🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣1️⃣* A sanyaye ta sake juyowa barin da suke tsaye Dan murmushi ta saukewa Hasan din ko zai sasauta irin hade fuskar da ya yi kafin ta sake mika hannu ta kuma tsayar da dan adaidaita sahu. Yana tsayawa ta ce" Bawan Allah anguwar mai shanu zaka kaini da yarana dari da sittin ce da ni" Kallonta ya yi sannan ya leko ya kalli yaren ya ce" Aman baiwar Allah kin san da kin so kanki ko? Yaya zaki ce a kaiki har anguwar mai shanu a dari da sittin da kuma yara?" Dan ajiyar zuciya ta sauke tana dan matsawa gefe dan ta gama gane shi dinma ba zai daukesu a haka ba, tun daga babar makarantarsu take janye da yaren dan su dan rarage tafiyar ko zasu samu a kaisu a haka din domin wannan cenjin shine kadai abinda ya rage mata a yar jakar sakarta da ta yi, sauran kudin kwata kwata ba na anfanin hakan bane, kudin makarantar ne take faman tarawa Bata ja maganar ba ta ce da dan sahun" Allah ya kawo kasuwa" Daga haka ta sake juyawa wajen biyun a hankali ta ce" Hassan dina idon ne?" Hassan ya sake murtuke fuskarsa sosai bai ce mata ci kanki ba, sai Usaini ne ya yi dariya da maganarsa mai ruwa ruwa ya ce" Mama mu karra yin tafiyar kadan zan ci gaba da jan hannunsa har mu samu masu kaimu a haka, na tabata ba za'a rasa na annabi ba" Murmushi ta yi tana kallon bayan dan sahun nan da sai da ya sake lekowa yana sake kallon fuskar Hassan din sannan ya ja adaidaitarsa ya yi gaba ya barsu a nan zafin ranar na sake tandar fatar jikinsu. Hannayensu ta kama tana tsakiyarsu tana jansu a hankali suna tafiya cikin salonta na sanyin jiki da magana tana dan tambayarsu idan suna jin yunwa ne da sauransu har suka yi tafiya mai nisan gaske sannan ta sake gwada sa'arta ta kuma tsahar da wani dan sahun, sai dai a nanma saboda talatin kadai da ta rage a kudin ya nuna ba zai iya daukarsu ba sai dai idan yaren zasu zauna a gaba ne, ita kuma abinda bata yarda da shi ba kennan watau ajiye biyu a gaban adaidaita, domin yaren nata ba dai kiriniya ba idan sunna cikin dadin rai zasu iya fadowa ta shiga uku, dan haka ta gwamace sake yin wata tafiyar. Usaini ne ya fara takwakwafa fuskarsa, domin shi din dama ba dai ragwonci ba, kadan ya sha wahala zata nuna a jikinsa, ya ga damar ya fara sheka kuka har inda zasu je ya ja ya tirje yana kallonta da fuskar kuka a shinfide wace ke nuni da tabas yana daf da fashewa da kukan. A sanyaye ta ce" USEIN din Mama, menene?" Useini ya juya gabas da yama, kudu da arewa ya ce" Mama ni gaskiya na gaji, ki duba baban titin nan kowa a cikin sahu yake dan ranar nan da ake kwalawa, daidaiku ne muke ganni sunna tafiya a kafarsu, suma babu yara a ciki, ni gaskiya ki goyani " Ido ta dan zarro jin ya ce ta goya shi, bayan tafiyar da sauransu sosai da sosai, bayan wannan ma yanzun idan ta goya shi Hassan zai murje ido ya kirta aikin da ba shikenan ba, dan haka sai ta age tsayinta sosai ta duka tana kallonsa ta ce" Ka ga dan albarkana ita tafiya fa tana da dadi, jikin mutun kan samun karin lafiya, ka san kuwa mai yin tafiya sosai a kafarsa baya yawan yin rashin lafiya bale a bashi magani? Zo maza dan albarka salihi dan Mamansa mu tafiyarmu mu karra kadan sai mu shiga dan sahu " Ido ya fara murzawa zai fashe da kuka, sai a lokacin Hassan ya bude baki ya ce" Ka san Allah idan ka mayar da katon kan nan naka baya ka fashe mana da kukan rainin wayo zan cire abin kan nan nawa na tatakaka a bakin titin nan, ka san da zan iya , kai ko kunya baka ji katon banza kai" Useini ya zaro ido ya juya wajen Maman tasu yana nuna kansa da nashi salon na rigimar sai dai ga dukkan alamu yana shayin dan uwan nasa domin uwar ya kafe da ido yama so ta yi magana a kan lamarin za'a tataka shi kafin ya samu kwarin gwuiwar yi shima. Zata yi magana wani dan sahun ya ja ya tsaya yana fadin" Hajia tafiya ne?" Shima bata boye masa gaskiyar abinda yake hannunta ba ta fada mas akuma wajen da zai kaisu, sai aka taki sa'a ta fada kan wanda nema ya fito da zuciya daya da kuma godiya ga Allah kan abinda zai samu da zarar zai samu fita to fa zai kwatanta adalci wa masu shiha adaidaitarsa ya basu damar shiga, wannan ya rufe babin fadan da suka ja dunda zasu dora a bakin titi wanda ta tabata da ace sun fara shin to fa lalle da sai ta kusan yi masu kuka koda zasu dajata, domin yaren akoy rigima sosai a tsakaninsu sannan akoy fahimtar junna a tsakaninsu da ita. Daidai gidan Baba Lauratu aka ajiye su, ta kuma kama hannayensu bayan ta biya dan sahun suka shige cikin gidan tana salama a bakinta tana kuma jin yadda Hassan kasa kasa yake dan jan tsakin biyowar da suka yi kafin su karasa gidansu. Har kasa ta duka tana gaishe da babar dake amsata da fara'a sosai a kwonce saman fuskarta kafin ta maida dubanta kan Hassan tana fadin" Ganninku alkhairi ne koda a saman dokinku kuke, ga maza ga biyu kyautar Allah, shin waye ya taba Alhassan bawan Allah ya kuma kumburan fuskar miji nake ganninta a hade haka?" Useini ya dan fara cika fuska shi ala dole shine mijin baba Lauratu , Hasan kuwa ya sake tamke fuskarsa yana sake cira kansa gefe Baba Lauratu ta ce" Kin ga *AMINA* ga cen kwanon da na dama fura harda siga dauko masu su shanye na tabata harda zafin rana ta hadasa rikicin biyu ba abin wasa ba" Ai kam har sai da ta sauke ajiyar zuciyar farin ciki kafin ta karasa ta dauko ta ajiye masu a cen gefe ta ja kowane tamkar makafi ta zaunar da su daya bayan daya sannan a sanyaye ta ce" Dama zasu min abin kirki su sha kama kama ba tare da sun yi fada ba?, Kai da na ji dadina sosai" Tana gama fada ta koma saman tabarmar Baba Lauratun ta shiga tayata kula lalenta na hausa da take kukulawa na siyarwa Kasa kasa sosai Baba Lauratun ta ce" Yaya mai baban sunna an dace kuwa?" Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye jakar tata ta saka tana ciro takardun ciki , ta bude baban litafin cikin ta ciro naira dubu hudu da dari bakwai ta mikawa Baba Lauratun ta ce" An gode Allah, aman cewa suka yi haka gwamnati ta rubuta kudin zana jarabawar, ba zasu iya rage min ba , ni kam yanzun na danganama Baba, Allah ya fido min da wata hanyar, kudin nan ki kuma ajiye min su zan je na ci gaba da buga bugar mu ga yadda Allah zai yi, idan da rabo badi zan zanna in sha Allah" Baba Lauratu ta sauke ajiyar zuciya, ita kam da yarinyar zata bi ta tata da ba haka take so da ita ba A sanyaye ta ce" AMINATU, Aure fa?" Da sauri ta kalleta, sai kuma ta samu kanta da maimaita kalmar Baba Lauratu ta ce " Eh aure nace" Amina ta yi murmushi ta juya tana kallon yaren dake shan furar, da farko sun fara fada sai kuma Hasan ya zubawa Husain din ido har ya fara koshi sai ya bara masa, domin shine dama bawan ciki ta sake juyowa wajen Baba Lauratu a hankali ta ce" Biyu fa?" Baba Lauratu ta girgiza kanta cike da rashin jin dadin lamarin ta ce" Kin ga Amina, rayuwa ba ke take jira ba, zan sake fada maki gaskiya kamar yadda na saba, kin ga iyayenki sun rasu, ke da y'ar uwarki suka bari, kunna da dangi ba baku da su ba, irin yadda suka yi watsi da lamarinku tabas abin a duba ne, aman kuma lamarin rayuwarkima abin a duba ce, kin san da tsoratar da maza kike?" Da mamaki take kallonta da son karrin bayani a kan wai tsoratar da maza take Baba Lauratu ta ce " yawancin wa'inda basu sanki ba idan sun ganki kina yawo da biyu zasu dauka naki ne koda kuwa yannayin jikinki bai nuna kin haife su ba, aman Amina ba kowa ne ya san cewa biyu y'ayan Firdausi ne, wainda suka sanki kuwa idan sunna da ra'ayin zuwa su aureki zasu iya tsorata da yannayin rayuwa ciyar da y'ayan mutun biyu ba kowa zai iya dauka ba, ki yi hakuri iya gaskiyar nake fada maki Amina kin zo kin sakkawa ranki wahala, wahala ce mana, Allah na tuba a kasar nan idan kai ba kowa bane ba dan kowa bane ko ka samu ka gama karatun sai dai ka san yadda zaka yi da shi aman ba dai ka anfana da shi ta hanyar da ta dace ba, gashinnan shekaru na ja Amina shekarunki nawa yanzu? Sai zuwa nawa zaki iya gane me nake nuna maki ki dauki matakin da ya dace ne?" Amina da idannuwanta ke lumshe tana sauraron dukkan bayanan Baba Lauratu zuciyarta na dan dokawa, ba dan komai ba sai dan ta san iya gaskiya ne Babar ke fada mata, aman kuma itama da nata maganar, tana da nata bayanin a kan maganar dan haka ta fuskanceta a nutse ta ce" Wani lokacin, du yadda bawa ya kai da son cenza yannayin kadarar rayuwarsa babu abinda ya isa ya aikata sai dai ya ci gaba da adu'a Baba, walau ala ni ban zo duniya dan na yi aure ba, ta yiwu kuma zan samu auren a hankali.......Abinda na fi rikewa da karfina Baba shine y'ayan nan y'ayana ne, yayan yar uwata ne, diyan zumuna ne, yanzu da nake cikin haka ina cikin niimar ubangiji, mijinta ya nuna nasa yayanma kama cen riko cen ne yake yi ina zan kaisu? Nawama suke yaren? Ba zan taba sakin hannayen biyu ba Baba, kin ga fa dangin mahaifinsu basa so, ina zan kaisu?......" Ta sauke ajiyar Zuciya ta dora da fadin" Ni bani da inda zan kaisu Baba, shi yasa na koyawa kaina zama mamansu da soyaya a zuciyata, na koyawa kaina kula da su da basu tarbiya, na tabata wata rana zan samu wani datijon arziki ya daukeni da yarana koda a gidan gadonmu ne mu zauna.......Abu biyu da na san ba zan bari ba shine ci gaba da neman ilimi ta hanyar da ta dace, da kuma ci gaba da kula da biyuna" ta karashe a sanyaye haka kuma jikinta na karra daukan sanyi ainun, bama kamar idan ta tunna irin abubuwan da take fuskanta a wajen wasu mazan dan kawai ya kasance itace mace tal a gidan da suke zaune sai yan yaren na y'ar uwarta, aman ta san ko menene adu'a na gaba da shi, kuma ta san Allah ne gatanta Baba Lauratun itama ta sauke wata ajiyar zuciyar ta ce" Allah ya dafa maki y'ar nan, Allah ya taya ki riko yarinyar nan" Da amen amen AMINA ke amsawa ta mike tana duba wajen su Hasan ta ce" Husaini zo dauki bokicin masar Baba mu je, mai tsuntsaye kai yau ba zaka rike komai ba?" Hasan ya kawar da kai yana sake hade gurarakinsa ya ki bata amsa Baba Lauratu ta saka daria tana fadin" Sai gwamnati baban kowa, yau mijin kulin wainar abokin naka ne ba zaka dauka ba? Zan kuwa yafa mayafi na je da kaina na bashi kannun labari sai ya san irin zaman da zai yi da kai a gabanan nan" Ita dinma bai tankata ba, yau gana daya yan hali ke tare da shi, shi yasa AMINA ke lalaba shi su wanye lafiya dan ba zata iya rigimarsa ba Amina ta sake kallon Baba ta ce" Baba ba'a gyara shinkafar ba kennan yau?" Baba ta tabe baki ta ce" kin ga Amina, ni ina yi masa hidima ne dan shi din mai hidima ne, aman matarsa ni fa ba zan iya ce maki ga kamaninta ba, a gaskiya ke kika ga kya iya wannan abin, ace waina sai kin yi kala biyu du juma'a ta Allah? Ita bata cin hatsi? Har yanzu bata san da ta tsufa ba ko dan bata samu haihuwa da wuri bane? Ga kuma Kumbar susa na kada mata gangar shedan, kin ga ki je ki gyara abinki da kanki Allah baki lada idan da ladan" Yar dariya Amina ta yi tana mata salama cike da nishadin halayar Baba Lauratun, ita bata ga abin sakawa kai damuwa ba a lamarin mam da duniya, yadda ya zo maka kawai ka je da shi mana in ba rigimar Baba ba? Hajia dai ba za'a ce mata muguwa ba, mutun ce dai mai hali irin na son kai a lamuranta da son kare mutuncinta ta kowace hanya, aman daidai gwargwado tana kyautata maka , rayuwar nan kuwa ai kowani bawa da kashinsa a kulle a mararsa ne, na wani ya fi ma wani, yau ita gani take ko me Hajia zata yi daidai da ita ne, ai masu gidan rana take rike da su, wa'inda sunne damuwar da yawa a yau Da haka sukaiwa Baba lauratu salama suka nufi gidansu a yanzunma ita da useini ne suka rike bokicin shi kuwa sarakin yana tafe yana sake daure fuska kai kace an masa wani laifi ne Hankalinta kwonce ta idasa bude gidan nasu bayan sun gaisa da mai kantin kofar gidan sannan ta tura da adu'a a bakinta ta shige ta dakata har suka gama shigowa sannan ta mayar ta rufe gidan sosai da makulin ta ciki kafin suka karasa shigewa cikin Gidan da tsaftarsa kamar yadda ta barshi, sannan komai a kilace yadda ta bari, cikin nutsuwa ta duka a gaban Hasan ta zuba masa ido tana kallon yadda ya zauna a cikin rana yana hararan wani wajen daban, ga zufa dake tsatsafo masa, bayan dan uwansa tuni ya cire takalmin kafarsa ya kilace ya nufi bayi dan yin wanka kamar yadda suka saba A hankali ta ce" Menene yarona?" Hasan ya maido dubansa saman fuskarta ya kafeta da ido yana kallonta, cen da ya ga dama ya budi bakinsa ya ce" Mama, me yasa kika cewa Aban baban gida da mai napep din dake kaimu makaranta bayan yace direba ya ringa kaimu? " Tsuru ta yi da ido tana kallon yaron tare da tunanin amsar da ya dace ta bashi, amsar da ba zai yi mata kallon tana masa karya ba, sannan ba zai riketa da wani abin a zuciyarsa ba, ko ba komai Hasan fa yaro ne wanda zai iya kallon du wani wanda zai tauye jin dadinsa a matsayin wanda baya sonsa, ko wanene kuwa, dan haka itama sai ta zame ta zauna a cikin ranar tana kallon fuskarsa, muryarta a sanyayen ta ce" Fadeel, ranar da kace abokinka ya matsawa byronka, kulun shi sai ya ara yana rubutu da shi, kai ka gaji ya isheka me yasa kace haka?" Yaron ya sake zuba mata ido yana tuna irin takurawar da Abokin nasa ya masa a aji, da farko shine da kansa yake ara masa dan taimakawa, daga baya sai ya zamto kulun kulun sai ya daukar masa byronsa, bayan shi kadai ne da shi , wani sa'in shi da abinsama aman sai ya jira abokin nasa ya gama anfani da shi kafin ya bashi, dan haka yace" To mama shi kulun kulun sai ya amsar min abina, bayan shima yana iya fada a gida a siya masa , ranar fa budewa ya yi ya hura shi gaba daya byron ya lalace sai da Malamarmu ta cenzan wani, ta bashi wani dan ya shafa min lafiya, aman a wasge garima yace wai na bashi, ni kuma na kiya!" Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce" To me yasa zaka kiya bayan abokinka ne?" Da mamaki yake kallonta ya ce" To kuma shikenan kulun sai ya amshe min ? Ni kuma fa?" Amina ta dan dage kafadunta ta ce" Ka gani Hasan, to kamar haka ne na hasaso a kan maganar motar da Baban baban gida yace a ringa kaiku school, sai nace da ace tawa ce sai ina kaiku kulun kulun, idan na zo na saka rai da motar zan zamto bani da wani anfani har na saba kulun kulun ana kaiku, idan direban ya gaji ya daina kuma yaya zan yi? Wa zai dawo kai min ku ba tare da kun yi lati ba? Shi yasa nake kaiku ina dawo da ku"....... Fadeel ya ce" Aman Mama, a gidan na baban gida motocin ai ba daya bane, ki dauko daya mana ki koya ki ringa kaimu?"......... "Aman Fadeel kana so kace min na je na dauko motarsu na ringa maku anfani da shi bayan ba ni na siya ba?" Ta fada tana sake kallonsa tare da auna irin yadda yake daukan maganar a saukake ba tare da ta rikita tunaninsa na yaro kamarsa ba, duda Hasan din nata yana da shekara takwas ne aman wasu abubuwan idan ya yi zaka dauka ya rufe goma ko ya haura ne, domin shiru shirun da yake yawan yi a yawancin lokuta yakan auna abubuwan dake zagaye da shi ne, dan uwansa ne mai zuba surutu ko ba ma'ana Hasan ya girgiza kansa sai kuma ya ce" To ke yaushe zaki sayi taki Mama?" Wannan karron har wani dan murmushi ya subuce mata tana kallonsa da manyan idannuwanta ta sake wara hannayenta tana tunanin in ba yarinta ba yau rigimar Hasan a kan mota ne yake yi? Ta ce" Zan siya idan Allah ya hore min , na ringa saka ka a ciki ina yawatawa da kai da izinin ubangiji, wai Jaririna kana adu'ar da nace ka ringa yi kai da dan uwanka kuwa?" Sai a yanzu ya saki dan murmushin da ya saka fuskarsa wadatuwa da ni'imtacen ni'ima yalwataciya ya shiga kunce takalminsa yana kuma magana da yannayin dake nuni da ya sauko ya saku har ya fara wasa ya ce" Sosai fa, dan ranar har Liman ya so barina a masalaci ina ta fadawa Allah cewa, Ya Allah ka sa kasarmu ta samu lafiya da kwonciyar hankali mai dorewa, ya Allah ka saka tausayin talakawa a zukatan magabatanmu, ya Allah ka sa mu cika da kyau da imani, ya Allah ka ba mamana dukkan abinda take bukata duniya da kiyama .....danma ina manta sauran " Dariya ta yi tana jin zuciyarta ta saku da daurewar yaron ta mike tana sake kilace kulin da bata san ta yadda zata sayo man suyarsa ba ta dage labule sosai dan su samu yalwataciyar iskan itaciyar mangwaron dake basu sanyi tana fadin" Mantawa kake yi ko? Kulun ka fara da neman gafara, ka yi fatan gamawa da duniya lafiya, ka roki Allah ya kareka da dukan sharin abin ki, ka kuma fadawa Allah ya hanneka cin haram da cin zalin bawansa....., Sannan sai ka kawo sauran bukatun duniya domin........" Daga bayin da Useini ya fito da dan gajeran wandonsa da bokicin wankan da kwondon sosonsa ya ajiye yana fadin" Domin duniyar ba matabata bace, lahira ce mai dorewa, dukkan bawan da ya san da haka zai yi kokarin neman lahirarsa fiye da duniya, wayo cikina Mama wollaj furar nan ta Baban nan taki ta yi gardi da yawa na koshi na koshi sosai zan shiga barci kafin ki samo na daren, ni yau da san samune na ci taliya yar murde da dan waken fulawa da man ja mai gardi walahi........" Da ido suka raka shi ya shige ciki yana wani dan sauri kar ya bata jikinsa Daria ta yi tana girgiza kanta tana jin dadin yadda nacin maimaita masu kalamai masu mahinmanci ya sa yaren suke rikewa harma suke maimaita mata da zaran ta dauko maganar dan sake tunatar da su,ita dai tana fata Allah ya bata ikon ba y'ayan nan tarbiya gwargwadon iyawarta, bata san hakan da take yi shine daidai ko ba daidai ba? Bata taba haihuwa ba duda shekarunta a yanzun sun kusan kaiwa talatin, bata taba raino ba sai a kansu, tana kamanta kyakyawan halaya na iyayensu da alakarsu ta shakuwa ne a kan yaren, sannan tana tambayar taimako na yadda zatana saka su a hanya a wajen malamai da manyan datijan anguwar dan samun nagartacen fahimta tsakaninta da y'ayan y'ar uwar tata, sai kuma ta shiga tunanin takiya da dan waken da ya fada ya shige barci abinsa a lokacin da Hasan ke fadin" Kai acici ko? Ba za'a dafa din ba wannan furar da muka sha ta ishemu har gobe, kai kawai ka ci ka je bayi shine kwonciyar hankakinka? Mtsssssss!" Ita dai bata tofa masu ba domin yanzu ne zasu rikice wannan yace ta bi bayan wannan wannan yace ai shine mai gaskiya, sai kawai ta shuge cikin itama dan ta cenza suturarta ta samu wankan idan Hassan ya fito daga bayin da ya nufa Wannan kenan. ______________________________________ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣2️⃣* Barci suka samu wadatace har yama ta kusan yi domin har an fara kiraye kirayen sallar la'asar A nutse ta mike ta dauro alwallah ta dawo dakin tana tashinsu ta umarcesu zuwa Masallaci da nasihar banda fada a hanya kuma kar daya ya saki ya bar daya a baya su dawo tare Tana tsaye sai da ta ga fitarsu ta rataya sakata ta sake komawa saman nata dardumar ta kabarta sallah Bayan ta gama adu'ar da ta saba ita ta ci gaba da yiwa naci, ba zata taba manta daren da aka shigo mata gidan nan ba, ba zata taba manta wannan rana ba, Allah ya tsaya mata ba'a cin mata ba, ama tunda daga lokacin take taka tsantsan da komai da addu'a, ta tabata wanda ya shigo mata ya nemi lalubarta ba yaro karami bane, abinda ya fi damunta yanzun gamawar da zata yi ta leka wajen mai kanti amsar kayan da zata hadawa kulin cen kar ya lalace Buga kofar ta sakata mikewa ta zira hijabinta dogo sosai ta je ta bude masu tana murmushi hadi da fadin" Oyoyo biyuna" Hassan ne ya fara shigewa yana cika yana batsewa, da sauri ta dan leka sai kuma ta ja baya kadan tana fadin" Au baba direba kaine ashe ke tafe" Yar dariya ya yi yana fadin" Gaske Mai tsuntsaye ke hade min fuska daga cewa zasu dawo gidana da zama ina son na auri aminsu, yanzu Mai baban sunna nine Baba?" Shiru Amina ta yi daga zauren bata leko ba haka kuma bata amsa ba, ita abindama ya fi damunta Husain dake tare da shi yake kuma jin abinda ya fada din Dan murmushi ya kuma yi ya ce" Ba zaki ce komai ba maman biyu?" A hankali ta ajiye numfashi ta ce" Uhum" Daga wannan bata dake cewa komai ba, dama ya san ba nisa maganarsu ke yi ba, ko gidan ta je jefi jefi dan gudun kar Mai Shanu ya tako da kansa yace shi ya zo a yi zumuncin bata kula mutane irin a yi ta hira da dariyar nan, sama sama ake dan gaisawa ta yi gagawar shigewa, a gidan Mai Shanu da matarsa samarin ma'aikatan gidan na mararin mu'amalantar wannan cakwaikwai din budurwa mai yan samari, masu auren wasu na son aurenta wasu kuwa abinda ke cikin hijab dinta suke son yayewa su ga wacece ita a fili, sai dai kamun kanta da mutunta mutanenta ya sa ake shayin kawo mata maganar banza bale har a nemi haye mata fuska, a lokacin da aka diro mata Mai Shanu ne da kansa ya zuba polisawa aka kusan sati ana bincike ama ba'a gano wanda ya diro mata ba, kuma ta ki ta kaura gidan Mai Shanun kamar yadda ya so, ta gwamace mu'amalantar gidan da mai gidan da matarsa mai shekaru madaidaita da manyan mata masu aji yan siyasa na kafawa a jarida suka malaka watau shekara hamsin da hudu a duniya Kudin dake hannunsa ya ba Husain yana fadin" Dama Mai Shanu ne yace a kawo wannan" Kudin Husain ya shigo ya miko mata ta yi raf da hannunsa rike da kudin tana hararsa kadan dan irin yadda yake da wani hali daban da dan uwansa na shigewa mutane , shi kowa abokinsa ne ta ce" To ama baba ai kudin watan da ta bada na Waina ba karewa suka yi ba" Ya ce" Eh sai da yace ta yiwu kice hala, yace ace maki a nan dubu goma kudin makarantar biyu ne, dubu biyar ki yi kudin adaidaita ki yi kokarin ki yi anfani da sauran yana so ki yiwa wainar hatsin nan miya ta gargajiya inaga dai ga dukkan alamu za'a samu ziyarar jikansa ne " Kai ta gyada kamar yana kallonta sai kuma ta amsa shi ta juya tana sakawa gidan sakata ba tare da ta bashi damar shiga gidanta ba Da dan gagawa take kimtsawa bayan ta gama yin wanka da rubuta dukkan abubuwan da tsle da bukata, sai kuma ta zauna tana tunanin inda ya dace ta je ta samo kwanuka masu sauki da kuma sauran kayan miyar da a yanzu ba zata iya samu ba gashi wainar tuyar asusuba take yi ta mika masu da sasafe Hannayen yarenta ta riko suka fito sunna tafia bayan ta rufe gidan da ky dinta Mijin Inar saude ne ya tsaya a gabansu da adaidaitarsa sabuwa dal sai walwali take yi ya leko kansa yana fadin" Uman biyu ce da kanta da yamacin nan? Sai ina ku shige mu je" Dan murmushi ta yi ta ce" Aban Saudat mune, ni da kaina ban san ina zan samu siyayata ba na dai fito na san ba zamu rasa ba idan mun shiga ciki sosai wajen bariki" "Me kike son siya ne?" Ya fada bayan sun shiga yana kunna adaidaitar hadi da wanata kadan Amina ta ce" Ina so na yi siyayar abubuwan da zan yi miyar gargajiya harma da kwano idan da hali" Dan jim ya yi sai kuma ya ce" Ni kuwa na san inda zan kaiki, mu je Rahusa gaba daya abinda kike so zaki samu da rahusa a shagon" Ita dai bata ce komai ba, hasalima bata dan inane Rahusa ba sai kawai ta yi shiru a bayan motar adaidaitar ya ja su ya tafi Sun yi tafia mai dan tsayi gaskiya , sunna karasowa ta kalli sunnan wajen ta kalle shi ta ce" Kayan miya fa nace Aban Saudat?" Daria ya yi ya ce" Kwarai kuwa, ai idan kika shiga nan babu ce kawai babu, komai kuma da layinsa da masu kula da layin, ki je ki gani da idannuwanki " Kai ta gyada a ranta tana ayana'" Masha Allah mutane sunna da hikimar nema, ama a wannan waje da tun daga nan zaka iya hango bayan ACn dake jejefe ace wai kayan miya ke ciki sunna shan sanyin? Su kayan miya an ci gaba" A hankali suke tafia, tunda ta shigo wajen ta karanta layin abinda take nema ta dauki hanyar ta nemi shagalta da kalle kalle da mamakin kayayakin dake cike a wajen Lalle babu ce kawai babu, harta da albasa sai da ta ga kala uku , dadawa ta kasa kasa, kai harta da atarugu gashi a kilace a wajensa, gaba daya sai ta shagalta tgana tura abin tana karanta kudin abubuwan tana dauka a hankali har ta gama siyayar ta koma zagayen kwanonin ta shiga bi tana karanta kudadensu tana zarro ido da mamakin yanzu wani fa sai ya siyi wannan kwanon mai kudin gadon budurwa na aure ya zuba abinci ko? Har ta gangaro wajen kannanun masu kannanun kudi tana karantawa tana waiga manyan ta jinjina kai tace gaskiyane, da bambanci ko a kallo, tana yi ne ba tare da ta kula da kowa ba, koda yake babu wanda ya damu da wani, daidaikun matan nema wata kan alli skin dinta a fuzge ta sake kallonta a fuzge ba tare da ta kureta da kallo ba a ranta ta ayana masha Allah, bata taba gannin black beauty mai lalausan kyau irin wannan ba, bakinta mai birgewa ne da shiga ido sosai, du kuwa irin yadda ya ciza haka yske da shiga ido da birgewa Sai da ta dauki kwano daya da miya tana duba kudinsu gabanta ya fadi ta juyo da sauri bayanta dan son gannin yarenta Wayam din da ta gani ya sakata sake wara idannuwanta tana dubawa cikin mutanen dake bangaren kwanonin ko sunna cikin su? Ama wayam babu su babu alamunsu Da sauri ta juyo kurar ta shiga bin bayanta hanyar da ta biyoa hankali tana furta" Fadeel? Farid? Hasan? Husain?" Rashin gannin alamunsu ko mai kama da su jikinta ya fara rawa, lokaci daya ta nemi rikicewa tamkar ba ita ba, bata taba jin tashin hankali irin na wannan ba bayan rasuwar iyayenta, kai ko halin da kanwarta ke ciki bai taba daga mata hankali irin wannan ba A hanzarce ta shiga tura kurar da dan gudu gudu sannan ta kara ware muryarta tana kiran sunnayensu Da karfi ta bangaji kurar wani mutumen da ya fito yana tura tasa kurar shima , mutumen ba yaro bane gaskiya baban mutun ne kuma kasancewar tasa kurar abinda ke ciki ba wani bane sai batirin da ya zo siya da abin gyaran gashin maza kurarsa ta kifa a wajen lokaci daya ta dafe bakinta da hannayenta ta fashe da kuka tana juyawa ta saki dayan hannun nata ta dora saman kanta da da dan karfi ta shiga fadin" Wayo na shiga uku kardai an sace min y'ayana? Wayo Allahna na shigo nan da y'ayana basa yin nisa da ni yanzu kuma basa tare da ni! Hasan? Husain!?" Ma'aikatan da suka kwashe kayan suka riko mata kurarta ne macen ta karaso tana kamota tana fadin" Calm down Madame, y'ayanki ba zasu bace ba akoy CCTV ta ko'ina a nan mu je cen baban dakin kusa da office din oga a hasko su na tabata sunna cikin nan sunna yawonsu ki daina kuka ba'a satar yara a nan" Ita dai bata daina kukan ba, haka kuma bata gamsu da kowa a wajen ba, da sauri take bin matar tana riko fari kal din hijab dinta da ya karra haska hasken duhun fatarta suka zo shiga wajenma abin kallo ne , watau wajen sai ka tsaya nanma an cajeka da abin nan na caje mutun sannan sai an maka daukan zafin zazabin wannan cuta ta zamani mai taken covid 19 Du ta kagauta, bata taba jin tana iya zma terrorist ba irin na yau, a cen kasan zuciyarta babu irin abinda shedan la'anane baya kitsa mata, ciki harda idan har dauke mata ya'ya aka yi ta tabata mai wajen nan ne ita kuwa da hannunta zata bankawa wajen nan wuta kowa ya kone, domin ta san wannan din ba abokin gabar gwamnati bane! Sunna shiha wani launin kanshi da sanyin daban da na baban filin sana'ar ya buso su, ama ita Amina sam bata ji shi ba, matatakala suka kama hawa sai da suka yi hawa biyu sannan suka shiga Lift ya hauda su hawa na nawa bata sani ba ita dai ta ga an bude nan da nan sun fito Yan tafia kadan ce suka yi yanzun suka ido mamakeken ofice din dake dauke da na'urorin da ma'aikata manya manyan masu ilimin dake kula da aiki da na'urorin wajen Sunna shiha kunnayenta suka ringa jiyo mata muryarsa da gura gura watau Husain yana fadin" To kai Hasan tsakani da Allah kaima baka ji ya birgeka ba biscuit din cen? Kuma fa ka ga yinwar yama nake ji, ni walahi dama sauran suka bani na cinye dan na san mama zata biya idan ta zo!" Hasan da haushi ya gama cika shi na maganar da matar dake tsayen cen ta fada a kansu cewa barayi ne su ko? Sun shigo ne da wa? Wa ya bari yara kananu suka shigo su yiwa mutane sata? Yau sai ta ga iyayensu sun biya kudin biscuit din nan gobema sa saki yara sunna masu barna a waje ya ce" Ka yiwa mutane shiru! Ba zaka ci biscuit din ba! Kai baka tunanin inda Mama take ne? " " Fadeel" ta fada a raunane tana fashewa da wani kukan da ya fito daga zuciyarta hade da dariya tamkkar wata tabarariyar yarinya lokaci daya fuskar yaren da take boyewa ta bayana a tatare da ita ta duka kasa sosai suka zo suka fada jikinta karfin soyaya da shaukin ganninsu ya debeta yana ta rungumarsu tana kukan hadi da fadim" Ashe ba'a sace ku ba? Ashe kunna nan? Me yasa kuka fita a bayana? Ina kuka je? Wa ya kawo ku nan?" Muryar matar ne fuskarta a hade tana tsaye cikin shiga ta sweet bakake irin uniform din du wani baban mahaukacin wajen mai dogon wando ne da farar riga daga ciki cikin yaren turanci ta waiga tana kiran wanda take gannin zai fasarawa wannan mai shige da village girl din ta ce" Wannan yaron aka kama yana satar kayan kwalam da makulashe yana budewa yana ci, irinsu ne ke zuwa su yiwa mutane barna a masana'anta, muna bukatar ki sadamu da iyayensu dan su biya barnar da ya yi sannan mu yanka masu kashedin kar su kuma zuwa da yara mararsa ji masu dauke dauke wajen nan, idan sun zo da su su tsaya iya park da su ba sai sun shigo nan ba!" Tunda ta fara maganar take kallonta, a hankali ta juya wajen yaron da aka nuna, watau Husain yana tsaye sai turo baki yake yi, Hasan kuwa yana hararar matar kamar zai fashe dan takaici da jin haushi A hankali kunanyenta ke jiyo mata fasarar da saurayin ke bata ama yana kiyaye mugwayan kalaman da matar ta fada kamar irin su kiran Husain da barawo da ta yi, da sauransu ya dai bata maganar a dunkule ne cewa yaron laifi ya yi ba'a bude abu a ci gashi yau oga na nan basa son abinda zai kawo hankalinsa kansu na rashin kula da wani abin Idannuwanta ta sake zubawa mutumen a hankali ta ce" Ka tabata haka tace ka ce min?" Sake kallonta ya yi,bama kamar lebenta dake dauke da kalar kasa kuma a kallonsuma sai kyalin laushi suke yi da fari tasss din idannuwanta masu dauke da siririn kwali zuwa hijabinta da ba zai iya fadin sunnansa ba gaskiy har zuwa takalmin dake kafarta dan soso da kuma irin na kafafuwan yaren wanda ya tabata wannan shiga ce ta saka Madame yanke mata hukuncin bata fa ilimin boko harma ta mata kallon talaka futuk da sauransu dai irin na wasu masu kudin da suka raina talaka daga kallon idannuwa suke ganne kai din su ya su ne ko kuma mu ya mu ne, ta haka zasu yanke hukuncin abinda ya dace da kai su yi maka ya sake gyada kansa zai maimaita mata matar da haushi haushi ta daki table din tana rankwafawa ta janye hannun Husain da ya juya zai dauko biscuit din ya nunawa mamansa cewa ba fa sata ya yi ba wannan ne kawai ya bude ya dauki daya shine aka kama su aka ce ina iyayensu aka yi ta nemanta wajen kayan miya ba'a ganta ba shine aka ce karya suke yi su kadai suka shigo, masu tsaron kofa suka ce aa ba su kadai suka shigo ba da mamansu ama aka ki yarda aka kawo su nan, tunda aka kawo su matar nan tale fada tana zaginsu da barayi, sai dai bata bari ya fadan ba ta ture shi da tsawa ta ce" Ka fadawa wannan bagidajiyar ta kira min uwar yaren ko ubansu na dalamesu su bani waje tun kafin sir ya leko ya ji karnin da Yaren nan suke yi da ganninsu a wajen nan ransa ya bace! Yaron nan da gani barawon anguwa ne!" 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣3️⃣* "please pull yourself together" Amina ta fada a sanyaye tana kallonta tana ta dane guguwar bacin ran da take tsoron fashewarta a irin wannan lokacin Dagowa ta yi ta karra daukota da kallo ta watsar, yin turancinta ba shine abinda zai sa ta sasauta mata ba , ta tabata turancin an koye shi ne a boyi boyi ko a titi , watau turancin tsakiyar titi ba na makaranta ba, dan haka ta dubeta ido cikin ido ta ce" Oh kennan kina gane abinda nake fada, ohk ki yi gagawar aiwatar da abinda na fada tun kafin lokacin zuwa sallar oga ya yi ya sameku a wajen nan!" Amina ta saki hannun Hasan ta matso daf da matar ido cikin ido ta dubeta sosai ta ce" Idan ban aiwatar ba fa?" Matar ta kalleta da mamaki, ta kalli mutanen da suka dan fara kawo hankalinsu kansu ta dan matsa dan bata so jikinsu ya hadu ta ce" Ke, ki matsa min kadan mana baki san ana fama da cutar covid bane? Idan kika ki kuma sai ki tafi ki barsu a nan na mika su hannun masu horar da barayi!" Da karfi Amina ta janyo atishawar karya ta maka mata sannan ta ce " Bismillah ki mika mu gaba dayanmu wajen masu horon tunda azalumai ne ku!" Hankalinta tashe take goge fuskarta da tissu tana fadin maza a kira mata security service! Jin haka ya kara tunzura Amina ita kuma ta shiga ihun wanda ake gudun ta gannin take son gani, da karfi ta ce" ba kina tsoron kar hankalinsa ya karkato wajenki ba? Shine zaki wulakantamu ki kirayi y'ayana barayi? Na san ke da gani baki san menene yaro ba baki san ciwonsu ba tunda ga dukkan alamu ko mage bakya ciyarwa! Na tabata shi din idan har datijon arziki ne zai maki fadan kira min yayana da sunnan barayi da kika yi!" A haukace Amina da nake yiwa kallon ko dan yatsana na saka mata a bakinta ba zata taba cizawa ba ta shiga watsar da dukkan abinda hannunta ya kai ta nemi haukacewa a wannan waje har daidai lokacin da secirity biyu suka shigo mata da sauri suka nufota daya ta samu ta damketa sai dai juyin da ta yi da ita ta kubce mata har ta nemi yin taga taga , hakan da suka gani ya daka dayar janyo bindigar teaser dinta ta nemi kashe gaban jikin Amina a lokacin da ta danna zata dora mata shi a lokacin Husain ya gantsa mata cizo a kafarta yana kukan kokowar da ake yi da mamansa , Hasan kuwa yana tsaye wajen mutumen nan da yaren turancin dake harshensa wanda su dukansu sun yi mamakin yaron dama haka yake da turanci a bakinsa yana fadin ya hannasu taba mamansa shima yana daf da fashewa da kukan da idan ya fara ta yiwu yin shirunsa da hakurinsa sai ko zuwa gobe aka danna baban office din da ogan wajen ke ciki da bakonsa da kuma likitansa da ya zo bashi magani domin a yau ranar da ya bi sosai ta bale masa habo har sai da ya yi kiran likitan dole Docter Mansur , likitansa kuma daya daga cikin abokinsa ne ya ga za'a jonawa yarinyar nan abin nan dake saka mutun yin bori a kasa kamar dan jaki kafin gaba daya jikinsa ya mace har fitsari ake saki fa da sauri yana fadin" stop that immediately!" Da sauri ta dakata tana kallonsa hadi da dan ja baya domin babu wanda bai san waye shi a wajen ba, da sauri ya dan karaso yana fadin" Subahanalah, me yake faruwa haka a wajen nan , hey boys me yasa kuke kuka? Hey saketa mana, ki saketa menene haka?" Sai kuma ya juya wajen babar mai kula da harkar cctv din ya shiga tambayarta abinda yake faruwa Kafin ta bashi amsar da zata gamsar da shi Amina dake share idannuwanta da suka cika da kwalla tana tare hijab dinta da aka yaga mata ta dube shi muryarta a shake ta ce" Dan girman Allah ina son gannin mai wajen nan, na yi rantsuwar ganninsa a yau kar kafars ta kamani, idan har ka san inda yake ko kana iya min iso ka taimaka min na ganshi" Kallonsa Mansur yake yi sannan ya dake kallon yaren dake kuka sunna rike hijabinta , sunnan da suke kiranta da shi Mama ya saka shi sake kallonta kafan sai kuma ya juya wajen da aka yi cirko cirko, a dan hade kadan ya badu umarnin kowa ya koma bakin aikinsa, sai kuma ya dake dubanta a hankali ya ce" Ina fata lafiya? Domin bashi da lafiya ne" Amina ta hadiyi yawu dake makogwaronta a hankali ta furta" Lafiya lau" Kofar office din ya nuna mata sannan ya juya wajen ma'aikatan da wace ke son nuna masa bai dace ta shiga haka kanta tsaye ba, bata da damar ganninsa kai tsaye haka bale ba abin kirki ne zai kaita ba , zuwa ne zata yi ta masa rashin kunya may be fiye da haka, sa sauri ya juyo dan idan har maganar cewa rashin kunya ne zata shiga ta yi a office din cen gwara ta zo ta yi wasan kurar da suke yi da kowa a wajen nan ciki kuwa harda shi, domin idan har wata magana marar dadi ta faru a cikin cen daga bakinta bai san me zai faru ba, du inda kake neman dan zafin kai mai tsutsotsin kai idan ka zo kansa ka ja ka tsaya ka dasa aya Sai dai ya makaro, bayanta kawai ya gani d ƴaƴanta dake biye da ita sun kutsa cikin office din Juyowa ya yi dafe da gaban goshinsa ya rasa abinda zai ce, sai dai ba zai bar wajen ba sai ya ga abinda zai faru dan baya so a samu matsala ya barsu da rigimarsa su kadai Da karfi ta bude wajen sannan ta kutsa kanta da salamar da ta zamto tarbiyar bakinta ta shiga baza ido dan ta ga abinda ta shigo nema watau mai wajen A hankali ya dago lumsasun idannuwansa ya sauke saman kanta da ƴaƴanta dake ta faman rike gefe da gefen hijabinta, tunda ya mike dan takawa bakin da ya yi da sauri ya dawo sanadiyar ihun kukanta, kansa tunda ya sarra yake tare hancinsa dan yana gudun wani habon ya same shi Wayar da yake yi bai katse ba haka kuma bai daina kallonta ba da yarenta dake kallonsa suma Da haushi ta sake kureshi da kallon raini, a ganninta idannba wulakanci irin na y'ayan masu kudi ba ta yaya za'a maka salama kana kallon mutane ka kasa koda amsa amincin da aka nema maka a wajen ubangijinka? Baki ta tabe ta ce" Ban san ko kana jin hausa ba fan saurayi? Ama dan Allah mahaifinka ko mai gidanka nake son gani, watau mai kampanin nan! " Kallon da yake mata da kuma dan juyar da kansa da ya yi ya waiwaiga hagu da damansa ya sakata bi itama da kallo, sai ta sake dubansa ta shiga tunanin ko kurma ne? Da wani bacin ran ta budi baki ta ce" Bawan Allah shin kai kurma ne? Ko kana daya daga cikin masu wulakanta mutun a wannan kampani? Koda yake kasancewarka a wannan kujerar ta yiwu kai din makusanci ne ga mai kampanin, ka fada masa cewa Allah ya halice shi, shi ya halice mu, ka fada masa cewa babu wanda ya san gobe sai Allah, idan da sanninsa ake wulakanci a karkashinsa Allah ya saka min wulakantani da aka yi har aka zagar min y'ayana!, Idan ba da sanninsa ake yi ba ya gagauta yin bincike ya tace ya rauraye! Wadannan din y'ayana ne! Yayana ne ! Ba bara.........." Idannuwanta ta rintse sai kuma ta bude ta dora da fadin" Ba barayi bane su, ina kafa kafa da abina, ina kuma fadawa Allah, yau koda sun iya hali irin na bera idan har an san ciwon haihuwa za'a kiyayi zaginsu da shi, idan kuma an san gobe ta Allah ce za'a kiyayi aibatasu da laifinsu na yanzu, domin laifin wani na iya kasancewa laifinsa na gobe!, Bai san me zai zama gobe ba, idan har shi din magidanci ne da ya san menene haihuwa to fa zai kiyaye ya saka tsari a tafiyarsa.....ka fada masa ni din uwa ce da hawayena ke zuba na ciwon wulakantamin y'ayana da aka yi, na san kai baka haifa ba bale ka sani dan girman Allah sak...................................." Dif ta dauke wuta a lokacin da ya mike daga cikin kujerar da ya lume ya tura kafafuwansa cen kasan tabel din office din , ashe irin zaman nan ne ya yi wanda ake tura kaffafuwa karkashin table a dafe kujerar, zama ne na masu tsayi ba gajeru ba gaskiya, shi yasa sam bata gane tsayinsa ba har sai da ya mike a yanzu Idan har ya mata magana a iffice din nan to fa takardun dake zube saman table dinma sun masa Wajen wayar tafi da gidanka ya nufa ya daga ya karra a kunnensa dannan ya shiga dadana numbobin da yake sin kira Cen kasan makoshinsa ya iya furta" EH " sannan ya ajiye ya kuma juyowa ya jinginar da bayansa jikin garun ya sake fuskantarta yana sauraronta Shiru ne ya dauki wajen, sosai shiru ana kallon kallo Kasa kasa Husain ya ce" Mama mu tafi kar ya zane mu " Hasan dake masa kallon da yake masu ne ya sake jan hijabinta yana fadin" Mama lets go please" Lebenta ta dantse cike da takaici, ta fa gane ba kurma bane tsagwaron wulakanci ne irin na yaren zamani, idan zata rantse ba zata yi kafara ba ta tabata wannan din ta girme shi nesa ba kusa ba, rashin kunya baya karewa a duniya! Juyawar ta yi, ba dan komai ba sai dan ta san ko menene uban gidansa ya jita!, Ta bar wajen ne dan ta kare mutuncinta, abinda ya so faruwa dazun ba zata so ya tabata a kanta a gaban ƴaƴanta ba, abin nan ta ji hirarsa a wajen yan school dinsu, tabas a dazu ta tsorata da ta ga za'a dasa mata shi Gana take sunna biye da ita har suka idasa sauka Bata tsaya ta kula kowa ba sula nemi ficewa a baban filin kampanin har an fara kiraye kirayen sallar magariba "Asalamu alaikum Hajia" muryar wanda ya kawo mata agaji a dazu ta daki dodon kunnenta da yannayi na ja baya ba matsewar waje ba Juyowa ta yi sai ta ga daya daga cikin ma'aikacin wajen rike da ledoji jigi jigi kusa da likitan A tausashe sosai ya furta" ki yi hakuri na san ke matar aure ce, ba wani abu bane dama dan na tambaya ne Ina fata ya saurareki?" Amina ta juyar da kanta tana shaƙar iskar magariba dake hurowa a sanyaye ta ce" Ban samu ganninsa ba, sia dansa, na fadawa ɗan nasa sakon na san zai sanar masa" Dan jim ya yi , sai kuma ya ce" Dansa kuma?" Amina ta gyada masa kai tana dubansa A hankali ya ce" Ai shine mai wajen fa, shi daya muka baro a ciki" Sai da ta saki baki da mamaki, ta waiga ta sake waigawa ta kuma kallonsa, ama sai ta barawa kanta abinda ya bata mamakin a zuciyarta , karshema sai zuba ido tana kallon yadda yake ta kokarin sai Hasan ya bashi hannu ama ina, a murtuke fuskar nan du inda rigima take ta tatare a saman fuskarsa, Husaini ne ya sake sosai da shi yana amsa tambayarsa, sai kuma ta juya ta fice gannin Aban saudat ashe dai bai tafin ba ta karasa tana kawar da fuskarta gannin ya fito a adaidaitar yana tambayar lafiya kamar wace ta yi kuka? Gannin ana miko masa ledojin ta juyo da mamaki tana fadin" Yaya kuke gannin salon zai je? Yaya kuke hangen cakwakiyar lamarin? Ku zo mu je sisters🥰🥰🥰🥰😍😍😍😍 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Wa'inda suke da matsala da harkar banki zasu iya turo kati ta numberna, ko su yi pos in sha Allah, kuma a kan number nawa kamar haka 93811618..... Sai kun zo Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣4️⃣* Da mamaki a saman fuskarta ta ce" Aa ba namu bane wannan fa" Mutumen nan dai ne rike da hannun Husaini dan nesa da su kadan yana fuskantar Aban saudat aa tunaninsa ko mai gidanta ne ya ce" Asalamu alaikum, dan Allah na biyo bayansu dan na karra bada hakuri, sannan ku yi hakuri ku amshi kayan nan, an samu matsala ne na rashin fahimta in sha Allah hakan ba zata kuma faruwa ba" Tsayen da take kallon bayaninsu take yi da mamakin ko menene abinda ya sa wannan mutumen biyosu mai daraja ne, shi din da kansa mai tausayi ne mutumen, a sanyaye ta girgiza kanta ta ce" Aban saudat ba zan amshi kayan nan ba, ga dai kudin a irga abinda suka kama sai a cire harda na biscuit din da ya ci" A nutse ya ce" Ama ai Aban aboki yace ki amsa ki yi hakuri ki amsa " Husain da sauri ya kalleshi yana fadin" Aa fa, ba abanmu bane wannan, akace abanmu ya rasu ko Mama?" Shiru ta yi tana kallon bakin Husaini, yaron ba dai surutu ba , kuma ba rashin kwaba bace haka Allah ya halice shi da saurin sabo da shegen surutu Masha Allah "Ay sorry ai na zata abanku ne , ama ki menene a dai yi hakuri, ni na kasa hakura ne dan na ga dan uwan aboki sai huci yake yi, " Gannin baban mutun ba wani karamin saurayi ba yana ta masu magiya a kan abinda ba shi ya bata ba ya sakata dan rage tsayinta kadan ta yi masa godiya sannan ta shige adaidaitar ta jinginar da kanta a jikin abin adaidaitar ta yi ta lumshe idannuwanta, a haka take jin magangannunsu har ta ji ya tada babur din sun dauki hanya Ana fitowa daga masalaci sunna karasowa kofar gidansu A daidai lokacin ne matarsa watau innar saudat ta fito zubar da ruwan wankin da ta yi, kasancewr anguwar ba wai mai duhu ce cen ba ya sa idannuwanta duka sauka a kan mijinta dake sauko da ledojin nan yana ajiyewa a kofar gidan Amina Baban abinda ya sakata sake zuba masu ido gannin Aminar na binsa da kudi tana magiya ama mijinta wanda ko tau naira dari da ashirin ce ya bara mata na cefanen safe da yama nata da ƴaƴansu yana nuna ba zai amshi kudin nan ba? Lalle yau abinfa take zargi ne zai tabata kennan? Juyawa ta yi wuuuuu ta shige ciki zuciyarta cike da sake saken irin yadda zata bullowa al'amarin Sunna shiga cikin gidan ta rufe ruf sannan ta bude baban dakin tana saka kayansu hadi da kunna wutar nepa da fatan samun wuta dan zafi take ji sosai Du da alwallah suka shigo suka shinfida abin sallah, itama ta fice dan dauro tata alwallar Tana zuwa ta shiga gabatar da sallarta a nutse, sai da ta gama sannan ta wuce ta bude kayan Macaronin da ta siyo masu ta dauko ta shige kicin dinta ta kunna fitilar kwai domin kicin din bata da fitila ta shiga dahuwar gagawa ta hade komai ta tsayar da ruwan miya ta koma dakin tana idasa fitar da abubuwan dake ciki Ido kawai ta zubawa garin kayan kwalam da makulashen da aka zuba a wata ledar shake, sai makaroni da shinkafa irin na leda masu tsadar nan kala daban daban a wasu ledojin shake summa wa'inda a sanninta dai ba ita ta saka a cikin kayansu ba Ajiyar zuciya ta sauke ta mayar gefe tana sake duban Husaini gannin sai kallon ledar kwalam da makulashen yake Bata bashi ba ta daure sosai ta ajiye gefe Da wuri wuri ta gama girkin lokaci daya tana gyaran kayan miyar da danyen naman da kifin da zata yi anfani da su , so take ta gyara su tun yau kar su kai gobe su cenza warinsu domin bata da freeza bale ta saka Juyewa ta yi a baban faranti ta ajiye masu karkashin karamar fankarsu da abin firfitu ta kama ruwan wanke hannu da na sha da yaren suka dibo ta ajiye Hannayensu suka wanke suka shiga cin abincin bayan sun yi adu'a Basu jima a kan cin abincin ba suka tatare ta kwashe komai da kanta ta darwaye abubuwan da suka yi amfani da shi da ruwan rijiyarsu mai kyan gaske sannan ta dawo ta zauna ta kirayi yaren Gabanta suka zauna su biyun, ta tsura masu ido irin yadda suke kama ita da kanta ta yannayin girman jikinsu da kuma kamanin idannuwansu kawai take bambance su A hankali ta ce" Waye ya baku izinin fita daga bayana bayan tafe muke tare da ku?" A tare suka kwashi magana wannan na cewa dan uwansa ne wannan na nuna dan uwansa Kausasa muryarta ta yi sosai ta ce" Ba zaku fadi gaskiya ba kennan?" Jiki a sanyaye Hasan ya ce shine, sai kuma Husainin shima ya ce shine, lokaci daya kuma sai Husainin ya dora kansa a gefen kafadar dan uwansa ya fashe da kukan da ya kusan sakata karaya harma ta rarasheshi bayan ta dauri aniyar yi masu fada da nasiha ne, koda zata yi rarashin ba yanzu ba, dan haka ta jure sosai tana kallonsa ta ce" Kai mike daga jikinsa kuma ka kama min bakinka ka yi min shiru! Yaya nace maku a kan abinda aka bakuma bale wanda kuka gani kuka dauka? Yaya na ce maku a kan haka?" Da sauri Husain ke rufe bakinsa dan kar ya kuma fashewa da kukan stlll yana son bada amsa ga kuka na hanna shi, dole Hassan ne ya ce" Kin ce ko bamu abu aka yi kar mu ci sai mun nuna maki, kin ce mu daina amsa bale idaan muka ga abu ko na waye kin ce kar mu yarda mu taba ko mu dandana , ba kyau, daukan abinda ba naka ba babu kyai, sata ne, sata kuwa kin ce haramun ne" A sanyaye Amina ta ce" Ba nice nace haramun bane Fadeel, Allah ne ya haramta sata, du wanda ya yi sata a hukuncin adinin musulunci ance a datse gundugwuilar hannunsa, " " Wayo Allahna hannuna, Mama walahi ni ba sata na yi ba, dauka na yi nace zaki biya shine na ji ina kwadayin abin na bude na diba kadan" Husain ya fada a raunane yana shirin kuma barke mata da kuka , abinka da wanda ya aikata laifin Ajiyar zuciya ta dauke tana fuskantarsa ta ce" Farid babu kyau, haramun ne, Allah ya haramta, ko me kake so a duniya ka fada min, in dai bai fi karfina ba in sha Allah zan yi maka shi, ka ji?" Kai yake gyadawa da sauri, hakama dan uwansa, Sai da ta tabatar sun gane fushinta a kan wannan lamari, sannan ta dawo nasiha a tausashe sai kuma ta saka suka yi salar isha'i suka kwonta Kamar yadda ta saba tunda ta salaci sallar asuba ta dora kaskon tuyarta a tsakar gidan ta shiga aikinta da murhu biyu da itace ba da gaz ba Safiya na yi aka ringa buga mata gidan daidai ta taso biyu ta sakasu yin wanka d shiryawa Zuwa ta yi ta tambayo waye, kafin ta bude Da fara'a suka gaisa ta yi baya ta bata hanya ta shigo hannunta rike da Saudat da ko ido bata wanke mata ba Kujera yar tsuguno ta mika mata tana mata murmushi ta koma ta ci gaba da toya wainar matar Mai shanu domin ta gama tashi tuni ta zuba a kwanon nan ta kilace Murmushi Innar Sauda ta yi tana fadin" Oh Amina ke kam jinninki ya hadu da mai gidan abanku, bayan kasa ta birni idoma bai yada ke ba, da ba dan Baba Mai shanu ya tsufa sosai ba ai da aurenki ya yi ya cencaneki sosai, ama yanzun idanma ya aureki anya zai iya da ke?" Amina ta dan katse zuba kulin ta kalleta da dan mamaki, sai kuma ta yi murmushi bata ce da ita kanzil ba ta ci gaba da zuba kulin wainar Haushi ne ya kamata a ranta tana ayana ' shegiya mai shegen taurin kan tsiya, maganarma ba zata yi min ba dan bakin hali!' Murmushi ta yi a bayane ta ce" Um, maza? Maza? Kin ga tunda na gama sallah na zo na tsaya nake jira ki gama ki bude dan na shigo na amshi wainar naj sadaka na ba yar nan, ki duba ki ga abanta a jiya naira ashirin daya da ya banu tun safe bai kuma waiwayarmu ba, wannan lamari na maza da me ya yi kama? Namiji ba kama gida, ba fara'a idan ya shigo gida bamu isa mu yi wata walwalar ba sai idan ya fice, shi kulun a babu yake, ko so yake na je wani wajen na samo mana ne?" Amina ta zuba masu wainar isashiya ta miko mata harda miyar da ta sha kayan hadi na gargajiya sai kanshi take a hankali ta ce" Allah shi kyauta" Maman sauda ta amsa tana ajiyewa gabansu da yin godiya ta ce" Ke kika san Allah shi kyauta, wai shine harda yin budurwa a cen bayan layi, ai nace ba damuwa ta kula shi idan har ya kawota sai mu ci idonmu baki daya" Amina ta yi murmushi tana idasa zubawa a kwanon Matar mai shanu ta kilace shima sannan ta zauna tana gadin miyar har ta daidaita ta zuba masu isashiya a dayan kwanon ta hade komai a cikin kwondon da take mika masu ta zubawa biyu suka zauna sunna karyawa sannan ta shige wanka Da ta fito ta shige ciki ta cenza tufafinta cikin shigar riga da sket na atampa ta zurmuka katon hijab dinta mai ruwan kasa har kasa mai hannuwa ta daka dan kwali sannan ta dake fitowa jin ana salama Ummu salma ce ta zo tambayar gyaran amarya , nan suka yi magana suka gama ta tafi harda bada rabin kudin Innar sauda kam kallonta kawai take yi, gata dai baka ce ita ama ko ita ta fita kyan gani, ita da kanta tana matukar kaunar kalar fatar Amina, ga shegen nutsuwa da dan uban miskilanci du yadda ka so ka daki cikinta ba zaka samu abin fada ba sai dai ka gaji ka hakura, Tare suka fito daga gidan na Amina ta rufe komai suka yi gaba neman abin hawan da zai mikasu gidan mai Shanu, da kallo ta raka su har suka bacewa ganninta, Tsaki ta ja a fili a ranta kuwa tana ayana' Yarinya karama ba miji ba komai aman ta gaje komai na anguwa, idan gyaran jiki ne ita, kitso ita, komai ita, kowa mutunci yake da ita! To walahi baki isa ki shiga gidana ba ki hanna min zaman lafiya da kwonciyar hankali da rawar gaban hantsi a gidana!' A hankali ta mikawa mai adaidaitar kudinsa tana kallon kofar baban get din da aka wangale ba'a rufe ba A nutse suke tafe yarenta na rike da wasu kayan itama tana rike da wasu suka wuce baban get din sula gaisa sosai da mai gadi sannan suka dauki bangaren Baba Mai Shanu Wani irin ja ta yi ta tsaya a lokacin da idannuwanta suka sauka a fuskar yaron nan na jiya wanda aka wulakantata a kampaninsa ta kai kara ya mayar da ita yar iska dan rainin wayo ya fito daga cikin wata galeliyar mota ya ja ya tsaya yaba karewa gidan kallo jikinsa sanye da dakakiyar shada ruwan sararin samaniya sai haska ido take fuskarsa daure yana kallon wani gayen dake masa hira yana ta nunawa yana dariya ama shi sai binsa da kallon nan na raini yake yi baya bashi amsa Mutuwar tsayen da ta yi na yan sekwani ne da sauri ta juya da nufin komawa Husain ya kalleta ya ce" Mama ina zamu je?" Daburcewa ta so yi sai kuma ta juyo gannin Baba direba ya taho da dan sauri hannunsa rike da wata jaka ya wuce su fuuuuuuuu yana sauri gaisuwarma sama sama ya iya yi mata ita A hankali ta ce" Baba ko dai yau Baban baya nan?" Baba direba ya ce" Yana nan yana ciki fa, jikansa ne ya zo yau ai ba kanta ki taho mana" "JIKANSA?" ta furta a saman lebenta, ta taho? Ta sake tambayar kanta, Abinsa ya faru a jiya ya dawo mata sak sak , irin abinda ya faru ya dawo mata, kwarai riketa da kokowar da take yi a kan idannuwansa ya koma ta kuma bishi ta dora daga inda ta tsaya A hankali ta rike kwondon da kyau a lokacin da ta ga ya juyo barin fa suke da nufin shigewa ciki Dan kallon second daya takk ya maka masu mai shige da harara ya dauke kansa ya shiga tatakawa ya shige ciki Da ido ta raka shi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce" 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣5️⃣* Da ido ta raka shi, kasa kasa ta ja tsakin jin haushi, sai kuma ta juyo kan yaran ta ce " Kumu je mu ba Saliss gayacen ya kai sakon Baba, yau bakine da shi ba zamu shiga mu dame shi ba" Gaba daya yaren basu so hakan ba, bama kamar Hasan, du miskilamcinsa da rashin son mutanensa sunna shiri sosai da Baba, koda yake baban ne datijo mai datako da iya mu'amalantar mutane kala daban daban, yakan zauna da Hasan ne da irin mood din da ya zo masa, idan yan hirar ne su taba kadan ana nasarwa, idan yan a zauna a kalli junnan ne sao su wuni a haka bai ce masa ufan ba, to shi da ya zauna da jikansama suka yi zaman lafiya bale hasan jariri, ga dai jikan nasa a yanzu ya kawo mizalin da ya dace ace ya ajiye iyali shima ya yi nasa gidan da mace zata dora tukunya ta masa sannu da zuwa idan ya dawo daga nema, ama sai gidan ba macen a ciki, shi gana dayama tale takensu da kakarsa ba wani dada yardarsa da kasa suka yi ba, ya dai zuba ido ne yana kallonsu Gaba daya sakon ta ba daya daga cikin yaren dake aiki a gidan wato Saliss suka yi tafiyarsu tare da yaren Salis ya nufi baban falon Mai Shanu ya yi salama sannan ya ja ya tsaya daga kofa, domin ya san yau madame na wajen ba zai so ya shige kansa tsaye ba ya samu matsala Mai Shanu dake zaune cikin sasaukar shiga ta hausa , lalausan yadi kansa sanye da hula ya sake waigowa kofar yana fadin" An amsa salama malan Salisu ka ja ka tsaya ka shigo mana?" Salis ya daga labule ya shiga da salama a bakinsa a karro na biyu ya karasa direcy gaban Mai Shanu yana kokarin dukawa da kayan dan ajiyewa wata murya mai cike da nutsuwa, furuci kasa kasa sosai, cike da cikaken aji da wayewa ta furta" Ka kai dining mana kar ka ajiye a nan" Mai Shanu ya dubeta sai kuma ya kalli Salis ya ce" Aa ya ajiye min a nan, wannan kamar kanshin Wainar maman biyu?" Salis ya ajiye din kansa a kasa sosai ya karra nutsuwa ya ce" Eh itace ta ajiye ta koma tace zata mika biyu makaranta ne" Dan jim ya yi sai kuma ya gyada kansa yana furta" ALLAH ya anfana, ya saka da alkhairi, ya yi mata albarka" Salis ya ringa amsawa sannan ya mike ya tafi Bayan fitarsa da kamar minti biyar Hajia ta kuma dagowa ta kalli mijinta a karro na hudu tun bayan maganar da ta yi ya take ko kallo bata ishe shi ba, ya wani kama yiwa yarinyar dake aikata aikin nan da kudin da yake tura mata godiya kamar wace ke ciyar da shi sadaka! Kanta ta cire ta maida kan Jikanta, abin kaunarta , farin cikin zuciyarta , abin alfaharinta taba cire gilas din karin ganninta hadi da ajiye jaridar hannunta ta ce" Cencenta ce ke nemanka ido rufe , ba kai bane ke nemanta *ABDUL RA'UF!*" Sau daya ya dago daga rubutun da yake yi a wani litafi ya sauke dubansa a kanta, sai kuma ya dauke dubansa ya maida cikin litafin ya sake dasa alkalaminsa ya dora daga inda ya tsaya Gefen da mijinta yake ta sake kallo, wannan karron abin ya taso mata daga cen kasan zuciyarta tana kallonsa ta ce" Ama ai sai ka yi masa magana ko Alkali?" Wainar da ya ciro ya dangwala miyar taushen ya sake kaiwa bakinsa, domin tuni ya fara karyawa da ita ya juyo inda take zaunen, Walwalin da take yi abin birgewa ne, ita din mace ce mai kwaliya, sam fatarta bata samun hutun rashin gyara, tun tana da jan sawunta da ya daukota ita din mai kwaliya ce, har yanzu da ta kawo shekaru hamsin da hudu a duniya ba zai ce ga wata macen da ta kaita iya saka kwali ba a idannuwansa, yyarintarta yake ganni ainun, a kanta ya gane bak'ar fata aba ce mai daraja da mahinmancin da ko ta zo tsufa idan da gyara sai shekaru sun yi mugun ja take nunawa, ita din ba farar mace bace, ama irin yadda ta iya daukan ado da gyara da ba kalar fatarta daraja ko farar fatar na mangarinta Da yawa masu shekarunta sun koma sun jabge, wasu tsabar lalaci da son jiki sun fake da sun tsufa ko kunshi sun daina yi, ama ita din wannan tasan da a yanzu shi tsufan ya masa zuwan gaske ita a danya sharat yake ganninta, baban damuwarsa idan ya kwonta dama shine ya bar wannan abokiyar rayuwa tasa mai wasu halayan da yake gannin hagu a tare da ita, giyar mulki , kaunar siyasa ba yau ba suka yiwa jinninta billin da ita da kanta bata fahimta ba!, Gatanan dai a zaune a kan siyasa sai ku haura sam ku fado wuyan kowa ya karye a huta, a yanzu haka rigimar da take kokarin janyowa a tsakaninta da jikan nata da ta san mutun ne mai zaune da ra'ayin kansa, wanda ya ki jinnin wani ya nemi yin iko da shi, shi yasa ya zama mutun mai ikon kansa da kansa ta hanyar kasancewa bos din kansa yake *NEMAN NA KANSA* da karfinsa da kuma guminsa ba tare da ya jira wani ya masa ba ko ya yi jira an bashi damar yi ba, shi din mutun ne da ya ki jinnin a ja shi a kasa a kan komai, shi yasa yake nema da karfinsa da kuma lokacinsa, wannan miskilin jikan nata take so ya tashi ya nemi takarar gwamnan garin nan, tana so ta bara masa wajen da take nema a cewarta aljihunta bashi da nauyin yin farfagandi, kuma bata da matasa a damarta , shine take so shi ya motsa ya bude aljihun wandonsa ya yi zuba na kudi sannan ya riko matasan dake tare da shi su hau wannan tsani mai nauyi da hatsarin gaske, dan kawai wannan din shine *Burinta!* Sai da ya taune ya hadiye ya yi dan murmushi yana fadin" Watau yarinyar nan Allah ya kara mata lafiya, a kulun abinda ke bani mamaki da wainarta bata konewa, bata yin yami, bata cika siga, idan kuwa ta rangada mata miyar taushe sai na ji du duniya babu miyar da ta kaita dadi, mahaifiyarta ta mata horon arziki, ita kam ta huta idan ta yi aure ba zasu samu matsala da miji ba wajen girki, mu kuma maza dama a kware wajen girkin kadaima ya wadatar" Wani irin tukuki ke turnikar zuciyarta tana kallonsa, lalle ta yarda bashi da kiyar kama mata a kan maganar nan, bayan ta san yaron na girmama maganarsa koda da salon wasa ya yita? Mikewa ta yi ta dauki jaridarya da gilas dinta ta maida a idannuwanta ta juya ta nufi ciki cikin takun nutsuwarta ba da fuuuuuu ba dan ranta ya baci, no, da salo irin na wayayiyar macen da ta gane idan ranta ya bace gwara ta yi shiru da ta daga muryarta ya zamto an samu mumunan furuci daga tsadafen bakinta ba! Da ido du suka rakata, sai kuma suka yi ido hudu shi da kakansa Goshinsa ya tatare sosai yana kallon kakan nasa , Dubansa ya maida wajen agogon dake bango ya duba ya sake juyowa wajen da yake ya ce" Sai yanzu kake karyawa bayan kana fama da ulcer?" Fuskarsa ya yatsina ya ce" Ka san kuwa tunda safe nake jin yinwar, har mafarkin wainar nan na yi, yau maman biyu ta yi rana shi yasa" Takardar ya mayar gefe gaba daya yana fuskantarsa , sai da ya gama ayana abinda zai fada masa a zuciyarsa sannan ya ce" Bana so,......" Ya yi shiru jin saukowa daga sama ya maida dubansa yana kallo, kakarsa ce ta fito cikin tsadaden shiri da abayarta mai walwali ga kanshinta dake sanar da zuwanta tun kafin ta iso Karasa saukowa ta yi daya daga cikin yan aikinta na biye da ita rike da jakarta ta tsaya tana kallon table din ta ce" Ki tatare breakfast din cen, a yi masa na rana, kar a cika mai sannan kar a saka masa magi da yaji a ciki, a dafa masa cuscus da miyar lambu......nd a tabatar an saka turaren wuta a ko'ina idan ya gama cin abincin" Cike da ladabi take amsata , sai da ta tabatar da cewa ta gane komai sannan ta sake juyowa barin da suke zaune Idannuwanta suka sarke da na jikanta, tarin damuwar dake tatare da ita ya fara karanta, sai kuma juyawar da ta yi ta wuce ba tare da ta ce da su komai na, uwa uba ko tambayar izinin fita bata yi ba a wajen mijinta ta kada ta yi tafiyarta ya saka shi rakata da kallo, sai kuma ya dawo da maganar da ya fara ya ce" Bana son kana zama har wannan lokacin baka karya ba, Waina, waina waina, na yi na yi na kawo ma'aikatan da suka kware wajen sarrafa waina su ringa sarafa maka ka kiya" Sosai jikan nasa ke saka shi a hali na kwonciyar hankali da farin ciki, uwa uba idan ya ga yana magana a kan abinda ya shafi lafiyarsa ko kwonciyar hankalinsa, tamkar wanda ya take shekara hamsin a duniya, rashin hayaniyarsa da tauna hharshensa wajen magana da matukar son girmansa na sakashi manta shekarunsa a duniya Murmushi ya yi masa ya ce" Babu mai wainar da zata fi Maman biyu iyawa a duniya, bayan wannan na yarda da tsaftarta ne ai" Ajiyar zuciya ya sauke ya ja bakinsa ya yi shiru yana kallon abincin da kuma irin cin fa kakansa ke yi Mai Shanu ya ce" A zuba maka ne?" A hankali ya girgiza kansa harda yatsina fuska, kwarai shi din mai matukar son abincin gargajiya ne, ama ba zai taba iya cin wanda bai yarda da shi ba! " Me yasa ba zaka yi mata biyaya ba ka shiga farfagandin da take da bukata?" Mai Shanu ya fada a tausashe bayan ya wanke hannunsa , ama bai sha ruwa ba , domin idan ya ci abinci baya shan ruwa a lokacin sanadiyar ulcer dinsa Yatsarsa ta tsakiya yake dannawa a hankali har sai da ta bada kara sau biyu sannan ya juyo gefensa a hankali ya ce" Saboda da na rintse ido ban ji ba dadin makanta" Mai Shanu ya girgiza kansa yana fadin" Ka bani a bude yadda zan fahimta" A tausashe, ba da yannayi na raini ba, ko isa, ko haikewa a kan maganar kakan nasa ya ce" Ita din misali ce a kan kalar rayuwar da ba zan so ta gabata a kaina da iyalina ba, ita din aya ce mai karfi da nake kokowa da ita dan burina ta farga ta zubar da dabi'un da ba adininta ba!" Mai shanu ya sake fuskantarsa ya ce" Wadine daga cikin dabi'un tawa matar ne baka so su zamto abin koyi a wajen naka iyalin?" Dan murmushi ya yi, domin ya fuskanci kakan nasa na son jan maganar ne kawai, ya gane komai ama sai takewa yake yi, yau hira yake ji sosai shine yake so ya yi ta jansa a kasa dan fin karfi, sai dai shi din kansa yana so yau Mai Shanu ya fahimci siyasa ba ra'ayinsa bace, ya yiwa matarsa magana ta barshi haka, idan maganar kudin ce zai zuba mata ta je ta gwada sa'arta, ama zai yi ta adu'ar kar Allah ya dafa mata a burin zamowarta gwamnar garin nan! A tausashe ya ce" Ni fa ba nufina matarka nada matsala ba Elhaji" "Aboki, ka yi maganarka sak, idanma iyalin nawa kake nufi da wata sirfar sai na baka amsa daidai da bayaninka, ai ka san baka kam ba tsami " mai Shanu ya fada shima yana murmushi Kafafuwansa ya tankwashe yana fuskantarsa ya ce" Bana tunanin zan iya jure wace Allah yace na kilace na bata kulawa fita yawon farfagandi dan ta tayani samun duniya koda babu izinina ba!, Zan so a wata ta yi fitar da bata fi uku ba dan sada zumunci da ta'aziya, bana tunanin zan iya fita na saurari maganar kowa da kuwar kowa dan na samo mana na gero , itama ta fita ta yi gogayar dan ta samo mana sunna ba! Na fi daukan haka a matsayin halaka da bacin sunna !, Damuwar ba zai yiwu na zama gwamna babu matar gwamna a gefena a jaridu da gidajen talabin ba, kowani kato zai kalleta kyauta harma ya aibatata, kowace katuwa zata nemi wulakantata dan kawai bata cikin tsarin wace ke birgeta! Matsalar kuwa itace ba'a gane shekaru na tafiya furfura na gama kai har sai ciwon ajali ya kama wanda ake tunanin stress ne kamar yadda aka saba jin dan damuwa na stress sai an tsinci kai a kabari!" Shiru ya yi yana kallon yannayin kakansa da gaba daya yaa cenza, duda irin karfin halin da yake yi dan ya nuna yana cikin nutsuwarsa , ama kana kallonsa zaka gane ya afka a hali na tunani, Kwarai ya so dakatawa haka, ko dan shima ya numfasa, sannan ya bar kakansa hakanan, sai dai bai dire abinda yake son sanarwar kakan nasa, ko yace tuntarwa, dan haka ya dora da fadin" Sai an tsinci ki a cikin kabari, daki matsatse mai duhu, wanda bin umarnin ubangiji ta hanyar bauta masa ne kadai zai sa ka samu wadatarsa da kuma haskensa, sai ka zo a panpanpan , watau biyu babu .....ukun lala, ba uwar ba ribar........me zai hanna k hadu da abokin *UKUBARKA* har a busa kaho ba?" Sake duban idannuwansa Mai Shanu ya yi, gaba daya maganar ratsashi take yi tamkar wanda bai san hakan ba, tunatarwar nan cikin hikima ta saka shi a halin rudu da karyewar zuciya A sanyaye ya ce" Tana sallah, tana azumi, na tabata ita din mai tsoron Allah ce, hali ne ya cenza a lokacin da ban yi aune ba, ni da kaina naa sake talafa mata dan samun farin cikinta da ci gabanta a rayuwa, arzikinta ya shiga, lokacinta ya shiga, lafiyarta ta shige, sosai an shiga fannin wasa da gobenta!, Kwarai ba haka ba nake hango tsufana, tsorona daya kar sai ta dawo wata rana ta tardo gawata bamu yi salama ba"................... A hankali ya saka hannunsa cikin na kakansa yana dan murzawa a lokacin da kakan nasa ke fadin" itafa ba rashin damuwa da ni bane matsalarta, kuma idan yau na daure fuska tana min biyaya, shi yasa nake saka ran koda kwana daya ya rage min a duniya na ganta ta dawo matar dakana, ta zubar da mulkin nan! Domin dama ni ba ra'ayina bane" Dan murmushi ya masa, bai amsa shi a kan wannan ba, har sai da ya kula ya saku da damuwar da ta shige shi farat daya sannan ya cika hannunsa ya sake komawa gefe ya dora da aikin da yake yi, wanda ya tanadeshi dama sai ya zo gaban Mai Shanu, domin ya fi shi sanni a wannan fannin sosai A hankali suke zantawa kan albarkar kiwon da ake yi wanda ya zuba masu kula masu ilimin abin da kuma yan mun gada, sosai suke zantawa kan shannin dake kim amsar abincin birni idan an sayo su daga jeji, a nan ya nuna masa cewa sunna iya sakinsu a baban filin wajen kiwon, su nisanta su da babura da mota da kwaramniyar bayan magariba, su yi kokarin rage masu hasken zamani na fitilu da sauransu , su barsu da hasken wata da kyalekyalin taurari, ya zamto sunna ji a jikinsu kamar a wajen da aka haifesu ne suka tashi, a hankali a hankali ake koya masu bakin lamuran birni sai ka ga sun saba daa sababin abubuwan sunna cin abinci sosai kuma basa ramewa da firgicewa Sosai sula zanta har sai da karfe goma sha dayan rana ta yi suka mike dan karra shiryawa su fita masalacin juma'a baba A cikin mot su biyu ne a baya, yanzun babu mai yiwa dan uwansa magana kowane na hailala a cen kasan zuciyarsa Sunna isawa suka tarar ana huduba dan haka suka ajiye carbi sunna sauraron hudubar har aka gama aka tayar da sallah suka yi suka gama A wajen sadakar da ya saba ta du ranar juma'a ta goma goma sababi kal kal yara sun zagaye shi, shi kuwa sai fara'a yake sosai yana basu sadakar nan cike da farin ciki har ya gama suka kuma shiga motar suka nufi gidan gona Sauka ya yi ya zagaya ya bude masa da kansa, ya kamo hannunsa ya fito da shi suka nufi wajen da suke hutawa da kuma hira da tsofafin dake zuwa su wuni tare Bayan ya gama gabatar masa da komai kasa kasa sosai ya ce" 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣6️⃣* Bayan ya gabtar masa da komai kasa kasa sosai ya ce " Ka hanneta yi min maganar siyasar nan, domin banna ra'ayi" Da ido ya raka shi da kallo domin bai tsaya ya ji amsarsa ba ya wuce ya nufi cen bangaren da zabi da su kaji dai da sauransu ke nasu kiwon cike sunna ta ihu irin kukansu ya tsaya ya harde hannayensa yana kallon yadda ake dauke kwaya kwayansu da irin kulawar da suke samu ____________________________________ Tunda Amina ta shigo gidan kanwar tata dukkan kuzari da farin cikin da ta riko na ƴaƴanta suke neman barinta sakamakon irin halin da ta samu kanwar tata a ciki Firdausi ta yi duhu sosai, ta rame, ga rashin fara'a dake damunta wace ta kasa boyewa du irin kokarin da take yi dan boyewar Tunda ta shigo ruwa wannan na rijiya da Allah ya basu kyauta Firdausi ta gagara tashi ta debo mata ta sha, hasalima hankalin kanwar tata na yawan duban kofar shigowa gaba daya ta kasa samun nutsuwa, ga cikin wata bakwai da ya nuna kansa sosai ya yi tirtsitsi sai rinjayarta yake yi, gaba daya ba nutsuwa a tare d Firdausi, kamar ba fido dinta ba Dan murmushin yake ta yi , ta ciro dubu biyun da ta kawo mata ta miko mata a sanyaye ta ce" Fido, dama jiya zuwa yau ne Allah ya kawo budi sosai, shine nace bara mu biyo mu kawo maki kya kara jarin kayan miyar da kike siyarwa a gida" Firdausi ta yi shiru tana kallon kudin, a sanyaye ta ce" Aunty ni ban kai maku talafi ba sai naku zan amshe? Aa gaskiya aunty ba zan amsa ba, babu kowa a wuyana da nake ciyarwa, iya bakina ko yayane ba zan rasa na sakawa bakin salatina ba" Amina ta girgiza kai tana fadin" Karbi mana, tunda kika ga na zo na kawo ai kin san muma mun samu ne, bale keda kike da wannan abu a gabanki ai sai da tanadi komai kankantar abin batarwar" Jiki a sanyaye Firdausi ta ce" Aunty yanzun bana siyar da kayan miyar fa, dama daidaiku ne ke zuwa siya irin wa'inda suka san halinsa suke da niyar talafa min, to gaba daya sai ya rikice mutun bai isa ya turo yaronsa amsar koda dadawa ne komai kankantar yaron , idan ya ci karro da dan mutane sai ya daka, nima na shiga uku kulun cikin fargaba da tashin hankali, kawai sai na daina siyarwar dan ba wani anfani" Ido Amina ta tsura mata, zuciyarta cike da damuwar wannan lamari, yanzun kayan miyarma ya salwantar mata da siyarwa? Ashe dole ta lalace har haka, dama da yar sana'ar ake samu ana kaiwa mai dan dadi baka, ta rasa ta inda zata bullowa al'amarin kanwar tata, ta ce ta je ta yi dinki ta koyi sana'ar dogaro da kai ya kafa kai da kasa ya kiya, ta nuna mata ta gwada siyar da awara ya kiya, ta ringa sana'ar kitso da gyara jiki domin itama ta iya nanma ya kiya, komai bawan Allahn nan idan an kawo na karuwar Firdausin sai ya kiya....wai sai ace kishi ne ke damunsa, wannan wani irin kishi ne bakin kishi? Yanzun dai ba'a kai ƴaƴan cikinta da ta haifa ba, ya yi masu katangar karfe wai hasan da husaini shekara shida shida a duniya yace sun zama samari su daina shigo masa gida, yanzu haka wannan rashin nutsuwar ta tabata tsoro take yi kar ya dawo ya tarda su a soron gidan da ta dakatar da su cewa tana zuwa, yaran kansu a yanzu idan ba ita ta kawo masu maganar Firdausin ba sun daina yi mata maganarta, shin yaya zai yi da haki da girman soyaya irin ta uwa da ƴaƴanta? Sam basa shiri a duniya , zata iya shiga gidansa ta fita yana nan basu gaisa ba, domin har akoy ranar da ya zageta ido da ido yace tana yawon banza ta ki fitar da miji baya son mu'amalarsu da matarsa, ita kuma tace sai ya dauki wuka ya yanka hannun matar ya tsiyaye jinninta dake gudu a jikinta ya cenza da wani, a ranar har ashariya ta kusa yanka masa dan bacin rai sai da Firdausin ta yi ta kuka da bataa hakuri ta hakura ta yi tafiyarta Amina ta sauke gauron numfashi ta ce"ki zauna waje daya mu yi magana, tsoro kike ji kar ya dawo ya tardo biyu a soro?" Firdausi ta zauna din tana jan numfashi ta ce" Aunty ai idan ya tardo sun ban san yaya zamu kwashe bane, kin sanshi da kulafirci da daukaka gaba da rigima" " Y'ayanki? Fido bakya missing dinsu? Bakya jin kamar zaki haukace dan rashinsu a gefenki? Bakya jin rashin dacewar hukuncinsa ? Ba zaki iya dakatar da shi ki nuna masa martabarsu da darajarsu ba? Shin bakya gudun shiga hakinsu?" Amina ta fada a sanyaye har idannuwanta na neman cika da kwala A hankali Firdausi ta dora kanta a kafadar Aminar kuka na kwace mata A kasa kasa sosai take kukan tana mai sake dora kanta a gefen kafadarta ta ce" Nakan wuni, na kwana da tunaninku, da matsananciyar kewarku baki daya, Aunty ina son su sosai fa, walahi ina son su, rikicin cenjin Rayuwar da na samu ne ke makani a kasa, Aunty bana iya tsalake maganarsa ko yi masa jayaya, ina ji ina gani ya haramtawa y'ayana shigowa gidansa bayan musulunci ya yi nuni ne idan D'a namiji ya balaga kana iya ware masa wajensa da sauran yayanka mata sannan ka saka ido sosai a kansu baki daya, shi din ko dan ba shi ya haifi nawa bane yake ki? Marayu ne.....yau da bani da ke yaya zan yi a rayuwa?" Sosai fushin dake zuciyar Amina yake narkewa yana komawa tarin tausayi da jinkai na yar uwarta A hankali ta ci gaba da dan bubuga bayanta a sanyaye ta ce" *KI YI MASA LADABI*, na tabata babu abinda yake dawamame a duniya dadi ko wahala, watarana zai cenza halayarsa ko Allah ya canza maki da wanda ya fi shi zama alkhairi" A hankali take amsata, Amina ta saka mata dubu biyun a hannunta ta ce" Ki adana wannan, du ranar da baki samu abinci ba ki yi kokari ki siya ki ci, in sha Allah zan dawo " A hankali Firdausi ta amsa ta mike ta boye tun tana zaunen sannan Amina ta tashi ta fito daga dan tsakuraren dakin Firdausin tana yi mata salama A hankali Firdausi ta ce" Aunty, dan Allah ki ce da su ina gaishe su, Allah ya yi masu albarka, ki ce masu kulun kulun ina yi masu addu'a sosai" Murmushi sosai Amina ta yi mata a sanyaye ta furta" Allah ya saka da alkhairi, zan sanar masu in sha Allah" Da wannan suka yi mata salama, basu hadu da mijinta ba sai a lokacin da suke tsayar da mai adaidaita sahu, ido cikin ido suka kalli junna da ita, ama sai ya cire kai tamkar ya ga wata abokiyar gabarsa Itama Aminar bata gaisheshi ko ta nuna ta sanshi ba, domin ta sani ne idan ta yi masa gaisuwarma da kyar ya amsa, koda ya amsa a kayade take zai ce da ita "Lafiya" yana cire kai, gaba yake yi da ita , yana jifanta cewa ta ki yin aure ta zauna zaman banza har tana neman tsofewa ta fake da nufin bata samu miji ba, to wa zai fito ya dauki ya'yan wani ya rike sannan ya kwashi sauran karti? Wannan kalamai nasa suka saka ta daina gannin mutuncinsa, dama mutuncin nasa kadan ne take gani domin mutun mai irin halayar mijin Fido sam baya cikin tsarin wanda zata iya yin zaman minti uku da shi a waje daya ba a rayuwa Firdausi dake gida zaune bayan tafiyar yar uwarta ta yi shiru ta zubawa waje daya ido zuciyarta cike da tunanin rayuwa da aune aune da sake sake ta yi firgigita tana mikewa tsaye da sauri sanadiyar jin rufe gidan mijinta ta hanyar saka sakata da komai sannan ya shigo gidan fuskarsa a hade sosai yana karewa ko'ina kallo da son gane abinda yake zargi Gannin bai fahimci komai ba ya fuskanceta fuskar nan a hade tana masa sannu da zuwa hadi da miko masa ruwan da ta ja a rijiya ta tanadar masa tunda ta gama dafa dukan taliya yar murdi ta adana Ruwan ya bi da tsinanen kallo ya sake dubanta fuskar nan a hade ya ce" Na tabatama ta zo gidan nan , domin na hadu da ita a bakin layi, abinda nake son sani shine ina fata bata shigo min gidana da kartin maza ba, kuma baki dauki ruwan gidana tsaftatace kika bata ba?" Kai Firdausi ta sada, zuciyarta na dokawa sosai, ciwon magangannunsa na ratsa zuciyarta, ita din ba mutun mai fitina bace, du irin sanyin Amina ta dameta ta shanye, ama duda haka wani lokacin sai ta ji tamkar asararen zama take yi da mai gidanta, sam bai san darajarta ba, bata tunanin gabar da yake yi da danginta dangin nata ya tsana, ta fi tunanin matsalar a kanta ne, itace damuwarsa, itace abikiyar gabarsa, takan yi tunanin da ace tafiyarsu bata dauki salon tsarce tsarcen yawu da tashin zuciya ba, da ta nema masa sauki itama ta samawa kanta , wani lokacin tana yin biyayar ne dan tsoro da tsoron Allah ba dan tana ji a ranta ya cencenci ta masa biyayar ba! A sanyaya ta ce" Sun zo, ama bata shigo da biyu ba, kuma ko ruwan gidanka ban bata ba" Daga haka ta juya ta shige cikin daki ta dauki carbinta ta zauna gefen gadonta ta shiga hailala da salatin annabi, domin shine kadai abinda take lazumta ta ji sauki a zuciyarta dangane da zamanta da mai gidanta Baki ya tabe ya daura alwallah yana ta mita da fadace fadacen shi da ya isa da gidansa da Amina ta daina shigo masa gida! Ita dai daga wannan bata ce masa ufan ba, sai da dare ya tsala ya sake biyota saman jigatacen gadonta ya yi mata turmusar da baya tsalake rana, kulun fa wannan sai ya biya shi baya tsalaken rana, da yinwa ko ciki koshe, da yardarta ko babu yardarta , idan ya tashi zuwa zai zo ne babu dan aike zai turmusa da dukkan karfinsa ya mike ya barta da wahalarta! Bayan kwana biyu Kasancewar amaryar gidan aunty Rukaya yarinya ce mai dan haske sai take yi mata gyaran hadin kurkum da zuma, sai kuma hadin dilkar tubawa tsumamiya wace a kwana na biyun nan da ta fara yi mata aikin fatar yarinyar har wani kyali take yi tsabar gyaran na kamata (gaba daya hadin zai zo da zarar na rufe free page) Yau gashin kanta ta raba gida hudu ta yi hadin gyaran gashi kamar haka : Nescafé, Kwai, madara, man shanu: ta kwaba shi sosai ta ringa bi daya bayan daya tana shafa mata har ya gama hade kan ta sakata saka leda sannan ta daura dan kwalinta a sama da zumar ba za'a wanke ba sai nan da kwana biyu domin yarinyar na fashin sallah ne, ta sake jadada mata kar ta damu da karnin kwan, idan bata kunce bama ba zata ji ba, domin turaran wutar da take yi mata kadai ya isa ya hanna karnin ya dameta Kamar yadda ta saba tataka mata , hakan ce ta faru yauma har kan kwanar gidansu sannan ta ja ta tsaya tana hangenta har ta shige gidansu Juyowa ta yi da zumar komawa gida, da sauri ta ja baya kadan tana kallon Muctar mai kanti dake tsaye daf da ita sosai Hade fuskarta ta yi kadan domin ta tsorata sosai bata san da mutun kusa da ita har haka ba tana sake dan matsawa hadi da fadin" Aa, Malan muctar kaine tsaye kusana har haka?" Muctar ya yi murmushi yana kallonta gannin tana sake jan kasan hijan dinta tana kokarin rufe fuskarta ya ce" Ba dole na ringa dakon hanyar fitowarko ba tunda na je zance sau uku kina kin fitowa? Amina shin kin dauka da wasa nake ne ko ba zaki iya auren talaka irina ba?" Kanta na kallon kasa take tunanin amsar da ta dace ta bashi, ita ko daya ba maganar talaka ko mai kudi ke gabanta ba, ita burinta ta samu datijo ko yayane wanda zai juri zama da ita da ƴaƴanta, idan ta auri Mutari ina zata kai biyu? Mutari kansa nada nasa ya'yan hudu da matarsa, matarsa sau biyu tana mata tataki da habaice habaice da komai, sai dai ita ba tsoront take ji ba, ba kuma wannan zai sa ta bar Mutari ba idan har ta yi niyar aurensa, matsalar daya ce zuwa biyu, wace ta fi karfi ƴaƴanta, sai kuma shi din kansa, mutari ba wani baba bane in ya yi nisa ya bata shekara hudu, irin saurin auren nan ne na mutanenmu na gida har ya tara ya'ya hudu, ita yanzu ta auri wanda ya bata shekara hudu ai ta auri yaro, salon su kama gardama a gida ya wanka mata mari ko? Ko ya kamata da kokowa? Bata tunanin hakurin da ta ji da shekara ashirin da tara zata cike talatin a duniya zata zo kuma ta dsa rayuwar wahala da wani namijin, ko kamaceceniyar rayuwar kanwarta, ba ztaa iya jurar a wulakanta mata yan bayin Allan ƴaƴanta ba A sanyaye ta ce" Ku zo fa mu je mata💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻, barkarmuda safiyar litinin 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣7️⃣* A sanyaye amina ta ce" Ka yi hakuri Muctar, zan karasa gida bana son tsayuwa a bakin layi" Da dan sauri ya daga kafarsa yana biye da ita dan har ta juya ta fara tafia, Bata yarda sun jera ba, ama idan ka gansu zaka gane tare suke, a tafiyyar da suke yi kuma kasa kasa maganar ya ci gaba da yi mata har suka karasa kantinsa Da mamaki yake tambayarta dama nan din zata zo ta ki bashi sako? Amina ta yi murmushi kawai ta mika kudi tana zayano abubuwan da take da bukata na kayan kosan da take son farawa na safe bisa shawarar inna lauratu Dagewa ya yi kan sai ta amshi kudinta, a dole ta fuskance shi a nutse ta ce" Muctar, ka san bana kulaka dan wannan, ka san ba yau ba ka nuna mu ringa amsar cefane na nuna maka aa, ka yi hakuri ba zan iya amsar kayan sana'arka ba, nima sana'a zan fara da wannan din, inada na jarin, ba raina maia na yi ba, na fi so na saka gumina dan na fi gane gaban nemana" Shi kam gaba daya irin yadda take zile masa na matukar damunsa, du yadda ta ki amsar wani abin sai da ya zuba wani ba tare da ta gane ba, sai da ta isa gida ta ringa cin karro da abubuwan da ya karra mata, sosai ta ji ba dadi domin dukkan abinda zai taba mata mutuncinta ko kwonciyar hankalinta takan yi iya yinta dan kiyaye alakar da zata taba mutuncinta, shi yasa a rayuwa du tsakaninta da kai bata yarda da kyautuka irin na yau da gobe koda na saurayi da budurwa ne Kilace komai ta yi ta gyara wakenta da nufin kaiwa markade gobe da karfe tara , domin kosan na yan gayu ne na masu karin karfe goma ne zuwa sama Washe gari da sasafe ta gama dukkan abubuwan da suka zamo mata jiki, yau din Alhamis ce tun kusan karfe takwas har rana ta fito ta fara kwalar kawunnan mutane, Su Amina na daya daga cikin wa'inda ranar ke kwala a bakin titi daf da kwata sunna jiran dan adaidaitan da suke wahala yau Husaini kan buda ruwansa ya didika ya rufe ya maida a jakar makarantar, yau fa basa yin karatu ama mamansu ta ki yarda tace ita jiya ba'a fada mata ba yau ba makaranta, shi kam gaba ta kaishi domin an saka masa bota a boredinsa ga kuma naira ashirin dinsa a jaka, kwanakin nan gidansu dadinsu kawai suke ci, sunne taliya, sunne shinkafa da miya ta gwamnati mai dadin hadiya, sunne biredi da bota, jiya harda alewar tsinke yar goma goma mamansu ta siyo masu, sun zama yan gayu , cin dadi suke yi ba kama hannun yaro, shi yasa shi kam fara'arsa har kamar zata yi yawa , baya fada da kowa baya jin haushin kowa, Hasan ne hali baya barinsa, du dadin nan ya ga damar ya tashi yana fushi ya ki kula kowa a gidan Ajiyar zuciya Amina ke saukewa lokaci zuwa lokaci tana sake hangen titin a zuciyarta tana karra ayana' ikon Allah, yau kamar an yi ruwa an kafe ? Basu da yawa yan adaidaitar kuma du a cike? Gashi har lokaci zai shige na makaranta gashi ban kai markadan ba, Allah la turo mana dan sahu na mika su na dawo' Gali mai ruwa ne ya karyo kwana da kurar ruwansa shake yana turi, Gali kan kaiwa Amina ruwa lokaci zuwa lokaci, bama kamar in zata fara sana'a domin ruwan pampo ne yake siyarwa sosai an yarda da tsaftarsa ga kuma sauki, Gali dai saurayi ne mai zuciyar nema, yana zaune ne a gidan mahaifiyarsa tare da mahaifiyar tasa da kannensa uku yan mata, gali shine komai nasu, jajircewarsa ta sa basa zama da yinwa, mutane da yawa na mamakin irin yadda Gali ke samun kudi, sandar ruwan dai gaba daya naira ashirin da biyar ce duka duka, a cikin kurar gali bai fi sanda goma ba, kuma a wuni in ya yi zagaye mai yawa ya yi zagaye hudu, domin harka ce ta ruwa kusan mutane da yawa nada rijiya a gidajensu, yawanci masu sana'ar shayi ne da kuma masu halin siyan na pampo dan sha a gidajensu yake kaiwa ruwan, ama yanzu haka wayar da Gali ke anfani da ita a kadan zata doshi dubu hamsin, kaf anguwar nan an san gali da gayu da ba naira kashi, abinda ba'a sani ba shine shin a ina Gali yake samun kudade zafafa haka? Da yawa abokansa sun fada sana'ar siyar da ruwan suma, harma sukan yi fita fiye da tashi a wuni, ama abinda aka fi karfi cimar kaiwa baka ce, bayanta du wata rigimar da kudi zai warware sai dai a yi kamo nan kama cen a yi wace idan ba'a yi ba ana iya mutuwa ko a jigatu, sukan kalli Gali a matsayin wanda ya iya sana'a fiye da su, basu san wanene Gali ba! Tunda ya shanyo kwanar ya tsaya dan kusa da su kadan yana dariya ya ce" Hajia Amina ikon Allah, yan matan jiya yan matan yau, kun ci zamaninku kun haye na kannenku har kun fi su kyan kamani" Amina ta sale tamke fuskarta, a duniya ta ki jinnin dukkan wani furuci ko lamari da zai saka yan ƴaƴanta dago kai su yi mata kallon Mama ke da kanki? irin kallon nan dai na mamaki da wasu lokuta zaka ga danka ya nuna a kan wani lamari da ya ga ya faru da kai ko a gabanka baka dauki mataki ba, Bata san dalilin da yasa Gali idan zai yi mata magana yakan saki jikinsa ya ringa yi mata tsokanar da ta wuce misali, ita dai sa'arsa bace, ita ba wani wasa take yi da maza ba irin da zaka ga budurwa tana shigewa maza da son yin wasan banza da su ba, hasalima samarin anguwar nan na mutuntata ta hanyar kuranta da aunty, ko wani ka ga zai mata ba daidai ba to fa bako ne kuma idan wani ya ji zai masa magana, kare mutuncinta da girmamasu da take yi ya sa suke girmamata itama, ama bata san shi me yasa yake yi mata irin haka ba, sam bata jin dadin irin wasan nan Bata bashi amsa ba, ama bai karyar masa da gwuiwa ba yana kare mata kallo yauma dai cikin hijab, ita dai kulun a hijab ya ce" Makaranta ba za'a kai biyu? Hajia Amina ai yanzu malan Muktar ke fada min yau fa akoy kosai, na ajiye jarka biyu ta ruwa a wajensa ya biya kudin, shine nace ko dai da yayan namu za'a shige daga cikin ne?" Da takaici ta juyo zata yi masa magana sai ji ta yi shaaaaaa ruwan dake kwonce na jikin kwatar nan an maka masu shi daga ita din har biyun, da Galin gaba daya A haukace du suka bi bayan motar da ta aikata haka, walahi bata san lokacin da ta saka ihu ihu ta daga hannunta da ya wawuro dutse ta daga kafarta daa dan gudu ta cila dutsen nan da dukan karfinta da karfi kuma ta ce" Allah ya isa mugu ko muguwar dake cikin la'annaniyar bak'ar mota! Allah ya isa rainin hankalin banza da woffffffffffi dan ba'a dan zafin haihuwa ba ina tsaye da y'ayana za'a watsan ru.......................!" Dif maganarta ta dauke, sakamakon abinda ya rubtu a idannuwanta, jifan da ta yi bata taba tunanin hannunta zai kai bayan madubin motar ba, dutsen kansa bata taba tunanin ko goshi ya daka zai fashe ba bale motar, itafa a da sai ta jima tana jifan wajen da kadangare yake ama da kyar take iya korarsa bata samunsa, sai gashi a yau wani tashin hankali jifan nan daya kamar ita fin jikar mahalba ce ya sauka a bayan motar nan da ta tabata ko kudinta aka yi ba zata kai kudin motar ba ya fasa madubin bayan motar Bata ji cikinta na neman hautsinewa ba sai da ta ga motoci biyun sun tsaya, lokaci daya kuma ta ga sun shiga yin baya baya a hankali A tsayen da take ta yi mutuwar tsaye, bata yi aune ba ta tsinci muryar Gali yana fadin" Kan uba, motar Jikan Mai Shanu kika daka yau Amina? WALAHI na tafi ni kam na yafe watsa kwatar da aka yi min, menenema a su kwata Allah na tuba" Da sauri ta sado dubanta jin Husaini yana jan hijabinta da karfi , bata yi wani aunen ba hijabin ya janye gaba dayansa ya sauka a wuyanta domin dama wuyan ya mata yawa dabara ta yi da tudun gahinta ta zaunar da hijabin dan ta san babu abinda zai kawo fitar hijabinta daga kanta lafiyar Allah A kidine, zuciyarta na dokawa ta dago jin innuwar motar da hucin tsayuwarta a gabanta Walahaula wala kuwata ila bilahil aliyul azim, Hasbunnalahu waniimal wakil, Wannan wani irin tashin hankali ne? Kudin jikinta dududu basu fi naira dubu goma sha hudu ba, a haka jinta take tamkar biloniya kwana biyun nan, ji take yi idan da waye zasu iya karawa domin aljihunta da nauyi, shagwaba ƴaƴanta take yi da kayan dadi dan idan ta laluba ta ji cukus sai ta ji hankalinta ya kara kwonciy, itace shinkafa rabin buhu, makaroni kwali, man kuli da na ja, harda su katihun kayan makulashe na biyu alewa da tuwon madara , sai ga mai samu ta sameta rana tsaka Motar dake gaba ce aka bude aka fito da sauri aka zagayo wajen motar dake daf da itan Mutane hudu ne suka fito din, ukun na sanye da suturar dake nuni su din masu ba sauran kariya ne, kamar Bodyguard haka, dayan kuwa na sanye da simple shiga ta malan bahaushe ta kama jikinsa sosai ta amshi jikinsa "Subahanalah, subahanalah, ashe ruwan tabo ne a wajen nan bamu sani ba? Ya salam baiwar Allah ki yi hakuri mun watsa maki ruwan nan ba da gangan muka yi ba" wannan bawan Allah da ba zata mantashi ba a kampanin siyar da kayan abinci wanda ya biyosu da kayan abincin har waje ya sa suka amsa yake fada yana sake jadada hakurinsa cike da kula Mutuwar tsaye kawai ta yi, a lokacin ne kuma yake dakatar da masu basu tsaron da suka so nufarta yana mai umartarsu da su koma mota su yi jira, lokaci daya ya shiga dan leka Husaini dake boye a bayanta sai kuma ya kalli hasan dake tsaye ya hade gabas da yama tamkar wanda yake jir a kara taku daya kusa da mamansa ya kifar da mutun Murmushi ya sauke a sanyaye ya ce" Ashe maman twins ce?, Sorry ina zuwa" Yadda ya fadi sorry yana zuwa din, da hakurin da ya fito ya ringa bata ya sakata sake daskarewa ta bishi da kallo tana dora hannunta na dama a hankali saman kan Hasan dan so take shima ya dawo jikinta ko hankalinta zai kwonta, idan kashe su ne za'a yi a kashe su tare Gefen da yake ya bude a hankali ya shiga sannan ya sauke gilas din motar daga baya gaba daya yana kallonsa a hankali ya ce" Me yasa muka tsaya ne? Ka ga fa mune bamu da gaskiya duba ka ga jikinta da yaranta gaba daya datin ruwan kwatar nan ne muka watsa masu" ABDUL RA'UF ya dan kalle shi a hanzarce ya cire dubansa ya ciro tissu din dake aljihunsa ya dan tare gaban hancinsa kadan da ya ji danshi danshi alamun habon dake masa yoyo du idan gari ana zafi ke son bale masa, kasa kasa sosai ya ce" Allah ya isa ta yi, ka kuma san bana kwonciya da hakin wani in dai na san da shi ko??" Dama ya san rigima ce ta dawo da ABDUL RA'UF wajen nan, ya san ba dai dan ya bata hakuri ya ja ya tsaya ba, dan haka ya shiga kokarin ganin sun bar wajen ba tare da ya nuna hali a anguwar nan ba, dama duba jikin Hajia zasu je, jiya tace idannuwanta dai sunna gannin biyu biyu kuma kaffafuwanta sunna daukan mijirya, tun a jiyan ya so su zo sai Allah bai yi ba dole sai yau, sai gashi sun sake haduwa da maman yaren nan , haka kawai yake jin yaren a ransa, bai san dalili ba, yaren na matukar shiga zuciyarsa, ko dan shi bai samu haihuwar ba har yanzu ne? Ko a wancen ranar sai da kyar aka bashi hakuri ya bar maganar a cire ma'aikaciyar nan a cenza da wada ta san darajar dan Adam, sosai ya ji zafin abin a zuciyarsa, a nutse ya shiga fadin " Ban san a kan me direbobinka suke irin tukin nan ba ABDUL RA'UF, ka ga fa ai an shiga hakinta shi yasa ta yi magana fa" Yanzun kam a kausashe ya dube shi , zai kuma yi masa magana sai kawai ya daina ya saka hannunsa ya bale marfin motar ta gefen da ba'a fita , watau hanyar da wasu ababen hawan ke wucewa bai tsaya ya duba masu wucewar ba ya fito ya rufe hankali kwonce ya zagayo ta dayan barin Da sauri Docter Mansur ya bale gefensa shima ya fito ya karaso wajen da ABDUL RA'UF ya karaso ya ja ya tsaya kikam a kanta A hankali yake son kwatanta masa cewa mutane fa sun fara tsayuwa kallonsu, a hankali sosai ya ce" Calm down Man, plz let's go, kar ka yi wani abin a wajen da ake gannin mutuncinka" Amina dake rike taf da hannun Husain da ya fara kuma yana fadin" Wayo Allahna za'a zane mu" Hasan kuwa sai huci yake zuciyarsa na yin sama tana yin kasa irin kirjinsa na daguwa yana yin kasa shima yana kallon Tsayin Docter mai kirki ko kafadar wannan mutumen bai kai ba A hankali ta dan matsa kadan, gaba daya ji take ya yi mata innuwa haka kuma hancinsa har kamar mura zata kamata sanadiyar matsewa kanshin turaransa guri da ta yi Bata idasa ajiye kafarta ta baya ba ta ji muryarsa for the first time a dake, sannan a rarabe, haka kuma a ajiye daidaya ya ce" *KE? BAKI DA KUNYA KO?