*_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ɗaya_ *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._ ........“Ango! Ango!! Ango!”. Itace kalma mafi rinjaye da tafi fita a bakunan taron matasan dake cike da ƙofar gidan. Yayinda wanda suketa faman kira da angon bakinsa ya kasa rufuwa dan farin cikin da yake a ciki a wannan rana data kasance ta aurensa da masoyiyarsa mafarkinsa. Magana da ɗaya daga cikin abokansa ya gwargwaɗa masa a kunne ta saka shi jan hannunsa suka koma gefe. Cikin ɗan nuna yanayin damuwa da hasala ya ce, “MB ya akai haka kuma? Nifa bana son matsala wlhy, duk abinda zan ɓatama Love rai bana son shi musamman a wannan ranar ma data kasance mana ta daban.....” “Na sani kwantar da hankalinka, kaima kasan dai bazan bari wani abinda zai ɓata farin cikinka faruwa ba JJ. Na faɗa maka ne kawai dan kar kaga an samu canji, dan yanzu haka ma nariga na daidaita matsalar, wajen da aka samu yanzu ɗin ma yafi wancan komai...” “Amma karka manta wajen farkon muka saka a invitation card”. “Hakan bazai zama matsala ba shima, dan kusa-da-kusa suke, dabarar da zamuyi zamu ajiye su Nure a ƙofar wancan hall ɗin duk wanda yazo sai su turosa inda aka canja ɗin. Yanzu sai ka sanarma amarya kawai, ko hakan baiyi ba?”. “A yayi, kunyi ƙoƙari, ALLAH ya bar zumunci bari na sanar mata”. *_DINNER HALL_* Matuƙar ƙyau da ƙayatuwa wajen yayi tamkar dama tun farko nan suka shirya yin shagalin. Kalar decoretions ɗin wajen kalar ankon ƴammatan amarya da suka sha ƙyau har suka gaji, haka suma abokan ango shar da su. Shigowar ango da amarya ta shafe duk wani ƙyawun kowa a wajen, dan adonsu na musamman ne. Atake hasken flash ya shiga tashi tako ina, tsakanin wayoyi da camaras, a gefe mc na faman kwarzantasu, yayinda dj ya saki wani cool music mai ratsa zuciya. Ta ko'ina dai taro ya cika taro kam sai masha ALLAH, abokan ango da ƙawayen amarya nata taka rawar gani irin na bajinta tare da dangi takowace ɓangare. A yanda aka tsara komai zaka iya saka masu bikin a layin masu hannu da shuni, sai dai sam ba haka bane ba, ana dai tsaka tsaki, wato babu tsiya babu hamshaƙin arziƙi. Sai dai akwai rufin asirin ALLAH ta kowanne ɓangarorin guda biyu. Anyi taro an tashi lafiya kusan ƙarfe ɗayan dare, ango na son maida amaryarsa gida da kansa yayarta tace karya damu yaje gida ya huta zasu wuce da ita. Babu yanda ya iya dole ya haƙura suka dunguma shi da abokansa zuwa hotel da suka kama. Amarya da danginta suma suka wuce nasu gida dan sai gobe in sha ALLAH za'a miƙata gidan mijinta..... *_WASHE GARI_* A kaf ƴan rakkiyar amarya babu wanda baiyi santin gidan da aka kawota ba. Dan kuwa dai gida ya cika ya tunbatsa komai zam. Tabbas angon yayi ƙoƙari sai kuma fatan a zauna lafiya. Bayan kammala ƴan kai da kawo na al'ada da rabe-raben kayan gara kowa ya kama gabansa aka bar amarya da ƙawayenta. Sune suka sake gyare mata gida ana faman raha da wasa da dariya komai ya koma kan saitinsa. Sai dai amarya bata da wani kuzari tattare da ita, ba komai ya jawo hakan ba sai ƴar fargabar da aka san duk wata amarya kamila da ita a irin wannan ranar, dama ita gata bamai yawan hayaniya bace, ko ƙawayen ma ba wasu ne daban ba, daga ƴan uwa sai maƙwafta da aka tashi tare. Bayan idar da sallar magrib kowacce ta shiga sake gyara kwalliyarta sukai zaman jiran abokan ango. Ƴan halak ɗin kam basu taushe hannu ba, dan idar da sallar isha kaɗan suka iso gidan. Amarya dai na lulluɓe, yayinda ango yay tsallen turare ɗan goma zuwa inda take ya zauna kusa da abarsa kamar zai rungume, itako tana ta faman matse jiki waje guda abinka da farin shiga ga kunyar baƙunta. Suko abokan ango nata faman masa shaƙiyanci da ido yana musu daƙƙuwa ta ƙasan riga da sakin murmushi. A haka dai akai ƴan abubuwan daya dace tsakanin abokan ango da na amarya, zuwa tara da rabi ango da yaga basu da niyyar basu filin ya murje idanu ya korasu waje. Sun fito suna dariya, yayinda MB babban amininsa ya sinna masa wasu ƙwayoyin magani tare da miƙa masa gorar ruwan hannunsa yana faman ƙyafta masa idanu da masa magana a hankali. “Adai yi tuƙi a hankali, dan wannan motar ƙirar larabawa ce, idan bakai wasa ba amaimakon horn ƙira'ar Alkur'ani zakaji”. A tare suka kwashe da dariya tare da cafkewa bayan ya afa maganin batare da tambayar na miye ba ya kora da ruwa. Ango JJ ya ce, “Shege abokina, kune malaman duniya, dan shugaban mai jan ƙyalli ma a ƙarƙashin koyarwarku yake baza komarsa”. Dariyar suka sake kwashewa a tare, MB yay gaba yana saɓa babbar riga da faɗin, “Idan da matsala kai dai kai kirana da wuri na turo makanike dan ka samu damar fita shan iskar yammaci, na barka lafiya a tuna da maƙota kar'a ishesu da...” bai ƙasa ba ya wani kashe masa ido ɗaya yana ficewa a gate ɗin. Shi dai ango JJ rufe gate ɗin yay yana cigaba da dariyarsa. Kafin ya juya cikin gidan ransa fes yau ranar baje koli ta duniya a cikin rayuwar sa... Shuuu!! Aka gitta kamar ta gefensa a dai-dai yana kai hannunsa ga handle ɗin ƙofar, kamar zai share da tunanin iskar sanyi data fara kaɗawa ce sai kuma dai ya ji an sake gitta masa yana ƙoƙarin tura ƙofar. Wawwaigawa yay damansa da haggu sai dai kuma babu kowa, cikin nuna halin ko'in kula ya ɗage kafaɗu da taɓe baki ya ƙarasa shigewa a falon. “Amarya kin sha ƙamshi, amarsu baƙya laifi koda kin kashe ɗan masu gida!”. Ya jero kalaman kirarin tamkar shine ya fara ƙirƙirarsu saboda tsaruwarsu a bakinsa kai kace waƙace a bakin shata ko barmani coge. Bai damu da jin ba'a amsa mar ba, ya murzawa ƙofar key harda gyara labulaye da ƙyau. Turus yaja ya tsaya ƙirjinsa na bada wani irin turururumm tamkar sautin gangar Ado gwanja a tsakkiyar filin biki. Wayam falon babu komai, duk kayan alatun nan da aka ƙawata falon da shi tamkar wata almara babu su babu alamar su. (Kai ina, wannan almara ce JJ dawo hankalinka) wata zuciya ta ayyana masa. Yawu ya haɗiye da ƙyar, tare da sakin murmushi mai kama da kuka shi adole yana son dawo da hankalinsa jikinsa. Bakinsa na rawa da karkarwa ya furta, “L-o-v-e!” a rarrabe yana runtse idanunsa da ƙarfi. Ba'a amsa mar ba yanzun ma dai, dan haka ya sake ƙarfin halin buɗe ido ɗaya da ƙyar, da sauri ya sake buɗe ɗayan ma ya shiga waige-waige yana haɗiyar yawu da sauri-da-sauri. Yanzu kam falon komai ya dawo kamar yanda yake a da, sai dai kuma kalar kayan ta canja. (JJ! Farin ciki fa ke neman juyar maka da brain, ka daidaita kanka mana). Kansa ya shiga gyaɗawa kamar tsohon ƙadangare cike da son gamsar da kansa akan dole, sai kuma kamar wanda aka ingiza ya nufi bedroom da sassarfa, yana tafiya yana waigen falon. Har ɗan datse hannunsa yake wajen ƙoƙarin rufe ƙofar bedroom ɗin da danna mata key saboda yanda jikinsa ke rawa. Cikin dauriyar azabar dake ratsa masa hannun da ya datsa ya jingina da ƙofar yana sauke nannauyar ajiyar zuciya irin ta na sha da ƙyar ɗin nan. Yakai minti ɗaya a haka kafin ya dai-daita kansa da ƙyar yana sauke ajiyar numfashi a jajjere. Kasancewar sai ka ratsa ɗan lungu daga jikin ƙofar kafin ƙarasawa tsakkiyar bedroom ɗin sosai saboda bathroom dake a wajen ya bashi damar share gumin ɗaya tsatstsafo masa da dai-daita yanayinsa da ƙyar sannan ya cigaba da tafiya a takun da bai gaza huɗu zuwa biyar ba. Bedroom ɗin ƙato ne, ga kayan gado yaji masu ƙyau dan iyayen amarya sun taka rawar gani suma. Ƙoƙarin hana kansa kallon komai yake saboda abinda ya baro baya, dan haka ya nufi gadon kansa tsaye dan yasan dai anan zaiga amaryar tasa sarkin kunya da nutsuwa. Sai da ya kai zaune yana faɗin, “Afuwan Love na barki ke ɗaya, na sallami waɗan nan ƴan matsalar ne, kin san in su MB na waje bakin mutum baya hutaw......” Ya kasa ƙarasawa sakamakon abinda idonsa ya gane masa. Wata irin murɗaɗɗiyar macijiya ce baƙa ƙirin an mata wata kwalliya da kalar jaja-jaja mai haske kamar ƙwan lantarki. Ba'a labaran tatsuniyoyi da wasanni ba, ko'a film ɗin ƴan India da suka sabayin na macizai bai taɓa cin karo da irin wannan maciji mai girma ba. Rawa jikinsa ya farayi kamar mazari, har takai yana zamewa a saman gadon zuwa ƙasa batare daya farga ba. Gab ya kusa kaiwa ƙasa daɓar yaji an riƙoshi... “D lafiya kuwa? Miya faru kake irin wannan kakkarwar har kana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa?”. Nutsatstsiyar muryar amaryarsa ta ratsa masa kunne, yayinda lallausan tafin hannunta da tunda ya riƙesa a wajen dinner jiya abin ya kasa barin ransa ke riƙe da shi a yanzu ma. Kusan a tare ita da shi suka zube a ƙasan, dan ya riga ya taho gaba ɗayansa, sannan ya fita nauyi. Faɗowarta jikinsa ya sakashi sakin wani irin ihu tamkar wanda aka farkar a barci da ruwa mai sanyi. Yay wani irin mamuƙeta illahirin jikinsa na rawa. A hankali ta saki ƙara da faɗin, “Wayyo D zaka karya min awazzu.” Kafin yau idan yaji wannan zazzaƙar muryar tata ji yake yafi kowa sa'a a duniya. Amma a yau maimakon hakan wani irin rawa da kakkarwa jikinsa keyi, ga zufa ta wanke masa illahirin jikinsa tamkar wanda yay wanka. Zumut ya miƙe tamkar wanda aka zabura ya shiga waige-waige, sam babu komai a gadon, sai ma gyaran da yasha na musamman ga filos da aka jera a kansa tamkar an zana a takarda. Sake juyowa yay da sauri yana kallonta da nuna gadon da yatsa, sai dai bakinsa ya kasa furta komai, sai ma rawa da pink lips ɗinsa sukeyi. Cikin rashin fahimta take kallon gadon itama, sai kuma ta dubesa da alamar tashin hankali a tattare da ita. “D! dan ALLAH miya faru, wlhy kana sake rikitani nikam. Jibafa yanda kake zufa. Kana nuna min gado kuma ni banga komai ba a wajen.” (JJ ka nutsu, karfa ka ɓata wannan daren mai muhimmanci a gareka mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya faɗa cikin tsawatarwa. Kansa ya shiga jinjinawa tamkar zuciyar tasa na kallonsa ne, ya haɗiye busashen yawu tare da sakin murmushin yaƙe ga amaryar tasa. “B..ba komai Love, dama fa ina gwada ki ne kawai naga amaryar tawa jaruma ce ko matsoraciya.” ya ƙare maganar yana damƙo hannunta cikin nasa da ƙyau. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, sai kuma ta duƙar da kanta tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi dan kunya. Yanayin nata ya sake sakashi dawowa hayyacinsa da tuna masa shi ɗin fa ango ne. Ƙoƙarin haɗiye komai yake yi, duk da hakan abune mai wahalar gaske a garesa, amma dai zai gwada yin wannan jarumtar ya gani. Ayatulkursiyyu ya karanta a zuciyarsa yana tattofawa a kaikaice. Sai da ya tabbatar ya ɗaure ɗakin ɗamm acewarsa, kafin ya ƙara ɗan samun nutsuwar sake maida hankalinsa ga amaryar tasa da kanta dai ke a sunkuye. A karo na farko ya jawota jikinsa ya rungume tsam yana sauke tagwayen ajiyar numfashi, yayinda ita kuma ta shiga masa rawar jiki irin na farin shiga, sai dai bata hanashi ba ko yunƙurin janye jikinta har kusan mintuna biyu daya saketa dan kansa. “Yau dai ga ni ga Love a gida ɗaya, ɗaki ɗaya a matsayin ma'aurata”. Ya faɗa yana sake riƙo hannunta duk biyu cikin nasa da ƙyau tare da gyara zamansa ya fiskanceta. Murmushi ta saki tana ƙara ƙasa da kanta tare da jan mayafinta ta rufe fuskarta. Shima sai ya saki wata ƴar siririyar dariya cike da nishaɗi, hannu ya kai ya yaye mayafin yana mai ɗago haɓarta ta yanda zaiga fuskanta da ƙyau.. Wata muguwar zabura yayi baya yana mai waro duka idanunsa waje jikinsa na karkarwa batare da ya ma sani ba ya furta, “Anoosha!!”. Cike da salo tai masa luuu da idanu tare da sakin sassanyan murmushin da a fuska ɗaya ya sanshi kuma ya taɓa ganinsa, bai kuma sake ganinsa ba. Tsabar kiɗimewa da shiga ruɗani har yana bugewa da gado wajen zabura da ƙoƙarin tattara babbar rigar jikinsa alamar zai kwasa a guje yaji caraf an riƙesa.......✍️ *_😂😂Tofa babbar magana, wai ango JJ mijin amaryar da ko sunanta bamu sani ba mi shika hwaruwa ne hakanga kuma? Anya kuwa ba....🥱Bara dai na iya bakina abinga walle bana hiɗi bane🤣🤣._* _Alhamdullahi inata alƙawarin gareku na yin free book ALLAH bai ƙaddara hakan ba sai yanzu. To Amin afuwa gani zan cika alkawarin in sha ALLAH. Ina fatan wannan littafi zai ƙawatar da ku tako wace fiska, cakwakiya, nishaɗi, ƙalubale, ƙaddara, son zuciya, kai abubuwane da yawa ya wawuso tako wace fuska, zakuma ku fahimci saƙon da yake son isarwa, dan salon na musamman ne, idan nace na musamman ina nufin na musamman a gaba ɗaya musamman ɗin😉👌. *Kumuje zuwa gidan ango muji yaya zai ƙare da wannan daren farko nasa, dan naga na musamman ne fa 🚴🚴🚴😆😆🤫🤫.* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na biyu_ ........“Ai babu gurin zuwa, saboda da hannunka ka rufe duka ƙofofin guduwar Mr JJ ango mijin amarya Alimah”. Muryar da baya jin zai manta a rayuwarsa ta ratsa kunnuwansa. Dauriyarsa ta ƙare, hakama ƙarfin halinsa ya kai ƙarshe. A take jikinsa ya fara rawa kar-kar. Gashi an riƙesa irin riƙon da ko numfashin kirki ya gagara yi. Jin saukar numfashin mutum a fuskarsa ta saka shi buɗe idanunsa da sauri. A matuƙar razane ya fasa gigitacciyar ƙarar data ɗauke numfashinsa gaba ɗaya sai gashi ƙasa wanwar a sume..... A firgice ta buɗe idanunta itama tamkar wadda aka farkar da ga nannauyan barci. Waige-waige ta fara ƙirjinta na wani irin luguden daka. To ita yaushe ma barci ya ɗauketa ne, ba yanzu babu jimawa suka shigo ɗakin nan tare da angonta JJ ba. Dan fitarsa babu daɗewa rakkiyar abokansa ko cikakken minti biyu baiyi ba ya dawo, batama jin yabar jikin ƙofar falon. Cike da zumuɗi da aka san duk wani ango da shi ya koma ya zauna inda ya tashi a kusa da ita. Batare da yayi magana ba kawai ya jawota jikinsa ya rungume yana shinshinar wuyanta. Kunya ta sakata shiga wani yanayi, a take jikinta ya fara mazari ta shiga noƙewa. Dariya ya sakar mata cikin kunne da faɗin, “Ai yau dai kunya ta ƙare Love, miya rage kin zama matar JJ, JJ ya zama mijinki. Please ki ajiye wannan kunyar da safe ƙya maidata dan kin san yau ɗin ta musamman ce fa”. Bata iya tace da shi komai ba, dan a matsanancin tsorace take ga kuma kunya. Sai dai hakan baisa ta hanashi yin yanda yaso da ita ba. Bayan ya gama shinshinar ta ne da rungumeta ya ɗakkota cak zuwa wannan ɗakin yana faɗin, “Yanzu dai muje muyi sallah kafin komai ko. Dan nasan matar tawa ustaziya ce”. A karo na farko ta sakar masa murmushi, tare da tura kanta a jikinsa dan kunya takeji matuƙa kamar me. Dan tunda take a rayuwarta bata jin wani ya taɓa riƙe mata hannu, sai a jiya wajen dinner da JJ ya aikata hakan gareta. To ita dai tasan sun shigo ɗaki, daga haka kuma bata san miya faruba sai ƙarar ihun nan da bata san daga ina ya fito ba da ya farkar da ita, a yanda kuma taga kanta alamu sun nuna barci tayi. Gadon ta sakko da sauri, sai kuma tai tsamm ta dakata saboda jin motsin ruwa a toilet ɗin ɗakin, hakan na nufin JJ na ciki kenan. Numfashi ta ɗan sauke a hankali, tare da komawa ta zauna tana gyara mayafinta, zuciyarta na tabbatar mata wanka ya shiga kenan, ita kuma barci ya ɗauke ta, ihun da taji kuma maybe a maƙwafta ne. To amma abin mamakin anan taya tayi barcin? Haka cikin ƙanƙanin lokaci? Rashin amsa ya sakata ɗan sauke numfashi kawai.. dai-dai nan JJ ya fito a toilet ɗin babu alamar wanka yayi sai dai ko alwala. Kanta ta duƙar ganin ita yake kallo, shi kuma ya saki murmushin da har ta iya jiyo sautinsa da ga inda take tare da faɗin, “Naga a takure kike, jeki falo ki jirani”. Kamar mai jiran jin hakan ta mike zumbur, har harɗewa take wajen fita tana mai sauke ajiyar zuciya, sai dai mamaki fal kanta dan sai take jin kamar wani banbarakwai hakan nan.... (Bake kaɗai ba amarya, ni kaina fa man kai na ya tsiyaye. Dan na gagara fahimtar komai, shin JJ ɗin ne ba mutum ba ko ke kanki? Masu karatu ko akwai mai amsa min?🥱😆🚴). ★★..... A ɓangaren JJ ango kam zubur ya miƙa tare da sauke nannauyan numfashi alamar farfaɗowa da ga sumar da ya tafi. Gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi a yanzu, dan tun bayan numfashin da ya kawo cikin zabura sai kuma ya koma laƙwas kwance yana maida idanunsa a hankali ya sake lumshewa. Falaƙi da Naasi ya fara karantawa a zuciyarsa yana ɗan buɗe ido kaɗan, shiru babu motsin komai, sai wata iska mai daɗi dake ƙaɗawa. Kamar wanda aka bama ƙarfi ya miƙe zaune dingangan, waige-waige ya shigayi idanunsa a buɗe sosai mamaki fal kansa na ganinsa a baranda kwance wanwar, tabbas a waje yake, ya kuma kasa iya tuna komai da ya faru. Babu alamar akwai wani abu da zuciyarsa ke ayyana masa kuma, sai ma wata nutsuwa da yake ji ga zuciyarsa na tabbatar masa faɗuwa yay kenan bayan yama abokansa rakkiya, dan abinda ya fara tunawa kenan kafin gittawar da akai masa lokacin da yake ɗaura hannunsa saman handle ɗin ƙofa, sai kuma abinda ya faru na shigarsa falo dama ɗaki, hakan na nufin komai daya faru a mafarki ne ba zahiri ba dai kenan. A take ya gamsu da hakan, dan kamar an masa wanki ƙwaƙwalwa ne ma ya kasa tuna komai a yanda ya kamata balle yayi tunani irin na mutane masu hankali. Sai ma amaryarsa da ta zo masa a zuciya. Miƙewa yay tamkar wanda aka tsikara, ya gyara zaman babbar rigarsa da hula sannan ya ɗaura hannunsa a handle ɗin ƙofar ya murza a hankali yana sakin wani murmushin farin ciki. A inda ya barta nan ya sameta, tana lulluɓe dai har yanzu cikin mayafinta. Sai ƙamshinta daya gama gauraye falon mai shegen daɗi. Taku ya cigaba dayi cikin shauƙi da bajinta zuwa gareta. Kusa da ita daf ya tsaya batare daya zauna ba ya zuba mata shu'uman idanunsa da suka sake ƙanƙancewa. Tsahon mintuna biyu kafin ya kai durƙushe ƙasa tamkar ɗa a gaban uwarsa. Hannu biyu ya saka ya ɗaga mayafinta ƙyaƙyƙyawar fuskarta mai alamun rashin yawan hayaniya ta bayyana. Ga kwarjini irin wanda aka san amarya da shi tattare da ita. A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da kamo hannayenta da take matsewa cikin juna ya riƙe, sun sha jan lalle da baƙi sai sheƙi suke. Ɗagosu yay zuwa bakinsa ya sumbata tsakkiyarsu ɗaya bayan ɗaya. Sosai ta sake ƙanƙame jikinta da sinne kanta na kunya... “Babu gaisuwa Love?”. Ya faɗa cikin wata irin siririyar murya. Kanta ta sake sinnewa cikin tata muryar da ke rawa ta ce, “Kayi haƙuri ina yini”. “Ai baƙya laifi amarya koda kin kashe JJ ne ma. Dama wannan golden voice ɗin nake son ji ne. Ina miki Barka da zuwa gidanki, fadarki. Alƙawarin ALLAH ya cika yau gani ga Love ɗina a gida ɗaya matsayin ma'aurata. Babu abinda zance da UBANGIJI sai godiya. Kisa a ranki har abada bake ba kishiya, ko'a aljanna ke kaɗai ce”. Murmushi ta saki a karo na farko, sai dai bawai ta amshi kalaman nashi bane da muhimmancin riƙewa, dan duk da ƙananun shekarunta kuma ita bamai yawan hayaniya bace da taron ƙawaye tanada iliminta. Tasha jin yayunsu na faɗin yarda da irin waɗan nan kalaman a bakin namiji yaudarar kaine kawai.. Shiko tuni murmushin nata ya kashesa, dan a tunaninsa kalamansa sunyi irin tasirin da yake buƙata. Tashi yay daga ƙasan da yake ya koma saman kujera kusa da ita, gaba ɗayanta ya jawo ta koma saman cinyarsa ya rungumeta tsam-tsam yana sauke numfashi da sauri-sauri. Dan maganin da MB ya basa ya fara aiki. Itako gaba ɗaya ta gama rikicewa da kunya da tsoro, sai dai batai yunƙurin jaye jikinta ba kamar ɗazun. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ya ɗago fuskarta, kallonta yake tamkar a yau ya fara ganinta, anan ɗin ma dai yaja wasu mintuna biyun cur sannan ya miƙe ɗauke da ita yana faɗin, “Muje muyi sallar godiya ga ALLAH sannan kici abinci da ga nan sai ki.....” ya ƙarasa faɗa mata cikin kunne yana sakin wata siririyar shaƙiyyar dariya. Itako jitai gaba ɗaya ta rikice, gashi yana ɗauke da ita, sai kawai ta sake cusa kanta cikin jikinsa har suka iso ɗakin bata yarda ta ɗago ba. Ba ɗakin da ya kaita bane ɗazun, ta fahimci hakanne lokacin da yake sauketa a kofar toilet ɗin yana faɗin, “Je kiyo alwala bara na rage rigar nan tamun nauyi. Kanta a ƙasa ta amsa da to, ya bita da kallo har sai da ta shige sannan ya juyo yana murmushi da ƙoƙarin cire babbar rigar tasa. Cikin sauri ya ƙarasa janye rigar daga fuskarsa ƙirjinsa na wani irin harbawa. Sai kuma ya waiga da sauri ya kalli ƙofar toilet ɗin, sake waigowa yay ya kuma kalli gadon. Amaryar tasa dai ce data shiga toilet akan idanunsa yanzu zaune a tsakkiyar gado kuma tana murmushi. (Kodai ƙwaya MB ya bani ne) ya faɗa a zuciya jikinsa na rawa, da sauri ya juya baya zuwa ƙofar toilet ɗin. Buɗewa yay ya leƙa. Alimah amarya dake ƙoƙarin fara alwala ta ɗago da sauri. “Sorry” ya faɗa bakinsa na rawa tare da ja mata ƙofar ya rufe yana juyowa. Yanzun kam gadon wayam babu kowa, yana nan tsaff da shi a gyare tamkar yanda suka shigo suka samesa.. Sautin kuka ne ya fara ratsa ɗakin a hankali har ana shashsheka, da sauri ya buɗe idanunsa daya lumshe na jin relief da farko ya fara waige-waige. Jin zai faɗi ya sashi kaiwa zaune bakin gado, a bisa tsautsayi bai zauna da kyau ba ya zame kasan carpet wanwar. Sai kuma ya miƙe zaune dingangan zuciyarsa na wani irin gudu a cikin ƙirjinsa. Ƙaruwa sautin kukan yake, sai dai babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai ɗin dai Alimah bata fito ba. Cikin tsumar jiki ya dafe hannayensa duka biyu ƙasa da nufin jan jikinsa koda da rarrafe ya kai ga toilet yaji ya camɓalasu cikin laima mai kauri da ɗumi, da sauri ya ɗago duka hannayen, yay bala'in waro idanunsa waje tare da maida kallonsa ga ƙasan. Tabbas jini ne malale a duka ɗakin tamkar yanda tiles yake, ga sautin kukan nan na ƙaruwa. A karo na farko JJ ya fashe da kuka kawai idonsa a hanyar toilet komai daya faru ɗazun na dawo masa a zahiri. “Na shiga uku ni Jazool. Mike faruwa dani?...” ya sake ɓarkewa da kuka..... Dariya ce ta karaɗe ɗakin a maimakon kukan da ake rairawa da farko. Kamar kaɗawar iska a cikin kunnensa aka gwargwaɗa masa, “Oh oh mazan fama kuma da kuka haka. Karka bada maza mana JJ ango” sai kuma aka ƙyalƙyale da dariya mai cika kunnuwa data sake rikita JJ. Kamar ƙyaftawar ido aka kuma ɗaga shi cak aka sauke saman lafiyayyen gadon ɗakin da yasha shimfiɗar alfarma. Yana ƙoƙarin zabura ya miƙe aka rungumeshi.. “Uhhm my D ina kuma zaka? Kasan fa wannan daren na musamman ne a garemu”. Aka faɗa masa a cikin kunne ana kaima wuyarsa sumbata. Bashi da zaɓin da ya wuce wage baki ya ɓarka ihu kawai ko zai samu agajin wannan tashin hankali da ga maƙwafta, sai dai me yana wage bakin caraf aka cafke harshensa cikin wani salo aka hau sumbata tare da sake ƙanƙamesa tamau. Duk yanda JJ yaso yin wani yunƙuri ya kasa hakan, yana ji yana gani aka suleshi zigidir. Kafin a sakar masa baki tare da jirkicesa ya koma ƙasa akai masa rumfa. Fuskar amaryarsa ce ta bayyana a idanunsa, ta sakar masa lallausan murmushi da kashe mar ido ɗaya cike da salon so da ƙauna... “My D! Ya kake abu kamar wani matsoraci. Karfa ka manta wannan shine dare mafi girma a wajenmu. Daren da kake ta faman zumuɗin zuwansa da lissafinsa.” ta ƙare maganar cikin wata iriyar shagwaɓaɓɓiyar murya tana shafo fuskarsa. Jujjuya kansa kawai yake hawaye na gangaro masa. Magana yake son yi amma da alama sautinta ya gagara fitowa, sai lips ɗinsa ke wata irin rawa ga hawaye ga majina ga zufa sun masa sharkaf a ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ma'abociyar shan gyara iri daban-daban. Sumbata ta sake kaima lips ɗinsa tana dariya, sai kuma ta ɗagashi zaune itama tana zaman harda tamkwashe ƙafa suna fuskantar juna. Ita dai sanye take cikin tufafinta harda mayafi, shiko an masa zigidir sai faman kare jikinsa yake da hannu. Dariya ta sake kwashewa da shi tana kallon yanda yake mammatse jiki. Cikin dariyar take faɗin, “Haba angona minene kuma na ɓoye jiki bayan so nake na kalleka da ƙyau yau ɗin nan. Karfa ka manta ka zama Alimah, Alimah kuma ta zama kai. Jiya aka ɗaura mana aure, yau aka kawoni gidanka. Miya rage kuma garemu banda baje kolin soyayya D?. Koka manta kana tare da Love ɗinka ce, ƴar shilar yarinyar nan mai shekaru goma sha bakwai kacal. Mai tarbiyya da ilimin addini. Kamila ga kunya kullum tana a cikin hijjab. Ƴar malamai da bata san komai ba sai zuwa islamiyya da aikin gida. Haba My JJ”. Ta ƙare faɗa da salon shagwaɓa a yanzun ma har tana turza ƙafafu a gadon. Sake ɓarkewa da kuka JJ yayi lokacin da idanunsa suka sauka akan ƙafafun nata. Dan amaimakon ƙafa shikam kofatai ya gani irin na shanu da dokuna. Ganin ƙafar yake kallo yana kuka itama ta kalli ƙafar, sai ta ɓarke da dariya harda kwanciya kafin ta tashi zaune da ƙyau tana haɗe fuska tamkar ba itace ta gama dariyar ba. Haɓarsa ta kamo tare da matso da fuskarsa gab da tata ta sumbaci lips ɗinsa, sai kuma ta zuro wani irin dogon harshe kamar ana fitowa da abu a rami ta fara lashe shi. Luuuu kawai yayi ya sake sumewa........✍️ _😂😂😂 Gaskiya JJ kana bada maza a wannan al'amari . JJ na buƙatar addu'a fa🚴🚴🚴🚴😆🥱_ *_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na uku_ ........Da murnarsa ya shigo gidan yana faman washe baki. Tun a farkon tura ƙofar soron gidan yake ƙwala kiran sunanta tamkar mai shela. “My Queen! My Queen! Kina ina ne? Wai nikam. Fito! Fito ki gani fito My Queen!!”. Har cin tuntuɓe take wajen saurin fitowa da ga bayin, tsabar yanda ta fito a rikice saboda kiran da yake faman ƙwala mata bama tasan da botikin wankansu da akoda yaushe yake a bayin ajiye ba ta fito. A ƙaramin tsakar gidan da bai wuce cin tabarma biyu ba sukaci karo. Kafin ma tace wani abu yayi wani kalar jawota ya rungume tare da ɗagata cike da farin ciki ya shiga juyi da ita. Ɗan ihu ta fara mara sauti tare da roƙon ya sauketa tana faman ɓoye fuskarta cikin jikinsa. Shiko duk da yasan bata son hajijiya sam bai sauketan ba, sai faman dariya ma yake abinsa yana cigaba da juyinsa. Sai da yay mai isarsa sannan ya afka ƙofar dake kusa da su, falone matsakaici dan kujerun da aka ƙawatasu da shi ma a mugun matse suke. Tsakar falon kuwa bai wuce girman sallaya ba, direta yay a saman doguwar kujerar yana hakki. Itako ta sake ƙanƙamesa har yanzu fuskarta na jikinsa. Sai da kusan mintuna biyu suka shuɗe taji hajijiyar ya saketa kafin ta ɗago kaɗan tana tura baki da kwaɓe fuskan tamkar zatai kuka.. a shagwaɓe ta ce, “Haba Husby so kake kaga bayana ne?”. Dariya ya ƙyalƙyale da shi, cike da nishaɗi ya furta, “Ai mai ganin bayanki sai kin juya My Queen. Wlhy wani farin ciki ne na shigo da shi wanda na tabbatar idan kika jishi yau ƙyautata sai ta kasance ta musamman ne”. “Woow Mijina bani nasha mana”. “Ai dole kisha kuwa Matata, sarauniya ta, dan haka rufe idanunki”. Ruf ta sufesu murmushi na sake ƙawata kansa a black beauty fuskarta mai wani irin sirrin laushi da sheƙi. Ga ɗan ƙaramin bakinta da yafi komai ƙawata sirrintaccen ƙyawun nata. Hannunta na dama ya kamo cikin nasa, yana cigaba da murmushin ya ciro abu a aljihunsa ya saka cikin hannun nata ya rumtse yana faɗin “Zaki iya buɗewa”. Buɗewar tai da sauri tare da ware tafin hannunta, ta ɗan zubama keys ɗin idanu zuciyarta na wani irin rawa-rawa. Sai kuma ta ɗago da sauri tana kallonsa da girgiza kanta. “Husby ka ɓaddani ALLAH. Keys ɗin miye haka?”. Ido ɗaya ya kashe mata tare da jawota jikinsa ya rungumeta har zanin dake ɗaure a jikinta na kwancewa. Basu damu da hakanba su duka, suka ƙanƙame juna. A cikin kunnenta ya gwargwaɗa mata maganar da ta sakata ɗagowa da sauri tana kallonsa idanunta gaba ɗaya a waje. Cikin rawar lips idanunta na ƙiƙƙiftawa ta furta, “Naka fa Dafeeq?! Taya hakan zata kasance bayan nasan ko key na keke bamu da hanyar samunsa a gidan nan balle mota har ma da gida”. “Ikon ALLAH kenan Deejoh na.” A hankali ta ce, “Hakane. Sai dai komai ai yana da sila. Tayaya hakan ta kasance?.” “Karki damu zan sanar dake komai. Amma fara mun haƙuri naɗan watsa ruwa ki bani abinci kuma naci. Dan yunwa nake ji ALLAH sosai. Banci komai a cikin nan nawa ba tun karin da mukai da safe”. Duk da zumuɗin son jin da take haka ta daure ta danne. Cikin ƙarfafa kanta da ture abinda ke tsikarin zuciyarta ta miƙe tana murmushi. Fita tai a falon, babu jimawa ta dawo. Kusan a tare suka ɗaga labule, dan haka ta ɗan jaye baya ta bashi hanya. Fita yay yana sakar mata murmushi, ta maida masa murtani cike da son ƙarfafa kanta. Numfashi mai nauyi ta sauke lokacin da take sake kaiwa zaune a kujera idanunta akan keys ɗin nan dai. Ta kafesu da ido zuciyarta na ci gaba da kai-kawo. Haka kawai take ɗan jin kamar tsoro a ranta, sai dai bata san dalilin hakan ba, domin a zahirance ba tsoron ya kamata ace tana ji ba, murna ya kamata ace tafi kowa da wannan alkairin da ya samesu. Badan komai ba sai dan tuna baya, tuna baya akan rayuwarta da Dafeeq kafin aure, tuna baya kafin zamowarsu ƙarƙashin aure. Tuna baya bayan zamowar tasu ma'aurata har zuwa yau ɗin nan da suka wayi gari a matsayin da suke kafin wanda ke neman canjasu a yanzun nan... Sunanta shine Khadijah, ɗiya ta farko a wajen iyayenta. Tana da ƙanne huɗu duk mata, sai namiji ɗaya daya kasance autansu. Mahaifinsu ba mai kuɗi bane, sai dai mai ƙarfin hali ne da wadatar zuci. Wannan imanin nasa ya sakasu tashi a gidansu matsayin ƴan gata, bama gidansu kawai ba har a cikin dangi da yaran anguwa sun kere tsara. Dan komai mahaifinsu tsaye yake wajen musu dai-dai ƙarfinsa. Hakama mahaifiyarsu tana nata ƙoƙarin da sana'arta ta saida kayan sanyi da kayan miya irinsu kuka, kuɓewa, magi, gishiri, daddawa. Kai duk dai wani nauyin kayan miya na gargajiya zaka samesa a wajen mahaifiyarsu. Dan haka gidansu ya kasace ɗaya daga cikin gidaje da ake zirga-zirga na sayayya. Ƙoƙarinta da ƙwazo a makaranta ya sakama mahaifinsu burin ganin tayi karatu mai zurfi ita da ƙannenta, amma kasancewar itace babba sai ya zam ita aka fara ƙoƙarin ginawa. Lafiya lau ta kammala primary ta shiga secondary ɗin dake ƙasan layinsu ta ƴammata, sai dai makarantar iyakarta jenior ce. Wato iya aji uku. Matuƙar ƙwazo da himma ta bada a karatunta, inda ta kasance ɗaliba mai ɗaukar first class a ajinsu tun daga jss 1 har zuwa jss 3. Sun zana jsce cikin nasara da jin kewar rabuwa da makaranta, musamman ita data kasance mai farin jinin malamai saboda ƙwazonta. Dan randa akai musu walimar fita ta samu ƙyaututtuka daban-daban da suka saka iyayyenta farin ciki tare da sake jin ƙaimi akan tsaya mata cigaba da karatu. Sun ɗanyi zaman gida har jarabawa ta fito, inda ta samu nasarar samun wata makaranta dake can wata anguwa, sai dai ita haɗe take ƴammata da samari. Makarantar babbar makarantace dan duk ɗalibin daya kasance a cikinta sai mai ƙwazon gaske. Saboda akan tsinto yara ne masu ƙwazo sosai daga makarantu daban-daban zuwa nan a duk shekara, itama ƙwazonta ya bata wannan damar. Tayi farin ciki matuƙa da zamowarta ɗalibar wannan makaranta mai farin jini da kowa ke fatan ganin ya sameta, hakama iyayyenta sunyi murna mara misali. Anan ɗin ma lissafin bai canja ba, dan ta matuƙar dagewa a tarm ɗin farko itace ta ɗauki ta ɗaya a ajinsu, ta kuma sami ƙyautar yarinya mai tsafta da kuma rashin yin latti. Iyayenta sunyi matuƙar farin ciki tare da ƙara ƙarfafata, dan har ƙyauta baba ya mata ma, hakama Inna ta siya mata kaza guda ta soya mata tace taita ci har ƙannenta na kukan an nuna musu wariya. Ta gama ss1 lafiya, a tarm ɗin da suka shiga ss2 komai ya fara, dan shine farkon labarinta tsakaninta da _Dafeeq Abubakar Ja'e_....... ★★★★ A hankali yake buɗe idanunsa da sukai wani masifar nauyi. Da sauri ya ɗan rumtsesu ya sake buɗewa again. Sai dai yanzun ma dai a hankali yake motsasu. Fankar dake juyawa kaɗan-kaɗan ya zuba ma su na tsawon sakanni goma. Tun yana kallonta dishi-dishi har idanun nasa suka fara gani tar-tar. Tabbas ba gidansa bane, dan anan ɗin normal selling ne saɓanin gidansa da akaima sabon lafiyayyen p.o.p da yasha fitulu. Sake ware idanun yay da ƙyau tare da motsa jikinsa, jin hannunsa na dama yay masa nauyi sosai ga zafin daya ratsashi saboda fisgar da yay masa ya sashi ambaton “Wash ALLAH na”. A karo na farko duk wanda ke ɗakin suka juyo garesa, sai kuma duk suka zabura kowa na ambaton sunansa. Idanunsa ya sake buɗewa da ƙyau yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Mahaifinsu ne, sai yayunsa biyu da abokinsa MB da SJ, sai ƙaninsa guɗa ɗaya. Jin yanda suka rufesa da tambaya da sannu ya sashi motsa bakinsa da yay nauyi a hankali ya furta, “Abba ina ne nan ɗin?”. “Asibiti ne Jazool, an kawoka ne baka da lafiya tun jiya”. Yayansa ya bashi amsa cike da nuna alhini da tausayawa. Da ɗan sauri JJ ya dubi hannunsa, ganin ruwa ake ƙara masa ya sashi yarda da zancen yayan nasa. Ƙoƙarin tashi yake zaune sai dai ya kasa, cikin sauri MB da yayansa na biyu suka kamashi. Zaunen suka tadashi, tare da jinginasa jikin bango da Nuhu ya gyara filo suna cigaba da masa sannu. Kai kawai yake iya gyaɗa musu shi dai, ransa fal mamakin miya kawosa asibiti shi kam.. Idanunsa ya rufe ruf, tamkar wanda ake sarrafawa da remote sai kuma ya buɗe da sauri jin abinda MB ke faɗa... “Sannu kaji abokina, gaba ɗaya ka ɗaga mana hankali, amarya da ya kamata ace ita ke jiyya sai kuma kai a naku labarin amarcin ya juye kaine kwance a gadon asibiti? Ni dai ALLAH yasa ba pills ɗin dana baka bane ya jawo maka wannan bala'in tun jiya ake abu ɗaya kamar bazaka rayu ba”. Rawa jikin JJ ya farayi, ya ɗan juya ya dubi sashen da Abba da Yayunsa suke, can ya hangosu a bakin ƙofa alamar magana sukeyi, sake maido idanunsa yay kan MB da SJ dake tare da shi kawai. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Yaushe aka kawoni nan? Waye kuma ya kawoni?”. SJ ne ya bashi amsa yanzun kam da “Tun jiya da safe aka kawoka. Amaryarka ce kuma tai kiran Rabi'ah tana kukan cewar azo a taimaketa ka mutu kamar yanda Nuhu ya sanar mana. Hankali tashe su Yaya Mujee suka nufi gidanka. Inda aka taddaka yashe a ƙasa baka numfashi kuma duk an jimaka ciwo a fuska da jikinka kamar da farauta, itama amaryarka jikinta duk jinin da yake biyo mata ta hanci da gefen baki alamar dukanta akai...” Da wani irin gudu abinda ya faru tun daga barinsu gidan zuwa komawarsa ciki ya shiga dawo masa. A take jikinsa ya fara kakkarwa. Muryarsa dake a disashe na rawa ya ce, “Duka? Ita Alimah ɗin?”. “Ƙwarai da gaske, dan tare ma aka kawoku asibitin nan, sai dai ita tun jiyan aka sallameta bayan Doctor ya dubata sosai, ya kuma tabbatar da marinta akai bakinta da ya fashe, jinin hancin kuma haɓo ne tayi. Kaiko an yayyageka da farauta ne aka jijji maka ciwukan nan. Dalilin sumanka ne dai har yanzu basu ce komai akansa ba, dan jiyan ma da ƙyar aka samu ka farfaɗo kusan sha biyun dare, shine sukai maka allurar barci sai yanzu ne kuma kake farkawa”. Cikin rawar lips mamakin zantukan MB ras akan fuskarsa ya buɗe baki zaiyi magana, sai dai shigowar likita tare da Abbansa da yayunsa ya hanashi cewa komai. Duk fita likita yace suyi, yayinda shi kuma ya shiga duddubashi yana jera masa tambayoyi akan yanda yake ji a yanzu. Da ƙyar ya iya bama likitan amsa da cewar shi yanzu baijin komai, sai kansa da yay masa nauyi da kuma mararsa. “Insha ALLAH suma zasu sakeka. Ciwon kan normal ne na daɗewa da kai a sume. Na maran ne dai ƴar damuwa itama kuma bamai tada hankali ba. Da ka samu kasancewa da matarka zaka koma normal. Pills daka sha ne suka haifar maka da hakan. Amma sai ka kiyaye gaba dan bincikenmu ya tabbatar mana daka jima kana amfani da irinsu, hasalima ƙarfin maganin da rashin sauke nauyin da suka saukar maka ne ya haddasa maka sumar nan kayi kuma nauyin farfaɗowa. Ka godema ALLAH ma kuma da baka samu haikema yarinya a wannan yanayin ba tunda naji ance amarya gareka, dan ƙarfin maganin nan zai iya sawa ka mata babbar illa musamman idan ta kasance virgin. Dan ALLAH ku dinga bincike akan abu kafin kuyisa, dan hakan wautace sosai. Musamman idan mukai dubayya da su yaran da ake kai muku basu san komai ba, binsu a hankali akafi buƙatar kuyi tunda al'amarin ba damben gwada ƙwanji bane ba. Kaga gashi nan wajen ceton kanta ta jijji maka ciwo itama ka jimata ciwon ta hanyar marinta da kayi. Hakan ai kaga baida amfani sam a daren farko fa kuma....” Likitan ya ƙarasa maganar cikin zafi-zafi. Shi dai JJ kallonsa kawai yake kansa a wani irin juye. Dan gaba ɗaya yama gagara auna maganar doctor ɗin a muzubin hankali kona fahimta. Shi harma a yaushe yay yunƙurin yin wani abu da Alimah. Ya san dai yasha pills kam tabbas, yana kuma cike da ɗokin yin shagalinsa, amma bai ko ɗau hanyaba. Kai shi bama wannan ba fa, abinda ya faru tsakaninsa da Alimah ɗinne abu mafi girman ɗaga hankali da buƙatar yin tunani, sai kuma yanda yaji labarin na neman canja kansa zuwa wani bigire daban a bakin wannan likitan. Ɗan zabura yay zai sauka a gadon har yana buge likitan. Da mamaki ya ɗago da ga rubutun da yake ya dubesa, ganin yana neman direwa a gadon yay saurin riƙesa da faɗin, “Ya ALLAHU! Lafiya kuwa?”. “Babu ita Doctor, Alimah nake son gani”. A halin da JJ ke ciki da yanda Doctor ya fahimci al'amarin akwai banbanci, dan haka yay murmushi yana ɗan laɓe bakinsa. “To baban soyayya kwantar min da hankalinka nan Please. Indai amaryace yanzu zaka ganta har nan inda kake duk da ma dai zamu sallameka ne muma kaje gareta a yau ɗin nan in sha ALLAHU kaji”. “Doctor plea....” “Shiii!!!” doctor yay saurin katsesa. Daga haka ya juya yana fuskantar ƙofar da faɗin, “Zaku iya shigowa”.........✍️ _😂To JJ dai ALLAH yasa kar a nuna hali anan ma🚴_ https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na huɗu_ https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc ........Dafeeq dai shima ɗaya ne daga cikin ɗaliban makarantar su Khadijah. Yaro ne mai ƙwazo da maida hankali a karatu sai dai baya jin magana. Shekara ɗaya ne tsakaninsa da Khadijah a makarantar, dan shi a yayinda ta shiga ss2 shi kuma sune suka shiga ss3. Yana ɗaya daga cikin waɗanda aka bama prefect, yana kuma cikin masu manyan muƙami. Sun haɗu ne a sanadin sayayyar kayan ƙwaɗayi da aka san ƴan makaranta a lokacin break. Tana tsaye gaban mai awara ita da ƙawarta Aminatu Dafeeq ya iso wajen tare da tawagarsa su huɗu shi na biyar. Shine a gaba suna take masa baya tamkar wani saraki ko malami. Hakan ba sabon abu bane, dan Dafeeq suna ɗaya daga cikin tsagerun ɗalibai, sai dai ƙoƙarinsa yasa malamai basa iya masa komai. Tunda ya shigo makarantar kuma da rashin kunyarsa ya shigo, dan baifi sati ɗaya ba wani prefect ya dakesa akan makara a wajen ya riƙe bulalar ya murɗesa ya amshe shi ya shiga zabga masa. Al'amarin ya bama kowa mamaki, dan kowa yasan dai akwai seniority a school ɗin musamman prefect nada ƙarfin iko sosai akan hukunta na ƙasa da su. Abinda yay yasa sauran prefect ɗin dake wajen rufesa da duka har sai da malamai suka fito aka dakatar da su da ƙyar. An hukuntashi akan wannan laifin tare da bashi suspecsion har na sati biyu, bayan yaje yayo babansa da aka buƙaci gani yazo ya bada haƙuri. Tun daga wannan abun da yay ƴan ss3 suka tsanesa, hakama ss2 suna cike da burin sauke masa iskancin kansa. Adalilin hakan yasha wahala sosai a cikin makarantar shima kuma ya wahal da wanda suke wahal da shi ɗin. Dan babu fashi ka dakesa a cikin makaranta kai kuma a waje zai saka a maka duka ko kuma shi ya maka da kansa. Daga baya ma daya haɗa daba sai yazam tare suke aikin su biyar. Wannan tsagerancin nasu da ƙoƙarin ya sakasu yin ƙaurin suna a school ɗin. Sannan kuma a wajen sayen kayan break basa saya, sai dai su saka yara su loda musu kaya su cinye suƙi biyansu. Idan an kai ƙararsu wajen malamai ana gama musu hukunci aka sakasu biya dole ana fita wajen makaranta suma yaro ko yarinya duka su amshe kuɗinsu. Tun suna ss1 suke halayyar nan har zuwa yanzu, su kansu masu tallan har sun gaji da kai ƙarar tasu idan sunzo sai su zuba musu kawai dan a zauna lafiya. Khadijah bata da yawan hayaniya, ba kuma ta da yawan shiga sabgar mutane. Dan haka ba wani sanin Dafeeq tayi sosai a fuska ba, sai dai takan ji ana labarin rashin jinsu a makarantar. Sai kuma duk sanda za'ai hutu idan an musu taro takan ga fuskar idan zai amshi ƙyauta dan duk tarm kam hakan baya wucesa saboda ƙoƙarinsa. Amma ita dai ALLAH bai taɓa haɗasu face to face ba balle magana ya shiga tsakaninsu sai yau ɗin nan da ya sameta a gaban mai awara ita da Amina. Ta juyo zasu bar wajan shi kuma ya kawo jikinsa duk da kuwa ya ganta sarai kuma ya fahimci ita bata lura da mutum a gabanta ba suka bangaji juna. Ledan hanunta ne ya faɗi, awaran ciki ya watse a ƙasa. Tsabar wulaƙanci Dafeeq yabi takansa ya wuce yana wani busar iska da fesarwa tamkar baiyi komai ba. Khadijah nada haƙuri, amma bata ƙaunar wulaƙanci. Ga shi kuma a yau tana cikin yanayin period sai zuciyarta duk take a ƙuntace kuma a kusa. Ranta a ɓace ta ɗago, sai dai har ya gotata zai wuce hankalinsa kwance. Hakan ya ƙona mata rai, batare datama san mitake ba a ƙufule ta furta, “Kai wane irin wawan daƙiƙin mutum ne mara sanin muhimmanci da kimar ɗan adam balle daraja abinci haka!”. Cak Dafeeq da yaji abin tamkar daga sama ya tsaya. Yayinda wajen yay tsitt a ƙanƙanin lokaci kasancewar a tsawace Khadijah tai maganar. “Kan babbar u.... can”. Ɗaya daga cikin abokan nashi ya faɗa yana wani kallo da ɗaga hannu zai zabgama Khadijah mari. Caraf ta riƙe hannun nasa tare da hantsilashi tana huci duk da ya fita tsayi sai dai shima babu ƙiba kasancewar dukansu yara ne. Jikin Dafeeq da bai juyoba ya faɗa har kansu na gware. Sai lokacin ya juyo a harzuƙe jin ƙarar da Hadiy ya saki sakamakon murguɗewa da ƙafarsa tai dalilin hankaɗawar da Khadijah ta masa. Tarosa Dafeeq yayi ya miƙar, dai-dai Khadijah na ƙoƙarin barin wajen yay wani kalar fisgota baya. Keeeee!! Kake ji hijjab ɗin jikinta ya yage har zuwa ƙasa jikinta da dogon gashinta suka bayyana kasancewar babu ɗan kwali akan nata sai hula. Fisgarta da yay kuma ya haɗo da hular. Taga-taga tai zata faɗi ciki rawar jiki Aminatu ta riƙeta, tana ɗagowa babu wani lissafi ganin hijjab ɗinta ƙasa wanwar jikinta da gashinta a buɗe ido a rufe ta ɗaga hannu ta sauke ma Dafeeq yatsunta biyar a saman fuska. Bai gama dawowa a hayyacinsa ba ta kuma ɗaukesa da mari na biyu hawaye masu zafi na wanke mata fuska. Dan a duniya babu abinda Khadijah ta tsana sama da aga jikinta. Itafa ko'a gida bata zama babu hijjab balle anan cikin makaranta da ko salla bata yarda tayi ba. Shiyyasa da'an tashi bata zama take ɗaukar hanyar gida dan ta samu damar yin sallarta acan. Tsitttt wajen yayi baka jin komai sai sautin kukan Khadijah, kowa ya zubama Dafeeq ido yaga wane mataki zai ɗauka akan wannan mari, wanda bai ragama senior ɗinsa ba taya jenior ɗinsa zatai masa wannan al'amari a zauna lafiya. Ganin yanda Dafeeq yay tsaye ƙiƙam tamkar wani soja ko wanda yay sumar wucin gadi yana kallon Khadijah kawai dan koda ta maresa baiyi ko gezau ba sai idanunsa da sukai matuƙar kaɗawa jazur, gaba ɗaya sauran abokansa 3 sukai kan Khadijahn a harzuƙe matuƙa. Sai dai da sauri ya ɗaga musu hannu alamar karsu taɓata. Basu iya ƙin bin umarninsa, sai dai da mamaki suke kallonsa. Ya wani kalar lumshe idanunsa da buɗesu a lokaci guda kan ƙirjinta da gashin kanta yana taune lips nashi na ƙasa. Sai kuma ya juya yana kallon sauran ɗaliban wajen. Cikin sauri suka shiga fashewa dan mugun tsoronsa ake saboda rashin mutuncinsa. A dai-dai nan ma aka kaɗa ƙararrawar komawa aji...... ★★★★ Daga shi har doctor ɗin ƙofar suka zubama idanu. Sai dai ba kamar yanda yay tsammani bane da tunanin ganin Alimah. Abbansa ne da yayansa. Doctor ya dubesa yana murmushin. Sai kuma ya ɗauke idanun ya maida kan su Abba dake jerama JJ ɗin sannu da jiki. Kai kawai yake iya ɗaga musu, yana mai jin wani iri a ƙasan zuciyarsa. Bayani Doctor yay musu a taƙaice, tare da tabbatar musu zai iya sallamarsu daga yanzu zuwa kowane lokaci. Idan kuma babu damuwa su bashi matarsa, kar suyi dubi da abinda ya faru, wannan ba komai bane akan ma'aurata sabbin aure. Nasu kawai su musu nasiha ne musamman ita yarinyar. Sosai Abba ya gamsu, yayinda JJ kansa ya sake kullewa gaba ɗaya, sai dai kamar an ɗinke masa baki ya gagara cewa komai har Doctor ɗin ya gama bayaninsa ya fice. Zama Abba da yayansa sukai kusa da shi suna sake jera masa sannu, yayinda yayansa ke haɗa masa shayi kamar yanda doctor ɗin ya bada umarni. Bayan ya kammala ya kawo masa tasan asibiti ya wanke bakinsa sannan aka bashi tea ɗin. Ya ɗanyi nisa da shan tea ɗin zuciyarsa duk a birkice da tunani kala-kala Abba ya katsesa da faɗin. “Jazool!”. A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Abban. Kafin ya ɗaga baki da ƙyar ya amsa da “Na'am Abba”. Nisawa Abba yay da cigaba da faɗin, “Jazool sam banji daɗin abinda ka aikata ba. Banda wauta irin taku ta yaran zamani abu kamar cin rabo. Yarinyar nan fa a gidanka take kuma tazo kenan har abada bawai damar daren shekaranjiyan ne da kai ba kawai. Yanzu da iyayenta fitinannu ne kana ganin maganar nan zata zama mai sauƙi ne kamar haka? Duk da kuwa sun riga sun mallaka maka ita. Auren soyayya fa kayi bana ƙiyayya ba balle kace taƙi amince maka zaka haike mata ta ƙarfi. Ka godema ALLAH daya kasance tai hankalin kiran ƴar uwarka ba wani ɗan gidansu ta kira ba ya ganku a wannan halin. Ina mai baka shawara da kazama namiji a gidanka, dan shi namiji mai dattako aka sanshi ba barahaza ba. Idan ka bita a sannu cikin lalama sai ka kai ga inda kake so batare da ita kanta tama san ta mallaka maka kan nata ba. Ban son na sake jin irin haka ta sake faruwa, in ba haka ba ranka zai ɓaci. Yara baku da hankali sam gaba ɗaya kun koma gina aure akan sha'awa kawai soyayyar ciki ƙalilance...” nan dai yay masa tass da faɗa da nasiha. Ya kuma hanashi cewa komai saboda shi Abba suna kallon komai ne a yanayin da suka fahimta kawai. A ta wani ɓangaren kuma shi kansa JJ ɗin bakinsa yay masa nauyin da ya gagara iya cewa komai batare da yasan dalilin hakan ba. Sai ma zaƙuwa da ɗokantuwar son ganin Alimah kawai yake a ransa.... Zuwa bayan la'asar aka sallamesu. Kamar yanda Doctor ya bada shawara gidansa aka wuce da shi. Sun sami mutane uku da suma suka dawo da Alimah babu jimawa dan tunda abin ya faru bayan an kaisu asibiti doctor ya tabbatar da ita bata buƙatar a kwantar da ita can gidansu JJ aka wuce da ita. Ƙannensa ne guda biyu sai sep mom nasu. Tana zaune a falo Alimah a kusa da ita tana mata nasiha, yayinda Rabi'ah da Sadiya ke tsaftace gidan duk da bawani datti yayi ba. A kusan tare JJ da Alimah suka kalli juna, tai saurin rissinar da nata kan cikin yanayin jin kunya da tsoro, shiko ya kasa yin hakan dan har sai da yayansa ya kamasa ya zaunar. Bayan Alimah ta gaida Abba da yayansa shi ta gaida da masa yaya jiki kamar yanda taji Umma ta faɗa cikin jajantawa. Itama da kai kawai ya amsa mata kamar yanda ya amsawa Umma. A haka su Rabi'ah ma suka fito suna masa sannu da yaya jiki. Suma amsa musu yay da kai. Nasiha mai ratsa jiki Abba yay musu su duka, itama Umma ta ɗaura da nata. Sun sallami Alimah ta koma cikin bedroom wajen su Sadiya, suka sake rufuwa akan JJ a matsayinsa na miji babba da ya fita shekaru. Shi dai saurarensu kawai yake dan baima san yaya zai fassara al'amarin ba. Zuciyarsa gaba ɗaya a rufe take ruff, babu wani abu a jikinsa dake aiki a sashen tunani irin na masu hankali. Abinda kawai ya sani yana jinsu yana kuma ganinsu da idanunsa. Rabi'ah Umma ta ƙwalama kira, ta fito aɗan gaggauce tana amsa mata. “Ki faɗama Alimah ta haɗa masa ruwan wanka ko? Dan ya kamata ya ɗan watsa ruwa ko jikinsa zai saki.” da to Rabi'ah ta amsa tana juyawa ciki, kusan mintuna shidda tsakani ta dawo ta sanar da an haɗa. Da taimakon yayansa JJ ya miƙe, yay masa rakkiya har bakin ƙofar sannan ya dawo. Daga haka suka miƙe su duka bayan an sake umartar su Sadiya akan su fito. Sosai Alimah ke hawaye dan bata son su wuce ita dai. Su dukansu sun fahimci tsorone a ranta, dan haka Umma ta sake lallashinta da tabbatar mata in sha ALLAH gobe su Rabi'ahn zasu dawo su yini mata. Kanta a ƙasa ta amsa da ta gode. Har tsakar gida tai musu rakkiya, suka wuce ransu fal tausayinta musamman ma Ummah da Abba da Yaya Mujee. Jiki a saɓule ta koma ciki, sai taji gaba ɗaya ma gidan ya fita mata a rai. Bata bi takan JJ ba ta wuce ɗakinta tana hawaye......✍️ _Ina fatan yau dai Yaya JJ zaisha amarcinsa da amarya Alimah 🥱🥱😆🚴_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na biyar_ https://chat.whatsapp.com/ImF9JpXmBISJCvMBGkTKLc ___________ 📲 *UMMUL~ADNAN DATA SERVICE*📲 We offer you the most affordable and cheapest data🥰 *MTN* 📲500mb ➖ 170 📲1gb➖340 📲2gb➖640 📲3gb➖940 📲4gb➖1250 📲5gb➖1550 📲10gb➖4000 Check balance=*131*4# or *460*260# *GLO* *CORPORATE GIFTING* 📶500mb➖150 📶1gb➖270 📶2gb➖540 📶3gb➖790 📶5gb➖1300 Check balance=*127*0# *AIRTEL* 🆒500mb➖150 🆒1gb➖270 🆒2gb➖530 🆒3gb➖800 🆒5gb➖1270 🆒10gb➖2510 Check balance=*140# *9MOBILE* ☑️500mb➖140 ☑️1gb➖240 ☑️2gb➖480 ☑️3gb➖660 Check balance = *228# All network valid for 30days👌 *PAYMENT* Through this acct 7032785536 ZAINAB SARKI AHMED OPAY CABLE SUBSCRIPTION ARE ALSO AVAILABLE Phone no 07032785536 ________ .......A sanadin wannan abu daya faru mahaifin Khadijah yazo har makarantar tasu, yanda yayma malaman tas akan abinda ya faru na rashin ɗa'a da akaima yarinyarsa amma basu ɗauki mataki ba yasa aka hukunta Dafeeq. Dan shima har sai da mahaifinsa yazo makarantar. Abinda ya bama kowa mamaki shine kai tsaye ya amsa laifinsa, ya kuma bama Khadijah haƙuri. Abune da bai taɓa faruwa ba, dan ko mi zai aikata duk irin hukuncin da za'ayi masa bai taɓa bama koda malamai haƙuri ba saboda shegen girman kansa da rashin ji. An sallamesu komai ya wuce. Tun daga ranar kuma idan suka haɗu sai ta hararesa ta murguɗa masa baki. Shiko baucewa da ita komai sai dai ya ɗauke kansa ko yay dariya kawai. Sabon salon nasa na bama abokansa mamaki, dan akwai randa akai taren masu latti ƙiri-ƙiri ya hana a daki Khadijah. Abun nasu kamar wasa a wani hutu sai ga Dafeeq a gidansu. Da farko nunawa yay baba yazo gaidawa, a dawowa ta biyu kuma ya ƙulle da ƙaninta. Tun yana zuwa ya tsaya iya ƙofar gida har takai baba ya bashi damar dinga shiga cikin gidan ya gaida Umma. Ko kallonsa Khadijah batayi da farko, amma kafin hutun nan ya ƙare sai gashi ta fara sassautawa har tana gaishesa. Sannu a hankali al'amarin nasu ya fara sauyawa har yana koya mata karatu ita da sauran ƙannenta, da farko iyayen Khadijah basu ɗauki al'amarin komai ba, dan daga Dafeeq har Khadijah yarane. Kasancewar Dafeeq ya ɗan samu matsala a harkar karatunsa a baya ya bama Khadijah kusan shekara huɗu, dan ita bazata wuce 16years ba, shiko zai iya kaiwa 20 gashi kuma da tsayi. A haka Dafeeq ya kammala makaranta su Khadijah suka shiga ss3 suma. Yawan zuwan Dafeeq da yanayin da suke kasancewa da Khadijah yasa Umma ta fara fahimtar akwai magana a kansu, dan haka ta faɗama Baba. Yayi matuƙar mamaki da jin batun dan yasan dai su ɗin yarane, dan haka ya zaunar da Khadijah ya mata nasiha da sake tabbatar mata da burinsa akan tayi karatu mai zurfi kuma yasan itama shine babban burinta. Shima Dafeeq ɗin baba ya sameshi da nasiha akan ya dage ya cigaba da karatunsa su ajiye maganar wata soyayya gefe idan ma yana son Khadijah ne ya bari sai nan gaba yanzu su yara ne, amma idan sun kai girma yayi alƙawarin zai aura masa ita. Kamar Dafeeq da Khadijah sunji wannan nasiha fa, sai kuma gashi bayan watanni kamar biyu aka kawoma Baba shaguɓen yafa saka ido akan Khadijah kada yaron nan dake zuwa gidansa ya lalata masu ita. Hankalin Baba ya tashi, sai dai baima Khadijah magana ba ya fara bibiyar al'amarinta batare data sani ba. Ilai kuwa sai ga Baba ya gano inda Khadijah da Dafeeq ke ɓuya yin hira wai. Ranar ya zaneta duka irin wanda bai taɓa kwatanta mata ba, ya kuma takama Dafeeq burki da zuwa gidansa gaba ɗaya. Al'amari kamar ya lafa sai kuma wasa da karatun Khadijah ya ɓullo, dan takai sam bata maida hankali har suna shirin fara jarabawar ssce. Tun Umma na lallashinta da mata nasiha a ɗaki su kaɗai har tadai faɗama Baba. Shi rasama abin faɗa yayi a wannan gaɓar, dan haka ya kira Khadijah ya tambayeta mi take buƙatane? Babu kunya babu tsoro kamar ba Khadijahrsa ba tace ita aure take so. Kuma Dafeeq take so. Kallonta kawai baba ya tsaya yi, sai da yaja wasu mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya da fuskantarta. Cikin lallashi da nuna kulawa yace to yaji zai mata auren, amma ta maida hankali akan jarabawarta da suke shirin farawa. Bayan ta kammala secondary ya mata alƙawarin tana fara jami'a koda wata biyu ne zai mata auren. Amma fa ta sani bada Dafeeq ba. Dan Dafeeq dai a yanzu haka yaƙi karatu, baya kuma sana'ar komai sai yawo da abokai, sannan iyayensa sunce ba aure zasuyi masa ba yanzu. Kuka ta fashe masa dashi tare da rantsewar itafa shi ɗin take so. Kuma idan ba'a aura mata shi ba zata bishi su gudu kamar yanda ya buƙata suyi aurensu acan wani waje. Cike da takaici da gatse Baba yace ga hanya nan ta tafi to. Daga haka ya buga babbar rigarsa ya fice a gidan ransa a ɓace. Maganar Khadijah tamkar a wasa ko ƙuruciya bayan kamar wata biyu aka nemeta aka rasa ita da Dafeeq. Hankalin kowa ya tashi, tako ina aka shiga nemansu amma babu labarinsu. Da ga ƙarshe aka samu saƙon wasiƙa daga garesu suna bama iyayensu haƙuri akan sunje suyi aure, amma in sha ALLAHU watarana zasu dawo garesu.. A take Baba ya yanke jiki ya faɗi, ranar sai a asibiti ya kwana. Yayinda iyayen Dafeeq keta tujara wai Khadijah ta janye musu hankalin yaro da asiri, ya daina jin maganar kowa sai tata da tasu Baba. Maganganu marasa daɗi dan har gida sukazo suka cima Umma mutunci da Baba dake kwance yana fama da kansa... Duk da wannan labari duk ya shiga kunnen Dafeeq da Khadijah basu koma gida ba, sai ma tattarawa sukai suka ƙara gaba. Sunyi aure kamar yanda suka shiryama kansu da taimakon hakimin yankin da sukaje. Dan sun haɗa masa ƙarya da gaskiya ne shi kuma ya amince. Sai dai bayan auren nasu ya basu shawarar komawa gida. Sun yarda da hakan, amma sun nema alfarmar a ɗaga musu ƙafa sai bayan lafawar abubuwa sosai. Wannan dalilin ne yasa ya barsu, tare da basu gida matsakaici, ya kuma zuba musu kaya a ciki masu ƙyau tare da nemawa Dafeeq aikinyi a wani Company. Aikin ba wani aiki bane babba can, dan na sharane acewarsa ya fara kafin a samu mafita, yadai samu abinda zai riƙe matarsa. Ansha amarci na nunama tsara tsakanin Khadijah da Dafeeq. Dan Son juna suke tamkar zasu cinye kansu. Kowa ƙoƙarin ƙyautatama ɗan uwansa yake. Sun manta da gida da iyayyensu gaba ɗaya. Sam Khadijah bata tuna jarabawarta da ta baro a lokacin da ake gab da farawa duk da tsananin son da takema karatu a baya. Idonta ya rufe gaba ɗaya babu wanda take tunawa da gani sai Dafeeq. A haka sukaci watanni huɗu, sai ga ciki. Sosai Dafeeq ya nuna farin cikinsa da samuwar wannan ciki, ya shiga tattalinta kamar ƙwai, sai dai bayan kamar sati biyar sai kuma tayi ɓari. Tasha kuka sosai dan ta mugun ƙwallafa rai a cikin nan, haka shima Dafeeq ya shiga damuwa, daga baya dai suka lallashi kansu suka cigaba da rayuwarsu ta faranta ran juna. Ba'a ƙulla wata biyu ba sai ga wani cikin dai, nan ma sunta murna, sai dai shima bai kai labari ba ya zube. Nan ma kuka suka dingayi rurus har sai da matar hakimi ta dinga musu nasiha sannan suka haƙura. Bayan shi Khadijah ta sake samun ciki sau biyu yana zubewa, zuwa lokacin kuma sun ƙulla shekara kusan biyu da barin gida. Tun daga ciki na huɗu daya ɓare bata sake samun ciki ba, tun suna damuwa har suka dangana, a yanzu haka kuma shekara ta uku suke. Khadijah nada shekara goma sha tara, Dafeeq nada Ashirin da uku cikin da huɗu. Basu da wata matsala sai ɗan faɗan masoya irin na yau da gobe, basa jimawa kuma suke shiryawa saboda ita Khadijah nada sauƙin kai, koda Dafeeq ya ɗauki zafi da ita takan nuna masa itace a ƙasansa ta bashi haƙuri tana kuka da roƙonsa da magiya. Har yanzu Dafeeq na aiki a companyn nan, da ga shi har ita basa zancen komawarsu makaranta, shiko bayan shara a kamfani baya sana'ar komai, dubu sha takwas ɗin da ake biyansa duk wata acewarsa ai ya ishesu rayuwa. Khadijah bata taɓa damuwa da haka ba, dan tana son mijinta, shi kaɗai ta sani a sabon garinsu, sai gidan baba hakimi da takan ɗan je lokaci-lokaci ta gaishesu. Shima kuma bayan ita da gidan baba hakimin babu wanda tasan ya sani sai abokan aikinsa na Company, amma abin mamaki yau sai gashi da key na gida da mota yana faman farin ciki da iƙirarin wai nashi ne. A ina ya samu? Waye ya bashi? A dalilin mi aka bashi?. Waɗan nan tambayoyin take zumuɗi da burin yazo ya amsa mata ko zata samu nutsuwa a zuciyarta itakam.... (To Khadijah muma dai zamu so san jin ina Dafeeq ya samo key na gida da mota haka. Amma bari mu leƙo JJ na amarya Alimah mu dawo dai🚴🚴🚴). ★★★..... Cikin ƙarfin hali JJ yay wanka ya shirya a ƙananun kaya marasa nauyi. Duk tunaninsa su Baba na falo ne basu wuce ba, dan haka ya fito cike da ƙwarin gwiwa. Amma sai ya samu falon wayam. Zuru yay yana kallon kujerun, sai kuma ya shiga laluben aljihunsa cikin tsumar jiki alamar neman waya. Babu komai, da alama ya barsu a ɗaki ne ko. Ya ayyana a zuciyarsa yana komawa da baya zuwa ɗakin. Babu wayoyin nasa duka biyu anan ma, dan haka abin ya bashi mamaki kuma. Fitowa yay da ɗan hanzari, sai hakan yay dai-dai da fitowar Alimah da ga nata bedroom ɗin. Suna haɗa ido tai azamar rissinar da kanta cikin jin kunya, sai kuma ta fara magana ƙasa-ƙasa da badan yana kusa da ita ba ba lallai yaji ba ma. “Ai ban san ka fito ba. Ga abinci to dan ka samu kasha magani kamar yanda Yaya ya faɗa”. “Sun tafi ne?”. Ya faɗa kamar cikin rawar murya. Kanta ta jinjina masa batare data ɗago ba ta ce, “Eh, ai kana shiga ciki suka wuce su kuma. Shine ma Yaya Mujee yace daka fito kaci abinci kasha maganinka”. Cikin kullewar kai da rashin makamar riƙewa ya jinjina mata kai kawai. Ga wani irin matsanancin tsoro na ratsa masa zuciya. Amma dai ya dake a zahiri dan yana son tabbatar da abinda ya faru a daren jiya. Murya a sanyaye ya ce, “To muje ki bani”. Babu musu tai gaba ya biyota a baya har zuwa tsakkiyar falon. A ƙasan carpet ya zauna kamar yanda yaga tayi itama a gaban kwanikan abincin. Ya zuba mata idanu yana kallon yanda take zuba abinci, sai ƙafafunta da yake kallo suma lokaci-lokaci. Zuwa can kamar wanda aka zaburar ya ce, “Alimah na tambayeki dan ALLAH?”. Duk da tayi mamakin jin ya kira sunanta kai tsaye sai ta jinjina masa kanta batare data bar abinda take ba ko ta ɗago. Shima bai damu da rashin ɗagowar tata ba ya cigaba da faɗin, “Daga bayan dawowata raka abokaina jiya zuwa sanda kika kira aka kaini asibiti miya faru?”. Cikin ɗan jin kamar mamakinsa ta ɗago ta kallesa. Sai kuma ta sake maida kanta da sauri ƙasa. Kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa a hankali. “Bayan ka dawo ka sake samuna a falo, shine kace muje ciki muyi salla, ka ajiyeni saman gado kace na jiraka anan kayi alwala, shine ka shiga bayi ni kuma barci ya ɗaukeni. Da'alama dai banyi nisa ba na farka a dalilin jin ihu da nayi, na tashi a firgice sai naji motsinka a bayi, baifi mintina biyu ba tsakani ka fito, shine kace na koma falo na jiraka kana zuwa. Ban jima a falon ba ka fito ka sake samuna, shine ka sake cewa na tashi muje sallar. Kaine ka kaini har ƙofar bayi dan nayi alwala, bayan na kammala na fito na sameka a ƙasa ka faɗi, na nufeka ina ƙwalama kira ka tashi ka maran, sai kuma ka sake sumewa, ni kuma kawai na fara haɓo. Nata kuka ina zuba maka ruwa baka farka ba shine nai kiran Rabi'ah lokacin kusan ƙarfe huɗu na dare, shine sai ita kuma ta gayama Yaya Mujee yazo muka tafi asibiti da asuba.” Tunda ta fara maganar jikin JJ ke rawa. Dan gaba ɗaya muryarta ta koma ta wadda bazai taɓa mantawa ba a rayuwarsa. Duk da kuwa bai kamata ace itace kaɗai zata zauna masa a zuciya fiye da sauran na baya kafin ita ɗin da bayanta ba. Jin shiru yasa Alimah ɗagowa a hankali. “Yayana wlhy ni fa duk a tsorace nake”. Wani irin yankawa ƙirjinsa yay na tsantsar firgita. Tuni ya zabura yay tsalle gefe cikin kaɗuwa. “Anoosh!” ya faɗa cikin rawar baki jikinsa na ƙara ɗaukar rawa.. “Anoosh kuma?”. Cewar Alimah tana masa kallon tsoro. Zaraf ya miƙe har yana taka plate data zuba masa abinci. Baibi takansa ba ya kwasa da gudu zuwa ƙofa, sai dai yana isa ruff ta rufe kanta da kanta. Baya yaja da wani irin rawar jiki yana zaro idanunsa gaba ɗaya waje. Sai kuma ya waiga bayansa da sauri. Alimah na tsaye tana kallonsa, da sauri ya juyo gabansa, nan kuma Anoosh tsaye jikin ƙofa itama tana kallonsa. Rigifff ya zube ƙasa kamar wani tsohon amalen raƙumi daya gama morar duniya......✍️ (😂 Uncle JJ namu🚴). *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na shida_ 📲 *UMMUL~ADNAN DATA SERVICE*📲 We offer you the most affordable and cheapest data🥰 *MTN* 📲500mb ➖ 170 📲1gb➖340 📲2gb➖640 📲3gb➖940 📲4gb➖1250 📲5gb➖1550 📲10gb➖4000 Check balance=*131*4# or *460*260# *GLO* *CORPORATE GIFTING* 📶500mb➖150 📶1gb➖270 📶2gb➖540 📶3gb➖790 📶5gb➖1300 Check balance=*127*0# *AIRTEL* 🆒500mb➖150 🆒1gb➖270 🆒2gb➖530 🆒3gb➖800 🆒5gb➖1270 🆒10gb➖2510 Check balance=*140# *9MOBILE* ☑️500mb➖140 ☑️1gb➖240 ☑️2gb➖480 ☑️3gb➖660 Check balance = *228# All network valid for 30days👌 *PAYMENT* Through this acct 7032785536 ZAINAB SARKI AHMED OPAY CABLE SUBSCRIPTION ARE ALSO AVAILABLE Phone no 07032785536 ____________ .......Kaff-kaff jikin nashi ke cigaba da rawa tamkar mai jin sanyi. Yayinda lips nashi ke nasu karkarwar suma. Sai ya kalli ƙofa ya kalli tsakkiyar falon, yanayi yana jan jikinsa baya da rarrafe. Hawaye tuni sun wanke masa fuska. Bammm ya dangane da kujerar 2sitter dake bayansa. Duk da azabar zafin data ratsa masa gwiwar hannu bai damuba. Sai cigaba da raba kallo yake tsakanin Alimah da Anoosh da har yanzu ke tsaye a inda suke suna kallonsa kawai. A karan farko tamkar wanda aka matsa ya fara karanta ayatulkursiyyu. Wata irin mahaukaciyar dariya data sake wargaza ƙwaƙwalwar JJ suka kwashe da ita su duka biyun. Sai kuma suka shiga takowa da wani irin salo a tare har zuwa gabansa. Zama sukai gefe da gefensa suka sakashi a tsakkiya. “JJ angon Alimah!”. “Ko kuma na Anoosh ba”. Dariya suka kwashe da shi a tare har ɗakin na wani irin jijjiga suka kuma tafa. Tsuuuu kakejin JJ na sakin gudawa a wandonsa. Fitsari kam dama tuni shi ya fara yin gaba. Kallon wandon nasa sukai a tare suka sake kwashewa da dariya. Sai da sukai mai isarsu Anoosh ta kalli Alimah. “Amarya! Ya kamata ki kawoma angonki abinci yunwa yake ji”. “Hakane fa”. Alimah ta faɗa tana juyawa ga kulolin abincin. Daga inda take ta miƙa hannunta sai gashi yayi dogo ziriri har inda kayan abincin suke. Yatsanta manuniya ta dangwala a samansu tayo baya da hannunta sai gasu sun biyota ta dire a gaban JJ da ya sake diriricewa. Ƙular data buɗe a ɗazun yaga shinkafa a yanzu data buɗe sai ga kunamu baƙaƙe kirin na motsi da ransu cike da kular. Kula ta biyu mai ɗauke da miya kam wani irin abune kore shar baima san yanda zai fassarashi ba. Kofi mai ɗauke da zoɓo kuwa ya koma jini. A yanzu Anoosh ce ta zuba kunamun a plate, tare da koren abunnan, Alimah kuma tasa jini a kofi. Jikinsa suka sake matsowa gab suna wani irin mugun murmushi. “Haaah!”. Cewar Anoosh tana ɗebo kunamun nan da wani irin zabgegen cokali zuwa bakin JJ. Kansa ya shiga jujjuyawa hawaye na zubo masa. Tsawa mai firgitarwa Alimah ta daka masa, tuni ya wangale bakin yana fashewa da kuka. Anoosh ta zuba masa kunamun a bakinsa. Cikin sauri ya fara taunawa yana wani kalar ɓarkewa da kukan azaba dan suma kunamun kamar jira suke ana zubasu suka fara ɗalla masa harbi a bakin. Cike da shaƙiyanci Alimah ta kai hannunta saman kansa tana shafawa. “Yauwa My D maza kaci mana kasha magani, ko kanaso Yaya Mujee ya ɗauka banji maganarsa ba. Haba ɗan sumilmilin mijina ƙyaƙyƙyawa tauraron ƴammata moouuch!!!”. Takai masa wani irin kiss mai shegen ƙara a gefen kumatu tare da ɗaura masa kofin nan mai ɗauke da jini cikin baki. Wata iriyar gigitacciyar ƙara ya saki na azaba. A take ya fara zazzago harshe waje zufa na wanke masa jiki. Sai kawai yay baya zai sume musu.. Saukar ruwa mai masifar sanyi a jikinsa ta sakashi buɗe idanunsa a hankali. Zumbur ya miƙe yana ware idanunsa, sai kuma ya ƙwalla ƙara da faɗin, “Na shiga uku na lalace ni Jazool. Dan ALLAH dan ALLAH azo a taimaka min. Wayyo Baba. Na roƙeku ku faɗa min ku su wanene? Dan ALLAH Alimah ina kika san Anoosh, ta mutu fa ta mutu, kice min ba ita bace wannan, zaku haukatani wlhy na haukace kodai mafarki nake.....” “Ai baba bazai taɓa jinka ba anan. Bama shi ba ko maƙwaftan da ke katanga ɗaya da kai bazasu taɓa jinka ba JJ. Ka ɗauka nan ɗin lahirarka ce, kasan kuwa ai duk wanda ya tafi lahira ba'a sake jin labarinsa kuma. Anoosh kuwa ashe baka manta da ita ba hhhhhh” Ƙatuwar magen dake a saman kujera zaune baƙa ƙirin da jajayen idanunta tamkar wuta ta faɗa cikin muryar Alimah. Gaba ɗaya ƙarfinsa ya gama ƙare wa. Ga harshensa dake masa wata irin azaba dama bakinsa gaba ɗaya. Mugun ƙanƙame jikinsa dake karkarwa yake waje guda ko kaɗan baya fatan ƙadangarun dake yawo cike da falon su taɓashi. Dan a rayuwa JJ na matuƙar tsoron ƙadangare da mage. Suko sai su taho kamar zasu taɓashi, sai kuma su zagayesa suna kaɗa kai. Gasu wasu irin tuma-tuma babu ko ƙyan kallo. “Dan ALLAH ku kasheni kawai na huta. Ku kasheni zaifi min sauƙi da wannan azabar da kuke min”. “Hhhh mutuwa kuma. Ai idan ka mutu a yanzu JJ kaci riba kenan. Dan koba komai ka kuɓuta da ga tari-tarin buhunan azaba dake zaman jiranka. Yanzu lokacin ɗaukar darasin rayuwane bana mutuwa ba.” sai tai wani irin kuka na maguna da ya sashi fashewa da kuka. A take ƙadangarun nan suma suka shiga rige-rigen nufar JJ. Ihu yake sosai yana ƙanƙame jikinsa. Suko suka shiga hayesa yuuuuu kamar an kori tururuwa da ga rami. Tsaff suka yanyamesa yanda kiyashi ke yanyame abu mai maiƙo. Wasu har cikin wandonsa da rigarsa. Harsunansu suka shiga zarowa suka fara lasheshi. Yayinda wasu ke ƙoƙarin shiga masa cikin bakin daya wage yana ihu iyakar ƙarfinsa. Miƙewa yay ya shiga zagaye falon yana tsalle-tsalle da ihu da ƙoƙarin kakkaɓesu a jikinsa. Da ƙayar ya iya kama rigarsa ya saɓule ya watsar ƙasa. Wandon ma ya saɓulesa. Cigaba yay da dire-dirensa yana kaɓar dana jikinsa. Sai da ya gama galabaita da jigata ƙarfinsa ya ƙare tasss ya zube ƙasa yaraff sannan magen nan tai kuka ƙadangarun suka ɓace ɓat. Gaba ɗaya jikinsa raɗaɗi yake masa na bala'i. Dan duk sun karceshi da jikinsu da farcinansu. Da ƙyar yake numfashi idanunsa nayin kamar zasu rufe sai dai sun gagara rufuwar. Sai buɗesu yake da rufewa kamar mai shirin suma. Ji yay ana wani kalar siɗeshi tun daga yatsan ƙafarsa. Yunƙurin zabura yayi sai hakan ya gagara. Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da sukai masa masifar nauyi da ƙyau kan abinda ke suɗesan. Wata irin mummunar hallita ce da tunda uwarsa ta haifesa bai taɓa gani ba duniya. Jikinta tamkar jan nama, kai irin na jaki, fuskar mutane da ƙahuna irin na shanaye. Tayi wani kalar tsaho mara misali da daɗin kwatamtawa. Idan ta lashesa ta lasa ta lasa saita fesa masa wani irin ruwa a bakinta mai azaba da raɗaɗi aka ciwukan nashi kamar ruwan attaruhu. Azaba ta hana JJ ko kuka. Jikinsa kam ya gagara koda motsawa. Sai hawaye da ke rige-rigen sakko masa a idanunsa. Zuciyarsa na addu'a da zuwan mala'ikan mutuwa ko hakan zai zama sauƙi a gareshi. Ji yake inama uwarsa bata haifeshi a wannan duniyar ba. Inama ya mutu kafin ya girma..... (JJ na buƙatar malamai a gidansa🚴🚴🚴🤣) ★★★★.... “Dan ALLAH ka taimakeni ka faɗamin yanda akai Husby. Wlhy gaba ɗaya zuciyata ta kasa samun nutsuwa, a tsorace nake, a firgice nake.” Sai da ya haɗiye laumar shinkafa da waken da ya zuba a bakinsa sannan ya saki ƴar dariya idonsa a kanta. Cikin nuna alamar rashin damuwa ya ce, “Tsoro kuma Dijoh, minene abin tsoro ko firgita anan. Gida fa nace miki an bamu halak malak da motar hawa ga kuma aiki da za'a dinga biyana albashi mai tsoka. Ai nakega abin muyi farin ciki ne mara misali”. “Dafeeq wake garemu a garin nan dazai mana duk wannan? Sannan karka manta iyakar karatunka secondary ne kawai balle muce ko girman takardunka zai baka wannan nasarar. Dafeeq ka faɗa min gaskiya mana!”. Yanda ta ƙare maganar kamar a tsawace ya sashi tsayawa cak da ga yunƙurin kai abincin da ya ɗibo bakinsa ya kalleta. Spoon ɗin ya ajiye a hankali yana mai harɗe hannayensa a ƙirji ya cigaba da kallonta. “Khadijah!” ya kirayi sunanta a hankali idanunsa na sake tsatstsareta. Nata idanun ta rissinar ƙasa, sai kuma ta amsa shi a hankali. “Ihu fa kike min kamar?”. “Kayi haƙuri. Wlhy hankalina ne a tashe. Ina jin tsoro Dafeeq matuƙar tsoro. Karka manta nabar komaina da kowa saboda kai tsahon shekara uku batare da nasan yaya suka kasance ba. Taya kake tunanin bazan shiga ruɗani ba a lokacin da naga sabon abu a wajenka tunda nasan mun bar komai namu ne a yanzu kuma bamu da komai sai kammu.” “Humm hakane, na fahimce ki. Sai dai ki sani barin komai da mukayi bashi ke nufin bazamu samu komai ba a gaba. Itafa duniyar nan da kike gani Khadijah tamkar tsanin hawa gini take. A lokacin da kika bar step 1 zaki ci karo da step 2 ne har zuwa ƙarshe kafin ki kai ƙarshen ginin da zai kaiki rufin soron. Naji bamu da wani karatu mai zurfi da zai iya bani aiki mai girma haka, amma kada ki manta mutanen kirki basa ƙarewa, sannan nasan abinda nakeyi fa ni ba shahsha bane.....” “Miya kawo zancen shashanci anan kuma. Indai maganata ce nikan ta ɓata maka rai ALLAH ya baka haƙuri. Gida da mota kuma bazan sake magana a kansu ba ALLAH ya sanya alkairi. Ya kuma sa matakin nasararmune su ɗin”. A ɗan gatsine ya ce, “Amin”. Da ga haka ya ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin abincinsa fuskarsa a ɗaure, bai kuma sake kallonta ba duk da ita yana jin idanunta a kansa alamar shi take kallo. Tsaff ya cinye abincin dan yana cin abinci sosai dama shikam. Batare da ya sake mata magana ba ya miƙe ya haye doguwar kujera ya kwanta ya lumshe idanunsa. Nata idanun kawai ta zuba masa zuciyarta na rawa sosai.... ________★ “Wai mi kike shirin yi da wannan yaron da kika danƙarama wannan ƙyautar haka? Kainaat!. Ni gaba ɗaya kin birkita min lissafi wlhy”. Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar da zata iya kaiwa shekaru talatin da huɗu ta saki. Sai kuma tai wani irin juya lafiyayyar kujerar office ɗin nata da salo irin na isa da ƙasaita tana kai bayanta kwance da lumshe idanu. Tsahon mintuna biyu kamar bazatace komai ba sai kuma ta buɗe idanunta a hankali akan wadda tai mata tambayar. Murmushi ta sake saki da motsa lips ɗinta dake ta shining na jambaki maroon ta ce, “Nadwa!”. “Na'am”. Nadwa ta amsa mata idanunta ƙyar a kanta. “Auransa zanyi”. Ta faɗa kanta tsaye babu shakku ko nuna damuwa balle kwana-kwana a zancen nata. A zabure Nadwa ta ce, “Aure!! Fa Kainaat? Da wannan abun dana tabbatar kin girma da kusan shekara goma? _Don_ ma da kuke shekarunku dai-dai da shi an miki sutu balle wannan jaririn. To ke da baki gama idda ba ma miya kawo miki wannan tunanin haka?”