KOGON ANNOBA MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Littafinyaki.com.ng 08137237071 ©️ Haƙƙin Mallaka Mansur Usman Sufi Shekarar bugu:- 2024 Website:- littafinyaki.com.ng GARGAƊI Ban yarda wani ya sarrafa min littafi ba ta hanyar yaɗa shi a soshiyal midiya, karantawa a rediyo ko manhajar YouTube, website da sauran su ba tare da izina na ba, yin hakan zai kai mu zuwa ga hukuma a kiyaye. Ko kuwa zuwa ga babban mai sakamako Allah (SWT). Sako daga MANSUR USMAN SUFI GODIYA Ta tabbata ga Allah SWT bisa iko da ya ba ni na rubuta wannan littafi mai taken KOGON ANNOBA. Tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama da iyalanshi tsarkaka. SADAUKARWA Na sadaukar da wannan littafi ga dukkanin masoyan Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama a ko ina suke a faɗin duniya. Bugawa da yaɗawa SUFI PUBLISHING COMPANY R/lemo Kano state Nigeria. 08137237071 BABI NA ƊAYA Ƙananan yara ne mace da namiji kyawawa na gaban kwatance ke ta faman tsala matsanancin gudu babu sassauci, saboda matuƙar gudun da suke yi idan ka gani sai ka yi tsammanin za su fita daga duniyar ne. kai duk sa'adda suka waiga bayan su idan suka yi arba da abin da yake biye da su, sai kaga sun ƙara ZAGE DAMTSE ƙarfin gudun su ya ƙaru ainun fiye da ɗazu. Babu abin da zai bawa mutum mamaki face idan ya ga yadda suke gudun sai ya rantse ya ce ba su kasance bil'adama ba, kallo daya zakayi masu ka fahimci cewa sun kasance 'ya'yan wani hamshaƙin attajiri ko BASARAKE, saboda tufafin da suke sanye da su masu tsadar gaske ne. Haka dai suka cigaba da gudu domin tsira da rayukansu daga sharrin abubuwan da suka biyo su babu alamun tsoro ko firgici a tattare da fusakunsu, har suka iso wani ƙasaitaccen birni ai kuwa sai suka kunna kai ta cikin wata yar mitsitsiyar taga ba tare sa sun jira masu gadin ƙofa sun buɗe masu ba. Lokacin da abubuwan suka biyo yaran suka sauka a birnin nanfa jama'a suka dinga guje-gujen gami da iface-iface kafin ka ce me gari ya kaure da ihun jama'a mutane suka dinga rugawa izuwa gidajensu suna ɗebo makaman yaƙ. A wannan lokacin sarkin dake mulki a birnin yana zaune akan karagarshi ta mulki fadar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatu nau'i daban-dabam dangin zinare da azurfa har da ma abin da ido bai taɓa gani ba. Duk inda ka duba a fadar kawunan jama'ane rututu tamkar dandazon kiyasai babu masaka tsinke. A gefe guda kuwa sarki SIYAMUL-AMSAR na zaune akan ƙasaitaccen karagar mulki yana sanye da doguwar alƙyabba akan shi yana ɗauke da KAMBUN MULKI da aka sana'anta shi da zallar zinare da lu'u lu'u. Sarki SIYAMUL-AMSAR ya kasance dogon mutum mai ƙirar samudawan farko yana da kyakkyawar fuska da ɗan siririn gemu mai tsawon kamu biyu wanda shine ya ƙara tona asirin kyawun surarshi. kallo ɗaya za ka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON JARUMI. 'Yan majalisar sarki na zaune a bisa shimfiɗu na alfarma waɗanda idan mutum ya taka su saboda matuƙar taushin su sai ya ji tamkar ƙafafuwanshi za su nutse a ciki a wannan lokaci babu abinda kunne ke ji face guje-gujen jama'a da kuma shirun da ya wanzu a fadar tamkar mutuwa ta gifta, daga can ga dakaru masu tsaron ƙofa sun shigo fadar hankulansu a tashe. Koda ganin halin da suke ciki sai sarki ya dube su ya ce ''shin me ke faruwa ne ? Cikin rawar murya ɗaya daga cikin dakarun ya buɗi baki daƙyar ya ce ''ya shugabana muna cikin gudanar da ayyukanmu na tsaron ƙofa sai ga su yarima NAZMAR sun janyo mana wata gagarumar masifa, ban tsammanin cewa akwai wata halitta da ta tsira da rayuwarta, mu kanmu tsananin razana ya hana mu mu tantance wace irin masiba ce''. Kafin badakaren ya gama rufe bakinshi sarki SIYAMUL-AMSAR ya zare sharɓeɓiyar takobi a gadon bayanshi ya sare mashi wuya, nan take kanshi ya yi fitar burgu daga gangar jiki jini ya yi tsartuwa ya kwaranya a ƙas. kawai sai sarki SIYAMUL-AMSAR ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu wanda ya firgita gaba ɗaya jama'ar dake fadar kuma ya amsa kuwwa izuwa cikin birnin, sai daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko mashi da saƙon mutuwa. Nan take ya yi umarni aka busa ƙahon yaƙi kafin wani lokaci MAYAƘA sun yi cincirindo a Ƙofar gidan sarauta. Shi kuwa sarki sai ya shiga izuwa gidan sarauta jim kaɗan sai gashi ya fito cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini da ban tsoro. Jim kaɗan da faruwar hakan sai ga boka ZULWAL ya bayyana cikin alƙalumman sihiri, sanye yake cikin shigar yaƙi irin ta manyan hatsabibai. Kawai sai ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa sarki ya dube shi cikin matuƙar fushi yana mai dakamashi tsawa ya ce ''shin kana ina ne masuba ta tunkaro birnina? Ina so ka gaggauta nemo mana mafita domin tserar da rayukan al'ummata". Cikin ladabi boka zirwal ya ce ''ya shugabana ka yi sani cewa mafita ɗaya ce, shine mu fita mu tari wannan masuba tun kafin ta iso gare mu ina mai tabbatar maka da cewa zamu samu nasara''. Gama faɗin hakan ke da wuya sarki ya kaɗa linzamin dokinshi ya shige gaba boka Zirwal ya mara masai baya, take miliyoyin dakarun yaƙi suka yi koyi dashi Babi na biyu Sarki Siyamul-amsar ibn Fannas ya kasance mashahurin BASARAKE kuma GAWURTACCEN attajiri da babu tamkar a kaf nahiyar Baitul-Wahid. Yana da matar aure guda ɗaya hal! Wata kyakkyawar gaske mai suna NUZRA BINTU SHA'ARAN. A rayuwar Siyamul-amsar babu wani rayuwar jin daɗi da ya nema ya rasa face rashin haihuwa, duk da irin tarin dukiya da ƙarfin mulki da yake da shi ya tashi a banza domin ba shi da wanda zai gaji karagarshi. Aƙalla ya ziyarci manyan bokaye sama da ɗari akan wannan matsala ta rashin haihuwa amma abu ya ci tira, a wata shekara ne ya ziyarci wani boka a can birnin ƘUFA mai suna Zirwal. Lokacin da sarki