta yi sallah sai da Abdurrashid ya shigo bai zauna ba ya ce ta zo su tafi, sun fito yake ce mata Mami ta kawo ƙarar ta cikin mamaki ta dube shi da tambayar me ta yi ɗauke kai ya yi "Ta ce in kin shigo ba ki shiga ki gaishe ta." Sanin ba shigar take ba ya sa ta yi shiru. Ya ce "Mu je yanzu mu gaishe ta." Suka karkata zuwa part ɗin Mamin, ba ita kaɗai suka samu ba su uku ne da wasu 'yammata su biyu. Sai da suka gaishe ta take ma Abdurrashid bayanin bai gane yammatan ba ? Ya ce "E." Ta ce "Yaran Haj Hanne ne babbar ɗiyar Haj yar Gambo yayar mahaifisa. Ya kaɗa kansa ta ce "Saboda sun tashi a Lagos ne shi ya sa ba kowa ya san su ba daga ba cika zuwa Arewan suke ba." Ta faɗi tana wani murmushi Ya miƙe Hamida ta mara masa baya suka bar falon ɗaya daga cikin su na cewa "Sai mun shigo Uncle." Ya ce "Ok. Washegari ya dawo aiki yana cin abinci sai ga su sun shigo sai mamakin shigar da babbar ta yi Hamida ke yi matsattsun riga da skirt ne na English wear sai karairaya take kamar tarwaɗa. Abdurrashid da bai wani sakar musu fuska ba daga gaishe shi da suka yi yana gama cin abincisa ya tashi ya shige ciki, Hamida ta ga kar ta bar su su kaɗai sai ta cigaba da zama ba ta bi bayan mijinta ba, tsaki dukkan su suka ja sai suka miƙe suka bar falon, ta bi su da kallon mamaki kafin ita ma ta miƙe ta bi mijinta. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH RAYUWA No.26 MARYAM LITEE Washegari ta fita game da karatu ta da take son ta jona masters ta tsaya restaurant ɗin Gwoggo,sun daɗe suna hira kan mutanen Daura dan sun kwana biyu ba su je ba ita da Gwoggon. Sun gama ta rako ta inda ta parker motar ta ta ga wucewar baƙin yammatan nan na part ɗin Mami wanda take jin sunan su Anisa da Amira,babbar ce Anisa, ta faɗa motarta ta bi bayan ta su motar. Ba ta shiga gidanta ba yankewa ta yi ta fara shiga wurin Aunty Karima ta gaishe ta don tana fama da mura,sai dai dokar da Abdurrashid ya sanya mata ta lallai ne ta shiga gidan sai ta shiga part ɗin Mami ba ta son ganin waɗannan yammatan 'yan rainin wayau da ta rasa uwar da ta yi musu indai za su gan ta sai sun ƙirƙiri abin da zai ɓata mata rai. Sun parker motar su ita ma ta parker kusan ma a tare suka fito tana rufe mota ta ji suna dariya "Ai ba ki san 'yar tuwo tuwo ba ce taɓ! Ai anan ya gan ta ana tallar abinci." Ƙaramar Amira ta fashe da dariya "Allah Aunty Anisa shi ne take wannan yauƙin kamar wata ɗiyar saraki? Anisar za ta yi magana sai ganin Abdurrashid suka yi da ba su san ta yadda ya zo wurin ba. Hamida wadda cin fuskar da suka yi mata ya yi matuƙar yi mata zafi ta fasa shiga wurin Aunty Karima ta gefen Abdurrashid da ita ma ba ta san ya aka yi ya zo wurin ba ta bi ta wuce gidanta, ɗakin barcin su ta wuce ta hau gado ranta na ci-gaba da suya,sai muryar Abdurrashid ta ji kanta "In kin samu lokaci ki je ki faɗa wa Gwoggoki na ce ta bar saida abincin nan." Saurin tashi zaune Hamida ta yi ta zuba mishi ido "Yes ta bari ta yi min lissafin abin da take samu a wata ki karɓo acc no ɗinta, ta kuma ba ki list na abincin da suke ci za a dinga kawo mata duk wata." Hamida ta karyar da kai "Anya za ka iya da Gwoggo Hamma? Da ka bar ta da sana'arta kar ta zo... Kina ganin ba zan iya riƙe ta ba ne, ko kina ganin duk abin da take samu ban da arziƙin ba ta? Kwantar da kanta ta yi duk yadda ranta ke ɓace ganin yadda ya hasala kuma bai san nufin ta ba don ba za ta fito kai tsaye ta faɗa mishi Gwoggonta ba ta da godiyar Allah duk yadda zai kai ga kyautata mata sai ta yi ƙorafi. "Ba ka gane ba Hamma ka bar ta da sana'arta saboda yau da.. ... "Yin sana'arta ba zai zama abin da za a riƙa goranta miki ba. Shiru Hamida ta yi gane cin fuskar da aka yi mata ya sa ya ce Gwoggonta ta bar sana'arta. Washegari ta shirya ta tafi wurin Gwoggonta a wurin sayar da abincinta sai da suka keɓe ta faɗa mata saƙon Abdurrashid duk da hango ci da ta yi sai da ta ciza "A'a fa Hamida kin san mijinki ba son taɓuwa yake ba." Hamida ta gyara zama "Kin san dai halinsa Gwoggo idan ba zai yi abu ba ba zai ce zai yi ba." Ta ce "Shi kenan, idan aka rubuta zan kawo ne? Hamida ta ce A'a ni zan rubuta miki Gwoggo yau ina nan tare da ke har ki tashi har abinci zan taya ki sayarwa." Gwoggo ta riƙe baki suka yi dariya a tare ta ce "Rufa min asiri. Ta tashi ta fita tana ci gaba da da dariyar. Nan Hamida ta zauna har sai da Abdurrashid ya koma gida ya kira ta a waya sai ta yi wa Gwoggon sallama ta koma gida. Washegari tana kwance a falonta sai ganin shigowar su Anisa ta yi, ba ta ko motsa ba har suka zauna. Sai dai ta ƙudura yau suka yi mata rainin wayo ci musu za ta yi, da ma tana ƙyale su ne don ba ta son wata fitina ta hada ta da dangin miji Amira ta fara magana "Na ƙosa Aunty a yi a yi ki shigo ki santalo mana baby kalar uncle daga ke kin gaji haihuwa ba juya ba ce, ba su cogal ba ana tafe ana dingisawa a haka a ka mutu kan su." Gabaɗaya Hamida ta miƙe sai dai kafin ta fara ce musu komai Abdurrashid da ke ciki ya tako tsakiyar falon kaca kaca ya yi musu ya ce su fita harkar matarsa kar ƙafar wadda ya kara gani. Ya dubi Anisa a fusace "A haka kike tunanin za a aure ki ballagaza kawai." Ta fashe da kuka ta ruga da gudu ta fice falon Amirar ta mara mata baya. Hamida ta koma ta kwanta ya tako zuwa inda take ya zauna kanta ya ɗora saman cinyarsa, sai ya yaye zanenta yana shafa ƙafarta da aka gama yi wa gori don ɗan adam tara yake bai cika goma ba tun Hamida na ƙarama ƙafarta ta ɗan buɗe tana girma tana raguwa to yanzu da ta girma sai ka sa ido da kyau za ka gane kafar ta ɗan buɗen. Kamar an tsikare ta ta tuna kalaman Amira ta tashi zaune ta tambayi Abdurrashid aka turo ƙofar Haj yar Gambo ce ta shigo a fusace tun kafin ta ƙaraso ta soma jidali "Ka kori yar'uwarka saboda matarka, to ko me za ka yi aure ba fashi,daga ko ubanka bai isa ya musa ba. Za a ɗaura aurenka da Anisa ko za ka samu rabo, kana zaune da mata kusan shekara goma ba haihuwa kai an haife ka kai kaɗai ba ka fatan ka haifa, shi ma uban naka da yake cewa ita ma ɗiyarsa ce don yar amininsa ce wa ya fi kusa da shi ita da Anisa?Cikin watan nan, za a sanya rana matar taka ta faɗi ta mutu." Ta juya a fusace. Aka shiga kallon kallo Abdurrashid da Hamida kafin ta fashe da kuka "Aure za a yi maka saboda ban haihu ba? Sai ta miƙe ta nufi ɗakinta ta rufe, ya yi bugun duniya da ban bakin ta buɗe amma ta ƙi. Da safe ma ba ta fito ba har sai da ya kira Aunty Karima, kira ɗaya Auntyn ta yi mata ta zo ta buɗe ta fito kanta a ƙasa tana gaida Auntyn. Aunty Karima ta dubi agogo "Hakanan ki azabtar da kanki, shiga kitchen ko Tea ki haɗo ki zo ki sha. Kitchen din ta wuce ba ta yarda ta dubi inda Abdurrashid ke zaune ba, ta haɗa ta fito a ƙasa ta zauna tana kurɓa a hankali. Aunty ta fara magana "Me zai sa ki rufe ƙofa? Ki yi haƙuri da abin da kika ji,ko Alh ba a san ransa yaya ta ƙulla wannan magana ba, amma ba yadda zai yi da ita. A maimakon fushi da addu'a kika kama kika yi ta yi inda sharri za a nufo ki Allah ya mayar wa Mutum abin sa. Haihuwa ta Allah ce, wanda ya so yake ba mu ba ga mu zaune ba, ita Haj Mariyar da ta ƙulla abin ta haihun ne? Ba hakana Alh ya zauna da mu ba? Haihuwa lokaci ne ko ni ban fidda rai ba ballantana ke da duka duka yaushe aka yi daren. Ki kyale su su yi ta abin su ,in sun aura mishi ita akan ki za ta zauna ki yi ƙoƙari dai ki kyautatawa mijinki shi ne ba wata kishiya ba,ki yi haƙuri don Allah. Hamida da ta kasa ci gaba da shan Tea jin da gaske dai kishiya za a yi mata, wata za a kawo su raba Abdurrashid da ita. Ta share hawaye ganin Auntyn ta mike ta fita Abdurrashid ya bi bayanta me mata aiki cikin masu aikin Aunty karima take ta kan taimaka mata saboda fita makaranta da take ta shigo sai da ta fara gaishe ta kafin ta soma ayyukan da take yi. Hamida kuma kitchen ta shiga don yi musu girki tana yi kuma tana share hawaye. Dole ta tilasta ma kanta haƙuri amma ƙasan zuciyarta kamar ta yi ta zunduma ihu. Su Anisan ma ba ta ƙara ganin su ba tun daga ranar don ko gidan ta shiga ba ta shiga part ɗin Mami,tunda ta ji Aunty Karima ta ce ita ta ƙulla a yi mata kishiya take jin haushin matar. Abdurrashid ya samu canjin wurin aiki shi da Usman zuwa barrack ɗin Abuja shi kaɗai ya tafi ya bar Hamida ranar da ya tafi sai ga yaran Mimi da Hanan. Hanan yaranta biyu Mimi tana da guda daya sai cikin na biyun, Affan yaron Mimi sai Afrah yar wajen Hanan, wai sun kawo yaran su taya ta zama kwana ɗaya suka yi suka tafi suka bar mata yaran, ta kan rungume yaran ta yi hawaye mai isar ta kafin ta share. Ta ji daɗin zuwan yaran sun ɗebe mata kewa sam ba ta gajiya da hidimar su, ana gobe za su tafi ya yi daidai da satin su biyu Abdurrashid ya ce mata ga shi nan zuwa. Cikin dare ya iso don kafin ta kwanta sun yi waya da Gwoggo Indo take tambayarta Abdurrashid yaushe zai zo? Ta ce bai faɗa mata ba. Ai kuwa sai ga Gwoggo ta yo sammako, a falo suka zauna Gwoggo na cewa "Bikin Yusuf dai na ta matsowa." (Ƙanen Hamida da ke bi mata) Hamida ta ce "E." Ta ce "To me za ki yi musu don mijinki ya kamata ace ya yi komai, amma ba zai iya ba." Shiru Hamida ta yi takaici ya hana ta ce mata yana ciki Gwoggo ta cigaba "To ni dai kuɗin da na faɗi ba su isa ta ki faɗi mishi." A ran Hamida ta ce ɗaya kenan. Kwantar da murya ta yi ta ce "Ke fa kika faɗi Gwoggo." "To daɗi miji,idan ba za ki faɗi mishi ba ke sai ki dinga ba ni, kina da miji mai kuɗi ba za ki dinga tambaya ya ba ki ba, yanzu ki duba gidanmu kowa ya gyara sasansu na ku fa mijinki ya gaza gyarawa, ke kuma ba za ki faɗi mishi ba " "Zai gyara Gwoggo,ba ya ba su gida ba sun ce ba za su koma ba wanda yanzu Yusuf zai zauna." Ta faɗi cikin takaici Gwoggon ma ina ta tsaya jin ta miƙewa ta yi Hamida ta bi ta a baya. Kwana biyu Abdurrashid ya yi har kuma ya koma bai nuna ma Hamida ya ji zancen su da Gwoggonta ba ita kuma ba ta ce masa komai ba, illa dai da suka tafi bikin ƙanen nata ita ma kam sai ta ji ba daɗi, kusan gabaɗaya gidan an tsara shi an mayar da shi ginin zamani kowa ya gyara wa iyayensa su Innawuro Engineer ya gina ma Malam tafkeken gida amma Malam ya ce ba zai tashi daga nan ba shi ne ya gyara musu sasan su. Laila ta gyara ma nata iyayen da daɗewa. Aina ta gyara nasu. Su Amina ne sasan su ba wani mai ƙarfi da Hamida ta tashi gyara nasu sai ta haɗa ta yi musu iri ɗaya ta mayar da shi na siminti a maimakon na ƙasa da, ba dai ta yi kamar na sauran ba. Abdurrashid da ya sai musu gida ƙi suka yi su koma. Abin da dai ya sanyaya mata rai da Abdurrashid ya haɗa wa Yusuf akwati har sadaki da abin da za a ci duka shi ya yi, nata da ta ruƙo za ta yi hidimar sai ta ba mahaifinta. Ana gobe ɗaurin auren Abdurrashid ya iso ya sauka gidan Engineer da ya saya don sauka idan ya zo garin. Da zai tafi masauki da daddare ya tilasta Hamida sai sun tafi tare,sulalewa ta yi suka tafi sanin ba mai ma gane ba ta nan don jama'a da ta yi yawa. Da ta tashi tun da safe yana barci ta zame ta gudu. Engineer ma ranar ɗaurin auren ya iso tare da Aunty Karima. Ana gama ɗaurin ya wuce Abuja,dama daga can ya zo. Ko da aka ƙare biki Hamida ta kwana biyu a Daura don ta daɗe rabon ta da garin nan Gwoggo da Laila suka tafi suka bar ta, Aina ma ta zo da yaranta biyu duka maza. San da ta koma Kano ta samu Abdurrashid ya zo kwanan shi biyu sati guda zai yi. Usman ma ya tafi da Jamila ta ma kira ta a waya ta yi mata sallama lokacin tana Daura. Washegarin da ta dawo ta idar da sallar sallar Isha'i tana shirin kwanciya, Abdurrashid ya shigo ya same ta, cikin jallabiya yake da Hamida ta ga ya matuƙar ƙara yi mata kyau a cikin ta, ta yi murmushi tana jin wata ƙaunarsa mai tsanani tana ƙara shigar ta "Zan je wurin Daddy in dawo." Ta ce "To ka gaishe da Daddy." Ta juya ta ci gaba da taje gashinta sai ta sanya hula ta sa rigar barci ta fito falo sai ta ji gabaɗaya zuciyarta ba ta kwanta da fitar Abdurrashid a daren nan ba. Ƙofar falon ta buɗe ta fita, ƙofar da ta haɗa gidajen nasu a buɗe take bai rufe ba turawa kawai ta yi ta ji ta buɗe sai ta shiga ta fara tafiya ta hango mutane biyu tsaye, kallon tsaf ta yi musu ta gane Abdurrashid ne, don inda suke ba wadataccen haske. Gabanta ya shiga lugude tabbatar da Anisa ce,ta ƙara takawa ɗaya biyu sai ta ja ta tsaya don ƙafarta da ta ji ta riƙe, Abdurrashid ya ba ta baya Anisa sai karairaya take daga inda take ba za ta zolayi kanta ba daddaɗan ƙamshin turaren yan Maiduguri har daga inda take tana shaƙarsa. Ta yi ta yi ta ja ƙafar amma ta kasa. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA NO.27 MARYAM LITEE Sun ɗauki ya yi minti ashirin kafin ya wuce, Anisa kuma ta yi part ɗinsu. Sai sannan ta samu ta ɗaga ƙafarta da ta riƙa ji kamar ba za ta ɗauke ta ba, ɗakin barcinta ta koma "Namiji munafiki.abin da take faɗi kenan a ranta yayin da ta rintse idonta hoton Abdurrashid da Anisa na gilma mata, ƙirjinta ta dafe da wani baƙin ciki ya tokare. Tana cikin da hawaye ta ji shigowar sa, ƙara rintse idonta ta yi "Yau nan za mu kwana kenan Madam? Ta ji muryarsa sai kuma ta ji ya fita. Ba a daɗe ba ya dawo gadon ya hau ya kwanta a bayanta ya rungume ta,jin ta ƙanƙame jikinta ya ƙyale ta ya shiga barci. Da gaske dai Abdurrashid aure zai yi kuma kanuri zai auro mata da take ji ake cewa sun iya riƙe miji, gaskiya ne ko da wannan fitinannen ƙamshin sa janye namiji, ita kam tana sayen turaren feshi da Air freshener amma su humra turaren wuta ba su gabanta, ta ina za ta soma ne? Ta tambayi kanta. Da ƙyar ta samu barci ya ɗauke ta. Da gari ya waye da wuri ta tashi ta fara ayyukanta, sai zuci-zuci take Abdurrashid ya fita gidan. Bai fita ba sai ƙarfe uku ta ce ita ma za ta je ma wata course mate ɗinta barka ta haihu. Ya ce ta zo su fita tare ya sauke ta ta ce A'a ya je kawai ita sai ta yi La'asar. Yana fita dama a shirye take jakarta da ta sanya Atm ɗinta da wayarta ta rataya sai matafinta,da kanta ta ja motar ta bar gidan. Wani Mall da suke zuwa ta yi wa tsinke, wani shago na saida turaruka da ke kusa da wanda take zuwa a saman shi an rubuta *HAJJA YANAH KANURI* ta shiga, a saman bene yake hawa na biyu. Masu aikin wurin sun tare ta da maraba ,mai wurin da ke zaune a wuri na musamman hango shigowar Hamida da ganin ta a jiƙe take jagab cikin Naira ya sa ta ce wa ɗaya cikin masu aikin ta ta kawo mata ita. Ta isa Hajiyar ta yi mata maraba aka ba ta wurin zama har da lemo aka kawo mata ta ce "Me kike so ƙanwata? Sai da Hamida ta ja wata gwauruwar ajiyar zuciya ta ce "Ina son humra masu kyau da turarukan ɗaki." Ta ce "Da waɗanne iri kike amfani? Ta girgiza kai "Ban amfani da su yanzu dai zan fara." Cikin mamaki ta buɗe baki kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa ta miƙe, Hamida sai kallon ta take yadda har ƙafafuwanta ke iya ɗaukar gangar jikinta saboda tsananin ƙibarta. Kala-kala ta zaɓo ta dawo ta ajiye su gaban Hamida "Waɗannan suna matuƙar kyau,sai dai suna da tsada." Hamida ta ɗauka tana shinshinawa tana lumshe ido ƙamshin su ya gamsar da ita. Ta kuma tashi ta ɗebo humrori "Waɗannan ma na musamman ne,su ɗin ma duk sun yi ma Hamida, a jikin kowanne akwai kuɗinsa, Atm ta miƙa masu su cire kuɗaɗensu Hajiyar ta ce "Daga kin ce ba ki amfani da su ƙanwata, ga abin da za ki dinga turara suturunki, ga kuma su bunner ya kamata ki s gaaya." Ba musu Hamida ta saisaya. Har ta miƙe ai yafuto ta Hamida ta dawo sai da ta rage murya ta ce "Ba za ki sayi na gyaran aure ba? Muna kuma yin gyaran jiki." Hamida ta ce "Ina so." Wani itatuwan turare ta ɗauko ta ce "Kin ga wannan sai mace ta isa, kina tsuguno da su mijinki zai ji ki daban,ba zan iya tsayawa yi miki bayani ba sai kin gwada,kar ma ki biya sai kin gwada." Hamida ta saki ajiyar zuciya "Na gode, ina so,ina ake gyaran jikin? Ta ce "Ciki ne,yarana ke yi, amma zan miki da kaina." Suka shiga inda ake yi, kamar yadda ta cen da kanta ta yi mata. Awanni suka ɗauka wanda ya ja lokaci. Yamma sosai aka kammala ta ce "Kyan ki sati guda za ki samu kina zuwa ƙanwata, zan gyara ki sosai." Hamida ta yi murmushi "Na gode sosai in sha Allah zan zo." Suka yi musayar lambar waya, ta sa yaranta suka ɗaukar wa Hamida amma ban da wanda ta ce na tsuguno ne ta ce Hamida ta sanya a jakarta ta kula da shi kamar yadda za ta adana da kudadenta. Sun yi sallama ta yi mata godiya sai da ta shiga mota fargaba ta rufe ta yamma ta yi sosai kar Abdurrashid ya riga ta dawowa,sai addu'a take har ta isa, ilai kuwa motar da ya fita da ita ga ta nan a ajiye, ta ɗauki kayanta ta nufi ciki yana zaune falo idonsa na kan TV motsin buɗe ƙofar da ƙarar takalmanta bai sa ya ɗago ba, ta isa inda yake jin bai amsa sallamarta ba ta ce "Sannu da hutawa." Ko motsi bai yi ba gabanta ya ƙara faɗuwa ta wuce ciki alwala ta yi jin an soma kiran sallah. Tana idar da sallah ta ciro kayanta bunner ta kunna ta ciro kayan da za ta sanya ta turara, sannan ta fita falo shi ma ta sa turaren sai ta wuce bed room ɗinsa don bunner uku ta sawo shi ma ta sanya mishi ta ƙara gyara shimfiɗar sai ta fito. Knocking ta ji ana yi ta isa ta buɗe mai aikin Aunty Karima ce ta kawo abinci don har yanzu daga can