Kangin Bauta 1 Littafin yaki Rubuta labari Mansur Usman Sufi Wthapp number 08137237071 Kyawawan samari ne majiya karfin damtse su uku, mai matukar kwarjini da ban tsoro. Na farkonsu yana rataye da waɗansu zaratan takubba guda biyu a gadon bayanshi kuma ya kasance mai matuƙar kaurin jiki fiye da 'yan uwanshi. Saurayi na biyu yana dauke da wani irin KWARI DA BAKA mai daukar hankali,jikinsa a murde yake ya tara kwanji, kallo daya zakayi masa kafahimci cewa ya fi sauran yan uwansa kirar sadaukantaka. Na ukun kuwa yana ɗauke da dauke da dogon nashi mai baki biyu, bakin yakasance daga farkon sa yayi fadi daga karshe yayi tsini ya fitar da baki biyu. Babu abin da zai burge ka ga samarin sama da yadda suka yi shigar yaƙi iri daya sak, kuma suna zaune abisa jajayen dawakai ingarmu. Samarin uku suna tafiya ne acikin wani daji ma,abincin dogayen bishiyoyi,koramu, tare da kwazazzabai.gaba daya yanayin dajin ya banbanta da sauran dazuzzukan da idanuwa suka saba gani. Domin hatta kwari da tsuntsayen dake cikin sa abin tsoro ne.awasu lokutan sai kaga tsuntsaye na dauke da fuskokin bil,adama,hatta bishiyoyin dajin suna canza launi zuwa launi, Tabbas dajin yana da matukar kwarjini ga duk jarumin daya tsinci kansa acikin sa dolane ya razana Haka dai zaratan samarin uku suka cigaba da tafiya adajin Babu alamun razani atattare da fuskokinsu Lokacin da suka shafe tsawon sa,a daya da dakika talatin suna tafiya acikin dajin,a dai dai wannan lokaci ne suka fara hango wani katafaren gida kwaya daya jal adajin, Al,amarin da yayi matukar basu mamaki kenan suka ce acikin zukatan su.taya za,ace wannan kasurgumin daji ace an gina wannan kerarrran gida a cikinsa. Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan, suka cigaba da tafiya, Da isar su bakin gidan suka tarar da gidan ya kasance tankameme Tamkar gari guda.gaba daya ginin anyi shine da waɗansu manyan duwatsun wuta wadanda ido bai taba gani ba, Katangun gidan sun kasance masu tsawon gaske.akwai ƙatuwar kofa guda daya jal mai tsawo da kauri inda za,a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ta. Nanfa samarin suka yi cirko-cirko suna nazarin kofar tsawon dakika arba,in dayansu bai ce uffan ba. Daga can sai daya daga cikin su wanda ake kira da suna Hilwas yayi gyaran murya yace "yaku 'yan uwana yanzu mene ne abinyi? Gashi yanzu mun iso gidan boka kimraz,naji ajiki na cewa dukkan baiwar da muke da ita bazata yi mana wani amfani ba face muyi Amfani da fasahar da muke da ita." Koda jin wannan batu sai sharwas yayi caraf ya tari numfashin Hilwasa yace"Ni shawarar dazan bamu muyi tunanin hanyar da zamu bude Wannan kofa, kunsan masu iya magana na cewa abari ya huce shi ke kawo rabon wani, kuma da zafi-zafi a kan daki karfe." Duk wannan tattaunawa da akeyi kahzib yayi shiru bai ce kala ba. Fuskar sa cike da damuwa, Kahzib yayi gyaran murya yace"yaku abokaina nifa ba wannan abu ne damuwata ba. shin kun mantane cewa rayuwar iyayenmu tana hannun sarki shardasu. A cikin ku wane yake da tabbacin sarki shardasu zai cika alkawarin daya daukar mana idan muka mallako masa abubuwan da yake buƙata na bamu fansar rayukan iyayemu. meyasa baza muyi tunani me yasa baza muyi tunani akan nemo musu maganin dazai warkar da lalurar dake samun su ba? Sa,adda kahzib ya zo daidai nan azancen sa sai jikin Hilwasa da sharwas yayi sanyi. Kuma hankalinsu ya dugunzuma ainun suka zurfafa izuwa kogin tunani, Su dai wadannan samari sun fito ne daga Wani birni da akewa lakabi da BAITUL-NA'IM. dalilin daya baro dasu daga gida shine kamar haka:- * Birnin baitul-na,im yakasance kasaitaccen birni daya shahara a fannin noma, kasuwanci. wanda ya haɗar da attajirai da manoma.kuma suna da ZARATAN MAYAKA masu juriya a filin daga. Sarkin da yake rike da Sarautar wannan birnin ana kiransa da shardasu ibn furais, Sarki shardasu yakasance Gwarzon mayaki mai tarwatsa maza afilin fama. mutum ne mai son abin duniya .dadin dadawa kuma yakasance AZZALUMI nagaban kwatance. Domin duk shekara a birnin sa ana noma abinda bokaye da masu hasashe suka tabbatar da cewa zai iya ciyar da kasashen dake nahiyar na tsawon shekaru biyu amma saboda zaluncin sa sai dai ya siyar da abincin ga manyan kasashen da ke wata nahiyar daban Duk yawan abin da mutum ya noma zai kasashi gida Biyar ya dauki daya kaso hudun na sarki shardasu ne. hatta dabbobi bai kyale ba duk shekara a kwai kason sa aciki, Sai da ya Zamo duk faɗin nahiyar babu attajiri kamarsa. Mahaifan Waɗannan samari uku sun kasance bayi ne ga sarki shardasu asali sarki shardasu ne ya cinye kasar su da yaki ya ribato su a matsayin fursunonin yaki. A tarihin samartakar su ba,a samu jarumai kamar su ba a can ƙasar su Mahaifan su sun samu lalurar dake jikin sune saboda bautar da suke yi a karkashin sarki shardasu. Mahaifin Hilwasa ana kiransa da suna Rukaisu , Rukaisu ya samu lalurar makantane saboda aikin ƙera dukkan nau,ikan kayan yaki,kofuna,da sauransu abubuwan da ake sana'anta su da zinariya da jauhari. Tunda Rukaisu yake Wannan aiki nasa ba,a taba samu ya ƙera wani abu ba yadda sarki ya buƙata ba amma saboda wata rana an samu akasi ya kera wadansu kofuna ba yadda aka umarta ba ya sanya aka soke masa idanu da wasu kibiyoyi na wuta idanunsa suka makance kuma aka aikashi izuwa kurkuku. Mahaifin sharwas kuwa ana kiransa da suna Rauzil ya kamu da ciwon kuturtane a hannayen sa da ƙafafuwan sa saboda aikin dafa sarki shardasu ruwan wanka wata rana rauzil ya kammala dafawa sarki ruwan zafi a bahon wanka bayan ya kammala zuba turaruka da sabulai masu kanshi, sai ya umarci wadansu kuyangi da sukai ruwan izuwa kewaye. Jim kadan sai ga sarki shardasu ya fito daga kewayen fuskarsa a murtuke tamkar an aiko masa da sakon mutuwa. kawai sai ya damki gashin kan Rauzil yana janshi akasa har izuwa inda wani ƙaton kasko yake a turakar sa. Kaskon yana dauke da wani tafashasshan ruwan zafi mai kauri baƙi baƙi. kawai sai sarki shardasu ya kama hannayen Rauzil ya tsomasu acikin kaskon. Tun Rauzil yana kwarara ihu har takai bana iyawa sai dai hawaye kawai yake zuba a idanunsa.lokacin daya fito da ƙafafuwan take naman jikinsu ya zagwanye Babu tausayi afuskar sarki shardasu ya damki hannayen Rauzil ya motsa akaskon, Hakika komai rashin imanin mutum idan yaga yadda Rauzil yake kwarara ihu yana zubar da hawaye dolane ya tausaya masa sai da naman jikin hannayen ya zagwanye sannan ya yi jifa dashi gefe guda Rauzil na fitar da numfashi sama-sama tamkar zai sheka barzahu daga nan aka kaishi izuwa kurkuku yazamo gurgu baya iya tafiya sai dai rarrafe Mahaifin kahzib kuwa ana kiransa da suna Hashim Shi kuma ya samu lalurar kurumtane saboda wani laifi da ya yi wa Sarki shardasu ya dunga dura masa garwashin wuta a baki yana hadiyewa Matayen su hasham kuwa sai suka kasance cikin matukar bakin ciki tare da kewaye mazajen su dare da rana Bayan shudewar wannan al,amari ne da kwanaki arba'in sai sarki shardasu na zaune a fadar sa. Fadar ta kasance makekiya mai tsawo da fadi.an kawatata da dukkan kayan kyale kyalen alatun jin dadin duniya. Duk inda mutum ya kalla bayi ne da kuyangi suna ta hidima, kowacce kusurwa a fadar dakarun ne atsaitsaye cikin matsananciyar shigar yaƙi mai matukar kwarjini da ban tsoro hannayen su rike da miyagun makamai Domin tabbatar da cikekken tsaro. Sarki shardasu Sarki shardasu na zaune a bisa kan ƙasaitacciyar karagar mulki da akayi da farin lu,u lu,u da jauhari. Ajikinsa yana sanye da yar karamar rigar Koriya mai gajeran hannu a hannun sa na hagu yana rike da wata ƙasaitacciyar sanda irin ta hamshakan sarakai sanye a kansa akwai kambun sarauta na zinare. A ƙafarsa yana sanye da takalmi baki da aka yi masa ado da nau,ikan gashin dawisu. A wannan lokacin ana tafiyar da harkokin mulki cikin kwanciyar hankali kwatsam sai aka hango Wani badakare ya shigo fadar yayin da rage tsakaninsa da karagar mulki bai huce taku goma ba sai kawai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa. sannan daga bisani ya dago da kansa yayi gyaran murya yace"ya shugabana labari ya riskeni cewa matayen su hasham sun sauka lafiya, kuma dukkanninsu sun haifi yaya maza, Koda jin wannan batu daga bakin bawa Durshuf sai fuskar sarki shardasu ta faɗa ɗa da murmushi tamkar wanda aka bawa SARAUTAR DUNIYA kuma ya mike tsaye tsam daga kan karagar sa daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi Bawa Durshuf yace"ina so kayi mini jagora izuwa inda matayen suke" Sarki na gama faɗin hakan sai bawa Durshuf ya shige gaba sarki shardasu yabi bayansa