*SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi ©ZAHRA ROYAL STAR 🌝 *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 1 *TSOKACI* Rayuwa cike take da ƙalubale, sai dai ko wani bawa da kalar nasa ƙalubalen. A nawa labarin Mahaifina shi ne ƙalibalena, duk yanda zan kai ga yin abu domin naiman albarkarsa ba na taɓa samu, duk yanda zan yi domin ganin na faranta masa ya ci tura. Duk abin da zan yi domin ya sa ya yabeni ba ya gani... Na amshi hakan a matsayin kaddarata, kuma zan kasance ina addu'a har zuwa lokacin da zan samu SAUYIN YANAYI. *Unguwar Dubantu Hadejia, Jigawa State Nigeria* "Salma Kinga yadda kika koma kuwa wai kwana biyun nan mike damunki ne?" A d'an firgice Salma dake zaune a kujerar parlo tayi saurin sauke numfashi tana duban Hajiya, dake mata magana tana kuma mata wani kallo na k'urulla. Da sauri Salma tayi k'asa da kanta. Wasu hawaye na neman zubo mata. Da sauri Hajiya ta d'ago fuskar Salma a firgice ta ce "Salma wai mike faruwa ne dake haka?, idan baki sanar dani a matsayi na na Mahaifiyarki ba, waye a duniya da zaki iya sanar dashi damuwarki bayan ni?". Ai kawai sai Salma ta fashe da kuka tana fad'awa jikin Hajiya. K'ank'ame bayanta Hajiya tayi tana k'ara jin wani sabon tashin hankali na neman rufeta. Da kyar Salma ta iya bud'e baki ta ce "Why Hajiya mi yasa bana gane karatu kwata-kwata komai a cikin aji sai an wuce ni. Gashi Abba ya tsane ni saboda banda k'ok'ari a Makaranta. Hajiya ya ce fa ko mutuwa zanyi sai nayi karatu, koma na sake na kwaso Kari Over sai ya kusa min baki". Ta karashe maganar hawaye na k'ara b'alle mata. Harga Allah abun na mata ciwo sosai ta rasa gane wane irin Kaine da ita kwata-kwata bata gane karatu kanta baya d'auka, ta rasa yadda zatayi kota matsama kanta dole karatun ya zauna tofa bazai tab'a zama ba. Gashi ta taso gidan da ake son boko fiye ma da komai na rayuwa, kowa na gidansu wajibi ne yayi karatun boko, ko yak'i koya so, wannan tsarin Abba ne. Sauk'e lumfashi Hajiya tayi tana sa hannunta ta sharema Salma hawayen dake zub'o mata har lokacin. Sai can Hajiya ta ce "nikam da Mahaifinku zaibi ta tawa, toni da aure kikai bawai karatun boko ba, harga Allah nafi son ki samu miji kiyi auranki. Ismail da Ahmad su na yarda suyi karatun tunda Maza ne amma ke mace hankalina nima bai wani kwanta da abinda Abbanku ya nace mawa ba dole sai kun......... Sallamar Abba ce ta katse ma Hajiya sauran maganar dake mak'ale a bakinta. A murtuke ya idasa shigowa cikin parlon yana duban Salma, fuskar nan a had'e. Ba shiri Salma ta tashi tana niyar barin Parlon da azama ya dakatar da ita, ta hanyar kiran sunanta. Koda ga jin yadda ya kirata ta tabbatar da yaji abunda Hajiya ke cewa. Gabanta ba abunda yake sai dukan uku-uku, a d'an tsorace ta dawo k'asa ta zauna tana kallon k'asa. Abba ya nisa yana kallon yadda Hajiya ta sha Mur itama dan cike take dashi dama. "Ke Salma ki bud'e kunnan ki da kyau kiji ni?. Karatu boko babu wadda ya isa ya hanaki yinsa sai dai idan mutuwa nayi. Kuma naji abunda uwarki ke miki karatu akansa tana son zugaki ki fara sama kanki son aure tun yanzu. To bari kiji idan na sake naji labarin ko soyayya kin fara wallahi ban yafe miki ba Salma, bare har ki tsaya da wani namiji". Ba Salma kad'ai ba hatta Hajiya saida tayi saurin kallon Abba. Bakin Hajiya na kyarma wajan cewa "Mlm Rabe ban gane mi kake shirin cewa ba?". "Da hausa nayi maganar bada wani yare ba" "Yo ai na kasa gane ina ka dosa ne. Taya za'ai yara sun isa aure kace wai dole sai yarinya tayi boko. Yarinyata kasan na sani bata da kan da zatai wani karatun boko, koma kowa da irin kaddararsa ai, ka barta tayi auranta shine mutumcin y'a mace" Tashi Abba yayi rai a b'ace kamar zai rufe Hajiya da duka yana nunata da yatsa ya ce "kinji dai mi na ce?, dan haka dole a gidana sai anyi karatu, koma karki sake ki hurema d'iyarki kunne dan wallahi zanyi maku abunda bakya tsammani keda ita. Kuma ba wadda baida k'ok'ari a duniya sai dai idan kaine ka maida kanka Jaki. To dan haka wallahi ki jama d'iyarki kunne. Ga sauran k'annanta can da yayyunta wasu sun gama karatun lafiya ace sai ita d'aya zata rink'a samin ciwon kai?". Itama rai a b'ace Hajiya ya tashi tana cewa "Rabi'u ba sai ka tsaya kana wata kwana-kwana ba, kawai ka fito fili kace kafi son Y'ay'an matakan ai dama sune abunso wadda basa laifi kullum sune abun yabo a wajanka. Dama ni nida Yara na ai ba k'aunarmu kake yi ba". Wani murmushi Abba ya saki yana niyar fita yana cewa "komiye zaki ce ki ce, nidai na gama maganata. Kuma ba ubanda ya isa ya aurar min y'a bada yawuna ba, idan kuma mace na aurar da Y'ay'anta mata to sai mu gani a fara ta kanki" Itama Hajiya yadda zaiji ta ce "ai ko tuni ake hakan ai ba dole sai da kai za'a d'aura mata aure ba, kuma wallahi na tabbata Salma sai ta zama wacce zata fara taimaka maka a rayuwa". Da sauri Salma ta shige d'aki tun lokacin da suka fara wannan musayar maganar da suka saba iyayen nata. Kuma kullum dai akanta ne. Dan wani lokacin idan suna yi har kuka Salma keyi. Hajiya bata iya shuru bata maida ma Abba da martani ba, saboda abun ya fara isar Hajiya itama. Kullum cikin yabon su Maryam yake wacce suke uba d'aya sune Y'ay'an so. Su kuwa komi sukai sune abun zagi a cikin gidan...... *Copa Cabana Estate, Lokogoma District Abuja Nigeria* "Keee Kande ubunmi ya sakko dage a hargitse haka?" A kid'ime Kande ke kallon Momy dake mata tsawa, tama kasa magana sai nuna mata sama take tana hawaye. Wani dogon tsaki Momy taja tana sake cewa "ke bana son gidadanci uban miye kike yi haka?" "Dama....damm...dama Hajiya uhmm....uhummm..." "Wai ke Kande mi yasa baki da hankali ne da natsuwa?, zaki fad'a min abunda ke faruwa ne ko kuwa zaki tsaya min in'ina ne?" Sharce wani gomi Kande tayi tana cewa "Hajiya dama abunda kika bani ne naje tsakiyar gadon Salman na binne shine na..... Kasa k'arasa maganar tayi ganin yadda Momy ta zare mata ido a kid'ime Momy ta shak'o Kande ta wanke ta da mari ji kake tassss tassss. Kande saida daga giftawar wasu taurari tsabar yadda marin ya shigeta. Bata gama dawowa daga hayyacinta ba taji saukar maganar Momy a tsawa ce wacce ta kusa sa Kande sakin fitsari. "Dan uwarki ba cewa nayi ki d'aga gadon kawai kisa kwaryar a tsakiyar k'ark'ashin gadon ba?. Ko cewa nayi ki bud'a kiga miye ciki iyeee?". Wani miyau Kande ta had'e tana sake cewa a rud'e "wallahi Hajiya tsautsayi ne, abunda na gani ne yasa na firgita na d'auka kodai baki san miye a cikin bane. Hajiya maciji nefa na gani kwance a cikin kwaryar in...... Wata tsawar ta koma bugama Kande wacce tafi ta farko tana cewa "idan kika sake maganar nan wani yaji ta to na rantse Kande saina kashe ki, kin bar duniya tun kan lokacin mutuwarki yayi" Wani irin zaro ido Kande tayi idonta a warwaje, ta kama bakinta ta matse da tafin hannunta y'an cikinta na bada wani sauti kulululuuuu. Bata san lokacin data zube a k'asa ba tana cewa "Hajiya dan girman Allah kimin aikin gafara na rantse da Ubangijin daya yoni ba wadda zaiji wannan sirrin naki" "Yafi miki dai" Cewar Momy, tayi zama inda d'akin Salman yake. Da kanta ba tsoron komai tasa hannu ta maida k'atoton Macijin bak'ik'k'irin dashi wadda ya fito daga cikin kwaryar ta maiyar dashi babu abunda yayi mata, ta maida katifar gadon a yadda take ta gyara gadon da kanta kamar ba'a tab'asa ba. Duk abunda take Kande na mak'ure waje d'aya tana kallonta cike da tsananin mamaki da kuma tsoro. Dama duk abunda Salman keyi wani lokacin kamar mai tab'in hankali duk dasa hannun Momy a ciki?. Shi yasa wani lokacin idan ciwonsa ya tashi duk wadda ke kusa dashi mugun duka yake Sha. Ansha aura masa mata amma suna guduwa saboda irin haka. Ansa masa hauka tuburan, idan yana cikin hankalinsa kuwa baka tab'a gane akwai abunda ke faruwa a cikin rayuwarsa. To itakam Momy mi take nema?, dan kawai Salman yazo a matsayin D'an kishiyarta wacce ta rigata sanin Alhaji, to yanzu da bata raye miye na abun kishi Kuma?. Jin saukar magana akanta yasa Kande katse tunanin data tafi na wani d'an lokaci. Ganin Momy a gabanta yasa Kande had'e wani miyau mai d'aci a mak'oshinta ba shiri. "Idan kunne yaji gangar jiki ta tsira" Momy na fad'ar haka tayi waje tabar Kande da sakin Baki. Ai itama da gudu ta fito daga part d'in harga Allah tsoron ma d'akin take. Da hankalinka da tunaninka dai bazaka tab'a kwana waje d'aya da wannan narkeken Macijin data gani ba da idonta wadda ya kusa sata zaucewa ba shiri.. *GURBI, K'ARAMAR HUKUMAR JIBIA KATSINA STATES NIGERIA* Da sauri-sauri take shiga gidan, ganin Inna na dakan surfen masara, yasa ta d'an tsaya tana sauk'e lumfashi. D'an kallonta Inna tayi na wasu y'an dak'ik'u, kamin ta ce "Nanah lafiya na ganki tsulum haka bak'o sallama?" Da sauri wacce aka kira da Nanah ta idasa shigo cikin gidan tana cewa "yo Inna ba dole ki ganni a hargitse ba. Ance wai masu satar mutanan nan sun shigo GURBI wai sun zagaye garin, wai wani suke son su d'auka" Ba shiri Inna ta saki tab'aryar tana dafe k'irjinta ta ce "kee Nanah bana son k'arya, yaushe rabon da su shigo mana nan Allah ya rabamu dasu, kuna kira mana su. Ke yama akai kika sani wai wani suna cikin garin nan?". "Inna mutane fa duk sunga alamar su a garin nan, karkigansu fa sun wani saje da mutanen gari akwai abunda suke jira ne k'ila". Ai da idasa maganar Nanah ko rufe bakinta batai ba suka fara jin k'arar tashin Bindigogi tare da ihun jama'ar gari. Can kuma garin yayi tsin sai k'arar Bindigogin kawai kake ji. Banda kuka ba abunda y'an cikin Inna suke ita da Nanah. Kamin ka ce mi sun dunkule waje d'aya a d'aki, banda zufa babu abunda suke sharcewa. Da kyar Inna ta samu bakin magana tana cewa "mun shiga uku Mlm fa bai shigo gida ba, shida Auta Innallihi wa'inna alaihir raju'on ke banga ta zama ba". Ta k'are maganar had'e da k'ok'arin tashi. Ai da sauri Nanah ta rik'e hannun Inna tana cewa "al'qur'an Inna bazan tab'a bari ki fita ba. Suma zasu nemi wajan b'oya ne" "Ke wai Nanah mi yasa baki da hankali ne?, Autan ne zaki ce zai iya kare kansa. Yaron da bai kai shekara Sha uku bama, ta sha biyu yake. Kinga ki cika ni na ce ko?". Duk abunda Inna ke fad'a hakan baisa Nanah sakin hannun tana ba. Suna haka suka ji an banko k'ofar gidan nasu. Su duka zabura sukai suna k'ara k'ank'ame junansu. Zaro ido sukai a tare duk zatonsu ko y'an Bindigar ne suka fad'o masu gida. Sai dai muryar Auta da Mlm da sukaji ne yasa ba shiri suka Fito suna ware ido waje. Ganin yadda Mlm yake a hargitse ya kusa sa Inna da Nanah dariya amma sai suka maze. Domin Mlm hula daban babbar rigarsa ma daban takalmi kuwa k'ila akan hanya wajan gudu ya watsar da d'aya domin d'aya ne kawai sanye a k'afarsa. Inna ce tayi saurin jawo Auta tana cewa "Mlm ina kuka tsaya haka?, kaida nasan ba cikin gari kuke kwana ba. Saboda irin haka, kun sanfa mutanan nan ba kyale garin nan zasuyi ba, ni dama nasan sai sun k'ara waiwayarsa. Mi zai sa Mlm bazamu tashi daga garin nan ba?". Wata zufa Mlm ya sharce yana cewa "Kinga Binta ni banda arzik'in tashi daga garin nan, masu tashi kam sunata tashi, dan yanzu hakama shigowar nan da sukai ashe D'an Liti mai shigo suka zo d'auka, kuma sunyi nasarar d'aukar tasa. Domin yana isowa daga Kano yayo uwar sayayya ta shigonsa suka cafke sa. Sunma kusa halbin K'aninsa Jafaru Allah ne ya tak'aita, wai suke cewa ai ba kisa suka zo yi ba dama d'aukarsa ne kawai aka basu ajandar yi. Da badan haka ba ai sai su iya hallaka garin gaba d'aya kinga yawansu kuwa?". Ba abunda zuciyar Inna take sai halbawa da k'arfi, cike da tausayawa Inna ta ce "amma Mlm kana gani suna d'auki d'ai-d'ai wata rana fa kar tazo kanmu muma, gara ace muma mu bar garin inaga hakan sai yafi mana kwanciyar hankali" Zama Mlm yayi akan dankalin dake tsakar gidan yana k'ara cewa "Kinga Binta ba irinmu suke d'auka ba, mi nake dashi da har zasuyi sha'awar d'aukata babu uwar dana tsinana bare na aje wai a sunan dukiya sai wannan gidan. Ai irin su D'an Liti mai shigo sune ake d'auka ba irinmu ba". Auta dake jikin Inna ya ce "Inna kinga yadda suke halba Bindigogi a bakin k'ofar shagon mutane sai gudu suke?. Kuma suna d'aukarsa suka tafi suka kuma kwashe komai na shagon masu tsadar suka d'iba" "Kai Auta gidan ubanwa kaji Hakan" Cewar Nanah dake tsaye. "Yo ba dole Auta ya baku labarin yadda akai ba, tunda nida shi muna bakin hanyar abun ya faru Allah ne ya tak'aita inaga wa'innan y'an Ta'addar ba masu kashewar bane dan naji ance wai Daba Daba ce dama" Inna ta nisa ta ce "to Mlm abunda nake gudu karfa wata rana marassa imanin su shigo mana gari, domin kasan basa kallon talaka da mai kud'i kawai jidar jama'a suke suyi cikin daji dasu". Mlm da bai son maganar ace ya tashi daga garinsa inda yake mutuwar so, yasa yama mik'e ya shige turakarsa. Ai yana shigewa Auta ya bud'e baki ya ce "Inna inama su sake dawowa, su ce zasu d'auki Baba, ai da, da gudu zaice mu koma birni, ina son mu tashi daga k'auye muma, kamar yadda abokina Ismail suka tashi suka koma katsina". Da sauri Nanah ta bige bakin Auta tana zare masa ido tana cewa "kai baka da hankali ko?, kake mana irin wannan fatan" Inna ta kalli Auta tana shafa kansa ta ce "kinga Nanah ba haka ya kamata kina masa fad'a ba, cikin hikima ake gayama yaro baiyi dai-dai ba. Kaga Auta babu kyau abunda ka ce, babu wadda zai so wa'innan mutanan su d'auki nasa, kuma daga yau karna sake jin irin haka ta fito daga bakinka kaji Auta na?". D'an murmushi Auta ya saki yana d'aga kansa alamar yaji. Hararar Nanah yake yacce ta bige masa baki kuma yaji zafi, itama hararar ta b'alla masa. Tana komawa inda Inna ke daga ta barsa tsabar firgita har turmin ya kusa kifewa k'asa. Dakan Nanah ta ci gaba da yi tana son yin dariya ganin yadda Auta ya wani mak'ale Inna kamar wani mai shan nono................