. Murmushi Kainaat ta saki tana wani limshe idanunta da sake buɗesu cike da yanga da ƙasaita. “Nadwa kenan, ai ƙarancin shekarun nasa ne suka ja hankalina da yin hakan garesa. Dan zan samu damar tafi da shirina yanda nake so. Rashin gama iddata kuwa ba matsala bace tunda ba yau nace a ɗauran aure da shi ba. Ina yin sharar fage ne kawai yanzu dan so nake ina gama idda a washe gari a ɗaura min aure da shi”. “Hummm wannan wane irin tunani ne yazo miki na rashin mafaɗi Kainaat? Kamarki matar riƙaƙƙen attajirin matashi ɗan ƙwalisa irin _Don Abaan_ ki rasa a inda zaki ƙare sai auren wannan gajan yaron da ko shekarun balaga bai gama cikawa ba. Anya duniya bazata miki dariya ba da kallon kinyi faɗuwar baƙar tasa kuwa? Ai shi kanshi Abaan zai sake jin izza da yarda ya fi ƙarfin naki kamar yanda yay iƙirari. Uwar tashi da ƙanwarsa da suka zama sanadin rabakun kuma sunci riba.” Murmushi Kainaat ta saki saki mai faɗi har ƙyawawan farare haƙoranta dake jere reras na bayyana. Idanu ta zubama aminiyar tata cike da ƙasaita. “Nadwa kenan, na fahimci har yanzu baki gama haddace ilimi akan halayena ba kenan. Ban so nace miki komai ba a wannan gaɓar amma ya kamata nace mikin domin ki tabbatar da ni Kainaat ba shasha bace. A tunaninki zan iya haƙuri da 1-0 a fagen wasa ne? Ai in har ba'ai 2-0 ba sai dai ayi draw wlhy, ko kuma a tashi babu ko ɗaya zai fi sauƙi ga abokin karawa. Bari na fito miki a mutum, saki ukun da Abaan yay min zan gyara na sake komawa gidansa dan aure ni da shi yanzu ne zai fara. Wlhy wlhy kinji na rantse, sai na raba Abaan da uwarsa da wannan shegiyar ƙanwar tasa mai kama da aljanu har abada. Sai na sakashi ya wulaƙantasu fiye da yanda suka sa ya wulaƙantani. Sai na shafe babinsu a zuciyarsa fiye da yanda ruwa ke shafe garin da aka gina akan hanyar wucewarsa. Zan ɗanɗana musu azaba sannan na wawashe kaf abinda ya mallaka a duniya ta yanda almajirin saman titi sai ya fisa kima da darajar kallo. Zan tabbatar musu ni Kainaat annoba ce a rayuwarsu. Talauci ga talaka kuma ba tambari bane adone” “Kin daina son Abaan ke nan?”. Wata siririyar dariya ta saki mai faɗin gaske. Kafin ta furta, “Bazan taɓa daina son Abaan ba har ranar mutuwata, sai dai kuma hakan bazai hana ni ɗan ɗana masa hukuncin laifinsa ba da na uwarsa da ƙanwarsa dan sabo da kaza a wajena baya hana na saka mata wuƙa a maƙoshi na yanka banza nai farfesunta na cinye”. “Humm amma kin san shi wannan yaron da kike son aure yana da mata? Sannan ba ɗan garin nan bane zuwa sukai nan aka ɗaura musu aure a gidan hakimi saboda mugun son da sukema juna shi da matar tasa”. “Wannan dalilinne yasa na zaɓesa ai. Batun matarsa kuwa idan ta kwantar da hankalinta ƙaruwarta ce. Dan bani da wata matsala da ita sai idan ta shiga gonata ne fa tabbas bazan barta ba koda ace zaman sati ɗaya nayi niyyar yi da mijin nata kuwa. Soyayya da kike magana kuma ni ban yarda akwaita ba. Dan naga abubuwa masu yawa a cikin idanun wannan yaron na hatsabibanci. Inda ace sonta yake da gaskiya bazai rabota da iyayenta ya kawota nan ya aura ba. Da sonta yake bazai dinga zubar mata da ciki ba a duk sanda ta samu....” “What! Zubar mata da ciki fa kika ce? Ke ko ina kika san duk wannan Kainaat?”. Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tare da maida bayanta jikin kujerar ta wani kwanta........✍️ _(Tofa wata sabuwa. Khadijah da Dafeeq laila da majnoon yaya dai?🚴🚴)._ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na bakwai_ INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.🥰🥰🥰 KAMA DAGA *FLYER *3D MOCKUP LOGO *2D MOCKUP LOGO *NORMAL LOGO *IMAGE LOGO *BANA *STICKERS *ADVERT VIDEO *PROFESSIONAL INVITATION *INVITATIONS CARD *BIRTHDAY VIDEOS *POSTER *CERTIFICATE.AND MORE...... CONTACT ME ON 👇 09035390383 ____________ .......“Please Kainat yaya kika san duk wannan wai?”. “Humm Nadwa kenan. Na faɗa miki Kainaat ba shashasha bace ba ai, kin san dai bazan jashi jikina ban san wanene shi ba. Inama da fiye da wannan game da shi, sai dai lokaci ne zai sa ki san sauran gaba ɗaya ba yanzu ba”. Idanu kawai Nadwa ta zuba mata cike da mamaki da tsoro. Maganar gaskiya bata son ƙawar tata tace zata shiga tsakanin waɗan nan ma'auratan dake tsaka da cin ƙuruciyar soyayyarsu. Amma ta santa tasan halinta, in har tace tana son abu sai ta cimma burinta a kansa, dan ita shaidace ko akan Don Abaan da yanda ya fara sonta har sukai aure shirine babba... ★★★..... “Ina ganin zuwa jibi zamu koma sabon gidan can dan mu samu albarkacin juma'a”. Da wani irin razana Khadijah ta jiyo tana kallon Dafeeq da ke magana a dake hannunsa riƙe da rigarta data miƙa masa zai shanya a igiya. Babu alamar wasa a kan fuskarsa ga shi ya wani tsareta da idanu. Nata idanun ta rissinar ƙasa tana ƙoƙarin saita rawar da jikinta ya fara. Sai kuma ta shiga jinjina masa kanta dan in har tai magana sai hawayen da take riƙewa sun zubo mata. “Miye wani ɗaga kai baki da bakin magana ne wai? Khadijah nikam wlhy na gagara gane miki gaba ɗaya. Da ace wani kemin wannan sabon halin naki sai na ɗauka baƙin cikine ko hassada. Gaba ɗaya kin hana kanki zama lafiya. Ki duba fa jiya na shigo da waya gidan nan amma koda na nuna miki baki ko taɓata ba a tsatstsaye kika wani ce ALLAH ya sanya alkairi kika kwanta...” Duk yanda taso riƙe kukan ta gagara yin haka a wannan gaɓar saboda yanda yake mata magana a zafafe kamar ba Dafeeq ɗinta ba. Miƙewa tai da sauri daga gaban kayansu da sike wankewar ta nufi ɗaki da gudu hannunta toshe da bakinta. A zafafe shima Dafeeq ya miƙe, tana shiga falon yana shigowa shima. Wani kalar fisgota yay baya tai taga-taga zata faɗi ya hankaɗata saman kujera. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa sun gama kaɗewa, cikin nunata da yatsa tamkar zai mareta ya ce, “K! Wai mi kike nufi dani ne? Dan Kinga ina lallaɓaki kike ganin kin samu hanyar wulaƙantani da jana a ƙasa. Ubanmi na miki ba dai-daiba anan?”. Kuka sosai Khadijah ta sake fashewa da shi, sai kuma ta kai hannu ta hankaɗashi baya iya ƙarfinta tana ƙoƙarin miƙewa. Taga-taga yay zai faɗi ƙasa ALLAH ya taimakesa ya dafe kujera. “Taauuu!!”. Kake jin wani lafiyayyen mari a fuskarta. A gigice ta dafe kuncinta tare da fashewa da wani sabon kukan. “Dafeeq ni ka mara?!”. “An mareki ko zaki rama? Ke har kin isa ki dinga jana a ƙasa kamar wani yaronki! Har kina da ƙarfin min wannan abun. Ko kuma dole sai nayi abinda kike so saboda haihuwata kikayi ƴar marasa tarbiyya”. “Dafeeq nice ƴar marasa tarbiyyar?!”. “Kina da ita ne. Ko ƴa mai tarbiyya ce zata bar uwarta da ubanta ta biyo namiji wata uwa duniya. K! Nifa na fiki iya iskanci. Har ni zaki dingama baƙin cikin cigaban rayuwata saboda ke butulu ce. To bari kiji ki kama kanki kafin na sassaɓa miki kamanni a gidan nan. Dan wlhy kaɗan da ga aikina ne na haɗa miki jini da majina wawuya kawai...” fuuu ya fice kamar zai tashi sama. Ragwaf Khadijah ta zube ƙasa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.. Tunda ta baro gidansu ta biyo Dafeeq yau itace rana ta farko datai mahaukacin kuka na tashin hankali da har ya saka mata masifaffen ciwon kai tare da jin wani abu kamar nadama nasan ɗarsuwa a ranta. Dan ko daren farkonsu tayi kukan azabar da taci a hannunsa amma baiko kai kwatankwacin wannan ba. Ita yau Dafeeq kema gorin bijirema iyayenta ta biyosa nan?, ita Dafeeq ya ɗaga hannu ya mara. Mari fa, mari mai suna mari da har take iya jin sayin yatsunsa biyar akan ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta. jama'a Dafeeq fa, Dafeeq ɗinta data zaɓa akan iyayenta da karatunta. Dafeeq data yarda ta bar komai ta koma mara komai ta ɗaukesa. ya arrahaman wannan wace irin rana ce haka da bata taɓa lissafawa a ciki lissafin rayuwarta ba. ya ALLAH kasa mafarki takeyi ba a zahiri bane ba. Ta sake fashewa da sabon kuka mai tsananin ƙona zuciya..... (Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye🤦🥲 dan zancen malam bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan). ★★★...... Iya jigata da galabaita JJ yayi a wannan dare zuwa safiya. Dan da salo-salo su Alimah suka dinga firgitashi. Gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa tamkar wani sabon kamu a hauka. Babu abinda yake iya ganewa tsakanin rayuwa da numfashi. Rana da duhun dare. Duniya da lahira, fari da baƙi. Abinda kawai ya sani a garesa komai ya gama ƙarewa kawai. Yayi masifar zama zuru-zuru cikin ƙanƙanin lokaci. Ba shi kaɗai ba hatta gidan kansa ya gama fita a hayyacinsa tamkar ba sabo ba, wanda aka ƙawata da kayan alatu. Dukan gate da akeyi da ɗan ƙarfi ya sashi buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi. Wani irin zafi da haske suka ratsa idanunsa da jikinsa a lokaci ɗaya. Tamkar wanda aka bulbulama wani irin ƙarfi ya miƙe zubur. Waige-waige ya fara, tabbas a tsakar gidansa yake kusa da gate gab. Idanu ya sake warewa na tabbatarwa. Farin ciki ya sake ratsashi ganin fa da gaske ƙofar gate ɗin ce dai. Ihu ya kurma na tsabagen jin daɗi mara misali, batare da tunanin komai ba ya miƙe a 360 zuwa jikin gate. Ƙofar ya shiga ƙoƙarin buɗewa yana waigen bayansa tamkar mai tsoron a biyoshi, yanda yake karkarwa da ƙyar ya iya buɗe ƙofa. Ko kallo bai yima wanda ke tsaye gaban gate ɗin ba alamar suke knocking ya wani kwasa a bala'in guje ji kake fiyyy-fuyyyy yana dukan iska, sai ya tafi gaba zai faɗi sai ya damƙi ƙasa ya miƙe yana waigen bayansa.... Tuni yara da ke wasa a tsakkiyar layin suka fara kwasa a guje suma suna ihu dan ganin ƙatoton mutum tsirara haihuwar uwarsa na gudu jikinsa yay wani irin butsaaa da ƙuraje ƙanana tamkar jikin kada. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ta ruɗe, yayinda JJ ke falfala gudun ceton rai da iyakar ƙarfinsa. A haka ya kai har titi, bai damu da tare abin hawaba ya ɗauki titin da ƙafa. Sake ruɗewa mutane sukai ana kiran mahaukaci-mahaukaci. A tare a tare. Sai dai ina babu mai tarewar sai ma darewa da ake ana bashi hanya a guje. Duk da wahala da jigatar da yay gudunsa yake sosai batare da nisan hanya da yanda mutane ke ƴar tsere akan ganinsa ya damesa ba. Sai dai duk mai hankalin daya gansa yasan wannan gudun bana lafiya bane, sannan ba a cikin hayyacinsa yake yinsa ba dan a haka ya isa har gidansu. A anguwar tasu ma tunda ya shigo ta rikice da iface-ifacen yara da mata da matasa. Dole akai dafifi wajen masa tara-tara da ƙyar aka iya kamashi. Ƴan gidansu hankalinsu yay masifar tashi, wasu ma kuka suke dan tun fitowarsa gida su Rabi'ah dake knocking gate yazo ya wuce su suna kuka sukai kiran iyayensu suka sanar da su. Tuni wasu sun nufo gidan nashi, sai dai a hanya suka gamu da shi, dole suka juya gida dan ganin komi zasuyi bazasu taɓa samun kanshi ba, ALLAH ma ya taimakesu hanyar gida ya dosa ba wani waje daban ba..... (🤦 Uncle JJ badai kuma ka haukace ba😩😩😫). ...★...★...★.... Duk yanda ya fito da ga gida da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya yaji zuciyarsa tai masa sanyi a dalilin shigowar kiranta. Cike da girmamawa ya ɗaga tare da kai sabuwar galleliyar wayar tasa iphone 14 data bashi shekaran jiyannan saman kunne yana ɗan murmushi. Sallamarsa kawai ta amsa da faɗin “Kana ina ne babban mutum”. Wani irin murmushi ya saki mai faɗi, dan yana matuƙar jin daɗin sunan nan da take kiransa da shi. Cike da girmamawa ya bata amsa da “Ina gida ranki ya daɗe”.. “A to bara na haƙura wannan lokacin uwargida ne ran gida ai. A gaidamin ita sai da saf......” Cikin sauri ya katseta da faɗin, “A haba hajiya, ai ko'a gidan giya akwai babba. Dan ALLAH kada ki katse ki faɗa min komi kike buƙata zan miki shi yanzun nan”. “A'a ai ba'ayi haka ba Dafeeq. Ka bari kawai gobe ma haɗu” Kainaat ta faɗa tana danne murmushin ta. “Hajiya bazanyi jayayya da ke ba, amma dan ALLAH ki bani umarni kawai ni mai biyayya ne a gareki”. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Ta ce, “Okay dama ina son ganinka ne wlhy. Yanzu haka ma ina office ban wuce gida ba. Idan ban takuraka ba ko zaka sameni?”. “Yanzu-yanzu kuwa ma Hajiya in ALLAH ya yarda”. Ya faɗa cikin sauri yana komawa cikin gidan. Ko kallon Khadijah dake durƙushe na kuka baiyi ba ya shige bedroom. Baifi mintuna bakwai ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga ta yadi mai ƙyawu sosai dan daga gani ma kasan sabon ɗinki ne. Sake tsallake Khadijah yay yayi wucewarsa ya barta da ƙamshinsa.... A cikin abinda bai wuce mintinan arba'in ba ya iso. Sakatariyar ta ce ta tarosa har cikin office ɗin duk da kuwa shima ya sani tunda Companyn ba baƙonsa bane ba. Tunda ya shigo Kainaat ke masa wani irin shu'umin kallo a ƙasan ido. Tabbas Dafeeq ƙyaƙyƙyawa ne. Dan daka ganshi kaga bafulatanin usil. Duk da har yanzu shekarunsa basu gama tsayar da shi a namiji ba, amma kai daka ganshi kasan nan gaba ba ƙaramin ingarma za'ayi ba. Sai dai fa duk da wannan ƙyawun nashi ko kama ƙafar Abaan ɗinta baiyi ba. Dan Abaan dabanne a cikin dubun mazaje tsararsa ma balle Dafeeq da'a gabansa bai wuce ɗan tsako haihuwar jiya ba. Wajen zama ta nuna masa tana mai tattare komai zuwa gefe. Batace da shi komai ba har sakatariyarta ta ajiye masa lemo da ruwa ta fita. Taja wasu mintuna tana rubuce-rubucen ta kafin ta ɗago. Ganin bai taɓa komai ba ta ce, “A'a babban mutum ya haka? Ko kana tsoron karna zuba maka wani abu ne na sace ka”. Murmushi yayi yana girgiza kai. “Kai haba hajiya wane sacewa kuma. Kawai dai bana jin shan komai ne dan yanzu na fito daga gida”. “Okay kace uwargida ce ta cika maka ciki dai kawai”. Murmushi kawai shi dai yayi baice komai ba. Itama bata sake cewarba sai tasowa da tai ta dawo kujerar kusa da shi suna facing juna. Lemon da aka ajiye masan ta ɗauka tare da ɓalle murfin takai baki, sai da tasha kusan rabi sannan ta miƙa masa. Kasa musa mata yay ya amsa yana godiya. Tai murmushi kawai da gyaɗa kanta. “Nasan kanata makin dalilin wannan kira na ujila. Dan haka bazan so barinka a duhu ba ko lalube muje kai tsaye ga abinda yasa na kirakan, dan ni macece mara son kwana-kwana ko kwalo-kwalo. Dafeeq nasan ka sanni kasan wacece ni a companyn nan. Ka mun tambayoyi bila adadin akan ƙyautar mota da gida danai maka sati ɗaya data wuce. Hakama shekaranjiya kamin tambaya akan waya duk dai ban amsa maka ba. To ina ganin yau ya kamata na baka amsa da kuma dalilin komai. Da farko dai magana ta gaskiya *_SONKA_* nakeyi.....” Da wani irin sauri Dafeeq ya ɗago manyan idanunsa yana kallonta. Sai kuma ya nuna kansa alamar (Ni). Kanta ta jinjina masa na tabbatarwa. Batare data bashi damar cewa wani abu ba. Ta ɗaura da faɗin, “Tabbas kai kuwa Dafeeq. Na kuma jima ina jin hakan a kanka tun randa na fara ganinka a company ɗin nan. Sai dai nata tunanin ta yanda zan tunkareka da batun gudun kada ka baɗa min ƙasa a ido. Amma dai na baka dama kaje gida kayi tunani dan ALLAH. Da gaske ina sonka kuma aure nake so muyi nanda ƙanƙanin lokaci. Dan banama son mu wuce sati biyu. Kada kuma ka damu da duk abinda za'ai na shagalin biki. Aikinka kuma zaka iya fara zuwa wannan Monday ɗin dan na tanadar maka kayan da duk zaka buƙata da kamfani ya bada umarnin ai amfani da su. Dan ALLAH kada kace a'a. Amma dai kaje kayi tunani akan maganata Please. ALLAH dai yasa bazakace na maka tsufa ba”. Ta kamo hannunsa tana murmushi tare da ɗora masa bandir na dollers. “Ga wannan ka riƙe a hannunka sai na jika. Ni yanzu zan tashi dan na gaji jikina ciwo yake mun ina buƙatar hutu.” Ta sakar masa hannu tana miƙewa fuskarta ƙawace da murmushi. Handbag nata mai azabar ƙyau kawai ta ɗauka da tarkacenta batare da ta sake cewa da shi komai ba tai ficewarta a office ɗin tana murmushi..........✍️ _😣🤌🏻Na rasa mima zance akanki Kainaat_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na takwas_ INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.🥰🥰🥰 KAMA DAGA *FLYER *3D MOCKUP LOGO *2D MOCKUP LOGO *NORMAL LOGO *IMAGE LOGO *BANA *STICKERS *ADVERT VIDEO *PROFESSIONAL INVITATION *INVITATIONS CARD *BIRTHDAY VIDEOS *POSTER *CERTIFICATE.AND MORE...... CONTACT ME ON 👇 09035390383 ___________ ........Cikin ƙarfin hali ta ƙarasa duka aikin da ya kamata tayi taja jikinta da ƙyar zuwa falo ta kwanta. Sosai kanta ke mata ciwo saboda kukan da tasha. Barci ya ɗan fara figarta sama-sama ya shigo gidan. Ciki-ciki yay sallama batare da ya kalli inda take ba. Har ya wuceta sai kuma ya dawo da baya yana kallonta. Gabansa ne ya faɗi ganin yanda idanunta sukai tulu-tulu alamar taci kuka, ga jijiyoyin kanta da sukai ruɗu-ruɗu suma. “Yanzu ke akan wannan ɗan abunne kika zauna kikai kuka har idanunki suka kumbura haka?”. Idanun ta buɗe a hankali ta sauke kansa, maimakon amsa masa sai ma ga wasu hawayen na zaryar sakkowa. Da sauri ya kauda kansa yana jan ƙaramin tsaki zai bar wajen ta riƙo hannunsa caraf. Cak ya tsaya, sai dai bai juyo ya kalleta ba. Ƙasa ta zamo daga kujerar ta durƙushe tare da sake fashewa da sabon kuka hannunta biyu riƙe da nasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka yafemin, nasan nayi kuskure amma in sha ALLAHU bazan sake ba, kada kayi fushi dani mijina na tuba”. Idanunsa ya lumshe yana jan ajiyar zuciya, kamar bazai kulata ba sai kuma ya juyo gaba ɗayansa. Idanu ya zuba mata na tsawon mintuna biyu. Ita dai tama durƙushe tana kuka mai ban tausayi. Kamata yay ya miƙar, batare da yayi magana ba ya zaunar da ita a kujera shima ya zauna. Nan ɗin ma baice komai ba ya dai zuba mata ido tana cigaba da kukan har tsawon wani lokaci kafin ya ɗan tsuke fuska da faɗin, “Amma kin san bana son kuka ko! To na gaji daji haka nan”. Da sauri ta shiga goge hawayenta, dan tasan tunda ya faɗi hakan to ya huce kuma kenan. Cikin dasashiyyar muryarta ta ce, “Nagode mijina.” Bai tanka mataba nan ma, bata kuma damu ba ta sake cewa, “A kawo abinci? Abinda kafi so na dafa maka”. “Ba yanzu ba, bani ruwa kawai”. Ya amsa mata cikin sauƙaƙa murya yanzu kam. Zaram ta miƙe baiwar ALLAH har tana cin tuntuɓe, ALLAH dai ya taimaka bata faɗi ba. Yanda bai motsa ba haka bai tanka mata ba, sai binta da kallo da yay harta fice. Bayansa ya kai jikin kujerar a hankali ya kwantar yana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, tabbas yana son Khadijah, duk da kuwa faɗa ne ya fara haɗasu, ya kuma fara jin sonta ne akan bigiren sha'awa, dan a lokacin daya yaga mata hijjabi a wancan lokacin yay tozali da cikakken halittar ta yaji wani abu da bai taɓa jiba akan mace ba ya tsarga masa, bayan an musu sulhu hararar da take masa da murguɗen baki a duk sanda suka haɗu ya dasa masa soyayyarta, dan duk da yaji sha'awarta a waccan ranar bai taɓa sama ransa wani mummunan al'amari a kanta ba. Tabbas son Khadijah yake, ya kuma yanke shawarar su gudo suyi aure ganin iyayensu sunƙi fahimtarsu. To a yau kuma ga Hajiya Kainaat a rana tsaka. A wata gaɓa da shi kansa yasan yana buƙatar kuɗi, dan kuwa bashi da wani buri a mataki na biyu bayan samun Khadijah da yaso sai mallakar dukiya. Sun baro iyayensu sun gudo nan sunyi aure, yasan dolene watarana su buƙaci waiwayar gida, komawa da tarin dukiya a wani matsayi shine abu mafi muhimmanci da iyayensu zasu kalla suyi saurin amsarsu. Wasu sukance idan aka samu akasi a irin auremsu da an haihu aka koma ga iyaye sukan amsheka dan waɗan nan ƴaƴan, sai dai kuma kash shifa magana ta gaskiya baya buƙatar haihuwa a yanzu, yo ALLAH na tuba shekararsa nawa ne ma kwata-kwata da zai yarda ya haihu a yanzu duk ya tsofe. Ita kanta Khadijah ya barta ta fara haihuwa ai sai tazo ta koma wata babarsa ne, shiyyasa ma yake zuba mata ƙwaya a duk sanda ta samu ciki batare data fargaba ta sha a lemo cikin ya zube. Da ga ƙarshe daya fahimci ba daina ɗaukar cikin zatai ba sai kawai ya saka likitan ya saka mata robar hana ɗaukar ciki tana tsaka da magagin ɓarinta na ƙarshe, sai bayan wani lokaci idan aikinta ya ƙare zai bi wata hanyar a sake saka mata wata batare data sani ba, dan ko zai yarda ta haihu gaskiya sai nan da shekara goma sha biyar haka sun gama more rayuwarsu. Amma yanzu baya buƙatar takura, ƴaƴa takurane kawai da salon tsofar da mutane, gashi ka zama wahalalle dan dole ka nemo suci ka biya musu kuɗin makaranta idan basu da lafiya kaine, kai abunfa ba sauƙi. To amma yanzu ga babbar dama ta samu, wato samuwar dukiya, dan duk da Kainaat ƙyaƙyawar mace ce fara tass shi baiji zai iya sonta ba, yo dakaɗan fa Ummansa ta girmeta, dan Ummansa ta sanar masa tana da shekara goma sha biyu akai mata aure kasancewarsu fulani, ta tare tana da shekara sha uku, ta haifesa tanada shekara goma sha biyar, yanzu shekararsa ashirin da huɗu, Ummansa nada shekara talatin da tara, matarnan zata iya kaiwa talatin da biyar, shekara huɗu Ummansa ta bata fa kawai. Taɓɗi babbar magana, yo ai koda take da ƙaramin jiki duk wanda ya kalleta yasan ba yarinya bace ba wlhy, amma kuma bazai bari damar nan ta kuɓce masa ba, dan a yanda ya fahimceta zata iya bashi dukiya mai yawa akan son shin da take, sannan in har ya mallaketa wannan companyn kansa da akace nata ne da tsohon mijinta ya gina mata zai iya mallakesa batare data farga ba....” Wani irin murmushi ya kufce masa har haƙoransa na bayyana. Idanu sosai Khadijah da tun ɗazun ke faɗa masa ga ruwa ta kawo bai jiba ta sake zuba masa. Mamaki na ƙara baibaye mata zuciya, dan yanayin nashi na sake tabbatar mata akwai abinda yake ɓoye matan tabbas. Amma tana jin tsoron cigaba da masa bore, dan haka haƙuri da shanyewa ta zubama sarautar ALLAH ido kawai ya kamata gareta a yanzu. “Ga ruwan”. Ta sake maimaitawa a hankali. Idanunsa ya buɗe a kanta, a take ya haɗiye murmushin da yake yi batare da yace komai ba ya amsa. Sosai ya sha ruwan har hakan ya bata mamaki, yana kammalawa ya miƙe ya shige bedroom. Kwance ya kai a can ma ya sake zurfafa a tunani, da ga baya kuma yama miƙe ya shiga kaiwa da komowa tare da ƙulla abubuwa da yawa akan Kainaat da dukiyarta..... __________★ “Wai kina nufin har kin zauna da shi Kainaat? Anya bakiyi gaggawa ba kuwa?”. “Humm Nadwa kenan, to miye amfanin jinkirin? Karfa ki manta kwana goma sha biyu ya ragen na gama iddata, kuma a washe gari nake son a ɗaura aure.” “To ni yanzu babu abinda zance tunda kin riga kin yanke hukunci, sai dai zan baki shawara gaskiya kiyi ƙoƙari bayan an ɗaura auremku ki tasashi gaba kuje ga iyayensa, kinga dai gara ita matarsa duk da gudowa sukai iyayensa sun san da ita, ke kuwa fa? Sannan yanda nake ganin idanun yaron nan a tsakar ka wlhy gara kisan tushensa koda ta ƙwaɓe kina da madafa”. Dariya sosai Kainaat keyi, Sai da tai mai isarta Nadwa na kallonta kamar ta samu tv kafin ta tsagaita. “Oh oh! ALLAH Nadwa kinada kayan haushi dana dariya. Yanzu ni banda abinki wannan ɗan yaron ne har zai iya sakani a wani tarko kike tunani? Sannan kuma idan baki mantaba bari na tuna miki, auren kisan wuta zanyi domin na koma gidan Abaan, bawai zama zanje yi da yaron nan ba. To niko har wace matsala ce zan hanga da zata sakani damuwa da wani sanin iyayensa da tushensa. Please karki hargitsa mini lissafi. Ke dai kawai ki tayani da fatan alheri, sannan ki samo min wanda nace miki ɗin dan ina son da ga gobe a fara bibiyarmin duk wani motsinsa”. Kaɗa kai kawai Nadwa tai da faɗin, “Okay shike nan. ALLAH yasa ayi lafiya a kuma rabu lafiya. Amma ya kamata kuma shima Abaan ki fara tabbatar da har yanzu kina a zuciyarsa, kar kiyi jifan gaffiyar ɓaidu. Dan yanzu haka yanda nake jin labari tunda kuka rabu yabar ƙasar har yanzu bai sake waiwayowa ba, amma akwai bikin buɗe katafaren companyn nan nasa na shinkafa da ake saka ran zai zo nan da wata uku da wasu satittika”. “Nadwa kenan ai duk nasan wannan. Hasalima duk wani tsare-tsaren buɗe Companyn nan nice na tsarashi a satin da tsinanninyar uwarsa zata saka shi ya sakan. Na kuma tabbatar dama duk inda yake sai ya dawo anyi bikin buɗe Companyn da shi, saboda muhimmancisa a wajensa. Wannan shine dalilin da yasa ma nake son ina gama Idda washe gari a ɗaura min aure da yaron nan dan sati biyu ko wata ɗaya nake son nayi da shi, kin ga zan sake wata iddar na gama kusan dai-dai da lokacin buɗe Companyn....” “Aiko bazai gamu ba kafin sannan lissafa kuma kiga”. “Hakan na matsala bane ai, fatan ba dai nayi auren na fito ba, duk sanda zai zo ƙasar ya san dai yana da damar maida aurenmu hakan ya wadatar dani”. “To ALLAH ya fidda a'i daga rogo”. “Suɓul kuwa zata fita gyara zama kisha kallo.” “A kallo kam mune a gaba ai. Sai dai a shirya tsaff dan irin yaran nan fa shap shooters ne wlhy zuwa ɗaya sukema yaƙin ƙasa da ƙasa su dawo da ganima. Karki saki jiki cewar kunata neman haihuwa ke da Abaan tun bayan haihuwar farko da kikai yaron ya rasu yanzu ciki bazai shiga ba”. Cikin ɗage gira Kainaat ta ce, “Uhhyimm! Sai akace miki kuma zan ma bashi kaina ne? Ai bana jin zan iya mallakama wani namiji jikina bayan Abaan Nadwa, dan Abaan da kike gani babban gwarzon mayaƙi ne da bayi da kwatankwaci a filin yaƙin nan...” “A wajenki ba”. Nadwa ta faɗa tana dariya. Dariyar itama Kainaat keyi, ta bata amsa da, “Muje a hakan a wajena ɗin”. Haka suka cigaba da hirarsu cikin nishaɗi da tsara zaman Kainaat a gidan Dafeeq da yanda al'amura zasu kasance. Duk da dai batun cikin nan da Nadwa tayi ya tsayama Kainaat a zuciya matuƙa.... _________★ Da ƙyar aka iya tara-tara wajen kamashi, wani dattijo maƙwafcinsu ya cire babbar rigarsa aka sakamasa. Gudun da yaci yasa numfashinsa gaba ɗaya ya koma fita da ƙyar, da ga ƙarshe ma ganin yana neman shiɗe musu dole akai gaggawar wucewa asibiti mafi kusa da shi, dan ya matuƙar birkice musu tamkar mai Asthma. An amshesu da gaggawa aka saka masa oxgyn kafin likita ya tsaya a kansa. Da ga ƙarshe dole akai masa allurar barci mai nauyin gaske dan doctor ya tabbatar da in har aka barsa ido biyu brain ɗinsa na gab da susucewa. Zuciyarsa kuwa bugunta ya wuce musali alamar yana cikin matsanancin tsoro ko tashin hankali. Bayan likita ya tabbatar musu su kwantar da hankalinsu sun ɗan samu nutsuwa, sai a lokacin suka samu tattaunawa akan batun wannan tashin hankali haka. An yanke shawarar barin wasu anan asibitin, wasu kuma suka nufi gidan JJ ɗin domin bincika abinda ke faruwa. Sun sami gidan kaca-kaca tamkar anyi yaƙi a cikinsa musamman ma falon. Dan komai an birkitashi da ga mazauninsa zuwa wani waje daban. Ba mamaki kawai ba harda birkicewar tunani ya samesu. Musamman ma Baba da yasan a jiya sune na ƙarshen barin gidan, kuma sun bar komai tsaff da shi tamkar an zana. Amma yanzu gaba ɗaya ya koma kamar ɗakin ajiye shara. Ruɗani na biyu shine rashin ganin Alimah da basuyi ba, hakan na nufin itama tabar gidanne kokuwa yaya ne?. Suna tsaka da dube-dube sukaji kamar ana kuka, da sauri Yaya Mujee ya nufi inda yake jiyo sautin kukan. Can bayan ɗakunan ne, fitowa sukai su duka zuwa inda kukan ke fitowa, tun daga nesa suka hangota a wani ɗan lungu takure. “Subahanallahi! Alimah kece anan?”. Yaya Mujee ya faɗa har yanayi kamar zaici tuntuɓe sai da Yaya Inusa ya ruƙosa. Su duka inda take suka isa suna kiran sunanta, sai dai babu alamar zata ɗago. Kusan mintuna uku suna faman lallashi da lallaɓata amma taƙi tako motsa sai ƙarama ƙarfin kukanta take. “To ko dai za'a kira iyayenta ne?”. Cewar Baba yana kallon ƴaƴan nashi. Yaya Inusa ne ya amsa masa da, “To gaskiya kam Baba hakan zaifi nake ga. Dan al'amarin naga ba ƙarami bane ba”. Waya Baba ya zaro da shirin kiran mahaifin Alimah, tamkar wadda aka zabura sai gata tai wani irin ɗagowa gashinta dake wargaje yayi bulahh fuskarta ta bayyana. A kusan tare Baba, Yaya Mujee, yaya Inusa suka zabura jikunansu na rawa. Dariya ta kwashe da shi tare da miƙewa tsaye gaba ɗayanta. Ai kafin ma kace takk ƙafa mi naci ban baki ba. Tuni tsakanin Baba da su Yaya Mujee an fara gudun wuce sa'a. Kowa burinsa ya kai ga ƙofa. Babu mai tunawa da girman na gaba da shi ko ƙanƙanta. Faɗuwar Baba biyu kafin suje gate, amma babu wanda yako waigo domin taimakonsa tsakanin Mujee da Inusa. Sai shi ke taƙarƙarawa ya tashi har dai ALLAH ya taimakesu suke fice. Tofa, ƴan anguwa da dama ke'a ɗari-ɗari tun daga fitowar JJ yanzu fa sun sake tabbatar da babu lafiya. Tuni aka fara ƴar rere ƴaƴa da mata kasancewar mazan duk sun fice wajen nema. Ga shi sabuwar anguwa ce dama. Bakajin komai sai ihun mata da kukan yara. Ga shi su Baba sunƙi tsayawa, dan suma kansu sun rarrabu kowa yayi titi. Duk wanda kuma ya samu abin hawa baya neman ɗan uwansa yake afkawa kawai..........✍️ _😂To gaskiya akwai matsala. Uncle JJ anya kuwa ba sarauniyar aljanu ka kwaso mana ba a family 🤣🙏_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na tara_ ......Da ɗai-ɗai suka dinga isowa gidan. Hakan ya sake ɗaga hankalin mata dake cike da gidan ana jajantawa. Dan duk yanda akaso suyi bayani kasancewar an san sunje can gidan haka ya gagara. Baba ne kawai ke iya maimaita kalmar, “Akwai matsala. Gidan Jazool babu lafiya ƙwarai da gaske”. Zugum-zugum akai kowa na sauraren baba cikin ƙara tsorata da jimantawa. Sai da suka samu nitsuwa kusan ta awa ɗaya sannan suka bada labarin abinda ya faru. Yanda Yaya Mujee ke siffanta sunga Alimah tamkar irin horror ɗin nan ya hargitsa zukatan mutane. Yanda wasu suka firgice ma sai ka ɗauka da su aka gano. Yaya Inusa da baice komai ba tun ɗazun cikin damuwa ya ce, “Baba dole ne fa a nema iyayen yarinyar nan akan lokaci. Dan abinda na fahimta gidan nan na Jazool akwai aljanu, kuma da alama sun shiga jikin matarsa”. “Gaskiyarka Inusa dole aɗauki mataki da wuri kam, dan barin yarinyar can a wannan halin ita kaɗai akwai tashin hankali. Bari muga a lalubo mahaifin nata”. Kowa dake wajen ya gamsu da zancen Baban. Yayinda tausayin Alimah da JJ ya sake mamaye zukatan kowa. Sam Baba ya kasa samun number ɗin mahaifin Alimah, dole ya yanke hukuncin idan sun idar da sallar la'asar zaije shi da Yaya Mujee gidan su Alimah ɗin. Bayan idar da sallar la'asar suna shirin wucewa gidan su Alimah kira ya samesu daga asibiti cewar JJ fa ya farka a wani yanayi. Dan a yanzu haka ma rirriƙe ake da shi. Dole su Baba suka saki zancen zuwa gidan su Alimah suka tafi asibiti. A yanayin da suka sami JJ kam abun akwai tausayi, ga likitoci sun tabbatar da su basuga komai a tattare da shi ba. Brain ɗinsa lafiya lau take. Hakama fatarsa babu wata damuwa amma ga wasu irin ƙananun ƙuraje sun maidashi butsaaa babu ƙyawun gani tamkar jikin kada. Su baba da suka fahimci komai a yanzu roƙonsu sukai kan su masa allurar barci kawai zasu wuce da shi gida. Dan sun gano bakin zaren shafar aljanu ce. Wannan shine dalilin dawo da JJ gida aka nemo malamai suka rufu a kansa. An masa addu'oi sosai duk da yana barci, sai aka kuma yanke shawarar bari har sai ya tashi. Har dare babu alamar JJ zai farka. Dan takai amma fara tsorata da barcin nashi. Ga su Baba ana idar da magrib suka fantsama gidan su Alimah, sai dai sun sami gida a garƙame da kwaɗo, da sukai tambaya kusan mutum uku suka sanar musu ai wannan gida ya kai shekara huɗu a rufe tun bayan rasuwar masu gidan, hasalima a yanzu ƙarƙashin kulawar ƴan sanda yake. Matuƙa kansu baba ya kulle, sai dai rashin lokaci ya sakasu yanke shawarar ajiye wannan batun har safiyar gobe suka nufi gidan JJ domin ceto Alimah tare da malam nan dan a barota da gidan. Dan malam ne suka bada shawarar a fara zuwa a ceto yarinyar da safe sai a nema iyayen nata saboda dare ya riga ya fara. Haka dole badan Yaya Mujee yaso ba suka nufi gidan JJ. Sun sami gate ɗin gidan yanzu a rufe. Iya ƙoƙarin suga sun buɗe hakan ya gagara. ALLAH ya taimaka akwai extre kay a hannun maƙwafcinsa, dan haka ya ɗakko. Da yawansu suka shiga gidan kasancewar mazan anguwa duk sun dawo, sai dai suna gama shiga ƙofar gate ta tafi da kanta ta datse ji kake gammm!!!. Gaba ɗayansu babu wanda gabansa bai mahaukacin faɗi ba. Dan duk a birkice suka juyo suna kallon ƙofar gate ɗin. Yayinda masu ƙarfin hali suka ɗauki addu'a a bakunansu. Cikin ƙarfin hali maƙwafcin JJ ya ce, “Iska ce ta rufe ƙofan, dama tanayin hakan tun ana aikin gidan”. Wasu sun ɗan ji mutsuwa, yayinda wasu dai sun haƙurane kawai dan ganin sunada yawa. Akwai wuta a gidan tako ina dan anguwar suna samun wutar nepa sosai. Cikin gidan suka nufa kowa na addu'a. Baba da malaman ne a gaba, sai ƴan anguwa da masu son ganin ƙwaf da suka biyosu daga can gida. Basu sami Alimah a inda suka bartaba ɗazun, sai dai inda ta zauna duk jini ne, sai kuma sawun ƙafarta da tambarin jinin ya tafi har hanyar back door na kitchen. Hankalin kowa ya tashi da ganin jinin nan, amma cikin ƙarfin hali haka aka ɗuru cikin falon kowa na karanta addu'a. Bbaaammmm!! Kake jin ƙofa ta datse kanta anan ma. A yanzu kam ai babu batun yarda da cewar iska ce ta rufe. Kusan gaba ɗayansu suka kalli ƙofar falon hankali a tashe. Bammm!! Ta Back door ɗin itama ta bada sautin rufewa harda ƙarar saka sakata. Yanzu kam rawar jiki ɗan gaske kowa ya fara, musamman ma ƴan son ganin ƙwaf ɗin nan da mazan anguwa. Malaman nan kam sun fara karatu cikin ƙarfin hali. Tsitttt babu wani abu da ya sake motsa kansa a gidan, zamaka iya ɗauka hatta iskar dake kaɗawa ta tsaya ne itama. Farrr-farrr wutar gidan ta fara rawa. Cikin sauri suka fara dunƙulewa waje guda, masu tsoron tsiya a cikinsu har fitsari ya cika musu mara, masu ƙarfin hali na taya malaman nan addu'oi. Ɗifff wutar ta ɗauke gaba ɗaya, duhu mai tsanani da ko tafin hannunka baka iya gani ya mamaye gidan duka. Sai ga mazajen fama na rungumar juna masu guntun fitsari na fara ɗiga..... 🚴🚴taɓ bara na fece alkur'an. Yo ƴan maza na cikin wanga yanayi mu ƴan mata sai muyi yaya, ai fecewar kawai ta ragemun tunda ni mai ɗaukar rohoto ina iya tashi sama kamar jirgi🤣🤣. _________★★★★ *_Aslm hajiyata miye matsalar gashinki? Rashin tsawo ne ko cunkushewa gareshi ko kuma baqi kikeso yayi da santsi ne? Ga garin itatuwa na kawo maki mai fito da gashi har har gadon baya cikin sati biyu kacal._* *_Sannan na kawo maki back to virgin wanda ko haihuwa nawa kikayi zaki matse cikin qanqanin lokaci ki koma kamar budurwa, har oga sai ya rasa gane shin wani aure yayine ko canza mashi mata akayi._* *_Daɗin daɗawa kuma ga saiwar breast wanda zata gyara maki boost ɗinki cikin qanqanin lokaci ki koma kamar budurwa abinki.....hmmm hajiyata wani abun sai kin gwada zakiyi man godiya......ke dai tuntubarni ta wannan number ɗin domin qarin bayani 09032237835._* ___________★★ Sati biyu ta cika a tsakanin Dafeeq da Kainaat. Yayinda ɓangarorin biyu kowa ke nasa shirin. Sai dai duk yanda Dafeeq ya ɗauki al'amarin ƙarami game da tunkarar Khadijah da zancen zai ƙara aure hakan ya gagara. Duk da yanzu ta tattarashi ta ajiye bata masa magana akan komai da zai zo da shi gidan amma sai yaji ya kasa tunkararta da batun. Ya fara zuwa aiki, yayinda nauyin cefanen gidansa ya koma kan Kainaat a yanzu. Kullum cikin kawo musu kaji da kayan daɗi yake, ya baza ɗunkuna na alfarma tsakanin yadika da shaddoji. Ita kanta Khadijah ya mata kala goma masu tsada. Sabon gida ne dai basu kai ga komawa ba, amma mota tuni Kainaat ta koya masa da kanta a yanzu haka ma ita yake hawa. Hankalin Khadijah a matuƙar tashe yake, kullum sai tayi kuka amma tsoro ya hanata sake tunkarar Dafeeq akan wannan sabon yanayin da suka tsinta kansu a ciki. Duk da yana fahimtar halin ƙuncin data saka kanta bai taɓa zaman lallashinta ba. Sai dai yana cin abincinta, yana kuma biyan buƙatarsa a jikinta duk da ita batajin wani shauƙin hakan a yanzu. Yakan fita gida da safe sosai, baya dawowa sai sha ɗaya, wataran ma sai sha biyu. Daya dawo yay wanka yaci abinci zaice ya gaji suje su kwanta. Dole take bin umarninsa, ya sameta ya mora ya hau barcinsa. Itako bata iya runtsawa, dan sosai take kewar Dafeeq ɗinta na da. Wanda baida lokacin kowa da komai sai nata, kullum suna manne da juna. Hatta da aiki yakan makarane a kullum kafin ya fita. Sannan idan ya dawo gida baya sake fita sai salla, da an idar yake dawowa gida su cigaba da sha'aninsu cike da farin ciki da farantama juna. Hatta aikin gida tare sukeyi, wankin kayansu da fita zuwa gidan baba hakimi. Wataran ma haka nan zai ɗauketa suje su zagaya gari suyi ƴar sayayyar kayan ƙwalam dinsu ko suci a can su dawo gida. Wanka idan har yana gida tare sukeyi. Amma yanzu duk babu waɗan nan tattalin da soyayyar. Iyakarsa cin abincinta da kuma sauke gajiyarsa. Dariyarsa ma ta gagareta gani, idan ta nuna damuwa ko'a fuska yace ita ta cika matsala. Tasan fa da da yanzu akwai banbanci, yanzu yana aiki uziri ya masa yawa kaza-kaza. Bata da bakin magana, dole take haɗiye komai sai ya fita taci kukanta. Ga kaɗaici na cimata zuciya, sam kayan alatun da yake faman zube musu a gidan baya wani birgeta, ita saima ta yini bataci abinci ba. Duk ta fige ta fita a hayyacinta. Shiko yana mulmula uwar ƙibarsa fatarsa na ƙara wani fresh. Yau ya kasance laraba, saura kwanaki biyu a ɗaura auren Dafeeq da amarya Kainaat, dan haka ya yanke shawarar tunkarar Khadijah da batun nan dan baya so taji a waje. Tayi mamakin ganin ya dawo aiki da wuri. Dan ana idar da sallar la'asar ya shigo gidan. Wanka yayi yace ta kawo masa abinci. Bayan yaci ya ƙoshi yana mata ƙorafin ramar da tayi itako tana ɗan murmushin ƙarfin hali kawai batare da tace komai ba. Bai sake fita ba har akai kiran sallar magrib sannan, bayan yayi har isha'i ya dawo gidan da tsarabar kayan ƙwalama. Tsareta yay sukaci tare, ganin kamar ya fara dawo mata a Dafeeq ɗinta na baya taji ƴar nutsuwa harta saki jiki taci. Bayan sun gama wanka sukayi da brush, tayi mamakin jin yace da wuri zai kwanta, amma haka ta danne komai na wasi-wasi a ranta ta biye masa suka shige bedroom tun ƙarfe tara. Tana kwance a jikinsa shiru bayan ya gama biyan buƙatarsa taji ya sauke ajiyar zuciya. Kallonsa ta ɗan yi, kamar bazatace komai ba sai kuma ta nisa itama tare da sake shigewa jikinsa. “Husby kanada damuwa ko?”. Shiru kamar bazaice komai ba, bayan wasu sakanni ya sake sauke numfashi da fuskantar ta shima. A hankali ya ce, “Tabbas inada damuwa Khadijah, kuma a kanki ne.” A zabure ta kallesa tana mai nuna kanta da waro idanunta. “Ni kuma dai? Dan ALLAH miyasa zaka shiga damuwa a kaina Dafeeq. Wlhy in dai abinda ya faru ne a kwanakin baya ni na ajiye komai, na kuma maka uziri, sannan ina farin cikin cigaban da ya samemu tunda nasan duk dan ka faranta minne. Fatana dai ALLAH ya cigaba da rufa maka asiri ta hanyar halak, dan bana fatan jikunanmu su zama a cikin jikunan da wutar jahannama zataci sakamakon ci daga haram. Bana zarginka bazan kuma taɓa zarginka ba in sha ALLAH”. “Nagode da hakan. Sai dai ni ba'akansa nake damuwar ba. Dan nasan dai hakkin ciyar dake a kaina yake Khadijah. Sannan inada ƴancin neman arziƙina ko zuwa miki da sabon abu batare da shakkar karki tuhumeni ba. Abinda kawai na sani bazan taɓa aikata abinda nima zai wargazamin rayuwa ba akan neman abinda zan ciyar dake ko ƙyautata ratuwarki.” Duk da maganganunsa sun mata wani iri haka ta danne harda sakin murmushin ƙarfin hali. Cikin son danne hawayen da suka cika mata ido ta ce, “Hakane”. Tashi yay zaune fuskarsa babu alamar wasa, hakan yasa itama ta tashi zaunen da ƙyau. Sai da ya zuba mata idanu na wani lokaci tamkar mai nazartar ta kafin ya ce, “Khadijah!”. “Na'am”. Ta amsa masa cike da girmamawa. “Mata nawa akace maza su aura a musulince?”. Ƙirjinta yay wata irin muguwar bugawa har sai da ta ɗago a zabure ta kallesa. Ganin yanda ya tsareta da nashi idanun ta haɗiyi wani abu mai kauri a maƙoshinta tana maida idanunta ƙasa cikin rawar murya ta ce, “Huɗu”. “Masha ALLAH” ya faɗa yana gyara zamansa. Batare da damuwa da yanayinta ba ya cigaba da faɗin, “To ALLAH ya karrama mijinki da zamowa cikin jerin maza da zasu ƙara aure, nima zan mallaki mace fiye da ɗaya kenan. Dan na samu wata baiwar ALLAH da muka dai-daita kammu har jibi juma'a ma za'a ɗaura auren in sha ALLAHU....” Sosai jikin Khadijah ke rawa Kaff-kaff tamkar wadda aka kaɗama gangi, yayinda idanunta tuni hawaye ya ɓalle a cikinsu. “Aure kuma Dafeeq!”. Ta faɗa cikin suɓutar baki da rawar lips ga hawaye share-share. Fuska ya sake tsukewa tamau, cike da gadara ya ce, “Ban cika namiji bane?”. Kanta ta girgiza masa da sauri. “A'a ba haka nake nufi ba. ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya”. A gatsine ya ce, “Amin” tare da komawa ya kwanta ya juya mata baya. Hannu tasa ta toshe bakinta jin kuka na neman kufce mata. Sai dai duk da haka sai da sautinsa ya shiga cikin kunnen Dafeeq. Ƙaramin tsaki yaja batare da ya juyoba ya ce, “Malama bana son wata damuwa fa. Idan kin kwantar da hankalinki ma ita wadda zata shigo ɗin ba sa'ar yinki bace ba. Sannan bata da lokacin wani yin ƙishi-ƙishin banzan nan dan tanada aji ta kuma san abinda yake yi. Ya rage naki ki kwantar da hankalinki kici arziƙi kema cigabanki ne”. Daga haka ya juya yay kwanciyarsa. Kasa daurewa Khadijah dake jin kanta na juya mata tayi, da sauri ta dira a gadon ta nufi falo........✍️ _Humm Khadijah 😕🤌🏻_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma_ _ADVERT👇_ _YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_ _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_ _MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_ _*YERWA INCENSE AND MORE*_ _DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._ _AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_ _ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._ _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_ _NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_ _YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED ___________ .......Ƙarfe ɗaya da mintuna goma sha shida duk wanda ke a massalacin ya shaida ɗaurin auren Dafeeq Abubakar Ja'e da amaryarsa Kainaat Usman akan sadaki naira dubu ɗari biyar. Kasancewar massalacin a anguwar su Kainaat yake gane wanene angon nata ya haddasa ƙananun maganganu a bakunan mutane. Kainaat sananniyace a anguwar tun tana budurwa, duk da mahifinta talakane ta tashi irin yaran nan marasa jin magana da son ƙarya. Za'a iya rasa masarar tuwo a gidansu Kainaat ka ganta da dressing na kusan dubu ɗari biyu a jiki. Gashi bata da mutunci ko kaɗan, dan ko gittawa tai ka gaya mata cuta sai ta dawo ta gaya maka mutuwa. Yanda Kainaat ke fantamawa a cikin dukiya yasa tuni kowa ke mata kallon ƴar iska. Sai dai kuma a baɗini sam ba haka bane. Dan duk rashin jin Kainaat bata aikata zina, amma fa ko kai waye a wayo in har ta ƙwallafa maka sai taci kuɗinka. Zatabi tako wace irin hanya taci saboda shegen wayonta. Kainaat ƙyaƙyƙyawa ce sosai, dan ta kasance buzuwa, sai dai anan Nigeria aka haifeta, dan nan ta tashi taga kanta da iyayenta nan kuma kaɗai ta sani ko Niger da aka san asalin buzaye suke basa zuwa. Ƙawayen Kainaat duk ƴaƴan masu kuɗine, ta kuma samosu ne a yazon bin joint-joint ɗinta. Dan duk inda tasan ƴaƴan manya suke nan ne wajen zuwanta. A wannan kutse-kutsen nata ta tattara ƴaƴan manya suka zama abokanta. Sometimes ma sune ke saya mata sutura, dan in har zasu shiga shopping to itamafa dole a mata. Tayi samari kala daban-daban kama daga kan alhazawan birni har zuwa matasan masu kuɗi dama yaransu, sai dai taci kuɗinsu ta gudu. Da taimakon Nadwa ta koma makaranta, dan ta kammala secondary ɗinta tuni. Nadwa mommy's girl ce. Dan babanta ya jima da rasuwa, kuma mai kuɗine sosai, ita kaɗai ya haifa dan haka ya barsu da tarin dukiya itada mahaifiyarta. Tunda taga Kainaat ALLAH ya ɗaura mata sonta, dan ita mutum ce mai son ƙyaƙyƙyawa. Tare suka fara karatu, daga baya Mommyn Nadwa ta turasu abroad. Da ƙyar baban Kainaat ya yarda, dan sai da Mommyn Nadwa ta lallaɓashi. Su Kainaat na shekarar ƙarshe a school Abaan yazo yin wani course na wata shida. Tunda Kainaat ta ɗaura idonta a kansa ta haukace. Haka ta addabi Nadwa sai da ta binciko mata shi ɗin ɗan waye. Hankalin ta ya sake tashi jin bama ubansa ba, shi akaran kansa gayyane. Dan matashin mai kuɗine a harkar noman shinkafa da shigo data waje gida Nigeria, ya kuma fitar da ta Nigeria waje. Kai a taƙaice dai shine kankat a harkar shinkafa a Nigeria bama arewa kawai ba. Wannan shine irin mijin da Kainaat ta jima tana burin mallaka, matashi ga kuɗi ga ƙyawu. Uwa uba miskilanci. Dan kallon fuskar Abaan kawai ya isa tabbatar ma da mai hasashenshi shi ba kanwar lasa bane. Duk da jikin Kainaat ya ɗanyi sanyi kaɗan da jin shekarunsu ɗaya na haihuwa, amma da ga baya sai ta ware akan hakan ba komai bane. Kainaat ta fara ƙoƙarin shiga jikin Abaan sai dai ko kallo bata ishesa ba, hasalima an sanar mata shi fa mata basa gabansa sam. Mahaifiyarsa da ƙanwarsa ne kawai taurarinsa a duniya. Jin wannan batu yasa Kainaat shiga ta fita harta jawo hankalin P.A nashi kanta, da taimakonsa ta fara kusanta kanta da Abaan, sai dai nan ɗin ma babu nasara, ganin bazai kulata ba ta canja alƙibla zuwa kan ƙanwarsa da mahaifiyarsa bayan sun dawo gida Nigeria sun bar Abaan acan. Yanda Kainaat ke kwantarma Hajiya Maryam kai yasa ta fara jin sonta a zuciyarta, gata kullum cikin shigar kamala. Noor ce dai ma aka ɗan sha wahala da ita, dan da ƙyar ta fara kula Kainaat saboda faɗan da Hajiya Maryam ke mata. Da taimakon Mommyn Nadwa Kainaat ta sake samun shiga jikin Hajiya Maryam, danta alaƙantata da cewar ɗiyar ƴar uwarta ce. Duk da Hajiya Maryam ba damuwarta dole sai ɗanta yay auren ƙwarya tabi ƙwarya bane sai taji ta amince Abaan ɗinta ya mallaki Kainaat matsayin mata. Dan koba komai ƙyaƙyƙyawace kuma nutsatstsiyar yarinya. (Nace Humm). Daga ƙarshe dai anyi auren Kainaat da Abaan badan yana sonta ba sai dan biyayya ga mahaifiyarsa. Yayinda komai akayisa a hannun Mommyn Nadwa matsayin itace uwa gareta iyayenta sun rasu. Mahaifiyarta tayi kuka sosai da irin wannan aure, dan tana son ƴarta, amma gashi a dalilin auren mai kuɗi ta kashesu ta ɗauki matar data santa da girmanta. Haka dai aka sha shagalin biki iyayen Kainaat basu da wani power a ciki. Amarya ta tare, sai dai babu kulawa daga miji, hasalima randa aka kaita yabar ƙasar, hakan ya ƙonama Kainaat rai sosai, taci kuka bana wasa ba, sai dai Mommyn Nadwa nata kwantar mata da hankali ta waya. Hakama Hajiya Maryam tasa Abaan ya dawo dole bayan tafiyarsa da kwanaki uku. Anan ɗin ma Abaan bai niyyar shiga sabgarta ba, amma babu wanda yasan yanda akayi kwanakinsa biyu da dawowa yakai kansa gareta har ma ya angwance a wannan dare. Samunta da budurcinta ne abu na farko daya kankaro mata mutuncinta a wajensa, duk da kuwa asiri na cinsa, dan kai kansa da yay gareta kam tabbas magani yaci a cikin abinci. A watan da Kainaat taje bata tsallake na ciki ya bayyana, kowa murna yake tsakanin Abaan da mahaifiyarsa da Ƙanwarsa. Tattalinta sukeyi kamar ƙwai, dan ko motsi tai sai ance mike damunta. Wannan al'amari yayma Kainaat daɗi, sai ta dinga langaɓe musu kuwa fiye da jin jiki na laulayi suko suna rawar jiki. A haka ALLAH yakai ciki watan haihuwa, ta ko haifo ɗanta namiji mai kama da ubansa sak. Farin cikin wannan family bama zai misaltu ba. Amma abin baƙin ciki mahaifiyarta da ƴan uwanta da mahaifinta sai zuwa sukai dubata a matsayin wai dangin babanta ne dake Niger, Mommyn Nadwa itace komai. Ranar ma mamanta sai da tai kukan baƙin ciki, yayinda ƴan uwanta sukai alkawarin bazasu sake raɓarta ba, dan yanda ta amshesu a wulaƙance ya ƙona musu zuciya sosai. Suna baro gidanta suka tattara kayansu dama gidan da suke gidan haya ne sukai tafiyarsu Niger. Wannan shine silar rabuwarta da iyayenta da ƴan uwanta, har yanzu bata kuma nemesu ba suma basu sake memanta ba. Ranar suna an zubar da kudi na tashin hankali, yayinda yaro yaci sunan Kakansa wato mahaifin Abaan da ALLAH yayma rasuwa tuni. A wannan ranar ne Abaan yayma Kainaat ƙyautar companyn nan, tare da maƙudan kuɗi daga mahaifiyarsa, ƙanwarsa Noor ma ba'a barta a baya ba ta siya mata danƙareriyar mota duk da kuwa Kainaat ɗin nada har guda biyu na lefe da aka saka mata da wadda Abaan ya bata matsayin tukuycin kai masa budurci. Ansha shagali an kuma samu dukiya sosai daga abokan arziƙi, dan kwarai da gaske yaro yayi goshi, Kainaat na alfahari da haihuwarsa. An fara rainon yaro matsayin ɗan gata, sai dai kuma ashe bamai zama bane, dan watansa ɗaya da kwanaki a duniya ya rasu sakamakon mura da dama aka haifesa da shi, dan Abaan nama shirin suje suga likita ne a waje ashe babu rabo. Kuka na tashin hankali Kainaat ta dingayi, dan kuwa dai taga samu taga rashi, harta fara alfaharin dukiya ta zama tata ta gida gaba ɗaya. Abaan da Mamah suka koma lallashinta ita da Noor, dan kuka suke sosai. Ansha fama Kainaat harda kwanciya asibiti kamar ba mutuwar ƙaramin yaro ba, da ƙyar ta dawo hankalinta..... ___________★ Guri ɗaya suka sake dunƙulewa sosai. Dan hatta malaman kansu a wannan gaɓar zukatansu bugawa suke da sauri-sauri. Sai dai basu yarda sun saki addu'oi ba. Masu ragguwar zuciya kam tuni fitsarin daya taru musu ya fara ɗiga, wasu ma gab suke da fashewa da kuka tsabar tashin hankali. Dan wannan al'amari ne da a film kawai suka sanshi bawai zahirin rayuwa ba. Tsahon mintuna biyar wutar ta sake kawowa. Wani irin ihu mai jijjiga gida suka saki kusan su duka idan ka cire Baba da malaman nan sakamakon bayyanar Alimah a mummunar siffar horrors dan bata da maraba da su. Fuskarta da jikinta sunyi wani irin fari tamkar an baɗa mata hoda. Wajen idanunta yay wani zummm kamar wadda tai kukan jini, hakama bakinta duk jini ne, ga gashi a wargatse da uban tsaho har yana jan ƙasa, ta saman kanta akwai ƙahuna guda biyu. Hakama ƙafafunta kofataine, hanyenta da wani irin farcina zaƙo-zaƙo tako ina dai bata da ƙyawun gani. Dan su kansu tunda sukai mata kallo guda idanunsu suka rumtse babu wanda yay gigin sake maimaitawa. Shuuuuu!! Ta wani irin zagayesu kamar mai tafiya a takalmin taya tana ɗaura zabgegen yatsanta a saman baki da faɗin, “Shiiiii!!!” alamar sumata shiru daga ihun da sukeyi. A tare suka shiga haɗiye ihun sai hawaye dake fita a fuskokin masu raguwar zuciyar cikinsu. Jaruman kuwa rawar jiki kawai suke yi, gashi a zagayesun da tai ɗin nan ashe ɗauresu tayi da igiyar da sudai basu gani a hannunta ba. Kwas! Kwas!! Kwass!! Ta dingayin wani taku tamkar wadda ke jerin gasar ƙyau ta duniya. Sai kuma ta wani kwashe da dariyar data nema fasa zukatan su. Sai da tai mai isarta tana faman zagayesu kafin ta tsagaita, da wata kalar kakkausar murya ta ce, “Ku miyasa bil adama kuke da son shiga abinda babu ruwanki ne? To gashi nan shishshigin ku ya jawo muku mutuwa!!!”. Cikin rawar baki da suɓutar baki Baba ya ce, “Baiwar ALLAH kiyiwa ALLAH ki haƙuri. Wlhy mu muzo ne domin ceton matar Jazool. Amma ki taimaka ki yafe mana”. “Hahahaha tsoho! Idan kai wannan ya kawoka su waɗan nan miya kawosu? Sannan da kukazo ɗazun ban muku gargaɗin farko ba?!”. “Kin mana wlhy, kin mana. Dan ALLAH kiyi haƙuri. Babu wanda zai sake maimaita kuskuren nan”. “Wanda ma ke son maimaitawa ya maimaita. Dan ganin gawawwakin ku sai ya saka ƙafar wani bazata sake tako cikin gidan nan ba. Ɗanka kuma yanzu ya fara amsar sakamakonsa a hannunmu, dan sai ya tabbatar da bakowace mace ake taɓawa a zauna lafiya ba. Sai mun barma ire-irensa tarihin tunawa a wannan duniyar”. A yanzu kam idan ka cire baba da malaman nan kowa kuka yake jin wai zata kashesu, sukam ganin ƙwam bai musu rana ba. Wata irin gigitacciyar tsawa ta daka musu. Sake dunƙulewa sukai waje guda suna mai sake ƙan ƙame junansu, masu fitsari na sake sakin second round. Cikin ƙarfin hali shugaban malaman ya fara karanto suratul baƙara. Da rawar jiki wanda suka iya suka fara suma. Kecewa da dariya Alimah tayi, sai kuma ta haɗe rai tare da tafa hannunta ta buɗesu. Sai ga bakunansu sun ƙage kowa ya kasa magana. “Hahaha!! Ni zakuma karatu. Ni nan kuke tunanin ƙonawa? To kafin ku ƙonani ni bari na shafe babinku.” ta wani irin sake tafa hannaye sai ga wasu mugayen halittu na fitowa ta cikin bangwayen gidan a kowace kusurwa. Gaba ɗayansu sun gama rikicewa. Hatta da su baba a wannan gaɓar kam babu sauran jarumta a tattare dasu. Kowa zufa yake kashirɓan jiki na rawa Kaff-kaff kamar waɗanda aka kaɗama gangi. Yanda suke sake curewa waje guda sai sun matuƙar baka tausayi. Masu ƙarancin ƙarfin zuciya tuni sun fara sumewa dan ganin halittun nan kawai ba ƙaramin tashin hankali bane mai rikita tunani. Balle kaga kai suke dimfarowa tamkar mayuntan zakuna suna wani irin nishi da fesar da wuta a bakunansu. Suna gab da isowa garesu ta sake tafa hannayenta suka ɓace. Dariya ta shiga ƙyalƙyalawa tana kallonsu. Kafin ta wani irin fesa musu ruwa da hannunta data ware a kansu kamar mai musu daƙuwa. Sharaf suka jiƙe, waɗanda suka suma duk suka farfaɗo. Kuka ƴan maza suka shiga fashewa da shi suna roƙonta tayi haƙuri sun tuba ta yafe musu. Tamkar bata jisu ba ma ta koma jikin bango ta maƙale. Shugaban malaman nan ne cikin galabaita da sauke numfashi ɗai-ɗai ya ce, “Baiwar ALLAH kiyi haƙuri. Ki sani akwai hisabi tsakanin aljan da bil adam. Yanda makomarmu take a tsakanin aljanna da wuta haka kuma makomarku kenan. Mu bamu zo nan domin cutar dake ba. Dan ALLAH kema kada ki cuta mana. Bamu san komai tsakaninki da Jazool ba. Amma zamu roƙeki shima ki yafe masa, ki kuma fita a jikin matarsa dan ALLAH ki barsu suyi zaman aure kamar kowa.....” “Har abada hakan bazata faruba! Nace maka har abada! Har abada JJ bazaiyi aure ya zauna da wata mace ba. Kuma bazan taɓa iya yafe masa ba!!” sai ta fashe da wani irin mahaukacin kuka daya sake firgitasu da gigita su. Sosai tai kukan kafin ta ɗago kanta dake lulluɓe cikin dogon gashinta tana kallonsu. Ƙasa duk sukai da kawunansu. Muryarta na rawa da karkarwa ta ce, “Zan baku dama ta ƙarshe saboda wasu dalilai. A cikinku akwai bayin ALLAH, akwai masu ƙananan yara, akwai masu taimakon marayu, akwai masu ƙoƙarin bautama UBANGIJI, akwai masu ƙyautatama iyaye, akwai masu yawaita karanta Alkur'ani. Duk da dai akwai tamtirai irin JJ kuma sun san kansu. To sunci alfarmarku, zan barku ku tafi, amma ku sani, duk wanda ya sake gigin shiga gonata saina sabauta masa rayuwa. Alimah kuma kuje JJ ya fara sanar muku *_WACECE ANOOSH_*, ni da kaina zanzo gareku da Alimah. Kuma ku sanar masa ko ƙoƙarin yin ƙarya yay akan Anoosh ina gefensa zaisha mamakina, dan duk inda yake ina a tare da shi kamar yanda zuciyarsa da jininin jikinsa ke tare da gangar jikinsa. Na barku lafiya”. Ta wani irin harba hannunta kamar mai san ture abu. Sai gasu a tsakar anguwa an watsosu kamar kayan wanki. Wayyo ALLAH zo kaga yanda ƴan maza ke rige-rigen tashi suna cika wandunansu da iska. Sai dai kaji garamm an buga ƙofar gida an shige. Wasu ma ba gidajensu suke ƙoƙarin shiga ba. Sai mai gidan ya farga ya jawosu waje shi ya shige yana faɗin, “Tafi gidanka”. Su baba da su Malam daba anguwar sukeba kam sun ma manta da motocinsu kowa ƙafarsa ce motarsa har zuwa titi. Babu mai sauraren ɗan uwansa kowa ƙoƙarin tare abin hawa yake. Burinsu kawai su gansu a nasu gidajen suma......✍️ _🚴🚴🚴To Bara nayi takaina Nima dai, malam na neman ƙafar zuwa gida, ni kuma Bilyn ku fa🤣🤣😂😂_. Mura ta rikeni kwana biyu🤧🤧🤧. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha ɗaya_ .......Tun daga lokacin bata da wani buri sai na ganin ta samu ciki, amma shiru kake ji malam yaci shirwa. Tun tana irga wattani har aka koma shekaru babu amo babu labari. Kwaɗayin samun jika ya fara damun Hajiya Maryam, da kanta ta saka Kainaat da Abaan gaba suka bar ƙasar zuwa asibi. Doctor ya tabbatar musu Kainaat nada ƴar matsala a cikin mahaifa, dan wani ƙurji ne ya fito mata, zasu iya mata aiki, sai dai akwai haɗari gaskiya, zakuma su iya ɗorata akan magani idan da rabo a hakan ma ciki zai iya samuwa. Jin batun haɗari yasa Hajiya Maryam cewa a bata magani kawai, yayinda Kainaat tace ai mata aikin ita dai, dan tana buƙatar haihuwa tako wane hali. Amma sai Abaan ya nuna mata bata isa ba, maganar mahaifiyarsa za'abi. Hakan ya mata ciwo matuƙa suka tattaro suka dawo gida Nigeria ta fara shan magani. Sai dai a hakan shekaru biyu suka sake shuɗewa babu labari, dan haka Hajiya Maryam tace Abaan ya ƙara aure, idan da rabo watarana itama Kainaat ɗin zata haifa musu. Tofa babbar magana, wannan zance ya hargitsa kan Kainaat matuƙa, dan a duniya bayan son haihuwa abu na biyu shine mugun son Abaan da Kainaat keyi. Tana kishinsa na hauka da ko ita mahaifiyar tasa da ƙamwarsa baso take taga ya raɓesu ba, tana dannewa ne kawai saboda irin son da suke nuna mata ga dukiya mai yawa ta mallaka ta dalilinsu. A dalilin wannan batun aure Kainaat ta fara fiddo da wasu sabbin halaye a gidan marasa ƙyau, tun Hajiya Maryam na kauda kai har dai ta fara magana, sai Kainaat ta fara mata rashin kunya. Abu kamar wasa ya fara zame musu kamar gaba a tsakaninsu, har Kainaat na neman raba Abaan da su. Hankalin Hajiya Maryam ya tashi matuƙa, tako miƙe kan ɗanta da addu'a ta kuma hanashi cin abincin Kainaat dan Noor ta kamata tana zuba masa abu ranar a kitchen. Rikici tun yana ƙarami har ya zama babba, a haka akai auren Abaan da sabuwar amaryarsa. Sai dai tunda akai aure Abaan ya gagara kusantar matar tasa, daga baya ma ta fara wani irin ciwo maiban tashin hankali har sai da aka raba auren. Ana cikin wannan rikici labari yazo ma Hajiya Maryam kan ainahin iyayen Kainaat da alaƙarta da mahaifiyar Nadwa. Nan fa aka sake kwasar wani sabon rikici ta tsare Abaan akan ya saketa, dan ba matar aure bace. Wadda zata iya gudun iyayenta saboda suna talakawa ta canja iyaye ai komai zata iya aikatawa idan ta samu dama. Abaan baya ƙetare maganar Mamah, dan haka babu wani ja'in ja yayma Kainaat one shika (🤣inji gwanja ba). Baƙin ciki da ruɗani suka rufe idanun Kainaat ta hau zagin Hajiya Maryam da tabbatar mata sai ta sakata nadama akan raba auren nan, Noor batama san sanda ta wawwanka mata mari ba, yayinda a take nan Abaan ya ƙara mata saki biyu suka zama uku ciff. Abin kamar almara haka suka koro Kainaat a gidan, sai dai da yake bayin ALLAH nan sun gaji arziƙi duk abinda suka mallaka mata basu ƙwace ba, hakama wanda ta sata duk suka barta dan su irin arziƙine gadonsa sukai ba haye ba. Wannan shine dalilin rabuwar Abaan da Kainaat, tunda ta fito kuma bata dai nema iyayentan ba, saima gida data saya ta tare a ciki, suka kuma cigaba da mu'amula da su Nadwa, ga company da Abaan ya bata na kawo mata kuɗu sosai, wanda a yanzu haka shine Dafeeq ke a ciki da kuma burin mallaka shima. Yayinda Kainaat ta aureshi da burin yin auren kisan wuta, tare da wani burin kuma data baima zuciyarta ita kaɗai. Babban burinta kuma shine komawa gidan Abaan, kullum saita masa text message naban haƙuri da safe, da dare kuma na good night daban haƙurin dai. Bai taɓa nuna alamar ya gani ba balle ya kulata, bata iya kiransa kuma alamar ya tosheta, ya kuma ɗauki matakin hana baƙuwar number kiransa. hakama duk wani shifinsa na yanar gizo ya tosheta, amma hakan bai hanata cigaba da bibiyar duk wani motsinsa ta hanyar yaransa ba..... ★★★_____ Ƴan gidan Baba Hakimi ne sukaima Khadijah karar taruwa a gidan sunata kwantar mata da hankali, dan a cikin kwana biyun nan ta sake wata irin rama da baƙi tamkar ba ita ba. Bata da aiki sai kuka, dan gaskiya tana jin kishin mijinta matuƙa. Matsala ta biyu yanda ya tattarata ya sake watsarwa tun randa ya sanar mata zancen auren zamansu ya sake ɗaukar zafi. Takai yama bar cin abincin nata, ya kuma daina yini a gidan gaba ɗaya, ya koma kwana a doguwar kujera a falo. Hatta yau da zai tafi ɗaurin aurensa harya gama shirinsa ya fito ko kallonta baiyi ba. Sai itace ke binsa da kallo kamar zata cinyesa. Dan yayi mata masifar ƙyau cikin ɗanyar shaddar da ya saka fara tass. Ga hula ya kafa sai ƙyalli yake kamar namijin ɗawusu. Ana ɗaura auren ya tura mata saƙo kamar haka _(Duk baƙin cikin tanda dai sai munci waina. Masu hassada sai a haɗiyi zuciya a mutu. Dafeeq ya zama angon Hajiya Kainaat. Zaɓi ya rage mutum ya kwantar da hankalinsa a zauna lafiya yaci arziƙi shima ko ya yanki ticket ƙofa a buɗe take)_ sosai jikin Khadijah ya dinga rawa da ganin wannan saƙo, dole ta shige bedroom ɗinta jin zata faɗi ga mutane a gida. Kuka taci sosai tana sake karanta saƙon kamar mai bitar karatu, mamakin Dafeeq na neman halakata. Shin dama haka yake ko yanzu ne ya canja saboda kuɗi? Dan ita saima yanzu take jin wacece ya aura ɗin a wajen ƴaƴan baba hakimi. Sai dai har suka gama hirarsu batace komai ba. Jin kanta na neman fashewa ta haƙura da kukan ta gyara fuskarta ta fito, duk da ba hira take ba tana zaune a cikin su Aunty Kareema dai daketa cigaba da mata nasiha. Gab da magrib suna shirin wucewa gidajensu Dafeeq ya dawo gidan. Daka ganshi kaga sabon ango, dan sai ƙamshi yake bazawa. Sama-sama ya amsa tsokanar da suke masa babu kunya ya shige bayi yin wanka bayan ya shiga ya cire kayan jikinsa yasa jallabiya. Ganin hankalinsa ma ba'a kansu yake ba suka tattara suka wuce zukatansu cike da tausayin Khadijah. Koda ya fito bai kalleta ba, sai ma a gadarance yace ya tashi ta ɗiba kaya a akwati su wuce. Da mamaki ta ce “Ina kuma?”. A zafafe ya amsa mata da “Ban sani ba. Ban san rainin hankali. Ina faɗa miki ki tashi ki shirya kina tambayata ma ina?”. Karan farko taji bazata iya haɗiyewa ba ta ja masa tsaki, a tsiwace ta ce, “Babu inda zanje to, aikin banza makwaɗaici kaw....”. Kafin ta rufe baki taji saukar mari. Bata gama dawowa a hayyacinta ba ga sake sauke mata wani. Sai da yay mata uku a jere masu gigitarwa sannan ya nunata da yatsa yana magana tamkar zai haɗiyi harshensa. “K! Dan uwar ubanki har kin isa kirana kwaɗayayye? To ubanki mai ƙaton kan nan da shegen miskilanci ne kwaɗayayye dan uwarki ƴar iska. An gaya miki nima da sona zan ɗaukeki zuwa inda nake ne banza daƙiƙiya baƙauya da ko secondary bata iya ya gama ba akan saurayi. Wlhy badan Hajiya ta dage atare dake gidan can ba na tafi sai kinyi wata bama ki ganni ba balle ki iya mun rashin kunyarki na rashin tarbiyya. Zan kuma tabbatar miki dani ƙwaɗayayyen ne ƴar baƙin ciki da hassadar cigaban wasu. Yanda ubanki ya ƙare a talauce haka kike fata nima na ƙare ko. To sai dai ke ki ƙare a wahale wlhy, dan sai kinje, kuma zakiga hukuncin da zan miki”. Wani irin kuka mai cin rai da zuciya Khadijah ta durƙushe tanayi. A karo na farko tunda suka baro gida take jin kewar yin nisa da iyayenta. Gatan da sukai musu ita da ƴan uwanta ya shiga dawo mata a rai. A wannan halin Dafeeq ya fito cikin sabon ɗanyar shadda yana baza ƙamshi.... _________★ Tuni anguwar su JJ ta ɗauki ɗumi akan abinda ya faru daren jiya. Dan su baba da wanda suka bisu gulma da ƙyar suka sami kansu a safiyar yau. Masu baƙin surutu suka kasa haƙuri suka shiga bada labari. Kowa jinjina al'amarin yake da mamakin mi JJ ya aikata haka shi kuwa da zafi? Babu mai basu amsar nan sai JJ ɗin, shi kuma yana kwance babu lafiya. Dan mafi yawansu ana idar da sallar asuba mazan anguwa da sama suka shiga gaisheshi kamar yanda al'adar anguwar take. In dai baka da lafiya aka kuma sani to maza kan shiga dubaka bayan kowacce salla daga massalaci. Duk wanda ya shiga yakan samu JJ na kuka da ihun jikinsa naci da wuta. A taimakesa a zuba masa ruwan sanyi kada ya ƙone. A zahiri kam babu wani abinda ke faruwa da shi. Hankalin ahalinsa gaba ɗaya ya ƙara tashi, a take yara da manya suka taru a kansa ana masa addu'a. Da ƙyar aka samu kansa kusan sha ɗaya na safe. Yay shiru sai wani irin mugun zufa da yake yi dan cikin duk bayan mintuna ashirin yakam jiƙe abinda aka shimfiɗa masa kamar wanda aka watsama ruwa, sai an ɗauke an canja da wani. Yayi wata irin muguwar rama ta tashin hankali jikinsa yayi baƙi sosai duk da kuwa JJ fari ne sol da shi. Tuni ƙyawun fuskar nan tashi ta gushe, baƙin sajen nan dake ɗaukar hankalin ƴammata kamar ma ya fara furfurar wahala. Baka iya hangen komai a tattare da JJ sai ƙwala-ƙwalan idanu da haƙora tamkar dillalin aljanu. Baba dake share hawaye cikin kasa daurewa ya ce, “Jazool mika jawoma kanka haka ne da zafi? Mika aikata ne da har muma yake neman shafarmu? Jibeka dan ALLAH cikin kwanaki uku kacal halittarka ta canja gaba ɗaya. Jazool ka faɗa mana mika aikatama bayin ALLAHn nan? Wacece Anoosha? Miye haɗinka da ita da ka shiga irin wannan bala'i a dalilinta ne?”. Duk da azabar dake ratsa JJ da wahalar ciwo a firgice ya kalli Baba jin ya ambaci sunan Anoosh. Yaya Inusa ne ya karɓe da faɗin, “Ba kallonsa zakai ba Jazool, ka sanar mana wacece Anoosh? Kamar yanda baba ya buƙata. Minene haɗinka da ita? Dan bayin ALLAHn nan sun tabbatar mana da har sai ka sanar mana wacece Anoosh sannan zasu bada matarka. Dan ALLAH ka sanar mana ko muma ƴan uwanka zamu sami nutsuwar zukata da kwanciyar hankali. Jiba kaga Baba ko taka ƙafarsa baya iya yi saboda wahalar da mukasha tsakanin safiyar jiya zuwa yammaci. Jibi fuskar Mujetapha yanda ya kwaye kumatu saboda gudun ceton rai. Kalleni kaga raunuka biyu naji a tsakanin hannu da gefen cikina duk a dalilin gudun kuɓuta daga gidanka. Dolene akwai abinda ka aikata Jazool, in ba hakaba miyyasa saboda kai duk zamu shiga bala'in nan. Hatta su baba liman basu tsira ba suna gidajensu suna jiyyar kansu. Mazan anguwar da gidanka yake ɗai-ɗaine jiya basuyi fitsari a wando ba banda tashin hankalin da idanunmu ya gani. Jazool wacece Anoosh! Mika aikata mata ne!!”. Yaya Inusa ya faɗa cikin ƙaraji da kaushin murya jikinsa har yana rawa. Shima JJ ɗin rawa jikinsa ya farayi yana mai kallon duk wanda ke ɗakin. A ƙufule Yaya Mujee ya amshe da faɗin, “Garama ka faɗa Jazool, kai dolene ma saika faɗa mana mika aikata. Dan tace idan ma ka ɓoye wani abu tana anan tare damu dan akoda yaushe tana kusa da kai. Ya rage naka ka faɗa da arziƙi koka faɗa da wahala. Dan kaga dai yanda ka koma a cikin kwana uku kacal tamkar wani dilallin aljanu. Har muma ana neman sabauta mana rayuwa a dalilinka”. Wasu irin hawayene masu zafi suka shiga ziraroma JJ a idanu. Tamkar wanda ake controlling murya na rawa ya ce, “Anoosh budurwata ce. Mun haɗu a ranar babbar salla ta shekarar 2020 da ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Dan fitowarmu da ga salla kenan ni da su MB a anguwar su Gwaggonsa da mukaje gaidawa.......”✍️ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha biyu_ ..........Tafe take cikin nutsuwarta tamkar wadda ke tsoron taka ƙasar. Hijjab ne a jikinta har ƙasa fari tas. Idanunta da siririn farin gilashi da kasancewarsa bai hana bayyanar ƙyawun idanunta da girmansu ba gamai kallo. Sam bata da alamar hayaniya akan fuska, sannan da ga ganinta kasan bata da yawan magana akwai kuma kunya da tarbiyya tattare da ita. “Woow! Ya arrahaman kaga wata halitta!”. SJ ya faɗa. Da ga JJ har MB ɗagowa sukai suka kallesa. Dan su hankulansu nakan wayar JJ ne suna kallon hotunan da suka ɗauka a wajen idi. Maimakon magana ita ya nuna musu da yatsa, dan harta gotasu kaɗan. Su dukansu babu wanda zuciyarsa bata harba ba, sai dai kafin su farga har JJ ya zabura zumutt, tamkar ƙyaftawar ido sai gashi a gabanta. “Assalamu alaikum ƙyaƙyƙyawa”. Ya faɗa cikin wani irin murya mai taushi da amo. Ko kallonsa batai ba, sai dai ta motsa jajayen ƙananun laɓɓanta da babu komai a kansu sai lips gloss alamar amsa masa sallamarsa batare da yaji sautin muryarta ba. Rabashi tai ta wuce, kafin ya zabura ta buɗe wani farin gate dake gab da su ta shige abinta. Kansa ya dafe cike da takaicin kansa da kansa. Yayinda MB da SJ ke faman masa dariyar ƙeta. Yana tsaye a wajen suka ƙaraso suna cigaba da dariyarsu. SJ ya ce, “Tuku-tuku mugun icce! daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi. Banda ma cin amanar abota nifa na fara ganin yarinyar nan amma ka zabura kamar wani kafilfilo kazo kamun yankan baya. To sai ka kama kanka ai dan wannan fa ba irin motocin titi bace ba”. Harararsa JJ ya ɗan yi, batare da yace komai ba yaja guntun tsaki ya barsu wajen. Inda motarsu ke ajiye ya dawo, ya jingina cike da damuwa yana mai lumshe idanunsa. Sake biyosa su MB sukai nan ma suna dariya, har sai da ya ƙufula ya shige mota. Ganin zai tada suka shige suma, dan kaɗan daga aikinsa ya tafi ya barsu a wajen duk da kuwa motar tasu ce su uku, dan tare suka haɗa kuɗu suka saya dan kawai burge ƴammata. A hankali JJ ke murza steering fuskar yarinyar na masa waiwayi a cikin idanu, ko sau ɗaya ya gagara saka baki a zancen su MB har sai da yaji SJ ya ce, “Ai inaga fa Gwaggo Ladi na mutunci da mutanen gidan, dan ina ƙyautata zaton ko abincin data bamu take faɗin daga maƙotan can natane masu farin gate to daga gidanne kuwa”. ƙuwww!! Kake ji JJ ya taka birki. Har sai da sukai gaba su duka suka bigi jikin motar. MB dake baya ya dafe goshinsa yana murzawa a hasale ya ce, “JJ halan kana hauka ne nikam? Yanzu dan ALLAH saboda mace kake neman kashemu a ranar salla”. Shima dai SJ masifar ya balbalesa da shi, amma a mamakinsu ko'a jikin JJ, sai ma ƙoƙarin gangarawa gefen titi da yay saboda yanda ake masa horn ya tsarema mutane hanya. “Wai lafiya kake kuwa?”. MJ ya sake tambaya a ƙufule. Kai JJ ya girgiza musu a karo na farko. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Gidan Gwaggo zamu koma dan ALLAH”. Kallon juna MB da SJ sukayi. Sai kuma suka kwashe da dariyar shaƙiyanci. JJ bai damu ba, da kuma kafiya-lafiyane masifa zai fara musu. Suna ji suna gani ya karya kan mota suka koma gidan Gwaggo Ladi. Shi ya fara fita a motar ya nufi gidan, dan ba baƙonsu bane ba kasancewar sun saba zuwa duk salla. Wani irin zuzuzu JJ yaji sakamakon yin tozali da yarinyar nan zaune a tsakar gidan Gwaggo tana cin abinci. Fuskarta ƙawace da wani irin murmushi da ya sake fiddo ƙyawunta. “Jazool kunyi mantuwa ne?”. Gwaggo data farga da shi ta faɗa. Cikin sauri yarinyar ta ɗago kanta, dan sam ita ba ƙofa take kallo ba. Idanu ta waro, sai kuma ta fisgi hijjab ɗinta dake saman jarkar ruwa a gefe ta shiga kiciniyar sakawa. A dai-dai nan su MB suka shigo suna dariya. Suma turus sukai da ganin yarinyar, sai kuma suka wayance tare da kamo hannun JJ da yay sumar tsaye baima amsama Gwaggo Ladi tambayarta ba. Shigewar yarinyar falon Gwaggo ya Bama SJ damar matsawa kusa da Gwaggo yana ƴar dariya. “Gwaggo ɗanki fa yay gamo, dan yarinyar nan fa ta dawo damu”. Da mamaki Gwaggo Ladi ta dubi hanyar falonta, sai kuma ta juyo ta kalla Sj. “Wai Anoosh?!”