take dakarun Sa suka mara masa baya. Suna fita wajen fadar aka kawo keken doki sarki Yakamata ya hau aka cigaba da tafiya. Tafiyar dakika talatin da hudu, su badakare Durshuf kadai su kayi suka iso wani bangare da bayi suke a cikin Gidan sarautar, Shi dai wannan bangare akalla yana dauke da dakuna fiye da talatin kuma musamman an Gina nasa ne domin bayi mata masu dauke da juna biyu. Da isowar su durshuf Sai wani badakare ya rugo izuwa inda suke tsaye ya sauke matattakalar keken dokin take Sarki shardasu ya taka matattakalar keken dokin Ya sauko kasa Sannan badakaren ya zube kasa Ya kwashi gaisuwa cikin ladabi yace"ya mai duniya ai Sai ku shigo izuwa ciki Sarki shardasu Ya karewa matayen kallo da nazarin jariran dake hannayen su na wani dan lokaci Sannan daga bisani ya mayar da dubansa ga shugaban dake kula da Gidan wani garjejen kato yace dashi cikin kakkausar murya "yakai Larbus kayi Sani cewa ban zo wannan gida ba Sai don na baka wani umarni. Abin da nake bukata shi ne ka kula da lafiyar wadannan mataye da jariran su. Tabbas nan gaba zasu zamo masu amfani agareni". Koda gama wannan jawabin Sai Sarki shardasu Ya juya ya nufi kofar fita daga gidan dakarun sa na take masa baya. yana fita ya hau bisa keken dokin Sa, Ya nufi hanyar da zata mayar dashi izuwa fada. Tun daga wannan rana matayen su Hasham suka kasance cikin kulawa ta musamman. Amma dai-dai da rana daya basu taba daina begen masoyan su ba, Gaskiyar masu iya magana da su kace sannu-sannu bata hana zuwa Sai dai adade ba,a je ba Sai gashi jariran su Hasham sun shekara goma, tun a wannan lokaci Sarki shardasu Ya umarni sarkin yaki Hatyal ya dauke su ya kaisu izuwa gidan horan yaki Nan fa yazamo cewa su sharwas sun kware ainun a fagen salon yaki iri daban-daban. A bangaren mahaifan su Hilwas kuwa tun da aka tafi da Yaya yen su Sai izuwa gidan horar da mayaka Sai Ya zama na sun kasance cikin KANGIN BAUTA Ya zama na duk wata kulawa da ake basu lokacin da suka haihu an dai na yi musu , domin a wasu lokutan dakyar suke samun abinda zasu ci. **** Kasaitacciyar turaka ce da aka kawata ta da nau'ikan kayan kawa da alatun jin dadin rayuwar duniya. Babban abinda ya kara fito da kyawun turakar shi ne wadansu fararen kushin na alfarma da aka kewaye turakar dasu kowacce kusurwa a turakar an kawata ta da wasu kawatattun fitulu na azurfa. idan mai kallo ya yi duba daga bangaren yamma a turakar bisa kayatattun kujerun zai yi arba da wani sadauki zaune shirye cikin gagarumar shigar yaki Mai matukar kwarjini da ban tsoro Duba daya zaka yi masa ka kawar da fuskar ka saboda tsananin munin sa, A bisa wata karaga ta alfarma wani mutum ma,abocin kyawun fuska da kwarjini, yana sanye da tufafin sarauta na alfarma sun yi matukar yi masa kyau kai da gani kasan yana jin dadin duniya. Shiru ne ya wanzu a tsakanin su Sai Daga bisani ne Sarki shardasu Ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar budar baki yayi gyaran murya yace "yakai dirkar birnin baitul-na,im kayi Sani Sani cewa ban kirawo ka nan ba Sai domin na tunasar dakai cewa lokacin gudanar da GASAR JARUMTA ya gabato nan da kwana talatin kacal! Lallai ina so a fara shirye shiryen wannan gasa. Kasani cewa awannnan karon akwai manayan sarakunan nahiyoyi hudu da zasu halarci wannan Gasa Sannan salon gasar zai canza izuwa rukuni uku .wato fadan takobi, Sai kuma na KWARI DA BAKA da kuma ta KARFIN DANTSE. Koda Sarki shardasu Ya zo nan azancensa Sai Ya zira hannun sa aljihunsa na Riga ya dauko wata doguwar takarda ya mikawa sarkin yaki, Cikin biyayya ya sa hannayen sa ya karba Sannan ya warware ta yafara karanta abinda ke kunshe a cikinta. Koda kammala karantawar Sai yaji zuciyar sa yayi bakikkirin bakomai ne ya sanya shi cikin wannan hali ba Sai domin a cikin sunayen jaruman gasar da aka bashi yaga sunan yarima kinzaru Wanda tsakanin su akwai rashin jituwa, Saboda sarkin yaki yana matukar kaunar kanwarsa gimbiya lashmira Tsakanin lashmira da yarima kinzaru akwai rashin jituwa saboda kowannen su na kwadayin ya gaji karagar mulki, Sa,adda Sarki yaki Ya zo dai dai nan a tunanin sa Sai ya cika da matukar bakin ciki yana cikin wannan hali ne Sai ya lura akwai sauran rubutu a ayan takardar. Cikin matukar farin ciki ya juya takardar ai kuwa Sai yayi arba da sunan gimbiya lashmira,Bawa Hilwas, sharwas da bawa kahzib, saboda farin ciki bai San sa,adda murmushi ya subuce masa ba, yayin da ya hada idanu da Sarki shardasu sai ya sunkui da kansa kasa cikin alamun rashin gaskiya Sarki shardasu Ya dubi sarkin yaki da duban dake nuna fahimtar wani abu game da murmushi nasa Sannan yayi gyaran murya yace " ya dirkar birnina kayi Sani cewa inaso ka gaggauta sanar da dukkan Wanda sunan sa ke kunshe a cikin wannan takardar jaruman Gasa kuma a tabbatar da cikekken tsaro daga yanzu har izuwa bayan gasa domin wannan gasa ce ta musamman. Koda gama fadin hakan sai Sarki shardasu Ya mike tsaye tsam! daga kan kujerar sa ya taka da kafafunsa ya nufi wata har siririyar kofa a turakar. Yana tafiya cikin kasaita da BAKAR IZZA! yana isa bakin kofar wadansu ZARATAN MAYAKA na sihiri suka bayyana su kimanin arba,in shirye cikin gagrumar shigar yaki suka Mara masa ba ya har ya kule izuwa cikin Gidan sarautar. Hakika Sarki shardasu Ya zurfafa acikin ilimin tsafi da kamo kafar shi sai mutum yayi da gaske. Nan take Sarki yaki Ya mike tsaye ya fice daga turakar zuciyar sa cike da tunane - tunane iri - iri. Mu hadu a kangin bauta 3 Don cigaban wannan kayataccen labari Daga mai debe muku kewa akoda yaushe MANSUR USMAN (SUFI) Wthapp number 08137237071 KANGIN BAUTA 6 Marubuci MANSUR USMAN SUFI Sarki Barsus na kwance bisa gado a cikin masaukinsa sanye da riga falmaran da dogon wando marar nauyi irin na hamshakan attajirai, kawai sai ya ji wani kwankwasa masa kofar shigowa turakar nan take ya mike tsaye tsam daga kan gadon ya je ya bude kofar. Wani saurayi kyakykyawa sanye cikin sulken yaki ya yi ido biyu da shi, Barsus ya yi guntun murmushi a gare shi. Saurayin ya zube kasa ya kwashi gaisuwa sannan ya budi baki cikin ladabi ya yi gyaran murya ya ce, "Ya shugabana tuni kyaumu sun iso tare da shugaban barayin wannan nahiya, kuma tuni ma sun fara yin kyau da ayy kyau, domin isa in da turakar sarki Shardasu da gimbiya Lashmira take. Koda jin wannan batun daga bakin saurayin sai sarki Barsus ya bushe da dariyar mugunta, a lokaci guda kuma ya turbune fuska kamar an aiko masa da WASIKAR MUTUWA. Cikin kakkausar murya ya ce, "Tabbas na yarda da kai ya kai Huzmal ina mai tabbatar maka da cewa da zarar burina ya cika na ganin bayan sarki Shardasu da gimbiya Lashmira a gobe za a yi nadin sarauta ta tare da yi maka wazirina, Koda jin hakan daga bakin sarki Barsus sai Huzmal ya sake zubewa kasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya tashi ya juya ya ficc daga cikin turakar zuciyarsa cike da farin ciki, koda ficewar Huzmal sai sarki Barsus ya janyo kofar turakar ya rufe ta ruf, ya kashe fitulun da ke ciki, sannan ya kwanta bisa kan gadonsa domin ya samu ya huta. Sa'adda gimbiya Lashmira ta yi arba da fuskar mahayin sai ta cika abin mamaki mamaki, ba komai ne ba ya ba ta mamaki ba sai bisa ganin gimbiya Shuraima 'yar sarki Husubul Dinar, Kallo ne ya wakana tsakanin gimbiya Lashmira da Shuraima na dan wani lokaci, har Lashmira ta budi baki da kyau ta ce wani abu sai Shuraima ta matso daf da ita ta rike hannunta ta tashe ta tsaye, ta yagi wani yanki a tufafinta ta goge mata jinin da ya zuba a bakinta suka shirya juna. Sannan Shuraima ta budi baki cikin tattausar muryar ta ce, "Ya Lashmira ina ncman afuwarki bisa ZUBAR DA JININ da na yi miki tabbas ban yi hakan domin kaskanta daraja da martabarki ba sai domin kare zuciyar ki daga kudurun da ke tattarc a al'adar. ki yi sani ccwa na san ba wani abu ne ya fito da ke a cikin wannan dare ba fuskantar tsananin soyayyar bawa Hilwas da ta addabi zuciyarki. Tabbas, matsalarmu irn daya ce, domin ni ba komai ne ya fito da ni a dai-dai wannan lokaci ba sai bisa kamuwar da zuciyata ta yi da kyau kaunar bawa Kahzib, irin son da ban taba yuwa wani da namiji ba, Saboda haka kinga yanzu tsakaninmu sai dai mu hada kai domin saduwa da masoyanmu kafin wayewar gari. Koda jin wannan doka daga bakin gimbiya Shuraima sai Lashmira ta saki tattausan murmushi, a gare ta sannan ta budi baki cikin annurin fuska ta ce "Ya ke Shuraima ki yi sani cewa tabbas na gamsu da dukkan bayaninki domin na san a cikin sarakunan da suka halarci GASAR JARUMTA mahaifin ki ne kadai ba shi da