ake kawo mata,ta kan faɗi abin da take so in kuma za ta shiga kitchen da kanta sai ta shaida musu. Sai da ta shirya tebur ta wuce ɗaki, bayan ta gamsu da daddaɗan ƙamshin da ko'ina ya ɗauka wanka ta shiga bayan ta haɗa wani ruwan turaren da ta sawo wanda Haj Yanah ta ce kar ta yi wasa da shi matuƙar namiji ya shaƙa sai ya biyo, ta gama ta fito ta yi kwalliyarta ta shafa humrorinta kayan da ta turara ta ɗauko ta sanya riga ne da skirt na material da suka yi mata dam! Ko'ina ya fito ta ɗaura ɗankwalin, ta tsaya shawarar ta yi turaren tsugunon ko ta bari sai anjima ƙarshe dai ta yanke ta yi yanzu, key ta danna ma ɗakin duk da sanin Abdurrashid na fushi da ita ba zai zo ba sai da ta gama ta fito ta samu Abdurrashid zaune ya fara cin abinci ta ƙarasa ta zauna "Sannu da zuwa." Wani kallo ya ɗago ya yi mata sai ya ci gaba da cin abincinsa, ta zuba ta fara ci "Ina kika tsaya har magrib? Ta tsinkayi muryarsa ba zato cikin kanta. "Shopping Mall na biya na sawo turare." Ta faɗi da sanyin murya "Amma kin san ban son ki fita ki kai magrib ko? Ta ce "Ka yi haƙuri don Allah." Bai ƙara magana ba har ya kammala sai ya koma kan kujerun falon ya zauna, ta tattara kayan abincin ta kai kitchen sai ita ma ta zauna, miƙewa ta ga ya yi ya nufi ɗakinsa ta bi bayansa da kallo a ranta tana faɗin "Fushin bai ƙare ba kenan ko da na bayar da haƙuri? Tun tana jiran zai fito sai ta ji shiru don suna daɗewa suna hira kafin su kwanta. Ranta ya ɓaci tana ta masifa a ranta ba don Aljanna da kake nema ba aljanna kuma ba ta samuwa ta sauƙi, yaushe za ka zauna a yi ta maka wannan latsin? Ta miƙe ta fara kashe kayan kallon da nufin ta wuce ɗakinta ta kwanta ta ji wayarta ta soma ƙara, hannu ta kai ta ɗauko ta sai ta ga shi ne tana picking ya kashe ta san kiran ta yake. Ta kama hanyar ɗakin nasa, tura ƙofar hango shi ta yi ya yi ɗaiɗai bisa gadonsa daga shi sai guntun wando ƙirjinasa ta kalla sai ta ji wani shauƙi ya kamata hannayensa ya miƙo mata ba ta yi saurin zuwa ba ta ce "Zan je in canza kaya." Ƙara miƙo mata hannun ya yi ta ƙarasa ya janyo ta ya sa ta cikin jikinsa,wasu tagwayen ajiyar zuciya ta ji ya fidda wanda ta san sai ya daɗe rabon shi da ita yake yin hakan. A wannan daren Hamida ta ga tarairaya da soyayya na musamman har safiya ji yake da ita. Sun gama break past ta yi wanka nan ma bin gaɓoɓinta ta yi da humrorin,ta turara kayan da za ta sanya doguwar riga ce, ta shiga ɗakin ogan don gyarawa sai ga shi ya shigo "Ki fito ku gaisa da Usman." Nan da nan ta sha mur ya gyara tsayuwa "Wai meye haka da na ce Usman sai ki ɓata rai? Shiru ta yi ba ta tanka ba "Ki fito ku gaisa." Ya faɗi sai ya juya ta raka shi da ido. Sai da ta kammala gyaran ta fito ta same su falon ta zauna ta soma gaishe shi yana amsawa cikin fara'a, knocking ɗin da ake ya sa Abdurrashid miƙewa ya nufi ƙofar ganin mai gadi ne sai ya fita suna magana. Usman na ganin ya fita ya juyo gabaɗaya wurin Hamida "Madam kenan sai ƙara kyau kike abokina na hutawa,dubi safiyar nan amma ko'ina ƙamshi yake mai kwantar da hankali, ke kanki ƙamshi kike mai tayar da sha'awa." Zumbur ta miƙe "A'uzubillahi minashshaiɗanir rajim, ina neman tsarin Allah daga shaiɗancinka Allah ya.. Jin ƙarar buɗe ƙofa ya sa ta yin shiru sai ta dafe kanta, Abdurrashid ya shigo ganin ta dafe da kai ya sa ya ce "Lafiya? Ta ce "Kaina ke ciwo." Ya ƙaraso inda take "Shiga ciki ki sha magani." Sai kawai ta ɗora kanta jikinsa ya fara tafiya zuwa ɗakinsa, suna shiga ta mamutse shi zuwa gado ganin abin da take yi duk da hankalinsa ya fara tashi ya ce "Me kike yi haka? Ga Usman can na bari a falo." Hannunta ta cusa cikin jikinsa wata irin shafa take yi masa wadda ta sanya shi manta komai, sai ita kaɗai yake so. Ta gamsar da shi matuƙa da gaske sai da ya dawo daga duniyar da ta kai shi ya ce "Kash yanzu me zan ce wa Usman? A ranta ta ce "Ɗan iska ba? Ya gaji ya kama gabansa. Jallabiya ya sa ya fita ta gyara kwanciya ta shiga barci don ba ta san yadda suka ƙare ba. Ta farka ta shiga bathroom ta tsarkake jikinta sai ta fito ta mayar da kayanta a falo ba ta ga Abdurrashid ba sai ta zauna tana taɓa wayarta. Cikin masu aikin Mami ta yi knocking sai ta buɗe goro da sweet da cingam take ɗauke da su niƙi-niƙi "Wai in ji Mami na sa ranar Anisa." Cikin ɗaure fuska tana hararar ta Hamida ta ce "Na sa ranar ta da wa? Sunkuyar da kanta ta yi cikin daka tsawa ta maimaita na ce "Sa ranar ta da wa? Jikin yarinyar ya ɗauki ɓari cikin rawar baki ta ce "Da yallaɓai." Juyawa kawai Hamida ta yi ta rufe ƙofarta yayin da ta bar yarinya da tararrabi, don ta san ba ta isa ta koma ma Mami da waɗannan kaya ba, ga wadda aka kawo ma wa ba ta karɓa ba,duƙawa ta yi ta ajiye su a ƙofar ta koma inda ta fito cikin sanyin jiki. Abdurrashid ya dawo daga fitar da suka yi da Usman yana buɗe ƙofa goro da sweet suka yi mishi maraba. Da mamaki ya wuce ya buɗe ƙofa ya shiga yana ƙwala kiran sunan Hamida,jin shiru ya sa ya nufi ɗakinta. Rub da ciki ya same ta tana zuba kuka, daga inda yake ya soma tambayar ta abin da ya same ta ba ta yi magana ba har sai da ya ce bari ya kira Aunty Karima ko ta san abin da ke faruwa. Saurin tashi zaune ta yi "Don za ka yi aure Abdurrashid, wani duba ya yi mata jin ta ambaci sunan sa da ko da wasa bai taɓa ji ta faɗi ba,sai dai ta kira shi Hamma kamar yadda ƙannensa ke kiransa. "Sai a riƙa ci min fuska,a aiko min kayan sa ranar ka." Ido ya zuba mata kafin ya ce "To ki yi haƙuri." Maganganu ta ci-gaba da saki da suke nuna tsantsan kishin da take ciki yana sauraren ta. Kiran wayarsa da daddynsa ya yi ya sa ya juya ya bar ɗakin, ita kuma ta yi amfani da hakan ta ja mayafinta ta fito ta bar gidan [2/9, 09:43] Original: *SHIRIN ALLAH....RAYUWA* NO.28 Tana tafe tana share hawaye har ta isa gidan Gwoggonta. Ita kaɗai ta samu tana kallo, ta zauna sai ta rushe da kuka. Gwoggon da ke duban ta tun shigowar ta hankalinta ya yi matuƙar tashi ta fara tambayar ta abin da ya faru, cikin kuka ta zayyana mata auren da za a yi wa Abdurrashid don ba ta haihu ba, har rana an sa. Hankalin Gwoggo ya ƙara ɗagawa sai haƙuri take ba Hamida ta ce "Na soma amso miki taimako na haihuwa sai ki kama min dariya ki ce ke ƙalau kike." Haka Abdurrashid ya shigo ya same su haƙuri ya yi ta bayarwa ƙarshe ya nemi Hamida ta tashi su tafi fafur ta ƙi Gwoggo kuma ba ta matsa mata ba don yadda ranta ya yi mummunan ɓaci, itam ma kamar za ta fashe da kuka. Da ya gaji ya ce ma Gwoggo ta ƙara ba ta haƙuri zai tafi zuwa dare zai zo su tafi, da safe zai koma Abuja tare da Hamida don ya gaji da waɗannan fitintinun. Gwoggon ta ce "Idan ka tafi da ita karatun da na ji tana faɗin za ta cigaba fa? Ya ce "Sai ta cigaba a can." Ya tashi ya tafi. Bayan tafiyarsa Gwoggon ta rarrashe ta ta yi shiru har abinci ta matsa mata ta ci. Yamma liƙis sai ga kiran Hajja Yanah,suna gama gaisawa ta ce "Sai na ji shiru ban gan ki ba ƙanwata. Ta ce "Wallahi kuwa da ma zan kira ki ban samu fitowa ba, mijina kuma ya zo daga Abuja ya ce gobe zai koma tare da ni can,ni fargaba ta idan na tafi can ya zan yi in samu kayayyakinki? Ga dilka da aka fara min." Ta yi murmushi mai sauti da har Hamida ta ji "Kar ki damu ƙanwata a Abuja ma muna da branch,zan turo miki address na wurin, kina shiga Abuja ki nemi wurin za ki samu komai har ma da waɗanda suka fi waɗanda na ba ki. Daɗi ya kama Hamida ta ce "Na gode Aunty." Ta ce "Ba komai ƙanwata ni ma na gode." Suka ajiye waya ta tura wa Hamida lambar da ta ce. Har takwas Abdurrashid bai dawo ba. Hamida ta shiga ɗakinsu suna yammata har yau komai na nan, kullum kuma sai Gwoggo ta gyara shi tana sauke baƙi idan ta yi. Ta haye katifar bayan Sheltos ɗin da ta fesa ya baje, barci ya fara ɗaukar ta sama-sama ta jiyo muryar Gwoggo tana kiranta,ta buɗe ido Gwoggon na tsaye "Ki tashi mijinki ya zo ku koma gida. Ba tare da ta tashi ba ta ce "Don Allah Gwoggo ki ƙyale ni in kwana anan ba na son gidan can." Gwoggon ta yi shiru cikin tausayin ta sai ta juya falo inda Abdurrashid ke zaune "Ta roƙe ni in bar ta kar ta koma gidan yau, ko za ka yi haƙuri da safe sai in rako ta ta ɗauki kayan da za ta tafi da su ? Ya yi shiru cikin tunani kafin ya ɗago "Ki yi min izni in shiga in fito da ita Gwoggo." Hanya ta ba shi ya tashi ya shige gefen katifar ya zauna yana jan ƙafarta, tunanin ta Gwoggo ce ta dawo cikin marairaicewa ta furta "Don Allah Gwoggo ki tausaya min ki bar ni ko na koma can ba zan iya barci ba." Sai kuma ta ji ƙamshin turaren Abdurrashid ɓigit ta buɗe ido amma ba ta juyo ba "Ki yi haƙuri ki zo mu koma, ki yi sallama da Daddy da su Aunty Karima, don sammako za mu yi ki kuma yi parking ɗin kayanki." Ko motsi ba ta yi ba ya matso kusa da ita sai ta ji ya kwanta bayanta "Mu kwana nan kenan? Gabanta ta ji ya buga meye haka Abdurrashid zai yi ? Ko da ta san ba ya jin nauyin Gwoggo ba ta zaci zai iya shige ta ya shigo ciki ba. Ba ta karaya ba ƙin ko motsi ta yi don ta ga idan ya ji ta ƙi tashi zai tashi ya tafi sai dai har suka kai minti ya yi ashirin ba shi da niyyar tashin sai ma wasannin da ya fara yi da ita "Tashi to mu je." Ta furta a hankali, zaune ya tashi bai yi magana ba,sai da ta ɗauki mayafinta ta bar dakin ya miƙe ya bi bayanta shi ya yi wa gwoggo sai da safe ita wucewa kawai ta yi. Suna zuwa gidan sun shiga sun yi wa Daddy da Aunty Karima sallama ba ta tsaya shiga part ɗin Mami ba tana ganin ya karkata zai shiga can ta wuce ta yi tafiyarta,ɗakinta ta shige ta datse shi ma da ya zo ya taɓa ƙofar ya ji ta datse sanin ko ya yi faman bugu ba za ta buɗe ba na shi wurin ya koma ya kwanta. Ita sai da ta gama shirya kayanta sannan ta kwanta. Kamar yadda ya ce da sassafe suka bar garin don haka sha biyu na rana sun shiga Abuja. Sai kallon barrack ɗin Hamida ke yi tana auna banbancin su da waccan ta Kano. Wasu rukunin gidaje masu kyau ya tsaya kafin tsayawar tasu sai da ya nuna mata wani gidan ya ce shi ne na Usman,kauda kai ta yi ba ta yi magana ba. Ta yaba da kyan gidan na su an kuma ƙayata shi da komai na more rayuwa. Kan Sopa ta miƙe tana jin wata gajiya na ƙara bin gaɓoɓinta,sai jin daɗi take sanin Aunty Ainarta anan barrack ɗin take,duk da ba wata jituwa a tsakanin su ta roƙe shi a washegarin zuwan su ya bar ta zuwa gidan Aunty Aina, a murtuke ya ce "Ba yau ba." Ya dai yi mata bayanin mai mishi kula da gida Namiji ne, amma ya sallame shi saboda zuwan ta. Sai dai zai nemi a samo musu mace ko dan makaranta da za ta koma. Ya fita sai ga Jamilar Usman ta zo mata wuni tana ta murna da dawowar Hamida, yamma sosai ya zo suka tafi.Da daddare Abdurrashid ya ce ta shirya gobe zai turo akai ta gidan Momi,idan ya tashi aiki sai ya je su dawo. Tana gidan Momin ta samu wayar Aina ta ce ta zo ba ta nan, kunya ta kama Hamida ta ce "Ki yi haƙuri Aunty Aina,jiya na tambayi zuwa gidanki ya ce sai weekend. Ta ce "Allah ya kaimu." Kafin wucewar ta sun yi maganar ci gaban karatunta da Momi Binta. Ta yi ta samun baƙi har satin ya ƙare Sai ranar Lahadi ta samu Abdurrashid ya ce ta shirya su je gidan Aina duk da ba ta samu wunin da ta so ta yi ba don sai La'asar suka fita dole ka gan su su ba ka sha'awa, Hamida cikin atamfa take ɗinkin riga da skirt da suka zauna dam a jikinta sai mayafi da ta sa iya kafaɗa wanda ba mai duhu ba ne ya bayyana kwalliyarta,jelar gashinta ta ɓullo kan kafaɗarta. Ga ƙamshinta da ke sukurkuta Abdurrashid yana tashi. Shi kuma ƙananan kaya ya sanya da suka yi matuƙar amsar sa. Sun jero suna hira kamar sababbin amare,akwai 'yar tafiya tsakanin gidajen su da na su Hamida. Aunty Aina ta tare su da murnarta. An cika musu gaba da kayan maraba da baƙo, sun ɗan zauna ta ce su zo su gaishe da Brigadier yana falonsa. Ita ta yi musu jagora yayin da Hamida ta zauna bayan yin sallamarsu Abdurrashid sara mishi ya yi, Aina ta nuna Hamida "Yau dai ga ƙanwata Hamida da ba ku taɓa haɗuwa ba." Ya yi murmushi "Gaskiya kam." Hamida ta gaishe shi asalin ƙato ne baƙi mai ƙaton tumbi kamar mai tsohon ciki. Hamida sai ta ga har ya fi kyau a hoto kan yadda ta gan shi a fili, duk tsawon shekarun nan Allah bai taɓa haɗa su ba don ba mutum ba ne mazauni har kuma wurin Abban Abdurrashid yana zuwa ba ta taɓa katarin ganin shi ba. Bai da muni a fuska sai dai baƙi. Sun koma falon Aina Abdurrashid bai zauna ba ya ce zai dawo anjima. Sun yi ta hirar su yaran Aina na maƙale da ita, da brigadier zai fita sai ga shi har falon Aina daga shi sai shirt da baƙin dogon wando,ya zauna yana jan Hamida da wasa ita dai nauyin shi take ji ya miƙe kuɗi masu nauyi ya ba Aina ya ce ta bai wa Hamida, ta yi godiya amma ƙasan ranta tana jin kuɗin sun yi yawa. Jamilar Usman tana ta mita da ciwon baki ta waya ta ƙi zuwa gidanta, dole ta daure ta je kamar tana kan ƙaya haka ta ƙosa ta bar gidan don kar Usman ya dawo ya same ta. Tuni Hamida ta saba da zaman Abuja. Ta je shagon Hajja Yanah na Abuja, ƙwarai take jin daɗin abubuwan da take saye a wajen, domin dai yanzu ta san ta ƙara matsayi a wurin Abdurrashid, fushi da ita yanzu bai iyawa tuni ya daina dogon fushin duk laifin da za ta yi masa, hakan ya sa ba ta jin ƙyashin kashe ko nawa ne ta saya. Tana zumunci sosai da Momi da iyalanta musamman Hanan da suke aminai Ga shi ta samu ta ɗora karatunta, ranarqranarq,p ta zuwa makaranta za ta je gidan Aina don Brigadier ya tambayi Aina me ya sa ƙanwarta ba ta yawan zuwa? Ta ce tana zuwa makaranta kuma mijinta ba ya yawan barin ta fita..Ya ce "Zancen kawai, duk garin nan tana da wanda ya fi ki ne? Zan yi mishi magana." Har office ya kira Abdurrashid ya yi mishi faɗan hana zumunci tsakanin yan'uwan biyu,hakan ya sa duk san da Hamida ta so zuwa ba ya hana ta. Idan ta je kuma idan Brigadier na gida falon Aina zai zo ya zauna Ainar kan ce mata "Janinki ya haɗu da na Brigadier, ga sunƙin kuɗi ba fashi ta zo sai ya ba ta. Hamida ba ta ƙara jin ɗuriyar auren Abdurrashid har sai da wata rana ta saci jin yana waya sai faɗa yake kan shi fa ba dole, don babanta ya kuma ɗaga waccan ranar da ya sanya shi meye na shi? Su suke abin su, in ma shekara goma zai ƙara kan waccan ɗayar da ya sanya da farko matsalar su ce. Da ta gama ji ta ji ba daɗi amma sai ta manta kawai. Lokaci na ta shuɗewa wata uku ya rage ta kammala karatunta da wani hantsi ranar ba za ta shiga Sch ba. Zaune take gaban mirror ta fito wanka shafe-shafenta take yi kafin ta yi wa fuskarta kwalliya,da ta ji ta ɗauki ƙamshi mai daɗi sai ta miƙe ta ɗauki kayan da za ta sanya daga inda ta turare su, doguwar riga ce ta atamfa ta kafa ɗaurinta jin shigowar saƙo daga wayarta ya sa ta kai hannu ta ɗauki wayar saƙon daga Aunty Aina ne take shaida mata ba ta jin daɗi in ba ta komai ta zo. Hankalinta ta ji ya ɗaga Aunty Aina ba lafiya? Mayafinta ta ɗauko ta yafa, saƙon kar ta kwana ta tura wa Abdurrashid ta nemi izni za ta gidan Aunty Aina ba ta da lafiya. Har ta zo waje tana rufe gidan kiran shi ya shigo jikin Ainar ya tambaye ta ta ce sai ta je ta gano. Mota ta ɗauka don ta isa da wuri. Tana parking fitowa ta yi ta shiga ciki, ba ta gamu da kowa ba cikin masu aikin Ainar, har ta isa falon Aina ganin ba kowa ta wuce bed bedroom nan ɗin ma shiru sai ta yi tunanin ta kewaya ne zama ta yi don ta jira ta sai ta ciro wayarta tunanin kiran wayar Ainar ya zo mata ta kira lambarta, jin ringing ɗin wayar na tunkaro ta ta katse kiran tana jiran ta shigo, sai dai a maimakon Aina mijinta ne ya shigo, gaban Hamida ya yi mummunan faduwa ganin daga shi sai guntun wando murmushi yake mata yana shigowa kuma ya mayar da ƙofar ya rufe tumbinsa yake shafawa yana ci-gaba da murmushi Tsaye ta miƙe "Ina Aunty Aina? Ta tambaya kamar za ta fashe da kuka [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA NO.29 Maryam litee Ina Aunty Aina? Ta kuma maimaitawa "Ni na aika miki da saƙo ba Aunty Aina ba." Ki nutsu Hamida na daɗe ina mafarkin wannan ranar,sai yau Allah ya cika min burina na samu damar kaɗaicewa da ke. Tun ranar da na fara ganin ki sha'awarki mai tsanani ta kama ni, ki bani haɗin kai in kauda kwadayinki da ke azalzala ta." Hamida ta toshe kunnenta "A'uzubillahi billahi minash shaiɗanir rajim. Ka rufa min asiri ka buɗe min ƙofa ni matar aure ce kai kuma mijin yar'uwata ne." "Sai me? Zan mallaka miki komai a duniyar nan matuƙar za ki mallaka mini kanki." Ya fara nufo ta tana ja baya hawaye na sauka daga cikin idonta "Sai na gaya wa Aunty Aina." Ya noƙe kafaɗa yana ci-gaba da shafa cikinsa "Sai me idan kin gaya mata? Ranar da kika gaya mata ranar zan mata saki uku. Ki ba ni haɗin kai ta lalama, ƙin amince min zai sa a tsinci gawar mijinki don ba zan bar shi ba." Jikin Hamida ya shiga wata sabuwar rawar ta saki kuka gabaɗaya. Ya ci-gaba da nufo tana ja baya yana faɗin "Gaya ma wani wannan maganar zai sa ki rasa mijinki, da auren yar'uwar taki da take riritawa." Har ya ritsa ta ƙarshen bango matse ta ya yi ta shiga kiciniyar hankaɗe shi yana kiciniyar raba ta da rigarta, ihu ta ƙwalla ya tura ta gadon ta faɗa ya yi azamar bin ta zai danne ta ƙwalla ƙara ta miƙe ta dira gadon ta nufi ƙofa ganin ba key ya zare shi ya sa ta faɗa wa bathroom