* " A haukace ta dago dubanta ta sauke idannuwanta cikin nasa, da matsanancin mamaki ta budi baki zata yi magana, sai dai bata kai ga yin ba ya katse mata abinda ta yi niyar fadan yana fadin" Ki tauna harshenki, ban san idan har zan iya cinye shirme yau ba!" Ya Allah, innalilahi, ita? Yanzu yaron nan ya dubeta ya dubi tsabar idannuwanta da girmanta, da darajarta, da mutuncinta, da ƴaƴanta yace da ita bata da kunya? Lamarin sangartatun yayan masu kudi abin sake hauhawa yake yi, idan ba rashin kunya da karancin tarbiya ba ya dubeta ya ce da ita bata da kunya? Ai yau idan me yake takama sai dai ya yi, walahi sai ta nuna masa ita bata daukan raini! "Kai kana da ita kunyar ne da zaka dubi idannuwan wanda ya girmeka ka ce da shi baya jin kunya? " Ta fada a tsitsikare, sannan a rarabe tana fada tana sake cire dubanta a kansa da matsawa domin tunda ta budi bakinta ya yi taku daya ya sake matse mata waje " Dan Allah, kar ka yi, ka duba yarenta sun rikice, duba wannan yana ta kuka, kuma idan matar aure ce yau matar aure zaka biya? Plz freind" Docter Mansur ya fada da sauri yana taro shi a lokacin da ya dago hannunsa da nufin yin abinda shi kadai ya san ko menene yake shirin yi 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 0️⃣8️⃣* A hankali ya sauke dubansa a kan Hasan Irin yadda yaron yake yi sai ya saka shi sake kura masa ido A hankali ya damu kansa da jin kamar zai yi murmushi da yannayin yaron a cen kasan zuciyarsa, irin kallon da Hasab ke yi masa tamkar zaki yana jira ya taba masa uwa ne ya far masa Sake kallonsa ya yi da kyau ya ga idannuwansa sun cika da kwala sosai fa, ama ya cije ya ki bari su zuba Wannan din shine mafarkinsa, shine burinsa, idan ya haihu yayansa su zamto jarumai ba akoki ba Yan so ya'yansa su ringa dukan yara ba wai a ringa dukansu ba Sai kuma ya kalli Husaini dake sake jan hijab din uwar sai sake lika mata shi yake yi a jikinta dama gashinta a fili tuni, da furucinsa na bakin yara sai ihun wayo Allah za'a zane su yake yi A zuciyarsa ya ayana' Um, Allah ya sa kar ku yi halin rashin kunyar uwarku, gwara ku gaji mahaifinku!' Bai ce komai ba ya juya ya koma motar ya bude gaba ya shiga ya ba direban damar su tafi, dan ya ga Mansur bai gama magana da su ba Docter Mansur kuwa Husaini ya janyo yana fadin" Haba jarumina, kai da kace min kana so ka zama likita kuma shine abu kadan sai ya rikitaka ka ringa rusa kuka kamar yar budurwa?" Husaini da ya raka motar da kallo yana ta hakin kukan ya ce" Ba uncle din cen bane zai zane mu? Dan Allah kar ya zane mu mamanmu bata iya jifa ba ko a gida ni fa Hasan muke korar mata kyankyaso daga daki tsoronsa take yi kamar me" A hankali ya dago da dubansa yana kallon maman nasu ya ga sai kiciniyar mayar da hijab dinta take yi kasa kasa sosai ya ce" To abanku fa? Shi ba zai korar mata ba?" Ido ya zarro hadi da kama baki yace" Kai, mu ai bamu da Aba ya rasu akace" A sanyaye yake kallon yaron, sai kuma ya mike ya rike hannunsa suka karasa wajen da bokicinta yake tana ta kakabar jiki ta dauki bokicin da jakarta da ta watsar du ta hade tana jan numfashi domin warin abin hawan mata kai yake yi sosai A sanyaye ya ce" Maman twins, ki yafe mana dan Allah" Sosai ta so jan maganar, sai dai mutumen nan tana matukar gannin girmansa, a haduwarsu sau biyu kadai alkhairi ya shiga tsakaninsu , ya kare mata mutunci sau biyu kuma ya rarashi Farid sau biyu, duda shi dinma bata tunanin idan ya girma sosai , ta yiwuma ta girme masa, ama tana gannin darajarsa, dan haka a sanyayen itama ta ce" Ba komai, zamu wuce gida" Ya so su bari ya kaisu, ama ta kiya, a dole ya hakura ya tafi ko kyautar da ya so ba Biyu ta tubure ta kiya, da wannan ya tafi da addu'ar Allah ya sake hada su, shi kam yana son taimakawa matar nan da ƴaƴanta, kamun kanta na matukar birge shi a rayuwa ___________________________________ A gajiye suka dawo gidan tare da Baba lauratu, domin kasa zuwa wajen markadan ta yi sai gidan baba lauratu ta je a nan ta fashe mata da kuka tana fadin an ci mata mutunci, karshe dai Baba laurantun sai ta rufeta fa fada tana fadin ta lura a kan lamarin Biyu sai ta tube a daku da ita, ta ringa sanyaya lamarinta, ina ita ina jifan motar masu kudi, masu kudin nan da daidaiku suka san yafiya da kyaliya ? Idan aka makata a cel yayazata yi kennan? Ta san basu da inda zasu je su kama a cirota , Allah ne kadai ya isa ya yiwa abin tsawa, ta kiyaye Allah ya taimaketa ta fada hannun na kirki Ita kam shanye abinta ta yi a ranta, ama ta san babu maganar na kirki, mutumen banza ne kawai Allah dai ya hada shi da aboki na kirki Da kaza kazar Baba Lauratu ta hasa wutar suyar kosan ta dora kasko ta shiga soya mata da siyarwa ita kuma ta shige ciki ta ja ruwan wanka ta dumama shi ta darje Hasan da Husaini da kanta , har kawunnansu sai da ta wanke da sabulu da soso sannan ta ji dama dama Itama ta yi wankan tamkar zata cenza fata ta fito ta gyara katifarta ta kwonta gashinta a barbaje dan ta samu ta huta, du wata kasala da bacin rai ke taso mata, ta so a bari ya mareta, da sai ta daka tsale ta shatawa jar fuskarsa mari sannan ta ciro sajensa a hannunta walahi! Karyar rashin kunya, ta rasa me yake yawo a kwakwaluwar samarin zamani A ranar dai bata wani sake yadda ya kamata ba, ƴaƴanta kansu basu haye mata ba sun kula ranta a bace sai suke shigowa idan ta kama su shigo din, sunna cen wajen Baba Lauratu sunna tayata ciniki, masha Allah sai zuwa siya ake yi taa ko'ina, dama samari sun fi gane irin haka, sai ragwagin matan da basa girki a gidajensu, sai yara da kwadayin abin ke saka su amso ashirin din iyayensu su siya su laka a hakoransu La'asar sakaliya Baba Lauratu ta gama gyara komai ta shiga ta hau dardumar da Amina ta yi sallah bata ninke ba ta shiga gabatar da sallar itama Tana salamewa ta yi addu'a ta shafa ta waiga barin da Amina ke zaune sai cika take yi tana batsewa Murmushi ta yi ta ce" ko dai na raka ki ki je wajen Baba Mai Shanu ki zane jikansa ne Amina?" Amina ta kalleta jin abinda ta fada da dan mamaki, sai kuma ta sada kanta tana turo bakinta hadi da jan numfashi kasa kasa sosai ta ce" wai bani da kunya" Baba Lauratu ta yatsina baki tana ciro kudaden itama ta ce" To ai ba'a yi abin kunya ba, ki ware uman Mijin shine kawai alkhairi, fushin bashi da dadi ai ko? Tunda dai ba ramawa zaki yi ba ai batawa kai lokaci ne, matso ki ga kuɗaɗen cinikin, masha Allah kasuwa na sonki Amina shi yasa nake ce maki ba dole sai da aikin gwamnati zaki ci abinci ba, baki taba kasawa kika kwashe ba'a siya ba, ama ke kin dage da maganar boko" Amina ta mike kamar an tuna mata tana fadin" Yauwa Baba kin ga tunda na fara kosan ga dubu gomar nan hadeta da ajiyar wajenki, kin ga har kudaden sun zarta wanda ake da muradi na jarabawar nan, sai dai lokaci ya kure, ama ba komai zan ta ajiyewa ana adanawa kafin badi idan ina cikin masu rai sai na kuma ajiyewa na zanna , Baba ina son boko, ko dan kaina ya karra wayewa, bale boko din fa tana biya baba" Baki Baba ta kebe, ita kam bata ga abin matsawa kai da maganar boko boko ba, a yi bokon a gama aikinma ya gagara? Ai kasarmu in dai baka da dogon hannu ko ka san mai dogon hannu ka shiga uku kennan, da zafin a kawo a kawo kawai ya isa ya koreka daga hanyar bokon, ta ce" Allah dai ya fito da miji da kudin na je na sa Lukman lafinta ya dandasa mana gado dandasheshe" Shirun da ya biyo baya ya saka Baba Lauratu karra kallonta, dama ta san a rina, da zarar an mata maganar aure sai komai nata ya tsaya, kamar wace bakin aljani ya aura, ta dauko damuwa ta ɗorawa kanta , a cikin manemanta mutun biyun nan tana gannin idan Allah ya yi aka yi da su ko yayane zasu kular mata da yarenta, domin a cikinsu babu na banza, daga baban Sauda har Muktar sunna da mutunci kuma an sheda sunna da riko da iyalansu da gaskiya, ba yinwa ba matsalar sutura, daidai karfinsu sunna kamantawa, bama kamar matar Muktar mai kanti, babu dashin da bata shiga na anguwa, kwanakin nan harda dashin gidan Baraka na dari uku a wata ta shiga dan tana samu, ama ita sai ture su take yi ta kasa sakin jikinta, idanma a nan take so su zauna da mijin ai ba damuwa sai su yi zamansu, duda da wahala mazan yanzu masu takaici su aminta da haka, ama ai hakan dinma ba laifi bane Ita dai Baba sai da suka ci abincin dare ta yi masu salama ta tafi Amina ta dawo ciki ta dage labulen dakin ta bude kofar dakin sosai, domin yau wani irin zafi take ji, biyuma da duka fara yin barci ta ga du sun rage suturar jikinsu babu mai riga a cikinsu , kowane kuma ya kama gabansa ya kwonta a gefensa dan yau basa so su likuma junna dan zafin da garin yake da shi Sake watso ruwa ta yi ta koma dakin ta dawo baki baki ta kwonta da daurin kirjinta sai hijab dinya da ta jiko ta rufa shi a jikinta ta shiga yin adu'ar tsaro ta tofawa yaren , itama ta yi ta tofa a jikinta sannan ta kwonta tana neman barci Barcin ne ya yi awon gaba da ita a nutse, sai dai a cikin barcin mafarki ne marar dadi ke dawainiya da ita Mafarki take yi wai ita da namiji, mafarkin da ta jima rabonta da yin irinsa A hankali ta ringa ji kan nononta na zafi sosai kamar ana tsikara mata allura, Juyawa ta yi domin gaba daya abinda take mafarkin tamkar a zahiri ne Dakatawar da aka yi na dan lokaci ya sakata sake neman barcin hadi da sauke ajiyar zuciya Sai dai bata jima ba ta ji ana shafar kasanta an kara shafawa Tun tana daukan abin da wasa sai ji ta yi ana mulmular abinda ke gabanta da yatsa ko da mene? Ita dai tana ji abin na sake shigarta dan haka ta kai hannunta cikin magagin barci dan kadewa, ko turewa, Hannunta ne ya yi raf da hannun dake kasanta ,lokaci daya barcin dake idnanuwanta ya dauke sakamakon fizge hannunsa da ya yi ya mike tsaye Wani irin razananen ihu ta saka hadi da wawurar hijabinta da zaninta tana sake ihun kwarto hadi da neman fitowa ko Allj zai bata sa'ar guduwa ta labe Jikinta rawa yake yi, kuka take yi, bata gannin gabanta hakan ya sa ta maku da jikin garun dakin nata ta yi baya ta zice a kas ta tafi a sume Ihun da yarenta ke yi sunna kiran sunnanta ya ankarar da daidaikun mazan dake fitowa dan zuwa masalaci Hankali ne ya fara tashi, domin daya na girgizata ne daya na ihun kiran sunnanta, uwa uba kofat gidanta a bude ham A hankali mazan suka fara dan taruwa a kofar gidan har suka kai mutun hudu, ciki harda yaron liman, shima magidanci ne kuma bai fi gida uku tsakaninsu ba A nutse ya ce" Malan Innusa inaga dole zamu shiga gidan nan, kafin a tado wata macen kar aje wani ne a gidan nasu, duba da kwanakin baya hakan ta faru?" Na'am suka yi da shawararsa, gaba dayansu suka shiga, sai daya da ya koma tado matarsa datijuwa da nufin ko menene mace sai ta fi su karfin taimakawa dan kare hakin musulunci A yannayin da suka same su da ƴaƴanta a dole suka fara bata talafin tsayar da jikin da goshinta ke yi, sai kuma Aban Saudat ya fice da sauri dan ya dauko adaidaitarsa a tafi asibiti Innar Audu itace da yarta suka talafi Maman biyu, sai Aban saudat din da kuma biyu suka nufi asibiti, su kuwa sauran suka je masalacin dan gabatar da sallah Bayan an gama sallah ne yaron Liman ya shaidawa Liman abinda ya faru, da yake baban masalaci ne dake cen tsalake , har sallar juma'a a nan ake yi ya saka Liman anfani da lasifikar masalaci ya dakatar da datawan da samarin baki daya ya shiga nasiha da jan hankali, da neman alfarmar kowa ya binciki ya'yan gidansa ko idan ya kula yaron anguwarsa nada irin halin nan ya fada a sanarwa hukuma su yi gagawar shiga lamarin, yaren sun ce wani ne ya shigo ya taba mamansu ta suma, an sako yarinya a gaba dan an ga miji bai fito ba kuma ba uwa ba uba ba dangin da suka yi jin kai? To b zasu zuba ido sunna ji sunna gani a salwantar da rayuwar yarinya ba, yau koda ace itace ke janyo mazan da rashin kamun kai datawan anguwa ba zasu bari hakan ya ringa faruwa ba bale yarinyar an yi mata shedar kamun kai da kare mutuncin kai! Sosai abin ya taba zukata, ciki kuwa Harda Mai Shanu dake yin doguwar tafiya a kafarsa shi da daidaikun ma'aikatan gidansa su zo har masalacin nan dan yin sallah, idan suka fita sukan zagaya ne a kafa su yi sport sosai dan jin saukin yannayin jiki Hankalinsa tashe ya karasa wajen Liman bayan an sake yin addu'a a raragu sosai yana tambayar wada ake magana a kanta? Liman ya san sarai mahaifinta ya masa gadi, hasalima gidan da take cikin Baba Mai Shanu ne ya malakawa mahaifinta suka fita daga haya suke ciki, dan haka ya sanar masa ko wacece da fadin anma kaita asibitin tafasa, shina yanzu cen din zai nufa Sosai hankalin Mai Shanu ya karra tashi, Tatare suka dungunzuma a cikin motar gidansa da ya sa Baba direba ya je ya dauko sula nufi asibitin Tasafar kowa hankalinsa tashe, zuciyarsa kuwa cike da tsoro da zulumin Allah ya sa wannan shedani bai samu galaba a kanta ba Baba Mai Shanu kam abubuwan dake cikin zuciyarsa yawansu da girmansu Allah kadai ya sani Ya shirya yin gaba da gaba da dangin iyayen yarinyar nan, idan zasu mayar da ita wajensu su mayar, idan ba zasu mayar ba to fa shi zai dauketa koda kuwa bata so! Ya isa haka, zaman tarenma da aka yi ai sai Allah ya tambaye su su da kansu bama dangin na iyayenta ba, sam an yi sake, an yi wasa da lamarin yarinyar nan, shi tunda ya kwatanta ta koma ta nuna ta fi son zama a nan tana gannin dakin mahaifinta da mahaifiyarta sai ya bar maganar, bai san ba baban tashin hankalinta zama tare da Matarsa bane, bai san ba Amina tana tsoron abinda zai taba mutuncinta komai kankantarsa, shi yasa ta iya garinta take tuka tuwonta Sun tarar an gama wanke mata goshin nata ta farfado ama tana kunshe cikin hijabi sai kuka take yi, Aban saudat ya koma gida ya dawo domin bai fito da isashen kudin da aka ce zai biya ba Baba mai shanu ne ya fito da fari kal din carbinsa ya je direct office din baban likitan wanda ya kwana a asibitin kuma bai sauka ba ya nemi izinin ganninsa Likitan na fitowa ya gaisar da Baba cikin mutunci, domin likitan akoy daraja dan Adam, kuma kana gannin Baba ka san akoy hutu a tare da tsohon A tausashe, da damuwa Baba ya ce" Jikata ce aka shiga gidansu jiya, nake so a duba min ita da fatan babu abinda ya sameta" Cike da jimami likitan ya yi gaba ya kirayi likita mace ya sa aka kirawo Amina sula shige ciki dan a dubatan Sosai aka sha daga da ita, domin sake rikicewa ta yi da nuna ba za'a dubata ba, ba zata kunce zanninta ba, sai da Likitar ta rarasheta ta nuna mata za'a duba ne idan bai yi mata komai ba sannan ta amince ta dubata Tare suka fito Likitar ta shedawa Baba cewa Allah bai bashi dama a kanta ba Gaba dayansu sai da alamun nutsuwa ta bayana a tatare da su Fuska a hade Baba ya ce" Amina Wuce ki shiga mota mu tafi gida" Amina da har yanzu bata wani dawo normal ba ta kalli Baba hankalinta na sake tashi ta ce" ASALAMU ALAIKUM WA RAHAMATULLAH 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* *PAGE0️⃣9️⃣* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* Bakinta na bari ta ce" Baba gida?" Carbin da yake ja ya hade ya daka a aljihun doguwar rigarsa fara sannan ya juya wajen da yaren suke ya masu nuni da su je mota gasunnan zuwa Juyawa suka yi suka nufi motar dan basa wasan musu da Baba A lokacin ya fuskanceta sosai ya ce" Eh gidana nake nufin ki wuce mu je mu ajiyeki, daga nan yau ba dai gobe ba zamu je mu samu dangin mahaifinki, yayansa daya daa na sani wanda da shi muka salaci gawar marigayi na masa magana a kanki, daga yau in sha Allah kin gama zama a gidan nan ke kadai, idan cen din suka ce zaki koma sai ki koma, idan gidan iyalinsa zaki koma sai ki koma, ama ba zai yiwu ki je gidan nan ke kadai ki yi rayuwa ba, zuwa yanzu na fahimci kin gane hatsarin hakan ya fi jin dadin gurbin da iyayenki suke zaune, ba zaki taba damun zaman lafiya ba mudin kina zaune ke kadai, babu wanda ya san mai zuwa maki gida da nufin cutarwa, idan na farko Allah ya kubutar da ke, na biyu Allah ya kubutar da ke, na uku ba'a san da wani shirin zai zo ba, idan ya barki a iya keta hadinki da sauki sauki, wa ya san ko yana fama da wata cutar? Idanfa Allah ya yi ke din mai kwai ce a kusa?, Wannan din gardame ce marar anfani, an riga an san ke kadai ce, Yaren nan ba zasu tare maki komai ba Amina, rayuwar y'a mace abin a bata kariya ce komai girmanta, yanzun shige mu wuce" Gaba daya tatareta suka yi suka hannata wani yinkurin bijirewa tafiyar, a hankali take tafe jikinta a mace tare da mugun tunani da tsoron abubuwa biyun dake shirin tunkaro rayuwarta Na farko gidajen yan uwan mahaifinta biyu ne kadai wa'inda suke shakikai a gareta, Kanninsa da yayansa Yan magana suka ce, abinda ya koro kura daga rami ta fada wuta ya fi wutar zafi Bayan rasuwar iyayensu babu gidan da basu gwada zama ba, suka gwamace zamansu su kadai daga ita sai yar uwarta A lokacin da suka zauna a gidan yayan mahaifinsu karen gidanma ya fi su daraja, babu abinda duka isa su raba , kasancewar gida ne na mata uku kowace da ƴaƴanta a gefe tana kalar nata ikon da kalar tata rayuwar, sai suka zamto kamar kishiyoyi ne na hudu aka zubo masu, abinci wannan basa samu sai ace ya yi kadan ne ba zai isa da su ba, abin takaicin yayan Aban nasu kuwa tunda ya nuna takardar gidansu yake so ya siyar ya raba masu gafo suka nuna basa so a siyar sunna so a barsu a kwana biyu , hasalima basa so a siyar da gidan a bara masu watarana wani sai ya shiga, gida dai nasu ne gadonsu ne mata suke, a yanzu idan suka siyar da shi sunna iya kade kudin ya zamto ba gurnon, ba kudin, idan halin rayuwa ya same su ina zasu je su zauna? To fa wannan lamari sai ya kular da shi, shi dai bai fito ya nuna ga dalili ba ama tun daga lokacin ya kawo ido ya zuba masu, in me za'a yi masu a gidan nan babu ruwansa, sau uku baban dansa na zane Firdausi tamkar zai kasheta da bulala da tatakawa da kutufo da komai, tun tana tunanin abu ne da zai wuce har ya gagara wucewar , aka zo aka yiwa Firdausi aure ko tsintsiya basu saka mata ba, a nan ta so siyar da gidan dan yi mata kayan daki mijin ya kiya yace aa shi zai yi mata, mafarin gabar family dinsa da Firdausin kennan, sam basa sonta basa kaunarta, gashi ana yin auren bai jima ba ya rasu suka tatarota suka watsar ta fito da cikin biyu Karshe dai zaman gidan yayan mahaifinsu gagararsu ya yi domin ga ciki ba zasu juri duka ba , suka koma gidan kannin mahaifinsu, wanda sai da suka gwamace kida da karatu, ashe tsohuwar gaba ke nanake a zuciyar bawan Allahn sanadiyar hanna shi auren dadiron matar da kowa ya san ba zama take yi ba, aurenta uku ana kamata da maza a gidajen, karshe dai ya bige da binta a haka aka aura masa itan suka zo suke zaune, har yanzun itace matarsa wace ta ja rantsuwar ba shi ba yayansa ko a kiyama! Ta kuwa hau ta zauna sai gasu sun fado gidansu, watau ta samu , sai da ta kai ido da ido matar nan ta nuna idan zaman lafiya suke so sai sun zama abokanan shashancinta, a ranar da kafafuwansu suka gudu , sanadiyar bak'ar wahalar ta saka Fido nakudar dole ta haihu a hannun Baba Lauratu, inda dangin mijinta suka bada abin yanka kawai suka nade hannayensu, ana gama sunna babu wanda ya kuma waiwayar yaren nan, su kuma sun daukarwa kansu alkawari zasu rike, Allah ya raya ya basu abinda zasu ciyar su shayar, su tufatar, su yiwa tarbiya! Tun daga lokacin ya zamto sai su kwashe wata daya ko biyu basu leka iyayen nasu ba, abinda ya sake yiwa Amina mugun tabo a zuciya shine haihuwar Fido ko a leke, suka barsu da kansu sai baiwar Allahn nake dake tare da su, dan auren Fido na biyu kiri kiri yayan mahaifinsu yace tafiya zai yi bashi da lokaci, aka ce a yi jiran dawowarsa sai a daura yace kawai limamin anguwar ya daura, wannan shine silar siya mata wulakanci a wajen mijinta, domin idan ya tashi gorinsa hadawa yake yi harda wannan Sai dayar damuwar itace Hajia, Walahi Amina na matukar tunanin zama da matar koda na awa daya ne bale na rayuwa tare da ita Ita dai ba zata ce ga ranar da wani abu marar dadi ya shiga tsakaaninsu ba, ama irin yadda ta san Hajiar da kyamar lamarin talaka tana tsoron zamantowa abar kyama a cikin gidan Tana tsoron kasancewa a karkashin Hajiar dan bata san wani irin zama zata yi a gidan ba, a kadan ta shekara uku tana yiwa Baba Mai Shanu waina tana kawo masa, ama maganar fatar baki bata hadata da matarsa bale godiya ko kamanta ta dan da zamanta, daidai da yin wainar shinkafa Baban ne yace da ita Hajia na son wainar shinkafa, ita kuma sai take yi dan kara girmama shi, ta fi tsoron zama da matar a cen kasan zuciyarta dan tana tsoron mutuncinta da son kare ratuwar ƴaƴanta Ama idan ta yi duba da abinda ke neman haye mata fa? Lalle da wata wahalar gwara wata Tana cikin tunanin nan suka karaso gidan Hankalinta du ba a jikinta yake ba ashe har Baba ya bada umarnin a kai su Malan Liman gida su kimtsa su karya zai zo zuwa karfe goma su wuce gidan iyayenta Sai da Hasan ya sake tba fuskarta ta dube shi a zabure , sai kuma ta shiga duban cikin gidan da datijan dake kallonta da tausayawa Malan Liman ya ce" Idan kin samu masauki, kafin ki kwonta ki tabatar kin rama sallar dake kanki , ki yi addu'a sannan ki kwontar da hankalinki, in sha Allah karshen fargabarki ta zo" Kai ta gyada a sanyaye sannan ta sauko ta shiga tafia a hankali Biyu na rike da gefe gefen hijabinta Baba ne a gaba, kadan kadan yana amsa gaisuwar daidaikun ma'aikatan dake aiyukansu na safe har suka shige falonsa A babar kujera ya mata umarnin zama sannan ya nufi sama cikin tafiyarsa a hankali na baban mutun mai shekaru irinsa A nutse ya tura kofar dakinta ya shiga da salama Hajia dake kwonce dan yanzu ta gama doguwar adu'ar da takan zauna ta yi bayan sallar asuba har sai rana ta fito sannan ta sake watsa ruwa ta kwonta dan so take ta fan huta kafin a jima wajen karfe goma ta fita cen wajen taron da suke yi yau dan ba mata masu fama da yoyon fitsari talafi da sunnan kungiyarsu A hankali ta dago tana kallon mijin nata Annurin musulunci daban yake, shi annurin musulunci tausasashe ne, ni'imarsa kuwa bata da iyaka, wannan bawa mai yawan sallah da nafila da ambaton Allah ya fi mata kowani namiji kyan kallo a duniya, annurin dake fita a murmushinsa kuwa ya fi mata komai dadina zuciya, gashi dai ya tsufa, fuskarsa du yabar tsufa ta bayana abinka da dogon mutun kuma fari tsufansa na gagawar nunawa, bale shi din ya kai tsufan shekara saba'in a duniya ai an sha ruwa, ama irin yadda yake da kuzari daidai gwargwado da kokari irin nasa na sakata jin nutsuwa a zuciyarta Murmushi ta sakar masa tana karra jan hular kanta ta rufe gashinta da furfura ta kusan hadewa tana fadin" Alkali yau kai fa kanka? Na so sauka fa sai barci ya ci karfina" Murmushi ya yi ya karasa bakin gadon ya zauna a ransa yana tunanin yau da gobe kayan Allah, tsufa labari, gashi yanzu shine kusan ba ruwansa da wannan lamari da ya yiwa naci a da, ita dinma da ta kasance cingan sarkin nacin miji a yanzu ba wannan a gabanta , abubuwan dake gabanta sun fi wannan fado mata a rai, kuma ana zaune, ana matukar kaunar junna da kula da junna, idan daya ya ce wash dan uwansa kaan rikice ya susuce A hankali ya kamo hannunsa tana sake fuskantarsa, duda kwana biyu sun yi yar tsama a kan maganar ABDUL RA'UF ta nuna cewa shine bai yi masa magana ba da tuni ya amshi tayinsu ya masu biyaya, sai a yau take jin ta yafe , kanshin turaran miskinsa mai taushi na mata dadi a hanci ta ce" Fari mai farin gemu ko yinwa ake ji?" Murmushi ya yi yana kallonta ya ce" kakar Fari bana jin yinwa, zuwa na yi da magana" Sake fuskantarsa ta yi tana sauraronsa dan ta san ko meye yana da mahimmanci a zuciyarsa A tausashe ya ce" Magana ce a kan Yarinyar nan, yarinyar nan marainiya ce, tana fama da kanta da neman hanyar da zata kare mutuncin kanta, sai dai hakan na neman gagara, har ya zamto wani marar jin tsoron Allah na dira mata gida da yara, ina so ta dawo gidan nan ta zauna har Allah ya fitar mata da mijin aure" A tausashe ta ce" Wa kennan?" Mai Shanu ya ce" Uman biyu nake magana a kai" Dan jim ta yi tana dan tunani, sai kuma ta sauke Ajiyar zuciya ta ce" Allah shi kyauta, to kuma Kakan Fari sai an nemi shawarata dan wannan? Ta zo mana ga cen bangaren su Nana sai ta zauna tare da su" Yana kallonta ya ce" Nana kuma?" Hajia ta gyada kai tana kallonsa Mai shanu ya girgiza kansa ya ce" Duda suma bana zaune da su a matsayin bayi ko wasu da na fi a duniya, ama su din masu aikina ne, ita kuma jikata ce, yarinyar nan na mutuntani tamkar ni na haifi mahaifinta, a nan tare da mu zata zauna " Naman goshinta ke dan tatarewa tana kallonsa, ta jima kadan a haka tana nazartarsa, sai kuma ta tabe bakinta tana kawar da kanta gefe ta ce" Ba damuwa, ama sai dai ta zauna a dakin kasa ba nan sama ba!" Murmushi ya yi a bayane ya mike ya kama hanyar fita , sai kuma ya dakata ya juyo yana kallonta ya ce" Idan kina da fita yau ki ajiyeta gefe ki kula da ita, zan so ki rarasheta dan kin san me ake nufi da abinda aka so yi mata" A tausashe ya yi maganar, sai dai wani irin gundumemiyar guduma da ta daki kirjinta ta hanna mata kyakyawan motsi ta raka kofar da ya ja mata da kallo A hargitse ta so mikewa dan bin bayansa, kwata kwatama ta manta shekarun yanzu da na da ba daya ba , sai daa ta ji kafafuwanta sun wani irin rike mata ta saka hannunta tana rike abin gadon hadi da rintse idannuwanta a bayane ta shiga karanta dukkan adu'ar da ta zo bakinta sannan ta koma ta zauna a bakin gadon Ido rufe ta shiga tunani a cen kasan zuciyarta da tarin takaici, ta zauna? Kar ta fita? Sabon salo kiran sallah da usur, yaushe rabonta da irin haka da shi? Me zata yiwa yarinyar da shekara ashirin da biyar kadai ta bata a duniya? Menene yarinyar bata sani ba? Yanzu shi dan ance an dira mata har wani daga masa hankali zai yi? A tunaninsa zata zauna har wannan shekarun bata san hanyar kashe kishirwarta bane? Itace MAI SHANU zai ringa jerawa wulakanci kala kala dan kawai an santa fa hakuri (🧐), walahi ba zai yiwu ba, bafa zai yiwu ba, bara kafarta ta saki ta sauka ta tarda shi a yi wace za'a yi! Ina dalili wai zai ringa caza mata kwakwaluwa ? Kiri kiri ya ki tankwasa fitinanen jikansa da ya yi gadon halinsa! To daga shi har shi din ba zai yiwu ba, gashinan yarinyar da yake nema ko jiya sai da ta mata maganar daga ce masa kwana biyu bai leka gidansu ba ya daina dan kiran da yake yi mata , gashi ya hannata kiransa kowani time yace baya so yana cikin aiki ko cikin jama'a ko ibada ta shagaltar da shi, wai a haka yana son yarinyar be kowama ya sani? Ita kam ta gaji da fitinarsu walahi! Baba bai sauko daga dama da wuri ba, sunna nan zaune dai Babar ma'aikaciyar gidan ta zo ta wuce baban dakin kasa da yan mata biyu a bayanta bayan sun gaisa duka shiga gyaran dakin, domin babu mutane ciki ba zai rasa kura ba, Sai kuma dakin kusa da shi nanma aka gyara tsaf har bayi aka wanke tasss Sunna gamawa suka bata kys din dakunnan biyu suka ce in ji baba , baban nata ne dayan kuwa na ƴaƴanta Ita dai amsa ta yi tana shafa kan Hasan da har yanzu fushinsa bai sauka ba sai cije lebe yake yi baya kula kowa A haka aka kuma kawo masu abinci shake da plate baba da cokula, ga jus da ruwan sanyi aka ajiye masu cike da kula da mutuntawa Da kyar ta samu Hasan ya yarda ya sauka dan cin abincin, shima dai sai da yace sai dai idan tare zasu ci, a dole ta ringa fan tsakura tana kaiwa bakinta , su kuma sunna ci sunna korawa da Jus A haka Baba ya sauko, cikin shigar manyan kaya na daraja a jikinsa, sai kanshi yake yi ga hula ya kafa a kansa Sosai ya ji dadin gannin sunna cin abinci, da kula sosai ya ce" Idan kun gama ku shige ciki ku huta kin ji Uman biyu?" Amina ta amsa kanta a kasa , biyu kuwa suka ringa yi masa adu'ar a dawo lafiya har ya fice a falon yana amsawa Gurin Man Liman suka je suka dauke shi da motar suka wuce gidan Iyayenta, watau yayan mahaifinta, wanda yake da dan teburinsa a kofar gidansa, sun tabata ko yayane zasu same shi a gida warhaka, sai dai idan rasuwa ko wajen daurin aure ya tafi, koma ina ne in sha Allah ya yi niyar sai ya hadu da shi a yau Sun taki Sa'a, sun samu Malan dan iya a gida , a kofar gida yan kukula kayan sana'arsa saman tabarmarsa A mutunce suka gaisa da junna, domin ya san waye MAI SHANU farin sanni, bai taba zuwa gaishe shi bai masa alheri mai girma ba A saman tabarmar suka zauna, Mai Shanu na tsokanarsa cewa yaya haka ya tsufa? Shima yana yar dariya da fadin to yaua za'a yi neman na gero kadai ya isa ya tsufar da talaka Mai shanu ya ce Allah ya dafa mana, suka amsa da amen A nutse Mai Shanu ya shiga bayanin abinda ke tafe da su, a tausashe da kalar fahimtarwa ya ringa fahimtar da shi abinda yake dauke da maganar , har ya dire aya da fadin" Wannan lamari na damuna Malan, yarinyar nan tana da bukatar taimako sosai, da ace zata samu da hankalinta zai fi kwonciya, ga rainon ya'ya bayan ita dinma yarinya ce" Malan dan iya da kansa ke sade yana sauraronsu har Mai Shanu ya gama maganar yana ta dannar harshensa da irin magangannun da yake tufka masa mararsa dadi a zuciyarsa, yana kwabar kansa cewa ya bi a hankali dan ya ci ribar zaman ya fuslanci mai Dambu a yannayin da yake tunanin maganarsa mai ma'ana ce ya ce" Haka ne, Allah gafarta malan da Elhaji gaba daya na ji maganar nan, kuma idan na fahimta da kyau so kuke ta dawo gidan nan ta zauna?" *Page 1️⃣0️⃣* Baba Mai Shanu ya ce" Kwarai kuwa, zan fi so Amina ta dawo gidan nan ta zauna kusa da mutane, cikin mata da jama'a yan uwanta, zata fi sakewa ta ci gaba da karatunta har Allah ya kawo miji a yi aure" Irin abin nan na wasu tsofin idan abu ya basu mamaki ko takaici ya yi yana dafe haba ya ce" Aure? Yanzu tsakaninku da huwa rahamanu baku gane yarinyar nan ta gama wulakantar da kanta bane ya sa ta kasa samun miji? To ai mai sunnan iya ko dan gidan na kawota na kawowa kaina fitina da balaki ne, domin a cenma da bata giga ba dan kawai yayansu ya daki kanwarta furduduwa take ko wa? Ta dauki ice tace ko shi ko ita, a haka wani sakarai ne zai dauka ya kai gidan watarana gardama ta hada su ta masa tsinanen duka? Ta zo ta kalli tsabar idona da nace a siyar a raba masu gado a saukewa bayin Allah nauyi a kansu tace aa su ba za'a raba masu gado ba, yarinyar nan a nan na hanneta maganar karatu da tace an ce iyayensu su zo nace me ake da boko? Boko ai lalacewa kennan! Tace da ni ba lalacewa a maganar boko , ilimi ne halal ne a neme shi!, Na kuma yi tataki na mata magana a kan rikon yara har biyu maza, da me zata ciyar da su? Waye zai aureta da yaren nan maza ? Zamanin nan waye zai iya rikon ɗan wani? Ama idona idon mai sunnan iya tace Baba zan iya ka bar min su kawai zan iya! Yarinyar nan gardama a kanta ta sauka kamar a kwakwaluwarta aka rawaito, ni kuwa yaya zan yi na iya rikonta? Ai kawai gidan nata zata koma ta je ta rayu da ya'yan ta ci gaba da gantalinta har ta tsufa, shi kam Uban mai sunnan iya ya yi asarar haihuwa walahi!" "Subahanalah, subahanalah malan, subahanalah, fal yakul khairan au li yasmut malan, yaya da girmanka da hankalinka malan da kanka zaka yi furuci irin haka? Yau kofa yar zumunka *LALATACIYA* ce ai zaka siranta,, harshenka ya bita da addu'a bale mu zahirinta da muka sani yarinyar tana da kamun kai, ba zamu yi shedar badininta ba, ama abinda idannuwanmu ke gani tana dauke da sheda ta alkhairi sosai, to ni a ganina ai rikon ƴaƴan y'ar uwarta da take yi dan tana da zuciya mai kyau ce, ga jajircewa a wajen baiwar Allahn nan, mai zuciyar alkhairi kan yi mata dan talafi a gareta, ka tausasa kalamanka malan a kan yarka" Liman ya fada cike da jin ba dadi a furucin Uba a wajen Amina Sai dai su suka san dadin abinda suke hange, basu san shi ya riga ya yi nisa baya jin kira ba sai da ya kara gyara zamansa yana dan kada kafarsa ya ce" Tototo, Aya, Allahu akhbar, kennan Man liman fadin gaskiyarma matsala ne? To Allah shi kyauta, ama ni kam Mai sunnan Iya ta fi karfina walahi, ba zan iya zama da ita ba" Baba Mai Shanu ya fi kowa jin takaicin bawan Allahn nan, wani irin mamaki ke lulube zuciyarsa da mamakin zumuncin zamani, y'ar zumunka? A gobe kiyama ita zaka gani fa! Itace kake wulakantawa haka? Maganar Liman ce yau ko bariki aka tare a kan yarinyar nan ai zai siranta ya bita da adu'a balle babu wanda zai ce ya taba gani ko ya ga wanda ya gani, shin menene a cikin rikon baki uku kawai? Yarinyarma bata da zubuwa, ko kyauta ka yi mata sai ka zare ido zata amsa, shine har zai kireta da sunnan idan ta gama dadiron? Ta tsufa? A cikin haka? Wannan dan uwa ne ko makiyi ne? Datijantaka da ilimi da salatin annabi da ya yiwa harshensa kawaya ya saka shi tausasa lafuzansa sosai hadi da iya kiyaye harshensa ya ce" Dama mun zo ne dan mun san a yanzu a duniya babu wanda ya kaika kusanci da ita, kuma babu wanda ya isa ya yanke hukunci ba tare da ya tuntubeka ba, Alhamdulilah tunda har ba zaka iya rikewa ba ni zan riketa, har Allah ya fitar mata da mijin ta yi aure, ko bayan raina na san iyalina zata rike min!" Malan Liman ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa, ai ko ni nan zan rike Baiwar Allah mai baban sunna, ka duba ka ga yau a masalaci irin taimakon da suka tara dan ance an tafi asibiti da ita, yanzu haka ana amsar kudin mai dari mai dubu kowa na bado talafi da kuma alkawarin za'a hadu a saka ido sosai dan a kama azalumin dake son karya mana haki a ido, ai in sha Allah yarinyar ba zata tabe ba, sai ta zauna a gidanka Elhaj idan Allah ya fitar mata da miji sai a daura mata aurenta ta yi tafiyarta gidanta" Da aka ce ko yaya ka yi da jaki sai ya ci kasa haka ne, kamar wanda wannan bawan Allahn yake gudun abin alkhairi da rahamar ubangijinsa, shin bai san falalar shafa kan maraya kadai bane a rayuwarsa bale kyautata masa da cireshi a kunci uwa uba ciyar da shi? Shi dai koda ya sani to fa shedan ya yi galaba a kansa a wannan lokacin da lada ke binsa yana zundumawa a guje tamkar mai gudun fanfalaki, a takarkare ya warware wani nadin na arzikin yana nuna hali ma rashin arziki ya ce" Ban taushi numfashinku ba, ba zaku gane abinda ni na gane dangane da yarinyar nan ba, kamar yadda ta fita daga gidan nan dan ta raina rikona da ikona ta gwamace zama a gidan ubanta haka zata koma yanzuma ta ci gana da zaman a cen! Walahi ba zan barta ta je gidan kowa ta zauna ba! Ba da yawuna ba, idan kuwa wata iyakar tawa zata nuna min bismillah sai na ga idan ta samu mijin wanda zai daura mata shi! Ai ta gani da kanwarta ta min rashin da'a yadda muka kwashe da ita!, Itama bata fi karfin hakan ba, babu abinda ya shafeni da barikinta ko kudinta, idan ta bijire min in na kama tsine mata sai ta bi duniya wa bilahilazi!, Alkawarina ne wanann!, Gwarama ta gyara halayarta ta koma ta kama mutuncinta ta zauna ko ta samu mashinshini, idan har ta bar gidan nan da nufin zama wani wajen sai dai idan da auren wani a kanta ne!" Daga Liman har Baba Mai shanu ido waje suke kallonsa Baba bai san lokacin da ya ce da Malan dan iya" Aman Malan me yarinyar nan ta yi maka da kiyaya hala? Ko dai kiyayar ta mahaifinta ce ke shirin shafarta?" Malan Dan iya har huci yake yi ya cire kansa gefe, irin wannan karron iko a hannunsa yake din nan , zai gwadawa Amina bata isa ba, ita din ba kowa bace , idan tana tunanin ta kai wani mataki ne dan tana da gida banzar bazara ce ita! Ya ce" Ba maganar gaba ranka shi dade, ai na yi rantsuwa ne sai dai idan da auren wani zata je gidansa ta zauna!" " Innalilahi wa inna ilaihi rajune, innalilahi wa inna ilaihi rajune, yanzu fisabililahi Malan wannan din ina anfaninsa? Idan fa bata fa maneman a yanzu? Shin baka gane cewa ana so a yaga mutuncin yarinyar nan bane ko me? Wani irin uba ne kai? Anya zaka so a yiwa ƴaƴan cikinka?" Liman ya fada da jimami yana kallon Dan iya Dan iya ya tabe baki ya ce" Liman ba zaka gane ba, mu mutanen karkara munada namu ka'idojin da ba'a takewa, a shekarun fa ta tara kadai laifi ne a kauye, tana yawo waje waje , bata zauna ba, baka san yaron mai garin garinmu sai da ya fito aurenta ba? Mahaifinsa ne da kanda yace aa wannan din ai ta tsufa sai dai ya nemi wata, wannan abu ya min ciwo a rayuwata, kwata kwata bata da sa'ar rayuwa ne!, Da yanzu ta malaki shanu uku ko hudu nata na kanta!, Sai karyar bokon tsiya, wannan din itace maganata, yarinyar nan ba zata je ko'ina ba ta koma ta zauna, wani mutuncin kuma? Kai ni fa dai na rantse bata da shi , kai baka ga rawar kanta ya yi yawa ba?" Baba mai Shanu tunda ya rufe baki da hannunsa yana kallon larkararen rashin ilimi da shirme ya kasa furta koda A ne, yana kallon yadda Malan ke iya kokarinsa dan ya dawo da Dan iya hanya, ama abin ya gagara, du inda ya bila sai ya bile, irin girman zumunci yake nuna masa da irin alkawarin Allah a kan wanda ya yanke zumunci, ama sai ya zile ya nuna masa ai yarinya ta lalace ba za'a iya talafa mata ba, Liman har zufa yake yi, gardama da mai lafiya ce da ita, domin ba za'a kirayeshi da jahili ba yana da nasa sannin daidai gwargwado!, A sanyaye Baba Mai shanu ya ce" Ka yi shiru abinka Liman, ba fa zai saurareka ba" Sai kuma ya fuskanci Dan iya ya ce" Shin yaushe ka yanke aurar da ita? Ina nufin zaka iya bata koda kwana uku ne ta dan saku daga wannan tashin hankalin a gidana? Idan ya so ni zan dawo maka nan da kaina da maganar aurenta, domin nima alkawari na daukarwa kaina ta gama zama a gidan nan ita kadai!" Dan iya kallon Baba mai Shanu yake yi, so yake ya kara kafewa ya kara zilewa, sai dai gaba daya mutumen yanzu da ya zo masa a tausashe sai ya kasa yi masa musu Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Ai ka isa da ni Elhaji, ba damuwa tana iya daukar har sati daya ta huta din, duda na san karya ne bata da wata damuwa, ama bayan nan idan bata samu mijin ba ta tatara ta koma rayuwar ta da, ba zata hanna kowa zaman lafiya da gidansa ba" Malan Liman gyada kai yake yi yana karra kallon mutumen, Baba Mai Shanu kuwa harda godiya da nunin ya gode da akai masa wannan alfarmar Ai kam kamar ya sani, alkhairin aka yi masa mai tsoka, yan dubu dubu sababi dal kafin su tafi, sunna daukan hanya shima ya dauki tasa hanyar ya nufi kasuwa dan ya yi sare sare, ba zai yarda ba matarsa ta ga kudin nan ta rabashi da su da jarabar lalurar yara! Mai Shanu ya jima a wajen su Malan Liman sunna tatauna maganar nan, karshe suka rabu bisa shawara daya tak, wace ta yiwa Malan liman dadi har cikin zuciyarsa, ya kuma dauki alkawarin daukan kwana uku yana fadawa Allaj da sake neman zabin Allah a kan lamarin Koda ya koma gida wajen hutunsa ya je ya dauki alkur'aninsa ya shiga tilawa, dan sosai zuciyarsa ta tabu da wannan lamari, hankalinsa ya tashi sosai da wannan abu, tausayin kansa ke lulube shi, da tunanin abinda dan Adam ya zama Baima koma saman hajia baba ba, bai sani ba dan rikewar kafar nan harda su docter ya zo ya dubata tana ta zubawa jikan shagwaba a waya ya mata alkawarin zuwa ya dubata shima, danma tafia ce ta fado masa wace dole shi da kansa zai je, a kan maganar taki ce da yake son buda kampaninsa na kansa dan ya fara fitar da takinsa yana siyarwa sannan yana anfana shima waa kansa Sarai Baba ya lura maganar da ya mata kan ta ja yarinyar a jiki bata yi, hasalima tunda ta yi wunin dayaa bata fita ba a na biyin shi da kansa da ya sauko bai sameta a gidan ba, Bai nuna damuwarsa ba ya kama hannun biyu suka wuce da kansa ya masu rakiya makaranta sannan ya bada damar idan baba Lauratu ta zo a barta ta shigo wajen Amina dan ta fada cewar a jiyama ta zo bata samu shiga ba, da wannan Amina ta wuni tare da baba dake karra tausarta da nuna mata hakan ya fi mata alkhairi, kuma da ta ji baba ya mata shiru a kan tafiyarta gidan yayan mahaifinta itama ta yi shirun kawai, ta tabata zai waiwayeta ko me ya yanke, sosai ta yi mata nasiha cewa ta yiwa matar gidan biyaya, ko menene ta tabata idan har bata taka dokarta ba ba zata wulakantata ba, kuma fa ba laifi tana da dan mutunci fa, kawai sun kalubalanceta ne Ita dai dadin da ta ji na gannin Babar ne, sosai suka wuni sunna shan hirarsu har yama ta yi baba ta mata salama zata tafi, a nan ne ta roki alfarmar ta biya ta sanarwa Firdausi, tace mata ba sai tace zata zo ba dan ta san ba barinta mijinta zai yi ba, ta fada mata babu abinda ya sameta, zata zo da kanta daga ta samu sararin hakan A wannan ranarma idonta idon Hajia bai hadu ba, Hajiar fa tamkar babu mutun a gidan haka ta mayar da ita, bata damu da lekata ba, bata damu da ita ta lekota ta gaisheta ba, takan fita dan ta gaishetan ama bata taba cin sa'ar haduwa da ita ba, yaranta kuwa sun zama sai hange, to sai hange mana sukan tare da Baba sai dai ta ringa jiyo dariyarsu da guje gujensu, karshema wani gem ya sa aka kafa masu tafkeke ya sa ana koya masu idan suka fito daga karatun islamiya yana zauna yana shan dariyar saurin fushin Hasan da kuma saurin kulan Hisaini, kamaninsu daya ama halayarsu sun sha bamban sosai, irin nutsuwar da yake kara ji da shawarar da ya yanke a zuciyarsa ya sa yale karra shirin hakan a ransa Yau kwanansu uku cif a gidan, a irgensa yau saura kwana hudu cif maganarsa da Dan iya, haka kuma a dazu da asuba sun sake zantawa da Liman kam maganar adu'ar da ya saka shi yi, ya sake tabatar masa shi kam alkhairin abin kawai yake gani , duda kwarai ya san akoy kalubale sosai , ama ya tabata alkhairin zai fi rinjaya idan aka tsananta da addu'a Shi yasa ya shirya fara tarban bama baman da ya san zasu tunkaro shi, harma ya sa aka kai abincin karinsa dakinsa sannan ya aika gayatar matarsa dakin nasa dan su karya Cikin wani rantsatswn lesh mai ruwan ash Hajia ta shigo falon mijin nata na sama da salama a bakinta Tafia take yi da classs, harufan manyan mata na yi mata wasali a goshinta Daurin kalabinta na wayayiyar mace ce, AC kuwa ya kara kwontar mata da kalar fatarta A nutse ta gama serving dinsa abinci ta ajiye a gabansa cikin plate a ranta tana ayana' Allah ka sa na ji alkhairi, wannan hade fuska haka a wajen alkali ba lafia ba' Baba Mai Shanu kuwa bai taba abincin ba, abinda le cikinsa ya fi cin abincin mahimmanci a yanzu Dan haka ya fuskanceta a nutse bayan sun gaisa sosai da sosai ya ce" Hajia Hauwa, dangane da maganar Abdallah ce, na yi masa Mace, kuma ina son daura auren nan da kwana hudu bi'izinillah, idan ya so a hankali kya yi taron bikinkkkkkkkkkkkkkk" Kwarewar da ta yi da ruwan jus din da ta kai bakinta zata surba ya saka shi saurarawa yana kallonta Tari ta ringa yi a hankali tana dan fifita fuskarta har ta daidaita, sannan ta dube shi da idannuwanta da suka dan cenza launi domin ba taron gangan bane ta ce" Sorry Alkali, na kwaru ne, to ama yaushe aka tsaida maganar auren da gagawa haka? Jiyama fa mun hadu da Honorable din a wajen taron yaye yan makarantar bording da suka samu shiga Universityn Kasar Spanish" Baba Mai Shanu ya ce " Aya, Allah ya sanya alkhairi, ai bama da y'ar gidan Honarable Alhasan Kwongilar bace, wannan sai daga baya, idan luwa ya zama wajibi sai a hade, yanzun da *MAMAN BIYU* ne nale magana......." Kaka kara kaka, lamarin fa ba karami bsne, rigimar ba ta nan bace, wai cakwakiyar idan kin san ba zaki jura ba karki fara bi, wannan rigima ta ina zata bile? Ba ga mahadan ba , ba ga wa'inda za'a hadan ba..........Rigiji gabji Dankaro da gudu ki turo naki katin ko shedar transfer ki same ki tsundum a gidan NI ZAN LADABIHHHH, sai ki min ladabi ki bi alkalaminsa, domin nima ladabin nake yi masu dan su bani danar fahimtar *WA ZAI YI LADABIH* a kokowar! Barka da yau😌😍😍😍😍😍 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 1️⃣1️⃣* Furucinsa, har zuwa kafiyarsa da yannayinsa, da suturar dake jikinsa , kai harta da kalar fatar jikinsa sai da ta shiga aunawa da idan yana cikin hayacinsa, a hankali da mugun kula ta karra dubansa kasa kasa sosai ta ce" NA'AM?" dukkan yannayinta yana kula, yana kuma hankalta, murmushi ya yi mata wanda ke tabatar mata da kwarai abinda ta ji shi yake nufi, ba gizo kunnenta ke yi mata ba, ba kuma a cikin hali na fitar hayaci ya yi bayani ba Da sauri ta saka hannayenta ta dauke farantin dake ajiye a gabanta ta kawar gefe ta zauna tana tataro dukan nutsuwarta da hankalinta ta ce" Alkali, wasa kake yi da furucin nan ama ko? Ka kuwa ji me ka fada? My big son , My hero, Uban gidan yan siyasa! Uban gidan masu mulkin! Dan yanada baban kowa a banki, shine zaka dauko auren fari kace zaka hada da macen da ta girme shi, macen da ta gama yawonta, macen dake fama da ya'ya, macen da bata waye ba, macen da take tuyar waina da kosai tana siyarwa, macen da bakin fatarta sai ya makanta mutun idan ya matsawa kallonta? Plz ka fada min cewa wasa kake yi da furucinka!" Mamakin abinda bai taba kawowa kansa cewa zai ji daga bakinta bane ya saka shi dora yan yatsunsa biyu saman lebensa, kwana uku da suka shige wanda ya yi maganar nan ya yi masa uzuri ya ajiye shi a matsayin wanda bai yi dogon karatu ba, yana fama da jahilci ya da ya yi aikin dana sani, a yanzu kuwa a wani bigiri zai ajiye iyalinsa? Shi dai sheda ne a kan irin karatun da matar gidansa ta yi, na bokon da na islamiya, shin jahilci shine sani a take sanin ko kuwa wannan din son kai zai kire shi da shi? Turw komai ya yi daga cikin zuciyarsa ya ce" Shin haramun ne aikata hakan?" Hajia kam abinda nema yake yi ya girmami tunaninta, har so yake ya ji idan haramun ne? Kennan so yake yi ya zauna a kan bakansa? Dan kwalin kanta ta cire ta ajiye gefe , lalausan gashin kanta mai dauke da furfura ya bayana a tufke a bayan keyarta da dan karamin ribom ta ce" Ba maganar haramun, shin ina hadi a nan? Idan miji kake son yi mata ka sama mata daya daga cikin ma'aikatan gidan nan mana, in ka raina su ka duba cikin ma'aikatan ka masu takardar gwamnati ka bata mana, ama sai ka dauko jirgi ka hada da mota? Ai ya fi karfinta walahi! Ita kuma ta girme masa a shekaru ai hadin sam bai yi ba, a cenza shi!" Kai ya gyada yana murmushi da tunanin lalle ya yi sake katon raini ya riga ya shiga tsakaninsa da iyalinsa, yana wanzar da rayuwar yanci da ita da shawara a dukkan abinda ya taso masu dan yana girmamata da darajata a rayuwa domin shi a ganninsa mace tana da damar zabi itama a tata rayuwar ba wai sai dai a ringa yanke mata hukunci da an yi niya ba, sai gashi tana neman maida hakan iko da isarta? Tana so ta manta yana raye kuma bai shirufce ba? Tana son take komai ta murje komai ta manta nata usulin?, Koda yake tana iya mantawa, domin halin rashin na dan lokaci ne suka yi kafin Allah ya warware, sai dai zai ji mamaki ainun idan ta ci gaba da nunawa talaka haka , takan manta Allah ya haliceta da ita da wanda bashi da shi, yana iya amshe dukkan abinda take gannin ta malaka ciki jarda jikan nata a lokaci daya kuma ya barta da ranta da hankalinta ta gani da idannuwanta? Kai Allah ya wadaran naka ya lalace! A tausashensa ya ce" To tunda dai ba haram bane ai an wuce wajen, nima da na aureki ai tserayar shekarun dake tsakaninmu nu har kunya na ringa ji a lokacin kar ace na auri yar cikina, gamu kuwa an yi tsayin rai du kanmu ya cika da furfura muna tare, wannanma ai aya ce Hauwau" "Alkali" Hajia ta fada tana tsareshi da manyan idannuwanta gannin ya mike tsaye yana shirin yin gaba ya bar mata dakinsa da itace ta tardo shi Juyowa ya yi fuskarsa a hade sosai ya ce" Look, ki saurara abinda kike shirin yi ko menene! Ki tausasa muryarki a kan tawa, ki saurareni da kunnen basira, Ni Alkali na ce na yanke hukunci Daura auren jikana da Maman Biyu nan da kwana hudu, na baki dama idan kina gagawar a hade da wace yaron ke kulawa matsayin soyaya ba damuwa, idan baki gagawa kuwa lokacin da kila shirya sai a daura masa ita, shi din ai mijin mace hudu ne a sanina, so bana son yawan surutu a kan lamarin nan, kuma na hanneki tarda yarinyar nan da wata maganar da zata zubar da mutuncinki a idaannuwanta, ki sani ya zama wajibi *KI YI MIN LADABIHHHH* , Idan ba haka ba lalle zamu bar abin kunya mai girma a duniya kafin kasa ta birni idannuwanmu!" Yana gama fada ya fice ya rufe dakin ya sauka kasa Hajia kam sai da ta yi summan hucin gadi kafin ta zabura tana sallalami da dora hannunta a saman kanta tana fadain" Walahi talahi ba zai yiwu ba, ni zaka wulakanta? Walahi ba zai yiwu ba, in ni ka fi karfina ai akoy masu yi maka magana, haka kawai dan tsufa ya zo maka sai ka hada yaro da abinda ba shikenan ba? Wani irin zaman aure ne zai iya yi da yarinyar nan? Ko hannunta zai iya tabawa ne? Kuma walahi ba za'a daura auren yar gidan honorable da gagawar nan ba, ni da nake shirya wannan rana ta yadda zan gayaci manyan yan siyasa su zo mu hadu a kashe koren arziki? Ba zaka taba sakani a jarida da yamadidin abin kunya ba, sauran titin zaka ba yarona? Haka kawai marayan Allah zaka wulakanta? Ba zai yiwu ba!" Tana fadan ne kuka na neman kubce mata tana dadana numbobi ABDUL RA'UF din ta fara kira, har sau biyu kafin ya kashe ya maido mata kiran Tana dagawa kuka ta fashe masa da shi tana fadin " ABDUL ko me kake yi ka zo gidan nan a yau yau, walahi Alkali ba zai kasheni ba, walahi ba zai kashe ni ba, bai isa ba, *Ba zan yi masa ladabin ba!*, A kan wannan bukatar tasa ba zan taba sada kaina kasa ba!" Du yadda ya so ya fahimci abinda ya hada su a yau kuma ya kasa, takan yi kiransa da korafin kakan nasa ya yi mata kaza ita kuma ta rama da kaza, ya yi mata nasiha ya hannata maimaitawa, ama bata taba kiransa tana rusa kukan nan haka kamar zata mutu ba, kuma kukan ba wai na wasa bane , irin yadda take yinsa zaka gane daga cen zuciyarta abin ke fita Hankalinsa ne ya yi mugun tashi, ya tabata ko kudi take so ya hannata, ko ya hannata yawon siyasa, a tunaninsa wadinnan ne kawai damuwar da zata rikita Matar Alkali, shi kam yaya zai yi da tsofafin nan ne fisabililahi? Sam basa girma, kulun cikin rikici suke, kuma shine a tsakiya, tsoronsa daya kar ciwon hawan jininta ya tashi, to wai inama shi Mai Shanun yake ya barta tana kukan nan haka? Ko menene ai sai ya rarasheta ya yi hakuri tunda ya fita girma kuma shine namijin ko? Kiran wayar Mai SHANU yake yi ba'a dagawa, ya shiga kiran yaronsa da fada masa maza ya sama masa waje a jirgin da zai juya gida, nanma aka sheda masa a yau dai sai jirgin yawo wanda a kadan zai iya kwasar awani ashirin bai je gidan ba, domin kasa kasa zasu sauka , baban jirgin Ethiopia ne, ya gwamace ya yi hakurin jirgin karfe bakwai din kawai da wahalar nan Sake kiran numberta ya yi ya sameta tana cikin waya Kansa ya girgiza ya jefar da wayar yana adu'ar samun saukin rigimar nan tasu, sunna daga masa hankali, sani ne basu yi ba, bashida damuwar da ta wuce tasu a duniya, yau ko rikicin neman kudi baya daukan hankalinsa irin wannan, shi fa samun kansa ya yi dumu dumu a cikin nema, kuma ya san da kudi da babu rayuwa zai yi normal, ama wadinan biyun da suka rage masa a cikin makusantansaa mafi kusanci da shi sunna taba kwonciyar hankalinsa Jin kukan wayarsa har gagawa ya yi ya dauko, a tunaninsa daya ne cikinsu, sai dai yana dubawa ya ga budurwarsa ce, wace bata san ya yi tafia ba, ya tabata ta samu labarin inda ya zo da numbersa ta nan din ne a wajen Hajia domin bai yi kiranta ba, fushi yake yi da ita, ya rasa rashin sannin ciwon kan nan nata da me ya yi kama, ba zata gane ba, shi fa baya son wulakantar da kai, ita ta dage wai ita yar kasuwa dole sai ta bude saloon? Tace aikin gwamnati yace sai dai ya dauketa aiki ta kiya, yanzu tace saloon ya nuna aa ta je ta bude, shi fa ba zai fita nema ba iyalinsa ta fita nema, idan karatun ne ba zai hannata ba, ta yi har ta ga makirkirin bokon, ama kuma ta yi zamanta, walahi ta fi karfin bautawa wani, kuma ta fi karfin wulakanta kanta a titi kulun tana yawo tana kama gashin wannan tana cudanya da karti wai ita mai saloon!, Yayan bankin yanzu haka na bankinta karamar mai kudi ce ita, idan sun mata kadan ya sake jibgawa, bahi da damuwa da hakan, ba kudin ne damuwarsa ba, a zauna masa a gida *A yi masa ladabi* sannan a tarairaye shi shine damuwarsa, a yadda ya jima da lamari mai girma rike da arzuzumin wandonsa ai dole ya bude filin sukuwa a gidansa ta kowani lungu da sako!, Ama shine dan raini yarinya karama ta ki bin umarninsa? No shi ba zai yarda da raini ba walahi! ( To fah, llale akwoy gwarama, to mu da muka saba da neman na kanmu fa? Ka zo da izala yaro!) Kafin yama ta yi tuni gidan Mai Shanu ya dauki haramar baki, na nesa da na kusa, duk wani wanda Hajia Hauwau ta dan yana jin kunyarsa ko nauyinsa ko sunna abotakata ta kud da kud sai da ta yi kiransa ta dora masa kukan mutuwa da fadin zai sakata a uku ya tona mata asiri, ciki harda Ɗan zumunsa, yaron da yale rayuwa a waje tare da iyalinsa, wanda a kusa kusan nan shine daya kwal yake laluba ya ji sanyi, dangi ne su mararsa yawa dama, sai ga lamari na dauki daidaya, sai ko taron dangin dake nesa sosai wa'inda sai a yi shekaru ba'a ga junna ba, kowa ya labe da iyalinsa yana toyawa yana kwashe abinda zai fishe shi, yau ta gigibo masu iya tasowa a ranar ta kawo su, wa'inda kuwa basa iya zuwa a ranar sun shiga shirye shiryen zuwa, domin ko ba zumuncin haduwa da junna , akoy na waya da kuma hannun Mai Shanu da na jikansa dake samun kowanensu, idan har da gaske ne Mai Shanun zai dauko ruwan dafa kansa kamar yadda Hajia ta fada za'a hafu a yi masa nasiha sannan a fadawa Allah ya kade lamarin, domin babu wanda ya isa ya yi masa dole, sai dai rarashin Tunda Mai Shanu ya fuskanci abinda yake faruwa ya yi murmushi ya kada kansa ya sa Direbansa dauko biyu suka wuce suka bar gidan Bayan sun tafi gidan gonar ABDUL RA'UF Baba Mau Shanu ya saka aka je aka dauki Baba Lauratu aka bata waya suka yi magana, dan haka aka wuce da ita gidansa kamar yadda ya umarta cewa a kaita direct dakin da Amina ta mayar da kanta yar kuryar daki a zo masa da ita Hakan ce ta faru, domin har suka fice a gidan Hajia Hauwau bata sani ba, rana sama kawayenta na danarta da rarashinta da nuna mata cewa lalle hadin naj sam ba zai haifar da alkhairi ba, ai bambancin shekarun ya fi komai daga hankali ga kauyanci, ba zai taba yiwuwa ba matar Gwamna ta kasance a haka ( uhum, su gwamna manya), idan aka yarda aka aurawa Honorable mace irin haka ai za'a samu matsala wajen zabe, ba matar gabam mota bace sam! Dole a cenza ra'ayin mai Shanu, wannan ke daga mata hankali, mijinta mutun ne mai masifar sanyi, a cikin sanyin nasa yake tafka maka abinda zai hadaka da juwa, ko a yanzu irin yadda ake buga masa waya baya dagawa ta tabata yana kallo, baban burinta shine a sakashi a tsakiya a tankwasa shi, idan ya daura auren nan mutuwa zata yi! Kai ama Allah ya tsinewa wata jarabar walahi, tana zaman zamanta, ita ta san tunda ta ki jinnin taren nan ta Mai Shanu da yarinyar nan da walakin goro a miya Takalmin dake kafarta slipars ne, hijabin dake jikinta baki ne sidik mai hannu, sannan ya kai mata har kasa tamkar zai kwasheta ya kifar, sai dai cizawar bakinsa ya sa fatarta haskawa ya zamto duhun fatar tata ya ragu sosai, danma ta yiwa kanta tanadin gyara ne idan ta tashi yin aure, da kalar fatarta mai hasken duhu ce sosai Manyan idannuwanta take karra zubawa a kan Hasan dake kyakyata dariya yana bin bayan Husaini da gudu, sakewar yaron a yanzu na bata mamaki, sosai yake sakewa yanzun bayan shi din mutun ne marar dariya a da, ko a yanzun ba wai cencen bane, ama da sauki sosai da sosai Suturar dake jikinsu ke karra shiga zuciyarta, yau bama ita ta shirya su ba, kuma sun je makaranta tana barcin asarar da ta aura, sai yanzu ta ga shirinsu, masha Allah sai haskawa suke yi cikin shigar gajerun wandunna daidai gwuiwa masu tauri watau gins daya blue, daya baƙi, sun ciza sosai da rigunnansu masu kyau masu dogwayan hannuwa, sai takalma kito kafa ciki blue da baki, masha Allah twins dinta har wata sabuwar kaunarsu ke karra bin sasan jikinta, saima idan sun juyo sun kirayeta da Mama, a zaune a wajen nan da take kamar ta yi ta taka rawa, ita kam wani kwonciyar hankali da jin dadi zata nema sama da wannan? Baba Lauratu da ta samu kebewa gefe da Baba tunda suka zo suka tatauna ce ta fito, fuskar nan tata kamar gonar auduga ta ce da Amina" 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ _*NI ZAN LADABI*_ 🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️ *NA* *SAJIDA NIGER* Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida Wannan Novel na kudi ne ba free bane Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka *NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰* *Page 1️⃣2️⃣* *Asalamu alaikum wa rahamatullah, karshen FREE page kennan yan uwa🥰🥰🥰🥰🥰, na gode* Fuskar nan tata kamar gonar auduga ta ce da Amina" Tashi maza ki je Mai Shanu na son magana da ke, Uman Mijin ki sani Mai shanu uba yake a wajen marigayi, Allah ya jikansa ya sa yana cikin rahamar ubangiji shi din mai biyaya ne a gareshi, bale marigayiya, ba zan taba tuna lokacin da na ga rashin kyautawa a tsakaninta da matar Mai Shanu ba du irin baudadan hali irin nata!, Dan haka ki je, ki yi kokarin yi masa biyaya, ko ba komai yanci yake kokarin kwata maki da rufa maki asiri, kasa zai tara maki ba wulakanci ba" Ita dai a tsaye take tana dauraron Baba har ta gama maganarta, haka kawai sai ta ji fargabarta na neman karuwa a kan tunanin abinda ya da suka zo nan, tana jin dadin yannayin wajen sosai, ama jiki sukuku ta karasa ta karra dukawa tana sake gaishe shi Mai Shanu yana murmushi ya ce" Uman biyu rabonki da ki min waina tun ta ranar juma'a, yanzun kikan ki yi min wainarma , bayan ni din ina son waina sosai" Murmushi take yi kasa kasa ta ce" A yi hakuri baba zan yi mai yawa , har sai kace ka koshi " Shima dariyar ya yi yana sake gyara zamansa ya ce" Yauwa, dangane da maganar wajen uncle dinki ne, yau kwaba uku kennan da na je na same shi ni da Malan Liman " Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi, a hankali ta kai zaune zuciyarta na saka mata abubuwa kala daban daban, baban fargabarta kardai yayan mahaifin nata ya yarda ta koma gidansa, shin yaya makomar rayuwar biyu? Tsoro da fargaba irin ta uwa ke darsuwa a zuciyarta, tunaninta ya kafe ya tsaya a kan murmushi da dariyarsu da ta barsu sunna yi yanzu, idanfa ta koma kuka a gobe? Baba Mai Shanu ya sauke ajiyar zuciya bayan ya hada abunda ya dace ta sani, ko ba komai ba zai saki baki ya yi ta yi mata bayanin abinda babanta ya fada ba, koda tana yarinya ba zata taba jin dadi ba, sam bai ga anfanin aikata hakan ba Dan haka ya ce" Sharadinsa daya ne tak a kan maganar zamanki a wani wajen, shine ya kasance kuna daure da auren wani a kanki , ki tare a dakin mutumen" Yanzun kam da sauri ta dago ta kalli Baba, dara daran idannuwanta masu dogayen gashin ido take ta kiftawa tana kallon Baba, sai kuma ta sake sada kanta Baba na hankalce da dukkan yannayinta ya ce" Harma ya bamu adadin kwanakin da ya diba bisa adalcinsa cewa nan da sati daya tak, watau nan da kwana hudu, Amina idan baki manta ba na yi ramtsuwar cewa ba zaki koma gidan nan ba, ban sani ba ko ni zan yi ta yin azumin kafara? Ko kina da tsayaye ne?" "Tsayaye?" Ta fada a hankali still tana kikifta ido tana kallon Baba Baba ya gyada kansa ya ce" Kwarai kuwa tsayaye, wanda kika tsayar a matsayin mijin da zaki aura, wanda ke zuwa wajenki kika ji kin aminta da son aurensa" Gaba daya sai ta afka a duniyar tunani, Aure? Ita? Nan da kwana hudu? Mutanen da suke tsayen da alamun sunna sonta biyu ta sani a duniya, Aban saudat da kuma Muktar, su din nan su ra sani a sanninta, sai dai bata karasa tunanin nan ba baba ya ce" Lauratu ta min maganar manema aurenki biyu, tun a washe garin da rigimar nan ta faru, Malan Liman ne da kansa ya tuntube su, su dukansu sunna da ra'ayin hakan, sai dai shi daya lokaci ya kure masa duda an nuna ba yanzu tarewa ba, dayan kuwa mahaifiyarsa ce ta yi karan tsaye kan lamarin, bayansu akoy wani ne?" Yanzun kam da hannayenta take dan watsawa, naman gaban goshinta na cakudewa a birkice ta ce" Aa, dama, dama su kadai ne suka ce, suka ce zasu aureni koda da biyuna, suka ce sunna son biyu, bayansu babu kowa" Dan murmushi ya subucewa baba, domin ko a yanzu baba cewa ta yi ba sai ya ji ra'ayin ko tana da wani ba kawai abinda ya yanke a zartar, shine yace da ita lalalala, ko daya ba zai so ace tana son wani ya katse hakan ba, ya fi so ace bata son kowa idan ya so su shirya kansu a gidansu A tausashe ya dubeta ya ce " Amina, idan babu, shin kin yarda ni na zaba maki miji, mai nagarta, wanda zai kula da maraicinki, ya rike yan biyunki, da ke kanki? Ina nufin zaki amince ki yi min biyaya kuwa? Idan har bakya jin zaki iya yin hakan ba zan ga laifinki ba, zan je na fara daukan azumin rantsuwar tun gobe, na san zan jure, ulcern tawa ai zata yi hakuri na yi ibada kar tsoho ya mutu ya je da bashi a kansa" Idannuwanta da suka cika da kwallah ta zuba masa, nazartarsa take yi , karara ta ga lalle da gaske yake, magangannun Baba suka fado zuciyarta, tsoro da fargaba suka shigeta, ta yi shiru ta rasa amsar badawa, hankalinta ya ringa neman karra tashi har sai da Baban ya kuma budar bakinsa a sanyaye ya ce" Amina, shin zaki iya yi min biyaya kuwa?" So take ta tambaye shi waye zai zaba mata? Ko baba direba ne? Ko mai ba shukoki ruwa ne? Ko Usman dan albarka ne? So take ta ji ko wanene, ama girman kunya irin ta cikakiyar budurwa ya danne curiosity dinta, kanta na kallon kasa a hankali ta daga kanta, sai kuma ta bude muryarta bakinta na rawa ta ce" Baba, zai, zai kular min da biyu? Kar kar ya min irin na mijin mamansu, kar sai ka daura auren yace ba zai rike yayan wani ba" Tausayinta zallah ya kama baba, ya kuma yi mata murmushi ya ce" Bari ki ji, bi izinillah zai rike biyu, ke da da hali harta tarkardunsu sai sun koma da sunnansa a kai, ni nan bani da haufi a kan haka, burina dama ki amince, domin na yanke hukuncin a gobe da yama zan daura aurenki bisa wasu abubuwa da suka bilo da take dokata da wace nake tunanin na isa da ita ta yi, ta manta cewa itace a kasana, *ITACE ZATA YI MIN LADABIHHH!*, dan tsufa ya kama ni, sannan na kasance mai son bata damarta na dan Adam mai daraja, har take son wulakantani da yi min bazawar sirri a kan abinda yake *MALAKINS?*, inada iko da dukkan *BAIWAR* da Allah ya bamu, bata san na fi mai rike da bulalar iko ba!, Tashi ki je Uman biyu, bana son kuka ko damuwa, ki shige dakinki ki yi alwallah ki fadawa Allah, yau Lauratu a wajenki zata kwana, Allah ya maki albarka" Idan ta iya budar baki tace ufan to fa takalmintama da ta saka a jirge ta nufi motar ya yi godiya ko ya yi magana, tunda suka shiga motar kuwa kanta a sade yake bata iya dagowa ba har suka karasa ta kuma ficewa ta nufi falon Tana budewa ta ga wasu mata biyu zaune sunna zantawa Ido hudu suka yi da junna, hakan ya sa ta duka har kasa ta gaishe su sannan ta mike ta nufi ciki Tana nan zaune Baba ta iso itama dakin ta zauna ta fuskanceta ta shiga tambayarta yaya maganar gyaran jiki? Da mamaki ta kalli babar, gyaran jiki? Wani irin gyaran jiki? Na me? Lallema baba ta iya hade hade a rayuwa Bata ce mata komai ba, dan ta san ta gama sannin komai, abinda ta so ta ji wanene a cikin ma'aikatan gidan? Dan a yanzuma da ta fito ta ga baba direba sai kallonta yake yi yana murmushi, ko dai shine? Ama ba zata iya tambayar ko babar ba, kunyarta take ji walahi Alwallar ta dauro ta dawo ta shiga gabatar da sallar magariba , a kan salayar bata tashi ba har aka yi isha'i, kai na takaice a nan harta abincinta nan ya iskota ta dan tsakura ta rufe shi ta ajiye gefe domin burinta ta dauki azumi goben! Ko menene ke shirin tarban rayuwarta Allah ya sa alkhairi ne, ta kasa gaskatawa, ashe itama zata yi aure? Aure fa? Gobe gobe? Shikenan shi babanta bashi da ta cewa kennan? Idanma waye a bata? Anya Baba dan iya zai iya bada y'arsa haka? Cire komai ta yi a ranta ta ci gaba da adu'arta Masu jiran Baba kuwa kowa sai kama wajen kwonciya ya yi ya kwonta, domin bai shigo gidan bama bale su hadu da shi ___________________________________ Washe gari Jirgin karfe tara ya sauka da shi a kasarsa ta haihuwa Yana samun ntwrk din kasarsa ya shiga kiran numbar baba da layinsa na gida Abin mamaki tana yin ringin aka daga, kuma muryar baban ce A tausashe baba ya ce" Ga dukkan alamu ka sauka Baban mutun?" Abdul Ra'uf ya sauke ajiyar zuciya jin muryarsa ram ya ce" What happened with u? Shin me yake faruwa ne? Ina Hajia?" Baba ya ce " Tana gida" Abdul Ra'uf ya ce" Kai kuma kana ina?" Baba ya ce" Yanzun dai na fito daga kasuwa ni da Malan Liman siyan goro, mu hadu a gidan dan nima cen na nufa ai" Yana gama fada ya katse kiran yana ta adu'ar da Liman ya karra bashi har suka karaso gida Gannin motocin Abdul Ra'uf din ya tabatar masa cewa ya karaso, lalle ya zaku ya ga kakarsa yar rigima Murmushi ya yi yana gyara babar rigarsa dake baza kanshin misk hannunsa rike wayarsa da kuma carbinsa ya doshi falon kansa tsaye Yana shiga mutanen da ya gani sai da bin ya so bashi dariya, haka kuma irin yadda ake nuna jimamin ba'a ganshi ba ya sake bashi dariya, kamar ya bace din nan? Shi dai da mutunci ya gaishe su, sannan ya karasa wajen abokinsa da ya sake zuwa da sasafe dan jin idan ya dawo gidan Hannunda ya kama yana fadin" Mu je saman mana Elhaji, na san Abdullahi ya karaso ko?" Du yadfa suka so dan fara dannarsa kowa sai ya yi shiru suka haura saman Tun daga kofar dakin nata yake jiyo muryoyi na mata da kuma nata, ita tana magana da kuka ne, matan kuwa sunna irin abin nan na zigi zigi da nuna sam idan aka yi haka ai wulakanci ne da tozarci, Hajia ta sake dubansa hannunta cikin nasa ta ce" Kar ka yarda Abdallah, ka tuna kana soyaya da yarinyar nan, yarinya yar gata gaba da baya, ga ilimin boko rututu a kanta, ga kyau ga kwalisa, aljannar duniya ce ita din, idan har ka yarda ya dauki y'ar fa ta gama yawace yawacenta kwararo kwararo ya aura maka ya cuceka, zai aura maka itane dan yana tausayinta, wai ita uman biyu, kulun tana tafe da yara sunna rike da hijabinta, bari ka ji ifan har ka aminta da haka ya wulakantar da girmanka da darajarka, da wahala Honorable ya yarda a makawa yarsa kishiya jahila!, Me take da shi na classssss? Me take iya yi na nuna halin girma? Zata bata sunnanka da nawa, kai ka ga duhun fatarta? Kar ka yarda da wannan hadin ka ji yarona?" Shi kam abin gaba daya wani iri ya zo masa, kallon kakar tasa yake yi a tsanake yana nazartar abinda take son fadi, shi fa idan za'a yi masa bayani da hargagin nan ba ganewa yake yi ba, ga kawayenta sun ki su yi shiru kowace sai fada take yi, A tausashe ya ce" Uma ku yi shiru mana daya ta yi magana, nu na kasa fahimta, aure ne za'a yi min?" A kusan tare suka amsa shi da eh Da mamaki yana jin murmushi zai subuce masa ya ce" To fah, sai kace yar budurwa? Shi mijin naki bai san ba an daina yayin auren dole ne ko ga yan mata?" Hajia ta ce" magana nake maka ta gaskiya fa son, ba maganar wasa bace, nufinsa aure zai daura maka nan da kwana uku kennan yau!" Ido ya dan zarro sai kuma ya dafe habarsa yana dan tunnani, a hankali ya ce" To yanzu kukan da kike yi a waya kika ce zaki mutu baki da lafiya ne? Jikin ne ya motsa?" Wace yake kira da Uma ce ta karbe maganar da fadin" Aa abin ne ya daga mata hankali mana Gwamna, ni da kaina sai da na ji kamar hawan jinina zai tashi , ka kuwa san me hakan yake nufi? Tun jiya take kuka baiwar Allan nan, duba ka ga yau ko dan kwalin kirki ban daura ba na fito daga gida , soma na yi na kwana sai kuma dai na koma gidan" Dan kwalin da tace ya bi da kallo, da magangannunta yana aunawa ya ce" Uma, kardai daga ke sai wannan abin na kanki kika fito?" Uma ta ce" Eh kana gani dai son, ai a mota ne da kyar na iya yin barci jiya, kar ka yarda da auren nan kai kadai ka isa ka bijire masa!" Mai Shanu da abikinsa, amininsa , datijon arziki da a jiya matar Mai Shanun ta rikita suka sake kallin junna Mai shanu ya saki murmushi ya dan ja shi gefe ya ce" Yarinyar nan ta wajen mai gadina ce ake magana a kanta, ka san bata samu aure ba.........." Gaba daya ya kwashe ya fada masa komai, ya dora da fadim" Shine Ni hauwau take neman tozartawa da tara kawaye ana yamadidi da korawa yarona bayani kan kar ya mik biyaya? Ashe basu da hankali? Ashe basu da kunya? Basu san sun girma ba? Kawunna cike da furfura basu gane a kusa suke da rami ba? Inace ba'a yi sati uku ba da daya daga cikinsu ta rasu , basu gane ana masu dauki daidaya ba suke neman izgili da lamarin ubangiji? Matan nan sunna da hankali kuwa?" Shima da madaukakin mamaki da takaici ya ce" Dama abinda ya sa Hauwau tara jama'a tun jiya har yau kennan? Hasbunnalahu waniimal wakil, hauwaun haka ta zama? Kai kace karfe nawa daurin auren?" Baba mai shanu ya ce" Shi dai uban yarinyar yace daga azahar har isha'i sunna sauraronmu Baba Rabi'u zai yi magana sai ga Abdul Ra'uf ya fito daga dakin yana dan tare gaban goshinsa, fuskarsa dauke da murmushin rikicin kakarsa da kawayenta, to rikici mana, wannan maganar ta wuce a zauna a tatauna tsakaninsu su uku a kashe wutar a wuce wajen? Shine take kukan nan? Uhum shi yanzu baima san inda zai lalubo Docter Mansur ya zo ya dubata ba, ya ga du ta kode abinka da farin mutun ido ya jeme mata ba kwaliya wai ita ta shiga tashin hankali za'a yiwa gwamna aure, shi idan sunna kiransa da gwamnan kamar ya fashe da dariya walahi Hannu ya fara mikawa Baba Rabi'u yana rage tsayinsa , sannan ya kalli Babab yana nazartar irin daure fuskar da ya yi ya ce" Ashe kana nan angin uley" Sukan yi haka da junna , yace da shi na bar maka shima yace aa aa tasa ce, ama yau sai ba'a bashi amsa ba, hasalima Baba Rabi'u ne ya shiga yi masa nasihar da ta saka shi zubar da dukkan wani yannayi na farin ciki da daukan maganar a shirme yana kallonsu baki daya, har suka gama suka dire Aya A hankalce ya ce" Ama, baba ka san ai inada wace na tsayar a matsayin wace zan dauka ko?" Baba ya fuskance shi da kyau ya ce" Ban hanna ka ba, ama a yanzu na cenza shawara sai na ga yannayin zamanka da yarinyar nan sai ka karra aurenka, ABDUL RA'UF na riga na sayi goro na kuma tsayar da magana, idan mun dawo daga daurin auren ma shigo mu zauna da iyayenku da ita yarinyar da kowa da kowa" Idannuwansa ya wara da mugun mamaki, a san kagauce ya dubi kansa, farar shada ce a jikinsa dinkin tazarce, simple bata da adon komai a jikinta sai hular dake kansa , kayan tunda asuba ya saka su, kai bama wannan ba sai kace mutuwa wannan abu a kagauce? "Ba zaka yi min ladabin ba?, Ba zaka bi umarnina ba? Nace ba zaka amsa maganata ba? Kana da damar bijirewa kamar yadda suka ce, kana da damar kiyawa tunda ai dama kaine mai kudin, hausawa kuwa suka ce mai kudi uban iyayensa!, Zamu yi gaba da jama'ar da na gayata, idan mun je cen din zamu daura auren, kafin nan kafin azahar ka yi kirana idan ka ga ba zaka iya ba kace da ni kar na saki na daura, domin ba zan so na yi maka auren dole ba, ai kai ba yar budurwa bace!, Rabi'u mu je" Baba ya fada a hasale ya fara yin gaba da tafiyarsa ta tsanake dan baya oya mugun sauri jikin tsufa Sosai baba Rabi'u ya dan kara tausarsa da nuna masa ya yi Ladabi wa kakansa, ya isa da shi kar ya bashi kunya, sannan ya bi bayan tsohon ba tare da ya yi masa tambayar waima wacece ne? Shi gaba daya gani yake yi ai mafarki ne wannan din, wani irin almara ce wannan? Aure? Aure fa? To da bai zo Bama za'a daura masa auren ne? Wannan wani irin abu ne? Wacece wai yarinyar nan da kakarsa ke ta fadin ta gama yawace yawacenta? Kuma shine shi za'a daura masa? Ya salam Jikinsa ya ji na damunsa da gajiya da kuma kasala dan haka sai ya koma ya dauki darduma a dakin hajia da ta daina kuka hankalinta kwonce ta san am gama tunda ta yaron ya kuma yarda da maganarta A hankali ya fice baya ya shinfida dardumar ya karasa wajen pampo ya daura alwallah ya koma ya zauna ya dauki carbinsa ya shiga ja, ko yinwar baya ji, ya fi irga lokaci da duban hanya, y kula samarin gidan sai ficewa suke yi a motocin gidan, har gidan ya dauki shiru , aka fara kiraye lurayen sallar azahar Kasa fita waje ya yi ya kabarta ya shiga bin sallar daga nan,, har aka salame ya sake Ubbawa wayarsa ido da tunanin in dai da gaske ne yanzun ana cen ko an daura masa aure da bakuwar da bai san ko wacece ba ko za'a daura masa Kai yau shi ya ga masifa lukuta walahi Sannu sannu har karfe biyu ta gota, dan haka ya mike ya dauki dardumar da nufin yin tsakar gidan Sai dai hango mnai gadi ya wangale kofa ya saka shi cenza akalar tafiyar ya dauki doguwar hanyar wajen mangoro dan burinsa ya dan labewa hayaniyar da ya tabata za'a yi a gidan nan a yanzu ,,. Dan baya so tta summe idan ta ji an daura masa auren nan, shi su bashi dama ya fahimci abinma sun kasa bashi, uhum wani abu sai hausa! Tunda ya taho tunani ya cika kwakwaluwarsa, haka itama dake tahoha dan ta koma dakinta ta kicin kamar yadda ta biyo ta zo ta wuni a karkashin mangwaron nan dan ta gujewa abinda Baba Lauratu a sakota a gaba da shi wai wani gyaran jiki har ta kama ta murza mata man ja da kurkum a jiki sai karnin man jan tale, shi yasama ta ki saka hijabinta ko daya dan bata shirya lalata hijabi ba a kan shirmen gyaran jikin auren da bata san da waye ba, kawai ta fito da doguwar rigarta sai dan kwalin rigar ta yane kanta da shi, kanta a kasa tana ta tunanin a wace ake ciki ne? Ina baba yake ne bata ganshi ba tun jiya? Shin yaya maganar da ya mata ne? Allah ya sa an fasa A zuciyarta ta ayana' Allah ya sa baban yace aa an fasa ba yanzu ba , ba zai bayar da................." Kim, kum duskarta mai dauke da man ja da kurkum tana kyalin mai ta kumun masa a gaban kirjinsa da farar shadarsa A rikice ta saka hannunta da ya dauki yellow din kurkum din ta damuki rigar tana furta" Aushhhhhhhh subahanalah wa........." Dif maganarta ta dauke a lokacin da ta yi arba da sajjen fuskarsa da kuma hasken fatarsa da kamaninsa Shima da hanzari ya rike damtsen hannunta ya janyeta baya yana yatsina fuska da binta da kallo da son tuno wacece wannan a ina ya san fuskar wanann, bale dan kwalin da ya yaye sak sai ya so tuna masa wata fuska daban Dan tsakin da bata dan da shi bane ya bale mata ta shiga jan hannunta, sai kuma da dan karfi ta ce" Malan cikani mana meye haka!" Idannuwansa ya wara a kanta, nan take a ransa ya ayana 'Fitsarariyar nan ce!' , A hankali hankali ya shiga dan nitsa mata hannunsa a damtsen da take gannin na mai karfi ce ita yana kallonta sai kuma ya dan matse hannun yana tsaye kikam yana kallon yadda ta kawo dayan hannunta tana zarro ido hadi da kokowar son kwace kanta a haukace ta ce" Kai baka da kunya ko? Ka cikani ni sa'arkace wai da zaka matsen hannu ? Kai ka........... Wai wai wai wai wai wai wai gwarama in ji kawata Nace ba, kin kuwa turo naki katin? Nan na tsayar da free, kuma in sha Allah shi din babu na aunty sajida a taimaka min da NI ZAN LADABIHHHH, domin a cikinsa zan baje basira na bada maganar gyara na sana'a ba cuta ba cutarwa .........garzayo yar uwa mu je da ke rikicin mai karfi ne.......wai yaya tafiar zata tafi ne? AMINA fa baba ce bata son raini, ga kuma wanda ya fita gannin shine baba , a samanta yake, uwa uba su din mata da miji suke a yanzu....wai yayane , *WAYE ZAI YI LADABIN?*, GA kuma hajia a gefe, kun tanadi ruwan watsa mata dan ta farka idan ta summa?, Wai yayane maganar yar gidan honorable? Iyayen gida mune da kambun wannan karo, tafiyar tamu ce! Ku buga mana tamburan aunty, hajia sannunki yah mama, kece uwar gidan gidan oga, kece za'a yiwa ladabin fa! Maman jariri nace ba? Yayane🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️ Sai kun zo *NZL PAGE1️⃣3️⃣* Kokowa take neman tafkawa da shi dan ta kwaci kanta, wani irin takaici da haushi suka hadun mata suka tsaya mata a wuyanta, so take ta fashe da kukan takaici na irin kusancin dake tsakaninta da shi, tunda take ko maza masu sunnan maza da suka girmeshi hakan bai taba faruwa tsakaninta da su ba sai a kan wannan? A kan me zai kama mata hannu? Ko ya zata yar iska ce ita? To ko iskanci zata yi ai ba da kannin bayanta ba walahi Kasa amshe hannunta da ta yi , ga ido ya cika da ruwan hawaye sai zuru zuru take ya sakata dago hannunta a haukace da nufin kifa masa abinda ta tabata idan har ta aikata din sai ta kulle kanta, dan bata tunanin in za'a kyaleta ta ci bilis, ta tabata Allah ne kawai zai tsaya mata ya kwaceta a hannunsa da kakarsa, ama ta yi niya a kan mutuncinta babu abinda ba zata yi ba Da karfi ta nufo fuskarsa da hannun nata, sai dai kasa karasawar hannun nata ya sakata neman kara dukewa da saurin kai dayan hannun da ya sakar mata ta damki gaban rigarsa wajen cikinsa tana haki hadi da kallonsa, domin da hannunsa daya ya tare marin yan dan zarro idon mamakinta Zai yi magana madaukakin salati da salalamin da duka fito daga falon nan du irin nisansu da falon ya sakasu a tare juyawa suka kalli hanyar falon Gabansu faduwa yake yi a tare, Ita dama taron jama'ar nan ya tsaye mata a kirji tans tunanin na menene, shi kuma a kasan zuciyarss fadi yake yi lalle ta faru ta kare Da dan karfi kadan ya yarfe mata hannun, wanda sai fa ta yi taga taga sannan ta iya rike kanta tana zarro ido Fuskarsa ya yatsina, domin ji ya yi ba zai iya buyar da ya so ya yi ba, ya san wace kakarsa a duniyar yan rikici, bale yau zagaye take da fadawanta yan zigata, baya so a yi abinda zai shiga uku Dan haka dole ya juya a nutse ya dake daukan hanyar cikin Amina dake haki tana hararan bayansa itama dole ta dauki hanyar falon, sai dai nesa take da shi sosai tana mamakin irin yadda yake tafiya da wani dan bubudewa kamar wani uba, uhum yaten zamani? Sai su Labulen dakin ya kama ya daga gaba daya ta yadda haske zai karru a dakin Dan tokarewa ya yi yana kallon ikon Allah, du an wani yayume kakarsa ana tausarta, shi kuma oga kwata kwatan yana zaune yana kallonsu a saman kujerarsa da yakan zama lokuta da dama, shi sai a yanzuma ya ga cousint dinsa hakan ya saka shi dan zarro ido sai kuma ya dauke ya shiga falon da salama a bakinsa ya ja ya tsaya yana kallon wajen kakar tasa a hankali ya ce" Hajia?, Hajia?" Hajia dake kuka ris ris ta dago da sauri jin muryarsa, sai dai wace ta gani a kusan daf da shi ya sakata dagowa tana nunata ta ce" Ke? Uban me kike min a nan ? Ko kin ga sa'anki a wajen n......" "Haba hajia, Haba hajia, wannan din ba girmanki bane, kar ki yi abinda zata rainaki tun yanzu mana" daya daga cikin kawarta ta fada, Amina kuwa ido ta zarro bayan ta waiga dan gannin da wace ake ta tabata da ita ake sai dam ta nemi juyawa dan barin dakin domin dama ita tsoron da ta ji kar aje mutuwa aka yi a gidan, kar aje wanda ya daure mata ne ya mutun, to wannan ihu da salalamin bakunna da dama ai ba dai karamin mugun abu zai saka su yi ba "Uman biyu, zo nan, dawi ki zauna cikin mutane" baba mai shanu ya fada a tausashe , sannan ya maida dubansa wajen da aka rike Hajiar ya kare mata kallo daga sama har kasa, da wa'inda ke ta tarotan A kausashe ya ce" Alhamdulilah, Allah ya saka da alkhairi, mun yi magana da Issuhu an fitar da motoci za'a maida kowa gidansa, wa'inda ba na gari ba kuwa za'a sakasu a hanyar da ta dace su koma gida, idan an tashi yin bikinsu kowa zai ji sai a dawo da dadin rai, wannan dai itace iyalinsa, gatanan in sha Allah mutu ka raba" Yanzunma gaba daya dakin aka bi inda Amina ke dan tahowa dan ta zauna a wajen da ya nuna mata, domin dan kusa da kafafuwansa kadan ya nuna mata kan ta zauna Itama ja ta yi ta tsaya da sauri , sannan ta kalli gefe da gefenta har bayanta da kujera ce kadai ba komai sai da ta waiga ta kalla, A dan rude ta kalle shi , hadi da salalamin da Hajia ke yi ta kai zaune a wajen da take tsaye tana faman fadim" Ban san irin girman laifin da na yi maka ba da kake wulakantani har Haka Alkali ba , ko menene ai sai ka fada min na nemi yafiyarka ko? Ina hadin aure tsakanin Abdul Ra'uf da yarinyar nan? Alkali shine ka je ka daura kuma kake son korar min mutanen da nake gannin sun isa da kai?" " Ki min shiru Hauwau tun kafin na saba maki! Idan ke baki da hankali baki gane kin kai wajen da zaki fara tsawatarwa ba maimakun a ringa tsawatar maki to ki iya bakikinki ki tausasa kalamanki, kar ki saki garin shirme irin naki ki yi furuci a abinda Allah ya boye maki sirrinsa!, Ke baki san waye zai rike hannunki idan kin kai gajiyawa ba! Kaf mutanen dake wajen nan da kike fadin sun isa da ni, ni Aliyu dan gidan Umar faruk karya ne a kan gaskiya, kai ko akoy wanda zai tirsasani yanke hukunci dan na yi abinda yake alkhairi ya saka a yanke igiyar auren nan? Bari ki ji Hauwau zaki yi sanadiyar da zan hanna maki siyasa, watau na haramta maki ita har duniya ta nade!" Baba Rabi'u ne yake son maida shi zaune, dan har rawa jikinsa yake yi, gaba daya ya fizge hannunsa yana juyowa wajensa ya ce" Ka barni da ita, me take takama da shi ne? In ba rashin godiyar Allah ba fa kudin zaki je kiyama? A kasarmu mace na mulki ne? Yaron nan da kike ikirarin ya hau kujera ya nuna baya so, na maku shiru ne dan na san idan Allah ya hukunta tabas zai yi mulkin kuma bi izinillah jinina ba zai kasa samu ba domin waye bai san sarkin matasa da kyakyawar mu'amallarsa da mutane ba?, Ama sai wani jahiltar siyasar kike yi kina wani irin abu tamkar kin kauro duniya da zama!, Hauwau idan daga zaunen nan baki idasa sauka kasa kika suma ba ke ba cikakiyar yar gayu mai kyamatar jinin talaka bace, Wai sai ikirarin bak'ar fata kike yi , ke kin manta yadda taki fatar take ne?" Da sauri Ya daga kafarsa ya karasa wajen kakansa da ya ki sauraron kowa ya saka hannunsa ya damki nasa hannayen ya shiga murzawa a hankali yana kallonsa , du irin halin da shi ya shiga a yanzu wannan da yake ciki ya saka kafa ya shure yace kau bani waje!, Muryarsa a tausashe ya shiga fadin" Aba....Abahnah, abah da baki fa a gidan" "Ka barni na yi, ka barni na tuna mata ita din mutun ce kamar kowa, bakin ai ita ta gayato su dan a hadu a taro ni, na haukace ko? Ita ta harhado su dan a yi min magana zan tafka sabo ko? Ai bakin makusantanta ne da nawa, idan summa sun haukace sai na gani, idan tunani take yi saukin halin da na dauka na zubar da komai nake rayuwa da ita dan samun sukunin zuciya tsoro ne ko dan ta fi karfina ne ta farka, Son ka barni a gaban bakin nata na tuna mata bata isa ba ta hanna wani abu a kan wannan, na daura maka aure zaka zauna da matar ko ta ki ko ta so, kuma sai matarka ta aminta zaka dauko ta biyun da take fada, maganar siyasa kar Allah ya sa su hau in dai son zuciya suka saka a gaba!, Hauwau kema zan iya haramta maki zumunci da kawayen nan dake mance abin rufa dan su zo su yi zigi a kan aikim lada da gyaran rayuwar wani, ki saurareni da kyau Hauwau, nace zan iya haramta mu'amalarki fa Uma, idan har ta fini a wajenki kuma sai ki bita, ki bita Hauwau!" Baba Mai shanu fada yake yi tun karfinsa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, gaba daya hakuri ake bashi ana fatan ya yi shiru ama ya gagara, zuciyar Aliyun Umar Farukun a kusa take yau, yau a kai kan gaba ya amaye abinda ya girgiza kowa, da yawaa yanzu suke kuka na tsorata da tashin hankali, ya jima rabonsa da rigima irin haka, ya dauki girmansa da hannu biyu ya zubar da komai tunda ya rasa dansa kwalin kwal da matarsa, ya daina saka hancinsa a wajen da ba'a saka shi ba, yana aiki ne dan ubangijinsa ba dan wani ba, yana kyautata mata ne da zuciya daya dan burinsa ya mace a hannunta ta yi masa takaba a gobe kiyama ta zamto uwar gidansa a aljannah idan Allah ya aminta, sai gashi lamarinta na kulafircin mulki na son haifar mata da ɗa ba ido, a fadansa da ya furta furtaciya fa? Wace koda da kome da kunya fa? Da sun dawo kowa ya yi dana sani, ABDUL RA'UF gannin abin zai zarce misali ya saka shi shiga kafadunsa ya rike shi da kyau ya shiga tafia da shi a hankali ya nufi sama da shi kasa kasa sosai yana fadin" Ka yi ta hailala, ka maye gurbin maganar da ambaton Allah, ka daina maganar haka, ka bar maganar haka" Sosai kirjinsa ke dokawa, bai taba tunanin da girmansa zai ga irin haka ba sai yau, tun ana yara ba'a yi haka ba sai yanzu? Gaskiya ta zo masa da sabon lamari a cikin rayuwarsa, wannan wace irin masifa ce? Tun jiya zuwa yau ta hannawa kanta kwonciyar hankali saboda abinda yake daidai da kuma alkhairi? Shi ba gori ya yi mata ba, ba kuma wulakanci ba, ya daki abin da karfi ne dan harta masu ririketan su gane bai zo da wasa ba a kan lamarin nan! Zaunar da shi ya yi a bakin gadonsa, a hankali ya dora masa kafafuwansa a samn bed din ya cire masa sabon takalmin da ya dandasha na amarci, sannan ya cire masa safarsa harda hularsa ya kai komai ma'adaninsa ya dawo ya janyo kujera ya zauna ya zuba masa ido yana kallonsa A hankali fushin ya fara sauka, har ya dawo yana ajiyar zuciya carbinsa a hannunsa yana ja Kasa kasa ya ce" Na kira Mansur ne?" Baba Mai Shanu ya bude idannuwansa ya sauke a kansa, shi yama zata ya fice ashe bai fita ba, tausayinsa ya ji ya kama shi a cen kasan zuciyarsa, ya sani sarai shima a cikin wani hali yake mai girman gaske, sai dai kamar yadda ya kasance mai saka bukatar wasu a gaba da taa, damuwar wani a gaba da tasa damuwar halaya kamara wani mai manyan shekaru ya sa ya dane nasa balin da ya sa zai masa ne a lokacin da ya fuskanci ya dace ya yi masan, a yanzu da ya ga yana fada ya cinye ya kawo shi dakinsa Kai ya girgiza a hankali yana bin shadar dake jikinsa da kallo irin jan man da ta yi Ajiyar zuciya ya sauke ya mike ya rage karfin ACn sannan ya dannan yadda zai ringa yin sama da kasa kar ya kafe waje daya , ya dawo ya sake gyara masa kafafuwansa yana ta dan matsa kafafuwan dan so yake ya gane idan sunna da kumburi ko basu tasa ba A hankali ya rufa masa bargonsa sannan ya mike da nufin barin dakin Muryarsa ciki ciki, dan har ta shake ya ce" ABDUL RA'UF" ABDUL RA'UF ya dakata, ya juyo ya dawo yana kallonsa da sauraronsa A sanyaye ya ce" Kar ka aikata aikin dana sani, kar ka saketa ko me zaka tarda ka ji?" Fuskar tsogon yake kallo da daraja tamkar ta mahaifinsa *Saki, ko me zai tarda,* yake ta maidawa zuciyarsa Wai dama auren da wannan yarinyar ne aka daura masa? Ya sake tambayar zuciyarsa A hankali ya sakarwa tsogon tatausan murmushi, dan ya kwontar masa da hankali sannan ya juya ya sake ficewa Ja ya yi daga sama ya harde hannayensa yana hangen dan karamin meeting din da ake yi a falon Maganar kakansa cikin fadansa ne ta fado masa a rai , inda yake cewa wace yake nema din bai is ya aura ba sai wace ya aura masa ta yarda Murmushi ya samu kansa da saki a saman lebensa Oh ahalinsa na shagalinsu Watau su a duniya kowane idan ya tashi yakan yi abinda yake birgeshi ne da rayuwarsa, ba ruwansu da nasa ra'ayin ko nasa burin, babu ruwansu da bin nasa tsarin Wani murmushin ya kuma yi yana gannin yadda abokin Baba ke masu fada hadi da nasiha, a haka jama'ar da hajia ta gayato ke dan raragewa domin da yawa dama da abin hawansu, wa'inda basu zo da abin hawan ba kuwa mota na jiransu Ji kake yi tsitt Hajia babu rigima da koke koke, gaba daya kamar an yi ruwa an kafe ta yi shiru kamar bata wajen Kawayen natama wasu tunda baba ya mike suka fece, sun san hali da zaki ya yi barci ne suke neman yin wasa da gashinsa Dayar dai itace ta tsaya, watau Uma, itama gaba daya jikinta ya yi mugun sanyi kamar an zare mata laka Umarnin da Baba Rabi'u ya bada kan ta raka Hajia dakinta ta dawo ta tafi gidanta ya saka suka mike Uma na rike da ita suka shiga haurawa A hankali ya ce da Hajia, dan ya san wacece ita, shirunta ba yana nufin ta dauka daga abinda ta hau bane, yana nufin tana kaunar mijinta ta kuma dan waye shi, yana nufin komai abinta idan ta taboshi takan yi laushi, ya san wacece ita a kak kafiya a abinda ta yi niya, dan haka ya ce" Hauwau, dan Allah kar ki yi abinda zai daga hankalinki ta kowace fuska, ki rike hakan a matsayin kadara da abinda Allah ya hukunta, ki bar yaran nan su shirya kansu, idanma da maganar aurensa ku barni da shi Aliyun idan komai ya lafa zan tado masa fa maganar tunda ai ya san da ita, tsohuwar magana ce, da ba dan shi din Abdallah din da kansa ya nemi da a dakata ba ai da an jima da yi, dan haka ku kiyaye kun ji?" Ita dai kai ta gyada masa, idannuwanta suka sake sauka a kan Amina da kanta ke hade da gwuiwarta , babu wanda ya ji muryarta ko ya gane abinda take ciki, tunda Baba ya fara fada da ta yiwa kanta haka bata kuma dagowa ba, a yanzu haka babu wanda ya san halin da take ciki, Kai ta dauke suka idasa haurawa Kasancewar hankalinsu a gaba basu lura da tsayuwarsa a barin dakin Baba Mai Shanu ba suka yi bangaren Hajiar A hankali ya sake juyowa yana hangen Baba Rabi'u da kuma yarinyar nan Kai ya sake girgizawa ya dago hannunsa dake maiko maiko da warin Man ja ya zubawa ido Page 1 bayan free🥰🥰🥰🥰 *NZL PAGE1️⃣4️⃣* 'shin su basu damu da nawa ra'ayin bane? Basu gane an kawo lokacin da namiji ko mace take da damar rairaya da tankada dan su dauki abokin rayuwar da suka gamsu zasu iya rayuwa fa shi duk rintsi duk wuya ba?, Shin yaya Baba yake tunanin shi ABDUL RA'UF UMAR FARUK ALIYU UMAR FARUK zai iya gabatar da rayuwar da mace zata bashi dama kafin ya dauki wata macen idan har yana ra'ayin hakan? Yaya suke tunanin shi din nan zai iya wata rayuwa da fitsarariyar nan?, Ganninta na farko da ya yi ana dambe da ita a wajen aikinsa ga yarenta masu kuka, na biyu da harare ta bi shi bai san me ya yi ba, na uku sun tsaya a bakin titi da kato yama zata mijinta ne Lukman ya watsa mata ruwa sakamakon tare hanyar da suka yi ga gefen hagu dinsu babar mota ce da ta shigo titin sosai, shigarsu ruwan ya zama wajibi ne ama ta kama masifa bata ko jin ta gaji harda jefa dutsi da yin Allah ya isa, sai yanzu da ta kwala masa kai uwa birgin bulo, ta cakumar masha riga da kazanta a hannunta karshema wai shi ta daga hannu ko zata yi menene ? Allah masani,itace aka daura masa?, Tabdijan' Dan kara saukowa yake yi yana sake kallon Baba Rabi'u da ya dage yake magana ba ko hutawa, har ya gama yana shirin tashi biyu suka shigo , Husaini yana aikin da ya saba, watau ciye ciye, hasan kuwa hannunsa daya a cikin aljihun shadarsa, dayan kuwa na reto kadan suka nufo wajen Mamansu dake zaune Husaini na fadin" Mama tsaya ki ji, tun kafin ya fada maki karya, na ranste da Allah bani ya yi, nace bana so, bana so ya dage ,karshema yace mai mayar da hannun kyauta baya dan wuta ne, sai kawai na amsa, kafin na kawo miki ne dai na dan bude na taba kadan, kai Hasan tsakaninka da Allah ba haka aka yi ba?" Hasan din ya wani maka masa harara yana cicijewa ya ce" Ka kuma ce min karya sai na fala maka marin mutuwa a gidan nan, sa'anka ne ni wai? Baka wani kin karba ba, na farkonma kana mika hannu kana kallona ne kace Mama ta hanna, shi kuma yace ai Mama amarya ce bata son rigima ba zata yi maka fada ba, sai kawai ka amshe ka kama ci ko wanke ledar ba zaka yi ba, kai dai ka ji kunya!" Baba Rabi'u na dariyar fadan biyu da baya karewa ya ce" Kun ga, yanzu dai ku je wajen Inna tana baya tana kiranku inaga ko me zata ce maku?, Ku je cen daga nan sai ku buga ball kun ji?" Da sauri Husaini ya fara juyawa, Hasan kuwa mamansa yake ta kallo , gannin tunda suka shigo bata dago ta kalle su ba sai ya ji ya kasa motsawa A hankali ABDUL RA'UF ya dan sake gyara tsayuwarsa yana karantar yaron Har Hasan din ya juya ya dan fara tafia, sai kuma ya ga ya juyo ya dawo daa hanzari ya duka kusa da mamansa ya saka tafukan hannayensa biyu yana dago fuskarta Abinda ke jikin fuskar nata ya sinsina sai kuma ya yi murmushi ya kalli Baba Rabi'u ya ce" Har gabana ya fadi na zata kuka take yi" Baban kansa sai da ya ji abin a zuciyarsa, yaro ne fa karami Hasan, ama irin yaran nan masu nacin uwa Dukkan motsinta a jikinsa a ransa, a bayane zaka ga shi din mai bata kariya ne duda karancin shekarunsa, dan uwansa kuwa a bayane zaka fahimci mai bukatar a bashi kariya ne a dukkan al'amarinsa A hankali ta dafe hannunsa muryarta cen ciki ta ce" Fadeel tafi mana" Sake tsura mata ido ya yi, sosai ya so fasa zuwan, sai dai daure fuslar da ta yi ya saka shi mikewa ya tafi yana waigenta Babanma sake mikewa ya yi yana jadada mata kalmar biyayya da hakuri, in sha Allah zata ga ribar abin Ita dai bata ce da baba ufan ba har ya fice a gidan shima Ta jima tana kallon waje daya, sai kuma ta mike tana dingisa kafarta da ta yi tsami ta nemi nufar dakin da aka bata dan ta harhada komatsanta ta san inda dare ya mata tun yau, ba da ita ba wannan rigima, ita? Ina ba da ita ba! "Ke zo nan" ya fada a kausashe yana saukowa gaba dayansa ya nufi babar kujerar dake falon Wani wawan birki ta ja ta ci, ta juyo a haukace cikinta na curewa waje daya Daga sama har kasa ta debo dubansa ta sauke masa kafin ta yatsina fuska ta juya da nufin tafiyarta A kausashe yana tsatsareta da kakausan kallo, muryarsa na kausasa ya sake fadin" KE ZO NAN NA CE!" "Ba ke sunna na ba malan, sunnana AMINA!" Amina ta fada bayan ta juyo ta dafe kugu da hannunta na dama zuciyarta na tafarfasa tana sake kallonsa yadda ya wani hakimce Hannunsa ya watsa irin du dayan nan , da idannuwansa ya yi mata nuni da wajen da yake nufin ta zo ta zauna Sosai ta zo yin tafiyarta, sai dai wani tunani da ta yi cewa ta yiwu ya sawake mata ta kama gabanta ya sakata dawowa ta zauna, ama ba a wajen da ya nuna matan ba tana kafe waje daya da ido Sai da ya sake kare binta da kallo yana ta nazartarta, yannayinta, girman fitsararta ( bai san a kansa kadai abin ke tashi ba ), sai kuma ya kada kai a rarabe ya ce" Kin san bana ra'ayin haka , gana daya hadin bai yi maching ba ko?" Amina ta juyo tana kallonsa, kallo daya ta masa ta dauke idannuwanta tana fadin ' Ni da kaina abin ya kasa zaunar min a cikin kwakwaluwana, wannan wani irin gaurayen abinda basa kamanceceniya ne?" "Ko?" Ya fada yana dan dage girarakinsa biyu "of course, menene ke damun Baba fisabililahi da zai tashi ya dauki kannin bayana ya bani a matsayin miji?" Ta fada wannan karron tana kureshi da manyan idannuwanta Wani irin haushi idannuwansa ke bata, irin kallon kasa kasan nan kamar tsohon kwarto ke bata haushi, bayan shi din bai tafasa bama bale ya kone, irin yadda yake yin kallonsa ke matukar kume mata zuciya da wuya, haka ta yi ta babatun magana a office dinsa ta zatama kurma ne ashe wai yana ji dan tsogon wulakanci da yarinya, ai sai ka yi fito na fito ka rama abinda na fada maka kau? Da haushi haushi ta juyar da kanta tana son jan tsaki, domin har ta hade labanta ta basu kalar turowa kamar za'a saka ribom tana shirin bude su kadan dan iskar da zata samu hanyar shiga ta tsakankanin hakoranta dake cije ta samu hanyar shigewa ta bada amon tsakin ta ci ya ce" Kin san tsaki raini ne, bai dace ka yiwa danka bama shi ko AMINA?" innalilahi wa inna ilaihi rajune, yaron da ya dace ya kireta da aunty ne yau ta yi faduwar tasar da wannan raini mai zafi ke shiga tsakaninsu? Shin me ta yiwa Baba ne? Du datijan dake zagaye da shi ya gaza dauko daya ya bata sai jinjirin da bai wuce goyo ba? , Shagwababen gaban kaka wanda a kansa kakarsa sai ta tada duniya? Uhum, dama Hajia ta kwontar da hankalinta, da ta daina daga hankalinta a kan abinda ba zai kai gobe ba! A kausashe tana mikewa tsaye ta dube shi ta ce" Ka san a kan mutuncina babu abinda ba zan iya yi ba, kudinka ko masu tsaronka ba su zasu hanna na rama ba idan na ga za'a wulakanta min girmana ba!, So kawai mu mutunta junna kowa ya tashi da mutuncinsa, ni dai ka san na girmeka nesa ba kusa ba, rashin sanni ne ya biyo ta nan da mu, yanzu da aka sani farar takarda sai ta sameni a ciki, bana son sa in sa da kai, domin ba mutunci bane ka gane ai!" Irin ta yayaba maganar nan, tana jira a yayaba mata ko ta samu ta sake amayar da takaicinta ta huce, sai ya karra tafka mata abin haushin nan ya sake yi mata shiru kuma yana kallonta Walahi kamar zata fadi ta saka ihun kula ta kama bori daga nan har bakin titi Wayo Allahna wulakancin dan Adam, dan tana talaka? Dan tana marainiya za'a yiwa haka? Juyawa ta yi da karfi karfinta ta nufi ciki, sai kuma ta dawo wuuuuuu ta warci dan kwalinta da ya fadi a kasa ta yafawa kafadunta ta sake hararar gefen da yake zaune ta kuma wucewa cikin dakin nata Murmushi ya yi ya maida kansa baya yana lalubar wayarsa dan ya kirayi direbansa ya zo ya kaishi gida ya yi wanka ya cire kayan maikon nan ko zai dawo cikin hayacinsa, ji yake abin na kama wuyanda sosai walahi, to ita du mayukan duniya ta rasa na shafawa sai wannan? Kai ya sake girgizawa kasa kasa ya furta" Yarinta kennan, kanwar hauka, Allah ya sa kar na karya y'ar mutane kafin na salameta" ( na shiga uku ni sajidede) Amina na shigewa dakin ta ja kofar ta rufe da karfi sannan ta dora hannayenta bibiyu a saman kanta ta silale a jikin kofar a hankali kuka mai daci na neman kubce mata ta ji wata zazafar dankwasa ta sauka a dandin kanta Da sauri ta dago gefen da ta ji abin zuciyarta na yankewa da faduwa da tunanin ko biyota ya yi ta rufe dakin da shi? Harda fargabar ko shine ya rafka mata dankwasar nan? To abu da yaro babu abinda ba za'a gani ba, sai ta ga Baba Lauratunta tsaye a kanta tana yi mata harare irin na fil'azal , harare na usulin kwararru a fannin juyar da ido bakin dake cikinsa ya bace bat farinsa ya tsaya yana mata mar mar mar "Ke yanzu in banda mayar da kai shashasha da neman fitina yarinyar nsn tunda na shafa maki abin nan kika bace min da azuminki a bakinki sai yanzu zaki shigo? Ina kika je kika zauna sai yanzu zan ganki ta nan? Ni me kike son mayar da kanki ne Amina? Gyaran nan inace ke kika koya min kin fini sannin yaya ake yinsa, shine zaki dauki kafa ki je cikin mutane a haka? Kin ganki kuwa? Kin ga da abinda kike kama? Daga ina kike ne?" Baba lauratu da ta biyo ta hanyar nan dan ta katse balin Aminar, domin abubuwan da duka faru babu wanda bata gani ba, karshema da ta ga rigimar ta koma tsakaninta da Sarkin samarin ne ta yi wuf ta shige daki dan ta san daga cen nan zata biyo, domin ta sani ne babu wanda zai risinawa dan uwansa a yanzu Amina dake dafe da kanta ta wani langwabe kai hawaye na ziraro mata ta ce" Aya, da kin san abinda na jiyo da sai kin yi takaicin bata naira dari ukunki wajen siyo madarar nan kika hada abin nan kila shafa min, da kin san abin kunyar da ya tunkaroni da kin tayani kuka Baba" Ikon Allah, Baba ta ayana a cen kasan zuciyarta, koda yake tunda Amina ta wayo gari da kula da kanwarta, da aurar da kanwarta, da rainon biyu ta dauki girman duniyar nan ta dora daman kanta, Amina kamar ita ta yankewa kasa cibiya, a kulun maganarta itace ka samu dan datijonka ka aura ka je ka yi zamanka, sai ga wayewar gari an tashi da Amina da auran yaro kanninta? Shekara fa bata fi daya da ta bashi ba in ta cike dayanma, kuma Aminar in ba karfin zuciya irin tata ba aa hadiye sai Abdul Ra'uf ya hadiyeta da yawun bakinsa ko asuwaki ba zai yi ba bale maganar kora ruwa kar a shake, ita mamakinma fa ta yi da take masa kallon yaro bayan a cike yake kuma ya ajiye saje irin na samari masu ji da kansu da tsafta suka kuma tada kai da yayan banki suka yi asuwaki da kafar dawisu!, Ta yiwu dan shirunsa, da bada amsarsa da murmushi irin na kililin kasau majicin kumba ne ya sa take saurin haye masa? Da ta san sari ka noke yake yana iya zuba mata gubar da zata kaita ga halaka da ta bi komai a hankali ta yadda zata kai ga ci ba tare da ta jigata ba A sanyaye Baba Lauratu ta ce" Allah ya rabamu da abinda kike fada Amina, Allah ya nisantamu da kunya da abin kunya, meye abin kunyar a ciki?" Amina ta ringa kallonta, kallo irin na son fahimtar ko ta san abinda aka yi mata ne? A hankali ta ce" Baba, Hala kin san yaron cen aka aura min?" Sai da baba ta kama habarta, sai kuma ta ce" Ki maida hankali, kin ji? Nace ki maida hankali sosai ki ringa yiwa lamarin nan muguwar fasara ta yadda bakinki zai tabo maki rigima danya, ke yanzu in ba abu irin naki ba mijin naki zaki ringa cewa irin haka? To ki hanzarta hawa ki tarda Mai Shanu mana ki ce masa kul kar ka konani ka kona kanka bana so ka kashe auren nan dan fitsarariya ce ni komai zai iya faruwa , nace ki je ki same shi a cen sama bashida lafiya ki tashe shi ya yi abinda kika yanke kar ya barki da abin kunya!" Sosai Baba abin ya kular da ita, gani take yi wannan din ai rashin hankali ne da rashin sannin ciwon kai A kaikaice take yaba mata magana da fada da sharar fage, domin tana yi mata fadan ta ce da ita" Tashi dan Allah ki shige ki wanke abin nan da sabulu da soso dan kin bata min gyara ga na kwan na hada maza ki fito mu shafa, kin san dai na kwai ba'a masa wasa ko? Da yama zan koma gida kulun da safe na dawo dan dazu mai Shanu ya bada kudin siyayar nan na gyaran jiki dole zan je kasuwa na sisiyo , a kadan ma kusan wata muna yi fa, tashi tashi tashi bana son bata lokaci!" Walahi sai Babar take neman cenza mata a idannuwanta da tunaninta, gyara na kwai? Yaushe ta samu kudin kashe kwaya kwayan yin gyara irin na kwai? Kwan da a kadan a kashe goma cikin madara da kurkum a murje jiki gaba daya da shi shine tace ta hada hadin? Ita kuwa kudin zata lalata hala a wannan abin? Har ta shige bayi tana waiwayen Baba da ta hade gabas da yama, kudu da arewa take jira ta sake daga mata hankali, wankan ta shiga tana tunanin ran Baba ya baci ne dan ta tafi yawo da kurkum a jiki, ta tabata idan suka zauna ta yi mata dala daka zata rakata wajen babban da kanta, dan haka sai ta shiga yi din ______________________________________ Hannunsa yake dan karra sinsinawa dan ji yake yi du irin wankan da ya yi warin man jan nan akoyshi a jikinsa, shi dama baya cin man ja , jin warinsa yake yi sosai har cikin kansa Du irin uban turaran da ya yiwa kansa wanka da shi shi kam yana jin warinsa a hancinsa A nutse yake tafia dan zuwa wajen dining ya dauki coffee ya sha, domin ba zai iya yin barcin a yanzu ba, kansa ya fi komai caza shi a irin wannan lokacin , baya son dogon tunani sam Idannuwansa ne suka sauka a kan MANSUR da RISALA dake zaune a falon Shi MANSUR din shi yake kallo da wani expression a fuskarsa, ita kuma tunda ya sauko ta sada kanta kasa, domin ba zata taba manta lokacin da ta zuwa gidan nan ta tardoshi da kananun kaya sosai irin yadda suka lwashe ba, batama taba gannin namiji mai shegen jin kunyar suturarsa irin ABDUL ba Dan sakw dubanta ya yi , hijab ne a jikinta , sai kafar wandon dake kasa da yake hange daga inda yake tsayen, sai tissu din da take ta faman murzawa wajen hancinta zuwa idannuwanta tana fyace hancin da buga hancin dan kukan da ta sha hancin ya done mata sosai A ransa ya ayana ' Ya Salam, ranar nan gaba dayanta ta hade min da abubuwa sosai, RISALA ta ji ga dukkan alamu, mtssssssss ni kam ba zan iya yin maganar yanxu ba' Da hannunsa ya yiwa Mansur alamar yana zuwa sannan ya nuna masa gajeran wandon dake jikinsa ya juya ya shiga haurawa Idannuwanta ta sake dagowa ta raka bayansa da kallo har ya bacewa ganninta Wani kukan ta barke da shi tana saukowa daga saman kujerar, lokaci daya Mansur na kokarin tausarta da bata hakuri , zai fara magana wayarta ta fara kuka Hannunta ta saka ta dauko dan ta zaci mahaifiyarta ce dake fada kamar zata ari baki tana cen gida tana bambamin sai me? Aure? ABDUL RA'UF din ne ya yi aure tun ba'a je ko'ina ba? Ta dage kan yarta ta rabu da shi ko shine autan maza, tana ta cin alwashin ai su irin kyau ne walahi karyane su yi tsawa, idan ABDUL RA'UF baya yi wani zai yi ta yiwu wanda ya ninka shi sau dubu!, In dai ita ta haifi yarta ta kare da shi, ba zai yiwu ta yiwa kato kuka ba!, Darajarsu ta wuce nan, bata san a irin wannan lokacin tuni yar ta silale ta sadado gidan dan ta fuskanceshi ba, bata san a yanzu daf take da rasa ranta ba, ta yaya mamanta zata yi tunanin zata iya rabuwa da zazafan gayen nan? Komai nasa baba ne, shi din baba dan baba ne, soyayarsa kuwa mai zafi ce, ajinsa kuwa zazafa ne, ita yaya zata iya soyaya da wani bayan ta dandana da shi? Ta sani ne ko wacece, ko y'ar gidan uban waye zata daka ta bara mata shi ne, idan me ta zo da shi gidan ta tarar, RISALA yar gayu sunnanta ya koma ko a kasar amerika bale a kasar hausa, in menene ta taka ta iya ta kware!, Ba zata taba sharing din Abdul ba sai dai ta rikeshi ita kadai, ko wacece ta shirya mata tsaf zata kuma gwabza da ita daga nan har duniya ta tashi in dai sunnada rai su dukansu! Gannin hoton zuciya da jinni kamar yadda ta yi seving din numbersa ya sakata jikinta na bari ta daga ta kara a kunnenta hadi da saurarawa A tausashe ya ce" RISLANAH, plz go, zan shigo gidanku yau, kin san na hannaki zuwa gidana? Nd yanzu bana iya doguwar maganar plz" Daga haka ya katse kiran Tamkar ya katse da numfashinta ne, domin mikewa ta yi tsaye da sauri ta juya wajen da MANSUR ke tsaye ta budi bakinta zata yi magana, sai dai ta gagara yi ta shiga jan maganar da bakinta da hancinta, karshema gaba dayanta ta rike gaban kirjinta ta kifa a wajen da take tsaye hannunta rike da kirjinta, idannuwanta sunna neman kakafewa......... Ya Salam, anya baku dauki lamarin nan da zafi ba kuwa? Happy wkdn mutanena🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰😊 *NZL PAGE1️⃣5️⃣* Gaba daya Mansur ya mike tsaye daga zaunen da yake A hanzarce ya karaso inda ta kife din, da irin abinda ta yi kafin ta ja numfashi ta dauke ya sake rikita shi Hannayensa duka ya kai da niyar daukanta Lokaci daya ya tsaya cak da abinda ya so yi din ya yi baya sannan ya juya da gudu gudu yana haurawa Yana karasawa ya ringa doka kofar dakin ABDUL RA'UF yana ambataon sunnansa ABDUL RA'UF dake idasa bala boturan rigarsa daga sama ya juyo da dan sauri yana sake saurarawa Jin sunnansa a bakin Mansur ya saka shi takowa a dan hanzarce kadan domin irin yadda Mansur din ke ambaton sunnansa lalle zaka san ba lafiya ba Yana budewa Mansur ya ce" Man, me ka fadawa yarinyar cen ne? Ta summa fa, ta summa?" Har ga Allah sai da ya ji kamar kansa zai sarra, Innalilahi wa inna ilaihi rajune, shine abinda yake ambata a kasan zuciyarsa hankalinsa na neman tashi, gaba daya kansa ke sara masa, cofee dinma bai sha ba bale a kai ga hutawa kafin la'asar ta shige 'Summa kuma?' ya saske tambayar kansa A dole ya fito ya bi bayan Mansur yana sauka a nutse suka nufi inda take yashe kafarta daya har a jirge dan bata fadi a daidai ba Duban Mansur ya yi girarsa na karra hadewa sosai na ciwon kai ya ce" Summan ne kuwa wannan Mansur?" Mansur ya dube shi, ya sake dubanta, a hankali ya ce" Na si na dubata da kyau duda ban fito da kayan aiki ba, to gani na yi iya din ba muharamata bace, sannan babu wani da ya bani damar hakan a makusancinta" Kwarai Mansur yanada gaskiya, sai dai shi dinma ai ba muharamar tasa bace, subahanalah, shi yasa kwata kwata baya son irin abinda take son nunawa, ta tashi ya zo gidansa su cewa junna me? So take yi mutuncinta da yake gani ya daina ne? Me yasa ta cika naci a kan abinda bashida wani anfani? Menene ya sumar da ita ne? Sai dai a yanzun ya zama wajibi su bata kula, abin takaicin a kasan hijab dinta wando ne dogo wanda a yanzu da ta fadin gayanan a fili a jikin kafarta ya bayana, shin me yasa yarinyar nan ke wasa da abinda yake dorata a kai? Shi yasa ya dakatar da maganar kai kudi gidansu, yana so sai ya gamsu da ita da tarbiyarta, ama a kulun sake baudewa umarninsa take yi A nutse ya ce" Ya zama wajibi ka bata irin kular da ta dace ai Mansur, kai din likita ne, idan muka ce sai mun nemi muharaminta ya riketanma karshe kai din zaka dubata, ka dubata kawai Allah ya bata lafiya!" Mansur ya yi gagawar fadin" To ai ka kamata mana, ina zaka je kuma?" ABDUL RA'UF ya ce" Zan koma na sha magani ne nima, kaina ke ciwo, nd zafi nake ji har cikin idannuwana" Da kula Mansur ya ce" To wa zai kama min ita?" ABDUL RA'UF ya ce " Ka san ba zan iya tabata ba ko? Kai kana da damar tabata dan talafawa rayuwarta likita ne kai, ni fa?" MANSUR dake ta kallonsa sai da ya ajiye wata ajiyar zuciya mai zafi, dan walahi yarinyar nan ta tsorata shi, kuma bai tabbata ba dan ya san waye abokinsa a kan matsalar kishi, shi fa yakan ce macen dake yafa mayafi wani kato ya kalla ya raya a ransa shi kam ya haramtawa kansa ita, yanzu haka a cikin rudun da yake da Baba Mai shanu ya sheda masa cewa ai maman biyu ce za'a aura masa, har suka je daurin auren a tare suka dawo yana cikin tunanin ra'ayi irin na ABDUL RA'UF, macen da ta auri wani har ta haihu aka aura masa ba da ra'ayinsa ba? Ya san abokinsa na son kakaninsa kamar ransa, ama kuma baya hada ra'ayinsa da na kowa ( kun san shima bai san cewa ba itace uwar biyu ba ) "Duda haka, ka tsaya kana tsaye mana, ka sani ko me ya summar da yarinyar nan yanada nasaba da kai, ka yi kokarin mutuntata kamar yadda ka saba, ka fi kowa sannin irin son da take yi maka, ba karya bane, ba kuma dan abin hannunka bane, so kuma ba karya bane " A hankali ya karra juyawa ya kalleta Idanuwansa ya lumshe, shi kadai ya san damuwar dake daskare a zuciyarsa Dawowa ya yi ya zauna saman kafet din a hankali ya tankwashe kafafuwansa ya mayar da kansa baya saman kujerar ya lumshe idannuwansa Mamaki ke neman halaka shi *SO?