wani mummunan kudiri a zuciyarsa a kaina da abbana. Amma sai dai kafin mi ci gaba da tafiyar mu ina so ka amsa mini tashin tambayoyi kamar haka: - Shin kuna yakinin cewa bawa Kahzib zai amince da soyayyarki? Tambaya ta karshe ita ce a ina ki ka samu irin tufafin da na sanya? Adabi24.com.ng Da jin wannan tambayar sai Shuraima ta yi murmushi ga Lashmira sannan ta dube ta ta hanyar gyaran lallausan muryar ta kawo gwauron nunfashi ta ajiyc ta ce, "Game da tambayarka ta farko, ki yin sani cewa duk da cewa bawa Kahzib bai furta min cewa yana kaunata ba tabbas na ga alamun hakan a kan fuskarsa, a lokacin da muka hada idanuwa da shi a filin gasa, kin san masu iya magana na ccwa LABARIN ZUCIYA a tambayi fuska Sannan game da tufafin da na sanya mai kama da naki kuwa labari ne mai tsawo, akwai bukatar mu samu lokaci mu zauna. Sa'adda Lashmira ta ji amsar wadannan tambayoyin sai mamaki ya turnuke ta ta ce a cikin ranta. "Shin wace alaka ce ke tsakanin tufafina da na gimbiya Shuraima, Kawai sai ta bar abin a cikin ranta su ka ci gaba da tafiya suna masu sakc rufe fuskokinsu da rawanin har suna hira kamar sun dadec da sanin junansu har suka iso masaukinsu, bawa Kahzib ba su hadu da wata matsala ba, sai da kyar da sidin goshi suka sadu da masoyansu. Wato bawa Hilwas da Kahzib kuma suka samu damar taron a ranar, ashe su ma da kyau Sun sun kamu da soyayyarsu. Kashe gari tunda duku-dukun safiya fadar sarki Shardasu ta cika ta batse da jama'a, duk in da mutum ya kalla kawunan bil'adama ne rututu babu masaka tsinke Babu abin da zai bawa mutum mamaki kuma iya daure masa kai fuska ganin yadda sarakunan da suka halarci taron ba su yi wani jinkirin fitowa ba, da yawa daga cikin jama'a a nan suka same su. Ana cikin wannan hali ne sai aka jiyo bushin algaita hade da bugun tambura, alamun sarki Shardasu na kan hanya. Kwatsam! Sai aka hango sarki Shardasu da tawagarsa sun shigo fadar sarki ne a kan gaba, gimbiya Lashmira tsaye aɓangaren hagu yarima Kinzaru a dama dukkansu sun caba ado mai girma daukar hankali, dakaru rike da kyau na take musu baya. Koda ganinsu sai gaba daya jama'ar da ke fadar suka mike tsaye domin girmamawa a gare su, Adabi24.com.ng domin masu iya magana kan ce ba a sarki biyu a masarauta daya, sai da sarki da su yarima suka zauna a wajen da aka tanadar musu sannan kowa ya zauna, fadar ta yi shiru kamar mutuwa ta kawo Ziyara. Aɓangaren da aka tanadarwa sarakuna kuwa sa'adda sarki Hukubul Ansab ya yi arba da tufafin da ke sanye a jikin sarki Shardasu sai takaici da bakin ciki suka suka mamaye zuciyar shi ya ji kamar ya kurma ihu daboda takaici. Ba wani abu ya sanya shi hakan ba face bisa ganin wannan dukkan kayan sarakunan masarautar daya sace a dakin masarauta domin ya samu nasar yiwa sarki Shardasu JUYIN MASARAUTA sarki Shardasu na sanye dasu wato alkyabba, kambu, takalmi da sauransu. Sarki Hukubul Ansab ya ce a ransa Shin yanzu duk wahalar da na sha ta tashi a banza, tabbas sarki Shardasu ya cika hatsabibi a ilimin tsafi, kuma wannan shi ne masu iya magana ke cewa kifi na ganiqnka mai jar koma. Sa'adda sarki Hukubul Ansab ya zo nan a tashinsa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe. Kamar hadin baki sarakunan da suka gabatar a bayyane suka mike daga kan kujerun zamansu suka je suka zube a gaban sarki Shardasu suka kwashi gaisuwa, sarki Shardasu ya karbi gaisuwar fuskarsa babu yabo babu fallasa. Duk wanda ya kalla daga cikin sarakunan sai ya ji hantar tasiri ta kada, ya sunkui da kansa kasa shi kuwa sarki Shardasu sai ya yi guntun murmushi a gare shi, sarki Husubul Dinar ne kadai bai ji wani abu a ransa ba har ya mayar wa da sarki Shardasu martanin murmushin, KANGIN BAUTA Rubuta labari MANSUR USMAN SUFI 08137237071 Sarakunan suka sake mikewa tsaye suka koma wajen zamansu suna yiwa junansu wani irin kallo mai tattare da kyayyar juna. Bayan kamar shudewar dakika talatin sai aka hango su bawa Hilwas sun shigo fadar dakaru na dauki musu baya, su duka ukun shigar korayen tufafi suka yi farin rawani, farin takalmi. Shigar da tayi kyau fito da tsantsar kyawunsu. Koda shigowarSu ya zauna gaba daya fadar ta ruɗe da shewa masu tafi da jinjina na yi su Hilwas na daga musu hannu, sai da suka zauna a wajen zamansu bayan sun kwashi gaisuwa ga sarki Shardasu sannan fadar ta sake yin shiru A karo na biyu, sarkı Shardasu ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar miƙewa tsaye ya fuskanci jama'a Sannan ya yi gyaran murya ya ce, "Hakika na girma jin dadi bisa ganin yadda jama'a suka bayar da hadin kai wajen halartar wannan fada mai albarka, domin ganin yadda za a bayar da manyan kyaututtuka ga jaruman da suka samu nasarar lashe gasar gasa rukuni uku da aka sake a jiya. Yanzu sai kowa ya saurara, domin ya ji sauraran bayanı. "Gama fadin hakan sai sarki ya koma kan kujerarsa ya zauna sarkin yaki Hatyal ya miƙe tsaye ya yi gyaran murya ya ce," Da farko yanzu muna bukatar ganin jarumi Hilwas wanda shi ne ya lashe kallon yaki da takobi, bayan ya samu nasara a kan abokin gwaminsa yarima Kinzaru. "Koda jin an ambacı Hilwas sai fadar ta rude da ya Koda hayanıya magoya bayansa na yi masa jinjina, har sai da je ya tsaya a da akc bukata. Koda tsayawar ta shi sai wani badakare va iso da wata madaidaiciyar akwatu ta bakin karfe ya ajiye ta gaban sarkin yaki a bisa tcburin da ke gabansu. Adabi24.com.ng Sarkin yakı ya bude akwatun ya dauko wata takobi da aka yi ta da zubar daji haɗe da wani kambu ya je ya risina a gaban sarki ya miƙa masa ya karba, shi kuma ya mike tsaye ya sanyawa bawa Hilwas kambun kuma ya damka masa takobin, Sannan ya rike hannun hilwas ɗayan ya saka a nasa ya daga sama. Nan take fadar ta rude da shewa gami da tafi, wasu ma har da kida da rawa, domin nuna farin ci kınsu bisa ba wa gwaninsu KAMBUM JARUMTA na gwarzon shekara. A bangarcn gimbıya Lashmira kuwa saboda tsananin muna ba ta san sa'adda ta mike tsaye ba tana yıwa masoyinta tafi da jinjina. Al'amarin da ya harzuka zuciyar yarima Kinzaru ke nan takama tafarfasa kamar zuciyar tasa za ta ƙone ya ji kamar ya zare takobi ya sare wuyan bawa Hilwas. Fadar ba ta samu nutsuwa ba sai da sarkı Husubul Dinar da sarki Hulbaru suka ba wa Hilwas kyutar dukiya mai yawa da adadinta ya kai dinare miliyan shida da ɗoriya sannan yaje ya zauna a kan kujerarsa a cikin yan uwansa Sharwas da Kahzib Sannan sarkin yaki Hatyal ya yi gyaran murya ya dora demunsa a kan takardar da ke magana game da shi, Jarumai na Kahzib da ya lashe zaben harbin KWARI DA BAKA, sai arumi Sharwas da ya lashe kallon jifa da mashi A lokaci guda tsakanin Kahzib da Sharwas suka mike tsaye suka nufi in da karagar mulki take sai nan take fadar ta sake kaurewa da shewa da tafi, gimbiya Shuraima kuwa farin cikin da ke zuciyarta ba a tonawa bisa ganin abin Kaunarta bawa Kahzib. Sa'adda ya rage bai fi sauran taku uku ba da girma da karagar mulki sai suka zube kasa suka kwashi gaisuwa ga sarkı Shardasu sannan wannan mummunan halin ya sake daukar manyan akwatu guda biyu ya ajiye su gaban sarkin yakı Hatyal, shi kuma ya bude ya dauko wata kasaitacciyar KWARI DA BAKA a cikin akwatu daya ya sake mikawa sarkı Shardasu shi kuma ya dankawa Kahzib, sannan sarkın yakı ya sake bude akwatu ta biyu ya dauko wani dogon mashi mai bakı biyu mai kyau launi da daukar ido ya mikawa sarki a karo na biyu, shi kuma ya damkawa Sharwas. Take fadar ta sake rudewa fiye da ko yaushe, a wannan lokaci ne Kahzib ya hango gimbiya Shuraima 'yar sarki Husubul Dinar, kawai sai ya ga ta jefe shi da wani inn tattausan mumushi mai tattare da tsantsar so da Kauna. Adabi24.com.ng Ai kuwa shi ma bai san sa'adda ya mayar mata da maratanin murmushin ba. Kahzib da Sharwas suka juya domin komawa wajen zamansu suna gaisawa da masoyansu Wasu kuma na ɗaga musu hannu, har suka isa in da kujerunsu suke suka sake zama, zuciyoyinsu cike da farin cikin farin ciki Maral Bayan komai ya samu dai daita sai kuma tsala tsalan Isalan mutanan kuyangi suka shigo fadar dauke da farin ciki da nau'ikan kayan abinci mai rai da lafiya. nau'i daban-daban Wadansu na dauke da tulunan giya, Nan take aka shiga hidimar ciye ciye da tanɗe-tanɗe, wani abu da zai bawa mutum mamaki kuma ya, daure masa kai shi ne duk tarin tsananin yawan jama'ar da suka halarci bikin sai da suka yi wadata da abıncı da abin sha har suka bar shi, sannan taro ya watse kowa yayi kama gabansa, baki suka koma masaukinsu Adabi24.com.ng kahzib, Hilwas da Sharwas na zaune a cikin turakarsu suna hira a tsakanınsu domin debewa juna ƙewa. A