TAKOBIN ƊAUKAKA Littafi na farko Rubuta Labari MANSUR USMAN SUFI Sarkin Marubuta Littafan Yaƙi Haƙƙin Mallaka ©SUFI Shekarar Rubutu 2/3/2021 Website:- arewanovels.com.ng Phone number :- 08137237071 BABI NA ƊAYA Saurayi ne kyakkyawa na gaban kwatance ke ta faman tafiya a cikin ƙasaitacciyar kasuwar birnin. sanye yake da tufafi riga da wando da aka sana'anta su da fatar damisa, hatta takalmin dake kafars an yi sa ne da fatar damisar, a hannunshi yana ɗauke da wata doguwar sanda, kallo ɗaya zaka yi mashi ka fahimci cewa ya kasance GWARZON MAYAƘI. Saboda da yadda ya tara ƙwanji tamkar duwatsu aka cusa mashi a ƙirjinshi. Babban abin da yakara fito da kyawun sa shine zara-zaran gashin kansa daya zuba izuwa kan kafaɗun sa da kasumbar sa gemun sa baƙaƙe siɗik, Haka dai saurayin ya cigaba da tafiya a cikin kasuwar babu sassauci, Lokacin da shafe tsawon rabin Sa'a yana wannan tafiya a dai dai wannan lokaci ne sarauniyar dake mulkin birnin ta fito yawon shaƙatawa tare da dakaru masu tsaron lafiyar mutum dubu biyar. Duk inda sarauniyar ta durfafa a kasuwar sai kaga jama'a sun da re sun bayan da hanya. Bakomai yasanaya hakan ba sai domin tsananin tsoron fushin sarauniya lasmirat. Ana cikin wannan hali ne sarauniyar lasmirat ta hango wannan kyakkyawan saurayi ya tunkaro inda take babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da fuskar sa. Al'amarin da yayi matuƙar bawa sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai Domin shekaru masu yawa tana fitowa wannan rangadi hakan bai taɓa faruwa ba Su kuwa dakarun dake bayan ta sai zukatan su suka harzuƙa jikin su ya kama kyarma yana tsuma saboda tsananin fushi. Kawai sai sarauniyar lasmirat ta daga hannun ta sama tana mai nuni da a tsayar da tafiya Sannan ta dubi saurayin ta daka masa tsawa cikin fushi tace dashi" yakai wannan saurayi me kake takama dashi da bazaka risina agare ni ba. Koda jin wannan tambaya daga bakin sarauniyar lasmirat sai saurayin ya kura mata idanu batare da yace da ita uffan ba Cikin fushi lasmirat ta sake dakama sa tsawa a karo na biyu tare da maimaita tambayar ta. Kawai sai saurayin ya saki wani tattausar murmushi daya karawa fuskar sa kyawu sannan ya dakamata sarauniyar lasmirat tsawa ya dube ta ya ce " Yake wannan sarauniya mai takama da abinda bazai dawwa ma agare ta ba kiyi sani cewa bazan taba girmama ki ba. Domin a halin yanzu abinda na sani kawai shi ne bambancin dake tsakani na dake shine ke ɗiya mace ce Ni kuma namiji, mulkin da kike takama dashi tamkar kumfar kogi ne akoda yaushe za'a iya neman sa a rasa shi, Kafin saurayin ya gama rufe bakin sa fiye da rabin dakarun sun zare makaman su yunkura izuwa kansa suna ihu da kururuwa mai firgitar wa Koda ganin hakan sai ya gyara tsayuwar sa gami da sandar dake hannun sa yana mai jiran karasowar dakarun Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da waɗannan dabaru suka ruga izuwa kan saurayi sai yayi tsammanin dandazon zakoki ne suka farma barewa guda ɗaya, saboda tsananin kwarjini daban tsoron su , Yayin da ya rage saura baifi taku uku tsakanin su ba sai kawai akaga saurayin ya dako tsalle daga inda yake tsaye tamkar an harboshi daga cikin baka yana saman ya sanya sandar sa ya daki kawunan dakaru mutum goma, Take dakarun suka tsandara ihu sannan suka zube a kasa magashiyan, Sannan ya dira bisa ƙafafuwan sa a turba cikin gwaninta, Nan take aka kacame da azababban yaƙi matukar muni ban tsoro daban Al'ajabi. Dakarun suka wanzu suna kaiwa saurayin sara da suka cikin matukar zafin nama JURIYA DA BAJINTA. Shi kuwa ya wanzu yana kare hare haren su cikin wani irin baƙin zafin nama, kuma yana makosu da sandar sa daga kan dawakan su suna yin MUGUWAR HALLAKA, Na fa waje ya yamutse da ihu da kururuwar mazaje, karar karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne, gawarwakin dakarun suka watsu a wajen gasu birjik kwance cikin jini. Sai da aka shafe tsawon sa,a ɗaya ana wannan gumurzun babu sassauci, Sa'adda sarauniya lasmirat ta lura cewa saurayin ya hallaka fiye da rabin dakarun sai ta cika da matukar mamaki, domin a tarihin masarautar tun a zamanin mahaifin ta bata taɓa samun wanda ya hallaka dakarun gidan sarauta mutum uku ba, Kuma zuciyar ta ta harzuƙa bisa ganin yadda dakarun ta keyin muguwar hallaka Duk inda saurayin ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun na zubewa kasa cikin mawuyacin halin dake tsakanin RAYUWA DA HALAKA Nan fa dakarun suka ɗimauce bisa ganin iri kisan da saurayi keyi musu, Amma koda kwarzane ɗaya basu samu nasarar yi masa ba. Daga can nesa jama'ar kasuwar suna kallon fafatawar da ake yi waɗansu ta tagogin gidajen su suke leken abinda yake faruwa. Kuma suka cika da mamaki bisa ganin yadda saurayi yazamewa dakarun sarauniyar lasmirat ANNOBA ƊARI wanda a tarihi hakan bai taɓa faruwa ba. Lokacin da sarauniyar lasmirat ta fahimci cewa idan har aka cigaba da wannan artabu a haka dukkan dakarun ta zasu rasa rayukansu sai kawai ta dakamusu tsawa suka ja da baya sannan ta dako tsalle daga kan dokokin ta tamkar an harbota daga cikin baka ta sanya ƙafafuwan ta biyu ta daki saurayin a kirji da dukkanin karfin ta. Saboda karfin dukan sai da saurayin ya yi katantanwa sau uku sai ya turje aka sake yin sabon kallon kallo tsakanin lasmirat da saurayin Lasmirat ta kasance mace mai madaidaicin jiki ba doguwa ce ba gajera ba, tana da kyakkyawar fuska mai ɗauke da fararen idanu dara dara tana da siririn hanci wanda aƙasan sa aka yanka wani ɗan madaidaicin baki, wuyan yana kyawu tamkar na barewa, gashin kanta baƙi ne siɗik mai sheki da ƙyalli,ya zuba har izuwa ƙasan kwankwason taqKirjinta a cike yake kuma a tsaye ƙyam bai rankwafa ba, cikin ta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba, daga sama ƙugunta ya tsuke daga baya baya kuma ya buɗe yayi tudu sosai, tana da zabga-zabgan cinyoyi, fatar jikin ta farace mai ƙyalli. Wohoho Hakika duk inda kyawu yake tabbas sarauniyar lasmirat ta kai, domin babu wani ɗa namiji mai hankali da zai yi tozali da lasmirat face ya kamu da matukar kaunar ta. Yayin da aka shafe tsawon dakika talatin ana wannan kallon kallo, sai lasmirat ta zare wata zabgegiyar takobi a damtsen ta kaiwa saurayin wani wawan sara da nufin tsinke masa wuya, Cikin baƙin zafin nama saurayin ya sunkuya takobin lasmirat ta sari iska, Kawai sai suka kacame da azababban yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA Ana fara wannan gumurzu ne lasmirat ta fahimci cewa tsananin KARFIN DAMTSEN saurayin ya nunka nata sau biyar gami da zafin nama. Sai da sa,a ɗaya ta shuɗe ana fafatawa batare ɗayan su ya samu nasarar lakutar jikin ɗan uwan sa ba, Bisa dole lasmirat ta sake zare wata takobin yazamana ta kai wa saurayin hari da takubba biyu, Ana Cikin wannan artabu ne saurayin ya shammaci lasmirat ya gabza mata wawan naushi a fuska saboda karfin naushin sai da sarauniyar lasmirat tayi sama tamkar an janye ta kugiya,sannan ta faɗo ƙasa a matukar galabai ce. *** Bayan gabatar mulkin sarki Hulbaru na birnin Misra anyi wata gagarumar sarauniya da ake yiwa laƙabi da lasmirat bintu kazmal Lasmirat ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance kuma gagarumar basadaukiya,mace mai kamar maza,daɗin daɗawa kuma mashahuriyar attajira ta shara ainun a fagen sanin ilimin tsafi, A gaba ɗaya nahiyar babu kasa mai karfin tattalin arziki kamar ta ta Sau tari manyan sarakunan duniya kan kaiwa lasmirat HARIN BAZATO domin mamaye ƙasar ta kuma su mallaketa a matsayin matar aure amma sai abu ya ci tira, domin duk sa'adda aka gwabza yaƙi sai dai sarakunan suyi asarar dakarun yaƙi da dukiya mai tarin yawa bisa dole suka janye aniyar su *** Lokacin da sarauniya lasmirat ta fara ƙwaɗaituwa da son ɗa namiji sai ta gudanar da bincike bisa halarar tsafin ta domin taga irin namijin da ya dace ta aura Abinda binciken ya tabbatar mata shine mijin da zata aura shi ne wanda yafi kowa talauci a duniya Binciken yakara tabbatar mata da cewa matsawar ta auri wani ɗa namiji ba shi har ta tara dashi tofa zata rasa komai nata da ta mallaka a duniya. Sa'adda sarauniya lasmirat taga wannan al'amari a cikin halarar tsafin ta sai ta cika da matukar baƙi ciki maral musaltuwa Taya za'ayi ace sarauniya kamar ni ace na auri wanda yafi kowa talauci a duniya, bayan cewa nafi kowa ne BASARAKE karfin mulki da tarin dukiya a wannan nahiya baki ɗaya. Tabbas hakan ƙasƙanta daraja ta ne da ƙimata a idanun sauran sarakunan duniya Kuma idan na auri talaka dukiya ta da mulki na zasu zamo bisa ƙarƙashin ikon sa. Lokacin da sarauniya lasmirat ta zo nan a tunanin ta sai hankalin ta ya sake dugunzuma fiye da ko yaushe kuma ta rasa abinda ke yi mata daɗi, A wannan lokaci lasmirat na zauna ne a bisa wata ƙasaitacciyar kujera amma sai ta miƙe tsaye ta shiga kai komo a cikin turkar ta. Daga ƙarshe dai lasmirat ta yanke shawarar ta ziyarci wani boka dake zaune a wani gari dake iyaka da Birnin misra. **** Lokacin da sarauniya lasmirat ta isa gidan boka Dayyubul-Barmas ta kaɗaita dashi a cikin turakar sa Nan take ta kwashe labarin abinda ta gani a cikin halarar tsafin ta ta zayyanewa boka Dayyubul-Barmas tun daga farko har ƙarshe, sannan ta ɗora da cewa Yakai wannan boka mafi girma a halarar tsafi kayi sani cewa Babban burina shi ne na auri mijin da yafi kowa Arziki a duniya sannan ina da burin na rayuwa kamar shekaru dubu biyu domin nazamo nafi dukkanin sarakunan duniya daɗewa a bisa karagar mulki. Yayin da boka Dayyubul-Barmas yaji irin buƙatar dake tafe da sarauniya lasmirat sai ya jinjina al'amarin a cikin ran sa. Tsawon daƙika arba'in bai ce uffan ba sai daga bisani ne ya dubi lasmirat yayi gyaran murya yace" ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa hakika kin zomini da al'amari mai girman gaske Hakika bakaramar hikima kikayi ba da kika bayyana bukatar a gareni domin shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka a cikin sa baza ka kwashe Abin da ke ciki ba, Kuma kinsan masu iya magana na cewa Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai hango ba, abin da bincike ya tabbatar mini ga me da bayanin ki shi ne. Matsawar kina son ki fi kowa ne sarki daɗewa abisa karagar mulki kuma ki auri mijin da yafi kowanne kuɗi a duniya to yazama wajibi ki mallaki abubuwa guda uku domin ki samu nasarar samun ruwan koramar matsafi Daryalu Da farko za,a nemo ruwan kogin ma'ul-hayatu, Sannan waɗansu zobunan tsafi dake ajiye a kogon fatalwa a can yankin kasashen Larabawa a wani daji da ake yiwa laƙabi da Husumul-kadar Abu na karshe shi ne kubar miftahul-daryal, Shi dai wancan ruwa zamu yi amfani dashi ne a lokacin da zamu shiga wani daji kafin mu isa inda koramar boka Daryalu takr, ruwan zai bamu kariya ne daga waɗansu musifu dake dajin, Su kuwa waɗancan zobuna zamuyi amfani da su ne a lokacin da zamu shiga gidan boka Daryalu rukuni na farko wajen sanya su a hannayen mu, Domin babu yadda za,ayi mutum ya shiga gidan face ya na ɗauke da waɗannan zobunan sihirin, Kubar miftahul-daryal kuwa zamu yi amfani da ita ne wajen buɗe gidan boka Daryalu Dazarar mun samu nasarar ɗebo ruwan koramar kinsha to shi kenan bazaki auri wanda yafi kowa talauci a duniya ba. Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai dai nan azancen sa sai hankalin sarauniyar lasmirat ya ɗugunzuma ainun Ta dube sa cikin alamun tsantsar damuwa tace" ya Sarkin bokaye shin taya ya zan mallaki waɗannan abubuwa kafin ajali ya riskeni Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa Sannan daga bisani kuma ya fashe da kuka. Al'amarin da yayi Matukar bawa sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai ta dube sa ta ce" ya uban bokaye shin ina dalilin wannan dariya,da kuka naka? Da jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya share hawayen dake sannan ya buɗi baki yace ya shugaba ta abinda ya sanya dariya shi ne bincike ya tabbatar mini dacewa a wannan zamani nine bokan da zan samu ɗaukaka fiye da kowa ne matsafi domin ya cika burin mahaifin mu. Abinda Ya sa ni kuka kuwa shi wani bakon jarumi zai rushe wannan ɗaukaka tawa ta yadda ko tarihina bata sake tunawa a duniya ba Kuma wannan jarumi ba wani bane face namiji da zaki aura har ki samu Haihuwa wanda yafi kowa talauci a duniya Sai dai iyakar bincike ne na kasa gano ainahin a nahiyar da saurayin yake, Domin jarumin yana yana ɗauke da waɗansu sirrika masu basa kariya, Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai -dai nan a jawabin sa, sai hawaye suka sake zubo masa, Nan take Sarauniya lasmirat taji ta kamu da matukar tausayin sa Dayyubul-Barmas ya cigaba da cewa ya sarauniyar kyawawa kiyi sani cewa bazaki taɓa fin kowane sarki daɗewa abisa karagar mulki ba face kin mallaki wata takobin da ake yi wa laƙabi da TAKOBIN ƊAUKAKA, A salin TAKOBIN ƊAUKAKA ta wani gagurtaccen mayaki ne ma'abocin addinin musulunci. Bayan shuɗewar jarumi Hilal ne wani mashahurin matsafin aljani ya sace takobin ya shiga halarar tsafi ta tsawon shekaru arba'in yana sana'anta takobin da sirrikan tsafi An kira takobin da suna TAKOBIN ƊAUKAKA ne saboda duk jarumin da ya mallake ta zai samu ɗaukaka a duniya Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya kammala halwar sa sai yaga wani Al amari da ya firgita sa kuma ya ɗimauta sa, Abinda ya gani shi ne bazai taɓa samun amfani da TAKOBIN ƊAUKAKA ba ajali zai riske sa. Wani jarumi wanda bai kasance kowan kowa ba shi ne zai mallaki takobin ya lalata sirrikan tsafin dake jikin ta kuma ya ɗaukaka a duniya, Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya ga wannan al'amari sai ya cika da baƙin ciki Kawai sai aljani Sautul-Hidar ya ɗauki TAKOBIN ƊAUKAKA ya caka a kirjinsa a saitin ƙahon zuyar sa, Faruwar hakan ke da wuya sai numfashin sa ya ɗauke komai na jikin sa ya daina motsi ya sandare,take gangar jikin sa ta zagwanye ta zama wani irin ɓakin ruwa mai yauƙi, Daga bisani sai ruwan ya rikiɗa izuwa waɗansu irin gabza - gabzan samudawan aljanu dukkanin suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini da ban tsoro a hannayen sa rike da waɗansu irin makaman yaƙi masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi, Koda bayyanar aljanun sai wani daga cikin su wanda da alama shi ne shugaban su ya ɗauki TAKOBIN ƊAUKAKA ya sanya ta acikin wata akwatu ta farin gilashi ya ɗauki akwatin da takobin ke ciki ya shiga sanya ta acikin waɗansu akwatin har guda dubu, Sannan ka sa dakarun aljanun izuwa kowace kusurwa ta gidan domin tabbatar da cikekken tsaro ga takobin Tun daga wannan rana waɗannan aljanun suke gadin gidan boka Sautul-Hidar dake kan tsaunin lauhul- azwar Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa duk ɗaya daga cikin wadannan aljanun yana iya kayar bil'adama guda miliyan daya Ke nan hakan ya nuna cewa aljanun zasu iya yakar duniya baki ɗaya. Tabbas a halin yanzu tunkarar gidan aljani Sautul-Hidar dai dai yake da mutum ya buɗe taskar ANNOBA DARI **** Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo daidai nan ajawabin sa. sai idanun sarauniya lasmirat suka zazzaro kuma tsoro ya kamata, ta shiga damuwa ainun kamar tacewa boka Dayyubul-Barmas ta janye buƙatar ta, Amma sai ta dube sa cikin karfin hali da ƙi faɗi irin nasu na sarakuna tace" ya uban bokaye shin yanzu yaushe zamu yi wannan gagarumar tafiya ta ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA? Dayyubul-Barmas ya gyaɗa kai yace"ya sarauniyar kyawawa ai komai ya na hannun ki duk lokacin da kika shirya tafiya a shirye nake, Koda jin batu sai sarauniya lasmirat tayi godiya a gare sa ta ɗebo dukiya mai mai yawa ta basa Wannan shi ne cikekken tarihin sarauniya lasmirat, **** Koda samun wannan gagarumar nasara sai kyakkyawan saurayin ya sakarwa sarauniya lasmirat dake kwance a ƙasa wani tattausar murmushi Har saurayin ya juya da nufin da nufin ya cigaba da tafiya a cikin kasuwar, sai yaji alamar motsin tafiya a bayan sa. Koda ya waiga sai yayi arba da ita fuskar cike da annuri ba wata ba ce face sarauniyar lasmirat. lasmirat ta dube sa tace" yakai wannan kyakkyawan saurayi ma'abocin sadaukantaka idan baza ka damu ba ina bukatar nayi maka waɗansu tambayoyi, kuma ina neman wata alfarma guda ɗaya a wajen ka. Koda jin wannan batu sai saurayin ya yi murmushi har fararen haƙoran sa suka bayyana ya dubi lasmirat yace" yake wannan sarauniya faɗi duk abinda kike son tambaya ni kuwa zan baki amsar ta dai dai abinda na sani. Lasmirat ta dubi saurayin da wani irin kallo mai ɗauke da alamar tambaya sannan tace "Yakai wannan saurayi shin mene ne sunan ka da ma Abinda Ya Kawo izuwa wannan birni nawa Alfarmar da nake nema a wajen ka ina so ka biyo ni izuwa gidan sarauta domin ina so mu tattaunawa wata muhimmiyar magana Yakai wannan jarumi kayi sani cewa kai ne jarumi na farko a rayuwa ta dana taɓa fafata yaƙi da shi har ya samu nasarar kai ni kasa Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tambayar ta sai saurayin ya dube ta yace " Ni dai da farko suna na yaslir ibn Hulzal na fito ne daga wata nahiya da ake yiwa laƙabi da Nashmir Game da Alfarma da kika nema a waje na kuwa bazan amince da ita ba Sai kin yarda kuma kinyi mini alkawarin cewa zaki dunga daraja kowane ɗan adam, Ma'ana za ki dai na azabtar da mutane da zaluntarsu, Sa'adda saurayi yaslir ibn Hulzal yazo nan a zancen sa sai sarauniya lasmirat ta zurfafa izuwa kogin tunani Sa'adda talakawa da sauran jama'ar kasuwar suka ga yadda sarauniya lasmirat ta ƙasƙanta kanta a gaban saurayin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi domin fiye da shekaru masu yawa hakan bai taɓa faruwa tunda lasmirat ta hau bisa karagar mulki Daga can sai ta ɗago da kanta da dubi saurayi yaslir tace"na amince da wannan sharaɗi naka yakai wannan jarumi, Koda gama faɗin hakan sai sarauniyar lasmirat ta yiwa wani badakare inkiya da hannu kamar badakaren yasan abinda take nufi sai kawai ya janyo waɗansu fafaren dawakai ya iso gaban ta ya risina ya rike ta linzamin dokin ɗaya,ta kama ta hau. Ta na mai yiwa yaslir nuni da yau bisa ɗayan dokin take ya kama dokin ya hau A lokaci guda suka sakarwa dawakan linzami sauran tsirarun dakarun suka mara musu baya a ka cigaba da tafiya, Jama'a suka bisu da kallo cike da tsananin mamaki **** A can kololuwar sararin samaniya inda Allah (s,w,t) yayiwa halittu iyaka a nanne sarki Hamras ibn zulaibu ya sanya aka gina masa ƙasaitacciyar fadar sa. Wacce masana suka tabbatar da cewa babu wata fada data Kaita ƙawatuwa da kayan alatun jin daɗin rayuwar duniya. Domin an ce sai da bakaken aljanu guda dubu shida suka shafe shekaru goma suna aikin ginin fadar dare da rana babu sassauci. Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa Sarki Hamras yakasance jinin wata Kabila da ake kira da Banu lahzar. Waɗanda aka tabbatar dacewa sun mamaye rabin sarakunan duniya, A rayuwar sarki himras fiye da abu uku, yana matukar adawar ace akwai wani sarki a duniya da ya fisa KARFIN MULKI Abu na biyu kuma shine ya tsani ma'abota addinin musulunci. Bakomai yasanaya hakan sai domin mahaifinsa sarki zulaibu ya mutu ne sakamakon kwabza yaki da wani jarumi ma, abocin addinin Musulunci, Akwai waɗansu muhimman sirrikan tsafi da mahaifin sa zai sanar da shi waɗanda da zarar ya sanar dashi ɗin zai mulki duniya baki ɗaya, Amma sai ya zamana waccan jarumin ya hallaka sa batare da ya sanar dashi sirrikan tsafin ba, Abu na karshe da sarki Himras ya tsana shi ne wani gawurtaccen jarumin ma,abocin addinin Musulunci,wanda binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa shine zai kawo karshen mulkin sa a doran kasa. Lokacin da sarki Himras ya ga cewa a halin yanzu basa da abokan gaba da suka huce ma'abota addinin Musulunci sai ya zurfafa izuwa cikin halarar tsafin sa domin ya gano wata hanya zai bi ya kawar da musulmi kuma ya mulki duniya baki ɗaya, Abin da bincike ya tabbatar masa shine bazai taɓa cika wannan buri na sa ba face ya mallaki wata tsafaffiyar takobi mai suna TAKOBIN ƊAUKAKA Amma koda ya mallaki takobin bazai samu nasarar sarrafa takobin ba face ya haɗiye gashin kan waɗansu mutum biyu, Waɗannan mutum ba wasu ba ne face" sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas, Sa'adda sarki Hamras yaga gagarumin aikin dake gabansa na mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA, da silin gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat sai ya umarci waɗansu gwarazan dakarun aljanun sa domin su yanko masa gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat Bisa jagorancin aljani Huruful-labarus. Aljani Huruful-labarus yakasance GWARZON MAYAKI da masu Bincike suka tabbatar dacewa a jinsin baƙaƙen aljanu babu mai karfin damtsen sa. Bayan Sarki Hamras ya tura Aljani Huruful-labarus sai ya shiga shiri sai da ya kwana arba'in ya na tsuma kansa da tsumin tsafi, sai ya fito ya shiga izuwa duniya domin mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA. Al'amarin saurayi yaslir da sarauniya lasmirat kuwa, tafiyar daƙika arba'in kacal suka yi suka iso izuwa gidan sarauta Gidan sarautar yakasance kasaitacce mai girma da faɗi tamkar gari guda, gaba ɗaya katangun ginin gidan anyi su ne da wani irin farin gilashi Babu wani BASARAKE ko attajiri dazai yi arba da wannan gidan sarauta face ya Zamo cikekken ɗan ƙauye, Tsayawa masalta tsaruwar gidan sarautar zai iya zamo wa ƙauyanci sai dai abinda idanu suka gani kawai Duk inda mutum ya duba bayi ne hade da kuyangi da barori na kai komo suna hadima Duk inda sarauniyar lasmirat da saurayi yaslir suka gufta a cikin gidan sarautar sai dai kaga jama'a na zubewa kasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa, Lokacin da aka iso wani bangare mai ɗauke da manyan falo guda uku haɗe da kewayen wanka, kayan more rayuwa sai Waɗansu tsala-tsalan kuyangi na kai komo a cikin turakar, Da sauri wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru hamsin ta rugo izuwa inda sarauniyar lasmirat take ta zube ƙasa bisa gwiwoyin ta ta kwashi gaisuwa Bakin ta na kyarma kuma kanta a sunkuye tace "me kike da buƙata ya shugaba ta? Lasmirat ta dube ta tace" yake zarima kiyi sani cewa bakomai nake da bukata ba face ina so wannan baƙo dake tare da ni a basa kulawa da dukkanin wani abu da ya buƙata kiyi sani cewa yana da matukar muhimmanci agareni Koda jin wannan batu sai zarima ta sake risina wa tace angama ya shugabata bin umarnin ki ai shi ne ibada ta, Tana gama faɗin hakan ta mike tsaye tana Mai yiwa saurayi yaslir nuni da ya biyo bayan ta Batare da bata lokaci ba yaslir ya kama linzamin dokin sa ya sauko sannan ya rufa mata baya Amma koda ya waiga ya haɗa idanu da sarauniya lasmirat sai yaga tana yi masa wani mayataccen kallo mai ɗauke da alamar tambaya. Cikin hanzari sarauniya lasmirat ta juya taɗa linzamin dokin ta ta nufi bangaren da turakar ta take, Lokacin da isa sai ta shiga izuwa kewaye ta tsala wanka sannan ta shiga tsaɓa ado tana mai fuskantar wani madubi Tana cikin wannan hali ne sai ta jiyo motsin tafiya a bayan ta Koda ta waiga sai tayi arba da shi ba wani bane face wazirin ta mai suna ukashat Waziri ukashat yakasance dattijo mai yawan shekaru amma duk da hakan babu gajiya a tare da jikin sa, Yana da kaurin jiki, dogo ne tsaka-tsaki,yana da tarin gemu da ƙasumba fararen sol, Fuskar sa tana da kwarjini Ukashat yakasance ɗan uwa a wajen mahaifin lasmirat wato sarki kazmal kuma babban aminin sa, bisa wannan dalili ne yasanya duk abinda lasmirat zata zartar sai ta nemi shawarar waziri ukashat, Bisa al'ada duk sa'adda waziri ukashat zai gana da sarauniya lasmirat yana sanya ayi masa iso,kuma zai shigo ne fuskar sa cike da annuri Amma a wannan karon sai ga fuskar sa a murtke babu annuri tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa, Kawai sai ya zaune a bisa wata kujera dake fuskantar lasmirat ya dube ta cikin tsananin fushi yace" yake lasmirat shin menene yasanaya za ki karrama wanda ya wulakanta ki a gaban talakawa?. Tabbas hakan zubar da darajar wannan masarauta ta mu ne da muka gada tun iyaye da kakanni, Shin yanzu da wane irin idanu zamu kalli sauran sarakuna abokan gabar mu? Wai shin ma bakya tunanin cewa wannan saurayi ɗaya daga cikin abokan gaba ne yayi ɓadda kama domin ya yaudare ki? Koda jin wannan tambaya daga bakin waziri ukashat sai sarauniya lasmirat ta dube sa a nutse tace"yakai waziri kayi sani cewa ko kaɗan bana taɓa da nasanin karrama wannan saurayi kuma jiki na ya bani cewa tabbas bazai cutar da Ni ba, hakika zai zamo mai amfani a gare ni. Ukashat ya katse ta ta hanyar ɗaga mata hannu yace " Haƙiƙa ke yarinya ce, tabbatas Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai iya gani ba. Ban yi mamakin maganar ki domin na fahimci cewa tsananin kauna da soyayyar wannan saurayi ce ta makantar da idanuwan ki, ta sanya har kika manta da burin zuri'armu na kare martabar wannan masarauta, Koda wannan batu daga bakin ukashat sai sarauniya lasmirat ta fusata ainun ta dakawa matsawa ta dube sa tace" yakai ukashat kayi sani cewa ni nake da ikon bayar da umarni a wannan masarauta don haka abin da naga ya dace shi zan aiwatar, Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta fice daga cikin turkar ta bar waziri ukashat a zaune Cikin alamun tsantsar damuwa waziri ya mike tsaye ya fice daga turakar zuciyar sa cike da takaici. Da shigar saurayi yaslir izuwa cikin turakar, sai ya tarar turakar takasan ce ƙasaitacciya da aka ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin jin daɗin rayuwar duniya. Gaba ɗaya turakar shimfiɗe take da wani koren kilishi mai taushin gaske, Bayan yaslir ya fito daga kewayen wanka wani wanzami yayi masa gyaran fuska da saje, sai wata kuyanga ta kawo masa waɗansu fararen tufafi masu taushi ya sanya a jikin sa, Nan take tsakanin kyawun sa ya fito fili ƙarara, kawai sai ya nufi teburin da aka tanadar masa abinci da abin sha ya shiga kimtsa cikin sa, Bayan ya kammala ne da yake a wannan lokaci duhun dare ya fara Kawo kai, Sai ya kunna fitulun dake turakar ta kaure da haske, Sannnan ya zauna a bisa kan gadon sa kuma ya zurfafa izuwa kogin tunani, Yana cikin haka ne sai yaji an turo kofar shigowa turakar Ai kuwa kofar na buɗewa sai ya yi arba da ita ba wata ba ce face sarauniya lasmirat ta caɓa ado wani irin daddaɗan ƙamshi na tashi daga jikin ta. Cikin Wata irin tafiya mai ɗaukar hankalin duk wani ɗa namiji,ta nufi wata ƙasaitacciyar kujera dake fuskantar yaslir ta zauna a kan ta, Cikin annurin fuska ta dubi yaslir tace"yakai yaslir kafin mu kai ga tattaunawa abinda ya taramu anan Yana da kyau ka sanar dani labarin rayuwar ka. Koda jin wannan tambaya sai idanun yaslir su ka ciki da kwalla ya dubi lasmirat yace" ya sarauniyar kyawu shin ina dalilin son kiji labarin rayuwa ta? Lasmirat ta numfasa tace"Domin sanin labarin ka ya na da matukar muhimmanci a gareni, Yaslir ya yi gyaran murya a karo na biyu sannan yafara dacewa *** Kimanin shekaru arba'in baya anyi wani ƙauye da ake kira da suna Darul-Na'am. Gari ne mai ɗauke da arzikin noma, kiwo, Sarkin dake mulkin kauyen yakasance adali mai tausayin talakawa Ana kiransa da suna Abu-salimat, Abu-salimat yakasance GWARZON MAYAKI mai tarwatsa maza a filin daga, Yana da ƴa guda ɗaya kyakkyawa tagaban kwatance ana kiran ta suna salimat ta gaji mahaifin ta a kyawawan halayen mahaifin ta. Ƙauyen Darul-Na'am na karkashin mulkin wata babbar masarauta da wani kasaitaccen sarki ke mulki mai suna Husnalu ibn kailub, Sarki Husnalu yakasance GWARZON MATSAFI, kuma mashahurin mayaki, daɗin daɗawa kuma yakasance AZZALUMI nagaban kwatance, Ƙwace,kashe rayukan al'umma,tare da farauce dukiyoyin su ba a bakin komai yake a wajen sa ba, A rayuwar sarki Husnalu babu abin da yake tsananin kauna fiye da ɗansa guda ɗaya mai suna Hatmal, Yarima Hatmal yakasance ɗan lele a wajen sarki Husnalu baya son ɓacin ransa ko kaɗan, Bisa al'adar Sarki Husnalu duk bayan shekara ɗaya sarakunan dake ƙarƙashin ikon sa kan biya sa haraji na dukiya da adadin ta yakai dinare dubu ɗari tara, gami da kayan amfanin gona da dabbobin ni'ima Tsakani na da gimbiya salimat akwai soyayya mai karfi, kasancewar mahaifina shi ne wazirin mahaifin ta,tun muna yara ƙanana muke kaunar juna. **** Wata rana daga cikin ranakun da sarakunan ke kaiwa sarki Husnalu haraji, kamar yadda aka saba duk shekara, Sai yazamana cewa a wannan shekara anyi tafiyar tare da ni da masoyayi ta gimbiya salimat, Bayan dukkanin sarakunan sun kammala hallara a fada, Bayan shiru da ya mamaye fadar na ɗan wani lokaci sai aka hango sarki Husnalu da yarima Hatmal sun shigo fadar, suna sanye cikin suturu iri ɗaya hatta takalmin dake kafar su iri ɗaya ne, Koda jama'a suka hango sarki sai suka miƙe tsaye domin girmama a gare su, Kai tsaye sarki Husnalu da yarima Hatmal suka huce izuwa inda karagar mulki take suka zauna a tare, Sannan sauran jama'a suka zauna, batare da bata lokaci ba sarakunan suka dunga tashi daga wajen zaman su suna zuwa gaban na Husnalu suka kwasar gaisuwa sannan su gabatar da harajin su da jama'ar da suka yi musu rakiya Sarki na farko da ya gabatar da harajin da ana kiransa da suna zulaibu, yana mulkin wani ɗan ƙaramin gari mai suna madinatul-shaswal, A gaba ɗaya sarakunan da suka hallara a fadar babu wanda yakai zulaibu yawan shekaru da kuma dadewa akan karagar mulki, Sai da sarakuna biyar suka gabatar da harajin sannan aka iso kan sarki Abu-salimat, Abu-salimat ya mike tsaye ni da gimbiya salimat muka mara masa baya, dakaru na biye da mu ɗauke da akwatin dinare gami da kayan amfanin gona, har mu ka isa inda karagar mulki take, muka zube ƙasa muka kwashi gaisuwa muna masu sunkuyar da kawunan mu. Kawai sai waɗansu dakaru daban a fadar suka karɓi wadannan akwatin dinare suka lissafa kuma suka bincike kayan gonar suka tabbatar da ingancin su sannan suka ɗauke suka fice daga fadar, Ana cikin wannan hali ne na ɗan saci kallon yarima Hatmal ai kuwa sai na ga ya ƙurawa gimbiya salimat idanu yana mai yi mata wani irin kallo daya sanya hantar ciki na ya kaɗa, Ku ma tsoro ya kamani. Domin kallon da naga Yarima Hatmal na yi mita kallo ne ma nuna kamuwa da soyayya. Jikina a ssnyaye na mayar da kai na kasa, sannan sarki Husnalu ya Umarce mu da mu fice daga fadar, Cikin hanzar sarki sarki Abu-salimat ya miƙe tsaye muka rufa masa baya muka fice daga fadar Fitowar mu keda wuya sai muka fara shirye-shiryen komawa izuwa ƙauyen Darul-Na'am Bayan an kammala ne muka hau bisa dawakan mu muka fice daga kasar Baitul-sharhal muka nufi hanyar da zata sadamu da ƙauyen Darul-Na'am, A wannan lokaci sarki Abu-salimat ne akan gaba tare da wani hadimin sa mai suna Haimar suna hirarrakin su cikin nishadi, Ni da salimat muna hira irin ta masoya, ana cikin wannan hali ne gimbiya salimat ta dube ni tace"ya masoyi na kuma hasken rayuwa ta shin nayi maka wata tambaya mana Cikin annurin fuska nace faɗi tambayar ki ya abar kauna ta Salimat tayi ajiyar zuciya ta ce " shin a halin yanzu yaya matsayin soyayya ta yake a zuciyar ka? Koda jin wannan tambaya sai na tuntsire da dariya na dubi lasmirat nace " shin kina kina tantama ne akan matsayin ki a rai na ko kuea. A,a kawai ina so naji matsayi na ne Salimat ta faɗa fuskar ta cike da annuri,. Murmushi nayi a karo na biyu nace" Ai matsayin ki a waje na tamkar hanta da jini ne domin babu abin da zai raba tsakanin mu face mutuwa, Salimat tayi murmushin jin daɗi tace " Ni kuwa ka zame mini tamkar numfashi a rayuwa ta, Nan take mu duka biyun muka fashe da dariyar farin ciki Ana cikin wannan hali ne muka jiyo alamun takun sawaye a bayan mu, Cikin firgici muka ja linzamin dawakan mu muka tsaya koda muka wai ga sai muka yi arba da waɗansu ZARATAN DAKARU masu matukar yawa Shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro, Har mun yunkura zamu zare takubban mu sai sarki Abu-salimat yayi mana nuni da mu dakata Bisa lura da yayi cewa basu bane dakarun face na sarki Husnalu Sannu a hankali dakarun suka iso har izuwa inda muke suka yiwa dawakan su Turkiya, Sarki Abu-salimat ya dubi wani garjejen kato mai kirar samudawan farko wanda da alama shine shugaban dakarun yace dasshi" yakai muraizu shin wane saƙo kuke tafe dashi izuwa gare mu ina fatan dai bamu saɓawa mai girma Husnalu ba, Sadauki muraizu ya bushe da dariyar mugunta mai kama da kukan jaki daga bisani ya murtuke fuska tamkar an masa da saƙon mutuwa, Cikin Wata irin kakkausar murya yace" ya kai Abu-salimat kayi sani cewa bakomai ne ke tafe da mu ba sai domin ka bamu yar ka salimat mu Kaita izuwa ga sarki saboda ɗan sa Yarima Hatmal ya kamu da soyayyar ta kuma yana so ne ya aure ta Cikin matukar kaduwa Abu-salimat ya dubi muraizu a lokacin da idanun sa suka zazzaro yace" shin wace irin maganar banza kake yi yakai muraizu anya kuwa a cikin hankalin ka kake kuwa? Muraizu ya bushe da dariyar mugunta har ya kusa faɗowa daga kan dokin sa daga bisani ya haɗe rai yace"Tabbas garau nake nasan Abin da nake faɗa ina cikin hayyacina, A halin yanzu ba neman shawarar ka muke yi ba face zartar da umarnin mai girma Husnalu, Koda jin wannan batu daga bakin muraizu sai na fusata ainun ya dakamasa tsawa cikin matukar