* Shima ai yana sonta! Sonta da yake ne ya sa yake hakuri da halayanta, lalle tana kular da shi da bashi haushi, ama ai shi dinma yana sonta To ama..................to ama fisabililahi................... To shi din nan a kan SO ko ciwon yar yatsarsa zai yi ne bale Summa? Wai har a kai ga mutuwa!, So ko wani dalili daban? RISALAH dama mai tsananin tsananta abu ce, ko abinta a gidansu babu mai taba mata, nata fa nata ne, domin ba zai manta wani lokaci da cousin sister dinta ta yi masa wasan cewa mijinsu, RISALA dan rashin wayo a ranar fata fata suka yi da yarinyar, kuma har yau basa magana, a gonakinsa hakan ta faru, ya je kauye ne ya kwana bakwai dan ya bi harkar nomansa da alkhairan gonarsa tace itama zata je kauyen wajen dangin mahaifinta, suka je da y'ar uwar tata, shi tunda ya fahimci karya ta yi ba wani dangin mahaifinta biyo shi ta yi ya cenza mata, kuma sai aka samu matsalar nan Yar uwar tata ke masa irin tsokanar nan, karshema sai shine ya bada mota aka maida y'ar uwar tata, bale yanzu ta ji an aura masa wata? Uhum Yana hakan MANSUR ya ringa zirga zirgar hanyar kicin da wajen da RISALA ke kwonce har na tsayin mintuna kusan ashirin Cen ya ji jan numfashinta, sai kuma ya ji kacaniyar da ya tabata ta kokowa ce A hankali ya sake lumshe idannuwansa dan baya so ya bude ya ga a wani yannayi ta farka da kokowar? Muryar kukanta, da ratsatsin abin da ya tabata na madubin gilas din dake dauke da ruwan lipton da lemon tsami da akan matsa masa mai yawa a ajiye masa dan bukatarsa ta kansa wace shi kadai ta shafa Sai kuma muryar MANSUR dake magana da ita yana ta ambatar sunnanta da fadin ta nutsu kar ta jima kanta ciwo, ta nutsu kar ta yi abinda zai ilatata, ko me ya daga mata hankali idan ta bi a hankali ai zata ji saukinsa Kuka ta kuma fashewa da shi a hankali ta kai zaune tana duka hannunta a saman cinyarta Idannuwanta da suka fara kumbura suntum , sunna dauke da gashin ido gazar gazar masu tsadan nan ta dauka ta sauke a barin da ABDUL RA'UF yake Hannunta ta kai daidai zuciyarta tana murzawa a hankali , hankalinta a karshen tashe ta dake kallonsa muryarta a raunane ta ce" Dama zan ga wannan ranar? Dama zan ji haka da kunnena ? Dama zan wayi gari My man, my heartbeat, my happiness my love ace min ya auri wata? , U'r are mine....ka tabatar min da haka da ka barni na kamu da soyayarka!" A hankali ya dago kansa, jajayen idannuwansa ya sauke a kan fuskarta, muryarsa mai karfin ta balagagun maza ba masu lankwasar harshe irin na launin muryar mata ya bude a hankali ya ce" Kina da matsala!" "What? U say inada matsala? Inada matsala?" " Ki min magana a tausashe, nd ki daina min ihu a kan shirmamiyar maganar nan RISALAH, sai da na ce maki ki koma gida, zan zo shine kika....................." Ya dan nuna wajen da ta summe din irin a rashin damuwa ya sake dubanta ya ce" Ke din ba yarinya bace, ke din ba karamar yarinyar da zata ringa yin shirme bane, ina tunanin kin kai wajen da sai dai ki yiwa wani nasiha da irin abubuwan nan" Ciwo take ji a zuciyarta, da rarafe ta rarafa da saurin gaske da niyar kamo hannunsa dan ta sake nuna masa irin halin da take ciki na tashin hankali Sai dai da sauri ya janye hannunsa yana kallonta wannan karron a hankali ya ce" RISALAH?" Lebensa da ya yi maganar take kallo, jan lebensa mai kama da na jariri take kallo, sajensa dake kwonce da dan madaidaicin gemunsa take kallo, ta san dalilin kiranta da ya yi a haka da kuma janye hannunsa "U knw, i lv u, i really really love u ABDUL, ka san ba zan taba iya rayuwa da kai da wata ba ko? Kai ka san ba zan iya hakurin hakan ba ko? Wacece ita? Soyaya ka yi da ita bayana? Me yasa baka zo ka aureni ba sai ita ka je ka aura? Yar siyasar su Mama ce tace a gidanku ma ta kwana, tace ka zo, ni banma san ka zo ba, tace aurenka ka zo.........ka daina sona ne ban sani ba? Ka daina ra'ayin aurena ne bani da labari? ABDUL ka daina sona ne?" Ta karashe da muryar kuka sosai, muryar kuka mai taba zuciya sosai, muryar dake taba cen kasan zuciya sosai Mansur ya kuma yin yinkurin fita a karro na uku A hankali ABDUL RA'UF ya ce" I said ka zauna tare da mu, domin bana so shedan ya yi tasiri a kaina ta kowace fuska!" "Ya salam" ya fada kasa kasa, shi da kansa shekara daidaidai hudu ya ba ABDUL RA'UF a duniya, taraiyarsu ba ta ya bishi bane dan yana da kudi, taraiya ce ta mutunci, sun hadu a aji daya tun secondary, shi ABDUL RA'UF an sakashi makaranta ne da wuri sosai, sabanin shi Mansur sai da ya kai shekaru kusan tara ya fara zuwa makarantar sakamakon cenje cenjen waje da tsatsauran ra'ayi irin na mahaifinsa, a sanninsa da ya yi, har zuwa yau da suke dinke matsayin abokai ya sanshi da yin taka tsantsan da harkar mata, ABDUL RA'UF nada kyankyami mai masifar yawa, haka kuma yanada kishi mai kargin gaske, Ba zaka taba sannin ABDUL RA'UF shima namiji bane sai ka yi zama da shi mai sunnan zama, kamewarsa ta sa baya shiga irin magangannun samari a kan lamarin mata, ko ya nuna zakewarsa ko ya nunaa yes shima yanada wani abu mai sunna feeling a kan mace Da yawa na masa kallon anya zai iya sakewa da mace kuwa? Da yawa na tunanin da wahala idan yana daya daga cikin maza masu anfani da damar da Allah ya basu dan su mori rayuwarsu ta hanyar badala da ƴaƴan mutane MATA da suka wulakantar da kansu, sai dai basu gane bane, shi din ya fi su more rayuwarsa domin ya guji harkar kazanta yana tanadar zamansa da *WACE ZATA YI MASA LAFABI!* Ko zamansa shi kadai a gidan nan sai da aka kai gauro aka kai mari kafin kakansa ya amince, kai kakansa ko a yanzu yakan yi masa ziyarar bazata, sannan ya ringa bin daki daki dan bincikensa, yakan yi murmushi idan ABDUL RA'UF din ya tsatsareshi da ido yace" Ka daina kallona a haka, ka san yaren zamani ba'a shedarsu, bale kanada masu bugawa bawa gangar shedan?, Shi yasa nake dan dubawa dan na ringa dan tunatarwa cewa idan aka daki layin an tafkawa kai kuskure mai zafin gaske" Sosai ya tausasa muryarsa aa tunaninsa, sannan ya yi iya yinsa dan gannin bai wulakanta lamarinta ba, cikin nutsatsun lafuza ya ce" RISALAH, da ni, da ke, da dukan wanda yake tare da mu bamu isa mu zanawa kanmu komai ba, munada ra'ayinmu da muke iya nunawa da karfin ikon da muke da shi a hannayenmu, a tunaninmu!, Bamu san komai da gobenmu ba, gaibunmu ne, ki kasance iyalina ko akasinsa ban taba zama da ke na maki alkawarin zan aureki na rayu da ke ke kadai ba, wannan kuma damata ce, ni a yanzu bani da isashiyar lafiyar da zan iya bi maki komai daki daki...................." Ya dan dakata yana kallon reaction dinta da son sake fashe masa da kuka, a hankali ya ce" Hey, hei RISALAH saurareni plz..........." Kanta ta langwabe tana kallonsa , dan murmushi ya yi mata a hankali ya ce" I love u too " Kanta ta karra langwabewa sosai tana kallonsa da son gaskata maganarsa A tausashe ya sakar mata da murmushin da ya sakata lumshe idannuwanta da jin tamkar zata dira ta fada masa ta rukunkume shi dan kauna da soyaya, yakan jima bai furta mata kalmar soyaya ba, yawancin lokuta idan ta furta masa yakan ce da ita "ME TOO", Du idan yace da ita I Love u takan adana maganar a kuryar dakin zuciyarta ( kar wanda ya ga laifinta, so ne fa, so ne mai tsanani, wadda na tabata babu wace batada wanda zuciyarta ke yiwa irinsa, sai dai wata ta iya danne shi, danne shin da hanna shi falasa baki dayansa shine alkhairi, domin zamanin namu ne ya zo da kalar gigitarwa!) A hankali yana kallonta shima ya ce" Zaki yi hakuri ki je gidan har na zo?" A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta waiga barin da Mansur ke zaune ta ga gefe daya yake kallo bayaa ko kallonsu, shi yasa mutumen ke birgeta, kuma Allah yana gani a duniya shine mai taimakon soyayarta da ABDUL, domin wani lokacin ABDUL kan cireta kwata kwata a rayuwarsa, idan ta kama Mansur da kuka sai ya shirya su, ita kam da yau zata ga yarinyar nan da aka ce an aurawa mijinta da sai ta shake wuyanta ta kasheta , sai dai itama a kashetan! A hankali ta daga masa kanta, dan ta san tunda yace zai zo din, to fa zai zo din ne, kuma ta san idan har ta saukar da kanta kasa suka yi magana to fa tabas zai saki yarinyar nan, dan itama ta san yana sonta Mikewa ta yi tana jan hijabinta da kyau stiilll tana kallonsa A sanyaye ya ce" *NZL PAGE1️⃣6️⃣* A sanyaye ya ce" wa ya kawo ki ne?" Itama a sanyayen ta ce" Ni na yi driving " Kansa ya gyada yana dan tabe bakinsa, sai kuma ya yi shiru yana kallonta tanai masa byby har ta fice a falon "Why ba zaka ce da ita auren hadaka ne aka yi da yarinyar dan hankalinta ya karra kwonci?" Mansur ya fada da mamakin irin yadda ABDUL ya ki fadin gaskiya dan ya kare kansa a wajen budurwar tasa dan su zauna lafiya ba sai an yi ta jan zancen ba ABDUL RA'UF ya yi dan murmushi yana kallonsa ya ce" A kan me zan zauna na bata labarin abinda yake sirrin gidanmu bayan bata zama sirrina ba?......koda sirrina ce idan abun zai iya haifar da fitina gobe ai zan rufe mata shi, bale auren da ba zai zarce gobe ba in sha Allah?" Da mamaki Mansur ya wara idannuwansa yana kallonsa ya ce" Kamar yaya?" ABDUL ya tsareshi da duban mamakin shima, tabas yayi mamakin da Har MANSUR ke tambayarsa kamar yaya idan auren nan ya zarce gobe, lolz auren na gigitar Baba? Tabas kakansa ya rikice ne a jiya zuwa yau da ya dauko nazawara uwar ya'ya biyu matar da wani katon ya aura ya saki ko yaya ne oho ya maka masa shi ga shashasha!, Y'ar fa ta daga hannu zata sharara masa mari? Shi fa bai taba gannin mai hayaniya irinta ba, bai taba haduwa da ita bata hadasa masa ciwon kai ba, wannan aure na *SA'O'I?*, Uhum....... Bai ce masa komai ba ya ciciba ya mike yana duban hanyar hawa sama ya ce" Barci, Mansur barci nake ji sosai, Ni kam bara na je na ga ko zai samu" MANSUR ya mike shima yana dubansa a lokacin da ya fara hawa ya dan daga muryarsa kadan ya ce" Sai ka sauko zan kalli balll, Hei Man?" ABDUL ya dakata yana juyowa MANSUR ya ce" Ka yi dogon tunani a kan lamarin nan" Murmushi ya sakar masa ya idasa hawa ya nufi dakinsa dan ya huta A ranar kwata kwata bai amsa kiran kowa ba, haka kuma bai nemi kowa ba, Mansur ne da dare da ya fito daga asibiti kafin ya isa gidansa ya biya ya duba Mai Shanu da Hajia, a nan ne ya hadu da biyu , Husain ya fada masa cewa mamansa na daki bata yiwa kowa magana Baba lauratu na shafa mata kwai a fuska karni jirr Hasan kuwa bai ce masa komai ba , ama kuma yau ya dan sake da shi dan yakan dan yi masa murmushi kadan , ama baya yi masa hira Da wannan ya wuce gida zuciyarsa cike da dariyar yar kakanin nasu, Shi Baba Mai shanu yana bangarensa hankali kwonce yana ibadarsa, matarsa kuwa ta kile ta kulle bata kula kowa ta labewarta itama a nata dakin, dan tunda ta shige bata sauko ba, bata nemi kowa ba, danma mai aikin nasu an jima da ita ta san kan gidan fiye da tunanin mai karatu, ita ke kula da abubuwa da dama, dana Hajiar kan bata umarnin a dafa kaza, ko a kiyaye da tsaftar gidanta , da irin cimar Elhajin wadda yawancin lokuta abinda zata ce a girka masan baya son cinsa a ranar sai an yi ya sa a tuka masa tuwonsa da man shanu ya rangada Washe garinma tun karfe tara ya wucewarsa bakin aikinsa, ya sauka a ma'aikatarsa ya shiga aikinsa tukuru, neman kudi a jinninsa yake, baya gajiyawa da mayar da biyar goma, ya fi sakewa a harkar neman kudinsa, a nan nema ya ringa samun kira jefi jefi daga manyan abokanan aikinsa ana masa barkar auren da aka daura a lulube Shi dai yakan amsa kawai idan ya kashe sai ya yi murmushi ya girgiza kansa A haka ya gama ya koma gidansa yauma bai nemi kowa ba, ciki harda kakansa A kadan sai da ya dauki kwana uku, hankalinsa ya kwonta, tunaninsa ya fiafaita waje daya, zuciyarsa ta dan samu nutsuwa, ya ji eh lalle yanzun yana iya zama da kowa su zanta a kan lamarin sannan ya turawa Risala sakon cewa zai zo gidansu a yau, dama su Hajia yana samun sakwaninsu ne daga wajen Mansur, domin summa daina kiransu ya yi Tunda ya fada mata ta tayar da tashin hankalin shirye shiryen tarbansa Du ta hargitsa ma'aikatan gidansu da basu umarnin a dafa wannan, a sauke wancen, har abin ya kular da mahaifiyarta dake binta da kallo Rai bace ta ce" RISALAH, ba zaki yiwa kanki da kyau a lamarin Yaron nan ba ko?, Ba zaki daina rawar kafar nan ba ko? Ke anya kinada zuciya a kirjinki? To walahi bari ki ji ni a kan y'ayana ba ruwana da maganar dukiya ko mulki!, Ko mahaifinku na ga zai sakaku a matsalar da ba itakenan ba zan nema maku mafita mai kyau, sakarcin banza sakarcin wofi" Har RISALAH zata tafi kicin dan ta karra masu maganar idan ya zo yana zama mutun biyu su kawo masa abin tabawa su gaishe shi kafin su tafi su basu waje ta ja ta tsaya A hankali ta dawo ta zauna a gaban mahaifiyarta ta sha kwaliya har ta gaji Hannayen mahaifiyarta ta kamo tana kallonta a hankali ta zauna gabanta ta ce" Mama, dan Allah ki yi hakuri, Mama na san kudinsa, kyansa ko sunnansa ke baya gabanki, na fi maki komai, Abane ke son tarayarmu ko dan sunnansa, Mama ni kuma.......ni kuma ina son shi, yanada halin girma, Mama a samarina kafin na tsayar da shi na jima ina bincike, kin ga yanzu da na tsayar da shi ina mai tabatar maki ya isa da hakan..... Please Mama idan ya zo kar kice zaki yi masa wulakanci a kan maganar aureb naj nasa, ki barni mu yi magana da shi, dan Allah kar ki shiga, idan baki manta ba mun taba yin fada da shi kika yi kiransa kika yi masa fada, Mama tsakanina da shi ne, ama kika shiga kika fatatakeshi, kin ga sanadiyar wannan da kyar ya dawo ya saurareni, har cewa ya yi dan shi bashida iyayen ne zai fuskanci haka? Shi bai maki rashin kunya ba ama sai ya shafa min lafiya.... Please Mama ki bani dama ni na san lagonsa, idan har na sada kaina zai turo a yi maganar aurenmu, ni kuwa na maki alkawarin ba dai ya zauna da wata mace ba ina raye! Mama ba zan je gidan da niyar zaman lafiya da kowace shegiyar dake tsakanina da ABDUL ba!, ABDUL nawa ne, idan ta min shigar sauri sunnanta kishiya uwar gida mai shishigi!, Ni na fi kowa sannin ABDUL dina, ni zan yaki abina.... plz Mama zaki yi min haka?" Sosai uwar ke tausayawa yarinyarta, ba komai ya sa take jin tausayinta ba sai idan ta duba ta ga zazafar soyayar da y'ar ke yiwa yaron nan, a bayane yake ta fi sonsa fiye da son da yake yi mata, a bayane take nuna masa zazafar soyayar da har take ikirarin tana iya mutuwa a kansa, wannan abu shi ya fi komai bata mata rai, idan ta kalli santaleliyar y'arta takan ji damuwa ta lulube zuciyarta, shin wace riba yarinyar zata ci da take kokarin wulakantar da kanta a kan Da namiji? Itafa inda ta rako mata kennan, itafa ba zata dauki irin abubuwan nan ba, shi yasa ko ubansu idan ya zo maraba, in ya tafi ya gaishe su walahi, Mikewa ta yi ta haye sama domin ba zata iya daukan takaici ba, dakinta ta fada ta dauki wayarta ta zauna a bakin gado ta shiga lalubar number HAJIA Hauwau wace rabonta da ita kusan kwana hudu kennan, ta yi kiranta sau kusan bakwai bata daga ba dan kwarai ta ji haushin abin nan, Tana ji lokacin da motoci ke shigowa, dan haka ta mike ta daga window tana hangowa daga sama Cikin rantsatsiyar shada yake sai walwali take ruwan baka sidik da dan zubi na bakin zare da dan rastsin ash color mai haske kadan ba da yawa ba Kafarsa sanye da takalmi kafa ciki ba mai tsini ba, mai daidaituwa da kafar mutun ruwan ash color, sai hularsa mai duhu da dan ash kadan Kayan sun matukar amsarsa, kuma duda shada ce haka ake gannin irin yadda wajen hannayen suka rike hannun taf suka kuma kama wajen kirjinsa kadan Irin tsayuwar da ya yi a jikik mota ya dan harde hannunda daya yana duban agogo ya sakata ayyana magana kamar haka' A kulun idan ya kawo mata ziyara yana gagawa ne ' Kwarai itama ta san sirikin nata ba dai a yi maganar haduwa ba, classs, gayu, uwa uba yan cenji, matsalarsa daya ce da bata tunanin in zai cenza mumunar akida da isa Tana hangen irin yadda Kyakyawar y'arta mai ji fa kyau da isa ke yi masa magiyar shiga ciki, da wani zumbulelen hijabin da ta zumbula a kan mahaukacin lesh din da ta sha, du dan kar ransa ya baci ya mata fadan ya zo da maza ta fito ba hijab, hum, ita gani take yi yarinyar tata ta cika azarbabi a kan lamarin yaron nan, tun bai zama mijinta ba yana dora mata dokoki haka ina da ya aureta? Lebe ta ciza kadan tana amda salamar Hajia Hauwau fa ta yi mata a nutse, a hankali kamar yadda ta saba magana idan zata yi in ba bali za'a yiwa dan tsoho mijin arziki ba Bakin gadon ta koma ta zauna itama cike da nata ajin ta ce" Kwana biyu Hajia?" Hajia Hauwau ta dan yatsina fuskarta daga ringeshen da take tana mamakin isa da raini irin na matar nan, in ba dan abinda take hangowa na harkar siyasar jikanta ba har ta isa ta ringa kiranta har sau bakwai bata amsata ba?, Shi yasa itama yanzu ta ki amsata sai da ta mata kira na biyar tukunnan A takaice ta ce" Fine " ta ja bakints ta rufe Wayar ta sake kallo, ta tabata hajiar ce sai dai irin yadda take bata amsa ya tabatar mata ko yayane hajiarma ta shaka Dan haka wannan karron sai ta dan sasauta ita mahaifiyar Risalar din a hankali ta ce" Hajia kennan, sai labari ya zo min na auren HONORABLE ko?" Hajia ta dan mike zaune daga ringeshen da take tana duban agogo, har karfe shida na yama ya shige dare na son sanyo kai ta ce" Uhum " ta kuma jan bakinta ta kyale To in ba rashin mutunci irin na uwar RISALA ba ita har ta isa ta wulakantata? Me take takama da shi ne wanda ita bata malaka ba? Kai idan bincike ko bibiyar asusu za'a yi ta dameta ta shanye a ya'yan banki da kuma hawa manyan motocin, dan ana wani lalabata saboda y'arta sai ta ni rainawa mutane wayo? Maganar siyasarma ba wai ana tare da su bane dan su din zasu bada wani abin, an hada karfi da karfe ne dan a cimma matsaya guda, mijinta shine dan siyasarsu shi ya kawo maganar ABDUL RA'UF din da nufin da zai amince da shi suka tsayar a takara, ABDUL din da har yanzu bai zauna sun zanta a kan maganar ba ya dai saurara ya yi shiru ne, shine zata wani dauki kanta ta kai inda Allah bai kaita ba? Ita yau mace ko ita ke ciyar da ita ai na zata dauki salon wulakanci ba, ta kama kanta dilla tun kafin ya gudu ya barta! Hajia ta sake gyara zamanta ta ce" Hajia sai nake gannin kamar ranki ya bace bayan ni aka wulakanta ni ya dace raina ya bace na yi dogon fushi a kan lamarin?, Kina gani fa irin wahalar soyayar da RISALA ke yiwa ABDUL, ama fisabililahi sai dai mu ji a duniya wai ya yi aure? Wannan wani irin tashin hankali ne, a kan maganar summar Risala biyu Hajia, yanzu haka bata cikin hayacinta, baban damuwarta maganar aurensu da kuma sakin yarinyar dan ba zata iya zama da ita ba a matsayin kishiya ba Hajia" Hajia ta mike tana bude kofarta ta dan shiga takawa kafarta sanye da takalmin bakin bed wanda take dan yawatawa da shi a cikin samanta bangarenta zuwa na mijinta ta ce " Ai a ranar da nake kiranki mun yi maganar da mijinki ne, yanzu haka mun gama maganar da shi kawai, kunna iya zantawa idan hakan ya yi fine, idan bai yi ba sai a hakura kawai dan bana ciki da abinda zai taba mutuncina da girmana !" Tana dasa aya ta katse kiran tana jan tsaki hadi da fadin" dan ubanki nada kudi sai me? Mijin naki da kike takama da shi yaron jikana ne, kuma ke din a kadan na baki shekara goma a duniya! Shine sai ki ba kanki damar raina ni? Ko mijinki karya yake ya san wacece ni kuma yana min *LADABIHHHH* dan ya samu abinda yake so a duniyar siyasarmu, da ake mutuntaki dan ana tunanin yar mutuncin kike, bayan wannan ABDUL yana iya daukan yar gidan ubanda yake so ba za'a hanna shi ba, kin yi kadan mu yi maganar cikin gidana da ke, duma abinda aka je aka fada maki hakan ne! Nonsence kawai!" Tana yi ne tana saka hannunta da nufin tarda Mai Shanu a yau, dan ta tabata ko meye ya kwontar masa yanzun A bangaren Hajiar kuwa sakalau ta yi da waya a hannunta cike da mamaki Da sauri ta shiga lalubar number mijinta Tana fara ringin ya daga dan shi din baya wasa da lamarin matar tasa, Hankalinta a dan tashe ta shiga labarta masa komai, har kiran da hajiar ta yi mata kwanaki bata daga ba, da zuwan ABDUL, da kuma yadda suka kwashe da hajiar Da mamaki ya shiga balbaleta da masifa, abinda yakan jima bai yi mata ba, domin sai ta yi laifi dari bai kula ba sai idan abin ya girmami tunaninsa yakam fadanta a kai Yana fadan ne yana salalami ya ce" Na rasa yaushe wannan girman kai naki na dan Aba yana da kudi zai barki, ki sani gaba da gabanta ne a rayuwa, kuma ko dan bawa ya ci ribar zama da mutun zai sasautawa kansa wasu abubuwan, ke na tambayeki meye ribarki a cikin nan? Kin sani ne idan kika matsa kika raba RISALA da Honorable kece sha wuya, domin a yadda kike da son Yar nan sai kin fi kowa shiga uku, dan kin san RISALA tana iya rasa ranta a kan HONORABLE, mts ku kam mata kunna bani mamaki, meye a ciki dan ya yi aure? Ke ace aurwn soyaya nema ya yi sai me? Ba hudu yake da damar dauka ba? Ni ina nan ina yakin a karshen watan nan a kawo nata itama ta je ta baza mulkinta son ranta domin itace matar so, ke kina kokarin wargaza min? " "Elhaj!" Ta fada da dan karfi kadan Shima da karfin ya ce" Na maki shiru na rufe maki baki kar na maki ihu ko?, To sai na maki ki gyara ko ki kwaba tuwonki ne, abinda zan tabatar maki shine kece da asara a wannan gem din, shi yana iya daukan wasu ukun bayan bazawarar da aka maka masa, kawai baku yin bincike a kan magana sai ku hau ku zauna? Ki yi kokarin matse lamba ta bangarenki kema ta yadda yaron zai turo a wuce wajen kin ji abinda na fada maki!" Kitt ya kashe kiran Wani gauron numfashi ta sauke mai zafi ta zubawa wahe daya ido Sai kuma ta mike ta dauki mayafinta dan yololo ta yafa a kanta zuwa kafadarta ta karra fesa turare ta juya ta shiga saukowa cike fa takama irin tata da isarta da nata ajin Tunda ta sauko sau daya da ya kalleta dan ya gane ko wacece bai sake yi mata wani kuraren kallo ba, ko dan rashin yalwatacen rufa ne? a mutunce ya gaisheta sannan ya dakatar da katse latsen wayar da yake yi dan bata girmanta Sosai ta fuskanci zaman nasu, da kuma karantar fara'ar dake kan fuskar yarta Ajiyar zuciya ta sauke, da kalar nata makircin itama dan ta kai ga ci a karro na farko bayan a kulun takan nuna ya bar yarinya ta hau kan nata ra'ayin da nata tsarin, ama a yau sai kunnayensa syka tsinci maganarta tana dan basarwa da dan murmushi ta ce" Ur excellency, ina fata ta sanar maka cewa na hannata maganar saloon ko?, Ai ni ban san wai hannawa ka yi ba, in ba shirme irin na RISALAH ba a kan me zata yi bayan ka hanna?, Ke da ake maganar turo da magabata a yi maganar aurenku kin tsaya shirme ne? Haba baby ai na yi mata fada tace zata baka hakuri ba zata kuma fita shagon ba, to mema ake yi da wani shago bayan ke din kece zaki kasance uwar masu gida? Uwar gida kuma amarya ke daya kwalin kwal?" A yanzun kam a dan fuzge ya dan kalli mahaifiyar Risalar, sai kuma ya dan kalli RISALAH Bai ce komai ba ya sake maida dubansa kan TV din dake kunne ama ba amo ko daya dan yana zama ya dauke amon baki daya, ya dan yi murmushi yana ayanna abubuwa a kan irin expression din dake saman fuskarsu baki dayansu Mahaifiyar Risala ta sake yin dan murmushi ta ce" Uhum, Elhaji mace ba, yaushene za'a turo a yi maganar? Abanta yace idan ka zo a yi maka tambayar" Sosai kunya ke son kama shi, mahaifiyarta? Lalle, ita kuma mamaki da farin ciki ke neman lulubeta, ta sake sinne kai ita ala dole kunya take ji bayan baban burinta shine ta mike ta kwaso shokiiiiiiiii gannin yau mahaifiyarta ce da kanta ta sauko a kan lamarin Abdul? Lalle ita kam alhamdulilah Sai da ya gama yanke abin fada sannan ya dubeta a tausashe ya ce" In sha Allah karshen watan nan" Daga ita har ita murna da farin cikinsu kasa boyuwa ya yi, kafin uwar ta mike sai da ta jadada koda an kawo bata so ya wuce sati biyu domin su sun jima da suka shirya Shi kam bai sake cewa komai ba har mahaifiyar Risala ta idasa hawa ta tsaya ta harde hannayenta tana murmushi mai daci a bayane kasa kasa ta ce" Ba takamarki jikanki ya isa ba shi wani ne ko Hajia HAUWAU? , Lalle sai ganninsa ya gagareki, takamar da kike yi da kudi kuma ya zamto maki tarihi!, Ke haye kika yiwa abin dole ya gigitaki!, Zaki gane cewa da ka haifi gwamna da matar gwamna gwara ka haifo matar gwamna!, In dai mice yar gifan Badasi fulasta sai na rabaki da ABDUL RA'UF kina ji kina gani daga ke har tsinaniyar da ya aura din!" To fahhhhhhhhh ana dara ga dare ya yi.......wata cakwakiyar wata rigimar, fitina kala kala, To kai da ka yanke lokacin kawo aurenka AMINAR ta yarda ne?🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️ Uhum ku mu je mutanena🥰🥰🥰🥰 *NZL PAGE1️⃣7️⃣* Ya dan karra kamar minti goma yana sake amsar kalaman soyaya har ya ji kansa ya fara daukan caji sannan ya mike da niyar tafiya Kamar yadda ya saba baya zuwa gidan bai bar kyauta tautunci mai saka farin ciki ba hakan ne yauma, ya ajiye chek ba dan sunna cikin rashi ba ko wani abin, ya sabarwa kansa irin haka ba dan a so shi dan hakan ba, sai dan ya kasance mai yin kyauta a kowani hali, ba iya su yake yiwa irin hakan ba, nasun dai na zuwa ne da karrin jadada mutuncinsa Har bakin mota ta rako shi, bayan ya bude ya shiga baya ya zauna ya waigo barin da take tsaye tana murmushi Murmushin ya yi mata a hankali ya ce" Kin tabata kin daina maganar shagon ki?" Sai da ta yi dan tsai, sai kuma ta gyada masa kai da sauri, dan ta san ko menene mahaifiyarta da ta fi kowa tsayawa kan maganar neman na kai ta kuma aikata haka da dalilinta, ta tabata ko menene zata samu gamsuwa idan ta koma yanzu, dan haka ta amsa shi da kwarai hakan ne Murmushi ya yi a hankali ya furta" Good night an mata" Itama murmushin ta yi ta ce" I love you My Man" Sai da ya lumshe ido da kalar nasa salon sannan ya furta" Me too" Daga haka ta ja baya kadan suka tayar da motar suka fice da mota uku cif masu kudi na garari, yana tafe da yan rakiya ne dan ya tabata zasu cika dare a yawo yau, domin daga nan kauye suka nufa da daren nan kuma a cen zasu kwana Tana tsaye sai da suka bacewa ganninta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya tana murmushi, sai kuma ta cire hijab din tun daga tsakiyar gidan ta shiga dan gudu gudu ta shige falonsu Hango mahaifiyarta zaune da chek din da ya ajiye a gefenta ya sakata karasawa da gudu ta rungume maman nata ta baya tanaa daria ta ce" Thank you mama, thank you love, ni na san zaki so shi, ni na san babu wanda zai ki ABDUL dina Mama, ni na saj zaki so shi watarana" Uwar ta yi murmushi tana janyota ta gabanta kamar wata yarinya karama ta ce" Ba tsanar Abdul dinki na yi ba baby, wasu halayarsa na iko na tsana!" Risalah ta ce" Mama, ki masa uzuri da maganar ikonsa, yana da damar yi mama, ki masa uzuri, ni kam ikonsa na daya daga cikin abinda ke karra sakani sonsa a zuciyata Mama " Baki ta tabe ta dauki takardar ta sake duba kudin, Kafadunta ta dan daga, ba maganar godiya ko nunawa yar ya yi bajintar da ta isa a gode masa, dama bata koya mata haka ba, ko duniya zai bata bata koyaa mata gannin wani abin a zo a gani ne, yau ta fara kama kudi ne? Yanzunma hakan take a dan takaice da isa da basarwa da nuna kudin har wani abu ne ta ce" Za'a karra injinnan gyaran jiki a saloon dinki da kudin nan" Tsare uwar ta yi da kallo ta ce" Saloon kuma? Inace kin ce an daina?" Da mamaki ta kalleta ta ce" An daina? Why za'a daina?" RISALAH ta ce" Mama yanzu fa kika cewa ABDUL an daina ?" Yatsina fuska ta yi ta ce" A daina? Kina bani mamaki Risalah!" Da wani mamakin ta budi baki zata sake yin magana uwar ta daga mata hannu ta ce" Look, ki ci gaba da nuna masa abinda nace muna kai a kawo a daura auren, kafin a daura auren ki tare kanwarku zatana zuwa saloon din ta kula da shi, idan kika zauna a gidanki kika mayar da ABDUL mutun ya zamto ba zai iya rayuwa ba sai da ke sai ki koma bakin aikinki ki nemi kudi Hajiata, idan baki da shi ko a cikin yan uwanki kece koma baya bale a duniya!, Ki rage kulafirci da shirme a kan da namiji!" Tana gama fada ta mike ta haye da takardar kudin, ita kuma ta rakata da kallo Sosai hudubar ta shigeta, da kyau kuma ta rike a ranta cewa dan ta yiwa Abdul karya dan ta samu cinma burinta ba laifi bane!, Haka kuma kudin nan da ya ajiye bata bishi da kalmar godiya ko Addu'a ba, daga naa wayar ta dauka kawai ta shiga tura masa kalaman soyayar da ta san da wahala ya mata replay ko ya bata amsa a takaice kamar haka" Thanx " Ama bata damu ba, ta san yana sonta, shi kawai ka barshi da nauyin bakinsa ( uhum hajiata ana yiwa wace bata isa bane nauyin baki walahi!) Yana zuwa gidan kakanin nasa sai da ya kusan minti goma sha biyar da ma'aikatan gidan sunna dan zantawa, bale mazan, matan da Hajia babar ma'aikaciyar gidan kawai suka zanta Sai da ya gamsu da komai sannan ya shige ciki Tunda ya shigo ya ga wayam ya samu kansa da sakin murmushi da tunanin kennan ba'a shirya ba tunda ba'a zaune a falo kallon dare kamar yadda aka saba Juyawa ya yi ya nufi hanyar hawa ba tare da ya kallo bangaren dakinta ba , kai ko a kansa hakan bai shigo ba sam Muryar Farid dake rusa kuka ya saka shi dan saurarawa da fara hawa ya yi tsai da tunanin kukan yaro kuma? Har zai sake hawa ya jiyo magana kamar haka "Wayo Allahna na shiga uku, Mama idan kika zane shi hala nima zaki zane ni? Mama dan Allah kar ki zane mu , ni jikina ruwa yake yi ya yi ta ciwo shi yasa bana son duka!" Muryarta ya tsinkayo tana fadin" Malan yi min tsittt da bakinka ko na farfasa maka jiki, kai Hasan zo nan na ce, yau zan ga uwar taurin kai da rashin ji a gidan nan, ba dai kulun a kan haka zamuna yin fada da kai ba? To yau jikinka ne zai fada maka!" A hankali ya saurara ko zai ji muryar wanda ya tabbata wannan yaron ne mai zuciyar nan, watau wanda ya birge shi a ranar da suka watsa masu ruwan kwata, Sai dai jin shiru ya saka shi dan juyowa a hankali ya sauko kafarsa daya ya kara saurarawa Jin karan saukar bulala da fasa ihun Husaini ya saka shi karra sauka da dan sauri ya karasa bakin kofar ya dan saurara yana son jin da gaske dukan yaron ne take yi ko me? A lokacin ne ya ji muryarta a hankali tana fadin" Ba zaka fahimtar da ni ubanda kake aikatawa a ajin ba ko Hasan? Watau ba zaka yi magana ba sai dai na kasheka ko?, To yau ni da kai a ga wanda ya fasa, kai kuwa Husaini idan bakinka bai min shiru ba sai na fafasa maka shi a wajen nan" "Wayo Allahna na kyale, Mama na kyale, Mama ki barshi haka kin ga baya wasa baya yin komai a ajin, nima ban san me yasa yake zuwa na buta ba mamanmu" Sake jin saukar bulala da karanta a kam wanda yake tunanin ake duka ya saka shi dora hannunsa a saman abin budewar a hankali ya bude kofar sannan ya dan guara tsayuwarsa ya leka dubansa dan so yake ya fahimci abinda yake faruwa, haka kawai yake son daina jin saukar bulalar kamar wani wanda abin ya shafe shi A tsaye take ta ba kofar baya, jikinta sanye da wando irin budaden nan sosai, domin iya kugunta kadai wandon ya rike kuma kalar ruwan madara ne, harda yar igiyarsa da bai san bata daure igiyar bane take reto ta tsakankanin kafafuwanta ba ko menene? Sai kuma rigar dake saman wandon ita ba budadiya ba ita ba damamiya ba, kuma hannu daya a yanke daya har tsintsiyar hannun, kanta sanye da hula ga bulala a hannunta tana rike da kugu da hannu daya ta saka yara a gaba tana cin zali Daga bulalar ta yi tana fashewa da kukan da ya kusan sakashi fashewa da daria, domin tana dagawa doka masa zata yi ama fadi take" Au baka tausayina? Na dake kan ko? Na mutu ko Fadeel? Na dake ka ba zaka yi min magana ba ko fadeel? To bara na karra maka idan na farfasa maka jiki ai shikenan!" Kukanta take yi bilhaki, ga kuma yaron jikinsa na rawa kuma yana so ya matsa jikinta ama ta ki bashi dama dan ta san idan ya rukunkumeta an kare ba zata dake shin ba Shigowa ya yi gaba dayansa yana sake kare masu kallo , a makoshinsa ya dan yi gyaran muryar da ta sakata juyowa a zabure dan bata san da an shigo dakin ba Ido ya zarro sakamakon yelow din kwabin kwan da ta shafawa fuskarta da tumaturi ya bushe mata ga kuma hawaye na zarya a kai Hannunsa ya kai wajen bakinsa yana dan sake kallon fuskar da nan take yake karantar shirye shiryen tafka masa fitsarar ake yi A hankali ya mika hannunsa wajen da Hasan ke tsaye bayan ya cire dubansa a kanta yana kallonsa bai yi masa magana ba, yana nufin ya zo wajensa, dan ya tabata yadda yaron ya cika hadiye harshe kalamansa na fita ne ta hanyar motsi da hannayensa ko yannayin idannuwansa Da sauri ta saka hannunta tana share hawayenta hadi da rarumar hijabinta ta zurma a jikinta tana hade fuska ta ce" Malan ya haka da shigowa dakin mutane ba ko salama, Allah dai ya sa lafiya?" Bai ce da ita uffan ba, a hankali ya sake rage tsayinsa ta hanyar dan dukar da gwuiwoyinsa kadan yana sake duban yaron da haka kawai yake ji yana so ya zo gareshi, sannan ya sake mika masa hannayensa duka biyu yana kallon fuskarsa da yannayinsa Hasan din dake ta haki ua ya cira dubansa ya sauke a kan fuskar Mamansu da ta cire kai ta turo baki gaba yadda ka san wata yar baby ita ala dole fushi take yi ya sake kallon ABDUL RA'UF wata ajiyar zuciyar na kwace masa , ya kalli hannayen ABDUL RA'UF din da kallo irin na nacewar nan sai kuma ya sake sada kansa yana ta wani iri shi ba kuka ba, shi ba hakin summa ba A hankali ABDUL RA'UF ya dantse lebensa na kasa yana sake kallonsa, bai janye hannunsa ba, haka kuma bai daina yi masa tausasashen kallon ba Tun Hasan na cire dubansa a kansa har ya dawo ya tsayar da duban nasa a kansa, sai kuma fuskarsa ta ringa nunawa, a hankali a hankali ta ringa wani irin shagwababewa, a hankali kuka ya kwace masa ya daga kafarsa da sauri ya karasa ya fada jikin ABDUL RA'UF ta hanyar shigewa cikin hannayensa ya rungume shi a cikin kirjinsa yana murzar fuskarsa a gaban rigarsa Daga ita har Husaini ido suka zarro na mamaki Matsanancin mamaki ne ya kama su na gannin a yau Hasan hankalinsa ya kai kololuwar tashi ya doshi wani mutun daban dake bako a gareshi Shi husaini kasancewarma tsoron mutumen nan yake tunda ya ganshi sau biyu baya masa fara'a na farko a office dinsa, na biyu a bakin layi ya sa ko a yanzu da ya shigo da sauri ya labe a bayan mamansa , gwara maman tasa ta masa dukan mutuwar kawai da wani bako ya daki banza!, Sai ga Hasan, Hasan dai Fadeel nasa, Hasan na gidansu ya rungumi wannan mutumen marar fara'a A hankali yake shafa kansa da ya fara tara suma yana jin kukan yaron a ransa Idannuwansa ya dago dake risine a bayan yaron ya sauke mata duban da zata fasara na ta ji kunya ne? Ko kuma shashasha ne? Ko irin kamar ta sato ɗan nan ne? Ko na zalinci ne? Ita dai duban gashi nan kala daban kamar na wata yar kidnaping, bayan shi din nan ba dansa bane, ya tardo mace da danta ya yi mata ba daidai ba? Lalle yaron nan ya cika raini da wulakanci ! Abinda take ayanawa a zuciyarta Bata ankara ba ta ga ya mike tsaye da Hasan ya daga shi sukut a jikinsa ya juya mata da ɗa zai tafin mata da danta Daga iya har Husainin ji suka yi kamar za'a tafi da rayuwarsu ne, dan haka da sauri ta biyo shi daidai ya sake bude kofar zai fita tana fadin" Ya haka wai, bani dana mana Malan!" Dan dakatawa ya sake yi ya juyo yana kallon fuskarta hadi da yatsina nasa fuskar, domin walahi karnin abin ke dukansa, shi ya rasa me ke damun yarinyar nan da take yaba abubuwan wari a jikinta haka, meye anfanin abubuwan nan ne? Wannan din dake jikinta sai wani iri ya mata da ta sha kukan ama bata kyankyami tana wani dakewa da fuskewa abinta Wajen da takardu ke ajiye biyu ya kai dubansa Da Hasan din a kafadunsa ya juya ya dauki takardun sannan ya janyo kofar ya rufe ya yi gaba da shi a jikinsa ya nufi sama wajen Baba Amina dake ji kamar zata haukace dan gannin ya fa tafin mata fa yaro sai da suka bude suka fito ita da shagwababenta, sai dai inda ta ga ya haura da ɗan ya sakata komawa tana sakin ajiyar zuciya tana rike da hannun Husaini taf a hannunta suka zauna a jikin kofar Husaini ya kwontar da kansa a hankali jikinta yana fadim" Mama Hasan fa? Zai dawo ne?" Kai ta gyada da sauri murya a rarabe ta ce" Zai, zai dawo, zai dawo in sha Allah, muna jiransa zai dawo ka ji? Mu yi jiransa a nan" A hankali ya saka hannunsa ya tura kofar ta Baba sannan ya shiga da salama Tunda ya shigo gabanta ya kwonci kwonci ya fadi abinda ta gani a rungume a jikinsa *NZL PAGE1️⃣8️⃣* Tunda ya shigo gabanta ya kwonci kwonci ya fadi sakamakon abinda ta gani a rungume a jikinsa Kureshi ta yi da ido, dukkan farin cikin da ta kwasa na rarashin mijinta da ta yi da kyar ya saurareta suka sasanta kansu, da kuma jin dirar motocinsa ya nemi bacewa battt A hankali ta sauke dubanta a wajen da ya ajiye yaron da irin zaman da yaron ya yi sai ajiyar zuciya yake saukewa ga dukkan alamu kuka ya sheka ko meye oho "Aa, subahanalah wannan kamar mai tsuntsaye na hadiyar zuciya, Abdallah ina ka samo Mai tsuntsaye haka ne?" Takardun ya ninke ya ajiye gefen kujerar shima ya zauna saman kujerar yana kallon kakanin nasa irin zaman da suka yi ya nuna masa sun shirya Baki ya tabe yana girgiza kansa da ya tuna irin bali da jama'ar da suka tara masu har ana wani ririke su gaba dayansu "Hum" ya fada takaici na tiko shi, yanzun du irin abinda suka raba da tataro mutane dan a shiga tsakaninsu a yiwa daya magana ana wani rike su sunna iface iface bama kamar Hajia har ya wuce sun mance? Ah to su sun mance sun rabawa duniya abin fada sun dinke abinsu a daka, uhum "Magana fa nake yi bawan Allah nace ina ka samo min mutumen ne na ga hankalinsa tashe?" A takaice ya ce" Wajen mamansa" Sai da ta kusan zabura a bayane, sai kuma ta dane kanta tana kallon ABDUL ddin da son su hada ido hudu da shi dan ta fahimci abinda yake nufi ama ya gagara, domin kiri kiri ya wani basar kamar bai san abinda ya fada da bakinsa ba Sai da ya gama shan kanshinsa shima yana gannin yadda kakansa ya taso ya kama hannun Hasan suka koma wajen zamansa ya raba yaron a jikinsa yana ta yi masa tambayoyin da yaron ya ki fadin koda A ne a cikin tambayoyin yana ta hakinsa dai Gaba daya abinda ya dan birge shi irin yadda hankalin Kakan nasa ya ki kwonciya a kan lamarin yaron, Murmushi ya saki a ransa yana ayanna ' Bafa zai yi maka magana ba, gwarama ka kyale shi' A bayane kuwa a dole ya amshi gaisuwar kakarsa da take ta tankwalowa ya shiga gaishe su gaba daya harda su tambayat yaya Risala? Ya bata amsar tana kalau............., Hajia ta gyada kanta tana sake kallon yaron da ya tsaya mata a wuya , si take ta yi tambaya, sai dai tana tsoron amsar da take iya samu a gaban mijin nata, bale yanzu suka gama sasantawa da kyar da walahaula da jibin goshi ABDUL kuwa kallon kakansa yake yi har ya ga ya dan rabu da tambayar yaron abinda yake damunsa dan ya ki ya yi magana Maganar anfanin gonar ya fara daukowa yana masa bayani a kan nomar da suke yi da talafin sababin kayan aikin da suka kawo, sunna yin noma ne irin na kasashen da suke da karancin wadatacen ruwan sama ama kuma babu wanda ya kaisu kayan alatu da na anfanin abinci domin sunna anfani da ruwa a lokacin da ba na damana ba su yi noma har su samu anfani mai yawan gaske da kuma gardi, Baba Mai SHANU ya dafe haba yana girgiza kansa ya ce" ABDUL RA'UFu, anya kuwa wannan anfanin gonar yana da inganci kuwa? Kai zamani na tafe da abin tsoro, yaushe za'a yi noma ba lokacin damana ba?" Yar dariya abin ya bashi domin haka suka sha da mai garin da gonakinsa suke , har jiya da ya bugo masa waya haka yake salalami yana fadin dawa ta yi tsayi har ta fito? Jama'a hatsi har ya yabanya? Tumaturi kwonce rututu jajajir rudu rudu? Santin abin dai ba'a magana, wai anya kayan nan ba cutarwa a cikinsu? Zamansa ya gyara yana fadin" zaka sha mangwaro a rani kuwa bana Elhajin Hajia" Murmushi Hajiar ta yi tana hango lamarin, gaba daya a kasar fa yanzu shi kadai yake da budaden kampanin da zaka samu kayan masarufi sabon fita ba dadadiyar ajiya ba, da farko da ta ga yana da nacewa a kan nema ta hanyar nan haka zata saka Mai SHANU a gaba da rigimar ga sana'a su gwal , su waye waye ama ya nace noma da wani kiwo da waye waye? Me zai tsinta a ciki? Sai Mai Shanu yace da ita abinda kika tsinta da kika auri makiyayi, watau shi, A yanzu kuwa har wani salo ake kiranta da shi, uwar mai sana'a goma bama kakarsa ba.....to ita kuwa wannan dadi har ina? Sosai suke dan zantawa tana jefo nata maganar itama, duda bata san dalilin da ya sa za'a bar yaro zaune cikinsu yana cika yana batsewa yana sauraron sirinsu ta hirarsu tsakaninsu ba, ama irin yadda hirar ta dauko dadi ana ta maganar kudi ya sa ta lume take shawagi da sauraron manyan kudade na harkar neman jikanta, kai Allah jikan iyayen yaron nan, su suka faro suka bara masa gadon da ya sake rarabawa yau ya zama haka, lalle da kudi ake neman kudi, ba irin zazabin da bata yi ba da aka bashi gadonsa, ta ringa hauka da iface ifacen a kan me za'a danka masa kudi yana da danyen kai da kadarori yaje a yi masa wayo? Akace da ita harkar gado ba'a mata haka, idan har da rabon ya tara nasa zai tara, ama ba wai a kN gado ba, kar ta kankara hakori da rigimar gado,kayadadiya ce, iska ce mai saurin wucewa Sai da ya gamsu da degrren saukowar kakan nasa sannan a nutse ya ce" Maganar wajen Risalah" A zabure Hajia ta dago tana kallonsa da dan zarro ido, wallahi abin sai da ya daketa, bata taba kawowa kanta zai tunkaro kakan nasa kai tsaye da maganar a irin wannan lokacin ba, ta yaya ABDUL ya aikata wannan shirmamen aikin? ME yasa bai yi mata shawara ba kafin ya kawo zancen? Ta gama daidaita cewa zasu zo da baba Rabi'u a masa zancen sai gashi shi ya masa haka kawai? Baba Mai SHANU ya dan yi jim, sai kuma ya ce" Uhum?" ABDUL RA'UF ya ce " Ina so a turaa karshen watan nan a gama komai ne" Baba Mai shanu ya gyada kansa yana fadin" Masha Allah, masha Allah, kace komai ya daidaita, nan da kwana goma sha shida kennan?, To yaya ina fata Uman biyun ta aminta da hakan?" Tsatsare babban ya yi da ido yana son gane wai da gaske yake abinda yake fada kuwa? Ta aminta? A matsayinta na wa? Shima yannayin sakewar tasa ya fara daukewa yana kallon Baban ya ce" Tana da hurumi a wajen da bata da zabi ne?" "Kake tunanin bata da hurumi a wajen da yake malakinta kafin watanta? " Baba ya bashi amsa shima da tare numfashinsa "Dama dunguru gum canki canka zai zamto malaki? Ko zabin rai kan malaki wani abin ne ba wannan ba, Baba dama akoy maganarta ne?" Ya fada shima yana sake kure kakan nasa da kallon da ya sa Hajia jin kamar ta zurma ihu ta dakatar da su, ama ba hali Baba ya yi murmushi yana gyara zamansa ya yi sak irin zaman da ABDUL din ya yi shima ya hade hannayensa waje daya ya ce" Akoy gadama ne a wajen tafka kokowa? Ko so kake ka ce min ka tsinke zumuntar da na hada ba tare da shawarata ba?" Abdul ya dantse lebensa na kasa da takaicin lamarin nan ya ce" Wai dama cencenta ka hango ? Ta wani fanni kennan?" Baba ya gyada kansa ya ce" Ta fannin da ya fi komai karfi, ta koyi da wanda ya fi kowa daraja, sannan ta dacewar kamarin, ko kana so kace min baka son bak'ar fata yar talakawa?" Hajia ta kalle shi a zabure, dan walahi sai ta ji kamar habaici ya yaba mata ABDUL RA'UF ya sake tabe bakinsa ya koma ya jingina da kujerar yana girgiza kafarsa kadan yana sake tunanin amsar da zai ba baba a dunkule ba tare da danta dake wajen ya ji zafinsu ba, dan gaba dayansu sun yi magangannun nan ne a dunkule dan yaron dake zaune, ba zasu so hakan ya zama wani cin fuska ko bacin rai ga yaron ba, ABDUL RA'UF ya yi murmushi yana kawar da kansa bayan ya gama ayana abubuwa masu zafin da suka fi kona masa rai, shi baba zai wulakanta? Ya dauko bazawara ya maka masa, ya kuma ce sai ya tambayi zabinta idan ta aminta a aura masa wace yake nema? Lalle A hade ya ce" Ladabin ya fi dadi idan aka cikawa kowa burinsa, naka burin ka cika baka cika nawa ba, anya hakan bai zama wani bigiri na danne haki ba kuwa?" Cicibawa baba ya yi daga zaunen da yake ya mike tsaye, wanda hakan ya kayar da gaban hajia ta yi tsuru tsuru da tsoron kar aje abinda ya yi zai sake maimaitawa, sai ta ga wannan karron ya kalli jikan nasa ido cikin ido ya ce" Baka fahimta ba kennan, du wani rikici da tashin hankali da kokowar a mace ko a yi rai na shirya mata tsaf a kan wannan lamari, ba gudu ba ja da baya ciki harda barazanar take hakin na dindindin, ni fa a gobe ina iya zuwa na sake daura maka aure da dayar idan mai wajen ta aminta da haka!, Ita din mataki ce ta tarda naka burin!, Idan kun shirya ta amince zan zartar, in kuwa kanada wani da ya fini yake iya wakiltata da raina da kafiyata kuwa fine, na ga sanarwar a TV ko a redio" Daga nan ya juya ya shige uwar dakansa harda rufowa da ky Sai da ta tabatar da ya gama rufewa sannan ta juyo hankali tashe kasa kasa tana fadin" Meyake damunka ne? Ka kuwa san irin girman abinda ke dawainiya da shi a kan yarinyar nan? Laifina ne da na yi sake take bashi Wainayana ci ba lokaci,zan iya rantsewa yarinyar nan ta asirce min mijina, yama yi kokari da ba kansa ya aurawa ita ba a yadda yake kaunarta!" Da sauri ya kalli kakar tasa, da idannuwansa ya mata alamu da Hasan Sai dai alamu sun nuna sam bata da niyar tausasawa, ita fa dama so take yarinyar ta ji, bata san a bayan kwarya take zuba ruwa ba, dama ace Husaini ne a wajen da ttsaf zai fadawa mamansa, ama hasan? Sai dai ya kulaceta , ba zai taba kaiwa mamansa maganar ba A hankali ya ce" Boy, je kofar daki ka yi jirana ka ji?" Hasan ya gyada kansa ya mike a hankali ya fice a dakin Hajia ta juyo tana fadin" Waima meye hadinka da yaron nan ne? Meye hadinka da shi a ina ka ganshi ka dauko shi? Ka ga ABDUL ka kiyayi abinda ya shafi yarinyar nan, ba kai ba ita ba ƴaƴanta, ina dalili ka sungumi yaron nan har kirjinka ya amsa?, Naa hanna ka, na rabaka da ita ka ji abinda na fada maka!" Bakinsa ya tabe yana girgiza kansa, to shi fisabililahi mema ya kawo maganar wani an hada shi da ita ko an raba shi da ita ne? Wannan duka ba matsalarsa bane, matsalarsa daya ne tak a kan wai shi ya je ya nemi izininta dan zai karra aure? Lalle kakansa ya dauko da zafi A kausashe ya ce" Me yake nufi da ni ne?, Ni zan je na nemi izinin yarinyar cen a kan maganar aurena?, To a fasa auren mana!" Hajia ta dafe haba tana kallonsa ta ce" Auren za'a fasa? Kennan ta ci galaba a kanmu baki daya, ina fada makaa yarinyar nan isashiya ce ta san abinda ta taka, tunda ta zo gidan nan bata taba takowa ta gaisheni ba dan ta san mai gidan na darajata fiye da ni!, Ka ga za'a yi magana da ita!" Ido ya zarro yana kallon Hajia, cece kuce dinta shi du ba shine a gabansa ba, idan ya ji ana neman dangantashi da zuwa ya nemi shawarar mace kan auren da zai yi ke kular da shi Hajia ta ce" ni zan ganta!, Zan bata abinda take kwadayi, wanda na tabata a kansa ta nace babar banza har ta auri kannin bayanta, zata amince ne da kanta, ka bari a yi auren ni na san yadda zan yi da ita!" Dan karamin tsaki ya yi yana mikewa tsaye ya dauki takardun nan dake ajiye ya dubi kakarsa ya ce" Allah ya bamu alkhairi" Hajia ta amsa shi tana sake jadada masa fita a harkar yarinyar da ƴaƴanta, sannan ta fada masa kar fa ya yiwa Alkali fushi, yana yin abubuwan nan ne ba a cikin hayacinsa ba, ita ta sani Shi dai ficewa ya yi a dakin ya shiga saukowa kasa A kusan hawa na karshe ya same shi a zaune ya jinginar da kansa a jikin karfe Zama ya yi shiga a wajen bai ko duba suturar jikinsa ba ya yi shirun shima Sun jima a haka, har sai da ya samu ya ji fushinsa ya ragu sosai sannan ya bude takardar dake ninke ya sake zuba idannuwansa yana nazarta A bayane ya fahimci dalilin da ya sa mahaifiyar yaron ta dake shi Shima abin ya dan bashi mamaki, dan haka ya dube shi wannan karron da yaren turanci ya shiga yi masa magana dan yana so ya fara nazartar yaron ya ce" Ama, kana kallon ina kai ka dauki wannan sakamakon, dan uwanka ya dauki na farko?" Ga mamakinsa, da yaren da ya yi masa magana, da shi yaron ya bashi amsa tamkar yaren shine asalin yaren haihuwarsa Hasan da ya yi kalar zai fashe da kuka ya watsa hannayensa ya ce" Nima ban sani ba, kulun haka nake kawowa, kuma tare ake koya mana komai, kuma ni da na zo zan yi sai bana gannin komai, kulun kulun haka ne" "Kamar yaya baka gannin komai?, Wani irin komai? Rubutun ko harda mutanen? Ko kana nufin baka fahimtar komai?" ABDUL ya sake tambayarsa yana sake kure shi da kallo duda ya fahimci barci ne ke cike da idannuwan yaron Hasan ya ringa tare kwalar idannuwansa yana ta kokarin fahimtar da ABDUL, domin damuwarsa ce da ta fi komai damunsa, sanadiyar wannan mamansa ke yi masa fada, a kan wannan ta sha yin kuka, ta sha zuwa makarantarsu ta yi ta tambaya, bata da hutu kulun tana koya masa, a gabanta yakan shanye komai ya fahimci komai, ama a aji ba hus ba gaba ba baya, shi yasa ta kasa fahimtarsa, har kuka take yi idan zata dake ahin fa tana dukan nasa tana yin kuka ne hakama dan uwansa Du irin kwatancen da yake yiwa ABDUL yana kallonsa ne har yaron ya kifa kansa a gefen kafar ABDUL din yana ta shasheka ya ce" nima ban sani ba, nine jakin ajinmu fa, kowa yanada ilimi banda ni? Kuma Mama sai ta yi fushi saboda wannan" Shiru ne ya biyo baya yana dan shafa sumar kansa mai nuni da rarashinsa yake yi A hankali ya ce" zaka je aski ne mu tafi ?" Dagowa Hasan ya yi ya zuba masa ido, Aski? Wani daban zai kaishi aski ba mamansa ba? Kulun kulun mamansu ke kaisu wajen aski , sai su tarda maza cike a wajen kowa babansa ko yayansa ya rako shi, ama su mamansu ce ke raka su Abinka da yaro, da kuma abinda ya bashi sha'awa sai murmushi ya nemi kubce masa, a hankali ya ce" Ama idan Mamana ta yarda, kuma da Hasan zamu je ko?" Shima murmushin ya yi yana dan kama kuncinsa kubulbul ya gyada masa kai Hasan ya ringa gyada kansa , a hankali sai gashi harda nuna irin askin da za'a yi masu yana murmushi da kada kai ya ce" Nima a makaranta sai na cewa Huzaifa Muma dai Elhajin gidan Papy ne ya kaimu aski ba mamanmu ba ko?" ABDUL ya sake sakar masa murmushi yana sake nazartar yaron A bayane yake yaron yanada ilimi, sai dai shima yana son sannin dalilin da ya sa yaron ke dauko irin sakamakon nan har uwar ke dukansa kamar jaki! Mikewa ya yi yana fadin" Mu je ko?" Hasan shima ya mike din ya sauko sai dai ya ja ya tsaya yana kallon kofar dakinsu ya kasa bin Abdul din ABDUL ya juyo yana kallonsa ya ce" Mu tafi mana?" Hasan ya takwakwabe fuska a hankali ya nuna masa dakin ya ce" mamana, da Husainin fa?" Hannunsa ya kai wajen habarsa ya kama yana kallonsa Dawowa ya yi ya dan rage tsayinsa ya ce" Baka tsoro ta sake dukanka ne zaka koma wajenta?" Hasan ya sada kansa , a sanyaye ya ce" Bata dukanmu fa, kuma wannanma da ta yi sai ta rarasheni ba zata kara min ba fa" Haka kawai ABDUL ya ringa kallonsa yana nazartarsa Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Mu je na raka ka toh" Kai Hasan ya gyada yana murmushi ya shige gaba ABDUL ya bi bayansa Sake bude kofar ya yi a hankali Hasan din ya shige sannan shima ya bi bayansa Gannin wayam basa dakin ya saka shi juyowa, sai ya gansu gefen kofar a zaune a kasa sun yi barci su dukansu,, Husaini a nanike da ita, ita kuma ta wani lankwashe har hijab din ya yaye gana barci da abin nan na fuskarta bata wanke ba 'ikon Allah ita kuma kawai kazama ce?' ya ayana a ransa Wajen bed din ya nunawa Hasan , ya kuwa je ya kwonta yana hangensu Dan gyarawa ya yi ya duka da nufin dauke husaini ya mayar da shi shima saman gadon idan ya so ita ta shekara a nan Sai dai yana kama yaron da nufin dauke shi Husainin ya rukunkume Amina, wanda hakan ya farkar da ita a gigice kuma a tsorace ta saka ihun tsoro tana dadamke hannunsa hadi da cakumarsa lokaci daya tana fadin" Kwartttttttt 😂🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️😌 kwar me? Mun shiga uku mu dai😂😂😂😂😂😂 Salam alaikum😍😍😍😍😍 *NZL PAGE1️⃣9️⃣* Furucin da ta yi na farko ya saka shi saka hannunsa ya janye nata daga jikin rigarsa sannan ya dauke yaron da ta rukunkuma da karfin da bata san daga ina ya janyo shi ba ya je saman bed din ya dora yaron sannan ya yi tsaye yana kallonsu, kamaninsu daya yaren, harta fatar jikinsu mai haske ce sosai, babu wani abu da suka yi na uwar, shi dai bai gani ba Kallon da yake masu ya saka Hasan sakar masa murmushi yana lumshe idannuwansa barci na dauke shi Murmushin ya yi shima ya juyo ya kama hanyar fita A tsaye take sai zaro idannuwa take yi kamar zata fashe da kukan takaici har ya bar dakin sannan da gudu ta nufi yarenta tana duduba su da magangannu kasa kasa tana jan tsaki hadi da fadin" Shirmen banza yaro zaka daukar min d'a ka tafi da shi ba ko ra'ayina dan ba'a san soyayar da da uwa ba, ko kashe shi na yi akoy mai magana ne?" (😌 Aa hajia mai sannin zafin haihuwa🤣) Yana fitowa suka yi ido hudu da Hajia, wace dama tunda ya zauna da Hasan take tsaye a sama tana hangensu Fuska ya sake hadewa ya fice gaba daya a gidan ba tare da ya tsaya ya ji wani zancen bama Da ido ta raka shi , sannan ta je ta saka hannunta for the first time ta bude kofar ta shiga tana karewa Amina kallo wace ta dago da sauri da tunanin ko shi din ne ta yanka masa kashedi a kan wannan abin da yake son bilowa da shi Gabanta sai da ya fadi, ta ji kamar zata summe da ta ga Hajia, tunda ta zo gidan nan anya sun wani hadu kuwa? Hajiar kuwa kallon sama da kasa ta yi mata ta kare nazartar ba wani abinda yaronta zai ci da yarinyar nan sannan ta tabe baki a dake ta ce" Gobe, karfe goma, ina son ganninki a bangarena" Bata tsaya ta ji amsarta ba ta yi tafiyarta ta bar Amina cike da tunani da fargaba kai harma da tashin hankali kala daban daban Sai dai abu daya ta fi barawa ranta shine zata amshi takardarta ne a hannun Hajia, domin ta fi kowa sannin Hajia itace babar makiyar hadin nan, bata san tana gaba tana biye da ita a baya bane, da ace idan ta je a goben nan takardarta zata bata da sai ta fi kowa yi mata adu'ar gamawa da duniya lafiya! A kan kari take A kan gaba take Abin nan na girmamar tunaninta da kwonciyar hankalinta Da kyar ta iya yin wankan da siracin lalle ya kamaa fatarta sosai sannan ta murje jikinta da dadadar humurar da Baba Lubabatu ta siyo, batama san a ina ta siyo humurar ba, ama tana tunanin Humurar daga garin maradi ta saka aka kawo mata ita, ta hadu iya haduwa, ta dai ji a laluwai tana maganar humurar Ramira harun, matar ta iya humura wai ba tsada ga dadi da kwontar da hankali (ku tuntubi Kwatena dan karin bayani a kan humura mai kkarko) Yayanta ta rungume bayan ta yi masu addu'a sannan itama ta yi ta neman hanyar da barcin zai dauketa Da kyar dai ta samu barci barawo ya yi awon gaba da ita tana ta jan numfashi da sauke ajiyar zuciya Kamar yadda Baba Lauratu ta auri yin safiya tunda aka daura auren nan hakane yauma Sai dai yau ta tarar da Aminar tuni ta kwaba Lalen hausan ta shafe jikinta da shi da hadin madarar tana zaune ga dukkan alamu har ruwan nata sun tafasa Farin ciki ta ji a zuciyarta ta koma da kanta ta juyo ruwan sai turiri suke ta kawo mata ta ajiye mata sannan ta rufa mata bargon ta shiga yin siracin hayakin na ratsa mata kofofin fatar jikinta tana lumshe idannuwanta dan sosai hayakin ke tashi Sai da ta gama siracin ta shige bayi ta yi wanka ruwan ya sauka da lallen ta dauko tawul biyu masu duhu da suka ware tunda suka fara gyaran jikin ta lulubo ta sake fitowa Kwabin Nescafe da kwai da madara ta bita da shi, wannan karron ta yi ta murzawa a jikin nata sosai abin na kama mata fatarta sosai har sai da ta gamsu sannan ta sake shafa mata shi wannan karron ya yi lumbuk sannan ta shiga yi mata na gashin shima sala sala sunna bi har kwan ya bushe ta sake komawa bayi Kafin ta fito Baba ta tatare komai ta karra kintsa dakin ta kawo turaran wuta na jiki da wani sabon zannin rufa ta zauna tana jiranta Ta dauki lokaci a ciki domin karnin kwon ne bata so ko daya, sai da ta wanke tass ama ba soson wanka sannan ta fito ta je saman kujerar ta zauna baba ta zuba mata turaran wutar na jiki mai dadi sosai a hankali ya shiga bin jikinta, sannan babar ta shiga shafa mata mayukan gashin na gyaran ne suma tana bin kan sala sala tana sakw gyara mata shi A sanyaye ta ce" Baba, banfa samu isashen barci ba jiya" Baba ta yi murmushi ta ce" Ai rabonki da barci tunda aka aura maki Mala" Kanta ta dago tana kallon Baba ta ce" Baba jiya fa Hajia tace yau tana son ganina karfe goma na safe, kina tunanin takardar sakina ne zata bani?" "Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallama ke wannan ya, wani irin takardar saki kuma?" Amina ta yi tsuru tana kifta idaannuwanta Baba Lauratu da takaici ta ce" ta isa ta baki takardar taki ne kike zaune a gidanta har yanzu? , Ke bakinki yaushe ya fara furta alkaba'inema ban sani ba?, Auren nan du ya mayar da ke wata shashasha bayan abu ne ya same ki sai dai in mutuwa kika yi zai sauka a wuyanki da izinin mai duka bayan mijin nan da kika raina ya saka ki a kabarinki, Ke Amina ki fa kiyayeni fa, walahi ki ji da kyau du wani wanda zai ja da ikon Allah sai dai a yi ba shi, kin ga auren nan da aka tashi daura shi irin yadda ya kawo rigingimj kuma Allah ya tsaya a daura shi ko? To du wanda yace ba zai gani ba sai dai kasa ta birni idannuwansa, wai wani takarda aa ranki zata baki a hannunki karshen kiyaya!" Amina kam sai ta ja bakinta ta yi gumm, yanzun har dungurinta Baba ke yi, bayan a da bata daga mata muryama da rarashi da komai take binta Abinda ta fi tsana ne ta hada mata watau ruwan lipton mai zafi aka kada masa kwai da madarar peak ra miko mata tana hade fuska ta mata tsaye a kai, sai da ta shanye ta yi bayi da gudu dan kuskure baki zuciyarta na tashi, takaici n cikata Babar ta bita da kallo tana tabe baki ta ci gaba da hade haden abinda ya dace tana ajiyewa dan haka take yi mata yau kwana hudu kennan ba ji ba gani kayan gyara da na sanyi dibgarsu take kamar ba gobe Tana dawowa ta tarar da sauran kayan ta zauna ta sha , domin ta dan ciwon da ba zai barka bane gwara ya kasheka ka huta, uwa uba ita ta san aikin banza ake yi, wannan shaye shayen na banza ne, dan ta san ko gawarta abar kunya ce a gaban Abdul bale ita da ranta, ai baba sai baba walahi! Baba Lauratu ta ajiye mata hijabinta sabo mai tsafta, dudu bai fi sakawa biyar da ta yi masa ba tana kallonta ta ce" Ki kimtsa ki je, goman ta wuce ina nan ina jiranki" Jiki a sanyaye ta dauka ta saka kayan ta dan fesa turare kadan a hamatarta dan ta ji dadin zama Baba Lauratu ta ambaci sunnanta Dakatawa ta yi ta dawo daga nufin fitar Baba ta ce" ki sani, farkon fara mu'amalarki da kakar mijinki ne, dama ban sanki da raini ba, ama a yadda abin nan ke bin keyarki komai kina iya aikatawa........dan haka nake gargadinki da ki kula, idan me zata ce da ke ki tauna amsar da ta dace da ita kafin li bata, ba hakan na nufin ki je a wulakanta ki ba!, Komai talaucin bawa idan ya bada dama za'a wulakantashi, baki zo gidan nan dan roko ba, hasalima baki taba takowa kika zo dan a baki gero ba, a yau da kuke zaune da daraja a kanki mafi girma a cikin darajoji, yin biyaya wajibi ne, haka kuma kare mutuncin kanki wajibi ne a gareki, ki kula Amina" Amina ta gyada kanta a sanyaye ta fita din Ashe mai aiki na zaune tun karfe goma tana jiran fitowarta, bata yi gigin shiga bane dab tunda aka daura aurenta Baba ya fada masu wacece ita yanzun a gidan, matsayinta yana da girman da basu isa su shige dakinta kai tsaye ba, Hajia ta turota tunda safe ita kuma sai ta zauna take jira har ta fito sai ta sanar mata sakon A mutunce suka gaisa, ta mike ta yi gaba fan nuna mata dakin domin hakan ne umarnin Hajiar Sun jima a kofar dakin sunna jira bayan sun buga an masu gyaran murya, har sai da aka basu damar shiga sannan suka shiga Gaba daya kanta so ya yi ya rikice a lokacin da suka dakin da yake ainahin na barcin Hajiar ne Daki kamar ba'a shiga cikinsa? Tsafta, kanshi, tsari abin ba'a magana Hajiar na zaune saman kujera ne cikin shiga ta shada ta kafa daurinta irin na manyan mata , ba kwaliya ko diz a fuskarta ama sai walwali fatarta mai hasken duhu take yi tsabar gyara da hutu ga shan madara (😌) A hankali Amina ta raka mai aikin da ta rakota tamkar zata bi bayanta da gudu ta rukunkumeta su juya tare A sanyaye ta sake juyo dubanta a lokacin da Hajia ke kare mata kallo tun daga sama har kasa, ba zaka taba gane yaya yarinyar take ba dan wannan jarababen hijabin dake janta tamkar zai kayar da ita, kulun a cikinsa tale, ba dare ba rana, ko a cikin gida ko a waje!, Shirmen banza wannan abar ce za'a hada jikanta da ita? Ai ba gami sam A nutse ta zauna a wajen da ta nuna matan, watau saman cafet, ya zamto ita Hajiar tana sama ne saman kujera kafarta daya kan daya, fuskarta a hade, ita kuma tana saman lalausan cafet din falon dan nesa kadan fa wasu tarin akwatunna kanta a sade a kasa Hannayenta dake fili Hajia kw kallo, wa'inda take dan murza su a hankali wanda hakan ya nuna mata cewa lalle tana dauke da strss wanda take son controlng a zaunen da take Bakinta ta tabe , a kadan ta dauki mintunna biyar tana sake karantar Amina A bayane yake Amina mahaukaciyar Black beauty ce, bama irin hancinta da ya tafi a mike zuwat ya sauka dan daidai kusa da labanta, manyan idaannuwanta masu hasken fari da duhun baki sidik na ciki, sai habarta mai dan tsayi kadan sannan daga tsakiyarta ta dana bile kadan Batada cikar kumatu irin kubulbul din nan, kuma batada ramar fuska, gaban goshinta kuwa kan iya sheda maka da ba zata rasa gashi mai kyau ba dan gayanan yana nuna kansa duda kindime shi da ake yi Sakw tabe baki ta yi a hankali, cike da iya sarafa harshe da basarwa ta ce" Wace fuska kika ba wannan hadi ne?" Sai da ta sake maimaitawa kanta tambayar har ta fahimta sosai , sannan ta dago a sanyaye ta dubi Hajiar cikin ido a sanyaye ta ce" Bakuwar fuska ce " Hajia ta dan kawar da kantan nan ta sake juyowa tana kallonta ta ce" Wace kike maraba da ita ? Ko kike hangen rashin dacewarta?" Yanzun sai da ta ji kamar ta bada amsar a zake, watau da zakuwa, sai dai ta dab kiyaye yanzunma ta bada amsar kamar yadda akai mata tambayar, a hankali ta ce" Ba cencenta, sam abin boyewa ne a wajena Hajia" Da mamaki Hajia ke kallonta, so take ta fahimci iya gaskiyarta kennan ko bariki zata nuna mata? "Idan hakan ya zamto tarihi ne, ina nufin abinda bai dauki lokaci ba ya shude zai dame ki kuwa?" Hajia ta fada ta a karra dubanta sosai da son idasa gane nufinta Sosai ta yi yaki da dukan abinda yake tare da ita dan hanna kanta sakin murmushin dake ciyota na farin cikin gannin adu'arta ce zata karbu, watau dai Hajia zata salameta ne? Da kyar ta iya hanna kan nata yin dariyar ko sakin kayatacen murmushin a hankali tace" Idan har hakan ne zabin da na barwa Allah, farin ciki ne in sha Allah Hajia" Tap, lalle a bayane Hajia ke karantar kamar yarinyar nan itama bata son auren nan, sai dai wani bari na zuciyarta ya shiga fada mata magana kamar haka' ta yaya kike tunanin zata fito maki a mutun ta nuna maki bata son abinda ta bi wani tudu ko wani gangare ta same shi bayan ta san bakya son hakan?, Ai dole zata boye maki dan a zauna lafiya, sai dai ta makaro, ita dinta ba'a so ba komai ba!' Hajia ta basar, ta dubi agogon hannunta na azurfa mai kyau dan karami ta sake fuskantar Amina ta ce" Na saka ki zi ne dan ina so mu yi magana da ke, ina so ki samu alkali ki nuna masa amincewarki da auren jikana, watau kin yarda ya auri yarinyar da yake so, ina so ki nuna masa cewa shi ya maki maganar ke kuma kin amince da hakan, " Kallon da Amina ke yi mata ya dakata itama kureta da kallo, kallon take son fahimta ko na menene? Sai dai bata gane ba, dan haka ta ci gaba da magana kamar haka" Amina, ke kin san ke din ba zabinsa bace, haka kuma ba zaki taba amsa abubuwan da ake da bukatar ki amsa dan huce takaicin zama matar gwamna ba, ABDUL RA'UF yanada yarinyar da suke soyaya, sun shirya kansu ana shirin aurensu maganarki ta bilo, a yanzu da kika samu hakan ina tunanin zaki yi masa adalci shima ya samu tasa wace yake so" 'waye ya ce maki jikanki shine abinda yake gabana?, Waye yace maki aurensa ko rashin aurwnsa ya dameni ne? An fada maki inada casss da abinda ya tsarawa rayuwarsa ne? Ko an fada maki ni din macen siyasa ce?, Hajia, dama zaki dubi maraicina, ki dubi karamin karfina, ki saka jikanki ya salameni, da kin rufan asiri duniya da kiyama kin kuma samu lada, domin bana tunanin zan taba yiwa kannin bayana *LADABAIH!*' wannan furuci shine Amina ke kokowa da shi a cikin zuciyarta da kuma kirjinta, sosai ya danne mata kirji yana son falasa kansa ama ta ki bashi dama ta rike shi da dukkan karfinta, bata so ya tonata ya saka ta raina baba, bata so ta yi abinda Baba Lauratu ta hanneta duda tunda ta zauna a wajen bayan ciwa kanta mutinci babu abinda ake yi Hajia ta dora da fadin" *NZL PAGE2️⃣0️⃣* Hajia ta dora da fadim" Ki duba kayan nan, suturunki ne da na saka aka hado maki aka kawo min, zan dora da makudan kudi da kuma mota dan ki rarashi mijina a yi auren nan, ina so daga yanzu har a gama maganar auren kar ki zamo matsala a ciki, ki bada hadin kai a yi komai da ke, idan ya so daga baya ko menene sai a sake zama a warware abinda yake cikin duhu" A sanyaye Amina da ta kasa kanta furta wannan furucin a yanzu ta dubi Hajia ta ce" Hajia, zai salameni ne?" Hajia ta yi mata duban bata fahimta ba? Sai a yanzu Amina ta fahimci abinda ta fada, dan haka ta ji nauyi da kunya na son lulubeta, harma ta kasa katabus Muryar Hajia ta sakata dagowa a hankali tana kallon Hajia Hajia ta ce" Ban fahimci maganarki ba" Amina ta sake sada kanta, ta riga ta furta, dole ta bayana ma'anar furucinta, A sanyaye ta sake dagowa , bata ko jin tsoron dakewar hajiar ta sake dubanya, ta kuma duban akwatunnan da suka firgitata, tarin alwatunnan da robobi manya dauke da takalma, a haka an yi abin ne irin jeka na yikan nan, ama ita gani take yi ta je ina da kayan nan? A sanyaye ta ce" Hajia, ni Uwa ce, na saba fita na kai yarana makaranta sannan na koma na dauko su, kafin na dauko su nakan zo na yi yan sana'a'o'ina irin gyaran amare da tuyar kosaina, na dakatar da karatuna dan jarabawar da zan zana a lokacin ban cike abinda ake da bukata ba, Hajia, kika ce za'a warware abinda yake cikin duhu, shine nake son sannin kina nufin idan aka gama maganar auren nasa, ni zai bani takardata ne? Dan na je na ci gaba fa tawa rayuwar kamar yadda na saba?" A hankali ta ajiye maganar, sai kuma ta sake duban wajen kayan ta ce" Hajia, bama sai an bani kayan nan ba, walahi zan yi ba sai an bani komai ba, in dai zai bani takardar shikenan, a lokacin da Baban ya yi furucin sama min miji da ya alakanta haka da na nuna masa cewa ya bani datijo, ko dan yan yarana" Ikon mai yi mana ruwa kawai Hajia ta tsaya tana kallo, gaba daya sai ta so shiga wani tunani daban a kan yarinyar, kai harma sai ta so afkawa a tunanin kiyaya ce ta saka haka ko kuwa kwarewa a iya wasan ne? Ta dan jima tana nazartarta a haka, karshe ta ba kanta amsa daya jal, koma meye ke dawainiya da yarinyar ita ba shine a gabanta ba, a yanzu abinda ya fi dadada mata rai da tace zata yi , ta zata idan ta ji maganar kishiya hakan zai daga mata hankali harma ta kasa boyewa, sai ta ga ba wannan bane a gaban yarinyar gaba daya Kai ta dan girgiza ta sake duban kayan, to ita kayan nan ai ko kyautar da ake yiwa ma'aikatan gidan idan zasu kai lefen aure ya fi haka yawa bale wai matar ABDUL Duda bata san abubuwan dake cikin akwatunnan na, ama ko meye a ciki ta tabata kadan ne a abinda matar ABDUL zata malaka harma ta anfana Motar kanta ba wata baba bace dan ba zata wuce million bakwai ba da ta sa aka kawo sannan ta zuba kudi a ambulop du saboda koda ta karkare ta siyeta da kudadan da ta tabata kaf danginta basu taba rikewa ba, sai ta samu mamakin furucin yarinyar Kafadunta ta dage ta ce" Kina nufin zaki yiwa Alkali maganar nan ba tare da kin nuna masa saka ki aka yi ba, kuma ki nuna masa da Abdul kuka tatauna maganar, irin kin aminta ne da son ranki?" Amina ta gyada kanta ta ce" Hajia, duka kaf zan yi, zan yi gaba daya , in dai nima zan koma bakin shagulgulana na yau da gobe" A gaskiya Hajia bata da cass da hakan, bata da matsala da hakan ko daya, dan fice da shigowarta kuwa bata tunanin zai damu wani, ta je inda zata je, ta dawo a lokacin da take so, bata da matsaya da hakan, in sha Allah ita kuma zata bata damar yin abinda take so har a yi auren nan, in yaso da laluma sai a saketa ta kama gabanta,....ashema abin ba wani wahala ko raini a ciki Murmushi ta yi na samun nasara tana gyada kanta ta ce" Ya yi, ama ki sani kayan nan da kudin nan duka ai hakinki ne, haka kuma motarma taki ce, kina iya hawa ko ki saida duka malakinki ne, ina so daga gobe ki same shi, idan har ya amince da maganar ki shaida masa karshen watan nan ne za'a tura din, kuma saka auren sati biyu ne suke so" Kai Amina ta gyada sannan ta karra yin shiru tana sauraron dukkan tsare tsaren da Hajia ke dorawa da abinda suke so a yi ita da jikanta Sai da ta gama ta salameta Tare da yan aiki suka sauko aka shiga shigewa da tulin kayan da aka batan ana jibgewa Baba Lauratu da ta kasa tsaye ta kasa zaune tana gannin hakan ta mike tana duban Aminar da yannayin son karrin bayani Sai da suka gama suka tafi sannan Amina ta samu waje ta zauna ya sada kanta zuciyarta na afkawa a kogin tunani Aure? Dan bata da daraja, an bata danar fita a lokacin da take so ta dawo a lokacin da take so? Lalle gaske hankalinta ya dugunzuma ya tashi a kan maganar auren dan gata, koda babu maganar shekaru rayuwar nan ba tata bace sam Baba Lauratu ta kalla dake yi mata tambayar wadinnan fa? A hankali ta ce" Baba, da kika je gidan Fido kin kuwa fada mata komai? Ama ban ganta ba?" Baba ta zauna fuskarta na cenzawa ta ce" Kin sani sarai fa yar nan, ga ciki ya tsufa ga rayuwar firdausi sai yadda Allah ya yi kawai, ana fatan samun cenji na alkhairi in sha Allah " Amina a wani sanyayen ta ce" Zan je gidan nata gobe in sha Allah, Baba ai cikin nata yanzu zai kai wata takwas ko?" A kufule Baba Lauratu ta ce"Ke Amina, yaya ina maki wata maganar ke kina yi min wata ne?, Ina maki magana a kan kayan nan ke kina min wani shirme daban? Wace irin fita? Auren naki dudu kwana hudu yau ki fara fita gobe ko bazawara kike ai kya gama amarci bale ko tarewa baki yi ba?" Amin ta yi murmushi tana sada kanta , sai kuma ta dago a sanyaye ta shiga labartawa baba duka kaf abinda ya faru, komai da komai bata boye mata ba, ta dora da fadi " Baba, ki yarda, sannan ki saka dangana da maganar nan, ba aure kike so na yi ba? Zan yi, daidai da ni, zan yi auren , ama ki bari lamarin nan yaa warware cikin ruwan sanyi, akoy cin zarafi a cikin lamarin, wanda ya hada din kuwa ba wanda zan ringa tararwa da kukana bane a kan wace take iyalinsa, sai abin ya fado a kan gabar nima bana ra'ayin hakan, Baba idan da halima ni din nanma ya fitar da ni ya dauko hudu tashi daya, shine isar namiji ba wai daya tal ba, kayan nan ko tsinke ba zan taba ba, kuma kin manta gobe juma'a ranar tuyar wainar Baba ce? A goben kuma nake son zama da Baban in sha Allah" Tabas abu ya daki Baba Lauratu, magangannun gaba daya sun shigeta ta yadda ba'a zato ba'a tsamani, haka kuma irin abinda Aminar kanta ta yanke ya bata mamaki Koda yake haka ne, idan kana cikin hali na wuya wuya din zuci babu abinda ba zaka fadi ba Murmushi ta yi tana kada kanta, a ranta ta ayana' Lalle akoy ranar kin dilaci, akoy ranar da zamu zauna da ke da kuma kakarsa da shi kansa mu nemo mafita a abubuwan kunyar da ake tafkawa, watau ita ta take dikar mijinta ta kuma kyamaci talaka, ke kuwa kin biye mata kin yi naki rashin kunyar kin nuna mata bakya son danta, shima uban tafiyar baima nuna ya yarda cewa mace aka bashi ba ko?, Ba damuwa lokaci ke raba gardama, rai dai da lafiya, ama da mamaki idan aka wayi gari kowa ya manta wanene MAI SHANU banda matarsa, yau ace Hajia da kanta ce ta manta waye mijinta? Lalle abin da matukar mamaki, wai har Mai SHANU ya dora doka a take? Uhum, ta manta ita din wacece, koda yake dadi kan sakawa a manga wuya.........' A bayane kuwa sai ta yi murmushi ta ce" Aa, ba zaki ki yin anfani da kayan cen ba, haka kuma ko kai kayan amaryarsa da ke za'a yi in sha Allah, dan ai ba zaki so mai Shanu ya irgaki cikin amsu bijire masa ba ko?" Amina da bata yi tunanin amsar nan daga Baba ba ta tsareta da ido tana son karantarta Baba ta dora da fadin" Wani nacinma bashi da anfani, ama ba zamu daina komai ba, haka kuma zaki ci gaba da yan shige da ficenki da ci gaba da kare mutuncin kanki, janyo kayan mu gani mu ware na dinkawa idan ba a dinke ba, mu yi sauri mu gama na je na hado maki kayan wainar ta Mai SHANU ko?" Wata ajiyar zuciya ta farin ciki ta saki ta mike ta shiga yin abinda babar ta ce hankali kwonce , cike da farin ciki Babar kuwa ta yi murmushi irin na manya a ranta ta ayana' Aya, ta yaro kyai take yi, bata karko, Amina...zaki saka kanki a ramin nan da kanki ne, haka shima zai zurma a lokacin da bai aune ba, ita kuma zamu ga irin nata hukuncin............sannan sai mu sake aunawa mu gani a cikin taron nan *WA ZAI YI LADABIN?!