SARAUTAR MUTUWA Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 Haƙƙin mallaka SUFI Shekarar bugu 2023 Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 GODIYA Ta tabbata ga Allah (SWT) bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai suna SARAUTAR MUTUWA. Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu (SAW) da iyalanshi tsarkaka da sahabbanshi masu haske. SADAUKARWA Wannan littafi sadaukarwa ne ga ɗaukacin masoya Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi a ko ina suke a faɗin duniya. Tsarawa da bugawa SUFI PUBLISHING COMPANY R/lemo L/ Pol Kano Nigeria. BABI NA ƊAYA A ƙarni na biyu bayan yaƙin duniya na ɗaya, a yankin arewacin larabawa anyi wani ƙasaitacce birni da ake yiwa laƙabi da zawatul-ifdar. Birnin zawatul-ifdar ya bunƙasa a harkokin kasuwanci, noma, kiwo da ƙarfin tattalin arziki. Sarkin dake mulkin birnin ya kasance gawurtaccen matsafi kuma mashahurin attajiri ana yi mashi laƙabi da Lazwar ibn kaulat. A gaba ɗaya nahiyar larabawa babu mashahurin sarki tamkar shi bisa wannan dalili ne ya sanya ya zamto GAGARABADAU a tsakanin sarakunan nahiyar. Duk waɗannan abubuwan da sarki Lazwar ya tara da ya danganci ƙarfin sihiri da tarin dukiya gami da ƙarfin masarauta ya tashi a banza, domin a daren kowace rana sai na kulle ƙan shi a turakarshi ya yi ta kukan takaici da baƙin ciki, har sai kuyanginshi sun shayar da shi barasa sannan yake samun barci. Ba komai ne yake sanya sarki Lazwar wannan kuka ba face wani dalili guda ɗaya jal! Dalilin kuwa shine bisa binciken da ya gudanar bisa halarar tsafin shi ya gano cewa har abada ba zai samu haihuwa da kowace 'ya mace ba face ya karya wani sihirin da abokin gabar shi sarki Darwazu ya yi mashi. Matsawar kuwa ya yi ganganci ya sadu da wata 'ya mace koda kuwa kuyangarshi ce, take dukkanin sirrikan tsafinshi da duk abin da ya mallaka zai ƙare zai dawo talaka (faƙiri). Tsawon shekaru biyar sarki Lazwar yana cikin wannan baƙin ciki dare da rana. Kwatsam! Wata rana sai kawai aka ji ya ƙwalla ƙara sannan ya bushe da dariya, sautin dariyar tashi ya amsa kuwwa izuwa gidan sarautar baki ɗaya. Al'amarin da ya yi matuƙar bawa kowa mamaki kenan, domin yau tsawon shekaru biyar ba'a taɓa jin shi ya yi hakan ba. Abin da mutane ba su sani ba shi ne bakomai ba ne ya sanya sarki lazwar wannan dariya ba, sai domin yau ne ya gano hanyar da zai lalata sihirin da abokin gabarshi sarki darwazu ya yi mashi. Abu na farko da zai mallaka shi ne hawayen wani gawurtaccen dodo dake zaune a dajin Darul-shatir dodo Murgazu ya kasance hatsabibi wanda ya addabi fatake da biranen dake maƙwabtaka da dajin Darul-shatir. Abu na biyu shine tsumin tsafin bokanya Lazira, bokanya Lazira ta shafe tsawon shekaru dubu biyu tana tsuma tsumin tsafin domin ta cika burin ta na tashin kakanta sarkin bokaye daga cikin kushewarshi, domin ya sanar da ita waɗansu sirrikan tsafi da zata mulki duniya da su. Abu na uku shine ruwan tekun Bahar-dawa'u, tekun Bahar-dawa'u na yamma maso arewacin duniya, yana ɗauke da waɗansu irin musifaffun kifaye da macizai da adadin su ya kai dubu biyar, tsananin ƙarfin damtsen ɗaya daga cikin halittun ya nunka na bil'adama sau hamsin. Abu na huɗu shine alƙyabbar sarkin bokayen duniya na ɗaya boka Murkatul-azab, a halin yanzu alƙyabbar na ajiye a fadarshi dake ƙarƙashin tekun Bahar-maliya, matsafa, bokaye da masu hasashe sun tabbatar da cewa a halin yanzu a duniya babu wani waje mai tattare da musibu tamkar fadar sarkin bokayen duniya. Abu na ƙarshe shi ne wata jaruma da ake yiwa laƙabi da Sharifa bintu Usman. A halin yanzu Sharifa na bauta ne a ƙarƙashin masarautar birnin Istanbul a matsayin baiwa, mahaifanta sun rasu ne a bisa KANGIN BAUTA a masarautar. Baiwa Sharifa ce kaɗai zata iya taimaka mashi ya samu nasarar mallakar waɗancan abubuwa. Sa'adda darki Lazwar ya ga wannan al'amari sai ya cika da matuƙar farin ciki, sai dai wani abu daya dugunzuma hankalin shi, shine halarar tsafinshi ta bayyana mashi cewa ba zai taɓa samun nasarar saduwa da baiwa Sharifa ba har ya samu damar bayyana mata buƙatar shi na son taimaka mashi ya samu don mallakar waɗancan abubuwan da zai karya sihirin ba, face shima ya mayar da kanshi bawa ya yi bauta a ƙarƙashin masarautar na tsawon shekaru. Sannan ma inda gizo ke saƙar shi ne, ba lallai ne Sharifa ta iya amincewa da buƙatar shi ba, tunda a halin yanzu ta rasa dukkan wani farin cikin rayuwar ta. Kasancewar masu iya magana na cewa biyan buƙata yafi dogon buri, kuma inda rai da rabo. Kawai sai ya yanke ranar da zai fita farautar baiwa Sharifa. BABI NA BIYU Kashe gari tun da duku-dukun safiya sarki Lazwar ya fara shirye shiryen tafiya izuwa birnin Istanbul , a dai-dai lokacin da rana ta fara haske ne ya kammala shirin tsaf! Tun daga kuyangi masu hidima, dakaru, gami da bayi. A can fada kuwa jama'a sun cika maƙil babu masaka tsinke. Duk inda mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu saka tsinke tamkar dandazon kiyasai. Kowa ya zuba idanu ana jiran fitowar sarki domin ganin wane zai baiwa riƙon sarautar shi. Tsawon daƙiƙa latalin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne aka jiyo bushin algaita haɗe da bugun tambura. Daga can sai ga sarki Lazwar tafe tare da tawagarshi yana sanye cikin surutu na alfarma da sukayi matukar yi mashi kyawu, kai tsaye ya huce izuwa kan karagarshi ta mulki ya tsaya sannan ya fuskanci jama'a ya yi gyaran murya ya ce "ya ku mutanen wannan fada tawa mai albarka ku yi sani cewa a yau ne zan yi gagarumar tafiya izuwa nemo abubuwan da za su warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki Darwazu ya yi mini. A bisa al'adar wannan masarauta sarki da kanshi yake zaɓar wanda zai bawa riƙon sarautar shi. Bisa ga nazari da kuma hasashe da nayi babu wanda zai riƙe sarautar wannan birni da amana face magajin gari Yasiran". Sa'adda sarki Lazwar yazo nan a zancen shi sai jama'a suka ruɗe da shewa da jinjina domin suna ganin shike nan sun huta da mulkin zaluncin sarki lazwar. Kaico! Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce rashin sani yafi dare duhu, inda a ce jama'a sun san wane ne magajin gari Yasiran da sun gwammace gwara sarki lazwar sau ɗari. Bayan an ɗora Yasiran a bisa karagar mulki sai kawai sarki Lazwar ya buɗe bakinshu ya ƙwala wa wani hadimin aljanin shi kira sau uku, yana gama rufe bakinshi sai kaga wata halitta shirgegiya na ketowa daga cikin gajimare tana sauka daga sararin samaniya. Nan fa suka ɗimauce suka fara guje-guje da ifice-ifice tamkar sun hango mutuwarsu, wasu ma saboda razani har sakin fitsari suke a wando basu sani ba. Aljanin ya sauka a turba yana mai shimfiɗe fuka-fukanshi a ƙasa, shi dai aljanin ya kasance shirgege tamkar tsauni yana da rafkeken kai mai ɗauke da kwala-kwalan idanu jajur tamkar garwashin wuta, hancinshu ƙato ne kofofinshi tamkar bututun shaƙar iska, bakinshi yana da girma tamkar bakin rijiya, maƙale a kwiɓin hamatarshi yana ɗauke da manyan fuka-fukai guda huɗu. Haƙiƙa wannan aljani yakasance mummuna kuma abin tsoro ga duk wata halitta mai numfashi. Aljanin ya kwashi gaisuwa cikin girmamawa ga sarki Lazwar. Sannan ya ɗago da kanshi ya dubi sarki Lazwar cikin ladabi ya ce cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya mai duniya gani na amsa kiran ka me kake da buƙata ya shugabana? Wani alfahari ya shiga kwanyar sarki lazwar jin aljanin ya ambace shu da mai duniya, cikin BAƘAR IZZA Lazwar ya ce " ya kai Za'aratun-layal ka yi sani cewa bakomai ya sanya na kira ka nan ba sai domin ka ɗauke ni da tawaga ta domin gudanar da wata gagarumar tafiya mai matuƙar haɗari. Sai dai ina so ka yi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zan 'yan ta ka ' daga ƘANGIN BAUTA a gare ni". Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai aljani Za'aratun-layal ya bushe da dariyar farin ciki, dariyar tashi ta haddasa wata gagarumar girgizar ƙasa mutane suka fara halaka, sai da sarki Lazwar ya daka mashi tsawa, sannan ya tsuke bakinshi, a sannanne komai ya samu dai-dai ta. Ba tare da ɓata lokaci ba sarki Lazwar da tawagarshi su ka hau bisa kan Za'aratun-layal da ya haɗar da sarkin yaƙin birnin da waɗansu zaratan bayi gami da kuyangi masu hidima suka zauna aka ɗora abin guzuri akai. Sannan aljani Za'aratun-layal ya yunƙura ya tashi sama yana mai kaɗa fuka-fukanshi tare luluƙawa cikin gajimare yana mai tsala azababban gudu, tun jama'a na daga masu hannu har suka dai na hango su. Sai da aka shafe tsawon sa'a bakwai ana tafiya a sararin samaniya ana keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. Lokacin da sa'a ɗaya ta shuɗe ne aljani Za'aratun-layal ya saki fuka-fukanshi ya sauka a turba,inda ya saukar yakasance wani daji ma'abocin kwarjini daban tsoro tun da aka shiga dajin kowa yasha jinin jikinshi, domin dole ne a samu wani abu mai cutarwa a cikin shi. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka ga waɗansu irin masifaffun kibiyoyi suna sauka a dajin, duk da irin ƙwarewa ta dakarun sarki Lazwar kafin su yi wani yunƙuri sai da kibiyoyin suka hallaka fiye da mutum ɗari. Al'amarin da ya fusata sarki Lazwar kenan ya karanta waɗansu ɗalasiman tsafi amma bisa mamaki sai kawai ya ga ya zama hayaƙi. Al'amarin da ya yi matuƙar bashi mamaki kenan kuma ya ɗaure mashi kai kawai sai ya zare takobinshi ya kama kalle-kalle da dube-dube a dajin cikin matuƙar fushi. Kwatsam! sai aka jiyo motsawar ganyayyakin bishiyun daga wani ɓangaren dajin, daga can sai a kayi arba da wata kyakkyawar yarinya mai kimanin shekaru goma sha biyu, zaune a bisa kan shirgegiyar damisa jikin ta sanye da kayan fata riga da wando da takalmi, a gadon bayanta tana rataye da wata zabgegiyar takobi, a hannunta na riƙe da wata irin kwari da baka, nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Lazwar da yarinyar. Lokacin da aka shafe tsawon daƙiƙa latalin ana kallon-kallo tsakanin wannan kyakkyawar yarinya da su sarki Lazwar. sai Lazwar ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar duban yarinyar cikin matuƙar fushi yana mai nuna ta da tsinin takobinshi cikin kakkausar murya ya ce "ya ke wannan 'yar ƙaramar ƙwaruwa shin wane irin rashin hankali ne ya sanya ki aikata wannan laifi a gare ni? Ina so ki bani amsar wannan tambaya kafin na zare miki ruhinki daga gangar jikinki kiyi mutuwar wulakanci. Ko da jin wannan tambaya sai kawai kyakkyawar yarinyar ta bushe da dariyar mugunta. Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa yarinya ƙarama da bata huce ayi mata kwab ɗaya ba amma ta yi GABA DA GABA da dandazon mayaƙa amma bata razana ba. A Lokaci guda yarinyar ta murtuke fuska sannan ta dubi sarki Lazwar cikin wata irin zazzaƙar murya mai ɗan karan daɗi tamkar sarewa ta ce "Ya kai sarki Lazwar ibn kaulat na birnin zawatul-ifdar ka yi sani cewa fiye da shekaru biyar baya na san da labarin ka kuma zaka yaɗa zango a wannan daji domin ka gudanar da tafiyar ka ta nemo abubuwan da za su warkar da kai daga sihirin da abokin gabar ka sarki Durwazu ya yi maka. Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar sai sarki Lazwar ya cika da matuƙar mamaki ya dubi yarinyar ya ce "shin ya aka yi kika san ko ni wane ne kuma mene ne buƙatar ki agare ni. Yarinyar ta ce "mahaifina mafarauci Murrasu kafin rasuwar shi ya sanar da ni labarin ka kuma ya bayyana mini cewa kai ne zaka iya taimaka mini na samu nasarar saduwa da mahaifiya ta dake ƘANGIN BAUTA a can birnin Istanbul bayan na taimaka maka ka sadu da Baiwa sharifa wacce za ka je farautar ta a cikin birnin Istanbul. Ko da jin wannan batu daga bakin kyakkyawar yarinyar sai sarki Lazwar ya sake cika da matuƙar mamaki, kuma ya taka da ƙafafuwanshi ya durfafi inda take ya yin da ya rage saura taku goma a tsakanin su sai ya ja ya tsaya. Cike da matuƙar mamaki ainun ya sake duban ta ya ce "ya ke wannan yarinya mai abin al'ajabi shin mene ne labarin ki? Kuma mene ne ya kai mahaifiyarki bauta a birnin Istanbul? Da jin waɗannan tambayoyi sai hawaye suka kwaranyo daga idanun yarinyar. Al'amarin da ya yi matuƙar bawa sarki lazwar mamaki kenan ya ce a ran shi, shin ina dalilin wannan hawayena yarinyar? Yarinyar ta share hawayen ta cikin alamun matuƙar damuwa ta ce "da farko dai suna na Shuraiba bintu Murrasu, ya kai Lazwar ka yi sani cewa mahaifina mafarauci Murrasu lokacin yana raye yakasance babban hadimi ga sarkin birnin Istanbul, shi ne mai kula da abin da ya shafi tufafin da sarki ke sanyawa da ma sauran iyalan gidan sarautar birnin baki ɗaya. Wata rana mahaifina ya fita farauta daji domin farauto wata dabba da sarki ya ce ke bukatar a yi mashi alƙyabba da ita. Tun safe ya tafi amma har la'asar ta shuɗe bai dawo ba nan fa ni da mahaifiyata mu ka shiga cikin matuƙar damuwa, muna cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai mu ka jiyo haniniyar dawakai a can ƙofar gida Kafin mu yi wani yunƙuri sai muka ga dakarun sarki sun shigo gidan, ina ji ina gani su ka kama mahaifiyata ta ƙarfin tsiya suka tafi da ita. Ina ta rusa kuka tamakar raina zai fita a daren wannan rana ne mahaifina ya dawo daga farauta hankalin shi a tashe idanunshi sharkab da hawaye kuma jikinshi duk jini. Ko da mahaifina ya ganni a cikin wannan hali sai ya janyo ni a jikinshi ya rungume a lokaci guda mu duka biyun mu ka fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya daban tausayi. Sai da muka ɗauki tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani mahaifina ya janye jikinshi daga nawa. Bata re da ya ce mini ƙala ba ya ɗauki wata jakar fata sai KWARI DA BAKAN shi da ke rataye a gadon bayanshi kawai sai ya kama hannuna muka fice daga cikin gidan muka nufi Kofar gari, har muka fice daga birnin muka nausa izuwa cikin daji, a kowacce rana sai nayi kuka wiwi ina mai tambayar mahaifina ina ummana ta ke. Amma sai ya lallashe ni ya kwantar min da hankali cewa ba wani abu ne ya same ta bazata dawo gare mu cikin ƙoshin lafiya. Bakomai ya sanya mahaifina yaƙi sanar da ni labarin mahaifiyata ba, sai domin ganin cewa ni yarinya ce ƙarama bansan komai a rayuwa ba. Sai bayan na girma ne mahaifina ya bani labarin irin zaluncin da sarki ya yi masa na mayar da ummina baiwarshi da yake saɗaka da ita, saboda al'adar sarki duk macen da ya ƙyallara idanu ya gan ta in dai har ta yi mashi to ko matar wane ne sai ya kwace ta ya aure ta ta ƙarfin tsiya. Baƙin cikin rashin mahaifiyata shine abin da ya yi sanadin mahaifina cutar ajali ta kama shi. A daren ranar da zai rasu ne ya mallaka mani KWARI DA BAKAN shu da dukkanin kayan farautar shi bayan ya sanar da ni dukkan sirrikan birnin Istanbul da shi kanshi sarki Ladiyas kuma ya ba ni dukkanin labarin ka ya kai Lazwar. Tun bayan rasuwar mahaifina ne na sha alwashin ceto rayuwar mahaifiya ta daga hannun sarki Ladiyas, dare da rana ina rayuwa a cikin ƙunci da baƙin ciki, babu abin da ke ɗebe mini kewa face wannan damisa da na gada daga wajen mahaifina. Sa'adda kyakkyawar yarinyar tazo nan a labarin ta sai ta fashe da kuka mai matuƙar tsuma zuciya da ban tausayi ga duk wanda ya ji shi. Bisa mamaki sai sarki Lazwar ya ga wannan damisa da yarinyar ke zaune akan ta ita ma ƙwalla na zubowa daga idanuwanta. Al'amarin da ya sanya Sarki lazwar da sauran tawagarshi suka ji sun kamu da matuƙar tausayin yarinya Shuraiba kenan shi kanshi aljani Za'aratun-layal da ya kasance aljani sai da ƙwalla ta zubo mashi saboda tausayi. Sai daga can sarki Lazwar ya dubi yarinya Shuraiba ya ce " ya ke wannan yarinya mai abin al'ajabi haƙiƙa labarin ki cike ya ke da ban tausayi matuƙa, kuma tabbatas sarki Ladiyas ya cika baƙin AZZALUMI, ina mai ɗaukar miki alƙawarin cewa zan taimaka miki har sai na ga kin cika burin ki na saduwa da mahaifiyarki da kuma ɗaukar fansa a kan sarki Ladiyas". Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yarinya Shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral musaltuwa. Ba tare da wani ɓata lokaci ba aka kafa sansani,nan fa kuyangi suka shiga aikin dafa abin kalaci, bayan an kammala ne kowa ya kimtsa cikinshi aka huta sai aka sake ɗunguma wa aka hau bisa kan aljani Za'aratun-layal aka cigaba da tafiya tare da yarinya Shuraiba tare da damisar ta. Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai sai a ka ga waɗansu zaratan dakarun aljanu ɗauke da waɗansu miyagun makamai da idanu basu taɓa ganin irin su ba, gaba ɗayan su suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro, adadin su ya kai dubu ɗaya da ɗoriya. Nan fa tawagar sarki Lazwar suka firgice, wasu daga cikin su har suna sakin fitsari a wando saboda firgici, sarki Lazwar ne kaɗai bai razana ba shi ma a matuƙar firgice ya ke, kawai dai ƙarfin hali ne da ƙi faɗi irin ta hamshaƙan sarakai. Shi kan shi Za'aratun-layal duk da kasancewar aljani sai da ya ɗimauce, domin iya tsawon rayuwarshi ko a labari bai taɓa ganin aljanu masu kwarjini da ban tsoro tamkar su ba. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su na tsawon daƙiƙa latalin, sai daga can wani mummuna daga cikin aljanun wanda da alama shi ne shugaban su ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai ban tsoro yace "ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa ban zo gare ku tare da rundunar mayaƙa na ba domin na yaƙe ku ba sai don ku ba ni yarinya Shuraiba, mu kai ta ga sarkin mu mai girma Zammar, domin ya yanka ta ya sana'anta jininta don ya yi wa matayen mu maganin cutar da ke damun su ta makanta fiye da shekaru hamsin. Ya ku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa matsawar ku ka yi taurin kai wajen damƙa Shuraiba a gare mu, ina mai tabbatar maku da cewa ɗayan ku ba zai ƙetare daƙiƙa goma a raye ba. Ko da jin wannan batu daga bakin shugaban dakarun aljanun sai sarki Lazwar ya yi ƙarfin hali ya tari numfashin shi yana mai daka mashi tsawa ya dube shi ya ce " ya ke wannan ƙaramin ƙwaro tabbas ƙaryar ka ta sha ƙarya, kuma ka yi ɓatan basira da ka ke tunanin cewa za ka iya raba mu da Shuraiba. Ina mai umartar ka da ka janye waɗannan rafkanannun mayaƙan na ka ka koma izuwa ga matsoracin sarkin ku ga faɗa mashi cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne". Kafin sarki Lazwar ya gama rufe bakinshi jikin aljanun ya kama tsuma yana kyarma tamkar za su ci babu. Kawai sai su ka yi wani irin ihu da kururuwa mai firgitarwa suka ɗauki kan su. Ko da ganin hakan sai su sarki suka zare makaman su, ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro da tashin hankali. Kaico! haƙiƙa tashin hankali ba'a sa ma sa rana, kuma duk wanda ya taɓa fita filin yaƙi shi ne ya gama ganin tashin hankali. Nan fa karafniyar ƙarafa gami da ihu da kururuwar dakarun aljanu da bil'adama ta cika dodon kunne, duk sa'adda makaman yaƙin ɓangarorin biyu suka haɗu sai ka ga walƙiya gami da tsawa tamkar za a ke ce da ruwan sama. Ana fara wannan arbu ne sai wani abin mamaki ya faru domin kuwa yarinya shuraiba ta zame wa dakarun aljanun alaƙaƙai kuma ƙadangaren bakin tulu, ya zamana cewa duk wajen da ta sanya a gaba sai ka ga aljanun na zubewa ƙasa matattu. Duk wannan artabu da ake yi tsakanin su sarki Lazwar da dakarun aljanun sarki Zammar ya gani a cikin madubin tsafin shi, a lokacin da yake zaune a fadar koda yaga cewa an kashe gaba ɗaya tawagar shi sai ya cika da matuƙar baƙin cikin maral musaltuwa kuma ya takarkare ya kurma ihu. A ɓangaren su sarki Lazwar kuwa bayan sun samu nasarar hallaka dakarun aljanun sarki Zammar, sai kowa ya shiga sanya magani a raunukan shi, amma aƙalla anyi asarar dakarun yaƙi mutum ɗari biyu da ashirin. Bayan komai ya samu dai-daituwa ne ba tare da wani ɓata lokaci ba sai aka sake ɗunguma aka ci gaba da tafiya. Ana fara wannan tafiya ne sai fira ta ɓarke tsakanin yarinya Shuraiba da aljani Za'aratun-layal, A inda Shuraiba ta dubi Za'aratun-layal tayi gyaran murya ta ce " ya kai wannan dattijon aljani wai kuwa idan ba za ka damu ba nayi maka wata tambaya mana. Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya ce " faɗi tambayar ki ya ke Shuraiba Shuraiba ta ce "wai kuwa a yanzu a cikin jinsin ku na aljanu akwai wanda yafi ka yawan shekaru? Koda jin wannan tambaya sai Za'aratun-layal ya bushe da dariya har da kyakyatawa ya ce "a halin yanzu ni ne ɗan auta a cikin jinsin mu na aljanu a ƙalla zan kai shekaru dubu ɗari uku da haihuwa'' . Cikin matuƙar mamaki shuraiba ta ce "ai kuwa in dai haka ne jinsin aljanu sun fi kowa daɗewa a duniya. Za'aratun-layal ya ce "kwarai kuwa zancen ki dutse". Shuraiba ta ce "amma kuwa mai yasa kuke yiwa bil'adama bauta alhalin kunfi su sanin halin da duniya ke ciki Za'aratun-layal ya ce "Tabbas ke yarinya ce ba ki san komai game da halin duniya ba amma bari na ba ki hikayar sarauniya ABIDAT ta birnin Sin wata ƙila ki shaida batu na. Za'aratun-layal ya yi gyaran murya sannan ya fara da cewa BABI NA UKU Wata mace 'yar kimanin shekaru ashirin da uku ɗauke tsohon ciki a jikinta sanye da tufafi na fatun dabbobi riga da wando. Zaune take a bisa kan wani ingarman doki baƙi, tafiya take a cikin wani irin daji mai tattare da sarƙaƙiya, kwazazzabai gami da duwatsu. Kallo ɗaya za ka yiwa mata ka fahimci cewa tana cikin mawuyacin hali. Kaico! Tana cikin wannan hali ne sai ta ji alamun naƙuda sun bijiro mata, kawai sai ta ja linzamin dokin ta tsaya cak sannan ta kama ta sauko ƙasa kawai sai ta taka da ƙyar ta durfafi kofar wani kogon dutse. Kafin ta isa sai kawai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, a cikin wannan hali ta haife abin da ke cikin ta. Cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa ta ɗauki abin da ta haifa domin ta ga mene ne, ai kuwa sai ta ga wata santaleliyar yarinya ce kyakkyawa ta gaban kwatance, duk da cewar tana cikin halin laulayi, ba ta san sa'adda hawayen farin ciki suka kwaranyo daga idanuwanta ba, a dai-dai wannan lokaci ne kukan jaririyar ya cika dajin baki ɗaya, cikin hanzari ta ɗauki wani ice mai kaifi ta yanke cibiyar jaririyar. Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai ta hango waɗansu dakaru sun durfafo inda take a bisa dawakai. Kafin tayi wani yunƙuri ɗaya daga cikin dakarun ya ɗame kibiyarshi ya harbe ta a gadon bayanta, saboda tsananin zafi da raɗaɗin da ta ji bata san sa'adda ta kurma wawan ihu ba ta sulale ƙasa sumammiya jaririyar ta shiga tsala kuka. Har badakaren ya sake yin shiri a karo na biyu da nufin ya sake harbin ta. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata murgujejiyar zakanya ta yi fitar burgu daga cikin wannan kogon dutse dake dajin, ta dako wawan tsalle ta daki badakaren a kirji. Saboda matuƙar ƙarfin bangazar sai da badakaren da dokin shi su ka yi sama tamkar an janye su da ƙungiya, sannan daga bisani suka faɗo ƙasa matattu ko shurawa ba su yi ba. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin zakanyar da mayaƙan. daga can sai zakanyar ta yi gurnani gami da hargagi sannan ta dako wawan tsalle izuwa kan mayaƙan. Ko da ganin hakan sai dakarun su ka ɗaga makamansu suka yi ihu da kururuwa mai firgitarwa suka yi ɗauki kanta aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni, ban tsoro da ban al'ajabi. Wohoho! Haƙiƙa yaƙi shi ne matattarar dukkan bala'i da musiba, kuma idan gwani ya haɗu da gwani JURIYA DA BAJINTA suka game waje guda, dole ne artabu ya zamo abin tsoro. Nanfa zakanyar ta wanzu tana hallaka dakarun, ya zamana cewa duk inda ta sanya gaba sai dai ka ga dakaru na zubewa ƙasa matattu, a inda za ka ga ta mako badakare faga kan dokinshi ta bishi ta turmushe. A duk sa'adda dakarun su ka kaiwa zakanyar hari sai ka ga ta wurƙila haɗe da zame wa ta kaucewa saran, kafin badakare ya sake daga takobinshi zakanyar ta dako tsalle sama ta sanya faratanta ta tsire mashi idanu ruwan cikin ya tsiyaye, take zai sulale ƙasa daga kan dokinshi yana mai kurma wawan ihu. Kai wasu lokutan idan ta daki badakare a wuya sai ka ji wuyanshi ya ƙara ya karye ya yi ƙara ji kake ruƙus!! Ƙas! Ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba. Haƙiƙa waɗannan dakaru suna ganin tashin hankalin da ba su taɓa ganin irin shi ba. Domin kafin cikar rabin sa'a zakanyar ta kashe fiye da rabin su. Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa da ihun mazaje, haniniyar dawakai haɗe da gurnanin zakanyar ya cika dajin baki ɗaya, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya saboda yadda dawakai ke yin turmutsutsu, kofatunsu na kartar ƙasa. Wohoho! tabbas masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce wuya ko da magani babu daɗi, kuma wuya mai sa dole. Hakan ce ta faru ga sauran dakarun, domin koda su ka ga cewa a kowanne lokaci za su iya baƙuntar barzahu sai suka cika wandunansu da iska domin GUDUN TSIRA da rayuka, sai zakanyar ta dunga ƙure masu gudu tana make su suna faɗuwa ƙasa matattu. Kafin wani lokaci ta zubar da gawarwakin su a ƙasa. Kawai sai ta juya ta durfafi inda wannan mata da jaririyar ke kwance a ƙasa tana fitar da wani irin gurnani. BABI NA HUƊU Lokacin da aljani da aljani Za'aratun-layal ya zo dai-dai nan a hikiyar sarauniya Abidat ta birnin Sin sai ya ja bakinshi ya yi shiru. Cikin alamun matuƙar damuwa Shuraiba ta dube shi ta ce "haba ya masanin HIKAYAR DUNIYA mene ne ya sanya za ka yanke ba ni wannan labari mai matuƙar daɗi gami tsantsar tausayi, haƙiƙa na matsu naji a wane hali wannan mata da jaririyarta su ke ciki? Kuma wace ce wannan zakanya da ta ceci rayuwar su? Shin mahaifiyar jaririyar ta na raye ko kuwa ta mutu sakamakon harbin kibiya da wannan badakare ya yi mata a gadon baya". Ko da jin wannan batu sai Za'aratun-layal ya cewa da Shuraiba ''shin baki lura da inda muka iso ba ne? Leka izuwa kasa ki gani". Da jin hakan sai ta sunkuya da kanta ƙasa aikuwa sai ta hangi wani irin baƙin daji mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. Sarki Lazwar ya dubi aljani Za'aratun-layal ya ce ''shin me ka fahimta da wannan daji dake gaban mu? Za'aratun-layal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu sannan ya ce " ya shugabana wannan daji dake gaban mu yana ɗauke da tsananin sanyi don haka dole ne kowannen ku ya sanya suturun kariya, sannan kuma dukkanin daji da ya kasance yana tattare da irin yanayin to dole ne a samu miyagun halittu masu shan jinin bil'adama da cin naman su, sai inda kizo ke saƙar shi ne bani da tabbacin waɗanne irin halittu ne. Ko da jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai kowa yasha jinin jikinshi. Cikin hanzari sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi ya ɗauko madubin tsafin shi da nufin gudanar da bincike, amma sai aljani Za'aratun-layal ya yi wuf da dakatar da shi ya ce ''ya shugabana ka yi sani cewa amfani da sihirin tsafi a irin wannan tafiya abu ne mai matuƙar haɗarin gaske domin baka da tabbacin cewa wanda za ka yi binciken bai fi ka karfin sihiri ba. Sannan shin ka manta cewa kowa a gidanshi sarki ne, mafita ɗaya ce a gare mu kowanne ku yakasance cikin shiri tun da gashi yanzu la'asar ta riske mu, ba zamu ɗauki wani tsawon lokaci ba duhun magariba zai gaba ce a dajin kenan dole yaɗa zango cikin dajin dole ne domin mu kwana mu huce gajiyar dake tare da mu. Da jin wannan batu sai kowa ya shiga sanyawa kanshi rigunan sanyi tun daga ƙasa har sama kuma kowa ya gyara riƙon makamin shi. Za'aratun-layal ya yi ƙasa-ƙasa ta fuka-fukanshi sannu a hankali har aka sauka a bisa turba . Sa'adda kowa ya yi arba da dajin sai tsoro ya kara kama shi. Shi dai wannan daji yakasance gaba ɗayan shi yana ɗauke da waɗansu irin dogayen bishiyu masu rassa masu matuƙar kaifin tsiya masu tattare da sarƙaƙiya, babu wani waje da mutum zai ajiye kafarshi face ya taka dusar ƙanƙara ce, Babu abin da zai ƙara firgita mutum kuma ya jefa tsoro a zuciyarshi sai jin shiru da ya wanzu a dajin tamkar babu wani abu mai rai a cikin shi, kai hatta irin tsuntsaye haka a saman bishiyoyin babu su. Nan fa aka fara tafiya a cikin ɗar ɗar domin shirin ko ta kwana, amma bisa mamaki sai ga shi an shafe tsawon rabin sa'a ba tare da an jiyo motsin wani abu mai cutarwa ba. Al'amarin da ya sanya kowa ya fara sakin jikinshi kenan, ana cikin wannan tafiya ne tsinin reshen wata bishiya ya yanki bawa zafiyar a cinyarshi jini ya zuba a ƙasa. Kawai sai a ka ji gaba ɗaya dajin ya kaure da wani irin gurnani mai ban tsoro ba shiri kowa ya tushe kunnuwanshi domin ƙarar na iya kurumtar da mutum. Abin da su sarki Lazwar ba su sani ba shi ne zubar jini a dajin shine alamun da halittun ke gane cewa bil'adama ya shigo dajin. Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin zaratan muradai na fitowa daga kowacce kusurwa a dajin. Muridan sun kasance masu matuƙar tsawo tamkar bishiyar kuka. Jikkunansu a mummurɗe suke tamkar duwatsu suna da rafkeken kai mai ɗauke da idanu ƙwaya ɗaya jal! Wanda ya kasance jajur tamkar garwashin wuta, fuskokin su munana ne babu kyawun gani, duk sa'adda su ka wangame bakunansu sai ka ga cewa wani irin yawun mai yauƙi na dalala, a hannayen su kuwa suna ɗauke da waɗansu irin masifaffun makamai na yaƙi da idanu basu taɓa gani ba, a ƙalla adadin muridan ya kai dubu uku da ɗoriya. Lokacin da muridan suka kammala yiwa su sarki Lazwar ƙawanya, sai aka fara kallon-kallo tsakanin ɓangarorin biyu,tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali sai daga bisani ne muridan su ka yi wata kururuwa mai firgita dandazon mayaƙa a filin daga, su ka yi ɗauki izuwa kan su, Koda ganin hakan sai su sarki Lazwar su ka yi kururuwa suka ruga izuwa kan muridan. Ana haɗuwa aka yi muguwar KARON BATTA. Wohoho! Haƙiƙa tashin hankali ba'a sa mai rana, kuma ita wutar bala'i kafin ta zo ne ake guje mata, amma idan tazo kawai miƙa wuya ake yi a tare ta ko dai a mutu ko a yi rai. Kaico! ana fara wannan arbu ne su sarki Lazwar suka fara gane cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin muridan sun zame masu tamkar GOBARAR ANNOBA. Duk sa'adda ɗaya daga cikin ya kai wa su sarki Lazwar hari da makaminshi, idan su ka goce saran ya sauka akan bishiya sai ka ga ta rabe gida biyu ta faɗi ƙasa rikica za ta danne su. Kafin ka ce me tuni muridan sun hallaka fiye da dakaru gami da kuyangi fiye da guda dubu. Al'amarin da ya yi matuƙar figita su sarki Lazwar kenen, babban abin da ya fi dugunzuma hankalin su shi ne yadda muridan suka kasance masu matukar zafin nama, tamkar jikkunan su na amfani da wata na'ura dake sarrafa su. Shi kan shi aljani Za'aratun-layal duk irin matuƙar karfin damtsen shi sai da ya zamana muridan sun zamto mashi ciwon idanu. A ɓangaren yarinya shuraiba kuwa ana cikin wannan yaƙi ne wani daga cikin muridan ya kawo mata wani wawan sara da gatarinshi da nufin tsinke mata wuya, Cikin wani irin baƙin zafin nama ta zille wa saran gatarin muridan ya shige cikin ƙarƙashin ƙasa. Kafin muridin ya zare gatarin na shi Shuraiba ta ɗame bakanta ta harbe shi da kibiya a idon shi guda, take ya fashe jini ya dunga kwarara tamkar an buɗe kan fanfo, nan fa muridin ya faɗi kasa yana mai kwarara ihu yana birgima zuwa wani lokaci ya sheƙa barzahu komai na jikin shi ya dai na motsi. Ko da yarinya Shuraiba ta ga wannan nasara da ta samu sai ta cika da matuƙar farin ciki, kuma a sannanne ta fahimci cewa ruhikan muridan suna cikin wannan idanu na su guda ɗaya dake tsakiyar goshin su. Kawai sai ta ci gaba da ta harbin muridan a idanun su cikin matuƙar ƙware wa da zafin nama. Wohoho! Gaskiyar masu iya magana da suka ce kyan ɗa ya gaji ubanshi, kuma ita sadaukantaka gadon a ke yi ba wai a kasuwa ake siyarwa ba. Haƙiƙa babu wadda zai yi arba da yarinya Shuraiba a cikin wannan hali face ya jinjina mata. A ɓangaren sarki Lazwar, sarkin yaƙi da su bawa Kuwait kuwa, sa'adda suka ga yadda yarinya Shuraiba ta gano lagon muridan har ta na samun nasarar hallaka su sai suka yi koyi da ita. Ya zamana cewa suna daka tsalle sama suna hawa kan muridan suna amfani da takubban su suna soke masu idanu. Aljani Za'aratun-layal kuwa hannunshi ya dunƙule ya shiga naushin muridan a idanuwansu. Duk wanda ya gabza wa naushin sai dai ka ga ya faɗi kasa matacce. Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan kiɗa ya canja dole ne rawa ta canza. Nan fa muridan suka fara gane kuren su suna yin muguwar hallaka a banza, komai hassadar mutum idan ya ga yadda sarki Lazwar ke ragargazar muridan dole ne ya jinjina mashi ya tabbatar da cewa tabbas Lazwar ya cika GWARZON DUNIYA kuma SARKIN SADAUKAI. Saboda yadda yake kashe muridan tamkar yana sassabe a gonar auduga. Lokacin da aka shafe sa'a ana wannan arbu sai ya zamana cewa duhun dare ya fara kawo kai, nan take tsananin sanyin dake dajin ya daɗa ƙaruwa. Nan fa su sarki lazwar suka shiga cikin wani tashin hankali, kuma tsawon lokacin da aka shafe ana wannan gumurzu bai huce muridan guda ɗari kacal ba aka hallaka ba. Koda ganin halin da ake ciki sai sarki Lazwar ya karanto waɗansu dalasiman tsafi domin samun mafita. Kaico! Hakikya rashin sani yafi dare duhu, inda a ce sarki Lazwar ya san abin da zai biyo baya da bai yi gangancin karanta dalasiman tsafi ba, domin kuwa faruwar keda wuya sai wata irin iska ta musamman ta mamaye dajin baki ɗaya wacce ta sanya sanyin ya kara tsanan ta. kawai sai ya ga jama'ar ya yanke jiki suna faɗuwa ƙasa sumammu. Ko da ya waiga bayan shi domin ya ga a wane hali yarinya Shuraiba ke ciki. Kawai sai ya ga wayam babu ita babu alamar ta, kafin ya mayar da duban shi zuwa ga su sarkin yaƙi sai kawai ji ya yi an gabza mashi wani wawan naushi a fuska take hankalin shi ya gushe ya dai na gane kanshi. Su sarki Lazwar ba su tsinci kansu a ko ina ba sai a cikin wani ɗakin duhu, wanda saboda matuƙar duhun shi mutum ko tafin hannayenshi ba ya iya gani, a bisa cikin wani irin ƙaton keji da aka yi shi da zallar waɗansu irin itace masu ƙwarin gaske. Jim kaɗan da farkawar su sai kawai su ka ga ɗakin ya gauraye da wani irin haske mai ban mamaki. Sai a sannanne sarki Lazwar ya gane cewa kowannen su an sanya shi a keji na daban ba tare da an gama shi da ɗan uwanshi ba, hatta aljani Za'aratun-layal na shi kejin daban, amma duk an daɗɗaure shi da waɗansu irin sarƙoƙi na baƙin ƙarfe. Sa'adda kowannen su ya sake buɗe idanuwan shi tarwai ya ga babu yarinya Shuraiba da gaba ɗaya sauran tawaga, sai hankulan su suka dugunzuma ainun, kuma aka shiga firgici, aka fara tunanin shin ko yarinya Shuraiba da tawaga sun rasa rayukansu ne. Shi kanshi aljani Za'aratun-layal da bai kasance bil'adama ba sai ya ji a ran shi yana matuƙar kewar Shuraiba tamkar da ma sun daɗe da shaƙuwa da juna. Tsawon lokacin ana cikin wannan hali sai daga bisani ne sai su kaji karar buɗe sakatun kofar ɗakin. Jim kaɗan sai Kofar ta buɗe sai ga waɗansu irin zaratan dakarun muridan su bakwai sun shigo cikin ɗakin. Kallo ɗaya su sarki Lazwar su ka yiwa dakarun suka sunƙuiyar da kawunan su ƙasa, saboda matukar kwarjinin da munin siffar su. Dakarun su ka durfafi inda su sarki lazwar suke, su na isa gare su suka ɗauki kejin da suke ciki su ka ɗora a bisa kafaɗunsu, wanda aljani Za'aratun-layal ke ciki kuwa dakaru biyu suka ɗauka, kawai sai su ka fice daga cikin ɗakin, suka durfafi wata hanya ta musamman su ka shiga izuwa cikin gari. Nan fa su sarki lazwar suka cika da matuƙar mamaki da al'ajabi suka kama kalle-kalle da dube dube-dube, tamkar ɗan ƙauye ya shiga birni, shi dai gaba ɗaya birnin muridan an gina gidajen shi da waɗansu irin manyan duwatsun wuta masu kwarin gaske, masu matukar tsawo da faɗi. Ko da jama'ar birnin su ka yi arba da su Lazwar sai suka cika da matuƙar murna, su ka suka shiga tanɗe bakunansu gami dalalar da yawu, saboda matuƙar kwadayin yau za su kalaci da naman bil'adama. Tafiyar daƙiƙa talatin kacal! aka yi aka iso fadar birnin. Fadar ta kasance tanƙamemiya mai matuƙar tsawo da faɗi, kuma gininta anyi shi ne da irin waɗannan duwatsu masu ƙyalli, sannan an ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya har dama abin da idanu ba su taɓa gani ba. A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza da mata yara da manya, babu masaka tsinke, bisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'an ta ta da zallar ƙarfen jauhari, aka yi mata feshi da koren ruwan yaƙut. Wani irin shirgegen mutum ne wanda yafi gaba ɗaya muridan girma kwarjini da cika idanu zaune bisa wata ƙasaitacciyar karaga. yana sanye cikin wata irin ƙasaitacciyar shiga irin ta su ta manyan sarakai, sanye da wata alƙyabba da aka yi mata ado da gashin ɗawisu kanshu sanye da wani KAMBUN SARAUTA na zinare. Zaune a gefen hannunshi na dama, wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa ce ta gaban kwatance. Budurwar tana da dara-daran idanuwa farare ƙal! Masu haske tamkar tacacciyar madarar shanu, ɗigon cikin su ya kasance siɗik mai kwarjini, girar saman su baƙa ce siɗik tayi luf-luf, hancinta dogo ne mai ban sha'awa, a ƙasan shi an tsaga wani ɗan madaidaicin baki da labbanshi suka kasance jajur, wuyanta dogo mai kyau tamkar na barewa, kirjinta kuwa ya yi tudu a cike yake kuma a tsaye ƙyam! Bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda, cikinta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, ƙugunta daga gaba ya tsuke daga baya kuma ya yi tudu tamkar idan aka ɗora tuffa za ta zauna, 'yan yatsun hannayenta da kafafuwanta sun kasance zara-zara masu ɗaukar hankali. Wohoho haƙiƙa Allah wannan budurwa ta cika kyakkyawa ta kece raini, babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da wannan kyakkyawar halitta face ya ɗimauce, kuma ya kamu da matukar kaunar ta a zuciyarshi. Ba wata ba ce face gimbiya Mashlira 'ya ga sarki muridan Kushuful-mannar Sarki Kushuful-mannar ya auri mahaifiyarta ne a cikin waɗansu a yarin larabawa da aka riba to a matsayin fursunonin yaƙi, bisa binciken da sarki Kushuful-mannar ya yi bisa halarar tsafin shi ya gano cewa 'yar shi Mashlira ce silar dauƙaƙar shi a duniya da ci-gaban zuri'arshi a doran ƙasa, bisa wannan dalili ne ya sanya ya ke matuƙar kaunar ta fiye da komai a rayuwarshi. Tun kafin dakarun da suke ɗauke da su sarki Lazwar su iso inda karagar mulki take gimbiya Mashlira ta ƙurawa Lazwar idanu ko ƙiftawa ba ta yi, a karon farko a rayuwar ta ta ji wani abu ya ɗarsu a zuciyarta. Shi kuwa sarki Lazwar koda ya ga irin kallon da budurwar ke yi mashi sai ya ji zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya kama shi jikin shi ya kama ƙyarma, abu na farko da jefa shi cikin wannan hali shi ne, a iya tsawon rayuwarshi tun da yake bai taɓa gani ko jin labarin 'ya mace mai matuƙar kyawun ta ba. Abu na biyu kuwa shine lokacin da da ya haɗa idanu da ita sai ya ji cewa a duk faɗin duniya babu wata budurwa da yake ƙauna tamkar ta. Yanzu ta ya ya zuciyarshi za ta kamu da soyayyar wata 'ya mace bayan cewa ba zai taɓa kusantar mace ba da niyar aure ba face ya karya sihirin dake jikinshi. Wai shin wane tabbaci ya ke da shi cewa waɗannan muridan za su bar shi a raye, Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai hankalinshi ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe. Lokacin da ya rage sauran kamar taku goma tsakanin su da karagar mulki sai dakarun su ka zube ƙasa, su ka kwashi gaisuwa cikin girmamawa bayan sun ajiye kejin da su Lazwar ke ciki. Sarki kushuful-mannar ya shin-shina su sarki Lazwar yana mai tanɗe baki tamkar wadda zai ci naman ɗawisu. Sannan ya busar da iskar dake hancinshi wani irin tiririn baƙin hayaƙi ya fita daga ƙofofin hancinshi. Kawai sai ya yi wa ɗaya daga cikin dakarun wata inkiya ta wutsiyar idanu. kawai sai badakaren ya buɗe kejin da bawa zailan ke ciki ya ɗauko shi ya kwantar da shi akan wani zagayayyen tudu, sannan ya ɗauko wata zabgegiyar takobi ya ɗaga sama ya datse wuyan bawa Zailan kuma ya shiga daddatsa naman shi. Koda ganin yadda aka yiwa bawa Zailan sai su sarki Lazwar su ka kamu da matuƙar tausayin shi har ƙwalla ta cika masu idanu. Badakaren na kammala daddatsa naman sai ya watsawa jama'ar dake fadar. Tun kafin ya kai ƙasa jama'a sun wawashe sun cinye suna ihun murna da kururuwa mai tayar da hankali. Badakaren ya sake sanya hannuwanshi a kan kejin da sarki Lazwar ke ciki ya buɗe sakatun, ya zira hannun sa ya ɗauko shi ya ɗora shi a bisa wannan tudu, a karo na biyu ya sake ɗaga takobin domin ya datse wuyan sarki lazwar. Kafin takobin ta datse wuyan Lazwar sai gimbiya Mashlira ta dakawa badakaren tsawa sannan ta dubi mahaifinta ta ce "ya abbana ina neman wata alfarma a gare ka da abar mani waɗanan fursunoni zuwa gobe, domin nima ina so na ga na hallaka su da hannaye na domin ɗaukar fansar kisan da su ka yiwa dakarun mu shin ko ka manta ne cewa fiye da shekaru ashirin hakan bai taɓa faruwa ba. Koda jin wannan batu sai sarki zammar ya yi murmushi mai taushi ga 'yarshi Mashlira ya ce "nayi miki wannan alfarma ya muradin zuciyata ai girma da matsayin ki ya huce haka, gaba ɗaya jama'ar wannan birni da abin da ke cikinsu mallakin ki ne". Ko da gama faɗin hakan sai ya yi wa badakaren inkiya a karo na biyu kawai sai badakaren ya mayar da takobinshi cikin kuben ta. Sannan ya ɗauki sarki Lazwar da hannunshi ɗaya tamkar ya ɗauki takarda ya sake jefa shi cikin kejin ya mayar da kofar ya rufe, sannan ya sake umartar waɗannan dakaru suka sake ɗaukar kejinan, har suka fice da fadar gimbiya Mashlira bata daina satar kallon sarki Lazwar ba tana yi mashi murmushi mai ɗauke da alamar tambaya. Al'amarin yarinya Shuraiba da damisar ta kuwa, a she lokacin da waɗannan samudawan muridai suka samu nasarar kama abokan tafiyarta ta rugawa ne izuwa wani ɓangare a dajin ta laɓe domin ta ga abin da muridan za su aikata Sa'adda ta ga muridan sun ɗauke su a cikin kejunan sun kunna kai izuwa cikin dajin, sai ta ci gaba da bin sahun su sannu a hankali, har sai da ta shige izuwa cikin birnin su ba tare da wani ya gan ta ba, da yake lokacin dare ya fara duhu sai Shuraiba ta maƙale a dai-dai ƙofar gidan da aka ajiye su sarki Lazwar, tana zuba idanu domin ta ga wanda zai fito daga cikin, tana nan tsaye sai kawai ta hango waɗansu dakaru su bakwai sun durfafo Ƙofar gidan har dakarun sun zarce gaba, sai kawai ɗaya daga cikin su ya dubi sauran 'yan uwanshi ya ce "haƙiƙa ni fa ina jin ƙamshin bil'adama. Sauran suka dube shi suka ce "kwarai tabbas zancen ka dutse, muma muna jin hakan kawai dai shiru mu kayi". Ko da jin abin da dakarun ke tattaunawa sai shuraiba ta yi wuf ta shiga cikin wani kwandon shara tare da damisarta, nan fa wari da ɗoyin