Siyamul-amsar ya bijirowa da boka zirwal da buƙatar shi ta samun haihuwa, sai kawai boka Zirwal ya bushe da dariyar mugunta har sai da ya faɗo ƙasa tim! Daga kan kujerar da yake zaune kuma idanunshi suka ciko da ƙwalla. Al'amarin da ya ɗaurewa sarki Siyamul-amsar kai kenan kuma ya fusata shi ya dakawa masjid tsawa ya ce da shi ''shin ina dalilin wannan dariya taka? Cikin nutsuwa da biyayya boka Zirwal ya koma kan kujerarshi ya zauna ya yi gyaran murya, sannan ya fara magana a karo na farko da shaƙaƙƙiyar muryarshi mai kama da kukan jaki yana mai cewa asi ya huci zuciyarka ya sarkin sarakunan masu isa kayi sani cewa ba komaine ya sanya ni wannan dariya ba face bisa ganin yadda ka wahalar da kanka wajen faɗin bukatar da take tafe da kai, bayan cewa ka zo gaban uban bokaye, ya sarki mai cikakken iko ka yi sani cewa tabbas a halin yanzu matarka na ɗauke da juna biyu nan bada daɗewa ba zata haihu, kuma ina mai farin cikin sanar da kai cewa 'ya'ya biyu zata haifa mace da namiji sai dai inda gizo ke saƙar shine 'ya'yan da za a haifa maka za su kasance hatsabibai marasa jin magana waɗanda sune zasu zamo ajalinka. Yayin da boka Zirwal yazo nan a jawabin shi sai hankalin sarki siyamul-amsar ya dugunzuma fiye da kowane lokaci ya dubi boka Zirwall ya ce ''ya sarkin bokaye shin babu wata hanya da za abi 'ya'yan da zan haifa ya zamto ba su kasance hatsabibaiba? Zirwal ya nisa ya ce sannan ya ce ''ai bakin alƙalami ya bushe lallai wannan al'amari haka zai kasance''. koda jn wannan batun sai sarki Siyamul-amsar ya sunkuiyar da kanshi ƙasa yana mai zurfafa cikin kogon tunani. Abu na farko daya faɗo mashi a rai shine yanzu babu wata mafita face kayi murna da waɗannan yara da za a haifa maka domin sune zasu gaje ka bayan ranka tabbas ba ka da nadama koda sun zamo ajalinka ai da a ce wani ne zai gaji karagarka gwara a ce jininka ne. Can kuma wata zuciyar ta ce ka cigaba da bincike ya za ayi a ce 'ya'yan mutum sune zamto ajalinshi. Lokacin da sarki yazo nan a tunaninshi sai ya ɗago da kanshi ya dubi boka zirwal ya ce ''tabbas na amince 'ya'yana su zamo ajalina matuƙar za su gajeni bayan raina''. Gama faɗin hakan keda wuya sai sarki ya ɗebi dukiya mai tarin yawa ya bawa boka Zirwal, saboda tsananin murna sai da Zirwal ya dinga birgima a ƙasa tamkar wanda ya samu ciwon hauka, domin tunda yake a rayuwarshi bai taɓa samun dukiya mai yawan ta ba kuma dama yana da wani babban buri akan adukiyar yana son ya haɗa wansanadarin tsafi da ita. Tun daga wannan rana sarki Siyamul-amsar ya kasance cikin tsananin farin ciki kuma ya zamana cewa dare da rana baya rabuwa da uwargidanshu Nuzra yana bata gudunmowa wajen rainon juna biyunta har ta sauka lafiya ta haifi 'ya'ya biyu kyawawa mace da namiji aka raɗa msu suna NAZMAR da HULAISA. Murna a wajen sarki kuwa ba a cewa komai domin a wannan rana ya dinga rabon dukiya da 'yanta bayi da barori sannan sai da aka yi kwanaki ashirin ana shirya walimar farin ciki, manyan sarakunan duniya sun sauka a birnin domin taya shi murna. Hakan ya sanya a lokaci ko ƙasa mutum ya kasa sai an siya saboda kawai ana farin ciki kuma ya zamana sarki ba shi da wani abokin shawara face boka Zirlwal. Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba, sai gashi kwance tashi yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa sun shekara uku a duniya kasancewar yanayin jikinsu irin na mahaifinsu ne sai ya zamana idan ka gan su lokacin da suka shekara uku sai ka ce sun shekara biyar da haihuwa. Tun suna waɗannan shekaru suke nuna hatsabibancinsu domin basa iya zama waje guda ko an kulle su a daki sai sunyi dabaru sun fita, a wasu lokutan idan suka rasa hanyar da za su bi su fice daga gidan sarautar sai su haɗa rigima tsakanin dakarun dake tsaron su sannan su sulale su fice daga gidan sarautar, Domin akwai wani lokaci da suka je suka tsokano wata qatuwar damisa ta biyosu har cikin gari ta dinga hallaka mutane sai dakyar da sidin goshi aka samu akayi maganin damisar kai in takaice maka kafin Nazmar da Hulaisa su shekara shida sun janyowa birnin masifu guda talatin kuma duk lokacin da hakan ya faru sai an samu salwantar rayuka da dukiyoyin al'umma wani abu da zai baka mamaki shine tunda aka haifi su yarima Nazmar arzikin kasar ya kara bunkasa amma sai dai mutane basu da kwanciyar hankali domin har kullum gani sukeyi su Yarima nazmar zasu janyo masifar da zata zamo ajalinsu ko asarar dukyarsu duk irin dakarun da sarki Siyamul ansar zai sanya domin tsaron su Yarima amma cikin hikima da basira sai Yarima nazmar sun samu nasarar gudowa shi kasansa sarki duk lokacin da ya tuna cewa su Yarima nazmar ne ajalinsa sai takaici ya turnuke shi har ya zubar da hawaye duk cikin mutanen birnin walau yan majalisa babu wanda ya iya kawowa sarki korafi su Yarima nazmar saboda ganin irin soyayyar da akeyi musu kuma babu wanda yake kaunar su domin ta sanadin su attajirai sun zamo talakawa wadansu sun zamo marayu. Duk lokacin da sarki ya samu labarin su Yarima nazman sun janyo wata masifa sai ya kara sanya matakan tsaro aturakarsa domin hanasu fita daga gidan sarautar. Lokacin da sarki Siyamul ansar da dakarun yakin suka fita daga kofar gari sai sukayi arba da wadansu irin jibga jibgan tsuntsaye sude wadannan tsuntsaye sun kasance suna da jiki irin na zaki amma kawunansu sun kasance na rakumin dawa suna dauke da kafafuwa guda shida akalla girman kowannensu yakai na qatuwar giwa fuka fukansu manya manya ne masu dauke da wadansu irin gashi mai kama da takobi awajen kaifi da tsini hakika ba karamin jarumi bane zaiyi arba wadannan tsutsaye face sai ya razana ainun yayi nadamar wamzuwarsa agaban kasa koda tsuntsayen su kimanin dubu sukayi arba da su sarki Siyamul ansar sai suka saki fukafukansu suka sauka aturba