* ( TOH FA) haka suka sake wuni, koda yama ta yi dukkan abinda ya dace kafin dare ya shigo yrenta suka dawo suka dinke a ciki, abinci baya gafce masu haka kuma a yau bayan muryar baban harda ta hajia ta ringa tsinkayowa a falon, ta yi murmushi abinta watau ta samu solution hankalinta ya kwonta ko? Rayuwa kennan Kamar yadda Baba ya saba zaman sasafe idan ranar juma'a ce, hakan ne yauma Sai dai zaman nasa na yau tare da uman biyu, da biyu ne ga wainarsa a gefe sai turiri take yi kanshinta ya gama cika masa hanci so yake yi su gama magana da Uman biyu wace ya gama fahimtar da magana a bakinta ya kama wainar nan ya ci iya cinsa Tsai ya yi yana kallonta, maganarta gaba daya dai ya ji bai gamsu da ita ba, yannayinta kansa ya tsargu da shi, furucin bakinta kuwa ya fi komai bashi mamaki Amina ta sake sadda kanta tana sake kamo ayoyin samun galaba tana ta yi da addu'ar da ta shiga bakinta, dan idannuwan Mai SHANU kaifin tsiya ne da su yana iya saka ka fadin gaskiyar da ka boye a cikin karyarka Murmushi Mai SHANU ya yi yana girgiza kansa a tausashe ya ce" Waye ya tsatsaraki ya tsara maki magana irin haka Uman biyu? Waima yaushe kika lakanci karya haka ne?" Da sauri ta dago tana kallonsa hadi da kai hannunta mai dauke da yelow din kurkum da bata wanke ba abinta ta ce" Lah🫢" Mai shanu ya yi yar dariya yana fadin" Fadi da kyau, Lah, to wai wa kike tsoro da za'a fara sako ki a gaba da tsararen zance ni kuma ki tardoni dan bakya jin tsorona?" Fuskarta ta takwakwabe ta sadda kanta tana ta rubububi da kalamai dan samun galaba a kansa Dagowa ta yi tana kallonsa a raunane ta ce" Ama Baba, ai ba haramun bane yin hakan ko?, Bayan wannan shi ABDUL din ai ya yi biyaya da ya yarda da zabinka ko Baba? Dan Allah a tura mana......" Baba Mai Shanu ya kada kai murmushinsa ya ki ya kau, hikimar yarinyar na kayatar da shi, sai dai du yadda ta so da boye masa gaskiya a bayane yake karantar gaskiyar lamarin, abinda dai yake son fahimta ABDUL son da yake yiwa yarinyar cen har ya kai ya yi maganar da uman biyu? Lalle da kuwa ya sarawa lamarin, dan kuwa ga dukkan alamu ba karami bane A tausashe ya ce" To ke kuwa wace irin mace ce za'a maki kishiya kike taya roko? Bakya kishi irin na mata ko kuwa Mai shanun birnin ne bakya so?" Kunya ce ta kamata, dan walahi baba har wani kasa kasa yake maganar da wani salo na tsokana irin na jika da kakansan nan, dama sun saba irin haka tsakaninsu sukan sha hira , dan dai a da yakan yi ta tsokanar ne ita kuma kanta a kasa tana murmushi da jin kunya, ama a yanzu ita ke ta magana dan tana so a saurareta Salamarsa a cen cikin makoshi kasa kasa da shigowar daya daga cikin masu aikinsa ya kawo kayan marmari na anfanin gonarsa da ya je kaya kaya ana ajiyewa ana sake shigo da wasu ya saka Baba kallonsa da fadin" Dan halak ya ki ambato, kai dan ka ga ina hira da amarsun ne ka wani diro kana huci? Yaro sha kuruminka ni da uman biyu mutu ka raba" Dan satar kallon gefen da take zaune ya yi kadan, sannan ya dauke kansa ya maida wajen Hasan da ya mike yana murmushi yana kallonsa, ama bai karasa wajensa ba, jira yake yi har ya ga fuskar yin hakan, duda rabonsa da shi da dadin rai suka rabu, ama shi din ba irin yaren nan bane masu shegen zakuwa da nacin abu ba, dan uwansa kuwa tuni ya labe a jikin babarsa dan shi tsoronsa yake ji Hannunsa na dama ya mika masa , hakan ya sa ya karaso inda yake tsaye ya saka hannunsa cikin nasa Basu yiwa junna magana ba, ama a hankali da hannayensu dake cikin na junna ya dan matsa kadan shima ya dan matsa nasa hannun , daga haka ya wadatar Cen gefe ya karasa ya zauna yana karra kallon sumar yaron, daidai lokacin da baba ke fadin" Lalle, hali da hali, Uman biyu wai kin ga mijinki da yaronki kuwa?" A tare suka kalli Baban, sai kuma suka kalli junna Wata hararar tsinin ido ta maka masa ta turo baki hadi da dauke kai, shi kuwa ya girgiza kansa a dan takaice ya dubi baban yana fadin" Na sameka lafiya?" Baba ya ce" Gani kuwa garas muna zantawa da uman biyu, kai ka yi mata nasiha ta san ciwon kanta da kishi irin na mata, wai ace uman biyu ke min maganar kun tsayar da maganar a karo mata abokiyar zama? Ko tarewarku fa ba'a yi ba, uwa uba ta dage wai karshen watan nan dan sun shirya dangin amaryar? Jama'a ni kam ka bani sirrin nan na aikatawa Hajia ko za'a dace, dan inaga da na gwada aure nan da shekara ashirin da hudu ta kusan wata a asibiti!" Sai da baba ya dire maganarsa, sannan ya sake kallon ABDUL da son gane yana sauraronsa kuwa? Kuma da son gane ainahin maganar uman biyu A hankali ta ciciba ta mike daga zaunen da take dan karara baba ke so ta dauke fuskar yaron nan da mari ta shiga uku, yaya zai ringa abu kamar na neman rigima ne? Ina hadinta da yaron nan? "KE DAWO NAN KI ZAUNA" ya fada a dake bayan ya mata kallo daya ya gane nufinta tafia ce zata yi bayan ta dauko maganar da shi bai san yaushe suka yi ba? Lah ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam ku kirawo hajia ABDUL zai ballo mata ruwa jama'a 😖😖😖😖😖😖😖😖😖😖 *NZL PAGE2️⃣1️⃣* A hankali ta juyo ta sauke dubanta a kansa, kai innalilahi walahi walahi jama'a da ita yake, subahanalah me yake yawo a kan yaron nan ne wai? Menene wannan lamarin na zubar da kima haka? A kaikaice ta sake dauke shi da hararar da tsaf Baba ya gani, haka kuma ya saka shi boye murmushi ya gyara zamansa tsaf yana son gannin karshen wasansu, dan ya tabata sunna daf da falasa kansu a wajen nan Juyawa ta yi da niyar sake yin tafiyarta dan ita ai ba sa'ar yara kanana bace A nutse Baba ya ce" Uman biyu mijinki yace ki dawo ki zauna fa" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, inama zata iya fashewa da kuka a wajen nan? Da ta yi kuka har kamar zata haukace Wai mijinki, wannan kalma na tsaye mata a wuyanta kamar zata kumeta ta sumar da ita Jiki a mace ta dawo ta zauna tana sake sada kanta tana hadiye bacin ranta "Ke baki iya gaisar da mutane bane?" Ya sake fada , dan kawai fitsarar yarinyar dariya take bashi, yauma kuwa warin nan na abin nan take yi dan gayanan a hannayenta , ko menene anfaninsa? Bai taba haduwa da ita ba bata wari, bau san menene take kwabawa jikinta ba sam! Idannuwanta da suka cika da kwala ta dago ta zuba a saman fuskarsa, numfashi ta ja tana fitar da kyatu ta dantse lebenta na kasa dan bata so ta fashe da ihun kuka Baba kansa dariya ke tikarsa, sosai abin ke titikarsa a ransa, gaba daya sai suka zamto wani nishadi nasa na sasafe, dan haka da kula yace "Uman biyu baki ji ba?" Amina ta sake kallon Baba, sai kawai ga hawaye tarrr ta bude bakinta ta ce" Baba wai na gaishe fa yake cewa fa?" Baba ya yi murmushi yana fadin" Eh haka, to ba shine gaba ba?" Kai kawai ta soke tana hakin kukanta Baba ya sake yin murmushi a hankali yace" Allah shi kyauta" Hijabinta ta saka tana dan goge hawayenta a hankali dan dagowar da ta yi ta ga Hasan ya kura mata ido so yake ya gane kuka take yi ko me? Idan kuwa ya gane haka ta san shima zata daga masa hankali Danta kuwa tuni ya yi waje, shifa mutumen nan da baya dariya ba tafiyarsu daya ba gaskiya, dan shi baya son bulala Baba ya sake yin murmushi gannin wani sirri da ya gani gannin idannuwansa a cikin lamarin Kai ya gyada ya ki yin lididddigar da ya yi niya Da kula ya ce" Yaushe kuka tsayar da mijin naki za'a tura maganar auren? Sannan yaushema kika ce za'a saka ranar daurin auren?" A hankali ta dab karra satar kallon yaron, ita baban takaicinta kar ya yi mata wata fasarar daban Ajiyar zuciya ta sauke ta sake maimaita masa abinda Hajia ta tsara mata Baba ya dubi ABDUL RA'UF ya ga shima shi yake kallo, so yake ya gani wai hala da gasken sai da ta roka zai yarda? Kai ama kuwa da ya sha mamakin baban, yaushe ya saka wata a wajen da yake da power ne? Lalle da an wulakanta shi shi kam! Kai ya gyada ya ce" Allah ya nuna mana, zamu je ni da Rabi'u, sannan za'a saka yadda kuke so, maganar tarewarku ne ban ji ba" Da dan sauri Amina na yiwa ABDUL kallon kasa kasa da turo baki ta ce" Wannan ai mun fi so idan aka daura natan sai mu tare baki daya Baba" Shiru ya ratsa wajen, na lokaci mai dan tsayi, domin Baban kawai kallonsu yake yi "Uhum" ya fada a cikin makoshinsa 'idan da raina ta yiwu na raba abin kunya' ya ayyana a zuciyarsa "Allah ya doramu a kan daidai, tashi ki bashi ruwa sai ki koma ki gama tuyarki na san Lauratun na cen tana fama da rigimar gaz, gaskiya Hauwa bata kyauta min ba, ai sai ta bari a min abina a itacen kamar yadda aka saba wai kar garu su dauki bakin hayaki, in ba Hauwa ba shekarar ginnin nan nawa? Itama dake namalakiyar ginnin bata ga ta yi furfura ba balle wai garu? Gaskiya Abdallahi ka yi mata magana ni kam in dai Uman biyu na nan du juma'a a toyan wainata da itace" Ruwan ta zuba ta kai daga cen barin dan so take ta yi masa maganar da bata so sai an jima dan gudun mantuwa ko ya bar gidanma bata sani ba Kasa kasa sosai bayan ta ajiye ruwan ta ce" Kake wani ce min ke zo nan gaskiya bana so kar a maimaita, kuma da kaji ana wata maganar daban nima so nake na yadda kwalon mangwaro na huta da kuda, Allah ya sa baka mance hausa ba!" Ajiye ruwan ta yi ta mike ta yi gaba Da ido ya rakata har ta bacewa ganninsa, ya dawo da dubansa Kan Baba domin shi yana kallonta ne shi kuma Baban na kallonsa A hankali ya ce" Tana fama da yarinta sosai yarinyar nan" Baba ya yi dariya harda dan kama haba ya ce" Ka ji da shi Abdallah" Shima murmushin ya yi ya karra duban kan Hasan ya ce" Inaga zamu je aski mu dawo kafin mu tafi masalaci da yaren nan" Wani farin ciki ya lulube zuciyar Baba, ya san cewa ABDUL zai kula yaran nan ne dan sun shiga ransa ba dan wani abu da yake da burin ginawa ko kulawa da uwarsu ba, dadin da ya ji shine Halayar ABDUL din kwata kwata sun yi nisa da na sangartacen yaro da kudi, halinsa na datako na sakashi a nishadi da kwonciyar hankali, ya tabata idan har suka samu sasantawa da Uman biyu sai ya fi kowa farin cikin hakan Sai dai tsoro kan kama shi Ya kula Uman biyun ma fa bata son hadin nan, domin a yadda ta yi wani abin kamar wace ba zuciya a kirjinta na kishi? Kishi ai halal ne, shi da kansa ABDUL din ya kula ya yi mamakin abin Salamarsa Abdul din ya yi suka fice, wanda Husain ya ki binsu sai da baba direba sannan ya shiga motar yana labe a jikin Baban yana hangen ABDUL da ya hade gabas da yama ya wani yi zama a hakimce cikin lalausan milk color din yadi yana wani basarwa irin na masu kudi Shi kuwa Hasan a haka ya ga wajen zama, dan kuwa shima ya yi zaman ne ya wani dauke kai yana kallon titi kamar wanda ya jima yana shuga mota, bayan ko kwarewa da bude motar basu yi ba, to a cenma su yan yawace yawacensu da mamansu a adaidaita sahu ne, bale a yanzu ____________________________________ Dukkan yadda suka yi da Baba ta sanarwa Hajia a yanzu da ta fito tsaf cikin lalausan shirinta da nufin tafia gidan yar uwarta Kanta ta sadda cikin shiga ta blue din Hijab mai tsayi har kasa sosai ta ce" Hajia zan tafi gidan Firdausi ne na dawo dn Allah in ba damuwa?" Hajia dake murmushin abin nan da mamakin yadda aka yi ya saurareta bai fatataki kowa ba, dan ita fa a shirye take tunda safw jiran ihun sunnanta take yi da balbalin balakin fadan ba'a isa ba, sai ta ji shiru , kuma gashi har yanzu bai dawo ba daga fitarsu juma'a, ita da kanta tana sin fecewa ama har yanzu bata fara fitan ba tukunnan, so take yi sai komai ya idasa lafawa Hajia ta ce" Kina ji, kina iya tafiya ai ba wani damuwa, ama ba zaki shiga taxi ba saboda Alkali gaskiya, ki je zan yi kiran direba daya ya kasance direbanki ne" Amina ta yi dan jim, sai kuma ta rage tsayinta kadan ta yi godiya sannan ta juya ta fice Hajia ta sake rakata da kallon da ta saba na harare harare da kuma haushi haushi a fili ta ce" Allah ya wadaran naka ya lalace, wai Alkali wannan ce zai sa ta juyani ni Hajia Hauwau? A dai daura auren zaka gani" Tare da Baba Lauratu suka je gidan Sun tarar da Firdausi tana sharar dan tsurut din balbalin gidan nata da wata tsintsiyar da bata fi a irga tsinken dake daure da yaloluwar leda fara ba Tana jin muryar Amina ta mike a zabure tana wara idannuwanta hadi da amsa salamar Da sauri ta daga kafarta dan ta zo da gudu ta rukunkumeta, sai dai amsawar da bayanta ya yi ga daskarariyar yinwar da take ji ya sakata dafe bayanta a hankali ta furta" Wash Allahna " Da sauri Amina ta karasa tana rikota ta rungumeta a jikinta a hankali tana fadin" Fido? Sannu ki yi a hankali mana" Firdausi ta yi yar dariya tana ji abin ya lafa mata a tsayen nan ta shiga dariya da murna da son dole sai ta yaye hijabin Aminar tana fadin" Uman biyi kece haka? Uman biyu kanshi kike yi wannan turaran fa? Uman biyu cirw hijabin nan na gani hannayenki bake ji wani santsi hakama jikinki ya dauka? Wayo Allahna farin ciki kasheni zai yi ni kam yau, Uman biyu kin ganki kuwa? Wayo Allahna da ke nake kwana ina tashi, damuwa ta cikan cikina, idannuwana kulun a kan kofar gidan nan, sakata yake sakawa ta baya du idan zai fita wai karma na saki na fita bai san tunda yace Allah ya isa idan na je ba na yi hakuri na biki da Adu'a, Uman biyu kuma da biyu kika tare? Shi mijin naki bai koro su ba! Uman biyu wai dan Allah........." "Fido wai ba zaki yi shiru ki huta bane?" Amina ta katseta tana ririke hijabinta, dan walahi ita kunya take ji irin yadda jikin nan nata ya dawo, kamar ba jikinta ba, wani irin santsi da yake yi har mamaki take yi, ga wani haske da fatar tata ta dauka har tana neman zarce fuskarta haske, ita kam wannan gyara ya fara damunta , gashi Baba tace bata ga ranar dakatar da gyara ba wai sai ta tare, hahahaa ta tare a ina? In ba rikicin Baba ba? Firdausi ta dan sasauta din, sai kuma ta sake rungumeta kadan saboda tirtsitsin cikin dake hannata motsin kirki ta fashe da kuka tana fadin" Uman biyu, aka daura aurenki wai babu ni? Innalilahi wa inna ilaihi rajune, ya Allah idan wani mumunan laifi na aikata ka jabaceni da wannan jarabawa mai tsauri bayan rasuwar mijina mai sona da ta iyayena , Allah ka sasauta min ka yafe min ka bani ikon cinye jarabawar nan, Allah kai ka haliceni kai ka dora min, Allah ka bani ikon cinyewa ya ubangijina" Baba Lauratun ce ke amsawa, Amina kam janyewa ta yi a hankali ta dauko wata yamutsatsiyar tabarmar firdausin ta shinfida a nan tana kaiwa zaune da kafafuwanta dake cikin safa Baba Lauratu ce ta ce" Dan bani jakar nan mana?" Amina ta miko mata jakar da kudin nan yake ciki, Baba ta fice a gidan A hankali suke hira hannayen junnansu a rike da junna Amina ta yi iya yinta dan kar ta yi kuka, ta yiwa kanta alkawarin in sha Allah ba zata kuma yiwa dan iskan nan kuka ba, ba Firdausi bace? Tunda ta nuna idan ta fito zata karra zama karin ci da sha da sutura ne a kan Aminar sai ta zauna gata ga shi, haka Allah ya rubuto tata salon kadarar, tana fata ba dare ba rana Allaj ya katse mata wahalar nan da take fama da ita Dawowar Baba lauratu da leda ta ja gidan ta rufe da sakata ta ajiye ledar ta bude tana ciro dunkula dunkulan kaji gasasu da jus dan kwali da manyan ruwan faro ya saka Firsausin da Amina zarro idannuwa Baba ta mikawa kowace nata itama ta ja daya ta ce" Yau ai juma'a ce, bismilarmu" Amina bata san lokacin da ta fashe da dariya ba domin yadda Babar ta yago kazar nan kamar sunna gaba da junna ne Itama Firdausin dariyar take yi, nan da nan yawunta ya tsinke tana kallon lazar da tsoron tabata To sai ta ji tsoro mana, ita rabonta da ta gantama ba ta manta ba, sai irin wani lokacin idan tsuntsaye suka dan sauka dan kama wani abin su ci su yi tafiyarsu dan kuwa ko na anguwa masu kiwo basa samun shigowa dan gidan a rufe yake kulun Ci suke sunna santi da dariya, Baba zuciyarta ta yi mata fesss tana kallon yan marayun da dariyar da suka samu A ranta take adu'ar Allah ya datar da su da farin cikin nan, ta san dadi ko wuya ba masu tabata bane har karshen rayuwa, wata rana dole a ji dadin, wata ranar kuwa a sha wuya, sai dai tana dakin ranar da zata ga farin ciki mai sunna farin ciki a fuskokin marayun nan Amina da ta koshi da wuri tana kora jus din nan mai shegen sanyi da dadi ta ce" Kai, anya akoy abinda ya kai kaza da yaji dadagage dadi kuwa?" Fisdausi dake hannu baka hannu kwarya baiwar Allah kamar zata tsinke yan yatsunta ta girgiza kai tana fadin" A duniya? Aa babu gaskiya" Baba ta yi dariya tana fadin" Akoy mana, miyar taushe ta sha dadawar batsi yara ta fi komai dadi" Aminarma ta yi dariya ta ce" Haka fa babanmu ke fadi Allah ya masa rahama, yace babu abinda zai dauke masa hankali da irin girke girken mai sunnana, watau mamansa" Firdausi ta kora ruwan ta yi shiru tana jin wata zufa mai sanyi n tsatsago mata sai gyatsa mai nutsuwa ta bi baya a hankali ta ce" Wayo Allahna, dadi zai kasheni, Allah ka sa mutu k raba auren Auntyna" A dan zabure Ameena ta kalleta zata yi magana Baba lauratu ta amsa da ameen, sai kuma ta ce" Bama kya tambayar biyu?" Firdausi ta yi murmushi tana fadin" ƴaƴan mamansu ni mamakin da na yi yau babu su a rakiyar kamar wutsiya du inda ta bi sunna lake da ita" Baba ta wani karkace tana share zufa hadi da yin murmushi ta ce" Sun tafi masalaci da babansu ne ai" Da mamaki Amina ta kalli Baba, waye baban nasu? Kai ita gaskiya ba'a kyauta mata a duniyar nan kwata kwata! Baba ce ta hsde sauran ta mika ma Firdausi ta ce" Kauda a kasan gado inda bera ba zai ja ba ki boye idan ya fita salar asuba ki janyo ki kauda sauran ki zuba a masai " Yadda ta yin ya karra basu dariya, irin karma ya ji koda kanshinta ne Murmushi ta yi a ranta tana ayana' Kaya, ai na rabaki da talaka mai zuciyar fir'auna, shi bama zai saki ransa ya cin ba in dai daga hannun Amina ya fito, a fili zan ajiye dan na tabata masu fada masa ta zo zasu fada masa, ni kuwa yau cikina a cike ai ko wace wace kawai!' Sake gididige watannin cikin suka yi, kafin su mike su yi mata salama Ji ta yi kamar zata dane su su tafi da ita, tana jikin kofar tana saurare har motar ta tafi ta koma cike da farin ciki ta idasa tatararta ta sake zubawa dubu goman nan ido ta yi wani murmushin hadi da godewa Allah da ya bata Amina a rayuwa Ta tabbata da kudin nan zata jima tana cin abinci, idan ya fita sai ta yi kiran yar gidan maman husnah ta bata ta amso mata abin tabawa su ci tare ta yi daidaya ta huta abinta..................... Talaka bawan Allah, shi baban burinsa ya ci ya cika cikinsa koda babu dadi, sannan ya samu kwonciyar hankali komai kankantarsa.....Allah ka karra rufa mana asiri duniya da kuyama, sannan ka kara ba ba mai bamu😍😍😍😍😍😍🤣 *NZL PAGE2️⃣2️⃣* Tun daga wannan rana Baba ya saka a yi masa bincike a kan lamarin yarinyar A hankali aka ringa kwana ana tashi har ya rage kwana hudu da son turawar da ake so ya yi , ama bai ce komai ba A kwanakin nan du wani kwontar da kai da biyaya yana samu daga Hajia, abin ba'a cewa komai domin harda Hajia a yan kicin dan yi masa yan girke girke Idan ya sauko yakan zauna da uman biyu, da biyu, su dan zanta sai kuma ya fice rawatawarsa da datijan anguwa da abokanansa na arziki Jikansa kan zo ziyarar kakannin nasa jifa jifa dan kuwa har tafiya ya yi ya yi kwana biyu ya dawo ita bata da labari, idan aka yi katari ya zo sun hadu ne a ajiye take sai sun taba yar tsamar da suka saba, yawanci kuma Aminar ce zata yi gaba rai bace tana gungunnin itafa bata son raini a kiyaye!, Shi kuma sai ya yi murmushi kawai ya cira kansa ya ci gaba da lamarin dake gabansa, A haka lokaci ya sake zuwa, a daren da ya rage kwana biyu a tura mahaifin Risalah ya yi kiran Hajia ya fada mata cewa yau su Alkali sun same shi a gida shi da aminansa biyu, har sun tsayar da maganar auren komai da komai, Alkali ya nuna yana so matan su tare su biyu dukansu a gida guda? Shin Hajia dama bata ce masa auren na hadi ne Honorable din kansa baya so ba? Yarinyar dai gatacen sai murna take yi, aman mahaifiyarta ta rikice kan ba zasu zauna gida guda ba, wai ba za'a wulakanta mata y'a ba Hajia tunda ta kashe wayar a zaunen nan da take ta kasa katabus Hankalinta ya yi kololuwar tashi da irin hanyar kuma da mijinta ya billo mata Shin yaya zata yi da Alkali ne? Ita dake jiran ranar da za'a je tambayar nan ta yi gaya ta kasa da kasa manyan mutane su je tambayar nan shine kamar aurwn bazawara Alkali zai je ya yi tambayarsa a boye ya dawo? Shin me yasa Alkali yake son wulakantata a rayuwa ne a kan auren nan na Abdul? Du salon ta nuna wani abin ne ya hana auren? Ta tabata so yake ta yi wani abin kiris ya fake da shi ya ki maganar auren Kasa fita ta yi, domin wata tsanar lamarin Aminar ya sake shiga zuciyarta, gani take yi ko menene akoy wani zagin kasa da yarinyar nan ke yi mata bata gane ba, ta yiwuma ita ta san da maganar nan bata fada mata ba! A kasa kuwa Alkali ne da Rabi'u suke tataunawa Da kula sosai Rabi'u ya ce" Aliyu, tunda muka je muka yi tambayar nan a haka kamar yadda ka bukata, in dai har mahaifiyar yarinyar bata watsa abin ba ka yi hakuri kawai a yi, kar ka manta jayayar kanta bata da wani anfani fa" Baba mai Shanu ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Na sani Rabi'u na sani, abinda ke damuna bincike a kan yarinyar da ubanta da mahaifiyar tata kanta, lalle ba'a fada min wani tabo ko wani gigitacen al'amarin da ya gyasa yan matan zamani masu yayi selfi ba, ama magana a kan kudo da mulkin nan ya tsaye min a zuciyata, sai kuma natacen so da burin yarinyar a kan jikana na dawainiya da ni, shi yasa na yanke mu je din nan a haka dan na tabata ita da kanta ta cikin idan har ta ji to fa ko ana cen an fara raba hali ko ana jirana, ka san da har yanzu ABDUL bai nuna bukatar tarewar matarsa ba? Menene aibun uwar biyu ne ni?" Baba Rabi'u ya yi dariya ya ce" Bata da wani aibu, kuma ai da kyauma da har yanzu take a matarsa, ita din uman biyun naka ba kai ke ce min ba uman biyu ba dai son girma ba? Aliyu mutanen nan biyu lokaci da garajensu zai shiryar da su ba tare da sun shiryawa hakan ba, ni bama na so ka saka damuwarsu a ranka, kamar yadda kace in dai sun baka amsar nan da kwana biyu sun shirya za'a daura auren nan da sati biyun to fa mu shirya mu kuma basu dama su yi bikinsu irin nasu na bajinta, kar ka hanna su yin komai , ka barsu su kashe koren arzikin su , su nuna murnarsu ka ji?" Da wannan suka gama tataunawa suka yi salama A daren bai leka dakin HAJIA Hauwau ba, sai da garin Allah ya waye ya shiga da sasafe A zaune ya sameta a saman salaya ta kure waje daya da ido Idannuwanta dake dauke da kunkumbali ya sheda masa bayan na shekarun da suka dan fara ja harda na rashin barci A nutse ya zauna yana amsa gaisuwarta Zai fara magana wayarsa ta shiga kuka dan haka ya janyo yana kankance ifannuwansa da dubawa Sunnan da ya gani ne ya saka shi dagawa ya saka handsfree kamar yadda ya saba amsa kira Gaisawa suka yi a mutunce, sannan mahaifin Risalah ke sheda masa ai har sun gama shawara sun yanke shawarar eh sun shirya Jim ya yi da mamaki da wayar a hannunsa yana kallon Hajia da ta zuba masa ido A nutse ya sake maimaita maganar da suka yi, Baban nata ya jadada masa kwarai kuwa hakan yake nufi Murmushi ya yi hadi da yin adu'ar Allah ya sa alkhairi za'a hada ya basu zaman lafiya, zasu zo dan tabatar da saka rana da dukan sauran tadar malan bahaushe Hajai kamar ta daka tsalen albarka ta saka ihun murna take ji , sai murza kafa take dan dadi tana kallon mijin nata Murmushi ya yi ya ce" Kin ga, shigowa na yi dan na sanar maku jiya fa mun je gidan su sarakuwar taki, sai ga amsar uban yace sun shirya, " tiryan tiryan ya maimaita mata abinda ta sani tuni Ai kam murna da farin cikinta ya kasa boyuwa har ya zuba mata ido yana murmushi yana kallonta Hajia ta sake matsawa kusa da shi ta dauki kafafuwansa masu hasken gaske ta dora a saman cinyarta ta shiga dan mamatsawa ta ce" Alkali?" Baba ya ce" Na'am Honorable?" Murmushi ta yi tana sada kai ta ce" Dan Allah ka barmu mu yi bikin nan yadda ya dace mana ka ji?" Murmushin ya yi shima ya ce" Ai ba zan hanna ba Hajia, damuwata daya ce zuwa biyu, ba za'a dauki sadaki dan duniya ta fada a maka ba, ba kuma za'a dauki kayan amaryar da ya wuce na uwar gidansa a maka mata ba, yadda aka yiwa Uman biyu za'a yiwa yarinyar itama, in sha Allah zan shiga dakin Uman biyun gobe da yama na ga kayan nata da kika ce an yi mata, idan ya so itama haka nake so a kawo mu zamu kai dan bana so mata su kai bi izinillah, albarkar abin nake nema da kuma kamanta adalci, domin bana so dan uman biyu ba zabinsa bace a nuna mata bambamci, koda ba zata yi magana ba ai mahalincinmu na gani, kuma har mu zia tsayar a kan wannan laifi, bayan haka na biyun shine ina so a ba Uman biyu dama itama ta yi gayarta ta yi bikinta ta yi wadakarta, ko ba komai ai ba Alkali bane zai karra aurw, mijinta ne zai karra ko?" Hajia ta kume tans kallon Alkali Gannin ya sake kafeta da ido yana tambayarta ta fahimta? Bayan wannan bashi da wata damuwa, gida kuwa zai sa a yiwa uman biyu jere a nata bangaren itama in sha Allah domin dama shi yake da alhakin yi mata kayan daki, ba yau ba ya daukarwa kansa wannan alkawarin Hajia tana ji tana gani Alkali ya gama ya fice a gidan, watau suka nufi gidan gona da yaren A haukace ta sauko ta fice a gidan tana waya da ABDUL Ah toh ina ta ga ta zama wani aikin na shirin balo mata? Dama maza ne zasu kai lefen, abinda dai ta tsara abokinsa da abokansu zasu kai a yi jeren motoci da kayan setinnan akwatunna na gigita kwakwaluwar karamin mai kudi mai baban buri a kai gidan, dan so take tun daga kan kayan lefen nan ta fara nunawa uwar yar ita ba sa'arta bace, da mijinta zata ja , shima ba wai dan ya isa ba, aa dan dai mutun ne shi mai baki da kazagi a wajen manya, sai gashi Alkali na son kasheta da ranta ABDUL dake cikin aiki gaba da baya , domin a lokacinma sunna cikin meeting ne ya yi excusing din kansa a sawake ya ce" Hajia, menene abin tayar da hankali a nan? Ki hada mata irin na wancen yarinyar mana menene a ciki?" "Abdul? Kayan da banma san me da meye a ciki ba? Saitin akwati daya dal ne fa aka hada mata, shine za'a hadawa RISalAH? Ka san da ba zai taba yiwuwa ba ko?, Ka ga ka yiwa kakanka magana kana ji fa jerema shi zai saka a yiwa yarinyar nan, ni tsorona daya kar ya dauki bangaren da ya fi kyau din a jerawa yar kauyen nan da tarkacen ƴaƴanta!" Abdul ya dafe kansa, tafia ce ke gabansa ta kusan sati guda cir kasar spain, harkar man fetur zata fitar da shi dan nan yake son fadawa kuma, ga kuma rigimar mutanen nan a gefe? Shi da ya gama magana da Risalah auren sai ya kusa zai sauka dan yanada abubuwan yi sosai, ama kakaninsa na son rikita masa lisafi? A tausashe ya ce" Hajia kina ji? Ki kwontar da hankalinki Please, du ni ban ga menene na daga hankali a nan ba, maganar lefen ki zauna dukkan abinda kike da bukata in a nan kike so a hado maki a hado a kawo, idan kuwa kin fi son fita ki hado sai a duba passport dinki ki je inda kike so, plz bana sin fadan nan ke da Baba" Hajia ta sake dafe kanta ta ce" Idan nace na fita zai ga kayan da na ba yarinyar nan, kawai gamunan zuwa NI da Uma kampani mu hada komai sai a loda a kai gidan, daga yanzu har gobe zan jure na yi zaben har mu gama".. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya kashe sannan ya koma suka gama meeting dinsu ya kuma fitowa ya nufi office din manager ya sheda masa a bude bangaren VIP na kayan lefe ga su Hajia nan zuwa, ko duka zasu kwashe a basu dama Nan da nan aka bude bangaren VIP din, baban bangare ne da idan yayab manya zasu hada lefe suke zuwa, domin ko akwatunnan ba kowa ke iya siya ba ko a manyan bale mu (🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️) Hajia da Hajia Uma sun rikice wajen daukan kayan amaren, sai dai a zaben nasu sun saka son zuciya a ciki, domin a duk wajen da ya dace su zuba abu iri daya wani abin sai su bambance su dauki wanda ya fi class su saka a kalar akwatunnan da suka daukarwa Risalah masu kyau da kalar yan gayu, sai su zuba sauran a sauran akwatunnan da suka daukarwa Amina color din zabin a cakule domin har kala biyar sula kwatsa mata A bangaren shadoji dinkaku bugagu yan waje masu zubin manyan dinkunnama sai da suka yi san rai, dan harta yawan shadojin Risalah sun fi na Amina yawa Haka a bangaren lafaya da abaya sun daukarwa risalah na lwaliyar amarya yar gata ne, su jefawa Amina na uwar gida sha gida zaunaniyar cikin gida Takalma ne da jakunkunna na alfarma a nan kuwa babu na koma baya, kowane ka dauka na gani na fada ne Atampopi da lesh , kananun kaya da kayan barci, sarka da yan kunnaye Masu tsaron bangaren sai da zuciyoyinsu suka karye gannin yadda ake kwasar kayan ana jidawa , sai da magariba ta gansu a kampani sannan suka koma gida bayan an shiga sakawa kayan irin abin nan mai kyalkyali na amare ana yin yadda Hajiar ta fada, ga sunnayen da ta bada cewa a kowane a saka sunna, Amina da RISALAH A daren hankali kwonce ta sha barcinta dan ta san an gama wannan rikicin kuma, yanzun ta shiga shirye shiryen biki ne na garari, duda haka tana cike da jin haushin wai Amina ce za'a ba wannan jerin kayan? Ta kaisu inama wai? Ta saka su ta yaya? Washe gari ya rage kwana goma daurin auren da kusan karfe goma sha biyu a falon Baba mai SHANU Matarsa ce da Baba Lauratu, da shi Baban ana ta shigo da kayayakin da kallonsu kadai sun isa su haukata mutun a cikin akwatunnan bama a waje ba Baba yana murmushi yana gyada kai har aka gama shigowa da komai ya dubi Baba lauratu ya ce" Allah mai iko, Laure wannan kaya ai sun isa a bude shago, Allah na tuba zamani mai tafe da rikici kin ga kayan yan mata biyu ne wannan, ai gwara da mun zo wannan zamani mun rufe daukowa bale mu gigice, kuma fa a haka sai ki ga ana saurin rabuwa da macen ta kwashe komai kana kallo kai ga shashasha ta tafi? Ai idan nine na zuba rabin wannan ba zan yi wasa ba gaskiya, kin san da lokacin Hauwa akwatin ta kwano ce mula kai kwaya biyar? Kar ki so ki ga yadda ake rububin kallo ana ka baki" Hajia ta karra hade rai cike da takaicin yadda baba ya bararahe yake ba wannan mata labarin aurenta, hum, shi kam ya iya zubar da mutunci walahi da girma, ina shi ina wannan dadadaur matar da ko a yar aiki ita ba zata dauketa ba? Baba ya sake yin murmushi ya ce" Masha Allah, to Hauwau kin ga wanda na zabarwa Uman biyu, ai uwar gida ce da daukan farko ko? Tunda na ga an raba abin biyu na tabata an gama gyara komai kai masha Allah " Cikin Hajia sai da ya yamutse waje daya kafin ya bada wani kuka kuuuuuuuuu a lokacin da ta ga Baba ya nuna kayan da suka zuba da sunnan RISALA yace wai su ya zabarwa Amina! Murmushi ta kakaro tana mikewa ta ce" Lah alkali, ka ga ai kowace da sunnanta a jikin nata, ka ga na uman biyun nan, wannan kuwa ai na Risalar ne ko? Duka kaf komai iri daya ne aka zuba ai" Baba ya yi murmushi a ransa yana ayana' Na san a rina' A fili kuwa ya ce" Kai masha Allah, ai kin ga nima kawai kalar ce wannan din ta fi birgeni, shi yasa na daukarwa uman biyun ita, ai tunda komai iri daya ne menene a ciki?, Kin ga Lauratu ga fa kayan uman biyu sun sauka ni kamar a saukar mata da ni mu sha kallo wannan kaya ai sai mu bude shago da su" Baba Lauratu wani irin farin ciki ya sakata fashewa da kuka a lokacin da Hajia ta tabatar da gaske Alkali yake kayan da ta zabo classs, masu dan uban tsada da tsarin kalar na yan gayu ne ya daukarwa bagidajiyar yarinyar nan ta juya da sauri domin ko gabanta bata ganni da kyau ta shiga sauka tana hade matatakalar da bibiyu tana rike kukan dake ciyota ta saka hannunta ta murda kofar amina ta bude da karfi ta shiga ranta bace, hankalinta tashe ta kai dubanta kan Amina ta ce" Rikicin cikin gida.....da mai rai ake yi 😍😍😍😍😍😍 Cmmnt dinku ya saka ni sakowa da sasafe jama'ata 😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍 *NZL PAGE2️⃣3️⃣* Kalaman da ta fara jifan aminar ta su ya saka Hasan dake samn gado yana daga kafafuwansa tashi zaune ya zuba mata ido Rai bace ta nunawa Amina hannu ta ce" Abinda nake so da ke shine, idan ya kawo kayan nan kar ki saki ki bude, ki bari idan aka kai wadincen din zan saka a kawo maki su ki bata nata, wa'inda yace a baki ba naki bane nata ne, kar ki saki ki kaini bango yarinyar nan!" A sanyaye Amina ke kallonta tana son fahimfar inda kalamanta suka nufa, domin ita dai bata san da maganar wai za'a karra mata lefe ba, wadinnanma da ko anfani bata fara da su ba dan gani take yi sun fi karfinta bale wasu? A hankali Hajia ta dafe gaban goshinta tana mai fashewa da kuka ta ce" Wannan wace irin masifa ce?, Da na san zan riski ranar nan da na shirya mata, ama ki me kike tunanin kin tanada ki zubar dan walahi na shirya maki tsaf zan yake ki da dukkan karfina!, Amina ki.........."......... Maganarta ce ta katse a lokacin da ta kai dubanta kan hannun da ya rike mata hannu Fuskar yaron har wani huci take fitarwa ya rike hannunta taf ya zubawa fuskarya ido Hannunta ta janye da sauri tana sake kallonsa Hasan haka kirjinsa ke sama yana kasa, Da sauri Amina da hawaye suka fara wanke idannuwanta ta karaso ta janyo shi jikinta ta rungume shi sosai tana kallon Hajiar itama haka kuma tana shafa bayansa Muryarta na bari ta ce" Hajia , na yi wani laifin ne kuma?" Hajia ta mata shiru itama tana jin zuciyarta na dokawa da daci da bacin rai Amina ta lumshe idannuwanta hawayenta suka gangaro sosai a hankali ta ce" Hajia, walahi walahi baya gabana, Hajia kudinsa basa gabana, Hajia asiri kuka rufa mana da kuka ajiye mu a nan, tabas asiri kuka rufa mana kuma Allah ne zai saka maku da alkhairi.......ama dan Allah ki yi hakuri ki daina yi a gaban yaron nan, ki yi hakuri Hajia ......." Sai ta fashe da kuka ta sake rungume yaronta wanda shima ya shiga nasa kukan, wanda dama ba zaka ji yana kuka ba sai idan abin ya shafeta ne Hajia ta rintse idannuwanta, fushinta bai sauka ba, haka kuma bata ji wani tausayinsu bama sai fitsararsu da ta gani ta juya ta fice a dakin ta bar gidan gaba daya, dan ta san da wahala a kai kayan nan a kuma dauko su Kayan aka fara shigowa da su , Baba Lauratu da sauri ta karaso tana kama Amina da mikar da ita hadi da fadin" subahanalah ke meye haka? Lafiya? Tare muke da Mai SHANU fa, menene? Lafiya?" Amina ta fashe da kuka ta fada jikin Baba tana kukan ta ce" Ki ce a sakeni mana, walahi na iya talaucina kuma na iya rike mutuncina, ki ce a sakeni nima fa ba sonsa nake yi ba, a kan me zan zama wulakantaciya har a gaban dana, a gaban Fadeel zata ringa wulakantani? Kin fi kowa sannin kowa zai hadiye banda Hasan ko?, Ki ce ta saka a bani takardata ni bana sin kayan nan, na je ina da su? Nace ni yar waye? Na saka na doshi ina wai? Haba haba wayo Allahna ni ba zan iya wannan rikicin ba walahi!" A hankali Baba ke kiran sunnanta dan bata so Baba ya karasa saukowa ya tarda wannan lamari, bata san me zai faru ba Amina ta ringa jan numfashi ta ce" Baba yaya ba zan yi kuka ba, kin ga fa hankalin Hasan take son daga min, abinda ba zan jura bafa, ni fa ban ce ina son yaron nan ba" Baba ta ja numfashi ta ce" Ya isa haka, kin ga fa da Baban muka sauko yace so yake ya zo ya ga murmushin marainiya da kansa, kina so ya ganki a haka ne hankalinsa ya tashi? Kin sani sarai fa yadfa yake daukan lamarinki da mahimmanci, ya dace ki sasauta ki yi masa adalci shima kin ji? Dan uwan mijin kuwa ki barni da shi zan rarasheshi kin ji? Maza share hawayenki ma yi maganar daga baya maza share kin ji?" Amina ta gyada kanta tana share hawayen ta dauko hijabinta ta zurma Baba ta juya dan gannin ko baban ya sauko? A hankali Baba ya juyar da bayansa ya dan matsa dan baya so su fahimci ya san wani abin Bismillah ta yi masa ya biyo bayanta yana murmushi Tunda ya shigo bai zauna ba, haka kuma bai idasa shigowa gaba dayansa ba, ya ja dai daga baki baki ya tsaya hannayensa a Harde a bayansa ya dan saci kallon Hasan da aka kwontar aka mayar da gabansa wajen bango dan basa so Baban ya fahimci ya yi kuka Murmushi ya yi yana fadin" Uman biyu, kin ga lefenki nan, zan je falo na dan jira dukan abinda yake na da naki ki tarkato ki hadawa Lauratu ta fito da su ta kai ta ba mabukata, ciki harda wannan hijabi naki da kuma takalmin dake kofar dakinki kin ji? Ni kam kayan nan kamar na tayaki dubawa kin gansu kuwa?" Amina ta tsatsare Baba da ido, murmushin yake ta kakaro tana sada kanta muryarta a cen ciki ta ce" Allah ya karra budi Baba, ama baba a bari a hankali idan na cire na yi wanki da komai sai na bada ko?" A dake, kansa tsaye , yana dan kama hanyar fita ya ce" Baki gane Ba Uman biyu, ina jiran hakan yanzu, ina nufin harda saitin akwatunnan cen gaskiya basu min ba, ai wanki ba damuwa bane idan ta kama nima sai na wanke fa, ke kuwa kina amarya kuma uwar gida ran gida ai ba'a isa a saka ki wanki yanzu ba" Da ido suka raka shi su dukansu Amina ta kai zaune muryarta a raunane ta ce" Baba ki bi shi dan Allah ki rarashe shi kar na taba kayan nan, kin ji abinda tace fa, bana son abinda zai taban mutuncina" Baba ta yatsina bakinta ta ce" Ke ki je ku yi maganar mana Amina, mutunci kuma ai kece mutuncin jikan da take tinkahon da shi, a dai juri zuwa rafi, watarana tulun zai fashe, tashi ki ban na je na aiwatar da abinda aka sakani, ai daidai yake da ku indai mai SHANU ne, kaya kuwa ta je ta same shi yadda suka yi sai mu ji idan ya zo ya dauke dama shi ya bada damar a kawo" Tana ji tana gani aka kwashe tsofafin kayanta Baba lauratu ta fita da su Baba gaba daya kayan nan ya umarci Baba da ta ware wa'inda ba'a dinka ba kala uku uku ma kanta, sauran kuwa ta je ta kai gidan Firdausi ta yiwu ta samu na anfanarwa kanta a ciki Sosai Baba ta fita da wannan farin cikin, da ta samu Firdausi har kamar nakuda zata taso mata ta farin ciki, kuka kuwa ta sha kamar zata hadiyi zuciya, daga baya tace Babar ta je da su gidanta dan idan ta bara mata a nan ba zata anfana da su ba zai kwashe, idan Allah ya sauketa lafia sai ta ringa dauka da kadan kadan tana anfanarwa kanta ________________________________ Hajia kam na fita gidan Uma ta je ta wuni a ranar, sun yi kiran wani gagarumin malamin adini ya zo da kansa Hajia ta gabatar masa da damuwarta, ta dora da fadin" Malan, wannan lamari idan ba aikin sihiri ba me zai haifar da shi? Mijina gaba daya ya birkice min ? Dan Allah a duba lamarin nan" Sosai Ustaz Laminu ya nazarci maganarta A tausashe ya ringa yi masu nasiha baki dayansu sannan ya dora da fadin" Da farko shi sihiri ba abu bane da ido bude ke ganninsa, haka kuma ba'a hawansa da hasashe ko zargi, kwarai zan baki adu'o'in da zaki dage da yi da fadawa Allah, idan har alkhairi ce yarinyar nan Allah ya kwontar maki da hankalinki a kanta, idan kuwa ba alkhairi bace Allah ya raba ba tare da hankalin kowa ya tashi ba, Shi Kuwa Alkali ki ci gaba da yi masa biyaya in sha Allah ko menene Allah zai warware mana baki daya" Sosai Malan ya basu adu'o'in da suka dace na karya sihiri, ya hada masu da na kariya kala daban daban sannan ya masu salama Umma ta ja numfashi ta ce" Kai kawata abin nan na damuna, wannan lamari sai hauhawa yake yi fisabililahi kuma ace ba sihiri bane? Kinsan fa shi malan Laminu dama haka yake, ko bincike fa baya yi kwata kwata, ko me ka kawo masa damuwarka a haka din nan ne zai durfafi abin, bi abinda yasa nake nace masa gaskiya abu da yawa da na saka a gabana na fada masa ala tayamu da Adu'a ina gannin hasken abin, ama yanzun kam na fi gane mu samu gagarumin malamin da zai buga mana kasa ya gano mana sirrin dake boye dan mu haye abin ta inda ya dace" Hajia Hauwa ta sauke ajiyar zuciya ta kurbi jus kadan tana kallon kawarta ta ce" Hajia Uma, kin san fa ni gaskiya ban cika son irin abubuwan nan ba, na fi so ko menene din na bi ta hanyar da ta dace, ina dalili sallar mutun ta lwana arba'in ba'a karba, idan halin mutuwa ya riskeni a haka fa? Kai ina tsoron bin bokaye wai sai ace malamai, wani malami ne zai aikata irin haka?, Ni yanzun abinda ya fi damuna kalar akwatunnan ne da muka dauka damuwata, ai ba classs a cakuden da muka yi, dan kayan dake ciki bani da darr da su, kayan nan ko uwar ta samu ai ta haye bale yar, balema ABDUL din yace zai min transfer na masu ranar da za'a kai kayan dazu da na kire shi ina kukan wani wulakancin na Alkali, ABDUL fa yanada damar ya bijirewa abin nan aman ya kyale alkali yana ta zubar masa da mutunci da sunna a kan banzar yarinyar nan mai manyan idannu!" Uma ta girgiza kanta tana tsaki ta ce" Ni kam abin nan na dauren kai, koda yake ai shima ba zata barshi banza ba, wainar da ake kawowa alkali ba kince wani sa'in tare suke ci ba? Ke dai dan kawia baki yarda da maganar boka bane da mun nemi mai kaifin wuka ya nuna mata ita karamar kwaro ce, ama walahi idan muka ga zata zame mana dan hakin da muka raina har ta kai ga tsole mana ido ko kw baki je ba ni zan je, domin ba zan yarda a wulakanta lamarin Gwamnana ba!" Hajia aka wani cira kai da isa an kira dan albarka da gwamna Uma ta ce" Kuma fa Hajia ke kika damu kanki da maganar kalolin akwatunnan nan, yanzun ba haka na ga ana yi ba sai ki ga an hada su red, su blue, su black, su fari du a tafia daya dan gadara ba, ba wani damuwa fa" Hajia ta tabe baki tace" A kalolin wannan yelow din mai kama da zawon baby ne ke ci min tuwo a kwarya, ke kika ce mu daukar mata ita kalar kalarta ce" Hajia Uma tace" Ni fa Allah itama bata da wata matsala, ke dai ba da kudi ba? Ki barsu ai sai mun nunawa maman Yarinyar nan mu ba sa'aninta bane, transfer din za'a yi mata ranar da mazan suka kai kayan a mata shiru, ta ga kudin ba bayani ta haukace, ita karamar yar bariki!" Hajia ta yi murmushi tana hango wulakancin yadda zai bada kala Shirye shirye ake yi ba kama hannun yaro Tunda maganar nan ta zauna har aka je aka kai lefe Hajia ta yi gadarar nan yan siyasarsu suka dauka garima ya dauka, saitin akwatunnan kayan ke yawo ta ko'ina, da hoton screen shot na transfer millioyin kudaden da aka dora wai na dinkin Amarya, kudin da sai a bude shagon dinkin na kasa da kasa da shi Daga kowani bangare fa aka mike kowane ya shiga shirye shirye Bangaren amarya kaya ake shirin zuba mata na garari, mahaifinta da mahaifiyarta da dangi sun hadu taf sunna bada himma Ta bangaren Hajia kuwa ta je da kanta gidan da za'a saka amaryar ta ga tsarin gidan , da kanta wannan karron ta ware bangaren da ya fi kyau din ma ABDUL din, ta gwamace hakan dan a yadda ta ga take taken mijinta idan har ta zabi nan ma Risala zata kwashi bakin ciki ne A event din auren diner daya jal ce za'a yi ta amaryar da ango bayan daurin aure da wunin biki Diner ce ta garari ta taron manya wace harda su davido mawakan yan gayu da manya manyan mawakan hausa aka gayata, tuni takardar gayar ta samu kowa harta da gagarumin Hl din da za'a gabatar da bikin Hajia ta tura kudinsa Kan Madame fa ya dau caji, bata da lokacin kowa, jikanta dake spain kawai take tabowa a kai a kai dan yan cenji, shima a gobe take sa ran zuwansa kasar domin daurin auren bai fi da saura kwana hudu ba a yau Happy juma'at yan uwa *NZL PAGE2️⃣4️⃣* Bangaren Amina, a lamarin yau da gobe na rayuwarta ta mayar da komai a kan tsari A cikin akwatunnanta tsararun hijabai irin na yadikan turkish kuka dinkin cen har kasa masu samfari kala daban daban da tsari na gayu take cakarewa da mora hankali kwonce Bata taba dinkunnan atampopin da sauran manyan kayan masu shegen kudi ba, ama ta taba irin dogwayan rigunna masu laushi da tsararen kyau A haka ta samu gyaran wata amarya wace take a tsohuwar anguwarsu, yarinyar a cen yar gayu ce kuma yar gata ce, ko a yanzu ta yarda Aminar ta gyarata ne dan ta ganewa idannuwanta idan har da gaske wai zaman da Amina ke yi a gidan nan a matsayin matar Hon ABDUL RA'UF ne? Domin maganar na zaga layi, yan mata kai ya dauki caji, kowace so take ta gazkata maganar nan dan ABDUL RA'UF din ba boyayen mutun bane, bale yawancin yan matan sunna jin maganar sunnansa ne a bakunnan samarinsu irin yadda suke koda shi da halayensa da kyautarsa da daukan wankansa da ajinsa tamkar wani saraki A yau sansanyar safiyar Alhamis, ya rage saura kwana uku a daura auren mutumen dake amsa sunnan miji a gareta, hakan ya sa gidan ya dinke da jama'a dangi da yan uwan dangi, wa'inda aka gayata da kuma Mu (😌😌😌😌 ni da kwate ai mun kusa wata a gidan) Bakin manyan mutanen sun rinjayi ya mu ya mu din , domin kuwa gidan kansa ya dauki motoci har ya zamto an cike wajen ajiyar motocin an fara ajiyewa a balbalin gidan Dafe dafe ake yi ta ko'ina ana ci ana wanke kwanoni, wata tukunyar na sauka wata take hawa Kayan aikinta ta kai cen baya wajen gardin din nan, hasalima itama tunda gidan ya fara daukan haramar mutane take guduwa domin har daki ake tardota ace an zo a gaisa ne a ringa kare mata kallo, ita kuwa hakan na damunta ainun, ga gyaran nata jikin da karara ta fadawa Baba Lauratu cewa ya isa haka in na so take yi fatarta ta cenza kala gaba daya ba, yanzu haka kunshin nan na gargajiya irin na gam din nan da aka yi mata ya hudo ya yi maroon sosai sai daukan ido yake yi a kan fatarta da ta dawo milk color tsabar gyara da anfani da su ruwan kwai da madarar ruwa, ita da kanta takan ji wani iri idan ta kalli fatarta , dan Husaini cewa yayi Mama ashe kema fara ce ba'a sanu ba?, Hasan kuwa sai ya kalleta ya yi murmushi irin ta birge shin nan Murmushi ta yi lokacin da Suraya ta ce" Oh Aunty Amina baki ga yadda hutu ya kamaki ba, ni kam dan Allah ki min irin gyaran fatarki Aunty, subahanalah dubi da kika cire hijabi, wai aunty harda gyaran Mama kina yi ba?" Kunya ce ta kama Amina, domin rigar dake jikinta ba wata mai dogon hannu bace, kuma ta cire hijabinta ne dan yanada haske domin kalar ash color ne mai haske idan har ruwan hadin gyaran nan ya taba shi zai lalace ne da kalar, gashi ko kanta babu wani abin kirki da ya rufe kan, batada kitso a kan dab kwalin wani mai sara sara ne ta dan yafa shi ta lauyo shi haka kadan a jikinta Dan murmushi kawai ta yi ta kasa bata amsar gyaran mamar da ta tambayeta ta shiga fadin" Surayah, kin ga hadin nan da na maki na hada kurkum ne da man ja da lalle na gargajiya, ana kwaba su a waje daya ne a shafe jiki gaba daya da shi sai a hau kujerar nan ta tsuguno mai kofa a zuba garwashi isashe a rufa wannan abin rufaf mai nauyi a bar fuska a waje ya yi ta bugun jiki, a kadan zaki dauki minti talatin a sama, dan haka dole ki jure , shi ake kira da DUKHAN, idan muka yi shi na kwana goma sai kin yi mamakin yadda zai kama maki fata, da farko fayar taki zata dauki duhu ne, a hankali muna murjewa da su dilka ana yin na kurkum da madara zai washe ki fara daukan annuri irin na amare, Yanzun sai kin mike tsaye na saka hannayena na shafe maki hadin sai ki zauna" Suraya ta yi murmushi ta ce" To aunty, ai in dai zan yi annuri irin naki ko meye zan jure walahi Mikewa ta yi tsayen ta juya ita kuma da dabara ta ringa shafe mata jikinta da hadin ko'ina da inanta harta da cinyoyinta dan koina ake shafawa, sannan ta zauna ita kuma ta yi wani shegen dukawa irin ka bada baya sosai din nan ta dan gantsarar da kugunta ba da gangan ba sai dan ya kama dole ta yi hakan a hankali ta sake debowa dan ta murje mata fuskarta da hadin da kuma kunnayenta da bayan kunnayen Shine a gaba, sai daya daga cikin masu bashi tsaro rike da wata akwatinsa sai babar rigarsa da ya cire a cikin mota ya bar na cikin , watau riga da wandon kayan suka biyo ta bayan ko zai samu saukin gaishe gaishen mutane da ya hadu da su tunda ya shigo Shi mamakima ya kashe shi gannin taron gidan nan, mamakinsa ta yaya suke iya jure wannan hayaniyar ne? Wai mema ya sa aka tara mutane ne har haka tun yau? A hankali ya ja birki daga karasawa ta kofar da yake da niyar yi daj ya shige ta kofar kicin Muryarta a sanyayen nan nata idan zata yiwa kowa magana a duniya banda shi ya ganar da shi itace a wajen a lokacin da ya kawar da kansa daga inda idannuwansa suka sauka kunnayensa suka jiyo magana kamar haka" Suraya ki gumtse bakinki kar ya shigar maki baki, kuma muna maganar turaren wuta, hajiyarki tace n dubu arba'in take so a hada maki, to ama baku yi maganar na ruwan ba, kin san fa babu wanda bana hadawa harda su humura duka kaf ina siyarwa" Sumaya dake son bude idannuwanta Aminar ta ce" Ki fa kula kar ki bude idannuwan nan ki bari har ki sauko saboda shi kwabin na fuskar harda kwai na saka ki bar idannuwanki a lunshe haka kar ki rintse su kuma kar ki bude su kar sikin namu ya koma baya" "Aunty?" Sumaya ta furta Gefen da yake kallo yana ta tunanin abinda ya dace ya yi, shin komawa ya dace ya yi ya bi ta tarin dumbin jama'ar cen dake iya hadasa masa zazabi, ko wucewa zai yi ba sai ya shiga harkar wannan fitsarariyar y'ar ba?, Wata zuciya ce tace masa'to idan ka koma a kan wani dalili?, Karewarta dai ace ka ga mace ba rufar kirki ka shigo ko?, Idan ta wani ka shigo ka tarar?, Ka je abinka' Juyowa ya yi ya fara kara takawa daidai Suraya na cewa" Shi na gyaran nonon fa?" Amina ta dafe goshinta ta ce" To wai ke ina hadinki da abin gyaran noni fisabililahi bayan ba auren kika taba yi ba, ba kuma shayarwa kika yi ba?, Ni dai kin ga nima ban yiwa kaina ba kuma gaskiya bana fadawa budurwa sirrin gyaran mama, idan har kinma ciko har wanda zai aureki ya zama ila a gareshi ai akoy matsala sai ki yi gagawar gyarawa, inma ba maza da iya wani abin daban ba ina idannuwansu ina zarce kallo?, Koda yake laifinku ne yan matan zamani, ko dinki kuma tashi yi sai a yi maku mai gidan mama ta yadda hakan zai dauki hankalin mai kallonku......ni kam mu yi maganar humurar dai bana son wancen" Sake ja ya yi yana juyawa ya mika hannu ya amshi jakar dake hannun wanda yake biye da shi kamar jela, domin da zarar ya tsaya shima yakan tsaya din ne har ya daga kafarsa Yana kallonsa har ya bar wajen kwata kwata sannan ya juyo daidai Amina ta juyo itama tana murmushin maganar Suraya Kwanon dake hannunta ta saki ya fadi kasa, lokaci daya kuma ta duka ta rarumo shi gabanta na yankewa ya fadi Daga duken ta rarume shi ta kusan kifa shi a kanta jikinta na rawa sosai ta hade kanta da cinyoyinta hankalinta a matukar tashe, bata taba hasashen cewa za'a iya biyowa ta nan haka kai tsaye ba, bata taba kawowa wani namiji zai zo nan haka kansa tsaye ba, ta manta dan masu gidab ya taba hadewa da ita ta nan din, sai dai ai rabonta da shi kusan sati fa ita tama manta da shi in ba jama'a ta gani ba ta tuna da taronsa ake yi A tsayen da yake in ba ABDUL ba maimakun ka yi gagawar shigewa tunda ka ga mutun ya gaza dagowa sakamakon shigarsa da ka tarar a haka, sai kawai ya zubawa gashinta ido da dan kwalin yan gayun ya zame ya bar mata gashi a fili, gashin Amina ba gashi mai santsi bane irin na larabawa, gashi ne sak namu na hausawa mai tauri a ido da cika sosai, sai dai guaran da yske samu da wankin karkashi ya sa gashin nata yake da laushi idan tabawa ne, kuma yakeda tsayin gaske domin idan kitsashi ne za'a yi haka wutsiyar ke yin bardan abinta Suraya ta ce" Aunty, indai irin kanshin nan naki nima fatata zata aura ni kam ina so, ina son humurar da turaren ruwa na zannin gado da akace kina hadawa shima kin ji Aunty?" Jin shiru bata amsata ba ua sakata itama jan bakinta ta yi gum da tunanin ko Aminar ta koma ciki, ko kuma yan shirun sun juyo ne Lalle Amina an dace, wannan gida haka? Lalle rayuwa Allah mai ba bawansa Samun kansa ya yi da nufar wajen da Hijabinta ke ajiye ya dauka yana rike numfashinsa dan ya tabata warin abin nan nata ba zai bar hancinsa ya huta ba Kawowa ya yi inda take tsugunen ya dora mata shi a kanta, hakan ya sa ta dago idannuwanta a firgice ta sauke su a saman fuskarsa Muryarsa cen cikin makogwaronsa ya ce" Kowama zai iya riskarki da suturar nan a jikinki" Hannunta dake cikinta a matse ta so fitarwa dan ta bashi amsa, a nan kirjinta dake daf da lekowa ya leko din ta saman rigar Dan bakinta mai zannen na mashaya ta murguda da balagagen rashin kunyarta ta ce" To ins ruwan mutun ko a yaya aka tardo ni ne?"....... Bakinsa ya tabe shima kasan sosai ya ce" Hakane kuma, to ama na nuna maki hanya shine daidai a matsayina na..............murmushi ya saki dan dama burinsa ya ga tataciyar fitsarar, ai kuwa ya ga alamu domin an fara masa mar mar da idannu irin za'a idasa hararensa da su din nan , Ya idasa fadin " A matsayina na jagoranki, bangonki, Uban gidanki.....kuma yayank....." Amina ta mike tsaye dan kusancin nasu na neman zama haramun, zomin har iskar furucinsa ke shiga hancinta tsabar yana kaifin harshe , rai bace ta ce" Kai!" Yanzunma tun daga kan nata har kasa ya sauke dubansa, sai kuma ya dan tabe baki ciki ciki sosai yace" Kwaila " Daga haka ya juya ya kama hanyar shigewarsa ta kicin din, inda ya bar Amina idannuwanta tamkar zasu zazago daga raminsu su manu a jikinsa dan mamaki da takaicin duniya da suka sameta da yamacin nan Har ya kusan shigewa ya dan saci kallonta ya samu kansa da sakin murmushi, sai kuma ya gimtse bakinsa a ransa yana ayana' Wai ita uwar son girma, in ba shirme ba ina hadin mace da namiji ta wannan fannin ne? Yau ko yaro dan shekara goma sha biyar da balagar ke masa kwalele sai ki ji tsoronsa bale ni, in ba dan takeki zai zamto min matsalar farin cikina ba da kafin mu saki hannun junna sai na take ki ta yadda zaki bambance waye yayan......shekarunki na sunne abin duba ba!' Amina kam da sauri ta juya wajen suraya du a tsarge tana kallonta da son fahimtar idan bata ji ko gannin fitsarar da yaron nan ya yi mata ba Gannin ta nutsu hayakin na hauhawarta ya sakata dantse lebenta da haushi ta dauki hijabinta ko hannun bata wanke ba ta zurmuka ta zauna a wajen zamanta abin na ciyo mata zuciya Shin jama'a ina zata kai wannan abin bakin ciki? Ace kannin bayanta ya dubeta ita Amina yace da ita kwaila? Shekararta da yannayin jikinta kadai ai ya girmi yara ama shii da balagagiyar rashin kunya ya kireta da kwaila? Kai , kai kafin ta bar gidan nan ko yayane sai ta dauke fuskarsa da mari , da yaa bataa takardarta wannan ne burinta na farko dan ta huce takaicin da ya guma mata na kwana da kwanaki a gidansu *NZL PAGE2️⃣5️⃣* Kokowa ce ke neman kaurewa a tsakaninsu, ko nace neman amsar kai, saurara mata ya yi ya bata dama ta ringa yakushi da son kwatar kanta har sai da girgizar da take ta gama kai masa sakon da yake ta daukan caji lamari ya amsa iya amsa duniya ta dauki dumi komai ya yi taurin da zai iya yaki sannan ya saka hannunsa ya janye hannayenta da ta rugfe mamanta da su ya zuba masu ido yana kallo Kalarsu gaba daya ya ji tana ruda kwonyarsa, dan duhunsu da bakin bakinsu ke ta harararsa Da dayan hannunsa ya taba su dan ya ji laushinsu domin ai ance wace ta san lamari lamari ya san sukan yi laushi ne sosai Sai dai tabawar da ya yi sai ya ji tauri ne da su maimakun laushi Ido ta rintse tana kukan dake fitowa daga cen kasan zuciyarta A rikice ta bude idannuwanta jin ya shiga mamatsa mata maman da ko bra bata saka masu ba Sake kokarin kwacewa take yi, a hankali ya saka kafarsa ya dane mata cinyarta da mugunta danma azabar zafin ta hannata wani motsin Ai kau zafin ya kai mata har cikin kwanyarta Sai da ta sake fashewa da wani kukan tana fadim" Kai, kai wai meye haka, meye wannan wulakancin? Me kake yi haka? Ka cikani kar ka janyowa kanka fitina, ka cikani haka ka ji na fada maka!" Kafafuwanta ya wara da dan karfi tana matsewa yana bi yana budewa har ya zamto ya wara kafafuwan nata ta yadda hakan ya zame mata bakon yannayin da ya sakata zabura kukanta ya dauke dif tana zarrar ido da kallonsa Bau wani kashe hasken dakin ba ko rage shi, tar tana kallonsa yana kallonta ya janye dogon wandon dake jikinsa sannan ya kama gajerun biyu na ciki summa ya yi masu diban albarka Da karfi ta dauki shahadar da ta zamo itace abinda ta farra zo mata bakints, sai kuma ta shiga kiran sunnansa tana kai masa duka a gadon bayansa Tana yi ne da dukkan karfinta dan a lokacin da karfin nata a tare da ita Bata taba sannin cewa bayan zare rai da akace azabarsa bata kamantuwa, da kuma haihuwa da akace sai wace ta dandana akoy wata azabar da mata suka cinye abinsu suka boye har suke zumudi ba sai a yau, a yanzu da yaron nan ya yi mata wata ratsawar da shi din da kansa sai da ya dauki dan lokaci idannuwansa a rintse sannan ya bude ya sauke dubansa a kan fuskarta kunnayensa na dodewa sakamakon tartsetsen ihun da ta tartsa lokaci daya tana fadin" Wayo Allahna zai kashe ni, Baba! BABA! BABA!" A haukace gabanta na faduwa ta ja wani mahaukacin birki da niyar kama hannun kofar dakin Aminar ta shiga da wayar dake kange a kunnenta tana neman SIR , domin Hajia ce a wayar kamar zata janyota ta wayar ta mamaka mata mari tana ihun ta kaima ABDUL wayar nan , wai yana ina! Jikinta ne ya fara rawa a lokacin da ta ji muryarsa da dan karfi ya furta" AHHHHHHHH!" A haukace hankalinta a kololuwar tashe ta juyo har tana neman kifawa ta abin matatakalar idannuwansu suka sarke da na Baba wanda ihun Amina ya fitar da shi daga dakinsa dake bude yana karatun Alkur'aninsa , bai rufe ba dan ya san gidan ba kowa sai daidaikun masu aiki dan ya ringa jin motsin mutane, Ihun Amina ba farko ya saka shi zabura har kafarsa na kamewa ya fito da alkur'anin a hannunsa, kiran sunnansa da take yi da dukkan karfinta da kukan dake tare da amon muryarta, da kalmar da ta fada mai nuni da abinda ke faruwa da ita, sai nishin da ya fito daga muryar ABDUL din ya saka shi gane ainahin abinda yake faruwar Al'ajabi ya damki zuciyarsa A hankali ya koma kofar nasa dakin bayan ya yafito yar aikin ya tsaya ya mika mata hannu ya amshi wayar sannan ya koma ciki Hajia dake tsaye har tana girgiza dan bacin rai ta ce" Umaima, yaya a kalla zaki mayar da ni shashasha ne? Nace maki ki duba min shi har gardin, da cen wajen masu aikin nan maza, ki duba inda ya tsiri kai yaran nan ki bani shi a waya, a kadab an dauki minti goma sha biyar ina jiranki kina min shirme? Ki bani ABDUL a waya ko walahi idan na zo na salameki tunda baki da wani anfani , shashashar banza da wofi kawai!" Baba a tausashe yana kaiwa zaune ya ce" Ta alkali wani laifi jikan nawa ya yi ne?" Sai da yi dif, sai kuma ta shiga magana kamar zata fashe da kuka tace" Alkali, yanzu fisabililahi kana kallon ABDUL sai yadda ya yi da mutane yana wulakanta mutane bayan haihuwarsa aka yi dan ubansa? Ya cewa yarinya kar ta yarda ta je wajen diner ya kashe wayarsa gaba daya ga yarinya da kawayenta nan sun rikice ba ita ba harta uwarta gatacen ta rikice ana ta doka number abdul ba'a samu , shine ita wannan marar anfanin ta kasa samo min shi ta bani shi na ji a kan wani dan uban dalilin zai hannata zuwa wajen dinern da muka kashe makudan kudade a kai kuma muka gayaci manyan mutanen da tunni wasu sunna cen a zazaune?" Gaban goshinsa ya shafa a hankali a tausashe yace" Hauwau, ki yi magana a hankali, sannan ku kwontar da hankalinki, shin akoy wani dalili da kika kula a lamarin dake iya cenza ra'ayinsa na son halartar taron naku?, Irin abinda kw iya taba adininsa, ko mutuncinsa?" Hajia ta fita daga cikin mutane sosai ta kwontar da muryarta ta ce" Alkali, wani irin abu ne zai taba mutuncinsa ko addinin da yake namu muma? Menene marar dadi a wajen nan ne Alkali? Da yawun bakinsa na tara taron nan, da yardarsa na yi komai, da aljihunsa na yi komai, yaya zai ce yarinya kar taje waje? ?" Baba Mai shanu ya ce " Haka yace da ita kar taje?" Hajia ta tabatar masa ta hanyar amsashi da kwarai kiranta ya yi ya fada mata ya katse kiran Alkali ya rasa ta inda zai bilowa lamarin, sosai yake jin shayin fitowa kansa tsaye yace da Hajiar ta daina dagawa kanta hankali ta tafi da iyalinsa ta kai masa gida, a kan umarnin da ya yiwa iyalinsa a barshi ta yi masa LADABI, sai dai bai san abinda haka zai haifar ba A nutse yace" Hauwau, kina ji? Ki yi hakuri tunda haka ya yanke harma ya kashe wayarsa, ta yiwu wani abin ne ya daga masa hankali dangane da diner din, ki taho gida kawai" Da mamaki a muryarta ta ce" Alkali, na taho gida fa kace?" A takaice ya ce" Eh " Hajia ta mike tsaye a saman kujerar ta ce" Alkali, wai me yasa kake min haka ne yanzu? Me yasa kake min haka ne? Ka san da hakan zai zama wani zagi ne a gareni a cikin gari ko?" "A zage ki dan jikanki ya hanna matarsa zuwa wajen diner? Ko a zage ki dan na tabata akoy baban dalilin da ya saka shi hannata zuwa wajen dinern?, Saurara Hauwau ki je ki binciketa tun daga kan kawayen dake zagaye da ita, da irin mutanen da kuka gayata harta da irin suturar da kuka saka mata, na tabata idan har kun yi wasa wajen suturarta ba zai lamunci haka ba, kin sani sarai yanada mutane a barbaje a ko'ina ko? Kin san ba zai yarda ya saka kafarsa ba tare da ya gamsu da yannayin wajen ba ko? So plz, i bg u, ki barni na huta da fitinar auren nan haka, ku kimtsata ku mikata dakin.........." Ihun da ya kara shiga kunnensa mai karfi na jigataciyar muryar Amuna ya sakashi dauke maganarsa dif ya sake mikewa daga zaunen da ya yi ya nufi hanyar fitar, sai kuma ya sake ja ya tsaya hankalinsa na neman tashi, fargaba na neman rinjayarsa Kwarai ihun nan a kunnenta ya sauka itama tana sauraron ihun nan kuwa na menene? Kofar ya kuma dosa domin gabansa faduwa yake yi, tsoronsa daya kar yaron nan ya kashe yar mutane a tunaninsa bazawara ce ya gana mata azabar da ta fi ta bazawarar dauka, bale yar tsamar da ya kula dake tsakaninsu wace kowani namiji zai so horar da wace ta raina shi irin haka "Alkali waye ke kula da kiran Baba?" Hajia ta fada hankalinta tashe tana fara tafia da dan sauri baba mai shanu ya kuma jan birki , jiki a mace ya ce" Ba kowa, sai kun zo" Kit ya katse mata kiran ya rasa yaya zai yi, shi dai ya san ko hauka yake yi ba zai shiga dakin nan a wannan lokaci ba, sai dai kulan Amina da yadda muryarta ta shake na sakashi a tashin hankali har yana son manta cewa ko menene sirinsu iya su A ciki kuwa lamari da yake samun kowani bakon shiga, saurayi ne ya samu ABDUL Ya samu nutsuwa da wuri sosai, domin a lokacin da ya ratsa tantanin Budurcin amina ko zuwa goma bai yi ba ya samu nutsuwar da ta sakashi sakin nishi tamkar zai summa Haka kuma lamarin dake faruwa da lafiyayen namiji farin shiga ko anda ya jike a harkar ya shiga sake motsa shi, watau samun nutsuwa ta farko ta zamto sharar fage ce a lokacin da ya so tashi a kanta yana ji zuciyarsa na wani irin fatfatfat tamkar zata faso kirjinsa ta fito, sai ya ji abinda ya fara laushi na fara wani irin mugun cika da dadaurewa A dole ya ki fitowa, a dole ya sake riƙe Amina dake fatan farkawa ta samu kanta a summe ace da ita ai summan kwana biyu ta yi har ta yi mumunan mafarkin nan, sai dai tana jin ya daina gana mata azabar da bata taba tunanin yaro dan tsurut haka zai aikata ba ya aikata mata ya ci gaba da motsi a jikinta ne ta sake gwada sa'arta ta hanyar sakw kiran wanda ya kawota gidan tana ihun ya taimaketa ko Allah zai sa a dace ya jita ya taimaketan, sai dai kashhh, karshema kukanta ya zamto tamkar busar sarewa da karin kaimi wajen taka rawarsa, tun tana jin gaban jikinta a jikinta har ta daina jinsu kwata kwata, tun muryarta na fita da karfi har ta disashe gaba daya Jiki a mace baba ya dawo matatakalar hawan ta kusan hudu ya zauna ya rafka tagumi yana Adu'a a kasan zuciyarsa da jiran tsamanin aikin yaro😭 Da sauri Hajia ta ringa tafia ta rasa number ya dace a yanzu ta yi kira Tana komawa ta tarar da Mahaifiyar RISALA ta dage sai fada take yi da fadin magangannu tana kallon kawarta kamar haka" Ke Hajia ki bar maganar nan, an yi ci gaban da namiji karyarsa ta sha karya yace zai yiwa mace haka, na tabata yaron nan wani salon raini ne da nuna isarsa a kan wajen da bai isa ba, a kan wani dalili zai saka min ya ta yi kuka?, Walahi kin ji na rantse bai isa ba, shi din banza shi din wofi, a kan yata zan iya aikata aikin da kare ba zai ci ba, dole ya fito a je a yi dinen nan a gama, du irin kwaliyar nan da Risalah ta sha za'a fito min da wani wasan na rainin wayo? Ai ni kaf a dangina babu talaka, in dan wannan ne, dan takamarsa kudi ai gidan ya tarar, walahi walahi karya yake shi karamin dan duniya yace zai zageni, shi da ya garwayu da talakawanma har yanzu talaucin ke bibiyarsa ya je ya dauko mace yar talakawa ba gaba ba baya futuk kamar beran masalaci? Idan har ABDUL RA'UF ya yi wasa da ni, tabas zan yi wasa da shi!" " Ke dillah rufewa mutane baki!" Hajia ta fada a kufule cike da matsanancin mamaki tana kallon maman Risalar Takowa ta yi ta karasa shigowa tana kallonta tamkar zata dauketa da mari a kausashe ta ce" Ke?, Har kin isa ke ki budi bakinki mai tsami ki zagi ABDUL RA'UF?" Hajia ta dire maganar tana sake bin dakin da mutanen dake ciki du da aka mike ana son basu hakuri baki dayansu Hajia ta mika hannunta ta dakatar da Uma ta ce" Ina yake kudin? I said ina yake kudin dan Uban Ubank.............." "Subahanalah Hajia zagi kuma da girmanki? Dan Allah kar ku yi haka a yanzu da kuka zama daya ai ba maganar haka ta fara shigowa a tsakani, maganar Diner kuwa idan wanda ya aurwta yace ya fasa ai inaga aljihunsa ne sai a ba baki abinci su ci su watse ai ba yau ba aka fara taro ba ango da amarya ko?" Auntyn Maman Risala ta fada tana son katse rigimar domin falon cike yake da yan zubawa wuta essence su hasata maimakun su kasheta, duda zagin da maganar ina kudin itama sun tsaye mata a rai harma tanada amsar ba Hajiar sai dai ba zata so a tafi da su haka a baki ba, uwa uba idan har mahaifiyar RISALA ta yi wasa da lamarin soyayar da y'arta ke yiwa ABDUL zata shiga uku ne da kanta, domin abinda take gudun ne zai faru, y'ar tata ce zata zama abin tausayi, babu wanda bai san cewa Risalah ta fi Abdul karfafa soyayarsu Saukowa take yi da gudu gudu daga sama, kuka take ci na maganar ABDUL, sai dai ana fada mata abinda ke shirin faruwa ta ji hankalinta ya karra tashi, Umanta ta zagi Hajia? So take yo a saketa ne? A haukace ta mike ta cakumi rigar amarenta ta shiga saukowa da gudu gudu tana fadin" Mama, mama dan girman Allah me kuke yi haka? Mama!" Ta idasa fada da karfi tana gurdewa a abin hawa na biyun ta rike karfen da ake dafawa ta fashe da ihun kukan da ya sake daukan hankalin jama'ar wajen dake ta bada hakuri sunna ririke Hajia da umanta tamkar zasu daku Hajia ta janye hannunta daga na wata datijuwa dake bata baki a hankali ta ce" Its ok Hajia" Sai kuma ta sake juyawa wajen da maman Risala ke tsaye ta ce" Ki gwada min aiki irin na isasu ki je ki dauki yarki ku je wajen diner ku raya daren nan, ni kuma a yau zan nuna maki aiki na wace ta isa na baki sakamakon hakan, ABDUL yace kar ta je na ga Ubanda zai taka dokarsa! Yarinya baki san maza ba sai kin ji kanki baya jikin wuyanki!" Daga haka ta juya ta nufi waje tana kokarin sake kiran number Umaimat dan hankalinta gaba daya ya yi gidanta irin yadda gabanta ke faduwa a kan lamarin ya fi komai daga mata hankali, bata san waye wannan mai kuka haka ba, koma waye Alkali na tare da shi, bata san wacece ke kiran mijinta haka ba, wacece ke neman ceto haka ba, loma wacece wani baban lamari marar dadi ya tunkarota............ Bayan motar ta bude da kanta ta shiga ta rufe tana fadiN" KAINI GIDA" A KAIKI INA? 🧐😫😫😫😫😫😫😫😫😫🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢 *NZL PAGE2️⃣6️⃣* Janta direban ya shiga yi cike da kwarewa sannan a hankali dan gudun tala dokar ABDUL RA'UF kan kar a ringa gudu da kakaninsa a cikin mota Hajia ta daga kiran Hajia Umma ta saka a kunnenta tana amsawa Abinda Umman tace ya sakata dan tabe baki a hankali ta ce" Uma kin gane, kuna iya yin dinern a tsakaninku, ku salami baki.ku ce masu wani abin urgent ya hanna mana halarta, sannan idan ta ga dama ta baku yarinyar ku mikata gidanta in ta kiya ta zaunar da ita a nan, indai ni HAUWAUN ALKALI ce zan je na daukota ta jima bata tare a dakin GWAMNA ba, !" Sosai Uma ke rarashinta dan ta bata hakuri ama Hajia ta katse kiran tana duban direban ta ce" Ka daga kafa mana" Da darajata ya amsa sannan ya ci gaba da tukin da gudu kadan Fitowa ta yi yanzuma tana dan jan karamin mayafinta dake saman kafadarta ta shiga nufar part dinsu Ja ta yi gannin Umaimat na kai kawo du a hargitse tana dubanta da haushi gannin ta sake firgicewa ganninta ta ce" Umaimat tabas a yau zan salameki daga gidan nan ba sai gobe ba tunda baki da wani anfani sai hauka da shashanci, wai nace ki kaiwa ABDUL waya sai ki kaima Alkali!" A rikice Umaimar ta ringa binta tana fadin" Hajia dan Allah ki yi hakuri, sir dinne nake ta nema nake ta nema dan ALLAH hajia karki koreni" Tana biye da ita tana bata hakurin ne har suka shige falon tana rike da jakarta Hajia bata tsaya ta kulata ba Turus Hajia ta yi gannin Alkali , Alkali nata zaune dangalgal a kasa wajen abin hawa, watau saman upstairs hannayensa biyubiyu a dafe da gefen fuskarsa yayi wani zuru zuru da shi kamar ya sha tsinanen duka Gabanta ne ya fadi domin abinda ya fadar mata da gaba a lamarin shine ABDUL RA'UF ne wani abun ya same shi, Gwuiwoyinta na rawa, hannayenta na rawa ta saki mayafin ta karasa gabansa jiki ba karfi ta ce" Alkali? Ina ABDUL din?" Tsakani da Allah ko a zamanin samartaka ba karamin abu ke hadasa masa faduwar gaba ba, bale a yanzu da tsufa ya zo ko wace wace baya wani shayin komai, ama ganninta a wannan lokacin kusan awa biyu kennan da Abdullahi ke dakin Amina baiwar Allah bai fito ba, sai ya ji gabansa ya kwonci kwonci ya fadi Fitinar Hauwau daukaka take yi a kulun safiyar Allah, hakan ya sa yake jin shayinta a cikin ransa tamkar itace mijin idan wani abin fitinar ya tashi Kokarin fashewa take yi da kuka ta ce" Ni na san ba banza ba jikana zai tayar min da hankali a kan maganar diner din nan, Alkali dan annabi Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam ka fadan inda yaron nan yake, me ya same shi ne? Me yake damunsa ne? Ina yake ne?............................" " Dan Allah ka fita, ka fitar min a daki nace........" Gajiyayiyar, shakakiyar sanyayar muryarta ke tashi a hankali, da yannayi na kamar a tsorace take da jin muryoyin dake tashi a kusa da dakin da take wa'inda a dazu bata ji ba sai a yanzu, haka kuma kamar an nufeta ne da wani nufin da ya sake dan hargitsa yannayinta, A waje kuwa, amon muryar du laushinsa kunnaye na jiyowa domin dare ne ya fara rabawa ba takun jama'a a gidan ba wata hayaniya, gashi ba wani gini bane mai sirrin nan dan irin gidin nan ne ko tsaki ka yi a dakinka ana iya jiyo shi a dakin makocinka "Ki bari mana " muryarsa shima tamkar bajimin zaki ta shiga kunnan kakarsa a lokacin da ta dago kanta ta kai dubanta dakin da aka saka yarinyar nan Da farko a rudu ta shiga na tunanin meye haka kuma? Daga baya sai ta zabura daga kusan mijinta ta sake kallon hanyar, lokaci daya ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi rajune Alkali? Ina Abdul? Me me me ABDUL yake yi a dakin cen? Ka cemin wani ne ya fada mata daki alkali kace min wani ne ya diro mata kamar yadda ta saba fada ba ABDUL dina bane" Da sauri Umaima ta bar falon hankalinta tashe, ta sani ne in ba ALLAH ya tsaya mata ba shan ruwanta ya kare a gidan nan, Gannin kallon da Baba ke yi mata ya sakata juyawa ta shiga hawa a haukace tana fadin" ABDUL? ABDUL? ABDUL?" Mikewar baba ya yi shima ya bita dan ya sani sarai Hauwau na iya afkawa dakin cen Da wani irin sauri ya mike daga saman gadon da yake zaune, domin yana ajiyeta ya zauna shima yana son warwarewa kansa abinda ke damunsa a kwakwaluwarsa Da takun cikaken namiji mai ji da karfi da girgizajen balagagen shiga hantsi ya karasa ya saka hannunsa ya dana kofar da tuni Hajia ta murda ya saka sakata sannan ya bar ky din a jikin kofar ya tsaya a jikin kofar ya rintse idannuwansa yana jin irin dokawar da ta fara yi da karfi tana kiran sunnansa, mamaki na neman kashe shi da tunanin wai idan da ya barta zata bude dakin nan ta shigo ne? Lalle da yau ya yiwa kakarsa abinda mamakinsa zaya kasheta, aa yana tunanin ya dace ko me zata yi ta ringa kiyaye limit, akoy abinda idan ka yi Allah ne zai kamaka da shi, da ta tardo su ba suturar kirki fa? Duda ko a yanzun shine mai suturar a jikinsa ita mai hararansan cen ta ki pantma ya maida mata bale a kai ga suturar Wani ihun kuka hajia ta barke da shi mai cin zuciyar nan ta kama abin budewar tana jijigawa a haukace ta ce" Abdul ka buden kofar nan kafin na tsine maka albarka! Ka buden kofar nan kafin ka kasheni" Baba bai san murmushi na iya samunsa a wannan lokacin ba sai da ta yi furucin nan, yana murmushin a tsayen da yake yana kallon sabon haukar Hauwau ya ce " Kina manta ba ɗan da kika haifa bane ABDUL? A kiyaye harshe dai dan gaskiya bana tunanin zai tsinu fa" Juyowa ta yi wajen Alkali , a hankali ta dawo gabansa ta sasauta muryarta da kukan ta ce" Alkali, dama kai ka hannashi zuwa dinern ka rufe shi da yarinyar nan?" "Ashe ke shashasha ce? Ashe baki da hankali?" Baba ya fada muryarsa dage a kan tata sosai dan ta fara kular da shi Itama da ihun kukan tace" Nice shashashar Alkali? Nice shashashar ? ABDUL ne a dakin nan? Me yake yi? Maganar me nake ji? Taimakon me zai mata? Me ABDUL yake yi a dakin nan da saka hannunka a cikin lamarin nan ko?" A kausashe Baba ya kama hannunta ya mata wani jan da bata taba zaton da sauran karfi haka a tsintsiyoyin hannunsa ba ya nufi nata dakin ya bude ya turata ciki ya ja ya rufe yana kallonta ya ce" Abinda kike tunani, shi ya je yi, ko kinada matsala da haka ne?" Ido ta kwalalo tana kallon Baba ta ce" Alkali, kana nufin ABDUL RA'UF ne ya tashi a yau ranar da nake shirin yi masa gata da yarinyar budurwar amaryarsa ya wulakanta wannan ranar ta hanyar zuwa ya samu matar da ta girme shi a duniya? ABDUL dina ne ya je ya samu wata mace cen marar daraja a cikin tsarin matan da suka isa ya duba har ya je mata a matsayin miji? ABDUL da aka daurawa aure da sabuwa dal din budurwa dake sonsa tamkar ranta wace zata tarairayeshi ta bashi soyayar da ta dace da shi ya zo ya tsinci me a wajen mai siyar da kosai?" Ta karashe tana dafe zuciyarta tana wani irin haki tamkar zata sume , sai cire shigar jikinta take yi domin ji take yi sikewa zata yi Alkali ya tabe baki ya gyada kansa ya ce" Ba mamaki ke kuwa abinda zai yi ajalinki kennan, watau yiwa lamarin ubangiji shishigi da saka damuwa a abinda bai dace ace ya dameka ba, sai dai ki sani idan kika mutu a haka sai ji je ki san abinda zaki fadawa ubangijinki Hauwau, dan bana tunanin in kinada abin fada gaskiya, kuma kin ga zan so Ki kiyayi furucinki, ki kiyayi harshenki, idan kina tunanin kin tara saloli kin tsaya a kan kafafuwanki a yanzu babu abinda zai daki rayuwarki ki sani da wanda ya juye duniyar kike son kawowa hali na marar godiya a gareshi" baba ya ajiye maganar a tausashe yana binta sa kallo har ta gama shan ruwan da ta kafa tana ta wani iri irin na mai jira a yi wace za'a yin nan Zama ya yi shina yana fuskantarta ya ce" kina maganar daraja aka kai uwar gidansa daraja ne? Ki fada min akoy namijin da zai kara mace bayan wace ya sani ta sanshi a farkon haduwa suka kasance aminen junna suke rayuwa ta mutuntawa da kaunar junna har ya auro watanta ya bata darajar da ta wuce ta wace ta sakashi a duniyar manya?, Hauwau kin yi sake tunda farko da aurenta ya dauru, kika kuma yin sake ta zauna dar a cikin gidan nan, kika hada mata lefe da kanki, har kika barta da mijinta, ya je ya samu abinda ya dace ace ya samu daga gareta kafin koda wata zata samu ya zamto mai wajen ce ta fara samu, Hauwau ki gane Aminar nan dai talaka itace mai ABDUL, du wata wace zai kawo da sunnan siyaya ko macewa a soyaya sunnanta amarya, dama zulumina tsorona kar yaje gaban Allah a tuhumeshi da wulakantar da marainiya, a yau da ya aikata haka koda ba a son ransa bane Alhamdulilah, da ke din, da shi din, babu abinda kuka isa ku yi, ita amaryar da kuke takama kema da bakinki kin kireta amarya, idan yar mutunci ce ta shigo da mutunci ta mutunta yayarta wace ta bata hanya su zauna lafiya, idan ba yar mutunci bace ni Alkali Aliyu na sayi rigimarku daga ke har duk wani wanda yake gannin ya yi ruwa ya yi tsaki a lamarin!" Baba ya sake tsayawa yana kallonta da fahimtar duka shirunta abinda yake nufi, watau jira take yi ya yi ya gama ta fita ko? Murmushi ya yi ya ce" Ki sani idan kika fito daga dakin nan sai dai dan ki je ki taimakawa matar jikanki , idan dan ki wulakantata ne Hauwau rigima zata kulu da ni da ke koda ita zata yi sanadiyar da ba zaki yi min takaba ba idan na rigayeki zuwa gidan gaskiya!" A zabure ta dago daga shashareshin da take tana jira ya gama yayaba mata maganar ta je ta nuna masa ta isa da jikanta ta zuba masa idannuwa da jin furucinsa na karshe wanda shi ya fi komai neman dakatar da bugawar zuciyarta Ikon Allah, ashe zata wayi gari ta ga halaya irin ta da namiji? Ashe zata bude ido ta ga wulakanci irin wanda karema ba zai ci ba daga mijinta abin kaunarta Alkalinta a kan wata cen? Ashe zata ga ranar nan ita Hauwau? Daga haka BABA mai shanu ya sake mikewa ya juya ya fitowarsa ya kama hanyar dakinsa, domin ko menene ya san a yanzu kam zata samu sasaucin farmakin da ake kai mata, domin maganarsa ta nuna masa cewa ya daga mata kafa ne, Murmushi ya yi yana ayanawa' rikicinma ya zi da sauki masha Allah, Allah kara tausasa halayar Hauwau' Shigewa ya yi ya rufe abinsa ya sake daukan Alkur'aninsa ya ci gaba daga inda ya tsaya , dan ya zame masa sabo idan bai yi karatun Alkur'ani ba du dare baya iya rintsa idannuwansa da dadi Jin shirun ya yi yawa ya sakashi cire kansa daga jikin kofar da ya kifa yana sauraron kalaman kakarsa Abubuwa ne goma da gomiyatara suka taru suka yi masa yawa a cen kasan zuciyarsa A hankali ya juyo da nufin sake kallon inda ya ajiyeta bayan ya talafeta ya sakata a ruwan zafin da ya farkar da ita daga yar kankannuwar summar da ta yi ta dora kukanta daga inda ta tsaya da tarin Allah ya isan da tana yi yaba nema mata yafiya a wajen Allah , tunda shi dai ya san ba abin a masa Allah ya isa ya yi ba, koda an yi masa ba kamashi zata yi ba tunda ai ba zuwa ya yi ya dage bujenta ya afka ba, sai da aka daura masa ita ai kau? kukanta ya dauke tsit tunda ta ji muryar Hajia da tsoron kar hajiar ta shigo dakin ta sameta a irin wannan yannayi ta yi tsuru tsuru tana jira ta ga abinda zai sake samunta sanadiyar wannan bawan Allahn da ya shigo mata rayuwa da garaje yake son Kaita kabarinta da ranta ba tare da rai ya bar gangar jikinta ba Walahi, wata mahaukaciyar faduwar gaba da ta sameta da ta ga ya juyo sai da ta rintse idannuwanta da karfi tana dantse lebenta da korar shedan a duniyarta, dan ta san ba komai zai sakaka jin tsoron kanninka ba irin aikin shedan a duniya Kallonta yake yi daga tsayen da yake, tarin tambayoyi ne dankam a cikin zuciyarsa, sannin cewa bashida amsosinsu a dole ya dan kara takowa wajen da take a giciye, wani irin kwonciya ita ba a kwonce ba, ita ba a ringeshe ba ta cakumi abin rufa ta cumuimuye jikinta da shi sai kikifta idannuwa take yi kamar an jijiga bera a kwano Tsoratar da ya ga ta yi a lokacin da ya nufota ya sakashi sake dan dakatawa yana kallonta, ajiyar zuciya take saukewa ta dauke kanta a kansa bakin fitsarar a cune tana kallon gefe hakan ya saka shi sakin dan murmushi sannan ya karasa ya dauki shadar zuwa diner dinsa a hannu ya kabe ya sake juyowa ya yi mata kallon da shi kadai ya san tarin tambayoyin dake cikinsa sannan ya juya bai ce mata komai ba ya fice a dakin Amina na kallon gefe sai da ta ji rufewar kofar ta maido dubanta a kan kofar A hankali idannuwanta suka sake cikawa da kwallah ta fashe da wani kukan da sam batada karfin yinsa da karfi A hankali ta shiga fadin" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, wayo Allahna na shiga ukuna, innalilahi wa inna ilaihi rajune ina zan kai wannan abin kunyar? Wayo Allahna ni Amina da girmana da darajata yaro karami ya min wannan wulakancin a kan abinda nake yiwa datijo tanadi? Allah ne zai saka min zalina da ka ci!, Me na yi maka da zafi haka da zaka rabani da prde dina bayan ka san na san aurenmu na yan dakiku ne?, Idan ka saba kaida kake da sabuwar amarya yarinya irinka ka je ka yi shirmenka a cen mana? Yanzu da wani ido zan kalli duniya ta kalle ni? ( Ah to, a dai san a yadda za'ayi ido hudu da jama'ar gidan Ni zan ladabi, inaga harda wace ta dora katuwar tukunyar gashi) Sosai Amina ta ci kukanta mai ratsa zuciya, kuka na takaici, domin bata taba kawowa a ranta cewa haka zai faru da ita Amina ba , duda ta san an daura mata aure da shi a tunaninta ai baba sai baba , yaro kuwa sai yaro bata taba tunanin cewa yaron nan zai saka hannu daya ya rike mata nata hannayen ya keketata uwa zannin atampa ba sai yau, mema ta taba yi masa? Me na arziki ya taba shiga tsakaninta da shi? A tunaninsa ga banza ya samu ko? Ga yar talakawa marar galihu shine zai wulakantata? In sha Allah ya yi daukan fari ba zai kuma dauka ba koda adashi ne ya zuba!, In sha Allah furucin kakarsa sai dai ya kare a kansa da wace take so ba dai ita ba, zata tsaya tsayin daka ya bata takardarta domin itama bataga ado a yiwa yaro kannin bayanta *Biyaya ba*, me zata ce a gaban mutane ? Yaro dan kannnin bayanta ya sauka a kan ruwan cikinta? Wannan shi ya fi kona mata zuciyarta ya fi sakata kuka, a dole take fashewa da kukan nan ba dan tana so ba Da kyar ta iya jan jikinta ta sake mayar da kanta bayi Ruwan da ya cireta a ciki ta zubar ta tara wani mai zafin gaske ama hannunta na iya zama a ciki Sosai ta jure ta rintse ido ta shiga ta zauna tana ambaton Allah a cen kasan zuciyarta, ta sani ta ji ciwo, domin tana gannin jini jinin dake fita daga gabanta Tsuru ta yi tana kallon ruwan yana dada dafa mata wajen har ya huce sannan ta fito da jan kafa ta koma ta sake dosanuwa a bakin gadon da ya yiwa wata irin jirkitaciyar shinfida tamkar makaho ne ya shinfida Sauka ta yi kasa dan kasa zaman gadon ta yi A ranta ta yi tsaki tana ayana' Ko me Hajia take tunani ne a kaina?, Nima ba shine nawa zabin ba, bani da wani hurumi a cikin lamarin, *wata kokowar* ba tawa bace, *neman na kaina* shi na fi hangowa a gabana, ni da na so na auri mutun tamkar dutse bashi da gaba bale baya?, Dan kawai *alkalamin kadarata* ya ajiyeni a nan ai bai gama zannani ba tunda ba raina ya fita daga gangar jikina ba, kasancewata *BAK'A* kuwa ba dan Allah ya tsaneni ya haliceni haka ba, inma ba mutun da raina mutun ba ai kowa nada tasa baiwa kamar yadda nake da *BAIWATA* ko?, Ba zan taka rawa a wannan *BADAKALAR* ba, idan ya bani takardata na bace sai na zamto tamkar zanen rubutu a saman farin allo a wajenki bi'izinillah' Radadin dake tsikararta ya saka dole barcin rabi da rabi ne ke surarta, har lokacin sallar asubahi ta zo ta yi iya yinta dan ta mike ta koma bayin ta dauro alwallah aman ta kasa hakan, daga kwoncen da take kafafuwanta a hade take matsar kwallah tana astagfari a zuciyarta, idannuwanta kuwa sun karra yi mata luhu luhu tana tunanin ita kam wa zai agajeta? Wa zai dubeta? Wa zai talafeta? Amare na kwonciya su tashi da miji koda ba mai kula bane yakan dan nuna kularsa a wannan dare, danginka kan kawo maka ziyara a taimakeka, ama ita gashi safiya ta waye bata da gaba bata da baya, tana jin zanninta da danshin da take tsoron ko jinni ne ama ta kasa motsin gyara kanta, kardai ace wannan yaro ya farketa ne ya sakata a uku? Lalle da saidai ta zauna a haka dan babu wani mahalukin da zata yarda ya san abinda take ciki ta tonawa kanta asiri da kanta Karfe bakwai ta gota, a lokacin ta fara jigatuwa da dukkan wani launi na azabar dake iya saka bawa fadawa a rashin lafiya irin su yinwa, kishirwa, ciwon jiki da kuma uban garin wanda du wata cikakiyar budurwar da ta kai mutuncinta zata iya haduwa da zazabin nan , bale idan akai mata irin hakar da aka yiwa wace ake tunanin ta fitar da biyu daga kasanta a lokaci daya Kwonkwasawar da ake yi a hankali ana dan saurarawa ya sakata bude lumsasun idannuwanta ta kai dubanta kan kofar sannan ta bude bakinta cen ciki duda ta san da wahala a jita tana amsawa da cewa a shigo Budewa Baba Lauratu ta yi ta shigo tana salama hadi da wara idannuwanta cikin dakin tana kiran " UMAN biyu? Ina kike ne?" Ido Amina ta rintse ta kasa amsawa Hello mutanen..... *NZL PAGE2️⃣7️⃣* Ido amina ta rintse ta kasa amsawa , Babar kuwa tana kalle kalle har idannuwanta suka sauka a kan Amina Da mamaki tace" Toh? Barci ne haka? Kefa akoy nauyin barci bale idan kika gaji, to maza tashi tashi mu tafi umarnin Baba" A hankali ta bude idannuwanta ta sauke a kan Baba Lauratu dake kallonta Ido Baba ta zarro ta ce" Subahanalah menene a idannuwan naki haka ne? Ko bakida lafiya ne Amina?" A hankali Amina ta iya budar bakinta tace" Lafiyana kalau Baba, lafiya na ganki warhaka? Ko Fido ce?" Baba Lauratu tace" Lafiya kalau, kiran Mai Shanu ne ya sameni daga direba tunda duku dukun asubahi yace a zo da ni, ina zuwa yace maza na sadaki da dakinki, nace da shi me zai hanna a bari sai da dare ? Yace aa haka yake so , baya so ace uwar gida bata gidanta a lokacin da zata tarbi amarya, ashe shi baima san bakida lafiya ba, tashi ki yi wanka ki kimtsa mu tafi ana jiranmu fa" Murya a raunane Amina ta ce" baba wani irin gidana?, Baba wani irin gida nake da shi da ya wuce na cen gidanmu? Baba dan Allah ki saka baki a bani takardata" Baba ta sake kura mata ido, lamarin Amina ya fara bata tsoro fa kuma, irin yadda take saka damuwar abin nan a ranta ya fara damunta itama A sanyaye tace" Amina, ina cewa mun yi da ke ki yi ta Adu'a ki fadawa Allah sannan ki yi hakuri ta tare a hankali sai a sake yin maganar nan?, Shin akoy wani abu da yasa zaki dawo ki take maganar da muka ajiye ne?" Amina ta lumshe idannuwanta sakamakon rashin amsar bayarwa A hankali Baba ta kama hannunta tana fadin" Ciciba ki tashi, keda kike fadawa Allah? Muma muke fada masa? Ki kwontar da hankalinki in dan rigimar kakar ABDUL ce, yanzu haka da na tambaya idan tana nan dan na gaisheta mai aikintace tace ta tafi asibiti, irin mutane masu halayanta Allah kadai ya isa ya daidaita su idan sunnada rabon shiryuwa, shi kuwa ai mun yi da ke ki kyale shi idan kun hadu gaisuwa ta hada ku, idan baku hadu ba babu ruwanki da shi ko matarsa ko?" Amina ta rintse ido hadi da damkar hannun Baba a lokacin da Babar ta zaunar da ita dangalgal a saman duwawunta Kasa bata amsa ta yi sai hawayen da ya shiga bin kumatunta Baba ta dakata tana kallonta sosai tana son gane abinda ya sakata cije lebe haka A hankali ta sake kamata tana son mikar da ita sai ta ga tana dudukewa haka kuma abinda take sin damkewa dan karta gani sai da ta ganshi domin hijabin dake jikinta fari ne tas Hankali tashe ta sake duban yannayinta , sai kuma ta samu kanta da kallon gadon dakin Sosai ta ji ta girgiza da tunanin da ya shiga kwakwaluwarta, kai harma ta so karyara hakan da ajiye haka a matsayin sharin kwatse kwatse ne na tunani Da kula ta ce" Amina ki mike da kyau mana ki shirya kina ganni lokaci na tafia?" Mikewar ta so yi, dan kwata kwata bata so asirinta ya tonu, duda Baba ce, ama Babar ce wace ya dace ta boyea tashin farko.sai dai ta makaro domin idan tace zata mike din kafafuwanta kuwa sai dai ta wara su A hankali Baba tace" Me ya samu kafafuwan naki ne? Kuma jinni ne kike yi haka baki sani ba ya bata maki jiki?" Amina ta dakata kanta a kasa, a hankali ta shiga shashekar kuka, sai kuma ta kasa rikewa ta fashe da kukan har ta kusan zubewa a kasa Da sauri Baba ta tareta a jikinta ta riketa sosai tana sauraron kukan nata, har ta tsagaita tana jan ajiyar zuciya Baba a hankali tace" Kin ji ciwo ne?" Amina ta cije lebenta , a hankali ta gyada kanta dan koda bata san meye ko yayane ake jin ciwon nan ba tana ji a jikinta tamkar yankan reza akai mata a wajen nan Baba bata ce komai ba ta rakata bayin ta taimka mata da komai a kusa ta ce" ki yi wankan ina zuwa" A hankali Amina ta gyada kanta dake sade Har baba ta bar bayin wannan karronma a ranta ji take yi ba zata iya yafewa yaron nan ba gaskiya Dukkan abinsa yake na bukatar Amina Baba ta daure taf sannan ta je ta kirawo ma'aikatan tana miko masu sunna saukewa wajen morocin dake jiransu wa'inda Baba ne da kansa ya bada umarnin a fitar da su Kasa inda Baba yake ta koma, cike da jin kunyar maganar dake bakinta da nauyi bayan sun gama magana a kan sauke kaya da komai, cike da kula da dan jimamin dake saman fuskarsa wanda yake nufi da ya san abinda ya faru kennan ya tambayeta Aminar?, Kanta a kasa cike da takaicin Hajia, wadda ya dace ace da ita aka yi maganar nan, ko dan kasancewarta mace, ama firrrr ta ki abin ta ture, ta ce" Alhamdulilah Baba, sai dai jikin nada bukatar gannin likita" Da kula Baba yace" subahanalah, aya, to ko zata iya yin jimirin zaman mota har zuwa gidanta ne sai likitan ya sameta a cen?" Baba ta amsashi da eh Baba ya ce" Allah ya bata lafiya, ku je Lauratu Allah ya tsare, zan zaunar da su idan kura ta lafa na masu nasiha, sannan za'a kawo biyu da yama idan suka sauko daga school, kin san tau litinin ta nasara muke" Baba ta amsa baba da biyaya sannan ta mike ta koma Ajiyar zuciya Baba ya sauke, yana fatan fitar da Hajia ta yi da nufin a kai Risala gidanta ya zamto Amina ta fara shiga gidanta kafin Risalar ta shiga, shifa ba yana hamaya da Risala bane, ko daya, hasalima zai so ace sun yi zaman lafia da fahimtar junna, sai dai take takensu da abinda aka fada masa na bincike ya saka yake taka tsantsan da son kankarowa Aminar nata itama mutuncin, yana yaki da matarsa , rufin asirinsa dan baya so a cuci marainiya, ya zamo mara uwa kuma uba dan alkhairin mahaifinta a gareshi yanada yawa, in ba Hauwau da manta alkhairi ba har ta manta irin taimakon da mahaifin Amina ya masa a lokacin da aka jefe shi ya kwonta, suka ringa fita kasashe neman magani abu ya faskara, shi dai mahaifin na uman Biyu ne ya samo masa magani na hausa Allah ya yi ta sanadiyarsa zai samu lafiya ya mike, ai da yanzu ta yiwu ko musakanta ta saka Hauwau ta barshi ko shi ya bar duniyar idan da karan kwana, shi ai in sha Allahu so yake yi ya samu nutsuwa dayarms ya bibiyi zaman auren nan nata, a yadda ya ga ana shagalin nan kaf babu ita ya fara saka ayar tambaya a kan hakan, rayuwa kennan, Sosai Baba Lauratu ta lulube Amina da zannin gado, wani abin kunyar tamkar wata yar yarinya karama za'a yiwa rakiya gidan wanda ya girmeta, suka lulubeta da masu aikin gidan na hannun damar Baba, domin shi da kansa ya badu umarnin rakiya ma matar ABDUL Wa'inda fuskokinsu ke bude suke da damar haukacewa ginnin gidan nan Amina da idannuwanta ke lumshe tana jin yadda ake santin gidan da ilimi irin na adini ba da furta Wauh wauh ba ta tabe bakinta tana sake gyara zamanta, danma ta dake shiga wani ruwan ta ji sauki saukin wahalar dake damunta, kuma jinnin ba wai zubar da jinni bane irin na mai bini ko wace ke jinnin al'ada ba, sam bai kai haka ba, ba zuba bane yake yi daga cen cikin jikinta, baki bakin da take tunanin da farcensa ya farketa dan wajen ya masa kadan ne ke dan fitar da jinnin kadan shima idan ta bige wajen dan haka nrmal bata jin zubarsa sai dai tana jinta da danshi danshi haka na wani abu mai yauki da bata san ki menene ba Du yadda Baba ya so wannan karron bai samu ba, domin irin yadda ya so ace Amina ta fara saka kaffarta gidan hakan bai samu ba dan kuwa motocin su Risala sun tsaya mata na fita sunna nufar bangaren da aka ce masu nan ne na amaryarsu motocin su Aminarma suka iso Mata ne, lamarinmu ne , kowa ya san ko masu nikaf watau malamanmu ne zasu dan dakata a gaisa a mutunce, bale wadinnan din dama daidaiku ne cikin zababun fitsararun makusantan mahaifiyar amaryar suka yi mata rakiya bisa jan idon mijin maman amaryar domin Hajia shi ta yi kira ta bashi umarnin a kai yarinya dakinta yanzu yanzu, shi kuma ya ba wace ya isa da uta umarnin shima "Abin al'ajabi baya karewa, wai kallo ya koma sama shawo ya dau giwa, meye wannan a luluben tamkar wata farin ciga duniyar ey yane? Ko tantagarin bariki ne irin na wasu matan? Lalle Risala kin kwaso da zafi, " Hajia Mabaruka ta fada tana janye gilas din dake saman hancinta tana kallon wajen su Amina kuma da karfi ta yadda kowama zai ji Dubu ta yi murmushi tana kada kai ta ce" Gane min hanya makaho ya so gulma, oh to wai inace ta jima da tarewa da gotai gotan makota ne?" A hankali Amina ta ja ta tsaya sannan ta saka hannunta ta yaye rufar da aka maka mata ta abin gado dake neman siketa, ga wasu kalamai da take tsinta a sama kamar da ita ake Yayewar da ta yi ne ya hadasa hardewar idannuwansu Risala dake rike da hannun kanwar mamanta , da Amina da hannunta ke cikin na Baba lauratu Kallon kallon da suka yiwa junna ya saka Risala cire idannuwanta tana sake kausasa fuskarta ta dubi Dubu ta ce" Momcy mu je mana, bana so wani abu na raini ya fara gitawa tsakanina da wadda ni da ita sai dai na dauketa aiki ta wanken bayi ta wanken tiles domin ko girkina bata kai wajen da zata dafa ba" Amina dai a tsaye take tana kallon ikon Allah, ita abinda ya fi daure mata kai wai a cikinsu wacece matar ne? Babu wace ta yi rufa ta mutunci kowace tamkar zata yar da dan yalolon mayafin da aka rufa dan cikashe gayu Wace dai take tunanin ta yiwu ko itace kuma sai ta ga ai yarinya ce karama ko menene? To wannan ai da ta yi auren wuri sai ta haifeta fa? Tunda anya zata wuce wata sha bakwai haka?, Sai dai furucin bakinta ya sakata yi mata kallon baba da yaro, watau ki yi aniya ki kama kanka kar na saka bulala na zane maki jikinki tasss, dan gaskiya ba ,zata so ta dauki rainin kannen matar tasa ba gaskiya "AMINA, mu tafi dan Allah ko jikin ne?" Baba Lauratu ta fada a sanyaye, dan ita kam mutanen nan sun samu galabar firgitata, wannan cakewa haka? Kowace kuwa ta sha suturar da ba dai talaka yace zai dana ba Fuska ta kwashababe ta so cewa baba ta daina tambayarta haka itafa ta warke, duda azabar dake sukanta, sai dai ta fasa dan itama ta bude fuskar nan ne dan ji take yi kamar tana tafia sama da kasa ne ga kuma numfashinta dake son tsayawa dan sun nadeta sosai walahi Sai kuma ta fasa cewa koman ta sake juyawa wajen babar ma'aikaciyar Hajia dake masu bayanin ga bangaren AMINAR nan, domin bayan an gama saka komai ita baba ya turo ta zo ta gane masa lamarin kicin komai ya ji? A hankali ta ci gaba da dan takawa, wanda dama tunda akace ko jikin ne ya tsayewa Hajia Mabaruka ta sake samun abin magantawa, wani yananayi ta yi na son sai ta dizga Aminar tace" To wai wace irin rashin lafiya bayan ga dukkan alamu kema yau kika samu tarewa a gidan bale muce ko an samu dan tayi ne na dan zaman da ake yi kafin mai wajen ta yi maki wahe rod?" Mtssss, itafa walahi bata son wulakanci, ita kwata kwatama mutanen nan bata ga abin mutuntawa a cikinsu ba, itafa tanada sanyin hali ne ga wanda ya nuna mata mutunci Da wani takaici ta dan juyo tana kallonta , da kakausan kallon da ya saka kowace duban tsagar idannuwanta, domin ido ne take dauke da shi mai bada umarni ba wai mai risinawar nan ba, idanma komai na Amina yanada sanyi banda idannuwan nan nata A hankali sosai da yannayin tashin amon muryarta mai cike da kasaitar da Allah ya halita mata ba wani ba ta ce" Kila hakane, kila kuma ko dan tayin ne, ta yiwuma uban biyu zai karra samun baby ne.........tunda lamari na ba zata da bakon al'amari, ta yiwu kwon biyu da aka samu ne za'a kara samun wani...........haduwar jinsi da jinsi kuwa ai kamar maganadisu ne,........sirrin dai ne bana son fayacewa dan lokaci ke nunawa!" Magana ce ta bada a sanyaye, a lalauye, a hargitse, sai dai dukkan wata mace dake wajen ciki Harda Baba lauratu sai da ta hangame baki da mamaki hadi da zarro ido jin furucin yar baiwar Allahn dake fama da kanta batada lafiya harda jinni A hankali ta sake juyawa ta bi bayan Umaima da suke ta shiga da kayanta wani sashen daban tana jin yadda Baba Lauratu ke basu hakuri da fadin dan Allah su yi hakuri , baki ta tabe a zuciyarta tana ayanawa' Bana tunanin zan iya hakurin wulakancin yarinya karama da danginta mararsa kunya da jin tsoron Allah, in da wata kuke kallona zan yi iya yina dan baku wace kuke son gani, mai kunya ko fitsarariya, ai ba a kanku aka fara min kallon biyu ni na haifesu ba, ko wa zai yi ya sani ina jin dadin hakan domin biyu dama nawa ne ba na wani ba, shirmen banza wai su nan a kan yaron nan ne har zasu nemi batawa mutun rai;' Tunda ta shigo Falon sai ta kasa yin wani motsin kirki a cikinsa, domin rantsatsiyar haduwar da ya yi ita ta san ba nata bane falon ta yiwu akoy wajen da za'a ratsa a karasa nata falon A kadan tana nan rakube ta ki motsawa du yadda ma'aikatan gidan Baba suka so ta karasa saman kujera ta zauna sai ta nuna nanma ya isa kawai, har sai da Baba ta karaso tare da mutumen nan mai kirki, mutun mai mutunci watau MANSUR da wata matar da bata santa ba Sunna shigowa ana ta sake saka turaran wuta a dakin, Mansur din shi daga bayansu yake, docter ce ta fara shigowa da mutuntawa duka gaisa da junna Tana kallin Amina ta fahimci itace bata da lafiyar, dan haka ta ce" Sorry Madame ki karasa ki zauna mana, keda baki da lafiya? Hajia ku zaunar da ita ko ba ita bace Madame din?" Gaban Amina da ya hargitsa ya fatatale ya fadi ta kurawa Baba ido adu'arta daya ce Allah ubangiji ya sa ba ainahin gane abinda ya faru da ita aka yi ba, har aka turo mata matar nan da sia yanzu ta gane farar rigarta me yake nufi, haka kuma ta gane bawan Allahn cen da take ganni take gannin mutuncinsa shi dinma likita ne ashe, sai dai tambayarta daya ce tal *SHIN WA SUKA ZO GANI NE?