cikin hirar ta su ne Sharwas ya dube su fuskarsa cike da tsananin damuwa ya ce "Ya 'yan uwana ku yi sani cewa wannan farin cıkı da muke a yanzu, kawai ina nuna shine ba dan zuciyata tana so ba, ta wata fuskar ma wannan farın cıkin ba shi da wani amfanı. Cike ma maganar mamakI Hilwas ya dubi Sharwas cikin murmushi ya ce, "Ya abokina shin ina dalilin wannan furici naka?" Sharwas ya sake haɗe rai ya ce, "Sanın kanku ne ke cewa mahaifanmu na raye kuma mun rabu da su tun muna yara kanana, to ina amfanin farın cikın mu tunda ba mu san halin da suke cikı ba. Ko da jin wannan batun daga bakın Sharwas sai hankalın Hilwas da Kahzıb ya dugunzuma ainun har kwallar takaici a zubo masu Hilwas ya buɗi baki da ƙyar fuskarshi cike da damuwa ya ce, "Haƙiƙa abokina ka sosa mini in da yake yi min Kaikayı. ka sani cewa a yau yau kafin wayewar gari sai mun gano in da mahaifan mu suke mun gana da su. Hakika mahaifa sune ginshiƙin rayuwar dukkannin wani ɗa na gari. Sa'adda Hilwas ya zo nan a zancensa sai ya fashe da kuka, al'amarin da ya narkar da zuciyar Kahzib da Sharwas ke nan suma suka fashe da kukan, Marubuci MANSUR USMAN SUFI 08137237071 KANGIN BAUTA 8 Marubuci Mansur Usman sufi 08137237071 Sai da suka shafe tsawon lokaci a cikin wannan hali sannan Hilwas ya share hawayen da ke fuskarsa ya mike tsaye zumbur ya fice daga cikın turakar Kahzib da Sharwas na bıye da shi. Da ya ke lokacı ne na dare sai suka huce kai tsaye izuwa kurkukun kasar, Duk in da suka huce sai dai ka ga kuyangi da bayı nayi musu musujina gamı ​​da miƙa gaisuwa. Su kuwa ko kallonsu baa yi suna masu fice daga gidan sarautar, Tafiyar daƙiƙa hamsin kacal suka yi suka iso kofar kurkukun wadda ta kasance murtukekiya da aka yi ta da zunzurutun bakın karfe, duk in da mutum ya kalla a sama da ƙasan kofar tarin muggan dakaru ne shırye cikın shigar yakı. Hannayensu suna rike da miyagun makamai sai mazurai suke yi suna kai komo kamar za su ci babu, haƙiƙa komai dakewar zuciyar jarumi da rashin tsoronsa idan ya yi arba da dakarun dole ne ya firgice saboda kwarjininsu. Koda shugaban da ke kula da kofar wani garjejen basamuden kato ya hango su Hilwas sai ya tako da katafunsa ya tare su ya risına a gare su cikin girmamawa. Hilwas ya dubi basamuden ya ce, "Ya kai Zamaru ka yi sani cewa ba komai ne ya kawo mu nan ba sai domin ka sanar da mu shin ina ne mahaifanmu suke. ''Da jin wannan tambaya sai idanun Zamaru suka zazzaro ya dubi Hilwas cikin alamun tsananin tsoro ya ce, "Ya shugabana na roƙe ka da ka yi min rai. ka sani cewa ba zan iya sanar da kai in da sarki Shardasu ya boye mahaifanku ba, domin ina ina tsoron ka da ya halakar da ni Sa'adda Hilwas ya ji wannan batun sai ya fusata ainun har idanunsa suka kaɗa suka yi jawur, ya dakawa Zamaru tsawa wacce ta sanya hantar cikin Zamaru ta kaɗa, ya dube sa ya ce "Na rantse da rayuwar mahaifan mu idan ba ka sanar da mu in da aka ajıye mahaifanmu ba sai mun yi maka kısa mafi muni ka bƙkunci barzahu. Nan fa hankalin Zamaru ya dugunzuma ainun ya rasa abin da yake yı masa dadɗiA. Abuna farko da ya faɗo masa a rai shi ne, shin yanzu idan ya sanar da su Hilwas in da aka ajıye mahaifansu yana da tabbacın cewa sarkı Shardasu ba zai gane cewa shi ne ya sanar da su ba. Sannan abu na biyu shi ne tabbas idan bai sanar da Hilwas abin da ya ke bukata ba zai rasa rayuwarsa a yanzu take, Wannan fa shi ne masu iya magana kan cewa gaba tsini baya siyaki. Wata zuciyar kuma ta ce da shı koma dai dai zai zai faru gwara ka sanar da Hilwas abin da ya bukata. Domin ka TSIRA DA RAYUWAr ka a yanzu. Koda barde Zamaru ya zo nan a tunanin sa sai ya dubi Hilwas da turɓunanniyar fuskarsa kai ka ce murmushi bai taba wanzuwa a kanta ba. Ya buɗe tafkeken bakınsa wanda ya fi kama da kofar gari ya ce, "Ya shugabana sarkı ya ajiye mahaifan ku maza ne a can Wani gida na musanman, bayan ɗauke su daga kurkuku, domin ka da ku yi yunƙurin zuwa in da suke. Shi dai gidan ya kasance a cikin kasa, wanda i dan har aka shigar da mutum baya taɓa fitowa face dai mutuwarsa. Gidan ya kasance a can ƙarshen gidan sarauta. Mahaifan ku mata masu suna a zaune a gidan horar da mata sana'o'i domin samar wa da sarkı dukiya mai tarin yawa, Ko da jin wannan bayani daga bakin barde Zamaru sai bawa Hilwas, Kahzib da Sharwas suka ji sun kamu da sananın tausayin mahaifansu bisa jin matsanancin halin KANGIN BAUTA da suke ciki". Ba tare da ɓata lokaci ba Hilwas ya umarci barde Zamaru ya kawo musu ingarmun dawakai, sannan suka kama musu linzami, suna masu tsala azababban gudu Kai tsaye gidan karkashin kasa suka nufa da ke karkashın gidan sarauta domin su fara saduwa da mahaifansu maza, Tafiyar rabuwa sa'a da daƙiƙa hamsin kaɗai suka yi suka iso ɓangaren tun kafin su karaso bakin kofar wajen suka fara fafata yaƙi da dakarun da ke tsaro. Lokacin da suka iso bakin kofar kuwa sai suka cika da matukar mamaki, Abin da ya ba su mamakin kuwa shi ne duk da irin yadda sararin samaniya ta mamaye da duhu, Amma ko ina a wajen haskake yake da wani haske na musamman wanda in da allura za ta faɗi a kasa da zarar mutum ya duba zai ganta Kai da gani ka san aiki ne na sihiri. Dakarun da ke wajen kuwa sun kasance ababan tsoro saboda kwarjininsu sai ka rantse ka ce ba su kasance bil'adama ba, tsananin yawansu kuwa ya huce musali. Yayin da suka bayyana suka yı arba da su Hilwas sai suka zare makamansu suka tare su aka kacame da KAZAMIN GUMURZU mai matuƙar muni, ban tsoro da ban al'ajabi. Ana fa wannan gumurzu ne dakarun suka gane shayi ruwa ne ba abinci mai nauyı ba, yawansu ya zamto banza, domin duk in da su Hilwas suka sanya gaba sai dai ka ga gawarwakin su na zubewa kasa, jini kuwa ya dinga feshi, fantsama yana malala a kasa. Nan fa ya zamana cewa bangarorin biyu sun wanzu suna kawai juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama JURIYA DA BAJINTA ta ban al'ajabi. Ana cikin wannan yaki ne wani daga cikin yanayin ya shammaci bawa Hilwas ya kawo masa wani nagartaccen sara da takobinsa wanda zai canza masa hannu. cikin bakin zafin nama Hilwas ya sanya takobinsa domin ya kare harin amma sai saran badakaren ya rinjaye shi ya kadɗe takobin Hilwas ta yo kasa za ta fadi. Kafin badakaren ya sake wani yunkuri Hilwas ya dunkule hannun sa ɗaya ya gabza masa wawan naushi a fuska, kuma ya miƙa ɗayan nasa ya cafo takobinsa saboda tsananin karfin naushin sai da badakaren ya banke 'yan uwansa dakaru mutum shida, suka zube kasa magashiyan. Tabbas jarumta da SADAUKANTAKA baiwa ce daga Allah, dukiya mulki ba sa bayar da ita face Allah. Kuma duk wanda Allah ya ba shi jarumta ya huta. In da a ce mutum zai ga yadda Hilwas, Kahzib da Sharwas ke ragargazar dakarun suna yin MUGUWAR HALAKA dole ne ya jinjina musu. Sai da aka shafe sa'a daya ana fafata baƙin artabu. sannan kuma Hilwas suka samu nasarar halakar da dakarun ba ki ɗaya, suka kutsa kai izuwa cikin gidan a nan amma sai suka yi GWAGWARMAYA da dakaru masu tarin yawa sannan suka samu shiga cikin ƙarƙashin ƙasa. Lokacin da suka shiga sai suka kama kalle-kalle da dube-dube suna masu duba dakunan da ke cikı domin su ga in da mahaifansu suke amina shiru babu labari sai fursunoni da suke gani maza da mata, Da ƙyar da sidin goshi suka gano a cikin mahaifan nasu suke a cikin waɗansu kejina na karfe hannayensu da kafafunsu ɗaure da sarƙoƙi. Cikın matuƙar farin ciki maral musaltuwa su Hilwas suka ruga izuwa in da kejinan suke Koda ya rage bai fi saura taku uku a tsakanınsu ba kwatsam ba zato ba tsammani sar wani wawakeken rami ya bayyana a gabansu wata irin gagarumar wuta na ci ganga-ganga a cikin ramin. Kuma wata irin kakkausar murya ta kece da dariya cike cike da matukar fushi da ɓacin rai Hilwas, Kahzib da Sharwas suka waiga bayansu domin su ga wanda yake dariyar. Ai kuwa koda waigawar tasu sai suka yı turus. Ba wani suka gani ba face sarkı Shardasu shirye cikin gagarumar shigar shigar yarima Kinzaru na tsaye a ɓarin hannun sa na dama, sarkın yaƙi Hatyal na tsaye a hagu. Waɗansu gabza-gabzan samudawan dakaru na kewaye da su cıkın shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini, hannayensu rike da muggan makamai Sai da sarki Shardasu ya yi dariya ta ishe shi sannan daga bısani ya murtuke fuska kamar an aiko masa da WASIKAR MUTUWA, ya dubi Hilwas, Kahzib da Sharwas sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya ya ce, "Ya ku jarumai masu dauke da KAMBUN JARUMTA ku sani cewa tun daga lokacin da kuka fice daga cikin masaukinku har kawo izuwa nan na ga dukkannin abin da ya faru gare ku. Ina