BUSA A MUTU!!! Littafi Na Daya (1) Part A Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini Marubucin ya fara da cewa... A YARIN Fatake ne da 'yan gudun hijira daga wata babbar kasa da ake kira Lairus. Yawansu ya kai dubu uku, wasu akan dawakai suke tafiya, wasu a rakuma da alfadarai. A kalla wadannan mutane sun shafe kwana tara suna tafiya a cikin daji suna keta kwazazza bai, koramai da duhuwoyi. A cikinsu akwai zaratan samari majiya Rarfi, sannan akwai mata, yara da tso fafffi kuma yawancinsu iyalai ne, wato wani zaka ga tarc yakc da matarsa da kuma dansa ko 'yarsa ko kuma 'ya'yansa guda biyu ko uku. Wani kuwa tarc yake da mahaifinsa ko mahaifiyarsa. Wani yana tare da dan uwa ko 'yar uwa. Kuma gashi suna daukc da dukiyoyinsu wasu ma har da dabbobinsu. Abin tambaya anan shi nc, ina wannan ayari suka nuta, kuma daga ina suka fito, sannan ina suka dosa? Ba wani abu banc ya sa wannan ayari suka yi gudun hijira ba face masifar yaki da ta 6arkc a kasar tasu ta Lairus wadda ta haddasa asarar miliyoyin rayuka da dukiya. Shi dai wannan yaki ya faru nc sakamakon wadansu 'yan tawaye wadanda suka yiwa Sarki Muraisu borc domin tabbatar da cewa sun tunkude mulkinsa da karfin tsiya saboda kawai ganin cewa shi. mutum ne adali wanda baya zalunckuma bai yarda da zalunci ba Su dai wadannan 'yan tawaye sai da suka shekara bakwai suna tanadi na wannan yaki suna tara dakaru a baye a can wata kasar daban gami da kayan yaki. Sai da suka tara mayaka miliyan biyu da rabi kuma ya zamana cewa kullum a cikin basu sabbabbin horon yaki ake. Babban abin takaici shi ne ba wani bane ya dauki nauyin wadanma Dakarun iawayc ba face Yarima Huraisu kanin Sarki Muraisu wanda suka kasance uwa daya uba daya. Tun Muraisu da Huraisu suna yara kanane suka taso basa jituwa saboda bambancin halaye sa ra'ayi suka zama tankar abokan gaba, ya zamar.a ccwa basa yiwa juna ga maciji. Babu abinda ya tsananta gaba a tsakaninsu face Huraisu ya san ceva idan mahaifinsu Sarki Salmar ya mutu, Muraisu ne zai hau kan karaga saboda tuni Sarki Salma ya yi nuni da hakan har ma ya bar wasiyar hakan. Halayen Sarki Saimar iri dayane dana Muraisu wato suna da son taiakawa,tausayi da taimako. Kwata- kwata abin duniya bai danesu ba. Begu da kari Muraisu ya kasance saurayin mai farin jini matuka a wajcn jama ar gari saboda ganin cewa ya taso da halaye na mahaifinsa. Duk inda ya wuce ma sai dai ka J1 ana yi masa kirari da Magajin Sarki. Shi kuwa Huraisu jama'a sun tsaneshi kamar yadda suka tsani Mutuwarsu saboda bakar zuciyarsa ta zalunci. Ko kallonsa mutum ya yi ya tsargu Sai ya zare makami nan take ya sareshi. Idan ya ga budurwa mai kyau ko 'yar gidan uban waye sai ya yi ma ta fyade haka kurma duk dukiyar da ya gani in dai ya ji yana bukatarta to fa sai ya kwaccta. A duk sa'adda Huraisu ya yi irin wannan mugun aiki baya yarda ya dawo gida sai dai ya shiga daji ya buya saboda sanin cewa saii Sarki ya sa an yi masa hukunci mai tsauri dai-dai da laifin da ya aikata. Sarki ya sha sawa a yiwa Yarima Huraisu bulala arba'in ko hamsin a farfasa masa jiki har sai ya yi jinya. Kuma duk sa'adda ya aikata laifin ya gudu daj babu mai iya zuwa ya kamoshi da karfin tsiya sai dan uwansa Muraisu. Muraisu da Huraisu sun kasance gawurattun Sadaukai na gaban kwatance kuma kwararrun mayaka wadanda suka yi shuhura a cikin nahiyarsu sai dai Muraisu ya fi Huraisu karfi, jarumtaka da iya yaki nesa ba kusa ba. Wani lokaci idan Muraisu ya tafka laifi sai Sarki ya sa a daureshi tamau a sama a jikin dirka a gasashi a cikin rana, ba ci ba sha har tsawon sa'a ashirin da hudu amma saboda naci da bakin hali idan aka sakeshi gobe ma sai ya kara aikata wani laifin da ya fi na baya. Azaba ko bazarana ba ta firgita Huraisu koda kuwa ya san cewa zai iya rasa rayuwarsa sakamakon azabar da za a yi masa. Sarki Samral yana matukar kaunar Yarima Muraisu saboda ladabinsa da biyayyarsa da kuma halayensa da ya gado gami da yadda ya ga jama'ar birnin Lairus ke tsananin kaunarsa suke girmamashi. Ko kara Sarki Salmar ya ajiye Muraisu ba zai ketarce ba. Mahaifiyar Muraisu ta rasu ne a ranar da ta haifesu suka zo duniya lokaci guda tagwaye. Muraisu da Huraisu suna matukar kama da junansu tamkar an tsaga kara. A wannan rana an cc Sarki Samral ya yi matsanaicin kuka da bakin ciki. Al'amarin da ya matukar baiwa mutanen kasar gaba dayansu mamaki ke nan, domin a tarihin rayuwar Sarki Samral tun daga kuruciyarsa kawo izuwa girmansa ba a taba ganin kwalla ba a idanunsa, amma sai gashi an ga ranar da yake ta kuka kishin6ar! da hawaye daki-daki, wani na bin wani. Sarki Samral kasaitaccen sadauki ne kuma gabjcjen mutum mai kirar mutanen farko, domin duk sa'adda yaje nahiyar da ba a sanshi ba da zarar mutane sun ganshi sai su firgice su kama guje-gujc, wasu su ce sun yi gamo da aljani, wasu kuma su ce ai fatalwa ce. Komai girman bishiya da hannu daya Sarki Samral ke hankadeta ta fadi kasa. Komai girman dutse da nauyinsa idan har ya ritsashi da hannayensa biyu to fa zai iya rabashi da kasa ya dagashi sama ya yi doguwar tafiya da shi ba tare da ya gaji ba.. Idan kuwa zai fita yaki saj dai a tanaji giwaye kamar guda arba in a matsayin ababcn hawansa, kumna babu wacce za ta , AA Misau Nake, iya daukarsa sama da tsawon rabin sa'a ba tare da ta gaji ba ta durkushe kasa saboda tsananin nauyinsa. Kai idan Sarki Samral ya fusata yana iya daukar ita kanta giwar ya yi wurgi da ita tamkar ya yi wurgi da hoge. Labarin Jarumtakar Sarki Samral ya bazu ko ina a nahiyarsu har ma da sauran nahiyoyin da ba nasu ba. Kuma ba a ta6a samun GWARZON MAYAKI ba kamarsa. A tarihin yake-yaken da ya yi a rayuwarsa tun kafin ya hau karagar mulki har izuwa sa'adda ya bar duniya ba a taba cinsa da yaki ba, kuma ba a taba ji masa ciwo ba. Idan yana tsakiyar abokan gaba yana saransu da sukarsu da takobinsa sai ya shafe sa'a goma sha biyu bai gaji ba, kuma tsananin zafin namansa da Rarfin gudunsa ya wuce misali kamar iska ce ke sarrafa gababen jikinsa. Da yake mutum ya kan haifi kansa sai gashi Sarki Samral ya haifo zakwakuran sedaukai da suka gado wannan girman jiki irin nasa da kuma jarurntaka tasa sai dai inda aka sami akasi Muraisu ya fi Huraisu komai ya ma ninkashi. Lokacin da fitinar Huraisu ta yi yawa kuma ta damu Sarki Samral ya zamana cewa duk irin azabar da aka vi masa da irin hukuncin da ake yi masa mai tsauri a duk sa'adda ya aikata laifi sun zama a banza sai Sarki ya kafa masa doka ta karshe ya sanar da shi cewa dukLa ranar da aka sake kamashi da laifin yin fyade ko sata ko kuma cin zali sai an yanke masa hannayensa biyu Domin kowa ya huta da fargabarsa saboda ya addabi Gaba dayan jama'ar birnin da Rauyuka. Sa'adda mutane suka ji wannan gagarumin bukunci da aka dauka akan azzalumi Huraisu sai suka cika da tsananin farin ciki. Tun daga wannan rana kyawawan 'yan mata suka sami 'yancin yawo a ko ina, attajirai suka rinka fatauci a ko ina a kasar cikin kwanciyar hankali, sabanin da can da 'yan fashi suka yawaita a ko ina a cikin kasar, kuma gaba dayan 'yan fashin yaran Yarima Huraisu ne. Lokacin da Yarima Huraisu ya ke kan sharafinsa na aikata duk irin laifin da ya ga dama ne ya tara yara a karkashinsa sama da dubu dari, kuma a kowanne birni da ke cikin kasar yana da wakilai. Duk sa'adda Fatake za su ratsa wata hanya ko kuma a duk inda za a yi wani gagarumin kasuwanci da dukiya mai yawa sai labari ya riskeshi sai dai kawai aga shi da yaransa sun baiyana a wajen sun tafka gagarumar 6arna. Ran biladama kuwa sun mai da shi tamkar na kiyashi. A wannan lokaci ne Huraisu ya tara dukiya mai tsananin yawan gaske saboda haka sai ya så aka gina masa wani tafkcken gida a tsakiyar waii daji da akc Kira Kirzufa, wanda ke tsakanin iyakar birnin Lairus da wani birni mai suna Hutaira. Shi dai wannan daji na Kirzufa dade ana rigima a Kansa a tsakanin kasashen biyu domin kowacce kasa kuma sau ashirin da daya ana yaki a zamanin Sarki Samral akan dajin, amma duk sa'adda aka yi yakin sai dai ayi ragas, duk da cewa Sarki Samral ya zama dodon maza kuma gagaraba dau. ba komai ne ya janyo Madakin Gini hakan ba face tsananin yawan mnayakan birnin Hutaira ya wuce misali. Akwai lokacin da Sarki Samral ya kwana arba'in Cif yana yaki da su shi kadai amma sai ya kasa karar da koda rabinsu, suma suka kasa hallakashi ko kaishi Ras. Duk sa'adda ya ga ya gaji ainun sai ya falfala da matsanaicin gudu su kasa cimmasa har yaje wani wurin ya buya sai ya huta sannan ya dawo a ci gaba da gumurzu. Gashi dai yana kashesu tamkar ana kakkabe ganyaycn bishiyoyi a daji, amma sai ka ga kamar matattu ne suke tashi saboda azabar yawansu. Kai a wannan zamani sai da masu bincike suka gano cewa ko mutan cn birnin Sin ba su kai rabin yawan mutancn birmin Hutaira ba. A karshe bisa dole Sarki Samral ya janye yakin da kansa ya koma birninsa ya hakura da mallakar dajin Kirzufa. Har Sarki Samral ya bar duniya da takaicin rashin mallakar dajin Kirzufa ya tafi, kuma kafin ya mutu sai da ya barwa Muraisu wasiyyar cewa duk yadda zai yi ya tabbatar da cewa ya mallaki dajin Kirzufa kafin shima ya bar duniya. Muraisu ya dauki alkawarin cewar koda kuwa zai rasa rayuwarsa a kokarin mallakar dajin Kirzufa ba zai Gaza ba Sarkin da ke mulkin birnin Hutaira, wani gawurtaccen boka ne mai suna Ishmar ibiní Suraifa. Shima Sarki Ishmar babu abinda bai yi ba akan ya ga bayan Sarki Salmar domin ya mallaki dajin Kirzufa amma abu ya gagara. Abinda yake daurc masa kai shi ne, "Me ya sa tsafī baya tasiri akan Sarki Samral? Babu irin binciken da bai yi ba a hallarar tsafi domin ya gano wannan matsala amma abu ya gagara. Kawai abin da ya iya ganowa shi ne akwai wani babban sirri a tarc da Sarki Salmar wanda yasa tsafi baya tasiri a jikinsa kuma ya ziyarci bokaye da yawa a duniya wadanda ma suka fi shi karfin sihiri amma dukkaninsu sun kasa gano wannan sirri. Abinda bokaye suka gaya masa shi ne duk duniya babu wanda ya san wannan sirri face shi kansa Sarki Samral kuimna kafin ya bar duniya sirrin zai koma kan dansa Muraisu, shima kafin ya mutu dansa zai gaji wannan sirri. Haka al'arnarin zai ta bibiyar zuri'arsu shckara da shekaru, zamani bayan zamani. Ba za a taba rabasu da wannan sirri ba face a ranar da aka kai mai sirrín kas a filin yaki aka sami nasarar hallakashi. A sannan nc za a tsaga kirjinsa a ciwo wannan sirri wanda ya kasance dan siriri tamkar silin gashin da ke wuyan doki guda daya. Sa'adda Sarki Ishmar ya ji wannan jawabi sai hankalinsu ya dugunzuma ainun, domin ya san cewa , AA misau nake, : shi dai abu ne mawuyaci a zamaninsa ya ga wannan rana sai dai nan gaba a zamanin 'ya'yansa ko jikokinsa. Akan haka ne ya rungumi kaddara bisa tunanin mallakar dajin Kirzufa a wannan lokaci amma sai ya ayyana a ransa cewa komai darcn dadewa sai an sami wani daga cikin zuri'arsa ya mallaki wannan sirri. Shi dai Sarki Ishmar Allah Ya albarkaceshi da yayye har guda talatin da tara, amma gaba dayansu mazane babu mace ko guda daya, kuma a binciken da ya yi zuri'arsa ba za ta taba samun damar mallakar wannan sirri ba na Sarki Samral face an haifi gagarumar BASADAUKIYA jininsa wacce za ta shahara a ko ina cikin duniya. Wani babban abin