. “Wannan dai data shiga falonki yanzu. In dai sunanta kenan to ita”. Tsaff ya kwashe komai ya sanarma Gwaggo. Murmushi Gwaggo keyi tana kallon JJ. Sai kuma ta kamo hannunsa ta zaunar kusa da ita. “Kaga kwantar da hankalinka Jazool. In dai Anoosh ce da yardar ALLAH ka samu kuwa. Na kuma tayaka murna dan yarinya ce mai tarbiyya da hankali. Sai dai bebiya ce dan bata magana amma tana ji. Tana kuma iya baka amsar da zaka iya fahimta ta motsin laɓɓanta. Zanfi kowa farin ciki da wannan al'amarin kuwa”. Ba JJ ba hatta su MB kallon Gwaggo suke jin wai Anoosh bebiya ce. Sai dai a cikinsu babu wanda yace komai. Gwaggo da bata lura da yanayin nasu ba ta ɗaga baki ta kira Anoosh dake cikin falo. Kusan mintinan biyu sai gata ta fito tana rabe-raɓe. Fuskar Gwaggo da murmushi ta nuna mata su JJ. “Anoosh waɗan nan ƴaƴana ne, sun zo min gaisuwar salla ne”. Jin jina kai Anoosh da idanunta ke ƙasa cikin gilashi tayi, sai kuma ta motsa ƙyawawan lips ɗinta a hankali alamar gaisuwa a garesu. Gwaggo ce ta sanar dasu tana gaishesu, cikin rawar lips suka amsa su duka, JJ kam yama kasa sai kallonta da yake kamar idanunsa zasu zubo ƙasa...... ____________★ Wani irin shurinta yay da ƙafa tare da cilla mata mayafi yace, “Tashi dan ...” ya mulmula mata ashariya. Ganin bata da niyyar tashi yay wani irin fisgarta tana tirjewa yana janta kamar wata dabba har waje. Kasancewar anguwar babu wuta gashi wata yay nisa ya buɗe motarsa ya cillata baya ya rufe. Gidan ya kulle shima ya zagaya mazaunin driver yaja motar a fisge. Har suka iso katafaren gidan Khadijah na kuka. Maigadi ya wangale musu gate ya shige. Koda ya fito nan ɗin ma janta yay zuwa ciki kamar abar banza, a wani haɗaɗɗen falo ya shigo da ita, ɗaki na farkon shigowa ya buɗe ya cillata ciki ya maida ƙofar ya kulle ya wucewarsa sama abinsa... Gaba ɗaya kukan da take ya tsaya cak saboda azabar wahalar buguwar da kanta yayi da gado a dalilin wullota da Dafeeq yayi. Tuni goshinta ya fara ɗigar da jini saboda fashewar da yayi. Kwanciya kawai tai yaraf tana sauke wasu irin ajiyar zuciya kamar wadda numfashinta ke barin gangar jikinta. Kafin dogon lokaci jikinta ya ɗime da zazzaɓi mai zafin tsiya. Gab-gab ta fara rawar ɗari saboda ac dake aiki a ɗakin. Tana kwance a cikin wannan wahalar take jin shigowar motoci da guɗe-guɗe alamar yanzu ne ma ake kawo amaryar. Zuwa can taji sun shigo falon. Yanda suke shewa da arerewa yasata fahimtar bama su da yawa ƴan rakkiyar amaryar. Zuwa can taji kiɗa ya fara tashi, sai kuma ta jiyosu suna ihu da shewar ango-ango. Hakan ya tabbatar mata da Dafeeq ne yaje inda suke kenan, da alama ma rawa yake shi da amarya kamar yanda take ji a kalamansu. Kusan awa biyu da wasu mintinan suka ɗauka a gidan, dan sai sha ɗaya taji gidan ya ɗauki shiru. Daga haka bata sake jin motsin kowa ba har dare ya raba tana dai kwance a wajen jinin dake ɗiga a goshinta ya fara rinjayar idanunta alamar jiri... A ɓangaren amarya Kainaat da ango Dafeeq kam bayan wucewar ƙawayenta su Nadwa cak ya ɗagata daga tsakkiyar falon cikin kuɗin da suka musu liƙi yay sama da ita. Dan Kainaat dai bata da jiki sosai can, amma fa a murjenta take suɓul-duɓul kamar alalar gwangwani. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce da ita suna faman sakarma juna murmushi, ya direta a tsakkiyar gadon yana hakki, dan duk da bata da ƙiba tanada nauyi, ƙarfin haline kawai da son ya birgeta ya sashi jurewa har ya kawota nan. Haƙuri ya bata akan bari yaje ya ɗakko wayoyinsu. Ta jinjina masa kai tana murmushi. Gudu-gudu sauri-sauri ya dawo falon, sai da ya waiga bayansa ya tabbatar Hajiya bata biyosa ba sannan ya durƙusa ya tattare dollars ɗin da ƙawayenta suka musu liƙin da ƴan dubu-dubu sabbi ƙal. Taf ya cika hularsa harda dannawa da ƙyar, bakinsa a washe dan yasan waɗan nan kuɗin ba ƙaramin kuɗi bane ba. Wayarsa da tata dake a Centre table ya ɗauka ya koma saman bayan ya kashe fitulin falon da kwasar ledojin kayan sayen baki. Da dabara ya zira hannu daga waje ya kashe wutar ɗakin sannan ya shiga, kai tsaye gaban gadon yaje ya tura hularsa mai ɗauke da kudin nan ƙarƙashin gadon sannan ya ajiye sauran kayan yana ƴar dariya da faɗin wasu maganganu wa hajiyar tashi irin shi ya kashe fitilar ne duk a cikin soyayya. Kainaat bata damu ba, dan itama dai zuciyarta ta tafi wajen tunanin ta yanda zata zille masa ne. Sai da ya gama ɓoye kudinsa da ƙyau ya kunna fitilar... Anci ansha tsakanin amarya da ango. Sannan ya buƙaci suyi salla. Kai tsaye tace masa tana period. Ƙarara taga damuwa a fuskarsa, a ranta tace shege ai maganinka zanyi, dan daga gani mayen yaro za'ai anan. Suna haɗa ido ta sakar masa murmushi, shima dai mayar mata yayi cikin yaƙe. Jiki babu laka ya tashi ya canja kayansa zuwa na barci, itama yaje ɗakinta ya ɗakko mata. Amsa tai ta shiga bayi ta canja, bata fito ba sai da ta turama Abaan saƙo kamar yanda ta saba a kullum naban haƙuri da good night. Koda ta fito bata kula Dafeeq ba ta kwanta, dan zuciyarta ta tafi wajen Abaan ne kamar yanda ta saba a kowane dare bata iya barci sai da tunaninsa, mafarkinsa shine abin yinta a kullum kuma. Babu zato babu tsammani taji Dafeeq a jikinta, hankalinta ne ya tashi, ta shiga son turesa, amma ya tabbatar mata shifa ko rage zafine sai yayi gaskiya. Bataƙi ba anan, dan koba komai tana kewar abokin rayuwarta, musamman daya kasance ita bata iskanci ko'a yanzun. Dafeeq shegen yaro ne, dan sai da yay yanda yay ya shagaltar da Kainaat har ya binciketa yaji babu wani period da takeyi batare data fargaba sai jinsa tai yana ƙoƙarin kai hari. Hankalinta ya tashi matuƙa, ta shiga turesa amma ya nuna mata shi sabon jinine, sannan ƙarfi ba'a shekaru yake ba, namiji kuma duk ƙankantarsa dai sunansa namiji... ★ Busowar iskar asuba mai sanyi da ni'ima ta farfaɗo da Khadijah. A hankali ta shiga buɗe idanunta tana karanto addu'a. Ganinta ba'a ɗakinta take ba ya sata maida idanunta ta rumtse komai na dawo mata dalla-dalla. Hawayene suka shiga sakko mata, itafa har yanzu kallon komai take kamar almara. Sannan wani gefe na zuciyarta na tabbatar mata Dafeeq ɗinta baya cikin hayyacinsa. Dole ne matar nan asiri ta masa. Ɗari bisa ɗari ta yarda da wannan tunanin, dan haka ta yinƙura ta tashi da ƙyar. Goshinta ta shafa, jinin ya tsaya, sai dai wajen ya mata nauyi kuma yana mata raɗaɗi. Mikewa tai gaba ɗayanta cikin ƙarfin hali ta nufi bayi. Bata damu da kallon ko'ina ba dan komai baya birgeta a gidan duk da ita kanta tasan ya haɗu. Ta jima tana kallon kanta a madubi kafin ta wanke busashen jinin goshinta zuwa fuska. Ashema raunin da taji ba wani babba bane can sosai. Alwala tayo tazo tai sallar asuba. Daga haka ta jingina da gado ta fara rera kuka, sai da taji kanta na barazanar tarwatsewa sannan ta haƙura. Har rana ta hasko windown ɗakin bataji motsin kowa na gidan ba, ga shi ya kulleta ta baya, dole ta haƙura ta zubama sarautar UBANGIJI ido kawai.......✍️ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha uku_ _ADVERT👇_ _YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_ _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_ _MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_ _*YERWA INCENSE AND MORE*_ _DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._ _AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_ _ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._ _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_ _NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_ _YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED _____________ .........A ɓangaren amarya da ango kuwa kowa ya tashi da mabanbancin yanayi. Ango na cikin farin ciki da nishaɗi, duk da kuwa ya shaida ya kuma tabbatar da amarya fa batako kama ƙafar Khadijahn sa ba. Dan a daren jiya ya tabbatar da zancen nan na mata sun bambanta. Tunda yake da Khadijah bai taɓa ganin tasha wani magani domin gyara jikinta ba yanda yake jin mata nayi, har bincike yasha mata amma bai taɓa cin karo da komai ba. Amma yarinyar nan ALLAH yay mata baiwa ta musamman da shi kaɗaine yasan wannan sirrin. Amarya kam da fushi ta tashi, duk da ango yayi wasan kura da ita tamkar ba ƙaramin yaron data raina ba taji a ranta Abaan ɗinta daban ne. A lokacin data samu kanta a hannun Dafeeq hawaye taitayi, dan gani take taci amanar Abaan ne. Ta jima tana hawayen kafin barci ya saceta. Basu farka ba sai yanzu da hasken rana ya hasko windown ɗakin. Itace ta fara tashi, ta zubama Dafeeq dake barcinsa hankali kwance ido ƙurr tamkar mai son tantance wani abu a jikinsa. Zuwa can kuma taja siririn tsaki tana ƙoƙarin sauka a gadon caraf taji an riƙe mata hannu. Da sauri ta jiyo, sai ko suka haɗa idanu da Dafeeq. Murmushi ya sakar mata ita kuma ta ɗan kauda kanta. Lips ɗinta dake motsi alamar tana son yin magana ya zubama ido, kamar wanda ya gama karantar abinda take son faɗa ya wani fisgota ta dawo baya. Idanunta ta rumtse da ƙarfi, cikin son sassauta fushinta ta ce, “Ranafa tayi, gashi bamuyi sallan asuba ba”. Bai tanka mata ba, sai ma shigewa jikinta yay da jan bargo ya rufesu yana magana cikin kunnenta a hankali. Idanu ta waro waje tana turesa a jikinta. Amma ko gezau, sai ma abinda yay niyya ya fara aiwatarwa. Tana ji tana gani sai da yay yanda yake so da ita kafin ya kalleta yana dariya cike da shaƙiyanci. “Hajjaju karfa ki manta sadaki na biya”. Harara ta zabga masa, a zuciyata tana faɗin (kaji ɗan iskan yaro. Ka biya kona biya maka) kamar yasan mi take faɗa, ya wani lakace mata hanci da faɗin, “Duk da fa ke kika bani na biya ni ne dai na biya a idon kowa”. “Hummm”. Tace kawai tana mai yunƙurawa ta tashi, da kallo ya bita harta shige toilet. Jin ta rufo ƙofar harda murza key yay wani kalar kwashewa da dariya. Sauka yay a gadon ya jawo handbag ɗinta mai ƙyau sosai. Tsaff ya bincike jakar, babu komai a ciki sai gold nata da ƴan kunne da sarƙa da su awarwaro data sanyo jiya da dare, ya jima yana kallonsu kafin ya wani taune lips ya maida ya ajiye. Da kansa ya gyara gadon, gamawarsa dai-dai tana fitowa. Baiyi magana ba ya shige bayin. Shima dai wankan yay ya fito, bata ɗakin, ta kuma ɗauke handbag ɗinta. Salla ya gabatar, sannan ya jawo hularsa dake ƙarƙashin gado ya shirya ƙuɗaɗen jiya tsaff ya nufi wadrobe ya ajiyesu a ƙasan kayansa. Cikin ƙananun kaya ya shirya. Kai tsaye ƙasa ya sauka yanata bulala ƙamshi, ɗakin da ya jefa Khadijah jiya ya nufa, yasa key ya buɗe... Tana zaune a inda tai salla har yanzu, gyangyaɗi take ga hawaye sun bushe mata a fuska. Idanu ya zuba mata na tsawon minti ɗaya. Haka kawai yake jin wani iri a ransa mai kama da tausayi. Da kyar ya ture tunanin gefe dan kuwa duk abinda ya shirya bazai fasa ba. Khadijah tana cikin plans ɗinsa akan mallakar Hajiya da komanta, sannan ita kanta Khadijah yay alƙawarin sai yay punishing nata akan baƙin ciki da hassada da kuma maganganun data gaya masa jiya dan nan gaba ta kiyaye. Saboda shi dai yasan wannan yaƙin da zaiyi sai tafi kowa mora ai. Saukar mari ya saka Khadijah farkawa a gigice. Yanda take shuri yasa Dafeeq daka mata tsawa. Babu shiri ta nutsu, dan harga ALLAH tana tsoron Dafeeq. Saboda tafi kowa sanin baida mutuncin. Gaidashi ta shiga yi jikinta na mazarin rawa. Bai amsa ba, sai harara daya zuba mata ya juya zai bar ɗakin yana bata umarnin ta biyoshi. Sai da ta share hawayenta sannan ta miƙe ta biyoshi, dan tayi alƙawarin matar nan tasa bazata taɓa ganin kukanta ba, yanda ta ƙwace mata Dafeeq da asiri itama zata ƙwato abinta da addu'a. Babu kowa a katafaren falon, sai ƙamshi mai daɗi da sanyin safiya. Wani banzan kallo yama Khadijah da nuna mata wata hanya. “Ga kitchen, ki haɗama amaryata break fast mai ƙyau da daɗi, awa ɗaya na baki. Bake kina da bakin yimin rashin kunya ba, zaki gane kuranki ne”. Komai batace masa ba ta raɓa ta gefensa ta wuce. Da kallo ya bita ƙasa-ƙasa harta shige, sai kuma ya kalli inda Hajiya take tsaye tamkar sai yanzu ne ya ganta. Kainaat da tun fitowarsu da ga ɗaki itama take sakkowa ƙasa da mamaki take kallon Dafeeq da shima tun fitowar tasu ya ganta amma ya basar. Kamar bazatace komai ba, sai kuma fuska a yamutse ta ce, “Dafeeq wannan fa?”. Tasowa yay ya kama hannunta, kamar wata ƴar yarinya ya kawota ya zaunar a cikin kujera. Zama yay shima kusa da ita yana wani kwanta mata a jiki. Idanunsa a lumshe yana shinshinar ƙamshinta ya ce, “Uwargida”. Idanu ta waro sosai, dan duk da tasan matarsa ance mata yarinya ce batai zaton haka sharaf ba sosai. Dan Khadijah nada ƙaramin jiki, sannan bata cika tsayi ba can. Idan ma baka sani ba bazakace takai 19years ba yanzu. Tana kallon fuskarsa sosai ta ce, “Haba Dafeeq. Yaya zaka saka matarka mana girki. Ni fa ban aureka dan ka wulaƙanta matarka ba, fatana ma mu haɗe kai mu zauna lafiya”. “Nima burina kenan hajjaju, sai dai ta nuna ita ba haka take buƙata ba. Jiya ban san munafukin daya kai mata hotonki ba na samu bata gida da yammar nan bayan gama ɗaurin aure. Sai bayan magriba ta dawo bata san zata saman a gida ba. Koda na tambayeta ina taje sai cewa tai gidan Baba Hakimi. Na ƙwace jakarta na duba sai ga ƙulle-ƙullen maganin asiri da hotonki da nawa, wai mu zata kai gidan boka ama asiri yarinyar nan”. Ruɗewa matuƙa Kainaat tayi, dan duk da tasan itama ta taɓa yima Abaan asiri bada kanta taje wajen bokan ba, Mommyn Nadwa ce ta aiki mai aikinta. Kuma tun daga nan bata sake amsar wani maganin tsubbu ba, wancan ma tayi ne dan bata da mafita akan Abaan. A tsorace sosai ta ce, “Na shiga ukuna ni Kainaat wajen boka kuma? Baby dan ALLAH idan da matsala ka sakan kawai nan da sati guda. ALLAH ina masifar tsoron harka da masu asirin nan”. Wata dariyar ƙeta Dafeeq yay a ransa, dan Kainaat bata san yasan duk manufarta na auren kisan wuta bane ba. A zahiri kam sai ya gimtse fuska kamar zai yi kuka. “Haba-haba Hajjaju daina wannan batu dan ALLAH. Ai ni da ke mutu ka raba takalmin kaza. Sai dai wata ƙaddara kuma amma bata wannan shashashar ba mara aji. Ki barni da ita zan horata a gidan har sai ta zama baiwarki, kema kuma na baki damar sakata duk aikin da kike so dan ki sallami masu aikin gidan nan suje su huta ita zata cigaba dayin komai”. “Kana ganin babu wani damuwa baby”. Kansa ya jinjina mata da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke a zahiri. A baɗini kam zuciyarta ce ke tafarfasa. Bata auresa dan shiga sabgar matarsa ba, balle ma wannan cilikowar da ko autan gidansu ya girmeta, ko shi Dafeeq ɗin sai dai suyi sa'anni da autansu balle ita. Amma kuma dolene kafin ta rabu da Dafeeq ta barma yarinyar nan tarihin ruwa ba sa'an kwando bane ba. Har ita zata kai gidan boka. An faɗa mata zama tazoyi ne. Fitowar Khadijah da tray bayan kamar awa ɗaya yasa Kainaat zuba mata ido, a cikin sakanni ta gama tsara gwada Khadijah taga shin da gaske yarinyar kishi take da ita ɗin.... ________★ Gwaggo ita ta shigema JJ gaba wajen mahaifiyar Anoosh, dan kuwa mahaifinta ya rasu. Akwai mutunci da girmama juna tsakanin Hajiya Lailah da Gwaggo. Dan Hajiya Lailah na ɗaukar Gwaggo tamkar uwa a anguwa. Bata huɗɗa da kowa sai ita. Jin JJ nada alaƙa da Gwaggo ta bashi damar neman soyayyar Anoosh. Tare da roƙonsa kar yaci amarta. Ya mata alƙawarin da tabbatar mata sai dai ya zamewa Anoosh garkuwa bawai shi ya kutsama mutuncinta ba. Kalamansa sun tasirantu a zuciyar Hajiya Lailah, dan haka taji ta sake yarda da JJ. Dan kuwa dai da fuskar musulinci yaje gabanta. Anoosh dai ita kaɗai iyayenta suka haifa. Mahaifinta ya rasu tun tana ƴar shekara bakwai a duniya. Mahaifiyarta Hajiya Lailah ta cigaba da kula da ita da bata tarbiyya duk da ta sake aure. Mahaifin Anoosh ya bar dukiya mai yawa, dan haka sabon mijinta yay amfani da wannan damar ya mamaye komai ya gudu. Lokacin Anoosh nada shekara goma. Wannan abu ya ƙona zuciyar Hajiya Lailah matuƙa, gashi bata san a ina zata nemosa ba, dan irin auren nan sukai na ƴan birni, tasan dai sunan garinsu amma bata taɓa zuwa ba shi kuma bai taɓa kaita ba. Gidansa da yake da matarsa zaune kuma sai bayan ya gudu tama san ba nashi bane, ya kwashe iyalan nasa sun gudu tare ashe haya yake. Haka taci kukanta ta haƙura dan ya bar mata takardar saki har uku. Taimakon da ALLAH yay mata sune sarƙoƙinta na gold da bai gani ba, wanda takema ɓoyo na tsiya, su kansu takardun kaddaririnsu ɓoyesu take, amma bata san yanda akai mijin nata ya gano takardun ba ya kwashe. Sarƙoƙin nan ta ɗiba dan hatta gidan da suke ciki ya sayar, ta tattara ƴarta mai lalurar rashin magana suka nufo garin Kano. A motar hayar da suka shigo ta haɗu da Gwaggo dake ta jan Anoosh da hira. Ance mai ɗa wawa, tuni Hajiya Lailah taji ƙaunar Gwaggo ta shigeta. Bayan sun iso Kano kowa ya sauka, Gwaggo tai musu sallama tanayi kamar karta rabu da Anoosh dan yarinyar ta shigar mata rai sosai, ga tausayi. Yarinya ƙyaƙyƙyawa ta gaske amma babu bakin magana. Har Gwaggo ta shiga napep Hajiya Lailah ta dakatar da ita. “Dan ALLAH Baba idan bazaki damu ba zan so mu biki gidanki”. Ɗan jimm Gwaggo tai tana kallonta, sai kuma tai murmushi da faɗin, “Karki damu shigo” dan dama ta lura matar na cikin damuwa tun a mota. Sosai Gwaggo ta karramasu, hakama mijinta. Bayan kwana biyu Hajiya Lailah bata ɓoye musu komai ba a kanta. Su Gwaggo sun tausaya mata, sun kuma cigaba da zama da ita a gidan har na tsawon wata bakwai, daga baya aka samu wannan gida dake kusa da su Gwaggo masu gidan zasu tashi sakamakon rasuwar mai gidan Hajiya Lailah ta saida gold nata suka saya. Duk da komawarsu wannan gida akoda yaushe Anoosh na nane da Gwaggo. Anoosh yarinya ce mai haƙuri sosai, bata da yawan hayaniya. Ga yawan murmushi. Duk da kasancewarta bebiya tana karatu, dan a yanzu haka ma jam'i takeyi anan b.u.k tana 100 level, suna gab da shiga 200. Tana da kaifin basira, gata ƙyaƙyƙyawa, duk wanda ya santa ya santane cikin hijjan akoda yaushe. Dan ko'a cikin gida zaka iya samunta da hijjab, sai ma idan Gwaggo ce ta tirsasa mata cirewa tasha iska. Shekararsu ɗaya a anguwar mijin Gwaggo ya rasu, mahaifin MB yaso ta tashi amma taƙi saboda su Anoosh, ga shi kuma gidansu ne sannan bata taɓa haihuwa ba. MB ba zuwa gidan yake ba sai salla-salla. Wani lokacin ma akanyi shekara biyu bai zo ba saboda karatunsa. Kusan yanzun ma hakanne, dan shekararsa biyu kenan rabonsa da gidan shiyyasa bai san batun su Anoosh ba sam. Sj da su JJ abokan juna ne da suka zama ƴan uwa ma. Dan anguwarsu ɗaya, tare sukai secondary school suka kuma wuce ƴar aduwa University katsina karatu. Akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu, dan tun suna secondary sun iya yaudarar ƴammata. Iyayensu basu taɓa damuwa da abinda sukeyi ba, dan ana kallonsa a shirmen ƙuruciya har suka kammala secondary. Shigarsu JJ jami'a alƙibalarsu ta sauya, dan kuwa sunzo inda babu uwa babu uba babu wani ɗan uwa mai tsawatarwa. Ƙoƙarinsu a aji da iya gayu gasu ƙyawawa ya fara jan hankalin mata garesu, to dama gasu gwanayen yaudara. Tun ana iya yaudarar har suka fara huɗɗa da matan, takai in har zasu koyar da yarinya karatu sai sunyi duk yanda zasuyi sunyi amfani da ita. Tun suna samun irinsu har suka fara hure kunnen salihan yaran mutane. Al'amarin su ya gawurta dan har kawalci sukema malamai. Wannan hali nasu yasasu zama ƴan gaban goshin malamai, dama kuma gasu da ƙoƙarin su. Sun kammala karatunsu lafiya suka baro Katsina ana kewarsu, koda suka dawo gida maimakon abu yay sauƙi saima ya cigaba. Dan kuwa ALLAH ya taimakesu sun samu aiki da taimakon wani lecturer nasu da suka dingama kawalcin students. Duk da aikin ba wani bane koyar da yarane a makarantar boarding babu musu suka amsa. Wannan ma wani lasisi ne na cigaba da lalata yaran mutane a cikin makaranta da wajen makarantar ma, dan in har suka kwallafama yarinya sai sun cimma burinsu a kanta. Sai akai sa'a sunfi samun irinsu lalatattu, wanda suke lalatawa ta yaudara ƙalilanne. A yanzu haka suna shekara ta farko da fara aiki, sun haɗa kuɗi sun sayi mota acewarsu matan sunfi amincewa da mutum idan yana da mota.......✍️ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha huɗu_ ........Sannu a hankali JJ ya fara shiga jikin Anoosh, tun bata kulashi harta ɗan fara sama-sama ganinsa kamar mutumin kirki. Dan a duk sanda zai zo gareta shigar mutanen ƙwarai yake yi, sannan kuma da fuskar musulinci. Bai sake yarda su MB sun masa rakiyya ba. A kuma gidan Gwaggo ake hirar. A haka suka share wata kusan uku, zuwa lokacin Anoosh ta fara sakin jiki da JJ sosai. Da wannan damar yay amfani ya dinga zuwa yana kaita school, idan ta gama lectures yaje ya ɗakkota ya maidota gida. Ganin babu wata matsala Hajiya Lailah ta barsu, sai dai tana saka musu ido sosai, sai da ta sake tabbatar da babu matsala sannan ta samu nutsuwar zuciya. Ta kuma faɗima JJ ya shirya Anoosh na shiga 300 level zata mata aure, karatu ta ƙarasa a ɗakinta. Ya nuna jin daɗinsa da hakan a zahiri, a baɗini kam dariyama abin ya bashi. Tayama kamarsa shi JJ mai buhu-buhu na ƴammata lafiyayyu dake binsa da roƙo ya ƙare da auren bebiya mai raunin gani sai da gilashi. Duk da dai Anoosh nada ƙyau sosai baya jin zai iya wannan sadaukarwar, adai cigaba da tirzawa ya samu abinda yake so yay gaba abinsa. Tun daga randa Hajiya Lailah ta masa batun shirin aure ya fara hillatar Anoosh akan ta ɗan dinga saka mayafi mana, taya shi da zai aureta ace baida ikon ɗan ganinta kamar yanda sauran ƴammata kema samarin su yaji daɗi. Takan nuna masa ita bazata iya ba tana jin kunya, sai ya koma nuna mata to idan ta shigo motar tana cire hijjab ɗin in ya kaita school sai ta maida. Nan ma ta nuna bazata iya ba, yay fushi sai da ya kwana biyar baya kiranta a waya dan dama vc sukeyi, baya zuwa kaita makaranta. Tun abin baya damunta harya fara, dan da gaske JJ ya dasa rassan ƙaunarsa a zuciyarta ta yanda bazata iya cisgeshi ba koda taso hakan. Koda Hajiya Lailah ta lura da yanayinta da kuma daina ganin JJ na zuwa ta tambayeta sai cewa tai yayi tafiya ne. Murmushi kawai Hajiya Lailah tayi, tana mai jin tausayin ƴar tata dan ta fahimci itama irinta ce mai zurfafa soyayya akan mutum. Zata tayata da addu'a ALLAH ya sassauta mata, dan ita taga illar zurfafa soyayya wa namiji. A kwana na shida JJ yazo sakamakon kiran da Anoosh taima SJ ta vc tana kuka tace ya bashi haƙuri. Ƙin mata magana da dariya yay har ya kaita makaranta ya ajiye, haka ta nufi aji jiki a saɓule. Bayan ta gama lectures nata ta kirashi kamar yanda ta saba, uhumm kawai yace mata ya yanke kiran. Babu jimawa sai gashi nan ga fuskarsa babu alamar yasan minene dariya. Sosai ta sake shiga damuwa, dan haka suna shiga mota ta zare jijjab ɗinta hawaye na cika mata ido. Amma yaya zatai bata son cigaba da ganin ɓacin ransa. Sannan kuma a ganinta da wautar tunaninta ko addini ya yarda wanda zai aureka ya ganka. Wata irin wawuyar ajiyar zuciya JJ ya shiga saki a jajjere jikinsa na tsuma, dan kuwa tabbas Anoosh cikakkiyar mace ce data amsa sunanta mace. Irin matan nan ne da ALLAH ya azurta da ƙira ta asalin gwalbar fantar da ake faɗi. Dan duk da tana a shekara ta Ashirin ko ina na Anoosh cike yake dam gaba da baya. Ga wata lafiyayyar fata mai santsi da ɗaukar ido a dalilin yawan zama cikin hijjab. Gata fara tas tamkar madarar shanu sabon tatsa. Kai komai yaji dai, rashin magana da raunin idanu ne kawai tawayar Anoosh a rayuwa. Amma shi kam ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba to a wajensa Anoosh ta cika harta zarta a ɓangaren halittar jiki. Da ace tana magana kuma idanunta na gani ras kamar a kowa shikam babu abinda zai hanashi yin wuff da ita. Jin yay ɗiff yasa ta ɗagowa ta kallesa. Da sauri ya ɗauke idanunsa dake mata kallon ƙurilla da gaba ɗaya ya kaucema shari'a. A kasalance yaja motar suka tafi. Sai da sukaje ƙofar gida ya ce, “To sa hijjab ɗin”. Jikinta har rawa yake ta saka, dan tunda take a rayuwa bata taɓa shiga takura da matsuwa ba irin yau. Tana gama sakawa ko sallama batai da shi ba ta buɗe motar ta fice tana cin tuntuɓe. Rakata yay da wani makirin murmushi yana zuƙar baki kamar wanda yaci yaji, dan maganar gaskiya ta kwance masa lissafi. Baya jin akaf ƴammatansa ya taɓa cin karo da mai irin surar Anoosh... _________★ A hankali ta fito daga kitchen ɗin hannunta ɗauke da tray. Rawa jikinta ya nema farawa sakamakon sauka da idanunta sukai akan Dafeeq dake kwance a cinyar Hajiya hannunsa cikin rigarta ita kuma tana wani shafa masa kai. Khadijah ta haɗiye yawu da ƙyar zuciyarta na faɗa mata (Khadijah ki dake, karki bada wata ƙofar da matar nan zata rainaki) da wannan shawarar ta zuciyarta ta samu ƴar nutsuwa. Batare data sake kallonsu ba ta ƙaraso inda suke ta ajiye tray ɗin. Hajiya dake binta da wani irin ɗan iskan kallo ta saki wata shegiyar ƙara ta iskanci tana ƙanƙame kan Dafeeq saboda abinda yake mata. A rikice Khadijah ta ɗago zuciyarta na wani masifar harbawa. Da sauri ta juya musu baya tana ambaton sunan ALLAH ganin iskancin da sukeyi a gabanta. Zuciyarsa kam tuni ta shiga wutsilniya a ƙirji tamkar zata fasashi tayo waje. Batama san ta saki wani shegen tsaki ba ta nufi barin wajen cike da sassarfa kamar zata faɗi. Sai lokacin Dafeeq ya ma farga da ita. Ji yay wata irin kunyar Khadijah ta lulluɓesa. Zaram yay ƙoƙarin tashi Hajiya Kainaat ta kanainaye sa cikin kissa da salo irin na manyan mata da suka san takan duniya. Tuni yamanta da batun Khadijah ya shiga maida murtani. Tsabar iskanci a falon nan suka shiga fagen yaƙin ƙasa da ƙasa. Sai ga Kainaat na kurma uban ihun da bataiba a daren jiya duk dan ta haukata Khadijah. Shima dai Dafeeq tuni ya saki layi dan Hajiya ta ɗakko wata hanya ne dake tabbatar masa da yaro-yaro ne. Kuka Khadijah ta fashe da shi da saka hannuwa duka biyu ta toshe kunnenta, dan gaba ɗaya sun cika gidan da ihun rashin mutunci. Kuka take sosai tana faman toshe kunne amma hakan bai hanata cigaba da jinsu ba. Ganin zuciyarta zata iya tarwatsewa dan Khadijah nada kishi sosai ta tashi a guje ta fito a ɗakin. Da rawar jiki tabar falon dan batai zaton anan suke iskancinsu ba. Cikin hajijiya da jiri ta fice aguje da ga falon, sai dai tana isa gate maigadi ya hanata fita, acewarsa Hajiya bata bada damar kowa ya fita ko ya shiga gidan ba. Ran Khadijah ya sake ɓaci, ta shiga zagin maigadi amma yay biris da ita. Dole ta zube a wajen tana kuka mai cin rai da zuciya. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sake komawa wujiga-wujiga kamar ba Khadijah ba. Bata taɓa sanin tanama Dafeeq irin wannan mahaukacin son da kishin ba sai yau. Ji take zata iya kashe Hajiyar nan. Kai har kanta ma da Dafeeq ɗin sai dai kowa ya rasa iyayensa suyi asararsa. Tana nan zaune a tsakar harabar gidan taci kuka harta godema ALLAH Dafeeq ya fito. Wani shegen taku na rashin mutunci yake yi da gadara da isa. Babu magana babu komai yana zuwa gabanta ya wani irin ɗauketa da mari. Kafin ta gama dawowa hayyacinta ya fisgeta zuwa cikin gidan. A falo ya watsar da ita kamar mara daraja, Hajiya na zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya. Kallo ɗaya tai musu ta watsar ta cigaba da danna wayarta. Sake ɗauke Khadijah yay da mari. Sai lokacin Kainaat tai magana a yamutse. “Baby nifa dama ka ƙyaleta wlhy, ba kanta ta ganarmawa ba. Kaga gobe idan taji ihun ma'aurata saita kiyayi fito musu banza ƴar iska. Ƙarama dake kin iya son kallon haram. To Alhmdllh sauƙin ma dai Baby sadaki ya biya ya auran ba baɗala muke ba.” Wani mugun kallon banza Khadijah da taƙi kuka duk da marin da Dafeeq yay mata ya shigeta ta sakarma Kainaat da jajayen idanunta. Sai kuma taja tsaki da ɗauke kanta batare datace komai ba ta miƙe. Tsawa Dafeeq ya buga mata cikin ihun faɗin, “Dan ubanki na sallameki ne?”. Ko gezau Khadijah tai wucewarta. Hakan yasa Kainaat sake tabbatar da yarinyar nan lallai shegiyar kanta ce. Dariyar tunzura Dafeeq ta saki da faɗin, “Yaro yaro ne, kaga kaima ta nuna maka baka isaba kenan. Yarinya aiki ya sameki kuwa in dai kikace da Kainaat zakiyi kishi sai dai kare ya mutu da haushin kura.” Cak Khadijah ta tsaya, ta haɗiye kukan dake neman ƙwace mata tare da juyowa ta na kallon Kainaat a wulaƙance. Sai kuma ta saki murmushin ƙularwa. “Tabbas karen kuwa zai mutu da haushin kurar ballagazar tsohuwar daƙiƙiya. Bari na baki fassarar zancenki dan naga girman shekarun ne kwai babu wayo a tare da ke. Ai kece karen, Khadijah kuma kura, kibar ganin asiri yay tasiri akan mijina yanzu, watarana ke da kanki zakiyi nadamar yinsa, dan Dafeeq nawa ne har abada, ki ɗauka yanzun ma aro na baki kafin na shafe babin tarihinki guzumar tsohuwa mai auren ɗan cikinta kawai”. Matuƙa maganganun Khadijah sun ƙonama Kainaat zuciya. Ta kalli kanta da ƙyau, dan a duniya ta tsani a kirata wai tsohuwa. Amma sai gashi harda su guzuma ma wai da ballagaza. Sannan yarinya ƙarama da inda auren wuri tai zata iya haihuwar kamartace ke faɗa mata magana haka akan wani banzan namiji data aura dan biyan buƙatar ranta. A fusace ta yunƙura zata miƙe cikin sauri Dafeeq dake kallonta yana wani irin farin ciki a zuciyarsa dan ya samu nasarar farko a plans ɗinsa kenan. Burinsa yaga suna faɗa irin na kishiyoyi a kansa. Hakan zai bashi damar tafiya plan b shi kuma. Riƙota yay cike da lallashi ya na faɗin, “Kinga hajjaju na kwantar min da hankalinki dan ALLAH. Ai wannan faɗan ba naki bane dani takeyi, kuma dolene ta amshi hukunci dai-dai da rashin kunyarta. Zauna ga ruwa kisha ina zuwa”. Ya zaunar da ita a kujera sannan ya nufi ɗakin Khadijah yana zare belt ɗin jikinsa. Khadijah na kwance a godon rufda ciki tana kuka mai ƙona zuciya babu zato babu tsammani taji saukar duka a jikinta kawai. Wani irin zabura tayi da ƙwala ihu ta miƙe zambar. Dukan ya cigaba da kai mata sai dai gefen gadon yake samu ba ita ba, da alama kuma yana sane yake hakan. Jin an bugo ƙofar an shigo yasa shi fara kai mata dukan gaskiya, dan kuwa Kainaat ce ta shigo tana faɗin, “Shegiyar yarinya yanzu ai kin tabbatar da waye kare waye kuran ko? Ka jibgar min shegiya Baby har sai jikinta ya farfashe dan ubanta”. Tamkar Kainaat ta zuga Dafeeq ne, ya cigaba da laftar Khadijah da a yanzu ta tsaya cak tamkar bama ita yake duka ba tana kallonsa kawai. Gashi ta daina kukan da take dan tanada shegen zuciya da kafiya. Ganin fa zai iya mata illa ya saki belt ɗin yana yarfe hannu. A marairaice ya kalli Kainaat dake kallonsa. “Baby wlhy hannuna ya gaji, yarinyar nan jakace bama jin dukan take ba fa”. Hannunsa ta riƙo, sai kuma ta kwashi belt ɗin itama tana faɗin, “Ni bari naci ubanta naga ƙarshen taurin kanta.” tana ɗaga bulalar zata zubama Khadijah ta riƙe. Wani murmushi ta sakar mata tana tsareta da jajayen idanunta. A kausashe ta ce, “Har abada. Har gaban abada ba'a haifi kishiyar da zan tsaya ta dakan ba, ke wadda ma zan tsaya dambe da ita babu ita balle har nai zaman ta dakeni. Shi dai zai iya duka yanda yake so domin sunansa miji, yaci darajar wannan sunan”. Ta fisge belt ɗin. Ba Kainaat ba hatta shi kansa Dafeeq ɗin kallon mamaki yake ma Khadijah. Ya san tanada zuciya da tsiwa kam, amma bai zaton tanada irin wannan jarumtar ba. Harara Khadijah ta balla musu su duka ta wuce toilet ta barsu da binta da kallo tamkar idanunsu zasu zubo ƙasa dan mamaki......✍️ _😂A nima dai Dijo taban mamaki kam. Amarya da ango sai ku sake sabon shiri_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha biyar_ _ADVERT👇_ _YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_ _INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_ _TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_ _MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_ _*YERWA INCENSE AND MORE*_ _DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._ _AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_ _ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._ _INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_ _NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_ _YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED ____________ .......Yini guda haka Khadijah ta yisa da zazzaɓi a wannan ranar. Idanunta sun mugun kumbura saboda kuka. Wani irin mamakin canjawar Dafeeq take a ƙanƙanin lokaci haka. Duk da zuciyarta nace mata asiri Hajiyar nan ta masa wani sashe yaƙi yarda da hakan. Gaba ɗaya sai hankalinta da tunaninta suka kasu, ta rasa gane wanne ne gaskiya. Halinsa ne haka? Ko asiri Hajiyar ta masa?. Waɗan nan tunani biyu sune suka hana zuciyarta sukuni gaba ɗaya a yinin har dare salla kawai ke tada ita, tsabar yunwar da takeji har jiri ke ɗibarta, a haka dai ta daddafa tai sallar isha'i ta sake komawa ta kwanta. Dan tun rikicin safen nan bata sake jin ɗuriyar Dafeeq da amaryarsa ba a gidan. Wani wahallen barci ne yay awon gaba da ita mai cike da mafarkin iyayenta... 2:23am ya sake duba agogon dake gefen gadon. Ƙaramin tsaki yaja tare da duban gefensa da Hajiya ke barcinta hankali kwance. Gaba ɗaya zuciyarsa a ƙuntace take, dan duk yanda yaso yau ma ya more taƙi yarda. Dataga ma zai takura mata sai ta jefeshi da bandir na 1k guda biyu wai ta saya. Duk da yaji zafin abinda tai masan haka ya ɗauki kuɗin yana binta da kallo. Itako ta ɗauke kanta tana wani faman cika da batsewa tai kwanciyarta tare da jan bargo. Dolo haka ya kwanta a gefenta ya haɗiye abinda ke masa kai-kawo. Sai dai duk yanda yaso barci ya ɗaukesa hakan ya gagara. Dan ya riga ya saba ba haka suke da Khadijah ba. In har ba tana period ba baya iya ɗaga mata ƙafa koda faɗa sukayi kuwa, kai koda ma tana period ɗin dole tai masa yanda zai samu nutsuwa. Amma sai gashi yanzu da matan har biyu bashi da wani ƙarfin iko a kansu. (Har Khadijah?) Wani gefe na zuciyarsa ya ayyana masa. “Kai ina, ita kam ai bata isa ba”. Ya faɗa a zahiri yana wani girgiza kansa da sake ɗaure fuska. Hajiya ya sake juyawa ya kalla, ganin barci take sosai ya sake jan ƙaramin tsaki, sai kuma ya lumshe nasa idanun yana fatan barcin ya ɗaukesa shima. Sai dai ina babu alamar hakan, sai ma wutar fitina dake sake ruruwa a jikinsa. Zaram ya miƙe ganin zai halaka, cikin sanɗa kamar wani ɓarawo ya sauka a gadon, da rarrafe ya isa ƙofa ya buɗe a hankali yana waigen Kainaat ya fita. Sai da yay ɗan jimm ya tabbatar babu wani motsi na alamun ta farka sannan ya miƙe ya sauka ƙasa, dan nasu ɗakunan na sama ne na Khadijah na ƙasa. Kai tsaye ɗakin ya nufa abinsa... Cikin barci taji ana taɓata, firgigit ta farka sai dai bata da wani kuzari a jikinta. Sosai ta ware idanunta na mamakin ganin Dafeeq. Zatai magana ya wani rungumeta yana girgiza mata kai alamar kartace komai. Ƙasa cewar tai kuwa, ta cigaba da binsa da kallo kawai. Hakan ya bashi damar sake shige mata jiki alamar dai akwai abinda yake buƙata. Cikin rawar murya da sanyin jiki ta ce, “ALLAH bazan iya ba yunwa nake ji”. Shiru yay yana kallonta, sai kuma yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa ya fita a ɗakin. Jitai kamar ta kurma ihu ta ce ya dawo amma tasan halinsa bazai saurareta ba. Tana nan kwance hawaye har sun fara ziraro mata sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da kwalin yogurt. Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi, kafin ma ya ƙaraso ta miƙe zaune. Kusa da ita ya zauna yana wani ciccin magani shi adole har yanzu haushinta yake ji. Da taimakonsa tasha madarar, ganin ta ɗan samu ƙarfi duk da jikinta akwai zazzaɓi sosai babu tausayi ya shiga neman hanyar cimmata. Sunyi nisa sosai a yanayin da suke ciki babu zato babu tsammani kawai sukaga haske ya karaɗe ɗakin. Matuƙar firgita Khadijah tai tare da fashewa da kukan baƙin ciki ganin Hajiya Kainaat tsaye a kansu babu kunya babu tsoron ALLAH idonta ƙyar a kansu. Ga Dafeeq baida alamar ɗagata balle nuna firgici da wannan cin zarafi na matar nan. Batama san wani ƙarfi yazo mata ba ta hankaɗesa taja bedsheet ta cikukuye jikinta tana kuka. Wani irin ihu Kainaat tai musu kamar zata kashesu. “Dafeeq ni zaka cima mutunci ka zubar min da kimata. Tsabar kai tataccen ɗan iska ne kwana na zaka ɗakko ka kawoma wannan kidahuman matar taka ɗan cin amana!! A ɗaura aurenmu jiya matsayin amarya kazo kana ɓarar min da mutunci a wajen wannan jakar da bata san ciwon kanta ba.....” Wani kalan yunƙurowar ɓacin rai Khadijah dake kuka tayi, sai dai da sauri Kainaat ta dakatar da ita a zafafe. “Ke kuma karki sakamin baki dan banzo kanki ba tukunna, hasalima baki isheni kallo ba kiji ma da matsalar gabanki wawuya kawai wadda ta rako mata duniya. Ya gama jibgarki ɗazun nan amma da yake ke karya ce har ki amince yazo yay yanda yaso dake yanzu da dare. Koda yake banyi mamaki ba, dan kekam na kula bakin iyaye ke ɗawainiya ma dai da ke. Tunda har kika iya haukan kishi da jure zama da wanda ko sha'awar haɗa jini baida buƙatar yi da ke, wanda ke ɓarar miki da ciki domin buƙatar kansa ai kekam sai a shafa miki lafiya. Wlhy kikai wasa wataran janki zai a tsakar anguwa a titi ya yardama bola ƙaramar daƙiƙiy......” “Kainaat!!!”. Dafeeq ya faɗa a tsawace illahirin jikinsa na ɓari. Da alama maganganun ta sun masifar shigarsa. Wani kallon banza ta masa ta sheƙe da dariya. “Karka sake min tsawa Dafeeq, danni ba irin wannan bace, a daren nan sai kabar gidan nan kai da ita wlhy. Ƙarya nayi bakai ke zubar mata da cikin ba? Ai gaka gata ka rantse ba kai bane. Ni kuma a safiyar gobe saina kawo likitan da ke baka ƙwayar da kake zuba mata ta sha, bakai kace ɗan iska bane, a kwana ɗaya har kake tunanin nuna min halin maza! To baka isaba kuwa dan a tafin hannuna kake. Ka rabota da iyayenta da yake itama daƙiƙiyace ta yarda ta bika kazo nan kana cutar da ita har kake tunanin babu wanda yasan kanayi. To barima kiji ba zubar da cikin ba kawai har abinda zai hanaki sake ɗaukar ciki ya saka miki, shirinsa ya gama morarki ya watsar yaje ya sake auro dai-dai da shi lokacin ke kin tashi aiki mahaifar ta gama lalacewa, kuma in baki sani ba ki sani a yau ke ya maida wawuya da bata san darajar iyayenta ba shiko yana zuwa duba nashi duk ƙarshen wata, wannan kwana biyun na ƙarshen wata da yake miki ƙaryar Company ya riƙesu su masa aikin gyaran wajen da za'a saka kaya ƙarya yake ganin iyayensa yake zuwa yi. Wannan kaɗanne daga jaridar yarinya idan kina son sabon labari ki ƙara shiga gonata. Kai kuma zaka zo ka saman ne, zan tabbatar maka akwai banbanci tsakanin Kainaat Usman da wannan ballagazar matar taka da bata san ciwon kanta ba ƴar rakiyar mata duniya”.... 🤔🤔Tofa __________★ Komai nada mafari, wannan rana itace mafari tsakanin Anoosh da JJ. Dan kuwa washe gari ma dazai kaita makaranta haka ya sakata ta cire hijjab bayan ta shiga mota, zuciyarta bata son abin, amma kuma bata so ta ɓata masa rai saboda soyayyar da take ji tana masa. Tana masa wani irin mahaukacin so da take jin komi yace tayi dai-dai ne, duk da kuwa ita tasan ba dai-dai ɗin bane. Da zai ɗakkota ma hakance ta kasance. Wasa-wasa sai ta ɗan fara samun nutsuwa ganin har kusan sati biyu iyakarsa kawai yace ta cire hijjab ɗin ne idan zai kaita makaranta ko idan zasu dawo. Sai da suka cika sati na uku a haka ranar wata alhamis yake tambayarta miyyasa bata son saka ƙananun kaya ne?. Murmushi kawai tai batace da shi komai ba, kanta a ƙasa. Cike da makirci da yaudara irin ta azzalumai ya sake kwantar da murya. “My Anoosh ina bala'in son naga mace tasa ƙananun kaya, musamman ma ke da nasan zasu fi miki ƙyau fiye da kowacce mace a duniya, dan kinfi mata dubu bisa dubu ƙyau. Irinku fa nada wahalar samu Anoosh. Please ki koya sakawa kafin auren mu dan ina so sosai. Idan kuma kinfi son na dinga kallon matan titi dake sakawa to?”. Da sauri ta girgiza masa kanta idanunta dake cikin glasses na cikowa da ƙwalla. Cikin alamar motsin lips ɗinta ta ce, “Ai Mommy bazata bari ba. Ko'a cikin gida na saka hijjab nake sakawa ko abaya”. Murmushi ya saki cikin kannewa ya ce, “Ai hakan ba damuwa bane my Anoosh, idan kika sanya nima basai ki ɗora abaya ɗin ba kisa kuma hijjab. Kinga Mom bazata taɓa ta gane ba ai ko? Ko baki son farantama mijinki rai ne? Kinfi son yana kallon matan dake yawo a titi?”. Kanta ta sake girgiza masa da sauri. Ya sakar mata murmushi yana riƙo hannunta a karo na farko. Duk da ya ga zaburar da tai da tsumar da jikinta keyi haka ya basar ya kai hannun bakinsa ya sumbata. Gaba ɗaya Anoosh ta gama daburcewa, sai dai ta kasa cemasa komai. Bayan ya sauketa har kuka tayi a aji cikin hijjab. Sam bata son abinda JJ ke mata amma ta kasa hanashi, ta kuma kasa faɗama wani. To wama zata faɗamawa? Ita ba ƙanwaba ba yaya ba, ba ƙawa ba. Sannan bazata iya tunkarar Mommy da wannan batunba ai, tasan zata iya halakata ma, kai ko Gwaggo bazata iya faɗawa ba. _(Iyaye! Iyaye! Iyaye mu kula Please and please. Nasan wayonka ko dabaranka bashi zai kare maka yaranka ba. Amma mu daure, mu rage sabgogin gabanmu wajen jan ƴaƴanmu a jiki musamman ma ƴammata. Mu zama ƙawayen ƴaƴanmu ta yanda bazasu taɓa yarda da wata Aminiya ba a waje sai mu, balle har suji shakka ko tsoron tunkararmu da matsalolinsu. Jan yaranmu jikinmu kansa muyi saurin fahimtar sabon yanayi da suka tsinta kansu a ciki. Dan irin yaran nan da samari kan yaudara zakaga a farkon fara koya musu abubuwa ko sakasu yin wani abu suna cikin tsoron da idan uwa mai lurace zata iya fahimta. Sannan mu daina bama samarin ƴaƴanmu amanar yaranmu hundred percent, hakan kuskure ne wlhy, dan kawai muna son yarinyarmu ta samu mijin aure, ko kuma kada ya kuɓuce sai mu ɗauki dukkan yarda mu basa. Abinda fa muka kasa fahimta mafi yawan irinsu JJ da fuskar mutanen ƙwarai suke zuwa ga ƴaƴayenmu bada ainahin fuskarsu ta azzalumai ba. Sannan a matsayinki na uwa ya kamata ki zama maisa ido wajen fahimtar raunin ƴaƴanki akan abu, ko kuma ƙarfin sha'awarta tun daga sanda ta fara balaga, kija abinki a jiki da samun hanyoyin kare mutuncinta inba hakaba wlhy kina nan hankalinki akan neman kuɗin da zaki saya mata kayan kwalliya dana kayan ɗaki wani sakarai zai miki sakkiyar da ba ruwa. Yaranmu na yanzu sunada wayo, dan kafin sukai ko'ina sun san minene ma ake nufi da ɗa namiji da alaƙar dake tsakaninsa da mace, karki sakankance yarinya ce bata san komai ba. Humm ƴar uwa a wannan zamanin babu wannan batun na sakankancewa game da shekaru ko wayon yaro, komai dolancinta ko ƙanƙanta zata iya baki mamaki wlhy. ALLAH ka shiryemu baki ɗaya, ka kare mana yaranmu da ga sharrin fasiƙan maza irin su JJ😩🙏)_ Washe gari kamar yanda JJ ya buƙata haka Anoosh tayi, ta saka ƙananun kaya a ƙasa ta ɗora abaya da hijjab. Tana shiga mota ya sakata ta cire hijjabin da abayar. Tsabar yanda ya rikice baima san ya rungumeta ba. Duk yanda take kiciniyar ƙwacewa bai saketa ba sai da ya samu ƙaramar nutsuwa a haka. Bayan ya saketa ta hau masa kuka, sai ya shiga lallashinta cike da daɗin baki irin na mayaudara. Wai wlhy tsabar rikicewa da ƙyan da tayine. Amma ta yarda da shi shi ko hannun mace bai taɓa riƙewa ba sai a kanta, kuma itace ta ƙarshe. Nan fa ya kanainaye ta da zance harda su wa'azi. Dole ta haƙura, sai dai tunkan suje makaranta ta maida hijjab ɗinta. Daga ranar kuma saita ɗan fara ɗari-ɗari da shi. Ganin damar daya samu zata kufce masa ya sake sabuwar dabara. Cikin weekend ya zo hira kamar yanda ya saba. Maimakon zama da Anoosh sai ya zauna da mamanta wai su tattauna akan kawo kuɗin aure. Hajiya Lailah taji daɗin wannan zance nashi. Bata ɓoye masa ba ta sanar masa zatama Gwaggo magana cikin dattawan layin nan mutum biyu su amshi kuɗin, dan bazata turashi wajen dangin mahaifin Anoosh ba saboda wasu dalilai da sai nan gaba zata sanar masa. Nunawa yay ai hakan babu komai, da yake shima zuciyarsa akwai tsatsa a ciki. Duk abinda suka tattauna Anoosh najinsu, sai taji ta samu matuƙar nutsuwa da sake jin ƙaunar JJ a ranta. Kwana biyu dayin wannan magana iyayen JJ suka zo aka zauna. Sun kawo kuɗin gaisuwar farko har dubu ɗari cif, akan a sake basu lokaci suzo da sadaki da komai a saka rana. Ranar Hajiya Lailah ta kasance a cikin matuƙar farin ciki, sai dai abinda bata sani ba shine JJ iyayen ƙarya ya kawo musu, dan hatta su MB abokansa basu san ya cigaba da zuwa wajen Anoosh ba. Sannan Gwaggo alaƙarta da MB ta ɓangaren mahaifiyarsa ne, bata wani san iyayen JJ ba sosai musamman ma maza. Yarda datai da shi kuma yasa bata taɓa kawoma ranta zai aikata wani abu makamancin haka ba, ga shi kullum Hajiya Lailah cikin yabonsa take. Ga soyayyar da Anoosh ke masa. Ita kanta kusan duk juma'a idan ya shigo yakan kawo mata kayan marmari wani lokacin harda sabulai da omo, randa ALLAH ya cidata ma harda kayan shayi da nama. Gashi duk ƙwaƙwƙwafinka baka isa gane ainahin fuskar JJ ba, dan makirin mutum ne da ya iya takunsa, duk wani salo na cimma mace ya sanshi musamman irin su Anoosh salihan yara masu tarbiyya. Kawo wannan kuɗi ya ƙara sakama Anoosh nutsuwa da JJ ita da mahaifiyarta, dan haka washe gari da yazo kaita makaranta koda ya rungumeta batai masa kuka ba, sai dai ta takure jikinta waje guda. Sai ca yay mata na murnar samuntane fa. Ko ita bata murna sun kusa zama ma'aurata. Cike da kunya tace tanayi. Hannunta ya kama ya sumbata, batare da ya bata damar sake cewa wani abu ba ya tada motar.........✍️ 🚶🚶🚶🧑‍🦯Humm *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha shida_ .......Sannu a hankali JJ ya cigaba da rungumar Anoosh. Abu kaɗan sai ya rungumeta yace cikin murna ne. Riƙe mata hannu kam ya sumbata yanzu ya zama ba komai ba. Tun tana noƙema rungumar harta fara jin daɗi itama tana biye masa. Idan ko suna zaune hannunta na cikin nasa. Ko shi bai kama ba ita zata kama nasan cikin dabara. Ranar sai gashi da kissing ɗinta wai yana tayata murnar ƙara shekarar haihuwa. Duk da taji abun wani iri sai ta samu kanta da jin daɗi. Da suka rabu ya kirata a waya ya dinga maimaita mata daɗin da yaji akan wannan kiss yana hura mata kai akan ita ta musamman ce, baida kamarta, har abada bazai iya ya rabu da ita ba. Kaza-kaza dai irin zantukan mayaudaran maza. Ya tunkari Hajiya Lailah kan sake kawo kuɗi harda sadaki a kuma saka rana, sai dai an samu akasi a satin Gwaggo ta tashi da ciwo har aka kwantar da ita asibiti. Hajiya Lailah ke jiyyarta, dan haka har Anoosh a asibiti take kwana, da rana ne dai take zuwa gida tai ayyuka tai musu abinci ta wuce makaranta, idan ta dawo ta wuce asibiti Mom taje gida tai wanka itama, idan ta koma sai JJ ya ɗauki Anoosh da suke tare a asibitin wajen Gwaggo ya maidata gida ya jirata ta shirya abinci ya maidota asibitin ya wuce gida.. Wannan yanayi shine ya bama JJ damammaki masu yawa akan Anoosh. Dan babu kunya a gidan nasu zai matseta yay kissing. Tun ana iya haka harya fara kai hannu a sassan jikinta. Idan ta nuna damuwa ya marairaice mata wai ta tausaya masa ko tana son yaje ya nema matan banza ne. _(Kuji shege fa. Da yaya yake yi kafin ya sanki, ƴammata wlhy kusan inda ke muku ciwo. Duk shegen namijin da zai kawo miki irin wannan ƙauli da ba'adin tofa ba sonki yake ba jikinki yake so kawai wlhy. Ku daina yarda wannan soyayyar iskar na kwasarku ana lalata muku rayuwa a barku da kuka ku da iyayenku. Mutuncinki shine kimarki a gidan aure, karki yarda wani shasha ya zubar miki da wannan kimar saboda farin cikinsa da biyan buƙatarsa. Duk namijin dake sonki dan ALLAH da aure tun kina waje zai kasance mai jin kishinki, idan ma kikai shigar da bata dace ba zai tsawatar miki ne, namijin ƙwarai duk ƙarfin buƙatarsa ko taɓa hannun budurwa tsantsenin yi yake wlhy. Sai ku nutsu ku dawo hayyacinku dan da yawanku ana yaudararku ne da ƙananun abubuwan dake buɗe hanyoyin zina koda ba'a kai babban ba). A ranar da JJ yaci galabar keta mutuncin Anoosh a ranar ALLAH yayma Gwaggo rasuwa. Wannan ruɗanin ya hana Hajiya Lailah fuskantar halin da Anoosh ke ciki. Yayinda Anoosh ke kuka biyu, sai dai JJ nata faman mata daɗin baki ta waya harda kukansa shegen. Ganin yanda ya nuna nadamarsa a zahiri ya sakata jin ɗan sassauci harta saki jikinta. A haka ranar addu'ar bakwai ya sake samunta ya more. Nan ma ta rikice masa da kuka ya koma lallashinta. Al'amari kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai JJ ya gama cin nasara akan Anoosh. Yakai yanzu idan ya ɗauketa maimakon makaranta sai ya kaita wani waje daban. Tun abin na damunta harta fara jin daɗinsa itama. Dan kullum magana ɗaya ce yake mata idan bata bashi ba zai je ya nema matan banza. (Kuji shege. Jeka nema mana bakai da ALLAH ba dan buhun bakon gidanku🙄😡). Sannu a hankali JJ ya gama sauyama Anoosh alƙibla. Sai ya gama moreta ta koma tana kuka da istigifari. Gefe kuma ya saki maganar kawo kuɗin aure. Idan ta tuna masa sai yace ta sake haƙuri rasuwar Gwaggo ta sake nisa kar ace bai damu ba. Ya riga ya ɗaureta da jijiyar kanta, dole take binsa da to kawai. Ita kanta Hajiya Lailah da abun ke damunta a rai ranar dai ta fidda kunya taima JJ magana, sai yace zasu zo a cikin satin zuwa weekend. Ta ɗan ji nutsuwa, dan burinta a yanzu kawai shine Anoosh tai aure itama ta samu tayi auren dan zama haka bazai cigaba da mata ba ana kallonta wani abu daban a anguwa, ga shi yanzu babu Gwaggo mai tsaya matan. Kwana uku da haka Anoosh ta fara ciwo, Hajiya Lailah bata kawo komai a ranta ba sai zazzaɓin cizon sauro kawai da canjin yanayi, dan haka takai ta camix. Ganin har washe gari zazzaɓin yaƙi sauka ga amai tanayi yasa ya ɗauketa suka nufi asibiti. Hankali tashe suka dawo gida sakamakon abinda likita ya sanar musu cewar Anoosh nada shigar ciki wata biyu da satittika. Daina gani Hajiya Lailah ta kusan yi, da ƙyar da addu'a suka iso gida. Anoosh nada matuƙar tsoro, dan haka Hajiya Lailah na tsareta da kurari bayan shigarsu gida babu wani ja'inja tace JJ ne. Sumar tsaye Hajiya Lailah tayi, ga hawaye na kwaranya a idanunta. Cikin rawar jiki ta ɗauka waya tai kiran JJ. Batare da tace masa komai ba akan ciki ta ce tana buƙatar ganinsa dan ALLAH. Haka kawai yasha jinin jikinsa da jin muryarta, amma sai yace mata zai zo zuwa gobe ko jibi yanzu yayi tafiya ne Babansa ya aikesa Kaduna. Dole ta danne tace masa babu damuwa har ya dawo ɗin. Hankalin JJ ya matuƙar tashi, dan ya fahimci Hajiya Lailah fa ba kanwar lasa bace ba. Sannan kanta a waye yake dan tanada iliminta gwargwado. Dan haka ya tattara ya gudu da ga Kano a ranar yacema iyayensa zaije Abuja wani abokinsa na nemansa akan aiki. Sun masa fatan alkairi ya tafi da shirin sai bayan wata guda zai dawo, dan yasan su Hajiya Lailah ba gidansu suka sani ba....... (Hummm😠) ____________★ Wani irin kalar rawa jikin Khadijah keyi fiye da farko. Ta ƙurama Dafeeq idanunta dake mar-mar kamar zasu zubo ƙasa. So take taji ya musa, so take taji yace ma Hajiyar nan ƙarya take ba haka bane. Amma harta wuce bai ce ba. Sai ma tana fita wani zabura da yay zai bita. Ƙarfin bugu zuciyarta ta ƙarayi jiri na neman ɗibarta. Batama san lokacin data buɗe baki cikin ƙaraji da karkarwar jiki ta furta, “Dafeeq da gaske kana zuwa duba iyayenka?!! Da gaske kaike zubar da cikin da na dinga samu?!!”. Harara ya juyo ya watsa mata tamkar zai cinyeta da idanun nasa. Sai kuma ya buɗe ƙofar a zafafe ya fita. Dama yana gab da fita ne tai maganar. Ihu Khadijah ta kurma jikinta na girgigizawa. Gaba ɗaya jitake kamar ta haukace ma ita kam... Da bibbiyu Dafeeq ke haɗa steps ɗin benan. Jikinsa na rawa kamar wani mayuncin zaki. Yanda yay wani irin kumburar ɓacin rai bazaka taɓa ɗauka yaron nan ɗan shekara ashirin da huɗu bane ba. Kai tsaye ɗakin kainaat ya nufa, sai dai yana ɗora hannunsa a handle ɗin ƙofar ya jita a rufe. Cikin ɓacin rai da ihu ya ce, “Hajiya buɗe ƙofar nan kona ɓallata!!”. Wani shegen murmushi Kainaat ta saki tana taɓe baki. A ranta tace haba yaro bakai kana jin kai ɗan iska bane kana a ganiyar balaga. Indai takamarka kai shege ne nan ma gidan ka taras, waya gaya maka ana shiga gonar Kainaat a fita lafiya babu tabon sarin maciji koda a yatsan ƙafa ne. Ai wasan yanzu ma aka fara, da kanka zaka min abinda nake so kafin ma cikar sati ɗaya. Amma hakan bazai hanani hukunta shegiyar matarka ba tunda ita batasan taci arziƙin a rabu lafiya ba. Taja tsaki tare da fisgar wayarta ta shiga danne-danne tamkar batajin hargowar da yake da jijjiga ƙofa. Wayar na gab da tsinkewa Nadwa ta ɗauka. Cikin yanayin barci ta ce, “Hello”. “K malama watsakke a wannan barcin nice”. Da mamaki Nadwa dake tashi zaune tana murzar ido tace “Amarya a wannan daren, ina kika bar mijin naki ke kuwa dan ALLAH. Wai badai da gaske kike bazaki bashi kanki ba?”. “Humm share ba wannan bane yasa na kiraki Nadwa, so nake da safe ki sanarma Mommy ina son a aika matar nan taje min wajan malamin nan da yay min aiki akan Abaan ina amarya. Ina son a gobe Dafeeq ya saki matarsa”. “What! Haba! Haba Kainaat mi kuma ya kaiki wannan tunanin? Dan ALLAH kada ki raba ma'auratan nan Please and please. Keda ba zama kikaje yi ba miya kawo miki wannan tunanin a daren nan? Ni dai babu ruwana dan ALLAH kada kiyi haka akan yarinyar nan da abinma tausayi ce. Ki barta da zalincin da yake mata ma na zubar mata da ciki”. “Haba kema kin san ganganne na ƙyale cuta ban rama ba. Ai rama cuta ga macuci ibada ce. Har ke kike tunanin wai babu ruwanta. Wlhy duk da ban auri mijinta dan na rayu da shi ba ita bata isa ta shiga gonata na ƙyaleta ba. Da ga safiyar yau zuwa daren nan tamun abinda sai ta san ta shiga gonata wlhy”. “Ya ALLAH calm down mana Kainaat. Mita miki?”. Kamar bazata faɗa mata ba sai kuma ta kwashe komai ta sanar mata. Tare da ɗorawa da wannan hukuncin nasu ne su biyu, duk da kuwa shima na tabbata dama wannan shine burinsa a kanta ƙarshe. Dan maza irinsu da sukai auren wuri kuma irin kalar auren nan daga ƙarshe mawuyaci ne basu sake su ba kosu ƙaro musu kishiya. To ni zan rabasu ne a gaɓar da suke buƙatar junansu dan ubansu. Duk da ban auresa dan na zauna dashi ba shi har ya isa ya ɗauki kwanana ya kai mata, tsabar son zubar min da mutunci a wajen ƴar cikina kwana ɗaya da auro ni. Ai wannan cin mutunci yakai cin mutunci”. “To amma baki ganin kema akwai laifinki? Maybe a matse yake bawon ALLAH kin hanashi kanki kin bashi kuɗi tayaya kike ganin tunda yasan yanada wata matar bazaije gareta ba. Ni dai dan ALLAH ki barsu, abinda kika faɗa mata ma kawai ya isa punishment a gareta, shiko nanda sati ɗaya zaki masa nashi punishment ɗin tunda ya saki jiki aure yay kamar kowa zaici banza, bai san nan da kwanaki komai daya samu ba ma zai rasa shi. Hakan kawai ya ishesa ai”. “Ina hakan yamun kaɗan, idan bazaki min yanda nake so ba barshi, bara na kira Mommyn da kaina dama dan naga darene bana son tadata a barci, kuma so nake tunda safe aje a amso min”. “A'a miyay zafi, saƙonki kam zan isar in dai nice. Ni dai shawara na baki dan ina tsoratar miki abinda zai iya zuwa ya dawo. Tunda ba gama sanin halin yarinyar nan kikai ba. Koda kike ganinta ƙarama maybe itama ta iya nata kalar hatsabibancin. Kigafa yanda ta maida miki magana har sau biyu”. “Mtsoww! Riƙe shawararki malama”. Kainaat ta faɗa tana yanke wayar. Jefar da ita tai gefe tayi kwanciyarta batare fatabi takan Dafeeq dake cigaba da kiran sunanta yana ƙwanƙwasa ƙofar ba. Sai ma taja headphones dake cikin bedside drawer ɗin ta ta saka abinta, daga haka tabar jinsa gaba ɗaya... Matuƙar tashin hankali Dafeeq ya shiga. Ta ina matar nan ta samo wannan sirrin nasa da yasan da ga shi sai ALLAH sai likitan nan suka sani. Sannan zuwa gida da yake yi kuwa shi kaɗai ya sani sai UBANGIJI. Dan tun bayan aurensu da wata biyar ya yanke shawarar zuwa ga iyayensa kasancewar labari ya sameshi mamansa ta samu karaya a ƙafa. Koda yaje bai wani sha wahalar shawo kansu ba dan suna son sa kamar mutuwa sakamakon shi kaɗai suka haifa a duniya. Bai yarda ya faɗa musu a ina yake ba, ya kuma sanar musu ya saki Khadijah tun kafin yazo garesu saboda yaga basa so, yanzu neman kuɗi yake yi dan ya koma karatu. Sun ji daɗi sosai suka dinga saka masa albarka. Kwanansa biyu batare da ya yarda kowa ya gansa ba ya dawo. Yayinda babansa ya shirya har gidan su Khadijah yaje yayima mahaifinta tas yace kuma su nema ƴarsu acan gidajen karuwar dan ɗansu ya sanar musu ya saketa. Hankalin iyayen Khadijah ya sake tashi, jikin babanta ya sake rikicewa sosai harta kaisa da samun paralysis. Yanzu haka yana kwance gefen jikinsa baya aiki. Karatun ƙannenta ya tsaya, sai da taimakon wani bawan ALLAH da yaga ƙanwarta mai bimata yana so ya maida yaran makaranta, ya kai Baba asibiti. Yanzu haka yana amsar magani jikinsa da ɗan sauƙi, ƙannenta biyu sun kammala secondary sun cigaba da karatu, an kuma saka musu ranar aure dan dama burin mahaifinsu shi dai su fara karatun sannan ya aurar dasu sa ƙarasa a gidan miji, amma Khadijah ta nuna masa bai isa ba. Ƴan anguwar su Khadijah kam da mutane da yawa sun yarda Khadijah tabi duniya saboda tsoron kada ta dawo gida Dafeeq ya saketa a mata dariya ko iyayenta suƙi karɓarta. Tun daga lokacin duk wata sai Dafeeq yaje gida, dan hatta auren nan na Kainaat iyayensa sun san zaiyi, hasalima a kuɗin data dinga bashi har gidansu yaje ya gyara tare da ƙarama babansa jari........✍️ _🥱 Dafeeq anya zakaga ANNABI ALLAH kuwa🤦🥲🚶_ _Khadijah ke kuma ƙya dawo hankalinki ai yanzu. Koda yake baki ji sauran labari ba ma😩_ _Ke kuwa Kainaat bakiyi wawtaba kuwa?, dan Dafeeq fa Hummm😆_ _JJ banda abin cewa a kanka kai kam yau🥲, na barka da masu karatu da su Alimah suci min ubanka bunsurun banza🧑‍🦯 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na bakwai_ INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 MAZA KU GARZAYO "UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN "TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.🥰🥰🥰 KAMA DAGA *FLYER *3D MOCKUP LOGO *2D MOCKUP LOGO *NORMAL LOGO *IMAGE LOGO *BANA *STICKERS *ADVERT VIDEO *PROFESSIONAL INVITATION *INVITATIONS CARD *BIRTHDAY VIDEOS *POSTER *CERTIFICATE.AND MORE...... CONTACT ME ON 👇 09035390383 ____________ .......“Please Kainat yaya kika san duk wannan wai?”. “Humm Nadwa kenan. Na faɗa miki Kainaat ba shashasha bace ba ai, kin san dai bazan jashi jikina ban san wanene shi ba. Inama da fiye da wannan game da shi, sai dai lokaci ne zai sa ki san sauran gaba ɗaya ba yanzu ba”. Idanu kawai Nadwa ta zuba mata cike da mamaki da tsoro. Maganar gaskiya bata son ƙawar tata tace zata shiga tsakanin waɗan nan ma'auratan dake tsaka da cin ƙuruciyar soyayyarsu. Amma ta santa tasan halinta, in har tace tana son abu sai ta cimma burinta a kansa, dan ita shaidace ko akan Don Abaan da yanda ya fara sonta har sukai aure shirine babba... ★★★..... “Ina ganin zuwa jibi zamu koma sabon gidan can dan mu samu albarkacin juma'a”. Da wani irin razana Khadijah ta jiyo tana kallon Dafeeq da ke magana a dake hannunsa riƙe da rigarta data miƙa masa zai shanya a igiya. Babu alamar wasa a kan fuskarsa ga shi ya wani tsareta da idanu. Nata idanun ta rissinar ƙasa tana ƙoƙarin saita rawar da jikinta ya fara. Sai kuma ta shiga jinjina masa kanta dan in har tai magana sai hawayen da take riƙewa sun zubo mata. “Miye wani ɗaga kai baki da bakin magana ne wai? Khadijah nikam wlhy na gagara gane miki gaba ɗaya. Da ace wani kemin wannan sabon halin naki sai na ɗauka baƙin cikine ko hassada. Gaba ɗaya kin hana kanki zama lafiya. Ki duba fa jiya na shigo da waya gidan nan amma koda na nuna miki baki ko taɓata ba a tsatstsaye kika wani ce ALLAH ya sanya alkairi kika kwanta...” Duk yanda taso riƙe kukan ta gagara yin haka a wannan gaɓar saboda yanda yake mata magana a zafafe kamar ba Dafeeq ɗinta ba. Miƙewa tai da sauri daga gaban kayansu da sike wankewar ta nufi ɗaki da gudu hannunta toshe da bakinta. A zafafe shima Dafeeq ya miƙe, tana shiga falon yana shigowa shima. Wani kalar fisgota yay baya tai taga-taga zata faɗi ya hankaɗata saman kujera. Cikin ƙanƙanin lokaci idanunsa sun gama kaɗewa, cikin nunata da yatsa tamkar zai mareta ya ce, “K! Wai mi kike nufi dani ne? Dan Kinga ina lallaɓaki kike ganin kin samu hanyar wulaƙantani da jana a ƙasa. Ubanmi na miki ba dai-daiba anan?”. Kuka sosai Khadijah ta sake fashewa da shi, sai kuma ta kai hannu ta hankaɗashi baya iya ƙarfinta tana ƙoƙarin miƙewa. Taga-taga yay zai faɗi ƙasa ALLAH ya taimakesa ya dafe kujera. “Taauuu!!”. Kake jin wani lafiyayyen mari a fuskarta. A gigice ta dafe kuncinta tare da fashewa da wani sabon kukan. “Dafeeq ni ka mara?!”. “An mareki ko zaki rama? Ke har kin isa ki dinga jana a ƙasa kamar wani yaronki! Har kina da ƙarfin min wannan abun. Ko kuma dole sai nayi abinda kike so saboda haihuwata kikayi ƴar marasa tarbiyya”. “Dafeeq nice ƴar marasa tarbiyyar?!”. “Kina da ita ne. Ko ƴa mai tarbiyya ce zata bar uwarta da ubanta ta biyo namiji wata uwa duniya. K! Nifa na fiki iya iskanci. Har ni zaki dingama baƙin cikin cigaban rayuwata saboda ke butulu ce. To bari kiji ki kama kanki kafin na sassaɓa miki kamanni a gidan nan. Dan wlhy kaɗan da ga aikina ne na haɗa miki jini da majina wawuya kawai...” fuuu ya fice kamar zai tashi sama. Ragwaf Khadijah ta zube ƙasa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.. Tunda ta baro gidansu ta biyo Dafeeq yau itace rana ta farko datai mahaukacin kuka na tashin hankali da har ya saka mata masifaffen ciwon kai tare da jin wani abu kamar nadama nasan ɗarsuwa a ranta. Dan ko daren farkonsu tayi kukan azabar da taci a hannunsa amma baiko kai kwatankwacin wannan ba. Ita yau Dafeeq kema gorin bijirema iyayenta ta biyosa nan?, ita Dafeeq ya ɗaga hannu ya mara. Mari fa, mari mai suna mari da har take iya jin sayin yatsunsa biyar akan ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta. jama'a Dafeeq fa, Dafeeq ɗinta data zaɓa akan iyayenta da karatunta. Dafeeq data yarda ta bar komai ta koma mara komai ta ɗaukesa. ya arrahaman wannan wace irin rana ce haka da bata taɓa lissafawa a ciki lissafin rayuwarta ba. ya ALLAH kasa mafarki takeyi ba a zahiri bane ba. Ta sake fashewa da sabon kuka mai tsananin ƙona zuciya..... (Hummm Khadijah kaɗan daga illar bijirema umarnin iyaye kenan. Ƴammata a dinga sassauta soyayyar da har zata iya saka ido rufewa a bijirema iyaye🤦🥲 dan zancen malam bahaushe nan fa na NAMIJI BA ƊAN GOYE bane gaskiya ne akan wasu mazan). ★★★...... Iya jigata da galabaita JJ yayi a wannan dare zuwa safiya. Dan da salo-salo su Alimah suka dinga firgitashi. Gaba ɗaya ya gama fita a hayyacinsa tamkar wani sabon kamu a hauka. Babu abinda yake iya ganewa tsakanin rayuwa da numfashi. Rana da duhun dare. Duniya da lahira, fari da baƙi. Abinda kawai ya sani a garesa komai ya gama ƙarewa kawai. Yayi masifar zama zuru-zuru cikin ƙanƙanin lokaci. Ba shi kaɗai ba hatta gidan kansa ya gama fita a hayyacinsa tamkar ba sabo ba, wanda aka ƙawata da kayan alatu. Dukan gate da akeyi da ɗan ƙarfi ya sashi buɗe idanunsa da sukai masa matuƙar nauyi. Wani irin zafi da haske suka ratsa idanunsa da jikinsa a lokaci ɗaya. Tamkar wanda aka bulbulama wani irin ƙarfi ya miƙe zubur. Waige-waige ya fara, tabbas a tsakar gidansa yake kusa da gate gab. Idanu ya sake warewa na tabbatarwa. Farin ciki ya sake ratsashi ganin fa da gaske ƙofar gate ɗin ce dai. Ihu ya kurma na tsabagen jin daɗi mara misali, batare da tunanin komai ba ya miƙe a 360 zuwa jikin gate. Ƙofar ya shiga ƙoƙarin buɗewa yana waigen bayansa tamkar mai tsoron a biyoshi, yanda yake karkarwa da ƙyar ya iya buɗe ƙofa. Ko kallo bai yima wanda ke tsaye gaban gate ɗin ba alamar suke knocking ya wani kwasa a bala'in guje ji kake fiyyy-fuyyyy yana dukan iska, sai ya tafi gaba zai faɗi sai ya damƙi ƙasa ya miƙe yana waigen bayansa.... Tuni yara da ke wasa a tsakkiyar layin suka fara kwasa a guje suma suna ihu dan ganin ƙatoton mutum tsirara haihuwar uwarsa na gudu jikinsa yay wani irin butsaaa da ƙuraje ƙanana tamkar jikin kada. Cikin ƙanƙanin lokaci anguwar ta ruɗe, yayinda JJ ke falfala gudun ceton rai da iyakar ƙarfinsa. A haka ya kai har titi, bai damu da tare abin hawaba ya ɗauki titin da ƙafa. Sake ruɗewa mutane sukai ana kiran mahaukaci-mahaukaci. A tare a tare. Sai dai ina babu mai tarewar sai ma darewa da ake ana bashi hanya a guje. Duk da wahala da jigatar da yay gudunsa yake sosai batare da nisan hanya da yanda mutane ke ƴar tsere akan ganinsa ya damesa ba. Sai dai duk mai hankalin daya gansa yasan wannan gudun bana lafiya bane, sannan ba a cikin hayyacinsa yake yinsa ba dan a haka ya isa har gidansu. A anguwar tasu ma tunda ya shigo ta rikice da iface-ifacen yara da mata da matasa. Dole akai dafifi wajen masa tara-tara da ƙyar aka iya kamashi. Ƴan gidansu hankalinsu yay masifar tashi, wasu ma kuka suke dan tun fitowarsa gida su Rabi'ah dake knocking gate yazo ya wuce su suna kuka sukai kiran iyayensu suka sanar da su. Tuni wasu sun nufo gidan nashi, sai dai a hanya suka gamu da shi, dole suka juya gida dan ganin komi zasuyi bazasu taɓa samun kanshi ba, ALLAH ma ya taimakesu hanyar gida ya dosa ba wani waje daban ba..... (🤦 Uncle JJ badai kuma ka haukace ba😩😩😫). ...★...★...★.... Duk yanda ya fito da ga gida da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya yaji zuciyarsa tai masa sanyi a dalilin shigowar kiranta. Cike da girmamawa ya ɗaga tare da kai sabuwar galleliyar wayar tasa iphone 14 data bashi shekaran jiyannan saman kunne yana ɗan murmushi. Sallamarsa kawai ta amsa da faɗin “Kana ina ne babban mutum”. Wani irin murmushi ya saki mai faɗi, dan yana matuƙar jin daɗin sunan nan da take kiransa da shi. Cike da girmamawa ya bata amsa da “Ina gida ranki ya daɗe”.. “A to bara na haƙura wannan lokacin uwargida ne ran gida ai. A gaidamin ita sai da saf......” Cikin sauri ya katseta da faɗin, “A haba hajiya, ai ko'a gidan giya akwai babba. Dan ALLAH kada ki katse ki faɗa min komi kike buƙata zan miki shi yanzun nan”. “A'a ai ba'ayi haka ba Dafeeq. Ka bari kawai gobe ma haɗu” Kainaat ta faɗa tana danne murmushin ta. “Hajiya bazanyi jayayya da ke ba, amma dan ALLAH ki bani umarni kawai ni mai biyayya ne a gareki”. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali. Ta ce, “Okay dama ina son ganinka ne wlhy. Yanzu haka ma ina office ban wuce gida ba. Idan ban takuraka ba ko zaka sameni?”. “Yanzu-yanzu kuwa ma Hajiya in ALLAH ya yarda”. Ya faɗa cikin sauri yana komawa cikin gidan. Ko kallon Khadijah dake durƙushe na kuka baiyi ba ya shige bedroom. Baifi mintuna bakwai ba sai gashi ya fito cikin sabuwar shiga ta yadi mai ƙyawu sosai dan daga gani ma kasan sabon ɗinki ne. Sake tsallake Khadijah yay yayi wucewarsa ya barta da ƙamshinsa.... A cikin abinda bai wuce mintinan arba'in ba ya iso. Sakatariyar ta ce ta tarosa har cikin office ɗin duk da kuwa shima ya sani tunda Companyn ba baƙonsa bane ba. Tunda ya shigo Kainaat ke masa wani irin shu'umin kallo a ƙasan ido. Tabbas Dafeeq ƙyaƙyƙyawa ne. Dan daka ganshi kaga bafulatanin usil. Duk da har yanzu shekarunsa basu gama tsayar da shi a namiji ba, amma kai daka ganshi kasan nan gaba ba ƙaramin ingarma za'ayi ba. Sai dai fa duk da wannan ƙyawun nashi ko kama ƙafar Abaan ɗinta baiyi ba. Dan Abaan dabanne a cikin dubun mazaje tsararsa ma balle Dafeeq da'a gabansa bai wuce ɗan tsako haihuwar jiya ba. Wajen zama ta nuna masa tana mai tattare komai zuwa gefe. Batace da shi komai ba har sakatariyarta ta ajiye masa lemo da ruwa ta fita. Taja wasu mintuna tana rubuce-rubucen ta kafin ta ɗago. Ganin bai taɓa komai ba ta ce, “A'a babban mutum ya haka? Ko kana tsoron karna zuba maka wani abu ne na sace ka”. Murmushi yayi yana girgiza kai. “Kai haba hajiya wane sacewa kuma. Kawai dai bana jin shan komai ne dan yanzu na fito daga gida”. “Okay kace uwargida ce ta cika maka ciki dai kawai”. Murmushi kawai shi dai yayi baice komai ba. Itama bata sake cewarba sai tasowa da tai ta dawo kujerar kusa da shi suna facing juna. Lemon da aka ajiye masan ta ɗauka tare da ɓalle murfin takai baki, sai da tasha kusan rabi sannan ta miƙa masa. Kasa musa mata yay ya amsa yana godiya. Tai murmushi kawai da gyaɗa kanta. “Nasan kanata makin dalilin wannan kira na ujila. Dan haka bazan so barinka a duhu ba ko lalube muje kai tsaye ga abinda yasa na kirakan, dan ni macece mara son kwana-kwana ko kwalo-kwalo. Dafeeq nasan ka sanni kasan wacece ni a companyn nan. Ka mun tambayoyi bila adadin akan ƙyautar mota da gida danai maka sati ɗaya data wuce. Hakama shekaranjiya kamin tambaya akan waya duk dai ban amsa maka ba. To ina ganin yau ya kamata na baka amsa da kuma dalilin komai. Da farko dai magana ta gaskiya *_SONKA_* nakeyi.....” Da wani irin sauri Dafeeq ya ɗago manyan idanunsa yana kallonta. Sai kuma ya nuna kansa alamar (Ni). Kanta ta jinjina masa na tabbatarwa. Batare data bashi damar cewa wani abu ba. Ta ɗaura da faɗin, “Tabbas kai kuwa Dafeeq. Na kuma jima ina jin hakan a kanka tun randa na fara ganinka a company ɗin nan. Sai dai nata tunanin ta yanda zan tunkareka da batun gudun kada ka baɗa min ƙasa a ido. Amma dai na baka dama kaje gida kayi tunani dan ALLAH. Da gaske ina sonka kuma aure nake so muyi nanda ƙanƙanin lokaci. Dan banama son mu wuce sati biyu. Kada kuma ka damu da duk abinda za'ai na shagalin biki. Aikinka kuma zaka iya fara zuwa wannan Monday ɗin dan na tanadar maka kayan da duk zaka buƙata da kamfani ya bada umarnin ai amfani da su. Dan ALLAH kada kace a'a. Amma dai kaje kayi tunani akan maganata Please. ALLAH dai yasa bazakace na maka tsufa ba”. Ta kamo hannunsa tana murmushi tare da ɗora masa bandir na dollers. “Ga wannan ka riƙe a hannunka sai na jika. Ni yanzu zan tashi dan na gaji jikina ciwo yake mun ina buƙatar hutu.” Ta sakar masa hannu tana miƙewa fuskarta ƙawace da murmushi. Handbag nata mai azabar ƙyau kawai ta ɗauka da tarkacenta batare da ta sake cewa da shi komai ba tai ficewarta a office ɗin tana murmushi..........✍️ _😣🤌🏻Na rasa mima zance akanki Kainaat_. *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha bakwai_ _________ https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* ____________________________ ........Duk yanda taso daurema zuciyarta haƙurin zuwa safiya ta gagara haka. A haukace ta fice a ɗakin zuwa upstairs da take jiyo hargagin Dafeeq. Yanda take tako steps ɗin da gudu-gudu ya sashi juyowa. Ɗauke kansa yay yana jan wani shegen tsakin takaici, sai dai me, a bazata, matuƙar bazata garesa yaji Khadijah ta wani irin fisgoshi baya har sai da yay taga-taga zai faɗi. Da ƙyar ya iya dafe bango yana bala'in zaro idanun mamakinta. “K! Kinada hankali kuwa?”. “Banda shi! Ka ɗauka banma san minene shi ba Dafeeq. Amsa kawai nake son ji daga gareka. Shin da gaske ne abinda matarka ta faɗa ko kuwa?”. Tsaki ya ja mai ƙarfi yana balla mata hararar takaici. Cikin matuƙar kaifin harshe ya furta, “Amma k jaka ce wlhy. Akan wannan banzar tambayar taki kika min wannan fisgar kamar wani sa'anki ko ɗanki.” “An fisgeka ɗin kayi abinda duk zakayi azzalumi macuci. Ka zugani nabar iyayena saboda kai amma ka zagaye kana zuwa wajen naka batare da sani na ba munafuki. Wlhy bazan taɓa yafe maka ba maci amana....” Tauuuu!!! Kake jin saukar mari, hannu biyu ta dafe kuncinta wata irin azaba na ratsata. Cikin rufewar ido itama ta ɗaga hannu ta sauke masa lafiyayyen marin tare da watsa masa jajayen idanunta dan Khadijah akwai zuciyar masifa. Tsabar kiɗimewa da mamakinta ya sashi sumar tsaye ya zuba mata ido kawai. Ta nunasa da yatsa jijiyoyin kanta na sake tashi ruɗu-ruɗu. “A da dai ka daka Dafeeq saboda ƙarfin soyayya. Amma a yanzu kaima kasan baka isa ba. Na rantse maka da ALLAH koda zaka kasheni ne da duka sai dai mu mutu tare a wajen ramawa azzalumi. Kai yanzu bakaji kunya ba? Ashe duk abinda kake faɗamin a iya fatar bakinka suka tsaya, na dinga wahalar ɓari a gabanka ashe kaine ke zubarmin da ciki saboda kai jahiline mara ilimi addini. Nayi dana sanin saninka a rayuwata Dafeeq. Nayi dana sanin barin iyayena waɗanda basu taɓa nuna gajiyawarsu a gareni ba tun daga haihuwa har girma saboda kai.....” wani irin kuka mai ƙona zuciya ya sarƙeta. Cigaba tai da nunasa da yatsa tana son yin magana amma hakan ya gagara. Wata shegiyar shaƙa Dafeeq daya gama cika tab da zagin da tai masa ya kawo mata. Kafin tai wani yinƙuri ya buga kanta da bango. Ƙarar azaba ta saki jikinta na rawa, yayinda hannunta ke kan nasa tana kiciniyar ƙwatar kanta amma hakan ya gagara, dan gaba ɗaya haushinta dana Kainaat ne ya tattara a kanta. Yanda yake jin kansan nan har shi wannan yarinyar zataima wannan zagin. Dolene ya nuna mata banbancin mace da namiji. Sai da ya tabbatar ta galabaita da irin shaƙar da yay mata sannan ya shiga jibgarta tamkar an aikosa. Bata da wani ƙarfin koda guduwa, dan tamkar ma numfashinta na barazanar barin gangar jikinta ne. Cikin abinda bai wuce mintuna biyar ba Dafeeq ya jima Khadijah ciwuka tako ina sai jini ke fita gashi ta galabaita ko motsin kirki bata iyayi balle kuka. Ga zagi yana mata na rashin mutunci ta yanda duk wanda ya kallesa yasan yana a cikin matsanancin fushi... Headphones ɗin data saka ta cire kunne ɗaya kaɗan dan taji koya haƙura ya tafi, a zabure ta miƙe jin yana dukan abu kamar mutum yana zage-zage. Abinka da dare gaba ɗaya gidan amsawa yake yi. Bama tasan sanda ta zabura zuwa ƙofa ba ta buɗe. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un ” ta ambata jikinta na rawa idanunta gaba ɗaya a waje. Ganin fa da gaske zai iya kashe yarinyar mutane a gidanta ya ja mata masifa tasa dukan ƙarfinta wajen hankaɗashi gefe da faɗin, “Kai ko kanada hankali yaron nan? Kasheta kake son yi ne?”. “Yaro yana bayan uwarsa ke kuma! Idan na kashetan miya shafeki? Ko kinada alaka da ita ne?”. Ya faɗa a zafafe. “A'a ALLAH ya rabani haɗa alaƙa da wannan. Kai dai da kaji ka gani kaita kaya. Amma maganar gaskiya bazakai min kisan kai anan ba. Ɗaukarta ku koma inda kuka fito idan ka gadama ma kayi bandarta bai daman ba. A gidana ne dai baza'ai kisan kai ba dan babu mai sakani a masifa ina zamana lafiya.” Harara ya zuba mata jikinsa na tsuma, ji yake tamkar itama ya rufeta da dukan ma. Sake watsa mata hararar yay da yarda belt ɗin hannun nasa ya shige ɗakin data fito. Itama hararar ta raka bayansa da ita, kafin ta nufi hanyar ƙasa dan ita kam bataga dalilin da zaisa ta bari su kwanar mata gida ba, musamman ma Khadijah dake nishin mutuwa. Babu jimawa sai gata ta dawo da maigadi. Khadijah dake kwance a sume ta nuna masa. “Kaga ɗauketa ka fitar min da ita a gida, inda ma zaka taimakan ka kaita can bakin titi dan ALLAH tunda ba wani nisa bane”. Cike da tsoro maigadi ya ce, “Hajiya bakin titi yanzu a daren nan, idan aka kamani fa? Karki manta mace ce fa wani ma sai ya ɗauka fyaɗe namata ai”. “Bamu da wani zaɓi ai Dauri sai wannan. Dan wlhy kaga wannan yarinyar ta mutu a gidan nan kaima bazaka sha ta daɗi ba. Inada dukiyar da zan iya tsallake ƙasar nan batare da ansan ina naje ba. Wannan mahaikacin dana jajiboma kaina wlhy a daren nan zai iya haurewa yabar garin nan shima faɗamin wanene a ruwa?”. Rawa jikin Dauri maigadi ya fara, dan tabbas gaskiya Hajiya tafaɗa. Shiko idan hakan ta kasance ai ya shiga uku. Kwata-kwata watansa na biyu kenan da yin aure. Amaryarsa nacan ya baro a ƙauyensu. Kuma Hajiya tasan garinsu koya gudu zata iya saka ƴan sanda su bishi. Ɗaff ya raba Khadijah da ƙasa cikin karkarwar jiki yay sauka zuwa ƙasa. Har cin tuntuɓe yake ga nauyin mutum ko yace gawa dan a yanzu Khadijahn bata da banbanci da hakan. Yana sauka Dafeeq na buɗe ƙofar ya fito, takarda ya jeho batare daya kalla sashen da yabar Khadijah ba. “Karna tashi na ganki a gidan nan da safe. Kije na sakeki saki. Abinda zaki tarar acan ɗin ma ya isheki daga ke har iyayen naki wawuya kawai ƴar iska. Ai ba'a haifi macen da zata maran ta zagan na barta ba, idan kina tunanin kinyi na farko kinci riba yanzu bazaki cita ba kuwa. Dolene kije ki ɗanɗana hukunci mafi tsauri dan nasan rabuwa dani shine mafi girman bala'i a rayuwarki, sai dai ki wuce Legas ki kama ɗaki matsayin karuwa dan waɗan nan iyayen naki masu kama da kafiran farko musamman ubanki ba sake kallonki zai ba”. Daga haka ya koma ciki tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da Kainaat da ke tsaye galala tana kallonsa da saurarensa ta zabura. Takardar ta ɗauka, cikin matuƙar mamaki ta ware idanunta, dan kuwa da gaske sakin ne har biyu ya rubuta. Ita dake shirin aje mata wajen malami akan hakan sai gashi ta samu cikin sauƙi haka. Kai gaskiya ita ɗin ƴar baiwa she ma to. Wani shegen murmushi ta saki mai ƙayatarwa da sanyaya zuciya, babu tausayi ko ɗar a ranta ta sumbaci takardar da kashe ido ɗaya ta ce, “Kin zama labari a tarihin rayuwar Kainaat Khadijah. Karki damu nima kwanaki biyar ya ragen na biyo bayanki, sai dai banbancina da ke ni wajen mijina masoyina abin alfaharina zan koma”. Dariya ta saki, sai kuma ta dafe bakin da sauri ta sauka ƙasa da gudu. Ta sami Dauri na ƙoƙarin buɗe ƙofar falo zai fita da Khadijah. Cike da nishaɗi ta saƙala takardar a cikin rigar Khadijahn sannan ta buɗema Dauri ƙofar da kanta ranta fes babu tausayi ko ƙanƙani a ranta.... (Hummm😶). ___________★ Sosai Anoosh ke laulayin cikin nan. Ga JJ yaƙi zuwa har kwanaki biyu sun wuce. Kullum cikin kiransa Hajiya Lailah tare yana kawo mata uziri. Ganin an tafi sati uku baida alamar zuwa ta fahimci yawo kawai yake da hankalinta. Ranta ya sake kaiwa ƙololiwar ɓacin da ta kasa cigaba da riƙe abinda ke ranta ranar tai masa wankin babban bargo a waya. Tare da tabbatar masa saita wulaƙanta rayuwarsa fiye da yanda ya wulaƙanta mutuncin ɗiyarta. Dan haka ya saurari sammaci. Ko tari JJ baiyi a wayar nan ba yayinda Hajiya Lailah ke masifa, sai da ta gama tsaff yaja tsaki kawai tare da kwashewa da dariya ya ce, “Lallai Hajjaju baki san wanene ni ba kenan. Ni kike tunanin wai ki wulaƙanta? To bissmilla ga fili ga mai doki saura sukuwa. Ƴarki kuma da kike maganar na shiga mutuncinta ki tambayeta ai tare muka ji daɗin, hasalima da kanta take kawo min kanta. Dan haka sai ki shirya wulaƙantani da wulaƙantata dan a tafin hannuna take saboda ni bana ƙwaina sai da zakara Hajiya. Ki duba WhatsApp naki ga saƙonan na tura miki, sannan ki shirya taki wulaƙantar ke da ballagazar ƴarki kafin ki shirya wulaƙantanin kinji. Dan na fahimci kin manta duk abinda NAMIJI yayi ado ne, MACE ita ce cikin ruwa tsundum. Na barki lafiya, idan ta haihu namiji a saka masa sunan babanta, idan mace ne kuma Lailah. Kar kuma a haifamin bebiya dan ALLAH hhhahahah”. Ya ƙare maganar da wata irin mahaukaciyar dariya data saka jikin Hajiya Lailah rawa. Gaba ɗaya ma ita ta kiɗime, tsabar yanda komai ke neman juye mata ta rasa ina zata kama. Da ƙyar ta iya kaiwa zaune ta shiga WhatsApp jikinta na rawa. Gigitacciyar ƙara ta saka mai firgitarwa tare da sakin wayar ƙasa ta sulale a sume. Da gudu Anoosh dake kwance a ɗaki cikin bargo ta fito, zubewa tai gaban mahaifiyarta tana mai kwala kiran sunanta da girgizata. Babu alamar numfashi a tattare da ita, baki ta sake buɗewa zata ƙwala kiran sunanta mararta tai wani kalar masifar ƙullewa. Da sauri ta saketa tare da dafe cikin da duka hannayenta biyu. Azaba ta sata kwanciya ta naɗe jikinta waje gudu hawaye masu zafi na tsiyaya a idanunta. Shirun ta ya sata jiyo sautin muryarta daga cikin wayar mahaifiyarta, sauti ne mara daɗin ji da gigitar ta tunani, duk da azabar da take ciki haka takai hannunta dake rawa da ƙyar ta ɗauka wayar, (innalillahi...) Kawai ta iya ambata a zuciyarta wayar na suɓucewa daga hannunta. Ɗaukewar numfashinta dai-dai da ɓallewar jini da ga jikinta tamkar an buɗe fanfo... Hajiya Lailah ta fara farfaɗowa gabannin asubahi, yayinda tana buɗe idanunta da ƙyar ta saukesu akan fuskar Anoosh dake kwance hawaye duk sun bushe mata a ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Ƙarnin jini da laimar da taji tana ciki ya sata zabura a firgice. Sai dai da ƙyar ta iya tashi saboda nauyin da kanta yay mata ga jiri na ɗibarta. “Ya ALLAHU Sadiyya!”. Ta kira ainahin sunan Anoosh ɗin da ƙyar jikinta na ɗaukar sabon rawa. Hannu takai da niyyar taɓata sai dai ta kasa, dan ƙirjinta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Yaraf ta koma ta kwanta, dai-dai da shigowar wasu ƙartan maza huɗu cikin falon fuskokinsu a rufe da ƙyalle. Dishi-dishi take iya ganinsu, amma hakan bai hanata ƙarfin halin ambaton, “Su wanene ku?”. Ba Ƙyallen ɗaya da ga ciki ya janye daga kan tasa fuskar yana wani kalan taunar cimgam kamar ɗan daudu. Ya kalleta sheƙeƙe yana kaiwa zaune tare da dire kakkaifar wuƙarsa ƙasa yana jujjuyata. Wuƙar Hajiya Lailah ta zubama idanu, sai kawai bugun zuciyarta ya ƙaru. Hannu biyu tasa ta dafe ƙirjinta, sannan ta fara magana da ƙyar. “Na roƙeku idan kashemu kuka zo yi kada ku aikata hakan, idan kuma yazama dole ne, ni ku kasheni ku barmin yarinya ta rayu. Dan ALLAH ku barta ko zamu samu mai mana addu'a ni da mahaifinta. Ita ɗin yarinya ce mai raunin ji da gani, bata san komai ba sai mu da neman ilimi. Na roƙeku kumin hukuncin da duk zaku mata duk da ban san laifin da mukai gareku ba......” tari ne ya sarƙe ta ta kasa cigaba da magana. Maimakon suji tausayinta ma sai suka kama dariya, tare da ɗaukar wayarta suka shiga kallon videon Anoosh da JJ dake cikin wani yanayi, sai dai ba'a ganin fuskar JJ ɗin sai Anoosh. Wani irin ihun shaƙiyanci suka saka daya ƙara ƙarfin bugun zuciyar Hajiya Lailah, a take ta fara aman jini. Sai lokacin sukai kanta, wanda ya buɗe fuskar tasan nan dake tabbatar da ogansu ne ya riƙota ya rungume yana wani abu na ƴan iska da faɗin, “A bari nima na more anan dan naga uwar da ƴar duk jirgi ɗaya ne, ba oga JJ bane kawai zaisha romon nan”. Dariya yaran nashi suka shiga yi, babu alamar tausayi a tattare da shi ya bama yaransa umarnin zuwa su bincike gidan duk wani abu mai muhimmanci su kawo masa shi, shi kuma ya shiga aikata sheɗanci da Hajiya Lailah da ita tuni ma ta fita a hayyacinta dan zuciyarta ta buga. Ko a lokacin daya ɗaga daga jikinta da alama rai yayi halinsa ma. Amma babu ko tausayi da imani tattare da shi, da alama ma baisan ta rasuba tsinannen.. Raba jikinsa da nata dai-dai da dawowar yaransa da tarkace a hannunsu. Na takardu dana wasu abubuwan daban-daban masu alaƙa da dukiya. Sai kuɗi da basu wuce 200k ba da suka samu a gidan. Cikin yaransa wani yaso haikema Anoosh shima amma ganin jinin dake fita a jikinta ya sashi haƙura cike da takaici ya shureta a ciki da shegen takalminsa yana faɗin, “Shegiya ƴar baƙin ciki”. Komai sai da suka tattare har wayoyinsu sannan suka kunna candles guda biyu suka ajiye a kusa da carpet da kujera, basu fita ba har sai da wutar ta fara kama kujerar sannan suka gudu lokacin anata kiran sallar farko ta asubahi. Ƙauri da hayaƙin wutane ya fara kai hankalin mutane masu fitowa sallar asubahi. A take aka fara binciken ta ina hayaƙin ke fitowa. Kafin hankali ya kai gidan wuta ta fara ci sosai. Kusan gaba ɗaya rukunin gidajen wajen aka ruɗe. Tuni har mata sun fara fitowa a guje da yara. Kafin kace mi an ɓalle ƙofar gidan da ƙyar aka shiga, tako ina ƙoƙarin kashe wutar akeyi, dan iya falonsu kawai ta kama bata fara zagaye gidan ba. Dalilin wani ma'aikacin ƴan kwana-kwana dake anguwar yasa aka samu nasarar isowarsu da wuri dan shi yay waya. Zuwansu ya bada gudunmawar samun nasarar kashe wutar akan lokaci, yayinda aka fito da Anoosh da Hajiya Lailah jikinsu duka a saɓule ko iya shaidasu ba'ayi. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Wannan tashin hankaline da ba'a taɓa ganin makamancinsa ba a anguwar, an wuce dasu asibiti duk da ba'a da tabbacin ma suna numfashi. Yayinda mutanen anguwa keta faman kuke-kuke. Dan Hajiya Lailah mutuniyar kirki ce, sannan Anoosh yarinyace mai tarin nutsuwa da hankali, sannan a dunƙule ma rayuwarta abar tausayice ga duk mai imani kasancewarta bebiya ga raunin gani, ga rauni na kasancewarta ɗiya mace. Kai koda maƙiyinsu a yau hankalinsa tashe yake. Gashi babu wanda yasan danginsu sai Gwaggo kuma itama ALLAH yay mata rasuwa. Sai kuma wanda kowa yasan Anoosh zata aura wato JJ. Dan haka ma wanda suka ɗan sanshi musamman waɗanda Hajiya Lailah ta wakilta suka amshi kuɗin auren Anoosh hankali tashe suka nemosa a waya, tare da faɗa masa ya maza yazo su Hajiya Lailah sunyi gobara.........✍️ _Nagode da addu'oin ku tare da kiran wayoyinku🙏🏻🙏🏻😘😘😘_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha takwas_ ______________ https://chat.whatsapp.com/CKY0xZDtpby6MTkGrPkXLr *_Assalamualaikum warahmatullah_* *_Kin dade kina neman gurin da zaki siya kaya amintattu masu quality cikin farashi me sauqi?_* *_ina marabtarku zuwa cikin wannan gida tare da kasancewa da juna,WANNAN GIDANNA HUGUMA CLOSET NA BUDESHI NE SABODA NA BAKU DAMAR SIYAN KAYA MASU KYAU QUALITY DA KUMA SAUQIN KUDI CIKIN AMINCI DAGA GURINA,MASU SIYAN D'AI D'AI DA MASU SARI,NATION WIDE DELIVERY cikin aminci da izinin Allah,Kayan haihuwa na jarirai har zuwa girmansu,ina muna fatan alkhairi ni da ku gaba daya_* _________________________ ......A matuƙar hargitse JJ ya iso anguwar. Hakan ya tabbatar da dama yana gari babu wata Kaduna da yaje. Amma da yake su basu san komai akan batun ba sai tausayin yanda yake kuka ana riƙesa kamar wani mace ƴan anguwar sukeyi. Da yaje asibiti yaga su Anoosh kuwa sai ya yanke jiki ya faɗi wai ya suma. Sai da aka yayyafa masa ruwa tare da bashi gado. Dan da gaske razana yayi ganin Anoosh bata mutu ba ita. Sai dai bata san inda kanta yake ba tana cikin wani hali mai wahalar fassara... JJ shine ya zama tamkar ɗan uwa na jini wajen jana'izar Hajiya Lailah, dan shine akan gaba, sannan shine ma ake ma gaisuwar. Shine ya kawo ƴan sanda akan shi bai yardaba sai a bincika a tabbatar da dalilin gobarar da alamu da yawa suka nuna akwai lauje cikin naɗi. Ba komai ya saka JJ yin hakan ba sai tsoron kar Anoosh ta rayu al'amari ya zama wani abu daban. Ƴan sanda sunyi bake-bake akan case ɗin, yayinda cikin ikon ALLAH suka samu wani ɗan alama da ya sakasu jin cewar lallai maganar JJ nada ƙamashin gaskiya, dan haka suka jajirce akan son binciko komai. A zahiri JJ na sake ingizasu da tsayawa tsayin daka akan binciken, a baɗini ko hankalinsa tashe yake da bin matakan toshe komai da zai bayyana gaskiya, tsabar son a yadda da shi ya kawo iyayen ƙaryar nan dai an ɗaura masa aure da Anoosh dan ya tabbatar musu da akowane hali take shi dai yana sonta. An jinjina ma wannan sadaukarwa tashi ƙwarai da gaske a anguwar, duk da ma auren an ɗaurashi ne kawai bayan idar da sallar magrib kamar yanda ya buƙata tare da waliyansa na ƙarya. Komai na Anoosh ya koma ƙarƙashin JJ batare da sanin kowa nashi ba, dan hatta ƴan san jin yanda akai idan sun so yin magana da shi baya yarda sai ma ya hau musu kuka akan shi su barshi yaji da abinda ya damesa. A haka Anoosh ta kwashe tsahon shekara kusan ɗaya kwance a asibiti. Tako ina al'umma na kawo taimako da gudunmawa, duk kuma abinda aka bada kai tsaye a asusun JJ yake tafiya. Duk da dai ana cire wasu ai hidimar asibitin. Tana da shekara ɗaya da wata uku likitoci suka bada shawarar fita da ita ƙasar waje yimata wani ai. Ɗari bisa ɗari JJ ya yarda da batun, har ma an fara shirye-shiryen hakan, sai dai kwanaki uku dayin maganar ALLAH yay mata rasuwa. Ta rasu idanunta ƙyam akan JJ tana hawaye. Yanke jiki JJ yay ya faɗi a wajen, sai da doctor ya tsaya kansa ya farfaɗo. Yanda yake wani irin kukan tashin hankali dole ka tausaya masa, dan harga ALLAH da gaske kukan yake yi. An kai Anoosh makwancinta na gaskiya JJ na a wani hali, bai kuma samu kansa ba sai a washe gari. Kamar yanda ya zama komai a yayin rasuwar Hajiya Lailah a ta Anoosh ma dai shi akema gaisuwar har akai addu'ar uku. Bayan ƙura ta lafa ya ɗan cigaba da zuwa anguwar har bayan wasu watanni, dan haka gidan su Anoosh ya cigaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar ƴan sanda da dattijan anguwar. JJ ma dake zuwa jefi-jefi ya rage zuwa. Watanta bakwai da rasuwa ya haɗu da Alimah. Ƙyaƙyƙyawar yarinya mai kama da larabawan Sudan. Dan Alimah ba fara bace, sannan bata kasance baƙa wulik ba. Mace ce har mace a tsaye da sura ga ƙyawun fuska da ko mace ta kalleta sai ta sake kallo. Alimah dai ƙawa ce ga Rabi'ah ƙanwarsa. Department ɗin su ɗaya a F.C.E. A wata ranar babbar salla tajema Rabi'ah yawo gida sukaci karo da JJ a ƙofar gida. Cikin masifa ya ɗago a zatonsa a cikin ƙannensa ne. Amma sai yaci karo da halittar data nema gigita rayuwarsa. Dan kuwa dai sumar tsaye yayi har Alimah ta gama magiyar bashi haƙuri baima san tanai ba sai da Rabi'ah ta taɓashi ya dawo hayyacinsa. Bai iya cewa komai ba, face gyaɗa kai tamkar wani dole. Bayan shigewarsu gida sai shima ya fasa fitar ya koma ciki. Zama yay a falo tare da su, dukkan wani motsin Alimah akan idonsa ne. Tun ma bata farga ba har dai ta tsargu. Al'amari kamar wasa dai sai ga magana ta zama babba, dan lokacin da Alimah da ƙanwarta suka tashi tafiya sai JJ ya dage akan zai kaisu gida. Badan taso hakan ba ta amince aka tafi harda Rabi'ah suka maidasu gida. Wannan shine sanadin da JJ yasan gidan su Alimah. Bayan sun dawo gida kuma ya titsiye Rabi'ah da tambaya akan Alimah. Itako ta sanar masa komai. Tun daga lokacin JJ ya koma kai Rabi'ah makaranta da kansa, yakan je kuma ya ɗakkota duk dan Alimah, sai dai duk yanda yaso Alimah ta kulashi hakan ya gagara, iyakarta da shi gaisuwa matsayin yayan ƙawarta Rabi'ah. Irinsu JJ idan ALLAH ya tashi kamasu ba'a magana, dan kuwa dai da gaske neman zaucewa yake akan Alimah, yayinda itako ta cigaba da jansa a ƙasa. Bawai wulaƙanci take masa ba ko zaginsa, kawai dai bata shiga sabgarsa ne bayan gaisuwa. Taƙi kuma bashi fuskar tunkararta koda da magana ne. Haka ya cigaba da haƙuri da jurewa dan so yakema Alimah na gaskiya, soyayya ta aure. Har faɗama abokansa su MB yake shikam ya samu matar aure. Hakama gidansu kowa yasan yana son Alimah. Dan danan JJ aka fara gini, sannan ya rage abubuwa da yawa musamman akan harkar mata. Da farko iyayensa sunyi mamakin inda ya samu kuɗin gini haka, dan filin kansa ba wannan suka sani nashi ba. Amma sai ya musu bayani akan kasuwanci ya shiga shi da wani uban gidansa aka samu yay albarka, hasalima ubangidan nasa ne ya bashi filin. Sanin wanda yake kira da uban gidan nashi yasaka su yarda, duk da kuwa ya kamata a matsayinsu na iyaye su bincika uban gidan nasa tunda bawai ya wani jima da kawoshi garesu ba ne. Amma tunda kudi na shigowa yana ɗaukar wasu daga cikin ɗawainiyarsu sai babu wanda ya sake masa magana akan hakan. Ya cigaba da ginin gidansa da yaƙin campaign ɗin soyayyar Alimah, wadda da ƙyar da ƙyar ya samu ta fara kulashi. Ya fara rawar jikin kashe mata kuɗi mahaifinta ya taka masa birki, tare da shimfiɗa masa dokoki na neman ƴarsa in har da gaske yake. Babu musu JJ yabi kowace doka, dan hatta hira bayayi da Alimah sai a falon mahaifinta tare da ƙannenta biyu. Sannan akwai cctv camara a falon da mahaifin nasu ke ganin duk wani motsinsu da ga bedroom ɗinsa. Sannan a sati sau biyu yake zuwa kawai hira, dokace bazai tsareta a hanya ko makaranta ba ko dan ya ganta a gidansu. Ako ina suka haɗu gaisuwace kawai, hira dole sai yazo gidansu. Da yake da aure JJ keson Alimah duk ya amshi waɗan nan dokoki da hannu biyu kuma yana kiyaye wa har iyaye suka shiga cikin lamarinsu. Ahakan ma dokar bata sauya ba, dan duk da mahaifinsu ba wani mai kuɗi bane akwai dai rufin asiri tsaye yake akan ƴaƴansa. Shekara ɗaya aka saka bikin, akwana a tashi ta cika aka shiga shagalin biki. A gidan su Alimah ɗaurin aure kawai sukayi babu wata bidi'a a ciki, sai dai bayan an kaita gidan su JJ ne suka ɗora da nasu bikin a yanda suke so. Shine akai dinner da dare bayan an kaita gidansu, washe gari aka kaita ɗakinta.... ★______________★ Hayaniyar mutane a kanta da zafin hantsin rana daya fara fitowa suka farkar da ita. A hankali take ƙoƙarin buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi, bata iya gane komai sai cakai-cakai ɗin mutanen da kowa ke faɗar albarkacin bakinsa game da ita. Wasu na ganin accident ne, wasu na ganin ɓarayine sukai mata haka suka yardata a bakin titin. Sai dai an kasa samun ko mutum ɗaya da zai taimaka mata. Hasalima kowa tsoron taɓata yake yi. Dai-dai tana ƙoƙarin sake buɗe idanunta a karo na biyu wata mota baƙa wulik mai ƙyawun gaske ta iso wajen. Kasancewar a hankali motar ke tafiya harta ɗan gotasu sai kuma aka gangara gefen titi ta gabansu kaɗan. Wasu hankalinsu akan motar yake, yayinda wasu ke cigaba da surutansu akan Khadijah. Da sauri drivern motar ya fito domin cika umarnin ogansa da yace yaje ya duba mike faruwa a wajen, ya nufo taron mutanen da ƴar sassarfa yana faɗin, “Bayin ALLAH lafiya kuwa? Mike faruwa kuka taru anan haka?”. “Wlhy wata yarinyace aka samu kwance anan kamar ma ta mutu duk raunuka a jikinta. Sai dai bamu san miya sameta ba ko dalilin yasar da ita anan ɗin. Gadai tanan da alama ta farfaɗo ma”. Wani magidancin dattijo ya bashi amsa cike da kulawa. Mamakine ya kamashi har ya bayyana a saman fuskarsa. Amma sai baice komai ba ya juya ya koma motar. Saitin sit ɗin baya ya tsaya tare da ɗan rissinawa yanda zai iya gani wanda ke ciki. Glass ɗin aka sauke a hankali, wani ƙyaƙyƙyawan kamilin matashin mutum ya bayyana. Cikin dattako da tausasa lafazi ya furta “Mike faruwa ne Awwal?”. “Wata yarinya ce Yaya aka yasar a wajen, sai dai suma basu san accident tai ba ko jefar da ita akayi, amma dai tana cikin wani hali kuma duk suna jin tsoron taimaka mata”. Shiru yay yana kallon Awwal ɗin cikin yanayin mamaki da ɗan ɓacin rai, sai kuma ya girgiza kansa batare da yace komai ba ya buɗe motar ya fito. Da sauri Awwal ya matsa ya bashi hanya. Tun fitowarsa motar ƙamshin turarensa ya baɗe wajen, hakan yasa mafi yawan mutanen waigowa suna kallonsa, sai kuma wasu suka shiga rawar jikin gaishesa duk da kuwa basu san wanene ba, sai dai kuma a duk inda mai kuɗi yake a cikin al'ummar mu ta yanzu zakaga an ɗaukesa ne da muhimmanci koda ba'asan wanene ba ko inda ya fito. Hannu kawai ya ɗaga musu cikin gyaɗa kai da faɗin, “Barka”. Sai kuma ya ɗan bisu da kallo da sake faɗin, “To mizai hana da wannan zagayetan da kukai ku ɗauketa ku kaita asibiti bayin ALLAH”. Ai kamar wanda yay shela a kunnuwansu, a take suka shiga darewa. Yayinda wasu ma suke ƙoƙarin barin wajen suna ƙunƙuni alamar dai su bazasu taimaketa ba kenan. Mamakine yake neman halakashi a tsaye, sai dai kuma bai gama haɗa mamakin nasa ba idanunsa suka sauka akan yarinyar dake kwance a wani yanayi mai ban tashin hankali da al'ajabi. Duk da shi ba ɗan sanda bane a kallo ɗaya da yayma Khadijah ya fahimci ba accident taiba dukane wannan. Bai ma san lokacin daya ƙarasa gareta da sauri ba yana baton sunan UBANGIJI.. Har ya kai hannu zai taɓata sai kuma ya dakata, sake ɗagowa yay yabi mutanen dake wajen da ido, babu abinda yake buƙatar gani, wato ƴar uwarta mace, hakan ya sashi ɗaukarta cak batare da ya kalleta ba zuwa motarsu dan gaba ɗaya mutanen wajen ma haushi suke bashi. Da sauri Awwal ya buɗe masa gaban motar alamar ya sakata anan. Amma sai ya girgiza masa kai da masa nuni da sit ɗin baya. Babu yanda Awwal ya iya sai cika umarni, a bayan ya kwantar da ita, shi kuma ya koma gaba ya zauna, yana ƙoƙarin rufewa Awwal ya miƙa masa takardar data faɗo daga jikin Khadijah. “Yaya daga jikinta ta faɗo.” Takardar ya ɗan zubama ido kamar bazai amsa ba, sai kuma ya amsa batare da yace komai ba ya ajiye gaban motar. Zagayawa Awwal yay mazaunin driver, yana ƙoƙarin ma motar key ya ce, “Zamuje asibiti ne Yaya?”. Kai ya gyaɗa masa alamar eh. Jin sun fara tafiya Khadijah dake jinsu ta kai hannunta da ƙyar saman fuskarta ta share hawayenta. Cikin muryarta dake fita da ƙyar ta ce, “Dan ALLAH na roƙeku kada ku kaini asibitin garin nan ku wuce dani Kano. Idan ma mutuwa zanyi na mutu gaban iyayena ko zasu yafemin kar naje ga UBANGIJINA yana mai fushi da ni”. Da mamaki Awwal da yasan ba lallai Yayan nasa ya tanka ba ya ɗan dubeta ta mirror da faɗin, “Haba ƴar uwa wane Kano za'a wuce da ke a wannan halin, babu abinda kike buƙata ai sama da kulawar likita a yanzu”. Kuka ta sake fashe musu da shi tana cigaba da magiya. Har sun ɗauki hanyar asibiti idanunsa akan wayarsa tamkar baima san mike faruwa a motarba a hankali ya furta, “Muje airport ɗin”. Sosai Awwal yay mamakin jin abinda Yayan nasa ya faɗa, dan shi dai yasan sun riga sun sayi ticket ɗinsu guda biyu tun a jiya da dare. Sai dai bai iya cewa komai ba sai amsawa da “to” cikin girmamawa. Daga haka ya ɗauki hanyar airport ɗin. Suna isowa airport ɗin yay kiran wani Attahir. Cikin mintuna kaɗan sai gashi ya isa. Fita yay yana bama Awwal umarnin zama a motar ya jirashi, shi kuma suka nufi wata hanya shida Attahir ɗin bayan ya leƙo yaga Khadijah da barcin wahala ya figa.... ★Koda gari ya waye Dafeeq yayi zaton Khadijah na gidan bata wuceba. Dan shi a tashi wautar bazata iya barinsa ta tafi ba kodan wasu dalilai. Ƙwaƙwƙwara a cikinsu shine bazata iya tunkarar iyayenta ba saboda tsoro. Sannan tana masa matsanancin son da bazata iya taɓa rabuwa da shi ba. Ko sakin da yay mata guda biyu yayine dan gargaɗi, zai kuma maidata amma sai ya wajiga rayuwarta ta yanda ko kallon banza bazata sake marmarin sake kwatanta yimasa ba. Sai ta koma masa tamkar baiwa ta yanda kozai maidata ƙasa dan takawa bazata sake koda tari ba. So yake ta koma jin tsoronsa fiye da yanda takeyi a baya. Baibi takan Kainaat ba sai ma hidimarsa yake hankali kwance kamar baida wata damuwa. Nan ko can ƙasan ransa addu'a yake ALLAH yasa Khadijah tazo ta bashi haƙuri da wuri. Anci Sa'a kamar yanda ya share Kainaat ɗin itama ta tattarashi ta watsar a wannan yinin ita a dole fushi take da shi. Hasalima yini tai a ɗaki kwance. Sai kusan uku na rana aka kawo mata order na abinci da tayi sannan ta sakko ƙasa. Sun fito kusan tare da Dafeeq da ke kwance shima a ɗakin, sai dai rashin jin motsin Khadijah ya damai ya ce bara dai ya fito ya duba. Sake tamke fuska yay lokacin da suka haɗa ido da Hajiyar tasa. Itama sai ta ɗauke nata kan batare da tace komai ba ta haura sama abinta cike da takun izza da taƙama. Ƙwafa yay da cije lips ɗinsa, yayinda yake ayyana abubuwa a ransa kawai. Sai da yaji shigarta ɗaki da rufe ƙofa sannan ya nufi ɗakin da Khadijah take da sassarfa. Sosai gabansa ya faɗi ganin ɗakin wayam, amma sai ya ƙarfafa kansa ya nufi toilet. Nanma babu kowa, babu ma alamar anyi amfani da ruwa dan ko'ina a bushe yake. Ji yay zuciyarsa na motsi a cikin ƙirji, dan haka ya fito har ƙafafunsa na harɗewa. Ƙofofin ɗakunan ƙasan ya shiga buɗewa, sai dai ko'ina babu ita babu alamarta. Shine har kitchen, nan ma wayam, ya sake komawa sama ya dudduba, nan ma dai shiru. Da sauri ya sakko ƙasa zuwa wajen maigadi........✍️ _Huummm Dafeeq. JJ 😡😡_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na goma sha tara_ _____________ METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da'ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained. METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba. Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah Yana da matakai 1....12 Level 1 anafarawa da 5$ Level 2 anadarawa da 10$ Level 3 anafarawa da 20$ Hakadai har zuwa level 12 Alkhairan metaforce Kingama register za'abaki TR coins na adadin level din da kika bude Samun reffaral bonus Ga garabasar spillover Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake Babu faduwa Babu asara aciki Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al'umma. Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah Phone number 07038708382/09069163665 _________________ .......Wani irin jijjiga zuciyar Dafeeq tai a dalilin jin amsar da maigadi ya bashi cewar ai tunda safe wai Khadijah ta fita a gidan. Baki ya buɗe zai masa masifa sai kuma ya fasa tamkar wanda ya tuna wani abu. Ciki ya koma, babu jimawa sai gashi ya dawo da key ɗin mota a hannu. Dan zuciyarsa na sanar masa Khadijah na can tsohon gidansu ne. Sosai ya dinga gudu duk da babu nisa sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso. Ji yay ya ɗan samu nutsuwa ganin gidan kamar ba'a kulle ba, dan haka ya afka ciki yana wani cika da batsewa shi a dole zaiyi hukunci. Sai dai me, tako ina babu alamar Khadijah a gidan, kai hasalima kamar babu wanda ya shigo gidan. (Kodai gidan Baba Hakimi ta tafi) zuciyarsa ta ayyana masa cike da ƙarfafawa. “Tabbas hakanne ma, dan nasan ko giyar wake tasha bazatace zata tafi Kano ba kuwa. To inama taga kuɗin motar tafiyar ne. Aiko bazan je ba, ta gama guje-gujenta har sai nan da kamar wata ɗaya ma zan leƙa gidan baba Hakimin sannan ta gama galabaita. Barima na cire layin da duk ƴan gidan suka sanni da shi ta yanda zan ƙara dafata da gigita rayuwarta”. Ya ƙare faɗa yana wani murmushi da ciro wayarsa a aljihu ya cire layin da yasan su baba Hakimi zasu iya samunsa da shi. Fitowa yay ya kulle gidan, daga haka ya tattara batun Khadijah ya watsar gefe, dan daga nan gidan abinci ya nufa yaci ya ƙoshi sannan ya fito zuwa wani hotel ya kama ɗaki dan itama Kainaat ɗin yay alƙawarin sai ya mata yaji na kwana biyu, sannan ya tsara yanda zai fara aiwatar da shirinsa a kanta dan ya fahimci itama ƙwalluwar kanta ce dole sai ya tashi tsaye... 🚴🚴🚴Hummm ___________ Babu wanda ya iya ƙwaƙwƙwaran motsi a tsakanin Baba da su Mujee. Sun zubama JJ dake kuka ido kawai zukatansu na duka tamkar zasu ɓallo ƙirazansu su fito waje. Tsahon mintuna biyar sannan cikin ƙarfin hali mahaiyarsu da suke kira Inna ta share hawayenta muryarta na matuƙar rawa ta ce, “Jazool kai ne ka aika aka kashe su kenan?”. “Wlhy Inna ni bance su kashesu ba.” JJ ya faɗa cikin shaƙewar murya da karkarwar harshe hawaye na kwaranya a idanunsa.... A fusace Yaya Inusa ya ce, “Munafuki ƙarya kake yi. In ba kai kasa su kashesu ba ya akai sunanka ya fito a bakinsu. Dolene dasa hannunka a mutuwar bayin ALLAHr nan Jazool. Ka zaluncemu ka ɓata mana sunan gida, ka zubar mana da mutuncinmu. Idan aure kake so miyyasa bazaka faɗa mu maka ba. Duk da mu bamasu ƙarfi bane na tabbatar bazamu gagara maka aure ba harda ginin muhallin zama. Miyasa ka aikata wannan zalincin Jazool? Miyasa kasa a kashe su? Mi suka maka innalillahi wa-inna ilaihiraji'un...” kuka ya sarƙeshi. Yunƙurawa JJ yay zai tashi amma ya kasa sai jikinsa ne ke rawa. Dole ya koma ya kwanta yana jujjuya kai ga hawaye na zuba kamar an buɗe fanfo. “Yaya wlhy bance su kashesu ba, na turasu ne kawai su amso min wayoyinsu su kuma kwaso min takardun gidan, nayi hakanne dan na ɓoye duk wani abinda Hajiya Lailah zata iya amfani da shi wajen tona min asiri. Takardun gidan kuwa zan mata barazana da shi ne bayan ta yarda bazata fidda maganar ba sai na maida mat.....” Tauuuu!!!!. Ka ke jin saukar wani gigitaccen mari a kan fuskarsa. A take kowa ya gigice a ɗakin aka shiga waige-waige. Yayinda JJ ya dafe kunci ya fashe da wani irin marayan kuka tamkar zai shiɗe. Wani marin aka sake ɗauke fuskarsa da shi, sai gashi zaune dingan gan yana kwara ihu da waige-waige. Amma abun mamaki babu alamar wanda ke marinsa. Sake ƙwala gigitacciyar ƙara yayi yana zabura da mamuƙe cinyarsa. Dai-dai nan Alimah ta bayyana a cikin idanunsa da wuƙa jazurr alamar an sakata a cikin wuta ne. Dan gaba ɗaya inda ta ɗora masa wuƙar ma ya yaye. Sai azaba mai ratsa kwanya dake shiga har a tsakkiyar ƙwalwar kansa. Sauran ƴan ɗakin ba ganinta suke ba, dan haka duk sukayo kan JJ ɗin suna tambayarsa mike faruwa da ƙoƙarin ganin cinyarsa daya riƙe gam. Bai iya basu amsa ba, sai kuma da yake yana faɗin, “Dan ALLAH kiyi haƙuri zan faɗi musu gaskiya, ki taimakeni ki bar ƙonani, dan ALLAH kada ki kasheni na tuba. Wlhy ni ne nace su sakama gidan wuta bayan sun ƙwace komai nasu, amma wlhy bance suma mahaifiyarta fyaɗe ba. Nayi tunanin kuma zasu gudu subar gidanne dan wlhy bance a saka musu wutar dan su mutu ba ne. Kuma koda sukazo suka sanar min abinda suka aikata na musu masifa har nace bazan biyasu sauran kuɗin aikin ba mukai faɗa da su, sukace zasu tona min asiri shine na haƙura na basu cikon kuɗin, ni kuma na cire kuɗin Hajiya Lailah dake account ɗinta dana Anoosh dan duk naga komai a cikin takardun gidan da alama ta rubuta ta ajiye ne saboda Anoosh ɗin. Sannan ko auren Anoosh dana yarda nayi batare da saninku ba nayi ne dan mutane karsu zargi komai a kaina, sai kuma sanadin hakan akaita kawo kuɗin gudunmawar kula da ita a asibiti daga ƴan anguwar da mutane, sai kuma Anoosh ɗin ta rasu kafin ayi aikin. Da kuɗinne na fara kasuwanci na kumayi gini na sai mota sannan na gyara gidan nan”. Salati aka sake ɗauka a ɗakin matan na sake fashewa da kuka. Mamaki da al'ajabin JJ na sake kashesu. Dan bazaka taɓa zaton zai iya aikata hakan ba. Duk cikin gidan yafi yaran shiru-shiru, idan ma ka kallesa saika ɗauka shine ustazun gidan saboda ƙarancin yawan kwaramniyarsa a zahiri. Ashe a can cikin rai sheɗanin kansa ne ƙanin iblis.... ★★★ Sun iso Kano cikin ƙanƙanin lokacin da ya bama Khadijah mamaki, duk da dai ba'a cikin hayyacinta take ba ma dan hankalinta sam baya tare da ita. Tun a airport ɗin aka sakata a wata ƙyakykyawar farar mota tare da Awwal aka wuce da ita asibiti. Ba haka taso ba, taso ace gida suka wuce da ita ko suka barta ta tafi, sai dai bata iya tayi magana ba dan tana jin jiki sosai. Ga ƙarfinta ya gama ƙarewa saboda jigatar dukan da tasha wajen ƙaton banza Dafeeq, ga yunwa ga barazanar fashewa da zuciyarya ke neman yi na damuwa da tashin hankali abinda zata iya tararwa. An kaita wani clinic mai ƙyau da bata ko san a wace anguwa ne ba. Babu ɓata lokaci aka shiga bata kulawa ta musamman mai nuni da cewar ansan Awwal a wajen, kuma yana da faɗa aji, ko kuma wanda taji yana kira da yayansan ne mai faɗa ajin tunda shine ya turosu nan ɗin shi kuma ya wuce sabgarsa... Yini guda curr Khadijah na samun kulawa a asibitin nan dan har ƙarin ruwa suka saka mata. Duk yanda take magiya da roƙon su barta ta tafi gida babu wanda ya saurareta, ga Awwal shima tunda ta farka bama ta gansa ba. Wata Nurse aka sa take kula da ita, a bakinta take jin cewar Awwal ne ya kawo abinci kuma shike tsaye akan komai yanzu babu jimawa ya tafi dan an kirasa a waya. Bata iya tace komai ba sai gyaɗama Nurse ɗin kai datai kawai. Da taimkonta ta gyara jikinta, ta bata wata doguwar riga wai ta saka inji Awwal. Batai musu ba ta amsa, ita dai fatanta su barta ta wuce kawai, dan babban burinta kawai a yanzu danganewa da iyayenta koda ace zasuyi gunduwa-gunduwa ne da ita. Da ƙyar ta ɗan tsakiri abincin tace ta ƙoshi, Nurse ɗin tayita lallaɓata amma ta dage kan ta ƙoshi, dole ta barta ta bata magunguna ta sha. Jingina tai da gadon shiru tana tunani kawai, sai dai jinta take kamar ta rumtse ido taga bata a asibitin nan. Bayan la'asar Doctor ya shigo dubata, matsawar da tai kan a sallameta yasa shi lallashinta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta zasu sallameta a yau ɗin anjima kaɗan. Taji daɗin hakan sosai duk da ranta fal fargabar yanda zata tunkari iyayenta kuma. Kusan misalin ƙarfe biyar Awwal ya shigo ɗakin bayan yay sallama Nurse ɗin dake kula da ita ta bashi izinin shigowa. Tana ƙoƙarin gaidashi kanta a ƙasa wani baƙon ƙamshin turare bayan na Awwal ɗin ya shige mata hanci. Duk yanda taso dauriyar karta ɗago hakan ya gagara. Dole ta ɗago a hankali. Wani kalar harbawa zuciyarta tayi sakamakon saukar idanunta akan kamilallen mutumin mai yanayin nutsuwa da rashin gaggawa. Ido suka haɗa ya kauda nashi a ɗan fisge. Hakan ya sakata maida nata kan ƙasa itama. Awwal ne yace mata, “Ƴar uwa kin tashi ashe? Yaya jikin naki?”. Kanta ta gyaɗa masa tare da faɗin, “Alhamdullah”. Murmushi yay ganin yanda take ta faman noƙe kai, sai kuma ya kai dubansa ga mutumin nan tare da sake juyowa gareta ya ce, “Ga Yaya zai dubaki dan doctor ya sanar mana zai sallameki yau ne”. Kanta ta jinjina a hankali, batare data ɗago ba ta samu kanta da faɗin, “Ina yini. Nagode sosai da ƙoƙarinku a kaina, ALLAH ya saka muku da alkairinsa. Kuyi haƙuri na saka ku ɓata lokaci a kaina.” Awwal ɗin ne dai ya amsa da faɗin, “Babu damuwa ai yima kai ne. ALLAH dai ya baki lafiya. Yanzu sai ki faɗa mana address ɗin gidan naku dan mu kaiki ko”. A ɗan razane ta ɗago ta kalli Awwal ɗin, sai dai karaf suka haɗa ido da mutumin nan da yake cema Yaya. Wanda tunda ya shigo waya ke a kunnensa da alama magana yake da wani, kuma wancan ne ke maganar tunda shi dai baice komai ba tunda ya shigo ɗakin. Kauda kanta tai da sauri gefe, sai kuma ta shiga kokawar haɗiye hawayen dake neman zubo mata. “Basai ma kun sake wahal da kanku ba ai, hakan ma Nagode da kulawarku. In sha ALLAHU zan iya kai kaina gida babu wata matsala”. “Mune zamu kaiki”. Dakakkiyar muryarsa ta daki kunnensu a bazata. Kusan a tare suka kallesa dan babu wanda yasan ya kammala wayar. Fuskarsa ba'a ɗaure take ba, amma kuma ba murmushi yake ba. Cikin nuna rashin damuwa da kallon da suke masan ya ƙara ɗan takowa gaban gadon sosai. Muryarsa a sauƙaƙe yanzu ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda muka ɗakkoki zamu kaiki ga iyayenki domin cika ladanmu. Ki kimtsa sai Nurse ɗin nan ta taimaka miki zuwa mota” daga haka ya juya ya dubi Awwal. “Ka tayasu kwashe kayan”. Da girmamawa Awwal ya amsa masa da “To Yaya”. Ficewa yay batare da ya sake cewa komai ba. Hakan yasa duk suka bishi da kallo ƙasa-ƙasa musamman ita da Nurse ɗin nan da tagama mutuwar zaune a kallonsa. Dan babu ƙarya guy ɗin ya haɗu kam. Gashi Suit ɗin dake sanye jikinsa sun sake haskaka shi tamkar wani baturen balarabe... Tafiya motar keyi amma tamkar tayoyinta na burgawa da bugun zuciyar Khadijah ne. Tunda take a rayuwa bata taɓa jin makamancin ruɗanin da take ciki a yanzu ba. Ji take kamar ta tsilga a motar tace ta fasa zuwa. Ko wata motar tabi takanta kawai a kai gawarta gidan nasu. To amma idan tayi haka ba lallai ta samu rahamar UBANGIJI ba, dan zata mutu iyayenta suna a masu fushi da ita. Bata taɓa tabbatar da ta cuci kanta ba sai yau. Lallai bata yiwa kanta adalci ba na barin iyayenta akan saurayi. Iyayenta jaruman nan masu jajircewa matuƙa da sadaukarwa akan farin cikinsu ita da ƴan uwanta. Duk da kasancewarsu ba masu ƙarfi ba, sun hidimta musu tamkar yanda masu arziƙi ke hidima ga ƴaƴansu. Sun basu ilimin addini dana zamani, sun suturtasu da sutura ta ƙawa koda su bazasu saka ba, sun ciyar dasu da abinci mai daɗi koda su bazasu ci ba. Sun hanasu barci a lokacin da suke buƙatar yin barcin. Amma ta rasa dame zata saka musu sai fifita saurayi a kansu. Ya ALLAH itako minene ya kaita wannan son zuciyar? (Soyayya) zuciyarta ta bata amsa. Jitai hawaye suna rige-rigen gangarowa a kumatunta. A karan kanta ta bama kanta amsa da (Ai babu soyayyar duniya sama data iyaye akan ƴaƴansu....) “Inaga nan ne ko ƴar uwa?”. Furucin Awwal ya dawo da ita hankalinta. Firgigit ta ɗago tamkar wadda ta farka a suma. Wani irin jijjiga ƙirjinta da zuciyarta da kanta sukai a lokaci guda sakamakon saukar idanunta akan ƙaninta autansu dake tsaye a ƙofar gidan sanye cikin uniform ɗin islamiyya alamar yanzu ya dawo dan abu yake amsa wajen wani yaro da zasuyi tsaho ɗaya shima dai sanye da uniform ɗin........✍️ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* AKWAI BONANZA TA MUSAMMAN TA 24HRS DAN SAMUN RANGWAMEN BIYAN 1K GA DUKA HUDUN💃💃💃💃💃💃💃 Daga yau 25 December zuwa gobe 26 December🔥🔥🔥🔥🔥 _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_KUYI MAZA KAFIN BONANZA TA ƘARE MASOYA😘😘_* *_ALLAH ya gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin_ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* AKWAI BONANZA TA MUSAMMAN TA 24HRS DAN SAMUN RANGWAMEN BIYAN 1K GA DUKA HUDUN💃💃💃💃💃💃💃 Daga yau 25 December zuwa gobe 26 December🔥🔥🔥🔥🔥 _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ _Kuyi maza kada bonanza ta ƙare babu ku_🙈 _________________ .........Cikin rawar hannu ta ɓalle murfin motar ta fita, hakan yay dai-dai da juyowar ƙanin nata da abokinsa ke nunama motar. Kallonta yake daga sama har ƙasa tamkar mai son tuna inda ya santa ko son gaskata ita ɗince ko gizo ne. Tana ɗaga ƙafa domin nufarsa kamar wanda aka zabura ya shige cikin gida da gudu yana ƙwala kiran “Mama! Mama!!.....” sai dai ya gagara cewa komai sai nuna ƙofa kawai yake yi yana hakki. Kusan a tare Mama da ƙannen Khadijah biyu Zuhrah da Jamilah suka fito a ɗaki a rikice. Jamilah ce ta daka masa tsawa da faɗin, “Kai Kamal wane iya shegene haka shigoma mutane cikin gida da gudu babu ko sallama sai ihun kira, waye ya biyoka ne?”. “Aunty Kha..di..jah a mota ƙofar gi.. gida. Wlhy da gaske nake, kuma kuzo ku gani”. Kasa cewa komai sukai su duka, sai kallan kallo kawai, kai kace suma sukai a tsayen. Sai mamace tai ƙarfin halin faɗin, “Shashancinka yayi yawa Kamal.” ta ƙare maganar muryarta na rawa da ƙoƙarin juyawa zata koma. Dai-dai nan Khadijah ta shigo gidan. Cak mama ta sake komawa ta tsaya, su duka suka zubama Khadijah idanu jikinsu na ɗan rawa kamar yanda nata keyi itama. Da ƙyar ta iya jan ƙafarta zuwa inda suke, ƙasa ta zube gaban Mama ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya tare da kama kunnuwanta duka biyu. Babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu, face zuba mata idanu da sukai kawai suna kallonta. Baka jin motsin komai a gidan face sautin kukan nata.... Tunda ta shige gidan suma suka fito a motar. Sai dai Awwal ne kawai a waje shikam yana daga cikin mota ya dai buɗe murfin ne kafafunsa duk a waje. Magana Awwal ya jiyo da nufin masa sai ga Baba an sauke a napep tare da Ni'ima, da ga asibiti suke, ta raka baba amsar magani. Ni'ima na kama da Khadijah sosai, dan haka a kallo ɗaya suka gane ƴar uwarta ce. Baba da tun fitowarsa a napep ɗin ke kallon motar ta su da Awwal ya ƙara so garesu yana mai dogara sandarsa, dan yanzu baya iya tafiya sai da ita. Sallamar Baba ta saka su juyowa su duka garesa. Bayan sun gaishesa yake tambayarsu ko suna neman wani ne?. Awwal ne ya amsa masa da faɗin “Eh Baba, muna neman mai gidan nan ne”. Murmushi Baba yay da jin jina kansa. Cike da dattako ya ce, “Ni ne mai gidan yaro. ALLAH yasa dai lafiya ba laifi nayi ba”. Murmushi shima Awwal yayi, sai dai kafin yace wani abu Yayansa da tun bayan gaisuwa bai sake magana ba ya ƙarɓama Baba da cewa, “A'a Baba bakayi laifin komai ba. Alkairi ne tafe damu.” “To masha ALLAH. Bissmilla. K Ni'ima shiga ciki ki amso tabarma ko”. Da to Ni'ima ta amsa masa bayan ta gaishesu. Sai dai tana nufar shiga gidan Yaya ya ce, “Baba bama sai ta amso tabarmar ba. Dan muna saurine”. Idanu baba ya ɗan zuba masa, dan haka kawai yaron ya birgeshi saboda nutsuwarsa da cikar kamala. Kansa ya jinjina tare da dakatar da Ni'ima, sannan ya sake juyowa garesu yana nuna musu dakalin dake ƙofar gidan. Shi da Baba ne suka nufi dakalin, Awwal na daga tsaye jikin motar. Sai da ya sake gaida baba sannan ya ɗaura da faɗin, “Baba dama muna nemanka ne adalilin wata yarinya datai mana kwatancen gidan nan muka kawota. Mun taho da itane tun daga Adamawa......” tsaff ya kwashe komai ya sanarma Baba, tare da miƙa masa takarda ya ɗora da faɗin, “Wannan a jikinta ta faɗo da alama itama bata san da ita ba”. A hankali Baba da jikinsa ke tsuma ya ɗago hannunsa ya amshi takardar. Sai kuma yay ƙoƙarin maida hawayen da suka cika masa ido da sakin murmushin ƙarfin hali ya ce, “Nagode yaro, ALLAH yay maka albarka. ALLAH ya kareka da sharrin duk wani abun ƙi. Ban san yanda zan misalta maka jin daɗina ba akan wannan taimako da kukai mata. Amma na maka alkawarin addu'a a gareku a kowace sallata. Zan so kuma ace kumu shiga ciki kusha koda ruwa ne”. “Kayi haƙuri Baba mun gode sosai. Hakan ma ALLAH ya saka da alkairi. Zamubi jirgin ƙarfe bakwai ne zuwa Abuja shiyyasa. Amma in sha ALLAH na maka alƙawarin watarana zan shigo domin gaisheka.” Godiya sosai Baba ya ƙara musu da sanya albarka. Sai da zasu shiga mota Awwal ya sauke wasu manyan ledoji yace a bama Khadijah... Bayan wucewar su Baba ya shigo gidan yara biye da shi da ledojin nan. Har yanzu Khadijah na zube a tsakar gidan tana kuka Jamilah da Kamal na taya ta. Yayinda Ni'ima da Zuhrah da suka kasance kamar sakonta suke tsaitsaye kawai ransu a ɓace. Dan sukam dai sunada wayonsu sosai a lokacin da Khadijah tabar gidan, sannan komai daya faru kafin ta gudun basu manta ba. Mama ko na zaune a yanzu kanta a ƙasa, dan tunda hajijiya ta nema zubar da ita Zuhrah ta taimaka mata ta zauna. Sallamar Baba ta saka Khadijah ɗagowa da sauri, idanu ta zuba masa. A take zuciyarta tai wata irin girgiza tamkar zata fito ta baki ganin yanda gaba ɗaya kamannin Baba suka sauya fiye da mama. Ya rame sosai yayi duhu ga shi yana jan ƙafarsa ga kuma sanda a hannu alamar itace ke taimaka masa a tafiyar. Shima dai kallon nata yake daga sama har ƙasa. Kusan mintuna biyu y kauda kansa batare da yace uffan ba ya nufi tabarmar da Ni'ima tai saurin shimfiɗa masa ya zauna. Rarrafowa Khadijah tayi har zuwa inda yake tana kuka. “Baba ku yafemin, dan ALLAH na roƙeku ku yafe min. Nasan nayi kuskure babba na bijire muku nabi wanda kansa kawai ya sani. Baba nayi nadama, nayi dana sani, wlhy bazan ƙara ba baba....” kuka mai nauyi ya sake sarƙeta. Maimakon cewa wani abu daga baba sai kawai ya dubi Ni'ima ya ce, “Kubata abinci”. Da ga haka yaja buta da Jamilah ta kawo masa ya fara alwala dan an fara kiraye-kirayen sallar magrib... __________★ METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da'ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained. METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba. Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah Yana da matakai 1....12 Level 1 anafarawa da 5$ Level 2 anadarawa da 10$ Level 3 anafarawa da 20$ Hakadai har zuwa level 12 Alkhairan metaforce Kingama register za'abaki TR coins na adadin level din da kika bude Samun reffaral bonus Ga garabasar spillover Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake Babu faduwa Babu asara aciki Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al'umma. Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah Phone number 07038708382/09069163665 ____________★ Kwana biyu cur Dafeeq na hotel abinsa hankali kwance a dalilin yarda da zuciyarsa kan Khadijah na gidan baba hakimi. Dama ya zare layinsa da yasan za'a iya samunsa da shi. Tsaf ya gama shirya yanda zai fara tafi da Kainaat tare da fara aiwatar da shirinsa kamar yanda yasan itama tana can ta gama shirya masa da batun jiran saki. Tunda ya baro hotel ɗin murmushi ya gagara barin ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Bai wuce gida kai tsaye ba, sai da ya biya wani waje ya amshi saƙo kafin yay sayayyar kayan ƙwaɗayi. Ana sallar isha'i ya shigo anguwar mara yawan hayaniya, tsayawa yay shima yayi sallar sannan ya ƙarasa gida. Ganin motocinta uku a harabar gidan ya tabbatar masa tana gida, amma duk da haka sai da ya tambayi maigadi. Maigadi ya tabbatar masa da ai tumma daya bar gidan bata fita ko ina ba tana gida, sister ɗinta dai tazo ta kwana jiya ta wuce gida. Kai tsaye ya fahimci Nadwa ce, dan ta sanar masa sister ɗinta ce batare da tasan yasan alaƙarsu ba. Cikin gidan ya nufa hannunsa ɗauke da ledojin tsarabar daya kwaso mata. Yana tura ƙofar ya shigo wani ƙamshi mai daɗi ya daki hancinsa ga sanyin ac. Shaƙa yay ya lumshe idanunsa tare da sauke ajiyar zuciya sannan yay sallama. Da sauri Kainaat da ke zaune cikin kwalliya ta ɗaukar hankali kamar tasan da dawowar tasa ta ɗago. Kallon ido cikin ido sukaima juna, a mamakinsa sai yaga ta wani sakar masa lalataccen murmushi, sai kuma ta taso a hankali cikin takun isa da yauƙi na ƴan ƙwalisar mata a bazata ta rungumesa tana kai masa kisses a kumatunsa da saman lips ɗinsa. Sosai Dafeeq ya shiga ruɗani a wannan gaɓar, amma da yake shima shegen kansa ne sai ya dake abinsa domin ganin iyakar gudun ruwanta da son gane manufarta. Hannu biyu yakai bayanta shima ya rungumeta da ƙyau. A cikin kunnenta ya raɗa mata, “Ki yafe min amaryata. Gwuyawuna bisa ƙasa Hajjaju na”. Makirin murmushi ta saki tana mai ɗagowa ta kashe masa ido ɗaya. Cike da kissa ta ce, “Ni ya kamata na baka haƙuri ai mijina, domin na fusataka da yawa har ka kai gamin yaji na kwanaki biyun amarcina. Dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake ba Baby”. “Ai ke baƙya laifi Gimbiya. Ni ne mai laifi dana tafi na barki, nayi hakanne kuma domin nesanta kaina da ke har sai kin huce. Ki yafe min abinda na aikata sharrin shaiɗanne, amma in sha ALLAH bazai sake faruwa ba, dan yanzu ke kaɗai ce mai Dafeeq babu wani shamaki a tsakaninmu na har abada” (Zakaci ubanka ne) ta faɗa a zuciyarta. A zahiri kam saita sakar masa murmushi da kai yatsarta saman lips dinsa ta ce, “Shiiii!!! Karka sake cewa komai. Abinda ya faru ya riga ya wuce har abada, na kuma yafe maka mijina muje kai wanka kazo ga abinci na shirya maka...” “Abinci fa? Sai kace wadda tasan da dawowa ta?” ya faɗa cikin tarar numfashinta. Sai da gabanta ya faɗi, amma sai tai azamar gyara yanayinta da faɗin, “Akoda yaushe cikin tsammanin dawowarka nake gareni ai, shiyyasa nake shirya abinci safe, rana, dare batare da jin gajiyawa ba Baby. Ba gashi an dace ba yau kuma ka dawo ka sameni a yanda nake fata”. “Hakane! Ina godiya Gimbiyar mata”. Ya faɗa yana shafa fuskarta da sakin murmushi. Sai dai a zuciyarsa yana jin lallai akwai wata a ƙasa. Fakar idonta yay ya watsa mata harara, a ransa ya ce, (Tsuntsu mai wayo, ta baki ake kamashi hajjaju). Shima kuma yana juya baya ta zabga masa hararar a zuciyarta tace, (Yaro yaro ne, yaro bai san wuta ba sai ya taka. Ƙiris ya rage na shafe tarihinka a nawa) 😂😂Cuta ta ɗau cuta kenan🚴🚴🚴🚴🚴. _________★ Kwanaki biyu kenan da dawowar Khadijah gida. Har yanzu daga Baba har mama babu wanda yace da ita komai. Hakama ƙannenta idan ka cire Kamal dake ƙarami babu mai shiga sabgarta. Garama Jamilah takan ɗan mata magana. Amma Ni'ima da Zuhrah ko kallo bata ishesu ba. Akan bata abinci wadatacce da zataci ta ƙoshi, idan ta gaida Baba kuma yakan amsa sau ɗaya ya tsuke bakinsa. Hakama Mama idan ta amsa sau ɗayan nan bata sake kulata. Idan su Zuhrah na aiki kuma ta taso ta ce zata tayasu suce ta barshi. Tayi kuka tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Dan da wannan shirun da suke mata gara ace dukan da yafi wanda Dafeeq ya mata Baba ya kamata yay mata zaifi mata sauƙi. Kuma data fara magiyar roƙonsu su yafe mata sai baba ya ɗaga mata hannu kawai alamar baya son ji. Mama kam ma tashi take tabar wajen batare data tanka mata ba. Gaba ɗaya duniyar ta mata zafi, ta rasa ina zata kama taji daɗi. A wajen Kamal take ji Baba baida lafiya yana fama da paralysis ne. Amma yanzu yaji sauƙi tunda har yana iya ɗan fita ƙofar gida. A wajensa taji an sakama Ni'ima da Zuhrah biki nanda wata bakwai ma za'ayi, sannan a gabanta suke fita makaranta tsaff da su. Tasan ta cuci kanta bana wasa ba, dan duk wanda ya kalla ƙannen nata a yanzu yasan ilimi ya ratsasu addini da boko. Shigowar wata makwafciyarsu a randa take cika kwanaki biyu yasa aka san da dawowarta. Tana fita kuwa ta fara bazama ƴan anguwa cewar ai Khadijah na nan ta dawo a mawuyacin hali. Da alama ma cikin farkunan nata na bariki wani yay mata duka dan jikinta duk bandage ne. Abu kamar wasa sai ga zance ya cigaba da zagayawa, har takai wasu sun kasa danne gulmarsu suna shigowa ganin Khadijah afakaice. Bata fahimci zaryar da mutane keyi gidan dominta bane sai da Kamal yazo yana bada labari wai yaji a majalissar ƙofar shagon Kalu Nigge ana gulmar Khadijahn. Ranar taci kuka sosai, sai dai abinda bata sani ba har su Ni'ima ma sunsha kuka a ɓoye. Dan duk da ta kasance mai laifi a garesu basa jin daɗin yanda ake aibantata a anguwa tunda suma komai na dawo musu a cikin kunne. Kawai dai maganarce basayi su. A randa take cika sati guda a gida sai ga mahaifiyar Dafeeq tamkar an jehota......✍️ METAFORCE online business ne Wanda malamai suntabbatar da halascinta masana suntabbatar da ingancinsa ba iri kasuwancin da'ake gudunmma mutane da kudin subane shi wannan an centralized ne ko Wanda ya kirkira bazai iya kulleshiba saboda Yana kan block chained. METAFORCE zakashiga da kudi kadan ka dauki da yawa ummu khalilwacce take zaune akasar Nigeria sananniyace akan harkar METAFORCE ta kawomana hanyar sauki dansamun cigaba. Zakasamu kudi Mai tarinyawa dawayar hannunka insha Allah Yana da matakai 1....12 Level 1 anafarawa da 5$ Level 2 anadarawa da 10$ Level 3 anafarawa da 20$ Hakadai har zuwa level 12 Alkhairan metaforce Kingama register za'abaki TR coins na adadin level din da kika bude Samun reffaral bonus Ga garabasar spillover Da dollars suke biya zaka iya cirewa kamaida kudinka account nantake Babu faduwa Babu asara aciki Kishiga kasuwanci Mai tarin alkhairi zaka kwashi kudaden musamman kana gayyato al'umma. Metaforce alkhairine ga duniya insha Allah Phone number 07038708382/09069163665 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da ɗaya_ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ .......A yanda Maman Dafeeq ta shigo gidan babu ko sallama ya saka kowa zuba mata ido batare da sun tanka ba har yaran. Dan kowa ya santa tunda ba wannan bane zuwanta na farko tai tujara a gidan. Hasalima zuwan da tai a baya rashin mutunci ne ya zama sanadin da Baba ya samu kansa a hanlin da yake ciki yanzu. Khadijah da ke zaune a ƙofar ɗaki cikin tagumi da damuwa taima kallon sama da ƙasa, sai kuma ta kwashe da dariya tana tafa hannaye da riƙe haɓa. “Oh ni jikar ta-rasulu kece ɗin dai ashe ba jita-jita ba. Barikin harta ƙwaɓe miki ne zuwa ajin ƙarshe na karatun natane ki ka dawo gida ko kuwa dai kinzo kawo musu abinda kika roro ne ki koma?”. Ba Khadijah ba, hatta ƴan uwanta a kiɗime suke kallon Maman Dafeeq ɗin, har Ni'ima ta buɗe baki da niyyar magana Khadijah ta rigata da faɗin, “Ban gane ba, ni Khadijah ce kuma a bariki? Na sojoji kona ƴan sanda?”. Wata dariyar rainin hankali Maman Dafeeq ta saki tamkar Khadijahn sa'arta ce tare da faɗin, “Oh halin naku zaki nuna kenan na matasan karuwai. Ai kin san wane bariki nake nufi. K yanzu bakiji kunyar kanki ba ƴar nan? Koda yake ma miye nawa, tunda ALLAH ya ƙwacemin ɗana da ga hannunki tun baku cika wata biyu ba. Da yanzu an kwaso ɗan dakan kuka an nana mana, dan da alama dama tun ana gida dai ake ƴan leƙe-leƙe ɗakunan samarin anguwa!”. Tunda Khadijah take a rayuwa ba'a taɓa faɗa mata kalmar data gigita rayuwarta ba kamar wannan. Zaram ta miƙe jikinta na ƙyarma. Ta bi mahaifiyarta da ƴan uwanta dake tsaye ƙiƙam babu mai alamar cewa komai sai ma zuba mata ido da sukai da kallo. Atake ta sake jin zuciyarta ta girgiza. Kenan kallon da suke mata ashe na wadda ta fito a yawan bariki suma kamar yanda mutane ke faɗa. (Ya arrahaman) ta faɗa tana mai girgiza kanta hawaye masu zafi na rige-rigen sakkowa saman kumatunta. Cikin sassarfa ta ƙarasa gaban maman Dafeeq da ke wani male baki da shan ƙamshi ita adole tayi tonon silili. Tsakkiyar idonta Khadijah ta kalla tare da nuna kanta. “Ni Khadijah ki ke ambata da sunan wadda ta fito a karuwanci? Ashe haka shi ɗan naki da yay sanadin komai yazo ya sanar muku? Naji zan ɗauka idan kince ni na jayeshi gareku kamar yanda kuke kallo bisa son zuciya, saboda ya zama hukunci a gareni nayin kuskuren bijirema iyayena nabi ɗan hau irin ɗanku saboda yaudararrun kalamansa gareni da ruɗanin wata abar banza wai ita soyayya. Sai dai ki sani idan ma ya ɓoye muku ne. Dafeeq ƙarya yake yi ni Khadijah shekararmu uku kenan tare da wasu watanni ba wata biyu daya sanar muku ba. Tun a satin da muka bar gida tare aka ɗaura mana aure a Adamawa. Bamu kuma taɓa rabuwa ba sai a satin daya shuɗe sakamakon jin da fahimtar shi ɗin wanene. To ashe ma halin nasa yasha ne gareki ban sani ba, a yanzu kam na daina mamakin halayensa dan madubinki ya sake haskamin ɗanki Dafeeq mayaudari daya zama sanadin rabuwa da iyayena ya dawo yana zuwa ku gareku, Dafeeq ɗin daya dinga zubamin ƙwaya batare da sani na ba ina ɓarin ciki, Dafeeq ɗin daya saka a asibiti aka sakamin abinda zai hanani sake ɗaukar ciki, Dafeeq ɗin daya auri sa'arki a yanzu saboda kuɗi. To idan kina tunanin daga karuwancin na fito tare da ɗanki mukeyi a ƙarƙashin igiyar aure. ALLAH shine shaidata, wanda suka ɗaura mana auren suna nan a raye suma shaidane, gidan da muka rayu da maƙwafta da yan anguwar duk shaida ne. Wannan tabbunan dukan da kike gani a jikina naɗe da bandage badaga kowane lalataccen ɗan barikin da kike tunani bane face lalataccen tataccen ɗanki a dalilin jin gaskiyar shiɗin makiri ne azzalumine mayaudari, dan har a yanzu kuma akwai igiyar aurensa a kaina.....” “Har abada kin masa nisa. Ɗaya daya rage ma bai ƙarasaba ni da kaina zan kaisa inda zai tsinketa!!”. Muryar Baba ta daki kunnuwansu a bazata batare da sun san da shigowarsa gidan ba. Batare da ya jira cewar waninsu ko damuwa da kallon da Khadijah ke masa ba ya nuna Maman Dafeeq cikin tsantsar ɓacin rai. “A baya kin shigo wannan gidan kinci mutuncin mu son ranki, kin kuma dawowa a karo na biyu kika ƙara dai. Kin san miyasa a wancan lokutan bance da ke komai ba?” ya saki murmushin takaici, batare da ya jira ta sake cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Saboda darajar igiyar auren da ke tsakanin ɗanku da Khadijah. Saboda bana son nai shishshigi akan al'amarin UBANGIJI. Saboda bana son na sake maimaita kuskuren farko. Saboda ni ɗin UBA ne. Shi kumai UBA a duk inda yake mai haɗiyewa ne, domin ɗan kuka shike jama uwarsa jifa. Da'ace Khadijah ta kasance mai jin magana da tausayinmu matsayin iyayenta da tabi nasiha da shawarwari da faɗan da mukai mata akan ɗanku da k baki isa ko kallon Kamalu dake ɗa na ƙarshe gareni ki ci masa mutunci ba balle mu. Da ace sanda ɗanku ya fara zuwa nan ƙofar gidan na taka masa birki akan ahalina, da ke baki isa ko kallon bangon gidana ba balle dafawa da sunan shiga ciki. Amma duk na amshi ƙaddarar data zama jarabawar da bazan taɓa iya gogeta a cikin zuri'ata ba da hannu biyu, Alhamdullah kuma ina ji a jikina mun cinyeta, tunda gashi ta tafi da ƙafarta taje tai rayuwa a ƙarƙashin igiyar aure, da kuma dawo da ƙafarta batare da aikata abinda kuka jima kuna jifanta da shi ba. Dan haka kije ki sanarma shi ɗan naki da yazo ya ɓata sunanta bayan tana acan matsayin matarsa cewar ku shirya, ku shirya sammaci dan zamuje gaban alƙali ya ƙarasa cikasa saki ɗayan daya rage bai rubutaba akan wannan biyun daya rubuta anan”. Ya nuna mata takarda daya warware. Cikin ɓacin rai da rawar jiki Maman Dafeeq ta ce, “Wlhy ƙarya ne, ku kun isa kuma yarona sharri, dan kuna son wanke ƴarku a wajen al'umma dan kar ace ta dawo daga yawan tazubar shine kuka kirƙiri takardar ƙaryarnan....” “Mu nan da kike gani munfi ƙarfin ma wani sharri balle ɗanki. Amma kije idan ma sharrin muke masa zai amsa a kotu. Na baki kuma minti biyu kibar min gida, in ba hakaba Ni'ima! Jamilah! Zuhrah! Kamal! Ku raka min ita da itace”. Ai tamkar dama wannan umarnin su Zuhrah dake faman cika da batsewa ke yi a cikin abinda bai gaza sakan uku ba kowa ya rarumi maɗaɗɗare dama duk abinda hannunsu ya kai sun raraki Maman Dafeeq da ta ɗauki abin wasa, dan harta buɗe baki zata fara zubama Baba tujara taga yaran sunyo kanta kamar an kama mayya a gidan yawa. Zo kuga gudu fiyyyy!! Fiyyyy!! Kamar kazar mayu dan dama haka take fingau-fingau babu wani ƙiba a jikin nata ko kaɗan. Har cikin anguwa suka bita atake aka ruɗe da ihu-ihu ana son hanasu amma ko'a jikinsu. Sai da ta faɗa wani gida ta banko murfin soron sannan mutane suka zagayesu ana basu haƙuri. Dan gaskiya abune da ba'a taɓa gani ba. Kowa a anguwar yasan su Ni'ima yarane kamilallu masu hankali da nutsuwa ga girmama mutane. Hatta ita kanta Khadijahn da ake kace nace a kanta yanzu kowa yasha mamaki lokacin da akace tabi Dafeeq sun gudu. Sai dai akoda yaushe mutum mai iya canjawa ne daga yanda aka sanshi, shiyyasa sanda yazo da batun sun rabu ta shiga duniya kuma mutane da yawa suka yarda, dawowarta a wani hali kuma ya sake saka zukatan mutane waswasi. Sai kuma a yau ga wani sabon zance ya fito dan tuni abinda ya faru a gidan Baban da kalaman Khadijah ga mahaifiyar Dafeeq dana baba har sun fara zagaye anguwar. Wasu ko dama akan kunnensu akai musamman ma maƙota. An lallaɓa su Ni'ima sun koma gida da ƙyar. In da suka tadda wasu a cikin dattawan anguwa zagaye da Baba a soro. A cikin gida Khadijah na durƙushe inda suka barta tana faman kuka. Ga Mamansu a gefe zaune itama tana nata hawayen ta juyama Khadijah dake magiyar su yafe mata baya.. Sun kai mintuna goma da shigowa gidan Baba ma ya shigo, kamar jira yana shigowa aka sake kwaɗa sallama. Komawa yay da baya ya sake fita, sai dai me yana fitowa yaci karo da ƴan sanda. Sun sanar masa cewar sunzo tafiya da shi ofishin su sakamakon ƙararsa da Maman Dafeeq takai wai ya saka yaransa su kasheta, sun kuma biyota da wuƙaƙe da iccina har cikin anguwa, da ƙyar mutane suka taimaketa. Murmushi kawai Baba yayi yace suje amma bari ya sanarma iyalinsa. Sun nuna basu amince ba, kawai ya bisu. Bai sake cewa komai ba ya bisun sai shigowa akai aka sanar dasu ai ƴan sanda sun wuce da Baba. A take hankalin kowa ya sake tashi a gidan, musamman Khadijah dake jin zuciyarta na barazanar bugawa ma...... ____________★ Tunda ya shiga bayin domin yin wanka da ruwan data haɗa masa zuciyarsa keta kai-kawo. Ya jima yana kallon ruwan da yay butsa da alamar akwai abinda aka saka a ciki, sai dai ƙamshin turaren dake tashi cikinsa zai saka kai tunanin turaren ne kawai. Lips ɗinsa ya ciza da ɗan ƙarfi, sai kuma yay murmushi da jan towel ya ɗaura ya fito a bayin. Dama a ɗakinta ta haɗa masa ruwan. Dan haka ya je ya sakama ƙofar key. Bincike ya shigayi a ɗakin tun daga cikin wadrobe ɗinta data cinye bango guda har zuwa ƙasan katifar gadon. Bai yarda yay wani motsin da zai iya jawo hankalinta ba, haka ma bai canja duk abinda ya ɗaga ba daga yanda yake. Itako tana can da tunanin ya gama wanka barci ya kwashesa kamar yanda malam ya faɗa zaiyi barcin kusan 1h kafin ya tashi, da ya tashi kuma komai zai iya faruwa. Idan a wannan step ɗin kuma ya tsallake da zaran yaci abinci yasha lemon data haɗa da magani shima shike nan rikici zai ɓalle tsakaninsu har takai su ga zuwa matsayin da take so. Abinda bai sani ba tun sanda yabar gida mai ɗaukar mata rahoto na biye da shi. Hakan yasa tasan duk motsinsa a kwanaki biyun nan da baya nan har zuwa kan tahowarsa gida. Ko abincin data shirya masa a table ba itace ta girka ba, sayowa akai da sauri, driks kam dama ta tanada a freight tun jiya, tana jin zai taho ta fiddoshi ta sake masa kwaskwarima, sannan itama ta gyara jikinta da turare da faudan malam da kwalli. Yanda taga kuma ya saukar da kansa sai take jin tarkonta na farko ya kamashi yanzu kuma ana kan na biyu tunda dai baya jimawa a wanka. Bazataje ɗakin ba saboda malam yace kar taje har sai shi da kansa yayi barcin ya tashi yazo inda take. Cike da nishaɗi ta buɗe ledar tsarabar daya shigo mata da shi batare da tunanin komai ba ta ciri shawarma ɗaya ta fara ci tare da buɗe kwalin yogout ta hau sha tana faman lumshe idanu da sakin murmushi. A ranta kam cewa take celebration ne take na cikar burinta. Tana kammalawa wani shegen barci ya fara rinjayar idanunta. Duk yanda taso hana kanta ta kasa saita ɗan kai kwance tana jan ƙaramin tsaki dan tasan barcin da bata sami tayi bane a kwanaki biyun nan saboda ƙulle-ƙullen da take akan Dafeeq ɗin, dama daurewa kawai take tun ɗazun, amma tunda yanzu ya riga yazo hannunta bari ta ɗan kwanta itama kafin ya kammala nasa barcin awa ɗayan. Wannan shine ya bama Dafeeq damar cin karensa babu babbaka batare da ita ya kawo komai a ranta ba game da dukiyarta yake hari. Tsaf ya tattara duka takardun daya tabbatar masu amfani ne, tare da golds ɗinta tun daga kan sarƙa, yan kunne, warwaraye zuwa zobuna. Bayan ya kammala tsaff bayi ya koma, ya zubda ruwan data haɗa masa ya zuba wani yay wankan sannan ya fito a ɗakin, a hankali ya fara leƙa ƙasan benan, cikin mamaki ya hangota kwance a kujera kwalin yogurt da takardar shawarma yashe a ƙasa. “Ƙuda wajen ƙwaɗayi....” Ya faɗa yana ƙyalƙyalewa da dariya. Ƙasan ya sakko a cikin sanɗa, wayarta ya ɗauka ya koma saman dan ya riga da ya gama gane password ɗinta cikin hikima tun kan aurensu.........✍️ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da ɗaya_ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ____________ ........Tsaf ya gama bincike wayar, cikin Sa'a kuwa ya samu abubuwa da yawa fiye ma da waɗanda yake neman. Hakan bai ishesa ba sai da ya saita wayar tata da tashi ta yanda duk sanda aka kirata ko ita ta kira shima kiran zai shiga wayarsa. Kuɗaɗen bankinta biyu dake kan wayar suma ya gama haddace pin nata batare data sani ba, a yanzu ya zauna ya kwashesu tsaf ya maida a nasa account ɗin ya bar mata kaso ɗaya bisa huɗu. Bai tsaya anan ba, ya kwashi wani numbers na abokan huɗɗarta masu muhimmanci harda na Abaan. Ya kammala yana ƙoƙarin miƙewa ya maida mata wayar duk da yasan yanada sauran lokaci saboda maganin daya zuba mata a yogout kira ya shigo. Nadwa ce, dan haka ya ɗaga ya kai kunne batare da yace komai ba. Cike da zumuɗi Nadwa dake tunanin Kainaat ce ta ɗaga ta fara magana kai tsaye, “Matar nan tun ɗazun nake tsumayen kiranki amma shiru kake ji. Ai ɗan Alhaji ya sanar min mutuminki ya dawo gida. ALLAH dai yasa kin aiwatar da duk abinda malam ya baki dai-dai dan mu samu a wuce wajen zuwa gobe. Yanzu ma inada albishir amma sai gobe zan baki idan komai ya kammala” sai kuma tai shiru jin ita kaɗai ke tsiyaya surutunta. Wayar ta cire a kunne cikin mamaki, sai kuma tai tunanin ko Kainaat ɗin na tare da Dafeeq ne shiyyasa taƙi magana. Da sauri ta yanke kiran tana dariya da faɗin, “Haka kawai kin ɗaukama kanki alaƙaƙai”. Ya jima tsaye yana cuɗawa da cakuɗa zantukan Nadwa a ransa. Kafin ya ce, “Hummm” kawai ya fita ya maida mata wayar dan ya fahimci komai. Wato gidan malam aka kai sunansa, wannan shine dalilin da yasa yaga magani a ruwan wankansa. Ya saki murmushi mai faɗi yana wani cije lips. Da ace ya samu dukan takardu da abubuwan da yake buƙata na Company babu shakka zai iya sakinta yau ma sai dai ta tashi taga doguwar wasiƙa da rubutu. Sai dai an samu akasi. Ba duka takardun Companyn ya samu ba akwai wasu masu muhimmanci da bai gani ba, dan haka sai ya amshesu sannan. Asiri kuma ta cigaba da nema itace a wahale. Matuƙar mamaki da ruɗani Kainaat ta shiga a washe gari, dan bata farka ba sai washe gari. Ta dinga kallon Dafeeq da yay fuska abinsa, sai dai ta gagara cewa komai. Ko salla batayi ba sai da tai kiran Nadwa. Sai dai ta yi shuka a idon makwarwa batare da ta sani ba. Dan duk abinda ta tattauna da Nadwa shima ya jisa. Dan haka tana gama wayar ya fara borin kumya sakamakon yin wani tunani. Exactly yanda yaji sun tattauna akan halin da malamin yace zai tsinta kansa a ciki ya fara gwadawa. Kafin wani dogon lokaci faɗa ya harƙe tsakaninsu. Ranta fes da farin cikin tunanin aiki yaci. Dan haka itama ta fuske ta biye masa kamar yanda malam ya bata shawarar kunnashi. Al'amarin kamar wasa sai ya zama gaske sakamakon fahimtar da tai babu wasu muhimman abubuwanta data adana a ɗakin a washe garin cikarsa kwana biyu da dawowa gidan. Dan faɗa sosai sukeyi ta buƙaci ya bata abubuwanta. Shi ko bai musa shine ya ɗauka ba dan kai tsaye ma har takai shi da tabbatar mata idan tana son saki sai ta bashi sauran takardun Companyn ta. Idan kuma tai tunanin sanarma wani shima zai sanarma Abaan ɗin da take harin komawa komai, ya ɗan balgata mata wani sirrinta daya ɗauka a cikin waya daya shafi Abaan ɗin. Matuƙar tashin hankali Kainaat ta shiga. Gaba ɗaya ma ta rikice. A take ta shiga bincike sosai a ɗakinta. Tako samu ya yashe komai harda kuɗin dake a cikin bank nata duka biyu. A takaice dai bata da wani ƙarfi ma da take tunani na dukiya da zaisa ta iya masa rashin mutunci ko gayyato hukuma cikin al'amarin nasu. Sannan maganar zai kaima Abaan wani yankin sirrinta ma wani tashin hankali ne gareta da bazata taɓa fatan ya kasance ba. A cikin ƙanƙanin lokaci komai ya canja a gidan. Ta fahimci hatta wayarta idan tai kira ko aka kirata shima tana zuwa cikin tashi wayar. Sai ma tarasa ina zata kama taji daɗi. Gashi ƙiri-ƙiri ya kulle ƙofar gate yama sallami Dauri maigadi da kuɗi masu yawa wai yaje ya huta zai nemesa. Yayi magana da Manager na Companynta da wayarta cewar a cigaba da al'amura shi da Madam sunyi tafiya zuwa Lagos honeymoon. A haka suka kwashe sati ɗaya a gida babu wani cigaba sai na tafka rikici da masifa. Kowa kuma yaƙi zuwa gidan sakamakon bin duk wanda yasan zai iya nemanta a waya ya tura masa text message cewar sun tafi honeymoon sannan ya kashe wayar ma gaba ɗaya. Tayi masifar tayi zagin tayi kurarin amma yaƙi bata wayar. Ta nema iya nema amma ta kasa gano a inda ya ɓoye. Shi kuma wayar hannunsa babu ma wanda yasan layin sai iyayensa kawai balle wani ya kirashi yasan suna gari. Tun Kainaat na ɗaukar al'amarin wasa harta fahimci yafi ƙarfin wasan fa yaron nan da gaske yake shirin mata ɗibar albarka yake da gaske. A yau suna cikin rikici ta maresa ya rama. A take dambe ya nema harƙumewa a tsakaninsu. Sai dai ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba, ya bubbugeta dan Dafeeq dai akwai zuciyar banza. Sannan duk da ƙananun shekarun nan nashi baya ƙaunar raini kowa ya sani tunma bai kai haka ba. Itama dai ta samu nasarar ƙwala masa plate a goshi harta jimasa ciwo. Hakan yasa shi nufar bayi domin wanke jini batare da ya lura da wayarsa data faɗi ƙasa ba. Yana shiga kira na shigowa, dan haka Kainaat ta ɗauki wayar da sauri, a mamakinta sai taga mamansa ce. A take zuciyarta ta bata shawarar ɗagawa, dan ta fara zargin lallai uwar tasa tasan komai dake faruwa tunda ita kaɗai ke kiransa a layin nan sai babansa. Ɗakin da Khadijah ta zauna ta shiga, ta maida ta kulle ƙofar sannan ta ɗaga wayar tana gab da tsinkewa. Tana kaita kunne Maman Dafeeq na kwaɗa sallama....... ____________★ Abubuwa sun rincaɓe sosai a gidan su Khadijah yau ɗin nan. Dan har dare an hanasu ko ganin Baba. Sai da Zuhrah da taga basu da wata mafita tai kiran saurayinta da zata aura. Hankali tashe ya zo station ɗin. Abinka da mai kuɗi a hannu, cikin ƙanƙanin lokaci da ya ga d.p.o aka basu Baba. Sai dai zuwa safe zasu koma da shi wai za'a turasu kotu dan laifin bin mutum da makami ba abune na wasa ba tunda mutane da yawa sun shaida hakan a cikin anguwa shima kuma baba bai musa ba. Kusan ƙarfe sha biyu da rabi na dare suka dawo gidan. Idan kaga Khadijah a wannan lokacin dolene ka tausaya mata. Idanunta sunyi masifar kumbura saboda kuka. Gaba ɗaya ta gama fita a hayyacinta fiye da kowa na gidan. Tunda suka shigo ta zube a gaban Baba kawai tana kuka da roƙon dan ALLAH su yafe mata. Ba su Baban kaɗai ba, hatta da ƴan uwanta roƙonsu ta dingayi akan su yafe mata duk laifinta ne, duk a dalilinta ne komai ke faruwa. Babu wanda dai ya iya cemata komai, sai maƙwafcinsu da aketa kai kawo da shi ya ce, “Suje su kwanta da safe koma minene ayi yanzu dare yayi Baba na buƙatar hutu. Dole duk suka shige ɗaki, sai dai sam Khadijah ta kasa barci, daga ƙarshe ta fito ta ɗaura alwala ta shimfiɗa ɗan kwalinta anan baranda ita kaɗai a tsakar gida ta fuskanci UBANGIJI mai share kukan masu kuka. Mai jin roƙon bayi da rahamarsa da jin ƙansa. Yanda take jero addu'oi da magiyar nan gafara a gun UBANGIJI cikin harshen larabci a cikin sujuda ɗinta ya jawo hankalin Baba da ya kasa barcin shima. Tsaye yay a jikin ƙofa kawai yana kallonta. Shi shaida ne duk cikin yaransa Khadijah dabance a fagen ilimi da ƙarancin kwaramniyar, tanada kaifin basira matuƙa, duk da suma sauran nada ƙoƙari amma tata basirar daban ce. Sai gashi ƙaddara da son zuciya ya ɗebeta aikata abinda ta aikata. Dan ALLAH shine shaidarsa yayi iya ƙoƙarinsa akan Khadijah hakama mahaifiyarsu. Sunbi duk hanyar data dace matsayinsu na iyaye domin dawo da ita hankalinta, nasiha, lallashi, kurari matsayinsu na iyaye duk sunyi amma duk da haka basuci nasara ba, ba kuma kowa zai fahimci ƙoƙarin su ba, wasu ma kallon sune masu kuskure sukeyi.... Khadijah da bata san da ana kallonta ba kuka take sosai bayan idar da sallar tana addu'a da roƙon ALLAH gafara da fatan ya ɗauki ranta a tsakanin nan, ya kuma saka iyayenta su yafe mata koda bayan ranta ne, ya wanketa da ga aibatantata da Dafeeq yayi a idon al'umma. Ta jima tana addu'ar anan ma kafin tai yunƙurin miƙewa tana layi dan ta gama yanke shawarar abinda zuciyarta ke ayyana mata. Daga baba har Mama dake bayansa tana hawayen tausayin ƴar tata binta da kallo sukai. Ganin ta nufi rijiyarsu gadan-gadan yasa Baba zabura cikin jan ƙafarsa da bai iya takawa. Tuni Mama ma ta rufa masa baya. Da ƙyar ya iya kaiwa dai-dai Khadijah ta tafi gaba ɗayanta zata afka kanta a rijiyar. Wani irin fisgota Baba yayi ya rungume a jikinsa dake rawa hawaye masu zafi na kufce masa. Mama ma ta haɗasu su duka biyun ta rungume itama tana mai fashewa da kuka. Sai ga Ni'ima da Zuhrah da ashe suma dai ba barcin suke ba a guje suma suka rungume iyayen nasu. “Baba dan ALLAH ku barni na faɗa, ku yafe min kuma dan girman ALLAH. Nasan na cutar da ku, kuma bazan iya yafema kaina ba. Kun haifeni, kun raineni cikin ƙyaƙyƙyawar kulawa da nagarta da bajinta irin ta jaruman iyaye da duk ɗa na gari zai so samu a duniya. Amma son zuciya da wata baƙar soyayya mara amfani da amfanarwa ta ruɗeni na bijire muku. Kaicona ni Khadijah, kaico da haihuwar ɗiya irina. Wlhy Mama naga illar saɓama iyaye, naga illar ƙuntata zuciyar Iyaye. Inama ace jiya zata iya dawowa a duniyata na goge da shafe abubuwan dana aikata a gareku. Sai dai kaicona, hakan bazai taɓa kasancewa ba. Na riga na ɓata sunana, na goga muku baƙin fentin da bazai taɓa gogewa a tarihin wannan gida ba. Dan ALLAH Baba, Mama, ƴan uwana ku yafe min ku barni na faɗa cikin rijiyarnan. Maybe idan na mutu ba'a gani na baza'a sake tuna muku da abinda na aikata ba balle a aibantaku da wanda ban aikata ba. Wlhy gara na mutu, gara ace mutuwarma nayi ko Baba?...” “Muna son ganinki a raye Aunty Khadijah. Dan ALLAH ki daina faɗar zaki kashe kanki. Muna sonki muna sonki sosai”. Zuhrah ce ta faɗa cikin kuka da sake ƙanƙame hannun Khadijah data kamo. Ɗagowa tai da sauri tana girgiza ma Zuhrah kai, sai dai kafin tace wani abu baba ya dakatar da ita ta hanyar ɗaura yatsarsa akan lips dinta ya ce, “Shiii!! Ya isa haka. Ku zaunar dani kun san yanzu babanku babu ƙafa.” Da sauri suka kakkamashi zuwa baranda, Ni'ima ta kawo tabarma da sauri ta shimfiɗa masa. Duk zama sukai shiru sai Khadijah dake durƙushe gabansu ta kama kunnuwanta har yanzu tana hawaye. Kusan kallon mintina uku Baba ya mata kafin ya ce, “Bamu labarin miya faru kika iya barinmu Khadijah? Miya faru a inda kuka je? Ya akai Dafeeq ya dawo ga iyayensa bayan watanni da barinku gida amma ke mace kima kasa hakan? Da gaske ne Dafeeq ya jima da sakin ki kika tafi wani waje daban saboda tsoron kar ki dawo garemu ai miki dariya?”