lokacin da dakarun sarki Siyamul ansar sukayi arba da wadannan tsuntsaye sai suka razana ainun da yawa daga cikinsu basu san sa adda suka saki fitsari a wandonsu ba kuma suka yunkura zasu koma da baya sai sarki Siyamul ansar ya daka musu tsawa suka tsaya cak jikinsu na tsuma gaminda karkarwa shi kansa sarki Siyamul ansar sai da yaji tsoro da razana sun darsu a zuciyarsa domin a iya tsawon rayuwarsa bai taba gani ko jin labarin tsuntsaye masu tsananin girma da ban tsoro kamarsu ba nanfa dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayansu suna nausawa cikin daji saboda tsananin dimauta su Yarima Nazmar kuwa lokacin da wadannan tsuntsaye suka biyo suka shiga birnin suka wuce kai tsaye izuwa turakarsu suka fara sharar bacci abinsu kai kace babu wani abu da ya faru agaresu al amarin da ya bawo kuyangi da barorin gidan sarautar mamaki kenan har wadansu suka raya zuciyarsu cewa anya kuwa su Yarima nazmar mutanene ba aljanu ba? ita kuwa mahaifiyarsu sai hankalinta ya dugunzuma ta kasa tsaye ta kasa zaune kawai sai ta dinga kai komo cikin turakar hawaye na zuba daga idanunta. Lokacin da aka fara kallon kallo tsakanin su sarki Siyamul ansar da wadannan jibga jibgan tsuntsaye sai ya zamana babu wanda yayi yunkurin afkawo abokin gabarsa awannan lokaci gaba daya mayakan dake wajen hankalinsu atashe yake shi kansa sarki Siyamul ansar hankalinsa atashe yake fiye da kowa yayi karfin hali ne na irin masu manyan sarakuna koda sarki Siyamul ansar yaga tsuntsayen sunki yunkurin afka musu sai ya umarci wasu dakaru dari biyar da su dana bakarsu su harbawa tsuntsayen take dakarun sukabi umarnin suka dana bakarsu suka harbawo tsuntsayen yayin da kibiyoyi guda dari biyar suka sauka akan tsuntsayen sai akaga tsuntsayen sun tsaya cak ko gezau basuyi ba hasalima idan kibiyoyin suka sauka akansu sai dai tartsatsin wuta ya tashi kibiyoyin su zube kasa saida dakarun suka karar da kibiyoyinsu sannan tsuntsayen sukayi wani irin kuka mai firgita manyan jaruman duniya suka afka musu da yaki take tsuntsayen suka yanyame miliyoyin dakarun kamar yanda dandazon kudaje ke yanyame kwallon mangwaro duk inda ka duba sune birjik babu abinda suke face hurowa dakarun wata dunkulalliyar wuta abakinsu ko su hallakasu da wadannan tsinin gashin dake fukafukansu masu tsananin kaifi da tsini. Cikin kankanin lokaci waje ya cikada ihun mazaje gamida karar karafkiya karafe gamida haniniyar dawakai mutuwar sadaukai ta cigaba da yawaita awajen nanfa aka kacame da azababben yayi tsakanin kowane bangare har yazama an shafe tsawon rabin sa'a su sarki Siyamul ansar basu samu nasarar kashe ko daya daga cikin tsuntsayen ba sai dai kaga tsuntsu ya wangame bakinsa ya hurawo badakare wuta sai dai kaga nan take badakare da dokinsa sun kama da wuta sassan jikin dakarun ya dinga shawagi a sararin samaniya kura ta turnuke kamar hadari ya gangamo akece da ruwan sama mala'ikan mutuwa ya wanzu yana shawagi asama dawakai suka dinga haniniya suna zubar da mahayansu kai duk inda daya daga cikin tsuntsayen ya sanya gaba sai dai kaga dakaru suna zubewa kasa matattu kamar ana sassabe agonar auduga sarki Siyamul ansar ya wanzu yana kare kansa yana saran tsuntsayen cikin bakin zafin nama juriya da jarumtaka. Yayin da yaga yanda dakarunsa ke hallaka sai takaici ya turnuke shi ya takarkare ya kwarara uban ehu ya dire daga kan dokinsa ya tari wani tsuntsu guda daya suka kacame da yaki idan tsuntsun ya wangame bakinsa ya huro masa wuta sai kaga sarki Siyamul ansar ya kaucewa harin cikin bakin zafin nama idan wutar ta zuba a kasa sai kaga wajen ya haddasa wani wawakeken rami mai zurfin gaske Lokacin da tsuntsun yaga ya kasa samun nasara akan sarki Siyamuk ansar ta hanyar kone shi da wutar bakinsa sai kawai ya dinga kai masa yakushi da zaqo zaqon paratan hannunsa da nufin yayi fata fata da sassan jikinsa. Faruwar hakan keda wuya sai sarki Siyamul ansar ya fara gano lagon tsuntsun domin yanzu takobinsa ya fara tasiri akan tsuntsun dan ayanzu takobinsa na samun nasarar yankar jikin tsuntsun duk inda takobin ya sara ajikin tsuntsun sai dai kaga ya dare jinina kwaranya. Abangaren boka zulwal kuwa yana iyakar kokarinsa wajen yakar tsuntsayen amma babu abinda ya daure masa kai sama da yadda karfin sihiri baya tasiri ajikin tsuntsayen face tsagwaron karfin damtse duk inda mai kallo ya duba ba abinda zai gani face gawarwakin dakaru fululu kwance cikin jini wasu a babbake suna kauri jini kuwa ya cakude da kasa babu kyan gani ana cikin wannan yaki ne wannan tsuntsu ya samu nasarar yankar sarki Siyamul ansar da faratansa a cinya take inda ya yanke shi ya haddasa wani qaton rauni jini ya kwaranya saboda zafi da zugin da sarki Siyamul ansar yaji bai san sa'adda ya sandara uban ihu ba ya saki takobin dake hannunsa cikin tsananin zafin nama ya daka tsalle daga inda yake tamkar an harbashi daga cikin baka ya dira akan wuyan tsuntsun ya sanya hannayensa biyu ya kama kan tsuntsun ya murde iyakar karfinsa nan take wuyan ya karye ji kake rukuss sarki Siyamul ansar ya daka tsalle karo na biyu ya sauka daga kan tsuntsun take tsuntsun ya fadi kasa yiff tamkar an jefar da giwa ko shurawa baiyi ba. Yayin da tsuntsayen sukaga abinda ya faru ga dan uwansu sai gaba dayansu suka tsaya cak da yakin kawai sai suka bude fuka fukansu suka luluka sararin samaniya suna masu daukar gawar dan uwansu da sarki Siyamul ansar ya kashe koda bacewar tsuntsayen sai akaga sarki Siyamul ansar ya sulale kasa sumamme cikin tsananin kaduwa boka Zulwal ya ruga inda yake ya umarci dakaru su dauko shi aka shigar dashi cikin gidan sarauta bisa wani kasaitaccen keken doki lokacin da masu magani suka dukufa akan sarki Siyamul ansar domin ceto rayuwarsa sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ba