fushi na dube nace " karyar ka tasha karya yakai wannan la'ananne kuma BAKIN AZZALUMI kayi sani cewa karyarka tasha karya baza mu taɓa lamunta da wannan magana taka ba, Kafin na gama rufe bakina sadauki muraizu ya fusata ainun ya zaro kibbau guda biyar a gadon bayan sa ya ya saka a cikin bakan sa yaja ya ɗame cikin wani irin zafin nama ya harba kibban Kafin ɗaya daga cikin mu yayi wani yunkuri kibiyoyin guda biyar sun sauka a kan waɗansu jama'ar mu mutum biyar sun faɗi kasa matattu Mutum biyar ɗin sun kasance dattijawa kuma manyan yan majalisar sarki da muke matukar alfahari dasu a cikin ƙauyen Darul-Na'am Koda sarki Abu-salimat yayi arba da gawarwakin yan majalisar tasa sai hawayen takaici da bakin ciki suka zubo masa, ** Lokacin da saurayi yaslir yazo daidai nan a labarin sa sai hawaye suka zubo daga idanun sa, Al'amarin da ya sanya sarauniya lasmirat ta kamu da matukar tausayin sa kenan. Har ta buɗi baki da nufin tace wani abu sai kawai suka ga sararin samaniya yayi dubu dunɗim! Cikin matukar firgici lasmirat da saurayi yaslir suka ruga mike tsaye zumbur suka ruga izuwa wajen turakar, suna fita suka ci karo da Sarkin yaƙi, Sarkin yaki ya dubesu cikin tashin hankali yace " ya shugabata muna cikin gudanar da ayyukan mu na tsaron kofa kawai sai mu kayi arba da wata gibgegiyar halitta mai matukar muni daban tsoro tana ta hallaka mutane, Ya shugabata na rantse da karfin mulkin ki babu wata halitta da zata tsira da ga sharrin halittar, Kafin Sarkin yaki yagama rufe bakin sa sarauniya lasmirat ta tari numfashin sa tace" A yi maza aje a busa ƙahon yaƙi, Batare da lasmirat ta jira Sarkin yaƙi ya furta wani abu ba ta shige gaba yaslir ya mara mata baya yana mai dogare da sandar sa, A can cikin gari kuwa halittar ta wanzu tana ta hallaka mutane jama'a suna ta guje-guje da ifice-ifice domin tsira da rayukansu, Duk inda halittar ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin jama'a birjik kwance a ƙasa cikin jini, A wasu lokutan ma sai kaga halittar ta sanya hannun ta ta yaye rufin ɗaki ta ɗauko mutum ya na ihu ta sanya a bakin ta ta laƙume tayi loma ɗaya dashi, Ana cikin wannan hali ne sai aka hango sarauniya lasmirat da saurayi sun rugo wajen a bisa dawakai cikin gagarumar shigar yaƙi suka tsaya cak, Kawai sai lasmirat ta dakawa halittar tsawa, Koda halittar taji an dakama tsawa sai ta tsaya cak a waje guda ƙurawa su lasmirat idanu tana mai nazarin su, Ita dai wannan halitta takasance,shirgegiyar aljani mai matukar tsawo,muni,gami da ban tsoro, Babu wata halitta da zata yi arba da wannan aljanar face firgici, Saboda matukar munin ta Duk irin dakewar zuciya irin ta lasmirat da saurayi yaslir sai da tsoro ya ɗarsu a zukatan su, Dakarun dake bayan su kuwa sai jikin su yakama kyarma yana tsuma tamakar ace kyat su cika wandon su da iska saboda tsananin tsoro, Sai da aka shafe tsawon dakika talatin a cikin wannan hali ana kallon kallo Daga can sai aljanar ta bushe da dariyar wanda ta haddasa girgizar kasa, Nan fa bishiyoyi suka dunga karairayewa suna zube ƙasa, gida je su ka dunga rushewa suna hallaka, ƙasa tana tsagewa dawakai da mahayan su suna rufta wa cikin ta, Ihun mazaje,mata, tsofaffi gami da yara ya cika dodon kunne, Sa,adda sarauniya lasmirat taga yadda jama'ar ta ke hallaka sai ta cika da tsananin baƙin ciki maral musaltuwa, Cikin fushi ta sake dakwa aljanar tsawa a karo na biyu tana mai cewa "yake wannan shu'umar aljana yau duhun ta cika idan har kin isa ki fito muyi fito-na fito na rantse da karagar mulki na sai na ga bayan ki, Koda jin wannan batu sai aljanar ta tsuke bakin ta komai ya samu dai dai tuwa bishiyoyi suka daina karyewa duwatsu suka daina fashewa kasa ta dai na tsagewa, Aljanar ta buɗe bakin ta wanda yafi kama da kofar gari cikin murya mai ban tsoro tamkar saukar aradu tace"yake wannan sarauniya kayi sani cewa bakomai ne ya kawo wannan birni naki ba sai domin ya kashe mutanen birnin ki kuma na mallake ki saboda wata muhimmiyar buƙata ta, Kafin aljanar ta gama rufe bakin ta saurayi yaslir ya tari numfashin ta yana mai daka mata tsawa cikin fushi yace"yake rafkananniyar aljana kuma yar tsakuwa a cikin jerin JARUMAN DUNIYA, kiyi sani cewa karyar ki tasha karya ina mai tabbatar miki dacewa bazaki tsira daga sharrin mu ba, Sai ki shirya ka maza nan bisa kanki, Yana gama faɗin hakan ya sakarwa dokin sa linzami yana mai gyara rikon sandar sa cikin hanzari lasmirat ta mara masa baya tana mai ɗaga takobin ta sama, Sauran dakaru mutum dubu arba'in sukayi koyi dasu Ana haɗuwa aka kacame da azababban yaƙi mai matukar tayar da hankali Domin kafin a haɗu sai da aljanar ta sanya hannu ta ta ɗebi dakaru mutum hamsin har da dawakan su ta watsa a bakin ta ta taunesu tayi kalaci dasu, Sannan ta afkawa su lasmirat. Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin shu'umar aljana da su sarauniya lasmirat, Sai lasmirat da yaslir suka wanzu suna kaiwa aljanar sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA Duk sa'adda makaman su suka sauka a jikin aljanar sai kaji sun bada kara ƙal ƙal !! Tamakar karfe suka sara In banda lasmirat da yaslir suna cikin kariyar tsafi da tuni sun hallaka, Idan aljanar ta kaiwa yaslir da lasmirat hari da hannayen ta, idan suka goce duk abin da hannun ta ya sauka akai sai dai kaga ya tarwatse,idan kuwa a ƙasa ne sai ya haddasa wani rami zurfin gaske, Take dakaru da dawakan su zasu afka cikin sa suna ihu da kururuwar neman taimako, Nan fa waje ya cika da ihun mazaje mata da yara da matasa, Karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne, JINI DA KASA suka cakuɗu, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, Lokacin da aka shafe dakika ɗari biyu da sittin ana wannan bakin gumurzu, Sai ya zama na cewa aljanar ta samu nasarar hallaka dakaru Fiye da dubu shida, Amma bata samu nasarar koda lakutar jikin su lasmirat ba sai ta cika da matukar mamaki kuma ta fusata ainun, Abin da ya bata mamaki shi ne ya akayi sarauniya lasmirat da saurayi yaslir suka kasance masu tsananin zafin nama, tabbas yau ta haɗu da takadiran jarumai, hakika rashin wannan nasara ƙasanta darajar ta ne da kimar ta, Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta canza salon faɗan ta yazamana cewa tana haɗa kai bugu da naushin hannu da ƙafa, Ai kuwa nan take labari yasha Bambam, domin a halin yanzu daƙyar su yaslir ke iya mayar da martani Idan ta daki gini ya tarwatse sai kaga duwatsun sun yiwa su lasmirat lugudan duka, Sai da aka shafe tsawon dakika dari da ɗoriya ana wannan fafatawa, Ana cikin wannan yaƙi ne aljanar ta kaiwa sarauniya lasmirat da yaslir wawan naushi da nufin yi musu farat ɗaya, Amma kafin hannun ta yakai gare su sai suka daka tsalle a sama tamkar an harbosu daga cikin baka suka bar kan dawakan su Sai gashi hannun ya sauka akan dawakan sun tarwatse tamakar an talitse tumatir, A daidai wannan lokaci ne yaslir da lasmirat suka sauka akan aljanar bisa tsakiyar kanta su shiga kafta mata sara babu sassauci, Nan fa yazamana sun riki ta aljanar yazamana cewa ta daina kaiwa dakaru hari Sai dai ƙoƙarin taga ta jefo su yaslir daga kan ta, ana cikin wannan hali ne aljanar ta samu nasarar damƙo su yaslir ta hannun ta ta matse su nan take suka sume sakamakon maƙurewar, Ashe ta samu nasarar karya ɗan yatsan yaslir, lasmirat kuma ta samu gocewar ƙashi, a hannun ta, Koda samun wannan gagarumar nasara sai aljanar ta bushe da shu'umar dariya Sai da tayi dariyar ta ishe ta sannan ta tsuke bakin ta kawai sai ta juya ta nufi kofar fita daga birnin tana mai koɗa kanta gami da yiwa kanta kirari, tana mai cewa " Saini GAWURTACCIYA uwar hatsabibai, GUGUWAR YAƘI nake mai share MAYAKA, ANNOBA ƊARI nake duk wanda ya Kusan ceni zai baƙun ci barzahu, Ni ne gararriya uwar gagararru, Haka ta cigaba da yiwa kanta kirarin tana lafiya a cikin birnin, Duk sa'adda ta ajiye kafarta ɗaya sai dai kaga ƙasa tana girgiza tamkar zata tsage abin da ke saman ta ya faɗa cikin ta Koda sauran dakarun suka ga abin da yafaru sai suka dunga ɗame kwari da bakan su suna Harbin aljanar Duk tsananin yawan kibban sai yazamana a banza domin ko gezau batayi ba Sai dai ma kaga ta sanya hannun ta ɗaya tana karkaɗe kibiyoyin kamar tana kaɗe ganyayyakin bishiya, Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ji aljanar ta kurma wawan ihu kuma ta faɗi ƙasa tim, Ta saki su sarauniya lasmirat suka faɗo ƙasa babu alamun rai a tare dasu , Kuma akaga aljanar ta ɗaga hannayen ta sama tana mai roƙon gafara Al'amarin da yayi matukar bawa dakarun mamaki kenan, suka rugo izuwa wajen domin su ga abin da ke wakana, Su na isowa sai suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya, Ai kuwa sai su kayi arba da wata kyakkyawar budurwa, Budurwur takasance dogowa mai matsakaicin kaurin jiki, cikin ta ashafe yake tamkar bata cin komai ba, Kuma a tsuke yake daga ƙasa, ƙugunta mai faɗi ne yayi tudu sosai, gashin kanta mai tsawo ne ya zuba har izuwa kan kafaɗun ta baƙi ne siɗik tamakar gilashi, a jikin ta tana sanye da tufafi irin na mutanen birnin sun, kanta daure da bakin rawani idanun ta kaɗai ake gani, A sannanne dakarun suka fahimci cewa wannan bakuwar budurwa ce ta ceci rayuwar su sarauniya lasmirat, Bakuwar budurwar ta nuna aljanar da ɗan yatsan ta na hagu take aljanar ta ƙame, tamakar gunki, komai na jikin ta ya daina motsi, Faruwar hakan keda wuya sai budurwur ta taka da ƙafafuwan ta izuwa inda su yaslir ke kwance, Kawai sai ta buɗe bakin ta ta karanto waɗansu kalamai da ita kaɗai tasan me take faɗa, Tana gama rufe bakin ta sai aka ga sarauniya lasmirat da saurayi yaslir sun mike tsaye zumbur tamakar babu wani abu da ya same su. Kafin wani daga cikin su yace uffan, budurwar ta sake nuna aljanar a karo na biyu da ɗan yatsan ta,take ruhin aljanar ya dawo jikin ta, komai nata yana yin motsi, Budurwur ta buɗi baki cikin wata irin zazzakar murya tamkar ana busa sarewa tace" yake wannan AZZALUMA kiyi sani cewa na yarda zan barki Lafiya kici gaba da rayuwa amma bisa sharaɗin cewa za ki dai na zaluntar al'umma, Cikin ladabi da ƙan-ƙan da kai aljanar tace Muryar ta na rawa saboda tsoro" Na amince ya shugabata na ɗaukar miki alkawarin cewa bazan kara cutar da wata halitta har abada, Koda jin wannan batu sai budurwur tayi wa aljanar nuni da ta tafi, Cikin hanzari aljanar ta miƙe tsaye ta buɗe manyan fuka-fukan ta tashi zuwa sararin samaniya tana mai keta gajimare cikin tsananin gudu keta Sa'a ta ɓace, Nan fa gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matukar mamaki maral musaltuwa, Abu na farko da ya basu mamaki shi ne yadda ta ceto rayuwar su sarauniya lasmirat kuma suka warke sumul, Abin da yafi basu mamaki kuma ya ɗaure musu kai shi ne yadda bakuwar budurwar take sarrafa aljanar tamakar tana juya waina (masa) a tanda, A ɓangaren sarauniya lasmirat kuwa, mamaki ne ya cika zuciyar ta ta kasa cewa uffan, Yaslir kuwa yafi kowa mamaki domin ko a mafarki bai taba ganin ya mace mai baiwar sarrafa irin wadannan aljanu ba, Kawai sai ya ƙurawa budurwur idanu yana nazarin ta, duk da kasancewar fuskar budurwur na rufe da rawani amma idanun ta kaɗai yaslir ya kalla ya fahimci cewa ta nunka sarauniya lasmirat a kyawun sura, Lasmirat da yaslir suka taka da ƙafafuwan su izuwa inda budurwur take tsaye, suka risina da kawunan su kasa domin girmama wa agare ta, Sannan lasmirat ta ta dube ta cikin murmushi mai taushi tace"yake wannan basadaukiya mace mai kamar maza shin mene ne labarin ki? Menene kuma dalilin da ya sanya kika ceci rayuwar mu ni da jama'ar birni na?. Koda jin waɗannan tambayoyi sai budurwur tayi shiru tana mai nazari, Daga can sai ta ɗago da kanta ta dubi yaslir, lasmirat tace cikin tattausar murya " Da farko dai suna na Sunaila na fito daga cikin wata nahiya da ake yiwa da Haurul-zamras, Abin da ya baro dani daga birnin mu shi ne domin na sadu da waɗansu irin mutane da ake yiwa laƙabi da musulmi, Babban burina shi ne na sadu da su kuma na karɓi Addinin su domin na samu nasarar ɗaukar fansa akan azzalumin sarki da ya rusa mini farin cikin rayuwa ta, Wannan nasara da kuka ga na samu na sarrafa wannan aljana ba tsafi ba ne kawai ina neman taimakon Ubangijin ma'abota addanin Musulunci ne, Sa'adda jaruma Sunaila tazo nan a bayanin ta sai mamaki ta turnuƙe su yaslir, Sunaila ta ɗora da cewa" Na shigo wannan birni naki ne na ɗan wani lokaci ne domin na bincika ko zan dace na samu irin waɗannan mutane ma'abota addinin Musulunci, Koda jin wannan batu Daga bakin Sunaila sai lasmirat ta ce"Kada ki samu damuwa yake Sunaila zan baki masauki har zuwa lokacin da za ki sadu da mutane ma'abota addanin Musulunci, domin ba za mu iya biyan ki taimakon da kika yi mini ba, Koda jin hakan sai sunaila ta cika da matukar farin ciki tace" Godiya nake ya shugabata, Da jin haka sai lasmirat ta matsa daf da ita ta yadda suna iya jin numfashin juna ta dafa kafaɗun ta tace da ita" yake Sunaila daga yau bana so ki kirani da shugabar ki face abokiyar ki ko Aminiya, Sa'adda Sunaila ta ji hakan sai ta gyaɗa kai cike da farin ciki, Cikin hanzari sarauniya lasmirat da yaslir suka juya suka nufi gidan sarauta,jaruma Sunaila na biye da su, Ana cikin tafiyar ne lasmirat ta lura cewa yaslir yana satar kallon jaruma Sunaila ta wutsiyar idanu, Nan take taji kishi ya turnuƙe ta, domin ta fahimci cewa yaslir yana yiwa jaruma Sunaila kallon SO ne, Kawai sai ta jefe sa da wata irin haramta, a lokacin da yake satar kallon, Take yaslir yaji hantar cikin sa ta kaɗa, kuma kunya ta kama sa ya sunkuyar da kansa ƙasa aka cigaba da tafiya,har aka isa gidan sarauta ɗayan su bai ce uffan ba, Har zuwa masauki lasmirat da yaslir suka raka jaruma Sunaila, Sannan kowa ya tafi izuwa bangaren sa, Lokacin da yaslir ya kwanta a bisa kan gadon sa domin ya huce gajiyar dake tattare dashi, sai barci ya gagare sa, Duk sa,adda ya runtse idanun sa sai ya yaga fuskar jaruma Sunaila rufe da rawani, Tana yi masa murmushi, nan take yaji tsananin SO da begen Sunaila ya mamaye zuciyarsa, Wani abu da ya faɗo masa arai shi ne shin hararar da lasmirat ke yi masa a ɗazu mene ne ma'anar sa shin tana tsananin kishi ne da kallon Sunaila da yayi, Shin ke nan hakan na nufin ita sarauniya lasmirat ta kamu da matukar kaunar sa kenan?. Amma yanayin tsayuwa da tafiyar da Sunaila tayi a ɗazu a filin yaƙi iri ɗaya ne sak da na masoyiyar sa gimbiya salimat, Shin jaruma Sunaila ita ce masoyiyar salimat? Sa'adda yaslir yazo nan a tunanin sa sai ya shiga cikin tsananin damuwa, Kuma yaji gaba ɗaya duniyar tayi masa ƙunci, nan take ya ƙudiri aniyar cewa sai yaga fuskar Sunaila kafin tabar wannan birni. *** 3 Kamar yadda ya wakana ga saurayi yaslir haka al'amarin yakasance ga sarauniya lasmirat, A inda ita ma barci ya gagare ta, Abu na farko da ya faɗo mata arai shi ne, shin Mene ne yasanya yaslir zai kamu da soyayyar Sunaila, Alhalin ta nuna alamun so, Sannan taya zai kamu da son wacce koda fuskar ta bai gani ba, Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tunanin ta sai taji zuciyar ta tayi ƙunci, kuma tasha alwashin cewa sai ta bayyana soyayyar ta ga yaslir a lokacin da suka gudanar da tafiya ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA, Da ɗebo ruwan ƙoramar boka Daryalu. Tun da tana so ne tafiyar ta kasance har da jaruma Sunaila za a yi ta, Daga wannan shawara ne sai ta ɗauko madubin tsafin ta domin gudanar da bincike don irin wainar da ake toyawa a duniya, *** Acan inda aka fafata yaƙi kuwa dakaru sun shiga aikin su na kwashe gawarwakin jama'a da waɗanda suka samu raunuka aka shiga duba lafiyar su, Kasancewar a wannan lokaci duhun dare ya fara Kawo kai sai aka kunna fitar ice aka cigaba da aiki Inda ace mutum zai ga yadda ake kwashe gawarwakin jama'a jini na kwaranya sai ya rantse yace a mahauta yake, Waɗanda suka rasa iyayen su, ya'ya da yan uwa gami da gidaje sai suka shiga rusa kukan baƙin ciki Domin a iya tsawon wanzuwar birnin Misra ba'a taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba, Kashe gari tunda duku dukun safiya sarauniya lasmirat ta umarci kuyangi suka shirya nau'ikan kayan abinci da abin shaye shaye da tanɗe tanɗe a bisa wani dogon teburin azurfa, a cikin wata ƙasaitacciyar turaka ta musamman, Kuyangi na cikin kammala aikace aikace a cikin turakar sai ga sarauniya lasmirat ta shigo, Cikin ƙayatattun tufafi irin na manyan sarakai, Koda shigowar ta sai gaba ɗaya kuyangin suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa Lasmirat ta amshi gaisuwar sannan ta umarci wata kuyanga ta tafi zuwa masaukin su