[10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI WANDA NA SABA MAWA DA WANDA BAN SABAMAWA, MASOYA NA NA GASKIYA DON KU NAI WANNAN DAN GUNTU LABARIN DON BAZAN MANTA DA KU BA HAR ABADA DON KUN NUNA MIN SO DA KAUNA . WANAN LABARI ALMOST TRUE LIFE STORY NE DA FATAN ZAKU DAN FAHINCI MAI YAKE NUFI. 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE A GIDAJEN MU👩‍👩‍👧‍👧 Zaune take tana wanke wanke a farfajiyan tsakar gidan nasu inda yarta yar wata tara take zaune daga baran da tana wasa kasan cewan yaran ta biyu da suka dan tasa sun tafi islamiya. Mama ce tafito daga nata dakin ta idon ta akan yar jikan ta dake zaune gefe tana wasa ita kadai. A,a Nusaiba kece zaune haka ga yamma ya kusa maryam ina fada maki kullun da zaran almuru yayi ki dinga goya yaran nan bai da kyau barin yaro a zaune shi kaida haka. Kiuya yai maku yawa yaran yanzu mu manyan mu ko yaushe suna fada muna mu kula da hakkin yaran mu don gujewa fadawa hannun shedanu. Umma so nake na gama wanke kayan nan na zo na dauke ta Allah ya kyauta kawai mama tace tare da daukan yarinyar dake zaune saman suminti tana wasa irin na yara yan shekara daya sai faman gwalaci take irin na yara. Daukan ta tayi suka koma cikin daki itako maryam hakane yasa ta jin dadin karasa aiyukan dake gaban ta kafin dare ya karaso mata. Bayan wasu yan mintina sai ga sauran yaran biyu sun dawo Ahmed dan shekara hudu da rabi sai kaunan shi Amira yar shekara uku. Suna dawowa gidan ya fara da baku bari ko dan fadan da suke a tsakanin su da yawan kawo kara mama kinga wani yai mun abu kaza ko. Oya ki zauna kuci abinci nai maku wanka nan ta kawo masu tuwon masara da miyan kubewa danya yaji attarudu sai kamshin daddawa dake tashi a cikin shi. Tsakar gida ta aje masu don kada su bata mata barandan da ta share dazun da yamma. Don maryam mace mai tsaba da tsanda bata son kazan ta ko kadan a rayuwan ta. Nan yaran suka zauna suna tacin abinci suna fada a tsakanin su daga inda uwar take tana aikin ta take tsawata masu. Umma ce tafito tana fada tana goye da Nusaiba a bayan ta sai kuka takeyi tace kai kuyi ku daga daga gurin nan ku koma ciki almuru yayi sosai. Maryam zo ki karbi yar nan ta damay ni da kuka tun dazun daga abin arziki zata saka min kuka na shegen kiuyan ta. Kai Nusaiba don Allah ki bari na karasa wanke tukunyan nan mana. Ni dai zoki karbeta ban iya kiuyan wannan yar taki mai shigen fitinan tsiya ita har yau bata saba da mutane ba uwar ta sai ubanta kawai ta sani. Maryam tadata daure hannunta tana dan gogewa da zanin jikin ta takaraso gurin tana dariyan maganan Umma. Ta karbi Nusaiba dake miko mata hannu daga bayan Umma da zata karbe umma takai mata dan duka a bayan ta. Sallama akayi daga kofan shigowa gidan Laure mai ganye ce Umma tace innalillahi ni gaskiya ban san mai ke kawo wanan matar da magariban fari ba haka gidajen mutane. Laure lafiya dai ko kika zo muna gida haka a lokacin da kowa ya ke kokarin natsa kan shi gida saboda yamma da yayi. A,a Umma Aliyu zuwa nayi idan kuna da dan gishiri ku bani don nawa ya kare kuma yanzu nasan masu shago sun rufe suna shirin zuwa sallah. Maryam don Alla debo mata gushiri ki bata inji Umma maryam ,ta juya da yarta a hannu ta nufi kitchen din su ta dauko gishiri a leda. Tana mika wa laure na karba taji kan ta yai wani irin uban sarawa a lokaci guda da sauri ta daga kai ta kalli laure dake tsaye a kofan dakin Umma. Idon laure akan yaran ta dake zaune a tsakar gida ganin haka Umma tai saurin gane may maryam ke nufi. Da sauri ta wuce inda yaran suke zaune tana cewa oyaya kutashi muje na wanke maku hannu ku koma daki. Nan tabar laure a tsaye tana kallon su, sai da ta dan numfasa tace to mama Ali ni zan koma na gode lokacin har an fara kiraye kirayen sallah ko. Futan laure daga gidan duk maryam sai take jin jikin ta ba dadi a lokaci guda kanta yana wani irin sarawa. Take jikin ta yai wani irin zafi radau dashi a dadafe ta samu tai sallah magariba ta samu guri ta kwan ta. Jin maryam shiru yasa Umma lekowa don da zaran tagama sallah zata koma dakin Umma suyi kallo duk da dakin ta akwai kayan kallo a cikin shi. Amma don su debewa Umna kewa a dakin ta suke zama ita da yara suna mata hira. Samu Umma tayi maryam ta rufe cikin wani katon zanin gadon ta tana rawan sanyi don zazzabi yariga ya rufe mata jikin ta ko. A,a maryam yaya haka kuma ikon Allah ina yanzun ne kike walwalan ki a tsakar gida kina aikin ki. May ke damun kine maryam Umma take tambayan ta tare da daukan Nusaiba dake kuka. Maryam ta bude baki da kyat tace Umma kaina jikina duk ban jin dadin shi wallahi. Tana taba jikin maryam yadda yai zafi a lokaci daya yaba umma tsoro tace a,a maryam ashe ba abin wasa bane. Take zuciyar ta tace mata laure a fili cewa tayi ina bako a gidan nan ba wallahi. Nan ta juya da sauri zuwa dakin ta sai gata da wani dan kulin magani ta kada a ruwa tace tashi ki sha maryam . Dakyat maryam ta mike tasha maganin ta koma ta kwanta fita umma tayi ta samo mata magani a chemest din unguwan su. Sai zuwa dare sosai maryam ta dan samu sauki ganin haka Umma ranan a dakin su maryam ta kwana da ita. Washe gari tun da sassafe bayan Umma ta sa maryam tai hayaki da wani garin magani ta fita gidan sai gidan laure. Babu ko sallama ta fada gidan ta samu laure zaune a dan madafin ta tana dama wani bakin koko a roba. Laure na ganin ta tace a,a mama Ali kece da farar safiyan nan haka Umma tace eh nine laure kin san ance a rama takwarkwari nazo ne yadda kika shiga muna gida da magariba shine nima nazo in maki kashedin hakan. Wallahi laure idan kina cin kasa ki kiyayi na shuri don kayan gidan malam mai Allo ba taki bace idan kuma kin ki ji bakyaki gani ba . Na fada maki wallahi ki kiyayi duk wani abin gidana in ba kina son watan tonon asurin ki ya kama a garin nan bane. Mama Aliyu ban fahinci may kike nufi ba ne ni tace zaki fahinta wallahi kiyi gagawan sake min matar da ko asirin ki ya tonu a garin nan. Wa ni mama Ali don Allah kada ki kulla min sheri idan ma sheri ne ai zaki gani kada ki sakar min sarakuwa kisha mamaki wallahi. Umma ta juya tafita gidan tana fada laure tai tsaki bayan fitan umma tana cewa ni dama gwadawa nayi wane ni da wanan yarinyar da take a tabaibaye bani ba jinin kuma ai. Umma na fita ta hadu da wata makwaciyar su tace a,a manan Aliyu ina aka fito haka da safen nan kuma. Tace daga gidan laure nake jiya daga shiga wai neman gishiri ashe sheri ne yakawo ta sai kawai ga yarinyar nan maryam jiki ya gashe mata a tsatsaye muka kwana da ita. Shine nazo nai mata kashedi akan gidana tace kinyi daidai wallahi watau ashe kudundumin nan da ake wa laure ta hurhura da gaskiya ke nan. Kafin wani lokaci sai maryam taji wani wasai a jikin ta nan ta mike kamar ba ita ba ta fara aiyukan ta kamar kullun. Tun wanan ranan Umma duk marance sai ta hake gidan nasu da hayakin miyagu don neman tsari. Maryam kan har ta manta da zancen laure don yanzu wasai take jin kan ta kamar ba abinda ya taba samun ta a baya. Maigidan maryam Aliyu dan Umma Rabi ma aikacin custom ne na kasa shi kadai Allah yabar wa umma duk haihuwan da takeyi basu tsayawa sai su koma. Akan Aliyu ne tun tana da ciki ake ta neman maganin wabi don ance wabi take yi ko ta haihu yaran da sun dan tasa sai su rasu. Allah da ikon shi saiga Aliyu an haifa sannu sannu Allah yaraya matashi har yakai ga girma yai karatun secondry inda ya tafi karatu a A B U zaria ya karanta engineering kuma ya fito da first class. Kasancewan yadda kasamu ta koma babu aiki ga fanin da mutu yai karatu dole ya joner da hukuma shige da fice na kasa watau Custom. Anan yanzu yake aiki da farko Enugu aka kaishi yai shekara uku acan yana can ne ya auri maryam diyar malam babba na garin su Auna wani gari dake can cikin yakin kasan kwantagora na Niger state. Tun da sukai Aure da maryam bai tafi da ita ko ina ba rana zaune ne tare da mahaifiyam shi na gida su na garin Auna. Har yakai sun kai ga haihuwan diya uku yanzu tsakanin su Umma tana jin dadin zama da sarakuwarta maryam don irin yadda maryam ke daukan ta tankar uwa a gare ta. Ko itace ta haifi maryam abin ya tsaya a haka don irin yadda maryam ke bata hakkin ta na uwan mahaifiya a gare su . Wani lokaci zakaga har suturan su kusa kala dayane da umma sai dai kala ya dan banban ta kawai. Umma ma tana matukar son maryam don halin maryam na dabian arziki a gare su. Maryam bata taba damuwa da rashin zuwa inda mijinta baiyi ba da ita don komai na bukatan su yana aje masu. Gashi kuma mutum ne Aliyu wanda yasan daraja da hakkin iyalin shi daga su har yaran su a wadace suke da sutura abinci da sauran su. Duk karshen wata Aliyu yake zuwa gida duba iyalinshi sai dai idan aiki ya tare shine zai kara yan kwanaki akai. Yauma ya kasance karshen wata ne don haka maryam take ta faman gyaran jikin ta irin yadda ta saba yi idan zai zo garin. Daga gida har jikin ta ita da yara wani lokaci ma har umma takan tilstawa sai tai mata kitso da kumshi don dai kada yazo ya samay su a kazance kawai. KUYI HAKKURI DA WANAN SAI KUN JI NI KUMA ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👨‍👩‍👧‍👦BAMU KADAIBANE 👩‍👩‍👧‍👧 GA MASU SON NOVEL DINA NA KUDI ZAKU IYA KIRA DA WANAN NOBAN 08036959257 DON SAMUN SARAUTAN MATA DA A LOKACIN MUKE,,, Da sauri yau na kamala komai don kada ya dawo ya samay mu a cikin kazanta daga girki har gyaran gidan mu duk da dai gidan namu bawai ginan zamani bane. Amma sai ta koma tsab dashi nai wanka na shirya cikin wasu material din buje da riga daga kasan buje a bude yake kamar fish tail daahi. Yaran suna gurin umma tun yamma nasan shigowan dare yake muna don isan dake tsakanin kaduna da mu. Dakin Umma na koma cikin su sai dai duk abinda nakeyi idona naa kofan gida don naji sallaman masu shigowa gidan. Gashi yar wayata nokia mai tocila babu caji tun da rana ta dauke ga neper basu kawo wuta ba har lokacin. Kawo wutan neper yai daidai da dirin motan da ya tsaya a kofan gidan mu a lokacin. Van kawo cewa shi bane don nasan baida mota shiga shi sai dai kuma baifi minti biyar ba muka ji sallaman shi a tsakar gida. Daga ni har yara rage rige mukeyi gurin taron shi har umma tafito dauke da Nusaiba da ihun mu ya tayar daga barci a lokacin. Yana tsaye cikin kanan kaya da leda a hannun shi mukai kan shi da murnan ganin shi. Yaran sun kankamay shi suna murna na karaso inda yake fuskana dauke da murmushi ina mashi sannu da zuwa. Common yau ba zan samu hoging din bane da ido nai mashi signal da ga Umma nan waje. Hakan bai hana shi dan rugomo ni ba a jikin shi nai mashi sannu da zuwa tare da karban ledan dake hannun shi. Dakin Umma na nufa da ledan inda na barsu suna gaisawa da ita a tsakar gida. Bai shigo ba ya juya yafita daga gidan sai ga yaran makwabtan mu dake wasan dare a waje suna shigowa da kayan tsaraban da yazo muna dashi. Duk a kofan dakin Umma aka jibge komai da yazo dashi sai yar jakar kayan shi kawai na dauka zuwa dakina. Nafito bayan na aje jakar ne nafito don na shiga da kayan daga cikin dakin Umma. Sai dai nai matukar mamakin ganin yawan tsaraban da yazo muna dashi wanan karon don yafi karfi abinda ya saba kawo muna abaya. Bayan nagama saka kayan daga ciki su doya da irish nabarsu a wajen juyawa nayi kitchen na juye mashi ruwan wanka a lokacin. Nasama shi tsaye a tsakiyan daki yana kokarin cire rigan shi don nasaba mai da ya iso yai wanka kafin ya zauna cin abinci yana ci muna gaisawa dashi. Juyowa yayi inda nake tsaye yana kallona cikin sha,awa yake cewa miss you maryam . Murmushi nayi nace nafi ka kewa ai baban Abba yanzun dai ga ruwa can kai wanka kazo kaci abinci. Yafita zuwa wanka nikuma na kara gyara dakin yadda naga ya kamata duk daba baci yayi ba kafin yafito nafitar mai da kayan da zai saka na aje mai a saman gado daga gefe daya. Koda ya fito ina zaune saman kujera ina shayar da Nusaiba nono a lokacin. Ina zaune ina kallon yadda yake shirin shi a tsanake tare da sake min murmushi yana tambayana ya bayan robo da kuma yara duk da dai muna waya dashi kusan sau biyu a rana. Yana gama shiri muka kwasa sai dakin Umma mun samay ta da yara suna fira muka shigo dakin nata. Nan suka kara gaisawa da Umma ga tv yana aiki daga gefe daya can cikin hiran su da Umma naji tana cewa yau sai muka ga tsaraba haka dayawa amma kan kasha kudin mota wanga uban tsara ba haka mai yawa. Murmushi yayi yace umma ban fada maku bane dai amma maryam ta samu kishiya ai. Da sauri na dago daga kallon tv da nakeyi nake kallon shi ita ma dai Umma din kallon mamaki take mashi. Yace tana waje yanzun haka da ita nazo ma sai da safe zaku fita ku gan ta aiko ? Baba kace min alheri ya samu ke nan bamu da labari nikan da nai mutuwan kasko a zaune ban fahinci maganan su kuma gashi naji umma har da murnan ta. Sai da naji yace ban dade da sayen taba don batakai sati biyu ba ma hannuna. Sabuwa ce dal Umma na samu dama na dade ina son sayen mota don nagaji da shiga motar haya hakanan. Sai a lokacin na dan saki murmushi a fuskana da na fahinci motace ashe yasayo nan muka shiga murna mun kagara ya gama cin abinci mu fita tare dashi mu gani. Sai da ya gama muka kwasa har yaran da basuyi barci muka fita waje ganin motan nashi. Sabuwar motace ta zamani 406 launin blue sai sheki takeyi a cikin farin wata. Ko ina na motan sai da muka duba muna yaba kyawon ta muka dawo cikin gida da murnan mu. Wanan karon bai koma dakin Umma ba dakin mu ya shiga nima ban bata lokaci va nabi bayan shi zuwa dakin. Shimfida na fara yiwa Nusaiba kafin na juyo inda yake zaune yana waya da abokin aikin shi. Fita nayi na kara watsawa jikina ruwa nazo na shafa maina mai kamshi daya sayo min wancan zuwan da yayi don ya san ni da balain son kamshi sosai. Ina gamawa ban tsaya bata lokaci ba naje naiwa su Umma sai da safe na dawo na rufe kofan dakin mu. Kamar kullun yadda yake dawowa a matse xa bukata na yau ma hakane ya kasance a tsakanin mu dashi. Sai bayan komai ya kamala ne yake cewa maryam ina ganin fa idan Umma ta yarda zan dauke ku dake da yaran mu koma kaduna don yaran nan su samu karatu ingantace a rayuwan su. Sosai naji dadin magan nan shi har na kasa boye farinciki na a ciki nace Allah yasa umma ta yarda ka tafi damu danafi kowa farin ciki da hakan kasancewan zamu zauna a guri daya dakai. Hira muke tayi dashi har barci ya dauke mu don yana da gajiya a jikin shi sosai ga kuma wanda yazo ya kara a tare dani. Washe gari tun da nai sallah ban kwanta ba kuma nashiga hada muna abin karyawan mu. Kafin sani lokaci na hada na shiga daki na samay shi still yana barcin gajiya wankan shiga kafin wani lokaci har na gyara jikina inda na saka wani dogon rigan wani atamfana ja mai kyau dashi. Sallama da yaro yayi ne yasani lekowa yana fadin wai ana sallama da baban Abba a waje inji malam hassan makwabcin mu ke nan. Komawa nayi zuwa bakin gado inda yake a kwance na dan taba kafan shi kadan. Abinda yasa shi bude idon shi ke nan yana kallo na a hankali cikin yanayin mai jin barci a lokacin. Nace wai baba hassan ne yake maka sallama a waje yanzun ya aiko yaro daga wajen. Dakyat ya bude idon shi tare da dan jan guntun tsoki yana fadin kai yanzun mutane bazasu bari mutum ya hutu ba wallahi gashi duk a gajiye nake . Dogon rigan jallabiyan shi dake gefe ya zura yafi gurin mai sallaman makwabcin mu ne dattijon kirki yana kula mu sosai kuma ya daukan yarana kaman jiko kin shi. Murnan motar da ya gani a kofan gidane yazo yi mashi inda yai mashi fatan alheri da fatan a gama da,karfe lafiya. Nan sauran makwabta suka samay su ana ta taya shi murnan samun karuwan da yayi na sayan mota. Sai zuwa rana da mutane suka rage ne ya samu ya shigo gida wanka yayi ya zo ya shirya ya zauna ya karya. Anan ne yakewa Umma magana kan yana son kwashe iyalin shi ya tafi damu can gurin aikin shi. Nayi zaton Umma zatai farin ciki da jin haka amma tace mai yanzu kai kaga ya dace ka kwashi iyalinka sunan cikin kwanciyan hankali ka tafi dasu garin da,baka da kowa a cikin shi. Murmushi yayi yace umma ai da ita kaduna ainihin sunan ta ke nan garin masaukin bakine tan arewa garin kazo na zo. Zakiga akasarin mazauna garin duk baki ne dako ina na nahiyar arewancin Nigeria dama sauran kasashen africa don gari ne da yaci sunan shi na bariki a cikin kasan nan yanzu dai abuja ce kawai zata nunawa yan kaduna wayewa kawai. Umma tace bakaji ba bariki fakace garin shege da shigiya ke nan ina tarbiya a gurin nan. Dariya umma tabashi yace umma ai idan tarbiya addini kike bukata to kije kaduna don acan addini ya yanke cibinsa sosai. Ni dai yanzu kabari sai nayi shawara don gaskiya ni hankalina bai kwanta da ka kwashi yaran zuwa har wata kasa ba inda ba kusa da gida ba. Yace tau Umma sai dai gaskiya ni nagaji da zama ni kadai a gida hakana ina bukatan zama da iyali a kusa da ni don na samu gida yanzun idan su bazasu tafi ba sai na samu wata yar can na aura ke nan. Dif naji kamar ruwa ya cinye ni a lokacin wani irin sakaiyya Umma da dan ta zasu yi min haka a daidai lokacin da nake ganin riban hakkuri na yazo min a rayuwa. Don yanzun alama ya nuna yaya yana a cikin budi da samu daga gurin aikin shi. Haka ya mike yafita zuwa cikin gari don ya gaisa da yan uwa da abokan arziki na gari. Nima mikewa nayi ba tare da nai magana ba na fice daga dakin umma tare da kayan da yaci abincin shi. Umma tabi ni da kallon tausayi don ta san indai hakkuri ne na yi shi a gidan nan akan komai yanzun kuma gashi yazo da wani magana mai wuyan sha,ani. Idan har da zasu tafi ne ya barta da yaran zasu dan debe mata kewa ai kila amma kuma yace zai kwashe su gaba daya har yaran gaskiya zaman kadaicin zai mata yawa sosai. Tasaba da hayaniyan su a gida suna debe mata kewan shi yanzun kuma yace zai kwashe su har zuwa wani kasa mai nisa haka. Nikan yinin ranan duk abinda nakeyi tunane ne yai min yawa kan yadda umma ke kokarin jawo min komawa baya a gidan. Ke nan fa idan yai auren bariki ni sai dai naci gaba da zaman hakkuri agidan ke nan don nasan halin mijina akan mata hankalin shi gaba daya zai koma ga sabuwar marar shi ke nan ni sai yadda akayi damu kuma. May zan gane nasan bani gane komai daga gare shi kuma gashi ina na da matular son ace na bishi inda yake aiki tun farko ban dai da yadda zan yine kawai na hakkura na zauna a gida. Ina ganin yadda anty na suwaiba keyi idan tazo daga minna yan uwa naji kamar su lashe ta daga ita har diyan ta don dan hausan su daya banbanta da namu da kuma shigan su daban yake dana yaran mu damuma kan mu iyayyen yaran sai kaga ta fito daban a cikin mu. Sallaman wasu makwatan mune da muke abin arziki dasu sunzo yi muna murna da arzikin sayen motan da sukaji yayi. Daga ciki har da kawata Lariya da tsohon cikin ta haihuwa ko yau ko gobe amma ta iya tasowa zuwa ganin abin arzikin da ya samay mu. Dakin Umma suka fara shiga sukai mata murna da fatan samun ci gaban da yafi wanan watarana. Suka fito muka shiga dakina nan muka fara gaisawa dasu suna min murna da samun sabuwar kishiya a cewan su. Suwaiba tace ai karfe kishiya ce don tafi kai matar gida cin abin hannun maigida sosai. Lariya dai tana gefe sai murmushi kawai takeyi a zancen mu nan nake fada masu labarin da yazo muna dashi na son tafiya da mu. Amma kuma ga cikas din da Umma take son ta kawo muna ga tafiyan. Sai a lokacin ne Lariya tai magana tace kai haba ita ko umma idan tai maku haka batai maki adalci ba gaskiya. Duk hakkurin da kikeyi kuma yanzun samu yazo zata tace haka ai wanan ba so bane ni yanzu fa ba aikin gwaunati yake zuwa yi ba amma da zai ce zai tafi damu lagos din da yake zuwa gurin cirani aida nabishi tuni wallahi. Nan dai kowa ke fadin maganan shi suke cewa gaskiya kada na yarda da zancen umma na gwada mata ina son bin mijina kawai. Lariya tace a,a ta kyaleta ai tasan abinda ya dace itama ai mace ce kamar mu tasan abinda ya dace da ita. Yanzun idan ta nuna mata rashin kunya ba umma ba har shi dan nata zai iya canza mata zaman su ya lalace ai ba abinda ya gagari Allah. Don haka kikai kukan ki ga Allah ya haushe ki akan umma da dan nata don tunda kikaji ya fara maganan aure killa ya shiryawa hakan ne kawai. Maganan lariya yai matukar tasiri a zuciyana sosai don haka na hau kan shi na zauna akan zan kai kukana ga Allah yai min jagora ga al,amarin. Sun dan dade muna hira dasu suka fito zasu tafi sukaiwa umma sallama na raka su ina cewa wai lariya anya wanan cikin naki abin baizo ba kuwa sukai dariya sukace gata nan dai wallahi. Bayan tafiyan su lariyane nai alawala na shiga sallah tun a lokacin na fara sallah ina kai kuka na ga Allah kan al,amarin. Shiko Aliyu sai harkokin gaban shi kawai yake yi ya murje yayi kyau sosai dashi sai annuri yakeyi kawai yana bushashan shi hankali a kwance . Niko ina cikin matukar damuwa a lokacin don nasaka zancen tafiyan nan a raina sosai. Kwanan shi biyu zai tafi yake cewa yana sauraren shawaran da Umma ta yanke don idan yai wani dawowa sai batun tafiya kawai da mu zai rage umma tace mai taji. Mukai sallama dashi ya tafi yana cikin farin ciki da jin dadi gashi ya murje yayi kyau duk macen da ta ganshi dole ne ta kyasa a kan shi. Don Aliyu ba dai kyau ba da iya shiga ga ilimin zamani da ya ke dashi kaman shi yasawa kan shi brain. ****** ********* ****** Tafiyan Aliyu washegari muka tashi da tashin hankali a unguwar mu don Lariya ce gurin haihuwa haihuwan yazo mata da matsala aka kwashe ta zuwa asibiti. Nan mayan uguwa suka kwashi jiki zuwa asibiti don diba matsalan ta a can . Sunyi dafifi a kofan dakin haihuwa Laure na zaune a saman wani gawo lokacin da likita yazo da kan shi zai shiga dakin haihuwan ne sai faman gaidashi mutane ke yi. Har ya dan zauda inda suke a zaune sai yadawo gurin tsofin ya tsaya can yai dan murmushi ya kalli inda laure take a zaune yace. Mama aida kin tashi saman wanan gawon naki ko zata samu ta haife abinda ke cikin ta kafin ku karasa ta. Yai matukar girgiza duk wanda yake gurin a zaune yadda ya likitan banufe yai tsaye akan su laure da wata kawar ta da,ba,a san tana maita ba. Shi bai wuce ba su kuma basu daga ba kamar yadda ya bukaci su daga a saman gawon da suke zaune akai. Ganin zai iya tona masu asuri yasa laure ta dan zauda kadan ta tura gawon baya ya fadi kasa baya table din da suke zaune sama, yana ganin haka yai murmushi ya shiga dakin theater sai ko ga kukan jariri ya kauraye dakin a lokaci guda. Ga murna ga kallon mamaki gaba daya mutane sai mamakin su laure sukeyi ga kuma murnan haihuwan Lariya da tayi. Likita ya kalli Lariya dake cikin wahala a lokacin yaji matukar tausayin ta ya kamashi don yasan is too late don sun riga da sun gama da ita ko lokaci kawai ake jira gare ta. Abin tausayi ga yan uwa da abokan arziki sai murna sukeyi na ta haihu lafiya a lokacin. Yafito yana share hawayen da ya dan zubo mashi a lokacin sai faman gaida shi mutane ke yi suna mashi sannu da kokari. Fitan shi daga dakin bai kokai office din shi ba sukaji an saka salati Lariya rai yayi halin shi lokaci yayi. Muna gida zaune wannan bakin labarin na,rasuwan Lariya kawata ya samay mu. Hankalina yai matukar tashi, ranan munga tashin hankali don haka a ka dauko gawan Lariya zuwa gida cikin tashin hankali kafin wani lokaci labarin abinda su laure sukai wa lariya yabi gari ko ga jariri ana mata wanka sai faman tsala ihu yakeyi a gidan hankalin kowa a tashe. Muna ji muna gani aka tafi da lariya gidan ta na gaskiya akabar mu da yaron ta kowa yazo gaisuwa yaga yaron sai hankalin shi ya tashi aita kuka. Haka aka wuni a cikin uguwan mu a cikin tashin hankali kowa sai tunanen yadda tashi zata kasance mai yakeyi. Bamu ga tashin hankali ba sai da dare duk gidan dake makwabtaka da gidan su lariya irin namu sai da muka wayi gari da abin al,ajabi. Har dani da Umma bata bari nabar koda kyalen mu a waje da tukwane duk dare sai na tattara kayan aikin mu nakai kitchen na boye. Amma ranan a can na kwaso su kofan gida a,watse haka mutane akai ta kwasan kayan su ana kaiwa juji ana watsar wa. Mutuwan sai ta girgiza mutane don yadda yazo da abubuwan al,ajabi wasu sukace ranan ma wa yan da ke cikin gidan sunfi shiga tashin hankali sosai. Don ga jariri na ta tsala ihu ga iska ya cika gidan kamar guguwa zai daga masu kwanon dakin su dan katfin shi. Sai da safe kowa ke fadin abinda yaji a dare jiya a gidan nan suka samu anfito masu dakayan gidan an kai waje cikin juji an tara masu tsibi guda. Hankalina yai matukar tashi ranan sosai don abin da,bamu taba gani bane ko ji. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE A GIDAJEN MU 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 3⃣ A kaita zancen Laure gari nan takoma abin tsoro ga manya da yara yan uwan ta da,suka zama dolen ta kawai ke hurda da ita ko su a cikin dari dari suke hurda da ita. Mun kan a gidan mu Umma a tsaye take a kan mu ba Laure ba shigowa a gidan mun don yai mata nisa amma dai nikan duk da abinda Umma take kirarin tana yi darr nake da,al,amarin laure tunda ta lashe min kawata har abada ta tafi ta bar mu. Muna waya da Baban Abba sosai don yana yawan kiran mu yaji lafiyan mu ko yaushe. Nan nake bashi labarin rasuwan Lariya da kuma sanadin mutuwan nata da,akace shine sila. Dariya yayi yace kai ku dai mata wallahi baku gajiya da shirmay wallahi ba,a mutuwan Allah sai kun canfawa mutum kun bata mai gawan shi. Nace nima abinda naji ana fadi ke nan na fada maka amma gaskiya akwai kamshin gaskiya a zancen. Yace adduan ku take bukata kawai yanzu ita nata ai yakare kuma tayi kyakyawan tafiya tafarki maikyau hanyan haihu. Har mun gama,waya banji yai muna zancen tafiyan mu gurin shi ba ni kuma ina jin nauyi na fito mashi da zance daga bakina matan hausawa ke nan akan kunyan bin hakkin su. A bangaren Umma ba,wani zance ita ma koda ma naji ta tayar da zancen daga bakin ta babu shi. Dalilin dayasa na yanke shawaran naje gidan mu da zancen ke nan naji shawaran da za,a bamu. Na shirya da yara na duka mukaiwa Umma sallama muka tafi tana cewa gaba daya zaku tafi ba wanda zai zauna dani a gida. Nace a raina ashe akwai aiki ke nan kuwa don umma da,wuya tabar mu da zancen tafiyan nan tamu. Ko da yake ba komai take wa haka ba sai shakuwan da mukayi da itane kawai yake damun ta a zuciyar ta. Mun fita ke nan daga gida sai ko mukai kicibis da Laure nikan banji kunya jaye yara a gefe ba muka wuce ta don Ance maye ko da ido yana daukan kurwa in yaso. Bin mu tayi da kallo nace a raina kurwan mu kur muguwa li,ilafi kureshin . A zaure muka samu mahaifina yana tila karatu kamar yadda ko yaushe mutum.yaje zai samay shi yanayi. Ko kuma ka samay shi da jama,a masu zuwa gurin shi tambaya abubuwan rayuwa. Yana ganin mu ya sake muna murmushi yana cewa ai mutanen Alangasa ne yau a gidan namu haka. Nan muka zube muna mika gaisuwan mu a gare shi yake tambayan mu Umma nace tana nan lafiya kalau. Yake cewa yaya shi wajen maigidan naki kuna jin labatin shi ko ? Nace cikin kunya lafiya yake baba yace ai kwanaki yazo yake ce min yana son ya koma da ku can wajen shi. Nace hakane Baba yace amma sai dai umma ce bata yarda ba da zancen har ya tafi ba tsayar da matsaya ba kan zancen. Yace subbahanallahi ita kuma Ige mai yakaita wanan halin yau ba dadin ta bane ace ya kwashe ku inda yake ai shine kamalan shi da ita ma. Yau har Allah yasa da kan shi yai magana zai tafi daku amma har zata kawo cikas ga maganan. Kai mata dai mata ne wallahi bata gudun fadawan shi a cikin halaka da kamuwa da cututunkan zamani da sukai yawa. Idan tai maku haka bata kyauta ba daga ke har maigidan naki zata shiga hakkin ku ne sosai. Baba yake cewa Abba abokina ga shi kayi sa,a andama hura yanzu sai ka dauka kaje kusha ko. Nace Baba kaifa idan suka shaye maka yace ai arzikin ke nan maryam mu godewa Allah da yasa har suka san mu yau ina Amina take cewa mahaifiyana nace hakane Baba yace su sha sai a sayo min wani a dama min. Na mike ina cewa bari mu shiga gida na gaida su umma kasancewa mahaifiyan mu mu ta dade da rasuwa a gurin kishiyoyin ta muka tashi kuma sun muna riko mai kyau baka cewa basu ne suka haife mu ba. Ga idona ya ciko da hawaye a lokacin fon tina min da mahaifita da Baba yai min a lokacin. Don mu shidda ne mahaiyar mu tabari nice babba a dakin mu saran duk kanne na ne su mu mata mu biyu ne sauran duk maza ne su. A yadda muka ji wai iskokaine suka saka mahaiyar mu a gaba wanda suka hanata lafiya har rai yai halin shi. Ina shiga na samu amaryam baban mu tana daka wa je tsakar gida tana ganin mu take cewa a,a yau mutanen Alangasa ne a gidan namu. Nai murmushi na shiga gaida ita nake gaisawa da yan uwa na yan mata dake zaune a tsakar gida suna cin tuwo a lokacin. Dakin Inna muka wuce don an ce muna tana ciki muna shiga na samu yayata tazo diyar mama da tayar dani nan muka baje muka shiga gaisawa dasu nakawo dan tsaraban da na kawo masu na basu tashiga saka min albarka da fatan gamawa da duniya lafiya. Ban dade da shiga ba itama Amaryan baban mu da muke kira innan sahura tashigo dakin gurin mu tana cewa. Dada maryam sai mukaji labarin rasuwar kawar ki boyan Allah ashe haka abin yazo mata da akasi nace wallahi innan sahura. Lariya boyan Allah ta tafi ta barmu anty lami dake zaune tace ba ance mayune wai makwaciyar ku suka kashe ta ba nace haka ake fadi wallahi anty aida kafin ita da dani tafara sharewa. Nan nake fada mata abin da ya faru tsakani na da Laure daga neman gishiri ya zama min alkakai a gurin ta. Innan sahura dake ta kofa a duke take cewa aiko da kashin ta ya bushe idan ta taba diyan malam a garin nan. Ita batasan kunfi karfin ta bane wai da zata jinjina ki haka mama dake sauraren mu tace wasa dai amma watan jin kunyata ko na tsayawa in takai gare ku. Mama tace kwanaki mijinki yazo yana gayawa malam yana son ya tafi daku can gurin aiki ko ? Na dan tabe bakina ce eh haka yaso mama sai anty tace wai dako nai maki murna maryam. Nace amma ai Umma ta hana anty lokaci daya suka hada baki suna fafin ta hana fa ta hana may zakiyi mata in kin zauna nan. Na marairaice nace to nima ban sani ba sai dai ina ganin kaman saboda yaran nan ne bata son mu rabu kawai don shakuwa. Don ko yanzun da zamuzo saida tace dukkan mu zamu kwashe mu bar mata gidan. Oh lalai shi takewa amma banda abin Ige ai hakan da yayi shine dai dai ko nace haka dai Baba yace yanzu ai. Kawai gaskiya baba yai mata magana inji anty na tace ta yaya zatai maku haka idan kin zauna nan ba wata zai karo muku can ba tunda yana da muradin zama da iyalin shi kusa dashi. A marairaice nace ni dai yanzu wallahi duk a rude nake don gaskiya kodan karatun yaran nan a can zaifi. Gaskiya dai idan tai maku haka bata kyauta maku ba dai wallahi dole ne ai mata magana ko zata sake shawaran ta. Nace yanzun dai yace idan ya dawo idan ta yarda damu zai tafi idan kuma bata yarda zai samu wata a can ya zarga da ita. Kai ba za akai ga haka musan bamu hana shi aure idan ya tashi amma aikece zata cuwa gaskiya haka ba adalci bane. Nan dai muka wuni muna zancen akan batun tafiyan har sisters dina suna cewa wallahi ke ta samu anty maryam da mune ai sai dai ta wayi gari kawai mun tafi abin mu. Wanan mara kunyan zata iya shi inji Innan sarahura tanacewa sahuran dake magana to bake bace dadin abin ke nan ita tana da ta ido. Sai da la,asar mukai masu sallama muka tafi lokaci daya mula fito da anty na daga gidan tana kara jadda min cewa na fa dauki mataki kada na yarda da zancen Umma nace haka za,ayi ai anty takama hanyan gidan su nima nabi nawa. Mun samu har umma ta aza min girki ko ina cire hijjab dina na fito don na karba a hannun ta. Nan nake fada mata mun hadu da laure ai da zamu tafi take cewa aniyar ta dai yabita wallahi. Nagama na kwashe kamar yadda muka saba yi kafin magariba na gama komai muka shige daki saboda tsaro. ****** ********* ****** Yana gurin aiki yake fadawa abokin shi zancen son ya dawo da iyalin shi da yakeyi garin. Mutumin yace kai amma kan ka kyauta gaskiya zama kusa da iyali shine kamalan namiji wallahi kuma zasu samu inganttacen rayuwa bisa ga zaman kauyen da suke a can. Yace sai dai gidan dana samu ba mutane sosai a gurin don can sabon easte din da aka gina ne a yakubu gawon road na samu gida. Aiko gurin ba laifi kaga ma ba nisa sosai da nan office din namu zai maka sauki sosai zuwa office. Kawai ka kama abinka idan gurin yai maka kyau da sannu zakaga mutane sun cika gurin ai. Akwai wani a malali yafi cikin mutane sosai amma dai wancan sabon easte din yafi kyau sosai gaskiya. Mutumin yace yafi kyau mana kasan an dade da gina su amma ba bude shi ba dai yanzun aka fara shiga. Yace kawai dai maganan shi zanyi da na bar nan gurin zanje gurin inchage din gurin muyi magana dashi. Muna zaune a dakin umma da yamma ya bugo waya suka gausa da faranta ga fuska suke gaisuwa da umma din can ban san may yace mata ba sai ji nayi umma na fadin kai kana ga zancen tafiyan ne wai har yanzu. Na fada maka ban da ra,ayin wanan tafiyan nasu can wani uwar duniyan na daban. Nafison ina ganin su a gidan nan a tare dani idan ka kwashe su ni dawa zan zauna a gidan nan. Ka tausaya min mana Baba kai dai fa Allah yabar min nake gani sai yanzun da kadamu iyali kuma suke debe min kewan ka. Ina ganin ce mata yayi to shikan sai dai yai aure don ba zai iya zama shi kadai ba don yagaji da hakan. Sai cewa umma tayi kaje kayi mana idan haka kaga yafi maka daidai a rayuwan ka. Wani irin mugun faduwan gaba naji a raina nace may umma take nufi da nine wai so ne haka ko dai kiyayya take min . Ranan ban mata ko sai da safe ba na mike abina na bar dakin tare da daukan Nusaiba a kafada na. Daki na koma sai kuka na kulle kofana ban sake fitowa ba again sai faman tunane nakeyi kawai a raina ni kadai a daki. Washe gari ma ban fito ba ina daki kwance har rana ya haska sai jin muryan umma nayi tana fadin oh yau maryam bazakiyi muna ko abin karin bane ? Gidan ko shara babu ban amsa mata har takai ta kawo kofan daki ta daga labule ina kwance na kunna redio ina saurare zabi sonka da akeyi a tashan redio kwantagora. Daga labulen da tayine tana fadin maryam yau ko lafiya kike ne na dan zauna kadan saman gadona nace lafiya nake Umma. Toowoo ko maganan da kika ji inayi da,Baba na jiyane kike wa fushi haka hmmm maryam baki gane manufa tane ke. Ke da,yaran nan fa kukadai nake gani inji sanyi ina zan barshi ya,kwashe ku zuwa wata uwar duniya can. Ni yadda duniya takoma yanzun ne nakeji wa baka kwana da mutum ba ya tashi dakai a ranshi. Ga kaduna ba karamin gari bane tun can baya don mu acan ne muka,fara jin labarin yankai kai da sace mutane . Nace Allah ya tsare mu umma amma dai ai bamu kadai zamu zauna ba aiko? To abun har yakai can to fito kiwa yaran nan girki su karya rana tayi ni na gama magana ta. Yaje can yasamu yar barikin da yace su zarga a tsakanin su yafi min sauki nikan. Wani iri naji a raina haka na mike banda yadda zanyi don ban iyayiwa umma rashin kunya naje na dora masu girki abin karyawa. Haka muka wuni ina share umma a gidan sai magana take sake min idan yyara sunyi abu nai masu fada sai tace kai ku kama kan ku kada a fashe haushin daba naku ba akan ku yau. Bayan kwana biyu anty na tazo don taji yaya mukayi akan zancen tafiyan namu nake cewa cikin kuka wallahi anty tana akan bakan ta ta hana. Don a gaba sukai waya dashi take cewa yaje ya nemi wata can a,bariki ya aura. Kai ashe haka matar nan take wallahi ni har ta zube min Allah ashe bata da imani bari zanje gida zan fadawa baba halin da ake ciki ai. Shiya hankalina bai kwanta ba nace bari nazo naji may ake ciki akan zancen don mu sanan abin yi kafin ku tafi don naga wata ya kusa karewa nasan zaizo ke nan. Nace wallahi anty babu zancen don ta hana tafiyan tace bazamu tafi mu barta ita kadai ba. A,a tace dai dama ita kike aure ba Aliyu ba ke nan da zata fadi haka kai tsaye. Ko da anty na zata wuce umma taga canjin fuska sosai a gurin ta don batai mata yadda ta saba ba inda tazo gidan. Direct anty na gidan mu ta wuce can take fadawa iyayyen mu yadda mukayi da Umma kan zancen tafiyan mu kaduna. Aiko sukai ta yanka fada suna aibanta umma da halin da ta tsiro suna fadin bata sona ashe duk sallon yaudara ne kawai. Sai da baba ya shigo gida ake fada mashi abin dake faruwa dani murmushi yayi yace kubarta ai zan ganta muyi maganan naji hujjan ta. Haka dai baba ya kashe maganan ya hana kowa ya kara magana sai yaga umma din. Aliyu ya bugo waya ban iya dauka ba sai kukan da nakeyi kawai hankalin shi ya daga ya shiga tambayana may akayi may ke faruwa ne wai. Na kasa magana sai dakyat nace mai ni abinda umma ta yanke a kan mune bai min ba ai wanan ba so bane ko gata gare mu. Maryam may ye abin tayar da hankali ga zancen nan ba ina zuwa gurin kuba duk karshen wata yanzun fa haka jibi ma zab shigo idan Allah ya yarda. Kada ki bari ajiku da umma ai maku dariya don son da Umma taje min ne ya koma a gare ku ai. A raina nace wani so ko kiyayya dai da yarta ne ni aida batai min haka ba wallahi. A fili cewa nayi ai baza aji mu ba amma ni dai gaskiya naso mu dan zo ko ma dai don miga gari kawai. Hakuri yabani yace mu bar zancen har yazo zai san yadda za,ayi idan bata yarda ba sai a hakkura mu zauna kawai. Nikan sam umma takasa gane kaina duk kwanakin nan harda dan kwaliyan da mukeyi idan zayazo yanzu wanan zuwa da zaiyi duk banyi ba hakana na zauna komai ban anyana ba akaina har yaran dagidan ido kawai tasamin tana kallona . ZAINAB IDRIS MAKAWA [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BAMU KADAI BANE A GIDAJEN MU,,,, 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 4⃣ Yashigo garin yadda ya saba amma kuma shi kan shi yanayin da ya riske mu ciki ya bashi mamaki sosai don ba haka ya saba samun ba don ko wanka ma ranan ban wa yaran ba har ni ina daure da wani tsohon zanin goyon Nusaiba a jikina. Sai bina da kallon mamaki kawai yake yi haka na shigo na dangware mai abinci tare da gaishe a tsatsaye n fita yabini da kallo har na bace mai ya sauke ajiyan zuciya kawai. Umma tana gefe tana kallon mu sai cewa tayi ikon Allah ko wai duk fushin tafiyan ne haka fa. Niko ba inda zasu su barni gidan nan ina nan a tare dasu idan ma ba rashin tausayi irin na maryam ba da take son kwashe yaran nan su barni da kewa. Haka yadda ka ganta haka ta koma ba maijin dadin ta a gidan nan dagani har yaran nata. Duk da baiji dadin maganan Umma ba amma kuma sai da yaji haushi irin hukuncin dana dauka kan dan maganan da bai kai ya taka kara ba kawai. Da dare ma ba wanan taron da rawan jikin da na saba mashi a baya can haka yai rawan shi da kidan shi ya,barni na juya mai baya kawai . Don yanzu daga shi har umma daukan su a makiyana nakeyi a gidan na,fahinci zaman amfani kawai dani sukeyi a nawa fahinta. Ina jin su da safe Umma tana ta sirfa masifa wai bazata dauki irin wullakancin da na dauko yiwa jikokin ta ba. Aliyu yana fita daga gida gidan mu ya,wuce gurin babana bayan sun gaisa dashi ne yai mashi sannu da zuwa tare da tambayan shi lafiyan mu. Yai dan murmushi yace suna lafiya sai dai ita maryam din ne nadawo na samu a cikin wani yanayi. Babana yace subbahanallahi na kamar may kuma ? Yace wallahi gaba daya ta sauya baba kamar ba maryam ba saboda kawai zancen tafiyan da Umma tace bazasu tafi ba can inda nake aiki dana so zuwa dasu. Murmushin manya babana yayi yace kai yaro dai yaro ne ita maryam ina ta samo wanan halin nata kuma haka don ban santa da halin banza ba a baya. Aliyu yace hakane baba shine nace bari na fada ma a dan tsawata mata ta,daina kada su samu sabani da Umma nan gaba. Babana yace ba matsala zanzo gidan yau da yamma insha Allahu kafin na zauna karatu. Sukai sallama yakawo kudi kamar kullun idan yazo gaida baban nawa yakan dan bashi har dasu Inna wani sa in yakan shiga yadan basu su ma. Bai dawo gida ba sai bayan sallah azahar yana,waje da,abokan shi na gida a,waje karkashin darbejiya sun shinfida babban tabarma akai. Yana shigowa ina alwala yake cewa wai na zuba mai ruwa butan kawai na karba na zubo mai ruwan na mika mai. Murmushi kawai yayi ya karbi butan don bai taba ganina cikin wanan halin ba sai a wanan lokacin. Kamar yadda, baba yai alkawarin zuwa gidan namu sai ko gashi da yamma tare da,yarashi biyu a,bayan shi masu daukan karatu a gurin shi. Umma yace ace anawa sallama baban maryam nan umma ta hau fada tana fadin yo karana akai ne gurin malam kuma? Lalai zance yakai to ni babu mai hadani da hatimi in lalace rayuwa na ya tashi ga banza. Daga waje Baba yana jin ta sai murmushi kawai yayi aka fito da tabar ma aka shimfida masu a waje. Can tafito tana yafe da zani irin wanda ta daura a jikin ta kamar ba itace tagama sababi a cikin gida ba. Sun gaisa tana durkushe daga gefe tana fadin malam yau kai da kanka kazo ai da ka aika nazo koma may nene. Malam yace a,a ba gurin ki nazo ba gurin yar ki maryama dai nazo don irin sabon halaiyar da naji ta tsiro dashi. Sai lokacin Umma tai murmushi tana cewa kai maryam maryam ai ba,wasa. Gaba daya ta hana zuciyar ta sakat kan zancen wai sai tabi mijin can inda yake. Shiru baba na yayi har umma tagama kawo hujjojin ta na rashin yardan ta ga tafiyan mu. To amma maman Aliyu bakiyi wa yaran nan ko adalci ba don yaron yanzu harkaji ya furta abinda ya dace da bakin shi to kamata yayi ayi dubaiyya ga alamarin. Amma yadda kika yanke masu wanan danyen hukunci haka ai dole ne yarinyar nan ta dau zafi haka gaskiya. Daya daga cikin wanda suka takawa babana baya ne ke wanan maganan haka. Umma ta dukar dakai babana yai gyaran murya yace to walilllahihamdu ban so ace nai wanan magana yanzu ba don bashine ya kawo ni ba yanzu. Yanzun tafiyan maryama ce ya kawo mu amma kuma sai gashi ke yanzun kin fito da zancen da kan ki. A gaskiya maganan malam iro ne abinda zamani yazo dashi mu yanzu sai hakkuri. Ko azananin da can baya nisanta da namiji da iyalin shi babban hatsari ne balle a,wanan zamanin da muke a cikin shi na karshen zamani. Ai sai naga kamar a gareki wanan nufin na yoron nan Aliyu abin farin cikin ki ne sosai yau da,bakin shi yazo maki da kudirin zancen son tafiya da iyalin shi a kusa dashi . Ai sai kawai abisu da addua da fatan alheri a gare su na gamawa da duniya dafatan albarka ga zuria. Umma tai shiru kawai tana,sauren irin nasihan da baba na yake zuba mata har yakai karshe yace sai abar zancen tunda baki ra,ayin tafiyan. A turo muna ita maryama din mugan ta sai mu tafi kuma don Allah aita hakkuri don Allah halin yaran yanzu sai su. Yanzu diyan zamani diyan agwagi ne suna gaba uwarsu tana baya haka yaran yanzun suka koma . Sai abinda zuciyar su ke so shine ra,ayi su ya zaba masu zabi suke gani. Umma ta mike tana cewa ta gode tashiga gida ta turo ni nazo na samu su babana ina gaishe shi ya amsa min dakyat tare da fara min fada kan sauyin da nayi da mutanen gidan mijina. Har baba ya kare min fada da nasiha ina duke sai kuka nakeyi a hankali kawai. Bayan babana yatafi ne da dare Aliyu ya,shigo Umma ta haushi da fada wai dani dashi mun hada baki munyi karanta gurin mahaifina. Mutumin dake ganin ta da mutunci amma saboda son zuciyar mu don bamu tausayin ta muna son rabata da jikokin ta zamu ce sai mun rabata dasu. Duk yadda yai mata rantsuwa shi baikai karan ta ba Umma ba yarda ba sai faman fada takeyi ran ta a bace. Nidai ina dakina ina jin su amma ban futo ba don umma ta riga da ta sure min ko. Haka Aliyu yai muna weekend zai komana yazo sallaman ta ne take cewa su sai yaushe zaka kwashe su kutafi din. Yace to ai umma baki yarda da tafiyan su ba don haka na bar zancen tafiyan nasu. Da sauri umma tace ka rufa min asiri kada gaba kuma akaini gidan sarki barni da sunan da Allah ya rada min da kowa yasan ni da Igena. Idan kayi niyya tafiya da su ka kwashi iyalinka ku tafi kada kuma kasa a kasa ni ga faifan gari ana zagi. Yace umma kiyi hakkuri don Alkah idan ranki ya,baci ne amma ni banyi karan ki fa kowa ba,wallahi. To ni dai yanzu kaji abinda na fada maka ai ka,kwashi iyakinka ka tafi da abinka idan ka tashi . Shiru tayi can ya,nisa yace naji umma amma ba yanzu ba sai in sun shirya wani zuwa idan nadawo sai na tafi dasu. Ya fito ina shanya kanyan fitsarin Nusai ba yake cewa sai fushi ya kare tunda Umma ta jaye kudirinta kafin nadawo sai ku shirya ko ? Haka ya yafi yabar mu wanan shigowa sam baiji dadi ba daga gurin Umma har ni din. ****** ********* ****** Sannu sannu na,dan fara,sakewa a hankali har takai dai na,sake din amma babu wani zance akan tafiyan namu da ita. Ranan ina nan da yamma zauns ina tankaden gari naji sallama Lawisa ce diyar makwabtan mu ta dawo daga school. Boarding school take sunyi huta dawowanta ke nan ta shigo gurin mu gaida mu makwabta ta gaida mu Lawisa tayi kyau ta girma kamar ba ita ba ce uwar goyon yarana kafin ta tafi makaran ta nan muka gaisa da ita har gurin Umma tashi suka gaisa tafito tana tambayan mutanen tanake cewa sun tafi islamiya dazun mun dan taba hira da ita tace zata tafi sauran gidaje su gausa. Tana fita tashi gidan dayan makwabtan mu da zata fito ne sukayi kicibis da Laure, ta dawo daga nika, Yarinyar ta tare da wasan jika da kaka da suka saba yi da ita a don dangin uwar lawisa ce sosai suke da zumunta da ita. Bayan ta Laure ta dan kai mata duka tana fadin jaira yaushe kika dawo halan ? Take yarinyar taji kamar an sara mata guduma akan tane kanta yai wani irin uban sarawa,a lokaci daya. Da kyat Lawisa ta isa gida dafe da kanta sai ciwo yake mata nan da na zazzabi ya rufe yarinyar sai ta fara sambatu ai ranan yarinyar bata kwana ba duniya. Da safe labarin rasuwan Lawisa ya karade ko ina kowa da abinda yake fadi a kan mutuwar yarinyar da ta dawo jiya jiya cikin uniform din ta,shiga gaida mutane. Sati biyu da rasuwan lawisa labari ya dan fara ya duwa wai wasu samari sunganta a,tsakar dare sun dawo yawon hiran su. Tana tsugunne da uniform din ta a jiki tana kuka, sannu sannu labari ya fara bin gari idan kayo dare a uguwan mu koda bayan goma ne zaka iya haduwa da wanan yarinyar a tsugunne tana kuka cikun uniform din ta. Duk gari labari yakai ko ina nan aka shiga kace nace kan zancen kkowa da abinda zai fadi ga zancen. Nikan ma dai saboda tsoro a dakin Umma na tare nake kwana don ance kishiyar maman ta tafito fitsarin dare ta ganta tsakar gida tsugune ta sa hannayen ta a fuska tana rusa kuka . Matar da taga lawisa sai da,akai kwana biyu ana burganta duk ta zauce ta zama kamar mahaukaciya sai fadin takeyi wallahi ashe ba karya bane na ganta tana fadin Laure Laure cikin kukan ta. Aiko zance ya bazu laure ce ashe ta cinye Lawisa ke nan nan dai da,abu yai yawa akaje tambaya,shine ake fada masu manya ce mace tai mata farat daya ta kashe ta. Bayani dai gashi nan babu dadi ko kadan akace wallahi sai dai aiwa laure ature tabarwa mutane uguwa amma ba,a zama da ita haka tanayiwa mutane ta,asa a gari. Tun da farar safiya akai mata koran kare daga uguwan da dan kayan ta ta bar uguwan don kada a kashe ta. Jifa mugu mai daukan rai shine wai kuma yake gudun mutuwa din wanzan baka so a jikin ka. Duk gidan da ka,shiga zaka samu ankafa incen aduruku a tsakar gida da kofan gida wasu har a dakunan kwanan su su yayyabe shi da ganyen don tsaro kawai. Muma Umma tashigo gidan da ganyen ta tayayaba shi ko ina a tsakar gidan. Zuwan da akayi gurin mai magani ne na mayu aka samu ta har aka daina ganin Fatalwan Lawisa karamar yarinya yana fitowa. Cikin wanan lokacin ne na tashin hankalin da muke ciki Aliyu ya iso garin. ****** ********* ****** Ya,samay mu a firgice da zancen abinda ya faru da yarinyar da yasani mai min rainon yarana idan na haihu ko yaushe muna like da juna idan aike ne ko girki duk itace mai min shi. Umma kan da taga fitina a,fili sai cewa tayi kai ni wanan abin ya isheni haka garama ka dauki iyalinka kutafi nisa yafi min wanan fitinan. Yau ace wanan gobe a ce wancan babu kwanciyan hakali a gari ko kadan . Kaga kwanaki ma wani abune yake yawo gida gida ba dama mace ta zubar da kanzon tuwo a bayan gida ko makwarara sai abin mai kama da maciji da kan jaki ya tasa gidan gaba duk dare sai yazo neman abinci. Umma tace dama mu an fada muna zuba abinci a makwarara yana kawo aljanne a gida ko macizai da wasu miyagun abu masu binda dare. Amma kaga su yaran yanzu sun yarda wanan al,adan suna daukan shi wai canfine kuma wallahi ba canfi bane. Gaskiyane duk gidan da ake irin wanan sakacin gidan nan bai rabuwa da ciwo da sauran saddabaru cikin shi. Allah ya kyauta yace tare da yiwa yarinyar addua umma tace gashi ance mutuwan mayu wuyan sha,ani gare shi. Ko kwanaki anan kauyen garin ake labarin yarinya ta mutu budurwa bayan wata biyar sai ga labari wai wani mahalbi ya tsunce ta a dajin zamfara ashe ba mutuwan Allah da Annabi tayi ba. Yace umma ai ban manta ba mutumin da ya mutu wani lokacibai irin hakane ya faru dashi mana. Nan gida ana cewa ya mutu sai ga,wani bayerabe zai dawo saman mashin din shi ya ganshi yana sauri ya tsaya su gaisa yake ce mashi sauri yakeyi baban shi ya aike shi ne. Amma idan yaje gida ya fadawa matar shi ta duba kasan gadon su akwai kudi idan ta haihu asai ragon suna dashi. Mutumin yana iso gari yaga antaru kofan gidan su wanda ya mutu din yake tambaya akace mai ai wanine ya mutu shinema yanzun aka dawo, kai gawan shi yanzu. Sai cewa yayi a,a wallahi badai wani ba kan wani da muka hadu dashi yanzu a hanya har yabani sako yace yana sauri ne baban shi ya aike shi, Yace nace matar shi ta duba kasan gadon su akwai kudi nan a dauka asai ragon suna idan ta haihu. Koda akaje aka duba akasamu kudin kamar yadda mutumin ya fadi nan aka gane cewa mahaufin nashine yakashe shi ta sihiri. Ai har nan akazo dashi gidan sarki yasa aka kore shi gari . Umma tace kwarai kuwa haka akayi wallahi aikai dai mutane yanzu sai addua wallahi don son duniya ya rufewa mutane ido sosai. Shiri muke tayi na tafiyan mu don ba lokaci sosai duk da dama ni kan na,shirya abina a asirce da safe ana gobe zamu wuce ne na tafi gidan mu in yi masu sallama. A zaure na samu mahaufina nake fada mashi gobe ne zamu tafi yai murmushi yace maryam uwar rigima sai da dai kika sa Ige ta yarda da zancen tafiyan nan ko? Dan murmushi nayi na dukar da kaina kasa can naji yana neman sani abu a cikin kayan shi yana fadin. Kin san yanzu duniya tayi nisa sosai bari na dan baku wani dan abu dake da yaran sai kuyi amfani dashi kafin ku bar garin nan ku tabbatar da kunyi shi yau din nan. Rubutu ne yabamu da kuma wani ganyen magani yace mu yi wanka da hayaki dashi nan yabini da addua da fatan alheri. Nashiga ciki na samu su Inna su ma nan suka dan bani nasu tsaraban tare da min nasiha. Tun a gidan mu mukayi abinda baba yaba mu muyi da kuma muka dawo gida muka kara yi ni da yaran harda maigidan a cikin hikima shima na bashi yayi. Duk wani dan abinda zamu bukata mun yaba da sai dai su kayan aiki ne yace kada nahe da komai duk a can zamu sayi wasu. Yaiwa umma sayayya sosai duk wani abin bukata sai da ya aje mata kafin mu wuce da safe duk yan uwa na sunzo gidan akan idon su motar mu ya tashi sai a lokacin naji kuma rashi jin dadin tafiyan da zamuyi mubar gida da kowa namu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE,,,, 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 5⃣ INA GODIYA GA IRIN KAUNA DA SOYAYYAN DA KUKE NUNA MIN A KULLUN MASOYA NA DA BAZAR KU NAKE RAWA ADDU,AN KU GARENI YANA MIN DADI ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA IMANIN UBANGIJIN MU A ZUCIYAN MU,,,, Tafiya mukayi sosai ban taba sanin ma ya iya mota haka ba sai da naga yadda yake sharara gudu damu a hanya saman titi. A gaskiya ba abinda yafi dadi ga rayuwan ma,aurata kamar su kasance a tare a ko wani lokaci. Zan iya cewa yauce rana ta farko a cikin tarihin rayuwan aure na da Aliyu da muka samu kebewa dagani sai shi a cikin ni shadi haka. Don duk abinda yagani a hanya zai dan waiga inda nake ko gurin yaran yace na saya maku abukaza ne. Wanda a gida ba dama ya sayo muna dan wani abin marmari umma ta kama mai fada ke nan wai yana son bata mu da kwadai. Iyakar mu dashi kayan girki kawai idan ma baya gari mun shiga cin tuwo ke nan da miyan yauki ko na taushe shine, na dadi idan anyi. Ga wani kulawa na musan man da yake nuna muna wanda bamu saba da hakan ba gare shi saboda ganin idon Umma . Yanzun ne na fahinci Umma ashe ba karamin takurawa rayuwan mu ni da yaran mu tayi ba . Duk da ban da wani matsala da ita a fili amma ashe a badili akwai kuntatawa a zaman mu kusa da ita. Gashi ko wani gari muka kai ko kauye sai ya fada mana sunan garin da dan tarihin shi har muka isa kaduna misalin karfe biyar da rabi na yamma. Sai bin garin muke da kallo garin ne wanda ganin shi ma yafi jin labarin shi sosai. Haka mukai ta tafiya har muka zo wani unguwa mai jama,a cikin shi sosai a hankali yake shiga wani titi mai tsawo har muka sha kwanan wasu gidajen dake jere da yawa duk kusan zubin su daya. A Gida kusan na karshe ya tsayar da mota yana fadin Alhamdullahi da,sauri na dan kalle shi tare da duban zubin gidan. Gida ne mai kyau ginan zamani komai a tsare yake a hankali na dan runtse idanuwa na tare da fadin Alhamdullahi a raina wanda yafito cikin irin gidajen mu na kauye yau mune a cikin irin wanan gidan . A gaskiya ba karamin arziki mukayi ba da umma ta amince da zuwan garin nan don komai abin birgewa ne gurin . A hankali ya bude motan shi ne ya fara fitowa daga cikin motan yana cewa oya bisimillah ko ? Nace Auzu bikalamatti llahi tamat min kulli shedanin rajim. Na sauko a hankali daga cikin motan tare da fadin La ilaha illa antta subbahanaka inni kuntu minal zalumin. Tau fa duk addua a ne haka maryam nace ba dole na nemi tsari ba ga Allah yaya da sabon gurin da zamu shiga. Shi ya hau matakalan da akayi three step kafin a hau baran dan gidan ya nufi kofan yana budewa a hankali. Muna bayan shi ina dauke da Nusaiba a hannuna muka shiga nace salamu Alaikum wa kikewa sallama kuma a gidan ko ance maki akwai mutane ne. Nace baba yace ko dakin kane zaka shiga kai sallama tukun kafin ka shiga ciki. Sai bin gidan nake da kallo gwanin ban sha,awa gida ne irin na ma,aikata akai tsarin shi daki biyu da falo ne sai kicin da bathroom sai ta baya a kwai kofa daga kicin inda zaka dan fita wani dan fili karami duka a cikin gidan. Ya sa kujeru a falon a cikin dakin kuma dayan dakin da gado dayan babu gado a cikin shi sai katifa katuwa a kasa. Falon akwai tv dan maudaidaici da fridge a cikin shi da labulaiya a ko wani windows din gidan. Na lumshe idona cikin jin dadin ganin sabon gidan namu na nufi dayan kujaran na zauna tare da shimfide Nusaiba sama. Dakin ya wuce direct bayan ya kunna muna fankan sama da wutan falo don yamma yayi a lokacin. Can ya fito ya sauya kayan jikin shi muna zaune da yaran yace ,a,a zama kukayi a nan Abba kaga sabon gidan ku ko ? Yau ka gudu kabar Umma ko ai bazaka ci masan safe ba nan dai babu masa kuma babu umma da ta saba baka masa duk safe kana ci. Nai dariya daga inda nake zaune nace ai Abba ya iya butulci ko yai kuka zai rabu da Umma yau am a yai wani kemaymay dashi. Baban shi yace nima fa naji mamaki yaron nan na dauka zai kuka da zamu wuce fa don ita wanan ya shafa kan Aisha yace ba tada damuwa taga baban ta. Muna nan zaune naga ya fara shigo muna da kayan mu ciki mikewa nayi na tsaya daga kofa ina karba kayan ina shiga dashi ciki. Har muka gama yashigo yana cewa wancan dakin dake da katifa dama cewa nayi sai ku zauna da yara a ciki kafin a gama gadon shi wanan kuma sai muyi sharing ni dake ko ? Nace mun gode dariya na bashi don shi mutum ne mai son dariya idan yaso yace barin fita in samowa yaran nan abinda zasu ci kafin suyi barci. Yana fita naji ta da motar ya barmu a gida sai ni da yara a hankali na bi gidan da kallo na mike daga inda nake zaune ina shiga ko ina ina dubawa a hankali. Gidan yayi gaskiya ba laifi idan mutum ya samay shi ko a gida ne ai ya gode shine mai hali. Nan na fara gyara kayan mu ina kai ko wani inda ya dace Abba yana tayani dauka da Aisha. Bathroom din nashiga naga akwai ruwa a fanfo yana zuwa ga shower daga sama kuma shima akwai ruwa a cikin shi. Na ce bari nai masu wanka kafin yamma ya karasa sosai kafin yadawo nayi masu wanka ko ina shafa masu mai ya shigo yana cewa kunyi sallah dai ko ? Nace anyi kiran sallah ne yace bakiga duhu yayi bane ba massalaci a uguwan amma munyi magana za,a gyara wanda aka gina na uguwan harda islamiya mun roka aimuna don yara saboda akwai nisa da inda ake zuwa karatu da nan. Namike na bar yaran na shiga nai alwala nazo falon nata da sallah bayan ya nuna min gabas. Na idar nai adduan sosai yadda na saba zama bayan magariba nai addua don yaran ne ma na mike na basu abincin da ya sayo muna kafin suyi barci. Tare na zuba masu sukaci basu wani dade ba barci ya dauke su nan muka zauna muna hira dashi sai misalin tara da wani abu na kwashi yaran zuwa daki da yace shine nasu yace amma da yake basu saba kwana su kaida gashi bakunta kukeyi ki kaisu daki sai mu kwana tare dasu nan nai masu shimfida a kasa na kwantar dasu su duka ukun na dawo na kwashe kayan da muka ci abinci nakai kitchen. Bai dade ba shima ya shigo dakin ina duke ina wa yaran addua akan su shirin kwanciya yakeyi shima. Nagama abinda nakeyi na kashe wutan na kwanta nima duk da gajiyan hanyan dake a kan mu bai sa ya huta ba ranan sai da ya sauke nauyi a kaina. Waahegari tun biyar muka tashi munyi wanka na shiga kitchen don yace bakwai yake zuwa aiki watarana ma shidda da rabi yake wucewa. Ina kamalawa na tayar dashi don har barci yaso ya fara daukan shi a lokacin ko. Wanka yayi ya shirya yafito ya zauna ya karya sannan yake ce min shi zai tafi zai aiko akawo min abinda zamuyi girki dashi da rana. Nan ya fita ya barmu nida yara ya wuce gurin aikin shi ban kwantaba don ban saba kwanci ba nan na shiga gyara fasalin falon yadda naga ya dace min dashi. Yaran suka tashi nai masu wanka na basu abin karyawa muka dawo falo na kunna masu tv suna kallo ganin muna da dan abin da muka zo dashi nai masu jeloup da kifin da mukazo da shi. Sai bayan har sun gama cin abinci ne mai kawo sakon ya zo gidan da kayan miya fresh one su tomatoes tattasai albasa dasu cabbage da sauran abubuwa girki dai. Nakai kitchen nai ma komai muhalin shi yadda ya dace ayi a kitchen sai zuwa rana na samu nai wanka nai sallah. Yaran na son fita waje na hana su na kulle gidan damu a ciki ba wani hayani ya sosai don mutane a gurin jefi jefine ake ganin su. Sai da na idar da sallah ne muka fito daga wajen gidan muna kallon uguwan. Nan naga yadda fasalin gurin yake dakyau na lular tsakanin gidan mu da gidan dake da mutane akwai gidaje biyu da suke empty ba kowa a cikin su sai namu can kuma zaka hango wasu suma daga nesa haka tsarin gurin yake a can ma gaban mu akwai wasu mutanen a wani gida don na hango mota a kofan gidan. Nan muka dan sha iska zaune a gaban gidan zuwa dan wani lokaci muka koma daga cikin gidan na fara kokarin gyara kayan miyan da zan muna girkin dare. Sai da nai sallah la,asar na dora girki ina jin yaran suna ta wasan su a falon gidan niko ina daga ciki ina aikina a cikin natsuwa. Har na gama mukai wanka na gyara ko ina a falon bai dawo ba sai zuwa biyar da rabi kusan shidda naji ana kwankwasa kofan dakin na nufi gurin na bude kofan. Shine a tsaye yana cikin uniform din shi kayan sun balain yi mashu kyau yana tsaye da leda a hannun ahannun shi nai mashi sannu da zuwa tare da karban ledan hannun shi. A tare muka juya muka shiga gidan dashi yaran dake zaune suka sheko suna mashi oyoyo ya daga su sama daya bayan daya. Nusaiba dake saman kujera tana wasa da ganin shi take wasan bakin ta don tasan uban ta sosai. Sai da ya dan zauna suka taba shirmay da yaran yamike ya shiga wanka yayi yafito cikin jallabiya a jikin shi. Sallah ya jamu mukayi a gidan sanan bayan mun idar ya,mayar ga,hankalin shi ga,tv yana kallon labaran duniyan da,akeyi. Saida mukai sallah ishau ne yabar gurin na kawo mashi abincin shi yafara ci nisaiba tazo gurin shi. Yana ci yana bata nace tafa ci abinci kwadai ne kawai irin nata yace da ta koshi aibazata karba taci. Nan muka zauna ana hiran abinda aka gani a hanya da zamu zo jiya daga gida. Yace yau na tafi school din da nake son sa yaran nan sunce zuwa Monday sai azo dasu su gan su. Naji dadi sosai a raina yarana zasu fara makaran ta abirni kamar yadda muke gani sunayi. Na zauna ina tunanen idan suma suka fara zuwa makaranta haka zan zauna ni kadai a cikin wanan gidan ga unguwa kamar daji. Naji muryan shi yana fadin badai har kin fara tunanen gida ba ko ? Nace a,a tunanen dai yaran nan nakeyi da zasu shiga cikin bakin fuska da basu sani ba. Yace ke da kikai karatu kin san su ne ba a hankali ake sabawa da mutane ba. Kada fa ki sakawa yara damuwa suje su kasa zama suyi karatu kuma. Aisha tace nikan baba akaini makaran ta ina so wallahi bazan ki yin karatu ba idan an kai mu. Abba dai ba mai yawan surutu bane kamar yar uwar shi hankalin shi yana can akan tv yana kallo abinshi. Yace akwai wani abinda kuke bukatane kuma a,sayo maku na gida nace ba komai sai dai yan bahohin aiki nake so kanana da yan manya don wanki saboda wanki da bucket bai da dadi wallahi. Bai min magana ba yaci gaba da kalon shi abinshi na mike zuwa kitchen na wanke kayan da yaci abinci na gyara gurin na dawo falo. Na samu yaran har sunyi barci a lokacin nace yau ga shirmay har kunyi barci ko yanzun karfe nawa? Yace suna da sauran gajiya ne a jikin su shiyasa sukai barci nace a gida fa suna kai dare sosai basuyi barci ba suna hira da umma ko kallo. Yace sai na samu kudi zan dan duba masu kayan sawa wanan duk subar sa su anan sun tsufa da yawa. Nace daya ke nan da agida muke ina zamu ga tsufan wanan kayan masu kyau haka. Shiya tayani daukan yaran mukai su cikin dakin kwanan mu bayan nayi masu shimfida sun kwan ta. Sai da na dawo falo na zauna nake cewa ashe uguwan nake ganin kaman ba mutane sosai cikin shi. Yace sabon guri ne ba akai shekara da,dawowa ba bamufi gida ashirin ba dake da mutane ina gani kuma gidajen zasu kai guda hamsim. Yace amma indai kaduna ne zakiga kwana biyu duk gurin ya cika da jama,a ai. Washe gari da muka tashi ma nai sauri hada mai komai yadda ya dace yafita ya bar mu ranan bai dawo da wuri ba sai bayan sallah magariba. Rashin shi a gida ya sa muka koma jigum jigum saida ya dawi aka dan fara hira da hayaniya a gidan. Cikin dare har muna,shirin kwanciyane aka kirashi a,waya wai yazo zasu tafi operation an ji cewa,wasu zasu shigo da kayan sumugal wani kauye. Ya mike yana fadin yes,sir gani nan zuwa kallon shi nayi da mamaki yace shi zai fita don zasu tafi gurin wani aiki ne . Cikin daren nan baban Abba yana shiri yake cewa ai haka aikin kaki ya gada dama ba kuna can kuna fanin kaman mutum yana nab yana jin dadi bane kawai. Yashirya yake ce min sai ki taso ki rufe gida idan na tafi don nasan ni sai da safe zan dawo gida ke nan tunda aikin dare zamu fita yanzu. Gabana ya fadi tsoro ya kamani nace a raina yauko anayin ta dani da yaran nan kawai zamu kwana a gidan nan ke nan. Binshi nayi a baya har zuwa kofan falon sai daya dan kai kofan zai fita ya juyo yana cewa ki kashe komai fa na,wuta idan zaki kwanta nace toh Yana fita na kargamay gidan da bisimilah don indai adduoi ne mun san gwargwado tin muna yara a gidan mu kasan cewan babana malami. Na juya na koma ciki na jashe wutan falon dana daki na shige cikin yarana muka kwanta abin mu. Ban falka ba sai can cikin dare naji kamar an tayar dani ne daga barji ni ban yi barci ba kuma na kasa tashi na yi koda nafila ne. Haka kawai naji tsoro ya kamani sai faman jero adduoi nake har dai barci ya zo ya sace ni ban sani ba. Ko da na fito da safe na shi kitchen kayan da na wanke dare jiya sai na samu kamar anyi amfani dasu ga garin tuwon mu a bude ba kamar yadda na rufe shi ba kuma har a kasa ya dan zuba. Naji mamakin ganin haka don dai nasan baya gani jiya babu wanda ya shiga kitchen din to wanene yai haka da kayan nan kuma ? Har na dan fara sa abin a raina nace kai kilama dai nice nabarsu a haka na mata kawai sai na gyara komai naci gaba da aikina. Sai rana yaya yadawo a gajiye tunda yai wanka ya kwanta bai falka ba sai bayan la,asar lis ya tashi ya dawo falo inda muke duk da ni ina kitchen ne aikin girkin dare. Yace yau da dare zamu fita zuwa wani guri sai ki shirya da auri haka yasa nai duk wani abinda zan yi kafin magariba har wanka munyi mun shirya. Cikin gari muka tafi gidan wani abokin aikin shi yana da mata shima da yara biyar matar ta tare mu sosai dakin ta muka zauna don mazan suna falo suna hira. Muma dai muna ciki tana min hiran garin da yake bata sa,wuyan sabo ita sai da yaga dare ya soma ne ya kecewa mu fito mu tafi dare yayi . Muna hanya ya tsaya damu wani shago na kayan yara da lashe lashe ya sai wa yaran kaya kusan kala biyu da kayan lashe lashe. Mun iso gida ina matukar jin fitsari da sauri bayan na suke nusai ba na fada ban dakin mu don in kewa ya lokacin ne ma shi yake shigo ciki da wasu kaya. Tau nidai a iya sanina mu kadai ne a cikin gidan nan amma sai dai gani nayi kamar yanzun wani ya gama wanka don har kamshi sabun da akai wanka dashi nakeji. Ga ruwa nan yana dan diga gowa ga, soson wankan a hankali kasan cewa soson a rataye yake a saman window dakin. Da mamaki nafito daga bayin inda suke zaune a falo yana barewa Nusai biscuit nake cewa akwai wanda ke cikin gidan nan ne bayan mu. Kamar yaya kuma nace wanka naga anyi kuma da alama yanzun aka fito daga gurin wankan . Dariya yayi yace wanka kuma ni ba wani wanda nabawa key din gidan nan balle kila ma ruwan shower ne yake dan digosa ya kike gani kamar wani ne yai wanka yanzun a ciki maganan don haka kawai na,share zancdn a raina n a ci gava da harkokina kawai. Shima bai kara zancen ba yaci gaba da hiran shi da yara yadda na samay su sunayi da farko. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BANE,, 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 6⃣ Tun ina saka zancen a raina har nagaji na share zancen naci gaba da normal life dina tun lokacin kuma ban ba kara jin komai ba a gidan. Sati yana kewayo wa yakai yaran makaran ta suka fara karatun su kamar ko wani yaro. Naji matukar wanan sabon rayuwan da muka,shiga dani da yara,a gidan. Don da ka gan mu kasan akwai canjin rayuwa matsalata data shine idan sun fita zaman kadaicin da nakeyi daga ni sai Nusaiba a cikin gida kawai. Rana sun tafi makaranta shikuma ya tafi gurin aiki sai naji ana nocking din kofan falon mu. Nafito don inga ko waye a wanan lokacin haka wata matace nagani tsaye a kofan gidan tayafa dan karamin gyale a kafadan ta. Ban santa ba yasa nake mata kallon mamaki daga ina tai murmushi tace min ina kwana na amsa mata sai take cewa sorry fa kiyi hakkuri tunda kuka zo ban da lafiya ban samu shigowa na tare ku ba. Nice makwaciyan ki ta nuna min gidan ta da hannu sai na fahinci gidan da akwai gida biyu da ba kowane a tsakanin mu. Jin abinda tace yasa nai murmushi tare da ce mata Allah sarki shigo mana muka shiga tare ciki da ita. Mun gaisa take ce min ance mu mutanen Niger state ne ko ? Nace mata eh tace ita yar lokaja ne itama mijin ta aiki ya kawo shi kaduna yana aikin banki ne tana da yara hudu babban yana jss one sai mai bi mashi yana primary four yanzu kaunan shi tana primary two ita sai wanda ta yaye bai fara zuwa school ba. Sunan ta Hauwa mijinta tana kiran shi baban mubarak. Nan nima na dan fada mata nawa dan labarin irin yadda ta bani tace unguwar ba dadi shirun shi yai yawa kasancewan shi sabon guri ne. Nan take ce min tana gani wancan gidan na gaba kamar kiristan ne su amma dai akwai mace da yara a gidan basu dade da dawowa ba suma kaman mu. Mun dan yi hiran garin muka fito waje nan muka tsaya muna karewa gurin kallo muna magana nai mata alkawari nima zan shigo idan yara sun dawo daga makaranta. Bayan mun rabu ne nadawo ciki naci gaba da aikin da nakeyi sai kallon da nakeyi jefi jefi. Yaran suna dawowa ne tare da yaran Hauwa don maigidan hauwa yana riga Aliyu dawowa gida kullun don yanayin aikin su ba daya ba. Wata rana su basu ma cikin gari sun tafi wani guri aiki yasa ya roki makwabcin namu ya taimaka mai da dauko yaran tunda makaran ta daya suke zuwa. Muna zaman lafiya sosai da makwabciyata don na dauke ta a matsayin ya don ta girmay min sosai. Saboda mu irin auren kauye ne kashiga makaranta da wuri ba nursery sai primary one ka gama da wuri daka gama secondary sai aure kuma sai saurin haihuwa. Don yanzun haka ko agida akwai yan mate din mu ma dabasu yi aure ba sun tsaya karatu wasu kuma lokaci ne dai baiyi ba tukun. Yaran sun dawo suna shigowa na saba masu da sun dawo su cire uniform sukai min can baya inda nake wanki zasu samu na fitar masu da kayan da zasu saka ajikin su. Tun suna saka kayan Aisha ke cewa anty yau anbamu aiki home work kuma anti tace wanda baiyi ba gobe bulala ne zatai mai. Nace to kici abinci kizo muyi homework din tare idan kin gama suna gamawa ne na zauna bayan na gama wanke masu uniform muka fara assignment din da ita. Naji dadin yadda yaran ke iya kokarin su da irin karatun birni duk da ba turanci ne suke ji ba. Yaran anty ne suka shigo gidan don alhamis ce basu zuwa islamiya ranan. Nan suka zauna muna hira,suna tambayana labarin wai da zasu dawo daga school yau sunga biri a hanya . Nake ce masu aikila na wanine sai fadila ke cewa baya cizo ne nai dariya nace yana cizo mana idan an tanlba shi amma bai cizon mai shi wanda yake dashi. Tace wai Allah yasa dai bangani ba daya cije mu ko maman Abba nace idan kinje kusa dashi ba zai cije ki. Tace shine fa yayan mu wai daddy mu ya tsaya mu kalla nace ai idan kin bashi banana bazai cijeki ba sai ku zama friend daga ranan. Yariyar tace No no bazan iya bashi ba nan suka shiga mussu a tsakanin su wanan yace ni zanbashi wancan yace sai na jefa mai na gudu nabar gurin. Ganin suna ta shirmayn su na,sulale nabar su suna ta hira akan biri yau zancen ke nan daya a bakin su tun dai Fadila dana fahinci bata taba ganin biri ba afili sai yau din. Har nagama girkin dare na zuba masu sukaci muna hira sai ga maman su tabiyo su. Nan muka gaisa da ita tace ku bakuga yamma yayi bane kuka zauna haka abinku har dare. Nace yanzun nake batun turasu gida ai tace wallahi idan yamma yayi haka ban son suna fita waje don kinga gurin namu kamar daji yake mussan ma wanan gidajen da babu kowa a cikin su tsoro suke bani wallahi don wani lokaci sai makiji kamar akwai mutane cikin shi da dare tun ma wanan naku kafin maigidan ki ya dawo ciki zaki dinga jin wallahi kamar akwai mutane a cikin sa. Sai ka natsu zakaga ba kowa kawai dai imagination ne mutum ke yi aini dawowan ku ba karamin dadi naji ba wallahi. Ina Allah Allah akawo mai mata mu zama mu biyu a kusa dama don zaman kadaicin yai min yaw nace ai zama shiru baida dadi wallahi. Nace da zasu tafi fadila ko na kawo maki birinki ne kije dashi da sauri yarinyar ta boye bayan mamanta cikin jin tsoro. Uwar tace ai wanan matsoraciya ce sosai bata fa fita nan da kofa idan dare yayi sai shegen tsoron tsiya gareta ga jan magana da son hira. Nace cikin murmushi ainaga alama yau Birin nan ya tsayawa Fadila a rai ko an manta sai ta jefo zancen birin ita. Uwar tace muje nidai kadai ki soma kiyi min mafalkin shi nai maki dukan tsiya wallahi ko. Sun tafi munyi saida safe dasu na juya muka koma ciki ni da yarana na kwashe kayan abincin da sukaci na shige dashi kitchen na wanke su kafin ai magariba. Bayan na idar da sallah ina zaune kiran wayan baban Abba yashigo min dama tunanen shi nakeyi ya dade bai dawoba yau duk da wani lokaci sai magariba yake shigowa gidan. Na dauki wayan da sallama tare da gaishe shi da aiki yake tambayan yaran nace gasu yanzun Aisha take tambayan ka ai. Nan yace na bata wayan ta dauka suna ta hira da baban wanda tambayanta karatun su yakeyi. Abba dake gefe zaune bai damu ba don yasaba hankalin uban yafi karkata ga Aisha basu faye shiri da Abba din ba sosai. Nan dai suka hira yace tabashi Abban basuyi wani dadewa dashi ba yaron ya miko min wayan. Yace kin gane ne maryam ki rufe gida don yau bazan dawo ba zamu fita operation din dare don akwai wasu kaya da muka samu labarin za,a shigo dasu ta barauniyar hanya. Don haka ku kwanta abinku ina ganin ni sai dai gobe idan Allah ya kaimu ke nan lafiya. Nace to Allah ya tsare ya kare muna ku lafiya yace Amin ina Nusaiba nace gata kwance tayi barci ko tundazun da nai mata wanka yace to ashafa min kan ta ko ? Bayan mun gama wayan ne naji raina ya baci don in akwai abin da naki jini ahine mukwana cikin wanan gidan mu kadai badashi ba. Gashi yau anty ta dan kara tsoratani akan unguwar da labarin sauran gidajen da babu kowa a cikin su. Karfe tara duk yaran sunyi barci nai masu shimfida na kai su daki na dawo na kashe komai na falon na rufe kofan dakin ban kwantaba na fara yiwa yara addua saina dawo a kaina. Can banyi barci ba saidai barcin ya fara daukana a lokacin sai naji kamar gaba daya kwanon ruffing din dakin ya kware naji wani irin kara kamar an sauke wani abu mai nauyi a kwanon gidan. Mikewa nayi zaune tare da kara jawo yarans kusa dani sosai muna nan shiru banji komai ba sai kallon yaran nakeyi suna barcin su hankalin su akwance. Addua nakeyi duk wanda ya fado min arai kasancewa na diyar babban malami tun muna kanana mun san adduoi masu karfi. Can dai naji shiru har tsawon lokaci na koma na kwanta shiru barci bai dauke ni ba can naji kamar anja tsoki mai karfi na kara mikewa zaune zubur. Can naji ba komai na kwanta nace araina kila dai tsoron da naji ne da farko yasani jin hakan. Barci ya dan dauke ni zuwa wani dan lokaci kadan musalin uku na dare sai ji nayi ana ta buruntu da kayan kitchen din kamar ana wurgaza kwanon dake gidan duk. Motsin yai yawa da burun tu na mike zaune tare da fitowa falo cikin sanda gabana sai faduwa yake yi ban san may zan gani ba a falon ko kitchen din. Amma ina shiga babu komai komai yana nan yadda yake a gurin a jere nai ajiyan zuciya tare da jawo kofan na koma na kwanta. Ina nan shiru ban kara jin komai ba can naji kara kamar anbuga kofa da karfi cikin hasala. Sai karfe hudu da wani abu na daina jin motsin komai a gidan lokacin ne kuma wani barci mai nauyi ya dauke ni ban falkaba sai bakwai a razane na tashi da sauri don na makara saida na dora ma yara idomie na,shiga nai sallah saboda na makara. Ina idar da sallah da sauri na karasa addua nai masu wanka na,shirya su duk a gurguje suka tafi saura ni da Nisaiba dake barci a lokacin. Sai bayan tafiyan su ne na fara tuna abinda ya faru jiya da dare a gidan tiryan tiryan nake tuna komai a raina. Gyaran gida nayi na saka kamshi na koma kitchen na dora abincin rana sai lokacin na shiga wanka. Ina ban daki naji ihun Nusaiba da karfi kamar sani abu ya samay ta da sauri nafito zuwa dakin yarinyar dake kwance saman gado na samu ta fado kasa har bakin ta ya fashe da kain ta. Da sauri na dauke ta ina jijigata sai ihu take tsalawa tana kalon bangon dakin a firgice. Ina nan na samu tai shiru naje nai mata wanka na gyara mata jiki saida nima na shirya na goya ta a bayana. Sai dai ban kawo komai ba don azatona fadowa tayi daga gado ta samu wanan raunin haka. Tun ranan ta firgice min ba dama na ajeta ita kadai sai tata tsala ihu duk na gigice. Yaran suka dawo gida zuwa sha biyu nan na dan samu ta sake jikin ta tana wasa a cikin su. Aliyu bai dawo gida ba sai bayan karfe hudu na yamma yashigo ya sayo muna kayan abinci da sauran abubuwa har da kayan yara ya sake sayo masu. Sai da yai wanka ya fito falo ya zauna daga inda nake zaune nake ce mashi abinci fa ? Yace No maryam ki bar abincin nan sai zuwa dare idan Allah ya kaimu zanci yanzun kan iam ok gaskiya. Kallon mamaki ne mashi amma bance komai ba nan suka fara bashi labarin sun ga monkey banana jiya da zasu dawo daga school. Aisha tamike tana mashi rawan wai monkey banana tace daddy har fa da cizo yakeyi inji maman mu. Nan shima yake basu labarin irin na birai nashiru tun ina sauraren su har nai zurfi ga tunanen abinda ya faru jiya da dare. Yana magana amma banji may yake fadi ba sai da yace maryam may kike tunane haka. Nai firgigit nai ajiyan zuciya ina ce mashi ba komao yaya kamar kada na fada mashi amma sai can na nisa nace wallahi Baban Abba gidan jiya da matsala. Ya duka yana dauko Nusaiba zuwa jikin shi yace matsalan may kuma maryam? Na fada mai duk abinda naji daren jiya sai kawai naga yana ta dariya yace kai maryam to ko Laure ce tabiyo ku nan din kuma ? Tsoro maganan shi yaban don ko ance maye har bangon duniya wai yana iya zuwa da dare. Munan nai shiru nama kasa maganan komai dan tsoro shiko ko a jikin shi naga bai damu ba ko kadan. Daren ranan lafiya kalau muka kwana banji komai ba a gidan haka yasani sake jikina nabar zancen komai. A gida yai weekend a tare da mu muna cikin farin ciki da so da kainan junan mu muda yayan mu. Ranan Monday suka fara kokarin shirin fita zuwa gurin aiki masu makaranta kuma suka shirya zuwa makarantar su. Yarage kamar kullun dagani sai Nusaiba a cikin gidan tana falo tana wasan ta nikuma ina yan aiyuka na nagida. Can naji ihunta da sauri nazo falon yarinyar ta nufo ni cikin dan tsoro na dauke ta na saka a baya don ko nono taki kamawa a lokacin. Da kyat na samu tai barci sai dai hankalina yaki kwantawa da yawan razanan da Nusaiba take yawan yi yanzu. Kafin wani lokaci jikin yarinyar yai wani irin zafi radau tausayi tabani gashi ko paracetamol banda shi a gidan. Na zauna nai addua a ruwa na bata tasha na shafe mata jikinnta dashi sai ta koma barci sai dai kuma taki yarda na kwantar da ita a falon kuma . Kiran wayan shine ya sani fitowa falon na dauka muka gaisa nai mashi yaya office yace Alhamdullahi. Ina Nusaiba ko tayi barci ne ? Nace eh gata nan a baya bata jin dadi jikin tane yai mugun zafi sosao tun dazun . Yace subbahanallahi kin bata magani tasha ko nace ba magani a gidan ai yaya nadai yi mata addua kuma ga jikin nata yana dan sanyi yanzu. Yace bari na sayo magani yanzun zan bayar akawo maku kibata nace to mun gode ya kashe wayan. Nan naci gaba da wankin da nakeyi a lokacin sai wani lokaci mai dan tsawo dan sakon ya kawo maganin na bata sai dai duk a lokacin ma jikinta yayi sanyi ko. Yaran na dawowa ta dan kara gyagijewa a tare da su sai da zasu islamiya ne na saka hijjab dina na rakasu har gidan su anty don da yaran ta suke tafiya islamiyan kullun. Zan dawo gurin gida jen nan biyu naji wani irin tsam ajikina nace la,ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minal zalumin. Nan na shige gida cikin tsoro gyaran gida nayi da yaran suka bata kafin su fita don na riga da na gama girki tuwone ya rage na tuka kawai. Can dai naji har lokacin tsoron bai fita min a raina ba nadauko waya na kira lamban wayan babana muka gausa dashi. Yake tambayana muna lafiya dai ko nace mai lafiya muke ba sai dai kawai akwai yan matsala ne. Yace subbahanallahi maryam matsalan may kuma nace wallahi baba gidan da muke sabon guri ne babu mutane sosai. Kuma akwai gidaje a kusa damu wanda babu kowa a cikin shi nan dai na koro mai duk abinda ya faru bayan zuwan mu gidan. Yace umm umm maryam Allah ya sawaka yanzun dai dai kiyi hakkuri zan duba al,amarin na gani amma shi mai gidan naki kin fada mashi ko ? Nace Baba na fada mashi amma bai dauki maganan tawa da muhin manci ba yace wai na saka tsorone kawai a rayuwana shine nake wahala. Yace babu damuwa maryam.insha Allahu koma may nene zan duba na gani sai nai maki bayani akai ke dai ki rike addua a bakin ki ko yaushe nace insha Allahu baba anayi yace dakyau. Mukai sallama dashi nace ya gaida mutanen gida yace zasu ji insha Allahu. Yaran suka dawo daga islamiya nai masu sannu tare da karban kayan su na wanke na shanya kafin mu kwanta sun sha iska. Da wuri ya dawo gida don Nusaiba da bata da lafiya tana zaune suna cin abinci da yan uwanta mukai mashi sannu da dawowa ya amsa muna idon shi na akan Nusaiba dake zaune a tsakan falo ita da Aisha suna cin abinci. Yace yaya jikin nata yana dan taba wuyan ta a hankali nace taji sauki ai tun dazun jikin yai mata sanyi. Wanka yashiga yayi ya dawo falo nan yai sallah ishai a gurin yaran suks samay shi saman sallaya suka haye shi Aisha da,Nusaiba. Shiko Abba ko ajikin shi sai kallon da yakeyi baban yace yaje daki ya dauko mai wayan shi saman gado. Yaron na,shiga sai gashi da gudu yafito yana hakki da sauri muna hada baki muna tambayan shi kai maynene wai jikin shi har kyarma yakeyi yana nuna dakin baban ya daka mai tsawa yace wawan banza kawai matsoraci kana zuwa ka dauko min wayana daki saman gado. Ganin da nayi yana kuka yana dan buga kafan shi a kasa yasani mikewa nabi shi narike mai hannu muka shiga dakin tare. Nadauko mai waya sai dube dube yaron keyi yana shishige min ajiki alaman yaga wani abu. Yakawo wa iban wayan ya amsa a hasale yana fadin kaidai wawa ne wallahi Aisha tafika wayo. Ganin yadda yaron ya takura yasani cewa kabae fadin hakana kasan ko may ya gani a dakin ya tsorata. Bai bari nakai karshe ba yace ai duk kece wallahi kika tsorata yaran nan yanzu kamar Abba zai ce wai yana jin tsoron shiga daki a wanan lokacin. May kike nufine wai maryam da kike son tayar da hankalinki ga gidan ne wai idan ma wani abu kike nufi to kisani ni banda karfin kama wani gidan dayafi wanan kyau. Mamaki maganan shi yabani don ban tsammaci jinhaka daga bakin shi ni ina nafito gidan mu dai ginan kasa ne iri rihewan na da ma gimshikin kasa har sama, Gidan shi kuma da nai aure ai gina ne akaja daki biyu sai baranda da kitchen da makewayi ni ina daya umma tana a dayan dakin. To may zaisa ya fada min haka da yake ban saba mayar mai da magana ba sai cewa nayi Allah yabaka hakuri amma ni ban nufin komai da gidan na ni ina nafito da zan raina wanan gidan kuma. Daga haka nai shiru shima shirun yayi ran shi a bace yana dan amsa ma yaran magana sama sama kawai. Shi kan Abba inda nake zaune ya dawo ya zauna sai dai hankalin shi baitare da shi kallon da yakeyi ma ya daina haka barci ya dauke shi abu ga kurciya. Ashe yana shiga dakin yaga mace tsaye a tsakiyan dakin da fararen kaya tana dube dube shine yaji tsoro ya gudo sai dai na godewa Allah da baice komai ba alokacin. Tun ranan Abba yake tsoron shiga daki shi kadai koda kuwa da ranane nikuma ban tambaye shi ba don ban son ya tayar da hankalin shi idan ya tuna. Da yake yaro ne kwana biyu sai ma ya watsar da zabce ya dawo normal din shi yana wasan shi kamar farko. Har aka gama weekends aka koma aiki na koma zama ni kadai sai nusaiba kawai a gidan zuwa sha daya babana yakirani muka gaisa natambayi lafiyan shi. Can bayan mun gama gaisawa ne yake ce min maryam nace na,am baba tace ataikace dai zance maki kidage da addua akanki da diyan ki don gidan yana da dan matsala kadan amma bai mai dorewa bane. Kada ki sa tsoro komai a ranki kema ki jajirce kifitar da tsoro a zuciyar ki don kina tare da,Allah ga kuma naku iskokan na uwar ku dake tare daku. Nace da sauri baba ko shine suke damuna suna son dawo wa akaina ? Yai dan murmushi yace kai haba Maryam ai iskan Amina bamasu cutarwa bane bakin da suka shige tane daga baya suka cuta mata akan wani bukatan su can da bamu yarda dashi ba amma aike naki ma yanzu sunfi karfin na uwarku nisa ba kusa basu yarda a cuta maku ko kadan. Addua dai zaki tsanan tayi Allah ya kareku ku baki daya kuma sai kin fitar da tsoro a ran ki. Na amsa a sanyaye da to baba insha Allah zan kula zan dinga yi yace zan kara dubawa idan na samu wanda zaizo zan bayar da sako sai akawo maki. Nai godiya mukai sallama na kashe wayan na zauna ina dan tunane don na fahinci baba ya boye min wani abu a dunkule wanda ban sani ba. Naci gaba da gudanar da rayuwana kamar ko yaushe ban sake maganan ba da Aliyu kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE,,, 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 7⃣ Ina tsaye tun safe nake wanke wanke sai abincin dake saman gas na yaran da,zasu tafi makaran ta dashi. Na dauraye hannaye na nafito falo na hada kayan break fast inda na saba ajewa komawa daki nayi na samu Aisha zaune tana saka socks a kafanta. Abba yana binciken wani abu a cikin school bag din shi abinda gagani cikin school bag din nashi ne ya ba kowan mu mamaki. Dabino ne da ruwan zamzam cikin wani leda light blue dagani zaka gane cewa kamar tsaraban kayan saudiya ne. Yana jin nashigo dakin ya juyo gare ni da sauri yana fadin mama wannan fa nace maynene haka tun ban karbi ledan ba . Yaron yace a cikin school bag dina na gan shi yanzun nan ai, nakarba ina dubawa dabino ne dan kasar saudiya da dan goran ruwan zamzam karami fari. Ledan na dauka na nufi dakin mu dashi yana zaune a bakin gado yana daura takalmin su na yan kaki. Jin na shigo yadago kai ina ce mashi ina kwana baban Abba ya dan saki murmushi a fuskan shi yana cewa ai na zata yau bazaki iya moriya ba da safe ? Dan murmushi na sake nace akan may kamar jiya farau haba dai nace Baban Abba kaine ka saka wa Abba wanan abin ga school bag din shi. Ledan dake hannu na yabi da kallo yana fadin may nene wanan din a ciki nace dabino ne da ruwan zam zam kamar tsaraba ne na kayan makka fa ? Ledan ya karba yana dubawa yace ina wanan kuma yafito nace yanzu Abba din ya gani acikin jakar shi. Abba din ya kwalawa kira sai gashi ya shigo yana goye da jakkar shi uban yace ina kafito da wanan kuma yace baba ban sani ba yanzu nagan shi a cikin jakata. Yace kodai wani ne yabaka a school ka manta dashi a school bag din ka Abba. Yaron yai sauri yana cewa a,a baba ba wanda ya bani jiyama ai da dare sai dana juye duk kayan jakan ina neman sharfiner na amma banga wanan ciki ba. Uban ya murde fuskan shi yace wai ba na hanaka karban abu a hannun mutane ba ko. Yaron ya marairaice yace wallahi baba ba wanda ya bani yanzun ne dai nagan shi a ciki. Ya juyo inda nake yana fadin Abba Abba wallahi ban san irin halin yaron nan ba da shegen shiru shiru haka. Yaya zaka aje abu kace wai kuma kai ba naka bane to idan ba naka bane nawaye ? Nan yai mai fada ya fita dakin ranshi a bace ubban ya aje dabinon saman side drower dakin . Suka fita suka karya kumallo sai da suka gama ina kallon yaron har lokacin bai sake jikin shi ba . Na dauko masu abincin su nakai masu suka fita suna min bye bye sai na dakatar da yaran nakaraso har inda suke nace masu duk wanda ya baku wani abu kada kuci shi kunji suka amsa da to mama. Nan na dawo cikin gida na ci gaba da aiyu kana ga zaman kadai cin dake damuna a lokacin. Falo na kwanta da niyar ba Nusaiba nono sai barci ya fara dan daukana sai naji kaman ana diban ruwa a cikin roban dake ta baya muna tara ruwa a cikin shi. Bude idanuwa na nayi a hankali ina ganin kamar mafalki ne nake yi ba mafalki bane haka din nake ji. Yadda kasan kana sheka ruwa a bucket yana bada sauti haka nake ji na mike zaune a hankali don nusaiba tayi barci ko a lokacin. Har yanzun ina jin sautin diban ruwa a cikin roban sai na nufi hanyan bayan a hankali. Tafiya naji a tsakar dan filin dake da suminti kamar an nufi wani guri sai dai babu kowa a gurin har lokacin. A hankali nabi filin da kallo banga kowa ba kuma roban yana a rufe yadda na barshi da farko. Na sauke ajiyan zuciya na dawo falo na zauna tunanen wanan bakon al,amarin duk ya cika min zuciya na. Firgigit nayi lokacin da naji ana buga kofan shigowa falon mu gashi lokacin sha biyun rana yayi nan tsoro ya kamani ina tunanen waye kuma a wanan lokacin haka. Daukan Nusaiba dake barci nayi na saka a bayana na nufi kofan falon da ake ta bugawa. Na bude a hankali ga unguwan namu yayi tsit bakajin komai sai sautin kukan tsuntsaye da kwari kawai. Wata mace nagani tsaye a kofan tai min murmushi tace sorry na damay ki ko nice wance ke wancan gidan na gaban ki ta nuna min gidan dake can gaban mu wanda nakan ga jan mota a kofan gidan. Tace sunana maman Stephen don Allah nazo ne ko kunyi ajiyan wake ki dan bani nawa ya kare na manta na fadawa daddy mu ya sayo muna. Nace mata ayya bari na duba maki na barta nan tsaye bata shigo ba nima ban damu da nace mata tashigo din ba . Na debo mata wake mai yawa a cikin wani dan blue roba na bata tace wiiii duk wanan mai yawa haka na gode fa nagode ina son nayi cooking ne kafin yan makaran ta su dawo. Mukai sallama matar ta tafi na dawo tare da rufe falon gidan gurin girkina na nufa yau ba lesson yaran da wuri zasu dawo gida. Karfe daya suka dawo gidan gida ya kaure da surutun su sai Abba ne ke ce min dana debo masu abinci mama ni fa kin san ban cin wake fa nace wallahi Abba na manta ne amma bari na dafa ma idomie idan zakaci lokaci daya na rana na dora tukunya a wuta yaran sun dan fita da Nusaiba takofan mu suna wasa. Na fita na jika kayan uniform din da suka cire a roban da nake wanki dashi. Koda na dawo sai samu nayi an kashe gas din an sauke tukunyan saman wuta. Tsayawa nayi da mamaki ina kallo don dai ni nasan na dora ruwan dafa mai indomie din. Na fita inda suke zaune suna wasan su nace waya shiga kitchen yanzu cikin ku ? Kowa yace basu shigo cikin gida ba suna waje suna wasan su kuma basu ga kowa ya shiga ba. Na juya na nufi kitchen din ina wasi wasi a raina towa ya sauke min tukunyan har da kashe gas kuma ? Na dauko abin kuna gas din zan kuna naji ance kada ki kunna shi na fada maki kamar a hasale akai maganan. Da sauri na juya don gani ko wacece take min magana babu kowa a kitchen din tso na aje tukunyan na fito kicin din na saka hijjab dina na dauki zanin goyon Nusaiba nafita inda yaran suke na karbi yarinyan hannun Aisha dake ta janjalanbo da ita don bata inmata ma sosai nace masu ina rufe gidan kuzo muje. Gidan Anty muka nufa kamar kullun gurin gidajen nan biyu sai naji tsikan jikina yana tashi idan nazo gurin. Gidan ta yana bude yaran ta duk suna ciki sina hayaniyan su mukai sallama na shiga nida yaran. Tana dakin ta kwance taji muryan mu sai tafito falon su nan muka gaisa sai hayaniyan yaran suna fira a tsakanin wanda hiran wani film ne yaron ta sa,an Abba yana bashi labarin gilm din na yarane. Tace maman Abba gaki kamar a firgice mana nagan ki tana mai kallon fuskana ido cikin ido. Na sauke ajiyan zuciya nace wallahi anty akwai matsala gaskiya nan na fara koro mata abinda nake yawan ji a gidan namu ko yaushe. Tace inkon Allah injin baki dora tukunyan ba nace ban dora ba shine ma nafito muka zo nan. Tace lalai ba,a rasa jinnu a gidan amma kuma shi Baban Abba yaki ya fahince ki asan yadda za,a bullo wa matsalan kuma. Tace wallahi muma hakane lokacin da muka dawo sai gidan ya kama juya muna idan da rana ne sai kiga gidan ya koma wani iri idan dare ne kuma sai a juya gidan ya koma part daban daban. Nace ni yanzu hankalina ya daga gaskiya ya mayar damu gida kawai ko ya sake muna wani guri . Tace gaskiya kan da matsala amma idan anyi sulhu dasu ai kila za,aci nasara su bar gurin kinga zan yi wa baban su Yasir magana yai wa maigidan ki magana ansan abin yi. Tace balle yanzu fa rana tsaka ne ance lokaci suke al,amuran su idan ka taba su a wanan lokacin suna iya cutata maka. Tace bari taba Abba din abinci yaci kada ya zauna da yunwa a cikin shi tace kindai yi arziki da baki kara dora tunkuyan ba da Allah yasan abinda zai faru da hakan. Nan muka zauna har wani lokaci sai da rana yai sanyi da la,asar muka nufi gida na shirya yaran zuwa islamiya suka fice. Hakana muka zauna yau dadi gobe madaci ina jin abubuwa barkatai a gidan. Gashi baban Abba yai min fada sosai wai ina son in tayar mashi da hankali da nasan ban son zuwa na zauna lafiya may yasa na matsa mai cewa zanzo inda yake shiga ba nan yake fita ba nidai nai shiru ina mamakin halin shi. Tun ranan ban kara mai magana ba kuma ba,a daina muna saddabaru ba a gidan. Yau watan mu daya cur a gidan muna zaman mu dai hakana na maneji da rayuwa irin tayau. Yace shi zasu fita operation zai kwana daya ko biyu a can komai da zamu bukata ya aje muna a gida kafin ya wuce nai mashi Allah ya tsare ya tafi yabar motar shi a gida. Lafiya muka wuni da yara ba komai har dare hankalin mu a kwance muna kallon super story da akeyi a N T A . Nan Aisha da Nusaiba su kai barci Abba da ni dake yan zirga zirgana ne kawai ke ido biyu shima dai nan barci ya dauke shi sai naga muyi kwanciyan mu a falon ma kawai mana. Can na gama ina shirin kwantawa akan shimfidan da nayi sai ji nayi ance to ni Ummi ina zan kwanta ga wanan ya kwanta min a guri. Dubawa nayi babu kowa a gidan sai naji ance zulkafalah kasan halin bani adam da son kai irin nasu sun tare muna ciki yanzun kuma nan din da muke kwanci kuma sunzo sun tare muna. Cikin karfin halin da ban san zan iya ba nace ai baikai na son kai ba bari na kwashe su na baku gurin ku a zauna lafiya. Muryan karamin yaro naji yana cewa dadai yafi sauki wallahi don ba yarda zanyi ba yau. Kallon yaran dake barcin su nayi na rasa daga cikin su waye zan fara dauka zuwa,daki don gudun kar na barsu wani abu ya samay su. Don haka na tayar da su gaba daya a lokaci daya na tasa su gaba muka shige daki cikin karfin hali na kara fitowa falon na kashe wuta tare da daukan abinda zan dauka nabar gurin. Nai alwala nan nafara sallah ina neman tsari tare da bude kur,ani na har safe ba wani motsin dana sake ji. Ban tashi jin tsoro ba sai da,asuba naji tsikan jikina yana tashi hankalina yai matukar tashi lokaci guda. Har barci ya dan dauke ni dole na falka ne masu abin karyawa dana zuwa school da safe. Ke nan ana nufi da wasu muke zaune a gidan ko may haka ke nufi bafa barci nayi ba balle ince mafalki ne nayi. Idona biyu duk wanan abin ya faru kenan fa gaskiyane wanan al,amarin yafaru really. Ga barci ina ji amma kuma tsoron kwanciya nakeyi hakana na zaune sai karatu nake fa Nusaiba da yanzu idan mu biyu ne a gida bata yarda na barta ita kadai ko kadan kamar wace ke ganin abin firgita a idon ta. Wa ma zan fadawa wanan zancen ince ga abinda naji Anty ce kawai tasan halin da nake ciki a gidan. Hayaniyan mutane naji daga waje shiya sani fitowa daga cikin gida na leka naga wasu ne sukazi zasu shiga dayan gidan dake a tsakanina da na su anty haka yasa naji dadi sosai a raina koba komai zan dan samu sauki a raina. Fatana dai Allah yasa musulmai ne nafi son makwabtaka da musulma yar uwata ba irin su maman Stephen ba da ko yau she kida ke tashi daga gidan su. Ina tuna haka dabara ya fado min a raina nace kawai na tsiri kai tashan da ake kira,a na dinga sake shi a gidan always tunda aljannu basu son karatun kur,ani. Ina shiga ciki kuwa na lalubu tashan da ake kira,a alkur,ani maigirma ko yaushe. Ina aikina ina bin karatun a hankali nima haka ya shagaltar dani na kara mantawa da damuwan da nake ciki. Abin mamaki na daina bin karatun amma sai nake ji kamar wata murya mai zaki ba,a cikin tv ba ana bin karatun a hankali. Saurarawa nayi haka din ne kuwa nace ya salam nashiga uku kuwa a gidan nan ashe har karatun ma bin shi akeyi . Sai naji anyi shiru muryan da naji har yafi nawa da na mai karatun dadin ji sosai. Ban kashe ba na barshi har rana yara suka dawo suna murna suna fada min sunga ana saka kaya a dayan gidan nan da babu kowa a cikin shi. Na ce masu ai nima nagani muna ciki naji ana nocking din kofa ina daga ciki nake cewa Abba duba waye a kofa. Yana bude kofan yaron da,ake kira Jonh ne a tsaye kofan dan maman Stephen da,roban da na ba uwar shi a hannun shi. Yace ga roba inji mummy mu wai na kawo maki nace ma yaron ya shigo har ya saka kafan shi kamar zai shigo sautin kira,an da yaji yana tashi ne yasa shi saurin ja baya yace No bazan shiga ba ya juya da sauri ya,wuce yabar gurin. Kallon mamaki nakewa yaron ban san may yakewa wanan wiki wikin ba da ido gashi har zai shigo ya juya da sauri yabar gidan. Nikan ban kawo komai ba,a,rai na nashare zancen yaron naci gaba da tsabgan gabana. Sai dare mun kwantane nai mafalki da yaron wai yana warning dina idan ya kara jin na saka kira,a a gidana sai ya kashe ni ya nuna min sani zundumaymay wuka a hannun shi. gani nayi wani abu ya daga yaron sama ya rade shi ga bango yaron yana wani gurjin ihu. Aiko a cikin barci na ke jin ihu har a fili daga gidan maman Stephen gashi dare ne tsoro ya kamani na zaci ko barayi ne suka shigo muna quarter din. Shirmay na sai motan baban Abba dake tsaye kofan mu na tuna nace shike nan sun sace dan motan ke nan mun huta. Ban yi barci ba ban kuma daina jin hayaniya ba a makwabtan mu abu ga yare sai ihun kuka da kiran juses takeyi. Can naji kara mota aka fita daga unguwar ashe sune suka fita da motan daga uguwan zuwa asibiti da yaron. Sai da safe tunda safe bakuwar makwabciyar mu da anty suke buga min gida na bude a gigice suke ce min ni jiya ana ihun neman taimako ban fito ba ? Nai saurin kai idona ga motan mu tananan tsaye inda take suke fada min wai John dan maman Stephen ne ba lafiya ankwanta smdashi lafiya lafiya cikin barci akaji yayi ihu sai ganin kan shi da, wuyan shi kamar ya kare jini yana fitowa sai da aka kaishi asibiti. Take mafalkin da nayi da yaron ya fado min a rai a zuciyata nace sabon matsala ke nan. To may kuma wanan al,amarin yake nufi kuma sai dai naja bakina na tsuke ban fadawa kowa mafalkin da nayi dashi ba. Don yanzun magana wuya gare shi ko banza suna iya fara zarga min wani camfi a kaina banji ba ban gani ba. Tun safe aka dauke wuta a layin namu don haka zafi ya ishi mutane muka fito daga waje mu sha iska. Dan zaman da kowa zafi ya ishe shi daga ciki ne yafito da yara ta,wajen gida a nashan iska hankalin kowa ya dauke. Sabuwar makwabciyata mutumiyar sokoto ne mijin ta dan sanda ne suma dai aikine yakawo su yaran ta biyar ta dara mu yara ke nan. Nan muka zauna muna hira da yaran ta da suka kwaso zuwa gurin mu suna wasa da sauran yara. Mikewa nayi in shiga daga ciki in duba girkin mu dana dora a wuta na samu an kashe gas din again. Naja na tsaya ina mamaki nace da karfi gaskiya ni wanan abin da ake min fa, ya fara isata wallahi mutum da gidan shi kuma a hana shi shakat wanan ai cin zalin ne in ma wani abune afito fili a fadawa mutum mana ya daina amma haka kawai don cin amana a saka mutum a gaba. Ga mamaki na sai kawai naga gas din ya tashi yana aiki na tsaya ina kallo da mamaki. Na juya zan koma naji ance min ku bamu gidan mu mana in baku san haka ? Nima yanzu na iya nace inba tsoro ba maishi yafito fili mana nagan shi nima amma haka kawai za,a hanaka shakat may mukai maku ne wai salaman salaman muke da kowa. Saida dare ina barci gashi ba wuta ga zafi nai mafalkin wata mata tsaye a kaina tana fadin kiyi hakkuri kin san halin yaran nan baji sukeyi ba yanzu. Tana fadin haka tajuya lokacin na bude idanuwana sai ko naga gilmawa kamar mutum daga dakin da fararen kaya. Zubur na tashi zaune har falo nake da yar toci na na haska ko ina babu komai a gidan na dawo daki sallah na tayar ina kai kukana ga Allah cikin damuwa da,wanan bakon al,amarin da ya samay ni a rayuwana kuma. Gashi mubar gida da fitinan mayi mun shigo bariki kuma ga fitinan da yafi na mayu ya taso min wanan rayuwa da may yai kama rana zafi innuwa kuma kuna. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 8⃣ Washegari da da safe haka na fito jikina kamar an dadake ni yai min mugun nauyi sosai. Da yake weekend ne ban tayar da yaran ba na barsu suyi dan barcin weekend su huta. Duk suna can cikin bed room suna barcin su ni ce kawai a falke ina zaune ina dan tasbihi duk da idanuwa na,nauyin barci ne sosai ke cina. Can kamar a mafalki naji shara daga back yard din mu da farko danaji sai na dauka daga gidan waccan sabuwar makwabciyar mu ne sautin sharan ke fitowa sai nai shiru ina,saurare sai ji bayi lalai lalai a cikin gidan ne kawai ake sharan nan. Nace oh Allah ni maryamu ni kuma nawa kaddaran ke nan gogaiya da aljannu ko may ? Ban daina jin abinda nake ji ba har lokacin ana ta faman motsi a gidan jefi jefi. Sai tsawon wani lokaci na mike na fito daga bedroom har lokacin yaran barcin su sukeyi hankalin su a kwance ba abinda ya damu yaro nace a,raina da ace shekarun su yakai su san halin da muke ciki a gidan nasan ko runtsawa bazasu yi ba balle barci hakan ga. Ina shiga kitchen komai yanan yadda na barshi ba,a taba min ba nace a raina Allah ka kare mu da kariysn ka ya Allah. Na kunna gas tare da dora ruwan zafi don yau ba tea nake da muradin musha ba a gidan so nake mucen kalar abin karyawan mu. Irish na debo na fara herewa a hankali daga inda nake a tsaye ne naji kamar gilmawan mutum a bayana. Nai matukar razana na juya da sauri banga komai ba a gurin sauke ajiyan zuciya nayi bakina tunkan nafito daki dauke yake da ayyatul kursiyu har zuwa wanan lokacin da nake aikina. Faten dankalin nai muna da ganyen alaiyahu yaji attarudu da albasa sai kamshi yake yi. Na kusa gamawa ne Aisha ta fara tashi wanda nasan yunwane ya falkar da ita bakin kitchen din ta iso na dan juya na ganta nace a,a Indo an tashi tace eh mama. Nace oya maza jekiyi alwala kizo kiyi sallah hankali ya dauke ga aikin da nakeyi ashe ba bathroom ta shiga ba can ta nufi backyard din da nake aiyukana ta dauki buta tafara alwala sai kuma ta hau wasa irin na yara ita kadai nake gani amma tana ta zuba surutu kamar wacce take wasa da wani yaro dan uwan ta a fili. Sai da na fito na shiga daki bayan na gama kwashe abinci ne na dora ruwan wanka sai dai bata dakin a lokacin shima Abba ya falka nace a,a ina kuma Indo ta shiga ne wai na bude bandaki bata ciki. Nafito falo sai lokacin naga kofan back yard a bude can na nufa ina kiran ta amma ta shagala da wasa ita kadai. Ina lekawa tana magana ita kadai har da dariyan ta tana nuna wani abu kamar mai dariya da wani. Na dan dade tsaye ina kallon ta bata san ma ina yi ba har tana nuna yatsa tana dariya tana fadin la bagashi can ba gashi gashi gashi hannuta daya a cikin bakin ta dayan ta rike buta dashi sai surutu take tana dariya irin na yara. Tsawa na daka mata sai ta zabura nace ke Aisha wani shirmay ne kikeyi ke kaidai haka a gurin nan tun dazu mazaki bar gurin nan. Sai naji tace mama wallahi nafi yaron nan iya alwala kallon mamaki ne mata nace yaro wani yaro kuma? Sai naga ta kalli inda bango yake tai shiru tana dariya nace maza ki bar gurin nan har na juya zan dawo falo sai naji ta sa dariya tana cewa bagashi ba hakka ake wanke fuska tana kallon sai saitin katanga inda bango yake na kara daka mata tsawa sai da ta kadu nace oyya taso mu shige daga ciki. Ina mai bin ko ina da kallo amma babu komai a gurin na tasa ta gaba sai na dauka shirmay ne kawai na yara take min . Tun wanan lokaci take zare jiki gurin ya zama mata gurin wasan yaran nan zata taita gwalanci irin nata na yara sai na kwalla mata kira ko in bubugi kanta tashigo daga ciki gurin yan uwan ta. Anjima kadan kuma bai hana ta mike ta sace jiki ta koma gurin wasa wasa ta hada kayan wasa irin na yara can zata zauna tai ta faman surutu ita kadai tana jera kaya tana yan dariya. Abin ya fara kaimin ko ina wallahi haka yasa na tura su gida Anty nace suje suyi wasa da yaran ta a can. Baban su bai dawo ba sai da yai kwana uku ya dawo muna falo zaune muna hira yai nocking na bude kofa tsaye yake cikin kayan kakin shi. Na dan saki murmushi nace sannu da,dawowa yace yawa barka da gida yaran najin muryan shi sukayo kanshi suna mashi oyoyo. Harda Nusaiba da bata iya magana ba tana koyon tafiya a lokacin ta nufishi ya cabe ta. Nan ya zauna falo dasu suka shiga shirmay su ya na gurin na kawo mai abinci ya ci sai gashi yau Aisha may matukar son daddy ta gashi ya dawo amma bata tsaya ta kan shi ba tana can ta sulale ta koma back yard gurin wasan ta. Sai da Baban ya shiga wanka ne na farga ai bata falon nace ina Aisha Abba yace umhumm. Namike a hasale Nusaiba na a hannu na tana shan nono na nuf bayan na samay ta kace kacekace ta baza kayan wasa irin na yara tana ta faman suraitai ita kadai. Rankwashi nakai mata tare da shuri da kayan na,watsar dasu ban san cewa hakan babban kuskurena bane kafan da nai amfani dashi ne naji yakoma min kamar turumi ban iya daga shi sai kuka takeyi tana waigen gurin dakyat nake iya daga kafana na tasa ta gaba muka shigo falo tana tsala inhu hankalin ta yana kan kayan wasan ta dana watsar can gurin kwata inda ruwa kebi. Zan shiga falo ne naji Nusaiba dake hannuna ta tsala wani irin ihu daga hannu na kan ta ya koma baya kamar anja mata suman kan ta. Nace subbahanallahi na kama yarinyar ina dube dube babu komai sai ihu take yi a razane. Jin kukan su yai yawa baban da ya fito wanka yana daure da towel yafito falon yana cewa kai kai wai yaya hakane may nene wai haka please. Nace bugunta nayi bata da gurin wasa yanzu sai backyard din can ta mayar dashi kamar dakin ta wallahi. Shine na watsar da kayan wai shine takewa kuka yace toke maryam inbanda abinki ana hana yaro wasa ne ? Nace haba duk fadin falon nan bai isheta ba sai ta tafi baya inda babu kowa in wani abu ya samay ta fa acan? Wani kallo ya,watso min yace may zai samay ta kuma acan din ke ti shiru kinji princess kyale mummy yau bakin halinta ya tashi ne ga Nusaiba ita kuma sai faman ihu takeyi a hannu na. Ya juya gurinta bayan Aisha ta zauna a saman kujera tai dan shiru amma idon ta yana kofan back yard din yace ita kuma wanan may takewa kuka hakane wai ? Nace ban sani ba ban san may ya firgitata ba gani nayi kawai ta tsala ihu haka kawai yace tsoron dukan da kikai wa Aisha ne mana yasa ta kuka ya juya yashige ciki. Da kyat na samu tai shiru ta kama nono sai dai kuma a take naji jikinta yai zafi radau ga kafata dake ta min zogi kamar bargona zai tsage daga ciki wani irin azaban ciwo ke damuna a lokacin. Yafito ya zauna falon remote ya dauka yana canza chanel ya kawar da inda nakai na kira,an Abba da dama tashan ya ishe shi ba dama ya canza don na hana ya sauke ajiyan zuciya. Nace Baban Abba jikin Nusaiba fa yai mugun zafi sosai ya ce may kuma ya samay ta ba yanzun take wasan ta ba nace kila kukan da tayi ne ya saka mata zafin jiki. Dan tsuki yaja yataso daga inda yake yazo inda muke zaune yakai hannun shi saman wuyan yarinyan. Wani irin mugun zafi yaji jikin nata yayi yace wai wai ashe sosai ne haka zafin. Tana da sauran magani ne ki bata nace wallahi wanda ka sawo muna ranan na nemi ledan gaba daya na rasa inda yake. Tsuki yaja yace bari na fita na samo mata magani yace yaran suzo ya fita dasu Abba yace yana kallon tom and jerry ba zai tafi ba. Suka fice shi da Aisha din jin kafana ya matsa min nace ya sheka ya fadawa Baban shi a sayo min maganin ciwon kafa ko na jiki. Na shimfide yarinyar na kama massage din kafan nawa da hannu ina bisimillah in tofa in kai daga sama zuwa kasan kafa in yarfar magani ne sosai na ciwar wata haka Baban mu yake muna a gida idan bamu da lafiya. Sai ko Allah da ikon shi naji kafan ya tsagaita min kamar an zare min allura a jiki naji. Na gyarawa yarinyar kwanciyar ta namike don kafan nawa ya lafa zuwa wanke kayan uniform din shi daya dawo dashi yanzu ya cire. Abin mamaki wai kayan wasan da na,watsar naga an kwashe daga gurin kwata an mayar inda suke da farko. Na dade tsaye ina kallo na jjuya falo cikin mamaki nace Abba yanzun Aisha duk dukan dane mata kan backyard din nan sai da takoma gurin ashe ? Yadan juyo duk da hankalin shi naga tv yace yana kada yatsan shi no no mama Aisha bata tafi can ba tun dazun tana ana zaune tare da ni. Da mamaki na juya zan nufi gurin kayan wasa sai naji kamar murya cikin hasala ance kada ki soma ki taba masu kayan wasan su shine fa arzikin yaro kada ki watsar da arzikin yarki. Cak naja na tsaya ina dan waige waige babu kowa a gurin gashi sha biyu saura a lokacin. A,uzu bikalamatil lahi tamatt min sheri minhalak. La ilaha illah antta subbahanaka inni kuntu minal zalimin. Kamar ance min humm naji na juya ban taba kayan bs don warning din da akai min. Cikin karfin hali ban bar gurin ba na wanke kayan na shanya duk zuciyata cike da tsoro tab. Sun dawo sayen maganin na bata maganin tasha sai kuma amai ya biyo baya haka na wuni da ita ba lafiya Aisha kuma ta sulace ga uwar rana amma ta koma gurin wasan ta ta hada zufa tai sharkaf amma bai sa ta fita daga gurin ba. Ganin na ba Nusaiba magani jikin bai sake ba nai shara dauko dan karamin cup nai addua aciki na bata tashs na shafe ta dashi. ****** ********* ****** Da yamma sai ga Anty sun shigo da sabuwar makwabciyar mu suka gaisa da baban Abba dake falo kwance nan suke ce min sun biyo min ne muje mu gaida yaron nan john da aka dawo dashi asibiti. Na fada mashi yace sai mun dawo nan nabar Nusaiba tare dashi da take barci. Mun shiga mun samu yaron kwance saman dogon kujera sai dai yana ganin mu yai zubur ya mike kamar yai mamakin shigowan mu kowa na gaida shi yana amsawa amma ni ina gaidashi sai ya mike yabar falon. Mafalkin da nayi dashi ne ya fado min a rai nace wata sabuwa kuma may haka yake nufi kuma ? Muna nan zaune maman su tana muna hiran abinda ya samay shi ne take cewa. Tana barci taji ya kwalla ihu tana bude ido taga yaron kamar an shake shi a bango wuya ya kare idanuwan shi sun firfito waje tace kai bari naga tashin hankali. Exactly yadda nagani a mafalki haka ta zaiyana muna ya faru da yaron duk sai nasha jinin jikina na kama bakina nai gum ban fadawa kowa komai. Mun dawo nashiga gida su kuma suka suce nasu gidajen suna magana akan zancen unguwar. Wasa wasa jikin Nusaiba yaki dadi haka muka kwana da ita ba dadi washe gari tunda safe muka kaita asibiti ganin likita. Sai gashi an bamu gado wai bata da jini a jikin ta haka na dole na zauna asibitin shi ya koma gida ya dauko muna abin bukata tare da nemo jinin da za,a kara mata. A gidan Anty ya bar yaran yace don Allah su zauna gurin ta ya rufe gida ya dawo asibiti gurin mu. Nan muka wuni dashi sai yamma akasa mata jinin shi da aka diba aka kara mata sai da,dare sosai ya dawo gida ganin jikin yarinyar yai dan sauki. Yana falo zaune ya hada tea yana sha yaran suna gidan Anty can zasu kwana gurin ta. Motsi yaji kamar an bude kofa ya dan tsaya ya saurara can yaji kamar kofan ban daki ne aka buga a lokacin. Mikewa yayi ya duba babu kowa a gurin saiya dawo ya zauna can yaji motsi ana diban ruwa a roban ruwan mu dake baya kamar yadda ranan naji. Gaban shine ya fadi ya mike ya nufi gurin a hankali sai baiga kowa ba ya rufo kofan ya dawo ya kwanta saman dogon kujera. Yana ci gaba da kallon film din da akeyi a tv sai yaji alaman wanka akeyi sosai yake jin ana wanka ana watsa ruwa kashe tv yayi yana saurare tabbas mostin ana wanka yake ji ya nufi ban dakin yaga gurin a rube kamar yadda ya jawo shi a baya. Ya dawo ya kwanta saman dogon kujera bai dade ba barci ya dauke shi a gurin . Can cikin barci yaga wata mace fara da,suma har kasa yana jan kasa yatsunta zara zara dasu tana tsaye a kan shi ga yaran ta duk cikin fararaen kaya sun kai kusan su goma tana tsaye saman kanshi sun zagaye shi tace. Bawan Allah katashi ka bamu guri kun tare muna guri kwanciya kun hana mu shakat damu da gidan mu kunzo kun damay mu matar ta duko kamar zatai mai kiss yai zubur ya falka tare da dan ihu. Ya juya ko ina babu kowa a falon sai shi kadai take ya hada wani uban zufa lokaci daya tsam ya mike tare da daukan gilon shi da yazo dashi ya shige daki ya rufe. Jikin shi sai kaduwa yakeyi yace may haka ke nufi ne wai kenan maganan maryam gaskiya ne koko itama dai mafalki takeyi take ganin haka ? Haka dai ya kwana gidan a,wahalce sai gabanin asuba ya samu yai barci sai motsi yakeji a cikin gidan. Yana tashi da safe ya shirya sai ga anty Hauwa ta turo akawo mai breakfast tace namu da zaikai muna ta hada idan ya tashi wucewa yazo ya dauke su zasu su duba mu suma ita da makwabciyar mu. Yagama yai wanka ya shirya ya biya ya dauko su sukazo asibitin tare dasu. Sun samu Nusaiba tana barci ya dade a kanta tsaye yana kallonta yai muna sallama yace zai tafi ya leko office sai ya dawo. Yace ko ya tsaya ya mayar dasu gida ne suka ce a,a zasu dan tsaya sai two zasu koma gida don yara na makaranta kuma yau akwai lesson basu dawowa da wuri sai four. Nan muka zauna dasu sai hira suke zuba min kan maman Stephen da yaran ta bakuwar mu akwai surutu take cewa ita fa yaron tsoro yake bata idan ta kalleshi takanji tsikan jikin ta na tashi mata. Mukai mata dariya nace kai wanan dan yaron Anty kawai dai don suna arnane kike ganin haka kila. Tace ita uwar ma wallahi kanta wani kala take kallon ta aini da muka,shiga bakiga na matsu mu taso ba. Sai muka saka mata dariya gaba dayan mu yadda ta zage tana aibanta matar mutane nasan halin yan sokoto da kyamar marasa sallah tun farko don su ko agaban su zasu ke arniya ta fa ko shi kafira ta bata sallah ai. Sai zuwa wani lokaci sukace su zasu koma nace wa Anty Hauwa don Allah ta kula da Aisha nan nake fada mata abinda nake ciki da ita a gidan. Makwabciyar mu yar sokoto yadda muke kiranta tace ke ke mutu wallah inji baki taba kayan ba nace ai danaji haka ban taba ba. Tace ai duk yadda yaro yatara kayan wasan shi kibar shi sunan wallahi don ance yadda yaro ka tara kayan wasa haka yake tara arzkikin shi. Idan kuma uwa ta zubar ta zubarwa dan ta da arzikine na nace oho shiya tace kada ki zubar da arzikin yar ki ashe? Yar sokoto tace ni walleh kun ma bani tsoro wallahi Anty Hauwa tace to ai gidan ku da kuke ciki kafin ku koma wani lokaci cikin dare sai kiji kamar a,kunna wuta har kida ake sakawa wallahi. Tace lokacin da muka dawo ba mutane da yawa gidan nan naku yana da ban tsoro sosai. Tace yadda naji ance ai unguwar wai tsohuwar makabarta ce aka murje shi bayan yai shekara arbain akai quarters din gurin. Yar sokoto tace aiko wallahi yau kun kashe ni wallahi kila ban kwana gidan nan muka sa dariya nace ina zaki kwana tace ai gara na dawo saman titi na kwanta da naga sanan mugun abin. Nace ai addu,a takobin mumuni ne nidai nasan insha,Allahu ina masune a gidan mu to musulmaine don naji suna karatun kur,ani. Tace na rabaki wallah inda wa yan nan na suka ganin mu bamu ganin su kinga ana zaman arziki a haka. Dariya muka kara saka mata yadda take hausanta tsakani da Allah ita bata ga abin dariya ba aciki. Mukai sallama suka tafi suka barni lokacin jikin Nusaiba ya kara tashi sosai tana ta kuka na rasa inda zan saka kaina gashi ni kadai ne a asibitin garin motane ban san kowa ba kuma ban ma iya ko kai kaina gida a lokacin don ban san ko ina ba. Muna cikin haka sai ga Baban Abba ya shigo tin daga nesa yake kallon yadda nake fama da yarinyar ya iso yana cewa yaya ne may yafaru ne wai kuma? Nake fada mai tana barci shine kuma ta tashi haka yanzun tana fitina yace bari yaga nurse yai masu complain. Sai gashi ya dawo da nurse ta dan dubata tace ai lokacin aluran ta ma yayi abata magani sai ai mata allura dayani. Haka yasa ta dan samu ta koma barcin ta ta daina fita yana gurin mu har dare yace zai koma gida nai mashi sai da safe ya tafi. Zance yau abinda yaji gidan yafi na jiya don yana kwance falo barci ya dan dauke shi tv yana aiki aka danne shi ya kasa koda motsawa sai da yaita addua yasamu aka sake shi ya mike ya hada zufa sharkaf dashi. A zuciyar shi yace yanzun kan na tabbatar da maganan maryam tana fadi ina ganin laifinta ashe da gaskiyan ta dole ne yasan abinyi tun wuri tun ba,a samu matsala ba. Cikin dare ma bamuyi barci da dadi da Nusaiba ba washe gari da yazo yaje gun likita sai ga likitan yashigo round nan ya dubata yace ikon Allah. Ai dole tayi kuka ba jini a jikin ta kamar ma ba,a kara mata ba da farko hankalin mu ya tashi yace sai an nemo wani jinin dole. Nan uban yafita zuwa neman inda zai samo jini gamu a garin mutane na kira babana na fada mai yace nai ta addua Allah zai kawo mata sauki. Na kira Umma ita ma na fada mata hankalin ta ya,tashi tace maryam kin ga abinda nake fada maki ko? Yanzu da anan kuke ai za,a samu jinin kara mata ba sai an wahala,ba wanan wani irin ciwo ne ace ana karawa mutum jini yana zukewa. Tai min Allah yakawo sauki muka kashe wayan muna nan zaune sai gashi da abokan aikin shi mutum uku za,a auna jinin su a gani ko zaiyi wa yarinyar akara mata. Munyi sa,a ansamu jinin wanda yai mata aka diba aka kara mata zuwa karfe uku mukai ma mutanen godiya suka tafi. Nan ya zauna damu yace ranan a gurin mu zai kwana tare da mu nan ya kwana asibiti da biyu ga tsoron gida ga jikin yarinyar dake wahala sosai. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE,,, 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 9⃣ An sallamo mu daga Asibitin likita yace bayan sati daya mu dawo akara dubata a gani yadda ta kara ji. Makwabta suna ta shigowa gaishe mu da dawowa har da wanda bamu hurda dasu. Halin rayuwan barki ke nan sai ku zama yan uwa a tsakanin ku da kuke a shiya daya. Yanzun tun dawowa na na ga Baban Abba sai yawan ce min yakeyi kifa rika yiwa yaran nan addua idan zaku kwanta. Na kance mai ai ina masu addua yaran da yasa mu raba daki dasu yanzu naga ta koma cewa na dinga masu shimfida a kasa su kwanta daki daya damu. Ni dai ban tambaya ba na dauka dai duk wani abune yasa yake hakan. Kwanan mu hudu da dawowa gidan ranan cikin dare gidan arna kun nan kusa da mu wani sabon al,amari ya faru kuma. Muna barci da dare ihun su ya tayar da mu nace kai a fili amma kafirci baiyi ba wallahi wanan ai daukan alhakine. Nakai kallona ga agogo karfe sha biyu da rabi na dare nace ikon Allah yau kuma komay ya faru haka dasu. Can dai na dinga jin hayaniyan yai yawa nafito falo don duk yara sunyi barci a lokaci ga maigidan bai gida sun tafi operation wani baki ruwa can wani gari. Window din falon mu na dan daga naga mutanen quarters din sai zuwa gidan zukeyi daya bayan daya duk da dare ya farayi sosai a lokacin. Can na hango yar sokoto da anty ta window shine ya sani fitowa daga gidan nima amma ban isa kusa ba na tsaya daga kofan mu ina kallo. Wai ashe matar gidan ce duk kwanakin nasai wasu kyankyaso guda biyu sun cije ta idan tana barci sai taita ciwo ba gaira ba dalili. Shine ranan ta kwanta da abu a kusa da ita batai barci ba kyankyason na fitowa Allah ya bata sa,a takai masu bugu suka fara shure shure. A can dakin da yaranta suke a kwance taji ihu tana zuwa tasamu yaran kamar yadda kyankyason data buge suma suna shure shure a dakin shine ta saka ihu. Ganin na fito yasa Anty da yar sokoto suka dawo inda nake tsaye muka tsaya a tare dasu don mazajen su suna cikin gidan a lokacin. Muna gurin aka dauko pastor din su na kiristan yazo gurin nan ya shiga irin saddabarun su take yaron nan John ya fara bayani kamar haka. Yana cewa shi da kaunan shi yan cult ne sune suke zukewa uwar su jini duk dare saboda an saka suyi hakane daga kungiyar su. Yace yar uwar shi Stephener ta daure baban su shiyasa kullun baida lafiya. Pastor din yace a ina suka samu wanan abin yace a school ne abokin shi ya bashi sweet yasha shine ya ga kanshi a cikin group din. Ita kuma kauna shi anty din class din su ce ta saka ta a group din cult ta basu biscuits shi ta shigar dasu. Duk wanda ke gurin sai da hankalin shi ya tashi a lokacin nan yaron ya shiga bada labarin abubuwan sherin da sukeyi wa mutane yace harda accident din da makwabci su na farko yayi ya mutu sune suka kashe shi. Kwanaki ma ciwon da yayi yaje ne ya kashe sabuwar makwabciyarsu da take saka wakan musulmai a gidan ta wanda abin yana matukar damun su . Shine ya samu ashe tana da sprint masu karfi a tare da ita agidan har suka kusa kashe shi. Yace yaso ne ya kashe matar har yaran ta don tunda suka shigo quaters din nan yake jin haushin su don yaran ta sunfi su sa,a. Pastor yace saboda may kake son kashe su basuyi maka komai ba yace ban son sune yaranta suna da baiwa da yawa wanda shi baida irin shi. Pastor ya tambaye shi yaya sukewa baban su yace sun daure shi ne sosai don yaso ya gane su shine suka mayar dashi hakana. Hankalin mutane yai matukar tashi sosai dajin yadda karamin yaro da baikai ko goma sha ba yake irin wanan ketan har da mahaifan shi. Mata don Allah mu saka ido akan yaran mu mu hana su cin abin hannun wanda ba jinin su ba,ako ina. Yaron yace wa pastor din ai idan suna son suyi cuta sukan zama babban mutum ne su dinga rabawa yara sadaka gurin amsan sadakane suke jayewa yaro destiny din shi gaba daya. Basu kadai ba har da,wasu witches suna hakanan yaron yace. Da kyat da addua aka samu hankalin yaran ya dan dawo gare su aka kwashe su zuwa church su da daren nan don yin irin abin su can. Nan mijin anty da suka fito suka samay mu suke bamu labari nace mun shiga uku may mukai wa yaran nan haka kawai su tsane mu har suna batun kashe mu. Labari ya kai ko ina dasafe zancen ne ko ina akeyi wanan abin mamakin da Baban su Abba ya dawo ne mijin anty yake bashi labari hankalin shi yai matukar tashi sosai da garin ma gaba daya. Yace wai maryam kodai don mun zo ba dason ran Umma bane muke ganin wanan jerabawan haka wai ? Nace nima nayi wanan tunanen a baya shiyasa ake cewa duk abin da yaron ka zai yi inda ba wanda ya sabawa addini bane kabishi da adduan fatan alheri kawai. Nace da yardan Allah ubangiji ba zai bari wani abu ya cuta muna ba na,sheri Allah yana tare da mu insha Allahu. Mun kai wani lokaci muna maganan wanan irin rayuwa yai ma yaran fada sosai tare da tsorata su akan duk wanda ya basu abu kada su karba kada ma suyi hurda da mai shi kawai. Duk suka tsorace kowa na fadin ni dai ba zanci bama zan karba ba gaba daya. Washe gari zamu koma kai Nusai ba ganin likita don haka na tashi da,wuri na kammala komai da zanyi muka wuce asibitin. ****** ********* ****** Muna zuwa muka samu mutane sosai a layin nan yake ce min idan ya tsaya zai makara zuwa gurin aiki . Don haka na karbi kudi idan mungama na dauki drop zuwa quarters din mu zan iya ko nace zan iya tunda drop zan dauka akaini har gida. Bai dade da,wucewa ba Nusaiba ta falka ta fara min fitina duk ta rudani saboda kukan da takeyi. Haka yasa na dan fito daga waje ina lalashin ta na dauko ruwa na bata akwai wata mata da muke zaune kusa da juna ta dan fito daga waje itama take ce min ta falkane nace mata eh wallahi gashi sai kuka take min tundazun na rasa gane may ke damun ta. Matar tace nakawo ta tagani na mika mata ita duk da nasan halin yarinyar da kiuya ba yarda zatayi ba da ita. Amma abin mamaki sai ta tafi gurin matar harda lafewa a jikin ta tana,sauke ajiyan zuciya a hankali. Matar ta dago kai tana murmushi tace yaro ke nan da ace zaku kaita wurin maganin gargajiya da zaifi kila ta samu lafiya. Don gaskiya ciwon ta bana asibiti bane wahala kawai kuke yi anan din amma gaskiya sai gargajiya matsalanta. Nace cikin murmushi ni ban san kowa ba a garin nan don mu bakine mijina ne kawai na sani shima ba kowa ne yasani ba don bai ma da lokacin zama. Tace da zakiyarda dani dana taimaka maki nakai ki wani guri insha Allahu za,a dace da yarandan ubangiji amma sai idan kinyarda da Allah kin yarda dani. Abin da da mahaifi gashi naga yadda take wahala ba sauki kullun ace ba jini a jikin ta. Yasa nace ai ba matsala tunda kince Allah gurin baida nisa sosai ko tace nan ne kusa sai muyi sauri muje kafin layi yazo kan mu mun dawo insha Allahu. Nai mata godiya muka fita tare zuwa bakin titi a daidai wani dan kiciron naga ta tsaya saiga wani taxi yazo ta tsayar dashi tare da fada mai sunan gurin da zamu tafi din. Muna shiga take ce min idan zaki watarana a daidai nan gurin zaki tsaya anan zaki samu taxi din da zai kai ki gurin. Tafiya mukayi bamai dan nisa ba sai ga mu a,wani dan kauye can bayan gari. Tace a sauke mu a wani guri muka sauka mukaidan tafiya gurine kamar kauye. Munzo dai dai wani gida ne take ce min bari don Allah mu shiga gidan nan na,gaidasu. Gida ne irin na kauye ga itace ankewaye a darnin gidan dake da zana ga icen zogala dana,aduruku duk ya kewaye gidan gwanin ban sha,awa dashi cikin gidan katon icen cediyane ya baje yai innuwa gwanin ban sha,awa. Matan gidan su uku ne daya tana daka a wani irin turmi da ban taba ganin irin shi ba sai a gidan. Daya tana sharan tsakar gida dayan tana wanki tufafi a duke jin sallaman mu ne suka daga suna cewa ,a,a maraba da mutanen saudiya ashe kun dawo garin. Muka zauna dayan ta karaso tana cewa Mukaddarasiyatu yaushe kuka dawo ina su baba tace duk suna lafiya nima na dawo ne na gyara gida kafin su iso garin. Sai faman kallona sukeyi na gaidasu suke tambayana yaya gida au bakuwa kika samu ne mukaddarasiya tace eh makwabciyata ce wallahi yar tace bata da lafiya muka zo ganin baba. Sukace malam malam yana nan yanzun ma nasan yana can da yaran suna karatu don basu taso ba tukun. Dayar matar ta debo muna ruwa a tulu ta kawo muna sai abokiyar tafiyana take cewa ita a koshe take nikan na karba nasha kada suga bamu sha ba dukkan mu. Ruwa ne da zance ban taba shan irin shi ba don dadi kamar ba,a randar kasa aka deboshi ba ga gardi ga sanyi kalau. Nasha sosai nai masu godiya tare da,aje kwanon dayan tace a tana da kirki matar dole ki taimaka mata gaskiya. Nan mukai sallama da matan muka fita suna bina da kallon mamaki wanda ni ban sani ba. Tafiya muke da kafa sai faman gaida matar ake a cikin mutunci haka yasa na gane matar tana da daraja a garin kodon ance a saudiya take zaune ne yasa haka oho. Wani dan lungu muka shiga wanda tun daga nesa muke jin sautin karatun yara yana tashi. Makaranta na hango irin na allo din nan yarane bila,adadin baka ko ganin iyakar su nai mamaki yadda dan wanan kauye haka aka,samu irin yaran nan haka da yawa gurin nan. Wani tsoho ne na hango tsakiyan su fari da fararen kaya yana zaune a saman wani kujeran katako wanda tun muna yara nasan irin wanan kujeran a garin mu yanzu babu irin shi ma nake gani. Kujeran katako ne na da wanda tsakiya ansa mai atamfa sai ana iya nade kujeran idan an daga sama ganin yana bada karatu tace mu shiga daga cikin gidan. Mun shiga da sallama mata su biyu a ciki kamillaun mata dasu masu daraja kamar ba,a kauye suke zaune ba in ka gan su. Mun gaisa dasu cikin mutunci suke mata sannu da,dawowa tare da,tambayan ta sauran mutanen gida. Sai faman kallo na sukeyi da mamaki can dayan tace ina kika fito bani adama mukaddarasiya ? Tace cikin murmush makwabciyatace yar ta bata da lafiya shine mukazo gurin baba ya ganta. Dayar ta mike can sai gata da,ruwa a kwano ta kawo muna matar da muke tare ta karbi ruwan tasha ta miko min duk da na koshi amma na karba na kafa kai na zuka sosai. Zan iya cewa ban taba shan ruwa mai dadi irin wanan ba a,rayuwana sai yau gardi dadi da,sanyi naji. Na aje kwanon cikin jin dadi nace nagode haba bako ai rahamane ga kowa ke bakuwar muce ai. Suka ce kaman wa yancan na farkon gidan da muka,shiga a,a ba laifi tana da mutunci gaskiya dole ki taimaka mata. Sai ga wani yaro yashigo cikin gidan yace wai ance bakin su shiga malam yana jiran su a waje. Muka mike muka shiga ina malam din yake tsohone sosai mai farin gemu yana zaune ya hakimce cikin kamala ta malaimai. Wani irin sanyi naji a furin kamar an,sa A C masu yawa gurin sai dai babu komai a gurin . Muka gaisa dashi ya kura min ido cikin murmushi yake cewa ikon Alkah yau zurian Amina ne a gida na. Nai matukar mamaki yadda yasan mahaifiyana haka kai tsaye yake cewa Mukaddarasiya ashe kin dawo yaya su wajen iyayen naki tace duk suna lafiya. Yace yauma kinyo barnan naki ko ban san mayasa kin san kina da tausayi ba kuma ke taba diyan Bil,adama haka ? Tai dan murmushi tare da dukan da kanta kasa tace wallahi malam akasi aka samu banice na taba taba su ba wallahi. Kasan yaran nan basa ji aikin Zalkafllahi ne shiyayi wanan aiki duk da nai masu fada amma sai da ya yaba mata yara. Yace ai ku din da ace kun san ko yar waye ita din da baku taba taba wallahi nijin sherck Mustafullah ne fa ita. Da sauri matar ta kalle ni tace haba naga alama tana da kafuwa sosai itama. Yace muga yarinyar ko na mika mashi ita cikin ladabi ya karbeta yana mata wasan jika da kaka yana yi yana shafan bayan yarinyar da jikin ta zuwa kafan ta,a hankali yana yarfawa gefe can ya dago ta yana shafan kanta shima kamar yana mata wankin kai yace don Allah ki bar ta mutanen nan makkaddarasiya idan kika kara kawo min wani kin mai illa dake da mai shi bazan kara ko kallon ku ba na fada maki. Nan dai bamu bar gurin ba sai ga Nusaiba harda rarafen ta tana,wasan ta hankali a kwance abinta mukai mai sallama na tambaya nawa zan bada tsohon yai murmushi yace kai haba aike yar muce jikan mu Allah dai ya tsare gaba kinji yakawo wasu ganyyaiyaki kuli yabani yabani wani abu kamar mai yace na shafawa duk yarana muyi amfani dashi. Mukai mai sallama yace idan wanan ganyen yafita baki na dawo na kara amsa mata don sau biyu za,ayi matar sai faman godiya take wa tsohon. Bamu jima ba sai ga mota a hanya muka shiga kamar kiftawa da bisimillah sai gamu a bakin asibitin. Layi ya kusa kawowa a kan mu da layi yazo na,shiga likita yace wonderful mai kuka bata haka gashi komai nata ya dawo normal da farko fa na katsewa yarinyar nan taku ne ban dauka ma zata kai wanan lokacin bata mutu ba,wallahi a yadda naga ta koma. Nafito ina neman matar nan muyi sallama kuma in mata godiya sai dai matar bata nan babu dalilin ta na tambayi matan dake wajen ko sun san inda ta tafi sukace su basu ga wata mata ba gaskiya bayan ni. Nai tsuki na ce shirmay ku dai kuna ta kanku amma na shigo da mata yanzu muke nan fa da ita na shiga na barta zata shiga idan nafito. Basu tanka min ba na fita ina bakin cikin rashin kara yi mata godiyan da banyi ba gashi naso na bata labarin abinda likita yace min. Nafita daga asibitin ina maijin dadi nace watau dai na,Allah basu karewa a duniya ke nan. Ina zuwa gida na dora tukuyan magani kamar yadda tsohon nan ya fada min nai mata wanka na bata tasha na shafe ta da maganin daya,bamu. Haka ma sauran yaran suma nai masu wanka na shafe su da maganin da aka bamu. Da baban Abba ya dawo na labarta mashi haduwana da matar da inda muka je yace kai amma maryam ban taba sanin baki da,wayo ba sai yau. Kin kuwa san inane kaduna kuwa kaduna fa ba Auna bane don sai a batar dake da yarki har abada kuwa. Nace nikan wallahi tunda naji tace tsakani da Allah zata taimakeni shiyasa har na yarda sai dai ban fada mai komai da ya faru ba acan da mukaje. Tun lokacin Nusaiba taji sauki sosai sai wasan ta takeyi niko tun ruwan da nasha a kauyen duk nasha ruwa sai naji kamar ruwan toka nake sha babu dadi kamar wancan dana sha a kauyen mai dadi. Yanzun kuma banjin komai a gidan ban kuma jin tsoro ko darr a raina na sake abina ina sha,anina. Shima baban Abba har yana batun canza gida amma yadda yaga na sake yasa ya dan kwantar da hankalin shi. Gashi yaga yadda muka saba da su anty da yar sokoto mun koma kamar yan gari guda muke dasu. Wanan yawan motsin da,nake ji a dare ban fasa jin shi ba kuma ban damu ba don ban fitowa koda naji sai dai kawai na dake abina. Maganin dai da malam tsoho ya bamu da,ban san sunan shi ba balle sunan kauyen ban fasa yi ba ina kanyi nida yara har da,baban yaran na hada mai a,man shafin shi bai sani ba yana,shafawa. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BAMU KADAI BANE A,, 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 🔟 Izuwa yanzu Nusaiba ta samu lafiya sosai a lokaci don idan ka ganta bazakace tayi irin wanan ciwon ba a baya yadda ta mulle tai kiba abinta sosai da ita. Komai na fitar a raina ban tsoron komai yanzun saina Allah da Annabinshi kawai. Nafitar da zancen wani abin tsoro a gidan cikin raina gaba daya yanzun haka. Abinda ke damu na shine rashin sanin wacece matar da ta taimaka min zuwa kauyen nan ? Ban san ta ba ban kuma da nomban wayan ta balle muyi communication da matar a waya. Haka bai hana ni ci gaba da shirin abin da zan kaiwa mutanen arzikin nan ba da nasha ruwa a gidan su a kauyen sa ta kaini. Don idan na masu alheri har matar ta samu labari tankar itace naiwa alheri din a hannunta. Don haka ina ganin saura kwana biyu mu koma kamar yadda malam baba ya umurce ni na,dawo da yarinyar bayan sati biyu inda yake ya kara duba lafiyan ta. Ganin ta samu sauki bai sa na kasa a gwiwa ba gurin komawa kauyen don in kaita akara dubata. Haka yasa na zabo omo clean maya har guda hudu sai sunki sabulun wanka parked hudu na duba cikin kayana na na zabo turaren Oud mai kyau da kamshin gaske sosai na jefa duk kayan ga wani handbag dina babba wanda zan fita dashi da safe idan Allah ya kaimu. Washegari tun da safe na tashi na fara aiyukan gida don na gama da,wuri na fita ko zan dace na samu matar nan da ta,taimaka min ranan. Baban Abba yana karyawa yake ce min ba zai samu saukeni asibiti ba don haka na shirya natafi ni kadai don ta dan makara zasu fita zuwa operation cikin daji ta barauniyar hanyar da,ake smogal ciki. Ban ji haushi ba yau sai ma dadin da naji kawai don zan samu yadda nakw so idan na fita ni kadai din. Na gama tare da rufe gida na nufo aaibiti can a bakin get na hango inda ake sayar da goro. Masu kyau mayan farare kursa kursa na zaba na dubu daya aka daure min a leda . Maimako na tsaya inda tace min sai na dan tsaya wani dan guri nisa kadan shiru babu alaman motar kauyen gurin. A hankali na gyara goyon Nusaiba na taka zuwa daidai inda muka tsaya,da ita a ranan. Sai ko ga mota na gani irin na ranan na tsayar dasu tare da fadin suna kauyen da zani . Mun dan taba tafiya muka kawo garin mutanen cikin motar sai kallon mamaki suke min amma ni ban damu da yanayin kallon da,suke min ba. Ina sauka na biya kudi na gyarawa Nusaiba goyo muka fara tafiya don ban manta da hanyan da muka bi a ranan da abokiyar tafiyana. Wanan gidan yan uwan nata da muka fara isa sukai mana taron arziki shi na shiga da sallama gaba daya suka sako idanuwan su suna mamakin sake gani na agidan su da,sukayi. Nagaishe su daya bayan daya tare da masu yaya bayan robon mu ranan sukace Alhamdullahi. Suma suka tambaye ni yaya jiki tare da kokarin karban Nusaiba da na sauke bayan na zauna saman kujera. Nasan bazata yarda ba don kiuyar tsiya gareta bata yarda da kowa in ba niba. Matar da tafisu fara,a a cikin su wace taso karban Nusaiba tace yau ina Mukaddarasiyya ? Nace ai tun ranan bamu kara haduwa da ita ba yanzun haka ina son ganin ta amma ban san inda zan samay taba kuma. Cikin fara,a da yar dariya matar tace aiko bazaki sake ganin ta ba sai Allah inda Mukkaddarasiyya ce. Nafito da dan tsaraban da na kawo masu ina fadin kuyi hakkuri da,wanan don Allah baida yawa aiwa yara wanki biscuits da sweet arabawa yaran shi. Sunji matukar dadi da abinda na kawo masu suna min godiya idona yana akan kayan da suke aiki dashi wanda ya banbanta matuka da irin wanda muke amfani dashi dana sani. Bayan na dan huta namike tare da goya Nusaiba ina cewa zan tafi naga malam babba ya duba yarinyar . Har kofa suka rakoni suna min godiya tare da min fatan alheri ina cewa ai insha Allahu idan na sake dawowa zan kara shigowa mu gaisa da su. Ina tafe yan garin suna bina da kallo cikin mamaki har nakai makarantar malam baba inda na samu yara ba iyaka masu daukan karatu a gurin shi. Cikin gida na shiga ban tsaya waje ba nai sallama matan shi a zaune na samay su suna hira. Suna ganina suka shedani ,a,a maraba da bakuwar mukkaddarasiya yau kece a gidan namu haka ? Suka bani abin zama muka gaisa dasu suna tambayana yaya jikin Nusaiba nace jiki Alhamdullahi. Nafito masu da abinda nazo masu dashi na basu sunyi mamaki matuka da wanan alherin da nazo masu dashi. Wani dan lokaci muna fira jefi jefi dasu akan al,amarin mijin su da irin baiwan da Allah ya bashi na sanin magani kala kala. Wani yaro kyakyawa fari ya shigo yace malam yace bakuwa tashigo a tare muka shiga da yan matar malam din dauke da tsaraban da na kawo masu zata nuna mai. Mun gaisa matar da mashi yaya bayan rabo ya amsa da Alhamdullahi yana tambaya yaya jikin Nusaiba din nace gata malam tun rana da na fara magani har yau bata kara kwanci ba. Matar ta nuna mai abinda nazo masu dashi yace ikon Allah yar gidan Amina tanan kuma kika fito min lalai halin ki na alheri ne dole mukkaddarasiya taji tsoro akanki. Yace wa matar da fatan kun yi godiya ko tace malam mungode ai don bamu san akwai masu halin mutunci haka ba a zaton mu? Tana fita na ciro goro da turaren da nazo mai dashi nace baba ga wanan ba yawa ayi hakkuri dashi. Ya kura wa abinda nakawo mai ido yace may yasa kika wahal da kanki haka akaina ? Na dukar da kai cikin murmushi da ladabi nace baba albarkan ka nake nema yasa nai hakan. Yace tona gode ubangiji Allah ya albarkaci rayuwan ki duniya da lahira yace miko min hannun ki nan na mika mai ba tare da ya rike hannun ba ya runtse idanuwan shi kamar yana min addua na dan tsawon lokaci can yace masha Allah, Allah ya kara tsare muna ku bakiya daya yafadi tare da mikwa Nusaiba hannu sai kawai naga yarinyar ta nufe shi. Da fara,a a fuskan ta ya dauke ta yana mata wasa tare da bin jikinta tana shafa mata magani. Yace min ba dai aljan ko mutum ba Fatima akan diyan ki tsakanin ki da su sai alheri ba dai sheri ba kan . In har dai kinyi masu abin da na baki a baya ki masu insha Allah ba abinda zai faru daku da yardan Allah. Yabani wasu yan abubuwa yace naje dasu gida tare da fada min yadda zanyi dasu nai mashi godiya har zan daga yake ce min banji kin min tambaya irin na bani adam ba ? Na koma na zauna ina murmushi nace baba sai idan ka fahintar dani don sani a gare ku yake Baba. Yace Fatima ke bakya sana,a ne irin ta neman kudi? Nace cikin kunya baba bana komai yace baki ra,ayine ko may nace ina da ra,ayi sai dai ban san yaya zanyi ba ya miko min wani dan kullin gari yace karbi wanan. Hannu bibiyu na mika na karba yace tun anan gabana ki diba ki shaka shi sai ki dan tauna kadan sauran ki murza a hannuwan ki har zuwa habar hannun ki. Yadda yace haka nayi yace to shafe fuskan ki da hannayen ki nayi yadda yace min yace ubangiji ya albarkace ki. Nace amin baba tace ke kadaice a gurin mijin ki zan baki wanan amma bazan fada maki amfanin shi amma zaki gane daga baya. Namike ina cewa baba na gode zan tafi sai na kara dawowa yace yana da,wuya ki dawo ki samay ni kuma amma duk sanda kike da wani bukata akaina zaki iya kiyastawa a ranki kamar kingani a gaban ki da yardan ubangiji zanji bukatan ki fatima. Ke abin tausayawace a gare mu don kina da kima da mutunci ga duk wani malami indai yakai malami a jinsin mu. Mahaifiyar ki ta wahala sosai agurin bakaken jinsin mu amma bata yarda ta kauce ba kamar yadda suka bukaci da tayi masu biyya akan ta kauce su taimaka mata. Karfin addinin ta yasa ta ki kauce wa bukatan su ta kommace ta mutu da ta kauce masu haka sukai ta,wahal da ita har Allah ya karbi ran ta ta tafi kowa ya huta. Sauran bayani watarana zan maki yadda zaki fahinci may ya faru da ita. Jikina yai matukar sanyi jin yadda mamana ta wahala a hannun wasu muggan mutane don bukatan su a kan ta. Nai sallama da malam na shiga gidan shi nai sallama da matan shi sukaita min godiya na barsu na tafi. Nai mamaki danagan ni a bakin asibiti sai ban damu ba na tare taxi aka dauke ni drop sai quarters din mu na dawo a gajiye dani . Tunda na dawo ban fadawa kowa ga abinda mukayi da Baba malam ba na bar zance kawai a raina. ****** ********* ****** Ina zaune yara sun fita zuwa islamiya don sunyi hutun boko a yanzu Anty Hauwa ce tashigo gidan mu muna zaune muna hira,da,wayan ta a hannu tana dan kallon abubuwa a cikin wayan. Can take ce min kai maman Abba zoki ga wasu bedshet haddadu masu kyau ina dubawa sukai matukar shan jinin jikina naga may zai hana nima na fara sana,an irin su tunda kayan mata ne kuma abin amfani. Nace gaskiya da zan samu kudi zan gwada sanan su insha Allahu kila na dace a kansu sanan ya karbu. To amma kuma kudi fa kudi sune matsalana yanzu ina zan samu kudin yin wanan sana,an nawa. Har mukai sallama da ita sai tunane nake a ina zan samu kudin da zanyi wanan sana,an da nake son yi yanzu ga zancen ya matukar tsaya min a raina. Sai zancen mu da malam Baba ya fado min a rai na son nayi sana,a nima na tsaya a kafana. Nasan halin baban Abba a gurin kudi idan bashi yai ra ayin bani kudi don kan shi kudi bai banbaruwa a hannun shi ko kadan. Kyautan shi dani dubu daya ne dubu biyu baima taba bani dubu biyar ba a rayuwan mu cur. Haka dai na yanke shawaran cewa zan daure na tambaye shi na fada mai manufana nason fara sana,a a gidan. Bayan ya dawo daga gurin aiki muna zaune yana hira da yara ina yan aiyukana a gidan. Sai da na gama komai na samay su a falon ina cikin atamfan wax da akai min dan dogon riga mai sharf dashi. Na zauna tare da fadin wai ya dan kallo ni yana cewa may kikayi da kike wash haka nace tunfa safe nake tsaye a gidan nan yanzun ko nagama ai dole na dan huta ko ? Murmushi yayi yace kinji dadin ki ke wallahi kina zaune gida baki baki baki fari amma har kina fadin wai ke kingaji a haka. NNace yauwa Baban Abba dama ina son fada ma wallahi sana,a nake son na fara na zannuwan gado sai na sara anan na,turawa anty Lami dashi can gida. Yace kina da kudi ke nan ashe nace ina naga kudi kai dai nake so don Allah ka ara min please. Take ya daure fuskan shi yace banda kudin da za,a salwanta Maryam kada ma ki soma wanan zancen don bazan bayar ba. Nasan tunda ya fadi haka har cikin zuciyar shi yake maganan nan kuma ya hau fada yana ta masifa inda yake shiga ba nan yake fita ba. Shiru nayi ina sauraren shi har tsawon wani lokaci naja bakina nai shiru kawai. Sakawa nake ina warwarewa ina zan samu kudi koda nace a sayar da kayan dakina nasan ba,wasu kudi sosai zasuyi ba kayan. Bayan kamar kwana biyu ina gyaran daki naga kudi a dakin yan dubu dubu masu yawa nai mamaki yadda yabar kudi hakanan bai fada min ba na boye. Sai da ta dawo da yamma nake cewa yaya akayi kabar kudi a fili haka baka fada min a boye ma ba duk da dai babu maishigowa gidan amma kuma komai yana son siri aiko ? Yace cikin mamaki kudi wasu kudi kuma maryam gaskiya ni ban bar kudi ba anan gidan. Na mike na shiga daki na kwaso kudin nace gasu fa wanan nake magana saman mirror na samay su fa. Ba kudina bane na bashi amsa da fadar haka. Yace maryam na fada maki ba kudina bane wallahi ki ajesu kila zaki tuna wanda ya baki ki boye mai. Nace ni wa zai ban kudi boyo kuma gidan nan bayan kai ka kuma ce wai banaka bane to na waye ? Kamar yadda yace din boye kudin nayi guri mai kyau ko zai zo ya tuna daga baya in bashi abin shi. Har yara sai da na tsure su na tambaye su suka rantse min ba nasu bane su basu ma san komai ba akai. Tsoro ya kama ni nace kodai sun fara irin harkan su John ne ban sani ba haka nakan raba dare ina,adduoin tsari akan yaran gaba dayan su ko zanga wani alama amma babu sign din komai a kansu. Bayan kamar wata daya na kara fito mai da zancen kudin yace shifa ba kudin shi bane bai san may su ba. Amma na barsu zai karba idan ba,a san ko na waye ba nace mai naji kawai. Ina zaune inda nai sallah magariba sai faman tunane nakeyi ba wanda ya fado min a rai naje na tambaya kan zancen kudin sai Baba malam kawai don haka na yanke shawara zan tafi gurin shi na tambaya akan kudin. Cikin dare muna barci ne sai ga Baba malam nagani a mafalki na ya shigo falon mu a cikin fararen kayan shi cikin kamala. Na rasa inda zan shi na kawo mai ruwa yace min ya gode a koshe yake yana rike da,sanda a hannun shi irin na manyan mutane. Yarana yake bi da kallo daya bayan daya yana murmushi yace maryama kin tara zuria masu albarka anan Allah ya tsare maki su. Nai mashi godiya yake cewa maryama kince kina son yin sana,a zanin gado shine na baki jari kiyi kuma gashi naga har yanzu baki fara ba wanan kudin da kike tambayan ko na,waye bana kowa bane nakine. Nine na baki su saboda Allah don ki fara sana,a dasu na bude baki zanyi magana sai naji an bude kofa ba kowa nagani ba sai wanan matar da ta kaini gurin shi da farko namike da fara,a cikin jin dadin ganin ta zan tare ta sai ta wuce ni zuwa gurin shi da fara,a tana cewa la Baba yau kaine a gidan namu da kanka. Yanunani da yar yatsa yace ga wace ta kawoni gidan nan nazo ne ba dadewa zanyi dama bayani ne nazo nai mata don na turo a kawo mata sako amma bata fahinci ko daga ina sakon yake ba. Ta juyo gare ni tace wanan abokiyar zamanane baba tana yawan takura min sai dai halinta yana da kyau don tasan hakkin makwabtaka. Tsohon ya mike yana cewa dake da ita duk jikokina ne don haka ku sulhunta kanku kafin ta baci maku yakai kofa ban samu cewa komai ta juyo yana min murmushi ya fice daga gidan. Najuya inda take a tsugune don in mata magana naga wayau bata gurin kuma ba alamanta ma agidan lokacin. Nan suka barni ina mamaki yau malam babane har a gida na da kanshi to ya gwada msi gidana ? Matar nan mai mutunci ne tafadi min a raina nace tace makwabciyata ce ita amma a ina . Zubur na falka daga barcin da nayi ama sai kamshi nakeji irin na turaren malam da nakanji idan naje gurin shi. Zufane ta fara karyo min ta ko ina sai yau ne karo na farko danaji tsoron abinda ke faruwa dani ya kamani. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU[10/27, 10:55 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE A,,,,, 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧 1⃣1⃣ Sosai mafalkin da nayi da malam baba da kamshin shi da nake ji ya tsaya min a zuciyana. Gashi kamar an daure min bakina don na kasa fadawa kowa irin halin da nake ciki har shi mai gidan nawa ma ban fada mai ba. Wani sabon yanayi da Baban Abba ya canza min yanzu yazo min da wani sabon sallo wanda ke nuna min rashin damuwar shi da mu. Daga ni har yaran yanzu bai damu da damuwar mu ba hatta Aisha da,suke dasawa dashi ba ruwan da ita sam ya daina yawan damuwa da al,amarin mu kamar baya. Da farko na dauka ko wani laifi ne nai mashi amma iya tunane na ni banga abinda nai mashi ba gaskiya. Ko da yadawo ne yaran sukaje gun su yanzu zaice kada ku damay ni please ku barni na huta don Allah. Tun abin yana damuna har nakai ga mashi magana ranan da ya dawo muna taron shi ya fada saman kujera a gajiye dashi. Aisha tazo kamar yadda ta saba idan ya dawo tana ta faman bashi labari makaranta. Wani tsawa ya daka mata yace for god sake Aisha ki barni na huta haka don Allah ba dama mutum ya dawo ya huta ku ishe shi da surutun tsiya kawai. Take wani yaro ya kama kanshi da shi suka fita batun shi yarinyar bata barshi ba sai jefi jefi yake bata amsa. Yafita yaje sallah ya dawo abinci kawai yaci ya koma daga cikin daki yana waya a cikin fara,a da nishadi. A haka na shigo dakin na samay shi yana wayan shi cikin nishadi kamar bashi ba na gani a falon a daure yan mintinan da suka wuce. Ni dai na dauki abinda zan dauka na koma falon gurin yarana mukaci gaba da abinda mukeyi dasu. Haka muka kwana ko kallon gurin da nake baiyi ba har takai tsawon sati muna cikin wanan halin na rashi kula da mu da bai yi kamar farko Idan yadawo kaga fara,an shi sai idan yana waya wanda da farko ma idan ya dawo gida kusan kashe wayan shi yakeyi. Amma yanzu ko wani lokaci zaka ganshi da waya makale yanayi yana dariya cikin shauki . Da naga abin yai yawa rana bayan yara sunyi barci nake cewa Baban Abba wai halan dai mun maka wani laifi ne ? Nace idan ma laifi mukai maka don Allah dai kayi hakkuri da mu kaine uwar mu kaine uban mu a garin nan bamu san kowa sai Allah sai kai. Zanci gaba yace for god sake maryam ki kyale ni please ban son yawan damuwan nan naki please ? Kallon mamaki nai mashi nace to Allah ya kyauta ni dai har nai barci yana kan wayanshi wanda na fahinci da mace ce yake wayan a lokacin. Ganin haka yasa na fita batun shi na kawo ido na,saka mai kawai duk da abin yana yawan damu na to amma yaya zanyi. Kwaliya, girki, gyaran gida ladabi da biyayya babu wanda ban mashi amma ya dauko min wanan halin daga sama. Ranan da zaman hakan ya ishe ni na,shirya naje gurin Anty hauwa na samay ta akan zancen sana,an da nake son yi na bedshet. Nan tai ta,duba min ta yi seaching din shagon da ake sayar da kayan muka,aje ranan da zamu tafi shagon da ita. Wanan kudin dai sune na dauko muka tafi muka sara kaya zanuwan gado da su takalma masu kyau sosai na hado har da kayan yara. ****** ********* ****** Yarinyar da yake waya,da ita ashe wata budurwan shi ce tun zuwan shi garin a unguwar da yafara zama kafin ya kwaso mu suke tare. Kuma har yai mata alkawarin cewa zai aureta da yardan Allah sai bayan ya zo da mune ya canza unguwa abin nasu yai sanyi sosai. Yanzun kuma ta nemo shi suka sake dinkewa da ita ba dare ba rana yana gurin ta ko suna makale a waya matan KD ke nan. Yau kudi take so a gurin shi wai tana da buki don haka rake son ya bata kudi don yasaba sake mata kudi ana karya. Gashi kwana biyu basu tafi operation ba yara ina ne zai samo kudi ya bata sai wanan kudin da maryam tai mai magana ya fado mashi a rai kawai don haka yana dawowa da dare yake cewa. Bayan yaga kaya birjit a saman kujeran falo na zube su a gurin yake cewa maryam dauko min wanan kudin da kika nuna min a kwanaki. Gabana ne ya fadi sai dai na dake a fili nace wasu kudi fa ke nan ? Yace cikin daure fuska kudin da nace ki aje a gurin ki har nai nazari a kan su mana. Nace kudin kan maisu ta karbi abin ta yau din nan yace kudin waye nace kudi anty hauwa ce mana. Kallona yake a cikin mamaki sai lokacin hankalin shi ya kai ga tarin kayan dake falon yace wanan kayan waye haka kuma ? Nakara cewa nata ne tasaro tabani nima nayi sana,a dasu zan tura gida ne akaiwa anty Lami. Kamar zaiyi magana sai yai shiru na lura ya shiga tashin hankali a lokacin can wayan shi tai kara ya dauka. Ya manta yasa handfree babu ko sallama take cewa yaya kabarni ina jiran kudin tun dazu ga kowa yasayo anko ni ban saye ba dubu hamsim ne fa kawai nace ka bani fa ? Kunya yaji amma sai ya basar ya mayar da,wayan silent yana cewa ki saurare ni mana Nadiya banace zan baki ba. Sai lokacin na gane abinda yake nufi da kudin dana kasosu yau a kasuwa. Duk da raina ya baci ban mashi magana ba na dake kawai kamar banji may yake a,waya ba. Sai da ya kashe wayan kunyane ya kamashi yace Aisha yau ba labarin makaranta ne. Yarinyar da dama zaman shiru ya ishe su a lokacin ta shiga bashi labarin game din da sukayi tazo na biyu gurin gudu. Kamar ban san sunayi ba na fita batun shi nan yake ta faman kamay kamay da yaran yanayi yana kallon fuskana. Ranan duk cikin kamay kamay da yakeyi fa,wayan shi yarinyar tana ta faman kira amma daga karshe sai ya kashe wayan kawai. Bayan yaran sunyi barci ne shi da kanshi ya kwashe su yakai daki ya kwantar dasu. Nagama komai nashige abina na kwanta tunda yanzun haka ya saba muna dashi. Can na fara barci naji shi a gefe na yana lalube na a hankali na bude idanuwa na nake cewa yau kuma ban yi laifin bane? Murmushi kawai naji yayi yana kokarin jawo ni jikin shi kawai duk yadda yaso haka na kyale shi har yayi abinda zaiyi ya kyale ni. Da safe na gama komai da zai fita yake cewa wai na shirya idan ya dawo zamu fita zuwa cikin gari gaba daya da yaran. Tun fitan su ranan ban yi komai ba sai faman tunane nakeyi akan maganan matar da naji jiya a wayan shi. Ana nufin cewa mace baban Abba yake nufin zai ba kudi har dubu hamsim gani ni matar shi ko goma bai taba bani ba a rayuwana. Na sani ba zan hana shi aure ba idan ya tashi kuma bazan mashi magana komai ba a yanzu balle ya dauka ina kishi ne akai. Yanzun badon Allah ya taimake ni ba yaya zanyi idan ta karbe kudin nan ni banci ba sai dai yaba wata yar iska can a waje ta cinye su a banza kawai. Kai maza Allah dai ya kyauta kawai ina zaku kai alhakin matan ku ne wai da wanan irin cin amanan haka ? Jifa yadda yazo min a daure wai na kawo kudin nan da tace na aje a baya kamar kudin shi ne fa ? Haka na gaji na mike na fara parking din kayan a wani katon jakar ghana most go don na daure su guri daya yadda za,aji dadin tafiya min dasu wani abu bai samay su ba a hanya. A karshe dai na yanke shawaran na koma gurin Baba malam nakai mai ziyar don na gaida su. Baima dawo gidan ba yadda yace sai yamma ya shigo gidan kuma a gajiye babu batun fita ke nan. Ina zaune na kurawa tv indo wanda a zahiri ba kallon nakeyi ba don ko antambaye ni may akeyi bazan iya fadi ba a lokacin. Yafito cikin shigar kananan kaya sai faman kamshi turare ke tashi a jikin shi. Yana daura agogo a hannun shi yake cewa ni zan fita sai na dawo nai mamaki yadda yau zai fita da dare haka abinda bai saba yi ba. Sai da yakai kofa yake cewa wai may ye babu shi a gidan na amfanin safe ya sayo ? Nace ban duba ba ban san ko mayye babu ba don ban saba fadin babu ba ya kalle ni kamar zaiyi magana sai kuma ya kyale yafita kawai. Bai dawo ba har munyi barci sai can cikin dare naji tana ta faman nocking da kyata na tashi na bude maigidan ya shigo. Ban tsaya tambayan shi abinci ba na juya nashige abina na kwanta shima yana gama shirin shi ya kwanta sai safe. Washe gari kamar yadda na saba idan na dora wa yara breakfast na dawo nai sallah na zauna na dan yi azkar haka ma da magariba nakan yi hakan. Yau ma ina gamawa na mike tare da ninke abin sallah na nufi kitchen na samu shimkafan da na,dora har ya tsane ko na mayar da miya saman wuta na dumama masu shi da kyau. Yafito a cikin shirin shi lokacin ina gyaran falo nan ya zauna yana breakfast sai da ya kusa gamawa nake cewa yau ina son zani unguwa nazaci zaice wani abu amma sai cewa yayi a dawo lafiya kawai. Bayan na gama shirina ne na kulle gidan na fita zuwa gidan baba malam da nai niya don na fada mai halin da muke ciki da baban Abba din yanzu saboda ya zama min kamar uba a guri na yanzu. Sai dai may har na karaci tsayi gurin dana saba tsayi babu motar garin ba,alaman shi zafin rana ya isheni haka najuyo na,dawo gida ban samu zuwa ba inda nai niyar zuwa din. Zaman da nayi a cikin rana yasa min kasala bayan munci abinci da Nusaiba na kwanta don na bata nono sai barci ya kwashe ni a gurin. Can a cikin barci nane nai mafalki gani zaune da matan makam harda tsaraban da na dauka nakai masu gashi wai ina basu suna min godiya. Na tafi gurin malam muka gaisa kamar yadda muka saba idan naje yake ce min kin manta cewa na fada maki cewa idan zakizo gurina ki kiyasta a ranki zaki ganni gashi kunje kun shawo rana dake da yar ki a banza haka. Maryama baki gudun yarki ta kamu da wani cuta na daban kuma bayan Allah ya bata lafiya yanzu. Yace yarona ne yagan ki kina jiran mota ya shigo gari dazun shine yake fada min yaganki kuma yasan nan gurina zaki zo. Nace Baba kayi hakkuri na manta ne dama sai ya tare ni yace dama zaki kawo min karan mijin ki ne ko? Yace mazan ku haka suke don haka kiyi hakkuri koda kince zaki tayar da hankalin ki a halin yanzu yai nisa baya jin kira da sannu zai gane gaskiya da kan shi. Yace naga kin saro kaya ai a shagon yaro nane na fada mashi idan kinzo ya raga maki yadda kema zaki samu sai dai duk abinda zakiyi kada ki cika riba a kayan ki don riba bai da kyau kin sani. Ya kawo wani dan karamin turare ya bani yace wanan kyautane na tafi umurah cikin satin na na dawo daga can. Nai mai sallama nafito a daidai lokacin na falka daga barci sai dai idona a bude amma kamshin falon malam nakeji a falon namu a lokacin waras na bude idanuwa na still har lokacin kamshin bai bari ba. Na dade a gurin ina kokarin tuna mafalkin da nayi da malam da iyalishi ina mamaki a raina kawai. Yaron da zaikai min sako wanda Anty hauwa taiwa magana yazo ya karbi kayan za,a kawo kwantagora nabashi nomban wanda za,akaiwa kayan a gurin shi anty zata zo ta karba. Har yara suka dawo daga school suka samay duk jikina kasalane ya damay ni ban iya yin komai ba a,wunin ranan kamar yadda na saba yi idan ina ni kadai. Ummumm mama falon nan yau yana wani irin kamahin dadi inji Abba Aisha tace nima naji kamshi sosai wallahi mama. Nace kai kun faye surutu bana hanaku idan kunji abu kuyi magana ba ashe. Har kwana biyu falon mu yana kanshin irin ta falon malam duk wanda ta shigo sai yai maganan kamshin dadin da yaji. Anty Lami da mukai waya take ce min Maryam.ina kika saro kaya haka masu kyau duk wanda yagani sai ya yaba kyawon kayan don kamar bana kasan nan bane wallahi. Tace har an wawashe su ai don an taba kyaun kayan nan da sati biyu zan turo maki da kudin ki sai ki kara turo muna da wasu don akwai masu so sosai wallahi. Naji wani irin dadi a raina nace a fili ALLAH na gode ma na goma Malam Baba hakika kai ubane na gari a gare ni. Nakuma godewa wanan matar Allah daka hadani da ita mata mai karamci da mutunci ko ina zan kara ganin ta in mata godiya in kuma fada mata alherin da taimin tazama min wani babban baiwa. Nace koda ban san inda zan ganki ba nagode ina maki fatan alheri a duk inda kike kema . Sai naji kamar murmushi a bayana bandamu in waiga ba don nasan babu kowa a gurin shirmay ne kawai da zolayar kunne ke rudina. Kamar yadda anty tace min bayan sati biyun takara ruro min da kudina tare da riba nakara zuwa wanan shagon na saro kayan na kara tura masu shi. Washegari sai ga wayanta wai har kayan sun kare ko nace ikon Allah anty ashe abin zai karbu haka ne sosai. Har lokacin baban Abba baida lokacin mu sai harkan gaban shi kawai yakeyi ba wani shakku a tare dashi. Nima ban sakawa raina abinda yakeyi ba don bai rage mu da komai ba a gidan na bukatan mu. Naga idan ma na saka a,raina,wahala kawai zanyi a raina nice da damuwa don shi ba abinda ya damay shi. Ranan zanyi wanki sai na tuna da clean din da ke a cikin jakata nace bari na dauko shi nayi amfani dashi. Sai dai babu komai a cikin jakan nawa sai wani kwalin turaren saudiya kawai nagani a ciki nai ta tunanen ko ina na samo shi amma na kasa tunawa. Na mayar na aje ainda na ganshi da farko na bude wani clean naci gaba da aiki na dashi. Ina wanki ne kyatan baba malam ya fado min a rai na turaren da ya bani a cikin mafalki. Da sauri na koma dakin na ciro kwalin tabbas shine din bawai mantuwa nayi ba wanda aka bani a cikin mafalki din. Mamaki ne ya kamani nace may hakan wai take nufi ne ana nufin daga cikin mafalki baba malam yabani kyauta kuma na ganshi a zahiri. Gaskiya akwai magana indai bada aljannu nake hurda ba ban sani ba sai kuma wata zuciya take ce min kai haba kin fasan manyan malamai da rafanai suke hurda kamar waliyyai suke kila haka yasa yace idan kina son ganin shi ki saka a ranki zaki ganshi din. Tunda malam baba yakai babban malami dubi fa yadda Allah yabashi bauwan tara yara yana koya masu kuma duk shi kadai ke basu wanan ilimin haka. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [10/27, 10:55 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BAMU KADAI BA NE A,, 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 1⃣2⃣ Alhamdullahi zance yanzu don sana,ata cikin wata biyu har ban san yadda zanyi musalin ci gaban da na samu ba akai. Yanzu ya kai har kitchen equipment nake turawa gida duk a gurin wanan costumer din nawa nake sarin su. Ya hadani da wani dan uwan shi yace ya dinga bani sarin kayan mata dogayen riguna masu kyau yakuma raga min naji yana cewa dashi kai mata sauki yar gidan malam SULAIMAN ne na tsibiri. Sai lokacin na tuna da malam naji ina son ganin shi kodon alherin da nake samu a kan shi yanzu yaci naje na godewa malam hakana. Sayayya nayi sosai na shirya sai gurin shiga mota ina rike da Nusaiba da yanzu tana tafiyanta da kafa tayi lafiya sosai ga,wani irin kiba da tayi kamar itace kadai ake kiwo a gidan. Naje bus stop na tsaya sai ko ga mota yazo na shiga ban tsaya ko ina ba sai tsibiri. Nashiga gurin matan nan da nake shiga don in tambaye su mukaddarasiyat. Mun gaisa nakawo tsaraba na basu har da zanin gadon da nake sayarwa nakawo masu yan 1,500. Suna tajin dadi dayar matar take ce min bamu dade da hiran ki ba fa munzaci kin bar mu ke nan ai. Nace haba ni daku yanzu ai mun zama yan uwa ko sai dai Allah ya kara dankon zumunci kawai. Nabasu tsaraba mamaki yai matukar kamasu sosai a lokacin sai wacce nake gani kamar itace babba a gidan take cewa dani. Amma kina da matukar kirki ke kamar ba biladam ba haliki ko shi yasa babu cutarwa a tsakanin ki da makwabciyar ki don halinki na kirki. Wanan kalman a kullun yana daure min kai sosai wallahi dayar tace gamu da nisa amma haka kike korin zuwa ganin mu ko yaushe kuma da tarin alheri. Ranan mijin su yana gida ashe yana fitowa naji kaina yai wani irin uban sarawa don ina ganin siffan shi gabana yai mugun faduwa. Dayar matar ce ta kirashi wai mu gaisa dashi don sun bashi labari na. Ya kura min ido na,wani dan lokaci kaina a kasa ban dago ba sai tsoron siffan shi dana gani amma da naji muryan shi yana fadin wanan ai costmer dina ce a kasuwa na dago kaina da sauri na kalleshi. Sai a lokacin naga ya koma min sak mutumin da nake sarin zanin gado a gurin shi a central market. Mun gaisai don ya koma min mutum sak wanda na sani nace a raina may yasamay ni ne kuma mutumin da ko yaushe nake sayan kaya a gurin shi har ya dauki yata ya rike min don Nusaiba ta saba dashi sosai. Nan na sake muka kama hira dashi matan ke nuna mai kyautan da na kawo masu yace ikon Allah. Kin saye a gurina kuma kin kawo wa iyalina shi yanzu sai yaya ke nan ? Nai dariya nace ai wanan tsakani da su ne kyauta nan nan ba,a fasa ba insha Allahu. Yai dariya yace masha Allahu to angode amma yaya akayi kike zuwa aanan garin namu mai nisa haka maman Nusaiba. Matan sukace lalai malam ashe ka,santa mufa har yau ma bamu san sunan yarta ba sai yanzu muke ji . Nace lah aiko ba nisa nan ne fa dan nesa da gari kadan yace akwai kayan da zasu shigo sati mai zuwa sai dai ba,a gama odo su bane amma suna da kyau sosai sai mun hadu a kasuwa idan kin shigo zan aje maki su insha Allahu . Nai mai godiya nace zan tafi in gaida malam sai suke ce min Allah yasa yau ki samu malam a gida don yau jumma,a shi kin san ba,a nan yake sallah ba a makka yake sallah jumma,a idan ya tafi sai dare yake dawowa gida. Makka kuma nace a fili sukai dariya sukace makka mana zuwa makka aiba wani babban wahala bane balle irin gurin su malam ma. Ikon Allah nace nidai na mike don in samu malam din don yanzu al,amarin malam ya fara bani tsoro malam ko yakai malam. Ace mutum yaje saudiya a rana daya ya dawo kuma ai abu ko ya shahara ya zama waliyi ke nan ko? Nashiga gidan malam da tsaraban manyan zannuwan gado dana kawo masu sukai godiya nace baba fa sukace ai kin makara duk ranan jumma da yafito sallah asuba yake wucewa babban harram yaje yai sallah sai dare idan anyi sallah ishai yake dawowa gida. Nace kai da na samay shi aidana bashi sako su kan malam Allah ya basu wallahi. Sai amaryan tace sakon may zaki bashi a fada mashi nace kudi naso na bayar a saro min turare yan saudiya don sunfi araha a can akace sai dai ai na makara yanzu kan. Mukai hira nace masu zan koma sai sukace na tsaya subani tsaraba kaya ne irin namu na mata da muke amfani dashi amaryan ta debo min masu yawa ita kuma uwargidan tabani wasu irin riguna na yarana masu masifan kyau da tsada wanda da wuya ma asmay shi a kasan nan. Nai sallama dasu bayan godiya ina tafe ina mamaki gasu talkawa a ina suka samu kudin sayen wanan kayan mai matukar tsada haka wai.? Malam kuma ace a saudiya yake sallah masha Allah insha Allahu nan da ranan talata zan shigo na gaida malam din da yardan Allah haka nadawo gida da tsarabata. Da yake ni ba ma,abociya amfani da kayan mata bane nan na,watsar dashi cikin jakar da aka bani shi. Tufafin dai ne nake ta murna akan su suma dayan gidan sun bani kyautan kayan miya irin namu. ******* ********* ***** Ba,wani zaman dadi a tsakanina da baban Abba yanzu don budurwace ko karuwa oho ta matukar dauke mai hankalin shi sosai a kaina. Ni ban damu ba sai business dina ya dauke min hankali ga komai yanzu. Mamaki take bani don yanzu ko a gabana zai sha hiran shi na soyayya zai dinga fadin magana na,so da kauna ba tare da wani shakkana ba. Ranan ya fito cikin shiri yake fadin shi zai fita sai kamshin turare yakeyi sosai a jikin shi. Aisha tace Baba ina zaka masalaci yai dariya yace kai Aisha akwai ki da shirmay masallaci da daren nan zan tafi hura ne gun sabuwar maman ku . Maman mu kuma baba baga maman mu a gida ba ka zauna kuyi hira mana da ita muma muji dadi. Yace maman ku yanzu bata iya hira ba sabuwa tafita iyawa sosai ina jin su ban tanka mashi ba. Sai Aisha tace ni Baba ban son sabuwa maman mu nake so yace aiko yarinya dole ki so sabuwa don baban ki yana so shi. Tace baba please ka zauna da mu mana baba ka kunna muna katun mu kalla don yanzu don bakin hali ko tv ya hana mu kunna a gidan wau muna cin kudin wuta da yawa sosai. Da har fridge ya hana sai da na jajirce mai don ba zan iya sayen ruwan sanyi ba a kullun. Yace Aisha bazan zauna ba idan kuma kika damay ni yanzu na bata maki rai don naga mugun halinki daya da uwar ki shegen kishin tsiya dake yar karama dake an koya maki mugun abu. Sai lokacin nai magana nace ni mugun hali ne dani ashe yace waya kaiki duk kinbi kin fige gurin bakin kishin ki. Nace wa zanyi kishi karuwa ko yar dadiro zanyi wa kishi nagane may sai ko yaya kaina don may nake kiranta da yar dadiro ko karuwa. Nace inba karuwa bane kuke taraiya har kake kwana da ita koshi hakan maynene matarka ce ita. Kamar zai mare ni ko may yagani kuma ya sauke hannun shi idanuwan shi sun kada sunyi ja jajir dasu sosai. Nace duk abinda kake min wallahi don kan ka Allah yana ganin ka ka kawo mu garin mutane kazo kana kuntata min ni dayaran ka. Yace wallahi maryam idan zaki tayar min da hankali ne zan mayar daku gida in huta dama kun kai min ko ina,wallahi. Nace ka mayar damu mana sai may dama ba acan nafi wayo ba kaine kila kake gudun kauye yanzu. Yace haka kikace nace nace ko yanzu ka mayar da mu mana wayai hasara ba kai ba naga kaga ina kyalewa don biyayya kawai amma shine har zaka kira ni da wai mai mugun hali. Ya kuta ya dauki keys din shi saman table yafice yana fadin zaki gane kuren ki wallahi nace naga alheri wallahi. Na juya yaran suna zaune saman kujera sun makure a guri daya cikin damuwa a fuskan su. Ina jin shi ya na tayar da mota a,waje motar taki tashi yayi yayi motar bata tashi ba . Ya fito daga motan ya bude ya dan duduba komai normal ya koma ya tayar amma motan bata tashi ba shiru kake ji. Duk yadda yaso motar bata tashi ba yashigo ciki yana tsuki ina jin karuwan tana bugo mai waya ya dago yana fadi hanna yaya ne tace naga shiru bakazo ba har yanzu. Yaja tsaki yace wallahi motatace take ta bani matsala taki tashi wallahi ban san may ya samay ta ba Tace bazaka shigo motar haya bane yace haba hannan motar haya tun daga nan har barnawa. Tace ba sai ka kwana an nan ba yace aiki fa da safe sai ta kashe wayan kawai. Shima tsuki yaja ya dan dago inda muke ya dan kalle mu cikin jin haushi yaran suna kallon shi. Yace a hasale may kuke kallona munafukai kawai gurin ku ya cika ban fatiba din. Dariya nayi kawai daga inda nake zaune yace ai kyayi dariya tunda ban fita ba yanzu. Nace waya hanaka fita batace kaje can ka kwana ba ai sai ka shirya kaje can din ka kwana tunda ka saba zzuwa ka kwana da ita a can. Yace na saba sai may tinda ke keda kafata ai saiki jani ki kaini nace ban saba kaika aikata zunubi ba don haka bani zan kaika ba ma yau. Kafin ya bani amsa sai ga kiran Hannan ya kara shigowa wayan shi again yana dagawa tace kataso ne ? Yace ban taso ba don dare yayi tace kai dai na gane shigiyar matar ka ta hanaka fitowa yau ke nan. Nace kece dai shegiya karuwan banza kawai kona hana shi na isa ne ai mijina nane fa. Sai ya kashe wayan dip yace a hasale maynene haka maryam dake take waya koda ni ? Nace dakai dai take wayan amma ta sakoni a ciki shine na bata amsa ni kuma daidai da maganan ta. Nan mukai ta sa insa dashi a karshe ya fashe haushi ga yaran yace muna fukai ku tashi kuje ku kwanta . Suka shige dakin su tara saura nima na gama abinda ya dace nayi na,shige na kwanta gurin su, na barshi nan falo suna ta rigima da Hanan din. Washe gari abin mamaki yana tayar da mota sai kawai motar ta,tashi ba tare da,wani matsalan komai ba. Yai mamaki jiya ba yadda baiyi da ita ba amma motar taki tashi mai a lokacin. Ina gama shiri na wuce banki na ciro kudin da aka turo min na kaya na nufi kasuwa don sarin kaya. Shagon mai bedshet na nufa muka gaisa na tambaye shi iyalin shi yace suna lafiya. Ina cikin zabar kaya don zanuwan da ya shigo dasu suna da matukar kyau sosai wallahi. Ina tsaka da zaben kaya wani yaro matashi ya shigo shagon yana magana kan wasu kaya da mai shagon dake rike da Nusaiba a hannun shi nace wanan kudin su nawa ne malam ? Sai matashin ya,juyo ya kalle ni yace a,a ba matar nan nagani a garin mu ba ranan jumma,a maishagon yace itace malam maryama ke nan ai. Nace da sauri malam.ina kasan sunan sai yai dariya ya basar yace kudin su ya haura wanda na,saba kawowa gaskiya. Nace malam don Allah a ina kasan sunana yace ni yanzu ai har gidan ku na sani harda mahaifin ki nace kai na mayar da hankalina gare shi. Yace ke diyar malam baba SULAIMAN bane ko ? Nai murmushi nace malam kan a garin nan yanzu shine Baba na,wallahi. Matashin yana tabina da kallo cikin mamaki yadda muke ta hira da mai shagon na gama zabe yai min kudin su na biya sai dai idan na biya duka kudin na bai kai ba gaskiya. Don bazan iya karasa sauran sayayyan da nake sonyi ba nace malam sai dai na rage kayan gaskiya don ina gani kudina basu kai wanda nake son saya ba. Yace duba dai malama insha Allahu zasu kai idan ma basu kaiba sai na baki bashi na biyo ki. Nace a,a malam bazanci bashi ba iya kudina zan dauka na bude jakata na ciro kudi sai naga a idona kamar kudin ya karu yawa. Nakirga kudin shi duka na bashi nabar kayan da Nusaiba nace zan shiga dayan shagon na saro kaya. A dayan shago na sai abun da nake bukata nafito zuwa shagon turare na gaida mai shagon zan fara saye yace min malama ga sako ance nabaki tun shekaran jiya yake aje a gurina baki zo ba. Na dubi katon ledan da take miko min wanda yake shake da turare nace sako kuma ? Yace eh sakonki ne baba malam yace na kawo maki wai abinda kikace ya sayo maki a saudiya ne ko wa yan nan zasuyi maki? Yace sauran bayani sai idan kun hadu zai maki nace baba malam dai na tsibiri kake nufi yace shi malama na ke nufi malama na karba ina cewa nagode yace sai dai kuma baida lafiya gaskiya yana fama da ciwon kafa sosai. Nace subbahanallahi aiko zan tafi na gaidashi yace yana da kyau hakan gaskiya. Maimakon na wuce sai na,shiga shagon islamic chamist nake tambayan maganin ciwon kafa na islamic. Na muma tuna babana yana bayar da magani ciwon kafa ai a gida don haka zan mashi waya naji. Na kwaso kayana a gajiye na dawo gida na samu baban su Abba ya dawo a lokacin ya bini da kallo tare da kallon kayan da,aka,shigo min dasu niki niki cikin gida. Yace wai ke Maryann ina kike samun kudin sayen wanan kaya haka masu yawa. Nace Allah ne ya bani daga,aro ya zama min alheri yanzun ma har na biya wacce ta bani jarin kudin ta nawa nake juyawa kawai. Yace dama ke nake jira kudi nake so aro har zuwa wani sati na mayar maki nace kudi kamar nawa yace dubu hamsin kawai nake son aro zanyi amfani dasu ne yau din nan. Nace anya ina dasu bari dai na duba nagani ina dubawa na samu akwai su na kirga na miko mashi ya karba tana sauke ajiyan zuciya. Jin waya yasa na bar gurin na shiga ciki na aje jakata na kewaya ina fitowa naji yana cewa nace ganinan zuwa na kawo maki mana. Fitowa falon yayi daidai da mikewan shi zai fita nace ina kuma zaka yace zama kike son nayi maki a gida dama. Ko na zauna wani abu zakiyu min ke dake guduna yanzu ma har yakai kofa nace Baban Abba ya juyo. Nace wallahi udan kaima karuwan ka amfani da kudina ban yafe ba. Yace don kin ara min kudi shine kuma zaki saka min doka a kansu ina ruwan ki da abinda zanyi da kudin kuma ? Nace nidai na fada maka wallahi ko yafice yana cewa wanan kuma matsalarki ce ai. Bai tsaya ba sai gurin hannan ya nufa yaba ta dubu talatin daga cikin kudin ta amsa a wulakance tana cewa talatin kawai zaka bani nidake son sittin a gurin ka. Yace tayi hakkuri tai maneji dasu ko su da kyat ya samo su don yanzu damane babu harka sosai yanzu. ****** ********* ****** Yana fita makwabta da suka gane ina sayar da kaya yanzu suka cika gida suna dubawa sai lokacin ne na bude ledan da Baba malam ya aiko min dasu. Turaren da na gani a ciki sun bani tsoro don masy matukar tsadane da kamshi sai manya zasu iya sayen su. Don ko a shago ban iya sayen ko daya a cikin su idan na tafi sarin kaya ga,wa yan nan sun cuna mana shagon kyau da kamshi sosai. Nan yar sokoto take cewa zata kaini gurin wasu yan garin su akwai buki sai na nuna jayan acan don manyan mata ne zasu hadu a gurin. Naji dadin hakan sosai nai mata godiya washe gari ko nace zan tafi in raka yar sokoto gurin buki na kai kayana bai hanani ba yabarni na tafi. Kayan kan sun karbu sosai wallahi kusan duk a gurin na rage wasu wasu sukace zasu zo har gida su duba su gani. Ban tsaya ba na bar mutumiyar a can na dawo gida abina ina murna nan na bugawa mai shago waya akan ya aje min sauran washe gari zan zo na dauka. Washe gari na shirya na tafi kasuwa sai dai ina son sai na tafi gurin Baba na ganshi idan na dawo sai na tsaya kasuwa. Mota na shiga kamar kullun sai gurin baba malam sai dai yau ba masu karatu kamar kullun na shiga cikin gida kai tsaye. Na gaisa dasu na basu tsaraban kankana da lemon da nazo dashi nasu daban wanda na rikowa babana daban. Nashiga gurin shi muka gaisa sai dai gaskiya yana jin jiki nace baba ashe kuma ba lafiya haka ? Yace wallahi kin san yaran bani adam basu da hankali kadan ne daga cikin ku masu hankali sune wallahi duk kaucewan da nayi sai da yahau kaina da mahakaciyar ku watau (mota) yabi takaina ya wuce. Yace shiyasa wallahi idan an hadu da mash rashin imani a cikin mi suke daukan mumunan hukunci a kanku din su rama ketan da akayi masu. Abin tausayi yarana sun bi yaron don su dauki fansa duk dana hana su amma sai suka samu ashe wai sauri yakeyi zai tafi asibiti uwar shi bata da lafiya nace su barshi Allah ya bata lafiya. Nace amin baba sannu baba na sa hannu a jakata na dauko maganunuwan da nazo mashi dasu na bashi yace ikon Allah mahaifinki ne ya aiko min dashi ko ? Nai mamaki yadda yasan hakan nace eh Baba matarshi ya kwalawa kira tazo yace ta shafa mai a kafan shi tana shafawa tana fadin sannu malam. Nima dake gefe daya sannu nake mashi yana amsawa da kyat dagani yana jin jikin shi sosai gaskiya. Muna nan zaune Baba yana zufa dayar matar ma tashigo muna tare dasu sai zufa yake can ya nisa yace ikon Allah naji matukar saukin kafan nan yau wallahi. Sai da naga ya samu natsuwa nake cewa Baba naga sakon turare sai dai ban san kudin su bane. Yai murmushi yace dubu ashirin zaki bayae na dago da mamaki ina kallin shi na sa hannu a jakkata zan dauko kudin yace min bani zaki ba ba ki aikawa wata boyar Allah a garin ku mai marayu tafini bukatan su kice na bata sadaka. Yai min bayanin matar nace nagane ta baba ai nasan har mijin nata ma da ya rasu. Nai sallama dasu nafito matan tai min rakiya sai lokacin take ce min baki daiyi amfani da abinda na baki ba ko ? Tace kiyi kokari kiyi amfani dashi zai maki amfani ga matsalan ki da maigidan ki don wanan karuwan da yake tare da ita abokiyar shedancin shi ba banza tabar shi ba. Nai matukar mamaki da tasan abinda Baban Abba ke aikatawa a lokacin. Nadawo kasuwa na,sari kayana na dawo gida a gajiye kamai nai wani tafiya mai nisa dani. Haka nakan ji kullun idan na tafi gurin su baba malam din sai na dawo a gajiye dani duk jikina ya mutu. Masu sayen kaya sunzo har gida sun sayi kayan daga ranan na fara samun costamars masu sayen kayana a cikin mutunci su zube min kudi na. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE A ,,,, 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 1⃣2⃣ ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI MUSULMAI INA MAI BAKU HAKKURIN JINA SHIRU DA KUKAYI KWANA BIYU NAYI RASHIN BABBAN YAYAN MU JIGON MU RILWANU IDRIS MAKAWA WANDA YA RASU RANAN ALHAMIS DA YAMMA, YARASU YABAR MU DA YARA HUDU DA MATA DAYA DAFATAN ZAKU TAYA MU YI MASHI FATAN DACEWA DA RAHAMAN UBANGIN MU DASHI DA DUK MUSULMAI DA SUKA RASU TUN ZAMANI ANNABI ADAMU HAR ZUWA YAU UBANGIJI ALLAH YA KAI HASKE GA KABARIN SU IDAN NAMU YAZO MUMA MU CIKA DA KYAU DA IMANIN UBANGIJIN MU A ZUKATAN MU ALLAHUMA AMEEN ALLAH,,,, WALAHI NAYI RASHI BABBA A RAYUWANA YAN UWA MUSULMAI,,, 😭😭😭😭😭😭 Abubuwa gaba daya sun rikice min a lokaci daya don yanzu takai Baban Abba ba ruwan shi da zance na dana yarana. Hanna ta riga tai nisa a zuciyar shi don yanzu takai ko albashi shi ya kwasa itace zata ciyen fiye da rabi gurin bukatocin ta na yau da kullun. Sauki na daya shine ya na sayo kayan abinci amma ba kamar yadda ya saba ba acan baya da yake sayo muna kalla kalla abubuwan bukatan mu. Hakan da yake muna ba mu kadai ya shafa ba yin hakan ya shafi har da Umma dake zaune a kauye watau mahaifiyar shi. Hakane ya sa,Umma din ta fara zargi a ranta cewa nice yamzu na shiga tsakanin ya da danta ina mai wayyo ina karbe mai kudin shi. Wai da su ne nake business din da nakeyi i na mai wayo ina karbe may kudin ina turowa a gidan mu. Anty Lami ta bugo min waya hankali a tashe tana sanar dani abinda Umma take fadi a makwabta har ya dawo kunnen yan uwana sukaji. Shine ran su ya baci suke gani koda ma kudin shi ne nake juyawa dashi ai naci na ci din don idan anyi la,akari da irin wahalan da nasha a baya can na zaman hakkuri a gida tare da mahaifiyar shi. Haka dai Umma take ta faman sake zamce a gari kamar a gaban ta ne ya bani kudin da take ikirari da nashi na ke ta saro kayan da nake sana,a dasu. Nikan hankali na a kwance nake al,amurana ban damu da,wani watsar da mu da yayi ba a cikin garin mutane ba. Don Allah ya rufa min a,siri ina sana,a a anan inda muke da kuma can gida da,ake juya min kudin sana,a ta. Yanzu takai ba ruwan shi da zance na dana yara iyakar shi da mu ya shigo gida idan mun yi sa a ya kwana a gidan ke nan. Tun sa,safe ba,zai tsaya ya karya ba zai ce zai tafi gurin aiki don yanzu aiki yayi masu yawa,a,sosai. Wai suna fita zuwa operation a daji don ana,smogal din kaya ta barauniyar hanya sosai inji shi. Komai a gidan Hanna yakeyi wacce ya mayar kamar mayar shi yanzu don komai yi mata yake yi. Wani abu daya da ya kasa ganewa shine duk lokacin da ya dauki kudina da nake sana,a dashi yai wa hanna amfani dashi daga shi har ita sai sun shiga uku don sai sunyi wahala a rayuwan su amma ya kasa gane hakan shi. Sa,an shi daya ba kullun ne yake daukan min kudina na ba sai zuwa lokaci mai tsawo haka yakan yi min dabara irin na maza yace na ranta mai zaiyi gyaran mota dashi ko zai turawa Umma a gida ne . Amma da zaran ya samu yakan yi kokari ya mayar min da kudina da ya,ara sai kuma wani jikon again. Yau ma kamar kullun haka yazo min da yake yana da bukatan kudi a gurina da dan sakin fuskan shi ya samay mu a falon zaune. Ya dan yi wasa da Nusaiba dake shan nono a jikina wance nake batun yaye ta yanzu don ta isa yaye sai ga Aisha ta shigo falon da har taso taron shi yadda suka saba da daddy oyoyo sai kuma taja ta tsaya daga inda take tsaye take cewa sannu da dawowa Daddy yace yauwa ido ya kuke ya gida kuma. Tace lafiya ta samu guri ta zauna can ya juya inda nake zaune hankalinana yana fa kallo yake cewa baza,a bani abinci bane yau. Nace naga ko nai ma tayin a kawo sai kace a koshe kake yaushe rabon ka da abincin mu a gidan nan nagani. Yace cikin murshi to yanzu dai na roka sai a bani naci ko ? Na mike ba tare da nace mai komaiba na jero mai abinci a kayan abincin shi zuwa falo inda yake zaune. Sai da yaci ya koshi yai nak dashi ya dan kai kishingide yana cewa, duk ya gaji har na shirya yara suka fita suka bar gidan zuwa islamiya don ya kasance asabarce ranan. Kamar mai jiran su fita yayo cikina amma na kauce yai dan murmushi tare da cewa idan kuma ban yi magana ba ace ban damu da iyalina ba. Ba tare da na juyo gare shi ba naci gaba da harkokina hannkali a kwance nake aiyu kana fuska ba walwala a cikin sa. Can dai ya gama murmukusan shi ya mike zuwa bakin kofa kitchen idana ke aikina hankalina a kwance ya dafa bangon kofan yana fadin. Maryam ina son ki ara min kudi kafin ai albashi don mota na tana son service sosai nai kamar banji may ya fada ba don dama nasan akwai abinda yake bukata a gurina da wanan sakin fuskan da ta shigo muna dashi yau. Ya kara fadan da karfi bakiji bane may na fada kudi zaki ara min na gyara mota ta da ita nace maki. Sai da naji shi gap dani yasa na dan juyo inda yake tsaye ina fadin kudi kamar nawa don gaskiya a,satin nan mai zuwa nake son zuwa na saro kaya da kudin dake a hannuna . Yace bazasu dade ba zan mayar maki da su insha Allahu, nace nawa zan bada ? Yake cewa koda zan samu dari zan so don gyaran yana da yawa sosai nake gani. haka na juya batare da nai magana ba zuwa dakina inda na dauko wasu kudin da aka kawo min na kayan da akasaya na kirga na bashi kudin. Inda bai kara minti goma ba a gidan ya juya ya bar gidan da sauri a cikin farin ciki yake. Bai ko tsaya mamaki matsayin shi na mijina wanda ya kawo ni birni da kauye na ina nake samun kudi irin haka a lokaci daya duk Sai da ya nufi gurin Hanna wace ta tayar mai da hankali a kan duk yadda zaiyi ya samo mata kudi don tana da bukatan da kudi. Yasan idan bai samo kudin da ta bukata daga gare shi ba babu lafiya ke nan a zaman su gashi duk ta bi ta susuta shi yanzu shiga nan fita nan duk akan zaman bamza kawai da sukeyi. Niko ba abinda ya damay ni da harkan su sai sana,ata nakeyi hankali kwamce inda mutane ke yaba kyaun kayana wanda ba kowane zai samay su ba idan ya,shiga kasuwa sari zan ma mutum kwatamce amma bazai gane shagon ba sai idan nice na shiga kasuwa da kaina na sayo wa mutum. Kayana suna matukar samun karbuwa a gurin mutane don wasu har cewa sukeyi wai a waje nake sayo wa ina dai masu bat da sau ne kawai. Dariya sukan bani idan sun fadi hakan har lakani suke min wai hajiyar Dubai don sun gane akwai wanda nake ba sakon kaya na a boye. ****** ********* ****** Shiru har ana batun sati biyu da karban kudin da yayi bai bani ba gashi na kula hankalin shi a tashe yake duk kwanakin nan. Sai dai bai fada min damuwan shi ba nima ban tambaye shi ba tunda yanzu ba shawara yakeyi dani ba kamar baya da komai a tare muke abin mu gwanin ban sha,awa damu. Abinda ban sani ba,shine ashe daga shi har hanna suna cikin tashin hankali kan kudina da ya karba ya bata. Don ranan da ya kai mata kudin ta karbe su a wulakance ba bu godiya ko yabawa a tare da ita. Sai da dare ta,shiya ta dauki kudin zuwa sayen abinda tai niyar sayowa nan tasha dan banzan mari a cikin Napep din da ta shiga ba tare da tasan wanda yake dukan ta ba sai da jikin ta yai rudu rudu aka watsar da ita a daji ba Napep ba dalilin shi haka ta dawo gida rijib da ita kuma ga kudin bata gan su ba sun bace daga hand bag din ta. Da kyat ta samu ta dawo gida ta sha dukan tsiya a kan kudin shiko gogan yana barin gidan ta yaga kamar mutum ya gitta mai a gaban shi. Yaja burki da karfi ya tsaya yafito babu kowa a furin ya sauke ajiyan zuciya ya koma mota yayi yayi ya tayar da motar shi amma motar taki tashi mai. Haka ya karasa office din su a gajiye ya kira bakanike ya duba mai motar amma taki tashi. Ba,a gane may ke damun motar ba anyi anyi motar haka kawai an kasa gane may ke damun ta. Hankalin yashi ya kasu biyu ga hanna dake kwamce akan dukan da tasha bata san mai dukan ta ba sai warning din da taji an mata cewa gobe ta kara karban alhakin wasu ta kashe. Ana haka aka bugo min waya cewa babana baida lafiya yana fama da ciwon ciki. Hankalina ya daga gashi dan abinda ke guri na na riga da na,sari kaya dashi a lokacin. Hakalina yai matukar tashi yadda nake samun labarin mahaifina yana jin jiki haka yasa na yanke shawara zuwa gurin baba malam na fada mashi na shirya tare da tsaraba da zan kai masu na shiga mota sai tafiya muke amma yau abin mamaki ko alaman garin dan kauyen su baba malam ban gani ba. Har muka fara shiga kauyukan garin plauto jos haka yasa hankalina ya fara dagawa na jawo wayana dake cikin jakata naga time din da kashe a cikin mota a zaune. Da sauri nace wa driver ya sauke ni a,wani dan kauye da muka kai. Nan na sake tare mota na juyo na dawo kaduna lokacin har magariba ya soma yi nakawo gida a gajiye dani. Na,samu su Anty hankalin su a tashe don sun dauka ko nabace ne ko an sace ni tunda ban taba yin haka ba. Idan na fita ban kai karfe biyun rana a,waje na dawo gida daga inda na tafi. Ranan ko girkin kwarai ban samu girkawa ba a gidan sai indomie na dafawa yaran sukaci kawai. Da dare ma,bamuyi wani dogon hira ba karfe goma duk mun shiga barci dagani har yaran saboda gajiyan dana kwaso. Can musalin karbi biyun dare na fara mafalki kamar an tashe ni sai ganin anty nan wace nake nema a rayuwana nayi. Tace min tashi muyi magana dake ban musa ba na mike zaune tare da cewa Anty mukaddarasiya may yasa kika bace bayan kin taimaki rayuwana kin hadani da mutanen arziki yan uwan ki masu mutunci da karamci. Wanda ta sanadin ki na zama wata abin alfahari a cikin yan uwana da abokan arziki. Murmushi tayi tare da dafa kafada na take cewa kwantar da hankalin ko don ke daga cikin jinsin bil,adam ta daban ce ke kina da mutunci da halarci maryama. Kin min abin da ban zataba daga cikin jinsin ku maryama shine ya hana na dauki duk wani matakin da naso dauka akanki a baya. Wanan gidan da kuke a ciki gidan mune ni da mahafana da yan uwana da mijina. Munyi tafiya ne zuwa kasan saudiya gurin bautan ubangijin mu bisa ga yadda sunna ta koyar da al,umman musulmai. Amma kassh sai gashi an turo ni ni da yara muzo mu fara gyaran guri na sami kunzo ke da diyan ki da maigidan ki kun mamaye muna guri. Duk da dai ba,yawa ne daku ba kamar mu don mu a gidan nan yanzun haka mukai mutum dari da dan kai don haka kinga mun fiku yawa ke nan. Yanzu haka iyayyena suna gap da dawowa garin nan ban san idan sun dawo yadda zamu kasance da ku ba. Sai dai baba malam yai wa mahaifina bayanin irin halin kirkin dake gare ki keda diyan ki. Hakan yasa aka hana kowan mu da ya cuta maku don yarana ne suka cutawa yar ki a baya shine sanadiyan da har na kaiki gurin baba malam don idan bashi ba duk nahiyar nan babu wanda zai iya taimaka mata. Ina son ki kwantar da hankali ki kada ki tayar da hankalin ki, don da yardan Allah babu abinda zai cutata maku a gidan nan idan har kinci gaba da tsare irin dokin da kike tsarewa wanda bamu son kina yi a gidan nan . Kina da matukar kirki maryama don haka baza mu bari wani ya cutawa rayuwan ki. Sai dai kada ki kara cewa zaki tsibiri don bazaki iya zuwa ba da kin san irin nisan shi da baki wahalal da rayuwan ki ba a dazun don zuwa can. Kamar yadda Baba malam ya fada maki idan kina son ganin shi ki nasa a ranki cewa zaki tafi can don ba,a kasan nan bane har fa birnin sin tsibiri yake kawai dai mu yan yankin wanan jinsin na kasan kaduna ne muna zaune ne daku kawai a nan cikin namu yanayi. Nadago kaina ina kalon ta da mamaki don a lokacin har ta mike tsaye daga zaunen da take a kusa dani. Nace birnin sin fa kikace anty tace min kwarai maryama kin san mu ba iriku bane yan adam mu jinnu ne ba mutane bane. Mikewa nayi tsaye da sauri na taka har gaban ta tace kina mamaki ne maryama ? Kwarai kuwa mu ba mutane bane nace a da sauri kina nufin harda babana baba malam ba dan adam bane ? Tace malam yai maki kama da dan adam ne maryama ? Malam ba mutum bane kawai dai mun juya maki ne ta tsigar yan adam don kada ki rana da kamanin mu idan kin gani. Amma ba zamu taba cuta maki ba sai dai ma mu taimaka maki don malam din yace min mahaifiyar ki tana da alaka sosai da su malam din wanda ni kaina na yarda da hakan. Kodon barin da akayi kina shiga cikin mu batare da wanin mu ya iya cuta maki ba don haka ni dake mun zama yan uwa daga yau ki rike a ran ki hakan. Maryama ban san irin son da kikewa malam ba haka wanda hakan har takai naga nawa mahaifin da yake yaya ga malam shima yana matukar son ki maryama. Don ko yaushe idan muna magana dashi zai tambayi lafiyan ki dana yaranki yakuma jaddada min akan na kula dake kamar yadda nake kula da sauran yan uwana dake nan. Kudin ki da mijin ki ya karba yakaiwa karuwan sa sunan nan a cikin jakar ki na sa an karbo maki su. Sai kuma wanan maganin gashi ta dora min a saman mirror dake dakin tace baba malam yabani magani na kawo maki . Yace na baki hakkuri bisa ga rashin ganin shi da baki samu yi dazun ba don yana aiki shiyasa bai sanda zuwan ki ba a bude maki hanyan ganin ki ba. Maganin mahaifinki ne yace ki hanzarta kaiwa mahafinki ya sha da kunu safe da yamma insha Allahu zai samu saraka sosai ga abinda ke damun shi. Sai kuma idan mun sake haduwa kinji kaunata ina tare dake a koda yaushe kada ki damu da nema na don muna tare dake akoda yaushe yar uwata kuma ke aminiyata ce don kina taimaka min sosai ta yadda baki tsanmani ba. Takai kamar taki biyu ta juyo tace min sana,an ki insha Allahu zaifi nan bunkasa nan da wani dan lokaci kawai sai naga ta bace min. A daidai lokacin ne naga kamar na falka daga barcin da nakeyi sai dai nayi zufa sosai a lokacin. Zubur na mike zaune daga kwancen da nake duk na sharfa wani irin zufa a jikina.[11/4, 10:17 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 BAMU KADE BANE, , , , , 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 1⃣4⃣ Aslamu Alaikum yan uwa da abokan arziki ina mai sanar maku da fitowan sabon littafina da zan fara typing na kudi mai suna maricin kan dutse ko Rayuwa nan da sati mai zuwa da yardan Allah insha Allahu sai dai na kudine shi ba free bane shi. Washegari na tashi har naso saka zancen mafalkin da nayi a raina amma sai na share zancen kawai na shiga harkokina nayau da kullun kamar yadda na saba yin abina a gidan Sai zuwa karfe sha daya na samu kaina a lokacin na kamala komai da nake bukatan yi a gidan sai hutun da nake bukatan yi kawai a raina. Wanka nayi don nusaiba ta dade da yin barci a lokacin na riga nai mata nata shirin ko. Bayan na fito daga wanka na zauna a gaban mirro ina shiri hankalina a kwance. Har na kusa kammalawa ne idona yakai akan wani kulin magani dake a saman mirro na aje. Kallon mamaki nakewa kullin don ban san wa ya aje min shi ba a gurin kuma ban san ko na may ye ba shi. Dauka nayi na bude sai naga magani ne irin na fargajiya a ciki nikakke dashi. Na mayar na kulle shi tare da kokarin ajewa a gurin da nagan shi aje don a zatona killa na baban Abba ne maganin. Take mafalkina na daren jiya ya fado min a rai inda na tuna a daidai gurin da mukkadarasiya ta aje min kullin maganin da baba malam yaba da sako nakaiwa baba yai amfani dashi a gida don warakan ciwon shi. Gabana ne yai wani mugun faduwa a lokacin tiryan tiryan abinda ya faru a cikin mafalkin yake fado min a rai na. Sai lokacin naji kamshin baba malama ga dan kullin dana gama daurewa wanda har hanaye na suma kamshin sukeyi a lokacin. Wani sabon faduwan gabane ta kara ziyartan zuciya na na mike da sauri zuwa falo inda Nusaiba take kwance tana barcinta hankalin kwace na dubata babu abin da ya samay ta nagani. A cikin tsoro nagama duk wani abinda zanyi a gida na goya yarinyar ta tare da saka hijjabina na bar gidan. Sai gidan anty hauwa na nufa cike da tsoro a zuciyata gashi ina son fada mata amma kuma na kasa kamar andaure min bakina nake ji. Allah dai ta taimakeni ban furta mata komai ba ga halin da nake ciki har yara suka dawo muka koma gidan mu cikin tsoro ni da yaran gashi ranan ba zuwa islamiya gare su. Suna cire uniform nabasu abinci sukaci Aisha tana gama cin abinci ta nufi back yard din inda ta saba wasan ta ita kadai. Nafito falo na samu Abba sai Nusaiba dake wasa a gefe daya shi kuma yana kallon katun a tv . Nace ina Aisha ya nuna min hanyan back yard da hannun shi har na fara hanya na kira ta sai tunanen abinda aka fada min ya zo min arai na. Na ba ita kadai bace take wasa a gurin tare da sauran yaran da mu bamu ganine take wasan. Tsayawa nayi daga kofa ina kallon yadda tai zufa ita kadai sai surutu take zubawa jefi jefi ita kadai a gurin tana faman jera kayan wasan ta data tara wanda ni ban ma san lokacin da ta tarasu haka ba a gurin. Kima ban taba kai hankalina ga sanin may takeyi ba ma sai yau da haka ya kasance a mafalkina. Dole ban da yadda zanyi na juya na koma falo cike da farga na zauna sai dai hankalina yana gurin yarinyar tunda sunce basu cuta muna su. A haka ranan na wuni a cikin damuwa da al, amarin dake damuna a raina ga waya ana bugo min kan ciwon mahaifina dake damun shi a gida. Sai da na idar da sallah magariba ne zancen kudin da tace nawa sun karbo min yafado min a raina na mike da sauri zuwa daki don na tabbatar da zancen da tai indan gaskiyane ko rudin kaina ne kawai nakeyi. Jakan farko dana duba babu komai a cikin sa hakan yasani sake ajiyan zuciya nasan mafalkine kawai hakan. To zancen maganin da nagani fa dazun saman mirro na wanda har a lokacin yana aje gurin da yake ban kawar ba. Ina jiran baban Abba ya dawo na tambaye shi ko nashi ne ya aje ban sani ba a gurin. Har najuya nakai kofa sai zancen jakar da na dauko wa baban Abba kudin a ranan ya fado min da sauri na juya inda jakar tawa take ajiye. Ina budewa kudine a ciki kamar yadda suke a farko suna daukan ido nafitar da sauri na kirga su cif dubu darin su yadda na bashi a ro a baya. Ban san lokacin da nakai zaune ba a bakin gado ina fadin na shiga uku ni maryam wanan magana ya tabbata ke nan gaskiya ko? Hankalina yai matukar tashi wanan ranan nakeji kamar na bude idona na ganni a garin gidan mu inda muka fito yafi min wanan bakon ala, amarin tashin hankali da na riski kaina a ciki a garin mutane. A haka muka kwana a gidan ga baban Abba yanzu halinshi sai a hankali ba damuwa yayi damu ba balle ma yasaurare ni. A cikin barci nai mafalki da uwargidan malam matar da nake kallon ta a matsayin mahaifiyata a gari tana kwantar min da hankali akan kada na saka tsoro a raina suba masu cutana bane sun fada min. Da suna da niyar cutamin da sun dade da cutata min ko tun zuwawa na farko gare su. Nan dai ta kwantar min da hankali tai min sallama ina falkawa na tashi da ciwon kai haka na mike na dauro alawa duk da tsoron da nake ji nakai kuka na ga Allah tare da neman tsari dani da yayana a gareshi. Wanan sallah danayi yasa na dan ji damuwan dake damuna ya rage min a raina sosai har na samu barci mai nauyi ya dauke ni a lokacin. Sai washegari da yamma baban su Abba ya dawo gida sai dana bari ya huta yaci abinci naga bashi da niyar fita da daren ranan. Nasamay shi da zancen maganan ciwon mahaifina dake cikin wani hali a gida. Fada ta hauni dashi don may ban fada mashi ba a waya na sanar dashi halin da babana yake ciki. Yace yanzun sai aga rashin hankalin shi na rashin buga mai waya ya tambayi lafiyan shi. Don ba za a san cewa bai gida bane a lokacin sai a ga kamar bai damu bane kawai da halin da yake ciki a can. Ni dai hakkuri na bashi kawai mutumin da kirikiri zan kirashi yanzu yaki daukan wayan idan ma ya dauka wani lokaci fada ne zai hauni dashi kan cewa yana tsakiyan aikin shi na damay shi da bakin kirana. Nan dai na bashi hakkuri tare da bukatan wani sati yara zasuyi hutu ina son zuwa gida na duba lafiyan mahaifina. A takaice ya bani amsa da sai yayi tunane akai kafin naji amsa ta. Haka na zauna tsawon kwanaki da zullumi iri iri a raina na halin damuwa da abu biyu ciwon mahaifina da anty lami ke cewa nayi kokari na shigo na gan shi da kuma zancen matsalan gidan mu na bamu kadai bane a gidan. Tare muke da mutanen da bamu gani kuma bamu san a ina suke ba ma gidan su. Matsa mashi nayi sosai akan zancen tafiyana wanda na tayar mai da hankalin shi haka yasa ya yanke cewa na shirya idan anyi hutun sai mu tafi. Amma ba lalai bane shi ya tafi tare da mu sai dai daga baya zai zo idan zamu dawo ta dauke mu idan hutu ya kare na yara. ****** ********* ****** Can gida kuwa Umma yakai ta tayar da hankaln ta har yakai ta fara zuwa gurin bokaye da malamai neman taimako wai na sake mata dan ta tillo daya yanzu sai abinda nace yakeyi. Haka take zuwa guraren malaimai wai a taimaka mata dan ta tadawo gare ta. Wasu su fada mata gaskiya cewa ba laifina bane halin shi daine ya sake nima hakkuri nake dashi a hakan. Wasu kuma suci kudin ta ba biyan bukatan da take so a gare su don ita takai kan ta ai. Nikan na shirya tsab daga sayen tsaraba tare da kayan da zai tafi dasu na sayarwa na a can idan na tafi don yanzu gaskiya Alhamdullahi ina da rufin asiri sosai akan harkan sana, ata da nakeyi. Basai na jira yai min komai ba don Hanna ta yi gaba da hankalin shi akan komai nashi. Saboda bata daukan abinda wasa akan shi kamar wani mijin ta can har shige shige takeyi don ta kara samun kan shi kawai. Wani guri idan ta tafi da sunana zasu ce mata tayi hankali da ni don idan ta matsa a kaina zata iya rasa rayuwan ta gaba daya don ba a banza nake ba. Haka yasa ta dan ja da zance na sai shi kawai take ta kokarin taga ta kamashi ta ko ina ta mallake shi. A kwai gurin wani malamin da ta tafi yana dubawa ya dago kai da sauri yace mata ke kin ko san da sunan wace kika kawo muna maza ki tashi ki bamu guri kada ki shafa min laifi. Idan kuma baki bari ba duk abinda ya samay ki anan gaba wallahi ki kuka da kanki don ma kawai an raga maki ne dayanzu sai buzun ki wallahi ko. Nan dai ta dawo gida cike da tunanen shi ita wanan matar ta Aliyu wata irin mace ce haka shu, uma da kowa ke tsoron yin aiki akan ta ne wai. Da yazo gurin ta take bugun cikin shi cewa wai matar ka halan waye baban tane yace mata diyar wani babban malami a kauyen mu mai koyar da almajirai karatu. Tace shiyasa haba ni dai nasan akwai wani babban al, amari a tare da ita kan. Yace al, amari kamar na may tace naga dai kana yawan son ta ne sosai har baka iya boyewa a ran ka. Yace haka dai kike gani yace zata tafi gida next week ita da yara don baban ta baida lafiya zasu tafi su dubo shi. Sai kawai tace Allah ya sa ma ya mutu mugun tsoho kawai kowa ma ya huta duk yabi a asirce mutane da mugun tsafin shi. Cikin mamaki yace mata kina da hankali kuwa hana tace ya mutu mana ubana ne halan ? Don kai an maka asiri baka san komai ba akai shine baka ganin laifin shi amma ina kai ina wanan matar taka yar kauye da ita kawai. Yace look Hanna duk abinda zakiyi kada ki fara ki zagi matata da yarana ko mahaifan don bazakiji dadina ba gaskiya. Tace don anzagi wanan tsohon mugun shine kake kokarin fada min magana may yake idan ba mugu ba munafuki kawai. Tsam ya mike ya dauki rigan shi yasaka yabar mata dakin tana kiran shi amma bai ko juyo gare taba don dama yayi niyar kwana a gurin ta ne ranan. Har mun rufe gida saboda yayi muna sallama cewa a gurin aiki zai kwana a ranan sai kawai gashi ya dawo yana buga gida na fito na bude mai. Bai ko tsaya takaina ba danake tambayan shi ya kuma dawo ne bayan yace yau a gurin aiki zai kwana gashi ban aje mai abincin dare ba. Ya shige zuwa daki ya canza kayan jikin shi zuwa jallabiya yafito falo gurin yara inda suke zaune suna kallon filin wasan yara. Na sake futowa daga kitchen ina tambayan shi a dafa mai wani abu mai dan sauki ne yaci. Yace no ki barshi naci abinci ko nikan na kyale shi naci gaba da harkokina da nakeyi na kawar da kaya tsakar gida komai na mayar dashi a inda yake. Nadawo falo na zauna muna waya da anty lami dake fada min wai wasu suna son a sayo masu atamfa mai kyau zasuyi ankon shi ne. Nace mata zan duba nagani idan da kudin da zai isheni zan sayo masu nazo masu dashi idan zamu zo din. Yana sauraren maganan da nakeyi sai dana kare nake ce mai amma sai naga ya kamata idan zamu tafi muyiwa Umma sayayya yan abubuwan amfanin ta. Ya juyo inda nake yana cewa gaskiya maryam banda kudi a hannu na don yanzun haka ma ina ta neman wanda zakuyi tafiya dashi ne. Nace amma Umma sai naga kamar ta dade baa aika mata da wani abin kwarai ba gashi kuma da kan mu zamu tafi ace bamu je mata da komai na azo a gani ba. Bai yi magana ba sai kaloon shi yakeyi Abba yana fada mashi yadda masu kamun kifi suke dubaran kama kifi a film din da suke kallo. Can cikin zuciyar shi kuma tunane ne yakeyi akan maganan da nai mashi na umma wanda yasan gaskiya ne na fada mai. Kwana kaman shidda ke nan da Umma din takirashi a waya tai mashi tas akaina amma yanzu gashi ni da kaina nake magana akan a taimaka mata kuma. Tausayin mu ne ya kamashi don yasan gaskiya bai muna dede daga mu har umma din kuma ni ban taba damuwa ba gashi ita umma a tunanen ta nice nake cinye mashi kudin shi ina mashi wayo. Shi yasa yanzu ya daina kula ta kamar yadda ya saba kulata a baya yana mata sakon kudi da yan kayan amfanin ta a gida. ****** ********** ****** Tun da safe musalin shidda saura karan wayan shine ya tayar damu daga barci. Ya dauka naji yana tsuki Hanna ce a layin yagani kaman kada ya dauki kiran amma sai ya daga cikin muryan barci yace hello. Sai yaji tana wani irin kuka cikin tashin hankali tana fada mashi wai yanzu aka bugo mata waya cewa mahaifinta ya rasu an samay shi ya mutu a dakin shi kuma lafiya kalau aka kwanta dashi. Don har gurin karfe goma sha daya na dare ana hira dashi da mutanen da suke haya a gidan su. Take zancen su na daren jiya ya fado mashi a rai inda takewa mahaifina fatan ya mutu kowa ya huta dashi. Allah da ikon shi sai gashi mahaifin ta ne ya mutu ba nawa din da tai ma fata ba. Da sauri ya mike yai wanka ya shirya ya tafi gidan gashi duk maganan da sukeyi a cikin kunne sukayi shi. Da zai fita kuma nasan cewa can gurin ta ya nufa duk da raina ya baci amma sai da ta bani tausayi sosai yadda naji tana kuka a wayan. Ya samay ta a cikin tashin hankali a gidan da take haya cikin gari don ita mutumiyar kafamchan ne ta dai shigo garine da sunan aiki kawai take bushe ayan ta da mazan banza irin ta. Samun Aliyun da tayi ta rike ne ma yasa ta dan daina harka da wasu mazan na daban can. Wanda ke fadin baida kudi sai gashi yana shirin tafiya kafamchan kai tsaye. Bai dawo gida ba ranan sai bayan sallah magariba ya shigo muna gida ya samu ina parking din kayan mu na tafiya da naje kasuwa na sayo a cikin manya manyan ghana most go. Nai mashi sannu da zuwa ya shige nikan naci gaba da shirina don banda gobe ne tafiyan mu insha Allahu. Nan ya shige bai fito ba kwantawa yay nima ban damu da rashin fitowan nashi ba naci gaba da abinda nakeyi kawai. Bai kara bi ta kan mu ba balle na san zancen tafiyan mu ina ya kwana a lokacin sai dai kuma ban fasa shiri ba naje saloon nayi kitso da gyaran jiki an kawo muna dinkunan da nai muna masu kyau ga kayan katin da na sayawa yara na masu kyau kala kala masu tsada da zamu tafi dasu. Da dare na tsura shi yana waya da wani abokin aikin shi yana fadin wai an mashi rasuwa ne a kamfanchan. Nan ma na gane cewa a garin kafancham take da zama ita don a zato na yar cikin garin kaduna ce ita. Yana ganina ya canza zancen da yake sai da na bari ya gama waya nake mashi magana akan tafiyan mu gobe da safe idan Allah ya kai mu. Nan yake fada dani wai ahi fa na matsa mai bayan ya fada min baida shiri akan tafiyan don haka idan zamuyi hakkuri har ya samu kudi wani karon mutafi muyi. Nace haba baban Abba bayan kowa yasan cewa zamu shigo yanzun kuma nace masu na fasa tafiya gashi a nan duk munyi sallama da mutanen arzikina cewa zan tafi gida. Yace to idan ke kin shirya ne sai ku tafi goben nace idan ka amince insha Allahu gobe tafiya ba fashi a gare mu da yardan Allah kuwa. Na fice a dakin raina a bace watau dan kudin da zamuyi tafiya dashi na fahinci sune ya kashe wa hana din. Gurin al, amarin mutuwan mahaifin ta shine yanzu yake min wani kamay kamay can dashi. Ranan falo nai kwanciya na a kasa tare da yarana duk da tsoron falon da nakeji banji tsoro ba a raina don bacin rai da nake ciki. Tun karfe hudu na tashi na hau shiri munyi wanka mun shirya ni da yara komai na adanashi wanda zai lalace na saka a fridge ko. Bakwai mun shirya na samay shi daki nace mun shirya ko yace ke nan tafiyan zakuyi ba zaki tsaya kigani ko zan samu kudin ba ko? Nace idan ka samu sai ka aiko muna dashi nikan zan tafi gida naga mahaifina yau ba fashi insha Allahu. Ya mike yana cika yana batsewa ya saka rigan shi yace muje ya sauke mu a tasha ni da yaran. Haka muka fito makwabta duk sunzo ganin tashin mu suna min adawo lafiya suna gaida mai jiki nace nagode muka kama hanya sai tasha ba wanda yaiwa wani magana a cikin mu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/4, 10:17 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👨‍👩‍👧‍👦 👩‍👩‍👧‍👧 BAMU KADAI BANE, , , , , 👩‍👩‍👧‍👧 👨‍👩‍👧‍👦 1⃣5⃣ Tafiya mukeyi muna ta bugun daji inda driver ke ta faman sharara gudu da mu a hanya muna cikin mota zaune hankalin mu a kwance sai faman tunane nakeyi a raina. Babu aabinda na fara tunawa sai irin halin da zan zamu mahaifina a cikin sa indan muka isa gida. Sai kuma tunanen yadda zamu samu Umma idan mun isa gashi baban Abba yana ta jaddada min cewa na tabbatar da cewa gida gurin Umma muka sauka idan mun tafi. Sai kuma daga karshe na fada cikin tunanen sabon bakon, yanayin da na tsinci kaina a cikin shi na hurda bakin fuskan dake zo min da tsigar mutanen boye. Tambayan kaina nayi shin mafalkina da mukkadarasiyyatu gaskiya ne koko just mafalkine irin wanda kowa ya saba yi as mafalki ya wuce. Abu biyu ya tsaya min araina shine zancen maganin da baba malam yabata tabani sai kuma kayan tsaraban da tace zangani nakai wa anty lami da babana. Yanzun ai ta haka zan gane idan mafalkina gaskiya ne don na kudiri aniyan zan ba babana wanan maganin na gwada na gani idan, zai yi aiki a kan shi. Zancen tsaraban da ni dai banga komai ba kamar yadda tace har na gama shirya kayana na wuto ba wani alaman sakon da nagani. Bamu isa gida ba sai ana sallah magariba muka sauka garin mu lokacin mutanen unguwan mu sun shiga sallah magariba. Umma ma mun samay ta daki ta tana sallah don bata san da zuwan mu ba a ranan. Nan aka shiga shigo muna da kayan mu manyan jakkuna ghana most go da sauran tarkacen kayan mu har jakka biyar da sauran abubuwan da nazo dasu don tsaraba dan amfanin mu nan gida. Jin hayaniyar mutane yasa Umma ra sallamay sallah ta fito tagan mu muna shigowa driver da ya kawo mu dan kwantagora don daukan motar mukayi dagani sai yara har gida ya kawo mu mukai sallama ya juya abin shi ya tafi. Nan umma ta shiga yi muna sannu da zuwa ta shiga dakin ta ta dauko key din dakina muka bude aka loda muna kayan mu cikin dakin. Fada takeyi yanzu ashe kuna hanya ban sani ba balle ai maku dan abinda zakuci gashi dare yayi yanzu ina zan samo abinda zakuci. Nace ba komai Umma akwai miya da mukazo dashi zasu ci bread dashi zai ishe su ai. Umma kan sai murnan ganin yan jikokin ta takeyi don gaba daya taga sun girma sun yi kyau dasu sosai. Sai da nai sallah na fito zuwa gurin Umma muka gaisa da ita tare da yaya bayan rabo. Badai yabo ba fallasa a yadda naga fuskan Umma din da akwai wani manufa dauke a fuskan ta. Tambaya ta jefo min cewa halan kun samu labarin rashin lafiyan malam ko ? Nace eh an fada min wallahi Umma hankalina bai kwanta ba yadda nake jin labarin ciwon shi yasa na matsa muzo mu gane shi yafi. Tace yanzu maryam dake da babana yadda kuka tafi kukai watsi damu haka kusan shekara biyu ake nema fa baku leko gida ba. Shi shiru ke shiru haka yayi daidai ke nan irin wanan abin nake gudun faruwan shi tun da farko yasa na hana tafiyan naku. Shiru nayi tana ta fada a yadda na fahinci fadan Umma laifina kawai take gani bana Baban Abba dan ta. Na dai ce ayi hakkuri umma abubuwan ne sai a hankali wallahi amma yadda kike tunane ba hakana bane. Yanzu ai dadade baiji baigani sai ke ke bidirin ki kawai da yan uwan ki komai nashi ya koma hannuki sai yadda kikayi dashi maryama. Maryam ki tuna fa ke ma watarana uwace kamar ni baku gudun alhakina ya kama ku ne wai ? Ace ina da da kamar babana amma abin duniya yana batun gagarana sai na je nema a makwabta. Duk wanda na fadawa cewa yaron nan bai min sakon komai yanzu ba yarda da zance na za, ayi ba . Sai aga kawai banda hakkurin ne na yana bani ban godiya ne kawai don na bata mashi suna. Nace Umma kiyi hakkuri kona fada maki ba yarda zakiyi ba amma yanzu baban Abba al, amarin shi sai hakkuri kawai. Haka zaki ce ai tunda ke ya rike maki kan maciji kina wasa da bindin sa badole ki fadi hakan ba tunda yana maki yadda kike