tareda anga yayi wani kwakkwaran motsi ba al amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin masu maganin da boka Zulwal kenan kuma hankalinsu yayi mummunan tashi babu abinda yafi dugunzuma hankalinsu sai bisa ganin yanda raunin ciwon sarki Siyamul ansar din ke zubar da jini da ruwa mai doyin gaske kamar kurji yana zubar da mugunya duk kuwa da kasancewar masu maganin sunyi iyakar kokarinsu wajen bawa ciwon kariya da wadansu magunguna. A bangaren Nuzura kuwa lokacin da su yarima Nazmar suka farka daga baccinsu sukayi arba da mahaifiyarsu tana kaikomo acikin turakar hawaye na zuba daga idanunta sai suka rugo izuwa gareta suka fada kirjinta cikin matukar damuwa suka hada baki sukace ya ummanmu shin ina dalilin zubar da wannan hawayen naki koda jin wannan tambaya sai Nuzura ta kara kankame su ajikinta ta fashe da kuka a karo na biyu koda ganin hakan su Yarima Nazmar suka fashe da kukan sai da suka dauki tsawon lokaci suna cikin wannan hali sannan Nuzura ta janya jikinta daga nasu ta dube su cikin tsananin damuwa tace yaku 'ya'ya na kuyi sani cewa ba komai ne ya sanya ni zubar da hawaye ba sai bisa takaicin mugun halin da kuka jefa jama'ar wannan kasa da mahaifinku aciki kunsan cewa ba wannan ne karo na farko ba da hakan ya taba faruwa koda jin haka sai hawayen bakin ciki suka zubowa Nazmar da Hulaisa dukkaninsu suka budi baki sukace ki gafarce mu ya ummanmu tabbas mun aikata babban kuskure kuma munyi nadamar abinda muka aikata kafin su gama rufe bakinsu Nuzura ta tari numfashinsu tace wai shin ma in tambaye ku wane laifi kuka aikatawo wadannan tsuntsaye ina son ku sanar dani idan kuka boye mini gaskiya zan gudu in barku in tafi wata nahiya in cigaba da rayuwa har ajali ya riske ni. Yayin da su Yarima Nazmar sukaji abinda mahaifiyarsu tace sai idanunsu suka zazzaro suka shiga damuwa fiye da ko yaushe alamun rashin gaskiya karara ya baiyana a fuskarsu har Nazmar ya bude baki da nufin yace wani abu sai aka jiwo ihu da kururuwar sarki ta cika gaba daya gidan sarautar al amarin da ya sanya gidan sarautar ya hargtse da guje guje da iface ifacen jama'a Nuzura da su Yarima suka fice daga cikin turakar da sauri suka rugo izuwa turakar sarki cikin tsananin tashin hankali koda isowarsu izuwa turakar sai sukayi arba da sarki Siyamul ansar akwance cikin mawuyacin hali raunin cinyarsa na zubar da wannan ruwa mai doyin gaske koda shigowar su Yarima Nazmar sai kawai akaga sarki Siyamul ansar ya mike tsaye zumbur ya ruga inda suke ya rungumesu a kirjinsa al amarin da yayi matukar bawa masu magani mamaki kenan bisa ganin irin mugun raunin dake cinyarsa amma har ya iya taka kafarsa ba tare da an bawo masu maganin umarni ba suka fice daga turakar boka Zulwal yabi bayansu ya zamana saura su Yarima Nazmar da sarki Siyamul ansar kadai koda ficewarsu sai sarki Siyamul ansar ya kama hannun su Yarima Nazmar ya jasu har inda gadon sarautarsa yake ya zaunar dasu suka fuskanci juna sannan ya juya ya dubi uwargidansa Nuzura yana mai kura mata idanu yace ya abar kaunata bazakiyi farin ciki ba da 'ya'yanmu suka kasance cikin farin ciki da koshin lafiya. Koda jin wannan tambaya sai Nuzura taje ta zauna a bisa lumtsattsiyar kujera da take fuskantar su sarki Siyamul ansar ta dubesu cikin nutsuwa tace ya uban 'ya'yana kayi sani cewa ba komai ne ya sanya ni cikin halin rashin walwalaba sai bisa tsoro abinda su Yarima Nazmar suka janyo mana yanzu gashi sunyi sanadin yi maka mummunan rauni mutane da yawa sun rasa dukiyoyinsu da rayukansu ya zama wajibi ka tursasa su Yarima su sanar dakai laifin da suka aikatawa wadannan tsuntsaye sannan kuma a gano shin wanne irin tsuntsayene da matakin da ya kamata a dauka koda jin wadannan tambayoyi sai idanun sarki Siyamul ansar suka ciko da kwalla sannan ya budi baki cikin karfin hali yace tabbas maganarki gaskiyace ya uwargidana amma ki sani cewa matukar su Yarima na cikin koshin lafiya bana nadama don na rasa wata gaɓa ajikina har kullum tunanina shine wacce hanya zan bi domin ganin su yarima sun gajeni to amma idan su Yarima suka cigaba da janyo masifu a wannan birni hakan zai janyo rushewar birni gaba daya a doron kasa a kundin tarihin duniya Nuzura ce tayi wannan furuci ga sarki Siyamul ansar cikin tsananin damuwa shiru ne ya mamaye turakar na tsawon lokaci shigowar boka Zulwal itace ta kade shirun da ya wanzu a tsakaninsu boka Zulwal ya zube kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya dago da kansa cikin kakkausar murya yace ya shugabana kayi sani cewa bayan na fice daga wannan turaka na gudanar da bincike bisa halarar tsafi nan take na gano wani mummunar al amari cikin firgici sarki Siyamul ansar yace me ya faru ya dodon bokaye boka Zulwal ya hada fuska yace ya shugabana kayi sani cewa ba komai ne al amarin da nagani ba sai gameda wadannan tsuntsaye sude wadannan tsuntsaye sun kasance mallakin wani hatsabibin boka da ake yiwa lakabi da suna JABARUL SIHIR bokayen duniya sunyi ittifakin a wannan karshen qarni babu wata halitta mai tsananin zafin nama gamida karfin damtse tamkar wadannan tsuntsaye babban burin boka Jabarul sihir shine ya tsafance wani sihirtaccen kwai wanda daya daga cikin tsuntsayen ta haifa wanda da zarar kwan ya kyankyashe kansa zaiyiwa duniyar juyin mulki da wannan tsuntsaye bincike ya kara tabbatar mini da cewa maganin da zai warkar da su Yarima Nazmar yana cikin gidan Jabarul sihir wato ma'ul diya'u lallai ya zama wajibi a tura Yarima Nazmar su maidawa tsuntsayen abinda suka dauko musu domin ina mai tabbatar maka da cewa tsuntsayen zasu dawo wannan birni namu nan da wadansu kwanaki kasani cewa babu wata halitta da zata tsira daga cikin jama'arka matukar suka dawo. Koda jin wannan jawabi daga bakin Zulwal sai hankalin sarki