yaslir ta yi musu iso, kuma ta ce tana gayyatar su walima, Jim kadan da ficewar kuyangar sai ga yaslir ya shigo Turakar,yana sanye cikin shiga riga da wando na alhariri masu taushi da ƙyalli, Yana shigowa ya risina ga sarauniya lasmirat sannan yaje ya zauna abisa wata kujera dake fuskantar ta, Ana cikin wannan hali ne Sunaila ta shigo, ta shigo turakar duk da cewar ta canza tufafin dake jikin ta amma har a wannan lokaci fuskar ta rufe da rawani idanun ta kaɗai ake gani, Bayan ta miƙa gaisuwa ga lasmirat sai ta zauna a kujerar dake fuskantar lasmirat da yaslir, Lasmirat ta dubi yaslir da Sunaila tace" yaku waɗannan baki masu daraja a gare ni, kuyi sani cewa na kiraku nan ne domin shirya muku walima bisa taimakon da ku kayi mini, Wanda bani da abin da zan saka muku dashi Koda gama faɗin hakan sai sarauniyar lasmirat ta tsiyaya ruwan inibi a cikin yan kananan kofunan zinare guda uku ta miƙawa yaslir da Sunaila kofuna biyu suka karɓa, Sannan ta ɗauki na uku a hannun ta, kamar hadin baki a lokaci guda suka kai kofunan bakunan su suka shanye ruwan inibi, Sannan aka shiga hidimar ciye-ciye da tanɗe-tande ana fira cikin nishaɗi, A cikin firar ne lasmirat ta dubi yaslir tace"In tambaye ka mana ɗazu da ka shigo naga fuskar ka akwai alamun damuwa shin ko me ya kawo hakan, Yaslir ya shafi sajen sa da gemun sa yace" na ɗan makara ne shi ne ya sanya Ni cikin damuwar, Koda jin amsar wannan tambaya sai lasmirat tayi murmushi ga yaslir mai ɗauke da alamar tuhuma, Sannan ta gyaɗa kai cikin gamsuwa, Al'amarin da sanya yaslir yaji hantar cikin sa ta kaɗa, Amma sai ya banzatar da abin aka cigaba da ciye-ciye da tanɗe tanɗe kamar babu wani abu. Bayan kowa ya kimtsa cikin sa an samu nutsuwa kuma shiru ya wanzu, Sai lasmirat ta dubi yaslir da Sunaila tace"yaku ababan soyuwa a rai na, kuyi sani cewa babbar muhimmiyar maganar da nake so mu tattaunawa Ita ce, ina so ku taimake ni muyi wata gagarumar tafiya tare daku, Nan take lasmirat ta kashe labarin abinda ya wakana tsakanin ta da boka Dayyubul-Barmas akan batun ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA ta zayyanewa su yaslir da ga farko har karshe, Sannan ta ɗora dacewa yaku waɗannan baki masu daraja a gare ni kuyi sani cewa idan har kuka taimake ni wajen cika burina Ina mai tabbatar muku dacewa zan raba kasa uku,dukiya, da komai nawa kowannen ku ya ɗauki ɗaya Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan azancen ta sai yaslir da Sunaila suka cika da matukar mamaki, kuma suka zurfafa izuwa kogin tunani, Sannan daga bisani yaslir da Sunaila suka dubi lasmirat Cikin haɗin baki suka ce mun amince da wannan bukata taki ya mai karamci, Koda jin wannan batu sai sarauniya lasmirat ta cika da matukar farin ciki mara musaltuwa, Kuma ta labarta musu ranar da zasu gudanar da tafiyarsu, Ranar da tafiya dajin Husumul-kadar tazo, sarauniya lasmirat, yaslir da Sunaila suka yi gagarumin shiri, Suka hau bisa dawakai suka nufi hanyar da zata sadasu da gidan boka Dayyubul-Barmas, Bayan lasmirat ta bayar da rikon sarautar ta a hannun waziri ukashat, Kuma waziri ukashat ɗin da sauran al'ummar gari sun yi musu rakiya har zuwa kofar gari, Lokacin da sarauniya lasmirat suka iso gidan boka Dayyubul-Barmas sai suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya, Su kayi cirko- cirko suna masu ƙarewa gidan kallo, shi dai gidan boka Dayyubul-Barmas yakasance ɗan madaidaici da aka ginasa da zallar duwatsun wuta masu ƙyalli, yana da kofa guda ɗaya da akayi ta da zallar karfen jauhari, Bakomai yasanaya su sarauniya lasmirat suka yi wannan cirko-cirko ba sai bisa ganin Kofar gidan a garƙame, kuma ya na lulluɓe da wata yanar gizo gizo Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai akaga boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum! a gaban su fuskar sa cike da annuri, Yana sanye cikin kyawawan tufafi na alfarma,sun yi matukar yi masa kyawu, a hannun sa yana rike da wata isgar tsafi,wacce take canza launi Lokaci zuwa lokaci, wani lokacin ta koma baƙa,shuɗiya ko Koriya, Lasmirat ta yi murmushi ga boka Dayyubul-Barmas daya ƙarawa fuskar ta annuri tace"ya abin dogaro na shin ina dalilin rashin bayyanar ka akan lokaci domin gudanar da wannan tafiya tamu? Dayyubul-Barmas yayi murmushi yace" ya sarauniyar kiyi sani cewa bakomai bane ya sanya ban bayyana akan lokaci ba sai domin na kara gudanar da bincike ne game da tafiyar tamu, Koda jin wannan batu sai lasmirat tace " ka gafarceni ya uban bokaye, Dayyubul-Barmas ya tari numfashin ta yace "ba sai kin wahalar da kanki wajen sanar da ni sunayen a bokan tafiyar ki ba, Yaslir da Sunaila, dukkan su ilimin tsafi ya bayyana mini abin da ya gudana tsakaninsu da su, Tabbas kin yi tunani mai kyau, domin Sunaila da yaslir zasu yi matukar taimaka wajen wannan tafiya tamu, Yanzu ina ganin abinda ya kamata mu fara yi shine tafiya domin ɗebo ruwan koramar boka Daryalu, domin hakan shi ne zai bamu damar fuskantar dajin Husumul-kadar, Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya kwallawa aljanin sa kira sau uku, Aljanin ya bayyana gaban sa ya kwashi gaisuwa, duk da kasancewar su lasmirat suna da dakakkiyar zuciya sai da suka razana da ganin aljanin, Aljanin yakasance garjejen kato karfaffan gaske,yana da rafkeken kai tamkar dutse,mai ɗauke da waɗansu manyan idanu jajaye,tamakar kwallon goriba,yana da katon hanci da rafkeken baki, sannan ya da manyan fuka-fukai guda shuda, Boka Dayyubul-Barmas ya dubi aljanin cikin nutsuwa yace"yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka ɗauke mu izuwa Husumul-kadar domin ɗauko zobunan sihiri a cikin kogon fatalwa, Daga nan kuma mu huce izuwa inda ma'ul-diya'u yake mu ɗauko kubar miftahul-daryal, Yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zaka samu ya ci Yayin da aljani Huzmal yaji wannan batu sai ya risina ya ce" An gama ya shugabana Yana gama faɗin hakan sai ya shimfiɗe gadon bayan sa boka Dayyubul-Barmas, lasmirat, yaslir da Sunaila suka hau suka zauna Sannan ya yunkura ya ya tashi sama ya na mai buɗe fuka-fukan sa yana mai keta gajimare, cikin sa wani irin azababban gudu na keta sa'a Tun da aka fara wannan tafiya babu wanda yace kala har yazamana an shafe tsawon sa,a uku Ana cikin wannan hali gyangyaɗi ya fara ɗaukar boka Dayyubul-Barmas koda ganin hakan sai dariya ta suɓucewa sarauniya lasmirat wanda ta sanya Dayyubul-Barmas dawo cikin hayyacin lasmirat ta dube sa tace" Haba dodon bokaye ai bai kamata ace irin ku suna suna barci ba, Koda jin wannan batu sai dariya ta suɓucewa boka Dayyubul-Barmas ya dubi lasmirat yace"Taɓ ɗi jan wannan fa shi ake cewa wai ana wata ga wata Dara ta ci gida ke yanzu wannan gyangyaɗi da nayi shi ne ya baki mamaki, tabbas da ace kin taɓa jin labarin boka shu'umanu da baki yi mini wannan dariya ba, Wane ne kuma boka shu'umanu? Lasmirat ta tambaya a ƙagauce, Dayyubul-Barmas ya ce" boka shu'umanu wani hatsabibin matsafi ne da ya shiga alwar tsafi ta tsawon shekaru uku domin ya karance wani muhimmin littafi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN JARUMTA, Babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki kundin ya karantasa baki ɗaya face ya mulki duniya, A daren ranar da boka shu'umanu zai kammala wannan karatun littafi ne wani irin barci mai nauyi ya ɗauke sa Sa'adda boka Dayyubul-Barmas ya zo nan azancen sa sai mamaki ya kama lasmirat, yaslir da Sunaila, Lasmirat ta ce" shi kuwa Boka shu'umanu da ya farka daga barcin me ya faru dashi, Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya ce"Ai wannan tambaya taki labari ne mai tsawo sai dai ki nemi littafi KUNDIN JARUMTA ki karanta, Lasmirat ta gyaɗa kai aka cigaba da tafiya, Kwanaki nabin kwanaki,mako nabin mako sai gashi su sarauniya lasmirat sun shafe kwanaki ashirin da uku suna tafiya, A iya tsawon wannan kawanki babu abinda ke sanyawa a tsayar da tafiya face idan wani daga cikin su zai yi bawali ko kuma lokacin barci yayi, Ana cikin tafiyar ne saurayi yaslir ya dubi Sunaila yace da ita" ya JARUMAR JARUMAI, shin mene ne dalilin daya sanya kika ƙi bayyana fuskar ki a garemu? Koda jin wannan tambaya sai sunailata sunkuyar da kanta ƙasa kamar mai tunanin wani abu, Daga can sai ta ɗago da kanta ta dubi yaslir tace"Ai wannan rufe fuska tawa yana da matukar muhimmanci agareni anan gaba zaka tabbatar da abinda na faɗa Idan kuwa har ka na so ne kaga fuskar ta wa to yazama wajibi ka amince da sharudda guda uku Da farko zaka yanko mini kan riƙeƙƙen zaki da ya shekara arba'in, Na biyu kuma zaka ceto rayuwar abokan tafiyar mu har sau uku Abu na karshe shi ne zaka farauto mini damisa guda biyu ka kawosu gare ni, Sa'adda saurayi yaslir yaji waɗannan sharuddan daga bakin Sunaila sai sai ya shiga nazari. Abu na farko da ya faɗo masa arai shi ne menene fa'idar waɗannan sharuɗɗa da Sunaila ta gindaya masa, To amma tun da a halin yanzu bashi da burin da ya huce yaga fuskar Sunaila dola ne ya amince da wannan sharuɗɗa, Kawai sai yayi gyaran murya ya dubi Sunaila yace" Na amince da wannan sharuɗɗa naki ya JARUMAR JARUMAI Duk wannan tattaunawa da ake tsakanin yaslir da Sunaila sarauniya lasmirat ta na sauraron su Koda taji yaslir ya amince da sharuɗɗan jaruma Sunaila domin ya yi arba da fuskar ta kawai Sai zuciyar ta takama tafarfasa tamkar zata kone kuma tsananin kishi ya turnuƙe ta, Lallai lokaci yayi da zaki bayyana soyayyar ki ga yaslir domin matsawar yayi arba da fuskar Sunaila Abin da kike gudu zai fara Koda jin wannan shawara daga zuriyar ta sai lasmirat sai ta bar abin a ranta Amma sai wani tunanin ya faɗo mata,shin wai ma me yasa zaki kamu da soyayyar wanda bazai ji kiranki ba,kuma Bayan cewa bashi ne namijin da zaki aura ki samu Haihuwa ba, Sa'adda tazo nana atunanin ta sai taji zuciyar ta tayi mata ƙunci, Har lasmirat ta buɗi baki zata ce wani abu sai boka Dayyubul-Barmas ya dubi aljani Huzmal yace dashi" Yakai Huzmal ai sai ka sauka a turba domin mun iso dajin Husumul-kadar Koda jin wannan umarni dai Huzmal ya saki fuka fukan sa ya sauka a turba, Boka Dayyubul-Barmas ne yafara saukowa sannan lasmirat, yaslir, Sunaila ce a ƙarshe, Nan fa aka yi arba da dajin Husumul-kadar yakasance mai ɗauke da manyan bishiyoyi masu tsawo tsiya babu duwatsu ko ɗaya a cikin sa face waɗansu manyan koguna guda uku masu ban tsoro, Wani irin farin hayaƙi ya mamaye dajin baki ɗaya babu alamar haske rana a cikin sa, Tabbas wannan daji yakasance mai ban tsoro, Tsawon daƙika arba'in su lasmirat na karewa dajin kallo sai daga bisani boka Dayyubul-Barmas ya dube su yace" yaku abokan tafiya kuyi sani cewa a cikin wannan daji ne zamu ɗauko zobunan sihiri, Sai dai ina so kuyi sani cewa wannan daji ne na ɗauke da musibu da bala'o'i da sai mun yi da gaske zamu tsira da rayukan mu,da wannan nake yi mana fatan samun nasara, Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya shafi sandar tsafin sa take ta rikiɗa izuwa wani ƙaton sungumi Sai kawai ya kunna kai izuwa cikin dajin yana mai cewa aljani Huzmal sai ka jira mu anan Lasmirat, yaslir da Sunaila suka mara masa baya, Tun da aka shiga dajin Husumul-kadar sai da aka shafe tsawon dakika ɗari biyu koda motsin tsuntsaye ba,a ji ba, Al'amarin da ya ƙara jefa tsoro a zukatan su sarauniya lasmirat kenan. Lokacin da aka iso inda wannan koguna suke sai aka shiga nazari Boka Dayyubul-Barmas ya dube su yace" A cikin waɗannan kogunan dutse uku ne zamu ɗauko zobunan sihiri sai dai ba za mu iya gane wanne ne wanda zobunan ke ciki ba, Karfin shirin tsafi bazai taba tasiri a cikin su face dole mu shiga izuwa kogo na farko ko zamu dace , Lasmirat ta dubi Dayyubul-Barmas cikin damuwa tace to mai hana bazamu koma baya ba domin mu gudanar da bincike mu gano kogon da zobunan sihirin ke ajiye a cikin sa, Dayyubul-Barmas ya ce "Ai bisa sharaɗin wannan daji idan mutum ya shigo baya fita kodai ya samu nasarar ɗauko zobunan sihiri ko kuwa ajali Ya riske shi a ciki, Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya matsa kusa da kofar kogo na farko ya ɗaga kansa sama ya karanta waɗansu haruffa da aka rubuta da tawadar za'afaran jikin wani allon karfe a saman kogon, Yana kammala karantawa sai kofar kogon ta buɗe wani irin tiririn bakin hayaƙi ya surnano daga cikin sa, Boka Dayyubul-Barmas ya tusa kai izuwa ciki, lasmirat, yaslir da Sunaila suka yi koyi dashi, lokacin da Sunaila wacce ita ce ta karshe ta sanya kafarta ta biyu sai kofar kogon ta mayar da kanta ta rufe ruf Tamkar bata taɓa budewa ba, Lokacin da su sarauniya lasmirat suka shiga izuwa cikin wannan kogon dutse na farko a cikin dajin Husumul-kadar, Sai suka ci-gaba da tafiya a cikin sa suna ganin abubuwan abubuwan al'ajabi kala daban daban, A wasu lokutan sai suji alamun takun sawaye a bayan su amma dazarar sun waiga sai su ga basu ga komai ba, Haka dai suka ci-gaba da tafiyar babu sassauci, har yazamana sun shafe tsawon dakika ɗari huɗu batare da an haɗu da wani abu mai cutar wa ba, Yana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai su lasmirat su kaji wani mahaukacin gurnani ya mamaye kogon dutsen gaba ɗaya ya kama girgiza tamakar zai rugurguje, sannu a hankali wani takun sawaye yafara bayyana, Kwatsam sai wani mutum ya bayyana tsulum Tamkar an jefoshi daga sama, Mutumin yakasance narkekeken kato, rabin jikin sa na gwaggwan biri ne, rabin kuma na bil,adama ne, Yana matukar tsawo tamakar tsauni, yana da tarin kwanji tamkar jikin sa yakasance na dutse,fuskar sa mummuna ce mai matukar kwarjini daban tsoro, mau ɗauke da gashin gemu da ƙasumba buzu buzu babu kyan gani, wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita daga hancinsa duk sa'adda ya busar da numfashi, Tabbas wannan mutum ya kasance abin tsoro domin babu wani jarumi da zai yi arba dashi face ya ɗimauce, Sa'adda su sarauniya lasmirat suka yi arba da mutumin sai suka firgita ainun Lasmiratda yaslir jikin su yakama kyarma yana tsuma tamkar nazari Dayyubul-Barmas da Sunaila ne kaɗai basu yi ba amma su ma a matukar razane suke,kawai dai karfin hali ne irin na GWARAZAN MAYAKA Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su lasmirat da Sai da aka ɗauki wani lokaci ana wannan kallon kallo, Sai daga bisani ne mutumin ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta wanda ta haddasa girgizar kogon kuma wani ƙara mai kama da aradu ya bayyana, Bashiri su lasmirat suka sanya hannayen su biyu suka toshe kunnuwan su domin ji sukayi kamar zasu kurman ce, Sai da narkekeken kato ya tsuke bakin sa sannan komai ya samu dai dai tuwa, kogon ya dai na raurawa,kuma su lasmirat suka dawo hayyacin su kuma har ma suka lura cewa ashe mutumin yana ɗauke da wata gabgegiyar jela wadda akalla tsawon ta yakai kamu arba'in, Narkekeken katon ya dakama musu tsawa data sanya hantar cikin su ta kaɗa ya dube su cikin wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki yace "Yaku waɗannan bil'adama ma'abota GAJERAN KWANA shin wane rashin hankali ne ya shigo da ku wannan kogo bayan cewa fiye da shekaru dubu uku babu wata halitta walau mutum ko aljan da taɓa yin wannan ganganci Sai dai nasan cewa bawai rashin sani ya kawo ku nan ba sai domin kwaɗayin daukar zobunan sihiri Dake ajiye a ɗaya daga cikin waɗannan kogunan dutse biyar na cikin dajin Husumul-kadar, Ina mai tabbatar muku dacewa kun tafka babban kuskure da zuciyar ku ta bayyana muku dacewa zaku fita daga wannan daji a raye ɗauke da zobunan sihiri Kafin mutumin mai siffa biyu yagama rufe bakin sa boka Dayyubul-Barmas ya tari numfashin sa Yana mai dakamasa tsawa yace "Yakai wannan mummunan halitta kayi sani cewa kwarjini da girman ka bazai bamu tsoro ba Shin ko ka manta ne cewa karfi a zuciya yake bawai a jiki ba, uma idan akwai rai to da rabo, kaga kenan akwai yiwuwar samun nasara akan ka kuma har mu ɗauke zobunan sihiri, Caraf mutumin ya tari numfashin boka Dayyubul-Barmas ya dube sa yana mai bushewa da dariyar mugunta a karo na biyu, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa, "Tabbas gaskiya ne maganar ka amma fa kar ka manta cewa masu iya magana na cewa" Alamar karfi tana ga mai ƙiba, Wani abu ma da baku sani ba shi ne shi kansa matsafi zarratu ibn lauhat da ya sana'anta zubonan sihirin a halin yanzu ba shi da iko dasu ballantana wani bil'adama karan kaɗa miya, Sannan ma yanzu idan kun samu nasarar hallaka ni taya ya kuke tsammanin zaku tsira daga sauran musibun dake cikin wannan daji, Bayan cewa ma kuma a cikin ku babu wanda yasan inda zobunan sihiri suke a cikin koguna biyar ɗin, Koda gama faɗin hakan sai narkekeken katon