dake ciki ya fara galabaitar da ita ga yunwa da addabe ta, take numfashin ta ya ɗauke, ta sulale ƙasa sumammiya, a dai-dai lokacinne badakaren ya haska gwandon sharar da wata fitar ice, dake hannunshi domin ya ga menene a cikin. Ko da haskawar ta shi sai ya ga babu komai a cikin shawara. cike da mamaki da al'ajabi ya sake shaƙar iska dake wajen amma a wannan karon sai ya ji ba ya jin ƙamshin bil'adama. Kawai sai ya juya izuwa inda yan uwanshi suke tsaye ya tarar da su ya dube su ya ce "babu komai a wajen tamkar yadda muke tunani, take sauran dakarun su ka cika da matuƙar mamaki, ɗaya daga cikin su ya yi gyaran murya ya ce cikin wata irin kakkausar murya "amma kamar yau na samu labarin cewa dakarun mai girma Zammar masu FARAUTAR MAZAJE sun samu nasarar kamo waɗansu fursunonin bil'adama,'. Wata ƙila wannan kamashi da muke ji yana da alaƙa da bil'adaman dake cikin wannan birni namu". Ko da gama faɗin hakan sai dakarun su ka juya suka ci gaba da tafiya. Kaico! Haƙiƙa yarinya Shuraiba da damisar baƙaramin tsallake rijiya da baya suka yi ba. Abin da dakarun ba su sani ba shi ne tabbas akwai bil'adama a cikin sharar, kawai dai saboda Shuraiba da damisar ta sun sume ne babu rai a tare da su shine ya sanya ba su ji ƙamshin su ba. Kuma bisa halayyar muridan matuƙar babu rai a jikin bil'adama ba za su ji kamshin shi ba. Tsananin sanyin da ya mamaye birnin bisa ketowar alfijir, shine abin da ya farkar da yarinya Shuraiba da damisar ta, koda farkawar ta su sai suka yunƙura suka fito sharar, nan take damisar ta fahimci cewa Shuraiba ta galabaita ainun da alamu ƙishi ruwa ce ta addabe ta, koda fahimtar sai kawai ta shiga tona ƙasa da ƙafarta ɗaya jim kaɗan sai ga shi ta tarar da ruwa. Kawai sai Shuraiba ta sunkuiya ƙasa bisa gwiwoyinta ta sanya hannayenta biyu, tana kamfatar ruwan ta na sha, duk da cewar ruwan yana da sanyi ƙarara har yana kama mata hakuri, amma haka ta cigaba da kwankwaɗar shi har sai da ta ƙoshi. A sannanne Shuraiba ta ji ƙarfi a jikinta, kawai sai ta yunƙura ta haye bisa gadon bayan damisar. Sannan ta cigaba da tafiya a cikin birnin, sai dai a wannan karon ba su haɗu da komai ba, haka dai su ka cigaba da tafiya a sannu-sannu, tana cikin tafiyar ne ta hango wani katafaren gida waɗansu irin dakaru tsaye a wajen, kuma shirye cikin gagarumar shigar yaƙi rike da miyagun makamai. Nan take Shuraiba ta sunkuiyar da kanta ƙasa tana mai zurfafa cikin kogin tunani. Daga can sai kawai ta durfafi ƙofar gidan, kafin ta isa sai ta hango waɗansu dakaru na daban ɗauke da waɗansu kejunan ƙarfe, kawai sai ta rakaɓe a wani waje tana hangen abin da ke faru, ba wasu ba ne a cikin kejin ba face su sarki Lazwar Ko da ta ƙwarewa kejin kallo sai ta lura cewa ƙofofin kejin suna ɗauke da waɗansu irin kwaɗuna, waɗanda ke nuna cewa akwai mabudin su, wani tunani da ya faɗo wa yarinya Shuraiba shi ne. Yanzu idan har ta ƙyale aka shige da su sarki Lazwar cikin gidan ba lallai ne suka kasance a raye ba, lallai dole ta yi dukkanin ƙoƙarin da ya dace don ceto rayuwar su kafin gari ya waye. Gama tunanin hakan keda wuya sai Shuraiba ta hangi wani tsuntsu a saman ta yana yana wani irin kuka da ta ga ya durfafi wani ɓangare na musamman a wannan gida da za shige da su sarki Lazwar, cikin matuƙar farin ciki ta dunga bin bayan tsuntsun, ba tare da waɗannan dakaru sun ganta ba. Koda isowar ta kusa da saitin inda dakarun suke a dai-dai lokacinne aka iso da su sarki Lazwar za a shiga da su cikin. Sai kawai ta ga wannan tsuntsu ya buɗe bakinshi ya busa wa gaba ɗaya dakarun wani irin koren haske, kafin ka ce me sun ɓingire ƙasa suna sharar barci har da munshari, kuma koren hasken ya shiga cikin kejunan su sarki Lazwar, take suka narke suka zama ruwa, sarƙoƙi da aka ɗaure aljani Za'aratun-layal suka ɓace ɓat!. Daga can sai tsuntsun ya rikiɗa izuwa wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa, ba wata ba ce face gimbiya Mashlira 'ya ga sarkin murida Zammar. Nan fa sarki Lazwar, Shuraiba, sarkin yaƙi da bawa Shaiban suka cika da matuƙar al'ajabi. Cikin wata irin zazzaƙar murya mai ɗan karen daɗi tamkar ana busa sarewa, gimbiya Mashlira ta dube su su duka huɗun ta ce "yanzu ba mu da lokaci da zamu tattauna domin a kodayaushe mahaifina zai iya biyo sahun mu, matsawar ya riske mu ɗayan mu ba zai tsira da rayuwar shi ba. Ko da jin wannan batu daga bakin Mushlaira sai sarki lazwar ya umarci aljani Za'aratun-layal ya ɗebe su baki ɗaya, zuciyarsu cike da matuƙar farin ciki bisa ganin cewa yarinya shuraiba ta na raye cikin koshin lafiya, kuma gimbiya Mashlira ta ce ci rayuwar su. A dai-dai wannan lokaci ne sarki Zammar da tawagarshi suka bayyana a wajen, koda ya ga dakarun kurku kwance suna sharar barci kuma babu su Lazwar da 'yarshi Mashlira, sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu, ihun shi ya haddasa wata girgizar ƙasa da ta sanya gine-gine suka dunga rushewa, nan fa birnin ya kaure da gujegujen jama'a domin TSIRA DA RAYUKA. Sai da sarki ya tsuke bakinshi sannan komai ya samu dai-dai ta gidaje suka dai na rushewa mutane suka daina hallaka. Kawai sai ya ɗauko madubin tsafinshi ya shafe shi da hannunshi na hagu, yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafi, yana gama rufe bakinshi hoton aljani Za'aratun-layal ya bayyana a kai, yana tsala azababban gudu ɗauke da su sarki Lazwar da 'yarshi Mashlira. Koda ganin hakan sai takaici ya ƙara turnuƙe zuciyarshi har ƙwallar baƙin ciki ta zubo mashi, kawai sai ya runtse idanuwanshi yana mai karanta waɗansu dalasiman tsafin na daban, koda kammala hakan sai ga wata irin halitta ta ketowa daga cikin ƙarƙashin ƙasa. Halittar ta nunka aljani Za'aratun-layal a girma, muni, da kwarjini gami da cika idanu. Ba wata ba ce wannan halitta ba face aljani Durusul-fannar, Durusul-fannar ya faɗi ƙasa ya yi sujjada ga sarki zammar, Zammar ya du be shi fuska a murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta kan ta. Cikin kakkausar murya mai ban tsoro ya ce "ya kai uban hatsabibai kuma kakan kangararru na duniya ka yi sani cewa, fiye da shekaru dubu ɗaya da ɗoriya rabon da na kira ka domin aiwatar da wani aiki sai yau, to ina so ka yi sani cewa na kirowa ka ne domin ka bi sahun su 'yata Mashlira da ta ci amana ta ta kuɓutar da waɗansu bil'adama da muka farauto. Ina so ka kawo min su a raye cikin ƙoshin lafiya domin ni da kai na zanyi hukunci, Koda sarki Zammar ya zo nan zancen shi, sai Durusul-fannar ya sake yin sujjada karo na biyu ga sarki Zammar cikin wata irin murya mai kama da saukar aradu ya ce "an gama ya sarkin sarakai, yin biyayya a gare ka shi ne ibada ta". Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya ya yunƙura izuwa sama domin ya bi sahun su aljani Za'aratun-layal, take ya shiga keta gajimare cikin wani irin masifaffan gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. Wannan shi ne abin da ya faru a acan birnin muridai. BABI NA BIYAR Al'amarin su sarki Lazwar kuwa lokacin da suka ci gaba da gudu a bisa kan aljani Za'aratun-layal, bayan gimbiya Mashlira ta ceci rayuwar su daga hannun mahaifinta, sai suka ci gaba da tafiya a sararin samaniya cikin hanzari. Ana fara wannan tafiya ne sarki Lazwar ya matsa kusa da Mashlira ya ce" ya ke wannan 'yar sarki ma'abociyar tausayi da jin ƙai, haƙiƙa ba mu san da wane irin baki zamu gode miki ba bisa ceton rayuwar mu da kika yi. Sai dai abin da muka kasa fahimta ni da abokan tafiya ta shi ne, mene ne dalilin da ya sanya kika biyo mu bayan cewa baki san daga wata duniya muke ba, kuma baki san ina zamuje ba. Ko da jin wannan batu sai Mashlira ta yi wani ƙayataccen murmushi da ya kara tona asirin tsantsar kyawun surar ta har fararen haƙoranta suka bayyana farare ƙal! Cikin daddaɗar murya ta ce "ya kai wannan sarki ka yi sani cewa kafin na fito daga cikin gidan sarautar birnin mu sai da na gudanar da bincike bisa halarar tsafina, na gano dukkan labarin ku da duk abin da ya baro da ku daga biranan ku, na nemo abubuwan da su warkar da kai daga sihirin da abokin gabar ka sarki Darwazu ya yi maka. Bakomai ne ya sanya na biyo ku domin gudanar da wannan tafiya ba, duk kuwa da irin haɗurran dake tattare da ita sai domin mahaifina ya gano cewa nan gaba zan samu ɗaukaka mai yawa wacce sai labari na ya yaɗu a duniya, bisa binciken da na gudanar a yau na gano cewa ta silar ku zan samu wannan ɗaukaka. Sannan kuma zan cika burina na samowa jama'ar birninmu maganin da zai warkar da su, su dawo ainahin surar su ta bil'adama. Da yake duk wannan tattaunawa da ake yi tsakanin sarki Lazwar da Mashlira kowa yana saurare, ya yin da aka ji abin da Mashlira ta furta sai kowa ya cika da matuƙar mamaki da al'ajabi. Sarki Lazwar ya dube ta cike da matuƙar mamaki ya ce "ya sarauniyar kyawawa shin dama jama'ar birninku bil'adama ne kamar mu ba muridai ba? Ko da jin wannan tambaya sai idanun Mashlira suka ciko da kwalla, fuskarta cike da matuƙar damuwa ta ce "Bbsa labarin da mahaifina ya ba ni ya tabbatar min da hakan, kuma ya sanar dani maganin da zai warkar da su daga wannan annoba, akwai buƙatar na sanar da ku labarina a taƙaice. BABI NA SHIDA A wani zamani can baya mai tsawo da ya shuɗe lokacin da jahilci ya yi katutu a zukatan bil'adama, ƙarfi da jarumtaka suka zamto jari, kuma ake yin gashin dankali wato babba a sama ƙarami a ƙasa A wannan lokaci anyi wata nahiya mai ɗauke da manyan birane guda biyar, biranen na ƙarƙashin mulkin wani gawurtaccen azzalumin matsafi da ake yiwa laƙabi da Sahibul-ukub Matsafi Sahibul-ukub yakasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa, domin an ce a filin yaƙi yana iya shafe tsawon kwanaki biyu yana yaƙi ba tare da ya ci ko ya sha ba. Idan ya je farauta daji kuwa yana iya saɓo giwa a kafaɗarshi, ya yi gudun sa'a ɗaya da ita ba tare da ya gaji ba, komai girman bishiya idan ya naushe ta da hannunshi sai ta jijjigo har saiwarta sannan ta faɗi ƙasa, Kai wasu lokutan ma idan zai kai farmaki wani birni ko alkarya, shi kaɗai yake fita ya yaƙi birnin a dare ɗaya ya farauto bayi, da dukiya mai da ganima mai tarin yawa. Bisa wannan dalili ne ya sanya duk biranen da suka ji labarin matsafi Sahibul-ukub zai kawo farmaki, ko da dai su fita su tafi izuwa gare shi su yi MUBAYA'A kafin ya zo, ko kuma su tattare ina-su-ina-su su fice daga birnin su yi hijira izuwa wata nahiyar daban. Batun ƙarfin sihirin tsafi kuwa, masu bincike da hasashe sun tabbatar da cewa a halin yanzu babu matsafi kamarshi, zaluncin shi kuwa ya huce yadda muke tsammani domin saboda matuƙar zaluncin shi yasa aka gina mashi kurkukun ƙarƙashin ƙasa da ake bautar da mutane da aljanu. A rayuwar matsafi Sahibul-ukub bai taɓa yin aure ba ballantana a ce yana da magaji da zai maye gurbin karagarshi. wata rana yana zaune a turakar shi sai kawai a ka ji ya taƙarƙare ya ƙwala ihu sannan daga bisani ya bushe da dariya mugunta, bakomai ne ya sanya matsafi sahibul-ukub ihu da dariyar ba face wani labari da sarki yaƙin sa ya kawo mashi, na wani ɓoyayyen birni mai tarin arzikin noma kiwo, da ma'adanan ƙarƙashin kasa. Birnin Madinatul-Adfal na yamma maso arewacin birnin Sin. Sarkin da ke mulkin birnin yakasance GWARZON DUNIYA mai karfi na Allah ya isa, yana shugabantar jama'ar shi bisa adalci da matuƙar tausaya wa, bisa wannan dalili ne ya sanya kullum tattalin arzikin birnin yake ƙara haɓaka. Wani abu da matsafi Sahibul-ukub ya gani bisa halarar tsafinshi shi ne, matuƙar ya mallaki birnin zai zamo mashahurin attajirin da babu kamarshi a faɗin duniya, kuma a wannan birni zai gina fadar da take babu kamar ta a duniya baki ɗaya. Kasancewar birnin yana ɗauke da dukkanin wani yanayi mai daɗi da bil'adama ke bukata. Bayan Sahibul-ukub ya kammala dariyar mugunta, sai ya juya ya dubi sarkin yaƙin da ke durƙushe a gaban shi tamkar zai yi mashi sujjada, cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da taƙama gami da BAKAR IZZA ya ce ''ya kai dirkar birnin Jauraful-harbat, haƙiƙa ba ka taɓa zuwa mii da labari mai daɗi kamar wannan ba, Amma lamarin ɓoyayyen birnin ya ba ni mamaki, da har na gasa gano shu bisa halarar tsafi na, amma ba abin mamaki bane domin masu iya magana na cewa shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka ba za ka iya ɗebe abin da ke cikin shi ba sai dai ka ɗebi iya gwargwadon ka. Yanzu abin da nake so shine a tanadar min dakarun yaƙi guda dubu hamsin, tare da magina dubu goma da kuyangi dubu, bayi da barori, a daren yau ina so alfijir ɗin a subahin gobe ya keto min a birnin madinatul-Adfal, domin wannan yaƙi na musamman ne a gare ni, ko da jin wannan batu sai sarkin yaƙi Shamsal ya risina ga matsafi Sahibul-ukub ya ce "an gama ya shugaba na". Yana gama faɗin hakan sai kawai ya miƙe tsaye ya fice daga turakar, domin aiwatar da umarnin da akayi mashi. A can birnin Madinatul-Adfal kuwa jama'a na gudanar da ayyukan su cikin lumana, masu saye da siyarwa na yi masu noma da kiwo na yi, sauran yara kuwa na wasanni a tsakanin su cikin nishaɗi, hakan kuwa ya faru ne sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya kamar da bakin ƙwarya ƙasa ta kwanta kuma gari ya yi daɗi korayen tsirrai sunyi luɓ-luɓ gwanin ban sha'awa, A na cikin wannan hali ne sai ka ga gari ya yi duhu dumɗum! Tamakar dare biyu ya haɗu waje guda, kai ka ce hadari ne ya gangamo zaa ɓarke da da ruwan sama, nan fa gari ya kaure da gujegujen jama'a gami da ifice-ifice yara da manya mata da maza. Ba wani abu ba ne ya haddasa wannan duhu ba face bayyanar rundunar matsafi Sahibul-ukub da ta iso birnin Sa'adda gimbiya Mashlira yar sarkin muridai Zammar ta zo dai-dai nan a labarin ta sai ta yi shiru, bakomai ne yasanya ta yi hakan ba, sai bisa ganin wata mummunar halitta da ta bayyana a gaban su, ba wani ba ne wannan halitta ba face aljani Durusul-fannar da mahaifinta ya turo domin ya farauto su. Ko da bayyanar aljani Durusul-fannar sai cikin kowa ya ɗuru ruwa, hatta shi kanshi aljani Za'aratun-layal da ya kasance aljani. Wannan fa shine masu iya magana ke cewa GABA DA GABANTA wai aljani ya taka wuta, kafin ɗaya daga cikin su ya yi wani yunƙuri aljani Durusul-fannar ya buda wata irin iska daga bakinshi, nan take su sarki Lazwar suka kama barci mai nauyi, kawai sai ya damƙe su ya makale su ajikin fuka-fukanshi tamkar ya ɗauko 'yan tsaki, ya juya izuwa hanyar da za ta mayar da shi izuwa birnin muridai. Tofa ana dara ga dare ya yi. Lokacin da aljani Durusul-fannar ya tsala da azababban gudu, ɗauke da su gimbiya Mashlira, sai ya ci gaba da keta gajimare cikin gudun huce sa'a domin ya isa ga sarki Zammar, yana cikin wannan gudu ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai ya yi kiciɓus da wani aljani agaban shi, Aljanin ya kasance ma'abincin kyawun sura fari sol. Zaune a bisa kanshi wani kyakkyawan yaro ne mai kimanin shekaru goma sha shida, wanda da kaɗan ya ɗara yarinya Shuraiba. Yaron yana sanye cikin fararen tufafi tun daga ƙasa har sama, a gadon bayanshi yana rataye da wata sharbebiyar takobi. Kallo ɗaya zaka yiwa yaron ka tabbatar da cewa kyakkyawa ne na gaban kwatance domin inda za'a ajiye shi daf da gimbiya Mashlira ba za ka iya tantance wane ne yafi kyawu a tsakanin su ba. Sa'adda Durusul-fannar ya yi arba da su yaji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya ɗarsu a cikin ta. A karo na farko a rayuwar shi ya ji wata halitta ta razana shi, nan fa ya cika da matuƙar mamaki ainun. Abu na farko da ya bashi mamaki shine duka aljanin bai kama ƙafarshi a girman jiki da surar jarumtaka ba, kuma wanda ke zaune a kanshi bil'adama ne yaro matashi. Kawai sai ya yi ƙarfin hali ya dakawa masu tsawon cikin matuƙar fushi ya dube su ya ce ''ya ku waɗannan ma'abota GAJERAN KWANA shin wane rashin tunani ya sanya za ku tare min hanya? Ba ku da labarin cewa nine GOBARAR ANNOBA mai tada hankalin duniya, ANNOBA ƊARI mai shayar da jarumai TASKAR AZABA? Kafin aljani Durusul-fannar ya gama rufe bakinshi kyakkyawan yaron ya tari numfashin sa yana mai cewa ''kaicon ka ya kai tsohon mushriki, ka yi sani cewa yau ƙarshen ka ya zo, kai maza ka miƙo min su sarki Lazwar da ka ɗauko su domin ka kaiwa sarki Zammar ya hallaka su. Sannan kuma ina kira a gare ka ka bayar da gaskiya da Ubangijin da ya halicci duniya da abin da ke cikin ta"; Ko da jin wannan batu sai zuciyar aljani Durusul-fannar ta kama tafarfasa tamkar za ta ƙone ya sake dakawa yaron tsawa a karo na biyu, tabbas yaro man kaza, bai san wuta ba sai ta narka shi, kuma haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka, tsautsayin akuya gai da kura, rabon da wata halitta da ɓata min rai yau shekara dubu hamsin, lallai daga kan ku hakan ba zai sake faruwa ba, domin zan koyar da duniya darasi akan ku". Gama faɗin hakan ke da wuya sai Durusul-fannar ya yi ɗauki kan su yana ihu da kururuwa mai firgitarwa, tamkar zai tashi duniya baki ɗaya, Ko da ganin hakan sai kyakyawan yaron ya buɗe bakinshi yana mai karanta waɗansu kalmomi, sannan ya zare takobinshi a gadon bayanshi ya tunkari Durusul-fannar suka yi KARON BATTA. Kaico! Haƙiƙa KARON MAZA babu daɗi, kuma tashin hankali ba a sa ka mai rana, nan fa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro gami da ban al'ajabi, nan fa yazamana cewa, abin nan da masu iya magana ke faɗi ya fara tabbata, wato ɗan hakin da ka raina shi ne ke tsoka ne maka idanu. Sai ga shi yaron ya zamto wa Durusul-fannar ƙadangaren bakin tulu kuma alaƙaƙai, Duka sa'adda da ya kai mashi duka da hannayenshi sai yaron ya zille gami mayar da martani cikin zafin nama, idan takobinshi ta taɓa jikin Durusu sai ka ji ya kurma wawan ihu. Bakomai ne ya sanya shi ihun ba face tsananin zafi da raɗaɗin da yake ji tamkar ana ƙona shi da wuta. Abin da Durusul-fannar bai sani ba shi ne takobin yaron na ɗauke da sirri na musamman, ana cikin wannan artabu ne yaron ya kaiwa Durusul-fannar wawan sara a kafaɗarshi, cikin sa'a ya yanke shi, take jikinshi ya kama da wuta, nan fa aljani Durusul-fannar ya kama ihu da kururuwar neman taimako. Indai ace mutum ya na tsaye a wannan waje yana kallon abinda ke faruwa, dola ne ya yi wa Allah godiya bisa ganin cewa mushriki maƙiyin Allah zai yi mutuwar wulakanci. Koda kyakyawan yaron ya fahimci cewa wutar zata iya kona su sarki Lazwar da har yanzu su ke cikin halin barci. Sai kawai ya ya yiwa hadimin shi umarni da ya kai masu ɗauki. Cikin zafin nama aljani ya miƙa hannayenshi biyu ya ɗauko sarki Lazwar, Mashlira, shuraiba, aljani Za'aratun-layal, sarkin yaƙi da bawa Shamsal, ya ajiye su bisa gadon bayanshi, sannan ya saki fuka-fukanshi ya yi ƙasa luu!. Ya sauka a turba a dai-dai lokacin da aljani Durusul-fannar ya ƙone kurmus tokar gawarshi ta sheƙe cikin iska. Ya yin da ya sauka a turba sai ya sauke su sarki Lazwar a ƙasa. Yaron ya koma gefe guda ya share ƙasa yana mai fuskantar alƙibila ya fara gudanar da ibadar shi irin ta ma'abota addinin Musulunci, kawai sai aljanin ya tsaya a gefen shi a yana mai koyi da shi, Sarki Lazwar ne ya fara farkawa daga barcin, sannan gimbiya Mashlira, bawa Shamsal, sarkin yaƙi, yarinya Shuraiba aljani Za'aratun-layal a ƙarshe. Lokacin da kowa ya wartsake ya dawo cikin hayyacin shi, suka arba da wannan kyakkyawan yaro da hadimin shi suna gudanar da Sallah, sai kowa ya yi turus! Cike da matuƙar mamaki gami da al'ajabi. Abu na farko daya bawa ko mamaki shi ne yadda yaron ke gudanar da ibadar cikin tsafta da tsari mai ban sha'awa, sannan ya aka yi su ka tsira da rayuwar su? Kuma ina aljani Durusul-fannar ya ke? Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kan su kenen, kawai sai suka zuba idanu suna kallo, har ya kammala ibadar sannan ya juya ya fuskanci su sarki Lazwar ya ce "ya ku waɗannan mutane ku yi sani cewa ban ceto rayuwar ku domin ku saka min da wani abuba, face kawai saboda Ubangiji na ya bayyana mini ku a cikin mafarki na. Kuma ta silar ku ne zan samu nasarar gano 'yar uwata da ta ɓace, kimanin shekaru bakwai. Bisa wannan dalili ne ya sanya na ce ci rayuwar ku bisa taimakon Ubangijina, duk da cewa ta mai bautar Allah maɗaukakin sarki, ku kuma kun kasance kuna bauta wa gumaka". Sa'adda su ka ji wannan batu daga bakin yaron sai kowa ya sake cika da matuƙar mamaki da al'ajabi. Ita kuwa yarinya Shuraiba sai ta ƙura wa yaron idanu, gami da yi mashi wani irin kallo da ita kan ta bata san dalilin yin shi ba, tana mai cewa a ranta. Shin wai dama akwai wani Ubangiji da ya halicci mutane bayan allolin mu? Amma addinin wannan yaro yana tattare da tsafta da kayatarwa, Nan take ta ji tana matuƙar ƙaunar yaron a cikin ranta tamkar ta daɗe da shaƙuwa da shi. Sarki Lazwar ya buɗi baki ya ce ''ya kai wannan yaro mai ban al'ajabi shin mene ne sunan ka da labarin ka? Ko da jin waɗannan tambayoyi sai yaron ya yi murmushi da ya ƙara wa fuskarshi kyawu ya ce "Ni suna na Imran ibn Nadir na fito daga ƙasar Yemen ne neman 'yar uwata wacce na rasa ta sakamakon farmakin bazato da aka kawo birninmu, ita ce kaɗai ta rage mini a cikin jinina, sannan babban burina shine kuma na yaɗa addini na gaskiya a doran ƙasa, game da tambayar ka kuwa mene ne labari na wannan hikaya ce mai tsawo yanzu babu lokacin yin shi sai dai a nan gaba". Ko da jin amsar wannan tambaya sai sarki Lazwar ya juya ya dubi sarkin yaƙin shi yana mai yi mashi raɗa a kunne ya ce "ya dirkar birnina shin yanzu kana ganin zamu amince da yaro Imran mu yi wannan tafiya tare da shi alhalin ya kasance mabiyin addinin Musulunci, kuma sanin kanka ne cewa iyayenmu da kakanninmu mun mutu ne bisa ƙiyayyar wannan addini. Sannan ka san babu yadda za'a yi sirrikan tsafi na su yi tasiri a wannan tafiya matsawar yaro Imran zai karanta abin da ya shafi addinin su, Abu ɗaya ma da nake tsoro ya kasance shi ne a koda yaushe zan iya rasa sirrikan tsafi na. Koda jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai sarkin yaƙi kara bakinshi dai-dai kunnen sarki cikin ladabi ya ce "ya shugabana tabbatas zancen ka dutse ne, sai dai wani hanzari ba gudu ba, baka ganin cewa dukkanin abokan tafiyar mu sun faɗa tarko da yawa amma sirrikan tsafin ka ba su tseratar damu ba. Yanzu da wannan yaro bai ceci rayuwar mu ba da yanzu kuma wani labarin ake yi daban ba wannan ba. Ni dai shawara ta shine ka ga dai Imran yaro ne ƙarami babu ta yadda za ayi ya canja tunanin ɗayan mu mu shiga addinin shi, kawai zamu yi amfani da shi ne, domin cimma buƙatar mu daga baya sai mu yi watsi da shi". Da jin wannan shawara ta sarkin yaƙi sai sarki Lazwar ya bushe da 'yar karamar dariyar mugunta ya dafa kafaɗunshi ya ce "an gaishe ka namijin duniya shi yasa dai-dai da sa'a ɗaya bana son a ce na rabu da kai saboda irin wannan al'amari, Ko da gama wannan shawara sai sarki Lazwar ya dubi yaro Imran ya ce "ya kai wannan Imran ma'abocin taimako haƙiƙa mun amince mu yi wannan tafiya tare, sai dai bisa sharaɗi guda, sharaɗin kuwa shi ne iya tsawon wannan tafiya da zamu yi har ka sadu da 'yar uwarka, ba za ka tilasta ɗayan mu cewa sai ya yi imani da Ubangijin ka ba"; Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Lazwar sai yaro Imran ya yi lallausar murmushi a gare su ya ce "ka kwantar da hankalin ka ya kai wannan sarki mai daraja ai addini ba a tilasta mutum ya shige shi face idan ya yi niyya da kan shi, Da jin wannan batu daga bakin Imran sai kowa ya gyɗa kai alamar gamsuwa, yaro Imran ya mayar da duban shi zuwa ga aljanin shi ya ce "ya kai Hadimul-khair ina mai umartar ka ka shiga izuwa cikin wannan daji ka samo mana abin da zamu yi kalaci gami da ruwan sha. Aljani Hadimul-khair ya risina ga yaro Imran ya ce "an gama ya shugaba na. Yana gama faɗin hakan ya kaɗa fuka-fukanshi ya nausa izuwa cikin dajin, Jim kaɗan bayan shuɗewar waɗansu 'yan daƙiƙu sai Hadimul-khair ya dawo ɗauke da waɗansu nunannnun kayan marmari da suka haɗar da tuffa, gwanda, ayaba, lemu gami da ibini. Ya ajiye a gaban Imran,shi kuma Imran ya yi umari kowa ya ɗebi wanda zai ishe shi, sannan kowa ya shiga kimtsa cikinshi, ita kuwa damisar yarinya Shuraiba sai ta kama kiwon a wajen tana kama kwari da kananan dabba tana lamushe su. Bayan an kammala ne an samu nutsuwa sai aka ɗunguma a ka ci-gaba da tafiya, inda aljani Za'aratun-layal ya ɗauki sarki Lazwar, sarkin yaƙi, bawa Shamsal da gimbiya Mashlira, amma sai yarinya Shuraiba ta ki yarda ta hau kan shi, inda ta nemi alfarma a wajen naaro Imran da ya amince mata ta hau bisa kan aljanin sa tare damisa Faizur. Al'amarin da ya yi matuƙar fusata sarki Lazwar kenan ya buɗe baki da nufin ya hana yarinya Shuraiba hawa kan aljani Hadimul-khair, amma sai sarkin yaƙi ya dakatar da shi yana mai yi masa raɗa a kunne ya ce "haba ya shugabana kar ka manta cewa Shuraiba tana da matuƙar muhimmanci a wannan tafiya tamu, domin ita ce ta san sirrin birnin Istanbul dama shi kanshi sarkin birnin, kar tun yanzu ka ɓata kiɗan da rawa, har Shuraiba ta fahimci cewa kana ɓoye mata wani abu game da yaro Imran har ta yi ƙoƙarin shaƙuwa da shi ta fahimci addinin shi. Idan kuwa har hakan ta faru to kuwa zamu rasa su baki ɗaya wato Imran da Shuraiba. Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai jikin sarki Lazwar ya yi sanyi ya koma ya zauna aka cigaba da tafiya. BABI NA BAKWAI A can birnin Zawatul-ifdar kuwa, jama'a kuwa sun fara yabawa aya zaƙin ta, domin magajin gari Yasiran yana yi masu MULKIN ZALUNCI da ya zarce na sarki lazwar. Domin ɗan ƙankanin laifi mutum zai aikata sai a yanke mashi hukuncin kisa ko zaman gidan kaso, yiwa 'ya'ya mata fyaɗe, ƙwace gami da fashi da makami ya yawaita a birnin Zawatul-ifdar. Duk wanda ya yi sabon aure to ba zai tare da matarshi face an kai ta ga magajin gari Yasiran ya tara da ita sannan zai karɓi amaryar shi kashe gari. Yan kasuwa aka matsa masu da karɓar haraji, nan fa ya zamana cewa hatta 'yan majalisar birnin sun fara ƙosawa da mulkin zaluncin Yasiran, suka shiga tunanin hanyar da za su kawar da shi daga kan karagar mulki, duk da cewar a halin yanzu sun fi matuƙar tsoron shi fiye da sarki Lazwar. Wata rana da hantsi lokacin zaman fada an cika maƙil da jama'a babu masaka tsinke, duk inda mutum ya duba kawunan bil'adama ne rututu tamakar dandazon kiyasai, ana jiran fitowar magajin gari Yasiran. Ana cikin wannan hali kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ji fadar ta kaure da wata irin mahaukaciyar dariya mai ban tsoro, daga can sai aka ga Yasiran ya bayyana tsulum! A fadar tamkar an jefo shi daga sama, hannunshi na dama riƙe da wata sharɓeɓiyar takobi, na hagun kuwa riƙe da wani mashi an tsire kan wani mutum a jikin shi jini na zuba. Sa'adda jama'a su kayi arba da kan, sai suka ɗimauce 'yan majalisa kuwa sai jikkunansu suka kama ƙyarma saboda matuƙar tsoro, ba komai ne sanya su ƙyarma face bisa arna da kan sarkin fada, wato ɗaya daga cikin yan majalisar magajin gari Yasiran ya ɗaga hannunshi sama fadar tayi tsit! Tamkar mutuwa ta kawo ziyara. Fuskarshi a murtke ya ce "ya ku al'ummar wannan fada mai albarka ku yi sani cewa, wannan shi ne darasi ga duk wanda baya goyan bayan mulki na a wannan birnin". Yana gama faɗin hakan sai ya yi jifa da kan sarkin fada a kas, cikin hanzari wani badakare ya shigo fadar janye da hannun wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa, tana ta rusa kuka sai ya iso da ita daf da ida karagar mulki take sannan ya risina ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa. Sannan ya buɗi baki cikin ladabi ya ce "ga ta nan na zo da ita ya shugabana"; Yasiran ya dube shi ya ce "sai ayi hanzari akai min ita turakata". Badakaren ya miƙe tsaye ya fice da budurwar wacce ke rusa kuka tana magiyar a rabu da ita, komai rashin imanin mutum idan ya ga halin da budurwar ke ciki, dole ne ya zubar mata da hawaye saboda matuƙar tausayi, da yawa daga mutanen fadar sai da su ka zubar da ƙwalla sabo da matuƙar tausayin budurwar. Wannan shi ne abin da ya faru a can birnin Zawatul-ifdar bayan sarki Lazwar ya ɗora magajin gari Yasiran a bisa sarautar shi ya shiga izuwa duniya. Haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce, sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba, sai ga shi an shafe tsawon kwanaki arba'in da huɗu ana tafiya tsakanin sarki Lazwar, gimbiya Mashlira, yarinya Shuraiba, sarkin yaƙi ,bawa Shamsal aljani Za'aratun-layal tare da yaro Imran. A iya tsawon wannan tafiya shaƙuwa mai karfi ta ƙullu tsakanin yarinya Shuraiba da yaro Imran, kuma Imran ya bayyana abubuwan mamaki gami da ƙarfin ikon Ubangiji. Domin sau talatin da bakwai yana ceto rayuwar su sarki Lazwar bisa taimakon Ubangijin musulunci. Bisa wannan dalili ne ya sanya Mashlira da Shuraiba suka fara kwaɗayin shiga addinin. A ranar da kwana hamsin suka cika ne aljani Za'aratun-layal ya sauka a bisa wani daji dake kusa da birnin Istanbul, nan fa farin ciki ya kama kowa shima aljani Hadimul-khair ya sauke Imran da yarinya Shuraiba Bayan kowa ya sauko sai aka shiga tattaunawa akan hanyar da kowa zai bi wajen shiga birnin Istanbul, inda Shuraiba ta dubi kowa sannan ta yi gyaran murya ta ce "akwai shawarwari da zan bamu waɗanda matsawar muka kiyaye su zamu shiga cikin birnin Istanbul lafiya kuma mu fito lafiya sumul. Da farko dole ne kowannen mu ya ƙaurace sanya tufafi masu tsadar gaske, ko wada ke nuna wata alama ta mulki . Na biyu gujewa ƙarya da ha'inci, sannan yin biyayya ga dukkan abin da ya shafi masarauta. Waɗannan sune shawararin da idan muka kiyaye su zamu cimma nasara. Koda Shuraiba ta zo dai-dai nan azancen ta sai ta juya da dubi Gimbiya Mashlira ta ce "ya ke Mashlira ya zama wajibi idan zaki shiga cikin wannan birni na Istanbul ke rufe fuskarki da rawani, har zuwa lokacin da zamu kammala samun abin da muka shiga nema, domin tsananin kyawun surarki zai jawo miki matsala. Koda yarinya Shuraiba ta zo nan a jawabin ta sai tayi bankwana da damisarta suna masu zubar da hawayen rabuwa da juna, har sai damisar ta ƙule izuwa cikin daji ta daina hangen ta. Ko da jin wannan batu daga bakin Shuraiba sai kowa ya gyaɗa kai cikin farin ciki, kawai sai sarki Lazwar ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya nuna aljani Za'aratun-layal da ɗan yatsan shi na hagu, take Za'aratun-layal ya riƙiɗa izuwa wani garjejen sadauki mai kwarjini daban tsoro, sannan ya sake karanto waɗansu dalasiman tsafin take tufafin dake jikin su ya canja launi zuwa makasƙanta, babu wanda zai ga sarki Lazwar da gimbiya Mashlira a wannan hali face ya cika da mamaki bisa ganin yadda suka koma tamkar almajirai saboda tufafin dake sanye a jikkunansu. kaico! Haƙiƙa masu iya magana sun yi gaskiya da suka biyan buƙata ya fi dogon buri. kuma ranar biyan buƙata rai da dukiya ba a bakin komai suke ba. Kawai sai aka ɗunguma aka durfafi ƙofar birnin Istanbul gadan-gadan, shi kuwa yaro Imran sai ya matsa kusa Shuraiba ya yi mata raɗa a kunne, sannan ya dawo da duban shi ga hadimin shi ya ce dash ''ya kai Hadimul-khair ina ganin ya kamata ka kasance a ɓoye, koda ka bayyana har sai lokacin da na buƙaci hakan" koda jin hakan sai Hadimul-khair ya risina ya ce ''an gama ya shugabana, kawai sai ya ambaci sunan Allah gami da yiwa Annabi salati take ya bace bat, tamkar bai taba wanzu wa ba. Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar lokacin da suka iso izuwa birnin Istanbul. BABI NA TAKWAS BIRNIN ZAWATUL-IFDAR Al'amarin wannan budurwa da magajin gari yasiran ya yi umarni a kai mashi ita izuwa turakar shi kuwa, ba wata ba ce face wata sabuwar amarya, kuma an ɗauko ta ne domin ya keta mata haddi. Lokacin da wannan badakaren ya isa da ita turakar sai ya tarar da kuyangi na ƙawata turakar da kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, wani irin daddaɗan kamshi na tashi a ko ina. A harabar turakar da bakin ƙofa kuwa dakaru ne birjik shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da miyagun makamai. Ya yin da amaryar ta tsinci kanta a ciki turakar sai ta sake fashewa matsanancin kuka mai tsuma zuciya, tsawon sa'o'i tana cikin fargaba da tsoron abin da zai faru gare ta, kuma tana tuna halin da angon ta ya ke ciki. Haka ta kasance a cikin wannan hali har duhun dare ya fara nisa, a cikin wannan hali ne ta ji motsin shigowar magajin gari Yasiran ba, nan fa tsoro ya kara kamata ainu. Tana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai kawai ta ga wani kyakkyawan tsuntsu yana fitar da wani sautin kuka mai daɗin saurare, yana shawagi a harabar turakar. Cike da matuƙar kwadaituwa da son ganin tsuntsun, ta matsa izuwa tagar dake turakar ta leƙa ai kuwa sai ta ga anyi wani rubutu a jikin fuka-fukan tsuntsun da harshen Larabci kawai sai ta furta a bakinta, faruwar hakan keda wuya, ai sai ta ji dukkan baƙin ciki gami da tsoron dake zuciyarta ya tafi, tamkar babu wani mugun abu dake shirin faruwa a gare ta. Cikin farin ciki mara musaltuwa ta cigaba da karanta kalmomin a cikin ranta A dai-dai wannan lokacin ta ji an turo kofar shigowa turakar, tana buɗe wa sai ga Yasiran ya bayyana, yana sanye da wani mayafi na alhariri da ya rufe daga cibiyarshi izuwa gwiwarshi. Sa'adda amaryar ta yi arba da shi saboda matuƙar tsoro ba ta san sa'adda ta faɗi ƙasa ba, jikinta na ƙyarma tamkar mazari, shi kuwa magajin gari sai ya nufi inda take yana mai bushewa da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa, Lokacin da ya matso daf da ita sai ya kawai ya miƙa hannunshi da niyyar ya cakume ta.amma sai ya ji wani irin tiririn zafi ya tunkaro shi tamkar an yana kusa tanderun wuta. Al'amarin da ya yi matuƙar ba shi mamaki kenan kuma ya fusata ainun, kawai sai ya buɗe baki da nufin ya karanta waɗansu dalasiman tsafi. Kaico! haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, in da ace Yasiran ya san abin da zai faru da bai yi gangancin karanta dalasiman tsafin ba, domin kuwa yana cikin hakan ne wata irin gagarumar wuta ta kama a jikinshi tana ci. Nan fa magajin gari ya shiga kurma wawan ihu yana mai kai komo a cikin turakar domin ganin ya kashe wutar, amma duk sa'adda ya zuba ruwa sai wutar da ƙara ruruwa. Ita kuwa amarya munirat koda ta ga wuta ta kama a jikinshi, sai ta ci gaba da karanta waɗannan kalmomi na larabci da taga ni a jikin fuka-fukan tsuntsun nan a cikin zuciyarta, kuma ta miƙe tsaye zumbur ta rugawa izuwa ƙofar fita daga turakar. Bisa mamaki duk ƙofar da ta tunkara sai ta ga ta buɗe da kanta, wani abu da ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai shi ne, gashi dai ƙiri-ƙiri dakaru suna kallon ta ta tsakiyar su take ratsawa, amma babu mai ɗaga mata yatsa ballantana ya ce mata uffan. Haka dai amarya Munirat ta cigaba da tafiya a cikin gidan sarautar, zuciyarta cike da matuƙar farin ciki maral musaltuwa gami da imani da ma'abocin waɗannan kalmomi da ta karanta suka ce ci rayuwar ta. A dai-dai wannan lokaci ne dakarun dake gidan sarautar suka dunga tuttɗowa suna zare makaman su suna rugawa izuwa ɓangaren sarki, bisa jin ihu gami da kururuwar magajin gari Yasiran da suka yi. kafin ƙiftawar idanun gidan sarautar ya hargitse da guje-gujen jama'a gami da ifice-ifice tamkar an busa ƙahon BUSAR MUTUWA. BABI NA TARA A can birnin muridai kuwa, sarki Zammar mahaifin gimbiya Mashlira ya ga dukkanin abin da ya wakana tsakanin yaro Imran da aljani Durusul-fannar. A cikin halarar tsafin shi a lokacin da yake zaune a fadar tare da 'yan majalisar shi. Ko da ganin hakan sai ya cika da matuƙar baƙin ciki maral-musaltuwa. Wata rana sarki Zammar na kwance a cikin turakarshi da ta ƙawatu da kayan alatun more rayuwr duniya, sai ya yi mafarki da yarshi Mashlira tana cikin ƙoshin lafiya. Kuma har ta gaya mashi cewa bata guje mashi domin ta ci amanar shi ba, sai domin ta shiga duniya ta samo masu maganin lalurar da ta addabe, su tun daga wannan rana Sarki Zammar ya kasance cikin matuƙar farin ciki, ya yiwa 'yarshi fatan alheri da samun nasara. Wannan shi ne abin da yafaru acan birnin muridai. Babi na tara Tafiyar daƙiƙa latalin kacal aka yi aka iso ƙofar shigowa birnin Istanbul, sa'adda aka yi arba da yadda ƙofar birnin takasance sai kowa ya cika da matuƙar mamaki, katangun birnin sun kasance masu matuƙar tsawo, a sama da ƙasan ƙofar birnin miyagun dakaru ne na mutum da aljan ga su nan birjik shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayen ɗauke da waɗansu irin masifaffun makamai Kai koda tsuntsu ne ya zo giftawa ta wannan waje waɗannan dakaru ba zasu bar shi a raye ba, tsananin kwarjini mayaƙan ya isa ya ɗimauta duk wata halitta mai numfashi. Idan har ƙofar birnin Istanbul takasance haka, to ya tsaron gidan sarautar birnin zai kasance kuwa? Sarki Lazwar ne ya yi wa kanshi wannan tambaya a cikin ranshi ba tare da ya furta wani ya ji ba. Wani narkeken sadauki mai matuƙar muni da kwarjini ya matso daf da inda su sarki Lazwar su ke ya kare masu kallo da yan mini-minin idanuwanshi jajaye tamkar garwashin wuta, cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya ku waɗannan baƙi shin daga ina kuke, kuma mene ne ke tafe da ku izuwa birnin nafi daraja a duniya?. Ko da jin wannan tambaya sai zuciyar sarki Lazwar ta kama tafarfasa tamkar zata ƙone. Bakomai ne ya sanya hakan ba, sai bisa jin badakaren ya ambaci birnin Istanbul da suna mafi daraja a duniya. Amma koda ya tuna cewa shi fa a halin yanzu sunan shi bawa ba BASARAKE ba, sai ya danne zuciyarshi, ya dubi badakaren ya ce "ya kai wannan badakare ka yi sani cewa ba komai ne ke tafe damu izuwa wannan birnin na ku ba face sai domin mu gudanar da kasuwanci, kuma a halin yanzu mun fito ne daga nahiyar ƙasashe larabawan gabas. Ko da jin amsar wannan tambaya sai badakaren ya bushe da dariya sannan daga bisani ya murtuke fuska ya ce "Za mu ba ku izinin shiga wannan birnin saboda muhimmancin abin da ke tafe da ku. Sai dai wani hanzari ba gudu ba idan muka samu ɗayan ku ya karya dokokin wannan birnin namu, to zamu ƙwace dukiyarku gami da tusa ƙeyarku izuwa gidan kaso. Ko da jin wannan batu sai hantar cikin kowa ta kaɗa da karfi tsoro ya kama shi. Kawai sai badakaren ya yiwa waɗansu dakaru inkiya ta wutsiyar idanu take dakarun suka shiga wangame kofar birnin, ƙofar na kammala buɗewa su sarki suka kunna kai izuwa cikin birnin zukatansu cike da matuƙar farin ciki. Lokacin da su Sarki lazwar suka tsinci kansu a cikin birnin Istanbul sai suka kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni, kuma suka cika da matuƙar mamaki gami da al'ajabi, bisa ganin yadda birnin ya kasance mai matuƙar kyawun gine-gine tamkar aljannar duniya. Kai tsaye yarinya Shuraiba ta durfafi hanyar kasuwar birnin, amma sai sarki Lazwar ya yi caraf! ya dubi yarinya Shuraiba ya ce "ya ke Shuraiba shin mene ne dalilin da ya sanya za ki kai mu kasuwa? Bayan cewa ba kasuwanci ne ya kawo mu wannan birni ba? Ko da jin waɗannan tambayoyi sai Shuraiba ta bushe da dariya ta ce "ai bakomai ne yasanya na kawo mu kasuwa ba sai domin kar ka manta cewa ka faɗawa dakaru masu tsaron kofar birnin Istanbul cewa kasuwanci ne ya kawo mu, tabbas dola ne a kowa ne lokaci dakarun sarki su kawo ziyarar bazato, domin binciken gaskiyar maganar abin da ka faɗa masu, Abu na biyu kuwa shi ne a lokacin da muka shigo wannan birni 'yan fashi da makami gami da 'yan damfara sun shaida shigowar mu, a koda yaushe za su iya kawo mana farmaki domin a tsammanin su za su samu dukiya mai tarin yawa a wajen mu. Waɗannan dalilai ne suka sanya na kawo mu kasuwa domin babu wani waje mai ɗauke da cikekken tsaro fiye da kasuwa". Ko da jin amsar waɗannan tambayoyi daga bakin Shuraiba sai kowa ya gyaɗa kai alamar gamsuwa gami da samun nutsuwa. Lokacin da aka shiga kasuwar sai aka tarad da takasance maƙiyaya mai faɗin gaske, tana ɗauke da gine gine cikin tsari, rumfunan masu siyan da tufafi dabam, kayan masarufi, komai dai an yi bisa tsari mai ƙayatarwa. Kai tsaye aka durfafi rumfar wani dattijo, da ta ƙawatu da kayan alatu na hatimin sarauta, da alama shine shugaba kasuwar. Tun daga nesa Shuraiba taga ya ƙura mata idanu ko kiftawa ba ya yi. koda shugaban kasuwar ya yi arba da su sai ya miƙe tsaye zumbu! Ya tarbe su cikin matuƙar farin ciki yana yi masu lale marhaban da zuwa, tamkar ya sadu waɗansu yan uwanshi na jini da ya jima bai sadu da su ba. Bayan shugaban kasuwar mai suna Sha'aran ya sauke su a bakin ƙofar rumfar, sai ya yi umarni aka kawo musu abincin kalaci aka jera a bisa wani dogon teburi, nan fa su sarki Lazwar suka shiga kimtsa cikinsu, har suna hannu baka hannu ƙwarya, domin rabon su da cin irin abincin yau wata huɗu kenan cif. Kuma suna mamakin irin karamci da shugaban kasuwar ya nuna masu. Shi kuwa yaro Imran da aka fara cin abincin sai ya yi bisimillah, loma bakwai ya yi sannan ya zare hannunshi ya kurɓi ruwa maƙwarwa huɗu sannan ya koma koma gefe gudal. Al'amarin daya bawa sarkin kasuwa Sha'aran mamaki kenan, ya ƙurawa yaro Imran idanu yana so ya tuna irin mutanen da ya taɓa gani suna irin wannan dabi'a wajen cin abincin su, Shi kuwa aljani ZA'ARATUN-LAYAL, da a halin yanzu sarki Lazwar ya canja mashi siffarshu dagaaljan ya koma bil'adama, cin abincin ya yi yana santi kamar tsohon mahaukaci. Bayan kowa ya kimtsa cikinshi ya dawo hayyacinshi, sai sarki Lazwar ya zira hannunshi a aljihun rigarshi domin ya ɗauko dinare domin ya biya kuɗin bincin da suka ci, da kuma kuɗin hayar gidan da za'a ba su. Amma sai kawai ya ga shugaban ya dube sa fuskar sa cike da annuri ya ce "ya ku waɗannan baƙi masu daraja ku yi sani cewa, ganin ku da nayi ya sanya jikina ya ba ni cewa ku mutanen ƙwarai ne. Yanzu ina buƙatar ku gabatar min da sunayen ku. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa, sarki Lazwar ya shiga gabatar da sunayen su ɗaya-bayan-ɗaya, Amma koda yazo kan yarinya Shuraiba sai sarkin kasuwar ya dakatar dashi ya ce "ba sai ka gabatar mini da ita ba. Al'amarin da ya bawa kowa mamaki kenan, har Shuraiba ta ce a cikin ranta shin me shugaban kasuwar ya sani game da ni. Kuma me ya sanya yake ƙura min idanu tun da muka shigo kasuwar? Ina dalilin rashin karɓar haƙƙin aikin shi daga gare mu. Amsar tambayoyin da yarinya Shuraiba ta kasa bawa kanta kenan. Shugaba sha'aran na gama faɗin hakan sai ya ƙwallawa wata budurwa kira. Budurwar ta bayyana a gare shi sanye da tufafi masu yalwa, tun daga ƙasa har sama, kuma fuskarta rufe da rawani mai ɗauke da wani hatimin sarauta idanuwanta kaɗai ake gani, ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa, sannan ta buɗi baki cikin wata irin lallausar murya mai daɗi tamkar sarewa ta ce ''ga ni ya shugabana me ake da buƙata? Shugaba Sha'aran ya dube ta ya ce "ya ke khadijat ki yi sani cewa bakomai nake buƙata a gare ki ba, sai domin ki yiwa waɗannan baƙi jagora izuwa unguwar Madinatul-dinar, masaukin manyan baƙi, ina so ki ba su dukkan abin da suke bukata na kulawa". Koda jin wannan umarni sai B Budurwa khadijat ta mayar da duban ta ga su sarki Lazwar tana ƙare masu kallo ɗaya-bayan-ɗaya. Ya yin da ta haɗa idanu da yaro Imran sai taji zuciyar ta buga ƙarfi kuma tsikar jikin ta ta tashi, kamar yadda ya faru gare ta shi ma haka yaro Imran ya ji wannan yanayi a tare da shi, amma saboda kada wani ya fahimci abin da ke faruwa sai khadijat ta kawar da idanuwanta a kan shi, a ɓangaren bawa Shamsal kuwa, tun sa'adda da ya kalli idanuwan budurwa khadijat sai ya ji hantar cikinshi ta kaɗa da ƙarfi, sannan wani abu ya ɗar su a zuciyarshi da ya kasa gane ko mene ne. Ita kuwa gimbiya Mashlira cikin idanun khadijat kawai ta kalla taji kishi ya kama ta, domin koda cewar fuskar khadijat a rufe take da rawani idanuwanta kaɗai ake gani, ta tabbatar cewa ta shafe ta a kyawun sura ne sa ba kusa ba. Tabbas idan masoyin ta sarki Lazwar ya yi arba da ita zahiri zai iya karkata zuciyarshi izuwa gare ta. Khadijat ta miƙe tsaye ta shige gaba, tana mai yafito su sarki da hannunta, tana mai yi masu nuni da su biyo bayan ta. Ba tare da gardamar komai ba, suka mara mata baya har suka ƙule a cikin kasuwar, duk inda suka gifta sai jama'a su bi su da kallo, haka suka wanzu suna ratsa saƙo da lungu na unguwanni, har suka iso wani ƙasaitaccen gida. Kai tsaye khadijat ta durfafi kofar gidan ta na isa dakarun dake gadi suka wangame makekiyar kofar shiga gidan suna masu risinawa a gare ta cikin girmamawa. Khadijah ta kunna kai izuwa cikin gidan, su sarki lazwar na biye da ita cike da matuƙar mamakin yadda masaukin ya kasance. Kowanne su ɗaki aka ba shi daban mai ɗauke da gado, kushin da kewayen wanka da sauran kayan more rayuwa. Kuma khadijat ta shaida masu cewa duk mai buƙatar wani abu ya sanar da ita har izuwa lokacin da zasu tafi. kasancewar a wannan lokaci duhun dare ya fara kawo kai, sai khadijat ta yi umarni aka kunna dukkanin fitulun dake gidan. A lokacin da dare ya tsala sai sarki Lazwar ya shiga izuwa masaukin kowanne ya bayyana masa cewa, dole ne su kasance cikin shiri, domin a kowannnen lokaci za a iya kawo masu harin bazato, kuma ba su da tabbacin cewa sarki kasuwa Sha'aran ba shi da wata mummunar manufa akan su, kuma a gobe da duku-dukun safiya za su shiga cikin garin domin gudanar da abin da ke tafe da su. A can masaukin yaro Imran kuwa bayan gabatar da kalacen dare, sai ya shiga izuwa kewayen ya ɗaura alwala ya dawo izuwa turakarshi ya shiga gabatar da Sallah isha'i yana cikin hakanne ya ji an turo kofar shigowa, sai da ya idar ya yi addu'a sannan ya juya domin ya ga kowane ne ya shigo ɗin. Koda ya yi arba da wanda ya shigo ɗin sai ya yi turus!, Ba wani ya gani ba face khadijat hadima ga Sarkin kasuwa Sha'aran, tana durƙushe a gefan shi na hagu ta yi zama irin na sallah. Cikin matuƙar mamaki Imran ya du be ta cikin girmamawa ya ce "ya ke hidima Khadijat shin ina dalilin shigowarki wannan masauki nawa a dai-dai wannan lokaci bakya tsoron sauran abokan tafiya za su zargi wani abu? Sannan jikina ya bani cewa kina kwaikwayon yadda nake gudanar da ibadar Ubangiji na. Shin baka tunanin hakan zai jefa rayuwarki da tawa a cikin haɗari ba? Ko da jin waɗannan tambayoyi sai khadijat ta yi murmushi mai taushi, sannan ta dubi Imran cikin murya mai daɗin saurare ta ce "ya kai wannan yaro ka yi sani cewa tun sa'adda nayi arba da kai a lokacin da ku ka sauka a rumfar mai gidana, naji ka burgeni sosai a zuciyata tamkar ina tare ɗan uwa na jini, kuma lokacin da ku ke cin abincin na lura cewa duk dabi'un cin abincin naka ya bambanta da nasu, wato naka irin na ma'abota addinin Musulunci ne, tun daga lokacin na ji cewa na samu ɗan uwa. Bisa wannan dalili ne ya sanya na biyo ka izuwa masaukin ka domin na bika sallah. Fiye da shekaru goma sha biyu kenan tun sa'adda an fito neman ɗan uwa na, wanda shi ne kaɗai ya rage mini da a duniya rabon da a ce na samu jam'in sallah sai a yau, Tabbas ina cikin matuƙar farin cikin da ba zai musaltu ba. Haƙiƙa da zaka zauna a tare da ni da ka ɗebe mani kewar mahaifina da na rasa. Tsawon shekarun da na shafe ina aiki tare da Sarkin kasuwa Sha'aran ban taɓa bayyana addini na a gare shi, saboda gudun matsala, domin duk wanda aka samu yana gudanar da wani addini saɓanin na birnin Istanbul hukuncin kisa ne a ƙanshin shi. Bisa wannan dalili ne ya sanya kai ma nake baka shawara da ka guji bayyana hakan, har ku kammala abin da ke tafe daku zuwa wannan birni"; Koda jin amsar waɗannan tambayoyi sai yaro Imran ya cika da matuƙar farin ciki yaji ya yi matuƙar shaƙuwa da hadima khadijat, kuma mamaki ya kama shi bisa jin cewa ta fito neman ɗan uwanta ne. Shin khadijat ita ce 'yar uwar shi da ya fito nema ? Amma ta ya zai iya gasgata hakan bayan cewa koda yaushe fuskarta a rufe take da rawani. Amsar tambayoyin da Imran ya kasa bawa kanshi kenan. Khadijat ta katse shirun da wanzu a tsakaninsu ta hanyar buɗar baki ta ce "ya kai ɗan uwa na idan ba za ka damu ba, ina neman alfarma a gare ka da ka amince min kullum na dunga zuwa wajen ka muna yin fira gami da ɗebe kewa Koda jin wannan batu sai Imran ya ce "na yi maki wannan alfarma ya ke yar uwanta". Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yaro Imran ma'abocin addinin Musulunci. A can masaukin sarki Lazwar kuwa, fira ce ta kare tsakanin Lazwar da gimbiya Mashlira, a inda Mashlira ta ci gaba da ba shi labarin abin da ya faru tsakanin matsafi Sahibul-ukub da mutanen birnin akan dalilin da ya sanya halittar su ta koma ta maridai inda ta ci gaba da cewa. Lokacin da rundunar matsafi Sahibul-ukub suka afkawa birnin Madinatul-Adfal sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro da ban al'ajabi. Nan fa su ma mayaƙan birnin suka dinga tuttuɗowa daga kowacce kusurwa ana yin KARON BATTA. Nan fa sassan jikkunan bil'adama ya dinga shawagi a sama suna zubo ƙas, hankakan mutuwa ya yi dirar mikiya a wajen ya wanzu yana kai komo wajen ɗaukar rayuka. JINI DA ƘASA suka haɗu waje guda, ihun da kururuwar mazaje gami da haniniyar dawakai ta cika dodon kunne. A wannan lokaci mahaifina sarki Zammar ya shiga izuwa cikin gidan sarautar yana shirin yaƙi, jim kaɗan sai ga shi ya fito izuwa filin daga kawai sai ya afka cikin abokan gaba ya hau su da sara da suka. Yazamana cewa duk inda ya sanya a gaba sai dai ka ga dakarun matsafi Sahibul-ukub na zubewa ƙasa matattu tamkar yana sassabe a gonar auduga. Sa'adda matsafi sahibul-ukub ya ga irin muguwar ɓarnar da mahaifina ke yi mashi, sai ya ruga izuwa inda ya ke ya tare shi suka kacame da azababban yaƙi mai matukar muni daban tsoro. Ana fara wannan arbu ne mahaifina ya fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa duk sa'adda matsafi Sahibul-ukub ya kai mashi hari da takobinshi idan ya kare harin, sai kaga ƙarfin saran ya cilla mahaifina sama ya yi ƙundumbala ya kife a ƙasa, amma saboda juriya da mafi irin ta GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur, ya ci-gaba da mayar da martani A wasu lokutan kuwa idan ya kai mashi harin ya kauce, sai ka ga duk abin da takobin Sahibul-ukub ta sauka a kanshi ya kama da wuta, kafin cikar rabin sa'a Sahibul-ukub ya galabaitar da mahaifina ya faɗi ƙasa magashiyan ya na amai na jini ta baki da hanci. Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin gimmbiya Mashlira 'yar sarkin maridai da Sarki lazwar. Kamar yadda ya wakana a masaukin gimbiya Mashlira da sarki Lazwar haka al'amarin yakasance a masaukin yarinya Shuraiba da aljani ZA'ARATUN-LAYAL A inda Za'aratun-layal ya ci gaba da bawa yarinya Shuraiba hikayar sarauniya Abidat ta birnin Sin. BABI NA GOMA Lokacin da wannan zakanya ta ruga izuwa inda suhaimat da jaririyar ta ke kwance, koda taga halin da take ciki sai ta ruga izuwa bakin wata ƙorama ta guntso ruwa a baki ta dawo izuwa inda take ta fesa mata ruwan a fuska. Faruwar hakan keda wuya sai suhaimat ta ja dogon numfashi gami da sauke nannauyar ajiyar zuciya, idanuwanta suka buɗe tarwai ta wartsake daga suman da tayi kawai sai ta miƙe zaune. Ya yin da tayi arba da zakanyar sai ta razana ainun ta ja da baya tana mai ɗaukar jaririyar ta ta ƙanƙame ta a ƙirji. Koda ganin halin da suhaimat ta shiga sai zakanyar ta juya ta ruga izuwa cikin wannan kogon dutse dake dajin. Cikin matukar farin ciki suhaimat ta mike tsaye taje bakin wannan ƙorama ta yi wa jaririyarta wanka, ita ma ta tsafta ce kazantar da ke jikin ta, sannan ta dawo izuwa ƙarƙashin wata bishiya ta zauna ta shiga sharar da jaririyar tana mai shafa gashin kanta, zuciyar ta cike da matuƙar farin ciki maral misaltawa. Kuma ta shiga tambayar kanta a cikin ranta tana cewa, dhin wane ne ya kashe waɗannan dabaru? Ko kuwa wannan zakanya ce? Amsar tambayar da ta kasa bawa kanta kenen,tana cikin wannan hali ne zakanyar ta dawo gare ta bakin ta rike da waɗansu tarin ganyayyaki ta a jiye a gaban ta, Bisa mamaki a wannan karon sai Suhaimat taji ko kaɗan ba ta tsora ta da ganin zakanyar ba, bata re da fargabar komai ba ta ta duba abin da ta kawo ɗin. Ai kuwa sai taga a she nau'ikan kayan marmari ne dangin su ayaba da inibi, kawai sai ta shiga kimtsa cikinta har sai da ta ci ta ƙoshi, sannan ta fasa kwakwa ta shanye ruwan cikinta. Zakanyar na tsaye na tsaye a gefe guda tamkar mai jiran umarni, a sannanne Suhaimat ta lura cewa jikin zakanyar akwai jini, take ta fahimci cewa ita ce ta kashe waɗannan dakaru domin ta ceci rayuwar ta da jaririyar ta. Lokacin da aljani ZA'ARATUN-LAYAL ya zo dai-dai nan a hikiyar sarauniya Abidat ta birnin Sin da yake bawa yarinya Shuraiba sai ya tsuke bakinshi ya yi shiru. Al'amarin da ya sanya yarinya Shuraiba ta dube shi cikin alamun tsananin damuwa ta ce "ya kai masanin HIKAYAR DUNIYA shin mene ne yasanya zaka katse min wannan daddaɗan labari? Tabbas ina so naji wace irin rayuwa Suhaimat da jaririyar ta za su yi a nan gaba, kuma menene dalilin da ya baro da ita daga birnin su? Shin ma mene ne ya sanya dakarun ke farautar Suhaimat? Koda jin waɗannan tambayoyi sai aljani ZA'ARATUN-LAYAL ya bushe da dariya ya dubi yarinya Shuraiba ya ce "ya ke Shuraiba shin baki gani ba ne har alfijir ya keto safiya ta yi". Koda jin wannan batu daga bakin Za'aratun-layal sai Shuraiba ta cika da mamaki, ai kuwa sai ta miƙe tsaye ta domin ta fara shiri kamar yadda sarki Lazwar ya yi masu bayani. Wannan shi ne abin da ya faru a masaukin yarinya Shuraiba. Kamar yadda ya wakana a masaukin Shuraiba haka al'amarin ya kasance a masaukin darki Lazwar da gimbiya mashlira. A inda Mashlira ta katse labarin bawa sarki Lazwar na matsafi Sahibul-ukub da mahaifin ta sarki Zammar. Saboda ganin ketowar alfijir a sararin samaniya. A ɓangaren masaukin yaro Imran kuwa, ya yin da ya ga alfijir ya gabato sai ya ɗaura alwala ya shiga gabatar da nafita, bayan nan kuma sai gudanar da sallar asuba, q lokacin da hadima khadijat ta bisa a baya a matsayin mamu. Lokacin da rana da fito ne ta yi haske sai khadijat ta yi umarni aka kaiwa kowannnen su bahon ruwan wanka, bayan kowa ya tsaftace jikinshi ya yi kalaci, sai aka ɗunguma izuwa cikin gari domin gudanar da abin da aka zo nema. Wannan shi ne abin da ya faru da su sarki Lazwar a lokacin da aka kai su izuwa masauki. Babi na sha ɗaya Lokacin da amarya Munirat ta ci gaba da tafiya a cikin gidan sarautar birnin Darul-usur bayan ta kuɓuta daga sharrin magajin gari Yasiran. Sai ta cigaba da tafiya a cikin gidan sarautar tana ratsa ƙofofi da dakaru iri daban-daban, zuciyarta cike da matuƙar farin ciki maral musaltuwa. Ta na cikin wannan hali sai wannan tsuntsu ya sake bayyana a gare ta a sama cikin iska Tsuntsun ya riƙiɗa izuwa wani kyakkyawan aljani mai kyawun sura, aljanin ya na ɗauke da sura irin ta bil'adama, sai dai yana ɗauke da fuka-fukai. Aljanin ya dubi Munirat ya ce "ya ke Munirat ki yi sani cewa da farko dai suna na Lailatul-azhar kuma ni hidimi ne ga sarkin musulmin aljanun duniya baƙaƙen fata. Ubangiji ya bayyana wa sarkin mu halin da ki ke ciki dama sauran mutanen birnin ku na irin baƙin zaluncin da magajin gari Yasiran ke yi maku, sannan kuma ya turo ni ne domin na kawo ƙarshen mulkin zaluncin shi baƙi ɗaya. Ki yi sani cewa kalaman da ki ka karanta a jikin fuka-fukaina har kika tsira daga sharrin magajin gari, ba wasu kalmomin ba face KALMAR SHAHADA wacce duk wanda ya furtata ta da tabbatar wa a zuciyarshi to ya yi imani da Ubangijin gaskiya da ya halicci komai da komai. Idan har kin bayar da gaskiya da Ubangijin ɗaya daya baki nasara akan magajin gari to tabbas zamu samu nasarar ganin bayanshi. Koda jin wannan batu daga bakin aljani Lailatul-azhar sai amarya Munirat ta cika da matukar farin ciki maras musaltuwa, ta dube shi ta ce "ina so yanzu ka shigar da ni addinin ka". Ba tare da wani ɓata Lailatul-azhar ya karanta mata KALMAR SHAHADA. Nan fa ya zamana cewa kafin mako guda fiye da mutanen birnin sun karɓi addinin musulunci a hannun amarya Munirat. Magajin gari Yasiran kuwa sai ya kamu da wata irin rashin lafiya, sakamakon wannan wuta da ta ƙona jikinshi, Nan fa aka rasa wanda zai gaje shi a kan karagar mulkin shi. 'Yan Majalisar suna ganin cewa tabbas yanzu hawa karagar mulkin Yasiran ana iya kiran shi da SARAUTAR MUTUWA. Domin su ganin a ko da yaushe magajin gari zai iya samun lafiya, ko kuma sarki Lazwar ya dawo daga tafiyar da ya yi. Saboda ba zai yiwu a zauna haka babu shugabanci bisa dole jama'ar gari suka ɗora amarya Munirat a matsayin sarauniyar su. Nan fa jama'a suka fara samun yanci, farin ciki gami da walwala sakamakon hasken musulmi da bayyana a gare su, Al'amarin Shuraiba kuwa Lokacin da ta cigaba da tafiya a cikin birnin Istanbul domin nemo mahaifiyarta sai ta wanzu tana tafiya babu sassauci, tana cikin wannan hali ne sai ta hango wajen waɗansu almajirai ke zaune suna bara a kasuwar, kawai sai ta matsa izuwa daf da inda suke ta shiga yin nazarin su. Abu na farko da ya faɗo mata a rai shine shin yanzu ina kike da tabbacin mahaifiyarki take, ki na ganin cewa mahaifiyarki zata kasance daga cikin waɗannan almajirai dake yin bara? An ya kuwa sarki Ladiyas bai mayar da mahaifiyar ki matar shi ba? Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenen. kawai sai ta ɗauki mayafi ta ɗaure fuskarta da rawani, kana ta ɗauki wani ƙoƙo ta ajiye a gaban ta, sannan ta shiga izuwa cikin su ta saje da su tamkar ba ita ba. Zaman ta ke da wuya sai wata dattijuwar almijira dake kusa da ita ta du be ta ta ce "ya ke wannan yarinya shin ke kuwa me kika rasa a rayuwar ki da za ki fito bara, baƙya duba wa ki ga cewa ke yarinya mai karancin shekaru". Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba ta cika da matuƙar mamaki ta dube ta ta ce "ya ke wannan dattijuwa ki yi sani cewa bakomai ba ne ya sanya ni aikata wannan bara ba sai domin na samu abin da zanyi kalaci. Mahaifina ya mutu tun ina da shekara bakwai a duniya, mahaifiyata ce take a raye ina neman ta ruwa a jallo, domin ita ce kaɗai ta rage min a duniya. Koda jin amsar wannan tambaya sai dattijuwar ta bushe da yar karamar dariya ta dube ta ta ce "tabbas yaro yaro ne kuma duk wanda ya riga ka kwana dole ya riga ka tashi, na san cewa akwai muhimmin al'amari daya sanya ki zuwa wannan waje domin, ban taɓa ganin ki ba tun da nake fitowa wannan bara tawa". Koda jin wannan batu daga bakin dattijuwar sai Shuraiba ta yi dariya ta ce "tabbas da akwai buƙatar hakan da na nema a wajen wani tun kafin na iso wannan waje, amma tambayar da zan yi maki wace matsalar dake tattare da wannan waje? Dattijuwar ta yi dariya ta ce ''ya ke wannan yarinya ki yi sani cewa bakomai yawan dinaren da mutum zai samu na sadakar da za a bashi, sai dakarun sarki Ladiyas sun zo sun karɓi haraji, da ƙyar za ka samu ka tsira da kaso ɗaya cikin goma. Idan kuwa aka yi rashin sa'a baka samu sadaka ba, to fa sai sarki ya sanya an kai mutum aikin horo a gidan sarauta domin ka yi aiki adadin wannan dinare da baka biya harajin ba"; Da jin wannan batu daga bakin almajirar sai yarinya Shuraiba ta ji ta ƙara tsanar sarki Ladiyas fiye da komai a rayuwar ta. Sannan ta dubi almajirar cikin alamun matuƙar tausayin ta ce "tabbas sarki Ladiyas ya cika azzalumi kuma maras tausayi, yanzu a ce almajirai ma sai sun biya haraji, Koda jin wannan batu sai mamaki almajirar har ta buɗi baki da nufin ta ce wani abu sai a ka hango dakarun sarki Ladiyas sun shigo kasuwar a bisa dawakai su kamanin ɗari biyu shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannayensu ɗauke da waɗansu murtuka-murtukan kulake. Nan fa kasuwar ta hargitse jama'a suka dunga kwashe kayayyakin su suna buɗa wa dakarun hanya, domin idan har suka iso mutum bai kwashe ba take za su bi ta kan kayan da dawakan su su tattake. Lokacin da dakarun suka iso wajen da su Shuraiba su ke sai suka shiga karɓar harajin a wajen dukkan almajiran dake wajen, suna cikin karɓar ne suka iso kan wannan dattijuwar almajira dake zaune kusa Shuraiba. Jikinta na ƙyarma ta zira hannunta cikin ƙoƙon barar ta lissafo dinare ta miƙa wa wani badakare, bakinta na karkarwa ta ce "ga shi ya shugabana har da harajin wannan yarinyar da ke zaune a kusa da ni, Kafin hannun badakaren ya kai inda dinaren yake yarinya Shuraiba ta shammace shi ta gabza mashi wawan naushi a maƙogaronshi. Saboda matuƙar ƙarfin dukan sai badakaren ya yi karanta wa sau biyu a sama, sannan ya faɗi ƙasa matacce ko shurawa bai yi ba, al'amarin da ya firgitarwa jama'a dake kasuwar kenan kuma ya harzuƙa zukatan sauran dakarun. Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya shuraiba a lokacin da shiga cikin gari domin neman mahaifiyarta. Al'amarin sarki Lazwar kuwa lokacin da fice da ga masaukin su ya kutsa cikin birnin Istanbul domin nemo hanyar da zai sadu da baiwa Sharifa, sai ya wanzu yana ratsa layu ka da unguwanni babu sassauci. Yana cikin tafiyar ne ya hango waɗansu cincirindon al'ummar a gefen kasuwar, cikin hanzari ya matsa daf da wajen domin ya ga wata irin waina ake toyawa. Sa'adda da ya matsa daf da wajen sai ya ga ashe waɗansu ƙarfafan samari ne guda biyu ke baiwa hammata iska jama'a sun kewaye su suna kallo. Idan ɗayan ya gabzawa ɗan uwanshi naushi sai ka ga ya faɗi kasa tim q matuƙar galabaice, amma saboda naci da juriya sai kaga ya miƙe tsaye zumbur ya mayar da martani. A gefe guda kuwa wani badakare ne mai ƙirar samudawan farko ma'abocin kwarjini da haiba, kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa, yana zaune bisa wata ƙasaitacciyar kujera ta alfarma, ya zuba idanu yana kallo yadda artabun ke wakana da alama shine mai kula da gasar da ake aiwatar wa. Sarki Lazwar ya matsa daf da wani mutum ya dube shi ya ce " Wai shin mene ne amfanin abin da waɗannan samari ke yi na yaƙar junan su? Koda jin wannan tambaya sai mutumin ya dubi sarki Lazwar ya bushe da dariyar mugunta ya ce "da alama kai baƙo ne a wannan birni ko? Sarki Lazwar ya gyaɗa kai alamar haka ne, Mutumin ya ce "ya kai wannan baƙo ka yi sani cewa waɗannan da ka gani bayi ne da aka farauto daga can wata nahiya daban, duk bayan mako ɗaya mai girma Ladiyas yana sanya a fitar mashi da GWARAZAN JARUMI a cikin su da zai kasance ɗaya cikin masu tsaron lafiyar sarauniya. Bisa wannan dalili ne ya sanya aka tara su a wannan waje domin fitar da zakara. Koda jin wannan batu daga bakin mutumin sai Lazwar ya cika da matuƙar farin ciki, domin kuwa dama ta samu wacce zata zamto sanadin kasancewar shi bawa a masarautar Istanbul. Domin dai ya cika burin shi na saduwa da baiwa Sharifa da za ta taimaka mashi wajen mallakar abubuwan da zai karya sihirin tsafin da abokin gabar shi sarki Darwazu ya yi mashi. A ɓangaren jarumai biyun kuwa tuni labari yasha banbam domin kuwa ɗaya cikin jaruman ya samu nasara akan ɗayan Inda ya yi masa jina-jina har layi na ɗibarshi yana faɗuwa ƙasa. Nan fa wannan badakare dake kula da gasar ya shiga ƙyalƙyala dariya bisa ganin yadda ɗayan jarumin ke yin nasara akan ɗayan, al'amarin da ya fusata sarki Lazwar kenan yaji ya kamu da matuƙar tausayin jarumin, kawai sai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye ya daki ƙirjin jarumin dake samun nasarar da dukkan ƙarfin shi. Saboda ƙarfin dukan sai da jarumin ya yi sama yana mai tsandara ihu sannan ya faɗo ƙasa a matuƙar galabai ce, hannayen biyu suka karye ji kake ruƙus! Ƙas. Cikin matuƙar al'ajabi jama'a suka duba domin su ga ko wane ne, ai kuwa koda suka yi arba da sarki lazwayr sai suka cika da matuƙar mamaki, domin sun san cewa tabbas koma wane ne shi baƙo ne kuma ya jifa kanshi a cikin bala'i, domin ba ka yi laifin komai ba ma sarkin yaƙi Darusu ya zalunce ma ballantana ka shiga gonar shi. Sarki Lazwar ya matsa izuwa inda ɗayan jarumin ke kwance ya tashe shi zaune ya karkaɗe mashi ƙurar dake jikin shi. Al'amarin da ya yi matuƙar fusata sarkin yaƙi Darusu kenan zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata kone, kawai sai ya dakawa dakarun shi tsawa suka zare makaman su suka yi ɗauki kan Lazwar. Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi nan fa artabun ya zamto abin tsoro da kuma ban al'ajabi, domin ga shi dai sarki Lazwar ba ya riƙe da makami amma sai ya zamtowa dakarun alaƙaƙai kuma GUGUWAR AJALI suka rasa yadda zasu yi da shi. Duk wanda ya gabzawa naushi a wata gaɓa a jikin shi sai ka ji ta ƙarye ta yi ƙara ruƙus! Ƙas. Kuma ya wanzu yana zillewa hare-haren dakarun cikin matuƙar zafin nama JUTIYA DA BAJINTA irin ta ZARATAN MAYAKA, Nan fa ihu da kururuwar dakarun gami da ƙarar karafniyar karafa ta cika dodon kunne, nan fa ya zamana cewa waɗansu dakarun na daban ya rugawa izuwa kan sarki Lazwar cikin matuƙar fushi, bisa ganin yadda yake ragargazar 'yan uwan su. Kafin cikar daƙiƙa arba'in sarki Lazwar ya bazar da dakaru fiye da saba'in, dukkanin su sun zube a ƙasa magashiyan suna nishin wahala. Nan fa zuciyar sarkin yaƙi Darusu dake tsaye a gefe guda ta kama tafarfasa tamkar zata fasa ƙirjinshi ta fito waje, amma kuma wani abu da ya faɗo mashi arai shi ne. Tabbas wannan baƙon jarumi ya cika GWARZON DUNIYA yadda ake bukata, kuma tabbas idan na kai shi ga mai girma Ladiyas zan samu ƙarin daraja da girmama wa, shin me zai hana ka kama shi a matsayin bawa ga tafi da shi ga mai girma Ladiyas? Koda gama yanke wannan shawara sai sarkin yaƙi Darusu ya shammaci sarki Lazwar ya lallaɓo ta bayan shi ya dunƙule hannunshi ɗaya ya kirɓa mashi wawan naushi a fuska a gadon bayan shi. Saboda ƙarfin dukan sai da ƙashin bayan Lazwar ya yi ƙara ya faɗi ƙasa sumamme. Cikin matuƙar farin ciki sarkin yaƙi ya yi umarci waɗansu dakaru suka ɗaure hannayen Lazwar da wata sarƙa suka ɗora shi a kan doki. Nan take Darusu ya kama dokinshi ya haye ya sakar mashi linzami ya durfafi hanyar da zata sada shi da gidan sarauta dakarunshi suka rufa mashi baya Waɗansu kuma suka shiga ɗaukar dakarun suka samu raunuka domin ba su taimakon gaggawa. Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin da ya shiga cikin gari domin saduwa da baiwa Sharifa. Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da fice daga masaukin su bayan ya kammala kalaci sai ya wanzu yana ratsa saƙo da lungu na birnin Istanbul. Domin cigiyar 'yar uwarshi, hakan ya sanya duk wajen da hango taron jama'a sai ya je ya tsaya, domin ya ga me ake gudanar wa. Yana cikin hakan ne ya iso wani waje mai cike da tarin al'umma, wani dattijo yana tsaye yana yi masu wani jawabi, kallo ɗaya za ka yiwa mutumin ka fahimci cewa ya kasance jagoran wani addini. Kawai sai yaro Imran ya ja ya tsaya yana sauraren jawabin sa. Malamin na cikin jawabin shi sai yaro Imran ya ɗaga hannunshi ya ce "ya shugabana ina da wata tambaya idan ba za ka damu ba. Koda jin wannan tambaya daga bakin Imran sai gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matuƙar mamaki. Domin ba a taɓa jin wanda ya yiwa matsafi Shamrul wata tambaya ba akan abin da yake bayani game da bautar gunki. Cike da matuƙar mamaki matsafi Shamrul ya dubi yaro Imran da fuskarshi ke rufe da rawani idanuwan kaɗai ake gani ya ce da shi ''ya kai wannan yaro faɗi tambayar ka ina sauraren ka". Yaro Imran ya yi gyaran murya sannan ya ce "ya kai wannan malami tambaya ta a gare ka ita ce, shin waɗanne mutane ne suka fara bautar gumaka a duniya kuma mene dalilin su na yin hakan? Tambaya ta biyu mene ne ya sanya gaba ɗaya gumakan da ake bauta mu ne muke sassaƙa su da hannayen mu, to ya ya abin da mune muka samar da su daga babu a ce kuma su ne allolin mu? Koda jin waɗannan tambayoyi daga bakin yaro Imran sai fuskar matsafi Shamrul sai ta sauya daga walwala izuwa fushi, kuma ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi tsoro ya kama shi ainun. Amma saboda kar jama'ar dake wajen su fahimci hakan sai kya basar. Abin da matsafi Shamrul bai sani ba shi ne haƙiƙa maganganu Imran sun yi tasiri a zukatansu baki ɗaya al'ummar dake wajen. Tabbas waɗannan tambayoyi da wannan yaro mai hikima ya yi sune abubuwan da ya kamata kowannen su ya sani kafin ya kasance cikin wannan addini na bautar gumaka, Nanfa mutanen dake wajen suka dunga cewa a amsa masu waɗannan tambayoyi haƙiƙa muna so mu ji ya tabban malami. Sautin muryoyin jama'ar ya sake ruɗa matsafi Shamrul, kuma suna amsa kuwwa izuwa cikin birnin, tare janyo hankulan sauran mutanen gari suka dunga tuttɗowa izuwa wajen, sa'adda da matsafi Shamrul ya ga cewa adadin mutanen da ke wajen yana cigaba da hauhawa, kuma ya tabbatar da cewa idan ya amsa tambayoyin abin kunya zai faru. Sai kawai ya yi wuf! Ya shafi wani gurun tsafi a damtsenshi na hagu, nan take cikin daƙiƙa biyu kacal hadari ya taso gadan-gadan sama ta yi duhu, a ka fara tsawa, walƙiya gami da iska mai ƙarfi, nan fa waje ya hargitse jama'a suka fara darewa suna rugawa izuwa unguwannin su domi kar ruwa ya yi masu ɓarna. A bangaren yaro Imran kuwa yana ɗaga kanshi sama ya kalli hadarin sai ya fahimci cewa, an samar da shi ne ta sihirin tsafi domin matsafi Shamrul ya kawar da hankulan al'umma daga amsar tambayoyin da ya yi nashi. Kawai sai ya yi dariya ya juya ya nufi hanyar koma gida, domin ya tabbatar da cewa idan har matsafi Shamrul ya kasa amsa wa mutane tambayoyin za su juya mashi baya su daina karɓar fatawar addini daga gare shi, sai da yaro Imran ya bar wajen, sannan matsafi Shamrul ya daina waigen shi ya na satar kallon shi Wannan shi ne abin da ya faru da yaro Imran BABI NA SHA ƊAYA Al'amarin Gimbiya Mashlira kuwa dukkan abin da wakana da masoyin ta sarki Lazwar a kasuwa tun daga lokacin da ya fafata artabu da waɗannan dakaru har izuwa lokacin da sarkin yaƙi ya yi umarni aka ɗauke shi aka nufi gidan sarautar, tana tsaye a gefe guda tana kallo. Koda ganin hakan sai hankalin ta ya dugunzuma ainun, bisa ganin cewa babu tabbacin za su bar shi a raye, bisa mummunan laifin da ya aikata. To kenan idan har hakan ta faru za bai samu damar cika burin shi na saduwa da baiwa Sharifa ba, harya bayyana mata bukatar shi, wai shin ma ta ya ya zan iya barci a daren yau matsawar ba na jin motsin masoyina Lazwar a kusa da ni, bayan cewa zuciyata ta kamu da matuƙar kaunar shi. Tabbas zan kasance a tare dashi duk TSANANI DA UKUBA koda kuwa bazai taɓa gane cewa ni ba ce Sa'adda gimbiya Mashlira tazo dai-dai nan a tunaninta, sai kawai ta dunga bin sahun su sarkin yaƙi Darusu a baya ba tare da wani ya gan ta ba , lokacin da ta ga cewa an kusa isa gidan sarauta sai kawai tayi ruf ta rafke ɗaya daga cikin dakarun, a cikin wani lungu ta maye gurbin tufafin dake jikinta da na shi, sannan ta kama dokinshi ta haye ta shiga cikin dakarun ta saje da su ba tare da wani ya gane ta ba. Wannan shi ne abin da ya faru da gimbiya Mashlira 'yar sarkin maridai Zammar, bayan ta fice daga masaukin su dake tsakiyar birnin Istanbul. BABI NA SHA BIYU Al amarin yarinya shuraiba kuwa lokacin da ta gabza wa ɗaya cikin dakarun dake karɓar haraji naushi a magoranshi ya faɗi ƙasa matacce, sai sauran suka zare kulaken su cikin matuƙar fushi suka yi ɗauki kan ta. Ko da ganin hakan sai almijiran dake wajen suka ruga suka bar wajen domin su tsira da rayukansu. Ita kuwa Shuraiba sai ta gyara tsayuwar ta tana jiran isowar dakarun a lokacin da jama'a suka buɗe masu fili mai faɗi sosai. Lokacin da suka iso sai aka yi KARON MAZA suka afkawa Shuraiba da azababban yaƙi, suka wanzu suna kai mata duka da kulaken cikin zafin nama domin su yi mata kisan farat ɗaya. Ana fara wannan artabu ne wani abin mamaki ya fara gudana, domin kuwa Shuraiba ta zamo tamkar shaidaniya a tsakanin dakarun, ta wanzu tana zillewa tare da hare-haren dakarun cikin matuƙar zafin nama. Nan fa ta dunga haɗa karo tsakanin dakarun, suna zubewa kasa magashiyan. Amma sai su yunƙurawa su sake afka mata da yaƙi. Lokacin da aka shafe tsawon rabin sa'a ana wannan karon batta sai ya zamana cewa Shuraiba da dakarun sun fara galabaitar da juna Ana cikin wannan yaƙi Shuraiba tayi wuf ta ƙwaci wani kulki a hannun ɗaya daga cikin dakarun, ta shiga gabza masu duka a ƙafafuwansu, kafin lokacin mai tsawo, ƙafafuwan dakarun sun sage, sun yi tsami gaba ɗayansu su sun zube a ƙasa suna nishin wahala Nan fa jama'a suka dunga shewa suna yiwa Shuraiba jinjina gami da kirari cikin matuƙar farin ciki bisa ganin cewa ta karya alƙadarin dakarun Kwatsam! Bazato babu tsammani sai akaga jiyo haniniyar dawakai gami da bugun tambura daga can nesa kaɗan, alamun dake nuni da cewa wani ma'abocin sarauta yana gab da bayyana. Koda jama'a suka waiga baya sai suka hango ashe tawagar gimbiya Lamrat ce. Cikin matuƙar firgici suka sunƙuiya ƙasa bisa gwiwoyin su, domin girmamawa a gare ta, sannu a hankali har suka iso izuwa wajen. Kawai sai aka ga keken dokin dake ɗauke da gimbiya Lamrat ya tsaya dai-dai inda yarinya shuraiba take tsaye Take Waɗansu dakaru mutum biyar suka ruga izuwa inda Kofar keken take suna masu durƙusawa ƙasa bisa gwiwoyin tare shimfiɗa gadon bayansu, sannu a hankali ƙofar keken dokin ta buɗe, sai ga gimbiya Lamrat ta fito ta taka gadon bayan dakarun ta sauko ƙasa. Sanye take cikin kariyar alƙyabba da aka yi mata cin baki da zaren lu'u lu'u da zubar daju, sanye a kanta akwai wani kambu na sarauta na zinare fuskarta rufe take da wani mayafi idanuwanta ma'abota kwarjini kaɗai ake gani. Kai tsaye gimbiya Lamrat ta taka da ƙafafuwanta ta durfafi inda yarinya Shuraiba ke tsaye wacce ita ce kaɗai bata faɗi ƙasa domin girmama a gare ta ba. Lokacin da ya rage saura taku uku a tsakanin su sai gimbiya ta ja ta tsay, ta kai duba izuwa kan dakarun da Shuraiba ta a raunata, sannan ta dubi Shuraiba tana mai ƙura mata idanu ko kiftawa ba ta yi. Nan take su duka biyun suka ji zukatansu na buga wa da ƙarfi wani abu ya ɗar su a cikin ta. Al'amarin da ya yi matuƙar bawa gimbiya Lamrat mamaki kenan, ta tambayi kanta a cikin ranta tana mai cewa. Shin mene ne ya sanya zuciyata ta buga lokacin da na yi arba da wannan yarinya? Shin ko kuwa hakan na nufin har yanzu 'yata ƙwaya ɗaya tilo tana raye? Amsar tambayoyin da ta kasa bawa kanta kenan, kawai sai ta cigaba da ƙurawa mata idanu. Daga can sai ta buɗi baki cikin zazzakar murya mai ɗaɗin sauraro ta ce "ya ke wannan yarinya shin wace ce ke kuma mene ne dalilin da ya sanya kika zaɓi ki yi bara ki ƙyale sana'a, wacce za ta ba ki damar ci da sha. Ko da jin wannan tambaya sai yarinya Shuraiba ta dubi gimbiya cikin ladabi da girmama wa ta ce "ya shugabata ki yi sani cewa ni baƙuwa ce a wannan birni, bani da kowa na shigo wannan birni domin neman mahaifiyata da aka rabu Ni da ita tun ina yarinya ƙarama". Da jin amsar wannan tambaya sai gimbiya ta sake jin zuciyarta ta buga da ƙarfi a karo na biyu Koda ta sake ƙurawa Shuraiba idanu sai ta taga tana ɗauke da kamanni iri ɗaya sak da na masoyin ta kuma uban 'ya'yanta sadauki Murrasu. Nan take abubuwan da suka faru da masoyinta da sarki Ladiyas ya fara dawo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta shiga tafarfasa tamkar zata ƙone. Tsananin ƙiyayyar sarki Ladiyas ta ci gaba da ruruwa a cikin ranta. Haƙiƙa babu makawa wannan yarinya ba wata bace face 'yata Shuraiba, wata zuciyar kuma ta ce da ita, amma a halin yanzu bai dace ki wani yasan da hakan ba, dole ki yi jinkiri ki sake nazari akai sosai. Koda gama tunanin hakan sai ta dubi Shuraiba ta ce "ya ke wannan yarinya idan ba za ki damu ba ina so ki zauna tare da ni, har izuwa lokacin da zan sa a nemo maki mahaifiyarki". Da jin wannan batu sai farin ciki ya kama yarinya Shuraiba ta ce a cikin ranta, tabbas wannan wata dama ce da zan ɗauki fansa a kan sarki Ladiyas da kuma gano inda mahaifiya ta ke. Shuraiba ta ce "na amince da wannan alfarma da kika yi min, amma nima ina roƙon alfarma a wajen ki da a daina karɓar haraji a wajen waɗannan almajirai har abada". Koda jin wannan batu daga bakin Shuraiba sai gimbiya Lamrat ta cika da matuƙar farin ciki ta dubi wani badakare a dake tsaye a gefenta ta ce da shi ''daga yau na haramta karɓar haraji a hannun dukkan wani almajiri dake wannan waje. Badakaren ya risina ya ce ''an gama ranki shi daɗe''. kawai sai ta kama hannun Shuraiba ta durfafi inda keken dokinta yake suka shiga izuwa ciki suka zauna a tare, sannan badakaren dake kula da keken ya zaburi dawakan kenan ya ci gaba da tafiya. Nan fa jama'a suka cika da matuƙar mamaki, almajiran dake wajen kuma sai sai farin ciki ya turnuƙe zukatansu, suka shiga yin shewa, kiɗa da rawa bisa ginin cewa Shuraiba ta ƙwato masu 'yanci a hannun miyagun dakarun. Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya shuraiba. BABI NA SHA UKU Al'amrin matsafi Shamrul kuwa lokacin da ya rabu da yaro Imran bayan ya kunyata ta shi a gaban mabiya addininshi. kai tsaye sai ya nufi hanyar da za ta sada shi da ɗakin abin bauta gunki Zallas. Da shigar shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa yana mai yi mashi sujjada, a karo na farko sai matsafi Shamrul ya ji wata irin kakkausar murya ya mamaye ɗakin baki ɗaya "ya kai Shamrul ma'abocin biyayya a gare mu dago kanka sama domin ka ji abin da zamu sanar da kai. Cikin matuƙar al'ajabi matsafi shamrul ya dago daga sujjadar, domin tsawon shekaru saba'in yana bauta ga gunki Zallas amma bai taɓa jin ya yi mashi magana ba sai a yau. Kakkausar muryar ma'abociyar tsoro da firgitarwa taci gaba da cewa "haƙiƙa mun san kana cikin matuƙar fushi da damuwa akan abin da ya faru tsakanin ka da hatsabibin yaro Imran, na kunya taka a barnar jama'a, haƙiƙa yaro Imran ya taɓo tsuliyar dodo, domin ba zai taɓa samun nasarar yaɗa addinin musulunci a wannan birni namu ba. Kuma lokaci ya yi da zamu kawar da dukkan wani musulmi a doron ƙasa. Abin da muke so da kai shine ka kwantar da hankalinka tamkar tsumma a randa, a ranar da za a gabar da bikin bauta zaka sha mamaki da idanunka, na mai tabbatar maka da cewa a ranar zai zamto gawa dama dukkanin wanda ya kwaɗaitu da shiga addinin shi. Sa'adda da muryar ta zo dai-dai nan azancen ta sai matsafi Shamrul ya cika da matuƙar farin ciki ya sake yin sujjada a karo na biyu ga gunki Zallas. Sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin bautar. Wannan shi ne abin da ya faru da matsafi shamrul bayan ya rabu da yaro Imran. Lokacin da su sarkin yaƙi Darusu suka cigaba da tafiya a cikin birnin Istanbul ɗauke da sarki Lazwar, ɗaure a kan doki cikin halin suma sai suka ci gaba da tafiya babu sassauci, tafiyar daƙiƙa latalin kacal kaɗai su ka yi suka iso kofar gidan sarautar birnin. Gidan sarautar yakasance mai dogayen gine-ginen zamani masu ƙayatarwa, koda isowar su sai waɗansu irin girɗa-girɗan samudawan dakaru dake shirye cikin gagarumar shigar yaƙi suka wangame makekiyar ƙofar shiga. Inda za'a sanya katti majiya ƙarfi mutum saba'in ba za su iya ture kofar ba, Kai tsaye Sarkin yaƙi Darusu ya kunna kai izuwa ciki dakarun shi na biye da shi, duk inda ya gifta a cikin gidan sai di ka ga dakaru, kuyangi, barori, bayi na zube ƙasa suna kwasar gaisuwa a gare shi Daga cikin gidan sarautar ya kasance ƙasaitacce tamkar aljannar duniya, babu wata halitta walau mutum ko aljan da za ta tsinci kanta a cikin wannan gida face ta tabbatar wa da kanta cewa gaba da gaban ta aljani ya taka wuta. Shin yanzu idan har gidan sarautar birnin Istanbul ya kasance haka to ya y turaka, da fadar sarki Ladiyas za su kasance. Tambayar da gimbiya mashlira ta yi wa kanta kenan wacce ta saje cikin dakarun ba tare da an gane ta ba Aka cigaba da tafiya har aka iso wani ɓangare a gidan sarautar, kawai sai sarkin yaƙi Darusu ya yi umarni aka shigar da sarki Lazwar izuwa ciki sannan ya dubi waɗansu dakaru mutum biyar daga cikin su ya ce da su "ku tsaya anan har izuwa lokacin da wannan baƙon jarumi zai farfaɗo, ku tabbatar da cewa wani abu mai taɓa lafiyar shi ba". Koda gama faɗin hakan sai sarkin yaƙi Darusu ya juya ya nufi hanyar da za ta fitar da shi daga gidan sarautar sauran dakarun suka mara mashi baya. wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin da su sarkin yaƙi Darusu suka ɗauke shi a cikin halin suma. Al'amarin abokan tafiyar sarki Lazwar sarkin yaƙi da bawa Shamsal kuwa, koda ficewar su daga masaukin sai sarkin yaƙi ya dubi bawa Shamsal ya ce dashi "wai kuwa me ka fahimta game da hadima khadijat akankallon da naga tana yi maka? Koda jin wannan tambaya sai Shamsal ya yi shiru kamar mai tunanin wani abu, daga can sai ya ɗago da kanshu ya dubi sarkin yaƙi ya ce "ya sarkin yaƙi ka yi sani cewa haƙiƙa ban fahimci wani abu ba game da kallon da khadijat ke yi min ba, sai dai a lokacin da muka haɗa idanu na ji zuciyata ta buga da ƙarfi". Da jin wannan batu sai sarkin yaƙi ya yi murmushi ya ce "ai kuwa dukkanin ku kun faɗa tarkon so ne ba ku sani ba, lallai nan da wani lokaci za ku cigaba da kasance a kogin SOYAYYA, amma wani hanzari ba gudu ba kai a yanayin da kake kallon khadijat kana ganin cewa halin talauci ne ya sanya ta yin aikatau a ƙarƙashin sarkin kasuwa Sha'aran? Jiki na ba ni cewa tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a tare da ita. Ko da jin wannan batu daga bakin sarkin yaƙi sai bawa Shamsal ya yi shiru karo na biyu sannan ya dube shi ya ce "tabbas maganar ka akwai ƙamshin gaskiya a ciki, domin a lokacin da muka sauka a rumfa su muna cin abinci na ga kallon da khadijat ke yiwa yaro Imran ya zarta misali. Bisa nazari da nayi haƙiƙa kallo ne mai ɗauke da tsantsar tausayi irin na 'yan uwa na jini. Amma dai ko ma dai mene ne komai zai bayyana domin masu iya magana na cewa, komai nisan jifa ƙasa zata faɗo, kuma a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe. Sarkin yaƙi ya ce "tabbas zancen ka dutse ya abokina"; Daga wannan furuci ne kowannen su ya yi shiru. Wannan shi ne abin da ya faru da tsakanin sarkin yaƙi da bawa shamsal a masaukin su. Al'amrin yarinya Shuraiba kuwa lokacin da gimbiya Lamrat ta ɗauke ta a cikin keken dokin ta suka durfafi hanyar da zata sada su da gidan sarauta, sai ya zamana cewa duk inda suka gifta a cikin birnin Istanbul sai dai ka ga jama'a na faɗuwa ƙasa suna gaisuwa tamkar za su yi mata sujjada. Haka dai aka cigaba da wannan tafiya har aka iso ƙofar gidan sarauta aka kunna kai izuwa ciki. Bisa wani ƙasaitacce ɓangare da yafi ko ina ƙawatuwa a gidan sarautar, keken dokin ya sauke su gimbiya Lamrat, kai tsaye ta kutsa kai izuwa ciki, hannun riƙe da na yarinya shuraiba dakaru na take mata baya, ɓangaren cike yake da kuyangi, barori, hadimai da bayi suna ta kai komo suna ta hidima. Nan fa ya zamana cewa yarinya Shuraiba ta zamto cikakkiyar 'yar ƙauye, ta kama kalle-kalle da dube-dube tamkar ɗan ƙauye ya shigo birni. Wata kyakkyawar budurwa daga cikin kuyangin ta rugo izuwa inda suke ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa ga gimbiya sannan ta ɓuɗi baki cikin ladabi da girmama ta ce "ya shugabata shin me kike da bukata? Gombiya Lamrat ta ce "ya ke Lazura ki yi sani cewa abi nda nake buƙata shi ne ki tafi da wannan yarinya a tsaftace mata jikinta a sanya mata tufafi masu kyawu, sannan a haɗa mana abin kalaci". Ko da jin wannan umarni daga baƙin Lamrat sai kuyanga Lazura ta risina ta ce "an gama ya shugabata" Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta kama hannun yarinya Shuraiba ta shige da izuwa wani ɓangare na daban. Sannan gimbiya ta shige izuwa turakarta dakaru masu tsaron lafiyar na biye da ita. Wannan shi ne abin da ya faru da yarinya Shuraiba da gimbiya Lamrat matar sarki Ladiyas. Al'amarin yaro Imran kuwa, lokacin da ya isa izuwa masaukin su sai ya shiga kewaye ya watsa ruwa kuma ya ɗaura alwala, sannan ya gabar da Sallar magariba, bayan ya kammala ya yi godiya ga Ubangiji Koda gama aiwatar da hakan sai ya ji an ƙwanƙwasa Ƙofar dakinshi. Kawai ya tashi ya je ya buɗe domin ya ga wane ne, sai ya ga a she hadima khadijat ɗauke da abin kalaci da taceccen ruwan inibi bisa kofin azurfa. Bayan ta ajiye a gaban shi sai ta samu waje ta zauna shi ma ya yi koyi da ita. Khadijah ta dube shi ta ce "na samu wani labari dake yawo a gari akan abin da yafaru tsakanin ka da matsafi Shamrul, tabbas idan hakan ya tabbata dola ne mu kasance cikin shirin ko ta kwana domin a kowane lokaci dakarun farmaki zasl su dunga kawo mana ziyara don ganin bayan ka". Koda jin wannan batu daga bakin khadijat sai yaro Imran ya jinjina al'amarin a cikin ranshi sannan ya dubi khadijat ya ce 'tabbas maganar ki gaskiya ce ya 'yar uwanta, kuma Ubangiji yana tare da mu a kodayaushe yanzu bari na yi kalaci sai ki dawo mu gabatar da sallar isha'i. Da jin hakan saikhadijat ta miƙe tsaye ta juya ta fice daga ɗakin tana mai waigen Imran. Wannan shi ne abin da ya faru da yaro Imran lokacin da ya isa masaukin su. BABI NA SHA HUƊU Lokacin da dare ya tsala sai sarkin yaƙi Darusu ya ɗauki sarki Lazwar ya gurfanar da shi a gaban mai girma Ladiyas Ladiyas, a lokacin da ya ke zaune a cikin wata ƙasaitacciyar turaka. tsayawa musalta tsaruwa da ƙawatuwar turakar zai iya zamowa ƙauyanci sai dai abin da idanu suka gani kawai komai ƙasaitar BASARAKE ko attajiri idan ya tsinci kanshi a cikin wannan dole ne ya zamto bagidaje kuma cikekken ɗan kauye. Bisa wata ƙasaitacciyar kejera wani mutum zaune a kai. Mutumin ya kasance mai ƙirar sadaukai ya tara ƙwanji, kyakyawa ne na gaban kwatance kuma ma'abocin kwarjini da haiba, Sanye yake da tufafi riga da wando irin na hamshakan sarakai, kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON DUNIYA mai ƙarfi na Allah ya isa. Ba wani ba ne wannan mutum ba face sarki Ladiyas ibn Fairuz. A wannan lokaci yana zaune yana hangen wani ɓangare na lambun shaƙatawar daga tagar turakar. Yana cin kayan marmari dake ajiye akan faranti na zinare bisa wani madaidaicin teburi na azurfa. Koda bayyanar sarkin yaƙi Darusu sai ya ajiye tuffa dake hannunshu ya juya yana mai fuskantar shi. Gami da ƙarewa sarki Lazwar kallo a lokacin da suke durƙushe a ƙasa bisa gwiwoyinsu kuma sun sunkuiyar da kawunansu ƙasa. Lokacin da sarki Lazwar ya ji shi durƙushe a gaban sarki Ladiyas sai baƙin ciki da takaici suka mamaye zuciyarshi, ya ji kamar ya ƙwalla ihu, wai yau a ce shi ne durƙusawa wani sarki saboda kawai neman biyan bukata, a matsayin shu na hamshaƙin sarki mai cike da taƙama da BAƘAR IZZA. Tsawon daƙiƙa ana cikin wannan hali, sai daga bisani sarki Ladiyas ya buɗi baki cikin wata irin kakkausar murya mai tattare da jarumtaka ya buɗi baki ya ce "ya kai dirkar birnina alamu sun nuna min baƙom bawan da ka zo da shi zai iya kasance ɗaya cikin masu tsaron lafiyar gimbiya, amma sai dai ba zai yiwu na amince da hakan ba face ya shiga izuwa ɗakin duhu kuma ya samu nasarar cin jarabawar FARAUTAR RAI, lallai ne gobe da safe ka gabatar da shi a fada domin yi mashi jarabawar"; Koda jin wannan umarni daga bakin sarki Ladiyas sai sarkin yaƙi darusi ya risina cikin ladabi ya ce "an gama ya shugabana". Yana gama faɗin hakan ya tashi tsaye ya juya ya fice daga turakar sarki Lazwar ya yi koyi da shi yana mai bin bayan shi, suka durfafi wani ɓangare daban. Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Lazwar a lokacin da aka gabar da shi a gaban mai girma Ladiyas. Al'amarin yarinya Shuraiba kuwa, lokacin da kuyangi suka kammala yai mata wanka da ado kuma suka ciyar da ita daddaɗan abinci, sai barci mai nauyi ya ɗauke ta. Ba ta farka ba sai da dare ya tsala, a wannan lokaci gimbiya na zaune a kusa da ita bisa kan gadon da take kwance. Sa'adda ta ga Shuraiba ta farka daga barci sai ta sanya hannayenta biyu tashe ta tsaye ta ja hannun ta izuwa wata ƙasaitacciyar kujera, da a gaban ta aka ajiye wani teburin azurfa mai ɗauke da nau'ikan abinci, bin sha da tanɗe-tanɗe. Cikin matuƙar farin ciki gimbiya ta shiga ɗibar abinci da abin sha tana bawa Shuraiba a baki. Nan take Shuraiba ta ji tamkar mahaifiyarta ce ke ciyar da ita, ita kuwa gimbiya farin cikin ta ba zai misaltu ba, bisa ganin cewa yau ita ce ke ciyar da 'yarta da hannunta da ta shafe tsawon shekaru tana kewar ta. Bayan gimbiya ta kammala bata abincin, ita ma ta kimtsa cikinta, sai Shuraiba ta shiga bawa gimbiya labarin rayuwar ta, tun daga lokacin da sarki Ladiyas ya raba ta da mahaifiyarta ya mayar da ita baiwar shi, har izuwa sa'adda suka koma rayuwa a daji ita da mahaifinta, har kawo lokacin da ta haɗu da su sarki Lazwar, tun daga farko har ƙarshe ta zayyane wa gimbiya. Sa'adda gimbiya ta ji wannan labari daga bakin yarinya Shuraiba ba ta san sa'adda ta rungume ta ba su duka biyun suna masu fashewa da matsanancin kuka mai tsuma zuciya. sai daga bisa ne gimbiya ta janye jikinta daga na Shuraiba suka fuskantaci juna. Kawai sai gimbiya ta sanya hannunta ta ya ye mayafin dake kanta fuskarta ta bayyana a fili ƙarara. Sa'adda Shuraiba ta yi arba da fuskar gimbiya ba ta san sa'adda ta sake rungume ta ba a karo na biyu tana mai fashe da kukan murna. Ba komai ne ya sanya ta hakan ba sai domin arba da ta yi da fuskar mahaifiyarta Lamrat, tana mai cewa ashe zan sake ganin ki ya ummina ashe daman kina raye? Daƙyar gimbiya Lamrat ta lallashe ta tayi shiru ta share mata hawaye, bayan ta samu nutsuwa ne sai ta dube ta cikin annashiwa da farin ciki ta ce "ya 'yata kuma farin zuciyata Haƙiƙa ina raye ban mutuwa, a kowace rana idan dare ya tsala sai nayi kukan baƙin ciki tare da roƙon abin bauta akan ya kare min ke kuma ya kawo min lokacin da zan ɗauki fansa akan BAKIN AZZALUMI da ya lalata rayuwar mu wato sarki Ladiyas. Sai gashi abin bauta ya dawo min dake cikin ƙoshin lafiya, ina so mu ɓoye sirrin dake tsakanin mu har izuwa lokacin da zamu ɗauki fansa. Saboda hakan ma ya sanya na ɓoye miki fuskata a lokacin da muka haɗu a kasawu, domin matuƙar wani ya gane hakan har sarki ya samu labari tofa dukkan shirin mu ya tarwatse. Sa'adda gimbiya ta zo dai-dai nan azancenta sai yarinya Shuraiba ta cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa, tana mai cewa tabbas na aminta da ke ummina kuma za mu ɗauki fansa akan sarki Ladiyas. Wannan shine abin da ya wakana tsananin yarinya Shuraiba da mahaifiyarta gimbiya Ramlat. Al'amarin yaro Imran kuwa tun sa'adda ya yi bankwana da hadima Khadijat bayan sun sun tattauna akan abin da ya wakana tsakanin shi da matsafi Shamrul a cikin kasuwa, sai ya shiga kimtsa cikin shi bayan ya kammala ne Khadijat ta dawo gare shi suka gabatar da sallar Isha'i Bayan kammala wa ne ya kwanta domin ya huce gajiyar dake tattare da shi. Wannan shi ne ya faru da yaro Imran ma'abincin addinin Musulunci. BABI NA SHA BIYAR BIRNIN ISTANBUL Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar sarki Ladiyas ta cika ta batse da jama'a maza, mata yara da manya, duk inda mutun ya duba kawunan bil'adama rututu babu masaka tsinke, tamkar dandazon kiyasai. Domin a yau ne aka samu labarin cewa za'a gudanar da gasar farautar rai, domin tsallake matakin ƙarshe da zai bawa sarki Lazwar damar kasance ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyar gimbiya Lamrat. Bayan jama'a sun hallara kuma sarki Ladiyas ya hakimce a bisa karagarshi ta mulki, sanye cikin ƙasaitacciyar shiga ta kece raini. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Sai aka hango sarkin yaƙi Darusu ya shigo izuwa fadar tare da dakaru sun tuso ƙeyar sarki Lazwar ɗaure a cikin sarari na baƙin ƙarfe. Sa'adda jama'a suka yi arba da sarki Lazwar sai fadar ta kaure da shewa, sai da sarkin yaƙi ya ɗaga hannunshi sama sannan fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta kawo ziyara. Sannan ya fuskanci mutane bayan ya yi gyaran murya sai ya buɗi baki ya ce ''ya ku jama'ar wannan fada mai albarka ku yi sani cewa ba komai ne ya sanya muka tara ku anan ba sai domin a yau ne mai girma Ladiyas ya bayar da umarnin a saka jarumi Lazwar izuwa ɗakin duhu. Domin ya yi gwagwarmaya da miyagun halittun da suke ciki kuma idan ya samu nasarar tsallake matakin zai zamto daya cikin masu tsaron lafiyar mai martaba sarki. Sa'adda sarkin yaƙi Darusu ya zo dai-dai nan a zancen shi, sai fadar ta sake kaurewa da shewa a karo na biyu, sai daga bisani ne sarkin yaƙi ya umarci waɗansu dakaru mutum hamsin suka wangame wata makekiyar kofar dake jikin bangon fadar, take wani makeken ɗaki ya bayyana mai ɗauke da waɗansu nau'ikan halittu dangin kuraye da zakuna gami da macizai. Cikin hanzari waɗansu dakarun na daban suka buɗe ƙofar ɗakin, su ɗauki sarki Lazwar suka jefa shi izuwa ciki, kana suka kwance sarƙoƙin dake riƙe da halittun, suka mayar da ƙofar suka rufe ruf! Sa'adda gimbiya Mashlira dake sanye cikin tufafin dakaru cikin ɓaddakama, ta ga an sanya masoyinta Lazwar a cikin ɗakin duhu sai takaici da baƙin ciki suka mamaye zuciyartq taji kamar ta ƙwallawa ƙara. Amma sai ta danne saboda ta san cewa ba don komai masoyin nata ya shiga wannan hali ba sai domin kawai ya sadu da baiwa Sharifa da zata taimaka mashi wajen mallakar abubuwan da zasu warkar da shi daga sihirin da abokin gabar shi ya yi mashi, sai kawai ta shiga yi mashi fatan samun nasara, amma har yanzu hankalin ta a matuƙar tashe ya ke ainun. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin sarki Lazwar da halittun, kuraye biyu zakuna biyu sai waɗansu rin mucizai masu kawuna biyar. Duk da kasancewar sarki Lazwar GWARZON MAYAƘI kuma GWARZON DUNIYA sai da hankalin shi ya dugunzuma ainun, domin iya tsawon rayuwarshi bai taɓa gani ko jin labarin halittu masu kwarjini da ban tsoron tamkar su ba. Tsawon daƙiƙa hamsin halittun na kewaye lazwar suna gurnani gami da hargagi mai matuƙar ban tsoro, sai daga bisani ne suka yi ɗauki kan shi suna kururuwa da ihu mai ɗimauta DANDAZON MAYAƘA suna masu kai mashi cizo da yakushi da faratansu, macizan na kai mashi sara gami da furzar da dafi daga bakunansu cikin wani irin baƙin zafin nama da ya ɗimauta hankali. Shi kuwa sarki Lazwar ya wanzu ya na zillewa tare da kaucewa hare-haren halittun cikin zafin nama JURIYA DA BAJINTA. Sai da sa'a ɗaya da rabi ta shuɗe ana wannan ɗauki ba daɗi ba tare da ɗaya daga cikin su ya samu nasara ba, a dai-dai wannan lokaci ne halittun suka fara galabaitar da Lazwar ya zamana cewa ba ya iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kanshi. Ana cikin artabun ne wani daga cikin zakunan ya yakushe shi a cinyarshi ta hagu take ya yi mashi mugun rauni, sarki Lazwar ya kurma wawan ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da ya ji jini ya kwaranya. Kafin ya sake yin wani yunƙuri wani maciji ya kafta mashi wawan sara a gadon bayanshi, saboda matuƙar azaba sai da sarki Lazwar ya faɗi a ƙas yana nishin wahala. Nan fa masoyan sarki Lazwar suka cika da matuƙar baƙin ciki har waɗansu na zubar da hawayen takaici bisa ganin halin da jarumin su ke ciki. Shi kuwa Sarki Ladiyas dake hakimce bisa karagar mulkin sai ya shiga ɓaɓɓaka dariyar mugunta har da kyakyatawa nan fa sauran 'yan majalisa da fadawa suka yi koyi da shi. Al'amarin da ya sanya zuciyar gimbiya Mashlira ta karaya kenan har kwalla ta cika mata idanu, bisa ganin halin da masoyinta ke ciki amma saboda tsoron kar wani ya gane halin da take ciki asirinta ya tunu sai ta yi sauri ta goge hawaye dake kan fuskarta, dai-dai lokacin ne ta hango bawa Shamsal da sarkin yaƙi a cikin jama'ar gari suka zubar da hawayen takaici bisa ganin halin da shugabansu ya tsinci kanshi a ciki, da koyaushe zai iya rasa rayuwar shi. Lokacin da sarki Lazwar ya tsinci kanshi a tsakanin RAYUWA DA HALAKA, kuma ya tabbatar da cewa haƙiƙa a koda yaushe zai iya sheƙawa barzahu, sai kawai ya fara amfani da zallar ƙarfin sihirin tsafinshi, amma sai ya zamana cewa tamkar yana inziga miyagun halittun wajen kai mashi farmaki. Kwatsam! sai yaro Imran ya faɗo masa a rai zuciyarshi na raya mashi cewa kawai ka nemi taimakon Ubangijin yaro Imran tun da dukkanin wata dubara ta ƙwace maka, domin masu iya magana na cewa da asara gwara gidadanji. Kuma wanda ya faɗa teku ko KAIFIN TAKOBI aka miƙa mashi sai ya kama domin ya tsira. Tun da a halin yanzu ba wanda zai gane cewa ka nemi taimakon Ubangijin Imran sai kai kaɗai. Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan a tunanin shi sai kawai ya yi kabbara yana mai ambaton sunan Allah a cikin ranshi yana mai cewa "ya Ubangijin imran ka tseratar da ni daga sharrin miyagun halittun nan". A dai-dai wannan lokaci ne wani ɗaya daga cikin zakokin ya wangame bakinshi da nufin ya cinye yan yatsun Lazwar na hannu. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Lazwar ya kurma wawan ihu cikin wani zafin nama na ban al'ajabi yana daga kwance ya kama wuyan zakin da hannayen biyu ya murɗe wuyan shi, take ya karye ya yi ƙara ji kake ruƙus! Ƙas ya sheƙa barzahu ko shurawa bai yi ba, sannan ya miƙe tsaye zumbur aka sake yin wani sabon kallon-kallo tsakanin shi da sauran halittun. Nan take fadar ta ruɗe da shewa masoyan sarki lazwar suka cika da matuƙar farin cikin bisa ganin gwaninsu ya miƙe tsaye. Shi kuwa sarki ladiyas fuskarshi a murtuke take babu annuri domin tsawon shekarun da aka shafe ana gwada jarumai, ba a taɓa samun wanda ya kashe dabba ɗaya daga cikin halittun ba. Daga can sai dukkan halittun suka afkawa Lazwar aka sake ruguntsume wa da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro. A wannan karon sai ya zamana cewa duk wanda Lazwar ya gabza wa naushi a cikin halittun sai kaga ya yi sama tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗo ƙasa tim. Amma saboda na ci da zafin nama irin na halittun sai su miƙe tsaye zumbur su sake afka mashi da dukkanin tsagwaron ƙarfin damtsen su. Kafin cikar rabin sa'a sarki Lazwar ya kashe gaba ɗaya halittun ya jefar da gawarwakin su a ƙas, nan fa fadar ta kaure da shewa da ihu jama'a suna ta mamakin wannan jarumtaka ta sarki Lazwar, domin a tarihin gasar shi ne mutum na farko da ya taɓa kashe miyagun dabbobin baki ɗaya. Ita kanta gimbiya Mashlira 'yar sarkin maridai bata san sa'adda murmushin farin ciki ya suɓuce mata ba. Al'amarin da ya sanya zuciyar mai girma Ladiyas ta ci gaban da tafarfasa tamkar zata ƙone kenan. Kodasamun wannan nasara da sarki Lazwar ya samu sai sarkin yaƙi Darusu ya umurci waɗannan dakaru mutum Hamsin suka je suka buɗe ƙofar ɗakin aka fito da sarki Lazwar, likitoci suka shiga ba shi taimakon gaggawa domin tsayar da jinin dake zuba a jikinshi tare sanya mashi magani akan raunukan shi . Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu dakaru mutum arba'in shirye cikin gagarumar shigar yaƙi sun tuso ƙeyar yaro Imran da hadima Khadijat, ɗaure cikin sasari na baƙin ƙarfe hannu da ƙafa. A gefe guda kuma matsafi Shamrul ne tare tawagar malaman addininsu sanye da tufafi irin na bauta. Lokacin da ya zamana tazarar dake tsakanin su da karagar mulki bai huce taku goma ba sai matsafi shamrul da sauran bokaye suka zube ƙasa bisa gwiwoyin su suka kwashi gaisuwa ga sarki ladiyas. Suna masu sunkuiyar da kawunansu ƙasa. Sai da suka ɗauki lokaci a cikin wannan hali sannan daga bisani matsafi Shamrul ya dago da kanshi sama ya buɗi baki cikin ladabi da girmamawa cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki ya ce "ya shugabana haƙiƙa abinbauta ya bada umurnin a yanka waɗannan mutane biyu mace da namiji da suka shigo mana da wani sabon addini mai suna musulunci wanda suke jan hankalin mutane wannan birni mai albarka, wanda a dalilin hakan zai janyo mana musiba da annoba da zata haifar da suɓucewar mulkin ka". Sa'adda da sarki Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin matsafi Shamrul sai zuciyarshi ta kama tafarfasa tamkar zata fasa ƙirjinshi ta fito waje, yaji ya tsani hadima Khadijat da yaro Imran. Kawai sai ya dubi Khadijat da fuskar ta ke rufe da rawani ya ce ''ya ke baiwa Sharifa haƙiƙa kin yaudare ni kin ci amanata da kika zo da wani sabon addini a wannan birni nawa, na aika ki zuwa ga sarkin kasuwa domin ki gane ki zamto 'yan leƙen asiri, domin ki taimaka min na samu nasarar ganin bayanshi, haƙiƙa a yau zan yanke miki hukunci dai-dai da laifin da kika aika ta a gareni"; Sa'adda da mai girma Ladiyas ya zo nan a zancen shi sai sarki Lazwar dake gefe guda likitoci na duba lafiyar shi ya cika da matuƙar al'ajabi da mamaki ainun, bisa jin sarki Ladiyas ya kira hadima Khadijat da suna baiwa Sharifa. Shin dama Khadijat ita ce baiwa Sharifa da ya fito farautar ta ruwa a jallo? Tabbas tsugunne bata ƙare ba wai an saci ɗan ɓarawo. Haƙiƙa dole ne ya yi sabon gumurzu domin ceton rayuwar Khadijat. Sarkin yaƙi, Bawa Shamsal da aljani Za'aratul-layal dake cikin siffar bil'adama tare da gimbiya Mashlira dake sanye da tufafin dakaru cikin ɓaddakama, sai suka cika da matuƙar mamaki bisa jin ashe hadima Khadijat ita ce baiwa Sharifa, wannan fa shi ne masu iya magana ke cewa "rashin sani kaza ta kwana akan dami". Ashe sarki Lazwar na tare da abin da yake nema bai sani ba har ya shigar da kanshi cikin uƙubar sarki Ladiyas. A ɓangaren jama'a kuwa sa'adda ji cewa yaron nan da yiwa matsafi Shamrul tambaya akan addininsu za'a yanke wa hukuncin kisa, sai suka yaɗa labarin izuwa cikin gari, nan fa al'ummar gari suka dinga tuttuɗowa suna cincirindo a fadar domin su ganewa idanuwan su. Domin a yau ne zasu tantance shin tsakanin Ubangijin wannan yaro Imran da matsafi Shamrul wane ne na abin bauta na gaskiya. Sarki Ladiyas na kammala wannan batu sai sarki Ladiyas ya koma kan karagar mulkinshi ya hakimce. Kawai sai wani garjejen ƙato ya ɗauki yaro Imran ya ɗora a jikin wani zagayayyan tudu a fadar sannan ya koma gefe guda ya ja ya tsaya, sarki Ladiyas ya yi wa sarkin yaƙi Darusu inkiya ta wutsiyar idanu dake nuna bashi umarni. Cikin dakewar zuciya gami da zafin nama sarkin yaƙi ya zare wata sharɓeɓiyar adda a gadon bayanshi ya durfafi inda Imran yake domin ya datse wuyanshi. Sarki Ladiyas, matsafi Shamrul da sauran bokayen suka bushe da dariyar mugunta har da ƙyaƙyatawa. Jama'a kuwa da yawan su sai suka fara zubar da hawayen takaici da baƙin ciki Ya yin da sarkin yaƙi ya isa daf da shi sai ya daga addar ya ɗora akan waya yaro Imran. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga wata kyakkyawar halitta ta keto daga saman fadar ɗauke da waɗansu mutane guda biyu. Ba wani bane wannan halitta da mutanen biyun ba face aljani Hadimul-khairi ɗauke da gimbiya Lamrat matar sarki Ladiyas da 'yarta yarinya Shuraiba. Kafin addar sarkin yaƙi Darusu ta yanka wuyan Imran aljani Hadimul-khairi ya ɗauko wata farar kwalba mai ɗauke da wani koren ruwa ya watsa inda Imran da baiwa Sharifa suke, take sarƙoƙin dake ɗaure a jikkunansu da addar dake wuyan Imran sun narke suka zama ruwa. Cikin matuƙar firgici sarkin yaƙi, sarki Ladiyas da sauran jama'ar fada suka ɗaga kawunansu izuwa sama. Yaro Imran, hadima Khadijat, sarki Lazwar, sarkin yaƙi, bawa Shamsal, gimbiya Mashlira da aljani Za'aratul-layal, kuwa sai suka cika da matukar farin ciki maral-musaltuwa. Aljani Hadimul-khairi ya a sauka a turba bisa diga-diganshi. Nan fa aka shiga kallon-kallo tsakanin sarki Ladiyas, da uwar gidanshi gimbiya Lamrat, matsafi Shamrul da yaro Imran da hadima Khadijat wato baiwa Sharifat, sarkin yaƙi Darusu da sarki Lazwar. Cikin matukar ɓacin rai mai girma Ladiyas ya dubi uwar gidanshi Lamrat ya ce "ya uwar gidana shin ina dalilin wannan zuwa naki a cikin wannan yanayi? Koda jin wannan tambaya daga bakin Sarki Ladiyas sai gimbiya Lamrat ta tari numfashinshi tana mai daka mashi tsawa, ta dube shi cikin matuƙar fushi ta ce "kai tsohon AZZALUMI kuma la'ananne ka yi sani yanzu kan mage ya waye, a yau ne zan ɗauki fansar jinin mai gidana maƙeri Murrasu daka ni da 'yata Shuraiba, haƙiƙa masu iya magana sun yi magana da suka rana dubu ta ɓarawo, rana ɗaya ta mai kaya, ka yi sani cewa tsawon shekarun da ka shuɗe kana azabtar da jama'ar birnin ISTANBUL kana yiwa mutane BAKIN ZALUNCI, to ranar ƙin dillanci ta zo maka. Shawarar da zan baka ita ce ka yi hanzari ka rubuta wasiyyar da kake son bar wa jama'ar kafin mu zare maka ruhinka daga gangar jikinka. Sannan ina so ka yi sani cewa ni da 'yata Shuraiba tuni mun karɓi addinin yaro Imran. A halin yanzu ni ba uwar gidanka ba ce face abokiyar gabar ka, dama dai-dai da rana ɗaya ban taɓa ƙaunarka kawai ina yi maka biyayya ne bisa dole don tana din gobe na". Sa'adda mai girma Ladiyas ya ji wannan batu daga bakin gimbiya Lamrat sai zuciyarshi takama tafarfasa tamkar zata ƙone ya daka mata tsawa a lokacin da idanuwanshi suka kaɗa suka yi jajur cikin kakkausar murya mai ya ce "kaicon ki yake Lamrat haƙiƙa kin tafka babban kuskure da har kika yi gangancin haɗa kai da maƙiya na domin farautar rai na, a yau ne zan yi maki hukunci mafi muni ke da 'yarki Shuraiba". Sa'adda sarki Ladiyas ya zo nan azancen shi sai ya miƙe tsaye zumbur daga kan karagar shi ta mulki ya cire alƙyabbarshi, take wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar firgici da ban tsoro ta bayyana a jikinshi. Kawai sai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye yana saman ya daga hannunshi sama wata irin sharɓeɓiyar takobin sihiri ta bayyana a gare shi, ya sauka bisa diga-diganshi a daf da inda Lamrat take. Koda ganin hakan sai yarinya Shuraiba tayi wuf ta zare kwari da bakanta ta yi shirin ko ta kwana. Sarki Lazwar kuwa duk da cewar jikinshi ya yi tsami akwai manyan raunuka, amma sai ya yi wuf ya kwaci wata takobi a hannun wani badakare ya falfala da azababban gudu izuwa kan sarkin yaƙi Darusu Baiwa Sharifa da yaro Imran kuwa sai suka yi ɗauki izuwa kan matsafi Shamrul suna masu ƙwala kabbara, bawa Shamsal da sarkin yaƙi kuwa sai suka tari dakarun dake fadar, aljani za'aratul-layal sai ya yi girgiza take surarshi ta canja daga ta bil'adama izuwa ta aljani kawai sai ya rufawa mai gidanshi sarki Lazwar baya, a lokacin ne gimbiya Mashlira sai cire hular ƙarfen dake kanta fuskar ta ta bayyana a fili, nan fa kowa ya cika da mamaki ganinta, kawai sai ta yi koyi da aljani Za'aratul-layal ta kaiwa masoyinta sarkin Lazwar ɗauki. Lokaci guda ɓangarorin biyar suka afkawa juna aka garƙame da azababban yaƙi mai matuƙar muni da ban tsoro. Wohoho! kaico haƙiƙa guguwar annoba idan ta taso babu mai maganin ta face Allah, kuma tabbas in da babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, domin KARON MAZA sai JARUMAN DUNIYA da suka ciri tuta a GUMURZUN SHEKARA DUBU, waɗanda komai TSANANI DA UKUBA a filin DANDAZON MAYAKA baya sa su gudu. Haƙiƙa komai dakewar zuciyar mutum idan ya ga yadda fadar ta yamutse da gumurzu dole ne ya ɗimauce ya fita daga hayyacin shi domin