takaici shi ne gaba daya 'ya'yan Sarki Ishmar manya wadanda suka yi aure duk wanda matarsa za ta haihu sai aga namiji ta haifa ba a taba samun wacce ta haifi 'ya mace ba bare Sarkı İshmar ya sa ran cewa ita ce za ta kar6i wannan sirri ga zuri'ar Sarki Samral. Saboda wannan dalili. ne duk sa'adda aka yi haihuwa Sarki Ishmar ya ga namiji aka samu sai ya kamu da tsananin bakin ciki ya rufe kansa a cikin daki ya yi ta kuka domin ya san cewa har abada ba zai ga ranar da zai raba Sarki Samral da wannan suri na sa ba Wanda zai sami damar cuiar da shi da zuri'arsa da Carfin sihirin tsafi. Babban abin takaici a gareshi shi ne lsufa ya riskeshi ya shekara tamanin da hudua dunivai ya san cewa ajali ko yaushe ajali zai iya riskarsa : De jin Kirzufa wani irin sihirtaccen daji ne wanda sama da shekaru dari baya ba a aba samun mahaluin da ya shiga cikinsa ya iya dauko wani abu ba face mutum aya rak, wato Sarki Samral. a wannan ikokinsa. Shi dai wannan daji na Kirzufa Allah Ya albarkaceshi da tsuntsaye iri-iri gami da dabbobin daji kala-kala masu yawan tsiya. Wata dabbar ma ko a labari mutum bai taba jin labarinta ba. Babban sirrin dajin Kirzufa shi ne, idan mutum ya shigeshi in dai bai yi ko Rarin đaukar wani abu ba ko cutar da wata dabba ba to fa zai shiga lafiya kuma ya fito lafiya, amma da zarar ya yi yunkurin daukar wani abu ko cutar da wata halitta, to fa sunansa gawa! Mafarauta da mayaka sun sha hada runduna su shiga dajin don đebo albarkatun cikinsa, amma dayansu baya dawowa a raye. Shi kansa Sarki Samral sau daya ya taba shiga dajin ya yi farauta inda ya kamo wadansu giwaye guda shida. Nan take ya kashe guda hudu ya ciro haure guda biyu kuwa ya sabosu a kafadunsa ya fito da su daga cikin dajin. Koda va iso inda ya bar Dakaru hamsin wadanda suka yi masa rakiya izuwa farautar suka ganshi da wadenan giwaye da kuma haure sai suka cika da tsananin mamaki suka rinka shewa suna yi masa iinjina domin shi ne mutum na farko da ya karya alkadarin dajin Kirzufa..... Sbd haka Nima Ku Tafamin😂 Dafatan Kowa yana lafiya SaikumA Mun sake haduwa a part B BUSA A MUTU!!! Littafi Na Daya (1) Part B Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gino Marubucin yaci gaba da cewa.... Nan da nan labarin wannan jarumtaka da ya yı ya bazu a ko ina a nahivar. Wani abin mamaki shi nc, hauren giwayen da ya farauto a cikin dajin sai da suka zamo sanadiyar samun dukiyarsa mai tsananin yawa irin wacce bai taba samu ba a rayuwarsa domin manya-manyan Sarakunan duniya ne suka rinka yin tattaki suna zuwa har birnin Lairus suna siyan hauren giwa daya jal akan miliyoyin dirhami. Duk wanda ya sayi hauren giwar sai ya kaishi masarautarsa ya adanashi a gidan tarihi mutane suna Zuwa suna gani suna biyan kudi. Shima ya sami abin samun kudi. Shima Sarki Samral sai da ya ajiye hauren giwar guda daya jal a tsakiyar fadarsa saboda barin tarihi, kuma yasa aka sassa ka gunki mai kamanninsa da girmansa sak! Yana gumurzu da giwaye shida na gumaka. Duk mutumin da ya shigo fadar Sarki Samral ya ga wadannan gumaka na giwaye shi da Sarki Samral dole ne ya yi sha'awarsu domin sun yi matukar kyau, kasancewar an yi su ne da zallan zinare, kuma masassakin ya kwarance ainun, da ka kallesu sai ka ga kamar za su yi motsi tamkar na gaske ne ba gumaka ba, Daga wannan rana da Sarki Samral ya shiga dajin Kirzufa ya yi wannan farauta ya dawo gida bai sake sha'awar sake zuwa daji ba Shekara na zagayowa ne ya kamu da cutar ajali. ya kwanta ciwo. Kuma a wannan lokaci ne Yarima Huraisu ya yi fishi ya bar birnin Lairus ya koma can daji inda aka gina masa wannan tafkcken gida ya zauna tare da yaransa manya-manyan 'yan fashi suka ci gaba da sharholiyarsu. A sannan ne labari ya riski Yarima Huraisu cewar mahaifinsa Sarki Samral ya kwanta cutar ajali. Koda samun wannan labari sai Huraisu ya cika da matukar farin ciki ya fara tunanin hanyar da zai tara mayaka masu yawan gaske wadanda za su zama 'yan tawaye su je su yaki birnin Lairus su karbi mulki da Rarfin tsiya tunda Sarki na kwance ba lafiya amma sai abu daya ya fađo masa a rai wanda ya firgitashi. Ba komai bane wannan abu ba face dan uwansa Yarima Muraisu wanda ya tabbatar da cewa ya fishi jarumtaka nesa ba kusa ba, kuma duk abinda Sarki Samral ya yi shima zai iya yinsa, don haka Muraisu shi kadai zai iya tarwatsa mayakan da zai tanada ya hanashi cika burinsa. Abu na biyu da ya kara dugaunzuma hankalinsa ya jefa masa tsananin bakin ciki shi ne, ya san cewa duk sa'adda Sarki va mutu lallai Muraisu ne zai gajeshi, kuma hatta wannan sirrin sihiri na shiga dajin Kirzufa sai ya mallaka masa shi. Babban burin Yarima Huraisu shi ne bayan ya Zama Sarkin Lairuf ya shiga dajin Kirzufa ya yi farauta a cikinsa kamar yadda mabaifinsa ya yi ya shahara A ko ina a duniya. A takaice dai yanzu burin Yarima huraisu guda biyu ne. Yana son ya zama Sarkin Lairuf kuma yana son ya sami daukaka irin wacce mahaifinsa ya samu a sanadiyar shiga dajin Kirzufa. Lokacin da tunanin wadannan abubuwa biyu suka yi tsanani a cikin zuciyar Yarima Huraisu sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi a duniya, ya kasa zaune ko tsaye, ya yi ta zarya a cikin wannan gida nasa na daji. A wannan lokaci manyan yaransa na zazAune sun zuba masa ido kawai an rasa wanda zai tambayeshi abinda ke damunsa. Daga cikin yaran nasa akwai wani jajurtacce, mara tsoro, wanda shi ne shugabansu, kuma ya kasance gawurtaccen mayaki wanda shi kansa Huraisu yana ji da shi, yana alfahari da shi, ana kiransa da suna Busara ibini Kalhur. Ba tare da fargabar komai ba Busara ya nikc tsaye ya tari gaban Huraisu ya ce, "Ya shugabana wai shin mene ne yake damunka ne a yau alhalin a jiya da daddare mun fita sana'a mun dace tunda mun. samo dukiya mai yawan gaske...Sannan ga giya ganga-ganga a gidan nan babu adadi, ga mata nan ba na banza sai Wacce kake sha'awa, komai na jin dadin duniya akwaishi a cikin gidan nan". Sa'adda Yarima Huraisu yajı1 wannan tambaya sai ya kyalkyale da dariya lookaci guda kuma ya murtuke fuska ya ce, "ya kai Busara, kayi sani cewa buri baya yankewa a zuciyar dan'Adam. Na sani cewa a halin yanzu na mallaki komai na jin dadin duniya. Duiciyar da na tara a yanzu har na bar duniya ban isa na karar da ita ba! Amma ai har yanzu ban sami mulkin birnin Lairus ba..AA Misau Nake, Har yanzu ban mallaki sirrin shiga dajin Kirzufa ba. Ta ya ya zan samu daukaka irin wacce mahaifina ya samu a duniya?" Sa'adda Yarima Huraisu ya ZO nan a zanccnsa sai Busara ya yi murmushi ya ce, "Ya shugabana ai babu wata cuta a duniya wadda bata da magani. Ina ganin cewa idan ka jc wajen Sarki Ishmar ibini Suraifa zai iya sanar da kai hanyar da za ka bi ka sami bivan bukatunka." Cikin matukar mamaki Huraisu ya dubi Busara ya ce, "Ta ya ya kake tsammanin ccwa Sarki Ishmar zai bani hadin kai alhalin ya kasance babban makiyin mahaifina. ?" Busara ya sake yin murmushi a karo na biyu ya ce, "Ai Sarki Ishrnar ya san duk abinda ke tsakaninka da mahaifinka, kuma ya san baka da wai buri wanda ya fi ka ga bayan mahaifin naka, don haka tabbas zai ba ka hadin kai tun da fadnwa ta zo dai-dai da zamna," Ya yiin da Huraisu yaji wannan shawara, sai nan Take ya cika da farin ciki, ya dubi Busara ya ce, A shirya mini tafiya izuwa bimin Hutaira gobe da safe Kuma mu uku ne kacal zanu tafi ni da kai da sadaulki Rauhaz". Sadauki Rauhaz shi ne na biyu a cikin manyan yaran Yarima Huraisu wadanda yake takama da su, kuma baya shakkar turasu aiki ko ina. Sadauki Rauhaz jarumi nc na gaske, kuma Allah Ya horc masa basira da kaifin tunani da hangen ncsa, don haka in dai ya shirya yadda za a yi sata sai an sami nasara. Ba a taba samun akasin hakan ba. Haka kuma idan aka shiga RINTSI ko wani bala'i da zarar ya bada shawarar abinda za a yi a kubuta, ana yin amfani da shawarar tasa take ake samun mafita. Bisa wannan dalili ne Yarima Huraisu in dai zai yi tafiya sai tare da sadauki Rauhaz, domin ya ri ga ya camfa cewa in dai suna tare duk abinda zai yi sai ya sami nasara akansa. Har ma kirari yake masa yana cewa da shi, "Kai ne mabudin hanya! Kai ne tutar Nasara Rauhaz!!m Kashe gari kuwa da sassafe Yarima Huraisu, Busara da sadauki Rauhaz suka yi shiri suka hau dawakansu suká durfafi birain Hutaira. Daga wannan daji wanda Huraisu da yaransa ke zaune zuwa birnin Hutaira, tafiya ce ta kwanaki ashirin da biyu. Haka kuwa su Huraisu suka shafe wadannan kwanaki suna tafiya. Kai tsaye suka rinka ratsa dazuzzuka ba tarc da fargabar komai ba tamkar a cikin gari suke tafiya, kuma komai dare ko rana basa jin tafiyar. Babu abinda yake tsaida su face gajiyar dawakansu da yankewar ruwan sha. Duk inda suka riski korama ko kogi sai su yada Zzango a wajen su huta, idan kuwa dare ya yi sosai sai su kwana a wajen. Duk lokacin da suka yi gamo da muggan 'yan fashi ko aljanu da sauran dabbobin daji ababan tsoro, cikin kankanin lokaci suke ragargajesu, su kashe na kashewa, na gudu su gudu. A haka suka isa birnin Hutaira lafiya sumul. Fadace Rasaitacciya wadda ta kawatu ainun fiye da tunanin mutum, kai a tsaya yin bayanin abinda ke cikinta ma kauyanci ne sai abinda mutum ya gani da idanunsa. Sarki Ishmar na zaune a bisa karagar mulki, fadawa sun kewaye shi, ga mutanen gari sun taru da yawansu, AA Misau Nake, wato dai fadar ta cika ta batse sai tafiyar da harkokin mulki ake. Sarki Ishmar ya kasance gajeran mutum mai katon ciki kuma kakkaura amma kuma kyakkyawane shi a fuska kuma yana da matukar kwarjini, domin mutum bai isa ya kura nasa idanu ba. Wata irin kyakkyawar shiga ya yi ta fararen kaya da doguwar riga da wando da farin alharini wanda akayi musu dajiyar baki da zaren lu'u-lu'u, sannan ya đora bakar alkyabba mai tsananin sheki da walwali. A kansa ya dora wani dan karamin rawani mai kyau gwanin ban sha'awa, takalmin kafarsa fari ne sol. Hakika shigar tayi masa matukar kyau kamar da kavan aka halecceshi a jikinsa. A hannun sa na hagu kuwa yana rike da farin kwagiri wanda saman sa sifface ta Zaki. Kallo daya mutum zai yiwa Sarki Ishmar a Wannan lokacin ya fahinmci cewa yana cikin farin ciki domin fuskarsaa cike take da annuri sai murmushi ya ke yi kamar wanda aka yiwa busharar samun Sarautar duniya. A wannan lokaci wasu Makada ne suka baje kolinsu a fadar, wadansu kyawawan 'yan mata na ta faman tika rawa. Babu abin da zai baiwa mutum mamaki face ganin yadda wadannan 'yan mata su ashirin da hudu kamanninsu ya zo duk iri daya tamkar tagwaye. Wani karin abin sha'awa a tare da su shi ne, dukkaninsu sun yi wata iri shiga co ta Zakara, wato da siffar Zakara aka dinka tufafin jikinsu. Duk sa'adda Sarki ishmar ya dubi wadannan kyawawan 'yan mata suna ta cashe rawa sai ya ji zuciyarsa ta yi fari, wani lokacin ma har yi musu tafi yake. Da zarar ya yi tafin sau daya sai ka ji gaba dayan jama'ar da ke fadar ma sun yi koyi da shi. Ana cikin wannan nishadinc aka ga wani. Bardc daga cikin Dakarun da ke gadin gidan sarauta ya ratso ta tsakiyar 'yan matan da ke rawa da sauri ya iso gaban Sarki Ishmar. Da zuwansa sai ya zubc a kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya budi bakı da nufin ya yi bayani, sai Sarki Ishmar ya yi masa nuni da cewa ya yi shiru. Cikin