ya zira hannun sa a cikin wata akwatu ta baƙin ƙarfe da ke kusa dashi a ɗauko wani zabgegen gatari na zallar mulmulallan farin karfe yana sheƙi,walwali da ɗaukar idanu ya yunƙura izuwa inda su sarauniya lasmirat suke tsaye, Koda ganin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya ɗaga sungumin sa sama yana mai kurma wawan ihu ya ruga izuwa kan halittar, Yaslir ne ya mara masa baya hannun sa rike da takobi tsirara, Sunaila da sarauniya lasmirat ta suka ru fa masa baya, Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari. Mansur Usman Sufi Littafanyaki.com.ng Takobin Daukaka Book 2 compelet Littafin Yaki Mansur Usman Sufi Ana haɗuwa aka kacame da azababban yaƙi mai matukar muni daban tsoro, Ana fara wannan gumurzu ne su sarauniya lasmirat suka fara gane kuren su, Domin ƙarfin saran su su duka hudun bai kai ɗaya na mutumin mai siffa biyu ba, Domin duk sa'adda daya kaiwa ɗaya daga cikin su sara idan ya zillewa harin duk sa'adda gatarin ya sauka a ƙasa sai kaga ya haddasa rami mai tsawon kamu ashirin, idan kuwa akan dutse gatarin ya sauka sai kaga yayi bindiga ya tarwatse Sai da aka shafe tsawon sa,a ɗaya ana wannan baƙin artabu babu sassauci, Ana cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗowa mutumin mai siffa biyu, Abin da ya faɗo masa kuwa shine shin mene ne dalilin da daya sanya ya kasa samun nasara akan waɗannan bil'adama alhalin baya ta ɓa fafata yaƙi da wata halitta a cikin abinda bai gaza dakika goma ba face ya zare mata ruhin ta daga gangar jiki, Tabbas akwai wani abu Ruwa baya tsami banza Koda narkekeken katon ya zo nan a tunanin sa sai ya fusata ainun zuciyar ta kama tafarfasa tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje, Kawai sai ya canza salon faɗan sa yazamana cewa ya sake zage damtse wajen kai wa su boka Dayyubul-Barmas miyagun hare haren fiye da ɗazu Gami da haɗawa da kai mu su naushi da bugu hannu da ƙafa, Kaico gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ma ta canza Faruwar canza salon faɗan keda wuya sai mutumin yafara samun nasarar naushin su boka Dayyubul-Barmas, Yazamana cewa idan ya naushe sun sai kaga sunyi sama tamakar an janye su da ƙugiya sannan daga bisani su faɗo ƙasa tim Idan fuska ya nausa sai kaga hanci da baki na yoyon jini, idan kuma ajiki yayi naushin sai wajen yayi tsami, jini ya tari, Amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA sai kaga sun mike tsaye zumbur an cigaba da artabu Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje a lokacin da ake wannan artabu yaga yadda su boka Dayyubul-Barmas ke yakin cikin juriya da nacin tsiya Dola ne ya jinjina musu ya tabbatar dacewa sun cika GWARAZAN MAYAKA masu dakakkiyar zuciya, Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne Sunaila ta kaiwa narkekeken katon hari da takobin ta a hannun sa a lokacin da yake ƙoƙarin tarwatsa mata kai Bisa sa'a sai gashi takobin ta tayi tasiri a jikin ɗan yatsan sa har jini yayi tsartuwa. A dai dai lokacin ne sarauniya lasmirat ta samu nasarar laftawa narkekeken katon sara a kafar sa take inda ta sara ɗin ya haddasa wani katon rauni jini yayi tsartuwa gami feshi, Al'amarin da yayi Matukar bawa sarauniya lasmirat da Sunaila mamaki kenan domin tunda aka fara wannan yaƙi hakan bai faru ba, domin idan takubban su suka sari mutumin sai dai suji tamkar dutse suka sara tartsatsin wuta ne kawai yake tashi gami da kara marar daɗin sauraro, Sa,adda mutumin mai siffa biyu naga raunuka biyu a jikin sa kuma dukkanninsu suna zubar da jini sai kawai yayi wurgi da gatarin sa gefe guda ya takarkare ya kwarara wawan ihu wanda ya mamaye kogon dutsen kuma ya haddasa wata yar ƙaramar girgizar ƙasa, Kafin ɗaya daga cikin su yayi wani yunkuri mutumin mai siffa biyu ya shammace su ya gabza musu wawan naushi a fuska cikin zafin nama a lokaci guda su duka huɗun suka zube kasa magashiyan numfashin su na fita sama Kawai sai ya wurgila jelar sa izuwa inda suke kwance,take ya samu nasarar kanannaɗo boka Dayyubul-Barmas, Sunaila da lasmirat da jelar sa, Nan take suka fara gani dishi- dishi sakamakon naushin da mutum yayi musu kuma suka ji tamkar ƙasusuwan jikin su zasu karye, saboda yadda jelar tayi kanannade su tayi musu ɗaurin Hunhun goro, Sa,adda Sunaila ta duba taga babu yaslir sai tace a ranta shin ina yaslir ya shiga ko kuwa ya rasa rayuwar sa ne? Amma idan har yana raye wannan itace damar sa ta farko dazai ceci rayuwar mu ɗaya daga cikin sharuddan da zai bi har ya samu nasarar ganin fuskata, Abin da Sunaila bata sani ba shi ne lokacin da mutumin ya kanannaɗo su da jelar sa yaslir ya gangara izuwa wani rani dake tsakiyar kogon dutsen, Lokacin da boka Dayyubul-Barmas ya ga irin mummunan halin da suke ciki sai ya shiga ƙoƙarin ceto rayuwar ta karfin sihiri,amma shiru kakeji malam ya ci shirwa, Koda mutumin mai siffa biyu yaga cewa Boka Dayyubul-Barmas na ƙoƙarin cewa rayuwar abokan tafiyar ta karfin sihiri sai ya sake bushewa da dariyar mugunta har da kyakyatawa, Ya shiga koɗa kansa yana yiwa kansa kirari yana mai cewa "" Nine gagarau uban gagararru Guguwa nake maganin karmami Wutar bala'i mai tada hankalin duniya, Mutum dubu kalacen dafe,aljanu dubu goma kalacen yamma"" Kammala yiwa kansa kirarin keda wuya sai kawai ya yi nuni da ɗanyatsan sa na hagu izuwa ga wannan akwatin bakin karfe daya ɗauko gatarin sa a ciki, Take wata irin gagarumar wuta ta bayyana a cikin akwatin tamkar dama can akwai ta, Kawai sai ya juyar da jelar sa izuwa inda akwatin take, nan take tiririn zafin ya sumar da su boka Dayyubul-Barmas. Mutumin mai siffa biyu ya bushe da dariyar mugunta bisa ganin wannan gagarumar nasara da ya samu akan su boka Dayyubul-Barmas, Dariyar tasa ta haddasa girgizawar kogon, a lokaci guda kuma ya tsuke bakin sa tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA kawai sai ya nufi wata kofa a cikin kogon dutsen, Kwatsam bazato babu tsammani sai mutumin yaji an dankara masa wawan sara a gadon bayan sa, Saboda karfin saran sai da sai da takobin ta nutse a gadon bayan sa, Kawai sai ya kwarara ihu tare da waigawa bayan sa domin ya ga wanda ya sareshin. Ai kuwa yana waigwa sai yayi arba da jarumi yaslir hannun sa riƙe da zaratan takubba masu kaifi da tsinin tsiya, A dai dai lokacin ne jini yafara kwaranyo wa daga inda yaslir ya sare shi , Mutumin ya dakawa yaslir tsawa wanda ta sanya kogon ya amsa da karfi, Bisa mamaki sai mutumin yaga ko gezau yaslir bai yi ba, al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan, Domin bai taba dakawa wata halitta tsawa ba face ta ɗimauce,ko ma ta rasa rayuwar ta, Wani tunani da ya faɗo masa shi ne, taya ya wani makami yayi tasiri akan sa Bayan cewa hakan bai taɓa faruwa ba, Lallai bakaramin kuskure kayi ba da ka manta da wannan bil,adama, Sa'adda halittar yazo nan a tunanin sa sai zuciyar sa ta kama tafarfasa tamkar zata kone jikin sa yakama kyarma yana tsuma tamkar mazari, Kawai sai ya miƙa hannun sa ya ɗauko wannan Gatari nasa Sannan ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa kan yaslir yana mai ɗauke da su boka Dayyubul-Barmas a ɗaure a jelar sa, Sa,adda yaslir yaga halittar ya rugo izuwa gare sa cikin mugun tanadi, Sai kawai ya gyara tsayuwar sa, lokacin da ya rage sauran taku Sai yaslir ya dako wawan tsalle tamkar an harbo sa daga cikin baka yana saman ya kaiwa halittar sara da takubban sa biyu a kafaɗa, Bisa sa,a sai gashi ya same Shi har jini na zuba a kafadar tasa Cikin gwanin ta yaslir ya yi katantanwa a sama sau uku ya dira ƙasa a bisa duga-dugan sa cikin gwanintar yaki, Sannan suka kacame da azababban artabu mai matukar muni,ban tsoro daban al'ajabi, Sai da aka shafe tsawon sa,a biyu ana wannan gumurzu babu sassauci, Tsawon wannan lokaci babu wanda ya samu nasarar lakutar jikin abokin gwamin sa, Duk sa'adda mutumin mai siffa biyu yakaiwa yaslir sara inda ya goce duk abinda gatarin ta sauka a kansa sai kaga wajen yayi rami mai zurfi, Idan akan Dutse ne sai Dutsen yayi bindiga ya tarwatse, Kafin cikar dakin talatin yaslir yafara galabaita saboda yadda yake zillewa harin mutumin, A dai dai lokacin ne kafafatun yaslir suka faɗa cikin wani rami a kogon kuma wani dutse ya danne sa, Wohoho! Wuya mai sa dole, shi kuwa tsoro na iya sawa mutum ya aikata abin da ko a mafarki bai taba tunanin zai iya ba idan yaga bala'o'i, Koda yaslir yaga halin da yake ciki kuma ya tabbatar da cewa idan har bai yi wani abu ba zai iya rasa rayuwar sa Sai kwai akaga yaslir ya sanya hannayen sa biyu ya ture Dutsen daya danne sa ta ƙarfin tsiya,kuma ya naushe sa da hannayen sa biyun cikin baƙin zafin nama take dutsen yayi sama tamkar an janye da ƙungiya ya daki fuskar mutumin mai siffa biyu, Take halittar ya ɗimauce ya gigice yayi jifa da gatarin sa ya sanya hannayen sa biyu akan fuskar sa yana rusa ihu, Koda yaslir ya duba hannun daya naushi dutsen sai yaga ko ɗan yatsan sa bai karye ba ballantana hannun yayi ciwo, Sai ya cika da matukar mamaki, kawai ya kama gefen ramin da ya faɗa ya fito waje, Yana fitowa sai ya zare wata takobin daban a jikin sa ya falfala da azababban gudu zuwa kan halittar ya daka tsalle sama ya soka masa takobin a ƙahon zuciyar sa, Nan take mutumin ya kurma wawan ihu sannan ya fadi kasa,yana shure-shuren mutuwa jini ya dunga kwarara da tsartuwa daga kirjin sa. Kafin wani lokaci komai na jikin sa ya daina motsi alamar rai yayi halin sa, Take wannan wuta dake ci a cikin wannan akwatu na mutu murus kuma jelar halittar dake daure da su lasmirat ta sake su, Sakamakon jinin dake zuba daga jikin halittar shi ne yayi sanadiyar farfaɗowar su boka Dayyubul-Barmas, Sunaila ce ta fara farfaɗowa koda ta buɗe idanuwan ta dake rufe cikin baƙin yanki koda tayi arba da yaslir a tsaye rike da takobi tsirara jikin sa duk ta ɓaci da jinin mutumin mai siffa biyu daya hallaka, sai ta cika da matukar mamaki, Sannan baka Dayyubul-Barmas, lasmirat suka cika da Mamaki bisa ganin bajintar yaslir. Bayan kowa ya samu nutsuwa kuma ya sanya wa kansa magani a raunin dake jikin sa, Sai aka sake ɗungumawa aka fice daga cikin kogon dutsen Lokacin da Sunaila wacce Ita ce a ƙarshe ta fita sai ƙofar kogon ta mayar da kanta ta rufe tamkar bata taɓa budewa ba, Haka dai su boka Dayyubul-Barmas suka dunga shiga kogunan dutsen yazamana cewa sun sha ɓakar wahala wajen yaƙar halittun dake ciki Sai a kogo na biyar ne bayan sun samu nasarar fafata yaƙi da wata SIHIRTACCIYAR mucijiya suka samu nasarar ɗauko zobunan sihiri, Amma kowannen su ya samu raunuka a jikin sa masu yawan gaske, Domin sai da su kayi kwana shida suna jinyar jikin su sannan suka fice daga dajin da fitar su suka tarar da aljani Huzmal ya bararraje yana ta sharar barci, Tabbas Bambancin aljani da bil'adama a bayyane yake yanzu duk tsawon kwanakin da muka shafe a cikin wannan daji Huzmal barci yake yi bai farka ba, Jaruma Sunaila da yaslir ne sukayi wannan furuci a zukatan su batare da sun bayyana kowa ya ji ba. Boka Dayyubul-Barmas ya katse shirun daya wanzu ta hanyar zungurar aljani Huzmal da kwagirin tsafin sa dake rike a hannun sa, Firgit! Huzmal ya ɗago kansa yana mutsittsike idanu cikin magagin barci, yace" Kai wane ne ya katse mini wannan daddaɗan barci da nake yi wanda ban fi daƙiƙa goma da farawa ba, Koda jin wannan batu sai boka Dayyubul-Barmas ya dakamasa tsawa yace" kai bana son maganar banza yi maza ka ɗauke mu izuwa tsaunin SHAFRAS domin ɗauko kubar miftahul-daryal Ka sani cewa daga nan izuwa tsaunin SHAFRAS tafiya ce ta tsawon kawanki arba'in bisa ingarmar doki, Ina so ka kai mu a cikin abinda bai gaza kwanaki uku kacal ba, Sa'adda Huzmal yaji wannan batu daga bakin mai gidansa boka Dayyubul-Barmas sai ya wartsake ya dawo cikin hayyacin sa ya dubi Dayyubul-Barmas cikin ladabi ya ce" Ka gafarceni ya shugabana naji dukkan bayanin ka amma ina so nayi maka wata tambaya wai shin kwanaki nawa kuka shafe a cikin wannan daji? Koda wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas yace " Kwanaki arba'in muka shafe Huzmal yace "Taɓ ɗi jan amma kuwa in dai haka ne ku bil'adama kuna hakuri da kuƙe yin barci sau ɗaya a rana, Amma ni gashi na shafe tsawon kwanaki arba'in i na barci amma ji nayi tamkar barcin daƙiƙa goma na yi, Ya shugabana na rantse da girman halarar tsafin ka inda za,a bani gaba ɗaya kwanakin rayuwar da kowannen ku zai yi a duniya a ace nayi barci iya adadin kwanakin a waje na bai huce kaso ɗaya bisa uku na barcin da na keyi a rana ɗaya ba, Sa'adda aljani Huzmal yazo nan azancen sa sai mamaki ya turnuƙe yaslir,Sunaila da sarauniya lasmirat har dariya ta kuɓucewa musu, Huzmal na kammala wannan furuci sai ya shimfiɗe gadon bayan sa kowa ya hau ya zauna Sannan ya bude manyan fuka fukan sa ya luluƙa izuwa sararin samaniya, cikin matsanancin gudu babu sassauci, ******. *****. ****** A,amarin su tawagar sarki Hamras kuwa, waɗanda ya tura domin su yanko masa gashin kan boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat domin ya samu nasarar mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA kuwa bisa jagorancin aljani Huruful-labarus kuwa Sun wanzu suna gudu a bisa sararin samaniya domin zartar da umarnin shugaban su, Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai tsulum suka ga wani ɗan wadan aljani ya bayyana tsulum a gaban su tamkar an jefoshi daga sama, Aljanin ya na ɗauke da ranƙwalelen kai mai ɗauke da manyan idanu ja jajur.wuyan sa ɗan siririn ne tamkar na barewa, kai bazaka taɓa cewa wuyan nasa zai iya ɗaukar nauyin rafkeken kan nasa ba, yana ɗauke da tafkeken kirji mai ɗauke da curi curin tsoka, Cikin sa rubdumeme ne tamkar an kifa kwarya, ƙafafuwan sa yan sirara ne tamkar sillan kara, yana ɗauke da wata murtukekiyar jela, Du dudu tsawon sa bai huce kamu ɗaya ba, Tabbas duk inda muni yake wannan aljani ya cika mummuna, idan kuwa za,a yi gasar muni ta duniya zai iya zama na ɗaya, Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su aljani Huruful-labarus da aljanin, Daga can sai Huruful-labarus ya dubi aljanin ya dakamasa tsawa ya dube sa a wulakance yace" yakai wannan ɗan ƙaramin kwaro a cikin aljanun duniya, shin wane ne kai, kuma wane irin rashin sani ne ya kawo ka nan wanen, Yi maza ka amsa mini waɗannan tambayoyi kafin naga irin hukuncin daya dace dakai, Koda jin wannan batu daga bakin aljani Huruful-labarus sai aljanin ya kyalkyale da dariya har da kwalla, Al'amrin da yayi matukar bawa Huruful-labarus da tawagar sa mamaki kenan kuma ya basu mamaki, Abin da ya basu mamaki shi ne taya ya wannan aljani da bai huce ɗaya daga cikin su ya maƙure shi ba zai dunga ɓabbaka musu dariya A lokaci guda ɗan wadan aljanin ya tsuke bakin sa kuma ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA cikin kakkausar murya yace" yaku waɗannan kananan jarumai kuyi sani cewa suna na Sahibul-Muluk, Kuma Ni ne shugaban yan fashin aljanun wannan nahiya baki ɗaya, Hakika kunyi babban kuskure da har kuka tsaya a gaba na kuke faɗa mini magana amma yanzu zan ganar daku kuren ku, Koda jin wannan batu sai aljani Huruful-labarus ya fusata ainun ya dakawa yaran sa tsawa su kayi ɗauki kan Aljani Sahibul-Muluk suka ihu da kururuwa mai firgitar wa, Nan take aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro daban al'ajabi, Sa'adda da aka yamutse da azababban artabu tsakanin shugaban Yan fashin wadannin aljanun duniya, Wato aljani Sahibul-Muluk, da tawagar aljani Huruful-labarus, Sai yaƙin yazamo abin tsoro gami da ban mamak, Domin kuwa duk irin girma da kwarjinin Huruful-labarus da yaransa sai ya zamo abanza, Domin kuwa Sahibul-Muluk yazame musu alƙaƙai sun rasa yadda zasu yi dashi, A inda zaka ga ya taƙarƙare ya ƙirɓawa ɗaya daga cikin su naushi yayi katantanwa sau uku ya faɗo ƙasa tim! A wasu lokutan idan hannun sa ya naushe su sai dai kaji kashi yayi ƙara ruƙus, Nan fa ihu da hargowar aljanun ta ci ka dajin baki ɗaya, Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje sai yayi tsammanin cewa YAKIN DUNIYA ya taso, Sa'adda da aljani Huruful-labarus dake tsaye a gefe guda ya na kallon artabun da akeyi yaga yadda aljani Sahibul-Muluk yazame wa yaran sa ANNOBA ƊARI, sai ya cika da matukar mamaki kuma ya fusata ainun, Abin da ya basa mamakin shine yadda Sahibul-Muluk ke ragargazar dakarun tamkar na'ura ce ke sarrafa shi, Tabbas wannan shine fa abin da masu iya magana ke cewa" GABA DA GABANTA Aljani ya taka wuta" Koda Huruful-labarus ya lura cewa idan har aka cigaba da wannan yaƙi a haka dakarun nasa zasu iya karewa sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu ya zare wata sharbebiyar