dola ne artabun ya zamo tashin hankali. Nan fa jama'a suka ɗimauce suka kama guje-guje da ifice-ifice domin tsira da rayukansu Ɓangarorin suka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare-hare cikin matuƙar baƙin zafin nama JURIYA DA BAJINTA tamkar jikkunan su basu kasance na bil'adama mai jini tsoka ba. Kaico! Haƙiƙa duk wanda bai fita filin yaƙi ba to bai ga ƙarshen tashin hankali ba, wanda bai san shi ba shi ne yake fatan zuwan shi, ana fara wannan ɗauki ba daɗi ne gimbiya Lamrat, yarinya Shuraiba da Aljani Hadimul- kahiri suka fara gane cewa tabbas shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba, domin kuwa tsananin zafin naman sarki ladiyas ya nunka nasu sai arba'in, Nanfa ya zamana cewa mutum uku sun kasa galaba akan ɗaya ya zame masu alaƙaƙai, duk sa'adda suka kai mashi hari da makaman smmsu idan ya kare da takobinshi, sai kaga makaman sun dakushe kuwa ko gezau bai yi ba. Idan kuwa Ladiyas ya kai masu harin idan suka goce sai ya zamana cewa duk abin da takobin ta saran sai ya yi bindiga ya tarwatse koda kuwa gini ne. Matsafi Shamrul, yaro Imran da hadima Khadijat kuwa tuni labari yasha banbam, domin kuwa sun hana tsafi Shamrul rawar gaban hantsi, har sai ya zamana cewa ya daina amfani da makami ya dawo yaƙar su da ƙarfin sihirin tsafi, domin wani lokacin idan Imran da Khadijah suka sare shi ta takubban su sai su ga raunin ya koma ya haɗe sumul, wasu lokutan ma sai ya rikiɗa ya zama haske. Sarki Lazwar, gimbiya Mashlira da aljani Za'aratul-layal kuwa sun wanzu suna masu kaiwa sarkin yaƙi Darusu hare-hare cikin gwanintar yaƙi tamkar za su cinye shi ɗanye. Amma bisa mamaki sai ya zame masu ƙadangaren bakin tulu suka kasa samun nasarar koda lakutar jikinshi, duk kuwa da cewar ƙarfin mutum biyu ne da aljani ɗaya akan mutum guda. A ɓangaren bawa Shamsal da sarkin yaƙi ku wa sun wanzu suna ragargazar dakarun dake fadar duk inda suka sanya gaba sai ka ga dakarun na zubewa ƙasa matattu, nan fa ƙarar karafniyar ƙarafa, ihun mazaje hade da hargowar aljanu gami da ifice-ificen jama'a ya cika dodon kunne, ƙura ta turnuƙe fadar baki ɗaya tamkar haɗari zai gangamo a kece da ruwan sama. Lokacin da aka ruguntsume da azababban yaƙi tsakanin manyan sarakuna biyu, aljanu biyu, gami da jarumai shida sai yaƙin ya zamto tashin hankali gami da ban tsoro ga yan kallo. Sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan ɗauki ba daɗi tsakanin jaruman ba tare da ɗayan su ya samu nasarar hallaka ɗaya ba. A bangaren sarki Ladiyas kuwa ya zamewa su gimbiya Lamrat ANNOBA ƊARI domin duk da cewar Hadimul-kahiri na amafni da addu'o'i domin su hallaka sarki Ladiyas amma sai hakan ya gagara domin sai sun datse wuyanshi suna tunanin ya mutu sai kawai su ga wani ruhun ya keto daga cikin ƙarƙashin ƙasa ya sake shiga jikinshi. Sai kuma a ɗora wani gumurzun, nan fa ya zamana cewa su Hadimul-kahiri sun kashe fiye ruhika arba'in na sarki Ladiyas. Al'amarin da ya sanya su duka ukun suka samu miyagun raunuka musamman yarinya Shuraiba. Haƙiƙa sarki Ladiyas bakaramin hatsabiba ne domin ya yi nisa a halarar tsafi wanda cimma mashi abu ne mai matuƙar wahala. A dai-dai wannan lokaci ne yaro Imran da hadima Khadijat suka samu nasarar hallaka matsafi Shamrul, ta hanyar amfani da takubbansu suka soka mashi akan ƙawon zuciyarshi, ya yin da suka hango su yarinya Shuraiba kuma suka ga irin mugun halin da suke ciki sai suka kai masu ɗauki. Nan fa ya zamana cewa labari ya sha bamban domin a wannan karon sai ya zamana tasirin sihirin dake tare da sarki Ladiyas ya fara karyewa, domin duk sa'adda hadima Khadijat da yaro Imran suka kai mashi hari da makamansu duk inda suka sara sai su ga sun tsarga jikinshi. Bisa taimakon Ubangijin halitta daƙyar da siɗin goshi suka samu nasarar hallaka sarki ladiyas, ta hanyar sare mashi hannaye da ƙafafuwanshi suka jefar da gawarshu a ƙas. In da ace mutum ya na wannan waje a lokacin da sarki Ladiyas da matsafi Shamrul suka yi mutuwar wulakanci dole ne ya yi farin ciki maral-musaltuwa. Bisa ganin yadda Allah Ubangijin halitta ya kawo ƙarshen azzalumai. A dai-dai wannan lokaci ne su gimbiya mashlira, Aljani Za'aratul-layal da sarki Lazwar suka samu nasarar hallaka sarkin yaƙi Darusu. Sa'adda al'ummar fadar da su bawa Shamsal suka yi arba da gawar sarki Ladiyas, da ta matsafi Shamrul sai dukkanin su suka durƙusa ƙasa bisa gwiwoyinsu suka yi mubaya'a, suna masu cewa "haƙiƙa mun bayar da gaskiya ga Ubangijin yaro imran Cikin hanzari waɗansu likitoci suka shigo fadar ɗauke da kayan aiki suka shiga duba lafiye yarinya Shuraiba, gimbiya Lamrat,da sarki Lazwar. Sannan yaro Imran ya ruga izuwa inda hadima Khadijat take suka rungume juna cikin matuƙar farin ciki maral-musaltuwa bisa sake saduwa da juna da suka tsawon shekaru. Daga bisani yaro Imran ya janye jikinshi daga na 'yar uwarshi Sharifa. Ya juya ya fuskanci jama'a sannan ya buɗi baki ya ce "ya ku al'ummar wannan birni mai albarka haƙiƙa na tabbatar da cewa a halin yanzu zukatanku sun gamsu cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah mai kowa mai komai. Saboda haka yanzu ba tare da wani ɓata lokaci ba yaro Imran ya faɗi kalmar shahada, take ɗaruruwan jama'ar dake fadar suka maimaita. Sautin muryoyinsu ya cika fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin baki ɗaya. Bisa mamaki sai Imran da hadima Khadijat suka ji sarki Lazwar da sarkin yaƙinshi haɗe da bawa Shamsal tare gimbiya Mashlira sun amsa kalamar shahadar. Nan fa suka cika da al'ajabi, sarki Lazwar ya tako da ƙafafuwanshi izuwa inda imran da Khadijat suke ya dubi Khadijat cikin girmamawa ya ce "ya ke Sharifat Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu, na zo wannan birni neman ki, ashe kina tare da ni ban sani ba, yanzu ga shi na karɓi addinin Musulunci shin ina makomar tafiya ta izuwa nemo abubuwan da za su warkar da ni daga sihirin da abokin gaba ta sarki Durwazu ya yi min, na karɓi Musulunci ne domin yadda a zuciyata, na samu tabbacin ne a lokacin da nake fafata yaƙi da miyagun halittun dake cikin ɗakin duhu, inda dukkan wata dubara ta ƙwace min na nemi taimakon Ubangijin imran". Sa'adda sarki Lazwar ya zo nan azancen shi sai Sharifa, yaro Imran da sauran jama'a suka cika da matuƙar mamaki. Sharifat ta ce ''ya kai wannan sarki mai daraja ka yi sani cewa ai shi addinin Musulunci yana shafe duk abin da ya tuve, saboda haka a halin yanzu sihirin da sarki Durwazu ya yi maka ya karye. Babu buƙatar sai na taimaka maka wajen mallako abubuwan da za su warkar da kai daga sihirin, domin abubuwan da za'a mallako dukkanin su na tsafi ne. A halin yanzu zaka iya kusantar kowace irin 'ya mace kuma har ka samu haihuwa ka yarda Ubangijin musulunci kawai a koda yaushe"; Koda jin wannan batu daga bakin Sharifa wato sai sarki Lazwar ya cika da matuƙar farin ciki wanda bai taɓa yin kamar shi ba. Daga wannan ne aka ɗunguma izuwa gidan sarauta domin kowa ya huce gajiyar dake tattare da shi. A cikin wannan dare ne hirar soyayya ta ɓarke tsakanin sarki Lazwar da gimbiya Mashlira 'yar shugaban maridai, yaro Imran da yarinya Shuraiba, Sharifat da bawa Shamsal. Kuma a wannan dare ne akayi shelar naɗin sarautar yaro Imran da wazirinshi Shamsal. kafin wayewar gari ciki da wajen birnin Istanbul ya cika ya batse da jama'a baƙin sarakuna daga kowa ce nahiya da 'yan kasuwa. Tun lokacin da alfijir ya keto bayan an gabatar da sallar asuba sai jama'a suka yi tsinke a fadar maza da mata yara da manya. Sarakuna da manyan baƙi an ware masu wajen zaman su daban, haka ma na talakawa, komai dai an yi shi bisa tsari. Sarkin fadar birnin Istanbul wani dattijo ya tashi ya gabatar da jawabin maraba ga mahalar ta taro. Sannan ma'ajin sarautar ya gabato da kayan sarauta da suka haɗar da alkyabba, rawani, kwagiri, takalmi da sauaran su. Sarkin fada Huzaifa ya ɗauki kayan ya shiga sanya wa yaro Imran a jikin shi, bayan ya kammala ne sai ya umarci yaro Imran ya je ya zauna bisa karagar mulki ya hakimce, nan fa tsananin kyawun surar Imran ya fito ƙarara yarinya shuraiba kuwa sai ta dunga satar kallon shi tana yi mashi kallo mai nuna alamun tsantsar so da ƙauna. Nan take jama'ar fadar suka yi mubaya'a a gare shi, daga bisani kuma sai aka shiga shagalin ɗaurin aure mutum shida sarki Imran da yarinya Shuraiba baiwa Sharifa da bawa Shamsal, sarki Lazwar da gimbiya Mashlira. A wannan rana anyi gagarumin shagalin da ba'a taɓa yin kamar shi ba tsawon kafuwar birnin Istanbul. Bayan an kammala ciye-ciye da tanɗe-tande, kowa ya cika cikinshi sai sarakunan da suka halararci bikin naɗin sarautar suka dunga zuwa, gaban sarki Imran suna karɓar KALMAR SHAHADA tare da jama'arsu, haƙiƙa farin ciki ya cika zuciyar kowa. Bayan tarewar angwaye uku sarki Imran, shamsal da sarki Lazwar. Sai sarki Imran ya umarci aljani Hadimul-kahiri ya ɗauki sarki Lazwar da amaryarshi gimbiya Mashlira da sarkin yaƙi haɗe da aljani Za'aratul-layal domin ya kai su izuwa birnin ZAWATUL-IFDAR, amma sai da aka fara zuwa ta birnin su gimbiya Mashlira aka musuluntar da sarkin maridai da mutanenshi kuma aka karya sihirin tsafin da aka yi masu suka dawo ainahin siffar su irin ta bil'adama suka daina cin naman bil'adama bisa taimakon Ubangijin halitta. An yi shagalin farin cikin dawowar yar sarkin muridai gimbiya mashlira. Sai da aka shafe mako ɗaya sannan aka sake ɗungumawa aka durfafi birnin Zawatul-ifdal, amma sai aka bar sarkin yaƙi imhal domin ya cigaba da bayar da ilimin addini ga jama'ar birnin, kuma sarkin maridai ya naɗashi wazirinshi. Lokacin da aka isa birnin Zawatul-ifdal sai sarki lazwar ya cika da matuƙar farin ciki, bisa jin labarin abin da ya faru tsakanin magajin gari Yasiran da amarya Munirat wacce a halin yanzu ita ce ke riƙe da karagar mulkin birnin. Jama'a sunyi farin cikin dawowar sarki Lazwar, ba tare da ɓata lokaci ba aka sake ɗaura auren amarya Nunirat da sarki Lazwar, sakamakon mutuwar angonta, amma da ƙyar da siɗin goshi sarki Lazwar ya shawo kan gimbiya Mashlira ta amince aka ɗaura auren. Sai aljani Za'aratul-layal da Hadimul-kahiri suka koma izuwa birnin Istanbul. Sannu-sannu bayan mako ashirin sai aka wayi gari matayen sarki Lazwar Munirat da Mashlira suna ɗauke da juna biyu. Farin ciki a wajen sarki Lazwar kuwa kamar ya zautu, ya dinga rabon dukiya da suturu na alfarma. Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya mamaye duniya baki ɗaya zaman lafiya ya wanzu, zalunci da bautar gumaka suka rushe baki ɗaya. Ƙarshe Alhamdulillah Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071 FATAUCIN BAYI Rubuta labari MANSUR USMAN SUFI Lokacin da su jaruma Nabihat suka iso izuwa bakin tanatin, sai Nabihat ta ɗauko hodar banju a cikin aljihun rigarta ta busa ta izuwa cikin tantin, jim! Kaɗan sai suka kunna kai ciki suna shiga suka tarar dakaru masu dafa abinci sun kama barci mai nauyi. kawai sai suka cire tufafin dakarun suka maye da na sannan suka rufe fusakunsu da hulunan ƙarfe. Kawai sai suka matsa izuwa inda dakarun suka ɗora sanwa akan wuta suka buɗe murafun tukunyoyin suka zazzaga wannan hodar banju a cikin, sannan suka mayar suka rufe ruf. Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sai suka zuzzuba abincin a cikin waɗansu ƙananan akushi, suka ɗora akan farantai na azurfa, sannan juya suka fice daga tantunan suka shiga rarrabawa dakarun dake cikin jirgin ruwan abincin mai dauke da hodar banjun har suka iso izuwa inda wani sadauki yake. Nabihat ta ɗauki akushi ɗaya ta miƙa mashi ya karɓa ya bude ya sanya hannunshi ya yi loma ɗaya, kawai sai ya dubi Nabihat ya ce "ya kai Himairu ya aka yi abincin nan ya yi ɗan karen daɗi haka? Koda jin wannan tambaya sai Nabihat ta yi murmushi gami da gyaɗa kai, kawai sai ta huce gaba ba tare da bawa sadaukin amsar tambayar shi ba. Haka dai suka cigaba da rabawa dakarun abincin, har suka iso inda suka bar saduki Hushaibu. Nabihat ta ɗauki akushin ta miƙa mashi ya karɓa. Har Hushaibu ya buɗe da nufin cin abincin kwai ya ji zuciyarshi ta buga da ƙarfi, kawai sai ya yi jifa da akushin ya durfafi madafa cikin hanzari. A dai-dai lokacinne su jaruma Nabihat suka kammala raba abincin suka samu wata maɓuya a cikin jirgin suka laɓe. A fusace Hushaibu ya kunna kai izuwa cikin tantin, ai kuwa sai ya yi arba da masu dafa abincin kwance suna sharar barci babu tufafi a tare da su. Cikin matuƙar fushi gami da tashin hankali ya zare takobinshi ya ruga izuwa waje yana mai ƙwallawa sauran dakarun kira. Al'amarin da ya janyo hankalin sadauki Sharkar kenan ya zare takobinshi da nufin dakawa dakarun tsawa. A dai-dai wannan lokaci ne hodar banjun da su Nabihat suka zuba a cikin abincin ta fara bugar da dakarun suna ɓingirewa kasa suna sharar barci. Kafin Sharkar da Hushaibu su farga fiye da rabin dakarun dake cikin jirgin ruwan sun kamu da barci mai nauyin gaske, cikin matuƙar kaɗuwa gami da tashin hankali sadauki Sharkar ya cigaba da falfala azababban gudu, yana mai kurma wawan ihu Nan fa sauran dakarun da ba su kai ga cin abincin ba suka firgice suka ɗauko makaman yaƙin suka dinga fitowa daga kowace kusurwa a jirgin. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga su jaruma Nabihat da sauran 'yan matan fursunonin sun yo fitar burgu daga maɓuyar su suna, suka yi ɗauki izuwa kan dakarun suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Koda ganin hakan sai dakarun suka yi ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAƘA a filin daga. Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan zaratan 'yan mata su ashirin kacal! Suka tunkari ɗaruruwan dakarun dole ne ya cika da mamaki kuma ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA, mata masu kamar maza. Ana haɗuwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matuƙar muni, ban tsoro daban al'ajabi. Nan fa gaba ɗaya jirgin ruwan ya yamutse da ƙarar haɗuwar makaman yaƙi, gami da ihu da kururuwar mazaje. Nanfa Nabihat da 'yan matan fursunonin suka wanzu suna kaiwa dakarun sara da suka cikin matuƙar zafin nama tamkar jikkunan ba su kasance na jini da tsoka ba. Cikin abin da bai gaza daƙiƙa arba'in ya zamana cewa sun samu nasarar hallaka fiye da mutum hamsin na dakarun sun rauna ta fiye da ɗari biyu. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin dakarun kenan kuma ya fusata su ainun, bisa ganin cewa a matsayin su na GWARAZAN MAYAƘA, amma a ce 'yan mata sun zame masu alaƙaƙai kuma GOBARAR ANNOBA. Nan fa dakarun suka ZAGE DAMTSE wajen kaiwa su Nabihat miyagun hare-hare. Ana cikin wannan artabu ne wani garjejen sadauki, ya kaiwa wata daga cikin 'yan matan wani wawan sara, da nufin tsinke mata wuya amma budurwa ta sunkuiya cikin zafin nama, takobin sadauki ta sari iska. Kafin ya sake mayar da martani, budurwar ta cire wata siriyar wuƙa a damtsenta s caka mashi a maƙogaranshi, sannan ta sanya ƙafarta ɗaya ta daki ƙirjin shi da dukkan ƙarfin ta. Saboda da matuƙar ƙarfin dukan sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya ya faɗa cikin tekun yana mai tsandara ihu. Kawai sai budurwar ta sake afkawa cikin dakarun ta ci-gaba da saran su. Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne SADAUKi Sharkar ya samu nasarar make Nabihat ta faɗi ƙasa, magashiyan nunfashin ta na fita daƙyar, kawai sai ya sanya hannunshi ya damƙo wuyanta ya tattare dukkanin karfinshi da nufin karya wuyan Nabihat. Kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka ga Nabihat ta dunƙule hannayen ta biyu ta girɓawa sharkar naushi a fuska. Saboda matuƙar ƙarfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau uku, sannan ya kife a ƙasa, yana mai tsandara ihu sakamakon zafi da zugin da ya ji, haƙorinshi guda ɗaya ya yi fitar burgu daga cikin bakinshi jini ya yi tsartuwa. Amma saboda karfin zuciya gami da juriya irin ta manyan GWARAZAN JIYA sai ya miƙe tsaye zumbur yana mai goge jinin dake bakinshi yana mai gyara tsayuwa. A dai-dai lokacin da Nabihat ta miƙe tsaye zumbur, aka sake sabon kallon kallo, sannan suka sake afkawa junan da yaƙi, ana fara wannan arbu ne Nabihat ta shammaci Sharkar ta gabza mashi naushi a kirjinshi da kafafuwanta biyu, saboda ƙarfin naushin sai da ya yi sama ta tamkar an janye shi da ƙungiya sannan ya faɗa izuwa tekun Baharul-sawara. Koda samun wannan gagarumar nasara sai jaruma Nabihat ta ruga izuwa inda 'yan uwanta suke ta kai masu ɗauki su ka cigaba da ragargazar dakarun.Cikin kankanin lokaci suka hallaka su baki ɗaya. Kawa sai Nabihat ta umarci 'yan mata uku da su tuƙa jirgin ruwan a cigaba da tafiya Cikin matuƙar kaɗuwa ɗaya daga cikin fursunonin ta dubi Nabihat cikin tashin hankali ta ce '' ya ke Nabihat ta ya ya zamu cigaba da tafiya bayan cewa yarinya Lazimat na cikin wannan teku, kuma bamu da tabbacin a wane hali take ciki tana raye ne ko ta mutu. Koda jin wannan batu daga bakin Sharimat sai idanun Nabihat su ka ciko da ƙwalla, ta dube ta ta ce "ya ke Shamirat tabbas a yanzu ba ni da tabbacin yarinya Lazimat na raye, shin yanzu zamu tsaya neman ta ne? Ko kuwa zamu cigaba da tuƙa wannan jirgin ruwa domin ceto daruruwan jama'armu da suka haɗar da yara ƙanana da mata gami da tsofaffi,'? Ina so ki kwantar da hankalinki idan har yarinya Lazimat na raye zamu sake saduwa da ita". Koda jin wannan batu daga bakin Nabihat sai Shamirat ta gyaɗa kai cikin alamun matuƙar damuwa ta matsa kusa da 'yan uwanta, suka shiga tuƙa jirgin ruwan domin koma izuwa birnin su. A dai-dai wannan lokaci ne shugaba Yasiran ya taso daga ƙarƙashin tekun fuskarshi a murtuke babu annuri, tamkar an watsa mashi garwashin wuta akan ta, gundulmin hannunshi da Lazimat ta sare mashi na zubar da jini. Sa'adda jaruma Nabihat ta cigaba da jagorantar sauran 'yan uwanta fursunoni, a bisa jirgin ruwan dake tafiya akan tekun Baharul-sawara, domin gudun TSIRA DAGA HAKA. Sai suka shafe tsawon sa'a biyu suna tafiya babu sassauci. Lokacin da ya zamana an shafe sa'a ɗaya ana tafiyar sai jaruma Nabihat ta yi umarni aka shiga ɗakin sirri dake ƙarƙashin jirgin ruwan, aka ɗauka gurasar gami taceccen ruwan inabi, aka shiga rarrabawa jama'arsu domin kowa ya kimtsa cikinshi. Ana cikin wannan hali ne kwatsam! Bazato babu tsammani sai aka hango waɗansu tawagar jiragen ruwa kimanin guda ashirin, sun bayyana a saman tekun a kowa ce kusurwa, wato gabas, yamma, kudu da Arewa, Cikin matukar kaɗuwa gami da tashin hankali Nabihat ta yi umarni aka tsayar da tafiya, kawai sai 'yan matan suka ruga izuwa wani ɓangare a jirgin suka ɗebo makaman yaƙi, sannan suka ruga izuwa tsakiyar birnin suna masu gyara tsayuwar su zukatansu cike da matuƙar firgici. Ya yin da ya zamana cewa jiragen ruwan sun matso daf juna, sai Nabihat ta sake ɗimauce wa, su dai jiragen ruwan suna ɗauke ne da waɗansu irin zaratan dakaru masu ƙirar samudawan farko, suna sanye cikin sulken yaƙi na baƙin ƙarfe, ɗauke da miyagun MAKAMAN ƘARE DANGI. Kaico! Haƙiƙa waɗannan dakaru sun kasance masu ban tsoro, domin babu halitta da za ta yi arba da su face ta yi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin su Nabihat da tawagar dakarun. Tsawon daƙiƙa arba'in ana cikin wannan hali, a lokacin ne su Nabihat suka hango shugaba Yasiran a ɗaya daga cikin jiragen ruwan, shirye cikin gagarumar shigar yaƙi hannunshi ɗaya ɗauke da wata sharbebiyar takobi, ɗayan kuwa da ya yi dungulmi ya naɗe shi da wani farin ƙyalle, fuskarshi a murtuke babu annuri har gyatsune take saboda matuƙar fushi. Al'marin da ya yi matuƙar ba su mamaki kenan, suka tambayi kansu a cikin ransu suna masu cewa, ya aka yi Yasiran ya rayu shin ina yarinya Lazimat take tana raye ne ko kuwa ta mutu? Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kawunansu kenan. Kawai sai Nabihat su ka hango dakaru masu tarin yawa suna dako tsalle daga inda suke suna sauka akan jirgin da suke suna shawagi a sama tamkar tsuntsaye, suna ihu da kururuwa mai firgitarwa. Koda ganin hakan sai Nabihat ta ɗaga takobinta sama cikin ƙarfin hali gami da ƙarfafawa sauran 'yan matan gwiwa ta falfala da gudu izuwa kan dakarun. Ya yin da 'yan matan suka ga haka sai suka yi koyi da ita, suna masu mara mata baya. Tabbas shi ƙarfi a zuciya yake ba wai a girman jiki ba, domin idan ba haka ba taya ya mutum ashirin za su za su tunkari ɗaruruwa. Amma dai masu iya magana na cewa shi bala'i kafin ya zo ne ake neman mafita, amma idan yazo babu abin da ya rage face a karɓe shi hannu biyu. In da a ce mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan dubban dakarun suka yunƙura kan su jaruma Nabihat, sai ya yi zaton DANDAZON zakuna ne suka farwa barewa guda ɗaya jal, saboda matuƙar kwarjinin su. Ana haɗuwa aka yamutse da azababban yaƙi mai matuƙar firgici da ban tsoro. Ƙarar haɗuwar ƙarafa gami da ihu da kururuwar mazaje ta cika dodon kunne. Ana fara wannan artabu ne su jaruma Nabihat suka fara gane cewa sun haɗu da gamon su. Domin kuwa kods ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza, kuma ruwa ba sa'an kwando ba ne. Tirƙashi muje zuwa domin jin wannan ƙayataccen labari mai taken FATAUCIN BAYI! FATAUCIN BAYI!! Ga shi nan tafe Daga mai ɗebe maku kewa a kullum da koyaushe. MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi 08137237071