so ke da yan uwan ki. Ku daiyi hankali da alhakina wallahi don idan ya tashi kama ku ban san yadda zakuyi ba da rayuwan ku don kuma kun haifa ba baki nake maku ba ni gaskiya nake fada maku. Yanzu dubi irin wanan shirgin kayan da kuka lodo saboda Allah amma ni dan abinda zaku tsakura ku turo min ya gagare ku. Na dai gane Umma tana ganin duk abindake gare ni na mijina ne wanda ita batasan cewa babu ko kwandalan shi ba a cikin bida na ba. Ban iya kwana ba nace zan tafi na duba jikin babana don ance kwanan nan jikin nashi sai a hankali sosai. Umma tace na bari da safe na tafi mana nace Umma bari dai tunda nashigo nadan je naga halin da yake ciki tukun. Ko Nusaiba ban dauka ba sai handbag dina na saka hijjab dina na fita na samu mashin na hau zuwa gidan mu. Nan na samu dukka yan uwana suna gidan don jikin baba na ya tsanan ta sosai kwana biyun nan. Yana cikin turakan shi sai nishi da kugi yake na ciwo na shigo da sallama na duk suka juyo suna fadin a, a maryam ashe kuna hanya tafe? Na kutsa kai dakin tare da basu amsa da eh yanzun muka sauka wallahi shine nayo nan don hankalina yana ga baba wallahi. Nan dai muka gaisa dasu tsatsaye na karasa har gaban baba inda yake kwamce ya dunkule sai nishi yakeyi. Nace sannu baba yaya jikin naka baba yaya ka kara ji kuma da jikin ? Ya bude udon shi da kyat ya dan dago kan shi yana kallona yace cikin halin ciwo maryama kin zone ? Nace eh baba sannu yaya jikin naka ka kara Ji kuma da sauki dai ko yace Alhamdullahi maryama da sauki kun shigo yaya maigidan naki da yara suna lafiya ko ? Nakai zaune jiki na duk yayi sanyi nake cewa duk suna lafiya baba da yaran ne ma muka zo nan ai sai dai suna gida na barsu a gurin umma ne. Nan dai kuma bai samu cewa komai ba ciwon ya taso ya dunkule guri daya yana nishi a cikin kugi kamar wani karamin yaro don wahala. Hakan yasa nasan cewa ba karamin jin jiki baba yakeyi ba sosai saboda yadda na san shi da karfin hali a baya. Duk na rude su dai sauran yan uwana sun saba ganin wanan halin da yake ciki sai sannu kawai suke mashi . Tsananin rudewan da nayi yasa na manta da zancen wani maganin da nazo dashi daga gurin baba malam. Sai da naji ana zancen wai an karbo magani a wani kauye a jika mai yasha ne abin ya fado min a rai. Naji mama tace aiko dazun an jika mai yasha amma kamar bai sha ba wallahi sai dai idan za, a kara jika mai ne yasha din kawai. Nan dai na yanke shawaran gabatar da wanda nazo dashi a gwada a gani ko Allah zai sa a dace. Nace cikin sanyin murya mama akwai wani magani da wani babban malami can da ya dauke ni a matsayin diya ya bani na kawo wa baba ai amfani dashi. Shiru naji sunyi ba wanda yai magana sai babban yayan mu ne yace to kawo a gwada bashi a gani nace amma yace idan za ai amfani dashi sai anyi alwala tukun za, a bashi dashi da wanda zai bashi din. Sai maman Aina tace ai yiwa malam alwala a wanan halin da yake ciki haka ? Yayan mu yace bari a gwada mai mana sai nima nayi na bashi mugani ko Allah zai sa a dace haka yadda suka ce din akayi akaiwa baba alwala tare da kma yayan mu yayi mai duk yadda nace ance ayi da maganin. Muna tsaye gefe daya muna kallon yadda baban mu yake wahala bamu da yadda zamuyi gashi ya hana akaishi asibiti wai yafi son ya cika a dakin shi idan ma mutuwa zaiyi yayi a dakin shi kawai yafi mai. Kamar minti goma da shan maganin sai ga zufa ya fara karyo mashi yana furta Alhamdullahi da bakin shi yace ya ji jikin ya fada mashi sosai. Bai kara wasu mintina ba sai barci ya dauke shi mai nauyi haka yasa muka watse a dakin don mu barshi ya huta ya samu barci a lokacin. Ganin dare ya soma nace zan tafi gida sai dai da safe idan Allah ya kai mu zamu shigo muka watse muna mai Allah ya nashi lafiya. Koda na fito lokacin dare ya soma yi sosai har yan mashin sun dan rage a titi don haka mun jima gurin bamu samu abin hawa ba. Sai can wani mai mashin yazo muka tsayar dashi na hau mukai sallama da yan uwa na don su da kafa zasu karasa gidan su don basu da nisa sosai da gidan. Mun dayi nisa da gida naji mai mashin din yace yaya jikin baban naki da sauki dai ko ? Cikin rashin damuwa nacd mai Alhamdullahi ya samu sauki sosai a zatona ko yasan ni ne nine dai bangane shi ba. Mun dan kusa da gida naji ya sake cewa ki fada mai ya daina fitowa zuwa ban daki da karfe biyu ya dinga barin sai zuwa uku da rabi ko hudu zaifi sauki da kariya. Nace kana gani fitan dare ne yajawo mashi matsala haka ko may yasa yake wahalan nan. Bai bani amsa ba muka iso kofan gidan namu don haka na sauka ban tsaya ba bita kanshi na ciro kudi na bashi amma yace na barshi kawai yaja mashin din shi ya tafi sai lokaxin na tuna bai bani amsa ba ya tafi. Dakin Umma na kwana ranan don dakina ba gyara ba zai kwantu ba a ciki hakana don haka muka kwana a dakin ta kawai ****** ********* ****** Washegari tunda safe na shirya sai gidan mu duk sakkon da nayi na samu yan uwana a gidan baba yana zaune a waje tsakar gida an mashi shimfida ya zauna ga kunu a gaban shi yana sha. Yana ganina yace maryama ashe kunzo ne sannun ku da zuwa yaya hanya yaya bayan rabo ? Nace Alhamdullahi baba yace ance kece kika kawo min magani daren jiya na sha na samu sauki haka ko ? Kenan ana nufin duk maganan da mukayi daren jiya babana bai cikin hayacin shi ke nan komay ? Nan dai muka dan shiga hira sama sama dashi duk da har yanzu yana jin zafin jikin nashi. Nace baba malam yace na gaishe ka da jiki sosai ko da zan wuto ban samu ganin shi ba yana wani aiki shiyasa ma bamu tattauna ba dashi sosai akan ciwon ka dashi ba. Yace maryama da alama dai kina ji da wanan baba malam din naki sosai gashi kuma da gani malami ne da yasan kan shi sosai. Don wanan maganin da ya bani akwai kyau sosai wallahi don ban taba shan maganin da naji dadin shi irin wanan ba tunda na fara ciwon nan. Gashi yau na samu barci sosai har sai da aka tayar dani sallah asuba. Cikin jin dadi nace ai baba baba malam dattijon kirki ne sosai wallahi mutum ne mai mutunci da son jama, a wallahi ya dauke ni tankar yar shi daya haifa na cikin shi. Sai dai kuma ina matukar mamaki yadda akayi yasan mama da ta rasu sosai har yace ne maka gaisuwan rasuwan ta. Da mamaki baba yace min yasan Amina fa kikace mutumin ? Nace cikin rashin damuwa kwarai kuwa baba yasanta sosai harda matsalan da ya samay ta sai da ya dan labarta min . Baba yace ikon Allah a can kasan aka samu mutumin da yasan Amina wacce duk rayuwan ta anan tayi shi bata san kowa ba, a can . Nace wallahi fa baba nima nai mamaki sanin hakan da yayi amma danaga babban malami ne shi sai ban kawo komai ba a raina. Baba yace Allah ya kyauta to nace Amin baba sannu da jiki yace yauwa sanu maryama Allah yai maku albarka na amsa da Amin baba. Sannu a hankali akaci gaba dayiwa babana maganin da na kawo mai shikuma Allah yana kara bashi lafiya sosai idan ka ganshi kasan yanzu ya samu sauki sosai a jikin shi. Ranan da hanna ta dawo kd daga makokin mahaifin ta tace tunda bani gari a gidan mu zata kwana don dakin ta ba gyara sai washe gari zata tafi ta gyara dakin ts da gidan da take ciki. Komai ya sayo masu na bukata wanda zasuci da wanda zasuyi amfani dashi da safe idan gari ya waye. Karfe takwasa suka shiga gidan don lokacin kowa yana cikin gidan shi ba ganin su za, ayi ba. Sunci sunsha suka yi wanka nan suka baje abinsu a falo suna kallo suna batun fara aikata masha , ansu. Daga bayan shi yaji kamar an kwashe shi da wani irin mari a bayan shi sai da ya gigice don zafi ya rike kumcin sa da sauri. Waige waige ya fara yi ko zaiga abinda yai mai wanan dukan haka da ba, a taba yi mai irin shi ba a rayuwan shi. Da sauri ya ja baya ya fada saman kujeran da yake zaune akai dafe da gefen fuskan shi. Take yaji jikin shi ba wani lakka a tare dashi sai wani bishi bishi yake gani a idanuwan shi na ya zube ya somay mata a falon. Hankalin Hanna yai matukar tashi ta mike da sauri ta debo ruwa ta zuba mashi amma bai farfado ba lokacin. Hankalin ta yai matukar tashi gashi daga shi sai ita a gidan ba kowa kowa yana cikin gidan shi gudu taso tayi amma sai kofan yaki budewa kuma. Gurin shi ta koma yana kwance a somay ta fara kiran sunan shi cikin tashin hankali amma shiru kake ji ba magana. Bulala taji an fara zana mata ana fadin gobe ki dawo gidan matan aure da niyar yin fatsikanci zaki kara fada sai da ta linkidu sosai ko ina jikin ta sai da shatin bulala yafito mata. Tana tsala wani irin ihu da karfin Allah amma babu maijinta don an toshe kunnuwan kowa da zai iya jiwo ihunta lokacin. Wani abu tagani mai wani irin tsawo ga hakora manya jikin shi da fuskan shi da jikin shi nan ta fadi ta somay itama. Bata falka ba sai asuba sanyi asuba yasa suka farfado duk kan su babu mai iya taimakawa wani a cikin su don kowan su ya gala baita. Da kyat ya iya mikewa ya nufi inda take kwance yashe yana tambayan ta may ya samay ta haka ? Bata iya bude baki tayi magana sai nuna gurin bango takeyi inda taga wanan abin da ya bata tsoro a daren jiya. Da kyat suka iya shiryawa suka fice a gidan a tsorace kowa da abinda yake nasawa a zuciyar shi ba mai ma dan uwa magana cikin su. Da kyat suka samu suka isa gidan Hanna din kowa hankali a tashe a cikin su. Suna shiga Hanna ta barke da wani irin kuka tana fadin dear ashe kasan gidan ka baida kyau kakaini don akashe ni ko? Cikin hasala shima yace gidana baida kyau koke baki da kyau tunda nake da iyalina ban taba jin komai ba agidan sai yau da kikaje min gida da naki masifan. Tace au haka ma zakace min dear duk da mutuwan da na tashi yi a gidan ka wani dodo ne fa nagani ban ko son na tuna kaman shi wallahi. Yace shoutup my dear don baki san ko ni may akai min ba akanki har zaki fada min haka ko yanzun haka idona ban ko gani sosai dashi don zafin marin da akai min. Dariya ya bata ta manta ma da abinda ke gabanta wai akan dan marin da akai mai zaice bai ganin guri da kyau. Itako da aikawa dan karsn dukan tsiya babu maceci tace may gawani mugun halitta da ya baiyana mata. Tace ba zan saks koda gigin zuwa gidan ka ba indai nice dama nace ma matarka ibilis ce gashi daga zancen mahaifinta ya mutu nawa uban ya mutu ba ciwon komai tare dashi. Yace will you stop dis rubish please duk kece gurin shegen shige shigen ki kika kwaso wa mutane wanan jidalin haka. Nan fada ya barke a tsakanin su ba karamin tashin hakali sukayi ba a ranan suka rabu baram baram a tsakanin su. Yafita daga gidan nata ranshi a bace gashi yana son komawa gida ko wanka yayi amma tsoron gidan nashi yake ji yau da kanshi. Office din su ya nufa hakana wijiga wijiga dashi babu shiri kowa ya gan shi sai kallon mamaki yake mashi yadda ya fito haka yau office babu shiri. Har yama abin duniya ya damay shi haka ya daure ya nufi gidan nashi a tsorace ko wanka ya dan samu yayi yaji dadin jikin shi gashi kuma bazai iya fadawa kowa abinda ya faru dashi da karuwan shi ba a gidan shi. Yana bude kofa ya shiga yaga komai tsab a gidan kamar babu abinda yafaru ba yadda ya barshi a hargitse ba a baya ba kafin su fita. Wayan shi ce tai kara yasa ya dan firgita ya jada baya ya ciro wayan noba tace yagani ya sauke ajiyan zuciya. Muka gaisa nai mashi yaya aiki ya amsa da kyat da Alhamdullahi ya tambayi jikin baba nace baba jiki Alhamdullahi ya samu sauki sosai yanzu. Har muka gama wayan naji shi ba yadda na saba jinshi ba kamar yana cikin wani irin damuwa yanayin shi. Na raya a raina kila baida lafiya ne ko kuma wani abinne ya samay shi kila. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/4, 10:17 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BAMU KADAI BA NE, , , 👨‍👩‍👧‍👦 👨‍👩‍👧‍👦 1⃣6⃣ ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI DAKE BUGO MIN WAYA SUNA NEMAN BAYANI YADDA ZASUYI REGISTER A SABON NOVEL DIN DA ZAN FARA KWANAN NAN. GA YADDA BAYANIN YAKE IDAN TA ACCOUNT ZAKI TURA MIN KUDIN REGISTER 300 ZAKI TURA MIN GA WANAN NOMBER DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK IDAN KUMA RECHARGE CARD ZAKI TURO NA 400 ZAKI TURO TA LAYINA NAGODE DA FATAN ZAKU FAHINCE NI MASOYANA MASU KAUNAN CIGABANA SAI NAJI KU NAGODE KWARAI DA HALARCIN DA KUKE GWADA MIN, , , , Tun tafiyan Aliyu daga gidan ta ta kwata jikin ta ba dadi sai ciwo yake mata ga wani zazzabi da ya rufe ta a lokaci daya. Da kyat kawar ta ta samu ta mike tai wanka ta kaita asibiti don a duba lafiyan ta. Har sai da Hanna, tai kwana biyu tana jinyar jikin ta ta samu sauki. Ga wayan Aliyu kota kira baya daukan wayan nata don ya dauki zafi sosai da ita. Sai dai kuma yana yawan mamaki sosai a cikin rashi na yaya akayi haka ya kasance a gidan shi gidan da yake zaune tare da iyalin shi amma su Allah ya kare mashi su daga duk wani mugun abu. A bayane ma farko Maryam ke yawan mai korafin baban Abba BAMU KADAI BANE A GIDAN NAN FA, Amma sai ya katse ta da sababi yana ganin wani sabon rigima ne kawai maryam take son dauko mashi ta aza mai yana zaman zaman shi. Haka yara suka dinga ciwo baji ba gani kamar ransu zai fita amma da tai magana yace ai don gurin sabon guri ne a gare su ya jawo hakan masu. Yanzu ma dai boyar Allah nan ya dai na jin ma tana mashi wani korafi akan gida lafiya lau take gudanar da komai nata a gidan. Gashi dan tafiyan su da yan kwanaki ya fahinci gidan nan da akwai abinda bai sani ba a cikin sa. Don ranan yai kokarin ganin ya kwana gidan amma abin ya gagare shi don tun da zai dawo gida ne misalin goma na dare da yake uguwar ana saurin shigewa gida gashi kuma lokacin sanyi ne take garin na kaduna yai tsit kowa ya boye don sanyi. Yana tafe yaga kamar abu ya gitta mai ta gaban shi yafito daga gidan su yar sokoto ya nufi bayan katangar gidan su ya kashe abin da hasken mota yaga ashe kyanwace bakakirin da ita sai idon ta da ke wani walkiya a cikin haske ba dadin gani sosai. Shiru yayi zaune a cikin motan yana nazari a ran shi na yadda zai fita ya duba ko may yagani a gurin ya gilma mashi. Ganin babu sarki sai Allah yasa ya daure yafito daga motan tafiya yakeyi zuwa step din da zai hau dashi barandan gidan shi amma sai yake ji ida ya taka daya kaman ana takawa biyu bayan shi gashi ya saka key ya bude gidan kofan gidan yaki saurin budewa a lokaci daya can sai ga wata mujiya mai rararan murya ta rangada kukan irin nasu jin kukan yayi har cikin tsakiyan kan shi lokaci daya yana fadin lah, ilaha ilah anta subbahanaka inni kuntu minal zallumin . Ya samu kofan ya bude mai da kyat ta fada gidan hankalin shi a tashe dashi yana hakki sama sama cikin tsoro. Yana zuwa ya bude frisge ya fara kwankwadan ruwan goran da ya jera acikin fridge din don zuwan Hanna gidan ranan. Basu yi amfani da komai da yasayo ba komai yana nan yadda ya barshi aje. Ganin ya samu ya shiga gidane ya samu guri ya zauna yana mayar da numfshi a hankali. Motsi sosai yake ji daga bayan back yard din gidan adduoi ne ya fara jerowa yanayiwa kan shi haka yasa shi dan samun sauki ga abinda yake ji. Sannu a hankali ya daina jin motsin yana kan addua har yaji zuciyar shi ya dan samu natsuwa, a rayuwan shi. Nan dai yai alwala yai sallah ya kwanta a tsorace ga bakin kiran layin shi da Hanna take ta yi mai amma halin da yake ciki yaki bari ya daga wayan shi. Can kuma hana sai ganin laifin shi rakeyi tana faman fada ni Aliyu zaiwa haka yana nufin zai watsa min kasa a ido ne ko may wallahi bai isa yace zai rabu dani ba a rayuwan shi sai nayi abinda na raba shi da wanan diyar malamai din da yake aure. Bayan ta samu sauki ta shirya da wata kawar ta da zata kaita wani kauye don ai mata aiki wanda zata samu kan Aliyu sosai sosai don sun yaba da aikin mutumin sosai a ran su. Suna zaune a cikin motar dayar kawar tace ta fara magana tace ai ni nai arziki ranan da nake dawowa daga gurin ki da nai dare baki ga abinda nagani bane wallahi. Sai Hanna take cewa kikai arziki ko ni nai arziki ni da gidan Aliyu aka tashi kashe baki ga irin abinda nagani bane wallahi sai driver Napep din dake tukin mota ta gaba yace mai kikagani haka har ya tsorata ki yar uwa tace bari kaidai ban san ma yadda zan maka bayani ba kai dai bari kawai sai sukaji yace may kika gani ne wai hajiya. Tace kai dai kawai bari na sha wuya wallahi ai dai nayi arziki dana samu kaina sai mai tukin motar ya juyo inda suke tare da fito da siffan shi a fili tare dacewa, Like dis👹 ? Gaba daya suka daga suna kallon shi ya bude baki hakkoranshi kamar kacan mashin fuskan shi kamar na wani halitta can take suka rude suka shiga tsala ihu. Sun dai bude ido sunga taron mutane a kansu ana tambayan ina suka fito don ba, a san su ba. A rude suke magana suna cewa a tare masu mota su hau zuwa gida sai a hankali suke kallon yanayin mutanen gurin ba irin yanayin mutanen kaduna bane da sauri kawar take tambayan inane suke nan wai aka ce masu suna kwatarkwashi ne yanzu haka. Gaban su yai mumunan faduwa suka rude gankalin su yai matukar tashi sosai dajin inda suke. Ga wani karon dute suna gani maigirma da ba iyaka a gefen su sai suka kara rudewa. Gurin maigarin aka kaisu sukai mai bayanin su daga kaduna suke sun shiga taxi ne zuwa wani unguwa shine suka gansu anan din. ****** ********* ****** Sosai na cinikin kayan da nazo gida dasu na sayarwa wanda haka ya tayar da hankalin Umma dake ganin yadda mata suke shige da fice a gurina Don sayen kayan kowa yana yaba kyawon su ga atamfan danakawo guda hamain ansaye kudi hannu an bani kudina don ban cika masu kudi ba har ana nema a kara guda talatin da dan kai. A cikin kayana naga wasu kunshin leda guda biyu wanda ban san dasu ba na bude don na duba sai na duba naga ashe atamfane guda biyu aciki masu masifan kyau dasu sai dayan ledan mai turare dan saudiya da dadumar sallah mai tsada acikin sa. Take na tuna zancen tsaraban da akace zan gani a kayana naba anty na Lami da babana nasu ne nagane kan sakon don haka na aje idan zan tafi nakai masu abinsu. Nan Umma ta shiga saka magana tana cewa yanzun kan ta sheda ita no kudin dan ta yake shiga watau nice nakarbe mai komai nashi nake juyawa don na fishi. Har yakai ta kira dan nata cikin fushi take fada mai bakaken magana duk yadda yaso ya fahintar da ita bata yarda da zancen shi ba. Yace wallahi wallahi umma babu ko kwandalana a cikin kudin da maryam take sana, anta dashi asalima ni ban san ida ta samu kudin ta ba ta dai ce min makwabciyar muce ta bata aron kudi take juyawa. Maganan shi bai sa Umma ta yarda dashi ba saima ta kashe wayan ta a karshe kawai. Na shirya ni da yara zuwa gidan mu wuni don tunda mu kazo ban samu zuwa mu wuni ba saboda gyaran gidan da nakeyi . Na samu mahaifina zaune a dakin shi bayan na gaisa da matan babana muka dan taba hira dasu na dauki ledan sakon shi zuwa dakin shi. Nan muka gaisa dashi yana dan wasa da yarana yake cewa mutanen kaduna kuna can abinku kun boye ko? Ya juyo gare ni yana cewa yaya shi maigidan naki kuma nace yana lafiya baba. Ledan sakon kayan shi na mika mai cikin ladabi nace baba gashi akace idan nazo na baka. Da mamaki yake kallon ledan yake cewa ikon Allah dagawa ke nan wanan sakon haka. Na gyara zama nace wallahi baba wata boyar Allah ce Allah ya hada ni da ita ban santa ba batasan ni ba. Sai dai haduwa da ita ya zama min babban alheri ga rayuwana yanzu. Baba yace dama haka duniya take idan Allah ya tashi ikon shi ga bawa babu mai hanawa . Yanzu kinga wanan ciwon danayi gashi mutumin da ban sani ba ya baki magani kin kawo min wanda shine makarun ciwon nawa. Nace yyawa baba raban wani mutum da ya daukeni da mashin nan kofan gida yai min wani magana akan ka. Yace na fada maka wai ka daina fitan dare misalin biyu zuwa uku na dare ka dan sahirta don lokaci ne na wasu daban ba namu ba. Ido baba ya tsura min yace maryama waya fada maki haka din ? Nace wani mutum ne mai mashin daya daukeni yai min wanan magana ni kuma gaskiya ban san shi ba a garin nan. Na kuma bashi kudin mashin yace wai na barshi saboda Allah ya sauke ni ya wuce abin shi. Maryama anya ba abubuwan uwarki bane kuwa suke bibiyan rayuwan ki ina tsoron kada ki gado Amina fa tun tuni don al,amarinki da siffan ki duk irin daya ne dana mahaifiyar ki. Nace baba idan zasu cuta min yadda suka cuta mata da bazan yafe masu ba gaskiya don irin yadda mama ta wahala kafin ta rasu ban taba mantawa da hakan a rayuwana. Yace Allah dai ya kyauta don kinga wanan magana da kika fada min yanzu ba wani mahalukin daya san shi sai ni da abin ya faru akaina. Ban kuma taba fadawa kowa shi ba balle nace ko maishi yaji ne a wani guri. Shigowan su anty Lami da yayan mu habbi bai hana baba fadan abinda yai niyar fadi ba. Yace na tashi wani dare don nai tsarki nayi alwala sai naga wata yarinya tsugune a tsakar gidan nan tana kuka. Nai mamakin yadda ga gida a rufe har tashigo gidan nan na haska mata toci ina fadin wanene a guein nan ? Bata daina kuka ba har na karaso inda take tsugune nace ke daga ina kike ne sai take ce min daga gidan malam mudi take ni dai a iya sani na garin nan ban san waye malam mudi ba. Nace may yakawo ki gidan nan kuma cikin kuka yarinyar ke fada min cewa tayi dare ne shine ta samu an rufe mata gida. Nace ke ko boyar Allah ina kika tsaya har dare yai maki baki koma gida ba nan dai nai mata fada kan ta kula da rayuwan ta daga karshe na saka ta gaba don nakaita gidan su. Ga mamakina a unguwar nan dai babu gidan sama amma sai naga ta runkari wani bene dani tace nan ne gidan nasu wanda sai an hau za, a samu kofan shi. Haka na daure muka hau sama da ita na buga kofan kusan sau uku aka bude kofan gidan. Mutumin da nagani ban san shi ba a garin nan nai mashi sallama tare da bashi hakkuri ta karbi yar shi ya daina fushi da yara wani kallo mutumin yake min kamar na tsana ban damu ba nidai hakkuri na bashi na juya don in sauko daga benen. Sai baba yai shiru tare da girgiza kan shi tace ashe ban sani ba gamo nayi don maimakon naga gidan sama sai kawai nagani a saman katon iccen kukan nan dake kofan gidan Tanko. Yaushe rabona da hawa icce koda karami ne balle irin wanan katon iccen haka. Da dabara da addua na sauko daga iccen lokacin har an fara kiran sallah asuba. Tun dana dawo gida zazzabi mai zafi ya rufe ni tun shine wanan ciwon haka ya sarke ni wanda ba, a san makarin shi ba sai da kika kawo min wanan maganin da mutumin nan ya bayar ki kawo min. Kinga ke nan akwai ayan tambaya ga bayanin da mutumin nan yai maki ranan ke nan ba mutum bane ta dauke ki kema a mashin din. Tsoro ya ziyar ce ni sosai da yake akwai yan uwa na a dakin sai ban fadawa babana halin da nake ciki ba a kaduna. Yanzu baba dama ciwon ka shafan jinnu ne gaka ashe shiyasa anata magani kamar ba, ayi ciwo sai gaba takeyi kawai. Baba Yace badon wanan maganan da maryama tazo min dashi ba yanzu da ban fadi wanan labarin ba har wani yaji don idan na fada gurin zai koma yana ba mutane tsorone. Mun dan dauki lokaci muna magana kan zancen ida baba ke kara fada muna abubuwan da zamu kiyayye kan jinnu kamar fita misalin sha biyun rana zuwa daya na rana haka kuma zubar da shara a wanan lokaci ko yin girki da rana tsaka da mata keyi da kuma lokacin da almuru yayi koda dakin ka zaka shiga ka dinga sallama a wa yan nan lokacin. Yace ai kinga kamar mahaifiyar ki da rana tsakane an aike ta tun tana karama suka shige ta. Shine dayake muggaine nata akwai mugu a ciki wanda ke yawan wahalal da ita shine yace sai idan zatayi bada magani zai kyale ta. Ni kuma ina zan yarda da wanan a gida tunda sai an kauce ma irin wanan sana, an nasu. Shine yakawo tunzuran zuciyar su har sukai mata illa ta rasu ta sanadiyan hakan. Amma tana da na kwarai tare da ita lokacin da abin ya faru da ita wai basu tare da ita sun tafi ibada shine har wanan mugun ya samu kafan yi mata illa haka saida tai wata daya baci basha ba barci kafin ta rasu. Anty lami tace kai gaskiya mama Amina ta wahala lokacin sosai wallahi ko. Don ban son jin labarin wahalan da mamana tayi saboda abin yana matukar tayar min da hankali sosai nace ma anty lami anty muje na baki sakon ki. Da mamaki take cewa sako kuma maryam dagawa ke nan nace daga anty na na kaduna mukkaddarasiyatu. Mukkadarasiyatu kuma suna sai kace sunan aljannu maryama ? Baba tace sunan su ne ai daji itace dai bata ganewa saboda tsigan da suke fito mata kawaine bata ganewa. Kai kaji baba kuma ina maryam zata hadu da aljanna tai hurda da ita kawai dai mutane ne dake saka sunaye yanzu any how. Ba karamin mamaki anty tayi ba dataga sakon tace maryama wanan zannuwan fa manyane super nace nima haka nagani anty don bata bani sakon tun can ba balle nai mata godiya tun can. Anty bata damu data tambaye ni ta yaya aka bani sakon ba sai murna takeyi tana sakawa mai sakon albarka ni kuma ban fada mata komai ba sai dai nabar zancen kawai a raina. Ga maganan da babana da yayi yanzu yana damuna a rai don hakka na kuddiri aniyar fada mashi komai don ya warware min matsalan daban sani ba. Sai da mukai sallah la,asar ne na sulale jikina zuwa gurin shi na samay shi ya jingina baya ga bango yana karatu. Ganina yasa ya sake fuskan shi yandan sauke littafin da yake karantawa na illimi dake a gannun shi. Yace zaku komane maryama ? Nakai zaune dakyau nace baba sai dan zuwa anjima dama dai nazo ne da wani magana dake damuna. Yace taufa nace baba kasan na fada maka run farkon zuwan mu kaduna abin dana fuskanta. Yace na sani nan na fara bashi labarin duk yadda abubuwa suka faru dani dakuma harkan sana, an danakeyi yanzu wanda nake ganin haske acikin sa sosai. Nace baba shine nace bari n fada ma ko zaka fahinci wani abu acikun magana ta. Yace cikin sauke ajiyan zuciya lalai maryama al, amarin ki abin dubawa ne sosai wallahi don haka ki bani yau zuwa jibi zan duba naga may nene matsalar taki ne hakan . Zanyi kokari nayi aiki akan matsalan ki ko Allah zai nuna muna gasken al, amarin naki don mu san abinyi akai. Kuma nagode da baki boye min halin da kike ciki ba kikakibarwa rayuwan ki matsalan ke daya har yai nisa. Nai sallama dashi bayan mun dan kara tataunawa da baba akan zance zuwa karfe biyar na yamma na shirya muka bar gidan na koma gida don yanzu ban yarda yamma kuma tai min a waje tunda har naji abin da babana ya fada da ya samu rayuwan shi. Mun samu Umma a gida tana jiran isowan mu a hasale wata makwabciyar mu ta zugata ta cika fam akaina ta dauki kudirin ranan sai tayi min tas akan cutar dan ta da nakeyi ina mashi wayau ina karbe mai kudi. Wai mahaifinane yai min asirin da na samu kan dan ta har na rabata dashi yanzu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU[11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👨‍👩‍👧‍👦 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE, , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 1⃣7⃣ GA MASU NEMAN LAYIN WAYA NA ZAKU IYA KIRANA DA WANAN NOMBA DIN SAI DAI BAN DA LOKACIN TURA WANNAN NOVEL DIN DAGA FARKO PLEASE KAMAR YADDA WASU KE BUKATAN HAKAN, , , 08036959257 INA DA SARAUTAR MATA DA ALOKACIN MUKE A KASA WANDA NA GAMA SU NA KUDI SU MAI SO YA BIYA YASHA KARATU DA KARUWA ACIKIN SA, , , , Muna shiga gida da sallama abakina tare da fadin umma sannu da gida mun samay ku lafiya ? Sai ji nayi tace muna fukan banza muna fukan wofi da ban wuni lafiya ba zaki ganni ne ? Dake da munafukin mahaifin ki mai maku tsubbu kuna cutan mazajen ku waiku diyan malami sai Allah ya tona maku asiri wallahi. Ni dana yafi karfin sherin ku ke da mahaifin ki wallahi maryama don Allah bazai baku ikon yin yadda kuka ga dama ba akan shi insha Allahu. Dama bayau ba nake jin cewa wai idan za, a kaiku aure sai an maku masan manta uwa kunci don miji ya manta da kowa nashi sai ku kadai. Ni da kuke ganina wallahi nafi karfin sherin ku balle jini na. Komai bazaki sakeyi wa Aliyu ba kai idan ma naga masa bata sure wallahi sai na raba auren ya auro min daidai ni wace zan iya juyata yadda naso. Duk fadan da Umma takeyi ina jinta don karshe ma a gaban dakina ta dawo ta tsaya tare dafa bango don naji ta dakyau. Nidai ban tanka mata ba don nasan rudin sgedan ne ke damun zuciyar ta yau ina zaune kawai a bakin gadona damuwa ya damay ni. Taci gaba dacewa dama tun farkon tafiyan ku nasan kulli ne munafukin tsohon nan yayi. Ya taso min nan da funtun nasihan shi don yaga zan wargaza mai shirinne ashe. Ai gashi yau sherin shi ya bishi da yakewa diyan mutane akan nashi haka zai kare a lalacen nan wallahi. Wanan magana da Umma tayi kan mahaifina shi ya bata min raina, ban san lokacin da nace wallahi Allah babana ba mugu bane kuma ba munafuki bane. Kuma ciwo ai yana akan kowa wallahi don mu munyarda da Allah shine mai sakawa bawan shi cuta aduk lokacin da yaso. Au zagina zakiyi maryam don na zagi munafukin ubanki in anyi magana yace wai shi na Allah ne. Karya na fadi ba asiri kukai wa gadanga bane ya manta da kowa sai ke kawai da diyan ki. Dubi tun zuwan ki garin nan yaran nan basu sake maida kayan da suka saka ba ajikin su sai sabbin kaya kuke sakawa kedasu. Gaiyan tsiya kawai gaiyyan na anya tun faeko kamar na sani naso hanashi auren irin gidan ku amma yanace shi sai yayi yau gashi da rana tsaka da raina da ladiya na kuna batun rabani da dana macuta diyar azzalumi kawai. Ta Allah bataku ba wallahi don sai na dawo da dana a hannuna yadda na saba na rabashi da sherin ku. Na fitowaje nace Umma kina daukan wa kanki alhakine kawai wallahi kuma ni ki daina zagin mahaifina da baici ba shaba akan daki. Wai ma wani danki kikewa wanan halakon haka badai dan naki macuci wanda bai san darajan iyalin shi ba wanda karuwai birni suka daukewa hankali akan kowa. Don kawai ina hakkuri dashi ina kokarin boye sirin shi don ko banza uban diyanane. Yadda kike ganin ya cuta maki muma haka ya kwashe mu yakai garin mutane ya watsar damu can don Allah ya rufa min asiri ban wulakanta ni da yaran yadda kuka so ganin mu ba kedashi. Shine yanzu bakin cikin ki damu umma ? Kaya kuma da kike cewa yara na sakawa na dauka alfaharinki ne hakan ai ba bakin cikin kin ki ba. Ni idan mata uku zaki aurawa Aliyu ba abinda ya damu maryama don ga Allah na dogara baga danki ba Umma. Kuma ki tambaye shi idan yabani Naira biyar din shi tunda muka taka garin kaduna dashi dasunan karuwana ko taimaka min sai wani abu. Don haka ki daina zagar min ubana dake fama da kanshi may danki ya ke bashi balle zargi ya biyo baya kuma? Umma tace wallahi koma may ye ai ba fadi zakuyi ba kuma sai kungani wallahi. Nace muga Alheri idan bamu da amanan ki sai dai wanda yabimu da mugun nufi yagani ga rabon shi wallahi na yarana a lokacin duk sun gudo sun dawo gareni don basu son tashin hankali. Sai cewa suke mama please live her alone don't fight with grandma please. Au zagina ma kuke waiku ga diyan nasara ko to nasara yaci abu kazan uban shi ni da naga mungun park karshen jankune ke nan. Ta juya a dusace zata shiga dakin ta cikin fada aiko kamar an wullo ta daga baya ji kakai kucaaa ta fadi kasa da karfi ta yanka wani irin ihu mai razana mutum. Ban tsaya ta kan ta ba na dauki buta zuwa alwala abina na share ta kawai nan don tai marukar bani haushi da mamaki yau. Yadda ta rufe idon ta tana zagina da mahaifina son zargi kawai da take muna kan abin duniya. Bayan da zanzo sai dana kashe mata kudi yafi dubu hamsim amma duk bata gani ba ita. Koda na fito na samu bata furin taja kafa zuwa daki nai alwalana na shige dakin na tare da yarana. Sai da na idar da sallah na kira dan anty lami ga waya yazo ya sayo muna abinda zamuci nida yaran ranan . Yaeon bai dade ba yazo na aike shi sai gashi da drinks snacks da nama na bashi dari biyar ya tafi yana murna. Nan mukaci mukasha muka kwanta abin mu har na kwanta nafito na rufe gida abina na kulle kofana sai safe. Yaron anty da yaje ne take fada mata cewa yana ganin ba lafiya gidan mu don yayi gaida Umma yau bata tanka mashi ba nima yangani raina a bace. Haka yasa tunda safe sai gata gidan mu har lokacin da na fito nai sallah banji motsin umma ba ni kuma ban bi ta kanta ba da zan muna abin karyawa ne na dan tsaya daga kofa ina mata ina kwana ban damu da ta amsa min ba na wuce kitchen abina kai tsaye na dora girki na. Sai bayan nagama tea ne na hada muna na zuba mata nata a jug naba Abba ya kai mata dakin ta. Shine yadawo yake fada min wai grandma is sick today Nasan bacin ran maganan jiyane kawai yake damunta a rai don haka ban tsaya bin ta kanta ba naci gaba da gyaran gida kawai. Shigowan Anty lami da sasaafe haka gidan mu yasa naji wani irin a raina muka shiga daki muke gaisawa da ita. Sai take tambayana ko may ke faruwa tsakani na da Umma ban boye mata komai ba na fada mata duk yadda mukayi da Umma jiya. Tace an ma matan nan dama abinda suke fadi a gari ke nan akan mu tunda sunga muna zaman hakkuri a gidajen mu da mazajen mu. Nan dai muka kara dan taba hira tana kara bani hakkuri take cewa ba anga Allah ya daukaka ki ba ai yanzi ki dinga jin zargi tako ina yana tashi akan ki sai kin toshe kunnuwan ki. Don kowa da irin abinda zai fadi saboda haka duniya ta gada dama da anga Allah ya rufa ma asiri sai an samu sherin da aka lakakawa mutum. . Da muka fito zata tafine ta tsaya daga kofan Umma tana gaida ita mukaji shiru bata amsa ba har ina cewa tazo kawai ta tafi da hannu. Sai ta daga labule kofan a hankali salatin danaji ta saka ta fada dakin yasa na mara mata baya hankali a tashe . Umma ce kwance cikin amai da zawo kace kace bata ko iya daga hanayen ta a lokacin. Hakali a tashe muka taimaka mata da gyara mata jiki muka nufi asibiti da ita. Nan aka bamu gado dole na shiga jiyar umma ba shiri nida yan uwan ta duk wani abinda za, a kashe nice mai bayarwa. Nakira Baban Abba yafi a kirga karshe ma a gabanta tanajin yadda yake min fada a cikin waya wai yaya nake son yayi shi fa baida ko kudin da zai kawo shi gida yanzu idan taji sauki mu mayar da ita gida kawai acigaba dana gida a gani. Naga lokacin da Umma ta lumshe idon ta nasan bakin ciki ne ya kumay ta a lokacin. Kwanata biyar a asibiti aka sallamota gida sai dai bata da lafiya har lokacin sai dai likita yace baiga abinda ke mata ciwo ba shi. Haka naita dawai niya da ita a gida amma ba wani sauki atare da ita saidai kawai ta daina amai da zawo sai dai ba baki kawai sai ido da take bin mutane dashi. ****** ********* ****** Zaune nake a gaban mahaifi na wanda zuwa yanzu ya samu sauki sosai na jikin shi. Dan shiru ya biyo baya kafin yai gyaran murya yace maryama nayi duba sosai kan al, amarinki wanda sai dana dauki tsawon lokaci kafin na iya warware al, amarin naki. Al, amari ne wanda ke cike da abin tsoro da al, ajabi acikin ga duk wanda yaji labarin ki. Shin maryama ko kin san kin hurda da mutanen boye kuwa ? Da sauri na dubi gefen da nake zaune kaikace ko akwai wani zaune a kusa dani a lokacin. Baba yace maryam Allah yai maki gyadan dogo a rayuwan ki da ya hada ki da aljannun kirki a rayuwan ki. Nace cikin wani murya na mamaki baba aljannu kuma yace kwarai kuwa maryama da jinnu kike hurda maryama. Shiru mukayi daga ni har baba din babu wanda yai magana kowa da abinda zuciyar shi ke kiyarsta mai a lokacin. Muryan babane ya katseni yana fadin ki kwantar da hankalin ki don munyi hira da baban naki sosai. Mutumin kirkine don ko a cikin jinsin su daban yake malami ne yana da ilimi sosai mai tarin yawa yasan darajan bil, adam sosai. Ya fada min dalilin taimakon ki da yakeyi wanda ba lalaine ni na fada maki ba don yanayi ne saboda Allah. Ke kanki maryama kin sai mutunci a gare su sosai don irin alherin da kike masu yakawo yarda da kauna a tsakanin ki dasu. Yanzun dai matsala daya ce shine idan kina son kanki da arziki duk dokikin daya fada maki kafin ki fara sana, a ki rike su don kariyan ki. Sun fada maki abinda basu so a gidan Alhamdullahi don kin kiyayye komai wanda hakan ya kawo taimako a gare ki don rashin masu taurin kai. Ko anan da kike yanzun haka a tare dasu kike don sunce bazasu bar ku ke da yan uwanki jinin Amina kuyi kunya ba sai idan ku kuka kauce wa dikokin su. Ki daina wanka da rana tsaka ki ki kuma kaucewa yin girki da tsakiyar rana wanda kuma gaskiyane. Mu da ba haka matan mu sukeyi ba yanzun ne mata suka lalace da kiuya son jiki zai sa mace sai rana yai tsakiya tace zata dora girki a gidan ta. Wanda bamu kadai bane a gidajen mu ba sunfi mu yawan jinsi saboda su basu mutuwa kamar mu, haka yasa sukafi mu yawa. Duk wanda yai niyar cuta maku sai ida karfin su ya kare gurin taimaka maku koda kuwa a cikin jinsin su ne. Don su na tare dake junsi ne masu martaba a cikin jinsin jinnu . Kinga ashe abin naki bana wasa bane ko ita uwar mijin ki ba komai ke wahalar da ita ba sai mutanen naki. Don ta bata maki rai ahine sukuma suka taba ta don su nuna mata kuskuren yin haka. Don haka ina mai rokon ki da ki daina fushi da mutane don kada kija wa mutane wahala. Saboda dazaran an taba ki su ko sai inda karfin su ya kare akan mashi gurin daukan maki fansa. Gidan ku yanzu lafiya bake ba har makwabtanki kuna a karkashin kulawan su ne akan ki duk suke wanan alherin haka. Maryama kinyi arziki don kinyi taraiya da jinsin daba naki ba har birnin su kike ziyara ba tare da kin sani ba. Amma don su dakatar dake da wahalan tafiyan da bakin mai nisa kikeyi ba yasa suka dakatar dake daga hakan. Ta hayan nuna maki ko da suwa kike hurda amma sai dai kurciya bai barki kin fahinci komai ba akai. Yanzu baba ashe ba mutanene nake zuwa gurin su ba dama ? Ba mutane bane maryama da jinnu kike hurda ba yan adam yan uwan ki ba da kika sani. Nashiga uku baba aiko na debowa kaina magana ke nan ban sani ba. Yace hukuncin Allah ne hakan maryama ai bake kadaine irin wanan ifitilain ke fadawa ba akwai ire iren ki da yawa da haka ke faruwa dasu sosai kuma babu abinda ke faruwa sai alheri kawai ke samun su. Don haka yadda suka rikeki amana ke ma kiyi kokarin rike su amana din sai dai duk abinda zakiyi kada ki yarda da hanyan kaucewa a rayuwan ki . Addinin ki yazamo gaba a kan komai da da zakiyi kada ki bari wani abu na kaucewa ya shafi addinin ki ko kadan don gujewa sabawa Allah. Duk da suma musulmaine kamar mu amma dole ne asamu wasu da ba su da rikon Addini sosai a cikin su suyi kokari ganin kin sabawa mahaliccin ki. Nace da sauri insha Allahu baba bazan yarda na sabawa mahaliccina ba koda kuwa zan rasa rayuwanane ta hakan. To Allah yai maki albarka ya tsare muna ke daga duk wani masheranci abu mutum ko aljan ko dabba ko kwaro dama abinda bamu sani ba ma. Na amsa da Ameen baba yace amma malam din yace min yana da kyau duk ranan jumna, a ki samu wani abu kiyi sadaka daga cikin wa yan nan abubuwan daya lissafo min kamar haka. Masa ko kosai ko kulikuli ko sugar ko sai abinci wanda akafison kibawa mubakaci don kariya. Bake ba duk wani musulmi ana son yai daya daga cikin wanan sadakan idan da halin yin haka ga mutum. ****** ********* ****** Baban Abba yana zaune a office akakirashi da waya cewa gasu Hanna acikin wani hali an kawo su a cikin wani hali mara dadi. Kamar kada ya tafi amma wata zuciya ta rudeshi da ya tafi ya dubasu yaga halin da suke ciki. Yadda ya samay su ne ya tayar mashi da hankali sosai don haka ya shiga ya fita asibitin gurin ganin ya taimaka masu ga halin da suke ciki. Don abinda taimai yana aiki sosai a zuciyar shi baibarsu va saida yaga ya shiga yafita komai kanmala yabar asibitin. Shi da kanshi ne ya kiragidan su ya fada masu halin da yarsu keciki duk wani lalurar asibiti shi yayi da kudin shi. Wayan da ya isheshi ne na mutane dake kiranshi akan rashin lafiyan Umma yasa ya shirya yazo gida. Yadda ya samu umma baiji dadin ganin halin da ya samay ta aciki ba, don ba karamin jin jiki umma din takeyi ba. Sai bayan fitan shi ne ya samu labari wai sanadiyan ciwon Umma fadane tayi sai ta fadi shine hakan ya samay ta. Wanda ba gurin wani ya samu wanan labarin ba sai gurin yaran shi daya fita dasu yawo suke fada mai abinda ya faru. Hankalin shi yai matukar tashi ya juyo gida ya samay ni a daki ina ba Umma abinci guri ya samu ya zauna yana cewa Maryam fada min may ya kawo sanadin wanan ciwon haka na Umma ? Shiru nayi naci gaba da bata abincin da nake bata jin nai shiru ne yasa ya kara tambayana kamar farko. Nace nidai ban sani ba kawai dai tagama fada ne tazo zata shiga daki ta fadi shine kawai abinda na sani. Fada min duk yadda abin ya faru please ban boye mashi ba na kwashe duk fadan da mukayi da Umma din da abinda ta fada min kan fadan da yadda ta fadi kasan harta samu wanan sanadin haka. Cikin wani murya yace haba haba Umma may yakaiki wanan aika aikan haka na fada maki babu kudin da naba maryam tun farko yanzu gashi alhakinta ya kamaki kin jawo wa kanki wani sabon matsala kuma. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BANE A 👨‍👩‍👧‍👦 👨‍👩‍👧‍👦 1⃣8⃣ Ganin yadda jikin Umma ya tsanan ta sosai ba wani sauki kuma gashi naga yana shirin tafiya. Yashigo dakin ya samay ni ina shafawa Umma magani da wani mutum ya bayar ai mata. Ya dan jima a tsaye yana kallon yadda nake mata da maganin batare da yai magana ba. Nice na kawar da shirun dakin nake cewa amma dai da Umma zamu tafi ko ? Ban gane da Umma zaku tafi ba kina nufin na dauke ta haka zuwa kaduna da ita. Nace to a gurin wa zamu barta ke nan idan mun tafi din mu ? Ke dai zaki zauna da ita ba ida zaku tafi ku barta a haka ba lafiya ita kadai. Murmushi nayi nace idan na zauna nan karatun yaran kuma fa yaya zai kasance ? Yace su dawo nan da karatu su mana ai masu register a Benjamin school. Shiru nayi don wani sabon balai dake shirin taso min kuma ke nan anan don ba zan taba yarda da wanan shawaran nashi ba. Har yakai kofa nace da Umma zamu tafi mukaita babban asibiti a duba muna lafiyan ta a can. Kina da kudi duban ta ke nan a can nace Allah zai hore muna insha Allahu amma zaman ta haka batare da mun san may ke damun lafiyan ta baiyi ba. Bai kara cewa uffan ba ya sa kai yafita daga dakin akarshe ma yama bar gidan baki daya yafice abin shi. Ina kokarin mikewa naga umma tana hawaye daga idanuwan ta haka yasani komawa na zauna kusa da ita ina cewa haba Umma ki daina saka damuwa haka a ranki insha Allahu zamu tafi tare dake can a duba lafiyan ki yafi zaman ki haka a gida dakikeyi ba, a san kan ciwo ba. Kiri kiri ya shirya ya tafi ya bar mu sai dai ban mashi magana ba don cewa yayi idan hutu ya kare zai dawo ya dauke mu. Haka ya koma yaci gaba wahal da kan shi akan hanna ga mahaifiyar shi da zai tafi dubu biyar ya bayar akan idon ta tagani kuma. Hankalina ya kasu gida biyu ga gurin mahaifina ga kuma Umma da ba lafiya komai na rayuwa nice ke yi mata shi yanzu . Yau sati biyu ke nan ga lissafina da komawa makarantar yara gasu zaune min a gida ba karatu sukeyi ba. Kudin da yace zai turo ma asakasu a makaranta nan Auna babu su babu dalilin su ga wayan shi ma sai yaga dama yake kiran gida. Koshi daya kira zai tambayi yaya jikin Umma dana fada mai halinda take ciki zai ce Allah ya sauwaka kawai ya kashe wayan shi. Ranan na gama sallah ida nai sallah ina zaune kamar barci ya dauke ni sai ganin anty mukkadarasiya nayi a gabana zaune tana min murmushi. Tace maryama kinzo kin zauna nan kin watsar da karatun yaran ki mijin ki fa bawai yadamu da halinda kuke ciki bane saboda shu, umar matar nan da yake tare da ita ko yaushe. Duk abinda kikeyi gobe goben nan ki shirya kibar garin nan ki koma gidan ki kada yaran ki su samu matsala. Zaman ku acan shine alheri a gare ki idan kn zauna nan zaki iya fadawa dake dasu cikin wani hali kada ki damu nasan zaki iya kawo kanki gida amna dai wanan ba matsala bane zan san yadda nayi akai kawai. Sai kundawo kawai tace min ta mike tana murmushi tabar dakin sai na falka firgigit dani barci nayine ko may wai ? Ina tambayan kaina don dai nasan koda barci ne ban kai minti biyar ba ma dayin shi kuma na tashi. Kamshin da naji ya gaure dakina bawani kamshi bane sai kamshi da gidan muna kaduna yakeyi ko yaushe. Wanda nidai nasan ban faye amfani da turare ba amma sai kaji gidan ko yaushe yana kamshin dadi idan ma mutane sun shigo sukan ce na san masu turaren da nake amfani dashi mana. Sai dai nayi dariya kawai don dai ni nasan ban amfani da komai gaskiya. Abinda ya fado min a raina shine maganan baba watau dai ya tabbata da jinnu nake hurda ke nan a rayuwana. Idan ko hakane dole ne nakoma gurin mahaifina naji shawaran shi don dai abin ya fara bani tsoro wallahi ko. Na shirya na leka dakin Umma ina cewa Umma zan dan fita yanzu zandawo insha Allahu. Ban tsaya ba sai gidan mu na samu babana na fada mai komai yadda mukayi da bakuwana da kuma abinda naji a dakina bayan tashina. Nan dai baba ya nisa tare dacewa maryama al, amarin naki ne sai taka tsantsan wallahi don dai abin akwai daure kai a cikin sa. Ni yanzu bazan hanaki bin mijin ki ba don ban san matsalan da suka gani ba a hakan . Don idan kinga haka akwai matsala kenan da suka hango suna son su warware maki shi ta cikin sauki. Don haka ki shirya goben ku kama haya kutafi sai dai don Allah idan kin tafi banda fitana duk abinda zaice kiyi hakkuri da halinsa har Allah ya warware maki komai insha Allahu. Nace insha Allahu baba bazanyi wani fitina ba da yardan ubangiji zaka samay ni mai biyayya tare dani. Baba yace amma dai da ita uwar naku zakutafi ko don in kun tafi waye zai zauna da ita nan din ita kadai cikin wanan halin haka. Nace baba da ita din zamu tafi gaba daya gara ma taje taganewa idon ta ko ta daina zargina hakana. Yace a dai ta hakkuri da jama, a don gujewan shiga wahalansu don da zaran kinyi fushi akan mutum zai iya haifar da daukan fansa akan mutum batare da sanin ki ba. Nace insha Allahu baba zan tsare da yardan ubangijin mu Allah. Nai sallama da babana nakawo kudi nabashi nace ya rike a hannun shi bayan kwana biyu zanyo mashi sako. Nafito na sallami mutanen gidan mu ina sheda masu cewa zan tafi gobe idan Allah ya kaimu. Nakawo abinda zan basu na basu suna godiya suna saka min albarka da fatan Allah ya tsare hanya. Tare da kanne na su biyu muka dawo gidan sune suka tayani shirya kayan mu Anty Lami ma tazo bayan na fada mata zancen tafiyan mu sai gata da saurinta tazo. Naima kanne na da yaran uan uwana kyautan kayan tufafin mu da mukazo dasu da zuman idan mun koma zamu sai wasu acan insha Allahu. Yayan mu yai maganan motan da zamu shiga wanda shatan shi za, a daukan muna har kaduna din. Har Umma da yara sai dana shirya komai don da safe da mun tashi sai tafiya kawai da zamuyi. Karfe shidda da rabi driver har ya iso kofan gidan mu yan uwa suka taru akan mu mun bar gidan hannun kanin Umma yace dan shi ne zai zauna a gida don ya fake muna. Suna daga muna hannu muka kama hanya inaji wani iri a raina na rabuwa da dangina jini na da zanyi mu koma cikin waau nauin mutane da ba kowane zan iya tatance jinsin shi ba acan don rayuwan dana fada ciki yanzu. Tafiya muke munyi nisa sosai da gida sai motar ta kiya muna driver yayi iya kokarin shi amma motar taki tashi. Ganin zai bata muna lokaci ne yasa shi cewa ya kamata ya samu wata motar yai muna juye dashi mu tafi. Ya tsare mota sun kai biyar ba wanda ya tsaya har mun debe rai ga tafiyan don rana ya somayi muna gashi ba wani nisa sosai mukayi da gida ba a lokacin. Sai ga wani driver tafe shi kadai cikin wata lafiyayan mota dashi ya sanya kira, a yana tashi. Driver mu na farko yai wa mutumin bayanin komai akan abinda yakeso damu driver motar yace shi har gaba ma zai tafi don jos zai tafi kwaso wasu kaya acewan shi. Akai muna juye muka kama hanya nai mashi fatan Allah yasa motar tashi ta tashi yace amin hajiya nagode Allah ya tsare hanya yakaiku lafiya nace amin Ragowan kudin da sabon driver mu yaiwa na farko abin akwai ban mamaki don bai karbi koda rabin kudin shi ba ma. Nashiga da addua ta tare da yaran muka dauki hanya sai faman sannu kawai nakewa Umma dake a cikin wani yanayi najin jiki a lokacin. Bamuyi wani nisa sosai ba kowa a motar cikin mu barci ya dauke shi sai driver motar ne kawai ke sharara gudun shi. ****** ********* ****** Ni dai a sani na koda barci nayi baifi na awa biyu ba ma kuma ga kaida sai karfe hudu zuwa biyar zamu shiga garin kaduna din . Amma wai ina bude idona nagan mu a unguwar kawo da sauri na zabura na mike zaune da kyau har a lokacin kira, a ne ke tashi a cikin motar inda driver ke bin kira, an a hankali shima. Cikin wani muryan mamakine nace inane nan don Allah dai malam ? Yace kawo muke mana nace hasbunallahu wa,ni, imal wakeel. Ban kara tsinkewa ba sai da naga driver ya sha titin da zai kaimu uguwar mu ba tare da nace mai uffan ba. Nace a raina bari naga iya fudun wanan mutumin dai a karya. Sai shiga kawai yake hanyoyin da zasu sada mu da gidan mu kawai ina bayan mota tare da Umma ina kallon ikon Allah. Bakin get din shiga easthe din mu driver ya ja motan shi ya tsaya kallon mamaki nake mashi kawai ga tsoron daya kamani har a fili. Bai min magana ba nima haka din sai cewa danayi duk da naga mutumin ustazu ne shi bai son magana da mata don bai muna magana ba tun shigowan mu motar tashi. Nace malam kai wanene please ? A ina ka san mune wai da har kasan inda zamu tafi ne wai nifa ban ganewa wanan tafiyan na mu ba fa ? Kamar bai son magana cikin murya kalar ta larabawa yace ni kanin kawar ki ce itace tace na rage maku hanya ai tai min kwatancen gidan ku kuma. Kawata wata kawata ke nan yace idan kun hadu zatai maku bayani da kan ta insha Allahu. Nace muna da kaya sai ka karasa damu don Allah kaga kuma mamana bazats iya tafiya ba da kanta. Yace insha Allahu kawai yaja mota sai kofan gidan mu nan ya sauke muna kayan mu yaja motar shi yabar mu nan a tsaye cikin mamakin shi. Ina faman nanatawa a raina kawata to wata kawar nawa ke nahiyar mu kuma har tasan gidan mu haka anan. Na dauko key din gidan dake hannuna acikin jakata don dama nasan da wuya mu samu baban Abba a gida idan mun isa. Na bude gida nice nafara shiga ciki da sallama na wanda yarana ma sun saba shiga guri da sallama don jin ko yaushe ina yi idan zan shiga guri. Gidan fes yake ba wani kazan ta ko ina a gyara sai walkiya yake yasha gyara sai kamshi ke tashi kawai ko ina na gidan. A raina nace ikon Allah ashe baban Abba zai iya gyara gida haka kamar mace. Na zaunar da Umma a saman dogon kujeran dake falon na juya na shiga shigowa da kayan mu dake kofan gidan dake bude. Sai dana gama shigo da kayan na bude fridge na dauko ruwa na kawowa yaran da Umma suka sha. Muna nan nace bari na zuba masu abincin dana dafa muna wanda da niyata muci a hanya Allah bai nufa muci din ba. Muna gama cin abinci na umurci kowa yaje yai sallah don lokaci yayi na sallah azahar lokaci sai mamakin yanayin tafiyan mu kawai nakeyi a raina. Inda nai sallah naiwa umma alwala itama tayi sallah nazauna nan barci ya dan kwashe mu lokacin. Can cikin barci naga mukkadarasiya tana muna sannu da zuwa tare da labarta min ai kanin tane ta tura ya dauko kuma itace tasa motar ya lalace don a dauko mu batare da mun wahala ba sosai. Tace wai ke maryama sai taushene zaki daina tsoron mu ne dakikeyi haka? Firgigit na falka naga kowa barcin shi yakeyi banda Aisha da bata a cikin falon lokacin. Take mafalkina ya dawo min a raina ina kallon kofan shigowa gidan yana a rufe kamar yadda yake da farko kafin na kwanta. Nakai dubana akan kofan back yard din mu nagan shi abude da sauri na karasa kofan. Aiko na hangota a cikin rana tayi zufa zufa da ita sai wasan ta takeyi ita kadai a cikin rana tana suraitai tana awon ruwa a wani goran room fresh tsoho. Nace ke Aisha taso ki cire kayan jikin ki ki saka masu sauki kin hada wani uban zufa haka a cikin rana ku bakujin zafin rana ne wai ? Jin muryana yasa yarinyar kaduwa sosai tamike dasauri a tsorace nace jiki sake kayan jikin ki hakana kada su baci. Tace mama idan na sake nadawo nayi wasana nace ki dawo Aisha amma kuma rana yai yawa yanzu ki bari anjima ko ? Sai bayan munyi sallah la, asarne naba Abba tsaraba yakaiwa anty Hauwa da yar sokoto sai lokacin ne suka san dawowan mu garin. Da yamma nai muna girki har dare mukaci muka jona kallo baban Abba bai dawo gidan ba. Ganin dare yayi yasa na kulle gidan kawai washe gari na shirya yaran nakaisu makaranta da kaina don nai masu bayanin rashin dawowan su da wuri. Har na dawo na samu umma idon ta biyu ta kurawa tv dake aiki ido kawai nace umma na dawo ba lalaine ta amsa min ba nace ko akwai abinda kike sone Umma batace komai ba sai mumushi kawai da tayi. Muna nan dai zaune namike na dora girki nai muna jeloup din shimkafa yaji kayan lanbun da nasayo dana fita. Har kwana uku da dawowan mu sadauki bai dawo gidan ba nima ban nwmay shi ga waya ba balle na sheda mai aishine ya kamata yakiramu yaji lafiyan mahaifiyar shi bamu ba. Na lura Umma ta shiga damuwa saboda yadda takan kurawa hoton shi dake manne falon ido yana tsaye a cikin kayan aikin sa. Nakan fahinci shi take tambaya tana son ganin shi amma ba baki balle ta tambaya din. Da yamman ranan ne mijin anty yaganshi a cikin gari shi da Hanna bayan sun gaisa yake cewa ashe baka san iyalinka sun dawo ba. Dazun zan kai yara makaranta suke fada min wai tunda suka dawo basuga baban su ba. Cikin mamaki yace sun dawo ne yaushe suka dawo garin banda labarin hakan.? Yace mai yau zasu kai kwana hudu ko biyar fa da dawowa ashe tsohuwa bata da lafiyane haka tare sukazo da ita ai gobe ma naji madam din na fadin zasu asibiti da ita. Kunya da mamakine ya rufe shi a lokaci daya shi dai mijin anty yaja motar shi ya tafi ya barsu nan. Amma wanan matar taka she is witch wallahi kodai ba mutum bace ita wai ? Cikin haushi yace ba mutum bace kece ko don Alla muje na saukeki na karasa gida da maganan takaicin ki can. Sai da ya sauke ta ya nufo gida cikin darrr dashi lokacin yara sun dawo gida daga islamiya . Ya tsayar da motar shi a kofan gida jin dirin motar shi yasa su saka ihu eh daddy oyoyo suka nufi kofan gida da gudun su. Ina zaune naiwa Umma wanka ina shafa mata mai yashigo gidan idanuwan shi a kan mu yana kallon may nake ma mahaifiyar shi. Umma sannu ku da zuwa yace tare da karasowa inda muke zaune da ita din. Ya dan riko hannun mahaifiyar tashi tabishi da idanuwa kawai ba baki ba lakka. Nan dai ya zauna tare dace min yaushe kuka dawo baki kirani ba yai wani kiban shi yai fresh dashi gwananin ban sha, awa hankalin shi da gani a kwance yake mai. Nace ka manta ka hanani kiran wayan kane idan ba kaika kirani ba da kan ka kace na daina damun ka. Yace amma da kika san zaku dawo ai sai ki kirani ki fada min ko don nasani . Nace yanzun ma daka sani bai baci ba ai dai duk abinda mutum keyi don kan shi don baya mutum ke barwa kura. Baiyi magana ba sai cewan da yayi yaya jikin nata yake yanzu akwai wani improvement ne akai ? Nace gata nan ai a gaban ka kagani sai dai a godewa Allah kawai don a sannu ake samun sauki ga ciwo. Shiru yayi duk guityness ya kamashi sai dan kamay kamay yakeyi kawai daganin shi baida gaskiya ga al, amarin shi. Ya mike tare da nisawa yana fadin Allah ya sauwa yanzu akwai wani magani ne da ake bata ne ? Nace ba wani magani bayan wanda aka karbo mata a tunga kawai shi ne har yanzu mukeyi. Gobe ya kamata muje asibitin a duba muna lafiyan ta aga may ke damuwan ta. Allah ya kaimu kawai nace mashi naci gaba da saka mata rigan jikin ta sai naga tana hawaye nace haba Umma idan kina tayar da hankalinki bazamu ji dadi ba mu. Don Allah dai Umma ko may ke damuwar ki ki barwa Allah kawai don kukan nan baida wani amfani wallahi. Ban bi bayan shi ba don banga abinda zance mai ba ko yace min idan na tafi inda yake din. Muryan shi ne naji yana kirana namike nanufi dakin indayake na samay shi tsaye a tsakar daki ya goya hannayen shi a baya. Nashiga da sallamana nace gani yace maryam wai may kike nema danine a rayuwan ki. Nace ban fahince ka ba fa yace bazaki fahince ni ba ai don may nace ku zauna gida zaku kwaso jiki ki kwaso su ku dawo. Watau kina nufin ni ban isa dake bakw nan ko komay kike nufi da hakan ? Kun dawo kuma baki nemay ni ba kunyi zaman ku kawai ba wani labarin komai balle nasan may kuke ciki a gidan. Wai ma yanzu da kika kwaso Umma kikazo da ita nan may kike son nayi mata anan wanda can gida an kasa yi mata. Ban san lokacin da nace wai baban Abba may ke damun kane yanzu haka mahaifiyar ka kai kadai a gareta kai kadai Allah ya bata amma har ka tsaya kana wanan maganan haka akan ta. Wallahi kaji tsoron alhakin hakin mahaifiya kada ya kama ka Allah. Idan banzo da ita nan ba can kake son mu barta ita kadai ko kuwa yaya kake so nayi da ita. Kace zaka turo da kudin makarantan yara asaka school acan amma kazo karuwan ka ta dauke maka hankali ka manta da zancen kowa a ran ka. Kasan dai ina da halin da zan iya sa su makaranta acan amma don naga kaima baka damu da su ba yasa na barsu hakanan. Yanzu shine kake bakin ciki don mun dawo dawowan namu akwai abinda zai hakanane daga halin da kakeyi kana sa yan uqanka suna zargina a banza don kawai na boye masu halin da kake ciki damu anan komay. Har yanzun zaka bode baki kace wai may mukadawo yi nan yanzu to kasani mundawo ke nan wallahi babu inda zamu tafi na fada maka. Yace ai idan baku tafi don Allah ba indai akan wanan gidan ne dole ku tafi kodon rigiman dake cikin shi don dai ni banda wani kudin da zan kama hayan wani gidan kuma yanzu a garin nan. Nace ba matsalan komai a gidan nan sai wanda yajawo da zafi ne yake ganin matsala dama a rayuwan shi gida ma ka huta akan shi bazamu canza gida ba nan dai inda muka saba zamu zauna din. Allah zai kare mu dayardan shi insha Allahu bamu ganin komai sai alheri. Umma kuma mahaifiyar kace idan ka kulata ruwan ka idan ka barta ma rukan ka ni dai duk abinda nake mata don Allah nakeyi mata ba don komai ba. Yace ai haka zakice waya ja mata aanan matsalan ba duk keba ai kin san komai kada ki mayar dani karamin yaro mana. Keda kikaja mata aikece mai wahala yanzu dawa kike wahalan bake kadai ba. Nace koba Umma ba bani fatan injawa wani wahala balle Umma da take a matsayin uwa a gurin na mahaifiyar uban diyana kuma. Yanzun dai sai ki shirya gobe aje asibitin ba ganin iyaka bane dama yasa kika kwaso kuka zo don ki kulla min sheri. Nace idan ni banga iyakarka ba ai karuwan ka zataga naka itada yanzu saboda ita baka hanin kowa da gashi a duniyan nan sai ita da uan uwan ta kawai. Kada kace ko ban san kudin da kake kashewa ne akan taba amma ga mahaifiyarka nan ba lafiya ko a jikin ka. Yace nakike nan dama bakin kishi kudinki nake bata ko nawa nace nawakan ai yafi karfin bata wallahi idan kuma mutum ya musa ne ya gwada kai mata inbai yabawa aya zaki ba. Nasani ai kada kice ban san yanzu kin sake daga maryam din danasani zuwa wata maryam din ba can. Kallon mamaki nai mashi jin abinda yace min don nasan akwai wani abinda ya sani gamay dani wanda ni ban sani ba ke nan. Yanzu aini maryam komai za, a iya kirana tunda karuwa ta hana mu dawo mun dawo zamu bata maku tsarin ku na cin duniya. Kamar zaiyi magana yadda ya tsura min ido sai kuma ya kasa furta komai sai kutawan da yayi kawai ya juya yafita daga dakin. Haka ya fito dakin ranshi a bace munyi kaca kaca dashi wanda nasan duk maganan mu yana a kunnen Umma din tanajin komai da kowan mu yake fadi. Ina fitowa naga fuskanta ya baci alaman bacin rai karara a fuskan ta ban tsaya ts kanta ba naci gaba da aiki koma maynene dai yau ai taji ma kunne ta hakin da tilon dan ta yake ciki. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , , 👨‍👩‍👧‍👦 👨‍👩‍👧‍👦 2⃣0⃣ Alhamdullahi don kwana biyun nan dana fara yiwa Umma maganin gurin baba malam, kuma na daina bata maganin asibiti wanda ke wahal da ita din. Aiko gaskiya Alhamdullahi don yanzu yakai Umma har tana dan iya mikewa daga zaune a inda take a kwance. Zata iya daukan wani lokaci mai tsawo a zaune idan kuma zata kwanta da kanta zata koma ta kwanta. Sai dai har zuwa yanzu babu baki a tare da Umma din sai dai kwatance kawai mutum zai fahinci abinda take so a rayuwan ta. Nan dai na dan samu saukin al, amarin do iyanzu ta rage sake najasa a gurin da take zaune don takan nuna min alaman bukatan ta. Zancen sakon baba malam gun matan da ya turani ne ya ke ta fado min a zuciyata. Haka dai yasa na yanke shawara washe gari zan rufe idona na tafi don kyaun alkawari cikawa. Na cewa baban Abba da zai fita da safe ina son zuwa na karbo kudina da sako a gurin wata mata a GRA don matar bata san mun dawo garin ba. Kallon mamaki ne yai min yace kin ko san inane GRA maryam ? Abin naki har yakai kin fara hurda da manyan matan gari haka ashe ban sani ba ? To ki dai yi a hankali don GRA ba unguwar zuwan tallakawa bane don ki sani. Nace insha Allahu nai godiya akan bari na fita da ya barni nayi batare da ya hana ba. Yana fita na shiga shiri na don ranan ba school yaran suna gida zasu zauna tare da Umma a gida. Tsab na shirya tare da daukan sakon maganin da baba malam ya bani na kaiwa matan nan biyu da yace nakai masu sako da kaina. Shatan mota na dauka sai unguwar Allah ya hadani da mai motan kwarai kwatancen gidan hajiya Aisha nai mashi kawai yace ya gane. Yace gidan matar tsohon shugaban kasa ko wancce take mininster mata na yanzu ko ? Nace gaskiya ban sani ba amma muje dai bai tsaya ba sai kofan gidan muka tsaya. Kallo daya naiwa girman gidan naji gabana ya fadi sosai amma yaya zanyi dole na daure na idar da alkawarin dana daukan wa baba malam din. Na rasa ko inane kofan shiga gidan Allah ya taimakeni naga wata mota tana fitowa daga cikin gidan haka yasa nagane kofan shi gidan. Na sallami mai motan daya kawo ba canji dubu daya nace ya tafi dashi nabar mashi yana ta godiya yaja motar shi ya tafi inda naga motar nafitowa na dan rabe daga gefe tafice nikuma na shiga gidan. Gidane irin ta manya wanda tsayawa fasalta shi bata lokacine don an kashe miliyoyin narai a ginin wanan gidan . Wasu mutane ne na hango saye da uniform duk iri daya a jikin su haka yasa na karasa inda naga kamar magana suke na siri a tsakanin su kuma suna rabon kudi. Suna ganina dayan ya taso kaina haikan yana fadin ke waya shigo dake gidan nan ki kuwa san inda kika shigo kuwa. Ba tsoro a raina nace dashi nazo ne naga hajiya yace wace hajiyan a ciki ? Nan fa daya sai naji bakina kawai yace hajiya babba din nazo gurin ta sai naga yana min wani kallo sama da kasa yana mamaki kamar ni zance nazo gurin hajiya a haka dani. Yace tasan da zuwan ki ne ko kuwa naki ya kawo ki gurin ta abinda kuka saba matan yanzu yin maula ? Nace idan ma nayi maka kama da mai maula ne sai ka canza tunanen ka don bashi nazo yi bani. Jinan malama ba,azuwa ganin hajiya babu appointment idan mutum ba dan uwan ta bane don ki sani. Nace kai tsaye a gadarance ka fada mata ga maryam tazo ganin ta kawai. Dariya naba mutumin bai gama dariyan ba yaji muryana ina umurtan shi da cewa zaka fada mata kona kirata na fada mata ka tsare ni da surutu a get. Yace au ashe ke zancen ki da gaskiyane bari nakira naji idan tasan da zuwan ki idan kuma tace min bata sani ba kinga karnunkan can na keji yanzu na kwance maki su suyi kaca kaca dake a gurin nan. Nace Allah ya baka sa, a dama haka kuke yan hana ruwa gudu asakaku ga rigar arziki kuce zakuyi wa mutane tsiya. Kallon mamaki yake min inda ya daga waya yakira wani layi yana bayani wai watace tazo sunan ta maryam tana son ganin hajiya babba. Ban san may akace mai ba nadai ji yace gaskiya ba wata bace can amma dai ta kafe lalai sai taga hajiya din. Nace don Allah malam kana bata min lokaci ni ina da abinyi kaji banan kawai zan tsaya ba please. Wacce yake wayan da ita taji muryana sai cewa tayi abani wayan na karba take cewa wacece ke hajiya tasan da zuwan ki ne ? Nace kifada mata ga maryam tazo kawai zata gane idan kin fadi hakan tace ok kijira ni ina zuwa. Sama ta hau ta samu hajiya a falonta na sama zaune tana ganin shigowan ta tabita da kallo. Tace hajiya sannu da hutawa tace yauwa sannu karimay. Hajiya wai wata ce maryam a bakin get take son ganin ki wai kin san da zuwan ta tace. Hajiya ta nanata sunan tace maryam ku maryam fa wata maryam ke nan ? Ta kada kai tace gaskiya ban san da zuwan ta bani sai dai idan ba gurina tazo ba. Wacce ta kira da karimay tajuya zata fita daga dakin har takai kofa mafalkin da tayi jiya tana fadin maryam nagode nagode kinji ne yafado mata arai. A take tace karimay karimay taja ta tsaya guri daya tace na tu kice tashigo please. Ta sauko kasa tace wa maigadi ance ya nashigo daga ciki . Yace kinyi arziki wallahi da na hadaki da karnun kan nan yau sun yaga min ke don naga baki da mutunci. Kalman nashi yabani mamaki na ja natsaya nace nice ban da mutunci kace yace kidai shiga tunda kinyi sa,a ance ki shiga din. Kallon mamaki kawai nake mai kaman zanyi magana sai kawai nasa kai na shige gidan kaman dama nasan kan gidan da farko. Ashe shigana da kaman second mutumin nan baiyi aune ba sai gani yayi kamar an sako karnukan nan dake a daure sun yo kanshi ba bata lokaci suka haushi da cizo da yakusa sai da sukai mai yagayaga da suturan shi. Da kyat yan uwanshi suka kwace shi ga karnun kan nan yana ta hakki yana mayar da numfashi guda guda yasha cizo. Da sallama na shiga falon wanda zance acikin film dai nake ganin makamancin sa a kasashen turawa ko indiya. Sallama nakeyi kamar ba kowa a gidan sai da ga can har na yanke shawaran na koma baya naji an karba min gaisuwa na. Wata matace fara doguwa maikarfi da ita tafi daga wani kofa tana cewa kece maryam dake neman hajiya ? Nace da ita nice atakaice. Wani irin kallo tai min kaman zatayi magana sai kuma take cewa bisimillah muje nakai ki gurin ta ko. Nace nagode. Sama muka hau sai bin gidan da kallon ikon Allah nakeyi bazakace a Nigeria kake ba idan kana wanan gidan. Falon da muka shiga na kasa tantance dashi dana kasa ko wani ne yafi haduwa dakyau. Can na hago matar dana zo gurin ta zaune saman wani kujera mai kama da royal cushion tana zaune a takure ta dafe kanta da hannun ta daya. Nai sallama ta dago kai da sauri tare da tsura min ido tace maryam sannu da zuwa. Yadda ta tare ni zakace ko tasan ni ne a baya tace karimay kawowa bakuwa abin motsa baki. Nace ai hajiya dakin barshi ba zama zanyi ba yanzu zan tafi nazo ne kawai nakawo maki sako. Wani hayaki nagani yana tashi daga kujeran da take zaune akai wanda nasan ba lalai bane kowa yana ganin hakan. Hajiyan take cewa ai dai ko bazaki dadw ba bakizo ki tafi babu abin tabawa ba ko ? Nace tona gode matar tana fita daga dakin sai naga alaman bata tafi ba tana daga bayan labule a tsaye nace dakin kawo min don yanzu zan wuce ni ina fadi ina kallon kofan inda karimay din take boye. Sai ta wuce sadip sadip da ita kamar munafuka tace au dama bata tafi bane ashe nace ina zata tafi ta tsaya taji damay nazo maki ne . Na juya inda hajiyan take zaune nace mama da zan baki shawara kiji da sai nace daga yau kada ki kara hawa saman kujeran nan dakike akai. Don kujeran yasha bakin sihiri don zaune kike a cikin wani irin bakin hayaki mai muni. Subbahanallahi tace da sauri tana kokarin mikewa sai naga ta kasa mikewa ta koma ta zauna. Haka yasa na fahinci bata da lakkan da zata iya mikewa ne a lokacin. Da sauri na karasa gurin ta na kamata zuwa saman wani dan timtim dake gefe nace ki zauna anan mama don shine kawai baida sihiri ajikin shi. Tace ikon Allah ashe zaune nake a cikin mugun abu ban sani ba ni. Kafin karimay ta shigo falon nai mata bayanin duk sakon da baba malam yabani. Tare da fada mata zancen yan aikin ta da yace ta canza su ta sake gaba dayan su kada tabar kowa agidan. Ashe karimay nacen tana sauri ta dawo ta dauko tiren data sa drinks aciki kamar an barar da kayan daga hannun ta suka zube dole takoma hada wani again. Namike ina fadin ni zan tafi mama Allah ya sauwaka yasa iyakan wahalan ke nan. Tace dakata maryam zaki tafi ban sanki ban san kuma idan kin tafi a ina zan ganki ba again. Don haka ki bani nomban wayan ki zan kiraki insha Allahu don karin bayani. Nabata nomban wayana ta saka a wayan ta ina batun fita sai ga karimay tashigo da kayan dauke a hannun ta. Nan hajiyan tace sai nasha wani abu daga ciki dole na tsaya na dauki cup ina tsiyaya ruwan lemon sai dai abinda nagani yasa nabi cup din da kallon mamaki. Na mayar gefe daya a cikin tire din na aje kallon gurin da karima take tsaye hajiya tayi tace ki bamu guri ina magana da diyata ce karimay. Sukusuku tafita daga falon tabar mu mukadai daga hajiya sai ni. Hajiyan tace ki sha mana diya ta na kalli cup din nai murmushi nace mama kiyi hakkuri bazan iya shan wanan abin ba gaskiya don da abu acikin sa kema kiyi hankali da da duk wani abinda zaifito daga hannun mutanen gidan nan don komai da suke baki ko bakin ki da sihiri a cikin sa. Wanda an riga an maku shi sai a sannu komai zai daidaita maku nan bada jimawa idan har kina amfani da abinda na kawo maki. Nace ni zan tafi sai wata rana kuma idan da rabon mu kara ganawa a tsakanin mu. Kudi ta dauko tabani wanda ni kaina ban san iyakan su ba. Na girgiza kaina ina cewa haba mama sako ne kawai na kawo maki banazo ne don na karbi koda kwandalla daga gare ki ba. Har nakai kofa sai najuyo na dawo zuwa inda take a zaune nace mata kamar mai rada kada ki yarda da kowa idan ba diyan ki ba don duk an saye su suna cutar dake ne kawai a gidan nan. Nace sai anjima nafice abina daga cikin gidan zan fitane naga wanan mutumin da karnuka sukaiwa ta, asa nace ikon Allah. Yaya akai haka ni basu yagani ba gashi kai sun yaga ka a lokaci daya Allah ya tsare gaba nafice abina na barsu nan suna bina da kallon mamaki. Mutumin yake fada masu yadda mukayi dashi da yadda yaga karnuka akan shi. Mamaki ne ya kamasu nan karima ta daga waya takira wani lanban waya tana fadin hello hajiya wallahi yau da matsala a gidan nan.. Da wani irin karfi matar da takira da hajiya tace matsala matsalan may karimay. Tace lalai hajiya tayi bakuwar wata yarinya danaji tana kiran ta da yar uwarta kuma yarinyae kamar dai ba ita kadai bace. Don ina gani har wanan abinda muka zuba saman kujerun falin hajiya sai da tagani don naga ta tayar da ita daga gurin zuwa wani wajen. Na bata abin sha taki tasha don nagane wani abu akan ta amma sam taki koda kurbawa ma balle tasha. Daga ina wanan bakuwar take abinciko min ita nasan ko wacece kada tazo ta bata muna tsarin mu muna ganin mun kusa cin ma nasara ga aikin mu kuma zata jawo muna matsala ta mayar damu baya ga aukin mu. Da sauri karimay ta bar falon takira daya daga cikin mutanen ta ta umurce shi dayabi bayana yaga inda na nufa. Sai dai yana fita bani ba dalilina na bace mai dagani nikan ina fita na samu mota ya sauke wasu mata nashige nabar unguwar. ****** ********* ****** Malali na nufa gidan hajiya Umma gidan shima ya hadu sosai kamar na farko don zan iya cewa yama fi na farkon gurin haduwa. Ban samu matsala sosai ba gurin shiga gidan don maigadin dana samu baida tsauri sosai kamar na aancan gidan. Yai min iso gurin hajiya Umma akace nashigo nashiga ina ta baza idanuwana gurin kallo. A raina nace ikon Allah baba ya hadani da irin manyan gidajen nan da sukafi karfina haka Allah dai ya ceceni daga kaidin irin manyan gidajen nan. Ina fadin gurin hajiya Umma nazo akai min iso gurin ta tana zaune saye da lafaya data lailaye jikin ta dashi. Dattijuwa ce sai dai da ganin ta ansha ilimi da duniya kudi kuma ba,a magana akan su. Nan dai muka gaisa da ita ta dago idon ta dake saye cikin farin glass tace boyar Allah ban sheda ki ba fa. Nace baki sanni ba mama baba malam ne ya aiko ni zuwa gare ke da wanan sakon ina kokarin ciro sakon daga cikin hand bag dina. Tace banko gane baba malam din nan ba dakikace nace mata yace in fada maki mutumin da kuka hadu ranan jumma, a a saudiya matar shi tana share mai zufa kina kallon su har wanan kyalen naki yafadi a kasa. Tace ukon Allah an koyi haka wallahi amma sai dai mutanen da nagani ba black bane su ina ganin kamar larabawane su. Nidai murmushi nai mata ban tsaya dogon bayani ba nafitar da sakon ta na bata tare da mata bayanin komai. Sai kallon mamaki kawai take min an kawo min abin motsa baki amma ban taba komai ba daga ciki. Sai kallon mamaki take min tace kinga ciwon kafan nan tun ina a senet comphress watarana naji kamar na taka wani abu tun lokacin nake fama dashi nayi magani har nagaji nabarwa Allah al, amarin sa. Yanzu idan nace zan shiga dakin nan da kike gani aiki ne babba a gare ni don ban iya taka kafan nawa da kyau sai naji shi har a cikin raina Na mike ina fadin gajiya ni zan koma tace tsaya na baki na mota ko nace a, a sako ne akabani na kawo maki kuma nakawo bazan karbi ko kwandalanki ba hajiya. Tace ikon Allah amma da kin karba ainice nabaki nace nagode mama Allah ki barshi kawai sakon dama ana son yazo gare kine kuma Allah ya nufa yazo. Nace sai dai kuma yace na fada maki zancen danki dake damun ki ki daina damuwa da hakan nan da sati uku mai zuwa insha Allahu zai dawo gida. Amma idan yadawo kada kice zaki mai fada ko magana akan rashin dawowan shi akasi aka samu ga hakan. Har na fara takawa ina fadin sai anjima tace dakata yarinyar naja na tsaya guri daya. Tace al, amarinki ya matukar daure min kai don dai ni na kasa fahintar komai akai. Nace hajiya kada ki damu idan har kin yarda da Allah to ki jaraba wanan maganin ki gani. Nace nabarki lafiya ni zan tafi tace dakata ki bani nomban ki pleaae ? Nabata nombar a gurguje na bar gidan ban tsaya ko ina ba sai gida nadawo agajiye dani. Kamar anbani kashi nakeji ga kaina yana wani irin sara min duk ban jin dadi a jikina haka na samu guri na kwanta sai barci mai nauyi yai gaba dani. Har dare haka nake kwance ba lakka ajikina sai faman kasala dake damuna kawai haka na daure natashi na ba Umma maganin ta. Tare da shafa mata nakoma na kwanta don gaba daya ban ganewa jikina ba a ranan zakace nai wani aikine. Sai daga baya abubuwan da suka faru suke dawo min tiryan tirya nake gani kamar a mafalki akayi su. Yadda ma akayi na shiga irin wanan gidajen haka nake tunane a raina ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👨‍👩‍👧‍👦 👨‍👩‍👧‍👦 BA MU KADAI BANE A, , , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 1⃣9⃣ Wshegari nagama duk wani abinda zanyi da wuri don zuwa asibiti da zamuyi zuwa kai Umma a duba ta. Shi ya kaimu asibitin ya sauke mu bai tafi ba sai da ya yankar muna kati muka bi layi don mun samu mutane da dan yawa a gaban mu. Mun dan dauki lokaci mai tsawo kafin layin yazo a kan mu aka kiramu muka shiga gurin likitan. Bayan yan dube dube da tambayoyi da akai muna muka gaya mai komai da yadda takeji. Daga karshe yake cewa ba komai ke damun ta ba sai hawan jini daya saka ta a gaba. Nan ya rubuta muna magani naje na sayo maganin nakama Umma muka nufi gida da ita. Baban Abba bai shigo ba sai goma na dare da yan mintina yashigo gidan agajiye dashi. Sannu da zuwa nai mashi ya nufi gurin da Umma take zaune cikin rashin jin dadi ga yanayin ta yana mata sannu da jiki. Maganin da aka bamu yake dubawa a hankali ya dago gurin da nake yana cewa hawan jini ke nan yake damunta ashe ? Nace eh haka sukace wai shine yai mata illa haka har ya mayar da ita hakan nan. Allah ta sauwaka yace yamike yanufi ciki abincin shi na dauko na shirya mai a falo don ya shiga wanka a lokacin. Yafito ya samu guri ya zauna yaci abincin shi ya koshi ba tare da ya tambayi inda na samo kudin cefane ba. Nan kuma ya juya yana cewa yaran yau may akai masu a makaranta nan suka shiga bashi labari yana biye masu wanda nasan ba komai bane kamay kamay ne kawai yakeyi don kunya. Ace mutum mahaifiyar shi bata da lafiya haka amma taki tsayawa ya mayar da hankalin shi akai. Ya koma kamar wani susutace dashi kan karuwa yar duniya da ta shige mai gaba da komai. Ni yanzu ban faye damuwa da al, amarin shi ba don al, amarin yarana da na majaifiyar shi da nake jinya yafi damuna a raina. Don nashi al, amarin ya fita min akai ko don yanzu na riga na saba da halinshi na rashin kulawan shi a kan mu. Mikewa nayi na shiga dakin da Umma da yara ke kwana nadan kara gyarawa tare da fesa masu sheltox don sauro da kwarin dake acikin dakin. Gurin Umma na dawo inda take dakyat na kamata da taratara nakaita dakin na kwantar da ita na kashe wutan dakin nadawo falo gurin su na zauna. Ina zama yake ce min kin fara bata maganin ke nan ko ? Nace eh tafara sha tunda muka dawo dayan ne wanda bamu samu ba kawai ban bata ba gama takardan nan. Ok kawai yace mun tare sa kawar da kan shi gareni yaci gaba da kallin wayan shi da yake charting. Karfin hali nayi nace ga takardan ko zaka sayo muna gobe idan kafita ko ? Bai dago ya dubi gurin da nake ba yace aje shi gurin yanzun dare yayi sai da safe a sayo. Tun wanan lokacin bai kara bi takan takardan ba don da safe nan naga ya fita ya barshi a gurin dana aje mai. Na fahinci cewa yanzu Umma ta kara langabewa fiye da baya ma don abin kara tabarbarewa yayi mata data fara shan na asibitin da muke mata. Don gaba daya bata lakka ko kuzari kamar baya da muke ganin sauki yana shigan ta a hankali. Yakai yanzun bata iya ma tasgin danake taimaka mata tana dan yi abaya. Hakan ya tayar min da hankali ga dan ta kona fada mai ba wani abu yake akaiba sai dai yace na bata magani tasha shine yake mata aiki. Ashe mu abinda bamu sani ba magani daban ciwo daban mukeyi don ba a hada aikin jinnu da maganin asibiti ga maganin yafi karfin jinin ta shine ke sa ta kara jin jikin da takeyi yanzu saboda ba hawan jini ne gareta ba. Nan dai hankalina yafara tashi akan al, amarin gashi danta ba ruwan shi da mayar da hankalinta gare ta. Idan ya fita tun safe sai dare sosai yake shigowa gidan zai samu tana barci ko a kwance da safe sosai kuma zai bar gidan sai kuma dare. Ranan da naga abin ya matsa mata yasa na tasa ta agaba ina hawaye gashi nice sillar zuwa da ita garin mutane kada wani abu yazo ya samayta a kuka dani dana kawo ta. Nace a raina da zan ga baba malam da sai na fada mai halin da take ciki ko akwai abinda zai taimaka mata dashi na lafiyan ta. Ina nan dai zaune inata faman sake sake a cikin raina da ga karshe dai na yanke shawara a rai na na gwada sa, at ko zan samu zuwa birnin dausayin tsibiri ko zanga malam din. Hakana kwana da zancen zuwa dausayin tsibiri washe gari ko Allah zai sa na samu motar da zai kaini can. Tunda safe bayan tafiyan yara makaranta nima nagama kimtsa Umma tare da bata abinci da magani na gyara ta yadda ya dace nazo gaban ta nace. Umma zan tafi gurin wani mai magani mu gwada mu gani ko Allah zai sa mu dace amma ba dadewa zanyi ba sai nadawo. Na dauki Nusaiba wace yanzu yarinyar tana iya zuwa ko ina da kafan ta don ta yi wayo sosai yanzu. Na kulle gidan daga baya da ita aciki na kama hanya zuwa inda zan hau taxi zuwa kofan asibiti. Masu motar haya suna tsayawa tambayan ina zan tafi idan nace dausayin tsibiri sai naga sun min wani kallon mahaukaciya don babu sunan garin a duk nahiyar kaduna. Ga rana na kudar mu ni da yarinyata da muka dauki lokaci tsaye a cikin ranan kusan awa biyu da rabi ba mota garin babu dalilin ta har lokacin. Na yanke shawaran nakoma gida kawai don nasan ba samu ma zanyi ba. Nace Nusaibs zo mu tafi gida kinji kada raban yai muna illa hakana gashi ma rana yasoma yi sha biyu da yan mintina yanzu. Na duka zan dauki yarinyar karaf kunnuwa na taji wani condester bus yana fadin Birnin tsibiri fa mai zuwa. Nai saurin tare motar na fada kawai duk da rana yai muna ga tafiyan a lokacin. Mutanen dana samu acikin motar sai kallon mamaki suke min ga tsikan jikina naji yawani tashi min a lokaci daya. Allah bai bani ikon yin addua ba a lokacin sai dafe kaina danayi kawai da rike yar diyata dake zaune a jikina. Muryan condester din nakara ji yana fadin masu sauka dausayin tsibiri su sauka mun kawo. Nai farat na mike na dauki diyata naba mai motar kudi na fita abina daga motar suka kwasa da wani gudun balai sukai gaba abinsu. Nagyara muka kama hanyan zuwa uguwar da zan nufa na yanke shawaran biya wanan gidan da nake shiga da farko idan na tafi. Sai dai yau na samu gidan kamar suna buki don naga mata sosai acikin gidan. Nashiga da sallamata idanuwan matan dana samu duk akaina yake gaba dayan su. Ina gaida matan ina raba ido ko zanga daya daga cikin matan gidan dan sani tafito a lokacin. Ke mari ga wata bil, adam fa tashigo gidan ku ko kun san da sanin zuwan ta nan ne. Matar da akakira da Mari tafito tana fadin bil, adam kuma a gidan nan yau wacece kuma ? Abinda nagani ne yasa naji wani faduwan gaba tare da sarawan kai ya kamani ban san lokacin dana dukar da idanuwana ba akan mari din. A, a maman Nusaiba yau kece a gidan namu lalemarhabi da dake jin muryan wace na sani yasana bude idon tare da dago kaina dake a duke yana sara min kamar zai cire nace nice anty. Murmushi dauke a fuskanta ta karaso inda nake tsaye tana cewa ai nazaci bazamu kara ganin ki ba ne yar uwa. Tace sai dai gaki kinzo gidan kin samu yau a cike yake waccan dayan abokiyar zaman tamu ta haihune ake buki a gidan yau. Daga kaina nayi ina kallon matan dake gidan ikon Allah sai nake ganin kowacen su a cikin irin hallitatanta da Allah yai mata nai suuu kamar zan fadi kasa. Matar ta tareni da sauri tana fadin kinga zoki tafi gidan malam kada ki makara don yau gidan namu bamu kadai bane kuma ko a cikin mu yau ba jinsi daya bane a gurin kada asamu mugu ya cuta maki. Da sauri taja hannuna zuwa hanyar fita daga gidan nan ma muka sake gaduwa da wasu gungun matan kaman dabbobi yanayin su kahonne a tsakiyan kawunan su gwanin ban tsoro dasu. Mukai sallama nabar gidan da sauri inayi ina waige kudun kada wata daga cikin su ta biyoni a baya. Gidan baba malam na nufa hankali a tashe nai sallama na shiga gidan nan na samu mutanen gidan suna cin abinci suna min sannu da zuwa. Muka gaisa dasu amutunci sai sannu da hanya suks min babban matar malam tace yau Allah ya taimakeki da matan gidan bukin nan sun maki illla don wasunsu basu da tausayi ko kadan. Yanzu Kafiya take sanar damu zuwanki gidan a cikin rudanin abin da kika sama agidan. Maryam ke mai arzikice da sa, a a rayuwan ki ko da yaushe don badon Allah yana tare dake ba ai da wa yancan shedanun don ba sallah sukeyi ba da sai sun cuta ma rayuwan ki kona yar ki a garin nan. Baban ki yana daga ciki yana jiran ki don tun dazu yasan da zuwan ki garin agurin shine ma muka samu labarin kina hanya tun dazun . Amaryan tace wai amma kunsha hanya ga rana bari na baki ruwa da abinci ki danci ko. Ikon Allah yau sai na tsinci kaina da tsoron su haka kawai nace a, a nagode. Murmushi tayi tace haba maryam ko da ace zamu cutawa wani dan adam aikema kin san banda ke ko don ke diyar malam ne kin zama diya a gurin mu. Murmushi karfin hali nayi don duk a rude nake iina dana sanin kafewan da nayi nazuwa garesu yau, nasa hannu ga jakar dana nazo masu da tsaraba acikin sa. Turare ne sai sabule masu tsada da clean kowa guda daguda nakawo masu. Takarba da murna da farin ciki tana min addua wanda duk na neman tsarine daga Allah. Uwargidan malam tace ke kan wai baki gajiyane da halin alheri maryama ? Nai murmushi nace mama ku iyayyena ne fada nake alfahari dasu a duniya don kun min riko da nuna min ku uwaye kuke agareni banda uwan da zanje gurin ta naji dadi na fata mata damuwana sai agurin ku. Kuma ku bani shawaran daya dace sai nan gurin ku. Ashe mai zasa da yagaji da kyautatawa iyayyen shi a duniya idan har yin hakan zai faranta maku rayuwan ku. Idonane yakawo hawaye a lokacin da nake wanan magana don tuna cewa banda mahaifiya ko yar uwan, uwa, wace zan iya kai damuwana a gareta ta share min hawayena ga bani shawaran daya dace a rayuwana kamar su a yanzu. Kuka ne yaci karfi acikin kukan ne nake fadin mama bazan iya guje maku ba don zaman mu yan jinsi daban daban ni daku duk da na san yin haka hatsarine a rayuwana. Amma kun nuna min kaunan da yasa nakejin kun zama iyayye a gare ni wanda duk duniyan nan yanzu banda ku da mahaifina banda wani makusancin dayafi ku a gareni. Kewan ku da damuwan makomata idan narasa ku a tare dani yana ci min zuciya don ban san yadda zan kasance ba daga baya idan har kuka barni. Haba maryama ai mu bazamu barki ba sai dai ke ki barmu ma don mu kin sn ba mutuwa mukeyi kamar ku ba. Muryan malam ne naji akaina wanda yasani dago kai a hankali na dube inda naji muryan. Yana tsaye cikin fararen kaya tun daga takalman shi tufafin shi har rawanin shi da sandan shi ta carbin shi duk farare ne. Zan iya cewa wanan ne karo na farko dana taba ganin malam din a tsaye kuma gani na sahihi da ban taba tantance kamannin shi ba kamar na yai din. Fari ne dogo kyakyawan balarabe dashi ga saje fari da yai kwance lub a fuskan shi gwanin ban sha, awa. Ko ba, a fada ba kaga lumana da malanta kwance karara a tare dashi. Maryam ya ta kada ki bata fuskan ki da kuka don ke yar muce Allah da annabinshi kawai yasan hikimar hadaki damu a duniyan nan. Yan adam nawa suke shiga a rayuwan mu amma baifi su gan mu sau daya ba idan ma har zasu ganmu din cikin wanan kama. Amma ke gashi Allah ya hore maki mu kina ganin mu kina zuwa gare mu a duk lokacin da bukatan hakan ya taso gare ki. Yau din ma ban so zuwan ki garin nan ba don garin namu yau ba dadi ko mu da muke yan jinsin su taka tsatsan muke da irin bakin mu don su bakake ne ba imani suka faye ba a rayuwan su duk da musulmai ne su ma amma suna da halin da kyaman dan adam tare dasu. Gabana ne naji ya kara faduwa karo na barkatai amma kuma sai naji yana fadin ganin da naiyi kin dade a tsaye kan kin nace sai kinzo gare mu yasa nasa a bude maki ido kiga motar nahiyar mu har ki samu zuwa. Idan ba haka ba ko kwana dubu zakiyi a gurin nan ai bazaki taba samun motan da zai kawo ki wanan nahiyar ba diyata. Kai na na dago a hankali na dan kalleshi nace nagode baba. Yace kici abinci ki huta kizo muyi maganan da ya kawo ki don yar kima tana jin yunwa gashi kuma ta wahala sosai a cikin rana kafin ku samu motan zuwa nan din. Abincine lafiyayye aka kawo min sai dai duk tsoro da fargaba ne ya cika min zuciya ta. Gudun su fahince ni duk danasan su san komai yasa na bude abincin tare da jawo Nusaiba a jikina na fara bata abincin a hankali. Amaryan malam take ce min bazakici ba ke kina fa tare da yuwan ajikin ki ga damuwan da kike dashi na mijin ki da mahaifiyar shi. Da sauri na dago kaina ina kallon ta don dai naga ban fada masu ko may yakawo ni ba gare su. Tace kin bani mamaki dana baki abinda zakiyi amfani dashi irin namata amma kikaki yin amfani dashi da farko na zaci ko rashin yarda ne dani yakawo hakan amma daga baya sai na fahinci abin ne ke bai damay kiba a rayuwan ki. Da ace kin gwada amfani dashi da a duniyan nan babu wata macen da zata iya shige maki a gaban ki komai hatsabibancin ta kuwa. Mazanjen ku shedanune maryam ma don abune mawuyaci asamu namijin da ya tsaya mu, amula da matar shi na sunna kawai a yanzu tundai mutane irin na alkaryan ku dabasu dauki zina da wani muhinmanci ba a rayuwan su. Yau zan kara baki wani don wancan na farko na dauki abina ganin baki amfani dashi ba . Sai lokacin na tuna na nemay shi ranan ina son bawa anty hauwa da ta tambayeni ko nai ajiyan kayan mata na nemay shi kasa da sama banganshi ba a gidana. Sai nai tsanmanin ko na jefar dashine ban sani ba kona sakashi wani gurin nai mai mugun boyo ne. Wanan abinci akwai dadi da test sosai ban san lokacin da na kusa cinye shi ba sai naji tana cewa akaro maku naman ko naman baunace Maryama kike ci kin san ku yanzu yan adam baku samun irin wa yan nan namun dajin a garuruwan ku kamar mutanen da suka gabata don namun dajin sun boye daga gare ku. Murmushi nayi nace na koshi mama na gode nace wani irin dabbane bauna kuma mama ? Kaman a mafalki naganni a cikin wani daji mai yawan dabbobi ga garke wasu namun daji masu girma siffan su kamar na shanaye dana sani sai dai su bakake ne. Sai kuma naganni zaune a ida nake da farko tace min kin taba ganin su a rayuwan ki na girgiza kaina tare da fadin a, a. Nan dai na gama cin abincin tana min bayani akan dabbobi wanda wasu nasan sunan su wasu kuma ban sani ba sai a bakin ta na tabajin su. Nan dai tabani wasu abubuwan masu amfani ga mace tare da jaddamin nai amfani dasu kuma zata bani wasu da zan dinga sayarwa ga mata yan uwa na idan ina da bukatan yin sanan an su don itama shine sanan ta, nace ashe kuma kuna amfani da wanan abubuwan tai murmushi take cewa haba muma ba maurata bane kamar ku ? Duk rayuwan da kukeyi munayin shi maryama dan banbancin rayuwa atsakanin mu daku kadan ne ai. Don akwai abubuwan daku yan adam zakuyi wanda mu bazamu iyayin shi ba don kunfimu hikima da fasaha da taurin kai. Mun dauki lokaci muna hira tare da ita tabani kayan masu yawa tace nagwada idan sun karbu zata dinga bani cikin saukin farashi. Ina gamawa da ita na shiga gurin baba malam na samay shi a zaune yana karatu rike da littafi a hannun shi. Jin sallama na yasa ya dago daga abinda yakeyi yana dan murmushi a fuskan shi cikin kulawa. Zubuwa nayi kasa ina gaida shi ya tare ni da fadin shiyasa muke cewa ku yan adam akwaiku da taurin kai a rayuwan ku. Na fada maki cewa idan kina son ganina basai kin wahal da kanki ba da zuwa dakin bukaci ganina zaki ganni ai maryama. Nace baba ina son zuwa gida ne naga su mama da sauran yan uwa, yace madalla maryama da irin son da kike muna. Nasan yanzu kinzo ne kan mahaifuyar maigidan ki dakike jinya ko ? Nace hakane baba. Yace ai ba aiki kowa bane sai mukkadarasiya da yaran ta sune suke mata wanan aikin kan abinda tai maki suka ji haushi. Kuma sunyi hakan ne don tasan muhin mancin ki a gareta wanda yanzun ta sani tasan komai kuma. Munyi magana da ita danaga kin shiga damuwa tace min akwai abinda take son matar ta fahinta ne akan ki. Sai dai kuna mata magani daban ciwo kuma daban wanda maganin da kuke bata na asibiti yanzu shine yakara kawo cigaban wani ciwon a gareta. Maryama naga jikin mahaifinki ya samu sauki sosai malam yana da mutunci ban san dalilin da yasa mutanen gidan shi da suke zaune shekara da shekaru suka cuta mai haka ba. Koda yake halinku ne na yaran zamani insha Allahi kuma bazasu kara cuta mashi ba bashi ba kowa ma na tare dashi. Yanzun dai ki karbi wanan kiyiwa surukarki amfani dashi kin dai manta na taba baki maganin waraka na wasu cututuka abaya da kin mata amfani dashi da ya wadatar daku ai dazata samu sauki sosai. Nakarba ina godiya zan bar dakin yace maryama akwai wani taimako danake son ki min akan wasu, mata da nake son ki taimakawa wanda hanya ne nake son nai maki ga hakan. Bazaki gane ba sai nan gaba nace baba wani taimako kakeso a gurina. Yace karbi wanan akwai wani gida a unguwar GRA wanda yafi ko wani kyau da girma a unguwar don haka ki kaiwa matar da ake kira da suna Aisha wanan maganin sha zatayi ta shafa ta kuma dinga alwala kafin ta kwanta barci. Sai dayan uguwar dake a malali zaki samu gida mai hawa uku daga barin daman ki ma launin shudi da yawan furanin idan kinje kice hajiya Umma kike son gani idan kin samu ganin matar sai ki bata wanan sakon tasamu ruwan massalaci ta hada dashi tana sha tana shafawa akafan dake damun ta insha Allahu zata warke itama. Kice mata mitumin da tagani ranan jumma, a a garin makka matarshi tana shafa mai ruwa a fuska ta tsaya tana kallon su shi ya aikoki gurin ta yace agaida ita. Zancen dan ta kuma ta kwantar da hankalinta nan da sati uku zai dawo gida da yardan ubangiji. Sai dai idan ya dawo kada taimai fada akasi aka samu ga rashin dawowan shi da baiyi ba na tsawon lokaci idan kikai min wanan taimakon dana bukata a gare ki ya wadatar min da komai a gare ki maryama. Nace amma baba kasan halin mutanen mu nayau zasu yarda dani kuwa har su karbi sakon nan. Yace ai ko wacen su tasan da zuwanki maryama sun sanki kece dai baki sansu ba kawai. Ita Aisha ki fada mata nace ta idan da hali ta canza duk yan aikin gidan ta gaba dayan su har maigadin ta haka shine saukin ta. Nace insha Allahu baba zanyi kamar yadda ka umurce ni dayi yace kada ki damu idan kinje komai ma da zaki fada zaki ganshi a zahiri kuma zaki aiwatar da shi. Yace zancen mijin ki kuma komai zaizo karshe da yardan Allah kada ki damu da komai akai. Nai godiya nafito mukai sallama da su ni dai nasan nakai zauren da zai fitar dani daga gidan baba malam din. Amma bayan haka ban karasanin yaya akayi ba kuma sai ganina nayi zaune tare da kayana dake gefena aje a falon mu. Firgigit dani ina cewa hasbbunallahu wa,ni,imal wakeel. Tabbas a falona nake zaune ba a wani guri ba na daban don na kara tabbatarwa yasa na mike da sauri na nufi dakin da Umma take kwance tana ciki a kwance idon ta biyu sai dai duk ta bata jikin ta da kashi da fitsari. Nace Umma kin yi lalurane ashe bana nan da sauri na fita na debo ruwa nafara gyara gurin na tsabtace ta da kyau na kawo kamshi na saka a dakin da gidan. Abinci na fara bata wanda dama na riga dana dafa shi ko kafin nafita sai data gama na kada maganin da baba yabani na fara bata. Tasha na shafe mata jiki dashi sannan nadawo da ita falo tare da kware labulen dakin don iska ya shiga sosai a dakin. Nan dai na shiga yin yan aiyukan da ya dace nayi nagama nai sallah nan barci mai nauyi yai gaba dani. Najima ina barci a gurin sai mafalkaiyyan abinda ya faru dani nakeyi ba abinda ya firgitana har na falka daidai lokacin da yaran ke shigowa sun dawo daga makaranta. Ba komai nagani ba sai matan da nagani a gidan buki dana shiga cikin wani irin hallita suna min wani irin kallo da tsoratani sai ga mari ta mika min wani leda wai abin buki ne da ban karba ba ta kawo min. Ina tashi kuwa idon yai tozali da ledan data bani a gefena wanda yake tap da kayan buki alkaki ne mai shegen kyau da nama sai nakiya mai kyau dashi. Ga yara sun zagane ni suna fadin sun dawo amma ni sai zufa ne ke karyo min a fuskana daduk illahirin jikina. Kafin na farga har yaran sun fara cin kayan bukin da suka gani suna fadin wai amma akwai dadi mama. Da sauri nakai idona gare su naga abinda sukeyi naikaiwa Aisha wacce nasan itace tafara daukan shi duka akai. Naji ance min akull kika kara dukan ta zamu hadu kina nufin yan uwa na zasu cuta maki ne ko may wai? Babu kowa kuma babu wanda kejin may aka fada min yadda naga su ko a jikin su haka yasa nasha jinin jikina. Ina kallo yaran naci ba halin na hanasu ci sai Abba ke ce min naci naji zakin dake akwai ga kayan. Na dan gutsura kadan a bakina nace gaskiya akwai dadi sosai don ban taba cin alkaki mai dadi ba irin wanan din ba a rayuwana sai wanan na gabana. Ranan nidai har na kwanta ban kara saka komai a cikina ba sai ji nake kawai a koshe nake tun abincin da naci a gidan baba malam din ga jikina sai ciwo yake min kamar nayi wani aiki mai yawa nake jin kaina. Hakama yaran kayan bukin da sukaci ya saka su basu jin cin komai ranan haka muka bar abincin dana dafa nan ya kwana sai da safe na zubar dashi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/9, 11:20 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BAMU KADAI BANE A, , , 👨‍👩‍👧‍👦 👨‍👩‍👧‍👦 2⃣1⃣ ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DAFATAN MUN WAYI GARI LAFIYA ALLAH YABAMU WUNI MAI ALBARKA. MASU SON NOVELS DINA ZAKU IYA REGISTER GA WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO RECHARGE CARD NA 400 ZAKU IYA NEMANA A WANNAN LAYIN KAMAR HAKA 08036959257 NAGODE DA KAUNAR DA KUKE NUNA MIN SAI NAJI KU, , , Alhamdullahi don tunda na kai sakon nan sai nake jin kaina shakat kamar an sauke min wani nauyi babba a kaina lokacin. Sai bayan kwana biyu na daina jin mutuwan jikin dake damuna wanda ban san dalilin yin sa ba lokacin. Alhamdullahi don Umma kan har baki ta fara samu a lokacin sai dai sai mutum ya saurara sosai zaiji may take fadi. Amma dai ko hakan ma mun godewa Allah matar da ke kwance sharkaf da ita yau da bin bango tana iya fita zuwa falo da kanta batare dana cicibeta ba kamar baya. Matsala daya ke ci min raina a yanzu shine rashin dawowan gida da baban Abba baiyi sai yaga dama kuma koda ya dawo din ba lalai bane ya kulani nida hoto daya muke a gurin shi. Duk yadda mutum ke tunanen hatsabibancin mace Hanna ta wuce gurin don tashiga tafita ta rabashi da kowa nashi a yanzu baya ganin kowa da daraja sai ita da yan uwanta da sauran tarkacen ta. Ko nawane zai iya kashe mata shi batare da yaji wani darr ba akai amma mu a gida bai damu da damuwar mu ba ko kadan. Kullun cikin ci da shan kaidin ta yake har ma da shafawa idan ya kwana a gurin ta. Hakan ke kara dauke mai hankalin shi gare mu yadda take bukata gani koda yaushe. Na gode ma Allah da bai saka min wahalan akai ba don ni harkan gabana kawai nasaka agabana. Yau nagama abinda nakeyi nace bari na shiga gida makwabciyar mu yar adamawa da ta haihu nai barka. Can na hade da su yar sokoto da anty hauwa aka zauna zaman hiran duniya. Har akazo akan zancen kayan mata sai lokacin na tuna da wanda nake dashi. Nace aiko ina dasu dana sarara kwanaki kuma suna da kyau duk matan dake gurin suka shiga tambayana don Allah mai kyaune maman Abba ? Nace ku gwada ku gani zaku bani labari ai na dinga gidada abin kamar nasan amfanin shi ni. Anty hauwa tace kai amma maman Abba ke muguwa ce yanzu kina da wanan kayan haka kikaki fada muna kika barmu muna sayen na banza a waje. Nace ban dade da na fara sana, an ba shiyasa baki sani ba nan dai muka aje magana da yamma zamu hadu kowa yaganin. Ina shiga gida na samu baban Abba da yai kwana uku bai gida ya shigo na samu ya shiga wanka. Na zauna falo gurin Umma da Nusaiba da bata fara zuwa school ba suna kallo. Nace Umma akawo abinci ko kai ta gyada min alaman a, a nace tau bari na dauko maki fruits kisha ko. Namike zuwa gurin fridge na duka ke nan naji muryan shi yana fadin ina kika fito haka. Sai da na dauko ledan fruits din na kalli inda yake tsaye ya rike labulen shiga inner room din mu. Nace daga gidan yar adamawa nake ta haihu tun jiya ban samu shiga ba sai yau. Yanzun abinda kikaga dama kikeyi gaban kanki ko don kin mayar dani mutumin banza ko ? Ita Umma da kika fita kika bari agida ita kadai wakike son ya kulata idan tana bukatan wani abu. Nace ikon Allah baban Abba akan Umma kan banda maraina gareta don baka san cinmu ba baja san shan mu ba haka kuma bakasan tashin mu ba. Oho shiyasa kike bugun gaba don ban sani ba ko nace naga bai dace har ka fada min haka bane idan ni ban fada maka ba. Yace nagane yanzu wuyan ki yayi kauri maryam kina ganin kamar ban iya rabuwa dake ne ko may ? Da mamaki na dago kai ina kallon shi don jin furucin shi nace rabuwa kuma na yaushe kuma. Ai sheda kawai ya rage ka gwadawa duniya na ka rabu damu ni banyi magana kan zubar damu da kayi a garin mutane ba sai kaine zakace wai zakai min wanan. Ai dai duk abinda kakeyi Allah yana ganin ka tunda karuwan ka tafi mu daraja da kima a furin ka. Nufoni yayi gadan gadan da nufin ya mareni ya daga hannun shi sai yaji hannun nashi yaki sauka ji yake kamar an rike hannun nashi daga baya. Gani nayi ya juya baya kamar yana kallon wani abu sai dai babu kowa a gurin yayi yayi ya sauke hannun nashi amma ya kasa. Sake shi nace rai a bace sai kawai hannun nashi ya sauka daga makalen da yake nace barashi ya buge barshi. Take idanuwana suka sake laune sun rine sunyi jajajir dasu nace cikin wani murya da ba tawa ba yau daka mareni da ka kwana a lahira. Kayi kuskuren daga hannuwan ka ka mari godiyar mu duk mutuncin da halarci da take maka tana maka bauta da mahaifiyar ja da ka watsar saboda karuwan ka hannan. Hanan hanan hanan ko ? Zaku gane kuren ku daga kai har ita idan baka fita harkan wanan karuwan taka ba. Ka sani tana gab da kashe ka idan ta samu abinda take bukata daga gareka don ymunafukace bakai kadai take hulda dakai ba idan ka musa ka tafi gidan yanzun nan kaganan wa idon ka ko wacece hannan din. Zata bada kai watarana nan bada dadewa ba yau kaje gurin ta karfe sha daya na dare zaka san ko wacece ita. Ina fadin haka na zube gurin a somay a kasa Umma dake zaune a gefe duk abinda ke faruwa a gaban idon ta sai ta fasa ihu da kuka tana son tasowa zuwa gare ni sai dai jikin ta da nauyi bata iyawa. Shi ya dauko ruwa da jan shi ya zuba min na sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi zubur namike ina mayar da numfashi a hankali tare da dan waige waige. Ina ganina a kasa abinda ya faru na zuwa mari na da yayi ya fado min a rai. Take na karasa mikewa zaune da kyau nakai tsaye kasa tafiya nayi na koma saman kujera na zauna. Kaina jin shi nake kamar zai tsage min gida biyu don ciwon da yake min. Wayana dake saman kujera ne yai kara shi ya dauki wayan a rikce yake a lokacin. Muryan mace yaji kuma da bakuwar nomban da ba suna akakirani ya amsa da hello matar ta ce don Allah maryam nake nema please. Maryam bata da lafiya mijin take magana matar tace idan ta falka ka fada mata matar tsohon shugaban kasa ce takirata tana son magana da ita please. Layin ya mutu da mamaki ya furta a fili matar tsohon shugaban kasa maryam ? A ina maryam ta san matan ko chairman balle matar shugaban kasa masu fada aji a kasan. Mamakine sosai ya rufe shi a lokaci daya yana cewa a ran shi kai al,amarin maryam fa ya fara bani tsoro gaskiya. Ga yadda ya kasance da ita a yanzu gaban shi yaga yadda ta juye takoma kamar namijin zaki. Ga hannun shi da aka rike yana mai wani irin zugi kamar zai balle mai don zafi da ciyon da yake mai ga Umma dake kuka wiwi a gaban shi abin ya taru yai mai yawa a lokaci daya. ****** ********* ****** Hajiya Aisha dake zaune tana kallon yadda ake kwashe kujerun gidan ta tace tabbas yarinyar nan mutunce ke nan da gaskiya. Tunda ga mijin ta har munyi magana dashi ya tabbatar min da tana kwance bata da lafiya. Taso ta gaiyace ni zuwa dakin tane na duba mata idan ba sihiri a cikin sa sai ta bar kayan dakin nata dama duk ko ina na gidan. Gashi yau har taji sauki ta fita zuwa gidan marayu kai ziyara kamar yadda takeyi acan baya. Ta dade idan tana barci tana ganin fuskan wanan yarinyar ana fadin zata taimaka mata itace zata taimaka mata a dalilin tane kawai zata iya samun sauki. Sai gashi Allah ya kawo mata maryam har gida da kan ta ta taimaka mata sai dai kuma yarinyar taki karban komai daga gareta ko abin gidan bata yarda ta taba komai ba. Dole ne ta nemo gidan wanan yarinyar a duk inda take a cikin garin nan ko kasan nan yazama wajibi a gareta don tanemo yarinyar na don lafiyan ta dana yaran ta. Mutunci da kamala da kuma tarbiyan da tagani ga yarinyar yasa taji son yarinyar ya shiga zuciyar ta farat daya a lokaci guda. Wayan ta dauka takara kiran layin yarinyar har lokacin mmijin tane ya dauki wayan again. Cikin kwantar da murya take cewa don Allah a wani unguwa kuke ne ina son na gantane please. Bai tsaya tunanen komai ba ya fada mata uguwa da gida da yadda zata ce idan tazo gidan. Ba bata lokaci ta shirya take cewa kanin ta da ta dauko yanzu ta aje shi a gidan ta don yanzu hajiya tsoron kowa take ji. Bashir ka shirya mota zamu fita ni dakai ban son ka fadawa kowa fitan mu kasan yadda kayi ka kawar da kowa a get yanzu ganinan saukowa. Asirtacen hanyan daba kowa yasan dashi a gidan ba tabi har tafice daga gidan su karimay basu sani ba. Uguwar da zasu tafi ta fada mashi nan Allah yakawo su har gidan mu lafiya. Baban Abba wanda yaki fita gidan don tsoro ga hannun shi dake ciwo yana son zuwa ya gaskanta zancen da yaji yanzu a bakina yanajin tsoro. Haka ya daure don tabbatar da zargin shi ya nufi gidan hanna din bai tsaya sallama ba ya sakai dakin. Suna kwance tsakiyan aikata masha,a da wanda take kira wai dan uwanta ne yasan mutumin farin sani don wani lokaci har tana sa sai ya taimakawa mutumin. Ganin su a haka yasa shi rimtse idanuwan shi suka dago a firgice suna kallon shi juyawa yayi yabar dakin da sauri yafada motar shi yabar unguwar. Ina kwance naji sallama a kofan falo da kyat na iya daga kaina ina kallon mai shigowa gidan. Tana saye da bakin abaya ta yafa dan kwalin shi a kanta rataye da jakarta a hannun ta. Umma dake zaune take gaiyawa jin yadda Umma ta amsa mata magana bai fita cikin daga hannu yasa ta fahinci umna din ba lafiya gareta ba. Namike zaune da kyat ina gaida ita da mata sannu da zuwa lokacin ne kuma yarana suka taso daga makaranta suka shigo gidan. Nace mama kece tafe shine baki kirani ba nazo kika taso tace na bugo waya ance baki da lafiya diyata shine na taso. Nace ni lafiyata kalau ina dan murmushi a fuskana mamakine baiyyane a fuskan ta karara tace to yaya kuke nace lafiya kalau mama. Mama kin dai ki koran mutanen gidan ki ko idan baki koresu ba sun kusa ganin bayan ki dake da dan ki Ahmed da zai dawo satin nan suyi shiri sosai akan shi don shine matsalan su dake, sauran diyan naki matane basu damu dasu ba sosai. Ikon Allah inji hajiyan ke ko diyata duk a ina kika samu wanan labarin haka dan Allah nace nima ban sani ba na dai gani ne a tare dake kawai. Ta gyara zama da mazaunin glass din idon ta da kyau tare da kura min ido sai wani hamma nakeyi kamar mai jin barci a lokacin. Kafin tai magana nace mama Alhaji Ibrahim ya sha alwashin rabaki da komai naki a duniyan nan har rayuwanki dana diyan ki sai dai kuma da yardan Allah bazai taba cin nasara akanki ba don halin ki na alheri garesu . Matsalan ki daya dasuke samun galaba akan ki shine sakaci da Ibadan ki da kuma saurin yarda da bokaye da malamai don dasu ake hada baki ana kara cutata maki. Duk wanda kika gani a gidanki an riga da an saye shi da makuddan kudi masu yawa. Aikin wasu sukeyi a gidan ki banaki ba kawai don sunfi ba da aminci ga wancan din dake biyan su fiye dake. Kinga hajiya halira da itace ake kulla maki komai gashi kuma itace ta kusa dake sosai kin watsar da yan uwan haihuwan ki kin kama yan bariki ajikin ki. Mama ki jawo yan uwanki ki saka ajikin ki zauna da abinki lafiya don sune naki naji. Yan adam suna sakaci da zumunci a wanan zamani zumunci kuma ba abin wasa bane. Idan kin bar gidan nan zaki shiga gida ki tabbatar da abinda hajiya harira ta kawo maki wata biyu da ya wuce antone wanan mugun abin a gidan ki don babu ke ba lafiya muddin wanan abin yana a tare dake a gidan ki. Yanzun nan kisa Bashir ya shiga bayan ban dakin ki dai gurin da ruwa ke zuba zaiga katon dutse sai ya daga dutse duk abinda yagani ya dauke shi a kona akan ki da yaranki akai wanan sihiri wanda haka kawai zaki dinga jin haushin su kina hattaran su kiji baki son hulda dasu ko kadan. Duk wanda yai maki aanan aiki nan da kwana biyu da kan shi zaizo neman gafaranki da bakin sa. Abuna karshe yar uwarki halima dake lagos itace kawai nake son ki dan ja dabaya gareta ki rike sirinki a cikin ki don tana maki zagon kasa sosai a rayuwan ku. Ni zan tafi lokacin kararu yayi idan kin tsare wanan abin dana fada maki da yardan ubangin ba abinda zai kara samun ki ki karbi wanan dake da yaranki kuyi wanka da hayaki kusha na barku lafiya. Suuu natafi na koma saman kujera sai atishawa na fara sakewa mai karfi har sau uku na mike zubur ina dan waige waige Umma nagani zaune tana barci a saman kujera sai hajiya da ke zaune cikin damuwa ta kura min ido kawai tana faman yi min sannu. Nace mama ni lafiyata kalau ba abinda ya samay ni fa kina min sannu haka. Tace ai na sani amma sannu da kokari maryam nagode nagode kinji. Kallon Mamaki nake mata don ban san may takewa wanan godiyan ba haka a gareni. Wani atishawa na sakeyi again nace hajiya Aisha barka da zuwa tace yawa dawa nake magana kuma tace mukkadarasiya ce diyar Alhaji malam kike magana da ita. Tace sannu dazuwa ko muryana sak ya koma kamar wata balarabiya dani nace yauwa hajiya. Kin dai yi arziki mahaifina yasa hannu ga aikin ki amma ke ma baki da dama hajiya duk abinda ya faru dake kece sillar sa. Zaki iya tuna baya lokacin da kika tafi wani kauyen kasan Ibo gurin wani hatsabibin boka keda kawarki Ajoke. Wacce yau shekaran ta goma ke nan da mutuwa to tun wanan lokacin matsalarki ta fara. A matsayinki na musulma da kika san Allah da Annabinsa kikaje gurin kafirai inda ake tsafi don kawai son duniya. Ku bil,adam kuna da taurin kai sai ku sani ku take sani kamar yadda namu jinnu suke da taurin kai sosai idan an hadu da miyagun mu. Wanan bokan ba kowa yasa akaiki furin shi ba sai makiyin ki dan uwan mijinki kuma abokin shi Ibrahim. Sun hada baki da wanan matar data kaiki inda ya bata makudsan kudi masu yawa. Da ace kin dogara ga Allah kin mika kukan ki gareshi da zakifi samun nasara da haske ga bukatun ki. Da adam Allah zai mai falala yatsaya ga taimakon dan uwan shi musulmi, kina ziyaran asibitocin ku kina taimakawa marasa lafiya kina taimakon maraya ko dabbobi da zaki samu haske ga duk wani bukatan dakike dashi a gurin ubangiji. Wanan godiyar tamu maryama boyar Allah ce da tana dashi zata taimakawa marasa galihu sosai a rayuwan ta sai dai kukukuku ta kada kai arziki bai zuwa gurin da bayi ke bukatan shi . Hajiya tace don Allah wama kikace sunan ki tace sunana yana da wuya a gareku. Hajiya tace yanzu idan ina tin wanan abubuwan dakika lissafo min kina ganin zan gyara tace dayafi maki alheri. Waccan kawar ki Ajoke tuni aka gama da ita akan wani aiki da akaso tayi akan ku amma takiya. Ku dinga sa tsoron Allah ga al, amarinku matan bani adam sun shaga da son duniya suna mantawa da komawan su ga mahaliccin su. Macen bani adam zata bushe zuciyarta ta aikata ko maynene akan abokiyar zaman ta ko wani dan uwanta mutum wanda hakan ba daidai bane a garemu bisa ga koyarwa da manzo yai muna. Akwai hanyoyi da dama da zaka kai ga nasarorin ka amma duk an watsar dasu ankoma ga hanyan shedan wanda dama shi gurin shine yaga ya halaka duk wani mumuni na Allah su kone a tare. Nakima yana da sauki sosai gana wasu don ke neman zaman lafiya da maigidan ki da farin jini kikatafiyi bakice ai mashi wani mugun abin ba can. Kuji tsoron Allah ga rayuwan ku akwai jinsin mi jinnu da aikin su halakar dakune kawai zuwa ga halaka duniya da lahiran ku ni zan barki don godiyar mu ta huta sai mun sake hadu wani lokaci. Na sake wani atishawa mai karfin gaske har uku sai sannu Hajiyan take ta faman yi min duk umma tana ta sharan barcin ta ba aikomai akan idon ta ba. Wanda nasan haka aikin sune kada taji sirin wasu ko taga halin dana tsinci kaina aciki a garin mutane. Maryam na gode ni zan tafi sai kuma kin karajina ki min godiya gurin Alhaji malam. Ban fahince taba na dai amsa mata da to mama insha Allahu zaiji take ce min zaki kara jina da yardan Allah amma don Allah ina son nai maki wani tambaya idan bazaki damu ba. Ba matsala mama kiyi tambayan ki don Allah nace koke mutumiyar wani gari ? Nai murmushi nace ni mutumiyar Niger state ne mama tace ikon Allah zamane yakawoku garin nan ko aiki. Nace aikine yakawo maigidana garin nan shi ma,aikacin custum ne na kasa, shine muka zonan din tare dashi. Tace yanzun na gamsu dake maryama kin san duniya abin tsoro ne sosai yanzu dole nayi bincike sosai akan ki don gudun kada wani ya turo ki gareni cikin rashin sani a yaudare ni. Don hakan yasha faruwa dani sai ka yarda da mutum yazo ya yaudare ka daga baya kuma haka yasa nake jin tsoron hurda da mutane yanzu. Amma kinga yanzu na gamsu na dai fahinci ke alheri ce a rayuwana maryam Don kafin kizo na dade ina mafalki dake duk dare idan na kwanta zan dinga jin sunan ki a mafalki na ana fada min cewa kece zaki kawo min maganin warakana. Da farko har ina daukan zancen zancd ne na mafalki kawai, amma daga baya danaga abin yai yawa sai na fara tunane akai. Kwasan ranan da zaki zone nai mafalki da nai bakuwa maryam sunan ta zato zo min da warakana. Ba karamin jin jiki nayi a gidan nan ba watarana ma sai naji dama na mutu na huta da wahalan duniyan nan kawai. Nace mama mutuwa dace ne ga rahamar ubangiji don haka bawa ya roki Allah sauki akan al, amuranshi shine mafita kawai. Tace hakane wallahi ina yawan kai kokena ga ubangiji kin ga Allah ya karba min. Ta saka hannun ta a cikin hand bag din ta tana cewa Aisha da tashigo dakin baby zonan ki karba a saya maki alawa kinji. Aisha tazo gareta tana cewa yaya sunan ki yan mata ? Sai Aishan take ce mata Aisha Aliyu Auna. Kai kice ke takwaratace ashe ? Ikon Allah to karbi mummy ta saya maku alawa keda yan uwanki kinji ki yi kokari a school kinji kada kiyi ragganci ba, asan Aisha da tsoro ba. Aisha tace na gode mummy abin yaba hajiya sha,awa yarinya karama ta san anbata abu tayi godiya haka. Murmushi nayi daga inda nake zaune ina jin yadda hajiya take yaba mai sunan su. Kudi ne sabbi rapper yan dubu daya mike dasu har guda biyu. Nace kai mama kudin nan sunyi yawa wallahi da dai ki rage su please. Tace haba maryam don baki san ko nawa na kashe akan jikin nan nawa ba ko .? Na kashe kudi masu yawa ga banza banyi nasara ba don dan wanan dana baki aiba komai bane don ban iya biyan ki abinda kikai min arayuwana. Sana dinki nake gani insha Allahu sauki ya samu a gareni da yardan ubangiji. Nace dama haka rayuwa yake ciwo daban magani daban sai an wahala kafin asamu nasara akai. Tana mikewa tana gyara tsayuwan glass din ta Aliyu ya shigo gidan ranshi abace. Tun daya shawo kwanan mu ya hango wani katuwar motar jeep tsaye a kofan gidan shi yake mamaki kowake da wanan motan haka ? Don iya sanin shi bai san wani ba aduk fadin garin nan da zai mallaki motar miliyoyin kudi har yazo gurin shi. Har ya fito idon shi yana akan motar yana kiyasta yawan kudin wanan lafiyayyen motan daya gani fake kofan gidan. Sun dai gaisa da bashir a waje amma bai mashi magana ba yashigo gidan. Lokacin ya samu hajiya tana shirin ficewa daga gidan ganin shi yasa hajiya dakatawa daga tafiyan da zatayi. Tace ko wanan ne surikin nawa ko ? Tace mai barka dai yaya aiki yaya iyali ya amsa adan darare don rashin sanin ko ita din wacce. Tace to ni zan tafi sai anjima ke nan nagode ko Aisha Allah yabamu Alheri. Tana fita daga gidan yakai idon shi kan kudin da Aisha take mika min a hannun ta. Cikin wani murya yake cewa maryam wacece wanan matar dana gani yanzu tafita. Nace nima ban san ta ba kawai dai Allah ne ya hadani da ita har tazo gidan nan amma nima ban sani ba wallahi. Sai dai naji ance kamar matar tsohon shugaban kasan nan ce ita. May yakawota gurinki yanzu kuma ina kika santa ma wai ? Nace sako tazo na bata kuma na bata abinta ta tafi sakon may naji ya jefo min tambayan abazata. Nace magani ne irin na maganan mata kawai tazo na bata kuma nabata ta tafi. Kallon sunkin kudin dake aje a gabana yakeyi yana kada kafan shi har lokacin Kudin nan fa nace yara taba kyauta tace, Yace mu gani nawane kudin kamar fa duk yan dubu dubu ne nace ban duba kalan su ba don basu gabana yanzu. Mikewa yayi yatako har gabana ya dauki kudin ya bude wrappers din dubu dubu guda biyu a ciki. Yace what kyautan dubu dari biyu kai tsaye haka ikon Allah. Nace wanan bakomai bane a gurin su don Allah ya hore masu shi basu hasaran bawa nabaya dasu. Kallona yake a cikin mamaki Ummace da tai magana yasa zancen ya katse bai samu furta komai ba again. Nake cewa Umma may kike so ne na karasa da kyat zuwa inda take don duk jikina yai nauyi sosai a lokacin kamar nai wani aiki mai nauyi. Ruwa take so na debo mata ruwa na kafa mata tasha tace Allah yai maki albarka. Amin umma nace har na zauna take cewa kuma tana son ta kewaya bandaki. Namike nakaita ta kewaya tafito duk yana zaune yana kallon mu duk abinda mukeyi da ita. Haka yasa ya dan nisa kadan tare da dan bubuga kafan shi a kasa don yaga irin faman da nake da mahaifiyar shi abin yai yawa sosai cikin ma wai ta samu sauki ke nan. Yace cikin dan sauke ajiyan zuciya amma yanzu naga kaman jikin na umma akwai sauki sosai don gashi har naji kaman tana magana ko ? Gashi kuma tana dan takawa da kafan ta a hankali dai sauki na shigowa ke nan. Har yanzu maganin hawan jinin ne kukeyi ko may ? Nace ba hauwan jini bane ke damun ta ciwo dai ne don maganin hawan jinin ai halakata ya so yayi. Sai dana canza mata da na gargajiya gurin dana taba karbawa Nusaiba ta samu lafiya can na karbo mata shine mukaga wanan saukin haka. Maganin hausa kukeyi aka samu wanan saukin haka ke nan ? Nace shi mukeyi da yardan Allah kuma zata samu lafiya takoma daidai da ita. Allah yasa yace tare da mikewa tsaye yana fadin shi zai fita ke nan ko akwai abinci yunwa yake ji. Kai Umma ta girgiza don takaici ni dai na mike na kawo mai abincin shi ya fara ci ga nama zuku zuku a ciki ya zauna yaci sosai can yace wai naman may ye haka kuka samu mai dadi ? Nace naman baunane aka bani nai miya dashi da sauri naga ya mike tsaye yace what naman bauna a ina kika samu naman bauna haka? Nace kaidai ba kaci ba may ye na tambaya kuma haka kaman wanda yaci naman mugun dabba. Look ina kika samu nama nace maki please ? Nace anbani ne a wani tsibiri danaje karbowa Umma magani. Yace what ? Sai naga ya fara kakaro amai kamar mai son amaye hanjin cikin shi lokaci daya. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU[11/11, 12:10 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BANE A, , , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣2⃣ Ya shiga damuwa don yasan tabbas akwai bakon al,mari ga zancen na a yanzu. Fita yayi daga gidan bayan ya gama kare karen aman shi a back yard yafito zuwa waje. Wayan shi dake a aljihu shi yaciro ya kira layin mahaifina wanda yake gani shi ya dace ya fara fadawa wanan zancen. Sun gaisa da babana tare da tambayan jikin shi shima baba tambayan jikin Umma yayi da aikin shi. Ya amsa alhamdullahi ba duk muna lafiya Umma ta samu sauki sosai don yanzu har tana tafiya tana magana. Alhamdullahi inji baba din yace, Aliyu yace baba dama nakiraka ne na fada ma wani magana akan maryam. Subbahanallahi inji baba din yace maryam kuma may samay ta kuma ? Aliyu yace baba a gaskiya maryam yanzu gaba daya ta canza wani bakon al, amari ne nake gani a gareta. Ga mamakin Aliyu din sai yaji baba yace na jinnu ko ? Yace a sanyaye haka ne baba. Yace gaskiya maryam tana tare da jinnu kuma masu karfi ne a tare da ita sai dai bama su cutawa bane. Dama kasan matsalan mahaifiyar ta ke nan shine yanzu suka koma kan yar ta. Kada ka damu da wanan don nayi iya yina akan hakan amma babu abin da zan iya akai dole mu barta da abinta don musulmai suma kamar mu. Al,amarin maryam da jinnun nan yai nisa Aliyu matsala daya ne ka kaucewa shiga harkan ta ta baya don kada su dauki fansa akan ka. Saboda duk wanda ya shiga harkan maryam a shirye suke da su dau fansa akan mayshi. Saboda son da sukewa mahaifiyan tane ya shafe ta har suke mata wanan irin son haka. Amma gaskiya al, amarin maryam nima yafi karfi na don maryam tasan abinda ni dakai da ma wani bai sani ba a yanzu. Kallo daya zataiwa mutum ta gane matsalan da mutum yake ciki kaga ashe al, amarin nata yayi nisa ke nan. Nisawa Aliyu yayi yace to yanzu baba yaya za, ayi ke nan ko haka zamu sa mata ido muna kallon ta. Murmushi baba na yayi yace Aliyu ka kwantar da hankalin ka akan al, amarin nan don abin yai mata nisa sosai. Kuma zuwan ku gidan nan na kaduna ne abin ya karu a kan ta don a gidan kuna tare dasu duk inda ma kake tunanen zaku yanzu a tare dasu kuke. Duk gidan da kake gani akwai su sai dai mu bamu sani ne sunfi mu yawa a duniya don su basu mutuwa. Muko kaga muna ragewa don muna mutuwa kuma bamu da shekaru kamar su. Maryam tare take da babban malamin jinnu wanda kowa ya sani da Alhaji malam Sunan shi sulaimana malami kamar shehi ko waliyi a cikin su yai taimako ne shi a duk inda yaga musulmi yana a cikin halin bukatan taimako. A sana diyar yar shi maryam ta hadu dashi wanda har yakai sun bude mata ido tana ganin su ko yaushe har tana zuwa biranen su ziyaran su. Ziyaran su baba ita maryam din ? Babana yace ita din kuwa duk sanda taso zuwa garesu suna bude mata ido zuwa tsibirin su dake kasan sin amma rayuwan su tankar anan ida kuke sukeyin shi don su a gurin su ba komai bane hakan. Shiru Aliyu yayi yana sauraren babana a cikin tashin hankali da ke mai bayani akai na. Su kai sallama da baba ya kashe wayan cikin tashin hankali yana mamaki yaushe ne wanan al, amari ya fara wa maryam haka har yai nisa bai sani ba. Cikin damuwa yake sosai haka yaja kafar shi yafita yabar gidan cikin damuwa yana ta faman sake sake a ran shi. Ji yake kawai ya nemi wani gida mu bar wanan tunda shine keda matsala. ****** ********* ****** Har yamma yana batun yi ban shiga gidan mai jego ba kamar yadda nai masu alkawari gashi sai faman jiran shigowa na sukeyi a gidan Ganin banzo ba yasa suka biyo ni har gida gurin na sun samay ni akwance cikin mutuwan jiki kan abubuwan da suka faru dani don ba sabawa da hakan jikina yayi ba. Yanzu mama Abba haka mukayi dake bayan kin san muna da appointment dake zaki share mu gidan maijego muna jiran ki. Mu dai fito muna da kayan mugani idan irin wanda nake dasu ne nabar maki kayan ki. Don ke san sokoto mune iyakan kayan mata ba a gwada muna kaya sai dai mu gwadawa wasu. Ni dai sai murmushi nakeyi kawai na mike zuwa dakin yara inda na aje kayan tun lokacin da nazo dasu gidan. Nake cewa dasu su shigo don Umma tana zaune a falon kuma ina jin kunya da nauyi tasan abinda mukeyi. Nan muka zube na fara fitar masu ina masu bayani akan komai suna gamsuwa. Yar sokoto take cewa gaskiya ita bata taba ganin wanan kayan ba tanayi tana dan danawa wai ita tasan kan su. Sosai sukai min ciniki don sun sai kayan yadda ya kamata su saya duk da ban cika masu kudi ba sosai. Sun fita na koma na kwanta abina don ina jin jiki na sosai a lokacin. Sai dai kafin subar gidan mu har yar sokoto tafara wani hamma tana mika na ce yaya dai mutumiyar sokoto takecewa ai ba magana kawai wanan kayan naki maman Abba akwai caji wallahi. Anty hauwa ta kara rudewa akansu sai dariya mukewa yar sokoto suka fice. Waahegari yara na tafiya makaran ta sai ga anty hauwa a gidan mu cikin hausan tana yare take ce min. Maman Abba zozozonan mu zauna yanzu kina da wanan kayan haka kika barni ina kashe kudi na a banza kan wasu. Nan dai take bani labarin yadda suka kwashe da mijin ta a daren jiya. A raina nace masu maza ke nan nikan rabona da nawa mijin ma aina manta rana. Sai dai naga jiya ya kwana a gida yana ta faman juyi yana tsuki ban bi ta kanshi ba don nima ina fama da kaina. Ganin na samu sauki washegari na shirya zuwa sarin kaya don na samu naci kasuwa gurin masu shigowa suna easthe din mu jibi. Na shirya sai kasuwa shagon bedshirt na nufa na samay shi zaune shagon ya karade da sautin kira,a na Sudes. Shima kanshi mai shagon sai ka dauka ko wani balarabd ne shi ga gemen shi mai tsawo kamar balarabe cikin kamun kai. Yana ganina yadan saki murmushi yana cewa maman Nusaiba yaya kwana biyu ? Yanzu bakya son zuwa da Nusaiba ta girma ko tayi wayo? Nace tana gida na barta da yan uwanta a gida ne yace aiko basu gida akwai mutane a gidan ku don babu ku kadai bane a gidan. Yace kina zaune tare da mutanen kirki masu halin alheri a tare dake. Azatona ko su anty hauwa yake nufi nace hakane fa suna da kirki da dadin zama. Yace lokacin da yake mikewa tsaye kwanaki mata suke fada min kin shigo gida sai dai kin samay mu da baki a gidan. Nace hakane nima ban san da zancen haihuwan ba dana tafi da shiri na ai ranan sai kawai na samu gidan da baki a cike. Yace sai dai kiyi hakkuri don na tambaya ko dai ba wanda ya razanaki ake ce min kin samu kulawa daga gurin Fati,a Kin san bukin mu ba irin naku bane don mu mutane ne daga nahiya daban daban suke zuwa muna kowa da halinshi kuma. Ba, abinda ya samay ni nace mai a gaiyar min dasu idan ya tafi gida. Bedshirt ne masu kyau ya fitar min dasu a gabana yana cewa wanan kayan masu kyaune yan bugun chaina ne kingan su nan . Saboda ke na ajesu don zaki samu alheri sosai akan su da yar da Allah. Nace anya zan iya saran su duka kuwa sai dai na saya daidai kudina kawai iya inda ya tsaya. Yace haba malama maryam damu dake yanzu mun zama daya kina zama a gida daya da yan uwana akan may bazamu taimaka maki ba. Nace abarshi kawai zan dai dauki iya kudina inayi ina juya kayan don kyawon su. Na koma fannin kayan yara ina dan dubawa a hankali muryan shi naji yana fadin . Ki zabi wanda kike so sai na aje maki don kinga Azumi ya kusa lokacin cinikin su yayi . Zan kuma dauki lokaci mai tsawo bana nan don bani azumi kin san a kasar na ina zuwa ibada ni da iyalina. Ina zaba yana ce min hada da wanan wancan ma zai dauko gareki har na tara kaya masu yawa ban farga ba. Na fita zuwa shagon turare na sai iya kudina da sauran tarkacen da nake bukata a kasuwan wanda nasan zasuyi sauri shiga gun mutane. Nadawo gida niki niki da kaya mai taxi ya dora min kan step ya tafi bayan na biya shi. Na dan zauna falo na huta har abinci sai da naci na dan sarara na mike zuwa dakina don na aje handbag dina. Sai may ? Kayan yaran dana zaba a kasuwa nace a je min idan na samu kudi zan tafi na kwaso ne nagani a dakin an tara min su daga gefe daya gefen gadona. Nace na shiga uku ni maryam cin bashi kuma harda na aljannu haka ? Sai ganin kaina nayi kamar a kasuwa cikin wanan shago tare da bin yusuf mai shago yana ce min. Ba bashi bane maryama ke yar uwatace bazakici min kudi ba yarda ne yasa na baki don halinki na alheri. Nace amma kuma gaskiya, , , , A, a maryam ki shigar da kayan nan zasu samu shiga sosai a gurin ku idan kin tallata su sai ki kawo kudin na baki wasu. Mussaman na dauko su don ke ki samu karuwa a rayuwan ki kada ki damu ke yar uwata ce. Daga haka ina fadin nagode sai ganina nayi zaune saman gadona nayi tagumi kawai. Tsoro ne ya kara kamani a lokacin duk na firgice nace nashiga uku ni maryam yanzu yaya zanyi ke nan da dukiyan mutane haka masu yawa Mama ga sauran kayan ki wai an kawo maki muryan Abbane ke fadin haka daga falon mu. Da sauri nafito ina mamakin wasu kaya kuma yake magana again ina fitowa sauran bedshirt din dana bari a shagon ne a cikin manyan leda. Cikin wata murya nake tambayan Abba waya kawo su kuma yace wanan mutumin daya sauke maki kayane, zaune nakai na dora hannun na akai ina fadin na shiga uku ni maryama. Haka na karasa wuni kamar kwai ya fashe min aciki sai na kalli kaya nakali kaina na dafe gefen fuskana. Haka baban Abba yadawo gida ya samay ni a cikin damuwa ya lura da yanayi na gashi ina son fada mai rigimar dana kwaso amma ina jin tsoro. Idan ma har zan fada mai may zance dashi akan kayan to may zamce dashi. Naja bakina nai shiru sai shi da idon shi suka kai kan kayan ne yake tambayana duk wannan shirgin kayan na may nene haka ? A sanyaye nake ce mai kayan sayarwa nane yace a razane duk wanan kayan haka masu yawa maryam naki ne sai nai shiru kawai. Washegari nashirya sai kasuwa hankalina a tashe sai dai ina zuwa shagon nasu a rufe yake na dan jima a gurin tsaye sai ga wani mutum yazo wucewa zai bude shagon shi nake cewa don Allah malam mai shagon nan nake tambaya ? Yace Oh Alhaji Bin Yusuf kike magana wallahi yai tafiya yace bazai dawo ba sai bayan azumi idan Allah ya kaimu zai dawo kin san azumi ya kusa zuwa. A daga can zai tafi umurah gurin ibada insha Allahu yanayin da mutumin yaga nashiga ne yake cewa hajiya lafiya dai ko ? Nace cikin girgiza kai a, a ba komai dama wasu kayane nazo na sara a gurin shi. Yace ayya ai sai dai kiyi hakkuri ki duba a wani shagon ko dayake shi kayan shi duk kasuwan nan na daban ne gaskiya. Naiwa mutumin godiya haka juya jiki a sanyaye cikin wani sabon tashin hankali ni yanzu yaya zanyi da dukiyan wanan bawan Allah haka daya jibga min a hannu na. Yazama wajibi a gare ni dole na sa ido naga kudin shi baiyi ciwon kai ba ko kadan a gurina. Ranan suna sai da na gama komai na fita don zuwa kama aiki saboda zama tare nima watarana , zanso aimin hakan a gidana. Yadda na samu baki yan uwan maijego sunzo har sun kwana wasu kuma yan gari sun soma hallara ko. Nazage na dan sake ana sha, anin buki dani sai bayan mun kamala ne na koma gida nai wanka nazo da kayana muka baje ni da su anty da yar sokoto. Nan mutane suka fara zuwa suna tabawa aikafin ace may sai ga masaya na ta bukin suna saye don sunga arahan su ga kuma kyau. Yar sokoto na ta faman dada kayan da quality din su bashi ne bamu yarda mubawa mutum sai dai ki saya ki zube muna kudin mu. Sosai nai ciniki a gurin nan sai ga yar sokoto ta ballo da zancen kayan mata. Haba nan sabon kasuwa kara buduwa min sun saya sosai wanan kan nai cinikin sa fiye da kima. Zance wanan taron bukin ba karamin jawo min alheri yayi ba sosai don ya zama min wani silar alheri a rayuwana. Don wani kofa ya bude min nan mata suka fara tururuwan zuwa har gida sayen kaya wasu har sari suka dauka a gurina na dan kara masu kudi a sama kadan. ****** ********* ****** Kamar yadda hajiya Umma take son tabbatarwa akan maganan mu yau sati uku ke nan da lissafin ta bayan ta idar da sallah la, asar take cewa. Yaudaran banza yaudaran wofi dani za, azo har gida aiwa 419 don kawai aci kudina don an hada baki a cuta min. Taja tsuki tace duk da dai maganin da takawo min yai min amfani na daina jin komai a kafana kuma yanzu yakai ma kamar banyi ciwon kafa ba a baya nake ji. Wanan bazai zama hujja ba a gare ni ai magani sa, a ce bawai yin mutum ba ko wani. Kawai ta samu wani wanda yasan sirin abinda ke damuna ya fada mata komai akaina gani tsohuwar banza yarinya karama zatazo har gida ta sani a kwana hakanan. Nan take zaune saman sallayan da ta idar da sallah da carbi a hannun ta tana dan karkada kafan ta a hankali. Kofan shigowa dakin ta aka turo da sauri ta daga idon ta tana kallon wacce tashigo dakin nata. Kafin maishi tai magana take cewa wai Fati saunawa zan fada maki idan ina daki ki daina shigo min dakina hakane ? Kai tsaye baki daga waya ki kirani koma may ye ki fada min may ye amfanin wayan dana saya maki har biyu don bukatana ? Mama ba hakana bane yaya Nasir ne ne yadawo shine nashigo na fada maki . Wa kikace Fati tace yaya Nasir ne yazo harda matar shi da yaran shi biyu baki gansu bane masu kyau dasu wallahi. Zubur hajiya ta mike tsaye cikin mamaki tace Nasir fa kikace Fati ? Wallahi mama shine shine ma don hoton shi dake manne a falon ki ina iya sheda shi. Ai kafin Fati ta karasa har hajiya takai kofan daki ko ta riga fatin fitowa waje. Yana tsaye gaban katon hoton mahaifin shi ya tsurawa hoton ido yana kallo bayan shi kawai ta hango. Tun bata karasa saukowa ba take ambatan sunan shi Nasir kaine ko gizo idanuwa suke min ne ? Yajiyo tare da kurawa mahaifiyar tashi ido kafin ta karaso gare shi ya zube a kasa gwiwa bibiyu yana kallon ta. Inda yake durkushe takaraso itama zubewa tayi a gurin tana kuka matarshi dake zaune a gefe tana kallon su tajawo yaran ta zuwa jikin ta ta rugumay su. Hajiya tana fadin Nasir ina kashige ne haka ka boye muna yadda taga ya fara dan ja da baya yasa ta tuna da gargadin da akai mata. Tace Nasir don Allah kazo gare ni idan ba mafalki nakeyi ba nagane ka. Jin haka yasa ya tako zuwa gurin mahaifiyar tashi suka rungumay juna baka jin komai sai kukan dake tashi a tsakanin su kawai. Sai da sukayi mai isan sune suka lafa yake gabatar da matar shi da diyan shi ga mahaifiyar shi. Bata jin hausa sai larabci da turanci koshi ba wani sosai take ji ba sama sama suka gaisa da hajiyan . Hajiya ta mika hannu wa yaran da nufin suzo gurin ta amma sukaki suna makale a jikin uwar su kawai. Nan hajiya tasa a gabatar masu da abinsha da sauran su a gaban su. Kafin wani lokaci Fati tasa an cika masu gaba da abinci da abin tabawa sukaci suka sha aka kaisu masaukin su. Sai da dare ne zancen wanan yarinyar da ta dauka a mayaudariya yazo mata a rai. Lalai ya kamata ta nemo wannan yarinyar don akwai abubuwan da zata bukata a gurin ta da take son sani. Godiyan ta ga Allah shine tayi dabaran karban nomban wayan yarinyar daba haka ba bata san inane zata zakulo taba a fadin garin nan. Ta sake sauke ajiyan zuciya tana cewa Allah nagode ma yau Nasir ne yadawo gida cikin mu harda iyalin shi. Idon ta ta runtse tana mai jin zafi a zuciyan ta abinda take tunane shine daga ina wanan matsalar na Nasir yafito mata. Dayasa kai yabar gida haka na tsawon lokaci batare da kowa yasan inda ya shiga ba ? Gashi kuma da zai dawo yadawo mata tare da iyali da alaman natsuwa kuma a tare dashi. Ba wani alama dake nuna yana cikin wahala a tare dashi ko wani mugun hali. Yanzu ma wazata fara fadawa dawowan shi cikin yan uwan ta. Wata zuciyane ta gargade ta da ta nemi yarinyar nan tukun tafara jin ta bakin ta shine mafita a gare ta don bata san daga inane matsalan shi yake ba. Takira nomban yarinyar amma sai ace mata is swich up haka ta hakkura ta kwanta zuciyar ta tab da tunane. Washegari na idar da sallah namike zuwa kitchen don na dorawa yan makaranta abinci don gudun makara. Sai lokacin naga wayana dana bari yashe a falo daren jiya dauka nayi don in duba time sai ganin ta nayi a kashe. Nasan ba kowa bane Abbane dake game da ita jiya da dare ya kashe min ita. Kamar anajira na kunna wayan sai ga kira ya shigo a wayan nawa da mamaki nake kallon wayan sai dai bakon nomba ne ake kiran dashi. Kamae kadana dauka sai na tuna kilafa mutanena ne da muke sana, a dasu suka kirani. Na dauki wayan da sallamana jin bakuwar muryan da ban sheda ba nayi tana karba min sallama na. Muka gaisa da ita acikin dadin rai take tambayan don Allah da maryam nake magana ? Nace nice insha Allahu. Sai naji ta sauke ajiyan zuciya tana cewa boyar Allah tun jiya nake kiran layin ki amma wayan a kashe yake. Nace ayya kiyi hakkuri wallahi yaro ne ya kashe min ita tun jiya da dare tace Allah sarki. Dama nakiraki ne na fada maki cewa Nasir yadawo jiya da yamma nan. Nasir na tambaya wani Nasir sai naga kamar abu ya gilma a cikin idanuwana lokaci guda. Nan take zance ya canza min nace dawa nake magana please ? Tace hajiya Umma ce au hajiya kin gama zargina ke nan kina ganin kamar ni yar 419 ce ko nazo na cuta maki har gidan ki. Ki sani niba macuciya bace taimakon ki kawai nayi don ganin halin da kike ciki. Amma runda kin zarge ni kada ki sa rai cewa zaki kara gani na don ban son mutumin da baida godiyan Allah. Mamakine yakama hajiya a bangaren ta tace cikin marairai cewa don Allah kuyi hakkuri duniya ne yanzu bata da tabbas kawai. Amma don Allah dai ayi hakkuri a yafe min Allah dakika ambata yasa zamu kyale ki da mun mayar maki dashi inda yafito inda bazaki kara jin labarin sa ba ma a duniyan nan. Nan dai ta shiga bada hakkuri hankali a tashe saida tai kamar tanayi aka hakkura mata. Nace kin kirani ne kiji wazaki fara fadawa dawowan dan naki ko ? Tace hakkane nace zaki iya fadawa kowa amma duk wanda ya amsa maki a cikin mamaki yakira sunan danki har sau biyu da mamaki shine munafukin ki shi yai maku wanan aiki akansa. Ba komai ne akansa ba sai kurciyan da akai mashi don son da kike mai keda mahaifin shi ya jawo maku haka. Tace ikon Allah insha Allahu zanyi kamar yadda kikace min din nagode nagode. Ina kashe wayan na yanka wani irin ihu wanda yasa duk wanda ke gidan fitowa a lokacin. Lamau nake tsakiyan falo ina wani irin gurji cikin wani irin sauti mai ban tsoro. Baban Abba yayo kaina cikin razana ya na kiran suna na a cikin tashin hankali. Yana kokarin tabani ne aka dauke shi aka maka shi a bango kumus ya buge. Bai hana shi dawowa ba ya kara cakumana cikin wani murya da ba nawa ba akece mashi kada ka soma taba muna godiyan mu. Don bamu yarda da kaiba kana cuta muna godiyar mu da mugun halin ka. Kana sa ana zargin itace take hanaka alheri kana fifita karuwan ka akan ta duk da munyi warning din ka bai hanaka komawa gareta ba. Zamu dauki fansa akanka nan ba dadewa ba daga kai har waccan matar banzan da kake hurda da ita. Zamu tozartaka a duniya zamu kwato ma mahaifiyar ka da yayan ka hakkinsu da kake tauyewa. Mun maka warning kakejin maganan mu hukuntaka ranan da ka kawota gidan nan da zuman aikata zina a gidan matarka ta sunna . Amma baisa ka daddara ba ka daina wanan harkan da kake yi yanzu duk abindaya faru dakai ka sani kaine kajawa kan ka don baku kadai bane a gidan nan kuna tare damu a ko ina sai dai a gurin da bai kamata mu shiga ba a lokacin da kake tare da godiyar mu. Yana duke a kusa dani ya kura min ido don sam wanan muryan ko kusa ba muryan maryam din daya sani bane tashi. Zamu tafi mubar godiyar mu ta huta hakana kada mu wahal da ita da yawa. Sai na kara mikewa na dan lokaci can na sake wani atishawa har sauku da karfi. Lokacin ne na bude idanuwa na da suka rine min sukai ja ina kallon duk wanda ke falon sai faman sannu suke min. A hankali na mike zuwa saman kujera na zauna lokacin Umm dake tsaye daga kofa ta karaso gurin duk abinda akayi aka fadi akan idon ta akayi shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/12, 11:23 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣3⃣ ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI INA MAI KARA SANAR DAKU FITOWAN SABON NOVEL DINA DAKE AKAN HANNYA SATI MAI ZUWA DA YARDAN UBANGIJI WANDA KE BUKATA YANA IYA KIRAN LAYINA DON YIN REGISTER A GROUP DINA NA KUDI NAGODE DA KAUNAR DA KUKE NUNA MIN A KULLUN TAKE KAUNAR KU DIYAR KU YAYAN KU ZAINAB IDRIS MAKAWA Baban Abba yana duke a kaina sai yan tofe tofe yake min tare da faman yi min sannu yake yi hankalin shi a tashe. Ina kada kaina dake sara min a hankali can dai na kara sake wani atishawan sai yar mikan da nayi na dinga binsu da kallo daya bayan daya duk suna tsaye akaina har yaran nawa a guri daya. Zubur na mike yana fadin ina zaki kuma nake cewa abinci zan duba na dora girki a wuta nake gani. Ki barshi a duba maki nace zan iya insha Allahu nasa kai na shiga sai da na gama zuba masu nai komai kafin su fita na samu guri don zazzabin da nake ji na kwanta a falo sai barci. Ranan yaran saida suka makara haka uban ya kwashe su hankali a tashe suka tafi tare da shi. Ban falka daga barcin danayi ba sai sha biyu da wani abu duk jikina sai ciwo yake min kamar an bani kashi nake ji a lokacin. Tunawa da mafalkin da nayi cewa na nemi hantiti na aje na dinga shakawa idan naji banjin dadin jikina haka. Na idar da sallah wanan nomban da aka kirani dashi da safe ne aka kara kirana dashi a lokacin. Kamar kada na dauka sai dai na dauka daidai lokacin da wayan yake batun tsinkewa. Muryan hajiya Umma ce take cewa kiyi hakkuri dani maryam na damay ki da kira please don Allah ko zakiyi min kwatancen gidan ki ina son turo maki da wani sako ne. Ba bata lokaci ba nai mata kwatancen ida nake tace min sai na gan ta mukai sallama na aje wayan. Baban Abba ne ya shigo gidan don sanin ya barni ban da lafiya yasa shi dawowa gida da wuri haka. Nai mashi sannu da zuwa yake tambayana yaya jikin nawa nace da sauki. Abincin ya zauna yaci wanda yazo dasu a take awaya don yasan bazan iya dafa komai ba a yadda ya barni kwance kafin ya fita daga gidan. Yamayi mamaki da ya shigo ya samay ni zaune saman sallaya na idar da sallah lokacin. Umma ma tafito daga daki tana min sannu da jiki suka zauna nan tare dashi suna magana. Dirin motan da mukaji ne sun tsaya a kofan gidan mu yasa shi mikewa ya nufi kofan ya duba ko waye. Bakin fuska ne ya gani suna fitowa daga motocin su kuma da ganin su masu fada ajine a gari don yanayin su da shigar su uwa uba motocin