ta danna key sai addu'a ta Allah ya kuɓutar da ita daga wannan fasiƙin take. Kukan wayar Aina da ya tura mata text ta jiyo, hankalinsa ne ya tashi ganin Aina ke kiran. Sai da ya saita kansa ya ɗaga kiran "Yaya lafiya? Ya ce mata "Gani nan dawowa, ka fita office ne? Gaban shi ya buga "Na fita na dawo, mantuwar wasu files na yi." Ok ni ma mantuwar na yi, sai da na fita na duba ɗayar wayata ban gan ta ba, kuma cikin ta lambar matar take." Ya ce "Ok sai kin ƙaraso." Ya matsa saitin ƙofar bathroom ɗin "Ga Aina nan, ki fito ni fita zan yi, amma ki sa a ranki haɗuwar mu ta biyu sai na samu abin da nake so, barin wata alama kuma da Aina za ta gane yana nufin mayar da ita har ke zawarawa.". Gaban Hamida ya kuma tsananta bugawa, ko da jin shiru ta kuma leƙawa ta kafar makulli ba ta gan shi ba hakan bai sa ta fito ba har sai da ta ji maganar Aina. Wanke fuska ta fara yi don yadda ko'ina na jikinta ke zubar da gumi,ta ɗan daidaita kanta sai ta fito "Haba ni dai na ga motarki ashe kina ciki? Hamida da ta kasa haɗa ido da ita ta isa gaban dressing mirror "I na shigo Aunty Aina, ina kika je? Takowa ta yi inda Hamida ta zauna tana murza ma fuskarta mai hannunta ta riƙe"Me ya faru da ke Hamida na fuskanci kina cikin damuwa? Ta sunkuyar da kanta don duk yadda ta so ta ware kar Aina ta fahimci komai abin ya gagara, hawaye ta fara hankalin Aina ya ɗaga "Kun yi faɗa da Abdurrashid ne? Ta girgiza kai tana kai hannunta tana share hawaye "Damuwar rashin haihuwar ne ko auren na shi da Gwoggo ta ba ni labari? Ki yi haƙuri Hamida,gara kishiyar gida da ta waje. Ni nan yanzu kowa kallona yake ina ba shi sha'awa ina cikin daula, amma zaune dai nake ina haƙuri, Brigadier kamar bunsuru yake shi da mata." Hamida ta yi saurin duban ta "Wallahi Hamida, kin san dai duk yaransa maza ne suna Turai ya tura su karatu yana holewarsa, har gabana waya yake da karuwai, in taƙaice miki har gidan yake shigo da mata in ba na nan." Hamida ta dafe ƙirji ", Wallahi na yi nadamar irin auren da na yi Hamida, a gani na kuɗi sune jin daɗin duniya sai na ga saɓanin haka, ga dai daula ina ciki amma wannan matsala ta sha min kai a halittata ta yaya mata matan da ke yawo bisa titi me suka fi ni? Amma ban ishi Brigadier kallo ba, ya gwammace ya bi har waɗanda ba su ko kama ƙafata ba. Ba abin da ban yi don ganin ya daina amma kamar ina zuga shi, kullum ina cikin nadama na son duniya irin nawa ga shi nan na tsinci kaina a halin kwaɗayi mabuɗin wahala. Ku godewa Allah da kika auri saurayi matashi kyakkyawa ba ya neman mata yana son ki, auren da suka dage sai ya yi ke kuma ki dage roƙon Allah akan haka, haihuwar ma yaushe aka yi daren da za a tsangwame ki kan ba ki haihu ba?Ni zuwa na yi aka cire min abin da na sanya wa mahaifa ta, kin ga yanzu ina da cikin fata nake idan na haihu yaron da zamu samu ya kusanto min da Brigadier kusa da ni don mutum ne shi mai tsananin son yara." Kallon ta Hamida ta ƙara yi ashe ƙara harƙewar da ta yi kamar za ta fashe ciki ne, ta hura iska sai ta cigaba "Domin duk yadda nake ganin munin halin shi ban kuma so aurena ya mutu, ina komawa gida ƙasƙanta zan yi, aure komai watsewar shi daraja gare shi. Yanzu ma tun fita ta na ji hankalina ya ƙi kwanciya da rawar da na ga yana ta yi da fitar da zan yi na kuma duba jakata na ga ba wayata ɗaya, na yi zargin shi ya cire ta duk da na kasa tuna mai zai yi da ita, na kira shi don ma idan yana tare da wata ya sallame ta kafin zuwana don ban shirya ganin tashin hankalin da zai yamutsa min tunani ba." Ta ja ajiyar zuciya "Na taho gabana na ta faɗuwa sai dai ganin ki a gidan ya kwantar min da hankali,duk da dai akwai alamar yana da plan na kawo wata daga yadda na zo na samu ya fasa masu aikina." Hamida ta girgiza kai "Ki yi haƙuri Aunty Aina." Ta dafa ta "Haƙuri ya zama dole Hamida, ƙarshen duniya muke kowacce da kalar haƙurin da za ki ga an manna mata a gidan aure, wata yanzu tana can ƙwaƙƙwaran abinci babu ba kuma sutura kuma yana bin matan." Hamida ta gyaɗa kai "Allah ya ba mu mafita." Ta amsa da "Amin me za ki ci a kawo miki? Hamida ta miƙe zuwa gado "Ba komai Aunty Aina." Ta kwanta ta rufe idonta. Ainar ta fita can sai ga ta ta dawo "Kin ga wayar da na bari Abdurrashid ya kira." Ba tare da ta ɗago ba ko ta buɗe idonta ta ce "Na ce mishi ba ki jin daɗi ne Aunty Aina,don kar ya ce na cika zuwa." Kai ta gyaɗa "Ok kira ya yi ya gaishe ni kenan? Ta zauna gefen Hamida sai dai duk yadda ta so su yi hira Hamida lumshe idanunta ta yi kamar me barci. Kwanciyar awa ta yi sai ta miƙe "Zan koma gida Aunty Aina." Ta ce wa Ainar da ta samu a falo tana cin Tuffa "Haba dai tun yanzu? Ki zauna mu yi hira kin ƙi." "Bari in je Aunty Aina." Suka jera har inda ta adana motarta ta shiga ta tashe ta sai ta bar gidan. Tana isa gida bedroom ta faɗa ta kwanta rub da ciki kuka ta shiga yi sosai na baƙin cikin jarabtar da aka yi mata da maza waɗanda suke makusantanta suke bibiyarta,bayan Usman aminin mijinta yau ga mijin yar'uwarta. Ko dai ta faɗi ma Abdurrashid take ta ayyanawa a ranta, wata zuciyar ta kwaɓe ta "Ki rufa wa kanki asiri." Ko na Usman da ta yi niyyar ta faɗa mishi sai tunanin wata ƙawarta da suka yi karatu tare ya faɗo mata ita wani lacturer ne ya so ya haiƙe mata ta gaya wa mijinta, bayan sammaci da ya yanko wa lacturer ita kuma abu kaɗan za ta yi ya yi mata shaguɓe. Haka ta yi ta kwanciya ko girki kasa tashi ta yi ta yi sai mai taimaka mata ta sanya ta yi. Ko da Abdurrashid ya dawo ya gan ta sukuku ya tambaye ta ce mishi ta yi kanta ke ciwo amma ta sha magani. Haka ta kwana cikin damuwa. Da safe tana zaune gefen gadon Abdurrashid yana ɗaura takalmi, ziyarar aiki za shi Maiduguri. Ko da take cikin waccan damuwar tafiyar shi zuwa Maiduguri sai ta ji ta yi mata tsaye,gani take wurin Anisa za shi don tun barin ta Kano ta samu labari sun koma Borno. Har wurin mota ta raka shi sai da ya ɗaga ta koma ciki ta fara shirin makaranta. Haka ta ci-gaba da rayuwa cikin damuwa da ta sa a ranta a tsorace take fita zuwa makaranta don sau biyu tana lura ana biye da ita dukkan su ta sha da ƙyar. Tana ta gaya wa Abdurrashid ita Kano za ta koma da zarar ta kammala karatunta,shi dai jin ta kawai yake yana mamakin ta ya rasa me za ta yo a Kanon da ta dage za ta koma ita kaɗai babu shi da ya kawo ta. Ranar wata Alhamis da ba za ta taɓa mance ta ba a tarihin rayuwarta. Tana ta sauri makaranta za ta tafi wayarta da ke kan mirror ta yi ƙara, ta kai hannu ta ɗauka tana barin ɗakin, ganin sunan Walida ya sa ta murmushi "Manyan gari kuna nan? Hamida ta furta tana gota mai aikinta da ke mata a dawo lafiya, hannu ta ɗaga mata ta wuce cikin sauri "Haba dai ka ji zolaya, mutanen birnin tarayya ai kune da garin, ya kwana biyu? "Hamida ta ce "Sai alheri." "Na shigo Abuja ki turo min address mu yi zumunci." "Ah lallai ai wallahi ba ki da kirki Walida, duk daɗewa ta a garin nan wai sai yau za ki zo gidana." "Ba gara ni ba ga shi na zo ke ba sai dai a ji kin shigo Kano ba? Hamida ta buɗe baki daidai tana barin gidan "Duka zuwana nawa ni da ke karatu, akwai san da na je na je gidanku Umma ta ce min ba ki nan." "An yi haka alhuda huda ni dai ina sauraren ki." "Ok. Hamida ta ce ta sauke wayar tana ƙoƙarin tura mata sunan barrack ɗin. Tana dawowa sai ga Walida ta yi mamakin yadda ta ga Walidar ta canza mata duk ba wannan ƙibar da ta narka. Tara sosai ta yi mata suka zauna suna hira ta ce biki suka zo na yaron Aunty Saratu,da yake nan ya samu aiki(Yayarta da mijinta ya ɗauki nauyin karatun su Walidar) Hamida ta ce "Don rashin kirki ɗan Aunty Saratu na aure ba za ki faɗi min ba." Ta ce "Na ga garinku za a yi bikin don har su Aunty Saratun ba wanda ba za ki gani ba, akwai liyafar da za a gudanar gobe na san ai za ki halarta? Hamida ta ce "In sha Allah, yaushe za ki bar garin? Ta ce "Sai jibi." Kafin tafiyar ta ta yi ta jaddada wa Hamida tana fa jiran ta ta zo mata wurin liyafar. Da Abdurrashid ya dawo suna cin abinci take ba shi labarin zuwan Walida da bikin da suka zo. Taɓe baki ya yi bai yi magana ba, murmushi ta yi don ta san da ma za a yi haka sanin ba wani haɗuwar jini ke tsakanin shi da Walidar ba. Ta roƙe shi za ta je ma Walidar Dinner ya ce "A'a." Magiya ta yi sosai sai da ya ja ranta ya bar ta. Washegari ta samu wayar Walida ta yi biyar tana jaddada mata tana fa jiran ta. Ta ce tana nan zuwa. Kwalliya sosai ta yi da duk wanda ya dube ta sai ya kuma ga ƙamshi na musamman tana fitarwa,ta fita a motarta. Ta kusa isa unguwar da Walida ta ce mata an kai amaryar don ta san unguwar nan ɗiyar Momi Binta ke aure sai ga kiran Walida ta ce "Ki ƙaraso View hotel anan za a gabatar da shagalin bikin,yanzu haka ina wurin." Tsaki Hamida ta ja "Wallahi kin wahalar da ni." Ta karya kan motar sannan ta faɗi mata daidai inda take ta ce "Sai ki faɗi min ta inda zan bi, don ban san inda hotel ɗin yake ba." Ta ce "Kin ji ki kina yar gari ma ba ki sani ba ina ga ni baƙuwa. Bari in tambaya. Muryar wanda Hamida ta ji ya yi magana kusa da Walidar sai ta ji kamar ta san muryar, ta ɗan zurfafa tunani sai kuma ta watsar don ba ta ga abin da zai kai wanda ta yi tunani wurin ba. Tana tafiya Walida na mata kwatancen har ta kai, ita ta zo ta tare ta sun jera bayan ta adana motar "Gaskiya matar nan kin samu duniya, kin ga yadda kike sheƙi." Walida ta ce wa Hamida Hamidar duka ta kai mata suna dariya har suka kai inda aka ajiye kujeru kusa da sweeming pool don zaman jama'a. Walida ta ja mata kujera ba ta zauna ba ta ce "A'a ya da zama kuma anan? Ta dafa kafaɗarta"Yanzu ake gyara wurin,mu zauna mu ɗan sha lemo kafin a fara." Amma shi ne maimakon ki bari in fara zuwa gidan bikin." Hamida ta faɗi tana zama "Kar ki damu ba wanda ba za ki gani ba har Aunty Saratu." Ba ta zauna ba ce ma Hamida ta yi tana zuwa, Hamida ta ciro wayarta tana dannawa har Walida ta dawo wani cikin masu aikin hotel ɗin na biye da ita da babban tray ya dire shi gaban Hamida sai ya juya, Walida ta zuba mata lemon sai ta zauna suna hira tana maimaita ma Hamida ta sha lemon, har dai ta ɗauka ta sha kurɓa ta uku sai ta ji kanta ya sara take ta ji ba ta yi,kanta ta dafe da ta ji yana juya mata. [2/9, 09:43] Original: *SHIRIN ALLAH....RAYUWA* NO.31 Duk da lugude da ƙirjinta ke yi bai hana ta isowa gaban shi ta zauna a ƙasa ba. Irin Video da aka tura mata shi aka tura mishi "Ranar wanka ba ɓoyon cibi Hamma, yau zan gaya maka abin da na daɗe ina ɓoye maka." Ta yi shiru, bai ko motsa ba ballantana ta sa ran zai tanka ta ci-gaba ta ba shi labarin tun farkon abin da Usman ya yi mata a haihuwar yar shi Hamida, har zuwa wanda Brigadier ya yi mata har kawo yaudarar da Walida ta yi mata ta kai ta Hotel da ganin da ta yi musu su uku Usman Walida da Brigadier a ɗakin Hotel har kare tan da Allah ya yi tana period a ranar, sai saƙon da aka turo mata yanzu fitar shi. Wayarta ta buɗe ta ajiye mishi kusa da shi ɗaukar wayar ya yi ya tashi zuwa ɗakinsa. Ta ɗauki awanni a wurin har lokacin sallah ya yi, Abdurrashid bai fito ba ta je ta yi sallarta ta shiga kitchen ta gama girkin ta je tana ƙwankwasa ƙofarsa shiru bai buɗe ba ta gaji ta koma ta zauna jugum har La'asar Abdurrashid bai fito ba ta miƙe ta sake komawa ta buga ya fito bai ko kalli inda take tsaye ba ya raɓa ta ya wuce. Sai tara na dare ya shigo shi ɗin ma bai saurare ta ba ɗakinsa ya shige ya datse, tashin hankalinta ta ji ya nunku me Hamma ke nufi da ita shirin kwanciya ta yo ta zo ta murza ƙofarsa a datse take ta buga ta koma ta tsaya jin shiru ta gane ba shi da buƙatar ta, ta ja ƙafa falo ta koma ta zauna kan carpet nan ta kwana. Da ya fito sallar asuba nan ya wuce ta inda ta ɓingire bayan raba dare da ta yi a zaune. Tana farkawa ta miƙe zuwa ɗakinta sallah ta gabatar ta san ba za ta zolayi kanta ba ta ce za ta kwanta ta yi barci daga ta san ba ɗaukar ta zai yi ba, samun kanta ta yi da yin wanka ta gyara jikinta wata doguwar rigar material ta saka wayarta tana hannun Abdurrashid sai ta rasa abin da za ta yi ya ya ɗan ɗauke mata tunanin halin da take ciki. Motsin ƙofa da ta ji ya sa ta ɗaga kai "Ina kwana? Ta ce tana duban sa. "Lafiya, ki shirya mota za ta iso ta kai ki gidanku, ki je ki zauna har sai na gama yanke hukunci kan wannan abun." Wani irin duka ƙirjinta ya yi ta sunkuyar da kai ya juya sai ya bar ɗakin wasu hawaye suka fara gudu kan kuncinta, ta daɗe zaune tana kuka shi kenan sun ja mata sun kashe mata aure. Ta jima cikin halin zubar hawaye ƙarshe ta miƙe ta shiga tattara kayanta duk wani abin amfanin ta ta ɗauka ta fito falo ta samu mai aikinta ta zo, sallamarta ta yi da alheri mai yawa ta ce tafiya za ta yi, haka ta juya cikin alhini don ba ƙaramin daɗin Hamida take ji ba. A hankali ta janyo akwatunan da ta sanya kayanta, waɗanda za su yi tafiyar tare sojoji ne guda biyu suka riƙa ɗauka suna sakawa a boot suka shiga gaba tana baya direban ya ja motar suka bar barrack ɗin. Lokaci lokaci tana share hawaye wayar da ta ji ɗaya daga cikin su na yi yana faɗin ya yi tafiya zuwa Kano ya sa ta gane Kano Abdurrashid ya ce su kai ta. Sai ta ce Daura za su. Daga Abuja zuwa Daura tafiya ce doguwa don haka kafin isar su gajiya liƙis Hamida ta yi. Ko da suka isa ba ta yarda ta furta komai ba ɗakin Innawuro ta sauka kamar yadda ta saba sai washegari suna karyawa da safe ta kwance wa Innawuron komai, tsananin tashin hankali Innawuro ta shiga ta sa aka kira iyayen su Hamida cikin su har da baban Hamida, ta kwance musu abin da ya kawo Hamida daga mai salati sai mai riƙe kai sun kiɗime sosai da wannan masifa da ta faru da ita. Zama suka yi suka tattauna kan wannan magana su bar ta iya nan ko iyalansu kar wanda ya faɗi ma wa, sai Gwoggo Indo ita kaɗai za a yi ma waya ta zo a shaida mata a kuma faɗa mata ta kama bakinta don ba zancen da za a bari wani ya ji ba ne, yadda za a yi shi daban yadda za a juya shi daban ƙarshen ta a ɓata sunan Hamidar, su zauna su saurare shi har san da zai gama binciken in kuma Malam ya dawo sai su saurari abin da zai yanke. Saboda idon Baban Aina kowa ya yi shiru kan abin da Brigadier ya yi sai shi ya ɗauki waya zai kira Aina ya faɗa mata yan'uwansa suka hana shi. Haka taron ya tashi kowa jikinsa a mace ran shi a ɓace. Suna fita Innawuro ta aika kiran Innar Hamida sai da ta zauna ta kwance mata abin da ya faru da Hamida, duk da tashin hankalin da ta ji ɓoye komai ta yi a ranta ta jajanta. Innawuro ta tashi ta ɗauko kuɗaɗe ta dawo kusa da Hamida ta zauna "Ki yi haƙuri kin ji Hamida? Jarabawa ce kowane bawa da ta inda ake jarabtar shi ki koma wancan ɗakin ki yi zaman ki." (Da yake an mayar musu Three bed bedroom flat bayan tanƙamemen falon da aka zuba musu komai na more rayuwa Malam an mishi bedroom ɗinsa Innawuro an mata two bedroom) Ba tare da mun zauna ɗaki ɗaya na takura miki ba. Wannan kuɗin Muzanbilu zan kira a zo a gyara miki Ac da aka sanya a ɗakin, a lokacin Muzanbilun ya ce ko me za a yi mata ta fara bada sanyi ba mu koma ta kanta ba ni da Malam." Nan ma ta sa aka kira mata Muzanbilun a waya abin da Hamida take ci da sha ta matsa mata ta faɗi ta bayar aka sawo. Zuwan Aliyu shi ma lallashi sosai ya yi wa Hamida ya fita ya yo mata sayayya mai yawa kafin ya yi musu sallama don shi ya koma gidan da Engineer ya gina ma Malam. Gatan da aka nuna mata ya sanyayar da ranta tafiyar Aliyu sai ta shiga ɗakin da Innawuro ta ce ta zauna gado ne da mirror da wardrobe yan waje sai tafkekiyardardumar da aka shimfiɗa saman tayels, labulayen ma na alfarma ne. Ta fara tuɓe kayan ta ji kaya-kaya ana sallama da shigo da wani abu ƙannenta ne da ƙaramin fridge wai Babansu ya sawo mata suka juya suka shigo da ruwa da drinks ɗin da Innawuro da Aliyu suka sawo mata. A sanyaye ta ce su ce ma Baban ta gode. Bayan fitar su ta kwanta bisa gadon tana tuna rayuwa, Hamma bai yi mata adalci ba. Ta janyo pillow ta rungume ta daɗe cikin tunani na baƙin cikin halin da take ciki kafin barci ya yi awon gaba da ita. Washegari sai ga Gwoggo Indo da aka yi ma waya aka ce ta zo. Zuwan ta zama suka yi ita da yan'uwanta aka kuma tusa maganar a gabanta, ranta ya yi mummunan ɓaci ta dinga surfa faɗa ana tausar ta ta ce "Aikin banza aikin wofi da zai turo yarinya gida bayan ya san ba laifin ta ba ne, in ma rabuwa zai yi da ita ai ba haihuwa ta yi ba miji wanda ya fi shi za ta samu ta aura. Da ma ni tun auren shi da ita haƙuri nake me yake ba ni? Innawuro ce ta taɓo ta sai ta waiwayo tana duban ta "Ke me batun raba aure tun da ba ki raba ba sai yanzu da abin nema ya samu." Kallon rashin fahimta ta yi wa Innawuron "Ban gane ba? "Ki kalli yar taki da kyau, ba ki ga addu'ar mu ta ci ba? Gaban Hamida ya buga me Innawuro ke nufi? "Kar dai ki ce min ciki gare ta? Gwoggo ta tambaya tana fidda ido "Ya wuce wai da kin dube ta kin san ba ita kaɗai ba ce." Gwoggo ta miƙe har tana neman yadda zane "Shi ne ba ki faɗi ba Hamida, Wannan abin farin ciki haka? Kunya ta lulluɓe Hamida cikin ƙarfin hali ta ce ita wallahi ba ta sani ba. Gwoggo ta tafa hannu "Ba ki sani ba sai ka ce wata yarinya? Bari in je a nemo mota mu je asibiti a