farin ciki ya mike tsaye sannan ya dubi wannan Barde da ke tsugune a gabansa, ya ce masa, "Ma za ka kona can bakin kofar gidan nan ka shaidawa masu gadi cewa su budewa bakona Yarima Huraisu kofa ya shigo da sauri. Kuma ka yi musu albishir da cewa ina sane da zuwansa, ina yi masa barka da zuwa." Koda jin wannan umarni sai Barden ya mike zumbur! Ya juya ya fice daga fadar. A sannán ne 'yar matan da ke rawa suka cigaba da rawarsu, sauran fadawa da jana'ar gari kuwa sai suka cika da tsananin mamaki bisa jin cewar Sarki yana marhabin da dan Sarki Salmar babban makiyinsa a rayuwa. Maimakon Sarki Ishmar ya koma kan karagar mulkinsa ya zauna, sai ya daga hannunsa na đama sama, ta ke masu kida suka daina, masu rawa suka kame, fadar tayi tsit! Tamkar babu nmai rai a cikinta Sarki Ishmar ya kada tafin hannunsa, kawai sai Makadan nan da 'yan rawar nan suka juya suka fice daga cikin fadar. Sarki Ishmar ya sake tafa hannunsa, sai ga wadansu kuyangi su tamanin sun fito daga can cikin gidan sarautar sun caba ado na gani na fada. Kuma kowacce daga cikinsu tana dauke da karamin Kwando wanda aka cika da fure mai ruwan dorawaa. Arba'in daga cikin kuyangun sun jeru a layi tun daga bakin kofar shigowa fadar har izuwa daf da karagar Sarkin hannun dama. ragowar arba'in din su ma suka jeru 6angaren hannun hagu. Tsakiyar fadar ta zama wajen babu kowa kuma ba a hango kowa face Sarki shi kadai tak! da karagar ta mulki ya tsaya cak! Yana kallon kofar shigowa, yana ta murmushi. A dai dai wannan lokacin ne aka ga Yarima Huraisu tarc da yaransa bivu Busara da Sadauki Rauhaz sun shigo cikin fadar. Huraisu ne akan gaba. Busara da Rauhaz na take masa baya, dukkanninsu a cikin gagarumar shigar yaki suke. Koda suka sawo kafafunsu cikin fadar, suka fara tafiya, sai wadannan kuyangi suka rinka debo wannan fure suna watsa musu a jikinsu yana ta zubewa kasa. Ya yin da kamshin furen ya doki hancin su Huraisu sai suka cika da farin ciki, domin alamace ta cewar ana nurna da zuwansu. Koda Sarki Ishmar ya hango tahowar Yarima Huraisu sai ya kasa jiran karasowarsa inda yake ya taho gareshi da sauri fuskarsa cike da annuri kamar wanda ya ga dan uwansa na jini wanda suka dade ba su hadu ba. Sarki Ishmar ya bude hannayensa biyu ya tari Huraisu shima sai ya bude nasa hannayen, ai kuwa suna haduwa suka rungume juna. Saboda murna har sai da Sarki Ishmar ya sumbaci gosbhin Huraisu ya ce, "Lale marhaban da haske mai yaye duhun bakin cikin Zuciya," Huraisu ya janye jikinsa daga cikin na Sarki Ishmar suka fuskanci juna ya ce,"Ya ya aka yi na zamo haske mai yaye duhun bakin cikin zuciya? Sarki Ishmar ya ce, "Ba komai bane ya sa na yi maka kirari da wannan suna ba face kaine mutumin da zai cika mini burin zuciyata burin da ya addabi iyaycna da kakannina." Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya kama hannun Huraisu ya ja shi suka nausa cikin gidansa sarautar. Har Busaru da sadauki Rauhaz sun yunkura za su bisu a baya, sai Dakarun Sarki Ishmar suka sha gabansu wani daga cikinsu ya ce, "Ai ku iyakarku ke nan." Kamar Sarki Ishmar ya bayansa sai ya waigo ya dubi Busaru ya ce da shi, "Akai su san abinda ke faruwa a Badakaren da ya tare su Busaru na su masaukin". Nan take Badakaren ya yiwa su Busaru jagora suka shige cikin wata kofa mai zurfi. Sarki Ishmar da Huraisu ma suka shiga cikin wata kofar dabam suka kulle. Faruwar hakan ke da wuya sai fadar ta fara watsewa, kafin a jima ta zama wayam kowa ya kama gabansa. Lokacin da Sarki Ishmar ya kama hannun Yarima Huraisu ya ja shi izuwa cikin gidan sarautar sai suka yi ta tafiya tamkar gidan bashi da karshe, duk inda suka wuce sai dai ka ga Dakarun tsaro suna rabc musu suna basu hanya. Abinda ya daurcwa Huraisu kai shi. ne yadda Sarki Ishmar ya saki jiki da shi kuma suke ta hira a ya yin da suke tafiyar tamkar dama can,sun saba da juna. Cikin wani katon falo suka tsaya. Da shigarg Huraisu ya ga babu komai a ciki facc wani katon zagayayyen tebur wanda a kansa an jcra farantan abinci iri-iri sama da kala dubu kuma a gaban kowannc faranti akwai Kuyanga guda daya wacce ita ce za ta zubawa mutum kalar wannan abinci idan yana da bukata. Madakin Gini Duk da cewa Huraisu dan Sarki ne sai da ya rinka hadiyar miyau domin kamshin abincin ma kawai ya addabi hancinsa, so yake kawai su zauna su fara cin abincin in ban da ma yana jin kansa da tun kafin ayi masa tayi zai fara gusar da yunwarsa. Kamar Sarki Ishmar ya san abinda ke ran Huraisu, suna zama ya dubi kuyangin gaba daya su dubu ya ce, "Kowacce ta zubo kalar a cikin falle biyu ta kawo. Aka tara kalolin abinci a gaban su. Sarki Lshmar ya dubi Yarima Huraisu ya ce, "Ya kai babban bakona ai sai kayi sauri ka ci abincin nan domin mua da aiyuka da yawa a gabanmu." "Ko da jin wannan batu sai mamaki ya kama Huraisu. domin shi a ganinsa bai ga wasu aiyuka da za su yi ba facc tattauna maganganu. Nan dai suka dukufa wajen cin abincin. Da farko sai Huraisu ya tsaya yana ruwan ido, domin va rasa kalar abincin da ya kamata ya ci. Duk wanda va kalla sai ya ga cewa dole ne ya yi dadi. Kawai sai ya rinka yin loma daya a cikin kowanne tamka yana dandanawa ne. Kafin ya ankara tuni ya koshi, kuma bai đancfana koda kala arba'in ba. Bisa dole ya hakura ya sha nuwan inibi sannan ya dauki tulun giya ya fara sha. Koda Sarki Ishmar ya ga Huraisu na neman shan giyar da yawa, sai yai sauri ya fisge kofin giyar da ke hannunsa ya ajiye a gefe daya ya dubeshi ya kyal kyale da dariya, ya ce, "Ya kai wannan dar Sarki, ina mai shawartarka da ka rage shan giya, in ba haka ba kuwa, wata rana za ta sa ka aikata abin da za ka yi ta nadamarsa har izuwa karshen rayuwarka. Yanzu haka fa kafin ku iso nan Kasata ka shanye ganga biya: ta giya a cikin kwana ashirin da daya. Kuma a can gidanka na dajin Hirzul, a kullum sai ka sanye tulu uku na giya." Sa'adda Sarki Ishmar yazo nan a zancensa, sai Yarima Hraisu ya yi gyatsa, sarnan ya ce, "Ya kai wannan Sarki mai daraja, ka y1 sani cewa giya tana kankare damuwa da bakin cikin zuciya, shi ya sa ba zan iya rage shanta ba a lokaci guda, sai dai a sannu. Bakin cikin da ya addabi zuciyata kuwa. komai ba ne face tsananin kiyayyar da ke tsak tia da mahaifina da kama đan uwana, na rasa hvar da zan bi na kar6o mulkin birnin Lairis daga hannunsu ya Zamana cewa na shafe Su a doron kasa." Lokacin da Yarima Haraisu yazo nan a Zncensa, sai Sarki Ishmar ya bushe da mahaukaciyar dariya har ia fadowa Rasa daga kan kujerar da ya ke zaune. Nima saboda jin wannan dariya haka yasa zan dakata anan saikuma lokaci na gaba Insha Allah Fatan Alkhairi MungyarA Matsalar ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part C Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini Likes and comments Domin Mu cigaba Al amarin da va matukar baiwa Huraisu mamaki ke nan. Ya mike da sauri ya taho gareshi da nufin ya tashe shi tsaye, kawai sai ya ganshi tsulum! A kan kujerarsa tamkar iska ce ta daukoshi ta mai da shi kan kujerar. Shi kansa Haraisu ya san cewa wannan abu aikin tsafi ne. Nan take Sarki Ishmar ya murtuke fuskarsa ya daina dariyar, sannan ya dubi Huraisu cikin tsananin damuwa tamkar zai fashe da kuka, ya ce, "Ya kai Huraisu, ka yi sani cewa lokaci ya yi da burinka zai cika, amma anan gaba bayan wadansu shekaru da za su z0, ni da kai zamu shiga cikin tsananin tashin hankali wanda idan tun yanzu ba mu yi wa tufkar hanci ba sai mun tozarta. Ina son ka saurarcni da kyau da kunnen fahimta, kuma ka kiyaye dukkan abubuwan da zan zaiyana maka domin idan ka yi kuskure daya sai nun shiga cikin fargabar da bana son mu shiga. Da farko dai, na san ka sani cewa a halin yanzu mahaifinka ya kwanta ciwo, kullum sai dai a kwantar a tayar, baya iya yiwa kansa komai. Bisa bincike da na yi na gano cewa abu nc mawuyaci nan gaba ya yi shekara guda a duniya ba tare da ya mutu ba. Tabbas wannan wata dama ce muka samu da zamu iya tara mayaka masu tsananin yawan da zamu iya cin birnin Lairis da yaki a cikin watannin kađan. Ka sani cewa, a halin yanzu ma yawan mayakana ne yasa Sarki Salmar da jama'arsa suka kasa samun nasarar yaRi a kaina. Koda yake, yakin da makayi a shekarun baya ne sa'adda kai da yayanka Muraisu kuna yara kanana bare kuma ayi yakin da ku, amma nayi imani cewa ko a yanzu ne za ayi yakin da ku ba za ku sami nasara ba akan jama'ata ba, musamman saboda na san cewa kai ba za ka yake ni ba. To yanzu fa Sarki Salmar ba zai iya yin yaki ba sai dai Yarima Muraisu ya wakilceshi. Na sani cewa, Sarki Salmar yafi Muraisu juriya, na ci, kwarewa da sanin tuggun yaki kuma koda ya koyar da Muraisu duk wadannan abubuwan Muraisu ba zai iya yin abin da ya yi ba, domin kama da wane bata wane. Shima Salmar ba zai yi irin jamurtakar da Kakanka ya yi ba. Bisa wannan dalili ne na ke son daga yau ka fara tanadin mayaka a can gidanka da ke daji, ya zamana cewa kullum muna basu horon yaki har tsawon kamar wata biyar, sannan sai mu yi gagarumin shirin yaki mu tasamma bimin Lairis. Tabbas idan har mu ka yi haka sai mun sami nasarar kama birnin. Matakin farko da zamu lura da shi, shi ne, dole ne mu hada karfi ni da kai mu yaki đan uwanka Maraisu a lokaci guda. Wannan ita ce, kadai hanyar da za abi a kai shi kas. Idan muka kuskura dayan mu ya tareshi har aka fafata sama da tsawon rabin sa'a sai ya sami nasara a kansa, Ina tabbatar maka da cewa, ni da kai zamu iya kai Muraisu kas idan har mun hada karfi. Da zarar mun kaishi kas kuwa, ni da kaina zan tsaga kirjinsa na dauko sirrin da za'a iya shiga dajin Kirzufa da shi. Ina so ka sani cewa duk fadin duniyar nan babu wata wuka da za ta iya bude kirjin Huraisu face wacce ake kira "Hirzul Subura". Ita dai wannan wuka ta Hirzul Subura, a yanzu haka tana nan acan birnin Darul Wasus, birnin da duk duniya babu kamarsa a fagen sarrafa karafa iri-iri, kuma 'anan ne makera na duniya kaf suka gama kure basirarsu ta kera makaman yaki da sauran kayan alatu na rayuwar yau da kullum. Fiye da shekaru dubu kawo i yanzu ba a taba kera Wuka mai kaifi ba tamkar Wukar Hirzul Subura, babu abin da bata yankawa, walau karfe ko dutse, kuma komai taurin abu ko kwarinsa, bayan ta yanka shi ba za aga ta dakushe ba, kuma kaifinta ba zai ragu ba. Idan akai yanka da ita sannan ne ma kaifinta ya ke karuwa. Wukar Hirzul Subura an bata mugun tsoro na gaban kwatance domin an ajiye ta ne a tsakiyar fadar birnin Darul Wasus, kuma an sakaleta a sama jikin rufin gini. Ba mna mutum ba, komai hatsabibancin aljani bai isa ya rabi inda takobin take ba, saboda karfin sibirin tsafin a ke jikinta duk abinda ya yi yunkurin taba wannan wuka take yake zama gawa. Bays ga haka, a kullum Dakaru dubu dari tara ne suke gadin wannan wuka dare da rana, kuma an kasa Dakarun gida biyu masu aikin rana dabam, haka ma masu aikin dare. Bisa binciken da na yi, mutum uku ne kacal a cikin fadin duniyar nan za su iya zuwa birnin Darul Wasus su iya dauko wannan wuka. Daga mabaifinka sai fan uwanka Muraisu sai kusna kai kanka." Koda jin wannan batu sai Huraisu ya dubi Sarki İshmar, cikin tsananin mamaki to mene ne dalilin da yasa Sai mu uku kacal za mu 1ya dauko wannan wuka?" Sarki Ishmar yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ainihin