so ku yi sani cewa ku da mahaifanku gaba ɗaya kuna karkashin iko na ne har abada ɗaya daga cikin ba zai sadu da mahaifansa ba face ya amince da biya mini wata mahimmiıyar bukata ta. "Koda gama fadin hakan sai sarki Shardasu ya yi nuni da hannun sa na hagu izuwa bangaren bangon yamma da ke wajen. Yana mai karanto waɗansu ɗalasiman tsafi, gama rufe bakinsa ke da wuya sai hoton mahaifansu Hilwas mata ya bayyana suna zaune a cikin wani gida suna aika ce aika ce Duba ɗaya za ka yi musu ka fahimci cewa suna cikin damuwa Domin sun rame matuƙa sun yi baki tufafin da ke jikinsu ya yi datti sosai duk ya yayyage, babu wanda zai gansu a cikin wannan hali face ya kamu da tsananin tausayinsu Sa'adda Hilwas, Kahzib da Sharwas suka yi. Arba da su a sannan ne mahaifin Kahzib da Sharwas da ke zaune a cikin wannan kejin suka fara zubar da hawaye. duk da mahaifin Hilwas idanuwansa a makance suke baya gan abin abin da ke faruwa, amma da ya ji kukan ɗan sa Hilwas da abokanan Rauzil da Hasham sai shi ma ya fashe da kukan. Sai da suka shafe wani lokacı a cikin wannan hali yarima Kinzaru na yi musu dariyar mugunta. sannan sarki Shardasu ya sake nuna bangon a karo na biyu hoton bat! Kuma ya sanya wani duhu tsakanin su da su Rauzil ya zamana ba sa iya ganin 'ya'yansu. Sarki Shardasu ya saki guntun murmushi ga su Hilwas da har yanzu hawaye ke zuba daga idanuwan su Sannan bushe da dariyar mugunta, kana ya murtuke fuska kamar an aiko masa da WASIKAR MUTUWA, ya ce, "Ya ku wadannan ZARATAN MAYAKA ma'abota karfin damtse ku yi saji cewa idan har kun ɗaukae mini Alkawarin da za ku samo mini abin da nake ji Bukata to zan 'yantaku tare da iyayenku ba za ku kara bauta a gare ni ba. Idan kuwa ku ka bijirewa buƙata ta ku da mahaifan ku za ku kasance a cikın KANGIN BAUTA har ajali ya riske ku, Yanzu dai shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Koda jin wannan batun daga bakın sarki Shardasu sa hankalın Hilwas, Kahzib da Sharwas ya dugunzuma ainun, kuma su duka ukun suka faɗa kogin tunani don samun mafita. Abin da ya faɗo musu a rai shi ne shin wace irin bukata ce za su biyawa sarkı Shardasu? An ya kuwa ba yaudararsu zai yı ba? To yanzu kuma idan ba mu amince mun biya masa bukatarsa ​​ba za mu ci gaba da zama a cikın kuncin rayuwa, tare da mahaifanmu? Amsar tambayoyın da suka kasa bawa kansu ke nan take hankulansu suka sake dugunzuma fiye da ko yaushe. Hilwas ne ya katse shirun da ya wanzu a tsakanınsu ta hanyar buɗar bakı ya sanya hannu ya share hawayen sa sannan ya ce "Mun amince za mu bıya maka buƙatar matsawar za ka ba mu FANSAR RAYUKAN mahaifanmu. Shin mece ce ake buƙatar taka?" Sarkı Shardasu ya yi murmushi a karo na biyu ya ce, "Abın da kawai nake buƙata shi ne za ku tafi izuwa gidan boka Kimraz domin ɗauko mini SANDAR SARAUTAR shi Kafin ku isa gidan za ku tarar da miyagun dazuzzuka guda huɗu masu matukar haɗari. Daji na farko ya kasance mallakin wani gawurtaccen matsafin dodo da ake yi masa masa laƙabi da suna Zamzaru. Dodo Zamzaru ya kasance gwarzon mayaki, kaifi da tsini ba ya tasiri a kansa, A wannan ƙarni ba ki ɗaya, domin saboda hatsabibancinsa ne ya zamana sarakunan da ke makwabtaka da dajin suka yi kaura suka bar yanayin. Kuma an ce shi kadai ne yake rayuwa a dajin. Daji na biyu ya kasance na waɗansu irin tsuntsaye ne masu kama da tsuntsun batoyi, babu wani nau'in makami da yake tasiri a kansu face tsagwaran KARFIN DAMTSE da basirar mutum. Masana da bokaye sun tabbatar da cewa adadin tsuntsayen ba zai kidayu ba, Domin kullum kara yawa suke yi. Daji na uku na waɗansu fatalwoyi ne na haske, mutum ba zai taba samun nasara a kansu ba face ya kashe shugabansu kuma dukkanninsu suna da kamanni iri daya sak!. Babu yadda za a yi mutum ya iya gane wane ne shugabansu. tsakanin zafin namansu kuwa ba zai musaltu ba sai dai abin da ido ya gani. Na karshe kuwa ya kasance daji ne na waɗansu zakunan sihiri da wani shu'umin boka ya ƙirƙira mai suna Sultan ibn Hammar. Bayan kun samu nasara shiga gidan boka Kimraz kun dauko mını sandar tsafinsa sai kuma ku huce izuwa wanı daji da ke ıyaka da gidan ku ɗauko mini ƙoƙon kan boka Mannaf da ke ajiye a cikin wata tsohuwar rijiya dake fadar Sarkin bokaye na duniya, Sa'adda sarki Shardasu yazo nan a zancen sa sai hankalinsu Hilwas ya dugunzuma ainun, Sharwas dubi sarki ya ce, "Ya shugabana a wace nahiya dazuzzukan suke?" Sarki ya ce, "Me ku ke ci ne na baka na zuba? Ai zan haɗa ku ne da wani hadimin aljanina ya yi muku jagora." Koda gama fadin haka sai sarki Shardasu ya rintse idanunsa ya kırawo sunan aljaninsa, wata irin kakkarfar iska ta mamaye wurin wacce ta haddasa gashin kansu bawa Hilwas da rigunan jikinsu kaɗawa. Daga can sai ga wani narkeken aljani ya bayyana tsum! Tamkar an jefoshi daga sararin samaniya. Aljanin ya kasance mai matuƙar tsaho, muni, girma gami da kwarjini. Domin duk dakewar zuciya irin ta su jarumi Hilwas sai suka firgita da ganin aljanın Shi kansa sarkin yaki Hatyal da yarima Kinzaru sun razana matuka. sarki Shardasu ne kadai bai tsorata ba. Aljanin ya faɗi ƙasa ya kwashi gaisuwa ga sarki Shardasu. Sarki ya dube sa ya ce, "Ya kai Kubuzul Haiman ka yi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina sai ka yiwa waɗannan jarumai rakıya izuwa dajin Darul Hashawar. Wannan shi ne abin da nake bukata." Koda jin wannan batun sai aljani Kubuzul Haiman ya risina ya ce, "An gama ya shugabana. Ba tare da wani ɓata lokaci ba Hukubul Haiman rankwafa gadon bayansa bawa Hilwas, Sharwas da Kahzib suka hau kan kansu suka zauna tare da dawakansu sannan Kubuzul Haiman ya yunkura ya tashi izuwa sararin samaniya. Kafin kiftawar ido ya ɓace ɓat a cikin gajimare, nan take sarki Shardasu, yarima Kinzaru da sarkin yaki Hatyal suka bushe da dariyar mugunta. Wannan shi ne dalilin barowar jarumi Hilwas, Sharwas da Kahzib daga birninsu na Baitul Na'im, domin su ɗaukowa sarki Shardasu sandar sihiri da kokon kan boka Mannal. SHIN WADANNE IRIN MIYAGUN MUSIBU SU HILWAS ZASU FUSKANTA A WANNAN TAFIYA TASU SUNA SAMUN NASARAR KETARE MIYAGUN DAZUZZUKA HUDU HAR SU ISA GIDAN BOKA KIMRAZ? KUMA SUNA SAMUN NASARAR DAUKOWA SARKI SHARDASU SANDAR TSAFI DA KOKON KAN BOKA MANNAF DOMIN FANSAR RAYUKAN MAHAIFANSU? SHIN YA SHURAIMA 'YAR SARKI HUSUBUL DINAR DA GIMBIYA LASHMIRA ZA SU KASANCE NA KEWAR MASOYANSU HILWAS DA KAHZIB? TSAKANIN YARIMA KINZARU DA GIMBIYA LASHMIRA WAYE ZAI GAJI KARAGAR MULKIN SARKI SHARDASU? INA LABARIN SARKI BARSUS, Sarkin marubutan yaƙi ANSAB DA SARKI HULBARU DA KOWANNENSU YA SHIRYAWA SARKI SHARDASU BAKIN TUGGU DOMIN RABA SHI DA KARAGAR MULKINSA, AMMA YA TSIRA DAGA SHARRINSU? SHIN A WANE HALI MAHAIFANSU JARUMI HILWAS YA ZA SU KASANCE NA RABUWA DA 'YA'YANSU? Mu hadu a 10 KANGIN BAUTA domin jin ci gaban wannan labarin nayataccen labari. Lokacin da su jarumi Hilwas suka yi cirko cirko a kofar shiga gidan boka kimraz Cike da matukar damuwa bisa halin KANGIN BAUTA da suka baro mahaifin su a ciki. Sai suka shafe tsawon daƙiƙa arba'in Batare da ɗayan su yace uffan ba. Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai suka hango wani mahayi bisa ingarman doki fari. Ya rataya wata sharbebiyar takobi a gadon bayan sa ya durfafo inda suke gadan gadan. Sai dukkanin su suka ƙura wa mahayin idanu suna jiran ƙarasowar sa. Sannu a hankali mahayin ya ci gaba da kusanto su, Har yazmana tazarar dake tsakanin su bata huce taku biyar sannan yaja linzamin dokin sa ya tsaya cak Yayin da suka yi arba da mahayin sai suka cika da matukar mamaki. Abu na farko da ya basu mamaki shine yadda mahayin ya yaksance ya mace ba namiji ba, Sannan ya akayi ta iya ketare miyagun dazuzzukan dake baya Wato dajin fatalwoyi na haske, dajin dodo zamzaru da kuma dajin zakunan sihiri masu ɗauke da fuka -fukai , Wanda su kansu sai da suka sha bakar wahala sannan suka samu nasarar ketare dazuzzukan. Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan Shi kuwa Sharwas sam bai ma san da wannan zancen ba, Domin tuni ya shagala da kallon kyakkyawar budurwar, domin lokacin da ya fara arba da ita sai yaji zuciyar sa ta buga wa karfi wani abu ya soki ya soki zuciyarsa a karo na farko yaji ya kamu da matukar kaunar ta a zuciyar sa, Tsawon daƙiƙu ana wannan kallon kallo tsakanin su Sharwas da Mahayin, Sannan daga bisani hilwas yayi karfin hali yayi gyaran murya ya dubi budurwar yayi gyaran murya yace" yake wannan budurwa shin wace ce ke ? Kuma ya akayi kika ƙetare miyagun dazuzzukan dake baya har kika iso nan?. Sannan mene ne ke tafe da ke izuwa gar mu. Sa'adda budurwar taji wannan batu daga bakin hilwas dai tayi gyaran murya cikin tattausar murya mai daɗin sauraro tace" yakai hilwas ɗan makaho rukaisu kayi sani cewa da farko dai ni suna na Husnat bintu abu-husein Na fito ne daga gabashin duniya a wani birni da ake yiwa lakabi da Darul--imfidal, Game da amsar tambayar ka ta biyu kuwa shine, Na samu nasarar ketare dazuzzukan dake baya ne bisa taimakon Ubangiji mahalicci,shine wanda ya halicci duniya da Abin da ke cikin ta, Amsar tambayar ta karshe ita ce bakomai ne ke tafe dani izuwa gare ku sai domin na taimaka muku da izinin Ubangiji na domin ku samu nasarar abin da kuka fito nema. Kuma na kuɓutar da mahaifan ku daga makircin azzalumin sarki sharadi, Sa'adda Kahzib, hilwas da Sharwas suka ji wannan batu daga bakin Husnat sai suka cika da ɗumbin al'ajabi da mamaki, Kahzib yace "yake wannan jaruma taya ya za ki iya taimaka mana wajen cimma burin mu bayan cewa mu ɗin Jarumai ne zamu iya nasara akan dukkan abinda muka sanya a gaba, Sannan naji kin ambaci wani Ubangiji shin dama akwai wani abin bauta bayan namu?. Husnat tayi ƙaytaccen murmushi da ya ƙarawa fuskar ta kwarjini sannan tace " na yar da cewa tabbas ku sadaukai ne kuka kuma zaku iya cimma nasara akan abinda kuka sanya a gaba Amma ina so ku sani zan taimaka muku ne wajen mallakar abin da kuka fita nema cikin ruwan sanyi batare kun sha wata wahala ba, Sannan ina so mu haɗa karfi da ƙarfe wajen rushe mulkin zalunci na sarki shardasu domin ku sani cewa koda mallaka sa abubuwan dake bukata sai ya ci amanar ku bazai taɓa baku fansar rayukan mahaifan ku ba, Sannan zan roƙi Ubangiji na ya warkar da lalurar dake samun iyayen ku, Amma sai idan kun ɗaukar mini alkawarin cewa zaki bayar da gaskiya ga Ubangiji na Sa'adda Sharwas, Kahzib da hilwas su ka ji wannan batu daga bakin Husnat sai jikin su yayi sanyi, Suna masu zurfafa izuwa cikin Kogin tunani Daga bisani sai Sharwas yace "Ɗan bamu Lokaci zamu tattauna da yan uwa na, Koda gama faɗin hakan sai shaewas da yan uwansa suka koma gefe guda suka yi ƙusƙus a junan su sannan daga bisani suka dawo izuwa inda Husnat take, Hilwas ya dube ta yace" yake Husnat haƙiƙa mun amince zamu zamu karbi addinin ki, Matukar kika cika alkawarin da kika ɗauka na taimaka mana wajen mallakar abubuwan da muka fito nema, Sannan idan har Ubangijin naki ya warkar da mahaifan mu, Munyi miki alkawarin cewa zamu taimaka miki wajen yaɗa addinin ki a wannan nahiya baki ɗaya, Koda jin wannan batu daga bakin hilwas sai jaruma Husnat ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa, Kawai sai ta kama linzamin dokin ta ta sauko ta durfafo ƙofar gidan boka kimraz Da isar ta sai kawai ta sanya hannun ta akan Mabudin kofar tayi bismillah ta tura ƙofar bisa mamaki sai gashi ta buɗe Al'amarin da yayi matukar bawa su hilwas mamaki kenan kuma ya ɗaure musu kai, Domin dai ko da a tarihi basu taɓa ganin jarumin da yayi wannan bajin ta ba. Domin kofar tana da kaurin gaske wacce in da za'a sanya karti majiya karfi mutun sattin ba za su iya ture ta ba, Batare da fargabar komai ba, Husnat ta zare sharbebiyar takobin dake gadon bayan ta ta kunna kai izuwa cikin gidan tana mai yafito su hilwas da hannunta tana nuna su biyo bayan ta, Batare da gardamar komai ba hilwas ya zare takobin sa ya bi bayan ta da sauri, Kahzib na rike da mashin sa mai baki biyu, Sharwas na rike da kwari da bakan sa suka shige izuwa cikin gidan, Wannan shi ne abinda ya faru da su bawa Hilwas akan hanyar ta zuwa gidan boka kimraz domin ɗauko wa sarki shardasu sandar sihiri. Acan birnin baitul-na'im kuwa al'amarin gimbiya lshamira da gimbiya shuraima yar sarki Husubul-Dinar kuwa, Tun sa'adda suka ji abinda ya da yafaru da masoyan su wato bawa Kahzib da hilwas, Sai suka kasance cikin tsanin damuwa yana zamana cewa sun kamu da rashin lafiya domin ko abinci basa iya ci, Koda sarki Husubul-Dinar yaga abin da ya samu yar sa sai ya yanke shawarar ya tafi izuwa Birnin sa domin yi mata magani, Amma sai sarki shardasu yace yayi hakuri har zuwa lokacin da zasu samu lafiya ayi musu magani tare da gimbiya, Al'amarin mahaifan su Kahzib maza da mata a cikin kurkuku kuwa sun kasance cikin kinci da damuwa dare da rana bisa tunanin halin da ya'yan su ke ciki. Suka ji sun tsani sarki shardasu fiye da komai a rayuwar su . Wannan shi ne abin da yafaru da su gimbiya lshamira da mahaifan su Kahzib. Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na 11 domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe Lokacin da su jaruma Husnat dasu bawa Hilwas suka shiga izuwa gidan boka kimraz, Sai suka tsinci kansu a wani makeken fili mai tarin rairayi, Sai suka ci gaba da tafiya Husnat tana mai dawo bayan su, Saboda ta lura yadda Sharwas ke satar kallon ta a fakai ce, Yayin da taga hakan sai ta dube sa ta sakar masa tattausar murya a lokacin da ya waigo ya haɗa idanu da ita ɗin. Koda yaga irin murmushin da Husnat ke yi masa sai yaji zuciyar sa ta buga da karfi, Kawai ya mayar da duban sa zuwa kan hanya yana mai tambayar kansa a cikin ran sa yana mai cewa shin Mene ne ma'anar wannan murmushi da Husnat tayi mini shin ko ita ma ta kamu da soyayyata ne. Amsar tambayar da Sharwas ya kasa bawa kansa kenan. Haka dai aka cigaba da tafiya sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana tafiya batare da an haɗu da wani abu mai cutar wa ba, Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ga waɗansu irin dakaru na taso wa daga cikin rairayin tamkar yadda danshi ke tsattsafowa daga cikin ƙasa, Dakarun sun kasance girɗa-girda tamkar samudawan farko suna dauke da siffa guda biyu, Tsagin jikin su na dama na karfe ne tsagin hagun kuwa na na haske ne Suna dauke da miyagun makamai masu barazana ga rayuwar bil'adama, Suna dauke da idanuwa jajur kwaya ɗaya jal a tsakiyar goshin su, Hancin su da bakunan su irin na gwaggwan biri ne, Haƙiƙa waɗannan dabaru sun kasance munana kuma ababan tsoro, Babu wata halitta mai numfashi walau mutum ko aljan da zayi arba da miyagun dakarun face tayi nadamar wanzuwar ta a doran ƙasa, Sa'adda su jarumi Hilwas sukayi arba da dakarun sai suka ɗimauce, Tamkar ace kyat su zura da gudu,amma saboda juriya irin ta zaratan Jarumai sai suka dake, Jaruma husnat ce kaɗai bata razana ba ita ma saboda tana karanta sunayen Ubangiji tsarkaka ne a cikin ran ta yasa hakan, Yayin da dakarun suka kammala yiwa su hilwas ƙawanya sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, Daga can sai dakarun su ka zare makaman su suka yi ihu da kururuwa mai firgitar wa suka ruga izuwa kan su. Ko da ganin hakan sai jaruma Husnat ta zare takobin ta ta kwala kabbara da karfi ta ruga izuwa kan dakarun, Sharwas, Kahzib da hilwas sukayi koyi da ita ta hanyar zare makaman su, Lokacin da aka haɗu sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini muni daban tsaro, Kowa ne ɓangare su ka wanzu suna kaiwa juna miyagun hare hare cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance, Wohoho ana fara wannan artabu ne wani abun mamaki ya fara guda domin kuwa duk irin zafin nama na su jarumi Hilwas yazama abanza, Domin kuwa duk sa'adda suka sari jikkunnan dakarun da makaman su sai suji tamkar dutse suka sara domin wani irin tartsatsin wuta ne yake tashi gami da kara marar daɗin sauraro. Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin su kenan suka fahimci cewa idan aka Cigaba da wannan artabu a haka dakarun zasu iya samun nasarar hallaka su. Abangaren jaruma Husnat kuwa tuni labari yasha bambam, Domin kuwa Husnat ta zamo gagarabadau a tsakiyar dakarun, Duk in da ta sanya a gaba sai dai kaga dakarun na zubewa ƙasa matattu tamkar tana sassabe a gonar auduga. Tabbas jarumtaka baiwa ce daga Ubangijin halitta ba'a siyan ta kuɗi ko mulki, Komai hassadar Mutum idan ya ga Yadda Husnat ke ragargazar dakarun doka ne ya jinjina mata ya tabbatar dacewa ta cika mace mai kamar maza kuma jarumar Asali, Nanfa ƙarar karafniyar ƙarafa,ihun mazaje haɗe da kururuwar dakaru ta cika dodon kunne, Sassan jikkunnan dakarun suka dinga shawagi a sararin samaniya suna zubowa ƙasa tamkar ana ruwan su ne daga saman, Jini kuwa ya dinga kwaranya, tsartuwa gami da feshi yana zubar a ƙasa tamkar an balle Teku, Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa babu sassauci, A sannanne dakarun suka fahimci cewa Husnat tayi musu muguwar barna. Domin ta kashe fiye da rabin su, Nan fa hankalin su ya dugunzuma ainun,kuma suka fusata ainun zukatansu suka dunga tafarfasa tamkar zasu kone, Kawai sai suka zage damtse suna cigaba da kaiwa Husnat hare hare ta ko ina, Al'amarin su Bawa hilwas kuwa sa'adda su ka ga irin gagarumar bajintar da Husnat ke yi sai suka cika da matukar mamaki suka ce a cikin ransa anya kuwa Husnat bil'adama ce, Taya ya za'ayi ce zaratan Jarumai kamar mu mun kasa samun damar hallaka koda badakare ɗaya amma Husnat ta kashe fiye da rabin su, Lokacin da sa'a biyu ta shuɗe ana wannan fafatawa a dai dai wannan lokacin ne Husnat ta hallaka ba ki ɗaya dakarun dake gaban ta, Kuma ta hango irin mawuyacin halin da su Bawa hilwas ke ciki, Domin dakarun sun galabaitar dasu basa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare kansu. Wasu lokutan idan dakarun suka kawo musu hari suka kare da makaman su sai kaga sun faɗi ƙasa magashiyan, Amma saboda juriya irin ta zaratan Jarumai sai suka muƙe tsaye aci gaba da yaƙin, Koda ganin hakan sai ta falfala da azababban gudu izuwa kan su Tana mai kwala kabbara da ƙarfi tare da yiwa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama salati, Domin ta kai musu ɗauki, Cikin daƙiƙa hamsin bisa taimakon Ubangiji mahalicci ta samu nasarar hallaka dakarun baki ɗaya, Faruwar hakan ke da wuya sai gaba ɗaya gawarwakin dakarun da makaman yakin gami da jinin da ya cakuɗa da ƙasa suka ɓace ɓat tamkar basu taɓa wanzuwa ba, Nan take filin ya rikiɗa izuwa wata ƙasaitacciyar faɗa, Da aka kawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya, Bisa wani zagayayyan tudu da aka shimfiɗe sa da wata irin Koriyar Darduma anan aka ajiye wata ƙasaitacciyar sanda wace akayi ta zallar zinare kuma aka yi mariƙin ta da zubardaju, Sandar tana canza launi lokaci zuwa lokaci Kai da gani kasan aiki ne na sihiri. Koda Husnat tayi arba da sandar sai ta dubi Bawa hilwas tace"sai kayi hanzari ka ɗauko mana waccan sandar sihiri domin mu tafi izuwa dajin kushuful-fannar domin ɗauko ƙoƙon kan boka Manaf. Ko da jin wannan umarni daga bakin Husnat Sai hilwas ya taka da kafafun sa har izuwa wannan gayayyen tudu yake ya dauki sandar sannan ya dawo izuwa inda su Kahzib ke tsaye. Kawai ya shige gaba ya durfafi kofar fita daga gidan, Sharwas, Kahzib na biye dashi jaruma Husnat ce a karshe, Lokacin da suka fita sai suka hango dawakan su acan gefe suna cin ciyayi, A sannanne Husnat ta lura cewa lokacin sallar la'asar ya giya, Don haka sai tayi istigfari sannan ta cire salkar ruwan ta ta ɗaura alwala, Bayan ta kammala ne ta fuskanci gabas ta tayar da sallah, Sa'adda Hilwas, Kahzib da Sharwas suka ga yadda jaruma Husnat ke gudanar da ibadar ta nan take suka ji addinin musulunci ya kayatar dasu, Domin ba su taɓa ganin addini mai tsafta da nutsu tamkar addinin Husnat ba, Nan take Sharwas yaji soyayyar Husnat ta daɗa mamaye zuciyar sa, Da yake yamma tayi liƙis duhun magariba ya fara kawo kai sai hilwas ya bayar da shawarar a kwana a dajin idan ya so da safe sai a durfafi dajin Kushuful-fannar, Mu haɗu a KANGIN BAUTA Littafi na 12 domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari, Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe Marubuci MANSUR USMAN SUFI Wthapp number &;call 08137237071 KANGIN BAUTA Marubuci MANSUR USMAN SUFI Wthapp&call 08137237071 Kamar yadda jarumi Hilwas ya bayar da shawara haka al'amarin yakasance, In da aka kwana a wajen da duku-dukun safiya bayan jaruma Husnat tayi sallar asuba anyi kalaci kowa ya kimtsa cikin sa, Sai kowa ya kama dokin sa ya hau ya sakaasa linzami aka cigaba da tafiya, Hilwas, Kahzib da Sharwas suna tafiya a jere kusa da juna, Husnat na biye dasu har a wannan lokaci fuskar ta rufe take da rawani idanuwan ta kaɗai ake gani, Nan fa aka wanzu ana ratsa duwatsu, koramu tsaunuka haɗe kwazazzabai gami da sarƙaƙiya, cikin matsanancin gudu ma keta sa'a , Wasa-wasa saka gashi an shafe tsawon Sa'a uku ana wannan tafiya,amma ba'a haɗu da wani abu mai cutar wa ba, Koda kuwa miyagun yan fashi da dakarun sumame, Lokacin da Sa'a huɗu ta cika a dai dai lokacin aka shigo dajin kushuful-fannar, Nan fa kowa yasha jinin jikin sa bisa ganin yadda dajin yaksance dole ne a samu miyagun halittu a cikin sa, Kuma yakasance cikin shirin ko ta kwana Tsawon tafiyar Sa'a aka yi sannan aka hango wata rijiya a can nesa, Don haka sai aka ƙara azama domin isa, lokacin da aka isa sai kowa yaja linzamin dokin sa ya kama ya sauka ƙasa, Ita dai rijiyar an gina ta ne da zallar dawatsun wuta masu kwarin gaske, Tana ɗauke da murfi guda ɗaya jal, da aka yi shi da zallar mulmulallan karfe, In da za'a sanya karti majiya karfi mutun sattin ba zasu iya buɗe murfin ba, Nan fa aka yi cirko-cirko aka rasa wanda zai buɗe murfin rijiyar. Daga can Kahzib ya matsa izuwa bakin Rijiyar ya sanya hannun sa ɗaya domin ya buɗe murfin amma sai yaji tamkar Dutse ya rike, sai da ya tara gumi ya jiƙe sharkab amma murfin ko gezau bai yi ba, Amma sai da hilwas, sa Sharwas suka gwada tasu dubarar amma murfin bai buɗe ba, Duk wannan abu dake da wakana jaruma Husnat na tsaye a gefe guda tana gani bata ce ƙala ba. Koda taga kowa ya kasa buɗe wa sai ta matsa daf da rijiyar ta karanta ayatul-kursiyyu tare da yiwa Annabi s'a'w salati. Ta sanya hannun ta ɗaya ta buɗe murfin tamkar ta yaye tufafi, Hilwas, Kahzib da Sharwas basu san sa'adda su ka dunga dalalar da yawu daga bakunan su ba saboda matukar al'ajabi. Koda murfin ya buɗe sai akaji wani irin mahaukacin gurnani na fitowa daga cikin rijiya, Daga can sai aka ga wani ɗan wadan aljani yayo fitar burgu daga cikin rijiyar tamkar an janyo shi da ƙugiya. Aljanin yakasance baƙi mummuna yana ɗauke da fuka -fukai irin na jemage, Du du du tsawon sa bai huce kamu biyu ba, A hannu ɗaya ana rike da wani ƙoƙon kai, ɗayan kuwa yana ɗauke da wani zabgeegen Gatari na zinare yana sheƙi da walwali, Aljanin ya bushe da dariyar mugunta tamkar bazai daina ba Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya ce" Kaicon ku yaku waɗannan bil'adama ma'abota taurin kai da GAJEREN KWANA, kuyi sani cewa haƙiƙa kun tafka babban kuskure da kuka kuke tsammanin cewa zaku iya ɗaukar ƙoƙon kan mai girma Mannaf kuma har ku fita a raye, Ina mai tabbatar muku dacewa dayan ku bazai fita a raye ba, Kafin aljanin ya gama rufe bakin sa Husnat ta tari numfashin sa tana mai daka masa tsawa tace "Kai tsohon maketaci kuma azzalumi la'anannan Allah kayi sani cewa, Ka sani cewa ai babu mai kashe wa face Ubangijin musulunci, Da yardar sa zamu ga bayan ka sannan samu abinda muka fito nema. Sa'adda ɗan wadan aljanin yaji wannan batu daga bakin Husnat sai ya fusata ainun idanun shi su ka kaɗa su ka yi jawur, gashin jikin shi ya mimmiƙe ya dubi Husnat yace "Na rantse da gemun mai gidana boka Mannaf sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikin ki ta yadda ƙananan tsuntsaye zasu ji daɗin tsatstsagar naman ki, Domin hakan ya zamo darasi ga bil'adama masu tsarin idanu irin ki, Kafin Husnat ta sake cewa wani abu Aljanin ya ɗaga gatarin sa izuwa sama ya falfala da azababban gudu izuwa kan ta yana ihu da kururuwa mai firgita DANDAZON MAYAKA Komai tsakanin yawan su, Koda ganin hakan sai Husnat ta kwala kabbara da ƙarfi tare da zare takobin ta ta ruga izuwa gare shi, Su na haɗuwa suka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban sha'awa, Su duka biyun suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance, Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan gwani ya haɗu da tsohon ƙashi , juriya da jarumtaka suka game a waje guda dola ne artabu ya zamo tashin hankali, Gaskiyar masu iya magana da suka ce fadan da yafi karfin sai ka koma ɗan kallo, Hakan ne yafaru da hilwas, Kahzib da Sharwas domin koda suka ga cewa Manyan GWARAZAN JIYA sun kacame da azababban yaƙi sai suka koma izuwa inda dawakan su suke suna hangen abinda ke wakana, Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa amma aljanin bai samu nasarar taɓa jikin Husnat ba, A zahiri ga wnada yake kallon yadda artabun ke wakana sai tabbatar da cewa aljanin ya nuna ka Husnat a karfin damtse, Sai dai ita ta fi shi salon kwarewar yaƙi, Al'amarin da ya fusata shi kenan ya kaiwa Husnat wani bahagon sara da gatarin sa sa nufin tsarga ta gida biyu, Cikin wani irin baƙin zafin nama Husnat ta wurkila tare da zamewa, Gatarin aljain ya sari iska, koda aljanin yaga cewa yakasa samun nasarar hallaka ta sai ya shiga aika mata miyagun sihiri kamar ,kibbau, duwatsu,mashi da sauran su, Amma Dazarar sun doshi inda take sai su narke su zama ruwa su ɗige a ƙasa, saboda addu'o'in da take karantawa na neman tsari a a gare sa, Da kyar da siɗin goshi ta samu ta hallaka aljanin ta hanyar soka masa takobi