✍️ *SAUYIN YANAYI* share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 2 *Villa for sale in Dubai hills Estates* Tsaye yake manne da waya a kunnansa. Ya juya baya gashin kansa kad'an daya sakko har bayansa ya d'ansa hannunsa yana shafawa. Ya d'an d'auki lokaci yana wayar kamin ya sauke wayar yana jan lumfashi kad'an. Turo k'ofar parlon da akai ne yasa shi juyowa gaba d'ayansa. Jasmin dake tsaye ta zuba masa mayun idonunta ji take kamar ta cinyesa wani irin bala'in kyau taga ya k'ara mata na fitar hankali. Wani irin miyau ta had'e tana k'ara binsa da kallo kamar idonta zasu fad'o. Saukar muryarsa taji yana cewa "what look?, that's enough" Sauke numfashi tayi tana k'ara takowa tsakiyar parlon tana binsa da mayan kallo har yanzu. Cike da yanga da iyayi ta ce "ai ka kai a kalle ka ne My Salman, babu macen da zata kalleka lokaci d'aya ta d'auke idonta daga kanka". Tab'e bakinsa yayi wadda yake jawur kamar na jariri.Of course, he also knows that he should be looked at, but he is not in front of him. Ko wa'inda ake aura masa bada san ransa ake yin hakan ba, kuma da k'afafunsu suke guduwa saboda lalurar da yake fama da ita wacce take tashi akai-akai. Muryar Jasmin ta katse masa tunanin daya fad'a. "Ya kamata Salman izuwa yanzu ka amince dani, ka aure ni wallahi ina bala'in sonka" Furzar da iska yayi yana bin Jasmin da kallo, kamin lokaci d'aya ya d'auke idonsa daga kanta. Kamar bazai magana ba, dan harta fidda rai da hakan, sai kuma taji muryarsa mai taushi da kaifi yana cewa "Jasmin nasha gaya miki nasha yin aure ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, duk wacce zan aure basa iya zama dani, because I can't curse those who have everything, even I have relieved the responsibility that God has placed on me. Dan haka please Jasmin ki manta da wannan maganar ta aure a tsakaninmu" "Wallahi ko kashe ni zakai naji zan iya zama da kai nidai kawai ka amince ka aure ni dan Allah". Kallon Jasmin kawai yake. Tausayi ma take basa wallahi, fad'a kawai take a fatar baki kyan nasa ne kawai yake rud'arta, bawai shi ainafin kansa ba. Shi yasa mata da yawa basa birgesa, da yawansu kud'insa da kyan da Allah yayi masa ne ke sawa su soshi ba wai wani abu ba. Bai sake magana ba ya fiddo wayarsa ya kira PA d'insa Fahad. Ba'a jima ba saiga Fahad ya shigo parlon. Kallon Jasmin Fahad yayi yana watsa mata harara harga Allah shi haushi take basa. Yadda take iya zubar da darajarta ta mace take zuwa wajan Ogansa kullum cikin magiyar ya sota kuma duk a banza tunda yasan ba saurararta zaiyi ba. Maganar Salman ce ta katse ma Fahad tunanin daya tafi. "Fahad ka tabbatar komai ya gama kammaluwa na tafiyarmu?". "Eh ranka ya dad'e k'arfe shidda jirginmu zai tashi" Yana idasa fad'ar haka Salman ya fice daga parlon bai k'ara kallon koda inda Jasmin take ba. Jasmin ji tayi kamar zata had'iye zuciya ta mutu tsabar yadda ya y'arfata, duk da ya saba mata hakan amma na yanzu tafi shik'a. Da kyar ta samu ta fisgo magana daga bakinta ta kalli Fahad cikin jin haushinsa ta ce "ina kuma zaije?". "Iska na wahalar da mai kayan kara. Kin san dai Mai gida ba mazauni bane, yana harkar kasuwancinsa k'asashe-k'asashe. Kuma koba wannan ba ai yana da dangi a Nigeria, ko baki san haka ba?, to zaije ganin gida ne". "Hmmm PA kenan ba kaine sa'an yina ba, wadda ya ajeka shine dai-dai ni" "Duk wannan haukan da kike hakan bazai sa Mai gida ya aureki ba. Saboda kyansa kika gani da dukiyarsa kike rud'e haka, amma ba dan Allah kike duk wannan haukan ba. Kuma na baki shawara Jasmin?. Mai gida koda yana da niyar aure yanzu to bazai tab'a auranki ba, domin baki dace dashi ba. Dube ki, dubi jikinki dubi kayan dake sanye a jikinki kwata-kwata kamar ba d'iyar hausawa ba. Kawai danki girma a ture sai akace ki yada al'adarki?". Jikin Jasmin tsabar b'acin rai har wani rawa yake so take ta gaggaya ma Fahad magana itama amma wani abu ya tsaya mata a wuya. Ganin bata da bakin magana yasa Fahad wucewa yana murmushi dan yasan ta shak'a iya shak'a. Ai wallahi baya fatan Mai gidansa ya auri irinsu Jasmin ai sai su lalata masa rayuwa gaba d'aya ma. *Canada Studio Faruk Galadima* Zaune yake a studios yana sauraran wak'ar da ya gama rerawa yanzu cikin harshan turanci. Dafasa akai ne yasa shi cire abunda ke manne a kunnansa yana duban Henry daya dafa k'afad'arsa. Henry ya ce "Ohhh Faruk, you should rest like this and work hard today, I see that your phone is being called and you should check" Sauk'e goran lumfashi Faruk yayi yana lumshe idonsa yana d'an murza dogon gashin kansa. Wadda daka kalla zaka san irin na Fulanin asali ne. Muryarsa a gajiye ya mik'e yana cewa "by God, I'm also planning to leave the studio and go home. I know, Amma I'm waiting for me". "You should do it because today we are working on this song" Computers guda biyu ya d'auka sai wasu y'an abubuwa yana shirin barin wajan yaji Henry na cewa "yawwa kaga nama manta babbar mawak'iyar nan tazo nemanka wai tana so tayi wak'a da kai" "Wa kenan?" "Enisa mana" "Ohhh, but I'm just singing, I don't release the video of the song, but some people sing my song if we sing normal, but honestly I won't sing, I can't sing" "Faruk na fad'a mata wannan duk da taso ku hau wak'ar tare amma ta amince zaku rera wak'ar kawai" "Okay yayi ba bamuwa ita ce ta rubuta wak'ar ne?". "Eh ita ce yanzu hakama taban wak'ar a rubuce zuwa gobe zata dawo domin ganinka.Then decide when you think you will sing the song" "Ba damuwa zuwa goben ma idan aiki bai min waya ba, zamu iyayinta kawai". Ficewa yayi daga studion yana fata yasa face mask ya rufe fuskarsa, gudun mutane suyo kansa, duk da dare ya tsala amma garin kamar safiya ce. Dan duk inda ya shiga a k'asar Canada to ansan sa ansan waye Faruk Galadima shahararran mawakin dake tashe a duniya. Ya fara wak'a tun yana k'araminsa da sun cikar burinsa na son zamowa mawaki. Kuma Amma ta basa goyin baya, sai dai duk da haka baisa ya manta shi d'in waye ba. Mahaifiyarsa kad'ai ta rage masa a duniya. Sunsha wahalar rayuwa acan baya amma wak'ar daya ke tasashi d'aukaka, d'aukakar da zato bai zata ba. Shi kansa baiyi tunanin zai zama wadda duniya take alfahari dashi kamar haka ba, it's a good thing for everyone to join him wherever he goes or where he goes. Abunda ya maido sa zama Canada shida Amma bayan wak'a yana aiki a wani kanfani na k'era wayoyi da computers da dai sauran na'oruri daya danganci electric. Yasan takan waya da computers duk idan sun samu matsala zai iya gyara maka a d'an k'ank'anin lokaci. All companies are proud of Faruk Galadima. Katse tunaninsa yayi dai-dai yazo gaban wata Mota mai d'aukar ido. Bud'e gidan baya yayi yasa abubuwan dake d'auke a hannunsa, bayan yasa ya rufe bayan ya dawo ya shiga ya tada motar yabar cikin studion, da shima mallakinsa ne yanzu, mawak'a wadda basu kaisa ba suna zuwa sosai domin su buga wak'arsu a studionsa ba tare da ka bada ko sisi ba. Da yawan mutane abunda ke k'ara sawa su soshi kenan sunansa yayi zarra a k'asar Canada, kai harma da makwaftan k'asashe. Wani ma dai-daicin gida wadda ya gaji da had'uwa yayi parkin d'in motar tasa kamin ya bud'e ya fito yana danna wani madanni dake hannunsa nan take get d'in gidan ya bud'e, shi kuma ya koma cikin motar ya data ita, ya idasa shigewa harabar gidan. Wajan aje motoci yayi parking. Fito yayi daga motar ya d'auki kayansa dake bayan motar ya nufi cikin gidan. Yana shiga babban parlon gidan ya iske Amma dake zaune zaman jiransa. Ganinsa ya dawo k'alau yasa Amma sauk'e ajiyar zuciya. Har saida Faruk yaji yadda ta sauk'e ajiyar zuciyar. Murmushi ya saki yana ajiye kayan dake hannunsa yazo kusa da Amma ya rungumeta yana cewa "Ohhh Amma idan na fita sai kace wani k'aramin yaro, wadda idan ya fita akesa ran bazai iya gane gida ba?. Amma nafa girma yanzu" Kumatunsa Amma taja tana cewa "kaci gidanku Faruk, yaushe aka haifeka ma da zaka wani ce ka girma yanzu?, ni a waje na kai yaro ne". Murmushi ya sakar mata ya ce "hakane fa Amma, ai kin san ina kan hanya gashi na dawo kuma lafiyata lau". "Kaji ja'iri baccin ka gama tada min hankali, ka kalli k'arfe nawa ne yanzu kuwa?" Da sauri Faruk ya kai dubansa akan tsintsiyar hannunsa dake d'aure da agogon hannu. Waro ido waje yayi yana cewa "Ohhhh sorry Amma sha biyu saura ashe na dare. Mi yasa baki kwanta ba?, aiki ne yau yayi min yawa wallahi" Shafa kansa tayi tana cewa "nayi tunanin hakan, amma kasan idan ba dawowarka na gani ba bazan iya bacci ba. Kaida kota ina mutane nemanka suke ya za'ai kullum hankalina bazai tashi ba idan zaka fita?". "Amma nemana mutane suke amma ai soyayya ce tasa hakan ba wai cutar dani zasuyi ba" Murmushi Amma ta saki irin na manya ta ce "har yanzu kai yaro ne Faruk, ai cikin hakan ake samun mak'iya, wad'anda basa son ci gabanka, kai dai kawaii Allah yayi mana tsari da su. Allah kuma ya k'ara k'are min kai a duk inda kasa gaba" Kiss ya kai mata a goshi yana amsawa da amin. Yana niyar tashi Amma ta ce "abinci fa?" "Bana jin abincin nan zai shiga yanzu Amma" "To miye kaci yau?". "Na d'anci wani abu a studio" "A'a bazan yarda ba saifa kaci abinci, nasan ba wani abinci kaci ba, yanzu haka Chacolate d'in daka saba ci kayan zak'i sune kayita sha. Kazo ga abinci nan akan darning table kaci" D'an tab'a cikinsa Faruk yayi sai yanzu nema yaji lallai yana jin yinwa, dan rabonsa da abinci tun safe da zai fita aiki. Sai Chacolate d'in da sha. Shigewa yayi d'akinsa dake sama. Yana shiga toilet ya fad'a ya watsa ruwa, bayan ya fito yasa wasu k'ayan bacci. Yana d'aukar wayarsa dake ta aikin ringing tun d'azo. Wayarsa ta gida wacce y'an uwansa na kusa da friend's nasa ne kad'ai ke kira ta cikinta yaji ta fara k'ara. D'aukan kiran yayi yana k'arawa a kunne. Cike da kulawa yake yin wayar wani lokacin yayi dariya daka gani kasan da abokinsa yake waya. Can ya ce "Okay kuna gaf shiga jirgi?. Ni banso ka koma Nigeria ba yanzu friend, miye zakai a Nigeria ne?, kasan kuma ciwonka yafi tashi idan kana can". Daga cikin wayar aka ce "to ya zanyi ina son k'asata kuma Daddy ya kirani yana son gani na nima nayi kewarsa sosai kasanfa rabona da Nigeria zanyi shekara biyu, tun sadda naje Momy ta matsa nayi aure, akayi a daran aka samu matsala dole na saki matar tun lokacin na bar k'asar" Faruk cike da kulawa ya ce "Salman ya kamata fa asan miye asalin mike damunka gaskiya ba yadda za'ai ka zauna ba aure" "Abunda bana so kana min maganarsa kenan Faruk ka sani. Nigeria is the only thing I don't want to come to where I went and Daddy pressured me to get married, kuma bayan yasan bazan iya zama da kowacce mace ba a haka" "Insha Allahu Salman komai zai wuce zamuyi waya idan ka sauka. Wai ina Jasmin ne taka?" "Kai ko? Bana son wannan zancan, ko kasan Jasmin bata da kamun kai?, kai kwata-kwata ma bata cikin jerin matan da nake so. Kuma duk fad'a take duk sadda a gaban idonta ciwo na ya tashi wallahi a ranar guduwa zatai" "Hakane aboki ai da yawansu badan Allah suke son mutane irinku ba" "Harda kai ma ai Faruk kaifa sele ne" Dariya Faruk ya saki yana cewa "kai Salman na kaika ne nifa wak'a ce ta d'aukaka ni kaifa tsaye kake da k'afafunka kaine ka kafa kanka da kanka, ai matsiyin da dabanne" "Ka cika wasa Faruk wallahi" Sun dad'e suna waya kamar kar su daina sai da jirgin su Salman zai tashi tukunna sukai sallama.......... *SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 3 *Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria* "Ance wai ana sallama da Babansu Auta" Inna dake tsakar gida ta dubi yaron daya shigo ta ce "kaje kace gashi nan zuwa" Juyawa yaron yayi ya fice daga gidan. Inna ta kalli Nanah dake cin abinci ta ce "Nanah shiga d'akin Babanku kice ana sallama dashi k'ofar gida" Tashi kawai Nanah tayi ta shiga d'akin Baba ta sanar dashi. Ba'a jima ba Baba ya fito ya fice daga gidan ya nufi waje. Nanah ta kalli Inna ta ce "wallahi Inna gidan su D'an Liti mai shigo tashi fa zasuyi daga garin nan" Inna ta aje redion dake hannu wacce take shirin kunnawa ta kalli Nanah, kamin ta d'an nisa ta ce "ai banga laifin su ba wallahi" "Da mukaje da Auta yi masu jaje wallahi sai had'a kaya suke gaba d'ayansu gidan wai zasu koma katsina" "Allah sarki ni kinga tun ranar dana je masu jajen ban gani ba, ashe barin Gurbi zasuyi. Kai wa'innan mutanan suna d'aukar alhakin al'umma. Haka kawai kana son garinka amma ya gagareka zama". A k'ofar gida Baba yana fitowa ya iske su Ibro da Balah duk abokansa ne. Ganinsu hankali a tashe yasa Baba k'arasowa da sauri yana mik'a masu hannu, gaisawa sukai kamin Balah ya ce "Baban Nanah akwai fa matsala a garin nan" Cikin Baba saida ya bada wani sauti kulululuuuu da kyar ya had'e miyau ya ce "ban gane ba Balah?" "To yanzu dai y'an Dabar nan dake yawan shigo mana gari masu satar mutane had'e da kashe su, sana su d'ibi dukiyarmu da muke nomawa sun waiwayo kanmu" "Subhanallahi wai kana nufin wadda suka so data garin nan baki d'aya?" Ibro ya sauk'e lumfashi yana mik'a masa wata farar takarda ya ce "kaga wannan takadar sak'o ne daga wajansu suka aiko wai suna nan shigowa garin muma shirya. Sana sunce duk abunda muka noma mu tabbatar mun barsa a gonakinmu domin suna zuwa zasu d'ibesa su k'ara gaba, kai harda kud'in haraji ma suka sama kowa dake cikin garin nan" Baba dake kallonsu ido a zare ya ce "wai wa'innan mutanan miye suke sone damu?, so suke su maida mu bayinsu kenan?". Balah ya nisa ya ce "kuma abunda ke k'ara tada min hankali ma shine, Gwamnati ta kasa kawo mana d'auki. Kun tab'a ganin wani shugaban Gwamnati ya k'ara zuwa cikin garin nan da sunan yazo yaji miye yake damun talaka?". "Inafa muka sake jin d'uriyarsu, ai tun gabannin zab'e da suke so muje mu dangwala masu k'uru'a. Sunci zab'en sun manta damu. Daga su sai iyalansu, ai wata shara'ar sai dai a lahira wallahi" Cewar Baba da duk jikinsa yayi sanyi. Baba ya sake kallonsu ya ce "to yanzu miye abunyi?" Ibro ya ce "nidai gaskiya yanzu haka naba matata kud'in mota ita da yara na ce taje garinsu, mugani kamin garin yayi lafiya. Dan yanzu haka dangin D'an Liti mai shigo suma, sun tashi daga garin nan gaba ki d'ayansu" Cike da tsananin tausayin kansu Baba ya ce "ashhsha yanzu muna ji muna gani garin nan zai dawo kamar mak'abarta?". "Toya zamuyi gara mu matsa mu basu waje, domin tsira da rayuwarmu". Cewar Balah. Baba ya ce "nidai gaskiya bani da inda zan kai Iyalaina wallahi, addu'a kawai zanyi Allah ya k'aremu gabaki d'aya. Sana yau can wajan gari zamuje mu kwanan?". Balah ya ce "Baban Nanah yo ni nima ai babu inda zan kai nawa Iyalan. Kwana wajan gari kuma mu maza ai ta kama mu, domin kasan can baya indai suka shigo gari suka taradda namiji a gida kashesa suke nan take, shi yasa gaba d'ayanmu yau ba'a gida zamu kwana ba". Ibro ma ya ce "Mai gari kuwa shi tuni ya kama gabansa shida Iyalansa an sai masa gida a cikin garin Jibia" "Yanzu dan Allah miye wannan?, ace Mai gari guda na b'uya shida garinsa an hanasa zama a cikinsa" Sosai suka tattaunawa kamin suyi sallama Baba bai koma cikin gida ba saida yaba su Balah kud'in harajinsa da y'an Dabar suka sa masu kowa saiya biya... *Unguwar Dubantu Hadejia, Jigawa State Nigeria* K'udundune take akan gado zazzafan zazzab'i ya rufeta. K'asusuwan jikinta sai kwankwatsa suke. Sosai take rawar sanyi yadda taji k'afarta na mata ciwo sosai, da cikin k'ashinta tasan ciwonta ne na Sikila zai tashi, hatta cikinta wani irin ciwo yake mata. Hajiya ce ta shigo d'akin ganin halin da take ciki yasa hankalin Hajiya tashi ba shiri ta rungumo Salma tana cewa "haba Salma mi yasa tun d'azo baki sanar dani ciwon ki zai tashi ba?" Da kyar Salma ta bud'e baki ta ce "Hajiya nima kawai ji nayi k'afata ta fara ciwo daga nan sai kwankwatsar k'ashi" "Subhanallahi tashi yanzu nasa a mik'a mu asibiti bari nayi ma Abbanku magana Ahmad ya mik'a mu" Hajiya na gama maganar ta fice daga d'akin. Hajiya na fita tsakar gidan ta iske yaran gidan su Maryam tare da uwarsu Hajara duk sun dabaibaye ta tana rabon abincin rana. "Yara kamar wasu mayu". Cewar Hajiya a zuciyarta. Wani kallon Mmn Maryam ta aikama Hajiya tare da su Maryam suna sakin shewa. Duk da Hajiya tasan da ita suke hakan baisa yau ta tsaya ta maida martani ba, domin abunda Salma ke fama dashi ma kad'ai ya isheta. B'angaran Abba ta shiga yana zaune yana jin redion sai Khadija dake zaune kusa dashi tana masa maganar kud'in karatunta, danta kusa komawa school. Hajiya na gani ya fiddo kud'i masu yawan gaske yaba Khadija, ta tashi rafka godiya take, ko kallon Hajiya bata yi ba, bare tasa ran gaida ita. Hajiya cike da tak'aici ta kalli Abba ta ce "Fisbilillahi Abban yara kana ganin yarinyar nan ta ganni na ganta amma ta wuce bata gaida ni ba, saboda ban isa ba?, dama uwarsu ta gama hure masu kunne akaina yaran Hajara gaba d'aya sun raina ni a cikin gidan nan. Amma ni nawa yaran suna bata girmanta a matsayinta na matar Ubansu" Abba dake danna y'ar k'aramar wayarsa bayan ya ajiye redion sai kuma ya sake aje wayar itama ya dawo da dubansa wajan Hajiya "Hajiya ya kike so nayi ne wai?, na tabbata akwai abunda ya kawoki, ba wannan ba ina sauraranki" Wani abu mai d'aci Hajiya ta had'e a mak'oshinta ta cewa a ranta "lallai Rabe wato ma babu abunda zaiyi, yara sun gama rainata suna taya uwarsu kishi, ai ko wallahi zata san matakin da zata d'auka, bazata zauna yara y'an cikinta suna raina ta ba wallahi bac........ Abba ne ya katse ma Hajiya maganar zucin data keyi. Ta kallesa cike da damuwar rashin lafiyar dake damun Salma ta ce "Abban yara, Salma ce ciwon nan nata ya tashi, shine nake so ka bamu key d'in motarka Ahmed ya mik'a mu asibiti" "Wato danta ji anyi maganar karatu shine zata wani ce ciwonta na Sikila ya tashi kenan?". Kallon tak'aici Hajiya tabi Abba dashi kamin ta ce "ban gane miye kake nufi ba?. Ciwon y'arka ya tashi wadda kasan tana d'auke dashi, kuma dama akai-akai yake tashi zaka ce kuma wai danta ji ana maganar karatu zata ce bata da lafiya, kana nufin k'arya take kenan?". "Ni bance ba, amma ta sani ko mutuwa zatai sai tayi karatu. Domin ita yanzu wannan ciwon da take fama dashi duk wadda zai aureta sai an sanar dashi, ba kowa ne zai iya auranta da ciwon nan ba". Wani dogon salati Hajiya taja tana kallon Abba. Ita yanzu abunshi ya daina bata mamaki sai dai tsoro. Kwata-kwata an gama dashi duk Y'ay'anta bai damu da damuwarsu ba, sai dai Y'ay'an kishiyata Hajara. Ahhh lallai Hajara ta dace Bokaye, yo idan ba aikin Boka ba ko Mlm tasan haka nan dai kawai Uba ba zai k'i Y'ay'ansa har haka ba. Shuru kawai Hajiya tayi tama kasa magana kwata-kwata. Ganin haka Abba ya mik'a mata key d'in motar kawai yana niyar tashi ya fice yabar mata d'akin. Da sauri Hajiya ta ce "baka bada kud'in magani, da za'a sai mata ba. Domin duk magungunan da take sha sun k'are gaskiya" Dubu biyar ya mik'o ya bata. Amsa tayi tana bin kud'in da kallo kamin ta dawo da kallonta garesa ta ce "haba Abban yara, yanzu wa'innan kud'in miye zasu siya a cikin maganganun Salma?. Kasanfa magungunan data ke sha masu d'an tsada ne, saboda lafiyarta fa ake saya, wannan kud'in ai ko ganin likita da siyan kati bazasu isa ba bare ace ajega magani" "Toni dai iya abunda nake dashi kenan" "Amma naga kaba Khadija kud'i masu yawa, saboda ita boko zata ko?, ita koma Salma ta mutu kenan kake nufi?". Ganin tana son sashi b'acin rai yasa ya idasa ficewa daga d'akin ya barta tsaye sake da baki. Hajiya dake jin wani abo ya tokare mata mak'oshi, kwafa tayi kawai ta fice daga d'akin itama. Tana shiga b'angaranta ta iske Ahmed rik'e da Salma. Da sauri Ahmed ya amshi key d'in yana kallon yanayin Hajiya fuskarta kamar akwai b'acin rai ya ce "yanzu haka Abba ya b'ata miki rai ko Hajiya?". "Hmm Ahmad ai kasan duk sadda ciwon nan na Salma zai tashi to irin haka saita faru tsakani na da Mahaifinku". "Kiyi hakuri Hajiya insha Allahu wata rana komai zai wuce. Nima yanzu nake shigowa na iske Salmar bata jin dad'i shine take gaya min kinje wajan Abba ya bada mota zan kaiku asibiti". Hijabi Hajiya tasa tana amsar Salma daga hannun Ahmad ta ce "eh muje ko mun samu ganin likitan". Suna tafiya Ahmad na cewa "insha Allah zamu samu ganinsa ai rana batai ba sosai duka sha d'aya yanzu". Har suka fita daga gidan mutanan tsakar gidan ba wacce ta d'aga kai ta ce dasu sannu ko ya mai jiki, duk da sun san ciwon Salman ne ya tashi. Suna tafiya Hajara ta saki wani murmushin mugunta tana cewa "aikin banza kawai, ai ko wannan ciwon ya hana d'iyarki auruwa wallahi, ai indai ina raye Hajiya baki ba jin dad'i ko walwala a cikin gidan nan". Khadija data fito daga d'aki ta ce "hmm Mama ai kina min dai-dai abunda kike sa Abba yana masu. D'azo fa naje amso kud'in school, ta shigo d'akin karki so ganin yadda ta nuna bak'in cikinta da kud'in da Abba ya bani" "Tayi ta gama, kad'an ma ta gani. Kuma d'iyarta ita da karatu sai dai idan anayi a lahira zatayi. Amma ni ce nan nasa Mlm ya toshema shegiya kwakwalwa" Maryam ta zaro ido dake kusa da uwarta, ta dafa Hajara ta ce "kee Mama dama kice silar maida Salma marar k'ok'ari?" Harara Mama ta banka ma Maryam ta ce "kee kiyaye ni, nasan halinki da shegen surutun tsiya, na sake naji maganar nan a bakin wani to wallahi sai nayi miki abunda baki tunani" Zaro ido Maryam tayi tana sakin dariya kamin ta ce "haba Mama ya za'ai na tona miki asiri ai kema kin san bazai tab'a yiwuba, kawai abunne yaban mamaki" Khadija ta kalli Mama ta ce "amma gaskiya Mama kin nakasata da yawa, kuma kin kyauta mana. Da yanzu shegiyar ta fimu komai wallahi dan daga gani ba k'aramar mai basirar karatu za'ai ba can" Mama ta saki dariya ta ce "yo ai dama sai da Mlm ya ce min haka, ni ko na ce a dod'e kwakwalwata, ta daina gane komai, yo ina zaune zan bari tazo ta kere yarana ku biyu da nake dasu duk duniya ai bazan tab'a bari ba. Ita d'aya da kuke gani zata iya zama wani abu wadda ku kuna ku biyu ko kwatarta baza ku kamo ba, ni kuma ina ji ina gani bazan tab'a bari hakan ta faru ba". Wani yaro ne yayi sallama yasa su duka suka bisa da kallo jin abunda yaron ya ce ne yasa Mama tashi tana cewa "kai mi naji kace?" Yaro ya sake cewa "ance wai ana sallama da Salma wani mai mota ne yana waje" Ai da sauri Mama ta ce ma yaron yaje gata nan zuwa. Khadija da bakinta ke kyarma wajan magana ta ce "kan uba can. Mai mota ne yazo neman wancan yarinyar mai d'auke da cutar Sikila?" Tashi Maryam tayi da sauri tana cewa "Mama kinyi shuru?", "Kin san mi za'ai?, ke Khadija zan baki wani turare ki fesa sa kamin kije wajan wadda yazo neman Salma. Idan kika je ki tabbatar ya shak'i turaran. Sana ki b'ata Salma a wajansa, na tabbata zai dawo wajanki " Maryam ta tab'e baki cike da jin haushin Khadija ta ce "haba Mama wai komai za'ai sai dai ace Khadija ni kuma fa?". "Ke kinga ki kwantar da hankalinki kema naki na nan zuwa" Duk da haka Maryam sai kunbure-kunbure take ta koma ta zauna kamar zata fashe da kuka, taso ace ita ce zataje taga waye ba Khadija ba. Dama ita ba wani samarin arzik'i ne da ita ba, duk na banza ne masu zuwa a soshale, a school d'insu. Kamin a rufe minti biyar saiga Khadija an fito ance uban gayu ana taku dai-dai. Harara Maryam tabi bayan Khadija dashi, ji take kamar ta fisgota ta dawo da ita. Khady na fita ta iske matashin saurayi a k'ofar gidansu. Jingine jikin wata mota sai kyalli take. Ganin wata sab'anin Salma yasa ya d'anbi Khady da kallon mamaki. Tana idasa k'arasowa inda yake yaji wani k'amshin turare kamar na bori yayi masa sallama a k'ofofin hancinsa. Kansa yaji ya fara juya masa, da k'arfe ya runtse idonsa. Sak'on d'aya biyu....... Ya bud'e su akan Khady sai ya samu kansa da sakar mata murmushi. Wani irin dad'i Khady taji ganin tarkonsu ya kama. Sallama tamai cike da iyayi da jan hankali. Saurayin a zuciyarsa yake cewa "kai wannan fa tayi Alaji ko ita na samu ai nayi sa'a" Bayan sun gaisa Khady cike da makirci ta ce "hmm naji ance wai Salma kake nema ko?" "Wacce Salma kuma?, ai ni ke na ce a kira ba wai wata Salma ba", Dariya Khady ta saki tana sake cewa "uhum kad'ai fad'i gaskiya, ai na d'auka Salmar kake son gani na ce baka da labarin bata da tarbiyya ko kad'an duk gidanmu itace zakka, gata d'auke da ciwon Sikila ba wadda ya tab'a zuwa da sunan yana sonta". Tab'e baki yayi kamin ya ce "mubar maganar wata Salma, baga ki yanzu ba kin maye gurbin duk wata mace a waje na yanzu. Ni sunana Jafar kefa?" "Ni kuma Khadija" "Wow so nice name" Sun dad'e suna fira. Zasuyi sallama ya bata wata leda daya ciko da kayan ciye-ciye da dai sauran su. Hannun Khadija har kyarma yake wajan amsa tana rafka masa godiya. Sai da tasa masa number wayarta shima ya amshi tata. Kamin ya shige cikin motar ya tayar yayi gaba. Juyowar da zatai ta koma cikin gida ta hangi Ahmad dayayi parking motar Abba yazo d'aukar katin Salma na asibiti da suka manta a gida. Ya baro su Salma na jiran ganin likita. K'arasowa yayi inda Khadija take yana cewa "keee dan Ubanki ba Abba ya hanaku zance ba?, har sai kun gama karatu koba haka ya ce ba?". Yadda ya daka mata tsawa yasa Khadija zabura tayi cikin gida da gudu. Bin bayanta yayi shima yana shiga cikin gidan. Ganin yadda Khadija ta shigo a hargitse yasa Mama tashi ta jawota tana tabbayar "ke lafiya?" Wani kukan makirci Khadija ta saki tana nuna k'ofar gida tana cewa "Mama ba Ahmed bane daga ya ganni ina zance shine yazo a gaban saurayina ya mare ni, wai ba Abba ya hanamu zance ba" Wata uwar ashar Mama ta dark'ara, dai-dai shigowar Ahmed cikin gidan kuma a kunnansa duk yaji abunda Khadija ta fad'a. Nunasa Mama tayi da yatsa tana cewa "kaiiii Ahmad ka fita ido na rufe bana son hassada da bak'in ciki, yo idan ba bak'in ciki kake data samu mai abun hannu ba uban mi kake mata?, saboda ba'a ce K'anwarka bace wacce kuke uwa d'aya, y'an ubanci zaka fara nunama Y'ay'ana. Shine zaka disgata a gaban saurayi saboda baka da kunya?". "Amma Mama kin sanfa Abba ya ce baya son ganinsu da samari tun.......... "Kai dakata na ce, ina ruwanka da rayuwar y'ay'ana K'anwarka ce wacce kuke uwa d'aya ita ce kake da ikon mata haka, amma banda su Khadija babu ruwanka dasu nama gaya maka. Idan kunne yaji gangar jiki ya tsira" Zai sake magana saiga Abba ya shigo gidan. Ai ganin haka yasa Khadija k'ara b'are baki tana sakin kuka. Hajara ma saita kama matse hawaye tana kama bakin zaninta tana fyace majina, alamar tasha kuka ta gaji. Ahmad yana tsaye yana kallon ikon Allah, had'e da kallon makirci tsantsarsa wajan uwa da y'ay'anta. Abba a d'an rud'e yake binsu da kallo kamin ya ce "mike faruwa ne?" Khadija saita k'ara b'are baki tana cewa "yo Abba ba Ahmed bane daga na fita waje wani d'an ajinmu ya kawo min wani book nawa dana ara masa na makaranta, shine kawai ya kamani da duka wai zance nake, wai ka hanamu zance, kuma ni ba zance nake ba d'an ajinmu ne fa". Ta k'are maganar tana matse hawaye. Hajara ta amshe da cewa "kuma dan rashin kunya ina masa maganar miye tayi masa shine kawai ya kaima Khadija mari nima yana neman kai min marin, tunda dama ba kunya ce dashi ba". Zaro ido Ahmad yayi kawai ya kama girgiza ma Abba kai, dake mai wani kallo na b'acin rai. Kai dama haka mata suke wasu?, haka suka iya kulla makirci, shi yanzu ko rantsuwa nawa zaiyi ma Abba to wallahi yasan bai isa ya iya kare kansa ba..... Tunaninsa ne ya katse jin saukar mari har biyu akan kumatunsa. Zaro ido yayi da mugun sauri ya dafe kumatun nasa. Yana kallon Abba daya sharara masa mari har biyu. Cike da masifa Abba ke nuna Ahmed da yatsa yana cewa "wato uwarka ce ta turoka kayi ma mutane rashin kunya ko?, saboda kawai naki bata kud'in maganin Salma yadda zasu isa, shine kai kazo rasa kunya b'eran tanka, ka rama mata ko?. Ai ba'a kan Hajara da yaranta zaka sauk'e fushinka ba, gani ni ya kamata ka duka basu ba". "A'a wallahi Abba ni Hajiya bata sanar dani komai ba, Allah ya baka hakuri". "Idan nak'i hakurin fa?, bani key d'in motata" "Abba suna asibiti fa suna jirana, kati nazo d'auka fa" "Babu ruwa da inda kaje ka ajiye su, ka taro napep ku dawo kaja masu, bani key d'in motata kawai na ce" Idon Ahmed jawur jijiyoyin kansa sun tashi tsabar b'acin rai, kawai ya mik'a ma Abba key d'in motar. Abba yasa hannu ya fisgesa da k'arfi ya juya ya fice daga gidan. Yana fita Ahmed yabi su Khadija da kallo yadda suke sakin murmushin jin dad'i. Kwafa kawai yayi yana shigewa b'angaransu. Yana jin yadda Hajara ke sakin shewa da dariya tare dasu Maryam......... *SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 4 *Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja Nigeria* A hankali yake sakkowa daga matakalar jirgi. Gilas ne manne a idonsa, wata irin iska ya shik'a ta k'asarsa Nigeria, wata irin nutsuwa na saukar masa a zuciya. PA dake janye da akwatunan su na kaya. Wasu jifga-jifga motoci ne suka zo d'aukar Salman sun kai su biyar a jere. Gaba d'aya Airport d'in kallo ne ya dawo garesa. Mata y'an gayu wa'inda suke ji da kyau da kud'i ko wacce na binsa da kallo kamar idonsu zasu fad'u, ko wacce mace dake wajan ji take inama ita ce matar bawan Allahn nan. Yazo giftawa ya shiga motarsa PA daya bud'e masa gidan baya na tsaye yana jiran k'arasowarsa. Yaji wasu y'an mata na rad'a a hankali suna cewa "kaii K'awata kinga wani gaye?, wow wayyo Allah na, wannan ka same sa gidan duniya ai ka gama samun komai" D'ayar dake kusa da wacce tayi maganar ta harareta tana cewa itama "to nan da kike ganinsa ba wani cikakken mai hankali bane, idan ciwonsa ya tashi cewa akai ko waye a kusa dashi mugun duka yake sha, da kyar ake kwace mutum a hannunsa. Sana auransa ya kai uku ko wacce bata iya zama dashi saboda baya iya tsinanama mace komai, nan da kike ganinsa bai cika namiji ba da'aAllah". Wani abu mai d'aci ne ya tukare ma Salman wuya idonsa ya kad'a yayi jawur danma a cikin gilas ne baka tab'a ganewa. Shi kad'ai yaji miye y'an matan ke cewa. Saboda Allah yayosa da mugun sauri jin magana, koda rad'a kuke zaiyi wuya baiji miye kuka cewa ba, indai tazarar ba wata bace. To yanzu ma a d'an kusa suke dashi koma a hakan wai rad'a suke suna galmarsa. Shigewa kawai motar yayi PA dake tsaye ya maida murfin motar ya rufe. Yana tunanin mike damun Mai gidansa?. Da alama ciwonsa kwanakin nan na gaf da tashi dama a Nigeria indai zai zo to kuwa sai ciwon ya tashi. *Copa Cabana Estate Lokogoma District Abuja Nigeria* "Kande ki tabbatar kin jera komai yadda ya kamata" Kande dake wajan darning table ta d'an tab'e baki tana maganar zuci "kaji makirar mata, a waje ta Allah a zuci shaid'aniya. Yanzu Fisbilillahi duk wannan rawar kan da take akan Salman zai dawo da za'a bata wuk'a a b'oye zata iya hallaka bawan Allah ko?". "Keee Kande ubanmi kike tunani ina miki magana?, kin mayar dani y'ar iska" A tsorace Kande ta kai dubanta wajan Momy dake jefo mata kallon wulakanci bakinta na kyarma ta ce "kiyi hakuri Hajiya wallahi banji bane. An gama jera komai ai" Tsaki kawai Momy tayi tana zama d'aya daga cikin kujerun parlon tana d'aukar wayarta. Wata number ta kira bugu d'aya aka d'auka. "Kinga Asiya abunda kike so fa bai zai tab'a yiwuba" Daga cikin wayar aka ce "haba Hajiya kinsan fa yarinyata Sakina tana mutuwar son Salman, mi yasa zaki ce bazai yuwu ba?. Bayan nasan komai na gidan Alhaji Bin Muhammad na k'ark'ashin ikonki ne" D'an sauk'e lumfashi Hajiya tayi kamin ta ce "bana son rayuwar d'iyarki ta salwanta ne, bana so ta zama k'aramar bazawara ne, domin bazata iya zama da nakashashshan yaron nan Salman ba, abunda nake so dake shine Asiya ina so a samomin yarinya wacce iyayenta suke da son kud'in tsiya wacce a gidansu anfi tsanarta wacce bata da gata gaba da baya, irinta nake son k'ara aura masa, wacce zatayi sanadiyar nakasa masa rayuwa. Boka ya ce min dole a samo yarinya wacce bata da galihu shine kad'ai zai iya zama da ita wacce koya bigeta tasha wuya babu inda zata iya guduwa dole dai ta zauna dashi. Danni burina kawai ace yau Salman ya kashe matarsa dole yaje gidan yari, duk wa'inda yake aure ba sonsu nakeyi ba, saboda suna da galihu Y'ay'an masu hannu da shuni ne. Kuma dama suma ba dan Allah suke sonsa ba, dan kyansa ne da dukiyarsa ke rud'arsu. Dasun zo kuma sunga ya yake sai su gujesa". Sauk'e goran lumfashi Asiya tayi dake cikin wayar kamin ta nisa ta ce "tabbas na gane ina kika dosa Hajiya, na gane nufinki kin iya taku gaskiya, komai a hankali kike binsa a sannu-sannu ta yadda wani mutum bazai tab'a gane ke muguwa bace, dole sai idan kice kikai niyar ya sani. Lallai na jinjina miki kuma insha Allahu a nan Hadejia zan bincika miki yarinyar data dace". Murmushi kawai Momy ta saki tana sauk'e wayar bayan sunyi sallama. K'arar tsayuwar motoci a cikin gidan yasa Momy tashi cike da fara'a kamar bakinta zai tsage tsabar makirci, harda fita k'ofar parlon gidan domin tarbar Salman. Kande dake lab'e a kitchen tana lek'en Momy ta rake baki tana cewa a fili "keee duniya ina zaki damu?. Yanzu waye zai kalli matar can ya ce bak'ar muguwa ce?". Ta idasa maganar tana kallon yadda Momy ta tarbi Salman ta rungumesa sai masa sannu da zuwa take, yadda kasan ta goyasa, baka tab'a kallonta lokacin d'aya kace ba d'anta bane. "Ohhh My Son kasha hanya sannu kaji. Kaje ka watsa ruwa an gyara maka part naka, an had'a maka ruwan wanka ga abinci akan darning table kai kawai yake Jira". Murmushi Salman yayi yana jin dad'in yadda Momy ke nuna masa so. Ya ce "Momy duk ni d'aya?. Ina Daddy ne?" Murmushin itama ta sakar masa wadda bai kai zuci ba ta ce "Ohhh Daddynka yana wajan aiki, nasan yanzu haka yana kan hanyar dawowa domin ya san da dawowarka. Danma suna da wani mitin ai da harda shi wajan d'akko ka Airport ma". Murmushi kawai ya saki yana juyawa ya nufi part nasa. Yana d'okin ganin Daddynsa. Yana juya baya Momy tabi bayansa da harara. Tana maganar zuci "hmm haka kawai tunda na auri ubanka ko b'atan wata ban tab'a yi ba. Sai kawai na zuba maka ido ka gaje dukiyarsa, baccin kaima ga irin arzik'in da Allah yayi maka, wadda yama so yafi na uban naka. Ina ai bazan tab'a bari kaji dad'in dukiyar bama, bare ka tafiyar da ita yadda ya dace, saina ruguza rayuwarka Salman". *8:00PM* Zaune Daddy yake shida Salman suna cin abinci cike da hara da soyayya. Maganar kasuwanci suke da kuma kewar juna da sukai. Sai Momy dake zaune a gefensu tana ta k'ara zubama Salman duk wani abu da yake so tana ta washe baki kamar ta Allah. Daddy ya kalleta yadda take ta nan nan d'ansa d'aya tilo abin sonsa ya ce "kai Momyn Salman anma manta dani kenan tunda anga Salman ya dawo ko?". Dariyar yake ta saki tana cewa "yo ba dole ba, d'ana ya dawo ai dole na kasa zaune na kasa tsaye. Sai dai kayi hakuri Daddyn Salman wannan lokacin d'ana ne kawai". Dariya suka saki a tare kamin Daddy ya aje cokalin dake hannunsa ya d'akko wayarsa yana cewa "abun y'ar hakane?. To shikenan kinci kyauta kawo account number naki yanzu kiji alart ai duk wadda ya kyautata ma Salman dole ne na basa kyauta" Murtuke fuska Momy tayi tana b'ata rai ta ce "haba Daddyn Salman na d'auka Salman ai d'ana ne wadda nake d'aukarsa kamar ni ce na haifesa. Yanzu idan wani yaji ai sai ya d'auka dama ban isa haihuwarsa ba, ka nuna dama bani ce Mahaifiyarsa ba". Da sauri Daddy ya ce "Ohh am sorry Momyn Salman ba haka nake nufi ba. Kyauta ce kawai zan baki, kin cancanta ne ba dan wani abu ba. Ni na isa na ce ba kece kika haifi Salman ba?". Murmushin makirci ta saki tana sake cewa "Ohh yanzu naji bato koda na ce, to mun gode Daddyn Salman" Dariya suka sake saki a tare Daddy na jin dad'in yadda Momy ke nunama Salman kulawa yana kallonta cike da so. Bayan sun gama cin abincin kai tsaye part d'insa Salman ya nufa PA dake tsaye tare suka jera da wasu takardu a hannun PA d'in yadda yaga Mai gidan nasa na rik'e kansa yasa PA d'an shakkar rab'ar inda yake. Duk da PA na matuk'ar sonsa amma yana tsoro ciwonsa ya tashi yana kusa, ai kowa na tsoron abunda zai cutar dashi. Sai dai addu'ar PA bata amso ba. Suna shiga parlon part d'in Salman kawai ba zato ba tsammani Salman ya zube a k'asa ba numfashi. Wata irin zabura PA yayi yana waro ido waje tsoron tab'asa yake dan indai ciwon zai tashi dama haka yake, sai ya fara fad'uwa k'asa kamar wadda baida rai. PA na tsaye a mugun tsorace shi bai fita ba shi bai idasa isa inda Salman yake ba. Baiyi zaton tashinsa a d'an k'ank'anin lokaci ba, amma kawai idonsa ya gane masa Salman ya mik'e tsaye a haukace. Kalar idonsa ta sauya ta koma jawur kamar wuta. Wata irin kururuwa Salman ya saki kamar Zaki. Ya fara yaga suturar dake jikinsa, yana yagar fatar jikinsa kota ina kartar jikinsa yake, wasu irin farata zak'o-zak'o sun fito masa a hannu. Mutuwar tsaye PA yayi ido a waje jikinsa ba abunda yake sai kyarma. Wani k'aton table dake gaban Salman ya wawuro, bai sauke sa a ko ina sai a akan PA wata irin zabura yayi had'e da sakin k'arar azabar data riskesa ba shiri. Ai da mugun gudu yayi k'ofa yana fita ya jawo k'ofar ya gark'ame. Wata irin zufa ce ke ketoma PA sai zare ido yake yana dafe da goshinsa inda Salman ya fasa masa. Da sauri PA yaje ya sanar dasu Daddy hankali a tashe suka nufo part d'in Salman d'in. Sai dai Momy ta rik'e Daddy ta hanasa shiga. Domin yadda suke ji Salman nata fashe-fashen abubuwa had'e da wasu irin surutai marassa kan gadu, kai da kaji yadda yake kasan baya cikin hankalinsa. Wasu hawaye suka shiga zuboma Daddy na tausayin d'ansa. Ba irin maganin da ba'ai masa ba amma ina shuru kake ji. An d'auka ma ciwon ya tafi saboda yaushe rabon da ace ciwon ya tashi. Gashi idan ya tashi sai yayi kwana biyu yana cikin yanayin hauka tuburan. Sai dai a kullesa shi d'aya hatta abinci sai dai a warga masa mudun yaga mutum to kuwa duka kawai yake kaiwa...... *Canada Bitor Estate* Fitowarsa daga wanka kenan sauri-sauri yake ya shirya domin yau ma yana da aiki sosai a studio. Bayan ya gama shiryawa k'ananun k'aya ne a jikinsa. Yana d'aure takalmin dake k'arfarsa, Amma ta shigo d'akin nasa. D'auke take da k'ofin shayi a hannunta, kallonsa tayi tana cewa "ba dai fita zakai baka ci komai ba?". Dai-dai ya idasa d'aure igiyar takalminsa ya amshe k'ofin shayin ya kai bakinsa, d'an kurb'a yayi ya sauk'e yana cewa "Amma na makara ne yau wallahi idan na dawo zanci kawai" Mik'a mata k'ofin shayin yayi wadda ba wani na kirki yasha ba. Yana kai mata kiss a goshi yana ce mata ya tafi. Addu'a tayi masa tana binsa da murmushi kawai. Yana cikin tafiya a motarsa kamar ance yabi wani titi ya hangi wasu dondozon y'an iska sunsha askin y'an iska daka kallesu zaka san basa jin magana ko kad'an ko miye zasu iya aikatawa. Ci gaba yayi da binsu da kallo ata cikin gilashin mota, yana gaf giftasu gaya ashe macece suka tsare sunata ci mata zarafi. Ai ba shiri Faruk ya taka birki bai san sadda ya fito daga cikin motar ba yana nufar inda suke. Duk da sanye yake da face mask hakan baisa wasu sun kasa shaida sa ba. Wani daga cikin y'an iskan ya ce "kai guys wa nake gani kamar Faruk Galadima?" Gaba d'ayansu suka waiga suna duban inda Faruk Galadima yake. Budurwar dake sanye da wasu y'an iskan kaya ganin y'an iskan sun kyaleta yasa da sauri zata bar wajan wani ya kamo hannunta yana murzawa da k'arfi. K'ara ta saki tana shirin sakin kuka. Da sauri Faruk ya k'araso wajan magana d'aya yayi masu suka kyaleta, wani na cewa "ai ranka ya dad'e ka wuce nan wallahi taci albarkacin ka". "Ko zan iya sanin miye tayi maku?" Cewar Faruk "Kawai ka share y'ar wahala ce mutumina bashin Oga ta ci shine ya bamu umarnin mu keta mutumcinta. Amma tunda kayi magana an gama boss taci albarkacinka wallahi. Boss ko zamu iya d'aukar hoto?" D'an murmushi ya saki yana cewa "zamu iya mana" Bayan sun d'auki hoto a tare ya basu kud'in da suka ce Budurwar taci bashi. Zai shiga motarsa kenan, Budurwar ta matsu kusa da motar ta rik'e murfin motar tana kallonsa ta ce "nagode sosai d'an uwa" Miskilin murmushi ya saki yana cewa "ba damuwa ai. Amma ya kamata ki rink'a kama kanki ba kowanne waje mace ya kamata ta rink'a shiga irin wacce kikai ba yanzu, mace tana da daraja ki kiyaye nan gaba" Amsa mai kawai tayi da kai tana kallonsa har motarsa ta b'ace ma ganinta.......... *SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 5 *Cottage Hospital: Kiri Kasama Road, Hadejia Jigawa State Nigeria* Ahmed a sukwane ya koma asibitin, yana zuwa ya iske su Hajiya wani doctor ya tara su sun kai su goma yana masu jawabin micece ma Sikilar kanta. Da yawan wa'inda ke wajan duk y'an K'auye ne. Duk da su Hajiya sunsan wasu abubuwa da doctor d'in yake fad'a amma bayanin da yake ya d'au hankalin mutane da dama. Shima Ahmad samun waje yayi ya zauna yana sauraron abunda doctor d'in ke fad'a, kamar haka. (CUTAR SIKILA(SICKLE CELL DISEASE ) *"Yakamata* ace kowa yana da ilimi akan wannan cutar... Mutane sun rabu gida uku(A sauqaqe amma) *AA* =sune wanda basu da cutar kuma baza su iya yaɗa cutar ba *AS* =Su ake kira da *Carriers,* ba suda cutar amma idan suka auri masu irin jinin su zasu iya haifar mai cutar *SS* =Sune masu cutar Kafin ku shaqu da wani wajen soyayya adalcin da kowa zayyi ma kanshi da yaran da zai haifa shine yasan wanne kalar jini ne dashi ta ɓangaren Genotype yaga ko zasu iya Aure *AA+AA=* ✓Za su iyah aure *AA+AS* =✓Za su iya aure *AA+SS=* ✓Za su iya aure *AS+AS* =×Ba a son suyi *AS+SS* =×Ba a son suyi *SS+SS* =×Ba a son suyi Ciwon Sikila(Sickle cell disease) Wata cuta ce da ta take shafar sinadarin da yake ɗaukar iskar da ɗan adam yake shaqa lokacin numfashi *Illolin da masu cutar suke fama dashi* 1-Ciwon gaɓoɓi mai tsanani 2-kamuwa da cututtukan infection Saboda garkuwar jikin su yana da rauni 3-Shanyewar jiki 4-Qonewar jinin jiki 5-mutuwar gaban namiji 6-Rashin girma sosai Da sauransu *Shin za a iya magance cutar?* Eh,ta wani bangaren kuma nace A'a Akwai abin da ake kira *Stem cell transplant* inda ake canjin ɓargon mai cutar yakan iya magance cutar... yana da tsada a qalla wasu asibitin ka kashe 10million kuma ba kowanne asibiti ake ba Zan tsagaita anan saboda kar rubutun yayi yawa Amma kowa yama kanshi adalci kar soyayya ta saka ka cutar ko ki cutar da kanka" Cewar Doctor d'in ya k'are maganar tare da duban mutanan dake wajan. Wata mata ce ta mik'e tana cewa "to idan masu cutar gaba d'aya sukai aure zasu iya haihuwar yaro wadda bai d'auke da cutar?" "Tabbaya mai kyau", Cewar Doctor d'in yana duban matar kamin ya gyara tsayuwarsa ya sake cewa "Eh zasu iya haihuwar yaro wadda bai d'auke da cutar, sai dai abune mai wahalar yiwuwa. Amma komai daga Allah ne, amma ina so ku sani gara ka aure wadda baza'a zo asha wahala ba, ku a wahale yara ma a wahale. Ina fatan kun fahimta?" Kowa ya amsa domin gaba d'ayansu sunji dad'i bayanin daya yayi masu. Daga nan su Hajiya suka nufi Office nashi, ya duba Salma sosai ya rubuta mata magunguna ya k'ara bata shawarwari sosai da wasu abubuwan daya kamata mai Sikila ya rink'a ci. Sosai Hajiya taji dad'in hakan. Bayan sun fito daga Asibitin Hajiya ta kalli Ahmad cike da mamaki ganin ya taro masu napep, ta kasa hakuri ta ce "wai Ahmad ina motar ne?" Wani murmushin tak'aici yayi kamin ya ce "dana koma gida na iske su Abba da abokansa ne zasu fita wani waje, to dama jiran motar yake, shine ya ce a baki hakuri mun dawo a napep" Wani kallo take bin Ahmad dashi na rashin yarda da abunda ya ce mata d'in. Can kuma sai ta ce "Abban naku ne zai fita unguwa? to ina zashi tare da abokai?" "A'afa Hajiya ba wani waje ne mai nisa ba zasuje, k'ilama mu koma muga sun dawo" Girgiza kai kawai Hajiya tayi tana kamo hannun Salma suka shiga napep d'in. Haka kawaii bata yarda da abunda Ahmad ya ce mata ba, akwai wani abu dai bayan wannan. Koda suka koma gida, Hajiya taga motar Abba sai bata ce komai ba. Hatta su Hajara data iske a tsakar gidan nasu bata tankama kowa ba, suma ko kallon inda suke basuyi ba, ko sannu ya mai jiki?, basu ce ba, Hajiya abun ya mata ciwo sosai, ai sannu bata cire ciwo amma ai tana da dad'i, kwafa kawai tayi tana jaddada rashin mutumci irin na Hajara da Y'ay'anta. Ta lura da taken-takensu kamar suna jiran ko zata ce masu wani abu ne, sai sukaga sab'anin hakan. Duk da Hajiya ta lura akwai abunda ya faru bayan Ahmed ya dawo gidan da sunan ya zai d'akko masu katin asibiti. To amma miye ya faru haka?. Ba mai bata amsa ganin kuma Ahmed d'in baya so ta sani, sai kawai itama ta kyale abun. Washe gari Salma ce kwance akan kujera sai kanta data d'orasa akan cinyar Hajiya, ba laifi ta d'an samu sauk'i. Hajiya tasa hannunta tana zare k'aramar wayar dake manne a kunnan Salma, data ke sauraron wani book mai suna Bak'ar wasik'a da abokiyar fira ta karanta, tayi nisa a sauraron book d'in taji Hajiya ta zare wayar. Tashi tayi tana kallon Hajiya. Hajiya ta kalleta ta ce "wai ke bakya gajiya ne da sauraron wa'innan labaran?" Dariya kawai Salma ta saki tana cewa "Hajiya da dad'i fa littafin, nima wallahi Hajiya ina son fara rubutun book, kiyi min addu'a Hajiya na fara a sa'a" Dariya itama Hajiya tayi tana cewa "da wace wayar zaki rink'a typing d'in to?" Sai kuma Salma ta tab'e baki kamar mai shirin kuka, data tuna cewa fa bata da babbar waya. Ahmed ne da Ismail suka shigo d'akin. Ismail yayi wajan Salma yana d'arewa akan cinyarta, murmushi ta saki tana k'ara gyara masa zama akan cinyat tata. Ahmed daya ji abunda suke cewa. Sai shima ya ce "Hajiya indai zata iya rubutu wadda mutane da yawa zasu k'aru da ita, to insha Allahu zuwa gobe zan kawo miki sabowar waya ki fara kawai" Ai da jin haka Salma ta saki k'arar murna ta fara zafgama Ahmed godiya bakinta tsabar murna yama ki rufuwa, kawai saita k'ara rungume Ismail dake jikinta tsabar jin dad'i. Dariya Hajiya da Ahmed suke mata yadda duk ta rud'e da murna haka. "Tohm Masha Allah ai ko ta gode, nima na bata goyan baya ba'a san inda baiwarta take ba ai" Cewar Hajiya tana kallon Ahmed. "Hakane Hajiya Allah ya bada sa'a Salma" Da amin Salma ta amsa tana ta aikin sakin murmushi. Washe gari kuwa kamar yadda Ahmed yayi mata al'k'awari ya cika sabuwar waya mai kyau ya kawo mata y'ar dai-dai wacce kud'inta bai wuce dubu arba'in ba. Sosai Salma taji dad'i kamar ta taka rawa. Bata b'ata lokaci ba wajan samun number Khadija candy domin cikin marubuta ita ce kad'ai Salma ke mahaukacin so da son kasancewa kamar ita. Kuma tayi sa'a Khadija candy ta amsheta hannu biyu-biyu, duk da dama tasha jin Khadijar bata da girman kai ko kad'an ta iya ma'amala da mutane kowa nata ne. Ita ta fara bata shawara ta fara typing kawai kamin tayi posting ta rink'a turo mata tana duba mata kamin ta samu kungiya ta shiga idan tana da ra'ayin hakan. Salma dama ta dad'e tana ya y'an rubuce-rubucenta ta aje cikin littafin makaranta. Kawai saita tuna da wani labari can baya data tab'a fara rubutasa tun kamin suyi candy, tasha wahala kamin ta samo book d'in, duk yayi k'ura duk da bata dad'e da gama secondary ba, dan har yanzu basu gama hutun da zasu tafi wata school d'in ba, shi yasa ma take zaune a gida har yanzu, jira kawai Abba yake hutun ya k'are ta sani ya sata wata makarantar. Cikin ikon Allah ta samu labarin hatta sunan labarin dama ta riga tasa mai, kuma bata canza ba, shine *YADDA K'ADDARA TA SO* Abun fa kamar wasa Salma ta fara typing d'in yadda kaddara taso cikin ikon Allah tana turama Khadija candy ita kanta tayi mamakin yadda book na farko amma ba wasu kurare da yawa, ga daga jin labarin zai d'au hankalin jama'a da yawa. Ita ta bata shawarar bud'e Facebook ta rink'a posting har a can, ta turo mata groups na novels a yawa ta shiga, a d'an k'ank'anin lokaci ta fara posting nasa a duniya kamin ka ce mi mutane sun karb'i littafinta na farko. Cikin nasarar Ubangiji daya bata da ikonsa, ta kammala book d'inta na farko, wadda tayi mamakin yadda mutane suka amshesa sosai ta yadda ma batai tsammani ko tunani ba. Bata tab'a zaton abokiyar fira zata karanta mata book ba, sai gashi tana gama book d'inta na farko Khadija candy tayi mata hanya ta had'ata da abokiyar hira ta fara bata kyauta ta karanta mata na farko kamin tayi wani zata siya. Karku so ganin yadda Salma taji dad'i kamar ta taka rawa, kowa na gidan sai da ya gane farin cikin da take. Hajiya dake kallonta yadda ta rik'e waya sai murmushi take yasa Hajiya cewa "nikam Salma wannan farin cikin duk na miye haka?" Murmushi ta k'ara sakar ma Hajiya kamin ta ce "Hajiya dole nayi murna, ina abokiyar hira nan wacce nake sauraron book's d'in data ke karantawa?" "Kware na tuna ta" "To yawwa Hajiya ita ce fa zata karanta min book d'ina wadda na ce miki na gamasa jiya" "Kai Masha Allah Ubangiji ya k'ara d'aukaka d'iyar albarka. Ai insha Allahu sai kin zama wani abu, sai kin zama abun kwatance da yardar Ubangiji". Khadija ce tsaye a d'akinsu ansha wata uwar kwalliya kamar wacce zata fita gasar kyau ta duniya, a fesa wannan a fesa wancan. Jafar ya kirata yana k'ofar gida yazo zasu fita yawo cikin gari. Sauri take dankar ma Abba ya ganta duk da ta gaya masa d'an ajinsu ne dama. Bayanta gama ta kalli Maryam dake kwance akan gado ta mak'ale waya a kunnanta, hula ce akanta tasa ta mak'ale wayar, tana sauraron book na ji. "Wai ni ko Maryam kin gama jin fitar tsoro kuwa?" Sauk'e lumfashi Maryam tayi ta zaro wayar ta kashe littafin data ke ji tana cewa "shine nake ji yanzu haka ma" "Ayya please karki gogesa dan Allah ina son nima na turasa. Domin naji k'awayena nata cewa yayi dad'i" "Ai wallahi da gaske suke yayi mahaukacin dad'i, bare akace miki kuma abokiyar hira ce ta karantasa ai dad'in ba'a magana. Nifa sai inkai sha biyun dare ina sauraron littafi, indai abokiyar hira ce zata karantasa to wallahi ina sonsa, babu book d'in da zata karanta bazan jisa ba" Khadija data fiddo wayarta cike da zumud'in a tura mata fitar tsoro ta ce "please y'ar albarka ki turo min kamin naje na dawo kanji. Akwai ma wani book a wayar tawa shima naji ne, amma D'an Hamza ne ya karantasa wai mai suna FANSA shima yayi dad'i amma fa horror story ne" "Wow ke dan Allah?, ai ko ina son horror story sosai ma. Ai ko kawo na tura miki sai nima na tura FANSAR" Mik'a mata kawai Khadija tayi, kamin ta fice daga d'akin. Tana fitowa taci k'aro da Mama dake fitowa daga shashin Abba. Tsayawa tayi Mama ta k'araso tana dubanta ta ce "wai dama tun d'azo baki fita ba?, tun yaushe naji yaro ya shigo gidan nan yana cewa ana sallama dake?". "Mama na d'an tsaya ne wajan Maryam zata turo min littafin abokiyar hira fa" "ke dan Allah harta k'ara yin wani sabo?, kinsan fa nima littafinta data karanta kawai nake iya ji, sai kuma na gidan redio" "Eh Mama ta sake karanta wani wai fitar tsoro, kije Maryam zata tura miki" Kamar zata tafi sai kuma ta tsaya tana cewa "ni ko Mama a cikin book baki ganin akwai inda ake cewa bin Bokaye da Malamai babu kyau kuma masu yin hakan kina jin yadda k'arshen su yake kasancewa. Mi yasa baza....... D'aga mata hannu Mama tayi tana zare mata ido kamin ta ce "Kinga duk nasan wannan tunkan a haifeki nake jin wa'azi, dan haka babu abunda zan fasa, indai hakan wancar matar ce da y'ay'anta dan haka tunkan waje ya k'ure miki kama hanya ki tafi inda zaki" Da sauri Khadija ta fice daga gidan gaba d'aya tana d'aga k'afad'arta irin ko a jikinta d'in nan. A waje kuwa Jafar ne tsaye yana waya da wani abokinsa yana cewa "haba abokina kasanfa motar nan maido maka da abunka zanyi ba wani dad'ewa zanyi ba zan dawo" Daga cikin wayar aka ce "kaga Jafar ya kamata wannan k'aryar ace yanzu ka daina ta. Tunda kana da mata da y'ay'a har uku, ace kuma hakan bai isa ba sai ka k'ara yin wata k'aryar ka auro wata kuma. Kana ganin rayuwa zata tafi a hakane?" Jafar ya murtuke fuska kamar yana gaban wadda suke wayar dashi kamin ya ce "kaga Baffa please ka rik'e gaskiyarka bana so. Amma aure saifa na k'arasa, idan ba haka kake ma matan yanzu ba tofa ko kallonka basayi, yo akan mi? ai wallahi kamar yadda na auri Hafsat ta gama haukanta wai bazata zauna a gidan k'asa ba, bazata ci tuwo ba, ta gama haukanta ba gashi dole tayi hakuri ta rungume kaddara ba. To itama haka wannan dole ne zatayi hakuri kota k'i kota so". "Ka dai rink'a sassauta k'arya a rayuwarka wallahi Jafar" "Kaga bawan Allah naji rik'e wa'azinka zaiyi anfani amma fa wata ran" Yana fad'in hakan ya tsinke kiran ganin Khadija na tahowa inda yake tsaye. Tana k'arasowa ya sakar mata murmushi yana cewa "Ohh My Khady wannan kyau haka?" Dariya ta saki tana sa tafin hannunta ta rufe fuskarta kamin kuma ta sauke tana cewa "ai duk kaine akai mawa" "Wow duk ni d'aya" "Eh man" "To yanzu dai da ina da ina kike so muje yau?" D'an fari tayi da ido kamin ta ce "eh ina so muje shopping da wajan cin abinci haka" Dariyar yak'i Jafar ya saki, danma yana da y'an kud'insa daya rantab'o ma kansa bashi, kullum cikin cin bashi yake da aron kayan jama'a, shine aro mota can, shine aro kayan sawa can shine kaza shine kaza. Bud'e mata mota yayi yana k'ara washe baki ya ce "Bismillah ki shiga" Shiga kawai motar Khadija tayi ta zauna, shima ya rufe motar ya shiga ya zauna. Ya data ita suka fice daga unguwar taso. *Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria* "Nanah kizo ku wuce Islamiya fa ko, gashi har shidda tayi safiya ta farayi, naga alamar baki son zuwa Islamiyar asubar nan" Nanah data fito daga d'aki tana faman murmuza idonta dake cike da bacci, ta kalli Inna dake bakin murhu tana dama Koko, ta ce "Inna wai Baba bai dawo bane?" Gaban Inna ne ya d'an fad'i har sai da ta d'an dafe k'irjinta kamin kuma ta samu kanta da addu'a a ranta, sai kuma ta dawo da dubanta wajan Nanah data k'araso inda take yanzu. Ta ce "bai dawo ba, nima nayi mamaki anayin sallar Asuba fa yake dawowa gida, indai sukai kwanan dajin nan" Murmushin yak'i kawai Nanah ta saki, dan itama taji irin fad'uwar gaban da Inna taji kawai ta d'aure ne dan kar Inna ta fahimci hakan. Auta ta jawo yasha Kokon kamin ta kama hannunsa zasu fice daga gidan taji Inna ta tsaida ita tana cewa "ke kuma fa bazaki sha kokon bane?" Wani abu Nanah ta had'e a mak'oshinta kwata-kwata yau bata jin dad'i, bawai rashin jin dad'i na jiki ba, a'a kwata-kwata yanayin yau bata jin dad'insa. Da kyar ta ce "a'a Inna na k'oshi, idan na dawo naci wani abu kawai" Itama Innar bata sake magana ba, har su Nanah suka fice daga gidan. Kawai saita samu kanta da tagumi hannu biyu-biyu ta rasa mike mata dad'i itama. Tafe suke kan hanya ita da Auta zasu dawo gida bayan an taso daga Islamiyar, Auta sai tsaida ita yake yana y'an wasanninsa. Tsawa ta daga masa tana cewa "wai kai Auta mi yasa baka da natsuwa ne?, muna tafe kan hanya ka natsu mana muje gida" Auta daya firgita da tsawar da Nanah tayi masa, yasa ba shiri ya natsu yana binta da kallo kamar ba itama ba, bata tab'a masa irin wannan tsawar ba. Kodai bata da lafiya ne?. Sai kuma ta kamo hannunsa suka cigaba da tafiya. Sun shawo kwanar gidansu kawai taji Auta na cewa "lahhh Nanah dubi k'ofar gidanmu cike da mutane" Kan Nanah a k'asa yake ai da sauri ta waiga inda k'ofar gida nasu yake. Wata wawar bugar zuciya ce lokaci d'aya ta riski Nanah had'e da wata fad'uwar gaba. Tunkan ace mata mike faruwa ta fara hawaye kawai domin jikinta ya bata ba lafiya ba. Da gudu Auta ya warce hannunsa da Nanah ta rink'e yayi cikin gida. Nanah ma ta tsakiyar mutanan ta rab'a ta wuce yadda taga sai binta suke da kallon tausayi, an shinfid'a tabarma ga Liman yazo wasu na alwala duk jikin mutane a sanyaye. Da sassarfa ta idasa shigewa cikin gidan. Tana shiga abunda idonta yayi mata tozali dashi shine Gawar Baba shinfid'e a har an gama shiryata duk jini ya b'ata jikin likafanin. Wata irin razananinyar k'ara Nanah ta saki a haukace ta nufi inda gawar Baba take wata irin wawar runguma tayi masa, kawai ta fashe da wani irin kuka mai zuma zuciyar mai saurare. Auta dake jikin Inna shima sai kuka yake duk da bai san mutuwa ba amma yasan idan aka tafi ba'a dawowa shikenan kaida mutum har abada. Da kyar aka b'anb'are Nanah da har sumewa tayi a jikin Gawar Baba sai da aka shafa mata ruwa bayan an fita dashi. Matsuwa Nanah tayi jikin Inna tasa kanta akan k'afad'ar Inna tana hawaye tana magana cikin muryar kuka ta ce "Inna miya faru da Baba?", "Nanah y'an Ta'addar nan ashe dajin dasu Babanku suke b'uya sun gane cewa dama b'uya suke subar matansu. Wani d'an lek'en asiri suka turo ya kwana a garin shine yaje ya sanar dasu komai har inda su Babanku suke. A daran sukai ma wajan dirar mikiya sun kashe da yawan mazan dake wajan hatta Balah shima sun kashe sa Ibro ne kad'ai ya tsira shima sunji masa mugun ciwo" Kuka kawai Nanah ta saki tana tsinema y'an Ta'addar nan a zuciyarta yafi a k'irga sai tsine masu take tana jawo masu bala'in duniya dana lahira. Gaba d'aya garin Gurbi ya zama shuru da yawan mutane a ranar basu k'ara kwana a garin ba, a hankali garin ya fara zama kamar ba gari ba. Duk wadda ka kalla a cikin garin bashi da natsuwar zuciya kullum da tashin hankali suke kwana suke tashi. Dan yanzu har tsakiyar rana y'an Ta'addar shigowa suke. Tsaye Inna take yau kusan wata d'aya da mutuwar Baba tana shirin saida gidan da suke ciki ta tattara y'ay'anta su koma cikin garin Jibia da zama, ko sun samu kwanciyar hankali, duk da taji Jibiar ma shiga suke idan sunyi niyya, amma ai gara can da yawan mutane a garin. "Yanzu Inna waye zai siya wannan gidan da daraja a garin nan?" Inna ta kalli Nanah dake mata magana. Inna ta nisa ta ce "na dai aika Auta gidan Saminu dallali, yaji idan zai iya siyan gidan nan, dan bana ma so mu k'ara wasu kwanaki a garin nan gaskiya" "To Allah yasa ya siya d'in, kin san yanzu tsoron siyan gida ake a garin nan ma" "Yo Nanah ba dole aji tsoron siyan gida a garin nan ba. Ai dan a zauna ake siyan gida, to k'iri-k'iri idan ka siya zai gagareka zama indai a cikin garin nan ne......... *SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 6 *Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria* "Kaiii Ismail tsaya na ce" Juyowa Ismail yayi yana duban Hajara data masa tsawa, rik'e k'ugunsa yayi yana kallon Hajara kawai. Wani duba take mai cike da mamakin yaron ta cije baki kamin ta ce "kai dan ubanka, ni ce zan aike ka kaje kayo min shirme?" "Mama bafa shirme nayo miki ba, haka kike ce na sayo miki Sigari" Dafe k'irjinta Mama tayi ido a waje take nuna Ismail tana cewa "na shiga uku Sigari?, ni ce nace ka sayo min Sigari?" Wani irin kuka ta fashe dashi na makirci. Tana matse hawaye Da sauri Maryam ta fito daga d'aki tana kallon Mama cike da mamaki take cewa "Mama lafiya na ganki tsaye da yaron nan dangin marassa kunya?" Mama ta dubeta ta ce "bari y'ar nan, yanzu ni wannan yaron zaima shirri?, wai ni ce zance yaje ya sayo min Sigari ni?, yanzu kamar wannan yaron d'an haka dashi ya iya k'ulla shirri?". Wani kukan kura Maryam tayi sai gata agaban Ismail batai wata-wata ba, ta tsinka masa mari. Wani ihu Ismail ya saki yana dafe kumatunsa. Duk da haka Maryam sai da taci kwalar rigarsa tana zare masa ido, a tsawa ce take masa magana. "Kaii dan ubanka, uban waye ya had'a maka wannan tuggun da har ka iya had'a munafurci, dan kaja ma Mama shirri kana yaro da kai?. Zaka fad'a min ko sai na faffasa maka baki?, ka tab'a ganin Mama nashan tab'a dan uwarka?" Hajiya ce da Salma suka fito a hargitse jin kukan Ismail. Ganin yadda Maryam taci kwalar rigarsa yasa Salma zuwa da k'arfi tajawo Ismail tana bin Maryam da kallo na mamakin miye yayi mata haka?. Mama ganin Hajiya ta fito, yasa dan d'aukar magana ta saki wata shewa tana cewa "yo idan banda abunki Maryam, ai uwarsa ce zata gaya masa yaje ya sayo Sigari domin kawai ya b'ata min suna, dama bata san zamana a gidan nan. Tota Allah bata mutum ba wallahi, duk wani munafurci uwarsa ya gadu ai". Wani murmushin manya Hajiya ta saki tana kallon yadda Hajara ke tujara. Batai niyar tanka taba amma jin maganar data keyi yasa Hajiya cewa "ke kin san y'ay'ana basu iya munafurci ba. Kuma ko kin d'auka kowama irinki ne?, kin d'auka duk wani makirci da mugunta da kikeyi a cikin gidan nan, kin d'auka duk mutane kalarki ne?". Maryam zatai magana Hajiya a tsawace ta nunata da yatsa ta ce "Kinga ke baki isa nayi ceceku ce dake ba, da uwarki nake bada ke ba, ke ba sa'ar yina bace kin gane?". Hajiya ta juya inda Salma take da Ismail ta nuna masu hanyar shashinta alamar su wuce ciki, wucewar su Salma yasa Mama hayayyak'o ma Hajiya kamar zata dake ta. Hajiya bata k'ara magana ba, tayi shigewarta abunta tabi bayansu Salma. Rik'e baki Maryam tayi tana cewa "kan uba, Mama wai wannan matar mi take nufi ne?" "Yo mi kuwa take nufi nidai nafi k'arfinta wallahi, kuma bari Abbanku ya dawo wallahi saina sanar dashi abunda shegen d'anta yayi min" Sallamar Khady ce ta mantar dasu maganar da suke kanyi. Ganinta nik'i-nik'i da k'aya cike da leda, yasa ba shiri suka jata sai cikin d'aki. "Yanzu Khadija duk wannan uba-uban kayan Jafar d'in ne ya siya miki?" Cewar Mama, tana yi tana fiddo kayan dake cikin ladar, kayan ciye-ciye ne kala-kala harda su chocolate. Maryam ma data fasa wata alawa tana tauna a baki ta ce "amma daga gani Jafar d'in nan yana da kirki sosai, daga gani yana da abun hannunsa" Dariya Mama ta saki tana cewa "yo daga gani ai, ba sai an gaya miki ba" Khadija ta saki murmushi tana d'aukar wata chocolate itama tana b'are ledar chocolate d'in tana cewa "wallahi kuwa Mama, ai harya fara min maganar turo manya a ciki, domin yana sona sosai nake gaya miki. Wai Mama kinga gidansa kuwa da yake ginawa har k'ofar gidan ya kaini, kai aljanar duniya". Zaro ido Mama tayi cike da zumud'i ta ce "ke dan Allah bari, har can kuka je?" Khadija ta amsa mata chocolate cike da bakinta ta ce "wallahi kuwa Mama karki so ganin gidan. Danma ban tafi da waya taba, na barta a nan gida, da ai har hoton gidan zan d'akko ku gani". "Na yarda, kuma insha Allahu suzo gida kawai ayi a wuce wajan. Dan jiran ya huce shike kawo rabon wani" Khadija ta zaro ido tana cewa "Mama kin manta ban gaba karatu ba?" "Shin wai ba saura shekara d'aya ki idasa bane?" "Eh Mama" "Yawwa ai dai-dai kenan, asa rana ayi komai asa ranar dai-dai lokacin da zaki gama school, a lokacin a ranar sai kawai a d'aura auran" "Kaii Mama nama manta da wannan dabarar fa wallahi, hakan za'ai ma kuwa zan masa magana ya turo manya kawai su gana da Abba" *Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria* Auta ne ya shigo ciki gidansu da gudu tare da taya yana garawa. Inna ta kalli Auta ta ce "yawwa Auta na, kaje aiken dana yi maka kuwa?" Auta ya aje tayar da yake garawa zaiyi magana Nanah ta rigasa tana cewa "Allah yasa yaje d'in, ya fad'i sak'on yadda ya dace, baiyi shirmen daya saba ba". "Kinga kibarsa ya gaya min ko?" Shuru Nanah tayi tana kallon Auta itama, tana son jin miye zaice. Auta ya ce "Inna naje ya ce zaizo gidan da kansa kuyi magana zuwa dare" "Yawwa Auta na, Allah yayi albarka" Gaba d'aya suka amsa da amin shida Nanah. Kamar yadda Auta ya ce, saiga Saminu dallali yayi sallama a k'ofar gida. Koda ga jin sallamarsa Inna data idar da sallah ta kalli Nanah ta ce "kije ki shigo dashi zaifi muyi magana a cikin gida" Da to Nanah ta amsa tana sa hijab d'inta ta nufi waje. Inna kuma ta baza tabarma a tsakar gidan ta dawo ta zauna akan sallayar data idar da sallah. Da sallama a bakin Saminu ya shigo gidan Nanah na gaba, tamai iso. Sun gaisa da Inna ta nuna masa wajan zama. Bayan ya zauna Inna ta nisa ta ce "abunda yasa na kira ka Saminu shine, ina so na saida wannan gidan ne, da muke ciki, ina so zamu koma Jibia da zama gaba d'aya". Saminu ya gyara zamansa ya ce "to wani hanzari ba gudu ba, yanzu dai gaskiya babu wadda ke zuwa ya ce zaisa gida a garin nan, na cikin garin ma tashi suke suna guduwa daga cikinsa. Danni kaina yanzu haka shirin tashi muke nida iyali na" Shuru ya d'an gifta na wasu sak'onni kamin Inna cike da tashin hankali ta ce "yanzu Saminu ba yadda za'ai a shigar da gidan nan?, wallahi nima garin tsoro yake bani baya ma ace dare yayi" Saminu cike da tausayi ya ce "gaskiya nima ban san yadda za'ai ba, amma zan miki taimako d'aya, zan ara miki kud'i idan kunje Jibia sai ki kama haya dasu. A nan kuma zansan yadda za'ai a shigar da gidan, idan ya so ana saida gidan sai na d'auki kud'ina" Girgiza kai Inna tayi, domin Allah ya sani bata son bashi ko kad'an, tana tsoron ace yau gobe ta mutu da bashi akanta. Ta ce "a'a Mlm Saminu bazan amshi bashinka ba, ina da wata sark'a tunta aure na, kuma ina da tabbacin zatai daraja, zan baka ka saido min a cikin birni zuwa gobe. Domin can baya naso na sayar da ita amma Babansu Nanah ya hana, gara na siyar da ita mu tashi kawai". Gyada kai kawai Saminu yayi yana binsu da kallon tausayi. Tashi kawai Inna tayi ta shiga d'aki ta d'akko sark'ar ta kawo ma Saminu. Amsar sark'ar yayi yana jujjayata kamin ya ce "kai ai kuwa sark'ar zatai daraja domin za'a iya siyanta dubu d'ari biyar harda y'an kai ma" Murmushi Inna ta saki danta san zata kai hakan itama. Sallama yayi masu inda yake cewa sai goben insha Allahu zai shiga birni ya saida ta........ *SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 7 *Garki Hospital: Tafawa B'alewa Way, Area 3, Garki, Abuja Nigeria* "Daddyn Salman please ka samu ka zauna zai samu lafiya fa insha Allah" Daddy dake safa da Marwa a harabar asibitin da aka kawo Salman, da kyar wasu Maza suka danne Salman aka kira Doctor ya danna masa wata allurar bacci. Duk da haka sai wasu irin surutai yake, jikinsa na sauyawa kamar maciji. Daddy fuskarsa cike da damuwa ya ce "bazan tab'a samun natsuwar zuciya ba, har sai naji ya yanayin jikin d'ana yake" Momy zatai magana saiga doctor ya fito daga d'akin da aka kwantar da Salman. Da sauri suka tarbeshi, sai dai ya d'aga masu hannu yayi masu alamar su biyo shi Office kawai. Shima kansa doctor d'in wata zufa ce yake sharewa, domin abunda ke damun Salman d'in yasha masa kai. PA dake tsaye baiyi gigin binsu Office d'in doctor d'in ba. Yana tsaye hannunsa d'auke da wayoyin Salman dake ta aikin ringing tun d'azo. Wani dogon tsaki yaja tana mitar cewa "wai su mutane mi yasa basa da hakuri ne?, sun kira sau d'aya ba'a d'aga ba, basai su hakura ba" Wayar dake hannun damansa ce tayi fara ringing wacce iya y'an uwa, da wadda suke da mahimmanci ne a rayuwar Salman kad'ai ke iya kira ta cikinta. Hakan yasa PA duba mai kiran, ganin Faruk Galadima rubuce akan wayar yasa shi d'auka. Sai da suka gaisa Faruk yake tabbayar ina Salman?. PA ya nisa kamin ya ce "wallahi yanzu haka muna asibiti jiya ne kawai ciwonsa ya tashi, dan gaskiya wannan karan yafi ma tsamari" Hankali a tashe Faruk ya ce "Subhanallahi, ya yanayin jikin nasa?, shi yasa tun jiyan nake neman wayarsa tana shiga ba'a d'auka" "To jiki dai sai dai ace Alhmdllhi, amma har yanzu dai sai a hankali" Sun dad'e suna tattaunawa daga k'arshe sukai sallama. A Office d'in doctor kuwa suna zama, Doctor ya dubi Daddy da Momy ya ce "gaskiya abunda ke damun Salman bana asibiti bane, saboda munyi iya yinmu amma abun yaci tura. Yanzu fa da nake gaya maku kalar jikinsa ce ke sauyawa tana komawa irinta jikin maciji, jikinsa na sab'ulewa yadda kasan shida kansa Macijin ne" Zaro ido Daddy yayi zuciyarsa na halbawa da k'arfi kamar zata faso k'irjinsa ta fito, tsabar rud'u da tashin hankali. Da kyar ya samu magana ta fito daga bakinsa ya ce "doctor maciji fa ka ce?". "Kware kuwa Alhaji, zama ku iya zuwa ta bakin window da aka kwantar dashi kuga halin da yake ciki. Mafita d'aya ce a samu wani Malami na addini ya rink'a masa karatu ko wasu taimako haka dai". Momy tana jin haka tayi wuf d'in cewa "haba Doctor ba wani Malamin da za'a kira, kuma ni ban yarda d'ana ba ciwon asibiti bane, saboda baida wani abokin fad'a bare har a samu mai masa asiri" Shi kansa Daddy ya yarda da abunda Momy ta fad'a. Domin iya saninsa Salman baida wani abokin fad'a ko d'aya. Shuru Doctor yayi duk yadda yaso fahimtar dasu amma ina, daya d'akko nan sai Momy ta toshe can. Dole tasa ya kama bakinsa yayi shuru. Fitowa sukai daga Office d'in, Daddy na niyar zuwa inda aka kwantar da Salman, Momy da makirci da wayo ta hanasa zuwa, bare ma ace ya yarda da abunda doctor d'in can ke fad'a. Ai ina bazata bari Ya rusa mata shiri, wadda ta dad'e tana shiryasa tun tsawon shekaru. Saima ta jasa suka koma gida, wai zuwa anjima zasu dawo, zata taho da kayan buk'ata, suka bar PA a nan da wasu masu tsaron d'akin da aka kwantar dashi. Suna zuwa gida ta haura sama da sauri tana wurgar da jakarta ta lalubo wayarta ta dannama Asiya kira. Tana d'auka ba gaisuwa ta fara cewa "Asiya na jiki shuru fa?" "Hajiya kiyi hakuri, ina d'an jiran wani abu ne, amma nama samo yarinyar, ina jiran wani abu ne ya faru a gidan su yarinyar ne, zanje kuma za'a bamu ita insha Allah" "Haka nake son ji, yana can kwance rai hannun Allah" Dariya suka saki a tare kamin Momy ta tsinke kiran. Wata dariyar ta sake kecewa da ita, kanta a sama tsabar dariya har wasu hawaye ke zuba mata a fuska. Rayuwarta ta can baya take tunowa, da abunda ya maida ita muguwa, abunda yasa ta tsani Salman shida uwarsa, wacce tana kawosa duniya Momy tayi sanadiyar barinta duniya. *Shekarun baya da suka wuce* "Yanzu Didi Alhaji Bin Muhammad aure zaiyi?, kuma yasan ina bala'in sonsa, haba Didi kiyi wani abu mana" Didi ta kalli Aysha dake kuka bil hakki da gaskiya. Duk da tasan Alhaji Bin Muhammad d'an uwa ne a garesu to amma tunda yaje ya d'akko bare yaya zatai dashi?, tunda yak'i y'ar uwarsa k'iri-k'iri ma ya nuna Hakan. "Kinga ki kwantar da hankalinki, indai ina da rai to sai kin auri Alhaji, kima sama kanki ruwan sanyi" Share hawayenta Aysha tayi, duk da taji dad'in maganar Dad'i tayi, to amma idan ta tuna dole fa su biyu zai aura koda ya amince da auran nata, sai taji zuciyarta tayi bak'i wani irin kishi na rufe mata ido. Tashi tayi ta shiga d'akinta tana zarya so take ta samu mafitar ruguza auran Alhaji da waccar Hafsa d'in, ta tsane ta, ita ba y'ar gidan kowa ba, amma tana son bata matsala. Ji take ko wuk'a aka bata zata iya yanka Hafsa wallahi. "My hayat ka tsaya mana tun d'azo nake fa faman gwala maka kira fa" Tsayawa Alhaji yayi yana bin Aysha da kallo, shi harga Allah bata birgesa. Yanzu ma abunda ya kawosa gida yazo wajan Dad'i ne shine take masa maganar dole ya had'a auran Aysha ya auri mata biyu, idan ba haka ba kuma bata yafe masa ba. Sun kasance Dad'i ita ce Kakarsu kuma ita ce kad'ai ta rage masu a duniya daga shi har Ayshar, itama Iyayenta sun dad'e da rasuwa, a wajan Dad'i take zaune, kuma tun tana k'arama take dak'on son Bin Muhammad. Ita kam Aysha dake kallonsa kamar zata cinyesa. Tun shigowarsa taji, ta sakko da gudu domin ganinsa kawai da jin muryarsa yana sata farin ciki. Ganin ta tsaya ita bata ce masa komai ba yasa shi cewa "kefa nake jira ina inda zani, kuma waje ne mai mahimmanci a rayuwata" Bakinta bata san sadda ya furta cewa "wajan wa zaka daya fi nan mahimmanci?" "Hmm wajan My Hafsa mana" Ya fad'i hakan yana shigewa Motarsa ya data yabar mata saurin k'urar motar a fuskarta. Rufe idonta tayi tana jin wani tuk'uk'un bak'in ciki na tokare mata wuya. Fad'awa tayi kan gadonta bayan ta shigo d'akinta da gudu. Tana fashewa da kuka.can Kuma saita tsayar da kukan tana tuno k'awarta kuma Aminiyata Asiya. Da sauri tajawo wayarta ta dannama mata kira. "K'awata yau kune da kanku kuke nemanmu?" Bayan Asiya ta d'auki wayar ta ce haka. "Kinga akwai matsala wallahi ina cikin damuwa ne" "Subhanallahi mike faruwa ne haka?" "Kinga maganar bata waya bace kawai kizo ina son ganinki" Daga haka ta katse kiran. Zuwa can da yamma Asiya tazo gidan. Zaune suke a d'akin Aysha. Asiya ta kama hannun Aysha bayan ta gama jin duk abunda ke damun k'awar tata. Ta nisa ta ce "tabbas idan baki d'au mataki ba, haka za'ayi auran, ki koma y'ar kallo, ki koma yi masu shara da wanke-wanke" A zabure Aysha ke kallon Asiya, cikin b'acin rai Aysha ta ce "ai wallahi hakanma bazai tab'a yiwuba ba, kin san wacece ni ai?" "Na sani duk da haka saifa kin mik'e tsaye kin kwato ma kanki y'anci" "Ban gane miye kike son cewa ba Asiya" "Kawo kunnanki kaji" Wani abu Asiya ta rad'a ma Aysha, wata dariya suka saki a tare had'e da tafa hannu. Aysha ta tashi tsaye cike da murna ta ce "kin tabbata idan muka je wajan Malamin nan zai min aiki Alhaji yaso ni kamar Hafsa?". "Harma yafi na Hafsa, ai aiki yake kamar yankan wuk'a wallahi" Duk wata hidimar biki cike da kuzari Aysha da k'awarta Asiya suke yinsa. Hatta Dad'i ganinta saki ranta itama ta d'auka ko Alhaji ne ya fara nuna ma jikar tata kulawa. Bayan an d'aura aure har yanzu basu je wajan Malamin ba, Asiya ta ce mata ta bari sai bayan bikin tukunna da kanta zataje mata kuma za'ayi aiki yadda ya dace. Bayan biki da wata d'aya, Dad'i ta rasu, abunda ya dakatar da Aysha kenan zuwa wajan Malaminsu danta ce da kanta zataje Asiyar ta raka ta. Domin kuwa har yanzu babu abunda yake shiga tsakaninsu da Alhaji sai kallo kawai, amma a wajan Hafsat kuwa soyayya take ganin yana nuna mata sosai. Aysha tasha kukan rashin Dad'i dan har saida aka kwantar da ita asibiti. Amma duk da haka mutuwar Dad'i bata sa Aysha saduda da duniya ba, domin tana samun sauk'i suka wuce wajan Malamin da Asiya ke fad'a mata. Bayan Malamin ya koro masu jabin cewa Hafsa na d'auke da cikin Alhaji na tsawon sati uku. Yasa Aysha rud'ewa zuciyarta a bushe ta ce "Mlm babu yadda za'ai cikin ya zube?" "Akwai yadda za'ai mana. Ga wannan maganin ki tabbatar kinsa mata shi a cikin abinci, sana wannan k'ullin kuma ki tabbatar Alhaji ya tsallaka sa, to komai sai abunda kika ce shine za'ai a gidan". Sosai Aysha taji dad'in hakan, ta zube masa kud'i masu yawa wadda bata sanma iya adadin nawa taba Malamin ba. Kamar yadda Mlm ya ce haka komai ta aiwatar dashi yadda ya dace. Kuma an samu nasara Hafsa taci abincin, Alhaji zaije kiran Aysha ganin yadda Hafsa ke juye-juye tana rik'e da cikinta, ga jini sai zuba yake mata duk ya b'ata mata jiki. Suna zaune daga cin abinci yaga ta fara haka. A rud'e ya nufi sama inda d'akin Aysha yake, a nan wajan ya tsallaka maganin, dama kuma tasan zaiyi wuya baizo sanar da ita ba, kawai saita yanke shawarar sasa a hanyar d'akinta. Ai ko yana tsallaka maganin yaji kansa ya juya kamar wani abu ya shige masa tunani. Yadda taga Alhaji ke mata magana cike da kulawa da soyayya tasan aikinta yayi, hak'arta ta cimma ruwa. Itama cike da makirci ta sakko k'asa hannunta cikin na Alhaji. D'aukar Hafsa sukai aka nufi Asibiti da ita. A sadda Doctor ke sanar da Alhaji cewa cike ne da Hafsa na tsawon sati uku, cikin yaso zubewa ne, kuma kamar wani abu tasha shine ya kawo mata hakan, amma Allah ya tak'aita abun, domin cikin na nan bai fita ba. A lokacin Aysha ji tayi kamar ta shak'e Doctor d'in nan. Tun lokacin duk wani makirci ta rink'a had'ama Hafsa. Hafsa tayi bak'i ta lalace ga cikin jikinta na matuk'ar bata wahala, haka ta d'aure ta cije take zaune a gidan. Yanzu ita da Alhaji sai dai kallo domin ko d'akin kwananta Aysha sai taga dama zata ce yaje ya kwana. Babu irin abunda Aysha bata yi ba, domin dai cikin jikin Hafsa ya fita amma ina Allah yayi al'k'awarin sai yazo duniya. A ranar da zata haihu a ranar Aysha ta koma wajan bokanta, a ranar aka had'a wani mugun asiri data dawo gida a bayan gidan ta binnesa. Asiri kuma shine wasu bak'ak'e aljanu aka turama Hafsa su shafi jariran data haifa, ita kuma su kasheta. A dai-dai lokacin data binne asirin a dai-dai lokacin kuma nak'udar Hafsa ta tashi gadan-gadan, gashi ita d'aya ce a d'aki sai wahala take tun d'azo. Koda Aysha ta shigo gidan tana iya jiyo ihun Hafsa da neman taimako da take, saima ta samu waje akan kujerun parlo tayi zamanta. Hafsa tasha bak'ar wahala ta shafe awanni kamin Allah yasa ta haifo d'anta namiji, sai dai tana haihuwa bata ga abunda ma ta haifan ba, taji kamar an shake mata wuya tana shure-shure har rai yayi halinsa. Sai da Aysha taji kukan jariri ya karad'e gaba d'aya gidan, ta daina jin matsin Hafsa, hakan yasa da gudu tayi cikin d'akin da Hafsa take. Wani mugun farin ciki ne ya lullub'e Aysha ganinfa Hafsa an tafi, tafiyar da babu dawowa. Cike da makirci, ta kira Alhaji tana wani irin kuka tana sanar dashi Hafsa ta haihu amma ita Allah yayi mata rasuwa. Shima hankali a tashe duk da dama an kauda hankalinsa daga gareta kwata-kwata, amma mutuwar ta shigesa dan har kuka yayi a sadda yaga za'a fita da ita. Tun lokacin ya dawo da soyayyar da yake ma Hafsa akan abunda ta haifa. Tun lokacin da Hafsa ta haihu Aysha taga namiji ne, nanma ji tayi kamar ta shak'e jaririn, amma wata zuciyar na gargad'inta da hakan, tunda ta tuna shima fa ta gama da rayuwarsa, zai taso ne kamar mahaukaci, ba mai cikakkar lafiya zai taso ba. Aysha taso ta kauda hankalin Alhaji daga Salman tun yana k'arami amma hakan ya gagara. Dole tasa ta yada makaman yak'inta, ta rink'a jawo yaron a jiki kamar wacce take sonsa Dan Allah. Shi kuma Alhaji ganin yadda take basa kulawa yasa ya k'ara jin sonta a ransa. Dan har idan zatai wani abu ko tana son amsar kud'i a hannun Alhajin sai kiga tana k'ara ririta Salman kamar ta maida sa ciki. Tunda Salman ya tashi ya bud'e ido ya gansa tare da Momy Aysha duk zatonsa ita ce ta haifesa. Sai dai ita da kanta ta fad'a masa cewa Mamarsa ta rasu wajan haihuwarsa. Domin Allah ya sani ta tsani yaron kamar yadda ta tsani uwarsa. Koda rab'arta yayi ji take kamar ta shak'e sa ya mutu haka nan take danne zuciyarta tana nuna masa soyayyar k'arya. Tun yana shekara goma, abunda Momy ta masa tun yana ciki ya fara tashi. Haka kawai sai aga yaro ya fad'i kamar mai farfad'iya, yayita fashe-fashen abubuwa, duk da k'ananun shekarunsa idan mutane sunzo rik'esa duk sai ya watsar dasu, ko kuma ya kama mutum saiya ji masa ciwo ko ya sumar da mutum. Alhaji ya shiga tashin hankali, ba inda baije ba domin neman magani har k'asar waje ansha fitar da Salman, amma abun yak'i sakinsa. Momy kuwa ita tak'i bari aje wajan Malaman Addini bare har a gano miye yake damun Salman d'in na ainafi. Sai dai duk da abunda tasa rayuwarsa a ciki hakan baisa Allah yak'i basa sa'ar rayuwa ba. Tunda ya fara karatu bai tab'a samun matsala ba, gashi da farin jinin jama'a. Kota ina ana ji dashi, komai zai tab'a sai Allah yasa masa albarka a ciki. School d'in dayayi da kansu suka d'au nauyin karatunsa aka turasa k'asar waje ya ci gaba da karatunsa. Yana gama karatunsa, bai jira wani aikin Gwamnati ba, kona Daddynsa, ya kama sana'ar saida motoci da gidaje, da kud'in da aka basa kyautar su a school d'in daya gama, yaci kyaututuka kala-kala iri-iri daban-daban. Hatta k'asar daya gama karatu sunso d'aukarsa aiki amma ya ce shi so yake ya tsaya da k'afafunsa. Cikin ikon Allah nanma Allah yasa masa albarka dandanan ya bud'e kanfanin k'era motoci. Companynsa kusan biyar a k'asar waje, harda na k'era Abayoyi irin na K'asar Dubai, da atanfofi da dai sauran su. Momy abunda ya k'ara sa mata tsanar yaron kenan, bata da wani buri yanzu saina ganin bayansa.... Sauk'e lumfashi Momy tayi tana zama akan gadonta bayan ta gama tuno gaba d'aya rayuwar data wuce baya.... *SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 8 *Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria* "Wallahi Abbansu Maryam k'iri-k'iri yaron nan Ismail, ya nemi min rashin kunya, saboda uwarsa ta d'aure masa gindin yayi ma mutane rashin kunyar" Mama ta idasa maganar tana hararar Hajiya dake gefe, sai Ismail dake gaban Abba. Dawowar Abba kenan gidan, Mama ta kai k'arar Ismail. Abba da b'acin rai ya aika a kira masa Ismail, shine Hajiya tajawo hannunsa suka shigo a tare d'akin Abban. Abba ya kalli Hajiya yana cewa "wato na ce yazo shi d'aya shine ke mai d'a, zaki kwaso k'afa ki biyosa ko?" "Amma Mlm abunda kake fa bai dace ba ko kad'an" Cewar Hajiya tana kallon Abba, dake masifa an tab'a masa mata. Rik'e baki yayi yana kallon Hajiya, sai kuma ya kama kunnan Ismail ya murd'e. K'ara Ismail ya saki yana ba Abban hakuri. Abba ya k'ara murd'e kunan Ismail yana cewa "dan k'aniyarka, miye ya had'aka da ita?" Ismail cikin muryar kuka ya ce "wallahi Abba, ita ce ta ce naje na sayo mata Sigari, shine fa dana dawo take cewa ita ba itace ta ce na sayo mata ba" Dafe k'irji Mama tayi ai kawai saita fashe da kuka tana nuna Ismail tana cewa "kaji irinta ko?, yanzu haka ita ta jashi d'aki saida ta shirya masa abunda zai fad'a, idan an kawo k'ararsa wajanka dama. Wallahi wannan maganar fad'a masa ita akai, wannan d'an yaron dai bazai iya shirya magana har haka ba. Yanzu tsakani da Allah Abbansu Maryam na tab'a sha maka Sigari a gida fisbilillahi?". Kamin ma ta rufe baki Abba ya kaima Ismail wani mangari a k'eyarsa. Yana cewa "bata hakuri dan ubanka, kuma ka tashi kabar wajan nan, marar kunya kawai" Zuciyarsa Ismail na zafi ya duk'a har k'asa yaba Mama hakuri, ciki-ciki ta amsa tana binsa da mugun kallo. Duk abunda ke faruwa Hajiya na kallo bata sa baki ba, zuciyarta na zafi, ta taushi zuciyarta ne kawai dan a zauna lafiya. Ismail na fita Mama ta kalli Abba ta ce "yawwa dama ina son magana da kaine, akwai maganar da nake so mu tattaunawa mai mahimmanci" Abba ya kalli Hajiya da bata da niyar tashi ya ce "maganar tamu kad'ai ce ko kuwa?, sai an bamu waje?". Murmushin jin dad'i Mama tayi ganin yadda Abba ke gayama Hajiya magana. Cike da makirci ta ce "a'a kowaye zan iya fad'a a gabansa, tunda mutum baida wuta baida Aljanna bare ya saka ni". Gyara zama Abba yayi yana bata hankalinsa, domin indai maganar samu ce ta kud'i to Abba yana gaba-gaba a wajan. Mama ta gyara zama itama tana cewa "yawwa abun arzik'i ne yazo har gida. Khadija dai ta samu miji, kuma da alama mai kud'i ne, baya ma so bikin ya d'auki lokaci da yawa, tunda kaga ta kusa gama karatun ta, yana son shigowa gida ne asan dashi, idan yaso akasa ranar auran sai asa dai-dai lokacin da zata gama karatunta. Koya kake gani Mlm?" Cike da farin ciki Abba ya washe baki yana cewa "kai Masha Allahu, haka ake so, kinga ita ta tsaya tayi karatunta kuma ga miji ta samo dai-dai ita, ba irin su O'a ba" Murmushin Hajiya dake gefe ta saki, batayi niyar tsoma masu baki ba, amma jin abunda Abban ke cewa ne, yasa Hajiya bazata iya hakura ba ta ce "karka manta Mlm dukansu fa Y'ay'anka ne, kuma komai lokaci ne dashi. Itama baccin kak'i ai da yanzu Salma ta dad'e da yin auranta" Girar Abba ce ta had'e waje d'aya, kamin ya dubi Hajiya yana cewa "Hajiya kima daina wannan maganar, domin kuwa Salma gata can ma tayi karatu, ke wai wani ya hanaki yin karatun ne?, ba da iliminki na ganki ba, miye karatun bokon baiyi miki ba, hatta aikin hajji da kika je, ba ta dalilin karatun bane?". Ganin maganar naso tayi tsayi yasa Hajiya tashi domin tasan ko kwana zatai tana gaya masa gaskiya tofa ba yarda zaiyi ba. Tashi tayi tana cewa "Allah ya baka hakuri, amma gaskiya ka rink'a kamanta adalci a cikin y'ay'anka" Tana idasa fad'ar haka ta fice daga d'akin. Wani tsaki Mama taja tana cewa a zuciyarta "kinyi ki gama Hajiya, amma Salma ba ita ba auran wani wadda zata huta a rayuwa, sai nasa ta auri wadda zai ida nakasa mata rayuwa, wannan al'k'awari ne wadda na d'aukarma kaina" Abba ne ya katse mata tunani, suka ci gaba da maganar Khadija da Jafar yadda komai zai kasance. Washe da safe. Salma ce ta fito daga d'akinsu tana k'ok'arin shiga babban kitchen d'in gidan. Fitowarta ta hangi su Maryam da Mama dake zaune k'ofar nasu d'akin. Fitowarta taji tsakin da sukai mata. Mama ce ta kunna redio, kawai taji suna karanto wani littafi waishe KADDARA CE, abunda ya k'ara hargitsa ma Mama da Maryam kwakwalwa shine yadda sukaji wacce ta rubuta book d'in. Salma duk da taji abunda yasa su firgita sai tayi shigewarta kitchen d'in ta nuna kamar bata ji ba. Duk da tasan book d'inta ne, to amma cikin gidan nasu babu wadda yasan tana rubuta book's daga ita sai y'an d'akinsu. Ita kanta bata san gidan redio na karanta book nata ba, amma taji dad'in haka. A rud'e Maryam ta ce "wai baku ji wane suna naji ana kira bane?" Dariyar rainin wayo Khadija ta saki tana cewa "naji mana, zai wuce wata ce can sabuwar marubuciya akai, dan naji wani book ma abokiyar hira ta karanta na marubuciyar yadda kaddara taso, duk ita tayi shi". Maryam ta ce "to amma ya akai sunan marubuciyar yake kama dana wancar Salman" Mama ta tab'e baki ta ce "ke kuwa Maryam da abun dariya kike, idan banda abunki ina Salma ina iya rubuta wani littafi, yarinyar da bata san komai ba, sai jakanci kwakwalwata babu komai ciki sai dusa" Dariya suka saki tare Maryam da Khadija har suna tab'awa. Dai-dai lokacin da Salma ta fito daga kitchen d'in. Duk taji abunda suke cewa, sai kawai ta girgiza kanta tana murmushi ta shige d'aki. Tana shigewa Mama tabi bayanta da harara tana cewa "yo yama za'ai hakan ta kasance, ai da nayi kukan bak'in ciki kuwa, ai insha Allah haka zaki k'are a gantale Salma keda uwarki" Bayan kwana biyu Mama na zaune kan gadonta taji Maryam ta tab'a ta, ba shiri ta tashi zaune tana kallonta. Ganin kamar gulma ta kawo mata yasa ta tashi da sauri tana cewa "ke lafiya na ganki haka?, kamar wacce aka biyo tayi sata" Maryam tama kasa zama, ta had'e hannayenta waje d'aya, sai kuma ta kama baki cike da tsananin mamakin abunda kunnuwanta suka jiyo mata a k'ofar d'akinsu Salma, sakin bakin tayi ta dafe kanta. Mama ganin cewa kamar fa Maryam d'in a kid'ime take yasa ta jawota ta zaunar da ita a kusa da ita. A hankali Mama ta waiga k'ofar d'aki wai ko wani abu ne ya biyo Maryam d'in, daya sa ta zama Haka. Ganin babu alamar komai yasa Mama cewa "wai minene naga fuskarki ta cika da mamaki?" Sauk'e wani goran lumfashi Maryam tayi kamin ta ce "yo ba dole Mama ki ganni a haka ba, ashe duk littatafan da muke ji a redio da You tub channel, wadda abokiyar hira take Karantawa, ashe duk na Salma ne, mu duk d'aukarmu ai suna ne kawai yazo d'aya ba ita ba ce, ashe kuwa Salmar gidanmu ce ba wata ba" A zabure Mama ta mik'e tana cewa "keeee Maryam bana son maganar banza kinji" "Na rantse miki Mama ita ce" "Ke ta gidan Ubanwa kika sani to?" "Mama ki natsu dan Allah kaji" Jawota Maryam tayi ta zaunar da ita tana cewa "Mama nazo shiga ban d'aki ne, kawai kamar ance na matsa k'ofar d'akin su Salma, sai naji Hajiya na cewa. "Salma ya kamata fa ki aje typing d'in nan haka nan, ki d'an huta, idan kika gama littafin nan, ki d'an huta, kamin ki d'ora wani" Sai kuma na sake jin Salma ta ce "Hajiya ai hutu ba yanzu ba, tunda ina da lokaci yanzu so nake sai nayi littafi kusan goma ko biyar tukunna zan huta. Dan har gasar Hikayata nake so na shiga shekarar nan" A haukace Mama ta mik'e tana cewa "kutumar Ubancan, ai ko bazai tab'a yiwuba wallahi, dole na d'au mataki, dole ne gobe naje garin Hayin fari, wajan Mlm, dole ne sai Salma ta nemi wannan basirar rubutu littafin ta rasa, dani suke zancan wallahi". Maryam ta sake kamo hannun Mama tana cewa "Mama kiyi a hankali dan Allah, kar wani yaji, nasan dama zaki d'au mataki ai, shi yasa zuciyata ta kasa yarda ba Salma bace tunda naji sunanta, na ce ni ko saina binciko, ashe-ashe b'oye mana ake dankar mu gane", "Hmm dole zasu b'oye mana, amma yanzun ma ba makara nayi ba wallahi". *Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria* Tagumin da Nanah ta zafga ne, tun fitar Saminu take jin wata fad'uwar gaba, Allah ya sani tunda Baba ya rasu take jin irin haka, kuma har yanzu bata sake ta ba. Inna dake mata magana tun d'azo, ganinfa kamar bama jinta take ba, yasa Inna mamakin miye Nanah take tunani har haka ne?. Ace duk uwar maganar nan da take bata ma jinta ashe?. Saida Innar ta dafa kafad'arta, ta d'ago a d'an zabure tana kallon Inna. Inna tana kallonta, ta nisa ta ce "Nanah lafiyarki kuwa?" Ai kawai Nanah saita fashe mata da kuka. Tana jin wani abu ya tsaya mata a wuya. Hankali a tashe Inna ta ce "Subhanallahi ke Nanah miye hakan kuma?", "Inna tsoro nake ji wallahi. Inna ina tsoron mutuwa yanzu wallahi, bana son k'ara rasa kowa Inna" Wani murmushin manya Inna ta saki tana cewa "haba ke kuwa Nanah ai mutuwa dole ce, ga duk mai rai. Ki kwantar da hankalinki insha Allahu sai Kinga y'ay'anki harma da jikoki, kinji bana son ganinki cikin wannan halin kinji?" Goge hawayenta Inna tayi. Nanah ta sakar mata murmushin yak'i wadda bai kai zuci ba. Cikin dare Nanah ta kasa runtsawa ko kad'an ga Auta dake kwance a jikinta, sai Inna dake gefensu. Tana baccinta hankalinta kwance. Murd'awar da cikin Nanah yayi ne tasa ta sauk'e Auta daga jikinta, domin zuwa ban d'aki, haka nan taji wani zawo-zawo ya kamata. Da sauri ta nufi ban d'aki. Tayi mamaki ba abunda taci amma cikinta ya b'aci domin zawo tayi mai ruwa ma kuwa. Bayan ta koma ta kwanta bata fi minti biyar da kwanciya ba, ta sake jin cikinta ya katsa. Wani d'an tsaki taja tana dafe cikin nata. Fitowarta kenan zata d'auki buta, ba zato ba tsammani kawai taji K'arar halbe-halben Bindigogi kota ina suna tashi a tsakiyar garin nasu. Cikin Nanah ne ya k'ara hautsinawa, ji tayi tana niyar sakin kashin a wando tsabar tashin hankali. Zaro ido tayi hankalinta a mugun tashe tama k'asa koda motsawa a inda take. Sai da taji saukar maganar Inna itama hankalinta a tashe tana cewa "keee Nanah kinji abunda naji kuwa?, kodai kunne na ne kawai ke jiyo hayaniyar mutane da halbin Bindigogi?" Nanah ji tayi kamar bacci take Inna ta farkar da ita. Bakinta na kyarma wajan cewa "mun shiga uku Innna, inama yau muka bar garin nan, na shiga ukuna, bana son mutuwa yanzu, bana son rasa kowa yanzu, wayyo Allah Inna ki taimaka mana, Inna ina zamu gudu?, Inna kina jifa gida-gida suke shiga". Ai kawai Inna itama saita ji wasu zafafen hawaye na zubo mata. Auta dake gefen Inna ya rungumeta yayi shuru kamar wadda baida baki, shima kansa hankalinsa a tashe yake. Banko k'ofar gidan da akai ce tasa Nanah da Inna zabura suna curewa waje d'aya. Ba abunda ke fita a bakinsu sai Addu'a, sosai Nanah ta rungume Inna da Auta. Abunda ya shigo gidan nasu ne ya k'ara hargitse masu kwakwalwa. Nanah kuwa zawon data ke rik'ewa ne ya samu damar kufce mata a wando. Zubewa kawai sukai a k'asa su duka. Ba abunda jikinsu yake sai rawa. Ganin wasu Y'an Ta'adda sun kai su biyar fuskokinsu duk a rufe rik'e da wasu Bindigogi wadda tunda aka haifi Nanah bata tab'a ganinsu da idonta ba, kai hatta Inna ma, sai dai su kallesu a cikin Film. Wata tsawa aka daka masu yasa su Inna runtse idonsu ba shiri suna fashewa da kuka. "Keee ina mai gidan nan yake?" Bakin Inna na rawa take cewa "mai gidan nan ya rasu da dad'ewa" Zagaye gidan suka farayi suna bincika ganin babu wani namiji cikin gidan yasa wani Babba cikin y'an Ta'addar ya ce "kaiii Tajo, ka kashe min matar nan, yarinyar nan kuma ku taho min da ita, da wannan yaron" Wata irin kururuwa Nanah ta saki tana ihu iya k'arfinta take cewa "na shiga ukuna, na lalace, dan Allah karku kashe min Innata, gara ni ku kashe ni, daku kashe ta, wayyo Allah dan Alla...... Maganar Nanah ta tsaya cakkk sak'on d'aya biyu...... Jin saukar k'arar Bindiga a kunnanta, kamin ta gama tantance waye aka halba, taga Inna ta zube a jikinta babu alamar sauran rai a tare da ita. Domin a saman kanta Tajo ya saita bindiga ya halbeta nan take. Yadda kasan batun-batumi haka Nanah ta koma. Hatta da d'an yatsan hannunta baya motsi. Tana iya jiyo kukan Auta yana girgiza Gawar Inna dake yashe a k'asa. Tana dai jin sadda wani ya sab'eta a bayansa, daga nan bata sake sanin mike faruwa ba. Shima kansa Auta tasa k'eyar yaron sukai suna zaginsa suna turasa da bakin Bindiga. Auta yana gani aka tasa su gaba aka bar gawar Inna. Auta yana ganin yadda y'an Ta'addar suka kaso mutane da yawa, dake cikin garin naso. Wasu suka d'ora su a Mashina, wasu a mota, wasu ma a k'asa, an d'aure su da igiya, kamar wasu dabbobi, yana gani akasa Nanah kan wani mashin, shima aka jefasa cikin wata bayan mota, suka fara tafiya cikin dokar daji mai duhun gaske, sunyi tafiya harta wuce hankali, tun yana iya gane ina suke har ya rasa ganewa, tun idonsa biyu suke tafiya har wani wahalallan bacci ya d'aukesa............ *SAUYIN YANAYI* Share Fisbilillahi *©ZAHRA ROYAL STAR 🌝* *ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION* *EPISODE* 9-10 END OF FREE PAGES *MAMA* POV "Mlm so nake a lalata mata basirar rubuta littafin data fara. Ina so asa mata rashin kwanciyar hankali tare da farkai masu ban tsoro, ta yadda bata da wata natsuwar rubutun bare harta k'irkiri wani labari" Mlm dake kallonta da jajayen idonsa, ya saki wani murmushi yana cewa "wani hanzari ba gudu ba Hajara" "Ina jinka Mlm" "Akwai wata k'awarki Asiya hakane?" "Kware kuwa Mlm Asiya k'awarta ce Unguwa d'aya ma muka taso da ita ai" "Yawwa to zata kawo miki ziyara a yau d'in nan. Zata zo da wani fahimmin zance, duk yadda zakiyi kiyi domin aba Asiya aurar Salma. Indai kina son ganin bayan Salma, to ki tabbatar Abbansu Maryam ya amince da abunda Asiya tazo dashi" "Mlm na kasa fahimtarka fa?" Murmushin gefen baki ya sake saki kamin ya d'akko wata kwarya cike da ruwa ya nuna cikinta, yana cewa "ki kalla tsakiyar kwaryar nan" Da sauri Mama ta kai dubanta a cikin kwaryar abunda ta gani ne ya bata mamaki. Da d'an mamaki take kallon Mlm. Mlm ya ce "miye kika gani ciki?" "To Mlm mutum na gani, kwance bashi da lafiya, kamar mai shirin komawa maciji, jifa fatar jikinsa yacce take komawa tana sabulewa kamarta aljanin maciji, masu komawa mutane, irin wadda nake kallo a cikin fina-finan India" "To kinga wannan mutunin shine za'a aurama Salma shi, zata zauna da mahaukaci har rayuwarta ta lalace, bata tsinana komai a duniya ba, tazo a wahale zata koma a wahale". Wata shewa Mama ta saki harda su bud'a tsabar dad'i. Ta k'ara duba cikin kwaryar tana cewa "ai Mlm dole ma Abbansu Maryam ya amince da wannan batu. Abu d'aya zaka min kasa shi ya amince kawai idan na masa zancan, karma yayi min gaddama". Mlm ya d'akko wani k'ulli ya mik'a ma Mama yana cewa "kinga wannan?, ki tabbatar kin sa masa a abinci yaci, kamin ki kai masa maganar, na tabbatar zai amsa bai shirya ba. Sana ita kuma zamu sa mata rashin natsuwar zuciya bata da lokacin ma rubuta wani littafi" "Idan kamin haka Mlm ka gama min komai ai" Mama ta fad'a tana bud'e jakarta ta fiddo da wasu kud'i, tana dank'ama Mlm sai washe baki yake. *Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria* "Hajiya yau ne fa na tura labarina na gasar Hikayata, kimin addu'a" "D'iyar albarka Allah ya bada sa'a kinji" "Amin Hajiyata" Cewar Salma tana kallon Hajiya da murmushi kwance akan fuskarta. Ahmad ne yayi sallama ya shigo hannunsa rik'e da wata leda. Zama yayi kan d'aya daga cikin kujerun parlon yana kallon Salma dake mik'a masa gaisuwa, ya amsa yana cewa "Salma kina shan magungunan ki kuwa?" Murmushi ta saki tana jin dad'in yadda Yayan nata yake bata kulawa sosai. Ta ce "eh man Y Ahmad Ina sha" "To amma naga kwayar idonki ta canza kala tana son komawa d'orawa?" "To nima ban sani ba, amma dai duk ina sha akan lokaci yadda ya dace" "Abinci fa kina kiyaye cinsa?, kin san fa ba kowane abinci ne ya kamata ki rink'a ci ba?" Hajiya ce tayi gyaran murya tana cewa "Ahmad kenan, kaima kasan ba komai take samu ta ci yadda ya dace ba, kai dai kawai Allah yasa mu dace ya bata lafiya kuma" Shima ajiyar zuciya ya sauk'e yana mik'a ma Salma ledar hannunsa ya ce "anshi wannan ki samu kici, ki ajema Ismail sauran" Da murmushi sallama ta amsa tana godiya. Tashi yayi ya fice daga d'akin. Bayan fitarsa Salma ta bud'a ledar tana kallon abunda Yayan nata ya sayo mata. Su kankana ne dasu Ayaba, da dai sauransu. Sosai Hajiya tayi murna dan ya kamata Salmar ta rink'a shan abubuwa irinsu dama. Sallamar da ake rafkawa a tsakar gidan ce, sawa Maryam fitowa daga d'akinsu. Ganin k'awar Mama Asiya ce yasa ta cewa "Inna Asiya sannu da zuwa, ai ko yanzu Mamar ta dawo daga unguwa, Allah yasa zaki tadda ita, bari na kira miki ita, tana d'akin Abba" "Yawwa y'ar albarka kira min ita, akwai magana yau ai", Bata tsaya jiran jin sauran abunda Asiyar ke cewa ba tayi gaba ta shiga d'akin Abban. Zaune ta iske Mama sai wani iyaye take ma Abba yana biye mata. Ganin Maryam ta shigo d'akin yasa Mama dubanta tana jiran jin miya kawota?. Maryam ta ce "dama Mama Inna Asiya ce tazo ", "Kai ai ko nasan da zuwanta, bari jeki gani nan zuwa", Maryam na fita Mama ta dawo da dubanta wajan Abba tana cewa "kaji abunda nake gaya maka ko?, dama na ce ma zata sake dawowa ne, domin tana so ayi abun da wuri" Abba ya nisa ya ce "kin ce yaron bashi da lafiya zata je kula dashi ne, za'a d'aura auran domin gudun faruwar wani Abu?, to amma a can zatayi karatu ne ko kuwa?", Kallon takaici Mama ke aikama Abba, yadda yake shirin mata musu, duk da ta basa abinci da abunda Malaminta ya bata, kuma ya ci, dan yana kanci ma. Ta ce "eh man zasu sata mana, babu abunda zata nema ta rasa. Ai kaga gara ma taje can tayi mai dalili, kai ka huta da kashe kud'inka akanta. Kuma tazo karatun ta kasayi kayi asarar kud'i akanta, tunda kasan ai ba k'ok'ari gareta ba, asarar kud'i kawai zakai, gara can taje tayi karatun acan" "Kuma fa hakane Hajara. Ai kawai na amince, ko gobe suka zo za'a iya d'aura auran babu wata damuwa" Wani almurin murmushi ta saki. Tana cewa "yawwa Abbansu Maryam shi yasa fa nake k'ara sonka, akwai saurin fahimtar mutum. Bari naje wajan Asiyar na sanar da ita abunda ake ciki" Tana gama maganar ta fice daga d'akin. "Ahh ahh Asiya yada zama waje kuma?, ga d'aki" Cewar Mama data fito daga d'akin Abba, ta iske Asiya zaune a waje. Asiya ta ce "wallahi kawai zama nayi nida Maryam muna d'an tab'a fira, ina Khadija ne ni kam?, ban ganta ba" Mama ta ce "wallahi Khadija sun fita ita da wadda zata aura sunje wata sayayya ne" "Ahh kai Masha Allah, kice an samo mana siriki kenan?" "Ai kuwa dai, na nunawa a sa'a kuwa" "Ayyiririiii, kice mun kusa zuwa aikin hajji?". Dariya Mama ta saki tana kamo hannun Asiya suka shige d'aki Mama na cewa "ai kuwa dai, gamu can a k'asa mai tsarki" Zama Asiya tayi tana cire gyalanta ta k'ara natsuwa ta ce "kinga akwai fa magana a bakina sosai", Dariya Mama ta saki tana cewa "tunkan kizo na riga da na gama da matsalar, domin nasan zancan daya kawo ki" Cike da d'unbin mamaki Asiya ke duban Mama, ta kasa hakuri ta ce "kamarya ban fahimta ba?" "Hmmm Asiya kenan, Malami na nasa yayi min duba, har ya sanar dani zuwanki, da abunda zaki zo min dashi, tunkan kizo, na riga da na sanar da Abbansu Maryam, akan wannan zancan, kuma na gama shawo kansa, kawai abunda zance miki shine su turo ayi auran kawai" Rik'e baki kawai Asiya tayi tana kallon K'awar tata, shaid'aniya uwar shaid'anu. Yo idan ba shaid'aniya ba, waye zai haka?. Kamo hannunta Mama tayi tana fiskewa ta ce "ke karkiyi wani mamaki fa, kamar kin manta wace ni?". Ture komai Asiya tayi tana cewa "tunda kin gama da wannan, kema tukaicinki babba ne, idan abun ya kasance" "Baki da damuwa komai zai kasance yadda muke so". Dariya suka saki a tare harda tab'a hannu. *Copa Cabana Estate Lokogoma District Abuja Nigeria* Waya ce manne a kunnan Momy suna waya da Asiya. Daga cikin wayar Asiya ta ce "Hajiya an gama komai fa, yanzu haka wakilanku kawai zaku turo a d'aura auran, ku tafi da amarya" "Da kyau, haka nake sonji. Zan turo miki naira million biyar, ki d'auki naira million biyu, kiba wacce tayi hanyar abun ya yiwu, naira million d'aya, shi kuma Abban yarinyar ki basa cik'on naira million biyun" Wata shewa had'e bud'a Asiya ta saki tana cewa "saike Hajiyarmu, uwar gida, a gidan Alhaji Bin Muhammad daga ke ba k'ari, Allah dai ya biya". Dariya kawai Momy ta saki tana kashe wayar. Ba'a jima ba kuwa saiga message na account number na Asiyar. Nan take ta tura mata kud'in gaba d'aya. Zaune take a gaban Daddy bayan ta gama koro masa jawabin abunda take so ayi. "Daddyn Salman, ina ganin yarinyar ita ce ta dace da zama da Salman, domin yarinyar tana da hankali da tunani, zata zauna dashi tsakani da Allah badan komai nasa na duniya ba, domin duk sauran da yake aura duk dan kud'insa ko kyansa ke rud'arsu". Daddy ya aje wani biro dake hannunsa yana rubutu a wasu takardu ya ce "kina ganin ita yarinyar ba'a danne mata hak'k'inta ba?, kin sanfa yadda rayuwar yaron nan take ciki" Kamo hannun Daddy Momy tayi cike da kissa ta ce "ba wani danne hak'k'inta da akai. Hasalinma taimakonta akai, saboda ita kanta tasan ko a hanya bata isa ganin Salman ba, yaro mai kud'i ga kyau ga nasaba, komai ya had'a, kawai wannan ciwon ne ke basa matsala a rayuwa, kuma da sannu komai zai shige, idan komai ya wuce ita ce da riba nake gani ai" Wani murmushin jin dad'i Daddy yayi, yaji dad'in yadda ta fahimtar dashi, kuma ya fahimta sosai. Inda daga k'arshe ya ce "to ita yarinyar y'ar ina ce?, yaushe kuma kike ganin za'aje domin tabbayo auran nata?" "Y'ar Hadejia ce, kuma tabbayo aure duk bai taso ba, d'aurasa kawai za'ai, domin duk na gama da wannan, yanzu haka Abban yarinyar yasan da maganar, ku kawai yake jira" "Ai shikenan tunda abu yazo gidan sauk'i. Zanje da kaina tare da wasu manya dana aminta dasu a d'auro auran zuwa gobe insha Allahu". Cike da farin ciki Momy ta baro part d'in Daddy. Tafe take tana maganar zuci. "Hmm Alhaji kenan, kaifa gani kake kamar son d'anka nake ko?, ina duk duniya ba abunda na tsana yanzu kamar shegen yaron can naka, amma da sannu zan kawo k'arshensa". *NANAH* POV Wani irin sansanin y'an Ta'adda ne su Auta suka tsinci kansu ciki. Auta ba abunda yake sai kuka yanata neman inda zai hangi Nanah. An zube su wani waje duk ciyayi ga rana ta kwanyare. Kowa ka gani wajan sab'anin y'an Ta'addar cike suke da tashin hankali. Kamar ance Auta ya waiga ya hango Nanah dake d'aure a jikin wata bishiya har yanzu a sume take bata farka ba. Gashin kanta ya sakko ya rufe mata fuska. Da gudu Auta ya nufi inda take, yana aikin kiran sunanta. Wani d'an Ta'adda ne ya matso ya kwasa masa tsawa, yana cewa "kaiii ina zaka je haka?, koma inda kake kar yanzu na fasa maka kai da wannan Bindigar" A tsorace ce Auta ya ke duban D'an Ta'addar. Amma duk da haka tsaye yake inda Nanah take ya rik'e tsintsiyar hannunta sai jijjigata yake. A hankali Nanah ta fara motsa hannun nata, kamin komai nata ya fara dawowa dai-dai, dashi-dashi take ganin mutane, hatta muryar Auta sama-sama take iya jiyota, kamin ta ware idonta akan Auta. Auta ko jin Nanah na motsa hannunta yasa shi sakin murmushin k'arfin hali yana sake kiran sunanta. Kallon Auta take kamar wacce ta samu tab'in hankali. Kamin komai a hankali ya fara dawo mata, duk abubuwan da suka wakana a daran jiya. Tana gama tunanowa ta fashe da wani irin kuka mai k'arfi jikinta na rawa, ta kama leb'en bakinta ta cije tana durzar kuka. Ganin yadda take kuka yasa Auta ma fashewa da kuka. Wani daga cikin y'an Ta'addar ne ya k'ara matsowa inda suke, bai tsaya wata-wata ba, ya damk'e gashin kan Nanah ya jashi zuwa baya da k'arfi, har saida ta saki wata k'arar azaba. Fuskarta ce ta bayyana. Hawaye duk sun b'ata mata fuska. Cike da rashin imani yake kallonta ya ce "zakiyi mana shuru a wajan nan, ko sai na kashe wannan bakin naki, maima mutane kukan banza?" Wani irin bak'in ciki ne ya rufe Nanah, data na dama wallahi saita kashe duk wani d'an Ta'adda dake wajan yanzu, to amma bata da damar hakan. Sakinta yayi yana maido dubansa inda Auta yake. Ya wani k'ankance ido ya ce "ni wai miye ma anfanin tahowa da wannan yaron?, ai da an rage masa wahalar duniya, an aikasa can kiyama". Zare ido Nanah tayi tana jin wani sabon tashin hankali na saukar mata. Tafiya suka farayi suka bar wajan da Nanah take. Suna magana, ganin haka yasa Auta rungume Nanah dake d'aure kamar wata akuya. Ba abunda y'an Ta'addar suke sai shan tab'a da giya. Ga y'an matan da suka dad'e da satowa suna faman dafa masu abinci, wasu ma sun maida su k'aruwan k'arfi da yaji, sun maida su kamar wasu matansu. K'iri-k'iri sai kaga k'aton gardi, daya ji sha'awar mace, zai d'auki mace kamar kayan wanki yayi cikin wata rufma da ita, ya biya ma kansa buk'ata, ya kuma tashi ya zuge wandonsa. Yadda suke afka masu kamar wasu dabbobi. Yadda Nanah ta lura da yawan matan wajan suna sato sune kawai dan su rink'a masu bauta, da biyan buk'atarsu kawai. Hakan yasa Nanah shiga wani sabon tashin hankali marar musaltuwa. Motsi kad'an tana nanik'e da Auta, wadda ji take kamar ta mayar dashi ciki. Wata irin yinwa ta fara addabar wa'inda suka sato, ciki harda Auta, ya fara kuka, yana gaya ma Nanah yinwa yake ji. Dan rabonsa da abinci tun jiya cikin dare gashi har gare ya waye rana na neman fad'uwa. Wasu hawaye ne suka shiga zuboma Nanah na tausayin Auta, ita dan ita zata iya zama a haka, zata iya jurewa na d'an wani lokaci, kai zama ta iya hakura har zuwa wata safiyar. Shifa?, yaro ne. Gashi anbi an wani d'aure mata hannu, tana son rarrashin Auta, tama rasa wacce kalma zata fara basa hakuri da ita. Kukan da Auta yake ne ya fara isar y'an Ta'addar. Hakan yasa wadda Nanah bazata tab'a manta sunansa ba, Mai suna Tajo ya nufo inda suke. Duk duniya idan akwai wadda ta tsana to bazai wace wannan Tajo ba, shine ya rabata da farin cikin rayuwarta, wato Innarta, shine ya ruguza masu rayuwa, shine ya rabasu da jigwan rayuwarsu. Da tana da dama saita kashe Tajo kamar yadda ya kashe Inna. Da jajayen idonsa yake kallon su Nanah, ganin irin kallon da Nanah ke aika masa dashi, na tsananin tsana da fusata, yasa Tajo shekewa da wata dariya yana nuna Nanah da hannunsa. Can ya tsagaita dariyar yana kallon Nanah da ba alamar tsoro yanzu a cikin idonta. Ya ce "keee uban mi yaron nan yake so ya ishemu da kuka?". Shuru tayi bata da niyar magana ga Auta daya k'ara balun d'in kukansa. Haushi abun ya bama Tajo, hakan yasa ya d'auke Nanah da wani gigitaccan mari. Wadda yasa taga giftawar wasu taurari. Duk da haka taji zafin marin daya kai mata, amma tayi shuru tana kallonsa da jajeyen idonta da suka kad'a sukai jawur. Ganin fa bazata tanka masa ba, yasa Tajo jawo Auta ya daka masa tsawa yana cewa "kaii kayi ma mutane shuru ko yanzu nasa wuk'a na yanka maka wuya wallahi" Auta bai daina kuka ba, majina da hawaye duk sun b'ata masa fuska. Wani dogon tsaki Tajo yaja yana shafa sumar kansa, ya d'an daga kansa sama, sak'on d'aya biyu....... Kawai ya kaima Auta wani bugu a saman kai, nan take Auta ya zube a sume. Wani sab'on kuka ne ya kufce ma Nanah tana kiran sunan Auta iya k'arfinta, duk tunaninta ko mutuwa yayi. Cikin muryar kuka take magana tana kallon Tajo cike da tsana ta ce "ku sani Allah bazai tab'a kyale ku ba, Allah saiya isar mana akan zaluncin da kuke mana. K'aramin yaro ma baku kyale ba, tsabar baku da imani, Allah ya isarmu wallahi bamu yafe ba". Dariya Tajo ya saki yana matsowa inda Nanah take, ya damko wuyanta yana cewa "au ashe kina magana y'an mata?, na d'auka ai kurma muka d'akko. Dama mu ai bamu ce ku yafe ba. Ya ishe mu da kukan banza ne, shine na sashi yin baccin dole, kin gane?, zai farka ai ba mutuwa yayi ba, amma ki sani ya sake mana irin haka, to zaibar duniya ne gaba d'aya. Ya kamata ki kula, bama son damuwa ne". Wani abu mai d'aci Nana ta had'iye a mak'oshinta tana bin Tajo da kallo. Ji take inama tana da dama data shak'e masa wuta shima harsai ya daina numfashi. Cikin dare Nanah tajiyo kukan Auta daya farka, sanyin dake cikin dajin ne ya farkar dashi, ga kuma inda yake kwance tsinnaku duk sun cijeshi a jiki. Da sauri Nanah ta kira sunansa a hankali. Da lalube ya k'araso inda Nanah take, yana zuwa ta rufe masa baki da tafin hannunta data samu Tajo ya kwance mata shi, d'azo daya gama gaggaya mata magana. A hankali Nanah ta ce "dan Allah Auta kayi shuru, kayi hakuri kaji?, zuwa safiya za'a baka wani abu kaci, kana kallo mutanan nan basu da imani fa, kana so ka mutu ne?". Da sauri Auta ya girgiza mata kai. Ta ce "to yawwa ka daina kuka idan baka so kaji?". Ba yadda Auta yayi dole tasa yayi shuru ya mak'ale a jikin Nanah. Suna haka, sukaji ihun wata matashiyar yarinya, daga jin yadda take ihun tana neman taimako, zaka san cewa so ake a keta mutumcinta ne. Yadda Nanah ke jin yarinyar na cewa "wayyo Allah, ku taimaka min zai kashe ni, na shiga uku ina zan kai wannan mutunin, zai lalata min rayuwa dan Allah ku ceceni". Waro idonta Nanah tayi tana kallon wata ruffa da abun ke faruwa hasken fitila ta gani a wajan, ihun yarinyar na fitowa daga cikin rufar. Tana iya jiyo yadda suke kokowa da yarinyar, tana son kwance kanta. Tana jin shi kuma yadda yake ta kai mata maruka ba k'ak'k'autawa. Allah sarki yarinyar duk da irin dukan da yake kai mata so kawai take ta kwaci kanta, sai kuka take tana kiran azo a taimaketa. Ganinfa tana son b'ata masa lokaci, gashi duk ta ji masa ciwo yasa ya harzuk'a bai san sadda ya d'akko bindiga ba ya sakar mata harsashi. A mugun rud'e Nanah ta toshe kunnuwanta had'e da k'ara rungume Auta daya fasa wata gigitacciyar k'ara yana sumewa a jikin Nanah, domin harga Allah ya mugun tsorota sosai. Nanah tama rasa wane hali take ciki, duk ta rud'e ta fice daga yaccinta. Ga Auta da bata jin motsinsa a jikinta, ga yarinyar da tana da tabbacin ita ce aka halba. Tana iya jiyo yadda D'an Ta'addar ke ta'asarsa saman kan yarinyar duk da halbinta da yayi, amma tsabar mugunta da rashin imani a haka ya afka mata..... _________________________ Mike shirin faruwa ne da Salma wai?, ya rayuwar Salman zata kasance a nan gaba ne wai?, shin Momy wacce irin zuciya ce da ita ne ta rashin imani?, kaiii wannan Mama ma akwai y'ar kwal uba fa🤭. Shin wai tsaya ma Hajiya zata amince da aurar da ake son d'aura ma d'iyarta wadda bata san dashi ba?, Yaya Salma zata ji idan taji an d'aura mata aure da wani, waninma wadda bata tab'a gani ba?...*KAIII JAMA'A AKWAI CAKWAKIYA A BOOK D'INGA, NA TSAYA A NAN DOMIN NIMA INA SON SANIN DUK AMSOSHIN NAN* _________________________ *To a nan na kawo k'arshen Free pages* *Game son ci gaban book d'in nan zai biya D'ARI BIYAR NE KACAL* Ta wannan account number d'in. 8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank Saika turo shaidar biya ta wannan number d'in 08130479973