wukar Hirzul Sabura wani mashahurin mayakine ya kerata wanda ya kasance Rasurgumin matsafi kuma shi ne, tushen zuri'ar dangin mahaifinku. A yadda ya kera muku wukar babu wanda ya isa ya yi amfani da ita face ya kasance jinin zuri'arku. Wani abin mamaki shi ne, gaba dayan zuriar tasa ta kare babu irinta a doron kasa face ku ukun nan kacal." Yarima Huraisu ya yi shiru yana nazarin al'amarina cikin zuciyarsa har izuwa wani dan lokaci sannan ya dago kai ya dubı Sarki Ishmar ya ce, "Na ji ka ce an baiwa wukar Hirzul Subura mugun tsarc ta ya ya zan iya kavar da tsaron har na daukate?"h, Ishinar ya yi munushi ya ce, "Ta hanyar hada karfi da ni gami da kiyaye dokokin da zan shimfida mana. Duk za ka san wadannan al'amura anan gaba kəfin ranar zuwanmu birninku ta zo. Mataki Da farko da za mu oi don cimma nasara b:sa wannan gagarimin aiki da ke gabanmu shi ne, doic mu baiwa juna horon yaki [ni da kai domin kowanncnmu ya kowa domin na koyar da kai abinda baka sani ba, kaima ka koyar da ni abinda ban sani ba. Ta haka ne san iyakar jarumtakar kadai zamu larwatsa Dakarun da ke tsaron wu kar Hirzul Subura Kuma mu sami nasarar a yakin da zamu je mu yi a Rasarku. iya hada karfi biyu wanda Mataki na biyu shi ne, dole ne mu ci gaba da tara nayaka wadanda ba za su gaza miliyan daya da rabi ba, kuma mu basu horon yaki irin wanda A kalla sai wadannan mayaka sun shafe Suna karbar wannan horo sannan za su kware ainun su Zama GUGUWAR ANNOBA mai shafe birni komai girmansa da karfin tsaronsa. Mataki na uku wanda shi ne na karshe kuma shi ne mafi hadari, dole ne mu kama Yarima Muraisu da hannunmu ya yin da muke yaki da su sannan mu kaishi kas mu tsaga kirjinsa mu ciro wannan gashin sihiri da ke jikinsa sannan ne burinka zai gama cika idan na sanya wannan gashin sihirin a cikin kirjinka yadda za ka iya zuwa dajin Kirzufa ka yi farauta a cikinsa kamar yadda mahaifinka ya yi har ya sami daukaka a duniya fiye da kowannc Sarki." nuke da shi. wata bakwai Sa'adda Sarki Ishmar yazo nan a zancensa sai hankalin Yarima Muraisu ya dugun Muraisu ya. dugunzuma saboda tunanin wasu al'amura guda biyar da suka fado masa a rai. Abu na farko shi ne, yanzu mece ce ribar Sarki Ishmar idan har ya taimaka mani na ci kasarmu da yaki, kuma na sarni damat shiga dajin Kirzuts? A bayaninsa bashi da wani buri wanda ya fi ya mallaki dajin Kirzufa, Babu yadda za ayi ya iya nallakat đajin Kirzufa face ya mallakí yashin sihirin mahaifina. Waninan yana nufin ke nan ba lallai bane idan ya ciro gashin sihirin a kirjin dan uwana ya mallaka mini ba. Ashe kuwa akwai alamun cewa Sarkí ya yaudarata, wato ya yí amfaní da ní don kawai ya biya bukatarsa, idan kuwa haka ne dole ne ya dauki tsattsauran matakí akan hakan," Huraisu na cikin wannan tunanin zuci ne shmar ya dafa kafadarsa ya ce, "Wai shin tunanin ne kakec yi ne haka ina ta nagana armma hankalínka ya tafi wani wurí? Huraisu ya yí firgigit kamar wanda ya farka daga barci sannan ya dubi Ishmar ya ce, "Ka yafarceni ya kai wannan Sarki, ka yi sani cewa hankalina ne ya dugunzuma bisa jin wadannan tsauraran matakai uku da zamu bi don ganin mun címma burinmu, ni kam guiwata ta fara yin sanyí, dornin ganí nake karmar ba zai yiwu ba," Koda jin wannan batu saí Sarkí Ishmar ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ai idan har mun bi wadannan matakai daí-daí tabbas bukata za ta biya. Yanzu sai ka tashi mu tafi na kaika izuwa masaukinka domin ka samí barci da isasshen hutu saboda gobe da sassafe zan turo a tashcka domín mu je filin motsa jini mu jarraba jarumtakar juna ni da kai". Koda jin wannan batu sai Yarima Huraisu dubi Sarki Ishmar ya yi masa murmushin mugunta sannan ya ce a ransa, "Ya zai hada jarumtakata da tasa kasance sa'an mahaifina. Lallai kuwa Zan nuna masa cewa sabon kashi da sabon jini ba dai-dai take da tsohon kashi ba ma za ayi wannan dattijon Ganin murmushin da Huraisu ya yi ne ya sa Sarki Ishmar ya yi zargin irin abinda Huraisu ya aiyana a ransa don haka sai shima va maida masa da mnartanin murmushin kuma ya ce a ransà, "Lallai yaro, yaro ne, domin bai san wuta ba sai va tabata da hannunsa. Tabbas sai na nunawa Huraisu cewar ko Zaki ya mutu gawarsa ta fi gaban wargi." Gama aiyana hakan ke da wuya sai Sarki Ishmar ya mike tsaye shima Huraisu sai ya mike tsayc suka kama harnun juna suka ice dana cikin dakin cin abincin, a sannan ne wadannan kuyangi guda dubu suka kwashe farantan abincin da ke kan tebur din suka fice a su zuciyoyinsu cike da takaicin an sa su sun dafa abincin da mutum dubu za su iya ci su koshi, amma gashi mutum biyu ne kacal suka taba dan kadan sai dai su je su ci iya Cinsu ragowar kuwa su zuba a shara. Kullum haka suke faman wannan aiki darc da rana, sbaoda wadatar da tayi musu yawa a gidan Sarautar. Lokacin da Sarki Ishmar da Yarima Huraisu suka baro cikin dakin cin abincin suka ci gaba da tafiya a cikin harabar gidan sai kwatsam! Suka hango wata: santaleliyar halitta abar kwatance daga necsa adan da ta nufo yaresu, fuskarta cike da annuri tana murmushi, wanda yasa tsigar jikin Yarima Huraisu ta tashi gaba daya ya tsaya cak a waje daya kuma ya Rame kamar gunki. Tunda Yarima Huraisu yazo duniya bai taba ganin tsaleliyar byaklyvwar budurwa ha ha kamar wannan. Kai ko a tarihi ko labaran duniya bai taba jin labarin mace mai kyau kamar na ta ba. Mace ce doguwa mai matsakaicin kaurin jiki, Kirjinta a cike yake, cikinta a shafe, kuma kugu mai fadi da matukar tudu daga Laya, grshin kanta baki ne sidik yana ta kyalkyali da shcki kuma ya zuba har kasan kwankwasonta. Idan tana tafiya sai ka ga kanuar dukkan gabban jikiría karyewa za su yi, domin ko ina motsawa yake. Fatar ¡ikinta fara ce sol irin farin nan mai kyau wanda babu ratsin komai, kuma tana sheki da taushi tamkar idan aka latse jini zai fito. Tun daga nesa kyakkyawar budurwa bude hannayenta biyu ta rugo izuwa ga rkr ishmar ta rungumeshi cikin farin ciki. Sarki Ishtaar ya janye jikinsa daga cikin na ta ya dubcta cikin damuwa ya ce, "Mene ne ya hanaki zuwA dakin cin abinci yau? Tun dazu ina tare da bakona a can har mun kammala cin abincin mun fito". Budurwar tayi murmushi ha kyawawan fararen hakorarta suka baiyana a fili ta ce, "Ka gafarceni ya: kai dana uwana, ka yi sani cewa jiya da daddarc na muka yi da kai wacce ta sa idanuna suka bushe, shi ya sa na yi ta barci har na makara ban fito da wuri ba". Sarki Ishmar "Ya ke ya yi murmushi ya ce, Husnaila rabin jikina, kin san cewa ba kya laifi a wajena koda kuwa kin karva dukkan dokokin da na kafe a garin nan, saboda haka ban ga dalilin da zai sa ki nemi gafarata ba. Yanzu zan raka bakona izuwa masaukinsa don haka ki je turakata ki zauna ki jirani Zan dawo mu tattauna muhimmanci." wani al'amari mai Cikin murna Husnaila ta juya ta nufi inda bangarcn turakar Sarki Ishmar take, ko kallon Yarima Huraisu ba ta yi ba, bare ma ta yi masa magana, tamkar ma ba ta san da shi ba a tsaye a wajen. Shi kuwa Huraisu tun sa'adda idanunsa suka yı arba da ita ya rude, ya kidime kuma ya dimauce ainun domin ji ya yi kamar an zare masa ransa gaba daya don haka sai ya kame kamar gunki kuma ya kura ma ta idanu ko kiftawa ba ya yi, har moa ya tafi duniyar tunani inda ya tsinci kansa a cikin wani kcrarren gida kuma akan wani luntsumemen gado shi da Gimbiya Husnaila suna morewa Soyayya. Yana cikin wannan tunani ne Sarki Ishmar ya girgiza kafadunsa ya dawo cikin haiyacin sa, sannan ya daka masa tsawa ya ce, "Koda wasa kada ka taba tunanin za ka kusanci wannan yar uwa tawa, domin ba: irin sauran 'yan matan da kake yiwa fyade bane a can Kasarku. Wannan kanwata ce uwa daya uba daya, kuma ita ce kadai ta rage mini a duniya. Ina sonta fiye da yadda nake son kaina, kuma na rantse da darajar iyaycnmu zan iya karar da dukkan mutanen wannan nahiyar tamu idan har aka taba lafiyarta ko mutuncinta. Duk wata alaka da ke tsakanina da kai za ta iya rushewa idan ka kuskura ka kusanceta. Abinda nake so da kai shi nc, ka dauka cewa a mafarki kuka hadu, mafarkin da har abada ba zai taba zama gaskiya ba. A karshe ina mai sanar da kai cewa kariwata Gimbiya Husnaila ba za ta yi aure ba kuma har ta bar duniya babu wani da namiji da ya isa ya santa 'ya mace koda kuwa bana numfashi a doron kasa, domin na cire ma ta sha'awar da namiji, kuma na tsareta da dukkan karfin sihirina na tsafi. Kai in takaice maka zan ce ko mutuwa tayi namijin kuda ma bai isa ya taba jikinta ba bare bil'adama ko aljan". Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya wuc gaba ya ci gaba da tafiya abinsa ya bar Yarima Huraisu a tsaye cikin tsananin mamakin wannan jawabi da ya yi masa. A sannan ne ya gano dalilin da ya sa Gimbiya Husnaila ta shareshi ya zamana cewa ko kallonsa bata yi ba a sa'adda suka hadu. Nan dai Sarki Ishmar ya kai Yarima Huraisu har masaukinsa inda suka yi sallama ya juya ya tafi ya barshi. Huraisu ya kunna kai izuwa cikin tafkeken: falon wanda Sarki Ishmar ya yi masa nuni a matsayin masaukinsa. Falo ne babba mai fadi da tsawo wanda ke shimfide da koren kilishi mai taushi, ga kujeru manya da kanana suma duka koraye. Kai hatta labulayen da aka sa a jikin tagogi da kokofi duk koraye ne, abin dai gwanin ban sha'awa. Da shigar Yarima Huraisu cikin wannan falo sai ya tsaya ya yi turus! Ba komai ne ya haddasa hakan ba face ganin abokan, wato manyan yaransa guda biyu Busaru da sadauki Rauhaz a kwance bisa wannan kilishi ga abinci nan a gabansu iri-iri birjik da 'ya'yan itatuwa sun ci sun bari. Sannan sai ya ga wadansu kuyangi guda shida a tare da su suna yi masu tausa. A can gcfe daya kuma wadansu kyawawan kuyangi ne guda goma a zaune waje daya suna jiransa domin su tayashi kwana. Kallo daya Yarima Huraisu ya yiwa kuyangin ya ji ko kadan baya bukatar su kusanceshi. Cikin hanzari Busaru da Rauhaz suka mike tsaye zumbur! Suka risina suka yi gaisuwa ga Yarima Rubaisu suna wadannan kuyangi gaba dayansu sai suka zube suka gaisheshi. Busaru ya yi gyaran murya ya cc, "Ya shugabana ga kuyangi nan masn tayaka barci suna jira, kuna akwai giya ganga-ganga guda a cikin dakinka an tanada Kafin Busaru ya gama rufe bakinsa sai Yarima Huraisu ya tari numfashinsa ya ce, Bana bukatar komai yanzu, zan shiga dakina na kwanta, kada kowa ya dameni Koda gama fadin haka sai Huraisu ya bude daki ya shiga ya kwanta akan wrani kasaitaccen gado wanda ke dauke da shimfida mai tudu da taushin gaske ya kwanta. Kwanciyarsa ke da wuya sai ya daga kansa sama ya kurawa rufin cakin ido. Nan take fuskar Gimbiya Husnaila ta baiyana akan rufin dakin, yaji wani farin ciki ya lullubeshi. Kawai kuma sai ya ga hoton fuskar ta ta ya Bace. A dimauce ya mike zaune daga kan gadon ya kama kalle-kalle a cikin dakin ko zai sakc ganin fuskar Husnaila a jikin bango ko a kasa, Nima kuma a dimauce Na tashi Na tuna cewa zanfita kasuwa sbd haka sai Anjima Likes and comments Zai bamu zummar cigabaa ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part D Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini Likes and comments Domin Mu cigaba Amma bai gani ba. Nan take ya gano cewa tsananin begenta nc ya sa ya ga kamar tana yi masa gizo. Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinsa ke nan domin shi a rayuwarsa bai taba yin soyayya ba kumna bai laba jin yana son wata 'ya mace ba face da lalata, amma sai gashi wannan karon yaji yana son ya mallaki Gimbiya Husnailaa matsayin matar da zai aura". Koda Huraisu ya luno da kashedin da Sarki Ishmar ya yi masa akan Husnaila da irin maganganun da ya shai ia masa sai hankalinsa ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi. Shi kam yanzu ya san cewa ba zai iya cire son Husnaila a zuciyarsa ba, kuma ba karamin tashin yankali ne ya ce zai nemi soyayyarta tunda ita ba ta ma san meye so ba, kuma ba ta taba yin soyayya ba. Huraisu ya ci pgaba da tunani cikin matukar damuwa har izuwa lokaci mai tsawo, daga bisani sai ya yanke hukuncin cewa ya yi hakuri har izuwa lokacin da zai zama Sarkin birnin Lairus, tabbas a sannan ne zai iya mallakar Gimbiya Husnaila ko da tsiya-tsiya tunda a sannan ma ya mallaki gashin sihirin da ke kirjin mahaifinsu, in kuwa ya mallaki wannan gashin sihirin ya san cewa babubwani tsafi da zai yi tasiri a kansa. Idan kuwa tsafi ba zai yi tasiri ba a jikinsa lallai ya fi karfin Sarki Ishmar. Koda Huraisu ya zo nan a tunaninsa sai ya cika da farin ciki ya ji kamar ma ya mallaki Gimbiya Husnaila ne. Kashe gari da sassafe bayan su Yarima Huraisu sun yi buda baki sai aka turo wani hadini ya yi musu jagora izuwa can filin motsa jiki. Wani katon fili ne mai tsawo da fadin gaske wanda aka kewayeshi da shingen karfe gaba dayansa, kasan filin an zuba ya shi mai taushi. Da isowar su Yarima Huraisu wannan fili sai suka iske Sarki Ishmar shi kadai a tsakiyar filin a tsaye ya yi gagarumar shigar yaki ta bakin sulke kuma ya rataya zabgegiyar takobi a bayansa. Sarki Ishmar ya dubi Yarima Huraisu ya ce, "Yau ne ranar da zamu fara bin matakin farko don samun nasara bisa bukatar da ke gabanmu. Ya kai Huraisu yanzu sai ka shigo Cikin wannan fli domin mu jarraba jarumtakar junanmu". Koda jin haka sai Huraisu ya yi murmushi ba tare da ya ce komai ba. Nan take ya cire alkyabbar da ke ikinsa ya zama daga shi sai doguwar riga da wando, sai kuma danarar da ya yi a kugun sa. Maimakon ya hude kofar shiga cikin filin ya shiga sai kawai ya daka wawan tsalle sama tamkar an cillashi, daga cikin baka ya dira a cikin filin nesa kadan da inda Sarki Ishmar ke tsaye. Nan fa suka fara kewaye juna suna kallon-kallo. Busara da sadauki Rauhaz suka gyara tsayuwarsu daga bayan filin domin su baiwa idanunsu abinci. Bayan Huraisu da Ishmar sun zagaya jauna kamar sau uku sai suka rugo da gudu izuwa kan juna. Sai da ya rage bai fi taku uku ba su hadu, sai kowannensu ya zare takobi, ai kuwa suna haduwa suka kacame da azababben yaki. Sai da suka shafe sa'a guda cur suna kaiwa junansu sara da suka amma dayansu bai sami nasarar koda yakusar jikin daya ba, kuma cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta suke yakin. Hakika sadaukantaka ta hadu da sadaukantaka, haka ma naci ya hau da naci. Da kansu suka rabu suka ja da baya, kowannesu ya kama haki kamar zakaru. Busara da sadauki Rauhaz kuwa basu san sa'adda suka kama yi mnusu tafi ba, domin su kansu sun san an yi jarumtakar da ta wuce saninsu. Bayan yan dakiku kadan sai Sarki Ishmar va dubi Yarima Huraisu ya yi murmushi ya ce, "Tabbas ka cika jarumi juriya. Yanzu kuma zan sauya salon fada domin na nuna maka cewa ni tsohon hannu ne kuma na fi ka kwarewa da Sanin makamna tunda na kara da mabaifinka ma bai sami nasara akaina ba. Duk sa'adda muka hadu sai dai mu yi jarumi ma'abocin jarumtaka da KARE JINI, BIRI JINI." Koda jin haka sai shima Huraisu ya yi murmushi sannan ya ce, "Tabbas na yarda ka fimi kwarevwa kuma na yarda cewa jarumtakarka tafi tawa tunda har kwanan gobe ni ban isa na kara da mahaifina ba, duk da cewa tsufa ya kamashi, amma zan nuna mmaka ccwa dole ne mahaifina ya fika iarumtaka da juriya, lallai sa'adda kuke haduwa in dai za ku yi gaba da gaba har tsawon sa'a guda Sa'adda Sarki Ishmar yaji wannan batu sai ransa ya sai ya hallakaka. " baci zuciyarsa ta kufulo, ya kasa cewa komai domin ya san cewa abinda Huraisu ya fadi gaskiya ne. Kawai sai ya sake rugawa izuwa kan Huraisu ya rufeshi da SARA DA SUKA cikin sabon salon yaki. Wannan karon dai tsalie-tsalle Ishmar ya kama yi yana shawagi a saman Huraisu tamkar tsuntsu mai fuka-fuki. Nan da nan kuwa Ishmar ya rikita Huraisu ya zamana cewa baya iya inai da martani sai dai kare hari. Koda Ishmar ya ga ya sami wannan nasara sai ya kara ZAGE DANTSE ya dada kuntatashi har ma ya sami nasarar yankarsa akan kirji. Duk da cewa yankan bai yi zurfi ba, amma sai da jini yai feshi. Koda Huraisu ya shafa kirjinsa ya ga jini kuma cewa rigarsa ta yage sai ransa ya baci, zuciyarsa kufulo, kawai sai ya ja d baya ya kama rigar tasa ya ketata gida biyu ya yi wurgi da ita. Kawai sai ya ruke takobinsa da hannu biyu sannan ya fuskanci Sarki Ishmar ya yi masa inkiya da ya sake kawo masa hari. Ai kuwa sai Ishmar ya ka bi tayin nasa ya rugo gareshi da gudu. Maimakon ya tsaya jiransa sai shima ya ruga kansa da gudu. Koda ya rage bai fi taku uku ba su hadu sai kowannensu ya daka tsallc suka hadu a sarma. Ishmar ya kaiwa Huraisu wawan sara a kafada ya goce cikin zafin nana amma duk da haka sai da takobin ta shafi jikinsa aka yi sa'a bata yankeshi ba, amma ta sarce gasin kirjinsa tamkar zabira aka sa aka askeshi. Shi kuwa Huraisu a cinya ya kaiwa Ishmar sara, maimakon takobin ta nutse a cikin cinyar sai ta shafci kadan daga cikin tsokar naman, jini yai tsartuwa. Tun a sarnan Sarki Ishmar ya kwalla ihu sakanakon tsananin zafi da zogin da yaji, amma yana durowa kasa sai yai sauri ya cire rawaninsa ya dauure raunin don tsaida jinin sannan ya sake afkawa Huraisu da dukkan karfinsa da zafin namansa kai ka ce da mutum dubu yake fada shi kadai. Sai da suka shafe sa'a daya da rabi suna gumurzu a wannan karon, gumurzu na tashin hankali wanda ya firgita 'yan kallon nasu domin gani suke yi cewa lallai a ko yaushe dayansu zai iya rasa rayuwarsa donin dukkaninsu neman hallaka juna suke Kamar hadin baki sai duk su biyun suka ja da baya suka tsaya cak! ga barin yakar juna sannan kuma sai suka bushe da dariya a lokaci guda, suka rungume juna. Sarki Ishmar ne ya fara janye jikinsa daga cikin na Huraisu ya dubeshi ya ce, "Hakika yanzu na gamsu cewa kai abokin tafiya nc, kuma albasa tayi halin uwa, domin ka gado wani abu daga cikin jarumtakar mahaifinka. Yanzu bani da wata fargaba akan matakinmu na farko domin nà san cewa idan muka hada KARFI DA KARFE ni da kai zamu iya kai Yarima Muraisu kas. Abu na biyu da zamu yi yanzu shi ne, mu tafi izuwa can gidanka domin mnu fara hada rundunar mayakan da zamu tafi da su yaki can kasarku. A kalla wannan aiki zai daukemu tsawon wata shida kafin mu kammalashi, domin ba zamu tafi wannan yaki ba da Dakaru kasa da miliyan biyu, kuma dole ne mu basu horon yaki na musamman irin wanda zai sa zuciyarsu ta kekashe ga barin tsoron komai. Tuni na aika da wasikar gayyata izuwa ga wadansu manyan sarakuna a wannan nahiya tamu wadanda suka kasance abokaina kuma aminaina na neman gudunmawar Dakarun yaki a wajensu kuma sun tabbatar min da cewa za su bani hadin kai dari bisa dari. Yanzu gobe da sassafe zan sake aikawa da wasiku ga wadannan Sarakuna na sanar da su cewa su turo mini Dakarun izuwa can gidanka mu samesu a can ko kuma su su samemu a can " Sa'adda Sarki shmar ya zo nan a zancensa sai Yarima Huraisu ya yi ajiyar zuciya ya ce, "To yanzu vaushe ne kuma za mu je mu dauko wukar Hirzul Subura." Koda jin wannan tambaya sai Sarki Ishmnar ya bushe da dariya sannan ya ce, "Ni kuwa dadina da kai ke nan ka cika hanzari a cikin al'amuranka. Kada ka damu kafin mu gama baiwa Dakarunmu horon yaki za mu je mu dauko wukar Hirzul Subura". Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya yi nuni da hannunsa na hagu izuwa ga raunin da ke cinyarsa wanda bai taba wanzuwa ba. Al'amarin da ya matukar baiwa Huraisu mamaki ke nan domin ya san cewa aikin tsafi ne kawai wannan". Koda Sarki Ishmar ya fahimci cewa Huraisu ya yi mamakin abinda ya faru sai ya bushe da dariya sannan ya sake nuna raunin da ke jikin Huraisu. Take shima na sa raunin ya warke sumul. Kawai sai ya kama hannunsa ya jashi suka fice daga cikin fillin motsa jinin suka nufi cikin gidan sarautar. Busara da sadauki Rauhaz suka take musu baya. Wannan shi ne abinda va faru a birnin Hutaira bayan Yarima Huraisu yaje ncmi hadin kan Sarki Ishnar domin ya biya bukatarsa ta ganin ya mallaki birnin Lairus. A CAN birnin Lain:s kuwa, lokacin da Sarki Salmar ya kamu da cutar ajali va kwanta ciwo sai hankalin Yarima IHuraisu ya dugunzuma ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya har ta kai cewa bashi da sukuni dare da rana, kuma baya iya cin abinci sosai baya saraun isasshen barci, al'amarin da ya janyo ya dinga ramewa ke nan tankar shima bashi da lafiya. Ba komai ne ya jefashi a cikin wannan mugun hali ba face ganin yadda ciwo nai zai ya kama mahaifin nasa a kankanin lokaci har ta kai cewa bakinsa ya kulle baya iya yin magana. Idanunsa sun rufe baya ganin komai ku.ma baya iya yin komai da kansa sai dai ayi masa. Bara Yarima Muraisu ba, gaba dayan jama'ar kasar Iarus birni da kauye sai da hankalinsu ya dugunzumna ainun bisa jin halin da Sarkinsu ya shiga saboda sun san cewa shi nc babban katangarsu wacce ta hana makiya yi musu dirar mikiya. Tabbas duk. ranar da aka ce babu Sarki Salmar to fa babu cikakkn tsaro a birnin duk da cewa an san akwai halifansa, wato Yarima Muraisu saboda kowa ya yarda da jarumtakar Sarki Saimar wacce tafi gaban tunani kuma kowa ya san kwarewarsa a yaki da kuma tsabar sa'arsa ta tsawon shckara da shekaru. Kullum Yarima Muraisu na zaune a gaban gadon Sarki Salmar yana kallonsa yana zub da hawaye domin a duniya babu mnutumin da ake shakka sama da Sarki Salmar tunda kusan shire ya renesu tun suna yara shi da Huaisu kamar yadda uwa ke rainon danta. Sabo da tsananin Raunar da Sark Salmar ke yiwa Muraisu da Huraisu hatta wanka da tsarkin kashi shi yake yi musu da kansa tun suna jarirai har suka rirma suka iya yin komai da kansu bai taba bari kuyangi da barori sun yi musu ba. Sai da Sarki Salmar ya kwana talatin da tara a kan gado yana jinya ba. A daren kwana na talatin da taran ne, Huraisu na zaune akan kujera dab da gadon Sarki ya fara gyan-gyadin dole bai sani ba sakamakon bashin barci da ya dauka na tsawon kwana biyu, kawai sai yaji an dafa cinyarsa. A firgice Muraisu ya farka daga barcin, sai ya ga ashe Sarki ne ya dafashi har ma ya kura masa ido hawaye na shatata bisa kumatunsa. Saboda tsananin murna da mamaki sai Muraisu ya yunkura da nufin ya rungume Sarki, armma sai Sarki Salmar yz daga masa hannu yana mai yi masa nuni da ya dakata. Muraisu ya koma kan kujerarsa ya zauna ya ci gaba da kallon Sarki a cikin nutsuwa domin ya ji abinda zai fito daga bakinsa. Sarki Salmar ya budi baki da kyr ya ce, "Ya kai dana, kayi sani cewa wannan sauki da na samu ba sauki bane na samun lafiya, tabbas sauki ne yazo mini dormin mu yi bankwanan karshe. Tabbas tawa ta kare domin zan iya mutuwa a cikin kowacce sa'a ko dakika mai zuwa nan gaba ko kuma a cikin yini ko kwana ko wata. Wata kila ma