takobi a damtsen sa yayi ɗauki kan Aljani Sahibul-Muluk, Aka ruguntsume da sabon azababban yaƙi, Sahibul-Muluk ya tare sa ya wanzu yana kare hare haren tare da mayar da martani ta hanyar kai bugu da naushi, Ana cikin wannan yaƙi ne Huruful-labarus ya samu nasarar laftawa Sahibul-Muluk wani sara, jini yayi tsartuwa ya zuba a ƙasa, Sahibul-Muluk ya kwarara ihu sakamakon tsananin zafida zugin da yaji, cikin zafin nama ya mayar da martani ta hanyar kai wa Huruful-labarus naushi a fuska, Huruful-labarus ya zille tare da zamewa harin sannan ya sanya takobin sa a karo na biyu ya tsarge Sahibul-Muluk gida biyu, take gangar jikin ta fado ƙasa rikica jini ya kwarara tamakar an buɗe fanfo, Koda samun wannan nasara sai Huruful-labarus ya ɗaga kansa izuwa sama ai kuwa sai yayi arba da wata yar ƙaramar halitta, Bata ba ce face Aljani Huzmal ɗauke da su sarauniya lasmirat, Nan take Huruful-labarus ya busa musu wata irin gagarumar Iska daga bakin sa, Tsananin karfin iskar ya tashi hankalin duk wata halitta dake rayuwa a dajin, kuma ta sanya fuka-fukin aljani Huzmal na ɓangaren dama ya karye take suka rikito daga sararin samaniya, Sai suka faɗo a kan tafin hannun Huruful-labarus Huzmal yana mai tsandara ihu sakamakon tsananin raɗaɗin da yaji a fuka fukin sa daya karye, Sarauniya lasmirat,boka Dayyubul-Barmas, yaslir da Sunaila kuwa sun galabaita ainun domin koda wata gaɓa a jikin su basa iya motsawa, Cikin matukar farin ciki aljani Huruful-labarus yace" yaku abokan tafiya kuyi sani cewa wani abin farin ciki ya same mu ku sani cewa waɗannan bil'adama da kuka gani akan tafin hannu na sune abinda muka fito nema wato sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas, Koda gama faɗin hakan sai ya nuna su sarauniya lasmirat da ɗan yatsan sa na hagu take wata igiyar tsafi ta bayyana a ɗaɗɗaure su tamau! Kawai sai ya jefasu a cikin aljihun rigar sa tamkar ya jefa kwallon goriba, Kawai sai ya yunƙura ya tashi zuwa sararin samaniya yana tsala gudu yaran sa na biye da shi. Huruful-labarus da tawagar su ka cigaba da tsala gudu a sararin samaniya ɗauke da su sarauniya lasmirat a cikin aljihun sa, Sai da suka shafe tsawon dakika ɗari huɗu sannan aljani Huruful-labarus yayi umarni a yada zango Inda aka yada zangon yakasance daji mai matukar kwarjini daban tsoro, Yana ɗauke da waɗansu dogayen bishiyu masu siffofin ban tsoro, Ko iya shirun da wanzu a dajin ya isa ya jefa tsoro a zukatan JARUMAI, Yayin da aka sauka a cikin dajin sai a kayi turus! Bakomai akaga ni face wani kyakkyawan saurayi sanye da fararen tufafi zaune bisa wani buzu na fatar damisa ya fuskanci alkibila yana gabatar da wata irin ibada mai ban mamaki, Nan fa aljani Huruful-labarus da yaran sa suka ƙurawa saurayin idanu cikin tsananin Mamaki, Abu na farko da ya basu mamaki shi ne taya ya bil'adama guda ɗaya ya shigo wannan daji mai matukar haɗari, alhalin shi bai kasance wani mashahurin matsafi ba, Wani abu da yafi ɗaure musu kai shi ne menene yasanya da saurayin yayi arba dasu bai firgita ba, Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan, Kawai sai suka zuba idanu suna kallon yadda saurayin yake gudanar da ibadar, Bisa mamaki sai suka ga ashe har ya kammala ibadar tasa ya ɗauki wata jakar fata ya rataya a kafaɗar da ya kunna kai izuwa wani bangare a dajin, Al'amarin da ya fusata Huruful-labarus kenan yasha gaban saurayin yana mai dakama sa tsawa ya dube sa cikin matukar fushi yace "Yakai wannan saurayi ma,abocin GAJERAN KWANA, shin wane ne kai a cikin bokayen duniya da har zaka nuna rashin ladabi a gareni? Koda jin waɗannan tambayoyi sai saurayin yayi murmushi da ya ƙarawa fuskar sa kwarjini da haiba kawai ya sake kunna kai izuwa dajin batare da ya bawa Huruful-labarus amsar tambayar sa ba Cikin fushi Huruful-labarus ya kai masa duka da fuka-fukin sa Kafin dukan yakai saurayin ya ɗaga hannayen sa sama ya karanta waɗansu addu,o,i na musamman ya shafa a fuskar sa, Kawai sai aka ga wata irin murtukekiyar igiya ta ta ɗaɗɗaure aljani Huruful-labarus da yaransa kuma igiyar tsafin da ta ɗaure su sarauniya lasmirat ta bace ɓat, suka faɗo daga cikin aljihun rigar aljani Huruful-labarus, Har a wannan lokaci a matukar Galabaice suke boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat kaɗai basu ji jiki sosai ba, Yayin da saurayin yayi arba da su lasmirat sai ya cika da matukar mamaki. Lasmirat ta miƙe tsaye da 'ƙyar boka Dayyubul-Barmas yayi koyi da ita, yaslir d Sunaila da aljani Huzmal na zaune dirshen a ƙasa cikin halin galabaita. Sa,adda lasmirat ta haɗa idanu da saurayin sai taji wani abu ya ɗarsu a zuciyar ta wanda ta kasa Bamban ce ko mene ne a iya tsawon rayuwar ta bata taɓa ganin namiji mai kyawun saurayin ba, Kallo ne ya wakana a tsakanin su na ɗan wani lokaci lasmirat nayi masa kallo mai ɗauke da alamar tambaya, Daga can sai lasmirat ta buɗi baki cikin wata irin tattausar murya mai rikita duk wani ɗa namiji cikin annurin fuska ta ce "Yakai wannan saurayia ma'abocin kwarjini da haiba shin wane ne kai? Kuma ya akayi ka samu nasarar ceto rayuwar mu a hannun waɗannan aljanu? Koda jin waɗannan tambayoyi sai saurayin ya zurfafa izuwa kogin tunani da ga bisani ya dubi lasmirat da fararen idanun sa masu haske tamkar madara cikin zazzakar murya yace "Yake wannan sarauniya ma'abociyar kyawu game da tambayar ki ta farko Suna na shamsuddin ibn Abbas na baro birnin mu ne domin ɗaukaka kalmar Ubangiji. Na samu nasara akan waɗannan aljanu ne ta hanyar neman taimakon Ubangiji na , Cikin matukar mamaki lasmirat ta sake budar baki a karo na biyu tace" shi wane ne wannan Ubangijin naka?. Shamsuddin yayi murmushi yace" Ubangijina shi ne wanda ya halicci duniya da abinda ke cikin ta babu abin da ya gagare sa komai yana iko a kansa, shine mai ciyar da tsuntsayen dake cikin duhuwar daji dama kifaye da ke karkashin Teku, Tsananin duhun dare ko na Teku baya ɓuya gare sa. Jarumi shamsuddin ya cigaba da jawabin sa bisa tambayar da sarauniya lasmirat ta yi masa, A inda ya cigaba da cewa Ubangiji shi ne ya wanzu tun babu babu ita kanta, Bashi da farko ba shi da ƙarshe, Sa'adda sarauniya lasmirat taji wannan jawabi sai nan take mamaki ya kamu ita da abokan tafiyar ta, Shiru ne ya wanzu a tsakanin su na ɗan wani lokaci daga bisani lasmirat ta matsa daf da inda shamsuddin yake ta yadda suna iya jin numfashin juna ta dube sa tace"yakai shamsuddin ina so ka ɗan bani lokaci zan yi shawara da abokan tafiyata, Da jin wannan batu sai shamsuddin ya gyaɗa kai Lasmirat ta matsa kusa da abokan tafiyar ta ta dube su tace" Yaku abokan tafiya ta shin me kuke gani game da wannan baƙon jarumi shamsuddin Ni ina ganin idan muka haɗa tafiyar dashi zai bamu wata gudun mowa ta musamman, domin ku duba fa kuga yadda Ubangijin sa ya bore masa sarrafa aljanu Koda jin wannan batu daga bakin sarauniya lasmirat sai boka Dayyubul-Barmas ya dube ta cikin kakkausar murya fuskar sa a murtke tamkar an aiko masa da WASIKAR MUTUWA, Yace"ya shugabata kiyi sani cewa ni ashawara ta bazamu haɗa tafiyar mu da wannan baƙon jarumi ba domin idan baki manta ba acan baya lokacin da kika ziyar ce nagaya miki cewa saurayin da zaki aura har ki samu Haihuwa shine namijin da yafi Kowa talauci a duniya, kuma shine zai hanamu cika burin mu na mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA, Shin yanzu bakya tsammanin cewa wannan baƙon jarumi shi ne saurayin da zai hana cika muradin mu, Tabbas jikina ya bani cewa babu wani alkairi a tare da wannan jarumi. Lokacin da sarauniya lasmirat ta ji wannan batu daga bakin Boka Dayyubul-Barmas sai hankalin ta ya ɗugunzuma ainun ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mai zurfafa cikin kogin tunani, Abu na farko da ya faɗo mata arai shin yanzu idan wannan baƙon jarumi shi ne wanda yafi kowa talauci a duniya shin taya ya zata iya cire soyayyar da ta kama zuciyar ta a Lokaci guda, To wai shin ma boka Dayyubul-Barmas da yake wannan magana yana da tabbacin cewa Wannan baƙon jarumi shine saurayin da zai hana su cimma muradun su na samun TAKOBIN ƊAUKAKA, Domin haka ai bashi da hujjar dazai zargi baƙon jarumin, haka dai lasmirat ta cigaba da wannan tunani ta saƙa wancan ta kunce wancan, Daga bisani ne dai sai ta dubi boka Dayyubul-Barmas tace" yakai Dayyubul-Barmas kayi sani cewa babu wata hujja da zata sanya mu janye tafiyar mu da wannan baƙon jarumi ba, Abu ɗaya ne kawai zai kawo mu janye kuɗirin na mu shine ka gudanar da bincike bisa halarar tsafin ka ka tabbatar mana da zargin da kake yi, Sa,adda boka Dayyubul-Barmas ya ji wannan batu daga bakin lasmirat sai ya dubeta yace "ya shugabata kiyi sani cewa da ace wani zai iya taimaka mana da bamu samu nasarar ɗauko zobunan sihiri ba, Amma masu iya magana na cewa"Ba,a kwacewa yaro garma" Zanyi duk abinda kika faɗa sai dai duk abin da ya biyo baya kada ki zargi ko a sai kanki, Koda jin wannan batu sai Hankalin sarauniya lasmirat ya ɗugunzuma ainun hantar cikin ta takaɗa amma sai kawai ta basar ta nufi inda shamsuddin yake tana mai sakar masa tattausar murmushi tace"yakai wannan jarumi ma,abocin kyawu da kwarjini kayi sani cewa na tattauna da abokan tafiya ta kuma dukkan mu mun roki alfarma a wajen ka da kayi mana rakiya izuwa mallako waɗansu abubuwa, Shamsuddin yayi murmushi yace" Nasan dukkan abinda kuka fito nema wato kubar miftahul-daryal da TAKOBIN ƊAUKAKA tunda kun samu nasarar ɗauko zobunan sihiri a cikin kogon fatalwa, Dajin wannan batu mamaki ya turnuƙe lasmirat ta dube sa cikin mamaki"ya akayi kasan abubuwan da muka fito nema ya jarumin jarumai Shamsuddin yayi murmushi yace"ya shugabata idan bazaki manta ba ko a baya na gaya miki cewa ikon Ubangiji na ya huce haka Hakika Ubangiji na ya bayyana mini dukkan Abin da ya gudana daku a cikin mafarki na. Sai dai kafin na amince da buƙatar ku tilas ne ku amince da sharudda na guda biyu Na farko shine duk sa,adda wani abu ya taso na neman taimako sakamakon wata musiba zan zuba muku idanu sai kunyi dukkan abinda zaku yi kun gaza sannan na gwada tawa dubarar, Sannan idan Ubangiji na ya bani ikon mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA kuyi mini alkawarin cewa za ku ƙarni addinina na Musulunci Sa,adda sarauniya lasmirat ta ji waɗannan sharuɗɗa daga bakin shamsuddin sai tace"Duka mun amince da wannan sharuɗɗa naka ai biyan buƙata yafi dogon buri, Koda gama faɗin hakan sai shamsuddin ya koma kan buzun sa ya cigaba da gudanar da ibadar sa, lasmirat ta koma wajen abokan tafiyar ta, Sai da aka kwana biyu a wannan waje aljani Huzmal yayi jinyar Fuka fukan sa su yaslir suka samu karfin jikin su sannan aka cigaba da tafiya A halin yanzu tafiya ta canza daga tawaga ɗaya zuwa biyu wato sarauniya lasmirat da su aljani Huruful-labarus da jarumi shamsuddin Maimakon a wannan karon a hau bisa aljani Huzmal sai shamsuddin ya ce kowa ya hau ɗaya daga yaran aljani Huruful-labarus bisa izinin Ubangiji ɗayan su bazai saɓa daga Umarnin da aka yi masa ba, Da yake a wannan lokaci da aka fara tafiya da hasken rana ne, Lokacin da duhun dare yafara kawo kai sai shamsuddin yayi umarni aka yada zango Take aljanu shida dake ɗauke da, yaslir,Sunaila, Dayyubul-Barmas, lasmirat da shamsuddin suka saki manyan fuka fukan su suka sauka a turba, Ana sauka aka kafa tantuna bayan an kafa ne sarauniya lasmirat ta shiga tanti ɗaya tare da sunaila, Boka Dayyubul-Barmas da yaslir, shamsuddin sai ya shiga nasa shi kaɗai Aljani Huzmal yana tsaye bisa bakin kofar tantin su boka Dayyubul-Barmas, su aljani Huruful-labarus kuwa suka karkasu izuwa kowace kusurwa a dajin domin tabbatar da cikekken tsaro, A cikin tantin sarauniya lasmirat kuwa bayan sun kammala kalaci ita da sunaila, Sai lasmirat ta kwanta Bisa kan gadon ta domin ta samu rintsawa amma duk sa,adda ta rufe idanun ta sai taga babu abinda take gani face fuskar jarumi shamsuddin yana yi mata murmushi, A wannan lokaci tuni Sunaila ta fara sharar barci har da minshari, Haka dai lasmirat takasance a cikin wannan hali har barci yayi awon gaba da ita, Tabbas lasmirat ta kamu da matsananciyar soyayyar wacce bata taɓa tsammanin zata shiga ba, Tabbas da ace jarumi shamsuddin zai zaɓeni a matsayin a matsayin abokiyar rayuwar sa Tabbas zan iya hakura da mulkina dukiya dama komai da mallaka domin na samu soyayyar sa , Kamar yadda ya wakana a masauki su lasmirat haka al'amarin yakasance a masaukin su yaslir Ina da bayan sun kammala kalaci sai boka Dayyubul-Barmas ya zira hannun sa a aljihun rigar sa ya ɗauko madubin tsafin sa ya shiga gudanar da bincike bisa halarar tsafin sa. Shi kuwa shamsuddin tun Kafin ya shiga tantin ya ɗaura alwala yana shiga ya dauko dabino da ruwan sa a cikin salka ya ɗan kimtsa cikin sa, Sannan ya shimfida buzun sa ya shiga gudanar da Sallah, batare da kalli abincin da su lasmirat suka kawo masa ba, Amma a ɓangaren su aljani Huruful-labarus kuwa suna cikin yin rangadi a tsakanin tantunan ne sai wani ɗaya daga cikin yaransa .mai suna Barbusa ya dubi abokin sa yace "yakai saltir wai yanzu haka zamu zauna muna ji muna gani wannan yaro shamsuddin yana juya mu tamkar yana sarrafa waina (masa) a cikin yanda Me zai hana bazamu shammace su ba mu hallaka su mu kama gaban mu, Baka tsoron mai girma Hamras zai aiko da wata musiba ta hallaka mu, Koda jin wannan batu sai idanuwan saltir suka zazzaro ya dubi saltir cikin alamun tsananin tsoro yace" A kul ɗin ka yakai aboki na kayi sani cewa tun ina yaro karami mahaifina ya gargaɗeni akan irin waɗannan mutane ma'abota addinin musulunci yace a halin yanzu a duniya babu hatsabibai kamar su Kafin saltir ya gama rufe bakin sa sai kawai su kaji wani sanyi gami daddaɗar iska ta mamaye wajen kafin kace me Gaba ɗayan su sun bungire kasa sun fara sharar barci har da minshari, Sarauniya lasmirat, Sunaila da yaslir suma nauyin barcin su ya karu ainun, Kuma wani irin gurnani mai ban tsoro ya mamaye wajen baki ɗaya. Sa'adda wannan iska mai ɗan karan daɗi ta bugar dasu aljani Huruful-labarus, tare dasu sarauniya lasmirat suka kama barci mai nauyin gaske kuma wani gurnani na mamaye wajen sai, Kwatsam bazato babu tsammani sai aljani Hafsul-Habarus ya bayyana a wajen, Yayin da yayi arba dasu Huruful-labarus sai ya cika da matukar farin ciki kawai sai ya taƙarƙare ya bushe da dariyar mugunta, Sai da yayi dariyar ta ishe sa sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa, Kawai sai ya miƙa gabza gabzan hannayen sa domin ya ɗauko su aljani Huruful-labarus, Yayin da rage saura kamu goma hannayen sa su isa sai wani mutum ya bayyana gaban sa tsulum, Ba wani bane face jarumi shamsuddin, Hafsul-Habarus ya ja hannayen sa baya ya dubi shamsuddin cikin tsananin fushi yana mai daka masa tsawa mai kama da saukar aradu Nan take bishiyoyin dake dajin suka dunga karairayewa suna zube ƙasa, duwatsu suka dunga bindiga suna farfashewa, kuma su lasmirat suka farfaɗo daga dogon barcin da suke yi suka fito daga cikin tantunan su a firgice suna masu zare makaman su, Sa'adda sarauniya lasmirat, Dayyubul-Barmas, yaslir, Sunaila, Huzmal, aljani Huruful-labarus da yaran sa sukayi arba da aljani Hafsul-Habarus sai suka firgice suka zube kasa, Sunaila, yaslir,da Huzmal suna masu sakin fitsari a wando saboda tsananin firgici, Shi kansa boka Dayyubul-Barmas a matukar firgice yake, Nan take a lokaci guda aljani Huruful-labarus ya tsuke bakin sa ya murtuke fuska, Take komai na dajin ya samu dai dai tuwa Cikin Wata irin kakkausar murya mai kama da kwaran kwatsa Yace"yakai wannan bil'adama ma'abocin tsaurin idanu shin wane ne kai dazaka hanani zartar da umarnin shugaba mai duniya sarki Hamras, Yi maza ka amsa mini waɗannan tambayoyi kafin na ganar dakai kuskuren ka, Sa'adda shamsuddin yaji wannan batu daga bakin aljani Hafsul-Habarus sai ya yi gyaran murya yace" yakai wannan mushriki makiyin Allah kayi sani cewa babu wani mai daraja face yakasance bawan Ubangijin musulunci mahalicci Abin da nake so dakai shi ne ka kadaina bautawa wanin Allah ka dawo izuwa TAFARKIN TSIRA, Wato addanin Musulunci,idan kuwa kaƙi yanzun nan zan roƙi Ubangiji na ya bani nasara na hallaka ka, Koda jin wannan batu daga bakin shamsuddin sai Hafsul-Habarus ya fusata ainun, idanuwan sa suka kaɗa sukayi jajur! Saboda fushi har wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita daga kofofin hancinsa, Kawai sai Hafsul-Habarus ya zare wani makami a jikin sa, Shi dai makamin yakasance dogo tamkar mashi, daga saman sa kawunan takobi ne guda biyu ɗaya na zarto mai cako-cako ƙasan kuma ya na da siffa irin ta lauje