da suka zo dasu har guda uku. Nan suka gaisa dashi ta gabarta da kanta gareshi yai mamaki don sunan ta ba bace yake ba a gari don kowa yasan ta sosai. Take fada mai suna son ganin matar shi ce maryam mamakine sosai yakama shi ida na san wa yan nan mutanen nan haka. Yace da ita bissimillah ko sai ta danyi murmushi tace sai dai tare da yarona muke ko zan iya shigowa dashi gidan nan. Dan jim yayi kafin ya daure yace bissimila ba matsala ku shigo daga ciki a tare dashi suka karaso har zuwa cikin falon mu. Ina ganin ta na sheda fuskan ta nake cewa sannu da zuwa Umma. Muka gaisa dasu gaba dayan su suma suka gaida Umma cikin mutunci. Nan ta fara magana maryam sai kika ganni a bazata a gidan ki ko ? Kiyi hakkuri yakama dole ne nazo don na nuna maki jin dadin abinda nai nasara ta dalilin ki nai maki kuma godiya. Yau dai ga dana Nasir Allah ya dawo min dashi gida bayan tsawon lokacin daya dauka baya gidan. Jin abinda ta fada ne yasa na daga kaina nadan saci kallon wanda ta gabatar da sunan dan ta daya bata da dadewa. Yau gashi da taimakon Allah a sanadinki mun samu Allah ya dawo muna dashi gida lafiya duk ta sanadiyar ki hakan ya samu. Haka yasa na wanko kafata nazo har gida nai maki godiya tare da baki dan sadaka da fatan bazaki raina dan kyauntan da nazo maki dashi ba. Sai ta mika hannun matar da sukazo tare ta miko mata key daga hannunta. Hajiyan ta dan zakudo daga saman kujeran da take zaune tana miko min key din tana fadin gashi motace sai dai ba wata babba bace 406 ce kika samu. Naso ace akwai kalar data dace dake ta mata sai wanda zai dace daidai, dake na kawo maki amma babu ita a kasa yanzu. Wanan da kike gani tare dani shine Nasir din daya bata tun mahaifin shi yana da rai yau kimanin shekara goma sha biyar ke nan bamu san inda yake ba. Munyi neman shi duk inda ya kamata amma Allah baisa andace ba sai da naji albishir din dawowan shi daga bakin ki kuma ban yarda da zacen ki ba a lokacin. Amma Allah da ikon shi sai gashi jiyan ya dawo gare mu daidai lokacin da kika fada muna dawowan nashi. Haka yasa idan da hali zanso nadanji wani karin bayani daga bakin ki akan batar nashi ko akwai abinda zamu iya sani akai. Kaina nadago a hankali nace hajiya kyautar mota haka kan wanan maganan kawai. Mamakin furci na tayi don cewan da nayi kan wanan maganan kawai a ranta take cewa yarinya baki san halinda na shiga bane yasa kika fadi haka. Naci gaba da cewa nima fa banice nai hakan ba ikon Allah ne sai sakon da baba malam yace na fada maki kawai yasa nane mi gidan ki na fada maki. Murmushi tayi tace maryam wanan ba komai bane idan da zaki san ko miliyan nawa muka kashe bazakiyi mamakin ba don na baki wanan motar kawai kinfi haka a gurina maryam. A daidai lokacin ne nafara wani hamma na ina yi ina dan murza hannaye na guri daya a lokaci guda take murya na ya canza zuwa sabuwar murya. Ina fadin salamu Alaikum hajiya duk suka karba min sallamata, gaba dayan su a falon. Nace da farko muna tayaki murnan dawowan jinjirinki a cikin ku da fatan zaki kwantar da hankalin ki ki saurare mu. Nasan kin na zargin wata da aikata maki wanan aikin akan danki wanda zarginki ba anan yake ba. Wanan matar da kike zargi har kan aiki ne kawai a tsakanin ku da ita abin baikai haka ba Bazan so fada maki wanda yai wanan aikin ba kai tsaye amma maishi zata fada da kanta. Mahaifin jinjirinki yana gwadawa jinjirinki so da kauna wanda har yakai bai iya boyewa kowa a fili cikin jinjiran da Allah ya bashi. Wanan ne dalilin da tsanarsa tai yawa a zukatan mutane da dama saboda suna ganin duk wani dama nashi zai kare ne akan danki. Sai na kada kai a cikin takaici nace kai bil, adam baku da kyau baku da tausayi a rayuwan ku. Ki godewa Allah jinjirinki yana rike da Allah a tare da shi sosai da ba iya abinda zai faru dashi ba ke nan. Ko zaki iya tuna matar da takawo maki tallan tufafin yara a office dinki a shekarun da suka wuce ? Har kukai sa,ainsa da ita kafin ki sayi kayan idan ma baki tuna ba bari na tuna maki yau . Kawar kice amma sai tana hurda da wata da baki yarda da ita ba haka yasa zargi ya shiga a tsakanin ki da ita. Wanan tufafin dakika sayawa jinjiranki agurin ta ne farkon sanadin batar danki don kin saya masu kayan dake da sihiri a cikin sa. Gaba daya yayanki hudu sun shiga tsana a zuciyar mahaifinsu wanda ke baki kawo komai a hakan ba a ranki. Hajiya tace anyi haka gaskiya amma ni ban san cewa Gajiye zata iya min haka ba gaskiya. Zata iya fiye da hakan don itama a lokacin tana son ta auri maigidan naki sai dai tana ganin baida kowa a gaban sa sai ke da zurian ki. Cikin mamaki hajin tace ita gajiye din ke nan ko ? Kwarai kuwa don haka yasa take hurda da abokiyar zaman ki wacce itama bata san cewa rudin ta takeyi ba a lokacin. Tare suka hada kai sukai mashi kurciya wanda ba zaku kara ganin sa ba a duniyan nan gaba daya. Allah ne ya taimaka yana barin nan bai tsaya ko ina ba ya fada dajin kashimil inda ya fada a hannun wani musulmi hafizi yake taimaka mashi. Wanan matar da yazo da ita wanan bawan Allah ne ya taimaka mai saboda sun yaba da hakalin shi sosai suka bashi yar su aure. Kurciyar da akai sihirin da ita ta mutu a daji cikin sahara acan muka nemo layan sihirin muka warware shi shine har hankalinsa ya dawo gida sosai kikagan shi. Idan da bamu samu dauko wanan layan ba danki ya bata daga gare ki ke nan har abada. Sai dai kuma anan gida ana bata mai sunan cewa ya saci makuddan kudin mahaifin shi ne yasa ya gudu ya boye dasu ko ? Hajiya tace haka ake fadi gaskiya amma ni nasan ba haka bane maryam. Murmushi nayi nace ni ba maryam bace zaki iya kirana da malam sulaimana ko Alhaji malam uba nake a gurin maryama, godiyar mu ce ita da muke aike kawai a gurin ku bani adam. Saboda ita tamuce jinin muce muna da alaka maigirma a tsakanin mu da ita cikin bil,adam. Za,a kawo wa danki abubuwa da dama da sunan murnan dawowan shi gida cikin ku , bashi ba koke kada ki taba ko daya daga ciki komai sha,awan da abin ya baki. Har zuwa wani dan lokaci bazaki fahinci danki ba don haka kibishi a sannu har komai ya daidaita akan shi. Na barku lafiya lokacin sallah ya gabato sai wani lokaci idan Allah yakaimu kuma. Shiru nayi na dukar da kaina yayin da kowa na falon ya numfasa don jin abin al, ajabin da sukaji daga bakina. Hamma na sake yi again ina dan murza hannaye na dana hade a guri daya a hankali. Matar da suke tare da hajiya take cewa kamar fa bai tafi ba sai murya sukaji ana fadin baba yatafi mukkadarasiya ce dai tazo tayaki murna dawowan jinjirin ki. Hajiya babana ya tafi bai maki bayani ba amma ni yanzu zan maki idan kina son ji. Da sauri hajiyan take cewa idan zan samu zanso naji komai gaskiya akai don nasan inda zamu dosa. Hajiya da farko kada ki bar dakin a garin nan don makiya sun maki yawa a tare da ke ba gida ba ba, a waje ba. Hajiyan ta amsa da fadi gaskiya ne haka maganan take makiya kan akwai su wallahi karma siyasan nan da nakeyi a yanzu. Dawowan shi zai jawo idon mutane akan shi donke kin yi sakaci sosai ga iyalin ki. Boko kawai kika saka a gaban ki baki damu da yi wa jinjiranki komai ba akan zaman duniyan nan da rayuwan su. Wanda haka ba hali ne da ya dace duk uwa tagari tayi watsi dasu ba a rayuwan ta cikin wanan zamanin da muke a ciki. Yau zamani yazo muna da sabon rayuwa da abubuwa iri iri a cikin sa wanda mu ada bamu daukan su da wani muhinmanci sosai. Amma yanzu ya zama dole duk uwa ta gari ta mike akan yayan ta tana masu addua tana kuma dan nema masu tsari daga cikin tsarin da ba sai an kaucewa mahaliccin mu ba. Koda ta hanyar yin sadaka ga mubukata da marasa lafiya da tsuntsaye zaki iya neman tsari ga jinjiranki. Akwai taimako da dama daba sai kin kauce hanya ba wanda sai dasu dole rayuwa take tafiya dasu a yanzu. Tun yaro yana karami yanzu iyayye basu hana shi yawan amsan sadaka daga makwabtan su wanda akasarin mutane a yanzu bawai sadakan Allah da Annabi ne sukeyi ba. Akasari sunayi ne da wata manufa da wasu miyagun mutane ke basu , sa,an kwashe baiwan yaro da yake dashi tun yana karami. Sai wanan baiwan da sa, an su koma ga wanan mutumin idan har sadakan gaskiya ce ai ga mubukaci ake son mutum yaba da sadakar shi. Amma zakiga mutum ya tara yara kanana a kullun yana mika masu sadaka da hannun sa wanda ba komai bane wasun su sukeyi sai sihiri a hakan. Bance duk masu sadaka haka suke ba sai dai gaskiya akasarin masu yi a yanzu da wani manufa suke yin hakan. Wani zai shafa kan danka da sunan so ko kauna wanda ba komai ne zai diba a cikin sa ba sai bawan da Allah yaiwa yaron ka kawai zai rabashi dashi har abada. Ko zaki iya tuna kin tafi kauye da yarki Nafisa to hakane ya kasance da ita kike ganin ta wata kala a cikin diyan ki. Ranan auren Binta yarki akwai matar da ba, abawa wanan abin da kuke rabawa ba na ledan buki. Wanan matar tun wanan lokacin take rike da mahaifar yarki Binta da yau shekara bakwai da aure amma ko batan wata bata taba yi ba a gidan mijin ta. Mamaki ne sosai ya kama hajiya jikinta ya shiga karkadawa cikin nazarin magana ta. Na girgiza kai nace dan adam ba kyau gaskiya zaku iya yin abinda mutum bai taba zaton zaku iya ba don ba imani ke gareku ba duka. Wanan rabon abinda kukeyi idan kuna buki yana iya kawo maku matsalolin aure da dama wanda ku baku sanda hakan ba a gurin ku ba. Zaku iya zama a gaban yaro karami kuna cin abu ba tare da kun bashi ko da kadan ne daga ciki ba shima ya lasa yaci wa ran shi koda kadan ne Wanda haka zai iya kawo sanadin da yaro karami zai iya tsiyaye zurian da Allah ya bashi gaba daya lokaci daya ga fitsarin sa. Wanda ke hajiya hakan yana daga cikin halinki a baya kina ganin ba yaro abu zai saka shi a kwadayi ko wani abu can da ban. Ba hakka abin yake ba ga zahiri gaskiya yaro yana tare da wani bawai ta musan man amma sakaci irin ta iyayyen yau yana kawo matsalar da dama ga yaran mu na yanzu. A da can baya idan mace tai ciki sai manya kawai ke iya gane hakan daga gareta su fahinci tana dauke da juna biyu basu magana sai dai su bar zancen ga zuciyar su kawai. Amma yanzu tun ciki yana mako biyu wata daya zuwa yan watanni kowa zai sani kamar an busa sarewa. Wanan shine matsalar dake damuwar yarinyar ki da kikaiwa aure a baya Aminatu yar wajan wanki da kika tayar abaya. Da sauri hajiyan take kallona da mamaki don jin abindana fada don tasan yarinyar nata na fama da yawan miscarage . Nace dazaran ta samu ciki gaba daya sai kowa ya gama sani kafin agama hallita shi a cikin ta, wanda yawan, bakin mutane ne ke yawan lalata shi koma da haihuwan tayi dan zai iya zuwa a lalace ko wani kala can daban. Baki ke nan, irin taku na yan adam duk yake haddasa hakan wani lokaci ga mataye masu haihuwa. Idan Allah ya bata wani cikin idan zata iya jan bakinta tai shiru ta dinga karanta malikki yumiddim, kafa goma sha daya da safe da yamma tana shafe cikin dashi, insha Allahu cikin zai zauna ajikin ta har ta haife shi lafiya insha Allahu. Hajiya tace insha Allahu angama in dai wanan ne kawai zan ja mata kunne sosai ga hakan. Nace Ni na barku lafiya lokacin sallah yayi zan bar godiyar mu ta huta haka na. Tana wucewa sai na kama kuka wiwiwi matar tace ikon Allah wani yazo kuma fa hajiya baban Abba dai yana zaune imani duk ya kashe maijikin sa. Wai yau maryam din shi ne a cikin irin wanan halin haka take wanan wahalan da wanan abin murya na ya koma kamar ta larabawa a lokaci daya alhalin ni ko Niger ban taba zuwa ba balle garin larabawa. Sukace dawa muke magana don Allah yanzu larabci na fara yi cikin gwanewa Allah yasa hajiya da Nasir suna dan ji. Suke tambaya ana basu amsa wani ma basu san may ake fada masu ba suna dai jin ana fada sosai ana kuka cikin harshen larabci ne kawai. Fada takeyi wai an bar Nasir ya wahala sosai a duniya don haka su sai sun dauki mataki akan duk wanda keda hannu cikin wanan abin. Don Nasir abokin karatun su ne tun suna kana a masar da sukai zama lokacin mahaifin shi yana ambasado acan. Kuka sosai mai shi takeyi tana fada ta wuce a jikina nan na sake atishawa masu karfi har kashi uku sai na lamay a saman salayan da nake zaune akai. Sai sannu kawai suke min da sannu maryam da kyat cikin daga kai nake karba masu na koma bayan kujera na dan jingina kaina a hankali. Shiru falon yayi ba mai magana daga cikin mu sai zuwa can hajiya Umma da duk imani ya cika ta shiga nazarin maganganun da taji yanzu take cewa. Wai nace ko ku mutanen garin nan ne ko baki ne ku ? Baban Abba yace cikin sauke ajiyan zuciya hajiya aiki ne ya kawo ni nan garin ok kawai tace can kuma ta kara cewa don Allah ku mutanen wani gari ne ? Yace daga Niger state muke hajiya ok ok nagane No warnder kawai tace. Sai dan shiru da ya kara biyowa baya a falon kowa da abinda yake nazari a ransa. Can tanisa tana cewa ok mu zamu koma ke nan sai kun kara jin mu ke nan. Malama maryam mungode zamu tafi zaki jini nan bada dadewa ba insha Allahu. Suka mike shima baban Abba mikewa yayi yabi bayan su nansan saboda darajan tane da kima yasa shi binta suna sallama dashi. Nan dai suka tafi suka bar mu da mota a kofan gida wanda wai yake a matsayin nawa. Motar dako mijina ba irinta yake shiga ba amma yau a dalilin wani sanadi nina mallake shi. Banso fada mai ya samo min hantiti kamar yadda akace na dinga yi sai dai yadda jikin ya matsa min dole nai mai magana akan iein yadda nake jin jikina ya damay ni. Ya fita yaje gurin nema min kafin yamma ya karasa yi sosai a lokacin bai jima ba sai gashi ya dawo min dashi a cikin dan wani bakin leda. Haka na kama shakawa kamar mahaukaciya kafin na samu naji dama a jikina. Cikin karfin hali irin nawa hakan bai hanani yin girkin dare ba ina yi ina kwantawa har nagama abinda duk zanyi . Ranan kafin tara na dare har na kwanta nai barci don duk jikina a dipge yake min bana jin dadi ko kadan a tare dani. Kasa hakkuri yayi ya dauki waya yakira mahaifina don yasan halin da nake ciki. Nan yake sheda mai halin da ake ciki yanzu har kyautan motar akai min kan wani matsala da ya taso na warware shi. Baba yace ikon Allah wanan abin kuma akan maryama ya sauka kuma ? To Allah ya sauwaka yasa ayi a cikin nasara abune na nufin Allah babu yadda zamuyi sai dai kawai musawa al, amarin Allah ido. Don idan mukace zamu bi zancen da zafi bamu san yadda al, amarin zai kasance ba damu. Fadan da baka ganin maishi sai a sannu addua zamu bita dashi akan Allah ya kawo mata saukin al, amarin a rayuwan ta. Don abin nasu kamar ya zama gado ke nan don kaga haka mahaifiyan ta tayi aanan wahalan da yake bamu fahince su yadda ita ta fahince su ba sosai sai abin yazo da akasi akarshe ma muka rasa rayuwan ta gaba daya. Allah ya sauwaka baba Aliyun yace tare da cewa amma wahala take sosai idan sun fita a jikin ta baba. Yace zan bincika naji may yakamata a dinga mata idan haka ya kasance da ita. Aliyun yace ta daice na sayo mata hantiti da yamman nan na kuma saya mata shine ta samu tai barci yanzun haka. Baba yace Allah ya sauwaka Allah yai mata saukin wanan al, amarin daya samay ta. Aliyu ya amsa da amin yai wa baba sallama kan zai kira shi idan sun natsu. Zancen Aliyu ya sai mota ya zagaye uguwar mu kowa sai cina da taran naki fada masu zancen sayen sabuwar motar dayayi suyi mashi murna. Hakkuri kawai nake basu ba tare dana fada masu asalin motar ba daga inda yafito ba. Don ban son yawan surutu saboda ina gudun mutane su fahinci halin da nake ciki. ****** ********* ****** Tun bayan komawan hajiya gida da labarin dawowan danta ya bazu a ko ina wanda yadawo cikin yan uwan shi da abokan arziki. Haka yasa mutane tururuwan zuwa taya hajiya Umma murna da mata farin ciki. Nasir yazama wani sheck din malami irin na kasan indiya yanzu ya aje wani gemay mai tsawo a fuskan shi. Sai dai matsala daya shine bai yawan magana dakowa kasafai haka ma Umma ta fahinci cewa koda iyalinshi ba wai yana yawan magana bace sosai dasu. Bata damu da matsa mai da hayaniya ba sosai daya gaisa da mutane zaici gaba da karatun shi ne kawai kan shi a duke. Hajiya Gajiye tazo da su cake da miyan kan saniya mai yawa wai don Nasir din tayo shi kawai da iyalin sa. Take Umma ta fahinci maganan mukkadarasiya ta hana ta cin komai a gurin kowa idan an kawo masu. Da batasan komai ba sai tace so da kaunane yajawo wanan alherin da takawo ma danta da iyalin shi. Sai dai ita kanta hajiya Gajiye tasha jinin jikinta irin yadda hajiya da yan uwanta suka karbe ta a yau. Ba kamar yadda suka saba ba abaya ita da hajiya suna matukar amintaka da junan su sosai komai a tare sukeyi. Duk da wani lokaci tasan gajiye na mata zagon kasa ga alamarinta sosai amma takan basar a matsayin hassadane hakan kawai. Ashe abin nagajiye ya wuce sanin ta yakai ga kashin kai don wanda ya raba ka da danka ai yana iya yin kissan kai. Haka tafita gidan tasha jinin jikin ta sosai takai kofa zata fita ne ta yanke jiki ta fadi kasa sai da aka kamata ta tashi tafita. Wanan faduwan ne yai sanadin kaita kwance tsawon wani lokaci sai fallasa da tonon asiri takewa kanta. Sherin da ta aikata kawai take labartawa har yakai ga sai da aka kulle ta a daki don abin yayi yawa sosai. Labari yazo wa hajiya Umma yadda hajiya gajiye ta koma yanzu tace ta karata a can ita ta sani don itace tajawa kanta koma may nene ya faru da ita din. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/14, 12:35 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BANE A, , , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣4⃣ Kwana biyu na samu dan shakat a rayuwa na banda matsalan komai a tare dani yanzu. Don dan kwanan biyun da nayi ba abinda ya samay ni daga fanin jinnun dake damuna yanzu. Haka yasa na ci gaba da harkan kasuwanci na danakeyi Allah kuma yana ta kara daukakani acikin sa sosai. Yarana ina matukar basu kulawa sosai yadda ya kamata haka ma uban su yanzu naga duk dare sai ya shiga dakin kwanan su ya tofa masu addu,oi kafin ya kwanta. Zan iya cewa yanzu a tsakani na dashi Alhamdullahi don gaba daya hankalinsa yana kan mu. Yana dawowa dara kamar ko wani magidamci yaci abinci agida idan kuma tara yayi na dare zai dawo sai kuma gobe idan Allah ya kaimu kuma zai fita daga gidan. Haka yasa hankalin hanna tashi sosai don yanzu dan jaye matan da yayi yasa ta shiga cikin wani hali na rashi. Saboda ta saba ansan kudi masu yawa a hannun shi tana shagalin ta dasu. Yanzu ko babu don bata ma ganin sa balle ya bata motar da aka bani yanzu shine yake shigan ta ya aje nashi guri daya. Haka ya jawo kace nace a tsakanin yan uwan aikin shi sai suke zargin ko ya samu wani deal ne yayi shi kadai ba da sanin su ba. Don har gurin controller din su sau da gulman shi ya kai amma ba a ga wani laifin daya aikata ba dole yasa suka kyale shi. Na fito daga daki zan shiga kitchen ke nan naji wayana yana kara na nufi gurin da wayan yake a saman kujeran falo na dauka. Wata abokiyar business dina ce tana yawan sayen kayana ta bani kudina acikin lokaci take fada min cewa akwai kawayen ta dake son kayan yara don Allah na kawo mata do yarta bata da lafiya ne yasa bazata samu zuwa ba. Nake ce mata bazan samu zuwa a ranan ba sai washe gari don maigidana yafita aiki ko. Bayan yadawo ne nake fada mai zan tafi gidan wanan matar don suna son sayen kaya na. Bai so ya barni ba amma da Umma ta sa baki yace sai na dawo sai dai yake ce min nayi a hankali na dai san halin da nake ciki a yanzu nake cewa ai da yar sokoto zamu tafi bani kadai zan tafi ba gidan. Washe gari bayan mun gama komai ne muka shirya sai gidan mun shiga da kayan da muka kwaso a cikin manyan ghana mostgo. Nai sa, a masu son sayan kayan har sun riga mu zuwa gidan suna jiran isowar mu. Kowace bata son yar uwarta ta zabi wanda yafi nata kyau yasa suka riga mu zuwa. Mun gaisa na baje kayan suka fara dubawa sai gida ya rude da suratai kawai irin ta mata. Matar gidan bata cikin falon nata tana daga ciki da yarta dake kuka cewa wai bata jin dadin jikin ta takewaya uwar tana mata tsarki . Yarinyar tana kuka tana cewa uwar tai mata a hankali wai ta haihu ne. Dariya yarinyan taba uwar ta tafito rike da hannun yariyar tana dariya. Nan take fada muna abinda yarinyar take fada mata yanzu a bayi wai tana mata tsarki yarinyar ke cewa wai don Allah mama ki min a hankali na haihu ne fa. Sai sauran matan suka saka dariya a lokaci daya suna tawa yarinyar dariya sosai wai ko a ina tasan haihuwa har take zancen sa haka. Ido na kurawa yarinyar har na wani dan lokaci naja tsuki mai karfi nace aiba karya take maku ba haihuwa tayi. Ido suka zaro suna kallo na take na fara wani irin hamma ina murza hannaye na . Lokaci daya murya na ya koma wanda ba nawa ba ina fadin ku mahaukantan inane. Yarinya ta haihu shine kuke mussa mata zancen ta da dariya haka babu tausayawa. Wanan da kuke gani haihuwanta uku ke nan yanzu ba wasa take fada ba wanan haihuwan yazo mata da dan wahala ne yasa har ta fada maku. Haihuwa fa maman Abba nace ba maman Abba bace mukkadarasiyatu ce ke magana da ku. Sai duk hankalinsu ya tashi a lokaci daya nace bil, adam baku da kula akan jinjiranku ko kadan. Yarinya tana a cikin wani hali amma kuna nufin baku fahinceta ba har kuna mata dariya haka. Kema ai maman siyama yar ki tana da sabon ciki yanzu haka ajikin ta ki koma gida zaki samay ta tana amai yanzu haka. Nashiga uku inji maman siyama din tafadi a cikin fargaba tare da dafe kirjinta cikin razana tamike tana fadin don Allah ku bari naje na leko wanan almaran da nake ji yau. Da sauri ta mike tare da saka hijjab din ta tabar gidan acikin sauri tafice duk suka bita da kallo. Shiru nayi kawai batare dana kara magana ba sai wata daga cikin su take cewa wanan magana akwai ban mamaki. Wani kallo na watso mata daga inda nake a zaune ina cewa ki min shiru kina cewa haka baki san halinda mijin ki yake aciki ba kwanan zai kawo maki abokiyar zama a gidan ki. Ta mike tana cewa kai ina yanzun kan ban yarda ba ni da mijina akwai alkawari bazai taba min kishiya ba don ni mijina dan kaki ne. Tana nufin barin falon nace idan kin shiga gida ki daga takardan dake gefen gadon shi zaki samu sheda a guri amma aure babu fashi a gareshi. Tsayawa tayi cak tana kallona nace jeki yanzu ki duba ki gani mana da sauri ta kwasa tabar gidan. Yar sokoto dake a zaune kamar ruwa yaci ta mamaki da al,ajabi sun rufe ta a lokaci daya don bata taba sanin wanan labarin ba akaina. Sauran matan da muke zaune kowace na gudun motsawa nata ya samay ta . Maman siyama ce ta shigo gida a rude rike da hannun yarta tana kuka tana fadin wallahi amai na samu tanayi ita kadai a bayi. Nace to ku tambaye su a ina suka samu hakan ai zasu fada maku nace Siyama fadawa uwar ki ko ke wacece yau don su sani. Yarinyar tai shiru tana kallona cikin wani tsawa nace bazaki fada masu ba ne ? Ta soma magana kamar muna fuka yarinya yar shekara bakwai tana cewa jecob ne yai min ciki. Wanene jecob inji uwan tace wani ne shine mijina yau shekara biyu da mukai aure kullun dare kuma yana zuwa ya dauke ni a gidan mu dake Abuja muke kwana. Nashiga uku inji uwar tace nice na aurawa baby deniel don yace min yana son ta. Sai ga baby har tafi ni haihuwa don yanzu baby tana da yara uku niko ina da na biyu ke nan. Waye jecob da Daniel yarinyar tace a school din mu daya dasu shine ya bani biscuit tun wanan lokaci muke tare dashi. Nace yaya kuke yi ku fita dashi tace wani lokaci muna hawa bawan gyada shine motan mu wani lokaci kuma muna amfani da takalma wanda ake bari a kofan daki shine muke fita dashi ya zama jirgin mu ( Gareku masu barin takalman sawan ku a waje idan zaku shiga kwana wanan ba wai labari bane it happen always don ba kyau barin abin amfanin ku awaje wallahi ) Nace gida nawa jacob din yake dashi siyama ? Tace mai kudine sosai yana da gidaje har a America mukan tafi wani lokaci. Yana da motoci masu yawa a tare dashi sosai da bodyguard masu bin bayan shi don shi ogane. Nace, matan shi nawa yanzu tace mu tara ne matan shi amma ya fada min yafi so na acikin su. Uwar yarinyar tace na shiga uku na lalace Siyama a ina kika san irin wanan maganan haka ? Nace ki barta tai bayani ki zaune da mugun abu a gidan ki tana halaka maki yan uwa baki sani ba. Itace ta bayar da jinin mahaifiyar ki takuma da na kaunar ki da suka mutu a cikin wata daya a lokaci daya. Nace ko karya nake maki siyama yarinyar ta dukar da kanta a kasa tare da girgiza kanta tace a hankali gaskiya ne. Nace may yasa kikaba Daneil baby tace saboda inajin haushinta kada mijina watarana yace yana son ta. Nace shi mijin baby din acikin cult din ku babbane ko karami a cikin ku ? Tace shima mai kudi ne sosai yana da dukiya mai yawa sai dai ita baby bata son shi kullun fada sukeyi dashi. Kuka sosai uwaye suka fara kamar ruwa yaci sauran matan dake falon lokacin. Nace kuyi muna shiru duk sakacine iein naku na uwayen zamani yakai ku ga hakan. Baku damu da damuwar yaran ku ba babu addua akan su idan zasu shiga barci idan kuma sun tashi haka kuke bari su fita agida. Gurin ku kawai suyi ilimin boko su samu duniya sunan ku ya daga shine naku kawai. Yaran ku da dama suna cikin matsalan rayuwa amma rashin kula irin naku yasa kunyi watsi da nauyin da Allah ya aza maku nasu. Yaran ku idan sun fita baku san dasu wa suke hurda ba baku san tambayan su damuwar su ba baku saka ido ga dabiun su ko kadan. Nace siyama yarinyar ta karba kamar muna fuka nace yau zan raba ki da Jecob din ki kina so? Kai ta girgiza min nace saboda may bakya so na rabaki dashi ? Tace I love him mummy. Kuka uwar ta ta kara nace amma kin san ba adinin ku daya ba ko dashi ? Tace na sani amma yace kadda mummy ta dake ni nayi addini na ba zai hanani ba. Idanuwana da sukayi jajajir na kafe yarinyar dashi nace zo nan take ta karaso inda nake zaune na kama hannunta a hankali ina murzawa kamar wasa nake mata. Sai ga yarinyar tana kuka cikin wani irin murya sautin wani yaro mukaji yana fadin don't live me Siyama please i love you . Iam dying becouse of you . Nace a cikin wani murya mai kaushi live her alone go back to your people don't ever come back to her life. Kuka sosai akeyi ana fadin mummy don live us please ? Ruwa nace abani da sauri wata matar ta miko min ruwa a cup na gunda ruwan abakina tare da matse yarinyar na dura mata a bakinta na shafe mata fuskanta da sauran ruwan. Nan ta kwanta tana wani irin birgima akasa cikin sauti kala kala na ban tsoro. Uwar zata tabata na hanata yadda naiwa yarinyar farko haka naiwa baby din ita ma take yaran sukai ta birgima a kasa sai zuwa wani lokaci suka lafa nake cewa karbi nan tare da mika masu hannaye na. Garin magani ne suka gani shi na basu nace asaka aman shafin yaran a dinga shafa masu daga yau ba abinda zai kara samun su da yardan Allah. Matar da ta fita zuwa binciken gidan ta tashigo da kuka tana nuna muna resist din da tagani na kayan lefen da mijin ta ya hada kusan miliyan daya da wani abu. Tana cewa ku cece ni wallahi ashe da gaske ne aure zai kara bai fada min ba. Nace ki rufa muna baki bakece kika jawa kanki ba kullun ba mutunci gare ki sai bani bani ya gajine da halinki yasa zai kara aure. Idan kuma kince zaki dauki wani mataki a haka zaki samu matsala sosai a rayuwan ki. Wai ma kuwa kin san wanda mijin ki zai aura kuwa to bari na fada maki sunan ta hajara diyar wani babban mutum ne a Abuja. Don haka kiba kanki lafiya shi ne zaman lafiyan ki don an wuce ki ga komai. Nace nabarku lafiya sai na fara wani irin atishawa a lokaci daya take na duka gurin da nake a zaune na lamay masu a kasa. Cikin karfin hali yar sokoto take kiran sunana maryam maryam maman Abba na amsa mata da kyat tare da nuna mata hand bag dina. Tamiko minjikin ta yana rawa da kyat na lalabo hantirina na shiga shakawa kamar zan tura shi a hancina duka. Sai lokacin na dan samu sa, ida a raina na mike ina fadin tashi muje gida please. Duk matan sun shiga tashin hankali sosai nan muka barsu cikin tashin hankali muka fice gidan. Koda muka iso gida a gajiye nake kaman an bani kashi jikina ba lakka tare dani. Nan na zube a falo ina mayar da numfashi haka baban Abba ya shigo ya samay mu. Cikin kidimay yake fadin may ya faru kuma please abin ya tashi ne kuma ko yaya ? Dama maman Abba tana da jinnu ne haka masu karfi a tare da ita ashe ? Nan dai ra kwashe labarin abinda ya faru take fada masu fada ya farayi bayan ya gama sauraren ta. Yana fadin ni wallahi maryam ina gudun kada wanan matsalan naki ya jawo min magana a garin nan. Wanan ai ba so bane basu taimaka maki sai dai su sakaki yiwa mutane tonon silla kawai. Gaskiya gara ku bar garin nan zaifi min kada a fahince halin da kike ciki kija muna matsala. Ni dai ina kwance ina sauraren shi ban iya cewa kallallahu ba don ko ni abinda akace inayi yanzu ya fara damun rayuwana sosai. Yar sokoto tai muna sallama ta tafi tana fadin zata dawo da yamma ta duba ni insha Allahu. Tana fita gulma bai bari ta shiga gidan ta ba tun a kofa take kwadawa anty hauwa kira. Anty hauwa dake kitchen tafito da sauri take cewa yau anty naga abin mamaki sosai ashe maman Abba tana fama da jinnu ne haka masu karfi ban sani ba? Jinnu kuma yaushe ta samay su haka nan dai ta shiga bata labarin abinda ya faru a gidan mutane damu. Sai da anty hauwa ta kewaya don tsoro da fargaban da ya kamata a lokaci daya. Nan dai suka shiga magana akai har yamma yai masu bayan magariba suka shigo gidan namu. Ina ganin su tare nasan takai gulma ko sun zo su tabbatar da zancen ta. Zaune nake a kasan ties gurin kafan umma muna kallo suka shigo gidan. Mun gaisa muyi komai take tambayana yaya jikin nawa nace masu da sauki. Ban yarda munyi zancen komai dasu ba akan zancen don nasan shine ya kawo su gidan. Har suka gaji suna cewa su zasu tafi don dare ya somayi a lokacin nai masu sai da safe suka fice. Ashe suns fita sukaga wata katuwar mage bakakirin da its ta kura masu ido. Da sauri suka wuce ta a razane sai suka ga kamar magen tana bin su a bayan su aiko binsu take cikin tashin hankali suka ruga aguje kowa ta shige gidan ta hankali a tashe. A cikin wanan daren ne shima baban Abba yai mafalkin ana mashi kashedin idan ya fara ya mayar damu gida zai hadu da tashin hankali a rayuwan shi da dama . Yana falkawa ne kawai yaji yana ta wani irin sufa wanda kamar ba sanyi akeyi ba a lokacin. Hankalin shi yai matukar tashi a lokaci daya yake sharan zufa tare da sauke ajiyan zuciya. Falkawa nayi nagan shi a zaune yayi tagumi kawai yana faman tunane nima hankali a tashe na mike zaune ina tambayan shi ko may ke faruwa kuma ? Nake cewa akan wanan zancen ne ko nima baban Abba abin ya fara damuna inaji wa kaina tsoron kada na jawo maka matsala a garin mutane . Komawa na gida naga kamar shine abinda ya dace dani da yaran nan don gudun abinda kaje yadawo muna nan gaba. Baiyi magana ba har lokacin da nai shiru yake ce min debo min ruwa nasha. Namike zuwa falon don na dauko mai ruwan yasha kamar yadda ya bukata, abinda idona yaganan min a falon namu ne ya tayar min da hankalina. Yara ne a zaune suna cin abinci wasu kuma suna kallon Tv wasu na karatu kai su nan dai birjit dasu kowa da abinda yakeyi. Hakana na ratsa a tsakiyan su ba wanda ya kulani a cikin su har na bude fridge na dauko ruwa da nufin nakai mashi. Sai naji wata murya na fadin kai maman su Abba din nan yanzun ma dan ruwan da zan sha idan nagama cin abinci shine kuma zata dauka ta tafi dashi. Wata kyakyawan mace ce tafito daga kitchen hannunta dauke da wani plate mai kyau dashi taci kwalliya sosai tana cewa. Kai Afir idan na sake jin kana wa babba rashin kunya sai na nayi maganin ka a gidan nan. Mayar da ruwan nayi na aje ina cewa yi hakkuri ban san ai naka bane . Ina fadin haka na juya zuwa gurin fanfo na debi ruwa nakai mai yadan kurba yadago kai ya kalle ni yana cewa babu mai sanyi ne zafi nake ji sosai. Nace kasha wanan kawai falon baida dadin zuwa yanzu yace kamar yaya ya mike zai fita daga dakin nai saurin rike shi ina cewa kada kafita baban Abba bamu kadai bane a gidan nan. Masu gidan suna falo suna hutawa a yanzu da sauri yadawo ya zauna yana kallo na acikin mamaki. Bamu kadai bane agidan kamar yaya na bude baki da zuman nai magana amma kuma na kasa yin hakan. Sai wani irin zazzabi mai radadi yazo ya rufe ni a lokaci daya haka na shige a cikin bargo ina rawan sanyi dani. A haka na kwana har gari yawaye gashi yana son fita amma kuma yana tsoron kalamina danai mashi na bamu kadai bane a gidan. Kalamin yai matukar firgita shi sosai hankalin shi yai matukar tashi dole da safe yakaini asibiti aka dubani. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU[11/15, 11:15 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BAMU KADAI BA NE A, , , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣5⃣ Sosai naji jiki ranan don na saka abin da nagani araina don ba wai a mafalkine naga wanan abin ba. Bayan mun dawo daga asibiti ne barci ya dauke ni misalin daya na rana nai mafalki da matar da nagani a mafalki tare da yaran nan a falo. Ta shigo dakina inda nake kwance mu ka gaisa da ita take ce min yaya jiki na dan yunkura na amsa mata da sauki. Tace kiyi hakkuri yar uwa ban san zaki fito ba a wanan lokacin dana boye mu daga ganin ki. Kin san halin yaran yanzu bajin magana sukeyi ba gashi kuma dare ku shine rana a gurin mu. Likacin da kuka kwanta kuke hutawa muma a lokacin muke samu muna rayuwan mu yadda ya dace. Fitan dare idan ba dole ba bai da amfani ga dan adam don gudun yin gamo da ire, iren mu jinnu. Yanzu ki karbi wanan ruwan kisha insha Allahu idanbkin tashi zaki daina jin komai akan mu. Daga yau kuma daga ke har duk wani wanda ke gidan nan bazaku kara ganin mu ba har sai idan kece kikaso ganin mu da kanki. Godiya nai mata na karbi ruwan nasha nashafa a fuskana kamar yadda tabukata nayi. Ta mike tabar dakin tana min Allah ya sauwaka tafice daga dakin a lokacin na falka daga barci nima. Fuskana da na shafe da ruwa naji alaman shi a fuskana na shafa naga kamar ba zufa bane nayi nan dai na dade a kwance sannu a hankali naji jikina yana sake min. Idanuwa na na lumshe a hankali ina tuna mafalkin da nayi nace a raina nikan maryam nawa kaddaran ke nan kuma hurda da mutanen boye a muraran haka. Nai adduan neman tsari ga Ubangijina na mike zaune falo nafito na samu su Umma zaune da Nusaiba suna kallo Na samu guri na zauna Umma tana min sannu yaya jikin nace da sauki tace min abinci fa nace na koshi Umma. Maryam tun safe fa bakici komai ba ki daure ki dan ci wani abu mana ko ? Nace umma tea zan sha maimakon namike na hada tea din sai ma nakai kwance kawai a gurin. Ina bin komai na falon da kallo yadda nagan su a daren jiya ne ya fado min araina komai ma yanzu na gidan tsoro yake bani. Tunda nasan bamu kadai bane mallakin komai da muke dashi agidan ashe muna sharing ne tare da wayanda bamu gani. Nace kuka ganin mu bamu ganin ku don Allah kuyi muna adalci akan zaman mu yan uwa musulmai. Umma take tambayana dawa kike magana nace ba kowa Umma ido ta tsura min tana zargina. Gani take kamar mutanen nawane zasu taso min sai cewa tayi dauko hantitin ki kusa maryam. Nace babu komai Umma magana kawai nakeyi amma lafiyata kalau. Gaba dayan mu yanzu munyi farin ciki da samun natsuwan baban su Abba yanzu a gida. Don idan bai gurin aiki yana gida tare da mu cikin kulawan da ya dace duk magidanci yaba ma iyalinshi. Haka yasa hankalin Hanna ya kara tashi gashi yanzu sai ta kira wayan shi fiye da sau goma bai daga wayan ta. Ni dai zan iyacewa tun lokacin da na fara amfani da abinda matar baba na tsibiri tabani yake min wanan irin likewan idan nabi ta nashi koda rana ma zamu kasance a tare dashi. Ya soma mantawa da zancen wata hanna can idan ba itace takira wayan shi ba. Koda takira din bai dagawa sai dai yaja tsuki kawai yabar wayan har ya katse. Idan ma ya dauka ba wani magana mai dadi da zataji daga gare shi karshe ce mata yayi please hanna live me alone for god sake is over now between me and you. Wanan kalamin ne yai matukar tayar mata da hankalinta sosai take gani idan ta rabu dashi wazata samu da zai kashe mata kudi kamar shi haka. Ta samu mahaifiyar ta da zancen uwar taita mata fada tana cewa duk yadda zatayi ta gyara tsakanin shi da ita tayi kokarin gyarawa gashi har sun fara shiga wani halin dan rasa shi sa da suka yi kwana biyu a tare da su. Hanna a cikin damuwa take sosai ta tafi gidan wata yar garin su dake zaune a kaduna ta fada mata halin da take ciki yanzu. Matar ta girmay ma hanna sosai ga shekaru take cewa ke dama baki shiryawa shiga bariki ba kika shigo ta hanna ? Kina da kaman wanan guy din zaki bari har ya kufce a hannun ki yaushe zaki kara samun kamarsa kuma. Nan dai take fada mata akwai gurin wa ni boka da zata kaita aikin shi kamar yanka yake da sun tafi komai zai koma daidai gareta. Hanna taji dadi sosai sai dai kuma can take cewa gaskiya anty akwai dan matsala sosai wallahi. Namau kuma hana ? Matar ta tambaya cikin son jin ina matsalar take kuma ? Hanna tace wallahi anty matar Aliyu muguwace matsafiyace ta gaske don yanzu haka ma idan nace maki tasan wanan maganan da mukeyi baza, ayi mussu ba. Dariya sosai mata mai suna Rabeca tayi tace amma har kin bani kunya hanna yaushe zaki tsaya wani tsoron matar shi kuma ? Ai kawai fito nafito zamuyi da ita komai tsafin ta bata kai wanan gurin da nake shirin kaiki ba ke dai kawai kisa ido ki gani yadda za, ayi da ga ita har mijin nata. Nan dai suka aje magana washe gari zasu tafi gurin bokan nasu a can wani kauye a yankin jos. Tunda safe suka shirya don su samu suje su dawo a ranan suka kama hanya. A gaban boka bai bari sun fadi abinda ya kawo su ba shi da kan shi ya labarta masu komai dake gudana tace mai hakane. Yan abubuwan su na bokaye yayi suna kallon shi daga shi sai dan bante a jikin shi. Yadago kai da sauri bayan ya watsa wasu farin kudi a kasa ya fara dan girgiza kan shi kadan kadan. Can ya dago da idanuwan shi da sukayi ja yana kallon su. Yace da zakubi shawarana sai nace ku rabu da mijin matan nan gaba daya duk son da kukemai. Don wanan matar banga kurwanta ba a nan shi dai mijin gashi nan amma kinga matar ba, a ganin ta. Akwai wasu abu da suka tare ta wanda basu bari ma aganta balle ai mata wani aiki. Matar tace boka a daiyi kokari a duba muna don idan ba, a kawar da ita ba ko munyi aiki a kan shi matar zata iya bata muna komai da mukayi. Nan dai take kara mai bayani akan maryam yadda zai fahinta yace ba sai kin fada min ba ai duk wanda na duba banga shi ba acikin nan nasan akwai matsala sosai ga mai shi. Sun matsa mai akan yai masu aiki akan maryam da mijin ta ba don yaso ba sai kwadayin kudin da sukace zasu zube mai yasa ya yarda zai masu aiki din. Sunyi dashi kwana biyu zasu dawo karban aikin da yayi masu sukai mai sallama tare da bashi na cin goro. Sun kamo hanya suka dawo gida cikin farin ciki da ganin nasara atare da aikin da za, ai masu. ****** ********* ****** Yanzu ban son fita ko ina haka ma baban Abba ya hanani fita zuwa ko ina don gudun kada na fita abubuwan kaina su tashi. Tunda idan na gani sai na fada yar sokoto sun shiga gulma a easthe din mu a kaina. Har magana ya dan fara dawowa a kunne na na lura dasu yanzu mun rage hurda da shakuwan da mukeyi a tsakanin mu dasu abaya. Ban damu ba dama can sune masu biyo ni ai banice mai binsu ba duk da dai sun girmay ni sosai. Maganan su bai sa sauran mutane sun yarda ba don haka suka koma jin kunya kuma don kansu ban san may suka gani ba suka dawo min kuma. Ban yarda na sake jiki dasu ba kuma don ban son yawan surutun da sukeyi. Duk yadda suka so mu fita tare bana yarda na fita dasu in ma har fitan ya kamani. Hanna ta koma ta karbo sakon ta gurin boka yadda yai mata bayani akan ta tunkare ni yasa ta shirya sai gidan mu. Muna zaune a falo gaba dayan mu ranan ba aiki duk muna gida har shi maigidan. Jin an yi nocking din kofa yasa muka mayar da hankalin mu a kofan muna kallo shine ya mike zai fita ya duba nace zauna kaci abincin ka na duba nagani. Na nufi kofan na bude tana tsaye sai yatsunar fuska takeyi tana cewa munzo zamu duba jikin mummy ne. Har zata kada kafanta a cikin gidan cikin wani irin murya nake cewa dakata anan. Kamar an daureta taja ta tsaya take yanayi ya sauya na nunata da yatsa ina cewa ki koma da abinda kika dauko ki fadawa bokanki daga kaina bazai sakewa wani sheri ba a duniya. Na nunata da yatsa nace ke kuma kinyi ganganci zuwa muna gida da kikayi da mugun abu ku tafi can kaikayi ya koma kan mashekiyar ta. Naja kofa na rufe na barsu nan tsaye a waje cikun mamakina mikewa yayi ya nufo inda nake cikin wata irin murya nake cewa kada ka tako gurin nan yanzu daidai inda ta taka na duka kamar mai cire wani abu sai ga hayaki na tashi a daidai gurin. Wani irin atishawa ne yazo min nan na mike kwance yazo da sauri ya kamani. Umma hankalinta yai matukar tashi take tambayan ko su waye suka zo muna da sheri haka har gida? Yarasa may zai ce mata sai kamani da yayi zuwa kan kujera ya kwantar dani da sauri ta koma daki ya dauko hantitina ya na shaka min a hanci na. Barci ne ya dauke ni hankalin shi yai matukar tashi sosai don abin ya dade bai tashi min ba. Jikun su sai rawa yakeyi don a zahiri abinda idon su ya gane masu yai matukar daga masu hankali sosai. Ga boka yace tabbas ranan dayace suyi amfani dashi idan basuyi ba akwai matsala ga tashin hankalin da suka samu a gidan wanda yai sanadin har faduwa sai da dayar matar tai tangarde a hannun ta. Basu kwana ba suka koma gurin boka a cikin dare suka isa sun samu a gidan boka ana kuka wai yana tsaka ga aiki akaji ya kyallara ihu sai abin ya koma mai kamar hauka tuburun dashi. A kauyen suka kwana ba yadda zasuyi suka aje mai kayan daya basu suka juyo tunda safe suka dawo kaduna. Wasa wasa suka fara dan ciwo wanda sherin da sukayi ne ya juye ya koma akan su. Dole mahaufiyar hanna tazo ta dauki yarta ta tafi da ita garin su cikin tashin hankali. Azumi ya fara kowa yanzu ibada yakeyi sosai babu babba ba yaro a gurin neman falala ga ubangiji. Na samu cinikin kayana sosai don har na hadawa bin yusuf mai kayana kudin shi cif na kulle a guri daya. Ga sauran kayan da suka rage a gurina duk a matsayin riba wanda idan zan sayar dasu zasukai kimani dubu dari uku da dan kai sama. Wayan hajiya Aisha ne yazo gare ni take cewa sunan shigowa tana son ta kawo min kayan azumi kada naga kamar ta manta danine bata kasan ne yasa mukaji ta shiru. Nace babu komai mama ai shiru alaman lafiya ne ga bawa. Munyi waya da ita da kamar kwana biyu masu sayen kaya sunzo muna tsaka da ciniki tashigo gidan da yaran ta mata. Mun gaisa dasu a cikin mutunci tana tambayana yarana nake cewa sun tafi islamiya karatu. Daya daga cikin ditantana idon ta yakai ga kayan dake a zube take cewa taga kayan yaran na mika mata dayan tace na miko mata bedshirt tagani. Sai naji yarinyar nata wace zata girmay min tace ikon Allah mummy kinga kayan da nagani a hongkong nai nema ban samu ba a lokacin. Itama mai bedshirt abinda ta fada ke nan bedshirt suka zaba har kalla goma suka sa na buga masu kudin shi cif suka miko min kudina a take. Maman tace dama suna ziyara ne don samun falalan watan azumi tace suzo gurina mu gaisa dasu. Nan ta zube min bandar din yan dubu har uku a kan table tace ga abin shan ruwa nan sai bayan azumi tana son yin magana dani idan Allah yakai mu. Zasu tafi taba Umma dubu hamsi tace tasha ruwa dashi mukai mata godiya na rako su har kofan gida suka wuce. Baban Abba yana dawowa na fada mashi zuwan su hajiya tare da dauko alherin da ta kawo muna na nuna mai. Ikon Allah yace tare da kurawa kudin ido yana tunane a cikin ranshi yake cewa. Yanzu ita kuma maryam nata hanyan samu ke nan ta wanan hanyan iskokan da suka hau kanta. Muryana naji ina fadin Abba dauki kudin nan ka mikawa baban ka da sauri ya dago kai yana kallo na a cikin mamaki. Yace amika min nayi may dasu ki rufa min asiri please ? Dariya maganan shi ya bani nace may kake tunanen zai faru dakai idan kayi muna amfani dashi matsalar dai daya ce idan ka dauki abina kai ma wata hidima dashi ko kabi wani hanyan dabai dace ba. Yace a, a maryam kibar kudin ki a hannun ki kawai keda ke sana, a ba sai ki kara ajarinki ba. Karban kudin nayi daga hannun yaron na raba biyu nabashi rabi ya karba yana godiya. Bai dauki lokaci ba yafita sai ko gashi yadawo muna da kayan abinci masu yawa da zamuyi amfani dasu don Azumi. Dama ba ai biya ba manage mukeyi kawai don bai sayo muna komai ba a gidan. Washegari wayan hajiya ya samay ni wai na kawo zanuwan gado da kayan yara da takalma ana son saya. Shi da kan shi ya kaini gidan nima da kyat na sheda gidan yana ganin gidan yai mamaki yadda Allah yakawo ni hurda mutane masu arzki irin haka. Na samu an canza masu aikin gidan duk sabbin fuskane nagani a gidan sabani wa yanda na samu a farko gidan. Taji gargadin da akai mata ke nan na zagon kasan da wa yancan suke ma rayuwan ta. A falon kasa mu ka zauna, nan da yake muna azumi babu wani abinsha da aka kawo muna sai dai hakkurin da suka bamu kawai na ana azamu. Tare da yaran ta da sukazo ne don zasu tafi umura suka sauka kasa cikin fara, an su muka gaisa dasu. Nan suka shiga duban kayan daya bayan daya suna yaba kyawon kayan sun zaba don kusan ince sun kwashe bedshirt din nawa. Suka ban kudina muna batun wucewa ne hajiya take fada muna cewa zata koma abuja gidan su dake Abuja da zama. Tana son don Allah idan zata koma bayan sun dawo daga Umura baban Abba ya taimaka ya bata aro na muje gidan don a akwai abin da ake da bukatan naje nagani a gidan kafin su shiga gidan. Ta cika mai ido bazai iya mussa mata ba akan komai yace kawai Allah ya kaimu lafiya. Take cewa kada ya damu ai idan za, ai tafiyan tare dashi za, a tafi don yaga guri a can. Haka mukai sallama bayan kuauntan da na samu dani dashi a furin hajiyan na atamfan super da dogayen riguna masu kyau guda biyu. Shi kuma shadda ne mai tsada aka bashi har kala biyu duk bardin masu kyau dasu. Kamar kada ta bari mu fito daga gidan har kofa ta rako mu tana muna godiya take cewa wancan ne motar taka mijin diya gaskiya wanan motar ma ai tayi karama sosai. Bude bakin baban Abba sai cewa yayi ai ta maryam ce ma nake shiga kyautan shi hajiya Umma ta bata. Da mamaki hajiyan ke tambaya wace hajiya Umma ke nan sai yake ce mata hajiya Umma sanda, . Cikin mamaki take cewa hajiya Umma dai wacce na sani seneter ita hajiya yabata amsa. Ikon Allah ashe tasan da zaman ki matar tana da mutunci sosai wallahi akwai taron da mukeyi na formwn ai tare da ita badai wani gaisawa sosai mukeyi ba. Nace haba baban Abba hakan baida kyau yin haka kamar fallasa sirin mutum ne ga wani. Ba wai lalai bane wani yasan abinda naiwa wani don hakan bashine alheri ba ga rayuwa. Magana sosai yaiwa hajiya dadi tace wanan gaskiyane diyata kuma har kin sa na kara son ki a raina sosai wallahi. Kada ki damu idan na dawo in Allah ya kaimu lafiya zamu hadu kada kiji komai diyata. Sai bayan mun kama hanyane muna tafe ganin raina ya baci ga abinda yai min yake cewa batare da ya kalli inda nake zaune ba. Iam sorry please bawai na fadi haka ne da wani manufa kawai dai maganace takawo hakan ai. Nace hakan baida kyau ne kasan kowa da sirin shi a duniya don Allah yabani ci daga karshin su bai kamata ace ina fallasa sirin wani ga wani ba sai mutane su dinga daukata mai yawan surutu. Har muka kawo gida babu wanda ya kara magana a cikin mu don raina yai balain baci ga maganan shi. Azikin shi daya shine watan azumi muke ciki da ranan nasan yadda raina yabaci daya dandana kuren shi gare su. Ko yanzuma ai ban debe ma katobaran shi tsanmanin ba gaskiya sai dai Allah ya gyara ba wani abinda ya faru damu har dare. Daga bangaren hajiya Umma na samu sako na alheri sosai alfarman watan azumi ta aiko min da kayan shan ruwa tare da kayan sallah nawa dana yarana har ma da Umma ta samu nata rabon a ciki. Nan dai mukai azumin mu lafiya wanan shekaran sai sam barka kawai zance naiwa iyayyena sako na ban mamaki a gida don duk yan uwana sai da suka samu sakona a lokacin. ****** ********* ****** Ranan sallah kowa yana murnan sallah muyi abinci mun akai wa mutanen da nake hurda dasu. Haka muka wuni lafiya har yamma sai nishadi muke da zagayowan wanan ranan mai albarja da Allah ya nuna muna zagayowan ta lafiya. Na idar da sallah namike ina nade abin sallah sai gani nayi kaman wani abu ya gilma min a gabana da fararen kaya ina dubawa da kyau wani haske ne har saida ya kashe min idanuwana. Abinda ban sani ba ashe nan na fadi kasa na fara gaisawa da yare davan daban wanda ba wanda yasan na iya yare kalan wanda nakeyi na harsuna daban daban . Ina nuna masu godiya da farin cikin ganin wanan ranan ta sallah da yazo. Hankalin baban Abba yai matukar tashi daga shi har umma da yarana don sai danai yare kusan kala tara kowa kuma da kalar yadda yake zuwa min idan zai zo ko zai tafi. Umma tace ni yasu babana ashe yarinyar nan ba sabbi ne suka sake shigan taba kuma ? Aliyu wanda kanshi a daure yake duk ya dabure ya rasa abinyi kai kawai ya iya dagawa umma. Sai daga karshe ne bahausa tazo sukayi magana sosai dasu na fahinta take sanar mai cewa sunzo yawon sallah ne gurina saboda so da kaunan da suke min. Shiyasa suka kawo min ziyar yau ranan sallah don yaune suka samu daman fitowa daga inda suka tafi hutu kuma sun tafi suna kewa na sun barni babu kowa a tare yace mata ai tana tare da Allah damu. Tace na dai yarda da tana tare da Allah amma kai banda karya babu abinda kakewa godiyar mu. Muna dai kyalekane don munga tana matukar son ka sosai a rayuwan ta idan bashi ba da tuntuni mun rabaka da ita. Amma a gaskiya abinda kake wa godiyan mu samsam bamujin dadin shi ko kadan. Yace to kuyi hakkuri kuyi min addua na daina mata abinda baku so. Tace koku bani adam kunsan yaudarar mace ba kyau amma kai kullun godiyar mu tana kokari akanka baka gani. Mun rabaka da waccan fasikar yanzun kuma ka koma akan wata bakasan wanan idan ka fada kaidinta ba tafi wacan hatsari agareka. Don kaga ita wanan tana sallah kuma tasan Allah sai dai tana da yawan shirka wanda mu bamu kauna maishirka bamu zama tare da wanda bai tsoron Allah zamu iya maka komai akanta duk ranan daka bari ran godiyar mu ya baci akan wanan sabuwar da kake kokarin daukowa. Shiru yayi yasan baida gaskiya duk abinda take fadi gaskiyane take cewa yanzu goron Sallah zaka bamu na rabawa yan uwana mu tafi. Yace bansan wani irin goron kuke so ba ai dariya tayi tana cewa godiyar mu ta san mau muke so don ta tanadar muna ka bude akwai zuma akayan ta shi zaka zuba akasa kawai ya ishemu komai kadan dinsa zamu raba a tsakanin mu. Ya mike zuwa daki da sauri yana dan dube dube yaga zuma acikin wani katon gora dana sayo ranan akasuwa. Har zan wuce sai mai zuman ya matsa min kan nasaya zai min amfani badon naso badai tausayi mai zuman yabani yadda naga yana qahalan talla a cikin rana. Ashe ban sani ba maishi yasan zan bukaci zuman yasa yai tabina sai na saya Allah ya taimakwni kuma na saya din. Kafin su barni nasha wuya sosai ranan haka na samu kaina daga garesu suka tafi suka barni da ciwon jiki. Nadai ji Umma na fadin wanan soyayyan da wahala yake ace ana son mutum haka kuma yai ta wanan irin wahala. Umma please ki kama bakinki don Allah tunda mun samu sun tafi ni wanan abin wallahi ya fara bani tsoro Allah. Na mike tare da bude idona lokacin har yamma yayi sosai sai mamaki nakeyi suko sai faman sannu kawai suke min. Da kyat na iya tashi nai sallah tare da watsa ruwa duk da wankan date ba dabia na bane amma ranan dole nagasa jikina. Ina daga daki najiyo muryan su a fallo kasa kasa umma tana fadin wallahi babana kakiyayi wanan neman matan da kakeyi kada su illata min kai. Ni banga abinda matarka ta rasa na rayuwa ba dake wanan shegen neman matan haka. Kudi na rudin ka har kana kokarin jefa rayuwan ka ga rudin duniya. Kana zaman lafiya da matarka amma kai kenan zuwa sunsune sunsunen matan banza a waje. Dama ace neman aure kakeyi ai babu mai hanaka yin abin da Allah yace amma kaike na neman matan da sukafi karfin ka kullun suna maka wayo suna karbe ma dan kudin ka. Badon Allah ya hadaka da yarinyar kirki ba kana ganin akwai macen da zata zauna dakaine cikin wanan rayuwan haka. Umma don Allah dai ki daina zancen nan tunda maryam bata san dashi ba a halin yanzu. Idan ma bata sani yanzu ba idan ka matsa kace baka kama kanka ai sani zatayi nan gaba. Kadai ji sunce sai sun maka illa a wanan karon yanzu dubara ai ya saura gare ka dai. Fitowa na falon yasa suka daina maganan da sukeyi sai bina da kallo kawai sukeyi cikin zargin ko naji abinda suke fadi. Ganin yadda na ga Nusaiba a kwance da kayan da suka wuni dashi a jikin su nake cewa Umma Nusaiba bata cire kayan jikin taba dashi ta kwanta hakana. Umma tace to bari a cire mata ai ban kula da tayi barci ba ma a hakan. Nidai na tayar da sallah na kawai nabarsu suna nan sun canza topic din zamcen su sun dauko wani sabon hira. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/16, 10:30 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣6⃣ Tun bayan jin bayanan da Umma take wa baban Abba yasa na fahinci ya kara komawa ruwa ke nan da wata macen Amma a ina Umma ta samu wanan labarin nai ? Ban nuna komai ba kamar naji maganan su muka dan ci gaba da hira jefi jefi dasu a falon. Wàshegari ne makwabtana suka shigo min yawon sallah kyautan danai masu yai matukar basu mamaki don ga al, ada cicin da drinks kawai zan basu. Amma sai na hada masu da kudi gar dubu goma kan su yai matukar daurewa sosai ga hakan. Sai dai da suka fahinci ni yar kasuwa ce suka basar da zancen a ransu amma sunji dadin kyaunta don dama suna da buka hakan. Zance zamana da su Alhamdullahi sai dai ban yarda sun fahinci komai ba a tare dani. Sallah da kwana biyu yar sokoto ta shigo gidan mu tana ce min anty hauwa yarta dake auren anan garin bata da lafiya ya. Shiru nayi ina nazarin fita daga gida bawai ban son zuwa bane kawai dai ina gudun abin da kaje ya dawo ne idan mun fita din. Tunda na zama fadi ba, a tambayaka ba yanzu dana gani sai na fadi ko ba, a sani ba. Nisawa nayi nace yar sokoto gaskiya bawai ban son zuwa bane amma kin san matsala ta a yanzu. Tai tsagal tana cewa wai matsalan iskokanki kikejiwa to ai ba ko yaushe suke tashi ba sai idan da matsala a ciki. Karfin gwiwan dana samu gurin yar sokoto ne yasa nace to zan shirya mu tafi tare din. Anty Hauwa bata san da zuwan mu gidan ba sai da mukayi sallama muka shigo ne taji mamakin ganin mu. Mun gaisa tare da ita muka shiga gurin mara lafiyan tana kwance sharkaf da ita da alama tana matukar jin jikin ta sosai . Waima cikin an sallamo ta daga asibiti ke nan a hakan da muka samay ta kwamce. Likita yace idan kwana biyu bata daina jin abinda take ji ba za, ai mata aiki ke nan. Muna zaune saman kujera two seater dake a cikin dakin muna fuskantar ta. Idanuwa na kura mata har tsawon wani lokaci ina kallon ta ban san yaya akayi ba na fara wani irin hamma. Abinda ya jawo hankalin su ke nan a gare ni duk suka tsura min idanuwan su akaina. Yar sokoto tana ganin haka tamike tsaye tana cewa tashi mu tafi maman Abba. Amma kamar da dutse take magana haka yasa tai karanbanin kai hannun ta da nufi ta tayar dani mu tafi. Idanuwa na da suka canza launi ne nadago kaina ina kallon ta idon ya sauya ya koma kamar ba nawa ba. Nace cikin kakausar murya kada ki soma tabani don baki da tsarki a jikin ki. Kallon mamaki taimin don idan ba ita da mijin ta ba amma gashi taji a bakina yanzu. Simi simi taja baya cikin kaduwa hankali a tashe suka tsura min ido sunan maralafiyan dake kwance wanda ko anty hauwa takan manta da sunan ta Adama sai lamin da suke kiranta ne ya amshe sunan nata. Nace Adama tashi ki zauna zamuyi magana dake ne ta fahinta tsakani da dake. Mikewa tayi kamar ba ita bace ke ta faman wulle wulle a saman gado ba yanzu. Nace ina son abani guri da ita ga murysna ya koma tankar na wata balarabiya dani. Hauwa ki dawo nan dake zamu zauna don ke ce yar uwarta ta jini anan yanzu. Na soma cewa bayan mun natsu yau rabonki da al, ada watan ki nawa shekaran ki nawa. Tace wata takwas ke nan danayi al, adana nake gani tace na dauka ko cikine da farko amma naje asibiti sunce ba ciki bane dani. Hannu na daga mata nace dakata baki da komai sai sakaci irin naku na matan yanzu. Ko zaki iya tuna tafiyan da kikayi zuwa gida buki a wani kauyen ku kina a cikin al, ada a lokacin? Ta dan yi tunane cikin yare su na yan lokoja suka juya harshen su ita da anty hauwa na basu amsan maganan su cikin ba yaren nake ji ba dai. Nace abinda ke faruwa shine zaki tuna jinin da kika bata wani bandaki dashi kika fito don babu ruwan da zakiyi flushing din gurin dashi. Shiru tayi tana dan kallona can ta dukar dakan kasa nace anan aka samu mai mugun halin data ga wanan abin ranta ya baci har tai maki sihiri akan sa. Wanan ba ciwon asibiti bane kece da kanki kika jawa kanki matsala bayan kin san cewa jini na al, ada jine abin siri ga mace. Mata da yawa suna sakaci wurin bari aga jinin al, adan su idan sunayi wanda yanzu duniya ta baci akwai sihirce sihirce da dama da za, a iyayi wa mace da wanan abin. Zakiga wata pad ko kyalen da take al, ada bata daukan shi da dara bata san cewa yanzu ko dan uwanta na jini zai iya mata illa da wanan abin ba. Don shi aladan nan da kuke gani wani abune na musan gashi kuma bautane na Allah amma sai kiga mata ayau suna sakaci gurin baein shi a fili. Tundai diyan ku da suke karatu a makaratina basu san cewa rayuwan su bane a wanan fannin duk yadda kikayi da diyan arna duk da dan bujen da suke sakawa a jikin su baki taba ganin wanan abin nasu don su sun san hatsarin dake cikin yin irin hakan. Ruwa na bukata abani a wani cup aka debo min addua kawai nai mata nace abata tasha ruwan a gaba tasha nace ki shafa aduk illahirin jikin ki gaba daya. Tana gama shafawa nace Alhamdullahi ubangiji ya tsare ya kare gaba dama sauran da basu sani ba ake masu zagon kasa a hakan . Ikon Allah Aishs na batun wucewa wata mace ta bude labulen dakin da muke ciki tana fadin. Sallamu Alaikum sai dana dago kaina kalli matar da kyau kamar ina nazarinta nace wa, alaikis sallam. Tace nazo ne don Allah nima a taimaka min akan, , , kafin tai magana nace akan yaron ki ko ? May kike son muyi maki da yaron ki bayan kece kikajawo wa kanki ni kuna bani mamaki bil, adam sosai sai kunyi abu zaizo yana damun ku kuma, Kin manta lokacin da danki yafara halinshi wasa wasa ana fada maki amma kike karyata mutane yan uwan ki. Nan gaba ma dake zaiyi kuka sosai don kece kika kara kaishi ga wanan rayuwan da yake a ciki yanzu. Abinda ma baki sani ba yanzu shine dan ki yayi nisa yaron da aka kawo maki riko wanan dan naki ya riga ya lalata mashi rayuwan shi ta hanyan yin luwadi dashi duk da kankanta dake ga yaron . Amma rashin saka idon ki waike kina son danki yaja anyiwa dan mutane illa a rayuwan shi saboda sakacin irin naku na uwayen yanzu. Akan may zaki ki dinga tafiya kina barin diyan ki su kadai haka a gida a tsakanin su bayan kin san dan ki baya ji magana tun yana karamin shi. Don Allah iyayye ku dinga kula da diyan ku saboda yaran yanzu sun riga da sunyi nisa sosai ta hanyan kallace kallace fina finan dake koyar da miyagun dabiu a gare su. Barin yara su kadai a gida ba abin alheri bane a wanan karnin da muke a ciki koda atsakan jinsi daya suka fito saboda baka sheda mugu a fuska yanzu. Ba wai lalai sai ka fita ba zaka hadu da mugu ko a cikin gidan ku akwai muggan diya da kuka haifa da kan ku. Saka ido ga rayuwan yaro abune mai matukar amfani yanzu ki tashi ki koma gidan ki wanan dan yayen da aka kawo maki ki fara duba lafiyan shi tukun zaifi maki alheri kafin mu duba al, amarin daki dake bukatan addua gareshi. Matar tamike jiki ba karfi don gwiwanta ya mutu idan har abinda aka fada mata gsskiyane yaya zatayi da dan marayan Allah datake riko. Wanda ta kulla da zaran awal ya shigo gida duk inda fahad yake baya kara fitowa sai lokacin da yaji fitan Awal a gidan zai fito waje daga inda yakw boye. Ashe ke nan mugun abinda yake aikatawa yaron ke nan ita hankalinta baikai ga yaron ba may yasa yake haka. Gashi idan zaiyi kashi sai yaita ihu yana cewa zafi ciwo amma ita sam bata kai hankalinta gare shi ba. Tana fita daga dakin wata mata tashigo da yarta ita wai bukata tazo dashi yar ta shekara hudu da aure bata taba koda batan wata ba agidan auren ta. Nace cikin dan kada kai ai wanan matsalar taku ce bakece ki zubar mata da ciki ba kafin tayi aure. To wanan cikin da kuka zubar shi kadai ne dama rabonta a duniya kuma kunzubar dashi. Yanzu sai ku koma ga Allah don ba abinda ya gagari ubangiji ya taimakawa bawan shi. Amma da kin daina wahalan yawon neman magani haka da kikeyi don kuka jawa kanku don gudun kunyan duniya. Kun manta da kunyan lahira yafi na duniya zafi da kibarta ta haihu don Allah shine masanin gaibu. Matar tafita da yar ta simi simi da ita take cewa lalai gurin nan kan akwai magana sosai ga wanda yazo. Haka bai hana wata shigowa dakin ba tare da yar ta tana biye da ita a baya. Suna zama nace tau duna nan kuma ka labe a jikin yar mutane kana cuta mata. Wai may sa ku bako so a zauna lafiya daku ne may yan adam suke maku haka kuke son yawa cutata masu a rayuwan su. Matar tace malama wallahi kamar kin san abinda ke tafe damu gashi ban fada ba harkin gani da idanuwan ki. Nace halin yarki yasa ya shige ta don wanan gashin da take dorawa ko yaushe akanta kin san shi duna baya son zama sai irin wanan guraren. Ida ake barin akaifa a yatsun hannu da gurin da ake barin gashin kai a sake ko da yaushe. Sai ko gidan da ba a tsabtace ana barin kwata yana taruwa a kwatamin gidan ko ana yawan barin kwanoka ba, a wanke su ba akan lokaci kai duk dai gurin da najasa yake anan ne zaki samay shi yana mafaka. Ku dinga horon diyan ku akoda yaushe su dinga daura dankwali ko hulla akan su su dai yawan karin gashi wanda basu san idan yafito ba a kawunan su. Dazaki ga wanan bakin aljanin danakira maki da duna zaki ga shugan shi da kaman shi kamar yadda diyan ku na wanan zamanin suke kwalliyan su sufito kamar mahaukata da sunan kwalliya a garesu. Wanan shiga da kuka saka ido diyan ku sunayi shike kara jan ra, ayin shi yana shiga jikin su yana jin dadin rayuwan shi. May yasa kuke ganin basu damun diyan ku maza a kasafai sai diya mata badon komai bane don suna morewa kurciyan su ne ta wanan hanyan kawai. Hannu nake murzawa ina mata bayani na miko mata hannun wanda magani ne ya baiyyana a cikin sa na mika mata nake cewa ta dinga yin hayaki da kuma shafawa a jikin ta har mugani zata ko kuma yi aure da zaran ya barta. Idan bai fita ba sai musan yadda zamuyi da su matar ta bude haban zanin ta dauko dubu daya tana cewa ga wanan sadakane na bayar saboda Allah. Kudin na kallo cikin mamaki nace kece mace ta farko da tasan wahalan da godiyar mu takeyi har ta bata wanan a matsayin taimako. Don haka jeki da abinki amma daga kanki yazama waji duk wanda zaizo neman taimako a gurinta dole ya san abinda zai aje mata da sunan sadakan da kikace a yanzu. Bamu bar gidan ba, sai musalin karfe biyu da rabi na rana, muka bar gidan wanda a lokacin Allah kadai yasan mutanen da sukaso gani na amma na basu hakkuri suka barni. Kai mutane suna cikin matsaloli musan man ma mata kamar sunfi kowa matsala a wanan lokacin da muke ciki. Mun iso gida duk jikina a gajiye yake min duk da na shaka hantitina a hanci ba iyaka. Ganin yanayina kawai ya sa Umma ta fahinci cewa abin ya taso min acan inda muka tafi yadda nazo na kwanta mata ragwab a gida. Tace yaya dai maryam ko abubuwan sun ziyarce kine kuma can ? Kai kawai na gyada wa Umma na gyara kwamciyana sai barci ban falka sai biyar saura koshi saboda sallah la, asar da ban samu yi bane yasana mike. Nan dai muke da yar sokoto da tashigo gurin ta duba jikina hira muke da ita da umma ina saka baki jefi jefi. Haka baban Abba ya shigo gidan ya samay mu ganin shi bai sa yar sokoto tabar mu ba don yanzu an saba sosai a tsakanin mu. Ga bakin ta ne yake jin abinda ya faru dani a unguwar da muka tafi da yadda abubuwan suka wakana. Nan dai yake fada yana cewa wanan dalilin ne yake sa yanzu sam bana son kina fita zuwa wani gurin. Umma tace ai wanan lalura ne kowa yasan ts kuma sai dai kowa da irin yadda tashi take zuwa mai. Jin maganan da Umma tayi yasa yaja bakin shi yai shiru don baida abin fadi kuma. ****** ********** ****** Sallah da sati biyu nashirya tare da daukan kudin bin yusuf da suka damay ni na nufi kasuwa dasu. Yar sokoto ta lake min cewa tare zamu tafi da ita don tana son zuwa shagon tagani nasan gulma ne zai kai amma tare muka tafi da ita. Allah ya rufa min asiri na samu wai ranan suka fara bude shagon su ashe daga dogon hutun da suka tafi koshi wai akan wani dalili yasa suka bude a ranan. Kudin shi cif na kirga na bashi tare da mashi godiya sosai. Bayan yagama kidayawa ne yake cewa masha Allah malama maryam kinyi alkawari sosai haka ake son samun mutum da cika alkawari. Don haka ina daga cikin wa yanda zasuyiwa bonanzan kayan shagon su na duba duk abinda raina ke so na zaba kada naji komai. Nan ta dinga taimaka min muka dinga zakulo kaya sai dana zabi duk wani abinda nake so a shagon. Yace bai kai yadda suke bauarwa ba na sake zaba haka muka zaba fiye da wanda na zaba da farko. Kudin daya fada na bayar yai matukar bani mamaki yace haka yakewa customers din shi don suma su samu duk shekara. Mun fita zuwa shagon da zan sari turare anan mukaga wani taro anyi dandazo ga wani yaro a tsakiya yana kuka yana faman rantsuwa. Har muka shiga muka fito shagon mutanen duk suna gurin ana ta faman rikici a tsakanin su wani mutum mai girman jiki yana kwadawa wanan matashin mari. Ni dai ban san yadda akayi ba sai ganina a tsakiyan taron nayi na dubi idon mutumin da idanuwa da suka canza launi nake cewa dashi. Kada ka kara dukan shi may yasa ku yan adam baku da imani ne ? Wanda ya dauki kudi ka daban wanda ka, ke duka haka daban don yana nema a karkashin ka, amma kazo ka kama wanan dan marayan Allah kana ta faman dukan shi da zargin shi. Kan san inda kudin ka suke ka koma gida tun bai kashe suba ka karbi kudin ka hannun dan ka Abdul don yafara taba su. Tsit mutumin yayi yana kallona cikin mamaki na kara cewa ka tafi gida saman silin din dakin shi kudin suna ciki ya boye. Ikon Allah wanan matar kuma fa? Wani daga cikin yan kasuwan yake tambaya nace sunana Rukaiyya daga haka na juya muka tafi Allah da ikon shi babu abinda ya samay ni ta fannin faduwan da nakeyi idan sun fita daga jikina. Muka kwaso kayan mu mota daya muka bar kasuwan kafin a dawo har mun bace ko. Koda mutanen suka dawo anyi nemana basu samay mu ba mun tafi, sai wani ne kece yasan ni ina yawan zuwa shagon bin yusuf sosai. Nikan na dawo gida kamar bani bace wani abu ya faru dani a kasuwa sai mamaki irin kayan dana lodo daga kasuwa yau Umma take yi tana fadin ikon Allah maryam duk wanan uban kayan haka naki ne ? Kice dai kece akazo wa kaduna maryam wanan irin alherin haka ? Murmushi kawai nayi ina kaiwa zaune saman kujera nan yaran dana samu sun dawo daga school suka kewaye ni kowa na son na basu tsaraban dana saba sayo masu idan nashiga kasuwa. Idan ka saba sayawa yaro dan abu idan kafita ko yaushe akwai yar shakuwa da yarda da aminci a tsakanin ka da dan ka. Haka yasa nasan sun saba da idan na dawo na basu dan abinda na sayo masu don ni bani taba basu kudi nace suje su sayi abu da kan su nice dai zan saya da kaina na basu. Don bawa yaro kudi yasaya abinda yake so kudi a hannun shi wani babban hanya ne na tallafawa lalacewan tarbiyan yaro a wanan zamani. Duk ranan da yaro ya bukaci ya sayo abinda yasaba baka bashi kudin ba yadda ka saba mai zai iya dauka koba da sanin kaba yaje ya saya. Wanda hakan zai kamaci gaba ga rayuwan shi har tai mai illa a gaba. A haka mahaifin su ya shigo ya samay mu sun kewayeni ina basu tsaraban alawa da biscuit. Idon shi kyam akan kayan da yagani na sayo yana mamakin ganin su haka da yawa. Nan ya zube yana cewa kun dawo ke nan daga kasuwan nake ce mai yau ai da kafan dama na shiga na samu ana bonanza na kwaso kaya haka da ace ina da kudin da yafi haka ai ba karamin kaya zan kwaso ba yau. Namike na dauko mai abincin shi ya soma ci ke nan akai sallama a kofan mu abinda yasa shi mikewa ke nan ya nufi waje gurin mai sallaman. Shiru shiru bai dawo ba har tsawon wani lokaci ya shigo sai dai fuskan shi a daure ina zaune a kasa gaban table ya zube min kudi masu yawa zasu kai kusan dari biyar. Bin kudin nayi da kallon mamaki kudin ki ne da kikai aiki a kasuwa aka biyo ki dashi nan. Kudina na taambaaya cikin mamaki yace eh kudin ki mana bakin shiga kasuwa ba yau kiika kashe wuta. Na kada kaii ina cewa gaskiiya bani bace don ban masan wanan maganan ba ni. Baiyi magana ba nima dai shiru nayi ina tunanen may nayi har za, a kawo min kudi masu yawa haka ? Ummace ganin yanayi take sake tambayan shi wai kai bakai mata bayani ne akan kudin ka zube mata kudi a gaban ta tace ma ba ita bace. Yace Umma ni may zance yanzu ace nayi laifi wasu Alhazai ne yan kasuwa sukazo wai taga suna rigima akan an sacewa chairman din kasuwa makuddan dollolin shi shine tafada masu inda kudin yake suna zuwa suka samu yadda ta fada din hakane shine suka kawo mata wanan a maysayin tukwaici gareta. Nace ni gaskiya ba abinda ya samay ni a kasuwa balle suce hakan bani bace ka mayar masu da kudin su don Allah. Kedawa kuka tafi kasuwa sunce min ku biyu ne ai ? Nace a hankali ni da yar sokoto ne muka tafi tare yace Abba kira min yar sokoto a gidan ta idan tana nan. Yaron yafita da sauri ya nufi gidan yarsokoto din shiko yaci gaba da fadin ni wallahi wanan abin ya fara isata wallahi dole na dauki mataki akai sai dai aga laifina. Tayaya mace zata dinga lamayawa a cikin kasa a gaban maza kuma a kasuwa akan wani dalili can na daban. Ai bake kadai bace a gari ga mata da yawa may zaisa basu bisu ba sai kece za, a saka a gaba haka kamar ke kadaice mai aljannu. Ka iya bakin kafa babana wallahi idan ba ita kadai bace kowa ba da kalan nashi ba da kuma irin yadda abin ke kasance mai. Yar sokoto tashigo gidan tare da Abba yanayin ta a cikin damuwa don bata san dalilin kiran da akai mata ba din. Tambaya ya jefo mata yana cewa don Allah yar sokoto da kuka je kasuwa may yafaru a can ki fada min gaskiya tsakanin ki da Allah. Bata rage ba bata kara ba duk abinda ya faru ta labarta mai nima sai lokacin ne na san may akayi. Yace bata zube ba a furin bayan su fita daga jikin ta tace a, a wallahi muna hanya dai naji tayi atishawa kawai abinda nagani ke nan amma har muka kawo gida ba abinda ya samay ta. Ajiyan zuciya ne ya sauke yana cewa yanzu naji magana amma gaskiya ni bazan yarda hurda da maza ba gaskiya. Kai al, amarin iskokan maryam fa masu taimako ne su aduk inda sukaga matsala don haka kaba kanka lafiya. Da yake musulmaine take tare dasu aikaga sun san kaida da darajan aure basu bari komai ya samayta ba a gaban maza. Nan zaka gane farfarun mabiyane tare da ita masu sonta da alheri ne ba tsiya ba. Yace ni gaskiya ya kamata na fara tambaya kan wanan al, amarin don abin ya fara bani tsoro wallahi. Kadai bi sannu na fada maka kada kajawo wa kan ka matsalan da zaka kasa fitar da kanka ciki. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU[11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BANE A, , , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣7⃣ Hankalina yai matukar dagawa akan wanan abin daya faru dani a kasu ba don komai ba sai don mutuncina na diya mace a matsayina na matan aure. Ranan zaman falo ma gagara na yayi nakoma daki abin duniya ya damay ni sosai a rai na sai tunanen yadda zan samu maraba da wanan abin nakeyi. Nayi dana sani yafi dubu a raina ranan nayi dana sanin haduwa da su danayi wanda nake ganin na hadu da mutanen kirki ne da farko . Ashe ban sani ba da jinnu nake taraiya yanzu ga abinda suke kokarin jawo wa rayuwan aure na matsala kuma. Shima fushin yake haikan haka muka kwanta kowa da abinda yake ji a zuciyar shi. Can cikin barcina na fara mafalki kamar an tayar dani akace maryam fito falo kinyi bako sai na dauki hijjab dina na saka na nufi falon da bakon yake. Baba malam ne yana zaune saman wani carpet na alfarma sai kamshi ke tashi gurin hannun shi rike da casbaha saye da fararen kaya kamar kullun. Zubewa nayi kasa ina gaishe shi da zuwa kai kawai ya daga min baiyi magana ba Ina duke gurin da na durkusa da farko har yakai karshen adduan da yakeyi ya shafa a fuskan shi. Ya dago yana murmushi a fuskan shi yace sallamu Alaikum maryama. Na kara amsawa tare da gaishe shi again yace yaya muke ya iyali nayi hakkuri baya kasan yatafi bauta tun cikin watan azumin tsofi bayan rabona dasu ke nan bada dadewa ba. Yake cewa yasan abubuwa da dama sun faru gareni da yan uwa suka jefani . Har yakai yanzu ina bakin ciki da nadama haduwa na dasu danayi na rashin ganin basuyi min adalci ba. Shiru nayi na sada kaina kasa cikin kunya yake cewa kin san halin ku yaran zamani da rigima bakowa bace sai Aisha da Rukaiyya . Son da nake maki ne tashafe su suma suke kaunan ki haka. Duk inda kika saka kafan ki suna tare dake sai dai nace kiyi hakkuri don ba zasu taba cuta maki ba ba kuma zasu bari a cuta maki din ba. Maryama ke tamuce muna tare da ku tun zamanin iyayye da kakan ni bazamu iya rabuwa dake ba yadda kike tsanmani. Wanan abin da kikeyi wani, taimako ne na al, umma da ya fado ta gare ki don haka hakkuri zakiyi da yanayin naki hallitan. Babu wani mahalukin da ya isa ya kankare maki wanan rayuwan sai ubangiji Allah da ya nufe ki da wanan rayuwan, haka taki rayuwan tazo maki a duniya. Bana son jin kin kara nadama da halin da kika riski kan ki a cikin sa shi mumuni ana son duk halin daya tsinci kansa a ciki ya dinga godewa mahalicin sa Allah da yanufe da zama haka. Daga yau bazaki kara wahala ba ko yin abinda ba daidai ba wanda zai iya sabawa ibadan ki. Muma musulmai ne yan uwanki musan abinda addini ya shimfida muna maikyau da marakyau na rayuwan bawa. Ni dai sauraren shi kawai nake kaina a kasa har ya gama min nasiha ina godiya kamar yadda na saba yi mashi godiya a duk lokacin da nake tare dashi. Karshe kafin ya tafi yake miko min wani jakka daga gefen shi yake min bayanin duk abubuwan dake cikin jakar ya kare da cewa zaki dinga karban sadaka ga kowa da kika bawa tai mako gwargwadon halin ciwon maishi. Godiya nayi bayan nasihan daya biyo baya yake ce min na dinga hakkuri da maigidana maza dama sai hakkuri don kowa da tashi kalar rayuwan. Gargadin karshe da yai min shine kada kiji kunya ko tsoro ko nauyi akan wanan lalurar taki don taimako ba sata bane taki hanyan samun kenan da Allah ya buda maki. Mukai sallama naga ya koma kamar hayaki yana bacewa gani na har na daina ganin shi. Ajiyan zuciya na sauke daga gurin da nake a tsugune na dafa wanan jakkan kayan maganin da ya bani na mike tsaye. A daidai lokacin na falka daga barcin da nakeyi tare da sauke ajiyan zuciya ga gumi na hada sharkaf a fuskana duk da yanayin sanyi irin na garin kaduna da akeyi. Baban Abba da ke barci a gefena naji shima yana mafalki kamar yana yanayin neman taimako sai fadi yake don Allah ayi hakkuri bazan sake saka mata ido ga al, amarinta ba insha Allahu. Ganin yana wahala sai faman motsumotsu yakeyi kamar mai neman taimako yana mika hannayen shi na kama hannunwan shi da sauri ina fadin baban Abba baban Abba lafiya kuwa ? Firgigit ya mike a zabure yana fadin ummum ummumm maryam nagode nagode. Nake cewa sun biyo ka ko kai ma ke nan ? Yace a firgice yanayi yana dan waige waige yace wallahi sun biyo ni maryam sunce yau sai sun hallakani badon Allah ya kawo ki ba a cikin wani katon rami mai namun daji sukaso jefani saida kikazo ne kika cece. Nace ka tashi muyi sallah mu roki Allah saukin wanan Al,amarin haka ni duk kaina ya daure da wanan abin gaskiya. Tunda muka tashi mukai sallah babu wanda ya kara runtsawa dagani harshi muna a gurin zaune har akai kiran sallah yafita zuwa sallah abinda bai saba yi ba ke nan sosai. Nan dai muka bar zancen kowa ya kama tsabgab gaban shi na shiga kitchen don dora abincin breakfast danai masu don tafiya makaranta. Muna shirin tafiyan su ne yafito daga daki yana shigowa falin yake cewa wanan kuma wani irin kamshine falon nan yakeyi haka ? Sai lokaci na farga da cewa nima naji kamshi kamshine na zauren baba malam sak yake tashi a falon lokacin. Ina jin abinda ya fadi mafalkina na daren jiya ya fado min a rai bankai ga karashe tunanen ba naji muryan Abba yana cewa mummy wanan bag din yana da kyau sosai . Gurin da yake nuna min bag din na kalla naga wannan bag din ne da baba malam yabani a daren jiya na magani. Gabana ne yai mugun faduwa nace a raina mafalkine ko gaskiya baba ya ziyarce ni a daren jiya. To amma kuma idan mafalkine kawai may ya kawo wanan bag din a falon mu yanzu. Bag din maye wanan baban Abba ne yake tambayana ganin yadda nai shock akan bag din. Ba boye nake cewa daren jiya baba malam ya kawo min shi . Abindana fadi ne yasa hankalin shi dagawa watau da gaskiya ina gana da mutanen boye ke nan murarar kamar yadda mahaifina yai mashi bayani ranan. Wahalan da yasha ne daren jiya yasa shi jan bakin shi alaikum yai gum bai furta komai ba. Saboda har wanan lokacin a firgice yake da mafalkin da yayi wanda yake gani kamar a zahiri ne yayi shi ba, a mafalki ba. Bayan fitan su gidan na gyara ko ina na gidan tare da dora girkin abincin rana don yanzu na daina barin koda sha biyun rana yai min ban gama aikina ba tunda abokan zama na sunce na kiyayye yin hakan. Wanan abubuwan da sukan yawa nuna muna alaman shi a gidajen mu akan mu dai wasu abubuwan da basu so. Amma rashin sani da rashin fahinta bai sai mu kiyayye sai muyi ta afkawa munayi su kuma sai su samu sa, an wahal da rayuwan mutum yadda suke so. Zaki ga wata idan sharane ba, a son ta dinga yi da rana ko da dare a gida da zaran tayi shi a wanan lokacin zata dinga jin ciwon kai ko ciwon jiki. Idan wanke wanke kikeyi da rana tsaka hakan zai ita faruwa dake ko girki ko wanki da sauran su saboda suna ganin kamar mun shiga masu hakkin sune a cikin sanin mu. Don Allah yan uwa na mata mu kula da abinda idan munyi a gidajen mu muke jin ba dadi saboda babu gidan da babu su a duniyan nan saboda tare muke dasu a gidajen mu bamu dai ganin su ne mu. Wanka naki na yaranki gap da sallah magariba yan uwa mata mu kiyayye yin hakan musan man ma macen da ta haihu ki take da ciki a jikin ta don sunfi saukin samun su sosai wallahi. Allah ubangiju ya tsare ya kare mu daga sherin shedan wanda muke gani da wanda bamu gani. ****** ********* ****** Ban sani ba ashe wanan abin danayi wa bawan Allah nan a kasuwa da aka sace wa dalolin shi ya jawo min wani sabon rayuwa na gaba. Ranan da yakai kamar sati uku da faruwan haka har na manta da zancen a raina. Sai ga baban Abba yashigo gida yake ce min maryam kina da bakin da ke son ganawa dake. Nace baki baban Abba wasu irin baki kuma ? Yace yanzu ina office mijin Hauwa yakirani wai nayi baki a gida danazo ne naga ashe wanan mutumin da kika taimakawa ne shi da wasu a waje suke son ganin ki. Nace gaskiya baban Abba duk da kaima nasan ba da son ranka zaka yarda naga maza ba don haka duk abinda zai samay ni sai dai ya samay ni wallahi amma bazan yarda na kaucewa mahalicci naba. Duk yadda yaso na fita kada mutanen suga an masu rashin mutunci naki sai dai cewan da nayi ya koma ya fada masu kada subi hanyan gabas da kayan su koma ta hanyan arewa su shigo dasu shine amsan abinda suke son ji a guri na kawai. Yadda na fada mai haka ya fada masu mamaki da imani duk ya kama su basu fada min abinda sukazo dashi ba amma gashi na basu amsa abinda ya kawo su. Shiru sukayi dayan na shirin yin magana wauan baban Abba yai kara nice a layin nake cewa bayan ya dauka nake cewa dashi Ya fada masu cewa kada su biyo dasu da dare sai karfe daya daidai na rana zasu biyo da kayan da yarda Allah shine mafita garesu. Yadda na fada mai yai masu bayani akan komai mutumin da wanan chairman din yan kasuwa ya rako yace anya Alhaji lukmanu kana ganin haka zai yi kuwa. Da dare ma yaya muka kwashe balle da rana haka kiri kiri ace za, a biyo da kaya. Suna hanyansu ta komawa inda suka fito ne suke wanan zancen haka. Alhaji Lukman yace mu dai jaraba mu gani kawai don ni al, amarin yarinyar ranan ya bani tsoro sosai don ban taba kawo cewa wai dana na cikina ne zai iya yimin haka ba a rayuwana ba sai gashi yadda ta fada muna hakane ya kasance din kuwa kudin na samay su kamar yadda tafada ya kuma fara tabawa. Baban Abba yana ciki gurina lokacin ina zaune tare da umma muna magana akan matsalan mutanen yanzu. Zama yayi duk muka bishi da kallon yanayin shi yace wai Umma yanzu may mutane suka zamane ? Yace mutumin da yazo ganin maryam yanzun fa ba karamin mutum bane a kasan nan wani irin hamshakin mai kudine sosai a cikin kasan nan. Umma tace may yake so kuma Aliyu yace tambaya ta ita tasan abinda yake so dai nikan ban sani ba gaskiya. Nace cikin mamaki wani ? Ni kan ma ina nasan shi balle har nasan ko may ya kawo shi gidan nan ni. Kallon mamaki yake min yace kai maryam wai ko kanki daya kuwa yanzun nan fa kika fada min abinda zan fada masu zakice kuma wai ke baki sani ba. Nace wallahi baban Abba ni ban san komai ba akan zancen da kake min ikon Allah to Allah ya sauwa kawai yake ce min don shi a zaron shi ko gatse nake mai. Nace wai wani mutum kake magana akai kuma wallahi Allah ban san ko wa kake magana ba. Nan dai ya fahinci al, amarin nawa akwai daure kai a cikin shi idan basu tare dani normal nake banda wani matsalan komai atare dani. Don haka ya zama wajibi a gareshi yasan yanayin da bani kadai nake ba don kiyayewa kawai. Gashi abin duniya ya dami zuciyar shi ba dama yace zai wala rayuwan shi a waje ai mashi tonon silar a gida. Nan dai muka bar zancen bakina dayazo min dashi muka shiga zance kan kayan dana tura gida kudi ya lake bai fito ba. Anty lami tayi bi amma matar da ta kwashi kayan a gurin ta, ta hana mata kudin har suna batun zuwa kotu don kudin yana da yawa sosai ba wai kuma bata dashi bane ra, ayine kawai. Jin haka yasa nace , a,a basai takai ta kotu ba akan kayan ta kyale ta kawai dasu bashi ke nan ba. Sai ga kiranta ya shigo a wayana na dauka da sallama muka gaisa da ita take ce min gata a gidan matar da ta kwashi kayana . Tazo don su kai karshen magana da ita nace bata wayan muyi magana da ita matar. Ina dauka matan take cewa aiko ina a kaje da ita dole a bari sai ta samu kudi tabiya kudin idan kuma za, a kwata ne da karfi sai ta gani. Allah yasa akwai mutane a gidan lokacin da muke wayan anty lami tasa handsfree a wayan kowa naji. Nace Asabe kin san dai akai kudi a dakin ki da zaki bayar ko don kudin kayana sunan nan ki sai diyan dorawa dasu kin tara don dogon guri. Akwai kudin Abbas da kika karba shima kin yaudare shi sunan kin sai gyada dasu kin boye. Shin da kudin mu kike ganin zakiyi arziki ba da yardan mu ba ki ci riban da kike son samu ? Idan kina son kanki da lafiya nabaki sati daya ki turo min da kudina idan kuma baki turo ba kinyiwa kanki. Aiko jin fallasan danai mata rashin sani yasa tashiga zagina da kunduma min ashar wai tun bata fara daukan kayana ba take da arzikin ta sheri zan kulla mata ko may ? Nace nadai fada maki in har kina son kanki da lafiya ki turo da kudin nan nan da sati daya kamar yadda na fada maki babu zancen zuwa kotu a kanki. Anty lami ta karbi waya na bata hakkuri don da ta kafe sai tayi karanta ga gobe insha Allahu. Ni kan tunda na samu komai ya lafa na fita zancen don nasan ya zama dole ta biya bashin nan koda tsiya koda arziki. Ashe taje tana yada magana cewa sai tayi maganin anty lami a garin nan ita zasuyiwa sheri da kake don ana bakin ciki tana da dukiya. Shine har ake mata hassada ita da kudin kudi ta rike taga uban da zai kwatar masu kudin su idan akwai wanda ya isa don lami tana kurin ubanta malami ne ko ? Anty din ta kara kirana akan zancen hakkuri na kara bata nace kwandalanki ba zaiyi ciwon kaiba anty kudin ki zasu dawo gare ki insha Allahu. Duk da haka bata yarda ba da zance na don tasan halin Asabe tantiriyar yar bariki ce kuma gashi tana hurda da manyan gari. Kamar yadda nai masu bayani haka Alhaji Lukman ya samu ya rarashi Alhaji Sada ya yarda a bin shawaran dana basu din. Dole ya hakkure yabi shawaran sai dai yana hango harsan da zai tafka sosai akan wanan gurguwar shawaran dana basu din. Mamaki sukeyi yadda akayi hanya lafiya kalau har suka shigo da kayan su basu hadu da wani jamin tsaro ba a kan hayan. Suna zaune falon Alhaji Lukman hankali a tashe sai jiran kiran wayan yarasu sukeyi suji labari mai dadi ko mara dadi akai. Shaddodine da atamfofi irin na kasan waje dasu bag, shoes, da sauran abubuwan amfani wanda yan custom ke shan kwace masu shi, gashi wanan lokacin kusan duk rabin dukiyan shi ya narka saboda kayan nan da yake son ya shigo dasu. Kiran wayan da akayi ne suna dubawa suka ga daya daga cikin babban yaron su ne da ke jagorantan shigowan kayan nasu. Da sauri ya dauka yana fadin hello mustapha yaya akayine sun kama ku ko? Dama ai nasan cewa wanan muguwar shawara ce dama yana fadin haka yakai zaune cikin dafe kai kwantena sun kai talatin da wani abu duk yayi hasaran su ke nan ake nufi. Alhaji Lukman ne ya dauki wayan yana fadin hello mustapha yaya may ke faruwa ne may ake cikine wai please. Wanda aka kira da mustapha din yace Alhaji Alhamdullahi komai normal don har mun shigo dasu inda kace batare da wani matsalan komai ba ko kadan a hanya. Kai masha Allah Allah mun gode ma jin yana hamdala yasa Alhaji sada dago kai yana mai kallon mamaki yana cikin wanan halin na tashin hankali. Hannu ne ya mika wa Alhaji sada yana cewa congratulaion Allah ya taimake mu Alhaji ya rufa muna wanan asirin. Ai yana jin hakan yace ban fahinta ba fa may kake nufi ne wai. Yace Alhaji sada kaya dai sun sauka lafiys har an adanasu indaya dace ko. Wai wasa kake min a cikin wanan yanayi ko may kake shirin fada min ne Alhaji ? Yace abinda dai kaji na fada ma din ne haka abin yake da gaske. Masha Allahu kai Alhaji wai yarinyar nan da kake fadi mutunce ko aljanna ita ? Yace bari kawai ni al, amarin wanan bakuwar fuskan yana matukar daure min kai. Baka ganta bane fa yarinya ce karama da ita Allah yai mata wanan baiwan haka wallahi. Kenan ashe ko acikin mutanen mu akwai irin yan baiwan nan sani sune kawai ba, a yi acikin al, umma ? Kwarai kuwa akwaisu da dama sune dai boyene ba, asanin su a cikin yan adam sai wanda Allah yaiwa katari dasu kawai zai san dasu. Allah bowayi gagara musali ita kuma wanan boyar Allah nata baiwan ke nan a haka. Dubi dan gidan da take zaune ciki tana rayuwa acikin sa tare da tarin baiwan Ubangiji a tare da ita. Alhaji sada ai ni wanan yarinyar yanzu ban ma san irin alherin da zan saka mata dashi ba a wanan duniyan. Nan dai sukai ta farinciki da jin dadi a tsakanin su har suka watse acikin farin ciki kowa ya hari nashi tsabgan cikin jin dadin junan su. ****** ********* ****** Sati dana fadawa Asabe ya cika tun da safe anty lami ta karasa gidan Asabe din cikin masifan son karban kudin ta a gurin ta. Amma sai bakar magana da cacan baki ne yabiyo baya har tana ikirarin taga uban da zai kwatar mata kudin ta a garurin ta. Tabar gidan rai a bace takirani a cikin masifa take fada min yadda sukayi da Asaben nake bata hakkuri nace ta koma gida kada ta damu da zancen ta. Aiko tai cikina da masifa ban san yaya akayi ba na daka mata wani irin tsawa sai da ta kadu cikin mamaki take kallon wayan kamar nice a fili take kallona. Haka kawai taji zuciyar ta ya aminta da magana na tace don Allah maryam kiyi hakkuri zan bar zancen kamar yadda kikace din. Ai ba, ai wasu awanni ba taji ana kwada sallama a kofa akece mata gidan Asabe ne ya kama da wuta kurmus komai na gidan ya kone amma ga kudin ta an samu wasu kudi a gidan gurin kashe wuta anji tana fadin kudin lami ne akai mata abinta. Mamakine sosai yakama anty Lami tace ita Asaben ne take fadin haka yan sakon sukace ai ta zare ne ta koma kamar mahaukaciya da ita sai sambatu kawai takeyi. Asabe dai bata tsira da komai ba a gidan ta har ginan gidan saida ya ruguje gabaki daya haka ta tashi ba komai. Ga kuma kudin da da bakin ta take rokon mutane akaiwa Lami kudi kudin Lami ne. Sai ga anty Lami ta bugo waya muna zaune take labarta muna yadda akayi kuma wai an rasa ta ina wuta ya shigo gidan don a lokacin ma babu wutan nepar a gari. Nace kudin ki dai sun dawo gare ki ko tace eh nace barta kawai kadan ta gani gobe ma ta kara in halinta ne . ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣8⃣ Gobaran Asabe duk yabi gari kowa da abinda yake fadi akan zancen gobaran gidan ta da ba, a san dalilin faruwan shi ba. Sai dai ta koma karba ta tabu saboda irin yadda take faman sake magana ita kadai tawa kanta tujara . Lami kudin ki dai nace bani basuwa, yanzun kuma gashi na baki kuddin ki ga kuma kaya min ajiye a gida kamar kullun. Lami dake da Abbas sai na ga wanda ya isa ya kwatar maku kudinku a hannu cikin fadin garin nan. Ganin ta soma haka yasa aka kamata akadaure ta cikin daki a gidan iyayyen ta duk da suma ba damuwa tayi da al,amarin su ba a matsayin su na iyayyen ta ba a baya. Amma babu yadda zasuyi ance naka sai naka ranan wuya kuma sai naka shine kawai zai tsaya akan ka. Haka suka fara shiga fita a kanta don nema mata lafiya gurin wani malamin suka tafi sai bayan yayi abin da zaiyi ne yake masu bayani abinda ke faruwa. Yace daukan magana tayi shine ya koma mata ta taba wanda sukafi karfinta ne yasa wanan iftilain ya sauka mata. Aka dan fara kus kus ana fadi ba, a tambaye kan fitinan ta da anty lami da sukayi na kudi. Haka dai zance yai ta yawo kowa da abinda yake fadi akan zancen duk da basu san komai ba . Sun yanke shawara tunda basu samun gani na kamata yayi su aika mace don zasu tafi gano masu gaskiya yadda abin yake. Hajiya saratu wata abokiyar sana, an su kuma yar siyasa ce aminiyar su, suka turo gurin na tafe da abin arziki. Kyauta ce ta ban mamaki sukai min wanda ban taba zaton samun shi ba a rayuwana suka aiko min dashi. Ya kasan ce ranan Jumma, a ne, Muna zaune ni da Umma muna kallo a falo bayan mu kare sallah Maigidan da yara sun tafi cikin gari mota ya tsaya a kofan gidan mu wanda yanzu har makwabta sun saba da zuwan bakin motoci dake yi na manyan mutane a kofan gidan mu. Wanda da farko idan sun gani suke shiga gulma ko a ina na samo manyan mutane haka nake hurda dasu. Hamshakiyar matar ta shigo gidan cikin tafiyan kasaita irin ta manyan mata sai faman raraban ido take yi sako da lungu na gidan namu. Mun tare ta a cikin mutunci tare da girmamata wanda dama haka rayuwan ta yake bukata ita a dinga mutanta ko yaushe. Ta zauna kamar mai kyankyami gidan namu sai bayan ta zauna dakyau take cewa gun malama maryam nazo don Allah. Umma tace to sannu da zuwa ta dubi umma da kyau tana tuhumar ko itace maryam din da tazo gurin ta. Amma sai taji Umma tana cewa ga tanan zaune a gaban ki itace maryam din ai. Wani kallon mamaki ne tai nmmin na jinki yafi ganin ki tafurta a fili karamar yarinyace ashe ke da wanan baiwan. Tace damaan turo ni ne zuwa gare ki ko zaki iya tunawa da mutanen da kika taimaka sati biyu da ya wuce ? Shiru nayi ina nazarin ko wa take nufi ya aiko ta zuwa gare ni bata fada ba kuma ban fahinta ba sai dana lura cewa so take ta gwada ni taga abinda suka fada mata akaina. Hannu na na hada guri daya nadan fara murzawa a hankali sai ko na fara hamma Umma dake gefe tafara magana irin na manya tana cewa. Ikon Allah sannun ku da zuwa ashe kuma kuna tafe a yanzu sannuku, sannuku da hanya. Aisha ce ko Rukaiya ko babban yaya nace Umma kuna lafiya yaya jama, an ku ? Ta amsa cikin jin dadi da Alhamdullahi sannu da zuwa matar dai da yake goggan yar duniya ce ta saba da ganin irin haka. Sai wani kallo take min kamar bata yarda da abinda take gani ba, zahiri. Umma take ce anzo gurin bakuwar mu ko sai nace Umma mukkadarasiya ce take magana nazo ne na bada sako na koma don ina akan tafiya ne. Hajiya dama baki tsaya kina wanan ba don ke yar soko ce zancen ki akan naki kayan da kike kokarin aikawa hakan bazai yi ba agare ki don kayan ki duk haramtatune dake da malka da kika ba sakon duk kasan saudiya zasu kama ku idan har kinyi yunkuri tura ta dasu cikin satin nan. May yasa kuke son yin kudi ko ta halin kaka dukiya bakomai bane sai tarin wahala a duniya da lahira amma ke kin kuke da wanan harkan bayan kin san ba alheri bane. Yaran mutane da kike turawa a kasa mai tsarki da kasashen turawa da zaki daina wanan harka da zaifiye maki alheri ki fada harkakin na tsiya dakike yi da farko don sabuwar gwaunatin da za, a kafa idan kin matsa zaki samu shiga sosai don zasu dama dake. Kallo na take a cikin mamaki nace hajiya kina ganin sakon da Alhaji sada ya baki na kudi da mahaukaciya ki kawo min kamar sun min yawa ko ? Kada ki soma taba kayan daba naki ba musan man irin wanan don zaki iya samun matsala babba a rayuwan ki. Yarda da son ki gano masu gaskiyan al, amari yasa suka turo ki nan don su tantance daga gare ki. Amma kuma ga shedan yana son rudinki ki aika wani abinda ba daidai ba akan sakon. Jikin ta yai sanyi sosai nace idan kin koma ki fada mai duk ritsi nan da jumma, a ya tabbatar da ya canza akalar maboyar dukiyan shi don daga cikin ku yan kasuwa kuma na tare dashi suna mai zagon kasa idan yaji walillahi hamdu. Ki shirya zuwa Abuja ranan laraba ranan samu ki shiga da ahabiyu akwai alherin da zai samay ki kan abinda kika dade kina nema acan. Nabarki lafiya zan koma dama nazo ne na walwale maki tuhumar dakike yi akan abinda idon ki ya nuna maki. Ajiyan zuciya ta sauke a hankali tana cewa ai min afuwa kusan dan adam da kwankwato amma yanzu na sheda komai da idona yadda ya kamata. Kuma ina fatan za, ai min afuwa sai don Allah ina neman alfarma ataimaka min kan kayan da akace bazasu shiga ba don su samu shiga don Allah. Nace sam haram kaya basu shiga ba don akwai haram acikin sa idan zaki iya ki tura su kasan turai zaifi maki alheri sosai. Take cewa ban taba aikawa can ba nace ki gwada kada kiji komai amma kuma wanan ba sana, an alheri bace duk kayan da zai iya kawar wa mutum da hankalin sa. Atishawan da nayi yasa Umma fadin ta tafi ai shike nan da zaki fake abinda ta fada zaifi maki alheri don ita wanan da kike gani yar kaidace da kannetane sukazo za ku iya fahinta amma ita magana daya takeyi. Kuma tunda kikaga tazo gun ki da kanta akwai matsala sosai don ita gaskiya bata faye zuwa ba sai idan abu ya baci zaki ganta ko ita ko Alhaji malam baban su. Ikon Allah hajiyan tace tana fuskantar umma dake shaka min magani a hanci tana ce min sannu maryam. Na dago ina cewa wai, tace sannu kinji balle sun dan kwana biyu basu taso maki ba. Yanzu mama ita wanan abin nata tun tana karama ne take dasu haka ko yaya? Umma tai murmushi tana cewa daga bayan nan dai ne bayan ma dawowanta garin nan Allah yakawo matasu haka. Sabbin hawa ne ma ke nan za, ace hajiyan take tambayan umma da hakan cikin kallon fuskan umma din. Umma tace tau sabbin ke nan za, ace amma gaskiya su abin nasu kamar gado ne don mahaifiyan ta ma haka tai ta fama dasu sosai a baya. Ikon Allah abin akwai mamaki basai ka fadi laluran ka ba sai dai kawai kaji ana ma tonon sillar haka ai wanan ba gurin zuwan mugun kai bane don sai mutum yasha kunya wallahi. Umma tace kin san musalaimane sosai kuma malamai ke tare da ita don haka nan kan ba gurin zuwa munafuki bane ko mugu idan ma yazo zai sha kunya don za, a fada mai komai kwata hilla. Hannu ta saka cikin jakar ta tafito da daurin kudi masu yawa tare da dan makullin mota tana fadin ga sako inji Alhaji sada kan taimakon da akai mai yaji matukar dadin wanan abin donnkayan shi sun shigo mai lafiya ba tare da matsalan komai ba haka yasa yace akawo wanan a matsayin goro. Umma tana kallon kudin tana fadin a, a a kai masha Allahu wasu idan an masu alheri a rayuwa sun sani sun san darajan alheri su saka da tukwaici mai tsuka haka ake so gaskiya. Daga inda nake zaune kaina sadde a kasa na dago kai ina kallon Umma dake wanan maganan haka. Nace Umma wanan abin baiyi yawa ba ashe taimako ne fa kada ya zama kuma hainci gare shi don an taimaka mai kuma ya zamanto na haince shi kinga haka baiyi ba . Hajiyan cikin mushi take cewa kai diyata baki san ko waye Alhaji sada ba ko a kasan nan ? Wanan shi ai bakomai bane a gurin shi don shi ko banza mutum ne mai sonyi alheri a rayuwan shi nasan ko wanan ma acikin shakkune yaba dasu. Don haka karbi abinki Allah ne ya cisheki daga gareshi kuma idan baki karba ba sai yaga kamar kin raina ne. Kudi ne sai kyautan mota ta hawa kawai yai maki yayiwa banza ma balle ke da kika taimaka mai haka. Umma tace mota ikon Allah kyautan mota ga mutum hajiya tace ai idan kana da halin haka wanan bakomai bane gamasu shi. Baki san irin nasaran daya samu bane wanda yace tun fara kasuwancin shi bai taba cin nasara irin haka ba. Nan dai bayan sundan taba hira da Umma tamike tana fadin zata koma amma zata sake dawowa nan gaba don nata bukatan idan ta dawo daga Abujan. Munyi sallama da ita ta tafi tabarmu a cikin mamaki da abin alherin da ta kawo muna gida. Umma na shiga wanka na kira mahaifina don na sanar dashi wanan alherin dana samu ta silar wanan al, amarin nakaina. Bayan mun gaisa dashi ne sai na fara kuka ina fada mai kamar haka. Baba shi ke nan ni na zama mai bada taimako ga jama, a duk yadda muka gujewa hakan baba abin sai da yahau kaina. Babana yace haba maryam may ye na kuka bazan tauye ki ba yadda na tauye mahaifiyar ki har abin ya zama sanadin rayuwan ta. Don kin san kafi ne dasu idan an masu ba daidai ba sai su koma akan maishi. Yace matsala dai daya shine kada ki kaucewa mahaliccinki da ibadan ki akan wanan abin. Ki rikr darajanki na ya mace da Allah yai maki haka kuma ki rike darajan auren ki da kimar mijin ki. Kin mayi arziki musulamaine kuma malamai a tare dake basu bari ki aikata wani abin ashaba a rayuwa. Nace a hankali cikin sanyin murya hakane baba baba yanzu fa kyau tan kudi ne zai kai miliyan daya da mots aka kawo min. Maryam kin kara samun kyautan mota kuma? Allah shi yasan daidai ga bawan shi wanan tafiysn naku maryam a zahiri dai tafiyan ki ne kukayi bana mijin ki ba. Don kece kikai gamu da alherin rayuwan ki a garin mutane don haka ki daina wanan kukan ki natsu ki san abinyi kafin ki makara da hakan. Lokaci yayi da zaki fara gina kan ki da diyan har ma da yan uwanki idan kin kwantar da hankalin ki komai zaizo maki a cikin sauki ta yadda baki taba tsanmani ba. Abinda nake boye maki tun kina yarinya maryam ina tsoron kada ki gado mahaifiyan ki da wanan abin don baki da gurin wasa tun kina karama sai gidin wanan iccen tsamiyan dake kofan gida. Duk neman da za, ai maki acan za, a samay ki saida nayi kamar inayi na samu kika daina zama a gurin. Wanda tun lokacin hasashe na yake a kanki kada dai ace kema kna da gadon wanan abubuwan tare dake. Nagode ma Allah da yasa ina a raye wanan abin naki ya baiyyana a kan ki. Insha Allahu bazasu taba barin ki tabe a hakana ba a rayuwan ki tunda na fahinci da alheri suke bibiyan rayuwan ki . Mun dauki lokaci dashi yana kwantar min da hankali wanda hakan ya sa na samu natsuwa a tare dani har nakejin zan iya tunkaran baban Abba ga duk yadda zai fahinci wanan kyauntan da akai min. Don ni dama ga nawa wautan shine kada ya zargeni akan wasu mazan waje ta wani fahinta na daban. Ga mota a kofar gida an girke min ga tulin uban kudi a cikin gida da aka zube min sai faman tunane nake araina. Anyya idan ana ban kudi irin haka rayuwana ba zai shiga wani hali ba kuwa don muddin idona ya bude da karban kudi masu yawa kan taimako to nan gaba bazan iya taimakawa mai karamin karfi. Zancen hajiyane ya fado min a rai da take cewa wanan abinda na gani ba komai bane a gurin hamahakin mai kudin daya bani wanan kyautan haka. Watau masu kudi suna nan a inda suke ke nan a kasan amma tallaka bawan Allah yake cikin wahalan rayuwa haka. Sai bayan karfe shidda na yamma ya shigo gidan tun da ya karyo kofan gidan ya hango wanan dirkekiyar motar parke a kofan gidan yake cewa a ran shi. Kai wanan kuma waye haka mutane basu dai bari mutum ya huta kowa ya dauko matsalan shi yakawo maka gida. Su gare su wani sabon hanya kuma ya bude ke na ga jama, a haka duk wanda ke bukatan ban kada ya kwaso matsalan shi ya kawo kamar basu san Allah ba. Haka ya shigo gidan fuska a daure yana zaton zai samu bakin nawa a falo zaune ne. Ga mamakin shi babu kowa a cikin falo sai Umma dake zaune ta kura ma shirin yara da akeyi a tv ido. Sina gaisawa da Umma yake faman raraban ido yaga bakuwar da ta shigo gidan amma babu kowa ga motsina daya ke ci a cikin kitchen ina daka kayan yaji da zanyi miyan dare dashi. Umma ce take kwala min kira daga falon nazo gashi ya dawo lokacin nafito ina yarfe hannuns dana dauraye da ruwa ina mai sannu da zuwa ya amsa a dakile. Na dauko mai abincin shi na juya na dauko ruwa ina ajewa ne naji muryan shi yana fadin wake da mota a kofan gida kuma. Kai tsaye na bashi amsa da cewa nawa ce kawai daga haka ban tsaya ba na shige dakin kwanan mu na dauko kudin nakawo mai. Cikin mamaki yake kallona don son jin karin bayani daga bakina sai bayan ba aje kudin ne nake cewa wanan mutumin da kazo dashi ranan ne ya turo matar shi da wanan kayan don hasken daya samu ga abinda akai mai. Cikin mamaki yace wai da gaskiya kina nufin kudi da mota ya bayar a matsayin tukwaici a gare ki haka ? Nace gasu ai a gaban ki kai ya girgiza yana cewa lalai ma al, amarin naki maryam bana wasa bane ashe don kin wuce sani yanzu kan. Ai har kin fi wani ma, aikaci samun riba a cikin wata don a iya lissafi na abinda kika samu faruwan wanan alamarin naki ba karamin abu bane gaskiya. ****** ********* ****** Hajiya saratu na komawa gurin su Alhaji take fada masu duk yadda abin ya faru sai dai ta boye masu wasu daga ciki. Nan suka ja mata kunne akan ya kamata su bar wanan zance iyasu don kada wasu su gane gurin azo a bata masu sa, an su nan gaba. Sai dai sin sha alwashi zasu dinga taimaka min idan hakan ya taso ta hanyan hajiya saratu tunda ina da aure ba gani na zasu dinga yi ba anytime. Itako zuciyar ta yaki aminta akan maganan dana fada mata kan zancen abinda take shirin aikatawa. Cikin sati kamar yadda tai niyya haka ta kudiri shiga da kayan ta kasan saudiya din. Aiko aka cafke kayan case yai kamari akace sai an kamata an tuhumay ta. Ta kira su Alhaji sada hankali a tashe take sheda masu komai kan su taimaka mata su ganni ayi magana asan mafita akan zancen. Haba hajiya saratu yanzu da hankalinki da wayon ki har kika bari wanan abin ya faru dake don kawai idon ki yarufe akan abin duniya ? Kece fa da kanki kizo muna da karin bayani akan wanan boyar Allah da irin abinda kika gani da idon ki a gareta. Sun cikin wanan case din sai kuma ga zancen yan matan data tura waje an kamasu a iyakan boarder ya taso nan abubuwa suka taru suka rikice mata a lokaci daya. Sunzo gurina da zancen kan asan yadda akayi ta kubuta nace ba na wanan aikin don ba, a bisa tubalin gaskiya aka dorashi ba. Duk yadda suka so gani naki yarda akan maganan sai da suka hafa da baban Abba shine yasani a gaba akan ataimaka mata ko don su Alhajin da suka saka bakin su ciki. Dole ba don naso ba na bukaci ganin baba malam akaro na farko da kaina kamar yadda ya umurce ni danayi indan ina da wani bukata a gareshi. Sai ko gashi ya taka akaina da kan shi nasha matukar wuya a ranan kafin akai ga mafitan zancen nata. Yadda duk aka fada haka akayi sai gashi ta samu kubuts sai dai su wa yanda aka kama an dan sasauta masu don ba wasu kaya masu aibu bane sosai goro ne sai su kayan mata da sauran tarkace aka yanke masu hukuncin shekara daya da rabi aka kashe zancen a cikin sauki. Na dan samu sararawa yanzu bana komai kuma sai harkan aiyukan gida da suka shige min gaba kawai. Hajiya Aisha kamar yadda tai alkawarin zamu Abuja a tare da ita sai gata da zancen ya taso mata don an kammala aikin komai a can. Kafin baban Abba ys yarda da tafiyan nawa tare dasu, sai da Umma ta saka baki ya amince da hakan . Amma ya nuna rashin yardan shi da hakan wanan tafiyan da nayi dasu naga duniya a furin wa yan nan mutane sosai. Gida wanda tsayawa fadan tsarin shi bata bakine gurin tsaruwan shi ga mai karatu. Muna shiga gidan naji kaina ya wani sarawa nan dai na samu daya daga cikin kujerun falon na kai zaune sama. Kowa na harkan gaban shi ina guri daya zaune sai lokacin hajiya ta hankalta da irin zaman da nayi take cewa, a, a diyata yaya komai baki taba ba daga ciki. Dan dago kaina nayi da idanuwa na da suka sauya min kalla a lokaci daya nace hajiya na koshi. Ta fahinci idan nace kalman hajiya agare ta bani kadai bace a lokacin hankalinta ta mayar gare ni tana kallona take cewa ko zan shiga daga ciki na dan huta ko ? Ina dai zaune gurin ban motsa ba ban yi magana ba kuma na dai yi shiru Nusaiba da nazo da ita tana makale a jikina. Nabila diyar hajiya ta biyu ce tafito daga saman steps take takawowa a hankali zats sauko kasa ta sauya kayan jikin ta zuwa kanan kaya wanan karon. Zubur na mike daga inda nake a zaune cikin wani kakausar murya nake ce mata tsaya anan kina kara tako daya sai dai kiga ana tafiya da kafa nan gaba. Cak taja ta tsaya guri daya a hankali nake hawa saman matakalan benen kamar zan fadi kasa a lokacin. Daidai step daya da ya rage ta taka na tsaya tare da dukawa agurin gaba daya wanda ke falon sun mayar da hankalin su a gare ni. Daben gurin nake bugawa da hannu na kai kasan idon tanice bazan ko iya banbaran shi da diga ba balle hannun da nake amfani dashi. Bugu biyu gana uku gurin ya tsake haka nasa faratana ina tonon gurin sai ga gurin ya bude hamza kanin hajiya ya karaso da sauri yana cewa wanan ma sabon shafi ne ba tarazo bane ai akai. Can na zaro wani kwalba a daidai gurin tare da wani laya da suma an nade a cikin shi. Take duk hankalin su yadaga gurin kowa na mamaki bin ginan gidan nayi da kallo kamar yadda dabba yake sun sunan wani abu don ya gano inda yake. Mikewa nayi a hankali nake bin matakalan har zuwa sama ban tsaya ko ina ba sai wani daki na shiga ina shiga na nufi daidai gurin gadon. Yaran sukace dakin mummy ta shiga hankalin hajiya yai matukar tashi sosai a lokacin jin dakin ta na nufa. Duk da karfin gadon dagawa daya nai mashi na dago shi sama gaba daya . Kasan gadon ma anyi kafi a cikin sa na ciro shi banyiwa kowa magana ba tunda nafito daga dakin hanyan fita daga gidan na nufa na fice zuwa waje. Sai da nai tafiya mai nisa sosai na samu guri na tsaya ina sake kwalllaben suka kama da wuta gaba dayan su wani bakin hayaki yatashi sama yabi iska. Na juya na dawo ina shigowa nai zaune ba umm, ba umm, umm haka na zauna kawai dani. Kusan awa daya ban tanka ba suma duk a tsorace suke a lokacin kowa yai tsuru tsuru a falon sun mayar da hankalin su a gare ni. Can da Allah zai bude min baki nace da karfi cikin dan zabura kamar zan mike tsaye, WALE. Wale wale kowan su ya fadi idan ba su ba sun san ban taba sanin wani walle ba can a duniya. Nace saike fadin Wale karo na biyu ina nuna gurin hamza yace walle ke nan ya saka abin nan ko ? Kai na daga masu kawai ban iya magana ba sai ga hawaye ya soma biyowa a fuskana wani bayan wani shar shar shar. Nace anba walle ya cutawa bayin Allah bayan yarda da amincin da akai mashi don may zakaci Amana Alhaji bashir ya cuta ma marayun Allah. Ran Hamza ya baci yace yaya kinga abin da nasha fada maki kan wanan kafirin amma sai ki ce min babu komai ko ? Nace cikin kakausar murya walle ya cuta maku ya zalunce ki zai zo yau din nan basai gobe ba zai fada maku komai da bakin shi. Ina fadan haka na kife a gurin ina sake wani irin hamma da atishawa duk a lokaci daya nake sake su tare. Hamza kabi sannu don gab suke dasu gama dakai don sun gane baka bari aiwa kowa gidan nan yadda suke son yi. Nan dai nake fada masu labarin inda Hamza ya tafi batare da sanin yar uwar shi ba don nema masu taimako da kuma yadda suka gane sukabi baya suka tone abin don Alhaji bashir shuumi ne hajiya ta hana shi yin yadda yake so da dukiyan su. Shi yasa yake kokarin ganin sai ya kawar da ita a doron kasa ya mallake komai nasu daga hannun yaran ta ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 2⃣9⃣ Door bell ke ta ringing alaman ana sallama a gidan lokacin duk muna falo a zaune abincin da hajiya ta tura kanin ta hamza ya sayo suke ci don ta hana su cin wanda aka girka a gidan. Duk da nace mata ba matsala amma bai sa hankalinta ya kwanta ba dashi. Uncle Hamza kamar yadda suke kiran shi dashi ne ya mike zuwa kofan ya bude wa mai shigowa gidan a lokacin. Ganin wanda ke danna bell din yasa shi dan kaduwa kadan amma sai yai kokarin boyewa hakan a ran shi. Tambayan shi yayi ko hajiya tana daga ciki ya bashi amsa da tana ciki yace yana son ganin tane please. Wani kallo uncle hamza yai mai na tuhuma sai yasha jinin jikin shi shima da irin kallon da akai mai din. Dakatar dashi Uncle Hamza yayi daga kofan shigowa cikin gidan ya juya zuwa fadawa hajiya zuwan shi. Cikin dakiya take cewa a barshi ya shigo daga cikin ganin mr Walle ne yashigo yasa gaba daya falon yai tsit ana kallon kallo dashi. Gaisawa ya fara yi da hajiyan amma ta amsa mai a dadare ba kamar yadda ta saba ta aminta dashi ba. Ganin haka yasa yaranta mikewa don su bar falon zuwa dayan falon nasu amma sai uwar ta dakatar dasu hikiman ta nayin haka shine ayi komai a gaban idanuwan su. Uncle Hamza yai setting din wayan shi batare da wani yasan abinda yakeyi ba a lokacin. Mr Walle ne ya fara magana yace Ma, nazo ne da wani magana wanda yake damuna sosai kusan sati uku ke nan abin yana matukar damu na a raina. Hajiya tace you can say it now tafada cikin rashin damuwa tana tsiyaya ruwa a cup zata sha. Ya kasa fadi sai dan kamay kamay yakeyi can dai ya daure yana cewa shi holy man ne addinin shi ya hana su yiwa dan uwan su hainci tundai, ga wanda ya yarda da kai. Yace hajiya da farko ina son ki gafarce abisa cin amanan ki da nayi bada sanin ki ba. Tace may kai min mr walle wanda ka haince ni har ban sani ba bayan na yarda da kai fiye da tsanmanin ka. Yace hakane hajiya na sani sai dai ni ban yi kokarin zama mai alkawari ba da rikon amana a gurin ki. Idan ban zo nayi confenssing din kaina ba agurin ki god will not forgive me . Mr walle may yakawo duk wanan zancen haka a wanan lokacin ban fahinci inda maganan ka ya nufa ba. Yake cewa hajiya bazaki fahince ni ba don an hada kai dani an cuta maki ta inda baki tsanmani ba ina tsoron kada wani abu ya samay ki ko yasamu daya daga cikin member of your familly. Dan gyara zama hajiya tayi da mamaki take kallon mr walle din a lokacin. Yaci gaba da fadin ba komai yasa nazo ba gurin ki don na fada maki cewa Alhaji Bashir brother din maigidan ki ya bani wani abu akan lalai sai nayi amfani dashi a gidan nan. Ban yi ba amma dai da sani ya karbi key din gidan bayan yayi barazanan ganin baya na da iyalina akan idan ban basho hadin kaiba zai cuta muna. Haka yasa na yarda tare dashi muka shigo don nike da keys din ko ina na gidan nan kin ya shiga bedroom dinki ya dauki lokaci a ciki haka nan kan steps din da zaikai ku sama shima yayi wani abu a gurin. Sai dai ni bazan iya cewa ga abinda yayi ba a lokacin don ina daga bayan shi tsaye. Kin ji abinda ke damuna nakasa samun sukuni a rayuwa na ko kadan a kan hakan. Yanzu na yanke a raina duk abinda zai min yayi min yafi min sauki akan na yarda a cuta maku don haka zaku iya duba wanan guraren dana fada maki ku gani ko zaku fahinci abinda nake fadi. Mr Walle how comes duk yarda da amincewan da nai maka a duk fadin garin nan har ka bari Alhaji bashir yai galaba akan ka. Yace Hajiya is god wish sai na yarda amma nima nasan ban kyauta maki ba wallahi. Shiru hajiya tayi tana nazari kafin tace dashi taji kuma ta gode amma yana ganin zats kara amincewa dashi kamar yadda ta amince dashi da farko kuwa? Yake cewa shi dai ko bata kara yarda dashi ba a yanzu bukatan shi, kawai, shine ya kasance ta yafe mai akan abinda aka aikata mata da sanin shi. Shiru hajiya tayi sai zuwa tsawon dan wani lokaci kamar mai nazari take cewa ba damuwa zai iya tafiya . Sai da yai dan jim guri daya kaman bazai tashi ba sai ya kara cewa tayi hakkuri dan Allah shima ba da san ranshi haka ya kasance ba. Ya dai mike gwiwa ba karfi yabar gidan don yasan cewa ba zata kara amincewa dashi ba kamar farko kuma. Yana fita hajiya take cewa ikon Allah wai may bashir yake so damu duniyan nan ne haka ? Uncle Hamza yace dukiyan marayun Allah shine a gaban shi mana bayan wanda sukai gaba dashi bai ishe su ba, wanda ya rage maku ne yake tsune mai ido kuma. Nabila tace mummy ni dama wallahi ban son al, amarin baba bashir din nan tun dady yana da rai kune dai kuke daukan shi da wani muhinmanci sosai a rayuwa. Nan dai suke ta maganganu mara dadi gamay da Alhaji bashir ba dadin saurare. Sai zuwa can nake cewa mama amma sai nake gani daga wanan abin da yayi yakai karshe insha Allahu don kaikayi zai koma kan mashekiyar ta duk abinda yake nufi daku Allah zai mayar mai dashi a kan sa. Daki daya muka kwana da yaran hajiya don sun ce wai suna jin tsoron kwana su kadai a dakunan su. Na fada masu da yardan ubangiji babu komai da zai faru dasu insha Allah don akwai tsarin ubangiji wanda su ba lalai bane su san dashi. Kwanan mu biyar a gidan tare dasu naji matukar dadin kasan cewa da wa yan nan mutanen na dan lokaci. Na shirya tare da tarin abin arzikin da na samu daga gurin hajiya da iyalinta wanda bazan iya tsayawa fadin shi ba har sai na manta da wani. Cikin lafiyan mota tare da tarin abin arzkina na iso gida na samu iyalina a cikin kewa na don ban taba tafiya haka ba na bar yarana su kadai. Irin abin arzikin da Umma taga na dawo dasu gidan ne yasa ta matukar mamaki irin wanan alheri haka mai yawa. Nan dai na shiga aikawa yan uwa da abokan arziki da abubuwan alheri dana samu suma su dana rabon su daga ciki. Rayuwan daula yana Abuja ko a abujan gida masu hannu da shuni suke cin karen su babu babbaka. Sai ina ganin mu ai kawai dai mun rako sune kallon duniya ashe shine dalilin da kullun mahaifin mu bai son muna shiga gidajen masu hannu da shuni don gujewa ganin wani rayuwan da ba irin namu ba. Yaro shi bai san banbancin mai kudi da tallaka ba sai yaga kamar abin duk daya ne laifin iyayyen shi kawai. Na fahinci hakan yanzu da hankalina yaikai lokacin da zan san haka din balle akan wanan daulan duniyan dana tafi na gano gidan masu abin. Ban ga laifin mahaifina ba da yake tsare mu daga shige shigen gidajen masu hannu da shuni. Wanda a da nake ganin kamar wani kuntata muna ake dayin hakan ashe ban sani ba gata ne akewa rayuwan mu da hakan. Sai washe gari ne muna hira Umma take fada min akwai wata matar da tazo har sau biyu gidan nan wai tana son ganin ki. Cikin mamaki na bar abinda nakeyi nake cewa Umma wacece ita ko bata fadi sunan ta bane ? Tace bata fadi ba sai dai matar kamar yar duniyace daganin ta gashi dai girma ya dan soma kamata amma dai shigan ta na kananan yara ne ba mutunci tare da ita. Dariya sosai maganan Umma ya bani nace kai Umma ho ai sunan birni ne ba babba ba yaro a gurin kwalliya sai wanda Allah yasa yagane gaskiya kawai. Umma tace ikon Allah ni dai sunan na shigo kaduna ne bubu inda na sani sai asibitin da muka tafi ranan. Umma kina son shiga garin ne kigani na tambaye ta cikin kallon fuskan ta don son jin may zatace min. Tace maryam idan ma nace zan fita ina zan tafi tunda ba kowa na sani ba a garin. Haka yasa na fahinci tana dai son zuwa ta danga gari kuma tana da gaskiyan ta ai. Itace ta kawar da zancen take ce min taji baban Abba yana zancen wai ya kamata ta koma gida hakana don kada abar gida babu kowa a can. A fahinta na Umma bata kaunan komawa gida yanzu don haka ya zama wajibi nasan yadda zanyi akan zancen . Yar sokoto ce ta shigo gidan muna hira take ce min gaskiya maman baki kyauta min ba yanzu ashe Abuja kika tafi shine baki gaiyaceni ba ni na ci arzikin ki. Yar sokoto haba dai yanzu ace mun kwashi jiki sa auren mu zuwa wani gari ba wani babban sha, ani ya faru ba ai sai a zarge mu ni dake. Tace kai haba maman Abba ina ruwana da zancen mutane idan zan tafi gidan harka irin wanan duk abinda wani zai fada ya je yai ta fadi ina ruwan ta ita. Aiko mun baje sai hiran rayuwa ake don tana jin dadin zuwa suna hira da Umma ko yaushe. Mukaji dirin mota har Umma na cewa ga babana nan yadawo gida. Sai mukaji an tsaya daga waje ana nocking din kofan shigowa daga falon mu. Haka ya tabbatar muna da cewa baki ne a tafe a lokacin sallaman da akayi ne tare da nocking a lokaci guda yasa muka gane mace ce take sallaman. Kusan amsa sallaman mukayi gaba dayan mu nida yar sokoto da Umma a lokaci daya. Fara ce ba doguwa can ba, shekarun ta ya dan kora kadan tana da alaman sakin fuska a tare da ita. Tufafin jikin ta kawai zai sa mutum ya fahinci ba karamar mace bace ita bin mu take da kallo daya bayan daya cikin son ta tantance gaskiyan abinda ya kawo ta gare mu. A bayan ta wasu mata ne dogaye baka da fara suna take mata baya sannu da zuwa Umma take masu a cikin fara,a ita da yar sokoto, sai dai ni ina bin su da kallo kamar ina nazarin su. Zama sukayi sai cikin yaren su na yan Niger dayan ke fadin wai kuwa gidan ne nan kuwa ita fa bata ga alaman abin kwarai ba anan. Daga inda nake zaune hannaye na a hade guri daya wanda ban san lokacin dana rufe su ba ina murzawa nake fadin. Ai kyawon guri bashi ne nuna sa,an guri ba don haka idan zatayi abinda ya kawo ta tsaya tayi. Nace cikin yaren zabarma wai ita yanzu tana nufi ra biyo Anarba ne zuwa karban taimako ko dai ta biyo ta taji abinda za, afada ne kawai. Na juya gurin mai suna ANARBA wace ina ga matan wani ne daga wani guri nace mata kina tafe da makiyiyar ki ne don mahaifan ki na a hannun su ita da uwar ta . Da Mamaki suke kallona suna cewa wai dama na iya zabarmarci ne haka ko yaya na basu amma da cewa yare guda gudane bana ji a rayuwan. Sam hamshakiyar bata yarda da magana ta ba sai dana fara bata labari ina fada mata duk yadda akayi ta auri mijin ta da sukayi auren gida dashi. Kallon mamaki take min tace yaya akayi nasan da zancen nan nace nasan har abinda bata sani ba akan zancen. Tiryan tiryan nai mata bayani yadda akayi auren ta da mijin ta da kuma irin gwagwamayar da yafaru a tsakanin yan uwasu a lokacin. Na nuna mata wanan ta farko tare da sake maimaita mata cewa maitat su na hannun kakansu Dijagal itace ta saka a daure maki mahaifan ki bazaki taba haihuwa da HAMMA MANDE ba. Don basu son hada zuria da jiniku sai irin nasu yan zabarma yar may kwairi kwarara. Kuka ne ya subbace wa matar a cikin damuwa take kuka tana sharan hawaye take fadin dama ita tasan yan uwanta basu son zaman ta da mijin ta don tafito daga tsatson mahaifinta da basu so a cikin ta. Bukatan ganin ta nayi ita kadai don haka kowa ta barni dagani sai ita a falon wanda hakan bai ma yan uwan ta dadi ba don basu so haka ba a ransu. Na fada duk yadda matsalolinta suke da hanyan da za, a magance su cikin sauki take matar ta riko min hannu tana fadin idan Allah ya nufe ta ta samu haihuwai tayi min alkawarin abubuwa da dama a rayuwanta nace a, a basai kin min komai ba bani da dogon gurin rayuwa akan alamurana. Ina dai taimakawa wanda Allah yabani ikon taimakawa ne a duk lokacin da hakan ya taso . Nace sun fada min wata mai iska ce ta turo su gurina tun daga yaimai na kasar Niger matan da ta turo su tafada masu ikokaina ne kawai zasu iya warware kullin da akai mata. Dalilin da yasa ke nan suka nemi da ai masu kwatancen ida nake iskan matar yai masu shine suka shigo daga Niger don su ganeni idan gaskiya akefa a kaina. Da zata zo ne sai tsohuwar gidan dake zaman kakan su ita da mijinta ta hada ta da wata daga cikin jikokin ta don tai mata rahoton abinda duk ya wakana tsakani na da ANARBA din . Gashi daga zuwan su na fara fasa masu kwai duk da sun san cewa za, a iya aikata abindana fadi din ga yadda yan uwa suka saka ta a gaba don matsalan rashin haihuwan da basu samu ba da maigidan nata. To amma kuma tsohuwar kakan su tasan duk inda matsalan nasu yake tayi hakane don ta aura mai daga cikin jikokin ta da take son ya aura daga jinin ta. Hankalin Anarba yai matukar tashi sosai yadda taji bayanin komai ta tausaya wa rayuwan ta da kyat na kwantar mata da hankali ta samu natsuwa a tare da ita. Tace cikin sanyin murya maryama kina ganin guri na zai samu cika nace da ita sanin gaibu sai lillahi yayata amma ki jaraba maganin dana baki nan da wata daya mu gani. A warwaron dake a hannun ta naga tana kokarin cirewa ido kawai na tsura mata sai bayan ta cire ne take cewa tare da miko min tana fadin maryam ki karbi wanan a warwaron bazan fada maki kudin shi ba amma nan gaba zaki sani. Nabaki shi ne a matsayin sadaka tsakanina dake ta bude jakkar ta tafitar da damin kudi masu yawa ta aje a gabana tana fadin. Wanan sako ne daga maigida yace nazo maki dashi sauran bayani idan Allah ya biya muna bukata zaki jimu. Nace kudin nan suyi yawa gaskiya da zaki rage su zanfi jin dadi a rayuwana. Murmushi tayi tace kada kiji komai yar uwa matsayin bukatan mu zai biya zakiga fiye da hakan a rayuwan ki daga gare mu. Tabani matukar tausayi na bita da ido nace da ita kiyi hankali da rayuwan ki koda ace kin haihu bawai zasu daina bibiyan ki bane daga ke har abinda zaki haifa nan gaba. Sai da ta share hawayen daya zubo mata take cewa tasani tasan da hakan a yadda take zama dasu gata marainiya a cikin su. Wani maganin nakara bata na fada mata yadda zatayi amfani dashi take cewa dani nai matukar kwanta mata arai yadda ta dan fahince ni. Nace babu komai Allah dai ya karba muna bukatun mu na alheri tamike tana fadin zasu koma don yau take son komawa Niger Republic din su don akwai taron da zata halarta a gobe insha Allahu. Take cewa da motan gidan gwanatin wani gwauna na kasan nan suka zo nan ida nake ga kwatancen da akai masu ne yakawo su inda nake. Munyi sallama dasu suka tafi inda taba anty hauwa da yar sokoto da Umma alheri mai yawa saida suka kadu. Bayan tafiyan su ne yar sokoto ke fadin ikon Allah, yanzu muma alherin ki maman Abba yana shafuwan mu. Yanzu sam na daina jin komai idan nai wani abinda ya shafi aiki wanan yana nuna alamane na cigaban alamarina da nake ciki. Gashi wani lokaci zan iya ganin mutanen nawa cikin siffa na yan adam wanda ba mafalki ko wani imagination nake ganin su ba. Zan zauna dasu muyi hira sosai bana jin tsoro kamar farko don ancire min tsoronsu a raina. Ga kudi na shigo min ta yadda ma ban taba tsanmani ba haka yasa na hada kudin makka wa mahaifina da nake son ya sauke farali a bana. Naso na biya su tafi da Umma sai dai hakan bai samu ba don wasu yan dalili da aka samu. ***** ********* ****** Ogan su babban Abba ya samu matsala dashi da wasu manyan su har ake ganin case din zai ya jawo masu adakatar dasu daga aikin su. Ganin yadda hankalin duk yan office din nasu ya tashi yasa baban Abba ya tausaya masu don duk suna acikin tashin hankali saboda shugaban nasu yana matukar taimaka masu sosai. Bai fada min ba sai nice a kafadawa kamar a mafalki naga damuwan dake damun su a office din su. Yana zaune ya tasa abinci a gaba ga Umma dake mai hira ta cika shi da zancen kanin ta da take son wai ya taimaka mashi. Yara kowa na harkan gaban shi hasken wutan lantarkin da ya haske falon namu zai iya nuna yanayin da kowan mu yake ciki a falon. Ban san yaya akayi ba nake cewa dashi amma da Oga zai amince ya datse Jibrin hassan akan maganan nan inaga zai samu mafita akai don daga gare shi matsalan take. Wani irin kallo ya watso min mai nuna mamaki ko tuhuma akaina na yaya akayi nasan da wani zance can. Nace eh Jibrin Hassan shike son yi maku zagon kasa bayan shine ya tura ogan ya aikata hakan kuma takardan da kuke nema da zai yi depend di ku yana gurin shi kai tsaye Oga zaice dashi ya bashi takardan daya dauka ranan hudu ga watan shidda a table dinshi daya shigs sallah zakuga yadda zai kadu kuma zai fito da takardan ba bata lokaci. Maryam are sure da maganan ki don wanan fa ba karamin magana bace. Nace nasan da hakan shiyasa nake son kai ka fada mai idan ma har baka fada mai bani zan fada mashi tunda naga yana da tausayi mutumin. Kara kallona yayi nace ina son hakan yafito daga gurin kane kawai don aikin kane kuma alherin hakan akan zaifi amfani. Shiru yayi kamar bai dauki maganan da muhinman ci ba a ranshi sai dai can kasan zuciya shi juyayin maganan nawa yakeyi yadda har nasan haka akan su. Washegari da zaifita na sake maimaita mai abinda na fada mai daren jiya din. Umma tace kai kayi abinda akace dakai kawai ban son abinda zai jawo matsala daga baya. Dariya umma ta bashi ganin yadda tai believe akan alamarin iskokai na haka. Ya isa office ke nan ya nayin da yaga mutanen office din nasu yasa yasan da magana yau a office din nasu. Ashe sun samu labarin manyan su zasu shigo bincike ne akan zancen takardan daya batan. Zancen mu ne ya fado mai aran shi yaga kawai ya kundunbalan yin wanan kasada ya fadi yadda nace dashi. Saidai idan kuma hakan baiyuyuba fa zata matukar kwabe dashi sosai don Jibrin din yana gaba dashi. Mikewa yayi don baida zabi ya fada office din shugaban yana zaune a cikin damu shi kadai a office din. Bayan sun gaisa ne yake mamaki shigowan shi direct haks don ba kasafai kananan ma,aikata ke shigowa gurinbshi ba anyhow. Yace og dama wani magana ne nazo dashi kozamu samu mafita akan wanan matsalan. Ina jinka Mr Aliyu Ogan ya fada cikin damu nan dai ya fada mai kamar yadda na fada mai din. Yace tare da shafo kansa yana cire hulan aikinsu dake kan shi yake cewa. Mr Aliyu ina wanan zamcen yafito haka bayan shi kan shi Jibrin din case din ta shafe shi sosai. Yace Oga kadai gwada mugani kawai zan maka bayani daga baya yadda case din yake. Oga dai baida zabi don haka Aliyu yana fita yakira Jibrin din yashigo cikin rashin damuwa da komai don yasan babu wanda yasan komai akan abinda ya aikata masu. Yazauna suka gaisa Oga yake cewa Mr Jibrin may yasa zakai ma rayuwan mu haka please ? Ina son ka kawo min takarda da ka dauka anan gurin nan dai yai mai bayanin komai kamar yadda akace dashi. Kan shi ya dukar kasa batare da yasan hakan mazai faru dashi ba kaman an matsi bakin shi yace Iam sorry sir sherin shedan ne kawai yasa nai hakana. Yace dauko min takardan baki alaikum na tura masu kafin su taso daga Abuja. Ba musu kamar ana izashi yafita bai dauki wasu awani ba ya dawo da takardu kamar yadda suke aje a gurinshi yamika mai. Bayan ya duba yaga komai intact yadda ya kamata ya sauke wani gwaron ajiyan zuciya a fili yace you can go. Yafice jiki ba karfi yana fita yaji kamar wani abu yafice mai akai yace a ranshi how comes har yai saurin yin confessing da sauri haka bayan saura kiris yacin ma gurin shi akai. Fitan Jibrin yasa oga ya kira wasu manya da abin ya shafa ya mika masu takardan sai mamaki da murna sukeyi kowa ya zama free ke nan akan takardan. Basu bats lokaci ba suka tura takardan can headquarter su komai ya shiga kamar yadda ya dace akan su. Sai da komai ya kammala ne oga ya nemi baban Abba a motar shi suka fice daga ma,aikatan nasu sundayi tafiya mai nisa yace. Mr Aliyu da farko zan fara cewa Alhamdullahi don komai ya tafi daidai har an kammala komai yadda ya dace ya kawo min takardan kamar yadda ka fada min. To amma abinda nake son sani shine yaya akayi kasan da hakan kao don Allah kada ka boye min komai please ? Aliyi bai boye mai komai ba yace sir mamatace keda matsala irin na jinnu da suka shafe ta itace jiya kawai ban fada mata komai ba wallahi take fada min hakan. Cikin mamaki yace matarka fa yanzu mace ce ta fitar dani daga wanan kangin balain dana shiga wanda zai iya jefani cikin rasa aikina gaba daya. Nan dai Aliyu yake fada mai duk irin halin da muke ciki da yadda al, amarin yafara yi min. Yace ikon Allah yanzu ashe muna da irin giftedness dinan acikin gida jen mu bamu sani ba haka. Yace dama shi baiwa na Ubangiji akwaishi a cikin aluman mu sai dai mutane basu ganewa da irin su ne Allah yakan boye su daga aluma don gudun cutuwa a garesu. Kagan ni nan nasan akwai jinnu a duniya dake shafuwan yan adam suna taimakawa bayin Allah irin haka saidai akwai da yawa da bana gaskiya ba daga cikin su. Irin hakane turawa suka fi mu don su da a kasan turai kuke da yanzu goverment din su sun dauke ta don amfanin su. Amma mu kaga anan sai a barsu a haka da tarin baiwan su sai dai wanda Allah yanufa da ya more daga garesu ne kawai Allah zaiba ikon ganin su. Yanzun haka ni kaina ina da yarinyar da take fama da irin wanan laluran a gida na sun hana ta aure don ko zancen aure bats so ayi mata. Zan samu lokaci muzo hargida da Iyalina don mu yi godiya ga matar taka sannan zakaji ni insha Allahu. Don Allah ka rike wanan sirin a tsakanin mu don ko shi jibrin bazan kara cewa dashi uffan ba amma daga satin nan isha Allahu zai bar nan . Kafara yi min godiya gurin ita mai dakin naks kafin muzo insha Allahu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 3⃣0⃣ Yanayin da ya shigo gida a cikin fara, a yasa na fahinci akwai nasara a tare dashi don na dade rabon da nagan shi a cikin farin ciki irin haka a cikin irin wanan yanayi. Ranan har yara sun sheda yana tare da farin ciki don ya shigo masu gida da abin tabawa. Sai murna sukeyi jin hayaniyan su ne yasa Umma fitowa daga dakin ta ta samay shi a tsakiyan su zaune yana bare masu chukulet din wa Nusaiba. Cikin murmushi da jin dadin ganin yanayin danta da jikokin ta ta zauna tana cewa a, a Nusaiba yau alawa aka samu najiki shiru ? Yace Umma kin fito ai na dauka barci kike da bangan ki ba a falo ? Tace ina ciki ina lazumi ne bayan na idar da sallah. Sun gaisa hankalin shi yana ga yara da suka samu kulawan shi yau shidai Abba da ba sabawa yayi da halin shi ba dawo yayi inda nake ya manne min ajikina tare da mika min nashi wai na bude mai. Bayan na bude mai yaron yamiko min wai na diba nima naci na girgiza mai kai kawai nace ci abinka abba nagode Allah yai maku albarka. Jin haka yasa Aisha dawo da gudun ta inda nake itama tana miko min ta wai nasa mata albarka. Nace sha abinki Aisha Allah yai maku albarka nima babana zai sayo min mai dadi wanda yafi naku. Tana jin haka tace wallahi mummy sai kin sha kada babakin ya kawo maki naki ki hana min. Na karba na dan gutsura kadan nace mata na gode nace wai amma akwai dadi shima Abba yana ganin haka yace sai nasha nashi dole na dan gutsura na mika mashi. Muryan shi naji yama cewa Nusaiba ke kai wa mummy tasha naki kada ta hana maki na baban ta. Sai taki don akwaita da shegen rowa Umma tace o bazaki bayar danaki ba ko to maryam kada ki bata naki idan an kawo maki ke ma. Can naji Umma tana cewa dashi yaya zancen naku akwai nasara a cikin sa ko har yanzu ba aikai iyaka ba ? Jin haka yasa na kasa kunne a gare shi don naji mai zaice gamay da zancen nasu. Yace bari Umma ai alamarin wanan yanzu tsoro yake bani maryam anya kuwa nan gaba ko ruwa nasha a waje bazaki gane su ga hanji na ba kuwa ? Umma tace ga tsiya abin ya koma mata maita ke nan kake nufi ko may ? Yace abin nata ne akwai abin alajabi sosai a cikin sa wallahi nan dai ya kwashe duk abinda ya faru daya fita yake fada muna. Nace ai Jibrin bazai dawo ba don kunya bai bari ya kara zama a cikin ku kuma. Nace ina gani ma nan bada dadewa ba kamar za, a watsa kune fa. Dasauri ya dago ya tsura min ido nace haka ne zai faru amma aiko ka tafi controler bazai bari ka tafi ba. Yace waye controler kuma nace Ogan naku mana shine zai zama Control wani sati da yardan Allah. Kaima sai nake ga kamar zaka samu dan sauyi sai dai matsalan takardunka ne zai kawo tsaiko kawai. Mamaki yayi yace kai maryam na barki inda na ganki don ba maryam dina bace wanan gaskiya ya fadi a cikin zolaya. Nan dai mukai ta hira akan irin aikin su na rashin imanin da basu dashi wanda yake jawo masu matsala a karshen rayuwan su wani sai kaga bai gamawa da duniya lafiya. Umma tace shine fa dalilin da mahaifinki lokacin da ya samu aikin nan yake ce min da zai samu wani da yafi wanan aikin da yafi. Nace baba ai ba karamin masani bane shima zaman kauye ne kawai ke cuta mai ba, a sanin ire iren su sunan da yawa. Maryam ina kika san haka ni zan fada maki akan wanan mijin ki din da kike gani irin taimakon da malam yai muna aiba kadan bane har Allah yasa na samu yakai haka. Sai dana hafa har tara suna macewa shine nan Allah ya bar min dataimakon Allah dana mahaifinnki . Murmushi kawai nayi Aliyu ya mike ta shiga daga ciki bai dade da shiga ba naji muryan shi yana kirana daga ciki. Ina shiga abin mamaki mutum da muke kamar baisan daraja na ba shine wai yau ya rugumoni zuwa jikin shi. Nokewa nayi ina fadin maye haka kuma yau yace ke tsiyanki ke nan wallahi da an dan taba ki yanzu ki kawo wani zance. Nidai Allah ma ya cece ni kada su rabani dake su ce maki kuma ina wari nan gaba. Dariya maganan shi yabani nace kai wani sabon sheri ke nan kuma da zasu rabani dakai ai da tuni sun rabaka dani tun lokacin da kake kwana gurin hanna. Yace kai akwaiki da tashin tashin may kuma ya kawo zance wata Hanna can ni nama manta yaushe rabona da ganin ta wallahi. Nace idan ba ta ai akwai wasu sabbin don ba fasawa za, ayi ba tunda kasawa rayuwan ka irin hakan. Yace da ke nan idan ma ina yi aida kin gani kun fada ni ai na rufawa kaina asiri da tonon sila da ake min bibiya akai. Nace dadai yafi ma alheri da wanan mugun rayuwan na alfasha murmushi kawai yayi yace wai ke su mutanen naki sune suka dakatar dake ne fa haihuwa haka komay ? Naga da can baki ma yayewa sai da ciki amma yanzu ga Nusaiba har tana batun shiga na ukku amma shiru ? Dariya maganan shi yabani don yaushe rabo danaji wani dadadan kalami haka daga gare shi. Maza ke nan ba kunya garesu ba su ko kadan idan idon su yarufe kai da banza daya idan ya bude kuma ace da kai akeyi. Nace nidai gani ka kirani bakace komai ba sai wani zance kakeyi haihuwa nice zanba kaina ko Allah zai bani idan yaso ni da hakan ? Aini na dauka ma baka damu ba wa yan nan sun isheka kawai da muka samu da kai ? Kai kajiki da wani zance ina bahaushe dan musulmai zance zuria sun isheni nace a zasu isheka dani mana sai sabuwa tazo ta haifa ma wasu kuma. Baiyi magana ba sai ma kamoni da yayi zuwa jikin shi ya shiga shafa na kamar yau ya fara sani na haka yasa na dakatar dashi nace. Amma kasan yaran basuyi barci ba dai ko zasu iya shigo muna daki fa. Yace bake kika saba masu da hakan ba ko ina nan zasu iya shigowa kai tsaye nace kadai fadi sai dai ban ki ba in Nusaiba amma bada sauran ba. Sai da yagama abinda yakeyi ba kunya yabarbi da jin nauyin Umma yai wankan shi ya fita daga gidan kafin magariba. Nan ya fice ya barni ina najin nauyi da kunyan Umma haka dai na tsarkake jikina na fito falo naci gaba da aiyuka na. Sai bayan ishai ne muna zaune da yaran Umma tafito daga dakin su tana cewa maryam dama ina son nai maki magana. Nace Umma ni tace eh maryam ba wani abubane dama zance dake ne don Allah kiyi ta hakkuri da mijinki Maryam shi kadai Allah ya barmin nake gani nake jin dadi sai kuma yaran nan da Allah ya baku nake kara jin dadi a rayuwana. Maryam ko bayan raina banyar da Babana ya kara wani aure ba a rayuwan shi muddin kuna raye. Don baki rage ni da komai ba aduniyan nan na fada mashi kin min abinda ko nice na haife ki ya tsaya nan hakana. Don Allah maryam kiyi hakkuri da mijin ki duk wanan halinda yake na rudin duniya nasan zai daina insha Allahu. Nace cikin murmushi Umma ai baban Abba yayana ne ni ban damu da abinda yake muna ba don kanshi yakewa don duk abinda yake min yana gani kamar yaran nan basu da wayyo wallahi sun san komai. Don haka ni ban sa zancen shi a raina ba balle har abin ya damay ni a raina. Harkan gabana ma kawai ya isheni yanzu ban zancen komai ni a raina. Tace nasan da haka amma dai kiyi hakkuri maryam ki dinga saka shi a hanya koda ba zai yi amfani da maganan ki ba dole dai wata rana yayi da wani. Nace insha Allahu Umma na gode bazaki taba samuna da abin asha ba a rayuwana ba. ****** ********* ****** Yau kwana uku da zancen gurin aikin su bayan yafita daga gida ranan kuma ba fita aiki can sai gashi ya shigo duk a gidimay yake. Yana cewa maryam muna da baki fa ga Ogan nan zasu shigo da iyalin shi yanzu yake min waya. Bai gama magana ba mukaji horn a kofan gida alaman sun iso ko ke nan yanuna don horn din da akayi a kofan mu. Dadtijone kamili dashi daganin shi ba mai son hayaniya bane sosai don yanayin shi ya nuna tafe suke shi da matar shi da yaran su uku. Mun gaisa dasu a cikin mutunci ban zauna saman kujera ba ina zube a kasan ties din falon. Sunji dadin wanan girman dana basu sosai har cikin ran su yace wanan ce malaman ya tambaya ? Aliyu da duk ya kasa zaune a kasa tsaye yau ga sugaba da kan shi a gidan shi saboda dalilina. Yace itace sir ikon Allah yace tare da nuna yar shi dake a zaune wacce nake gani da alama ita ce babba a cikin su. Ogan yace nai farin ciki haduwa da wanan family din a rayuwa na da fatan Allah yasa mu kasance da junan mu a cikin amana. Yace diya ta nazo da iyalina gareku ne don na mika godiyana akan taimakon da Allah ya nufa kikai min. Don badon Allah ya kado ki cikin alamarin ba da bamu san iya iyakar inda abin zai tsaya ba. Murmushi nayi tare da dukar da kaina kasa cikin kunya yace na zone da kaina muyi maki godiya har gida abisa amin cewan maigidan ki don sai da yardan shi zan shigo har cikin iyalin shi. Nan dai yake mika godiya ga taimakon da akai mashi shida sauran abokan aikin shi. Hannu naji na dan fara murzawa a lokacin da yake maganan sai hamma ya biyo baya again. Gurin da yarsu ke zaune na juya nace mama hajo tare ake dake ashe anan kika zauna kuma ? Matar Ogan tai dariya tace ai ba sunan ta hajo ba Amina take. Umma tace Umm, Umm kyale ta ba ita bace akwai abinda tagani tare da ita tunda kikaji sun fadi hakan. Ikon Allah inji matar ta mayar da hankalinta a gare mu sosai daga ita har kowa dake falon. Nace mama hajo uwar ruwa in babu ke babu ruwa inda ke ruwa ya gyaru. Sai wacce suka kira da Amina din ta fara hamma ita ma sannu a hankali kamar yadda nayi zamowa tayi kasa kamar yadda nake zaune muna kallon junan mu. Nace ba, asan ki da barna ba kamar Inna doguwa inna uwar manya, inna uwa maba da mama wanda baida uwa yazo ga Inna. Tace hakane ni da ina banbancin mu kadan ne don ni bani zama jikin mai muni kuma bani zama ajikin kazami sai wanda ya amsa sunan shi gurin kyawo. Kadai kai nayi nace hakane mama amma yau sai gaki gaban malam Alhaji musulmi mai aikin musulunci bani baiyana sai inda yadace. Tace nasani malam nakuma yi mamaki ganin ka a cikin wanan karamin gidan. Muryan mu duk ya canza daji kasan na larabawane ko wani jinsi na wata nahiyar. Nace shi musulmi ko kin manta duk daya suke a gurin Allah mahaliccin mu ? Ai damu da karami duk daya muke ga Allah don Allah ne kadai yasan wanda yafi wani a gare shi. Tace hakane malam nace kin fadi gsskiya yanzu may kike nema a jikin wanan boyar Allah dakike wahalwa haka. Wani irin gyatsa tayi mai karfi kamar wacce ta koshi tace malam Amina godiya tace ban son naga wani bil, adam ya rabe ta ko kadan. Shiyasa ko yaushe nake nisanta ta da kowa sai wa yan nan marikan nata kawai kosu don suna matukar son tane na barsu da ita da tuni nagama dasu. Nace amma kin san kin shiga hakki ko hakkin daba naki ba kina cutawa boyar Allah. Tace na sani malam amma Amina tana da abubuwan da nake son hutawa a cikin sa. Nace tun ysushe kike tare da ita tace malam tun tana yar shekara biyu da rabi. Ina matukar son mace mai yawan gashi kasani kamar yadda nake baka da gashi har baya haka nake matukar sha,awan mace mai gashi sosai. Iyayyen ta sun kasance masu gyara mata kai akoda yaushe suna barin kan asake yadda jama, a zasu gani su yaba wa kwalliyan ta. Nikuma a irin gurin nake samu ina shigewa a jikin mace ya zama gurin hutawa na. Ina matukar son yaron da ake barin kansa a sake ko yaushe wanda ake yawan gyarawa a ko wani lokaci. Kai ba yaro ba ma koda babbace idan tana barin kan ta a bude zan shiga na yi yadda nake so a raina don nan ne gurin hutawa na. Zan iya hana mace aure idan makinyi sa, a kinyi aure zan iya hanaki jin dadin duniya watau haihuwa. Idan ma kina haihuwan zan iya hana diyan zama a duniya ta hanya fito maki ta wani siffa cikin mafalki na kashe yaron. Subbahanallahi ke kuwa musulmace hajo ? Tace malam aika sani ko ta gurin sunana dakaji hajon ni sunana hajjo ruwa. Murmushi nayi nace nasani amma a ruwa aka sanki ba zama a jikin mutane ba irin haka. Tace malam ke nan amma aikasan ni a gurin keta ko ? Haka kawai idan naga mace mai yawan sake jikin ta zanji na shiga jikin ta na dinga cutawa rayuwan ta kawai. Wani lokaci zamu jona dani da karuwa kasanta gurin keta itama sai mu dinga saka mace tana abubuwan shedana don a zage ta kawai. Muna yawan yin hakane ga yan mata masu sha, awan sake tsiraicin su ga wasu mazaje da sunan kwalliya kawai. Amma mace mai yawan ibada bamuga guri ba ma balle mu zauna da ita don kariyan da takewa jikin ta. Abinda bamu so shine mace mai yawa saka lalle ajikin ta don bama son warin shi. Warin lalai yana matukar cutawa jinnu sosai munyi arziki matan yanzu basu son amfani da lalai wanan ne yasa muke matukar samun sauki gurin shige masu. Da ace suna saka lalle koda a yatsun hannuwan su ne baza mu samu kafan shiga jikin su ba haka. Amma yanzu Allah kadai yasan yawan matan da muke zama a jikin su wanda su basu sani ba muna matukar cuta masu don sun bar suna mai karfi da aka umurce su dayi. Wanan hakana ne amma da ku shige su aida kun sanar dasu gurin matsa masu su dinga yin abinda addini ya koya masu ba na nasara mai jan kunne ba. Tace malam munyi kuskure anan gaskiya amma muna matukar jin dadin zaman ajikin su dan yazamo muna gurin hutun mu. Nace yanzu naji wanan zaki bar jikin Aminatu ta samu ta sarara a rayuwan ta ko kuwa bazaki fita ba ? Dukar da kai tayi kasa can ta dago tana hawaye tace malam idan kace nafita zan fita amma da sharadi. Nace muna jinki sharadin may kike son saka mata kuma ? Tace malam sai tayi alkawarin bazata dinga zama kanta a sake ba koda ko agida take. Sai kuma idan zata fita ta tabbatar da jikin ta yana a rufe ko yaushe a cikin mutunci saboda mun saba zama a jikin ta mina jin dadin yadda take bamu mmasauki a jikin nata. Idan ta daina zaku barta har abada kunyi alkawarin hakan tare da ku dake da yaran ki da sauran yan uwan ki ? Tace malam munyi amma aisu bil, adam kamar sune suke kiran mu yanzu a jikin su don basu tsare rayulan su daga ire iren mu jinnu masu sha, awan su. Shiya kaga matan su sunfi kowa samun wanan matsalar a rayuwan su don irin yadda suke kasan cewa a yanzu babu kimtsi sam a tare dasu yadda ya dace da dan musulmi. Mama hajjo baki ganin wanan zamani ne yakawoo masu hakan ? Maimakon kukan da takeyi sai ta koma dariya tace ai zamanin muke bi muna aiwatar da shirin mu gare su. Malam wani lokaci fa har da kazama muna shiga don wanan doyin dake fita daga jikin su muna matukar jin dadin shi sosai. Zakaga mace kazama ce amma muna tare da ita muna morewa don karuwan mu gare ta. Yanzu ina son daga nan ki bar jikin boyar Allah nan har abada kada ki sake shiga jikin ta idan ba haka ba zan kona ki ko na daure ki. Ta dukar da kanta kasa tace malam mun san zaka iya muna fiye da hakan ma don haka zamu barta har abada. Ko yanzun ma da mun san nan za, a zo da ita da ban tsaya har ka ganni ba don ai an kaita gurin masu magani da dama amma sai mu shiga mu bata maganin ko mu halaka mai maganin gaba daya kowa ma ya huta. Nace to ina son don Allah ku fita daga yau kubar jikin ta ba sai mun hadu da ku ba. Tace an gama malam amma tai min wani abu daya a rayuwan ta don taci gaba da zama lafiya. Shine duk ranan jumma, a ya kasance ta daan yi sadaka da abinda ya sauwaka a gareta. Ba wai duk ranan jumma, a ba a, a idan dai ta samu halin yin haka zaifiye ma rayuwan ta alheri sosai. Kasan yanzu biladam su watsar da taimako kansu kawai suka sani bayan kuma Allah ya hore ma wasu sun su abinda zasu iya bayawar ga mabukatan su. Yace to ki fita daga jikin ta kuma har abada tace angama malam insha Allahu. Daga haka tai wani dunkulewa guri daya tare da murdewa kamar cikin ta yana ciwo tana sake wani irin atishawa mai karifi da sauri nace wa uwar ta dake gefe tajaye tabasu hanya su wuce. Sai gata ta mike kwance tana mayar da numfashi wani iri kamar zata shude ranta zasu taba ta nace su barta akwai saura. Nace baku san hajjo ruwa ba ko ita wata aljannace da ke zama a cikin ruwa tana da matukar kyaun sura tana da gashi har bayan ta mai yawa. Bata faye baiyyana ba sai tayi barna sosai a jikin mutum kafin agane cewa itace tare da mutum don ba kasafai take baiyana ba. Acikin yan adam wanda duk tafitowa asuran ta mutun kan kasance kamar ya haukace don siffan ta akwai kyau akwai kuma ban tsoro sosai da ita. ( Don haka kalubali gare mu mata mu kula da kawunan mu akan abinda bamu gani kuma bamu san dasu ba a tare damu ) Ban dade ba bayan tafiyan ta na juya kan mahaifinsu nace Malam Iliyasu kana wa iyalinka sakaci kaida matarka. Gashi kai mutum ne mara rigima amma hakan yasa har kake sakacin kyale iyalinka gurin yin yadda sukaga dama ga rayuwan su. Kai kanka kana da sakaci gurin saurin amincewa dana tare da kai. Aikin ka ba na saurin aminta bane gama yanzu da wani nauyin zai kara karuwa a kan ka. Sai dai don Allah kamar yadda kake sa tausayi ga dukiyan bayin Allah ayi kokarin ganin a kara tausayawa wanda baida laifi gurin neman nakansa. Aiku yana da matukar hatsari sosai shiyasa akasarin ku suke karewa a nakashe don yawan yasin din damasu haki ke ja maku. Duk da wasu mutanen suna da laifi gurin shigo maku da haramttatun kayan da ba, a son amfani dashi to amma adinga dubaiyya da yakamata. Duk wanda aka hada da Allah baiyi ba sai ubangiji ya jarabe shi da cuta mai tsanani a rayuwan shi idan kunne yaji jiki ya tsira ni zan koma na barku lafiya. Daga haka na dukar da kaina kasa sai wani irin atishawa mai karfi adaidai lokacin da Amina itama ta mike zaune ta dan dube duben gefenta ganin ta da tayi a kasa zube. Nan dai suka fara muna sannu Umma ce ta mike tashiga kitchen sai gata da roba dauke a hannun ta ta dauko goran ruwa takawo min. Nawanke fuska na nasha nace mika hannu da sauri Aliyu ya dauko min hantiti na na shaka sai na sauke wani numfashi da karfi nabi lafiyan kujeran dake kusa dani na yadda kaina a sama. Ikin Allah hajiya kinji magana kamar ta almara yanzu mu ina muka san da aanan bayani badon Allah yai sanadin haduwan mu da mutanen nan ba. Da haka uwata zatai ta zama da mugun abu ajikin ta basun mafarin sa ba mu. Dama na dade ina hasashen cewa suke bata maganin da muke mata da anfara magani sai abu ya lalace kamar an tayar dashi ne. Umma takada baki tace ai mafi yawan matsalan nan mune ke jawa kan mu to abinda baka gani kuma bakasan dasu ba. Gashi dai dole kuma ayi rayuwan ba fasawa za, ayi ba tunda mata muke. Oga yace amma hajuya sai ayi ahi a cikin kima tunda kinji abinda suka fadi mai kazantar ma ba barinta zasu yi ba. Sun dauki lokaci tare damu har yake tambaya ina aikine umma tace a, a sana, a nakeyi. Yace ikon Allah banyi karatu mai zurfi bane Aliyu yace mai ina da NCE danayi tun kafin muyi aure. Yace gaskiya dole a duba kuma ya kamata na koma makaranta ai hakana tunda ma ina da takarda na. Umma tace kuma Alhaji ayi hakan yace shi karatun yana da amfanine ba wai sai lalai mace tayi aiki ba don kinga tana sana, a akwai inda karatun zai taimaka mata ne ai. Munyi sallama dasu suka fice suna godiya muka rakasu har gurin motar su hajiya tace na bata nombana tana bukata. Bayan kwana biyu ta bugo min waya tana cewa wallahi sunga haske sosai yanzu akan yarsu don duk halaiyarta na da yanzu ta daina. Nace hajiya sai a fake dokokin da suka aza maku akanta don samun lafiyan ta tace insha Allahu. Tace tana bukatan watarana na kawo masu ziyara naga mazaunin su suma nace zan fadawa maigidan idan ya yarda. Har zan katse kiran takecewa dani wai ba ance kina sana, a ba nacs eh hakanane hajiya. Tace why not ki hada kudi akwai kayan da akai Options din su daga gurin su maigida zaki samu sosai a garesu. Nace mama idan nai haka ban sabawa Allah ba kuwa ? Dariya magana na yabata tace tayaya zaki sabawa Allah ba saye kikayi ba aiba cin hanci aka baki ba. Idan ma baki saye ba wasu ne zasu saya kuma su sayar dashi da kudi mai yawa. Nace to zan duba nagani idan sayen ba matsala muka kashe wayan tabarni ina nazari a raina. Assalamu Alaikum yan uwa dafatan munyi jumma lafiya. Ina mai baku hakkuri don yanzu bazaku dinga jini ba kamar kullun saboda yau insha Allahu zan fara novel dina na kudi mai so tana iya yin register don jin labarin sadaukar da rayuwa ga jajartun mata masu imani a zukatan su. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BANE A, , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 3⃣1⃣ . Ni kadai nake ta faman nazarin zancen da mukayi da hajiya Binta a raina na kasa kuma fitar da zancen a cikin zuciyana. Saboda ina ganin kudin dake gareni ina zai isheni sayen kayan contener dungurun gun. Gashi kuma ko baban Abba na kasa fadawa wanan maganan sai cina yake a raina saboda ina gudun yai min masifa akai. Don abune wanda ya shafi bangaren aikin shi sosai bazan so na ja matsala ga inda yake samu ba. Sannu a hankali na fara koyon mota wanda yar sokoto ce ke koya min tukin wani lokaci kuma baban Abba da kan shi zai fita dani ya koya min. Yau sati daya cif da case din mu da diyar Ogan su Baban Abba da keda lalurar aljanne a kanta da mukai artabu wanda hajjo ruwa take zama a jikin ta na tsawon shekaru. Kitchen nake ina aiki da safe yayin da wayana dake aje a falo yake ta faman ringing shikadai. Sai da kiran ya kusa tsinkewa ne na iso gurin da sauri na daga wayan. Bakuwar Nomba ce ake kirana dashi daga kasan waje nombar yanuna min daga kasan Chaina ne. Nace a fili ina daukan wayan chaina kuma ina dagawa murya ce na mace ke magana dani a layin tana fadin. Yau maryama dama na kiraki ne na fada maki yau zamu dawo da dare insha Allahu don haka nasan sai cikin dare zamu iso gari don jirgin yamma zamu biyo. Ina son ki gyara gida ki muna abinci don kin san yaran ki suna matukar son cin girkin ki. Mamaki ne fal a zuciyana don ban san dawa nake magana ba a lokacin gashi dai maishi tana min magana akan tasan ni kuma a tare muke. Don Allah maryam duk da ban sanki da kazanta ba ina son ki gyara ko ina don ba dadi kai tafiya na tsawon lokaci kadawo ka samu gida ba tsabta haka baida dadi ga macen kwarai. Lokacin da nake ni kadai a gida bana tafiya ban tsabtace gidana ba yanzu ko kin sa damu da kune a gidan. Gabana ya fadi take Mukkadarasiyatu ta fado min a rai na nace kardai ace da ita nake wayan nan kenan. Watau shirun da naji bana mafalkinta kwana biyu tayi tafiya ke nan basu gidan ? Muryan tane yadawo dani daga tunanen dana keyi tana cewa nagode sai mun iso zuwa dare insha Allahu. Nace kamar nafahinta Allah ya kawo ku lafiya Allah ya tsare hanya yasa ku samay mu lafiya ta amsa da Amin yar uwa mai albarka nagode nagode. Ina kashe wayan nakai zaune guri daya hankalina a tashe na dafe gefen huskana da hannu na daya ina fadi a raina. Yau ni na shiga ukku ni maryama abin nawa ba wani sauki sai kara ci gaba da al, amarin yakeyi ma yanzu. Yau har takai ina waya da mutanen boye kai tsaye ba wani shamaki ko dar a tare da ni. Na jima a gurin na mike ina fadi a fili zama ai bai ganni ba ni maryam ko banza kyaun alkawari cikawa. Daki na koma da saurina na shiga shiri ina dakin ne ina faman tunane mutumiyata yar sokoto ta fado min a rai nace ita zan laluba naji a raina don munfi balain shakuwa sosai da ita. Ban kaiga idar da abinda nakeyi bane naji wayan nawa yana ringing da sauri na fito zuwa falon na dauka a zatona ko itace ta kara kira na sai naga ba ita bace a layin. Baban Abba ne yake kirana da sauri na daga kiran nashi da sallama muryan shi a cikin yanayin farin ciki yake magana. Maryam lalai ke yar halas ce wallahi wai kin san may har na kasa bari na dawo gida nai maki albishi nace a, a cikin girgiza kai kaman yana a gabana. Yace wallahi yanzu takarda ya samu Oga an mayar dashi controler na costom baki daya na Nigeria. Nima murna nayi sosai nace masha Allahu kai ashe abin farin ciki ya samay mu baki daya yace wallahi maryam. Yace waiko kin san jiya fa yai min magana a kanki yace yana son ki fadada kasuwancin ki zasu taimaka maki a baki daga cikin kayan da akai Option dinsu ki sara ke ma ki samu. Amma wai na tambaye ki wani kike bukata daga cikin kayan sai na manta zancen faduwan Aisha yasa na manta da komai ban fada maki ba. Mun dan dauki lokaci a wayan muna magana dashi yana min bayanin yadda abin yake yadai ce na bari sai ya dawo gida zai karasa yi min bayanin komai. Har zamu kashe na marairaice nace dama yanzu nake son kiranka don Allah zan dan fita na shiga kasuwa ne. Yace may kuma zaki sawo maryam kin san fa kudi ya kamata yanzu ki hada wanda zakiyi business don kin kusa zama big hajiya. Nace ba kaya zan saro ba kayan abinci nake son sayowa kawai. Da mamaki yace kayan abinci har yaushe na sayo komai a gidan nace ba wanan ba baban Abba baki zanyi shiyasa nake son sayowa. Dan shiru yayi yana mamakina yace baki daga ina kuma maryam nace daga waje . Ikon Allah yace to adawo lafiya ai zaki iya fara driving da kanki ko sai ki fita da motar ki ? Nace tare da yar sokoto zamu fita yace hakan yana da kyau sosai sai kun dawo. Ban san Umma tafito ba tana tsaye take cewa baki zakiyi yau gidan maryam ? Najuya ina murmushi nace eh Umma yau masu gidan zasu dawo daga tafiya shine zan girka masu abinci. Masu gida ta tambaya cikin mamaki ? Ban bata wani dogon amsa ba don nasan ba ganewa zatayi bana dai ce eh afili kawai. Nai mata sai na dawo ina sauri sai gidan yar sokoto nai mata bayani kasuwa zata rakani mu sayo kayan abinci zanyi baki ne. Bata bata lokaci ba muka fice daga easthe din mu sai kasuwa tafini sanin kayan fita kunya don haka itace ta dinga zaba nawa biyane kawai. Mun dawo gida a gajiye da kayan mu niki niki har cooler manya guda biyu na fita kunyan baki saida na sayo muna. Mun dan huta yar sokoto ta leka gidan ta bata dauki lokaci ba tadawo tare da anty hauwa muka fara aiki sosai. Abinci mukayi naji da gani kamar zamu tari wani gwauna sai yamma lis muka gama komai mun zuba a cikin manyan kuloli na alfarma sai kuma na shiga aikin gyara guri. Na sayo kayan kamshi masu kyau da kamshi har sabbin labule saida na saka ko ina gidan ya koma neat dashi. Sai tambaya suke wai wasu irin bakine zasu zo haka maman Abba wana gyara haka kamar shugaban kasa zaizo. Amsa daya nake basu shine baku sannu ba amma sunan tafe munyi waya dasu. Baban Abba yana shigowa gidan yaga yadda guri ya juye mai gwanin ban sha, awa ga kulolin tap da abinci masu dadi anjera na abinci sai plates kusan ashirin da dan kai ajere abin sha ba adadi. Yake cewa rangas yau wasu irin bakine haka zamuyi maryam amsa dana ba Umma nabashi shima. Masu gida ya tambaya da mamaki nace mashi eh kai kawai ya kada min batare da yai wani magana ba don ya fahinci da mutane na nake nufi. To amma ta yaya zasuyi suci wanan abincin dana girka haka agidan yace zamu gani ai yau gamu gasu. Har dare su yar sokoto ana lekowa ko zasu ga bakin sunzo su lakaci arziki amma shiru sai hiran mukeyi. Takasa kannewa tace amma dai bakin sun fasa zuwa ne ko aiko da wanan aikin da mukasha ko basu zo ba da sun biya mu wahalan mu. Nace sai dare zasu iso don jirgin dare ne zai sauke su sukace komai dare zasu zo ai. Karfe tara da rabi na tura yara suka kwanta har Umma ranan nace da ita don Allah ina son a kwanta da wuri don akwai baki a gidan. Kallon mara hankaline suka fara yi min don abina ya zarce na mai hankali. Goma da rabi gaba dayan mu sai wani irin mugun barci muke ji kowa ya shiga shirin kwanciya ba baki na babu dalilin su na gyara ko ina na falon tas baban Abba shine ya kashe wuta ko ina ya kulle gida don ni barci nakeji sosai saboda aikin da muka sha da rana duk nagaji. Can cikin dare kamar a mafalki nake jin hayaniyan mutane kamar gidan duk ya cika da suratan mutane amma kuma na kasa tashi kamar an daure ni sai na fara jin motsin plates ana cin abinci ga kamshi dadi ya gauraye gidan. Da safe baban Abba da ya rufe gida yana min dariyan keta a ranshi na babu wanda zai zo nayi barnan abinci saboda haukana. Ai zaiga yadda zanyi da wanan tulin abincin dana girka haka mai uban yawa, ya kulla a ranshi sai yai min sheri sosai da safe. Sai dai may yasan dai shine ya rufe gidan da hannun shi kuma anan yabar komai dana girka amma yana fitowa zuwa sallah sai yaga wayau babu kulolin babu dalin su a falon. Juyawa yayi zuwa kitchen do yaga kona fito da dare na kwashe su ne sai ya samu gasu aje anci komai naciki ga gorunan drinks nan ansha an aje su a gefe daya. Ikon Allah yace yaushe yai barci haka har baki suka shigo gidan bai sani ba har akai wanan didiman duk yana barci. Kai amma dai ba mutane kadan bane sukai wanan hidimar haka mai yawa ikon Allah. Ko da yadawo daga sallah ina zaune saman salaya na ina addua yashigo yana zama yake cewa maryam ashe bakin naki sunzo ne daren jiya ban sani ba ina barci ? Nace ai na fada ma daga tafiya zasu dawo sun iso ke nan ashe ya juyo da mamaki yana kallo na yake cewa ke baki masan sun iso ba ke nan nace barci nayi mai nauyi wallahi amma dai sai naji kamar a mafalki sun shigo da dare. Allah ya kyauta yace ya koma ya kwanta don ranan sati ne ba aiki nima haka yasa a inda nake zaune nakai kwance saman sallaya na. Sai barci ina cikin barci nagan ta wai tashigo tana murmushi a fuskan ta ta zauna a bakin mirro na tana ce min yaya bayan rabo? Na amsa da lafiya lau anty yaya hanya yaya yan uwa tace alhamdullahi mun ma zo dasu baba sunzo suga gida su koma don yafi gane ma zaman su can yanzu. Nace Allah sarki ashe hardasu baba akazo tace eh ai yana godiyan girkin da akai masu sosai naji matukar dadi maryam yadda kika karama mu nagode hakika ke yar uwace tagari abin alfahari ga wanda ya samay ki. Halinki na alheri yasa nake kara son al,amarinki a raina Allah yai muna jagora ga alamarorin mu nace amin anty. Ta mike tana cewa ga tsaraban ki nan dana yara sai dai naga makwabtan ki sun tayaki aiki ga nasu sakon nan a dan karamin leda kiyi min godiya a furin su. Nace mun gode Anty Allah ya bamu hakkurin zama a tsakanin mu daku tace tama bamu sai dai ya kara muna maryama. Zamu dauki lokaci mai dan tsawo da iyayyen mu gidan nan kafin su koma koda yake ma ba wai zama zasuyi ba na dindindin don zasu dan zagaya dangin mu a cikin kasan nan da fatan zamu samu halarci a gurin ki sai kin kara jina yaran ki suna gaida ke sunji dadin girki ki wallahi. Daga haka tafice daga dakin ban dauki lokaci mai tsawo ba kukan Nusaiba ya tayar dani naje na mike ne nai karo da wanan jakar kayan data kawo min a mafalkin da nake ganin nayi. Da mamaki nabi jakar ina kallon ikon Allah don nasan koda nai sallah babu shi a gurin. Ga yar leda datace sakon su yar sokoto a gefen namu ledan daganin shi na kasan wajw ne bana kasan mu ba. A hankali na mike na nufi gurin da nake jin kukan Nusaiba a dakin su Umma na samu Umma tana lalashin ta nake tambayan ts may yasa may tane? Umma take cewa wai ta na barci taga ta tashi tana kuka haka a raina nasan aikin yaran boye ne sune sukai mata wani abin. Amma ai idan da alkawari babu cutarwa a tsakanin mu dasu don may zasu saka min yarinya kuka. Kamar a mafalki nake jin kukan yaro a back yard din mu sai lokacin na juya banga Aisha ba a makwancin ta nace ina Aisha ta tafi kuma da safen nan. Fita nayi falo da sauri bata ciki kofan back yard din mu na nufa yana abude koda na leka tana tsugune tana wasa harda dariyan ta. Nace ke Aisha da safen nan kike wasa ke kadai a cikin sanyi bakya gudun mura ya kama ki ne ? Tace mummy kiga yaron nan maman shi ta dake shi wai ya taka Nusaiba bai sani ba tana barci. Nace Allah sarki don Allah anty kiyi hakkuri tunda bai sani ba ya take ta harkan yara ne kawai. Ina magana kamar ina ganin ta a lokavcin nace wa Aisha tashigo ta saka rigan sanyi a jikin ta don ban da ikon hana ta wasa naja mata matsala koni kaina. Kitchen na shiga bayan nagama shirya Aisha cikin rigar sanyi tafice da gudun ta. Abin karyawa na hada muna sai na gyara gidan ko ina tsab dashi harda back yard din duk da baiyi wani datti ba amma sai da nai mashi kwal na shiga nai wanka na shirya. Suna falo a zaune na jawo jakar kayan tsaraban da aka kawo muna idon Umma akan kayan har na iso inda suke na fara bude jakkan. Dogayen riguna ne irin na matan larabawa masu matukar tsada da kyau kala biyar, sai kayan yara kowani na daga size din su mun fahinci mai shi. Na baban Abba mai matukar kyau da laushi irin kayan yan Pakistan din na ne yasamu har kalla uku. Sai na Umma dogon riga itama ga atamfofi na waje manyan super dake cikin kayan desgn masu kyau letes. Ban bude na su yar sokoto ba sai nakai masu zamu gani mamaki ne fal a zukatan kowan mu sai dai cikin karfin hali suke fadin mun gode Allah ya saka da alherin sa. Mun gama gani na saka hijjab dina sai gidan su yar sokoto ina fita ne daga gidan Umma tace wanan alamarin haka kamar a mafalki ban taba sanin ana haka ba arayuwa da labarin hakan aka bani sai nace labari ne kawai ba gaskiya ba ne. Yace Umma alamarin sai dai ayi shiru kawai don abin sai gaba yake mata ni yau din nan a cikin mamakin ikon Allah nake a gidan nan. Nifa na rufe gida da kaina ban kuma ga wani bakon da yashigo gidan nan ba amma wai wanan abincin alfarman da ta dafa jiya koda gari zai waye ba abinci ba kula agurin dana barsu. Da ace ba, a gaban idona ne haka ya faru ba koda rantsuwa ne zan iya yi nace ba gaskiya bane wanan zancen. Ni kan ina isa na samay su a waje zaune kofan gidan anty hauwa suna hira muka gaisa dasu nai masu ban gajiyan aikin jiya. Bamu kai ga karasa gaisuwan mu ba yar sokoto ke fadin jiya muna tajiran muji baki sun iso muzo mugaida su sai mukaji shiru. Ledan hannuna na mika masu nace ga tsaraban ku sunce a baki ikon Allah harda tsaraba muka samu ashe sun zo din kuwa ? Nace sun dawo jiya cikin dare wanan akace na baku suna kokarin bude ledan riguna ne dogaye masu laushi da kyau sai turare kwali biyu a ciki. Murna sukayi sosai tare da nuna farin cikin su akan kaya cikin zakuwa Anty hauwa ke fadin wata mata ce tai muna wanan kyautan haka maman Abba ? Anty mukaddarasiya ce abokiyar zamana da muke zama a gida daya sunyi tafiya shine suka dawo daga tafiya jiya. Kallon kallo sukeyi wa junan su ga kayan sai wani irin kamshi ke tashi a cikin sa. Wai ban gane ba maman Abba kina nufin cewa mutanen ki ne dama bakin naki da mukai wa aiki jiya na bata amsa a takaice da sune. Mun shiga uku mun lalace don girman Allah da gaskiya kike zancen nan mama Abba ? Nace ga zahiri kin gani ni nayi tafiya ne balle na samo maku wanan tsaraba mai tsada ko makka naje ina zan iya sayo maku wanan rigunan haka ? Aiko boni yaci mu inji anty hauwa kada fa su san damu ? Murmushi maganan ta yasani nace tun yaushe anty hauwa mutanen da muke zaune tare dasu koda yaushe. Da firgice tafara dan dube duben gefen ta kamar tana neman wani abu da ya bace mata . Nace ni a ina na samay su ba a nan din ba don dai ban dasu da farko anan muka hadu dasu. Mun shiga uku wai da gaskiya kike fadi maman Abba nace to anty ina wasa dake anty wallahi gaskiya nake fada maki. Don Allah kuke ganin mu bamu fanin ku kutaimaka muna kada ku taba mu mun kuma gode da sakon ku Allah ya saka maku da alheri. Mun dayi hira dasu amma a tsorace suke sosai sai da na kwantar masu da hankali suka samu natsuwa. ****** ********* ****** Motoci ne har guda hudu dirka dirka dasu suka shigo easthe din mu su yar sokoto suna waje suna hira da maigidan ta suka bi motocin da kallo. Maigidan ta ke cewa wa yan nan dagani daga wani gidan gwaunati suka fito don wanan motan bana kananan mutane bane. Ba su tsaya ba sai a kofan gidan mu nan aka shiga bude motocin ana fitowa da sauri security ne ke wanan aikin. Bayan wata mota daga ciki aka bude yayin da wata farar mace tafito daga cikin motar tana gyara lafayan dake jikin ta. Sai da taima easthe din kallon kyawo tafara dan takawa zuwa matakalan hawa gidan na mu. Yayin da wata mace yar sanda take nocking din kofan na mu duk su yar sokoto suna kallon su daga inda suke a zaune da mijin ta. Ina falo zaune tare da Umma naji kwankwasa kofan namike ina fadin waye kuma ke nocking din kofan. Bakin fuska nagani a daidai lokacin da nake kokarin bude kofan hakan yasa na gane munyi baki ke nan a gidan. Cikin hausan yare yar sanda ke min magana muna neman hajiya maryam anan gidan take don Allah ? Nace eh anan take sannun ku da zuwa tace ok ki fada mata her excerllency zata shigo gurin ta yanzu. Nace ki fada mata excerllency ana mata sannu da zuwa ta dan kalle ni da mamaki kamar zatai magana sai kuma ta juya da sauri cikin zafin nama irin nasu na yan kaki. Ko second ba ayi ba sai gasu sun shigo tare da yar sanda tana take mata baya. Ba laifi don matar abin kallo ne sosai saboda kyauwon ta ta hadu sosai dagani kuma naira ya samu gurin zama. Sannu da zuwa nai masu tare da nuna masu gurin zama don su zauna ba musu ta zauna yar sandan tana tsaye a bayan ta. Tace maryam muke nema don Allah ko anan take da zama muna son magana da ita ne ? Nace cikin murmushi hajiya kina magana da maryam ne yanzun haka a gaban ki. Tace tare da dan kara min kallo to ikon Allah don Allah sorry fa na dauka zan ganki wata babban mace ce wallahi. Nace ba damuwa ai rashin sani ne yakawo hakan don baki san ni ba ne ai. Tariza ki bamu guri please ta umurci yar sandan da haka don tafice zatayi siri ke nan. Yar sandar ta juya bayan ta sara mata ta fice daga gidan ba bata lokaci bisa umurnin da aka bata. Matar ta juyo gare ni tace nasan baki sanni ba amma sako ne na kawo maki, , , kafin tace wani abu nace daga guri Adisatu ko ? Kallon mamaki ne tai min tace ta fada maki zanzo ne dama ? Nace ban ma da contact din ta kawai dai nagani ne ta turo ki ki min albishir da bukata ya biya ko ? Sai kuma ke da kikazo da matsalan ki gamay da maigidan ki da baki gane komai akan shi yadda kike so ? Tace subbahanallahi haka ne ikon Allah a ranta tace nako zo karshw a rayuwana ashe don bankada. Nace amma hajiya ya kamata ki godewa Allah da baiwa da niiman dayai maki a rayuwan ki. Kin fi kowa sanin kina samu sosai a gurin shi amma hakan bai maki ba hajiya? Kada ki manta da nauyin alumman dake a kan shi shi kadai idan bai sauke wanan nauyin ba gobe lahira shi Allah zai tambaya shi kadai. Kina ganin duk tarin dukiyan dake gaban ki bazasu isheki rayuwa har jikokin su samu a ciki ba ? Zan cen dakin yusuf yakamata kizo min dashi kafin akawo maki shi kasan nan a daure ba wanan zancen ba. Ku dinga tuna ranan gobe kiyama da Allah zai tsayar daku kan irin mulkin da kukaiwa alummanku . Tace nagode maryam da wanan fadakarwan dakikai min nace ki gode ma Allah daya saka maki fahinta na. Tace naji kin min zancen dana Yusuf ga maganan ki wanda zancen ya daure min kai sosai ban fahinta ba gaskiya ? Zakicce min baki san halin da yake ciki ba acan inda kuka turashi karatu ko may ? Wallahi ban sani ba maryam wani hali Abban baba yake ciki nace bazan fada maki ba amma idan da hali ki shirya kikai mai ziyara na bazata duk abinda idon ki ya gane maki zaki iya dawowa nan mu san abin yi. Hankalin ta yai matukar tashi amma duk yadda taso na fada mata ban fada mata komai ba sai ta gano wa idon ta kafin musan abinyi akai. Jakar hannun ta ta bude tafito min da kudi a daure masu yawa tace wanan sako ne daga gurin Adisatu tace na kawo maki don halin da take ciki ba dama tabaro Niger tazo Nigeria yanzu. Na kalli kudin dake tare agabana masu matukar yawa nace da ita kudin sunyi yawa ki raba biyu ki mayar mata da sauran ace mata muna godiya gareta. Allah ubangiji ya raba su lafiya yabamu mai albarka. Tace ai bamu kyauta mu mayar wanan rabonki ne Allah ya tsaga daga gare ta don haka ki rike naki ne nima ganawa akara taciro daurin yan dubu har uku ta aje min saman table din falon. Nace hajiya kudin nan sunyi yawa matuka da ku rage yawan su kawai albarkan aiki yafi yawan ladan shi ai. Tace nasan da hakan amma na hango nasarori mai tarin yawa a zamana dake wanan ba komai bane idan har bukata zai biya ? Nagode nace mata tare da fadin idan kin tafi ki fada ma Adisatu cewa ta dan rage yawan fita koda yaushe ta dan zauna har cikin ta yakai wata hudu tafara fita idan zata iya. Insha Allahu zataji zan fada mata ai mun gode don Adisatu tana a cikin wani hali na tsangwaman yan uwan mijin ta sosai wallahi. Zasu daina don zasu sota yanzun haka ma wasun su sun fara daina hattaran ta sosai. Allah yasa hakan wallahi don tana matukar bani tausayi sosai irin yadda suke nuna mata banbanci a cikin su. Insha Allahu har kakan nasu zakusha mamaki sosai akan ta bari cikun nan ya baiyyana kawai. Ta dai ja bakin ta yi shiru sai idan angane shi kawai a jikin ta komai zai fara baiyyana. Muna gamawa tai min sallama suka fice a gidan tausayi tai matukar bani sosai don dan ta yana cikin mugun rayuwa a kasan turai amma ita tana ganin yana can yana karatu ne. Bata san cewa yana can yana hole rayuwan shi da irin makuddan kudin da suke tura mashi daga nan kasan. Kudin nake kallo a gabana dole nai saurin kwashesu kada wani ya fado gidan yagane su a haka . Ban dade da kaisu daki ba sai ga yar sokoto tashigo tana fadin maman Abba ashe baki mukayi haka yau masu fada aji na kasan. Ai na taso nazo security suka tare ni a waje wai ba zan shigo ba ciki her excerllency tana ganawa dake. Ki ce min abin har ya kai ga zuwan excerllencys gidan yanzu baki ga yadda suka taso min ba kamar zasu cinye ni danya gani dama da tsoron bindiga atare dani na juya da sauri nabar gurin kada su halakani ga banza. Mun jima muna hiran wata makwabciyar mu Ibo da muka samu a cikin easthe din mu mai daukan kai bata gaida ko idan taga mutum. Nace yanzu ke ina ruwan ki da ita bako addinin ku daya ba bakuma kabilan ku daya ba da ita. Duk hiran da mukeyi sai yanzu hankalina yakawo kan bangus watau awarwaron da Adisatu ta taba bani a baya. Bayan fitan ta gidan namike na nufi daki na bude gurin dana boye shi yana nan gurin a ajiye kamar yadda na boye shi. Namayar daniyar zai kan shi kasuwa a auna min gram din shi don naji kudin shi. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 3⃣2⃣ Hajiya tana barin gidan mu da komawan ta gida abu ya dinga damuwanta a zuciyar ta yadda zata gaskan ta zancen da na fada mata. Amna wanan karamar yarinyar ne za,ace tabawa Adisatu magani kuma ya karbu anyi nasara akai . Ta girgiza kanta tana cewa ina wanan ma ai shirmay ne kawai amma akwai dai kawai dai lokacin samu ne yayi mata. Da dare bayan ta dawo gida tana kwance saman dofon kujera duk gaban jikin ta ciwo yake mata don dan tafiyan da tayi na ranan. Maigidan nata ya shigo falon yana saye a cikin dogon riga ta maza irin na zama a gida da manya ke amfani dashi a gida. Idanuwan shi a kan ta ya zauna a cikin murmushi yana fadin duk gajiyan tafiyan ne kamar wacce tai tafiya mai nisa haka ? Tace bari kaidai his excerllancy tafiyan ne sai bayan nayi ta ne na raina kaina don wallahi baka ga yarinya karama da na samu ba agidan wai itace mai bada taimakon da ake fadi. Wai may yasa mutane suka baci da karaya ne yanzu saboda son kudi kawai sai kaga murane wai harda yara kanana a cikin wanan harkan ta bada magani. Don kawai ido ya rufe da son kudin kota halin kaka sai dai kowa yayi kudi a duniyan nan. Kai in banda abinki ai kudi abin so ne ga kowa ko da kike cikin wanan daulan bakiki ki kara samun wasu kudin ba fiye da haka. Yanzu fa jira kike na sa maki hannu ku fara shirin ku na wayar wa mata kai akan tsarin iyali wanda ba karamin kudi ne za, a kashe ba a hakan. Tace kai gaba yallabai ta nan kuma ka biyo min watau kowa dai baki kudi ba ke nan ? Yace ai na kanta take nema ko ba biyoki tayi ba har gida ke ce kika kai kanki gare ta ai. Tace ni saboda Adisatu na tafi ba wai kaina nakai ba amma sai gashi kawai don hali irin na masu magani ta jefo min maganan Abba a bakin ta. Da sauri ya dago yana kallon ta a cikun mamaki yace zancen Abba kuma tace may akai ? Dariya tayi har da dan kyalkyatawa ta mike zaune tana fadin waini zata mayar doll don an fada mata kila ina da da Abba shine wai nayi saurin taimaka ma rayuwan shi don yana a cikin wani hali kafin akawo muna shi kasan nan a daure. Subbahanallahi wa, iyazu billahi ita matar ce ta fadi haka akan Abba din a ina tasan Abba din wai ? Kin taba sanin tane ke yake kokarin tambaya don kalamin bai mashi dadi ba don shine dan su namiji babba yanzu da suke gani. Matar tace cikin rashin kulawa kaima kasan ai zamanin median din nan komai mutane suna dashi akan gidajen wasu don barnan sunan su kawai. Yace look wanan maganan ba maganan wasa bane koda kuwa karya ne takeyi akai mu yakamata muyi duba sosai cikin al, amarin don mu fahinci gaskiyan zancen. Amma ke sai naga a matsayinki na uwa a gareshi kuma kece aka fadawa wanan zancen sai naga kamar zancen bai damay ki ba ke ? Tace haba yallabai urin burgan aikin nan ne fa kawai tunda tace Abba sai na dauki abin serious na hau na zauna na dinga mata barin kudi akai. Look ki fada min exactly yadda kukayi da wanan matan dan kamay kamay tafara yi bata son ta fada mai komai duka haka dai tai mai bayani ya fahinci lalai fa akwai matsala duk yadda akayi tunda sunan yaron yafito daga bakin mai maganin. Yace dole ne muyi yadda aka fada muna muyi don tsira da mutuncin mu da rayuwan yaron nan saboda nan gaba. Tace sai naga kamar ka dauki zancen da karfi kai har cikin ran ka ? Yace haka kawai naji maganan ya tsaya min a zuciyana don haka zan sa ai min wani abu akai mu gani. Daga haka ya mike zuciyar shi duk a jagule ya bar falon zuwa dakin kwanan shi yana jin kan shi a cikin wani irin yanayi. ****** ********* ****** Sosai naji dadi da na samun wayan hajiya balaraba yusuf matan sabon controler na custom na kasa tana nema na a gidan ta. Ban tsaya wani tsaiko ba nake cewa da baban Abba don Allah ya bari na tafi na amsa gaiyyatar ta. Yace idan ma zaki tafi ne tare da ni zaki tafi nima nai masu murna idan mun tafi din.. Don haka washe gari muka shirya har Umma da yara zamu tafi, kamar an jefo min mutumiyata yar sokoto a gidan. Ganin muna shiri take cewa yau kuma sai ina haka nace zamu gidan Ogan su baban Abba ne muyi mashi murna an bashi controller nasu na custom tace ai nima baza a barni ba dani za, a tafi gaskiya. Ina dariya nace ai sai ki shirya mu tafi, bata dauki lokaci ba sai gata ta dawo a cikin shirin ta muka kama hanya. Nice ke jan mota muna zaune da baban Abba a gaba yar sokoto da Umma da yara suna baya a zaune. Da kwatancen da yake muna ne muka isa gidan a GRA katon gida ne irin na manyan kusan gwaunati. Gidan ya matukar tsaruwa gurin tsari sosai don babu ne babu a gidan zamu shiga muka hade da Amina tafito saye da hijjab din ta mai hannu da alama fita zatayi a lokacin. Tana ganin mu ta sheda mu ta dan saki murmushi a fuskan ta na jin dadin ganin mu. Mun gaisa da ita a cikin mutunci take cewa ashe kuna tafe amma mama bata sani ba don tafita sai dai ba dadewa zatayi ba bissimillah ku shigo mana. Tajuya muka bi bayanta zuwa cikin gidan nasu wani katon falo muka zauna har ita ta ciro wayan ta daga cikin jakjar ta tana neman layin mahaifiyan ta. Sunyi magana take fada mata tana da baki a gida uwar ke tambayan ta ko su waye ? Tace mama matar nan da kuka kaini gurin ta ne na easthe din nan . Tace ace gata tafi wata mace Aminan ta kira daga cikin gida tazo ta kawo muna abin sha. Ba,a dauki lokaci ba uwan ta shigo gidan da alaman dama ba nisa ta tafi ba daga gidan. Mun gaisa tana jin dadi tace kai amma baku kyauta min ba da baku sanar dani yau zaku shigo ba ai da mun dan hada maku abin taron baki. Nace aiko haka ma mun gode take cewa maigidan ranan yai tafiya ya tafi yin reporting gurin aikin shi. Tace ita ma tafita ne zuwa gurin masu shirya masu bukin da za, ayi na taya maigidan murna. Nace mama da fatan ba wani shagali zaku shirya wanda zai jawo magana ba akai ? Tace to kin san yanzu haka akeyi da zaran ka dan samu abin farin ciki sai ka gaiyaci yan uwa da abokan arziki sun taya ka farin ciki. Nace hakane kuma fa mutane suna son abin da za, ai bida,a sosai yanzu, wanda basu ganewa ne a haka shedanu ke samun dama shiga mutane har suyi barna ba, asani ba. Wata kila ga mai bukin ko wani wanda ya halarci bukin nashi ya samay shi a lokacin. Don fa duk abinda zamuyi bamu kadai bane ke gudanar dashi a gurin dole ne sai an samu kasancewa jinsi daban daban wanda ba lalai bane mu gane hakan mu. Kai maryam har kin sa jikina yai sanyi wallahi nace hakan ne ke kasan cewa yadda alumma suka kasance ne yakawo hakan ai. Yanzu yaya za, ayi ke nan shiyasa fa dama na bukaci na ganki kafin hakan ya kasance, musanman ma akan ita wanan din kada wani abu kuma ya skasance da ita. Don yanzu gaskiya alhamdullahi ta samu lafiya sosai a wannan lokaci gashi kina ganin ta takoma kamar ba umma da muka sani ba abaya. Muna gidan baban Abba yake cewa zai tafi ya dawo sai ya dauke mu nan muka zauna dasu cikin jin dadi zakace ko mun saba da dewa dasu ne. Hira muke sosai dasu cikin jin dadin yadda muka samu karbuwa a gidan don maman bata da girman kai ko kadan. Umma na kula da yau taji dadin fitowan mu daga gida kodan yadda taga an tare mune a gidan oho ? Nan hajiyan ta ke be dani don wani muhinmin maganan da take son yi dani. Wanda ba komai bane illa akan zancen maigidan ta ne dakuma yaran su wanda yanzu shine matsalan mutane da yafi damun su. Mun tatauna da ita sosai daga karshe ne take tambaya na wai may yasa bana son zancen sayen kwantainan da tai min ne ? Cikin murmushi nace ba hakana bane mama kawai dai don naga kamar banda zarahin hakan ne sai nake ganin yafi karfina. Idan banda abinki maryam dama ai sai wani ya dafa wani yake tashi ai haka duniya ya gada don haka kada kiji komai please ? Akwai guda biyar da aka ware min don haka sai na baki daya ko biyu daga ciki kema ki more na kan ki. Nace wai mama dayan ma na samu na hada dai mu gani tace a cikin sauki ne fa muke samun shi muma mu karu. To amma mama sai nake ganin kamar haka ai cin amana ne ga bayin Allah. Dariya zance na yabata take cewa ba haka abin yake ba ai maryam mutane ne da sun riga da sun ginu amma basu bin ka,idan da gwaunati ta shimfida masu gudun kada a tuhumay sune yake sa su watsar da kayan subar wa yan custom shi a gurin su. Nace insha Allahu satin nan zan hada kudin dake gurina zaki jini da yardan ubangiji tace toke fa maryam ai a haka kike ganin mata na tashi yanzu. Akwai na atamfofi da takalma da kayan yara wani kike so ne daga ciki su ? Nace sai naga kamar atamfan da kayan yaran zaifi saurin karbuwa ko don su nake business din su dama . Tace da kyau yanzu yadda za, ayi zan hada maki dana takalma sai mu raba ayi maki cumbunation din su ina ga zai fi ki gwada kawai ki gani zasu karbu don kayan suna da matukar kyau sosai . Nace mama na gode Allah yasa mu dace tace amin ya ta haka nake son ji daga gare ki. Na rasa may zan maki a rayuwa da zamu saka maki akan alherin da muka samu daga gurin ki idan maigidan ya dawo zan mashi bayani nasan zai taimaka maki sosai shima. Sai bayan munyi sallah azahar yazo daukan mu mun sha kyauta sosai na alfarma a gurin ta daga ni har yara umma da yar sokoto kyautan atamfane yan super masu kyau da tsada naga inda karyan business din mata yake a gurin ta namu ashe dan mali ne. Yar sokoto tace tabbas zama na dake maryam alheri ne babba ga rayuwana zanin da nake bin baba Iman ya sayo min fiye da shekara gashi Allah ya bani har biyu a lokaci daya. ****** ********* ****** Mijin ne yake cewa da ita ta shirya zasu tafi waje amma bata taba kawo cewa gurin dan su zasu tafi ba alokacin saida suka biya kasashe biyu yaga likitan shi suka wuce inda dan nasu yake karatun shi na likita. Tun isan su kasan ne take kirsn layin dan nata ta sanar dashi zuwan su amma wayan nashi a kashe yake. Haka yasa suka kama hanya zuwa gidan akai tsaye tun da suka shigo layin kida ke tashi gidan sai haske disco light ke tashi a cikin sa. Suna karasawa maza da mata ne matasa zakace a tsirara suke sai masha,an su sukeyi sam basu damu da ganin su ba da sukayi. Nan hankalin hajiya ya fara tashi dirct dakin sama suka hau inda dakin shi yake. Yana kwance tare da yan mata uku suna ta aikata mashaa a dakin suna ganin su bai sa sunji ko gezau ba a jikin su har shi yaron nasu. Ga kayan maye a ko ina dakin abin ba, a cewa komai uban ya nufe shi yadago shi duk da yana a cikin maye bai hanashi sheda mahaifin nashi ba. Amma abu ga wanda yai nisa sai ya fara cewa daddy you are welcome enjoy your self please ? Tas tas ya fara kwasanshi da mari sai da ya gigice a gurin zai kara kai mari karo na uku ne Abba shima ya dunkule hannayen shi kamar zai rama lokacin mahaifiyan ta shigo dakin tana gani tace kada ka soma Abba. Ya dago kai yana kallon ta lokacin yan matan dake kokarin mikewa wata baka daga cikin ukun take cewa don may za, a bata masu jin dadin su haka ? Abban ya fada gado daga baya gashi tsirara yana cewa o shirt cikin dafe kan shi sai barci. Kuka uwar ta sake don magana ya zama gaskiya ashe abinda yarinyar nan tagani ke nan take nufi da zancen ta. Juyawa mahaufin yayi ya fita zuwa falo inda kida ke tashi sun kai wa makwabta ko ina ya kashe kidan tare da daka masu tsawa sufice mai daga gida. Daya bayan daya suke ficewa da bakar magana a bakin su na an katse masu jin dadin su da sukeyi. Ranan haka suka kwana a zaune babu wanda ya uya runtsawa a cikin su don takaici. Abban bai farfado ba don mugun mayen da yayi sai bayan an kwana a wuni likitan da aka kira ya duba shi yake ce masu drugs ya kusa yiwa lafiyan shi illa sosai. Gashi anbinkota makarantan da yake karatu sunce ya daina zuwa ma yin karatun kusan wata hudu ke nan. Maigidan yace kinga irin haukan ki ko ? Mata ta fada maki abinda ake ciki amma kike ganin abin hannun ki take son ci an fada maki irin mutanen nan ana watsi da baiwan da Allah yai masu ne ? Komai da zasu bar kasan da yaron sun kammala shi tare dashi suka dawo gida Nigeria don basu iya barin shi kasan ba. Kowa yagan shi yasan yaga dan maye ba wanda ya tafi karatu ba don babu kimtsi ko ga irin shigan shi. Sai bayan sati daya da dawowan su ne mahaifin ke tambayan ta inda matar nan take yana son ganawa da ita. A lokacin ne ta tuna mun yi musayan lamban waya da ita shine tabayarbwa maigidan nata. Ina zaune a falo tare da kowa na gidan muna hira a falo wayana yai ringin na dauka bakon nombane nagani ake kirana dashi. Ban ki dauka ba na daga wayan muryan namiji ne naji yana min sallama gashi layin special nombane irin ta manya. Na dauka muka gaisa yake cewa bayan mun gaisa din kina magana ne da gwauna jaha kaza. Na kalli wayan cikin mamaki kamar mai maganan yana a gabana a lokacin. Yake cewa idan babu damuwa don Allah ina son muyi magana dake ce ta fahinta akan matsalan yaron da kika fadawa matana. Cikin mamaki nace ina ga bani bace gaskiya murmushi naji yayi yace don Alkah ki saki jikin ki ba wani matsala bane ai. Dama zancen da kika fada ne ya zama gaskiya shine nake son muyi magana akai don yanzun haka yaron yana nan kasan mun dawo tare dashi. Sai dai yana cikin wani yanayi na bukatan taimako ne shine dalilin da yasa na kiraki yanzu. Kin san ba girma na bane a ga nazo gurin ki kai tsaye sabo da tsara gashi kuma ko banza ke din matar aure ce. Don haka ina son jin yadda zaayi mu gana dake idan ba damu zanso satin nan ki shigo garin mu gana . Nace ga maigidana zaku iya magana dashi duk abinda yace shike nan na mikawa baban Abba din wayan dake rike a hannu na yana tambayan wane a layin. Amsa yabashi da fadin shi gwaunan jaha kazane matsalan dan shi ne yataso yake son ya taimaka mai yaga matar shi don kila akwai mafita a gurin ta. Baban Abba ya aje appointment dashi bayan ya saurari bayanin shi cewa zamu shigo a karshen mako lokacin ba aiki ranan. Haka ya kasan ce muka shirya har yaran da Umma zuwa jahan cikin tanadin da gwaunan yai muna na zuwa ganin su. Ban taba tunanen zan ziyarci wanan jahan ba don banda kowa a can kuma ba wani dalili da zaikai ni. Sai gashi yau a bisa wani dalili mun shigo jahan kuma ta jirgi mukai tafiyan namu. Yadda aka tare mu zakace ko wasu mafada ajine akasan nan din musha taro na mutunci gaskiya. Sai dare muka samu ganawa da wanan iyalin cikin girmamawa sosai da ba sai na fada ba. Daga nan aka fara zance baida wani matsala na iska sai dai miyagun abokan da yake hurda dasu ne kawai suka mayar dashi haka. Nace za, a bashi magani wanda zai daina sha har abada da yardan ubangiji bazai sake ba insha Allahu. Mahaifin yace don Allah na taimaka masu don shine babba a cikin diyan shi ga kuma halin daya fada ciki. Nace sai dai idan har anbashi zai galabaita amma kada su damu zai dawo daidai insha Allahu. Duk yadda suka so yaron yasha maganin yaki a ranan dalilin da yasa ke nan suka kirani a cikin daren. Mun samay su cirko cirko a tsaye yana tsula masu tsiya wai shi ba zaisha maganin hausa ba cikin shi yai tsatsa. Kallo daya nai mashi cikin yanayina daya sauya nace kamar da tsawa karbi kasha shi maza. Ya dago kai da nufin yai min tijara ban san may yagani ba a gare ni ba mussu ya karbi cup din daga gurin uwar shi ya shaye shi tas. Takawa nayi har inda yake a tsaye nace miko min hannun ka nan ba mussu ya miko hannayen nashi gare ni. Kamawa nayi kamar ina fitar mai da wani abu sai wani hayaki yafito daga hannayen shi nan ya kife ya fadi kasa baisan inda yake ba. Nace akama shi akai shi dakin shi zuwa safe zai farfado kuma zasuga sauki gare shi da yardan ubangiji. Godiya suke min sosai kamar ba a kasa garesu nake ba banyi magana ba sai hannu dana daga masu kawai alamam godiya na juya na fice daga falon gidan. Sai bayan na shiga dakin mu ne na saki atishawa wanda ke nuna alaman abinda ya hau kaina ya fice a lokacin. Barci sosai mukayi duk jikina da gabobina suna min ciwo da kyat na falka da safe a hakanan ba dadi. Munso juyowa washe gari amma hakan bai samu gare mu don sun dakatar damu akan mu dan tsaya suga yadda jikin yaron zai kasance mai. Munji dadin bakuntan da muka kai masu sosai don har tataunawa munyi da gwaunan yana bukatan a warware mai wasu yan matsalolin da suka sha mai kai. Ba laifi yasamu nai mashi bayani sosai ya kuma gamsu mun juyo mun dawo kaduna tare da tarin alherin da ban taba tsanmanin samun shi ba daga gare su. Mun samu hartan bukin samun girman shugaba su baban Abba naga karyan naira a gurin kamar ba gobe. ****** ********* ****** Nasha fadawa baban Abba don Allah ya daina yin dare idan ya fita amma sai yake daukan zance na a tsurku ne kawai. Sai yaga dama yake shigowan shi easthe din mu a lokacin da da duk ya bushi iskan hakan . Ranan yakai sha biyu da rabi yabaro gurin aikin su ya nufo gida kai tsaye ba wani damuwa a ran shi. Tun shigowan shi easthe din yaji tsikan jikin shi ya tashi mai sosai amma bai san dalilin hakan ba yana dai tafe gida kai tsaye. Gani yayi kamar gurin ya juye mai a lokaci daya ya hasko hsske fitilan motar shi sai yake ganin kamar yara suna wasan su babu damuwa komai. Mamaki ne sosai ya kamashi ina yara suka fito a cikin daren nan haka kuma baima san su ba a uguwar namu gasu kamar yaran turawa daganin su. Kamar ancd ya daga kan shi sama sai gani yayi kamar mutum zaune ya tokaro har rufin gidan mu zaune da fararen kayan shi yana shan iska abin shi. Take yaji gaban shi ya Fadi tabbasa yau ya shedavda idon shi ba mukadai bane a gidan kamar yadda nakan sha fada mai hakan. Ya isa da sauri yaji duk jikin shi ba dadi ga tsoron da ya mamaye mai zuciyar shi. Da karfi yake bugun kofan gidan a gigice Allah yasa banyi barci ba dama naji dirin motar shi yadawo. Nafito da sauri na bude gidan sai yafado ciki da sauri ya mayar da kofan ya rufe yana fadin wuce da sauri mu shiga please. Ina fadin lafiya bai iya magana ba sai karkarawa yake kamar maijin sanyi a lokacin haka nan ya kwana a firgice kuma ya kasa cewa dani uffan jikin shi yai wani irin mugun zafi radau na rufe shi da bargo amma sai rawan sanyi yake yana sambatu. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU [11/27, 9:32 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 BA MU KADAI BA NE A, , , 👩‍👩‍👧‍👧 👩‍👩‍👧‍👧 3⃣3⃣ SALAMU ALAIKUM YA MASOYA DAFATAN MUN WAYI GARI LAFIYA ALLAH YA SADA MU DA RAHAMOMINSA ALLAHUMA AMEEN. INA MAI KARA SANAR DAKU SABON NOVEL DINA DAKE TAFIYA A GROUP DINA WANDA KEDA MATUKAR AFANI AGARE MU MATA, MAISO ZATA IYA KIRAN LAYINA DON JIN KARIN BAYANI DON BA KOWA ZAI SAMAY SHI BA SAI IDAN KINYI REGISTER 08036959257 SAI NAJI KU, , , Kafin gari ya waye yai matukar wahala sosai koda gari ya waye idan ka ganshi zakace yai wata daya yana ciwo duk ya zabge ga baki daya. Gashi nayi tambayan duniya may ya samay shi ni da Umma amma ba baki sai sauke ajiyan zuciya yakeyi da ya fara dan barci zai zabura ya mike yana leken window kamar yana duban wani abu. Haka yasa hankalin mu yai matukar tashi sosai ga halinda yake ciki don akwai matsala gaskiya. Muna ganin haka nake cewa Umma ya kamata mu tafi asibiti dashi gashi sai rawan sanyi yake rufe a cikin bargo. Shiryawa nayi bayan na daure na hada abin karyawa a gida umma tana zaune tare dashi a dakin mu. Na ce bari na tadashi ya karya mu tafi na dan taba shi kadan yai wani irin firgita ya zabura zaune yana kallon mu. Nace a hankali tashi ka karya mu tafi asibiti yanzu, wani kallo ya watso min tare da girgiza kan shi. Umma tana ganin haka tasha jinin jikin ta ta fice daga dakin daga falo naji muryan ta tana kira na nafito zuwa inda take. Na samay ta zaune tayi tagumi da hannun ta daya nace Umma gani ta dago kai a cikin damuwa tana kallona ido da ido tace. Anya maryam baki ganin kamar mutanen boye ne suka shafi yaton nan ? Naji gabana yai wani irin faduwa nace Umma muranen boye kuma kuma ? Tace baki ganin irin yadda yanayinsa yake ne kamar mai neman wani abu can ? Nace amma sai nake ganin kamar zafin zazzabine yake sashi yin haka kin san wanda bai ciwo bai iya yin ciwo ba sai ya tada hankalin na tare dashi randa yayi. Nace bari dai mu tafi asibiti dashi kawai don hankalina ya daga kwarai ban taba ganin yai ciwo haka ba ? Umma tace nima dai haka din ne gaskiya na juya da nufin na koma daga cikin dakin abinda ban san yadda akayi ba na yake jiki na fadi a kife a gurin tare da sake wani irin ihu mai karfi. Umma tace yau na shiga uku may zangani haka ni kadai a gida Abba maza kira min yar sokoto. Yaron ua sheka dagudu sai gidan yar sokoto yana saye cikin shirin makaranta sai hakki yakeyi. Yace mama wai kizo inji Umma baban mu da maman basu da lafiya daga yar sokoto har mijin ta suka nufo gidan mu da saurin su. Yanayin da suka samayni ciki yasa ta fahinci mutanen ne suka hau kan na. Yar sokoto ke fadin sannu da zuwa yau kuma shigowan safe haka kukaiwa godiyar taku ? Wani irin juyi nayi sunajin yadda kassan jikina ke ba da sauti kas kas tace don Allah ko waye yayi magana musan may ya kawo shi nan. Sai zuwa can babu magana tsawon dan wani lokaci nace cikin wani murya haba haba haba bil, adama yaya kuke son muyi ne wai? Rana takuce kuyi yadda kuke so a cikin sa daren ma da Allah ya zaba muna mufito muyi yadda mukeso bazaku bar mu bane ? Yar sokoto tace hakane mun sani amma muna kiyayye daren gare ku ai don a lokacin muke hutawa muna. Kun kun kun nace cikin kada hannaye na idan haka ne yaya akayi marikin godiyar mu yagan mu daren jiya. Yagane mu yaga yaran mu yaga tsohon mu sarkin mu malamin mu yana shan iska. Bamuyi mashi komai ba don albarkacin godiyar mu yaci amma min razana shi sosai don bai kyauta ma jin dadin mu ba. Umma tace Allah sarki kuyi hakkuri don Allah rashin sani ne aida baza a aikata haka ba. Nace kunce asibiti, asibiti, asibiti, asibiti suna da maganin jinnu ne sai dai idan kuna son kashe kudin ku ga banza ne. Sui,ufil hayat jinnu oud, sui ufil hayat jinnu oud, suka tambaya cikin son karin bayani nace masu eh, ai godiyar mu ta san shi. Godiyan mu ga Allah ta san shi, sosai shi zata ta shafa mai shi a jiki zai samu waraka daga kaidin yaran mu da ya batawa rai. Sarkin mu yana shan iska ya gane shi ya haska mai hasken mota a fuska haka ya batawa yaran rai suka shafe shi. Ku kiyaye fitan dare don dare ba naku bane sai idan fitan ya kama dole na dago kai gurin mijin yar sokoto nace hayatudeen sai nai murmushi. Nace kayi a hankali da kudin mutane don ka kusa fadawa cikin hau, ilwala,I. Yace subbahanallahi ni kuma ya gyara zaman shi nace kwarai kuwa don akwai wani arne dake son ku hada halaka dashi kada ka soma arne ba abin yarda bane makiyan ku ne basu da tsoron Allah ko kadan atare da su. Matar da iyayyen ka ke son ka aura kayi a hankali babu babu babu lafiya ba alheri a tare da ita ko kadan. Gidan da kake son saye a garin ku an yaudare ka na guri bane mai kyawo shiyasa maigidan ke son sayarwa akwai huwa,i gurin bai bari kowa ya zauna don shi keda gurin sa. Tsohuwa tsohuwa kin bar gida har gidan ya zama maboyan shedanu makwabciyar ki ta samu gurin aje ruhin yan adam yan uwanki ko zaku koma cikin gidan nan yanzu sai anyi burgan sa sosai. Don ta samu dama da furin boye sirin ta a gidan ki don gidan yai mata dadi agidan ki suke meeting din su na mayu unguwar ku. Abba yaron kirki saidai kassh akwai shedanun yara dake sa ido gare ka amma bazasu iya ba don kafi karfin su da tuni sun gama da kai don akwai baiwa a gareka nan gaba mai tarin yawa. A garinku makwaciyar ku tasan da wanan tarin baiwa taso ta gama da yaron tun yana a cikin godiyan mu . Sai dai hakan bazai yiyu ba don abubuwan dake a tare da godiyan mu bazasu bari a lokacin a cuci jinin su ba. Godiyar mu mu tana da matukar kirki amma ke tsohuwa mai kalwa ta cusa maki mumunan ra, ayi a kan ta haka yasa muka gwada maki ba ai wa godiyar mu haka. Yanzu kin ganan wa idon ki gaskiyar alamarinta don haka sai dai idan halinku na yan adam ne ya taso maki kuma don har gobe baki daina hassadan ta ba a ran ki . Don kina ganin kamar ta taushe maki baiwan danki ne tafi shi arziki yanzu kin manta abin daga Allah yake. Zamu koma don haka ke yar sokoto gare ki don godiyar mu ta yarda dake amma kina kyashi akan ta kina yada magana wanda bai dace ba akan ta, kiyi hankali da fushin mu watarana kada mu waiwaye ki akan hakan. Sai watarana ku ceci rayuwan marikin godiya don shi yai muna katsalandan a rayuwan mu ba komai ba. Tsit falon yayi yayin da nake sake wani irin atishawa mai karfi har sau uku daga inda nake kwance. Sun tafi yar sokoto ta fadi haka nan tare da kiran sunana maman Abba sannun kinji. Na gyada mata kai kawai alaman amsawa tace bari na baki ruwa ki wanke fuskan ki. Ina tashi da kamar minti uku Umma tace dani maryam kin san sui, ifil hayat jinnu oud na kada mata kai alaman nasan shi. Tace sunce ki shafawa mijin ki tare da hayakin shi yanzu wai ba na asibiti bane gamo yayi da su a daren jiya. Da sauri na dago kaina na kalli Umma nace gamo kuma Umma a ina ya gamu dasu. Sai na fashe da kuka tace haba nace Umma ni ina fama da haka ace kuma yau baban Abba shima abin ya shafe shi kuma. Tace basu shige shi ba sun dai bashi tsoro ne kawai sukace don ya gan su ya haska masu haske akan su. Lokacin wai akwai tsohon sarki a waje yana shan iska shi kuma ya biyo gurin su. Da sauri nace baba ke nan ba kanin baba malam mahaifin mukkadarasiyya. Kallo na suke da mamaki nace tabbas yana kasan nan yazo ziyar na san da hakan nasani kuma sunce mu kiyaye su har ya wuce. To yanzu dai idan kina iya tashi ki tashi ki dauko maganin kiwa mijin ki yadda suka ce. Na yunkura zan tashi naji wani irin jiri ya kwashe ni da sauri na koma na zauna inda nake zaune da farko na dafe kaina. Yaya dai kuma suka tambaye ni kusan a lokaci daya nace babu komai jiri nake ji kawai sannu suke min. Sai bayan dan wani lokaci na mike zuwa daki na shiga neman maganin wanda sune suka bani shi dama. A hankali na yaye bargon da yake rufe dashi nakai hannu a jikin shi jikin nashi yai wani irin mugun zafi sosai. A hankali na soma shafa mai na daba mai ta gurin hancin shi da kunnuwan shi da saman kan shi. Bai fi minti goma ba ya sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi cikin murya kamar ihu yace maryam maryam nagan su tabbas BA MU KA DAI BA NE A GIDAN NAN. Nace haba ya Isa mana haka kayi shiru Allah yabaka lafiya ya koma ya lumshe idanuwan shi a hankali sai kuma ya koma barci mai nauyi. Haka yasa muka barshi ya samu barci da kyau muka dawo falo sai lokacin ne yar sokoto da mijin ta sukai muna sallama suka tafi gida. ****** ********* ****** A gidan su maigidan ke cewa murjan wai kin san ban taba yarda da zance wasu jinnu ba can sai yau din nan. Mata kamar ibishiya komai da ta kalli mutum tasani akan shi haka ? Kai dai ka fadi haka ni babu ruwana wallahi kadai ji warning din su kai min yanzu don haka koda gigin barci ba zan kara maganan ta bani. Dama Anty hauwa ce mai kawo maganan niko nake zakewa na yi daga yau kuma na dai na indai ni murja ce. Sai lokacin ta juya gare shi tana cewa ashe kai har aure ake nema ma ban sani ba a gida ? Yace kai zancen anty Fatine fa wata wai diyar kanin mahaifin mijin ta shine wai ta kama min ita na kara. Yanzu ai dai kaji in kunne yaji gangan jiki ya tsira yace ai dole sai na bincika. Yace haba no warder ashe gidan nan sukace na kawo kudi a yadda na taya ashe sun san sherin dake gidan suke son lakaka min shi. Yar sokoto tace to wani mutum ne ke son cutanka da suka ce yace bakowa bane Devid ne na fahinci haka tun soma maganan ta. Dama shakiyi ne shi yana da alaman yaudara tare dashi Allah dai ya rufa min asiri ban zurma a hannun shi ba da wallahi ya cuce ni har abada. Nan dai suke ta magana akaina har ya shirya a makare ya fita zuwa office don ya makara ranan kan case din mu. Baban Abba bai falka ba sai guraren karfe daya na rana ya tashi daga dogon barcin da yayi. Koda na shiga ya hada wani irin zufa sharkaf dashi kamar ba shine ke rawan sanyi ba da safe haka na. Jin muna magana dashi Umma dake cikin matsanacin damuwa ta fado dakin tana fadin ya tashi ne ? Nace ya falka Umna wai wanka yake son yi ko zai ji dadin jikin sa. Bathroom na shiga na hada mai ruwa ya mike dakyat jikin shi babu lakka daganin yadda yake tafiya zuwa ban dakin. Yana fitowa tare da alwala yai sallah nai mai maganan abinci yake cewa nabashi tea kawai yasha a lokacin. Falo ya fito anan na samay shi nafito da kayan tea na hada mai tea mai kauri ya sha ya koma saman three seater ya kwanta sai faman sannu umma take mai a raina nace uwa ke nan. Wanan abin na juya daki na dauko da niya na na kara shafa mai da sauri ya cire hannun shi da ya kare fuskan shi dashi yana cewa maynene haka kuma ? Umma ce ta tare ni da fadin tsaya mana ta shafa don Allah ko zaka kara walwalewa. Yace may ye shi din kuma tace kai dai bari ta shafa ma kawai badon Allah ya taimake mu tana dashi ba a gida yaushe zamu samay shi har aima amfani dashi kaji sauki haka ? Murmushi yayi tace ke shafa mai kinji ban tsaya ba na fara shafa mai turaren maganin a jikin shi. A hankali naji yana sauke wani ajiyan zuciya zakace ko yai nisa ne ga tunane a lokacin. Idanuwsn mu a kan shi wani sabon barci ne ya dan kara daukan shi a gurin bai falka ba wanan karon sai karfe biyar na yammaci. Yai sallah na gabatar mai da abinci yace maryam bar abincin nan please bakin nan nawa babu test ko kadan. Nace ai dole ba karamin jin jiki kayi ba ai Allah dai ya kawo saukin alamarin ai. Da asibiti muka tafi da kana can killa ma sai sun rike a can su kwantar da kai a yanayin da ka kwana ciki. Kwanan shi biyu ya walwale ya koma kamar baiyi ciwo ba ma alokacin ya koma normal life din shi. ****** ********* ****** Kudi na tsab na hada nakaiwa hajiyan controler taban kayan da sai dana gigice don yawan su. Na kalli yawan kayan da akace wai duk a matsayin nawa suke nan na fara kasuwanci sosai ba kama hannun yaro. Allah ya kama min abin sosai har manyan mata suka san da zamana moton da nake shiga na sayar na tura kudin a gyara gidan mahaifina dashi. Don na samu kyautan mota tagani ta fada daga gurin gwauna don yanzu zance na zama tankar yar gida a gurin su. A cikin haka wata rana suka bugo min waya wai Adisatu ta haihu a Niger nai matukar farin ciki sosai da samun wanan labarin. Ga matar gwauna tace tare zamu yafi Niger suna da ita don Adisatu tace azo dani wai. Suna saura kwana biyu muka bar kasan nan zuwa kasan Niger a tare da aminiya ta yar sokoto da tai min rakiya. Munga daula sosai a gurin wa yan nan mutane nayi mamaki daganin haka don a yadda muke jin labarin wai kasan basu kai kasan mu Nigeria arziki ba. Sai gashi mu munga sabanin hakan gare su ko don gidan masu akwai ne muka tafi oho ? Zan iya cewa wata kila su arzikin su na gado ne don duk dan wanan zurian idan ka ganshi kaga masu akwai. Don munga karyan gwalagwalai a gurin su duk wacce zata shigo acikin dakkakiyar shedda ce ga sarka da yan kunne da munduwa duk na zinare. Muma mun lakaci arziki don akwati guda na irin tufafin su na samu ta ranadar min na fitan suna da zan saka ajikina. Ganin nazo da yar sokoto itama sai ga nata daga cikun nata tufafin bazakace an taba amfani dasu ba ma ajiki. Duk wacce tazo zakaji Adisatu tana fadin ga sisters din ta daga Nigeria suka zo suna sai kaga ana mutunta mu da ta fadi hakan. Mun saje dasu sai ka dauka muma yan kasan ne saboda irin tufafi na alfarma dake a jikin mu. Ko wani kaya yasha aiki har kasa dashi da zani har dan kwalin su ga gwal a wuya yana muna sheki. Washe gari ne da dare ta gabatar dani ga maigidan ta wanda da ka gan shi basai an fada ma ba kaga buzu sak dogo siriri dashi amma akwai naira. Adusatu ce ke gabatar damu tana nuna matar gwauna yace ai yasanta yace yaya maigidanta yace yayi tafiya bai samu zuwa ba ko ? Tace hakane yaso zuwa amma tafiya ya kamshi tare da shugaban kasa sunfita zuwa waje. Tace hone ga malama maryam daga Nigeria da na tafi gurin ta kwanan baya kan matsalan mu. Ya dago da sauri cikin harshen hausa mai surki da yaren su na can yake cewa au wanan ita ce kika tayar min da hankali akan ta sai kin shiga nigeria kin ganta ? Tace kuma zuwan yai muna amfani ba don gashi yanzu Allah ya azurta mu d Abdoullah. Nan muka gane sunan da dan ta yaci watau Abdoullah. Murmushi yayi yace malama mun fa gode Adisatu kin san rigima gareta a lokacin naso ta bari muzo tare amma ta matsa dole ita zata fara hanya. Ya kara min godiya tare da yaba ma kokarin da akai masu yace zan iya cewa tun wanan lokacin komai a garemu Alhamdullahi. Muma muka gode mai ga irin halarcin da yai muna na sakon daya aika min dashi daga baya yace haba haba wanan ba komai bane ai. Muna kokarin mikewa mu bar falon ne nace sai dai akwai matsala dana hango wanan bakin dokin da aka shirya ma zaka hau kada ka haushi saida safe kasa a shirya ma farin adaidai lokacin da kake kokarin fitowa. Kallona yayi cikin mamaki yace cikin yar murya kina nufin dokin da zan hau gurin kilisa gobe gurin suna nace shi din. Ikon Allah ke nan da a kwai matsala ga bakin dokin nawa ke nan ?. Nace kwarai kuwa don yau sati daya ana asirce shi don jiran wanan ranan gare ka. Cikin mamaki ya kara cewa ko zan san wanda yai wanan abin haka ? Nace Allah zai baiyyana mai shi ta hanyan jarabtan shi da irin ciwon da mai shi yaso kayi ne don kaikayi zai koma ga mashekiya tun a gurin taron zai yanke jiki ya fadi a haka zaka gane maishi. Muka barsu da matar shi cikin matukar mamakin abinda na fasa masu zai faru. Bayan fitan mu yake cewa anya Adisatu wanan zancen gaskiya ne kuwa dokin da ko yaushe nake hawan shi tafiyan nan da nayi ne kawai ban haushi ba Tace kadai yi hakkuri kayi yadda tace ma mu gani don gujewa wahalan rayuwa. Buki ne sosai akeyi anci ansha anyi karyan arziki ko wace mace a gurin takai ta isa anan naga wanan masifaffan kakar tasu da ta sa Adisatu a gaba kan auren ta da mijin ta don basu so shi ya aureta ba sai daga cikin tsatson ta . Tsohuwar na gani na ta kasa dauke idon ta a kaina ina ganin ta kira wata hadimarta tana tambayan ta ko ni wacece Wacce ake tambayan take cewa daga Nigeria muka zo wai yan uwan Adisatu ne dake can. Ta dago kai ta kalle ni na sake mata wani lalausar murmushi mai sake ma,ana ga maishi don karyan su ya kare ke nan. Can maza suka fito saman dawa kan su sun saka mijin adisatu a tsakiya daga shi har dokin shi sun sha kwalliya sosai. Sun na rafe suna dagawa mutane hannu har lokacin da suka karaso daidai wani rufa sun dan bada baya gurin wani mutum maji karfi daga mutanen dake zaune saman kujerun alfarma ya yanka wani irin ihu. Take hankalin kowa ya koma furin shi nan ya zube a kasa wani farin kumfa yana fitowa daga bakin shi. Aka kwashe shi zuwa ciki nan taro ya hargitse yan uwa da abokan arziki sai cewa suke subbahanallahi hamma alkasim ne . Daga saman dokin da yake yakai idon shi a rufan da muke muna zaune saitin bayan matan shi idanuwan shi a kaina kai kawai na daga mai alaman hakane. Haka aka karasa wanan bukin cikin sabon tashin hankali kakan su mai fada aji duk ta rikice ta rude sai cewa take a taimake ta bata son ta rasa alkasim din ta. Komai yadda nai masu baya ni ya kasance masu Allah ya taimake su ba hamma Haroon ne ya hau dokin ba da sai buzun shi. Don su bakin cikin su ya fara samun magaji ba zasu kai fa samun cin dukiyan shi ba da suks so shiyasa aka yanke shawaran a nakasa shi kowa ya huta. Mun dawo gida da tarin saifa fam a tare da mu inda ban iso gida ba sai da matar gwauna tasa aka canza min kudin yakoma har miliyan uku da rabi namu na nan kasan. ****** ********* ****** Yanzu al, amari na zance Alhamdullahi ga karatu na koma inayi ina son hada digree dina don na rike kwalin a hannu na. Ga harkan kasuwanci na abin ba, a cewa komai ba kasafai nake samun tsayawa yin aikin jinnu ba sai idan mutum ya tsurani ya zama dole nakeyin sa. Nayi kudi fiye da tsanmanin mutum a wanan fannin na alamarin jinnu din dake kaina har yakai nakai yan uwana saudiya don sauke farali. A shekaran da ya kewayo kuma maigidana ya samu cigaba don controler ya dauke shi ya mayar dashi Abuja suna aiki tare. Shekaran da ya wuce ne na kara haihuwa lokacin na gama karatuna ranan suna mutane suna ganin bakin fuska dasu mukayi shagalin buki sai dai basu san iyalin baba malam ne dana mai shagona da su mukkadarasiya suka zo min wunin buki. Yanzu idan kin ganni na koma wata hamshakiya dani ba kasafai nake son ina al, amarin jinnu ba duk da har wanan lokacin da nake baku labarina suna tare dani babu abinda ya canza a gareni na al, amarina dasu ban dai da lokacin yin wanan harkan ne don irin ci gaban rayuwan dana samu a yanzu din. Da fatan yan uwa zasu dinga kiyayyewa a gidajensu da tsaron lafiyan mu dana yaran mu don kaucewa shiga hakkin wasu da bamu ganin su. Amma su suna ganin muna ganin su da gangan muke shiga hakkinsu. Na tabbatar da zamu kiyaye rayukan mu daga abubuwan da sunna ya koyar damu mukai watsi dasu insha Allahu babu abinda zai samu rayuwan mu. Don wanan matsalar a yanzu babu family din da basu shafi wani ba amma mu bamu sanin hakan don ba ganin su mukeyi ba. Nima zainab ina ce maku anan zan talaita maku labarin maman Abba don samun ci gaba da sabon novel dina dana farawa mosaya na da fatan Allah ya tsare ya kare muna rayuwan mu dana yayan mu da yan uwan mu musulmi. Nagode kwarai da so da kaunan da kuke nuna min a kullun da dan lokacin da kuka bamu gurin bin karshen wanan labarin. Allah ya kare mu ya tsare mu sai kuma wani lokaci idan Allah yakai rayuwan mu lafiya nagode nagode kwarai gareku yan uwa musulmai ga fahintar sakon mu a gare ku ma,assalam. ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU