*🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* Masarauta Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🎠ELEGANT ONLINE WRITER'S🎠 *Page~1* بسم الله الر حمن الر حيم A WANI YANKI NA INDIA. KUDU MASO YAMMA.. Gudu take na fitar hayyaci tana k'wala masa kira da iya k'arfin ta bata da burin da ya wuce ta cimmasa tana zuwa gaff dashi wata gagarumar iska me had'i da guguwa ta fara kad'awa. Hakan yasa yayi taga-taga k'afar sa ta zame yayi baya ya fad'a k'asa. Cikin ihu ta furta sunan sa tana k'ara waro gwara gwaran idanun ta, cikin sanyin jiki da wani irin taku ta k'arasa wajen tana lek'awa, ganin da gaske ya fad'a d'in yasa ta dafe k'irjin ta tana wata irin shak'uwa idanun ta suka k'ara firfitowa ko k'yaftawa basayi,, zubewa tayi a wajen kamar sumammiya ta durk'ushe akan k'afafunta. Wani mutum ne ya zagayo ta bayan ta ya kama damtsen Hannun ta ya fara janta k'irrrr kamar ba mutum. Babbar Harabar TAJMAHAL PHURLA. Cike take da mutane iri daban daban bayi da hadimai haka ma dogarai mawak'a da masu bushe bushe. Ko ina kid'a ne ke tashi da wata irin busa me d'auke da wani take da wani kyakkyawan salo da k'warewa. Rukunin y'an mata sun sha ankon riga da wando burguza burguza sunyi k'awanya a tsakiya suna rawa da karairaya cike da k'warewa da kuma sabo. Gefe guda kuwa sai watsi ake da furanni da garin fure da kuma kaloli. Da alama ana gudanar da wani babban shagali ne a wannan masarauta. A cikin Mahaal a hawa na bakwai. Wani k'ayataccen d'aki ne wanda yaji ado irin na sarauta ta ko ina, acan ciki, Zaune take bisa wani katafaren lilo yana lila ta cike da isa gami da izza ba'a iya ganin fuskar ta sakamakon juya baya da tayi. Gefen ta kuwa wata kyakkyawar Hadima ce tsaye kanta a k'asa tana wasa da yatsun Hannun ta, cikin sanyi da kuma zak'in murya tace, "Hazoor Ki yafe ni, amma masarauta ta cika ta ko ina ke kawai ake jira" Ba ta ce komai ba sai mik'ewa da tayi cikin wani irin salon mulki da gadara. A take fitinanniyar surar ta ta bayyana kanta. Budurwa ce me ji da lokacin ta, Kyakkyawa ce ta azo a gani jajur da ita kamar ka ta'ba jini ya fito jikin ta ko ina kayan ado ne na gwal da azurfa sark'ok'i duk wani sassan jikin ta babu inda babu su hakan yasa duk wani motsin ta sai kaji k'arar su bare kuma idan ta taka, ta had'e cikin wani Saarie ruwan ganye, kore, yayi matuk'ar kwanciya a jikin ta tayi kyau kamar ba gobe kasancewar ita d'in kyakkyawa ce, babu wata kwalliya a fuskar ta sai kwalli da yaji bajau a idanun ta hakan ya k'ara musu kwarjini da wata irin barazana. Wannan hadimar ta kalla, take ta sako wani shu'umin murmushi ta kauda kai cike da izza, a hankali ta lumshe idanun ta tareda motsa bakin ta alamun magana, cikin dadd'ar muryar ta ta furta Arjulaa??? Wata tsuntsuwa fara tass ce ta nufo inda take suuuu,, itama kanta tsuntsuwar kyakkyawar gaske tana zuwa ta sauka akan kafad'ar ta tana wani kuka tareda karkad'a jela, hakan yasa ta saki murmushi. Kamar me tsoron k'asa ta fara takawa a hankali idan tayi taku d'aya sai ta girgije sannan zata k'ara d'aya a haka tayi gaba, Hadimar tabi bayan ta kanta a k'asa. Hannun tasa ta janye tufafin jikin ta ta d'anyi sama dashi sakamakon jan k'asa da yake sannan ta sako k'afar ta a wajen d'akin. Tin daga k'ofar d'akin sojojin masarauta ne rerass baka iya gano iyakar su, suna ganin ta na farko yayi wata irin busa, daga can ma wani ya k'arayi haka abun ya d'auka har ya fito harabar masarauta wane gayawa wane, ai kuwa take Salo ya k'ara canjawa yanayin kid'i da busar da akeyi ya canja zuwa wani salo me bala'in d'aukar hankali. Da takunta irin na wahainiya har ta fito harabar duk inda ta ratsa zubewa suke kan guiwoyin su tareda sunkuyar da kansu k'asa su k'ame kamar abu mara numfashi har sai ta wuce tabar wannan sashin sannan zasu mik'e, mata da maza manya da yara haka sukeyi. daga can wani d'an bene aka tanadin gurin zaman ta ita da na kusa da ita, kai tsaye can ta nufa kafin ta zauna ta d'aga musu hannu a take gurin yayi tsittt kamar ba sune suke hayaniya ba. Sihirtaccen murmushin ta ta sakar musu. Hakan yasa kowa da yake gurin murmusawa sannan suka dunk'ule hannayen su na dama suka d'ora kan k'irjin su gami da d'an rank'wafawa, kansu a k'asa. Jinjina kai tayi taja wani yalwataccen numfashi. Wanda yake da alhakin sanar da umarnin ta yayi busa hakan yasa kowa ya d'ago, masu kid'e-kid'e suka fara kid'a da busa me sautin taken ta. Zama tayi ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya, tana kallon ko ina da fararen idanun ta,, bayan wani lokaci ta tuna da Hadimar ta da take a tsaye kallon ta tayi fuska a sake tace, " Farhanaa zauna" Wadda aka kira farhanaa ta sadda kai k'asa cike da ladabi tace, "ina godiya Hazoor" Bata sake kallon inda take ba taci gaba da kallon mutanen ta, wato mutanen masarautar Phurlaasirie. Bayan an d'auki lokaci ana wannan sai aka tsagaita. Yayin da idon kowa kuma ya dawo kanta. Wata kuyanga ce ta turo wani abun saka jarirai na gargajiya wanda yasha ado ganyayyaki kala kala jaririn sai baza ido yake yana kallon kowa, a gaban ta aka ajiye shi kuyangar tayi gefe tana me sunkuyar da kanta k'asa. Wasu mace da namiji ne suka k'araso duk kansu yana k'asa suka kwashi gaisuwa ta musamman sannan sukayi gefe suka tsaya, cike da ladabi namijin yace, "ranki ya dad'e wannan d'an mu ne nida matata wanda a dalilin haihuwar sa ne kika shirya mana wannan gagarumin shagalin, mun gode da wannan karramar Hazoor, wannan d'a mun sadaukar dashi gare ki duk abunda kika yanke a kansa mun amince ba dan kanmu muka haifeshi ba sai dan ke mun mallaka miki shi ranki ya dad'e. Kyakkyawan murmushi tayi tareda mik'ewa tayi tsaye akan jaririn,, ido ta zuba masa shima ya zuba mata ido suna kallon-kallo har wani lokaci kafin tasa hannu cikin nutsuwa ta d'auke shi ta rungume, kallon iyayen sa tayi cikin k'asaitacciyar muryar ta tace, " menene Lak'abin sa??? Uwar yaron tace, "ranki ya dad'e yanzu ba namu bane naki ne duk hukuncin da kika zartar akan sa ya zama dai-dai ko da kuwa yanka shi zakiyi ki sadaukar da jinin sa ga abun bauta" Baban yaron yace, "ranki ya dad'e mu mun kasance bayi ne a wannan masarauta tin iyaye da kakannin mu kuma har yau bazamu gajiya da hidimta muku ba bakin rai bakin fama nayi alk'awari ga abun bauta zan mutu ina me bautawa wannan masarauta" Murmushi tayi ta d'an yi taku biyu kafin ta juyo, girgiza kai tayi tace, "na k'aunaci yaron nan dan kuwa yana da k'warin zuciya tamkar mahaifin sa bazan bawa kowa shi ba shi d'in mallaki na ne kamar yadda kuka mallaka min shi dan haka zan rad'a masa suna yanzu. Share hawaye mahaifiyar yaron tayi har cikin ranta tana jin kewar d'an ta wanda ba lallai ta sake ganin sa ba. Ita kuwa lumshe ido tayi tana motsa baki da alama addu'a takeyi bayan ta kammala ta hura masa iskar bakin ta a kunne,, hakan yasa yaron ya k'ara zazzaro ido tareda k'ank'ame jikin sa, bud'e idon ta tayi ta zubawa yaron su, tana murmushi tace, " AbdulKareem" Da sauri baban yaron ya d'ago kai yana wani irin murmushi tareda k'walla jikin sa har rawa yake ya mai-mai-ta AbdulKareem?? Zubewa yayi kan guiwoyin sa yana kuka yana cewa, "mata ta na gode miki da kika haifa min AbdulKareem, Ranki ya dad'e kin biyani ubangijin AbdulKareem ya saka miki da mafificin Alkairi. Uwar d'an kuwa jin sunan da d'an ta yaci yasa ta dena sharar k'wallar bak'in cikin rabuwa da shi , farin ciki ya wanzu a tattare da ita itama ta zube a k'asa tana mik'a godiyar ta. Fure ta dank'a ta watsa musu tana murmushi tace, " ina muku fatan samun wani d'an bayan wannan kunyi babbar sadaukarwa bayan tarin shekarun da kuka samu ba tareda kun samu d'a ba kuma kun haifa kuka sadaukar dashi gare ni tabbas kun cancanta da komai a gareni Udday" Mik'ewa Udday yayi cikin d'aga murya yace, "ku saurara kowa ya maida hankali,,, ni Udday d'aya daga cikin bayi kuma y'an bayi na wannan masarauta na sadaukar da d'a na da na haifa ga Uwar wannan masarauta, Uwa me adalci ta sanyawa yaro suna AbdulKareem!!!!!!!!!!! Sai da wajen ya girgiza gaba d'aya saboda fad'ar wannan suna take wasu suka fara zubda hawaye wasu kuwa razani da firgici gami da rud'ani ya d'arsu a zukatan su, wasu kuwa jikin su har kakkarwa. Wani tank'amemen faranti wanda aka lullu'be da wani k'yalle me ado da Hatimin Phurlaa Mahaal ta kar'ba a hannun wata baiwa tana murmushi ta mik'owa Udday sannan ta kar'bi d'ayan ta bawa matar sa. Farin ciki da murna ba kama hannun yaro,,, ba su kad'ai sukaji dad'in wannan kyauta ba har da sauran jama'ar wajen,, take aka k'ara rud'ewa da fad'in, " Godiya ta musamman da jinjinar ban girma ga Uwar Masarauta" Shagali akeyi sosai ko gajiya basayi. Mik'ewa tayi da zummar komawa tana rungume da AbdulKareem, ta fara tafiya kenan wata murya ta dakatar da ita, cikin d'aga murya ba tareda tausasawa ba ya kira sunan ta. "Mahalakhshmie??????? Juyowa tayi tana waro masa idanu cikin wani mugun zafin nama ta d'auke shi da wani gigitaccen mari, cikin tsawa da kuma kwarjini tace, " MAHARANIE MAHALAKHSHMIE " sassauta murya tayi tak'ara cewa, "ka sai ta harshen ka ba'a kiran sunan Uwa haka kawai" K'asa yayi da kansa zuciyar sa na rad'ad'i kafin yayi wani yunk'uri yaji an sark'e k'afafunsa da wasu mazajen sark'ok'i ido ya zazzaro yana kallon mahaifiyar sa wadda itama idanun ta suke warwaje. Da sauri dattijuwar matar ta k'araso ta durk'ushe a gaban ta cikin k'ask'antar da kai tace, "kiyi hak'uri ki yafi d'a na k'uruciya tana damun sa shiyasa kiyi hak'uri Mhaa" Da hannu tayi musu alamar su sake shi. suka kwance shi suka ja baya. Nuna shi tayi da yatsa tace, "RamRaj shine kawai sunan ka rik'e matsayin ka" K'ara yin k'asa da kai yayi tareda cewa "zan kiyaye" (Kuci gaba da bibiya ta a cikin wannan k'ayataccen labari domin jin ya abun ze kasance. Wacece Maharanie mahalakshmie?? Shi kuma RamRaj waye shi?? Meyesa baya girmama sunan ta kamar kowa?? Shin meye yasa ta kasance uwar masarauta duk da kasancewar ta k'aramar yarinya budurwa?? Wannan sunan da ta rad'awa yaron Udday sunan waye?? Meyesa wasu suke farin ciki dashi wasu kuma suka razana?? Waye shi in ya girma??? Duk amsoshin suna cikin gundarin labarin sannu sannu bata hana zuwa,ku biyo ni domin jin yadda zata kasance..) Taku. INDO Ce *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* Masarauta Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~2* بسم الله الر حمن الر حيم Cikin tsantsar izzar ta taci gaba da tafiya har ta koma sashin ta, kafin ta zauna ta mik'a Abdullkareem ga Hadima Farhanaa ba tareda tayi magana ba. Hadima Farhanaa tace, " Maharanie?? Umarnin ki nake jira" Murmushin gefen baki tayi ta tsurawa Arjulaa ido ba tareda ta kalli Hadima Farhanaa ba tace, "ki kula dashi " Hadima Farhanaa ta kalle shi sannan ta kalli Maharanie tace, "kiyi min Hak'uri Hazoor amma sai naga kamar abun yayi min yawa in kula da jariri in kula da mamallakiyar jaririn, bazan iya ba" Fuska a had'e ta kashe ta da idanun ta masu bala'in kaifi, taku d'aya biyu tayi kafin ta juyo,, ta kuma juyawa sannan tayi magana cikin k'asaitacciyar muryar ta tace, "kiyi duk yadda zakiyi dashi ko da bazaki iya ba in yaso ki jefa shi a ruwa ya tafi dashi, sai ki sani ko lafuci ya samu yaron nan ranki ne fansa" Ido Hadima Farhanaa ta zaro a razane tace, "Hazoor ki gafarce ni da alamu an samu rashin fahimta ne,, ina nufin ba nice zan rene shi da kai na ba amma, Maharanie ki dena saurin ambaton kisa kai tsaye hakan yana girgiza jikima ta" Y'ar dariya tayi tana ci gaba da takawa ta k'arasa wajen taga tana lek'en k'asa gami da shak'ar kyakkyawar iskar da take kad'awa kamar me koyon magana ta tattaro kalmomin tace, "ke kad'ai ce kike da nasara a zuciyar Maharanie ina jin ki tamkar k'anwa ta ta jini, shiyasa nake iya hak'uri da duk wani shirmen ki ba dan haka ba da tuni na hukunta ki hukunci me tsauri akan abubuwa da dama, Ki nemi amintacciyar Hadima ki bata renon Abdulkareem sannan ki kula da ita da duk wani takunta bana so wani mummunan abu ya faru dashi hakan ze sa rayuka su 'baci, wannan nake nufi" Murmushi Hadima Farhanaa tayi tace, "ina Godiya Uwar masarauta, nasan matsayi na a gurin ki ya wuce na kowa hakan ne yasa nake da damar fad'a miki duk abunda yazo kan harshe na ba tareda tsoro ba dan nasan in anjima zan kasance me nutsuwa ko Maharanie??? Nima tamkar Yaya ta nake jin ki, Ni kad'ai ce kike zama kiyi doguwar magana dani, ni kika amincewa na shiga hurumin ki ta ko wane fanni, Ni kuwa me ze hana nayi miki duk abunda kika so?? Na d'auki alk'awari wa wannan masarauta zan kasance amintacciyar ki komai wuya bazan ta'ba juya miki baya ba" Murmushi Maharanie tayi tasa tafin hannun ta ta shafi kumatun Hadima Farhanaa, juya gwarazan idanun ta tayi zuwa sama kafin tace, " ki d'auka cewa Abdulkareem d'a na ne wanda na haifa tareda miji na, irin wannan kulawar nake so ya samu a ke'bantaccen gurin da ba kowa ne ze san inda yake ba, nima zan kasance me bibiyar sa a lokacin da ya dace" Hadima Farhanaa tayi k'asa da kai tareda cewa, "ubangiji na ya sakanya miki da Alkairi Maharanie yadda kika ce haka za'ayi" Daga haka ta fice ta nufi sashin Hadimai dan kuwa ita tasan wadda zata bawa shi komai ya tafi dai-dai. Wata dattijiwar Mata ce tana zaune tana sa'kin wani abu na zaren itaciya, tana ganin Hadima Farhanaa ta mik'e tana dai-dai ta kanta tareda cewa, " sannu Hadimar Hadimai a gaida Hannun daman Uwar marayu" Murmushi Hadima Farhanaa tayi tace, " Uwar Hadimai Urmiey sannu da gida,, rik'e wannan jariri na Maharanie ne" Ido Uwar Hadimai ta zaro tace, "Maharanie Mahalakshmie??? Jinjina kai Hadima Farhanaa tayi tace, " AbdulKareem shi d'in jinin Udday da Surekha ne iyayen sa sun kasance masu bautar gunki shi kuma ze kasance Mabiyin Addinin Islam ne ubangijin Da nake bautawa shima shi ze bautawa" Kar'bar AbdulKareem Uwar Hadimai tayi tana cewa, "Barakallah AbdulKareem ibni AbdulKareem?? Masha Allah, Tinda ka kasance musulmi da hakan ya kamata na sa maka albarka duk da ni ba musulma bace, amma Hakan yana nufin kenan akwai daru a Mahaal?? Meyesa Maharanie ta aikata haka, itace tace miki Musulmi ne??? Hadima Farhanaa ta jinjina kai tace, " Maharanie tinda ta rad'a masa sunan musulmi tabbas musulmi ne baze yuwu yayi wani addinin ba bayan wannan" Uwar Hadimai Urmiey tace, "abun bauta ne kad'ai yasan abunda ke k'unshe a cikin wannan Mahaal har ma da wanda yake 'boye a zuciyar Maharanie da bainar duniya baki d'aya amma akwai alamar bayyanar wani abun me k'arfin da ze girgiza wannan Mahaal" Hadima Farhanaa tace, "koma meye nayi imani da ubangijin Amintacce Almustafha kuma nasan yana tare dani harma da Maharanie nasan baze bari mu tagayyara ba ze ku'butar da ita a ko wane irin hali domin kuwa tana yawai ta Bauta masa tana yin azumi tayi sallah duk ranar Jumu'at duk da bansan dalilin hakan ba amma da alamu akwai wani sirri ne dangane da hakan dan kuwa bayan wannan ranar bata yin wani abu da ya kasance yayi koyi da dinul'islam sai dai a wannan ranar kuma bata fashi indai har ranar tayi to zatayi wannan bautar" Uwar Hadimai Urmiey ta jinjina kai tace, "akwai k'ulle k'ulle rifaffu a wannan Mahaal dan dai ke a yanzu kika zo yarinya ce ke, amma anan gaba ma akwai gagarumar k'urar da take tinkaro mu" Sosai jikin Hadima Farhanaa yayi sanyi ta yarda da maganar Uwar Hadimai Urmiey dan kuwa tasan bazata yi mata k'arya ba kuma akwai abubuwan al'ajibi da ta kasa gane me suke nufi. Fuskar ta a rufe take hakan yasa baza'a iya gane wacece ba, da sauri take tafiya har da gudu-gudu ta nufi wani 'bangare na TajMahaal, kasancewar duk masu tsaron yankin sun sani yasa basuyi k'ok'arin tare ta ba duk da cewar fuskar ta a rufe take, Cikin wata turaka ta kutsa kai ba tareda neman izini ba. yana kashingid'e hannun sa d'auke da wani kyakkyawan kofin azurfa yana kur'bar ruwan inibi yanayi yana lumshe ido. Tsaye tayi a kansa ba tareda tace komai ba har sai da ya ankara, da sauri ya tashi ya zauna tareda bud'e mata hannayen sa alamar ta rungume shi, fad'awa tayi jikin sa tana murmushi. Ya ajiye kofin tareda gyara mata zama a jikin sa ya fara lalubar ta yana wani mugun murmushi, cikin wata murya me cike da mugunta yace, " gaya min me yake faruwa?? Hannu tasa ta shafi sajen sa kafin tace, "TajMahaal ta rikice saboda Maharanie Mahalakhshmie ta rad'a wa yaro AbdulKareem kowa yana cewa meye fa'idar hakan, ina ganin dama ce ta zo mana cikin sauk'i da zamu iya juya zancen" Ture ta yayi daga jikin sa a burkice ya mik'e yana cewa, "Me ne??? Kika ce ta rad'a AbdulKareem????? Meyesa!????? Ya jefo mata tambayar cikin tsawar da sai da ta razana. "K'warai yaron Udday yaci wannan sunan" Jingina yayi jikin garu yana maida numfashi a take wani gumin wahala ya shiga keto masa, ya lumshe idon sa ya bud'e sannan yace, "meyesa ta kasa sallamewa kanta wannan masoyiya?? Wadda ya kira masoyiya ta gyara zama kafin tace, " dad'i na da magajin karaga saurin fushi, da kayi shiru baka firgita ba da sannu zakaji mafita ta fara zuwar maka cikin tunanin ka" Dawowa yayi ya zauna kusa da ita cikin salon yaudara ya rik'o hannun ta yana d'an murzawa cikin sassanyar murya yace, "fad'a min menene?? Murmushi tayi tace, " zamuyi amfani da hakan mu jefa rud'ani cikin zukatan mutane ta yadda zasuji sun tsane ta" Yace, "kin kawo magana yaci ki samu kyauta me kike so na baki?? A kunne ta rad'a masa kafin suka kwashe da dariya sannan suka ci gaba da shirya yadda zasuyi su rusa Maharaniey. Idanun ta a lumshe suke yayin da take k'ok'arin d'aure gashin ta da wata kyakkyawar sark'ar azurfa har ta kammala, Hadima Farhanaa tana gefe ta zuba mata ido har ta gama sannan tace, " gaskiya Maharanie ke kyakkyawa ce" Murmushi kawai tayi ba tareda tace uffan ba. Hadima Farhanaa taci gaba da cewa, "Hazoor kenan yanzu ina zakije??? Jin batayi magana ba yasa Hadima Farhanaa ta canja magana dan kuwa tsananin baiwar surutun da Allah yayi mata baze barta tayi shiru ba. Cike da son k'arin bayani Hadima Farhanaa tace, " Maharaniey?? Shin meye dalilin da yasa kike hidimtawa Addinin muslumci lokaci lokaci??? Sannan kuma waye Abdullkareem?? Akwai abubuwa da dama wanda na kasa fahimtar su daga gareki har sai yaushe zakiyi min bayani?? Kin barni a cikin duhuwar da na kasa gane gaba da baya" Kamar baza tayi magana sai kuma ta murmusa sannan tace, "baya tarihi ce gaba kuma gwagwarmaya, gani yafi ji dan haka ki tsammaci zuwan lokacin da zaki gani da idon ki, tarihi kuma ba abunda ya zama wajibi bane kiyi k'ok'arin yin tunanin gobe ba jiya ba dan ta riga ta wuce tariyar ta ba amfani, idan ta riga ta dawo kuwa ba lallai abun yayi kyau ba" Ta k'arasa maganar tana zuba mata idanu. Gyad'a kai Hadima Farhanaa tayi tace, "kenan dai ba dama?? Haka zan ci gaba da rayuwa kenan ba tareda nasan iyaye na ba?? Bansan wacece ni ba kenan a haka zan gudanar da rayuwa ta?? Ina buk'atar sani musamman akan mahaifi na" Kamar wadda take tsoron yin magana tace, "da haka kika taso idan kin ci gaba da rayuwa a haka ba damuwa" Mik'ewa tayi tana takun ta irin na giwa cikin nutsuwa ta nannad'e jikin ta da k'aton mayafin Sariey wanda ya sha ado ko ta ina ba ta kalli inda Farhanaa take ba sai ma kiran Arjula da tayi suka doshi hanyar fita. Da sauri Hadima Farhana ta biyo bayan su. Suna fitowa kowa ya d'au saiti. Kai tsaye wani ke'bantaccen guri ta nufa wanda kai tsaye za'a kira shi da kurkuku, cikin nutsuwa take takawa har tabar harabar kurkukun ta shiga wani d'aki bayan me gadin d'akin ya bud'e mata. K'arewa d'akin kallo ta shigayi kafin ta k'arasa a hankali ta tsugunna a wani waje. Duhun da d'akin yayi yasa ba'a ganin komai bazaka iya gane menene a ciki ba. Cikin wata irin murya kamar ba ta-ta ba tace, " Yaushe??? Taku. INDO CE.. [25/02, 10:41 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~3* بسم الله الر حمن الر حيم "Yaushe ne zakiyi magana??? Meyesa bazaki bani amsa ta ba?? Sai yaushe ze zo??? Kinyi shiru ki fad'a min!!!" Tayi maganar a tsawace. Me gadin gurin ne ya shigo da fitila yana haskawa.. Wata Mace ce a tsakure a jikin bango ta had'e kai da guiwa gashin ta yayi buzu-buzu kaca-kaca ga tarin datti, Tsawar da Maharaniey, (Sarauniya) ta daka ce tasa ta d'agowa tana zuba mata firgitattun idanun ta wanda sukayi jajur,, daka ganta ka ga mahaukaciya saboda irin d'aud'ar da take jikin ta da kuma yanayin ta. Ido ta zuba mata suna kallon kallo ba tareda tayi magana ba. Maharaniey ta k'ara da cewa, "kiyi magana kafin ranki ya 'baci, ki fad'a min mana, meyesa kika dena magana ki bud'e baki kiyi min bayani" Jijjiga ta ta shiga yi tana cewa, "kiyi magana ki fad'a min yaushe ne??? Hadima Farhana ce ta matso zuciyar ta na k'una cikin 'bacin rai tace, " gaskiya ranki ya dad'e ta wata fuskar ke muguwa ce, sai yaushe zaki dena azabtar da wannan matar??? Meyesa zaki za'ba mata wannan rayuwar?? Shin menene abunda kike so daga gareta da har kika kasa jin tausayin ta dan tak'i fad'a miki?? Wannan be dace ba" Da mamakin maganganun da Hadima Farhanaa ta gaya mata ta juyo a fusace tana zazzare mata manyan idanun ta, cikin Hasala tace, "ki rufe min baki, kece zaki fad'a min abunda ya dace ne?? Yaushe ne kika samu matsayin da zaki duba tsabar idanu na ki fad'a min irin wannan maganar??? Me kika taka ne Farhanaa???????? Hadima Farhanaa tace, " ban taki komai ba tinda ni bani da mulki bani da dalilin sa, amma gaskiya ce nake fad'a miki me wannan matar tayi miki da zaki kulle ta anan shekara da shekaru?? Kuma ace bazan fad'a ba ya kamata kiyi adalci, kullum kin takura mata da tambaya, shin ranar mutuwar ki kike tambayar ta ne ko meye???? A fusace Maharaniey (Sarauniya) ta zaro wata takobi da akayi mata mazauni a jikin bangon d'akin wanda aka gina shi da zallar dutse, Cikin tsananin Fushi ta kai mata Takobin da niyar raba kanta da gangar jikin ta ba tareda tunanin kuskuren da take shirin aikatawa ba. Wani irin gurnani matar tayi tareda yunk'urawa ta mik'e tana girgiza kanta da iya k'arfin ta tana fizge fizge, tana wani irin ihu, kamar me cutar iska. Dakatawa Maharaniey, (Sarauniya) tayi jikin ta na rawa saboda tsabar 'bacin rai, ta dad'e a haka kafin tayi wurgi da takobin ta kalli Hadima Farhanaa, cikin Izza tace, "Farhanaa ki dinga banbance matsayi na da naki, karki manta nice silar zuwan ki duniya, ki dena d'aukar kanki a wata abu ke ba komai bace face baiwa ta" Daga haka tasa kai ta fice daga kurkukun a fusace, kai tsaye bayan masarautar ta nufa bakin wani k'aton kududdufi k'oramu suna ta gudana da ruwa ta ko ina ga sanyi da yake tashi a wajen tsuntsaye sai yawo suke suna lelewa, tsayawa tayi ta rungume Hannuwan ta cikin k'irjin ta tana babbaza ido, har wani lokaci kafin zuciyar ta ta fara yin sanyi. Hadima Farhanaa ce ta k'araso wajen cike da nadamar abunda ta aikata, durk'ushewa tayi kan guiwoyin ta- ta maida hannuwan ta baya ta hard'e su, kanta a k'asa tace, "Hazoor, (Ranki ya dad'e) ki gafarce ni idan har zuciyar ki zata iya hakan, idan baki huce ba ki d'auki mataki a kaina na d'auka, tabbas nayi kuskure ama sharrin zuciya ne ba da son rai na ba, kwata-kwata bani da niyar 'bata miki rai bansan hakan zata faru bane" Lumshe ido tayi tareda sauke wani zazzafan numfashi, ba tareda ta kalle ta ba tace, "ina Abdullakareem??? Hadima Farhanaa tace, " yana nan cikin kwanciyar hankali ba abunda yake damun shi" Jinjina kai tayi ba tareda tayi magana ba ta juya ta koma cikin Tajmahaal. Da tsakar dare ta tashi ta shiga wani d'aki, babu haske sosai sai kad'an-kad'an, tarkace ne na abubuwan da suka fi kama da na tarihi, kan kujerar da ke tsakiyar gurin ta zauna ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana d'an karkad'a ta a hankali, k'arewa d'akin kallo ta shiga yi kafin janyo wata akwati ta bud'e ta, zuba wa akwatin ido tayi har wani lokaci kafin ta saki murmushi, cikin wata maraitacciyar murya tace, "yaushe zaka dawo??? Meyesa zaka guje ni?? Sai yaushe zaka zo gareni??? Murmushi tayi ta k'ara cewa, " nasan zaka zo, ko ba dad'e ko ba jima, nasan fushi kake dani, nima yanzu na canja na dawo kamar yadda kake son gani na meyesa bazaka zo ba?? Ita kad'ai take y'an surutan ta har wani lokaci sannan ta tashi ta koma turakar ta. Babbar Fadar Masarautar Phurlasirie, Cike take mak'il da jama'ar masarautar yayin da kowa yake hirar sa cikin nishad'i da walwala hayaniya ce kawai ke tashi. Shiru fadar tayi kamar wucewar tsawa, sakamakon busar da ta iso cikin fadar wadda take nuna alamar Maharaniey mahalakhshmie ta doso cikin fadar, Kowa tashi yayi tsaye ya k'ame tareda sunkuyar da kansa k'asa gami da dunk'ule hannuwan su na dama suka d'ora gefen k'irjin su, ba babba ba yaro haka tsoho da tsuhuwa haka maza da mata, kowa mik'a ban girma yake gareta. Tsaye tayi a bakin fadar ta lumshe idanun ta, cikin wata irin siga take motsa bakin ta a hankali ba tareda sautin abunda take fad'a ya fito ba, sai da ta d'auki d'an lokaci a haka kafin ta bud'e idanun ta, take suka k'ara rikid'a suka k'ara wani irin kwarjini da razanar da duk wanda yayi gigin tsoma nasa idon cikin su, Idan baka lura sosai ba bazaka ta'ba cewa tana k'ifta su ba sai in kayi mata kallon k'wak'waf hakan kuwa ba kowa ne yake iyawa ba, Cikin takun ta me cike da zallar izza da gadara ta saka k'afar ta ciki tareda k'ara rarraba idanu tana kallon mutanen da suka koma kamar basa motsi,, Har sai da ta dangana da kyakkyawar kujerar mulkin ta ta zauna sannan kowa ya zauna. Kowa yayi shiru yana tsammanin abunda ze fito daga bakin. An kwashi lokaci sosai kafin tayi magana cikin d'aga murya tace, "ina buk'atar sanin duk abunda yake gudana a ciki da wajen masarauta" Da sauri Wanda suke da Alhakin hakan suka taso tareda hawa kan tudun da ke gefen kujerar wanda aka tanada saboda su. Subbhu ne yayi gyaran murya kafin yace, " Ranki ya dad'e wasu daga cikin mutanen masarauta suna cewa sun kasa gane dalilin da yasa kika rad'awa yaro Abdulkareem sannan kuma kin enta Udday fiye da ko wane bawan ki ta dalilin haihuwar wannan yaro basu fahimci meye hakan yake nufi ba, har wasu suna cewa ko dai kina da alak'a ta jini da yaron" Jinjina kai tayi tareda zubawa Hadima Farhanaa ido. Hadima Farhanaa ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki. Kamar baza tayi magana ba sai kuma ta mik'e, ta fara takawa cikin k'asaita hannun ta rik'e da gefen mayafin Sarin ta, Juyowa tayi tana fuskantar jama'ar ta, cikin d'aga murya tace, "abu ne me kyau kaso wanda ya so ka da gaskiya, kyautatawa ga wanda ya kyautata maka abune me matuk'ar muhimmanci, kar ku manta da waye Abdulkareem kar ku zama butulu saboda wasu y'an tsirarun mutane suna son hure muku kunnuwan, ku tsarkake zukatan ku a koda yaushe kar ku bari wani yayi tasiri a zuciyar ku, ya kasance kuna yin komai da yak'ini ba tareda bin fad'ar wani ba, idan kun kasance wanda basu san waye shi ba kuyi tambaya ga iyayen ku da kakannin ku, nasan ma ba lallai ne ace baku san da hakan ba, enta wanda ya enta ka shima abu ne me kyau, be zama dole sai wanda ka had'a jini dashi ba zaka kyautatawa, akwai su da yawa wanda su d'in jini na ne amma a hakan sune suke tunzura ku dan su jefa ku cikin wasi-wasi, Komai na yiwa udday ban biya shi ba domin kuwa shi kyautar d'an sa yayi min, har gobe shi mutum ne me daraja a idon masu daraja, yaro kuma na d'auka a matsayin d'ana ne, kuma wani abunda baku sani ba, koda bana raye ku sani Abdulkareem bin Abdulkareem shine magajin karaga ta, Yafi kyau ku maida hankali wajen kishin kanku da y'ancin masarautar ku da kuma yankin ku domin dubban halittu suna son ganin bayan Tajmahaal wadda kuka taso cikin ta tin kakannin kakannin ku, Ni dai na aminta kuma na tsaya ga al'uma ta na fansar da raina gurin kare su da basu y'ancin su, ban yarda da zalumci ko nakasu a wannan masarauta ba, duk wanda yayi k'ok'arin hakan?? Yasan meye hukuncin duk wani kaifi a fadar nan" Shiru tayi tareda k'ara taku biyu zafafa tana kallon su d'aya bayan d'aya. Shiru fadar ta k'ara yi kowa da tunanin sa, jikin su yayi sanyi matuk'a domin kuwa sun san a cikin zantukan ta babu na watsarwa. Wasu kuwa furucin ta na mallakawa Abdulkareem karaga shine ya k'ara hautsina tunanin su yayin da zuciyar su ke raya musu duk yadda akayi Abdulkareem d'an ta ne. Babbar tambayar kuma itace da wane mijin ta haifi Abdulkareem????? Kuma a yaushe???? Subbhu ne ya d'akko wata takarda yana dubawa, cikin d'aga murya yace, "ku saurari k'orafin da Shugabar mu zata saurara da kuma hukuncin da zata yanke a yanzu" A take nutsuwa ta k'ara wanzuwa a gare su kowa ya cigaba da sauraron su. Subbhu yace, "Hazoor !! ( Ranki ya dad'e) "Janela tana d'auke da juna biyu wanda ya kasance ya samu asali daga Narayan, Sakamakon keta haddin ta da yayi saboda son zuciyar sa ba tareda son ranta ba, iyayen ta sun mik'o kukan su gareki tareda sa ran samun adalci" Udday yace, "wanda suka san dasu ake su fito gaban shugaba" Fitowa sukayi suka durk'usa kamar yadda tsarin masarautar yake suna tsammani daga gareta. Zama tayi tareda lumshe ido ta sauke 'boyayyar ajiyar zuciya kafin ta bud'e su ta juye akan Narayan wanda jikin sa yake kyarma saboda tsabar tsoro da fargabar azabar shugabar tasu, a Take wani abu ya fara kwaranyowa cikin tunanin ta, Jinjina kai tayi tace, "wajibi ne auren ta gare shi bayan yayi zaman kurkuku na adadin lokacin da zata rabu da abunda yake jikin ta, kullum ze d'auki hukuncin bulalai hamsin ba tareda ya motsa ba, Bayan wata d'aya sai a koma yi masa duk mako d'aya, Ban da shan ruwa sai me zafi abinci kullum sau d'aya, Kulawa da d'an sa da matar sa ya wajabta a kansa indai ya 'bata mata rai ko ya goranta mata koda na lokaci d'aya hukuncin kisa ta hanyar jifa ya tabbata gareshi" Daga haka ta mik'e da niyar fita daga fadar jiki a muce. Tashin hankalin abunda take fad'a ya hana shi aiwatar da abunda yaso k'addamarwa akan ta, idanun sa sun kad'a sunyi jajur saboda azabar rad'ad'in da zuciyar sa take masa ya kafe ta da idanu yana wani irin huci, zuciyar sa tana raya masa irin mummunan matakin da ya dace ya d'auka a kanta. (Waye????????? Mu had'e a next page insha Allah) INDO CE.. [26/02, 8:29 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~4* بسم الله الر حمن الر حيم Free page Da sauri mahaifin sa ya rik'o hannun sa wanda yake kakkarwa, cikin razani da shakka yace, "Arveen wannan be dace ba kasan wacece yarinyar nan kuwa??? Kai kad'ai ne ka rage min a yanzu dan haka karka sake kayi abunda zata cire maka kai a banza" Yana shirin yin magana ta juyo tana kallon su saboda ji a jikin ta da tayi ana firar ta. Ganin haka yasa sukayi saurin fuskewa dan gudun matsala. Kawar da idon ta tayi daga kansu kafin tace, "Arveen ka kula da hukuncin da na zartar, karka bari a samu matsala" Daga haka ta juya ta fice ba tareda ta k'ara kallon sa ba. Fizgewa yayi daga rik'on da Waziri yayi masa, a fusace yace, "wai yaushe ne har yarinyar nan tayi girman da zata iya ja dani??? A gaban mu fa aka haife ta, amma Baba ka kalla yadda kowa yake jin tsoron ta, idan haka ne meye amfanin rashin iyayen nata?? Da sauri waziri ya shiga jansa dan kuwa akwai mutanen ta a kusa,, da wani yaji abunda yake fad'e ze rattaba mata kuma yasan hukuncin baya wuce kisa, baza tayi duba da cewa d'an uwan ta bane kawai gamawa zatayi dashi. Sai da suka koma sashin su sannan ya sake shi, Yaja tsaki tareda cewa, " Arveen kana da matsala meyesa kake haka ne??? Kasan halin yarinyar nan, ina ruwan ka da zancen yarintar ta tinda dai har ta riga ta girma??. Yanzu abunda yake gaban ka shine wanda ya dace ba wai hurumin ta ba. Arveen ya zuba dogon tsaki cikin k'unar rai yace, "yarinya duk ta addabi kowa?? Kenan mu haka zamu k'are a bayin ta?? A k'a'ida ma fa sarautar tawa ce, Kaji fa abunda take cewa wai nine zan kula mata ma da hukuncin da ta yanke wa wannan yaron, saboda tsabar zalumci ai ni banga laifin shi ba, ai kuwa wata rana hakan zata faru akanta itama sai muga me dakatar dani idan zata iya" Waziri yace, "Arveen tinda dai na tabbatar baka son ta shikenan kawai kayi shagalin ka d'a na" Ya fad'a yana wani irin murmushi me cike da ma'anoni da yawa iri da kala. Cikin nutsuwa ta zauna a bakin makeken gadon ta tana maida numfashi saboda irin bugawar da zuciyar ta takeyi, cikin sassanyar murya tace, "Arjula?? " Cikin sauri Arjula ta k'araso kusa da ita ta sauka tana kallon ta. Itama kallon ta take har wani lokaci kafin tace, "Farhana" Tashi tsuntsuwar tayi ta fice daga turakar cikin sauri, Ba tareda wani 'bata lokaci ba sai gata ta dawo tareda Hadima Farhana. Da sauri ta durk'ushe a wajen tareda cewa, "Hazoor, (Ranki ya dad'e) na amsa kiran ki" Ido ta zuba mata har wani lokaci kamar wadda bata ta'ba magana ba da kyar ta iya cewa, "Abdulkareem a nomo min Hadima Urmi" Hadima Farhana ta jinjina kai ta tashi da sauri tana cewa, "yanzu kuwa Ranki ya dad'e, amma kafin na fita ya kamata kisha ruwa, abunda dai bakya so d'in ni kuma karanbani yayi min yawa bana son ganin ki cikin wani yanayi, kisha ruwa zuciyar ki zata samu salama Insha Allah" Kamar bazata kula ba sai kuma ta jinjina kai tace, "zan sha amma bayan na ganshi" Hadima Farhana tasan halin kayar ta dan haka tace, "yadda kika ce haka za'ayi, nagode da amsa tayi na" Bata kalle ta ba sai ma hannu da ta mik'awa Arjula, ita kuwa tayi d'araf akai. Basu 'bata lokaci ba suka dawo tare. Uwar Hadimai Urmi ta mik'a gaisuwar ta. Bayan ta amsa ta mik'e ta nufi hanyar fita. Hadima Farhana tace, "Uwar Hadimai Urmi Shugaba tana son ganin d'an ta ne" Hadima Urmi ta mik'e tana cewa, "zan cika aiki ya shugaba ta" Sashin gaba d'aya yara ne wasu sun tasa wasu k'ananu ne. suna ganin ta suka fara murna,, d'aya bayan d'aya suke zuwa suna ta'ba k'afar ta ita kuwa sai sa musu Albarka take, Masu kula dasu ma sai mik'a gaisuwa suke. Hadima Urmi ce tayi gaba zuwa cikin wani d'aki k'ayatacce wanda yaji ado da dukiya me yawan gaske ko ina tsaf sai walk'iya yake. Da murmushi akan fuskar ta ta shiga kai tsaye wajen d'an madai-dai-cin gadon da aka kwantar dashi yana shan baccin sa ta nufa, tsayawa tayi ta zuba masa ido tana k'ara jin k'aunar sa tana ratsa duka sassan jikin ta, a hankali tasa hannu ta shafi kansa har zuwa fuskar sa tareda furta, "Masha Allah" Ta'ba shin da tayi ne yasa yayi firgigit ya bud'e idon sa yana waro su a kanta. Yalwataccen murmushi ta sakar masa ganin yadda ya k'ara wayo ya girma, hakan ya tabbatar mata yana samun kulawar da ta dace, cikeda kulawa ta d'auke shi ta rungume shi tareda binsa da addu'o'i har wani lokaci sannan ta mik'a shi ga Hadima Urmi, Hannu tasa ta share y'ar k'wallar da ta fara k'ok'arin sakkowa daga cikin idanun ta, A zuciyar ta tana cewa, "ranar kuka bata zo ba tukunna" Ficewa tayi daga shashin ta koma nata. Ramraj ne zaune gefen k'afafun mahaifiyar sa, Kallo d'aya zakayi masa ka gane yana cikin damuwa. Rausayar da kai yayi yace, "Mama Shikenan Maharani Mahalakshimi bazata saurare ni ba??? Wani shu'umin murmushi gimbiya Sunaya ta saki kafin tace, " ina ta murna na haifi namiji, namijin da ze iya yak'ar masarautar nan dan cika muradin mahaifin sa amma sai dai kashh, be cika namijin ba, Raj a yanzu ba soyayyar ta ya kamata ka nema ba, Fansar jinin mahaifin ka ya kamata ka nema kuma ka nema masa cikar burin sa ko da ze samu salama, Idan baka sani ba Maharani Mahalakhshimiey, (Sarauniya Mahalakshmi) itace ta kashe maka Mahaifin ka ta ruguza cikar burin sa, wannan yarinyar shaid'aniya ce da suffar mutum a memakon muyi k'ok'arin kawar da ita sai kuma kace kana sonta?? Nace ka hak'ura ka k'i kaga yadda take wahalar da kai har yau tak'i saurarar ka bata ta taka ma baki d'aya, amma da Arveen ne na tabbata da zata saurare shi, Kana kallon fa idan aka zauna a fada ma wuyacin abu ne bata bashi abunda zeyi ba, kaga wannan ma matsayi ne wanda kai baka same shi ba, Mu bata d'auke mu matsayin jinin ta ba tafi ganewa Waziri da d'an sa saboda shi yafi mu nuna mata k'auna da kulawa, motsi kad'an idan kayi sai ta hukunta ka amma shi bata yi masa haka, Ka dawo nutsuwar ka Raj kisan mutum a gurin ta tamkar shan ruwa ne bana so ta kashe ka ba tareda mun cika muradin mu ba" Shiru Raj yayi maganganun Mahaifiyar sa suna ratsa shi, ya d'an d'ebi lokaci beyi magana ba sai kuma yace, "ita d'in ba wai wadda zamu kawar bace domin kuwa mutanen da suka fi mu k'arfi harda iko suna sun hakan amma sun kasa, Lakhshmie sarauniya ce wadda ta gagari duniya manyan masarautu suna da irin wannan buk'atar ta son kawar da ita dan haka idan muka kawar da ita kawai munyi yak'in ne amma ba mune da nasarar ba, sune zasu zo suyi kane kane akan komai, Fansar jinin mahaifina ta hanyar kashe ta ko nakasta ta ba shine mafi kyawu ba, sai dai ta haifa min wani,, auren ta zanyi kawai kuma yadda tsarin yake wanda ya aure ta shine da mulki dan haka wannan ne ya dace damu, Kiyi tunani akai sosai, yanzu lalla'ba ta zamuyi mu shiga jikinta sosai mu nuna mata komai ya wuce sai mu dinga binta a sannu muna hak'e jijiyoyin ta lokaci d'aya sai dai taji ta fad'a tarkon mu" Dariya sosai Gimbiya Sunaya take sai da tayi me isarta sannan ta rungumo shi tana cewa, "ashe kana da fasaha d'ana gaskiya kai jarumi ne na dena ce maka ba jarumi ba kaji ko?? Bari ma gobe zanje nace mata baka da lafiya dan haka ka zauna gobe kar kaje ko ina kaji ko?? Zanje ma na nemo sa'a" Yace, " ai kuwa ta haka zamu fara kama ta kinyi shawara me kyau" Zaune take ita da Arjula suna hira sai surutu take zuba mata duk da cewar tsuntsuwar bata magana amma hakan be hana ta zama ta fad'a mata damuwar ta ba har ta bata labari,har abunda ya wuce baya ma suna tattaunawa, Koda baza ta ce komai ba takan nuna alamar amsa ga abunda Maharani ta fad'a mata, idan na damuwa ne zata nuna alamar damuwar ta haka idan na farin ciki ne zata nuna, Tsuntsuwa ce me ban mamaki sai dai kowa kawai ganin ta yake be san sirrin dake tattare da ita ba. Kallon ta tayi tana murmushi tace, "Arjula!! Kin tuna a Fadar Maharanie Abunda ya faru? Karyar da kai tayi hakan ke nuna alamar bata tuna ba. Maharani tace, " kina nan fa Har maa take min dariya? Lokacin da yayi min.. Da sauri Arjula ta baza fuka-fikin ta tana fiki-fiki dashi, Hakan yasa Maharani tayi shiru tana kallon ta fuskar ta d'auke da murmushi tace, "Yanzu dai kin tuna ko?? Kare kanta tayi da fuka-fikin ta ta cusa shi ciki tana karkad'a jela. Dariya Maharani tayi tana cewa, " oh kunya ta ma kike ji?? Ni banji kunyar ki ba? Sassauta murya tayi tace, "Arjula na kasa manta wannan ranar tana yawan dawowa cikin tunani na ko meyesa hakan?? Rausayar da kai tayi tareda yin kalar tausayi. Maharani ta gyad'a kai kafin tace, " lokacin lek'en sirri yayi Arjula ki zagaye ko wane sashi na Mahaal kizo min da labarin abunda yake faruwa, ki tabbatar babu wanda ya ganki, ki bi iska yadda ko kusa da mutum kika je baze sani ba " Tashi Arjula tayi ta fice cike da son cika umarni. Hadima Farhana ta k'araso tana d'an murmushi tace, "Sannu da hutawa Shugaba" Bata ce komai ba sai Jinjina kai tayi ba tareda ta kalle ta ba. Hadima Farhana tace, "Ranki ya dad'e taya kike iya yin magana da Arjula? Shin tsuntsuwar tsafi ce ko kuwa?? Naga bama ita kad'ai ba kema kina iya jin maganar ta" Mik'ewa tayi daga kishingid'en da take ta d'ora k'afar ta d'aya kan d'ayar, Cikin Izza tace, "daga ina kike??? " K'asa tayi da kai tareda cewa, "ina neman afuwar shugaba, naje Sashin marayu Abdulkareem ya girma sosai, daga nan na wuce 'bangaren bayi dan kula da abunda suke aikatawa na tarar ba matsala, amma wata daga cikin manyan bayi na 'barin ciyar da mutane abinci na kama ta da laifin hantarar na k'asa da ita gami da wahalar dasu ko tayi musu horon yunwa haka kuma abincin sai son ranta take bawa mutum bata ba su wanda zasu ci ya k'osar dasu, sun bani k'orafi ne sai kuma nayi bincike na gane hakan nayi shigar bayin ne na shiga cikin su sai kuma naga hakan tana faruwa nima ta faru a kai na" Jinjina kai Sarauniya tayi a hankali ta bud'e baki tace, " kin nuna mata kanki?? Wane mataki kika d'auka?? Da sauri tace, "Maharani ban d'auki mataki ba bata san ma naje ba" Gyad'a kai tayi tace, "ki mayar da ita 'barin share share ba'a matsayin wata ba itama ta shiga cikin wanda shugabar su zata dinga basu umarni, a wajen abinci kuma ki nemi wata ki d'ora sannan ta dinga yi mata kamar yadda itama ta yiwa mutane, Bayan haka idan ta k'ara yin hakan ga wani zata kar'bi tsatstsauran hukunci" Hadima Farhana tace, "Zanyi hakan ranki ya dad'e" Wata Hadima ce tayi gyaran murya a bakin k'ofa tareda cewa, "zan iya shigowa Ranki ya dad'e??? Hadima Farhana tace, " shigo" Shigowa tayi tana d'ibar gaisuwa cike da ladabi tace, "nice Sabuwar Hadimar da zata dinga nemawa mutane iso zuwa gareki Hazoor" Jinjina kai tayi alamar ta gamsu, ta k'ara zuba mata ido alamar tana sauraron abunda zata fad'a. Godiya tayi sannan ta cigaba da cewa, "Hazoor gimbiya Sunaya matar Tsohon Galadiman wannan masarauta tazo hankali tashe tana son ganin ki" Shiru tayi na wani lokaci kafin ta gyad'a kai. Hadima Farhana tace, "a iso lafiya" Tashi tayi ta fita cikin sauri. A hargitse gimbiya Sunaya ta shigo fuskar ta yare yare da k'walla ta zube a wajen k'afafun Maharani tana cewa, "ya shugaba ta d'a na ya kamu da cuta mara warkewa yana cikin tsananin rashin lafiya, ki tausaya masa kije ki duba shi na rasa me zanyi masa ya warke" Kauda kai tayi a yatsine tace, "Hadima Farhana kije ki duba shi" Baki Gimbiya sunaya ta saki tana kallon Sarauniya saboda jin abunda ta fad'a, a ranta tana cewa, "wannan gallababbiyar yarinyar fa ta fini dubara, ai kuwa yanzu zan shawo kan ki" Fashewa tayi da kuka tana cewa, "Maharani Mahalakshmi, sunan ki suna ne me daraja da kima abar bauta me matuk'ar tausayi da jink'ai, Hazoor d'a na maraya ne bashi kowa sai ni sai ke mune dangin sa kece y'ar uwar sa mahaifin sa ya riga ya mutu, Bamu sani ba ko shima ciwon ajali ne ya kama shi kije kuyi ban kwana kar ya mutu be samu kulawar ki koda sau d'aya ba, yana son yaga kin kula shi a matsayin sa na d'an uwan ki amma be samu hakan ba, Nasan ze mutu ne da bak'in cikin wannan, ki tausaya masa shifa jinin ki ne Maharani, Yanzu yana mutuwa shikenan na rasa kowa wayyo abar bauta Mahalakshmi ki sassauta min wannan bak'in cikin" Ta k'ara rushewa da kuka tana kallon Maharani dan ganin matakin da zata d'auka, shin zata amince ko kuwa?? Cikin zuciyar ta kuwa tana k'issima, "ai kin gama yawo Lakshmi indai kika sake kika amince kina zuwa aikin gama ya gama burin mu ya cika " (Fans zata yarda ko bazata yarda ba???🤣😂) INDO CE.. [27/02, 7:11 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~5* بسم الله الر حمن الر حيم Free page *Tajmahaal na kud'i ne Naira 100 kacal cikin rahusa😄* *Domin magana dani ta prvt ga link👇* https://wa.me/message/45UKV47T7IM2F1 Shiru tayi tana nazari na wani lokaci kafin taja wani dogon numfashi, kamar me tsoron abunda zata fad'a tace, "kije zanzo" Ba tareda jan lokaci ba ta tashi jikin ta har rawa yake saboda farin ciki, sai da tayi godiya sannan ta fice, Tana komawa sashin su ta fara rawa saboda tsabar farin cikin da take ciki, Raj da yake gefe kwance yana shan wahala da kyar ya iya cewa, " nifa Inajin ba dad'i meyesa zaki bani guba saboda kawai cikar burin ki Mama idan kuma ta kashe ni fa??? K'arasawa tayi gurin shi tana murmushi cike da rawar kai tace, "kai ragon maza ka shanye kawai, idan ba haka ba kasan dai zata gane ciwon k'arya kake dan haka na baka wannan gubar ai nasan bazata cutar da kai ba, ba abunda ze faru, ka daure kawai kai fa matsalar ka rashin juriya rago kawai" Maida kai yayi ya kwanta cike da azaba ba tareda ya k'ara ce mata uffan ba. Ita kuwa cigaba tayi da murna. Lokacin da Maharani ta iso ya gama galabaita, Sai a lokacin Gimbiya Sunaya ta nuna tsantsar damuwar ta akan sa sai kuka take kamar na fitar rai, duk a tunanin ta ba abunda gubar zatayi masa a ganin ta kawai ragonta ce take sa shi yana mata wai-wai. Cikin nutsuwa ta k'arasa kansa ta zuba masa zaratan idanun ta. Gimbiya Sunaya ta zube a wajen ta dafe kai tana kuka tareda cewa, "Maharani kina ganin halin da d'ana yake ciki kice wani abu dan Allah" Kallon ta tayi cikin tsawa-tsawa tace, "meye abunda yaci??? Ido ta zazzaro a firgice zuciyar ta ta fara tsalle tana dako sama ta dawo k'asa, cikin razani ta saki wata yar dariyar tsoro wadda batasan lokacin da ta su'buce mata ba tana cewa, " ha ah aha Maharani ai babu abunda ma yaci kawai kinsan da yake rago ne" Kafe ta tayi da ido kamar wadda take shirin cinye ta. Irin mugun kallon da take watsa mata yasa taji hantar cikin ta ta fara hargitsawa, cikin rashin sanin abunyi tace, "uhm ,Maharani ki dena min irin kallon nan yana da ban tsoro" Tayi magana tana y'ar dariya. Kauda kai tayi daga gareta ta maida kallon ta ga Raj wanda zuwa yanzu ko idanun sa ma ya kasa k'i bud'ewa, ganin irin matsanancin halin da ya shiga yasa taji zuciyar ta tafara harbin iska, A kausashe tace, "Ram!!!" Da kyar ya iya d'aga ido ya kalle ta a wahalce. "Kayi magana mana tashi ka fad'a min" Yunk'urawa yayi ya tashi da k'yar dan k'arfin hali da kuma shakkar ta da yake, Jiri ne ya d'ebe shi ya fara wata irin shak'uwa yayi baya ze fad'i. Cikin sauri ta rik'o hannun sa a razane tareda cewa, "RajKumari!!!!!" Ba Gimbiya Sunaya da shi kad'ai ba ita kanta Hadima Farhana sai da mamaki da al'ajabi ya kashe ta. Zama tayi gefen sa tana rik'e da hannun sa, k'ara zuba masa ido take tana binsa da kallon tuhuma. Shi kuwa k'amewa yayi ya bita da ido ko motsi ya kasayi. Gimbiya Sunaya kuwa farin ciki yasa takejin kamar ta nutse a wajen, yau d'an ta ya samu matsayin da Sarauniya ta kira shi da suna tsadadde haka, Ba dan kar ta gane lumbu lumbu tayi mata ba da ta taka rawar murna. Lumshe idanun sa yayi tareda sauke 'boyayyar ajiyar zuciya. Cikin sassanyar murya tace, "Kumari?? Me kaci ne?? Me yake damun ka haka?? Girgiza mata kai yayi alamar babu komai, cikin ransa kuwa yana mamakin yadda akayi ta damu dashi lokaci d'aya, abunda ko da sunan wasa bata ta'ba nuna tasan da shi d'in d'an uwan ta bane, Abun mamakin ma yadda tayi saurin kai hannun ta jikin sa matar da ko ra'bar gefen ta mutum yayi sai ta hukunta shi koda sunan tsautsayi bare kuma ya ta'ba jikin ta shikenan tashi ta k'are sai dai Allah ya tseratar dashi, amma yau itace da kanta ta rik'o hannun sa, Duk da ya fara fita hayyacin sa amma mamakim wannan be barshi ba. Kallon Hadima Farhana tayi a tsawace tace, " ki nemo masu kula da lafiya mana!!" Da sauri ta juya tana cewa, "Yanzu kuwa ranki ya dad'e" Maida kallon ta tayi gareshi cikin sanyi tace, "Rajkumari karka damu zaka samu lafiya" Duk da wahalar da yake sha bata hana shi sakin murmushi ba. Gimbiya Sunaya ce ta matso kusa tana cewa, "abun wasa ya zama gaske?? Raj?? Ya naga kamar kana cikin mugun hali ne?? Me yasa haka?? Karfa kace min ka illatu" Tsawa Maharani ta doka mata da cewa, "yi min shiru!! Koma menene ai laifin ki ne, yaro d'aya a gurin ki kin kasa kulawa dashi??? Tatta'be baki tayi ta fara k'walla cikin k'issa tace, " Hazoor, ina kulawa dashi sosai kawai tsautsay ne" Cikin 'bacin rai tace, "kuma kika barshi yaci guba Meyesa zaki barshi yaci abunda ze cutar dashi waye ma ya bashi gubar???" Goge k'wallar ta shiga yi tana cewa, "Maharani!! tashin hankali da rud'ani yasa na fara kasa gane ina na dosa, ance min fa gubar bata cutar da mutane shin ba da gaske bane?? Da mamaki Maharani tace, " kenan ma kina sane da abunda ya faru kece kika bashi ko kuwa da hannun ki a ciki??? Zuwa yanzu lamarin ya fara bata tsoro jikin ta ya hau kyarmar tsoro ganin abun ya fara rinca'be mata gashi Maharani tana son gano ta ga irin halin rayuwa ko mutuwar da d'anta ya shiga, wanda da take ganin wasa amma yanzu ta gane gaskiyar lamarin hakan yasa hankalin yayi tsuntsuwa zuwa sama.. A diririce tace, "haba Maharani meyesa zan bawa d'an ciki na guba?? Na rantse da abun bautar mu bansan anyi ba, Hazoor ki duba ki gani fa yadda aka mayar min da d'ana" Jinjina kai tayi tace, "ko waye kuwa na gane shi to bazeji dad'i ba, Kuma idan bazaki iya kulawa da RajKumari ba zaki iya mayar dashi gareni, shi jinina ne dan haka ki kula dashi, bayan yau idan na k'ara jin wani abu ya same shi zan d'auki mataki akan ki" Da sauri tace, "to ai kuwa zan kula dashi da gudu. ma Kuwa" Maganin gargajiya ne aka shiga yi masa ba ji ba gani domin ceto rayuwar sa. Bata da lokacin 'batawa a wajen dan haka ta barsu tareda basu umarnin bashi kulawa ta musamman. Sai da sukayi da gaske sannan suka samu kansa bayan ya amayar da gubar ya dawo dai-dai sai dai rashin k'warin jiki da d'an abunda ba'a rasa ba. Hadima Farhana ce ta kalle ta tayi k'asa da kai cikin ladabi tace, "Maharani ki gafarce ni, amma ina ganin kawai duk shiryawa sukayi ita da d'an nata, a gani na suna son cimma wani muradi nasu ne" Waro mata gwaragwaran idanun tayi cikin kausassar murya tace, "karki k'ara, koma meye d'an uwa na ne, na gani da ido na irin halin da yake ciki kina nufin ba gaskiya bane?? Ko kuma zata bashi guba ne kawai dan wani abu???? Rissinawa tayi tace, " naga kamar ranki ya 'baci ina neman afuwa ranki ya dad'e" Zazzafar iska ta furzar kafin tace, "yau ne karon farko da naji na damu da damuwar wani, ashe dama ina da tausayi haka? Nayi zaton na barbad'ar dashi kamar yadda aka tambad'a min farin ciki na, ban zata zan iya ji'bantar lamarin wani cikin sauk'i haka ba " Hadima Farhana tace, "Hazoor kina da kyakkyawar zuciya ta wata fuskar, amma rashin yafiyar ki shine yasa bana jindadi, shin wacece wadda kika kulle a kurkuku? Bakya tausayin ta,, ko meye tayi miki yaci ki yafe mata ta wahaltu ta bautu tin da hasken ta har ta koma mahaukaciyar k'arfi da yaji,, Bana jin dad'in azabtarwar da kike wa matar nan shin wane zunubi ta aikata miki kika rufe ta har kika kasa yafe mata?????? *INDO CE..* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 *AURAN DIJAN GALA* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 *Shaharar ran book din nan mai matukar nishadantarwa ga fadakarwa hadi da ilimantarwa* ```ni oum siyama nashirya tsaf domin nishadantar daku, akan farashi mai sauki 200 kada kibari abaku labari``` *indai ba ki karanta AURAN DIJAN GALA anbarki baya yar uwa*, *maza Ku garzayo domin nishadinku* *200 only* *Ku tuntubeni a 08100437976 domin kira kuma 👉08108353370 sainaji Ku* ```koda kudinki saida rabonki``` *Oum siyama ce* Tinda ta fara maganar ta tsura mata ido har takai k'arshe, jikin ta yayi wani mugun sanyi lokaci d'aya, mik'ewa tayi tana taku d'aya bayan d'aya, A wajen taga ta tsaya tana lek'a waje , a take yanayin ta ya canja, taja dogon numfashi kafin tace, "Banida abunda zan gaya miki Farhana nima kaina bana jindad'in hakan sai dai ya zama dole ne ba yadda na iya, d'an murmushi tayi ta k'ara da cewa, " ke yarinya ce Farhana, kije kawai na gaji da magana, wancan yaron Raj ya saka ni surutu, Abun beyi ba gaskiya yanzu bana son hayaniya lokacin buk'atar huta yayi" Tashi Hadima Farhana tayi tana cewa, "zancen dai d'aya ne kullum ba amsa, sai yaushe ne kuma zaki bani labari akan iyaye na??" A zafafe ta juya tana kallon ta fuska a had'e ba alamun wasa a tattare da ita. Duk da rashin tsoro da jarumta irin ta Hadima Farhana sai da ta tsora tayi waje da sauri tana cewa, "Allah ya huci zuciyar Sarauniya" Tin daga wannan lokacin kulawar ta da nutsuwar ta ta karkata zuwa ga Abdulkareem da kuma Ramraj, Musamman Abdulkareem irin bada hankalin da tayi a kansa har ya wuce inda mutanen ta suke zato abun har ya fara girgiza su sun kasa gane wace irin k'auna ce tsakanin ita da yaron da ya kasance d'an bayin ta. Mahaifiyar Ramraj kuwa sun samu mafaka a gefen Maharani, Ita ta d'auke shi a matsayin d'an uwan ta wanda ya dace ya samu kulawar ta,,,, yayin da su kuma suke mata zagon k'asa suna k'ara ganin sirrin ta suna shiri dan ruguza ta. Arveen ne ya kalli Mahaifin sa cikin 'bacin rai da bak'in ciki yace, "Baba kana kallon fa abunda yarinyar nan takeyi, meyesa kake tsoron ta ne??? Ni idan bazaka iya ba ka barni na tinkare ta muyi gaba da gaba meyesa haka ne?? Haba Baba ni nagaji kana cewa komai lokaci ne sai yaushe ne zan samu wannan k'arfin ikon??? Tayaya ne zan zama me mulki a wannan fada me tsohon tarihi??? Su kuma mutane kowa ita suke so sun kasa juyuwa ta riga ta shigar da tsoron ta a cikin zukatan su, ni kuma zan gusar da wannan tsoron nata da sukeji, shakka babu nine magajin Masarautar Purlasiri Baba" Dafa kafad'ar sa waziri yayi yace, "ah d'ana kwantar da hankalin ka ba dai ina nan ba?? Sai dai amma ka sani tinkarar yak'i da wannan yarinya dai-dai yake da sadaukarwa gunki jinin ka, ba shakka sai tayi fata fata da kai, dan haka yanzu muna buk'atar wanda zasu taya mu yak'ar ta" Arveen yace, "to yanzu ya za'ayi kenan Baba?? Ka duba ka ga yadda take kula da yaron nan Abdulkareem babu tantama yaron nan d'an ta ne dan kuwa abun ya wuce tunani, tsoro na d'aya kar sai tafiya tayi nisa kawai baya ta bayyana a gaban mu, Baba ka tabbatar ya mutu????? Kar muje ta mutu ta bar mana baya da k'ura" Dariya waziri yayi sosai kafin yace, "lallai yaro na ka girgiza da wannan lamarin, ya riga ya mutu, duk da cewar ita d'in yarinya ce me dabara amma Baban bazata iya dawo dashi ba, Na rik'e maka kan macijin d'ana kayi wasa da jelar sa yadda ranka yake so, Yaron nan kuma ya zama dole dama mu kashe shi domin kuwa jarumi ne tinda har kaga ta k'aunace shi sosai har ta rad'a masa wannan sunan tabbas yaron nan ze bamu matsala, Kamar yadda tak'adirin Aljani ya gaya min wannan d'an shine bak'in duhun da muka dad'e muna ganin ze bayyano a garemu, dan haka ya zama dole ne mu kawar dashi" Arveen yace, "k'warai Baba" Kwance yake ya tayar da kai da cinyar ta yayin da fuskar ta take lullu'be da bak'in k'yalle. Dariya yayi yace, "gaskiya kin cika shaid'aniya ina jin dad'in ki kina yi min aiki yadda ya kamata, Yanzu waye na gaba a shirin mu??? Ya zama dole mu tashi tsaye, Sai mun kashe wannan yaro Abdulkareem sannan haske ze bayyano mana a lokacin ita kuma duhu ze lullu'be ganin ta, amma duk da hakan sai mun nemi matemaki wanda ya kasance jigon ta, Wa kike ganin zeyi mana haka??? Ko mu nemi matar Uddaiya?? Girgiza kai tayi tace, " a'a ba wannan ba, Hadima Farhana, ita zamu nema ta dawo tsagin mu indai hakan ta faru shikenan mun karya lagon ta, to amma ta wace hanya zamu biyo wa Hadima Farhana??? Indai dukiya ce bata da matsalar ta ba abunda zamu bata wanda zata yarda damu, idan kuma kayi mata barazanar kisa ko wani abu hukuncin Maharani Mahalakshmi ze tabbata ne gareka" Mik'ewa yayi ya zauna tareda janyo ta jikin sa yana cewa, "ke kad'ai ma gayya ce kina shiga jikinta ba tareda ta sani ba ganin ki take kamar wata ta kirki batasan nan makashin ta take tare dashi ba, Zanji da Hadima Farhana dan haka ki cigaba da abunda ya dace, goben nan zanyi maganin ta" *INDO CE..* [28/02, 7:43 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~6* بسم الله الر حمن الر حيم Free page *Tajmahaal na kud'i ne Naira 100 kacal cikin rahusa😄* *Domin magana dani ta prvt ga link👇* https://wa.me/message/45UKV47T7IM2F1 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 *AURAN DIJAN GALA* 🌹🌹🌹 🌹🌹 🌹 *Shaharar ran book din nan mai matukar nishadantarwa ga fadakarwa hadi da ilimantarwa* ```ni oum siyama nashirya tsaf domin nishadantar daku, akan farashi mai sauki 200 kada kibari abaku labari``` *indai ba ki karanta AURAN DIJAN GALA anbarki baya yar uwa*, *maza Ku garzayo domin nishadinku* *200 only* *Ku tuntubeni a 08100437976 domin kira kuma 👉08108353370 sainaji Ku* ```koda kudinko saida rabonki``` *Oum Siyama* Maharani. Tana zaune kan k'ayatacciyar kujerar ta tana hutawa, Haka kawai takejin zuciyar ta tana bugawa ba tareda tasan meye fa'idar hakan ba. Hadima ce ta kutso kai tareda nemawa kanta iso. Ba tareda tayi magana ba tayi mata alamar ta shigo. Ta shigo tana cewa, "ranki ya dad'e, nice dai wadda aka kawo ni domin iso da mutanen ki gareki, Sunana Fadya, Gimbiya Jusiyya tana son isowa ni kuma na hana ta, da fatan banyi laifi ba domin kuwa ta tabbatar min da cewar ba'a yi mata shamaki da shiga duk inda kike" Zaratan idanun ta ta d'aga ta juye akan ta cike da tuhuma tace, "ban tambaye ki bayani akan ki ba, na sanki, meyesa zaki hana Gimbiya Jusiyya shigowa?? Shin ba'a wannan masarautar aka haife ki ba??? Baki san wacece Gimbiya Jusiyya a guri na ba??? K'asa tayi da kai tana cewa, " A huce ranki ya dad'e, akan aiki na nake ni sabuwa ce a wannan fannin nayi zaton shigowar ta kai tsaye ne ze sa nayi laifi amma a yafe ni kuskure ne bazan kuma mai-mai-ta shi ba" Ko kallon ta batayi ba sai ma lumshe ido da tayi. Da sauri Hadima Fadya ta tashi ta fice. ba 'bata lokaci wata mace ta shigo, babbar mace ce me kamala da dattaku, tasha ado ta ko ina, fuskar ta d'auke da murmushi ta k'araso kusa da Maharani, cikin ladabtacciyar murya tace, "Maharani Mahalakhshmi?? Sannu da hutawa zan iya zama??? Gyad'a kai tayi ba tareda ta kalli inda take ba. Gimbiya Jusi ta saki yalwataccen murmushi ta zauna a bakin gado, Kallon Maharani Mahalakhshmi tayi cikin amintacciyar murya tace, " Yarinya ta kinci abinci kuwa?? Girgiza kai tayi alamar a'a. Da sauri gimbiya Jusi tace, "meyesa??? Ki dena damuwa ki bari komai ya wuce be kamata kina zama kina saka tunani a zuciyar ki ba har ya hana ki cin abinci, Idan baki inganta kanki ba taya kike ganin zaki iya inganta wasu?? Be kamata ba, komai da maslaha akeyin sa, meye damuwar ki yanzu??? Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, " Gimbiya Jusiyya babu abunda nake tunani" Dafa kafad'ar ta tayi cikin sanyi tace, "haba y'a ta?? Ina ganin damuwa k'iri k'iri a tare dake amma kice min baki da damuwa? Rausayar da kai tayi tace, " damuwa ta d'aya ce kawai ita kuma ba buk'atar kowa ya sani, zanci abincin amma ba a lokacin da kikace naci ba" Murmusawa tayi tace, "har yanzu kin kasa sauyawa y'a ta, babu wanda ya isa yasa kiyi babu wanda ya isa yasa ki bari, Ni dai ki rufamin asiri Maharani ki dena damuwar nan, Duk alhakin ki a kaina yake, har sai na tabbatar na saki farin ciki sannan ruhina ze samu salama, kin cire yarda da kowa, amma ina so ki sani ni bazan iya cutar dake ba, duk wanda naga yana shirin hakan sai inda k'arfi na ya k'are, Koda bazaki yarda dani ba Na rok'e ki ki dena kallo na amatsayim wadda zata cutar dake" Ta k'arasa maganar tana sharar k'walla kamar me shirin durgujewa da ihu. Dogon numfashi Maharani taja bata ce uffan ba. Mik'ewa gimbiya Jusiyya tayi tana cewa, "kar na cika miki kunne bari na koma sashi na, ki kula da kanki" Lumshe ido tayi ba tareda tace komai ba. Hadima Farhana. Tana cikin tafiya wata kuyanga tasha gaban ta, Tsayawa tayi tana kallon ta cikin rashin fahimta, ita da ba'a ra'bar ta saboda tsoron hukuncin Maharani kuma yau itace wadda za'a tarewa gaba, mamaki sosai abun ya bata. K'arasowa tayi a ladabce tace, "A gaida Hadimar Hadimai" Gyad'a kai kawai tayi tareda zuba mata ido. Tace, "kiyi hak'uri na tare ki a hanya, sak'o ne akace in isar miki wannan wasik'a ce" Tayi maganar tana mik'o mata wasik'ar dake hannun ta. Kar'ba tayi cikin tsananin mamaki, gaba d'aya kanta ya kulle ta kasa gane me hakan yake nufi. Kafin ta farga taga kuyangar har ta 'bace tayi nata guri. Cigaba tayi da tafiya cikin sanyin jiki da kuma rud'ani gami da firgici, waye wannan wanda bata sani ba???? Ko alamar shiga batayi ba ta kutsa kai turakar Maharani , Tana zaune suna had'a wasik'ar jaki ita da Arjula suna hira cikin kwanciyar hankali, A k'asa tayiwa kanta mazauni tareda yiwa Maharani Sannu. Amsawa tayi gami da binta da ido zuciyarta tana tsalle, kai tsaye tace, "Ina Abdulkareem??! Hadima Farhana tace, " ranki ya dad'e Abdulkareem yana cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali" A zahirance ta sauke ajiyar zuciya gami da lumshe kyawawan idanun ta, k'ara bud'e su tayi kafin tace, "kina da damuwa! Meyesa??? Hadima Farhana tayi k'asa da kai. Kamar yadda ya buk'ata da daddare ta kimtsa tsaf harda shirin ko ta kwana sannan ta nufi inda akace mata taje, Shi kad'ai ta tarar dashi sai surutu yake kamar wani Aljani, K'arasawa tayi cikin tsoro tsoro tace, " Meyesa kake nema na??? Kallon sa ya mayar gareta yana dariya tareda cewa kinzo?? Kawar da kai tayi tace, "a'a" Kwashewa yayi da dariya ya mik'e ya nufo inda take ya tsaya gaf da ita yana kallon ta, Sassauta dariyar yayi kafin yace, "kema fa kyakkyawa ce tamkar mahaifiyar ki" Ido ta zaro a kansa tana mai-mai-ta abunda ya fad'a a cikin ranta. Hannun ya kai ze ta'ba ta tayi sauri daka masa tsawa. Ba shiri ya janye hannun sa yana cewa, "to ai shikenan tinda bakyaso ba matsala,,, abunda yasa na nemo ki dama ina so ki dawo tsagi na ne" A kausashe tace, "a matsayin ka na wa?? " Kai tsaye yace, "magajin izza, ina so ki rabu da uwar d'akin ki -ki dawo guri na mu had'a kai don nemawa kan mu y'anci" Ba tareda ta tsaya k'arasa jin zancen shi ba ta yarfa masa wani kyakkyawan mari. Raj. Suna zaune shida gimbiya Sunaya suna tattaunawa, Rausayar da kai yayi yace, "Mama gaskiya aikin mu yayi kyau inama ze d'ore a haka" Dariya tayi tace, "haba d'ana kwantar da hankalin ka mana!! Ai tukunna ma wannan ai farko ne ka zuba ido kaga k'arshen, ai in gaya maka mu ai mun riga mun haye yanzu bamu da wata damuwa tinda har muka samu kusanci da ita, Yaro na mahaifin ka dalilin kashe shi kenan akan gaskiyar sa, dan yace ze k'waci sarautar sa, ai sarautar tamu ce ba ta-ta ba amma muguwar yarinyar nan sai ta kashe mana shi gashi yanzu ta bar mu mu kad'ai ai nayiwa kaina alk'awarin bazan k'yale ta ba har sai na d'auki mummunar fansa akan ta, yaro na ka bita a hankali kayi mata ladabi har zuwa lokacin da zamu gama jefa ta cikin tarkon mu a lokacin ne zata rasa gabas ta rasa yamma, Mu kuma lokacin mun zama masu karaga" Ta'be baki Raj yayi yace, "sune basu kashe ta sun huta ba,, da tini ba wannan zancen ake ba, munafukar mata, Ni dai wannan d'an da tasa ake bashi kulawa irin ta y'ay'an sarakai shine yafi tayar min da hankali ba akuya ta lullu'be mana da fatar kura ba kuwa?? Dafa kafad'ar sa tayi tareda cewa, " sa ranka a inuwa d'ana ai mun riga mun kusa zurma ta, ni a guri na jariri ba komai bane, cikin sauk'i zan talitse shi wuyar abun kawai ita d'in amma dan ta jariri ai me sauk'i ce" Raj yace, "to shikenan, ni dai yanzu jindad'i na nake ba abunda ya dame ni tinda ina samun kulawa" Tsaki Gimbiya Sunaya tayi tace, "kaji kai dama ai ba'a abun arziki da kai, na lura kwata-kwata baka damu da jinin mahaifin ka da aka zubar ba, lusarin namiji" Tayi magana cikin nuna alamar fushi. Dariya yayi ya tashi yana cewa, "bari ma ki gani tafiya zanyi" Tsaki kawai ta raka shi dashi batace masa k'ala ba. *Indo ce..* Dafe kumatunsa yayi tareda rintse ido,, zuciyar sa ta fara tafarfasa lokaci d'aya,,, ji yake kamar ya hau kanta da duka amma sanin hakan ba riba yasa ya k'wak'ulo murmushin yak'e, 'Dan girgiza kai yayi yace, "banji dad'i ba, ba haka naso ki fahimta ba, ya kamata ki nutsu ki saurare ni,, Ki dawo guri na hakan zefi miki kwanciyar hankali da nutsuwa idan ba haka ba kuma zakiji a jikin ki ne zanyi maganin ki" Murmusawa tayi tace, "barazana kake son yi min??? Ai ba sai ka bi ta wannan hanyar ba, me kake so kayi min??? Kana so ka rabani da Shugaba ta ko?? To ka bada k'ok'ari, Har ni zaka tsora, meye kakeji dashi?? Kashe ni zakayi?? Ko kuwa lalata ni zakayi?? Shiru yayi cikin k'unar rai ya kauda kai daga gareta cike da rashin sanin abunyi. Ta k'ara murmusawa tace, " duk wata barazana da zakayi min baza tayi amfani ba sai dai ma ta hallakar da kai, nace bazanyi abunda kace ba duk abunda kaga zakayi ina jiran ka, ka jaraba ka gani ko akwai riba" Daga haka ta juya zata bar masa wajen. Da sauri yace, "yarinyar nan a zahiri take nuna miki son ki take amma a zuci ba haka bane, ita d'in muguwar yarinya ce wadda duk irin halaccin da kayi mata bazata ta'ba ganin sa ba haka zata sakanya maka da sharri, Nasan kina son sanin suwaye iyayen ki, To ni nasan su" Tsayawa tayi cakkk tana saurarar maganganun sa, a take jikin ta yayi sanyi zuciyar ta ta kwad'aitu da son taji labarin iyayen ta, Dawowa tayi ta nemi guri ta zauna sannan tace, "ina sauraron ka" Mugun Murmushi ya saki kafin yace, "iyayen ki sun kasance bayi ne a wannan masarauta tin asalin ta, Amintattun mutane ne masu gaskiya da kuma bin umarnin na sama dasu, basa ta'ba cutar da mutum, Rana tsaka wannan yarinyar tazo ta zama sarauniya, muguwar shugaba kenan, tayi kashe kashe ta zubda jini, nima a lokacin na rasa mahaifiya ta, Mahaifina dan yayi magana akan kashe masa mata da akayi shina sai ta tsira masa mashi a k'ahon zuciyar sa, ina kallo akan ido na ta kashe min iyaye na" Shiru yayi yana share k'walla cike da tausayawa kanshi. Jikin Hadima Farhana ya k'ara d'aukar zafi ga tasa nan in tausayin sa da ya lullu'be ta, jinjina kai tayi tace, "Ka dena kuka kayi hak'uri" Share k'wallar yayi yace, "Bayan tayi wannan ta'asar ta zama shugaba haka take gudanar da mulkin ta tin asali duk wanda ya ta'ba ta koda kuwa dangin ta ne sai tasa a gutsire masa d'an yatsa, haka take wannan zaluncin har yanzu bata dena ba, Nima a wannan hannun nawa na dama har yanzu akwai tabon ta wanda taje fad'uwa na rik'o ta tana juyowa ta keta min hannu ta zubar min da jini har sai da nayi kamar bazan rayu ba, Ai kema kin gani dai har yanzu bata dena ba, Wanda yasha gaban ta kuwa sai tasa a d'aure shi da sark'ok'i ai ta jansa a k'asa har sai anji masa munanan ciwuka jikin sa yayi ta zubda jini, Kina kallo take irin wannan aikin,,,,,,,, Hadima Farhanaa kinsan wacece mahaifiyar ki?????? Girgiza kai tayi cike da k'agara. Yace, " mahaifiyar ki itace wannan matar da take d'aure a kurkuku, kullum azabar safe daban ta dare daban karki zata kawai kulle ta tayi a gurin nan, a'a azabu take mata iri-iri, mace me kyau ga hankali da nutsuwa, amma zalumcin Mahalakhshmi ya mayar da ita mahaukaciya, Mahaifin ki kuma mutum ne me daraja amma yarinyar nan ta zubar masa da mutuncin sa tasa yayiwa mahaifiyar ki fyad'e har aka haife ki, bayan tasa ya aikata wannan mummunan abu sai ta kashe shi, Ita kuma mahaifiyar ki tasa aka kulle ta ake wahalar da ita, Ke kuma take amfani dake wajen bata kariya da biyan buk'atun ta, ita muguwa ce muguwar da ta wuce duk zaton masu zato, Kar kiyi tunanin mutanen gari suna binta ne saboda nagartar ta, su sunsan halinta ne shiyasa, kawai saboda tsabar zalumcin ta ne yasa idan kana son zaman lafiya ka nuna mata so amma badan suna sonta bane, Farhana ki zo mu had'e mu yak'e ta domin mu kawar da mulkin zalumci daga wannan yanki namu me tsohon tarihi" Cikin kuka Hadima Farhana tace, "kana nufin ba ta hanyar halak iyaye na suka haife ni ba??? Yace, " k'warai da gaske itace tayi sanadin hakan, shiyasa tak'i baki labarin suwaye iyayen ki, haka take ce miki ma itace ailar zuwan ki duniya. *INDO CE..* [01/03, 6:28 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~7* بسم الله الر حمن الر حيم Free page *Tajmahaal na kud'i ne Naira 100 kacal cikin rahusa😄* *Domin magana dani ta prvt ga link👇* https://wa.me/message/45UKV47T7IM2F1 *(Sanarwa!!! Assalamu'alaikum masoya littafin TAJMAHAAL na fara kar'bar kud'in sa daga yau (1 March 2022) 100 ne ba yawa😊 ku hanzarta mallakar naku tin kafin ya koma 200 😅 Domin neman k'arin bayani ku tuntu'be ni ta wannan link na sama👆sai na jiku🥰)* Ya k'ara da cewa baya ta wuce kiyi tunani akan goben ki, idan kika k'waci mahaifiyar ki daga wannan k'uncin nasan zatayi matuk'ar farin ciki" Girgiza kai tayi tana cewa, "sai naji kamar k'arya ne kamar hakan bata faru ba, meyesa zatayi min haka?" Murmushin gefen baki yayi yace, " dama ba lallai ki yarda ba domin kuwa ta riga ta tirke ki, amma kiyi tunani sosai duk hukuncin da kika yanke ina jiran ki- ki same ni anan" Daga haka ya cigaba da tafiya ba tareda ya k'ara cewa uffan ba. Kuka ne ya kufce mata ta shiga rero shi. Dai-dai lokacin hadarin da ya had'o ya fara wani irin rugugi yana tsawa gami da walk'iya tareda iska, ruwa me k'arfin gaske ya sakko lokaci d'aya. Mik'ewa tayi domin gudun dukan ruwan dan kuwa sanyi takeji saboda zazza'bin da ya rufe ta saboda mugun jin da tayi, Cikin sauri sauri take tafiya kamar daga sama ta fara jin kukan Abdulkareem, Hankalin ta ne ya k'ara tashi ta shiga dube dube a gurin cike da rashin tsoro, Tana cikin dubawa tayi karo dashi an yasar dashi a sararin Allah ruwa sai jibgar sa yake, Cikin sauri ta k'arasa ta d'auke shi ta rungume tana k'ara rarraba ido, gilimin mace ta gani ta wuce da gudu ba tareda da tabari ta shaida ta ba, taso binta amma sanin bazata iya ba saboda rawar sanyin da take yasa ta fasa, Kai tsaye sashin Maharani ta nufa zuciyar ta na tsinkewa fargaba da tsoron irin yadda Maharani zata fuskanci abun ya cika mata zuciya, A bakin k'ofa ta durk'ushe cikin rawar murya tace, "Maharani??" Cikin nutsuwa ta sakko daga kan gadon ta ta nufo inda take zuciyar ta na wani irin bugawa a dari da sittin, Hannu ta mik'a mata ba tareda tayi magana ba. Cikin sauri ta bata shi tareda cewa, " a gafarce ni Ranki yadad'e" Ido ta tsura masa har wani lokaci kafin tayi magana cikin matuk'ar razani tace, "waye??? Hadima Farhana tayi k'asa da kai cikin sanyi tace, " bansan ko waye ba Hazoor (Ranki yadad'e) kawai na tsinkayi kukan sa ne ina cikin tafiya koda na duba shine na ganshi cikin wannan halin ruwa yana dukan sa, sai kuma naga gilmin wata mace amma ban shaida ko wacece ba, wannan shine iya abunda na sani, ki fuskance ni dan Allah kar kiyi min gurguwar fahimta" Jinjina kai tayi tace, " kenan akwai masu son ganin bayan sa?? Hadima Farhana tace, "sosai duk wanda yake son ganin bayan ki ze iya ta'ba yaron nan domin hakan yana girgiza ki. Rungume shi tayi tsam a jikin ta tana k'ara zuba masa ido, murmushi me tafe da hawaye ne ya su'buce mata cikin sanyi tace, " duk abunda yayi tsanani yana tareda sauk'i, wata rana hakan ze zama tarihi kamar yadda abubuwa da dama suka zama, Ya zama dole a ninka tsaro akan sa, ki nemo min Uwar Hadimai Urmi kuma ki had'o min da Subbhu Da Uddaiya gobe ina da magana dasu a k'aramar fada ta, sannan ki kula da kanki kema" Mik'ewa tayi tana cewa, "ina godiya Sarauniya, zanyi kamar yadda kikace" Batace komai ba sai ma komawa da tayi ta kwantar dashi kan gado, Arjula ta kalla cikin rauni tace, "wai sai yaushe ne ze dawo Arjulah?? Tin inada sa rai har na fara karaya, tabbas idan be zo ba mak'iya zasu hallakar dani sannan su cutar da mutane na, bana son abunda ya faru a baya ya k'ara faruwa, ya kamata yazo gareni tin kafin k'arfi na ya k'are, Na mallaka rayuwar wannan yaro gareshi ne a matsayin mahaifi idan be zo ba tayaya Abdulkareem ze san yana da uba?, Ina son yaron nan kamar yadda nake son sa hakan ta faru ne tin lokacin da na fara d'ora ido na akan sa, idan aka cutar dashi tabbas anyi min matuk'ar illa a rayuwa ta, bana so hakan ta faru Arjula, yanzu shikenan ya gujeni??" Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro kan kumatun ta, Goge su tayi kafin ta fara k'ok'arin bawa Abdulkareem temakon da ze dawo hayyacin sa. Washe gari kamar yadda tace hakan akayi, tattaunawa ta gaggawa sukayi yayin da ta tuhumi Hadima Urmi akan abunda ya faru, sai dai itama lokacin da za'ayi hakan make ta akayi ta fad'i a sume, hakan yasa ta bar zancen domin kuwa batajin Hadima Urmi zata bada kai wajen cutar da ita. Waziri. Zaune yake kan wani k'awataccen lilo ya kashingid'e sai wani irin murmushi yake me cike da tarin manufofi. Arveen ya kalle shi cike da k'aguwa yace, "Baba wai wane irin tunani kake haka wanda yake sa ka wannan murmushin??? Kai tsaye yace, " farin ciki, inaji a jiki na lokacin nasara ta ya fara, amma idan muka bari Gimbiya Sunaya ce zata cike mana ramin da muka dad'e muna ginawa ba tareda mun cimma ruwa ba, yanzu kuwa mun fara ganin idon ruwa tayaya zamu bari ta dawo mana da aiki baya?? Wannan tunanin nayi kuma na gano mafita shiyasa nake murmushi yaro na" Shima murmusawa yayi tareda cewa, "na san kaci dubu sai ceta Baba na, ni kuwa ban ta'ba tunani akan Sunaya da d'an ta ba, kuma tabbas zasu rushe mana tubalin mu, ya zamuyi dasu Baba?? Waziri yace, " yarinyar nan ta cika ta tumbatsa hallau kuma ta shahara, tinda ta hau mulki bata ta'ba nema na a matsayin wazirin wannan masarauta ba komai ita take yankewa da kanta, tayi fatali da dokokin masarauta da tsare tsaren ta babu rawan ta da shawartar wani sai wannan d'iya musulmar nan Farhana, to nima a wannan lokacin na yanke mata hukunci a matsayi na na yayan uban ta zan nemo mata auren wani yarima d'an Sarauniyar da takeji da kanta take takara da ikon Mahalakhshmi, yaron yana da mugun son mata kuma ita d'in macece wadda kowa yake sha'awar ta dan haka idan na had'a su sai na koma gefe na zuba ido, idan ya aure ta kaga shikenan mu kuma sai mu shigar da k'udurin mu" Dariya Arveen ya farayi kamar sabon mahaukaci. Cikin rashin ganewa Waziri yace, "yaro na?? Meye kuma na irin wannan dariyar??? Arveen yace, " Maha? Mahalakhshmi ce zata amince kayi mata za'bin aure ina ai bazata amince ba" Waziri yayi murmushin manyan ce ya rausayar da kai kafin yace, "Yaro na ka girmi Mahalakhshmi sai dai kuma duk da hakan nine na haife ka, na haifi kamar ka ma bare kuma ita?? Na riga na shirya tin kafin na fito, shiyasa nace maka shi d'in yana da son mata bare kuma ita, nasan a nashi gigin dole ze kai hannu jikin ta, kasan meye abunda zatayi?? Y'ar k'aramar wuk'ar da take sokewa a k'ugu zata zare ta yanka masa tafin hannun sa, ta yuwu ma harda wani hukuncin zata had'a masa idan yayi wasa ma a ranar ba lallai yaga uwar sa ba, kuma kana ganin mahaifiyar sa zata amince??? a lokacin da ta haruzuk'o tace bazata yarda ba nasan zatayi ta tunanin hanyar da zatabi don ta rama abunda Mahalakhshmi tayi mata zata shiga tashin hankali dan tasan Maha tafi k'arfin ta, ni kuma a lokacin zan tunzura ta akan cewa idan bata aurawa d'an ta Maha ba bazata ta'ba rama abunda akayi mata ba, kaga daga haka na had'a hatsaniya tsakanin manyan masarautun nan guda biyu idan yaso su kashe kansu, mu dama ai dukan su adawa muke dasu domin kuwa sunyi mana tazara sun nuna mana iyakar mu" Arveen yayi dariya tareda cewa, "lallai Baba na kana da matuk'ar basira wannan abu yayi" Farhana ce tsugunne a gaban Mahaifiyar ta idanun ta suna zubda k'walla, cikin rawar murya tace, "Mama??? 'Dago zararrun idanun ta tayi ta zuba a kanta tana binta da kallo irin na mamaki. Farhana ta rik'o hannun ta gami da Fashewa da matsanancin kuka, sai da ta sassauta sannan tace, " Mama kiyi hak'uri a bisa shareki da nayi shekara da shekaru, bansan cewa ke d'in mahaifiya ta bace amma yanzu insha Allah zaki samu kulawa daga gareni bazan k'ara barin ki ba Mama, dan Allah kice wani abu, kiyi min magana ko zanji dad'i kice kin yafe min Mama ko kina fushi dani ne??? Girgiza kai tayi alamar a'a idanun ta suna zubar da hawaye kamar famfo sai dai ko motsa baki batayi ba bare sa ran magana. Hadima Farhana tasa gefen mayafin ta tana goge mata k'wallar cike da k'auna gami da tausayawa. Mik'ewa tayi tana cewa, "zan dawo na k'ara duba ki Mama bazan k'ara bari a zalumce ki ba" Raj. Yana kwance ya tada kai da cinyar Gimbiya Sunaya yana kallon sama sai murmushi yake. d'an dukan sa tayi a kafad'a gami da cewa, "kai d'ana na lura yanzu soyayya tasa ka fara zauncewa, wannan murmushin da kake sunan sa me??? Bana son lalaci fa, kasan ita sarauniya sai dai jarumi amma kai gaba d'ayan ka rago ne, bana so ta saka gasar shekara ka kasa cin gasar hakan ze zubar maka da martaba da kimar ka kaji ko?? Dan haka kayi k'ok'arin zama jarumi kafin lokacin" Dariya yayi yace, "Mama?? Ai nasan tana so na ko banci gasa ba amma dai zanzama jarumi kamar yadda kike so Mama ta" Dariya tayi tace, "shashashan d'ana" Kamar yadda yace su had'u haka suka k'ara had'uwa a gurin waccan ranar. cikin k'unar zuci da 'bacin rai Hadima Farhana tace, " na amince da buk'atar ka, zanyi duk yadda zanyi na k'wato mahaifiya ta daga wannan mugun k'arnin bazan iya cigaba da kallon ta a haka ba, na yarda na had'a hannu da kai domin kawo k'arshen zalumci, daga yau na dawo tsagin ka, tin yanzu ma a fara daga wane mataki zamu d'ora??? Jinjina kai yayi yace, babu shakka kinyi tunani me kyau Hadima Farhana fatan zaki cigaba da bada k'ofa, yanzu abunda zaki fara shine jiyo mana sirrin ta da duk wani shirin ta haka ne ze sa musan ta wace k'ofa ya kamata mu shigo mata" Hadima Farhana tace, "zanyi hakan ba tareda na nuna mata wata alama ba, zan zauna a matsayin yardarjiyar ta sai dai kuma ba hakan bane yanzu bakin alk'alami ya riga ya bushe, zata gane kuren ta tabbas tinda abun nata haka yake nima bazanji tausayin ta ba" Da haka suka rabu kai tsaye ta koma wajen ta domin lokacin cin abinci ta yayi. Bayan an kammala zaman fada waziri ya taso ya dawo kusa da ita, cikin nutsuwa da nuna kulawa da kamilanci yace, " y'ata? Be kamata ki zauna ba aure ba har yanzu,ya kamata kiyi aure kodan mu k'ara samun k'warin guiwa akan ki, baza mu so rasa jinin ki ba y'ata, ki manta da abunda ya wuce ki gina rayuwar ki ta gaba" Girgiza kai tayi tace, "waziri ka tsaya a matsayin ka karkace zakayi kutse a cikin lamari na domin baka da wani amfani gareni banajin zanyi wani aure dan haka ka k'yale ni" K'ara marairaice fuska yayi yace, "haba y'a ta? Gimbiya Jusiyya kina jin abunda y'arki take cewa?? Ke kad'ai ta yarda dake dan haka kiyi mata bayani yadda zata fahimta, ya kamata tayi aure domin shine cikar y'a mace" Gimbiya Jusiyya taja dogon numfashi gami da jinjina kai sannan tace, "shikenan zanyi nazari akai" Sosai Gimbiya Jusiyya tayi tunani akan goben y'ar ta a take taji ta aminta da shawarar Waziri, hakan yasa ta lalla'ba Maharani Gami da binta da nasihu masu ma'ana har ta amince. Waziri jiki na rawa ya aikawa masarautar sakon gayyata, abunka da me jiran kad'an ba 'bata lokaci suka amsa tareda tsayar da ranar zuwa. *Karku manta ku biya domin ku karanta cikin Aminci😊* *INDO CE..* [03/03, 11:56 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* Marubuciyar SIRRIN K'ETA. A JINI 'DAYA. 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~8* بسم الله الر حمن الر حيم Last Free Page *Tajmahaal na kud'i ne Naira 100 kacal cikin rahusa😄* *Domin magana dani ta prvt ga link👇* https://wa.me/message/45UKV47T7IM2F1 *(Sanarwa. Ga masu buk'atar siyan littafin TAJMAHAAL har yanzu k'ofa a bud'e take ku gaggauta mallakar naku ku karanta cikin aminci da kwanciyar hankali😊 Kuyi min magana ta wannan link na sama👆 sai na jiku😊)* *(k'arshen shafin kyauta, daga yau indai kuka ga littafi na a waje to ba da izini na ba, ku daure ku siyi naku 100 ba yawa)* Kamar me tsoron taka k'asa haka take takawa har ta isa cikin kurkukun. Kamar yadda ta saba tana ragu'be a gefe ta kifa kanta cikin guiwoyin ta tareda rungumo k'afafun ta da hannayen ta. Cikin nutsuwa ta k'arasa, a kanta ta tsaya gami da zuba mata wadatattun idanun ta, Ta dad'e a haka kafin ta durk'usa kan guiwoyin ta tana fuskantar ta, Cikin wata irin murya me cike da aminci tace, "Ummeeh??? 'Dago idanun ta da sukayi jajur tayi ta zuba su a kanta. Kallon kallo suka fara yiwa juna ido cikin ido babu wanda yayi alamar janye kowa kallon tuhuma yake watsawa kowa, (Maharaniey Mahalakhshmiey,,) ce, (Sarauniya Mahalakhshmi ) ce ta katse shirun cikin maraitacciyar murya tace, " Ummeeh!?? wannan ne karon farko da na fara karya miki alk'awari, kiyi hak'urii nima ba'a son rai na hakan ta faru ba, Farhana ta matsa ne shiyasa amma ba da son rai na bane Ummeeh, karkiyi fushi dani, kiyi magana karkiyi shiru kice min wani abu Ummeeh!! Ba tace komai ba sai zuba mata idanun ta da tini hawaye suke zirya a cikin su tayi. Hannu tasa tana share mata k'wallar sannan ta Dafa guiwar ta cikin rauni tace, "kenan?? Bazan k'ara jin muryar ki ba? Shikenan bazaki k'ara ce min komai ba?? Kiyi magana Ummeeh dan Allah, Magauta zasuyi nasara a kaina sun fara cin galaba ta , Na fara gajiyawa komai ya fara k'are min, sun kusa yin nasara a kaina, Ina jin bak'in ciki sosai zuciya ta tana k'una idan na ganki ina tuna abubuwa da dama,, na kasa mantawa, komai ya juya min yanzu, na kusa sarewa Ummeeh kiyi magana, Idan na 'bata miki rai ne akan Farhana kiyi min hukunci amma karkiyi fushi dani, hakan ze k'ara jefa rayuwa ta cikin yanayi , yanayi mara dad'in gaske, idanun ki suna zubar da hawaye Ummeeh, ashe akwai wannan ranar? Da zata zo min da irin wannan barazanar tana nuna min hawaye a idon ki???????, ki dena kuka Ummeeh , meyesa zuciya ta take gaya min abu da dama?? Yaushe ne komai ze dawo dai-dai?? Surutu na bashi da amfani gareki kenan?? Ko meye zan fad'a baza kice komai ba? Fad'awa tayi jikinta tana kukan zuci me tsananin rad'ad'i da k'una. A hankali ta d'ago hannu ta d'ora a kanta tana shafawa har zuwa gadon bayan ta cikin sigar rarrashi. A hankali ta fara sauke sassanyar ajiyar zuciya har wani lokaci kafin ta janye jikin ta tana kallon ta kallo me tarin ma'anoni, Cikin sanyi tace, " Ummeeh inaji a jiki na kamar baya zata dawo" Mik'ewa tayi tana goge fuskar ta ba tareda ta k'ara cewa uffan ba ta juya tabar wajen.. Kamar yadda suka tsara haka komai ya tafi dai-dai, Ba dan taso ba suka shirya komai, kamar yadda waziri yayi zato hakan ta faru Maharani kuwa ta balle tace bata san zance ba, Mahaifiyar sa kuwa ranta yayi bala'in 'baci, haka aka tashi wasu da farin ciki wasu akasin haka. Bata tsaya cikin masarautar ba har sai da ta danga da waje sannan ta tsaya tana kalle kalle zuciyar ta na zafi, bak'in ciki da takaicin abunda Waziri yayi mata ya hanata sakat. Gimbiya Jusi ce ta k'araso wajen cikin sanyi tace, "Maharani! Ina ma baki aikata abunda kika aikata ba? Meyesa baza kiyi aure ba? waziri gaskiya yake fad'a ba k'arya ba a gani na hakan ze fi mutumci da daraja gareki, Meyesa kuma zaki ta'ba yaron mutane? Shifa ba d'an Tajmahaal d'in mu bane Kuma Kin sani masarautar su jiran k'iriss sukeyi akan mu sun dad'e suna neman abunda ze had'a su da mu da kin k'yale shi ai ba kuskure ya aikata me girma ba" A zafafe tace, "na k'yale shi kika ce?? Laifin sa ma ba babba bane!! Dama ba kowa ne ze kalli abun da girma ba amma ni a waje na babban laifi ne kuma ba sai d'an wannan masarautar ba ko d'an waye dole ne ya kar'bi hukunci na idan yayi kuskure a duk inda yake bare kuma masarauta ta ya shigo, babban kuskure ne mutum ya kai hannan sa kaina dan kuwa hakan yana ta'ba jikima ta k'warai da gaske, kuma ko kece kikayi hakan tabbas bazaki tsira ba" Jinjina kai Gimbiya Jusiyya tayi tace, "Maharani Maha gaskiya ne kina da darajar da kin wuce hakan to amma ina fargabar abunda muguwar matar nan zatayi bata da mutunci ko kad'an musamman ga duk wanda ya ta'ba d'an ta, Tabbas waziri ya fad'i gaskiya da yace kiyi aure matsalar da ta faru da ba d'an mutunci yaso had'a ki dashi ba, Amma Maharani? Sai yaushe ne zakiyi aure kuma waye za'bin ki?? Kallon ta tayi kafin ta maida hankalin ta kan ruwan da yake ta gudana, girgiza kai tayi tace, " ni bani da za'bi face za'bin Allah, Ban sani ba ko yana raye ko ya mutu? Ko yana duniya ko akasin haka?? Ta yuwu ma a k'addara ta babu aure a ciki, Na kasa gane meyesa kuke da son shiga sharafin da babu ku a ciki , ni bana tsoron ta haka bana shakkar ta duk abunda zatayi ina tsammatar ta, Amma sai dai inaji a jiki na kamar hakan shiri ne, anyi ne domin a samu makamin tarwatsani" Murmushi tayi ta k'ara da cewa, "Sai dai bana jin hakan zata yiwu abun bauta ze kawo min makamin da zan yak'i duk wani me shirin yak'a ta ko a gida ko a daji" Gimbiya Jusi taja numfashi kafin tace, "naji dad'in jin hakan daga gareki, dama tsoro ba na jarumi bane, ina alfahari dake y'ata, Zan wuce ciki sai kin shigo ko zaki zo tare dani!? Girgiza kai tayi tareda cewa, " ki turo Farhana" Murmushi tayi tace, "Sarauta izzarki tana burge ni yarinya ta, zan turo ta" Daga haka ta juya ta nufi ciki. 'Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tareda dafe kanta da yake juyawa, tabbas wata rayuwar tana shirin kutso kai cikin rayuwar ta shin wane abu ne ze bayyana haka?? Suna zaune suna tattaunawa Farhana ta k'araso wajen a tsaye ta tsaya kafin tace, "meye shirin ka na gaba yanzu?? Maharani yanzu a cikin matuk'ar tsoro take domin kuwa abunda ya faru bazaka shigar da wani abu ba?? K'asaitaccen murmushi ya saki kafin yace, " gaggawar me kike ne?? Zuba ido zamuyi muga ta ina zasu fara 'bullo mata mu ma sai mu samu hanyar shiga hakan shine a tunani na bansan a naki ba amma meye ke abunda kike gani?? Farhana tace, "muguwar mata ina da wani mummunan kwanto a kanta zamu tsara komai a nutse, ni fa nace bazan iya k'yale ta ba, hankali na baze ta'ba kwanciya ba indai da ita a cikin gidan nan" Kowa hada hadar sa yake a masarautar kowa yana ta kai kawo,, Tana sama tana shan iska yayin da take kallon abunda yake faruwa a k'asan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, jefi jefi idan ta tuna wani abu takan sauke gwauruwar ajiyar zuciya, Gefen ta kuwa Fadya ce ta zuba mata idanu kamar wadda zata had'iye. Jin ana kallon ta yasa ta juyo, Da sauri Fadya tayi k'asa da kai tareda rintse idanun ta da k'arfi, Cikin mamaki Maharani tace, "Meye abunda kike ne anan?? Na riga na iso inda zanje ai zaku iya tafiya domin kuwa ina son kad'aici ba buk'atar zuwa ku sani gaba" Cikin rawar jiki Fadya tace, "Ranki yadad'e a gafarce ni, aikin mu ne tsaron ki sai dai bamu san hakan bakyaso ba da tini mun tafi, ina godiya sarauniya" Jinjina kai tayi kafin tace, "zaku iya tafiya" kafin su kaiga tafiya wani tsuntsu ya nufo inda suke, tsayawa sukayi kallon sa da mamaki, Kai tsaye wajen da Maharani take tsaye ya nufa yana bud'e fuka-fukai. Zuciyar ta na dukan tara tara tasa hannun ta ciri wasik'ar da yake tafe da ita tana cirewa ya juya yabar wajen, Da ido ta bi wasik'ar cikin zuciyar ta tsoro da firgicin abunda zata gani ya gama lullu'be ta sai dai ko da wasa bata nuna alamar hakan ba. Cikin nutsuwa ta fara warware ta, idon ta ya fara sauka kan Hatimin Masarautar Maruda, Bugun zuciyar ta ne ya k'ara tsanan ta cikin k'aguwa ta k'arasa bud'e ta tafara karanta sak'on ciki. "Maharani Mahalakhshmi tabbas kin aikata kuskure akan d'a na, kamar yadda baki aminta a ta'ba jama'ar ki ba sai kin d'au mataki haka nima ban amince a ta'ba tawa ba bare kuma d'an ciki na, ya zama dole ki biya abunda kika d'auka shine cikar kwanciyar hankalin ki, yanzu ne lokacin da zaki nunawa jama'ar ki son su kike ko kuwa kinfi son kanki ne, zasu fuskanci mummunan iftila'i daga gareni idan kin za'bi hakan idan kuma ba haka ba ki amsa kira na ki shigo cikin Masarauta ta ba tareda kowa naki ba, sai kinzo zaki iya banbancewa zaki fita ko kin shigo kenan, Sannan idan zaki zo kiyi shirin amarci domin kuwa auren ki da d'ana shine kawai ze iya biya miki bashin da kika d'auka, Kiyi tunani akan kanki da kuma mutanen ki za'bi ya rage naki duk hukuncin da kika yanke ki sanar dani,, kuma ki sani ko a yanzu akwai mutane na a cikin masarautar ki idan ma baki zo ba to tabbas za'azo a d'akko min ke har cikin fadar ki" Dafe k'irji tayi saboda wani irin kad'uwa da tayi ta jigina jikin bango gami da lumshe ido. Jiki ba k'wari ta koma turakar ta zama kawai tayi tana k'ara zubawa wasik'ar ido tarasa meyesa take jin gaba d'aya ta rasa wani karsashin ta da k'warin guiwar ta duk wata jarumtar ta ta k'wace mata sai wani mugun tsoro da firgici da ya sako ta gaba. Tin daga ranar bata da wani kwanciyar hankali ko abinci bata iya zama taci duk da an k'ara tsananta tsaro a masarautar tana tsoron kar wani abu ya samu mutanen ta a dalilin ta, Gashi har lokaci yana tafiya ta kasa tsayarwa zuciyar ta hukunci d'aya. Kamar macijin da babu dafi take tafiya sululu har ta isa kurkukun tana shiga d'akin ta fad'a jikin ta tareda fashewa da wani hatsabibin kuka, taja lokaci tanayi kafin ta sassauta cikin rawar murya tace, "Ummeeh idan ban dawo ba dan Allah karki cigaba da irin wannan rayuwar yanzu zan saka kaina a kasada domin ceton jama'a ta duk sun ta'allak'a ne gareni bazan bari a cutar dasu ba, yanzu lokaci yayi wanda k'arfi na ya gama k'arewa zan amsa kiran Sarauniya Samina duk abunda tayi min zan d'auka ko zan fito ko bazan fito ba, banida masaniya akai nidai buri na d'aya ne kiyi min magana kafin tafiya, lokaci ya k'ure babu wani abu da ze iya dakatar da wannan abu da ya tinkaro ni, kuma na tabbata Waziri ne ya shirya min komai, nasan ke kin fahimta Ummeeh Amma Mama Jusiyya ta kasa fahimtar wanene shi, Amma nasan indai har yana raye komai daren dad'ewa ze dawo kuma shine ze ceto rayuwa ta daga ko wane irin k'angi, ki gazgata min haka Ummeeh" Mik'o mata wani abu tayi tana Gyad'a kai alamar haka ne, Kar'ba tayi tana kallon abun kamar Rakhee da d'an mamaki tace, "menene wannan?? Bata magana dan haka bata da hanyar da zata iya yi mata bayani. Share k'wallar ta tayi tana murmushi tace, " Nagode Ummeeh" Cikin sauri ta tashi tabar kurkukun wani lungu ta shiga wanda ko mutane babu sojojin ma sai d'ai-d'ai da tafiyar tayi zurfi kuwa sai ya zamana babu kowa a wajen. Wata Babbar k'ofa ce ta zallar k'arfe ta bayyana a gaban ta, cikin sauri ta shiga gurin take wani gunki ya bayyana a ciki, k'arasawa tayi a hankali tana kallon gunki fuskar ta cike da hawaye, durk'usawa tayi a gaban sa zata fara kuka kenan taji wata murya ta dakatar da ita da cewa, "Mahalakhshmiey Sarauniya ce kuma ita d'in jaruma ce wadda abun bauta be amince da zubar hawayen ta ba, hakan kuskure ne kike aikatawa abun bauta be amince ki zubda k'walla ba domin kina da k'arfin dantse da kuma k'arfin iko, ke d'in kin kasance jigo ce ga dubban Al'uma kece k'arfin su kuma k'warin guiwar su, idan suka ga hawayen ki hakan yana nufin kin gaza kenan hakan zesa su rasa duk wani karsashi, meye yayi zafi yasa ki cikin wannan hali yake wannan Sarauniya?? Da sauri ta tashi tana murmushi gami da goge hawayen, da farin ciki tace, " Guru Ummeeh " Da sauri yace, "meye ya same ta?? Girgiza kai tayi tana murmushi, tayi taku biyu sannan ta juyo mik'a masa abun tayi tareda cewa ta bani wannan amma ta kasa magana sai yaushe zata fara magana Guru???" Kar'bar abun yayi ya lumshe ido tareda damk'e Rakheen a hannun sa yana karanto wasu yan abubuwa, bud'e ido yayi ya mik'o mata cike da k'warin guiwa yace, "wannan naki ne a duk inda yake ze kasance tare dake, Kuma ita d'in baza ta k'ara magana ba har sai ranar da ya bayyana a cikin Masarautar Purla a lokacin ne komai ze dawo mata dai-dai indai kikaji maganar ta to tabbas yazo, ki rik'e wannan duk inda kika shiga karki bari ki rabu dashi shi d'in kariya ne gareki" Jinjina kai tayi tace, "Nagode kuma yanzu na samu k'warin guiwa amma Guru zan shiga Masarautar Maruda ban sani ba ko zan fito" Kai tsaye yace, "kar kije, akwai matsala a shigar ki wannan Masarautar ki jira lokaci" Had'e fuska tayi tana girgiza kai alamar a'a cikin k'asaita tace, "Guru iya abunda kake iya gani kenan ni kuma ina ganin goben mutanen wannan yanki nawa ne, zanyi komai domin na zama kariya garesu dan haka bana buk'atar ka dakatar dani ko meye ze faru zanje" Yasan ba'ayi mata musu dan haka yace, "ina miki fatan nasara a rayuwa" Juyawa tayi ta fice ba tareda ta k'ara tanka masa ba, Tana dawowa turakar ta ta d'akko Alk'alami da abun rubutu domin rubata wasik'a zuwa ga Masarautar Maruda, Arjulaa sai k'ok'arin hana take amma tak'i ji har ta gama rubutawa sannan ta aika Arjulaa domin isar da sak'on, babu yadda Arjulaa ta iya haka taje ta isar. Yau ce ranar da zata amsa kiran ba tareda ta bari kowa ya sani ba daga ita sai Farhana sai kuma d'ai-d'ai daga cikin wanda ta aminta dasu. Farhana tashin hankalin ta ya kasa misaltuwa kwata kwata bata son zuwan Maharani amma ta rasa yadda zatayi ta dakatar da ita. Tana zaune tana shiryawa ta zuba kayan ado a jikinta ta ko ina sai k'yak'yali take tayi kyau kamar ba gobe, fuskar ta fayau sai kwalli rad'au a idanun ta, A zahiri mutum baze iya gane irin fargaba da tsoron da take ciki ba amma a zuci har yanzu addu'a take akan za'bi mafi kyawu ko zuwan ko akasin sa. Wani irin bugawa zuciyar ta ta fara yi duff duff d'aya bayan d'aya, A razane ta kalli Arjulaa tana cewa, "Arjulaa kina jin abunda nake ji?? A cikin Bugun zuciya ta nakejin Takun sawun gwarzon Doki tamkar a cikin zuciya ta yake tafiya, meye hakan yake nufi Arjulaa ki fita maza kiyi min bincike ki gane abunda yake faruwa. Waziri yana kwance akan gadon sa suna hira shida d'an sa cikin farin ciki da nishad'i, lokaci d'aya ya fara jin bugun zuciyar sa ya fara canjawa ta ko ina yake jin takun Doki yana tinkaro sa da mugun k'arfi har gadon da yake kai yana amsawa, cikin sauri ya rik'o Hannun Arveen yana cewa, " Arveen duhu nake gani duhu!! duhu!!! Arveen, zuciya ta zata tarwatse jiki na rawa yake ka rik'e ni d'akin ya fara girgizawa Arveen" Arveen kuwa ya kasa yin komai ga mahaifin sa saboda shima tini wannan iftila'in ya afko masa jikin sa ya d'auki wani mugun zafi. Gimbiya Sunaya tana rik'e da abinci ta nufo turakar ta yayin da Raj yake kwance yana baccin sa cikin kwanciyar hankali, wata muguwar Tsawar da ta ratsa kunnuwan su ce tasa suka firgita a lokaci d'aya, Watsi tayi da kayan abinci ta nufu Raj da gudu suka rungume juna a matuk'ar tsorace, Raj da yake yana da mugun tsoro ga ragon ta tini ya fara kuka yana cewa, Mama Ido na ya dena gani Mama zuciya ta tana bugawa tamkar Takun fusataccen doki, ko dai yak'in da za'a rusa Tajmahaal yazo Mama?? K'ara rungume shi Gimbiya Sunaya tayi tana cewa, "'dakin mu yana girgizawa ko ina yana amsawa Raj wane irin Duhu ne yake tinkaro mu?? Nima inajin abunda kake ji d'ana karka damu kanka ko mutawa zamuyi tare zamu mutu bazan bari komai ya same ka ba" Zamewa Gimbiya Jusiyya tayi yiifff ta fad'i a tsayen da take babu alamar numfashi a tattare da ita. A firgice Hadimar ta tayi kanta tana kiran sunan ta amma ina, jijjiga ta ta shiga yi tana cewa ki tashi karki mutu banyi miki komai ba" 'Jakadiya ce tayi saurin k'arasowa tana cewa, "Ranki yadad'e me yake faruwa ne suma kikayi ko mutawa" Hadima tace "bata numfashi anya ba mutuwa tayi ba??? Shiru sukayi suna kallon ta saboda bugawar da zuciyar ta ta farayi lokaci d'aya dufff dufff dudufff, kallon kallo sukayi take tsoro ya k'ara ziyartar su, a firgicr Jakadiya tace, " Takun Doki kuma Jarumin Doki tareda mugun duhu Hadima kinga mu tashi muyi ta kan mu domin kuwa mu abun bauta ya tseratar damu bamu shiga irin wannan hali ba dan haka kar laifin ya hau kan mu mu tashi mu gudu" Kafin Jakadiya ta k'arasa magana tini Hadima taje wajen k'ofa suka rufa da gudu gudu suka bar sashin" Tsananin Hargitsewar da kansa tayi da kuma irin rikicin da zuciyar sa ta shiga yasa ya fara fizge fizge da tirjiya yana ihu, da sauri tayo kansa tana furta sunan sa tareda tambayar lafiyar sa amma kafin ta k'araso ta yanke jiki ta fad'i, Da kyar ya iya furta, "Zuciya ta zata fashe" Hayaniyar da taji Masarautar ta kaure dashi ne yasa tayi saurin tashi ta d'akko abun hangen nesa ta lek'awa. Hadima Farhana ce ta zuba a gaban ta tana haki tace, "kiyi sauri ki fito Hazoor akwai babbar matsala a Tajmahaal ki fito ki gani masarauta ta hargitse. Da gudu gudu ta fito tana numfarfashi. Inda take hawa domin yin sanarwa ta hau cikin d'aga murya tace, " kowa ya nutsu, maza a shirya Tarko akan ko wace hanya ta ko wace kusurwar Yankin purlasiri sannan a kulle ko wace k'ofa a bar guda d'aya itama a saka tsaro a kanta sannan a tura sojoji Dari uku wajen Masarauta domin yin bincike akai, a kad'a k'ararrawar yak'i domin tabbatarwa wanda basu sani ba, masu kibiya su dai-dai-ta kowa ya kasance cikin shiri domin fuskantar ko wace irin k'ura ce take tinkaro mu, muyi k'ok'arin bawa junan mu kariya" Zuwa yanzu ta kasa magana saboda k'ara tsananta da bugun zuciyar ta yayi. Bayan wani d'an lokaci... *(karku manta wannan shine K'arshen shafin kyauta indai kuka ga littafi na a waje daga yau to ba da izini na ba, kuyi k'ok'arin mallakar naku kar ku bari a abar ku a baya )* *INDO CE..* [16/03, 8:37 p.m.] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GhmvkCVguNJ004XgclluXD *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~9* بسم الله الر حمن الر حيم *(k'orafe k'orafen da kuke min akan cewa na k'ara free pages yasa na k'ara muku😊😊 ina fatan zakuyi farin ciki da hakan🥰🥰)* Arjula ta dawo tareda nufar inda shugabar ta take ta sauka kan kafad'ar ta. Ido Maharani ta zuba mata cike da k'aguwa da son jin abunda take tafe dashi, lokaci d'aya jikin ta yayi wani mugun sanyi. K'ara hargitsewar da masarautar tayi ne yasa ta matso domin ganin abunda yake faruwa. Wata K'ararrawa aka shiga bugawa wadda ta k'ara gigita duk ilahirin mutanen cikin masarautar na ciki da waje kowa sai da ya bayyano kuma kowa ya mayar da hankali kan k'ofar masarautar domin kuwa k'ararrawar da aka kad'a tana nuni ne da cewar wani babban abu ya tinkaro cikin masarautar. Kar'bar takobun ta wadda take cikin wani kyakkyawan kube tayi a hannun Hadima Farhana cikin sauri ta sakko k'asa cikin shirin ko ta kwana. Dakaru kusan talatin ne rik'e da wasu mazajen sark'ok'i wanda suka yiwa wani mutum dabaibayi da su sai fizge fizge yake yana cewa su sake shi, Har sai da suka dangana da gaban Shugabar su sannan suka tsaya. Subbhu ne ya kalle ta cikin ladabi yace, "Ranki yadad'e wannan da kike gani wani bak'o ne ya shigo cikin yankin ki ba tareda izinin ki ba kuma ba tareda yabi dokoki ba ya shigo kai tsaye kuma gadan gadan a kan dokin sa ya razana duk mutanen mu dake wajen masarauta kuma shi d'in mutum ne me matuk'ar kafiya, fuskar sa a rufe take amma ya tirje ya hana mu bud'e ta gashi bamu san wane irin mutum bane, munyi amfani da tarkunan da kika bamu umarnun had'awa ne mun kama shi da kyar, ranki yadad'e yanzu wane hukunci kika yanke akansa?? Lumshe ido tayi tareda jan wani gwauron numfashi tana karanto addu'o'i Bud'e ido tayi ta zuba su a kansa sannan ta kalli Subbhu a k'asaice tace, "ku sake shi" Cikin k'aramin lokaci suka warware shi daga zargen da sukayi masa,, mutum ne kamar kowa amma duk da fuskar sa a rufe take kallo d'aya zakayi masa ka fahimci cikar haiba da zallar kwarjini gami da k'arfin dantse a tattare dashi. Ido Maharani ta zuba masa zuciyar ta fall tunane tunane kala-kala,,, bayan shud'ewar lokaci me tsayi yau ce rana ta farko wadda ta d'ora idon ta akan abu kuma taji bata son saukewa" Ajiyar zuciya ta sauke tareda lumshe zaratan idanun ta, takawa ta shigayi har sai da tayi taku uku sannan ta tsaya cikin zallar zarra tace, "bud'e min fuskar ka" Shiru kamar ba dashi take ba ko motsawa beyi ba. Ba tace masa komai ba dan bata son jayayya cike da jarumta ta k'arasa inda yake ta shammace shi ta janye abunda yayi nad'in dashi, take kyakkyawar fuskar sa ta bayyana, Ido ya zuba mata kamar yadda itama ta zuba masa, Suka shiga yiwa juna kallo na rashin tsoro da kuma rashin shakkar juna. Sun d'ebi lokaci cikin wannan yanayi kafin ta sauke numfashi, murmushin izza tayi tareda cewa, "Ya kai me wannan fuska ma'abociyar kwarjini ina son sanin waye kai" K'asa yayi da kai ya d'ago ya k'ara kallon sannan ya koma kallon gefe cikin kamalalliyar muryar sa yace, " bawan Allah" Har cikin ranta sai da maganar ta ratsa ta lokaci d'aya ta tafi da bugun Zuciyar ta, jinjina kai tayi ta k'ara da cewa, "Dani da kai dasu duk bayin sa ne sai dai mun kasance muna addini mabanbanta, masarautar Purlasiri tana cike ne da mutane iri iri kuma masu addinai daban daban Ba mu kasance mabiya addini d'aya ba, irin lafazin bakin ka kai tsaye ya tabbatar min da cewar kai d'in mabiyin addinin islam ne, Sai dai kuma mabiya addinin nan babu su yanzu a wannan masarauta sun riga sun shud'e cikin wata tafiyar ruwa da ta ta'ba wanzuwa a cikin wannan masarauta, Daga ina kake??? Ya sunan ka???? Kamar da dutse take magana yayi mata banza ko kallon ta baya yi bare ta gane yasan tana magana. Murmushi tayi gami da yin tattaki sannan tace, " Kana da jinkai, sai dai kuma nan fada ta ce, kai d'in baka yi min kama da wani d'an sarakai ba, kafi kama da irin mutanen dajin nan" Kai tsaye yace, "tunanin ki ya baki dai-dai ni na rayu ne a daji" K'ara ware masa idanu tayi cikin gadara da tsantsar izza tace, "sunan ka" "ARUUF''!!!!!!!!!!! ARUUFUL-ANSAAR!!!!!!!!!!!!!!!! Ya fad'a cike da karsashi. Sai da tsigar jikin ta ta yarfa saboda yanayin yadda yayi maganar me bala'in tsargawa mutum lokaci d'aya, akan la'b'ban ta ta mai-mai-ta "Aruuful'Ansaar " ta fad'a tana jefa idanun ta cikin k'wayar idon sa. Shima kallon ta yake cike da jarumta. Matsowa ta k'arayi kusa dashi sannan tace, "Aruufu'Ansaar? Tabbas wannan suna ne me dad'i sosai, uhm, ya sunan baban ka???? Kafin ta rufe baki yace, "Abu Ansaar " Girgiza kai tayi tace, "sunan sa nake magana" Ya k'ara mai-mai-ta mata cewar "Abuu Ansaar" Ganin nema yake ya 'bata mata lokaci yasa tace, "mahaifiyar ka fa??? Kara tsaye yace, " Ummu Ansaar" Zuwa yanzu zuciyar ta ta fara turnuk'owa ranta ya fara 'baci amma sai ta danne ta jinjina kai kafin tace, "dangin ka fa?? K'asa yayi da idon sa tareda cewa, " Ummu Ansaar Abu Ansaar sune kawai dangi na ban rayu tareda kowa ba sai su, sune na sani" Jinjina kai tayi tace, "na yarda da hakan amma dole mahaifan ka suna da cikakken suna na gaskiya kowa ya shaida su d'in iyayen ka ne ba buk'atar k'ara mai-mai-tawa, Meye sunan ta? Sai da ya kalli cikin k'wayar idon ta sannan yace, " Ummu Ansaar " Zuwa yanzu ji take kamar ta zaro takobin ta daga cikin koben ta ta falle masa kai saboda 'bacin rai gaba d'aya ji take ya gama zubar mata da mutunci kimar ta ta gama ta'buwa, Mik'awa Hadima Farhana Takobin tayi ta k'ara matsawa kusa dashi, ba tareda shakka ba tasa hannu ta tallafo ha'bar sa tana cewa, "ya kamata ka gane cewa kaifa ba yaro bane da za'ace sunan Maman kawai ya sani" Cikin zafin nama da zafin zuciya ya yarfa mata wani shigaggen marin da sai da taji duniyar ta tsaya mata cakkkk lokaci d'aya. Cike da k'warewar aikin su sukayo kansa har sun fara zarge shi cikin sark'ok'in suna shirin hukunta shi. Cikin tsawa tace, "ku dakata!!!!! Dakatawa sukayi kamar yadda ta buk'ata, tasa hannu ta kwashe gashin ta da ya rufe mata fuska sakamakon hargitsuwar da tayi saboda azabar marin, Cikin d'aga murya tace, " shi d'in ya kasance bak'o ne yayi kuskure a bisa rashin sani tabbas ya kamata yasan wacece Sarauniya Mahalakhshmi yana da kyau kuyi masa bayani yadda ze iya fahimta amma tabbas yayi kuskure" Kallon ta yayi tareda cewa, "mafi girman kuskure shine wanda kika aikata, Ni musulmin k'warai ne kuma addini na be baki damar d'ora hannu a kaina ba, ina ke'ban ce kaina da duk wata mace dan haka ki shiga taitayin ki" Murmushi tayi cikin k'asaitacciyar muryar ta tace, "Aruuful'Ansaar kasan hukuncin duk wanda ya d'ora hannun sa a kan Maharani Mahalakhshmi koda kuwa macece?? Za'a yanke masa babban d'an yatsa indai da niya yayi, a rashin sani kuma ko a kuskure? Za'a yanka tafin hannun sa ne yadda ze gane kuskuren sa, Yau ce ranar farko da na ta'ba yiwa wani mutum da ya d'ora hannun sa a kaina sassauci ka godewa Allah" Cikin d'aga murya tace, "ya cancata da zaman kurkuku har zuwa lokacin da na umarci a fito dashi, ku d'akko jadawalin dokokin masarauta a karanta masa da yadda ze iya fahimta ko na rana d'aya kar ku barshi yabar wannan masarauta daga yau ya zama bawa na" "Yarinya ce ke baki da hankali shiyasa kike irin wannan tunanin, daga ni sai Mahaifina muke rayuwa kuma yanzu sai in zama bawan ki shi kuma in barshi kenan? Ke sarauniya ce ban damu da hakan ba, ban aminta ma da wata halittar mutane a duniya bayan ni da mahaifi na da mahaifiya ta ba bare kuma nasan akwai wata sarauniya, Abu Ansaar yana can yana jirana dan haka zan koma gare shi" Murmushi tayi tace, "Abu Ansaar ma kansa laifin Ansaar ya shafe shi dan haka babu kai babu komawa amma idan ka damu da ganin sa shi ma ze zo kuma yadda ka kasance bawana haka shima ze kasance, zan waiwaye ka cikin lokaci, koda yaushe ka tsammaci zuwa na" Daga haka ta juya tabar wajen cikin takun ta me nuna zallar jinin sarautar dake yawo a cikin jikin ta. Kafin yayi wani yunk'uri sun d'aure shi cikin hanzari dan kuwa sun tsorata da lamarin sa duba da yadda ya basu bak'ar wuya kafin su same shi, kamar yadda tace haka sukayi suka wuce dashi kurkuku. Zuciyar sa kawai k'una take, tinda yake be ta'ba fitowa tudun k'asa cikin mutane ba, yau ce ranar da ya fara tozali dasu amma sun saka masa da wannan rashin albarkar, tunanin irin halin da Abu Ansaar ze kasance kawai yake yasan yana can hankalin sa tashe, ko yawo ya shiga yaga ya d'an jima yanzu hankalin sa zeyi k'ololuwar tashi gashi ba da sanin sa ya fito daga dajin su ba kullum cikin gargad'ar sa yake da fita cikin mutane amma yau tsautsayi yasa dokin sa ya jawo shi garin wasa, Ashe dai Abu Ansaar yasan halin mutanen ne shiyasa yake cewa koda wasa kar yayi marmarin zuwa domin cakud'ad'd'iyar rayuwa sukeyi, Kamar ya zunduma ihu haka yakeji" Raj da jikin sa yake ta tsuma har yanzu yayi lakur a bayan mahaifiyar sa, A razane tace, "Raj meye yafaru ne haka? Waye shi wannan mutum da ya tinkaro mu mukayi wannan girgizar? A tsorace nake har yanzu" Raj yace, "Mama kema kinji tsoro bare kuma ni? Nima ban san ko waye ba kuma har ya d'auki hannu ya mari Maharani kuma ba'a yi masa hukunci ba" Gimbiya Sunaya tace, "Gaskiya ne Raj nima tsoron sa nakeji" Arveen ya kalli mahaifin sa cikin rud'ani yace, "Baba na wai meye dalilin faruwar hakan ne? Ya zama dole ka shiga d'akin tsafin ka yanzu domin ka dubo mana shin wannan na asalin ne ko kuwa wani ne? Tabbas mutumin nan ya kasance me k'warin zuciya da matuk'ar kwarjini, shi d'in jarumin jarumai ne, tinkaro mu da yayi yasa masarautar mu tayi girgizar da ko yak'i ne ya taso sai haka, lallai na dasa alamar tambaya ta akan sa Baba, kuma yanzu k'iyayyata ta dawo gareshi na tsane shi" Bakin makeken gadon ta ta zauna tana k'ara mai-mai-ta tunanin abunda ya faru, na dak'ik'a d'aya ji take bugin zuciyar ta yana k'ara tsanan ta, ta rasa inane inda zata sa kanta taji sanyi, tana matuk'ar jin zafi idan ta tuna yadda ya d'ebi yatsun sa biyar ya tarfa mata tafi a fuska, take taji zuciyar ta ta gaya mata idan bata wahalar dashi ta mayar dashi k'ask'antaccen bawan ta ba baza ta ta'ba hucewa ba, idan ta tuna shid'in musulmi ne kuma takanji wani abu yana sukar k'ahon zuciyar ta. Farhana ce ta matso kusa da ita cikin sigar rarrashi tace, "Hazoor dan Allah ki yi hak'uri ki yafe masa shi d'in yayi kuskure ne a rashin sani amma ze gyara da zarar yasan wacece ke, ni dai ba ta shi ma nake ba, wannan 'bacin ran naki ne na tsani ganin sa bana so maharani ki dena dan Allah" Jinjina kai tayi kafin ta mik'e ta shiga takawa har zuwa wajen taga, murmushi tayi tace, "Farhana ta?? Afuwa ga wanda yayi kuskure hakan yana sawa ne ya k'ara mai-mai-tawa rayuwa ta koyar dani darasai masu tarin yawa, karki damu a kaina indai kina son ki dena ganin fushi na to sai kin dai-dai-ta nutsuwar jama'a ta, sannan zaki gane kaina" Hadima Farhana tace, "ni kuwa zan jarraba Ranki yadad'e" Daga haka tasa kai ta fice ta barta. Hannu ta mik'awa Arjula tareda cewa, "meye kike gani game da Ansaar yanayin sa yana nuni da...... *INDO CE..* [18/03, 9:36 a.m.] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhUTxJ28ext83rI6uvV1xB *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~10* بسم الله الر حمن الر حيم *ga masu buk'atar shiga group na musamman ina nan ina cigaba da posting kullum domin jin k'arshen labarin Naira 100 ne kati kuma 200 domin k'arin bayani ku neme ni ta wannan number 08146838480 gani ya kori ji kar ku bari a baku labari😂* Da Cewa shi d'in jarumi ne, yanayin sa da yadda yake tafiyar da komai tamkar jarumi na, a lokacin da na fara ganin fuskar sa naso ace ba wannan fuskar na gani ba,,, ba dan na riga na sani ba da babu abunda ze hanani cewa shi d'in jinin Abu Abdulkareem ne, sai kace shine,, amma kuma ba shid'in bane, nasan shi a koda yaushe ze kasance yana kama dani ne" Ta k'arasa maganar tana y'ar dariya kafin ta cigaba da cewa, "Ya matuk'ar girgiza ni, zuwa yanzu na riga na yankewa kaina cewa, Alhinin bayyanar AruufulAnsaar ne yasa nakejin bak'on yanayi, Arjula a lokacin da na riga na d'ai-d'aita imani da tausayi na banyi tunanin cewa a duniya akwai wani d'an adam wanda ze zo yafini zarra ba, ban ta'ba kawowa akwai wanda ze iya kallon tsabar ido na ya zabga min mari haka ba, tabbas ina jin rad'ad'i da k'una Arjula, ban zaci akwai mutum wanda yake jin kansa kuma yake da matuk'ar jarumtar da ze iya ja dani akan ido na gaba da gaba, Waye shi Arjula?? Na gigita kuma na k'agu da matuk'ar buk'atar sanin tarihin sa da asalin sa, sai dai ko sunan iyayen sa yak'i furta min bare nasan inane bakin zaren, Arjula yana da kafiya ni kuma inaji da izza da zamu sauke wannan tabbas da zamu iya kawar da matsalar cikin k'aramin lokaci, amma bazan iya ba, babu wanda yake iya samun kaina sai shi kad'ai har mamakin yadda akai na mallaka masa rayuwa ta gaba d'aya nake, gashi yanzu na kasa yarda da kowa na kasa samun kusanci da kowa shi kuma ya riga yayitazara dani, Lokaci lokaci nakanji tamkar ni marainiya ce abu d'aya nake tunawa ya gusar min da duk wannan tunanin tabbas bazanyi kukan maraici ba nan gaba, Arjula ina ta surutu ni kad'ai baza kice komai ba?? Wunin yau ko abinci Waziri be tsaya yi ba ya duk'ufa wajen gano waye Ansaar sai dai har rufewar Almuru manufar abun bata bayyana gareshi ba har sai da ya k'ara raba dare, Zazzafar iska ya furzar tareda zubawa Arveen ido. Cikin sauri Arveen yace, Baba na ka fad'a min shine ko?? Me yake faruwa?? Waziri yace, "Arveen ba shi bane!!! Tabbas wancan ya mutu sai dai yabar baya da hazo!!! Wancan ya mutu mma ta samu wani wanda ze kasance bango a gareta kuma makamin ta, kaico, shi d'in ba kamar ko wane mutum bane dole ne mu san takun mu Arveen yanzu canja Salo zamuyi tabbas" Arveen yace, "Baba na tabbas ina bayan ka indai zebamu matsala kawai mu kawar dashi mu huta" Gimbiya Jusiyya tinda ta farko take faman numfarfashi jikin ta yayi zafi d'auu sai da temakon Jakadiya suka mayar da ita turakar ta sai bata fifita ake ita kuwa tana faman nishe nishe. Hadima Fadya ce ta shigo bayan ta nemi izini, zubewa tayi tana gaisuwa kafin ta k'ara da cewa, "Ranki yadad'e Uwa Jusiyya tana cikin matsanancin yanayi na rashin lafiya" Ido ta zuba mata har wani lokaci kafin tace, "su waye masu kula da ita? Kafin ta rufe baki Hadima Fadya tace, " Ranki yadad'e Hadimar ta da kuma jakadiya sune suke kula da ita yanzun haka hadima ce tazo ta sanar dani kuma tace in sanar miki" Wata rikitacciyar tsawa Maharani ta doka mata, "karki k'ara gauraya maganar ki da tawa, duk saurin da kike ki jira sai nayi shiru sannan ki d'ora karki k'ara musayar yawu dani" Tsananin firgitar da tayi yasa ba shiri taji fitsari ya fara zubowa jikin ta ya d'au kakkarwa gumi ya shiga keto mata ta ko ina, da kyar ta iya cewa, "tuba nake ranki yadad'e sarauniya a gafarce ni a rashin sani ne hakan ta faru na rantse da abun bauta kuma nayi Alk'awari da Maharaja Bazan k'ara kuskuren nan ba" Bata ko kalle ta ba bare tasa ran samun amsa hakan yasa ta tashi tayi waje har tana shirin yin tuntu'be. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi ta gyara mayafin ta ta nufi hanyar fita, Kai tsaye sashin Gimbiya Jusiyya ta wuce ta same ta kwance ta kishingid'a da filo sai maida numfashi take, Ido ta zuba mata kamar bazata d'auke ba sai kuma ta kawar da kai ba tareda tayi magana ba. Gimbiya Jusiyya tace, "jakadiya kuje waje zan neme ku" Jakadiya tace, "Ranki yadad'e yanzu ma kuwa" Sai da suka fita sannan ta nemi guri ta zauna a bakin k'aton gadon, kamar wadda take fizgo maganar da k'yar tace, "Mama Jusi? Meye abunda ya faru dake haka?? Gimbiya Jusiyya tace, " Yarinya ta waye wannan?? Wanda ya shigo wannan Masarauta tamu?? Mayar da kallon ta tayi zuwa gefe a fiffik'e tace, "Ba shine abunda ya kamata ki furta ba ya dace ki bani amsa ta tukunna ki tsirko naki zancen, Aruuful'Ansaar shine sunan sa bayan haka bansan ko waye shi ba, sai dai daga yau zaki iya kiran shi da bawa na a cikin wannan masarauta domin kuwa bashida matsayin da ya wuce wannan" Zazzafar ajiyar zuciya Gimbiya Jusi ta sauke kafin tace, "Kiyi hak'uri a bisa rashin baki amsa da nayi, amsar itace tinda Aruiful'Ansaar ya nufo wannan masarauta naji duk na fita daga cikin nutsuwa ta, na rasa gane neye sirrin hakan, har yanzu na kasa dawowa dai-dai" Numfashi taja sannan tace, "na dasa ayar tambaya a kanku, Gimbiya Sunaya da Gimbiya Jusiyya tabbas naji abunda kuka fad'a sai dai ban shiga irin wannan tashin hankalin ba, tabbas Aruuf mutum ne me tasiri, zan saka wannan a cikin tunani na, ki mayar da hankali akan maganin da ma'aikatan lafiya suka d'oraki a kai dan yanzu kin manyanta dole ki kula da kanki, karkiyi k'ok'arin jefa kanki Hurumi na hakan ze wulak'anta kimar ki" Daga haka ta tashi tana k'ok'arin fita, Dakatar da ita tayi da cewa, "zaki iya fad'an komai a kaina domin kuwa rashin sani yafi dare duhu, Na sani k'warai Aruuf yana da tasiri sosai hakan ne ma yasa zuciyar ki ta fara son yarda dashi tin kafin ki gane ko shi d'in waye, Ki sani kece sarauniyar da kika gagari kowace masarauta ta duniya haka kuma wanda suke son mallakar duniya, mutane ne daban daban a ko wane yanki daga ko wane sassa na duniya haka kuma k'abilu daban daban kowa yana iya k'ok'arin sa dan ganin ya mallake ki ko kuma ya rusa ki, Haka kuma kina da abokan gaba, Ni bana yarda da kowa yanzu sai ke tin daga lokacin da aka tarwatsa farin ciki na aka tarwatsa ahali na haka miji na ma ba'a k'yale shi ba haka d'an cikin ciki na shima be tsira ba, Mahalakhshmiey tabbas idan na zamanto me cutar dake na zama babbar asararriya, bazan iya hakan ba, Zuciya ta tana shiga k'unci idan na tuna yadda kike d'auka ta tamkar wani abu me cutarwa, ni jinin ki ce Maharani Mahaa,, Amma bazance dole sai kin fahimce ni ba nasan zaki gane hakan a duk lokacin da kika zauna kika nutsu, Amma bana so ki yarda da Ansaar cikin lokaci kad'an kiyi bincike me tsauri akan sa, zansha magani na, ki kula da kanki yarinya ta" Shiru tayi tana d'an tunani kafin ta saki wani yalwataccen murmushi sannan tace, "zanyi hakan" Gimbiya Jusiyya ma murmusawa tayi a ranta tana tausayin yarinyar ta-ta. Zaune take ta dafe goshi sai tunane tunane take, ji take kamar kwanyar ta zatayi bindiga saboda irin rud'ani da rikicin da take ciki, Ji tayi an dafa kafad'ar ta ta juyo a hankali, Wasik'a kuyangar ta mik'a mata ba tareda tayi magana ba, Kar'ba tayi ta fara dubawa kafin ta mik'e cikin sauri ta nufi wata sark'ak'iya dake cikin Masarautar, cikin wani madai-dai-cin gida wanda akayi sa ginin dutse da dutse, ta shiga babu komai sai duhu a ko ina kamar gidan fatalwa loko loko a gidan anan ne fa ta rasa ina zata dosa, Wata murya ce ta katse mata tunanin ta da cewa, "Barka da zuwa, ki biyo ni" Cikin sauri ta marawa budurwar wadda ta rufe fuskar ta ruff baya cike da fargaba da tunanin ina aka kawo ta haka?? Duk da tasan waye me kiran nata tasan bazata samu matsala ba. Wani lungu suka shiga suna fita sai gasu a wani babban d'aki wanda hasken kendir da fitulu ya wadata, can ta hango shi a kashingid'e kan wata hamshak'iyar kujera irin ta sarauta sai lumshe ido yake da alamar yana tunanin wani abun ne ko kuma wani abun yayi masa dad'i. Murmushi ta saki kafin ta k'arasa gefe ta tsaya tareda cewa, "Sannu da hutawa magajin izza" Wani sukurkutaccen murmushi ya saki tareda jinjina kai ba tareda yace komai ba. Murmushi tayi tace, "da alama yau Sarautar ta motsa ne" Budurwar ce ta kar'be zance cike da kishi tace, "k'warai Sarautar ce ta motsa kinsan abunka da jinin abun sai anyi hak'uri" Ta k'arasa maganar tareda zama kan makekiyar kujerar da take kusa da ita ta hard'e k'afa d'aya kan d'aya, cike da izza taci gaba da cewa, "naga ma kina da matuk'ar amfani gareshi har da yake iya shareni ya saurare ki, ina kishi da hakan gaskiya" Murmushi Hadima Farhana tayi cike da jarumta tace, "wai ke wacece ke ne?? Naga koda yaushe fuskar ki tana rufe ne, bansan wace fuska bace bare na gane ta ishe ni kallo ko bata ishe ni ba, ki zauna a iya matsayin ki domin ba take nake ba" Cike da takaici tace, "me kike tak'ama dashi ne da har kike fad'a min duk maganar da tazo kan harshen ki?? Zatayi magana ya dakatar da ita da cewa, " barka da zuwa Hadima Farhana zaki iya zama anan" Ya fad'a yana yi mata nuni da gefen sa. Cikin gadara ta k'arasa ta zauna ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya. Cikin sauri ta sauke ta-ta k'afar ta kalle shi rai 'bace tace, "meyesa haka Kumar?? Wannan fa baiwa ce a wannan Masarautar meyesa zaka bata y'ancin da har zanyi abu tayi?? Rausayar da kai yayi tareda sakin wani malalacin murmushi yace, " kwantar da hankali mana, Farhana karki damu akanta tana da kishi ne sosai" Farhana tace, "ohh ita d'in matar ka ce?? Girgiza kai yayi tareda cewa, " bazance a'a ba kusan hakan dai" K'asa Hadima Farhana tayi da kai cikin ranta tana wasu y'an maganganu. Gyara zama yayi tareda cewa, "game da zuwan wancan Bawan, yanzu wane hali shugabar taku take ciki? Hadima Farhana tace, " indai akan wannan ne tabbas tana cikin damuwa domin kuwa marin ta da yayi da kuma nuna mata iyakar ta hakan ba k'aramin tayar mata da hankali yayi ba" Kumar yace, "ya batun zuwan ta Masarautar Maruda? Da kuma auren da Waziri yake son shirya mata? Lumshe ido tayi ta bud'e kafin tace, " bana jin wannan k'udurin nasu ze kai ga cin galaba akanta, zuwan Ansaar ya tarwatsa komai ya tarwatsa manufofi da shirye shirye da dama ni kaina zuwan sa ya rusa min shirin da na tsara, yanzu nasan ita kanta Maharani Sameena tana can cikin rud'ani da tashin hankali, domin kuwa tarihi ne yake k'ok'arin mai-mai-ta kansa kamar yadda kuke fad'a" *(Kuyi hak'uri da wannan dan Allah,, ina bala'in yin ku VIP grp musamman Ummu Taslim Ummu Sulaiman Maman Najwa sai kuma Waziriya ta ta hannun daman wato Salmaji Ce, sai kuma babbar Aminiya ta Jiddah Shajarafi y'ar Mutan KT da sauran su,,, ina godiya Allah yabar k'auna)* *INDO CE..* [20/03, 11:03 a.m.] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhUTxJ28ext83rI6uvV1xB *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~11* بسم الله الر حمن الر حيم *Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480* Jinjina kai yayi tareda cewa, "k'warai haka wannan yake sai dai dole akwai matakin d'auka kafin abu ya rinca'be amma yanzu bamu da makama ya zame mana dole mu dakata na wani lokaci kafin mu gane bakin zaren" Hadima Farhana tace, "na yarda da hakan" Zaune yake ya zuba tagumi yayi zurfi cikin tunani, sama ta ka yaji muryar ta ta ratsa dodon kunnen sa, Yamutsa fuska yayi ba tareda ya kalli inda take ba, K'arasawa tayi kusa dashi ta tsaya tana kallon sa har wani lokaci kafin ta durk'usa dai-dai shi sannan tace, "Sannu da hutawa Aruuf" Ba tareda ya kalli inda take ba yace, "Barka da fitowa" 'Dan murmusawa tayi tareda lumshe ido sannan tace, " da fatan babu wata damuwa" Gyad'a kai kawai yayi ba tareda yace komai ba. Cikin nutsuwa tace, "Aruuful''Ansaar ko zaka iya fad'a min ina mahaifiyar ka???" 'Dan kallon ta yayi ya kawar da kai sannan yace, "na rasa ta tin ina k'arami" "Kenan baka san lokacin da ta mutu ba??" Girgiza kai yayi tareda cewa, "a'a na rayu da ita na wani lokaci har na fara girma sannan ta mutu" Tace, "ooh na taya ka bak'in cikin rasa ta domin kuwa rashi abu ne me tsanani ga wani sai dai kuma wasu garesu rashin shine abunda yafi dad'i, babu yadda muka iya tinda mu dai mun riga mun rasa, Banji dad'i ba Ansaar, kenan yanzu kana tareda mahaifin ka ne?? Kai tsaye yace, " hakan ne ma yasa nakejin ba dad'i saboda tsallake umarnin sa da nayi" 'Dan kallon sa tayi ta gefen ido cike da son gane gaskiya da kuma banbance tantamar da take tace, "kenan bazaka iya sanar dani sunan sa ba?? Ba tareda ya jira wani abu ba yace, " Abu Ansaar, da haka nake kiran sa dan haka kema ki kira shi da hakan" Jinjina kai tayi tace, "na yarda da hakan, To amma a wane yanki kuke zaune?? Kace a daji kuke rayuwa baka san mutane ba kuma wai da gaske ne hakan?? Gyad'a kai yayi yace, " muna rayuwa ne a cikin wani daji da yake mak'ota da wannan k'asar mu ba'a cikin ko wane yanki muke ba, cikin wannan dajin shine kawai duniyar mu banida wasu abokanai sai dabbobi da tsuntsaye, nasan ma yanzu suna can cikin damuwa suna nema na, Ki barni na koma ga mahaifi na" Jinjina kai tayi tace, "na gamsu da maganar ka, amma na kasa yarda cewa kanada mahaifi kuma shi mahaifin naka shine wanda ya haife ka da gaske, ka tabbatar iyayen ka ne su d'in?? Kuma baka da dangi ko da guda d'aya bayan iyayen ka?" Zuwa yanzu ya fara gajiyawa da irin tarin tambayoyin da take aza masa, a k'agauce yace, " sune suka haife ni idan ba haka ba ai bazanyi miki k'arya ba domin ni na yarda da hukuncin Addini na duk wani mak'aryaci yana kan hanya mara kyau shiyasa na za'bi fad'en gaskiya akan k'arya, kuma banida wasu dangi Ummu Ansaar da Abu Ansaar sune kawai dangi na, ina fa da hankali na meye kike tunani ne a kaina?? Banajin yin surutu amma kin sani magana, ki fitar dani daga wannan kurkukun ki barni na tafi gurin Abu na" Girgiza kai tayi tace, "zan k'ara tsananta bincike akan ka, idan kuma na gane k'arya kake wani ne ya aiko ka ko kuma kai d'in wani ne ba wanda ka fad'a ba ka sani ni a guri na gutsire maka kai abu ne ne sauk'i, idan kana son fita daga nan ya zama dole ka cike sharrud'a na bin dokar masarauta ta sahu da k'afa, haka yin abunda duk wani bawan wannan masarauta yakeyi, Girmama na sama da kai a cikin bayi na ya zama dole kai d'in k'ask'antacce ne a cikin su domin kuwa ranar ka ta farko a cikin yankin da bakasan suwaye suke rayuwa a cikin sa ba, ka aikata kuskuren da ze ta bibiyar ka har k'arshen rayuwar ka, Ka yarda da sharrud'ai na sannan na fitar da kai daga sijn idan ba haka ba rayuwar nan ta kama ka, zan aikawa mahaifin ka wasik'ar gayyatar sa zuwa wannan masarauta kuma koda yazo bazan bari ka ganshi ba" Shiru yayi yana nazari har wani d'an lokaci sannan yace, "na amince zan zama bawan naki indai zaki fitar dani daga nan, ban saba irin wannan rayuwar ba, kuma ina son ganin Abu na" Mik'ewa tayi tareda cewa, "kayi tunani me kyau" Daga haka ta fice zuciyar ta tana sak'a mata abubuwa daban-daban. Kai tsaye wajen Ummee ta nufa. Tana tsaye ta jingina a jikin bango idanun ta a lumshe, Cike da sa ran jin muryar ta wanda ze tabbatar mata da cewa jarumin ta ya bayyana tace, "Ummee????" Shiru batayi magana ba hakan yasa taji zuciyar ta tayi wani wawan zillo lokaci d'aya taji ta fara sarewa, Cikin rawar baki ta k'ara furta " Ummee??" Idanun ta kawai ta bud'e ta zuba mata, har lokacin bakin ta gum kamar bata ta'ba magana ba. Maharani ta k'ara ware Ido tana kallon ta a razane, cikin kad'uwa tace, "Ummeeh? Hakan yana nufin kenan baze dawo ba?? Kenan Ansaar ba shine Jarumi na ba??? Na shiga rud'ani na kasa ganewa Ummeeh dan Allah yau dai kiyi magana" Ta k'arasa maganar a ma-rai-rai-ce. Jin Ummein ba tace komai ba yasa taji wasu zafafan hawaye sun gangaro kan fuskar ta, tafin hannun ta tasa ta goge su, cike da tausayin kanta tace, "zan cigaba da zaman jiran sa har lokacin da ze zo, bazan ta'ba gajiya ba har lokacin da ze bayyana gare ni, nasan baze guje ni ba ko Ummee??" Ummi kam ta kasa magana sai wasu hawaye da suke ta gudu kan fuskar ta. Cikin sanyin jiki ta koma sashin ta, cikin ranta taji gaba d'aya Ansaar ya fice mata a rai tamkar wani babban mak'iyin ta takejin sa. A ranar tasa aka fito dashi daga kurkuku sai dai duk da haka yana tareda tsaro a duk motsin da yayi, har mamakin yadda ta mayar dashi kamar wani dabba yake. Lokacin da aka zauna a fada ta rubuta sak'o ta aika dakaru suyi tafiya zuwa inda Ansaar yayi mata bayani ba dan komai tayi hakan ba sai dan ayi mata bincike sosai banda haka da Arjula kawai zata aika. Da gudu gudu gimbiya Sunaya ta shiga turakar ta tareda k'walawa Raj kira. Da sauri ya tashi yana tambayar ta lafiya. Jikinta har rawa yake tace, "Raj yau Maharani tace ka shirya zaku shiga daji tare, hakan ya sani farin ciki sosai" Cikin rashin fahimta yace, "Mama wai dajin gaske?? Nifa tsoro nakeji" Tsaki ta rafka cike da takaici tace, "kai kuwa anyi soko Raj, a memakon kayi murna zakace wani tsoro kakeji?? To ai kuwa tace jarumtar ka take son gwadawa sai ka shirya kafin ranar zata sa gasa tsakanin kai da ita, kuma na rantse idan ka tsaya jin tsoron nan sai na shak'e ka ka mutu" Cikin sanyin jiki yace, "Shikenan Mama zan shirya amma dai gaskiya inajin tsoro" Dafa kafad'ar sa tayi tace, "kwantar da hankalin ka yaro na kar kaji tsoron komai ai nasan baza ta cutar da kai ba, Kawai kayi k'ok'ari sosai kaji??" Gyad'a mata kai kawai yayi ba tareda ya gamsu ba. Hannun ta hard'e a bayan ta tayi tsaye tana tsammanin zuwan sa, Bayan wani lokaci dattijon ya k'araso bakin sa d'auke da wasu Addu'o'i Sai da ya kai matsaya sannan ya dakata cike da kulawa yace, "Maharani Mahalakhahmi" Cikin sanyi tace, "Guru banyi zaton cewa wanda ya shigo cikin mu a yanzu ba jarumi na bane, shin da gaske ne hakan?? Jinjina kai yayi yace, " k'warai ba shi bane, sai dai kiyi hak'uri Amma wannan ba shine wanda kike jira ba, amma wata rana shi d'in ze bayyana" Kamar zatayi kuka tace, "kenan wannan