* , 😖😖😖😖😖😖😖 Har yanzu bata jigatu ba jama'a da sauranta *NZL PAGE2️⃣8️⃣* "Amina ki karasa ki zauna mana wai me yake damunki ne yau?" Baba Lauratu ta fada tana tsatsareta da ido, domin gana daya Aminar sai wani abinda bata santa da ita ba take yima mutane a yau , kamar wata mai tashin balagar rashin kunya Amina ta sada kanta, kunya na neman hadiyeta baki daya A hankali ta sake dagowa a lokacin da ta ji Mansur ya yi dan gyaran murya ya shigo gaba dayansa ya dubi wajen Hajia da docter ya ce" Baba, ba saman kujera zara zauna ba, ta wuce ciki kawai, Docter ki shiga ciki ki dubata ba zai yiwu ta zauna a falo ba domin ba'a san tashinta daga nan din ba" 'innalilahi' Amina ta ayana a zuciyarta tana cire dubanta a kansa ta maida kasa Rasa abinda zata yi cikin kin zuwa din ko zuwan ya sakata sake damkar zannin gadon dake rabe da jikinta ta juya jiki a mace ta nufi dakin da ya nuna din, domin idan akoy abinda ta yarda da shi a lokacin nan daya ne tak, shine ba zata iya hada ido da mutumen nan da tsoron kar aje ya san abinda ya faru da ita ya cika mata ciki Du yadda ta so tafia da sauri a dole ta tafi a hankali ta shige dakin tana tafe a hankali Muryar doctern a nutse da ta nuna mata bed din dake kasace da wata niimtaciyar shinfida tana fadin" Madame, a nan zaki kwonta dan kasa ba zai maki dadi ba" domin ta kula kamar Aminar nema take ta yada zango a saman cafet din dakin shi yasa ta katse mata hanzari Amina ta ka numfashi ta karasa ta zauna a ringeshe tana rintse idannuwanta Zama likitar ta yi ta fuskanceta sosai , a nutse ta ce" Madame?" Amina ta kalleta sannan ta sake sada kanta hawayen da ya cika gurbin idannuwanta ya ringa hayewa jikin gashin idannuwan nata Yannayinta ya saka matar sake fahimtar abinda docter Mansur ya dan kwatanta mata a gajarce Murmushi ta yi a nutse ta ce" Kin ga, tun kafin na dubaki yannayin tafiyarki ya sheda min kina cikin halin bukatar taimakon gagawa, kin san shi wannan waje waje ne mai hatsarin gaske, babu wajen da ya kaishi bukatar taka tsantsan da samun isashen kula a duniya, kin ga idan ido ya makance zaki iya rayuwa normal, ama idan shi ya rube ba zaki anfanu ba da dadi a rayuwa, koda kin rayun tofa a cikin wahalar rayuwa ne, karshema kina iya yinta rayuwar ke daya a kauye daya dan gujewa wulakancin mutun, ina so ki yi aiki da iliminki, ki bani dama na dubaki a yi maki dukkan abinda ya dace a maki, Ni likita ce, Gynécologue ce ni, na jima a saman aiki a kadan na shekara goma sha daya, ina duba Hajia ne kawai a familly dinku sai yanzu kika shiga layi bisa umarnin SIR, zan so ki yi anfani da iliminki mu taimakeki ki ji saukin jikinki, ina fata kin fahimta?" Kan Amina a sadden take tunani kala kala a cen cikin zuciyarta Muryarta a sanyaye ta ce" Aunty, wanene SIR?" Docter ta yi murmushi itama da kula tace" SIR ABDUL RA'UF sister" Amina ta dago idannuwanta a hankali tana kallon matar Eh lalle matar nan ta fada mata gaskiya, idan ta yi wasa da jikinta da lafiyarta itace a ciki, yau idan ta lalace a kwonce wa zai kular mata da biyu?, Kuma matar ai ba yarinya bace dimin ko a haka da take wanke jikinta ya nuna ta bata wasu shekaru goma ko sama A hankali tace" Aunty na cire kayana ne?" Docter ta sake yin murmushi da kula sosai ta ce" Aa ba duka kayanki ba, iya zanninku ne mu duba wajen" Karshe dai tabas Amina ta samu kari, kuma a lokacin Docter ta hada allurar dinki ta yi mata shi, wanda saida Amina ta ringa hawaye tamkar zata summa dan azaba, domin wajen ya kwana ya sake rinewa da wahala, ana yi mata tana tunanin anya akoy wahalar da ta kai wace ta sha daga jiya zuwa yau? Sosai ta karra daukan zafi da yaron a zuciyarta, dinki? Kamar wace ta haifo kan dan mutun daga jikinta? Wannan wani irin cin zali ne? Docter na gama yi mata tana mata sannu ta bata magungunna na zazavi da kuma na samun sasaucin radadin, cikin nutsuwa bayan Aminar ta rage jin radadin harma ta taimaka mata ta cenza wata riga yar yololuwa dan ta samu hutun mai dadi sannan ta sake bata shawrwarin yadda zata kula da kanta, ta fada mata cewa karta einga gasa kanta yanzu, ta bari zuwa jibi dinkin ya fara neman hanyar warkewa sai ta fara gasa kanta Amina ta gyada kanta barci na fuzgarta dan ba wani isashen barci ta samu bafa a hankali ta ce" Aunty, dan Allah karki fadawa kowa cewa har kari na samu sanadiyar wannan, sanadiyar sa" Docter ta zuba mata ido na dan dakikai, sanadiyar wannan din da ta hadiye ya dan so ya sakata a tunanin wannan me? Sai kuma ta ture tana murmushi tace" Karki damu, in sha Allah wanda ya dace ya sani kawai zai sani, ba zan sanarwa wani hakan ba" Amina ta gyafa kanta tanai mata godiya sannan ta rakata da ido har ta fice a dakin A hankali dan sanyin Acn na dan ratsata har barci yayi awon gaba da ita a saman lalausar shinfidar gadon , barci mai nauyi da kuma ragewar radadin wajen, hakan ya sa ta lula a barcinta har tana sauke ajiyar zuciya Sosai Docter ta sake yiwa Baba lauratu bayanin abinda ya dace a yanzu ta ringa ci dan jikinta ya samu wadatacen kulawar da zai yi gagawar warkewa, ta sake jadada mata kar a ringa shiga ruwan yanzu, ta kuma yi nata maganar zama da hade kafafuwa da kula sosai domin kofa ba da kanta ta haihu ba idan zafin dinki ya sa a yanzu ta ringa zaman da iska ke iya shigarta sai ta shigeta ta zo tana fama da tusar gaba Sosai Baba ta mata godiya ta rakata sannan ta dawo itama ta ringesa tana yiwa Allah godiya da sake duban falon nan, sai ta saka harshen hijabinta ta share hawayenta a fili ta furta" Mahakurci mawadaci kennan, ashe mijinki na nan rantsatse Innar marigayiya? Kinga yyau harda yan aiki ne da ke , Allah dai ya maba maganin sabon halin da ya sameki uman biyu, ki yi hakuri ki yiwa mijinki *LADABIH*" Tunda suka fito suke dan tafe haka a hankali tana yi masa bayanin matsalar da kuma solution din da ta dauka , sosai ya gamsu da komai harda maganin da ta bata, Har bakun motarta ya rakata yana sake yi mata godiya domin a aiki ita din gaba take da shi, kuma irin yadda rake mutuntashi da sauran ma'aikatan dake karkashinta ya sa summa suke mutuntata a rayuwa Yana tsaye har Motarta ta fita a gidan sannan ya juyo wajen da ya hange shi tunda suka fito ya daga kansa Yana tsayen kuwa hannunsa daya a harde a bayansa, dayan kuwa ya dafe abin madubin shima yana kallonsa Murmushi ya yi ya tunkari part din nasa ya bude ya shiga falon ya ratsa ya shiga hawa matatakalar A gajiye ya idasa hawa ya tsaya ya bubuga sannan ya murda ya shiga Dafe da bayansa ya shiga yana kallon ABDUL dake zaune saman wata lalausar yar madaidaiciyar kujerar da ta yi masa kadan yana fadin" Kaikaikai, wannan idan na yarda na yi hawa goma a wata guda tabas zaunewa zan yi, wai ku yan gayun nan me kuke ji a gidan sama ne? Du ku bi ku mutu shekarunku basu kai mutuwar ba?" ABDUL ya yi murmushi yana dauke kansa a kan Mansur ya ce" Idan ka ga ka mutun dama a rube kake man , ba laifin Upstairs bane" Shima dariya ya yi dan yadda ya yin wai irin ya tsokale shin nan Zaune ya kai kusa da shi kadan yana bashi hannu ya ce" Yaya kake? Ya jikinka?" Abdul ya amshi hannun suka gaisa sosai a hankali yace" Mansur bani da lafiya ne?" Mansur ya dage kafadarsa yace" na sani, na ga ka zama na daki kamar wani sabon ango........" Abdul ya ce" Uhum" sannan ya yi shiru yana sake zubawa waje daya ido Yan sekwani sun ratsa tsakani a hankali ABDUL ya ce" Wa ya dubata ne?" Da gangan Mansur ya ce" Wace?" ABDUL ya zuba masa ido, sai kuma ya tabe bakinsa yana kawar da kansa ya yi shiru Yanzunma sun sake daukan lokaci Mansur ya ce" Da gangan ka yi, ko a rashin sani ka yi? " ABDUL ya sake kallonsa, ya kuma cire kansa bai bashi amsa ba Mansur ya yi murmushi ya ce" Ban taba tunanin zaka yi irin aikin nan ba, domin kanada ilimi" "Ka daina magana kamar wanda kaima baka cikin mamakinta, abinda nake son sani a lamarin nan shine....mata ana yi masu halitar virginity biyu a rayuwa ne ko.......ko TWINS ba, ba ita ta haife su ba?" ABDUL ya fada a dake yana murza gaban goshinsa kadan MANSUR ya ce" Sai dai idan Twins ba ita ta haife su ba, ama babu macen da aka halita da budurci biyu a duniya, fannin likitan mata ka karanta, kasuwanci ya kamaka ne, ya zame maka dole ne, ko kana so ka cemin akoy abinda ke iya rudaka ka shiga tunanin anya abinda ka gani haka ne ko ba haka ba?" Da ido ya tsatsare Mansur, sai ya ga kamar wani wanda ke jiransa ya kwonkwonce masa nagangannu, to a ganninsa menene na sin titsiye shi? Me yake son fadi a maganarsa na cewa akoy abinda zai rikitashi a kan wannan lamarin ne? A hade ya ce" Me kake nufi da na rikice na kasa fahimta?, Emotion mai karfi irin na MACEN DA AKE YIWA gagarumar soyaya, ko karfin kauna irin ta iyaye?" Mansur ya yi murmushi a zuciyarsa, a bayane kuwa ya ce" tambaya na yi" "Amsarka itace ba dayan biyu" ABDUL ya maida masa yana sake dauke kansa Mansur ya dake yin murmushi yana ta kallon ABDUL, he can't believe it, ABDUL abokinsa , amininsa ne ya wayi gari da wannan farin cikin da yake dannewa karfi da yaji, ya kasa fahimtar alkiblarsa a yanzu, idan ya yi kamar ya tsani lamarinta, sai kuma ya tare mata wani abin Mikewa ya yi yana murmushi yace" Ya dace ka dauki magani kuma ka yi sleep, ND.. .......nd ........." Ya dakatar da maganar yana kallonsa kamar tadda shima yake kallonsa Mansur ya ce" Nd kana da tarbiya, u'r a gentle Man, ya dace ka kwatanta kula a gareta............, Kamar yadda ka fada ne, tanada shekaru kadan a saman kanta.... but tamkar baby haka take....she need ur care " ABDUL dai da ya yi shiru baisake ce masa komai ba, dan ya kula Mansur sai wani nemansa da masifa yake yi, wai wani ya dauki magani dan kawai ana cewa ko namiji idan dai yinsa na farko ne yakan fadi rashin lafiya, ya manta ba kowa da kowa ba? Hm! Sai da Mansur ya tafi sannan Abdul ya sake mikewa daga zaunen da yake ya karasa kusa da wayarsa ya dauka ya sake gwada number kakarsa Sai dai still bata daga ba Murmushi ya yi ya yi kiran mijinta suka sake gaisawa a mutunce sannan ya ce" Tsoho, ina fata ka leka asibitin wajen Hajia?" Baba Mai shanu ya kadakai yace" Ka ganni nan a gidan gona bangaren shanu mun kada shanu ni da Rabi'u muna rakasu kiwo , ka san me Abdallah? Wannan rufe shannu da kuke yi ku yan birni bashi da wani anfani, shi yasa shanayenku basa sakin karinsu su dauki girman jiki sosai............., Abincima kulun kunna kayade masu wanda zasu ci ta yaya kuke so su yi kiwo?" "Baba, kalli wancen farar ta ki yin gaba ta ki yin baya sai wani irin abu take yi" Muryar Husaini ta shigo cikin wayar, sai kuma muryar Baba Rabi'u yana fadin" Aliyu wancen fa haihuwa zata yi, ka ga fa ta hau gwuiwa" Baba da dan sauri ya karasa yana sauraron ABDUL dake fadin" TWINS na tare da kai ne?" Baba yace " Eh ai daga makarantar tasu nake na dauko su sai muka wuce nan " Dan shirun ya sake yi, sai kuma ya samu kansa da fadin" Ina iyayensu suke?" Baba ya dakata da tafiyar da yake yi dan tambayr ta zo masa a ba zata, kwarai ya dan zai tambayeshi hakan , dama da gangan ya boye masa dan yana so ya fara gane idan har yaron ya fara damuwa da wani abu nata , duda ya san zai yi wahala ama kuma yana tunanin idan har ta samu gurbin zuciyarsa sai ta yi fata fata da duk wani tanadinsa Yana kallon yadda ma'aikatan ke taimakawa sanuwar dake dan fitar da kuka irin na sanuwa mai karfin nan tana ta faman haihuwar ya ce" Umansu ba tana gidanka ba? Ko dai basu je ba da na turo su ne? Likitan ya ganta kuwa?" ABDUL ya dafe gaban goshinsa a hankali ya ce" tell me father, ka fada min abinda ka san ina son ji mana?" Baba ya yi murmushi ya ce" *NZL PAGE2️⃣9️⃣* Baba ya yi murmushi ya ce" Mahaifiyarsu na nan gidan mijinta, mahaifinsu kuwa ya rasu, ita mahaifiyar tasu itace kanwar Uman biyun ai, uman biyu ta saki nono ita ta kama, su biyu kadai iyayensu suka haifa, sun rasu ne iyayen nasu kai a lokacin kana yawo da naka uban baka san ihayensu ba sam, Allah dai ya jikan marigayi da matarsa, mutane masu karamci da halaci a rayuwa" ABDUL ya lumshe idannuwansa yana tunanin lamarin kakansa, yanzu dama maganar nan haka take sau nawa yana kawo irin haka bai taba fada masa ba? Yanaga Hajiama bata sani ba ai, kuma yanzu daga tambayarsa yar tambayar nan ya bashi amsar nan a haka kamar wanda ya tambayeshi abin a haka Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kashe ya ce" Za'a kawo su ne?" Baba ya kada kai ya ce" Eh to, gamunan dai, ka san yaran nan ne da shiga rai walahi, in ba dan umansu ba zara iya rayuwa babu su ba ai da na yi ruwa na yi tsaki na amshe, ama ko a yanzun dai muna shawartawa udan har yama ta yi mai halinka bai nemi umansa ba a wajena zasu kuma kwana, ka san jiya tsakuyar dare ya farka yace ina Uma? Nace ta tafi makaranta, yaron da ya mun wani kallo sai da na ji kamar na masa wani mugun laifi ne Abdallah, uhum nace kai kam kamar daga tsatson Abdullahi ka fito yaron nan" ABDUL ya ja numfashi kasa kasa yace" Yau ka cika surutu sosai Alkali, Sai an jima" Baba ya tabe baki ya katse yana sake kallon har Sanuwar nan ta haihu ya ce" Allah ya yankan na magana na gumtse dan nine sarkin mararsa rabon duniya? Karya ne walahi" Sai kuma ya karasa yana fadin" Masha Allah Masha Allah ashe an sauka, to Husaini maza jeka ka amso mana kwano a bamu sabuwar tatsa mu je mu yi dakashi, kiwo kennan alkhairainsa yawa ne da su" _________________________________ ABDUL kuwa baki ya tabe ya koma wajen gadonsa ya cire rigar da ta rage masa ya kwonta a saman gadon Rashin Sa'a ya taka a lokacin da ya kai dubansa saman zannin gadon ya yi arba da kalar zannin gadon mai ruwan peak mai haske ne sosai, kuma harta da fan kwaliya kwaliyar jikin sak irin zannin gadonta ne na jiya Wani irin yarrrr yarr yarr da jikinsa ya dauka a lokacin da ya hasko irin rikon da ya yi mata itama ta yiwa zannin gadon har kamar zata yaga shi da hannunta , da idannuwanta da suka girmama wajen kallonsa irin ya zo mata fa bidiar nan Idannuwansa ya rintse da dan karfi yana jan hannayensa ya yi mika sosai a hankali ya furta" YA SALAM" sai kuma ya hade kafafuwansa ya rufe jikinsa da kyau yana ambaton Allah kamar yadda ya saba a irin lokutan nan idan ya samu kansa a irin wannan yannayi mai wuyar fasara wanda ke sako shi a gaab lokutan da ya ga dama Nan da nan jikinsa ya gama karba, a yanzu maimakun ya dan lafa sai ya sake murde masa Idannuwansa ya bude hana jin lalle ba damar samun barcin fa a yanzu ya dan zubawa waje daya ido Haka kawia ya samu kansa da sakin murmushi a zuciyarsa yana ayana' Ga rashin kunya, ga tsoro kamar farar kura......wai kaida baka san ciwon haihuwa ba, ashe ita dinma bata san komai ba, jaririya ce , kofarma a matse kamar kofar hanci sai iya rigima' ( Maman jariri inaga ya dace yanzu kam ki makashi a kotu, wai fa da kawarki yake😭😭😭😭😭😭😭😭😭🤣)..... Wahala ya sha da kansa kafin ya samu barcin shima ya yi awon gaba da shi, domin shi din kansa ba wani barcin kirki ya damu ba , dan tun a jiyan yake cike da tunani harma da tuhumar kansa irin yadda ya jema wace bata san komai a kan lamarin ba Amina na farkawa daga barci da yama sosai Baba Lauratu ta sakata a gaba sai da ta ci ta koshi ta sha maganinta sannan ta shige wanka ta sake yin wanka ta dawo ta saka wata rigar yanzuma irin ta zaman gida mai laushi kuma marar nauyi ta zauna tana fuskantar Baba dake yi mata hirar Irin rikicewar da Firdausi ta yi kan sai ta zo wajen taron bikin nan Amina ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana ayana' gwarama da bata zo ba, da fa wani ido zan kalleta?' A fili kuwa ta girgiza kai da takaici ta ce" Mijin Fido, Allah ne kawai zai saka mata wulakantata da yake yi Baba" Baba Lauratu ta ce" Allah ya shirye shi tun kafin lokaci bai kure masa ba ya gane matar rufin asiri yake tare da ita su hadu su rufama junna asiri su talafi junna, ama lamarin yaron akoy ban haushi" Haka suka yi ta zantawa har Babar ta mike da nufin tafiya Amina ta shagwababe fuska tana kallonta ta ce" Baba, kuma ki barni da wa a wannan katon dakin? Ni walahi tsoro nake ji" Baba ta yi murmushi ta ce" ke kuwa tsoron me Allah na tuba ga katuwar tvn nan kadai ai ta isheki hira, ai dai ba zama zan yi mu yi ta labari a gifan siriki ba ko? Ko yanzu ai an jima a zaunen ke dai Bara na tafi, zan fara biyawa gidansu Asmaun da kika ce na masu kwatancen nan din ko? Kuma fa kin ga su Rabiama sun ce sunna son gyaran amaren gidansu watau biyu, kuma auren fa saura sati biyu dudu, shine nace anya zaki iya kuwa?" Amina ta ce" Zan iya sosaima, ko gobe suke son fara zuwa su zo kawai mu fara Baba" Baba ta dan zuba mata ido, sai kuma ta yi murmushi ta ce" Sa zo, ama ba gobe ba, nan da kwana biyar in sha Allah sai su zo ku fara, idan suka samu wadatacen gyara abinda sati guda ya isa su yi fess da su, ke dai ki dauki maganinki yadda aka ce kin ji ko?" Kai ta gyada ta dauki hijabinta tana tafe a hankali wai ita a dole sai ta yiwa Baba rakiya Ita dai bata hannata ba dan lalabata take yi, karma ta tubure tace sai ta bita gidan, babu abinda ya gagari uman biyu yanzu Tana kallo aka ja Baba a wata mahaukaciyar mota aka tafi da ita Ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe ido da shakar iskar waje mai ni'ima da dadi, ga shuke shuken mangwaro da sauransu balbalin gidan ba karamin kyau ne da shi da dauke hankali ba A nutse ta koma dakin ya rufe bata saka sakata ba ta wuce ciki ta sake shiga bayi ta dan wanke dan danshi danshin da ya hannata sallah ta sake fitowa ta dauko akwatin kayayakin hade haden HUMURARTA ta koma falo ta baje kayanta bayan ta shinfida wata leda ta shiga ciciro kayan hadin BAK'AR humura kamar su: *Hadin BAK'AR Humura* *Ruwan turare irin na jarirai mai dadin kanshi, irin kanshin dake birgeka* *ALKAMUS* *TURARE Na madara MAI KAURI , CONCENTRÉ MAI DADIN GASKE* *Garin sandal* *Musk, musk ba muski ba, musk shima murje shi zaka yi ka hade a ciki* Yadda ake yin hadin kawai zaka harhadasu a cikin butali guda mai dan girma ne suma ka girgizasu su hade jikinsu sosai, shikenan sai ka barta ta jiku, domin Humura ta fi dadi idan ta tsumi sosai komai ya hade jikinsa.....Wannan itace sasaukar Bak'ar humura, kana iya yin hadin karamin kudi ko baban kudi, ya danganta da murdinka ko muradin mai siya a wajenka Turaren ta hada kunnayenta na jiyo mata salamewar kiran sallar magariba, sai kuma ga daya daga cikin ma'aikatan bangarenta ta fito da karkon turaren wuta ga dukkan alamun turaren ne zata saka Gannin Amina a falon a zaune sai da ta duka har kasa tana gaisheta cike da ladabi da biyaya sannan ta ce" Hajia zan saka turare ne dare ya yi kafin na koma bangarenmu" Wani irin banbarakwai Amina ta ji kuma ta ga lamarin, sai dai bata ce komai ba illa gyada mata kai da ta yi tana kallonta ta sasaka ta ajiye sannan ta ja ta tsaya sai da dakin ya dauki kanshin turaren wutar mai dadin gaske sannan ta dauke kaskon ta fita da su bayan ta yiwa Amuna salama Ajiyar zuciya Amina ta sauke tan lunshe idannuwanta ta kau hannunta gaban hancinta tana sinsinawa dan son jin kanshin humurar a hancinta sosai Budewar da aka yi ya sakata sauke idannuwanta a kan kofar Hasan ne ya fara shigowa, yana ganninta a guje ya karasa itama ta ajiye dukkan abunda ke gabanta tana kyakyata dariya ta rukunkume shi a jikinta tana fadin" My son, my boy" Hasan na rukunkumarta shima ya ce" my mama, my mom, mama i misss u so much........." Itama harda son ta fashe da kuka tana fadin" Ina dan uwanka? Ina Husainina? Ina fata bai yi kuka da ya ga bana nan ba?" Hasan ya yi dariya yana danewa saman cinyoyinta ya zauna abinssa ya ce" Mama ya yi mana sosaima, kuma da aka bashi madara sai ya yi shiru, yanzu haka yana wajen DaD yana masa fadan shan nonon Sanuwa da ya yi ba'a tafasa ba, wai kawai dan ya ga Baba tsoho ya sha.....Mama yanzu a nan kuma zamu zauna ne?" Mamansa ta yi gagawar fadin" Aa, ba zamu jima ba a nan zamu koma wancen gidan namu , kace waye DAD kuma?" ABDUL dake tsaye hannunsa rike da Husaini yana sauraron dukkan abinda take fada ita da Hasan ya dan karra kallon Husainin dake ta ajiyar zuciya dan ya gindaya masa kashedin daga yau idan ya kuma jin ya ci wani abu a waje sai ya yanka masa lebe ya soya ya ba mage sun cinye, shine fa ya ringa hawaye yana rantse rantsen ba zai kuma ba Shima hannunsa ya saka ya bude kofar ya shigo Da ba dan Hasan na daf da kasa ba da wannan mikewar da ta yi tabas sai ta hantsila shi ta yadda zai ji ciwo a wani sashe na jikinsa A yanzunma a kwonce ya fado sai dai bai wani damu ba domin bai doku da karfi ba Tsaye take tana kallonsa har ya karaso inda take tsayen yana kallon gefe kadan wajen da Hasan ya fadi Ciki ciki ya ce" Ke, ki yi a hankali mana kar ki yiwa YARONA rauni, tashi son ku je ciki ku tube ku shiga wanka" Yaron na mikewa ya nufi inda aka nuna masan itama zungwai zungwai ta juya zata bisu, ko kulashi neman masifar da ya yi mata bata yi niyar yi ba, domin bata tunanin zata iya tsayawa su yi wani dauki ba dadin da junna Sai dai bai barta ta shige ba ya saka hannunsa ya kamo nata hannun na hagu sannan ya janyota baya kadan har sai da bayanta ya dan doku a kirjinsa kadan A hankali maganar da ta so yi a cikin ranta ta fito fili ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, na shiga uku me kuma zai min?" Tana fada ne hawaye na son kwonce mata A hankali ya dan juya da ita ya shiga nufar dakinta da ita ba tare da yace da ita ci kanki ko daina kuka ba Baki Amina ta bude tsakaninta da wanda ranta ke hannunsa ta takarkare ta ce" " Wayo, kai, meye haka? Kai Abdul meye haka?" Dakatawa ya yi da tafiar da yake yi da ita yana kallonta kamar bai gane yarenta ba Amina ta shiga murza hannayenta ta juya ta ji ya sake riko hannunta A haukace ta juyo tana sake matsawa nesa da shi hadi da zuba masa idannuwan itama Murmushi ya yi kasa kasa ya ce" Dama, cewa na yi, yaya jikin ki?" Me Amina zata yi a yanzu da ya wuce kuka? Dukma wace zatace mata kar ta koka dan ba ita abinnan ke samu ba, dole ta yi kuka , dole ta zubar da hawaye A raunane tana kallonsa ta ce" *NZL PAGE3️⃣0️⃣* A raunane tana kallonsa ta ce" Ka ga, ko a anguwarmu ni bana wasan maza, bana shiga harkar maza, dan haka dan Allah ka fita a harkata kafin ka bani takardata, ka daina yi min maganama kwata kwata" Sake matse mata waje ya yi hakan ya saka AMINA, da girmanta da komai ta kwala ihu tana rintse idannuwanta, domin ita abinda ta yi tunani daban, sai ta ga ya tsaya yana kallonta Tana bude idannuwanta suka sake yin ido hudu sai ta ga ya sakar mata murmushin da ko a gaban sarki aka gurfanar da ita zata iya rantsewa murmushin rainin wayo ne Juyawa ya yi bai ce nata komai ba ya kama hanyar ficewa Har ya kama kofar ya dakata ya juyo kasa kasa yace " Ki tabatar kin saka masu kayan barci sannan ku masu addu'a ki rufe masu dakinsu" Baki bude take kallonsa zuciyarta na raya mata abubuwa irin na rashin kunya da ya dace ace ta yayaba masa ko zai shiga hayacinsa ya gane yarenta Bai bar dakin ba sai da ya sake fadin" Kar ki saki ki hada daki da su AMINA" Ido ta kwalalo tana kallon kofar da ya rufe ya fice ta karaso tana fadin" Idan na hada din sai me? Ina ruwanka da hada dakina da y'ayana? Malan sai shishigi ni zaka nunawa raini? Ka bari na warke walahi sai na koya maka biyaya wa manyan gabanka, kuma zalina da kake ci kai da Allah.....shima Hasan....Hasan? Hasan?" Ta nufi dakin da aka ce nasu ne wanda ko shiga bata yi ba tanai masa kiran da yana ji ya yi turus dama fitowarsa kennan daga wanka Husaini kuwa yana ciki Tana shigowa ta ja da mamaki tana kallonsa Rigar wanka ce a jikin Hasan jama'a ya wani yi fresh kamar dan yan gayu na kasa da kasa shi kadai sai shinning yake ga abin ruwa dake nuna fitowarsa kennan a wanka Farin cikin ganninsa a haka ya so mantar da ita abinda ta shigo yi, har sai da ta zauna gefe ta tuna sannan ta sake hade fuska ta ce" Kai zo nan, zo nan" Fuskarta yake kallo kafin ya shiga matsowa ya tsuguna a gabanta Tsayinta ta rage tana sake hade fuska ta ce" Waye yace maka ka ringa fadawa wancen dady?" Dagowa ya yi da mamaki yana kallonta, sai kuma ya ce" Ba dady bane Mama?" Amina ta yi tsuru ta rasa amsar da ya dace ta bashi Hasan ya sake soke kansa ya ce" Dama dazu ne da yama ya je cen gidan gona, shine Baba yace ga dadynmu nan, muka ce masa akace dadynmu ya rasu? Sai yace eh wancen ya rasu, yanzu kuma ga dadynmu nan, mu je masa dady, ni dai sai nace masa dady sai yace da gaske ina so ya zama dadyna?" Amina dake kallonsa tsigar jikinta na kwonkwoncews tana sagewa a hankali ta ce" Sai kace me?" Sake dagowa ya yi yana kallonta, sai ya sakar mata murmushi ya ce" Mama, kin manta dama munna ce maki mune bamuda dady a school? Yanzu muma fa mun samu kennan?" Zuciyarta ne ta ji ta yi mata nauyi, amsar da yaron ya bata kuwa ta tabatar mata lalle baban burinsa ne ya cika, domin karara take karantar farin ciki a tare da shi idan yana maganar wancen mutumen Fitowar Husaini da saurin cin birkinshi y saka Amina da Hasan waigawa sunna kallonsa Kiri kiri ya yi ya ce" Mama ai na cewa Dady ba zan kuma cin abin kowa ba , walahu ba zan kuma ba Mamana" Ajiyar zuciya ta sauke ta sakar masa murmushi ta mika masa hannu, haka kuma ta mikar da Hasan din ta nufi wajen da take tunanin a nan suturunsu suke, suturun da ita dai bata san lokacin da suka samesu haka ba, batama san yaushe aka zuba su ba, kai karshe bata san wa ya zuba ba Sai da ta tsorata da ta bude wajen kayan Kayan gasunnan birjik kala daban daban, kuma kowani launin tufa an yi gefensa daban Ajiyar zuciya ta dauke ta nemo wajen kayan barcin ta ciro masu wando da riga kowa da color din da ya fi so ta basu , suka shiga sakawa ta dauko masu turare ta zo gabansu ta shiga dan fesa masu Sai kawai ta lumshe idannuwanta tana jin wani irin sanyi da nutsuwa a cen kasan zuciyarta Sai kuma ta ji wani gefe na zuciyarta na katse mata farin cikinta ta hanyar fadin' Amina, duka wannan jin dadi na dan lokaci ne, ke kin sani, duda mafarkin da kike yiwa yaranki samu kennan, watau irin wannan rayuwar, ama hakan ba yana nufin ki ringa mantawa da komai dake gabanki ba' A hankaki ta sauke ajiyar zuciya bayan ta gama shafa masun suka haye saman gado daya su biyun kowane na yi mata murmushi Itama murmushi ta yi masu a hankali ta shiga yi masu addu'a tana kallon askin dake kansu mai kyau sak dai irin na yan gayu, Murmushi ta yi , ta samu kanta da yiwa koma waye ya kular mata da ƴaƴanta haka adu'ar fatan alkhairi a zuciyarta Bata tashi ba sai da ta ga sun yi barci sannan ta tashi da kyar ta nufi nata dakin tana ayana' Bara dai na yi wankan nima na dawo mu yi kwoncin mu , ba wani yaron da zai hannani kwonciya daki faya da y'ayana ba, idan fa suka motsa tsakiyar dare bana kusa suka yi kuka? Nima ba zan iya barci ni daya a dakin cen ba ai' Tunda ya bude bangarenta ya ga sai hasken fitilu da TV dake yi ama bata falon ya yi tunanin tana dakinta A nutse ya nufi dakin nata ya murda ya shiga da salama a bakinsa yana wara dubansa dan son gannin inda take A jikin kofar ya jinginu yana kallonta, zaune take a saman gadonta da shiga irin ta sasaukan wando dogo da riga , kitsonta a daure a tsakiyar kanta, fuskarta a hargitse kamar ta sha kuka Itama kallin take yi tana sauke ajiyar zuciyar bacin ran dake nukurkusarta, yanzu fa ta gama yanke cewar zata je ta same shi, sai kawarta tace da ita aa ta bari ya zo, kar ta manta amarya take, kuma gashi gida da kishiya kar a fara saka mata ido, ita dai ta saurareta ne ba wai da nufin zata yi aiki da abinda ta fada ba, sai gashi ya shigo Murmushi ya saki gannin da gaske a shake take, dan haka sai ya dago ya karasa bakin gadon y zauna yana sake fadin" Amincin Allah ya tabata a gareki Risalah, ina nema maki amincin Allah kin yi shiru?" Risala ta lumshe idaannuwanta tana rike hawayenta, domin idan akoy abinda mahaifiyarta ta yi ta jadada mata shine ta kiyaye yawan kukan nan, bashida wani anfani, idan ya kasance komai zata sakashi a gaba tana yi masa kuka to fa zai rainata ne A hankali ta ce" Huby, yanzu fisabililahi ace yau kwana biyu da daura aurenmu sai yanzu na ganka? Kamar baka dokina? Wani irin kira ne ban yi maka ba bayan ka san kai ya dace ka neme ni? Irin kiran da ake yiwa mace ana murnar an daura din nanma baka yi min ba, nd mun ware babar ranar yin diner kace kar na fita? Why? Me yasa kake min irin haka ne?" A hankali ya sake fuskantarta ya ce" Risala, tsarin gidanku ne sai an yi diner a kawo ki gidana shi yasa na baku dama, na hannaki zuwa diner ne dan baki saka suturar da zaki je gaban kowani kato ki wuce ya biki da kallo ba, ita diner din nan ai ba'a ce ba za'a yi ba, ama me zai hanna a yi shiga ta musulmai?" RISALA ta tsare shi da ido bayan ta kamo hannunsa ta ce" Kishina ne ya saka ka hanna ni tafia?" Sai da ya zubawa fuskarta ido mai dauke da kwaliya da su gashin ido, kwaliya kai mai kyau din nan , a hankali ya gyada kansa yana tunanin kwaliyar nan ai ta yi yawa fisabililahi Murmushi ta yi tana komawa kusa da shi ta ce" Dama na sani, sai da na fadawa Mama ta daina fushi na tabata da dalilinka mai karfi, gashi kuwa da dalilin" Murmushi ya yi shima, domin ko ba komai ya ji dadin da ta dauki maganar da mahinmanci A nutse ya ce" Zuwa na yi na ganki, na yi maki oyoyo sannan na maki sai da safe" 'Sai da safe?' ta ayanna a kasan zuciyarta, tana kallonsa ta ga ya mike yana dube dubensa ya sake juyowa ya ce" Hop komai lfy baki da bukatar wani abu?" Da mamaki ta ce" Sai da safe?" Juyowa ya yi ya fuskanceta ya ce" Eh " Da mamaki ta sake dubansa ta ce" U said sai da safe, safe? Hakan na nufin zaka je part dinka ka yi sleep ? Ko kana nufin na taso mu tafi sai da safe na dawo nan?" Ita da kanta da ta yi furucin sai da ta ji wani iri, ama kuma abinda take hange ya fi mata wannan jin nauyin a zuciyarta ABDUL ya dan lumshe idannuwansa yana jin wani iri a furucinta, duda ya san gaskiya ta fada kuma ƙarin haske take so a furucinta, ama sai ya ga zuwan kai tsaye ai na namiji ne, a duniyar hausa Dan sake matsota ya yi kadan ya zauna yana fuskantarta ya ce" Oh sorry, kin san a hukunce dole sai na yiwa UWAR GIDANKI sati kafin na yi maki ko?" "Uwar gidana?" Risala ta fada idannuwanta na kankancewa Abudl ya sake fuskantarta ya gyada kansa ya ce" Eh, yar uwarki, yayarki, ko kin manta ne?" Gaban Risala na dukan tara tara, ranta na neman jagulewa ta sake dubansa ta ce" ABDUL, wannan wace irin magana ce? Kana magana kamar wanda ya tare da matar cen?, I said uwar gidana, yar uwata....kamar wata wace take da isa da takama a wajenka wace kuka yi auren soyaya da ita irina?" ABDUL ya dafe habarsa dan magangannun sai ya ga kamar ba wani ilimi a cikinsu gaskiya A hankalinsa ya ce" Risala, tanada daraja mana, ba magana ce ta na yi auren soyaya da ita ko akasin hakan, tunda har igiyar aurena ya rataya a wuyanta ai tanada daraja, nd maganar tarewa kuwa ai inaga sirri ce ko?" Risala yanzun kirjinta ya fara dokawa da karfin da har gaban goshinta ke dokawa, a yamutse ta ce" Please, please ka yi shiru..... Please ka rufa min asiri ka yi shiru da maganar nana haka ......kar ka saka na tsorata da furucinka mana?......................, Na san an aura maka ita ama darajarta bata kai tawa ba, domin ni kake so ita kuma hadaku aka yi....., Nd maganar tarewa wannan ai inaga ba wani maganar da zan iya fahimta a cikinta tunda an jima da daura maku aure, kuma bayan wannan idanma maganar wace ta fara zuwa ne ka tambaya mun rigayesu zuwa gidan nan, wai bama wannan ba kamar wata budurwar yarinya zaka ce idan ka yi mata sati? Wani irin sati matar gotai gotai da yaranta da komai?" "Risala, are u okey?" ABDUL ya fada a hankali yana kallon Risala da mamakinta Risala ta kamo hannayensa tana mai tabatar masa lalle a cikin hayacinta take Hakan ya saka shi fuskantarta ya ce" Am, RISALA, kina ji? Ina so ki kiyaye dukkan abinda zai shafi irin magangannun nan idan har bai shafe ki ba, sam bana tunanin zan lamunci haka ta fara fitowa daga kowace daga cikinku, maganar daura aure hakane ama bata tare ba sai a jiya" Risalas da jikinta ke neman daukan zafi da wani irin yamutsa da ske yi mata a cen cikin kanta kamar zata haukace ta ce" No, no, ba jiya bane yau ne , kuma yau dinma na rigayeta" ABDUL ya sauke numfashe ya ce" Jiya ta tare, ban san me kuke kira da tarewa ba, wanda na sani nake maki bayani a kai, kuma ta dauki karfin fara yin kwanakinta ne dan ba a rana daya aka daura aurenku ba, kin ga idan har hukunci zamu bi bisa adalci kwanakinta ne muka fara.....so ki yi hakuri koma menene abinda yan kwanaki ne zasu shige na dawo?" Walahi, ita ba mashayiyar abin maye bace, ama a yanzu sai ta ringa jin ana yi mata mugun kida a cen cikin kanta kamar wace ta saba busawa bata busa ba Kasa maganar da ta yi ya saka shi mikewa bayan ya mana mata pk a goshi ya fice yana janyo mata kofar, domin kansa shima har ya kwashi ciwon , dama ya wuni da abinsa ya nufi bangarensa dan yin wanka yana tunanin ba zai juri yawon dakunnansu ba, idan komai ya lafa na maganar bakunta zai dora dokar du wace keda shi ita zata zo turaka ( wo wo wo malan, wai kai yaya haka? Mufa sakinmu muke jira me kake jira da mu ne) ABDUL na fita RISALA ta silale kasa daga saman bed din tanaa kunce daurin kanta ta warware shi sosai tana cusa hannayenta a cikin kitson tana yamutsawa da kardi ta kama jela guda ta ringa ja har sai da kan ya kama sara mata da wani irin karfi sai kuma ta dakata tana kallon waje daya ta ce" ABDUL, ABDUL, kana nufin dakin wancen matar zaka je ka kwana? ABDUL kana nufin dakin wancen matar zaka tafi? Me ma'anar ta tare? Me husarka ke nufi? .....Abdul!" Ta fada da karaji tana sake damkar gaban rigarta da kanta da hannunta ta sake fadin" ABDUL, don't tell me abinda ta fada cewa ta yiwu cikinka ne a jikinta dazu da irin tafiyar da take yi da komai cewa ka sadu da wannan matar?" Da karfi ta daki abin gadon da hannunta ta ce" ABDUL!, ABDUL!, Kar ka ce min burina da rike kaina da na yi dan darenmu ya zamto unik,na kasance ta farkonka kai har ka ba wata wannan darajar ba ni ba?" Da wani ihun kuka ta sake fadin *NZL PAGE3️⃣1️⃣* Da wani ihun kukan ta sake fadin" ABDUL, ka kirayeta uwar gidana, yar uwata, yayata.....kana son nuna min cewa ne kana sonta itama bayan an fada min grandfather dinka ne ya aura maka ita, an kuma fada min ita din ko wacece?, An fada min har ta haihu? Zaka kai mata kwanakina ne dan cin zali har sati daya dan ta asirceka ko me? Tunda dai kowa ya san ga yarenta nan a kan me zaka wulakanta ni? Waye bai sheda cewa na rigayeta zuwa gidan nan ama sai a bata kwanakin da suke nawa?!, Abdul uwar gidan banza uwar gidan wofi bayan nice amarya koda auren so ka yi da ita ka fi dokina ?, Abdullllllllllllllllllllllllllllllllll kisa kake so na yi? Wayo Allahna, wayo Allah................." Ta karashe da kukanta, sai kuma ta zabura ta rarumo wayarta ta shiga dokawa nahaifiyarta waya A irin wannan lokacin maman nata kanta tana dakin mahaifinta sunna hirar dare kira ya shigo wayarta na Risala Tana dagawa Risala ta shiga labarta mata duka yadda suka yi tana sheka kuka Mahaifiyarta ta shaka iya shaka, rai bace ta ce" Tun ba'a je ko'ina ba kin ga ilar zurfafawa da namiji soyaya ko? Ba laifi yana iya yin abinda ya ga dama tinda an asisrceshi an nashi ya ci a waina, ama ba zan taba lamuntar wannan wulakancin ba, in sha Allah zamu zo a zauna gobe da safe a kan maganar nan, ina hadin bazawara da budurwa? Kuma mu ina ruwanmu da maganar wai itace uwar gida bayan kin rigayeta shiga gidan?, Ai walahi ba zan lamunta ba tsaf ya dawo dakinki idan ya maki sati ke mai darajar a tare da ke sai ya koma mata ya yi mata kwana uku irin na zawarawa irinta, in bandama cin zali ina hadinki da naa wata bagidajiya.....? No ba zan dauki haka ba, ki kwontar da hankalinki in sha Allah goben zamu zo gidan , saima na faraa biyawa na dauko kakarsa mu wuce dan ba zai yiwu ba walahi, a kan haka sai na amshi takardar sakinki!" Sosi ta hau take zage zage har ta kwontarwa da y'ar hankalinta sannan ta juya ta fuskanci Mahaifin Risalar da yake fadin" Meye kuma daga zuwa yau yau har ta fara kawo kararsa, kin ga ki yiwa yarnan tsawa fa, na kula so take yi ta saka ni a cikin jin kunya , yaushema har zata fara an yi mata an yi mata, aa ni fa bana son irin haka nan gaskiya, ki kwabi yarki ko zata zauna a gidan miji kar ta kaso auren ko sari bai yi ba!" Mahaifiyar Risala ta mike tana fadin" ai kuwa elhaji sai fai ka shiryawa jin kunya, domin ba zan taba yarda a cutar min ya ba a banza a wofi, shi yasa bana yarda da siyayar dangi dan idab danka ya yiwa yarana na tsaya tsayin daka na hukuntaka daidai da laifinka, danginama ban dagawa kafa ba a kan y'ayana bale jikan yar talakawa? Ai Walahi ba zai yiwu ba"..... Yana kallonta ta shige ciki sai mita take yi da rantse rantsen ba zata sabu ba bindig a ruwa, ta yaya za'a ba ƙatuwar mace kwanan y'arta, ko amarci basu fara da miji ba Kai ya kada ya yi kwonciyarsa bai bita ba, abu daya ne ya sani idan takamarta ita karyar kudi hajia Hauwau ta dameta ta shanye, kuma a kan jikanta sai ka ga rashin wayonta, bata hada jikanta da kowa fa a rayuwa , ita nan har so ne take nunawa ya? Ta bi a hankali dan yana guje mata garajenta ya hadasa mata husumar da ta fi karfinta, domin lalle ita din yar mai kudi ce, ama ta kasa ganewa gaba da gabanta, su kam sun yi biyaya ___________________________________ Dakin yaren ya fara zarcewa bayan ya rufe falon da ky yana mamakin Uman biyu da shiririta ta kwonta ne bata rurufe ko'ina ba? A hankali ya bude dakin ya shiga da salama kasa kasa dan ya tabata warhaka ai sun yi barci Turus ya yi yana zuba masu ido su uku a saman gadon Uman biyu ta bararaje abinta a daman gadon yaran nan du ta takurasu ta matse masu waje har kamar zata tunkudo Husaini kasa tunda tsakiyarsu ta shige abinta Habarsa ya kama da hannu biyu, irin idan abu ya bashi mamaki ko haushi da yakan yi dan nuna girman mamakinsa ko jin haushinsa a abun yana kallonta a hankali ya ce" Bata jin magana fa yarinyar nan ko kadan" Kai ya girgiza ya shige bayi ya duba an kashe dukan abinda zai iya zamowa damuwa wa barcinsu, ya dawo falon, a nan ya ga kaskon turaren wuta da hayaki kadan kadan na dan tashi irin ya cinye din nan saura dan kadan ne a ciki Ido ya zubawa kaskon yana tunanin anya wannan aikin aikin daya daga cikin ma'aikatan familly dinsu ne? A formation da ake basu na kula da gida idan suka saka turaren wuta sukan tsaya ne har ya gama waje sannan su dauke su tafi da shi Sake juyowa ya yi ya dake kallon wajen AMINA Dan kankance idannuwansa ya yi a kanta , sai kuma ya karra tabe bakinsa ya dauke ya fitar ya kashe ya yarda mata kasko a cen ya dawowarsa Adu'a ya shiga yiwa yaren a hankali yana dafa kansu daya bayan daya har ya gama sannan ya sake kallonta da mamakin nauyi barci ne haka ko dai summa ta yi? Hannayensa ya saka bayan ya tatare hannun jalabiyar tasa a hankali ya saka a hamatar Amina ya yi mata dagowa irin ta yara sannan ya talabi bayanta ya cicibota gaba dayanta ya mike tsaye da ita a hannunsa Ido ya sake zarrowa gannin bata farka ba, Kai ya gyada ya juya a hankali ya fito da niyar mayar da ita dakinta sannan ya dawo ya rufewa yaren dakinsu A hankali yake tafe da ita yana sake wara dubansa a kan fuskarta domin har wani dan lilo lilo take tana murmushi ga dukkan alamu mafarki take yi ko kuwa idannuwanta biyu neman fitina take yi da shi A daidai zai shige da ita dakinta ya gwara mata kai da garun wajen, hakan ya saka Amina bude idannuwabta da sauri jin an kwala mata dutsi tana barcin Ido hudun da suka shi da shi ya sakata sakin ihu ta kubto ta dirmiyo kasa , sai kuma ta saka wani ihun tana kokarin mikewa da dan wara kafa domin ai dinkine a kasanta jama'a Tsayuwa Abdul ya yi yana binta da kallo tana dan kai kawo tana yarfe hannu yana tanbayar kansa hala dinkin da yawa ne akai mata? Ko kuma an bar mata abin zare na sukarta a wajen? "Yanzu ni zaka dauka? Ni Amina? Wai kamar wata kanwarka? Mema ya dawo da kai dan girman Allah? Me yasa kake shiga harkata ne ni? Me na yi maka kuma yanzzzzzzzzzzzz" Gannin yana matsowa kusanta maganarta ta dauke tana zaro ido tana kallonsa Hannunta ya kama ya nufi bakin gadon da ita ya zaunar da ita yana kallonta cen ciki ya ce" Ina zuwa" Juyawa ya yi ya fice, hakan ya sa Amina kokarin tashi dan ta rufe dakinta da ky ta zo ta yi tunanin yadda ya dace ta yi da wannan yaron, domin bafa zata yarda ya ringa raina mata wayau ba da girmanta! Dawowarsa da rufewar kofarta da ky da ya yi ya sakata komawa ta zauna a saman gadon tana zarro ido tana kallonsa Fitilar dakin ya kashe sannan ya kunna ta kusanta mai hasken ja mai ragagen haske Yana yi yana fadin" Ki kiyaye barin abin turaren wuta kuma ki yi barci kin ji? Ita wuta batada kadan, kuma aikinta mai girma Ne Amina" Amina dake binsa da kanta kamar zai karye dan son gannin me yake nufi da ya kama sunnanta gatsau sai da ta ji wani iri, ace kanninka na kama sunnanka fisabililali? Da gunguni ta shiga fadin" Ko wa'inda suka girmeka Aunty suke ce min, dan ka dauki karfe ka wani ja dare kamar daren mutuwa shikenan sai ka nemi raina wanda ya girmeka?" A lokacin ABDUL ya gama dube dubensa ya karaso inda take zaunen ya duka kasa hannayensa a saman katifar, hakan ya sa ta ja baya tana son hantsilawa hadi da fadin" Kai wai meye haka?" Da sauri ya rike kafafuwan nata daria na son kwace masa, shi walahi har yanzu ya kasa yarda bata wuce wata sha bakwai haka ba, wannan shiririta haka? A hankali ya ce" Me kika ce?" Amina dake hadiyar yawu da sauri da sauri ta ce" Me zaka min dan Allah?" ABDUL ya yi dan murmushi ya ce" Ba komai fa, cewa na yi me kika ce?" Amina ta ringa dauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Cewa na yi wai da, ka ga tunda na girme maka da yawa na ce min aunty , wa'inda na girma haka ka fahimta?" Kai ya gyada , a hankali ya ce" Nima na ringa ce maki Aunty ne?" Amina aka wani mane baki aka gyada kai, ita ga Aunty Murmushi ya yi ya ce" To Auntyna" Amina ta dan tsatsareshi da ido dan sai ta ji kamar da gatse ya kireta auntyn A hankali ya shiga dage doguwar rigar barcin nata, a gigice ta daka hannunta tana rike nasa taba kallonsa bakinta har yana hadewa ta ce " ABDUL , menene haka kake shirin yi? Me zaka min? ABDUL ka tashi daga kusana kuma ka daina tabani , ka ga lokaci nake jira ka bani takardata ko? Dan Allah ka barni haka ya isa" Kansa ya dago a cikin ragagen hasken yana kallon yadda du ta rikice, tsoro na dawainiya da ita karara A hankali ya ce" Ba komai ba fa zan yi maki" Amina ta ringa girgiza kanta tana fadin " Ka sake ni, dan Allah ka bani takardata na koma gidana da y'ayana mu yi zamanmu, dan Allah kar ka sake min abinda ka yi min kar ka wulakantani" Idannuwansa ya dan lumshe a hankali sai kuma ya shiga ambaton Allah a cen kasan zuciyarsa, haka kuma fargaba na cika masa ciki Shi bai taba haduwa da rigimar dake nufo shi baya son kulawa ba irin wannan, shi a rayuwarsama fadan mutun biyu kawai yake gujewa, bayansu idan rigima ta yi salama yakan nema mata amincin ne shima ya rikota a yi ta yi Ama wannan yarinyar sam sai ya ringa jin baya so su yi tashin hankali, kuma baya so ya fada mata maganar da zata ji mata ciwo A hankali ya cire hannayen nata ba da kwaramniya ba ya ce" Dubawa ne zan yi, kar aje da ta maki dinkin ta bara maki yan tsirarun zare, kin san yanada dan kaifu da kuma tsini yana iya damunki ya hannaki sukuni , ko zama kika zo yi a karkace dan kar ya ringa sukar maki wajen, bari in gani?" Amina, ta kasa fahimta idan ta yi magana baya gane yarenta ne ko kuma bata isa ya ba maganarta mahinmancu bane ya sa baya bi ta kan abinda ta fada, sake maido hannunta ta yi zata kuma rike shi, sai dai yanzun da dan karfi ya tare mata hannunta ya dago da idannwansa da suka fara dan cenza kala, dan Walahi ta cika caza masa kwakwaluwa ya ce" I said , ki barni na gani " Daidai da amon muryarsa yanzun a wani irin kusashe ya yita, kuma yana yi kamar sai ta bari zai gannin ne bayan tuni ya kaita kwonce ya saka kafafuwansa ya yiwa cinyoyinta yannayin da idan tace zata yi wani motsi mai karfi tana iya jiwa kanta ciwo mai masifar zafi, a dole ta rintse ido jikinta na rawa kadan kadan tana suararonsa hankalinta tamkar zai bar kwakwaluwarta a lokacin da ta ji ya dora hannunsa a hankali yana shafa saman jikinta sannan ya kunna fitilar kusa da gadon ya haske da kyau yana kallon dinkin, harma ya kai yar yatsarsa wajeb zaren ya dan danna a hankali Kwarai ta zabura, ama ba irin zaburar da idan da sauran zaren zata yi ba, hakan ya sa a hankali ya cire hannunsa yana kallon wajen, dan makoloton wuyansa na ta kai kawo , tunaninsa na neman cenzawa a irin wannan lokacin, inda harshensa keta neman zirowa ya kai ziyara a wajen, sai dai irin yadda jikinta ke rawa a hankali ya ja mata rigarta yana dan jimke hannunsa da ya fara dan bari kadan sannan ya haura saman gadon a hankali ya ja bargo ya luluba mata bayan ya jata saman gaba dayanta Idannuwanta a rintse suke, ita dai ta kasa kwakwaran motsi domin tsoron da take ji ya fi komai yin tasiri a kanta a yanzu A hankali ABDUL RA'UF ya shige cikin bargon da ta kudunduna yana lumshe mayatatun idannuwansa ya janyota jikinsa a hankali ya rungumeta yana kai hannun nasa a hankali yana lalubar jikinta da tunanin yadda zai yi ya samu dan rage wahalar da ta fi da kunno masa kai A hankali ya dora hannun nasa a saman mamanta yana zagayawa da shi, inda Amina ta ja wani irin numfashi ta sauke hadi da saka hannunta ta rike nasa da karfi tana son hannashi abin nan Da hannun nata a saman nasa ya ci gaba da yi a sanyaye yana sake zagaye shi, Muryarta mai hade da dacin da take ji da kukan dake ta danno mata a hautsine ta ce" ABDUL?" Cen ciki da kyar ya iya amsawa a takaice Amina ta sake rike fuskarsa a hankali ta ce" Dan Allah ka barni haka, kai baka jin kunyata ne?" Idannuwansa ya lumshe a hankali ya ce" bana ji" Amina ta sake rike shi sosai ta ce" Baka jin kunyar tawa?" ABDUL ya gyada mata kai yana sake lalubar abinda a hannunsa yana jin yadda ya fara taurara , watau tana amsar sakonsa ama tana turewa A hankali ta ce" ABDUL ni fa yayarka ce?, Abdul babu soyaya a tsakanina da kai, kuma ka ga dinkine a jikina ko? Dan Allah ka tashi ka yi tafiyarka dakinka!" A hankali ya juyar fa hannun nata yana kallon idannuwanta yaa janyo hannun nata a hankali har ya kaishi babar eriyar da ta gama cika ta tumbatsa wace ta hadasa mata samun dinki ya dora a saman wajen yana kallon yadda ta zavura, ta tsorata, ta janye hannunta, ya yi murmushi a hankali ya ce" Bafa yi zan yi ba Aunty, mamamaan zan sha , kuma sai ki rike min nan shima sosai ki dan murza min ....ki riken da kyau kin ji? Zaki min?" 😧😧😧😧😧😧😧😧😧😧😧😧😧😧😧😧ni dai ba luwana🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️🧎🏻‍♀️ *NZL PAGE3️⃣2️⃣* Amina ta fashe da kuka tana kakauda kanta cike da matsananciyar kunya ta ce" Hasbunnalah, ya salam, ABDUL ka daina yi min abubuwan nan tamkar wata yar iska, bayan ni ba yar iska bace, ka dagani nace" ABDUL ya tabe bakinsa ya sasauta sosai sannan ya dage ya janye rigar tata gaba daya yana danneta ta yadda ya san ba zata iya yin kokowar kwatar kanta ba ko dan radadin dake kasanta sannan ya sake hayewa jikinta a hankali ya ce" Na sani mana ke ba yar iska bace, abinda raminma dan tsugul ne........, Kin ga nima nan zan sha shikenan fa, idan kuwa ta kama kema ki yi abinnan kau......? Ya karashe yana dadage mata girarakinsa idonta cikin nasa A hankali ta cire nataa duban domin bakinta ya mutu murus sai kallonsa take yi Ido ta rintse da karfi tana dora hannunta a saman kansa a lokacin da ita da kanta bata san ta aikataa hakan ba , ta nemi mimikewa tana sakin dayan hannunta a saman gadon tana sake rintse ido hadi da sakin wata irin ajiyar zuciya dan guntun hawayenta ya shiga biyowa ta gefen idannuwanta Tun tana turewa, har abin ya zo ya girmami tunaninta ta mance da wa take, a ina take, da kuma ciwon dake jikinta , ya zamto idan ya kai hannunsa ya shafa mararta sai ta yi kamar ta farke dinkin da kanta su koma ruwa, domin ita kadai ta san abinda take ji, radadin kansa daukewa ya yi gaba daya ta shiga ambaliyar niimar gyare gyaren da ta kwasa a jikinta wanda da kyar ya iya hanna kansa sake afkawa a koramar da wannan feshi ke fitowa A rikice ya riketa a jikinsa ta zamto tamkar wata yar baby ya juyar da ita gaba daya saman bed din ya rukunkumeta sosai a jikinsa yana yin iya yinsa a tsakakanin cinyoyinta dan ya samu nutsuwa Da kyar ya iya samun nutsuwar wanda a daidai lokacin sai da ya sake yi mata wata damka a rikice yana fitar da nishin da ya sake tsoratata ta sake rintse idannuwanta gam, domin nishi ne kamar na wani dankareren bajimin kato A ya dawo nutsuwarsa ya kasa daga jikinta Wannan ni'imtacicen kanshin dake shiga hancinsa bayan ya yi zufa itana ta yi zufa ke karra manar da shi a jikinta Wannan dadadan laushi da santsi da fatar jikinta ke yi ya fi komai bashi mamaki da sake shafa fatar yana kallon yadda take sheki a cikin karamin hasken dakin Muryarta cen ciki sosai ta furta " ABDUL........ ABDUL?" A hankali ya iya amsawa da "ummm?" Itama a hankalin ta ce" Ka dagani, bana iya numfashi da kyau" Dan motsawa ya yi a jikinta kasa kasa ya ce" Wai da ban koshi bane Aunty" Amina ta rintse idannuwanta a hankali ta ce" Kasheni kake son yi ne?" ABDUL ya girgiza kansa bai bada amsa ba Amina ta sake jan numfashi ta ce" Ka tashi to, ni bayi zan shiga fitsari nake ji!" Ido ya sake lumshewa yana jin wani irin abu na sake ratsa sasan jikinsa Juyo da ita ya yi a hankaki yana kallon lebenta dake ta kyali ya kashe girman idannuwansa cen ciki ya ce" Kin tabata fitsarin ne kike ji ko kuma dai wani abu ne a nan ya maki nauyi ya dane maki nan?" Ya karashe yana nuna mararta a hankali yana shafawa Da mamakin gannin ya gane ina ke damunta ta ce" Lah......, To ai fitsarine ko?" ABDUL ya yi murmushi yana kallon fuskarta, a hankali ya ce" Aunty Amina ni shekarunki nawa?" Amina ta wani maze irin an tabo filin da ta fi auki ta ce" Na kai talatin fa a kadan" Murmushi ya yi ya kai hannunsa gaban goshinta yana shafa kwontacen gashin gaban goshinta, sai kuma ya rage muryarsa ya ce" To mu je mu yi fitsarin" Amina ta kura masa ido, ita tunanin da take yi a mararsa kunya a anguwarsu bata hango wannan yaron ba, koda yake ba komai bata da kafiya dole zata sada masa, idan ya bata takardarta ba shikenan ba, Samu ta yi ya dagata, cike da jin kunya ta ja zannin gadon ta rufe jikinta yaron nan na kallon dukan motsinta, ta juya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta nufi bayin Sai da ta bude ta shige ta karro ta juyi fuska a hade ta ce" Ka tashi ka bar min dakina walahi ka ji na fada mak............mmmmmmm" Kit ta yi ta mako kofar tana zarro ido domin mikewa ya yi ya nufo kofar.. Samun kansa ya yi da tsayawa yana kallon kofar da ta maki, haka kuma kunnayensa na jiyo masa gungunninta A hankali ya karasa ya dan tsaya a jikin kofar yana sake sauraron dan fadan da take yi irin na itafa bata son rainin wayo fa, karfa ya dauka ya samu damarta ne dan yana cin zalinta, ko abinda ya shiga tsakaninsu shi da ita ya dauka zakinta ya ci kuma ba zai kuma samun wannan dama ba, ita takardarta take so tun kafin ya jaza mata abin kunya a zageta a gari ace ta auri kanninta, in sha Allah ta je ta auri datijon da zai iya kula da ita A hankali ya janye ya juya saman abinda ke shinfide a saman gadon ya zauna Yan yatsunsa na kafa yake kallo da kuma tunanin abubuwan dake masa yawo a cen kasan zuciyarsa Ta dauki lokaci sosai a ciki sannan ta fito ta sako rigar wanka mai ruwan pink mai haske ta daura igiyar rigar haka kadan a bayanta , sannan ta dan nado dan tawul fari kal a saman kanta Tunda ta fito a wankan ta dan kalle shi sama sama ta dauke idannuwanta, domin irin zaman da ya yi gaba daya wani irin gida gida gida a jikinsa irin na gagararun samarin nan masu ji da karfi da kula da jiki, irin yanda cikinsa ya yi wani gida gida kuwa har sai da ta ringa dan satar kallonsa, kula da ta yi ita yake kallo ya sakata rasa sukunin sakewa ta yi abinda take so Mikewa ya yi a hankali ya karaso inda take tsayen ya yi tsaye a bayanta, ya zamto sunna kallon junna ta madubi A hankali ya ce" AMINA, anya kuwa zaki iya jure karar da kika yi kika yiwa Mai SHANU biyaya?, Idanma kin iya jure hakan, anya *zaki iya yi min Ladabihhh?* kuwa?..............ina nufin, zaki iya jure rayuwa da ni ba tare da kina jadada min kiyaya a bayane ba?" Amina ta juyo tana kallonsa jikinta a sanyaye, kalmar jadada kiyayar da ya yi sai ta jita wata iri, ita ai bata jadada masa kiyaya ba, ita gaskiyar dake tare da ita take fada A hankali ta ce" ABDUL, ba kiyaya nake jadada maka ba, hasalima ni din ba mai irin hakayan nan bace ba.........." Ta yi shiru tana kallon kasa, a hankali ta sake dagowa dan har yanzu hucin numfashinsa take ji ta sauke idannuwanta a cikin nasa bayan ta dago dubanta kadan A sanyaye ta ce" ABDUL shekarunka nawa a duniya?" Abdul ya dan kashe lebensa na kasa da ya dan bushe masa kadan, bai ce da ita uffan ba, hasalima a yanzu haka ya kasa fita ne dan maganar nan tata sau hudu Kennan yana jinta daga bakinta, Ba wai maganar ta tsaya masa a rai bane dan wani abu Maganat ta yi tasiri a ransa ne dan shi yana jadada magana ne idan ya zamto ta zama babar damuwa a rayuwarsa, ko ta farin ciki yakan yita sama sama ne ya barta, Gannin uman biyu tana neman saka damuwa a ranta ne abin ke dan son ya dame shi Shima, bai tare da ita dan tunaninsa zama zaunewa da ita ba Daga jiya zuwa yau ne ya yi tunanin ya dace ya zauna zaunewa da ita har mutuwa ta rabashi da ita, bale da Husain da hasan suka kireshi da DADY Ya dace Uman biyu ta sani shima babu maganar soyayar ko dis a cikin zuciyarsa, ya dace ta yiwa kanta adalci ta daina wata shiriritar Shi mutun ne cikin mutanen dake kamanta adalci ga duk wani wanda suke zaune tare, Zama na yan sekwani ko na jimawa yakan kamanta zama da kai ne da ra'ayin kanka Shi bai taba kamanta takurawa mutun a komai na rayuwa ba bale a ra'ayi irin na zaman aure A yanzu, kafin ta fito maganar da ya yi ta kamantawa a zuciyarsa shine' Saki take so? Me yasa take son saki? Idan na saketa ina zata koma?, Ko dai na kauracewa shinfidarta? Shin mace idan namiji ya kauracewa shinfidarta ba a nan take shiga uku ba? Ko ita nata ra'ayin daban ne da na sauran mata? Shin shekara daya tak dake tsakanina da ita ne take aiki ko riketa da nake yi a hannuna na zuba mata madarar da mararta sai ta dauki nauyi da dumi na lokaci mai tsayi ne abin duba?, Shin ita ba zata duba dauka, sunna uwa uba tsarin hakitar da dubunta je wawura dominsu?, Me ya dace ace na yi mata ne? Bara ta fito na bata takardar tata, idan ya so sai ta samu kwonciyar hankali tunda na kula hakan na daga mata hankali' Wadinnan sunne abubuwan da ya yi ta tunani har ta fito daga bayin ta wuce ta gabansa ta karasa gaban madunin ta shiga kimtsa kanta A hankali ya dauko dubansa tun daga kafafuwanta da suka sha gyara irin na Alewa da ake yiwaa mata a dauke gashishikan kaffafuwansu da sauran sasan jikinsu, wasun harma da fuskarsu irin masu tarin gashin nan, Alewa wace ke daukewa sumul bata barin kuraje ko wani tanbo tanbo na gashi , sannan fatar ta dauki sheki kamar gashi bai taba tsirowa a wajen ba, irin yannayin hakitar kwaurinta zuwa gwuiwarta da batada mugun bakin da ya zarce na jikinta, bakinma kusan daya ne da sauran jikinta da nan, a hankali ya kai duban nasa kugunta sannan ya sake hauda duban nasa har zuwa kirjinta, sannan ya ajiye a saman fuskar da ake ikirarin an tsufa da ita yana kallon fuskar zuwa gashin kanta da ya dan leko daga tawul din nan baki sidik da shi Yar yatsarsa ya kai wajen hancinsa a hankali ya dan murza gefen hancin sannan ya juya ya nufi hanyar fita ba tare da ya bata amsar tambayarta na son sannin shekarunsa ba Da ido Amina ta rakashi tana jin kamar ba dadi haka, Sai kuma ta ture ta juya ta ci gaba da shafa turarenta domin ta kwonta Sai da ta cenza zannin gadon sannan ta kwonta tana ta turo baki na abinda ke zube a saman zannin gadon da jin haushin yaron nan Asuba ta gari auntyn abdul🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🤣 *Yadda ake hada ALAWA ta cire gashi irin kwauri, cinya, da fuska* Da farko anada bukatar _*Siga Kofi daya* *Rabin kofin na lemun tsami, lemun ki siyo ki matse kamar rabin kofi* *Sai kuma rabin kofin na ruwa* Da farko zaki kunna wuta kasa sosai sai ki kawo ruwan ki juye hadi da zuba sigan nan, ki kula wutar fa kasa sosai fa, sai ki zauna kina kula kina dan juyawa kadan ba sosai ba hat sai ya dawo maroon sigan, sai ki sauke a kasa ki zuba ruwan lemun nan ki juya su a hankali su hade jikinsu, zaki ga ya fara kauri sosai, sai ki kawo wani abin zubawa na kwalba, na kwalba, sai ki juye a ciki sai ki barshi ya kara hucewa kadan sai ki rufe, idan kin tashi anfani da shi zaki ciro ne, ki yi ta jansa , ki yi ta jansa sosai har sai ya kasance yana wani irin jayuwa sosai sai ki kawo ki fara anfani da shi wajen cire gashin ta hanyar ɗorawa kina ja , da zafi kadan ama kuma result din mai kyau ne😍😍😍😍😍😍 __________________________________ Kiran da ta samu daga mahaifin Risalah ya saka barcin dake dan fuzgarta marar dadi sakinta A hankali ta zauna saman gadon da ta kwana a dakin dake gidan aminiyarta watau Uma tana jin murjirya na neman hade mata jiki lokaci daya Muryarta a sanyaye ta ce" Ka fada mata ina gidan Uma, ka barta ta zo Elhaji ba damuwa" Tana gama wayar ta katse ta zurawa waje daya ido still jikinta na yi mata wani irin yam yam yam kamar ana bin jikin nata daya bayan daya ana zukar jinnin jikinta *NZL PAGE3️⃣3️⃣* Da kyar ta iya tashi ta shiga wanka jikinta a mace, babu karfi ko daya, damuwar dake ciciyar kirjinta ta kore komai, dama da kyar ta iya rintsa idannuwanta zuciyarta cike da mamakin ALKALI, yanzu alkali yana sane ance masa ta fita bata da kafiya zata je asibiti, ama shine babu abinda ya dame shi? Alkali har ta kwana a wani wajen bai nemeta ba? Tana gannin kiraye kirayen ABDUL ta ki dagawa , dan ta fara lura wannan abin harda yardarsa yake faruwa, ta fara yarda cewa ABDUL ne ke bada dama ana wulakantata Suturar da ta fito da ita ta cenza , watau doguwar bak'ar abaya mai shegen kyau ta dauki mayafinta ta yafa sannan ta bude jakarta ta hannu ta shiga fesa turare tana tunanin abinda ya dace ta aikata Batama san ta inda ya dace ace ta fara ba, ama ko menene zata fuskanceshi, ta yi kuka a jiya ta huce, a yanzu lokaci ne da ya dace ta fuskanci damuwarta Karfe tara na yi da yan mintunna ta fito sakamakon kiranta da Hajia Uma ta zo ta yi cewar ta yi baki Zama ta yi kamar yadda ta saba a kimtse, zama mai birgewa, kafafuwanta a hade, abayarta ta dan bazu kadan ta bi jikinta masha Allah, kanshin jikinta kuwa ya hade ko'ina domin tana fitowa kanshin turaran Channel gangariyarsa ya baje ko'ina ya hade ko'ina ya doke kowane da aka yi anfani da shi a wajen Da kyar Hajia ta iya jurewa bayan Maman Risalar ta gaisheta ta amsa mata sannan ta sake hade bakinta da fuskarta tana kallon TV Hajia Uma ta yi murmushi, domin ta kula kawar tata fa ta karra kankaro wulakanci, dan haka itace ta fara yin magana tana duban Maman Risala ta ce" Hajia ki yi mata bayani mana?" Maman Risalar ta tabe bakinta kadan tana kallon yayarta da ta mintsineta, domin dama itace tace sai sun zo sun dauki wace ta isa da shi su je gidan ta ce" Hajia, dama jiya ne Risala ta yi kirana tana kuka take fada mun yadda suka yi da ABDUL, cewa wai sai ya yiwa yarinyar nan sati daya kamar wata budurwa wai ai itace uwar gida tunda an rigayi daura aurenta kafin ya yiwa Risala nata kwanakin, bayan a jiyan da kika ce a kai Risala ko wankan kirki bata yi ba aka kaita, shine kuma haka zai biyo baya?" Hajia ta sasauta gilashin idannuwanta na karin karfin ganni tana kallon Maman Risala Ita abin mamaki ya fara bata, sai kuma ta samu kanta da jin haushin lamarin Da basarwa ta ce" Kina nufin, auren da aka daura yau kwana uku cif, ta tare jiya a jiyan ta fara kawo karar mijinta?" maman Risala da yayarta suka kalli junna, sai yayar tata ta yi gagawar fadin" Aa hajia ba haka take nufi ba" Hajia ta fuskanceta dan ta kuka itace uwar maganar ta ce" Yaya take nufi kennan?" Mama Risala ta dubeta ta ce" Hajia, ya dace a yanzu idan akoy wani abu da ya shiga tsakani mu mayar da shi gefe mu fuskanci abinda ya dace ace mun fuskanta" Hajia ta yi murmushi tana sauke kafarta dake saman dayar ta fuskanceta sosai, a hankalinta ta ce" Ke da kina tunanin akoy wani abu da zan rike a tsakanina fa ke Hajia?, No, bama ke ba, ko wanda ya girme maki ba zan iya hakan da shi ba.....dama cewa na yi than.........abinda kika ce kin shirya ni na jima a kai......" Ta saje duban jus din da mai aikin Hajia Uma ta ajiye a gabanta da cofin kwalba mai kyau ta dauke kanta ta sake dubanta ta ce" Idan dabi'arta ce, ya dace ki kwabeta ,domin mijinta ne ai , kuma yanzu suka fara rayuwar, a duka lamarin itace a baya , ya dace ta daina kawo maki kararsa, bayan wannanma ai na wani abu zaki yi masa ba ko?" Baki ta bude zata ba Hajia Amsa da sauri yayarta ta tareta tana murmushin yake ta ce" Haba dai Hajia, wa zai ce zai tarbi wannan aradun da kai? In ba shakikinsa ba a wannan zamani ai babu wanda zai yiwa mai kudi haye, hajia wasu masu kudin da sun fi karfin kowama? Ciki harda shakikan nasu? Dama maganar ce muka ga ya dace a kawota gaban wace ta isa da shi , shine muka zo " Hajia ta koma saman kujerar tana sake buga masa waya, sau hudu kennan bai daga ba a ranta tana ayana' ramawa kake yi ko?' A hankali ta yi salama a lokacin da ya daga, sannan ta saurara har ya amsa mata a nutse Hajia ta ce" Zan zo gidan ne, ina fata baka fita ba" ABDUL da dawowarsa kennan daga kampani ya dawo ya dan huta ne ya fita gonaki domin tunda duku dukun ya fita ya je Kampanin ya amsa hajia cewa yana gida Bata ce komai ba ta kashe ta juya ta fuskance su ta mike tana kallon Hajia Umma da izar hajiar ke birgewa kamar ace itace ta ce" Uma zamu je, ta yiwu daga cen na wuce gida ko na dawo yadda hali ya bada" Umma ta mike tana yi masu Rakiya, Hajia ta shige motarta direbanta ya ja , suma suka shiga tasu Maman Risala sai masifa take yiwa yayarta da yaren turanci kamar zata ari baki ta ja masu motar suka bi bayan ta Hajia Tunda Hajiar tace masa gatanan dama ya gane ba lafiya ba, shi yasa ya kimtsa kansa ya dawo falonsa na kasa ya zauna yana jin kamar hayakin Turaran wutar da aka saka ya dan yi yawa, ko kuwa dan ya fito daga cikin kura ne ya shaki kurar da yawa? Ga kayan karinsa saman table ko tabasu bai yi ba suka karaso Tunda suka zauna ya gaishe da wa'inda ya dace ace ya gaishe da su ya dan kalli Risala sau daya ya dauke dubansa ya maida kan kakarsa dake cicin magani ita a dole fushi take yi da shi A hade Hajia ta ce" Meye gaskiyar maganar da matarka ta fada?" ABDUL ya sake fuskantar Hajia yana rage sanyin ACn domin sanyin ya yi yawa sosai a nutse ya ce" Dangane da me fa?" Hajia ta dube shi, ta dubi Risala ta ga sai sake sinne kai take, ta sake dubansa tana tunanin ta inda ya dace ace ta yi bayanin ta ce" Kan maganar tarewarta" ABDUL ya lumshe idannuwansa yana komawa saman kujerar gaba dayansa yana jin nauyi da kunya na son kama shi dangane da maganar, sake dagowa ya yi idannuwansu suka sarke da matarsa, yar budurwar matar da ya dauko wace a tunaninsa ko wata ya yi bai taba hannunta ba zata yi kawaici har sai abin ya zarce misali, sai gashi a kan kishi ne ko wauta ce, ko sabo da yi ne ya saka har ta fitar da maganar cikin gidansa a jiya tsal zuwa yau? A dake yana dan fara cenza yannayinsa ya ce" Gaskiyar kennan" Daga Hajiar, har iyayen na Risala sai da suka zuba masa ido Hajia ta dan so daburcewa, sai dai ba zata yarda da haka ba, komai hardewar fuskarsa gaskiya ce ta zo sanar masa sai ta fada Da kuka ta ce" A kan me zaka dauki kwanakin wata ka ba wata bayan ita ta rigayi dayar shigowa gidan nan?" A dakensa ya ce" Dan aka hukuncin yake, ke kin san Uman biyu ta rigayeta tarewa...............kuma an rigayi daura aurenta a kan na Risala" Ido Hajia ta shiga kiftawa, watau ABDUL dan rashin kunya yana so ya nuna mata cewa ita ta dan ya kwonta da uman biyu ko me? Mahaifiyar Risala ta ce" Ka yi hakuri Abdul, ai ba haka tsarin yake ba, inaga ya dace ka bi gaskiya dan gudun wasu fitintinnun, inm ba abinka ba ina kai ina tsohuwar macen da ta girmeka nesa ba kusa ba?, Sannan matar nan harda ya'ya menene abin bata har sati guda fisabililahi?" ABDUL ya sake jinginar da bayansa yana dan ciciza lebensa a lokacin da yayar mahaifiyar matarsa ke fadin" Ai abin ba wani bane son kai ne irin nata, ita tana gannin ai idan ta gaskiyar za'a bi bata da riba, shi yasa zata fara hada shi da bokaye da sauransu da kuma kirsa irin ta tsohuwar mace, Allah ya sa Risala ba marainiya bace tanada iyayenta zasu tsaya mata, na san an jima ana sonka dama ana dabonka yanzu da aka samu za'a yi aiki irin na zalunci, ina anfanin haka?" "Bata SONA fa" ya fada a hankali yana duban agogon dake hannunsa Ya sake dagowa gannin kowace ta masa tsuru tsuru tana kallonsa Murmushi ya yi ya ce" Ita soma take yi na saketa, ko jiya sai da tace na saketa ta koma gidansu......ina nazari ne a kan abinda ya dace, tunda kun ga ai AMINA MARAINIYA CE, ina matukar kwadayin samun ladan rikon Marainiya da marainun ƴaƴanta " Hajia kamar ta kurma ihu, idannuwanta kamar ta ciro su ta lika masa haka take ji Maman Risala takaici kamar zata hadiyi zuciya ta ce" Ta yaya zaka ringa maganar cewa bata sonka? Idan ka saketa ba sai ta shiga uku ba a duniya gaba daya?, Ai ana yi maka haka ne dan kara damkeka a bar yar yarinya karama da ciwon zuciya na wulakancin d'a namiji, tunda tana so ka saketa ka saketa mana, babar banza kawai" ABDUL ya fuskanceta, a nutse ya ce" Hajia, itafa du yadda ake dan hasashe a kanta bama haka bane, twinsma ai na kanwarta ne, ita dinma yarinya ce karama fa sosai, kuma maganar bata sona da gaske ne, bata da ra'ayin zaman itama" Hajia da kyar ta iya budar bakinta da rarashi dan ta fara yarda da maganar yayar maman Risala cewa an hada danta da malamai, in ba malamai ba fisabililahi ina bakin ABDUL ina kiran Amina da yarinya karama? Yace wai bata sonsa kuma har yanzu bai rabu da ita ba? Ai an gama da jikanta tana wasa da yawon siyasa A hankali ta ce " SON, ka saketan mana?" Risala ta gyada kai da sauri ta ce" Eh, dan Allah ka saketa mana?" ABDUL ya ringa kallonsu daya bayan daya yana tunanin anya sunna da adalci kuwa? A tausashe ya dubi Hajia ya ce" Idan na saketa yaya zaki yi da Alkali?" Hajia ta kalle shi tana kure shi da duba ta ce" Kamar yaya, ni kuma ? Kai dai" Murmushi ya yi yana kowama ya zauna da kyau, a nutse ya ce" Zan so ace, ko menene tsakanina da su dukansu, mu iya zama mu sasanta mu fuskanci junna, zan so ace idan na dora doka a gidana koda ta son rai ce ba wai ta gaskiyar da ake son takewa dan wasu dalilai daban ba a zauna da ni da iyalina mu yi maganar mu sasanta komai........." Ya saurara , ya kausasa muryarsa sosai ya sake dubansu ya ce" Da wahala na iya daukan jeka ka dawo ga kuma kasuwa da jama'a, sam a cikin neman na abinci wanda dole sai da shi za'a rayu , da wace ya dace ace ta zamto wajen hutuna wajen nutsuwata, wajen da na fi komai farin cikin zama mu zanta ko mu yi shiru a waje daya.....uwa uba wajen da.........." Ya dauke maganarsa yana dan murza hancinsa kadan ya ce" Wajen da nake da ikon ajiye hudu, koda wa'inda ke nan mun kasa zaunuwa ba dan na kasance mai sake sake ba, sai dan ba zan iya jurar RAINI ta WATA FUSKAR ba!, Su zamto hargitsina, kwonciyar hankalina ba, .............kwarai zan so ya zamto na farko hakan, kuma na karshe, ba dan raini ba, ba dan na raina manyana ba, sai dan gudun abon rainin ya shiga tsakani....domin farawar hakan tsakiyarsa cin mutunci ne, karshensa kuwa bakin ciki............." Yana dire ayarsa ya sake bude idannuwansa ya zuba a cikin idannuwan mutane hudun nan da kowace girman nata idon ya fi gurbinsa dan kowace da irin fasarar da ta ba maganarsa a dunkule, kowace da irin abinda ya shiga kwakwaluwar a maganar jikam Hajia Maman Risala da mamaki ranta bace ta ce" *NZL PAGE3️⃣4️⃣* Maman Risala da mamaki ta ce" ABDUL, yanzu a kan wacen matar ne zaka sakamu a gabaa ka nemi rainamu har ka nuna kana iya rabuwa da RISALA yau daya kwana daya?" A zabure Risala ta kalli Uwar hankakinta tashe ta ce" Mama sakina kuma?" Abdul ya sake sauke ajiyar zuciya ya mike gaba daya bai kuma cewa dayansu ufan ba , ciki harda kakarsaa ya haye sama Mikewa Hajia ta yi harta jakarta da wayarta ta bari a nan ta shiga binsa saman da dan sauri, inda gaba daya suka rakata da kallo Yana shiga tana shigowa ta bude kofar da karfi ta jiga ta kamo shi ta juyo da shi yana dubanta a rikice ta ce" ABDUL, yau ni zaka wulakanta? Abdul ni zaka watsawa kasa a ido a cikin mutane ka wulakantani?" Abdul ya ja numfashi a hankali ya kama hannunta ya nufi bakin gadonsa da ita ya zaunar da ita, sannan ya tsuguna a kusa da ita kadan yana dubanta a nutse ya ce" Hajia, me yake faruwa ne? Me yake damunki ne haka?" Hajia ta ce" Ni za'a tambaya abinda yake damuna ko kai Abdul? Kai za'a tambaya abinda yake damunka da har ya rufe maja ido haka" ABDUL ya yi shiru kadan, sai ya sake riko hannunta yana dubanta ya ce" Menene abin daga hankali acikin abinda Allah ya hukunta?, Du da ake wannan rigimar idan Allah ya yi sai mun zauna zaunawar fa zamu yi, idan kuwa Allah bai yi ba muna kallo sai dai mu yi hakuri fa Hajia" "Dama kanada niyar zama da ita ne Abdallah? Dama kana soyaya da ita ne?, Dama ka jima da sanninta ne ko menene? Abdallah ta girmeka fa?" Hajia ta fada tana tarar numfashinsa A hankali ya ce" Hajia , halal ne, kuma sunna ce mai girma wace Ma'aiki ya raya SAW, ita shekara daya ce tsakanina da ita wace idan za'a zauna a duba yarintarta sai ace na bata shekara takwas ko goma a haife............, Hajia shekarunta be matsalar ko mene?" Ya idasa a sanyaye yana kallon Hajiar............ Hajia ta ce" Magana kake yi a kan shekarunta kadai?, Kosai fa take saidawa, kwararo kwararo tana yawo da yayanta da kake cewa wai ba nata bane" "She's virgin Hajia" ya fada kasa kasa sosai wanda hakan ya saka su dukansu yin shiru kamar an yi ruwa a dauke, domin shi din da kansa ya zame masa dole ne fadin hakan, ita kuma hajiar wata irin kunya da nauyi ne suka zo lulubeta, gaba daya ta rasa kallonsa zata yi ko sada kanta zata yi kamar tana gaban sirikanta? Dan tarin karfi da yaji ya yi kadan yana cire nauyin da ya tsaye masa a gaban idannuwansa a sanyaye ya ce" Kin san cewa ba kyau tsananta kiyaya ko soyaya ko?, Kuma kin sani wannan hadi na Alkali ne.........a kan haka kin ga irin fushin da Alkali yake yi da ke ko?" Hajia ta lumshe idannuwanta ta ce " ABDUL, sam ita din ba tsarinka bace, shin ka manta burina ka tsaya a takarar gwamna a sabon zabe ne?, Ka san me ake so a matsayin matar gwamna uwar gida, nifa ba wai wani damuwata Risala ko iyayenta ba, no, ni damuwata kai, ina wannan yarinyar ina amsa kiran sunnan matarka a gaban manyan mutane?" Murmushi ya yi a hankali ya ce" Ki kwontar da hankalinki, in sha Allah lokaci zai nuna mana komai Hajia" "Ni so nake ka salameta" hajia ta sake nanatawa, wanda hakan ya sake bashi mamakinta, bai taba sannin haka Hajiarsa take ba gaskiya Murmushi ya yi bai ce komai ba, har Hajia ta gama saukowa, domin shi ya san hanyoyin sauko da ita koda tana cikin fushi ne, a nan ya yi mata abinda ta fi kauna watau ya tura mata ƴaƴan banki yana fadin" Ina so a koma gida yanzun daga nan.....Hajia, ina mamakin irin yadda har yanzu kike yarda wasu na shiga tsakaninki da Alkali, bayan kin fi kowa sannin wanene shi" Shiru ne ya biyo baya mai dauke da tunani kala daban daban daga Hajiar har shi din Cen ta mike tana yi masa salama ta sauka A lokacin da ta sauko basa nan gaba dayansu dan haka itama bata tsaya nemansu ba ta fice da gagawa ta shige mota aka nufi gidanta da ita ABDUL kuwa wayoyinsa ya kashe gaba daya ya kwonta dan hutawa __________________________________ Kwanaki uku da suka biyo baya ABDUL bai kuma komawa dakin Amina da nufin tabata ko kwonciya yin barci tare da ita ba Hakan da ya yi sai ya samar mata nutsuwa da ragewar faduwar gaba har ta zo ciwonta ya fara yadda zare dan haka ta shiga gasashi sosai har yanzu ya zamto ta saka Baba turo mata Asma'u dan su gama gyaranta sannan tace biyunma su fara zuwa ta yimasu nasu zata iya A bangaren ABDUL kuwa wata irin shakuwa ce ta shiga tsakaninsa da Biyu, a yanzu haka a cikin tractation din cenza masu makaranta yake , ama bai sanar mata ba, domin makarantar tasu gaba daya bata yi masa ba, ba dan tana makarantar gwamnati ba, aa, dan matsalolin da ake fuskanta na irin bambance bambance karara ba tsawatarwa ya saka shi neman takardunsu da komai ya rubuta su a wata babar makaranta ta ƴaƴan manya, yanzu haka lesson da aka ce sai an masu na wata daya kafin su ci gaba da cen din ne ya dan dakattar da su, idan aka dauke su akan mikasu wajen lesson din ne da kayansu na makarantarsu a dawo da su gida, ko a wuce da su gidan gona su sha kiwo da Baba, ko a tafi da su Kampani a sake su, su sha yawo da ciye ciyen kwalam da makulashe ana dubansu ta camera ana gannin mouvement dinsu da komai ciki harda ma'aikaciyar da ta kirayi husaini barawo, sai dai ta ringa binsu da kallo bata da bakin magana, domin a lokacin da ya zo da su sakon da ya bada a fadawa duk wani mai ruwa da tsaki a wajen a matsayin mahaukaci cewa ya kula tikiten karshen shan ruwansa a kampanin ke yawo a kusa da shi, dalilin wannan suka zama yan gata a wajen ma'aikatan, da masu yi dan kar a kore su, da masu yi domin Allah ABDUL ya tatara du wani abu dake iya zamowa damuwa ya ajiye shi gefe, duda abin damuwar ya kula shigarsa ne yake yi da karfi da yaji koda baya so, ba wai shawararsa yake nema ba, a tsakakanin iyalinsa yakan ji bugun zuciya mai tsanani na yawo da shi Ya bata fili, ya bata damar da zata yi mu'amalarta da dan kai kawonta yadda take so, idan ya shiga sun hadu da farko takan daure fuska tamau ta nemi rurufe jikinta, shi kuwa sai ya yi mata murmushi ya kireta da AUNTYNA sannan ya tambayeta idan ta tashi lafiya? Hakan ke sakata rakashi da kallo har sai ta tuna wa ta bi da kallo sai ta cire dubanta tana tura lebenta da tunanin yanzu haka da yace mata Aunty ba har zuciyarsa ba.........sosai take so su zauna ta amshi takardarta, ama du idan ya shigo sai ta ji bara dai gobe ta masa zancen har ta cike kwana biyar cif a matsayin mace cikakiyarta a karkashin ikonsa ya zamto yai zata fara gyare gyarenta bayan ta dan yawata a gidan da yamaci tare da Baba sun samu wajen da ya dace ace ta fara din Baba Ta fuskanceta ta ce" AMINA ya dace ki ga ABDUL RA'UF ki sanar masa da maganar nemanki, kafin ki fara, domin yanada yancin sani a yanzu da yake mijinki......" Wannan magana ta tsaye mata a kahon zuci har yanzu da take kan murjewa Asma'u gyaran da ta yi mata tana tunawa Sunma gamawa ta rako Asma'u har bakin get, daidai an wangale get din motoci har biyar suka shigo Daga ita har Asmaun raka motocin suka yi da ido har suka kulewa ganninsu , Asma'u ta gyada kai tana yi mata salama ta tafi A sanyaye Amina ke nufar Bangarenta ba tare da ta kalli kowa ba A hankali tafiyar taya ta fara yin nauyi sakamakon jin kamar ana kallonta Da dabara ta dago dubanta ta sauke a wajen da ta fi kyautata zaton a nan ne ake kallon nata Tsaye yake kikam Hannayensa duka biyu zube cikin aljihun wandonsa yana kallonta da kallon da ya saka gaba daya ta tsargu da kanta A hankali ta cire idannuwanta daga kansa ta sake daga kafarta ta yi taku biyu ta ji ta kasa yin na uku, a dole ta sake dakatawa ta juyo gaba dayanta ta tsaya tana kallonsan itama Rabonsu da su yi irin kallon nan gaskiya har ta manta A hankali ta nufo inda yake tsayen, hakan ya saka shi dan sake waigawa dan gannin idan umarnin da ya ba garadansa sun tafin ko sunna nan, sannan ya sake zubawa Uman biyu ido har ta karaso inda yake tsaye ta ja ta tsaya tana harde hannayenta biyu a saman doguwar rigarta wace ta dan lafe kadan a jikinta ta dan bi shap din jikinta kadan ta matukar kayatar da halitar jikinta Kanta ta dan langwabe ciki ciki ta ce" Hi" Fuskarta ya zubawa ido da yadda ta yin, kamar in Husaini na son abu yake yin haka, Hasan dama shi halayansa kamar na wani baba ne A hankali ya dan matso kusa da ita, ta yadda sosai ya sake kerewa tsayinta yana kallonta cem ciki ya ce" Yanzu fa kin girma......ina hijab dinki?" Idannuwa ta wara, sai kuma ta kausasasu tana kallonsa ta ce" Me yasa idan kana yiwa manya magana baka tausasawa?" Murmushin gefen baki ya yi kadan ya zuba mata tsaurarun idannuwansa a kanta a hankali ya ce" Kin tabata kin warke?" Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi......, A hankali ta dan cire idannuwanta a cikin nasa kasa kasa ta ce" Hala murna kake ji dan ka ci zalina?" Kansa ya girgiza yana kallon yadda ta turo bakin ita a doke amsa take so Baki ta karra turowa tana kawar da kanta ta ce" Baba Lauratu ce tace nace maka wai, wai ina yin sana'ar gyaran amare, zasunna zuwa nan ina yi masu kafin mu tashi daga nan" Baki ya tabe ya ce" Tashi zamu yi daga nan din Aunty?" Har sai da ta kama habarta ta ce" Kai, harda kai kuma?" Ya dage kafadunsa irin ya sani?, Sai kuma ya ce" Ba damuwa, ama idan muka zauna na ji million nawa ake baki dan wahakar dukawa da darzar fatar wata?????, In ya min.....idan bai min ba gaskiya aaaaaa......." Idannuwanta ta kankance ta ce" ABDUL me kake nufi?" Sai da ya kausasa nasa idannuwan ya ce" Abinda kika ji AMINA" muhamadu rasululahi Sallallahu alaihi Wasallam, tana kallonsa har ya bacewa ganninta, gaba daya ya yi tafiyarsa, ita da za'a tambayeta waye fitsarare a cikin fitsararun zamani da ta fadi cewa ABDUL ne dan gidan Baba Mai Shanu walahi, idan ya kama sunnanta kirat har gabanta faduwa yake yi, inda dalili jama'a? Ana ce mata aunty da mutuncinta da komai ta zo zamanin da kannin bayanta zayana ce mata wai AMINA? AMINA fa? Ko su iyayenta ce mata suke mai sunnan Ina, dan mahaifinta har ya rasu ce mata yake yi Innata, shin shi ABDUL bai san sunnan Maman abansu ta ci bane hala? (Ah to....tambayeshi dai) Juyowa ta yi sai cika fuska take yi suka yi ido hudu da Risala dake tsaye wajen tagar bangarenta ta yaye tana kallon Aminar da wani mugun kallo tamkar zata kasheta da mari Kanta ta dauke ta tataka ta nufi bangarenta, sai ga Biyu an dawo da su sunna ta maganar result din da Hasan ya samu yau da malaminsu dake masu lesson ya masu exercise Da gudu Husaini ya kawowa uwar a lokacin da take bude bangarenta ya mika mata, sam basu lura da fitowar Risala da doso wajensu da ta yi yana fadin" MAMA, Mama albishirinki, dubi result din Hasan, dama Dady yace idan ya maida hankali zai siya mana tap da kuma babur irin na yara muna tukawa a gida , yau Dady sai ya yi dariya idan ya ga result din nan" "Wanene dadynku?" Risala ta fada da mamaki tana kallon Husaini yadda yake dira ya karra kiba fatarsa ta karra murjewa bul bul da shi sak irin ya'yan gayu Amina ta ninke takardar itama abinda ta so kwabarsa kennan da ya dage yana ihun yau dady kaza yau dady kaza ta kalli yarinyar nan da kallon basira bata ce komai ba a lokacin da Husaini ke fadin" Baki san dadynmu ba hala?, Ke din wacece wai?" Tambaya ce ya yi dan harga Allah bai santa ba, kuma ta fito ne irin a cikin gidansu, abu da yaro shi ai yanzu a tunaninsa ya fi kowa iko da fada a gidan nan tunda an fada masa cewa gidansu ne "Ni kake tambayar wacece ni?" Ta fada a zafafe tana ruruko masa ido, hakan ya tsoratar da shi da sauri ya labe a bayan mamansa yana lekota AMINA ta dubeta da kyau tana tunanin abunuwa da dama a ranta, abu daya ne ta sani a yanzu a wajen nan, shine, idan har yarinyar nan ta zo ne dan ta raina mata wayau zata dauko tsimingiya ta darwaye mata jiki tas har sai ta summa dan wahala, dan bata tunanin wannan yar ficikar y'ar zata iya rainata ta kyaleta A dake ta ce" A dake Amina ta ce" Am, lafiya?" RISALA ta dawo da dubanta kanta tana sake daure fuskar itama ta ce" Magana na zo mu yi, mu shiga daga ciki ko?" Har Amina ta zo kiyawa, sai ta tuna ai a cikin ba zata rasa bulala irin ta caza ba haka, dan haka ta janyo hannun Hasan dake tsaye yana jiran ko ta kwana ta fara tura su ciki fuskarta hade ta ce" Maza ku je ku yi wanka ganinan zuwa" Cikin suka wuce gaba dayansu yaren, ita kuma ta karasa wajen da soket take ta ciro cazar wayarta ta yi tsaye irin tsayuwar nan da kake yi idan zaka zane yaronka tana kallonta ta ce" Bismillah " Hannun nata ta bi da kallo, a ranta tana ayana Allah ubangiji ya sa ABDUL da ta gani ysaye yana kallonsu ya biyo bayansu ya tardo Amina da bulakar dukan nan, da ta ji dadi taa gode Allah da ya bata damar gala mata sharin da ABDUL zai saketa, dan ta tabata ba zai kyaleta ta masa aikin nan a gidansa Risala ta yi tsaye a saitin da zata iya gannin mai zuwa tana kallonta ta ce" Zuwa na yi mu yi magana a kan Mijina!" Amina dai tana kallonta bata tanka ba RISALA ta sake fadin" A kan mijina na zo mu yi magana......" " Wa fa kike magana a kansa?" Amina ta fada tana sake fuskantarta Risala ta ce " Wane kuwa da ya fi wanda kika san hanyar da kika bi kika aura, ABDUL nawa ne, mun yi soyaya da shi mai karfin da na kori duk wata yar iska ko wata mai tunanin ta isa, haka na juri wuya ko dadinsa, na yi ta dakon gannin aurena da shi, tabas kin ci galaba da kika same shi ta hanyar Waina, ama in sha Allah daga yanzu zan dawo da Abdul nawa ni kadai abina, domin bana tunanin zan iya rabashi da wata, ko budurwa bale ke, bana jin zan........." " Ki saurara haka!" Amina ta fada a kausashe tana warware hannunta dake nade Ta dubeta sama da kasa ta ce" Wama sunnanki plz?" Risala ta wani rike kugu tana jijiga ta ce" RISLA, RISLA" AMINA ta tabe baki ta sake dauko dubanta tun daga sama har kasa ta watsar ta ce" Ke kika san dadinsa, ke kika rayu da tsarin yadda zaki rayu da shi, ke yake gabanki!, In kin kula ba ni na roka ba, haka kuma da ina ra'ayin da na tabatar maku kwalelenki a kansa, domin yadda kika ga a ayo na fiki, to fa a shekarunma haka ne, haka kuma a iya tuku sitiyarin balagage!, Ki kama kanki ki juya ki barmin daki, domin idan kika yarda maganar batanci ta shiga tsakani RISALA kike ko? Walahi sai na wanke maki jiki da dukan da za'a kasa gane ki, dan ni ba saarkkkkkkkkkkkkkkkkkkkkk" Wani irin ihun yan bori da Risala ta saka sannan ta aniya ta maku a kasa ta sake kwala wani ihun tana fadin" Daga magana sai ki dake ni? Daga magana sai ki dakeni? Innalilahi na shiga uku jama'a wayo a ceceni............." Baki sake Amina ta tsaya da bulalarta a hannunta tana kallon Risala Ita abinda ta shiga tunani ko mahaukaciya ce, sai dai kafin ta gane hakan ta ga shigowar ABDUL RA'UF, hakan ya bata amsar tunaninta Da ido take ta kallon ikon Allah ABDUL ya nufi Risalar ya yi tsaye a kanta yana karra son fahimtar wai da gaske Amina zane Risala ne take yi? Amina wani irin abu ya tsaya mata a wuya ta nunota da bulalar ta ce" Ni zaki yiwa shari a kan abinda baya gabana?, Ni zaki yiwa karya har a falona?, Bara na zane kin sai ki yi mai dalili......." Kun san fa wanda bai iya munafurci ba baya iya boyewa, shi yasa Amina ta kasa daukan wasan Rislaa itama ta dana, sai kawai ta yi irin abin nan na mai fitowa kwado kwado ya fadi gaskiya ta fadi hakan harma ta nufi Inda Risalar take Hannunsa daya ya saka ya tareta sannan ya fuzge bulalar dake hannunta yana binta da kallon dake nuni ransa a matukar bace yake Sake tirzawa Amina ta yi da nufin sake dosar Risala da ta mike ta labe a bayansa tana kukan karya bilhaki ita Amina dukanta ta yi Sai dai bata kai ga isawa ba ta ji yaa yiwa hannunta wani riko daya tal a tsayen da yake yana kallon yadda take haki ita a dole sai ta daki Risala sannan ya janyota ta bayanta ta hadu da kirjinsa yana dan sasauta rikon da ya yi mata a wajen kunnenta dake fitar da kanshin nan mai saka zuciya nutsuwa ya ce" Ki nutsu mana aunty kar ki sa a maki fasarar cewa kina kishin ABDUL ne?" Kamar ya wanka mata mari haka ta farka daga zuciyar da ta dabeta ta dago tana kallon sajen fuskarsa da idannuwansa dake nunin ransa a bace yake Muryarta a cec ciki ta ce" Ama ai kai ka san ba haka bane ko?" Kallonta yake yi, komai nata sai lamarin yarinta ya bayana, du yadda ta so mazewa dan a ga girmanta sai ta shagalar da shi da abinda ke sanyaya zuciyarsa A hankali ya ce" Eh to, kin san daga aikinka ake fasaraka yanzu duniya" Amina ta wani turo baki kasa kasa ta ce" raina ni fa ta yi, wai kashedi take min, ni banma fara dukam nata ba ta fara wannan haukan fa ABDUL" ABDUL ya yi murmushi yana tare Rislaa dake son jin abinda suke fada ya kara rage amon muryarsa sosai ya ce" Gwara dai kar ki biyata ke ai baba ce ko?" Amina ta gyada kai Abdul ya ce" To kyaleta kawai kin ji?" Amina ta gyada kanta tana dan lumshe idannuwanta dan yadda yake maganar cen kasa sai ta nutsu koda zata iya jinsa A hankali Abdul ya zarro harshensa ya dan lashi gefen kunnenta da shi Zabura ta yi tana wartsakewa ta ja gaba kadan tana kai hannunta hadi da sosa kunnenta ta juya tana fadin" Kin ci Sa'a, gobema ki zo min nan ki gani, dilla malama yara kanana sai raini......" Su dukansu sunna kallon kofar da ta rufe ne a tsaitsaye, shi har ga Allah da tace yara kananan ne ta saka masa stop, in ya fahimta dai kamar matarsa ta janyo masa wajen uman biyu Ita kuma abinda take son fahimta shin maganar da ta yi ya gane mai take nufi ne ko menene ya cewa Aminar? A sanyaye tana dubansa ta ce" AR, dukana fa ta yi da bulalar nan" ABDUL ya dawo da dubansa a hankali kanta, samun kansa ya yi da dan tsura mata ido, sai kuma ya budi bakinsa ya ce" A haka kuke yawo a cikin gidan kema gardaye na yawo? Wai ko so kuke yi na fitar da ma'aikatan gidan nan ne na zuba maku mata ? Koda yake yanzun matanma sai mutun na kula kar a sakashi uku ........" Ya idasa yana nufar hanyar ficewa a dakin Amina Dan daga kafarta ta yi sai kawai ta yi luuuuuuuuuu ta tafi da karfi ta kifu a kasa Da sauri ya ja da tafiyar da yake yi ya juyo inda ta fadin Cikin sasarfa ya karaso wajen yana fadin" Subahanalah, Risala, Risala" Mace, du yadda ta so tafiyar da tsarin rayuwarta a sila na daukan alhaki ko cin galaba a wani abin sai dai idan bata saka kanta ba, shi yasa ko me take yi a yawaita yi mata nasiha, Adu'a, fada, da kuma uzuri Du yadda ya gane cewa harda shari a lamarin Rislaa faduwar nan da ta yi take rike numfashinta sai ya daga masa hankali Cike da damuwa ya nemi aboki kuma amininsa ya zo ya dubata harma ya banka mata allura ta dexa domin shi lamarin numfashi a yadda ka sarafashi ake ganninsa, haka masu ciwon huka idan ba a lokacin da ta tashi ba aka yi masu hoton wajen ba za'a taba gannin ciwon haka ba Bata da shi, batada dalilinsa ta ringa jan jumfashin tana hucin mai huka a dole aka yi mata allurar da ta hadasa mata rawar jiki da bugawar zuciya , domin haka take ko baka da lafiyar ne ana yi maka ita take hadasa maka haka a hankali kuma ta saki Dukka wannan azabar Risala ta ji ta gani ta dauka, zata iya jurewa in dai a kan Mijinta ne Du yadda ya so mayar da ita nata bangaren abin ya gagara, da sauran kwanan Amina daya Risala ta kwana a bangarensa, sai dai bai yarda wani abu ya shiga tsakaninsu ba, du irin yadda ta bale mabalin riga ta langwabe da gangan sai ya tashi ya bar mata dakin, domin ba zai taba bari yana cikin hayacinsa ya saka kansa a uku ba..............ita dai ta karra daukan hakuri dan ta san ai daga gobe komai ya kare ta kama aiki, a nan zata nunawa Amina menene kula da miji ________________________________ Washe gari, kusan karfe takwas da rabi Amina ta karasa bakin kofar dakinsa ta tsaya tana tunanin ta yadda zata iya bugawa A kadan ta dauki minti ashirin a nan, domin har zama ta yi ta rafka tagumi tana kallon dan rainin hankalin da ya hannata fita a gidan Tunanin da ta yi da sake duba message din cewa daga yau har zuwa kwana bakwai je kake da damar ajiye takardunka , ta kuma san cewa tanada gyare gyaren da zata yiwa takardun nata, ga kuma gyaran kulin wainar Baba domin gobe ne juma'a ya sakata yin safiya dan ta je ta gama komai da wuri ta dawo, ga yar uwarta da ta kwana a ranta, idan tana tune da irgen bai fi sati biyu ba Fido ta cike lokacin haihuwarta, a irgensu fa , domin ba asibiti ta je aka fada mata ba Sake mikewa ta yi ta kai hannunta a hankali ta shiga kwonkwasawa sannan ta dan dakata Sake saka hannun nata ta yi ta kuma kwonkwasawa sannan ta saka hannunta wajen abin budewar ta murda da fatan Allah ya sa ya tashi ta shiga da salama a bakinta Ido ta zuba a abinda ta samu tana kallo Da wani irin langwabewa Risala ta rigo hannunsa tana furta" Weshhhh baby ba zan iya zama ba ka bani a bakina plz" A hankali ya kamata da kyau ya zaunar da ita Risala ta karkatar da zamanta tana wani irin dantse lebe tamkar a kasanta ne take jin zafi A hankali Amina ta bi yannayin nata da kallo, ta samu kanta da sake zuba mata ido na yan dakiku sai kuma ta dawo da dubanta kan ABDUL dake tsaye yana kallonta, yar simple din makup din da ta yi ta fi komai shiga idannuwansa, abinda ba koda yaushe take yi ba shi yasa komai kankantarta idan ta yi takan yi kyau sosai A hankali ta bi shigar jikinsa da kallo, farar riga ta ciki irin ta maza fara kal kal ta lafe a ginanen jikinsa ta dan hau saman wandon dake jikinsa na yadi ruwan madara wanda har arzuzumin dake jiki ana ganni da kuma irin yannayi dai na tsarin hakitar gamjin namiji sannan ta hauda dubanta har zuwa lebensa mai ruwan na jarirai ta kai wajen hancinsa sannan ta sauke idannuwan nata tar a cikin nasa idannuwan suka yiwa junna kallon ido cikin ido A hankali ta janye ta juya tana manta kwata kwata abinda ya kawota dakin "Aminah".....ya furta a sanyaye yana kallon bayanta, tar saman bayanta dake cikin hijab har kasa ja, ama irin dinkin hijaban yan matan zamani hijab kamar doguwar riga jama'a ya bi ya lafe a jikin matar mutun? A hankali ta juyo tana sake kallonsa Sai a lokacin ta tuno abinda ya kawota dakin Ido ta dan lumshe a hankali ta ce" Dama, zan fita ne, wai sai yace ka saka dokar sai ka sanar masu idan wani zai fita a gidan.....gashi ina sauri inada muhinman abubuwan dake gabana" Har ta dire aya yana biye da hannunta na dama da take dan nunawa da shi tana dan wanawa da shi kadan kadan haka.........., Sannan ya sake zuba mata ido da yannayin da ta ajiye maganar tana sake kai dubanta wajen da Risala ta kara karkacewa tana furta" Baby....zafi nake ji......................" A hankali ya dauke dubansa bayan ya sake kallon Risala da tunanin hukar nata har hanna mata zama yake yi?, Ya sake duban Amina ya ce" Uman Biyu, ina da ina zaki je ne?" Amina ta kai hannunta gaban goshinta ta dan murza tana fadin " Zan je gyaran takarduna ne, sannan na biya wajen Baba" Zaunawa ya yi saman kujerar yana dauko kofin lipton din still yana binta da kasalalen duban nan ya ce A'a baza ki tafi ba Ku gafarceni dan Allah, abubuwa ne a kusa kusa hidimun biki Na gode sosai😍😍😍😍 A hankali Amina ta zubawa fuskarsa ido Daure fuskar da ya yi, da irin zaman da ya yi yana zuba lipton din a kofi mai dan girma ya zuba madara isashiya ya mikawa Risala yana fadin" take" Sai ta ji wani abu ya tsaya mata a wuyanta, A kan wani dalili zai ce mata wai ba zata fita ba kamar wani wanda yakeda hurumi a kan hakan? Ya zauna gaban yarinya shi ga jarababe sunna wani abu kamar basu san ciwon kansu ba zai hannata fita? A hankali ta ce" ABDUL" Abdul ya dago yana sauke mata kausasun idannuwansa a kanta A kausashe ya ce" Idan zaki zauna mu karya ne bismillah...., Idan ba wannan bane ki tafi dakinki kawai" Magana ce mai nauyi take son fada masa, magana ce mai masifar nauyi take son yayaba masa, sai dai kuretan da suka yi da ido daga shi har fitsarariyar matarsa sai ta ji ba zata fada ba Abu ya zo mata wuya ya yi mata katutu ta juya da sauro sauri dan bata so ta yi kuka a gaban kannenta ta jawa kanta raini ta fice a falon ta nufi nata dakin Tunda ta fita ya kura kofar ido na yan sekwani, sai kuma ya saki murmushi a ransa yana ayana' Na san yanzu itama wanda ya daure mata ya yi kirana ya ja min kashedi, oh ni ABDUL RA'UF da gidanka da iyalinka ana saka maka ido" "Baby bana iya sha da kaina" RISALA ta sake fadi tana hayewa jikinsa dan ta mantar da shi dan cenjin mood din da matarsa ta hadasa masa yanzu tana sake makalkaleshi cen ciki tana ayana' madallah, haka nake so har sai wahala ta isheki kin bar gidan da kanki, wai Ni za'a nunawa bariki ki zo da gardawan ya'ya wai su ringa kiran min miji Dady?, Ina ji ina gani ya ringa kulaki? Zaki yi bayani ne!' A nutse ABDUL ya dan tareta a jikinsa yana kallon fuskarta, Tun jiya ya gane take takenta, irin abubuwan da ta ringa yi masa ne ya saka shi a yau kasa ficewa da sasafen nan domin kusan tsirara ta fito a bayi tana ihun kyankyaso yan biraren mamanta sai sama da kasa suke, da yan duwawunta kamun cokali saia dan babarbabar suke abinsu......da kyar ya hanna kansa turmusheta a lokacin , ama a yanzu fitar nan da makociyar dakinsa ta yi tana sababar sababar ya sake motsa shi har kamar ya ci babu, domin irin harbawar da ake masa a cikin wandonsa tamkar za'a tsaga wandon ne a fito a samu abinci a koma barci A saman kujerar ya juye da ita gaba dayanta, ya zamto tana kasansa, shi kuma yana samanta Du irin yadda take amsarsa da romancing ya kasa jin abinda yake son ji a lokacin da ake ture shi ana masa ihu da fade faden magangannun ba'a son raini Murmushi ya yi yana tunano tsoron da ya gani karara tun a lokacin da ya daneta ta yi wuki wuki ido ya raina fata, baki ya fara mutuwa, aa dangane da Risala kuwa sai shanye girman idannuwanta take yi tana riko shi iya rikowa harma da kanta ta kai hannunta wata hajar ta shiga laluba da mulmula Gaba daya sai ya ji dokin abin ya fara sare masa Risala ba wai dan ta taba yi bane ko ta kware a harkar bane, irin abin nan ne na amaren zamani da ake koya masu wai iya kulawa da miji, ko su dadage su koyi abinsu a karance karancen da shekarunsu basu kai ba, su koyi jarabar da wata uwar macenma bata iya ba su zo sunna ta fama da shi har a ringa masu wani irin kallo bayan basu san abin ba Irin yadda take fitar masa da harshe, harma ta cire yar rigarta ya zamto yan berayenta a fili sun yi kiri kiri ta kawo hannunsa ta dora tana murzawa a hankali hadi da sake bankaro masa kirji da kokarin cire pant dinta ya saka shi dan dakatawa yana kallonta........................... Rashin sa'ar da ta takaa shine, shi dai ABDUL ba zai so ace yarinyar da ya dauko a matsayin budurwa ta zo masa da sabon salo irin wannan ba Gaba daya gwuiwarsa ta sage, jikinsa ya yi sanyi yake kallon yadda Risala ta rikice, ko wata rikakiyar macen ba zata iya yin haka ba Shi yasa ake cewa ki kasance mai kunya, ki rike kunyar nan domin ado ce, koda namijin irin masu son ki masu rawar disko ce tsirara ki bari idan an zama daya an zama jiki sai ki yi, ama a daren farko fisabililahi ki kamo abinda yake boyewa ki aniya laguda ai sai ki saka masa tsoronki a ransa Dagowa Risala ta yi jin shirun ya yi yawa, du a kokarinta na son nuna masa kauna tsantsa wace ta zarce iyawar kishiyarta ta saka idannuwanta cikin nasa , sannan ta hade bakinsu ta ci gaba da gurnaninta cen ciki tamkar zata hadiye masa harshe Ido ya rintse zuciyarsa na dokawa da karfi Shi ba haka ya faru da shi da Uman biyu ba Shi abinda ya faru tsakaninsu da Uman biyu har yanzu idan ya tuna shi kadai sai ya saki murmushi hadi da mahaukaciyar tsumamiyar mika, domin sai ya ji har tsigar jikinsa na tashi dan dadi da tsumuwa.........................., A lokacin da ya dora hannunta ta janye a zabure hadi da sallalami kuwa ji yake kamar ya mayar da abin kacete ya ringa kallo ba dare ba rana yana shan dariya, Da ta fara yi masa magiyar kar ya hudata kuwa har tsakiyar kokon ransa yana jin abin..........., Bai san me yasa ba har zumudin son ya ga ta so abin yake, sai gashi ana nuna masa ana son abin , bai wani debe shi ya dada shi da kasa ba Kasa kasa ya ce" Risala, bamu yi nafila ba fa....." Risala dake ji gaba daya jikinta ya dume da kaikayi ta kawo kansa kusa da mamanta da ya yi jajajir dan so take yi ya yi romancing dinta tamkar a film din india, kuma ya riketa kamar idan tana kallon americain film A hankali ta nufi bakinsa da shi tana fadin" Bb, plz sck me.............." "Ya salam" ya fada a hankali yana lisafin duka kaf yannayinta A hankali ya saka hannunsa ya janye dan guntun sket dinta, sannan ya ringa kallon tudun pant dinta shima ya janye shi a hankali yana kallon jikinta Cike da son sake birgeshi ta kwonta tanaa gyara yannayinta, domin akoy wani serie da take kallo, wanda yan matan rikaku ke irin kwonciyar nan namijin ya kafa bakinsa...................... Ta sha mafarkin ita ake yiwa Baban burinta ta samu haka, bale ta rike kanta ta bari ta ga haka ne daga Abdul dinta, ta ki yarda da namiji lalatace ko yar iskar macen da zata yi mata haka, ta yi hakuri du irin jarabar kalace kalacenta har ABDUL dinta ya yi mata, ta sani ne ta haukata shi da ta watsa masa kafafuwan nan Bata san eh lalle ta haukatashi ta wata sigar daban ba Du kallon da yake yi mata shi kadai ya san fasarar dake cikin zuciyarsa Abinda ya rage a jikinsa ya janye ya sauka kasa daga saman kujerar ya dora gwuiwayinsa a kasa sannan ya kamo kafafuwanta ya juyota gana dayanta ta yadda zai ji dadin fuskantarta Wajen da dan maiko maiko, ama du irin jagular da ya mata bai kai abinda ya lalubo a jikin Uman......a jikin Uman biyu ba. A hankali ya matsota sosai sannan ya riko lamarinsa yana sake kallon yadda ta shirya, ko me take jirama oho Saitata ya yi ya auna mata abinda take jira, ya auna mata abinda take masifa kansa, ya auna mata ABDUL dinsa, ya antaya a lokacin da bata san haka yake ba, ya nutse duda iyakarsa rabi a wajen da bata san haka zafin ya kai ba, domin idan tana taba kanta a gida ba haka take jin zafi ba, ya sake rike kugunta gannin ta dauke wuta hadi da son zaburowa daga kwoncen da take ya mayar da ita a hankali ya ce" Ki kula ba'a fara ba" Sai kuma ya sake turawa da dan karfi da dan mugunta domin har ga Allah shi wannan rawar kan kwata kwata bai masa ba! Ihu Risala ta saka tana sake son dagowa, sai dai ta makaro, du yadda ta so mayar da abin ba haka ta zata ba, ta makaro, bata san wa ke tare da ita ba, a tunaninta yadda zai yi maka magana a sanyin nan hakan take cenma, a tunaninta sai ta koya masa komai, a tunaninta ba zai iya da ita ba Sai gashi daga fara hakarta ta shiga sanarwa duniya komai Kuka take yi da ihu kamar yana kasheta, shi kuwa ya bata damar ramar da muryarta dan ta karra bambance aya da tsakuwa............ Haba, wannan rawar kai ta kayar masa da gaba ainun, ko ba komai ya san ta matsa da kale kalen abubuwan banza ne, uwa uba du yadda ya so ya samu satisfaction abu ya gagara, a dole ya sake bada hima dan samun nutsuwa, gaba daya ta gakabaitar da kanta da shi din kansa domin ta ki tsayawa sai hade kafa take tana ihun ta tuba kar ya kasheta Tabas RISALA ta ga haza Gaba daya sai da kalmar mai saka wando da arzunzumi ta fice mata a rai Kuma ko aummar ta ki zuwa idonta biyu kamar zata mutu komai ta gwada harda jan numfashi ama abin ya gagara Sai da ABDUL ya gama hora wajen da ba shine mai laifi ba sannan a jigace ya samu samun nutsuwa yana fitar da huci ya tsare jikinsa dan zafin da yake ji a ciki ya wuce misali Ihu Risala ke yi, a bayan ya dagatanma, ihun da yanzu sam bama ya fita da kyau Idannuwanta gam a runtse fadi take" Kuka ce min da dadi, Allah ya isaana tsakanina da ku, wayo Allahna bayana, wayo ya hadeni na shiga uku na lalace wayo ya hadeni" Ido kawai ya tsura mata, ko a yanzu sai ya ji bayan tausayinta ya fara wani tunani daban Gannin zai sake daukan lokaci tana masa wannan kururuwar ya mike, gashi sai a lokacin ya tuna a inda suke, duda abu ne mai wahalar gaske bako ya shigo kai tsaye ko ma'aikata in dai yana gidan, ama gudum bacin rana.....yarinyar ce take wani irin abu na gayata, gashi ya amsa gayatar kuma tana neman sakashi a uku Bayan ya fito daga wankan ya dauko wayarsa yana sake jiyo kukanta daga bayi da fadin ita bata iya wanka ba, kuma karya tabata kar ya kasheta ya kirawo mata mamanta Duba wayar ya yi, domin a tunaninsa zai tardo kura ne barkarai na wanda ya daurewa Uman biyu take abinda ta ga dama, sai ya ga ba kira ko daya a wayar, hakan ya saka shi tunanin ta yiwu a gaba ta kai karan, dan ya san fitar dai ba samun yinta zata yi ba, ya hanna hakan, in bama uman biyu da yarinta ba tana saka kaya a dame a jikinta haka ina take tunanin tafia? Ai yadda ta motsa yaro mai gani ya kasa motsawa tabas ya san zata motsa dubaj, ta yiwuma la'antacen dake dira mata kwadayin na hijabin nan yake, shi kam zai je da kansa yau bangaren hijaban Kampani da kansa ya duduba, shin haka suke kawo damamun hijabai ko dai Uman biyu ce a aune sosai? Murmushi ya yi ya saka kayansa ya sake komawa bayin dan ya kula wani aikin ne ya sake barowa kansa, ga bakin nan ba dai tonon asiri ba, indai yau akoy mutane a kusa kusa ya tabata sun ji komai da komai.......to shi ai abin ne ya fi karfinsa, shi ya zata ai wannan bamkare bankare da gayata ta san abin ne shi yasa ya bata isashe yadda zata koshi, da ya san karambanu ne irin na yan matan zamani da ya barta da halinta ya bita a hankali Amina, zaune take a falonta, ta cire hijabin dake jikinta , sannan ta cire riga da zanninta ta ba TV baya da wayarta yar latse tana jiran kiran Baba da tace mata tana gidan rasuwa zata yi kiranta, ta ci kuka har ta gode Allah An dauki lokaci kusan minti arba'in domin baba bata fito daga gidan rasuwar ba sai da yan rakiya suka dawo aka yi Adu'a sannnan ta fito ta sa aka saka mata kati a tata wayar itama ta samu guu ta zauna ta kwalawa Uwar biyu kira tana fadin" Na'am kina jina uman biyu?" Amina ta gyara zamanta ta sake fashewa da sabon kuka har tana murza idannuwanta A rikice Baba ta ce" Allah ka sadani da gannin manzo ba dan halayana ba, ke kuwa me ya faru haka ne? Me aka yi miki da zafi Amina kike kukan nan haka? Ina biyun me ya faru ne ke kike kuka?" Amina ta shiga magana har tana shasheka ta ce" Wai sai kace saarshi, sai kace wata y'arsa ko wata kanwarsa? Ni ? Ni Baba?" Baba kam bata gane komai ba, ama ko menene ta san ba zai wuce mutumen nata ba, dan haka ta ce" Me ya faru kina magana kina shan kwana" Amina ta ce" Yanzu fisabililahi, ya rasa wai wa zai ce zai yiwa tsakani da fita sai Ni?, An fada masa ni matar kulle ce? Ko mijin da zan yi zaman dindindin da shi ai ba maganar kulle bale shi?, Tsakani da Allah da Annabi ace wai ni Amina ya cewa ba'a zuwa? Yo ko biyu yanzu da suka girma ai yar shawara ce bake ni gotai gotai da ni?," Sai yanzu Baba ta gane inda maganar ta nufa, dan haka ta ce" ke in ba rashin ta ido ba ki fita ki je ina kuma bayan ko lafiyyar kirki bakida ita? Ina zaki je yau kwana bakwai da tarewa?" Amina ta ce" Kin ga, maganar jarabawar nan ne aka sake ba talakawa dama, to talakawa mana wa'inda nasu samu sun ajiye a kan lokaci ba, shine na so in yi gagawa in zo gidanki in amshi ajiyar na je na dauki takarduna a gida na je na gyara ma gyarawa na ajiye sannan na siyo kayan wainar Baba, shine wai ya wani ce wai ba'a zuwa, kuma kin ga har yanzu Asma'u fa bata zo ba, a jiya na ji yana cewa bai yarda da aikina ba in ba million ake bani ba, kin ga kar ya min abinda ba shikenan ba ina zaman zamana ya rabani da nemana ya sakeni in shiga uku, dan idan ya watsar min da customa ina zan saka kaina ga y'ayana?" 