Siyamul ansar ya dugunzuma ainun ya tashi ya dubi boka Zulwal yace shin kanada tabbacin cewa zamu iya zuwa gidan boka Jabarul sihir har mu debo ruwan ma'ul diya'u? wadanda zai warkarda su Yarima su daina rashin jin da sukeyi? boka Zulwal yace akwai wani jarumi mai suna HUZAIFAL BN MASNUR ma abocin addinin musulunci lallai kashe gari ya kamata mu gudanar da tafiya domin mu ziyarce shi domin ya amince da bukatarmu da wannan nakeyi maka bankwana na barka lafiya ya shugabana koda boka Zulwal ya gama wannan jawabi sai ya shafi kasa da hannunsa na hagu ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen take sarki Siyamul ansar da Nuzura suka cika da farin ciki mara misaltuwa. **** BABI NA UKU Kamar yanda boka Zulwal ya fada haka al amarin ya kasance wato tun da dukun dukun safiya sarki Siyamul ansar da su yarima Yarima Nazmar sukayi shiri bayan sun rabu da mahaifiyarsu suna masu zubar da hawayen rabuwa da juna suka dauki hanyar tafiya tare da dakaru masu yi musu rakiya mutum dubu biyu tafiyar sa'a uku sukayi suka iso wani daji mai tattareda kayan ni'ima nau'i nau'i daban daban koramai na gudana acikinsa atsakiyar dajin akwai wani dan madaidaicin gida shi dai wannan gida da zallan duwatsun wuta masu kwarin gaske da isowarsu bakin kofar gidan sai sarki Siyamul ansar ya sauka daga kan dokinsa yaje ya kwankwasa kofar gidan wanda ta kasance mai tsananin tsawo da kaurin gaske saida ya kwankwasa sau uku ba tare da yaji motsin alamun za a bude taba koda ganin haka sai su yarima da boka Zulwal suka sauko daga kan dawakansu suka tako har izuwa kofar gidan suna masu yin cirko cirko domin suga an bude kofar tsawon dakika dari biyu shiru ba aji sautin bude kofar ba al amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin sarki Siyamul ansar ya dubi boka Zulwal yace ya sarkin bokaye shin yanzu me nene abinyi? har boka Zulwal ya budi baki da nufin yace wani abu sai kawai aka hango wani kyakkyawan saurayi mai cikar kamala da annurin fuska ya tunkaro kofar gidan kallo daya zakayiwa saurayin ka fahimci ya kasance gwarzon mayaki mai karfi na Allah ya isa saurayin yana sanye da kayan fata riga da wando takalmin dake kafarsa anyi shine da patar damisa akafadarsa yana dauke da wata qatuwar zakanya. Koda isowarsa inda su sarki Siyamul ansar ke tsaye sai ya bisu da kallo cike da mamaki ba tare da yace da dayansu uffan ba yasa hannu daya ya tura gofar gidan ta bude ya kunna kai izuwa ciki yayin da sarki Siyamul ansar da tawagarsa sukayi arba da qatuwar zakanyar dake dauke akafadar saurayin kuma sukaga yadda ya bude kofar gidan da hannu daya wanda sai karti majiya karfi mutum ashirin sun taru sannan zasu iya bude kofar sai suka cika da tsananin mamaki domin basu taba gani ko jin jarumin da yayi wannan jarumtaka ba suna nan atsaye a kofar gidan sai sukaga saurayin ya fito daga cikin gidan ya tako da kafafunsa har izuwa inda suke ya dubesu cikin nutsuwa yace aminci ya tabbata agareku yaku wadannan baki shin menene ke tafe daku izuwa gareni koda jin wannan tambaya sai sarki Siyamul ansar yayi gyaran murya yace yakai jarumi Huzaifal bin masnur kayi sani cewa ba komai ne ke tafe dani izuwa gareka ba face wata muhimmiyar bukata bukatar kuwa itace inaso kayi mana jagora izuwa gidan boka Jabarul sihir domin nemowa wadannan 'ya'yan nawa maganin da zai warkadda su larurar dake damunsu ta rashin jin magana kuma har su mayar da abinda suka daukowa wadansu tsuntsaye wadansu tsutsaye inason ka fadi dukkan abinda kake bukata da ya danganci dukiya da mulki ni kuwa zan baka shi. Koda jin wannan jawabi daga bakin sarki Siyamul ansar sai.jarumi huzaifal yayi shiru yana mai sunkui da kansa kas ya shiga dogon nazari daga can sai ya dago kai ya dubi su Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa sannan ya dubi sarki Siyamul ansar yace yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa fiye da shekaru goma ubangijina ya baiyana mini cewa zakazo gareni da wata bukata na amince zanyi maka wannan aiki amma sai dai bisa sharadi guda daya jal wanda sai ka 08137237071amince dashi zanyi wannan gagarumar tafiya da jin haka sai sarki Siyamul ansar yace fadi sharadinka ya jarumin kwarai Huzaifal yayi gyaran murya a karo na biyu sannan yace sharadina shine bayan na samu nasarar debo ruwan ma'ul diya'u wanda shine zai warkar da su Yarima zaka yarda kayi imani da ubangiji kai da jama'arka baki daya idan ka daukar mini wannan alkawari shikenan ka biyani dukkanin aikina ba tare da ka bani dinare da ko wani yanki na masarautarka ba koda jin wannan batu sai sarki Siyamul ansar yayi shiru duk tattaunawar da akeyi tsakanin Jarumi Huzaifal da sarki Siyamul ansar boka Zulwal da su Yarima Nazmar suna sauraro koda Boka Zulwal yaji sharadin da jarumi Huzaifal ya gindayawo sarki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya tabbatar idan sarki Siyamul ansar yayi imani cewa zai karbi addinin musulunci duk shirinsa zai tarwatse na son mallakar birnin SARIRUL AIWAN da ya dade yana muradi yana cikin wannan hali ne wani tunani ya fado masa tunanin kuwa shine tunda sarki Siyamul ansar umarninsa yakebi bana jarumi Huzaifal ba lallai akwai tabbacin burinsa zai iya cika sa'adda yazo nan a tunaninsa sai ya cika da farin ciki a ransa sarki Siyamul ansar ya kada shirun da ya wanzu a tsakaninsu ta hanyar bude baki yace yakai jarumi Huzaifal hakika na amince da wannan sharadin naka matukar 'ya'yana zasu daidaita yanda nake bukata amma kuma wani hanzari ba guduba menene batu a gameda cewa su yarima sune zasu zamo ajalina da jin wannan tambaya sai murmushi ya subucewa jarumi Hullzaifal har fararan hakoransa suka baiyana farare qal ya dubi sarki Siyamul ansar cikin annurin fuska yace kada ka damu ya shugabana kasani cewa matukar kana