. “Sam ba haka bane Baba. Wlhy ba haka bane ba. ALLAH kuma shine shaidata duk abinda zan faɗa muku shine gaskiya. Sannan inada shaidu akan abinda zan faɗa mukun tun daga wanda ya ɗaura auren mu har zuwa inda muka zauna da dalilin farkawata a barcin kuskuren bijire muku na dawo gida. Duk da wlhy tunda na barku ban taɓa jin salamar haka ba a raina. Kawai ina dannewa ne dan kar naima Dafeeq laifi a wautata da son zuciya. Amma kullum a cikin mafarkinku nake, nakanyi kuka a ɓoye da jin kamar na dawo na baku haƙuri, sai dai ina jin tsoro, ni burina da nawa hangen shine idan na haihu zan zo muku da yaƴan maybe kufi yafe min kuskurena. Sai kuma aka samu akasin hakan abinda nake burin ya zamar min jagoran zuwa gareku ya gagara samuwar.......”✍️ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da uku_ ___________ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ___________ .......Tsaff ta basu labarin komai da ya faru tun daga randa suka bar gida har ɗaura aurensu zuwa samuwar cikinta da yayta zubewa dama daina samuwarsa duka. Shigowar al'amarin Kainaat da ya zame mata wata fitila data haska mata hanya a yanzu. Turke Dafeeq da tai da dukan da yay mata zuwa tsintar kanta da tai a titi bayin ALLAHn da suka kawota gida suka taimaketa. Komai bata ɓoye musu ba. Duk dauriyar Baba sai da yaji hawaye sun cika masa ido. Sai dai kiran sallar asubahi da aka fara ya sakasu kasa cewa komai dole duk suka miƙe domin ɗaura alwala kamar yanda Baban ya basu umarni. Kasa haƙuri Mama tai dan tana tsoron shiga ɗaki Khadijah ta sake tunanin jefa kanta a rijiya. Anan baranda ta shimfiɗa sallaya domin yin tata sallar yayinda su kuma suke cikin ɗakinsu. Baba da Kamal kuma sun fice massalaci...... __________★ Maman Dafeeq data rangaɗa sallama a waya batare da jiran Dafeeq ya amsa ba ta cigaba da maganarta a ƙugule Kainaat na saurarenta. “Duk inda kake kazo gida a gobe, dan wannan shegiyar yarinyar daka jajibar mana a cikin zuri'armu ta dawo gida tace ƙarya kake baku rabu da juna ba. Hasalima raunikan data dawo dasu a jikinta na duka kaine kamata su ka kuma zubar mata da ciki. To nadai taƙaice maka zance yanzu haka nasa an kulle ubanta saboda yasa yan uwanta biyoni da makamai wai su kashe ni. Dan haka kazo maza muna nemanka ni da Babanka dan wannan sharrin datai maka sai an zauna kotu. Wlhy bazamu yarda ba. Kama taho da matarka ƴar arziƙi irin albarka dan tai maka shedar itace matarka a yanzu ba shegiyar ba. Ato kaji sai kai azamar tahowa”. Ɗiff ta yanke wayar tsabar bala'i da ke cinta bama ta gama tantance dawa take wayar ba. Harga ALLAH Kainaat ta razana da mamakin wai Khadijah na gidansu Kano. To ta yayama akai ta iya tafiya a wannan yanayin? Wama ya bata kuɗin motar tafiyar to?. Koda yake ita miye nata ma. Ai wannan wata damace itama gareta da zata jijjiga rayuwar Dafeeq. Murmushi mai ƙayatarwa ta saki, tare da saka wata number ta rubuta text message. Tana turawa ta goge shi akan wayar tana sakin wani lalataccen murmushi. Kafin a fili ta furta, “Yaro mu zuba mu gani. Ni da kai ɗan halak ka fasa, dan CUTA CE TA ƊAU CUTA...” daga haka ta fita a ɗakin, wayar ta maida a inda ya barta ta haura sama itama..... ___________★ Kamar yanda jami'an tsaro suka buƙata an maida baba police station. Sai dai yanzu ba'a kullesa ba an dai yi shirin miƙasu kotu ne. An gama komai suna shirin barin station ɗin ne sai ga wani maƙwafcinsu da baƙi a mota. D.p.o ya bada umarnin a shigo da su. Shi dai baba koda suka shigo kallon rashin sani yake musu, sai da Khadijah da kanta ke ƙasa tana hawaye ta ɗago ne cikin zabura ta ce, “Baba Hakimi! Baba Harɗo! Aunty Mariya”. Murmushi duk suke mata, yayinda aunty Mariya ta buɗe hannu alamar tazo gareta. Babu musu Khadijah taje ta shige jikinta tana kuka mai ban tausayi. Sun jima a haka sannan suka kai zaune bisa umarnin d.p.o, daga haka aka fara gaggaisawa. Iyayen Dafeeq dai nata harare-harare tunda suma basu san su Baba Hakimi ba a zahiri sai dai a labari wajen Dafeeq. Shi kuma bawai ya taɓa zama bane wajen sanar musu komai akan alkairin su Baba Hakimi garesu. Bayan an lafa da gaishe-gaishe Baba Hakimi ya sanar musu shi wanene da dalilin zuwansa nan ɗin... “A jiya da dare wani yaro ya samemu da zance akan Khadijah da mijinta. Al'amarin ya bamu mamaki dan bamu san mike faruwa ba duk da kuwa suna a ƙarƙashin kulawarmu ne. Da farko zan fara da bama iyayensu haƙuri akan kasa maidosu gida tun a lokacin da suka zo garemu kam mu ɗaura musu aure. Munyi hakanne saboda gudun kada mu dawo dasu su sake wani takun guduwa tunda sun ƙudiri aniyar hakan dan dan yau ka haifesa ne baka haifi halinsa ba, shiyyasa na ɗaura musu auren na kuma katangesu a kusa da ni duk da nakan basu shawarar ko zasu koma ɗin amma suce ba yanzu ba. Na barsu ne har zuwa lokacin da zasu ji babu wannan zaƙin soyayyar dake ɗibarsu ta ƙuruciya. Zasu fi sanin muhimmanci da martabar kuskuren da suka tafka fiye da su dawo a sanda suke jin zaƙin soyayyar. Tabbas gaskiya ne Khadijah matar Dafeeq ce kuma ni shaidane da mutuncinta taje gareshi kamar yanda iyalina suka sanar dani, hakan ya ƙara ma bani ƙwarin gwiwar rungumarsu dan na fahimci wautar ƙuruciya da son zuciya irin ta yaranmu na yanzu ya fisgosu aikata abinda suka aikatan. Amma alhmdllh tunda ma aure sukai tunanin suyi bawai wata masha'a ba kamar yanda wasu yaran kanyi domin neman mafita.......” Tsaff ya kwashe komai ya sanar musu tamkar yanda Khadijah ta faɗa a gaban su baba, ta kuma sake maimaitawa a gaban su D.p.o yanzu babu jimawa. Tunda Baba Hakimi ya fara magana babu abinda Baba ke saki sai ajiyar zuciyar sake samun nutsuwa. Yayinda iyayen Dafeeq suka birkice da borin wai ƙarya ne duk shiri ne. Dan haka a take sukai kiran Dafeeq a waya suka sanar masa... ________★ Lokacin da kiran ya shigo masa yana gida kwance a falo, dan gama sa'insarsa da Kainaat kenan ta dinga masa dariya da faɗin ya gama da matsalar gabansa sannan yazo su ɗaura daga inda suka tsaya tai shigewarta. Shine ya kwanta a wajen yana tunani da nazarin son gano inda maganarta ta dosa. Kamar bazai ɗauki kiran ba sai kuma ya ɗaga. Jin abinda mahaifinsa ke faɗa kaɗan ya rage ya wantsalo ƙasa da ga kujerar. Baima san ya lailayo wata bagidajiyar ashariya ba da faɗin, “Baba Hakimi tare da Khadijah a Kano?”. Kafin Baban nashi ya bashi amsa d.p.o ya amshe wayar. Cikin bada umarni yace yazo Kano suna buƙatar ganinsa daga nan zuwa gobe. Zai kuma riƙe iyayensa a station ɗin har sai yazo. Bai jira cewarsa ba ya yanke kiran. Matuƙar tashin hankali Dafeeq ya shiga kuwa. Duk ya wani gigice da ruɗewa kamar wanda ya zare. Kuma shi a karan kanshi bama zai iya fadin abinda ya sakashi ruɗewar ba ma dan bai taɓa hasashe ko tsammanin Khadijah zata iya sanarma su Baba Hakimi abinda ke faruwa ba balle komawa gida a wannan halin, sakamakon imani da yay da ɗunbin soyayyar da take masa..... __________★ “Kamar yanda nai alkawarin sanar muku wacece ni? Sunana shine Alimah kamar yanda kuka sani. Sai dai ni ba mutum bace kamar yanda kuke tunani...” Babu wanda baiyi zaburar firgita ba a ɗakin, itako cikin rashin damuwa ta cigaba da faɗin, “Kamar yanda kuke rayuwa a gidajenku haka muma wasu a cikinmu nan ɗin ne wajen rayuwarmu. Dan haka na kasance ɗaya daga cikin masu rayuwa a gidan su Anoosh. Na shigo rayuwar ɗanku ne dan rama cuta da cuta. Saboda na fahimci bazai daina abinda yake ba cikin sauƙi. Na tsara shiga rayuwar ƙanwarsa Rabi'ah ne domin cimmasa ta inda bai zato ko tsammani ba. Dan haka ni da shi *_CUTA CE TA ƊAU CUTA_*. Abinda nai masa a baya kuma ba komai bane face sharar fage. Dan sai na sabauta rayuwarsa fiye da yanda ya ruguza ta ƴaƴan jama'a. Sai na bar babban gargaɗi wa ƴan baya masu irin halinsa a kansa ta yanda idan suka tinashi zasu shiga hankulansu yayin aikata makamancin abinda ya aikata. Dan haka JJ muje zuwa mataki na biyu dan yanzu ne wasan zai fara na gaskiya tsakanina da kai”. Wani irin gigitaccen ihun tashin hankali JJ ya buga, jikinsa na wata irin jijjiga da magiyar dan ALLAH tayi haƙuri, ya tuba ya tuba ta taimakesa tayi haƙuri. Ina ko saurarensa batai ba tama ɓace ɓat a ɗakin. Daga iyayensa har ƴan uwan nasa suma a rude suke ta yanda bama fahimtar ihunsa da magiya suke ba. Dan tuni wasu ma sun bar ɗakin a guje. A ƙanƙanin lokaci labarin JJ ya fara zagaye anguwa da ga bakin waɗanda suka jiyo komai a gidansu. Dan danan ko'ina ya ɗauki zance, har aka samu mai ƙarfin halin zuwa anguwar su Anoosh ya fesa labarin da ya zarce cikin anguwa ya fara zagaye gari har kunnen ƴan jarida sai ga zance a gidajen rediyo. Yayinda wasu ma suka fara zuwa gida wai jin ta bakin JJ. Hakan kuwa bamai yiwuwa bane, dan ganin JJ ya zama abu mafi wahala, wanda ma sukai ƙarfin halin iya juriyar ganin nasa da sun shiga ɗakin suke dawowa hankali a tashe sakamakon abinda idonsu ke gane musu. Dan batare da cin wuta ko ƙuna na gaba ɗaya fatar JJ tai wani irin saluɓewa kamar wanda ya ƙone a cikin man gyaɗa ko wata gagarumar wuta. Babu abinda yake a kwana da yini sai kuka da ihun magiyar a taimakesa jikinsa na ci da wuta. Sai dai abin mamaki a zahiri babu abinda ake gani sai jajur da jikin nasa yayi kawai. Tausayin rai duk da ana ALLAH wadai da abinda JJ ya aikata malamai suka haɗu ana masa addu'a da fatan Alimah ta bayyana kanta. Amma ƙiri-ƙiri babu Alimah babu dalilinta. Sai nau'o'in azabar da take ganama JJ kawai ke bayyana kansu. Dan bayan ƙuna sai ga JJ kuma na kukan son yin fitsari amma yaƙi fita. Ranar ma sunga tashin hankali akan wannan matsalar dan sai da dai takai an ɗaukesa zuwa asibiti. Shi kansa bai taɓa tunanin fitsari zai iya zama azaba ga mutum ba sai a ranar. Iya ƙoƙari likitoci sunyi dan ganin JJ yayi fitsari amma abu ya gagara, sai da takai har suma yake sannan aka samu ɗan kaɗan ya zuba, sai kuma zubar kaɗan ɗin ta sake zame masa wata sabuwar azabar data nema zama fin ta farko garesa har yana gigicewa kamar wanda ciwon hauka ke neman kamawa. Mutane ƙalilan ne ke tausayin JJ, amma mafi yawa sai ALLAH ya ƙara da ALLAH wadai sukeyi. Lokacin da hotunansa da labarinsa suka fara zagaye social media batare da an san wanda ya ɗora su ba sai wasu a cikin ƴammatansa daya lalatama rayuwa da irin yaudarar da yay ma Anoosh suka shiga binsa da mugayen addu'a suma. Harda masu zuwa dubashi har gida ko asibiti. Abin kamar wata almara labarin JJ ya zama latest a yanzu musamman a media da gidajen rediyo.. Bata canja ba kuma akan abokansa suma nasu ya fara fitowa duk da dai bai kai ta'addacin na JJ ba da ya haɗa harda kisan kai.... __________★ Kamar yanda d.p.o yay alƙawarin riƙe iyayen Dafeeq haka kuwa akayi, dan saurayin Zuhrah da ke tsaye akan case ɗin ya nuna suma bazasu yarda ba har sai Dafeeq yazo ya bayyana gaskiya wa mutane sannan domin wanke Khadijah. Hankali tashe Dafeeq ya iso Kano tare da Kainaat daya taso gaba. Da farko batai niyyar zuwa ba, sai dai bisa ga tunanin shukama Dafeeq tsiya a Kanon ta yanda zai saketa ya kuma bata takardunta kan dole yasa ta yarda ta biyoshi. Kusan ƙarfe sha biyun dare suka iso Kano, dole yay haƙuri suka wuce gidansu dan su kwana. Sai dai Kainaat nata yamutse-yamutsen fuska wai tana ƙyanƙyamin gidan tsabar iskanci. Ba itace a gabansa ba dan haka ya watsar da ita. Washe gari daga sallar asuba a police station yay masa, sai dai kuma bai samu ganin iyayen nashi ba ance sai d.p.o yazo ƙarfe goma. Hankali tashe ya juya gidan su Khadijah, inda ya tadda su Baba Hakimi da suka kwana anan. Sai dai ƙiri-ƙiri Baba Hakimi ya nuna shi bazai sauraresa ba sai sunje gaban d.p.o. dan gaskiya labarin abinda Dafeeq ɗin yazo ya aikata na ɓata Khadijah anan Kano ya matuƙar girgizashi da mamakin yaron. Yaso ganin Khadijah amma sai hakan ya gagara gareshi nan ma, sai ma wani abin mamakin daya sake cin karo da shi, wato ganin Kainaat ta fito a gidan ita da wata yarinyar makwaftansu da alama itace tai mata rakkiya. Wani shegen murmushi take masa cike da salon iskanci da nuna halin ko ina kula da mamakin da take karanta a saman fuskarsa........✍️ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da huɗu_ __________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ____________ ......Wani irin duka zuciyarsa keyi matuƙa da ganin Kainaat ɗin. Dan duk yanda yaso dakewa yay fuska hakan ya gagara gareshi. Cikin ɗan rawar harshe da shan jinin jikinsa ya furta, “Mi kikeyi anan haka Hajiya?”. “Zuminci”. Ta bashi amsa a gadarance a kuma taƙaice. Batare data jira cewarsa ba tai gaba abunta ƴar rakiyarta biye da ita. Sosai yaji kansa yana juya masa, dan magana ta gaskiya ya fara tsoron shegiyar matar nan. Dan ya fahimci dole akwai abinda take ƙullawa, kai anya ma ba'itace ta saka aka kawo Khadijah da su Baba Hakimi Kano ba? Lallai biri yayi kama da mutum, dan ya kamata ma ace yay wannan tunanin, to amma bai zama lallai ita ɗin bace tunda yasan in har Khadijah gidan Baba Hakimi ta tafi a safiyar daya saketa dole Baba Hakimi zai iya cewa zai rakota gida. Gaba ɗaya kansa ya kasa haska masa komai game da abinda Kainaat take son shiryawa, bai da zaɓin kuma daya wuce tafiya su haɗu a police station ɗin kamar yanda akace masa. Koda ya koma gida duk haukan daya dinga yi akan Kainaat ta sanar masa mitaje yi gidan su Khadijah ko kallonsa batai ba balle ma ya samu wata amsa. Hasalima ta tattarashi ta watsar ne tai kwanciyarta. Cikar lokacin tafiya station ya sakashi ƙyaleta ya wuce yana rayama ransa dole zai yi maganin ta ne. *_POLICE STATION_* Kowa da ake buƙatar gani ya iso, har D.p.o ya bada umarnin fito da iyayen Dafeeq da suka kwana a rufe. Sai dai abin mamaki sam hankalinsa ma baya kansu ya zubama Khadijah idone tamkar zai cinyeta. Shifa badan kar ace yay ƙarya ba sai yaga a kwanaki kusan goma sha ɗayan nan da rabuwarsu kamar harma ta canja. Tai masa wani irin fresh da ita, babu bandage ko ɗaya yanzu a jikinta sai ɗan alamun tabbunan ciwukan. Ga wani ƙamshi mai tada hankali da take zubawa. Tana sanye cikin doguwar rigar abayar Ni'ima baƙa da aka wadata da duwatsu sai walwali take. Shi shaida ne Khadijah ƙyaƙyƙyawace. Dan irin black beauty yaran nan ne masu taushin fata da ƙyalli tamkar ƴaƴan masu kudin na da rana bata ganinsu kullum suna ac. Gata da murzajjen jiki dan babu rama tattare da ita sam kasancewarta cikakkiyar mace da ALLAH ya wadata da komai dake tabbatar da mace a mace. Tunda suka haɗa ido tai masa wani banzan kallo daya girgiza zuciyarsa ta ɗauke kanta bata sake kallon ko sashen da yake ba. Amma shikam sam ya gagara daina kallonta. Jima yake kamar yaje ya rungumeta, dan wani irin mahaukacin sonta ne ke ƙara azalzalar zuciyarsa. Da gasken gaske yana matuƙar ƙaunar Khadijah, baima san miya shiga kansa ba ya saketa shikam, shiyyasa sam ba'a son yanke hukunci cikin fushi..... Maganar d.p.o ce ta katse masa tunani, dole ya nutsu ya maida hankalinsa can. D.p.o ya fara bama Khadijah damar yin bayani akan duk abinda ya faru. Itako kanta tsaye babu ko shakka balle gargada ta shiga jero bayani tun daga marin da taima Dafeeq a makaranta har zuwa randa ya daketa ya kuma saketa bata ɓoye komai ba. Shima Baba hakimi ya maimaita tun daga randa sukaje wajensa har zuwansu nan Kano, wanda ke tare da shi suma sun tabbatar da hakan akai. Karo na farko ran mahaifin Dafeeq ya ɓaci. Bawan ALLAH muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Amma kai ba haka ka faɗa mana ba Dafeeq. Yanzu nan kana tare da yarinyar nan tsahon shekara uku amma kazo kace mana ka saketa harma baka san inda take ba? Dafeeq wace irin rayuwa ce wannan ka zaɓama kan ka? Yanzu gatan da mukai maka a matsayinka na ɗa ɗaya tilo garemu domin nuna godiyarmu ga UBANGIJI kuma sai ya zama laifi kenan da ɗoraka akan wata hanya mara ɓillewa. Anji yarinyar nan itama nada laifi tunda bawai ka jata ta tsiya bane ka tafi da ita, da kanta ta zaɓi binka kuka tafi. Sai dai duk mai hankali da son faɗar gaskiya yasan Dafeeq ka fita laifi. Dan ita mace rauni ne da ita, sannan duk ƙanƙantar namiji a kanta zai iya yaudararta ya canja mata tunani, musamman ku yaran nan na zamani da kukai ma soyayya bahaguwar fahimta. Banji daɗi ba, dan kasa nida mahaifiyarka faɗa akan abinda ba haka yake ba. Duk da wlhy itace nidai ke zugani, koda naji bai kamata nayi abinda mukayi ba sai naji na kasa musa mata saboda soyayyar da nake muku kai da ita. Malam Muhammad dan ALLAH kayi haƙuri ka gafarcemu. Tabbas mun cutar daku kuma mun cutar da kammu. Dan kai mutumin kirki ne ka nuna mana dattako akan wannan al'amarin, saboda tunda aka fara bakace komai ba koda ɓatancine ga ɗanmu sai mune keta hauka a cikin anguwa batare da yin nazari da tunani irin na iyayen ƙwarai ba. Wannan shine mafi yawan kuskuren iyayen zamani akan kin amsar kuskuren ƴaƴansu saboda soyayya. Sai lokacin da abu ya ƙwaɓe yaro ya shiga cikin wani bala'i kuma mu kasa zaune mu kasa tsaye koma muce wani ne ya jefesa da asiri ko baki alhalin mune da kammu muka rusa masa rayuwa saboda gurguwar soyayya. Dan ALLAH ku yafe mana Malam Muhammad kai da iyalinka gaba ɗaya, yanzu da sanadin ciwon nan ka rasa ranka ina zamu saka kammu ne”. Murmushi irin na dattako Baba ya saki, sai kuma ya nisa a hankali tare da furta, “Babu komai Malam Abubakar. In sha ALLAHU komai ya wuce a yanzu. Kuma dama can ni dai ban riƙe waninku ba face addu'ar kariya da nake bin su Khadijah da shi akan ALLAH ya hanesu aikata alfasha a ƙarƙashin inuwar shaiɗan. Kuma Alhmdllh na godema UBANGIJI daya kasance sun rayu ne a ƙarƙashin inuwar aure. Ko lokacin da kukazo kuke cemana Dafeeq ya saketa ta shiga duniya ban fasa gayama UBANGIJI na ba duk da mun shiga tashin hankali. Amma sai na dinga ganinta a mafarki cikin aminci akoda yaushe, na kuma dinga jin bana kokwanto akan tanada aure. Nayi imani da ƙaddara zata iya faɗawa akan komai, amma ina alfahari da fatan yanda ban taɓa taɓa ƴar kowa ba da nufin zina ko ɓata mata rayuwa nima in sha ALLAHU ALLAH zai bama nawa ƴaƴan kariya. ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, ya kuma shirya mana yaranmu damu kammu dan aduk sanda suka aikata kuskure yakan zama wani lokacin muma iyaye da gudunmawarmu a ciki, duk da dai akwai tsayayyun iyaye da wlhy suna iya ƙoƙarinsu akan ƴaƴan amma zakaga abun sai dai addu'a kawai. Wasu kuma duk da suna ƙoƙarin zata iya yiyuwa suma sunma iyayensu wani kuskurene da suke girban abinda suka shuka akan ƴaƴan nasu kuma. Dan abinda muke mantawa idan fa ka aikatama iyayenka ƙyaƙyƙyawa kaima ƙyaƙyƙyawa zaka girba a wajen ƴaƴanka, idan mummuna ne kaima zaka girbi dai-dai da hakanne. Ni kaina ina danganta abinda Khadijah ta aikatamin da bijirewar da naima nawa iyayen akan auren mahaifiyarsu a farko, dan sai da takai bayan an aura min ita nai tahowata nan Kano kusan watanni biyar wai dan duk suji haushi su rabamu, amma koda na koma saina samu dai tana nan a gidanmu. Daga nan na karaya na sallama bayan ita da kanta tamun nasiha da tabbatar min itama ba sona take ba umarnin iyaye tabi, tana roƙona koda bazamu so juna ba muyima iyayenmu biyayya kodan darajar da ALLAH ya basu da fifiko a kammu na haihuwa. Wannan shine sanadin gyara komai harna ɗakkota muka dawo nan cikin Kano da zama. Duk da na roƙa iyayena gafara sun kuma yafemin gashi sai da na girba abinda na shuka ga ƴata ta fari dana ɗauki burin duniya na ɗaura a kanta da tunanin zata zama madubin ƙannenta a komai na rayuwa.” Kuka sosai Khadijah ta saki hankalinta na ƙara tashi. Dan wlhy zuciyarta zata iya bugawa idan ƴaƴanta anan gaba akace zasu rama abin nan da taima mahaifanta. Cikin rawar jiki da kuka take roƙon dan ALLAH su yafe mata. Cikin murmushi Baba yace, “Ai komai ya wuce Khadijah na yafe miki. Mahaifiyarki ma ta yafe miki tun ma kan ki dawo garemu. ALLAH ya ƙara shirya mana ku”. An amsa da Amin, yayinda Dafeeq ya durƙusa shima gaban Khadijah cikin sanyin murya ya ce, “Dan ALLAH nima kiyi haƙuri to ki dawo gareni Khadijah. Na miki alƙawarin wlhy zan koma miki kamar da yanda muke a farko. Abinda ya faru ma wlhy tsautsayi ne. Amma zan cigaba da riritaki fiye da yanda nai miki a farko”. Wani banzan kallo ta masa hawaye na sauka mata. Sai kuma ta nuna kanta da faɗin, “Wai ni kake tunanin zan koma gareka Dafeeq? To kayi kuskure. Wlhy koda ace baka aikatamin komai ba hakan ta faru, zan hana kaina komawa aurenka saboda ya zama horo ga kuskuren dana aikata na bijirema iyayena. Koda ace kuwa ina jin soyayyar ka zata halakani wlhy. Balle ma a yanzu bana jin koda ɗigon soyayyar ka a raina. Kuma wlhy! Wlhy! Wlhy koda ace soyayyarka zata halakani, koda ace kaine autan maza na barka har abada Dafeeq.....” Cikin rawar jiki da bugawar zuciya Dafeeq dake ƙoƙarin riƙo mata hannu ke furta, “Dan ALLAH Khadijah, dan ALLAH kada kice haka, kada kimun haka. Wlhy ina sonki, kuma kema nasan kina sona. Sharrin shaiɗanne kawai da munafuncin matar can. Amma wlhy kika barni zan iya rasa kaina gaba ɗaya. Sannan ni wlhy nama maidaki, na maida auren mu tun randa na ce nai sakin, kin san dai akwai sauran igiya ɗaya”. Murmushi mai ciwo Khadijah ta saki. Sai kuma taja tsaki da taɓe baki. “Ka ɗauka ka maida banza Dafeeq, dan zama ni da kai har abada ya ƙare. Maganar matarka kuma kadai sone kawai ka ɗaura mata laifi. Amma ni zuwanta alkairi ma ya zame min. Tunda a sanadin zuwanta nasan kai ɗin nan, kai da kanka kake zubar min da ciki. Sannan kana zagayowa kazo ga iyayenka, ka kuma gyara mu'amalarka da su yayinda ni ka gama ɓata mun suna da mafi munin ɓatanci a wajen nawa iyayen da mutanen anguwa. Wai na shiga duniya! Kai jama'a na rasa miye ribarka kan aikata wannan shaiɗanar. Kaico da miji irinka, kaicona da bijirema iyayena nabi mutum irinka mara zuciya a ƙirji. Dan sam kai ɗin ba cikakken mutum bane Dafeeq. Kai azzalumi ne, kuma na barka da ALLAH, na kuma godema matarka dan alkairi ce nikan a gareni. Idan ma mafarki kake ka farka. Dan har abada ka rasa Khadijah Muhammad Kura, kasa wannan a ranka kama hutar da kanka okayyy”. Sosai jikin Dafeeq ke mazari. Zaiyi magana d.p.o ya dakatar da shi. “Uhhm kaga magana taƙare kuma. Daga yau nima na kashe wannan case ɗin. Abinda ya rage shine dole ka bayyana ma duniya kai da iyayenka gaskiyar lamari domin wanke Khadijah kamar yanda kuka ɓata ta. Zamuyi a rubuce dan ya zama konan gaba wani abu ya taso ni da kaina zan ɗauki mataki akan duk wanda ya aikata”. Baba ne ya amshe da faɗin, “Hakan yayi dai-dai yallaɓai kuma mun gode sosai. Sannan ina so yanzu a gabanka a gaban iyayensa dasu yallaɓai Hakimi ya janye maganar cewar ya maida Khadijah, yama cika mata ɗayan sakinta dan maganar gaskiya ni kaina bazan bar wannan auren sake komawa ba ya isa hakan nan. ALLAH ya haɗa kowa da rabonsa na alkairi”. Sake rikicewa Dafeeq yay, hatta mahaifinsa roƙon baba yake akan yay haƙuri kada ya raba auren. Amma Khadijah ta rantse in bai saketa ba zata kaisa kotu kokuma ta faɗa rijiya ta mutu sai ya zauna da gawarta. Jin kalamanta yasa D.p.o tsare Dafeeq akan saifa ya janye maganar maida khadija da yace yayi. Dafeeq ya koma roƙon Baba Hakimi da Baba Harɗo. Suko sukace babu ruwansu, wannan zaɓin Khadijah da iyayenta ne ba nasu ba, basu da hurumi akan wannan batu. Dole Dafeeq naji na gani tare da zugar mahaifiyarsa data cika da takaici tai fam tun sanda babansa yay magana da bama Baba haƙuri ta shiga rantsuwar itama Dafeeq ɗin bazai sake zama da Khadijah ba. In ko ya cigaba da dagewa zata tsine masa ne. Garama ya saketa, idan kuma ya saketa bazai ragu da komai ba, shida keda mata ƴar arziƙi irin Kainaat miye dan ya rabu da wata Khadijah can da har zai wani damu kansa a banza a wofi har ana raina masa hankali da nuna tama fisa wani fifiko ne.......✍️ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da biyar_ ____________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ __________ .......Saki dai dole Dafeeq yayi sa, sannan akai komai a rubuce kowa ta saka hannu aka bama kowa nasa copy ɗin d.p.o ma ya ajiye nasa. Khadijah ta dinga sakin ajiyar zuciya da jinta sakayau tamkar wadda akaima rahama. Haka suka taho gida Dafeeq na kallonta harda cin tuntuɓe mahaifiyarsa na jansa tana masifa da hararar Babansa. Dan gaba ɗaya yama fi kowa bata takaici daya kware musu baya ya zaɓi bare akansu har yana gurfanen bada haƙuri akan abinda ita bataga inda sukai laifi ba. Sosai Baba ya sake jerama su Baba Hakimi godiya. Suka kuma haɗa musu shatara ta arziƙi dan sun ce yau kam gida zasu kwana tunda an gama komai. Sanda zasu wuce Khadijah harda kukanta. Haka dai sukai musu sallama suka tafi badan rai yaso ba. Amma dai in sha ALLAHU Baba yace zuminci ya ƙullu kenan. Khadijah batai ƙasa a gwiwa ba bayan wucewar Baba Hakimi ta sake neman gafarar iyayenta dama ƴan uwanta. Suma basu ja zancen ba sukace komai ya wuce ai sun yafe mata. Baba da Mama suka sake mata nasiha da nuna mata illar abinda tayin. Ranar ma taci kuka dan harda su zazzaɓi tasha da ciwon kai. Daga ƙarshe dai ƴan uwanta suka koma tarairaiyarta suma... ★ A gidan su Dafeeq kam bala'i ne ya nema kaurewa tsakaninsa da Kainaat daya tattara laifin komai a kanta mahaifiyarsa na kareta. Amma ita sai tai biris da shi saina murmushi da take dan a ganinta dai ta baƙanta masa rai. Kuma koba komai iyayensa sun kwana a bayan kanta. Duk da ma ba haka taso ba wlhy. Taso ace anyi bala'i iya bala'i da iyayen Khadijah ta yanda sai Dafeeq ya wajigu kamar na wata ɗaya ya fita a hayyacinsa. Amma koba komai dai hakan ma nasara ce. Tsawatawar iyayensa ya taƙaita wannan fitina. Sai dai a ransa ya ƙudiri aniyar wlhy sai tayi dana sanin masa wannan abun datai masa. Oho bata damu ba, dan itama dai ta shirya masa tsaff. Bai yi niyar su koma Adamawa ba sam. Sai dai fa maganganun mutane da ALLAH wadarai da akema iyayensa da shi kansa akan Khadijah ya hanashi sakat a anguwa. Musamman ma da akace yanzu Kainaat ya aura tare da jin labarin tushen auren nashi. Shike nan mutane suka samu nayi dan duk wanda dai ya kalla Kainaat yasan ba sa'ar auresa bace duk da dai a addinance bawai haramun bane. Amma dai ana fassara shi nashi auren akwai manufa a ciki tunda ance Kainaat nada kuɗi. Hankali tashe ya tattara Kainaat suka koma inda suka fito akan sai komai ya lafa zasu dawo. Dan ya ƙudiri aniyar baro Adamawa zai dawo gida Kano da zama. Kainaat kuwa da ita wasan yanzu aka fara.... *_BAYAN WATANNI_* Tafe take cikin ɗan sauri-sauri, sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarta ba irin ta ɗiya mace. Hijjab ne har ƙasa a jikinta da niƙab dan babu ta inda ake ganin komai nata sai ƙwayar ido. Komai ya canja a rayuwarta, canjawar da take tabbatar da ita a sabuwar Khadijah Muhammad Kura. Duk da watanni bakwai ɗin nan da suka biyo bayan abinda ya faru sun sake zuwa mata da wasu abubuwa ne mabanbanta wanda tai tsammani babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya. Taso komawa ta cigaba da karatunta, amma sai Baba ya tabbatar mata da cewar ta makaro kuma. In dai a gidansa ne ta gama karatu kenan wannan shine horon da zai mata akan kuskurenta. Sai dai zai barta ta koma islamiyya bazai taɓa tauyeta a neman ilimin addini ba, na boko kam sai dai idan aure ta ƙara mijin ya maidata amma shikam badai shi ba. Duk irin roƙo da magiyar da taima baba bai saurareta ba. Haka tanaji tana gani dole ta jingine maganar makarantar boko ta koma islamiyya kawai ƴan uwanta ma bata sha'awa. Dama dai ta kusa sauka ta tafka waccan tsiyar, dan haka a yanzu ta sake dagewa sosai fiye da da gashi har tayi saukar tunda dama tana gab. Zakuma ai bikin saukar da ƴan uwanta ne a ranar ɗaurin aurensu da ya rage saura kwanaki huɗu kacal a yanzu. Sam bata kula kowa a yanzu. Kai ko kallon wani namiji da wata siga batayi, dan duk ta haɗasu ta musu kuɗin goro a littafin rayuwarta. Bayan kammala iddarta samari da yawa harma da magidanta sun fito da niyyar aurenta amma ta dakatar dasu. Shi dai Baba dama baice mata komai ba, hakama Mama iyakarta da ita nasiha da shawara. Sai su Ni'ima ne keta zugata akan ta fidda miji a haɗa bikinsu dan ALLAH. Murmushi kawai take musu tace ba yanzu ba, ita da aure ma tana jin har abada. Sukan nuna jin haushin maganarta, itako ta tattarasu ta share kawai.... Isowar napep da take jira ya katse mata tunani. Sai da ta sanar masa ina zata sannan ta shiga tare da fiddo wayarta ƙarama ta daddana dakai kunne. Daga can Zuhrah ta amsa mata. “Aunty kin taho ne?”. Kai tsaye ta ce, “Eh, ina fatan dai kun gama gyaran jikin”. “Eh muna kammala, kema muke jiran dan har an gama mana komai ma. Dan ALLAH ki maza kizo a miki kema. Kefa kaɗai ya rage”. “K nifa ku rabani da wannan gyaran jikin. Kunbi kun takura min kullum aka gama muku sai kun takura an yaɓamin wannan kayan naku a jiki ina dalili. Yau ma kawai zanzo ne saboda biyanta kuɗinta da kuma Baba daya ce dole nice zan tsaya a kanku muna komawa gidan”. Dariya Zuhrah tai da faɗin, “Aunty Khadijah masifa, shike nan sai kinzo mudai muna jiranki.” wayar ta yanke itama tana taɓe baki, minti kaɗan suka iso anguwar. Ta biya mai napep ɗin ta shiga. Ta samu an kammalama su Ni'ima komai. Kamar kullum yauma sukai kanta su da mai gyaran jiki sai da aka mata aka kuma tsareta tasha abubuwan da ake basu wai maganin sanyi, ƙyalesu kawai take ana tasan wani ba maganin sanyin bane ba. Dan kusan sati biyu kenan ita ke kawosu ta wuce islamiyya, idan an tashi ta biyo ta ɗaukesu su koma gida. Baba ne ya sata wannan aikin badan komai ba sai dan tsoron yau da gobe. Sai da aka gama mata komai batare da jira ya daɗe ba ta maida kayanta da hijjab suka wuce gida akan idan taje can tayi wanka. Dama haka take yi ita kullum. Daga haka sukai sallama da mai gyaran jiki akan ita zata samesu gida gobe dakai ƙunshi... Washe gari akai kamu, a kuma ranar akama amare ƙunshi, tare da tsare Khadijah itama akai mata exactly kalar nasu. Tun a ranar baƙi suka fara cika gida musamman ƴan uwansu da zasuzo da ga kura asalin garin babansu kenan. Duk da sun san da batun Khadijah kowa yazo ya ganta sai ya tanka da sake maido da zance baya. Hakan yasa ta dinga jin hawaye sai dai ta faki ido ta share kawai. Ganin zance yana neman fara yawa a kanta Mama tace su koma gidan makwafciyarsu Maman Daddy tunda mijinta baya nan. Hakan ne ya bama Khadijah salama. Idan ba doleba kuma bata yarda ta shiga gidansu sam. Washe gari ta kasance ranar ƙunshi na ƴammata. Ga baƙi nata sake kunno kai dan wannan shine biki na farko da za'ayi a gidan tunda dai Khadijah ba'a gida akai nata ba. Cika iyakar cika gida yayi, Khadijah dai tana tare da amare amma bata shiga cikinsu ta barsu da ƙawayensu. Tana daga gefe matsayinta na babba ta kama kanta. Ana gobe ɗaurin aure ne ta kasance ranar dinner da anguna suka lallaɓa baba da ƙyar ya amince musu ayi a ranar, dan da an ɗaura aure yace bai yarda da wata bidi'aba kuma. Hakan yasa suka saka dinner ɗin daren ɗaurin aure. Washe gari ayi walima da saukarsu bayan an ɗaura aure. Da dare a miƙa amare ɗakinsu shike nan. Sam Khadijah batai niyyar zuwa dinner ɗin nan ba. Amma aka sakata gaba. Kai har sai da takai Ni'ima tai rantsuwar in har Khadijah bazataje ba wlhy itama bazaje ba. Jin haka yasa itama Zuhrah tace itama ta fasa sai dai anguna suyi abinsu su kaɗai. Khadijah ta ɗauka wasa suke, sai da taga mai kwalliya tazo sunƙi yarda a musu sannan ta yarda zataje. Haka suka tsaya a kanta aka fara mata kwalliya ƴar dai-dai misali sannan suma akai musu tasu irin ta amare tare da zuba musu ado na gani na faɗa. Su duka sunyi ƙyau sosai cikin lassai masifar ƙyau ja sai Masha ALLAH. Haka itama Khadijah tai wani kalar ƙyau na masifa kamar ka haɗiyeta. Balle yanda jikinta da fatarta suka wani sake murjewa dayin fresh tamkar bata shiga rana. Ƙamshin gyaran jiki ko da akai musu yasa koya suka motsa zakaji wani shegen ƙamshi mai motsa zuciya da ratsata kwanya. A yanda komai na Khadijah ya canja saika rantse bata taɓa aure ba ma. Dan kusan yanzu ne take kan ganiyar zama cikakkiyar macen ta. Sosai material ɗinta fari da adon pitch flowers da akaima fitet gown yay masifar kwantawa a jikinta tamkar an zana shi. An mata ɗaurin daya kwanta sosai ta gaba gashinta ya fito hakama baya jelar da aka naɗe da ribbon sai ƙyalli suke. Ba ita kaɗai ba yaran gidansu duk suna da gashi dan sun gada a wajen mahaifiyarsu ne, Jamilah ma duk ta fisu. A wajen saka mayafi ne aka fara rikici, tace ita bazata iya fita da mayafi a kafaɗa ba da wannan gown ɗin. Su Ni'ima sai roƙonta take itako ta dage hijjab zata saka. Sai da Zuhrah ta hau mata kuka sannan ta yarda badan ranta yaso ba ta saka gyalen pitch color shima dan bata son taga ɓacin ran ƴan uwanta a yanzu, sai dai a saman kanta ta ɗora ta lulluɓa duk da bawani ya sauka mata ƙasa sosai bane yanda take so. Dan bayanta da bata so a gani dai sun fito ƙirjin kawai ya rufe. Ganin hakan yasa ta saki jelar gyalen ta baya na gaba kuma ta yanashi ta yanda ya rufe mata ƙirjin, sai hakan ya taimaka mata sosai amma kuma ta gefen data saki gyalen ana gano gashinta baƙi siɗik da aka faka a tsakkiyar kan ya fito tsakkiyar ɗaurin ɗan kwalinta. Haka dai ta haƙura suka fito kasancewar abokan ango na zaman jiransu. Duk da mijin Zuhrah dana Ni'ima sun girmeta matukar girmamata suke kamar yanda ƙannenta ke mata. Dan haka tunda suka fito suke faman tsokanarta da faɗin, “Kai kai Aunty Deejoh wannan ai kece ma amaryar kawai gaskiya. Gaba ɗaya ai kinsa kwalliyar amaren ɓoyewa. Murmushi tai mai sanyi tana girgiza kanta, dan tasan dai tsokanace kawai. Inata ina amare da suka fito tamkar taurarin dake jikin wata ɗan daren sha bakwai. Mota guda suka ware mata wai ita kaɗai za'a ɗauka ai babbar ya uwa. Ita saima suka bata dariya. Haka dai ta shiga dan shima wanda zai ɗauketan duk ya wani rikice abokinsu ne. Ganin yanda yake wani rawar ƙafa yasata jan girma dan ita a yanzu kam duk maza haushi suke bata saboda kallon Dafeeq take musu. Duk yanda ya isheta da surutu bata tanka masa ba har suka iso inda za'ai dinner ɗin. Waje kam yay ƙyau sosai matuƙa. An masa docoretion irin ankon ƙawayen amarya da abokansu. Alhmdllh daga mijin Ni'ima har na Zuhrah matasan masu kuɗine kuma abokan juna tunda a dalilin saurayin Zuhrah shima na Ni'ima yaga Ni'imar ya maƙale, dan kowa naji da kansa, dan haka suka haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen shirya komai yanda zai ƙayatar. Yako ƙayatar ɗin. Lokacin da za'a buɗe taro da addu'a mc ya shelanta ganin malama Khadijah Muhammad Kura babbar yayar amare. Ji Khadijah tai kamar ta fasa ihu, ganin bata da niyyar tashi Ni'ima ta tura mata saƙo a waya, cikin magiya take roƙon dan ALLAH taje. Ido ta ɗago ta kalla Ni'imar, sai taga duk sun ƙwaɓe fuska ita da Zuhrah kamar zasuyi kuka.. Dole ta daure ta miƙe zuwa inda ake buƙatarta ta amshi mp ɗin ta fara addu'a. Tsitt hall ɗin yay kawai ana saurare zazzaƙar muryarta mai fita da matuƙar sanyi da nutsuwa. Wadda ake iya ji harta waje kasancewar ƙofar dake a buɗe. Tana kammalawa ta miƙa wani a cikin abokan ango yazo yana gwargwaɗa ma mc magana a kunne. Ita dai wucewa tai ta koma wajen zamanta. Yayinda mc ya fara shelar faɗin, “Masha ALLAH! Masha ALLAH!! Tofa jama'a sai mu sake gyara zama domin kuwa oga kwata-kwata, mai gayya da aiki ogan waɗan nan anguna guda biyu. Gwarzon matashin nan uban matasa ya iso wannan waje mai albarka tare da tawagarsa domin taya angunan biyun nan murna. Dan ALLAH a tafama bango goya marayu uban marasa uba, kai masu uban ma ubansu ne fa. Dan yarone amma mai zuciyar dattawa. Kai dan ALLAH ku bashi tafi”. Ji kake raff-raff!! Kowa ya zubama ƙofa ido da fatan son aga waye zai shigo. Duk da kuwa wasu a wajen sun san sunan wannan oga na anguna, wasu ma sun sanshi a fuska musamman abokansu da danginsu.........✍️ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da shida_ ________________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ____________ ......Sallamar sassanyan ƙamshin turarensa kafin bayyanarsa ya sake zama wani ɗan jagora a fisgar mutanen hall ɗin da suka ƙwaɗaitu da son ganin wanene wannan ogan anguna da mc ke kwarzantawa da kurantawa haka da kirari. Masha ALLAH na ambata a ni karan kaina a lokacin da matashin cikakken mutum ya bayyana. Lallai babu ƙarya, dan mai kallo ya isa fassarawa da yarda da kalaman mc akan wannan matashin mutum. Bawai zamu kirashi ɗanyen kai sharaf ba, dan shekarunsa a ƙalla zasu iya kai 37+ ma. Sai dai yanayin jin daɗi da kwarjinin da ALLAH yay masa ga cikar kamala zai iya sa kace bazai iya kai shekarun ba ma. A take flash na camaras ya fara harska shi tun daga farkon shigowa har zuwa mazaunin da aka tanada domin sa. Sai da ya zauna tamkar wani gwamnan jiha kafin muƙarrabansa da suka tako masa baya suma su sami wajen zama. Ƙus-ƙus ne ya fara tashi a tsakanin ƴammata da zawaran dake wajen, kai hatta ma masu auren wasu sun gaza haƙuri sai da suka tanka. Dan kuwa dai tabbas babu ƙarya wannan oga na anguna ya kai ace wani abu akansa. Ƙyawu da kwarjini ziryan da babu gauraye ALLAH ya azurtashi da shi, cikakken bafulatani ɗan usil, ga nera da ta zama babban ado wa rayuwar koda mai ƙarancin ƙyau ne a wannan rayuwar. To shi sai ya zam UBANGIJI ya haɗa duka biyun ne garesa. Dan ko adon dake jikinsa ka kalla kasan naira ta zauna koda baka san minene darajar kuɗin kaya ba kuwa. Abun zai baka mamaki idan nace duk wannan kai kawo da kace nace da ake akan ogan anguna ko sau ɗaya Khadijah bata ma kalla sashen da zai shigoba balle inda ya zauna. Ta tattara hankalinta ne gaba ɗaya a wayar Ni'ima dake hannunta tana buga game hankalinta kwance. A haka mc ya sake jera kirarin barka da zuwa ga babban baƙo. Kiran sunan Khadijah da mc ya sake yi tare da roƙon sake zuwa ta sake buɗe wannan taro da addu'a a karo na biyu ya sakata jin tamkar ta fasa kuka. Amma yaya zatayi, bazata iya bari ƙannenta shiga damuwa ba. Dan haka bayan ta kwashe kusan mintuna uku da har sai da mc ya tako inda take sannan ta miƙe tana ɗan harararsa ƙasa-ƙasa. Cikin takunta na nutsuwa ta fito sautin takalmanta na shiga kunnuwan duk wanda ke wajen sakamakon komawar hall ɗin shiru. A inda ta tsaya ɗazun yanzu ɗin ma dai ta tsaya, cikin nuna takura ta fara karanto addu'oi zazzaƙar muryarta na ratsa kunnuwan duk wanda ke'a wajen. Cak ya dakata daga latsa wayar da yake, ƙirjinsa na wani kalar harbawa da motsawa tamkar ɓera na sukur-sukur a drower. Wani irin ratsa ɓargon jikinsa muryar tata tai kamar wanda aka watsama ruwan sanyi cikin jijiyoyi maimakon jini. Wayar ya damƙe sosai cikin hannunsa tare da ɗago idanunsa ƙasa-ƙasa ya sauke a kanta. Sai dai baya iya gano fuskarta sai bayanta da gashin kanta dake a tsakkiyar ɗan kwali samakamakon zamewar gyalen daga saman kanta... Duk jinta take a daburce ganin yanda aka zubo mata idanu fiyema da ɗazun, dan haka tai addu'ar a takaice tana miƙama mc m.p ɗin harda balla masa harara. Shiko babu sirri ya ce, “Oh ƙyaƙyƙyawa irin wannan harara haka ai sai ki hanani barci wlhy”. Ya ALLAH ji Khadijah tai kamar zata zube a tsakkiyar hall ɗin sakamakon yanda ya sake jawo attention ɗin mutane kanta musamman mazan wajen. Da ƙyar dai ta iya maida kanta mazauninta tana sauke numfashi guda-guda. (Tsarki ya tabbata ga UBANGIJI) zuciyarsa ta sake ayyanawa tare da bugawa da ƙarfi kamar an daki ganga sakamakon saukar idanunsa kan black beauty face ɗin Khadijah da akaima kwalliya a taƙaice ta yanda kamanninta sam basu ɓace ba. Haka kawai yaji a ransa kamar ya taɓa ganin fuskar, to amma a ina? Wannan shine ya kasa tunawa sam. Isowar anguna inda yake domin miƙa masa gaisuwa ya katse tunaninsa. Yanda suka gaishesan ma da matuƙar girmamawa ya sake tabbatar ma kowa dake gurin shiɗin na musamman ne a garesu. An musu hotuna a tare kafin su koma wajen zamansu. Da ga haka aka fara abinda ya tara mutane. A dai-dai lokacin da ake kiran babban abokin anguna domin faɗar tarihinsu a lokacin wani baƙon matashin saurayi kuma ke isowa hall ɗin shima. Shima dai mc ya sanar da zuwansa matsayin Uncle ɗin mijin Ni'ima. Sai dai kasancewar sa'an ango ya zama abokine, ya kuma taso tundaga kudancin Nigeria domin wannan biki. Sai da aka bashi wajen zama sannan abokin angunan yay bayani akan tarihinsu su biyun. Yana gamawa akai kiran Khadijah matsayin wadda zata bada na amare suma. Taji kamar taƙi zuwa, amma ganin fuskokin su Zuhrah yasata miƙewa badan taso ba. A yanda kansa ke duƙe bazaka taɓa tunanin ita yake kallo ba, amma kaf hankalinsa na kanta, ƙoƙarin son tuno inda ya santa kawai yake yi dan tabbas shi yasan wannan fuskar. A hankali Khadijah ta fara abinda aka kirata tayi cikin harsuna guda uku datai matuƙar birge mutane jin yanda take fidda kowanne da ƙwarewa duk da a rubuce koman yake. Hausa, larabci, turanci. A bazata kawai akaga saurayin nan daya iso yanzun nan Uncle ga mijin Ni'ima ya iso gabanta ya fara zuba mata liƙin ƴan 200. Ihu mc ya ɗauka yana wani zigashi, shiko idonsa ya rufe sai zubama Khadijah da ke jin wani irin tashin hankali sabbin 200 yake yi yana mata wani shegen kallon daga sama har ƙasa dan tun fitowar Khadijah yaji ta gama tafiya da duka imaninsa. Dan haka ya kasa jurewa kawai ya zaɓi hanyar da zata ɓille masa tun da wuri. Duk yanda yaso daurewa da danne ransa hakan ya gagara. Duk da ya kasa tuno a inda yasan yarinyar sai yake jin kamar yana da wata babbar alaƙa da ita. Sai kuma yanda saurayin ke mata liƙi da zagayeta yana mata wani kallon gogaggun maza yaji ya zafesa. Wayarsa da saƙo ya shigo ya duba, kamar wanda aka zabura tsamm ya miƙe cikin nutsuwarsa da cikar kamala batare da kowa yay tunanin ina zaije ba shima dai aka gansa gaban Khadijah. Ƴan 500 sabbi ƙal da yaronsa ya iso da sauri ya miƙa masa kawai yayma wata kalar farkewa ya fara liƙama Khadijah. Ganin haka saurayin nan da yaji zuciyarsa ta sosu shima ya watsar da ƴan 200 da suka rage hannunsa ya zaro dubu-dubu. Ihu hall ɗin ya ɗauka yayinda jikin Khadijah ke neman fara rawa dan ita bata fahimci manufar hakan ba gareta face kallon al'amarin a wulaƙanci da son nuna fariyya. Ɗagowa tai cikin ɓacin rai idonta karaf akan yaronsa. Ai ko a magagin barci bazata mance wannan fuskar ba, shima Awwal da tun fitowarta ya ganeta ya sakar mata wani murmushi. Da sauri ta janye idonta a kansa ta maida ga ogan nasa da ke kallonta shima, sai dai saɓanin yanda ya tasanshi yanzu fuskarsa a ɗaure take. Awwal da dama gaba ɗaya saurayin nan ya gama baƙanta masa rai da ganin yana son nuna takara da yayansa cikin sauri yakai kunnensa ya gwargwaɗa masa maganar da Khadijah bata ji ba, sai kuma ya miƙa masa wasu kuɗi da bata taɓa gani a zahiri ba sai a hoto ana ce dasu dollars. Wani irin jan gadara yayma takardar samansu yana wani yamutse fuska ya fara zuba mata su saman dubu-dubun da saurayin nan ke liƙa mata. A yanda fa hall ɗin ya ɗauki ihu yanzu sai ka rantse zai fashene. Ina Khadijah bazata iya jurar haukar nan ba. Da sauri tai ƙoƙarin barin wajen amma suka cigaba da binta suna liƙa mata kuɗin har wajen zamanta. Mc ya matuƙar haukacewa, dan ogan anguna dai sai farke dollors yake kamar baisan ciwon kuɗin ba. Yayinda ran wancan guy ɗin ya ɓaci matuƙa ya koma liƙama Khadijah bandir na dubu-dubun a dunƙule. Mijin Ni'ima da ya gama sanin waye Yassar a fitina da kuma sanin waye ogansa a rashin son raini yasa ya aiko wani cousin brother nasu jan Yassar ɗin daya gama cika fam da takaicin wannan mutumin. Taya ma zai fara nuna interest ɗin sa akan yarinya shi ya fito yana nuna masa gadara akan kuɗi. Waye shi! Ɗan uban waye ne!. Awwal da ke jin kamar ya fasa ihu dan daɗi akan abinda yayan nashi yayi sai murmushi yake yi. Dan duk wanda yasan yayansa yasan babu abinda ya damesa da mace duk ƙyanta, duk jin kanta. Amma lokaci ɗaya ya nuna damuwarsa akan Khadijah. Duk da yana tunanin yayi hakanne saboda tuna wacece ita amma dai zuciyarsa na ƙaryata hakan. Tuni yaran mc sunzo sun fara tsince kuɗin dake zagaye da Khadijah da tunda ta zauna kanta a ƙasa taja mayafi ta rufe fuskarta tana hawaye. Kirari mai suna kirari mc ya fara ga ogan anguna. “Tabbas idan kaji ana ƙi gudu sai idan sa gudun bai zoba. Ai na faɗa muku shi ɗin uban mara uba ne, har masu uban ma fa ubansu ne. Oga *_ABAAN OMAR MODIBBO_* ake faɗa muku, sune shinkafa a ƙasar nan, dan sai sun so a dafa muku a tukwanan gidanku kuci zaku ganta. Sawun giwane take na raƙumi koda kuwa raƙumin tsohon amale ne....” yanda mc ke zabga kirari zai tabbatar da ruwan kuɗin na ya gama gigitashi. Shiko tunda ya koma mazauninsa ya sake maida kansa ga waya baiko ƙara kallon kowa ba sai dai abinda basu sani ba idonsa nakan Khadijah ne ƙyam ko yaya ta motsa. Gashi taƙi sake yarda ta buɗe fuskarta a cikin mayafi har lokacin da amare da anguna suka fito sannan ya tashi nan ma ya zuba musu liƙi da ƴan dubu-dubu. Taro ya cigaba da tafiya sai dai duk yanda mc yaso Khadijah ta sake hawa sama bai samu ba. Dan ko da amare da anguna suka fito aka buƙaci ganin jinin amare suyi rawar jini da jini ita bataje ba. Sai amaren ne sukazo inda take sukai mata liƙi tare da angunansu amatsayin girmamawa ga babbar yayarsu. Sai hakan ya sake ƙayatar da mutane sosai. Awarsa kusan biyu a wajen ya miƙe, a tare da muƙararransa su Awwal suma duk suka miƙe dan kowa yasan yayi ƙoƙari, babu ma wanda yay zaton zai yi mintuna talatin a wajen, amma sai gashi da awanni har kusan biyu. Ya amshi mp daga zaune yay addu'a da fatan alkairi ga anguna da amare harma da godiya ga jama'a sannan yay sallama. Idonsa ƙasa-ƙasa akan Khadijah har sai da ya gota ta sannan ya ɗauke... Fitarsu da kamar mintuna goma sai ga Awwal ya dawo wajen, kai tsaye inda anguna suke yaje yay magana dasu batare da kowa yasan miya faru ba akaga angon Zuhrah ya tashi. Fita yay, baifi minti biyu ba shima sai ga Jamilah tazo har inda Khadijah take ta kama hannunta bayan itama ta gwargwaɗa mata magana. Da alama dama Khadijah kamar akan ƙaya take, dan kafinma Jamilah ta gama maganar tamiƙe. Bata buɗe fuskarta ba a haka Jamilah ta taimaka mata suka fice a hall ɗin gaba ɗaya kamar wata amaryar da za'a kai gidan miji. “Aunty to ki buɗe fuskar tunda mun fito”. Cewar Jamilah tana ƴar dariya. Ajiyar zuciya Khadijah ta sauke mai nauyi tare da janye mayafinta a hankali. Tana ƙoƙarin yin magana da ƙara sauke ajiyar zuciya mijin Zuhrah ya iso wajen fuskarsa da murmushi. “Auntyn mu tuba muke. Gaba ɗaya sun hana mana ke sukuni ko. To ayi mana afuwa dan ALLAH. Idan babu damuwa kizo a maidaki gida kawai dan na fahimci gaba ɗaya a takure kike a wajen nan muma yanzu zamu tashi ma insha ALLAHU ”. Jitai hakan ya mata, dan haka a sanyaye ta ce, “Nagode sosai Ya Ibrahim. ” yanda Muryar tata ke fita da sanyi sosai zai tabbatar maka kuka tayi. Murmushi Ibrahim ɗin yayi da faɗin, “Babu komai auntynmu ai yima kai ne. Bissmilla ko”. Bata kawo komai a rai ba ta bisa har zuwa inda ƙatuwar zuƙeƙiyar baƙar mota ke a fake. Baya ya buɗe mata da matsawa gefe. Itako a tunaninta babu kowa a ciki kamar ɗazun, kanta tsaye ta shiga tana masa ɗan murmushin ƙarfin hali da faɗin, “Ya Ibrahim thanks you”. Murmushi ya mata da rufe motar bayan ya gyara mata mayafinta da ya ɗan sakko waje.......✍️ _🥱🥱Gaskiya zanci ganda irin mai yajin nan da romo da ake cema ragadada sanda muna yara😩. (🚴🚴🚴Kai jama'a Bily da son girma, irin mu mun girma ɗin nan yanzu fa ko🤣 wai sanda muna yara🤣)._ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Ashirin da bakwai_ __________________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ _______________ .......Jin kamar mutum a gefenta da azababben ƙamshin daya gama ɗaure motar ya sata juyawa gefenta kamar a ɗan razane. Wani irin bugawa ƙirjinta yay da ƙarfi har tana ƴar zabura. Sai kuma duk ta daburce cikin lalube take son kama handle ɗin ƙofar amma tama kasa sai dibi-dibi take. Yanda take yi ɗin harga ALLAH ya bashi dariya, dan sai yi take kamar makauniya na laluben hanya. A hankali ya saki wani ɗan gajeren murmushi batare da ya daina abinda yake a laptop ɗin saman cinyarsa ba ya furta, “Awwal muje”. Murmushi shima Awwal ya saki cikin ƙunshe dariya. Harga ALLAH yana a cikin matukar farin ciki da yanda al'amarin nan ya kasance haka. Dan jin komai yake ma kamar wani mafarki ko almara gaskiya. To amma ikon ALLAH yafi gaban komai ai. Fara tafiyar motar ya saka Khadijah jin kamar ta fasa kuka. Idanunta cike da ƙwalla ta sake kallonsa a karo na biyu. “Dan ALLAH ku sauke ni zan koma ciki nayi mantuwa”. Kusan mintuna biyu kamar bazaice komai ba, ga Awwal kuma baida alamar tsayawa. Itako jikinta sai wani tsuma yake zuciyarta na duka kamar zata fito waje. “Wannan shine gaisuwa?”. Ya furta cikin sassanayar muryarsa mai cike da kamala da dattako batare da ya ɗauke idanunsa a laptop ɗin ba. Gaba ɗaya sai kunya ta lulluɓe Khadijah. Cikin sanyin jiki da jin bata ƙyautaba ta sake ƙasa da kanta. Ai koba komai basu cancanci haka a gareta ba kodan alkairin da suka taɓa mata a rayuwa, dan tun ganin Awwal shima yayan nasa ta ganesa. “Ina yinin ku”. Ta faɗa muryata na ɗan rawar jin kunya. Murmushi ya sake saki mai sanyi hankalinsa dai na ga aikinsa. Shiru bai amsa mata ba har tsawon wasu sakanni, kafin ya rufe laptop ɗin ya ɗago yana mai juyowa gareta. “Mi kika manta acan ɗin?” ya faɗa maimakon amsa mata gaisuwa. A hankali ta ce, “Abu ne!” Shima a hankalin ya furta, “Bashi da suna?”. Shiru ta gagara amsawa. Sai ya zubama yatsun hannunta da taketa faman cuɗawa ido, yanda ƙunshin yama hannun nata ƙyau a take yaji wani iri a ransa. Idanunsa ya kauda da sauri yana jan numfashi. Laptop ɗinsa ya sake buɗewa a can ƙasan maƙoshi yana furta, “Ki faɗi ko miye kika manta ɗin, in har ana saida shi za'a saya miki shi”. Yanzu kam jitai kamar ta tsilga a motar ma kawai ta hutama. Jikinta har wani yamm-yamm yake saboda yanda sautin muryarsa ke wani ratsa mata zuciya. Ga ƙamshin turarensa yay masifar addabarta kamar yanda shima nata ke matuƙar masa daɗi da sakashi a wani yanayi. Jin tai shiru ya sashi ɗan ɗagowa ya kalleta, sosai ta takure jikinta a jikin murfin. Kamar ance ta juyo itama karaf suka haɗa ido. Da sauri ta sake maida kanta. Murmushi kawai ya saki ya ɗauke nasa kan shima. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai sai shi da kan amsa waya lokaci-lokaci yana ta aiki a laptop har suka iso ƙofar gidan su Khadijah. Kafin ma Awwal ya gama kashe motar harta buɗe ta fita ita, “Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi” ta faɗa dai-dai lokacin da take ƙoƙarin rufe motar. Shi dai kallonta kawai yake dan ya fahimci burinta kawai tabar wajen ne, kafin kace mi ko harta faɗa gida cikin sassarfa da harɗewar ƙafafu. Kansa ya ɗan girgiza da sakin guntun murmushi kawai ya maida kansa ga laptop ɗin yana faɗin, “Awwal muje”. Cikin girmamawa Awwal dake ta jin daɗi kamar ya taka rawa ya ce, “To Yaya”. Wata ajiyar zuciya mai ƙarfi Khadijah dake jikin ƙofar soron tana leƙensu ta saki tana mai dafe ƙirjinta. Tama rasa wane kalar tunani zatayi akan al'amarin. Kenan mutumin nan daya taimaketa a randa ta baro Adamawa nada alaƙa da mazajen su Zuhrah. UBANGIJI kenan mai hikima. Ita tamayi zaton bazata sake ganinsu ba a rayuwarta har abada. Ashe akwai alaƙa a tsakani duk da dai bamai ƙarfi bace ba... Fara isowar motocin da suka kwaso ƴan dinner ya sata barin soron ta ƙarasa shiga cikin gidan itama... Tunda ƴan dinner suka dawo aketa labarin abinda ya faru a hall ɗin yau akan Khadijah da ogan anguna Abaan da kuma matashin saurayi mai suna Yassar. Kowa da yanda yake fassara al'amarin da kuma fatan da yake yi akai. Ita dai Khadijah ko kanzil batace ma kowa ba, ta kuma ji daɗin yanda babu wanda ma yasan ogan angunan ne ya kawota har gida. Bayan sun wuce gidan makwafciyarsu da zasu kwana Ni'ima ke cemata itafa sai taga kamar mutumin nan shine suka kawota ɗin nan dan Awwal bai ɓace mata ba. Shiru Khadijah tai mata taƙi ta tanka, dole Ni'imar ta ƙyaleta itama dai dan tasan halin auntyn nasu in bataso asan abu ba..... _______________★ Watanni shida kenan da faruwar komai daya buɗe sabon littafin babin rayuwa a garesu. Dan tun randa suka baro garin Kano bayan ƙarasa gundile igiyar aurensa da Khadijah komai ya sake kwaɓewa. Dafeeq bai sake tabbatar da yana son Khadijah haka da yawa ba sai a wannan lokaci. Dan ji yake tamkar bazai iya rayuwa babu yarinyar nan ba. Luff Kainaat ta masa tare da komawa gefe tana kwasar dariya. Dan duk yanda ta takalesa suyi faɗa baya tanka mata a lokacin nan saboda halin jiyyar zuciya da yake a ciki. A haka suka cinye wata ɗaya da dawowa. Anan ne fa hankalinta ya fara tashi dan babu abinda tafi buƙata sama da saki a yanzu. Saboda a lissafinta Abaan na gab da shigowa Nigeria ne bikin buɗe katafaren Companyn sa anan Adamawa, ita kuma bata fatan ya dawo ya sameta da auren wani a kanta. A yanzu kam ta tabbatar shiru bazai mata ba, dan haka ta ɗauki salon kissa. Tabbas mace mace ce in har taso nuna kanta a macen, dan kuwa a cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sanyaya yanayin Dafeeq ɗin ya ɗan rage yanayin ƙuncin da yake ciki akan rasa Khadijah . Cikin kissar ta fara hillatar sa da son karɓe takardun hannunsa da wayarta, sai dai fa anan ya nuna mata shima ɗin namiji yake. Dan tamkar ta farkar da shi a nannauyan barcin daya tafi ne na kwana biyu. Rikici suka fara a hankali game da hakan inda fa Kainaat taga lallaɓa Dafeeq bazai kaita ko ina ba sai ɓata mata lokaci, dan dama tana lallaɓashinne saboda bata son wasu mutanenta su san irin auren da tayi. Ƴan sanda tasa su kama Dafeeq, labari kuwa ya dawo masa. Hakan ya sashi tattara inasa-inasa da duk abubuwan nata daya sata ya bar garin Adamawa baki ɗaya. Sai wayar gari Kainaat tayi babu Dafeeq a gidan. Haukacewa kawai ya rage Kainaat tayi dan tashin hankali. Dan kuwa duk inda ake tunanin zaije ƴan sanda suka gama bincikawa babu shi babu dalilinsa. Kamar wasa ƙaramar magana ta nema zama babba. Dan kuwa dai har Kano Kainaat tazo neman Dafeeq tare da jami'an tsaron amma sun samu baima zo ba, sai ma birkice masu da mahaifiyarsa tayi akan Kainaat tasan ina ɗanta yake. Tayama za'ai su tafi tare sannan azo ace mata wai ana nemansa. Zance kamar waya ya zama babba. Dan kuwa komai ya juye akan Kainaat ne. Wasu abokan Dafeeq da Kainaat bata san dasu ba sun haɗe kai da Mamansa sun kai ƙara police station akan Kainaat ta sace Dafeeq. Case ɗin dole ya baka mamaki, dan tako ina an gagara fahimtar gaskiya, tunda babu wanda yaga sanda Dafeeq ya gudu. Tuni aka fara tuhumar Kainaat akan laifin kidnapping. Zo kaji yanda ƙananun magana ke tashi, ruɗewa yasa Kainaat kasa kare kanta. A cikin wannan harmutsin nasu har akai bikin buɗe Companyn Abaan batare data tuna ba, dan lokacin ma tana a hannun ƴan sanda. Sai da akayi da kusan sati biyu sai ga ƴan sanda wai sun gano inda Dafeeq yake a wani gida a kulle. Sai dai yace shi ba Kainaat bace ta saceshi wasu mutanene da bai sani ba. An wanke Kainaat daga laifin sannan Nadwa taje ta fiddo ta. Gaba ɗaya Kainaat ta gama fita a hayyacinta da tashin hankali, tsakaninta da Dafeeq sai kallan kallo. Bayan an kaisu asibiti an duba lafiyarsu aka sallamesu suka dawo gida. Suna shigowa Dafeeq ya fara dariyar shaƙiyanci. Cikin ɗage gira sama da kallonta sheƙeƙe ya ce, “Wannan kaɗanne daga makircin da Dafeeq zai iya shiryawa Hajiya Kainaat. Dan haka ya rage naki ki kama kanki, ki bani takardu salin alin na baki sakin ki ko kuma mutafi batch b dan inada plans daban-daban na makirci, idan kuma na ƙulleki a wani wlhy bazaki taɓa iya kwance kanki ba. Wannan ɗin ma nayi niyyar kwancekin ne shiyyasa kaka fito”. Ya ƙare maganar da kashe mata ido cike da salon iskanci. Mutuwar tsaye Kainaat tayi a wajen kawai, sai kuma ta rushe da kuka mai cin zuciya. Tabbas ta ɗakkoma kanta CUTA a rayuwarta, amma zata nuna masa itama shegiya ce. Tun daga ranar ta tattarashi ta ajiye gefe, bayan ta bincika cewar Abaan yazo an kammala bikin buɗe Companyn har ya koma taci kuka harda zazzaɓi. Dama dai wannan itace damarta, gashi ta kuɓuce mata, dole sai ta sake sabon plan kenan tunda ɗan iskan yaron nan ya wargaza mata komai. Salon gidan ya canja a watannin da suka cigaba da shuɗawa, kowa yana ƙullama ɗan uwansa ne, duk sanda ta masa batun ya saketa, Shiko zai mata batun ta bashi takardu idan tana buƙatar sakinta, shi bata gabansa takardun kawai yake buƙata. Takan ji kamar ta shake banza ya mutu kawai, sai dai tasan hakan ba abune bamai sauƙi ba dan Dafeeq shegen kansa ne. Dan kuwa duk yanda suke damben tsiyarnan hakan baya hana idan yaji buƙatarsa zuwa gareta ya nema hakkinsa. Haka zasu ci uban fitina su wajiga rayuwar juna ya kuma sami abinda yazo neman. Duk da abin nan bawai ita kaɗai ce a tashin hankali ba, shi kansa a cikin damuwar yake dan kullum kamar sake kunna masa wutar soyayyar Khadijah akeyi, a kuma biye yake da al'amarinta dan koda yaushe yana a hanyar Kano ne a watannin nan kamar mara aikin yi... *_WASHE GARI_* Alhamdullah yau an wayi gari safiyar ɗaurin aure. Amare sun sha ƙyau iya ƙyau kamar ka sacesu ka gudu. Hakama Khadijah duk da taƙi yarda dai ai mata kwalliya sam. Tadai saka kaya da sukai matuƙar amsar jikinta tai kwanciyarta dan ji take kamar ma zazzaɓi na neman rufeta. Ga ƙirjinta wani irin zutt-zutt yake mata batare data san dalilin hakan ba. Sai kawai ta dinga addu'a a zuciyarta har taji nutsuwa, sai dai jikinta duk babu wani ƙarfin kirki. Zuwa sha biyu layin nasu ya rage hayaniyar maza sai mata dake ta isowa da baƙi. Maza kam sun wuce massalaci sallar juma'a da ga can kuma za'a ɗauro auren... A massalaci ana idar da sallar juma'a aka fara ɗaure-ɗauren aurarraki. Dan bana su Ni'ima ɗin bane kawai za'ayi akwai wasu daban. Kusan aure bakwai aka ɗaura. Mijin Zuhrah shi ya fara kiranta ya sanar mata an ɗaura aurarrakin. Cikin sanyin jikin da aka san duk wata amarya a irin wannan lokacin ta sauke wayar a hankali hawaye na silalo mata. Daga ita har Ni'ima a jikin Khadijah dake zaune tsakkiyarsu suka kwanta suna kuka. Hakan ya sakata hawayen ita ma. A take falon ya ɗauki ihun ƙawayensu harda masu guɗa. Suna tsaka da wannan shaƙiyancin wa amaren biyu sai ga wata abokiyar wasan su Khadijahn da aka zo da ita daga kura. Kai tsaye inda Khadijah take ta nufa. Khadijah na lallashin su Zuhrah kawai taji ana mata wanka da turare tare da callara guɗa a kanta dake ratsa mata har tsakkiyar ƙwaƙwalwa........✍️ ___________ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da takwas_ ________________ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ _______________ .......Shiru falon yay kowa ya zubama aunty Kubra idanu dake ma Khadijah guɗa da zazzaga mata turare. “Aunty gafa amaren nan”. Wata Rumaisa ƙawar Ni'ima ta faɗa tana nuna su Zuhrah. Kai tsaye Aunty Kubra ta bata amsa da “Ai itama amaryar ce”. Kallon juna aka koma yi, yayinda Zuhrah da Ni'ima suka wani irin miƙewa daga jikin Khadijah a zabure. Khadijah kam kamar wadda ta suma a zaune idanu kawai ta zubama aunty Kubra kamar ta sami hoton bango. “Aunty Kubra kin san mi kike cewa kuwa? Aunty Khadijah ce amarya?”. “Kwarai ma kuwa, itama an ɗaura mata aure tare da ku. Ayyyiririrrrriiii!!!!!”. Ta sake sakin ghuɗa akan Khadijah da su Zuhrah gaba ɗaya. Dai-dai nan Inna Zulai ta shigo kiran amaren su duka. Ganin tace harda Khadijah yasa mutane suka fara gaskata zancen aunty Kubra da kowa ke tunanin tsokanar Khadijahn take da farko. Sake dabircewa Khadijah tai dan har tana neman faɗuwa sai da Inna Zulai ta riƙota tana faɗin, “Hankali mana Khadijah”. Bata iya cewa komai ba, sai rawa da jikinta ke cigaba dayi. A haka suka fito ƙofar gidan dake cike da maza ƴan ɗaurin aure. Yawanci duk dangi ne sai ƴan anguwa da abokan Baba. Anguna daga ɗaurin aure sun tafi walimar da suka shiryama kansu, sai anjima kaɗan zasu iso nan wajen saukar Alkur'anin da za'ayi mai haɗe da walima da islamiyyasu Khadijahn ta shirya musu. A ɗakin soro aka shiga dasu, inda Baba ke tare da shiƙiƙan ƴan uwansa harma da kawunai. Bayan an zaunar dasu suka gaishesu, sai dai Khadijah har yanzu da alama bata gama dawowa dai-dai ba. Nasiha kowa ya fara musu mai ratsa jiki, hakan ya sake rikita Khadijah ganin su dukansu kamar ana musu ishara da sabuwar rayuwar da suka shigan, tsabar yanda komai ke mata yawo ji take kamar tacema kawunan nasu itafa banda ita. Sai dai babu damar hakan dole ta nutsu har suka gama faɗansu da nasihar. Kiran sunanta da Kawu Bala yayi ne ya sa gabanta sake faɗuwa. Muryarta har rawa take wajen amsa masa da “Na'am Kawu”. “Matso nan kusa”. Matsawa tayi kamar yanda ya buƙata. Sake cemata yay ta ɗago fuskarta, anan ma babu musu tai yanda yace. Dukansu dake ɗakin ya nuna mata, murya a dake ya ce, “Miye matsayinmu a wajenki?”. Da rawar murya ta ce, “Iyayena”. “Kin tabbatar da wannan sunan mun cancancesa a gareki?”. Kanta ta jinjina musu hawaye na silalo mata a kumatu. “Alhamdullah” ya faɗa tare da cigaba da faɗin, “Munji daɗi da kika tabbatar da mu ɗin iyayenki ne. Dan haka a matsayinmu na iyayenki mun ɗaura miki aure kema a yau tare da ƴan uwanki. Kuma insha ALLAHU zakiyi alfahari da hakan da mukai miki. Ba kuma muyi haka dan ƙasƙantar da ke ba ko tauye miki hakki. A'a haka ALLAH ya ƙaddara wannan kuma ikonsa ne da tsarawarsa. Amma muma abin yazo mana ne a bazata. Dan kwata-kwata bai wuce sati biyu da suka shige zancen ya shigo ba, ba kuma muyi tunanin zai zama gaskiya ba sai a kwanakin satin nan da suka gabata. Mun ɓoye miki ne saboda gudun komawa ƴar gidan jiya. Muna fatan zaki kasance ƴa mai biyayya a wannan lokacin, dan in sha ALLAHU sai kinyi alfahari da wannan auren Khadijatul-Kair. ALLAH yay muku albarka. Ya baku zaman lafiya ku da mazajenku da zuri'a mai albarka. Ku zauna lafiya dan ALLAH kodan ku sake kwantarma mahaifinku da hankali kun daiga halin da ya shiga ciki a baya. To yanzu ku ya rage ku sakanka masa da ƙoƙarin sa gareku ta hanyar zama lafiya da mazajen aurenku kamar yanda kuka ga mahaifiyarku tana zaune da shi lafiya kunji. Aita haƙuri kuma, dan shi aure ba zaman nanaye bane da shargalle kamar yanda ku yaran zamani kuke kallo. Auren bautar UBANGIJI ne. Shi kuma bautar ALLAH sai da jajircewa ake yinta da tsafta sannan ai mata kwalliya da haƙuri sai a samu aljanna da ake fata.” Sosai Khadijah ke ƙoƙarin riƙe kukanta. Harga ALLAH gaba ɗaya ma ta gama ruɗewa da gigicewa. Itafa aka ɗaurama aure a yau. Ya arrahaman ya akai haka ta kasance? Rashin amsa yasata ƙara daurewa, dan tayi alƙawarin a wannan gaɓar, koda mijin nata zai kasance gurgu ne. Makaho ne. Zata zauna dashi kasancewar su iyayenta suka zaɓa mata shi. Kai koda ace ƙazami ne, ko da ace jahili ne. Kai koda ma ace yanada wani mummunan hali in har bazai sakata saɓama UBANGIJI ba, zata zauna da shi. Ta kuma san ma iyayenta bazasu taɓa aura mata wanda zai ɗorata a hanyar zuwa wutar jahannama ba. Nasiha sosai akai musu a ɗakin har iyayensu mata suma sun shigo suka ɗora nasu kafin a fito dasu saboda kiran sallar la'asar. Cikin gida aka shiga dasu wajen Mama. Kasa daurewa Khadijah tayi ta faɗa jikinta tana hawaye mara sauti. Rungumeta kawai mama tai batace komai ba. Dan harga ALLAH tana tausayin ƴar tata. Amma tana mata fatan alkairi a wannan auren. Suma su Ni'ima jikin Maman suka shige suna kuka. Hakan yasa dangi abokan wasa sukai musu caa da sheri wasu na karesu.... Bayan idar da sallar la'asar duk aka ɗunguma babbar harabar islamiyyar su da za'ayi taron. Komai an gama shiryawa manyan baƙi kuma duk sun iso dama sallar dai ake buƙatar fara gabatarwa sannan. Zaman amare da aka sakema shiga cikin dogayen rigunan abaya farare da adon golden da mintuna kaɗan tawagar anguna ta iso wajen. Nan take wajen ya ƙara cika taf. Sauka aka fara gabatarwa, inda komai ya tafi a cikin tsari da birgewa. Yayinda bakunan anguna ya kasa rufuwa. Sai dai babu wanda yasan wanene angon Khadijah har zuwa yanzu idan ka cire iyayenta maza. Sun sami ƙyaututtuka da suka bada mamaki musamman wanda suka fito da ga ogan abokan ango Abaan Omar Modibbo. Dan kuwa mukullayen motoci har uku ƙanana dai amma masu ƙyau da ɗaukar hankali ya bama amaren su duka ukun dan sun birgesa matuƙa. Bayan wannan ma wasu ƙyaututtukan sun biyo baya dan islamiyyar sun gayyaci manyan mutane sosai, hatta da su Baba Hakimi da suka taso tun daga Adamawa basu wuceba suma sun tsaya domin saukar, kafin a fara gudanar da lectures masu ratsa jiki ga anguna da amare. Har zuwa yanzu bawai Khadijah ta fita a ɗimuwar da take ciki bane ba. Dauriya kawai take da son tilasta kanta zama a dake, amma duk da haka jikinta zazzaɓi ne mai zafi sosai dan tunda suka zauna a wajen ma kanta na a kafaɗar Ni'ima kasancewar duk sanda ya ɗago sai ta kama ogan anguna da ake kira Alhaji Abaan Modibbo na kallonta, sai ta daina ɗagowar har sai da aka kirasu wajen sauka. Suna dawowa bayan an kammala ma dai kwance take shiru a jikin Zuhrah data koma kusa da ita a yanzun. Sauka ta ƙyatar sosai. Ansha hotuna kamar babu gobe. Anan ne ma dai mutane suka fara tsarguwa da hasashen wanda kowa kema kallon angon Khadijah ganin duk sanda za'ai hoto yana a kusa da ita ne, amma kuma basu da tabbas har aka tashi gab da magrib. Bayan sallar isha'i akai shirin miƙa amare ɗakunansu. Sai dai kuma banda Khadijah. Ayanzu ne fa sukai asalin kukan rabuwa. Dan da ƙyar aka raba su Ni'ima da ga jikin Mama da Khadijah. Da aka kaisu yima Baba sallama ma nan ma ansha ɗan ƙaramin bidiri kafin. Har ƴan kai amarya suka je suka dawo Khadijah na kwance a ɗaki zazzaɓi yay mata rijif. Koda mama ta bata magani ma fakar idonta tai ta ajiye ta koma ta kwanta. Anata sam barka da gidajen amare. Abin farin ciki kuma suna a jere da juna ne komai nasu kuma iri ɗaya kamar wanda suka aura tagwaye. Koda yake Ibrahim da Adams kowa na iya kallonsu da tagwaye saboda shaƙuwarsu da ƙaunar fa sukema juna. To sai muce ALLAH ya sanya alkairi ya kuma basu zaman lafiya mai ɗorewa.... *_WASHE GARI_* Duk da yanda Khadijah ta tashi a yanayin rashin lafiya Baba ya tabbatar da yau za'a wuce da ita nata ɗakin mijin. Dan kuwa ya tabbatar da ƴan uwan ango da motocin ɗaukar amarya tun jiya suna Kano yau kuma zasu wuce da ita. Dan haka ƙarfe goma duk wanda zai rakkiyar Khadijah ya shirya tsaff. Dan motocin har sun iso tare da masu amsar amarya. An musu tarba ta mutuntawa kamar yanda suma suka shigo da dattakonsu. Matane guda biyar sai abokan ango da galla-gallan motoci har kusan ashirin. Al'amarin ya bama kowa mamaki daya kawo maganganu suka fara tashi a anguwa. Kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Ƴan ɗaukar amarya ke sanar da amarya ita a jirgi zata wuce tare da mutum biyu, dan haka motocin da suka ɗauki dangi tuni sun ɗauki hanyar Abuja. Bayan kammala shirya Khadijah dake ta faman kwasar kuka aka kaita ga baba. Sai da ya sanya mata albarka tare da nasiha mai ratsa jiki da addu'a kamar yanda yayma ƴan uwanta jiya sannan ya ɗora da faɗin, “Naso ace na baki damar zaɓar Miji da kanki Khadijah domin ki tabbatar da na huce na kuma yafe miki. Sai dai tsarin UBANGIJI ya banbanta ne dana kowa. Amma in sha ALLAHU idan kikayi haƙuri a yanzun ma zakiyi farin ciki fiye da zaɓin da zaki iyama kanki. Dan mutumin nan mutumin kirki ne da tabbas aurenki da shi wata hikima ce ta UBANGIJI. Naso na faɗa miki dukkan yanda al'amarin ya kasance haka. Sai dai ya roƙi alfarmar na barsa ya sanar miki da kansa. Dan haka dan ALLAH ina roƙonki kije kuyi haƙuri a gidan aurenki Khadijah. Kima mijinki biyayya, ki ƙyautatama ƴan uwansa da maƙotanki. Ki manta da abinda ya faru baya sunansa ƙaddara. Ita kuma ƙaddara ai babu mai iya tsallaketa. ALLAH yay miki albarka ke da sauran ƴan uwanki”. A tare aka amsa da Amin. Yayinda Khadijah ta sake fashewa da kuka da faɗin, “Baba in sha ALLAHU zan kasance mai biyayya a gare ku. Kuma dan ALLAH ku yafe min ku yafe min. In sha ALLAH zan tabbatar muku da ni ɗin ɗiyace tagari akan wannan auren”. “Mun yafe miki tuni Khadijah. Fatanmu dai ki bama mara sa ɗa kunya kawai. Ki zauna lafiya ki kuma ringumi sabuwar rayuwarki ta yanzu da hannu biyu da kuma haƙuri”. “In sha ALLAHU Baba”. Sauran ƴan uwa sun sake mata nasiha sannan aka fito da ita zuwa motar da zata kaisu airport ɗin ita da wasu dangin angon 2 da aka bari, sai Inna Zulai da Gwaggo Safina da zasu mata rakkiyar suma. Har suka isa airport kuka sosai Khadijah keyi Inna Zulai dai na lallashinta. Sun ɗan yi zama saboda kai kawo da jiran lokacin daya rage dan sai 12:30 jirginsu ya ɗaga. Khadijah ta sake hawa jirgi a karo na biyu. Yayinda su Gwaggo Safina ya kasance musu na farko. Cikin mintuna ƙalilan suka iso Abuja. Anan ma sun tarar da motoci na jiransu har guda biyu. Ɗaya Khadijah da iyayenta suka shiga. Ɗayar kuma ƴan uwan ango biyu dake tare da su ne. Khadijah dai na kwance jikin Inna Zulai har suka iso inda taji suna faman santi ƙasa-ƙasa, duk da dai dama tunda suka fito airport bakinsu bai huta ba sai faman ƙus-ƙus sukeyi. Tun daga gate su Gwaggo Safina suka sake tabbatar da ƴarsu Khadijah ta sake shiga cikin zuri'ar fulani kamar dai mijinta Dafeeq na farko. Banbancin kawai shi Dafeeq sun jima a birni a yanzu ko fillancin ma babu maiji a iyayensa. Suko wannan sunata yara yarensu a baki tabbacin basu bar gida ba. Tarba akai musu ta girmamawa da mutuntawa. Yayinda suma suka nuna nasu dattakon. Dan duk da an nuna musu sashen amarya basu yarda sun nufi can da ita ba suka buƙaci a kaisu sashen mahaifiyarsa tunda ance suna tare ne a gida ɗaya. Aiko sunji daɗin wannan ƙarancin. An fara kai Khadijah wajen surukata. Katafaren falo na gani na faɗa da yaji kayan more rayuwa kamar ba'asan ciwon kuɗi ba. Kai tsaye suka gane wacece mahaifiyar angon. Dan dai-dai Khadijah da fuskarta ke lulluɓe da mayafin da aka rufa mata na kaiwa duƙe kamilalliyar dattijuwar matar dake zaune cikin kujera 2sitter ta kamo hannunta ta zaunar a kujerar kusa da ita tare da rungumeta. Ta tsufa kam, sai dai ba wani tsufa ba irin na takwarkwashewa. Dan akwai jin daɗi sosai tattare da ita. Kasa daurewa Khadijah tai ta zamo ƙasa kusa da ƙafafunta ta zauna. Hakan datai ya sake birge ƴan uwan ango dama mahaifiyarsa sosai..........