gwada." Gwoggon ta faɗi tana ficewa ɗakin. Ba a jima ba ta dawo ta ce Hamida ta ɗauko mayafinta. Wata asibiti mai zaman kanta suka je don haka ba wani ɓata lokaci suka ga likita gwajin jini aka yi mata inda aka tabbatar musu tana ɗauke da ciki har ya shiga wata na uku. Ai kuwa suna dawowa tun daga tsakar gida Gwoggo ke rafka guɗa abin da ya ja hankalin mutanen gidan, kafin ka ce me zancen ya je kunnen kowa har na gidan ma'aura,wasu ba su bari an kwana ba sai da suka dangano da gidan, ana ta murna iyayen su maza ma sai da suka dawo suka ji Gwoggo ta so kiran Abdurrashid aka hana ta aka ce ta bar shi har ranar da zai zo. Hamida ba ta samu keɓewa ita kaɗai ba sai da ta zo kwanciya,kayanta kaf ta tuɓe ta tsaya gaban mirror tana ƙare wa kanta kallo ƙwarai akwai canji a tare da ita wanda rashin sa rai bai sa ta taɓa maida kai ba komai nata ya daɗa cika musamman ƙirjinta, al'ada kuwa tun wadda ta yi gamuwarta da su Brigadier har yau ba ta ƙara ba rashin kwanciyar hankalin da take ciki sai ya ɗauke mata hankali ya hana ta tunanin ko ciki ne. Ta sa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta "Allah na gode maka." Ta furta cikin siririyar murna. Da gari ya waye ta bada aka sawo mata sabuwar waya da layi sai layinta da take jin alert ta yi welcome back ɗinsa. Samun cikinta ya ɗauke mata kowanne baƙin ciki ga iyaye da yan'uwa da ke kewaye da ita suna taya ta farin ciki, Aina ma wadda ta yo waya ta yi nauyi sosai a yanzu ta kusa haihuwa. Ta sa aka kawo ma Hamida waya sai faɗa take mata tahowar da ta yi ba ta sanar mata ba da aka ce matsala suka samu da Abdurrashid da ta zo gidanta ko Brigadier ba zai sasanta rikicin ba sai ta kama tafiya gida. Hamida ta ba ta hakuri cikin ƙarfin hali don wani mugun takaicin Brigadier da take ji yana taso mata. Zaman Hamida gida a wannan lokacin ya kusanta ta da Innarta, duk safiya can take tafiya. Mahaifiyarta ba ta da tashar kallo sai su Sunna TV Africa TV 3 inda za su yi ta saka wa'azizzuka na malamai daban-daban anan za ta tafi Islamiyya ta bar Hamida wa'azin za ta yi ta ji, yawan jin wa'azin har ya kama ta ko ta dawo wurin Innawuro shi ta kan kunna. Watarana aka saka Sheck Aminu Daurawa wa'azi yake kan shigar mata da yadda suke fita a wannan zamani. Jaddada duk matar auren da ta shafa turare ta fita har wani namiji ya ji ƙamshin, to idan ta dawo ta yi wanka domin tamkar ta yi zina ne ya sa Hamida tashi zaune, duniyar tunani ta faɗa ba ta dawo ba sai da ta ji yana faɗin yawaitar zinace-zinace a yanzu mata sun bar hijabi ana shiga ta son rai, domin Ubangiji cewa ya yi mu nisanci zina, shigar bayyana tsiraici kuma tana cikin kusantar zina, kallace-kallacen fina-finan batsa da karatun labaran batsa suna daga cikin manyan fadadi a wannan lokaci da muke ciki. Tsaye Hamida ta miƙe don jin da take tamkar zazzaɓi zai rufe ta can ƙuryar Innarta ta shige ta haye gado tana jin nadama na rufe ta A rayuwar ta bari boko ya rinjaye ta ta saki komai na koyarwar addininta in banda sallah da ta riƙe. Take ta ɗora ma kanta laifi kan abin da ya faru da tsakanin ta da Usman da kuma Brigadier tana yarinyar mace kyakkyawa mai cikakkiyar sura mai ɗaukar hankali ga shiga wadda mijinta kaɗai ya halakta ya gani sai muharramanta amma za ta yi ta shiga ko'ina,ga ƙamshi mai tsayawa a rai da ba ta tarar yaushe ya kamata ta sanya. [2/9, 09:43] Original: *SHIRIN ALLAH...RAYUWA* NO.32 MARYAM LITEE Ga ƙamshi mai tsayawa a rai da ba ta tarar yaushe ya kamata ta sanya, koyaushe cikin sa take. Kenan duk namijin da ya shaƙa zai zame masa fitina duk da dai a ƙarshen zamanin nan da muke mai hijab ma yan iskan maza ba su bar ta ba don ko ƙawarta da lacturer su ya yi ma maganar banza kullum cikin hijab take.a "Zan shiga Islamiyya." Ta faɗi kamar mai magana da wani "Zan ƙarar da rayuwata wurin bauta ma Ubangijina." Sai kuma ta dafe kai don sabon tunanin da ya shige ta Ba abin da ke samun ta a rayuwarta ta tsaya ta fuskanci Ubangiji ta yi addu'a, dubi duk wannan bala'i da ya same ta daidai da rana ɗaya ba ta taɓa dagewa da sallar dare ba kan Allah ya kawo mata ɗauki ba. Shigowar mahaifiyarta daga Islamiyya ya katse mata tunanin, lafiya ta shiga tambayar ta ganin fuskarta yau cikin damuwar da kwana biyu suka daina ganin ta cikin ta. Ta ce "Ba komai." Zama ta yi ta yi ta gaya kalaman kwantar da hankali da imani da ƙaddara tare da jaddada mata ta yi ta addu'a ba abin da ya gagari Allah. Buɗe bakin Hamida ta ce "Zan shiga Islamiyyarku Umma." Kai ta girgiza "Ba za a yi haka ba ki riƙa fita ba iznin mijinki,ki dai bari har Allah ya kawo daidatawar ki da mijinki kika koma ɗakinki sai ki shiga." Ta gyaɗa kai"In sha Allah zan shiga Umma." Sun daɗe har sai da Innawuro ta aiko ta zo ta ci kwaɗon zogale da ta ce tana so ta miƙe sai ta bar sashen. Watanta guda sai ga Gwoggo Indo ta zo duba ta bayan ta tafi sai ga kiran Momi Binta sai faɗa take mata tana tambayar Hamida me ya haɗa su da Abdurrashid da har ta taho ba su sanar mata ba? Ta kasa magana. Kwana biyu tsakani sai ga Momin da Aunty Safiya sun ce Daada ta zo su taho tare to kwana biyu ciwon ƙafa ya sanya ta gaba ga hawan jininta ya tashi. Sun zauna da iyayen Hamida aka gaya musu matsalar da aka samu suma jimamin suka shiga tare da bayar da haƙuri kan matakin da Abdurrashid ya ɗauka tare da neman a ba su Hamida su tafi tare, su ma haƙurin suka ba su tare da yi musu godiya amma sun ce su bari har Abdurrashid ɗin ya zo da kanshi, wanda suka faɗi baya ma ƙasar, sai yamma suka bar ƙasar. Su Hanan da Mimi sun zo mata suka kwana guda suka koma. Wata da suka yi karatu tare mutumniyar Kaduna da ke saye da sayarwa na yadikan hijabai da ɗinkakku da safuna masu kyau ta yi wa magana tana son ɗinkakkun hijabai ne nuna mata ta yi ta zaɓi kala-kala da safuna ta zaɓi irin ɗinkin da za a yi mata ta bayar aka sanya a mota Hamida ta aiki ƙanenta ya amso mata, ta yi alƙawarin canza shigar ta za ta koma rufe jikinta kamar yadda musulunci ya yi umarni duk da ba inda take zuwa sai awon ciki da ta fara zuwa Asibitin da suka je aka tabbatar mata tana da ciki. Watarana daga wurin awon ta wuce gidan yar'uwarta Amina, wadda yanzu yaranta hudu. Mimmiƙe ƙafafu ta yi a tsakar ɗakin Aminar suna hira tana kallon Aminar tana haɗa garuka da su gumba su tsimi za ta sha. Ta jinjina kai "Kuna ƙoƙarin shan magani Amina, ni kam sai ta ƙure nake rufe ido ba kuma kowanne ba." Aminar ta kai bakinta sai da ta sha ta sauke kofin, "Shan na dole ne Hamida, ni ma kin san ba son magani nake ba." Hamida ta ce"Kamar ya dole? Ta ƙara kai kofin sai da ta sauke ta ce "To in ba ka gyaran ba akwai matsala, musamman mu masu kishiya." Hamida ta yi murmushi "To ai sai in ji ana ta yi wa masu saidawar tsira a ce ki gama kashe kuɗaɗenki duk daɗin da namiji zai ji bai hana ya nuna miki shi ɗin namiji ne. Wai duk masu sayarwar ma yawancin su ba su da aure in yana da amfani da ba a sake su ba." Amina ta gyara zama "I ba abin da ba a faɗi amma ni wurina yana da amfani, kin ga kafin ayi min amarya basu dame ni ba Baban Amar yana yin aure ya daina nema na a shimfiɗa sai mu yi wata ni dai sai dai in ji mata na hirar abin nan don ni har manta ma ina da miji nake, sai ya zam ririta ni da yake da abubuwan buƙata da yake mana ni da yayana ya rage hakanan dai nake zaune duk wani farin ciki na shi ya mayar da shi wurin amarya, na tashi haiƙan ina amfani da magungunan nan ashe kuma sanyi ya yi min mugun kamu hakan ya hana ni gane amfanin abin da nake shan, na gaji na watsar na ci-gaba da zaman haƙuri. Ana nan sai Allah ya haɗa ni da wata mai sayar da magungunan mata da ƙyar ta sani na ɗauki wani ta ce in gwada, na dai karɓa na biya ta na zo na ajiye ya yi wata uku da safe ban koma ta kanshi ba sai watarana na ɗauko shi na yi amfani da shi a ranar na ga abin mamaki don gabaɗaya susucewa ya yi, in taƙaice miki magani ya yi daga nan bunu-bunu mutum na manne da ni, abubuwan cikin gida da duk ya maƙale hannunsa duk ya saki ya dawo yana mini hira da da ta soma gagara tsakanin mu. Zai yi ma yarana hidimar duk da ta kama, tun daga nan na kama matar nan na riƙe da ta samu masu kyau za ta kawo min. Amir (Yaronta na farko) da ya ga matar ta shigo sai ya yi ta jin haushi wai in ta kwashe kuɗina ina ba ta, a raina sai in ce yaro har kai wannan matar tana ma amfani. Wato ni Hamida abin da na fahimta game da waɗannan magungunan, ba wai za ka mallaki namiji ba ne ko ya yi ta kwasar abin duniya yana ba ka, a'a za ka tsira dai da ƙimarka, Hamida ta gyaɗa kai "Na gamsu da bayanan ki, ni ma ban da ban iya sha da na saya." Ta ce "Ai akwai masu daɗi irin su zuma da gumba, za ki iya ci." Ta ce "Sai na tashi amfani da su zan sa ki saya min, ke ma zan ba ki nawa da nake amfani da su." Wayar Hamida da aka shiga kira ta katse su Hamida ta ɗaga kiran tana murmushi ganin sunan ya Aliyu ne kan screen ɗin ta ce "Ya Aliyu, yayana ni kaɗai." Murmushi ya yi mai sauti har ta ji "Yanzu dai kina ina? Innawuro ta kira ni hankali tashe wai har yanzu ba ki dawo ba." Murmushi ta yi "Ita Innawuron? Sai dai in ta soma ruɗewa amma na gaya mata zan shiga gidan Amina, in gaishe ta ta samu miscarrige ka sani." Kai ya gyaɗa kamar tana kallon sa "Zan zo in kai ki gida." Ta ce "To ya Aliyu." Ta ajiye wayar suka ci gaba da hirar su har ya kira ta ya shaida mata isowar sa, hijab ɗinta ta janyo dogo har ƙasa ta sanya Safa sai ta miƙe Amina ta biyo ta don mata rakiya sai da suka zo zaure Hamida ta tsaya ta buɗe jakarta kuɗi ta ciro masu kauri ta kama hannun Amina ta damƙa mata Aminar tana meye haka ta ce "A sayi kayan gyara a ƙara gyarawa Baban su Amir." Suka yi dariya ta ce "Ya za a yi in amshi kuɗinki ke da kike zaune? Murmushi ta yi don ta san ba ta da matsalar kuɗi duk wata sai Abdurrashid ya turo mata kuɗaɗen da ya saba ba ta. Ta ce "Kar ki damu ina da kuɗi." Ta kaɗa kai "To na gode sosai." Suka isa inda ya ajiye motar Amina ta gaishe shi sai suka wuce. Yammacin wata Laraba ta fito wanka ko da zaman ta gaban mirror sai ta samu kanta da son yin kwalliya wacce tun da ta zo ba ta yin ta, ta murza hoda ta gyara girarta ta goga wet lips sai ta sanya turare. Jin ƙamshin ya tuna mata da rayuwarta da Abdurrashid hannayenta ta haɗe ta shiga tumani, ta jima kafin ta miƙe ta nemi kayan da za ta sanya cikin ya fara fitowa duk da ya sa ta yi ƙiba jikinta ya kuma yin lukwi-lukwi ta dai yi kyau irin na mata masu ciki. Wata doguwar riga ta zura ta wani yadi mai taushi, sai ta sanya hijab takalmi flat da jakarsa. Ta fito Inna Innawuro na zaune a falo tana kallon shirin Kwana casain da ake gabatarwa ganin ta da hijab ya sa ta ce "Ina kuma za ki? Ta ɗan zauna hannun kujera "Ka ji Innawuro sai ka ce wadda ke fita kullum, ya Aliyu zan dubo." Baki ta riƙe "Yau kaɗai da bai shigo ba za ki duba shi son yawo dai." Ta langaɓe kai "Kai Innawuro ina nake zuwa? Ya Aliyu fa ya ce yau ko fita bai ba ciwon kai ya matsa mishi." Tausayi ta ji ta ba ta ta ce "Shi kenan, ke da wa za ki? Ta ce "Keke napep yara za su samo min.". Ta fita falon Innawuro ta bi ta da kallo. Sasan su Aina ta fara shiga ta yi wa matar Baban Aina barka don Ainar ta haihu ta samu ya mace, da ta fito na su Laila ta shiga akwai yaron da ke kwance yana fama da gaida, nasu sasan ta shiga ƙarshe ta samu Innarta na girkin abincin dare, nan ta zauna suna hira har aka aka samo mata mai napep ta fita suka tafi. *********** A falo ta samu Aliyun yana zaune ta zauna tana duban shi yana mata murmushi "Sannu ya Aliyu." Ta faɗi tana langaɓe kai, Asabe da ke kallon su tana goge goge daga nesa takaici ya rufe ta. Hamida ta zame hijab ɗin jikinta don wani zafi da take ji "Asabe ba ki ga zuwan Hamida ba? Aliyu da ya san da wanzuwar ta a wurin ya faɗi "Ki ba ta ruwa." Ya kuma faɗi yana waiwayawa inda take ta tako zuwa tsakiyar falon ko da Hamida take da aure sai ta yi ta ganin za ta iya zama kishiyarta, yanzu zaman da suka yi wuri ɗaya wata dacewa take ganin sun yi, da ƙyar ta iya cewa Hamida Sannu da zuwa. Ita kam ta gaishe ta cikin fara'a da tambayar ta yara ta ce suna Islamiyya. Sun ci gaba da hirar su har aka kusa kiran magrib ta ce za ta koma gida, ya ce a'a ta bari ya yi sallah sai su tafi tare. Ko da Hamida ta yi alwala ba ta ga fuskar shigar ma Asabe ɗaki ba, sai ta yi sallar a falo nan saman carpet tare da yarinyar Aliyun mai sunan Innawuro, wadda take goyo kuma sunan Hamida ya sanya mata, tana idarwa Asabe ta zo kusa da ita "Ba wai mutum ya baro ɗakinsa ba yana bin gidajen mazan mutane." Da mamaki Hamida ta ɗago "Aunty Asabe ban gane me kike cewa ba? Gabaɗaya ta taso "Ina nufin mutum ya fita hanyar mijina." Ta buɗe baki za ta yi magana Aliyu ya shigo ganin Asabe tsaye kan Hamida ya ce "Lafiya." Asabe ba ta tanka ba sai wata cika take Hamida ta ƙirƙiri murmushi "Ba komai ya Aliyu." Ta miƙe, ya ce "Mu je ko." Yarinyar ta ce "Zan bi ki gidan Innawuro Aunty Hamida." Ta ce "Gobe akwai Sch maama." Ta ciro kuɗi "Ku yi break ke da su Baffa, gobe a Sch." Ta bi bayan Aliyu. Sun bar gidan har ya hau titi yake ce mata "Aure zan ƙara Hamida." Gabanta ta ji ya faɗi don tuna fargabar da ke cikin cewa za a wa mutum kishiya "Kai Ya Aliyu me Aunty Asabe ta yi za a yi mata kishiya? Ta gefen ido ya yi mata wani irin kallo "Sai ta yi wani abu zan ƙara aure? Ina da buƙatar hakan ne, a cikin garin Katsina yarinyar take. Ina so a yi da zarar ta ƙare karatu." Hamida ta jinjina kai "Karatu take kenan? Ya ce "Ƙwarai ɗaliba a jami'ar Umaru Yar'adua University karatun digiri take tana shekarar ƙarshe. Ajiyar zuciya Hamida ta fidda tuna Anisa da zaman da take da ba ta san makomarta ba. Ta ce "Allah ya tabbatar da alheri." Murmushin da ba koyaushe yake yi ba ya yi ya ce "Amin." Suna isa ɗaki ta shige ta bar su suna maganar dawowar su Malam gobe, duk kuma yadda Innawuro ta so ta ci abinci ƙin ci ta yi sai hura ta sha ta kwanta. Ta daɗe tana zubar da hawaye, abin har ya kai a fara tozarta ta? Sai da ta ji kanta ya fara ciwo ta ba kanta baki ta yi barci. Da safe da ciwon kan ta tashi ta ce ma Innawuro za ta asibiti don ba ranar awonta ba ce. Sai da ta karya ta shirya ta tafi, napep ta hau tana kuma wucewa motar Abdurrashid na tsayawa ƙofar gidan. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH....RAYUWA NO.30 MARYAM LITEE Walida ta duba da ta ga ta ƙura mata ido sai ta ga Walidar ta taso ta kamata bayan ta rataya jakar Hamidar da ake ajiye. Da taimakon ta suke takawa zuwa cikin Hotel ɗin, dan Hamida daf take da ficewa hayyacinta. Wani ɗakin Hotel ɗin ta kai ta ta dire ta bisa gado bishi-bishi Hamida ke kallon ɗakin idonta na lumlumshewa, Walida ta kece da dariya "Sorry ƙawata, tun farkon fara ƙawancen mu nake fama da takaicin a komai kin fi ni, don haka da aka nemi in kawo ki za a ba ni maƙudan kuɗaɗen da ban taɓa mafarkin riƙewa ba sai ban yi wasa da damar ba." Usman Hamida ta ga ya shigo ɗakin yana wa Walida tafi"Kin yi namijin ƙoƙari." Ya faɗi yana duban ta, murmushi ta yi masa ta miƙa mishi hannunta "A ba ni balance ɗi na." Ya ciro wayarsa "Zan miki transfer yanzu." Ya matso kusa da Hamida ya kama hannunta sai ya sake shi hannun ya tafi yaraf, dariya ya kece da ita sai ya ɗauke ta hoto. Shigowar Brigadier ya ɗauke ji da ganin Hamida. Sara mishi Usman ya yi suka juya shi da Walida don barin ɗakin, Brigadier ya bi bayan su ya murza wa ƙofar key, ya dawo yana murza hannuwa yana ƙare wa Hamida kallo. Ya zauna gefen gadon so yake ya cire komai na jikinta kafin ya gabatar da ƙudirinsa, amma matsuwar da ya yi ya ji shi cikin jikinta ya sa ya fara kwance zanenta, ya zare skirt ɗin da ke ciki kyawawan cinyoyinta suka ƙara ɗimauta shi ya ja fant ɗinta pad ɗin da ya gani ya sa shi janye hannunsa da sauri, sai ya dafe kai komai ya tsaya mishi, ɓacin rai ya maye gurbin farin cikin da yake ciki, tsaye ya miƙe sai ya zura kayansa da ya tuɓe ya bar ɗakin. Ganin motar Usman a harabar Hotel ɗin ya ba shi mamaki ya isa ya ƙwankwasa glass ɗin, Usman ya fito yana sara mishi "Ya ba ka wuce ba? Ya tambayi Usman kame-kame ya hau yi don saƙe-saƙe yake yadda zai samu damar ɗaukar hoton Hamida yayin da brigadier ke kwance da ita da vedio yake so ya yi mata barazana ta ba shi kanta, don shi ba zai amfani da ita tana wata duniya ba ya fi so ta faranta mishi da kanta hakan zai sa ya samu gamsuwar da kullum yake mafarkin samu. "Yallaɓai ka fito kuma? Usman ya tambaya yana wani sunkuyar da kai "Mance kawai, abin su na mata take zan jira har ta tashi, idan ta wuce sai in tafi." "Ok Sir" Usman ya faɗi ya faɗa motarsa ya ja ya bar wurin jin Brigadier ba tafiya zai yi ba, don da ya san zai fito yanzu da ɓoyewa zai yi har sai ya wuce ya shiga ya rage zafi. Awa uku Hamida ta ɗauka tana barci sai ta farka zaune ta tashi ta dafe kanta da ke saDra mata. Ta ɗan jima a haka kafin abin da ya faru ya fara dawo mata zumbur! Ta miƙe tsaye salati take tana ƙarawa ganin zanenta da skirt a yashe tunanin sun keta mata mutunci ya sa ta fashe da kuka, sai dai tuna halin da take ciki na al'ada ya sa ta shafa wurin, fant ɗinta na nan haka pad ɗin, sai ta yi wa Allah