tare dani kuma kayi imani da ubangijin musulunci mahaliccin sammai da kassai da abin dake cikinsu babu yanda za ayi 'ya'yanka su zamo ajalinka yanzu dai abinda za ayi shine ku biyoni izuwa cikin gidana kudan shakata kafin abinda ya kamata ayi tunda na lura cewa kun gaji ainun kuma a tsarin addininmu ubangiji ya umarce mu da mu girmama ma'abota mulki matukar basu hana mu bauta masa ba. Koda gama fadin haka sai jarumi Huzaifal ya juya ya shige gaba yana mai.kunna kai izuwa cikin gidan yana mai yafito su sarki Siyamul ansar na hannunsa ba tare da bata lokaci ba sarki Siyamul ansar Yarima Nazmar gimbiya Hulaisa boka Zulwal ne a karshe suka suka biyo bayan Huzaifal yayi musu jagora har izuwa cikin gidan da shigarsu izuwa cikin gidan sai suka cika da tsananin mamaki abinda ya basu mamaki shine yadda aka tsara gidan bisa tsari da kayatarwa gidan yana dauke da manyan dakuna guda uku masu girma da fadi suna da kofa ɗai ɗai da tagogi guda biyu a wani daki ne dake kallon yamma cikin gidan jarumi Huzaifal ya sauki su sarki Siyamul ansar aciki dakin cike yake da kayatattun kujeru kuma an shimfide kasansa da kilisai masu taushi wani daddadan kamshi ya mamaye turakar bayan jarumi Huzaifal ya sauke su acikin turakar sai ya fice daga cikin dakin jim kadan sai gashi ya dawo dauke da wani dogon paranti cike da nau'in kayan marmari da gasasshen naman zakanya gamida tatacciyar madarar shanu ya ajiye agaban su sarki Siyamul ansar a bisa wani dan madaidaicin tebur na katako a tsakiyar turakar yana ajiye abincin ya dubesu yace ai sai ku dan kimtsa cikinku ko yana gama fadin hakan ya fice daga dakin sarki Siyamul ansar da boka Zulwal suka bishi da kallo cike da matukar mamaki tayaya akayi har ya sarrafa naman zakanyar da ya farauto acikin kankanin lokaci haka kuma a inama ya samu wannan tatacciyaro madarar shanun al halin babu wata dabba dake rayuwa acikin dajin saida suka kammala kimtsa cikinsu suka huta sannan aka dunguma gaba daya suka fice daga gidan har jarumi Huzaifal suna ficewa ya mayarda kofar gidan ya rufe ta ruf kawai sai suka ga ya kusanci wani bangare adajin mai tattare da sarkakiya sai gashi ya janyo wani ingarman doki fari sol mai kyawun launi bayan ya hau dokin ne kowa ya hau abin hawarsa sai aka nausa cikin daji aka fara tafiya dakaru masu rakiya na biye dasu ana fara wannan tafiya ne jarumi Huzaifal yaki yarda ya jera da kowa face Yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa yana mai satar kallonsu fuskarsa cikeda annuri ana cikin hakan ne Yarima Nazmar ya dube shi yace yakai wannan jarumi a dazu da kuna magana da abbana naji kace akwai wani ubangiji da kake bautawa wanda ya halicci sama da kasa bayan abin bautarmu. Koda jin wannan tambaya sai Huzaifal yayi murmushi ya dubi Yarima Nazmar yace tabbas akwai ubangijin da ya halicci duniya da abinda yake cikinta kuma yake aiwatar da duk abinda yaso da ace zaku gwada neman taimakon ubangijin nawa da kun kasance jarumai kamar yanda har kullum kuke muradi sa'adda Yarima Nazmar yaji amsar wannan tambaya sai ya cika da mamaki yace wacce hanya zanbi in samu taimakon ubangijinka Huzaifal yace ai abune mai sauki kawai duk sa'adda wani abu ta taso maka kace kana neman taimakon ubangijin gaskiya ubangijin da yayi rana da wata yayi mutum da aljan dabba da tsuntsaye ruwa da iska ubangijin da babu wani ubangiji bayan shi a ranka ba tareda ka furta wani yaji ba lallai kai da yar uwarka inason ku boye mini wannan sirri dake tsakanin mu Yarima Nazmar da yar uwarsa sukace ai kuwa babu wanda zaisan da wannan sirri har sai gaskiyar abinda kake gaya mana ya baiyana daga wannan kuma Huzaifal ya shiga basu daddadan labarai masu sanyaya nishadi da annashuwa haka dai aka cigaba da wannan tafiya babu sassauci ana cikin tafiyar ne kwatsam ba zato babu tsammani sai aka hango jibga jibgan mutane masu tsawo da kauri qirar mutanen farko yawansu yakai dubu biyar suna da miyagun makamai masu baraza ga rayuwar mutane da aljan nan fa gaba daya dakarun sarki Siyamul ansar suka firgice sukaji tamkar su cika wandunansu da iska amma sai sukaga mutanen sunyi musu kawanya suna masu fitowa daga kusurwar dajin. Lokacin da mutanen suka kammala yi musu kawanya sai aka fara kallon kallo daga can sai akaga mutanen sun ɗane sun sake bayar da wata yar siririyar hanya a tsakiyarsu da mutum zai iya wucewa sai ga wani garjejen qato ma'abocin kwarjini da ban tsoro ya ratso hanyar ya fito izuwa gaban mutanen ya dubi su sarki Siyamul ansar a wulakance sannan ya bushe da mahaukaciyar dariya mai kama da haniniyar doki sannan daga bisani ya turbune fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya bude wawakeken bakinsa mai dauke da wadansu wargatsattsun hakora cikinsa marasa kyan gani cikin kakkausar murya yace yaku wadannan kwari maza ku sallama kanku izuwa gareni kafin in zare muku ruhinku daga gangar jikinku kafin garjejen qaton ya gama rufe bakinsa jarumi Huzaifal ya tari numfashinsa yana mai maida masa da cewa shin wanene kai kuma menene nufin ka agaremu garjejen qaton ya bushe da dariya a karo na biyu sannan ya kurawo Huzaifal idanu masu kama da garwashin wuta yace eh lallai da kyau yan samari shin har kanason kasan wanene ni to inaso kai da abokan tafiyarka kusani cewa nine sadauki RAUZAM shugaban yan ta'addar wannan nahiyar baki daya amma fa na yaba da jarumatarka matuka ganin yanda ka iya yin magana baki da baki dani amma lallai bazan bar dayanku a raye ba jarumi Huzaifal ya katse shi da cewa amma idan har ka cika namijin duniya muyi fada da juna kuma kada dayanmu ya rike makami a gwada yar qashi idan nayi nasara akanka na cinye ka da yaki idan kaine kayi nasara ka kashe ni sai ka kashe abokan tafiyata. Koda jin abinda Huzaifal yace sadauki Rauzam ya takarkare