✍️ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na ashirin da tara_ ______________ Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846 Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria Ummu khalifa 01017018846 _______________ ......Sunyi zama na kusan mintuna ashirin an gaggasa da ƙyau kafin ai musu rakkiya inda akace sashen amarya. Ai su Gwaggo Safina ma sai suka gagara cewa komai ganin daular duniya. Salla sukai zaman gabatarwa yayinda Khadijah ta kwanta dan zazzaɓi ne sosai a jikinta. Zuwa yanzu ma har ɗan rawar sanyi take yi. Amma tanata ƙoƙarin daurewa ta kuma ƙi sanarma kowa har sauran mutanen da suka taho a mota suka samu isowa. Anan fa gida ya sake ɗaukar harama. Ga tarin abinci iri-iri an kawo musu al'amarin dai sai sambarka kam. Aunty Firdausi ce ta fahimci Khadijah babu lafiya. Dan an zuba mata abinci tace ta ƙoshi. Tsoffin iyayenta suka mata caa da faɗa wai tana abu ita ba budurwa ba. Ya kamata ace ta haƙura haka ta kuma godema UBANGIJI da wannan ni'ima da yay mata. Taso matan da sukai ya tilastata yin lauma ɗaya ta abincin sai ga amai. A sannan ne Aunty Firdausi data kawo mata ɗauki taji jikinta da zafi sosai shine ta ke sanar musu bama ta da lafiya. Duk kuma sai jikinsu yay sanyi suka shiga mata sannu da jera mata kalaman lallashi. Dole wanka ta samu tayi da ruwa mai zafi ta canja kaya. Sai kuma aka shiga tunanin ina za'a samo magani, gashi su ba gama wayar ango sukai ba balle a nemosa ace amarya babu lafiya. Da kunya kuma aje wajen mahaifiyarsa daga zuwa ace mata amarya babu lafiya. Dole suka haƙura har zuwa yamma da aketa shirye-shiryen Fulani event ɗin da suka shirya zasuyi anan harabar gidan. Dan har an gama tsara ko'ina da adon fulani ma. Ana idar da sallar magrib aka kawo kayan da amarya zata saka itama. Sosai kayan sukaima Khadijah ƙyau tamkar ka saceta. Ga shi itama kuma ALLAH ya azurtata da gashi, dan har Aunty Firdausi na tsokanarta da ai da ansan zasuyi wannan wasan da an mata kitson fulanin itama tunda dai ta alaƙantu da su ta fannin uwa. Dariya wanda ke ɗakin sukayi kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Ita dai Khadijah bata tanka musu ba dan takanta take. Ga zazzaɓi ga fargabar tunanin kowane irin miji kuma zata tarar a yanzu. Shin shima irin Dafeeq ne ko yamafi Dafeeq abubuwan mamaki. Dan itakam a yanzu bata jin bayan mahaifinta al'amarin wani namiji na birgeta a wannan rayuwar. Kawai dai ayi sha'ani ne. Sai da aka yafa mata gyale aka rufe mata fuska sannan suka fito. Duk da ba ganin fuskarta akeba sai ambaton masha ALLAH dangin ango keyi ganin yanda kayan sukai matuƙar zama a jikin amaryar tasu. An zaunar da itane kusa da surukarta daketa faman jin daɗin sake ganin wannan rana da ranta, ta riƙe hannunta cikin nata. Zafi taji sosai da ya sakata ambaton “Ya Salam daughter baki da lafiya ne haka amma baku faɗa ba?”. Kasa cewa komai Khadijah tai, dan duk da bataga fuskar matar ba har yanzu wani kalar kwarjini da girmanta take ji cikin ranta. Jikinta ta ɗan saka Khadijahn tare da kiran wata ƙyaƙyƙyawar matashiya mai tsananin kamanni da ita. Gabansu ta tsugunna tana murmushi da dafa ƙafarsu su duka biyun, sai kuma ta ɗaga gyalen zata leƙa Khadijah. Harararta Mamy tayi da buge mata hannu. Tai ƴar dariya da faɗin, “Kai Mamy na ƙagarane fa naga amaryan Hamma”. “To bazaki gani ba”. Mamy ta faɗa tana hararta. Hannu ta ɗaga alamar surrender tana murmushi. “Shike nan na haƙura Mamy, amma kamar jikinta da zafi.” “Eh shine dalilin da yasa ma na kiraki nan ai. Yayanki basu iso ba har yanzu, inaga kiyi magana da Yafendo ayi komai a takaice Dota ta koma ciki, sannan ki nema min number doctor”. “Okay Mamy”. Ta faɗa tana miƙewa. Kamar jira tashinta babu jimawa aka wangale gate. Motace ta shigo, rashin wadatacce fili kasancewar sun mamaye harabar gidan yasa sukai parking can nesa. Kowa yasan ango ne ya iso, dan can Kano suka barsa sai yanzu yake isowa. Jirgin ƙarfe bakwai suka biyo alhmdllh kuma gashi har sun iso. Driver da yaje ɗaukarsu ne ya fara fitowa. Sai Awwal dake gefensa shima ya fito. Shiko yana baya bayansa jingine da kujera idanunsa a lumshe. A kallo ɗaya zaka fahimci a gajiye yake. Dan koda driver ya buɗe masa motar ya ɓata kusan minti ɗaya kafin ya fito. Cikin rashin hayaniyar nan tasa yacema drivern “Thanks you Baba. Mun hanaka barci ko”. Murmushi Baba yay da faɗin, “A haba Alhaji ai yima kaine. Sannunku da zuwa dai, ALLAH kuma ya sanya alkairi a cikin wannan aure. Yasa yanda muka taru anan baɗi i war haka muna nan muna shagalin suna kuma”. Awwal ne ya amsa da amin yana ƙumshe dariya. Shiko ya ɗan murmusa kawai batare da yace komai ba sai dai a zuciyarsa ya amsa da Amin. Dan sosai yake son yara shima, kawai dai ana ganin kamar bai damu bane saboda bai cika yawan furtawa ba. Idanunsa ya kai inda ake taron, hankalin wasu duk na garesu ne, yayinda wasu kuma ke hidimarsu batare da sun farga da su ba. Tunanin ta yanda zai shige sashensa batare da wani ya tsaida shi ba yake. Sai dai bai kai ga samo mafitarba ma ƴan uwa suka fara zagayesa ana masa sannu da zuwa da jera masa kirarin ango ango kasha ƙamshi. Kamar yanda ya saba ne, murmushi kawai yake musu a taƙaice. Ganin suna neman cika wajen ya zare jikinsa ya gudu ta baya zuwa sashensa dake manne dana amarya. Sai dai da yake akwai ƙofa ta gaba da baya da basai dole yabi ta cikin falon Khadijahn ba yasa zaka iya ɗauka ma daban-daban ne. Shigewarsa babu jimawa Mammy tasa aka maida Khadijah ciki dan rawar sanyi take yi. An cigaba da gudanar da shagali Noor kuma taje ta sanar ma Yayanta amarya bata da lafiya a kira Doctor. Fitowarsa kenan daga wanka sallamarta ya sashi zira jallabiyya ya fito falon. Agogo ya ɗan kalla sai kuma ya dubi ƙanwar tasa ɗaya tilo a duniya. “Amma miyasa tun ɗazun k baki kirashi, yanzu fa kusan 10 ake tafiya. Sannan kun zo da ita a wannan sanyin ita da bata da lafiya kuma”. “Sorry Hamma Ab. Ai ba'asan bata da lafiya bane fa sai yanzu Mamy ta gane. Kuma yanzu haka ma an maidata ciki. Na kuma kira Doctor ɗin bai ɗauka bane maybe baya kusa”. Baice komai ba face ƙoƙarin sarrafa wayar hannunsa da ya ɗauka. Inda ya fito ya koma yana kai wayar kunnesa da yima Noor alamar taje kawai... Noor na zaune a bakin gadon da Khadijah ke kwance ƙudundune cikin bargo kiran Yayanta ya shigo mata. Tana ɗauka umarnin kawo Khadijah kawai ya bata sashensa ya yanke kiran. Koda ta sanarma su Aunty Firdausi cewar Hammanta yace ta raka Khadijah likita yazo babu wanda yay yinƙurin hanata. Sai ma sake birgesu da take dan Noor akwai surutu, tun ɗazun hira take musu abinta kamar wata ƙaramar yarinya. Khadijah ce ma taso taɗan turje Inna Zulai ta fara mata faɗa, dole ta miƙe Noor ɗin ta kama mata hannu suka fice tana tafiya cikin ƙarfin hali dan jikinta sai rawar sanyi take. A hankali ya ɗago idanunsa dake kan tv yana sauraren hirar da doctor ke masa ya zubama ƙofar tare da amsa sallamar Noor akan lips. Khadijah da ke tafiya a hankali ya zubama idanu har suka iso gabansa, sosai tai masa ƙyau a cikin kayan fulanin dan ma akwai mayafi jikinta. Kai tsaye Noor ta zaunar da ita a kujerar 1sitter da ke gefensa na dama. Itako da dama da rabin fuskarta gyale ya rufe bata yarda tama kalli ko ina ba sai sassanyan ƙamshin turaren wuta dana fresheners dana jikinsa harma dana doctor ke rige-rigen shigar mata hanci. Noor na zaunar da ita ta naɗe ƙafafunta zuwa saman kujerar ta wani irin dunƙule waje ɗaya kamar ƴar mage. Wani irin fisgarsa yanayin nata ke yi, amma sai ya dake tamkar babu komai tattare da shi yama ɗauke kansa ya maida ga television. Doctor ne ya taso inda take yana jera mata sannu. Kanta kawai ta gyaɗa masa tana ƙoƙarin rufe ƙafarta da ƙyau da mayafin jikin nata. Tambaya doctor ya fara mata tana bashi amsa, yanayi yana ɗan rubutu harya kammala. Dubansa ya kai ga Abaan ɗin cikin girmamawa ya ce, “Sir tana buƙatar abinci haka mai ɗan ruwa-ruwa dan akwai yunwa tare da ita. Sai kuma ƴar damuwa nake gani da malleria haka. Taci wani abun ɗin sai tasha magungunan nan a kuma mata wannan allurar in sha ALLAHU zuwa safiya zata ware”. Cike da gamsuwa Abaan ya dubi Noor. “Ki sama mata tea”. Amsa masa tai da “To Hamma” tana nufar ƙofar fita. Babu jimawa sai gata da kofin tea daketa turiri. Yanda ta fita ta barsu haka ta dawo ta samesu musamman ma Khadijah dake cure a cikin kujera. Tea ɗin ta miƙama masa tana danne dariya, ya ɗan zuba mata ido tamkar bai gane mi take nufi ba. A ɗan shagwaɓe ta ce, “Hamma zanje na kawo maka abinci ne kaima fa in ji Mamy”. Amsar kofin yay da bata amsa a taƙaice. “No ni am ok bazanci komai ba”. “Amma Hamma Mamy zatai faɗa, bari dai ko madara mai zafi na amso maka”. Tai maganar tana ficewa wuff batare da jiran amsarshi ba. Kansa kawai ya ɗan girgiza dan shi kam bai san randa Noor zatayi hankali ba kuma. Da'ace ALLAH baima mijinta rasuwa ba da yanzu ƙilama tanada ya ra biyu itama. Ture lamarin Noor yay gefe yana mai maida hankalinsa kan Khadijah, dai-dai nan shima doctor ya miƙe tare da masa sallama ya wuce. Cikin alamun gajiya dake tattare da shi ya maida hankalinsa ga Khadijah bayan fitar doctor. Kamar wanda baya son yin magana ya furta, “Zaki iya tasowa nan?”. Jitai kamar ta sharesa, amma kuma sai ta dai kaɗa masa kai saboda tuno nasihar Baba, sannan shi a karan kansa yana da wani girma da kima da hatta a cikin muryarsa zaka iya jin hakan. Dan haka ta miƙe a hankali bayan kamar minti ɗaya. Yanda take ɗan yin kamar layi ya sashi kai hannu ya riƙo nata hannun. Sosai zafin zazzaɓin jikinta ya ratsa nashi hannun har sai da ya ɗan yamutsa fuska. Itako jitai tana neman daburcewa, domin kuwa ta sama ranta wani abu daban akan maza. A gefensa ya zaunar da ita kusa da shi gab dan a 2sitter yake zaune. Da sauri ta ɗan matsar da jikinta tana sake naɗewa gefe sosai dan sanyi take ji, shima kuma ya shaida hakan saboda rawar sanyi da take kaɗan-kaɗan. Idanu ya ɗan zuba mata na kusan sakan ashirin, kafin ya janye a kasalance tare da kai hannu ya ja mayafin ta dake rufe da fuskarta ruff zuwa ƙasa. Kaɗan ya ɗan duƙo gareta yana miƙa mata kofin shayin. Sai hakan ya basu damar samun kusanci da juna, har kowa na iya jin ƙamshin turaren ɗan uwansa sosai. Sosai ta wani rumtse idanunta da yamutse fuska kamar mai shirin sakin kuka ta yanda har shi sai da ya zubama black beauty face ɗin nata ido sosai. “Sorry, ki daure kisha shayin ko kaɗanne sai ki sha maganin”. Kanta ta girgiza masa hawayen da take riƙewa tun ɗazun na rige-rigen silalowa. “Uhhm-Uhmm! Shi dama kukan kai amarya baya ƙarewa?”. Ya faɗa a hankali cikin tausasawa da ƴar tsokana. Baki ta ɗan tura kaɗan da ƙoƙarin jan mayafinta zata sake rufe fuskar. Hannunta ya riƙe shima yana ɗan murmushi, a hankali ya sake furta, “Pleasseee!”. Yamutsawa tsigar jikinta tai saboda yanda ya kirayi Please ɗin a wani can ƙasan maƙoshi tamkar mai raɗa ko yaro da ke jin ɗan shwagwaɓan nan nason yima Mamansa wayo ta bashi abu. Bata da zaɓin daya wuce amsa kawai, dan ji take wani abu na mata kai-kawo acikin hannunta daya riƙe. Hannun nata ya saki tare da sake jan gyalan saman kafaɗarta sannan ya ɗan matsar da jikinsa yanda yake da ya zauna da ƙyau. Saboda ya bata damar shan shayin sai ma ya maida hankalinsa ga tv. Karo na farko ta ɗan saci kallonsa, ganin ba ita yake kallo ba takai kofin bakinta dan gaskiyar Doctor ne yunwa take ji. Rabonta da abincin kwarai tun jiya da safe a gida kano.........✍️ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin_ ____________ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ________ ......Kurɓarta kusan uku ta fara jin yunƙurin amai. Ita dama zazzaɓinta kenan. Bata son abinci, dan ko an takurata taci zata iya amansa. Da sauri ya amshe mug ɗin tare da riƙota. A bazata, matuƙar bazata ta jita a jikinsa hannunsa saman bayanta yana shafa mata kamar yanda akanma yara idan ana son lallashinsu. Wani irin yuuu ta sake ji saboda tasowar aman da shaƙar ƙamshin turarensa. Jikinta taja da sauri tana toshe bakinta da hannu, kafin ma yay wani yinƙuri ta dire ƙasa. Ƙofar da ta gani a falon kawai ta nufa da gudu fatanta kawai ace bayi ne a wajen. Takoyi sa'ar hakan, dan kuwa ƙaramin toilet ne dake tsaf-tsaf yana ƙamshi alamar ana kula da shi yanda ya kamata. Bama wani aman kirki tayi ba saboda babu komai a cikin nata sai shayin nan da ɗan malt.. da Gwaggo Safina ta matsa mata tasha sanda suka iso. Yanda take yunƙurin aman ya haddasa mata rashin ƙwarin jiki. Daga duƙen da take ta dinga jin kamar juwa zata kwasheta, baya tai da nufin jingina da bango taji an riƙota. Bata da zaɓin daya wuce kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke numfashi guda-guda. A hankali cikin nuna damuwa da yanayin nata ya furta, “Sannu! Kin gama”. Kanta ta ɗan ɗaga masa tana lumshe idanunta. Sosai jikinta ya sake ɗaukar zafi. Taimaka mata yay ta wanke bakinta, a bazata kawai taji ya ɗauketa gaba ɗayanta. Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta maidasu da sauri ta rumtse sakamakon haɗa ido da sukai da shi. Bata sake gigin buɗe idonta ba sai da taji ya direta akan wani lallausan abu, ga sanyi da wani irin ƙamshi mai shegen daɗi na ratsata. Kaɗan ta buɗe idon tana dunƙule jikinta waje guda. Gado ne babba da yaji shimfiɗu na alfarma, sai dai rashin yawaitar hasken ɗakin yasa bata iya tantance sauran abinda ke cikinsa ba. Dan shi kansa ba wani ganinsa take sosai ba da ƙyau. Jin ya yafa mata ƙaton blanket ɗin gadon mai shegen laushi ta sauke ajiyar zuciyar da har sai da yaji sautin hakan. Baice komai ba yaje ya kashe ac ɗin gaba ɗaya. Wani ƙaramin freight dake a ɗakin ya nufa. Madara ya ɗako mara sanyi sosai da ruwa ya dawo bakin gadon ya ajiye, sai kuma ya sake fita a ɗakin babu jimawa sai gashi ya dawo da tarkacen maganin da doctor ya bada da allura da zai mata da kansa dan ya iya. Zama yay a bakin gadon saitin cikinta har tana iya jin kamar ya jingina da jikinta kaɗan, dan haka ta sake ɗan takurewa waje guda a cikin bargon. Allurar ya haɗa sannan ya yaye bargon batare da yayi magana ba ya ɗaga farar rigar ƙasan ta fulanin dake sama kaɗan, ya kuma zama zanin shima. Wani irin dukan uku-uku zuciyarta keyi amma ta dake da son tabbatar da abinda zai yi. Jin shigar allura jikinta yasata rumtse ido sosai, dan akwai ɗan zafi kaɗan. Shi da kansa ya murza mata wajen dan haka ta kasa buɗe idanunta har ya ɗagota ya zaunar. Madarar nan ya saka mata a baki cikin lallashi ya ce, “Daure kisha kaɗan sai kisha maganin”. Sam bata so, amma girmansa da yanda ya cika mata ido ya hanata iya masa musu. Haka ta daure ta ɗan sha kusan kwata ɗin robar sannan ta kauda kanta. Baice mata komaiba ya ajiye ya bata maganin. Tana gama sha kanta a ƙasa muryarta na rawa ta ce, “Bara na koma can kar su Gwaggo suga na daɗe”. Idanu ya ɗan zuba mata kamar bazaice komai ba, har sai da ta tsargu ta ɗago ta kallesa. Maidawa tai da sauri cikin dabircewa. Ɗauke nasa shima yay tare da miƙewa ya kauda kayan maganin daga gaban gadon sannan ya dawo inda take. Batare da yayi magana ba ya kamata ya kwantar a hankali, blanket ɗin yaja ya rufa mata zuwa ƙirji, sai kuma ya ɗan zuba ma fuskarta datai takwaf-takwaf kamar zatayi kuka ido. Kamar mai raɗa ya furta, “Miyasa baki son nan ɗin?”. Kamar mai jira da rawar murya tai saurin faɗin, “Su Gwaggo duk suna nan fa. Kuma ance musu kawai zanga doctor ne na koma kaga babu daɗi suji shiru ko?”. Yanda ta ƙare maganar cikin sigar tambaya ya sashi sakin ɗan murmushi, sai kuma ya saki bargon dake cikin hannunsa har yanzu ya ɗan shafo black beauty face ɗinta mai santsi da laushi. Rumtse idanunta tai da sauri tsigar jikinta na wani irin tashi. Hannunsa na akan fuskar batare da ya janye ba ya ɗan ƙara duƙowa kanta sosai har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskar tata. “Su Gwaggo bazasu taɓa jin rashin daɗi ba sai dai ma suji farin cikin kwananki a nan tare da mijinki, in dai nine ki kwantar da hankalinki zan baki isashen lokaci na hutawa, sai dai ba hakan na nufin bazan iya canja shawara ba okay”. Ya ƙare maganar da ɗan bubbuga kumatunta kaɗan ya miƙe daga ranƙwafar da yay a kanta. Da kallo ta bisa zuciyarta na wani kalar tsitstsinkewa, sam tama kasa fahimtar kalamansa na ƙarshe balle gane ina suka dosa. Bayi ya shiga, babu jimawa sosai sai gashi ya fito. Ya shimfiɗa sallaya tare da daidaita tsaiwarsa ya kabbara salla. Ajiyar zuciya ta ɗan saki kaɗan tana gyara kwanciyarta, a haka barcin dake rinjayar idanunta yaci galaba a kanta. Can cikin barci sama-sama taji hawowarsa gadon, bargon ya gyara ya shiga, tana ɗan jiyosa sama-sama yana addu'ar barci, harya kammala ya shafa mata itama sannan ya kwanta a gefe yabar ƴar tazara a tsakaninsu. Daga haka bata sake jin motsinsa ba barci mai nauyi yay sake sureta..... _____________★ Abin duniya ya gama dabaibaye Kainaat, ta rasa ta inama zata ɓulloma mayen yaron nan daya zame mata akwatin maciji. Tayi haukan, tayi kissar, tayi lalashin amma kamar tana ma ƙaramasa ƙarfi ne. Har sallamarsa tai daga Company aiki amma ya tabbatar mata bata isaba. Idan kuma ta dage to wlhy zai tona mata asiri wajen staffs dinta game da aurensu. Kainaat mace ce mai son girma, sannan tana da son adana sirrinta ga na ƙasa da ita shiyyasa ta kasance mai matuƙar taka tsantsan. Hakan yasa ta janye maganar sallamarsa dan sam bata buƙatar abinda zai zubda mata daraja a wajen staffs nata. Sai dai ta sake kasawa ta tsare akan komai na Companyn ta yanda Dafeeq bazai iya mata suruf bahana ba. A tare kullum suke zuwa aiki su kuma dawo tare, dan sun adana matsalarsu a iya gidansu batare da wani a gefe ya sani ba idan ka cire Nadwa da Kainaat kan sanar mata domin ta bata shawara. Sai dai ma kamar Dafeeq ɗin na gani har hanji ne, dan duk shawarar da Nadwan ta bata sai ya wargazata. Yauma kamar kullum a tare suka baro office ɗin. Dafeeq ne ke tuƙi ita kuma tana gefensa tana danna sabuwar wayar data saya, tuni ta maido komai nata na waccan tsohuwar wayar dake a hannunsa anan. Ta kuma sami nasarar dawo da kuɗaɗenta na bank da Dafeeq ya kwashe ta hanyar wani ɗan uwan su Nadwa Manager ɗin bank ɗin da kuɗin ke a ciki. Dan sun kai report bisa shawarar Nadwa akan cewar ɓarayine suka sace mata bag. Sa'ar da aka samu shi Dafeeq bai kwashe kuɗin daga account nashi ba. Baifi kwana uku kenan da dawowar kuɗin ba, sunci uban faɗa kuwa dan harda marinta yay ta rama. A yau ne ma suka ɗan shirya har suka nufi office ɗin tare. Dafeeq kuwa ya sakko ne saboda wani shiri da yake ƙullama zuciyarsa, yayinda ita kuma ke faman masa shan ƙamshi. Kallonta ya ɗan yi yana mai sakin murmushi, sai kuma ya sake damƙe steering da ƙyau tare da maida idonsa ga titi yana faɗin, “Dan ALLAH bamu birgeki ba, jibemu shar damu kamar ka sace ka gudu. Hajjaju mu kauda wannan abubuwan mu zauna lafiya mana Please”. Shiru kamar Kainaat bazata kulashi ba sai kuma ta ɗan ɗago ta kallesa. Ganin hankalinsa na akan hanya ta maida kanta ga wayarta da faɗin, “Wani abun kake shiryawa kenan?”. “Oh oh, ke shikenan baza'ai zaman lafiya ba sai ana shirya wani abu. Hajjaju karfa ki manta soyayya ce ta haɗamu, kece kuma kika fara min tayinta, sai da na zurma sosai kike neman mani illa kuma”. “Oh saboda ni na fara maka tayinta shine ka amsa da manufa?.” “Ko ɗaya baki canka dai-dai ba. Da zuciya ɗaya na amshi soyayyarki, tunda ke shaidace saboda ke na rabu da matata da nake tsananin so da ƙauna. Idan ma kina faɗin hakane saboda kwashe kuɗinki na banki da takardu ni nayi duk wannan ne saboda gano kece kika aureni da manufar rabuwa da ni bayan cikar kwana bakwai. Haba hajjaju, wane sakaraine zai sami zuƙeƙiyar mace irinki ya saki. Da ace tun farko kin sanrmin auren kisan wuta zakiyi bazamu kai ga wannan matsalar ba, amma kika shirya mun rufa-rufa. Ni kuma shiyyasa na kwashe kuɗi da takardun Companyn danna ɗaureki. Nasan dai suna hannuna bazaki taɓa rabuwar dani ba zaki ce saina baki”. Tsaff kalamansa suka tsaru akan Kainaat, dan kamar wadda jikinta yay sanyi ta ɗago tana kallonsa. A bazata yaji ta furta “Yanzu a ina kaji wannan zancen haka Dafeeq?”. Murmushi yayi mai bayyana haƙora, sai kuma ya ɗan kalleta da faɗin, “Zancen duniya ai baya ɓuya Hajjaju. Amma karki damu in dai nine ban ɗauka da zafi ba duk da da farko naji haushi. Amma yanzu na yafe miki. Fatana kawai shine ki janye ƙudirinki nima zan janye nawa harma na baki sauran takardun hannun nawa. Amma zan baki lokaci kiyi tunani dai”. Kai kawai ta jinjina masa zuciyarta na wani irin rawa kamar zata faɗo. Amma batace da shi komai ba ta fita a motar dan sun riga sunzo gida. Da kallo ya bita yana wani cije lips, sai da ta shige falonsu ya kwashe da dariya yana buga sitiyari da faɗin, “Shegiya zaki gane kuranki tsohuwar guzuma kawai kin sa na rabu da ƙyaƙyƙyawar mamata ƴar shilax, wlhy kika yarda kika faɗa a wannan tarkon nawa kin gama kaɗewa. Khadijah kuwa tana gab da dawowa gareni. Dan wani zan nema ya aureta ya saketa batare da shi da ita sun san plan ɗina ba. Zan saida Companyn naki na ɗauke Dijoh na mu bar ma ƙasar gaba ɗaya”. Ya sake ƙyalkyalewa da dariya harda ƙyaƙyƙyawa na ƙeta.. A falo ya samu Kainaat kwance tana hutun gajiya, ido suka haɗa, a bazata ta sakar masa murmushi. A ranta kuwa faɗi take (shegen kaya kenan, ai nasan wannan kwantar dakan naka na sabon shiri ne. Amma babu komai zanyi amfani da shirin naka na gama da kai cikin sauƙi batare da ka kawo min wata tangarɗa ba. Kafin ka farga ka dawo tafin hannun Kainaat. Zan tabbatar maka ni da kai CUTA CE TA ƊAU CUTA... shegen yaro mai wayo kamar ɗan dila). Martanin murmushin ya mayar mata, tare da takawa a hankali inda take ya zauna. Ɗagota yay ya rungume a jikinsa. Hakan yasa itama rungumesan suka saki ajiyar zuciya a tare. Daga haka labarin ya fara canja salo. Duk da Kainaat taso dojewa daga baya ya hanata kowacce irin dama.. Sai da ya tabbatar ya samu abinda yake so sannan ya barta yana dariyar ƙeta. Danne zuciyarta kawai tai tana biye masa da murmushin fatar baki, a haka sukai wanka tare, sannan suka dawo ƙasa ta dafa musu noodles sukaci a tare. Bayan sun gama falo suka sake komawa suka kunna kallo, tana zaune shi kuma yana kwance yay filo da cinyarta. Lokaci-lokaci sukan kalli juna su saki murmushi, a ƙasan rai kuma kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa, dan su duka babu wanda hankalinsa ke akan kallon.. Dafeeq ne ya katse shirun da faɗin, “Bakice komai ba Baby. Dan ALLAH ki ajiye makamanki mu zauna lafiya mu rungumi junanmu. Na tabbatar miki zan koma miki fiye da bawa a gidan nan”. “Humm Dafeeq ina tsoron na sallama ne kaci amanata”. “Babu wannan maganar ki yarda dani”. Ɗan jimmm tayi kamar mai nazari, sai kuma zuwa can ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Okay shike nan na amince. Amma zamuyi komai a rubuce ka yarda”. “In dai nine baki da matsala dani a yanzu. Tunda kin san gidanmu, kin san iyayena, mi kuma ya rage to”. Cike da gamsuwa ta ce, “Hakane”........✍️ _Ni dai nace Humm😂. Kufa masu karatu kuna da abin faɗa?🥱._ _________ Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846 Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria Ummu khalifa 01017018846 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da ɗaya_ _____________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ______________ ......A hankali take buɗe idonta jin kamar ana ja mata yatsan ƙafa. Sunanta da ya sake ambata kamar mai raɗa ya sata buɗe idanun da ƙyau. Shine kuwa tsaye cikin tattausan jallabiya sai ƙamshi yake kamar ba asuba ba. Sake faɗin, “Tashi asubahi yayi kiyi alwala” da yay ya sata jin jina masa kanta cike da kunya. Sai dai ta gagara motsawa dan ji take bazata iya hakan a gabansa ba. Fahimtar hakan da yay ne ya sashi juyawa yana ce mata, “Na wuce massalaci ni”. Bata iya sake cewa komai ba harya fice. Cikin sauri ta sakko a gadon dan Alhamdullah bata jin komai yanzu zazzaɓin ya tafi. Harta nufi ƙofa sai kuma ta koma. Gadon ta shiga gyarawa a gaggauce ta gama tsaf tamkar ba'a shine suka kwanta ba. Gani komai ya mata yanda yake so ta fita. Sashen gaba ɗaya ta bari dan jiya da Noor ta mata jagora duk da kanta a rufe yake tana gane hanya. Da sanɗa ta shiga sashenta. Motsin ƴan rakiyarta da taji a ɗakuna biyun dake a sashen nata yasa ta saurin shigewa na can ciki da aka kaita. Tana maida ƙofar ta juyo da jingina jikinta idonta a rumtse tana sauke ajiyar zuciya. Buɗe idon da zatayi suka haɗa ido da aunty Firdausi, sai aunty Luba dake salla. Daburcewa tai, amma ganin Aunty Firdausin ta ɗauke kanta cike da basarwa itama saita wuce toilet da sassarfa kamar zata faɗi. Kai kawai aunty Firdausi ta girgiza tana sakin murmushi. Ta jima kafin ta fito a bayin, dan bayan tai alwalar sai tai tsaye tana shawarwarin fitowa da tunanin kallon da su Aunty Firdausin zasu mata. Jin massalatai har sun fara idar da salla ya sata fitowa a sanyaye, sai dai ta tsuke fuska ta yanda karma su mata wata tambaya. Tama samu basu idar da sallar ba, dan haka itama ta saka hijjab ta kabbara tata a bayansu. Koda suka idar da sallar babu wanda yace mata komai. Sai ma bayan gaisuwar datai musu suka koma hirar irin karamcin da akai musu a gidan da yanda wasan jiya yay matuƙar ƙayatar da su. Khadijah dai na saurarensu bata saka baki ba, a haka ma barci ya saceta sai da aunty Luba tace ta tashi ta koma gado sannan ta miƙe... Kallon juna sukai suka saki murmushin shaƙiyanci kawai. Sai dai babu wanda yace komai... Misalin takwas da rabi Gwaggo Safina ta shigo ta tada Khadijah wai taje tai wanka haka nan su kaita ta gaida surukarta. Suma zasuyi shiri ne zuwa goma zasu wuce in sha ALLAHU. Jiki a sanyaye tabi umarnin Gwaggo. Tsaff tai wankanta Aunty Nabela tai mata kwalliya kaɗan ta shirya cikin atamfa datai mata matuƙar ƙyau da amsar jikinta golden, sai ƙyalli take da ɗaukar ido ga kwalliyar stones tasha mai sheƙi. Ga wani uban ƙamshi na tashi a jikinta kamar fadar miss xoxo ta haɗa turate. (Mai son YERWA INCENSE AND MORE ya nemi wannan no ɗin 👉08095215215. Kayan ƙamshi ƴan gaske na maidugiri guys karku bari ayi babu ku😘😘👍) An kawo mata abincin karin da aka kawo musu mai rai da lafiya. Dan farfesune har kala biyu da kayan shayi da soyayyen doya da masa. Shayin kawai ta ɗan sha kaɗan tace ta ƙoshi, duk yanda su Aunty Luba ke mata faɗan ta dinga cin abinci bata iya tacin ba sai kuka da take neman yi musu, dole suka ƙyaleta. Su Gwaggo sun kaita ta gaisa da Mamy, anko karramasu sosai dan suma sun ji daɗin girmamawar da dangin Khadijah suke musu. Khadijah dai yau ma kanta a ƙasa ta kasa kallon kowa. Sai ma Noor ce tazo ta leƙata a mayafin tana dariya. Mamy dakema Noor daƙuwa ta tambayeta yaya jikinta. A kunyace ta amsa da cewar alhmdllh taji sauƙi. Murmushi kawai Mamy tayi dan ta fahimci surukar tata badai kunya ba. Basu wani jimaba sukai musu sallama aka dawo da ita. Zaman sake mata faɗa akayi, yayinda iyaye ke haɗa kayan garar da sukazo da shi dana rabo domin miƙawa sashen Mamy. Dai-dai nan Noor ta shigo da sallama, amsa mata sukai da fara'a, cike da girmamawa ta sanar musu Hammanta zai shigo ya gaidasu ne gashi a ƙofa. Da sauri suka shiga gyarawa dan kusan duk iyayene a wajen babu mai son suruki ya shigo ya gansa a mummunar kama. Amsa mata sukai daya shigo, dan haka ta koma wajen ta sanar masa. Ita ta fara sake shigowa kafin wata sassanyar murya tai sallama a ƙofar falon. Kasancewar ba wani surutu sukeyi sosai ba yasa suka jisa, dan duk isu-isu mayanne a falon wanda ke a cikin ɗakunan ƙalilanne irin su Khadijah da auntys nata ke can sun saka tsakkiya da nasiha da sake koya mata dabarun riƙe miji suna kuma sake banka mata abubuwa. Kamar ko yaushe ƙamshinsa ne ya fara shigowa kafin shi. Kansa a ƙasa cike da girmamawa ya kai duƙe yana gaishesu. Suma dai kawunan nasu a ƙasa suke. Sai masu ƙarfin halin satar kallonsa ƙasa-ƙasa suna gulma da zukatansu da tsarkake sunan UBANGIJI dan kuwa Abaan cikakken bafilatani ne zirryan babu gauraye ƙyaƙyƙyawan gaske. Ya jera musu godiya sosai da addu'a kafin ya miƙe. Inna Zulai da bata san Khadijah a ɗakinsa ta kwana ba, dan su duk tunaninsu bayan Doctor ya dubata nan ta sake dawowa. Cikin dattako da hange irin na manya ta ce, “Ka shiga suna ciki ai su Khadijahn tare da sauran ƴan uwanta”. Kasa yimata musu yay, dan haka ya kalli Noor data masa rakkiya ƙasa-ƙasa, da ido yay mata alamar tayi gaba. Dariyar dake taso mata ta haɗiye, dan tasan wanene Hammanta akan kunya. Yanzu ma da ƙyar Mamy ta kaɗoshi zuwa gaisuwar nan. Anan ɗin ma sai da Noor ta shiga ta sanar da zuwansa sannan ya shiga. Tuni su Aunty Luba sun kimtsa suna ma tsatstsaye ne. Khadijah kuma na zaune a bakin gado yarinyar Aunty Saddiqa na hannunta tana ɗaura mata ƙananun band a kai, sai mutsu-mutsu yarinyar keyi alamar bata so. Itako ta dage saita mata dan yarinyar akwai gashi masha ALLAH. Kafin ma ya gaishesu su tuni sun fara gaidashi saboda yanda kwarjininsa ya wani cika musu ido. Shiko kansa a ƙasa tun kallo ɗaya da yayma Khadijah bai sake ɗago kansa ba. Da ɗaɗɗaya suka dinga fita, hakan ya sashi miƙewa da ga ɗan ɗofanar da yay a hannun sofar dake ɗakin ya koma gaban mirror dake facing Khadijah da sam taƙi yarda ta kalla inda yake. Aikin ma Baby Zeenat kitso kawai takeyi duk da tunda ya shigo gabanta ke faɗi ta daure bata kallesa ba. Ga kunya dan abinda ya faru jiya yana yin sallama komai ya shiga dawo mata dalla-dalla. “Boddo kin tashi lafiya?”. Ya faɗa cikin muryarsa mai fita da nutsuwa da sanyi. Jitai kunya ta sake lulluɓeta dan tasan fassarar Baddo ɗaya kirata. Kamar aɗan daburce ta ce, “Ina kwana” batare data yarda ta kallesa ba. “Uhhm dama haka ake gaida miji?”. Kamar zata fasa ihu taji, dan wlhy kunyarsa take ji sosai. Amma taga shi ko'a jikinsa kai tsaye yake mata magana kamar sun wani saba. Ƙoƙarin gyara baby Zeenat dake zamewa take, sai son matse yarinyar take itako taƙi yarda shima take miƙama hannu alamar son ya ɗauketa. Murmushi yayi da tasowa daga jinginar da yay a mirrorn ya ɗauka yarinyar. Hakan ya bama hannayensu damar haɗuwa waje ɗaya. Da sauri ta janye nata kamar wadda lantarki ya taɓa. Duk da shima yaji shock cikin dakewa ya fuske abinsa yana komawa jikin mirror da ɗan ɗaga yarinyar sama yana mata wasa. Itako sai faman wangale masa baki take. Mamakin yanda ya shagala da yima yarinyar wasa yasa Khadijah zuba masa ido batare data sani ba. Karaf kuwa suka haɗa idon, da sauri ta janye nata cike da kunyar kamata tana kallonsa. Cikin son ƙara bata kunyar ya furta, “Ina matuƙar son yara da yawa. Ina fatan kin shirya bani nan da wata tara Boddo!”. Sosai kuwa ta rikice ta daburce da kalaman nasa. Har yanda tayi ɗin yaso bashi dariya. Dan dama ya faɗa ɗinne dan yaga yaya zatayin. Aiko ya gani fiyema da yanda yay tsammani. Dan har sai da ya ce, “Uhhm ayi haƙuri to wasa nake. Yaya jikin naki? Babu zazzaɓin dai ko?”. Ya faɗa cikin son kauda waccan maganar. Ajiyar zuciya ta ɗan sauke da jinjina masa akai alamar eh babu. “Alhamdullah ALLAH ya ƙara afuwa. Bara naje Awwal na jirana dan ina da baƙin da zan gani nanda awa ɗaya. Ina dai fatan babu wata matsala ko?”. Nanma kanta ta jinjina masa, sai kuma a hankali ta ce, “Babu komai”. Ya ce, “Masha ALLAH. Mamy tace min yanzu baƙinmu zasu wuce. Naso su bari sai zuwa gobe su sake hutawa amma sunƙi yarda da hakan.” A take idanun Khadijah suka ciko da ƙwalla, muryarta a karye ta ce, “Dan ALLAH ka sake roƙonsu, bana son su tafi nima”. Cike da tsokana ya ce, “Idan kin yarda zaki sake kwana ɗakina yau ɗin ma mizai hana na roƙesu sumayi mana sati”. Da sauri ta maida kanta ƙasa kunya kamar ta nutse a ƙasa take ji. Ƙaramar dariya yayi da dire mata Zeenat kan cinya. A wata bazatar taji saukar sumba a gefen kuncinta. Kaɗan ya rage ta saki Baby Zeenat ƙasa. Shiko ya nufi hanyar fita yana murmushi da faɗin, “Ki kula da kanki sai na dawo. Banda kuka, banda tunani”. Kasa amsa masa tayi dan ya riga ya gama kaita ƙarshe a kunya..... __________★ Kamar yanda Dafeeq ya buƙata Kainaat ta amsa da hannu biyu kam, dan akwanikan nan da suka gabata suna zaune lafiya sai dai ta ciki na ciki. Yanda yay alƙawari ya dawo mata da duka takardunta, hakan ya sakata jin matukar farin ciki har wani sashen zuciyarya na mata kokwanton anya kuwa bada gaske Dafeeq keyi ya zubar da makamansa ba? Sai dai wani sashe na kwaɓarta da hakan kuma. Dan haka ta cigaba da saka masa ido kamar yanda ta shirya masa, tare da fara aiwatar da plan ɗinta itama. Idan ka gansu a yanzu zaka ɗauka wasu masoyan arziƙi ne. Dan kowa na ƙoƙarin ɓoye mummunar manufarsa akan ɗan uwansa. A zukata kam da wahala a haɗu ba'a zagi juna ba. Kullum tare suke zuwa aiki su dawo. A gidan ma suna manne da juna ko yaushe. Kamar yanda ya saba zuwa gida Kano duk ƙarshen wata wannan watan ma yay shirin hakan. Harda yima Kainaat tayin ko zataje. Kamar tace a'a sai kuma ta canja shawara tace da shi zataje. Sun gama shiri tsaff tun a daren jiya yau da safe ta wayi gari da ciwon ciki mai tsanani. Hankali a tashe tun asuba suka nufi asibiti, tako samu kulawar gaggawa kasancewar likitan nada alaƙa da Abaan, dan kusan ma shine silar saninshi da tayi. Bayan sun rabu kuma bata daina zuwa wajensa ba, shi kuma bai taɓa tunanin bama sa tare da Abaan ɗin ba tunda alaƙar likita da maralafiya ce kawai ta haɗasu. Ko aure da yasamu labarin yayi a kwana uku da ya wuce wani abokinsa ne ke faɗa masa, shine ma ɗazu yay kiransa ya tayasa murna. Ganin Kainaat kuma a yanzu ta sashi tunanin toko suna ma a Adamawa ne anan akai bikin? Sai dai yayi mamakin ganin wanda ya kawota dan shi Awwal kawai ya sani makusancin Abaan dakan iya kawo matarsa ko ƙanwarsa ko Mamansa asibiti. Amma dai sai baice komai ba ya shiga bata kulawa yanda ya kamata. Har kusan azhar sannan ya sami nutsuwar zama, result ɗin gwaje-gwajen daya bada amata aka kawo masa. Cike da farin ciki da zumuɗin ganin abinda sakamakon ya bada ya shiga laluben neman Abaan a waya batare da yayi tunanin fara magana da wanda ya kawota ba. A kiran farko ba'a ɗaga ba, sai baiyi tunanin komai ba tunda yasan Abaan da sabgogi. Kusan mintuna goma tsakani sai ko ga kiran Abaan ɗin ya shigo masa. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗauka tare da rangaɗa sallama ta girmamawa.......✍️ _😂Kai dai wannan likita sam baka da man kai gaskiya_ Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846 Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria Ummu khalifa 01017018846 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da biyu_ ____________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ___________ .......Alhamdullah ƴan rakkiyar amarya da wasu a dangin ango duk sun wuce. Sai gidan yayi tsitt kasancewar babu mai yaro a wanda suka rage. Kuka sosai Khadijah tasha a sashenta daya rage babu kowa sai ita kaɗai. Mamy dai ta tura mata masu aiki sun gyara ko'ina tsaf. An kuma kai mata abincin rana. Sai da akai sallar la'asar kuma sai ga Noor da baƙi ƙawayen Mamy. ALLAH yasota babu jimawa tai wanka. Dan ɗan barcin da tayi bayan ta gama kukanta yasata jin nauyin jiki, shine ta watsa ruwa lokacin data shiga yin alwalar la'asar. Cikin girmamawa take gaida ƙawayen surukar tata. Wayayyun mata ƴan boko da naira ta gama nuna kanta a jikinsu. Duk da acikin su akwai wanda sukaso Abaan ya auri ƴaƴansu hakan bai hanasu yaba ƙyawun Khadijah da nutsuwarta ba. Sun kuma tabbatar da Abaan ɗin ya samu dai-dai shi a yanzu ba irin Kainaat ba mai buɗaɗɗen ido sa'ar shekarunsa. Haka dai suka fito suna sambarka da ambaton masha ALLAH. Koda Noor ta musu rakkiya nan wajen Khadijah ta dawo ta ɗan tayata zama, dan ɗazun dama tazo ta samu tana barci. Hakan yayma Khadijah daɗi sosai, dan ta rage kewa, sannan Noor ɗin ta taimaka mata sun gyaro sashen Abaan kamar yanda ta bata shawarar suyi. Sai gab da magrib ta koma nasu sashen, tabar Khadijah da kewa da zullumi. Dan ji take kamar tai tsintsuwa ta koma Kano, sai dai kuma tasan bakin alƙalami ya riga kuma ya bushe..... _________★ Ƙarfe biyar da kusan rabi motarsa ta shigo gidan. Kamar kullum yana tare da Awwal. A yanda ya fito motar a kasalance zai sa ka fahimci a gajiye yake. Dan hatta ƴar saman suit ɗinsa riƙe take a hannunsa ya ɗan sagalata a kafaɗarshi. Kai tsaye sashen Mamy ya nufa, ya bar Awwal na tattare masa tarkacensa kamar yanda ya saba. Sassanyan muryarsa ta fargar da su Mamy dake hira zuwa garesa. Duk da tunkan ya shigo dama ƙamshinsa ya musu sallama. Cike da girmamawa ya gaida gwaggonninsa biyu da suka rage basu wuce ba. Sai wasu mata biyu da suma suka gaishesa cikin girmamawar. Sai Noor da itama ta gaishesa, sannan shima ya maida hankali ga Mamy dake binsa da kallon tausayi, dan gani taima kamar ya ɗan rame mata yau ɗin. Amsa masa tai da kulawa, tare da ɗorawa da faɗin, “Baffah kaci abinci kuwa yau ɗin nan?”. Murmushi yay mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya ce, “Mamy naci snacks da drink....” “Baffah na drinks da snack aiba abinci bane. Shiyyasa naga ka rame min a ido wlhy. Kaga maza jeka wajen matarka an kai muku abinci dan ALLAH ka zauna kaci, sannan itama ka tabbatar taci kaga baƙuwace ita”. Murmushin ya sake yi nan ma yana miƙewa, sallama ya musu ya fice dan shima dai yasan yana matuƙar buƙatar hutawar kam... Tsaye take gaban mirror tana fesa turare dan kammala gyara jikinta kenan kamar yanda su Aunty Firdausi suka gargaɗeta da yi. Ratsa kunneta da sassanyar muryarsa tai yasata ɗan daburcewa, cikin sauri ta ɗauki ɗan kwalinta da bata kai ga ɗaurawa ba ta shiga ƙoƙarin warwarewa tana amsa sallamar tasa. A hankali ya janye idanunsa da ga kan gashinta dai-dai tana ɗora ɗan kwalin da faɗin, “Sannu da zuwa ina yini”. Rigarsa dake saman kafaɗa ya sauke a ɗan kasalance ya amsa da, “Ya baƙunta? Badai kiyi kuka da zasu tafi ba dai ko?”. Kasa bashi amsa tayi, sai ma idanunta da suka ciko da ƙwallan, amma tai dauriyar riƙesu. Freight ɗin dake ɗakin ƙarami ta nufa, ruwa ta ɗakko da kofi ta nufesa. Yanda ta zuba ruwan a nutse da ɗan rissinawa yayin miƙa masa ya sashi sakin siririyar ajiyar zuciya. Jin kaifin idanunsa a kanta ga shi ya haɗa hannunta da kofin ruwan ya riƙe yaƙi ya saki ya saka tsigar jikinta fara tashi yaam. Ji tai ta kasa daurewa ta ɗago a hankali itama, kai tsaye cikin idanun nasa natan suka shige, ji tai ta ƙara rikicewa ma, dan mijin nata akwai kwarjini da cika idon mai kallonsa. Ganin yanda tayi ɗin ya sashi sakin murmushi, magana ta gaskiya yana matuƙar son mace mai kunya da sanyin hali irin na Khadijah, dan haka komai nata ke birgesa kai tsaye. Yanda baida hayaniya haka yake son mace mara hayaniya da rashin kauɗi. Kofin ya kai bakinsa batare daya sakar mata hannunta ba, sai da ya shanye duka batare da ya saki hannun nata ba dai ya jawota zuwa jikinsa a hankali ya zagayeta da ɗayan hannunsa, cikin kunneta ya raɗata mata “Haka ake tarbar miji dama Baddo?”. Ji Khadijah tai inama ƙasa ta buɗe kawai ta shige dan kunyarsa. Yanda yake tafi da ita nasata mance ta taɓa aure, dan kunyarsa take irin sosai ɗin nan, kodan ya girmi Dafeeq a shekaru ne, ko kuwa yanayin kamewarsa da cikar kamalane ke sata jin hakan ita bata sani ba. Sun yi kusan minti biyu a haka kafin ya saketa, sai kuma a ɗan kasalance ya ce, “Bara nayi wanka na zo nai sayen bakin amarya dan naga dai take-taken ki kenan”. Da sauri ta juya masa baya tana ɗan murmushi. A ranta tana jin mutumin nan nadabanne a cikin daban. Komansa na tabbatar mata lallai a duniya akwai maza akwai kuma mazaje. Jin yana ƙoƙarin fita muryarta acan ƙasan maƙoshi ta ce, “Mamy ta aiko da abinci a kawo maka?”. Sai da ya kalla ƙyaƙyƙyawan agogon hannunsa da ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci ɗaya shima murya can ƙasa ya bata amsa da, “Zan dawo anan naci after isha”. Kanta kawai ta jinjina masa batare data iya kallonsa ba. Sai da taji ya fita ta ɗan sauke ajiyar zuciya tare da ɗagowa, idanu ta ɗan tsurama inda ya tsaya ɗin sai kuma ta saki murmushi, ita kanta tana mamakin yanda take tsintar kanta a wani shauƙi da kunya mai tsanani a duk sanda suka kasance tare. Ga wata kasala dake saukar mata da jin nutsuwa. Bayi ta shiga tai alwalar magrib duk da da ɗan sauran mintuna, amfani tai da sauran lokacin da ya rage tai zaman karatun Alqur'ani har sai da lokaci ya cika ta tashi ta gabatar da magrib, koda aka idar karatun ta cigaba dayi har isha'i. Ta jima tana addu'oi sannan ta tashi, gaban mirror ta koma tai ɗauri mai ƙyau tare da sake gyara kwalliyarta simple data sake fidda mata ƙyawunta. Ta sake saka turare sannan ta ɗauka mayafi ta yafa kamar mai shirin fita. Tayi ƙyau sosai, sai kwalliyar tata ta sake tabbatar da ita a amarya. Falo ta fito ta saka turaren wuta a kusan burner uku data gani, duk da kuwa falon yana ƙamshinsa abinsa. Kitchen ta shiga ta haɗa abincin dan tunda aka kawo anan aka ajiyesa. Ta kawo kulolin ta koma ɗakko sauran ta samu ya shigo. Sai dai waya yake yi, yana zaune a kujera sanye cikin milk jallabiya datai masa ƙyau sosai kamar wani balaraben Saudiyya. Ga ƙamshin turarensa mai daɗi ya cika falon. Yanda yake wayar cikin yaren filatanci haɗe da turanci dolene ya birgeka. Duk kai kawon da take tsakanin kitchen zuwa dining idonsa na kanta, ta masa ƙyau sosai, haka kawai sai wayar da sukai da Doctor Giɗaɗo ɗazun ta faɗo masa a rai, wai Kainaat nada ciki. Da sauri ya ture tunanin gefe cikin halin ko'in kula, dan shi ko kaɗan baiji wani abu na kishi akan hakan ba, shi yama manta da wata Kainaat can a babin rayuwarsa, yama yi zaton ta koma ga iyayenta tuni ashe wai tana Adamawa harma ta sake wani auren, gaskiya bai taɓa sake tabbatar da Kainaat kidahuma bace sai yanzu, yayi nadamar auren yarinyar nan a rayuwarsa, amma ba komai ai yayine domin Mamynsa, gashi kuma yaci ribar biyayyar da yay mata a farko tunda gashi a karo na biyu ta sake haɗashi aure da choice ɗinsa, hakan kaɗai garesa Alhmdllh. Isowar Khadijah wajen ya sashi yin sallama da wanda yake wayar tare da ture batun Kainaat gefe, cikin ɗan risinawa kanta a ƙasa ganin ya kammala wayar ta furta, “Hamma ga abincin (yanda taji Noor na kiransa). Wani kalar ɗan waro idanu yay waje, sai kuma kamar a ɗan shagwaɓe ya ce, “Hamma kuma baddo! Wannan ai salon hanani rawar gaban hantsi ne”. Cikin rashin fahimta da jin yanda yay maganar a wani can ƙasan maƙoshi ta ɗan ɗago ta kallesa. Manyan danunsa ya lumshe mata tare da wani kalar ɓata fuska a daƙile ya ce, “Eh mana, miya haɗa ango a daren farkonsa da wani Hamma can. Inama laifin irin su kankanar zuciyata, madarar raina, gobar ruhina haka sai na san ango nake.” Dariya sosai Khadijah keyi, dan harga ALLAH ya bata matuƙar dariya, irin waɗan nan sunaye haka. Ganin yanda take dariya har fararen jerarrun haƙoranta na bayyana ya sa ya saki murmushi shima. Haka yake son ganinta cikin farin ciki, dan yasan ya tsamota cikin danginta tana cike da damuwar kewarsu dannewa kawai take. Miƙewa yay har sannan fuskarsa da murmushi ya nufi dining ɗin, hakan yasa itama haɗiye sauran dariyar tabi bayansa. Ita da kanta ta zuba masa abincin, sai dai kaɗan ta saka kamar yanda ya buƙata. Ganin ta zauna bata da niyyar zuba nata ya sashi kallonta da fararen idanunsa masu maruƙar rikita mata lissafi. Ƙasa tai da kanta tana wasa da yatsunta. Komai baice da ita ba ya ɗauke idanun, sai kuma ya ɗauki spoon ya saka a plante ɗin nasa a bincin. “Bismilla muci”. Ya faɗa babu alamar wasa a tattare da shi. Ji tai gaba ɗaya ta kasa musa masa. Dan girmansa da kwarjinin sa a idonta bana wasa bane. Kasa sakewa taci abinci tayi, sai juya spoon take a ciki da tsakura kaɗan-kaɗan. Shiko bai mata magana ba yana cigaba da ci a nutse rabin hankalinsa akan tvn dake dining ɗin yana kallon news. Ya ɗan ci sosai ya ajiye cokalin sai kuma ya zari tissue ya goge bakinsa yana kallonta. Tana jin yanda idanunsa ke yawo a jikinta amma sam ta kasa ɗagowa, har sai da ya fara ƙara mata abincin sannan ta ɗago da sauri. Kansa kawai ya ɗan ɗaga mata alamar taci yana miƙewa yabar dining ɗin, can falo ya koma ya sake zama a inda ya tashi yana buɗe laptop daya ajiye ya shiga aikin gabansa da duk bai wuce bincike akan noma ba dai. Dan in dai ka gansa da laptop aikin kenan kawai. Tashinsa a wajen ya ɗan taimaka mata taci abincin, bayan ta kammala ta tattare wajen ta kai kitchen, sauran abincin take ta tunanin yanda zatai da shi, dan bata son barinsa ya lalace babu daɗi. Gashi ita ba waya ba balle ta kira Noor tace a zo a ɗauka. Ta manto wayarta a Kano, tun ɗazun take son magana da su ma hakan ya gagara. Rashin mafita ya sata fitowa, kanta a ƙasa ta nufo inda yake. Sai da ta ɗan saci kallonsa, ganin hankalinsa gaba ɗaya a screen ɗin laptop ɗin yake ta sauke ajiyar zuciya can ƙasa. A hankali ta ce, “Hamm....” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa. Murmushi ya ɗan saki batare daya kalleta ba, idanunsa akan screen ɗin laptop ɗin ya ce, “Uhumm ina jin ki! Batun Hamma kuma zan canja shi ai da kaina dan ni dai ba Hammanki bane”. Duk da zancen nasa ya sata jin kunya haka ta daure ta sanar masa batun abincin. Karan farko ya ɗago ya ɗan kalleta ya sake maida kansa, ji yay ta birgesa, dan ta sabbatar masa ita ba almabazzar mace bace ba. Gefensa ya nuna mata ya ce, “Bismilla zauna bara na kira Noor sai ta aiko a ɗauke”. Kanta ta jin jina masa itama kawai, dan har ya riga yakai wayar kunnesa. Dai-dai tana ƙoƙarin zama a ƙasa ya ajiye wayar yana kallonta, kansa ya girgiza mata da faɗin, “No akoda yaushe nafi buƙatar jin iyalina a jikina in har ina gida. Karki sake kwantanta cewa zaki zauna ƙasa dan ina kujera. Dan haka bissmilla”. Ya nuna mata kusa da shi, inda ta tabbatar idan ta zauna dolene a jikin nasa zata kasance kamar yanda ya ambata.........✍️ Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846 Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria Ummu khalifa 01017018846 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da uku_ ___________ Ina kuke manyan mata da hajiyoyi munsamar muku sauqi Ina masu shaawar futa Egypt karatu ko yawan bude ido to gadama tasamu kaidai kawai kaiwa wannnan number magana 01017018846 Ba nan ummu khalifa ta tsaya ba tana kawo original Egyptian abaya da shoes da duk abinda mutum keso tana kawowa zuwa gida Nigeria Ummu khalifa 01017018846 ______________ ......Zama tai a ɗan takure, sai dai a bazata taji ya saƙalo hannunsa ta bayanta ya kwantota saman kafaɗarsa, batare da ya sake magana ba ya cigaba da aikinsa. Ta jima idanunta a runtse dan kunya, kafin ta buɗesu a hankali tana kallon abinda yake a laptop ɗin. A haka masu aikin Mamy da suka kawo mata abincin sukai sallama. Zata tashi ya sake maidata yana amsa musu sallamar, sai kuma yace su shigo. Kamar Khadijah zata fasa ihu dan kunya, amma shi sai taga aikinsa ma kawai yake. Ta gefen ido ta kalla masu aikin, sai taga tunda suka musu kallo ɗaya basu sake yi ba. Ko gaishesu da sukai kawunansu a ƙasa suke. Shi hannu ma kawai ya ɗaga musu, sai itace ta amsa musu. Koda suka shiga kitchen ɗin ma suka fito sam basu kallesu ba har suka fice, a hankali ta sauke ajiyar zuciya har yana iya jinta. Sai dai baice komai ba face ɗan murmushi daya saki kaɗan ya cigaba da aikinsa. Kusan awa ɗaya suna a haka, tun tana noƙe jikinta harma ta saki wani barci-barci ya fara rinjayar idanunta dan ƙamshin turarensa ba ƙaramin ratsata yake ba da saukar mata kasala. Laptop ɗin ya rufe ya ajiye tare da sauke ƙafafunsa dake a table ƙasa. Sai kuma ya ɗan kalleta yana mai kai hannunsa saman fuskarta ya shafa. Firgigit ta buɗe idanun, ganin yanda fuskarsa ke gab da tashi ga hannunsa akan tata fuskar ya sata ɗaga kanta a kafaɗarsa da ɗan sauri. “Da'alama kin gaji da yawa, ansha rawa wajen party shekaran jiya ko?”. Juyowa tai da sauri batare data tuna dawa ma take maganarba, idanunta a ɗan ware bakinta na nuna alamun ƴar shagwaɓa ta ce, “Ni wlhy bana rawa, kuma dai ai kowa yasan banyi ba”. Wani irin harmutsawa jinin jikinsa yayi saboda yanda tayi ɗin, ga idanunta sun sake wani haske har ƙyalli suke, baƙin ya ƙara baƙi, lips ɗinta sun ɗan tattare kaɗan. Samun kansa yay da jinjina mata kansa, idanunsa na a cikin tsakkiyar nata idanun, kamar mai raɗa ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Uhmm nima shaida ne bakiyi rawan ba, amma yanzu zakiyi min nawa a ɗaki ko....” “Rawan!”. Ta faɗa cikin ƙara waro idanunta sosai waje, irin nuna alamun matuƙar mamakinsa ɗin nan. A wani irin sake kasancewa a kasalance ya jinjina mata kansa yana lumshe idanunsa da buɗewa cikin nata ya furta, “Uhhumm Baddo”. Kamar wadda aka maido hayyacinta ta miƙe zabar, sai kuma cikin sassarfa ta nufi barin wajen da bashi amsa muryarta na rawa. “Ni ALLAH bana rawa”. Wuff ta shige ɗan lungu bedroom ɗin ta. Murmushi mai bayyana haƙora ya saki, sai kuma ya taune lips ɗinsa da ƙarfi yana ɗan kaima kansa ƙaramin mangari ya ce, “Abaan kai ɗin nan ko”. Sai kuma ya sake sakin murmushin da komawa cikin kujerar ya wani lafe. Shi gaba ɗaya ma ji yake yana neman rasa control ɗinsa akan yarinyar nan. Anya Ibrahim da Adams ba saida suka tofeshi ba kafin su kawo wannan batun ga Mamy. Abin da mamaki fa, sam mantawa yake da cewar Khadijah ta taɓa aure kafin shi ɗin, kallon wata ƙaramar yarinya budurwa sharaf yake mata, koda yake yarinyarce ai, 20years fa, ko ƙanwarsa daya bama shekaru masu tazara sosai ta girmeta fa. Ai dami a kala kawai ya tsinta... Tafi minti takatin da shigowa sannan ya shigo, dan harta canja kayanta zuwa na barci. Wando da riga ne masu santsi da basu kama jikinta ba, sai hula data saka amma duk da haka kwantaccen gashin gaban kanta sai da ya fito. Zaune take a saman gadon ta jingina da fuskarsa littafin addu'oi a hannunta. Ta rage fitilar ɗakin sai lamp na side drawer kawai da take amfani da shi wajen ganin rubutun littafin. Shigowar tasa sai da ta ɗan sakata razani, dan duk ta saki jiki akan bazai biyota ba. Ta ƙasan ido take binsa da kallo har ya hawo gadon, ganin ya ɗan zuba mata ido ya sata ɗauke nata ta maida ga littafin. Tsahon wasu sakanni kuma sai ya matso jikinta gab. Wani yarr taji saboda jin saukar kansa a kafaɗarta amma ta dake. Hannunsa ya ɗaura saman nata dake riƙe da littafin ya ɗan jawo kaɗan shima yana kallon rubutun larabcin. A haka suka cigaba da karantawa a tare batare da yayi magana ba. Ganin sun kammala karanta na barcin tana neman buɗe wani shafin kuma ya sashi zare book ɗin a hankali, jikinta ya ɗan ranƙwafo har tana ɗauke numfashi ya ajiyesa a side drawer ɗin, sai kuma ya nufi sauka gadon yana faɗin, “Kina da alwala?”. Kanta ta jin jina masa alamar eh. Shima sai ya jin jina nasa da bata umarnin ta sakko. Sun gabatar da salla raka'a biyu, ya kama kanta yay addu'a tare da yi musu addu'ar zamar lafiya da samuwar zuri'a mai albarka sannan suka sake komawa garon. Zama ta sake yi kamar ɗazun, batare da yace mata komai ba ya rage ƙarfin lamp ɗin ƙasa sosai. Sake maida kansa yay a kafaɗarta kamar ɗazun ya riƙo hannunta cikin nashi ya matse har sai da ta ɗan zabura kaɗan. “Mrs Abaan Omar Modibbo!”. Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa idonsa akan hannunsu dake cikin na juna. Zuciyarta na bugawa da sauri-sauri a hakanli itama ta ce, “Uhmyim”. “Thanks you Baddo da kika amsheni a matsayin miji duk da ban taɓa zuwa gareki na nuna kaina ba, bazan ɓoye miki ba kin matuƙar burgeni da kika amshi auren nan a yanda yazo miki batare da nuna koda a fuskarki an miki ba daidai ba. Lallai ke kin cika ɗiya tagari abin alfaharin kowaɗanne iyaye. ALLAH yay miki albarka, ALLAH ya yarda dake fiye da yanda ni mijinki nake jin na yarda dake. UBANGIJI ya yafe mana kurakuran mu baki ɗaya. Baba ya sanar dani komai akanki, ina son ki manta da abinda ya faru baya domin kuwa ƙaddararki ce, ita kuma ƙaddara duk iya gudunka baka isa tsere mata ba. Tun randa muka tsinceki a bakin hanya tabbas naji tausayinki sosai a raina, duk da kuwa ban san minene dalilin shigarki a halin da muka gankin ba. Bayan mun kaiki gida na tafine da tunaninki a wannan yinin, sai dai kasancewata mutum mai yawan sabgogi ina komowa Abuja namance komai daya shafeki na cigaba da harkoki na. Kasancewar irin rabuwar da mukai da matata ta farko Mamy kullum cikin roƙona take kan na fidda matar aure. Nakan bata amsa da cewar ba yanzu ba, idan kuma naga ta damu sai nace mata ta zaɓamin kamar yanda ta zaɓa min ta farko. Hakan kansa ta ƙyaleni, dan tana ɗaurama kanta laifin a kan yanda matar data zaɓamin ɗin ta kasance a baya. Sam lokacin da muka kaiki gida ban san su Adams nada alaƙa da gidanku ba, duk da nasan an saka musu date ɗin aure kuma zasu auri yara ƴan gida ɗaya ne. Ban taɓa maganarki kuma da su ba duk da su ɗin sun wuce yarana na business sun zama tamkar ƴan uwane gareni saboda gaskiyar su da riƙon amana. Dan sukan iya zuwa cikin gidan nan suci su sha suyi hira da Mamy harma suyi kwanaki, haka nima nakan ziyarci iyayensu a duk sanda na samu dama in har na shiga Kano. Mamy itace ta haɗa lefensu su duka, bayan ta kammala haɗawar ne tai kiransu dan su gani, sannan baifi saura sati uku bikin nasu ba, ni lokacin ma bana ƙasar. A randa sukazo ɗin ne Ibrahim na waya da ƙanwarki sai maganarki ta shigo ciki akan miki ɗinkunan fitar biki, alokacin Mamy na tare dasu, dan harta gaisa da Ni'ima ma. Bayan ya gama wayar yake cewa Mamy zai bada a saya miki kaya kema kamar kala biyar haka dan kayan lefen nan sun masa ƙyau, anan ne Mamy ke tambayar wacece ke ɗin kuma, dan duk zatonta wata budurwarce kuma daban, shine suke bata labarinki. Mamy macece mai tsananin tausayi, sannan da kike ganinta nan ƴar gwagwarmaya ce akan mata, a take ta nema ganin hotonki, tare da alƙawarin tsaya miki kiyi ilimi. Su Adams duk basu da hotonki sai da suka kira su Zuhrah suka tura musu. Ta jima tana kallonki fuskarta da murmushi, a bazata sai ji sukai ta ce, “Ni dama ɗan rigimar ogan nan naku zai amince ai da sai yay mana wuff da wannan black beauty girl ɗin kawai. ALLAH yarinyar ta shiga raina matuƙa”. A take maganar tata ta ɗauki hankalinsu, musamman ma Noor da tai ta zigawa akan a min magana akuma turamin hoton. Tun Mamy bata ɗauki zancen serious ba harta amince a washe gari tai kirana, kai tsaye tace tamun mata na duba ga hoto nan ta tura min ta email ɗina na gani idan tamun. Duk da maganarta ta shigeni, kuma ba auren ne a gabana ba sai kawai na amsa mata da cewar na amince in har yarinyar ta mata. Harga ALLAH banga hotonki ba, dan ko buɗesa ma banyi ba na goge. Farin cikin da naji Mamy da Noor na ciki ya samun jin zan iya amsar auren koda bazan soki ba, dan matata ta baya ta gama ciremin sake jin son wata mace a rayuwata. A ranar Mamy ta aika su Adams Kano domin yin magana da Baba, ban san hidimar da suke ba dan tun a ranar na manta da batun wani tayin aure da Mamy tamun, ashe su suna nan sunata kai kawo dan da farko Baba yaƙi amincewa har sai da Mamy taje kano da kanta sannan, lokaci baifi saura kwana takwas bikin su Adams ba aka tsaida namu zancen. Ban dawo Nigeria ba sai ana saura kwana uku, na kuma zo ne da shirin bikin su Ibrahim. Sai kawai na samu an gyara gidan nan tsaf harma wasu a baƙin Adamawa sun fara isowa. Humm abin yaban mamaki, amma yanda naga mamy ta ɗauki abin da muhimmanci ya sakani danne zuciyata na cigaba da binsu da ido. Sam banyi niyyar zuwa dinner ɗin nan ba amma Mamy ta matsa tare da magiyar su Adams dole nai shiri aranar nabi jirgin ƙarfe shida zuwa Kano. Kin san wani abu?”. Yay maganar ƙarshe cikin sigar tambaya yana ɗan matsa hanunta dake cikin nashi da ɗan ɗaga ido ya kalleta. Kanta ta girgiza masa a kasalance. “Tun kafin mu shigo cikin hall ɗin nan na fara cin karo da zazzaƙar muryarki da tai matuƙar ratsani kina addu'oi. Jinai na kwaɗaitu da son ganin mamallakiyar muryar tunkan na shigo ciki, sai dai muna shigowa muka samu kin gama. Ni ne na turama Awwal saƙo cewar a sake sakaki ki fito kiyi addu'a.....” da sauri ta waro masa idanunta alamar mamaki, murmushi ya sakar mata da cigaba da faɗin, “Lokacin da kika miƙe jinai kamar na zama tsuntsu naje naga fuskarki, dan sam bana ganinki da ƙyau, har sai da kika kammala kika koma mazauninki. A lokacin ne na iya ganin fuskarki, ji janai zuciyata na neman fitowa ta baki, da ƙyar na iya controlling kaina, abinda zai kuma baki mamaki har lokacin banfa gane ki ba, dan kin canja gaba ɗaya daga waccan ranar. Sannan kuma ban san kece matar da Mamy ta zaɓamin ɗin ba har sai da aka sake kiranki matsayin yayar amare da zata bada tarihinsu. Anan ne zuciyata ta shiga waswasi har lokacin da tsageran yaron nan ya fito ya fara miki liƙi, kawai saina samu zuciyata da shiga ƙunci harna kasa dannewa na turama Ibrahim saƙo, amsar daya bani ta sakani miƙewa zimbir na nufeku, sai kuma ga Awwal yazo min da batun wai kece ai muka kai gida watanni takwas da suka wuce. Bayan mun kaiki gida na koma masauki ban iya barci ba Khadijah, kwana nai ina jerama UBANGIJI godiya dan wlhy a ƙanƙanin lokaci ya dasa min ƙaunarki a zuciya irin wadda ban taɓama wata ɗiya mace da sunan soyayya ba a rayuwata. A washe gari na matuƙar jin ƙagara a ɗaura mana aure, dan kawai saina samu kaina da tsoron karfa tsohon mijinki ya dawo yace bai sake ki ba, ban samu nutsuwa ba har sai da naji an ɗaura mana aure. Ina sonki Khadijah, ina matuƙar sonki har cikin jinina, ina fatan nima zaki soni ki ƙaunaceni koda ƙanƙanine dan ALLAH. Karki wahalar dani domin ni mai rauni ne akan soyayyarki”. Hannunta dake a cikin nashi ya ɗorasa saman ƙirjinsa, cikin sake raunana murya da kafeta da mayun idanunsa masu matuƙar haske da girma ya furta......✍️ _____________ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da huɗu_ _____________ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ___________ .......“Taɓa kiji yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri. Na kuma fara fuskantar wannan yanayin ne tun a rannar dinner ɗin nan dana fara tozali dake. Ni na tabbata zaki iya juyani fiye da yanda kike zato saboda ƙaunarki Khadijah, abinda kawai na tsana shine cin amana, wulaƙantamin mahaifiya da ƴar uwa, duk a yanda nake jin ƙaunar nan taki bazan iya amince miki hakan garesu ba. Domin su ɗin rayuwata ne, fatana ke da su ku dunƙule ku zame min abu ɗaya dan ALLAH Khadijah. In sha ALLAHU zakuyi alfahari da ni, sannan zaku sameni fiye da yanda kuke zato da tsammani ku duka dan na kasance rawani a tsakanin kalluba ne gareku.” A hankali hawayen da Khadijah ke riƙewa suka silalo, murmushi ta saki mai sanyi da raunana zuciya. Hannunta dake cikin nasa ta juya, sai nasan ya koma cikin nata. Kaɗan ta matsashi hakan ya sashi kallonta, ganin hawaye ya sakashi tashi daga kafaɗarta da sauri, hannu ya kai kan fuskarta amma sai ta kauce ma hakan, sai kawai ta sake saki kuka ta faɗa jikinsa. Baida zaɓin da ya wuce ƙanƙameta da ƙyau, ya wani lumshe idanunsa sautin kukan na ratsa masa zuciya. Kusan mintuna biyu ta ɗauka a hakan, jin bata da niyyar dainawa ya ɗagota daga jikinsa gaba ɗayanta, ƙoƙarin son kallonta yake amma taƙi yarda, sai da ya kamo fuskarta cikin tafin hannunsa duka biyu biyu. Yanda ya zubama fuskar tata ido ya sata rumtse idanun da sauri wasu hawayen na sake silalowa. Sake lumshe nasa idanun yayi yana jan numfashi da fesa mata akan fuskar, sai kuma ya matsar da tasa fuskar a hankali ya saukar da lips ɗinsa masu ɗumi kan nata da hawaye ya jiƙa sukai sanyi da santsi ga taushi. Ƙanƙame jikinta tai da farko gabanta na faɗuwa, sai dai yanda yake aika mata salon sumbatar yasa cikin ƙanƙanin lokaci ya birkita mata dukkan lissafi batare data farga ba ta fara maida murtani itama. Sake rikicewa Abaan yayi, dan baima san shi ɗin yana cikin kewa da buƙatar abokiyar halittar tasaba sai a yanzu. Tuni salon ya sauya da wani irin zazzafan yanayi mai ɗunbin tarihin da su kansu sun san bazasu taɓa iya mantawa ba har gaban abadan, dan wannan rana ta kasance musu ta daban a cikin daban a rayuwarsu. Dan ta kasance musu a mafi daraja da girman dare da kowaɗanne ma'aurata kan ƙalla kuma su rubuta su ajiye a kundin sirrinsu mafi zama ƙololuwar sirri da babu wani mahaluki dakan iya bincikowa, dan koda ace da bakinsu suka faɗeshi ga wani sai dai su kamanta badai lissafinsa dalla-dalla ba dan wannan wani al'amari ne mai girma daga ƙyautar UBANGIJIN al'arashi mai rahama da jin ƙan bayi... _________★ Jikin doctor Giɗaɗo ƙalau ya sauke wayar daga kunnesa. Yayinda matuƙar mamaki ke ratsashi jin yanda Alhaji Abaan ɗin ya amsa masa batun albishir da yay masa kan batun cikin kainaat. Ba haka yay zato ba sam, tabbas bai yi tsammanin samun hakan ba. Dan a zatonsa idan ya sanar masa Abaan ɗin zai kasance cikin ɗunbin farin ciki tamkar ya fasa wayar dan daɗi, dan shi shaidane irin wahalar da suka dingayi da matar tasa akan neman irin wannan damar. Amma sai gashi yanzu yaji sabanin hakan. (ayyah) kalamarfa da Abaan ɗin ya amsa kawai kenan da ita lokacin daya sanar masa da maganar ciki a jikin Kainaat na kwakin da basu wuce sati ɗaya ba ma, daga ƙarshe kuma yace masa yanada uziri sai kawai ya yanke kiran. Shigowar Nadwa ya sashi jan ajiyar zuciya ya fesar, sai kuma yaji wani daɗin ganin nata dan koba komai zata fiddashi a duhun da yake ciki yanzu.. Sun gaisa da girmamawa, batare da ya jira jin miya kawota ba ya jeho mata tambaya. “Hajiya Nadwa nikam ko zan sami wata number ɗin Alhaji Abaan a hannunki, dan inata kiransa nai masa albishir amma yaƙi ya ɗagamin, kin san manyan nan da uzirori”. Ɗan jimm tai, sai kuma can ta ce, “Wani abu ya faru ne kake neman number ɗin sa?”. “A'a babu abinda ya faru sai alkairi, kawai ina son masa albishir ne game da rashin lafiyar Hajiya Kainaat”. Da sauri cikin waro idanu ta ce, “Albishir ɗin mi?”. “A ke kam na faɗa miki kuma na ragema kaina lissafi, ai nai alƙawarin sai mijinta ya fara sani kafin kowa”. Kallonsa ta tsaya yi kamar bazatace komai ba sai kuma ta ja numfashi, cike da kissa ta ce, “Kasani ko idan ka faɗamin ɗin na zama silar da za'a ninka maka goron albishir ɗin naka. Common faɗa min mike faruwa in har kana son number”. Yasan halinta, tunda tace hakan saifa ya faɗa, ƙasa ya sake yi da murya ya ce, “Dan ALLAH amana fa, dan nafi son ya sani ta bakina kafin kowa”. “Baka da matsala ina dai wannan ne”. Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya matso da fuskarsa a cikin raɗa ya ce, “Na gano tana ɗauke da cikin kwanaki takwas ne”. Sosai Nadwa ta waro idanu waje har tana ƴar zabura ta furta, “Ciki kuma doctor?”. Da sauri yay mata alamar ta rage murya, sannan ya amsa mata da, “Tabbas kuwa ko tantama babu ciki, Kinga kuwa ai wannan albishir ni ya kamata na fara sanarma Alhaji Abaan”. “Ai ba nashi bane. Domin kuwa kusan shekara ɗaya da wata biyu kenan da rabuwarsu. Wannan yaron da kaga ya kawota shine mai cikin dan shi ta aura. Idan kace zaka kira ABAAN maimakon goron albishir ɗan karen bugu zakaci ma. Sannan idan ka sanar da Kainaat ko mijinta batun wannan cikin ma komai zai iya faruwa. Dan haka inada da bara, idan ka bani haɗin kai ni da kai duk sai muci arziƙi mu bar arziƙi a inda yake, kadai san ni ai bana kawo maka aikin banza”. “Tabbas hakane Hajiya Nadwa yanzu yaya kike son ayi?”. Wani shegen murmushi ta saki da kashe mar ido ɗaya, sai kuma ta miƙe tana ɗan duƙawa saman decks ɗin ta yanda har yana iya ganin jikinta. Yawu ya haɗiye da ƙyar yana sake ware ido shi yaga banza. Cikin kunne ta gwargwaɗa masa maganar da nima banji ba, a take suka saki ƴar dariya, ta bashi hannu alamar su tafa, cikin rawar jiki ya miƙa mata nashi shima yana wani karkatar dakai da leƙata. Yi tai kamar bata fahimci ina ya dosa ba suka tafa ta koma ta zauna a mazauninta.... “Doctor har yanzu baka sanar min mike damun matata ba, ko result ɗin bai fita bane?”. Kai doctor Giɗaɗo ya jinjina yana yana jawo wani file a gefensa. Sai kuma ya kalli Dafeeq yana ɗan murmushi. “Afuwan abokina, result ɗin matarka ya fito, sai dai muna jiran na ƙarshe ne shiyyasa bance da kai komai ba. Amma tunda ka damu bari na baka wannan ɗin. Alhmdllh ba wani abu ke damunta ba sai infection, yayi tsanani ne sosai da har yake sakata ciwon mara, sai dai kada ku damu yanzu haka mun fara treatment ɗinta kuma komai zai zama normal”. Wani shegen kallo Dafeeq ke masa, dan abinda Doctor bai sani ba duk tattaunawar da sukai da Nadwa yaji ta, abinda kawai bai ji ba maganar datai masa a kunne, itama kuma ya gama tsara hanyar da zai san ko minene. Da yake makirine bai nunaba ko a fuska, sai ma damuwarsa daya nuna sosai akan ciwon Kainaat ɗin. Babu musu kuma ya amshi takardar magunguna yaje ya saya. Ɗakin da Kainaat ɗin take ya koma, ya samu Nadwa na bata shayi, zama yay a kusa da ita cike da kulawa yana jera mata sannu, ƙasan ransa kuwa ji yake kamar ya shaƙe banza dan ba abinda zancen cikin nan ya ƙara masa a zuciya face ƙara jin tsanarta. Da gaske shifa bai shirya haihuwa ba yanzu, koma zai haihu bada wannan tsohuwar guzumar ba mai bakin iyaye aka. Da Khadijah kawai zai iya yarda ya haihu, dan itace kawai ta dace da hakan. Kulawa sosai da hidima yake mata har abin na bama Kainaat mamaki, harma tana tunanin akwai abinda yake shiryawa a ransa amma ta gagara gane komai. Kwanansu biyu aka sallamesu. A ranar kuma Nadwa ta sanar mata tana da ciki. Shiru Kainaat tai tana kallonta kamar wata wawuya, sai da Nadwa ta zungureta tana murmushi. “K wai lafiya naga kin saki baki. Murna fa ya kamata muyi, dan ni tun a asibiti da doctor ya gaya min na gama shirya planing ɗin komai wlhy. Wannan cikin ai alkairi ne garemu baki ɗaya, ga shi kwata-kwata sati ɗaya ne da wasu kwanaki, kin san dai doctor Giɗaɗo kamar maye yake wajen gano ciki komai ƙanƙantarsa.....” “Yaron nan Dafeeq yasan da batun cikin?”. Kainaat ta jeho mata tambayar cikin katse ta. Kai Nadwa ta girgiza mata, “No bai sani ba, dan na hana doctor sanar masa. K hasalima ni kaɗaice na sani sai ke yanzu dana sanar miki”. “Alhamdullah yau zan koma asibiti a zubar da shi”. “Zubarwa fa?”. Nadwa ta tambaya cikin zare idanu, a zafafe Kainaat ta bata amsa da “Yes zubarwa, dan bana buƙatarsa. Abaan kawai nake fatan haifama ƴaƴa. Bandama rashin adalcin wannan cikin bai shiga a inda nafi buƙatarsa ba sai a gidan ƙazamin shashashan yaron nan. Ai ni abinma kunyane gareni ace inada cikin wannan ɗan tayin yaron wlhy. Dukiyata duka ta dawo hannuna, lokaci yayi da zan rabu da shi na komawa Abaan ɗina....” “Wannan shine dalilin daya sa bazan bari ki zubar da cikin ba ai Kainaat”. Nadwa ta katseta itama. Kallon Nadwan ta tsaya yi kamar ta samu tv. Kai Nadwa ta jinjina mata da faɗin, “Yes Kainaat bazaki zubar ba. Dan wannan cikin shine makamin da zai kai nasararki komawa ga Abaan kuma kici riba. Dan haka ma na hana Doctor Giɗaɗo sanarma sakaran yaron nan kinada cikin yace masa infection ne dake. Bari nayi miki kai tsaye, doctor Giɗaɗo zai kwantar mana da cikin nan na jikin ki, ke kuma zakiyi duk yanda zakiyi yaron nan ya sake ki a cikin watan nan. Zamu je wajen malamin nan da Mom, wanda yay miki aikin farko akan Abaan yazo da kansa ya maida ki. Bayan kin tare da kamar wata ɗaya sai a tada cikin, kinga zai zama matsayin na Abaan kenan, dama abinda kike fata shima yake fata hakama mahaifiyarsa kenan.” “Woow Nadwa dama haka kike sona ban sani ba?”. Kainaat ta faɗa cikin wani irin farin ciki hawaye na zubo mata, sai kuma ta rungumo Nadwa jikinta tana sake fashewa da kuka. Ta jima a haka kafin ta ɗagota. “Amma Nadwa kin manta doctor Giɗaɗo likitan Abaan ne, hasalima ta sanadinsa na sanshi. Kina ganin bazai ci amanarmu ba”. “Ko kaɗan bazaiyi hakan ba. Dan na shirya masa abubuwa kashi-kashi da koda wasa bazai taɓa iya cin amanarmu ba. Shine kuma kawai zai iya mana aikin Abaan ya yarda saboda da kike gani komai nasu nada ƙa'ida da tsari, idan ba likitan daya sani bane yace masa kinada ciki zargi zai iya shiga tunda nasan babu yanda za'ai batun aurenki bazai je masa ba. Dolene ma ai tunda yasan sai kinyi auren zaki halatta garesa”. “Tabbas hakane wannan kuma gaskiya ne Nadwa, nagode sosai ALLAH yabar zuminci. Shiyyasa a kullum nake sake jin banda wani ahali a duniya sama da ke da Mom. Kumin abubuwa da yawa wanda iyayena suka gagara mun.” “Common baby share kawai, ai ALLAH ne ya haɗa wannan ƙaunar tsakaninmu. Yanzu dai abinda zance miki mataki na gaba shine ki tattaro duka takardun kaddaririnki da kuɗaɗenki ki maidosu wajen Mom kafin ki fara yaƙin amsar sakin ki. Dan wannan yaron hatsabibine wlhy, bar ganin ya dawo miki da komai akwai abinda yake ƙullawa ne” “Na sani wlhy Nadwa, shiyyasa na shirya ta yanda zan san minene shirin nashi. Amma shawararki tayi kam, daga nan zuwa Monday in sha ALLAHU zan kammala haɗa komai na danƙashi ga Mom, na miki alƙawarin kafin cikar sati ɗaya wannan auren ya zama tarihi”. Dariya suka kwashe da shi harda tafawa, sai kuma duk suka gimtse bakuna suna kallon ƙofa. Kainaat ce ta fara sakin nata da faɗin, “Oh ashefa shegen baya nan ya fita. Sai kuma suka kwashe da sabuwar dariya suna tafawa. Wani kalar cije lips Dafeeq dake ta bayan windows duk yana jinsu yayi, sai kuma ya saki wani kalar makirin murmushi da faɗin, “Ni da ku za'a banbance shegun ai. Dan zan tabbatar muku CUTA CE TA ƊAU CUTA”.........