godiya da ya kare ta. Usman, Brigadier, Walida. Ta riƙa kallon hotunan su a cikin ɗakin da Walida za a haɗa baki a tarwatsa rayuwarta? Komai na ta ta ɗauka sai takalmanta ne ba ta gani ba, ba ta damu da tsayawa neman su ba ta fita dakin, sai da ta je gaban motarta ta lalubi key a jakarta, yana ciki da wayarta, tana tayar da motar ta fara kuka iya ƙarfinta. Har ta kusa gida ta tuna da Abdurrashid, agogon motar ta kalla takwas saura na dare gabanta ya yanke ya faɗi me za ta gaya mishi yau? Ba ta son ce mishi komai har sai ta nutsu ta yi tunani, tana ajiye motar kusa da ta shi ji ta yi kamar kar ta fito,don shi ma tana jin tsoron abin da zai ce mata ta dai daure ta fita, a hankali take takawa har ta isa ƙofar falon ta yi sa'a ta ji ta a buɗe sai ta shiga da sauri ta miƙe zuwa ɗakinta "Ina kika tsaya sai yanzu kike dawowa? Cak ta tsaya jin muryar Abdurrashid cikin kanta wanda sam ba ta lura da shi a cikin falon ba. "Ban san sau nawa zan faɗa miki ba na son ki fita ki kai irin wannan lokacin matuƙar ba tare muka fita ba, amma kin raina ni, zan ɗau ki mataki a kanki." "Ka yi haƙuri." Ta furta ba tare da ta waiwayo ba "Kar ki damu ki cigaba sai dai kar ki yi kuka da matakin da zan ɗauka kanki." "Don Allah dai na ce ka yi haƙuri." Ta ƙara bada haƙurin cike da ƙosawa ta samu ta shige ɗakinta jin ya yi shiru ta san ba zai ƙara cewa komai ba sai ta wuce ɗakinta kamar ana tunkuɗa ta. Gado ta hau ta rufe idonta takaici take ji kamar ta rufe kanta da duka, me ya sa ba ta tona mishi asiri maganganun banzan da ya gaigaya mata da yau ko me Abdurrashid zai yi mata sai ta faɗi abin da suka yi mata a yau shi da Walida, abin da zai taka mata burki Brigadier da ya shigo tsakiyar su, ba za ta so auren yar'uwarta ya mutu ba ɓullar maganar zai iya shafar zumuncin su har a can gida, don haka ta yanke yin shiru kawai tana kammala karatunta ta bar garin. Wayarta ta lalubo sai ta gan ta a kashe ta kunna tana neman sunan Walida sai saƙo ya shigo ta tsaya dubawa gargaɗi ake mata kan idan ta tona abin da ya faru a yau kiran sunan wani a cikin su ukun abu biyu zai faru mutuwar auren Aina da tsintar gawar Abdurrashid. Wani busasshen miyau ta haɗiya ta ci-gaba da neman lambar Walida sai dai ba ta shiga, goge ta ta yi gabaɗaya daga wayarta don wani abu da ke tokare ta idan ta ga sunan ta tuna cin amanar da ta yi mata. Tana nan zaune cikin alhini da baƙin ciki ba ta ankara ba sai ta ga ƙarfe biyu da rabi na dare, ta shi ta yi ta shiga bathroom ta tsaftace jikinta sai ta fito ta tuɓe kayan jikinta ta kashe wutar ɗakin ta kwanta shiru cikin wani sabon tunanin. Asubar farko barci ya yi awon gaba da ita wanda ya ja mata muguwar makara, sauƙin ta ma da ba sallah za ta yi ba shi ma bugawar da mai mata aiki ke yi ya tayar da ita, don Abdurrashid bai bi ta kanta ba saboda yana fushi da ita ya gama shirin sa ya bar gidan. Ta buɗe mata suka gaisa sai ta koma ciki ta yi wanka, da fitowar ta wata doguwar riga ta zura ko mai ka sa shafawa ta yi. Ta fito ta haɗa Tea zalla tana sha bakinta ba daɗi don yadda ranta ke ɓace, gamawar ta ɗaki ta koma tana ci-gaba da tunanin da ya fara addabar ta ta rasa wa za ta kira su raba wannan abu da ya faru da ita ko za ta samu shawara, Hanan da Mimi sune aminan ta amma kuma su ɗin dangin miji ne ita kam tana tsoron dangin miji komai daɗin ka da su. Tana nan har ta ji dirin motar Abdurrashid ta miƙe ta fita tarar sa jakar da ya shigo da ita ta karɓa tana mishi barka da zuwa ya amsa fuska ba walwala, ko da ya ke fushi da ita yana mamakin abin da ya sa duk ta yamutse bai dai tambaye ta ba ko da suka zauna cin abinci yana kula ba wani na kirki ta ci ba. Haka suka ɗauki kwanaki uku yana ta tunanin abin da ya same ta, don ya san hakanan yake fushi da ita ba ta bari a kwana za ta yi shigar da za ta ɗau hankalinsa ta sha turarukan da ƙamshin su ke kiɗima shi wanda jikinta ma da gidan sun riga sun riƙe ƙamshin,ta kawo kanta tana kukan kissa tana ba shi haƙuri shi kenan ya wuce. Ya dawo aiki tana makaranta wanda tun faruwar abin a tsorace take fita sai ta ga kamar za su sace ta su idasa mugun nufin su a kanta, ji take kamar ta haƙura da karatun da aski ya zo mata gaban goshi ta tattara ta koma Kano. Yana zaune ta dawo ɗakinta ta shige ta fito tana kankare jan ƙunbar da ta sanya a farcenta, kallo ɗaya ya yi mata ya faɗi a ransa ta samu tsarki kenan? Don haka da daddare tana kwance a ɗakinta ya shigo a wannan daren Allah ya yi ikon sa rabo ya shiga a tsakanin su wanda da wata ya zagayo Hamida ba ta ga al'adarta ba hakan bai wani ɗaga mata hankali ba don ta sha yin haka sai sun gwada su ga ba komai. Ba abin da ta canza na daga ɗabi'unta ma'ana ba ta wani laulayi kuma Allah ya ɓoye abin sa ko shi likita bokan turan bai gane ba. A haka ta kammala karatunta ta shiga magiya ga Abdurrashid ya bar ta ta koma Kano shi kuma ya ƙi amince mata. Wata safiya ta yi waya da mutanen gida mutum na ƙarshe da ta yi wayar da shi shi ne Malam da za su tashi zuwa ƙasar Singapore shi da Engineer, Malam ɗin na fama da ciwon sugar Engineer kuma zai je kan harkokin kasuwancinsa kuma shi ma za a duba shi kan ciwon shi na zuciya. Engineer ne ya shirya musu tafiyar, zai tafi har da Aunty Karima. Hamida ta yi wa Malam fatan nasara da dawowa lafiya. Har ta ajiye wayar sai ta ga ya kamata ta kira Daada kwana biyu ba ta kira tsohuwar ba, duk da dai idan ta ji shiru Hamidar ba ta kira ta ba sai ta kira. Sun gaisa ta ajiye wayar, Abdurrashid ya shigo ya dube ta yadda ta harɗe ƙafa tsakiyar gado "Wai me kike a ɗaki? Murmushi ta yi "Yan Daura na kira da Malam mai tafiya." Shi ma ya murmusa "Ya yi kyau, ni fita zan yi, zan ga wani abokin aikina amma ba daɗewa zan yi ba wani saƙo zan karɓa." Ta diro gadon ta bi bayan shi sai da ya fita ta dawo, gadon ta koma ta ɗauki wayarta Whatsapp ta shiga bayan ta kunna data, shigowar wani saƙo daga wata baƙuwar lamba ya sa ta dubawa, wani ɗan short video ne sai saƙo a ƙasa vedio ta fara dubawa abin da ta ganin ya sa ta miƙewa tsakiyar gadon, sai kuma ta koma ta zauna gabanta na masifar bugawa zufa na wanke fuskarta. Vedionta ne kwance shame-shame a ɗakin Hotel, har sunan Hotel ɗin ga shi nan ta dafe ƙirji tana karanta saƙon da aka turo ƙasan Video *"Ina neman haɗin kanki idan kina son rufin asiri wurin mijinki, in ba haka ba zan tura mishi vedio nan."* Wani baƙin ciki ya turnuƙe zuciyar Hamida, ko da dama ta san ba su ƙyale ta ba ba ta san Usman zai iya zuwa mata da wannan rainin hankalin ba, ita da kanta ma yau za ta faɗi ma Abdurrashid komai. Voice note ta yi masa ta dandanƙara masa magana kafin ta kwasa ta fito falo tana jiran dawowar Abdurrashid wanda take jin kamar ta bi shi don ƙosawar da ta yi ya dawo. An samu kamar minti talatin ta ji dirin motarsa. Bugun da yake wa ƙofar shigowa falon kamar ba na lafiya ba ta ƙarasa ta buɗe sai dai yanayin da ta gan shi tuni ya sare mata gwiwa, tashin hankali take hangowa a tare da shi gabaɗaya ya birkice. Zama ya yi a kujera ya cusa hannayensa cikin sumar kanshi kafin ya ɗago ya dube ta da idanuwansa da suka canza kala, take ta ji ƙafafuwanta sun ɗauki rawa. Ya ciro wayarsa ya nuna mata "Meye wannan Hamida? Wane zance nake ji game da ke Hamida? [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA NO.35 MARYAM LITEE Wuya sosai ta sha hannun Abdurrashid har sai da ta fara mishi kuka ya sarara mata. A jikinsa ya rungume ta hannunsa kan cikinta cikin kunnenta yake raɗa mata zancen cikin Aunty Karima, buɗe idonta ta yi daga lumshe sun da ta yi ko da Aunty Karima ta tashi daga ganin abinci ba ta kawo ciki ne da ita ba ta taya Auntyn murna a ranta. Hira suke a hankali har sai da aka kira sallar magrib ya raba ta da jikinsa ya shiga bathroom. Ita ma anan ɗakin ta yi sallah don ba ta gyara ɗakinta ba har sai da suka yi sallar asuba tana ganin Abdurrashid ya fara barci ta zare jikinta, ya buɗe ido ya dube ta sai ya mayar ya rufe, ta fita sai ta ja ƙofar. Ɗakinta ta wuce ta shiga kakkaɓe kakkaɓe da goge goge ta canza labulayya da zanen gado sai da ta ga ɗakin ya yi mata yadda take so sai ta fita zuwa kitchen, tun a jiya aka kawo mata abin da ta buƙata daga wurin Aunty Karima, Abdurrashid ta haɗa ma abin karyawa ita kunun gyaɗa take sha a Daura don ba ta iya shan madara, ta san Innawuro ta manta ta haɗo mata da markaɗaɗɗiyar gyaɗarta don duk abubuwan da take ci ta haɗo mata su. Tana farawa mai taya ta aiki daga wurin Aunty Karima ta yi knocking ta je ta buɗe sai da suka gaisa Hamida ta ce ta gyara falo. Lifton ta dafa ma kanta sai ta fita kitchen ɗin, wanka ta je ta yi ta gyara kanta sai ta fita zuwa ɗakin Abdurrashid ta samu ya farka yana kwance yana danna wayarsa ta zauna gefen gadon tana gaishe shi sai ya tashi zaune da ta faɗa mishi ta kammala abin break tare suka fito, motsin mai aikin ta ji a kitchen tana gyarawa. Abdurrashid yana cin abincinsa yana kallon Hamida da ke shan ruwan lipton tsura ya ce "Ba abin da kike ci ne? Sai ta yi mishi bayanin kunun gyaɗa take sha kuma babu abin yin, ya ce ta nema yau. Ta ce "To." Ya kusa kammalawa aka yi knocking Hamida za ta miƙe mai mata aiki ta fito daga kitchen ta je ta buɗe suka dubi wurin don ganin wanda zai shigo Maman Walida ce, haɗa idon su wani abu Hamida ta ji ya tokare mata ƙirji tuna abin da Walida ta yi mata, miƙewa ta yi ta nufi wurin ta ta ce mata maraba ta nuna mata wurin zama sun gaisa fuskar Hamida ba yabo ba fallasa, ta ce "Taimako na zo nema Haj Hamida." Cikin mamaki Hamida ta ce "Wane irin taimako? Sai ta fashe da kuka" Hamida ta danne zuciyarta don ji take kamar Walidar ce gabanta ta ce "Subhanallah ya kuma kike kuka Umma? Ta share hawaye "Ƙawarki Haj Hamida. yau kimanin watanni biyu kenan ba mu gan ta ba ko sama ko ƙasa." Hamida ta ce "Innalillahi, ba ku gan ta ba? Ta fyace hanci "Wallahi tafiya ta yi kwana biyu da tafiyarta mun yi waya, daga nan shi kenan ko an kira wayar a rufe take." "Duk kuma an je inda take zuwa? Hamida ta tambaye ta "Ba inda ba a je ba shi ne na zo neman taimako wurin maigidanki ya taimake ni yadda Allah ya taimake shi daga shi Soja ne, ko Allah zai sa in san inda take." Abdurrashid ya tashi zai wuce wurin shi ta sauka kan kujera ta soma gaishe shi, shi kuma tunda ya gane uwar Walida ce ya yi matuƙar ɗaure fuska ta soma shessheka"Ka taimaka mini yadda Allah ya taimake ka." Amsawa ɗaya ya yi ya shige ciki. Ta ci-gaba da roƙon Hamida ta ce kar ta damu za ta yi mishi magana za su yi iyakar ƙoƙarin su. Ta miƙe Hamida ta kai ta zuwa ƙofar falo ta dawo ta zauna tana tuna cin amanar da Walida ta yi mata baƙin cikin abin ta ji ya taso ya rufe ta, tuna Abdurrashid na ɗaki ya sa ta miƙewa zuwa ɗakin, wanka ta samu ya fito yana goge kansa ta samu wuri ta zauna sai ta rasa ta inda za ta fara mishi magana don har ga Allah Umman Walida ta ba ta tausayi za ta saurari maganar ne don ita, amma ta ma fi ƙarfafa zargin Walida yawon barbaɗarta ta tafi. Ta yi ƙarfin halin fuskantar sa, "Kana ji Hamma abin da ta zo da shi? Ka taimaka mata don Allah." Wani kallo ya yi mata da ya sa ta kauda kai sai ya ja tsaki "Ki fita harkar mutanen nan na faɗa miki, ko za ta fito ba yanzu ba sai ta gane matar wa ta taɓa." Galala ta yi da baki gane da hannunsa a ɓatan na Walida. "Kai ka ɓatar da ita Hamma? Ƙara ɗaure ya yi sai ta fasa faɗin abin da ta yi niyya illa ta ce mishi za ta dubo Aunty Karima. Kwance yau ma ta same ta ita ta yi mata gyaran bedroom ta haɗa mata ruwan wanka, da bin bango ta shiga ta yi ta fito ta nuna ma Hamida kayan da za ta ɗauko mata ta shirya sai mai aikin ta ta zo ta ce mata Dr ta zo, tare suka fito da Hamida, Hamida ba ta zauna ba ta ce za ta koma gida. Sai da ta biya ta gaida Engineer da bai daɗe da dawowa daga Daura ba sai ta koma gida. Kitchen ta shiga ta fara shirin abincin rana shinkafa ta yi ma Abdurrashid da miya duk son ta da shinkafa da miya yanzu ba ta son ta, ita cikin sai ya cika wata uku sannan ta fara ba ta cin wannan, tana cin wannan kuma ga shi har ya shiga wata na biyar ba ta daina ba. Ita dambu ta ɗora ma kanta da tsakin da ta taho da shi. Jin Abdurrashid ya shigo daga sallah da ya fita ta ɗauko abincinsa ta ajiye a dinning sai ta koma kitchen ta fito ɗauke da flet sai ta nufi inda yake tsaye yana tuɓe jallabiyar jikinsa ya juyo ya dube ta, ta ɗan karya wuya "Bari in kai ma Aunty." "Me za ki kai mata? Ya tambaye ta yana kallon flet ɗin da ke hannunta "Dambu na yi shi ne zan kai mata ko za ta iya ci." Juya kai ya yi yana canza tasha da remote ɗin da ke riƙe a hannunsa ya wuce dinning ɗin. Ɗaki ta koma ta sanya hijab ta fito kwance ta samu Auntyn a falo ta ba ta ta kuma wuce kitchen ta ɗauko mata cokali, ba ta zauna ba ta koma gidanta. Ta samu Abdurrashid har ya yi nisa da cin abincinsa, tana yaye hijab ɗin kitchen ta faɗa ta fito da nata danbun,don da ma flet biyu ta yi. Abdurrashid dai bin ta ya yi ta yi da ido ganin yadda take ci, yana kammala miƙewa ya yi ya shige ciki ya fito cikin shiri, ya ce mata zai fita ta yi mishi fatan dawowa lafiya tare da roƙon zuwa La'asar za ta leƙa Gwoggonta. Ya ce a'a daga dawowa sai yawo? Bai jima da fita ba ta ji knocking ta tashi ta buɗe sai Gwoggonta ta gani fara'a "Shigo Gwoggo,sannu da zuwa." Ta shiga tana faɗin "Tun ɗazu na shiryo in zo in gan ki, sai ga Laila ta yo yaji." Hamida ta fidda ido "Yaji kuma Gwoggo? Ta ce "E wai aure zai yi shi ne suke ba ta kashi." "Hamida ta dafe kai "Innalillahi, wayyo Aunty Laila, kishiya za a yi mata? Ta ajiye ma Gwoggo lemo tana zuba mata "Ke dai bari yau duk hankalina a tashe yake yadda Laila ta fita hayyacinta, ya jikin ke kuma? Hamida ta ce "Na ji sauƙi." Suna ta hirar su har cikin hirar take ba Gwoggo labarin cikin Aunty Karima ta yi ta mamaki ta ce "Ikon Allah kenan, ashe rabon naku a tare yake." Sai La'asar ta tashi tafiya Hamida ta yi mata alheri na kuɗi da turare. Ganin Abdurrashid bai shigo ba ta yi ma kanta tuwon dawa miyar kuka, shi ba ya cin abinci mai nauyi da daddare. Nan ma kallon ta ya yi ta yi da take ci yana shan fruit salad ɗin da ta haɗa mishi. Da ta kammala ɗakinta ta koma ta yi wanka da duk shirin da za ta yi na zuwa turaka. Ta fito cikin wata yaloluwar rigar barci mai hannun shimi ga cikinta nan ya turo,tsawon rigar iya gwiwa. Ta lura tunda ta fito Abdurrashid yake kallon ta ta zauna tana taya shi kallon film ɗin da yake kallo, sosai take son shirin series Film ne kuma ta yi sa'a ana farawa ta fito Miƙewa ya yi sai ya soma kashe duk kayan wutan da ke falon ganin ya kashe TV ta ɓata fuska "Haba mana Hamma,ina son shirin nan." Ya ce "Kwanciya zan yi " Ta dube shi "Zan taho idan an gama." Ya girgiza kai " A'a, a jikinki zan yi barci, ina jiranki." Ya wuce ta bi shi da kallon takaici ya hana ta ta kalla. Ta miƙe ta mara mishi baya, yana shiga tana shiga, ganin ya hau gado ita ma ta haye ya janyo ta ya sa jikinsa tana jin ajiyar zuciyar da yake fiddawa. Sai da suka yi nisa da wasanni ta yi mishi tambaya kan batun Walida, take ya amsa da cewa shi ya sa a ɓoye ta amma bai ce a mata komai ba yana so dai ta ɗauki darasi. Ajiyar zuciya ta fidda sai ta cigaba da abin da take masa wanda ya ƙara rikita shi sai ta kwantar da murya ta roƙe shi ya saki Walida kawai ko dan uwarta, ya ce zai yi hakan. Washegari ta kammala shiri da hantsi za ta gidan Gwoggonta sai ga Maman Walida ta kuma dawowa. Wata magiyar ta dasa mata a taimake ta a nemo mata Walida. Hamida ta ce Kar ta damu ganin Hamida cikin dogon hijab da Safa ta ce "Hala fita za ki yi na tsare ki? Murmushi Hamida ta yi ba ta yi magana ba ta ce "To mu je, ni ma gida zan koma." Tare suka fita a ƙafa ta yi niyyar tafiya amma saboda Maman Walida ta janyo motarta ta buɗe mata gaba ta shiga suka tafi. Suna tafiya tana faɗi ma Hamida tashin hankalin da take ciki wanda ko barci ba ta iyawa. Sun zo gidan Gwoggo Hamida ta tsaida motar, Maman Walida ta ce"Ni ma zan shiga mu gaisa da Haj Indo." Hamida sai fargabar haɗuwar Maman Walida da Gwoggonta take don ta san sam ba za ta yi daɗi ba. Suka sauka tare tana kulle motar Gwoggo ta turo ƙofa ta fito, ganin Hamida da Maman Walida ya sa ta ƙara buɗe idonta, tabbatar da abin da idon ke nuna mata ya sa ta balbale Hamida da faɗa "Wane irin rashin hankali ne haka kuma?Me ya kuma haɗa ki da mutanen nan Hamida ko sharrin ne bai ishe ki ba? Maman Walida ta matso "Gwoggon yara ina kwana? "Riƙe gaisuwar ki Marka, ban da buƙatar ta, me ya kawo ki wurin Hamida? Ko yar ki bata faɗa miki tarwatsa rayuwar Hamida da ta tashi yi sai dai ta Allah ba ta ta ba? Cikin rashin fahimta Uwar Walida ta ce "Wai me ya faru Haj Indo? Ta yi ta ba Gwoggo haƙuri kan ta faɗa mata abin da ya faru. Gwoggo ta gaya mata saƙare ta yi kunya ta baibaye ta da takaici kafin ta shiga ba Hamida haƙuri da rantsuwar ba ta sani ba. Nan dai ta wuce a sanyaye, Gwoggo da Hamida suka wuce ciki sai surfa ma Hamida faɗa take da ta tsaya sauraron uwar Walida. Ganin Laila Hamida ta yi duk ta yi wani firgai-firgai, ta matsa kusa da ita tana gaishe ta suka ji sallamar Ahmad ya shigo, sai da aka gaisa ya bada haƙuri tare da cewa Laila ta tashi su tafi ta yi funfurus, sai Gwoggo ce ta ce ya yi tafiyar sa za ta maido ta da yamma. Cikin damuwa ya tashi ya tafi. Sai kuma bayan tafiyasa Hamida ta ji duka-duka auren saura sati biyu. Tana zaune tana cin kwakwa tana sauraron Gwoggo na ba Laila shawara. Ƙarfe uku ta yi shirin komawa gida Gwoggo ta ce ta bari su kintsa sai ta sauke su. Sai da Laila ta yi wanka ta shirya suka tafi Gwoggo sai mita take a mota "Don za a yi maki kishiya sai kuma ki zama ƙazama, tunda kika zo fa Laila ba ki yi wanka ba meye haka? Sun samu gidan Laila kaca-kaca don ba ta da mai aiki sai yaranta su hudu, Amir shi ke komai na aikin gida. Hamida ta cire hijab ɗinta ta shiga kintsa wurin a ranta kuma tana fargabar haɗuwar ta da Abdurrashid don ta daɗe. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA NO.34 MARYAM LITEE Shigowar Aliyu suka gaisa da Abdurrashid, Innawuro ta shaida mishi abin da kenan. Ya isa ɗakin ya samu Hamida shi ya yi aikin rarashin da har ta haƙura ta tashi ta yi wanka ta shirya cikin riga da zane da dogon hijab ta fito zuwa cikin gida don ta yi sallama da mutanen gidan, ta wuce Abdurrashid da Aliyu kowanne sashe ta shiga sai Allah ya kyauta gaba ake mata da Allah ya kiyaye hanya ta yi tunanin kowa ya ji maganar kenan? Sasan su ta shiga ƙarshe Innarta na zaune tana kallon tashar Sunna TV sai ƙannenta su biyu, zama ta yi Innar ta ce "Kin tashi kenan? Ai don mijin naki da ke zaune ya hana in shigo in ci miki, Innawuro ke sangartaki." Ta tura baki sai hawaye"Ni Inna ba a ga abin da ya yi min ba? "In an gani fa rayuwar duka guda nawa take? Babu abin da ke isa sai haƙuri, ki yi haƙuri jarabawa ce." Nan dai ta yi ta mata nasiha ta share hawaye sai ta miƙe ta tuɓe hijab ɗin ta yo alwala don ta ji an fara kiran sallah sai da ta idar ta murza farar hoda,ta je ta zauna gaban Innarta, haƙuri ta ƙara ba ta da yi mata nasiha sai hawaye ke zubo mata. Sallamar da Abdurrashid ke yi daga bakin ƙofa bai sa ta motsa ba ya shigo cikin nutsuwa Innar ma ƙara sunkuyar da kanta ta yi ya gaishe ta tare da ba ta Haƙuri kan abin da ya faru duk da bala'in kunyar sa da take ji sai da ta yi musu nasiha da su je su yi ta haƙuri, rayuwar aure yar haƙuri ce. Da ta gama ta tashi ta shige ɗakinta ya yi mata godiya da bankwana, sunan Hamida yake kira a hankali yana faɗin ta tashi su wuce banza ta mishi tana share hawaye, shigowar ƙannenta ya sa ta miƙe ta bar falon tana goge ido, shi kuma ya ciro kuɗi ya ba ƙanenta Jabir ya ce idan sun wuce ta ba a ya miƙe ya bi bayan Hamida. Mutanen gidan sun fito suna mata Allah ya kiyaye hanya ƙannenta suka saka tsarabar sauri da Innawuro da Innarta har ma da mutanen gidan suka haɗa mata, ta zauna cikin motar tana mamakin wannan zalama ta Abdurrashid da kamar dole sai ya tafi yau tsoron tafiyar dare take saboda hanya da ba ta da kyau, duk lol maganganun da yake mata ba ta ce uffan ba sai can ta ce "Saboda Allah ka san hanya ba kyau meye na tafiyar dare? Ɗan murmushi ya yi mata yana zaro bindigogin da ke jikinsa"Kuma yarinya ba ki ga motar da na ɗauko ba? Kauda kai ta yi a ranta tana cewa "Ka ji shi waɗannan masu kama mutanen ina ruwan su da wani Soja? Sai ta ji yana kiran wayar Aunty Safiya bayan ya gaishe ta ya ce yana hanya bai daɗe da tasowa ba ta yi haƙuri ya so tsayawa amma yamma ta yi. Faɗa ta yi mishi kan tafiyar dare ta ce maza ya iso Katsina, gobe da safe sai su wuce. Inda Hamida ke zaune ya duba sai ya ajiye wayar a gefensa, ita da ba ta san me aka ce mishi ba har ya canza hanya ba ta ce komai ba. Ganin sun shiga birnin Katsina ya sa ta mamaki a ranta ta ce da ma Katsina zai tsaya? Ya shiga masarautar Katsina aka kuma kiran wayarsa, har kuma ya yi parking bai gama wayar ba ya fito cikin motar ya jingina jikinta ya ci-gaba da wayarsa. Hamida ta fita ta kama ɓangaren Aunty Safiya, tana ta shan gaisuwa daga barorin gidan aka yi mata iso kafin aka zo aka yi mata jagora zuwa wani shiryayyen falo da take hutawa, daga inda take kishingiɗe kan kilishi take ma Hamida murmushi da barka da zuwa,ta zauna gefen ta tana miƙa gaisuwa, aka shiga hidimar kawo mata abin tarar baƙi, Abdurrashid ya shigo apple ɗin da ke gaban Auntyn ya ɗauka sai ya zauna daf da ita sai sannan ta tashi zaune gaisawa suka yi cike da bayyana so da ƙaunar da ke tsakanin su. Suna nan zaune har aka kira sallar magrib, Aunty suka tashi ita da Hamida maimakon inda take saukar baƙinta bedroom ɗinta ta kai Hamida ta yi sallah, ƙaramar yarinyarta ta shigo ta ce mommynta ta ce ta fito su ci abinci, ta ɗaga mata kai sai ta miƙe da hijab ɗin ta fito wani wuri na musamman da aka shirya don cin abinci ta gano su zaune Aunty Safiya da Abdurrashid, ta isa ta zauna kan tattausar shimfiɗar sai ta ƙara gaida Aunty Safiya. Kowannen su ya zuba abin da yake so amma Hamida ƙamshin da suke fitarwa ma tayar mata da hankali yake saboda Aunty Safiya ta zauna suka zuba har sun fara ci Abdurrashid dai ganin idon Auntyn ya hana shi mata magana sai Aunty Safiyan ce ta ce "Yaya dai Hamida ki zuba mana." Ta ce "To." Ta zuba kaɗan sai dai cin ya gagara ta ce "Ko akwai abin da kike so a yi miki? Da sauri ta ɗaga kai "Idan akwai tuwo ina so Aunty, na dawa ko na Semo." Take Auntyn ta zargi wani abu wanda take fatar ya tabbata. Kira ta yi ta sa a tuƙa ma Hamida tuwon Semo, suna kuma gama cin nasu abincin ana kawo tuwon su Auntyn suka koma falo ita kuma ta zauna ta ci tuwonta wanda ta ji daɗin shi, da ta gama ba ta zauna inda Abdurrashid da Auntyn ke hira ba wuce su ta yi ta je ta hau gado ta yi kwanciyar ta ba ɓata lokaci kuma barci ya yi awon gaba da ita. Sama sama ta ji muryar Auntyn tana cewa "Anya Hamida kwanciya da wannan dogon hijabi." Ba ta yi magana ba ta gyara kwanciya, kukan wayarta ya tashe ta ta ɗauka ta kai kunne Abdurrashid ne ke faɗa mata ta zo ta same shi cikin muryar barci ta ce ba ta san inda yake ba. Ya ce ta fito za ta gan shi. Ta ce "Haba ga Aunty ya za a yi in fito? Ya ce "Ba Aunty daga ta bar miki ɗakin, da asuba sai ki dawo." Ta ce ita dai ya yi haƙuri tana jin kunyar Aunty ta gane ta kashe wayar ya sake kira bai shawo kanta ba ƙarshe ya turo mata text ƙyale shi ta yi ta sanya wayar a silent ta tura ta ƙarƙashin pillow ta shiga barcinta. Da asuba ko da ta farka sallah ta yi karatun Alqur'ani don akwai complete Quran a wayarta, da azkar da yanzu ya fara zame mata jiki. Sai ta koma saman gado ta koma barcinta. Ƙarfe takwas ta shiga bathroom ta yi wanka ta yi kwalliya wata doguwar riga ta sanya ɗinkinta mai girma ne don haka ya ɓoye cikin da ba ta so a gani, tana fesa turare Aunty Safiya ta shigo ta ɗan ranƙwafar da kai ta soma gaishe ta ta amsa cikin fara'a ta ce ta zo su je ta gaida mai martaba, suna dawowa suka samu Abdurrashid ya shigo cikin shiri yake Aunty Safiya ta ce "Duk saurin ka dai ka tsaya ku yi break past." Kamar jiya ma tare suka yi zaman karyawar cikin ya sa Hamida ba ta iya shan madara sai Lipton ta sha ta ci wani Farfesun kaza. Suna gamawa Abdurrashid ya ce za su wuce kyautar wasu turaruka Aunty Safiya ta yi wa Hamida. Sun ɗauki hanya babu mai magana duk da mamakin canjin da ya gani tattare da Hamida na mu'amala da dogon hijab da Safa bai mata magana ba. Ƙarfe Sha biyu suka shiga Kano. Suna shiga Estate ɗin ta kira Gwoggo Indo ta waya ta ce ta dawo, yana sauraren ta har ta ƙare wayar sai ta dube shi "Ka fara sauke ni wurin Aunty Karima." Jin bai tanka ba ta ce "Don Allah." Can ɗin ya yi horn aka wangale gate ya cusa hancin motar. Masu aiki na ta mata barka da zuwa ta isa falon Aunty Karima Abdurrashid masallaci ya wuce ta tambayi Aunty Karima suka ce tana bedroom ɗinta. Can ɗin ta isa ta yi knocking ta ji muryarta ta ce a shigo ta shiga da sallama kwance ta samu auntyn ta tashi zaune da ƙyar, cikin mamaki Hamida ta ce "Ba ki da lafiya ne Aunty? Ta janyo tissue ta zubar da yawu sai ta yi murmushi "Ai na kwana biyu." Hamida ta nuna damuwarta ta yi mata fatan samun sauƙi. Anan ta yi sallah suka fito falo ana kawo abinci Hamida na buɗewa Aunty Karima ta tashi da sauri tana toshe hanci ta ɗan jima ta dawo Hamida ta yi mata sannu sai ga Abdurrashid ya gaishe da Aunty Karima ya ce Hamida ta zo su tafi, ta miƙe ta yi wa Auntyn sallama da addu'ar samun sauƙi sai ta bi shi a baya, part ɗin Mami da ta ga ya nufa ya sa gabanta bugawa tunawa da Anisa. Fara'a sosai Mamin ke yi da suka shiga, da suka gaishe ta ba su jima ba ya miƙe sai suka bar part ɗin. Ba ta yi mamakin ganin falonta fes ba don ta san Abdurrashid na zuwa, a hand bag ɗinta ta ciro keyn ɗakinta sai ta nufi can ya yi ƙura sosai ta fara gyarawa Abdurrashid ya shigo "Ki bari a kira masu aikin Aunty mana su gyara "Ta ce "Zan iya." Ya ce "To zo mana." Ya juya ta ɗan bi bayansa da kallo sai ta taka ta rufe ƙofar bunner ɗinta ta jona sai ta ɗauko turare ta ɗan turara gabanta, ta shafa wata humrarta sai ta fito. Tana tura ƙofarsa ta hango shi ya yi ɗaiɗai bisa gadonsa, a bakin gadon ta zauna sai hannunsa ta ji ya janyo ta, yana samun nasarar kai ta gado sai ya ɗora mata nauyinsa "Wayyo numfashina." Hamida ta ce cikin haki, jin nunfashin da take ya sassauta dannetan da ya yi sai ya fara ƙoƙarin raba ta da rigarta, bai sha wahala ba ya cire ta sai bin ta yake da kallo ganin ainahin canjin da jikinta ya samu ba kamar tana da kaya ba, yana zuwa cikinta wani abu ya ji ya buga a ƙirjinsa, hannayensa duka ya sanya kan cikin "Faɗi min da bakinki Hamida, alherin da na daɗe ina roƙon Allah ya ba ni shi na samu kika ɓoye min. Sai ya sake ta ya sauka gadon ya yi sujjada, ya daɗe kafin ya ɗago ya dawo gadon ya rungume ta tsantsan har sai da ta ƙara cewa numfashina sai ya sassauta mata "Gaya min Hamida tun yaushe ne,wata nawa kenan? Da hannunta ta nuna mishi ya shiga wata na biyar mamaki ya kashe shi yadda aka yi ya kasa ganewa tun tana Abuja. "Me ya sa ba ki kira ni kin faɗa min ba? Ya ce yana kafe ta da ido ta ɓata fuska "Ka kore ni sai in kira ka? Yar dariya ya yi wadda bai faye yin ta ba sai ta ƙure "Korar ki ma na yi? Kunnenki na ja." Ya faɗi yana jan hancinta. Tambayoyi ya ci-gaba da yi mata kan cikin tana ba shi amsa abin da ya shagaltar da shi bai samu yin abin da yake ta kwaɗayi ya samu su keɓe da matar ta sa ba, sai kiran sallar la'akari suka ji, tilas ya janye ta daga jikinsa ya shiga bathroom ɗauro alwala. Ita ma ta tashi ta yi ta ta sallar. Yana fitowa sallah yan'uwan mahaifiyarsa suka soma kiran sa suna tambayar ya Hamida ba wata dai matsala kansa ya ɗaure bai samu amsa ba sai da Daada ta kira shi hamdala take ta yi da Allah ya sa tun tana raye za ta ga wannan rana Karima da matarsa na da juna biyu tana ta addu'ar Allah ya sauke su lafiya. Abdurrashid da ya yi shiru yana sauraren ta ya ce "Wai Daada wa ya gaya miki Daada? Ta ce "Karima ta kira ni ta ce yanzu mahaifinka ya kira ta ya ce shi ma yanzu ya samu labari a Daura, Karima kuma jiya ta faɗa mata na ta, yana shiga falo Hamida ma wayar take da su mimi suna murna don gabaɗaya labarin cikin ya karaɗe family ɗin su har sai da Abdurrashid ya gaji ya ce "Wayar ta isa ina jiranki." Ya faɗi yana wucewa "Mijina na kira na sai anjima. Ta ce wa hanan da suke waya a lokacin ba ta saurari sharrin da take mata ba ta bi bayansa. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH...RAYUWA NO.33 MARYAM LITEE Da zuwan su ta sallami me nafef ɗin, a hankali ta shiga asibitin sai da ta karɓi babban katin ta samu wuri ta zauna inda sauran mutane ke zaune suna ganin likita. Abdurrashid ya ɗan jima bai fito cikin motar ba yana duban gidan, ya dai gyara farking sai ya fito kai tsaye ya shiga gidan wanda yanzu kowa ya ja doguwar katanga ba wanda zai san ka shigo sai wanda ka shiga wurin sa. Sasan Innawuro ya shiga da sallama wadda ke taya me aikinta girkin tarar tsohon mijinta, ta amsa tana fitowa daga kitchen mamaki ne ya rufe ta ganin me sunan mijinta, duk da daman kullum addu'ar ta kenan Allah ya kawo mijin jikarta ta ta koma ɗakin ta. Ta faɗaɗa fara'arta tana mishi sannu da zuwa ya zauna yana gaishe ta cikin girmamawa sun ɗan yi shiru ya ce Malam yau za su sauka Kano." Ta ce "Ma sha Allah, Allah ya kawo mana su lafiya." Ya ce "Amin zan je in gaishe da mutanen gidan." Ta ce "Ai kam mazan duk sun fita." Ya ce bari ya gaido Mama. Ta san maman Hamida yake nufi ta ce "To." Ko da ya je ya gaishe ta ya dawo suka ci gaba da zama ya ji Innawuro bata da niyyar kira masa Hamida sai ya tambaye ta ta ce "Da ciwon kai ta kwana, ta je Asibiti." Da damuwa a fuskarsa ya ce "Ina ne asibitin? Ta ce "Bari dai in sa a raka ka." Ta fita ta samo yaro ya miƙe suka fi ce. Asibitin babu nisa da gidan, yana yin farking ya sallami yaran ya shiga ciki. Wani mai saida kati ya tambaya ko ya ciro katin wata Hamida Ibrahim a yau? Ya ce "Bai ciro ba." Ganin Abdurrashid babban mutum ne ya sa ya ce bari ya tambaya mishi, fita ya yi yana tambaya wata Nurse ya samu ta ce ya tambaya wurin masu ciki, ilai kuwa yana zuwa aka ce ta zo, ya duba ta wurin ganin likita, sai ya koma ya faɗa wa Abdurrashid hannu ya sa aljihu ya yi masa kyautar girma, ya shiga godiya ya bi Abdurrashid ɗin shi ya tambayi Hamida Ibrahim wasu mata biyu suka faɗi yanzu ta shiga wurin likita. Abdurrashid ya nemi ya nuna masa Office ɗin likitan, ya nuna mishi knocking ya yi daga ciki likitan ya amsa ya murɗa handle ɗin ya shiga, sun kalli juna da likitan ya ƙarasa ya bashi hannu suka yi musabaha Hamida wadda zaman ta kenan cikin dogon hijab ɗinta da safa jin ƙamshin turaren Abdurrashid ga kuma ƙarin mamakinta kamar muryarsa, ID Card ɗinsa Abdurrashid ya nuna masa wanda yasa likita ya ƙara shiga nutsuwarsa ya ce "Me ke damun Madam ɗi na? Likitan ya ce "Ciwon kai ne ranka ya daɗe ka san mata masu irin lalurarsu, can na ciwo nan na ciwo." Kan Abdurrashid ya ɗaure wace irin lalura ce da matata?"Kafin likita ya bada amsa ya kai wurin Hamida hannayenta ya lalubo cikin hijab ɗin ya ɗan rankwafo har suna jin nunfashin juna "Wa ce lalura ce da ke Hamida?" Ba ta yi magana ba hasali ma ko motsi ba ta yi ba "Wata biyu bana nan, ban san me yake faruwa da ita ba." Abdurrashid ya fuskanci likita ba tare da ya ɗago ba likitan ganin kamar Abdurrashid ya manta yana wurin ya miƙe "Yallaɓai bari na dan tsahirta muku ina ganin tunda ka iso za kayi maganin ciwon kan.". Da haka ya bar kujerarsa ya fita ya ja musu ƙofa. Ajiyar zuciya Abdurrashid ya fidda gabaɗaya ya cafko ta ya miƙar tsaye ya sa ta jikinsa sai ya ji cikinta da ya yi tauri ya cire hannun ya kama hannunta suka fito Office ɗin, sai da suka kai inda ya adana motarsa ya buɗe ya cusa ta ciki sai ya shiga glass ɗin tintek ne hakan ya ba shi damar ƙoƙarin cire mata hijab, duk da riƙewar da ta yi sai da ya yaye shi cikinta yake lalube taurin da ya kuma ji ya ce "Me ya same ki a ciki? Jikinsa har rawa yake don son jin amsar da za ta ba shi amma ta ƙi magana "To koma gaba mu tafi." Nan ma banza ta mishi ya gaji ya koma gaban ya ja motar. Ganin ya nufi GRA gidan Daddynsa inda yake sauka idan zai kwana garin ya sa ta ce "Ina za ka kai ni? Ya ce "GRA za mu in yi rarashin a can." Ta ce "Wallahi ka kai ni gida ba zan je ba." Ganin ba shi da niyyar canza hanya ya sa ta ce "Ko ka tsaya ko in buɗe ƙofa in fita, wallahi ba zan je ba." Wawan burki ya ja ya mayar da motar gefen hanya "Ki yi haƙuri ranki ya daɗe." Ya faɗi sai ya tashi motar zuwa gidan su Hamida yana tsaida motar ta riga shi fita ta shige ciki ba ta ga Innawuro ba ta shige ɗakinta kan kujerar mudubi ta zauna kawai ta rasa wane ma tunani za ta yi? Ta samu ya yi minti talatin a zaune Innawuro ta turo ƙofa sai da ta tambaye kan wanda har ta manta da ciwon ta ce mata ana kiran ta a falo. Da ma ko hijab ɗin ba ta tuɓe ba ta miƙe cikin sanyin jiki sai ta isa falon bayan kujera ta ɗan raɓe ganin duk babanninta na wurin. Sai da aka buɗe taro da addu'a sannan Baban Laila ya nemi Abdurrashid ya bayyana matsalar da ta haɗa shi da matarsa har ya turo ta gida ta zauna tsawon watanni biyu." Tiryan tiryan ya faɗi abin da ya sani da sakon da aka turo mishi da wanda Hamida ta ba shi labari." Baban Amina da duk cikin su shi ne mai zafi ya ce "To ka amince da abin da aka turo makan shi ya sa ka turo mana ita gida wata biyu? Abdurrashid ya yi ɗan jugum kunya da nauyi suka kama shi ya yi ƙarfin halin amsawa da cewa "Ban turo Hamida gida don ina zargin ta ko na yarda da abin da aka turo min, na turo ta ne don in ja kunnenta na ji zafin abin da ta yi min ƙwarai na ɓoye min abin da yake faruwa, abokina Usman wanda yake aminina na tunkare shi a ranar da Hamida ta tafi ya kasa fuskanta ta ƙarshe sai gudawa ya yi yanzu haka iyalansa da iyayensa ba su san inda yake ba. Ya turo min text yana neman gafara ta tare da bayyana min komai, ya kuma ƙara wanke Hamida kan mace ce ta ƙwarai kuma Allah ya kare ta kan mummunan ƙudirunsu akan ta. Falon suka ɗauka da faɗin Alhamdulillahi. Sai da suka tsahirta ya ce yana roƙon a ba shi Hamida su wuce yau. Baban Amina ya ce Hamida za ta koma amma ba yau ba sai Malam ya dawo. Dafe kai kawai Abdurrashid ya yi ya rasa yadda zai roƙe