wanda ido bai taɓa gani ba, Tabbas wannan makami abin tsoro ga dukkan wanda yayi arba da shi, Sannan ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa kan shamsuddin, Koda ganin hakan sai shamsuddin ya dunkule hannayen sa ya ruga kan Hafsul-Habarus aka tari juna aka kacame da azababban yaƙi mai matukar tayar da hankali da ban tsoro, Wohoho Hakika gaskiyar masu iya magana da suka ce, Ranar bikin gwanaye sai wane da wane ne ke fitowa a taka rawa, Kuma idan ana babbakar Giwa ba,a jin ƙaurin bera Tabbas fadan da yafi karfin ka sai ka zamo da kallo, Hakan ne yafaru da su sarauniya lasmirat, Ba shiri su lasmirat suka rike tsaye suka runtuma da gudu izuwa cikin dajin , suka laɓe a bayan waɗansu bishiyoyi suka hangen artabun da akeyi tsakanin shamsuddin da Aljani Hafsul-Habarus, Nan take su jarumi shamsuddin suka tashi hankalin duk wata halitta dake dajin ya kama girgiza kasa ta dunga tsagewa tana zaftarewa bishiyoyi na faɗa wa cikin ta, duwatsu suka dinga murginawa kan juna suna karo. Wani abin mamaki da yafaru shine, duk yawan hare haren da Hafsul-Habarus ke kaiwa shamsuddin yana samun nasarar zillewa koda sau ɗaya makami bai taɓa jikin sa ba, Idan kuwa shamsuddin ya naushi wata gaɓa a jikin Hafsul-Habarus sai aji ya kwalla kara,. Bakomai ne yasanya hakan ba sai domin duk sa'adda shamsuddin ya naushe san sai yaji wajen tamakar an ƙonashi da ruwan zafi yana yi masa raɗaɗi da zugin tsiya, Al'amarinn da yayi matukar bashi mamaki kenan bisa ganin yadda yakasa samun nasara akan shamsuddin, Shin wannan wane irin jarumi ne da za,ace na kasa samun nasara akansa alhali koda makami bai riƙe ba , amsar tambayar da Hafsul-Habarus ya kasa bawa kansa kenan, Kawai ya sake zage damtse yana cigaba da kai Hafsul-Habarus miyagun hare haren babu ƙaƙƙautawa, Daga can nesa su sarauniya lasmirat na hangen artabun da ake yi tsakanin ZARATAN MAYAKAN biyu, Sa,adda sukaga yadda Hafsul-Habarus ke yakasa samun nasara akan shamsuddin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi kuma suka tabbatar da cewa shamsuddin ya cika jarumin kawarai mai karfin Allah na isa. Nan take sarauniya lasmirat taji soyayyar jarumi shamsuddin takara shiga zuciyar ta, Ita kanta Sunaila sai taji a cikin ranta cewa i na ma dai ace masoyin ta yana da jarumataka irin ta shamsuddin Abin da su duka biyun basu sani ba shine tsananin taimakon Ubangiji ne, Ke ɗawainiya dashi bayin kansa bane, Sai da shamsuddin da Hafsul-Habarus suka shafe Tsawon sa,a ɗaya da daƙika ɗari biyar suna ɗauki ba daɗi batare Hafsul-Habarus ya samu nasarar lakutar jikin shamsuddin ba, Nan fa Hafsul-Habarus ya sake fusata ainun ya haɗa da kai bugu da naushi hannu da kafa Sa,adda shamsuddin ya fahimci cewa wankin hula zai kaishi dare sai ya cigaba da riƙon Allah a zuciyar sa yana mai cewa, Ya Ubangiji ka taimaki bawan ka mai rauni akan mushirikin bawan ka. Don matsayin annabin ka, Ai kuwa yana kammala hakan sai shamsuddin ya taƙarƙare ya ƙirɓawa Hafsul-Habarus naushi a ciki, Saboda karfin naushin sai da cikin Hafsul-Habarus ya yi ƙara fam fam! Tamkar an daki Tanki, Ya faɗin ƙasa yana murginawa gami da turmutsutsu Cikin sa yana murɗawa, Kafin yayi wani yunkurin jarumi shamsuddin ya sake ƙirɓa masa wani wawan naushin a cikin sa, take. Cikin nasa yayi bindiga ya fashe tamkar an buga katuwar ganga, kayan cikin sa suka fito waje jini ya dunga tsartuwa yana feshi yana malala a ƙasa tamkar an balle ƙorama, Sa,adda su sarauniya lasmirat suka ga irin nasarar da shamsuddin ya samu sai suka fito daga inda suke laɓe suna masu yi masa jinjina suna cewa G ausheka GOGA SHA YAƘI, SADAUKIN SADAUKAI Ciwon idanun kananun kwari JARMAI SHA YAƘI uban maza DODON MAZAJE Amma boka Dayyubul-Barmas sai ya murtuke fuska tamkar an aiko masa Da sakon mutuwa, Kafin su kai inda yake gangar jikin sa ta zagwanye ta narke ruwan ya tsotse a cikin ƙasa, Suna karasowa sai shamsuddin ya dubesu yace fuskar sa cike da annuri yace " Yakamata kowannen ku yaje ya kwanta a samu ishashshan barcin saboda tafiyar dake gaban su, Koda gama faɗin hakan sai shamsuddin ya juya ya shiga izuwa tantin sa, Take kowa ya shiga nasa tantin a ka cigaba da barci, Acan birnin misra kuwa tun daga ranar da sarauniya lasmirat ta tafi izuwa ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA domin ta samu damar ɗebo ruwan ma'ul-diya'u, Waziri ukashat ya cigaba da tafiyar da sha,anain mulki bisa tsari da adalci, Wata rana waziri ukashat na zaune a fada, Wata kyakkyawar budurwa na zaune a gefen sa na dama cikin ado na keta raini ba wata ba ce face gimbiya Hulaifat yar waziri ukashat, A gefe guda kuma fadawa ne a zazzzaune bisa shimfiɗu na alfarma fadar ta cika maƙil ana tafiyar da sha,anin mulki, Kwatsam bazato babu tsammani sai kawai akaga wani waje ya zabtare a fadar ya rufta izuwa kasa Kwatsam sai ga wani narkekeken dodo ya fito, Shi dai wannan dodo yakasance jibgegen basamude ,fuskar sa mummuna ce babu kyan gani Hannayen sa tafka tafka ne tamkar bishiyar kuka,tafukan kuwa su na da faɗi tamakar faranti, ƙafafuwan sa manya ne tamkar da dutse aka yi su, kirjin sa ya kumburo ya tara kwanji, kofofin hancinsa manya ne idanuwan sa jajawur tamkar garwashi girman kowanne daga cikin su yakai girman lemon zaƙi, Tabbas wannan dodo ya cika abin tsoro domin babu wani jarumi da zai yi arba dashi face ya firgice Nan fa yazamana cewa fadar ta kaure da guje-guje gami da ifice-ificen jama'a Cikin matukar tashin hankali waziri ukashat ya miƙe tsaye zumbur daga kan karagar sa ta mulki yana mai zare zare takobin sa take fadawa da sauran dakarun dake fadar suka yi koyi dashi Aka fara kallon kallo tsakanin su da dodon, *****. *****. **** Kashe gari tunda duku dukun safiya bayan su sarauniya lasmirat sun yi kalaci an kammala shiri tsaf! Sai kawai kowa ya bisa kan ɗaya daga cikin yaran aljani Huruful-labarus aka cigaba da tafiya domin isa izuwa tsaunin SHAFRAS, Tafiya kwanaki talatin kaɗai akayi aka iso tsaunin DARUL-SHAFRAS a iya tsawon wannan tafiya babu abin da ke sanya wa atsayar da tafiya face idan jarumi shamsuddin zai gudanar da ibadar sa, Inda aka tsaya ɗin yakasance daji ne ma,abocin kwarjini daban tsoro, Tsakanin su sarauniya lasmirat da inda tsaunin DARUL-SHAFRAS yake ake tazara mai yawa don haka sai suka cika da tsananin mamaki bisa Ganin yadda tsaunin yakasance Tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance mai matukar tsawo inda ace mutum zai kalle sa daga nesa sai yaga cewa har ya shige cikin gajimare, Babu wani ɗan itaciya da yayi tsiro a wajen face waɗansu irin duwatsu masu ɗauke da siffofin bil,adama da dodanni masu ban tsoro Sai da aka shafe tsawon lokaci a cikin wannan hali sai daga bisani boka Dayyubul-Barmas yayi umarni aka tashi aka nufi tsaunin gadan gadan Nan fa jarumi shamsuddin ya dunga kallon abubuwan kudirar Ubangiji na halittun sa da tajallin sa iri daban daban, Yayin da aka sauka a tsaunin sai kowa yasha jinin jikinsa kuma hankalin sa ya ɗugunzuma ainun, Bakomai ne yasanya su hakan sai bisa ganin yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance Daga sama tsaunin yakasance mai ɗauke da manyan gine gine da aka yi su da zallar duwatsun wuta kirar mutanen farko mai ɗauke da manyan ɗakuna tamkar akwai wata halitta da ta taɓa rayuwa a wajen Babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafar sa face akwai ƙasusuwan bil,adama ko wasu sassa na jikin sa yana duk ta lulluɓe su,alamun dake nuna cewa wata halitta ta daɗe bata ziyarci wajen ba, A wasu lokutan sai kaga mutum an rataye da igiya har ya zagwanye yazamana kwarangwal, Babu abin da zai firgita Mutum shine yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance shiru tsit tamkar babu wata halitta a cikin sa domin koda yan kananan tsuntsaye babu, Nan fa hankalin kowa ya ɗugunzuma ainun, amma bisa mamaki sai kaga shamsuddin bai razana ba Nan fa su duka raya a ransu cewa shin menene yasanya shamsuddin bai razana da ganin kwarjini tsaunin ba, Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan Boka Dayyubul-Barmas ne ya katse shirun da ya wanzu budar baki sannan yayi ajiyar zuciya ya kawo gwaron numfashi yace "Yaku abokanan tafiyata kuyi sani cewa mun iso tsaunin DARUL-SHAFRAS inda zamu ɗauki ruwan ma'ul Daryalu, Sai dai kafin hakan ina san na samar daku waɗansu dokoki Da farko dole ne kowannen ku ya kiyaye amfani da dukkanin wani abu da danganci sihirin tsafi, Abu na biyu kuwa shine dole ne kada wani ya shiga wani waje face yasanar dani na basa umarni, Yana gama faɗin hakan sai ya juya ya dubi shamsuddin fuskar sa babu annuri tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce " yakai shamsuddin kada ka manta alkawarin dake tsakanin mu dakai na fito rayuwar mu a lokacin da wata musiba ta taso mana muka kasa tseratar da kan mu idan har ka gaza ceto rayuwar mu Tabbas zamu yanke tafiyar mu daki domin hakan ya tabbatar mana cewa Ubangijin ka ya gaza wajen taimakon ka, Koda jin wannan batu sai jarumi shamsuddin ya yi murmushi yace"Da yardar Annabi mai daraja Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Ubangiji na bazai bani kunya ba, Dajin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya zare wani makami a jikin sa ya kunna kai izuwa cikin wani falo, Sarauniya lasmirat, yaslir, Huzmal, Huruful-labarus da yaransa, da Sunaila tana mai gyara rawanin ta suka mara masa baya , jarumi shamsuddin a ƙarshe har yazamana sun basa tazara mai yawa, Da shigar su izuwa cikin falon sai suka tarar yakasance makeken mai tsawo da faɗi ba'a iya hango ƙarshen sa, sai suka ci-gaba da tafiya suna kallon abubuwan ban al'ajabi iri daban daban Yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wata ƙasaitacciyar fada, Fadar an ƙawata ta da mau,ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, Ko ina a fadar a tsaftace yake, tunda karagar mulki har na yan majalisa babu kowa akai Nan fa kowa ya cika da matukar mamaki bisa ganin ƙawatuwar fadar, Musamman sarauniya lasmirat da take ganin cewa idan aka kwatanta fadar ta da wannan fadar ta tan bakomai ba ce face kango, Koda koda a tarihi bata taɓa ganin fada mai ƙawatuwa da tsaruwa tamkar wannan fada ba, Babu abin da yafi bawa su boka Dayyubul-Barmas mamaki kamar yadda aka shirya kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe a bisa wani kayataccen teburin na azurfa, kamshin abincin ya mamaye fadar baki ɗaya, taimakar an haɗawa wani BASARAKE walima Nan fa aljani Huzmal da Huruful-labarus suka fara tanɗar baki,har su na dalalar da yawu daga bakin su basu sani ba saboda tsananin kwaɗayi, Kafin su farga ɗaya daga cikin yaran aljani Huruful-labarus mai suna Barbusa ya ya faki idanun su ya sunkuci wani katon faranti ɗaya mai ɗauke da wani farfesun naman tsuntsu yayi loma ɗaya dashi ya tanɗe bakin sa Tabbas rashin sani yafi dare duhu inda ace Barbusa yasan abinda zai faru da yayi hakuri da cin wannan naman tsuntsu ya cigaba da dalarar da yawun sa saboda kwaɗayin abincin, Domin haɗiye abincin nasa keda wuya sai kwatsam aka ga waɗansu jibga jibgan samudawan muridai suna ratsowa daga bangon fadar suna fito wa, hannayen su ɗauke da miyagun makamai, dangin gatari,al'amudi',majaujawa,takobi da mashi, A dadin su yakai dubu hamsin da ɗoraya, Gaba ɗaya gurnanin muridan ya cika fadar baki ɗaya, Muridan sun Kasan masu damatsa,suna rafka rafkan kawuna, suna da matukar kwarjini da muni,duk sa'adda dayan su ya ajiye lafceciyar ƙafar sa a fadar sai kaji ƙasa ta amsa saboda karfin takun, Haƙika waɗannan muridai sun kasance ababan tsoro domin duk da irin dakewar zuciya irin ta Boka Dayyubul-Barmas, lasmirat,Sunaila , yaslir sai suka ɗimauce, tamkar ace ƙyat suka zura da gudu,aljani Huruful-labarus,saltir da Barbusa har sakin gudawa sukayi a wando saboda da firgici, Shi kansa jarumi shamsuddin a matukar razane yake kawai saboda addu'ar da yake ne yasanya tsoro ya kau daga daga zuriyar sa , Nan fa nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su Dayyubul-Barmas da muridan lokacin da muridan suka kammala yi musu kawanya sai suka buɗe wata hanya a tsakiyar su ta yadda mutum goma zasu iya tsaya a jere Take wani gurnani ya dunga bayyana a hanyar gami da karfin takun sawaye, Sannu a hankali sautin yana ƙaruwa jim kaɗan sai ga wani narkekeken muridi ya bayyana, Shin dai muridin yafi sauran girma da kwarjini sannan ya na ɗauke da rigar sarauta a jikin sa alamun dake nuna cewa shine shugaban muridan, Shugaban muridan ya karewa su Boka Dayyubul-Barmas kallo, kawai sai ya bushe da dariyar mugunta mai kama da haniniyar doki, Sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAKON MUTUWA Sannan ya buɗe wawaken bakin sa daya fi kama da bakin rijiya saboda girman sa cikin kakkausar murya " Lalle marhaban da zuwa fadar uban muridai KIRMALU IBN SHAMSHAN, Yaku wadannan bil'adama kuyi sani cewa yau fiye da shekaru dubu shida babu wata halitta da ta taɓa zuwa tsauni na DARUL-SHAFRAS sai ayi Na tabbata cewa abinda ya kawo ku baya rasa nasaba da Ruwan ma'ul Hayat Ina so kuyi sani cewa kun kawo kanku gidan musiba da bala'o'i na rantse da gemun mai girma Baddadul-sihir ɗayan ku bazai sauka kasan wannan tsauni a raye ba, Domin hakan ya zamo darasi ga bil'adama masu taurin kanki da wauta irin yaƙi, Koda shugaban muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN yazo nan azancen sa Sai ya sake bushe da dariyar mugunta a karo na biyu Koda can sai ya murtuke fuska kawai sai ya dakawa yaransa tsawa dake nuna su afkawa su boka Dayyubul-Barmas Take yaran suka ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgitar wa Nan fa ana haduwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro gami da tashin hankali, Al'amarin sarki Hamras kuwa tun sa,adda da ya tura hadimin aljanin sa wato Huruful-labarus domin ya ɗauko masa gashin kan sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas sai ya shafe tsawon kwanaki ashirin batare da yaji ɗuriyar su ba Sai kawai ya nutsa bisa halarar tsafin sa domin yaga abinda ke wakana, Ai kuwa nan take ya ga dukkanin abinda ya faru tsakanin Huruful-labarus da jarumi shamsuddin, tun daga inda Huruful-labarus ya rusawa su sarauniya lasmirat wannan iska sihiri suka kamu da barci mai nauyin gaske, Har kawo inda shamsuddin ya samu galaba akan Huruful-labarus a lokacin da suka fafata artabun, Duk daga farko har karshe ya bayyana a cikin madubin tsafin sa, Sa,adda Sarki Hamras yaga wannan al'amari a cikin madubin tsafin sa sai ya cika da matukar bakin ciki maral musaltuwa, Kuma yasha alwashin cewa komai daren dadewa sai ya ɗauki fansa akan jarumi shamsuddin Kwanaki nabin kwanaki mako nabin mako sai gashi sarki Hamras ya shafe tsawon kwanaki arba'in cif yana da tafiya A ranar kwana na casa'in ne sarki Hamras yana tafiya a sararin samaniya cikin sauri yana mai keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya Yana cikin wannan hali ne yaji gajiya yafara kamashi Kawai sai ya yanke shawarar ya sauka ya huta idan yaso sai ya cigaba da tafiya, Koda gama kammala tunanin hakan sai kawai ya shafi wani gurin shafi a damtsen sa na hagu take yayo ƙasa sulu lu lu luh! Ya dira a bisa turaba tamakar yakasance mai fuka-fuakai Inda ya sauka yakasance daji mai ɗauke da manyan tsaunuka da bishiyoyi, duwatsu da ƙwazazzabai, Hakika dajin yatara dukkan wata sifa ta kwarjini Daga can nesa sai sarki Hamras ya hangi wani kerarran gida kwarya ɗaya jal a dajin Al'amarin da yayi matukar basa mamaki kenan kuma ya ɗaure masa kai ya ce a cikin ransa Shin ko wane ne. Mai mallaki wannan gida kawai sai ya yanke shawarar ya shiga izuwa gidan domin yaga ko mene ne a cikin sa Koda gama yanke shawarar hakan sai kawai ya durfafi gidan gadan gadan Idan ka ɗauke karar takun sawaye sarki Hamras dake haddasa motsawar busassun ganyayyakin bishiyun da suke zube a ƙasa babu abinda kunne keji Wannan shi ne a binda ya faru ga sarki Hamras na mai mulkin Daular aljanu, *****. *****. ***** Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin su boka Dayyubul-Barmas da yaran Uban muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN Sai yaƙin yazamo mai matukar firgici daban tsoro Karar karafniyar ƙarafa ta cika tsaunin Darul SHAFRAS baki ɗaya Suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA Nan fa su boka Dayyubul-Barmas suka fara gane kuren su domin tsananin zafin naman muridan ya huce tunanin bil,dama Kai iya hargowar muridan ta isa ta firgita duk wata halitta mai numfashi, Abangaren jarumi shamsuddin kuwa wani abin mamaki ya faru domin dai gashi a zahiri muridan na kallonsa amma