✍️ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da biyar_ ________ *_ZAFAFAN DAI_*🫡🫡🔥🔥🔥🔥 *_NEW HOT BATCH 2024 DA ZAI TASHI KANKU FIYE DA NA BAYA IN SHA ALLAH_*🥵❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥🔥🔥🔥 *_KASANCE D'AYA DAGA CIKIN ZAFAFA FAMILY NA WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA HANYAR SIYAN TIKITIN SHIGA GROUPS NASU NA ZAFAFAN LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA_* 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥 _WANNAN DIN WATA DAMA CE TA MUSAMMAN A GAREKU WAJEN ZAMOWA CIKIN AYARIN IYALAN ZAFAFA_ *_LITATTAFAN SABUWAR SHEKARAR SUNE KAMAR HAKA_* *KWANKWASON JIMINA miss xoxo* *TSUTSAR NAMA Billynabdul* *GUDUN K'ADDARA Huguma* *AMEENATU Mamuhghee* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA LALE DA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ ___________ ......Kwance take shiru akan abin sallar data idar da sallar asubahi. Tayi wani irin fayau da ita da ke tabbatar da ita ɗin amarya ce a yau ɗin. Daren jiya ne ke dawo mata daki-daki tamkar a yanzu komai ke faruwa. A hankali ta sake lumshe idanunta da cije lips ɗinta tana murmushi. Kafin daren jiya ɗauka take duk duniya babu ya Dafeeq a fannin jarumta, sai dai daga daren jiyan zuwa safiyar yau ta tabbatar da cikakken gwarzon namiji abin nunawa tsara. Lallai a baya tanada kundi, kundi mai ɗauke da tarin ƙaddara abar a tausaya mata da rububin son a karanta. Sai dai a yanzu ta tabbatar da cewar sake buɗe sabon kundi mai ɗauke da sabon babin rayuwa, rayuwa mai matuƙar ƙayatarwa da sanya zumuɗi a zuciyar duk wanda zai nazarci sabon kundin nata dan a yanzun ne kam tayi miji mai amsa suna namijin duniya, ba'a shimfiɗa kawai ba har a al'amuran rayuwa duk da kuwa kwanaki biyu kacal tayi da shi a matsayin mijin. “I love you Hamma Abaan”. Ta furta a hankali saman lips nata. “I love you too Adda Khadijah”. Aka gwargwaɗa mata cikin kunne. Zumbur ta miƙe zaune jikinta na ɗan rawa, sai kuma ta waro idanunta cike da mamakin ganinsa. Sam bataji lokacin daya shigo ba balle sanin yana durƙushe a kusa da ita haka. Jitai kunya mai tsanani ta sake lulluɓeta. Miƙewa tai da shirin barin wajen shima ya miƙe yana murmushi. Hannunta ya riƙo ya figota ta faɗo jikinsa. Yanda ya rungumeta tsam a jikinsa da shinshinar wuyanta da yake yana sakar mata sumba yasa ta ƙamƙamesa itama batare data sani ba. Sai dai sai ƙoƙarin son ɓoye fuskarta take yi shi kuma ya hanata hakan. “Anya bai kamata ace kunyar nan ta raguba kuwa Baddo. Yanzu fa kika gama faɗin You love me, bai kamata kuwa a nuna min love ɗin nan a zahirance yanda zan manta hanyar gate ɗin gidan nan gaba ɗaya ba. Yanda nake ji banƙi ace daren jiya ya sake maimaita kansa a safiyar nan ba koma har abadan. Dan ya kasance dare na musamman a kaf dararen dana rubuta a kundin tarihina da bazan manta da su ba ya gama danne girmansu da cikar nasu tarihin. Khadijah ke ɗin ta dabance, dan kin min ƙyautar da bazan taɓa mantawa da ita ba, sannan kin tabbatar min da mata ma fa suna suka tara. ALLAH yay miki albarka, yanda kika kasance haka cakwai ALLAH yasa rayuwar aurenmu ma ta kasance haka cike da farin ciki da ƙaunar juna koma fiye da hakan. I love you so much alheran”. Ya ƙare maganar yana sakar mata wasu tagwayen sumba a wuya. Jin tsaiwa na neman gagararsu ya ɗagata cak zuwa saman gadon. Wani sabon shafin mai cike da tarihi suka sake buɗewa. Yayinda Khadijah ta sake tabbatar masa da itama mace ce fa, dan kuwa ta cire kunya wajen nunama Abaan da gaske tana son shi duk da kuwa tana ji a jikinta dan Abaan ba namijin wasan yara bane. Bayan nutsuwa ta riskesu suka nufi bayi domin tsaftace kansu. Sosai Khadijah ke jin kunya amma babu yanda ta iya dole ta haƙura sukai wankan tare. Dan shi Abaan mutum ne kai tsaye. Baya kwana-kwana akan duk abinda yay masa. Gadon ta sake kimtsawa sannan suka kwanta ramuwar barci tana lafe a cikin jikinsa kamar wata ƴar mage... Barci suka sha sosai kasancewar dama yau ya ɗauki hutun zuwa office. Dan sai sha ɗaya suka tashi. A yanzun ma tare sukai wanka tanata noƙe-noƙe. Bayan sun fito yace ta ɗauka masa kaya a ɗakinsa. Babu jimawa kuwa ta dawo da kayan. Da taimakon juna suka shirya tsaff, kasa ɗauke idanunsa yay daga kanta, dan tayi matuƙar ƙyau a cikin atamfar data saka. Ita kam data ɗago ta kallesa suka haɗa ido sai ta sunkiyar da kai tana murmushi. A haka suka fito falo, inda suka samu an gyara ko'ina tsaf hatta breakfast ɗin su nakan dining a tsare. Zaman karyawa sukai da lafiyayyen abincin da Mamy ta shirya musu da kanta. Suna kammalawa sashen Mamy suka nufa gaisheta. Sun sameta ita kaɗai a falo dan Noor da sauran baƙin da suka rage sun fita kasuwa. Cike da farin ciki da sha'awa take kallonsu. Yayinda Khadijah kanta ke a ƙasa. Cike da girmamawa ta kai durƙushe tana gaida Mamy. Hannunta ta kamo ta ɗagota, kusa da ita ta zaunar da ita tana murmushi, ta ɗan bata site hug da faɗin, “Daughter kunyar ce dai har yanzu. Nifa mamanki ce karfa kice zaki ɗaukeni a suruka. Da ke da Baffana da Noor duk ɗaya kuke kinji”. Kai Khadijah ta jinjina mata tana murmushi. Gaisheta shima Abaan yayi, ta amsa masa da kulawa sannan ya tambayi ina su Noor. Sanar masa sun tafi kasuwa Mamyn tayi tana maida hankali ga Khadijah da duk ta kasa sakewa. Har akai kiran zuhur suna sashen, anan ma ya barta ya wuce massalaci. Fitarsa babu jimawa su Noor suka dawo. Nanfa Khadijah ta sake miƙe ƙafa aka shiga hira. Har akai la'asar. Sai da Abaan yay kiran Noor a waya yace tazo sannan ta miƙe badan taso ba. Noor ta mata rakkiya har sashen nata sannan ta koma. A falonta ta sameshi zaune yana waya. Zama tayi a kujerar gefensa har ya kammala. “Dama haka amarya keyi ta manta da mijinta Baddo?”. “Kayi haƙuri”. Ta faɗa a hankali. Kansa ya ɗauke da ga kallonta yana faɗin, “It's ok bani rowa”. Tsam ta miƙe zuwa kitchen. Ya bita da kallo yana wani lumshe idanunsa a kasalance. Sai kuma ya ɗan cije lips ɗinsa da sakin murmushi mai ƙayatarwa. Shi kaɗai yasan irin farin cikin da nishaɗin da yake ji a yau ɗin nan. ALLAH dai ya basu zaman lafiya..... ____________★ Sosai al'amari yay matuƙar tsamari a ɓangaren JJ. Dan tun ana kiranyen Alimah har an haƙura sai addu'oi da aketa masa da neman magani. Matuƙar ƙawanya cututtuka da aka kasa gane kansu sun masa. Gaba ɗaya ya canja daga JJ ɗin nan ɗan gayu ɗan ƙwalisa. Ya rame sosai kamar kai cutar sida. Kullum cikin masa saukar Alkur'ani ake. Tun ma al'amarin na bama mutane tsoro har ya koma bada tausayi. Watanninsa biyar cikin tsananin jiyya a wani dare gobara ta tashi da shi wadda ba'asan musabbabinta ba. Sosai anguwa ta ruɗe, dan abin mamaki iyakar ɗakin da yake jiyya ne kawai ya kama da wutar a gidan. Da ƙyar da ƙyar aka samu aka kashe wutar, yayinda aka fiddo JJ cikin wani yanayi naban tashin hankali. Kai tsaye asibiti aka nufa da shi, in da likitoci sukai masa karɓar gaggawa dan gaba ɗaya jikinsa ya gama saluɓewa, hatta da fuskarsa ba'a iya tantancewa. Zuwa safiya labarin wannan gobara ya gama zagaye anguwa har da kafafen sada zumunta. Yayinda hotunan JJ suka fara yawo tare da labarin tsiyatakunsa na baya. Abin yi fa ya samu, dan dama duk sanda irin haka ta faru kakanji bakuna daban-daban musamman a social media. Ka shuka alkairi ma yaya kakare balle sharri. Al'amarin JJ ya zama wani abin tattaunawa a kowace kafar sada zumunta. Yayinda ƴammata da iyaye ke addu'a akan masu irin halin JJ ALLAH ya sake nuna musu iyakarsu. Wasu ma ko a zahiri suke bayyana sunayen waɗanda sukai musu irin yaudarar JJ ɗin. Nanfa rikici ya ɓarke tsakanin ƴammata da samari, kowa na faɗin albarkacin bakinsa akan ɗan uwansa da ƙoƙarin kare kansa. To komadai minene ta JJ kuma ta ƙare ai. Dan halin da yake a ciki babu tabbacin zai sake wata doguwar rayuwa kuma. Ga taimakon da ake nema ma wasu da sun ji tushen labarinsa sai suji ƙyashin badawa. Sai dai kawai idan kaje kaji yanda yake ihun kuka da roƙon likitoci su taimakesa su kashesa dan azabar ƙunar da yake ji zakaji tausayinsa kasancewar ka mai imani. Watannin JJ kusan takwas nannaɗe cikin bandage a gaba ɗaya jikinsa sai idanu kawai ALLAH yay masa rasuwa. Mutuwa ce data matuƙar girgiza duk wanda yasan sa a zahiri dama wanda ya san labarinsa da hotunansa a kafafen sada zumunta. Dan yanda hotunan nashi da labarinsa suka dinga yawo a baya a yayin mutuwar tasa ma hakan ce ta kasance. To shi dai tasa ta ƙare kuma ai. Sai fatan ALLAH ya shiryi ƴan baya idan masu shiryuwa ne. Idan kuma bazasu shiryu ba ya UBANGIJI ka fimu sanin miya dace akan azzaluman nan. Ka mana maganinsu ka kare ƴaƴayenmu da ƙannenmu dama mu kammu da ga shiga tarkon yaudararsu. Ya rabbi ka yafe mana kurakuran mu. Ka sanya duniya a tafukan hannunmu ka hanata tasiri a cikin zukatanmu. Ya rabbi ka wajabta mana tsoronka da soyayyar ANNABIN MU tsira da amincinka su tabbata a gareshi shi da iyalan gidansa. Ya rabbi kasa ranar mutuwarmu ta zama ranar farin ciki a garemu. Ya sabbi ka saka gaskiya a harsunan mu, zukatanmu, jikunmanmu da ayyukanmu baki ɗaya🙏😭.. ___________ A washe garin da aka sallamo Kainaat asibiti ta tattara komai nata ta danƙa a hannun Mom ɗin Nadwa da tazo dubata. Dan hatta kuɗaɗenta na banki kaf ta turasu a account ɗin Mom ɗin. Bayan Mom ɗin ta wuce gida ta kammala nata shirin tsaff akan Dafeeq. Dan zama tai a falo tare da ajiye biro da takarda tana jiran shigowarsa. Kusan awa biyu kuwa sai gashi ya dawo. A kallo ɗaya da yay mata ya gama karantar shirinta. Amma sai ya danne zuciyarsa ya ƙaraso cikin falon. Kusa da ita ya zauna cike da kulawa da kwantar da murya ya ce, “Hajjaju yaya dai! Badai jikin bane ko?”. Maimakon bashi amsa sai ta miƙa masa takarda da biron data ajiye. Kallonta yake cikin nuna alamun rashin fahimta, kafin yay ƙarfin halin faɗin, “Namiye kuma wannan ɗin?”. A gatsine ta ta ce, “Takarda ce da biro. A yau ina buƙatar saki na Dafeeq. Dan bazan iya zama da kai ba Dafeeq. Ka sanya min ciwon sanyi saboda tsabar son zuciyarka. Miyasa tun kafin aurenmu baka sanar min kana da infection ba ne?”. Murmushi yaso saki dan harga ALLAH tama bashi dariya amma sai ya dake. A ɗan ɗage cike da gatsen shima ya furta, “Ai auren mu auren zobe ne Hajjaju, babu saki babu yaji har abada. Banda abinki ma k yanzu ina zaki je da wannan abun da ke a tare da ke”. A wani kalar razane ta ɗago ta kallesa da faɗin, “Kamar ya?”. “Kamar yanda kika ji na faɗa mana. Hajjaju tunda har kin tabbatar na saka miki wannan ciwon bai kamata ai mu rabu ba dan kema zaki iya zuwa ki sakama wani. Kawai muyi haƙuri da juna a haka shine zai fi”. Wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, dan da farko ta zata cikin dake a jikin nata ya gane. Harara ta watsa masa da miƙewa ta jefa masa takarda da biron. “Babu ruwanka da abinda zai faru a rayuwata ta gaba, na baka awa ashirin da huɗu ka saken da arziƙi ko ka sakeni ta wuya.” fuuuu ta wuce rai a ɓace. Murmushi ya saki da kaiwa kwance jikin kujera yana wani cije lips. Sai kuma ya ciro wayarsa da ke aljihu yay ɗan danne-danne da kaiwa kunne. Cikin wata iriyar murya dake nuna tsantsar basanci ya furta, “Doctor aikin ka ya fara.” Murmushi mai ƙayatarwa Doctor Giɗaɗo ya saki da ga can, har Dafeeq na iya jiyo sautinsa. Cike da isa ya furta, “Yes Abokina.” Yanke wayar Dafeeq yay yana sakin wata shegiyar dariya harda ɗan bubbuga kansa a jikin kujera irin na na gama cin nasarar nan.. *_WASHE GARI_* Ƙarfe kusan goma na safe Kainaat dake ta shirye-shiryen matakin da zata ɗauka akan Dafeeq ta sakko ƙasa. Kitchen ta nufa neman abinda zata sakama cikinta saboda yunwar data tashi da ita mai tsanani. Tana ƙoƙarin ɗora tukunya a saman gas sabon maigadin ta yay sallama. Daga kitchen ɗin ta amsa masa tana ɗan leƙowa. Ganin yanda yake kamar a ruɗe ya sata tsayawa kallonta. Sai kuma a ɗan tsawace ta furta, “Ɗanjuma lafiya kuwa?”. “Babu lafiya Hajiya, dan wasu baƙine gasu can a tsakar gida suna dudduba gidan nan, sune suka ce a sanar muku wai masu gidan ne su suna buƙatar magana da ku masu hayar ciki”. “Haya kuma? Wace kalar haukace kuma wannan, kodai ka fara shaye-shaye ne Ɗanjuma? Kai ubanwa ya faɗa maka haya nake a gidan nan?”. Sai kuma a fusace ta nufi ƙofar fita batare data jira cewarsa ba.......✍️ _Tofa Hajiya Kainaat mike shirin faruwa haka ne kuma?_. _Amin afuwa da jina shiru kwana biyu, cikin ƴan hutuna ne ta saka bit a hanci gaba ɗaya hankalina ba'a kwance yake ba kwanakin nan🤦._ ____________ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da shida_ Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR MUNA SAYAR D KAYAN KITCHEN D FURNITURES N TURKEY D ABAYA AKAN FARASHIN SARI DA CAPSULES MASU KYAU D INGANCI. _________ *_ASHE SUN DAWO😱???!!_* _Su waye🤔?_ *_ZAFAFA BIYAR MANA_* *_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._* *_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA'ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_* *_ILMANTARWA!!_* *_NISHAƊI!!_* *_SOYAYYA_* *_BARKWANCI_* *_ƘAYATARWA_* *_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_* *_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._* *_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_* *_GUDUN ƘADDARA🏃‍♀️_* _(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za'a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za'a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_. *_KWANKWASON JIMINA...🦃_* _(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_ *_AMEENATU🧕🏻_* _(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za'a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_. *_TSUTSAR NAMA....🥩_* _(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 _________ .......“Sunana Alhaji mai-kuɗi. Ni ne mamallakin gidan nan a yanzu. Nazo ne nai magana da masu hayar gidan. Dan haka ina mijinki?”. Wani shegen kallo na amma ka haukace Kainaat taima dattijon mutumin. Kafin cikin rainin wayo ta ce, “Dama yanzu shaye-shaye ya wuce kan matasa har dattijai ma ɗorawa suke yi. To idan hankalin naka baya a tare da kai bari na dawo maka da shi jikinka. Sunana Kainaat, wannan gidan kuma mallakina ne. Idan ma wani sakaran ɗan damfarar ne ya siyar maka kai maza kafin ya ɓace ma ka karɓa kuɗinka.” Sheƙeƙe Alhaji mai-kuɗi yay dariya, shima dai kallon ke wawuya ce ya jefeta da shi, kafin cikin gadara da ƙyaɓe fuska ya dubi yaransa a umarce ya ce, “Wannan naga ƴar hau ce. Tunda bata buƙatar masalaha ku gaya mata na bata nan da kwanaki uku in ma ita kaɗai ce, in ma da mijinta suke tare su tattara su barmin gidana dan ina da buƙatarsa. Ku nuna mata shaida maybe ta farka a mafarkinta”. Yana gama faɗa ya fice yana wani takun faɗi kamar bajimin san da girma yayma yawa... Wani kalar ihun rashin mutunci Kainaat ta musu lokacin da suke ɗaga mata takardun, kafin ta koma ciki fuuu. Kai tsaye ɗakin Dafeeq ta nufa. Jin ƙofar gam-gam ta shiga masa bugun hauka. A fusace ya buɗe ƙofar, daka kallesa kaga wanda ya tashi abarci. Ranta ɓace ta ce, “Kazo nan kana barcin asara na rashin aikin yi. To sai ka fito ga wasu ƙadangarun bariki nan sunzo wai gidan nan nasu ne. Harda bamu notes na kwana uku”. “Kamar ya Notes?”. Ya faɗa cikin mamaki. Bata amsa masa ba ta juya a fusace. Da kallo ya bita, sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana komawa ɗakin bayan ya sakama ƙofar key. Tsalle ya dirga saman gado yana wani ƙaramin ihu. Sai kuma gimtse bakinsa yana waro idanu. Wayarsa ya ɗauka ya shiga dannawa, kafin yay dailing wata no da aka sakama Dr G. Tana fara shiga ya wani yi baya a saman gadon ya kwanta ƙafa ɗaya kan ɗaya like saraki ɗin nan dai. Yay filo da hannunsa ɗaya ɗayan na riƙe da wayar. Harta tsinke ba'a ɗaga ba, bai kawo komai a ransa ba ya ƙara kira. Nan ma dai ba'a ɗaga ba har sai da yay kira kusan huɗu sannan aka ɗaga ana ƙarshe tana gab da tsinkewa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yay sallama a gadarance. Daga ɓangaren Doctor Giɗaɗo ya amsa murya a sauƙaƙe tamkar yanama murmushi ko yanayin nishaɗi. “Aboki kana kira ina cikin aiki ne. Ykk?”. “Normal”. Dafeeq ya amsa a gadarance. Kafin cikin yamutsa fuska kamar yana gaban doctor ɗin ya cigaba da faɗin, “Naga mutanenka sun zo. Harya bada kuɗinne?”. Wata ƴar dariya doctor ya saki, sai kuma ya bashi amsa da, “Yes ai harma na damƙa masa takardun. Suma kuma yanzu haka duk sun iso hannuna.” Karan farko Dafeeq ya saki murmushi, sai kuma a ɗan zumuɗe ya furta, “Okay good. Yanzu mu haɗu da kai a inda muka saba haɗuwa. Amma kafin nan ka bama yaron nan nasu 1mil..”. “Okay an gama abokina, amma baka tunanin bama yaron kuɗi zai sa su Nadwan su fahimci abinda ya aikata. Ya kamata mu bari har sai ka bar garin, koma ka tafi da shi mana Please”. “No no, ai ni bana aiki da mutum sau biyu, na tafi da shi nima wataran zai iya cin amanata. Batun su Nadwa kuma ai bashi kaɗai yay aikin ba da taimakonka ne. Tunda da bata yarda ta sanar maka ina suke ba ai bazaka sani ba?”. “Yes kuma hakane. Amma inada shawara, bai kamata mu haɗu yau ba, mu ɗan bada ƙafa 3days okay”. Ɗan jimm Dafeeq yay kamar zancen bai shigesa ba. Sai kuma zuwa can ya furta, “Hakan bazai yiwu ba, nasan yau gidan nan akwai ƙura, anjima kaɗan zan nemeka kazo saika saman anan kawai”. Doctor ya amsa masa da “To babu damuwa”. Daga haka suka yanke kiran. Sai da yasha dariyarsa sannan ya saka jallabiya ya sauka ƙasa. Ya samu Kainaat zaune a falon da waya a hannu, da alama wani take nema amma ta gagara samunsa. Cikin wani irin sauri ya ƙaraso gareta. “Am sorry Baby. Na ɗan zagaya toilet. Please yimin bayani yanda zan gane ɗazun kin barni a duhu nikam”. Kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta shiga masa bayani a zafafe. Ta ƙare da faɗin, “Dafeeq narasa miyyasa hankalina ya gagara kwanciya. Yanzu haka kuma kiran wayar Nadwa da Mom nake amma babu wacce ta shiga.” “A'a miya haɗa wannan maganar kuma da su Nadwa?”. Cikin rasa control ɗin ta ta ce, “Takardun gidan nan fa dama duka documents ɗina suna hannunsu. Ina son jin ko an samu kuskurene da ga wajen su da har mutumin nan ke jin ƙarfin gwiwa, dan wlhy na hango tarin rashin mutunci a idon mutumin nan fa”. Wani kalar gyara tsaiwa yay cike da salon karyar da murya ya furta. “Oh yanzu Baby tsana da rashin yarda har takai haka a tsakaninmu. Ki ɗauki komai naki ki fita da su a gidan nan saboda ni?....” Da sauri ta shiga girgiza kai, sai dai ta gagara cewa komai. Shima bai sake cemata koman ba ya koma gefe ya zauna shi adole yayi fushi. Duk da taji wani iri sai dai batashi take ba. Ta cigaba da kai-kawo da neman layin Mom da Nadwa. Sai dai samun ya gagara. Da ga ƙarshe dole ta yanke shawarar fita. Ko kaɗan baiyi yinƙurin binta ba. Itama batako masa tayin hakan ba ta figi key ɗin mota ta fita. Mintuna kaɗan suka kawota ƙofar gidan su Nadwa, sai dai ta samu gida garƙame da kwaɗo. Mamaki ya kamata, tana tsaye tana ƙullawa da kwancewa maigadin maƙwaftansu ya leƙo. Da sauri ta nufesa tana tambayarsa ko ina masu gidan? Cikin rashin damuwa da kuma sanin da yay mata ya bata amsa da, “Ai sun tashi anan, sun kuma saida ma gidan jiyan nan. Ga wannan ma sukace a baki dan da alama dama sunyi tunanin zuwanki ma ashe”. Ya ƙare maganar yana miƙa mata brown envelope. Hannunta har rawa yake wajen amsa. Harta kama zata buɗe suka ji an tada mota. Da sauri suka waiga a tare, sai me har an birka motar a guje. Ihu ta shiga kurmawa tana tsalle da kiran ɓarawo-ɓarawo. Nan fa masu gadin gidajen layin suka shiga firfitowa a guje. Sai dai kamar asiri basu ko kama hanyar cimma ɓarawon ba. Hasalima ya ɓace ma ganinsu ɓat kamar abin rufa ido...... __________★ Tunda ya koma aiki kamar yanda ya saba ƙarfe biyar yake dawowa gidan. Yau ma hakane. Sashen mahaifiyarsa ya fara shiga suka gaisa kafin ya nufo nasu sashen. Tun kafin ya shiga wani ƙamshin turare mai ratsa zuciya ya gama cika masa ƙofifin hanci. Lokacin da ya gama shiga tsakkiyar falon sai yaji kamar ya shiɗe dan daɗin ƙamshin turaren wutar. Kamar mai jin zazzaɓi-zazzaɓi a hankali ya furta, “Baɗɗo am”. Murmushi Khadijah dake laɓe bayan labule ta saki, kafin ta yaye labulen a hankali jin ya sake kiran sunan nata. Wani kalar luuuu yay da idanunsa kamar mai shirin suman tsaye sai kuma ya buɗesu a slowly. Tabbacin ita ɗin ce dai ya saka shi jin numfashinsa na wani fita guda-guda. A hankali Khadijah da ke kallonsa ta sake sakin murmushi, sai kuma tai ɗan yi juyi a hankali. “Habba Baɗɗo am kasheni zakiyi? Maza zo gareni karna sume, Baɗɗo am Hammanki mai rauni ne akan ki common zo zo”. Yay maganar yana yafito ta cike da nutsuwarsa. Nufosa ta shigayi a ƙasaitance. Yayinda shi kuma ya buɗe mata hannayensa alamar ta shige jikinsa. Sai da tazo gab da shi ta wani saki murmushi da sakar masa gwalo da sauri ta koma ta bayansa ta ɗane tare da zagayo hannayenta duka biyu a saman cikinsa ta kwantar da kanta a bayan nasa ta lumshe idanunta tana murmushi da rungumesa ƙam-ƙam. Ajiyar zuciya mai ƙarfi suka saki a tare. Musamman ma shi da kwalliyar tata tai masifar hargitsa lissafinsa. Da ɗan tsumar jiki ya kama hannayenta da ke saman cikinsa ya zagayo da ita gabansa. Idanunta ta rufe gam tana murmushi. Shiko ya tsareta da kallo tun daga ƙafafunta har zuwa kan bomshot ɗin data saka na jeans blue da akaima adon stones masu ƙyalli, zuwa kan ƙaramar farar shirt data saka ta ɗaureta a saman ciki har kana iya ganin cikinta dake buɗe a yanayin gayu, zuwa ɗaurarren gashinta data raba biyu kowanne ta ɗaure kamar wata matashiyar budurwar turawa. Sai dai ita dan kawai baƙa ce. Sake kamota yay ya rungume tsamm a jikinsa, cikin raɗa a kunnenta tamkar mai tsoron a jisu ya furta, “ALLAH yay miki albarka Baɗɗo am. Yanda kike sanyani farin ciki, ALLAH ya faranta miki da sakamakon gidan aljanna ke da iyayenki da ahalinki baki ɗaya. I love you Baddo am”. “Amin ya rabbi Hamman Baɗɗo. Tare da kai da zuri'arka baki ɗaya. I love you too”. Ta faɗa itama tana manna masa sumba a dai-dai maƙoshinsa dan iya inda tsahon nata ke zuwa kenan. Fuskarta da take ƙoƙarin janyewa ya damƙe da tafukan hannunsa duka. Kallon juna sukayi cikin ido, a wani irin salo ya kashe mata ido ɗaya da sakar mata murmushi kafin ya kai lips ɗinsa kan nata. Ajiyar zuciya suka saki a tare, sai kuma suka lumshe idanu a taren nan ma. Sun jima a haka kafin su rungume juna na wasu mintuna. Sai da suka gama dai-daita kafin ta bar jikinsa, hannunsa ta kama suka koma cikin falon, ruwan data ajiye a Centre table domin shi ta zuba masa, sosai yasha yana saka mata albarka, kafin ya miƙe muryarsa acan ƙasa, “Baddo saura wanka.” Babu musu ta ɗan masa kallon shagwaɓa, sai kuma ta noƙe kafaɗa da faɗin, “Uhm-uhm ni hannuna ke ciwo da ƙafafu na”. “Please Baɗɗo am, nifa jikinne duka ke min ciwo, baki tausayina daga office fa nake nema muku na tuwo”. Ya faɗa shima cikin marairaicewa. “To sai in ka yarda zaka goya ni”. “Abu mai sauƙi” ya faɗa yana duƙawa. Ƴar dariya ta saki tare da hayewa bayansa tana ɗora fuskarta a wuyansa tare da hannayenta tana ƙanƙamesa. Murmushi yayi kawai shima yana ɗan lumshe idanu. Dan siririyar dariya tata ta shiga har ƙasan ɓargon jikinsa, ga ƙamshinta dake ratsashi. A haka ya nufi sashensa da ita, duk da tana da ɗan nauyi bai damu ba. Shi dai fatansa tai farin ciki kamar yanda shima take sakashi akoda yaushe. Shi kaɗai yasan yanda yake jin sati biyun nan da suka kasance a tare a cikin ransa. Dan sun zo da ɗunbin tarihi da bazai taɓa iya goguwa a ransa ba. Ko aurensa na farko baya jin ya shiga irin wannan nishaɗin. Kodan ita ɗin wannan ƙaramar yarinya ce yanda yake so haka yake juyata ta kuma masa biyayya babu gardama, saɓanin waccan da take sa'arshi idanunta kuma a buɗe oho shi bai sani ba. Har bedroom ɗinsa ya kaita, da taimakonta ya cire kayansa, sai dai duk yanda yaso kauda kai a kanta ya gagara hakan. Bai ma san sanda labarin ya canja ba sai tsuntar kansa da yay a wata duniya da fassarata badai baki ba. Yana jin farin cikin yanda sam bata masa musu. Ko yanzu tai kwalliya ya ɗakko hanyar ɓatata ko a fuska bazai taɓa ganin ɓacin ranta ba. Idan zai zo mata sama da babu adadi bata musa masa ko nuna gazawa koda kuwa ta cancanci ta gaza ɗin. Da ga ƙarshe tare sukai wankan, ya shirya itama ta saka rigarsa t-shirt data sakko mata sosai. Fita yay sallar magrib, itama ta koma sashenta tayi tata. Har isha'i sannan ya dawo, kamar yanda suka saba suka nufi sashen mamy dan can ne dandalin cin abinci da hirar dare. Duk da anan ma ta kusan raba yininta tare da Mamyn a yanzuma cikin zumuɗi ta tarbesu. Gaskiya Mamy nada daɗin zama sosai. Mace ce kamila mai tarin dattako. Dan halayen Abaan da yawa ya gajesu daga gareta ne. Abinda zai birgeka duk wannan soyayyar dake tsakanin Abaan da Khadijah da zaran sun je gaban Mamy sai kaga kowa ya kama kansa, yanda suke share juna bazaka ɗauka ma sunada wata alaƙa ba. Komai cikin dattako da girmamawa yake kasancewa. Bayan sunci sun ƙoshi aka buɗe babin hira. Tara da rabi nayi Mamy ta korosu sashensu. Cikin nuna ba haka suka so ba suka fito, Noor ko na musu dariyar tsokana. Suna fitowa Khadijah ta dogare tana tura baki gaba. Kallonta yay sai kuma ya saki dariya. Gwalo ya mata da faɗin, “Ai Mamyn ce ma maganin ki”. Baki ta sake turawa tana kai masa mintsini. Kaucewa yay, ta sake kai masa ya kauce. Sai kuma ya fara ɗan gudu tana binsa........✍️ *_ASHE SUN DAWO😱???!!_* _Su waye🤔?_ *_ZAFAFA BIYAR MANA_* *_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._* *_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA'ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_* *_ILMANTARWA!!_* *_NISHAƊI!!_* *_SOYAYYA_* *_BARKWANCI_* *_ƘAYATARWA_* *_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_* *_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._* *_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_* *_GUDUN ƘADDARA🏃‍♀️_* _(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za'a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za'a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_. *_KWANKWASON JIMINA...🦃_* _(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_ *_AMEENATU🧕🏻_* _(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za'a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_. *_TSUTSAR NAMA....🥩_* _(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_**_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da shida_ Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR MUNA SAYAR D KAYAN KITCHEN D FURNITURES N TURKEY D ABAYA AKAN FARASHIN SARI DA CAPSULES MASU KYAU D INGANCI. _________ *_ASHE SUN DAWO😱???!!_* _Su waye🤔?_ *_ZAFAFA BIYAR MANA_* *_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._* *_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA'ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_* *_ILMANTARWA!!_* *_NISHAƊI!!_* *_SOYAYYA_* *_BARKWANCI_* *_ƘAYATARWA_* *_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_* *_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._* *_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_* *_GUDUN ƘADDARA🏃‍♀️_* _(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za'a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za'a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_. *_KWANKWASON JIMINA...🦃_* _(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_ *_AMEENATU🧕🏻_* _(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za'a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_. *_TSUTSAR NAMA....🥩_* _(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 _________ .......“Sunana Alhaji mai-kuɗi. Ni ne mamallakin gidan nan a yanzu. Nazo ne nai magana da masu hayar gidan. Dan haka ina mijinki?”. Wani shegen kallo na amma ka haukace Kainaat taima dattijon mutumin. Kafin cikin rainin wayo ta ce, “Dama yanzu shaye-shaye ya wuce kan matasa har dattijai ma ɗorawa suke yi. To idan hankalin naka baya a tare da kai bari na dawo maka da shi jikinka. Sunana Kainaat, wannan gidan kuma mallakina ne. Idan ma wani sakaran ɗan damfarar ne ya siyar maka kai maza kafin ya ɓace ma ka karɓa kuɗinka.” Sheƙeƙe Alhaji mai-kuɗi yay dariya, shima dai kallon ke wawuya ce ya jefeta da shi, kafin cikin gadara da ƙyaɓe fuska ya dubi yaransa a umarce ya ce, “Wannan naga ƴar hau ce. Tunda bata buƙatar masalaha ku gaya mata na bata nan da kwanaki uku in ma ita kaɗai ce, in ma da mijinta suke tare su tattara su barmin gidana dan ina da buƙatarsa. Ku nuna mata shaida maybe ta farka a mafarkinta”. Yana gama faɗa ya fice yana wani takun faɗi kamar bajimin san da girma yayma yawa... Wani kalar ihun rashin mutunci Kainaat ta musu lokacin da suke ɗaga mata takardun, kafin ta koma ciki fuuu. Kai tsaye ɗakin Dafeeq ta nufa. Jin ƙofar gam-gam ta shiga masa bugun hauka. A fusace ya buɗe ƙofar, daka kallesa kaga wanda ya tashi abarci. Ranta ɓace ta ce, “Kazo nan kana barcin asara na rashin aikin yi. To sai ka fito ga wasu ƙadangarun bariki nan sunzo wai gidan nan nasu ne. Harda bamu notes na kwana uku”. “Kamar ya Notes?”. Ya faɗa cikin mamaki. Bata amsa masa ba ta juya a fusace. Da kallo ya bita, sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana komawa ɗakin bayan ya sakama ƙofar key. Tsalle ya dirga saman gado yana wani ƙaramin ihu. Sai kuma gimtse bakinsa yana waro idanu. Wayarsa ya ɗauka ya shiga dannawa, kafin yay dailing wata no da aka sakama Dr G. Tana fara shiga ya wani yi baya a saman gadon ya kwanta ƙafa ɗaya kan ɗaya like saraki ɗin nan dai. Yay filo da hannunsa ɗaya ɗayan na riƙe da wayar. Harta tsinke ba'a ɗaga ba, bai kawo komai a ransa ba ya ƙara kira. Nan ma dai ba'a ɗaga ba har sai da yay kira kusan huɗu sannan aka ɗaga ana ƙarshe tana gab da tsinkewa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin yay sallama a gadarance. Daga ɓangaren Doctor Giɗaɗo ya amsa murya a sauƙaƙe tamkar yanama murmushi ko yanayin nishaɗi. “Aboki kana kira ina cikin aiki ne. Ykk?”. “Normal”. Dafeeq ya amsa a gadarance. Kafin cikin yamutsa fuska kamar yana gaban doctor ɗin ya cigaba da faɗin, “Naga mutanenka sun zo. Harya bada kuɗinne?”. Wata ƴar dariya doctor ya saki, sai kuma ya bashi amsa da, “Yes ai harma na damƙa masa takardun. Suma kuma yanzu haka duk sun iso hannuna.” Karan farko Dafeeq ya saki murmushi, sai kuma a ɗan zumuɗe ya furta, “Okay good. Yanzu mu haɗu da kai a inda muka saba haɗuwa. Amma kafin nan ka bama yaron nan nasu 1mil..”. “Okay an gama abokina, amma baka tunanin bama yaron kuɗi zai sa su Nadwan su fahimci abinda ya aikata. Ya kamata mu bari har sai ka bar garin, koma ka tafi da shi mana Please”. “No no, ai ni bana aiki da mutum sau biyu, na tafi da shi nima wataran zai iya cin amanata. Batun su Nadwa kuma ai bashi kaɗai yay aikin ba da taimakonka ne. Tunda da bata yarda ta sanar maka ina suke ba ai bazaka sani ba?”. “Yes kuma hakane. Amma inada shawara, bai kamata mu haɗu yau ba, mu ɗan bada ƙafa 3days okay”. Ɗan jimm Dafeeq yay kamar zancen bai shigesa ba. Sai kuma zuwa can ya furta, “Hakan bazai yiwu ba, nasan yau gidan nan akwai ƙura, anjima kaɗan zan nemeka kazo saika saman anan kawai”. Doctor ya amsa masa da “To babu damuwa”. Daga haka suka yanke kiran. Sai da yasha dariyarsa sannan ya saka jallabiya ya sauka ƙasa. Ya samu Kainaat zaune a falon da waya a hannu, da alama wani take nema amma ta gagara samunsa. Cikin wani irin sauri ya ƙaraso gareta. “Am sorry Baby. Na ɗan zagaya toilet. Please yimin bayani yanda zan gane ɗazun kin barni a duhu nikam”. Kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta shiga masa bayani a zafafe. Ta ƙare da faɗin, “Dafeeq narasa miyyasa hankalina ya gagara kwanciya. Yanzu haka kuma kiran wayar Nadwa da Mom nake amma babu wacce ta shiga.” “A'a miya haɗa wannan maganar kuma da su Nadwa?”. Cikin rasa control ɗin ta ta ce, “Takardun gidan nan fa dama duka documents ɗina suna hannunsu. Ina son jin ko an samu kuskurene da ga wajen su da har mutumin nan ke jin ƙarfin gwiwa, dan wlhy na hango tarin rashin mutunci a idon mutumin nan fa”. Wani kalar gyara tsaiwa yay cike da salon karyar da murya ya furta. “Oh yanzu Baby tsana da rashin yarda har takai haka a tsakaninmu. Ki ɗauki komai naki ki fita da su a gidan nan saboda ni?....” Da sauri ta shiga girgiza kai, sai dai ta gagara cewa komai. Shima bai sake cemata koman ba ya koma gefe ya zauna shi adole yayi fushi. Duk da taji wani iri sai dai batashi take ba. Ta cigaba da kai-kawo da neman layin Mom da Nadwa. Sai dai samun ya gagara. Da ga ƙarshe dole ta yanke shawarar fita. Ko kaɗan baiyi yinƙurin binta ba. Itama batako masa tayin hakan ba ta figi key ɗin mota ta fita. Mintuna kaɗan suka kawota ƙofar gidan su Nadwa, sai dai ta samu gida garƙame da kwaɗo. Mamaki ya kamata, tana tsaye tana ƙullawa da kwancewa maigadin maƙwaftansu ya leƙo. Da sauri ta nufesa tana tambayarsa ko ina masu gidan? Cikin rashin damuwa da kuma sanin da yay mata ya bata amsa da, “Ai sun tashi anan, sun kuma saida ma gidan jiyan nan. Ga wannan ma sukace a baki dan da alama dama sunyi tunanin zuwanki ma ashe”. Ya ƙare maganar yana miƙa mata brown envelope. Hannunta har rawa yake wajen amsa. Harta kama zata buɗe suka ji an tada mota. Da sauri suka waiga a tare, sai me har an birka motar a guje. Ihu ta shiga kurmawa tana tsalle da kiran ɓarawo-ɓarawo. Nan fa masu gadin gidajen layin suka shiga firfitowa a guje. Sai dai kamar asiri basu ko kama hanyar cimma ɓarawon ba. Hasalima ya ɓace ma ganinsu ɓat kamar abin rufa ido...... __________★ Tunda ya koma aiki kamar yanda ya saba ƙarfe biyar yake dawowa gidan. Yau ma hakane. Sashen mahaifiyarsa ya fara shiga suka gaisa kafin ya nufo nasu sashen. Tun kafin ya shiga wani ƙamshin turare mai ratsa zuciya ya gama cika masa ƙofifin hanci. Lokacin da ya gama shiga tsakkiyar falon sai yaji kamar ya shiɗe dan daɗin ƙamshin turaren wutar. Kamar mai jin zazzaɓi-zazzaɓi a hankali ya furta, “Baɗɗo am”. Murmushi Khadijah dake laɓe bayan labule ta saki, kafin ta yaye labulen a hankali jin ya sake kiran sunan nata. Wani kalar luuuu yay da idanunsa kamar mai shirin suman tsaye sai kuma ya buɗesu a slowly. Tabbacin ita ɗin ce dai ya saka shi jin numfashinsa na wani fita guda-guda. A hankali Khadijah da ke kallonsa ta sake sakin murmushi, sai kuma tai ɗan yi juyi a hankali. “Habba Baɗɗo am kasheni zakiyi? Maza zo gareni karna sume, Baɗɗo am Hammanki mai rauni ne akan ki common zo zo”. Yay maganar yana yafito ta cike da nutsuwarsa. Nufosa ta shigayi a ƙasaitance. Yayinda shi kuma ya buɗe mata hannayensa alamar ta shige jikinsa. Sai da tazo gab da shi ta wani saki murmushi da sakar masa gwalo da sauri ta koma ta bayansa ta ɗane tare da zagayo hannayenta duka biyu a saman cikinsa ta kwantar da kanta a bayan nasa ta lumshe idanunta tana murmushi da rungumesa ƙam-ƙam. Ajiyar zuciya mai ƙarfi suka saki a tare. Musamman ma shi da kwalliyar tata tai masifar hargitsa lissafinsa. Da ɗan tsumar jiki ya kama hannayenta da ke saman cikinsa ya zagayo da ita gabansa. Idanunta ta rufe gam tana murmushi. Shiko ya tsareta da kallo tun daga ƙafafunta har zuwa kan bomshot ɗin data saka na jeans blue da akaima adon stones masu ƙyalli, zuwa kan ƙaramar farar shirt data saka ta ɗaureta a saman ciki har kana iya ganin cikinta dake buɗe a yanayin gayu, zuwa ɗaurarren gashinta data raba biyu kowanne ta ɗaure kamar wata matashiyar budurwar turawa. Sai dai ita dan kawai baƙa ce. Sake kamota yay ya rungume tsamm a jikinsa, cikin raɗa a kunnenta tamkar mai tsoron a jisu ya furta, “ALLAH yay miki albarka Baɗɗo am. Yanda kike sanyani farin ciki, ALLAH ya faranta miki da sakamakon gidan aljanna ke da iyayenki da ahalinki baki ɗaya. I love you Baddo am”. “Amin ya rabbi Hamman Baɗɗo. Tare da kai da zuri'arka baki ɗaya. I love you too”. Ta faɗa itama tana manna masa sumba a dai-dai maƙoshinsa dan iya inda tsahon nata ke zuwa kenan. Fuskarta da take ƙoƙarin janyewa ya damƙe da tafukan hannunsa duka. Kallon juna sukayi cikin ido, a wani irin salo ya kashe mata ido ɗaya da sakar mata murmushi kafin ya kai lips ɗinsa kan nata. Ajiyar zuciya suka saki a tare, sai kuma suka lumshe idanu a taren nan ma. Sun jima a haka kafin su rungume juna na wasu mintuna. Sai da suka gama dai-daita kafin ta bar jikinsa, hannunsa ta kama suka koma cikin falon, ruwan data ajiye a Centre table domin shi ta zuba masa, sosai yasha yana saka mata albarka, kafin ya miƙe muryarsa acan ƙasa, “Baddo saura wanka.” Babu musu ta ɗan masa kallon shagwaɓa, sai kuma ta noƙe kafaɗa da faɗin, “Uhm-uhm ni hannuna ke ciwo da ƙafafu na”. “Please Baɗɗo am, nifa jikinne duka ke min ciwo, baki tausayina daga office fa nake nema muku na tuwo”. Ya faɗa shima cikin marairaicewa. “To sai in ka yarda zaka goya ni”. “Abu mai sauƙi” ya faɗa yana duƙawa. Ƴar dariya ta saki tare da hayewa bayansa tana ɗora fuskarta a wuyansa tare da hannayenta tana ƙanƙamesa. Murmushi yayi kawai shima yana ɗan lumshe idanu. Dan siririyar dariya tata ta shiga har ƙasan ɓargon jikinsa, ga ƙamshinta dake ratsashi. A haka ya nufi sashensa da ita, duk da tana da ɗan nauyi bai damu ba. Shi dai fatansa tai farin ciki kamar yanda shima take sakashi akoda yaushe. Shi kaɗai yasan yanda yake jin sati biyun nan da suka kasance a tare a cikin ransa. Dan sun zo da ɗunbin tarihi da bazai taɓa iya goguwa a ransa ba. Ko aurensa na farko baya jin ya shiga irin wannan nishaɗin. Kodan ita ɗin wannan ƙaramar yarinya ce yanda yake so haka yake juyata ta kuma masa biyayya babu gardama, saɓanin waccan da take sa'arshi idanunta kuma a buɗe oho shi bai sani ba. Har bedroom ɗinsa ya kaita, da taimakonta ya cire kayansa, sai dai duk yanda yaso kauda kai a kanta ya gagara hakan. Bai ma san sanda labarin ya canja ba sai tsuntar kansa da yay a wata duniya da fassarata badai baki ba. Yana jin farin cikin yanda sam bata masa musu. Ko yanzu tai kwalliya ya ɗakko hanyar ɓatata ko a fuska bazai taɓa ganin ɓacin ranta ba. Idan zai zo mata sama da babu adadi bata musa masa ko nuna gazawa koda kuwa ta cancanci ta gaza ɗin. Da ga ƙarshe tare sukai wankan, ya shirya itama ta saka rigarsa t-shirt data sakko mata sosai. Fita yay sallar magrib, itama ta koma sashenta tayi tata. Har isha'i sannan ya dawo, kamar yanda suka saba suka nufi sashen mamy dan can ne dandalin cin abinci da hirar dare. Duk da anan ma ta kusan raba yininta tare da Mamyn a yanzuma cikin zumuɗi ta tarbesu. Gaskiya Mamy nada daɗin zama sosai. Mace ce kamila mai tarin dattako. Dan halayen Abaan da yawa ya gajesu daga gareta ne. Abinda zai birgeka duk wannan soyayyar dake tsakanin Abaan da Khadijah da zaran sun je gaban Mamy sai kaga kowa ya kama kansa, yanda suke share juna bazaka ɗauka ma sunada wata alaƙa ba. Komai cikin dattako da girmamawa yake kasancewa. Bayan sunci sun ƙoshi aka buɗe babin hira. Tara da rabi nayi Mamy ta korosu sashensu. Cikin nuna ba haka suka so ba suka fito, Noor ko na musu dariyar tsokana. Suna fitowa Khadijah ta dogare tana tura baki gaba. Kallonta yay sai kuma ya saki dariya. Gwalo ya mata da faɗin, “Ai Mamyn ce ma maganin ki”. Baki ta sake turawa tana kai masa mintsini. Kaucewa yay, ta sake kai masa ya kauce. Sai kuma ya fara ɗan gudu tana binsa........✍️ *_ASHE SUN DAWO😱???!!_* _Su waye🤔?_ *_ZAFAFA BIYAR MANA_* *_🤥AMMA NAKE ZAUNE NAN WANGALAU DA BAKI😨 KAMAR ƘOFAR RIJIYA. KAI AMMA DAI GASKIYA TAWAJENA BAKI ƘYAUTABA. MU ZAFAFA BIYAR NA FARA HARKA AI ZAMA YA ƘARE MANA, CIN DATA A BANZA DA GANTALI BABU WAJEN ZUWA A MEDIA KUMA YAZO ƘARSHE. BARI DAI KIGA DA SURUTUN NAN NIMA NAJE NA YANKO NAWA TIKITIN SHIGA A DAMA DAMU. KIN SAN IN ANA ZAFAFA BAKAI BABU DAMUWA, NISHAƊI ZALLA A LITTAFAN SU, KAI HARMA DA GIDAN COMMENTS._* *_WANNAN GASKIYA NE, INA KUKE MA'ABOTA KARANCE-KARANCEN LITATTAFAN HAUSA. KU GARZAYO MAZA GA WATA SABUWAR DAMA TA SAKE SAMUWA FA. DOMIN KUWA ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN DA KUKE TA JIN LABARI SUN SAKE DAWO MUKU DA WASU DABBIN SALO NA SABUWAR SHEKA MASU ƘAYATARWA_* *_ILMANTARWA!!_* *_NISHAƊI!!_* *_SOYAYYA_* *_BARKWANCI_* *_ƘAYATARWA_* *_ƳAR UWA KE MI KIKE JIRA ANATA YANKAR TIKITIN SHIGA JIRGIN ZAFAFA BIYAR AMMA KE KINA A NIGERIA GASHI KUMA YANA GAB DA TASHI. KIN YARDA DUK WANCAN ABUBUWAN NA SAMA SU WUCEKI? KENAN?_* *_HABA TAWAJENA MAZA GARZAYO A DAMA DAKE KEMA A WANNAN TAFIYAR. NASAN ZAKIJI DAƊINTA ZA KUMA KIYI ALFAHARI DA ITA. DOMIN MASU IYA MAGANA KANCE SAYEN NAGARI MAIDA KUƊI GIDA. TO SAYEN ZAFAFA HAR RIBA MA ZAKI MAIDA INSHA ALLAHU._* *_Ƙayatattun littafan naku sune kamar haka👇🏻_* *_GUDUN ƘADDARA🏃‍♀️_* _(Na SAFIYYA HUGUMA. kai daga jin sunan kasan za'a ɗauki darasi tare da ilimi harma da soyayya mai ƙayatarwa. Dan kun san HUGUMA bata kawo muku labaran banza. Za'a warwasa matuƙa da nishaɗi mai gamsarwa🥰🫡)_. *_KWANKWASON JIMINA...🦃_* _(HAFSAT MISS XOXO. Masu iya magana kance kwankwason jimina mai wuyar shafawa. Daga ji babu tambaya wannan littafi na ɗauke da darasi, ilimi na musamman, tare da gagarumar cakwakiya, ilimi harma da nishaɗi. Kun san dai Miss xoxo a fagen ƙayatar daku, ga soyayya mai tsayawa a zuciya kaji kamar ana zanata ne a cikin kanka.😍🫡)_ *_AMEENATU🧕🏻_* _(NA MAMU GEE. Kun dai san Mamun taku a fagen iya tsara labari, ta kasheku da sinƙi-sinƙin ƙauna ziryan mara gaurayen algus. Daga jin sunan littafin ma kasan za'a kwashi romon ƙauna da ilimin ƙulle mai gida a haɓar zane kai soyayya fa tayi. Kun san dai Mamu gee bata kawo muku labaran banza😘🫡)_. *_TSUTSAR NAMA....🥩_* _(NA BILYN ABDULL. Tofa cakwakiya. Lallai akwai tsallen tsalli watsanga kenan a wannan littafi. Kun san dai Bilyn taku wajen kawo muku darasin rayuwa, ilimi, nishaɗi, cakwakiya, kai harma da soyayya mai sa kaji kamar dan kai akeyi. Ƴan uwa akwaifa ƙura hummmm🫶🫡)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da bakwai_ __________ *_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._* *_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_* *_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*. *_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_* *_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*. *_TSUTSAR NAMA....!!_* _(Bilyn Abdull)_ *_AMEENATU_* _(Mamu gee)_ *_KWANKWASON JIMINA...._* _(Mss xoxo)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _(Safiyya Huguma)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 ___________ ........A kujera ya zube yana cigaba da mata dariya tsokana. Itako ta koma gefe ta zauna ta zabga tagumi kamar zata fasa kuka. Yatsa yasa yana ɗan cakularta taƙi kulashi, ya zame ɗan kwalinta ya ja mata gashi, nan ma taƙi ko motsi, ita a dole dai tayi fushi. Dariyarsa ya danne da ƙyar, ganin bazata kulashin ba ya fizgota ta faɗo jikinsa. Ƙankameta yay yana dariya da sakar mata kisses tako ina. Tun tana ture masa kai da zizzilewa harta nutsu luff a jikinsa suka koma dariyar tare. Daka gansu kasan suna cikin farin ciki da matuƙar ƙaunar juna... Washe gari yana dawowa daga massalaci sallar asuba a kitchen ya sameta tana ƙoƙarin haɗa masa breakfast. Rungumeta yay ta baya da sakar mata sumba a gefen wuya yana faɗin, “Good morning Baddo am”. Idanunta ta lumshe tare da sakin murmushi tana kai hannunta ta shafo kansa duk a lokaci guda. Sai kuma cikin sauƙaƙa murya a hankali ta furta, “Morning Hamman Baɗɗo. Ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya da yalwatuwar nutsuwa”. “In dai kina gefena akowane dare tashi da waɗanan abubuwan biyu, haɗe da farin ciki tamkar wajibi ne a gareni Baɗɗo am. ALLAH yay miki albarka ke dai, ya wadata zuciyarki kema da farin ciki ke da zuri'arki baki ɗaya. ALLAH ya ƙara min sonki, ya bani ikon ƙyautata miki da yi miki adalci a rayu. ALLAH ya haneni ƙuntata miki koda da mummunar kalma ne”. Wasu hawaye ne a hankali suka silalo a kumatun Khadijah. Soyayyar mijinta na ƙara ratsa mata ɓargo da zuciya. Ji take, inama duk mata su kasance kamar ita a gidajen aurensu. Da tabbas an samu farin ciki da wadatar zuci harma da ƙauna da farin ciki mara iyaka. Tayi imanin da mata da yawa sun daina shirka a domin maza.... “Uhm-uhm ni bana son kuka Baɗɗo, idan ba hakaba nima zan tayaki”. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan, yayinda shi kuma yake share mata hawayen. Cikin son canja yanayin nasu ya buɗe tukunyar dake kan wuta yana faɗin, “Mi surukar Mamy ke dafa wa mijinta?”. Hannunsa ta ɗan bige kaɗan tana hararsa, ba shiri ya saki murfin tukunyar. Baki ya tura mata, ita kuma ta hararesa da faɗin, “Sirrine babu mai gani sai a kwano.” bakin ya sake turawa irin nayi fushin nan. Ta masa gwalo da faɗin, “Oho dai bazaka gani ba. Tafi wanka ma an yafe taya hiran”. “Ni naki nake so”. Ya faɗa yana ƙara ɓata fuska. Cikin marairaicewa ta ce, “ALLAH Hamma rigimarka yawa gareta. Yaushe na gama aikin nan akaje wani wanka”. “Oho, nidai koma yaya ne ke zakiyi. Shiyyasa ma yanzu a office an fara cewa yanzu ina latti kuma duk kece baki saurin shirya ni”. “Kai Hamma ALLAH babu ƙyau sharri”. “Gaskiya dai”. Ya faɗa yana ja mata hanci da sakin murmushi. Itama sai ta saki dariya. Haka suka cigaba da aikin tare cikin nishaɗi. Bayan sun kammala ya jata part ɗinsa sukai wanka tare suka shirya tsaff sannan suka fito sukai karin. Sashin Mamy suka je dan tare zasu fita, zai maidata ganin likita. Tun cikar satinta guda yay mata magana game da inplan na jikinta. Sai ta sanar masa ai Baba da kansa yasa Mama da Ni'ima suka kaita asibiti aka cire tun bayan warware matsalarta da Dafeeq. Ya gamsu da hakan, amma dai ya kaita asibiti bisa shawarar Mamy. Doctor ya dubasu su duka ya kuma ɗaurasu akan magunguna da fatan ALLAH yasa iyakar wahalarce tazo. Tom yau sune cikar kwanakin da yace su sake komawa. Sun samu doctor ma na jiran zuwansu. Komai an musu shi cikin girmamawa da kulawa. Dan ba shi uban ginsamin ba hatta ita kanta Hajiya sama Hajiya ƙasa ake kiranta. Basu ci awa ɗaya ba cikakke suka fito. Shi suka fara ajiyewa a office ita kuma Awwal ya wuto da ita gida. Kai tsaye sashen Mamy ta wuce, dan tasan tana can cikin kaɗaici dan ma akwai masu aiki... __________★ Komai ya gama hargitsewa musamman a ɓangaren Kainaat da gaba ɗaya kanta ya gagara gane yanda abubuwan suke ma tafiya. Dan duk wanda tasan nada alaƙa dasu Nadwa ta nemesa a waya. Amsa ɗaya ce su basu san ina suke ba. Bama su san sun bar gari ba. Sannan nan fa Adamawa garin mahaifin Nadwa ne kawai. Mahaifiyarta ba ƴar nan ɗin bace, hasalima su basu san ƴar ina bace ba. Wasu suce Jos, wasu Lagos babu dai matsayar kamawa, itama kuma shaida ce akan hakan, sai dai ita sukan gaya mata Lagos da Jos ne garin su Mom, amma abin ALLAH ita bata taɓa binsu taje, su kuma bawani taron biki sukai taga danginsu ba tunda Nadwa dai har yanzu bata taɓa aure ba, ita kaɗai kuma suka haifa. Da ƙyar Dafeeq yake danne dariyarsa yana lallaɓata da faɗin ta kwantar da hankalinta. Sai dai kuma bayan sun buɗe takarda sun duba abinda ke ciki labarin ya canja salo, dan kuwa dai yanke jiki Kainaat tai ta faɗi a sume. Anan kam duk da Dafeeq na jin ransa fes shirinsa ya gama cika a kanta sai da yaji bazai iya guduwa ya barta ba kamar yanda ya tsara. Hankali tashe ya ɗaga waya domin kiran Doctor Giɗaɗo. Sai dai me, Number switch off. Cigaba yay da nema, amma dai still amsa ɗaya ce switch off ɗin dai. Da farko bai kawo komai a ransa ba ya jajibeta suka wuce asibitin su Dr Giɗaɗon. An musu tarba ta gaggawa saboda halin da Kainaat ɗin ke ciki. Dafeeq bai samu nutsuwa ba har sai da yaji ance ta farfaɗo tana ma barci. A lokacine ya nufi office ɗin Doctor Giɗaɗo. Sai dai ya samu a rufe, wata Nurse ke sanar masa ai duk yau ma Doctor Giɗaɗo bai shigo asibitin ba. Zuciyarsa taso ɗan shiga ruɗani, amma sai wani sashe ya gargaɗesa akan ba hakan bane. Kwanakin Hajiya Kainaat biyu a asibitin aka sallamesu. Sai dai har yanzu babu Doctor Giɗaɗo babu labarinsa. Tun Dafeeq na ɗaukar al'amarin wasa har lissafinsa ya fara canjawa. Gashi bai san ainahin gidan su Doctor Giɗaɗo ɗin ba, sai gidansa kawai ya sani, yaje ya samu kuma a rufe wai sunyi tafiya masu gidan. Yata bin Nurses na asibitin su sanar masa ko Dr Giɗaɗon nada wani gidan bayan wannan sun ƙi, da ga ƙarshe wani ke sanar masa Doctor Giɗaɗo fa ainahinsa baɗan Adanawa bane, kuma zaune yake shi kaɗai babu matarsa. Hasalima ba ɗan Nigeria bane. Ɗan Cameroon ne. Neman faɗi Dafeeq yayi, amma ya daure ransa da ƙyar suka bar asibitin zuwa gida a napep. Sun iso kowa da abinda yake tattaunawa a ransa, sai kuma mi, suka sami ƙofar gida danƙare da kayayyakinsu duk an fiddosu waje. Sai mai gadin makwabta ne ke sanar musu ai aikin wanda suka sayi gidan ne. Sannan kuma wani yazo ya bada saƙo a bama Dafeeq. Baibi takan saƙon ba hankalinsa ya karkata ga Kainaat dake tambayar ina sauran motocinta biyu. Da mamaki maigadin ya bata amsa da ai ƴar uwar nan tata da wanda ya bada wannan saƙon a bama mijinta ne suka ɗaukesu suka wuce. Neman yanke jiki ta faɗi tayi dan tasan dai Nadwa ce kowa ya sani matsayin ƴar uwarta, nan ma sai da Dafeeq ya riƙeta. Ganin mutane sun fara taruwa Dafeeq ya lallaɓata akan tazo suje gidan da ya zauna da Khadijah dan shi ya kasa fahimtar komai. Bata da zaɓin daya wuce binsa, dan wlhy jitake kamar kanta zai fashe... Sosai gidan yay kura, dan ba zama ake ba. Shi kansa yayi kusan wata biyu ma bai zo ba. Da dai yakan zagayo ya ɗauki kayan Khadijah yana shin shina wani lokacin harda hawaye. Sai dai wannan abin daya tasa gaba akan dukiyar nan ta Kainaat ta ɗauke hankalinsa kwana biyu. Kuka sosai Kainaat keyi na tashin hankali. Babu abinda ke juya mata a rai da ƙwaƙwalwa kamar batun wai Abaan ɗinta yayi aure sati ɗaya kenan daya wuce. Yanda take kukan ne ya sake hasala Dafeeq, a kausashe ya ce, “Wai minene kuma?!”. Cikin suɓutar baki tana ƙara fashewa da wani sabon kukan ta ce, “Yayi aure fa, kana ji wai ni Nadwa ke faɗama Abaan yayi aure”. Wani harara ya wulla mata zuciyarsa na tafarfasa. Sai dai yay dauriyar yimata banza ya ɗauke kansa kawai. Sai ma warware babbar envelope ɗin da maigadin nan ya bashi yake. Wayace a ciki, wayar da shi da kansa ya bama Doctor Giɗaɗo akan suna waya. Baima san sanda yay saurin shiga wayar ba, kamar an saita da video ya fara cin karo. Nadwa da Doctor Giɗaɗo da Mom suka bayyana. Wani shegen zabura da ya maido hankalin Kainaat kansa yayi. Ƙoƙarin miƙewa yake ya fita Kainaat ta warce wayar ta danna play. “K miye haka?!!”. Ya faɗa cikin daka tsawa. Ko kallonsa batayi ba ta maida hankali akan videon. Dan abu na farko da mutanen uku suka fara shine dariya a tare. Kafin Doctor Giɗaɗo ya ɗaga hannu ya ce, “Hy Dafeeq mijin Kainaat. Oh Hajiya Kainaat.” sai kuma suka kwashe da dariya. Sai da sukai mai isarsu sannan ya cigaba da faɗin, “Nasan zakuyi mamaki, matuƙar mamaki. Amma karku damu. Dafeeq kai tsuntsune mai wayo. Sannan ALLAH ya baka kwanya sosai. Sai dai matsalarka ɗaya ce baka da ilimi. Ƙarancin iliminka yasa ko kayi lissafi yake wargajewa batare daka farga ba. Zan fayyace farkon alaƙarmu saboda ko ita Hajjajun taka zata gani dan saƙon ya isheta. Hajiya Kainaat kamar yanda kika sani nasan Nadwa da mamarta ne a dalilinki kamar yanda na sanki a dalilin Alhaji Abaan. Mun ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakanina da Nadwa da jimawa lokacin kina tare da Abaan, sai dai mun rabu daga baya sakamakon wasu matsaloli. Tunda muka rabu bamu sake ganin juna ba sai randa aka kawoki asibiti, a dalilin gano kina da shigar ciki na nema number Alhaji Abaan domin na sanar masa. Sai dai yanda ya karɓi batun cikin naki yaban mamaki. Ina tsaka da taraddadi sai ga Nadwa. A wajenta nake jin ai kun rabu, yaron daya kawoki shine mijinki yanzu. Nasha mamaki, amma sai wani zancenta ya shafe min mamakin nawa. Ta nema mu ƙulla dil, in har na taimaka mata muka mallaki dukiyarki to lallai ko zata auran. Humm naji daɗi kamar zan mutu, dan ina son babyn nan”. Ya wani shafa ƙirjin Nadwa yana dariya da kashe ido duk da kuwa mahaifiyarta na wajen ko'a jikinsa balle ita. Cike da shaƙiyanci ya cigaba da faɗin, “Mun sami nasarar hakan, bayan ta amshe takardu da komai naki cikin siyasa sai kuma ga mijinki, shima yazo min da barazana, wai yaji duk abinda muka tattauna da Nadwa a office dan haka in ban bashi haɗin kai ba zai yimin miye-miye so soki burutsunsa na ƙuruciya dai da rashin ilimi. Niko na zarmashi ya shiga, nama nuna masa tsaronsa nake ji. Shine ya bani duk wani point dazan iya cimma gaci. Ada munyi niyyar barinki da motocinki da gidan da kuke ciki, sai muka fahimci ai ke da shi CUTA CE TA ƊAU CUTA. kawai mukazo suma mukai packaging nasu. A yanzu dai ki sanar masa ya daina wahal da kansa. Dan ni da matata Nadwa da Mom namu bama ma ƙasar, har abada kuma bazaku sake ganinmu ba byeeee”. Ya wani warwatsa yatsu kamar ɗan daudu. Dariya Mom da Nadwa suka sanya. Sai kuma can suka tsagaita. Mom ta fara magana, “Humm Kainaat Kainaat. Nasan zaki shiga mamaki, sai dai ki sani ba abun mamaki bane dan kece kika jama kanki. Kina da son zuciya, yanda na riƙeki a rayuwa ban taɓa tunanin zaki saka mana da mugun hali ba. Ke kin samu dukiya tsakaninmu dake sai dai kiɗan tsakura mana ko. Ƙyauta 500k bata taɓa haɗamu ba duk wahalar da mukai miki a rayuwa. Har ƙasar waje na kaiki karatu saboda ƴata, amma da kika samu mijin nunama Sa'a sai kika maidamu wawaye ni da ita. Sai abinda kikai ɗan niyyar sammana. To dama binki muke sannu a hankali har zuwa gaɓar data dace. Gashi mun kai, karma ki wahalar da kanki a neman mu. Yanzu haka mun sayar da kaf kaddaririnki har company ɗin, mun tsallake ƙasa, saboda lawyer ɗin da duk wani mai motsin kirki a companyn dama mune muka haɗaki da su. Ki taya ƙawarki murna sunyi aure da Doctor kuma, nima zan sami wani mai jini a jikan nai wuff da shi kamar yanda kikayi da wannan yaron Dafeeq yake ko mima oho muku. Dama ita bariki alalan gero ce, wanda bai iyaba saita kwaɓe masa. Tun barowarki gidan Alhaji Abaan muke fakon dukiyar nan, sai zuwan yaron nan ya sauƙaƙa mana aiki. Muna masa godiya, ga ladan aiki nan mun bar masa ya rage zafi 500k ne babu yawa.” itama tai mata wani salo tana kashe ido ɗaya.........✍️ *_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._* *_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_* *_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*. *_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_* *_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*. *_TSUTSAR NAMA....!!_* _(Bilyn Abdull)_ *_AMEENATU_* _(Mamu gee)_ *_KWANKWASON JIMINA...._* _(Mss xoxo)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _(Safiyya Huguma)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin ta takwas_ *_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._* *_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_* *_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_* *_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_* *_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_* _Littatafan sune kamar haka 👇🏻_. *_KWANKWASON JIMINA....._* _(NA MSS XOXO)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _( NA SAFIYYA HUGUMA)_ *_TSUSTAR NAMA....._* _(NA BILYN ABDULL)_ *_AMEENATU_* _(NA MAMU GEE)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 _________ ........Murmushi Nadwa tayi, sai kuma ta gyara kwanciya a jikin Doctor Giɗaɗo tana faɗin, “Ni dai shawara zan baki kamar yanda na saba. Kainaat ki nema iyayenki ki koma garesu, dan in dai Abaan ne ya miki nisa, kamar yanda yaƙi yarda da tayin aurena da naketa jelan masa, kema wlhy sai dai ki rasa dan ya miki nisa. Nisa irin na tsakanin samaniya da ƙasa. Shiyyasa nake ta fargar dake. A yanzu haka yana tare da ƙyaƙyƙyawar matarsa a gidansa cikin aminci da kwanciyar hankali. Dan haka ki riƙe shuga boy ɗinki yafi miki. Nasan zakiyita tunanin mune kuwa. Humm mune ɗin dai, a tunaninki bazan taɓa jin kishi a raina ba ne. Kefa ba ƴar kowan kowa bace. Mune mika ɗauke ki muka suturtaki da sutura ta ƙawa, muka kaiki ƙasar waje kikai ilimin da ya fiddoki har irinsu Abaan ɗin suka kalleki. Saboda mu ahalinsa suka yarda ya aureki ma. A tunaninki banda zuciyar da zanji a raina ni ya kamata na samu wannan bake ba. Nice fa keda komai ɗin, amma sai kika koma komai a kaina. Shiyyasa nai alƙawarin sai kin gama tattara mana mu kuma muji daɗin, dan na lura sam ke ba ƴar halak bace ba baki san halacci ba. Akwai fa lokacin da har gwadaki nai nace ki aramin 10mil zan fara Business amma matar nan kika nuna min baki da shi, ashe ƙarya kikeyi sai daga baya na gane hakan. Hummm kar dai na cikaki da surutu maybe idan kin haihu zan zo suna, ko in matar Abaan ta haihu nazo miki barka, a gaida angon jego Dafeeq byeeeee!🖖”. Ba Kainaat ba hatta shi uban gayyar jikinsa kakkarwa yake yi. Jin hajijiya na neman yadda shi ya wani zube a kujera. Dai-dai nan Kainaat ta fita gabansa. A bazata ta ɗaukesa da wani kalar wawan mari irin na bazatan nan. Domin kuwa bai tsammani zuwansa ba sai saukarsa yaji. A gigice ya ɗago, ta kuma sake ɗaukesa da wani haggu da dama. Rikicewa yay har kunnensa na masa wani dommmm. Nuna shi tai cikin fashewa da kuka ta ce, “Matsiyaci ɗan mage baka daɗin goyo. Azzalumi tsinanne, ashe da kai ma aka shirya komai” ta sake kai masa wani dukan. Gam ya riƙe hannunta yana huci, yanda nata jikin ke tsuma haka nashi keyi. Cikin rufewar idanu ya shiga kaimata duka tako ina. Ƙarfin mace da namiji ba ɗaya ba koda ace ta girmesa. Amma duk da haka tayi ƙoƙari itama ba kamar Khadijah ba. Dan duk abinda taci karo da shi wawusowa take tana ƙwala masa. Cikin ƙanƙanin lokaci sukaima kansu jina-jina. Sai da maƙwafta suka shigo aka rabasu anata mamakin yaushe ma suka zo gidan tunda ansan yanzu Dafeeq ɗin yayima gidan ƙaura. Tuni kuma an garzaya an sanarma Baba Hakimi abinda ke faruwa. Yanda suka jigata juna da raunika yasa dole suka nufi asibiti da su. Baba Hakimi kuma ya hana a sallamesu a ranar dan yamma tayi sosai sai washe gari. Da farko daya tambayesu abinda ya haɗasu shiru sukayi, sai dai bafade ya musu tsawa sannan Kainaat ta shiga zayyane komai tana kuka. Dan a ganinta mafitar da zata rabu da Dafeeq ɗin ce ma tazo mata. Sai dai me, maimakon samun yanda take ai nasiha Baba Hakimi ya musu. Batare daya kawo komai a ransa ba ya ce, “Kai Dafeeq in ma Khadijah ce ka kwantar da hankalinka. Dan yanzu haka tana gidan mijinta tai aurenta. Garama ka riƙe matarka ku zauna lafiya ku kuma ɗauki abinda ya faru matsayin ƙaddara. Dan kai da ita ɗin duk CUTA TA ƊAU CUTA ce kawai”. Tashin hankali kenan. Dan yanda Dafeeq ya miƙe zambar yana ɗura ashariya sai ma ka ɗauka ya haukace. Fadawa zasu saka a masa duka Baba Hakimi ya hana. Sai dai ya saka an fiddashi a fadar. Aiko a ɗimauce ya nufi gida ya fara haɗa kayansa sai Kano. Wannan al'amari ya sake haukatar da Kainaat, dan duk wanda ya ganta a ranar sai ta bashi tausayi. Kamar ba Kainaat ɗin nan ƴar gayu ƴar ƙwalisa mai ji da kuɗaɗe a gidan sanyi ba. Ta harmutse, ta hargitse, ta gama fita a hayyacinta abun ba'a magana.... A haukace Dafeeq ya iso Kano, sai dai kuma ya samu amsar da yaji inama bai zo ba. Dan ta tabbata dai Khadijah tayi aure. Yanda ake zuzuta masa labarin ta auri wani babban mutum mai kuɗi a Abuja ya nema saka zuciyarsa bugawa. Sai ga Dafeeq da kwanciya ciwo rejiff. Mamansa taso wannan karon ma taje tayi tujara a gidan su Khadijah baban Dafeeq ɗin ya taka mata birki da tuna mata gargaɗin d.p.o, dole ta haƙura ta cigaba da tsine-tsinenta a cikin gida kawai. Washe gari sai ga Kainaat itama ta iso Kanon kamar sabuwar kamu a hauka. Ta tada musu hankali akan sai fa Dafeeq ya saketa. Babansa yace idan har ya saketa sai ya saki mamarsa shima ya kuma tsine masa. Ai sune dai-dai da juna dan haka su cigaba da kasancewa a tare. Dan kuwa a haukar Kainaat ta kwancema iyayen Dafeeq ɗin komai ne wai dan su sakashi ya saketa. Sai kuma ta ɗaure kanta da kanta. Da farko itama Maman Dafeeq ta ce ya saketa jin kuɗi dai babu su. Sai dai furucin mijinta ya gigitata. Sai kuma cikin da Ƙainaat ke ɗauke da shi ya sake saka jikinta yin sanyi, dan duk duniya kuma babu abinda take buƙatar gani a yanzu sama da jinin Dafeeq ɗin. Wannan shine sanadin zaman Kainaat da Dafeeq a Kano dan su duka biyun ciwo ya kwantar dasu. Ita laulayi shi jiyyar zuciyar rasa Khadijah. Akwai randa harda su aman jini, sai da aka garzaya da shi asibiti. Kusan satinsa uku sannan aka sallamosu. Itama jikin Kainaat ya rikice, nanma suka garzaya asibiti, sai ake sanar musu ai cikinta a bayan mahaifa yake, dole sai sun lura da bata kulawa har lokacin haihuwa a ciresa ta hanyar cs dan yana cikin ƙoshin lafiya. Ina kainaat ta birkice musu akan sai dai fa a cire ciki, dan wata ƙawarta data samu irin hakan cire mata akayi tun yana wata uku. Anta tafka bala'i Dafeeq da Mamarsa sukace bazasu yarda ba, daga ƙarshe dai sai da aka dangane da police station, acan ne aka musu iyaka. Babu yanda zatayi dole ta haƙura dan bata da gurin zuwa yanzu, saboda satinta ɗaya da zuwa Baba Hakimi ya lodo kayansu a mota da ƴan rakiya aka kawo Kano. Acewarsa ya amshi gidansa Dafeeq ya cigaba da zama a gidansu. Dole fa aka share musu ɗakin ajiye-ajiye na gidan suke zaune anan. Idan fatara ta ishesu a zari wannan a siyar, a cire wancan a siyar, wataran ma Maman Dafeeq ɗin ke sata ta sayar basu sani ba. Dama dai kayan Ƙainaat ne masu daraja a ciki. Ga faɗa kullum kamar kaji. Yanzu basa jin nauyin ɗaga hannuwa su shararama juna mari. Saboda yana marinta itama take ware hannu ta sauke masa. Sai in zasu harƙume dambe ne Babansa ya tsawatar tare da tuna musu lalurar dake jikin Kainaat ɗin.... __________★ Yau ta kasance weekend, dan haka tun kusan sha biyu Abaan da Khadijah suka fita domin ɗan hutama ransu. Tunda aka kawota bayan asibiti babu inda ta taɓa zuwa sai yau. Yawo yayi da ita sosai wajaje daban-daban da suka nema juye kan Khadijah ta sake tabbatar da ganin Abuja yafi jinta ma. Dan wani wajen ma idan suka shiga ita mantawa take Nigeria ce fa. Bata wani ɓoyewa taita santi abunta da nuna al'ajabinta. Shiko Abaan na mata dariya da tsokanarta wai baƙauya. Sunsha hotuna, dan duk inda akeje cewa take suyi hoto dan ta nuna ma su Ni'ima. Tun yana tayata shikam harya gaji ya miƙa mata wayar tasa ta cigaba da ɗauke-ɗaukenta. Sai yamma lis suka dawo gida a gajiye. Washe gari kuma yace ta shirya zai fara koya mata mota. Jitai kamar ta suma a zaune dan sai da ya taɓata tai firgigit. Muryarta har rawa take ta ce, “Hamma mota fa?”. Murmushi ya sakar mata mai sanyi, sai kuma a hankali ya kwanto da kansa saman cinyarta. Hannunta ya kamo yasa a ƙirjinsa ya rungume. “Ko jirgi kike son koya zan kai ki a koya miki na sayo miki shi Khadijah. Kin san waye mijinki kuwa. K dai kawai kiyita bani farin ciki wlhy zan zame miki fiye da bawa. Ba koyan mota kawai ba, nan da sati uku zaki fara zana waec ɗinki in sha ALLAHU. Dan ina son ki samu kwalin Sakandire sai mu tattara inamu-inamu mu koma abroad ki cigaba da karatunki har sai kin kammala zamu dawo. In sha ALLAHU sai kin gogema iyayenki hawayen da kika sakasu zubarwa a shekarun baya. Sai kin zama abar kwatance. Yanda mutane da dangi suka dinga jifanki da ALLAH wadai a shekarun baya sai sun koma sanya miki albarka. Yaron nan daya zaluntar min ke sai kin koma kece mai taimakonsa a rayuwa. Fatana ni dai ki zama mai gaskiya, mai amana, mai kuma jajircewa......” A hankali hawayen da suke kwaranyo mata suka shiga ɗiga a kan fuskarsa. Murmushi ya saki tare da kai hannu ya share mata su. Sai kwai ta rungume kansa ta saki kukan mai ƙarfi. Tashi yay camak ya ɗauketa yay bedroom da kayarsa. Daga haka labarin ya canja salo... Kamar yanda yay alƙawari ya fara koya mata mota da kansa. Sai dai a wajen koyar motar nan ma babu abinda ake sai shan soyayya ziryan. Komai suna yinsa cike da farin ciki da nishaɗi ne. Cikin sati guda ya fara sakar mata steering. Khadijah mai ƙwazo ce tun acan baya. Kawai taso zubar da damarta ne a dalilin busar shaiɗan data Dafeeq. Sai dai yanzu kam alhmdllh. Lokacin da ta cika sati biyu ai sai dai ace Alhamdullah. Bata motar ake ta fita ita kaɗai ma. Sai dai abinda bata sani ba Abaan na biye da ita a ɓoye. Dan shi dai a tsorace yake. Sai da ya tabbatar komai Alhmdllh sannan ya iya dinga daina binta. A haka ta fara exam. Abinka da makarantar masu kuɗi komai ya riga ya mata da kansa, sai abinda ba'a rasaba ne ya kaita ta ƙaƙƙarasa yi kafin farawar, ya kuma dage da koya mata abubuwa shi da Noor. Kai har Mamy ba'a bari a baya ba ta bada tata gudunmawar. A haka dai ta fara jarabawar, cikin amincin ALLAH kuma suka kammala lafiya. Tana cigaba da zuwa ganin doctor duk sati, dan gaskiya zubar mata da ciki da Dafeeq ya dingayi da abinda suka saka mata a jiki yaso mata illa. Amma Alhmdllh da yake akwai kuɗi yanzu kam Abaan ya dage sosai. Sai dai bai taɓa sanar mata abinda Doctor ɗin ya faɗa mata game da matsalar da taso samu ba a mahaifarta. Dan har ɗan ƙaramin aiki sukai mata batare da an warware mata al'amarin kai tsaye ba. Ya kuma gargaɗi likitan akan kada ya taɓa sanar mata komai ya riga ya wuce kawai. Watansu uku da aure ya ɗauketa suka nufi Kano. Inda ta samu iyayenta cikin ƙoshin lafiya da wadatar zuci. Ga gidansu yasha gyara sosai kamar bashi ba. Babanta na sake samun kulawa ta musamman ashe har Egypt Abaan ya kaisa amma yace kar a faɗa mata. Sai da suka zo ɗin nan ta sani a bakin Jamila. An buɗema Baba ƙaton store na shinkafa a bakin titi. Aiko bawan ALLAH yay fes da shi kamar bashi ba, duk da dai har yanzu yana ɗan tafiya da sanda haka dan ƙafarsa na shagiɗawa. Jitai kima da darajar Abaan da mahaifiyarsa ya sake girma a idonta. Kai ita kam bata san mizata sakakankama mutanen nan da shi ba a rayuwa. Tururuwa matan anguwa da yara da ƴammata suka dingayi ganinta. Dan tuni anguwa ta ɗauka Khadijah tazo a wata mahaukaciyar mota. Dan tsiyar da Abaan yay musu ita kaɗai ya bari ta shiga anguwar tasu a wata zazzafar mota yace mata zuwa dare zai ƙaraso dan yana da meeting a gidan gwamnati. Aifa ta janyo magana, dan har gidan su Dafeeq aka kai ma mamarsa labari. Sai ta dinga koro mutane da zagin cin mutunci da tsinuwa. Mutane kam nata mata dariya sun maidata mahaikaciya. Alokacin Dafeeq da Ƙainaat na asibiti sun je ganin doctor dan sam bata jin daɗi, cikin na matuƙar wahalar da rayuwarta, gashi a bayan mahaifa, ta kumbura matuƙa babu ƙyan gani. Koda suka dawo kuma dare yayi, Mama ta katsatstsare dan kar Dafeeq yaji labarin Khadijah tazo. Washe gari da asuban fari ta sashi gaba suka tafi wani ƙauye wai amsar magani, sai da tai yanda tai suka kwana acan. Sai washe gari suka dawo a randa su Khadijah suka wuce.........