su su yi haƙuri su ba shi matarsa ita ya hukunta amma ya fita shiga damuwa na rashin ta kusa da shi bai ankara ba sai dai ya ji suna yi mishi sallama kowa ya fice Hamida ma da ke raɓe ta miƙe ta shige ciki Abdurrashid ya bi ta da kallo. Sau biyu Hamida tana leƙowa sai ta gan shi zaune,kuma hakika yunwa take ji, ana ukun ne ta ga ya fita ta fito ba ta ga Innawuro ba a falon ta wuce kitchen ɗanwake take sha'awa da miya tana da garin ɗanwaken da Innawuro ta sa aka yi mata rogo ne da dawa da alkama da wake da gujjiya har kuka an sanya wurin niƙan. Akwai jiƙaƙƙen ruwan kanwa sai ta kwaɓa ta ajiye wuri ɗaya sai ta soma haɗa muryar akwai tantaƙwashi da ganyaye a fridge ta haɗa lafiyayyar miyar gyaɗa, sai da ta gama haɗin ta kunna ɗaya kan gas ɗin ta sanya ruwan ɗanwake da ta riga ta tafasa ruwan a kettle nan da nan ta fara saki tana gamawa ta koma kan miyarta tana cikin juyawa ta ji muryar Abdurrashid yana kiran sunan ta, ƙofar ta harara ta ci-gaba da abin da take. An ɗan jima yana kiran ta kafin ta ji shigowar sa kitchen ɗin gyalen abayar jikinta ta yi saurin warwarewa ta rufe kanta zuwa kafaɗa sai kallon ta yake daga sama har ƙasa duk da ta ba shi baya "Hamida." Ta kuma ji ya kira sunan ta, ko motsi ba ta yi ba har ya iso inda take sai ta ji ya rungume ta da sauri ta zabura "Meye haka kake yi ka manta nan ɗin ko'ina ne, za ka shigo har kitchen? Hancinsa yake gogawa a wuyanta "Ni ko na san ko'ina ne, Innawuro ta bar mana wurin ta san rabon miji da matarsa watanni biyu ta san akwai kewa." "To ka sake ni in sauke miyar." Ta faɗi tana ɓata fuska ya sake ta ya matsa jikin bango ya harɗe hannayensa, ta harhaɗa komai ta ɗauki tren za ta fita suka haɗa ido ta yi saurin sunkuyar da kai a falon ta ajiye ta zauna ta soma zubawa shi ma ya fito gabanta ya zauna yana kallon ta ba zai ce bai taɓa ci ba don idan ya je Yola Daada na yi, amma shi kam ba cimarsa ba ce. "Ba tayi? Ya faɗi yana tsare ta da idanuwansa mamaki yake yadda ta koma mishi ta yi ƙiba komai na ta ya ƙara cika ga kyau da ta ƙara wadda kullum ya tuna ya tura matarsa ƙauye ya yi banza da ita fargaba ke rufe shi yadda za ta koma, Allah kuma bai ba shi ikon ya fahimci ciki ne a jikinta kuma wata dakakkiyar doguwar riga ce ta sanya kalarta ash sai aka yi mata kwalliya da baƙi ba ta kama ta ba don haka cikin da ya soma fitowa ya ɓace cikin rigar. "Ka zo ka ci mana." Muryarta ta dawo da shi daga tunanin da ya lula, ajiyar zuciya ya fidda ya ƙara gyara zama kusa da ita ta tsaya da ci ta zuba mishi duk da miyar ta yi mishi daɗi ka sa cin na kirki ya yi, ganin ta gama cin wanda ta zuba ta sha ruwa ya kamo ta suka hau kujera kan cinyarsa ya ɗora ta "Lallai ma yarinyar nan. Ya lakaci kumatunta "Har ma wasu kumatuna kika ajiye ba ki ma damu da ba mu tare ba." Ya daki mazaunanta "Komai naki ya ƙaru kin ƙara kyau ya riƙe ta da kyau "Ki shirya anjima mu je GRA." Saurin zabura ta yi za ta ƙwace jikinta ya ƙara riƙe ta "Allah ba inda zan bi ka yau ... Jin kamar za a buɗe ƙofa ya sa ya yi saurin sakin ta ta tashi da gudu ta shige ɗaki. Abdurrashid dai ya ƙi tafiya yana zaune falon Innawuro wadda ita ma duk ta takura ya yi ta kiran wayar Hamida ta ƙi ɗauka ya tura text yana roƙon ta fito su tafi ta yi banza da shi dole hakanan ya yi sallama da Innawuro ya nufi GRA. Washegari tun hantsi Malam ya iso gabaɗaya gida ya ruɗe da murna ana ta sannu da zuwa sai da Hamida ta fita ta ga tare suke da Daddyn Abdurrashid gaishe su ta yi ta koma ɗaki. Sai da suka kintsa sannan aka haɗu kan matsalar Hamida da Abdurrashid bayan mayar da magana kamar jiya Abdurrashid ya ƙara da cewa "Ni da ma Daddyna nake jira ya dawo zan yi ƙarar Brigadier kan keta hurumin iyalina da ya yi." Ɗakin ya yi shiru kowa da abin da yake tunani haɗe da zullumin yadda mijin Aina da Hamida za su zauna kotu. Malam ne ya yi gyaran murya ya ba Abdurrashid Haƙuri iya iyawar sa kan kar ya yi ƙarar mijin Aina, ya bar musu su za su zauna da shi, sun kuma shirya hakan da Engineer tun kafin su dawo. Sauran mazauna wurin ma haƙurin suka ba shi Baban Aina dai ya dafe kai. Abdurrashid ya ƙara bada haƙuri ya ce yana so ya wuce da Hamida, Malam ya ce "Ba laifi." Kowa ya fice sai Malam aka bari da Engineer. Kwanciya Hamida ta yi bayan ta koma ɗaki. Tana nan kwance Innawuro ta shigo kusa da ƙafafunta ta zauna "Sai ki yi ƙoƙari ki shirya mijinki ya ce zuwa La'asar za ku wuce." Tagumi ta rafsa hannu biyu "Haba dai Innawuro, sai ka ce wata kaza ya wulaƙanta ni ya koro ni tsawon wata biyu sai kawai daga zuwan shi a ce in bi shi? "Haƙuri za ki yi tunda su Malam ba su ce a'a ba, kuma da ma addu'armu kenan ya zo ki koma ɗakinki in kin zauna nan ɗin me za ki yi? Hamida ta saka kuka, Innawuro ta yi lallashin amma ta ƙi yin shiru ta fita ta ja mata ƙofar. Har uku saura Hamida ta ƙi tashi ta shirya ga Abdurrashid sai sintiri yake mata a haka Aliyu ya shigo gidan. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA END MARYAM LITEE Ta zauna tana pasing ɗinsu, ba ta damu da kallon da suke mata ba ba wanda ya yi mata magana sai ita ta gaida Abdurrashid. "Ba ka shigo ba." Ta ce da ta ƙare gaisuwar, ƙara ɗaure fuska ya yi bayan shakkar Haj yar Yaya da yake da tuni ya kore ta ya yi mata fata-fata. "E ban shigo ba. Ya amsa mata a taƙaice." Ta ci-gaba da zama tana jan shi da magana, Hamida ta ƙi magana don tana son ta ga ƙarshen rashin kunyarta, idan ma ta yi magana tana ganin ta mayar da kanta baya. Ta gama firiritarta ta tashi za ta tafi ganin Abdurrashid ya yi banza da ita daga inda yake ko motsi bai yi ba ta fice. Hamida ma ta cicciɓa ta miƙe tsaye ta fara takawa ya kira sunanta ba tare da ta waiwayo ba ta amsa "To zo mana." Ya ce mata Nan ma ba ta tsaya ba ya miƙe taku ɗaya ana biyu ya cim mata,hannu ya riƙe mata sai ya janyo ta suka koma kan kujera "To fushin na mene ne? Uhm na ce na mene ne? Ta turo baki "Wallahi wannan ne na ƙarshe da za ta shigo min wuri wai ta zo wurin ka." "Ina ce yanzu ba za ta dame ki ba? Ya g faɗi yana shafa cikin ta. Hamida dai ba ta samu sukuni ba sai da Haj yar Yaya ta zo kan batun auren Abdurrashid da Anisa ya basu tabbacin ba zai auri Anisa ba don dama an ce don ya samu haihuwa to shi yanzu ba shi da wannan matsalar. Da Mami da Haj yar Yaya ba a san wanda ya fi shiga tashin hankali ba da wannan hukunci da Abdurrashid ya yanke. Hamida ta ziyarci Asibiti a hanyarta ta dawowa ta yi karo da baban Amir mijin Laila ya ce ta ƙi zuwa ta ga amarya ta ce za ta zo. Don haka da ta tashi zuwa gidan Gwoggonta sai ta fara biyawa ta can part ɗin yar'uwarta ta fara shiga ba ta nan sai yaran, da yake Weekend ne. An gyara wurin don ta yi sabuwar mai aiki, yaran suka kewaye ta ta raba musu Chocolate ɗin da ta ruƙo musu har da abin wasa ta sawo ma ƙananan su biyu, ta kama hannun ƙaramar daya ta bi ta a baya zuwa part ɗin amarya. Da ta yi knocking aka amsa shiru ba a zo an buɗe ba sai da ta ƙara yaran ma suka ƙara ta ce su bari sai ga wata mata ta buɗe cikin matuƙar kwalliya take tana ganin yaran ta ɗauki ƙaramar ta kama hannun ɗayar ta yi ma Hamida maraba da tayin shigowa ta bi bayan ta ta zauna kan ɗayan daga cikin kujerun falon da ya sha gyara yana fitar da ni'imtaccen ƙamshi. Baban Amir da ke zaune kan dinning ya ce "A'a ƙanwata ke ce a gidan? Barka da zuwa." Ta ce "E tana gaishe shi matar ba ta zauna ba sai da ta kawo ma Hamida abinci ta zubo ma yaran ta sanya ƙaramar a cinya tana ba su tana gaishe da Hamida. Kaɗan kaɗan Hamida ke amsa hirar da baban Amir ke mata, da yaran suka ƙoshi ta shiga ciki ta kwaso musu kayan wasa ta basu tana taya su wasan Hamida tana karantar su, awa biyu ta yi ta miƙe ta ce "Na ga amarya baban Amir, Allah ya sanya alheri." Ta yi ma amaryar sallama wadda ta ce ta bar mata yaran. Ta fita ya raka ta har waje ta tafi. A gidan Gwoggo ta samu Laila tana ta razgar kuka wai yanzu baban Amir bai son ta amaryarsa mai shegen sanabe nema take ta karɓe shi ita kaɗai. Duk da nauyin ta da Hamida take ji zama ta yi ta faɗi mata gaskiya yadda za ta yi mu'amalarta da mijinta,tun kafin a karɓe mata shi gabaɗaya. Ta yi mata alƙawarin turarukan ɗaki da Lailan ta ce tana so ina Hamidar ke saye. Sai La'asar Abdurrashid ya zo suka koma gida. Washegari tana zaune a falonta ta ji ana knocking daga inda take zaune ta bayar da izinin a shigo, aka buɗe aka shigo. Ƙura wa wadda ta shigo ido ta yi don son tuna inda ta san ta. Ta tako cikin falon sai ta zauna a ƙasa "Barka da hutawa Haj." Ta furta cikin sunkuyar da kai "Rabi! Hamida ta ambaci sunan cikin wani irin mamaki da ya rufe ta "Na'am Haj Hamida." Hamida ta yi murmushi "Da ma Rabi kina duniyar nan? "Ina nan Haj Hamida, bayan tafiyar da aka yi da ni aka yi min aure, auren ne ba daɗi shekara guda kenan da mutuwar shi, zaman ƙauye sai a hankali shi ne na yanke dawowa wurin Haj (Gwoggo Indo) sai kuma na iske ta bar sana'ar, da na tambaye ki sai ta bani labarin kina nan shi ne na taho ki taimaka min ki bani aiki a wurin ki kowane iri ne." Hamida da ke ta kallon Rabi cike da tausayawa don ganin yadda ta koma gabaɗaya ta rafke ta yamutse saboda wahala. Ta ce "Ina da mai aiki Rabi, sai dai hakan ba zai hana in ɗauke ki ba." Ta cicciɓa ta miƙe Rabin na mata sannu ta isa kitchen abinci ta zubo mata ta fito ta kawo mata ta amsa tana godiya tana ci suna ɗan taɓa Hamida ta tambaye ta ba ta da yara ne ta ce haihuwa shida ta yi ukun da ta haife su suke mutuwa saura uku yanzu suna gidan uban su. Sai da ta ƙare cin abincin Hamida ta shiga ciki yan suturu daga cikin nata ta zaɓo mata don ganin tana buƙatar su, da sabulai da man shafawa har da kuɗi dubu uku ta zo ta ba ta ta ce ta koma gidan Gwoggo za ta sanar da mai gidan idan ya dawo. Ta yi ta godiya ta tashi ta tafi. Da Abdurrashid ya dawo ta faɗi mishi bai ƙi ba don haka ba ɓata lokaci Rabin ta tare a gidan ɗaki ta ware mata can ta baya tana taimakon ta ƙwarai musamman da cikinta ya tsufa sosai, zuwa yanzu duk sun gama sayayyar kayan haihuwa sai jiran haihuwar kawai inda Hamida ta dage da roƙon Allah ya sauke ta lafiya. Innawuro ta zo daga Daura Daada ma ta zo daga Yola. Ana gobe babbar Sallah kowa ya ɗauki azumin arfa Hamida ma duk da faɗan da Abdurrashid ya yi kan ta bar azumin hakuri kawai ta ba shi ta ci-gaba da azuminta. Bayan Rabi wadda ke mata aiki kafin zuwan Rabin ta shigo suka haɗu suka yi mata aikin sallah zuwa yamma sun kammala komai. Ta yi wanka ta ɗauki kunun ayan da ta yi da cincin ɗin da suka yi su take so ta fara buɗa baki da su idan an kira Sallah,ɗakin su Daada ta nufa ta zauna kan carpet ta buɗe ƙafafuwanta suna mata sannu, ba ta fi minti biyar da shigowa ba aka fara kiran sallah ta d ɗaga kofin kunun tana ta addu'a ma fi yawan addu'ar ita ce Allah ya raba ta da cikin nan lafiya, sai ta kafa kofin ai kam tana shanyewa mararta ta amsa da ciwo ta miƙe ta kabbara sallah a ɗakin, har ta idar marar tana ɗan taɓa ciwon tana bari sai dai duk yadda ta so ta yi buɗa baki kasawa ta yi har suna haɗa baki wurin tambayar ta lafiya dai ta ce lafiya lau, Abdurrashid ya yi sallama daga bakin ƙofa saboda Innawuro ya ƙi shigowa ya gaishe su da yi musu barka da shan ruwa sai ya juya ta samu ta miƙe ta bi shi a baya, ba su hawa dinning saboda halin da take ciki ledar cin abincin da aka shimfiɗa suka zauna nan ma kasa cin komai ta yi da ya tambaye ta ta ce ta ci wurin su Daada,yana gamawa aka kira Isha'i har ya fita sallar ya dawo tana nan zaune ya kama ta suka tafi ɗakinsa. Wasu dogayen riguna ya sawo mata ya ce ta gwada ta gwada ta farko ba ta gama sauka ba ko dan saboda cikin, cikinta ta ji ya yi wata irin murɗawa ta saɓule rigar da sauri sai ta juya ta bar dakin dakinta ta isa ta hau gado tana ta jin ciwon da mararta ke yi, a haka ya shigo ya same ta yanzu kam yana tambayar ta ta ce mararta ke ciwo ya ce ta tashi su je hospital shi ya ɗauki kayan da ta shirya sai da ta zauna a mota ya koma ciki don sanar ma su Innawuro da suka ce ba su ga ta zama ba Asibitin su na sojoji ya nufa da ita cikin sauri suka karɓe ta aka shiga ba ta kulawa Abdurrashid na tare da ita, har sai ƙarfe sha biyu na dare ta haiho santalelen ɗanta mai kama da uban shi sai da aka gyara su aka canza mata ɗaki su Daada sun shigo baki har kunne don Daada ma har da kuka. Zuwa safiya kowa da ya kamata ya ji ya ji har Engineer da safen ya zo shi da Mami da Aunty Karima wadda ta yi matuƙar nauyi. Kwana biyu ta yi suka sallame su suka koma gida inda suka shiga karbar jama'a daga ko'ina da ke ta zuwa barka da murna, suna aka yi na ji da gani da ya tara dubban mutane. Ta samu saƙon Jamilar Usman da ta ce ta kasa zuwa ta yi mata barka amma tana mata fatan alheri. Ta ci-gaba da kula da ɗanta wanda ya ci sunan Engineer suna kiran shi Affan duk safiya Engineer ke aikowa a zo a ɗaukar mishi shi haka ma idan ya dawo Office, kwanan su arba'in da biyar Aunty Karima ta haihu ta samu budurwa sunan mahaifiyar Abdurrashid aka mayar mata tare suke renon yaran da suka zama kamar yan biyu. Sai da suka yi watanni biyu ta samu tafiya Daura tare suka tafi da Innawuro a can ta haɗu da Aina wadda kunyar abin da mijinta ya hana ta je wa Hamida sai dai saƙo ta tura mata. Haƙuri ta yi ta ba Hamida wadda ta ce ba komai Aunty Aina,sai dai ina fatan hakan ba zai raba zumuncina da ke ba. Tana can ta samu labarin rasuwar Haj yar Yaya dole daga yin sati ta juyo maimakon kwanaki goma da ta samu Abdurrashid ya ba ta da ƙyar. A gidan mutuwar ta ga su Anisa daga zuwa daya ba ta kuma yarda ta koma ba sai ranar bakwai. Sannan ta bi gidajen su Momi Binta ta kai musu Affan. Wata uku da haihuwarta ta shiga Islamiyar da take ta burin shiga ta cikin Estate ɗin. Rayuwa ta yi wa Hamida daidai don tsakanin ta da Ubangiji sai dai godiya bayan Affan ta kuma haihuwar Abubakar Siddiq sannan ta haifi Fatima sunan mahaifiyar Abdurrashid Aunty Karima dai daga fatimarta ba ta ƙara ba. Alhamdulillah Sai Allah ya haɗa mu a book dina na gaba idan mai kowa da komai ya raya mu mai suna Bilkisu mai gadon zinare. Maryam ɗinku ce. [2/9, 09:43] Original: SHIRIN ALLAH... RAYUWA No.36 Yamma liƙis suka fito tare da Gwoggo. Ƙin zuwa ta yi gidansu ta sauka wurin Aunty Karima,yau dai ta same ta da ɗan sauƙi sai da Engineer ya shigo duba Auntyn ta tashi don komawa gida sai ga Abdurrashid ya shigo ta raɓa shi ta wuce. Da ta koma ba ta yi tunanin yin girki ba don ta gaji, turare ko'ina ta yi da turarukanta masu ƙamshi sai ta yi wanka ta yi sallah sannan Abdurrashid ya shigo, a falo suka zauna tana ta sauraro ta ji ya yi mata faɗan daɗewar da ta yi sai ta ji shiru har suka kwanta. . Washegari da daddare sai ga Ahmad mijin Laila, anan gidansu ya yi hira ta zubo mishi jallop ɗin da ta dafa ma kanta don Abdurrashid ba zai ci ba. Ya kuma cinye tas sauka ci-gaba da hirar su tana sauraren su har ta ji barci ɗakinta ta miƙe ta shiga brush ta yi sai ta yi alwala ta yi turarukanta sai ta sanya riga da wando masu taushi sun lafe a fatarta sai ta ɗaura dogon hijab ta fito ta yi mishi sai da safe ta wuce ɗakin mijinta, gado ta hau ta karanta falaƙi da nasi, da Suratu Ikhlas, da ayatul kursiyu sai ta rufe da Amanar rasulu. Ta rufe idonta ta shiga barci, cikin barcin ta ji an birkito ta ana shafa cikinta ba ta buɗe ido ba don ba abin da take so irin ta yi barcin, a kunne yake raɗa mata "Jibi fa za mu wuce Abuja, gobe ki fara shiri." Ai gabaɗaya ta buɗe idonta "Ni Hamma na gama zama garin nan." Ya ce "Saboda ke ke iko da kanki? Ta ce "Garin ya fita a raina ba za ni ba." "Ai ba shawara na ce mu yi ba, ki shirya gobo jibi in sha Allah za mu wuce. "Ta tashi a jikinsa ta koma kan pillow"Ni na faɗa maka Hamma ba za ni ba." Ƙwafa ya yi ya kwanta don bai saba tana musu da shi ba. Har washegari ya ga ba ta da niyyar soma shiri, ya kai ta asibiti don ta mayar da awonta anan har Scanning ya sa aka yi mata don ya ga lafiyar abin da ke cikin. Sun dawo ya kuma mata zancen shirin tafiya, ta ce ita fa ba za ta ba ita Islamiyyar ma take son shiga Ya ce "A'a ba yanzu ba sai kin haihu." Ta ce "Islamiyyar nan cikin Estate ɗin fa shi ne sai na haihu." Ya ce "Haka na ce. Ya miƙe sai ya fice. Jin wayarta tana kuka ta duba sai sunan Aunty Karima ta gani ta ɗaga ta ce ta zo part ɗin Engineer ta same ta. Ta sanya dogon hijab ɗinta sai ta fita. Har Abdurrashid a falon ta same shi ga Engineer zaune, kusa da ƙafar Aunty Karima ta zauna ta gaishe da Engineer sannan Aunty Karimar fuskarta na ƙasa. Engineer ya ce "Ya aka yi ɗiyata, Mijinki ya ce kin ce ba ki bin shi Abuja? Shiru ta yi don ba za ta iya magana gaban shi ba "Ki yi haƙuri ɗiyata, ki shirya ki bi mijinki kamar yadda yake so ba ma daɗewa zai yi ba ai Abujar bai fi saura wata biyu ba ya dawo nan ɗin." Ita dai ko motsi ba ta yi ba har ya ƙare maganganun lallashin ta ya sallame ta. Ta ce musu sai da safe ta tafi ba ta tsaya ko'ina ba sai ɗakinta, hijab ɗin jikinta kawai ta yaye ta haye tsakiyar gadonta ta fara kuka a haka ya shigo ya same ta tsaye ya yi yana kallon ta kafin ya ce "Duk maganar da aka yi miki ba ki haƙura ba kenan? Ba laifi." Ya sa kai ya fita ta share