shekara, bani da tabbaci dai. Kafin na ce da kai komai yanzu ina son ka tashi ka garzaya gidan boka Rafyan yanzu-yanzu ka ce da shi ya zo ina son ganinsa." Cikin tsananin damuwa Yarima Muraisu ya mike tsaye jikinsa a sanyaye kamar zai fashe da kuka domin gani yake kamar idan ya tafi gidan bo ka Rafyan kafin ya dawo Sarki ya mutu. Haka dai ya daure ya tafi. Cikin gudu Muraisu ya isa gidan Boka Rufyan ya isar da sako. Nan da nan kuwa suka juyo suka dawo gidan sarauta suka shiga cikin turakar Sarki. Koda Sarki Salmar ya yi arba da boka Rufyan sai ya yunkura da kyar ya juyo da fuskarsa sosai ya fuskancesu, su kuma sai suka yi sauri suka zauna a gabansa suka fuskanceshi. Sarki Salmar ya kama hannun boka Rufyan ya rikeshi gam a cikin nasa sannan ya ce, "Ya kai amintaccen bokana gaya mini iyakar gaskiya kamnar yadda ka shaida mini a baya kimanin shekaru ashirin da biyar da suka gabata. Mene ne zai faru bayan mutuwata anan birnin Lairus?" Koda jin wannan umarni sai boka Rafyan yai tsuru-tsuru yai shiru bai ce komai ba, ya dinga raba idanu tsakanin Sarki da Yarima. Koda ganin haka sai Yarima Muraisu ya dakawa boka Rufyan tsawa ya ce"Saboda me za ka tsaya kana Jinkiri bisa bin umarnin mahaifina, ko kuwa don ka ga vana kwance nea cikin wannan hali?" Sa'adda boka Rufyan yaji wannan tambaya sai hawaye ya zubo masa sannan ya dubi Sarki cikin matukar damuwa ya risina ya ce, "Ya shugabana shin ka mantane cewa mun yi alkawarin cewa ko ni ko kai dayanmu ba zai tona wannan sirri ba, saboda mc yanzu ka sauya shawara?". Koda jin wannar tambaya sai hawaye ya sake zubowa Sarki Salmar ya cc, "Ai dole ne na sauya shawara tunda bakin al kalami ya bushe ko mun baiyana ko bamu baiyana ba sai wannan al'amari ya faru, kuma ka sani cewa idan ba mu yiwa Y arima bayani ba tun yanzu to fa asarar da za ayi ta rayuka da dukiya sai ta wuce yadda duk ake zato. Na umarceka da ka hanzarta yi masa bayanin komai tun kafin an koma cikin mugun halin da na kasance n rashin' gani da kasa yin magana". Koda jin wannan batu sai boka Rufyan yai shiru isawon 'yan dakiku bai ce komai ba. Dega can kuma sai ya dubi Yarima Muraisu cikin nutsuwa ya ce, "Ya kai gwarzon jarumi magajin ubansa, ka yi sani cewa bayan rasuwar mahaifinka mummunan yaki zai 6arke anan kasar wanda babu mai iya kare rayukan jama'a da dukiyarmu. Tabbas sai an cimu da yaki, kuma ba wani bane zai kawo wannan yakin ba face dan uwanka Yarima Huraisu. A yanzu iaka Yarima Huraisu ya bar nan kasar gaba daya, ya jevcan ya hada kai da makiyanmu suna hada rundunar mayakaa ta mutane masu yawan gaske wadanda Za su yakemu. Tabbas nan da wani lokaci burinsu zai cíka burinmu". Koda boka Rufyan ya zo nan a zancensa sai Yarima Muraisu Ya tari nun:fashinsa ya cc,Tunda dai Yanzu an san da haka me zai hana sarki yayi mini izini na debi dakaru masu yawa mu tafi har can sansanin su huraisu mu yakesu shida wadanda suka hada kai mu kawar da su?", Caraf! sai Sarki Salmar ya ce, "Shin ka manta ne cewa wannan abu da zai samcmu kaddara ce kuma bamu isa mu kaucewa kadiara ba? Babu makawa sai an cimu da yaki, lallai babu abin da za mu iya yi face kawai mu yi kokari mu rage asarar da za ta samemu. Ya kai Rufyan yanzu mcne re abin yi?" Boka Rufyan yai shiru yana mai sunkui da kansa kas tamkar mai daukar karatu ashe tunani da bincike yake yi a cikin hallarar tsafir.sa. Tsawon lokaci bai ce komai ba, can kuma sai ya dago kai ya dubi Sarki Salmar ya ce, "a shugabana idan har muna son mu rage asarar rayuka da ta dukiya da za ta biyo baya dole ne Yarima Muraisu ya gaggauta yin aure a cikin watannin da basu wuce biyu zuwa uku ba, kuma dole ne matar da zai aura ta zamo daga cikin zuri'ar abokan gabarmu. Lallai idan ya yi wannan aure zai sami haihuwa da ita kafin zuwan ranar da warnan yaki zai Zo kuma Allbarkacin dan da za su haifa ne ita da dubunnan daruruwan mutane za su iya yin ayari guda su yi gudun hijira su bar winnan kasa tamu. Suma ba Zai yiyu ba dukkaninsu su tsira da rayuwarsu da dukiyoyinsu ba face sun isa dajin Kirzufa." Sa'adda Boka Rafyan yazo nan a zancensa Sal Yarima Muraisu ya cika da tsananin mamaki ya dubeshi cikin tsananin damuwa ya ce, "Yanzu ta yaya zan auri 'yar abokan gabar mu a cikin wannan yanayi da mahaifina ke ciki? A ina ma zan ga 'yar abokan Gabar tamu har na aureta alhalin bani da lokacin da zan tafi ko ina?" Boka Rufyan ya tari numfashin Muraisu ya ce, "Ai kuwa zema bai samcka ba dole ne ka mike ka yi shiri ka bazama neman matar da za ka aura. Kuma bincike ya nuna cewa ta hanyar farauta za ka hadu da sirikarmu wacce za ta zamo uwar dan da zai gaji sarautar kasar nan a nan gaba, wanda shi kadai ne zai iya karbar mulkin da za a kwace daga hannunmu da karfin tsiya. Bincike ya dada tabbatar da cewa baka da sasshen lokaci na zama a gida, ya zama wajibi ka gaggauta shirin fita farauta a daji idan har muna son wannan bukata tamu ta biya Sa'adda Boka Rufyan yazo nan a jawabinsa sai hankalin Yarima Muraisu ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, saboda jin cewa dole ne ya yi shiru ya fita farauta a wannan wannan lokaci da Sarki ke tsakanin MUTUWA DA RAYUWA. Nan take hawaye ya subutowa Muraisu ya durkusa a gaban Sarki ya đora kansa akan cinyarsa. Sarki Salmar ya đaga hannunsa na dama da kyar ya dora akan Muraisu yana wasa da gashin kansa a lokacin ne shima hawaye ya kubuce masa domin yana Ji yana gani zai rabu da babban masoyinsa a duniya. Hakika ko a mafarki Sarki Salmar bai taba Tunanian cewa wannan rana za ta zo masa ba a rayuwa. Shi kansa boka Rufyan saadda ya ga Sarki da dansa suna zubar da hawaye sakamakon wannan rabuwa ta dole da za su yi sai da ya kamu da tsananin tausayinsu, domin ya san irin shakuwar da ke tsakaninsu ta fi gaban kwatance. Boka Rufyan ya mike tsaye sannan ya ce, "Ya kai Yarima Muraisu, ka tashi ka je ka fara shirye shiryen wannan tafiya da za ka yi gobe, kuma ka tabbatar da cewa ka dawo gida a cikin kwanakin da basu haura arba'in ba tare da matar da za ka aura." Da jin haka sai Muraisu ya mike zumbur! ya dubi boka Rufyan cikin rashin fahimta da damuwa ya ce, "To wai shin yanzu wane daji zan je na yi farautar har na hadu da wannan mace wadda zan aura, kuma ya za a yi na san ita ce wadda zan aura din? Wai shin ma ta ya ya za ta amince da ni har ta biyoni nan birnin mu zo a daura mana aure?" Koda jin wadannan tambayoyi sai boka Rufyan ya ce, "Amsar wadannan wannan tafiya da za ka yi. Amma a yanzu duk duniya babu wani boka da ya isa ya baka amsar komai bincikensa da matsayin a hallarar tsafi........ To NimA dai Bari Naje FarautAr Yarinyar da Zan aura Daga India Ko zata Amince Ta Biyoni Gida Nigeria hhhhhhh Anan Zan Dakata Saikuma Wani lokaci Insha Allah ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part E. Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini babu wani boka da ya isa ya baka amsar komai binciken sa da matsayin sa a hallarar tsafi". Koda gama fadin haka sai boka Rufyan ya juyo sosai ya risina ga Sarki ya cc, "Na barka lafiya ya shugabana. " Nan take ya juya ya fice. Har Muraisu ya yi yunkurin ya sake zama a gaban Sarki sai ya yi masa nuni da cewar ya tashí yajc ya fara shiryc-shiryen tafīya. Cikin sanyin jiki Yarima Muraisu ya juya ya nufi kofar fita. Har ya sa kafarsa guda wajen kofar sai ya kira sunansa ya waigo suka dubi juna. Sarki ya yi masa wani dan guntun murmushi, ya ce, "Kafin ka tafi a goben ka zo mu yi sallama domin na baka gudunmawata ta kariya, domin ba lallai bane ka dawo ba ka riskeni a rayc". Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta karaya, nan da nan idanunsa suka ciko da kwalla amma sai ya daure ya juya ya fice daga cikin urakar zuciyarsa cike da sake-sake yana mai cewa a ransa, "To wai shin wacce irin kariya Sarki zai bashi alhalin ya yarda da kansa kuma ya san zai iya kare kansa daga kowacce irin masifa?". Tun da Yarima Muraisu ya bar turakar Sarki ya koma tasa sai ya kasa zaune ko tsaye, tunani da fargaba suka cika masa zuciya. A haka dai ya samu ya Byara kayau yakinsa kuma ya kimtsa kayayyakinsa Wadanda zai yi wannan afiya da su. A sannan ne ya zauna ya yi tagumi ya shiga sabon tunani. Abinda y fara fada masaa rai shi nc wai shin waccc irin sabuwar rayuwa ce ne ta zo masa haka? Ya ya shu da bai taba yin soyayya ba, bai ta6a magana da budurwa ba ta tsawon dakiku za a cc da shi ya tafi neman wadda zai aura a lokaci guda haka?" Muraisu ya sake zurfafawa a tunaninsa sai ya fahimci cewa akwai alamun cewa wannan sabon yanayin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki yana da matukar rikitarwa da tashin hankali domin ya fahimci cewaa lokacin da zai rasa komai da kowa nasa ne ya zo tunda an cc lallai za a ci su da yaki. To abin tambaya anan shi ne shi yana ina har za a zo a cisu da yaki? Abinda ya yi imani da shi shi ne, idan har za cisu da yaki, tabbas baya nunfashia doron kasa. Muraisu na cikin wannan hali hali ne wata Kuyangarsa mai kula da abincinsa ta shigo cikin turakar ta ajiye masa abinci da ruwan inibi a cikin tambulan da kofi a gabansa. Maimakon ta juya ta fita sai ta zauna a gefe daya ta zuba masa ido kawai. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan domin sama da shekara bakwai kenan wannan Kuyanga tana yi masa wannan bauta amma duk sa'adda ta kawo masa abinci ajiyewa take ta fita. Hasali ma basu ta6a yin magana ba da juna a tsawon shckarun zamansa da ita. Ita dai wannan Kuyanga kyakkyawa ce sosai kuma launin fatar jikinta ruwan kasa ne mai ban sha'awa, sannan akwai kuruciya a tare da ita, domin sa'adda ma ta fara yiwa Muraisu bauta ba ta fi shekara goma ba a duniya, don haka yanzu tana da shckara goma sha bakwai ne kacal, kuma ana kiranta da suna Sabirat. Lokacin da Yarima Muraisu ya ga Sabirat ta zauna kuma ta Kura jnasa idanu sai ya daka ma ta tsawa ya ce, "Ke kuma fa, lafiya, akan wane dalili za ki zauna mini a cikin turakata?". "Ka Cikin firgici Sabirat ta mike tsaye zumbur! sannan ta durkusa bisa gwiwoyinta ta ce, gafarceni ya shugaban a, Sarki ne ya ce lallai yau idan na kawo maka abinci kada na fita sai na tabbatar ka ci ka sha tukunna sannan na korna na bashi labari". Koda jin wannarı batu sai Yarima Muraisu yaji wari irin dadi ya shigeshi, bai san sa'adda ya sakia murmushi ba ga Sabirat. Wannan shi ne karo na farko da ta taba ganin ya yi ma ta murmushi a iya tsawon rayuwarta da shi. Shi dai Yarima Muraisu ko kadan mace bata dameshi ba, domin ba a taba ganian ranar da ya bukaci wata baiwa ba ko Kuyanga, kai har ma wasu suna zargin ko bashi da cikakkiyar lafiya. Babu abinda ya sa a gabansa kullum dare da rana face horar da kansa yaki da kuma yin ladabi da biyayya ga Sarki yana gudanar da duk aikin da aka umarceshi da yi. Lokacin da Kuyanga Sabirat ta ga Yarima Muraisu ya dubeta har ya yi ma ta murmushi sai hankalinta ya kwanta ta mikc tsam daf da shi ta zauna yadda har suna iya jin num fashin juna ta ce, "Shin ka yi mani izini na civar da kai da hannuna? Maimakon ya ba ta amsa sai ya dubcta kawai ya sake yin murmushi. Nan take Sabirat ta dinga đebo abincin tana bashi a baki. Fara hakan ke da wuya sai ta ga hawaye ya zubo masa, al'amarin da ya matukar girgiza ma ta hankali