waye???" Yace, "kamar yadda ya fad'a miki haka gaskiyar sa take, Sai dai wani abunda baki sani ba, koda jarumin ki baya tare dake to tabbas wannan ma bango ne a gareki shi d'in abun bauta ya jefo shi gareki ne domin ya temaka miki" Murmushi tayi tace, "nagode amma bana jin akwai wani, wanda ze iya maye min gurbin sa dan haka bani da wata alak'a da Aruuful'Ansaar bana buk'atar ko wane temako nashi, Ya zauna a matsayin sa na bawa, Na barka lafiya guru" Daga haka ta juya ta fice zuciyar ta cike da takaici. A can dajin kuwa sun tarar da Abu Ansaar cikin kid'ima da tashin hankali duk ya rame yak'i cin abinci yayi kuka har ya gaji ya bari, Ba k'aramin farin ciki yayi ba da yaji inda d'an sa yake se dai yaji takaici sosai da suka sanar dashi hukuncin da Maharani ta yanke masa na zama bawan ta, Babu yadda ya iya haka ya tarkato y'an komatsen sa ya biyo su suka dawo cikin masarauta. Tinda suka shigo ta zuba masa ido tana daga sama a kishingid'e kan wani madai-dai-cin gado wanda yaji ado irin na tambarin masarautar, jinjina kai tayi kafin ta mik'e ta ta taka zuwa gaba, cikin d'aga murya tace, "ina yi maka barka da zuwa wannan masarauta Abuu Ansaar da fatan zaka kar'bi hukunci na" Da mamaki yace, "wane irin hukunci kuma ranki yadad'e?? Murmushin gefen baki tayi tace, " hukuncin da na yanke akan d'an ka sannan ina buk'atar jin dalilin ka na turo shi cikin masarauta ta ya tayarwa mutane na hankali" Dafe goshi yayi cike da tsoro yace, "ranki yadad'e ba da nufi ne hakan ta faru ba, ba nine wanda na turo shi ba domin kuwa babu abunda ze iyayi gareku yake wannan Sarauniya, Ni yaro na ragon maza ne ko rik'on wuk'a be iya ba face wuk'ar da ze yanka nama, Bare kuma ya iya rik'on takobi ko kuma wani mugun makami, Shi ba wani jarumi bane kamar yadda kukayi zato, bashi da k'arfi haka kuma bashida wata dabara, amma ubangijin mu Allah yayi masa halitta irin ta jarumai amma sam ba haka yake ba, ki gafarce shi Sarauniya, a bisa rashin sani ya shigo yankin ki, be ta'ba shiga duniyar da mutane suke rayuwa ba sai yanzu, yana cikin wasa ne ma akan dokin sa har ya shagala yayi nisan da ya kai ga shigowa nan dan haka zan d'auke shi mu tafi ba fad'a ba tashin hankali, ni ban iya fitina ba bare na koya wa d'ana, dan Allah kiyi hak'uri" Jinjina kai tayi tace, "Na yarda da abunda ka fad'a, amma barin ku wannan masarautar ya sa'bawa k'a'ida ta, d'an ka dole ze kasance anan domin kuskuren da ya aikata kuma kai ma ta shafe ka" Rai 'bace Ansaar yace, "wannan zalumci ne, meye abunda mahaifi na yayi miki? Ni nayi miki laifi dan haka karki sake ki ta'ba mahaifi na" A yatsine tace, "ba'a musayar yawu dani Aruuf ka kiyaye" Abu Ansaar durk'ushewa yayi a wajen ya fashe da kuka tareda cewa, "haba d'ana koda ka tsallako iyakar duniyar mu meyesa ka za'bi wannan duniyar ka shigo cikin ta, kazo duniyar da ake zubda jini ake yin zalumci, gashi ta raba ni da kai" A hankali ya durk'usa gaban Abu Ansaar zuciyar sa na rad'ad'i, cikin son kwantar masa da hankali yace, "karka damu Abu na, babu abunda waccan yarinyar ta isa tayi maka indai ina nan, na amince zanyi komai da ta sani indai har zan k'waci kimar ka Abu na, ka dena kuka Allah yana tare damu" Rungume d'an nasa yayi cike da k'auna irin ta d'a da uba, A hankali ya shiga shafa bayan sa yana cewa, "Abu Ansaar dan Allah karka damu ko ina ne zata kai ka ka sani zanzo gareka, kuma idan ta cutar da kai to fa bazan ta'ba k'yale ta ba" Abu Ansaar yace, "yaro na nasan ma bazata cutar dani ba, kawai ina tsoron kar ta wahalar min da kai ne" Murmushi yayi tareda shafar kumatun Abu Ansaar yace, "indai a kaina ne kar ka damu babu abunda ze faru kaji Abu na??" K'ok'arin raba sun da dakarun suka shiga yi ne yasa ya janye jikin sa ya mik'e yayi gefe, yana kallo suka tafi da mahaifin sa, duk da ransa baya so haka nan ya hak'ura" Ko ina ciki da waje ya d'auka Maharani zata shiga daji tareda Raj. Tana cikin shirye shirye Arveen ya sanar mata da buk'atar sa ta shiga gasar, ba dan taso ba tace ta amince. Tana cikin tafiya ta dawo daga wajen Abdullkareem taga ya sha gaban ta, Da tsananin mamaki ta zuba masa ido ba tareda tace masa komai ba. Tini sojojin ta suka zagaye shi suna shirin kai masa hari tayi saurin dakatar dasu. Gyara tsayuwar sa yayi yace, " a gani na tinda masu shiga gasa sun zama biyu ke ba girman ki bane kice zaki gwada dasu ki hak'ura ki bar su su biyu" Shiru tayi na wani lokaci kafin ta d'an murmusa tace, "nan masarauta ta ce, mutanen cikin ta mutane na ne, Arveen da Raj su kuma jini na ne, kaga baka da alak'a da tsara min yadda zan tafiyar da komai nawa, kuma in jaddada maka ba'a shiga gaba na idan ina tafiya nakan sa yankewa mutum k'afa, to amma kai bak'o ne kana buk'atar uzuri ka kiyaye gaba" Murmushi kawai yayi yana mamakin yadda take d'aukar kanta kamar itace tayi kanta, yana mamakin yadda mulki yasa takejin gaba d'aya itace sama da kowa a duniya. Anyi gumurzu sosai tsakanin su biyu ita da Arveen sai dai duk da hakan itace ta kayar dashi a gasar ya rage daga ita sai Raj, Bayan sunyi nisa ta kalle shi cike da kulawa tace, "Raj kasan meyesa nace mu shiga daji tare domin farauta?? Girgiza kai yayi yace, " a'a" Tace, "mahaifiyar ka ta haife ka ana tsaka da yak'i ne, a memakon kazo a jarumi sai ka zama tamkar mace, Rajkumari?? Ina so ka zama jarumin namiji wanda masarautar Purlasiri zatayi Alfahari da kai har na tsawom tarihi" Murmushi yayi yana binta da ido cikin shauki yace, "Maharani meyesa kike kira na da d'an sarki?? Suna ne wanda ba nine na dace dashi ba tinda mahaifina ba sarki bane" Dafa kafad'ar sa tayi cikin sassanyar murya tace, "Rajkumari kai ma fa jinin Sarauta ne, abunda yayi mahaifin ka shine yayi mahaifi na kaga kuwa da kai wannan sunan ya dace, kai fa k'ani na ne Raj ka kasance kamar ni mana" Murmushi yayi yace, "zanyi k'ok'arin hakan kamar yadda kike so sarauniya" Murmusawa kawai tayi bayan an kammala suka koma gida. Farin ciki a wajen Raj ba kama hannun yaro idan ya tuna kalamanta gareshi sai yaji tamkar shine mutum mafi sa'a fiye da kowa a duniya. Bayan kwana biyu. Cikin sauri sauri take tafiya cikin wasu lunguna wanda babu kowa a wajen sai d'ai-d'ai d'in dakaru, Kamar da wasa taji kukan wucewar mashi ta gefen kunnen ta, Da mamaki ta juyo domin ganin ko waye sai dai bata ga kowa ba, ta cigaba da tafiyar ta. Ba zato ba tsammani taji an k'ara kawo mata hari da wasu guda uku a lokaci d'aya, sai a lokacin ta gane abun ba na wasa bane koma waye maharbin kibiyar nan to ita yake hari, waige waige ta farayi ko zata ga wani amma bata ga kowa ba,, tana cigaba da tafiya kuma zataji an k'ara watso mata su. Takawa tayi da wani mugun gudu, yayin da aka shiga harbo mata su akai-akai cike da k'warewa da kuma son cimma wata manufa....... *INDO CE..* [21/03, 7:10 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~12* بسم الله الر حمن الر حيم *Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480* Cikin zafin nama ta k'arasa ga takobin da aka yiwa mazauni a jikin bango, ta zaro ta cike da k'warewa ta juyo tareda kai masa wani mugun hari, Cikin zafin nama ya kauce mata tareda farmakar ta da tashi takobin, Karewa tayi cike da zullumi da kuma tsananin son taga ko waye dan kuwa ko farce be bari a waje ba face idanuwa wanda take ganin kamar tasan me su amma ta kasa ganewa, gashi iya k'arfin sa yake kai mata hari sai dai beyi nasarar samun ta ba saboda k'warewar da tayi. Ba tareda ya gajiya ba ya cigaba da farmakar ta. 'Dan k'aramin yak'i me d'auke da babban gumurzu sukayi har sai da ya kai ta k'asa warwas sannan ya bud'e fuskar tasa gami da mik'a mata hannu alamar ta rik'e shi ya tashe ta. Sai da numfashin ta ya kusa tsayawa saboda mamakin abunda idon ta ya gane mata, cikin kad'uwa tace, "Aruuful'Ansaaar!!!!!" Gyad'a kai yayi tareda cewa, "ni ne" Cikin sauri ta tashi tana karkad'e jikin ta, kanta ya fara kullewa duk yadda tunanin ta yaso bata abun ya gagara, cikin tsananin mamaki tace, "kenan mahaifin ka k'arya yayi min??? Kai d'in gwarzon jarumi ne wanda kai tsaye zaka amsa suna Khiladie Yonkha khiladie (Jarumin Jarumai) amma yace min baka iya rik'on takobi ba amma har ka kai ni k'asa???" Jinjina kai yayi yace, "wannan kad'an ne daga cikin ikon Allah, tabbas Abu Ansaar yayi miki k'arya sai dai kuma ba shine da Alhakin ta ba saboda yayi ne dan tsoron ki da yakeji, ni kuma bana shakkar ki Lakhshmie hakan ne yasa na yanke hukunci bayyana miki asalin zahiriyya ta, ni ma'abocin irin wannan abunda kika gani ne, ina wasa da makamai sosai, ba ni kad'ai ba har mahaifiya ta mukanyi irin wannan wasan da ita haka Abu Ansaar, muna rik'e makami amma mu ba dan zubda jini muke rik'e shi ba abun wasa muka d'auke shi" Ido ta zuba masa cikin k'unar rai, ta d'an jima tana kallon sa bayan ya gama maganar,,, sannan tace, "kuma har kakejin kana da zarrar da zaka iya gwada wasan ka dani?? Kuskure na biyu kenan wanda ka aikata kuma ka sani bazan k'yale ka ba" 'Dan murmushi yayi tareda cewa, "Naji kuma na d'auka nayi kuskure kuma bazaki k'yale ni ba,, sai dai ki sani ni hakan ba'a gaba na yake ba tinda dai sak'o na ya riga ya isa gareki, kuma na sanar dake abunda nake son sanarwa" Da d'an mamakin tace, "meye kenan?? Ansaar ya kamata ka shiga tai-ta-yin ka yanzu, ka sani nan fa ba a dajin Allah kake ba masarauta ta ce ka gane??? Girgiza kai yayi yace, " idan ban gane ba zaki iya ganar dani?? Kin san meye abunda nake son sanar dake??? Kaifin kafirci da izzar mulki da k'arfin iko gami da ji da kai da girman kai harda rashin sani sun tare miki sun sa kina ji da ganin cewa duk duniya kece tauraruwa mafi haskawa, gani kike kinfi kowa k'warewa jarumta da wayo, Kin nuna bajintar ki akan ragwayen mazancan, ba Ramraj ba kawai shi kansa Arveen ban yarda da jarumtar sa ba, Kin nuna dukan su kece tauraruwa a cikin ku, Hakan ba kuskure bane tinda hakan ta faru, gaskiya ne a cikin su kinfi kowa jarumta sai dai ki sani duniya fa da fad'i, baki ta'ba kawowa zan shigo rayuwar ki ba sai gani katsidim kuma kece kika gayyato ni, Kinga kuwa tinda ni kaina baki sanni ba hakan yana nufin akwai dubun ki kuma akwai wanda baki ishe su komai ba, Ki dena d'auka cewa kinfi kowa domin kuwa dukan mu bayin Allah ne, Gashi duk wannan ji da kan naki nazo na rusa shi domin kuwa abun kaico ne ace na shigo masarautar ki na ciki da yak'i, Na kai ki k'asa abunda a rubuce jikin littafin tarihin masarautar ba'a ta'ba yi ba,,, kisan da a cikin jama'ar ki ne sai sunyi tunanin wani abu??, Ki dena jijji da kai d'innan bashi da amfani, Kinga yanzu na isar da sak'o na, Amma fa ke jaruma ce duk da hakan, sai dai kinsan duk iyawar ka akwai wanda ya fika" Daga haka ya bar mata gurin ba tareda ya k'ara cewa komai ba. Da ido ta bishi har ya 'bacewa ganin ta sannan ta cigaba da tafiya, koda ta dawo turakar ta ko maganar kasa yi tayi tunanin ta be wuce Ansaar ba, kalaman sa sunyi matuk'ar sosa mata rai, ga kuma cin galaba da yayi a kanta sai taji duk hankalin ta ya tashi, bata da burin da ya wuce nuna masa iyakar sa. Arveen kallon Waziri yayi cikin salon fusata yace, "Baba wai yarinyar nan me takeji dashi ne??? Taci mutunci na a gaba dubban jama'a, haka inaji ina gani kenan Raj ze k'wace kambu na?? Shine fa wanda bata saurara a daa amma yanzu gaba d'aya ta mayar da nutsuwar ta kan sa ne" Waziri ya dafa kafad'ar sa cike da manyance yace, "yaro na fad'a min gaskiya shin kana son Maharani ne??" Ture hannun nasa yayi tareda cewa, "a'a amma dai kasan daa duk cikin masarautar nan daga Farhana sai ni, amma yanzu bata bin ta kaina, hakan yana min ciwo Baba" Waziri yace, "d'ana kayi tunani sosai karka 'batawa kanka lokaci indai kana son ta ni me baka duk abunda kake so ne kaji ko?? " Girgiza kai yayi yace, "nifa nace bana son ta" Waziri yace, "to shikenan, indai wannan ne matsalar ka zata warware, ni nace ma zan ajiye matsayi na na d'ora ka a kai, tinda kaga kai matashi ne sabon jini inaga idan taga haka zata dinga tsoma ka cikin wani abunda ya shafi masarautar nan, na gaji da yanke hukuncin da takeyi kai tsaye bayan ga manyan masarauta amma tana y'ar yarinya ta dinga juya mu" Da sauri Arveen yace, "da gaske?? Naji dad'in hakan, ko babu komai zan dinga yin kutse cikin lamarin ta koda bata nemi hakan ba" Waziri yace, "yauwa d'ana ai nasan kanada fahimta" Hadima Farhana ce zaune a gefen k'afafun ta tana taunar kayan marmari cikin kwanciyar hankali. Maharani tana kwance kan d'an madai-dai-cin gadon ta na hutawa, ba abunda take tunanu sai Ansaar lamarin sa yana matuk'ar d'aure mata kai, d'an kallon Hadima Farhana tayi ta kauda kai sannan tace, "Hadima Farhana na rasa ta inda zan shawowa Aruuf ya nuna min iyaka ta, ya nuna min gazawa ta, ina buk'atar d'aukar fansa akan hakan domin kuwa raina ya k'onu da yawa" Hadima Farhana ta gyara zama kafin tace, "Maharani, nagode Allah da ya kawo min wanda ya iya fahimtar dake way'annan abubuwan da kika kasa fahimta, kinga yanzu ma sai ki gane ba wai jarumin ki ne kad'ai jarumi ba akwai dubun sa" Girgiza kai tayi tace, "jarumi na daban yake, kuma idan ya dawo zaki gane hakan" Farhana tace, "Maharani da bakida tabbacin cewa yana raye? Baki sani ba ko ya mutu ko yana nan, kedai kawai lokacin dawowar sa kike jira" "Ruhin sa da nawa aminan juna ne, da ya mutu tabbas zanji hakan a jiki na, damuwa d'aya kawai bansan a wane hali yake ba, amma nasan ze dawo Farhana" Ta'be baki tayi tace, "bayan zuwan sa Tajmahaal ban k'ara saka ido na a kansa ba ina son ganin sa, Amma Kinsan ya zakiyi ki rama?? Kawai kiyi amfani da k'arfin ikon ki hakan ne ze sa ya gane akwai tazara a tsakanin ku" Murmushi tayi ba tareda tace komai ba. Raj yana kwance bisa hamshak'in gadon sa ya kalli sama sai tunane tunane yake, Gimbiya Sunaya ce ta shigo tana cewa, "Raj!! Wai kai baka da aiki sai kwanciya ne?? Tashi zakayi fa ka dena wannan kwanciyar dan a haka bazaka ta'ba cimma burin ka ba, kai naga yanzu ma baka da burin da ya wuce ka mallaki soyayyar ka, mahaukaci ka ma manta da rashim Albarkar da yarinyar nan tayi maka, ta kashe maka mahaifi amma kai ba ta wannan kake ba, ni buri na kawai d'aukar fansa yaro gara ma ka gane, ta maida kai shashasha bafa wai matsayi ta baka ba dan tace ku shiga farauta tare, kawai tana so taci zarafin ka ne" Mik'ewa yayi ya zauna kafin ya rik'o hannun ta yace, "zauna Mama" Zama tayi tana binsa da ido. Murmusawa yayi sannan yace, "koda ita bata d'auki hakan a matsayin komai ba ni na d'auka, bazan manta da hakan ba domin yana d'aya daga cikin babban abu na tarihin rayuwa ta, batun d'aukar fansa kuma bana ta ita domin kuwa shi ya riga ya mutu, kinga gara mu k'yale batun sa mu gina sabuwar rayuwa, idan ba haka ba kuma kema zaki bishi ne domin kuwa kashe ki a wajen ta ba komai bane sai dai nasan ni bazata kashe ni ba, Mama ki bi a sannu dan kuwa bana so na rasa ki" Shiru ta d'an yi kafin tace, "wannan haka ne amma gaskiya bazan hak'ura ba idan kaga na janye to nayi bakin k'ok'ari na har na gaza" Raj yace, "to Mama ina miki fatan Nasara" Tsaki tayi tace, "tashi kaje ka kai mata wannan abincin kace inji ni kaji ko??" Kallon ta yayi sama da k'asa kafin yace, "in kai mata abinci inji ki? Anya kuwa ba guba kika zuba mata ba???" A razane tace, "rufamin asiri d'ana idan na zuba mata wani abun ai zata gane kuma k'arshe tawa ce baza tayi kyau ba, na rantse da abun bauta Ram ban zuba mata komai ba kwata kwata ba da niyyar cutarwa na bata ba, kawai gani nayi a masarautar nan mune dangin ta amma bama kulawa da ita shiyasa" A ranta kuwa cewa take "kai yaro ne fa Raj baka da wani wayo, sai abunda ka gani dai kawai kai dai kaje ka kai mata, idan kuma da rabon ka kashe masoyiyar taka da hannun ka to" Jinjina kai yayi yace, "to zan kai mata" Kar'ba yayi ya kama hanyar sashin nata, ko ina ya ratsa kallon sa ake domin kuwa kowa yasan kai tsaye sashin ta ya nufa kuma da kayan abinci hakan shine na farko dan haka abun yazo musu a bazata. Yana cikin tafiya yaji an kirashi. "Hee!!!! Nirbal" Duk da ba sunan sa bane amma yaci amsa sunan dan shine rago dan haka ya gane cewa dashi ake, tsayawa yayi yana waige- waige, can ya hango shi yana tawo wa cikin k'asaitaccen takun sa, ido Ya zuba masa yana k'ara kad'aita buwayar wanda ya halicce shi, shi ba jinin sarauta ba amma yanda kasan sarki Ganesh haka yake da k'asaita, sai dai indai kana da nutsuwa zaka gane halittar sa ce a haka bawai jinin sa ba. yayi zurfi a cikin tunani hakan yasa besan ya k'araso ba sai ji yayi yace, "Nirbal, kana namiji meyesa ka bari Lakhshmi ta fika jarumta" Ido ya zaro tareda mai-mai-ta "Lakhshmi??" Cikin sigar tambaya. Gyad'a kai yayi tareda cewa, "eh Lakhshmi" Cikin tsoro da firgici yace, "Hazoor, Maharani Lakhshmi, kuskure ne kiran sunan ta haka kai tsaye, kai fa bak'o ne kuma karka manta fa kana da mahaifi a wannan masarauta ka samu ka lalla'ba ka bita a sannu har ku rabu lafiya ka samu ka d'auke mahaifin ka ku tafi, amma baka gama biyan wani abun ba karka d'aukarwa kan ka wani, ni ma fa ta kusa cire min kai" Murmusawa yayi yace, "kana tsoron ta da yawa, kamata yayi ka zama jigon ta ba wai ta zama naka ba domin kuwa a ko ina namiji shine aka sani da jajircewa ba mace ba" Raj yace, "kanayin kuskure fa, baka san wacece Maharani bane shiyasa, ni yanzu abinci akace na kai mata dan haka karka 'bata min lokaci ka bani guri na shige" Aruuf yace, "k'warai na san fuskar ta amma bansan 'boyayyen halinta ba, zaka ganar dani abunda ban gane ba???" Da sauri yace, "eh gobe mu had'u a bayan masarauta cikin lambu yanzu sauri nake" Bashi hanya yayi tareda cewa, "zaka iya tafiya zamu had'u goben" Ya wuce da sauri... *INDO CE..* [22/03, 10:51 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~13* بسم الله الر حمن الر حيم *Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan👉🏻 08146838480* Har ya d'an yi nisa sai kuma ya juyo yace, "karfa ka manta" Shafar sumar kansa yayi kafin yace, "Nirbal Aye wahan, ( zo nan)" Dawowa yayi ba musu dan kuwa shakkar sa yake tin daga lokacin da ya zumbud'awa Maharani mari kai tsaye. Mik'a masa hannu yayi tareda cewa, "bani tarkacen nan kaji ko?? " Nok'e kafad'a yayi yace, "a'a bazan bayar ba, babu ruwa na aike na akayi" Dafa kafad'ar sa yayi yace, "ka bani sai kace mata yana guri na kace mata nace ta fad'a min inda mahaifi na yake sai na baka ka kai mata, idan kuma kayi min gardama yanzu zan tumurmusa ka" Da sauri ya mik'a masa yana cewa, "gashi amma ba ruwa na kai da ita kuma zance mata kaine ka kar'ba" Jinjina kai yayi yace, "dama ai dan ka fad'a d'in na kar'ba kace mata ta fad'a min inda Abu na yake" Gaba yayi yana cewa, "ni ba ruwa na" Cike da fargaba ya k'arasa sashin ta kafin ayi masa iso wajen ta tuni ya fashe da kuka ra'be-ra'be, Ba 'bata lokaci Hadima Fadya ta dawo tace ya shiga amma tana can gurin hutawar ta, Cikin tsoro ya shiga ya ratsa ya wuce, ya same ta zaune bakin wani d'an k'aramin ruwa wanda aka k'awata shi da adon furanni jajaye da Farare, ta zubawa ruwan ido tayi zugum da alamu tunani me zurfi take. Shashshekar kukan sa ce ta dawo da ita hayyacin ta da sauri ta dawo da nitsuwar ta gare shi cike da kulawa tace, "Raj!! Kya huwa?? ( Raj Me yake faruwa??) . Cike da ga'bonci yace, " Aruuf, Mama ta bani abinci na kawo miki shine ya k'wace yace sai kin fad'a masa inda mahaifin sa yake sannan ze baki" Ido ta zuba masa har wani lokaci kafin ta kauda kai, kamar baza tayi magana ba sai kuma tayi murmushi tace, " haka ne?? Ka fad'a masa yana masaukin bak'i sashi na musamman, amma ya cinye abinci ni na k'oshi shine yake da buk'ata" Cikin sauri Raj yace, "kina nufin kin hak'ura ba zaki yi min komai ba??" Murmushi tayi gami da rik'o hannun sa cike da manyance tace, "Mera bhai!! Kuma shine abun kuka? Bazance komai a kai ba domin nasan ba yin kanka bane, ba nace ka zama jarumi ba wai??" Gyad'a kai yayi alamar "eh" Ta murmusa kafin tace, "sai yaushe kenan??" K'asa yayi da kai cikin k'asa k'asa da murya yace, "nima ban sani ba" Y'ar dariya tayi tace, "ka saba da shagwa'ba, da na sani tin kana yaro na kar'be ka daga hannun Maman ka domin kuwa be kamata ace kana jinina ka kasance haka ba, Da ka taso a hannun Uwa Urmiy nasan zaka zama jarumi kamar yaro na Abdulkareem, Farhana ma da aka haifa a bayan ka kuma ita mace gashi ta zama jaruma, ya kamata kai ma ka zama namiji ba me tsoron mata ba" Gyad'a kai yayi tareda cewa, "to" Shafa kumatun sa tayi kamar k'aramin yaro tareda cewa, "ka nutsu Raj, tashi kaje" Da sauri ya mik'e tareda amsa mata, yayi hanyar fita har neman yin tuntu'be yake. Yana fita taga an harbo wani mashi ya sauka a gefen ta, ido warwaje take kallon mashin ganin wasik'a d'aure a jikin sa, zuciyar ta fal fargaba ta d'auka ta warware ta ta fara karantawa. "Lakshmie Mahalakhshmiey, Lakhshmie Ganesh Maharaj, Hahahaha lokaci. Ya gabato da zan rushe Masarautar Ganesh Maharaja" Idanun ta ne suka k'ara girma yayin da gudun zuciyar ta ya ninku lokaci d'aya, wani razanannen numfashi taja kuma ta kasa mayar dashi ya dai-dai-ta, Kamar hoto haka ta koma, idanun ta suna kan wasik'ar bata fasa kallon ta ba, ta karanta ta mai-mai-ta ba adadi. hadima Farhana ce ta shigo a ladabce tace, "Ranki yadad'e, ganin ta a firgice yasa ita ma ta firgita tayi saurin k'arasawa tana cewa, " Hazoor kaise hai?, (ranki yadad'e ya akayi?)" Jin shiru yasa ta mik'a hannu da nufin kar'bar wasik'ar. Cikin sauri ta dunk'ule ta tareda luma hannun ta cikin ruwan, girgiza mata kai tayi tareda cewa, "Farhana kar kiyi bincike akan wannan baze amfana miki komai ba" Cikin sanyi tace, "kiyi hak'uri Hazoor, ki huta lafiya" Daga haka ta tashi tayi nata waje. Koda ya koma ya sanarwa Aruuf abunda tace yayi mamaki sosai dan kuwa be ta'ba zaton hakan ba, take tunanin sa ya bashi da alama bata cin abincin kowa, kuma ba sune suke bata abincin ba shiyasa bata damu da shi ba, A gefe guda kuwa farin cikin matsayin da Abun sa ya samu ya lullu'be shi a tunanin sa Kurkuku ta kai shi ko wani gurin dai mara kyau, amma da yaji haka sai yaji hankalin sa ya kwanta, Komawa yayi can gefe ya bud'e abincin, ko d'aya daga ciki babu abunda ya burge shi domin kuwa irin abunda ya saba ci ba shine wannan ba, 'Daya daga cikin magunan da suke gurin ya fara kira, Ta'be baki yayi yace, "kuma mage baza'ayi babu ku ba dan haka kuzo kuci abinci ni kam bazan iya ci ba" Sauran duk sunyi gaba sai d'aya ce ta tsaya tana kuka da alama tana jiran abunda ze bata ne, mik'a mata yayi duka, ita kuwa ba jira ta fara ci. Tana cikin ci ta dakata tana wata irin shak'uwa lokaci d'aya kumfa ta fara fita daga bakin ta idanun ta suka firfito sukayi guru-guru, kallo d'aya zakayi mata ka gane tana shan bak'ar wahala. A razane ya zuba mata ido,, ya kalle ta ya kalli abincin cikin mamakon mamaki, yana kallo ta fad'i a wajen tana shure shure daga haka tayi lak'was alamar ranta baya tareda ita, "Subhanallah" Shine abunda ya fito daga bakin sa yana k'ara binta da kallon mamaki, zuciyar sa sam babu dad'i, ji yake kamar shine ya kashe ta kai tsaye ma shine silar mutuwar ta, kamar yayi kuka dan kuwa yana matuk'ar son dabbobi, Tattare sauran abincin yayi yaje ya watsar a inda babu wani abu da ze gani yaci, Da tambaya ya samu inda mahaifin sa yake. cikin gata da wadatacciyar kulawa ya same shi, a sashin da yake komai yaji ko 'bangarorin wasu daga cikin wanda suka ji'banci gidan be kai nan kyau da tsaruwa ba, Ko ina dukiya ce kamar banza. Da murna ya k'arasa wajen sa yana cewa, "Abu na kana lafiya?" Rungume shi yayi cikin farin ciki da tsantsar k'auna yace, "ina lafiya d'a na Allah yasa kaima haka ne" Yayi murmushi tareda gyad'a kai yace, "nima ina lafiya, ina cikin farin ciki sosai" Yayi dariya tareda cewa, "ina farin ciki a duk lokacin da naga farin cikin ka, Sabse Baada khiladie, (Babban Jarumi) naji dad'in zuwan ka" Murmushi yayi yace, "farin cikin ka shine nawa, Abu indai bakayi farin ciki ba nima bazan yi ba" Da sauri ya janye shi daga jikin sa yana cewa, "Allaah!!! Sabse baada Kiladi, meye yasa zuciyar ka take bugawa? Wani abun mara dad'i ya tsinkaye ka d'a na" Ya k'arasa maganar cike da yak'ini akan abunda ya fad'a kamar ze fashe da kuka. Cike da kulawa yace, "Abu Kuch nahi hai, (Abu Babu komai) Girgiza kai yayi yace, " kar ka 'boye min d'ana Alk'awari be ce haka ba" Murmusawa yayi yace, "Abu na Sarakan Alk'awari, Abu an bawa yaron wannan masarauta ya kaiwa Sarauniya abinci shine na kar'ba dan ta fad'a min inda kake tsautsayi yasa na bawa mage shine ta mutu" Abu Ansaar ya dafe goshi tareda cewa, "ya Allah, d'a na ka kwantar da hankalin ka babu komai tinda ba da sani ka bata ba, tabbas yaro na kai d'in daban kake daga cikin mutane, zuwan ka kenan masarautar nan amma Allah ya baka ikon ceton rayuwar Sarauniya Lakhshmi, Allah ya albarkaci rayuwar ka har bayan bayan ka yaro na" Murmushi yayi tareda cewa, "Amin" Shiru yayi yana tunanin abun, lallai akwai surkulle a cikin masarautar wanda ba lallai ya waru cikin dad'in Rai ba, kaida dangin ka amma kana neman kashe ta, Kenan itama duk wannan girman kan nata ana nan ana shirye shiryen ganin bayan ta, Da ita taci abincin nan fa da tuni ta mutu ko?? Ya jefawa kansa tambaya. Abu Ansaar yace, "k'warai d'ana da tuni itace a matsayin wannan magen, Allah be k'addara mutuwar ta a dai-dai wannan lokacin ba" Aruuf yace, "Abu kenan d'an uwan mutum sai ya nemi kashe shi a kan mulki??? Indai haka ne kuwa na tsani mulki, Bare kuma Lakhshmi tana had'awa da son zuciyar ta, Abu sai naji na kamu da tsanani tausayin ta, shin zan iya temaka mata?? Tinda nazo na lura akwai damuwa da yawa a tareda ita wanda bata bayyanawa, akwai babban abunda ya faru da ita kuma take 'boyewa ,, idan nayi bincike na gane damuwar ta-ta na temaka mata, banyi kuskure ba Abu???" Abu Ansar yace, "bakayi kuskure ba Aruufu, a koda yaushe temako shine abu me kyau, Allah yace mu temakawa wanda suka gaza yin abunda mukayi temaka musu yana da kyau domin kuwa dama ce ta kyawawan ayyuka, ka jaraba da iya k'arfin ka da baiwar da Allah ya saukar maka Aruuful'Ansaar" Murmushin jin dad'i yayi yace, "zanyi k'ok'ari sosai Abu na" Da yamma suka halacci gurin da Raj ya fad'a domin had'uwar su. cikin sanyin jiki Aruuf yace, "Raj waye yace ka kaiwa Lakhshmi abinci??" Kai tsaye yace, "Mama ta ce, yayi dad'i ko?? Ai Mama ta iya abinci sosai" Ido ya zuba masa yana jinjina kai ya lura da yanayin sa shi be san abunda mahaifiyar tasa ta shuka ba dan haka ya yanke shawarar baze fad'a masa ba domin shi zuciyar yara gareshi. Ganin yayi zugum ne yasa yace, "Aruuf lafiya" 'Dan murmusawa yayi cikin son kauda zancen yace, "kai tsaye?? Aruuf babu d'an rissinawa??" K'asa yayi da da kai tareda cewa, "a'a mantawa nayi" Yace, "to ina jin ka" Gyara zama yayi kafin ya fara cewa, "Ganesh Maharaja shine mahaifin ta, Gimbiya Jusiyya k'anwar sa, Baban Arveen da Baba na yayyen sa ne, kuma su baban su be basu mulki ba saboda yasan bazasu iya ba, Ganesh Maharaj ya fisu jajircewa da jarumta kuma ya ma fisu Adalci su ta kansu kawai suka sani basu damu da talakawa ba shiyasa baban su ys bawa Ganesh Maharaj mulki, bayan sun Haife ta aka zo akayi yak'i aka kashe su tin daga lokacin ita kuma ta koma hakan nan da kake ganin ta duk ta rikid'a ta koma kamaf muguwa to amma maganar gaskiya idan ka fahimce ta ba haka take ba, sai dai bata yafiya ba kuma ta sassauci ga duk wanda ya karya mata doka, idan kayi kuskure babba kuwa kashe ka zatayi hakan ne ma yasa ta kashe mahaifi na shima Arveen ta kashe mahaifiyar sa, amma Mama bata gaya min asalin laifin da sukayi mata ba, Ni kuma a yanzu so nake kawai naga ta dawo mutum kamar kowa idan ta zama kamar mahaifin ta nasan duniya ma sai tayi alfahari da ita, amma a yanzu ko wace masarauta tsoron ta kawai akeji" Numfashi Aruuf ya sauke kafin yace, "shikenan abunda ka sani??" Yace, "eh mana amma dan Allah idan kasan cutar da ita zakayi kawai ka tafi ka barta" Murmushi yayi tareda dafa kafad'ar sa yace, "karka damu k'ani na Lakhshmi zata canja kamar yadda kake so" Da mamaki yace , "to taya kenan?" Yace, "da ikon Allah kasan yafi k'arfin komai, fad'a min to ta kashe wanda suka kashe iyayen ta??" 