hawayenta ta tashi ta soma haɗa kayan da za ta tafi da su, ba ta kwanta da wuri ba sai sha biyu, hakan ya ja mata makara don ba ta tashi buɗe idonta ba sai da haske ya fara shigowa ta window ta ta tashi da sauri tana salati sai ta dubi agogo, bakwai tuni ta wuce cikin matuƙar baƙin cikin rasa sallar asuba da ta yi ta shiga bathroom, ta fito ta kabbara sallah tana idarwa ko azkar da karatun Alƙur'ani da ta saba yi ba ta tsaya yi ba ta tuɓe hijab ɗin ta nufi wurin Abdurrashid tsaye ta same shi cikin shiri ya waiwayo ya amsa sallamarta a hankali ta ce mishi "Ina kwana? Tana kaiwa zaune bakin gado amsawa ɗaya ya yi ta ce "Na makara, shi ne ba ka tashe ni ba? Ya noƙe kafaɗu "Na san don in yi fushi in tafi in bar ki ne kika ƙi tashi, kuma kin samu nasarar yin hakan zan tafi in bar kin sai dai ki sani ba ƙaramin cutar da ni hakan zai yi ba, tsawon watanni biyu muka ɗauka ba kya tare da ni yanzu daga dawowar ki ki guje min, sai dai kar ki ga laifina idan ban zo ba don sai kin neme ni." Hawaye Hamida ta ji suna zubo mata na baƙin cikin juya maganar da ya yi ta sauko gadon ta durƙusa ƙasa ta shiga kuka sosai. Ya dubi inda take sai ya ajiye jakarsa da ya ɗauka ya tako zuwa inda take tsugune ya kamo ta ta ƙwace ta ci-gaba da kukan ƙarfi ya sa mata ya ɗago ta sai ya haɗe ta da jikinsa tana sane ta shiga goga fuskarta a jikin fara ƙal ɗin shirt ɗinsa, duk ta goge masa hawayen da ya damalmale fuskarta. Zuwa bakin gado ya ja ta ya zauna tare da ita tana cikin jikinsa da dukkan hannayensa ya rungume ta "Me ya sa kike so ki yi ta ɓata ranki alhali kin san ba ke kaɗai ba ce? Ya shafa cikin "Me kike ma kuka? Ta ƙi magana ya kuma maimaitawa nan ma ba ta ce uffan ba. "To ki yi haƙuri daga ba ki son zuwa zan ƙyale ki." Da sauri ta ce "Daddy zai ga na raina maganarsa." Ya zare hular kanta ya soma shafa calabar kanta "Ba zai ce ba zan mishi bayani." Ganin ya zare rigar barcin jikinta ya soma tube tashi ta san abin da kenan, zagewa ta yi ta faranta mishi tana mishi kukan shagwaɓar ɓata mishi rai da ta yi daren jiya ya yafe mata. Bai raba jikinsu ba bayan kammala komai barci ya ɗauke ta shiru ya yi yana duban fuskarta, a hankali ya zare jikinsa sai ya miƙe zuwa bathroom wani wankan ya sake ya fito ya sake shiri cikin wasu ƙananan kayan sai ya ɗauki jakarsa ya dubi inda Hamida ke barci sai ya dubi agogonsa lokaci ya fara tafiya, ya fita ya ja ƙofar. Sai da ya zauna a motar ya zaro wayarsa ya tura ma Hamida saƙo, ya tayar da motar mai gadi ya wangale gate yana wa mai gidan nasa fatan sauka lafiya. Wayar Hamida da ke kan gadon ta tayar da ita da rurin da ta ɗauka, ta buɗe idonta tana duban ɗakin da yadda suka yamutsa shimfiɗar gadon sai dai ba Abdurrashid, tunanin ko ya tafi ya bar ta ne ya sa hankalinta tashi ta gaza ɗaukar wayar har ta tsinke. Ta rafsa tagumi tana duban agogon bango sha ɗaya saura, wayar ta kuma ɗaukar ƙara a karo na biyu cikin sanyin jiki ta miƙa hannu ta ɗauko ta, Ahmad ne mijin Aunty Laila, cikin mamakin kiran ta yi picking sai ta soma gaishe shi cikin girmamawa kamar yana ganin ta, ta tambaye shi su Aunty Laila da yaran ya ce duk suna lafiya. Ya ƙara da tambayarta "Oga ya wuce ne? Ta amsa da "E." Ya ce "Da ma wata magana nake so mu yi da ke saboda yaba hankalinki da nake yi da ɗabi'unki." Ya ɗan tsahirta ko za ta ce wani abu, jin ta yi shiru ya cigaba "Game da zamantakewa ta da Laila ne tun kina ƙarama na san kin san komai ina zaune da Laila ne don ina son ta, shi ya sa nake haƙuri da ɗabiunta, amma yanzu an kai lokacin da dole ina buƙatar sama ma kaina mafita shi ya sa na nemi ƙarin aure, Laila ta dira ta yi tsalle ba za ta yarda ba. Me Laila ta riƙe wanda zai hana a yi mata kishiya? A ran Hamida ta ce "An zo wajen." Ta daɗe tana ma yar'uwar ta ta fargabar ranar da za a zo haka. Ta ja ajiyar zuciya ta ci gaba da sauraren shi. "Komai da ake wa miji ban san shi ba daga Laila ba abin da ta sani sai ta ci ta kwanta ta ɗauki wayarta, yarana su za su yi ma kan su komai har ni ma su yi min, wanka da kwalliya su kaɗai nake samu daga Laila su ma ɗin ta watsar ta rungumi waya. Ni dutse ne da ba zan buƙaci inda zan samu kula ba? Don haka na kawo koke na gare ki, kina da hankali da sanin ya kamata ki yi mata nasiha ta nutsu ta gyara aurenta." Jin ya yi shiru ta ce "Ka yi haƙuri Baban Amir." Ya ce "To na gode." Suka yi sallama ta ajiye wayar ta zauna shiru cikin tunani ita ya ma za a yi ta fuskanci Aunty Laila da zancen za ta yi mata nasiha duk girmanta? Amma tsakani da Allah ta san Laila tana da buƙatar a zauna a yi mata nasiha ta gyara yadda take tafiyar da rayuwar gidanta, in kuwa ba ta gyara ba aka auro mata wadda ta san kanta Aunty Laila ta kaɗe har ɗan ganyenta. Ta daɗe cikin tunanin ƙarshe ta miƙe zuwa ɗakinta, wanka ta yi ta gyara jikinta sai ta gyara ɗakin. Ta fita zuwa dakin Abdurrashid ta gyara nan ma sai ta fito don barin gidan suka yi kaciɓis da mai yi mata aiki sai da suka gaisa ta ce ta ce ta zo ta yi ta knocking ba a buɗe ba. Ta ce barci take. Tare suka tafi wurin Aunty Karima can Hamida ta wuni har girki ta yi mata ta ci kuma ya tsaya mata ba ta yi amai ba. Yamma sosai ta koma gida. Washegari ta nemi iznin Abdurrashid ta je gidan Laila, zagewa ta yi ta yi mata gyaran gida amma ta kasa ce mata komai domin dai Laila ba sa'ar ta ba ce ko da wasa. Sai da La'asar ta yi mata sallama ta koma gida. Har Abdurrashid ya yi sati biyu bai zo ba, tuni zaman ita kaɗai ya gundure ta. Suka sha bikin Ahmad mijin Laila yan Daura sun zo sosai cikin su har da Innarta wadda ta ji daɗin ganin ta sosai. Ranar wata Laraba da hantsi ta shiga wurin Aunty Karima Auntyn ke faɗa mata Mami ba lafiya kan dole ta tashi ta tafi gaishe ta ba dan ta so ba. Su uku ta samu falon Mamin, Mamin sai Haj yar Yaya sai wata mata da ba ta san ta ba. Su biyun suka yi mata caa! Da ido, don duk da ƙaton hijabin da ta sanya cikin ya turo ya fito. Wuri ta samu ta zauna tana gaishe su da tambayar Mami jiki Haj yar Yaya ta taɓe baki "Bikin Anisa kafin ta haihu za a yi shi." Mami ta ce "Da an bari in ta haihu sai a haɗa da suna." Suka cigaba da zancen auren Anisa da Abdurrashid kamar ba ita ce a gaban su ba. Ta miƙe ta yi musu sallama sai ta bar sashen zuciyarta na mata zafi jin waɗannan mutanen ba su haƙura ba da ƙarin auren Abdurrashid. A falonta rasa inda za ta zauna ta yi tana cikin haka kiran Abdurrashid ya shigo wayarta, ta ɗaga sai ta kama mishi kuka hankalinsa ya tashi don tunanin ko wani abu ya faru, ya shiga tambayar ta ta ce ita dai yaushe zai dawo? Ya ce ba yanzu ba ta ci-gaba da kukanta tare da magiyar ya zo ya ce to zai dawo da ƙyar suka rabu. So take ya dawo don idan yana can gani take za su yi ta soyayya da Anisa hankali kwance ita tana nan. Tashi ta yi ta rufe ƙofar falon ta dawo ta baje a falon cikin damuwa a taƙaice kasa shiga ɗakin ta yi a falon ta ƙaraci damuwar ta barci ya yi awon gaba da ita. Cikin barcin ta ji ana shafa ta ta tashi a razane sai ya riƙe ta "Ke ni ne." Ta buɗe idonta da ta rufe don tsoron da ya rufe ta ta gan shi tsugune gaban ta, tare da ita ya miƙe hannunsa na kan cikinta suka nufi ɗakinsa. Sai da ta wartsake ta tambaye shi hanya har yake gaya mata ko lokacin da suka yi waya ya shigo garin yana barrack ɗin da ya bari, ta nemi ta yi masa girki mai sauƙi ya ce a'a dare ya yi bai tare da yunwa. Ba su jima ba suka kwanta don dare ya fara nisa. Kwana biyu kawai ya yi mata ya koma. Rayuwa tana ta tafiya cikin Hamida yana ta girma da na Aunty Karima. Nata ya kai watanni takwas na Aunty Karima shida Abdurrashid ya dawo Kano da aiki, wai sai ga Anisa ta dawo gidan tunda Hamida ta gan ta hankalinta ya tashi don ba ta san da zuwan ta ba sai wani dare suna zaune a falo ita da Abdurrashid ita tana zaune kan Sopa ta bubbuɗe ƙafafu shi kuma yana zaune a ƙasan carpet kusa da ƙafafun nata yana cin apple ta yi knocking shi ya amsa yana duban agogo cike da mamakin waye me zuwa musu yanzu, Anisa ta shigo cikin karairaya. SHIRIN ALLAH... RAYUWA END MARYAM LITEE Ta zauna tana pasing ɗinsu, ba ta damu da kallon da suke mata ba ba wanda ya yi mata magana sai ita ta gaida Abdurrashid. "Ba ka shigo ba." Ta ce da ta ƙare gaisuwar, ƙara ɗaure fuska ya yi bayan shakkar Haj yar Yaya da yake da tuni ya kore ta ya yi mata fata-fata. "E ban shigo ba. Ya amsa mata a taƙaice." Ta ci-gaba da zama tana jan shi da magana, Hamida ta ƙi magana don tana son ta ga ƙarshen rashin kunyarta, idan ma ta yi magana tana ganin ta mayar da kanta baya. Ta gama firiritarta ta tashi za ta tafi ganin Abdurrashid ya yi banza da ita daga inda yake ko motsi bai yi ba ta fice. Hamida ma ta cicciɓa ta miƙe tsaye ta fara takawa ya kira sunanta ba tare da ta waiwayo ba ta amsa "To zo mana." Ya ce mata Nan ma ba ta tsaya ba ya miƙe taku ɗaya ana biyu ya cim mata,hannu ya riƙe mata sai ya janyo ta suka koma kan kujera "To fushin na mene ne? Uhm na ce na mene ne? Ta turo baki "Wallahi wannan ne na ƙarshe da za ta shigo min wuri wai ta zo wurin ka." "Ina ce yanzu ba za ta dame ki ba? Ya g faɗi yana shafa cikin ta. Hamida dai ba ta samu sukuni ba sai da Haj yar Yaya ta zo kan batun auren Abdurrashid da Anisa ya basu tabbacin ba zai auri Anisa ba don dama an ce don ya samu haihuwa to shi yanzu ba shi da wannan matsalar. Da Mami da Haj yar Yaya ba a san wanda ya fi shiga tashin hankali ba da wannan hukunci da Abdurrashid ya yanke. Hamida ta ziyarci Asibiti a hanyarta ta dawowa ta yi karo da baban Amir mijin Laila ya ce ta ƙi zuwa ta ga amarya ta ce za ta zo. Don haka da ta tashi zuwa gidan Gwoggonta sai ta fara biyawa ta can part ɗin yar'uwarta ta fara shiga ba ta nan sai yaran, da yake Weekend ne. An gyara wurin don ta yi sabuwar mai aiki, yaran suka kewaye ta ta raba musu Chocolate ɗin da ta ruƙo musu har da abin wasa ta sawo ma ƙananan su biyu, ta kama hannun ƙaramar daya ta bi ta a baya zuwa part ɗin amarya. Da ta yi knocking aka amsa shiru ba a zo an buɗe ba sai da ta ƙara yaran ma suka ƙara ta ce su bari sai ga wata mata ta buɗe cikin matuƙar kwalliya take tana ganin yaran ta ɗauki ƙaramar ta kama hannun ɗayar ta yi ma Hamida maraba da tayin shigowa ta bi bayan ta ta zauna kan ɗayan daga cikin kujerun falon da ya sha gyara yana fitar da ni'imtaccen ƙamshi. Baban Amir da ke zaune kan dinning ya ce "A'a ƙanwata ke ce a gidan? Barka da zuwa." Ta ce "E tana gaishe shi matar ba ta zauna ba sai da ta kawo ma Hamida abinci ta zubo ma yaran ta sanya ƙaramar a cinya tana ba su tana gaishe da Hamida. Kaɗan kaɗan Hamida ke amsa hirar da baban Amir ke mata, da yaran suka ƙoshi ta shiga ciki ta kwaso musu kayan wasa ta basu tana taya su wasan Hamida tana karantar su, awa biyu ta yi ta miƙe ta ce "Na ga amarya baban Amir, Allah ya sanya alheri." Ta yi ma amaryar sallama wadda ta ce ta bar mata yaran. Ta fita ya raka ta har waje ta tafi. A gidan Gwoggo ta samu Laila tana ta razgar kuka wai yanzu baban Amir bai son ta amaryarsa mai shegen sanabe nema take ta karɓe shi ita kaɗai. Duk da nauyin ta da Hamida take ji zama ta yi ta faɗi mata gaskiya yadda za ta yi mu'amalarta da mijinta,tun kafin a karɓe mata shi gabaɗaya. Ta yi mata alƙawarin turarukan ɗaki da Lailan ta ce tana so ina Hamidar ke saye. Sai La'asar Abdurrashid ya zo suka koma gida. Washegari tana zaune a falonta ta ji ana knocking daga inda take zaune ta bayar da izinin a shigo, aka buɗe aka shigo. Ƙura wa wadda ta shigo ido ta yi don son tuna inda ta san ta. Ta tako cikin falon sai ta zauna a ƙasa "Barka da hutawa Haj." Ta furta cikin sunkuyar da kai "Rabi! Hamida ta ambaci sunan cikin wani irin mamaki da ya rufe ta "Na'am Haj Hamida." Hamida ta yi murmushi "Da ma Rabi kina duniyar nan? "Ina nan Haj Hamida, bayan tafiyar da aka yi da ni aka yi min aure, auren ne ba daɗi shekara guda kenan da mutuwar shi, zaman ƙauye sai a hankali shi ne na yanke dawowa wurin Haj (Gwoggo Indo) sai kuma na iske ta bar sana'ar, da na tambaye ki sai ta bani labarin kina nan shi ne na taho ki taimaka min ki bani aiki a wurin ki kowane iri ne." Hamida da ke ta kallon Rabi cike da tausayawa don ganin yadda ta koma gabaɗaya ta rafke ta yamutse saboda wahala. Ta ce "Ina da mai aiki Rabi, sai dai hakan ba zai hana in ɗauke ki ba." Ta cicciɓa ta miƙe Rabin na mata sannu ta isa kitchen abinci ta zubo mata ta fito ta kawo mata ta amsa tana godiya tana ci suna ɗan taɓa Hamida ta tambaye ta ba ta da yara ne ta ce haihuwa shida ta yi ukun da ta haife su suke mutuwa saura uku yanzu suna gidan uban su. Sai da ta ƙare cin abincin Hamida ta shiga ciki yan suturu daga cikin nata ta zaɓo mata don ganin tana buƙatar su, da sabulai da man shafawa har da kuɗi dubu uku ta zo ta ba ta ta ce ta koma gidan Gwoggo za ta sanar da mai gidan idan ya dawo. Ta yi ta godiya ta tashi ta tafi. Da Abdurrashid ya dawo ta faɗi mishi bai ƙi ba don haka ba ɓata lokaci Rabin ta tare a gidan ɗaki ta ware mata can ta baya tana taimakon ta ƙwarai musamman da cikinta ya tsufa sosai, zuwa yanzu duk sun gama sayayyar kayan haihuwa sai jiran haihuwar kawai inda Hamida ta dage da roƙon Allah ya sauke ta lafiya. Innawuro ta zo daga Daura Daada ma ta zo daga Yola. Ana gobe babbar Sallah kowa ya ɗauki azumin arfa Hamida ma duk da faɗan da Abdurrashid ya yi kan ta bar azumin hakuri kawai ta ba shi ta ci-gaba da azuminta. Bayan Rabi wadda ke mata aiki kafin zuwan Rabin ta shigo suka haɗu suka yi mata aikin sallah zuwa yamma sun kammala komai. Ta yi wanka ta ɗauki kunun ayan da ta yi da cincin ɗin da suka yi su take so ta fara buɗa baki da su idan an kira Sallah,ɗakin su Daada ta nufa ta zauna kan carpet ta buɗe ƙafafuwanta suna mata sannu, ba ta fi minti biyar da shigowa ba aka fara kiran sallah ta d ɗaga kofin kunun tana ta addu'a ma fi yawan addu'ar ita ce Allah ya raba ta da cikin nan lafiya, sai ta kafa kofin ai kam tana shanyewa mararta ta amsa da ciwo ta miƙe ta kabbara sallah a ɗakin, har ta idar marar tana ɗan taɓa ciwon tana bari sai dai duk yadda ta so ta yi buɗa baki kasawa ta yi har suna haɗa baki wurin tambayar ta lafiya dai ta ce lafiya lau, Abdurrashid ya yi sallama daga bakin ƙofa saboda Innawuro ya ƙi shigowa ya gaishe su da yi musu barka da shan ruwa sai ya juya ta samu ta miƙe ta bi shi a baya, ba su hawa dinning saboda halin da take ciki ledar cin abincin da aka shimfiɗa suka zauna nan ma kasa cin komai ta yi da ya tambaye ta ta ce ta ci wurin su Daada,yana gamawa aka kira Isha'i har ya fita sallar ya dawo tana nan zaune ya kama ta suka tafi ɗakinsa. Wasu dogayen riguna ya sawo mata ya ce ta gwada ta gwada ta farko ba ta gama sauka ba ko dan saboda cikin, cikinta ta ji ya yi wata irin murɗawa ta saɓule rigar da sauri sai ta juya ta bar dakin dakinta ta isa ta hau gado tana ta jin ciwon da mararta ke yi, a haka ya shigo ya same ta yanzu kam yana tambayar ta ta ce mararta ke ciwo ya ce ta tashi su je hospital shi ya ɗauki kayan da ta shirya sai da ta zauna a mota ya koma ciki don sanar ma su Innawuro da suka ce ba su ga ta zama ba Asibitin su na sojoji ya nufa da ita cikin sauri suka karɓe ta aka shiga ba ta kulawa Abdurrashid na tare da ita, har sai ƙarfe sha biyu na dare ta haiho santalelen ɗanta mai kama da uban shi sai da aka gyara su aka canza mata ɗaki su Daada sun shigo baki har kunne don Daada ma har da kuka. Zuwa safiya kowa da ya kamata ya ji ya ji har Engineer da safen ya zo shi da Mami da Aunty Karima wadda ta yi matuƙar nauyi. Kwana biyu ta yi suka sallame su suka koma gida inda suka shiga karbar jama'a daga ko'ina da ke ta zuwa barka da murna, suna aka yi na ji da gani da ya tara dubban mutane. Ta samu saƙon Jamilar Usman da ta ce ta kasa zuwa ta yi mata barka amma tana mata fatan alheri. Ta ci-gaba da kula da ɗanta wanda ya ci sunan Engineer suna kiran shi Affan duk safiya Engineer ke aikowa a zo a ɗaukar mishi shi haka ma idan ya dawo Office, kwanan su arba'in da biyar Aunty Karima ta haihu ta samu budurwa sunan mahaifiyar Abdurrashid aka mayar mata tare suke renon yaran da suka zama kamar yan biyu. Sai da suka yi watanni biyu ta samu tafiya Daura tare suka tafi da Innawuro a can ta haɗu da Aina wadda kunyar abin da mijinta ya hana ta je wa Hamida sai dai saƙo ta tura mata. Haƙuri ta yi ta ba Hamida wadda ta ce ba komai Aunty Aina,sai dai ina fatan hakan ba zai raba zumuncina da ke ba. Tana can ta samu labarin rasuwar Haj yar Yaya dole daga yin sati ta juyo maimakon kwanaki goma da ta samu Abdurrashid ya ba ta da ƙyar. A gidan mutuwar ta ga su Anisa daga zuwa daya ba ta kuma yarda ta koma ba sai ranar bakwai. Sannan ta bi gidajen su Momi Binta ta kai musu Affan. Wata uku da haihuwarta ta shiga Islamiyar da take ta burin shiga ta cikin Estate ɗin. Rayuwa ta yi wa Hamida daidai don tsakanin ta da Ubangiji sai dai godiya bayan Affan ta kuma haihuwar Abubakar Siddiq sannan ta haifi Fatima sunan mahaifiyar Abdurrashid Aunty Karima dai daga fatimarta ba ta ƙara ba. Alhamdulillah Sai Allah ya haɗa mu a book dina na gaba idan mai kowa da komai ya raya mu mai suna Bilkisu mai gadon zinare. Maryam ɗinku ce.