a ƙahon zuciyar sa. Kuma ta ƙone shi ƙurmusa ta hanyar karanta masa ayatul-kursiyyu, Haƙiƙa su Bawa hilwas sun ga iko da ƙidira ta Ubangijin talikai bisa ganin yadda Husnat tayi masara akan aljanin, Bayan an fito da abin guzuri an yi kalacin rana. Sai kowa ya sake kama linzamin dokin sa ya hau ya sakar masa linzmai a ka cigaba da tafiya domin fi cewa daga dajin kushuful-fannar. Mu haɗu a Littafi na 12 don cigaban wannan labari Marubuci MANSUR USMAN SUFI mansurusmansufi@gmail.com Kangin Bauta 14 Rubuta labari MANSUR USMAN SUFI 08137237071 A wannan karon da aka fara wannan tafiya sai fira ta ɓarke tsakanin su jarumi Hilwas, Domin a wannan karon sun samu nutsuwa a zukatan su cewa jaruma Husnat za ta cika musu dukkan burikan su bisa taimakon Ubangijin ta, Gaskiyar masu iya magana da su ka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba, sai gashi an shafe tsawon kwanaki ashirin da uku ana wannan tafiya, A ranar kwana na ashirin da huɗu ne da la'asar aka iso birnin Baitul-na'im, Tun daga nesa aka hango kofar birnin cike da miyagun dakaru ɗauke da miyagun makamai, Al'amarin da ya sanya su hilwas su ka sha jinin jikin su kenan, Domin da gani ruwa baya tsami banza, don haka sai hilwas ya ɗauki sandar sihiri ya sanya ta a kirjin sa ta yadda babu komai wanda zai iya gane ta, Kuma ya ɗauki ƙoƙon kan boka Manaf ya sanya shi a cikin wata jaka ya rataya a gadon bayan sa, Sannan ya zare takobin sa. Da ganin hakan sai Kahzib ya zare kwari da bakan sa, Sharwas ya ciro mashin sa ya rike a hannu, Husnat riƙe da takobin ta aka durfafi kofar birnin Baitul-na'im, Yayin da ya rage saura taku talatin tsakanin su da kofar birnin. Sai kawai aka ji wani ƙara daga cikin birnin sai kofar ta buɗe, Sai ga sarki shardasu, yarima kinzaru da sarkin yaƙi hatyal, Waɗansu irin girɗa -girɗan dakaru na take musu baya, Bisa tsakiyar dakarun mahaifan su hilwas me maza da mata sanye cikin sararin baƙin ƙarfe hannu da ƙafa, Koda ganin hakan sai su hilwas suka ja linzamin dawakan su suka sauko ƙasa, Suka durfafi in da su sarki shardasu suke domin tarar juna, Sa'adda sarki shardasu yarima da sarkin yaƙi suka yi arba da jaruma Husnat sai hantar cikin su ta kaɗa da karfi tsoro ya ka masu. Sarki shardasu ya tambayi kansa a cikin ran sa shin wace ce wannan bakuwar jaruma? Shin ya akayi halarar tsafi na bata bayyana mini ita ba a lokacin da na gudanar da bincike akan su hilwas ɗin, Amsar tambayar da sarki shardasu ya kasa bawa kanshi kenan, Amma saboda kada yarima da sarkin yaƙi su fahimci wani abu sai Kawai ya shiga sakar wa su hilwas murmushi mai taushi, Amma har a lokacin zuciyar shi bugawa take da karfi tamkar zata faso cikin kirjin shi ta fito waje, Abin da bai sani ba shine kamar yadda ya kamu da tsoron haka yarima da sarkin yaƙi su ka kamu dashi, Yayin da ya zamana an iso daf da juna sai sarki shardasu ya dubi su hilwas cikin annurin fuska tamkar wanda aka bawa SARAUTAR DUNIYA ya buɗi baki yace "lale marhaban da zuwan JARUMAN DUNIYA sai a yau ne na tabbatar da cewa kun cika MAZAJENI DUNIYA kuma GWARAZAN JIYA da babu kamar ku a wannan KARSHEN ƘARNI, yaku waɗannan jarumai kuyi sani cewa a yau ne zan cika muku alqawarin da na ɗaukar muku na baku yanci da mahaifan ku daga KANGIN BAUTA a karkashin iko na, Don haka yanzu sai ku danƙamin sandar sihiri da ƙoƙon kan boka Mannaf, Koda jin wannan batu daga bakin sarki shardasu sai hilwas ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi Sarki yace " ya shugabana ni da yan uwa mun amince zamu damƙa maka abubuwan da ka buƙata amma bisa sharaɗin cewa bazaki yaudare mu ba, Idan kuwa har ka saɓa alkawarin zamu bar ka tare da wannan jaruma ta yanke maka hukunci dai dai laifin da ka aikata, Kuma sai mun rushe mulkin zaluncin ka daga doran ƙasa, Koda jin hakan sai sarki shardasu yace na amince da sharaɗin ku, Da jin haka sai hilwas ya ciro sandar sihirin boka kimraz tare da ƙoƙon kan boka Mannaf ya miƙa wa sarki shardasu ya sa hannu ya karɓa zuciyar cike da matukar farin ciki, Kawai sai ya nuna dakarun dake bayan sa da ɗan yatsan shi na hagu take su ka ɓace ɓat kuma sasarin ɗaya daure mahaifan su hilwas ya ɓace a daga jikin su, Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa hilwas, Kahzib da Sharwas, suka ruga izuwa in da mahaifan su suke domin tarar juna. Yayin da ya rage saura kamar taku goma sha biyu a tsakanin su sai sarki shardasu ya yi nuni da hannun sa izuwa wajen take wata ƙarama ta tafasasshiyar darma ta bayyana a tsakanin su ta yadda babu damar su haɗu da juna, Sannan sarki shardasu ya ɗauki ƙoƙon kan boka Mannaf ya sanya kansa take ya ya zauna a kan tamkar ya saka hular ƙarfe. Ya riƙe sandar sihirin a hannun sa gami da bushewa da dariyar mugunta, Yarima kinzaru da sarkin yaƙi su ka yi koyi dashi, Daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi su hilwas a lokacin da hawayen takaici ke zuba daga idanuwan su, "Haƙika yaro man kaza ne bai san wuta ba sai ta nar ka shi, kuma tabbatar duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, Yanzu kuna tsammanin cewa zan barku a raye ne, Ku sani cewa a halin ku da mahaifan ku baku da wani amfani a waje na, Yanzu batare da ɓata lokaci zan hallaka waccan jarumar da kuke takama da ita, Koda Gama faɗin hakan sai sarki shardasu ya daga sandar sihiri izuwa sama ya kwarara wawan ihu sannan ya falfala da azababban gudu izuwa kan jaruma Husnat, Koda ganin hakan sai bawa hilwas ya riga izuwa kan yarima kinzaru, Kahzib da Sharwas kuwa suka tari sarkin yaƙi hatyal, rike da makaman su, Lokacin da aka haɗu da juna sai aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar kwarjini daban sha'awa. Ɓangarorin uku suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta tagaban kwatance, Wohoho haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce idan gwani da gwani suka haɗu a yaƙi juriya da bajinta suka game waje guda dola ne yaƙi ya zamo tashin hankali daban tsoro. Sai da aka shafe tsawon Sa'a ɗaya cur ana wannan artabu, Tabbas a wannan rana Allah ya nuna ikon sa domin Husnat ta samu nasarar hallaka sarki shardasu ta hanyar karya masa waya, Amma ita ma tasha matuƙar wahalar gaske, Hilwas da Kahzib suma sun kashe abokan gabar su, Amma sai da Husnat ta kai musu ɗauki bisa taimakon Ubangiji, Tabbas inda ace mutum yana tsaye a wannan waje zai ga yadda gawar sarki shardasu ke kawance a ƙasa cikin ƙaskanci da wulakanci dole ne ya gode wa Allah bisa ganin yadda ya kawo KARSHEN ZALUNCI da azzalumai. Koda samun wannan gagarumar nasara sai wannan ƙorama da ta raba tsakanin su hilwas da mahaifan su ta ɓace ɓat tamkar bata taɓa wanzuwa ba. A sannanne su hilwas suka ruga izuwa inda mahaifan su suke suka rungume juna suna masu zubar da hawayen farin cikin. Al'amarin da ya sanya Husnat dake tsaye a gefe guda ta kamu da matukar tausayin su kenan har kwalla ta zubo mata, Daga can sai ta taka da kafafun ta har zuwa inda suke ta durƙusa kasa bisa gwiwar ta ta dube su cikin tausaya tace "yaku waɗannan jarumai kuyi sani cewa a yanzu ne zan cika alkawarin da na ɗaukar muku na warkar da mahaifan ku bisa taimakon Ubangiji na, Koda Gama faɗin hakan sai Husnat ta fito salkar ruwan ta ta kofa ayatul-kursiyyu da falaƙi da nasi, Ta umarci mahaifan su Kahzib maza su shanye ruwan. Haƙiƙa tsarki ya tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki, Faruwar hakan ke da wuya sai idanun mahaifin hilwas suka buɗe garau yana iya ganin komai, Mahaifin kahzib kuwa bakin ya buɗe ya dawo yana iya magana tar-tar. Sharwas kuwa duk kuturtar dake jikin mahaifin shi ya warke jikin sa yayi kyau sumul, Batare da bata lokaci ba su hilwas da mahaifan su suka karɓi kalmar shahada a wajen Husnat Sannan aka dunguma izuwa cikin birnin Baitul-na'im aka musuluntar da kowa dama sun gaji da mulkin sarki shardasu, Bayin dake kurku kuwa aka fito dasu aka basu yanci. Nan fa gari ya kaure da shewa da murna, Kashe gari tun da duku-dukun safiya aka shiga shagalin nadin sarautar bawa hilwas a matsayin sabon sarkin birnin Baitul-na'im,tare da auren sa da gimbiya lashmira, Kahzib a matsayin waziri, hilwas a matsayin sarkin yaƙi tare da daura auren su, Kahzib da gimbiya shuraima yar sarki Husubul-Dinar, Sharwas da jaruma Husnat, daga wannan rana aka rushe KANGIN BAUTA kowa ya samu 'yanci gaba ɗaya jama'ar birnin suka kasance cikin matukar farin ciki maral misaltuwa, Hasken musulmi ya mamaye ko ina a nahiyar baki ɗaya Alhamdulillah Ƙarshe Daga mai ɗebe muku kewa a kullum da ko yaushe MANSUR USMAN SUFI Sarkin marubutan Yaƙi 08137237071