'Dage kafad'a yayi ya nok'e ta alamar be sani ba. sai kuma yace, " eh ta kashe shi tabbas a cikin masarautar nan ma ta k'ona gawar sa" Aruuf yace, "shikenan tashi kaje wajen Maman ka, sannan ka tsarkake zuciyar ka a koda yaushe karka bari duniya ta rud'e ka ka aikata kuskure kamar yadda iyayen ka suka aikata" Gyad'a kai yayi yana maimaita kalaman nasa ya tashi yabar wajen. Dafe kai yayi cikin juyayi da al'ajabi lallai ashe besan komai a duniya ba face daji, ashe ana irin wannan rayuwar a duniya be sani ba?. Yana nan zaune yaji an dafa kafad'ar sa, be motsa ba sai mayar da hankali da yayi akan wanda ya dafa shin yana fahimtar yanayin sa domin gane da me yazo masa, Fahimtar da yayi babu komai yasa ya juya suka had'a ido, kauda kai yayi tareda cewa, "Udday babban amintaccen Maharani meye kuma zakayi min??" Zama Udday yayi cike da damuwa yace, "d'an uwa Aruuf kaji kad'an daga cikin labarin shugabar mu sai dai a yanzu haka tana cikin rud'ani da tashin hankali, bazaka iya temakon ta ba??" Da d'an mamaki yace, "tashin hankali name?? Kuma tayaya zan iya temakon ta??" *( masu yi min k'orafi ta prvt akan bana saka yaren su a cikin labarin, to sai dai fa ku d'an yi hak'uri an bani shawarwari ne akan cewar rubuta labarin da hausa yafi shiyasa, amma ko jefi jefi ne zan dinga sakawa insha Allah, amma fa ba irin sosai d'in nan ba, ina godiya da k'aunar ku gareni Allah ya saka da khairan)* *Alk'alami na abun Alfahari na😊* *INDO CE..* [24/03, 8:51 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~14* بسم الله الر حمن الر حيم *Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480* Udday yace, "kwantar da hankali d'an uwa amma tabbas lamarin akwai rud'ani, wata azzalumar masarauta ce wadda take kiwon shugabar mu tin yarintar ta har zuwa yanzu, a wannan k'adamin kuma sun turo da wasik'ar zasu fara kawo mata hari, Mun kasa gane yadda zamuyi d'an uwa, muna da buk'atar ka a wannan masarauta karka gujemu" Jinjina kai yayi ya ta'be baki yace, "wannan tsakanin su ne ni kam bata shafe ni ba ni kuma indai ba itace tace na temaka mata ba to fa banida hannu a wannan lamarin, da zarar ta bani Abu na tafiya zamuyi yankin mu, inda bamu da wani shugaba bare ya kafa mana sharud'a" Udday yace, "kar kayi haka d'an uwa Aruuf tabbas Sarauniya Lakhshmi tana da jin kai bazata yi abunda kake so ba" Kai tsaye yace, "ashe bazan dai saka hannu na ciki ba" Daga haka ya tashi ya bar wajen. Hadima Farhana tana cikin tafiya sukayi arangama, Da ido ta bishi har cikin k'ashin ta take jin wani irin yanayi ya tsinkaye ta, take zuciya ta fara raya mata abubuwa da dama da masu kyau da marasa kyau" Tin be gane tana kallon sa ba har ya fuskanci hakan, cikin shirin ko ta kwana yace, "ke baki iya kallon hanyar ki bane kike bin mutum da ido?? Bana son rashin kamun kai" Sosai maganar sa ta sosa mata zuciya, a sarari tace, "har wannan bawan ne ze dinga fad'a min wannan maganar banzar?" Sake kallon sa tayi cike da jarumta tace, " ban iya ba, baka san cewa ra'bar gefe na ma kuskure bane?? Yanzu zansa ayi maka hukuncin da baka shirya ba, Ku dinga sanin ya kamata ku gane tsaran ku da kuma wanda ba tsaran ku ba" Cike da mamakin tsageranci irin nata yace, "Farhana!!! Ni bawa ne amma ba bawan wani ko wata ba bawan Allah ne, ra'bar kusa da ke kuma banga abun burgewar ma da ze sa na ra'be ki ba, idan arziki ne ban damu dashi ba dan ban san ma amfanin sa ba, mulki kuma kema baki da gado a kansa, ke kawai ta kusa da masu mulkin ce ba wai d'aya daga cikin su ba, kema ki dinga banbancewa mana" Sosai ranta ya 'baci musamman da ta duba taga yadda ake kallon su, k'wafa tayi tace, "zaka gane kuma ka tabbatar da abunda na fad'a maka" Daga haka ta wuce ta bashi guri, Tana zuwa wajen Maharani ta zube a wajen sai had'e fuska take, da kyar ta iya yi mata sannu tana kaiwa ta fara zayyana k'orafin ta k'arya da gaskiya ta had'a ta fad'a" Jinjina kai Maharani tayi kafin tace, "hukunci ya tabbata ga Aruuful Ansaar domin kuwa yana da yawan kutse cikin lamura na kuma hakan babban kuskure ne wanda yakan iya jawowa mutum zaman kurkuku na har abada ko kuma hukuncin kisa, Yanzu kuma yazo ya tozarta ki Farhana, wai me yake tak'ama dashi ne?? Ina ganin fa sai na nuna masa iyakar sa, tin kafin ya wuce sa'ar sa" Hadima Farhana tace, "ranki ya dad'e ina bayan ki d'ari bisa d'ari" Cikin ranta kuwa farin ciki ne ya lulllu'be ta domin kuwa haka take so burin su ya cika na son muzanta shi a wajen Maharani, indai aka cigaba da hakan to wata rana da kanta zata kashe shi" Washe gari bayan kammala zaman fada ta yanke hukunce hukunce ga duk wasu masu laifi haka shima ta yanka masa nasa hukuncin, sharar wata k'atuwar haraba da take a sashin bayi da tsakiyar rana idan ta bud'e tayi k'walll ba takalmi sannan baze tsaya ba har sai ya gama, kuma sai yayi har tsawon kwanaki goma" Tin daga wannan ranar Maharani ta samu hanyar cin karen ta ba babbaka akan Aruuf,, wahala da bautuwa iri iri babu wadda bayayi mata, yawancin ayyukan wasu bayin musamman tsofaffi duk ta yaye musu ta mayar kansa, lokaci d'aya yayi bak'i kallo d'aya zakayi masa ka gane yana shan bak'ar wahala, tak'i bashi dama koda sau d'aya ya ida nufin sa na son temakon ta, Tsananin tausayin da yake dashi yana kyautatawa talakawa da marasa k'arfi da gajiyayyu a cikin masarautar hakan yasa suke bala'in tausayin sa, gaba d'aya sai ya zamana duk shine kusan shugaban bayin kamar su bauta masa haka sukeji saboda nuna k'aunar su gare shi, yawanci suna kiran sa abun k'auna. Yana kashingid'e kan lafkekiyar kujerar sa sai lumshe ido yake,, gefe kuwa Farhana ce zaune fuskar ta fayau da alamun farin ciki a tattare da ita. Tana murmushi tace, "Ranka yadad'e hak'ar ka tana gab da cimma ruwa" Cike da gadara da jin kai yace, "dama nasani ai nasan dole zanyi nasara, yak'in da aka fara shi tin bata da wayo ai dole ne a gama shi bata isa ta dakatar dashi ba" Hadima Farhana tace, "wannan haka yake yalla'bai idan da ace banyi k'ok'arin jefa Aruuf cikin wannan halin ba nasan da yanzu komai ya warware mata, Shiyasa nayi wannan k'ok'arin domin kuwa Aruuf mutum ne, Kuma kowa cewa yake shine makamin ta, Ina ta tunanin ko shine wanda take jiran zuwan sa sai yanzu na gane ba shine ba" Yace, "gaskiya ina jin dad'in aiki dake Farhana kinsan abunda kikeyi, naji dad'in hakan" Murmushi tayi ba tareda da tayi magana ba. Yawan turo mata wasik'un da akeyi daga masarautu biyu yasa ta shiga tashin hankali, yanzu kwata kwata ba ta mutanen masarauta take ba, Aruuf d'in da tak'i shine me basu kulawar da ta dace, da lura da duk abunda sukeyi, Hadima Farhana dama tini ta tsame hannun ta, yanzu duk nutsuwar ta tana ha Kumar duk abunda zatayi tasa shi farin ciki shine abunda take yi, Ita kuwa burin ta kawai ta nema musu mafita tasan ta yadda zata shawo kan lamarin amma duk tunanin ta ta kasa gane ina ne bakin zaren, Gashi komai k'ara ta'azzara yake sun jefa mata fitina. Yana zaune suna tad'i tareda wani dattijo Udday ya k'araso wajen, zama yayi tareda gaida dattijon, Ya amsa kafin ya tashi yabar wajen, cikin mamaki Udday ya kalli Aruuf yace, "wannan kuma waye?? Daga ina ka same shi? Ba kace baka da dangi ba??" Aruuf yace, "haka ne Udday Abu na kawai shine dangi na, shi kuma wannan a cikin masarautar ku yake" Girgiza kai Udday yayi yace, "a'a gaskiya wannan ba irin mutanen mu bane, ka lura sosai mana ba d'an masarautar nan bane sai dai idan an turo shi ne" Cikin kad'uwa Aruuf yace, "an turo shi?? Kana nufin ya banbanta da mutanen ku?? Nifa a wannan masarautar nake ganin sa shine ma har muka zauna hira" Cikin son kawar da zancen Udday yace, "to shikenan ina ganin kamar gane shi ne banyi ba, Aruuf meyesa baza ka iya ganar da shugabar mu gaskiya ba?" Yace, "akan me fa??" Udday yace, "akan gaskiyar ka tana wahalar da kai kuma ni na sani tanada buk'atar temakon ka Ansaar kaji tausayin ta, rashin sani ne yasa take aikata abunda take aikatawa" Jinjina kai yayi kafin yace, "to amma ita da bata son gani na? Kuma ku na kusa da ita kun kasa ganar da ita sai ni? " Udday yace, "ai mu sai mu fad'a ta kasa ganewa kai kuma ta gane maka" Girgiza kai yayi yace, "a'a tashi kaje kawai Udday dan Allah ka rabu dani" Ya fad'a tareda had'e tafukan hannayen sa guri d'aya. Jiki ba k'wari Udday ya tashi ya bashi guri. Tsaki yayi zuciyar sa cike da takaici. Da daddare yana cikin tafiya kamar yadda ya saba zagaye da shiga ko ina a cikin Masarautar a ko wane dare domin duba abunda yake faruwa, yau ma hakan ce ta faru. Yana cikin tafiya yaji kukan yaro, Da sauri ya fara dubawa domin gane inda yake, Wata mata ya gani tana cin gudu wasu mutane su biyu suna binta hannun su rik'e da takobi sun shafe fuskar su da farar kala yadda baza'a iya gane su ba, Tana ganin sa tayi sauri dawowa bayan sa tana kuka tace, "yaro na nice Hadima Urmi wannan yaron Maharani ne shine suke son kashe mu mu duka" Su kuwa mutanen ganin Aruuf yasa sukayi turusss, Shi kuwa Aruuf kansa ya gama kwarkwancewa mamaki ya lullu'be shi da ya akayi Maharani ta samu d'a?? 'Dayan ne ya kalli d'an uwan sa cike da rashin imani yace, "idan fa bamu kashe su yau ba bamu da sauran lokaci" Cikin tsawa Aruuf yace, "Ku dakata!!! Akan me zaku kashe su?? Laifin me sukayi muku??? To zanga wanda ze iya ta'ba su" 'Daya yace, "wannan Fa Aruuful Ansaar ne zefi sauk'i mu gudu kafin ya gano mu" Kafin yayi wani yunk'uri sun bar wajen da gudu kowa yayi ta kansa. Hadima Urmi tace, "na gode maka d'an nan ka cece ni daga wannan azzaluman mutanen" Ido ya zuba mata yana mai-mai-ta sunan ta Hadima Urmi, jinjina kai yayi yace, "karki damu, kece Uwa Urmi ko??" Tace, "eh nice" Yace, "ko zaki iya bai labarin abunda ya faru cikin nutsuwa ina son sanin d'an waye wannan" Zama tayi sannan ta fad'a masa iyayen yaron har zuwa barwa Maharani shi da sukayi, cikin tausayi ta cigaba da cewa, "Maharani tana son yaron nan sosai hakan nema yasa ake son kashe shi sabo da indai ta rasa shi zataji ba dad'i yanzu nima kaina ina cikin wanda suke son ganin bayan mu, rayuwar mu tana cikin had'ari, haka suke kawo mana farmaki a ko wane lokaci ba zato ba tsammani Allah ne kawai yake temakon mu" Jinjina kai yayi yace, "zan yi mata magana, amma wace masarauta ce suke son sace ta" Da sauri tace, "Marudha ce" Jinjina kai yayi tareda cewa, "karki damu komai ze wuce insha Allahu" Cikin farin ciki tace, "nagode sosai d'an nan Ubangijin ka yayi maka Albarka" Murmusawa yayi har cikin ransa yana mamakin k'arfin kafirci irin na mutanen masarautar ace duk yawan su ba musulmi. Tana zaune a wata haraba had'ad'd'iya Tasha ado, Arjula ce ta sakko kusa da ita tana karkad'a jela. Ganin hakan yasa ta gane akwai magana, hannun ta mik'a mata, ta haye, Kallon ta tayi a marairaice tace, "Arjula?? Fad'a min me yake faruwa" Shiru tayi na d'an wani lokaci kafin ta zaro ido tareda cewa, "Aruuf ya baki wasik'a ki kai masarautar Marudha kuma?? Me yace?" Daga masarautar Purlasirie. Na shirya tsaf domin taren ko wane k'alu bale da zan fiuskanta daga gareku, sai dai fitina ba itace a gaba na ba yanzu, zefi mana sauk'i muyi sulhu tsakanin mu kuma mu had'e kan mu, be cancanta mu zauna muna raba gari ba bayan kuma akwai wanda suke son ganin bayan mu mu duka, kamata yayi mu had'a k'arfi da k'arfe mu yak'e su kuma mu nema kan mu da mutanen mu y'anci, nakasta junan mu ba shine mafita ba, kiyi tunani Maharani Sameena, idan baki hak'ura da d'aukar fansa akan abunda nayiwa d'an ki ba? To ki zo har inda nake ki rama, ni na zubar da makamai na bana shirin yak'ar ki domin hakan bashida wani amfani, daga Maharani Mahalakhshmi" Muryar sa ce ta tsinkaye ta, Da sauri ta zuba masa ido cikin ranta tana mai-mai-ta abunda bakin sa yaje furtawa har ya kammala kafin ta mik'e cikin gadararren takun ta ta k'araso gaban sa, a dake tace, "me kake nufi da hakan??? Karanbanin ka har ya kai nan koma ya wuce?? Har kana ganin kayi isar da zaka rubuta wata wasik'a da yawun masarauta ta?" Murmushi yayi yace, "dad'i na dake bakya cin riba, ni a nawa tunanin hakan shine dai-dai ina amfanin fitina Lakhshmi?? Ni bansan ana irin wannan yak'in da ake karkashe mutane ba, kuma Marudha zata iya temaka miki akan way'an da suke hak'on su cimmi ki, dad'i na dake girman kai amma idan kinyi tunani zaki gane hakan shine dai-dai addu'ar da zakiyi a yanzu itace Allah yasa su amince da hakan" Shiru tayi tana d'an tunani kafin tace, " idan aka samu matsala ka yarda ka d'auk hukunci na??" Yace, "na amince, tinda Allah yasan da kyakkyawar niya nayi hakan, amma mutanen ki suna cikin wani yanayi, Mahalakhshmi me ze hana ki dawo da Abdulkareem kusa da ke? " Ido ta zuba masa kamar wadda take shirin had'iye shi sun ja lokaci suna kallon kallo kafin tace, "a kan wane dalili??" Ba tareda shakka ba yace, "akan ana son kashe shi!!! a gani na ki dawo dasu nan har Uwar Hadimai Urmi " Murmushi tayi tace, "na amince da hakan ka nemo min Hadima Farhana" Juyawa yayi ba tareda yace mata k'ala ba ya bar wajen. Ta raka shi da ido tanajin wani yanayi yana riskar ta, har ya 'bacewa ganin ta bata dena kallon hanyar da ya tafi ba, lumshe ido tayi tareda sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, akan la'b'ban ta ta mai-mai-ta "AruufulAnsaar " *INDO CE..* [26/03, 10:39 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~15* بسم الله الر حمن الر حيم *Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480* Kallon Arjula tayi cikin nutsuwa tace, "Arjula? Meyesa Aruuf yake kiran suna na haka kai tsaye?? Jarumi na ne kawai yake kirana Lakhshmi ko Mahalakhshmi kai tsaye, yana da abun Al'ajabi a tattare dashi" Da sallama ya shiga inda Abu Ansaar yake ya same shi zaune ya zuba tagumi hannu bibbiyu, da sauri ya k'arasa yana cewa, "Abu lafiya kuwa?" Tatta'be baki yayi cike da rigima irin ta tsoho ya fara hawaye yana cewa, "d'a na ni dai kazo mu tafi gidan mu mubar wannan masarautar ina jin tsoro, akwai abubuwa sosai a cikin ta harda marasa kyau, Yau wata mata tazo tace min in gaggauta d'auke ka mu tafi idan ba haka ba sai ta kashe mu duka, kuma shak'e min wuya tayi banyi tunanin ma zan zo yanzu a raye ba, d'a na ka rufa min asiri ka tashi mu bar wannan masarauta tin kafin su kashe mu" Ido Ansaar ya zuba masa zuciyar sa tana wani irin harbawa, Baki a sake da tsananin mamaki yace, "Abu na wacece??'" Abu Ansaar yace, "ban santa ba yaro amma duk inda taje tazo y'ar cikin masarauta nan ce, tayi ado irin na sarauta sosai amma ni ban santa ba bata fad'a min sunan ta ba kawai tace min na d'auke ka mu tafi wai kana yi mata shigar kutse a cikin rayuwar ta" Aruuf yace, "Abu dan Allah zaka iya kwatanta min yanayin ta? Ina son sanin ko wacece, ni dai a sani na bana shiga hurumin ko wace mace idan ba Lakhshmi ba ta yaya kenan zan shiga rayuwar wata?? Ko dai Farhana ce? Abu babba ce ko yarinya??" Abu Ansaar ya ta'be baki kafin yace, "naga duk ka firgice ne, da alamu dai bakayi musu laifin komai ba, kawai ganin ka ne basa son yi, dama su mutane haka suke dan haka d'ana kawai mu bar musu masarautar su, ita babba ce ba yarinya bace, nima ba dan nasan lakhsmi Maharani d'in ba da zance ko itace dan tayi ado irin nasu amma ita wannan babba ce dan kuwa zata iya kaiwa tsarar mahaifiyar ka, tace wai rayuwar ta da d'an ta kake shiga shiyasa" Shiru yayi yana d'an tunani kafin yace, "tace ina shiga rayuwar ta da d'an ta?? Kenan wannan wacece? Kuma kace tayi ado irin na Lakhshmi ko? Ba kuma mahaifiyar Ramraj bace?? Ita kuma bata da gatan da zatayi irin wannan adon sosai a masarautar nan, kuma ita ba wata babbar macece ba, Abu kai na ya kulle anya kuwa ba Gimbiya jusi bace?? Idan haka ne kenan ita ma tana da wani k'uduri mummuna akan Lakhshmi?? Kuma a hakan kake cewa na bar masarautar nan Abu?? Kasan had'arin da mutanen cikin ta zasu fuskanta idan bana nan?? Lakhshmi duk tunanin ta yana ga wani da take jiran zuwan sa ta rasa yadda zatayi komai ina son temaka mata sosai Abu" Jinjina kai yayi yace, "nima ina so ka temaka mata d'ana amma rigimar sarauta sai y'an sarauta su d'in ma ba kowa ne yake iya ta ba, kuma wadda kake zato be zamo lallai ace itace ba domin kuwa nasan gimbiya Jusiyya sosai ba itace tazo guri na ba, wata ce daban, 'Dana kayi k'ok'ari kamar nan da kwana uku kayi abunda zakayi mu gudu kaji ko?? Ka nema mana alfarma a wajen Rani" Jinjina kai Ansar yayi yace, "shikenan, amma ni yanzu duk na kasa fahimta, na zauna ina hira da wani tsoho Udday yace ba d'an masarautar nan bane kai ma gashi wata tazo wajen ka kuma bana jin itama y'ar wannan masarautar ce, gaskiya akwai rikici" Abu Ansar yace, "d'ana ni dai duk inda ka shiga ka dinga addu'a Allah ze warware maka komai" Ya gyad'a kai tareda amsawa da "to" Arveen da Waziri suna zaune suna tattaunawa akan abunda ya shafe su, Arveen yace, "Baba ni fa har na fara kwatanta yadda zan gudanar da mulki na, kowa sai ya tabbatar an samu canji ni bazanyi yadda Maharani Mahalakhshmi takeyi ba, zan bawa kowa damar sararawa da y'an mata ba tareda hukunci ko doka ba, Amma fa bayan wannan babu wani abu me sauk'i, hukunci na kuma sai yafi nata tsauri" Waziri yace, "idan ka zama sarki ita kuma ya zakayi da ita??" Kai tsaye yace, "zan maida ita baiwa ta ko kuma na kulle ta a kurkuku ko Baba?? Ko kuma ta zauna a me kula da matata" Waziri ya shek'e da dariya yace, "lallai d'ana mulkin ka zo ze da abun mamaki, ina son ganin wannan ranar ni kaina sai na dinga gwangwajewa ta" Arveen yace, "karka damu baba" Wani matashin ba fade ne ya shigo yana kai gaisuwa suka amsa tareda bashi umarnin ya fad'i abunda yake tafe dashi. Da sauri yace, "ranka yadad'e Shugaban mu na gobe wato Aruuful Ansaaar dai ya aikawa Masarautar marudha wasik'a akan neman sulhu a yanzu zancen nan da muke Sarauniya Sameena ta amince da hakan haka itama Sarauniyar mu ta amince yanzu gaf suke da had'e hannayen su guri guda su zama tsintsiya mad'aurin ki d'aya, sannan wannan Aruf Ansar da kuke gani makirin mutum ne yanzu ya riga ya gama mamayar zuciyar sarauniyar mu, abubuwa da dama shine yake tsara mata yadda zatayi, sai kun tashi tsaye a kansa idan ba haka ba ze baje tsarin ku kuna zaune, kuyi hanzarin sanin abunyi ranka yadad'e" Tini zuciyar Arveen ta fara tafasa yayi kicin kicin da rai. Waziri ne ya kalli bawan yace, "yanzu ka zo da labarin da ya fusata d'ana dan haka ba kai ba samun kyauta yau ka tashi kaje" Sim sim ya tashi ya fice, ko babu komai ya isar da abunda yake son isarwa. Waziri ya kalli Arveen cikin son kwantar masa da hankali yace, "haba jarumin d'ana be kamata abu kad'an ya dinga fusata ka ba, Zamu san abun yi" A harzuk'e yace, "kar in bari abu kad'an ya fusata ni wannan kake kira abu ka d'an?? Haba kace ka samo mana mafita ashe hanyar da bata 'bullewa ka kai mu, A memakon masarautar Marudha ta tarwatsa ta yanzu sai su had'e kai dan temakon juna? Meyesa hakan???" Yayi tambayar a tsawace. Waziri ya dafa kafad'ar sa tareda cewa, "yi hak'uri d'ana kwantar da hankalin ka ni nasan hakan ma baze yuwu ba" Maharani tana zaune Ansaar ya iso inda take, ba tareda ya jira umarni ba ya nemi kujera ya zauna kusa da ita. Ido ta zuba masa tana jin wata irin kibiya tana sukar zuciyar ta. Da d'an murmushi akan fuskar sa yace, "ba abu ne fa me wuya ba Lakhshmi, ki bawa masarautar Marudha hak'uri baya nufin kin fad'o, domin kuwa shi shugaba da son zaman lafiya aka san shi, hakan da zakiyi shine ze k'ara kankaro martabar ki a wajen wasu, kiyi k'ok'arin danne zuciyar ki karki bari girman kai yasa ki fad'a halaka, ki rubuta wasik'a yanzu yanzu Lakhshmi, Gobe ki tashi mutanen ki suyi tafiya zuwa can domin isar da sak'on, kiyi komai da tsari kuma da mutuntawa" Daga haka ya tashi yana shirin barin wajen. Sunan sa da ta kira ne yasa ya fasa tafiyar ya juyo yana kallon ta. cikin murmushi me cike da shauki tace, "Aruuful Ansaar, Tumhara har kaam bahut khub hota hai" (Aruuful Ansaar Ko wane aiki naka yana kyau) Murmushi yayi tareda d'an rissinawa. Hakan ya sumar da ita a zaune, yau ne rana ta farko da ta ta'ba ganin ya risina mata, hakan ya sata cikin nishad'i, ita kad'ai tayi ta murmushi tana tunanin irin yanayin sa da d'abi un sa. Da daddare ta kaiwa Ummee ziyara, Cikin sanyi ta zauna kusa da ita tareda rik'i hannun ta, a marai-rai-ce tace, "Ummee na yak'i dawowa gare ni gashi har wani yana nema ya gaje fadar sa, ko dai ya mutu ne??" Girgiza kai tayi alamar a'a ko kuma bata sani ba. Murmushi tayi tace, "Ummee mutum d'aya ne ya ta'ba sanya shauki a cikin tunani na bayan shud'ewar wani lokaci" Duk da irin yanayin da take ciki be hana kyakkyawan murmushin ta bayyana ba, ta lumshe ido tareda had'iye wani mugun yawu. Maharani tace, "zan iya tafiya?" Gyad'a mata kai tayi. Ta tashi tana murmushi ta koma turakar ta. Hadima Urmi ce ta shigo hannun ta rik'e da Abdulkareem wanda yayi wayo ya girma har ya fara irin gwaranci na yara. Tana ganin sa fara'ar ta ta k'ara fad'ad'a da sauri ta taso ta kar'be shi tana cewa, "Abdulkareem!! Ido ya zuba mata ko k'iftawa baya son yi. Ta saki murmushi tareda hura masa iska a fuska sai kuma ya k'yalk'yake da dariya. Sake rungume shi tayi tareda sumbatar goshin sa tace, " ina fatan nasara wa rayuwar ka Abdulkareem " Uwar Hadimai Urmi tace, "Ranki yadad'e naji kamar yana buk'atar ganin ki ne shiyasa na shigo miki dashi ina godiya k'warai da gaske da ya kasance kin dawo damu kusa da ke, anan zamu fi samun kwanciyar hankali" Ta murmusa tareda cewa, "uwa urmi ai wannan ba komai bane gareki, kije kawai yau zan kasance tareda Abdulkareem" Tayi godiya sannan ta fice. Yau ta kasance rana ce wadda ake lullumi babu rana sai hazo da hadari da suka zagaye sararin samaniya iska tana kad'awa kad'an kad'an,,, sakamakon Albarkar shuke shuke da tsirrai da suke dasu a yanki yasa k'amshin su yake tashi yana bazawa ko ina. Cikin nutsuwa take shiryawa cikin wani Sari ruwan makuba (coffee ) wanda aka yiwa ado da ruwan gwal (golden ) yayi matuk'ar dacewa da jikin ta yayi mata kyau sosai, ta d'auki wata dank'areriyar sark'a ta zuba a wuya har sai da ta kai kan cikin ta kallo d'aya zakayi mata ka gane ta madarar gwal ce sai shek'i da walwali take, haka tayi ta saka kayan ado ta ko ina sosai tayi kyau kamar sabuwar amarya, tana gama shiryawa ta zura takalmin ta, Wajen taga ta nufa tana lek'awa, sassanyar iskar da take kad'awa ta shak'a taja numfashi kafin ta sauke ajiyar zuciya, murmushi ta saki saboda tunanin da ya fara bijiro mata, A duk lokacin da yanayi ya kasance irin wannan takan kasance a mak'ale dashi domin kuwa tana matuk'ar jin dad'in irin wannan yanayin yayin da ta kasance a tareda shi, idan bazata fita ba haka shima bazata barshi ya fita ba sai dai ya rungume ta kawai, tayi bacci ta farka shi kuma yana ta gadin ta, idan kuma zata fita ko a ina take ko a wane yanayi take ko yawan mutanen da suke guri baya hana ta shigewa jikin sa, amma sauyin rayuwa ya sa itace me fita ko wane irin lokaci ana ruwa ana rana ana sanyi ko ana iska baya hana ta fita domin al'umar ta. A take wata muguwar kewar sa ta tsirga mata tin daga sama har k'asa , idanun ta suka cicciko da k'wallah, tafukan hannun ta tasa ta goge su kafin ta fara takawa cikin nutsuwa tayi hanyar waje. Ko ina ta ratsa d'iban gaisuwa ake da mik'o jinjina, da kyar take iya amsa musu saboda yanayin da ta tsinci kanta a ciki, Haka ta cigaba da ratsawa har ta isa bayan masarautar,, bakin tank'amemem ruwan da yake gudana ta tsaya tana kallon furrai da tsirrai tana matuk'ar jin dad'in daddad'ar iskar da take gudana. Ta dad'e anan tana tunanin rayuwar baya da kuma wadda zata kasance nan gaba, tana jin zuciyar ta na mata barazana akan irin abunda yake shirin faruwa, duk da tana da k'warin guiwa amma tana matuk'ar tsoron wannan Azzalumar masarautar domin kuwa d'aukar fansa ce zata dawo dasu wajen ta. Tana cikin tunanin taji an rungume ta, Wani bahagon numfashi ta fizga tareda zazzaro ido a razane. Muryar sa ce ta daki dodon kunnen ta cike da kulawa yace.... (Su o'o har an baza kunnuwa aji me yace hhh😂😜😜a dena sa ido😎) *INDO CE..