ya kwarara uban ehu da ya firgita gaba daya jama'ar dake wajen sannan yace da kyau jarumin kwarai haka akeson namiji da zuciya irin ta manya yana gama fadin hakan sai kawai ya daga annayensa sama ya falfala da gudu izuwa inda Huzaifal ke tsaye duk sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai dai kaji kasa na amsa kuwwa tamkar zata rufta Yana gama fadin haka kawai sai ya daga hannayensa sama ya falfala da gudu izuwa inda Huzaifal ke tsaye duk Sa'adda ya ajiye kafarsa daya sai sai dai kaji kasa ta amsa tamkar zata rufta koda ganin haka sai Huzaifal ya sauko daga kan dokinsa yana mai gyara tsayiwarsa gamida dunkule hannayensa biyu da isowar sadauki Rauzam yakai masa wani wawan naushi a fuska ya sunkuya hannun Rauzam ya naushi iska sannan duka kacame da azababben yaki mai matukar ban al'ajabi da ban mamaki ana fara wannan gumurzu nefa Huzaifal ya fahimci cewa Rauzum ya fishi tsagwaron karfin damtse domin idan ya naushe shi a fuska ko a jiki inda ya nausa din sai jini ya taru Huzaifal ya daka tsalle tamkar an harbo shi daga cikin baka ya daki kirjin Rauzum da kafafunsa biyu saboda karfin dukan sai da Rauzum yayi sama tamkar an janye shi daga qugiya yayi katantanwa a sama sau uku cikin gwaninta jarumi Huzaifal ya daka tsalle sama yayiwa Rauzum luguden naushi sau goma sannan suka sauko kasa a tare yana mai dora kafarsa a wuyan Rauzum alokacin da jini ke juba a hannayensa a hancinsa da bakinsa kuma numfashinsa ya fara sargewa Huzaifal ya dube shi yace yakai wannan dan ta'adda kayi sani cewa matukar zaka bayarda gaskiya ga ubangijina kuma ka daina wannan haramtacciyar sana'a taka zan kyaleka ka cigaba da rayuwa koda jin haka sai Rauzum yayi murmushin karfin hali ya furzadda gudan jini a bakinsa cikin kakkausar murya yace ai da inyi mubaya a agareka gwara ka kashe ni domin za a shaida cewa ni jarumi ne kafin Rauzum ya gama rufe bakinsa Huzaifal ya zare takobinsa ya datse masa wuya. Koda sauran yaransa sukaga abinda ya faru ga shugabansu sai sukayi kururuwa suka afkawo su jarumi Huzaifal aka kacame da azababben yaki sai da aka shafe tsawon sa'a biyu ana wannan yaki sannan Huzaifal suka samu nasarar hallaka gaba daya yaran Rauzum a inda kowanne daga cikinsu Rauzum a kashe dakarun rakiya mutum saba'in dayake duhun dare ya fara kawo kai sai kowa ya sanyawo kansa magani kuma aka kafa tantuna sannan akayi kalaci saida aka shafe tsawon kwanaki biyu a wannan daji a iya wannan kwanaki jarumi Huzaifal ya koyawo su yarima yadda ake yaki kuma bisa mamaki sai gashi suna rike duk abinda aka koya musu al'amarin da yayi matukar bawo sarki Siyamul ansar mamaki kenan domin sau tari yana koya musu yaki amma basa rikewa da hantsi aka sake yin shiri aka cigaba da tafiya saida suka shafe kwanaki hudu ana keta miyagun dazuzzuka amma bisa taimakon ubangiji basu sake haduwa da wani abin cutarwa ba sau tari idan miyagun dabbobi suka hango su sai kaga sun tarwatse sun bazama izuwa cikin daji al'amarin da yayi matukar bawa sarki Siyamul ansar da boka Zulwal mamaki kenan abinda basu sani ba shine kawai tsananin addu o in da jarumi Huzaifal ke karantawa ne suka tsare su daga sharrin dabbobin a iya tsawon wannan kwanaki babu abinda ke tsaida su face idan lokacin bacci yayi ko lokacin gabatar da sallan jarumi Huzaifal a ranar kwana na biyar ne da yamma sakaliya suka hango gidan boka Jabarul sihir akan tsakiyar wani qaton dutse da ba a ganin karshensa. Lokacin da ya zamana saura taku ashirin atsakaninsu sai kowannensu yaja linzamin dokinsa ya tsaya suka sauko sannan suka raka da kafafunsu suka durfafi gidan suna masu zare makamansu da isarsu izuwa bakin kofar gidan suka tarar kofar ta kasance doguwa mai tsawo da fadi kuma anyi tane da zallar mulmulallen karfe Huzaifal ya matsa kusa da kofar ya karanta ayatul kursiyyu da tsarkakakken sunaye yana mai tofawa ajikin kofar sai gashi ya tura kofar da hannu daya tamkar ya yaye labule kawai sai ya kunna kai izuwa cikin gidan sarki Siyamul ansar boka Zulwal yarima Nazmar gimbiya Hulaisa dakarun rakiya ne a karshe suka bi bayansu da sauri da shigarsu suka tarar da wata hangamemiyar fada ta gaban kwatance gaba daya fadar gidan anyi shine da zallar farin gilashi idan mutum ya kalli ko ina a fadar sai yaga hoton surar jikin gilashin aqalla girman fadar yakai gari guda kai tsayawa misalta tsaruwa da kawaitar fadar yakan iya zamowa kauyanci sai dai abinda ido ya gani wani abin ma idan mutum ya gani bai taba gani ko jin sunansa ba abangaren yamma afadar bisa wata matattakala mai hawa shida aka ajiye wata qasaitacciyar karagar mulki ta gaban kwatance boka Jabarul sihir ne zaune bisa karagar fuskarsa cike da annuri tamkar wanda aka bawo mulkin duniya boka Jabarul sihir ya kasance garjejen qato mai tsawo da kauri tamkar toron giwa duk da kasancewar shekarunsa sun dan ja kallo daya zakayi masa ka fahimci cewa ya kasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza afilin daga a wannan lokaci boka Jabarul sihir na tsaye ne cikin doguwar alkyabba da akayi mata cin baki da zaren lu'ulu'u akansa yana sanye da kambun mulki da akayi shi da zallar zinare yana walwali da daukar idanun mai kallonsa duk inda mutum ya kalla ajikinsa guraye ne da layun tsafi zaune bisa wadansu qayatattun kujeru afadar yan majalisansa ne na jinsin mutum da aljan kuma gaba daya fadar kewaye take da wadansu irin zaratan dakaru masu matukar muni da ban tsoro suna dauke da makami masu barazana da rayuwar bil adama lokacin da boka Jabarul sihir yayi arba da su sarki Siyamul ansar sai ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ya tako matattakalar fadar ya sauko kasa yana mai takowa da kafafunsa yana kusantar inda suke fuskar cike da annuri tamkar zai sadu da yan uwansa na jini. Koda ganin