'bakinki ya sari danyen kashi, Allah ya kiyaye ya sakeki, shashasha!' shine abinda Baba ke ayanawa a ranta A fili kuwa ta ce" *NZL PAGE3️⃣8️⃣* A fili kuwa Baba ta ce" Kin ga dago, komai gide dan a hankali ne, kina jina , ki kwontar da hankalinki Allah na tuba ai shi namiji a hankali ake binsa ba wai a yi masa gatsau ba, kuma min ga ki kula da bakinki fa, ko zama na wuni daya ne tunda aka daura maki shi mijinki yake, kar shiririta ta saka ki aikata aikin zunubi mai girma fa Amina, nu yanzu ki sanar min inda takardun suke sai naje na bude na dauko, sannan maganar waina zan kai nikan da kaina na hado maki komai na kawo ai da kudi a wajena sai mu ga yadda za'a yi, shi miji ko shekara ashirin ka bashi idan ka yi wasa fa sai ka kone Amina kin ji?" Amina bata ce komai ba sai shasheka take yi Baba ta ce" Ko kin fafada masa magana ne?" Amina ta girgiza kanta ta ce" Aa ban masa ba a gaban yarinyar nan, ai da jiransa nake yi yana shigowa yiwa yara Adu'a kullun sai mu yita ta kare" "Kada, ki daina yiwa yaron nan haye walahi, kin ga ki fa kiyayi lamarin wanda Allah ya nada ja gabanki, ki kuyayi bakin nan naki da sin girman tsiya ke dai na fada maki" Amina ta sake turo baki sai maganarta take yi kasa kasa na jin haushi har suka yi salama da Baba ta mike ta nufi ciki dan ta tabata tunda Asma'u ta kai warhaka da wahala ta zo a yau, sosai take shake da haushin da bata san ko na menene ba, kiris take jira wani ya shiga harkarta ko waye ta yi masa abinda ba shikenan ba, domin ko abincin rana da aka kawo da ta bude ta ga kazi sunna nishi haka ta hau fadan cewa ta ga alama bakin cikin jikinta dan daidai ake yi a gidannan ko kuma an dauketa maiya nema oho, an wani dage ana kawo mata kaji ita ga wace bata saba ci ba ko? To a shafa mata lafiya da kazi ita malmala ta sani.......... Ta yi fadan kaji an kwashe an yo mata malmala ƴaƴanta sun dawo da magariba , sun sake komawa masalaci da abansu sun yi saklah sun dawo suka nufi wajen cin abinci dan sunna gama ci sai kwonciya, a lokacin ne kuma shimaa ya shigo dan baya so sai sun yi barci ya shigo domin irin lokacin yakan ji abubuwan da suka yi a wuni cikin hikima, da haka yake karra gane damuwar Hasan kuma yake kokarin kamanta yiwa tufkar hanci da Adu'a da komai, domin yaron a ransa yake cen ciki, ya fuskanci kwata kwata baya son harkar pression ne, duk wani abu da zai zamto damuwa a wajensa to fa rikitashi take yi, Hasan yanada ilimi fiye da tunanin mai karatu, wannan azalzalar ta amsar takardun jarabawar ke saka shi rikicewa, wani lokacin kuwa idan an daki wani yaron sai ya rikice , shi baya kuka ama kuma du abinda zai yi bafa daidai zai yishi ba Sunna zama Amina ta fito cikin shiga ta riga da sket ta nufo wajen cin abincin sai karra cika kumatunta take yi ita a dole ba wani raini da take so a yau, kwata kwatama ita kunya yaron nan ke bata , wai ace shi haka aikinsa? Lalle ta kwashi kunya daidai gwargwado! ( To wane aikin a ciki amine?) Cen wajen da ta ajiye kayan wainar Baba ta sake dubawa ta rufe da mayafi mai shara shara ta dawo wajen cin abincin dan zubar nata Budewa ta yi ta dauki plate da nufin zubawa sai jin muryar Husaini ta yi yana fadin" Kai, tuwo kuma?" Dan dakatawa ta yi ta dan kalle shi, sai kuma ta ci gana da zuba abincinta Hasan ya ce" Tuwo Mama?, Ina mu ina tuwo?" A zabure har gabanta na faduwa ta kai dubanta kan Hasan tana ajiye abin zuba miyar ta kama bakinta cike da madaukakin mamaki tanna kallonsa,sai kuma ta kalli tuwon ta sake kallonsa "Bakwa son tuwo ne Boys?" Ya furta kasa kasa sosai cike da basarwa yana dubansu Kusan hadewar baki suka yi daya na girgiza kansa, daya na fadin karara shi kam baya son tuwo A hankali ya dago kansa ya fara kure lebenta da kallo wanda aka tabe ga dukkan alamu tak ake jira a yi kowace wace ya ce" Aunty, bama son tuwo fa" Amina ta zuba masa ido na yaan sekwani, ta cire kai tana kyabtu taki cewa komai ta zuba nata ta zauna ta saka cokalintaa zata fara ci A hankali ya rike cokalin yana sake dubanta ya ce" Aunty mu bama son tuwo muka ce" Da haushi haushi Amina ta ce" Ka ga ka rabani da rikicin duniya, ka rabani da karyar ya'yan nan, ku yanzu in ba karya ba ina ku ina kib tuwo? Tuwon da a da sai mu neme shi mu rasa? Wai Hasan harda kai ko? Harda kai a karya ko?" Ido ya zuba mata har ta dasa aya tana hararar biyu, wa'inda suka nemi zuba tuwon su ci dan harga Allah su sun fadi ra'ayinsu ne dan sun ga ai yanzu akoy komai na abinci A hankali ya shigaa tunanin kalmar da ta fada ,cewa a da sai su nemi tuwon watarana su rasa a cikin zuciyarsa Murmushi ya yi kasa sosai ya ce" Aunty, ki yi hakuri tunda bama so a sama mana ko kunnu ne mu sha, nima bana iya hadiye tuwo fa nauyi yake min kin ji?" Abin al'ajabi da baya karewaa ta zubawa ido harda rafka tagumi tana kallonsu, sun mata tsuru ita suke kallo Abincinta ta ajiye ta mike tana mita ta shige kicin ta rufo sai mita take yi Murmushi Ya yi yana kallon Hasan da yace" Dady ka ga tunda tana so mu ci tuwon mu ci fa?" Sake yin murmushi ya yi ya rurufe tuwon da shima sam bai yi masa ba domin ya yi duhu sosai wama ya san ko na bak'ar dawa ne aka tuka mata, ya tabataa ita ta bukaci hakan, bai cewa yaren komai ba duda irin tarin tambayoyin dake cen kasan zuciyarsa dankame na shin ita kadai ta ciyar da su, ta shayar da su, ta kula da komai nasu? Shin ina dangin mahaifinsu suke ne ? Domin nata dangin ya san komai a kai............ Ama ya san ba maganar da zai yi daa yaren bane, dan haka sai ya share suka ci gaba da dan zantawa kan maganar karatu Abinda ta fi iyawa a wayewarta ta yi, watau makaroni ta dafo shapshao ta juyo masu a baban plat sai turiri take ta sha kayan lambu da kifin gwongwani , kana kallo sai ka hadiye yawu koda baka shirya ba ta ajiye masu a saman table sannan ta dauki tuwonta tana fadin" Allah na tuba tuwo ai zaune yake darrr , duma wanda ya wulakanta shi zai nemeshi ne , in dai tuwo ne, karma a ci mana masu sonsa ai da yawa......yaushema in ba karyar biyu ba" Su dai babu wanda ya tanka, hasalima ABDUL ke jujuya abincin hayakin na raguwa yana kuma sauraron habaicin da harda shi ake yiwa yana murmushi a cen kasan zuciyarsa Tsaf suka ci abincin suka gama ta kwashe komai ta kai kicin ta dawo ta idasa tatare wajen ta kimtsa a ranta tana tunanin yanzu yaya za'a yi da sauran tuwon nan mai yawa ne? Ta tabata za'a zubar ne fa ko mene? Har ta zo zata shige ciki ta ji ya kamo hannunta ya janyota baya , bata ankara ba ya zaunar da ita darr a saman cinyarsa A zabure ta mike tana ruruko ido ta ce" Kai" Hannunsa ya saka ya maidata saman cinyar tasa sannan ya saka hannayensa ya rungume bayanta ya hadeta da kirjinsa Marmar ta fara da ido gabanta na dan faduwa ta sake neman surmiyowa tana fadin" ABDUL wai menene haka ne ?, Ka cikani mana dan Allah nifa bana son abubuwan nan na rashin kunya da kyakyashewar ido haba dan Allah, ka tashi ka tafi wajen matarka kar yarana su manta wani abu su fito su ga wannan abin taba hankalin yaron" Murmushi ya yi yana sake zaunar da ita dandar a jikinsa cen kasa yace" Ita ai an tafi da ita gida batada lafiya fa" Amina ta yi shiru sai kuma ta juyo cike da son tsegumi ta ce" to me ya sameta ne?" ABDUL ya murmusa har sai da kumatunsa suka lotsa ya ki bata amsa sai idannuwanta da ya kafe da kallo A hankali ta cire dubanta tana sake som tashi "Ita maman biyu, i mn wace ta haife su inane gidanta ne? Yaya aka yi ban taba ganninta ba?" Ya fada cen kasa yana sake kai hancinsa yana sinsinar wuyanta dake kyali zuwa kirjinta da yake jin kamar ya warto shi da karfi ya ciro..................gaba daya wunin yau haka ya wuni cikin zaburar zuciya da tunani.....ya kasa ci gaba da sharetan har cikin ransa, ya gaza samun sukuni motsi kadan sai ya saki murmushi idan ya tuno wata diramarta, Risala na kiran gidansu da ya fita sallar azahar yana dawowa ya tardota cikin kukanta ya sake kamanta rarashinta , fir ta ki sauraronsa har aka zo daukanta daga gidansu, abinda ya bashi mamaki da haushi har ya shige ciki bai ce masu komai ba mamanta ce da kanta da kanwarta suka zo daukan Risalar, ana wani fuzge fuzge irin sun gano ya kwonta da yar ne, suka nuna da ita zasu tafi dan sun yi tunanin yanzu ya fara ratsa duniyar mace ne, a tunaninsu zai kwonta ya ringa magiyar kar su rabashi da duniyar maji dadi ne, sai suka ga ya masu fatan alkhairi ya shigewarsa, da haushi uwar ta tatara y'arta suka tafi da nufin sai ta yi jinya ta warke zata dawo, kamar a kanta aka fara kai bidurci gidan miji? Kamar ita ta fi kowa gata a duniya?, Watau su nasu iyayen sun rasu ko? Itace mai iyaye................... "Tana nan, tanada tsohon ciki ne bata iya fita" Amina ta fada muryarta na nuna damuwa ƙarara a cikin furucinta A hankali ya dubi fuskarta yana son karantar abinda ya fahimta a muryarta Amina ta saka idannuwanta cikin nasa ta ce" ABDUL, ina so na je na ganta ka ga kwana biyun nan sam bana barci ban yi mafarkinta ba...., ABDUL ni kadai takeda a duniya..... dan Allah kar ka zamto miki a rayuwata ta hanyar shiga tsakanina da y'ar uwata" Ashe ta iya tausasawa? Ashe tanada baban rauni bayan Biyu? Ya zata biyune kadai idan aka taba ake cin mata koda bata shirya ba, sai yanzu ya gane bayansu akoy watansu Murmushi ya yi yana sake kallon cikin idannuwanta da suka cika da kwalar son ta fashe da kuka, bakinta da ya tabe kamar na yar baby , fuskar gaba daya ta dauki kala na son yin rigima.......... A hankali ya samu kansa da rungumeta a jikinsa ya dora kanta a kafadarsa yana dan shafa bayanta Sun dauki lokaci a haka Amina ta ce" Zan tashi" Murmushi ya yi yana gyada kansa ya saketa ya bata dama ta tashi tana ta murje murjen da bai san ba shin Uman biyu wanka ne bata yi ba ko irin abin nan ne na yara idan wani abu na damunsu da zaka ga sun rikice da soshe soshe Dakinta ta nufa tana fadin" Sai an jima" Kai ya gyada yana kallon bayanta har ta bacewa ganninsa Mikewa ya yi a hankali ya nufi dakin yaren bayan yaa kashe komai ya rufo ya shige ya samu kamsa da kwonciya a tsakaninsu yana kallon fuskar Husaini yar kutub da ita yaron ya karra kiba mulmul A hankali ya ce" ko dai tanada wani da take so na tauyeta?"............ A hankali ya ce" Ko dai tanada wanda take so ne na tauyeta??????" Sai kuma ya samu kansa da faduwar gaban jin abinda ya fada din, bai san dalili ba A hankali ya juya a saman bed din yana lumshe idannuwansa hadi da sake neman barci Da asuba sunna dawowa daga masalaci tare da yaren ya rakasu dakinsu domin yana son komawa nasa bangaren ya ja carbi har rana ta fito Yana fitowa ya ringa jiyo kwaramniya kamar daga cikin kicin take fitowa A nutse ya nufi kicin din da tunanin waye da duku dukun safiya yake kwaramniyar nan? Gannin ba kowa a kicin din ama fes fes yake sai cokula dake zube nan ga dukkan alamu an cirosu ne, ya nufi hanyar da ya fi jiyo kwaramniyar domin ya ga kofar bayace a bude, dan haka a nutse ya fice sai ya ja ya tsaya yana kallon ikon Allah Amina ce ta sauka kasa ta duka sosai wajen itacen nan tana hurawa da bakinta domin wutar ta mutu ne kuma du abubuwan fifitar nan Amina ta fi gane hurawa da bakinta, ga wani daurin zani da ta yi a saman wata riga mai siririn hannu ruwan copee Hular kanta ce ta fadi , ta dakata ta dauka tana lalubar birke ta daidaita ta shiga kunnawa tana fadin" Kayan aiki du na nasaru, yanzu ace wannan abin mai ruwa a ciki ne zai bada wuta? To wai kananzir ne a ciki ko ruwan nasaru ne?, Shi yasama ya kasa hasa wutar gashi zubi daya tak na yi tunda duku dukun duhun asubahi kar safiya ta waye Baba ya yi jiran wainarsa ina nan ina gantali da itace!" A hankali ya jingina da jikin kofar ya harde hannayensa yana kallonta fuskarsa dauke da yannayin da shi kansa bai san ya kai cen ba Murmushi yake yiwa dukkan motsinta, ya shagala da kallonta, komai take yi sai ya daukeshi daban, ya bashi fasara daban, ya nemi waje daban ya ajiyeshi mai matukar girma da son daukaka lamarin a bayane, ita batama san yana wajen ba domin hayakin nan da aikinta ya fi komai daukan hankalinta Hayakin ne ya fara janyo hankalin ma'aikatan gidan masu kula da gidan, maza kennan, domin ko'ina shukoki ne, hayaki dai irin haka a gaskiya basa fatan gani domin ko shara ba konata ake yi a gidan ba bale ace hayakin shara ne, dole zasu duba su ga ta inda yake fitowa "Aminu, ka ga ka bi ta cen ni bara na bi ta nan mu yi gagawa mu ga ta inda hayakin yake fitowa, ka ga wannan hayaki haka ai ba lafiya ba" usman ya fada yana sakin hanyar ya nufo dayar hanyar, shi kuma Aminun ya nufo hanyar da Amina take Da dan sauri ABDUL ya fito ya ratsa ya wuceta ya nufo hanyar da ya tabata ta nan za'a bilo a tardo uman biyu ta bararaje tana buga tsugunon nan a haka ita ga mai tuyar waina Sai da ya wuce ta lura da shi Samun kanta ta yi da yin dogon wuya tana karra tabatarwa kanta shine, sai kuma ta koma ta dauki hijabinta ta saka ta dauko mafici tana fifita wutar , Allah ya taimaketa ta tashi ta ci gaba da suyarta hankali kwonce, kanshi kuwa ya gama gidan tuni, masu kaunar waina bakinsu ya gama rikicewa da hadiyar yawu Kusan zubewa ya yi a kasa dan gaisar da uban gidansa Yana dan dube dube ya ce" Sir dama hayaki ne muke ta gani shine muke neman wajen" ABDUL ya gyada kansa a nutse ya ce" Ni na hasa shi" Kai Aminu ya gyada ya mike yana mai yi masa fatan a yi sallar juma'a lafiya ABDUL ya dan yi gyaran murya yana fadin" Ji mana Aminu?" Aminu ya dawo ya sake dukawa Abdul ya ce" Kana ji, du ranar juma'a zakunna gannin hayakin nan, Uman biyu ke tuya, bana son gannin kowa a nan wajen ka fahimta?" Aminu ya amsa shi sosai sannan ya mike ya tafi Ajiyar zuciya ya sauke ya koma wajen da take tuyar yana kallon an saka hijabi ashe Karasawa ya yi wajen wani kyakyawan kwano mai rike zafi an rufe shi da wani farin tawul ya dan tsuguna ya bude yana ciro guda hadi da jujuyata sannan ya yi bismillah ya kai bakinsa ya gutsura yana taunawa a hankali, sai kuma ya saki jikinsa da taunawar domin ta masa dadi a bakin nasa Amina dake kallonsa kasa kasa ta ce" Baka tsoron kar aje na yi bade baden magani a ciki na asiri?" Kalonta ya yi da dan mamakinta Sai kuma ya yi murmushi yana idasa cinyewa ya ce" Uman biyu zan ci nima yau wainar, tai min dadi a bakina.....zaki bani?" Samun kanta ta yi da sada kanta dan wollah sai ta ga kamar maganar da bata so ce ya yi mata, kawai sai maganarsa ta zai sha ta fado mata a rai jama'a, Gaba daya tsigar jikinta sai da ta tashi, ta sake sada kanta tana dan bubuga tandar suyar dan gaba daya nema take ta rikice Mikewa ya yi ya shige ciki ya dauko plate ya dawo ya sake budewa ya zuba kwaya hudu sannan ya koma gefe ya zauna yana kallonta tana tuyar kanta a gefe sam bata so su hada ido Kunyarta na saka masa nishadi, bai san dalili ba Koda ya gama cin sai da ya ga ya matse mata waje ya hanna mata motsi yadda take so sannan ya mike yana fadin" ki fa shirya karfe goma mu ajiyeki gidan Fido kafin mu wuce wajen baba" Da sauri ta dago kanta tana kallonsa ta ce" Allah wai?" Turus ya yi ya juyo, dan har ya kusan shigewa ya tsaya yana kallonta, to wai hala so take ya ja rantsuwa da ta tsatsareshi da ido, hm Amina kennan yanzu idan wani abin ne ta iya bude baki tace ita babace Sharewa ya yi ya ce" Idan kika saka suturar dake lafe maki a jiki kuma sai dai mu yi tafiyarmu mu kadai" Dariya hadi da farin ciki suka hade mata tana fadin" aa aa, in sha Allah bama zan saka ba, wayo Allahna dadi yau zan ga fidona" Juyawa ya yi ya tafi dan ya koshi ainun so yake ya dan huta koda na awa daya ne kafin su fice gidan Baba su yi hirar safe sai su wuce masalaci tare Da zumudi ta gama tuyar ta zubawa masu aiki , ta zubewa baba sauran ta rufe ruf ta dora miyar da yake ci da ita ta wuce dakinta Tun a lokacin ta shiga shiryawa cike da zumudinta , yara kuwa sunna ji sunna gani barcin ya gagaresu domin kiri kiri mamansu ta hanna masu barci ta sakasu yin wanka ta ciro masu jalabiyoyi biyu iri daya da takalmansu ta koma falo tana ta aikin murmushi tana duba lokaci a wayarta Karfe goma ta gota ya shigo da salama a bakinsa yana dan kallon falon da mutanen ciki Zamanta ta gyara tana sake baza hijabin jikinta irin ya gani din nan bai matseta ba sannan tana washe bakinta da murmushin da sai ya rantse dai ba na Allah bane dan kawai yace zai fita da Uman biyu ne take washe masa baki har haka Ratsawa ya yi ya shige dakin biyu, suka rakashi da kallo baki dayansu Jim kadan ya dawo hannayensa rike da shadoji iri daya ya mimikawa kowane yana fadin" ku cenza kayan nan" Amsa suka yi , kowane ya nufi inda zai labe ya cenza suturarsa, Da kallo ya bisu ya juyo yana murmushi ya ce" Wai zuzuzu dinsu zasu boye miki" Ido Amina ta zarro ta juya da dan sauri tana nufar wajen table dan dauko kwanonin wainar nan a zuciyarta tana ayana' Sam ba kunya a lamarin ABDUL' Tana kawowa ta ajiye ya bi kwanonin da kallo ya gyada kansa ya ce" Kin san na kula yannayin tafiyarki ne yannayin nuna halitar jikinki, kawai ki daina tafiya da sauri sai bombom din su daina dancng......" "Kai jama'a" ta fada kasa kasa ta sake yin shiru, dan dai burinta ai su kaita inda zata je , bata so ta biye shi su yi wani fadan ya sake hanna mata fita Cikin motar suka shige, biyu a gaba su biyu, ita da shi a baya a zaune, sai sasada kai take yi tana tunanin idan aka ganta a make a wannan shareriyar motar ai ta gama siyawa kanta zunde da yagalgala, bama irin wa'inda suka nuna mata soyaya ta kiya, ai har ance dama kudi take so ba wani datijo ita kuma du wanda ya fasarata haka ya cuceta Allah ne zai saka mata A hankali yake jansu, sai da suka je anguwani uku sunna sauka da biyu da shi kadai da direba su shiga su fito sannan suka dauki hanyar gidan Fido tana kwatanta masa yana fadawa direban kamar wani wanda aka saka dole sai shi zai fadawa direban har suka iso kofar tsakuraren gidan Fido din direban na tuki a guje kamar zai tashi sama, ta kula da direban da ABDUL din du kamar yan daba Walahi Ido ya zubawa kofar yana kallo, sai kuma ya dubeta ya ga tana washe baki ta kama kofar ta bale ta fita harda yi masu byby abinta ta tsalaka kwatar ta nufi soron kofar gidan Basu tashi ba domin a tunaninsa zata dawo ta yi masa iso ne su gaisa da kanwar tata, haka kuma a tunaninsa ai biyu zasu sauka su gaisar da mahaifiyarsu, sai ya ga basu motsa daga inda suke zaune ba Da kulla ya ce" Boys ku je mana" Husaini ya juyo ya kalle shi, sai ya juya yana girgiza kansa ya ce" Dady ai bama shiga, idan muka shiga mijin Aunty ke dukanmu , itama ya doketa, yace maza basa shiga gidansa wai" Daga Abdul din har direban a zabure suka kalle shi, Abdul ya sake fuskantarsa da kyau ya ce" Husaini, ba nan ne gidan mamanku ba?" Husaini ya kalli Hasan, Hasan ya kalle shi, Hasan ya juyo yana kallon ABDUL ya ce" Dady gidan kanwar mamanmu dai ko? Gidan aunty ne nan, mu mamanmu ba a gidanmu sabo bane kace gidanta cen ne gidanta ko?" Sai yanzu ya tuna wa suke duba uwa a duniya Sai ya ji haka kawai ya kasa bada umarnin su tafi Haka kawai ya ji yana so Uman biyu ta fito su tafi gida kafarsa kafarta, bai san dalili ba sai ya ji gaba daya hankalinsa na kan gidan A hankali ya bude bangaren da yake ya fito ya tsalaka wajen mazan dake zaune sun zubawa motar ido tsuru sunna kallo Hannu ya basu suka ringa gaisawa da kula sosai sannan ya nemi waje ya zauna a kan bancin da aka marmatsa masa ana yi masa bismillah mana Habu mai teburin ya ce" Malan bako ne ba? Sai na ga kamar gidan Mudi kuka sauka?" ABDUL ya yi murmushi yana gyada kansa ya ce" Eh, na kawo madame ne ta ga kanwarta, inaga matar gidan itace kanwar tata" Saley ya sauke ajiyar zuciya yana fadin" Alhamdulilah, dama yanzu muka gama maganar yarinyar, muna yi mata ADU'A, muna fatan Allah ya amsa, ace yarinya a kan gwuiwa yau kwana biyu tana fama ama ya ki a mikata asibiti? Yanzu da kai ya waye Allah na tuba ai ba'a haihuwar gida, mata na wahala ana kallonsu har sai sun lalace a yi watsi da su, ko idan abu ya zo a mace ko su su mace sai kaji ana fadin lokaci ya yi, eh Akoy maganar lokaci,wanda idan ya yi ba tsumi ba dabara, ko a ina kake ko a karkashin kulawar wa kake zaka tafi ne, ama kuma akoy mugun hali na wasu mazan,Allah na tuba wannan asibiti ta gwamnati da yan kudaden da zaka kashe basu taka kara sun karya ba kake yiwa macen bakin ciki?" Audu ya ce" Kai fa saley kanada matsala, aishi wannan mutumen bama maganar kudin bane inaga, wannan bakin hali nasa sam bai masa rana ba, wai sai ace maza sunnada kishi basa so namiji ya bude masu mace ya amshi haihuwarta, ni fa nan da ka ganni da innar baban gida ta jigata gwara namijin ya amshi haihuwar tata, to Allah na tuba lafiyarta ai ta fi min komai a duniya" Saley ya amshe da fadin" Kai kace, bale yanzu fa mata ke amsar haihuwar nan,mata ilimi suke yi sun amshe abin fa, maza kuwa su duba maza yan uwansu, dama in ba mai laluwai a hannu ba ina kai namiji kato ina karatun feraye matar wani? In ba so kake yi ka ringa shiga hurumin da ba naka ba" "Ku dai kun shiga uku da bakinku walahi, kun ga sai maganar nan kuke tunda safe matayenku sun zigo ku kun zubawa kofarsa ido kun kasa aikata komai sai saka da warwara kuke yi, inace yanzu na gama maganar mu kai kara wajen mai gari a fitar da yarinyar cen a kaita asibiti kuka nuna aa aa wannan ba huruminku bane, sai da mutun ya zauna zaku saki baki kunna cakalkalarsa, idanfa dan uwansa ne?" Mubashir ya fada da dan fada fada, domin tunda safiyar juma'ar nan ta waye suke kan maganar nan, ama da Mudin ya fito siyan garin kwakin ashirin hannu hannu suka ringa bashi sunna gaisawa shi kuwa yana wani cire kai kamar wani tsiya, wai shi baya shiga hurumin yan anguwa baya son tsegumi, wani tsegumin kuma, na nawa? Shi kulun kamar zai hadiyi zuciya dan bacin rai Audu ya kama baki yana yar dariya da jan hakorinsa a bakinsa ya ce" Karan uwan nana kaya, gacin uwanan kayasa, ai da mun shiga uku, to ama ai da wahala a dangin Mudi a samu mai fara'ar wanann, Elhaji ko ba haka ba?" ABDUL da komai suke fada ke karra dan tunzura jinnin jikinsa , da kara fahimtar wa kanwar matarsa ke aure, da son shiga gidan kai tsaye ke karra shigarsa ya rafka tagumi yana kallonsu har suka dasa Aya ya mike ya yi masu salama ya tsalako ya shiga kai kawo yana duban kofar yana tunanin ba zai iya motsawa ba sai ya ji daga bakin Uman biyu A cikin gidan fido Rungume Amina take da Firdausi tana magana hankalinta tashe tana fadin" Tun yaushe kike yashe a tsakar gidan nan haka Fido? Ina makotanki? Fido ina Mudi yake?" Firdausi dake numfashi da kyar tana sake rike hannun yayarta muryarta cen ciki ta ce" Aunty, wayo Allahna Aunty mutuwa zan yi, Aunty mutuwa zan yi , bana iyawa na gajiya Aunty, dan Allah ki yafe min zan tafi nima na barki da nauyi a kanki Auntyna" A zabure Amina ta mika hannunta jikin kofar dakin ta shiga bugawa da wani irin karfi tana fadin" Kai Mudi? Mudi? Mudi? Ga takalmanka nan kana jina ga takalmanka nan ka fito Mudi kana jina?" Wani wawan tsaki ya ja ya taso daga kwoncen da yake yana son yin barci, domin daren nan kwana ta yi tana hailala da kiran Allah shi du ya zatama ba zata waye ba a irin yadda take haukan nan, ta saka makota sai binsa da kallo suke matayensu yan saka ido sun kai masu gulmar gidansa ko? To baki daya daidai yake da uban kowa, inda ubanda ya isa dan Allah ya fito ya fitar da Firdausi daga gidan nan ya gani! Iskancin banza iskancin wofi yanzu yayarta ta zo shine zata wani langwabe ita ga kwalba sarkin shari ko? To ya fisu iya iskanci, wa suke da shi da ya tsaya masu a duniya? Wai wani Amina ta yi aure ta auri mai kudi, ai ko kudin ta aura yana nan a yadda yake zata dawo ne zaman anguwar yana jiranta! Da tataciyar fuskar rashin mutunci ya bankade labulen tsuman atampa roba robar dake kare kofar ya fito yana jan ido ya kalli Amina ya ce" Mudi Ya fito yana jan ido ya kalli Amina ya ce" Gani,menene da kira haka kamar na bar duniyar?" Amina ta yi masa kallon ka ji kaina, ta yi masa kallon tarin tarwatsewar da zuciyarta ke neman yi, wanda ya sakashi faduwar gaba da tsurata mata ido tamkar zai hadiyeta danya, muryarta na rawa ta ce" Ka dubi Allah, ka dubi girman Allah ka bani dama na fita da ita asibiti, duba ka ga halin da take ciki? Ka tausaya mana ka barmin ita na sadata da asibiti ka ji? Walahi na rantse maka ba zan bari namiji ya duba maka ita ba, kuma ko kwabo ba zan nema na maganinta ko abinda zata haifa ba, dan Allah yaya Mudi ka min rai ka barni na kai kanwata asibiti........" Ta idasa tana hade hannayenta da ta shafo ruwan da Firdausi ke zubarwa jikinta sai rawa yake tana malolowa tamkar tana fitar rai, Da mamaki ya rike habarsa ya ce" Yau nine yayan? Yau zan yi maki rana ko Amina? Nine zaki kalla ki kiraya da yaya? Ai ki ci gaba da raininki da salon wulakancinki, kema sai na haramta maki shigowa gidana in ga ta tsiya da karyar zumuncin munafurci, kin ga ba inda za'a kaimin matata, a barta a nan idan lokacinta ne ya yi ai haka Allah ya nufa ko akoy dan iskan likitan da zai hannata mutuwa ne?" Amina ta ringa kallonsa hawaye wani na korar wani Wani irin nishi da Firdausi ta yi ta kakafe gaba dayanta ya saka Amina fashewa da matsanancin kuka ta mike tana ajiye Firdausi gefe ta yi waje da gudu tana ihun a taimaketa Idannuwansu ne suka sarke, dama gaba daya hankalinsa ba wani a jikinsa yake ba yana kai kawo Kafa daya ya daga zai nufeta sai gata ta rigayeshi zuwa Tana zuwa ta fada jikinsa ta rukunkume shi tana sakin wani kukan muryarta a hade, a cakule tana fadin" Wai ba za'a kaita asibiti ba, nakuda take yi ABDUL, wayo Allahna ABDUL ka taimakeni, ita kadai ta rage min, ita kadai nakeda ita ABDUL " Biyu har rige rigen fitowa daga cikin motar suke domin tun fitowarta da ihun kukanta suka saki wayar direba Muhamat da suke buga game da ita sunna kallon mamansu hankali tashe Da kyar ya iya bambareta a jikinsa yana kallonta ya ce" Amina, ki nutsu mana Amina, me yasa ba za'a kaita asibiti ba? A ina take?" Zuwa lokacin mazan dake tsalake su sun tsalako, haka mata na anguwa dake kusa du sun garzayo da yara, duda Amina na rukunkume ne a jikin ABDUL a yau ba wannan suke ganni ba, rashin mutuncin Mudi da son kashe baiwat Allahn yarinyar dake tare da shi ya fi komai bakanta masu, yaren ne dai ke zarro ido gannin baba da baba sun kama junna namiji da mace kuma, abin mamaki (🧐) Amina ta yarfar da hannunta tana fadin" ABDUL, wai ba za'a kaita asibiti ba ABDUL, wai ya haramta mata zuwa asibiti da aurensa a kanta ABDUL, shin ya halata irin wannan abin kuwa ABDUL? ABDUL cewa ta yi wai mutuwa zata yi, Abdul da hannuna na rufe idannuwan Mamanmu, ba zan iya rufe na Firdausi ba tare da zuciyata ta buga ba Astghfrullah Abdul, dan Allah ka taimakeni ABDUL" "Shuiiiiiiit, ya isa haka, ya isa....." Ya fada a hankali yana kallon kofar da hangen kamar mutun ne a tsaye yana hangensu Biyu ya kama ya umarcesu kan su koma mota, sannan ya kama hannunta suka nufi gidan kansa tsaye , ba ko dar bale dari dari ko wani dan tsaye tsaye, jama'a kuwa suka nemi mara masa baya Shi ya fara saka kansa zauren da salama a bakinsa ciki ciki yana janye da hannunta Summa ne kadai Mudi bai yi ba a lokacin da ya ga mutumen dake rike da hannun Amina Wannan shine mai kampanin da ya je neman aikin share share da gyaran filin wasan yara aka ce masa ya je ya yi jira idan an tashi kara ma'aikata a duba a ga cencentar wanda ya cencenta idan yanada rabo za'a neme shi Wannan shine ABDUL RA'UF fa? Ko menene? Meye hadinsa da Amina? Hannu ABDUL RA'UF ya mika masa ya sake yi masa salama Kukan da Amina ke yi ya saka ABDUL RA'UF katse masa tasa salamar da ya kwasa wata doguwat salama yana fadin" Idan ba damuwa zamu je asibiti da ita" Mudi ya wani gyara tsayuwa, halin wulakanci na bibiyarsa ya ce" Ai damuwar Elhaji mu a gidanmu har rantsuwa muke yiwa babanmu cewa matanmu ba su ba asibitin nan ta yahudawa, idan kuwa suka taka suka je a bakin aurensu" ABDUL Ya sake fuskantarsa ya ce" Kana dai nufin idan har muka fita da ita zuwa asibiti ka saketa kennan?" Mudi ya wani gyada kai shi ga azalumin karshen zamani, mace na kwonce a halin summa ciki na mata wani iri har ya daina motsi ama ya kafe kan akidar da bashida ilimi a cikinta dan tsabar duhun kai, da kafiya irin ta jahilci yana sake maimaita eh a kan bakansa yake Ran ABDUL ya baci, bacewa irin mai tsananin nan, bai taba gannin marar tausayi da imani irin mutumen nan ba Fita ya yi da wani irin sauri Jim kadan ya dawo da litafi da takarda fara a samansa da byro ya mika masa yana fadin" Tabatar min da sheda,, dan samun ingantacen zawarci in sha Allah" Ido Mudi ya wara a kansa, yana kallon takardar a hannun ABDUL, uwa uba yadda ABDUL din ya kere tsayinsa da cika fiye da shi, kana gannin Abdul ka ha rikaken dan dambe! sai ga direbansa da ya biyo baya, jikeken kato maji karfi wanda a da ya yi zaman yin fashi da makami , sanadiyar ABDUL din ya shiryu ya dawo yi masa aiki, shine direbansa ko tafiyar mota ta barin gari ne shi ke jansa, sunna tafe sunna shan hira kamar ba mai gida da yaron gidansa ba, ko salama bai yi ba ya dubi Mai gidansa yana fadin" Sir yaya dai, ta cije ne na kwonceta?".....da irin muryar nan ta dabamci, domin sai da ya matsar da jama'ar bakin kofar gidan ya ja masu kashen ba kyau leke sannan ya shigo ABDUL ya girgiza kai yana duban Mudi da ya shiga zazaro ido ya shiga fadin" Aa, yaya haka a shigo min gida da karti fisabililahi bayan matata a yashe jiki a waje ? To wai da kake cewa na saketama a matsayinka na wa zaka iya amsar sakinta ne? Ina cewa ko daurin aurenta liman din anguwa ya bani tsabar batada da dangi bale kuma wai wani kato ya sakani sakinta?" Ido Muhamat direban ABDUL ya zarro ya ce" Kai rasa kunya ne kai hala?, Dadi kasheni zan daki yaro yau, kai wannan din ai babanta ne, mijin hajia ne fa, miji kuwa Allah na tuba ai uba ne kau?" ABDUL ya taka ya karasa gabansa, a kausashe ya ce" Ka san Allah, idan ka yi mana rashin da'a a nan sai mun gwada maka danyen kai sannan mu barka a kwonce, da kake fadin wanene dinta, nine jigon yayarta, hakan ya bani damar zama uba a gareta;" ABDUL ya sake duban yadda Amina ke kife a kan Firdausi ya dafe goshinsa ya ci gaba da fadin" Baka sani bane a sakefa take tunda na sani ne abinda zai hannani sadata da asibiti daga nan raina ya bar gangar jikina, KE UMAN BIYU KI RUFEN BAKI KE KUWA!" Ya daka tsawa yana kallon wajenta dan walahi sai wani katse masa fada take yi yana kora jawabi , Ya dora da fadin" Irinku sam baku cencenci auren mace ko wace iri bace, domin baku da da'a da kunya da adini, kuma rakakun da ake yi ana kyaleku ne ke baku kwarin gwuiwa, kunna fakewa da ku masu adini ne kunna cutar yayan mutane dake karkashinku, .....bara ka ga karshen gardi ya shigo maka gida" Yana gama fada ya karasa inda Amina take ya kamata ya mikar da ita ya nuna mata hanyar fita a hankali ya ce" Yi shiru mana kema haba uman biyu, jeki mota ganinan" Ta so jan maganar, sai dai gannin ABDUL din du ya rikide kamar ba shi ba sai huci yake yi ya sakata juyawa ta fita da sauri tana karra rufe bakinta da hanna kanta sake fashewa da kukan tana ambaton sunnan kanwarta da fadin Allah ya bata lafiya Dukawa ABDUL ya yi ya cicibi Firdausi dake da mugun nauyi ga na ciki ga na sakewar jiki , ko hijabinta ba'a saka mata ba ya juya ya nufi fita da ita a hannunsa fuskar nan a hade Da garaje Mudi ya nufo shi yana ihun fadin a ajiye masa matarsa, walahi idan aka fita nan kofa da ita ya saketa saki uku! Dau Muhamat ya daukeshi da wani bahagumen mari a kan kunnensa wanda ya bada wani sauti *GAB* dan karkacewar amonsa da zazafan sautinsa sannan ya saka kafarsa daya ya shure shi yana nanade hannayen rigarsa ya ce" Kai baba, baka yardaba kennan da Sir yace zamu iya kasara maka jiki, kai in ba rashin kunya ba maza suka ce maka ubanta ke magana ai sai ka saurara, haba elhaji kai har namiji ne kana wulakanta gidan hutunka kana wani hobara kamar jaki? A waje ake dawa, a cikin gida kai nama ne yaro, domin idan ba su ba mu, ko kana iya take mai jela irinka dan uwanka ne bamu sani? Shege arne mai bakin ido ka wani furta saki shashasha to Allah ya tashi kafadunta ta sha madara ta murje ka zo kama kukan jini !" Ya karashe da babar muryarsa yana hararan Mudi dake kasa yana ihun an cire masa kunne, a fasa masa keya Muhamat ya ce" Kai daina yin ihu mana kar na kwashe maka hakora oga na kusa baya son hayaniya walahi, shege sauran daba kai nan har mafarauci ne? Ai ko daba bama son sakarai irinka wawa dillah! Kai dana irin tawa matar ka samu wa bilahilazi kana daga hannu ta fara sharara maka marin kuma ba inda zaka kaita sai hakuri" Labulen dakin ya bude dan a sanninsa ai da kayan haihuwa ake zuwa asibiti, sai dai gannin ba komai sai wani yankwamamen gado da abin shinfida a yakune ya saki labulen yana kara kallon dan tsakuraran gidan ya yi daria ya ce" Shege wai ba'a shigo masa gidansa, maza basa shigowa, akurkinka dai, dama yan iskan sun fi samun salihan bayi.......ka tashi ka yi wanka ka nemi na dare domin ka shiga uku ka saki y'ar Elhaji Wawa marar rabo!" Mudi na ji yana ganni ya yi kittt da bakinsa har sai da Muhamat ya bar gidan sannan ya fashe da kukan dake cen cikin zuciyarsa mai dacin da ya jima yana yawo da shi a duniyarsa Yayi nadama, ya yi dana sani fiye da a irga, da farko abinda ya so dauka yana zuwa ya cenza ra'ayi da ya ga fara, ya dauko farar ya gaza samun abinda yake so domin in dai bak'ar ta gilma ta gabansa to fa sai ya ji kamar zai fada mata, ya dawo ya saka kansa da kansa a ukuba bake wace suke tare, tun ba'a je ko'ina ba yana fatan ta mace ya dauki yar uwar su rayu abinsu ta dauki wani ciki, haka kuma du irin galazawa cikin bai karta ba saima karra kwari take yi, yanzu an wayi gari wai ta yi aure....aure? Ko uban wa take aure sai ta dawo hannunsa, fatansa fitar da aka yi da uwar nacin nan daga motar nan sai kabari!, Idan dai Fido ta kauce komai zai zo masa da sauki! ( 🤔 Na fara tsantsamta a kanka mahaukacin kare!) Asibitin su Mansur aka wuce da ita direct Sunna zuwa aka dorata saman gado na turi aka gurgurata aka wuce dakin emergency da ita Biyu sun ci kuka suma har sun gode Allah domin mamansu kuka take yi ba ji ba gani Muhamat ne ya bude ya fita da su balbalin asibitin yana kwontar masu da hankali da salon iya kwontar da hankakinsa ABDUL dake zaune shadar jikinsa ta jike hannunsa rike da hannun Amina da ta bude ta so fita ya dawo da ita ya rufe yana kallonta tana kukanta ya kai dubansa wajen da Mansur ya zo rike da sabon file din da aka bude mata dan batada komai na gannin likita ya tsaya yana fuskantarsu ya ce" Cikinta nada matsala ne tun daukansa, gashi ba'a je asibiti ba, ba'a yi awo ba, ba'a yi allurori ba, bale likitoci su fuskanci matsalar cikin su tura su gannin baban likita, yanzu dai mun fara farfadota domin summa ne ta yi, matsalar abin cikin ne babu, kuma biyu ne....dole zamu yi mata aiki domin ba zata iya haifowa da kanta ba ta jigata sosai ba zata iya jure haihuwa da kanta ba" "Wayo Allahna, innalilahi wa inna ilaihi rajune na shiga uku, biyu ne kuma babu? Wayo Allahna fidona aiki?" ABDUL ya dubeta yadda du ta zama wata irin akoke , sam ta ki saurarawa sai kuka take sha abinta, ya maida dubansa kan Mansur ya amshi file din yana dudubawa, sannan ya bashi ya ce" A yi dukkan abinda ya dace Allah ya fitar da ita Lafiya " "Wayo ABDUL zan je na ganta" Amina ta fada tana sake fadawa jikinsa ta rukunkume shi tana barkewa da wani sabon kukan "Ya Allah" ya furta, bai taba gannin mutun mai kukan uman biyu ba, a kusa kusan nan ko daya A hankali ya dago fuskarta yana tsurawa cikin idannuwanta ido, hannayenta ya samu kansa da kamowa ya rike yana duban irin kallon kurular nan Amina na cikin kuka ta ji hannunsa a cikin hijabinta ya saka cikin rigarta ya hauda cen wajen mamanta a hankali ya dan matsa, hakan ya sakata dauke kukanta tana yi masa kallo mai kama da harara ta ce" Meye haka mutane na cikin halin kaka naka yi kana taba masu nono?" Sai da ta fadi nonon ta rintse ido, ita kam wannan yaro me yake son mayar da bakinta ne? A hankali ya ce" Au, hakane kuma, Sorry uman biyu, ki yi shiru mana kema idan kina kukan ni du sai na ji kamar haka kike so na yi maki mana shi yasa na yi" Kin yin magana ta yi ta kwontar da kanta a saman cinyarsa tana ta jan numfashi kuka na zo mata tana rike shi, dan ta kula kamar da gaske fa yake kau? A hankali ya jinginar da bayansa ya kai hannunsa wajen hancinsa yana jin yadda zuciyarsa ke neman tarwatsewa da madaukakin abinda ya shigeta yanzu yanzu na abinda yake hasashe A hankali ya kai hannunsa daga bayanta har zuwa wajen cikinta ya dora a hankali ya dan shafa a cikin zuciyarsa ya ayana ' YA ALLAH, Ya Arahaman, Ya rahim, ya razak......hasahena ne ko gaskiyar lamarin kennan?' "Idan ta mutu fa?, Ance mutuwa ake yi a dakin tiyata" Ta fada muryarta na rawa tana dagowa ta dube shi A hankali ya saka hannunsa ya mayar da madubin motar mai duhun haske sannan ya janyota jikinsa gaba dayanta ya hade bakinsa da nata ya lumshe idannuwansa ya shiga kissing dinta a hankali yana lailayar lebenta da sake talabar kumatunta a hankali yana sake tarota jikinsa domin so take yi ta zile masa sai ruruko ido take ta gaza tsayawa waje daya a tsorace take sai wuwulga ido take yi kar aje ana kallonsu har ya samu ya cire mata hijabinta gaba daya ya kwontar da ita saman cinyarsa ya ja zif din rigarta daga baya ya sasauta rigar yana sake kallon mutanen nasa da kawunnansu du suka yi wiki wiki sunna kallonsa, Hannunsa dake dan rawa ya kawo a hankali ya dora saman kan daya ya shiga mulmulawa a hankali yana dan matsa kan a hankali a hankali har ya ga ta bude lumsasun idannuwanta tana kallon fuskarsa muryarta cen ciki ta ce" Abdul, meye haka wai? Ni akoy zafi fa, kuma ka daina tabani ni, a nan a wajen nan, kuma a cikin mota baka gannin m......................" Hadiye maganarta ta yi domin bakinsa ya kafa a kan maman nata a hankali ya ringa lasa Da karfi ta ja numfashi tana rike fuskarsa ta dagota gaba daya tana kallonsa ta ce" Tana dakin tiyata fa, ka bari mana meye haka wai" A hankali ya ce" to kin ki yin shiru bayan nace ki daina kukan sai yi kike yi fa, idan na bari zaki daina yin kukan?" Kai Amina ke dagawa sai hadiyar yawun wuya take yi Murmushi ya yi ya saketa ya daga yana kallonta ta mike da sauri ta gyara rigarta ta mayar da hijabinta sai sada kai take uwa tana gaban sarkin garinsu kunya cike da cikinta da mamakin yaron nan! Sai da ya ga ta samu nutsuwa sosai sannan ya ce" Kin ji an ce abin cikin ba rai ko?" Amina ta gyada kanta jikinta a sanyaye Ya sake fadin" Hakan na nufin za'a cirosu ba rai, za'a bamu su ko?" Amina ta sake gyada kanta tana kallonsa yana mata magana kamar ya samu mai shekara biyar Abdul ya ce" Ba maganar kuka, kin ji? Haka Allah ya hukunta, idan an ciro za'a nuna mata abinda ta samu suka koma dan ta samu dangana sannan a kaiwa mahaifinsu su ya masu sutura domin shi yakeda ikon hakan kin ji?" Amina ta kalleshi gabanta na faduwa, a hankali ta ce" ABDUL, kuma harda Fidon zaku mayar masa itama ya kashe min?" A hankali ya girgiza kansa ya saka hannu ya bude kofar yana fadin" Ai ba aure tsakaninsu ya saketa " Allah yana ganni wani farin ciki da sanyi ne suka ratsa zuciyarta, Astagfrulah, ance an yi saki maimakun hankali ya tashi? , Sai ta ji wata nutsuwa na shigarta, ko ba komai Allah ya raba kanwarta da wahalar mutumen nan, abinda ya fara dawo mata a rai shine to yanzu Fido ita daya zata je gidan nan da ake shigo mata ta zauna kafin su dawo ko me?????, Da wannan ta bi shi wajen zaman jiran har a fitar da su daga dakin tiyatar suka zauna su biyu kowane da abinda yake rayawa a ransa, bama ABDUL da ya tsareta da ido har ya zamto ta kasa samun nutsuwa tana ta gyara hijab da sauke ajiyar zuciya, Biyu kuwa sun bi direba Muhamat sun tafi kaiwa baba Wainarsa da kuma sanar masa halin da ake ciki............. Docter Mansur ne ya fito , jikinsa a matukar sanyaye ya tunkaro inda suke zaune A tare suka mike sunna kallon abinda yake rungume da shi, shi da docter Umi A hankali ya saka hannunsa ya bude abinda ke rufen yana kallo, hakama Amina dake gefensa a hankali ta dora kanta a gefen kafadarsa tana kallon baby face din yarinyar da cikaken gashin dake kwonce a gaban goshinta, fari fat da ita domin ba rai a jikinta Wani numfashi ta ja, gaba dayanta ta ja wani irin abu ta ......... 40😍😍😍😍😍😍 Wani numfashi ta ja mai zafi, gaba dayanta ta sake lumshe idannuwanta a saman kafadarsa tana kallon fuskar jaririyar Jikinta babu karfi ko kadan, muryarta cen ciki ta ce" Ka ga, mamaci sai fuskarsa ta yi fari fat haka, ko baki ne sai ka ga ya kara haske irin hasken rashin jinni" A hankali ya kalleta, hakama doctors din A sanyaye ya ce" Haka kamanin mamaci ke yi?" Amina ta dago tana kallonsa, a sanninta shima ai nasa iyayen sun rasu ko?, Gaba dayansu Idannuwansa ya lumshe yana sake duban fuskar namijin ya ce" Kin san ni ban samu gannin haka ba.....ban ga komai ba" Sai da wani irin abu ya soki zuciyarta, a hankali ta kai dubanta kan fuskarsa tana janye hannunta daga jikin abin rufar yaran A saman lebenta ta furta" Allah ya rahamcesu" Shima a saman nasa leben ya amsa da "Amen summa amen " Da kansa ya rakata dakin da aka kai Firdausi Idannuwanta biyu, dama ba na dogon barci akai mata ba ta tsurawa waje daya ido tana kallo tamkar kurma , idannuwanta a soye tass babu hawaye, ciwon dake cikin zuciyarta da na jikinta ji take yi idan ta bude baki da nufin yin kuka tana iya yin aman jini......bata tunanin idan har zata iya yin kuka normal irin na mai fama da wani miki a zuciyarsa Hannunta ya saki ya juya ba tare da ya cewa Firdausi komai ba ya tafi......itama a hankali ta karasa kusan Firdausin ta zauna tana kallonta Sun dauki kusan minti biyar a haka , muryarta cen ciki ta iya budat bakinta ta ce " Aunty, gidansa zan koma ko?" A hankali Amina ta girgiza kanta hawaye na zubo mata kamar ruwa , muryarta na rawa ta ce" Koda zan rasa raina a kan yaki da dukkanin ahalinsa, ba zan yarda a mayar da ke gidansa ba......kuma Abdulma ya ce ba zaki koma ba Fido" Firdausi ta gyada kanta tana sake mayarwa ta dora a hankali saman matashin da aka saka mata mai laushi tana kallon sama, kennan yanzu mutun biyar ta birne a rayuwarta.............. A cen kasan zuciyarta ta ringa maimaita adu'ar da Amina ke karanta mata kasa kasa sosai tana lumshe idannuwanta hawaye na diga a gefe da gefen kumatunta Tsayuwa ya yi ya yi kiran gida , ya samu Baba na sanar masa yanzu zai taho da suka zo ya dan fita ne Baba na kashe kiran ya kai dubansa saman kular da Hajia ta kawo masa waina mai sunnan waina, waina irin ta yan gayu ta sha su yankakiyar albasa da komai da komai , a kala yau an yi sati da take wannan abin dan ya kulata, bata san cewa bashida lokacin haukanta bane, a garin da take dakawa ta kara kaimi ta daka sama da shi, tsaf ya shirya mata ko me take takama da shi Mikewa ya yi bai ce komai ba ya ja hannun biyu zasu tafi Jiki a sanyaye ta ce" Alkali, ina zaka je kuma baka ci wainar da na yi ba?" Gannin da yara dole ya dakata ya juyo yana kallonta ya ce" Zamu tafi asibiti ne, uman biyu ke cen da kanwarta an mata aiki" Hajia dake neman shiri harda dan mikewa tana fadin" To ko na zo mu je ne?" Sosai ya ji sasauci a guguwar fushin da yake yi da ita a zuciyarsa, sai dai ba zai yarda da ita haka kai tsaye ba , dan haka ya ce" Aa, ki yi zamanki, idan tsoro ya fita tsakaninku kwa yi zumunci" Daga haka ya fice da biyu yana tunanin sai sun biya an dauki Baba Lauratu su je tare ko dan ta kula da biyu , domin asibitin ba'a barin yan jinyama sam, ko kwana nawa zata yi ba zasu yarda da yan jinya ba, zadai a ringa zuwa ganninta ana dawowa har a sake su Kofar ta zubawa ido na lokaci da dama a tsaye Ta rasa ta inda zata kamo tunanin mijinta Koda yake, ta fi kowa sannin waye Alkali a kan kafiya kan abinda ya nacewa Zama ta yi tana maida kiran Maman Risala a ranta tanaa ayana ' matar nan kiran wace jarabar kuma take min tun jiya da yama!' Gaisawa suka yi a mutunce, maman Risala tana basarwa ta ce" Na ji shiru ne Hajia tun jiya na zatama zan ganki?" Hajia ta dafe goshinta dan ta tabata wata jarabar aka yi ta ce" Lafia dai ko?" Maman Risala ta ce" Lafia kalau hajia, na ga abin alkhairi ya samu haka kuma na ji shiru?" "Hajia ni du ban fahimta ba, wani abu ya faru ne na alkhairi bani da labari?" Hajia Hauwau ta fada a dan kagauce dan dama zuciyarta du a cinkushe, yanzu du irin yadda ta sa aka koya mata tuyar waina ta siyo tanda irin ta jonawa da wutar lantarki ta sa aka yi mata hadin waina naa karshe na manyan yan gayu ama Alkali ko budawa bai yi ba ya tafi wai asibiti ko kanwar uman biyu ko me? Ashe har kanwa gareta yarinyar! Maman Risala ta yi murmushi ta ce" Au, na san kunya ta hanna masa sanar maki ne Hajia, ai jiya raga raga muka daukota mun kusa kai isha'i a asibitima, sai da muka ga likita baba, ai lamarin kai budurci kan zo da salo daban daban , ita kam ta jigata baiwar Allah, kin san abu da wace bata saba ba, a kilace a tsaftace shi yasama na dawo da ita nan dan ta yi jinya" Tsuru tsuru HAJIA ta yi da mahaukacin mamakin maman Risala, du wayewarta bata kai cen ba walahi Yanzu dama wannan maganar matar nan zata fada mata ta saka ta nutsu take sauraronta?, Wata irin kunya ta kama Hajia, harma ta rasa amsar da ya dace ace ta bada A hankali Hajia ta iya furta " Uhum" Maman Risala bata dauki hanya ba, bata gane ba, ta ci gaba da yamadidi da maganar tana karra jadadata, har ya zamto Hajiar ta fahimci inda ta dosa, watau kyauta da ake yiwa amare idan sun kawo daki, shi matar ke son nunawa A nutse ta ce" Allah ya bata lafiya, zan hau sama " Maman RISALA ta yi dan murmushi tanaa sake fadin" To na damuwa HAJIA sai an zo dubiya, ai yar gidan naki gatanan sai nishi abu da rashin sabo mijin sam bai saurara mata ba ai in fada maki kwata kwata bai........" "Kai lahaula wala kuwata na shiga uku , dan Allah maman Risala bakya jin nauyin maganar nan ne?, Haba dan Allah manan Risala wai wasu irin mutane kw zagaye da ke basa baki shawarar da ta dace ne tunda ke ai na kula sam ma bakya tuna irin haka, Maman RISALA ace kin je kin dauki yarinya daga dakinta dan kawai abin daukakawarta ya sameta?, Ke na kula ina yaki kina kuncen hanyar yaki ne gaba daya walahi, ama ba komai idan alkhairi ne ai zaki gani kwana kusa Maman RISALA, wannan kamari har ina wani abin ai ba sai an fada maka ba tsakani da Allah, a kanta aka fara? To bari ki ji itama dayar ai budurwar ce du yadda ya ki kar na ji sai da kika kwasheni kika kaini shi kuma ya fada min idan ya so na ji da shi ko? Ni kam kin ga bafa cen na dosa ba, mu irin wannan abin boyewa ake yi ba abin a yi yawo da shi kowa ya ji bane ba fa Hajia, ni kam kin ga kamarin kyautar wannan abinma idan ya yi niya ya yi tsakaninsu, idan baya irin haka kuma ra'ayinsa ne ba zan tofa komai a kan wannan ba, haba , yaya ina yaki dan yarinya ta samu wurin zama kina kunce min? Yanzu da kike kwasheta kika kaita gida ai fili na Amina ne, sai ki yi ta yi tunda ke bakida masu fada maki a kusa da ke" Hajia ta fada da bambami tana katse wayar hadi da ci gaba da masifa kamar zata ciki kasa, ita abin ya bata mamaki Walahi meye a su budurci da ake fada da wani isa, to hala yar ta yi yan yawace yawacenta ne da ake cika baki dan bata barar da budurcin ba?, To da me take tunani ne? Budurcin banza budurcin wofi idanma ta barar da shi ai gata ga ABDUL din, batama san waye ABDUL bane, ta dai rike y'ar ta tabata ba zai lekata ba tunda ba wani ciwo mai dalili bane , ciwon iya shege ne, yo ko fafarketa ya yi ai abin kunyarku ne yamadidi da shi bale da ace ya farketan na tabata sai kakansa mai SHANU ya ji , mutane sai shegen iyayi da dan banzan nuna kai bayan ba komai kowa ba!, Shirmen banza da ita da budurcin sun ci kaniyarsu. ( To fa) A bangaren Maman Risala karma tana jin an katse kiran ta shiga zage zage tamkar zata hadiyi harshe, har sai da Risalar ta fashe mata da kuka tana fadin" Mama, sai da nace maki dan Allah kar ki yi kiran hajia, ki bari na daidaita tsakanina da ita, kin ga dama ba wani yin wancen matar take ba, idan na samu na sake sayeta ko menene sai aa yi, ama mama kece ki yi fada da ABDUL, ki yi da Hajia? Mama yaya kike so na yi da raina?" Da takaici uwar ta ce" Ki hadiyi ran mana Risala? Shashashar banza da wofi, sam ban ga anfanin wannan aure ba, ace ya fatatakeki haka ama bai biyo bayanmu ya yi mana magiyar a bada ke yaa mayar da ke? Wai HAJIA ni zata cewa wancen guzumar tasamaa budurwace? Ina ruwana ni, tsohon budurci da sabo ai ba daya bane, ke da ita ba zaku taba kasancewa daya ba har abada, shirmen banza da wofi wai ita a komai sai ta wulakanta mutun" Ita dai Risala kukanta ta ci gaba da yi da wayarta a hannu tana sake buga numbar Mijinta A daidai lokacin sun karasa gidan iyayen Mudi sun kai masu gawarwakin yaren, sannan Baba ya sanar masu duka kaf abinda ya faru Ga mamakinsu Mahaifinsa ko a kwakar rigarsa, vawarwakin yaren kawai ya yi gargadaf yana fadin su zasu birne , ba zasu bayar ba, tunda yaro ya saki kuma ai shikenan, dama shi sam yarinyar bata wani yi masa ba, abinda yana saurayinsa danye shataf ya je ya wani lakewa bazawarar da miji ya mutu ya bari da cikin gardawa har biyu, ai kawai an gode uma ta gais da asha Baba mai SHANU baki da hanci ya bishi da kallo a lokacin da ya mike yana mai ci gaba da balakinsa ya shige da nufin kiran ɗan nasa dan ya fada masa ya zo su je ko su biyu ne su birne yaren Yana shigewa mahaifiyarsa dake rame baiwar Allah tana share hawaye ta duka gaban Baba tana fadin" Dan Allah Elhaji ku yi hakuri kun ji?, Ku yafewa yaron nan, ban taba dana sannin aurena irin haka ba, ba sauki ba alamun sauki, hali zanen rai ne yake dawainiya da su, mugun hali marar amfani, yarinyar nan tunda ya aureta sau biyu kawai na ganta, ita bata samun fita, bale ni da a wajen ubansa ya gani ya gada, Elhaji ba zan taba manta bawan Allahn nan ba, mahaifina ya rasu har aka yi suturarsa bai sanar min ba, an zo daga gidanmu dan a fada min yace zai fada mij, sai da aka yi sati mahaifiyata ta zo da kanta take fada min, a ranar na yi kuka kamar raina zai fita, kuma bana iya fita nan da kofa, idan na saka kafata zan fita kamar zan mutu nake ji, ina rokon Allah ya nuna min bayan wannan wahala domin abin ya wuce tunanin bawa Dan Allah ku yi hakuri ku bata hakuri itama sannan ku yi mata barka , domin ko ni na samu haka ina so Elhaji" Kai baba ya gyada cike da al'ajabin wannan ahali, yana tsinkayo wayar da uban ke yi da ɗan nasa, waya ce mai amo mai karfi, baki dayansu sun ji ihun fadin da Mudi ke yi cewa an kashe masa ya'ya dai, ba zai taba hakura ba, ba zai yarda ba sai ya kai karansu mikewa Baba mai Shanu ya yi yana dafa kafadar ABDUL da ya yi wani iri alamun rikici sun bayana a fuskarsa ya ce" Mu je Magaji, mu tafi , Allah ya sa masu ceto ne" Mikewa ya yi shima ya bi bayan Baba suka fice a gidan Ko a cikin motar shiru ne ya ratsa motar, babu mai magana a cikinsu Sai da suka shigo farfajiyar asibitin Baba ya dubi ABDUL gannin bashida niyar yin magana ya ce" ABDUL, ka yi hakuri ka ji? Haka Allah ya hukunta, ita kuma Allah ya sa karshen wahalarta kennan, Allah ya shirye su su kuma idan masu shiryuwar ne, idan ta warke ka ga sai ta koma gida ta zauna tare da mu har Allah ya fitar mata da miji ko?" A hankali ya dago kansa da idannuwansa da suka yi ja yana kallon Baba yana ta cije lebe da saki kadan kadan ya ce" In sha Allah" Ya yi shiru, sai kuma ya sake duban Baban ya ce" Amma idan ta fito daga nan tare da Uman biyu zasu zauna dan idan ta je nesan ba zata daina kuka ba" A hankali baba ya ce" Aya, ita Firdausin kau? Kuka take ta yi ko? Baiwar Allah ai ko ba'a fadan komai ba yarinyar ta wahala, Allah ya saka mata da mafificin alkhairi a cikin alkhairan duniya da kiyama " A nutse ya ce" amen, amma ba ita ba, ni ita har yanzu bamu yi magana ba, ita Mom twince din ce ai idan aka tafi babu kanwar tata zata yi ta yin rigima ne" A hankali Baba ya kalli Muhammat da ya dago shima ya juyo yana kallon Uban gidan nasa Ya sake juyowa ya ce" Ita dai Uman biyun ce mai rigimar?" Kansa ya gyada yana budewa ya fita yana fadin" Bara na leka Mansur na ji kwana nawa ya dibar mata" Da Baban, da Muhammat din basu daina binsa da kallo ba sai da ya bacewa ganninsu "Allah mai alkhairi, ka ga rashin rabo , saifa da kakar gwamna ta ce min zata zo na kiya, da na san hakane da na zo da ita ta ji batun gwamna......kai jama'a" Baba ya fada yana kame haba Muhamat ya ringa dariya kasa kasa Baba ya ce" To ka ji,, Muhamadu kaini dakin yarinyar nan na sake ganninta baiwar Allah na yi mata nasiha, Allah dai ya shiryi wasu mazan" Yana murmushi ya bude ya shige gaba Baban na bin bayansa suka nufi ciki A office din MANSUR "Man, na jima ban shiga wani hali a rayuwata irin na yau ba, na jima ban ji zuciyata na girgiza irin na yau ba, Man wannan mutumen yana nan a raye baka babalashi ba? Namiji uwar yaren nan tsabar abu ya dira mata zuciya ta kasa koda kuka, yaran ta amsa ta kalla daya bayan daya ga ciwo CS a hankali ta masu addu'a ta mana masu kiss a goshinsu ta miko mana, du yadda muka so gannin hawayentama bamu samu ba.....Man dan Allah kar ku yarda ta koma gidanta idan har baku zaunar da shi kun ji meye damuwarsa ba, kar aje mahaukaci ne ba'a sani ba fa" Mansur ya fada hankalinsa tashe , ko a cikin amon muryarsa zaka fahimci ransa a bace yake shima ABDUL ya sauke ajiyar zuciya yana dubansa ya ce" Man, ba zaka gane ba, ni da kaina kadan na tsinta a cikin maganar, har yanzu ban san duka maganar ba, ama in sha Allah ba zan bari haka ba, idan shi dan duniya ne zamu buga kwallon duniyancin,....... Daga shi har ubansa!" Da mamaki ya ce" Man kana nufin mahaifinsa da rai dama ya bar rayuwar yarinya a wulakance haka?" ABDUL ya sake cije lebensa da bacin rai ya ce Nzl 42 ABDUL ya sake cije lebensa da bacin rai ya ce" Yana nan da ransa , ka gane abin ya wuce tunanin mutum, ya zamto talaka bashida wani gata sai na Allah, wa'inda suka isa su tsawata sun nade hannu kowa na tsoron tofawa, mahaifiyar yaron kanta a ha'ula'i take, ai ba maganar aure cewa ya yi idan na fito da ita ya mata saki uku, ni kuwa na fito da itan a summe" "Saki?, Uku? Hasbunnalah, wannan wani irin marat imani ne? Wani irin rashin godiyar Allah ne? Ni ina nan haihuwar nake nema ido rufe Allah bai kawo ba ka gaan sameta a wani wajen ana wukakantawa? Dan Adam bashida godiyar Allah, wanin baya jin tsoron Allah sam" ABDUL ya sake daukan file dinta ya bude yana komawa ya zauna ya ce" Allah zai yi maganinsu, kwana nawa ka daukan mana ne?" Mansur ya ce" Na daukar mata kwana uku ne, idan komai ya tafi daidia jinninta ya daidaita in sha Allah zan salameta" ABDUL ya gyada kansa yana duba duka kaf magungunnan da aka rubuta mata harda na kafe ruwan nono dan kar su dameta da suba da zogi Sosai ya gamsu da komai ya ajiye yana sake zama yana ta cicira tunanin dake zuciyarsa, sai dai ba zai fadawa kowa yanzu ba, zai bari ne har ya tabatar sannan ya san abin yi, shin yaya zasu rayu bayan bata son rayuwa da shi? Idan kuwa har furen dake tare da ita ya yi tsiro har ya yabanya wace irin gagarumar rigima ke gabansaM "Hum" yace har sai da Mansur ya dube shi yana ajiye masa jus yana fadin" Man kayanka sun baci gashi an kusa shiga masalaci, ya dace ka je ka kimtsa" Ajiyar zuciya ya sauke ya mike yana masa salama da nufin sai sun hadu da yama idan ya dawo daukan Uman biyu Tafiyarsa ya yi ya bar Baba da biyu dan ya san sa wuce masalacin tare , shi kuma ya koma gida A cikin dakin kuwa Baba ke yiwa Amina nasiha kasa kasa, Firdausi kuwa ta samu barcin wahala tunda ta saka hannunta cikin na yayarta sai da barcin ya kwashetama Amina ta janye a hankali ta zauna aa gefenta tana kallonta Kasa kasa Baba ya ce" Haka nata salon kadarar yake, kuma kin sam cewa Allah baya dorawa bawa abinda ya fi karfinsa, ki daina kuka ki bata kwaron gwuiwa, ta haka sai ta shanye dukkan wahalar har ki ga ta mike kamar ba ita ba kin ji Uman biyu?" Amina ta gyada kanta tana sake share hawayen nata, idannuwanta har sun kumburo dan kuka, bata taba jin maraici har cikin kirjintaba irin na yau, kafin Abdul ya fito da Firdausi babu irin abinda bata tuna ba a duniyarta, ta yi kuka da boda kamar zata fasa motar Shigowar Baba tana rike da bokici da yan kayayakin dake ciki , Husaini na yi mata surutu ya saka Baba sakin murmushi yana kallon Hasan ya ce" Yau sam ba fara'a a fuskar mai tsuntsaye, Allah dai ya sanyaya fushinsa" Baba ta yi murmushi itama tana sake gyaraa matashin kan Firdausi ta zauna tana kyatu ta kama Hassan ta zaunar ta ce" Allah ubangiji yaa sa karshen wahalar kennan" Da amen suka amsa, du suka ci gaba da zama har karfe goma sha biyu ta yi suka fice tare da Muhammat da ya dawo daukansu dan kaisu masalaci Da yama da kyar Uman biyu ta fito , har zuwa lokacin Firdausi bata farka ba, kuma ance idan ta farka ba za'a bata abinci ba , sai dai ta sha jus Ji take abin nan sam bai dace ba ace za'a rabata da kanwarta, shi dai a bayan motar a zaune waya yake amsawa , yau sam bai leka nema ba, gashi da zafin nema, suka nufi gidan Baba domin yau bai je ba, rabonsa da Hajia kwana biyar ciffffffffff A asibiti Tsaye suke a kanta, docter da Mansur sunna bata baki a kan kin amsar koda bakin ruwa ne ta sha, ta nuna Alhamdulilah bata jin cin komai Docter ta janyo kujera ta zauna tana kallonta ta ringa yi mata nasiha da bada baki da nuna mata mahinmancin lafiyarta Ama Firdausi sam ta nuna bata jin yinwa ne Da kula Docter ta dubi Docter Mansur ta ce" Likita, inaga sai an tabo makusancinta, ka san ba zai yiwu ta ki shan jus din nan ba, shi zai taimaka mata samun karfin jikinta kafin ta samu iska ta fara cin dan salak da dai wani abin marar nauyi ko?" Kai MANSUR ya gyada, cike da tausayi yana kallonta ya ce" Na gode sosai Docter da kika zo, zan dubata....." Docter ta amsa ta mike ta tafi, Mansur ya amshi jus din dake hannun Nurse din da ta shiyata da komai , itama ta fita , ya maida dubanta kan Fido da kanta ke sade tana kallon waje daya Aa sanyaye ya ce"baki dangana ba Firdausi?" Fido ta dago a hankali ta yi masa kallo daya ta sake sada kanta, muryarta a sanyaye ta ce" Dangana da me likita?" Mansur ya ce" Da rashin da muka samu, ko kuma aban yaren ne mai baban laifin?" Sake dagowa ta yi tana kallonsa, ta sake soke kaanta Mansur ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Akoy ciwo Firdausi, akoy ciwo matuka, ama ya dace ki yi duba da jama'ar dake zagaye da ke masu zubar da hawayensu dominki, a kan laifin daya tak, kar ki hukunta kanki da hukuncin da zai damu masoyanki, kin ga wace zata fara jigata yayarki ce, a gangaro kan biyunki, mu da kanmu sai hankakinmu yaa tashi Firdausi, karma ki saka damuwar wani a ranki ki kasa nutsuwa kin ji?" Firdausi ta sauke numfashi yinwar fa na cinta, a sanyaye ta ce" Docter, dama wata sharaar ai sai a kiyama......., Luuuu luuuuuuuuuu Nake gani kar aje nima mutuwar zan yi na shagalta da kurbar juss, shi yasa nake ta Adu'a a zuciyata......ka ga kuma biyu ba nawa bane ba fa, na uman biyu ne" Tausayinta, madaukakin tausayinta, shi ya fi komai rinjayarsa, Da dabaru irin na likitoci ya samu ta amshi juss din har ta yi masa sha na mamaki Tana gama sha ta koma barci domin akoy allurorin barci a lamarin dole sai da hutu Ido ya zuba mata yana kallonta, kallon da shi kansa bai san ya zarce a kallon ba Gata dai a cikin hali na rama, duhun fata du hasken fatarta wahala ta rinar da ita, rashin walwala, girman ciki irin na wanda ya sauke ciki yanzu, tarin tausayinta ya sakashi zuba mata ido yana mai cike da madaukakin tausayinta a zuciyarsa Ajiyar zuciya ya sauke ya mike domin a lokacin tuni har isha'i ce ke shirin kawo kai ya sake duba komai na dakin sannan ya tafi ya kimtsa ya nufi gidansa dan tun karfe shida yau rabonsa da gidan nasa ___________________________________ Daga gidan Baba suke, fuskar Amina tamkar an saka balan balan , ita kafai ke hauhawa tana hucisakamakon abinda biyu suka yi mata, wai ba zasu zo ba yau a gidan baba zasu kwana a cen zasu yi weekend Tana ji tana ganni akace wai ta bar ƴaƴanta ta dawo gida ita kadai, ita lamarinsu ya fara bata tsoro, tana janye shakuwarta da ahalin gidan Mai Shanu yaran nan na makalata Sai da ta bacewa ganninsa ya dawo da dubansa wajen Muhammat, ya ga ya tsareshi da ido yana wani murmushi irin na saman leben nan A kausashe ya dage girarsa daya ya ce" menene?" Muhammat ya dora yan yatsunsa biyu daidai bakinsa ya ja irin ya yi zif din nan sannan ya sake mayar da kansa gefe yana murmushi ABDUL ya bude ya fice yana dan mimike kafafuwansa fa fadin" Sai gobe idan A'lah ya kaimu" Muhammat ya ce" Allah ya tashemu lafia Oga, a huta lafia" Bangarensa ya shige ya haura sama Ko'ina fes fes an gyara ko'ina sai kanshi yake yi, masu gyara harta da dakin barcinsa su suke gyarawa Wanka ya yi ya dauro alwallah ya dawo saman salaya yana sake dafe cikinsa da suka sake cin wainar Uman biyu shi da yara da baba gaba daya, cikin nasa ya yi nauyi da yawa bayan baya cika kulunsa har haka da dare, a dole zai dan motsa jikinsa idan ba haka ba , ba zai iya samun barci mai dadi ba Yana gama sallah ya dan buda computernsa ya dadana ya gama aikin da zai yi sannan ya mije ya sake fesa turare ya sauko yana kallon table din abincinsa an shake da kuloli kala kala ya yi gaba , yau ba zai leka komai ba ai ya koshi sosai ne A Hankali yake takawa, da fara kar din jalabiyarsa a jikinsa ya shiga dan tafia a tsakar gidan, nufinsa ya fita haka ya zagaya anguwar a kafa ko zai ji cikinsa ya sauka kadan Idannuwansa ne suka sauka a kanta, ta cenza shigar jikinta ama da hijabinta tana tsaye ta dan dafa jikin garu a balbalin kofar bangarenta tana kalle kalle "An mata" ya fada a hankali yana kallonta a tsaye Itama tunda ya fito ta ganshi, shi yasama ta cire dubanta a kansa take kallon wani wajen daban, da yace an mata, a dole ta juyo tana kallonsa da mamakinsa Murmushi ya sakar mata yana kallonta ya ce" Me ake yi a waje da dare?" Amina ta dan sadda kanta , sai kuma ta cuno baki tana fadin" to ba twins bane ba zasu zo ba, su ba ruwansu idan na ji tsoro ko?" "Da ruwansu mana" ya fada a hankali Sai kuma ya sake kallonta ya ce" Tsoro kike ji?" Mazewa ta yi ta ki bashi amsa Dan murmushi ya yi ya ce" To zo mu fita yawo a cikin anguwa" Samun kanta ta yi da son fitar, domin ita kadai du wani kadaici ke damunta na ba gaira babu dalili A sanyaye ta sauko suka shiga tafia, kadan kadan da dabara sai ta saba jerawar da suka yi, shima da dabarar sai ya daidaita A hankali suke takawar har suka fita a makeken get din suka shiga tafia a anguwar dake dauke da fitillu manya a kofar gidaje, ya zamto ba duhu sosai, sannan akoy mutane jifa jifa sunna dan tafiyarsu, wasun kuwa a zaune zaka gansu nesa sosai sunna dan zantawa, harda mata kuwa, domin anguwa ce ta gayu mai dauke da yayan yan gayu da jikakun yan gayu masu son yannayi mai dan sanyi na dare haka kafin dare ya dan tsala su shige gida "Me yasa kake son shiga tsakanina da nemana?" Amina ta fada a hankali tana kallon hannunsa daya dake saman kirjinsa a rungume Dan juyowa ya yi ya kalleta, sai kuma ya dauke kansa ya shiga nuna mata wata shuka yana fadin" Kim ga wannan shukar, a shekara daya take girma, kuma ita bata son mai dati ya tabata, idan kanada dauda irin haramtaciya ka tabata mutuwa take yi, Aunty kin ga tanada kyau ko?" Amina ta kalli shukar, ba shukar komai bace sai ta zogale, zogale dai zogale , ta ce" Uhum" Takawar suke yi har suka kusa kaiwa wata kwana , Dan daga kafarta ta yi ta je ta gabansa tana kallonsa ta ce" ABDUL, me yasa kake son shiga tsakanina da nemana?" "Bani da nutsuwa a kan neman ki" ya fada a takaice Amina ta ce" Why?, Ka san kuwa shi ya rufa mana asiri ni da y'ayana da kanwata har muka kawo yanzu?" A hankali ya dakata yana kallonta ya ce" Yanzu kuwa ba gani ba, sai na zamto rufin asirinmu baki daya in sha Allah" "Na dan lokaci?, Na kayadadan lokaci? ABDUL na dan lokaci? Yaya kake tunanin zan yi sake da barci bayan na san ni mai nemo shinkafa ce?, Ba zan kuma yarda Fido ta fada hannun wani azalumin ba in sha Allah, haka kuma ba zan iya amincewa ka korar min wa'inda nake yiwa gyara a yanzu ba, idan ka barni kuma na koma ina nema ana kin kulla ni, tun ba yau ba sana'ata ce, haka kuma inada burin habaka karatuna ABDUL " Amina ta fada tana rage amon muryarta domin ya juyo gaba dayansa yana kallonta ne har ta dire aya A hankali ya ce" Waye ya ce maki zan barki?" Amina ta tsatsareshi da ido Gabanta na wani irin dokawa Muryarta tana kin fitowa da kyau ta ce" Me, me kake nufi ne?" ABDUL ya juyar da kansa gefe yana basar da maganat, sannan ya sake juyowa yana kallonta ya ce" Manta " Amina ta sake matsowa tana kallonsa ta ce" Na manta me ABDUL? Me zan manta?, Ka min magana a kan bayanin nan, ni fa bana son magana a rufe!" "Ki ringa tausasa lafuzanki mana Aunty, mu tafi kin ji?" Ya sake fada a tausashe Amina ta sake neman tuburewa tana kallonsa, irin ai itace baba ita ya dace ta ringa masa irin haka ba wani shi ba Tana kallonsa ta ce" Ka ga , ba wani maganar tausasawa babe ko rashinsa, magana ce ta gaskiya, dama Baba tace na bari matarka ta tare, ta tare ai har na ga aikin tarewa kun aikata kau? Yanzu ni sai ka salameni na je na ji da rayuwata, na je na ji da ta y'ayana da ta kanwata, bana so Biyu su ci gaba da shagalta da abinda ba dindindin ba, ni kawai ka..............." Da wata irin murya ,a mugun kausashe, ya sake matsowa yana dora dan yatsarsa daya a saman lebenta ya ce" Cewa na yi, Ki tausasa harshenki, sannan ku tauna kalamanki, bana son aiki irin na yarinta da shirme a nan" Amina ta zarro idannuwanta ta bude bakinta zata sake yin magana ta ga ya watsa mata wani mahaukacin kallo mai dauke da namijin hatsari, mai firgice da yaren zane, Sannan ya saka yan yatsotsinsa biyu rak ya rike lebenta da su ya ce" SHUIIIIIIIIIIIIIIIIITTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTT!" TAKAICI, MAMAKI, BACIN RAI, TASHIN HANKALI suka hadun mata, suka hannata barkata komai,yawo idannuwanta ke yi a saman fuskarsa, hadewar fuskarsa ya girmami tunaninta, Hannunta ta saka ta janye lebenta da kyar , ta sake zubawa fuskarsa ido, sannan ta juya da wani irin gudu gudu,sauri sauri ta koma hanyar da suka biyoita da shi tana rufe bakinta da hanna kanta kuka a gaban yaro! Da ido Masu gadi sukabita, harda Muhammat dake shirin tafia nasa gidan Murmushi ya yi da ya tuno furucin ABDUL na dazu yana tabatar da gaskiyarsa ashe, maman twins ba dai rigima ba Tana bude falonta ta shiga suka yi ido hudu da Hindatu tana sake saka turaren wuta Huci take yi na wanda ke son fashewa da kuka tana kallon Hindatun ta ce" Nzl 43 Huci take yi na wanda ke daf da fashewa da kuka tana kallon Hindatu ta ce" Hindatu, hala turaran wutar ne? Nace maku juwa yake sakani Hindatu kin cika masa muski hawar mun kai yake yi Hindatu, wayo Allahna Hindatu". Sai kawai Amina ta fashe da kuka tana zama a kasa kamar wata yar baby Ido Hindatun ta zarro tana yin waje da turaran ta hanyar kicin da gudu sannan ta dawo hankali tashe sai fadi take"Na shiga uku na lalace, Hajia,dan Allah ki yi hakuri ban san bakya sonsa ba HAJIA, dan Allah ki yi hakuri ki daina kukan na shiga ukuna" Amina ta tuje hijabin, wani mahaukacin kyau da ta fara yi na daban fiye da gyaran amarcin da ta sha, da wani irin luf luf da gashinta ya karra yi sai wanda ya gani, tana tuje kafafuwanta ta ce" Ki daina ce min Hajia, ni ba HAJIA bace, hasalima filin jirgin kansa ban san a wace anguwa yake ba, kawai sai ki ringa min abinda raina baya so bayan ban maki komai ba?" "Annabi Muhammadu Rasulullah salalahi alaihi wa ahlihi wa salam, na shiga uku ni Hindatu jikar Maryama, Hajia ki yafe mib baki daya rankatakaf laifin da na yi maki, ki kuma dauka kan ba za'a kuma ba, duka kaf abinda bakya so zan daina yi miki har karshen rayuwata a gidan nan kin ji Hajia?" Hindatu ta fada tana sake dukawa gaba daya hankalinta a tashe, ita tama manta tana sake maimaita Hajiar da aka hannata fada Da haushi Amina ta mike tana jin juwar na daukanta, dan walahi juwa take ji sosai , gaba daya hadin turaran nan ya mata karfi shi yasa ita bata anfani da turaruka masu karfi, dan sunna cutar da ita ko cenma Hijabinta ta amshe tana hararar Hindatu dan ganu take yi ai du laifinta ne, ta hannata ce mata HAJIA ta wani sake fada mata Dakinta ta nufa tana fadin" Sai ki yi ai , ki yi ta cewa Hajiar Hindatu, nace ki kwana kina fada"...... Tsuru Hindatu ta yiwa kofar , sai kuma ta yi hanyar kicin har kamar zata kifa tana adu'ar Allah ya sa kar Hajia ta koreta, ita ta rasa me ta yi da zafi haka har Hajiar take kuka? Wayo duniya Tana shiga dakinta ta yi bayi tana wurgar da abubuwan dake jikinta Wanka ta sake yi dan zafi take ji du irin sanyi sanyin garin Tana fitowa ta dauko yar yololuwar riga fara ta saka , sannan ta dauki hijabinta ta zurma ta fita falo Wajen abincin ta bubude tana dubawa, gannin abubuwa irin na turawa sak ta rufe tana jan dan tsaki ta nufi kicin din da kanta ta dauko dadawa da tafarnuwa da dan kayan yaji mai kanshi sai magi , Friza ta bude ta babako kaza guda ta tsomata a ruwa ta zauna tana jira Sai da kazar ta saki sannan ta yayankata ta cire bindin ta sakata cikin tukunya ta zuba dadawar nan da komai da komai sannan ta dora saman gaz ta sake hayewa tana dan balancing din kafafuwabta tana jira Kanshin dadawar ya sakata hadiyyar yawu har kazar ta silalu sosai ruwan ya janye saura kadan, ta juye a kwano ta yi zamanta a cikin kicin din ta ringa dangwalar kazar nan da yajin dadawa tana ci, har wani lumshe ido take yi, a irin wannan lokacin babu abinda ya kai mata kazar nan dadi du duniya Kwafa ta yi ta ce" Husaini harda kai a kin biyoni ko? To gashinan ina cin irin dahuwar da kake so ni kadai" Tana gamawa ta kimtsa komai ta koma dakinta ta sake wanke bakinta taa kuma murza humurarta sannan ta hau saman gadon ta zauna tana zubawa waje daya ido Samun kanta ta yi da yin kwafa kasa kasa ta ce" A me ka dauki kanka? Me kake tunani a kaina? Ko me kake tunani daidai nake da kai walahi!,ina nan gobe sai ka bani sakina malan!" Ta jima tana fama da tunani da fadace fadace sannan ta koma saman gadon ta kwonta ta yi Adu'a ta yi shiru tana tunanin ta yaya zata iya yin barci a irin wannan lokacin , sam bata jin barcin walahi, gaba daya ranta a wani bace yake bata san dalili ba Sai da karfe goma ta gota ya shigo dakin bayan ya kashe komai ya sadada a hankali saman gadon ya haye ta bayanta ya sanyo hannunsa a hankali wajen mararta yana dan shafawa Matsawa ta yi tana son juyowa dan ta mike lokaci daya ta fashe da kuka Da mamaki kasa kasa ya ce" Na shiga uku mai kuka ne shi kuma" Tana kukan ta ce" Ka sakeni, ba dai nice abin wulakantawar ba ko?, Mema na maka a duniya da zafi ne wai? Haka kawai ka ringa sakani kuka , da me kake so na ji ne? Harda zaka yi magana kuma ka ki bani amsa a bayane , kuma ka min alamun zaka zabga min mari? Abdul yayarka ce fa ni idan ka mareni ina zaka kai abin kunya?, Ka sani sarai a duniya Hajia batada makiyi irina, bata so, ta taki Sa'a nima bana so, kaima baka so to ba shikenan ba? Babane zamu san yadda zamu bashi hakuri ya yafewa kowa idan yana so dan ya huce ya bani wani datijo mu je mu karata ko?" A hankali ya sakata a jikinsa ya yi mata rumfa ya juyo da ita barin da yake ya sake riketa a jikinsa sosai yana jin yadda kanta ke sarawa ama rigima ta ki ta daina kukan IA hankali ya ce" To ki yi hakuri kin ji?" " Na yi hakuri fa kace fa, cewa fa ka yi na yi hakuri? Bayan kana kallona na dawo baka biyoni ka bani hakurin ba, ni kawai ba'a yi min adalci a gidan nan" ta kuma fada tana dago idannuwanta tana kallonsa Shima tsai ya yi yana kallonta, har ga Allah tausayinta da son fashewa da dariyar rigimarta ke dawainiya da shi Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya ce" Ni kam ban san me yasa yanzu kike da kuka ba Uman biyu, Haba auntynmu wai menene na kukan a ciki? To maganar ba mun san da zamanta ba me ya sa za'a ringa maimaitata?, Kuma ni babar damuwata Baban ne, shi nake jira na yiwa wayo ta yadda zai yarda ya yafe mana ko? Ko baki damu da fushin Baba mai shanunki bane?" Aminaa ta dan kikifta ido tana ta jan ajiyar zuciya, a zuciyarta tana aauna furucinsa Ya dora da fadin" Ranar da na ce masa soma kike a rabu cewa ya yi da kuwa ba shi ba mu gaba dayanmu ko a lahira" Gabanta sai da ya fadi ta dago tana kallonsa da alamun maganar ta tsoratata Abdul ya ce" Ni kuma da na ga haka sai nake ta son samo hanyar da zan yi masa wayo, baki gani ba ko yanzu da yace maza mu tafi gidanmu na kamo hannunki a gabansa? So nake yi idan ya zo abin kawai ya dangana ya dauka haka Allah ya hukunta ba tare da ya yi mana fushi ba Ko Uman biyu?" Amina ta gyada kanta a hankali cike da tunanin maganar Ta dago tana kallonsa ta ce" ABDUL kuma sai ya fita a harkar tamu?" ABDUL ya gyada kansa ya ce" Sosaima, shi kam yana son hadin nan sosai bayan mu ba wani so muke yi ba" A hankali ta ce" Hakane" Abdul ya ce" Shi yasa nake so mu bi komai a hankali ta yadda zamu kai ga ci a hankali ko?, Kin ga akoy abubuwan da ya dace ace kin fara a matsayinki na ke, irin su fitar da taimakon gajiyayu, taimakawa marayu dai da sauransu ko?" A hankali Amina ta ce" A matsayina na ni wa?" ABDUL ya zubawa fuskarta ido, shinning din da bakinta ke yi idan tana kuka ya fi komai daukan hankalinsa A hankali ya ce" Wai da a matsayinki na Matata ko?" Fuskarsa har zuwa karshen karen hancinsa ta zubawa ido har sai da ya dan dage mata gira ta ankara ta dauke idannuwanta A hankali ta ce" Kennan kafin mu rabun ka rabani da sana'ata?" "Kece bakida hakuri, ba zan rabaki da nemanki ba, za'a fara yi maki gyaran baya ne a zuba maki kayan gyaran amaren.......gyaren nima ai na anfana da shi ko?" Ya idasa yana kane mata ido daya Kunya ta sakata turo baki hadi da son juyawa Riketa ya yi a yadda take kasa kasa ya ce" Amina, da gaske sai da na kusa suma fa......" "Ya Allah" ta fada tana zuba masa ido Murmushi ya yi ya dora da fadin" Takardunki na amsa a wajen Baba, zaki zana ko me kike so, amma........" Da dan zumudi tana kallonsa ta ce" Amma me ABDUL?" "Amma bana son maganar aiki Amina, bana son ki fita aiki ne, kin ga ai ga aikin nan a gida ko? Tunda na gida ne ni ba zan hannaki ba" ya fada yana sake kasheta da kallon da bata san me yasa bata sonsa ba A ranta kuwa ayanawa take yi' Alhamdulilah, dama nima ai ba son sana'a a titi nake yi ba, kafin a rabu dai da sana'ata, kuma indai na zana jarabawar nan ai shikenan du wani tashin hankalinama ya ragu in sha Allah' Da sauri ta saka hannunta tana damkar nasa jin ya shiga yin wani abin daban Da matsananciyar kunya ta ce" Menene haka kuma?" Fuska ya shagwabe ainun yana kallonta ya ce" Marata ke ciwo fa" "To ni kuma me hadina da haka?" Ta fada muryarta na gargada, tsoro na fara kamata Kasa kasa ya ce" Ba yi zan yi ba ai, kadan ne zan dan yi wani abin ko?" "Ka ga babu wannan a tsakaninmu" Amina ta fada idannuwanta na yin rauraurau "Na sani aunty.........just wannan.....".........ya fada yana hade bakinsa da nata a hankali ya shiga kising dinta Ya dan saki kadan yana sake hade jikinsa da nata ya ce" Kadan ne zan dan taba......" ..........."uman biyu dan kadan ne nake son yi.....mmmmmmmm ......mmmmmmmmmm" A hankali ya ringa tareta a jikinsa, du yadda ta so kaucewa ya juyota ya tarota a jikinsa, a hankali ya ringa ribatarta, har ya zamto ta daina son kwace kanta ta ringa binsa da shanyayun idannuwanta da sukai mata wani irin nauyi Irin yadda yake yi mata ya girmami tunaninta Wani abin kamar ta kurma ihu ko zata ji sanyi sanyi, ama ta maze ta matse ta rike Ba karamar dambe suka sha ba a lokacin da ya ringa lalubar wajen da ta sha dinki Kiri kiri ta ce da shi tana iya barinsa da Allah tunda ya zo ne dan ya kasheta Sai dai suna wannan Hali ya sameta da wayo har bata san lokacin da ya kai harshensa wajen ba Ihun kam a yanzu fitowa ya yi Kar ku yi mata muguwar fasara, ihu ne na tsoro da mamakin dan Adam Bata taba tunanin ana haka ba gaskiya, Bata taba sannin ana yin haka ba A haukace ta so dagoshi tana zarro idannuwa , sai dai bai bata damar hakan ba a lokacin da ya danna harshensa a wajen da bata iya ambata Shidewa ta yi, ta yi summan wucin gadi idannuwanta a bude tana kallon sama A gaskiya idan haka ne abin sai a yi Du irin nauyi da take ji gaba daya komai ya barta ta ringa sake sakin jikinta ma kanninta (🧐) A haka ya sake neman hanyar nan a karro na biyu bayan ya yi addu'ar saduwa da iyali Du yadda ya bita a hankali, ya ringa bin wajen a hankali, du yadda wajen ya jike sai da ya tausaya mata Domin shi da kansa ya san a jigace take, a wahalce take Shi da kansa ya san a wannan fannin ita din daliba ce wace ke karamin aji Da tausayawa ya rungumeta a jikinsa yana dan bubuga bayanta Ba kuka take yi ba, amma jan numfashi take yi tamkar mai cutar huka Jikinta du ya yi laushi ba wani karfi a tatare da ita Gashin kanta yake kallo domin gaba dayanta ta shige jikinsa ya yi mata rumfa da fafadan jikinsa A hankali ya kara shafa bayanta yana lumshe idannuwansa Muryarta cen ciki ta budi bakinta da kyar ta ce" ABDUL ka yagani ko?" Idannuwansa ya bude yana kallonta, murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce" Aa fa, keda kika ce kara Abdul karra?" Idannuwanta suka cika da kwallah ta sadda kanta tana fadin" Ka daina yi min sharri mana, yanzu ina zan kai wannan abin kunyar?" Dariyarsa ya danne ya ce" To wama zai sani? Babu wanda zai sani ai balle har a miki wani kallon" A zuciyarta ta ayana' Hakane kuma, amma da na shiga uku da kunyar jama'a ' Nanauyan barci ne ya yi awon gaba da ita, Barci mai tatare da gajiyar da ta sake kwasa da kukan da ta sha Sai da ya ji jikinta ya sake Sosai sannan ya janye nasa jikin ya luluba mata zannin gadon yana kallonta A hankali ya kai hannunsa wajen lebenta ya dan shafa yana kallon fuskar tata A bayane kasa kasa sosai ya ce" Allah ya bani ikon gane cikinki, ta yadda zan tankwasa ki cikin ruwan sanyi......domin ba zan taba yi maki dole ba Amina' Sai kuma ya yi murmushi yana kallon cikinta, abubuwan dake ransa da yawa a kan tunanin nan....uhum wata rigimar ko kansa zai iya dauka kuwa?, Yana da fargaba a cikin hakan. ______________________________________ Washe gari tunda safe aka kaita asibiti, Muhammat ne ya kaita , a cen ta tarar da Baba da biyu sun zo suma daga masallaci suka wuce Fido ta farka daga barcin da ta sha ta dan taba hira jifa jifa da y'ar uwarta da Baba, Biyu kuwa tsakaninsu da ita ido ne, su basu wani shaku da ita ba, ita kuma sam bata jansu a jiki du irin masifar da Amina ke yi a kan hakan ...........SANNU a hankali , a kwana a tashi sai da Firdausi ta yi kwana hudu a asibiti sannan aka sake su A ranar da zasu koma ita ta fito da ky din tsohon gidan da nufin idan sun je zata saka a je a siyowa fido dukkan abin bukata, sai ta ji Muhammat yace gida Oga yace a koma da su Sunna zuwa gidan tare da su Baba ta samu kiransa a wayar falonta Tana dagawa ya fada mata a bar Firdausi ta huta banda shan kai da hayaniya, a tabata ta ci wani abin......magana dai irin ta manya, tamkar wani baba a tsaren nan, sannan ya kashe Dakin da Firdausi ke kallo kamar idannuwanta zasu fado ta juyo tana fadin" Baba wai nan dij kuwa nan dinnne dakina? Ko dai mun yi batan kai ne? Wannan daki haka ?" Baba ta yi yar dariya tana gyara mata ringeshenta ta ce" Naki ne ke kam yar nan, Ai Allah sai ya karra daukaki a kan cin zalin nan na mijinki, kin ga dai gidan yayarki ne duka wannan" Murmushi ta ringa yi ta ce" Baba dagaske Nan din? anan auntyna take zaune? Ynz duk wannan Ni kadai? Murmushi baba ta sakar mata tace ke kadai firdausi, ai ina ga ma idan bai miki ba za a iya canza miki Murmushi ta kara saki tana sauke numfashi a hankali gyara tsayuwar babbar tayi tace bari naje na samo miki abinci ina zuwa Da kallo tabi babar tana sake kallon iya kofar dakin kawai, ba komawa bana ta dawo da abinci ta aje a gefanta ta taimaka mata ta zauna da kyau sannan ta zuba mata ta ci ta koshi sbd babar na sake nuna mata mahimmancin koshin mata a hali da take ciki, tana ganawa ta dauke kwanukan zata fita tace toh ynz ki kwanta ki huta haka aka bani umarni Jinjina kai tayi da farin ciki to baba Nagode sosai Juyawa tayi ta fita ta sake rufi mata dakin ita kuma ta gyara ta kwanta tana lumshe idanun dan neman bacci ido rufe Daga yanayin zaman nashi zaka san lallai yana girmama na sama dashi, qara gyara zama yayi yana murmushi yace toh shiyasa nace bari na kiraka naji dan naga shirun yayi yawa ita tana zaune haka kuma ko sau daya ban ga kazo ko dubata ba. Shiru yayi kanshi sadde kasa yana mammatsa tafi kan hannayen shi da suka dauki sanyin Acn motan daya fito daga ciki kamar bazai yi magana ba sbd lkcn daya dauka bai ce komai ba yana nazari kan lamarin na risala da mamanta sam ya sarewa lamari ta tunda tayi mai wannan tereren a gani shi sam bai cancanci ta mai haka ba, hakan ma da tayi ba birgewa ba ce ita bata fi yar uwar ta sanin zafin jiki ta ba, yadda yaje mata haka yajewa yar uwarta, amma sai da ta sanarwa duniya abinda ya faru daga karshe mamanta ta wani zo ta kwashe ta suka bar gidan toh mai zai musu? Ya dinga zartar zuwa ganinta yana rawar jikin aka ta? Sam hakan baya daga cikin tsarin shi Dan shiririn numfashi ya sauke kafin cikin natsuwa yace Abba Ni bansan da zuwa ta gida ba ban ce a tafi da ita ba shiyasa ma bani ba Kallo mai dauke da mamaki ya bishi dashi jin abinda yace sai yaji kunya na don rufe shi na abinda matar shi tayi sam bai dauka ta dauko risala dan ra'ayin kanta ba hakan yasa shi ɗan sadda kan shi yace ah to shikenan ai ina ga tunda taji sauki ma zaka iya tafiya tare da ita ko? Shiru yayi na wasu dakiku yana tunanin ya tafi da Itan ne? Samun gamshasshiyar amsa yasa shi jinjina kai alamar to amma bai ce komai ba, tashi yayi ya shiga dakin matar tashi inda anan risala tafi zamanta tunda tazo gidan Yana shiga ya sameta zaune akan gado tana daddanna waya fuskanta cike da damuwar shareta da Abdul yayi, mayar da dubanshi yayi kan mamanta data fito daga bandakin kanta daure da karamin towel Dantse kebenshi kawai na kasa yayi ya sake kallon risala da karar kofar ne ya sata kallon shi tace Abba sannu da zuwa Fuskar shi a hade ba alamar wasa yace tashi ki bi mijinki yana nan falona. Rarako idanu tayi da mamaki dama Abdul yazo gidan nan ne? Shine bata sani ba, manta kuma a sukwane nufoshi tana aje towel ɗin tace "A'a! Ban gane ba Abban Risla, ya za ka ce kawai ta tashi ta b..." Irin arnen kallon daya jefo mata yasa ta ɗauke kanta tana harareen bango, Risala ya sake kallo a tsawace yace "Malama zaki tashi?" Da sauri ta shiga kiciniyar saukowa daga kan gadon ta zuro ƙafafunta ƙasa, wajen kayanta ta nufa da Mamanta ta aje mata a nan ta zaro dogon hijabi ta saka akan dogon wandon dake jikinta da ƙaramar riga, jakar kayan nata ta ɗauka da sauri ta kama hanyar fita. Ta cika iya cika tamkar za ta fashe tsabar hassala, saida Risala ta bar ɗakin sannan ta sake kallonshi da yanayin ɓacin rai tace "Abban Risla, a gaskiya ni baka kyauta min ba, ya za ka wani ɗauketa ka miƙa masa haka kamar wata yar tsana? Yaron nan kwanan Risala nawa amma ko sau ɗaya bai zo ya dubamu ba, shine daga zuwanshi za ka ce ta je kawai, kenan ma an bashi dama ya sake wulaƙantata?" A matuƙar tsawace cike da ɓacin rai yace" Ya wulaƙantatan, ke yanzu dama ba shi ne ya ce ki ɗaukota ba shine kika taho da ita nan? Anya kuwa kina nemawa kanki mutumci da daraja a wajen mijin ƴarki? Me ye ya faru? Kasheta yayi ne da san an ɗaukota nan? Haka kawai ki dinga ja wa mutane zagi." Da mamaki ta kalli fuskarshi tace" Ni ce ma zan ja maka zagin? Bayan duk abinda ka aikata, yanzu da ka ɗauketa ka miƙa masa ba salon ya rainata bane, me ya bata a matsayinta na budurwa? Yaron nan fa kusan halakata yayi da zuwa ɗaya..." A tsawace yace" Ke shiru dallah! Da wani bakinki da bai san me yake faɗa ba, wa kika ga lamarin nan ya kashe ne? Ke ba ta haka kika sameta ba, to ki ji ni da kyau..." Cike da gargaɗi ya shiga nunata da yatsa yace" Wallahi kika sake min irin haukan nan Allah ranki idan yayi dubu sai ya ɓace." Juyawa yayi ya fice daga dakin ta bishi da kallo ita ma a hassale sosai ta jinjina kai irin za ka sani ɗin nan! Ita kula Risala shine ta tafi ɗin dan ya ce ta tafi ba ko wani gardama da jan aji, to ta ya ma Abdul ɗin nan zai darajtata ne da wannan rawar kan? ________________ Tunda ta fito kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kanshi ya miƙe ya fice a falon ta bi bayanshi tana mai turo baki da jin ta ya zai mata haka? Ko fa waya ba sa yi tunda ta zo gidan nan bare kuma maganar zuwa dubata. Abu ɗaya da ta ji daɗinshi shine karɓan jakar hannunta da yayi ya buɗe mata ƙofa ta shiga sannan a shige shi ma tare da aje jakar a tsakiyarsu. Bai sake kallonta ba bare ya ce mata ƙala, ganin bai da niyyar yi mata magana yasa ta ɗan matsawa kusanshi kaɗan tare da ɗauke jakar ta ɗofata a kan cinyoyinta, a hankali ta zura hannunta na hagu ta sakalo a na shi hannun ta dora kanta a kafaɗarshi a sanyaye ta furta "Babbbb." Tunda ta rike hannunshi yayi jim tare da tsayar da idanunshi yana kallon ƙeyar Muhamat dake masha Allah dagaa zaune ma za ka gane ba ƙarami bane. Shigar da leɓenshi na ƙasa yayi cikin bakinshi ya ɗan ciza kadan sai kuma ya sake maida dubanshi kan wayarshi da yake dannawa bai kulata ba, tunkuɗo baki tayi gaba ta sake lafewa a kafadarshi ita ma bata sake cewa komai ba dan ta lura bai da niyyar yi mata magana, sai dai ita ai bata ga abinda ta mishi ba, kuma tunda har ya zo gidan da kanshi ya nemi ta koma, to tabbas yana buƙatarta ne a gidan, dan ta san wannan uwar biyun ta bakinshi ba abinda za ta iya tsinana masa dan ita ce sabuwa fil a leda. Sai dai bata san Abdul ya amsa kiran mahaifinta ne ba wanda ya na girmamashi fiye da yadda a yanzu yake ganin mutumcin Mamanta, ba dan ya kirashi ba da ya so ya barta ta yi ta zama a gidan, idan an tamayeta dalili ta ce dan ya je mata ne ta zo jinya gida, aikin banza kawai! Shi bai ma taɓa ganin irin wannan rashin hankalin ba a rayuwarshi. Sunna karasawa gida yanzu bai ciro jakarta ba, hasalima bangarensa ya nufa yana amsa waya da ta shafi kasuwancinsa Itama fitowa ta yi tana yatsina, ita ga matar oga matar so, Da isa ta dubi Muhammat ta ce" Kai ka daukon jakata ka kaita bangarena" Da mamaki Muhammat ya kalleta, sai kuma ya dauke idannuwansa da sauri domin hijabin ta kwashe ta bi bayan Abdul Tana shigowa yana gama wayar a zaune saman kujera ta shiga fadin" Bab, yanzu fisabililahi kana yi min adalci a rayuwa kuwa?, Ka duba ka gani a yadda aka daukeni aka tafi da ni, ashema kanada bukatata a gefenka ka wani shareni ba kira ba amsa kirana?, Bab soyaya fa ba karya bace, ni masoyiyarka nake ba makiyiyarka ba" Da mamaki yake kallonta, zai bata amsa aka sake kiransa A dole ya duba ya daga ya shiga amsawa A kalaman da yake yi karara ta fahimci gini ne aka yi a cikin gidan nan da ya dauki sunnan Mom twins gyaran amare, wanda ta ji da kunnayenta yana maganar cewa yanada bukatar wajen ya yi fili, kuma dukkan abubuwan bukatar da aka kawo na ginawa a saka a tabatar sun shiga wajensu a tsare kamar yadda ya bada a hoto Sun dauki dan lokaci sunna wayar dan mutumen famar da yake yi ya leko wajen, ama yace aa shi ba yanzu ba yana dai so a gama komai idan an gama zasu zo tare ta gani shima sai ya gani, abinda bai yi mata ba sai a cenza mata Risala har idannuwanta ke neman rufewa da duhu da tashin hankali Kallonsa kawai take yi har ya katse kiran ya juyo sashenta ya ce" Sorry, mema kika ce?" Maimakun ta dawo kan maganarsu, sai ta sake dubansa tana fadin" Abdul, gini menene ake yi ne?" Idannuwansa ya lumshe , sannan ya sake budewa ya ce" Wajen gyaran are ko mene, Na maman twins ne" Sake dubansa ta yi ta ce" Kuma a cikin gidan nan?" Shima dubanta yake dan son gane me take nufi Risala ta dafe gaban goshinta ta ce" Bama wannan ba, wai ba kace ka hanna mace sana'a ba?, Ba kace ba zan yi aikin saloon dina ba?, Ba kai da kanka ka shiga tsakanina da nawa neman ba?, A kan me ita zata yi?" Da farko ya so hawa ta hanyar da ta hau, watau kalubalantarta ita da kanta kafin ya tsigeta daidai da laifinta Sai kawai ya ga ciwon kai ne zai dorawa kansa mai zafin gaske Dan haka yana dubanta ya ce" Ba sana'a na hanna mace yi ba, bana son sana'ar da mace zata yi a waje ne, idan kema kina so sai a maki naki a nan cikin gida sai ku ringa yin abinku a cikin gida, ai nema hallal ne, ama ni na fi gane na cikin gida wa iyalina" "ABDUL, kennan kana nufin zama zaka yi na aure na dindindin da wannan matar da har kake kirrarin iyalinka? ABDUL hakan na nufin matar aure take a gidanka mai darajar da har ta samu wajen sana'a a cikin gidanka wanda yake nufin bakada niyar rabuwa da ita?" Risala ta fada a sanyaye ABDUL ya dago daga ringeshen da yake yana kallonta Risala ba zata daina bashi mamaki ba a rayuwa A nutse ya ce" Kina ji, da san samu ne mu ringa kauce irin wannan magangannun, kin ga kamar yadda kike da daraja a wajena haka takeda ita, maganar na zauna da ita ko aa wannan kuma ni ta shafa, haka kuma maganar abinda zan iya yi dan kyautatawa dayarku, Risala bana mayar da abu dole idan ba adininane ya koyar da ni ba......Amina matata ce, bayantama ban maku alkawarin auren zobe ba bale ki damu kanki, tsakaninku baki daya kuwa kowa ya yi ta kansa kawai, wanda ya iya allonsa ya wanke .....ai fili ne a gabanku!" Yana dasa aya ya mike ya haura sama dan futa zai kuma yi, ga wayar da Baba ya masa a kan auren jikar Baba Rabi'u na yana son ganninsa dan gudunmuwar da zasu kai, ga kuma zuwa da zai yi kauye su ga wasu dabobi da aka ce magada nada bukatar kudinsu, garke ne har shida na mahaifansu, zasu raba gado Shi kam abubuwan dake gabansa da yawa , ba zai zauna Risala ta ringa bata masa rai ba! , Tunda batada wayau ai sai ta yi ta yi. _____________________________________ Tunda Risala ta dawo aka ci gaba da gabatar da zaman kwana daidaya a tsakanin iyalinsa, rigimarsu suke yi a cen tsakaninsu a dalilin ginin gyara, kasancewar kowa da part dinsa ba lale ka san me dan uwanka ke ciki ba idan ba zumunci kuke yi ba, ko kuma kunna yaegumtar junna A wannan rigimar Harta baba sai da ya shiga, yace kuwa yana bayan jikansa, idan zata yi aiki a cikin gidanta ba laifi ta yi, in ba haka ba ta hakura, shima da ya yarda macen ta fita gashinan abinda ya haifar masa! Karshe dai mahaifiyarta ta tsaya kan ya zuba mata kudin da ya kashewa Amina tunda hakinta ne ai itama a asusunta, a zuciyarta kuwa ta kudurta a dai zauna zama mai sunnan zama, da kansa zai yarda ta koma bakin aikinta ne Kwanaki daidaya da yake masu sam Amina bata gane hakan sosai ba, domin yakan daga mata kafa ne idan ya gaza yake tarda ita da dabara da wayo ya cin mata, sai komai ya lafa ta gaza dago ido ta kalleshi dan kunyarsa da kunyar kanta, shi kuwa babu abinda yake sakashi daria irin lokacin, da ganganma yake mikewa yada ya fado duniya a gabanta ya yi tsaye, watarana har ihu take ta fice bayi da gudu tana fadin sam bashida kunya wannanba hali bane!, Ya yi ta dariarsa shi kuwa......... Baban abinda ke saka Amina a farin ciki a yanzu idan ta daga ido ta ga irin walwalar da kanwarta ke tsinta a hankali a hankali Bama idan ABDUL ya masu shigowar yama, A da takan gudu ta barsu da yaren da su Firdausin A yanzu kuwa sai kawai ta zauna nesa ta ringa mamakin tadinsu, da walwalarsu, da wasa da dariya Bama abinda ke sake sakata dariya sai Fido ta ce masa wai wani Dady, shi kuma ba kunya ya amsa abinsa Takan ji wani irin farin ciki idan ta ga sunna kus kus da Fido, Sam bata taba sannin me suke fadi ba, ama a yadda suke dinkewar su yi kuskus harma da Baba idan tana gidan sai ta ji wani irin kwonciyar hankali na samunta a cen kasan zuciyarta Da wannan ta je ta zanna jarabawarta, jarabawar da ta ringa shan wahala a kan ajiyewa kadai bama har ta samu damar zannawar ba Jarabawar da babu abianda bata ganni ba a kanta Har an so a wulakanta mutuncinta a kanta Har an so a wulakanta mutuncinta a kan jarabawar nan An nuna mata idan tana so ana iya bata hanya ama idan itama zata bayar da wani abin da take da shi kuma takeda iko da shi Kiri kiri saboda dan cikon da bai taka karra ya karya ba aka rike mata hannunta harma aka so a nuna mata itace ta ki ci gabanta a duniya Sai gashi ta zannata a mutunce, a kamilance, a hakimce a bayan motar da Muhammat ya ja bayan ABDUL ya yi mata adu'ar Allah ya tsare ya bada Sa'a Suka je ta shige aji ta zanna ta fito ta samu Muhammat na jiranta, harda abin karin da ta sha mamakin yadda aka yi ya san yinwa take ji, har mamakin kanta take yi kafin ta fito fa sai da ta karya tare da Fido da ta yi dan wake tun da asusuba, ta ci dan waken nan kamar ba gobe, kuma sai gashi tun kafin a fito wata yinwar na yi mata wawushe da kayan ciki, kuma yinwar nan fa idan tana ji bata jin kunyar cin abinci a gaban kowa Bata san tana ci hannu baka hannu kwarya ba a cikin motar sai da ta cinye tana lumshe ido tana kora ruwa mai sanyi ta dubi wajen Muhammat ta ce" Ama muhammat wannan dambu ya yi dadi, a ina ka siyo shi?" Muhammat ya yi murmushi yana kadda kai, watau abinda ya faru ogansa ne yace da shi a ina za'a samo abincin gargajiya, dangin abinci dai na gargajiya, idanma da hali harda dadawa Shine ya je ya samu Matarsa ita kuwa ta kaishi gidan da ake yin dambun nan suka siyo Yana kai masa yace aa ya je daukan Uman biyu da shi zata so samunsa a wannan lokacin Har yana mamakin dambu kuma uman biyun?, Sai gashi ta cinye tsaf Muhammat ya ce" Mom twins ai a gidan wata kawar madame na siyo shi" Amina ta gyada kai tana fadin" Muhammat ta iya dambu, man kulin nan da ta saka ya yi dadi sosai, mu je mu karro in ajiye da yama na ci, sai na ji ko kulun shi zan ringa ci ba zan gajiya ba, ama ka san wannan dambun ba na gaz bane ko Muhammat?" Muhammad da ya dauke wuta tunda tace su je su siyo yana tunanin ai bama zai tarki zuwa da ita ba Sir ya nadi hancinsa ya ce" ai da itace take yi, ko man da itace take soyawa, ai bakiga ba tsaftarta, ama yanzun gida zan kaiki sai na koma na gani idan akoy na karro maki" "Aa Muhammat, ba gida zaka kaini ba gaskiya, zuwa zamu yi na siyowa baba, na tabata idan ya taba dambun nan gobema sai ya sa an siyo masa, mu he mu sayi da yawa a kai masa nasa nima na tafi da nawa gida" Amina ta fada tana buda yar jakarta dan ta ga tanadin jakar, kar aje ba nauyi