* [26/03, 10:41 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~16* بسم الله الر حمن الر حيم *Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480* "Mad'aurin rigar ki ne ya kwance shine zan gyara miki" Duka ta tattaro k'arfin ta ta bangaje shi, a zafafe ta yarfa masa wani shigaggen mari, fuska a had'e tace, "ka shiga tai-tayin ka Aruuf,, Maharani Mahalakhshmi ni ba kamar ko wace mace bace, bana buk'atar gigi, ban amince wani ya kusanci kusa dani ba shine zakayi min irin haka saboda ka samu fuska?" Hannun sa dafe da kumatun sa cikin wata sassanyar murya yace, "kenan har ranki ya 'baci!?? Bana son hakan kiyi hak'uri, a bisa kuskure ne na aikata hakan nima kaina na sa'ba doka da k'a'ida ta, wannan baya d'aya daga cikin d'abi'a ko ak'ida ta ina neman afuwar ki" A tsawace tace, "rufe min baki Ansaar!!! idan zuciya ta ta riga ta buga batajin magiya bata gane meye hak'uri bare ta tausayawa mutum iya abunda ta sani kawai hukunta duk wanda yayi mata kuskure, ka cancanci mummunan hukunci sai dai bazan iya yi maka shi ba, kuma hakan ya samo asali ne saboda ina mutunta addinin ka da kuma duk wani mabiyin addinin banda haka tabbas kai da kwanan farin ciki daga yau sai dai tarihi, Aruuf" Kallon ta yake ido cikin ido a dake yace, "tabbas nayi kuskure amma irin hukuncin da kike yankewa mutane wani laifin sa be kai girman hukuncin ba, kin mayar da zubda jini tamkar ado ko kuma wani abu me kyau, Na tsani wannan d'abi'ar taki, Mutum ya aikata kuskure kad'an kiyi masa hukuncin kisa kin mayar da takobi abun k'arar da rayuka, Ki jaraba koda sau d'aya ki dena irin wannan hukuncin ki samu jituwa da kusanci da jama'ar ki na tabbata hakan ze sa kiji sauyi sosai a tareda ke, Bayan wanda kike so kuma kike jiran zuwan sa kin kasa sakin jiki da kowa, Ba dole sai ahalin ka ne zasu ji'banci lamuran ka ba idan da kina jansu a jiki sosai nasan zaki fi haka samun salama domin nasan zaki samu masu d'ebe miki kewa ba adadi, Nayi bincike akan mahaifin ki wato Sarki Ganesh, tabbas shi shugaba ne me adalci wanda yake iya zama yaci abinci tareda bayin sa, yakan zauna yayi hira ta fahimta dasu ya d'auki kowa a matsayin d'an uwa yana kyakkyawar kyautatawa gare su baya zargin kowa haka ya d'auki yarda ya bawa kowa, tunane tunane ba aikin sa bane ya mik'a lamarin sa ga ubangiji, meyesa bazaki kwaikwayi baban ki ta wasu 'bangaren ba??" Shiru tayi tana nazari kafin ta girgiza kai tace, "baka san komai ba dan haka ka janye jikin ka, duk da cewar na d'an yi mamakin yadda ka zayyano min wasu daga cikin halayen mahaifi na, amma wannan kad'an ne tunanin ka baze iya d'auka ba kwanyar ka bindiga zatayi idan aka fara karanta maka tarihi na da na mahaifi na har ma da mahaifiya ta Sarauniya Rukhshah, Rukhshahnaa, tunani kuma abu ne wanda ya zama wajibi ga wanda yake tafiya ba gaba ba baya kuma hanya ta k'ure masa ya zama dole yayi nazari akan meye mafita, ka dinga tunanin abunda ze yuwu Bin Abu Ansaar " Daga haka ta fara takun ta me matuk'ar jan hankali da shagalarwa da nufin komawa ciki. Cikin zafin nama ya rik'o hannun ta tareda finko ta tayi baya, dai-dai inda wata k'orama take kwararar da ruwa ya tara ta, Sai da ta jik'e jalaf har ta fara kakkarwa saboda sanyi da kuma yadda ruwan ya ratsa k'ok'on kanta sannan ya sake ta. Cikin hanzari ta fito tana girgiza kanta tareda k'ok'arim shak'ar kyakkyawan numfashi, ta d'auki lokaci kafin numfashin ta ya dai-dai-ta sai sauke ajiyar zuciya take a kai a kai ta furzar da wata sassanyar iska ta bud'e idon ta garass a kansa tana binsa da wani kallo me cike da tuhuma da kuma tsantsar 'bacin rai. 'Dan murmusawa yayi yace, "Lakhshmi nasan ba lallai idan kin fahimci me hakan yake nufi ba, ni nayi ne dan na sa kiji sanyi har cikin zuciyar ki ba da wata muguwar niya nayi ba, Ranki ya 'baci sosai a dalili na be kamata in bar hakan ba, kuma yawan tunanin da kike ya jefa ki a damuwa hakan ne ma yasa nazo gareki domin nema miki salama, tin zuwa na da haka naso in iso miki sai dai kuma ban samu damar hakan tin farko ba, Idan kika d'aga murya kece zakiji dan kuwa mutanen ki zasu raina girman ki, Idan kuma kika koma cikin Tajmahaal a haka mutane zasu d'auka kinyi wankan Al'ada ne na addinin ku, ni kuma nayi ne kawai dan rage miki damuwa, na barki lafiya" Daga haka ya juya ya bar wajen cikin takunsa irin na cikakken jarumi. Ido ta bishi dashi take tunani ya k'ara bijiro mata, a zahiri tace, "yanayin takun sa yanayin salon sa haka ma tafiyar sa murmushin sa da kuma yadda yake gudanar da komai cikin kyakkyawar manufa da k'wak'k'warar hujja Sakkk,. Murmusawa tayi tareda cewa, " na k'aunaci hakan Aruuf, kuma salon ka yana burge ni" Wani shauki ne ya shiga d'ibar ta sai murmushi take ita kad'ai,, Cikin nutsuwa ta shiga cikin masarauta kamar yadda ya fad'a kuwa kowa yayi zaton tayi wankan Al'ada ne shiyasa suke ta kwasar tabarraki, Gaf da zata shiga sashin ta tayi karo da Gimbiya Jusiyya hannun ta rik'e da wani d'an abu na zuba wuta, fuskar ta d'auke da murmushi ta saka mata Albarka sannan taja hannun ta suka shiga ciki, Kaya ta ta d'akko mata ta bata tareda cewa, "y'a ta kisa kaya kinji ko!? Kar sanyi yayi miki yawa" Gyad'a kai tayi ta kar'ba tana murmushi. Cikin hargagi Arveen yace, "Baba wai me yarinyar can take nufi da mu ne a wannan masarautar??? Ta d'auki wancan k'azamin bawan tamkar wani abun bautar ta, kusancin su yayi yawa, ina jin zafin hakan Baba" Waziri yace, "yaro na? Nace ka dena saurin fushi dan kuwa mutum me saurin fushi be cika tunani ba, Ka zauna kayi nazari sosai akan abu shine mafita ba kai ta fusata ba, karka damu d'ana" Tsaki yayi yace, "haba Baba na, haka kake ta cewa kar na damu gashi yanzu duk ka lalata komai kwata-kwata ma yanzu ba ta mu take ba, zanyi abunda nake ganin shine dai-dai fa" Waziri yace, "d'ana kwantar da hankali bana son ganin 'bacin ran nan naka, na gaya maka sannu sannu bata hana zuwa" Arveen ya juyar da kai tareda cewa, "haka dai" Gimbiya Jusi ce ta kalle ta cike da kulawa tace, "Maharani?? Naga kwanan nan kina cikin damuwa duk kin canja me yake faruwa ne?? Me yake saki irin wannan yanayi Maharani??" Lumshe ido tayi tareda kamo gefen le'ben ta ta taune shi, kamar baza tayi magana ba sai kuma tace, "Mama Jusiyya masarautar da muka yak'a a baya tana son dawowa garemu domin d'aukar Fansa na tabbar yanzu magajin masarautar ne yake k'ok'arin tinkara ta abun bazeyi kyau ba domin kuwa nasan ya girma ne da muradin fansar jinin mahaifin sa" Gimbiya Jusi iya tashin hankali ta gama kaiwa k'ololuwa, ko motsin kirki kasa yi tayi sai girgiza kai da take idanun ta sun cicciko da k'wallah. Da sauri Maharani ta dafa kafad'ar ta tareda cewa, "Haba Gimbiya Jusi meyesa kuma zaki tashi hankalin ki haka shiyasa fa nak'i fad'a muku gara na shiga tashin hankalin ni kad'ai k'anwata Farhana ma ban gaya mata ba saboda bana son ku shiga irin rud'anin da nake ciki ina fata a cikin wannan k'adamin masoyi na ya dawo Gimbiya Jusi daga nan ne duk wani k'warin guiwa ta ze dawo, rashin sa ya sa rayuwa ta ta samu babban nakasu, Mama Jusi dan Allah ki dena damuwa babu abunda ze faru sai Alkairi, ubangiji baze basu ikon cin nasara a kan mu ba, domin a koda yaushe gaskiya itace a sama" Gimbiya Jusiyya ta share k'walla cikin tausayi da juyayi tace, "y'ata ke me nasara ce kuma zaki cigaba da nasara a rayuwar ki, har yanzu jinin masoyin ki yana bibiyar jikin ki, akwai abu me matuk'ar daraja a tsakanin ke dashi, darajar wannan abun baze bari ya nisan ta da ke ba, yana tareda ke y'ata" Murmushi ne ya su'buce mata ta lumshe ido a k'asaice tace, "naji dad'in hakan Gimbiya Jusi" Farhana tana zaune gefen sa suna hira kad'an kad'an mafi yawanci ma tambaya ce yake mata sai ta bashi amsa, Wannan budurwar me rufaffiyar fuska ta shigo kai tsaye Kumar ta fara kira, Yayi saurin bud'e mata hannu ta fad'a jikin sa tareda sauke wata zazzafar ajiyar zuciya. Cike da kulawa ya rungume ta yana kallon ta cikin muryar sa me cike da jin kai yace, "kyaa hua??" Numfashi ta sauke kafin tace, "masarautar da ta dad'e tana bibiyar Maharani itace yanzu take k'ok'arin jefo harin ta gidan nan, yanzu lokacin da ze d'auki fansar sa yayi" Kece yayi da dariya, har sai da yayi me isar shi sannan ya tsaya, cikin k'warin guiwa yace, "ban damu da kashe kashen da za'ayi ko 'barnar da za'ayi ba, ban damu ba idan an rushe masarautar nan ni dai buri na a wulak'anta Maha" Farhana tace, "wannan gaskiya ne Khumar nima babban buri na shine naga an tarwatsa ta, ban ta'ba muradin mulki ba kawai naga an kawo k'arshen ta shine cikar buri na" Devi tace, "shikenan to yanzu me kuke ganin za'ayi??" Khumar yace, "baku da damuwa a kan wannan yanzu hukuncin da na yanke shine za'a bi zanyi nazari naga abunda ya kamata, sai mun cika muradhen mu" Zaune take a bakin gado ta rufe fusksr ta da tafukan hannun ta duka biyun, ta dad'e a haka kafin ta tashi ta fice. sashin da aka mayarda Hadima Urmi ta nufa, ta tarar da ita zaune tana yiwa Abdulkareem wasa. Tsayawa tayi tana kallon sa har cikin rai tana yaba wa irin mugun wayon da yaron yake dashi, a hankali ta tsungunna dai-dai shi cikin sassanyar murya ta kira sunan sa, ya dawo da kallon sa gareta yana fara'a. Murmushi tayi tareda shafar kansa tace, "zanje kurkuku na duba Ummee na ko zaka raka ni??" Hadima Urmi ta murmusa tareda cewa, "me zamani y'ar mulki yaro Abdulkareem be iya magana ba, zan iya amfani da yawun sa??" Kallon ta tayi ta kauda kai sannan tayi mata alamar eh. Hadima Urmi tace, "godiya nake uwar marayu ta dai Abdulkareem yana son ya bi Ummeen sa alamun sa ma sun nuna hakan" Hannu ta mik'a masa tana murmushi tareda cewa, "kana da son yawo kenan?? Yanzu ma kaci girman da zaka fara sanin ciki da wajen masarauta zan dinga d'aukar ka nayi komai tareda kai dan ka fahimci komai" Shi kuwa cikin sauri ya mak'ale mata sai rarraba ido yake. Hadima Urmi tace, "Abdulkareem ya gode haka ma me rainon Abdulkareem ta gode" Bata kula ta ba ta d'auke shi suka fita. Tana kwance can gefe ta tsakure sai d'an numfashin ta da yake fita a hankali ne ze tabbatar maka da tana da rai. A hankali ta k'arasa ta durk'usa a gaban ta, cikin sanyi tace, "Ummeen mu!!! Ki tashi nazo ki tashi kiga Abdulkareem, cikin hanzari ta bud'e ido tareda mik'ewa ta zauna tana kallon su. Mik'a mata shi tayi tana cewa, " daga Udday da Surekha" Rungume shi tayi tareda gyad'a kai cikin nuna kulawa da zallar k'auna, sumbatar goshin sa tayi take waye suka shiga jerangiya akan fuskar ta kamar famfon da ya lalace. Maharani bata hana ta ba sai ma nata hawayen da suka fara zuba..... *INDO CE..* [27/03, 11:08 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠* (Masarauta) Mallakin *INDO CE..* 🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼 *Page~17* بسم الله الر حمن الر حيم *(WANNAN SHINE K'ARSHEN SHAFIN KYAUTA DAGA YAU NA GAMA FREE PAGE. KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI😊)* *Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480* Cikin sanyi ta dafa ta kafin ta share k'wallar ta tana murmushi tace, "ba kuka zakiyi ba Ummee Addu"a zakiyi mana wata rana muma zamu haifa miki y'a me kama da ke nasan zakiyi farin ciki sosai musamman idan ta kasance me sunan ki, nasan zatayi irin halin ki da kyawun ki Ummee, kuma zata kasance jaruma sak jinin mahaifin ta, ina son ganin Murmushi a fuskar ki ba hawaye ba, idan ina ganin kina kuka nakaniji gaba d'aya bazan iya yafewa kaina ba, Gashi kin k'i magana Ummee kin kasa fad'a min kin yafe min ko kuwa?? Duk da ko kin yafe min ba lallai ubangiji ya yafe min kuskure na ba, Ummee idan kinso zan iya bada raina fansa akan abunda nayi, Farhana ta kasance me karaga nasan koda bana raye indai hakan ta faru tabbas ruhi na ze samu salama Farhana nasan zatayi fiye da abunda nayi a wannan k'asar bare kuma da temakon ki, za'a shimfid'a mulki na adalci, Ummee meyesa baza ki za'bi hakan ba?? Meyesa sai zaman kurkuku kika za'bawa kan ki?? Mu kuma iyalin ki meye makomar mu Ummee?? Dan Allah ki dena kuka kiyi farin ciki a koda yaushe nasan wannan yaron tabbas ze zamo Fansar wasu daga cikin rayukan da muka rasa, ki kalle shi sosai duka yanayin jinin Abdulkareem ne dashi hakan ne yasa naji ina k'aunar sa domin kuwa Ahalin Abdulkareem ba abun k'i bane, Kiyi Murmushi Ummee na" Share hawayen ta shiga yi sai dai tana sharewa wasu suna k'ara zubowa, ido ta zubawa Abdulkareem wanda yake kallon ta kamar wanda yake mata kallon tuhuma, wani yalwataccen Murmushi ne ya buwayi fuskar ta, jinjina kai tayi tareda mik'awa Maharani shi, cikin ranta tanaji kamar tayi magana sai dai bakin ta yayi nauyi ya rik'e gamm baza ta iya motsa shi ba indai da sunan tayi magana ne, girgiza kai kawai take yayin da wasu zafafa hawaye suke kwararowa daga cikin idanun ta, tabbas tana da abun fad'e tana da muhimman abubuwan da ya kamata ta sanar mata sai dai k'addara ta hana ta wannan damar" Jin tana neman fashewa da kuka ne yasa tayi saurin tashi tana rungume da Abdulkareem ta fice daga wajen tana tafiya cikin sanyi da tsanani tausayin rayuwar su" "Lakhshmi" Muryar sa ce ta doki dodon kunnen ta,,, tsayawa tayi cak ba tareda ta juya ba kuma bata cigaba da tafiyar ba. K'arasowa yayi cikin nutsuwa da kamala yace, "Lakhshmi bana jin jefa kanki cikin wani k'angi shine mafitar damuwar ki, da haka me yasa baza ki baza sojojin ki ba tinda suna da yawa su je su nemo miki wanda kike so??? Kuma ina so ki tattara nutsuwar ki guri d'aya indai baki yi hakan ba banajin zaki iya yin tunani me kyau, Akwai jarrabawa a rayuwa haka kuma akwai k'alu bale, wani tashi k'addarar zalla ce wani kuma tayi gauraye, rashin nutsuwa yana gusar da hankali kuma idan hakan ta faru k'arshe bata bada abu me kyau, Ya kamata ki dinga nutsuwa ki bawa zuciyar ki damar yin tunani me kyau" Sai da ya gama maganar sannan ta d'ago idanun ta wanda suka cika tafff da hawaye zuba a kansa ta d'an kwashi lokaci tana kallon sa kafin ta bud'i baki a hankali tace, "Zanyi amfani da abunda ka fad'a amma sai nayi dogon nazari kafin na amince na bar mutane su shiga inda basu sani ba, domin kuwa ta ko ina farauta ta ake, kuma mutane na sune komai nawa idan na bari aka ta'ba su tamkar zubar da kimar iyaye na ne nayi Alk'awari gare su bazan gushe ba zan tabbatar da adalci ga mutanen su, Wasu suna ganin kamar abunda nake zalumci ne, a zahiri hakan ne sai dai wanda yasan ciki yasan waje yasan gaba da baya ze gane meye amfanin hakan, ni ina da k'wak'k'waran dalilin da yasa bana yin afuwa,,, Ansaar kayi min addu'a kawai domin kuwa bani da matemaki sai ubangiji, shine kawai yasan asalin halin da nake ciki" Jinjina kai yayi ba tareda yayi magana ba yabar mata wajen, yau ce ranar farko da ya ta'ba jin tsananin tausayin ta ya bulale shi. Lumshe ido tayi tareda sauke 'boyayyar ajiyar zuciya sannan taci gaba da tafiya. Ba tareda ta ankare ba sai ganin mutum tayi a gaban ta, idanu ta waro masa tana binsa da kallon tuhuma. Ya sosa k'eya cike da makirci yace, "Sarauniya Mahalakhshmi ki gafarce ni a bisa shigar sauri da nayi miki kai tsaye, ina son gaya miki ne cewa Mahaifi na yana Son magana da ke, yazo sashin ki ne ko kuwa zaki zo sashin mu,, ko gurin had'uwa??" Kauda kai tayi cikin k'asaitacciyar murya me nuna tsantsar isa da izza tace, "Arveen, ya same ni a k'aramar fada ta sai dai yau bani da lokacin ganin sa sai zuwa gobe, yanzu lokacin yaro na ne" Har cikin ransa abun yayi masa k'una sai dai be nuna alama ba dan kuwa yana son gyara hanyar sa ne dole sai ya jure, murmushin yak'e yayi tareda cewa, "ranki ya dad'e Sarauniya Malakhshmi y'ar sarki Ganesh da Sarauniya Rukhshanah , duk abunda kika ce haka za'ayi domin kuwa girman ki da darajar ki har sun wuce nan, a isa turaka lafiya me gadon izza" Ko kallon sa batayi ba tayi gaba cike da rashin damuwa da kulawa. Da wani mugun kallo ya bita yana jin kamar ya shak'e ta ta mutu ya huta . Ta kasa zaune ta kasa tsaye tunanin maganganun Aruuful Ansaar ne kawai suke dawo mata, ta rasa gane me ya kamata tayi amincewa ko akasin haka, kwata-kwata zuciyar ta ba dad'i gashi bata da wanda zata fad'awa ya taya ta kuka,,, Abdulkareem da Arjula kawai sune wanda tasa gaba tana zubawa magana iri da kala. Farhana kuwa yanzu ba koda yaushe take shiga inda take ba, taci gashin kanta kawai shiga gari take ta ko ina a cikin masarautar har ta fara gina ta-ta fadar domin kuwa ta fara had'a mabiya ta hanyar nuna musu tausayin ta a zahiri hakan yasa suke son ta kuma suke girmama ta sosai. Abu Ansaar yana zaune dafa'an akan Sallaya bayan ya idar da sallah ya 'buge da kuka domin kuwa tin safe yasa a nemo masa d'an sa sai dai shiru ba'a ganshi ba ba labarin sa, hakan ba k'aramin tayar masa da hankali yayi ba dan ya riga ya saba basa iya nesanta da juna. Yana cikin wannan yanayin Aruuf ya shigo sai k'asa k'asa yake da ido. Da sauri ya tashi ya nufi inda yake yana cewa, "d'ana meyesa zaka tafi ka barni??? Yanzu har ka iya yawon da zaka dinga nesa da mahaifin ka?? Karfa ka manta kai kad'ai ne d'ana kaine nake kalla naji dad'i gashi na rasa matata bare nasa ran zata haifa min wani, idan na rasa ka komai ya k'are min d'ana" Rungume shi Ansaar yayi yana d'an bubbugar bayan sa alamun rarrashi, Cikin salon kwantar da hankali yace, "Abuu ka dena cewa haka dan Allah bazan nesanta da kai ba fa, koda yaushe ina tareda kai, ni d'a ne kawai a wajen ka amma ni kaine duniya ta ban canja ba har yanzu Aruuf d'in ka ne ni" Turo baki yayi kamar me shirin sake fashewa da wani kukan, yace, "d'a na to ai naga baka tafiya ka barni ne yau kuma naga ka tafi baka dawo ba ina ta neman ka" Jan hannun sa yayi ya zaunar dashi sannan yace, "Abu kana da abun mamaki sosai, baka tsufa sosai ba sannan kuma kai ba yaro k'arami bane amma kana da irin abun yara ko tsafaffi ai bazan 'bata ba kawai dai na d'an shiga gari ne" Ya fad'a yana goge masa k'wallar cike da kulawa. Abu Ansaar yace, "yaro na ba dai kana so na ba?? To ai kuwa yanzu zaka shirya gobe mu fita da assubuh mu bar wannan k'asa na gaji da zaman cikin ta yana da kyawu mu koma yankin mu, karka manta muna da y'an uwa muna y'ay'a da abokai a can kuma sun shak'u damu bazasu ji dad'in rashin mu ba, ko ka manta dasu ne?? Tsuntsayen ka da dabbobin ka??" Jinjina kai yayi yace, "Abu meyesa baza mu cigaba da zama anan ba?? Nifa naji dad'in zama tareda su" Da sauri Abu Ansaar yace, "o'oo yaro na nan fa rayuwar su ba irin tamu bace, kar kace haka, kar ka fara jin dad'in zama dasu ni kam tsoron su nakeji, ni dai mu tafi kawai nasan Sarauniya baza ta hana mu ba" Aruuf yace, "Abu kwana biyu fa??" *(Last Free Page)* Dafe goshi yayi ya rashe da kuka yana cewa, "yanzu Aruuful Ansaar jindad'in ka da zama da mutane har yasa kana tunanin baza mu koma dajin mu ba? Ni kuwa ina zan kai Alk'awarin da na d'aukarwa mahaifiyar ka?? Me kake so in gaya mata idan nima na mutu?? 'Dana ka biyo ni mu koma inda muka fito anan nafi jin dad'in rayuwa bana son mutane, kuma yanzu duk sun tsane mu duk cewa suke ka addabe su, bana so su kashe min kai Aruuf" Shiru yayi yana nazari har cikin ransa yakejin k'unar kukan mahaifin nasa, hannun sa ya rik'o cikin nutsuwa yace, "Zamu tafi Abu amma ba da wuri ba, zan sanar mata kar mu tafi ba'a son ranta ba a samu matsala kasan ta zubar da jini baya yi maya wahala, idan na gaya mata ko zuwa da yamma sai muyi tafiyar mu, nima bana son zama anan tinda baka so Abu, mu koma muyi rayuwar mu tareda tsuntsayen mu da dabbobin mu, sune abokanan mu be kamata muyi tarayya da mutane ba, ka kwantar da hankalin ka Abu" Share hawayen yayi yana murna, cikin fara'a yace, "to d'ana bazan kuma kuka ba amma indai bamu tafi gobe ba zanyi kuka na gaji da zaman nan ba'a yawo ba'a zuwa ko ina ba'a farauta ba'a wasa koda yaushe ina a wannan turakar jinake kamar ta d'aure ni ne, ai nasan ma zata bar mu mu tafi ai laifin da kayi mata tayi naka hukunci nasan yanzu ta hak'ura" Aruuf yace, "eh mana ai yanzu ta hak'ura kuma zata bar mu mu tafi" Washe gari, fitowar ta kenan daga turakar ta ta nufi fada, Cikin hanzari ya tari gaban ta, ba tareda ya jira shan k'amshin ta ba ya fara isar mata da sak'on Abu Ansaar. Ido ta zuba masahar wani lokaci kafin ta rik'o hannun sa ta fara jan shi. Tin yana tirjewa har ya gaji ya bita zungui zungui. Har sai da ta dangana da turakar ta sannan ta tsaya ta saki hannun sa, a tsawace tace, "mai-mai-ta abunda ka fad'a" Ba tareda shakka ba yace, "mahaifi na baya son zama a cikin mutane kuma nima ba tareda su na taso ba dan haka muna son komawa yankin mu, Abu Ansaar yace na nemi Alfarmar ki ki bari mu mu koma" Zuwa yanzu tini jikin ta ya d'au wata irin kakkarwa idanun ta har sun fara canja kamanni, takobin ta ta zaro a fusace ta tsarga rigar da take jikin sa,, a take faffad'an k'irjin sa ya bayyana.. Cikin tsananin mamaki da al'ajibi ya tsaya yana binta da ido. Itama k'are masa kallo tayi sama da k'asa, ganin bata ga abunda zuciyar ta da idanun ta suka dad'e suna muradin gani ba yasa tayi wurgi da takobin tareda fashewa da wani gigitaccen kuka ta durk'ushe kan k'afafun ta. Zuwa yanzu abun ya fara zame masa kamar almara ko motsawa ya kasa yi sai binta da ido kawai da yake ya kasa fahimtar komai. Sai da ta d'ebi d'an lokaci tana kuka kafin ta tsagaita, be ankara ba sai jiyayi ta rungume shi tsamm tana sakin wani sabon salon kukan. Take yaji yanayin bugun zuciyar sa ya canja shi kanshi jin sa yake kamar ba shi ba, da kyar ya iya cewa, "Maharanie Me yake faruwa??? " Sakin sa tayi ta juya masa baya cikin shashshekar kuka tace, "kowa cewa yake Mahalakhshmi ta samu me temakon ta ashe ba haka bane?? Meyesa ka za'bi tafiya ka barni bayan ka bari zuciya ta ta shak'u da kai??? Baka ta'ba tunanin dalilin da yasa kowa yake ganin kai jigo ne gareni ba?? Idan bazaka iya tausaya min ba Aruuf ka tausayawa dubban mutanen da suke baya na kuma suka dogara dani suka d'auki yardar su suka d'ora ta a kai na, kaji tausayin su karka tafi ka bar mu Aruuf ka kasance tareda mu, zuciya ta ta Alak'antu da kai fiye da yadda zaton ka yake baka, Aruuf ka tausaya min banida kowa,, bayan wani lokaci kaine wanda zuciya ta ta k'ara amincewa dashi, ina ji tamkar na samu wanda zan dinga gani ina jin farin ciki ashe kai a gurin ka ba haka bane, idan abunda nayi maka ne ka yafe min, Bana so ka tafi ka barni zan shiga wani yanayi, kayi tunani akan goben mu yadda zata kasance, gaff suke da tarwatsa sansanin mu zasuyi min illah Aruuf kowa yana farin ciki an samu canji daga zuwan ka, ashe tafiya zakayi ka bar mu"" Sake rungume shi tayi tareda fashewa da wani sabon kukan. Kamar bishiya haka ya tsaya kyamm, take yaji kansa yana wani irin juyi, wani wahalallen rauni ya ziyarci zuciyar sa kukan da take ya dasa masa miki a cikin ransa, lokaci d'aya yaji duk duniya bashi da za'bin da ya wuce ya zauna tareda su.............. *(Karku manta shine shafin k'arshe na kyauta🥰)* *(shafin yau page 26 ni kaina nasan yayi wuta🔥🔥🔥🔥🤣😂😂😂)* *INDO CE..*