hakan sai su jarumi Huzaifal suka dafe takubbansu lokacin da ya zamana saura taku goma tsakaninsu sai boka Jabarul sihir yaja ya tsaya ya dubi su jarumi Huzaifal ya bushe da dariyar farin ciki sannan ya budi baki cikin kakkausar murya yace lale marhabun da manyan baki masu daraja na dade ina jiran zuwa wannan rana mai cike da farin ciki agareni yanzu sai ku miko min kwan sihirin da su yarima suka dauke mini akogon Annoba koda jin wannan batu sai sarki Siyamul ansar ya daka masa tsawa yace kai tsohon la'ananne kai sani cewa baka isa mu damka maka kwan sihiri ba face ka amince zaka debo mana ruwan koramarka wanda dashi ne zan warkar da 'ya'yana koda gama fadin haka sai sarki Siyamul ansar ya zura hannunsa a aljihu sai gashi ya fito da wani kwai mai girma tamkar gwanda yayin da boka Jabarul sihir yayi arba da kwan sihiri sai ya takarkare ya kwarara uban ihu paruwar hakan keda wuya sai gaba daya duhun ya yaye sai ga boka Jabarul sihir cikin gagarumar shigar yaki a hannunsa yana rike da wata zabgegiyar adda mai tsawo da tsinin tsiya koda ganin hakan sai sarki Siyamul ansar ya zare takobinsa boka Zulwal yayi koyi dashi suka ruga izuwa kan dakarun fadar jarumi Huzaifal kuwa ya zare takobinsa ya ruga kan boka Jabarul sihir aka kacame da azababben yaki ana cikin hakan ne sai su yarima Nazmar sukaga wadannan miyagun tsuntsaye na ratsowa ta saman fadar tamkar yadda danshi ke ratsa kasa suna dura a gabansu daya bayan daya koda ganin hakan sai yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa suka falfala da azababben gudu izuwa kan tsuntsayen suna masu rayawa azuciyoyinsu cewa muna neman taimakon ubangijin musulunci ba tare da sun riki wani makami ba suka afkawa tsuntsayen da yaki su kuwa dakarun rakiya sai suka zare makamansu suka tari wadansu dakaru afadar dake bangaren yamma aka yamutse da fada abu kamar wasa sai gashi jarumi Huzaifal da boka Jabarul sihir sun shafe tsawon sa'a biyar suna yaki ta hanyar kaiwa juna miyagun hare hare. Lokacin da boka Jabarul sihir ya fahimci cewa ya kasa samun nasara akan Huzaifal da karfin damtse sai ya fara amfani da karfin sihirin tsafi har ya zamana yana yin amfani da dukkanin sirrikan tsafinsa tabbas boka Jabarul sihir ya hadu da gamonsa dakyar da siɗin goshi ya samu nasarar zabgawo Huzaifal daushi aciki ya bazadda shi kas koda Huzaifal ya fahimci halinda yake ciki sai ya kira sunan ubangiji karfi yana mai neman taimakonsa take ya samu wani gagarumin karfi kawai sai ya mike tsaye zumbur yayi tsalle sama tamkar an harbashi daga cikin baka ya dira akan boka Jabarul sihir yana mai rarraba kafadunsa cikin zafin nama ya sanya hannayensa biyu ya murde masa wuya sannan ya dako tsalle ya dira bisa kafafunsa cikin gwaninta adaidai wannan lokaci ne gawar boka Jabarul sihir ta fadi kasa racaca jini ya kwaranya nan take dakarun gaba daya da suke yaki da su sarki Siyamul ansar suka qame suka zama gumaka kuma komai na fadar ya sandare ya zamana saura tsuntsaye dasu yarima suke cikin yaki nan fa jarumi Huzaifal boka Zulwal da sarki Siyamul ansar suka zuba idanu suna kallon fafatawar da akeyi babu abinda yafi basu mamaki sama da yadda su yarima Nazmar ke ragargazar tsuntsayen babu sassautawa a inda za kaga sun kirbawa tsuntsu naushi sun karya kafa ko fukafuki nan fa ya zamana ihu da kururwar tsuntsaye ya mamaye fadar jini kuwa ya dinga kwaranya yana malala tamkar an balla teku su kansu su yarima sunyi matukar mamakin irin wannan gagarumin karfi da suka samu sai da dakika dari da sittin ta shude sannan yarima Nazmar da gimbiya Hulaisa suka samu nasarar kashe gaba daya tsuntsayen amma gaba daya jikinsu ya rine da jini tamkar an tsomasu cikin tekun jini cikin matukar farin ciki sarki Siyamul ansar ya ruga inda 'ya'yansa suke ya rungumesu a kirjinsa cikin tsananin farin ciki daga can su yarima suka janye jikinsu daga na mahaifinsu suka dube shi sukace ya abbanmu kayi sani cewa dukkanin wannan nasara da kaga mun samu akan wadannan tsuntsaye mun samu taimako ne daga ubangijin jarumi Huzaifal saboda haka munyi imani da ubangijin musulunci koda jin haka sai sarki Siyamul ansar boka Zulwal da dakarun tsakiya sukace muma munyi imani da ubangiji mahalicci cikin matukar farin ciki jarumi Huzaifal ya karanta musu kalmar shahada suka maimaita. Faruwar hakan keda wuya sai sukaji gaba daya fadar ta kama girgiza koda ganin hakan sai jarumi Huzaifal ya falfala da gudu izuwa kofar fita dake fadar yana mai yiwa su sarki nuni da su biyo bayansa ai kuwa suna kammala fita daga fadar sai gaba daya ginin fadar ya dinga rushewa kuma gaba daya ya nutse cikin karkashin kasa Huzaifal ya dubi su duka su hudun yace bamuda bukatar nemo ruwan ma"ul diya'u dan warkar da su yarima imani kadai da sukayi da ubangijin musulunci ya warkar dasu daga lalurar dake damunsu ta rashin jin magana koda gama fadin haka sai jarumi Huzaifal yaje ya kama dokinsa ya hau sannan kowa ya hau nasa aka cigaba da tafiya sa'adda lokacin sallah yayi sai jarumi Huzaifal yayi umarni aka tsaya da tafiya bayan an samu ruwa a wata korama anyi alwala su yarima sun sauya tufafin dake jikinsu sai Huzaifal ya shige gaba yayi musu limanci sa'adda su sarki sukaga yana yin ibadar bisa tsari mai ban sha'awa sai sukaji kaunar addini ta kara shiga ransu bayan an kammalane aka dauki hanya yayin da aka isa birnin sarirul aiwan sai aka kafa tutar musulunci jarumi Huzaifal ya auri wata baiwar sarki Siyamul ansar mai suna ZARIMAT BINTU FANNAS daga wannan rana jama'ar birnin suka kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali ya zamana babu manyan jarumai kamar su yarima Nazmar da sanin ilimin addinin musulunci. ALHAMDULILLAH Marubuci MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubutan Yaƙi Wthapp number 08137237071