tana ta maganar aje ta sayi dambu Waje ya samu ya parker yana fadin" to bara na amsa kira na dawo mu tafi Daga motar ya fita ya koma gefe ya danna kiran ABDUL da fatan Allah ya sa ya daga da wuri, duda ya san da wahala ya ki dagawar , ama kuma idan aiki ya masa yawa yakan ki dagawarma Koro masa bayani ya yi dala dala, wanda hakan ya saka ABDUL neman excus ya fito daga dakin meeting din da suke yi da bakinsa yana sake fadin" Wai kai wa ya aikeka fada mata ga inda ka siyo? Muhammat bakinka ba dai magana ba, yanzu idan babu fa?" Muhammat ya ce" Nima abinda nake ta tunani kennan, kar dai ta yi wannan kuka nata na shiga uku" ABDUL ya dafe gaban goshinsa ya ce" Kana ji, ka fara kiran matarka, ta je ta yi jiranka a zuba a daure, ka yi ta yawo da ita kafin ku karasa a tabatar an daure komai , kawai a miko maku , ku je wajen baban daga cen sai ka maida ita gida" Muhammat ya ce" In sha Allah sir" Har zai katse ya ce" Kana ji?" Mummamat ya amsa da "eh sir ina ji" "Muhammat kar ka yi tukin ganganci da ita ka ji?" ABDUL ya fada a hankali yana duban agogon hannunsa. Muhammat na murmushi ya sake fadin" Bi'izinillah Sir" Ai ko gidan suka wuce, Muhammat ya fita daga motar ya jira kaɗan matarsa ta miƙo masa dambun sannan suka wuce gidan Baba mai Shanu. Tunda suka shiga bayan sun gaisa, bata nemi hawa wajen hajia ba, domin ba haka tsakaninsu, idanma ta je zata dauki wulakanci a hannunta ne na gori kala kala, Da zumudi ta masa tayin shin ta zuba masa dambu zai ci? Baba ya kalleta da mamaki yace "Uman biyu yau kuma dambu aka yi?" Da fara'a a fuskarta tace "A'a Baba, ai a hanya ne na sa Muhammat ya tsaya muka siyo, wallahi Baba baka ji dambun ba? Na zuba maka ka ci za ka ji daɗ..." Yar sauran harafin daya rage ne ya makale dan ita wallahi kallon da Baban yake mata kamar wanda ya ga wani abu a jikinta, irin kallon mamakin nan ne da kuma son gano wani abu........, Dan kallon jikinta ta yi , kar aje ko abincin ta zuzuba a jikinta bata sani ba? Murmushin da ya saki tare da girgiza kanshi gefe daya ya sake tabbatar mata da lallai fa Baban wani abu yake tunani a kan ta. Amma tunda ba tambayarshi za ta yi ba sai kawai ba ta ce komai ba aka bar zancen, amma kam yannayin nasa kamar wasu lokuta yaron nan dake sakata a duhu kuma ya barta da duhun kai yake mata shi ma. Dake kwanan Risala ne yau kuma ba wani damuwa take da shiga harkar yarinyar ba, har fridge din falon ta zo dan daukar kakkaurar madarar da suka rage dazu ita da Fido, dan wallahi idan tana sha ji take kamar za ta tsinka harshenta Tafiya take tana jan kafafunta dake sanye da silifas masu laushi na daki tana susar bayanta da yar yatsarta, kuma a ganinta darene ai kowa yayi bacci, shiyasa ta fito da riga da wondonta na cotton da suka dan saketa har jikinta na rawa a ciki, iya hula ce a kanta wacce ta tsaya a rabin kanta kamar za ta fadi. Har ta buda fridge din ta dauko farin bidon ta kalli madarar mai kaurin gaske da sanyi, rufewa tayi ta juya da niyyar komawa dakinta. Hada ido sukayi da Abdul da ya fito daga dakin Biyu zai koma makwancinsa, domin Risala har yanzu bai idasa sake mata ba, dan tunda ta dawo ya kan je dakin ne ya ga lafiyarta, amma yana so ya barta tayi hankali kafin ya sake nuna ita ma matarsa ce, dan ba zai iya da wannan kwaroroton tereren tara masa dangi ba daga abinda bai kai bai kawo ba.........sirrinsa abin boyewa ne da karfin gaske ba abin watsawa bane! Kyaɓe baki ta fara yi tana lullumshe idanu, sai kuma ta ɓoye madarar a bayanta ta zura hannunta cikin bayan rigar ita a dole kar ya ga me ta zo yi, a nutse ta shiga takawa ba ta sake kallon inda yake ba sai ma gunguni da take kasa kasa a kan me bai yi bacci ba shi din? Shi dai yana tsaye bai ce mata kala ba har ta shige dakin ta maida kofar ta rufe, wani tattausan murmushi ya saki yana girgiza kai a ranshi ya ayanna 'Uman biyu kennan' *Bayan kwana biyu* dukansu gidan Baba Rabi'u suka je bikin jikar tasa, duk da ba wani shaƙuwa ce tsakaninsu ba amma dai tare suka tafi bisa bukatar Baba da shi ABDUL din , harma suka kwashe awannin nan tare, ama kowa da inda ya fi karkata, domin Hajia na cen wajen tsofafin wajen sunna nasu shagali na iyaye,Amina na wajen amaren sunna nasu shagali , Risala na nata eriyar tana nata shagalin har lokacin dawowarsu gida yayi Abdul da kanshi ne yake tuƙasu Hajia na gaba tare da shi sai ita da Risala a baya, inda Muhamat ke tuƙa Baba da biyu, ya zamto motar sunna bibiyar junna ne, watau daya a gaba daya a baya Motar shiru da fari ba mai wani magana, sai kuma Hajia da Risala da suka fara yar hirarsu da Abdul ma shi tsakani da Allah yana jin me suke fada amma baya gane gaban zancen, gyara zama Hajia ta sake yi ta buɗa jakarta ta lalubo dabinonta irin na kwalin nan ta fara ci, dan bata ci abincin bikin ba, sam lamarin matar Rabi'u ba classs, yaushe zata barawa mutanen gida su yi girkin abincin auren jikarta? Ga kampani na ma'aikata dake girki kala daban daban maimakun su je su dauko a yi girki a tsare da kiyayewa ...aaa, sai ta bari yan gida suka jamalmala, shi yasa ta kasa ci gaskiya, dan a matsayinta ba zata wanke goma ta durmiya biyar a cikin abincin vilagggssss ba! Ɗan kallonta Amina tayi daga baya, dan a barin da ABDUL yake ta zauna, tana iya gannin hajiar da abinda take yi har zata ɗauke idanunta sai kuma ta sake kallon dabinon, irin yanda ya jeru raras a gidanshi yayi ja mai kyau da alamar masifaffen zaƙi, sai kawai ta ji yawunta na wucewa ba tare da ta ankara ba alamar dai so take yi sosai Ba ta ankara ba, ba ta kula da ta kasa dauke idanunta akan dabinon ba har saida Hajia ta ci mai isarta ta maida sauran a jaka tana korawa da ruwan roba. Abdul da tun fara kallonta ga dabinon ya kula, da fari ita yake ɗan satar kallo ta madubi, da ya ga ba ta ko kyabtawa sai ya maida hankali kan abinda take kallo, hakan yasa shi kallon hannun Hajia ya sake kallon idanun Aminatu ta madubi. Yanzu kuma da Hajia ta maida abunta sai ya kula da yadda ta dauke kanta da yanayin rashin jin dadi tare da dan turo bakinta gaba ta jinginar da kanta sosai irin na yaro dai idan yana son abu aka hanna masa, murmushi kawai ya saki yana ci gaba da tukinsa A ƙofar gidan Baba Mai Shanun aka tsaya dan sauke Hajiar da motar su Baba dake bayansu, Hajia na buɗewa za ta fita Amina ta rigata fita tare da bude bakinta ta kwaranyo aman da ya tuƙota yanzun nan ba tare da sanin dalilinsa ba Da sauri ya fito daga motar Hajia kuma ta zagayo duk suna kallonta da yi mata sannu a tare, dan dukawa ta yi tana yi harda rintse ido yatsina fuska Risala tayi ta ɗauke kanta tana jin kamar zata yi aman itama dan kyankyami tana duduba jikinta kar aje iska ta dauko aman ta watsa mata a jiki tace "Cussss, wata ƙazama da ita." Da yanayin kulawa Hajia tace "Dama ba ta lafiya ne ko kuwa abuncin cen ta kama ta yi ta nanaga??" Abdul da hankalinshi ke kanta ne yace "Ban sani ba Hajia, sannu ko Amina? Taso ga ruwa" Ya sake fada ma Aminatu dake share fuskarta da gumin data fara hadawa, ta mike da kyar ta miko hannu ta amshi ruwan goran da ya dauko ya miko mata, hankalinsa gaba daya a tashe, sai ya nufota kamar zai rikota sai ya ga ta dan kauce dan idannuwan Hajia da kuma su Baba da suka karaso har suka zo summa suna tambayar lafiya? Abdul ne ya fada mishi a taƙaice, hankalinsa a tashe, sannan yana ta auna abinda ke iya sakata a wannan halin, domin dukkan motsin Amina biye yake da shi sau da kafa Ya fita sannin abinda ke tare da ita da dukkan hanyoyin da ya dace ace ya bi dan taimaka mata A gidan Firdausi ta sani, Baba kauratu ta sani, su din da kansu sunne suke sake sakashi a hanyar da mai ciki keda bukata dan samun kwonciyar hankali irin su kwadayinta dai, da yan rigingimmun da na Amina ya zo mata da shi, domin bata laulayi sai na harshe da kuma ciye ciye Da farko ita din da kanta ta fara damuwa da ciye ciyenta, sai kawai suka hada baki idan ta dan nuna yanzu batada aiki sai ci, sai a nuna mata ai hanjinta ne ya warware dole ta ringa ciye ciye, ai cenjin yannayin kennan Sai kawai ta hau ta zauna, tunda ba taba yin cikin ta yi ba, bata sani ba ai Ba zai manta lokacin da ta ce tana son cin abincij nan da ake kira da ABACHA na Yoruba, kafin a samo masa mai yinshi ta yi aman nan A hankali ya kalli Hajia yace "Ina ga fa kamar dabinon da kika ci ne ya jawo hakan." Da wani kallo ta bishi ta ce "Ban gane ba? Guba na ci ne? To me ya hada cina da amanta" Girgiza kai yayi yace "A'a, nufina ko tana so ne, dan na ga tana ta kallo" Kallon Amina tayi tana mata kallon sama da kasa, aman da ta yi ta kwaye hijabin da ya rufawa dima diman duwawunta asiri , yanzu da ta dan duka suka dan bayana kadan cikin tsalelen lesh din dake kasa wanda aka yiwa dinkin doguwar riga ya kamata sosai dan dinkin kamar cif da cif ne a jikinta tace "Sai ka ce wata dangin mayu? Dan kawai tana so sai ya kaita ga amai." Murmushi Baba mai Shanu yayi Abdul kuma ya kyaɓe baki ransa na neman bacewa Baba mai Shanu ya sake duban Amina da kyau, juyawar da Hajia tayi za ta shige cikin Baban bangarensu yasa Alhaji faɗin "Au! Ba za ki bata dabinon ba Hajajjuna?" Juyowa tayi duk sun tsatsareta da idanu, sai kawai tayi kamar za ta fashe da kuka tace "Saboda Allah me ye haka? Kawai daga ganin abu sai a ce shi ya sakata amai, to idan na bata ta ci ta kara amai sai a ce ni ce kuma ko? Ga dukkan alamu itama yarinyar nan ba wani kaunata take yi ba ake min dole sai na sota" Girgiza kai Mai Shanu yayi yace " Bafa haka ake nufi ba ke kuwa, Kin manta lokacin da kika taɓa ganin goriba a hannun almajiri daga mun tsaya a bakin danja?" Ƙura masa idanu tayi irin tana son tunawa, sai kuma tace "E, lafiya?" Saida ya saci kallon Abdul yace "Da na hana miki saboda a ganina a hannun almajiri yana cin abinsa yaushe zamu tsaya ya baki goriba tsakani da Allah, ba saida kika kwanta asibiti ba?" Da yanayin rashin fahimta tace "E, sai me to ai a lokacin ni banida lafiya ne" Shafa wuyanshi yayi da hannunshi mai carbi kamar mai rad'a yace "Sai ya zama dalilin da ya kwantar da ke ne ita ma ya sakata amai ai ur excellency ." Zazzaro idanu tayi ta kalleshi da kyau, sai kuma ta maida dubanta kan Amina da ka rantse kuɗin aika ta ci tana tsatsare Alhajin da kuma Hajia da idanu, da muryar rawa rawa ta nuno Aminar da yatsa tace"... ke ciki ne da ke?" A zabure Amina ta muke tsayinta gaba daya tana kwalalo idannuwanta, Risalama ta juyo a zabure gabanta ya yanke ya fadi kamar zai fito ta bakinta ABDUL kuwa a nutse ya yi taku biyu ya tsaya jikin mota ya zubawa Amina ido zuciyarsa na begen abinda baya kwana da shi bale tashi da shi a zuci Baba kuwa murmushi ya yi ya sake tsayawa kan kafafuwansa lokaci daya shi da Amina suka yi magana, Amina ido a waje tana dafa kirjinta ta ce" Wa ni? Aa aa banida komai......m" Baba kuwa ya ce" Kwarai kuwa shine dai " A haukace Amina ta juya barin Baba ta ce" Nzl 46 A rikice, tare da tarin tsoro, da mugun son kare kanta, da tsoron kakarsa da ya shigar nata zuciyarta tana kallon Baba ta ce" Baba, ni kuma? Baba banida komai, Baba walahi banida komai, Baba ni tsakanina da shi babu komai , gayanan a tambayeshi ni walahi baba bana shigama harkarsa, , Baba dan Allah ka rufa min asiri da maganar nan, idan kuwa inadama cikin Nan walahi sai a zubar shikenan ya bani takardata na tafi, dan Allah Baba kar ya zamto inada ciki" "Ke!, Kinada hankali kuwa?, Kinada hankali?" Hajia ta fada da wata irin murya mai girma da bacin rai Amina ta girgiza kanta tana neman tsugunnawa ta ce" Hajia, walahi walahi ba maganar soyaya bale a kai ta son ajiye iyali a tsakanina da shi, gayanan ku tambayeshi zai baku amsa, ABDUL, ABDUL, ABDUL dan Allah ka ce banida komai ka ji ABDUL?" A irin wannan lokacin , ko baka san Amina ba sai ta baka tausayi, domin magana ne take yi dan ceton ranta, magana take yi dan a fahimceta, hankakinta a tashe burinta a fahimceta, a yi mata uzuri, sai dai ba kowa ne a wajen nan ya fahimci inda ta dosa, shin ina zata saka ranta ne?, Ina zata dosa ne? A gaban Hajia matar da ta tabata ba kaunarta take yi ba, ta tabata abinda zata guji ji a duniya kennan cewa ta dauki cikin jikanta daya kwal a duniya, ita din da kanta tashin hankalinta ne hakan A rikice tana girgiza kai ta ce" Hajia, dan Allah, idanma haka din ne Hajia a zubar , a zubar Hajia" "Dan tsananin kiyaya ne ba zaki haihu da Jikana ba?, Dan bakya sonsa?" Hajia ta sake fada a kausashe, Baba dake tsaye jikinsa ya dauki wani irin sanyi yana kallonsu shima, Gefe daya ABDUL na jingine da motar nan Amina kawai yake kallo, Uwa uba Risala da take ji duniyar tai mata zafi, take ji kamar zata mutu a tsayen da take itama tana kallon Hajiar da Aminar Amina ta girgiza kanta ta ce" Hajia ba maganar Kiyaya bane, Hajia ba maganar kiyaya bane a lamarin, rashin cencentar ne Hajia" Da haushi Hajia ta ce" Kin ga saurara, ki saurara min haka da magana kamar zaki summa, daj walahi kin ji na rantse maki idan wani abu ya samu cikin nan sai na yi shara'a da ke!, Ke har zaki yi maganar rashin cencenta? Kina nufin jikana bai isa ya zama uban danki ba ko me? Ki kalleshi da kyau, daga sama har kasa, ke kin san Allah ne ya wanke ya baki, kar ki saki ki yi gigin taba lamarin cikin nan , walahi walahi kin ji na rantse maki!" Tana gama fadan ta juya ta cara hawa yar matakalar biyu, sai kuma ta juyo jin Risala ta fashe da kuka ta shiga fadin" Ciki? Ciki fa? Ciki gareki? Dan Allah ciki gareki? ......" Sai kuma ta juya wajen ABDUL tana kallonsa ta ce" Ni me ka min na adalci kennan?, Kamar bambanci ke wakana karara tsakanina da kai ABDUL, haka ka mara gini a cikin gida nace zan koma aikina kace nima sai dai idan ginnin nake so, bayam ni ba zan iya sana'a a cikin gida ba, dama ba maganar aikina kace ba zan yi aiki ba, kuma yanzu ABDUL ciki ne da ita? Ni fa wani laifi na yi mai tsauri da ya zarce sonka da ni baka bani cikin ba?" Hajia Kanta sai da ta zarro ido tana kallon Risala, Baba kuwa kansa ya dauke , Abdul kuwa ya zuba mata ido itama yana kallonta Hajia ta dawo ta ciro ledar dabinon har biyu ta kamo Hannun Amina for th first time a rayuwa ta damka mata dabinon tama fadin" Wuce ku tafi , Allah kiyaye" Daga haka ta yi ciki, suka sake binta da kallo su duka, Harda Aminar, haka kuma lokaci daya yawunta ya sake tsinkewa da ta sake kallon Dabinon, ama sai ta dauke kanta ta ki ci ABDUL ya bude motar ya shiga kansa na sarawa, Risala ta yi tsaye bata shiga ba hakama Amina Baba ya dubi Amina ya ce" Uman biyu, jeki falo ganinan zuwa kin ji?" Amina ta gyada kanta ta juya ta shige ciki Baba ya dawo wajen Risala yana dubanta a tausashe ya ce" Risala, ki yi hakuri da jarabawar rayuwa kin ji?, Na san kina son mijinki, kuma shima yana sonki, wasu yan halaya ne da suka yi sabani da ra'ayin mijinki kike yarda sunna faruwa a tare da ku, da ace zaki duba ki gyara da kin ji dadin zama da mijinki fiye da tunanin ki, ki sani yata mijinki bai tsane ki ba, hasalima yana ra'ayinki, domin da akasin hakan ne na tabata da tuni ABDUL ya salameki, dan na san waye ABDUL, koda ya yi biyaya idan baya ra'ayin abu zai sabule masa ne bale babu wanda ya tsaya da bindiga a kansa dangane da ke, ki iya rike masa sirrinsa, ki masa biyaya da zuciya daya, na tabata zaki fi kowa jin dadin zama da shi kin ji?" Risala dake hawaye bilhaki ta gyadawa Baba kai tana sake sada kanta hawayenta wani na korar wani Baba ya sake fadin" Idan kin jw gida ki yi nazari a hankali ki ga idan har kin amince da maganar a yi maki ginnin a gidanku ki sanar min kin ji ko? Kar ki yi nauyin baki ko ki ce ai an baki kudin hakan, ki sanar min, kwonciyar hankalinku ake nema baki daya" Risala ta sake amsa baba sannan ta je ta bude motar su Muhammat ta shiga, dan irin kallon da ABDUL ke mata ta tabata idan ta bishi a haka sai ta raina kanta , dan abinda ya fi damunta zai yi mata, watau ya yi watsi da ita baki daya Baba ya je wajen motar ya bude gaba ya shiga ya zauna yana dafe habarsa hadi da zubawa madubi ido Cen ya yi murmushi yana gannin har an rufewa Su Muhammat kofa sun tafi shi kuwa bashida niyar tada motar bale ya tafin, ya tabata kulafurcin abinda bai yarda bane ke damunsa Dan murmushi ya yi ya ce" Karen uwan nana kaya, ka san na shirya tare Kakar gwamna kuwa? Na zata tana jin cewa Uman biyu nada junna biyu summa zata yi, ka ga sai ta yi wani abu mai kama da tana son cikin, ko dai bonono take son min ta lahanta yar mutane yar marainiyar Allah?" ABDUL ya kalleshi da haushi haushi ya cire kai yana gyattu, shi fa gaba daya Baban yau ya kunnashi fiye da tunaninsa, wai ashema ya fada ne saboda matarsa ta ji, shi abin haushinma waye ya ce Masa Mom twins nada ciki? Ya wani zo ya bude haka kaai tsaye ? Baba ya ce" Toh fa, yo ABDUL RA'UF ni menene laifina a ciki? Ai dai ba tsoron tace bata sonka ke damunka ba ko?" ABDUL ya dube shi ya ce" Ka ga kawai ka yi shiru, aiki ne ka riga ka yi sai ka je ka sha juss ka huta, in bama abu ba ta yaya zaka kunnan mata biyu ka wani koma gefe kana kallonsu? " "To nima tawa matar ba na bata mata ran ba?" Baba ya fada yana kallon Abdul ABDUL ya ce" Wannan ku ta gano, yau kuke yaki ne? Haka kawai ina lalabawa ka zo ka bude a cikin jama'a, yanzu ka kyauta kennan?" Baba ya karkato yana nuno shi da yar yatsa ya ce" ka ga Abdul RA'UFu ka ji tsoron Allah, yo ni meye laifina a nan kuma? Ni nace ta yi aman ne ko ni nace a tambayi me yake damunta ne? Daga fadin gaskiya sai ka rufeni da fada ni da ka raina ko? Ai su baka yi masu fadan ba , du abinda Uman biyu ta yi maka ai bakaa yi mata fadan ba dan kana jin tsoronta" ABDUL ya sake kufula ya ce" Ninema nake jin tsoron matanaa ko? Na ga ai ni da na hannasu aiki sun yi? Ka ga kawai dai ji ka sakani a uku ka ji dadi!" Haba Abdulahi, ni banma taba gannin jarumi tsaye gaban mata ya maze masu irinka ba, ka san ko yayane namiji a matansa akoy wace ke masa kwarjini, koma nace kawai take bashi tsoro....ama kai ana rikici ko a baka ce da ko daya ba, ai wannan sai mazaje" Da mamakin Baban ya kame haba yana kallonsa Daria Baba ya yi kadan sannan ya yi shiru yana dan girgiza kansa , bai taba tunanin zai ga reaction irin haka daga Hajia Hauwa ba, shi har ga Allah a ransa tsoro daya ya ji kar aje ta summa su nufi asibitin dole, duda magangannun da ta yayabawa Uman biyu ba dadin ji, ama abinda shi ya hanga a tatare da ita wanda shi kadai ke iya ganninsa, tarin ruwan da ya cika idannuwanta da son ta rukunkumi Uman biyu, ama ta gaza ko kunya ce ko menene oho, a bashi mamaki, to shi a tunaninsa ai du yadda take kaunar Allah ya nuna Mata ya'yan Abdul ya zata idan Amina ce dauke da cikin ba zata so abin cikin ba "Shin, Shin , ba zata taba ajiye maganat girma a gefe ta fuskanceni ba? Ba zata taba yin hakan ba?......... ALKALI tauye yarinyar nan nake yi ne ko me?" ABDUL ya fada a hankali sosai, yana idasawa da dan jimke hannunsa kadan ya kai wajen hancinsa, sannan ya juyo yana kallon Baba da ya yi tsai yana kallonsa "Kana son ta ne?" Baba ya fada a hankali yana kallonsa ABDUL ya yi shiru, shiru na dan lokaci A hankali ya sake duban hanyar falon, a sanyaye ya ce" Ban san me take tunani da shekara daya tak da ta bani ba......................, Ko kuma abinda ke riketa soyayar wanina ne?" Baba ya sauke ajiyar zuciya, ABDUL dinsa abokin shawararsa ne, babar shawara ko karama, tun mahaifansa da rai , yakan yi masa hira mai girman gaske , a yanzu haka, duda harshensa yai masa nauyi a lamarin nan shi ya fahimci yana cikin zuciyarsa ya yi masa riko mai wuyar fasara A sanyaye ya ce" Kar ka riketa da furucinta ABDUL, ka sani ta fadi haka ne dan tana cikin tsoro da firgicin abinda Hauwau zata yi mata a kan hakan" "Koda da maganar tsoro, da maganar abinda yyake cikin zuciyarta, idan am tsorata ba karya ake nemowa ba, gaskiya ake fada Baba" ABDUL ya fada shima yana tare numfashin Baba Baba ya sake fuskantarsa yana karantarsa A nutse ya ce" Ko me ka fuskanta kar ka yanke hukunci cikin fushi ko rashin nazartar Abu ....... Ka yi mata Uzuri ka ji?" Shiru ne ya dauki wajen, na lokaci mai dan tsayi domin Har baba ya fara kama abin motar zai fice dan ya kula sun juyo yan miskilancin ga kuma bacin ran da yake cinyewa baya so ya saki a fahimta A hankali ya ce" Ko me zata yi, ta yi kokari kiyaye abinda yake cikinta.....Baba ina son abina ko menene, idan abin kunya zai zamto a gareta ta haifo min sai ta bar min, ko shege ne ba zan ji kunyar rikeshi ba bale dan halal" Baba ya lumshe idannuwansa ya sake jadada masa kalmar hakurin dai sannan ya fice a motar yana tafe a hankali duba da yannayin girma da kuma yan ciwace ciwacen jiki, a dole kuzari zai rage sosai, danma ana cikin kula ne Sai da Baba ya shige sannan ya ja motar ya wuce gidan gona direct, dan baya jin zai iya binsu gida a yanzu Da salama Baba ya shigo falon yana fadin" Gafararku dai Uman biyu" Nzl 47 Kafafuwan da Amina ta watsa tana hawaye ne ta tatare tana jan Hanci muryarta a shake hadi da fadin" Shigo Baba" Murmushi ya yi ya shigo din yana fadin" Kai kai kai masha Allah, uman biyu wai kwonci tashi yau Rabi'u ya aurar da jikarsa mai sunnan Kulu, ni kam a da idan yar ta zo gaisheni sai ni kadai na ringa yunani, sai na samu kaina da tunanin oh sunna zannen mutun, to Uman biyu zanen mutun mana yarinyar nan baki ganta ba yar tsakure da ita yar kadan, ama akoy iya kwaliya da daukan wanka fa iya tafia , wani lokacin sai ka yi zatonma yar faransa ce" Maman Biyu dake sauraronsa tana binsa da kallo har ya nemi waje ya zauna yana zuba sam bata gane ma maganar wa yake yi ba, ita abinda ke ranta yana ranta ne Baba ya idasa zama yana fadin" Ya zuljalalu wal'ikram" Dubansa ya maida wajen Amina ya ce" Uman biyu yau fa inada shekara Saba'in da kwanaki a sama, tsufa kam ya zo, Alhamdulilah, Allah dai ya sa mu yi tsufa mai alkhairi mai tatare da abin alkhairi sannan ya sa mu cika da kyau da imani" Amina ta bude bakinta a hankali ta ce" Amen Baba" Dabinon dake ajiye ya mika hannu ya dauko ya bude shi sosai yana kallonta ya ce" Maman biyu amshi ki ci dabinon mana" Amina ta kalli dabinon, haushinsa da son cinsa na mata yawo a zuciyarta A hankali ta girgiza kai tana son sadda kanta Baba ya ce" Ba kyau ai mayar da hannun kyauta Baya, amshi yar albarka maza amshi, bara na dauki biyu nika na dandana, irin dabinon nan irin dadinsa, gashi bashida ila shi dabino ko kadan " Tana kallonsa ya ciri biyun ya fara ci Jiki a mace ta rarafa ta amsa ta koma ta zauna ta bude ta shiga ci Ci take yi har tana lumshe idannuwanta, shi kuma Baba yana kallonta yana murmushi har ta kai koshi, domin yanada yawa a nanage yake, ga ruwa gefe na goran da ABDUL ya bata ajiye ta dauka ta kora tana jin yanzu kam batada wata matsala a duniyar da ta wuce maganar ciki, Murmushi Baba ya yi zuciyarsa cike da farin ciki ya sake mayar da dubansa kanta bayan ta gama shan ruwan tana sauke ajiyar zuciyar samun nutsuwa domin cikinta ya cika ba laifi ya ce" Su Uman biyu sai kike dubi tsabar idannuwan kakar gwamna kika nuna bakya son jikanta da dan tayin shalelen da na tabata idan har kakar geamna ta yi tsayin rai sai kun ga kauna gannin idannuwanku tsakaninta da dan jikanta, shine nake shan dariya, oh dan fari kam sai shi" A hankali ta fara shashekar kuka tana jan hijabinta ta kai wajen fuskarta tana sharewa Tsakani da Allah wata irin kunyar baban ce ta kamata wace a dazu bata jita ba Maganarsa ta doketa fiye da tunaninsa A hankali tana shashekar kukan ta ce" Baba, ni fa ba wai cewa na yi na tsani kowa ba fa baba, kai ai ka sani Baba" Baba ya gyada kansa yana fadin" Na sani sosai Aminar Gwagwo, nima ai na san zakiji kunya , to ama kuma abinda na gaza ganewa ta menece kunyar?" "BABA Abdul kanina ne fa......" Ta fada tana rushewa da kuka Baba ya kama bakinsa a hankali ya ce" Toh fa, haba ni kam nace kukan nan da kika samu Uman biyu ba kalau ba, ashe dai na gane, To Allah ya baki hakuri share hawayen mu yi magana kin ji?" Kai ta gyada tana share hawayen tana sauke ajiyar zuciya Baba ya sauke ajiyar zuciyar shima, yanzu kuma sai kalar damuwa ta bayana a fuskarsa A tausashe ya ce" Shin dama bakya son hadin nan kika yarda na yi? Ko wani abu yake maki na cin zali ne ban sani ba?" Amina ta rasa amsar da ta dace ta bashi, kanta a sade ta samu kanta da gyada kai da kuma girgizawa lokaci daya, irin amsar da mutun zai rasa me kake nufi, watau ita kanta a cikin rudun amsar dake zuciyarta take Baba ya karra tausasawa ya ce" Amina, ba zaki iya zama da Aban Biyu bane? So kike ya sawake maki ne?" Haba, kofa itace yar fari a wajen iyayenta ta dan halaci A duniyar kaf bayan rasuwar iyayenta Baba shine wanda ya fara talafata, sai Baba Lauratu, sai daidaikun datijan anguwarsu Mutumen da bai kyamaceta ba, bai nuna mata bambamci dan tana talaka ba, karshe yake cin abin hannunta da take jan ruwan rijiya ta girka masa, ya zo ya hada aure da ita da gudan jinninsa kwalin kwal wadda itace zata fadi girma da soyayar yaron a zukatan kakaninsa, idan ta bude baki a karro ba biyu ta yi wata wautar da kanta zata ba kanta amsar abinda ya dace da ita A yanzu haka abinda yake faruwa tsakaninta da bawon Allahn cen ma gidan cen zata ce a maza da ta sani babu wanda ya kaishi kima a idannuwanta Kawai ita dai bambancin shekarun nan ne baban damuwarta , bayansu batada wata damuwa da shi Baba ya sake tausasawa gannin ta lume a tunani ya ce" Idan har wannan din shine burinki, ki sani, ni Uba nake a wajenki, da farko zan fara baki shawarar ki je ki yi nazari, ki yi dogon nazari na rayuwa, ki sani koda kin rabu da Abdallah ba zaki koma gidan cen ba wannan alkawarina ne, ni zan zame maki gata a gidan duniya har na bar duniya, kar ki yi tunani a kan kaka naka yi ta rayuwa , ina nufin ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, muhali, da dukkan hutun da ya dace........tunanin da zaki yi shine na mutuncinki, abinda yake cikinki, yayanki dake kiransa Aba, uwa uba shi din da kansa Amina......., Ki yi tunani a kansa da kansa kin ji? Ki auna ki gani, shin wannan mutun ya cencenci zama da ke? Na san ke ba jahila bace, ba zaki yi riko da karfi dan kar ace ba, ki saki maganar kar ace, ki gyara Amina............. Kar ki manta komai girman abinda ke tare da na farin cikin da kike sama masa wata na iya bashi, haka kuma wannan baban abin dake tare da ke mai daraja mai mahimmanci kina iya rage kimarsa a zuciyar mahaifinsa............., Idan har kika yi tunanin nan kika yanke hukuncin ba zaki iya zama da shi ba, in sha Allah zan sama maki nutsuwar zuciya kin ji?" Amina da kanta ke kasa bata iya yin kwakwaran motsi ba tana sauraron Baba Baba ya sake maimaita cewa " Uman biyu kina jina kuwa ?" A hankali ta gyada kanta tana sake sauke ajiyar zuciya Baba ya ce" Zaki je ki yi nazari a hankali ko?" Kai ta gyada tana sake sada kanta Baba ya yi murmushi ya ce" Masha Allah, ki cire damuwar komai a ranki kin ji? Zamanin nan da shegema am daina boyewa bale dan Abdul? Ai ni nan in fada maki shagali kawai da kakar Gwamna, na tabata yau idan ta fara sadaka harda ni" A hankali Amina ta samu kanta da yin murmushi, domin irin yadda Baban ya yi dole ya saka ka darawa Dan shiru ne ya biyo baya, a lokacin Hajia ta sauko daga sama da waya a kunnenta tana amsawa ta nufo falon ta karasa kusa da Baba ta zauna wayar a kunnenta dai tana amsa abinta Baba kasa kasa ya ce" Ai in fada maki inaga harda party zamu sha" Amina ta sake sada kanta gabanta na faduwa, tsoro ya cikata, tana ji kamar zata tashi sama dan tsoro ta tsere Hajia na gama wayar ta sake Bin Amina da kallo sannan ta kalli Baba ta ce" Ita kuma me yasa bata bi mijinta ba?" Baba ya yi murmushi ya ce" Zantawa muke yi, kin san yar dakina ce , zancen sirri muke yi ai" Hajia ta tabe bakinta tana sake kallon kafafuwan Amina dake nanade ta ce" Ki mike kafafuwanki , ki daina dogon zama a haka, kuma kin ga miyar bikin nan da magi da komai kika tashi kika ci, ki daina haka yana da ila wa mai ciki kin ji?" Cike da kunya da tsoro Amina taa gyada kanta tana sake sinne kan nata Hajia ta dubi Baba ta ce" Kun gama sirrin ne Alkali?" Baba ya dubi Amina ya ce" Uman biyu, mun gamaa sirrin ?" Da sauri ta gyada kanta Baba ya ce" To bakua marmarim waina, ko dambu, ko kauco, ko tafasa, ko agwaluma, ko rake dai da sauransu? Ko madasho bakya son ci?, Idan kina son daya ki fada sai Kakar Gwamna ta maki ko a siyo maki kin ji?" Da mamakin Baba da neman rigima ta kafe shi da ido, tana jira ta ji saukar masifar matarsa kan yace wai ta mata abu ta ci? Sai ta ji shiru, asalima itama kallonta take kamar mai jiran amsarta A sanyaye ta ce" Bana son komai Baba " HAJIA ta dauki wayarta ta yi kiran Baba direba Minti kalilan ya shigo, ta dauki kudi ta bashi tace" Ka kaita gidanta, wannan idan ta ga wani abin a hanya ka siya mata yadda zai isheta, Ke tashi ku tafi gida mana yama na karra yi" Cicibawa ta yi ta mike tana kallon dabinonta da ya rage ta kasa dauka har sai da Baba ya ce da Baba direba ya daukar mata yana murmushi suka fice A cikin motarma kanta a hade da jikin madubin motar ta lumshe idannuwanta tana jin maganar direba sai tambayarta yake yi me za'a siya? Ama ta kasa bashi amsa har ya gaji da yawatawa da ita ya kaita gidan Tana fitowa daga mota Twins dake buga balll suka nufota da gudu sunna murnar dawowarta Hasan ya ce" Mama, kin ga wai ball dim da dady ya siya mana? Mama dady dinmu yana sonmu, muma muna sonshi Mama" A zabure ta kalle shi, Husaini ya katse mata kallon yana fadin" Bakiga fadan da ya yiwa prncipal din makarantarmu ranar da kb yace wai mu kamar shegu bamuda uba ne? Yace mata laifinsu ne da basa tsawatarwa yara har yaro ya iya fadawa dan uwansa haka sunna kallo, daga nan ai ya ciremu a makarantar yace shine ubanmu!" Numfashinta ta ringa ji yana mata sama da kasa A hankali ta ce" A makaranta ya cire ku?" Husaini dake rike da hannunta jin yannayin muryarta ya dago dubansa yana kallonta ya ce" Mama bakida lafiya ne?" Amina ta girgiza kanta ta ce" Mura nake Fadeel, nace a makaranta ya cire ku?" Hasan ya ce" Eh mana mama an jima ai, an sakamu a wata baba mun je da uncle ya biya komai kuma Dady ya je ya gani yace ta masa, sai ake yi mana lesson akace sai mun yi lesson na wata guda kafin mu shige aji da sauran yaren Ko Husaini?" A hankali ta dakata tana fadin" My boys, ku tafi ku buga ball din mana" Kai Husaini ya gayada ya tafi da gudu, Hasan kuwa ya sake zuba mata ido kadan, sai kuma ya saki hannun nata ya juya a sanyaye damuwar yannayinta na kama shi Sai da ta ga sun fara buga ball din ta idasa karasawa bangarenta ta kama abin budewar ta bude ta shiga falonta Nzl 48 Sai da ta ga sun shiga buga ball din sannan ta karasa bangaren nata ta kama abin budewar ta bude ta shiga tana jin tunaninta na sake harhade mata Daga kicin take jin dan motsi, bata nufa ba dan ta tabata ba zai wuce Fido ke girki ba , ya zama hajiar girke girke na gargajiya tana ta dura mata bata san abinda ke tare da ita ba, du sunna tunanin cenjin yannayi ne , basu san abinda ta kumsa ba Dakinta ta shige ta rufe ta karasa bakin madubi a hankali tana cire hijabinta Rigar dake jikinta ta lesh ta ja zif dinta kasa a hankali tana kallon kanta a madubin Jikinta ta zubawa ido, kan cikinta Shafewarsa ke son karyata maganar da ba likita bane ya tabatar mata A hankali ta dora hannunta tana kallo , tunani na yi mata yawa a ranta A hankali ta idasa tubewa ta kwashe ta kai wajen shanya ta shanya su sannan ta wuce bayi dan yin wanka Bayan ta fito harda alwalarta ta dauro ta dawo ta zauna ta sake daukan carbi tana ja hadi da zama ta hade jikinta waje daya A ciki ta yi sallar magariba, bayan ta gama a dole ta fito dan Firdausi sai bugawa take yi , suka ci abinci tare da yaren da Firdausin dake ta faman tambayarta maman biyu shin menene? Bakida lafiya ne? Hakama twins sai tambayarta suke yi shin lafiyarta? Batada lafiya ne? Ama amsar daya ce barci take ji Sai da suka gama ta mike tana duban Fido ta ce" Fido, dan Allah ki tabatar yarana sun yi wanka ku masu addu'a kafin su yi barci kin ji? Ni yau barci ke damuna" Firdausi da ta fahimci bayan barcinma akoy wata damuwar a tatare da yayarta, sai dai ba zata matsa mata da son ji a yanzu ba dan bata san me hakan zai haifar ba a hankali tana murmushi ta ce" Aunty, keda kin san ko sun yi barci Abansu sai ya kuma dubawa idan an masu komai yadda ya dace? Ke dai jeki ki yi sallah ki kwonta, Allah ya tashemu lafiya" Amina ta dan kura mata ido, sai take tunanin du kamar da gangan suke yawan sako maganar mutumen da take so ta kawar da maganarsa a ranta dan ta manta da shi kwata kwata Baki ta tabe ta juya ta nufi dakinta bata ce komai ba Firdausi ta bita da kallo tana sauke ajiyar zuciya, a koda yaushe ta dora kanta saman abin sallah adu'arta itace, Allah ya sa yayarta ta sauko dubanta gabanta ta gane me ke tare da ura na alkhairi, ta sani sarai yayarta ba dai son girma ba, tunda abu ya kasance haka kuwa sai a hankali, ama baban dana sannin da ba zata so ya tabata a garesu ba baki daya shine yayarta ta ki mijinta Mijinta shine mijin da kowace mace zata yi burin samu a rayuwa Wanda ya cancaleka, ya cancali ahalinka? Wanda ya mayar da naka nasa da zuciya daya? Bata taba tunanin akoy namiji irin wannan a duniya ba, ta zata masu kirkin basa tsayin kwana suke tafia su bar matan, lalatatun sunne cika gari, gashi dai jibi zata zubar da wankan haihuwar da ta yi da kuma rabonta da gidan ukuba, ita kam ta san ba ita ba aure, ba zata kuma ba, ba zata yarda ta kuma ba koda wasa, mijinta da ya zo babu wanda ya kaishi adini da nuna talaucinsu baya damunsa, ya kasance yakan talafesu da nasiha da yin uzuri, ama tana shiga gidansa ta zama tamkar makiyiyarsa, basa shan innuwa guda, a kulun kuma abin sake lalacewa yake yi.....bata yarda da bashida imani da tausayi ba sai a nakudarta, ba kowa ya kashe mata ƴaƴanta ba sai ubansu, wannan kalma tana fatan maimaitata a gaban mahalincinta da Mudi! __________________________________ Tunda ta shiga dakin nata ta yi shirin kwonciya barci ta kwonta da carbinta a hannunta bayan ta gama yin sallah tana saurare Kunnayenta ke sauraron falo har karfe goma na dare ya yi ta ji shiru ba ihun yara ba hayaniya ba komai A hankali ta tashi zaune tana duban agogon dakin da wani tunani na daban a cikin zuciyarta Sai da ta ga batada mai bata amsa ta koma a sanyaye ta kwonta ta sake yin addu'a ta lumshe idannuwanta Da kyar barci ya dauketa , barcinta mai nauyi A cikin barcinta kiraye kirayen sallar asuba ya farkar da ita , ta mike jikinta da nauyi na abin barci ta nufi bayi ta dauro alwallah bayan ta watsa ruwa dan ta saku, sannan ta fito ta gabatar da sallah still kunnayenta a waje,sai dai yanzunma babu hayaniyar komai, shiruya fi yawa Barci ta koma dan shi ya fi cin karfinta, har sai da kusan takwas na safe ta tashi a gigice sakamakon yinwar dake kwakular hanjinta A gagauce ta kimtsa kanta ta shafa turare sosai sannan ta fito falon Murmushi ta yi gannin Baba da Firsausi zaune sunna cin abinci Karasawa ta yi ta zauna kusa da su ta shiga hannu Baka , hannu kwarya tana gaishe da Babar lokaci guda Baba ta yi murmushi ta ce" Amina ki ci a hankali mana" Amina ta gyada kanta tana tausawa har ta hadiye sannan ta ce" Baba, wannan cenjin yannayi da saka cin abinci yake , bakiji cikina ba, jikina har rawa yake yi fa" Baba ta ce" Aya, hakane kin san sai a hankali dama , yanzu daga yannayinki ya saba shikenan, sai ki ga kin daina" Kai ta gyada a ranta tana ayana' Ba zan fada maku komai ba in sha Allah bale ku min wani kallon ' Sai da cikinta ya dauka sannan ta iya samun nutsuwa tana share zufa ta gyara zamanta tana kallon Baba dake yi mata bayani a kan maganar kwana arba'in din da Fido zata yi da haihuwa, waina da ake toyawa a yi sadaka koda abun ba rai, bale za'a hade da ta arba'in din yaren dai da sauransu Amina ta gyada kanta ta ce" To Baba , in wannan ne nima sai na bada kudin hatsin ai da kudi a wajena fa, ba sai na fada masa ba inaga" Baba ta dubeta da kyau ta ce" Aa Amina, ai dole ki fada masa, kin ga yanada hakin sannin hakan, bayan wannanma ai Uba ne baban wa uba ne Amina" Amina ta tsare Bakin Baba dake taunar goro yana kira mata ABDUL uba ne a wajenta Baki ta tabe ta kawar da kanta ciki ciki ta ce" Zan sanar masa" Baba ta kureta da kallo, Hakama Firsausi Baba ta gyada kanta ta ce" Allah shi kyauta, ni yau banma ganshi ba ai da ban tsaya shiriritar baki sako ba, na san ya fita tunda safe ko? Abdallah kennan sarkin nema" Firsausi ta ce" Nima jiya har na yi barci dai bai shigo ba, ama na san ba zai ki shigowa gannin ƴaƴan ba komai dare in dai ba tafia ya yi ba?, Uman biyu ko ya yi tafia ne?" Amina ta ciciba ta mike ciki ciki ta ce" Je ki gani mana dilla sai tambaya" A ranta kuwa ayanawa take ' Yaya za'a yi ya zo? Bai zo ba ai, dama ni ba wani son zuwan naka nake ba, kar ka zo din ma mana!' Baba ta cire kanta daga rakiyar Amina da ido ta maido dubanta kan Firdausi ta ce" wannan ya dai Allah ya tarota yarinyar nan" Fido ta talabe haba ta ce" Amen Baba, haka jiya bata tsaya ta kula kowa ba, tun nan na gane ba lafiya, shi yasa na ki kwonci sai da ya shigo gidan nan, wai ace Aunty ta bude baki a gabansa da gaban hajia ta ce baya sonsa?" A zabure Baba ta dafe kirji ta ce" Na ga annabi idan na yi hali na gari, ita Aminar? Kice ta lalatamu ta sa an saketa?" Firdausi ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Ya ki fada min komai, wannanma da kyar ya fito daga fatar bakinsa, shi dai damuwarsa ta yi hakuri ta kula da cikin nan, daga nan ya shiga dakin nata ya dan jima ya fito ya shiga na biyu ya fito yace min kar na nuna ya zo kwata kwata " Baba ta sake talabe kumatunta, tunaninta faya ne har ga Allah kar aje Amina na fama da aljannu masu taurin kai basu sani ba? Aa ita kam zata fara nemo taimako na rubutu da dan turare na aljanu ta fara yi mata ko a dace Nan suka wuni tare, kowa na walwala banda Amina dake cicin magani, abubuwan dake ranta gani take ya fi na kowa muni, shi yasa da ta ga su basuda wata damuwa ta saka hijabinta ta fice ta ringa kale kalen tsuntsaye da yannayin ginnin gidan ABDUL, tamkar ba za'a mutu ba, an yi gini kamar ba a duniya ba jama'a kuma mamalakin abin ya sheka a shekashi kabari daga shi sai likafani ko matashin kai babu A haka ta karasa wajen ginnin da akai mata Tun daga yannayin wajen take ta kallon tsaruwar ginnin da irin zannen da aka yi na gyare gyare kala kala, zane ne aka yi a jikin ginnin ba hoto bane aka lika Tunda ta karaso mai ba fulawowin da aka shushuka ruwa ya gaisheta sannan ya tambayeta shin ya amso ky ne? Samun kanta ta yi da zubawa wajen ido,da tambayar kanta shin a amso mata ky din ne? Zuciyarta na zumudin a amso, wata na gargadinta A hankali ta girgiza kai ta juya tana sake maimaita sunnan wajen a cikin zuciyarta ta koma cen bangarensu Tun daga nesa ta hango Risala ta yiwa wata cencadediyar budurwa rakiya, hakan ya sa ta dan rage tafiyarta gar suka gama matar ta shige motarta ta tafi, ita kuma ta juya ta nufi nata bangaren A hankali ta dauke dubanta a kanta, dan da farko ido ta dan zuba mata sannan ta shige bangarenta Sai bayan magariba Baba ta tafi, watau sai da ta yi jira ABDUL ya dawo ta samu ganninsa da kanta ta sanar masa komai, domin ita kam ba za'a yi haka da ita ba walahi, yadda yaron nan ke mutuntasu ba zata kasance cikin shiritar Amina ba Ai kuwa, halayansa na girma ne ya gabatar A yadda ya dauki abin da irin yadda ya yi maganar sai da ta ji kamar ta fasa kukan dadi Bayan sun gama maganar duka kaf abinda za'a yi wanda sai da kyar ya yarfa aka dan rage ya fuskanci Baba a nutse ya ce" Baba, dama a kan maganar Firdausin nake son mu zauna da ke, sai gashi yau kin zo" Baba ta gyara zamanta a saman kujerar falonsa da ya yi ya yi da kyar ta zauna , domin da farko a kasa ta so zama gannin yana sama, ama firr ya nuna shima ai kasan zai sauka idan har ta sauka A hankali ya ce " Kasancewar ba takaba bace take yi, tana da damar fita, shine nake son sannin a fannin makarantar boko da ta islamiya a daidai ina ta tsaya? Domin ina so ta je ta ci gaba da karatu dan ta karra warwarewa ta manta komai" Sai da idannuwan Baba suka cika da kwallah, harda tarin jin kunyarsa tana sake sada kanta kamar shine baban , itace karamar ta ce" Oh, Elhaji da wannan wahala haka, Allah ubangiji ya saka da alkhairi, yadda kake talafin marayun nan kaima Allah ya dubeka ya ji kanka, ya kareka a duk inda kake, Allah ua saka maka da mafificin alkhairi ka ji? Allah dai ya karra rufa asiri sannan Allah ya shiryi Uman biyu ku yi zamanki lafiya lau" Da farko shiru ya dan yi, sai kuma ya sadda kansa a hankali ya furta" Amen summa amen" Baba ta sake fadin" A yi ta hakuri, a yi ta hakuro, ka san mace da namiji yannayin hankalin ba daya ba, a dauka yarinta ce da kuma hankali irin namu na mata, a yi ta hakuri da komai dan Allah" Yanzuma kasa kasa ya amsa da" In sha Allah " yana lumshe idannuwansa sannan ya sake bata damar yin magana Baba ta ce" To dai, a sanina ita Fido karatun nata sam bai yi wani nisa ba, dama Aminar itace mai nacin makaranta ko a lokacin da ran marigaya, ita Firdausi ta taso da irin gyare gyaren nan dai irin na Aminar, sai kuma son koyon aiyuka irin na hannu da burin kasancewa babar mai girke girke na zamani , dan takan ce idan ta samu haki zata je ta biya ta koya ta bude wajen siyarwa, to ama duka wannan yanzu ban san yayane ba, ina iya zuwa na kirawota sai ku tatauna lamarin" Zai ba Baba Amsa Risala ta shigo ta sha wata mahaukaciyar kwaliya sai baza kanshi take ta ko'ina da salamarta sannan hannayenta dauke da wani faranti mai shegen kyau da jug mai dauke da jus mai haske ta yiwuma na aya ne ya sha hadi Kansa ya cire bayan ya amsa salamarta a nutse ya dubi Baba dake gaisheta ita kuma tana amsawa ya ce" Baba?," Baba ta dube shi Ya ce" Aa ba sai kin kirawota ba, in sha Allah zamu yi maganar idan na leka su" Baba ta amsa ta mike tana karra risinawa tana yin godiya ta fice a falon tana karra kallon Risala da kwaliyarta Falon Amina ta koma da salamarta Daidai Amina na kora ruwa masu sanyi a cikinta tana lumshe ido dan dadin da take ji na koshin da ta yi ta ce" Uhum, mata na kwaliya a duniya" Amina ta dubi Baba tana fadin" Sosai fa Baba, wata amarya ba kika gano ko me?" Baba ta ce" Hakkun, ai amaryar Elhaji ce kar ki so ki ga kwaliya kamar aljana a kyau, sai baza kanshi take" Daga ita har Firdausi sai da suka dago sunna kallonta, Ita Firdausi dariya ta danne dan ta gane inda Baba ta dosa Ita kuma Amina baki ta tabe bata tanka komai ba Baba ta aniya sake zuzuta abin har fiye da inda ya kai, har sai da Amina ta kai iya wuya, a ganninta meye a ciki yo? Yau ta fara gannin kwaliya ko kawai ta shiga hakkin wa'inda basa son hayaniya? Mikewa ta yi ta nufi dakin Biyu tana fadin" Bara na ga dana, Ke kuma Fido walahi kar ki kuma dungurinsa, ki bar min abina kar ki rikita min yaro, kin ji na fada maki" Baba ta dan daga murya ta ce" To Uman biyu ni fa ba zaki tardoni ba, zan wuce, kai ni dama Amaryar Elhaji ta dan tsakura min turaren cen , baki ji kanshi ba" Turus Amina ta yi, ta juyo a kufule tana kallon Baba ta ce" Nzl. 49 Turus Amina ta yi, ta juyo a kufule tana kallon Baba ta ce" Ke kuma yaushe kika fara kaunar turare haka? Inace du turaren da nake hadawa sai kice aa bakya son turare kinada cutar turare, idan kika shaka yana hadasa maki ciwon hanci da wuya?" Baba ta karkace zamanta tana kantsar goronta ta ce" An yi haka, sai dai ai turarenma sunna ya kama, wannan nata ai inaga ba na kasar nan bane" Yanzuma da haushi haushin da ita sam bata san ya kai cen ba ta ce" Du turare dai turare ne, Allah na tuba ai ba'a kai turarukan Madina ba, ni kuma da su nake aiki , da su nake hada turarukana, ko menene dai na Madina ya fi kyau da karko da komai, kuma sai maganar kwaliya kyau kyau kyau ai Allah na tuba du kyanta idan ta ga wata sai dai ta ja gefe ta yi shiru!, Kuma ai farin ne ta fi mutane ba dai kyau ba walahi!, Fari kuwa a me? Ai fari banza ne ni nan Amina na fada!" Harda buga kirji da sake kallon Baba irin tana jira ta ji ta bakintan nan Firdausi tamkar zata saki fitsari a zaune yanda take mutsu mutsu da kafarta dariya na tukarta, a dole ta shiga tarin dole dan kar ta fashe da dariyar ta shiga uku Baba kuwa ta sake gyara zama ta ce" haƙa ne kuma, ama fari ai karshen kennan, wani fa cewa yake yana son fara ko maya ce, kuma ni banma ga me yasa abin ke bata maki rai ba, bayan ba layin abinda ya shafeki bane uman biyu, sai na ga kamar fada ne muke yi a kan maganar ABDUL " Turus ta sake yi tana kallon Baba Sai kawai ta cire kai ta kama kofar dakin yarenta ta shige a fusace Tana mako kofar Firdausi ta kama ciki tana kakaba dariya har fadowa take yi daga saman kujera Babama dariya take yi bilhaki ta ce" Walahi idan ta tarar da su sunna rashin ji zasu ci kakansu a dakin cen" Firdausi na dariya ta ce" gwarama su ci kakan nasu yaren cen sai ita, kim ga wai yadda Hasan ke cika yana batsewa, ni kuwa na gaura masa mari , shegen yaro kai ba dan kowa ba sai shegen hobara?" Baba ta ce" Kin ga, ki rufawa kanki asiri da dukan ƴaƴan nan walahi a kansu sai mamansu ta zaneki tsaf idan ya so in me za'ai mata a yi mata" Firdausi ta ce" Na ga kat, dan walahi da ya je ya rukunkumeta harda tara hawaye a idannuwanta ta min kaca kaca tace aa bata son wasan duka in daina dukansu, in masu nasiha in masu addu'a ya isa, fadama ba'a yarda na yi ba" Baba ta ce" Kadan daga soyayarta da ƴaƴan nan, Allah dai ya biyata sannan ya shiryeta, dan baki ga yadda maganarta ke cenza yannayin mijinta ba, muna magana da karsashinsa da na kamanta hirarta nan take yannayi na rashin jin dadin mu'amalarsu ya bayana a tatare da shi, na tabata abinda ke zuciyarsa dangane da ita mai girma ne, bana so wannan firgitaciyar y'ar ta kwace komai, Uman biyu kuwa na shirme" Firdausi ta sauke ajiyar zuciya mai zafi, ta ce" Baba, walahi tana sonsa, rikicinta ne ya fi komai karfi a cikin lamarin, ama ai wannan hanya da ya dauko zamu gani ita ko shi wanda zai saki ya nemi sulhu" Baba ta amsata ta mike tana mata salama dan so take ta yi ta je ta gayaci makota su tayata aikin nan tun yau a rarage Yauma hakan ta kasance, sai da dare ya tsala ya shigo ya samu Firdausi na karatun Alkur'ani mai girma Ya zauna suka gaisa sosai, ya karra yi mata nasiha da rarashi a kan lamarin rayuwa, sanann suka tatauna a kan lamarin abinda suka tatauna da Baba Sosai Firsausi ta ringa kuka tana sake dukawa tana yi masa godiya, har sai da ya nuna bacin ransa ya fara fada sannan ta share hawayenta ta shige kamar yadda ya umarceta Tana shiga bayi ta wuce ta dauro alwallah ta haye saman salaya ta shiga Adu'a a kan wannan mutumi da yayarta da dukan alkhairin dake tare da su Shi kuma abinda ya saba ya yi, yaransa ya yiwa adu'a sosai sannan ya karasa kofarta ya tura a hankali ya shiga A hankali ya karasa bakin gadon ya tsuguna yana kallonta Kumatunta yake kallo da ajiyar zuciyar dake masa nuni kamar ranta a bace ta kwonta A hankali ya dora hannunsaa saman mararta ya shafa yana dan sakin murmushi A hankali ya kai bakinsa ya manna mata kisss mai zafi a wajen sannan ya dago ya sake zubawa fuskarta ido da gashin kanta dake waje wanda ke wal wal wal wal na hasken duhunsa da kyansa A hankali ya dan shafa shi yana sake kallon fuskarta zuciyarsa na dokawa da mugun karfi Kasa kasa sosai ya furta"u'r sleeping like a baby" A hankali ya sake shafa fuskarta ya kuma furta " U'r a baby , my baby, Wifey" ya idasa yana dan sakin murmushi kadan yana kallonta A hankali ya ci gaba da tofa mata Adu'a har ya yi ya gama ya mike ya fice ya rufe mata dakin Ta baya tmya rufe ya duka ya tura masu ky din ciki sannan ya koma nasa bangaren cike da bege da jin rashi a cikin zuciyarsa, sai dai kamar yadda ya kudurta ba zai takurata ba, idan dai hakan shine burin Amina zai hakura, ko menene ai in sha Allah ya tabata Allah zai sanyaya masa, balema ba wani abu mai karfi da ya wuce tarin kaunar abinda ke cikinta! Sosai suka raya daren nan, bayan Risala ta yi masa rantse rantsen cewa ba zata kuma bari wani ya ji abinda ya shiga tsakaninsu ba, ta bashi hakuri na wanda ya faru, sun karra tataunawa a kan furucinta na gidan Baba mai shanu sun ganewa junna Ta sha wahala a yauma , ta sha wahala sosai, domin ya kwana biyu da abin shima, a dole ya barta daga karshe domin irin nishin da take fitarwa kar ta summe masa Da kyar shima ya samu barcin bayan sun tsaftace jikinsu yana jin yadda mararsa bata sakar masa yadda yake so ba, ama ba halin sake koma mata dan shi ba makaho bane ya gane kwarai ta yi hakuri ta jure kuma ta gaji dole ya tausaya mata ya barta ta huta ___________________________________ Washe gari ta kama asabar, ranar da ya ware ta hutu ce tunda ya tare da matansa, ya kasance yana gida ne tunda safe har wata safiyar, sallah kawai ke fitar da shi sai ko idan ana wani abu mai mahimmanci irin zuwa taaziya, ko zuwa wajen daurin aure, ko zannen sunna, da zarar an gama yake dawowa gida dan ya ware ranar ne dama wa iyalinsa Kusan karfe goma bayan an kai Biyu wajen aski ta fito a nutse ta nufi bangarensa ba tare da ta yiwa Firdausi salama ba, dama ko da ta tashi a cike ta tashi kamar yadda ta kwonta a kufule, kamar zata tashi sama dan haushi da take ji na kowa da kowa A nutse ta tsaya bakin kofar tana dan bubugawa kamar yadda ya zame mata jiki, bata fadawa waje ba tare da ta nemi izini ba sannan ta yi salama a amsa mata A karro na biyu ta sake yin salamar , sannan ta ji muryarsa, duda bata yi tunanin samunsa a falo ba, dama ta tsaya a falon ne da nufin idan ta yi salama uku ba'a amsa ba ta shiga ta haye sama ta same shi a samansa A hankali ta tura ta shiga tana baza dubanta dan ya lalubo shi a cikin kwayar idannuwanta A hankali ta karru da kujerar dake gabanta wace bata san ta kawo inda take ba sakamakon kallonsu da ta shagalta da yi dan mamaki dake ciciyar zuciyarta "Be careful please, don't injured ur ur self " Ya fada yana dan son tashi da dan karfi daga zaunen da yake kan Risala na saman cinyoyinsa yana dan shafa hannayenta dake waje sanadiyar karamar rigar dake jikinta, idannuwansa kuwa tarr a cikin na Amina A hankali ta dauke idannuwanta ta dan juyar da kanta tana gyara tsayuwarta dan kar ya karaso ya tabata Shima dan dakatawa ya yi bayan ya tuna da Risala a samansa ya koma ya zauna yana lumshe idannuwansa hadi da lalubo hannunta a hankali ya jimke dan abinda zai rike hakan yake so dan samun kwarin gwuiwar fuskantarta Yawu mai dacin gaske Amina ta hadiye ta sake juyowa tana dan kallonsa, a ranta tana ayana' Namiji kennan, buhun kaya, watau ga Maina kaya ko? Har ka hau ka jida mata aiki ka sauka ka rike yar shila?, Shine ina fama da ciye ciyen cikin da ka dura min babu ruwanka na rayu ko na mace kana nan ka labe a jikin yar yarinya kamar a karyata dan shegen kasusuwa a wuya ko? Ba damuwa ni ba makashiya bace, zan haife maka na dire maka dan walahi babu wanda zai sakani zawarci da malulun yaro, an jima baa zageni ba!' A fili kuwa , a dake ta ce" Wajenka na zo, ina son zamu yi magana" Fuskarta da ta hade da cire kan da take ya saka shi shima a dan hade ya ce" Bismillah" Juyowa ta sake yi gannin kadangaruwar tasa sai sake dago kai take kamar ta sha rana tana son innuwa kadan ko jin ƙishirwa, sannan ta sake kallonsa ta ga ita yake kallo da idannuwansa dake daf da kasheta dan kaifafan kallonsa sam ba risinawa a ciki A hankali ta sake juyawa da nufin tafia, dan ta ga soyayar irin mai hawa kan nan ce tanada bukatar a basu waje A hankali ya dubi Risala kasa kasa ya ce" Bab, dan bamu waje kadan kin ji?" Sai da ta dan dago yana kallon idannuwansa ta mana masa kisss wanda tsaf a idannuwan Amina sannan ta mike taa nufi ciki firki firki tamkar zata karye biyu Ita amina Al'ajabinema ke neman kasheta, oh yaren zamani jarabace cike da cikinsu, yanzi wannan yar ita kuma halin da ta saka kanta kennan a rayuwa? Jarabar maza? To Allah ya sanyaya Zamansa ya gyara yana nuna mata wajen zama dan nesa da shi, a tsare ya ce" Bismillah" Kujerar ta kalla, tana nesa da shi ainun, sannan ta kalli ta dan kusa da shi Haka kawai sai ta ga harda rashin adalci a lamarinsa Ama sai ta kyale shi ta barshi da halinsa ta je ta zauna a kujerar, itama ai gani take ta fi mata alkhairi fiye da kowace A nutse ta ce" Dama, dama dangane da maganar makaranta ne, jiya twins ke ce min ashe ka cire su a wancen makarantar tasu, ni ban sani ba, kuma har ka saka su wata ta kudi duka ni ban sani ba, shine nace dama zan zo na ganka a kan hakan" Sai da ta dire aya yana kallonta, shima a hankali ya ce" Eh an yi haka, ashe ban nemi izininki ba Amina, na cire su ne baki yarda ba?" Idannuwanta ta dago cike da jin wani irin abu marar dadi, tana kallonsa a hankali ta ce" Aa ba haka nake nufi ba fa" Gannin ya yi shiru ya sakata ci gaba da fadin" Dama na zo mu yi maganar ne, saboda na ji wace makarantar ce suka koma, saboda halin rayuwa idan bata yi mugun tsada ba, kuma na yi godiya" Yanzunma jin shirun ya yi yawa a dole ta dago idannuwanta dake sade ta zuba masa ido Sai ta ga ita yake kallo, ama ba da kallon nan na kamar zai cinyeta danya ba, kallo ne normal kawai wanda zaka yiwa irin wani wanda baka sani ba haka Basarwa ya yi yana kauda kansa ya ce" Allah zai badaa yadda za'a yi in sha Allah" Amsar tasa a dunkule, kuma yua ja ya tsaya, kamar ya gama maganar yake nufi Ta dan jima tana cicira maganar, har dai ta rasa abin bilowa a kan maganar sai ta ce" Kuma, Kuma fido yau take ce min an ce ta shirya gobe ta fara zuwa, ta fara tafiya makaranta da kuma koyon girki da.........." "Amina, abinda ya Kawo ki kennan?" Ya fada yana katseta Tsuru ta masa da ido ABDUL ya ce" Idan shine kina iya tafia it's ok" Sake zuba masa ido ta yi zuciyarta na kunna da tafarfasa, watau ta tafi ta basu waje su dora daga inda suka tsaya ko? Rai bace ta mike ta juya zata yi tafiyarta tana dana sannin zuwa yi masa godiyar nan, farin cikin da ta tsinta a fuskar kanwarta ya sakata nufo dakinsa, sai gashi yana wulakantata "Zaki fara awo gobe, dan ya kai wata daya da sati biyu , zaki je wajen Mansur ya hadaki da doctern da zara ringa maki awo in sha Allah" ya fada yana kallonta Rai bace ta juyo ta ce" Awon me zan je? A dake ya ce" Awon ajiyar dake tare da ke " "Ni babu awon da zan je, kuma da kake fadin adadin lokacinsa wani ya fada maka ne?" Ta fada cike da neman a yita ta kare ABDUL ya tabe bakinsa yana gyara zamansa ya ce" Anya wani ya isa ya fada min bayan ni kadai na diga abina?, Sai dai na fadi ranar da lokacin da tsayin lokacin da ya dauka, Allah dai ya fido shi lafiya" Kukan da yake ta so ya ganin ne aka fashe da shi, ta nuna kanta, sannan ta nuna shi ta ce" ABDUL, ni kake wulakantawa ko? Ba damuwa Ai damarka ce, ka wulakantani son ranka, ni ga banza ko? Ai na laifi samu ka yi ABDUL, kuma babu inda zani!" ABDUL yana kallon fuskarta da kukan da ba hawaye ya yi dan murmushi kasa kasa ya ce" Ai ba damuwa idan baki je ba ni sai na aunaki a gida,sai an jima Amina" Tsuru ta masa kukan na daukewa cik, itace Abdul ke wulakantawa haka? Jama'a ga mari ga tsinka jaka? A guje ta juya tana sake fashewa da wani kukan Bilhaki, wanda ya saka shi dan mikewa kadan yana kallonta har ta bacewa ganninsa ta shige bangarenta Labulen ya saki ya dawo a ransa yana Adu'a kamar haka ' Ya Allah, ka kare min ita da abinda ke cikinta, sam bata bi a hankali , gudu fa take yi da cikina a jikinta" Amina naa shiga falonta ta karasa wajen Fido ta fada jikinta tana kukanta hadi da neman yin burgima A rikic Firdausi ke tareta dan kar ta jima kanta ciwo tana fadin" Aunty, subahanalah aunty lafiya?" Amina na kuka ta ce" wai ni ce zai ringa kora?, Nice zai ce na je awo ko ya ringa aunani a gida?, Nice zai ringa wukakantawa dan ya rungumin wanncen abar kamar karauki tana tafe frikyau firkyau kamar diban raba? Duwawu a shafe kamar bayan plat sai wasu shangalalun hannaye kamar kanlemun fara cici kashi?" Firdausi ta kwalalo idannuwanta cike da alj'ajhabin wannan ba'a layayiya ta ce" Awo na me aunty? Aunty, wayo Allahna aunty ko dai ciki ne da ke?" Cak ta tsayar da kukan tana zarro idannuwanta tana kallon Fido ta ce" Ciki kuma?" Firdausi ta kureta da kallon itama ta ce" Eh mana aunty, na ji kina cewa an ce ku je awo, kowani abu ne za'a auna? A sanina ciki ne ake zuwa awonsa asibiti ko?" Amina ta sake hade fuska ta ce" ciki kike min fata ne ke?" Firdausi ta sake zubawa karfin Hali irin Na Amina ido,kafin ta ce" Aa, Aunty ana zancenma? Ai baban farin cikina da na twins a duniyar nan ki bamu baby, baki ji yadda muke fatan gannin haka ba" Amina ta shiga tureta daga jikinta tana silalewa kasa ta ce" Ta yiwuma bakinku ne ya kamani, ta yiwuma kunne kuka min fatan nan abin nan ya sameni, shikenan na shiga uku kin sani Fido, ciki ne na kanina a jikina Fido" Firdausi ta shiga tafa hannu ta kwashi kururuwar da ta saka Amina yin wuki wuki tana kallonta Salati take tana salamewa da sanarwa ubangijinta, a rikicen da gangan ta ce" Wannan da ace su Uma da rai har sai sun sakaki a ukun da gaske, mijin naki kike wani cewa kannenki? Yo ko kin bashi shekarun haihuwarsa tunda ya zama mijin ki ai komai ya kare, Kunya? Abin kunya? Halal din? Allah ya rabamu da abin kunya, kuma walahi kinga awo ko? Tsaf zamu je awo gobe, ni nan zan rakaki abinda yace shi za'a yi gaskiya, kuma a dai ringa tunawa da mutuwa, idan ta zo a hali irin haka ai an shiga uku , me za'a amsa a gaban Allah? Mace marar yiwa miji biyaya ake sak, kuma dai ai an yi islamiya an san makoma, ko shi yasa kwana biyu ba ruwanki da kowa kike ta masifa? Mu kam abin dadi ya same mu sai sallah da sanarwa ubangiji walahi aunty , haba dai ai godiyar Allah ya dace ba wai a nuna rashin gldiya ba" Har baki Amina ta kama da mahaukacin Mamakin Fido ta ce " Ke, kin ci kaniyarki,na ce kin cikaniyarki kin ji? To sai ki kaini asibitin na gani!" Ta mike ta wuce ciki tana fafa tamkar zata ari baki Firdausi kuwa ta yi tsit sai da ta shige ta mako kofar sannan ta mike tana dariya hadi da zagayawa tana sake godewa Allah Karshema dakinta ta wuce ta shiga duba abinda zata saka na fitar da zata fara yi a gobe, har Allah Allah take yi goben ta yi, a jiyama har yar dariya Yaya ABDUL ya bata da ya yi maganar ida, wace idar kuma ita da ta yi jinnin haihuwa? Ai an wuce wajen kawai kowa ya yi ta kansa, ita dai yanzun zata maida hankali ne ta gina kanta da taimakon ahalinta, namiji kuwa sun yi hannun riga da shi, ai an gwada tunda ba riba an hakura Wainar Baba ce ta raba dan Amina fushi take yi, Baba kuwa ta tsaya a kanta da jan ido ta ja rantsuwar gobe da sasafe maza a shirya a je maganar miji , idan ba haka ba ai ta san ana mutuwa kuma ba'a yafewa kowa ba! Kukanta ta sha, kuka da biyu, dayan abinda ke mata ciwo wai ita ABDUL ya kora, dayan kuwa na zuwa awo ne Da kyar ta yi barci, haka kuma safiya na yi Firdausi ta tasheta, lahadi ne ama da yake clinik ce, kuma ya san da zuwansu haka ta shirya rai bace suka tafi asibitin ta su Mansur A asibitin sunna karasawa Muhammat ya fita ya shiga ciki Jim kadan ya fito tare da Mansur din da waya a kunnensa yana magana yana tsaye gefe guda Muhammat ya daka hannunsa ya bude gefen da Fido ke zaune yana fadin" Bismillah kanwata ku fito " Firdausi dake karra tausar Amina tana yi mata maganar ta daina to hade ran ta fito da dan gudu sakamakon daga hannun da Amina ta yi tana cik alwashin sauke mata biyar a kumatunta Birki ta ja tana kallon barin da MANSUR ke tsaye ta ce" Ina kwana?, Zata fito yanzu in sha Allah" A hankali Mansur ya dauke dubansa daga kanta yana maidawa kasa, dan haka kawai ya ji haka ya dace ya yi , sai kuma ya dago da murmushi yana jin furucin ABDUL dake Fadin" Mansur, ka ga idan docter ba zata dawo yanzu ta duba min mata ba kawai ka sakata a office dinka kai ka fita ka tafi wani office din ni na zo na aunata, kar ka bari wani kato ya mata tambayoyin da bai bata ajiya ba, ka ga rantama a bace yake, inaga ba zasu wanye lafiya ba fa?, Docter ita ta san yadda ta vi da ita wancen karronma , kawai ka nemota zai fi" Docter Mansur na murmushi ya ce" Ka ga wasa fa nake maka tun jiya na sanar mata, yau bama ta aiki ama tuni ta zo tana office dina , su ladai take jira ta tarda mujinta da ƴaƴanta park" Ajiyar zuciya ya sauke mai dan dumi ya datse kiran yana dan sosa kansa a hankali da jin haushin nemansa da fitinar da Mansur ke yi, shi kuwa sai ya wani manta komai ya biye masa su yi ta yi kamar wasu yara ƙanana Koda yake gaskiya ba zai iya lamuncewa a yiwa iyalinsa dala dala ba! To ai bama kyau hakan a adinance Sun ga likitar, sosai suka zanta cikin hikima da iya aiki, Abinda docter ta fuskanta ya sakata fara dauko strategi na sakawa Amina cikin nan a ranta, ko tace na bayana mata tsantsar kaunar da take yiwa cikin ama takw dannewa dan wani dalili nata, domin uwa ba zata taba kin cikin dake jikinta ba ko a wani irin hali, sai dai wasu lokutan wani tashin hankalin kan dane soyayar , idan ya yi mugun karfi harma yakan rinjayi soyyayar, sai wani gyara na Allah Hotunnan da ta ringa hasko mata na yayan larabawa da turawa cikin kyan kama da kyan shiga, da yayan hausawa cikin kyan shiga da yannayi na farin ciki, da tarin kaunar dake idannuwan iyayen ta ringa kallo har suka gama bayan ta tabatar batada wata matsala na laulayi da ya wuce cin abinci da barci, ta karra mata nasiha sosai a kan yadda zata kula da kanta sannan ta fada mata ainahin lokacin da zata fara awo mai sunna awo, ama kafin nan ko me ta ji marar dadi to fa ta dawo ko ta yi kiranta ta sanar mata bama sai Sir ya sani ba, sunna iya yin magana a tsakaninsu Sosai ta sakata ta saki jikinta da ita suka cenza number sannan suka fito ta rakata Ofice din Docter Mansur domin Fido na cen zaune tana jiranta Sunna zuwa suka tarar da Fido din zaunenta ga su jus a gabanta ama bata dauki ko daya ba, hasalima kamar a takure take a zaunen da take har suka zo ta mike suka yi masa salama suka wuce dan zuwa wajen da zata fara nata karatun da sauransu Kwonci tashi, a hankali Amina ta ci gaba da rainon cikinta, A fannin ci, da sha, da sutura sai dai tace abin har ya wuce tunaninta, daga gidan Baba mai shanuma ya zamto bini bini za'a turo mata da kayan kwalam da makulashe, irin abubuwan kwadayin da wasu har mamakin inda aka samo su ke kamata, haka kuma du ranar Juma'a Baban ne da kansa da Hania zasu zo gidan, duda ba maganar dake hadasu da Hajiar sai tsatsareta da ido da zatana yi da yawan fada mata ta ringa kiyayewa , ta ringa cin abu kaza ta daina cin kaza, daga hala ba wata hirar kuma a tsakaninsu, karshema takan tafi lamuran gabanta ne sai Baba ne zai baje abinsa ya wuni a gidan a sha hira tare, kuma harda Risala yake sakawa a kirawo yana tsakiya abinsa idan ya dauko wannan hirar ya tsoma su baki daya, wanin su amsa gaba dayansu, wannin kuwa wata ta yi shiru, kowace dai da kalar nata isar da kalar nata nuna kulawar da sauransu, har sai yama ta yi a mayar da shi gida abinsa, wani lokacin Biyu su bi shi, wani lokacin kuwa su kiya su nuna gobe asabar abansu na gida zasu buga game da shi Abinda ke damunta kuwa ta gwamaci barawa kanta a zuciyarta, domin bata san me zata fasara haka ba Kiri kiri ABDUL ya dauki kwananta ya hadewa Risala Babu abinda ya dame shi da ita Ba gaba yake yi mata ba, ama kuma babu irin wancen kulawar Rabonsa da ya shiga dakinta tub ranar da aka samu matsalar nan a gidan Baba Tun daga ranar tana tunanin ko dakin biyu ya daina shiga ya masu addu'a Gaba daya ya yi watsi da ita Abinda yake mata a rayuwa shine ci, sha sutura, bayan wannan idan ka ga ya mata magana ido da ido dan ya tambayeta ne yana fatan cikinsa lafiya kalau? Yana fatan tana tune da ranar awonta, awon da ya fita irgen lokacinsa, har mamaki take yi a kan haka Risala sai tunkaho da daga kai take yi mata a cikin gida, domin ba dai an fada mata ba, da idannuwanta ta isa ta gane miji ya mayar da ita banza a cikin gida, gaba daya ta zuba masa ido ne, jira take yi ta haihu sai ta bashi gidansa ya yi yadda yake so da wadda yake so! Yau kwanakin watan musulunci ashirin da daya, haka watanin cikinta wata bakwai ne cikinta ya riga ya fito da kansa, ba maganar buya, domin ko tafia take yi shine a gaba, shi yasa sam bata fita in ba abu ya zama dole ba balema irin girman da ya yi ne abin a dubeta a yi mata sannu, dan ya kai girman cikin da ya isa haihuwa, shi yasa take komai a hankali da kuma lalaba lafiyarta, idan Baba ya zo nema yake sakata dole yawatawa a cikin gidan wai su je su yiwa ma'aikata ziyara, ba dan ta so ba, a dole take binsa dan bata da yadda zata yi masa Ya zamana a yanzu ABDUL kan ajiye fitar juma'a koda bayan sallar juma'ar ne ya yi tsaye daga dakinsa yana hangensu Yakan yi murmushi mai taushi yana kallonta n cikinta A irgensa, nan da wata biyu da yan kwanaki abinda ke cikinta zai fito duniya , shima zai rungumi baby a hannunsa daga Aminansa Harta da ranar da aka bata a asibiti na haihuwa ya ware sati kafin ranar, da kuma sati biyu bayan ranar, koda takan haihu kafin lokacin, ko kuma bayan lokacin in sha Allah, ba zai fita ko nan da nan ba bi'izinillah, zai zauna kusa da ita har ta sauka ........ In dai yana raye _________________________________ Kamar yadda aka saba, sabon sati na sabon watan watani takwas din Amina da ciki A juma'ar yau falon nata ya dauki Harda ABDUL ne, sakamakon zazabin da ta tashi da shi, wanda Firsausi kafin ta fita ta sanar masa, domin jikinta da zafi sosai, gashi ba'a so mai ciki da irin haka, dan yana gagawar ratsa babyn da ita kanta, yana haifar da matsala Daga kicin ta fito rike da plate din da ta je ta yanyankowa su Baba fruits ba tare da sun san abinda ta shiha yi kennan ba, da Hajiar da kanta ce zata hannata, domin Hajia bata hada cikin nan da komai a duniya A hankali ya mike ya nufeta dan amsar plat din, domin baba ne ta ciko, kuma tafiyarta kanta wata iri ce baiwar Allah, gajiya na tatare da ita a bayane ba a boye ba A hankali ya rike Plat din hadi da hannunta, hakan ya sa ta dago manyan idannuwanta ta saka cikin nasa, dama abinda yake bukata kennan A saman lebensa ya ce" Yaya jikin ki?" Amina ta lumshe idannuwanta itama a saman lebenta ta ce" Ya dameka ne?" ABDUL ya tsatsareta da ido ya ce" Ya fi damuna fiye da kowa a duniya " Amina ta tabe bakinta, kasa kasa ta ce" Ka fafi gaskiya , ko kana tunanin Risala ke gabanka?" Idannuwanta ya tsatsare da ido, so yake yi ya ga abinda Mansur ke fada masa dangane da ita da shi, ama shi a kulun ganu yake yi bata ra'ayinsa bata ra'ayin kasancewa kusa da shi A hankali ya budi Baki zai yi magana Kukan Fido ya karade wajen, ta shigo da gudu hannunta saman kanta tana kuka, ta rasa ina zata nufa domin Hajia dai ta san ba wace ke ra'ayin janta a jikinta bace Da sauri ya Rike Amina gannin zata je da sauri Wajen Fidon da ta nufi Baba da ya mike yana kiranta da salalami yana tambayarta lafiya? Zaunar da Amina ya yi saman kujera sannan ya dubi Fido dake kukanta hankalinta tashe tana wani irin haki ABDUL ya ce" Firdausi menene kike kuka haka, zo nan taho nan na ji?" Firdausi ta karasa inda yake ta duka kanta a kasa, Hajia dake dadana wayarta ta dan dago ta sake duban Fido, ta sake maida kanta kan wayar tana ci gaba da dadanawa Firdausi na shashekar kuka ta ce" Dady, wai , wai Mudi ne ya tarda ni cen wajen koyon girkina, yau muna koyawa baki ne , muna tsakiya da aikinmu ya cewa security wai shi mijina ne, aka barshi ya shigo, a cikin mutane ya ringa zazagina yana ce min wai karuwa ce ni na kashe aurena ina yawon cakuduwa da maza, na kashe masa ya'yansa har biyu ina zaune ina yawon ta zubar, Dady ana rikeshi yana fadin a barshi sai ya yi ajalina, da kyar Bintu ta fitar da ni a motarta ta kawo ni gida " Da mamaki ABDUL da ya mantama waye wai Mudi, dan shi ba wani rike sunnan yaron ya yi ba ya ce" Mudi? Tsohon Mijinki Kennan?" Fido ta gyada kanta tana sake tare hawayenta Amina haka jikinta ke rawa, wata irin dunkulaliyar Ashar ke makale a wuyanta, wace a zaunen da take gwara ta saka ihu da ta yita, domin irin zaburariyar ashar din nan ce mai sakawa a maka kallon lalatace komai girmanka da darajarka, ji take tamkar ta hira ta je inda yake yau ta kwakulo idon marar kunya! ABDUL da bacin rai ya dubi Baba dake tambayarsa wai yaron nan bashida kunya ne ko me yake nema da mutane ne kuma? ABDUL ya dan dantse lebensa na kasa, sannan ya saki ya ce" Bashida kunya, kuma bai gane an kyale shi ne dan takardar rashin kunyarsa bata kai inda za'a yi fito na fito da shi ba, ama yanzu na amshi tayin, ina zuwa!" Mikewar da ya yi daga zaune ya saka Hajia mayar da wayar gefe tana kallonsa a tausashe ta ce" Honorable ina zaka je?" ABDUL ya dakata dan ya dan shine ai Honorable din dai da Hajia ke kira kulun, Aminama da ta fara murmushi tana jin inama a je da ita ta ga yadda ABDUL zai ci uban dan iskan cen dakatawar ta yi tana kallonsa ta ji ya ce" Zan je na dawo ne" Hajia ta yi murmushi tana fadin" Koma ka zauna, kai da matarka bata da lafiya?, Wannan ai ba aikinka bane, ka ga ya kule kansa fa yaron da kansa, tunda yace zai halakata a cikin jama'a, kuma ya je har wajen da yake na gidansu ya zageta, tunda wajenka ne kai kuma Uba kake a wajenta, sannan ya yi karyace karyace da yawa.......ka barshi kawai ya kule kansa ai" Alkali ya zuba mata ido, yadda take maganarta a nutse hankali kwonce ya san abin kansa zai karkato Ai kuwa ta dube shi tana daukan wayarsa da sam bai cika anfani da ita ba ta mika masa ta ce" Alkali kana ji jikarka za'a kashe, ka dan yi wani abu mana" Amina dake zaune sai da ta ji kamar numfashinta zai katse dan wani abu dake ratsa mata zuciya da jiki Alkali kuwa murmushi ya yi yana dan rage girman idannuwansa dan ya lalubo sunna, ama ya kasa a dole ya mikawa Amina da ta fi kusa da shi ya ce" Uman biyu, lalubo min DPO Mustapha na sojojin ba polisse ba" ABDUL ya saki murmushi yana gannin yadda Amina ke danne dariyarta, wada karars ya fahimci dariyar farin ciki take son saki ama tana hanna kanta har ta lalubo ta dannawa Baba kira sannan ta kara matsawa tana sauraron maganar da Baba da DPO Tsaf Baban ya gama bayaninsa, amsar da DPO ya bayar da tambayar su Hajia da Honorable ya saka ABDUL sake yin murmushi, watau gaba daya makaraban Hajia Honorable suke kiransa, bayan kasa ya gama nikawa wace zai watsa masu a ido, domin shi ba dan siyasa bane, ba kuma zai tsaya a takarar neman kujerar gwamna ba, bashida ra'ayin hakan gaskiya Amsa ya yi suka gaisa sosai, ya sake jadadawa , ya bada kwatance tak tak , harda na gidan ubansa , ya sake fadin irin rashin mutuncin mutanen a takaice da kuma tayarwa da ahalinsa hankali da suke son yi DPO ya yi murmushi ya ce" Wannan aiki ai nawa ne da kaina, zamu zauna da su, idan nan ya isa to, idan bincike ya saka su a uku kuma sai mu maka su kotu, domin sai mun bincike su kaf dinsu, daga ɗan har uban Honorable" Da wannan suka yi salama Amina ta saka hannayenta ta talabe habarta, wani tsadaden murmushi ya kubce mata tana kallon yadda Fido ke murmushin itama tana sauke ajiyar zuciya ta mike bayan ta yi godiyar da aka yi mata fadanta ta nufi ciki, cike da gayunta Hajia ta rakata da ido tana jin wani irin tausayinta a cen kasan zuciyarta Abinda bata taba yi ba ne ta yi, watau shiga hurumin Amina bayan cikin dake hada su Tana kallon Amina ta ce" Nzl 51 A hankali Hajia ta dubi wajen Uman biyu ta ce" Na kasa fahimtar komai, twins kannenku ne? Ko kunnada wata sister din da ta haife su? Dan na ga ai Honorable ya ce min ke din............" Ta yi shiru dan sai ta ji kamar nauyin maganar take ji a bakinta A nutse ta idasa da fadin " Ya ce min ke yarinya ce ko?" Baba ya sake dane kafa yana murmushi yana kallon Hauwa Amina kuwa ta sada kanta, na farko bata taba magana haka da hajia ba, na biyu wannan magana ta sakata a kunyar da bata taba tunanin zata jita ba a rayuwa ABDUL ya dan sauke numfashi yana jinjinawa Hajia a ransa Baba ya ce " Ai ita din nan dai itace maman biyun , ita ta haife su ama ba'a fadi, kuma itace ta samu wasu biyun suka koma" Hajia ta dubi baba, wani farin ciki na ratsata Murmushi ta yi ta ce" Ama mijinta akoy sakarai Alkali, idan ba rashin mafada ba ta yaya zaka samu mace mai zubo bibiyu ka yi wasa? Muma Allah ya sa mu dace da samun biyun, Wai Honorable me yasa ka hanna a yi mata scan ne?" ABDUL ya sake dubanta yana murmushi ya ce" Na fi so ya zamto surprise a garemu baki daya, tunda batada wata matsala a kan haka ya sa na hanna a yi" A hankali Amina ta ciciba jin kunya zata kasheta ta mike tana dan nishi ta nufi ciki, zuciyarta cike da mamakin lamari irin na yan gayu, a zauna a waje daya ana maganar cikin fari da iyaye? Ai ba za'a kiresu kakani ba iyaye ne sak, shima yana sakin jiki hankalinsa kwonce yana bada labari? Allah dai ya sawakawa yan gayu Gyaran murya Hajia ta yi a karto na biyu tana kallonsa A hankali ya dawo da dubansa kanta , kallon ido cikin ido suka yi na yan dakiku ya dauke dubansa a cikin nata ya mike yana fadin" Bara na ga idan boys sun gama karatun mu dan fita" Da ido ta raka shi har bakinta a bude dan mamaki har ya bacewa ganninta A hankali ta dawo dubanta kan Alkali dake kallonta shima Damuwa a kan fuskarta ta ce" Me yake faruwa a tsakaninsu?, A matsayinsu na yaran ma'aurata kula da junnansu ya dace ya zarce haka, sai na ga kamar ya fi damuwa da ita?" ALKALI ya gyada kai yana murmushi ya ce" Hakkun" Hajia ta zuba masa ido da kyau ta ce" Menene Hakkun Alkali?" Alkali ya ce" Abinda kika fada ne na dafa, ai ita uman biyu sam jikanki baya gabanta" "Ina ba zai yiwu ba, a duniya ban ga macen da ABDUL zai yi tsaye a gabanta a matsayin wace zai iya yiwa soyaya ba ta zumunci ba zuciyarta bata motsa ba, babu ita!" Ta fada tana dafe cinyarta dan ta tabatar masa Alkali ya mayar da bakinsa gefe yana murmushi ya ce" Sai kace wanda ya yi farin jinina?, Sam bai tako Sa'a a gaban Uman biyu ba, shi ke sonmu mu baya gabanmu, ai kin ganni da idannuwanki" Wani irin shiru Hajia ta yi, ga dukkan alamu kamar abin na dan damunta Sai kuma ta basar a zuciyarta tana ayana" In sha Allah bama zasu raini dansu ko yarsu a rabe ba" __________________________________ Da dare, kusan karfe bakwai da rabi, ABDUL ke zaune saman doguwar kujerar falonsa yana rike da remot din TV yana son sake kallon maimaicin labarun da aka yi na yau wanda bai kalla ba A hankali Risala ta karaso ta bayansa ta sanyo hannayenta a hankali tana dan murza kafadunsa ta ce" Barka da warhaka Husband" A hankali ya saka hannunsa yana janye nata yana dagowa ya kalleta, sam hankalinsa ya tafi a wajen kallo bai ji shigowarta ba, koda yake bai kai ga rufe kofar ba ya zauna kallon Shigar dake jikinta da ita da babu du daya, haka kuma dai ya ga after drss dinta baka ajiye saman hannun kujera Kansa ya dan dauke yana sake maidawa saman TV ya ce" Baki kwonta ba?" Risala ta yi farrr da idannuwanta tana zagayowa ta zauna daf da shi tana kallonsa ta ce" Ban kwonta ba, na kasa barcin, so nake na yi a nan" Abinda yake yi ya dakatar dan kirjinsa take nunawa kuma tana son kwontawa a kai, ita fa a yanzu ba zaku gane bane, dwara da bata samu cikin ba, dan ta kula zumudin cikin kadai mijinsu ke yi, bai damu da mai dauke da cikin ba!, Dan haka gwara da aka yi haka ai A hankali ya janye hannayenta yana kallonta ya ce" Kin san ai bama haka" Risala ta turo baki tana cewa" Me yasa kake hannani rabarka a ranar da ita din bata gefenka?, Tunda ba zuwa take yi ta kwana ba ni na zo ai sai ka bani kulawa ko?" "Ranakun da suke naki zan iya baki kulawa, wanda suke na yar uwarki baki da wannan damar, mu kiyaye kar ki shiga abinda kuma bai shafe ki ba" ya fada a tausashe yana sake dan matsawa kadan, domin du abinnan a idannuwan Uman biyu suke shigagu dadadu , koda ta nace ta kwana a bangarensa idan ranar ba tata bace ko daki basa hadawa, ya gwamace ya shige ya rufe ya kwonta idan ya je ya bi dare ya gano Uman biyu da cikinsa, da kuma twins ya masu addu'a A hankali ta kawar da kanta gefe ranta na kuna, wannan jaraba da me ta yi kama ne? Bata san me yasa ABDUL ke yi mata haka ba, duda ita dadinta ne babu wanda ya san ainahin abinda yake faruwa a dakansa daga ita sai shi , sai mahalicinsu, ama idan yana mata haka sai ta ringa tunanin ba zai taba zubar da matar cen kwata kwata ba!, A hankali ta ce" Dama zuwa na yi dan na yi godiya, kuma sai na kasa barci, shine zaka ki ko rabarka na yi ko?" ABDUL ya yi shiru yana kallon TV din bai ce mata komai ba, dan ya gama magana ai da ita kuma A hankali Amina ke sake rike kofar shigar zuciyarta na dokawa Wayar da suka yi da dan gidan uncle dinsu, watau yayan mahaifinsu ya rikitata, bata san a inda ya samu numberta ba, batama san gaskiya ya fada ko karya ba, bata taba sannin idan ta ji dangin nata a wani hali zata girgiza haka ba, tunda ya fada mata maganar mutuwar zuciyarta ke bugawa da karfi, abin cikinta kuwa wani irin juyawa da ya yi ta tabata daga sama yanzu kasa yake kallo ko menene, uwa uba ciwon dake tashin mata wanda ta tabata na tsoratar da ta yi ne ya sakata haka Ta rasa wa zata nufa da maganar, dole abin ya rikitata, gashi Fido na wajen lesson dinta, Biyu ne kawai a zaune da kayansu na masalaci sunna kallo Sai da ya lafa mata sannan ta murda ta shiga zuciyarta na daf da tsintsinkewa Wanda zata yiwa kuka ta ji sanyi sannan ya rakata take nema ido rufe Da wani irin sauri Risala ta shige jikinsa lokaci daya ta nemi lalubar bakinsa a lokacin da su dukansu suka yi arba da Aminar da kana ganninta zaka fahimci hankalin ta ba a kwonce yake ba A hankali ta sake dafe cikinta, sannan ta juya a hankali ba tare da ta furta koda A ba Da karfi ya matsar da Risala gefe tamkar wata yar jaririya dan irin kautar da itan da ya yi da mamakinta yana mata wani kallon da ya tsoratata ya mike da dan sauri yana fadin" Aunty?" Amina ta dan ja wani tukukin bakin ciki ya murdo ya sake murda mata cikinta Da karfi ta duke dan har wani irin abu ta ji kamar yana bin kafarta ta rintse ido sosai tana ambaton Allah a zuciyarta Dukowa ya yi hankalinsa tashe ya kamata yana dagota hadi da fadin" Aunty, menene? Bakida lafiya ne? Me yake damunki plz?" Hannunta cikin nasa yake, a damke take da hannun nasa dan abinda ke mata zabtu zab zab zab kamar zai summar da ita Gaba dayansa ya zauna a wajen yana kokarin rungumota jikinsa, Sai da ya rungumeta sosai yana shafa bayanta a hankali a hankali yana duban wajen da Risala ya ce" Ki dauko min wayata mana " Rai bace ta mike ta nufi ciki, ya sake rungumo Amina a jikinsa daidai ciwon ya lafa mata ta samu a hankali ta ringa janye jikinta har ta raba jikinta da nasa tana rintse idannuwanta Cike da damuwa ya ce" Aunty?" Amina ta bude idannuwanta ta sake zuba masa su, wannan wani irin wulakanci ne marar misali ne a rayuwa? Me ta yiwa wannan mutumen ne? Ai dole ya kireta aunty mana, tunda ya hadata da kayan nauyi ya zo yana kwakular yar yarinya Hannunsa ya kai zai tabata, a hankali ta janye nata hannayen muryarta na rawa tana kallonsa ta ce" ABDUL, kar ka taba ni dan Allah, cin kashin ya isa hakanan, sannan ka sawake min, wanda na gani ya wadatar!" Kirjinsa sai da ya mugun doka masa, yana kallonta da kallo mai dauke da mamakinta n kafiyarta da kuma mamakin kennan ba zata taba sonsa ba? Ya ce" Me yasa kika kasance mai furtawa miji ya sakeki bayan ba kyau? Babu kyau mace ta nemi saki a wajen mijinta haka kawai ba laifin da na maki?" "Kake kiran ba laifin da ka yi min?, ABDUL babu laifin da ka yi min?, ABDUL tunda na dauki cikin nan ka yi watsi da ni, da ni da banza duka daya a wajenka, babu ruwanka yaya na kwana, ko yaya na tashi? Babu ruwanka da komai nawa, baka zuwa ind.................................................................." Idannuwanta ta rintse wani ciwon na sake murda mata Cikin ciwon ta dake ture shi da dan karfi ta ce" Ka daina tabani nace, idan takamarka ni hadaka aka yi da ni, ka sani nima hakan take! Hadani aka yida kai, bayanshi ba wani abin!, Ka salameni na je na karasa haka, ya isheni haka!" A sanyaye , jikinsa da zuciyarsa na tsintsinkewa ya sake tareta a hankali ya ce" Ki yi a hankali Plz, ki yi a hankali, ki tashi na kirawo docter dinki ta duba min ke, tun yaushe kike jin ciwo ne? Amina dan Allah ki bar rigimar nan haka kin ji?" Fashewa ta yi da kuka tana sake tureshi ta ciciba a hankali ta mike daidai Risala ta fito da wayar tana kallonsa ido cikin ido ta ce" Ka bani waje na wuce, ka sani ko kaine autan maza kafata ba zata kuma takowa nan ba!, Idan kana so ka mayar da ita cikinka dan so, hakina da kuke shiga ku je ku kuka sani!" Gaba daya ta rikice ta rikitashi ta hannashi rabarta ta kuma ki saurarawa Wayar ya fizga a hannun Risala ya wuce ciki yana lalubar jalabiyarsa dan ya bita bangarensa, gaba daya hankalinsa a kololuwar tashe Ya dan jima ciki dan bai iya rudewa ba a rayuwa, da kyar ya samo rigar da ya saka ya fito Abinda ya sake bashi haushi da Risala, tan tsaye hannayenta harde sai jikiga take yi Kallonta ya yi ya ce" Baki bita ba?" Risala ta wani kalle shi ta ce"ina zan bita ni kums?" ABDUL ya yi wani irin kwafa ya fice da sauri bai ce mata komai ba Dorect bangeren Aminar ya karasa Yana zuwa ya tambayi ko tana dakinta? Domin dawowar su Fido kennan , ita da Biyu sunna zaune Yannayinsa ya shedawa firdausi ba lafiya ba, mikewa ta yi ta shige dakin Amina, sai dai ta tarar kayan aminar a watse a kasa, kamar wani abu ta dauka, ko wani ya daukar mata Hankalinta ta ji yana neman tashi ta fito da sauri ta yi kicin, Cenma bata sameta ba, ta dawo tana fada masa bata ganta ba, kuma ga yadda ta samu kayanta A tsayen da yake sai da ya ji kamar za'a maka shi da kasa dan wani irin juuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu da ya ji kansa ya kwasa Labulen dakin ya sake rikewa da dan karfi idannuwansa rintse har ya ji numfashinsa na dawowa a hankali sannan ya fita Wasa wasa nan da nan aka tada hankalin du wani wanda ya kwana ya tashi a gidan nan ana neman UMAN biyu Abinda ya fi komai dagawa wa'inda ke tsaron kofar gidan hankali shine, sun raja'a , a kallon ball din da ake ce ta chealsy da baban club din da suke support , ya zamto kowa hankalinsa ya dauku wajen ihun ball din da aka saka wace ta shiga a ba zata, babu wanda ya san idan ta fita ko tana cikin gidan......nan fa suka rarabu, suka haukace kowa ya kama hanyar da zai nemeta a cikin gidan, wanda ABDUL bai taba dana sannin yin ginni mai girma ba sai yau a rayuwa Dare kara yi yake ama basu ganta ba A hankali ya karasa wajen mota ya bude ya shiga yana danna kiran Muhammat Muhammat ya karaso da sauri yana amsa shi Ky din mota ya tambaya yana duban sitiyarin motar Muhammat ya ce" Sir koma gefen cen na tuka ka" A hankali ya girgiza kansa yana kallonsa ya ce" Ka bani ky plz" Miko masa ky din ya yi sabban ya je da sauri ya shiga wata motar ya tayar ya dakata yana kallonsa har ya tada ya fita a gidan Biye yake da shi a hankali har suka karaso kan kwanar da zata idasa shi gidan Baba mai shanu, yana ta dube duben hanya domin ya tabata idan ta fito daga gida ba zata tarbi kowa da bacin ranta ba sai wanda zai saurareta Ido Muhammat ya zarro lokaci daya yana taka wani wawan birki sakamakon wani mai baban babur da ya shawo kwana a guje ya maku jikin barin da ABDUL din ke tuki, watau bangaren da yake zaune yana tuki A haukace ya bale motar ya fito ya nufi wajen da tuni aka fara tsayawa ana son fara yiwa wajen taro Mutanen dake wajen kofar ya kautar ya kama ya bude kofar hankalinsa tashe Da sauri ya dago Abdul dake kwonce jikin sitiyarin motar kansa saman sitiyarin a haukace ya ce" ABDUL?" Ido ABDUL ya rintse dan ihun ya ratsa masa kunne sosai yana bude jajayen idannuwansa ya kalli Muhammat Muryarsa cen ciki ya ce" Ta yiwu ta shige cikin gidan Baba ko?" Masu gadi da suka zaburo jin an ce an yi hatsari du suka nemi rudewa gannin wanda ya yi hatsarin, sai dai yadda ya ki a talabeshi ya fi komai damunsu Cike da damuwa Muhammat ya ce" Sir buguwa ka yi fa ka tsaya mana a rikeka mu karasa gidan" ABDUL ya juyo yana nuna masa marfin motar ya ce" Ka manta wace irin mota ce?, Muhammat nakuda take yi, ban san inda ta shiga ba" Muhammad ya bi bayansa yana bashi baki dan motar tuni mutanen gidan Baba sun shiga kulawa da wanda ya bugun mata da motar kanta, duda shine bashida gaskiya kuma shima bai wani ji ciwo ba, babur din dai ne ya dan tatabu A hankali ya karasa wajen da Baba ke tsaye yana jira a dawo a sanar masa Allah ya sa ba'a ji ciwo ba, an fada masa an yi accident a kan kwanar gidansa shi yasa ya fitoya tsaya kamar wani mai anguwa yana jiran dawowarsu, ai ga motar gidan ABDUL RA'UF ta shigo Hankalinsa a kan ABDUL RA'UF din har suka zauna yana jin gabansa na faduwa, yana duban Muhammat ya ce" Muhamadu, lafiya? Me yake faruwa ne?" Muhammat ya cire takalman ABDUL ya nufi waje yana fadin" Ina zuwa baba bara na janyo motar cen , walahi kar aje su raunatata " Baba ya kalli ABDUL yana jin kamar ba zai iya tambayarsa ba, dan yana tsoron amsar da zai bashi Da kyar ya daure ya ce" abdulahi me yake faruwa ne? Lafiya?" ABDUL ya jinginar da bayansa a jikin kujera yana fitar da zazafan nishi , da kyar ya ce" Baba, ban san inda ta nufa ba, kuma dai inda ta tashi na ga har kamar ta fara zubar da ruwa, nakuda take yi" Baba ya fuskanceshi da kyau ya ce" Kana bani magana a dunkule, ina Uman biyu? Dan na san itace da ciki a tare da kai" ABDUL ya furzar da iskar dake bakinsa da daci ya ce" Nld 52 Abdul ya furzar da iskar dake bakinsa da dacin harshe ya ce" Ta shigo ne, sai irin ta tarar da Risala......to yau din ba lokacin Risalar bane, sai dai abin ya bata mata rai, ta yi fushinta sosai harma irin dai ta ce sai na saketan nan, Baba damuwata ban ganta ba, bata dakinta, bata bayi, bata ko'ina " Baba ya dafe gaban goshinsa, a sanyaye ya ce" sai da na fada maka, horon nan da kake yi mata ya isa hakanan, sai da na sanar maka ya dace ka dubeta, ka yi mata uzuri, abinda nake son fahimta a kanta na fahimta, Abdul matarka na sonka , ba bata sonka ba, ama ka ki ka bude idannuwanka ka yi hakuri ka bta kulawar da ta dace da ita, ko dan abinda ke tare da ita......, Shin idan ba'a hakuri da mata za'a zauna da su ne? Kuma ita ai na ga da saukima ko?, To yanzu da ka fito ina kake tunanin ta tafi ne?" Abdul ya dafe goshinsa shima , jikinsa du ya dauki ja abinka da farin mutun, ya ce" Nima ban sani ba, na yi tunanin ko wajenka zata zo?" Hajia ta idasa saukowa har tana hade kafafuwanta ta Karaso da sauri tana fadin" Macen da lokacin haihuwarta bai cika ba kace tana nakuda ABDUL hankali ka daga mata har ya kaita da fara nakuda ko menene haka?" ABDUL ya lumshe idannuwansa ya rasa amsar da zai basu,da ace zasu iya gane hallin da yake ciki, da sun hanzarta sun gabatar masa da ita a gabansa Hajia ta ringa kai kawo tana ji Alkali na maganar ko gidan Baba Lauratu ta nufa? Ko gidansu? Ina zata je da daren nan ga ciki ga bacin rai? Hijabinta ta gyara a jikinta tana nufar kofa ta ce" Ba inda zata je, nakuda ai ba abin wasa bace, tana cikin gidanta" Kusan a tare suka mike sunna mara mata baya, kowane da abinda ke bakinsa suka shige mota daya baki dayansu Muhammat ya ja su suka sake komawa gidan Cirko cirko suka same su ana ta maganar babu wanda ya fita da waya tsakanin Muhammat din da Sir din bale a yi kiransu a fada masu an ganta Ido Abdul ya lumshe yana jinginar da bayansa a jikin motar yana hangen kakaninsa da suka nufi dakinta kowane na saurin da Allah ya bashi ikon yi Gaba dayansu a rikice suke a kusa da ita A fitarsu har Fido ta yi kiran baba Lauratu dan ta ji ko gidanta ta tafi? Babar ta zo itama hankali tashe suka sake komawa dakinta a nan suka sameta a labe bayan sif jikinta na bari hankalinta du ba a jikinta ba, furucin bakinta shine ya sawake mata, ba zata iya ba, kasheta yake so ya yi ne? Ta gaji da wulakancinsa, ta gaji da komai da yake mata na wulakanci a rayuwa, ya barta ta tafi inda za'a san darajarta, tunda ba sonta yake yi ba, yana kiranta da AUnty! Hankali tashe Hajia ta karasa tana duban Baba dake gurfane tana sake dafata ta ce" Wai a kan gwuiwa take ne?" Baba ta gyada kai tana fadin" Haka muka sameta a kan gwuiwa take, inaga an sanar mata cewa an kashe yar gidan babansu ne a dakin saurayinta, kuma gongonsu da ta ga gawar itama ta rasu, shine kuma ya hadu da wani rikicin na Uman mallan" Baba ya ringa kama sunnan Allah yana salatin Annabi Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi wa salam yana gannin abin ya lafa mata tana sauke numfashi ya ce" Ni kam abin nan ya fara damuna, Uman biyu sannu kin ji? Allah ya raba lafiya, an zarce wata takwas abu ya isa haihuwa kam bale haihuwar fari, kin ga mijin fa da ya rikice har hatsari ya samu " A gigice ta dago fuskarta jin abinda Baba ya ce Hajia kuwa ta kalli Baba bayan ta cire hijabinta tana kiran docter ta ce" Haba alkali ya yaka kuma?" Amina kuwa daga zaunen sai gata ta ciciba ta mike tsaye , Fido da baba na tareta ama faman sumewa take yi Tana kallon Firdausi muryarta na rawa, daidai Abdul ya shigo a hankali dan kar ya yi hayaniya aje bata son ganninsa ya karra rikitata ta ce" Firdausi, Ab Ab Aban biyu ne ya yi hatsarin? Fido yana ina? Innalilahi wa inna ilaihi rajune..........." Ta idasa fadi tana daf da idasa zubewa dan gaba daya kafarta ta nemi gaza daukanta Da fido da Baba sun saka iya karfinsu dan talabeta, Haka hajia dake amsa kiran Docter tana fada mata sosai abin ya matso itama ta karaso ta talaba....uwa uba mai gaya mai tafiar shi ya fi kowa talabota a jikinsa a hankali ya zauna da ita a jikinsa yana ci gaba da shafa bayanta a hankali yana kallon yadda du ta rikice ya kama hijabinta ya ja ya cire mata shi domin du ya jika da zufa haka kuma ya janye ribom din dake kanta ya kasance gashin kanta ya saku ko zata ji saukin zafin nan, ya kai dubansa kan Fido da suka sakjar masa kuma suka kawar da dubansu yana fadin" Karra mana ACn cen Fido, kuma ki bude min dakin cen na ga idan zata iya zaman mota mu wuce asibiti ,......Hajia kirayi numbar Mansur plz ki sanar masa" ya idasa yana kallon Hajiar dake ta kai kawo kamar wace ke shirrin kwasawa da gudu, du ta rikice abinta kamar itace mai nakudar Da sauri ta shiga lalubar number Mansur din tana buga masa kira Baba kuwa kofi ya zuba ruwa masu dan dumi kadan ya zauna yana tofa Adu'a A hankali ta kwontar da kanta saman kirjinsa dan hakan shine baban abinda ta ji tana bukata a zuciyarta A hankali ya ci gaba fa shafa bayanta yana shafawa a hankali ya ce" Amina? Zaki taimaka min mu shiga cikin dakin cen na duba ki? Plz zaki iya?" Amina dake galabaice tana sauke ajiyar zuciya a hankali ta dago idannuwanta tana kallon fuskarsa Muryarta a raunane ta ce" ABDUL, wai nice auntyn ko?" ABDUL ya zunawa fuskarta ido, shi kam idan za'a nada sarakan rikici na duniya zai fara bada sunnan Mina, bashida tantama ita zata ci walahi A hankali ya girgiza kansa, dan bai san eh ko aa zai ce ba, hasalima bai san fadin sunnan take so ko kar a fadi ba Numfashi ta ja tana sake maida kanta saman kirjinsa a sanyaye ta ce" Haka kake ce min aunty mana, kai ga mai yar yarinya mana, Abdul baba yace ka yi hatsari? Ka ji ciwo ne?" Wata irin bugwa da zuciyarsa ke yi, da Amina ta sani, da ta bi shi a hankali kar ta halaka shi A hankali ya mike ya samu ya dagota da taimakon Hajia sannan suka kaita dakin Daga kofa hajia ta koma ta tsaya tana ta zufa, ita kam ta fi kowa rikicewa, kuma a yanzu kam haushin Honorable take ji, me yasa shi ba zai yi hakuri ba ko me ta masa ne sai ya ringa nemanta da rigima ne? Haba dan Allah Da kyar ya lalabata ta yarda ya dubata, Ai kam nakuda take yi sosai da sosai, ama idan suka maida hankali zata haihu a asibiti Cikin gagawa yake bada umarnin maza a hada kayan haihuwa, maza a yi kaza a yi kaza, sannan suka kamata suka sakata a mota Muhammat ya ja suka nufi asibiti a lokacin dare ya tsala sosai aka bar Bab lauratu da tsaron Biyu, domin Fido kasa zama ta yi ta shige motar su Baba mai Shanu A asibitinma gwagwarmayar ake sha, fama take baiwar Allah, nakuda sai sake nuna take ga likitoci a zagaye da ita A hankali bakin rikicin da mita ya mutu , ta dawo sai ido sai adu'ar da take yi a cikin zuciyarta Bata taba gannin namiji a hausa, a dakin haihuwar mace ba sai a kanta, Mijinta na zaune rike da hannunta a lokacin da ta zo kan gaba haihuwarta ta salamo gabanin asubahi, domin haihuwar sai da asubahi ta sanyi kai sannan ta samu ta sulube ƴaƴanta kwaya biyu, mace da namiji Yayan ake gogewa dan dora mata su a saman cikinta kamar yadda aka saba, ita kuma tana sake rintse ido da maida numfashin jin kamar an cire mata kaya zafin radafin na tafia yana barinta Jikin ABDUL gaba daya rawa yake, ya rasa yayan zai kalla, ko ita dake damke da hannunsa bata saki ba? A hankali ya rankwafo saman kanta yana shinshinar dukkan inda hancinsa ya kai, bama kamar wajen idannuwanta, da su hancinta, da sauransu, sai sinsina yake hannayenta cikin nasa a hankali yana kama sunnanta har ta bude idannuwanta tana kallonsa , shima yana kallonta A hankali ya sauke numfashi mai sanyi a saman fuskarta yana kallonta, muryarsa a bayane ya furta" I love you, I love u so much Minah, i love u, i love u meenah" Idannuwanta ta lumshe kirjinta na dokawa a hankali tana sauraron yadda yake lashe lebunnanta da suka bushe mata kayau kafin ya kame harshenta a hankali ya ringa tsotsa a yadda yake a rankwafen nan ta saman gadon tamkar zai cinyeta danya ........... Ido Docter ta zarro tana juyawa daria na kubce mata ta ce" Docter ka bari ta sauka daga saman gadon mana mu kimtsata ka ga mun mika yaren , Hajia kuma so take ta shigo ta ga yannayin jikinta" Da kyar ya iya barinta yana son jin amsa daga gareta, fuskarta yake kallo yadda idannuwanta ke lumshe A hankali ya ce" Ba zaki ce min kema kina so na ba?" Amina ta sake lumshe idannuwanta wani irin abu na ratsa ilahirin jikinta "Kai yau na ga abu, ABDUL me kake yi haka ne wai? Ka matsa a idasa fitar mata da gudan jinni mana a gani idan da dinki a yi a kimtsata jama'a, wannan haihuwa mai wahala ka tare mata numfashi idan ta summa fa?" Hajia ta fada tana karasowa , a yau harta da rawar nan ta tsofafin da ake janyowaa kiiiii sai da ta yi, kuka kuwa risris ta rusa shi ana bata hakuri, ƴaƴan nan da kyar ta ba alkali da Firdausi, ta rasa ina zata tsoma kanta dan farin ciki, ta rasa me zata ce me zata yi? Ashe Amina itace uwar ƴaƴan jikanta? Biyu? Namiji da mace? Haihuwa da ta masu karanci a familly dinsu? Ai su lamari yana da zafin gaske a zuciyarsu, a yanzu bata san me zata yi na nuna farin cikinta ga yarinyar nan ba, to ita arzikin ya'yan nan ai ya ninka maganar hawa kujerar gwamnati sau million a wajenta Haka ya saki hannunta ba dan ya so ba ya mike da kyar, domin a rankwafen nan a kadan ya dauki awa biyu, ita na nakuda ne shi yana nishi, kuma sai a yanzu ya ji kamar idan an jima jikinsa tsami zai yi har ya fadawa yan garinsu Murmushi ya yi bayan ya sake juyowa ya ga yadda Hajia tta shiga taimakawa Docter da nurse din dake kan Amina dan gyarata Hannunsa ya kai daidai zuciyarsa a hankali ya furta" Allah ka bani ikon haukatata a so na, domin idan abin ya kasance na zuciya daya ne tak, dayar bata ra'ayi, kwarai zan cutu" Yana fitowa ya ga wani shagalin, Fido na rike da Yar, Maansur na rike da yaron, Ita fido yar take ta karra budewa cikin lulubinta hakoranta a waje tamkar gonar auduga Shi kuwa yana rungume da ɗan a kirjinsa yana binta du inda ta yi, kuma yana kallonta kamar zai dauke idannuwansa ya lika mata Baba kuwa ya tafi masalaci domin hawaye ya ringa yi kamar ba baba ba, ya tafi yace ya tafi ya hantse a masalaci ya godewa wanda ya basu, Tsayawa ya yi yana kure Mansur da kallo, irin kallon nan na kankance idannuwa da dage gira guda ya ce" Kai ya haka?" Sai da Mansur ya zabura, dan bai san ana kallonsa ba, ya juyo yana rike dan da kyau ya ce" Man ka fito?" ABDUL ya karra kankamce ido ya karaso yana fadin" Ka ga bani na ga magajin ya ganni, kuma ka dan dawo daga nan bana so ana matsewa y'ayana waje haka, yaya yarinya na kwana kana binta?" Ido da baki Mansur ya saki yana kallonsa, irin yadda ya sha murr kuwa kai kace baban na Fido ne sak Fido ta karaso ta kawo masa macenma ya hade yana kallonsu Murmushi ya dago yana yi zai yi magana ya sake gannin Mansur Fido yake kallo, Fuska ya sha ya ce" Kai ba nace ka daina kallon yar ba?" Mansur ya dube shi yana fadin" Dan Allah wai meye haka? Ba za'a yita ta kare ba?" Firdausi ta yi gaba da dan sauri, dan bata kaunar abinda ke fitowa daga bakin Docter mai kirki Sam bata so, bata tunanin idan har tana ra'ayin haka a kurkusan nan Mansur yaa kai zaune yana fadin" Me ka yi kennan? Haba Man, yaya ba zaka kama min ba bayan ina so?" ABDUL ya tabe baki ya ce" Yaren nan ka tabata basa bukatar kwalba?" Da haushi haushi Mansur ya ce" Kai dan Allah ka rufa min asiri, kwalbar me yayan masha Allah babu na kasa da kilo 3?, Ina maka magana ta a bani na raya sunna kana kawar min da zancen?" ABDUL ya yi murmushi ya ce" Man, sai ka bita a hankali.....idan kace zaka takura ba zaka samu abinda kake so ba.....ka ga tanada tabo na maza a rayuwarta, sai ta gamsu da kai a aikace ba a furucin bakinka ba........so kawai ka yi ta kanka, domin nima ta kaina zan yi da rigimamiyata" Mansur ya yi murmushi yan saka yaran a irin gadon nan na turawa ya lulube su ya mika masa hannu yana yi masa congratulations A nan dai suka hantse aka kimtsa Amina sosai aka kaita dakin hutu bayan ta sha dinki aka barta tana hutawa, domin awa shida zata yi a saketa, ta haihu lafiya bata samu matsalolin haihuwa ba sai na kari kadai Ana dawowa daga masalaci aka mayar da baba gida, ama HAJIA tace aa sai sun je ta daidaita masu harkar Ac da sauransu dan kar a yi wasa a kama masu mura, yaran ta masu hoto fiye da a irga, hawaye kuwa daukewa take yi tana karrawa ABDUL ya nemi waje zai zauna da jalabiyar nan da suka sha kokowa da komai da ita, HAJIA ta nuna Aa, kawai ya wuce gida gasunnan, ai zuwa karfe goma za'a salameta a fara shirya zuwansu gida Har ya yi gaba ta sake kiransa ya dawo ya dan zauna yana kallonta Fuskarta a hade ta ce" ABDUL, matarka bata san y'ar uwarta na asibiti bane?" ABDUL ya yi dan tsai, sai kuma ya gane inda ta nufa, a nutse ya dan yi yannayi na bai sani ba Hajia ta tabe baki tana gyada kanta ta ce" Nzl. 53 *KU JI?, KUNNA JI? KU JI......KUNNA JI? KU GARZAYO DAN SAMUN NAKU, ZAKU SAME SHI NE DA FARIN CIKI, ANNASHUWA MUTANENMU, KWATENA CE, ALKALAMINTA NE, AKOY ZAKI, GA FARASHI MAI SAUKI 300 KADAI, TAKENSA TASBIWUL DABE, WATAU CARBIN KWAI...... SAI KUN ZO* Hajia ta tabe baki tana gyada kanta ta ce" Ok, idan ka koma ka sanar mata, idanma wani abu ke bin bayan kanta ta warwareshi, dan bana son iskanci?" Da dan mamaki ya kalleta, sai kuma ya yi murmushi ya mike ya fice Ko a cikin mota sau uku Muhammat na masa magana irin ta yanna taya shi murna, ama baya jinsa sai da suka tsaya bakin danja Muhammat ya yi murmushi ya ce" Su oga soyaya ta yi raf da su" A hankali ya dawo da dubansa wajen Muhammat, wanda sai da ya zabura, dan bai san zai ji shi Suka yi ido hudu, ya janye dubansa da sauri, shi kuma yana dan kallonsa, sai kuma ya yi murmushi kasa kasa yana dauke dubansa ya sake komawa cikin kujerar ya zauna yana tunanin yaya zai yi da tafiyarsa? Gaskiya ba zai je ba, ba zai iya zuwa ba, idan ya tafi yaya zai yi da tunaninsu? Ya tafi ya barsu su kadai? Aa zai ba kowa hakuri taron da zasu yi a China na wani aikinsu kan harkar kasuwanci da kofar shigo da kayan order wanda zai daukar masu sati guda ba zai halarta ba, dama ya zata zata karra wata guda da sati biyu kafin ta haihu da sai ya je ya dawo, tunda ta haihu yanzu shikenan ba zai je ba A haka suka karaso gida, suka tarar da gidan sai murna ake, babu mai ba dan uwansa hakuri kowa murna yake, bama kamar ma'aikatan su mata, mutanen sunna matukar jin dadin zama da ita, ba ruwanta, bata takuraka, bata wulakantaka, bata cin zalinka, idan kuma ta yi wainarta du mai rabo sai ya more, ya zamana har jiran juma'a suke ta zagayo a yi waina, domin yanzu yan tuya wainar sunna da yawa da ake taimaka mata, ga tsufa na ciki ga kuma yawan da aka karrawa wainar dan yan amsar sadaka, su kam uwar gidansu sunna alfahari da ita fiye da tunanin mai karatu Murmushi kawai yake yi na yadda ake masa barka, sannan ya shige bangarensa ya haura sama dan yin wanka , ko su Baba bai leka ba dan harda jini jini a kasan rigarsa, ko sallah bai yi ba saboda babu abin sakawa sai yanzu zai gabatar da ita a nutse A cikin bangaren Amina kuwa gyare gyare ne aka tada ba ji ba gani, sababin labulaye aka fitar aka kafa , harta da cafet sabo sai da aka saka, bangaren ya dauki kanshin turaran wuta komai sai haskawa yake yi, Biyu sun kasa sun tsare sai tambaya suke bin Baba da ita kan wai mamansu ce zata zo da baby biyu? Gaba daya murna da farin ciki ke tare da su sun kasa koda cin abinci har karfe goma sha daya ta gota sannan bakin asibiti suka dawo A hankali Hajia ke rike da ita dan taimaka mata, haihuwar ya'ya biyu ba wasa bane, sai a hankali karfi zai shigeka, shi yasa aka talafeta har aka dorata saman katifa madaidaiciyar da aka shinfida mata a falo dan ba zai yiwu a wuce ciki da ita ba ko dan baki, idan hutu take so ba zata rasa ba za'a fita da kowa ta huta Hajia ta dubi Baba ta ce" Laure, a dora ruwa dan a mata wanka sannan ta koma barcin" Baba ta dan risina ta ce" Hajia ai ruwan nan ya jima yana tafasa" Hajia ta ce" Masha Allah, maza a juye, ke Hindatu ke kuwa a juyo zabin da nace a dafa mata da ruwa ruwa ina fata baku zuba magi ba?" Hindatu ta amsa HAJIA itama ta tafi dak zubowar Hajia ta sake cire hijabinta ta zauna tana dauko macen dake tsala kuka har lebenta na kasa rawa yake yi karkarkarkarkar irin alamun zata yi kukan nan Ruwan zamzam ta dauko ta ringa diga mata tana murmushi ta ce" Firdausi wannan baki na yarki anya ba gidan rigima ba kennan?" Fido ta yi yar daria tana ajiye bokicin kunnun kanwa da Baba ta bata ta kawo ta ce" Hajia ai fa wannan baki na prncsss nima ina kallonsa da idannun basira, yana bani tsoro" Hajia ta ce" Nono take so, sai mamanki ta fito daga wanka zata shayar da ke kin ji amnana?" Fido ta yi murmushi tana talaba Amina suka nufi dakinta da aka kai ruwan wankan zuciyarta fesss da tarin farin ciki Sunna shiga ta taimaka mata ta cire hijabin da aka luluba mata sannan suka karasa wajen bayin Amina da muryar wadda ya sha wahalar nakuda ta ce" Fido, hala yi mini wankan za'a yi?" Baba dake daga ciki ta dan dago daga gyara ruwan wankan, da ruwan gyaran da tun yau ta dauri aniyar fara shi na jego ba ja da baya ba gudu ba sasautawa ta ce" Kwarai kuwa maza tube malama " Baki ta turo tana karasawa kasa kasa ta ce" Ai inaga ke baki damu ba ki ringa sala min wanka abinki, haka kika min ai na nonon rakumi" Baba ta yi daria ta ce" Bakin nan ba zai mutu ba, Fido taimaka min ta cire komai" Ido ta zarro ta ce" Ah wannan fa daya, fido fita dilla, kin wani tsaya a gaban manya zaki tubeni, jeki jeki kawai" Su duka daria suka saka dan a yadda ta yin tana hararar Fidon dole a dara Tubewa ta yi da kyar ta zauna saman kujera, Baba kuwa ta shiga kwatanta mata komai dan kar ya zo mata a ba zata sannan ta shiga kwatanta mata zafin ruwan Ai kuwa an sha daru, domin da kyar ta zauna aka yayaba mata ruwan wankan jegon, sannan aka mayar da shi gefe aka matso kayan gyara Kayan take kallo, a zuciyarta tana jin eh lalle tana na'am da su, haka kawai wannan karron take jin har sai ta karra gyaran jiki na zama cikin dumamar madara da kurkum, ji take yi a cen kasan zuciyarta tun kafin ta gama jinnin haila zata fara dafa kaza da bankanr dukkan abinda ya dace na gyara, haka kawai take ji idan bata yi haka ba, ba zata iya fuskantar du wani mai ruwa da tsaki a hargitsata ba......... Sosai ta nutsu Baba ta darjeta, sannan Fido ta sake kawo wani ruwan aka sake sirka shi sosai aka sake binta da shi Tana fitowa Fido da ta gama hada mata danyar madara sabuwar tatsa da maganin gyaran noni ta mika mata ita kuwa ta zauna ba gardama ta kafa kanta ta shanye tasss Baba ta ciro mata abin daure ciki, Fido kuwa ta sauko kayanta da ta turara mata sasaukan kaya mararsa nauyi, riga da sket na yadi mai laushi da rigar mama harda wani tsuma mai kyau wanda ta tanadar mata shi ne dan idan nononta na zuba ta ninka shi ta saka shi a wajen dan kar ya bata mata jiki da karni Tana zaune da tawul din sai da Fido ta busar mata da gashinta sannan ta daure da dan ribom karami tana jin wankan nan sosai take jin jikinta ya yi dama dama , gajiya ce dai ta haihuwa wannan sai a hankali, ama ba ita zta hannata kimtsa kanta yadda ya dace ba Sai da ta turara jikinta da sansanyan turaran wuta, ta dauko kwalin da ta jima bata saka ba ta sakawa idannuwanta , sannan ta dauki jan bakin da ta yi dan tsai tana kallonsa, sai kuma ta yi murmushi ta dan gogawa lebenta ƙadan ba da yawa ba sannan ta daure cikin nata ta saka bra din da rigar , kuma ta saka sket din tana dan buda kafarta ta ce" Fido kin tabata zan iya barcin kirki da sket din nan?" Fido ta ce" Sosai aunty, ko kim fi son zani ne?" Baba ta dago daga tatare kaya tana mayarwa ta ce" Ke rabani da wani zani, wannan din ya isa ai gayanan yana jayuwa sosai kuma ya zauna mata bai matseta ba, barta ta fara abin kirki kar ki sa ta fasa Abaya fara mai haske sosai , watau shara shara ta dora sai mayafin abayar ta ce" Baba wannan abayar fa sabuwa ce kamar wace zan je anguwa?" Firdausi ta ce" Aunty kin san yanzu baki zaku yi ta yi, da abokansa da yarensa da matansu da mazansu, ga mai wancen dakin itama ko?" Amina ta yi murmushi a ranta ta ayana' Ga shima da kansa mai gidan, wanda sai na bambance masa kalar nawa rike wuyan namijin da na wace ke lasarsa!, ABDUL........... Mutu ka raba da ni da kai, na yi aniyar zama da kai, babu mai rabani da kai...... Ciki ko kai ne!, Sai dai JARABAWA!'