ke nan ta firgita ainun ta ce, "Ya shugabana ka yafeni, idan wannan abu da na yi maka ya bata ma ka rai?" Da jin haka sai Muraisu ya yi mnurmushi sannan ya dubeta ya ce, "Mene ne sunanki?" Cikin matukar mamaki ta ce, "Sunana Sabirat." Ba komai ne ya sa Sabirat tayi mamakin jin wannan tambaya ba face sanin cewa bata da matsayin da zai tambayi sunan na ta kuma ta san lallai bai sani ba, tunda a shi da wani amfani a wajensa. Muraisu ya sake yin murmushi a karo na biyu a gareta, sannan ya sa hannu ya share hawayen da ke zuba a idonsa ya ce, Ya ke Sabirat kiyi sani cewa a iya sanina ke ce mutumn na biyu a duniya wanda ya taba ciyar da ni a hannunsa. Mahaifina shi ne mutum na farko. ba wani abu bane ya sa ni kika ga ina zubar da wannan hawaye ba face na tuna cewa a rayuwata ban san dadin uwa ba, tun ina jariri ta mutu ta barni. Mahaifina ne ya ci gaba da renona har na girma, yau gashi shima mutuwa za ta rabamu a ko yaushe daga yanzu. Yanzu an umarceni da na fita neman matar da zan aura gobe, kuma zan tafi na bar mahaifina a cikin wannan hali na matsanaiciyar rashin lafiya. Bani da tabbacin zan dawo na sameshi a rave. bani da tabbacin zan zamo abinda zan tafi nema, Shin mene ne karshen rayuwata? Ga dukkan alamu zan rasa komai da kowa ke nan tunda dan uwana ma guda daya da ya rage mini ya zama abokin gabata, kuma ya gujeni. Ashe haka rayuwa take da rashin dadi idan mutum ya rasa masoyi?" Sa'adad Yarima Muraisu yazo nan a zancensa, Sal Kuyanga Sabirat taji ta kamu da tsananin tausayinsa, bata san sa'adda ta rungumeshi ba, suka fadi kasa, kawai sai ta shiga shafar gashin kansa. Ashe abinda ta bashi ya ci akwai banju a ciki. Nan take kuwa barci ya kusanceshi, cikin tsananin farin ciki ta mike tsaye ta kura masa idanu. Nan take taji ta kamu da tsananin kaunarsa, domin shi ne da namiji da ta taba runguma a rayuwarta a lokacin da balaga ta zo ma ta. Kasancewar babu inda tayi bauta face a wajensa, kuma musaranan Sarki Salmar yasa aka siya ma sa ita domin ta rinka debe masa kewa, kuma ya yi saboda ita tunda tun tana karama aka siyota, shima a lokacin bai fi shekara ashirin ba a duniya, amma sai gashi bai yi sabon da ita ba, kai ko sunanta ma bai taba sani ba sai a yau din nan. Lokacin da Kuyanga Sabirat ta kurawa Yarima Muraisu idanu sai ta ce a cikin ranta, "Hakika duk macen da ta auri Yarima ta garma morewa, dormin duK abinda mace take so akwai a tarcd a shi. Ga kywawan halaye, kuma gashi dan Sarki. Ina ma dai a ce ni ce matar aurcn da zai tafi ncma a gobc. hakika da na Zama tauraruwa a cikin matan wannan zamani. Koda gama fadin haka sai Sabirat ta tafi da baya da baya ta fice daga cikin turakar tana kallon Yarima kamar za ta fasa fitar ta koma ta zauna a gabansa. Fitarta ke da wuya sai ta wucc kai tsayc izuwa turakar Sarki Salmar. Da shigarta sai ta iske an gyarawa Sarki kwanciya, wannan karon an sanya bayansa bisa matashin kai an jinginashi da jikin gadon shi ba a kwance ba kuma shi ba a zaunc ba. A wannan lokaci akwai hadimai hudu a cikin turakar, biyu maza, biyu ma ta. Koda Sarki ya ga shigowar Kuyanga Sabirat sai ya ce da wadannan hadimai su fita su basu wuri. Nan take kuwa Hadiman suka fice suka turo kofar dakin ya zamana cewa saura su biyu kacala cikin fakin. Sarki Salmar ya daga hannunsa da kyar ya yafito Sabirat yana mai yi ma ta nuni da ta zo ta zauna daf da shi. Cikin hanzari taje ta zauna a gefen gadon da yake kwance suka kuawa juna ido, sannan ya ce, "Ya ke Sabirat bani labarin abinda ya faru tsakaninki da dana iyakar gaskiya". Ba tare da ta boye komai ba Sabirat ta zaiyane masa komai. K.oda gama jin hakan sai Sarki ajiyar zZuciya sannan ya dubi Sabirat cikin alamun tausayawa ya ce, "Yarinya buki da rabo, inda ace baki zuba masa banjua cikin vannan abincin ba, sai a cikin ruwan inibi da sa'adda kica rungumeshi din nan ku ka fadi kasa kika rinka shafar gashin kansa da tabbas sai ya tara da ke, duk macen da dana ya fara tarawa da ita sai ta sami juna biyu da shi. ldan kuwa haka ta faru sai na 'yantaki kin aureshi, kn ga ke nan da tafiyar da zai yi gobe an fasa yin ta, kin ga ke nan abin da za ki haifa shi ne anan gaba zai gaji sarautar garin na. Tashi ki tafi, amma ki sani cewa gobe kina daga cikin mutum uku wadande za su yiwa Yarima rakiya izuwa taftya Deman matar da zai aure. Maganata ta karshe a gareki ita ce, idan kin rayu nan gaba, ki zamo bai kula da ikana da za a haifa, ni kuma ladan da zan biyaki da shi mai tsoka ne, amma ba zai zo hannunki ba sai bayan jikana ya dawo nan birnin ya karbi kujerarsa ta mulki". Sa'adda Sarki Sainar ya zo nan a zancensa sai Kuyanga Sabirat ta cika. da mamaki kuma ta kasa fahimtar abinda ya ke nuii, ta ce a ranta, "To mene ne zai sa jikan naka ya tafi wani wuri sannan kumna ya sake dawowa ya karbi karagar tasa?" Nan dai Sabirat ta mike tsam! Ta fice daga cikin turakar Sarki zuciyarta cike da tsananin bakin ciki bisa damar da ta subuce ma ta ta zama matar Yarirna Muraisu. Kashe gari da sassafe Yarima Muraisu ya yi wanka ya kintsa. Yanafitowa daga wanka ya iske abincin kalacinsa a aiive inda aka saba ajiye masa, amma bai ga mai kawo abincin ba, wato Kuyanga Sabirat. Har ya yi nufin ya kwala ma ta kira ta zo domin ya tambayeta yadda aka yi ya yi barci a jiya da daddare nan da nan cikin dakiku kadan, sai kuma ya fasa. Nan dai ya zauna ya ci abincinsa, da ya kammala sai ya dauko damararsa ta yaki ya daura, ya kwashi dukkan kayan farautarsa sannan ya fita domin yaje turakar Sarki su yi sallama. Lokacin da Yarima Muraisu ya shiga cikin turakar Sarki sai ya iske boka Rufyan, Kuyanga Sabirat da wani barde wai shi Kurzal zaune a gefe daya. Al'amarin da ya matukar ba shi mamaki ke nan, domin bai ga abinda suke yi ba a turakar Sarki a wannan lokaci. Shi dai Kurzal, wani kwararren masanin hanya ne da daji, ko kunnensa ya kara bisa kasa yana iya gane abinda ya wuce a kanta sama da tsawon sa'a guda. Duk irin sawun da ya gani a kan kas, walau na mutum, aljan ko dabba yana iya shaidashi ya yi bayani a kansa. Idan ya kallo hanya yana iya fadin inda za ta kai mutum, walau wajen da za a riski ruwa, tsauni ko bishiyoyi ko duhuwa. A zamanin da Sarki Salmar ke fita farauta daji duk sa'adda zai fita tare da Kurzal yake fita. Idan kuwa Kurzal bashi da lafiya sai dai shima ya fasa fita farautar. Kai tsaye Yarima Muraisu ya nufi gadon da Sarki ke kwance. Da zuwa sai ya sumbaci goshin Sarki, a lokacin ne yaji jikin Sarki ya dume da zafin zazza6i gaba daya. Al'amarin da ya matukar daga hankalinsa ke nan, ya zauna daf da shi ya rike hannunsa a lokacin da suka kurawa juna ido, kowannensu sai kwalla ta cika masa idanu. Sarki Salmar ya budi baki ya ce, "Ya kai dana kayi sani cewa yau ne babbar rana ta bakin ciki a gareni, saboda abu ne mawuyaci mu sake jin muryar Juna daga yau. Haka kuma, yau ne babbar rana ta farin ciki a gareni, domin kana daf da taka babban matsayi irin wanda na taka a rayuwata. Wadannan mutane uku da ka gani yanzu tare da mu su ne za su yi maka rakiya a cikin wannan tafiya da za ka yi, wacce nake son ka je ka dawo a cikin kwanaki arba'in cif-cif. Hakika duk Su ukun Suna da matukar muhimmanci da amfani, amma ba za ka san hakan ba sai kun yi tafiyar." Sarki ya juyo da fuskarsa ya dubi Boka Rufyan, zal ya ce, "Ku yi mini a dana bisa amana". Je, "Mun yi alkawari za Kuyanga Sabirat da Barde alkawari cewa za ku Cikin hadin baki su ukun. mu yi iya kokarinmu wajen kare rayuwar Yarima daga dukkan abin ki". Koda jin haka sai Sarki ya yi guntun murmushi sannan ya ce, "Shi ke nan, ku fita ku bani wuri zan gana da dana, kuma ina son ku rufe marna kofa da dukkan tagogin turakar ran". Ba tare da gardamar komai be su Boka Ruf'an suka cika wannan umarni. A sannan ne Sarki ya dubi Muraisu ya ce, "Bude bakinka ya kai dana". Ta ke Muraisu ya bi umami ya bude bakinsa, shima Sarki Salmar sai ye bude nasa bakin, kawai sai wani silin gashi guda daya tamkar na wuyan doki ya fito daga cikin bakin Sarki ya shiga cikin bakin Muraisu. Faruwar hakan ke da wuya sai Muraisu vaji wanı Iin gagarumin karfi ya shigeshi irin wanda bai taba jin kamar sa ba a rayuwarsa. A sannan ne Sarki Salmar ya turnuke da matsanaicin tari A dimauce Yarima Muraisu ya yi saurin zuba ruwa a kofin zinarc ya baiwa Sarki ya sha, sannan farin da yakc yi ya lafa. Tsawon 'yan dakiku suka ci gaba da kallon juna sannan Sarki Salmar ya yi ajiyar nunfa shi kamar wanda ya farfado daga dogon suma, ya ce, "Ya kai dana kayi sani cewa daga yanzu habu wani sihirin tsafi da zai yi tasiri a jikinka, kuma babu wani daji wanda ba za ka iya shigarsa ba. Babu wala jarumt:aka da ba za ka iya yinta ba. Amma idan makiyanka guda biyu suka hada karfi za su iya kaika kas su rabaka da wannan sihiri da na baka a yanzu. A sannan ne za a ci birninmu da yaki ayi masa ado da jini da gawarwaki. Abinda za ka yi kawai kafin makiya su kai ka kas shi ne, ka tabibalar da cewa ka tscrara da rayuwar matarka da wadansu daga cikin jama armu domin kada a shafemu a doron kasa mu zama Tarihii... Nima Zan dakata anan Sai kuma wani lokaci insha Allah ßµŠÅ Ä MµTµ Littafi Na Daya (1) Part F. Karshen Littafi Na (1) Marubucin Littafin Abdulaziz Sani M/Gini matarka da wadansu daga cikin jama'armu domin kada a shafemu a doron kasa inu zama tarihi. Wannan shi ne kalamina na karshe a garcka. Sauran bayani za ka įi a ɔakin Boka Rufyan. Ina mai yi maka fatan sa'a da nasata bisa abinda za ka fita nema. ldan ka dawo gida ka islc na mutu ka ziyarci kabarina tare da matarka, itama ta sumbaci kabarin nawa ta shatashi da hannunta, wannan shi ne kadai bukatata a garcka" Koda Sarki Salmar ya zo nan a jawabinsa sai hawaye ya zub0 masa.. Nan take zuciyar Yarima Muraisu ta karaya ya dora kansa akan kirjin Sarki ya fashe da matsanaicin kuka. Sai da suka jima kankamc da juna duk suna kuka sannan Sarki ya janye jikinsa daga cikin na Muraisu, ya ce, "Tafi abinka ya kai dana, daga yau kada ka sake yin kuka komai bakin ciki ko wuya, sai dai zubar da hawaye. Idan za ka fita yanzu daga cikin turakar nan kada ka waigo mu sake ganin fuskar juna". Koda gama fadin haka sai Sarki ya lumshe idanunsa a lokacin da hawaye ke shatata bisa kurmatunsa. Cikin matukar sanyin jiki Yarima Muraisu ya mike tsaye ya taka sawayen sa ya nufi kofar fita daga turakar. Kafin ya isa bakin kofar sai ya tsaya sau uku ya yi kamar ya juyo ya yiwa Sarki kallon karshe, amma sai ya kasa saboda biyayya ga furucin Sarki. Tun Yarima Muraisu na yaro karami bai taba ketare maganar Sarki ba, kuma ko a cikin wuta ya ce ya shiga sai ya shiga. A wannan lokaci ne Yarima Muraisu ya rinka tunowa da duk abubuwan da suka faru tsakanin sa da Sarki a baya tun sa'adda ya fara wayo kawo izuwa girmansa. Kawai sai yaji ya kasa daurewa, bai san sa'adda ya fashe da matsanaicin kuka ba ya yi sauri ya fice daga cikin turakar. Yana fita sai shima Sarki ya fashe da matsanaicin kuka, domin ya san cewa shi ke nan har abada ba za su sake ganin juna ba, domin Boka Rufyan ya gaya masa cewa duk ranar da ya rabu da wannan gashin sihirin da ke jikinsa ba zai Rara kwana arba'in ba a duniya, kuma gashi wannan tafiya da Yarima Muraisu zai yi ba zai dawo ba sai bayan kwana arba'in