sai ya zamo basa iya ganin ballantana su tunkari inda yake, Su kansu su boka Dayyubul-Barmas sai da suka cika da matukar mamaki da ganin hakan, Abin da basu sani ba shine addu'o i da shamsuddin ke karantawa shine ya makantar da idanuwan muridan. Basa iya ganin sa Sai da aka shafe tsawon dakika ɗari biyar ana fafata artabun babu sassauci Yazamana cewa su boka Dayyubul-Barmas basa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kansu kawai. Al'amarin daya fusata muridan kenan kuma ya basu mamaki, Domin a iya tsawon wanzuwar su a saman tsaunin Darul SHAFRAS basu taɓa yin gamo da halitta mai karfin damtse tamkar su sarauniya lasmirat, Koda su kazo nan a tunaninsu sai suka sake zage damtse suna kaiwa mu hare haren bazato Tabbas masu iya magana na cewa idan kiɗa ya canza dola ne rawa ta canza Faruwar hakan keda wuya sai ya zama na cewa a wannan lokacin muridan sun fara samun nasarar kaftausu sara a sassan jikin su, Duk wanda ɗaya daga cikin muridan ya kafta sara sai kaji ya tsandara ihu jini yayi tsartuwa, Kuma ya kife a kasa yana nishin wahala, Cikin abinda bai gaza dakika ɗari biyu ba muridan suka zubar da su boka Dayyubul-Barmas kasa babu wanda yake wani kwakkwaran motsi a cikinsu, Sai nishi kawai suke yi numfashin su na fita sama sama Koda samun wannan gagarumar nasara sai muridan suka bushe da dariyar mugunta suka shiga buga ƙafafuwan su a kasa, Nan take sautin ɗariyar yayi sanadin sumewar su boka Dayyubul-Barmas, A lokaci guda tamkar haɗin baki muridan suka tsuke bakunan su tamkar an aiko musu da WASIKAR MUTUWA kai kace basu taɓa dariya ba tunda Allah ya halicce su, Sarkin muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN ya sake ratso wannan hanya ta tsakiyar yaran sa ya taka da kafafafun sa har izuwa inda su sarauniya lasmirat ke kwance, Yaran sa nayi masa kirari suna cewa Gaisheka KIRMALU mai duniya Hadari sa gaban ka inda kake so! Daji kake ba,a yi maka ƙyaure koda mahaukacin kafinta, Kai gajimare mai zubar da ruwan musiba da bala'o'i Kai ne. SARKIN SADAUKAI na duniya, Sa,adda uban muridai KIRMALU yaji kirarin da yaransa ke yi masa sai ya wangale bakinsa yana mai ɓaɓɓaka dariyar farin ciki, Duk wannan abu dake wakana jarumi shamsuddin yana tsaye a gefe guda yana kallo A lokaci guda KIRMALU ya murtke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA Kawai sai ya zare wani mashi a gadon bayan sa mai baki biyu ya daga sama da nufin ya farka cikin sarauniya lasmirat da Sunaila, Koda ganin abinda ke shirin faruwa sai shamsuddin ya falafala da azababban gudu izuwa kan uban muridai yana mai karanto waansu addu'o'i na musamman a cikin ransa tare da maimakon Ubangijin musulunci, Yayin da rage saura taku goma tsakanin su, sai a sannanne muridan suke iya ganin shamsuddin da idanuwan su, Kafin aya daga cikin su yayi wani yunkuri shamsuddin ya shammace shugaban muridan ya gabza masa wani wawan naushi a fuska, Bisa mamaki sai aka ji uban muridai KIRMALU ya kurma wawan ihu sannan ya jefar da mashin dake rie a hannun sa, Al'amarin da ya harzua zukatan sauran muridan kenan kuma fusata ainun suka afkwa shamsuddin da azababban yai suka wanzu suna kai masa miyagun hare haren Shamsuddin ya wanzu yana karewa tare da zillewa harin muridan tare da maida martani cikin bakin zafin nama ta hanyar amfani da hannun sa da kafa wajen kai bugu da naushi, Tabbas ikon Ubangiji ya huce tunanin an Adam domin abinda mutum yake ganin bazai yiwu ba sai kaga Ubangiji ya samar dashi, Domin kuwa duk wanda shamsuddin ya nausa a cikin muridan sai kaji inda ya nausa in ya ya karye yayi kara as ruus, ya kurma wawan ihu, Nan fa ihu da kururuwur muridan ta cika dodon kunne da tsaunin baki aya, Duk inda shamsuddin ya sanya gaba sai dai kaga muridan na zubewa kasa matattu tamkar yana sassabe a gonar auduga jini yana kwaranya, Wohoho Hakika duk wanda ya iya ya huta inda ace mutum yana tsaye a wannan waje yaga yadda shamsuddin ke hallaka muridan dola ne ya jinjina masa ya tabbatar dacewa ya cika SARKIN SADAUKAI, Kafin shuewar dakika ari shamsuddin ya hallaka gaba aya muridan ya zubar da gawarwakin su, Sa'adda uban muridai KIRMALU IBN SHAMSHAN ya yi arba da gawarwakin jama'ar da sai kawai ya mie tsaye zumbur yana mai kurma wawan ihu Take wata irin gagarumar Iska ta dunga fitowa daga hancinsa da bakinsa wacce ta sanya gashin kan shamsuddin ya mimmike , Kuma tayi sanadiyyar farfaowar su sarauniya lasmirat daga dogon suman da suka yi. Sa'adda sarauniya lasmirat,boka Dayyubul-Barmas, yaslir, Sunaila,saltir, Huzmal,Barbusa, Huruful-labarus, suka yi arba da gawarwakin muridan kwance cikin jini kuma jikin shamsuddin duk ya aci da jini muridan sai suka cika da matukar mamaki, Suka ce a cikin ransa shin taya ya akayi shamsuddin ya samu gagarumin karfin da samu nasarar hallaka muridan Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu domin suga abinda zai faru tsakanin shamsuddin da uban muridai KIRMALU, Uban muridai KIRMALU na kammala kururuwur sai kawai ya zare wata zabgegiyar adda a ugun sa mai kaifin tsiya ya falfala da azababban gudu izuwa inda shamsuddin yake duk sa'adda ya ajiye afarsa aya sai kaga kafar wajen ta tsage ta rufta izuwa ciki, Koda ganin hakan sai shamsuddin ya zare takobin sa ya kwala kabbara da karfi ya ruga kan uban muridai don tarar juna, Lokacin da ya zamo saura taku goma a tsakanin su sai shamsuddin ya zamo an wada agaban uban muridai tamkar an ajiye yanwa a gaban kare, Lokacin da aka hau sai aka ruguntsume da azababban yai mai matukar firgici daban tsoro, Shamsuddin ya wanzu yana kare hare haren uban muridai tare da mayar da martani cikin bain zafin nama JURIYA DA BAJINTA, Duk sa'adda uban muridai ya kai masa hari da addar sa idan ya goce duk abinda takobin ta sauka a kansa sai kaga yayi bindiga ya tarwatse yazama gari koda kuwa gini komai warinsa, nan fa shamsuddin da uban muridai suka tashin hankalin duk wata halitta dake fadar, Gaskiyar masu iya magana da suka ce fadan da yafi karfin ka sai ka zamo an kallo, Kuma tabbas idan gwani da gwani suka hau, juriya da naci suka ci karo da juna dole ne yai ya zamo tashin hankali daban tsoro, Hakan ne yafaru dasu boka Dayyubul-Barmas domin koda suka lura cewa duwatsun da su shamsuddin ke rusawa a fadar suna neman danne su sai suka rarrafa da afafuwan su izuwa bayan waansu duraku a fadar suka lae suna hangen abinda ke wakana Sai da aka shafe tsawon sa,a aya cur ana wannan bain artabu Shamsuddin bai samu nasarar koda lakutar jikin sa ba duk kuwa da cewar yana karanta addu'a na musamman a cikin zuciyar sa Ana cikin wannan artabu ne uban muridai ya samu nasarar make takobin dake hannun shamsuddin a lokacin da ya daka tsalle da nufin ya hau kan kafadar sa Kawai sai uban muridai KIRMALU ya canza salon faan sa a inda ya shiga kaiwa shamsuddin hari da karfin damtse bada makami ba , Shamsuddin ya wanzu yana zillewa harin tare da amfani da dubaru da hikimomi, yana mai kwala kabbara gami da neman taimakon daga sunayen fiyayyan halitta annabi Muhammad s,a,w, Nan take wani irin gagarumin karfi ya shige sa kawai sai ya daka tsalle sama ai ku wa sai gashi a saman uban muridai tamkar an janye sa da ungiya, Kawai sai ya dunkule hannayen sa biyu ya irawa uban muridai KIRMALU naushi a wuya, Saboda arfin naushin sai da asusuwan wuyan sukayi ara ruus as! Uban muridai ya kurma wawan ihu, Kafin ya sake wani yunkuri shamsuddin ya sake gira masa wani naushin. Kawai sai akaga jikin uban muridai ya sandare ya yi asa zai fao, Koda shamsuddin ya lura cewa zai rikito daga saman uban muridai sai kawai ya dako wani wawan tsalle naban al'ajabi da mamaki ya sauka abisa turba, A lokacin da gangar jikin uban muridai KIRMALU ta fai asa rikica, tamkar an jefar da toron Giwa ko shurawa bai yi ba Nan fa mamaki ya turnue su sarauniya lasmirat Bisa ganin gagarumar bajintar da shamsuddin yayi na hallaka uban muridai KIRMALU da yaran sa. Al'amrin su shamsuddin kuwa sai da suka shafe tsawon kwanaki huu a saman tsaunin Darul SHAFRAS,kowa ya warke sumul daga raunukan dake jikin sa, Bayan shamsuddin ya samu nasarar ebo ruwan ma,ul- hayat a wani bangare a tsaunin, Sannan su aljani Huzmal suka sake aukar su aka cigaba da tafiya, Ana cikin wannan tafiya ne a lokacin da rana ta take sai sarauniya lasmirat ta dubi Sunaila tayi gyaran murya sannan ta kawo gwaron numfashi ta ajiye tace " ya Sunaila inyi miki wata tambaya mana idan bazaki damu ba, Sunaila tace " ina sauraren ki fai tambayar ki, Lasmirat ta ce" A can baya lokacin da kika samu nasarar akan wannan aljana acan birni na lokacin da na tambaye ki labarin rayuwar ki kin faa mini cewa baban Burin ki shine ki sadu da mutane ma,abota addanin Musulunci, domin aukar fansa akan wani azzalumun sarki shin Jarumi shamsuddin baya aya daga cikin mutanen da kike nema ne? Koda jin wannan tambaya sai sunaila tayi murmushi Duk da kasancewar fuskar ta na rufe da rawani sai da lasmirat taga alamun loawar kumatun ta a lokacin da tayi dariyar, Sannan ta dubi lasmirat yace" ya yar uwa ta kiyi sani cewa bawai ina tantama Game shamsuddin ba ne tabbas yana daga cikin ma, abota addanin Musulunci da nake nema sai dai ina so na kammala haa waansu hujjoji ne sannan na kari Addinin sa, Koda jin wannan jawabi daga bakin Sunaila sai lasmirat ta gyaa kai Sannan ta bui baki akaro na uku da fara wannan tattaunawa ta ce"Amma kina ganin Ubangijin shamsuddin bashine abinda dogaro ba kuwa ki dub kiga yadda ya samu nasara akan su aljani Huruful-labarus da uban muridai wanda boka Dayyubul-Barmas yagaza kare mu, Koda jin wannan batu daga bakin lasmirat sai sunaila tace"Tabbas duk abinda kika faa akan shamsuddin haka ne harma ya huce haka inda ace kin taa karanta jarumi Hilal da irin nasarar da ya samu a rayuwarsa da ke kunshe a cikin littafin KARSHEN ZALUNCI, da zaki tabbatar dacewa girma da sha,anin ma,abota addanin Musulunci ya huce yadda ake tsammani, Koda jin wannan batu sai sarauniya lasmirat tayi ajiyar zuciya sannan ta kawo gwaron numfashi ta ajiye tace" Ta ijan idan kuwa har haka ne abinda shamsuddin yayi abaya bakomai bane. Face sharar fage domin ke gaban mu yafi na baya yawa, Tafiyar kwanaki arba'in akayi aka iso kogon Garul- barzahu inda kubar miftahul-daryal take Sai da shamsuddin yasha gwagwarmaya dakyar da taimakon Ubangijin halitta ya samu nasarar kashe miyagun halittun dake ciki,kuma ya samu nasarar auko kubar miftahul-daryal, Hakika su sarauniya lasmirat sun ga iko da kudirar Ubangiji a wannan rana Bayan kwanaki biyu sai aka sake cigaba da tafiya domin isa gidan boka Daryalu domin ebo ruwan koramar sa Yayin da aka iso cikin koramar sai aka tarar tana auke da waansu irin halittu masu auke da fuka-fukai irin na jemagu suna da kawuna irin na bil,adama, suna wani irin gurnani mai sanya firgici daban tsoro. Nanfa aka ruguntsume da azababban yai mai matukar firgici daban tsoro yazamana cewa kowa ya gane kuren sa, Sai da aka wuni cir ana artabu babu sassauci, sannan aka samu nasarar hallaka halittun amma kowa ya samu manyan raunuka a jikin sa Nan fa yazamana cewa tsananin azabar dasu lasmirat suka sha tasa jikin su yayi sanyi kuma gwiwoyin su sukayi sanyi dukkanin su suka yi nadamar yin wannan tafiya domin wata buata ta jin dain duniya musamman sarauniya lasmirat, Bisa wannan dalili ne yasanya dukkanin su suka yanke shawarar karbar addinin Musulunci Bayan sun karbi kalar shahada ne a wajen shamsuddin Sai shamsuddin ya bayyana wa sarauniya lasmirat cewa dukkanin bayanin da boka Dayyubul-Barmas yayi mata aiki ne. Na bokaye ma,ana sihiri shi kuma sihiri karya ne Saboda haka imani da tayi da Ubangijin musulunci zai biya mata dukkan bukatun ta kuma muradin ta ya cika na samun aukaka a duniya da ma tsawon rayuwa A sannanne Sunaila ta cire rawanin dake kanta fuskar ta ta bayyana a fili arara Sa, adda kowa ya yi arba da fuskar sulaina sai mamaki ya kamashi , Yaslir kuwa bai san sa,adda ya ruga izuwa inda take ba ya kura mata idanu hawaye na zuba daga fuskar sa Nan take ita ma Sunaila kwalla ta zubo mata Bakomai ne ya sanya hakan ba sai domin a yanzu ne yaslir ya tabbatar da zargin sa cewa Sunaila ita masoyiyar sa gimbiya salimat Kawai sai suka rungume juna cikin matukar farin ciki maral musaltuwa gami da tsantsar soyayya hade da shauin juna, Ana cikin wannan hali ne sai kawai akayi arba da boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum hannun sa rike da wata zabgegiyar takobi ta haske mai matukar kyawu ba wata ba ce takobin ba face TAKOBIN AUKAKA Abinda basu sani ba shine. A lokacin da yaji dukkan su sun karbi addanin Musulunci sai ya faki idanun su ya bace yaje ya haa kai da sarki Hamras mai gidan su aljani Huruful-labarus, da tsohuwa zahira wacce sarki Hamras ya shiga gidan ta a cikin wannan daji a lokacin da ya fito farautar shamsuddin , Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su shamsuddin da su boka Dayyubul-Barmas, A lokaci guda boka Dayyubul-Barmas,sarki Hamras ,tsohuwa zahira suka yi kukan kura suka afkawa shamsuddin da azababban yai mai matukar firgici da tashin hankali, Dakyar shamsuddin ya hallaka su duka bisa taimakon Ubangiji dukkan su sukayi mutuwar hulakanci Tabbas da ace mutum yana wannan waje zai ga yadda gawar boka Dayyubul-Barmas ta hulakanta dole ne takaici ya kamasa bisa ganin yadda duk wahalar da boka Dayyubul-Barmas yasha abaya gashi ta tashi a banza yayi mutuwar asara Tabbas rayuwar kafirci wahala ce kuma arasa ce Amma shamsuddin yasha wahala tamkar ransa zai fita, Koda su aljani Huruful-labarus suka ga abinda ya faru da mai gidan su sarki Hamras da kuma irin abubuwan al,ajabi da shamsuddin yayi sai nan take suka bayar da gaskiya da Ubangiji suka amshi kalmar shahada, Batare bata lokaci ba jarumi shamsuddin ya auki TAKOBIN AUKAKA ya tofa mata Ayatul- kursiyyu take takobin ta canza launi kuma rubutun sunayen fiyayyan halitta annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama dake jikin takobin suka fito raau, Shamsuddin ya dubi su lasmirat yace" waannan sunaye su ne suka bawa su Boka Dayyubul-Barmas nasara akai na har nasha bakar wahala, Haia duk wanda yayi rigo da kamun kafa da mai sunan wato annabin rahama s,a,w zai samu nasara. A komi nasa koda kuwa kafuri ne Allah zai jinkirin ta masa na wani lokaci kafin na kamashi Koda jin wannan jawabi daga bakin shamsuddin sai kowa ya sake jin kaunar shugaban halitta ta arsu a zuciyar sa , Batare da wani bata lokaci ba su aljani Huzmal suka sake aukar su shamsuddin aka nufi hanyar dazata kai su birnin Misra Bisa mamaki a wannan lokaci sai su Huzmal suka ga cewa karfin gudun nasu ya karu ainun Abin da basu sani ba shine sirrin hasken MUSULUNCI ne a tare dasu ya basu karfin gudun Tsawon kwanaki huu aka auka a wannan lokaci bisa taimakon Ubangijin halitta aka iso birnin Misra Nan fa waziri ukashat da jama'ar birnin suka fito tarar su sarauniya lasmirat da tawagar ta Bayan an sauke su an haa liyafar Abinci da abin shaye shaye nau'i daban daban, Take kowa ya shiga kimtsa cikin sa ana fira cikin nishai Su ma su Aljani Huzmal sai akawo musu tasu liyafar abisa wadannsu manyan tukwane dake auke da farfesun naman rakuma da shanu Nan fa suka fara tanar baki suna rafka koma, Al'amarin da ya sanya har dariya ta subuce wa yaslir da Sunaila kenan bisa ganin aljanu nayin kalace, Bayan kowa ya samu nutsuwa ne waziri ukashat yakashe labarin abinda yafaru bayan tafiyar lasmirat ya zayyanewa lasmirat daga farko har karshe, Da abinda yafaru tsakanin su da wannan dodo daya bayyana a fada Batare da bata lokaci ita lasmirat ta shiga bawa jama'a labarin tafiyar su da abinda yafaru tsakanin su da shamsuddin da abubuwan al,ajabi da ya nuna Sa,adda jama'a sukaji wannan labari sai suka cika da inkin al'ajabi kuma suka ce tabbas munyi imani da Ubangijin jarumi shamsuddin take sarauniya ta biya kalmar shahada Dubban miliyoyin jama'ar ta suka amsa, Sai da aka nako guda shamsuddin na koyar da jama'a yadda ake gudanar da ibada kuma yana jinyar raunukan dake jikin sa Sannan aka shiga shagalin bikin aurin auren sarauniya lasmirat da shamsuddin, yaslir da Sunaila, Bai daga sassan duniya sun halarci taron bikin Akayi shagalin da ba,a taba yin kamar sa ba Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya mamaye ko ina arzikin birnin Misra ya kara bunkasa Bisa dole sarakunan dake nahiyar suka dunga zuwa da kansu suka karbar addinin Musulunci, Jarumi shamsuddin yazo sabon Sarki birnin Misra,jarumi yaslir yazamo shugaban majalisar sarki, Musulunci ya cigaba da bunasa. Karshe Alhamdulillah