. ( ABDUL mata bisa kanka fa) A hankali take takawa yanzun , Fido na gefenta , Baba Kuwa tana idasa kimtsa dakin da saka turaren wuta Dan dakatawa ta yi tana hutawa, Fido kasa kasa ta ce" Aunty mijinki sai kallonki yake" Amina da ta sani sarai, domin tunda ta fito ta tsinci idannuwansa a jikinta ama ta basar ta dan harareta tana fadin" Zan fa mare ki" Firdausi ta yi dariya da sauri tana tare yaren da suka saka ihu sunna nufo mamansu ta ce" Kai meye haka dilla ku nutsu kar ku kayar da ita!" Amina ta dubeta ta ce" Firdausi kin ga bana son haka kin ji, matsa min na ji dumin y'ayana mana haba dan Allah" Firdausi ta dan matsa tana karasawa ta ce" Ai sai ku yi tunda sabonku ne!" A hankali ta ringa rungume su tana ta aukin tambayarsu sun ci abinci? Sun yi kaza? Sun yi kaza?, Tamkar wace ta shekara bata tare da su A hankali ya karaso hannayensa rungume saman kirjinsa yana kallonta , girman cikin nan ya ragu sosai ga daure shi da aka yi, sasaukar shigarta ta tafi da imaninsa, nutsuwar kan fuskarta, da dogon karan hancinta, zuwa lebunnanta na gigita duniyarsa A hankali ya ce" Amyn Farid, Fadeel......Amna nd Ammar?" Wani irin tsammmmm. Ya sake ratsa dukkan jikinta, a hankali ta dago idannuwanta tana dan son riko Hasan da ya rage domin Husaini tuni ya koma wajen Hajia dan ta bude yaren a karro na biyu tana jajen a zo a basu nono su sha Hannunsa ya janye cike da farin ciki shima ya nufi cen din harda dan tsalensa ya barta da Abdul Ido ta zarro a hankali tana rakashi da kallo, sai kuma ta dawo dubanta kan Abdul A hankali ya yi murmushi a saman lebensa ya furta" I love you" Da sauro ta dauke dubanta, kirjinta na bugawa ta nemi rabe shi dan komawa wajen katifar A hankali ya karasa gefenta kadan ya riko hannunta cikin nasa yana dan murzawa ya ce" Hajia, kin ga wai kar na taimaka mata" Hajia ta juyo , daidai Amina ta yi tsuru tsuru ta ce" Amina zaki karaso ki basu hakinsu ne yaren nan ko sai sun fara galabaita?" Amina ta gala masa harara tana turo baki a hankali ta karaso din ta zauna saman kujera ta zuba masu ido yadda suka zuba mata tana jira kowa ya fira sai ta ba yaran nonon ko? Ai ja za'a sakata tubewa a cikin jama'a ba ko? Hajia ta sauko wajen katifar tana duban Fido ta ce" Kawota ita sarkin kukan a sakasu tare kin ga shima ya fara gajiyawa bawan Allah Gyara zamanki mana Amina?" Ido ta zarro tana kallon Hajia muryarta a sanyaye ta ce" Hajia, ba sai na shiga ciki ba zan basu?" Hajia ta kalleta da mamaki ta ce" Cikin ina?, Amina bude rigarki ki ba yara nono mana?" Da ido da baki ta sake budewa da mamaki tana kallon Hajiar, kasa kasa ta ce" Hajia da maza fa a dakin" Hajia ta juyo tana neme nemen mazan, maza dai hudu ne a dakin, Mijinta, yarenta biyu, sai shi dan jaririn dake cikin tsuma Abdul kuwa ya gyara zama daria na son kubce masa, so yake sai ya ga nonon, shi fa nonon zai gani da kuma yadda za'a ba yaren, ya san sai an yi wannan rigimar, shi kuwa abinda zai saka shi nishadi kennan Hajia ta kama abayar ta yayeta har ta hada da dan kwalin, hakan ya bayanar da lalausan gashinta mai cika da baki da daukan ido Hajia ta fara fada tana cewa" Kai ku ji min yarinya, yaren nan tun a asibiti suke rarume rarume kina kallonsu kina sada kai kamar gaki a gaban sirikanki, ki bude ki badu kalaci tun muna mu biyu" Amina zata yi magana tana tare hannun Hajia da zata ciro mata nono aka yi salama Risala ce, da mahaifiyarta, da auntynta suka shigo cikin shiga irin ta kece raini sa nan suka ja suka tsaya sunna jiran gannin idan wajen ya isa su zauna ko su gaisar da su daga tsaye su juya? Juyowar da hajia ta yi , ganninta da suka yi, a irin wajen da suka ganta a zaune, da kallon da ta masu ta fauke kanta, bama kamar Risala da take jin haushin sai yanzu ta shigo gannin yar uwarta da ta haihu? Haihuwa fa? A fitarta ana iya dawowa da gawarta fa? Ama ko ta lekota? Ita bata tsoron itama ta sameta ne? Idan ta sameta daga ita sai ita a gidan fa? Ko ta isarwa kanta komai ne ita mai iyaye? Kusan kimuwa a kasa Maman Rislaa ta yi gannin kamar goshin Amina da na hajia zai hadu ana kiciniyar ciro nono ta ce" Kamar Hajia Hauwau a nan?" Hajia ta sake juyowa bayan ta ciro nonon ta amso yar, shi Kuwa ABDUL daga zaune har dadage yake yana leka nonon da mamakin ya karun kuwa ya ji Hajia na fadin" Eh nice wai ba zaku shigo bane kunna tsaitsaye a kan dokin kofa?" Mamakinta kasa boyuwa ya yi, ta ce" Ke ce? A nan? Hajia?" Hajia ta juyo da Yar a hannunta tana dan zizigaTA ta dubeta da mamaki itama ta ce" Eh nice hajia nace ku karaso mana kun tsaitsaya a bakin hanya?" Maman Risala ta dafe haba, irin mamakin nan, da tarin abin al'ajabi ta ce" Ikon Allah, abin mamaki baya karewa, yau ga hajia a dakin mai waina rike da y'arta" Ba kalacin Hajia ba, yau harta Risala sai da ta juyo a zabure, dan ta tabata maganar mamanta a ciki ta so yi ta fito waje ABDUL kuwa kallo daya ya mata ya sake maida kansa kan Amina dake ta kare nononta yana murmushi, shi fa Allah yana ganni matar du ta sare masa walahi Hajia kuwa sai da ta mata kallon anya kinada hankali? Sannan ta ce" Hajia ta tabe Baki tana gyada kanta tace " Nifa kwata kwata ban fahimci inda kika dosa ba, me kike nufi ne? A hankali Abdul ya e hajia ki saka yarinyar a nono mana kar ta mayar? Hajia tace ko ina zuwa Ta sake gyara Amina da kyau ta ciri nonon duka biyu ta tallaba hannunta ta nuna mata ta saka macen a hannun dama, sannan ta saka namijin a hannun hagu ta saka gizo tallabe mata shi kafin ta iya da kanta tana fadin sai kin jure fa akoi zafi Amina ta guda kanta tana rantse idanunta domin namijin kamar jira yake yayi rage dashi macen ce ma ake ta koya mata a hankali a hankali Karasa wa tayi tana kallon Risala ta ce" Ke tun jiya kina ina har mu na waje muka shigo muka raka yar uwarki haihuwa bakya wajen? Sannan har aka sakomu yau sai ciro waya ya koma ya gyara zamansa yana daukanta hotuna a dabarance yana murmushi bata san kin sauko daga kiyayar da kike yiwa matar jikan naki ba shi yasa ta yi mamaki har ta furta, kin san ita batada munafurci ko cem, takan fadi abinda take tunani komai muninsa ne sai dai ka yi hakuri idan ya maka ciwo" Hajia ta gyada kanta ta ce" Hakane, ba mamaki, halaya ne ai na mahaukata, gashi ita kuma cikin kyakyawar shiga" "Hajia nice kike zagi da mahaukaciya kuma yau?, Hajia nice mahaukaciya? Walahi ni ba mahaukaciya bace, ai ba karya aka yi maki ba, da baki nuna mata kiyayar ba ai da ba zan zo na fada ba, ko kin ga na maki kage a nan ne? Maman risala da itama ta harzuka ta fada har tana cire hannun yar uwarta dake mayar da ita baya dan bata so ko kadan Maman risalar ta zubar da mutuncinta a idannuwan sirikinta, duda aikin gama ya gama sunne basu sani ba, a hausa ai ba'a haka, bahaushe da kunya da kara aka sanshi ba shirme ba Rai bace ta ce" Dan Allah adda ki daina turani haba dan Allah, ita komai ya tashi sai ta wani nemi ta wulakanta mutane , ai nima ba yar talaka bace bale a zageni da arziki, ita yarinyar da kika tsana din ai dan yar mai datin hula ce, ko karya aka yi? Kema da bakinki kin ce jikanki ba zai zauna da mai tuyar waina tana bi kwararo kwararo da ƴaƴan shegu a hannunta ba, shine yanzu zaki wani hade kai da ita a cutar min ya? Ba zai yiwu ba tunda aka fara haka Risalar ba zata ga da kyau a wajenki ba, Risala kuwa yar gata ce gaba da baya ba zan bari a wulakanta min yata ina ji ina gani ba, koda banida da shi ba zan yarda abinda kika yiwa wancen ki yiwa yata ba walahi!, Ke risala wuce mu tagi gida wuce min!" Sama sama take maganar danma du wanda bai ji ba ya ji, gaba daya zagin da ta juyewa su Amina da wulakanci tasss kowa ya ji haka kuma sirikinta dake murmushi gaba daya murmushin ya dauke a fatar bakinsa A nutse ya mike cikin shigar dakakiyar shadarsa ya karaso yana kallonsu Aa hankali ya ce" am, ku yi hakuri ku koma waje, yanzu ta fito daga asibiti hayaniyar nan ba zata haifar mata da abin alkhairi ba................" Maman Risala ta tabe baki, bata sake wata muguwar maganar ba dan ko HAJIAR gaba daya bakinta a mace tana kallonsu ne Maman Risala ta sake lekowa ta ce" Ke wai ba da ke nake ba dan kutumar ubanki?" Risala ta juyo ifannuwanta sun cika da kwallah ta fara taku daya biyu ta tsinkayi muryarsa a dakensa ya ce" Idan kika fita daga get din gidana a yau ba tare da izinina ba na yanke igiyoyin aurena dake kanki" A haukace ta ci birki tana juyowa ta kalle shi idannuwanta na firfitowa waje Haka mahaifiyarta da yar uwarta, haka hajia ta juyo tana kallonsa zuciyarta na karra tsintsinkewa Bakinta na rawa ta ringa nuna kanta, da shi tana son furta wani abin ama ta rasa mene Mahaifiyarta ta sake shaka ta saka hannunta ta fardota tana fadin" Sai me, ai mai kyai baya tsawa , wuce mu je Alhamdulilah ba ciki bs goyo bale abin duniya ya isheni, menene a auren da ya wuce cusa bakin ciki da kaskantar da mutun da darajarsa da komai? Wuce mu je zaki samu sama da shi a komai, ai ba shi bane autan maza a duniya!" Janyo hannun yar take yi , yar na tirjewa Da karfi ta sake juyo da ita dan ta fuskanci kamar bata jinta, sai dai abinda y'ar ta yi ya sakata zuba mata ido, domin hannunta ne ta janye a hankali hawaye na zubowa yana neman bata kwaliyar da idan biya ne zasu yi a yi mata zasu iya kwararar dubu hamsin A hankali ta ce" Risa, mu tafi mana kar rana ta yi zafi ta taba maki fata kin ji?" A hankali Risala ta langwabar da kanta tana kallon Mamanta ABDUL kuwa ya kama hannun Hajia da ta zama tamkar gunki ya shige ciki da ita, direct dakin Fido domin ya kula tana da bukatar dan kadaicewa ko yayane A hankali Maman Risala, dan kar su Amina su jiyota ta ce " Me kike nufi da dakatawa a nan bayan kina gannin wulakancin da ake mana , ni uwarki da ke din kanki?" Risala ta fashe da kukan da take rikewa ta kasa yin magana Mamanta ta zarro idannuwanta tana nuna kanta ta ce" Risa, risa namiji zaki zaba a kaina?" Da sauri ta girgiza kanta tana kallon mamanta ta ce" Aa mama, ba maganar na zabeshi bane mama, mama a shekara ashirin da takwas na same shi, na so shi, ya so ni, mun yi aure, yanzu na kai ashirin da tara a duniya, idan har ba zanen kadara ta fitar da ni ba zaki so na dawo na sake maki wani zaman? Mama banida matsala da shi, ban rasa komai ba, kema kin san a aurena zuwa yanzu na tara abinda ban tara ba kafin auren nawa......., Mama kakarsa ce, itace mamansa, itace duniyarsa, idan tana fada s kansa bana gannin laifinta, kamar kece da mu fa......... , Mama, babar matsalarma ina son shi, mama ina son mijina, idan na biki muka tafi na dawo ina neman saka kanmu a uku baki dayanmu fa? Dan na tabata wata rana sai na tarda ABDUL, idan yau ya koreni, gobe ya koreni, jibi ya koreni, wata rana ina iya samun galaba a kansa, ina iya sakashi a uku, uwa uba na saka kaina...Mama ribar me zaki ci?....." Dau mahaifiyarta ta dauketa da wani mahaukacin Mari tna nunata da yatsarta ta ce" Ni zaki watsawa kasa a ido a kan Kato?" Risala da ta duke tana kuka tana girgiza kai, yayar mahaifiyarta na rike mahaifiyar tata har suka janyeta suka fita da ita a falon Amina sannan ta mike da gudu itama ta fita ta nufi bangarenta tana cire abubuwan kwaliyar da aka bata lokaci ana mata dan ta yi kira ta sanar kishiyarta ta haihu , mahaifiyarta ta zabo mata leshen dake da kyau da tsafa aka caka mata dauri, ama abin ya kare a haka? Yanzu yau ita da mahaifiyarta ne wannan abu ya faru? Ina zata shiga da ranta? Shin ABDUL da mamanta wane zata zaba? Idan ta yarda ta zabi Abdul din ya wulakantata da gaske fa? Shin yaya zata yi da rayuwarta? Wayarta ta dauka ta ringa kiran mahaifinta, sai dai ya fada mata yana cikin aiki, da zarar ya zauna zasu yi magana, a dole ta kashe ta ci gaba da kukanta, domin an saba mata tana samun damuwa takan yi kiran mamanta ne ta zo inda take, ama a yau da maman nata ne damuwar a dole ta rasa inda zata saka kanta ____________________&__ A cikin daki, Tunda ya zaunar da ita ya fice ya je ya samo mata ruwa mai dan sanyi sannan ya dawo ta wajen su Firdausi dake zaune jigum jigum yana dan murmushi ya ce" Sorry an mata mun shiga dakin cen dan lokaci?" Fido ta yi murmushi tana fadin" Dady mu da muke nan muna dan hirarmuma" Shima ya yi murmushin ya kalli Amina kkasa kasa ya ce" Sun sha?" Manyan idannuwanta ta dago ta dora saman fuskarsa, a hankali ta dan masu kasa kasa sai kuma ta mayyar bakin hanyar da Fido ta bi dan basu waje Murmushi ya yi ya sake fadin" kins da kyau, jan ajin kuma ya amsheki Hajiar ABDUL" Yanzuma baki ta dan tabe bata ce masa komai ba har yaa mike ya nufi ciki yana jin dan damuwa na rashin kulashin da take yi A hankali ya zubawa HAJIA bayan ya bude ya mika mata sannan shima ya zauna a gefenta ya yi shiru yana sauraron hucin dake fita daga bakinta A hankali Hajia ta sauke numfashi tana girgiza kanta ta ce" Ka san a duniya, babu wulakantace sai wanda ya wulakanta kansa ta hanyar daukan duniyar nan a wani abu mai dorewa, bayan tunda aka haifeka kake gannin jariri, yaro, saurayi, mai aure, uba, tsoho, mace ko namiji na mutuwa sunna zuwa wajen da ba'a katse rayuwar sai dai ka yi ta girban abinda ka shuka na dindindin, ama a haka muke manta komai muna aikata abubuwan da suka fi karfin kawunnanmua........" ABDUL ya sake dubanta a hankali ya ce" Daj Adam din kennan, alkhairinsa ya kasance mai rokon gafarar ubangijinsa sannan ya tuba da gaskiya da daukar niyar ba zai kuma maimaita laifin da ya aikata ba" Hajia ta gyada kanta tana sake sauke wani numfashin ta ce" Yanzu ace da furfurata, na wulakanta kaina har yarinyar bayana tana irin haka da ni? Gaba daya na manta darajata ta shekarun da Allah ya bani, na manta mutuncina , da girman darajar da Allah ya luluba min,na wulakanta marainiyar Allah,na wulakantata bata taka min ba, bata kashe min ba, du a kan son kai, gashi yanzu an zageni ko budar baki na kasa yi dan gaskiya aka fada min, a kan son kaina da rufewar idannuwana................" Abdul ya sake fuskantarta bai ce komai ba yana kallonta Hajia ta sake girgiza kanta ta ce" baka sani ba fa, ita fa siyarma du haka take, ka ga zamu hadu da yayan cikinmu, wasu mun yi jikoki da su mu yi ta abubuwa kamar ba zamu mutu ba, a yi ta iface iface da manyan da kananan, mu yi ta tsare tsaren yadda zamu samu mu ci kudade ko na waye, mu yi ta shiga hakin junna, uwa uba ABDUL RA'UF kulun bama koshi da abinda muke samu, kulun burinmi mu samu sama da abinda muka samu, ba ruwanmu da wa zai ritsa ko wa zai jigata, idan dai kawunnanmu suka wucewa jifa to ya fada kan kowama......, Abdul bama kaunar a rabamu da talaka, ba ruwanmu da talaka, mun manta mu menene tushenmu, da yawanmu sun rasa aurensu a haka, wasu a cikin haka sun rasu, wasu sun dimiya basa tuna komai irin Allah ya kyalesun nan..... Abdul yau nice na jawa kaina wulakanci irin haka? Wai a kan dan cikinka ake gannin bak dace na taba ba dan kawai na nunawa yarinya tsana? Bata min komai ba dan kawai bata kwaliya irin ta yan matan zamani, bata gwali da abubuwan yan matan zamani shikenan ni ga kakar Gwamna dole gwamna ya auro matar gwamna ko? A haka idona ya rufe na dauko yar mararsa kunya na hada a cikin ahalina, idan da haihuwa itama ta haifo ta kuma bada tarbiya irin wace ta damu a gidansu.........." A hankali ya kama hannunta yana murzawa A tausashe ya ce" Hajia ya isa haka kin ji? Ki kwontar da hankalinki, abinda ya faru ki kadara wani mataki ne na samun cenji a rayuwarki, ke mutun ce, baiwa ce ke, ba zai taba yiwuwa ki rayu ba laifi a rayuwa, baban laifi shine na daukan alhakin bawa, Allah baya yafe wannan, ki yi kokari ki gyara mu'amalarki da kowa, ki kokarta ki daidaita mu'amalarki da jama'a, ba wai Mom twins kadai ba, kowama, bama kamar Alkali, a kusa kusa ban ga namiji mai hakuri da iyalinsa irinsa ba, ki yi kokari ki gyara hakan, sauran du saura ne marar karfi, domin kamar yadda kika ce, dama kika bada har yau aka ci maki zarafi haka, idan ba wannan damar dole a mutuntaki, mutun dama shi yake fara mutunta kansa , sai ki ga ana mutunta shi, hakan kuwa ta yannayin mu'amalarsa da mutanen dake zagaye da shi ne........." Hajia kai take gyadawa har ya dasa Aya A hankali ta yi murmushi ta ce" Ban taba tunanin zan ji kunyar Amina ba a rayuwa irin na yau" Shima murmushin ya yi ya ce" bata rike ki ba, koda ta ji haushi ba zata wulakantaki ba" "Hakane, tanada hakuri sosai, ta jima tana bautawa mijina , ama ba abinda ke shiga tsakanina da ita sai mugwayan kalamai..........na yi dana sannin wasu halayana, kuma in sha Allah sai na gyara abinda zai gyaru idan har inada sauran numfashi a duniya" Hajia ta sake fada tana kallon ABDUL ABDUL ya ce" Allah ya aminta" A nan dai suka ci gaba da dan zantawa, harta da masu girki da komai sai da ta sanar masa ga yadda za'a yi, uwa uba kayan da Amina zata yi anfani da shi na sunna, a gangaro kan irin kular da za'ana badawa na uwar da ƴaƴanta baki daya, abubuwa dai wanda shi da kansa sai da ya samu kansa da yin murmushin jin dadin hakan a zuciyarsa, Ya san Uman biyu zata dube shi, ya san zata amsa shi, ya san yanzun da bata son Aunty hakan na nufin tana iya amsarshi a matsayin miji, idan kuwa ba haka ba bai san yaya zasu kare rayuwa ba, tunda shi dai ya san ita din kaunarsa ce, zuciyarsa ce, soyayarsa ce, jarabawar da zata rabashi da ita mai zafi ce, baya fatan ganninta, kai da ba dan kar ace wani abin sai yace gwara ta mutuwa da ita, wace ya san ya bar duniyar ne kwata kwata da ya yi wani tunanin daban ___________________________________ A hankali aka ci gaba da samun baki, aja amsar baki tare da alkhairansu Kwonci tashi har ranar sunna ta zagayo yara suka dauki sunnan iyayensa mahaifa , ama suke masu kiranye da Ammar da amna dan kare sunnan Taro ne aka yi na mamaki, taron da ya tara al'uma masu yawa, masu dauke da position din rayuwa kala kala ABDUL RA'UF mai mutane ne, matasa da datijai babu wanda babu, masu hannu da shunni da mu du gamunan, taron da ya yi niyar cenza sutura sau uku irin na Uman biyu, tun ta farko da ya saka bai sake zaunawa bama bale ya cenza Yana waje tare da jama'arsa ana shan sunna A cikin gida kuwa tunda Risala ta bar bangaren nan sai a yau wunnin biki ta fito, shima a zuwan mahaifinta fatiha ya sameta ya yi mata wankin baban bargo da fada mata gaskiya mai dacin gaske, ya fada mata cewa idan ta yi wasa tana iya yin biyu babu, gwara ta sauke kanta ta yi zumunci da uwar gidanta su zauna lafiya A dole ta shirya kanta cikin rantsatsiyar shada da gwala gwalai da rantsatsen mayafi ta je ta samu kujera ta kame tana dan dane danenta da dan kallon abinda ke faruwa, taron cike yake da manyan mutane jama'ar hajia da na ABDUL, wai abin arzikin da ake shigewa da shi dakin da aka ware dan kar a rikita dakin mai jego du na wannan matar ne? A dole ranta ya ci gaba da kunna na rufewar ido sai da ta yi da gaske sannan ta hanna kanta kuka tana biye da motsin kowa Gani take yi kowa ya tsaneta Gani take yi kowa a bayan kishiyarta yake Gani take yi kishiyarta ta asirce mijinsu da danginsa ne Gani take yi ba banza ba, wannan abin ba banza ba Ba zata iya amincewa cewa matar da aka yi auren hadi da itane take da wannan taron a kanta da soyayar dangin miji, ita matar da aka auro dan soyaya an maida ita gefe ace kuma lafia ne Sai dai ita ba zata iya wulakanta kanta haka ba Babu wanda zata lashi kafarsa dan ta samu fada walahi Kuma bata san kofar boka ba Haka kuma.malami ba zai ci kudinta dan a karya ba Ita kam ta bari da Allah kawai!, A ci gaba da nuna mata fifikota bari da Allah kawai! Alhamdulilah taro ya ci lafiya ya tashi lafiya, jama'a na nesa da na kusa kowa ya kama gabansa an bar ma'aikata da gyaran gidansu, Tun karfe bakwai yau Amina ta kwonta Yaren kansu bata tsaya nemansu ba , sunna wajen Baba lauratu da ta dora ruwan zafi zata gasa masu jiki, idan sun gama tace su goya su, kanta tarwatsewa zai yi tsabar gajiya da ciwo A hankali ta kwonta saman lalausar shinfidarta tana jan abin rufarta ta maida shi gefe ta kurawa waje daya ido ta afka a duniyar tunani A yau ta ga abubuwan da bata taba tunanin zata iya gani ba a rayuwa na arziki da kauna da kwonciyar hankali Kuma duka sun tarun mata ne dan ABDUL DINTA!, Dan murmushi ta yi tana juyowa da dan karfi dan ta gyara kwoncintsa, sai dai me? Ido hudun da suka yi da shi ya sakata dan zarro ido tana dan mikewa tana kallonsa ta ce" A hankali ta dan gyara rigar barcin dake jikinta, mai hasken fari da mannewa a jiki tana dan son wara idannuwanta dake shanyewa dan kansu tamkar wace ke masu haka da gangan, muryarta a dan shake ta ce" Hi " Idannuwansa ya lumshe, hannunsa daya a cikin aljihun wandon barcinsa irin budaden nan mai dan kauri mai ruwan blu , watau hasken sararin samaniya, sai rigar ciki singileti da kuma ta sama ta wandon wace bai balla boturan ba haka ya ratso al'uma ya taho , hannunsa daya kuwa a saman kirjinsa yana dan shafawa a hankali, yana son dauke yar damuwar dake tattare da shi wace bata wuce rikicin da suka yi daa Baba da Hajia kan maganar Amina, cewa Amina gida zata je ta yi wanka, wai gidan Baba, bayan shi yana niyyar fasa tasa tafiyar dan ya sake raya duniyarsu shi da ita da ƴaƴansu hudu? Shikenan sai a wani ce za'a tafi da ita? Bakin nata da ta ce Hi, da amon muryarta ya nemi cenza tunaninsa A hankali ya karasa inda take zaune, ta yi irin zaman nan da ake matsewa a cen saman gado, ta dan hade bayanta da jikin abin gadon , kafafuwanta kuwa ta dan dago su ta dora hannayenta samansu A hankali ya haye gaba dayansa saman gadon ya yi zaune yana kallonta Bai san a yadda zai fasarta lamarinta a tare da rayuwarsa ba Tanada girma mai girman da girma bai isa ya kayade ba Yana gannin mutuncinta, kimarta, da dumbin soyayarta a zuciyarsa Bai taba tunanin zai samu wannan jarabawa a kan Amina ba A hankali ya kamo hannunta ya sakaa cikin nasa, sannan ya shiga murzawa kadan kadan yana kallonta, muryarsa a ciki ciki ya ce" Ba zan iya barinki ki tafi ba " Amina ta bude lumsasun idannuwanta ta zuba masa su, ba zai iya barinta ta tafi ina ba? Ina yake tunanin zata tafi? Hala a tunanin ABDUL tana kan bakanta na neman saki? Lolz lalle Iska ya furzar daga bakinsa mai zafi ya ce" Shi wankan, a nanma ba sai ki yi ba? Idanma babu mai maki ba gani ba?" Sai a yanzu ta dago zancen, kuma sai abin ya bata kunya A hankali ta dan cicira idannuwanta gefe na alamun kunyar, wanda tsaf ya karanceta bar ya samu kansa da sakin murmushi, domin dama yana tunanin gannin haka daga gareta, Aminansa ba dai kunya ba Ni tuni na ce masu ba zaki tafi ba, suka ce sai kin je, shi wancen Alkalin harda fadin da kansa zai zo ku tafi sai kin yi wankan jego a gabansa, baya ciki da cin amana.....Wifey Ni ai ba dan cin amana bane ko?" Ya salam, gaba daya nema yake ya cenza duniyarta da dukkan wani tunaninta A hankali ta janye hannunta taana kallonsa da lumsasun idannuwanta ta ce" Yanzu zamu tafi ko gobe?" Shiru ya yi sshima yana kallonta, sai kuma ya budi bakinsa a hankali ya ce" Binsu zaki yi?" Da idannuwanta ta bashi amsa tana masu luuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuuu sannan ta dage su Jajayen lebunnansa ya dan cije yana kallonta ya ce" Tafia zaki yi ki barni ni kadai?" A hankali ta dan sake matsawa dan matsota yake yi kasa kasa ta ce" Dama ai ba tare da ni kake ba, ko na tafi ba kai kadai bane" "Meenart" ya fada aa hankali yana katseta Amina ta sake bude idannuwanta aa hankali ta ce" Aban Amnahhhhhhhh" Abinda zai fada ya samu kansa da mantawa har ya dan daburce, wannan ne karron farko da ta budi baki ta ce masa Aban Amnahhhhhh, ba ABDUL ba ko kai ka bari fa Murmushi ya dan saki a hankali ya ce" Bakya tausaya min ko?" Baki ta dan tabe, sai kuma ta dannawa gefe harara kasa kasa ta ce" Aban Amnah kai ka tausaya min ne?" Ido ya zarro har yana dafe habarsa , da madaukakin mamaki ya ce" Lah hararata kika yi?" Amina ta bude idannuwanta tarr tana kallonsa, ta turo bakinta hadi da shagwabe fuskarta ta ce" Ni aa, gefe na harara fa" "Umum um um Uman twins da ni kike " ya fada yana sake matse mata waje Amina ta dire kasa hakan ya bayanar da iya tsayin rigar barcin nata da kwata kwata duwawunta kadai ta dan dara A hankali ta duka tana bashi baya ta dauki takalminta na kusan bed ba dan sai ta yi haka zata saka ba, aa , kawai hakanan ta yi hakan har tana wani irin dan girgiza ta saka takalmin sannan ta mike ta dan gantsare tana yin hammar da ba ta gaskiya ba sai kuma ta janye ribom dinta ta dan girgiza kanta kadan, hakan ya sa gashin kan nata bajewa ya dan watsu gefe da gefe sannan cikin tafiyar izgili ta nufi bayi kasa kasa tana fadin" ABAn Fadeel, bana ciki da rigima, kawai Allah ya bamu alkhairi, yo Allah na tuba yau ka fara cin amana kuwa, ka je kawai wajen dayar na san tana cen tana kyarkyara" da gangan da zata ce kyarkyarar har sai da ta kama kofar bayi ta juya duwawunta son ranta sannan ta shige ta datse kofar tana zarro ido hadi da dafe kirjinta dake dokawar tsoro ta rufe idannuwanta da hannayenta biyu wata mahaukaciyar kunya na son halakata ta rufe bakinta dan kar ta kurma ihun kunyar da ta rufeta "Dady?, Dady?" Muryar Husaini da ya shigo yiwa mamansa sai da safe ya yi ta salama shiru ba'a amsa ba sai da ya karaso ya taba gefen hannun babansu da ya tarar a zaune tamkar matacen mutun ya kurawa kofar bayi ido ko kiftawa baya yi ya ringa ambaton sunnansa ama shiru, dan haka ya dafa shi yana sake kiran sunnan da karfi Wani irin ajiyar zuciya ya sauke, a zabure ya kalli Husaini, sai kuma lokaci daya ya kalli jikinsa Cikin dabara ya dora kafa daya kan daya yana kallon Husaini muryarsa a cen kurya ya ce" Son, ?" Husaini ya sake kallonsa a hankalin sshima ya ce" Dady baka da lafiya ne?" ABDUL ya dan fitar da idannuwansa irin bai san me yasa ya ce haka ba ya ce" Rashin lafiya? Me ya sa kace banida lafiys?" Husaini ya shafo gaban goshinsa da zufa ke tsatsafowa ya ce" Dady kalli fa goshinka?" ABDUL ya ringa sauke ajiyar zuciya a boye cikin dabara ya kakaro murmushi ya ce" No lafiyata kalau Boy, wai mema kake so?" Ya karashe yana dage masa gira daya Husaini ya yi murmushi yana kallon gashin girar babn nasu kamar wanda ke gyaran gira, ga cika gaa tsari ya ce" Mama ne ni ban mata good night ba, shine na zo" ABDUL ya yi murmushi ya shafa kansa yana fadin" Mamanka tanaa bayi, zan sanar mata ka tafi ka kwonta saboda school fa gobe" Husaini ya gyada kansa ya juya yana masa byby A hankali ABDUL ya yi masa by din shima sannan ya sake maido dubansa kan kofar Mikewa ya yi ya karasa ya kama abin budewa ya murda, ama a garkame ta rufe ruf A hankali ya dora hannunsa saman kofar ya dan shafa kofar yana sauraron ciki ko zai ji motsi, ama baya jin komai Wata ajiyar zuciyar ya sauke kasa kasa ya ce" Na san kina jina............." Amina dake like da kofar tana jinsa ta sake lumshe idannuwanta tana sauraronsa, domin bata iya motsawa daga jikin kofar ba tana jin maganarsa da Husaini ABDUL ya sake sauke numfashi a hankali ya ce" I'm sorry, plz ki yafe min kin ji?" Amina ta sake lumshe idannuwanta tana dafe gaban kirjinta dake doka mata A hankali ya ci gabaa da fadin" Ni ban taba rainaki ba a matsayinki ko nasabarki, u seee ko da na ga kece aka bani na yi niyar idan aka zauna aka tatauna zan ga na yi abinda ya dace a lamarinki.............." Ya sake dan cije bakinsa ya ce" Meenart a namiji ko mace babu wadda ya taba min ihu ban dauki mataki a kansa ba, haka kika min son ranki a ranar ina ciwon kai, ama na kasa kwakwaran motsi sai dai kallonki.............." ABDUL ya dan dafe gaban goshinsa ya dora da fadin" A lokacin, ba maganar so, kyau, ko halitar jikinki ta sakani kafeki da ido ba, kawai haka na samu kaina da yi har kika gaji kika yi tafiyarki.....................u know kin takani sosai fa Madame" A hankali ta ringa bude idannuwanta kamar yana gabanta , ta samu kanta da yin dan murmushi still tana sauraronsa Ya ci gaba da fadin " Ko da maganar tsoron Hajia, ko ba so, Ko ba jin kunyar ido, ko ba jin nauyi , ya dace ki tausaya min, a lokacin na jima ina jan farin cikina na samun cikinki sai kawai kika ce ke ba sona kike yi ba, ke a zubar da cikina dake jikinki?.......kin kuwa san matsayin girman kalaman nan.................. Amina sun raunata ni, sun jigata ni, ba dan a lokacin kika fara nuna min baki zo dan zama da ni ba......no dan a lokacin kin fadi abinda ke cikin zuciyarki ne da dukkan gaskiyarki.........." Amina ta zubawa kofar ido tana jin wani irin abu kamar tuhumar kanta, kamar zata ji haushin kanta ABDUL ya ce" Tell me, idan kece ba zaki bani space ta yadda zan duba na gani idan zan iya rayuwa da ke ko akasinsa ba? Na tabata a yadda meenart kike da zuciyarnan kin barni har abada!" Amina ta sake turo baki tana dan kai kawo tana sauraronsa Ya ce" A haka na ringa naci , du dare sai na leko na tsotsi dan abubuwan tsotsa na dan shafa na shafawa na dan yi um um um sai na koma bangarena" Ido ta zarro da dan karfi ta ce" aban amna a jikin wa?" Murmushi ya yi mai dan sauti ya ce" Hala zaki ce min baki taba farkawa kika ga babu jan bakin da kika shafa ba? Baki taba tunanin a ina ya goge ba?" Yanzun kam har sai da ta so budewa sai kuma ta fasa tana jin mamaki na neman kasheta, haba da farko dan wani iya yi zata shafa jan baki ta kwonta, idan ta farka sai ta ga babu, ta sha duba abin shinfidarta ko a jiki take gogewa garin barci? Sai ta ga ba komai, sai ta bar hakan a matsayin shanyewa take yi da kanta, ashe ashe ABDUL ne? "Ama ai hakan bai hannaka daukan kwanana ka ba yarinyar cen ba har take bubude min a cikin gida ko?". Ta fada tana turo bakinta tamkar za'a saka mata ribom Yar daria ya yi, dan a yadda ta fara amsa shi ya tabata alamu ne ta fara saukowa, a hankali ya ce" Sai kace jahili? Kina tunanin zan yi saken da zan kona kaina da kaina? Aa, ba zan yi haka ba, dan ina tsoron Allahna" Amina ta dafe haba, gaba daya mamakinsa na isar duniyarta Yanzun kuwa sai ta saurari muryarsa cen kasa sosai yana fadin" Meenart kasheni zaki yi, idan har kika ci gaba da wahalar da ni kasheni zaki yi gaba daya kin ji?, Ki sasautawa ABDUL dinki kin ji? In sha Allah zamana da ke zan kamanta adalci wa kaina ne ba a wa kowa ba, idan na cuta maki nine a cikin damuwa Meenart, plz ki sasauta min kin ji?" Lahaula wala kuwata ila bilah, kai jama'a, gaba daya jikinta ne ya dauki bari, sauraro take tana mana kunnayenta kamar zata shige ta shige cikinsa ta huta Ita da ace zata ga masu cewa ta yiwa ABDUL dogon fushi gaskiya da ta yada masu magana Tsakani da Allah mema ya yi mata? Bawan Allah mai halayan yan aljana😌 Gaskiya zata shirya da mijinta maki gani kuma ya rintse idannuwansa, haba jama'a, yo ita anya kaf duniya akoy wanda ya kai mijinta kuwa?, Ina ba kyauma ai gaba da daukewa miji kai da hararansa, sam ba kyau A hankali ya idasa tsumata yana fadin" In sha Allah, zan tafi Chaina jibi, idan mun je gidan mun wuni tare zan tafi kan harkar aikina, dama ace bakya jinni Meenart, dama ace ya tsaya Meenarnahhhhh" 'annabi muhamadu Sallallahu alaihi Wa ahlihi wa Salam, Allah ya karra kusanci a tsakaninka da shi da muka ribanci sunnarka, sunnarka itace sunna mafi dadi a duniya, kai jama'a ashe auren kani shine riba? Yau ni Aminar Abanmu da ABDUL ya sakeni da na lalace, dama bana jinnin nan ABDUL, tsaf zan fito mu jone du wandama yace aa kansa ake ji' Amina ke ayanawa a zuciyarta tamkar zata summe dan tsumuwa ABDUL bai bar dakin nan ba sai da ya gaji da rarashi da ban baki da tsuma zuciya sannan ya juya jikinsa a mace ya fice a dakin da tunanin bata yafe masa bane, Mansur babu irin abinda bai masa ba da ya fada masa tana masa fushi ne dan ya dan nuna mata tare yake da Risala harta ranar kwananta, Mabsur yace masa kai tsaya ka ji mata ba'a yi masu haka, idan ka yarda ka masu haka sunna iya tsanarkama, sam ba'a yiwa mata haka fa, shi ua karra rikita shi a wunnin yau din nan, sun koma gefe sun tatauna sosai Jiki a mace ya shige bangarensa ya karasa wajen diner yana kallon Risala dake zaune saman kujerar dinern tana jiransa Kwanaki ne da matarsa ke jinnin haihuwa, idan ta zo marabarta, idanma bata zo ba kanta A hankali ya zauna dan ya dan ci salak din da yakan ci kafin ya kwonta bayan ya amsa gaisuwarta da murmushin da shi kadai ya rage masa a fatar bakinsa, jama'a wai sittin saba'in din nan na jikin Uman Biyu ba ciko? Kai jama'a mata na abubuwa a duniya, ta karkace ta masa tuka tuwon baban gida yana zaune yana kallonta? Oh tsaf so take ta kaishi kiyama A hankali Risala ta ce" A sanyaye Risala ta ce" Bab, ka je da ni mana Chainar, me yasa zaka tafi kai daya bayan kanada mace?" Idannuwansa ya dan lumshe ya dauki ruwa dan ya jika makoshinsa ya kurba kadan sannan ya fuskanceta ya ce" Risala, na fada maki , aiki ne zai kaini chaina, aiki irin mai wahalar nan, idan na fice tunda duku duku idan da rai da lafiya sai da wani duhun zan shigo, na barki ke daya a dakin hotel, chaina gari ne na aiki, ba zama , ba wasa, idan na je da ke ba zamu ribanci zuwan ba, ke me zai hanna ki zauna ne har Allah ya dawo da ni?" Risala ta juyar da fuskarta gefe tana ta tunani, sake rage garajen muryarta ta yi sosai tana dubansa ta ce" Kennan ni kadai za'a bari a gidan? Sati daya fa ba wasa ba, ga gidan nan da girma" ABDUL ya ce" To ko zaki je gidan Hajiar ne kema?" Da sauri ta zarro ido tana girgiza kanta, ita kuma me zai kaita gidan hajia ? Ai har an yanka mata wuya saboda kiyaya, matar da ta tsaneta ta zabi kishiyarta a kanta? Ina ba zata je ba walahi ( Ina jiran irin wannan lokacin dan na kawo wani misali kadan a garemu baki daya, ba dan na fiku sanni ba, ko dan zan koyar da ku ba, ban kuma isa na cenza wanda ya dauki maganata da zafi ba, naci ne irin nawa ya sakani zan yi maganar nan, Yan uwana mata, mun san cewa aure abu ne dake kamawa ba dole sai an tsani mace, ko dan ta gaza ta wani fannin ake kawo mata abokiyar zama ba, ta yiwu laifin nan na mijinku ne, ko kuma haka kawai kika tankadawa kanki garin wahala mai cike da tsakuwa, kina tunanin ke kece mace ke kika isa ki kawowa namijin nan da ya auri matarsa ta farko shekara a kadan biyu, ko uku, har zuwa goma ko sama cenje cenje da jin dadin rayuwar da bai taba yi ba? Albishirinki, itama a ledarta ya daukota, yar shila sabuwa dal, ya murza ya dannan son ransa, komai lalacewarta da ita yake kwana saman gado daya, yan yayan da kike ganni nasu ai kin san ba fyade yake mata yana bata su ba ko?, Soyaya mai sunnan soyaya ta yiwu wace suka yi ba zaki taba ganninta a wajensa ba, ta yiwu lamari ne na bukatar karo ki dan karrin jin dadi na namiji, kina sane da cewa namiji na karra aure dan ra'ayi, yana karra aure dan karin gidan hutu, yana karra aure dan matarsa na kyautata masa ya karra samun kyautatawa? Yana karo ki dan yana so a cika masa gida da ya'ya, yana karro ki dan shi din mai yawan koyi ne da wanda ya isa a yi koyi da shi sugabanmu Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wa salam, ama sai ki tashi, ki cika kwakwaluwarki da abubuwa, tunani kala kala, ke kece mace kece isashiya kece matar so, wata zata shigo ne da kudurin mayar da matarsa banza ya zamto komai ya dawo hannunta itace mai waje mai tabarmar ta nade?, Wata dama nufinta waje zata yi da uwar ya'yansa bayan ita ko yayan ba zata iya rike masa da zuciya daya ba, wata da nufin lalata gidansa wargaza gidansa ya zamto kowa bai ji dadin zama ba, wata da nufin haifo wa'inda zasu gaji gida, abubuwa dai gasunnan barkatai subahanalah, ta yiwu wannan namijin da kike hobara a kansa shine asalin wanda zai kasheki kamar yadda ya kasheta, idan nace kashewa ba na kai mutun kiyama ba, yau wani namijin irin mumunan zaman da yake da wata macen kamar zaman kiyaya, kamar wace aka kawo dan ya kashe, ya daureta ya ringa yi mata kisan mumuke, bai saketa ba bai jiyar da ita dadin zama ba,sai kin zauna ki gane, idan kuwa ba haka bane kika samu macen nan a gidanta, macen da ta san kanta, take zaune da ciki daya da jama'ar dake zagaye da ita, ta samu kyakyawar mu'amala, idan bakida wayo kika kasa yin koyi da ita kika samu kema naki waje har kika gina taki rayuwar sai ki dawo kina batun cewa ta asirce kowa ta malake miji baya gannin kowa baya ganne komai sai ita sai zancenta, baki san irin wahalar da ta sha na biyaya da takewa da gannin kaskanci kafin su zamto aminan junna ita da mijinta ba, baki gane a haka dinma yakan birkice ya rufeta da fada ama kanta a sade bata dagowa ba dan haka suka saba rayuwarsu dan haka take masa biyaya, saima ki ce ai ke ba zaki dauki wulakancin namiji ba, itama matarsa kissa ce, ke baki yardaba kennan da ana iya yin biyaya domin Allah ba dan a yi kissa da kishiya ba ko? A haka da yawa zaman ya gagara a ringa cewa ta fitar da ke, a ringa magangannu, idan kuwa zaman ya zaunu a wahalce, kulun cikin cin zarafin junna? Ki sani idan da kika tardota ta dan yamuge ne, fatarta ta dan ja ne, ko kwali ta saka baya mata ram ya zauna mata dasss hakan rayuwa ce, yau da gobe ne, kwonci tashi ne, haihuwa ce, shekaru ne, Mace daman ta fi namiji tsufa, namijin nan naku da kike gannin kin zo ki ririta kema haka zai didirka maki naki cikin a hankali ki fara janyewar fatar shi kuwa ram abinsa..........dan Girman Allah mu ringa yiwa kanmu fada, mu rayu da sannin ko me muke takama zamu mutu baki daya, ban yi maganar nan dan na fi wata ko ni ba zan yi kishi da kishiyata ba idan Allah ya kadarto min ita ba, na yi be dan baki daya mu ringa tunani a kan lamuranmu, kishi halal ne, kishi akoyshi, ba karya bane, ama kuma wani kishin mu da kanmu zamu hanna kanmu sukuni da kwonciyar hankali/ Maganata ba wai iya Amaren da suka tardo iyayen gidansu nake ba, harta ke hajia uwar gida, ki sani yarinyar nan da aka kawo maki idan kika dauketa kika riketa dan ki cutar da ke Allah zai saka mata, idan dan kinada dama wajen mijinku kike anfani da damar nan kina kunna mata wuta Allah na jiranki, idan dan kin fita sannin danginsa ba zaki sakata a hanya ba kina kallonta ta ringa aikata abinda zasu tsaneta kema kin haifa!, Idan dan kece Hajia mama uwar gidan Elhaj zaki rike kambun nan ki munana mata, ki wulakantata, ki sakata labewa a daki dan tsoronki da tsoron kaidinki sai ki yiwa kanki karatun ta nutsi ki kalli fatar hannunki, na tabata zaki gane tsufa kike kara yi yau da gobe, yau ko ba mutuwa a barki da tsufan nan zaki zo shekarun da kanki ba zaki gane ba bale wani, DUNIYA AI MAKARANTA CE, du abinki ba zaki kasheta ba idan lokacinta bai yi ba, dan an aurota ne ta maki laifi sai ki bada hima a takaitaciyar rayuwar ki munana mata, idan kin je kiyama sai ki amshi sakamako daidai da laifinki!, Sai kai baba, idan ba zaka iya rike biyun nan ba ka yiwa girman Allah kar ka karro, ko ka salameta ka dauko tunda bakada adalci!, Kaine gyaran gidanka, kuma kaine mai batawa!, Idan ka yi aiki irin na munafurci ka bata daya a wajen daya dan ka faranta ran daya ka lalata gidanka da kanka!......Na gode ) Risala ta girgiza kanta tana fadin" Aa, wai da cewa na yi nima na je gidanmu har ka dawo?" Shiru ya yi na dan lokaci yana tunani a zuciyarsa Shirunsa ba a kan komai bane sai a kan tunanin abinda ya dace ya yanke, wanda ba zata ga an tauyeta ba, ba kuma zai tauye kansa ba Tsakani da Allah har a cikin ransa ya ji dadin da bata bi su ba, kuma dalilin wannan shima ya daga mata kafa a kan abinda ya so yi mata na rashin kyautawarta dangane da yar uwarta, sai ya daga mata kafa dan ko ba komai ta ji naganarsa duda yana hankalce da ita ba ruwanta da harkar sunnan ya'yansa sai a wunin biki kawai ta je ta zauna a gefe tana kallon mutane tana amsa waya da dane danenta Ama duka wannan ya yi niyar a hankali zai kwatanta hada kansu , zai kwatanta hada zumunci a tsakaninsu, ba zai dira kai tsaye ya yi haka ba dan abin ne tunda farko a rikice yake, dole ya bi a hankali A nutse ya fuskanceta ya ce" Kina ji? Risala ki yi hakuri kin ji? Idan bakya zaman nan din ne ku je gidan Hajiar baki dayanku, ama bana son maganar zuwa gidanku ki yi har sati guda dan kawai na yi tafia, a nan dinma ai ba ke kadai bace sai idan kin so zama ke kadai din, ga masu aikinki ga komai, kuma kina iya sakawa daga gidan naku kannenki su zo su tayaki zama ko?" Ya fadi nagabar kannenta ne kawai, domin ba zasu taba zaman minti goma basu yi fada ba, sam basa zaunuwa waje daya, akoy lamari na rainin junna a tsakaninsu Risala ta yi tsai, a hankali ta ce" Ama husband, ita fa da ka barta ta tafi gidan hajia ba zabinta bane? Sai nice zaka hanna?" ABDUL ya dafe kansa, wai dama haka ne hada biyun? Bale idan masu jinini ne? Wannan tace wannan, wancen tace wannan A tausashensa dai ya ce" Risala, haihuwa fa ta yi, ina zata je ta yi wanka ne? Wankan jego zata yi a gidan ai, kuma kema nace idan kina son cen din ku tafi tare ko?" Risala ta cire kanta idannuwanta na cika da kwallah Zuciyarta na haharbawa Muryarta a raunane ta ce" Allah ya sa dai ba bakin uwa zan gani a zamana da kai ba, du inda na bi sai ka hanna ni, ita kuma du abinda take so ka baza mata, yanzuma daga wajenta kake, kamar wanda ke sonta bayan asiri ne, babu wanda zai ji labarinku bai tabatar min da asiri ta yi ba, ta rabani da Hajia , yanzu tana son rabani da kai gaba daya, na ce ka je chaina da ni kace aa, gidanmu ka ce aa, Allah ya nuna min karshen masifar nan, dan ni da Allah na dogara!" A hankali ABDUL ke girgiza kansa yana kallonta Niyar bude Salak din ya fasa ya ajiye ya juyo da kyau yana fuskantarta Da siga ta nasiha ya ce" Risala, kin san a duniya bawan da ya saka irin tunaninki ya fi kowani bawa wahala a rayuwa kuwa?, Da yawama wa'inda ke bin bokayen suke fama da irin wannan matsalar, zaki ga kullun su cikin maganar an jefe su, an masu asiri, an shiga gabansu suke domin sun ba dan kasuwa yardarsu wanda abubuwan siyarwarsa wannan buga kasar ne ya fada maka karya dan a ciki abincinsa yake, idan ya fada maka cewa lafia kake ai ba zaka dawo neman magani ba, a haka wa'inda ke fama ke fama, sai gashi kema kina irin tunanin nan?, Zan so ki ba kanki lafiya, ki cire wannan tunani a ranki, ki rungumi abinda yske gabanki, babu abinda ya kai gaskiya dadi a duniya, domin itace raminta ba kurare ba Risala, ko me zaka yi kuma gwara ai ka yi shi a kan gaskiyarka ko? Da ka yi shi a kan hasashe ko son zuciya, Risala Amina matata ce, kamar yadda kike matata, ina sonta kamar yadda nake son ki, ke da ita ba bambanci, yadda zan kare mutuncinki haka zan kare nata, ki cire tunanin an hadani da ita dan dole an min dole, ke babu wanda ya isa ya min dole fa ? Ra'ayina ce ita , kamar yadda kike ra'ayina, ki kwontar da hankalinki, ki nutsu, ki cire komai a ranki, ki fuskanci me ya dace ki gyara ko me ya dace ki daina, zaki ga mu'amalarki da kowa dake tare da ke ta daidaita, koda ba yadda kike so ba zaki ga akoy fahimta kin ji?" Risala ta ringa daka tissu tana goge hawayenta, domin ita dukka kaf jadadawar soyayarsa wa Amina da ya yi ta dauki haka a matsayi aiki irin na sihiri!, ABDUL dinta? Haba dai, haba!, Tana hawayen ta ce" Kennan dai ba zan je gidan namu ba, dan kana tsoron kar a lalatani ko me kake nufi ?" ABDUL ya kureta da ido, kennan dai ba zata gane me yake nufi ba? Ajiyar zuciya ya sauke ya dauki jug din ruwa ya mike ya nufi ciki, kwata kwata ba zai ci salak din bama, Allah kuma ya shiryeta idan tanada rabon shiriya ( kina fa da dama, kina iya tankwasashi har ya yarje makin, kina iya morar kuruciyarkin, da kyanki, ama A haka, a haka ko?, kwonci tashi, tun ana sauraronki, za'a zo a daina, zai zamto da kin bude baki ba'a ba abinda ,aki fada mahinmanci, domin an san me zaki jajanta, koda bakinki na dauke da magana mai mahinmanci......dan Allah ina anfanin kashe kai da kai? Ai gwara a hakura walahi a gabatar da kishin da ya dace, ke mu fa a kishi muna iya yin burgima abinmu😂😂😂🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🙇🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️ i com in peace) Mikewa ta yi itana ta fice ranta a bace, ta sani rayuwar bambanci in dai da aikin asiri ai kadanma ta gani, yau zata yi ta kiran mamanta koda zata kwana tana yi ne dan su shirya, domin batada wanda zata kaiwa matsalarta sama da ita, a hankali zata kwatanta mata ba gida zata bita ba, aa ta tayata da Adu'a ko menene ya karye itama ABDUL dinta ya dawo nata ita daya. _____________________________________ A gidan Baba mai shanu A tsaye suke gaban madubi, ko nace ita tana tsaye tana saka dan kunne a kunnenta bayan ta fito daga wankan yamma ya shigo dakin nata harda murza ky A hankali ya rungumeta ta baya , ya zamto malunmalun din jikinsa ta dan dagu ta kareta sosai a jikinsa Kasa kasa ya ce" Zan tafi......" Amina ta lumshe idannuwanta, wani irin abu mai girma irin na rashin son mutun ya yi nesa da ita na neman damunta A hankali ta juyo tana dago dubanta tans kallon kyakyawar fuskarsa da cikaken sajensa Murmushi ta yi a hankali ta dan shafa gefen fuskar tasa ta ce" Da wuri Haka Taem ruhi? ( Abincin ruhi)" Kallonta yake yi kasa kasa, zuciyarsa na hatsiltsila.......... A hankali ya ce" Ni ne abincin ruhinki?" Amina ta sadda kanta tana dan wasa da yan yatsunta Murmushi ne ya subuce masa da dan gagawar magana ya ce" ki ce min na zauna..... Ni kuma ba zan ki zama ba" Fuskarsa take ta kallo, tana yaki da son ce masa eh zauna din da zuciyarta ke ingizata Da kyar ta iya budar baki kasa kasa ta ce" Neman na shinkafar fa?" ABDUL ya bata fuska ya ce" Allah ba zai hannamu ba ai" Murmushi ta yi a hankali ta shige jikinsa tana dora kanta a saman kirjinsa Shiru ya ratsa na dan lokaci Kasa kasa ta ce" Aa, ka je Aban Amnah, Allah ya dawo mana da kai lafiya Aban Fadeel, ai tafiya mabudin ilimi ce ko Abbansu?" Dan makwaloton wuyansa ke sama da kasa a hankali a hankali yana sake talabo fuskarta , har sai da ya dagota yadda yake so a hankali ya shiga kissing din lips dinta Tun sunna yi a tsaye har ya karasa bakin bed da ita ya zauna ya dorata saman cinyarsa stll yana kissing dinta A hankali ta dan janye kasa kasa ta furta" ABDUL........" ABDUL ya sake talabota shima cen ciki ya furta" Meenart........i ndd u" Da kyar ta iya hannashi kaita kasa, domin du ya cire mata su dan kwalin harta da rigar, da kyar ta iya jadada masa tana hali na rashin sallah, da kyar ta iya dawo da shi a hayacinsa, hannayensa jimke da cinyoyinta ya lunshe idannuwansa kanta a saman kirjinsa, kirjin nasa na bugawa pat pat pat Da kyar ya samu ya dawo hayacinsa, muryarsa cen ciki ya furta" Meenart?" Amina ta ja amsar a cen cikin makoshinta A hankali ya ce" Ki kular min da kanki, ji ringa cin abinci sosai, dubi cikinki fa ya koma ya lafe kamar ba shine bulele ba" Yar daria ce ta kubce mata, shima ya saki murmushi yana shafa gashin kanta, a hankali ya ja numfashi a wajen gashin nata yana shakar kanshin turaran gashin sannan ya furta" Zan tafi.........." Idannuwanta ta lumshe tana jin kamar zata yi kuka ABDUL ya sake dagota yana kallonta, ya sakar mata murmushi ya mike yana gyagyara malunmalun dinsa da ya yakunne sannan ya dan rage tsayinsa dan ta dauko hular ne ta yi dadage ta kafa masa tana taya shi kabewa, a hankali ta ce" Allah ya tsare" Amsata ya yi da amen, yana tafia tana biye da shi a kan dokin kofar ta tsaya tana kallo ya kama ya bude, sai kuma ya sake juyowa ya ce" I love you wife........." Murmushi ta yi ta juya da dan sauri Shima ya yi murmushi yana lekata har ta boye, sannan ya rufe kofar ya juyo da nufin karasawa ya yiwa Baba salama da sauran jama'ar gidan suka yi ido hudu da Baba Wani irin kallon kurullah da Baban ke masa sai ya ji du ya dan tsargu kamar wanda ya shiga dakin matar wani jama'a Rigarsa da ta yakune ya sake kakabewa yana dan kokarin daidaitawa har ya karaso falon ya zauna yana hade fuska danma kar a ga damarsa Baba ya kada kai ya dan rankwafo a hankali ya ce" Ai ba zata daidaita ba sai dai ka je ka cenza wata, wannan rigar ba zata daidaita ba" ABDUL ya kalleshi yana kankance ido ya ce" To me kake nufi?" Baba ya dan watsa hannayensa ya ce" Aa ba komai, ama ABDUL sam bakada kunya, yaya zaka tardo yarinya har gidan iyayenta? Kai nifa sirikinka ne ko? Kar ka karra shiga dakin yata gaskiya a ringa aro kunya koda babu ita a kusa kusa" Haba ya dafe da shegen mamakin Baban, zai bashi amsa Hajia ta fito daga kicin tana tuta abin gungurawa na yaran a hankali wanda yake dauke da abin jarirai biyu ya zamto Amna na daya , Ammar na daya sun sha wankansu kowane da abin tsotsa a bakinsa yana dab tsotsa, dan Ammar barcima yake, Ambar ce ke kallon abin wasan dake jiki yana bada kaloli da yar wakar dauke hankalin jarirai haka, gefe guda kuwa pidarsu ne da ruwa da kuma madara, domin ana hada masu da madara nonon kadai ba zai ishesu ba Baba ya yi murmushi ya ce" ka san Hauwa kamar ita ta haifi yayan nan? Na kusa cewa jego ya karbeta " ABDUL ya dafe goshinsa dan yau ya kula Baba ido rufe wanda zasu yi yake nema, ya dubeshi ya ce" 56 Ya dubi Baba ya ce" Allah dai ya karra lafiya" Baba ya yi murmushi yana sake gyara zamansa daidai Hajia na ciro yaran ta fara mikawa ABDUL macen, sannan ta ba Baba namijin ta zauna tana girgiza pidan Domin Amna tamkar mai acici a cikinta ta fuskanci ABDUL ta ce" Magaji, me yasa wai Firdausi ta ki sauraron MANSUR? MANSUR ai mutumen kirki ne, na ga gaba daya baya gabanta, bawan Allah sai kai kawo yake a zamanmu a gidanka har zuwansu yau tsal yana kai kawo , ama ta yi mursisi kamar bata san me yake nufi ba, ni fa bana son iskanci a ringa wulakanta mai so domin Allah, MANSUR ya yi iya yi, gwara ta amince ta aureshi, matar nan tasa da ita da solofiyo du daya, mace tamkar irin matan da, baiwar Allah hakurinta ya cika yawa, ta yiwu da wuci zata mutu" "Kai Hauwa, kai Hauwa, Muhamadu rasululahi salalahu alaihi Wa salam " baba ya fada yana karashewa da daria Itama dariyar ta yi tana kallonsa ta ce" Alkali, ka taba gannin mai hakurin nan mai kwontacen ido irinta ya jima? Matar Mansur fa ko marinta ka yi kanta a kasa baiwar Allah, irin matan zamanin da ne irin yan aljannar nan, Allah ya sa mu dace baki daya" ABDUL ya girgiza kai yana sake mana Amna a kirjinsa yana shafa bayanta, kakanninsa sun fi karfinsa shi kam, zai bisu da Adu'a kawai, dan ita suke da bukata, lamarinsu sai su, A nutse ya ce" Eh dazu ai mun yi magana da ita,....." Sai kawai ya yi shiru ya ci gaba da dago Amna yana so a dole yar wai sai ta bude ido ta kalleshi, fadi yake dady ne ta masa daria mana? Hajia ta shaka, barda talabe habarta dan haushi ta ce" Kai Magaji wai ba zaka min magana a mike bane?, Alkali wannan hali na menene nu Hauwa?" Baba ya kebe baki ya ce" Ai sam Gwamna ba hali, kin ga fa soyaya ce yake nunawa ya'yan fari a gaban sirikai, ni dai na masa magana kar na kuma gannin rashin kunyar shiga dakin yata, ina dalili yo Yar da danyen jego a ringa shigar mata daki ana zaunewa? Mema za'a fada mata" Hajia ta yiwa Baba tsuru tsuru dan kam bata san abinda zai fada ba da bata ja maganar ba ABDUL kuwa ya tabe baki yana sake manawa Amna kiss a idannuwanta a hankali ya ce" Babyn dady ba zaki farka ba?, Ki farka mana tafia zan yi fa, bude idon ki ga dady, dady, dady ne?" Hajia ta sake cafa ta ce" Kamarma zai fi son macen a kan namijin, kia ba'aiwa tagwaye haka, sunna iya mane maka ido" Baba ya ce" Kwarai ko su mane masa duwawu ya gaza yin kashi ba" A tare suka kalleshi, Hajia t ace" wai Alkali yu me na maka kake nemana da fitina ne? Tun dazu kake nemana da rigima, kuma me ya kawo magana duwawu a nan?" ABDUL ya rintse ido, kai jama'a, Allah ya gode maka Alkali kuwa ya ce" Kakar gwamna me yasa bakida abin fada ne ke? Mema to ni nace a tarin abubuwan fadana?, A ringa sasauta fushi dai ana yiwa tsoho hakuri, yanzu yaya maganar matar gwamnan?" Ajiyar zuciya ta sauke tana girgiza kai ta dubu ABDUL ta ce" Yauwa, dangane da Uman biyu, za'a koya mata mota, da kuma dai dukkan abinda ya dace, idan fita ta kama zata fita" Tsam ya dago ya sake zuba masu ido, Kuresu ya yi da kallo ya ce" Waye yace yana so a koya mata mota, wa zai koya mata motar?" Tsuru sukai masa su dukansu, Hajia ta kalli Baba mai Shanu ta ce" Alkali bashi amsa" Baba ya gyada kai ya gyara zamansa yana sake rike Ammar dake barcinsa hani'an ya ce" To dai , ka ga gwamna ni din nan sunana Aliyu, ita kuma wannan hauwau, mu muka yanke zamu kai gwagwon malan koyon mota da sauransu na zamani, kai dai ka yi fata kar Hajia ta koya mata siyasa, domin ka shiga uku, ni kuma da ka gani a nan mijin kan tace ne, tunda ta fada an yarda, a lamarin Siyasa ce kawai ba dadi, bana so ta koya, ama duka kaf sauran abubuwan ka yarda da ni alkhairi za'a koyawa Matarka ka ji Gwamna?" ABDUL ya lalubo wayarsa dake zuzuzutttt ya daga ya karra a kunnensa Sanar masa da aka yi jirgin da zai dauki masu tafia chaina ya kusa sauka ya saka shi maida hankali ya yiwa yayansa Adu'a sosai yana ta sake rungumarsu abinsa sannan ya tafi bai idasa fadawa Hajia yadda suka yi da Fido din ba, bayan tana son ji, shi gaba dayama sun shaka masa kutu ne, ya gwamace ya tafi ya barsu da Halinsu, yana fatan Allah ya taro su, shi kam da san samu ne kar a bar Uman biyu fita, to wai dama wankan fita ake yi ne? Ya ga yau duka duka kwananta tara da haihuwa, dama sun kawota kusa dan su koya mata yawo da abubuwan da ba za'a rasa bane?, abu daya ya sani shine koda za'a fara ba yanzu ba, ta yiwu sai ya dawo, idan kuwa haka ne du zai iya da su baki dayansu! A gidan Baba Gata, mai sunnan gata, gatan da ko a gaban iyayenka ne da wahala ka same shi, shi Amina ke gani a gidan nan Gyara takanas Hajia ta dauko mace tun daga garinsu ta zo ta zauna take gyara Uman biyu, a wajentaa Uman biyu ta karra daukan yadda ake gyaran mace idan ta haihu, gyara har kamar za'a juyo cikinta a zuba mata sabo, wani irin gyare gyare abin ba'a magana, ga ruwan noni da ake samu ya zamto koda yaushe ana tatsa ne a cikin pida anna kaiwa wajen Baba inda yaren ke wuninsu da Hajia a ajiye a cikin dan abin ajiyewa, idan ba dare ba bata saka su a nono, shima ba wai ta kwonta da su ta kwana rungume da su ba, no a dai basu su sha sosai su yi gyatsa a kaisu dakin Fido cikin gadajensu, ita kuwa ita ke dan motsawa idan sun motsa ta basu madara su koma barcinsu, sam basu saba masu da kwana da su gado daya ba, uwar kanta da farko a ranta ta ji kamar tana missing dinsu, sai dai tana samun wayar mijinta da ya tambayeta yarensa ta shaida masa ga abinda aka ce ya yi murmushi yace Allah ya tsare su, ai hakan kam ya yi, dan lamari na dare sai manya.....a dole ta gane yarensa ta yi shiru dan ABDUL kam sam ba tsari a harshensa A hankali har lokacin dawowarsa ya yi, watau ranar asabar zai sauka A wannan rana da ido kawai suka ringa bin Uman biyu yan zaman falo, domin da katon hijab dinta ta ringa shige da fice kicin, du idan zata wuce kuwa sai Baba ya ce da ita sannu, tun tana dan ja ta tsaya dan ta ji ko akoy magana ne, har ta kula kus kus suke yi shi da kakar Gwamna dan haka ta ajiyesu gefe ta zagine a kicin din nan ta yi girki mai sunan girki har kala biyu, da jus da dan abin motsa baki ta saka aka fitar da kwanuka masu kyau na kwalba aka zuba aka gyara komai, suka ringa fitarwa sunna kaiwa saman table sunna jerawa Baba ya kalli Hajia, Hajia ta kalle shi suka yi murmushi ta sake saba Amna a kafadarta tana mata tawai Baba kasa kasa ya ce" Hauwa, wai me yasa kwana biyu bakya zuwa taronku na manyan mata ne?" Hajia ta yi masa banza Baba ya yi murmushi yana kada kafarsa ya ce" Kyale miji dai ba kyau Ule" Hajia ta juyo tana kallonsa ta ce" Alkali kai ba za'a yi makotaka da kai ba sai ka ja fada ne? Haba jama'a " Baba ya yi murmushi ya ce" Gani na yi masha Allah kwana biyu matar aure sak kike, ga yan yayanki da suka sace maki zuciyarki, bakya zama sai da su a gefe, anya zaki iya ba Mamansu su kuwa? " Murmushi ta yi ta ce" Zan bata mana, jarirai ne ai, amma kulun sai a kawo min su su wuni a nan, Alkali ai ka san burina na samu yan biyu ko?"............. Shigowar da Fido ta yi kamar hankalinta a dan tashe ta gaishe su zata wuce ya saka Hajia kiranta tana kallonta, domin yannayinta ya nuna hankalinta ba a kwonce yake ba Dawowa ta yi ta duka kanta a kasa kusa da Hajiar A tausashe Hajia ta ce" Firdausi lafiya kuwa kike?" Fido ta dago idannuwanta da suka cika da kwallah, domin daga dakin Amina take ta wanketa soso da sabulu , a hankali ta ce" Lafiya kalau HAJIA " Hajia ta ce" Inafa lafiya kina magana hawaye na zirara a gurbin idannuwanki? Hala Uman biyun ce ta dake ki?" Firdausi ta girgiza kanta da sauri, Baba ya dafe haba yana fadin" Kai duka kuma?" Fido ta sake girgiza kanta a sanyaye ta ce" Hajia, dama Dady ne yace idan ya dawo zai dauran aure da Docter....shine shine....." Hajia ta sake zuba mata ido dan gane damuwar tata ta ce" Shine hankalinki ya tashi ke bakya son auren ko Mansur din ne bai maki ba?" Kanta ta sada, hawayenta yaa karra balewa, hannayenta har rawa rawa suke, idan ta duba ci gaban da ta samu na rayuwa, irin yancin da ta samu da farin ciki da kwonciyar hankali na rayuwa a yan kwanakin nan, kuma ta tuna gidan aurenta takan ji ba zata taba iya yin aure da kowa ba, gwara ta yi rayuwarta haka a gefen yayarta da danginta hankali kwonce ba tare da wulakanci ko matsawar namiji ba, Mansur namiji ne cikake ma kuwa, domin ko a samfari na kyan fuska yana da shi ba mumuna bane, maaikaci ne, kuma mutun mai sauraron mutun ne, sai dai mazan ai haka suke, jira suke su malakeka a matsayin nasu shikenan su wulakantaka, jira suke ka zamto yi na yi, bari na bari su juyaka kamar ba dan Adam ba, ta tsorata da duniyar maza, yaya namiji mai mace zai zanto alkhairi a rayuwarta ita kuwa? Bata tunanin zata iya samun haka, namiji dayama ya wulakantata bale mai mace? Zama hajia ta gyara ta ce" Fido taso li zauna saman kujera" Firdausi ta sake sada kanta dan ba zata mike ta haye saman kujera dar ba ta jeru da HAJIA ba Hajia ta girgiza kai, ta kula kam Fido ba dai dagewa ba, dan haka ta dubeta yanzu a kausashe ta ce" Ke zaki taso ko sai naa tsinkawa fuskarki mari ne?" A zabure ta tashi ta hau saman kujerar tana kallon Hajia da sin gane me ya yi zafi? Baba kuwa ya yi murmushi abinsa yana kallonsu, domin so yake ya ga abinda zai faru, ya tabata ba za'a tashi lafiya ba domin Firdausi akoy sanyin hali,, Hajia kuwa da kagauta, shi yasa tafiyarsu ke tafiya da Amina, domin ita batama sake ba bale ta sha ashar din, dama ita batada sanyin hali Hajia ta mayar da Amna cikin shinfidarta ta runguma mata dan filo tana dan shafa gashin kan yarinyar mai cika da baki ta ce" Ki saurareni da kyau, rayuwa bawa na haduwa da jarabawa kala daban daban, ki kadara mijinki wanda kuka rabu dama shine kadararki mai karfi, ki sani haka Allah ya hukunta maki, a yanzu kuma ba shi zai hannaki duban wani ba, ba shi zai hannaki auren wani ba, ba shi zai sa ki yiwa maza kallo iri daya ba, ke a kadarama Mansur dan iska ne ko? Ni da kaina zan tarda shi na nuna masa bai isa ya wulakanta min jika ba!, Ban ce zaman duniya zaki rayu kamar wata wace ta shiga aljana, ba bacin rai, kulun sai farin ciki, aa aa, ko daya, dole watarana zaki ga bacin rai, ai zama ne da iyayenkama kana haduwa da haka bale da miji, wannan shine zaman, ama fa ina mai tabatar maki idan kika auri Mansur kin samu miji, ki je ki share hawayen nan kina wani abu kamar an zare maki laka, ki yi da jiki ki yi kaza kaza bana son lalaci, tashi ki share hawayen ras ki je ki kimtsa tare zasu zo ya sauka tun dazu yana gida Mansur din zai je su zo tare, maganar aurenki an yi an gama saura idan ya zo na ji wata maganar " Zungui zungui zungui ta mike ta tafi jiki du a mace dan Hajia batai mata da sauki ba ta bude dakinta ta shige zuciyarta cike da tunanin shin zata ba Mansur damar ne ko kuwa ta fada masu gaskiya cewar ba zata iya zaman aure da kowa ba, a barta ta rayu ita kadai shine burinta?, Idan ta tuna maganarsu da Uman biyu sai ta ji hankalinta ya sake tashi, yaushema Uman biyu ta fara cewa wai abinda dadynsu ya yi ita bata da ja? Ta yi tunanin zata ce ne aa bata cikin a yi nata aure yanzu domin ta fi kowa sannin me aure ya mata, ama da ta yi insister sai ta nuna mata ai ba zata zauna ba aure ba, shekarunta duka duka nawa? In ba fan an mata aure da wuri ba itama bata fi a raineta ba, dan haka ita bata cikin wannan maganar ta tafi kawai ta bata waje Jiki ba karfi ta shirya itama , ta samu kanta da dan shafa dan jan baki , sai kuma ta yi murmushi da ta tuna abinda ta baro a dakin Auntynta, Auntyn nata ta dora kayan sakawarta a saman turaren wutar da matar nan ta hada mata mai mahaukacin dadi ta bude kayan gyaran fuskarta , alamu sun nuna harda fuska zata fence da son ranta........? Murmushi ta sake yi tana hayewa da kyau saman gadon tana bin fatar jikinta da kallo, sun murje, sun wanku, harta maganarsu ta zama irin ta yayan gatan nan ....bama kamar Hasan da Husaini jama'a, sun zama basa doguwar maganama da hausa sai turanci, sun zama wasu irin rikakun yayan gatan nan, a yanzu da suka yarda da HAJIA itama ta yarda da su ta karra rikitasu da ruwan gayu, har wani koya masu shan madara mai dumi da sasafe ta yi, ita da turancima sak take masu hira, Baba da Umansu nema ke masu hausa wadinnan kuwa irin tunaninsu dawa, gargajiya sak wai Sai da yama sosai suka karaso, su dukansu sunna cikin sasaukar shiga mai kashe zuciyoyin yan mata, ashe su Hasan ana dauko su daga makaranta wajensa aka wuce da su, yara sai ihun kayan wasa suke sun zo da wasu sun ce wasu na gida, harta kayan jikinsu sababi ne suka ce Abansu ya sa Aunty ta gida ta shirya su, Sosai a nan aka baje a falo kowa da kowa ana ta labari kamar wanda ya shekara baya nan, amna da Amman sun sha shirinsu sai kanshi suke abinsu, shi kuwa sai shinshina yake yana sake hangen mamansu dake cen barin Hajia cikin hijabinta har kasa domin ta sanshi, ta san waye shi, idan ta bude kwaliyarta haka a gaban Mansur sunna iya hautawa sama, bata san me yasa yakeda kishi har haka a kanta ba, ko a yanzu idan sun hada ido sai ya dan lumshe mata idannuwa , ita kuma sai dai ta yi dan murmushi kawai ta sada kanta Hajia ta Umarci Fido ta kaiwa Mansur abincinsa cen bangaren baki, ba dan komai ba dan su dan karra zantawa ko yayane, bangaren dai ba waje bane mai mugun shiru, waje ne mai jama'a, yanzu kuma zata mike da kanta ta fadawa datijuwar ma'aikaciyarta ta ringa dan kai kawo a wajen, ba dan wani abu ba, sai dan gudun lamari na shedan, Firdausi dai ba yarinya bace, hakama Mansur, rashin zamansu yaren nema matsala, domin hakan na iya haifar da wani abin daban.....Allah ya sawaka basa fatan hakan sam shi yasa ta mike ta fita bayan Fido din ta dauka ta tafi jiki a sanyaye Ya kasance saura Baba, da ABDUL, da Uman biyu Ya kasance sauran Baba, Abdul, da Umman biyu a falon, Abdul ya kalli Amina, da wata tattausar murya yace MEENAL," Baba ya dago da sauri daga kama yatsun amma da yake yi ya kalle shi, ya kalli Amina ido ya kanka ce yace waye meenalu kuma? Kamar bawan rake? Sunanta Amina ko kace gwaggon malan" Abdul ya kalle shi, shi da aminar, Amina ta sadda kanta tana yar dariya shi kuma ya gyada kai a tausashe ya kuma cewa meenah nima a zuba min abincin yunwa nake ji Baba ya kalle shi kallo irin na basira, baki ya tabe yace gwamna ina ga daga gidanka ka fito? Mene na san a baka abinci kuma a nan? Matar ka ta chan fa? Amina ta dan saka birki daga mikewar da tayi ta koma tana sadda kai tana kumshe dariyarta Abdul ya kalli baba, kallo irin na su fahimci juna a tausashe yace baba ya maganar wannan dokin daka ce kana so, na gidan gona fari kal din nan? Bana yace fari na saraki wanda ka cimin amana ka siya daya tal ba kace Ni hawa zan yi ko kuwa na dame ka? Abdul ya jinjina kai yace shi fa' yanzu ka zabi daya ka dan je wajen su Hassan kadan gobe sai kaje ka dauki dokin ka idan ma nan kake so ka aje shi sai zai dashi" ko ka zauna anan kana abinda ba shikenan ba kuma kayi asarar dokin ka Baba yayi tsai na dan lkc sai kuma ya dafa gefe yace kawo yar nan na tarbi kakar gwamna dashi kar ta ce zata shigo nan bayan mutun da matar shi haka kawai azo a dame shi, Kawo ta nan kasan ta shanu da ya'yan nan kamar ta maku kwace bayan ba bata zaku yi ba,Bara muje chan Bata mu zauna ai yau yanayin garin da dadin zaman waje yake , Allah dai yasa mu cika da kyau da imani gwamna. Abdul ya mika mishi yar hankali kwance ba kunya ba wani Dar, inda Amina taji kamar jinin jikinta zai kafe da tsananin kunya, kanta a kasa sai mirza yan tatsuniya take kamar ta fashe da kuka dan kunya Ba za a zo ba ko? Ko na zo? Abdul ya fada yana murmushi dan ya lura qarara ta aka cikin duniyar kunya ne Fuskar ta ta dangi ta shagwabe fuska tace ynz ka kyauta kenan Abdul ya dage mata hira irin mai anyi? Amina tace haba annan amna ai sai kasa malam ya min wata fassara ta da ba dadi ko, Abdul ya mike tsaye dan ya kula yan mulkin ke san dawowa a daidai wannan gabar su cire shi, a nutse ya karaso inda take ya rage tsayin sa sosai ya kamo hannayenta ya mikar da ita sannan ya sa hannu ya janye hijabinta baki daya ya tsaya yana kallan kwalliyarta ta malam bahaushe atamfa riga da skirt an kafa masa sauri ya zauna das a gaban goshi Ajiyar zuciya ya sauke ya rungumeta a jikin sa tsam a hankali yace "har ynz wai jinin nan bai tafi ba dan Allah? Amina ta hadiye yaqin wuya da tsoro ta gyada kanta a hankali tana kakkaucewa domin lalubawa yake tsakanin shi da Allah, janye wa ta samu ta danyi da sauri tana nufar wajen table tana cewa Bismillah kazo kaci abincin Abban amna, sai da ta kule wa ganinsa yana kallon kayan kallon data hasko masa ta baya, sannan yaja mika yana murmushi a hankali yace gwaggon malan Allah dai ya qara lfy da nisan kwana dani a gefe na ringa mulmula da mulmulawa dan samun ingantacciyar lafiya. Da wannan suka janye table suka fara cin abinci da zuba soyayya tsaftatacciya da tsari..... A bangaren fido kuwa a darare take tunda ta shigo falon, sosai taki yarda su hada ido dan ita wlh kunyarsa ma take ji, Ma sur kuwa ya bata dama ya mata uzuri sosai domin shi fa ya idasa fitar da jaririyarta daga cikin cikintq, yana cikin wa'inda sukai mata aiki kodan wannan lamarin mata sai taki amincewa auren sa bayan shi kam ba wannan bane ya sa shi kwadayin ajiye ta a matsayin iyali, ta masa ne yana so ya aje ta su rayu a matsayin iyali Bayan ya gama taba abinda ya aje masa ne ya bata damar kashewa sai da yazo dauka ta duka zata kwashe a nutse yace fido? Firdausi taji gabanta ya fadi a hankali ta dago ta kalle shi mamaye ya sakar mata murmushi a hankali yace Allah saka da alkhairi nagode sosai, sai firdausi ta rasa godiyar mai cece tama rasa amsar da zata bashi, a sanyaye ta dauke ta nufi hanyar fita jikinta ba kwari Mamaye ya sake ambaton sunanta yana kallon ta hijabinta sakakke ne har kasa ba a ganin jikinta ko kadan ko lafewa baya yi a jikinta, a sanyaye yace fido ' Ina son ki irin sosai din na fa kuma daddyn ku ya bani ke..... Ido ta zaro hannayenta suka nemi zubar da babban farantin dake dauke da kayan kwalam da kwamulashe, da sauri ta sadda kanta karshema nan ta dungura abin ta balle da gudu domin ji tayi idan tace zata gudu da kayan zubarwa zata yi kuma gudanar ita ce abinda yafi sauki a gareta a irin wannan lkcn, kirjinta na dokawa kamar zai ballo ya fito daga bakin ta, ta samu waje ta labe tana Dora hannu a saman kirjin nata.... Da wannan Abdul da doctor suka rikita yan amtan hajia da kalar nasu salon, suma suka rikita su da kalar nasu innocence din da sassa yar soyayya har ma ya fadi cewa zai turo wacce zata musu lesson na koyan tukin mota, idan an gamsu da kwarewar su sai a basu takardun tukinsu Bai tafi ba saida ya nunawa hakka motar daya dauko musu Amina da risala da gudu, sai dai tasu Amina iri daya ce kala ce kawai ta banbanta ta dodo kuwa jakarta daban, motocin dai baki dayan su irin hawan mata ne sannan ya tafi cike da kewaye iyalinsa da tunanin ta a zuciyar shi da kuma ya'yensa dake dariya duk da basu san abinda duniyar take ciki ba amma da zarar an dan tattauna kumatunsu sai su d,inga dariya wannan ya kara sanyaya masa zuciya Bayan kwana biyu haj suka shirya suka fita tare da matar da zata yi aikin koya musu mota, saida suka fara zuwa gidan ya'yan mahaifin yaran tare da yaran, domin tunda aka yi haihuwar bata je wajen rasuwar ba, Abdul da baba ne kaɗai suka je sai yau da suka fito suka nufi can yana cikin shiga irin ta larabawa watau bakar abaya bakar nika Safar kafa data hannu, sun tarar da ya'yan mahaifin nasu cikin shiga mai kyau ba laifi saidai yar rama da yayi da tunanin rayuwa dake damunsa, gidansa kansa ba laifi domin a gyare yake ga kuma mutun biyu dake kula da tsaftar gidan da kuma ta abincin sa mata da miji ne a gidan Karshe dai da jikansa da komai ya dinga labarta musu irin abinda ya faru, ya fada musu ai yana cikin halin rashin sanin inda kanshi yake mijinta ya mayar dashi babban asibiti da kakanshi aka dinga bashi kulawa har ya dan daidaita, ba laifi ya'yan mahaifinsu yayi nadama amma kanin mahaifin su abin ba sauki gidan shi ya zama tamkar gidan karuwai yana ji yana gani sai ya taso kato dakin shi bai isa yace komai ba haka suke rayuwar su Sun yafe masa dayan ma sun nema nashi sauki a wajen Ubangiji domin babu abinda ya gagari Allah shima ana iya wayar gari aga ya samu canjin rayuwa, da suka fito sun gaisa da dayar matar tashi wadda kanta ke sadda kasa a dole sbd hajia tsaye cikin shigar nan Tata ta Alfarma ga kanshi tana ta badawa ga kyauta ko baka mata biyayya dan komai ba kayi mata dan kyautata, hajia hauwa kenan matar Alkali. Hart's cousins din su saida suka gani suka sake jajanta wa juna sannan suka wuce wajen koyan motar, hajia ta zauna cikin rumfar da jarirai ta da wayarta tana shan iska tana kuma cin wariyar rikici irin ta yan siyasa, a ynz ma bata daina siyasa ba Abinda ta daina makauniyar siyasa mai tura bawa cikin rami irin siyasar dake sa mutun har addini shi ya manta,daga nesa take yin siyasar ta wadda ba tana yin ta bane ynz dan ayi mata wani abu ba a gwamnati, tana yin tane dan ra'ayi, tana son siyasa a jinta take amma kuma kaunar jariran nan tazo ta make komai bazata iya fita nesa dasu ba, bazata iya wuni basu a gefanta ba wani irin son su take kamar ranta murmushi tayi ta kai idon ta chan gefe inda biyu ke buga gama a iPad dinsu suna gardama da kyautata dariya, idannuwanta ta lumshe tana yiwa Allah godiya da kadaice kadai ya ishe ta babu wadannan a kusa da ita idanuwanta sun rufe bata gane komai..... A ynz kuwa gata ga su ga farin cikin rayuwa a tare da ita ko a ynz ta koma ga mahaliccin ta Alhamdulillah 58 A hankali aka dinga koya musu mota wani ikon Allah tun a fitar su ta uku suka ba mai koya musu mamaki tukin a hannun Amina ras abin ba a magana, a kadan sai da aka musu lesson takwas sannan suka shiga gari tare watau ta dauko su suka tukata cikin gari hanyoyi mafi hatsari wajajen da motoci, mashina da manyan motoci ke yawo san ran su sun tsira da farko domin harda ihu Amina ta saka da suka iske wani dogon go slow amma tana kwantar mata da hankali sai gashi sun fita amma sun sha nawa domin koda wasa bata yi tukin ganganci ba ko nuna iyawa a hankali ta tuka har suka fita, a kwana na goma sha biyu ta kawo musu takardunsu shedar sun gama iyawa bata da darr akan su ai kuwa an sha murna domin da Abdul a cikin gidan ya shiga Umman biyu ta yawa ta dashi a Hakim ce irin madame tukin nan, ya zamto kwanan su talatin da uku ne a kirgen shi sauran kwana bakwai umman biyu tayi kwana arba'in din da ake yi ta tattara ta koma inda tafi wayau A ranar da wuri ya koma sbd kansa na dan damunsa da ciwo a washegari kuma yayi safiya ya leka ya amshi magani ya sha sannan ya wuce office ya kwanta domin kansa ke masa ciwo ya sha magani ya kwanta don samun barci wayarsa kan ta ya manta ta a gida dan samun barci.... Tunda ta farka daga barci take ta gwada kiran layin shi amma amsar daya ce a kashe, tun bata damu ba har dai ta kasa hakura ta fito cikin shigar abaya baka da dogon wando a ciki da mayafin abayar haka yafe saman kanta taje dakin hajia tana tambayarka ko sun yi waya da Abdul? Anan hajiyar tace mata itama ta neme shi Bata same shi ba sai muhammet ta kira yake ce mata bashi da lfy ne amma ya amshi magani Yana office, hankalinta ne ya tashi har ta kasa boyewa a saman fuskanta ta samu ta jingina e da bayanta a jikin kujera a dakin hajia bayan bata taɓa zama haka a dakin ba duk tsakanin su tayi shiru kanta a sadde, har hajia ta fito daga wanke Ammar domin ya bata pampas din sa ta gan ta a yanayin nan, murmushi tayi tace Amina da sauki fa jikin nashi kar ki saka damuwa a ranki mana ai shiru sauƙin kenan inda ba sauki da an nemo mu ko? Amina ta gyada kanta jikinta a mace dai ta mike a sanyaye zata tafi kasa Hajiya ta kira yi sunan da juyo tana kallon hajia idanuwanta sun cika da kwalla hajia tayi murmushi tana nuna mata saman sif tace kinga laluba chan kin ga key din mota ta chan dauki kije wajen aikin ki ganshi sai hankalinki ya kwanta tunda na aiki direba ke kuma naga kamar zaki suma dan rashin kunya. Amina taja numfashi da dan sauri ta dauki key din ta juya har tana hade ta sauka da dan saurinta ta fice bata tsaya daukar hijabi ba balle ta tuna da wando ne a jikinta ta qara wajen mahaukaciyar motar hajia baka sidik ta bude ta shiga tayi mata key tayi addu'a a hankali tayi ribass ta nufi hanyar fita daga gidan mai gadi ya bude mata yana kwararo mata addu'a yana mai washe baki cike da mamakin Amina da hajia, ya yarda cewa Allah shi ke gyara komai,. Nutse ta dinga tukin tana gane hanyar rass har ta iso tafkeken kampanin, a hankali ta karasa wajen da aka bata damar shiga sannan ya aika motar ta wajen ajiye motoci tana hangen daidai kun mutane dake shawagi su ciki harda muhammet daya Qura wa motar ido yana tunanin hajia ce ta zo domin matar hajia ce mota mai masifar tsada da bakin glass, mota ta manyan alhazzai duniya guda. A nurse ta bude ta fito takalmin dake kafata flat ne ba wani mai tudu ba simple ne bashi da wani kwarafniya Asalinsa na fido ne ta zira ta bar na cikin dakin ta anan falon hajia tayi gaba, du idan tana tafiya kuwa ana ganin wando dake ciki mai roba roba, abayar mai botira ce kuma mai dan shara shara ce, mayafin kuwa bashi da girman a zo a gani dama mayafin bayar ne ta dan yafa a saman kanta, ido Muhammad ya zaro yace uban wa, baiwar Allah jaraba kike san ja mana baki dayan mu. Nufo ta yayi yana cewa hajia ce da kanta? Amina ta dan dakata sai kuma tayi murmushi tace muhammat kana nan kai ma ashe? Dan Allah yimin iso ko sa bar Ni na je wajensa, ya jikin nashi ne? Muhammat ya rasa ta yaya zai fada mata dama hijabi ta saka, bafa dan shigar tayi muni bane, no a wajen mijinta ne zata yi muni dan wani irin birkitaccen namiji ne balle a kanta bashi da hankali, a kanta baya kara, kowa ya fahimci kishinsa a kan ta bayyananne ne shiyasa ake guje masa bacin Rai akan hakan ana kiyayewa. Saidai bazai iya maganar nan da ita ba a dole yayi mata ja gaba suka shiga ta lifta ya haura dasu ya kai su har babban wajen ma'aikatan nan da aka sha rigima da ita a wajen, magana daya ya fadawa wanda ke tsaye a wajen cewa matar oga ce suka saki hanya gaba dayansu suka wuce har kofar office din sa Camerar dake haska ko waye muhammat ya daga kai ya kalla ya saki murmushi irin na cikin hancin nan sannan ya nuna umman biyu, yan saka Ni kadan kofar ta bude muhammat ya koma gefe yana mata nuni data shiga sannan ya juya abinsa ya rufo yayi gaba. A hankali ta shiga tana tuni yanda taga office din sa a wancan lkcn ynz an kara chanja masa waje hakan yasa ta dinga dube dube har ta waigo inda yake tsaye da dan abin goge ruwan da wanko fuskar ynz daya tashi daga bacci kuma alhmdl kansa ya daina ciwo ya samu barci maganin ya masa aiki. Tun daga sama har kasa ya dinga kallon ta ta karaso kusa dashi tana murmushi tace abban amna ashe ka mike? Yaya jikinka? Ni na damu sai dana taho Daga bakin mai maganar har kalaman nata sai da ya cije ya ba kansa hakuri sannan ya fahinci me take nufi" a nutse yace zo nan Amina ta kalli fuskarsa dan kamar a kausashe yayi maganar, sake kallo da take shima yana kallonta, a hankali yace cewa nayi kizo nan umman biyu, yawun bakinta ta hadiye sannan ta daga kafa ta karasa inda yake a tsayen kara kafewa da ido yayi yana jin yadda zuciyarsa ke qara hawa sama saman sama, lebensa ya cije ya juya ya dauki wayar office din ya danna lambobin bangaren suturu ya bada umarnin irin abinda yake da bukata sannan ya zauna yana mata kallan Ni zaki yiwa ba dadi. Amina tayi tsuru tsuru har aka zo da kayan ya mike ya tare chan kofa ya amsa ya dawo ya mika mata yace chanja kayan nan mu tafi, sai ynx ta fara gane laifin ta, bata yi masa gardama ba ta karba ta cire abayar yana zaune yana kallonta ta chanja doguwar riga da hijab na Turkiya Masu kauri da rufe jiki sannan ta dauki abin nikaf din su mai dan haske ta kade tana murmushi ta kai daidai fuskar ta tace kasan gaggawa sam bata da wani amfani, ina gaggawa ne na fito a haka ko yara ban leka ba. Kai ya gyada yana kallonta saida taga tsaf ya dauki hularsa ya dora a kansa sannan ya kamo hannunta ya juya suka cigaba da tafia, har suka sauko ana gaishe shi, shi kuwa duk inda yaga taron maza sai ya kauce da ita har suka karaso inda muhammat ya gyara mota yana jiran karasowar su, motar ta shiga tana abban amna ya za a yi da motar hajia, daka bari na tura na bi bayanku mu koma gidan hajiyar ko? Yanzu ma shiru yayi mata ya janyo ta jikinsa ya kwantar a gefen kafafarsa muhammat yaja suka tafi, gidansu aka nufa dasu kuma bata ankara ba sai da aka tsaya ta miko mata hannu sannan, ido ta zuba masa tace me kuma ya kawo mu nan yau,? Bai dai ce mata komai ba sai da ya fitar da ita ya nufi bangaren ta da ita. Hindatu ya samu tana tsaye a kofar rike da keys a hannunta da sauri ta bude tana sake tsungun nawa tana gaishe su, Amina har da tambayarta gida da ce mata tana zuwa shi kuwa bai ce mata komai ba har suka shige, dakin ta direct ya nufa da ita yana sake kallonta Ita kuwa dan dari dari take dashi a dan tsorace tace abban amna kasan fa nayi arba'in ba na bar su amna a gida ko nono ban basu ba mu tafi su sha Kaji. Dan murmushi yayi yana kallonta yace umman amna kiji tsoran Allah rabon ki da biƙi tun satin dana dawo amma na kyale ki tunda ynz yawo kike san koya shikenan ai"" Amina tace toh me kake nufi? Saman bed din ta ya tura ta da hannu daya ta fada da baya baya ta dangi da sauri tana cire nikaf din tana kallonsa. Murmushi yayi yace ina nufin Allah sa ki samu ciki yNz dama amna ai kinsan ba bamu su zasu yi ba, jira suke a yaye su a ynz ma da ba a yaye su ba ai kinga ba namu bane balle,....ai kin dawo gidanki hajia Amina ta zaro ido tana mike wa tsaye tana cewa haba dai, haba dai mu da ba fitsararru ba, kaga nifa cewa aka yi baka da lfy shine naje ganinka kuma sai aji wata magana ta ɓillo? Murmushi yayi yana kama hijabinta yana janye shi gaba dayan shi sannan ya kama zip din rigar ya sauke shi kasa gaba dayanshi da sauri ya tare ta ya hanata boye mishi abinda yake san kallo yana murmushi ya dora hannun shi a kai ya dan matsa kadan kasa kasa yace fitsara kuma ta nawa ai su ji suke tun a gabansa zaki fara zubar da dan yawu dan su a tunanin su tun a gaban su na jima da danne ki fa umman biyu muga abin cikin wandon nan? dan Allah mu gani Ido ta rufe tana kife kanta a saman kirjin shi zuciyar ta na dokawa abin tsira shine bata da alamun zata kiya bata jima a ranta ba wai zata iya kiyawar kawai gaba daya ma sai ta samu kanta da daukakuwar rashin kunyarta. Finkewa suka yi tamkar zasu hadiye juna, haukata shine kawai bata yi ba dakin nan har Allah ta godewa da basu zo da yara ba kuma ba kowa a bangaren nan domin lamura kam sun kankama sai gyaran Allah. Bayan komai ya kafa har sun tsaftace jikin su suna kwance a kan kujera tana lumshe ido tace Wai dagaske kake mun dawo? Wlh baba kadai ya ishe mu a garin nan. Murmushi yayi a hankali yace ba Kya tausaya min ne? Kenan kinsan nayi kara sosai ynz kuma har an fara tunanin taba min zaman lfy ta, dubi a yadda hajia ta barki kis fito fa, Amina ta dan dago tana kallonsa tace da rufata fa da sututata fa, kasan ai na lullube jikina abban amna. Kai ya gyada a hankali yace nafi jin dadi idan kina gefe na shi wankan nan na malam bahaushe nima na daukaka ta tunda na barki kinje kinyi satittika Ni kam ya isa hakanan Amina tayi murmushi a sanyaye dai dan ta lallaba shi tace toh ka bari na koma sai mu dawo da yaran ko? Abdul yayi murmushi ya sake juyawa da ita kan kujerar yana kallan fuskarta yace muhammat ya tafi fa minti waya da baba da kika shiga wanka tuni na kashe bakin.......yana chan yana fadan a ba yaro matarsa ai yay ladabihhhhhhhhh umman biyu kenan kina san nayi LADABIHHHHH ko? Ynz muyi maganar shirye shiryen auren fido Nan da kwana bakwai kinsan lkc naja sannan mijin fido yace gidan cen na kan kwana zata shiga. Da mamaki da kuma farin ciki Amina tace wai gidan chan da kuka yi iri daya? Gira ya daga mata dariya tayi ta dago ta manna mai kiss a lebe tace ngd Abban 4 shima murmushi yayi ya cigaba da lalubarta. Wannan itace soyayyar dake wakana tsaftatacciya a gidan abdul, yan wanka sun dawo lfy saidai sun mugun shakuwa da hajia har ya zamto Hassan da Hussaini sun fi so a tattara su su tafi su da su amna da Ammar su wuni a wajen hajia domin gata irin na kakanni suna samu kowa abinda yake so yake yi ba dan a gidan su babu ba, no soyayyar kakanni ce da suka tsinta a sama ya zamo farin ciki da kwanciyar hankali a gare su. Risala na Tata kalar rayuwar itama ynz ta rage kwasar karamin abu ta maida shi babba, watau ta rage daukar bacin rai fuuuuuu domin tayi yafi a kirga bata kuma ga amfanin shi ba kuma rashin haihuwarsa da kansa ya dauke ta suka asibiti aka gane qari ne ya haddasa haka ynz haka tana kan daukar maganin da likita ya tabbatar idan ta gama shan shi zata iya daukar ciki domin bai yi girman da za a yanke ba. Itama tana nata kasuwancin a cikin gidan ta kaya take kawo wa manya manyan masu tsada na manyan Mata, mata na zuwa suna dauka tana badawa har da sari, mahaifiyarta kuwa na kula dana shafin gyaran jikinta. Mu'amalarta da Amina ba za a Kirata perfect ba, amma kuma ba cuta ba cutarwa, tunda Amina taja girmanta take shagalinta tana gabatar da rayuwarta da adalci a kangin kanta sannan da abokiyar zamanta kodan sama .a mijin kwanciyar hankali a cikin gidan sa, tana kula da yan yaranta, kanwarta kan leko su sha hirar su wani sa'in su wuni tare, idan fita ta kama su su kan yi ta a mota daya, ga itama nata wajen gyaran jiki dake qara haɓaka domin gyara suke ba ji ba gani harda baba lauratu Kan zo ayi gyaran a gargajiyance abin sai godiyar Allah sai ya zamana kishi na fadsce fadace ba shine a gaban su ba, suna kishi Dan kishi amma sun fi bada karfi a irin kishin nan na yan gayu da kuma wayo Abinda bazai sauku ba shine ita risala na daukar kanta yar masu dashi Amina kuma na rayuwarsa ne akan babu wanda ya halicce ta balle ya wulakanta ta idan da zumunci za a gaisa idan babu kuma tayi GIRMAN DA BAZATA KULA YARINYA karama ba, tsakanin su magana ce ta LAFDABIHHHHH, a duk duniya ma mutun daya ta girma amma ta gwammace ta aje girman dan UBA ne shi, GARKUWA ne shi, ABOKI ne shi, YAYA ne shi, MASOYI ne shi, shi din DANGINTA ne, RAYUWARTA ne......... Takan sune shi tayi murmushi idan yana mata tsiya ta sadda kanta ta furta kalma kamar haka NI ZAN LADABIHHHHHHHH ABBAN 4 ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH Alhamdulillah Daga alkalamin Sajida