din. Da fitowar Yarima Muraisu kofar turakar Sarki, sai ya iske Boka Rufyan, Kuyanga Sabirat da Barde Kurzal tsaye a jere suna jiransa. Ko kallonsu bai yi ba sai ya wuce gaba ya mufi can bakin kofar fada. Cikin sauri suka bishi a baya. Da zuwansu kofar fadar sai suka iske an tanadar musu dawakai guda uku, gami da guzuri. Nan take suka kama dawakan suka hau, Muraisu ne a kan gaba, sannan Kuyanga Sabirat a tsakiya, sai Boka Rufyan da Barde Kurzal a baya. Haka dai suka ci gaba da tafiya har suka fice daga cikin birnin Lairus suka nausa cikin daji. Ba su gushe ba suna wannan tafiyar har sai da rana ta take, a sannan ne dawakansu suka fara sassarfa, kai da gani ka san cewa suna bukatar su sha ruwa, kuma su huta. Koda ganin haka sai Boka Rufyan ya dubi barde Kurzal ya ce, "Wane irin nisa ne a gabanmu kafin mu riski Rorama ko kogi?" Koda jin wannan tambaya sai Kurzal ya yi murmushi ya ce, "Ya kai abin dogaronmu ai bamu yi nisa ba da barin gida ba fa, ca nake kowa a cikinmu nan ya san a inda muke. Nan da tafiyar zango daya tal zamu riski koramar Salzas". Koda jin wannan batu sai kowa ya cika da murna, saboda sanin cewa koramar Salzas wani wuri ne mai ni'ima inda ruwa ke zubowa kasa daga saman wani dogon dutsc, kuma akwai tarin 'ya'yan itatuwa wadanda suka yi tsuro a wajen. Shi dai wannan wuri ya yi kaurin suna domin ya zama tamkar sansanin Fatake, inda sukan yada zango su huta kafin su shiga birnin Lairus. Wani lokacin ma sai Fatake sun kwana sun yini a wajen suna gyara kayan kolinsu sanann su Rarasá cikin birnin Lairus. Kamar yadda masanin ya Kurzal ya yi bayani, haka al'armari ya kasance, walo sai da suka kara tafiyar Zango guda sannan suka iso daf da koramar Salzas. Tun daga nesa kadan Kurzal ya daga hannu sama yana mai yi musu nuni da su tsaya. Nan take duk su ukun suka yi turjiya da dawakansu suka tsaya cak. Kurzal ya sauko daga kan dokinsa da sauri ya dubi hanyar, sai ya ga sawaycn dawakai, kawai sai a tsugunna ya dora kunnensa akan kasa, har iZuwa tsawon dakiku goma sannan ya mike tsaye ya rike kugu yai ajiyar zuciva ya dubi Yarima Muraisu ya ce, "Ya shugabana wadansu mutane masu yawa sun zo bakin koramar nan sun yada zango, kuma eun huta har tsawon kamar sa'a guda, sannan suka tashi Suka ci gaba da tafiya, kuma maimakon su bi hanyar da za ta kaisu birninmu sai suka bi wata hanyar dabam wacce babu inda za ta kaisu face cižkin muggan dazuzzuka masu matukar hadari". Koda jin wannan batu sai Yarima Muraisu ya dubi Boka Rufyan ya ce, "Duba mana mu ga ko su waye, kuma mu san daga ina suke da inda suka dosa" Boka Rufyan ya ce, "An gama ya shugabana. Amma zai fi kyau mu karasa bakin koramar tukunna mu sauka mu sami nutsuwa". Ba tare da gardamar kormai ba kuwa Yarima Muraisu ya amince da wannan shawara suka karasa bakin koramar suka yada zango. Sai bayan dawakansu sun sha ruwa, suma sun sha, kuma aka ci abinci sannan Boka Rufyan ya share kasa ya rintsa idanunsa ya karanta wadansu dalasimai na tsafi sannan ya tofa akan kasar, sai ga hoton cikin birnin Hutaira ya baiyana akai, aka nuno cikin gidan sarautar Sarki Ishmar. Sarkin yana tsaye tare da 'yar uwarsa Gimbiya Husneila suna sallama zai yi tafiya, duk su biyun suna kwalla. Husnaila ta dubi Sarki Ishmar cikin matukar damuwa ta ce, "Ya kai dan uwana kayi sani ccwa bamu taba rabuwa ba facc idan za ka tafi yaki, kuma ko yaki ka tafi baka wce sati biyu zuwa uku baka dawo ba, amma yau gasni ka ce dani zamu rabu har tsawon wata bakwai, ta ya va kake tsammanin cewa zan iya jure kewar rashinlka a tare dani?" Sarki lshmar yaji wannan tambaya sai hawayc ya Zubo masa ya ce, "Ya ke 'yar uwata ki sani cewa bisa dolc zan tafi na barki ba don ina so ba, kuma wannan tafiya zan yi ta ne don cika babban burin rayuwata wanda idan ya tabbata sai mun sami daula, đaukaka da arziki irin wanda bamu taba samu ba. Na sani cewa za ki cikin kewata matuka, amma akwai abinda zai kawar miki da wannan damuwa. Na sani cewa rayuwarki babu abinda kike so sama da yin rangadi a cikin daji kina kallon kyawawan tsuatsaye da kyawawan namun daji, saboda haka na shirya miki wannan rangadi. A duk bayan wata guda za ki fita tare da Dakaru dubu dari uku wadanda za su baki tsaro, amma duk sa'adda kuka fita kada ku sake ku haura kwana goma baku dawo gida ba. Abu na biyu, akwai dajin Kirzufa wanda ba a shigarsa, lallai ku nisanceshi. Abu na uku wanda shi ne na karshc, kada ku kuskura ku bi hanyar da za ta kaiku birnin Lairuf. Koda kun bi hanvar kuwa ya kasance iyakarku ita ce koramar Salzas, daga nan sai ku juyo ku bi wata hanyar dabam". Sa'adda Sarki Ishmar ya zo nan a zancensa sau Gimbiya Husnaila tayi ajiyar zuciya ta ce, "Ya kai dan uwana shin yanzu kana ganin ccwa wadannan Dakaru da za su yi mini rakiya ya yin da zan fita rangadi za su iya karcni daga dukkan mugun al'amari?" Sarki Ishmar ya yi murmushi sannan ya ce, "A1 koda ba za su iya kareki ba babu wani tsautsayi da zai iya hawa kanki saboda na karc lafiyarki da dukkan karfin sihirina" Da jin haka sai murna ta kama Gimbiya Husnaila ta rungume Sarki Ishmar ta sumbaci goshinsa, sannan ta ce, "Ya kai dan uwana hakika yanzu hankalina ya kwanta kuma na san cewa har watanni bakwai su cika ba zan shiga tsananin damuwa ba tunda zan dinga fita wannan rangadi. Amma abinda nake so da kai shi ne, da zarar watanni bakwan sun cika ka gama shirinka to kafin ka tafi yakin ka dawo gida ka daukeni mu tafi tare". Sarki Ishmar ya ce, "Ai wannan mai sauki ne, na yi miki alkawari cewar lallai haka za a yi". Nan takc Sarki Ishmar ya rungume Husnaila suka yi bankwana sannan ya juya ya tafi. A dai-dai nan ne Boka Rufyan ya goge kasar da ke gabansa, hoton komai ya bace. Yana dago kai sai ya ga ashe Yarima Muraisu, Barde Kurzal da Kuyanga Sabirat sun kame kamar gumaka. Ba komai ne ya haddasa musu hakan ba face tsananin rudewa da dimaucewa da suka yi sakamakon ganin kyawun Gimbiya Husnaila. Ita kanta Kuyanga Sabirat da take mace sai da ta rude matuka, domin tun da tazo duniya ba ta taba ganin mace mai kyanta ba. Ya yin da Boka Rufyan ya ga su Yarima sun dimauce sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya. Al'amarin da ya janyo suka dawo cikin haiyacinsu ke nan. Yarima Muraisu ya dubi boka Boka Rufyan ya ce, "Yanzu dama akwai mace mai irin wannan kyau a duniya? Ni kam yanzu na ga matar aure". Koda jin haka sai Boka Rufyan ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, sannan ya murtuke fuska kamar an aiko masa da sakon mutuwa. Ita kuwa Kuyanga Sabirat sai taji kishi ya turnuketa kamar ta fashe da kuka. Boka Rufyan ya duk arima Muraisu cikin matukar damuwa ya ce," gabana kayi sani cewa mallakar Gimbiya Husnailaercka ba karamin aiki ba ne. Zan iya cewa dai-dai yake da tafiya neman Jaki mai kaho, ko kuma ace SIYAN AJALI, tun gabannin ajali ya zo. Za ka iya mallakarta, amira za ka iya rasa rayuwarka a ko karin maliakarta, sabod tsananin Rarfin sihirin da ke iikinta wanda xi kaina ban san makarinsa ba. Da farko dai ina so ka sani ccwa Gimbiya Husnaila bata ta6a vin sovavya ba, domin babu ni da namiji da zai burgeta kornai kyansa ko jarumtakarsa. Abu na biyu, an circ mata sha'awa irin wacce ke tsakanin mace da namiii barc tayi sha'awar yin aurc. Duk wadannan abubuwa Sun faru sakamakon sihirin da dan uwanta ya sanya ma ta a Jikinta. In har kana son ka karya wannan sihiri da ke jikinta dole nc sai ka je ka vaki Dakarun da ke tsaron lafiyarta a yanzu su dubu dari uku. Ko ka tarwatsasu ko kuma ka kashesu gaba dayansu sannan ka daukcta ka shigar da ita cikin dajin Kirzufa ku yi rayuwa ta tsawon kwana uku a cikin dajin, kuna ci kuna sha daga dabbobin dajin da 'ya'yan itatuwansa. To fa a sannan ne sihirin tsafin da ke jikinta zai karyc, sai kuma ka san hanyar da za ka bi ka sami soyayyarta har ta amince ta biyoka izuwa birnin Lairus domin ayi bikin aurcnku. Babban abu mai hadari a cikin wannan al'amari guda biyu ne Abu na farko shi nc, yaki da wadannan Dakarn guda dubu dari uku masu tsaron lafiyar Gimbiya Husnaira ba karamin bala'i bane, domin Dakaru ne na musamman wadanda aka siyesu daga can birnin Romaniya. A duniya kaf, babu wadansu mutane masu girma da karfi kamarsu, sannan an tsumasu a cikin tsafin da' babu wani kaifi ko tsini da zai yi tasiri a jikinsu, kuma basa gajiya da yaki koda za a kwana uku ana yakin da su. Duk wuya, duk gumu basa gudu a filin daga. Abu na biyu shi ne, tunda dajin Kirzufa ya wanzu ba a taba samun tnahalukin da ya taba kwana a cikinsa ba. Shi kansa mahaifinka da ya shiga dajin sa'a uku kawai ya yi a cikinsa ya fito saboda bala'i da masifar dabbobin da Ke cikin dajin. Shi kansa ya lura cewa idan ya ce zai kwana a cikin dajin yana farauta to zai iya shiga mugun hali ko kuma gaba daya ma ya rasa rayuwarsa, shi yasa ya hakura ya yi sa'o'i kadan a ciki ya fito. Idan har ka iya yin wannan kwana uku a cikin dajin Kirzufa tarc da Girabiya Husnaila kuma har ka sami soyayyarta ku ka yi aure, tabbas sai kun haifi da wanda ba a taba yin jarumi kamarsa ba a duniya wajen tsananin Karfi da jarumtaka. Amma kuma rayuwarsa a doron kasa za ta zama annoba ga dukkan manyan Sarakunan duniya, matsafa da manyan attajirai, domin za su rinka rasa 'ya'yayensu akan kari, saboda haka za su bazama wajen farautar rayuwarsa. Dalilin da zai sa su rinka farautar rayuwarsa shi nc, akwai wani narkekcn kahon tsafi a cikin dajin Kirzufa wanda ake viwa lakabi da suna BUSA A MUTU. Kullum sai wannan da da ku ka haifa ya daga kahon ya dubi kudu ya busa shi sau uku. Da zarar ya busashi kuwa 'ya'yan manyan mutanc uku za su mutu a kasashc uku. Shi dai wannan kaho idan ya busashi sai an ji sautinsa a ko ina a cikin duniya. Ba wani abu bane zai sa ya inka busa wannan kaho ba sai domin yana son ya ta fita daga cikin dajin Kirzùra ya koma can birnin Lairus domin ya dauki fansar kisan gillar da aka yiwa jama'armu, kuma ya karbi karagar mulki daga hannun dan uwanka azzalumi Yarima Huraisu. Ba zai sami damar fita daga dajin ba, inda anan nc ya girma har sai ya busa kahon sau adadin yawan dabbobin da ke cikin dajin Kirzufa. Har yau, har gobe babu wani matsafi da ya iya gano yawan dabbobin. Amma dai bincike ya nuna cewa yawansu kaf bai kai dubu daya ba.!" Topah Aikin Aikineh *SHIN YARIMA MURAISU ZAI IYA TARWA TSA DAKARUN DA KE TSARON GIMBIYA HUSNAIRA DOMIN YA DAUKETA YA SHIGA DAJIN KIRZUFA DA TTA DOMINv SIHIRIN TSAFIN DA KE JIKINTA YA KARYE HAR TA AMINCE DA SOYAYYARSA? WANNE HALI SARKI SHMAR DA YARIMA HURASU SUKE CIKI? YAUSHE NE ZA SU GAMA DUKKAN SHIRYE-SHIRYENSU DON SU IE BIRNIN LAIRUS SU YẤKESHI HAR SU SAMI NASARAR MALLAKAR GASHIN SIHIRINV DA KE JIKIN YARIMA MURAISU? *WADANNE IRIN HADARURRUKA SU YARIMA MURAISU ZA SU RISKA A YA YIN WANNAN TAFIYA TASU? YAUSHE NE ZA SU HADU DA SU GIMBIYA HUSNAILA DA DARUN U HAR A FAFATA AZABABBEN GUMURZU? YAUSHE ZAA HAIFI JARIRIN DA ZAI ZAMO GUGUWAR ANNOBA GA AL'UMMAR DUNIYA, WANDA ZAI RINKA BUSA KAHON BUSA A MUTU? Mu hadu a kashi na biyu, don jin ci gaban wannan kayataccen, kasaitaccen labari. Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe. ABDUL'AZIZ SANI M/GINI. (King of Adventures Story) . Dafatan labari ya kayatar Kowa ya ajiye mana hasashenshi...