✍️ *_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._* *_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_* *_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_* *_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_* *_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_* _Littatafan sune kamar haka 👇🏻_. *_KWANKWASON JIMINA....._* _(NA MSS XOXO)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _( NA SAFIYYA HUGUMA)_ *_TSUSTAR NAMA....._* _(NA BILYN ABDULL)_ *_AMEENATU_* _(NA MAMU GEE)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na talatin da tara_ Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR MUNA SAYAR D KAYAN KITCHEN D FURNITURES N TURKEY D ABAYA AKAN FARASHIN SARI DA CAPSULES MASU KYAU D INGANCI. ___________ ........Rayuwa taima ango Abaan daɗi fiye da yanda yay hasashe. Hakama amarya Khadijah dake samun kulawa a garesa da ahalinsa. Idan kaje gidan dolene rayuwar cikinsa ta burgeka musamman yanda kowa ke girmama ɗan uwansa. Tsakanin ango da amarya kam ai ba'a cewa komai. Dan soyayya ce mai tsafta da tarin birgewa, tuni Abaan ya kaɓar da ƴar sauran kunyar Khadijah musamman idan an shiga daga ciki. Yanda soyayyarta tai tasiri garesa haka itama tashi tuni ta mata shigar sauri saboda nagartattun halayensa. Bayan sun dawo Kano ya bar ƙasar. Ya barta da damuwar rashinsa kusa da kaɗaici, sauƙinta ma ta koma zuwa wata babbar islamiyya anan kusa da su. Sashenta kawai masu aiki ke gyarawa, nasa kuwa ita da kanta take wannan aikin batare da jin gajiyawa ko ƙosawa ba kullum duk da baya nan. Takan shiga sashen Mamy susha hirarsu, dan Noor ma tana zuwa aiki. Satinsa biyu ya dawo aka cigaba daga inda aka tsaya. Ita ke tsaye kan hidimar mijinta da safe. Hakama idan lokacin ɗora abincin rana yayi tayi musu da kanta dan in har Abaan na Abuja zuwa ake a amsar masa abincin rana daga gida akai masa office. Dan haka nan ma ta riƙe ragamar girkin rana. Bana safe da rana kawai ba, na daren ma ita ke shirya musu abincin mara nauyi, sannan ta koma sashensu tarbar mijinta duk da in har ya shigo gidan ƙa'idarsa ce sai yazo ya fara gaishe da mahaifiyarsa sannan, hakama idan zai fita sai yazo ya mata bankwana. Idan sun kamala ƴan hidimominsu kamar taimaka masa yay wanka da sauransu zai wuce massalaci har sai anyi isha'i ya dawo. Sukan nufi sashen Mamy ita da shi suyi dinner acan. Daga haka ai zaman hira. Goma nayi Mamy ke korosu, wani lokacin ma tara da rabi tace suje sashensu su ƙarasa hirar acan tagode. Noor kan dinga musu dariya dan su sunfi son ayi hirar anan. Saboda Mamy mace ce data san kanta. Dolene ma idan ka zauna da ita komanta ya dinga birgeka. A koda yaushe cikin gyara Khadijah take batare da Khadijahn ta farga ba. Dan ita dai sai dai kawai a bata abu ace ta shanye ko ta ci. Ita kuma saboda biyayya bazata taɓa tambayar Mamyn minene wannan ba balle ta musa sha kota zargi wani abu. Halayen Khadijahn na sake saka ƙaunarta a zuciyar mijinta da mahaifiyarsa harma da ƙanwarsa ɗaya tilo data zame mata ƙawa a yanzu duk da ta girmeta. A wannan hali kwanci tashi Khadijah da Abaan suka cika wata goma da aure. Akan samu sassaucin yawan faɗa ko rigima ta ma'auratan zamani, ba komai yasa hakan ba sai kasancewar su su duka biyun masu haƙuri ne. Sannan Abaan ya girmi Khadijah nesa ba kusa ba, takanyi abu da yawa yay masa kallon ƙuruciyace kawai ya share. Wanda kuma ya zama dole yay magana a kansa sai ya zaunar da ita cikin nasiha ya ankarar da ita kaza ba dai-dai bane kazane dai-dai. Hakan da yake na ƙara saka girmansa da kimarsa a wajen Khadijahn, dan takanyi ƙoƙarin ganin ta kiyaye duk abinda zai ɓata masa rai. Takanyi waya da iyayenta a wayarsa, dan ita har yanzu bata da waya, bai siya mataba ba kuma ta taɓa masa magana ko nuna ta damu da son a sai mata ba duk da tana buƙatar hakan. Ko magana yake son yi da ita idan yana office sai dai ya kira wayar Mamy yace ta bata dan yasan da rana suna a tare idan bataje islamiyya ba. Idan kuma zatai waya da ko su Zuhrah ne tashin take amsa kota Mamy ko Noor. Bata taɓa nuna damuwar hakan ba garesa ko waninsa ko taji a ranta ana raina mata wayo. Sai dai ma takan ɗan ji kunyar cewa su ara mata tai wayarne wasu lokutan, koda tana da buƙata sai kawai ta haƙura. Abinda Khadijah bata sani ba Abaan na gwadata ne kawai, dan Mamy tasha masa faɗan ya saya mata waya sai yace tayi haƙuri zai saya akwai abinda yake yi ne. Mamy tasan halinsa, dan haka ta saka masa ido kawai akan hakan. Dan daga baya itama sai ta fahimci dalilinsa akan ƙin sayen wayar. Ana cikin haka yay tafiya waje ya barta bata jin daɗin jikinta, takuma ƙi yarda suje asibiti, to anan ne fa shima abin ya fara cin ransa. Dan da rana dai yakan kira su Mamy su bata. Da dare kam yana son waya da matar tasa ko zaiji raguwar kewarta da lafiyarta babu dama. Da farko ya fara saka Noor ta bata tata, sai kuma nata saurayin yayta kira, wani lokacin kuma sanda shi zai kira saurayin Noor ya riga ya kira sai hakan ya ƙona masa rai. Ai fa babu arziƙi kwanansa goma sha biyu sai gashi ya dawo. Sam babu wanda yama san da dawowar tasa, dan ita Khadijah ma ranar jikinta ya takura mata ko sashen Mamy bataje hira ba, tadai je ta gaisheta ta dawo sashenta ta kwanta. Cikin barci sama-sama take jin ƙamshin turarensa na hawar mata kai. Idanunta da sukai matuƙar nauyin barci ta buɗe a hankali. Lumshewa ta sake yi, sai kuma ta sake buɗewa domin tabbatar da shi ɗinne ko mafarkin data saba take yi. Shi ɗinne dai ba mafarkin take ba. Tashi tai da sauri, sai dai mi, ƙamshin turarensa na bugarta a guje ta nufi toilet sai amai. Hankalinsa ya tashi, ya taimaka mata ta gyara jikinta suka fito yana mata faɗan ya akai take barin ƙofa buɗe sauro na shigowa, dan shi zatonsa malleria ce, tunda yaga sanda aka kawota haka taita amai tana zazzaɓi. Ita dai batace da shi komai ba, sai faman toshe hanci ma takeyi. Karon farko Mamy tazo sashensu tunda Khadijah tazo gidan, itace ta fahimci halin da Khadijahn ke ciki, tai mata tambayar ƙamshin miye bata so. Da ƙyar ta sanar musu turaren jikin Hamma. Idanu sosai ya waro waje, mi Noor zatayi inba dariya ba. Har sai da ya harareta sannan ya miƙe fuuu ya fita shi yaji haushi. Ita kanta Mamy sai da tai murmushi. Koda ya fitan ma Khadijah ta kasa sukuni, dan tace har lokacin tana jin ƙamshin. Dole aka haɗa turaren wuta da yawa Noor ta saka ako ina. Sai da aka ɗauki lokaci ga ac sannan tace ta daina ji, lokacin kuma Mamy ta kira Abaan da tunda ya tafi sashensa bai dawo ba tace yay kiran doctor. Duk wanda ke a cikin wannan ahali yau kasan yana cike da ɗunbin farin ciki mara misali, dan hatta doctor daya tabbatar da ciki a jikin Khadijah yasha ƙyaututtuka. Tuni Abaan ya rungume Khadijah a gaban Mamy babu ko kunya, turaren ko da tace bata son ƙamshinsa duk da tsadarsa haka ya ɗauka ya bama Awwal shi, yace an bar sakawa. Sai ya koma idan ma zai saka turare sai ta zaɓi wanda ƙamshin yay mata koda shi baya so kuwa. A haka ta cigaba da rainon cikinta da kulawa, dan kowa tattalinta yake kamar ƙwai a cokali a gidan. Batun tafiya karatunta kuwa dole ya tsaya dan boss yace sai ta haihu kuma. Bata damu ba, dan abinda mijinta ke so shi take so itama. Cikinta na wata shida Ni'ima ta haihu. Da farko dai Abaan yaso ya hana zuwan, amma ta saka masa rigima dan tunda sukai aure zuwanta ɗaya Kano bata sake ba. Sai dai Auta da Jamila sun zo mata hutu sau biyu, yanzu haka ma so take jamilar ta dawo kusa da ita saboda yanayin cikinta. Sai da Mamy tasa baki ya yarda taje jin cewa har Mamy zata je. Haka suka ɗunguma sai Kano ta dabo. Sun sami tarba ta mutunci da girmamawa. Dan Mama tata roƙon Mamy akan su sauka anan, hakan kuwa akayi. Kasancewar ana gobe suna suka je washe gari tunda safe suka nufi gidan Ni'ima mai jego, inda suka sami itama Zuhrah na fama da nata cikin, dan tsakaninsu da Khadijah kaɗan ne. Babu zato sai ga Abaan, ta dinga harararsa dan bata san zai zo ba. Shiko yana mata dariya ƙasa-ƙasa dan yana tare da su Adams ne da wasu abokansu. Yaro kuma an masa takwara da Abaan ɗin ne. Zokaga murna wajen Khadijah da Abaan. Aiko yaron nan yasha ƙyautuka. Suna ya ƙayatar sosai, Abaan yasa rigimar ranar zai koma da matarsa har sai da Mamy ta tsawatar masa. Aiko yace in dai bazata koma Abuja ranar ba shima bazai koma ba yana nan Kano har sai sanda zasu tafi. Mamy tace yaje ya ƙarata. Kwanakinsu uku a Kano sukai shirin dawowa Abuja. Kusan sha ɗaya na safe Khadijah ta shirya dan zuwa ta gaida wani kawunsu dake can ƙasan su. Hakan yasa Abaan da yazo yace tazo ya kaita. Dama tare suke da Noor. Tafe suke a mota cike da nishaɗi suna hirarsu. Da wani kalar sauri Abaan ya taka birki dan kaɗan ya rage ya buge wata yamutsatstsiyar mata goye da yarinya a baya ta fito a wani gida a guje da icce a hannu tana ɗura ashar manya-manyan. A harzuƙe ya taka birki, sai dai kafin yay magana sai ga wani mutum shima ya fito da nasa iccen a hannu yana zagin shima na rashin mutunci. Matar ya wulwuloma iccen, saura kaɗan akan Khadijah da ke ta saitinsu tayi zuru tana kallonsu kamar mai son tuna ina ta sonsu. Tofa, an taɓo abinda Abaan bazai iya haƙuri ba, tuni ya ɓalle murfin mota Noor na take masa baya. Amma mi yana fitowar ya iso gabansu da nufi masifa yaja yay turuss kamar yanda matar nan mai goyo tai tsaiwar sojan badakkare ta zuba masa ido kamar zata suma. Dan namijin har ya ƙaraso gareta zai wanka mata mari sai kuma shima ya tsaya cak jin cikin wata irin murya mai rawa da karkarwa ta ambaci “ABAAN!!”. Kasa amsa mata Abaan yayi, dan shi ƙoƙarin tuno ina yasan fuskar tata ma yake amma ya kasa. Sai da Khadijah data kasa haƙuri ta fito da sassarfa. Kainaat ta nuna sai kuma ta kalli Dafeeq da ya wani mugun rama yay rakwaf a tsaye kamar wani ɗan shekara arba'in da ɗoriya saboda wahala. Cikin son tabbatarwa ta ce, “Wai da gaske Kainaat da Dafeeq ne?”. Da sauri Abaan ya kalleta ya ce, “Kainaat kuma Baɗɗo am?! Dama kin santa ne?”. “Yess Hamma nasanta, ai itace ta auri Dafeeq gashi nan.” Juyawa yay ya kalli Dafeeq ɗin da jikinsa ke rawa. Dan wani kalar kallon Khadijah yake kamar idanunsa zasu zazzago ƙasa dan tashin hankali da ruɗanin Ganin Khadijahn tamkar wata baƙar balarabiya, ga cikinta ya fito ɗas yay mata ƙyau. Wani shegen kishi ne ya ziyarci zuciyar Abaan. Hannun Khadijah ya kamo ya riƙota jikinsa. Batare da yace komai ba ya nufi mota da ita. Sakata yay, shima ya shiga ya zauna. Hakan yasa itama Noor dakema Kainaat wani kallon ƙyama da tsana ita da Dafeeq ɗin taja tsaki ta shige mota. Ko kallansu Abaan bai sake yi ba ya birga motar sukai gaba. Har sukaje gidan kawun babu wanda ya sake magana. Kusan awarsu ɗaya a can suka sake dawowa gida. Ƙofar gidan da suka bar su Dafeeq suka samu cike tamm da mutane, Abaan yayi niyyar wucewarsa sai dai kuma ya tsaya jin mike faruwa?. Wata mata ce ke sanar musu ai Dafeeq da matarsa ne wani mai napep ya buge yay tafiyarsa. Yay musu horn yay musu amma suna tsaye a tsakiyar titi kamar gunkina shiko yabi takansu dan barikinsu ba ɓoyayya bace a anguwar. Kullum ne sai sunci uban dabe har titi, a garin dabben nasu ne ma suka makema uwar Dafeeq ɗin ido yanzu haka ido ɗaya ne da ita ɗayan ya tsiyaye. Ubansa kuwa tuni ya gudu garinsu yay aurensa. Har Kainaat ɗin nada ciki haka suke zuba dambe, yanzu ma data haihu kuma basu daina ba, a kullum faɗan nasu bai wuce kan abinci sai kace karnuka. Dan shi dai Dafeeq ɗin baya aikin komai balle sana'a sai zaman gulma a majalisar abokai, yanzu haka suma sun gaji sun korosa. Ita kuma Matar tasa wahala tasa tana bin gidajen mutane tana wankau ana bata sauran abinci da kuɗin da basu taka kara sun karya ba. Shi kuma da son zuciya idan ya gani yace zai ƙwace hakan ke haɗasu faɗa kullum a tsakkiyar anguwa. Yau kuma ance wai shi tsohuwar matarsa ya gani, ita kuma tsohon mijinta sun zama mata da miji suma shine sukai sumar tsaye har mai napep ɗin yazo yay awan gaba da su. To yanzu dai gasu can anyi cikin gida da su...... Noor ce taja tsaki saboda gajiya da surutun matar, cikin hasala tace, “Please Hamma mutafi Mamy na jiranmu muka zauna jin wannan shirmen banzar”. Numfashi ya ɗan sauke kawai yana ƙoƙarin tada motar Khadijah ta ɗaura hannunta a saman nashi. Kallonta yay kamar yanda take kallonsa itama. A hankali ta sakar masa murmushi mai sanyi. Shima murmushin ya sakar mata, sai kuma ya girgiza kansa kaɗan ya ce, “Ya akayi Baɗɗo am”. “Hamma mu taimaka musu, Aunty Noor kiyi haƙuri kinji. Babu abinda yafi rama sharri da alkairi nasara a rayuwa. Mu musulmai ne, masu tarbiyyar koyarwar MANZON ALLAH (S.A.W). Ya mana dukkan ni'ima ta rayuwa badan munfi saura daraja da kima ba, sai dan kawai haka yaso. Wannan wata damace UBANGIJI ya bamu, idan mukai amfani da ita mune da riba har abada”. Kusan a tare Abaan da Noor suka saki ajiyar zuciya. Wata irin ƙaunar Khadijah na sake ratsasu.... Da ƙyar suka sami ganin su Dafeeq da aka zagaye anama fifita. Ga mahaifiyarsa da alamu suka nuna bata gani da ƙyau nata kuka a gefe. Haka yarinyarsu sai tsanyara kuka take itama da rauni a goshinta. Hannu Khadijah tasa ta ɗauke ta, duk da kuwa yarinyar duƙu-duƙu take da datti har wani tsami-tsamin dauɗa take da zarni. A zabure Dafeeq da Kainaat suka tashi kamar basu ne kwance magashiyan anama firfita ba suna nishi da ƙyar. “Da gaske ku ma'aurata ne a yanzu?”. Cewar Kainaat cikin rawar murya da zubar hawaye. Kafin Abaan da Khadijah suyi magana Noor ta amshe a gadarance. “Yess su ɗin ma'aurane. Masoyan juna na bugawa a sararin samaniya bama bango ko dutse ko jarida ba. Gasu ma har ALLAH ya azurtamu da samu rabo, nan da watanni uku in sha ALLAHU ɗanmu ko ƴarmu sun shaƙi iskar duniya. Ya kukaga haɗin dan ALLAH”. Ta ƙare zancen da ƙyalkyalewa da wata shegiyar dariya har sai da Abaan ya harareta. Kuka Dafeeq da Kainaat suka fashe da shi a lokaci guda tamkar wasu ƙananun yara. Yayinda Mahaifiyar Dafeeq ke tayasu. Cikin kuka tana faɗin, “Yanzu duk ƙoƙarina na kar Khadijah kiga Dafeeq dai ko ya ganki haƙata bata cimma ruwa ba kenan. Oh ni oh ni duniya haka zakimin. Yau ga Khadijah gaban ɗana tamkar matar shugaban ƙasa. Ga ɗana a ƙasƙance gabanta kamar almajirin gidanta. Dafeeq ka cuci kanka ka cucemu daka kwaso mana wannan KARA DA KIYASHIN da bakin iyaye ke ɗawainiya da rayuwarta. Gamunan ta goga mana ƙashin tsiyarta matsiyaciya kawai tsinanniya mai yawo da tsinuwar iyaye aka....” “Ashaa mama haka bai ƙyautu ba. Ai daga ɗanki har matarsa duk ɗaya suke a gareki. Hakan garesu kuma rubutaccen al'amarine da babu hannun da ya isa ya goshesa a cikinsu. Haka ALLAH ya tsara, batare da mun taɓa sanin juna ba amma ya auri mace ya saka na aura, na saka nima ya aura. Wannan wani hukuncine da ga UBANGIJI......” “CUTA TA ƊAU CUTA... ALKAIRI YA ƊAU ALKAIRI ba Hamma”. Noor ta katsesa tana wani balla musu harara. Aiko atake jama'ar da suka cika tsakar gidan duk da ana korarsu sun ƙi fita suka shiga faɗin, “Wannan haka yake.dan babu wanda bai san soyayyar da Khadijah ta gwadama Dafeeq ba. Amma yaci amanarta shi da uwarsa. To gashi nan ya rabu da ita saboda abin duniya ya auro dai-dai da shi mai fama da bakin iyaye. Dan tuni a surutun Dafeeq da mahaifiyarsa sun fayyacema mutane wacece Kainaat. Kullum cikin mata gori ake a anguwa. Tana son zuwa ga iyayenta bata da ko kuɗin motar barin Kano. Data fara tarawa kuma Dafeeq ke sacewa. Haka zasu ci uban dambe su jigata juna ta haƙura. Hakan kuma bai hana ta sake tarawa ya sace su. Jin al'amarin nasu dai babu daɗin ji Abaan ya basu kuɗi. A take Khadijah ma ta basu daga jakarta sukace suje asibiti suka fito suka barsu dan Mamy nata kiransu lokaci zai ƙure musu gashi jirgi zasu bi. Haka dai suka dawo gida jiki a sanyaye. Yayinda suka bar Dafeeq da Kainaat da mahaifiyarsa na rusar kuka. Da ga ƙarshe faɗa ya nema hargitsewa tsakaninsu akan kuɗin. Dafeeq na son nuna musu ƙarfa-ƙarfa daga uwarsa har Kainaat ɗin sukace bai isa ba kowa yaje yaji da kansa. Dan haka maimakon asibiti ma camix suka je aka duddubasu kowa ya matse kuɗinsa. Burin kainaat gobe asubar fari ta nufi Niger neman iyayenta ta nema gafararsu ko hakan zai sa ta samu sassauci kamar yanda mutane keta bata shawara. Maybe hakan zaisa ta samu Dafeeq ya saketa ta dawo ta auri Abaan. Shiko Dafeeq nasa hangen ya haɗe kudi ya fara kasuwanci ko shima ALLAH zai azurtashi Khadijah ta dawo garesa....... ✍️ _Niko nace Hummm hauka maganinka ALLAH. Ai an baro shiri tun rani Kainaat da Dafeeq 🥱🥱😆🧑‍🦯._ *_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._* *_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_* *_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_* *_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_* *_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_* _Littatafan sune kamar haka 👇🏻_. *_KWANKWASON JIMINA....._* _(NA MSS XOXO)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _( NA SAFIYYA HUGUMA)_ *_TSUSTAR NAMA....._* _(NA BILYN ABDULL)_ *_AMEENATU_* _(NA MAMU GEE)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏_*i *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na arba'in_ *ZAFAFA BIYAR FAMILY*🫂🫂🫂🫂🫂 🔥 *me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba* *_ZAFAFA BIYAR_*❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥 ❤‍🔥 *_SABUWAR SHEKARA_* ❤‍🔥 *_SABON TSARI_* ❤‍🔥 *_SABBIN LABARAI_* ❤‍🔥 *_TSUMAMMIYAR SOYAYYA_* ❤‍🔥 *_CAKWAKIYA_* ❤‍🔥 *_LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO_* ❤‍🔥 *_SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA_* ❤‍🔥 *LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_* *_KWANTAR DA ZUCIYA_* *_CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA_* *QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA* *KWANKWASON JIMINA* _ME WUYAR TABAWA_ (miss xoxo) *TSUTSAR NAMA* _ITAMA NAMA CE_ (Billynabdul) *AMEENATU* (Mamuhghee) *GUDUN K'ADDARA* _GUZURIN TARAS DA ITA_ (Huguma) *_KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI_* *_Biya naki ta wadannan lambobin domin ki zamo cikin ZAFAFA FAMILY HOUSE_* *TSARIN SHINE KAMAR HAKA* _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *THANKS FOR CHOOSING US*🫂🫂🫂🫂 _______________________ ........*_YEARS LATER_*. Shekaru sun ja, rayuwa ta canja. Tuni jiya ta sauya daga yau zuwa goben wasu. Al'amarin tamkar mafarki ko labari suma sun zama iyaye. Wannan Abaan ɗin da kowa ya sani a matsayin matashi yanzu sunan dattijo yake amsawa. Hakama Khadijah ɗin nan ta zama babbar mace uwa mai ƴaƴa har huɗu jinin Abaan. Ɗiyarsu ta farko suna kiranta Mimi, wadda taci sunan mahaifiyar Abaan ne. Sai na biyu Muhammad. Na uku Abubakar Sadiq. Sai auta Umar Fharooq. Dukansu kamanni suke da Abaan, babu wanda ya ɗako Khadijah a kamanni sai dai jini shi baya ƙarya, duk wanda ya gansu dai yasan itace mahaifiyarsu. Ƙarfe biyar da wasu mintuna zuƙeƙiyar mota ta shigo ƙaton harabar gidan. Driver na kammala parking a gaggauce ya fito domin buɗe mata. Hamshaƙiyar mace da hutu ya nuna kansa a jikinta ce ta fito cikin yanayin gajiya. Tana sanye cikin shiga ta alfarma. Dan wani lass ne mai masifar ƙyau da ɗaukar idanu a jikin nata. Sai farar riga ta likitoci ƙal dake tabbatar da ita ɗin wacece. Sannu direban ya shiga jera mata ganin yanda take ta faman yamutsa fuska alamar a gajiye take. Ta sakar masa murmushin nan nata mai sanyi batare da tace komai ba. Kafin ta raɓashi ta wuce zuwa cikin gidan. Tarkacenta dake a mota shima ya tattaro ya biyota. A kusan tare ƙyawawan samarin yaran dake a falon kowa na harkar gabansa suka ɗago. Sai kuma duk suka miƙe suka nufota kowa na faɗin oyoyo Ammie. Hannayen ta ta buɗe musu duk suka shige abinsu. Jikin nata suka bari kowa na jera mata sannu da nuna tausayawa. Itako na faman musu murmushi. Babban da zai iya kaiwa shekara goma sha biyar ne ya kama hannunta har tsakkiyar falon ya zaunar. Sai kuma ya duƙa gabanta yana mai kama ƙafarta ya zare takalmanta ya na danna mata ƙafafun da sukai ɗan fushi. Da sauri autanta da zai iya kai shekara goma shi kuma ya iso gabanta da ruwa yana faɗin, “Ammie tun ɗazu na fito miki da shi a freight ya huce dan kar kisha mai sanyi kiyi mura.” Fuskarta da murmushi ta furta, “Oh my AUTA ALLAH yay muku albarka. Yanda kuke ji dani ALLAH ya baku mata da zasu ji daku kuma da ƴaƴa”.. A tare suka amsa da Amin cikin ɗoki harda na tsakkiyar da zai iya kai shekaru sha uku. Shi kuma kayanta dake hannun driver ya amso. “Daddy fa?”. Ta faɗa tana kallon babban. Sauran ƴan uwansa ya kalla sai kuma ya kwashe da dariya. Harararsa Khadijah tayi da faɗin, “Miye abin dariyar?”. AUTA ne ya matsar da bakinsa saitin kunnenta. Cikin raɗa ya ce, “Ammie ya ɓuya a sama ne. Wai idan kin dawo muce bai dawo ba. Kuma ya kashe phones nashi sai kin ruɗe sosai zai sakko. Ammafa kar kice ni na faɗa”. Murmushi Khadijah tayi mai sanyi tana girgiza kanta. Sai kuma ta miƙe tana kallonsu da kulawa. “Shike nan bari naje na watsa ruwa. A haɗamin shayi kar a saka suga. Ina Mimi?”. Shiru yaran sukai saboda tambayar ƙarshe. Sai kuma babban ya ja numfashi muryarsa da alamun ɓacin rai ya ce, “Ammie ta fita. Kuma da alama wannan shegen yaron ne yay kiranta. Ta ƙofar baya ta fita batare da tasan na ganta ba. Naso binta sai nai tunanin kar Daddy ya ji”. Shiru Khadijah tai tana kallon yaron nata. Sai dai gaba ɗaya fara'ar dake saman fuskarta ta gushe. Wani kalar bugawa zuciyarta keyi da sauri-sauri. Dan al'amarin yarinyar tata ya fara caja mata ƙwaƙwalwa. Ɗakinta ta nufa, sai kuma ta fasa ta nufi upstairs. Da kallo samarin yaran nata duk suka bita fuskokinsu cike da damuwa. Dan sun san al'amarin yayar tasu shine abu mafi zama damuwa ga mahaifiyar tasu a kwanakin nan... Tun kam ta ƙarasa hawo steps ɗin ƙamshinta ya gama cika masa hancinsa. A hankali ya ɗago daga abinda yake ya zuba ma hanyar fararen idanunsa dake cikin glasses fari tass da alama na ƙara gani ne. Saurin ture laptop ɗin saman cinyarsa yay yana mai riƙota ganin yanda take tafiya kamar zata faɗi. Muryarsa na rawa alamar ruɗewa ya ce, “Boddo am mike faruwa? Yau ma daga asibitin ne? Ko kuwa n.....” Da sauri ta girgiza masa kai hawayen da take ta son riƙewa na gangaro mata. Sai kuma ta faɗa jikinsa tana mai ƙanƙamesa da sakin kuka mai ƙarfi. Sake rikicewa Abaan yayi. Dan babban abinda ya tsana a rayuwarsa shine ganin matar tasa cikin ɓacin rai ko damuwa. Yana ƙaunar baiwar ALLAHr nan. Ƙauna irin wadda baisan yaya zai misaltata ba ga mai saurarensa. Domin ta gama masa komai. Ta riƙesa amana. Ta ƙautata ma mahaifiyarsa a lokacin da take jiyya har ALLAH yay mata rasuwa. Ta haifa masa yara har guda huɗu. Ta tsaya tayi karatu kamar yanda yay fata ta zama babbar likita saboda shi yana son hakan. Ta bama yaransa tarbiyyar da suka zama abin sha'awa a wajen duk wanda ya sanshi dama wanda bai sanshi ba. Tayi hakuri da abubuwa masu yawa domin shi..... “Hamma har abada bazan daina nadama ba. Bazan daina takaicin kaina ba akan bijirema iyayena. Duk da sun yafe min kafin su bar duniya hakan bai hana tarihi neman maimaita kansa ba. Ashe da gaske ne duk abinda ka aikata ga iyayenka kaima sai ƴaƴanka sun aikata gareka....” “Haba Boddo am miyasa kike irin wannan maganar ne. Abinda ya faru ya riga ya wuce ai. Baba da bakinsa ya sake maimaita ya yafe miki a randa zai bar duniya. Hakama Mama bata gushe ba sai da ta sake nanata yafiya a gareki tare da sanya miki albarka ke da zuri'armu. Miyasa zaki faɗi haka?”. “Dolene na faɗa Hamma. Domin kuwa Mimi data kasance ya ɗaya mace tilo a garemu. Ta kuma farko da muka fara gani a duniya ta fara ɗakko irin wacan hanyar da nabi da har yau ban daina nadamar binta ba. Na ɓoye maka ne da tunanin zan iya control ɗinta. Sai dai ba hakan bane. Sati uku kenan Sadiq ya sanar min duk sanda driver ya kaisu school ya ajiye sai ta koma ta fita. Hankalina yay masifar tashi da jin zancensa. Amma sai bance da shi komai ba washe gari na kaisu school ɗin da kaina. Bayan na ajiyesu sai na samu wani waje na ɓuya. Ban rufa mintinan biyar ba sai gata ta fito. Da ƙyar na iya riƙe kaina saboda hajijiya data nema ɗibata ganin wani saurayi da bai wuce shekara ashirin ba ta nufa. A mota ya ɗauke ta suka bar makarantar, hakan yasa na bisu da sauri ta yanda bazasu gane ba har zuwa wani sabon garden da Fharooq keta maka nacin muje ɗin nan. Na ɗanji nutsuwa ganin ba wani wajen ashsha suka nufa ba. Haka na ɓata lokaci a wajen har awa kusan uku suna tare kafin ya ɗauketa su koma. Makarantar ya sake maidata ta shiga shi kuma ya tafi. Ranar nayi kuka, na kira Ni'ima na sanar mata ita da aunty Noor. Shine suka bani shawarar kar nai mata magana kaima haka na cigaba da bibiyarya na sati guda. Haka nabi shawarar tasu har sati ɗayan kullum ina zuwa school ɗin nasu batare da ta sani ba kaima haka. Kuma kullum sai sun fitan sai dai garden ɗin nan dai yake kaita suje suyi zaman awa uku ya maidata. Ranar da sati ya cika Aunty Noor taje ta ritsasu a garden ɗin. Tun a can ta faffalesu da maruka su duka ita da yaron sannan ta ɗaukesu zuwa gidanta. Nasiha tai musu sosai bayan ta tambayi yaron ya sanar mata yana lavel 100 ne a jami'a baima cika wata hudu da farawa ba. Bayan ta musu nasiha da faɗa sosai muka cigaba da bibiyarsu. Sai naga ya daina zuwa ɗaukarta akaf satin can daya gabata. Ganin haka yasa na saki jiki nabar bibiyarsu saboda ayyuka sun min yawa ma a asibiti a satin nan gaba ɗaya. Hamma ashe yaran nan basuji faɗa da nasihar Aunty Noor ba. Yanzu na shigo gida shine yaran nan ke sanar min tana ganin ka hawo sama ta fita ta kofar baya. Muhammad ya kuma tabbatar min yaron nan ne yay kiranta. Hamma duka shekarar Mimi nawa ne? Hamma wlhy ji nake kamar zuciyata zata fashe.....” “No Please calm down Baɗɗo am.” ya faɗa cikin jarumtar danne nashi tashin hankalin tare da saka mata ruwa a baki. Da ƙyar ta iya shan makwarwa biyu. Ya rungumeta a jikinsa yana shafa bayanta batare da yace komai ba. Sun ja tsahon lokaci a haka kafin ya miƙe da ita zuwa ɗakinsa. Shine ya taimaka mata ta cire kayanta ya jata zuwa bathroom. Sun ɗan jima a ciki kafin su fito. Da alama wanka ya taimaka mata tayi, kasancewar tana da kaya a ɗakin ya taimaka mata ta shirya. Shayin da tace Muhammad ya haɗa mata da kansa yaje ya amso yazo ya bata tasha. Sannan cikin lallashi yace mata tai salla shima zasu je massalaci. Kanta kawai ta iya ɗaga masa. Shi kuma ya sakar mata murmushi tare da sumbatar goshinta sannan ya fito. Ya iske su Muhammad duk sunyi alwala shi suke jira. Baice da su komai ba ya shiga ɗakin Mimi da ke kusa dana Khadijah. Babu kowa alamar bata dawo gidan ba. Baice komai ba ya maida ya rufe. Inda samarin yaransa suke ya dawo. Ya kama hannun Auta su Muhammad biye da su zuwa masallaci. Ana idar da salla ya fito a massalacin. Duk da kuwa hakan ba ɗabi'arsa bace dan sai yayi isha'i yake fitowa. Gaban gate ɗin gidansa ya dawo. Da sauri maigadi ya kawo masa kujera daya buƙata. Bayan ya zauna wayarsa ya fiddo ya shiga traicing layin Mimi. Ya jima yana kallon alamar da aka nuna take. Sai kuma ya ajiye wayar yana mai lumshe idanunsa da fara karanto addu'oi a ransa. Yana a wajen har akai kiran sallar isha'i. Miƙewa yay zai koma massalacin. Yana gab da shiga ya hangota tana tahowa cikin dogon hijjab har ƙasa. Yanda take tafiyar tana waige-waige zai tabbatar maka a tsorace take. Sosai take kama da shi itama. Dan kasancewar ta mace ma yasa har tafi sauran ƙannen nata ƙyau da haske. Sosai ya jima yana kallonta har sai da taje gaban gate. Ta kai hannu zatai knocking idanunta na kallon massalacin suka haɗa ido. Wani kalar rikicewa tai da diriricewa jikinta na rawa sosai, sai kawai ya ɗauke idonsa ya shige massalacin kamar bai ganta ba... Bayan an idar da salla kamar yanda ya saba ya taso yaransa gaba suka shigo gidan. A falon ƙasa suka sami Ammie da masu aiki suna ƙoƙarin shirya table domin yin dinner. A kallo ɗaya da yay mata yasan tasha kuka. Bai ce komai ba suka zazzauna. Fharooq ya kalla cikin kamilar muryarsa yace masa yaje ya kira Auntynsu. Kai yaron ya ɗaga masa da faɗin, “To Daddy” ya tashi ya wuce. Babu jimawa sai gashi ya fito. Itako sai da taja kusan mintinan huɗu dan harma Ammie ta kammala zubama Daddy nashi abincin zai fara ci sai gata ta fito tana rabe-raɓe kanta a ƙasa. Babu wanda yace da ita komai. Dan hatta Ammie batako kalleta ba ma. Hakan ya ƙara sakata shan jinin jikinta har sai da Daddy ya ɗago ya kalleta. “Kina lafiya kuwa Mamina? Ko bazaki ci abincin bane?”. Yanda yay mata maganar kamar yanda ya saba ya sata zabura. Sai kuma ta shiga ɗan rawar jiki na rashin gaskiya. “Za...z...zanci Daddy. Ammie ina yini”. Ta faɗa duk a tare muryarta na rawa. Murmushi Abaan yayi da ɗan girgiza kansa yana kallon Khadijah da ko kallon inda Mimin take taƙiyi. Kansa ya ɗauke tare da maidawa ga Mimin ya ce, “Zoki zauna”. Zaman tazo tayi, sai dai idonta nakan Ammie cike da tsarguwa. Shi kansa Daddyn yanayinsa da yanda ya nuna tamkar bai ganta ɗin ba firgitar da ita yake yi. Haka dai ta zuba abincin ɗan kaɗan ta fara tsakura dan a ƙoshe take. Fitar da sukai da Yazeed wani haɗaɗɗen gidan abinci ya kaita suka ciwo kayan ƙwaɗayi..........✍️ _🤦Kunga na ɓata ɓat ko, Hummm abubuwa sai addu'a. Kudai ku sani a addu'oi ku kawai dan ALLAH 😭🙏_ _INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_ _KU MARMATSO KUSA...🔊_ _ZAFAFA BIYAR 2024_ _ZAFAFA BIYAR!!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _ZAFAFA BIYAR!!_ _SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_ _YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_ _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_ _________ _1_ *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_ _2_ *_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_ _3_ *_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_ _4_ *_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na arba'in da ɗaya_ *_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._* *_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_* *_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*. *_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_* *_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*. *_TSUTSAR NAMA....!!_* _(Bilyn Abdull)_ *_AMEENATU_* _(Mamu gee)_ *_KWANKWASON JIMINA...._* _(Mss xoxo)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _(Safiyya Huguma)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 ___________________ .......“Minene sunansa?”. A matuƙar rikice Mami ta ɗago ta kalli Daddy da yay maganar. Sai dai a mamakinta hankalinsa nakan tv ne da ake labarai ma. Juyawa tai ta kalli inda Ammie take. Itama dai ba ita take kallo ba shayi ma take ƙoƙarin zubama Daddy ɗin. Sashin su Muhammad ta juya, sai taga wayam alamar sun tashi gaba ɗayansu daga falon.... “Nace minene sunansa?”. Daddy ya sake maimaitawa a karo na biyu yana mai katse Mimi dake dube-dube. Kuka ta fashe da shi tana girgiza masa kanta. “Dan ALLAH Daddy kayi haƙuri natuba. Wlhy bazan sake kulashi ba. Na maka alƙawari”. “Fateema! Nace minene sunansa?”. Kaɗan ya rage kam a yanzu zuciyar Mimi ta ɓaro jin ainahin sunanta a bakin mahaifin nata. Abu mai wahalar gaske kaji ya faɗa kuwa. Ƙaruwa rawar jikinta ta ƙara. Cikin matuƙar rawar harshe ta ce, “D...d...daddy Ya...zee...d!”. “Waye babansa?”. “Abdul-kareem Waziri. Ministarn Abuja”. “Tun yaushe kuke tare?”. Kuka ta fashe da shi har sai da Daddy ya daka mata tsawa. “Nace tun yaushe kuke tare?!”. “Ka k....kayi haƙuri Daddy wata huɗu kenan. A wajen dinner ɗin bikin Uncle Awwal”. “Fateema aure kike so?”. “Daddy wlhy wlhy kaji na rantse maka a'a. Shima na faɗa masa ya daina zuwa ni karatu zanyi. Amma yaƙi yarda Daddy. Shine yake bini har school. Ko nace bazanje ba sai yayta roƙana kamar zai yi kuka. Wataran ma har kukan yake min. Amma wlhy Daddy ba aure nake so ba. Kuma wlhy na maka alkawarin bazan sake binsa ba”. “Bani Number sa”. “Daddy Dan ALLAH na roƙe ka...” Tsawa ya sake daka mata mai firgitarwa da har sai da ta sakata zabura tana sake fashewa da kuka. Cikin ɓacin rai da bata taɓa sanin Daddyn nasu ma da shi ba dan shi mutum ne mai saukin kai sosai. Yakan zauna yay hira yay wasa da dariya da su. Wani lokacin ma Ammie ta fisa zafi. Wayarta gaba ɗaya ya amshe ma. Sannan yace ta tashi ta bashi waje. Haka ta tashi tana kuka da magiyar roƙon suyi haƙuri su yafe mata shi da Ammie bazata sake ba. Amma babu wanda ya saurareta ya korata. Koda tabar falon da ga shi har Khadijah babu wanda yace da ɗan uwansa komai. Dan wayar tata ma gefe ya ajiye ta ya cigaba da kallon labaransa. Sai goma dai-dai suka tashi suka haye sama bayan sun leƙa ɗakunan yaran nasu har Mimi ɗin. Sun sameta a saman sallaya tana karatun Alqur'ani. Babu wanda yay mata magana a cikinsu suka maida mata ƙofar suka rufe. Sama suka haye. Sai bayan sunyi shirin barci Khadijah na daga jikin mirror tana saka turare shi kuma yana a bakin gadon zaune ya ɗauki wayar Mimi. Bincike ya farayi lungu da saƙo na wayar dan babu password, hakan dokace da ga Ammie. Sai da ya gama bincike wayar tsaf yana ɗan sauke ajiyar zuciya ganin babu wani abin tada hankali sai text messages na soyayya mafi yawa ma yaron ne ya tura mata. Sai wasu ta WhatsApp da hotunanta data tura masa shima ya tura mata nashi. Dukansu kuma da hijjab ma tayi su. Shima kuma cikin kamala yake. Iskar samun nutsuwa ya furzar. Kafin a hankali ya ɗago ya kalli Khadijah dake kallonsa. Hannu ya miƙa mata alamar tazo gareshi. Babu musu ta nufesa. Jikinsa ya jawota suka faɗa saman gadon. Da ga haka yaja musu bargo yana sumbatar kumatunta da faɗin, “Ki ɗan yi murmushi mana Baɗɗo am”. Murmushin ta ɗanyi da sake shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Shima sai ya sauke tasa ajiyar zuciyar yana sake rungumeta da ƙyau... *_WASHE GARI_* kamar yanda suka saba duk suka fita aiki. Yaran kuma makaranta har Mimi. Sai dai yau Daddy da kansa ya kai su makarantar. Ya kuma hana Mimi fita. Suna zaune a mota ita da shi sai ga kira ya shigo a wayarta dake hannunsa. Miƙa mata yay babu alamar wasa a fuskarsa yace “Ki amsa masa kamar yanda kika saba”. Kanta ta jinjina tana share hawaye. Ganin yanda mahaifin nata ya tsareta da ido dole ta amsa ɗin. Suna gamawa ya amshe wayar yace mata taje inda yake. Kuma koda wasa ta sanar masa tare suke sai ya mata dukan mutuwa. Tana hawaye ta amsa masa. Tsawa ya mata akan ta share hawayen. Haka ta gogesu tsaff ta gyara yanayinta sannan ta fita bisa umarninsa. Tana shiga motar suka bar wajen . Bayansu yabi har garden ɗin da Ammie ta dinga bibiyarsu. Sai da suka fita a motar suka sami wajen zama Mimi dai duk a ɗarare sannan ya fita zuwa inda suke. Koda Yazeed yay tozali da Alhaji Abaan gabansa rikicewa yay. Dan kuwa mahaifin Mimi ba ɓoyayyen mutum bane. Sannan duk wanda ya kalleta ya kallesa yasan shine mahaifinta. Jikin Yazeed na rawa ya kai har ƙasa yana gaida Abaan. Amsa masa yay tare da masa nunin ya tashi. Batare da yace komai ba yace su biyosa. Ganin babu alamar wasa a tattare da shi Yazeed ya bisa babu musu. Ita dama Mimi yasan bata isa yin musun ba. A motarsa ya ɗebesu su duka aka bar ta Yazeed anan. Mami na baya Yazeed na gaba kusa da Daddy. Hankalin Yazeed ya tashi ganin gidansu suka zo. Bai sake ruɗewa ba sai da aka buɗe musu gate yaga motocin mahaifinsa na nan alamar bai fita ba. Ita dai Mimi bata san nan ne gidan su Yazeed ba. Sai da akai musu iso ciki suna shiga tai tozali da mahaifin Yazeed ɗin. Duk sai itama taji ta sake rikicewa. Tarba ta girmamawa Alhaji Abaan ya samu a wajen Ministar. Domin kuwa akwai sanayya batun yanzu ba, sannan akwai huɗɗar kasuwanci. Tun kuma a daren jiya ya nema ganinsa ta hanyar tura masa saƙo ta waya. Hakan yasa batare da wani kace nace ba suka haɗu a gida kai tsaye kamar yanda Ministar ɗin ya bashi dama yau da safe ta hanyar kiransa. Dan Alhaji Abaan ko shugaban ƙasa ya buƙaci gani duk da a ƙurarren lokaci ne hakan bazai gagaresa ba. Dan ya wuce duk yanda mai hasashe zai iya hangowa yanzu a ƙasar nan. To ada can baya ma da suke matasa akayi dasu balle yanzu da gwamnatin ma sune suka kafata da dukiyarsu da iliminsu. Bayan gaisuwa da ɗan barkwanci tsakanin dattijan guda biyu Alhaji Abaan ya nuna Mimi da Yazeed dake zaune ƙasa kawunansu a ƙasa tamkar masu neman gafara. Yazeed ya nuna da faɗin, “Nasan kasan wannan. Wannan kuma first born ɗina ce Fatima”. Fuska cike da murmushi Ministar dake kallon Mimi ya ce, “Masha ALLAH dota yaki nan. Wato girman dai ɗan mutum babu wahala. Yanzu Alhaji Abaan yarinyar da muka sha shagalin sunan ta ce ta girma haka oh ALLAH”. Murmushi kawai Daddy yay batare da yace komai ba. Yayinda Mimi ta taso a ɗarare har gaban ministar ta sake zaman gurfane. Daka ganta kasan hankalinta baya tare da ita. Gaishesa ta sake yi cike da girmamawa. Ya amsa mata da kulawa yana jera mata tambayoyi. Har suka kammala Daddy baice komai ba. Sai da sukai shiru sannan Daddy yayma Yazeed nuni da shima ya matso. Tasowa shima Yazeed ɗin yayi a ɗarare ya gurfana kusa da Mimi kansa a ƙasa kamar yanda take. Daddy ya maida dubansa ga ministar da yayma ɗan nasa kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Batare da ɓata lokaci ba Daddy ya shiga yima Ministar bayanin abinda ya faru a jiya game da fitar Mimi gida. Har bayanin da Ammie tai masa zuwa abinda ya faru yau. Sannan ya miƙama ministar wayar Mimi dake hannunsa. Shima duk sakwanin da suka shiga tsakaninsu ne ya dudduba. Bayan ya kammala ya ɗago ransa a ɓace yana kallon Yazeed. Magana yaso yi amma Daddy ya dakatar da shi. “Kasan miyyasa na kawosu gabanka?”. Kai ministar ya girgiza masa rai a jagule. Daddy yay ɗan murmushi. Sannan ya cigaba da faɗin, “Saboda mu fiskancesu tare. Da farko naso hukunta yaron dake tare da itan ne koda ɗan waye. Sai dai jin yaronka ne yasa naji bazan taɓa iya hakan ba. Sam ba soyayyar tasu ko alaƙarsu ta ɓatamin rai ba. Hanyar da suka ɗora kansu wajen gina soyayyar ne ya zafeni ya kuma tayar min da hankali. Domin hanyace mara ɓillewa. Wlhy wlhy ko ɗan maigadin gidana Fatima ta kawo gabana tace min Daddy ina son wannan da aure shima yana sona bazanji komai ba sai farin ciki, zan kuma goya musu baya na bama alaƙarsu ƙarfi ta yanda basuyi zato ba. Amma soyayya a bayan fage da ɗaukar salon cutar da iyaye koda ɗan wanene bazan ɗauka ba. Dibesu, dukansu basu haura shekaru ashirin ba a duniya amma sun san su yaudari iyaye ta hanyar barin makarantun da muka turasu su tafi lambun soyayya. A da fa iya makaranta ake bari zuwa garden, amma yanzu ta fara kaiwa matsayin barin gida babu izini zuwa gidan cin abinci. Daga haka mi kuma muke tunani zai biyo baya....” ya dafe kansa cikin takaici. Batare da ya jira cewar ministar ba ya cigaba da faɗin, “Wannan ta riga ta faru, ba kuma na fatan ta cigaba da faruwa. Dan haka nazo da su gabanka. Idan ka shirya yima Yazeed aure ka turo min magabatansa na bashi auren Fatima. Ba kuma nason komai ya wuce nan da wata biyu. Taje tai karatun a gidansa idan tana da ra'ayin hakan, idan kuma bata buƙata duk ya rage nata. Ni dai Alhmdllh nasan na sauke nauyinta da ke kaina matsayin mahaifi. Hakama mahaifiyarta na iya ƙoƙarin ta a kanta. Sai dai na sharɗantama Yazeed kar ya sake tareta a waje da sunan soyayya, kada ya sake zuwa ɗaukarta makaranta da sunan soyayya. Kada ya sake kiranta ta fita a gida saboda sunan soyayya. Na bashi dama yazo gida a duk ranaku uku na cikin mako, suyi hira a falona daga nan har zuwa randa zan bashi ita a matsayin mata. Yazeed wannan alfarmar kawai nake buƙata a gareka dan ALLAH dan ALLAH ka taimakeni”. Ya ƙare maganar yana kallon Yazeed dake hawaye kansa a ƙasa. Hakama Mimi kuka take kamar ranta zai fita dan maganganun Daddy sun matuƙar gigita mata zuciya da sata a ɗimuwa. Shi kansa Ministarn kallon ɗan nasa yake cike da matukar mamaki da al'ajabi. Dan da wani ne yazo ya sanar masa Yazeed ɗin zai aikata haka wlhy bazai yarda ba. Saboda kaf a cikin yaransa babu wanda ya kamo ƙafar Yazeed hankali, nutsuwa da biyayya. Yaro ne nagartacce da ƙyawawan halaye. Sannan gashi shiru-shiru kamar idan ka saka masa yatsa bazai iya taunawa ba. Cikin tsananin ɓacin rai ya rufe Yazeed da faɗa, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Sai da yay masa biji-biji Yazeed ɗin na hawaye sosai sannan Daddy ya riƙo hannunsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Ya isa haka tom”. Kansa ya girgiza tare da maida dubansa ga Daddy. “Nagode sosai da wannan halaccin da kaimin Alhaji Abaan. Wlhy wlhy kaji na rantse daga ni har mahaifiyarsa bamu san hakan na faruwa ba. Dan kullum ya shirya ya fita a saninmu makaranta ya nufa kawai. Yanayin rayuwa da taɓarɓarewar abubuwa yasa mahaifiyarsu bata yarda su ƙetare ƙasar nan domin yin karatu ba, musamman ma su mazan, matan kuma idan mazajensu sun amince su tafi dasu dan da sun kammala sakandare muke aurar dasu. To ashe shi shaiɗani yana can yana hurema yarinya ƙarama dake aji biyar na makaranta kunne saboda zalunci. Kai idan akaima ƙanwarka haka zakaji daɗi? Duka nawa kake ma Yazeed. Just twenty years fa, amma kake.....” Sake riƙo masa hannu Daddy yay yana murmushi. “Oh calm down ya isa haka. Ai kuskuren ba nashi bane shi kaɗai harda ita Fatiman. Amma in sha ALLAHU ni zan magance matsalar in dai kun shirya masa aure. Dan ita dai in sha ALLAHU bazata sake min wata biyu a gida ba koba Yazeed ba zan aurar da ita ne na riga na yanke hukunci”. Sake rikicewa Mimi tai da kuka.........✍️ *_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._* *_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_* *_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*. *_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_* *_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*. *_TSUTSAR NAMA....!!_* _(Bilyn Abdull)_ *_AMEENATU_* _(Mamu gee)_ *_KWANKWASON JIMINA...._* _(Mss xoxo)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _(Safiyya Huguma)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na arba'in da biyu_ *_WAI KINA SHIRIN WUCEWA NE BAKI KARANTA BA😨._* *_TO MAZA DAWO BAYA KI DUBA. IN BA HAKA BA ZA'AYI BABU KE NE_* *_INA KUKE MASOYAN ZAFAFA BIYAR DAMA WANDA BAZU TAƁA SIYA BA SAI DAI SU KARANTA A HANYA_*. *_MAZA KU MARMATSO KU MALLAKI NAKU DAN GAB JIRGIN YAKE DA BARIN ƘASA. MA'ANA GAB ZAFAFAN SUKE DA FARA SAKAR MUKU ZAFAFAN LITTATAFAN SU NA SABUWAR SHEKARAR 2024_* *_KAR KUYI MAMAKI IDAN NACE MUKU TAFIYAR FA TA BANBANTA DA BAYA. SABODA SALON NA DABANNE, NA KUMA MUSAMMAN NE_*. *_TSUTSAR NAMA....!!_* _(Bilyn Abdull)_ *_AMEENATU_* _(Mamu gee)_ *_KWANKWASON JIMINA...._* _(Mss xoxo)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _(Safiyya Huguma)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 _______________ ........Cikin jinjina kai Ministar ya ce, “Wlhy ka birgeni, kuma hukuncinka yamun dai-dai. Aure kuwa tare da shi daya hure mata kunne zamu musu in sha ALLAHU. Suje su ƙarata dan ni dai babu ɗan da zai bani ciwon kai in sha ALLAHU Alhaji Abaan. Na kuma gode da wannan karamcin naka. ALLAH yabar zuminci. In sha ALLAHU zuwa weekend zamu shigo mu ganka. Sannan ina sake bada haƙuri da neman afuwa dan ALLAH”. Murmushi Daddy yay da ɗan harararsa. Daga haka sukai dariya irin tasu ta manya. Cikin kuka Yazeed ya rarrafa kusa da Daddy. Haƙuri ya rinƙa bashi da cewar ya yarda yayi kuskure. Amma dan ALLAH Daddy da Abban nasa su yafe masa. Kuma shi wlhy ba laifin Mimi bane laifinsa ne. Murmushi kawai Daddy yay da shafa kansa da faɗin, “ALLAH yay muku albarka. Ya shirya mana ku baki ɗaya.” daga haka ya miƙe abinsa. Har mota Ministar yay masa rakkiya. Har lokacin Mimi kuka take na fitar hankali Ministar dake riƙe da hannunta na lallashinta. Shi ya sakata a mota da kansa, yayinda Daddy ya shiga mazaunin driver abinsa. Ko a hanya duk kuka da magiyar da take masa baice da ita uffan ba. Makaranta ya maidata. Ta fashe da kuka zata fara roƙonsa ya daka mata tsawa da faɗin, “Get out of my car my friend!!”. A rikice ta fita jikinta na rawa. Ko kallonta bai sake yi ba yay reverse ya fice ya barta anan tana kuka. Office ya nufa bayan yay kiran Awwal ta waya yace ya samesa can. Dan dama da safen ya kira shi akan basai yazo kaisa Office ba zaije wani waje da kansa... ★★★ Kuka sosai Khadijah keyi da jin hukuncin da mijin nata ya yanke akan tilon ƴarsu mace. Cikin sake ƙarfin kukanta ta ce, “Hamma dan ALLAH kada kamin haka na roƙe ka. Wlhy zai iya zama fiye da Dafeeq a gareta. Ƙarya yake ba sonta yake ba ƙuruciya ke ɗibarsu. Wlhy daga ita har shi basu da hankalin tantance dai-dai da akasin sa. Hamma zai cutar mana da yarinya ne kawai amma ba sonta yake ba.....” A fusace, matuƙar fusace Abaan ya katseta da faɗin, “To yaya kike so nayi ne Khadijah! Na barsa ya lalatamin rayuwar yarinya a saman titi ne ko mi? So kike na matsa na hanasu tarayya wataran ya jata su gudu. Tunda har Fatima zata iya fita a gidan nan a dalilin namiji yaya kike tunani idan nace sai sun rabu. Kima kanki adalci mana dan ALLAH Khadijah. Wlhy idan yarinyar nan tabi yaron nan suka gudu zuciyata zata iya bugawa. Na fiki jin wannan tsoron, dan tun daga jiya zuwa safiyar yau hatta da bugun zuciyata ba dai-dai yake ba. Ni bazan iya jure abinda su Baba suka jure akanki ba Khadijah, dole ne na ɗauki matakin da zai zame min masalaha dan bazan iya jurar rasa yarinyata ba, zan aura masa ita, suje hakan zai fi bani kwanciyar hankali akan ace sun bijire mana zuwa wata duniyar..” hawayen dake neman zubo masa ya sashi kasa cigaba da maganar. Sai kawai ya juya ya shige bedroom dan dama a tsaye yake, ya shige yana ƙoƙarin maida hawayen. Da kallo Khadijah da tun furucinsa na (Ni bazan iya jure abinda su Baba suka jure akanki ba Khadijah) hawayenta suka tsaya cak. Illahirin jikinta ya shiga rawa. Dan ba ƙaramin ratsata waɗan nan kalaman sukai ba. Sai zuciyarta ke gaya mata kamar fa gori mijin nata ya mata. Gori yake mata akan abinda ta aikata da ya zama ya shafi ƴarsu a yanzu. A take ta sake fashewa da wani matsananci kuka. Domin wannan shine karo na farko da irin wannan babban saɓanin ya shigo tsakaninsu. Bawai basa samun saɓani ba. Wannan dole ne a gidan kowane aure na kowace ƙabila. Amma a tsahon shekaru goma sha takwas da aurensu bata jin Abaan ya taɓa ɗaga mata murya irin haka, dan shi ko faɗa zaiyi yakanyi ne cikin yanayin sanyinsa da rashin hayaniya. Amma a yau yanda yake ihu mata akai ta tabbata hatta yaransu dake ƙasa duk suna jiyosu... Ilai kuwa hasashenta yay dai-dai, dan ta iske Auta da Fharooq na kuka sosai a falon ƙasan. Yayinda take jiyo muryar Muhammad a ɗakin Mimi yana mata masifa yana kuka da ƙalibalantarta akan yau a dalilinta ga iyayensu suna ɗagama juna murya. Yayinda ita kuma take kuka kamar ranta zai fita. Ji Khadijah tai hajijiya na neman kwasarta, dan komai ya gama rikice mata tama rasa ina zata dafa. Al'amarin kamar wasa sai abu ya zama babba. Dan gaba ɗaya a cikin satin gidan dake kamar aljannar duniya ha ma'abota rayuwar cikinsa ya zama kamar wani gidan mutuwa. Magabatan Yazeed sunzo. Dan Ministar da kansa tare da vice president da ƙanensa biyu sunzo neman auren Mimi kamar yanda Alhaji Abaan ya basu dama. Bai kuma ja komai da nisa ba duk da raɗaɗin da yake ji a ransa na rabuwa da yarinyarsa da bata gama mallakar hankalinta ba suka gama komai hatta ranar ɗaurin aure. Dan gaba ɗaya wata biyu kacal ya saka musu a lokacin su Mimi na cikin hutu. Aifa ranar sosai Khadijah ta birkicema Alhaji Abaan akan itafa bata yarda ba, bata amince ama Mimi aure a wannan shekarun ba. Dan tana matuƙar tsoron ɗiyarta ta faɗa a makamanciyar rayuwar data faɗa itama. To anan nefa rikici ya ɓarke. Alhaji Abaan yace bata isa ba. Babu fashi zai aurar da Mimi dan haka shine kwanciyar hankalinsa. A gefe kuma Mimi na kuka da roƙon Daddyn nata akan yayi haƙuri kada yay mata aure. Ita wlhy bata son aure a yanzu. In dai Yazeed ne ta rabu da shi har abada. Ko saurarenta ma Daddy baiyi ba. Ranar ma data ishesa da magiya da kuka a karo na farko na tarihi ya faffaleta da maruka biyu da suka matuƙar gigita mata rayuwa. Dan abu ne da bai taɓa faruwa ba. Duk rintsi Alhaji Abaan baya dukan yaransa. Wani lokacin ma idan suka ƙure Khadijah ta dakesu har haushi yake ji. Yafi gane ya zaunar da yaro ya masa nasiha idan yayi ba daidai ba. Amma a ranar sai da Mimi ta samu rabonta har ana ganin shatin hannunsa a farar ƙyaƙyƙyawar fuskarta mai tsananin kamanni da tashi. Aunty Noor ta shiga zancen itama tana beging yayan nata. Amma a karo na farko yaƙi saurarenta akan shifa babu fashi akan aurar da Mimi. Idan sunga zasu je su fara shiri matsayinsu na iyaye suje su fara. Idan kuma bazasuyi komai ba daga an ɗaura aure zai ɗauketa shi kaɗansa ya miƙata gidan miji ne. Komai ya caɓe, ƙura ta tashi sosai da ya kai har rashin jituwa yasa a karo na farko Khadijah tai shiri ta wuce Kano. Kai tsaye kura ta nufa wajen dangin iyayensu. Inda takai ƙarar Abaan wajen kawunan ta. Aranar ta dawo cikin Kano ta yada zango a gidan Ni'ima. Inda suka tattauna tare da ita da Zuhrah da mazajensu dake tamkar ƙanne ga Alhaji Abaan ɗin. Basu ɓoye mata ba sun fito fili sun sanar mata kuskurenta na tun farko ko muce maimaita mata tunda kowa ya daɗe da tabbatar mata wannan tun iyayensu nada rai. Suka kuma nuna mata kar taga laifin Alhaji Abaan da yawa a tsorace kawai yake dan yana ganin tarihi zai fa iya maimaita kansa Mimi tabi Yazeed su gudu kamar yanda itama tabi Dafeeq a wancan shekarun. Bata ko musa ba wajen amsar laifinta, ta kuma yi kuka ta sake nadama da roƙon gafarar iyayensu da suka jima da kwanta dama. Haka dai washe gari suka ɗunguma suka koma Abuja wajen Alhaji Abaan, sai dai ita bata bisu ba nan suka barta a Kano ɗin. Suma dai sun je sun zauna da Alhaji Abaan tare da lallashinsa da ban haƙuri musamman ganin yanda Mimi itama ke kuka da magiya da roƙon yay haƙuri ta tuba. Dan yanda yarinyar ke a firgice har asibiti aka kwantar da ita na kwana biyu. Duk ta zabge ta rame ta sake yin haske abin tausayi. Ga ƴan ƙannenta ababen farin cikinta sun juya mata baya gaba ɗaya. Musamman ma Muhammad da yafi kowa ɗaukar zafi da ita kasancewar yafi sauran ƴan uwansa wayo. A su ɗin ma dai Alhaji Abaan ya murje idonsa, sai ma haƙuri da ya basu akan shifa yana akan bakansa dan babu fashi. Garama su faɗama Khadijah ta dawo in zata dawo. In ko ba hakaba za ai bikin Mimi ko bata nan. Waɗan nan kalamai nashi sun sake tada musu hankali. Dan dole fa suka komo Kano jiki a sanyaye. Sunta lallashin Khadijah akan ta haƙura kawai ta koma ta barsa yay abinda ya tsara akan ƴarsa. Dan ya riga ya hau sama irin yanda kowa bai san ya iya fushi haka ba. Kuka ta dinga musu dan gani take ita kowa fa baya hango abinda take lurar dasu. Tana tsoron a aurar da Mimi Yazeed ya dawo yaci dunduniyarsu kamar yanda Dafeeq ya mata. To bayan dai sun sake tattaunawa dabarar zuwa ga Baba Hakimi ta zo musu. Haka sukai shiri suka ɗunguma garin Adamawa. Inda suka je suka tattare komai suka sanarma Baba Hakimi daya ƙara tsufa sosai. Haka dai badan yana jin ƙarfi ba suka kwashesa zuwa Abuja. Shine yay zama da Khadijah da Abaan da Mimi, sai da ya gama jin komai sannan yay murmushin su na manya. Sannan ya sallami Mimi ya fara magana da Abaan da Khadijah. Sun tattauna sosai inda daga ƙarshe ya sa Alhaji Abaan ɗin kira masa Ministar da ɗansa Yazeed aka sake sabon zama harda Mimi. Wannan zama shine ya kawo masalaha a tsakani. In da Baba Hakimi ya kawo masalaha akan komai. Yazeed zai yi haƙuri Mimi ta kammala secondary ɗinta. A lokacin shima karatunsa yay nisa. Amma da sharaɗin bazai sake zuwa ya ɗauketa a school ba ko ya fiddata daga gida bada sanin iyayenta ba. Zai dinga zuwa hira wajenta akowane ranar juma'a da yamma, zakuma suyi hirar ne a nan falon gidansu. A take Yazeed ya amince. Dan shima hankalinsa a tashe yake sosai da yanda Mimi ta birkice masa tamace su rabu, ta kumayi blocking nashi a waya da kowanne account nata na media. Shi kuma harga ALLAH so da ƙaunarta yake na gaskiya. Ya kuma fahimci wawtarsa da kuskurensa saboda mahaifiyarsa ta masa faɗa sosai kasancewarta mace mai dattako. Anan dai aka sasanta komai aka dai-daita zancen biki ya fasu... Bayan ɗan fushi da shashshare juna na kusan sati guda bayan sasantawa Alhaji Abaan da Boddonsa suka shirya kansu. Suka kuma sake ɗaura ɗammarar jan Mimi jikinsu. Yayinda a ɓoye Alhaji Abaan yay mugun sakama Mimi ƴan leƙen asiri ako ina da zata iya kasancewa. Haka itama Dr Khadijah ba'a barta a baya ba wajen sakama ƴar tata idanu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Mimi ta kammala karatunta na sakandare. Yayinda Yazeed ma ke cigaba da nasa karatun. Abin kuma birgewa bayan ta kammala ɗin koda aka tada batun aurensu sai sukace ba yanzu ba sai Mimi ta fara karatunta na Jami'a, shi kuma ya kammala nasa. Hakan yayma iyayensu daɗi sosai, musamman kasancewarsu duk ƴan boko dama. A haka Mimi ta fara karatu a jami'ar, tana lavel 200 Yazeed ya kammala nashi karatun. Ya shiga hidimar bautar ƙasa. Yana kammalawa Babansa ya sama masa aiki mai tsoka, bai zauna ba ya sake shirin joining masters nashi. Zuwa lokacin soyayya ce mai ƙarfi da shaƙuwa a tsakanin Mimi da Yazeed. Ga zuminci ya sake ƙulluwa a tsakanin iyayensu fiye da da. Dan yanzu in ma baka sani ba saika ɗauka Yazeed ɗin ɗan gidan ne. A dalilin Masters da Yazeed zai wuce abroad aka yanke shawarar saka bikinsu. Daya dawo za'a sha biki Mimi ta ƙarasa karatunta a ɗakinta. Haka kuwa ne ya faru, dan shekarar Yazeed ɗaya da wasu watanni ya dawo gida Nigeria. Inda aka shiga shirye-shiryen biki na ƴan gata. Dan daga ango har amarya iyayensu duk masu hannu da maiƙo ne. Kafin kace mi zance auren waɗan nan iyalai biyu ya karaɗe shafukan sada zumunta. Inda aka shiga biki na nunama tsara. Amarya da ango duk sun sha ƙyau. Komai suke zaka fahimci cike da so da ƙaunar juna ne. Hakama iyayensu na a cikin matuƙar farin ciki da ganin wannan rana a gare su. Dan Khadijah tayi kuka har bata san iyaka ba. Ansha shagali amarya ta tare ɗakinta. Inda tabar iyayenta da ƙannenta da kewa. Duk da ma zuwa yanzu duk ba zaman ƙasar yaran suke ba saboda karatu. Auta ne kawai a gida sakamakon bana ya kammala nashi secondary ɗin shi. Shima dai ana shirye-shiryen miƙashi abroad ɗin ne........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na arba'in da uku_ *_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._* *_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_* *_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_* *_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_* *_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_* _Littatafan sune kamar haka 👇🏻_. *_KWANKWASON JIMINA....._* _(NA MSS XOXO)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _( NA SAFIYYA HUGUMA)_ *_TSUSTAR NAMA....._* _(NA BILYN ABDULL)_ *_AMEENATU_* _(NA MAMU GEE)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 _______________ .........A watan da su Mimi ke cika bakwai cif da aure iyalan Alhaji Abaan suka nufi Kano halartar auren yaron Ni'ima da ƴar wajen Zuhrah. Harda amarya Mimi mai fama da ciki ɗan watanni biyar. Sai langaɓewa take a jikin Khadijah tana tureta da mata faɗa akan ta dinga ƙarfafa jikinta. Shiko Alhaji Abaan na faɗan ta bar damar masa yarinya ta barta da abinda ya dameta. Ita daga uban ma har ƴar dariya suke bata. Dan bataga ƙyau a makanta ba sam. Da taga zasu isheta ta ce aiba dole bane zata kira Yazeed ɗin yazo ya ɗauki matarsa basai taje bikin ba ai. Aiko ta sanya ma Daddynta kuka akan ita dai tana son zuwa dan ALLAH. Aiko ya ɗaure mata ƙugu dole Khadijah ta kawo ido ta saka musu. Sun isa Kano ranar talata, inda suka tarar su ake jira da shirye-shirye musamman Khadijah da ayanzu itace matsayin uwa ga ƙannenta. Washe garin laraba suka shirya fita duba matar autansu da ke a asibiti sakamakon miscarriage data samu a daren jiya. Mota biyu sukayi, daka gansu kaga nagartaccen family na gogaggun ƴan boko da naira ta gama nuna kanta a jikinsu. Dan daga iyayen har ƴaƴan tsaf-tsaf suke kamar ka taɓa jin daɗi ya maka ihu. Koda suka shigo asibitin kwarjininsu yasa kowama ya haɗu da su sai ya kallesu ya sake kallo. Bayan sun duba matar ƙanin nasu da akama sallama suka ɗunguma suka fito. Autansun ne ya ja su akan su rakashi wani waje Please. Babu wanda yay musu sai ma Mimi dake faman masa rakin ita dai a koma gida barci take ji. Aunty Jamilah na riƙe da ita tana riritata kamar wata ƙwai. Yayinda Khadijah ke faman harararta. A gaban gadon wani yamutsatsen tsoho da wahalar rayuwa ta gama nuna kanta a jikinsa suka tsaya. Yana kwance sai idanu luƙu-luƙu da haƙora daka gansa kaga wanda yunwa ta gama cinyema hanji. A yanda yake kwance kuma zai baka tabbacin yana tare da lalurar shanyewar ɓarin jiki ne. Dan bakinsa har ya ɗan karkace. Da alama kuma idonsa ɗaya baya aiki sosai. A gefensa mace ce akan tsohon wheelchair irin na ƙarfen nan da akeyi a Nigeria. Itama duk ta fita hayyacinta fatar fuskarta tai wani faci-facin nan baƙi nan jaa nan brown. Itama dai a rame take sosai, sai haƙora gayau na gaba ma guda biyu sun fita sai uban gate kamar ƙofar gari. Babu ƙafa a tattare da ita sai dungulmi. Sai wani kalar tsamin dauɗa take ga kayan jikinta duk a ciccinye saboda tsufa da gajiyar da sukai suma. A kaf su Khadijah babu wanda ya gane su wanene, sai dai sun gaishesu da tambayar mai jiki. Amma abin mamaki daga matar har mijin da alama su sun shaidasu musamman ma Khadijah da Mimi da suka tsurama idanu. Dan atake hawaye suka fara bin kumatunsu. Khadijah dai ta ɓalle handbag dinta ta cire rafa na dubu guda biyu 200k ta ajiye musu dan haka kawai suka bata matuƙar tausayi. Tasan kuma tunda auta ya kawo su nan ya san mutanen. Ƙoƙarin tafiya suke saboda naci da shagwaɓar da Mimi take musu kan a tafi ita bata son warin asibitin. Cikin rawar muryar yamutsaten mutumin da ke fita gururu ya ce, “Khadijah!”. Cak Khadijah ta tsaya tare da juyowa a firgice dan jin ya ambaci sunanta. Hawayen dake bin kumatunsa masu zafi suka sake ɓulɓulowa kamar yanda na matarsa ke ɓulbulowa. Batare da ya damu ba ya cigaba da faɗin, “Nasan baki ganeni ba. Dafeeq ne.” Ba Khadijah ba kowa ma dake wajen sai da ya razana. Idan ka cire Mimi da sauran yaran da basu san komai ba. Sai auta da ya san wanene ɗin shi daman. Dafeeq dake kuka rurus ya cigaba da faɗin, “Kinga yanda ALLAH yay dani Khadijah. Kinga yanda Dafeeq ya koma. Tabbas nasan alhakinki dana iyayenki bazai barni ba Khadijah. Dan na zalunceku ƙwarai da gaske. Nayi wasa da zuciyar data soni don ALLAH. Na bar soyayya ta gaskiya da amana saboda kuɗi. Na ɓata miki suna da tunanin ni ɗin mai wayo ne. Amma wlhy a duk abinda ya faru ban taɓa jin rashin sonki kona daƙiƙa ɗaya ba. Dan ALLAH ne shaida ta son gaskiya ke kaɗai na taɓamawa bayan iyayena. Sai dai ban san wace wauta da son zuciya ne ya jagoranceni aikata miki dukkan abinda ya faru ba. Kaicona. Inama nayi haƙuri nabi shawarar Baba alokacin da yace na bari ki gama karatunki da kansa zai aura min ke. Inama nayi haƙuri da abinda yace. Da nasan har yanzu muna a tare cikin farin ciki da zuri'armu. Amma na biyema son zuciya da wauta na ɓata komai. Na zugaki, nai amfani da soyayyar da kikemin ta gaskiya na sakaki bijirema iyayenki. Na kuma dawo na shirya da nawa kika cigaba da zama cikin fushin naki iyayen. Hakan bai isheni ba na ɓata miki suna a wautata wai duk dan na samu damar nisantaki da kowa sai ni kawai. Kiji bazaki taɓa iya rabuwa dani ba. Duk da hakan kuma ban haƙura ba naje na kawo wannan ƙarfen ƙafar cikin rayuwar mu. Na ɗakkoma kaina CUTA da hannuna gashi nan na gagara warkewa daga gubarta, saima sake wargazani da tayi gaba ɗaya. Khadijah kamar yanda Kainaat ta bijirema iyayenta da ƙyamatarsu matsayin su na iyayenta ta ɗauki iyayen bariki tarihi ya sake maimaita kansa. Dan a yanzu haka muma tamu ƴar ta jima da jefar damu da nunama duniya mu ba iyayenta bane ba. Talauci baisa mun sakata a makaranta ba. Sai talla da suyar awara a bakin layi. A haka ta samu saurayi daya dinga jan ra'ayinta har ya sakata a makaranta. Bayan ta kammala karatu ya tsaya mata ta shiga jami'a. Acan ne ta haɗu da ƙawaye da sabbin samari. Shima ta butulce masa dan acewarta ta gama da ajinsa. A haka ta zama koda yaushe cikin ƴaƴan manya. Inda ta samu damar aure baban wani yaro da suke abota kasancewar baban babban ɗan siyasa ne. Babu zato sai ganin aurenta mukai ana nunawa a tv tare da wasu iyayen bamu ba. Munsha kuka matuƙa, dan a ranar na yanke jiki na faɗi na samu paralysis. Koda akaje aka sanar mata sai cewa tai bama ta sanmu ba. Dan bata da wata alaƙa damu bayan ta ni wai mai gadin gidansu ne mamanta gata nan mai aikinsu. Haka naita jiyya a gida bata taɓa ta waiwayemu ba. Sai dai mu ganta a tv tare da mijinta. A haka akaja wajen shekara guda, ranar kwatsam sai ga labarai an nuna wai ta kashe mijin nata a sakamakon ya gano sirrinta na ƙarya data masa da iyayen bogi. Rikici ya hargume tsakaninsu ta daɓa masa wuƙa. In dai takaice muku yanzu tana prison anata Shari'a. Munma ji ƙishin-ƙishin ɗin kasheta zasuyi, koda yake nasan kuma duk kun san wannan labarin, dan labarine daya zaga lungu da saƙo na ƙasar nan. Munsha wahala a rayuwa Khadijah, dukiyar da akaso tarawa bata tarun ba. Ƴa ɗaya tak da muka mallaka a duniya tace mu ba iyayenta bane. Shekarata kusan uku kenan a wannan halin na jiyya, Babu mai taimakonmu, sai a kwanan nan da ɗan uwanki ya samu labari yazo ya kawoni asibiti. Ita kanta Kainaat kinga yanda ta koma. Duka ƙafafu babu, ta rasa a sakamakon haɗari lokacin data nufi Niger neman iyayenta......” Cikin Kuka Kainaat ta amshe da faɗin, “Tabbas alhakinku ke da Abaan dana iyayenmu bazai bari mu rayu cikin salama ba Khadijah. Dan bayan kun bamu kuɗin nan ke da Abaan na shirya zuwa na nema iyayena kamar yanda kowa ke bani shawara. A haukana ƙila idan nayi hakan zan samu sararin sake komawa cikin rayuwar Abaan. Sai dai kaicona na baro shiri tun ran tubani. Dan kuwa a randa na tafi Niger batare da jiran yardar Dafeeq ba a hanya muka gwabza babban haɗari muna gab da shiga maraɗi. Kasancewar jeho mai sunaki Khadijah da muke kira Banan da nayi ita bataji ciwo sosai ba. Niko ƙarfe ya dannemin ƙafafu dan ɗaya ma tun sanda aka zaroni tama rabu da jikina. Ɗayar kuwa sai daga baya aka yanke min ita. A dalilin wannan haɗari ƴan uwana suka ganni cikin wanda ake cigiyar danginsu dan ni bana iya magana ba saboda buguwa a tv. Nanfa suka rankayo suka saman a asibiti. Bayan na dawo hayyacinna na nuna farin cikin ganinsu. Sai dai koda na tambayi ina iyayenmu dan na nema gafararsu sai aka tabbatar min da duk sun rasu. Nayi kuka sosai Khadijah irin wanda bazai taɓa ya misaltu ba. Amma yaya na iya haka na haƙura ƴan uwana suka kwasheni zuwa gida kasancewar an kira Dafeeq amma baizo ba. Nasha fama matuƙa da jiyya ta kusan shekara huɗu babu Dafeeq babu alamarsa. Gani ina cikin tsangwamar mutane da habaici da zagi akan abinda na aikata. Kowa faɗi yake ai banga komai ba, domin kuwa a silata zuciyar mahaifiyata ta buga dare ɗaya tabar duniya. Hakama babana hawan jini ne ya kasheshi kuma duk akan baƙin cikina ne. Dama ƴan uwan nawa bawai kowa ke kulani ba sam. Tun ina iya jure abinda mutane suke faɗa harna gagara haka. Dan tsantsar ƙyara da tsangwama da izgilanci nake gani kala daban-daban ni da Banan. Har takai ni da fara shiga a wani halin da yasa ƴan uwana dake ɗan kulawa dani suma suka fara janyewa saboda zugar mutane. Ganin bazata haifar min da ɗa mai ido ba dole na tattaro na baro Niger zuwa nan Nigeria. Haka na dawo ga Dafeeq. Inda shima na tarar tasa mahaifiyar ta rasu. Rayuwa ta masa zafi sosai komai ya ƙwace masa. Da farko yace shi bazan zauna da shi ba, daga baya dai darajar Banan daya ɗauki son duniya ya ɗaurawa saboda sunanki ya haƙura mu zauna tare. Sai dai tsangwama da kyarar da yarinyar ke fuskanta yasa dole muka canja anguwa. Haka mukaita wahala akan Banan, mune bara mune aikatau domin mu saya mata sutura mu bata abinci. Amma a hakan bamu tsiraba, dan bayan ta girma tasan kanta saita bijire mana. A sakamakon hakan Dafeeq ya rasa ɓarin jikinsa shima. Shine muketa fama har zuwa yanzu amma dai ga'anan. Dan kullum sai nayi Bara muke samu ma muci abinci sau ɗaya a yini. Mun rasa komai, mun rasa kowa har ƴar da muka haifa Khadijah. Na tabbata alhaƙinku ne. Wlhy alhaƙinku ne ku da iyayena ke da Abaan. Kaicon haɗamammiyar rayuwa irin tamu. Nabar iyayena nabi son zuciyata. Yau ga su Nadwan dana ɗauka da muhimmanci sunci amanata kamar yanda naci ta Abaan da iyayena. Inda suma sukaje sakamakon dukiyar da suka ƙwata a hannun nawa basu mori komai ba. Dan Dr Giɗaɗon shima ya wankesu tass harda nasun ma ya gudu. Inda shima dai bai cin ba ya tararma ajalinsa yay accident a motar komai daya ƙwace a hannunsu ya ƙone ƙurmus dashi kansa sai tokarsa aka tattara aka binne. A yanzu haka suma suna can sabon gari sunama ƴan tuwo-tuwo wanke-wanke da girki ana tsammusu na abinci dana shan sigari. Gaskiyar Noor ƙanwar Abban da tace ni da Dafeeq CUTA TA ƊAU CUTA. ke da Abaan ALKAIRI YA ƊAU ALKAIRI. A yau kuwa ga amsar ta fito. Dan randa mukaga shagalin bikin ƴarku da kukayi a tv munsha kuka sosai muna masu tsinema kammu da ALLAH wadai. Kuma nasan bazamu gushe ba muna masu amsar wannan furucin ga jama'a har ƙarshen rayuwarmu. Fatanmu dai ALLAH yasa mu zama izina ga ƴan baya masu sha'awar irin rayuwarmu koma wanda suke kan aikatawa”........✍️ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_* *_Typing📲_* *_CUTA TA ƊAU CUTA_* _(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_ _𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_ _Shafi na arba'in da huɗu_ *_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._* *_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_* *_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_* *_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_* *_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_* _Littatafan sune kamar haka 👇🏻_. *_KWANKWASON JIMINA....._* _(NA MSS XOXO)_ *_GUDUN ƘADDARA_* _( NA SAFIYYA HUGUMA)_ *_TSUSTAR NAMA....._* _(NA BILYN ABDULL)_ *_AMEENATU_* _(NA MAMU GEE)_ _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 _______________ .........Sosai Khadijah tasha kuka da ganin irin wulaƙantacciyar rayuwar da su Dafeeq suke a ciki shi da Kainaat. Kasa haƙuri tai tun a daren ta kira Alhaji Abaan ta zayyane masa komai. Shima dai al'amarin ya matuƙar girgizashi. Dan haka washe gari da suka zo ɗaurin aure bayan an kammala da yamma ya ɗauki Khadijah da autansa da autan su Khadijah sukaje har asibiti yaga su Dafeeq. Kuka sosai Kainaat ta dingayi da ganin Abaan. Ya sake zama babban mutum duk da shekaru sun fara nuna kansu. Amma dayake akwai kuɗi da hutu da jin daɗi yana nan a ɗan gayunsa ga aji da rashin son hayaniyar nan tashi. Babban abin sha'awa yanda yake tattalin Khadijah sa da ƴaƴansa biyu dake tare da su. Dan Muhammad da Fharooq suna makaranta su. Kasa iya cewa komai Abaan yay sai rungume Khadijah da Mimi dake kuka yay a jikinsa yana lallashinsu. Dan bayan komawarsu gida sai da Mimi tai yanda tai Aunty Jamila ta bata labarin tushen komai da basu taɓa sani ba. Anan ta fahimci tushen rikicin da aka sha a lokacin shirya aurema Yazeed ita sanda suke a shekarun ƙuruciya. Wanda da ƙyar suka sha a dalilin marigayi Baba Hakimi. A take Alhaji Abaan yasa aka canjama su Dafeeq asibiti zuwa Abuja kamar yanda Khadijah ta roƙa. Dan kafin ma su gama shagalin biki su an wuce dasu. An kuma fara basu taimakon da duk ya dace kodan matsayin Khadijah na babbar likita a asibitin na Abuja. Lokacin da suka kammala biki suka dawo Abuja Dr Khadijah ta cigaba da treatment ɗinsu su duka tare da taimakon likitoci. Yayinda Alhaji Abaan ya zuba maƙudan kuɗaɗe da ake basu cikakkiyar kulawa ta musamman. Kafin kace mi abubuwa sun fara daidaita a kansu. Dan kuwa an sakama Kainaat ƙafafun roba duka biyu. Yayinda jikin Dafeeq ya fara murmurewa. Kafin cikar shekara guda sun ɗan dawo hayyacinsu musamman da yake akwai lafiyayyun abinci ga kulawar lafiyarsu. Sai dai Dafeeq bai iya tafiya sai a wheelchair. Gara ita Kainaat ɗin takan ɗan miƙe akan sanduna. Sai dai itama tafiyar tata bata wani nisan zango. A kullum cikin kuka suke da nadamar rayuwarsu musamman ma Kainaat data rasa iyaye da dangi baki ɗaya. Dan tun da ta baro Niger babu wanda ya sake waiwayenta a ƴan uwan nata. Ga rashin ƴaƴa. Ƴar ɗaya tilo ta musu nisan da ko labarinta ma basu da ƙarfin ikon ji sai kukan zuci. Ko ƴan aiki da Khadijah ta ɗiba musu suke tare da su a ɗan gidan da suka basu dan bayan sun sami lafiya Kano aka sake maidosu haka zakaga suna musu wulaƙanci da daka musu tsawa. Yanda masu aiki ke tsoron iyayen gidansu su ga waɗannan ba haka bane. Iyayen gidan ne ke tsoron ƴan aikin. Dan basu musu komai sai hantara da wulaƙanci. Suna zama dasu ne kawai dan amsar kuɗaɗen albashinsu. Su kuma sun gagara iya gayama su Khadijah gaskiya dan kar suga sun cika ƙorafi. Saboda komai a rayuwa su Khadijah sun musu bai kamata su damesu ba kuma. Lokaci-lokaci idan su Khadijah sun shiga Kano sukan leƙa su duba su. Musamman ma Khadijah dake yawan shigowa saboda harkar aikinta na likitanci data samu ɗaukaka daban-daban saboda ƙwazonta. A yanzu haka akowane ƙarshen sati biyu akwai jihar da take zuwa bisitin matsayinta na gawurtacciyar likita da ake ji da ita a Nigeria ma baki ɗaya ba Abuja kawai ba. Ga mijinta daya kasance shahararren ɗan kasuwa lamba ɗaya musamman a fanin shinkafa. Dan zuwa yanzu bama a Africa kawai ba, a duniya kamfanin Alhaji Abaan yana cikin wanda ake matuƙar ji da alfahari dasu a harkar shinkafa. Kuɗi dai kam Alhmdllh akwaisu. Ga ɗaukaka ga suna ga taimako duk ALLAH ya basu. Dan Khadijah ta kafa wata ƙungiyar wayar da kan mata musamman ƙananun yara da iyaye akan harkar soyayyar ƙuruciyar nan da dayawa take kashe rayuwar yaranmu da nakasar zukatan iyaye. Tare da ƙarfafa iyaye akan tsayawa akan ƙafafunsu wajen ganin sun tallafawa ilimin yaransu musamman mata. Dan ɗiya mace tana matuƙar buƙatar ilimi kodan sanin yanda zata tafiyar da rayuwar aurenta ma da tarbiyyar yaranta. Domin kuwa wannan ƙarancin ilimin ya taka rawar gani akan mahaifiyar Khadijah a lokacin da soyayyar Dafeeq ke ɗibarta. Maybe da tanada ilimi data kasance mai tsayawa da bin matakan jan ra'ayin ɗiyarta. Hakama iyayen Kainaat. Maybe da sunada ilimi da basu yarda ƴarsu ta zubar da su ba a idon duniya ta ɗauki wasu iyayen barikin. Duk da dai idan mukai dubi da wani faninin kuma Kainaat nada ilimin ai, amma bai hana ƴarsu Banan ta bijire musu ba itama harta maimaita abinda Kainaat ta aikatama nata iyaye. Hakan na nufin koda ilimin sai an haɗa da ƙyawawan halaye da tsayawa wajen biyayya ma iyaye. Dan iyaye basu kasance abin wasa ba a wajen kowanne irin ɗa komai lalacewarsu da baƙaƙen halayensu. Dan kuwa dai Banan taga hakan, dan duk da baƙin halin iyayenta Kainaat da Dafeeq hakan bai hanata itama ɗan ɗana kuɗarta ba. Tunda da ga ƙarshe ta ɓige da ƙasƙantacciyar rayuwar prison. Ta kuma ratayama kanta alhakin rai. Inda ta koma ba dukiyar babu iyayen babu nasarar rayuwar. Hakama a fannin Khadijah sai da ta girbi abinda ta shuka duk da kuwa ita nata iyayyen ma ta roƙa gafararsu kuma sun yafe mata kafin subar duniya. Amma duk da haka sai da UBANGIJI ya ɗanɗana mata irin wannan zafin data ɗanɗanama iyayenta domin taji ta tabbatar da iyaye ba abin wasa bane ba. Hakama bijire musu babbar musiba ce kuma illa ga rayuwa. Sai dai ALLAH ya taimaketa kasancewa mijinta mutumin kirki mai tsarkin zuciya yasa komai ya daidaita cikin sauƙi suka cimma burinsu na aurar da ƴarsu cikin salama ga wanda taso kuma yake sonta a kuma lokacin da sukai fata. Haka dama rayuwa take cike da ƙalubale kala-kala da kuma nasarori. A wasu lokutan gaggawarmu ke hanamu zuwa ga nasarorinmu. Wani lokacin kuma son zukatanmu ke yanke mana igiyoyin nasararunmu. Mun manta cewar UBANGIJI ya ƙaddarara dukkanin ƙaddaririn namu tunkafin haihuwarmu. Babu kuma mahaluki ko alkalamin da takardar da suka isa canjawa daga abinda zuciya ke so zuwa ga abinda ke a rubuce a taskar ALLAH. Dan haka mu kasance masu tsoron UBANGIJI a duk inda muke a kuma duk yanda muke. Mu kasance masu jin soyayyar MANZON ALLAH a zukatansu akowane hali dan ita a garemu wajib ne. Mu kuma kasance masu biyayya da hakuri da iyayenmu koda abinda suke so mu bai mana ba mu so shi in sha ALLAHU zamu ribatun a wata rana koda ƙasa ta lulluɓe idanunsu. Sannan namu ƴaƴan muma zasu kasance masu biyayya a garemu. Ya rabbi ka shiryemu ka shiryamana yaranmu. Ka tsaremu katsare mana zukatanmu. Ka saka gaskiya a harshenmu, ka saka gaskiya a zukatanmu, ka saka gaskiya a ayyukanmu da gaɓɓanmu. Ya rabbi ka hanemu saɓa maka da ganganci ko akan rashin sanin ka tsaremu daga aikata ZINA. ka shiryi masu aikatawa idan masu shiryuwa ne. Idan ba masu sjiryuwa bane ya rabbi ka nisantamu da su ka nisantasu da ƴaƴayenmu. Ya rabbi ka shiryi masu irin halayyar JJ idan masu shiryuwane. Idan ba masu shiryuwa bane ya rabbi mun kawo ƙarar su gareka ka fimu sanin yanda zakai mana da su.. Ya rabbi ka gafarta mana baki ɗaya. Ka ɗaukaka ayyukanmu da rahamarka.🙏😭✍️. *_ALHAMDULLAHI!!_* Ya rabbi Nagode maka daka bani ikon kammala wannan ɗan littafi nawa. Kuskuren da nayi a ciki rabbi ka yafe mini ni da masu karantawa.🙏 Duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan labari ya yafe Mani. Nima na yafema kowa.🙏 Ina sake tallata muku littatafan ZAFAFA BIYAR dake shirin zuwa muku da wani sabon salo na musamman masoya. Dan tafiyar wannan shekarar fa tanada banbanci da saura matuƙar banbanci. Soyayya ce za'a shata kwarya-ƙwarya😋 babu algus. A fanin ilimin ma mun tanada muku romo mai yawa. Hakama faɗakarwar munzo da sabon tanadi. Kai cakwakiyar ma fa da zamantakewar rayuwa duk ba'a barmu a baya ba. Kudai kawai ku kasance da zafafan biyar ɗin nan naku domin samun nishaɗi fiye da yanda aka saba.😁👍👌 Masha ALLAH sai mun haɗu a ZAFAFA BIYAR dan suna nan shirye tsaff da zafinsu. Kuma gab suke da zuwa gareku in sha ALLAHU suma😁🙏 Bilyn Abdull ce🤙. _Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._ _GUDA DAYA:400_ _BIYU:700_ _UKU:900_ _HUDU: 1200_ _BANK NAME:KEYSTONE_ _BANK ACC NO:6019473875_ _ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_ _ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_ __ _IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_ _*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_ *09033181070* *_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_* _MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥 *_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*